Skip to content ummu-abdoul MENU Diya mace by khadija sidi Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17, 2016 ​[16/10 21:43] .: 7/24, 11:46 PM] Salmah Ateeku: [11:40pm, 4/30/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣ Jin an idda sallar isha’i,ga jama’a na ta fitowa daga masallaci ya sanya Hajara wacce ake kira da hajjo kara sauri,ji ka ke kululu! Karar kugin yunwa da cikin ta ke ma ta kenan,silifas din ta hadin bauta,daya ya tsinke saboda haka sai cire shi ta yi,ta ruke a hannu. Dauke ta ke da katuwar kwaryar dawa wanda ta je aka niko domin Innar su ta samu ta tuka mu su na dare,hajjo ta dada sauri,cikin ranta fadi take yau dai Inna za ta yi tuwan dare,wata kila ma sai goman dare za mu ci,ko da yake mu ma godewa Allah baba yau ya kamana dawa mai tarin yawa,ma huta da shan garin rogo kwana biyu. Titi ta tsallaka,ta wuto ta wajan mai shayi,kamshin tuyen wainar kwai ya daki hancin ta,ba ta san san da ta mayar da mugun yawu ba,ba ta da buri da ya wuce ta gifta ta wajan,dan har dan tsayawa a wajan ta ke,taitahura hanci,ita a lalle sai ta shaki kamshin wainar kwai ko Allah ya sa ta ji shi har cikin ta kamar ta ci ta koshi. Wannan karan ma tsayawa ta yi ta na baza hanci,ga wata bakar yunwa da ta addabe ta,tini ta shagala ta ma manta da dawar da ke kanta,ba ta ankara ba sai ga mahaifin ta zaune cikin rumfar mai shayi,gaban sa katan buredi ne,ga kuma wainar kwai manya manya cikin faranti,ya na yagar buredin ya na hadawa da wai nar kwai,ga kuma shayin sa a gefe ya na korawa. Da sauri Hajjo ta matsa ta na fadin laa Baba,Baba ne wlh,Baba! A fusace ya waigo ya dube ta,ganin Hajjon ce ba kunnen sa ke zagi ba,ya daka ma ta tsawa,ke uwarki! uwarki na ce! Hajjo ta sha jinin jikin ta,sauran jama’a da ke zaune cikin rumfar su ka zubo mu su na mujiya. Na ce Uwarki! Ya ma ta dakuwa,shegiyar kaya! Ki kai ma ta dawar ba za ki kai ma ta ba kin tsaya gantali! Tafi gida dan uwarki! Ya daka ma ta tsawa,jiki na bari ta juya,har da tuntume Allah ya sa ta ruko dawar ba ta zube ba,Baba ya ce assha,kun ga dai shashasha,maza zubar da dawar kwa yi kwanan yunwa dan uwar ki!! Ita dai Hajjo ta ti maza ta kama hanyar ta,jiki na bari,ta ma manta da wani kamshin wainar kwai da ta ke bala’in so,shi ko Baba buredin shi ya ci gaba da yanka ya na hadawa da wainar kwansa ya kaiwa baki,sai gunguni ya ke kamar kuturu!! Tin da ta dau hanya,ba ta zame ko ina ba sai cikin gida gaban Inna ta dire kwaryar har lokacin jikin ta be daina rawa ba,Inna ta dube ta tace sai yanzu Hajjo? Layi ki ka tadda a wajan ne? Lfy ya na ganki ba nutsuwa jiki na bari haka? Hajjo ta zauna ta na maida numfashi ta ce Inna wai fa dan na ga Baba ya na cin buredi da wainar kwai wajan mai shayi,ba fa emmin zance ya yi ba,kawai dama magana dai kawai na ma sa shi ne ya fatattako ni,kamar na ce ya emmin!Inna ta dafa kafadar ta kema Hajjoo me ya kai ki yi ma sa magana tin da kin san ba ya so,yanzu haka sai ya time ki idan ya dawo. Tsigar jikin Hajjo ya tashi tuno dukan mahaifin ta,kana ta ce wlh Inna rai na ne ya biya ban san sanda ma na ma sa magana ba,ni dama ya emmin da yayyai ta bugu na bazan damu ba ma,yunwa na ke ji kamar na ci babu. Inna ta ce inbe emmiki ba ai ya emmiki bugu,yunwa kuma ga danwake cen dazu da fitar ki yayar ki Indo ta aiko ma na da shi sai…. ba ta jira Inna ta gama magana ba ta tashi da gudu ta nufi inda danwaken ya ke ta ja kwanan ba tare da ta wanke hannu ba ta afka ma sa,hannu baka,hannu kwarya,Inna ta bita da kallo ta ce oh Hujja kamar kin shekara ba ki ci komai ba? Allah dai ya yanke ma na wannan bakar wahalar da mu ke ciki,amen. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [11:49pm, 4/30/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣ Hajjo kenan,Hajara Mamman Mansur,diyar Mallam Mamman Mansur,wanda suke zaune a kauyen Kumurya,na yankin birnin kano. Wato Mallam Mamman wanda su Hajjo ke kira da Baba mutum ne mai rufin asiri matuka,ya na daya daga cikin ma su kudin yankin,amma kash mako gare shi,be san ya wadatar da iyalan sa ba,gidan sa kullum cikin faci-faci ake,mafi munin halin Baba shi ne kyamar haihuwan ‘ya’ya mata,ya ki jinin ‘ya’ya mata dan a nashi wahala ne kawai babu wata riba,a wannan dalili ya sa ya auri mata shida ya na saka a dalilin sun haifar ma sa diyoyi mata,duk wacce ta haifi diya mace da sai ta bar ma sa gida ita da diyar da ta haifa,wacce ta ci sa’a Allah ya zaunar da ita ita ce Inna,uwar gidan sa wato mahaifiyar su Hajjo,ita ma din dan Allah ya nufe ta da haifar da namiji a haihuwar ta na fari wanda aka radawa Mahmud,ake kira Mudi,da wannan dalili ne ya sa ya saki cikin sa ya zauna da ita,bayan shekara biyu ta dada haifa ma sa wani jinjirin Namiji mai suna Ayuba,murna gun Baba ba a magana,ita kanta Inna sai da ta zama yar gata dan cikin matan da ya aura ita kadai ce ke haihuwar maza,ko da Allah ya sake ba ta ciki a karo na uku,sai fa Inna ta haifo diyar ta mace,bakin ciki gun Baba kamar ya zaune diyar ya huta,yayyai ta masifa da bala’i wai an haifo masa jidali,wacce ba za ta amfana komai ba sai dai kai ka amfana ma ta,ai ta dawainiya ana jidali a karan banza a karan hofi,haka dai ba dadi aka sanyawa yarinya suna Indo. Tin daga nan Inna ta fara ganin sauyi,abunda ta ke gani Baba ya na wa matan da ya aura na shirin afkuwa kan ta. A haka zaman ba dadi,sam be san rayuwar Indo ba,sai dai na Mudi da Ayuba,su ka ci gaba da zama,Baba na auran mata ya na saki,gashi kuma kudira na Ubangiji har ya yau babu wacce ta haifa ma sa da namiji in ban da dai Innar. A haka ba dadi har shekara goma ya shude,an fidda rai da sake haihuwar Inna,kwatsam sai Allah ya ba ta wani cikin,tin ya na karami Baba ke ma ta kashedi kar fa ta haifo diya mace,ya dai fada ma ta,da ke abun na Allah ne bayan wata tara Inna ta sillibo diyar ta mace,Baba ranar har da zage zage,ai fa Inna ta kwashe kayanta ta bar ma sa gida,da kyar yan uwan sa suka sa baki ya bar ta,a fadar sa ta ci darajar yaran ta maza. Ranar suna aka radawa yarinya suna Hajara,shekara biyar da haihuwar Hajara aka aurar da yayar Indo wacce ta ke da shekara goma shabiyar. Kwanci tashi,yanzu Hajjo ta kai shekara goma shabiyu cif a duniya,amma daidai da rana daya Baba be taba fada ma ta magana ta arziki ba sai kyara da tsangwama. Hajjo yarinya ce da ba ta fiya jiki ba,yar fiyot ta ke kamar ka hure,kuma ba ta da wani tsayin azo a gani. Ba wani sifar kyau gare ta ba,amma kuma ba laifi tana da wani irin boyeyyen kyau wanda har ka kare zama da ita ba dai ka ga munin Hajjo ba,sai dai ma ka ga tana kara ma ka kyau. Hajjo ba fara ba ce,ba kuma baka ba,an fi danganta ta da wankan tarwada,idanun ta ba manya ba ba kuma kanana ba,haka zalika hancin ta be da wani tsini,ba ba’a ba hancin na ta ya so yayi gajarta sai Allah ya taimaka be yi ba,ba ta da gashi,amma kuma gaban kan ta rufe ya ke ruf da gashi .dan ko ta daura dankwali gashin be buya kamar ta sa hula ka ganshi lub lub a kwance kai ka yi zaton irin mai gashin nan mai yawa na gaske ce. Ba a kira ta mai karamin baki ba,amma girman leben na ta ba me muni ba ne,shi ne wanda turawa ke kira full lips,abubuwa biyu da ke karawa Hajjo kyau shi ne lotsewar da kumatun ta keyi duk sanda ya yi magana bare kuma uwa uba fara’a,dama ga ta gwanar murmushi,ga kuma yar wushiryar wanda ke dada bayyana kyanta cikin nutsuwa DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [12:01am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 3⃣ Washagari da safe Inna ta na wanki Hajjo ta shigo a guje ta na waka.. “Wata tafi wata a gashi ko Ni na fi a gashi,wata ta Fi wata a hanci ko ni na Fi a hannci…” Ta fada bayan Inna ta na dariya,Inna ta ce Hajjo hankali!za ki karasa min bayan nawa,yau kuma wannan wakar aka yi a dandalin kenan!Hajjo kyalkyale da dariya ta ce wlh Inna shi aka yi,amma kin se me Inna? Inna ta ce sai kin fada auta,Hajjo ta ce da ance wata ta fi wata,sai ki ga wata ta fito ta ce ko ita tafi,Mairo ta ce ta fi a gashi,Bintu a Ido,Hanse a hanci,ni kuwa ban fito a kowani baiti ba,da aka gama na ce ni me ya sa ba a bani nawa fitowar ba sai Mairo ta ce wai ai ban da abun fitowar dan babu abunda na fi su da shi,wai gani kwakwido,kuma komai nawa kadan ne! Inna ta murmusa,kyale su Hajjo,ai shi ya sa ki ka fisu kyawu saboda komai na ki daidai ne ba kuma kadan ba,dan haka ne ki kin fi kowa a kyawu! Hajjo ta saki Inna ta zura a guje..ke ke ke Hajjo! Ya ki nan! Inna ta kwalla ma ta kira,Hajjo ta dawo ta na haki,cike da mamaki Inna ta ce ina kuma za ki? Cikin haki Hajjo ta ce zuwa zan yi na fada mu su na fi su a kyauwu! Inna ta girgiza kai auta hankali! Ki yi hakuri idan kun sake haduwa anjima kya fada mu su,ko fa karyawa ba ki yi ba,ga kokon ki da dumame can maza ki dauka ki karya. Ba dai haka ta so ba,ta ce toh,ta karasa ta dauko koko da kwanan numame ta ya haye kan tabarmar da ke shimfile karkashin bishiyar mangaro ya yayi rumfa a tsakiyar gidan. Babban gida ne mai dauke da dakuna shida a jere,sai kuma guda daya mai ciki da falo,shi ne wanda Baba ke kwana ciki,sai daya na Inna da Hajjo,na biyu na Mudi da Ayuba,daya dakin girki,daya kuma dakin aje kayan abunci duk da ba aje mu su kayan abuncin ya ke ba,sai kuma dayan dakin da ke kulle cike da kayan takarce har da wani tsohon gado mai rumfa. Da ke Inna mace ce mai tsaftar gaske kullum gidan tsaf sa shi. Sai da ta fara kai loma sannan ta daga ido ta kalli Inna ta ce laa Inna wankin ki ke ashe,ni da na ce zan na taya ki. Inna ta dara,Hajjo hankali,ke tin shigowar ki ba ki lura da wankin ba sai yanzu? Baki cike ta ce eh wlh Inna,bara na gama sai na sa mi ki hannu,Inna ta ce a gama lfy auta. Inna! Hajjo ta kwada ma ta kira,na’am auta,menene kuma? Hajjo ta ce ni ma dan Allah ki ce da Baba ya sani makarantar gaba da firamari kamar yanda ya sa su Mudi da Ayuba…..ba za a saki din ba! Baba ya fito a fusace,ya ci ado da babbar rigarsa aska shida,ashe ya na daga daka ba ta sani ba. A fusace ya ke duban Hajjo da tini ta sha ruwan jikin ta,ta yi tsumu tsumu. Shegiyar kaya,ke dubanni nan!ke wacece da za a saki makarantar gaba da firamari? Inna ta dauke kai ta ci gaba da wankin ta,ba da ke na ke magana ba! Ido na shirin kawo ruwa ta ce ni Hajjo ce… Baba ya ce Hajjo me? Hajjo ta ce diyar ka mutum! Ungu nan! Ya ma ta daguwa! Hajjo diya mace ba diya ta ba za ki ce! Ke diya mace ce,su Ayuba da Mudi maza ne shiya na sanya su makaranta koba komai idan su ka gama ma amfana da su,ke kuwa fa? Ita diya mace jidali ce,a haifo uban ku yayi dawainiya da ku,mu aurar da ku mazajen ku su yi dawainiya da ku,ku tsufa ‘yayan ku su yi dawainiya da ku,shegiyar kaya na ki na yi asara,bazan sa ki a makarantar ba! Da ma ki ka samu na.sanya ki firamari din?Har kina sa bakin magana dan kin ga ban buge ki jiya ba ko? Ya kama kunnen ta sai da Hajjo ta dan yi kara dan zafi,in kara gani kin maimaita abunda ki ka min jiya sai na lahira ya fi ki jin dadi! Ya saki kunnan,Hajjo ta durkushe ta na kuka,ko a jikin sa,hannu ya sa a aljihu ya fiddo da damin kudi,ya zaro naira hamsin ya karasa wajen Inna ya na fadin ke Amenatu ungo nan kudin cefane,sai Allah ya dawo da ni,na tafi daurin auren Garbati dan Alhaji Baso,ta dago ta karba tare da ma sa fatan dawowa lfy,ya fice ya na baza babbar riga. Inna ta dubi Inda Hajjo ta ke durkushe ta na kuka,tace maza tashi diyar albarka ka karasa cin tuwan ki,kar su Mairo su shigo su cinye mi ki fa! Hajjo fuskarta cike da hawaye ta ce Inna dama ni ma namiji ce kamar su Mudi da Baba ya soni ko da dan gutsire ne! Inna ta baro wajan wankin ta zauna kusa da Hajjo,ta ce kul Hajjo,na godewa Allah da yaiyo ki diya mace,kin san darajar ‘ya’ya mata kuwa? Ai darajar diya mace da yawa take Hajjo,yanzu in tambaye ki,da ki zama kamar Inna da ki zama kamar Baba wanne ki ka so? Hajjo ta ce caf! Gwara na zama kamar Inna ta wlh,Inna ta rungumo ta yauwa diya ta,shi ya sa na ke san ku,Baban ma fa ya na son ki,har ya fi gutsire,kawai baya nunawa ne. Hajjo ta dara Allah Inna? Shi ya sa ma jiya da ya dawo ya ga na yi bacci be buge ni ba ko? .Inna ta gyada kai kwarai da gaske,maza ci tuwan ki toh sai ki zo mu yi wankin,ko kin fasa taya ni ne? Hajjo ta ja kwanan tuwan ta, zan taya ki mana Inna,bara na yi sauri na zunzunduma loma! Inna ta tashi ta na dariya,ta ce a dai ci a hankali,ta koma kan wankin ta,ta bar Hajjo ta na zunduma lomar kamar dai yanda ta ce DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [12:11am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣ Babban Masallacin Kumurya,jama’a an taru,Baba tare da aminin sa Alhaji Baso baban ango zaune cikin masallaci suna jiran waliyan amarya su karaso,shiru ba su karaso ba,har rana na shirin takewa,Baba ya dubi Alhaji Baso ya ce anya kuwa lfy? Ka ga fa yanda aka shanya mu kamar kayan wanki? Alhaji Baso cikin damuwa ya ce ni ma dai jiran ya fara damuna Alhaji Mamman! Daga can gefe su ka hangi Garbati,yaci babbariga tare da abokansa. Garbati kato ne mai girman gabobin jiki,gashi dai yaro ne mai kimanin shekara ishirin da biyu a duniya,amma sai kayi zatan ya haura haka,fari ne mai zubin gwabaye. Kai Garbati,ya ka nan! Alhaji Baso ne yayi kiran sa,Garbati ya karasa da sauri ya durkusa gaban su,gani Baba,Alhaji Baso ya ce ya haka ne? Ya da girman mu a gari ana shirin maishe mu kanana mutum ne? Mun tara Jama’a amma ba waliye na amarya? Cikin maganar sa irin ta gwabaye,da karfi ya ke ya ce yo ni ma Baba hakan na gani!har raina ya fara baci! Aw Baba ka ga yayan Jummalan ma ya karaso! Ya yi nuni da wani matashi da ya shigo,Illo ga mu nan! Ya kwalla ma sa kira,Illo ya karaso ya gaida su Baba,Baba ya ce ya haka ku ka makara kuma? Illo ya durkusar da kai ya ce ai an sami matsala ne daga wajan amarya,ta ce maganar aure ba ta san shi ba,ta fasa auren Garbati…..lahailahaillallahu Mahammada Rasulillahi Sallallahu alaihi wasallam! Su duka su ka doka salati!Garbati ya fara muzurai! Alhaji Baso ya ce wannan ai yashashshen zance ne! Mu za a maida kanana mutane! Tintini ba ku san ku fasa auren ba sai da mu ka tara jama’a! Dan Allah Mallam Mamman taya ni jin maganar kananan mutanen nan! Shi de Illo ya yi kasa da kai kawai,Baba ya ce to a wani dalilo yarinya ta fasa aure? Illo ya ce a dalilin kin ware ma ta gida ita kadai ba tare da ya hada ta iyayen sa ba! Zancen banza zancen hofi! Alhaji Basu ya dakatar da shi ya na kumfar baki,an ki a ware ma ta gidan! An ki din! Ta fasa auren dan iyayenta! Mu nan mu mu ka hana shi ware ma ta gidan,tashi ka bamu waje! Illo ya ce na bar ku lfy,ya tashi yayi gaba ya bar su cikin takaici,ga Jama’a an tara. Baba ya dafa kafadar Alhaji Baso ya ce kar ka damu,ba dai yau aka sa za a aura auran Garbati ba? Aure kam kamar an daura an gama,kai Jama’a a saurara za a fara abunda ya kawo mu,Garbati dai sarautar Allah ya zubawa ido kawai. Can gida kuwa Inna ta aiki Hajjo siyo daddawa,dake Hajjo akwai san gudu,ta taho a guje ga daddadawar ta a hannu,ba ta ankara ba ta gwabje Idi dan makota ya dauko tallar manja,tini farantin manjar ta yi kasa,manjar ta zube malale a kasa,Idi ya bi manjar da kallo ya ce kan uba! Wlh sai an biya ni ko na daki kudina!mahaukaciya wacce ba ta san tafiya a hankali ba! Jin haka Hajjo ta dada zurawa a guje ta na fadin ba sai ka biyo ni ka daki kudin na ka ba in za ka iya kama ni! Ai kuwa shi ma bin na ta yayi,tsabar gudu ba ta hango Baba tafe ba,da gudu ta shige gida. Baba ya shigo ya na fadin komai aka yi shegiyar kayan nan wani masifar ta jangwalo ma na ya sa take gudun fanfalaki haka! Amenatu ki na ina ne! Inna ta fito daga dakin ta yayinda shi ma Idi ya shigo a guje,ya tsaya gaban Baba ya na haki. Baba ya ce kai lfy? Menene? Idi da kyar ya ke magana dan haki ya ce Hajjo ce ta baran min da manja ta ta gudu,wlh sai ta biya ni! Ko na daki kudi na! Inna ta ce Hajjo kuwa? Daddawa fa na aike ta ta siyo min! Baba ya murmusa,ya ce ni na ga abunda ba ki gani ba,kai yaro nawa ne manjar ta ka ga sadakin ta na biya ka a ciki! Inna ta dafe kirji SADAKI kuma! Baba ya ma ta banza,yayinda ya fito da kudi daga aljihun sa,Idi ya ce dari uku ne,Baba ya dirga dari uku ya mi ka ma Idi,ka ci sa’a yanzun nan na karbi sadakin ta,da wlh sai dai ka daki kudin na ka dan da kudi na dai ba zan cira na biya ba. Idi ya karbi kudi ya kama hanyar fita ya na fadin Allah ya so ki yarinya! Inna ta ce Mallam magana na ke fa,na ce wani sadaki ka ke magana akai ne? Baba ya ce sadakin Hajjo mana,Allah ya yanke min wahala ai,yarinyar da Garbati zai aura ta ce ta fasa auren,sai ni kuma na samawa kai na sauki na Hajjo dan na fitar da abokina kunya! Inna ta fara salati ta na sallallami,ta ce Mallam aure fa ka ce? Hajjon nawa ta ke Mallam!kwanan nan fa ta cika shekara goma shabiyu Mallam,Kai kuji wani yashashhsen zance,Hajjon nawa ta ke? Zama zan yi da ita in ta dawainiya da ita?kin manta motsin gado ce ba yarinya ba,ina ma ta ke ne? A gaban ido na ta shigo a guje kamar walkiya! Ke Hajjo ki na ina ne wai! Za ki fito ko sai na sabar mi ki! Inna ta ce Mallam na ce da kai na aike ta siyan daddawa…Baba ya ma ta banza,ya cigaba da fadin Hajjo wlh na dirga uku ba ki fito ba sai na mi ki dukan kawo wuka,ya fara dirge daya,biyu…. Tim!kamar daga sama sai ga Hajjo ta diro daga kan bishiyar mangaro,Baba ya ce shegiyar kaya! Ki ganta nan bishiya ta haye kamar birinya,Inna kallan Hajjo da ta yi tsumtsumu da ido ta ke cike da mamaki da tausayi. Ke tashi! Baba ya daka ma ta tsawan da ba ta san sanda ta saki daddawar Inna ba ya zube kasa,jiki na bari ta tashi,Baba yace daga yau dawainiyar ki ta tashi daga kai na kuma ya koma ga mijin ki,ya mikawa Inna kudin hannun sa,ta ma kasa karba sai da ya ce ke karbi mana! Kun ga shashanci,jiki ba laka Inna ta karba,Baba ya ce dubu biyar ne ba dari uku,dari ukun na biya kudin barnan da ta yi kin dai gani,sai ki siyo ma ta langa tuwo da miya da kuma dai abunda ki ka san za ta bukata,kudin sadakin ta kenan,na ce da Alhaji Baso ba sai sun kawo lefe ba dan ni ma ba gara zan yi ba,zan kira kafinta ya ma tsohon gadon da ke dakin can fanti,dan gobe za a yi jere akai Hajjo dakin ta….. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [12:16am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭 DIYA MACE👭👭👭 5⃣ Yauwa Allah ya sa na yar da kwallan mangwaro zan huta da kuda! Ya na ware babbar riga ya shige ciki,Inna sakin jiki ta yi ta na kallan sa,wannan abu da me ya yi kama? Ganin Baba ya shige Hajjo ta kwaso daddawar da ya zube,ta tashi da sauri ta mi kawa Inna ba tare da ta san abunda ake ciki ba,dan dama ta saba da ganin bala’in Baba dan haka ba ta kawo komai a ram ta ba,fadi take Inna ungo daddawar ai wannan dan rainin wayon ne ya biyo wai dan ban sani ba na buge shi manjan sa ya bare! Maimakon Inna ta karba kawai sai ta fashe da kuka,hakan ba karamin dagawa Hajjo hankali ya yi ba dan ba ta taba ganin Innar tata ba a cikin wannan hali,ita ma kukan ta sa tana fadin wayyo Inna ta me ya same ki ki ke kuka,ni Hajjo na shiga uku na lalace!Baba dukan ki yayi Inna? Baba ya na jiyo su ya musu banza,Mudi da Ayuba su ka shigo,sun dawo daga makaranta. Gani uwa da ‘ya na kuka tini hankalin su ya tashi,da kyar su ka shawo kan Inna ta yi shiru ta fada mu su dalilin da ya sa su kuka,Mudi da ke ya mallaki hankalin kansa shi ya shiga bawa Inna baki,ya tura Ayuba gidajen yan uwa domin sheda mu su abunda ke faruwa,kan ka ce me? Kafin la’asar tini gida ya fara cika da yan uwa,ita dai Inna ta zubawa sarautar Allah ido,bare ita amaryar da ba ta ma san ana yi ba,tin da ta samu Inna ta dai na kuka ta shiga sabgarta irin na yara,Baba kuwa tin da ya sa kafa ya fita be sake waiwayan su ba. Yanda Baban yace haka ko aka yi,gado mai rumfa ke aje shekara da shekaru aka fidda aka shiga ma sa fenti,haka kuma Inna tace a hada da gadon Hajjo mai spring,sai a hada ma ta har shi,tinda dai amare ma su gata gado biyu ake hada mu su. Indo yayar Hajjo ta karaso,gaba daya ranta yayi matukar sosawa,daka su ka zauna ita da Inna suna jin jina al’amarin. Hajjo ta ci danmara,fuskar ta cike da kwalliya an zane da gazar,ta faki idon jama’a,ta fito sim sim,ba ta ankara ba ta ci karo da Ayuba dauke da su langa tuwo da miya da Inna ta aike shi ya siyo. Wayyo dan Allah yi hakuri Ayuba,yasin ban san ka taho ba!Ayuba ya ce Hajjo hankali! Dama ina za ki san na taho? Sai a sannan ya lura da dammaran da ta ci,ga fuskar an bi an zane,ya ce ke ina za ki wai? Cikin yanga tana tafa hannu ta ce ai Mairo ce ta gayyace ni fatin yayan ta Garbati,ta ce ma ba sai na kawo kudin fatin ba ma! A fusace ya ce ku ji shasha,fatin kaniyar ki,ba ki san yanzu ke matar aure ba ce? Ai kece amaryar Garbatin! Hajjo ta murguda baki caf Allah ya sauwake! Ya ma samo amaryar sa kafin dare ya masa,ta yi gatsine. Wuce ciki kafin na bata mi ki rai! Sakarya kawai! Hajjo ta cije ta ki motsawa,ya ce ba da ke na ke magana ba Hajjo? Ta na buga kafa bakin nan cure ta shige ciki Ayuba na biye da ita,suna shiga Jama’a su ka fara waya taba amarya? Ta mu su banza,kai tsaye gun Inna ta shige,ta tadda ta tare da Indo,kan ciyar Inna ta zube ta na ihu an hana ta zuwa fati! Ayuba ya biyo ta ya na fadin kiyi kukan jini ma ba inda za ki je! Indo ta ce ayya mana Ayuba ka bi ta a hankali dan Allah! Ayuba ya ce anki a bita din,yarinya ace har aure an daura ma ta amma ta gaza hankali,ba dan Allah ya hada mu ba ai da an tafka abun kunya,ganin ta fa na yi za ta gidan sun Garbati wai Mairo ta gayyace ta fati. Inna ta kama baki,ai kuriciyar kenan Ayuba,kuruci dangin hauka,shi ya sa gaba daya hankali na ya gaza kwanciya kan lamarin auren nan wlh,yi shiru auta,Allah zai zama gatan ki. Indo ta ce amen,amma ba a kyautawa Hajjo ba gaskiya,ko nima sai da na kai shabiyar aka min aure,bare kuma Hajjo da ta ke shabiyu. Ayuba ya aje langar a gaban su,ya ce da Indo kar dai ki bari Baba ya ji ki yarinya,za ki yi bayani. Ya sa kai ya fita Indo ta na fadin ya ji ni din,ba gaskiya na fada ba!Inna ta ce kul Indo,ban san tsaurin ido. Indo ta ce na yi shiru Inna,Inna ta duba fuskar Hajjo sai gani ta yi ta yi bacci,ta gyara ma ta kwanciya zuciyar ta cike da tausayin ta. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [16/10 21:44] .: [7/24, 11:57 PM] Salmah Ateeku: [12:22am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣ Biki dai gadan gadan yin shi ake,da daddare aka yiwa amarya kunshi. washagari aka yi jere da wuni,da magrib aka fara shirin kai amarya sai aka nemi Hajjo aka rasa,da kyar Ayuba ya gano ta cikin duhun bishiya ta na ta shan mangaro,ya daka ma ta tsawa ta sauko. Da gudu ta shige dakin Inna,jama’ar biki sai dariya su ke. Ta na shiga ta ga an aje kayan sallan ta bisa gadan Inna,Indo ta ce maza ta sanya. Hajjo ta daka tsalle ta na fadin Indo yau sallah ne? Ashe ban sani ba! Ita dai Indo banza ta ma ta,jiki na rawa sai da ta yi tik sannan ta sanya kayan sallan na ta,ta bazama za ta fita Indo ta ruko ta ta na fadin ina kuma zaki amara? Baki washe ta ce su Mairo zan je na nunawa dama Inna ta ce na fi su a kyawu!Indo ta ce ba sai kin je ba,dama mu ma gidan zamu. Hajjo ta ce Allah? Za ku da ni? Indo ta ce eh dole mu je da ke,ungo mayafin ki sanya,Hajjo ta karba za ta ci dammara,Indo ta dakatar da ita,ah ah Hajjo ba haka ba,a ka za ki rufa,ta karba ta rufa ma ta ruf,Hajjo ta yi saurin yayewa,ta ce wayyo Allah,alquran tsoro na ke ji! Indo ta ce ke fa shasha ce Hajjo,Allah ki ka ci gaba da kullar ni buge ki zan yi! Inna ta shigo ta na fadin yi ma ta a hankali Indo,auta yi hakuri ki yafa,Hajjo ta ce toh Inna,ke ma da ke za a gidan su Mairo? Inna ta kwauda kai ta ce ah ah. Hajjo ta ce saboda me ya sa? In ce ba iyalle ta aiko mi ki da cingam ba….? Kafin Inna ta ba ta amsa sai guda ya fara tashi,da alama dai masu daukan amarya sun zo,yayye da kannan Inna su ka shigo suna fadi toh Hajjo Allah yayi lokaci yayi,maza Innar ki ta karasa mi ki fada ku yi sallama kuma sai watarana! Inna ta kwauda kai da alama kuka ne ya ciyo ta,Hajjo ta ce fada? Toh me na yi da za ta min fada? Daya daga cikin yayyen Inna ta ce nasiha za ta miki,maza karasa gefan ta ta mi ki. Hajjo ta karasa wajan Inna ta ce Inna yi min nisihan toh za mu tafi…..Inna ta fashe da kuka! Hajjo ta ce laaaa toh menene eh? Ke ma so ki ke ki bi mu? Yo ki biyo mu mana ko Baba zai yi fada? Da Allah ki bar kuka Inna wlh zan rago mi ki kwili da kunun zaki! Gaba daya dakin ba wanda be tausaya mu su ba,ita ko Indo tini itama ta sa na ta kukan. Yayar Baba ce ta kamo hannun Hajjo ganin Innar ba ta da niyar yiwa Hajjon nasiha,har sun kai kofa Hajjo ta fizge ta dawo da gudu ta fada jikin Inna ta na fadin ni ma na fasa zuwa alqur’an na fasa!nan fa ana jan Hajjo Hajjo na dada kamkame Inna da kyar aka samu aka bambare ta,Inna na fadin Allah ya mi ki albarka,Allah ya zama gatan ki,Allah ya sa ki je a sa’a Hajara. Hankalin Hajjo ya tashi,ko by h da su ka kai kofar gida sai ta cije,aka yi aka yi ta saki kofa ta fito ta ki,ana haka sai ga Mudi,ko da ya ga halin da a ke ciki,ya kuma san halin Hajjo,idan ta kafe ko Baba be iya tankwasa ta,sai kuwa ya cincibi Hajjo,ta na buri ta na ihu,mata su ka sa su tsakiya,aka nufi gidan su Garbati,gaba daya ta cika kunnan jama’a da ihu. A haka aka shigar da Hajjo har kuryar dakin mijin ta. Mudi na dire ta ya daka ma ta tsawa,amma ko a jikin ta,ita dai ya mai da ta gidan Innar ta! Da dai ya ga jan ido ba zai kai shi ko ina ba sai ya shiga rarrashin Hajjo tare da alkawarin zai mai da ta gun Innar sannan ta yi shiru,su Yayyen Inna da Baba su ka sami damar damkata amana gun uwar mijin ta wato Iyalle,shi ko Mudi gida ya dawo abun sa. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [12:29am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 7⃣ Tafiyar su Indo ma fa sai da dabara,sai da su ka mata wayo wato su ka ce bari su leka makota suna zuwa,ganin yayar Mairo tare da Mairon sun shigo dakin na ta sai ta yarda su ka tafi,ta saki jiki suna ta hirar su kamar ba ita ce mai kukan dazu ba. Kande wacce ta ke sa’ar Indo amma ita bazawara ce ta ce da mairo ta taya Hajjo hira ta na zuwa. Da fitar ta Hajjo ta ce yarinya kin ga kayan salla na!ai Inna ta ce na fi kuwa a kyawu,wai ina amaryar Garbatin na? Mairo ta ce lalle ma ke Hajjon nan! Ga ba ki nan ba! Ba ki da wayo da ki ka yarda aka aura mi ki yaya na Garbati! Hajjo ta harare ta,waya ce mi ki aurar Garbati na yi? Allah ya sitiri bukwi! Mairo ta ce yarinya an sha ki ai,ni ce fa na sa Jummala ta fasa auren Garbati,wlh shekaran jiya da safe dan ban sani ba na dan tankwabar ma sa da kokan safe ya kamani yay ta jibga,ni kuwa da dare yayi na je wajan Jummala na fada ma ta gaskiya. Cikin kaguwa ta ji Hajjo ta ce wani gaskiya? Mairo ta ce aw kema ba ki sani ba ki ka yarda aka aura mi ki shi? Hajjo ta ce wlh Mairo za mu yi fada idan ki ka kuma cewa an daura min shi! Ni ki fada min dallah! Mairo ta ce hmmm ai Garbati mugu ne,wlh mugun ma na gaske,dan ya sibirbide ki ba wani aiki ba ne,gashi ba ya wanka da buroshi sai ranar juma’a,warin Garbati sai ya kar mutum har lahira…Hajjo ta toshe hanci ta na fadin Allah da gaske Mairo? Mairo ta ce kwarankwatsa da gaske na ke,idan karya na ke ki kwace yar babyn roba na,ke ki ma tambayi Kande ki ji! Kande ta shigo,Mairo ta ce yauwa dan Allah Kande Garbati ba mugu ba ne? Ai har kema bugu ya ke ko? Dan Allah ba baya wanka ba ba…..ke Mairo! Kande ta katse ta,ba ki da hankali ko? Na kuma ji sai na hada ki da iyalle,kai wannan diya akwai surutu,karya ta ke mi ki Hajjo kin ji ko? Hajjo ta dubi Mairo,Mairo ta kifta ma ta ido tare da kada ma ta kunne alamar dai Kande karya ta ke. Muryar Garbati su ka jiyo daga waje,Kande ta ce ga angon nan ke Mairo ta shi mu tafi,Mairo ta tashi da sauri Hajjo ma tashi ta yi za ta biyo su,Kande ta ce ah ah ai ke Hajjo nan dakin ki ne,ba ki san Garbati mijin ki ba ne? Hajjo ta yi zuru zuru da ido,ta ce wallahi karya ne,ba miji na ba ne! Kun ga na ce ba na so…ni gun Inna zan tafi….kai su waye cikin dakin nan? Muryar Garbati suka ji ya na maganar nan na shi kamar ya na yi da sama,tini jikin Hajjo da Mairo ya fara bari! Labule ya daga ya ce ke kande azo a wuce daki ko? Su ka kama hanya sim sim za su fita Hajjo ta ruke Mairo,Garbati ya dube su ya ce ke Hajjo! Sau ta! Ki sau ta na ce! Kar ki bata min rai na! Jiki na rawa ta sake ta,Mairo ta fice da sauri,Hajjo ta gama tsorata da Garbati,ta bi bayan Mairo ya daka ma ta tsawa,ke wai ke ina za ki? Koma ciki dallah! Jiki na rawa ta yi baya ta na wayyo Inna,ni gida zani! Ta daga ido ta dubi Garbati,ya kusan yin biyun ta ma,ga tsayi ga jiki! Garbati ya ja kofa karaf ya rufe,ya daga fitar acibulbul da ke ci tsakar dakin ya haska fuskar Hajjo,murya a sama ya ce kan uba! Ku ga kwailar da Baba ya aura min dan Allah! Hajjo dai gaba daya ta gama tsorata,dan jikin ta har bari ya ke,gani take Garbati rufe ta zai yi da bugu tinda dai Mairo ta ce halin sa kenan! Kamar daga sama ta ji ya ce tube! Ta yi zaton kunnan ta ke zagi dan haka ta ce iye? Ya ce ki tube rigar ki na ce Hajjo! Kar ki bata min rai na!!!!!!!! Jiki na rawa a gigice Hajjo ta ce wayyo Allah wayyo Inna wai fa na tube! Wlh ba zan tube ba! Ke Hajjo! Wlh zan buge ki! Kar ki bata min rai na!!! Ya dada ma ta tsawa,ya yiwa Hajjo kwarjini,ba shiri sai ga Hajjo ta cire rigar ta. Garbati ya dada haske ta,ya ce ahaf! Dama wlh na san kwailace Baba ya aura min! Ku duba ku ga ko nawa ya fi nata! Dirgan dangin ma yanzu ta fara! Dallah mai da rigar ki! Yo ni me zan yi da ke yanzu! Wlh Baba ya bata min rai na,ki sa rigar na ce!!! Jiki na rawa ta mayar da rigar,ta fara shirin fita,ya ce yo ke ina zaki? Ta na kuka ta ce gun Inna zani!! Ya ce Innalo ba Inna ba! Haye can ki kwanta! Ya ma ta nuni da karamin gado,ta ki hawa,ya ce kar ki bata min rai na!!!!! Ya daka ma ta tsawa,jiki na rawa ta haye gadon ta na kuka,ya dada ma ta wani tsawar ki min shiru kwaila!!!ko tarin ki ba na son ji!!!Hajjo ta sa hannu ta toshe bakin ta tana ta ajiyar zuciya,shi ko Garbati gado mai rumfa ya haye,ba tare da ya cire babbar rigar jikin sa ba,ko min ti biyar be yi ba ya shiga numfashi kamar ba mutum ba,bacci yayi gaba da shi… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [12:33am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 8⃣ Jin munsharin sa ya sa Hajjo saukowa,cikin sanda ta nufi kofa,ko da ta ja sai ta ki kam ko motsawa kofar ta ki yi,Garbati ya sakace,gashi sakatar can sama ne ko ta taka kujera tsayin ta ba zai kai ba. Nan ta durkushe ta na kuka amma a hankali gudin kar Garbati ya ji ya jibgeta,a haka bacci ya sace ta. Washagari sai karfe takwas rana ta fito Garbati ya tashi,ko sallar asubahi dama ba ya tashi,sai gari ya waye tangaradau ya ke yi,ko da ya Hajjo kwance a kasa bakin kofa sai ya tsallake ta abun shi cikin nuna ko in kula yay ficewar sa. Bayan kusan minti talatin cikin bacci ta jiyo muryar Mairo ta na fadin Iyalle na. tafi dandali sai na dawo!!! A firgice Hajjo ta tashi,ta ma manta inda ta ke,ita ma ta fito a guje ta na fadin ke Mairo tsaya ni mana dallah!Mairo tace tsaya ta na fadin toh ki yi saurk ki wanke bakin ki da ido mu tafi dan wlh Garbati ya na ciki ya na shan koko,cikin sauri Hajjo ta dau buta tana fadin toh Mairo….gidan ubanwa za ku?muryar Garbati suka ji kamar daga sama,Hajjo ta saki buta ya fadi kasa hannu na rawa. Ya nuna Mairo da yatsa ke zan ci uban ki Mairo,ba ki san Baba ya aura min ita ba? Iyalle! Ke Iyalle! Sai ga mahaifiyar su Iyalle biye da ita Kande ce sun fito daga daki da sauri dake tsakar gidan daya ce,ba wani girma kuma gare ta ba. Iyalle ta bi su da kallo ta ce kaka an kayi Garbati? Garbati ya ce wlh Iyalle ki shiga tsakani na da mairo,yo ban da rashin mutunci Hajjo fa ta gayyata su ke dandali,har da ta yo sauri ina ciki! Iyalle ta ce ke Mairo ba ki san ita Hajjo matar aure ce ba? Cikin gunguni tace yo ni na ce ta biyo ni? Ba ita ta ce in jira ta ba! Karya ta ke,makaryaciya!Garbati ya katseta,Mairo ta murguda baki tace ba dai ni ba! Hajjo kuwa tini ido ya kawo ruwa. Garbati ya yunkura zai bugi Mairo Iyalle ta hana shi,ta ce Mairo je ki abunki,haka kawai akan wata ba za ka dakar min diya ba Garbati!Garbati ya ce wlh Iyalle ke ki sa yarinyar nan ta na dada rai na ni,Mairo ta juya za ta fita,Hajjo ta bi ta,ina za ki? Ya daka ma ta tsawa sai kuwa ta sa kuka. Iyyalle ta ce ni dai ba za ka bugi diya ta ba,je ki abunki. Hajjo ta na ji ta na gani Mairo ta fice,Garbati ya fizgo hannun ta ya wulga ta daki ya ja ya rufe ya na fadin za ta dawo ita ma ta sa me ni ne. Iyyale ta ce in ka taba Mairo sai na bata ma ran ka! Ta dubi Kande shige mu tafi kin ji! Su ka shigewar su ciki. Garbati ya fice shima ya huci,ita ko Hajjo inda ya jefa ta nan ta durkushe ta na ihu,fadi take na shiga uku na lalace!wayyo na shiga uku wayyo Inna! Su Iyalle da kande suna ji su ka mata banza,har ta gaji ta yi shiru,sai ga Kande ta shigo dauke da kwanan sha ta aje gaban Hajjo,ta ce ga Koko da kusai inji Iyalle. Hajjo ta ture ta ce ba na so,ni gidan mu zani,ni wajan Inna zani! Kande ta dube ta ta ce yarinya zancen ki ke so,ta juyo tai fitowar ta. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [12:38am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 9⃣ Hajjo tana nan kwance ta jiyo sallamar Indo,da.sauri ta tashi ta na fadin yauwa Indo sai yanzu ki ka dawo wlh sai na hada ki da Inna! Ta bude kofa ta fito,sai ta hangi Indo cikin dakin Iyalle suna gaisawa,ai kuwa ita ma Hajjon kofar dakin ta nufa,ta tsaya hannu a kugu ta na fadin ku gama gaisawa ki fito mu tafi dan Allah! Iyalle ta ce ina ruwan Hajjo,har yanzu ba ta fahimci ta girma ba,ki dai ma ta fada Indo,Indo murmusawa ta yi ta na duban Hajjo,cikin ranta kuwa sanyi ta ji dan daga ganin Hajjo Garbati be ma ta komai ba,ashe dai ya na da tunani. Indo ta nisa ta ce zan ma ta Iyalle,za ta gane inshaAllahu. Iyalle ta ce toh amen dai. Ta fito hannun ta dauke da jakar buhu,ta ja hannun Hajjo,ko da Hajjo ta ga Indo na shirin shigar da su dakin ta sai ta ce Indo wlh ni ba na so na kara ko minti biyar ne a gidan nan,dan Allah kawai mu tafi kafin Garbati ya dawo wlh shi ya hana ni zuwa dandali,kuma dan iska ne wlh,jiya fa da daddare cewa ya yi na tube….shhhh! Indo ta toshe mata baki,dan Allah Hajjo ki rufa min baki,muje dakin ki bani labarin kafin mu tafi din. Hajjo ta ce ina gama baki lbry za mu tafi yasin! Indo ta ja ta suka shige dakin. A tsakar daki Indo ta ce yanzu Hajjo dubi dakin nan da kyau,ki ga yanda aka jera langa tuwo da miya,jibi akwatin karfen can,dubi sif din can fa,dubi gadan can mai rumfa ga kuma na ki an hado mi ki da shi,duka na ki ne Hajjo,ke ma kin zama ‘yar gata an mi ki aure kamar yanda ni ma aka min..Hajjo ta zumbura baki ta ce yo ni ban ce a min auren ba ai! Indo ta ja hannun ta suka zauna bakin gado,ta ce ki na nufin duk damin kayan nan ba kya so Hajjo? Hajjo ta ce ina so mana,amma ni Garbati ne ba na so,wlh jiya sai da ya yay ta min fada,ce min yayi na tube riga ta…nan ta kwashe yanda su ka yi da Garbati ta fada ma ta,Indo ta saki ajiyar zuciya jin yanda ta kasance tsakanin su,ta kuma kwabeta da kar ta fadawa kowa ko da kuwa su Mairo ne za su yi ma ta dariya da ihu da gori,ta ga dai su ba a musu aure ba,komai ya faru kar ta bari kowa ya ji,batun komawa gida kuma babu,nan ne saban gidan ta shi ya sa ma Inna ta ce ta kawo ma ta sauran kayan ta,ga su cikin buhu. Hajjo ta dubi kayan ta kalli Indo ta ce wai shikenan an min aure ni ma zan ta haihuwa kamar yanda ki ke yi? Indo ta ce eh idan lokaci yayi za ki haihu,ke ma ki sami katuwar bebin ki da ta fi ta roba. Hajjo ta daka tsalle ta ce wayyo farin ciki,wlh da ko sai na yiwa su Mairo kambo,ba zan na ba su dani ba yasin! Indo ta ce dama mana,da ke sai abun ki babu mai taba mi ki,har fa kudin cefane za a na baki,da kan ki za ki na girki abun ki,idan kin so ma sai ki na toya wainar kwai. Hajjo ta mayar da mugun yawu ta ce Allah Indo? Indo ta ce sosai ma kuwa,can ba kwanan abuncin ki bane? Hajjo ta dubi kwanan da Kande ta ce eh wai ni kande ta kawowa,Indo ta tashi ta dauko ta tisa Hajjo a gaba,ta na ci ta na mata dan nasihohi cikin dabara dan a samu dai ta zauna dakin mijin ta Garbati… DEDICATED to The Women OF Virtue💁👰🙋(group) [12:43am, 5/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣0⃣ Shi ko ango Garbati kai tsaye wajan abokin sa Nuhu ya wuce,ya tadda shi cikin dakin sa kaca kaca kamar ba mutum ke kwana ciki ba. Nuhu na ganin sa ya fara ango ango ango ka sha kamshi….! Garbati ya zube kan katifa ya na fadin yo wani kamshi na sha Baba ya aura min kwaila! Ai wlh an bata min rai na! Jummala ta cuce ni,wlh kwaila Baba ya aura min,kai da ta tube jiya ko ni na fita awk yasin ni da na ke na namiji….hahahahahaaha! Nuhu ya sheke da dariyar mugunta,yo in ban da abun ka Garbati me za ka gani jikin Hajjo? Kasan yarinya ce danya sharaf! Garbati ya buga kafa! Ni wlh Nuhu Jummala ce ta cuce ni! Ta bata min rai na! Nuhu ya ce ka ce dai kai ma ba ka gama lalube yan matan tasha ba!hahaha ashe da saura! Garbati ya ce indai Hajjo ce mata ta yanzu na fara lalube yan matan tasha! Ta shi ma muje dan Allah! Bazan iya jira gari yayi duhu ba! Nuhu ya tashi har yanzu be dai na dariyar ba,ya dau wata rigar sa,dan dauda har annakiya datti da jirwaye ta yi,ya zura,su ka fito ya ja kufar shago ya rufe,kai tsaye tasha su ka nufa…. Gidan su Garbati kuwa wuni Indo ta mata,sai da ta tabbatar Hajjo za ta iya zama sannan ta saki ranta,dama Inna ce ta turo ta saboda hakan,kafin Indo ta tafi yan uwa sun dan lekowa Hajjo,ita ko Hajjo tin da Indo ta ce za ta haihu ta saki ranta,dama yarinya ce mai san yara,gashi za ta na girki,kuma komai na dakin na ta,ai sai kuma lamari ya fara ma ta dadi. Indo ta sa ta yo wanka aka cancada ma ta ado,ta ce haka za ta na yi kullum tin da ita matar aure ce. Hajjo ta ce toooh,abun nema ya samu! Iyalle ce ta kawowa bakin Hajjo abunci,sai yaban ta su ke kuwa ta karrama su. Da la’asar sakaliya kowa ya kama hanyar gida,ko da Indo za ta tafi sai Hajjo ta fara shirin yin tsiya,da kyar ta lallaba ta,ta yarda ta zauna a daki shiru ita kadai. Da abun ya ma ta yawa sai ta zari mayafi ta ci dammara,ta yi sa’a ba kowa a tsakar gidan sai ko ta yi ficewar ta. A waje ta tadda su Mairo suna enter,ta ce ku da Allah zan yi,kun ji? Mairo ta ce yarinya idan Garbati ya kamaki ba ruwana! Hajjo ta murguda baki ni ina ruwa da shi,za ku yi da ni ko kuwa? Hanse ta ce za mu yi da ke mana,ai sai a fara daga fari,ta yi saurin daga hannu ta ce fess! Mairo ta ce sakan! Hajjo da Habi suka hada baki su ka ce los! Da kyar aka raba gardama Hajjo ta zama los din Habi ta biyo ta a baya,sai kuma sauran wasan suka zabi na su,ya dai danganta da wanda ya riga fada,sun kai su bakwai. Kan ka ce me,enter yayi enter,amma sai aka cinye Hajjo ta zama kariya,ai kuwa nan aka shiga ma ta waka…. “Wacece wacece?wacece Kariya,Hajjo ce Kariya! Ta yi cikin dan tsako ta Buye a gajeran wando Kariya!ku fada mana Ko kuna tsoran ta ne Yar ficika ta Alhaji Baba ta ci tuwo ta Na mana yanga….” Suna ma ta wakar ta na bin su za ta kama dan ta shafa kan su ta tsira amma ta kasa,gaba daya ta hada zufa,ko da Mairo ta gifta ta gaban ta sai ta yi kanta da gudu,idanu rufe ba ta ankara ba sai ji ta yi ta yi gware da jikin mutum,azatan ta Mairo ce,fadi ta ke yarinya na kama ki,ko da ta ga kafar namijj sai fa ta sha jinin jikin ta,ta daga kai a hankali,yayinda ta yi ido biyu da jajayen idon angon na ta Garbati….. DEDICATED to The Women OF Virtue💁👰🙋(group) [16/10 21:44] .: /25, 12:39 AM] Salmah Ateeku: [11:03am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣1⃣ Gaba daya rudewa ta yi,su Mairo ma su waka tini suka yi shiru babu wanda be tsorata da ganin Garbati ba. Cikin tsawa da daga muryar nan ta sa da ya saba ya ce ke Hajjo!Hajjo ta daura hannun ta biyu bisa kanta,ta cure gu daya a durkushe,tana jiran saukan duka,ya ci gaba da fadin uban me ki ke a waje sai ka ce shashasha! Kai ni wlh an cuceni! Yau sai kin gane kuranki yarinya! Ya fizgi hannun ta,Hajjo ta sa kara wayyo Allah Inna zai kashe ni! Cikin takaici ya saki hannun,a fusace yace wlh Hajjo kar ki bata min rai na,ki wuce mu tafi na ce! Hajjo ta ki ta motsa,shi ko Garbati ya gama kulewa,sai ya sunkume ta ya aza a kafada ta na ihu da bori,gaba daya warin dadti da gumi da ya ke ma kadai ya isa sata ihu,sai Mairo su ka sa ihu,wooooyiii an dauke ta,ya nufuso da sauri kowa yayi ta kansa,Mairo ta shige gida a guje,Garbati biye da ita,a tsakar gida su ka tadda Iyalle ta na tuka tuwan dare,dan ko dakin girki ba su da shi. Saura kiris Mairo ta sa ta bari ta tsallake ta a guje ta shige dakin Iyalle ta banko kofa garam! Iyalle na fadin wakika tsokano ke ko Mairo za ki lalata min kyaure…sai ga Garbati ya shigo,ya na huci ya saki Hajjo ta fadi gaban Iyyale sharaf kamar kayan wanki fuska cike da hawaye ta dada curewa. Kai Garbati ina ka samo wannan fitinanniyar diyar da aka aura ma ka? Cikin daga murya ya ce Iyalle! Iyalle ki bar ni na jibgi Mairo! Mairo daga daki ta ce yo ni ina ruwana! Ni na ce ta fito? Iyalle ta ce gaskiya Mairo ita daya ta fita abunta,ita wannan mata taka ita ya kamata ka jibga ba diya ta ba! Ina ruwan Mairo? Kande ta fito daga bayan gida dauke da buta,ta gifta gaban Garbati ta ce kwarai ko ni ma na ga fitar ta,sannan ta aje buta ta shige dakin Iyalle. Cikin takaici ya ke duban Hajjo,ya ce Iyalle,wai ya zan yi da yarinyar nan ne dan Allah? Ya zan yi ta daina fita kar fa watarana kuma uban ta ya zo ya ga abun da na gani yau? Iyalle ta ce aiki za mu ta jibga ma ta,duka aikin gidan nan ita za ta ke yi,ka ga ba ma za ta sami damar fita ba. Garbati ya ce Iyalle ita fa wannan babu abunda ta iya sai fitina,za ta iya aiki kuwa? Iyalle ta ce ba dai diya mace ba ce? An gama magana,koya ma ta za’a yi. Garbati ya saki ajiyar zuciya ya ce indai zan sami sauki a tula ma ta aikin,dan wannan ko dukan ta zan yi sai dai na daki kashi! Iyalle ta ce daga gobe ma kuwa. Ya dubi Hajjo cikin zafin nama ya dada cincincibar ta yay daki da ita,kan gado ya aza ta,tini warin sa ya game daki,Hajjo ta na so ta toshe hanci ta na tsoro,ya nuna ta da dan yatsa ya ce ki ka sake fita sai na jibgeki,shashasha kawai. Ya ja tsaki ya fito ya rufo kofar dakin,dama gashi tagar dakin yar karama,ga Garbati ya gume daki da wari,ga shi kuma ya ja kofa ya rufe. Ai ko da gudu Hajjo ta biyo bayan shi,ta ja kofa ta ki buduwa,tayi kuka,tayi kuka har da birgima kamar za ta shide. Sai bayan isha’i ya shigo,ya tadda har ta yi bacci wahala,be damu ya tada ita ta yi sallah ba ko ta ci abunci,ya tsallake ta nan inda take kwance a kasa bakin kofa ya dauko tuwan sa miyar kuka da ta ji daddawa,ya ci ya koshi,ya wanko hannu ba tare da kuskure baki ba,bare sauya kaya,tin babbar rigar jiya ce jikin sa,ya haye gado ya saki gabba da su labba ya fara munshari.. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [11:04am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣2⃣ Washagari da sassafe,kafin ma Garbati ya tashi Iyalle ta zo ta buga mu su kofa,tini Hajjo ta tasha ta na murje ido,shi ko Garbati da ko sallar asuba be tashi yayi ba da kyar ya tashi ya na gunguni,ganin ya nufo kofa Hajjo ta matsa da saurin ta,be ma lura da ita ba ya bude kofa ya na fadin wai menene Iyalle! Ita kanta Iyalle sai da ta ja baya jin yanda Garbati ke tashi,gashi da yayi magana sai ka ji kamar za ka sume. Iyalle daga baya baya dai ta ce Hajjo na zo tashi ta fara shirin hada mana karin kumallo ai ba kai ba. Ya fara ware ido,ke Hajjo,ya ki ki bita dallah! Dama ita Hajjo burin ta ta fita,da saurin ta ta fito,Garbati ya ja kofa ya rufe ya haura gado ya ci gaba da bacci. Iyalle ta dubi Hajjo maza wanko ido ki zo ki sa min hannu wata rana ma ke zan sakarwa,Hajjo da ke yarinya ce me san aiki,sam ba ta sa kiwa,bare kuma an ceto ta daga warin Garbati,ta ce toh,bara na yi sallah,banyi magariba da isha’i da asuba ba. Iyalle ta ce maza je ki dungura ina jira. Hajjo ta ce toh. Ta dau buta ta yi bandaki. A dakin Iyalle ta yi sallah wai gudun kar ta tada Garbati,wato Iyalle mace ce mai shegen san lallaba yaran ta,amma na wani ko oho. Ta na Sallah Alhaji Baso ya fara wai ina kokon ne? Iyalle ta leko ta ce ke ki fa yi sauri dallah,Mallam ina zuwa be sauka ba tukun. Da sauri Hajjo ta idar,ta na ganin Mairo da kande sai baccin su su ke,haka ta fita ta fara tular aiki ba kakkautawa,duk da ba ta iya ba,amma Hajjo akwai saurin dauka,wuyar ta a koya ma ta,shikenan. Ranar dai Hajjo ba ta sami hutu ba,hatta wanki ita ta yiwa Iyalle,ta na ta zuba ido ko Indo za ta zo shiru,tin tana kuka har ta fara sabawa da rayuwar da ta tsinci kanta,kullum cikin aiki,ta zame mu su kamar baiwa,ta ma fara tunanin Innarta ma ta yada ita,ga Warin Garbati na bata wuya duk da kowa da gadan sa amma daki daya su ke. Wasa wasa haka rayuwar ta ta kasance,gashi har ta cika wata dakin mijin ta. Iyalle ta tura Garbati wajan wani malamin sauro ya na karbar ruwan rubutu,wai dan ya kafe Hajjo,ya kuma mallake ta dan ta na jin maganar sa,duk daren Allah sai Garbati ya tisa ta gaba ya bata ruwan rubutu ta sha,idan ta ki sha ya nuna zai buge ta,haka dai sai ta karba ta sha,idan ta yi karfin hali ta tambaye shi na menene sai ya ce maganin dangana da hana yawo ne,tin abun ya na damun ta har ya zame ma ta jiki. Rannan ta hada zufa da tsakar rana ta na ta wanke wanke,ba kowa a gidan sai ita kadai,an tula ma ta aiki,kamar daga sama ta ji sallamar Indo,ta daga ido ta ga Indon ce,sai ta saki kwanan da ta ke wankewa ta zuru wajan ta a guje,tana fadin wayyo Indo sai yau za ki dawo! Ganin yanda Hajjo ta rame ta yi baki ya dagawa Indo gankali,har ta rungumeta Indo kallan ta ta ke,ta ce Hajjo sai ka ce da ke ake miya wannan rama taki? Ina mutan gidan? Hajjo ta ce sun fita,daga ni sai baban su Garbati,kuma sun hana ni fita,Garbati ya ce duk randa na sake fita sai ya kusan kashe ni. Kashe ki? Indo ta kama baki,ta ja hannun Hajjo su ka yi daki,ga dai dakin tsaf da shi Hajjo ta gyara ko ina,sai dai kuma dakin gum ya ke da warin Garbati,Indo ta zauna tare Hajjo bakin gado,ta ce Hajjo ya dakin na ki wari haka? Hajjo ta ce kayan wankin Garbati ne,idan ya sa kaya ranar juma’a baya sauya su sai wata Juma’ar in yayyi wanka dama juma’a juma’a ya ke wanka,toh kayan na sa can bisa kyaure su ke warin…. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [11:04am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣3⃣ Indo ta dafe kai ta ce hoo Hajjo zama da kazamin miji sai hakuri,Hajjo ta ce wlh ba na san shi Indo,na fi san zama da Inna ta,dan Allah ki mu su magana su bar ni na koma gida. Indo ta ce ki yi hakuri Hajjo,ki yi hakuri,sai da na biya ta wajan Inna kafin na zo,ta fito da kayan kamshi,su kananfari,jitta da dai sauran su,ta mikawa Hajjo ta ce ga tsarabar Inna. Hajjo ta ki karba,ta ce Inna ba ta so na,ta ki cewa a mayar da ni ta kuma ki zuwa. Hankalin Indo ya dada tashi,nan ta ci gaba da ma ta bayanin Baba ne ya hana Inna zuwa,ita din ta na kewar ta,sannan ta hakura ta karba. Indo ta tambaye ta ya zaman ta a gidan,ta na jin dadi kuwa? Nan ta kwashe komai da take ciki,har da ruwan rubutun da Garbati ya ke bata,Indo ta ce oh ya Allahu,Allah sarki Hajjo shi ya sa na ga kin zama shiru shiru haka,asirce ki ya ke,so ya ke ya maisheki baiwar sa nan gaba,kai wannan akwai azzalumai,nan gaba ya baki kar ki sha,ki faki idon sa ki zubar,kin ji ko? Hajjo ta gyada kai alamar eh. Indo ta ce wannan duk aikin ke kadai ki ke yi Hajjo? Wlh da sake,da gida zani amma na fasa wajan Inna zan koma dole a kwatar mi ki hakkin ki! Tashi mu je na taya ki aikin! Hajjo ta ce laaa zan iya,ai har na fara sabawa,har fa girki na ke,da na sa hannu na ke gama komai. Cikin tausayawa Indo ta ce Hajjo Allah ya zama gatan ki,mu je na taya ki dan Allah. Hajjo ta wuce Indo biye da ita. Ta sa ma ta hannu su ka gama aikin gidan tas. Kamar yanda Indo ta fada,wajan Innar ta koma,jin halin da Hajjo ta ke ciki ran Inna be so ba,amma sai ta buye ta ce in banda abun ki dan an sakarwa Hajjo aiki wani abu ne? Hajjo diya mace ce,aiki ga diya mace ai taimako ne,kin ga za ta tashi a kwararriyar mace mai himma,kuma zancen asirce ta Indo ba su isa su yi ma ta abunda Allah be kaddara ba,wannan shiru shirun da ki ka ga Hajjo ta zama wlh adduar uwa ce,nutsuwa ta ke kasencewar adduar da na ke ma ta na Allah ya nutsar min da diya ta gidan mijin ta,adduar iyaye ga ‘ya’yan su karbabbiya ce,dan ko asirin Garbati ya ci Hajjo,to kadan zai yi tasiri kanta,zan kuma ci gaba da ma ta addua,kuma ki na yawan zuwa ki na duba ta dan Allah,ba komai ai diya mace dama da aiki aka san ta. Jiki a sanyaye ta ce toh Inna,Allah ya sa mu dace,Inna ta ce ameen,Allah ya ci albarka. Indo ta ce amen,gami da mikewa ta ce Inna bara na koma toh. Inna ta ce a sauka lfy,Allah ya tsare,ta ce amen amen. Washagari da wani irin matsanan cin ciwan mara Hajjo ta tashi,haka a daddafe ta dinga yin aiki,duk da Iyalle ta lura da haka,sai ta yi kamar ba ta gani ba,sai Mairo ce ma ta zo fita dandali ta ga Hajjo durkushe gaban murhu ta ce ke Hajjo mene wai? Baki da lfy ne? Ta dago idanun ta sun kada ta ce Mairo kasan ciki na ciwo,Mairo ta ce sannu toh!ta kama hanyar ta ta fice. A haka tai ta fama da hura wuta ta na gyarawa Iyalle har Iyalle ta gama girkin ta,Hajjo ta yi shara ta yi wanke wanke… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [1 [16/10 21:44] .: 05am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣4⃣ Ta na gamawa ta koma daki ta kwanta,ciwo ya ki ya barta,daga bisani kuma ta ji kamar wani abu na fita daga jikin ta,ta nan kwance ta ki motsawa sai ga Kande ta shigo ta na fadin Hajjo wai me ke damun ki ne? Hajjo ta ce kasan ciki na ke min ciwo,yanzu na ji kamar wani abu na fita daga jikina,kande ta ce mugani? Dan matsa na gani,ko da ta matsa Kande ta ga halin da Hajjo ta ke ciki,ita ma Hajjo sai a sannan ta gani,sai ta sa kuka. Kande ta ce menene na kukan? Ai al’ada ce,kowace cikakkiyar diya mace ta na yi,ke ma yau kin zama cikakkiyar diya ma ce,hukunci ya hau kan ki,ki bar kuka,ita dai Hajjo ta ki ta yi shiru,gani ta ke mutuwa za ta yi,da kyar Kande ta shawo kanta,ta ce auduga ake siya ake sawa,ko kuma kyalle,itama ba ta da audugar,Hajjo ta kawo kyalle mai kyau sai ta koya ma ta,cikin kayan Hajjo ta sami wani dankwalin ta,ta yanka,sai da ta kai ma ta ruwa bandaki,sannan ta gwada ma ta yanda za ta sa kyalle,dake ciwan diya mace aka ce na diya mace ne,Kande ba ta nuna kyama ba,taiwa Hajjo kara kafin ta fito ta cire zanin gadon da Hajjo ta bata ta wanke ta shimfida ma ta wani,sai da ta tabbatar Hajjo ta yi tsaf,ta ba ta Panadol sanan ta ce da Hajjo ta kwanta kafin Garbati ya dawo sai ta tambaye shi ya bada kudin auduga ta siyo mata,Hajjo ta na fama da ciwan mara,ta ce ma ta toh kawai,idanu runtse. Ko da Garbati ya dawo Kande ta fada ma sa halin da Hajjo ke ciki,ya ba da kudi ta siyo ma ta auduga,sai ya kalle ta yace yo wani kudi zan ba ki? Ina na gan sa? An fada mi ki tsintar su ake a kasa? Ta yi kunzugu in za ta yi,idan kuma ba za ta yi ba tai ta zama haka,kar fa ki matsa min Kande,dallah bace min da gani. Cikin takaici Kande ta tafi,ta na Allah ya sauwakewa matsolo. Ya ce kar ki nemi ki zage ni sai na kwade ki wlh! Kande ta yi tafiyar ta abunta. Da Hajjo ta tashi,sai Kande ta ce da ita idan akwai zani ta kawo ta yayyanka ma ta,sai ta ke amfani da shi tin da audugar ba ta samu ba. Duk da ba ta wani sitirar arziki,wani zanin ta ta bayar,Kande ta yayyan ka,ta ce da ta ji ya jike ta sake wani,Hajjo ta ce toh,ta yi godiya. Ranar dai a takure ta wuni,Allah ya so Iyalle ta daga ma ta kafa ba ta kara ma ta wani aikin ba,shi ko Garbati bin ta ya ke da kallo kawai,ashe wannan yarinyar ma ta cika diya mace,lalle ya kusa dai na kawar da kai ya na shuka dusa kullum ba riba. Kwana biyu Hajjo ta daina ciwan mara,ta dan fara samin nutsuwa,kuma yanda Kande ta koya ma ta hakan ta ke yi,gaba daya wasa da su Mairo ya fita da ga kanta,ita yanzu kullum lissafin ta shi ne wani aiki za ta fara,wanne zai fi ma ta saukin yi. Ga tsafta sosai,ba za ka taba ganin kazantar Hajjo ba. Rana na hudu sai ta ga ya dauke,ko da ta fadawa Kande sai ta ce ta dan jirkin ta ta tabbatar ya dauke sai ta yi wanka,ta dai san yanda ake ko? Hajjo ta ce waye be iya wanka ba?ba dai a dirje jiki da soso da sabulu ba? Kande ta ce ba wannan na ke nufi ba,irin wanda addini ya koyar fa,wankan tsarki,Hajjo ta ce ayyo,dama akwai shi?ita ba ta taba ji ba ai,Kande ta yi mamaki,ko a islamiyar ku ma ba a koya mu ku ba?Hajjo ta ce ta allo na ke zuwa da ai,kuma aramma be taba koya mana ba. Kande ta ce toh,bari na koya mi ki,ba wuya ai. Nanan ta gwada ma ta,tare da ma ta bayanin hukunce hukuncen wankan. A ranar da ta cika kwana biyar,da daddare Ayuba da Garbati tage tafe,sun dawo ne daga gun matan matan tashan da su ka saba lalubewa,Garbati ya ce da Ayuba kai aboki na na fa yi hakuri alkura’an,dan haka wannan yarinyar Hajjo ta cika diya mace,tinda har ta fara jini…kai ta fara? Ayuba ya katse shi da tambaya. Garbati ya ce yasin. Ayuba ya kame baki cike da mamaki,ya ce caf Garbati na ga kokarin ka,ai da ni ne da tuni na afka ma ta! Ya da aure na zan je ina samin faci faci wajan yan tasha? Garbati ya ce kai dai bari ayuba,yau din nan kuwa,a daren yau za a yi ya ta kare,afka ma ta zan yi yasin! Ayuba ya ce atoh ko kai fa,haka su ka ci gaba da tafiya suna hirar su da karfi murya a sama,ko da su ka zo kofar gidan su Garbati sai Ayuba ya bashi hannu su ka tafa,kana ya ce kar fa ka bani kunya mutumi na,na san ka da himma,Garbati ya washe baki,ka dai jira lbry gobe,suna dariyar shakiyanci su ka yi sallama su ka rabu,Garbati ya shige gidan su,Ayuba ya kama hanyar shagon sa DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [11:05am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣5⃣ Hajjo na idda Sallar ta na isha’i ta yi baccin ta,da ke tin a jiyan da daddare ta samu ta yi wanka. Garbati ya shigo ya ja kofa ya sakace,ya jima a kanta ya na kallan ta,ya cire babbar rigar da ta yi kusan sati jikin sa ya wulgar a kasa,tini warin zufa ya gume dakin,ba wani nafila bare neman yardar ubangiji,ba lallami da lumana,ba tausayi bare soyayya,kamar yanda ya ce zai afka ma ta din,haka ko ya afka ma ta kamar dabba. Tini Hajjo ta fara neman ceto,tana kokarin kwacar kanta,tana ihu da kuka,Garbati ya sa hannu ya toshe ma ta baki,sai fa inda karfin sa ya kare……… Hajjo tinda Garbati ya tashe ta ta hanya mafi muni,har ya gama biyawa kansa bukata ya mingina ya fara munshari kamar rago ba ta rintsaba,ta ma kasa kuka da baki sai hawaye da ajiyar zuciya kawai,ga warin Garbati da ya addabe ta da ke gefen ta ya ke kwance,yanda ka san ya sami sa’ar sa haka ya gwada ma ta karfi,dan haka ta ma ka sa kwakkwarar motsi,dan ita kam jira ta ke kawai ta Allah ta kasance a kan ta,ta mutu ta huta. Idanun ta biyu,ba ta samu ta runtsaba har asuba ta yi Iyalle ta zo tashin ta yanda ta saba yi da an idda sallar asuba. Ta fara buga kofar ta na Hajjo! Ke Hajjo Allah ya yi dare gari ya waye,a fito aiki!Hajjo ta na fama da kanta ko motsawa ba ta yi,Garbati ne ya amsa ma ta cikin bacci,ya ce Iyalle Hajjo fa ba za ta iya ko motsawa ba,yau dai a barta ta huta. Iyalle ta ce a barta ta huta? Zancen banza zancen hofi! Wani hutu kuma Allah ya wayi gari? Yau ga saban salo! Ta ci gaba da buga kofa,Hajjo,kai Garbati tashe ta mana!!!! Iyalle! Na fa fada mi ki Hajjo ba ta iya tashi ba. Iyalle ta ce a wani dalili wai? Garbati ya ce Iyalle kin fa dame ni,tam! Na ce ka tada min matar ka kace ba za ta iya motsawa ba,dole na dame ka! Da ke Garbati gabo ne,da karfi ya ce Iyalle! Afka ma ta na yi jiya da dare,kuma na ma ta tilis! Aradu ko motsawa ba ta iya yi in kina musu shigo ki ganta!!!!! Shiru ake ji,Iyalle ba ta kara tankawa ba ta juya ta koma dakin ta,maganar Garbati ta rufe ma ta baki,shi ko Garbati ko ajikin sa ya ce Iyalle? Iyalle? Dama ai sai da na ki fada mi ki ki ka dage sai kin ji,kuma na fada kin min kunne uwar shego! Yo ai shikenan! Ya juya ya ci gaba da baccin sa,ba batun wanka bare kuma sallar asubahi. Iyalle ko ba ta sake waiwayen su ba. Sai da rana ta take sannan Garbati ya tashi,ya dubi Hajjo da ke kwance kamar ba kashi a jikin ta,ya ce ke Hajjo! Kin fiya raki wallahi,dallah tashi,kar ki bata min rai na!!Hajjo ta sa kuka,dama kukan kwance ya ke kasan makogoranta,maimakon ya tausaya ma ta,sai ma ya ja tsaki,mtsw yo kukan na menene? Kan ki aka fara? Idan kin yi mai isar ki kya tashi,ya kwashi kayan sa masu datti ya mayar ya fita ya na mika,Iyalle da Kande da ke zaune tsakar gida su ka kalle shi su ka kau da kai,cikin ko in kula ya dau buta,ya shiga yayi wanka dan sami tsarki ba tare da yayi na soso da sabulu ba,kayan nan na sa mai taddi dai ya mayar,ya fita abun sa ya na taku dai dai,gani ya ke daidai ya ke da kowa,sallar asubahi ma wa ya sani ko da azahar zai hada. Da fitar sa,Iyalle ta ce da Kande,Kande je ki gano yar mutane,Allah ya sa bai karta ba. Jiki na rawa Kande ta ce toh,ta shiga dakin da Hajjo ke kwance,duk da Garbati ba ya nan dakin be daina warin sa ba. Ta na yi tana dauke numfashi ta karasa gadon da Hajjo ke kwance sai kuka ta ke,ganin Kande kan ta,sai ta fara dan Allah Kande kira Indo,dan Allah kirawo Inna ta da Indo,cikin tausayawa da ke Kande bazawara ce,ta san halin da Hajjo ke ciki,bare kuma Garbati kan fanka ne mijin ta,da sauri ta ce toh. Ta fito ta fadawa Iyalle,Iyalle ta ce ai sai ki maza ki yi kiran Indon,Kande ta ja mayafi ta fice,ta bar Iyalle cikin zulumi,can sai ga Kande da Indo,sama sama su ka gaisa sannan ta shige wajan Hajjo,ganin halin da Hajjo ke ciki Indo ta rabka salati,ta na fadin sannu Hajjo,ki yi hakuri,girman kenan,diya macen kenan,ita dai Hajjo sai kuka. Da taimakon Kande aka hada ruwan zafi a daki aka dan gasawa Hajjo jiki,da ta dan ware sai aka kai ma ta ruwa bayi,da kyar ta ke iya tafiya,kamar mai koyan tafiya sai da Indo ta dan dafa ma ta,ta kai ta bayi,sannan ta barta ta yi wanka,Kande ta ce har da wanda na koya mi ki jiya za ki yi,niyar za ki banban ta kamar dai yanda na ce kin ji ko? Hajjo ta ma ta banza,Indo ce ta tsaya ma ta,sai da ta tabbata ta yi,ta kamo ta su ka dawo daki,ta taimaka ta shirya,da kyar ta yarda ta sha kokon da Kande ta kawo ma ta,ita wallahi gidan Inna za ta koma,Garbati zai kashe ta…. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [11:06am, 5/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭CIWAN DIYA MACE👭👭👭 1⃣6⃣ Indo ta barta ta na shan kokon ta je ta wanke zanin gado,ko da ta dawo sai ta tadda Hajjo ta sami bacci,ta gyara ma ta kwanciya,sannan ta yiwa su Iyalle sallama,ta ce ta bar yara gida. Hajjo ba ta tashi ba sai da la’asar ta yi,ko da ta ga Indo ta tafi sai ta sa kuka,gaba daya tsoran gidan ma ta ke,har abun ma ya fara kullar da su Iyalle,tin suna ba ta baki su ka ma ta banza,da ta ga dai ba mai rarrashin ta sai ta yi shiru. Ta fito ta na takawa da kyar za ta yi alwala,Mairo da ke zaune a tsakar gidan ta kwashe da dariya har da mirginawa,ta ce ke Hajjo! Kin ga yanda ki ke tafiya kuwa kamar yar kaciya yasin! Hajjo ta kalle ta ta daka ma ta harara,ta ce yarinya ke ma Allah ya sa a mi ki aure! Mairo ta tafa ta ce ai min din mana,sai mai? Ji ta da Allah! Ta dada kwashewa da dariya,Hajjo ta cije lebe,Kande ta fito ta na ke Mairo wlh idan ba ki dai na tsokanar ta ba sai na hada ki da Iyalle,kyale ta Hajjo,ba ta da hankali. Mairo ta fara gunguni,Hajjo ta gyada kai ta yi shigewar ta bandaki,ta na jiyo dariyar Mairo,Kande na kwabarta amma ta kasa shiru. Shiko Garbati tin fitar shi be dawo ba sai bayan isha’i,Hajjo na jin shigowar shi ta suri filonta ta fito duk da da kyar ta ke takawa sai ga ta tana sauri sauri,har karo ta yi da Garbati,ya na ke bakya gani ne? Ta ma sa banza,dakin Iyalle ta shige,kamar daga sama su ka ganta a kan su hannun ta ruke da filo,lfy Hajjo? Iyalle ce ta tambaya,Hajjo ta ce Garbati ne ya dawo,kuma wlh bazan sake kwana a dakin ba….sai ta sa kuka har da shassheka. Iyalle ta tashi tsaye yayinda ita ma Kande ta bi sahun ta,ita ko Mairo tini ta yi baccin ta. Iyalle ta ce ah ah ba a yi haka ba Hajjo,yi hakuri ki koma…..ke Hajjo! Tahooo, muryar Garbati ce ta katse Iyalle,labulai ya daga hannun sa ruke da aci balbal. Ganin sa Hajjo ta kara ciki da sauri ta buya bayan Kande. Garbati ya ce Hajjo ki taho na ce! Kar ki bata min rai na! Hajjo ta ce na ki na taho din,na ki,wayyo wlh kashe ni zai yi!!! Ta kamkame Kande! Iyalle ta ce da Garbati kai kuwa Garbati yarinyar nan ta tsorata,ka dan bar ta ta kwana a nan din mana. Garbati ya ce Iyalle! Wlh sai na hado ki da Baba! Ina aka ce mace ta na gudun mijin ta! Yo ina ya dace ta kwana idan ba dakin ta na sunnah ba! Ke Hajjo taho mu tafi na ce! Iyalle ta kame baki,ta ce Hajjo zo ki bi mijin ki…Hajjo ta kurma ihu ni wlh bazan bi shi ba,wayyo na shiga uku na lalace! Wayyo yau mutuwa zan yi!!!! Garbati ya na huci ya ce wlh sai kin kwana dakin ki!!! Yo toh menene amfanin aura min ita da aka yi! Hajjo ta ce bazan kwana din ba,ni ban ce a aura min kai ba dama,Garbati ya ce Hajjo! Kar ki bata min rai na,ke Iyalle ki ma ta magana mana! Iyalle ta ce ni da ka ce za ka hado ni da Baban ku? Ina ruwa na ban kuma sa baki,ga ka ga ita ai. Ya ce ke Kande turo ta nan! Hajjo ta kamkame Kande ta na ta ki ta turo ni din,ba za ta turo ni ba,ni wlh ban bin ka,mugu azzalumi. Garbati ya fusata da jin kalaman Hajjo,ya ce Hajjo kar fa ki zage ni!ke Kande matsa ki ga ai ba karfina ta fi ba,ya ture Kande saura kadan ta fada kan Mairo,Mairo ta farka ta na fadin wayyo Allah Iyalle a mafarkin ma Garbati ba zai bari na huta da bala’in sa ba! Ita duk ana ta mafarki ne,ganin Garbatin a kanta ya na shirin rarimar Hajjo ta yi gefe da rarrafe kar ya hada da ita. Da sauri ita ma Hajjo ta yi ta kanta,amma ina sai da ya caf ko ta ya daga ya aza a kafada,ta na ihun neman ceto. Iyalle fadi take kai amma Garbati ba ka da imani,ka bar yarinya ba za ka bar ta ba? Ya ma ta banza yayi ficewar sa….. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [16/10 21:43] .: 5, 12:42 AM] Salmah Ateeku: [5:40pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣7⃣ Dallah malama ki rufa ma na baki! Ya daka mata tsawa yayinda ya aje ta bisa gadan ta,ko a jikin Hajjo,maimakon ta yi shiru sai ma kudundunewa ta yi,ta dada daga murya,Garbati ya dube ta rai bace ya ce Hajjo! Na ce ki min shiru! Wai me na ce zan mi ki toh? Ko kina tunanin zan kara ne? Yo dallah ni ma mutum ne! An fada mi ki ke kadai ki ka wahala sokuwa kawai mai shegen san kanta! Ai dai wlh dan nima ba na jin dadi ne da sai kin bani hakkina in ya so na ga karshen gudu!ki min shiru Hajjo! Ya juya tura kofa ya sa sakata,sannan ya haye gadon sa yanda ya saba ba tare da ya rage kayan jikin sa ba. Sai mita ya ke wai an raina ma sa hankali,kan ka ce mai tini barci yayi awan gaba da shi,sai da Hajjo ta fara jin munsharin sa kamar kukan rago sannan hankalin ta ya kwanta ta dai na kuka,ta sauko cikin sanda ta yi kwanciyar ta bakin kofa. Haka su Iyalle ma,ko da su ka daina jin kukan Hajjo sai su ka yi kwanciyar su,ba Hajjo ba ko suma hakurin zama da garbati su ke. Hajjo ta yi sa’ar Garbati,ya kwashe kusan sati daya da dori ba tare da ya sake kusantar ta ba,tawarke,kuma ta cigaba da ayyukan ta da ta saba,duk da haka dai a takure ta ke muddin dare yayi,gani take zai iya sake zuwa ma ta. Ile kuwa ta na cika sati biyu Garbati ya dawo da jarabar sa,kuma ba ya tashi zuwa ma ta sai dare ya raba yanda babu mai ceton ta,tin ta na gudu dakin Iyalle ya na zuwa ya na dauko ta har ta ma dai na gudu,da gari na fara duhu gaban ta ke fara faduwa ta san lokaci ya kusa. Hatta Iyalle tausayin ta take ji saboda haka ta sassauta ma ta ayyukan da ta ke ba ta,Haka ta share watanni hudu gidan Garbati. Wata ranar alhamis Hajjo ta tashi da kasala da matsanancin ciwan ciki,ga shi sai ta na jin zuciyar ta na tashi,sam ba ta sha’awar cin komai,dan ko ta ci ma ba ya zama. Ta na kwance cikin dakin ta,gaba daya duniyar ta ma ta kunci,sai ga Indo. Sai da ta gaisa da su Iyalle sannan ta shigo dakin,a tunanin ta ma bacci ta ke,sai ta ga idanun ta biyu,Indo ta ce aw ki na ji na Hajjo ai na aza bacci ki ke,yau ba za a tarbe ni ba kenan,an gaji da gani na…. Hajjo ta tashi a hankali ta na murmushi ta ce haba ai ke na fi son gani duk duniyar nan idan aka dauke Inna,wlh ban jin dadi ne…Indo ta zauna bisa gadon,ta ruke hannun ta,ta ce me ke damun ki? Ko da Hajjo ta ma ta bayani,sai ta tambaye ta yaushe ta yi al’adar ta karshe? Hajjo ta kame baki,wannan abun? Ai tunda na yi be kara zuwa ba wlh,dama ana yi ne a tayi a tayi? Indo ta murmusa ta ce eh duk wata ya kamata diya mace ta ke yi. Hajjo ta ce ai kuwa ni sau daya na yi,kin ga wata uku kenan da yi ma,toh idan ba ka yi wata wata sai me zai faru? Indo ta ce ai dole kowani wata cikakkiyar diya mace mai lafiya ta yi,indai ta kai munzali,sai dai ko ba ta kai ba,ko kuma shekaru sun ja ta dai na,ko kuma ta na dauke da juna biyu… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [5:48pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣8⃣ Juna biyu!! Hajjo ta dafe kirji. Indo ta gyada kai ta ce haka Hajjo,tabbas ciki gare ki tinda kin ce ba ki sake gani al’adar ta ki ba. Farin ciki ne ya fara bayyana fuskar Hajjo dan ta na san ita ma ta haifo na ta yar jinjirar,sai kuma daga bisa damuwa ta maye gurbin farin cikin na ta,ta ce Indo ni ma haihuwa zan yi? Garbati zai daina zuwa guna duk dare tin da ina da cikin ko? Indo ta murmusa,haihuwa za ki yi Hajjo nan da wata shida ko bakwai inshaAllahu,ya danganta da watannin cikin na ki ayanzu,zance Garbati kuma ki yi hakuri Hajjo,ko wata diya mace da ki ka gani gidan ta haka ta ke rayuwa da mijin ta,ke ma za ki saba ne ai. Kwalla na fita da ga idanun Hajjo ta ce wlh Indo na kasa sabawa,kullum azaba kawai na ke sha,ba na so,ba na son yanda Garbati ya ke min. Indo ta dafa kafadar ta tace kar ki damu,ai ba a banza ba,aure bautar ubangiji ne. Hajjo ta share kwalla ta ce sai dai bautar ubangijin,bari na kawo mi ki ruwa,za ta tashi Indo ta dakatar da ita,ta ce ki na fama da kan ki,ban jin ishi,na hutasshe ki,Hajjo ta koma ta zauna,cikin tausayawa Indo ta ke kallanta,a dan kankanin lokaci girma ya kama Hajjo,gaba daya ta canza,ta yi sanyi kamar ba ita ce yarinyar nan mai tarin kuriyaciya da wasa ba,lalle aure shi ne maganin mace!ga shi kuma ta zo ma ta da mummunar lbry….na ce ya Inna? Tambayar Hajjo ce ta katse tinanin Indo,Indo ta yi ajiyar zuciya,ta ce toh,Inna dai ba lfy,kusan watan ta daya ta na fama…na shiga uku na! Hajjo ta dafe kirji,me ke damun ta? Tooh wa ya sani ne ma,wai fa dan kurji ne ya fito ma ta a wuya,da ya ishe ta da zafi ta bincine shi,shi ne fa ya zame ma ta ciwo,abu kullum sai rami ya ke. Wayyo Inna ta!Hajjo ta daura hannu biyu bisa kai,amma Inna ta kai wata ba lfy shi ne ko ki fada min Indo,Allah sarki,tashi mu je na gan ta dan Allah. Indo ta girgiza kai,kin gan ki ko? Shi ya sa ma Inna ta ce kar a fada mi ki,ta san yanzu sai ki daga hankalin jama’a,ina za ki ba ki tambayi mijin ki ba,ki jira ki tambaya sai ki je. Hajjo ta turo baki ta ce yasin ko ya hana ni bazan yarda ba,ai tintini na ke tambaya ya ki ya bar ni! Indo ta ce yi hakuri Hajjo wannan karan zai barki. Da kyar da lallami ta samu Hajjo ta hakura ta fara jiran dawowar Garbati,a karo na farko kenan da Hajjo ke jiran dawowar ta sa. Ba shi ya dawo ba sai cikin dare,ganin Hajjo ido biyu sai yayi tunanin shi ta ke jira akan abun da ya saba ma ta kullum kenan yau ba sai ya tada ita ba,ita ma ta na so kenan. Ya na murmushi,hakoran sa yalaye suka bayyana,ya ce Hajjo mata ta ta kai na,ni ki ke jira ko? Zuciyar ta daya ba tare da ta gane inda ya dosa ba ta ce eh,ya ce ina zuwa,bari na ci na dare,ya ja kwanan tuwan da aka aje dan shi,ya na budewa daddawa ta daki hancin sa,ya ce daddawa sarkin kamshi,ya shiga kai loma kamar wani mayunwaci,dan takaici ma Hajjo sai sauke kan ta tayi,gashi alahimis ne raban shi da wanka kwana shida kenan,sai gobe juma’a zai yi. Ya na gama cin abunci ya wanko hannu ba kuskuran baki,sai gashi ya dawo,ya na washe baki,ya sunkuyo ta hanyar dafa gadan Hajjo ke kai ya ce da Hajjo toh gani na zo toh toh gyara!ya dago ya na cire babbar rigar sa. Hajjo ta dan ja da baya jin yanda ya ke tashi,ta ce in gyara kuma? Magana za mu yi… Garbati ya ce Hajjo yanzun ga a gwiwa na ke,idan na gama biyan bukata ta ma yi maganar,ki gyara min mana karfa ki bata min rai na! Hajjo ta sa kuka,ya ce aw haka za mu yi? Ni ko ban fasawa. Yanda ya saba ma ta yau ma haka yayi,ya na barin ta tashi da sauri ta fice sai bakin rariya,nan taita amai kamar hanjin cikin ta zai fito,ta dau kusan minti goma a bakin rariyar sannan ta koma daki,ina tini gogan na ta yayi nisa da baccin,ta so ta tashe shi,amma sai ta sake shawara gudun kar a kuma,sai kawai ta fito ta yi wanka dan duk san da Garbati ya kusance ta ba ta iya bacci sai ta yi wanka komun dare,ji take kamar ita ma din warin Garbatin ta ke. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [5:55pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 1⃣9⃣ Da sassafe da amai Hajjo ta tashi,ta na durkushe gaban rariya,Iyalle da Kande tsaye kan ta suna ma ta sannu,Garbati ya fito ya na mika,ya ce Iyalle,wai me ke sa yarinyar nan amai ne haka? Iyalle ta dan taba bayan Hajjo ta na sannu Hajjo,ta dubi Garbati ta na fara’a tace ai Garbati girma ne ya hau kan ka,matar ka dai ta yi tsintuwa,eh juna biyu gare ta. Garbati baki washe ya ce ashe? Kai ashe ni ma na isa da,bari na je na fadiwa Nuhu,ni ba sa’an shi ba ne! Ya juya zai fita ba ko sallar asuba bare wanke ido,Hajjo ta tashi da sauri ta ce Garbati dan Allah ka barni na je na duba Inna ta ba ta da lfy. Ya juyo ya ce ke ki bari na dawo ma yi maganar da Allah! Yayi ficewar sa,Iyalle ta ce Ameenatu ba ta ji dadi ba ashe? Allah ya sauwake. Cikin kunci Hajjo ta amsa ma ta da amen ta shige dakin ta. Nuhu zaune gaban shagon sa Garbati ya zo ya same shi,ya ce kai mutumin nan ni fa jindadi ya same ni! Ya bashi hannu su ka taba,Nuhu ya mi ka ma sa asuwaki ya ce kai goge wannan bakin na ka da ke tashi kafin ka karni! Zama ya yi kusa da Nuhu,ya ce shege ai ni da kai duk kanwar ja ce!! Da lbry na zo dallah! Aje asuwakin yayi da dai ya ga Garbatin ba karba zai yi ba,amma fa suna magana ya na dan kau da kai,ya ce wani dadi kuma? Garbati ya ce ina fatawar da mu ka samu game da mace mai ciki? Nuhu ya ce aka ce sun fi armashi….Garbati ya daga kafa ya dire ya na wata irin dariya ya ce toh yasin Hajjo ciki gare ta!!!! Nuhu ya dara ya ce shege Garbati! Murnar ta ka ta za ka zama uba ne ko kuwa na matar ka ta dado armashi? Garbati ya shafa kyeya ya ce yo ni ina ruwa da wani zama uba! Ka ji wani dundurusu da kai,wake ta wannan,ni murna ta na dada jin dadi da zan yi ne,dan wlh bazan rangwanta ba sai na samu rabo na kan ta haihu,caf ga ni’ima daga sama ina zan yi wasa! Nuhu ya gyada kai,Allah sarki dadi inji barawan zuma,wlh ko ni ne haka zan yi,dan haka kai fa Allah ya kashe ya baka. Garbati ya ce wlh mutumina,shi ya sa ko karyawa ban yi ba na taso ka taya ni murna,kai dan uban ka kace a ma ka aure! Nuhu ya ce ahh ni tukunna dai,bari dai ka ci gaba da lasa min lbrn kafin na yi. Garbati ya bashi hannu su ka gaisa sannan ya ce abubuwa dai na wuce ka,ni kam bari na koma gidan,Nuhu ya masa a sauka lfy,dama Allah Allah ya ke ya tafi ko ya sha iska. A gidan kuwa Hajjo Alhaji Baso ta kaiwa korafi,dan ta ga take taken Garbati ba zai barta ta je wajan Innar ta ta ba,Alhaji Baso ya ce ya ko ji lbryn rashin lfyar na ta wajan Alhaji Mamman,ah ya kamata ta je,ina Garbatin? Hajjo ta ce ai ya fita,sai kuma gashi ya shigo,ganin Hajjo durkushe gaban Mahaifin sa ya fara menene toh? Baba me ta ce na yi? Alhaji Baso ya ce ba komai,ta dai tambaya ne za ta gida,dan haka ka barta ta tafi. Budar bakin Garbati sai cewa yayi toh Baba ka fada ma ta ta dawo da wuri,ka ga dai ciki ne da ita….Alhaji Baso ya ce an ki a ce din! Sakarai me ya hada cikin na ta da tafiya gida? Ciki ya shige ya na fadin kar ma ta dawo ne dare yayi ta ce ta gaji,atoh dan yasin bazan hakura ba….Alhaji Baso ya yi kamar be ji shi ba ya ce ta yi maza ta shirya ta tafi abunta kafin lokacin masallaci. Tana murna ta ce toh,ta tashi da sauri ta fara shiri,shi ko Garbati sai kashedi ya ke ma ra,karfa ta je ta zauna,dan shi fa bazai saurara ba. A haka a haka Hajjo ta samu ta fito…. Ko da ta shiga soran gidan su,ji ta yi tafiya ma bata lokaci ne,ta manta da auren da aka lika mata,da wani cikin da ake cewa ta na da shi,ta zura a guje ta na fadin Inna!! Inna ta!!!Inna!! DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [16/10 21:45] .: 3pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣0⃣ Inna na kwance tana fama da kan ta cikin uwar daka,gidan ba kowa su Mudi sun tafi makaranta,jin murya kamar na Hajjo ta tashi da sauri ta fito tsakar gida,nan ta ci karo da Hajjo,Hajjo ta daka tsalle ta rungumo Inna,ta manta da ciwan da ke wuyan na ta,sai da Inna ta ce hankali dai da ciwo bisa wuyan Innar taki,sannan Hajjo ta sake ta da sauri ta na fadin yi hakuri Inna,na manta ne wlh. Inna ta na fara’a take kallanta,ta ce Hajjo hankali,Allah sarki auta,zo mu shiga ciki. Ta ja ta suka shiga ciki,nan fa aka fara hirar ya bayan saduwa,Hajjo ta na mata mitar ta ki ta zo ta ganta gashi Garbati ya ki ya barta ta zo,wlh ita ba ta san shi,Inna ta ce ki yi hakuri diya ta,komai zai wuce ai da yardar Allah,babu abunda ya ke madauwami. Sai a sannan Hajjo ta ce Laa Inna ban ma gaishe ki ba,ina wuni? Inna ta murmusa ta ce Hajjo hankali,auta hankali,Allah sarki Hajara ta,Lfy lau diya ta,Hajjo ta ce ya jiki? Inga ciwan? Inna ta ce da sauki,ta sunkuya ma ta dan ta ga ciwo,ganin yayi rami sosai sai hankalin Hajjo ya tashi,ta ce Inna Baba ya kai ki kemis kuwa? Shi ne ya ke saki zazzabi wannan ciwan? Inna ta ce eh ya na sawa Mudi ya na raka ni ai,kar ki damu auta,ai ba wani abu ba ne. Hajjo ta ce toh,Allah ya sauwake. Ta cire mayafi ta aje gefe sannan ta haye gadan Inna ta ce Inna yau dai bari na dana gadan Inna ta,Inna ta ce maza dana auta. Sai da ta kwanta ta kwada ma ta kira,ta ce Inna! Inna ta na daga kasa ta ce na’am auta! Hajjo ta rufe fuska da tafikan hannun ta,ta ce wai kin ji wai ciki gare ni!!!! Inna ta kame baki,maganar ta ma ta ba zata,amma sai ta buye ta ce toh! Auta hankali! Allah ya raba lfy. Na ce dai kin rage hargowar nan taki,kin ga dai kin girma,ki na hakuri ki kuma bi mijin ki Hajjo,na ce dai ba kya ma sa wannan tsiwar ta ki ko? Ta ji shiru ba amsa,ko da ta dago ta duba sai taga Hajjo ta yi baccin ta. Inna ta shafa fuskarta zuciyar ta cike da tausayin Hajjo. Hajjo ta sha baccin ta koshi,sai da la’asar ta tashi,su Mudi da Ayuba sun dawo daga makaranta,sai tsokanar Inna Mudi ya ke,wai ta ga auta dai hankali ya kwanta,shi ko Ayuba Hajjo yay ta zolaya. Bayan ta ci abunci ta amayar ne Mudi ya fita ya siyo ma ta ‘ya yan itatuwa,ta na zaune cikin yan uwa cikin jin dadi ana hira ta na cin ‘ya ‘yan itatuwan da Mudi ya siya ma ta sai ga Baba nan kamar an jefo shi,ganin sa tini Hajjo ta nutsu,gaba daya fara’ar da ke fuskarta ta gushe,a tsorace ta tashi sannan ta koma ta tsugunna ta ce sannu da zuwa Baba, Rai bace ya ce ke ce da sannu ke da ki ka baro gidan mijin ki tin safe ki ka rashe a nan,toh gashi can kofar gida ya biyo sahun ki,ki tashi ki bishi. Idanun Hajjo yayi rau za ta yi kuka ta ce wlh Baba ba tin safe na zo ba,ga dai Inna nan ita ce sheda ta. Ke rufa min baki! Ya daka ma ta tsawa,ni ina ruwa da lokacin zuwan ki,maza tashi ki bi mijin ki! Hajjo ta sa kuka,cikin girmamawa Inna ta ce Mallam za ta tafin ne ai,amma dai ya bari ku gaisa ko? Wa? Da wa za a gaisa wai? Inna ta ce da kai wai Mallam. Baba ya ce ahab ka ji wani zance,wani gaisawa kuma za mu yi da ya wuce wanda mu ka yi yanzu,ke wuce ki tafi. Inna ta dauko mayafin Hajjo ta rataya ma ta,ta na fadin dai na kuka ki tafi gidan ki Hajjo,shi zai fishe mi ki alkhairi,Baba ya shige ciki ya na fadin na fito na same ki sai kin gane kuran ki. Hajjo ta ki motsawa,sai da Inna ta fara nuna ma ta bacin ran ta sannan ta yarda Mudi da Ayuba su ka raka ta. A kofar gidan kuwa su ka sami Garbati,da ke juma’ar Allah ce sai ga Garbati an yi fes an sami wanka kenan,wata kodaddiyar babbar rigar sa ce a jikin sa,ya kafa wata hular shi irin ta mutan da har goshi. Ganin su Mudi yayi saurin ba su hannu su ka gaisa,sannan su ka yi sallama da Hajjo,ko ta kula su,ita dai rera kukan ta take,Garbati ya tisa ta a gaba ya na fadin da ba ki tashi zuwa gidan ba sai da ki ka ga kina da ciki dan ki min asara,toh wlh ba ki isa ba. Cikan ka ba tace ma sa ba,suna tafe jama’a na kallan su har su ka shige gida… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 9:35 AM] Salmah Ateeku: [6:18pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣1⃣ Wasa wasa cikin Hajjo ya girma ya fito sosai,ta sha laulayi,ga jarabar Garbati da ya karu ba dare ba rana. Yanda Allah ya so ta da rahama sai warin Garbati ya dai na damun ta,sanadiyyar cikin da take dauke da shi. Duk dare sai dai ya zo ya ce Hajjo gyara,da ya sami abunda ya ke so ya zube ya na munshari,ita ko baiwar Allah har ta ma soma sabawa. Sanda cikin na ta ya kai wata tara sai fa jikin Inna yayi tsanani sosai,gashi Mudi da Indo ne masu kula da ita,dan Ayuba dai ya shiga layin yan shaye shaye. Ko da Indo ta fada ma Hajjo halin da ake ciki,ita take kula da ita da rana,saboda yara sai ta ke komawa gida da magrib ta barwa Mudi kula da Innar. Hajjo ta ce ai jinyar mace sai mace,bari Baban Garbati ya dawo za ta tambaye shi in ya so ita take kwana da Innar,Indo ta ce da wannan tsohon ciki Hajjo za ki iya? Hajjo ta murmusa kwarai ma kuwa,ina iya komai fa. Da haka su ka rabu. Baban Garbati Alhaji Basu be yiwa Hajjo mu su ba,dama ya san halin da Innar ke ciki,dan haka da Hajjo ta fada ma sa bukatar ta sai ya sa Mairo ta yi kiran Garbati. Ko da gogan na ta ya ji zancen sai ya ce sam ba da shi ba,ya ce Baba ni wlh ban iya kwana ba Hajjo,caf wannan ba ma maganar dauka ba ne Baba! Gaban Hajjo ya fadi,ta fara karanto addu’oi cikin ranta,ba ta da buri da ya wuce dai na kwana rumfa daya da Garbati. Garbati ya dube ta ya ce yo Baba idan ta tafi bukatata kanwa zan na sauke ta eh Baba? Alhaji Baso dai da ya gane in da Garbati ya dosa sai cewa yayi toh toh na gane,toh ke Hajjo kin ji daga bakin mijin ki. Hajjo ta ce wlh Baba Inna ta na bukatar taimako!! Garbati ya ce wlh nima ina bukatar mata ta!!! Hajjo ta watsa ma sa harara,ji take kamar ta kurma ihu. Alhaji ba so ya nisa,ya ce ina ke Hajjo,yanda za a yi ki na zuwa wajan Innar ta ki da safe ma na,in ya so da magariba ta yi yar uwar ta ki ta karbe ki ki dawo dakin mijin ki,ko kuwa? Hajjo ta san idan ta yi wasa wannan damar zai wuce ta,dan haka ta amsa da toh Baba,na gode,da ga gobe zan fara zuwa. Alhaji Baso ya ce Allah ya sauwake. Bayan tafiyar Hajjo Garbati yay ta mi ta,wai fa ana ma sa katsalandan fa,Allah ya bashi kudi ya tashi ya bar gidan ya huta,Alhaji Baso ya ma sa banza,Mairo ce ma ta taya sa da ameen,mu ma ma huta da masifar ka,ya bita zai daka,Iyalle ta hana,kawai sai ya fice ya na ta bala’i,wai ana so a kar shi a gidan. Jikin Inna dai ba dadi,kurji ya zame mata ciwo mai cin jiki. Yan da Alhaji Baso ya ce hakan Hajjo da Indo su ke,suna ba ta kulawa matuka,duk da kuwa ta so hana Hajjo amma ta dage,dan haka ta kyale ta tana ta ci musu albarka,fadi ta ke in ban da diya mace wai zai ma ka wannan gatar? Wanda ba su da shi Allah ya ba su. Alhaji Garbati kuwa da Magariba ta yi za ka gan shi kofar gidan su Hajjo,gudun kar ma ya ji shiru ta ce za ta kwana,kullum ta na mita ta ke bin shi zuwa gida,wata rana ta ki fitowa da wuri amma sai ya jira ta ya tisa kyeyar ta zuwa gida. Bayan an idar da sallah magariba Hajjo zaune tsakar gida tare da Inna,Inna ta sa ta dauko wata fanteka,kayan jarirai ne,riguna uku da wandunan su,sai kuma atamfa da sabulun wanka da na salo,dai kuma kayan yaji da ga can kasa. Inna ta ce Hajjo wannan kayan uwa ne,gashi nan na mi ki na fita hakkin ki na baki tin yanzu kar ki haihu ba na nan. Ido cike da kwalla Hajjo ta ce dan Allah Inna ki dai na magana haka,ki nan mana,ina za ki kuma? Indo da tuni ta zo ta fito daga daki ta na fadin Inna kuwa,ai kin san zancen ta kenan Hajjo. Inna ta murmusa kawai,ta ce da Indo ta dai aje kayan gun ta,hankalin ta zai fi kwanciya. Ana haka sai ga yaro wai Hajjo ta fito in ji Garbati. Hajjo ta ja tsaki. Indo ta ce sai ki tashi ki tafi kafin ya ta jero aike,Inna ta ce aifa! Cikin sirniki kamar ba za ta fita ba take shiryawa,Garbati ya yi aike har yara biyar,sannan Hajjo ta mu su sallama,za ta fita kenan Inna ta ce ya ki nan Hajjo,Hajjo ta dawo ta zauna gaban Inna,Inna ta ruko hannun ta cikin musabaha ta ce diya ta Hajjo,Allah ya mi ki albarka,Allah ya azurta ki da ‘ya’yaye na gari,ya ba ki diya mace mai kamar ki wacce za ta tausaya ta ji kanki kamar yanda ki ke min. Idanun Hajjo cike da kwalla ta ce amen Inna,ameen Allah ya baki lfy. Cikin zolaya Indo ta ce Inna yau kuma har da musabaha..yaro ya kara shigowa wai Hajjo….gani nan dallah! Hajjo ta katse shi kafin ma ya karasa. Inna ta murmusa,ta ce Allah ya sadu mu da alkhairin sa Hajjo,tashi ki bi mijin ki. Hajjo ta saki hannun Inna ta ce amen,sai da safe Inna,ta yiwa Indo sallama ta tafi. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [6:34pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣2⃣ Garbati na ma ta mitar ta jirga shi ta ki fitowa ta ma sa shiru,gaba daya ji ta ke ba ta jin dadi,ta rasa me ke damunta. Washagari da asubar fari Mudi ya buga musu gida,ya zo yayi kiran Alhaji Baso,Hajjo na bacci ba ta ma san an yi hakan ba. Da tashi sallah ta ga Garbati ba ya nan tai ta mamaki,yau wata rana Garbati an tashi sallar asuba. Gari yayi dan haske ta fara aikace aikacen ta sai ga Garbati ya dawo,biye da shi Mudi ne,gaba daya a rikice ya ke,ganin sa gaban Hajjo ya fadi,ta daure ta ce maraba da Mudi,fuska cike da damuwa ya ce Hajjo shirya mu je gida jikin Inna yayi tsanani…..wayyo Allah Inna ta na shiga uku na lalace!!!!! Ihun da ta sa kenan! Ihun na ta ne ya fito da su Iyalle da Kande daga daki dake da ma su sun san halin da ake ciki,Hajjon ce dai ba a fadawa ba. Ke dallah ba na san shashanci! Wani abu na ce ya sami Innar? Za ki sa fa na fasa tafiya da ke idan hauka za ki min!!! Hajjo ta ruke bakin ta tana fadin na yi shiru,wlh na yi shiru dan Allah kai ni wajan Inna ta! Garbati ne ya dauko ma ta mayafin ta,su Iyalle ma sai ba ta baki suke,su ka kama hanyar gidan su Hajjo. Ko da su ka Isa Hajjo ta ga Jama’a a kofar gida,wasu suna alwala,sai ta kara fasa kuka,Mudi ya ja hannun ta ya na fadin kar fa ki yiwa kan ki illa,ki yiwa mutane shiru Hajjo,shigar su gidan ta kara ganin mata a tsakar gida,ta ns shirin faduwa Mudi ya ruko ta,dakin Inna ya shige da ita. An yi mata sutura dama Hajjon ake jira su yi sallama a tafi da ita,tsakar dakin ta ke kwance,Indo zaune gaban ta,hawaye na kwaranya. Mudi ya karaso da Hajjo gaban gawar Inna ya ce ga Inna nan ki ma ta addua ba kuka ba….Hajjo ta yanki jiki za ta fadi,Mudi ya ruko ta,nan jikin shi ta zube sumammiya. Sai bayan da aka kai Inna aka dawo Hajjo ta farfado,gaba daya idanun ta sun kafe ta ma kasa kuka,sai dai surutai kamar wacce ta fara zarewa. Gidan na su tai ta kwana,randa Inna ta yi uku Garbati ya ce ta dawo gida,su Mudi su ka ba shi hakuri,su ka ce ya bari a yi bakwai tin da aka yi rasuwa Hajjo ba ta sami cikakkiyar lfy ba. Bayan da zai yi ya hakura,amma dan an fi karfin shi ba dan ya na so ba. Ranar da aka yi bakwai Hajjo ta tashi da naguda,ta sha wahala matuka har sai da aka fara shirin kai ta asibitin gwamnati da ke gari sai kuma Allah ya sauke ta,ta silbo diyar ta mace,sai dai ta karu sosai sanadiyyar girman yarinyar,Fara ce ga tsayi ga jiki kamar dai Garbati,amma kuma fuskar ta Hajjo ce sak,kamar ta yi kaki ta tofar…. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7 [16/10 21:46] .: 7:11pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣3⃣ Unguwar zoma ta ce da su Indo da Hajjo ta sami kanta sosai sai su kai ta asibiti a ma ta dinki,suka ce toh,ga koshi ga kwanan yunwa,an rasa Inna an kuma sami karuwa. Hajjo zaune,ta na ta kuka dan tin da Inna ta rasu ba ta yi kukan ba sai yanzu,dan haka sai su ka barta ta yi mai isar ta,dama dai sun damu da rashin kukan na ta. Ta yi ta koshi,sai ajiyar zuciya ta ke,kanwar Inna ta fara ma ta nasiha na da ta dangana,Allah da ya bada Inna shi ya karbe ta,ya kuma ba ta wata diyar mace. Da haka Hajjo ta yi shiru,jaririyar ta na ta tsala ihu,aka ce ta ba ta nono mana,Hajjo ta ki saboda da yarinyar ta kama sha cikin ta ke ma ta ciwo,sai da aka sa ta gaba,ta na kuka haka ta ke shayar da diyar ta ta. Duk wannan abun da ake Garbati be tako kafa ya zo ba,kayan da ke jikin jinjirar ma kayan da Inna ta bawa Hajjo ana gobe za ta rasu ne. Shiru shiru an aika be zo ba,da Mudi ya ga haka ya ce da Hajjo wani suna su Hajjon su ka yanke za a sawa diyar ta su ne? Dan ya kamata a yi ma ta huduba Hajjo ta ce ba su taba zancen ba,amma dan Allah ya ma ta da sunan Inna,Ameena ta san shi ma ba zai ki ba,Mudi ya ce toh a kawo masa yarinyar,ya ma ta huduba da Ameenatu,Inna ta tafi Inna ta dawo. Washagari bayan Hajjo ta yi wanka ta shirya,ta yi tsaf da ita,ta ciko sosai kamar ba Hajjo ba. Indo ce ke wa jariyar wanka,ta ce Hajjo? Hajjo ta ce ummm kin san kuwa jiya ki ka cika shekara gomasha uku? Hajjo ta gyada kai kawai ba tare da ta ce komai ba. Har aka gamawa yarinyar wanka sai cilla ihu take,dake yarinyar akwai kuka. Indo ta daura ta kan cinyar Hajjo,ta ce ki daure ki ba ta tasha Hajjo,Hajjo ta yamutsa fuska ta ce wlh da ta fara cikina ciwo ya ke,gashi ba ta koshi,Indo ta ce ki yi hakuri Hajjo,ya za ki yi tin da kin haifa dole ki shayar ai,daure ki ba ta. Hajjo ta turo baki ta sa ma ta nonan a baki,caraf diyar Garbati ta karbe ta fara sha kamar wacce aka koya ma ta. Sai da yamma su Iyalle su ka zo,sun zo da sakon Garbati na a yiwa yarinya huduba da suna Katime,sunan Iyalle. Indo ce ta mu su bayani cikin ba da hakuri akan yarinya da aka ji shiru an ma ta huduba da suna Ameena,an yi tunanin hakan zai yi daidai da ra’ayin Garbati. Toh ai ba komai,Allah ya jikan Ameenatun,amsar da Iyalle ta bayar kenan,amma sai da fuskar ta ta nuna ba a mu su daidai ba,dan haka ba su jima ba su ka tafi. Har suna ya zagayo ba Garbati ba alamarsa,ko ragon suna be aiko ba. Mudi da Indo da Ayuba sun yi cirko cirko a tsakar gida,ana tunanin ko bin sawun Garbati Baba ya shigo ya ce ya aka yi cirko cirko haka?lfy? Mudi ne mai bayanin,ya ce Baba muna tattaunawa ne akan lamarin Hajjo,Allah ya waye mu suna amma mai gidan na ta shiru haka yan uwansa,ko rago ba su turo ba bare kuma ayi batun abincin da za a bawa yan suna. Baba yace yo ba ku ku ka jawo ba,ai na zuba mu ku ido ne kawai,yaro tin da aka yi uku da rasuwar Ameenatu ya ce mai dakin sa ta koma,ku ka kiya,ta haihu ku ka ma ta huduba da sunan da kuka so ba tare da kun jira shi ba,yanzu ga irin ta nan,sai kusan yanda za ku yi dan na sadu da Alhaji Baso dazu ya ke fada min an yiwa Garbati ba daidai ba dan haka ya ce tin da ku ka rada sunan ku siyi ragon suna,kuma kwayar shinkafa tawa ban yarda a dafa dan sunan asara ba,kun dai ji na fada mu ku! Kuma gobe goben nan Hajjo za ta koma dakin mijin ta,na gaji da hidama da ita da diyar ta ai ta cinye ma hatsi!Ya shige ciki ya barsu suna kallan kallo,Indo ta ce toh kun ji fa,yaya kenan? Ko dai cikin ragunan da maigida na ya ke kiwo za mu ranci guda a yanka? Ayuba ya ce zai ba mu ne? Indo ta ce mai zai hana,ai Sani be da matsala. Mudi ya ce ai Indo Mijin na ki ne balalle a same shi ba. Ta ce ya na gida,be tafi kanan ba tukun,ku yi azama ku riske shi. Su ka ce toh su ka tafi,ita kuma Indo ta koma daki wajan Hajjon da tun safe ta ke kuka,ga Ameena da take kira Inna sam ba ta barin ta ta sami bacci da daddare. Ta ce Hajjo ki rufa min asiri dan Allah ki bar kukan nan haka. Mu fatan mu a samu a yi yankar nan,na so ace an mi ki wannan dinkin kafin ki koma gidan ki amma Baba ya ce gobe za ki koma,saboda haka bayan kin koma din ma samu mu je asibiti a mi ki kin ji ko? Komai zai wuce,yanzu Ina Inna? Gaba shi yau mun wayi gari ba ita ba,haka duk za mu wuce komai mai wucewa ne ai. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7:16pm, 5/15/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣4⃣ Hajjo uhum kawai take iya cewa,ita kadai ta san abunda ta ke ji. Ba a jima ba sai ga Mudi da rago,har da shinkafa kwana biyar Sani mijin Indo ya hada su da shi. Ba bata lokaci aka yi yanka,Yan uwa sun ka fara zuwa,da taimakon dangi aka sarrafa shinkafar zuwa dafa duka,aka hada kunun zaki…a haka da faci faci aka yi suna aka gama da ke ba wani taro aka yi ba,dama ga babu ga kuma rasuwar Inna. Washagari Hajjo ta koma gidan ta,Mairo da Kande kadai ke hidima da ita,su kan daukar ma ta Innar na ta sosai,ita kuma Iyalle bakin cikin ta na an ki a sa sunan ta,an sa na Inna. Shiko Garbati bakin cikin sa da yawa,gashi Hajjo ta tafi ta ki dawowa sai da ta haihu,gashi an sa sunan da ba shi ya ce a sa ba,gashi diyar ta Hajjo kukan dare gare ta,ta hana sa bacci,dan haka ko kallan inda ta ke be taba yi ba bare ya dauke ta,ko tsinke be taba siyawa yarinyar ba kayan barka na yan uwa da abokan arziki ake sa ma ta. A haka Hajjo ta yi arba’in. Da la’asar ta na sallah,Mairo ta goya ma ta Inna, kwatsam sai ga Garbati ya shigo,ganin Hajjon ta na sallah sai ya fara bala’i,kut! Ke Hajjo da ma munafunta ta ki ke kin fara sallah ba ki fada min ba? Munafukar aure! Sallah ta ke amma sai da gaban ta ya fadi,ta dade da fara sallah,amma kiyayyar da ta kewa Garbati ya sa tai ta buye ma sa,da ke shi din ma ba zama ya ke ba,yanzun ma dubun ta ne ya cika. Ta tsora kwarai,ji take kamar tai ta sallah har illa mashaAllah. Garbati ya sami waje ya zauna ya ce toh sai ki idar ki bani hakki na,dan wlh bazan jira dare yayi ba,munafuka kawai!! Badan gaban Allah ta ke ba da taki sallma,amma bayanda za ta yi dole ta yi sallamar. Ta ce yau fa na fara sallar,dama zan fada ma…ya ce na ji toh gyara! Hajjo ta ce ka jira mana dare yayi,ya ce ban jira,ya tashi ya sakace kofa,yayi wulgi da babbar riga ya ce maza ki gyara na ce Hajjo! Yanda ya ke so haka aka yi,amma fa ko da ya gama biyan bukatar sa,sai labari ya canza. Rai bace ya ke kallan ta,murya a sama ya ce Hajjo! Wai ya na ji haka kamar kofar gari? Yaya haka ne? Hajjo ta mayar da hijabin ta,ta takure gefe guda. Ya ce ke Hajjo ba da ke na ke magana ba! Ya na ji haka ne! Murya kasa kasa Hajjo ta ce dama da na haifi Inna ne aka ce na karu sai an min din ki….kin karu? Ana nufin kin yage za a dinke ki? Kai diya mace ta na yagewa ana dinke ta kamar tsumma! Wai wannan yar mitsilar abar da ki ka haifa ita ta maida ki sai ka ce kofar gari? Caf da sake kuwa! Wannan ai ba zan iya ba,wlh bazan iya zama da mace wankakekiya haka ba!!! Sauki zan yi! Ke wlh na ma sauki,ki hade kayan ki na sauki saki daya……! DEDICATED to The WOmen Of Virtur💁👰🙋 [7/25, 9:36 AM] Salmah Ateeku: [7:17pm, 5/18/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣5⃣ Hajjo ta daga ido ta kalli Garbati,maganar ta sa ce ta ma ta ba za ta. Ta ce kunne na ke zagi ko kuwa dai sakin na ji? Garbati ya na hura hanci ya ce eh sauki na yi kofar gari! Hada na ki ya na naki,ki hada har wannan abar da ki ka haifawa kan ki ki bar min gida! Wani irin farin ciki ne ya lullube Hajjo,ji ta yi kamar an cire ma ta kaya,cikin sauri kafin Gatbati ya sake shawara ta tashi ta na fadin kai amma fa na gode Allah ya saka da alkhairi. Ya na huci ya ce idan ma ba’a ki ke min amen,na dai ci moriyar gangan,kar na dawo na same ki a gidan nan wlh! Ya fice tare da banko kofa. Dan farinciki ta ma rasa da mai za ta fara,Ghana must go din ta ta ja ta shiga zufa komatsenta,sannan ta hade kayan Inna cikin fanteka guda. Ta fito da sauri neman Mairo ta karbi diyar ta. Mairo ba ta nan sai dai Kande. Saki? Kande ta kame baki cikin jimami,Iyalle ta fito jiyo maganar Kanden,ta ce ya na ke jin batun da Allah ba ya so ne? Wa aka sau? Tana fara’a kamar wacce aka yiwa albishir din hajji ta ce ni ce,wlh ni ce dai Garbati ya sau…lahailahaillallhu! Kai Garbati ya isa maras hankali! Ya sauki da danyan jego?? Ba inda za ki….. gwiwowi biyu a kasa Hajjo ta durkusa, ta na magiya ta na tafa hannu,dan Allah dan annabi dan ya rasulillahi Iyalle ki bari na tafi,wallahi na rantse da Allah ya ce ya sau niii…sai ta sa kuka. Iyalle ta ce ah ah dai na kuka,ai sai ki tafi din,za ki tafi,Allah dai ya sa haka shi ne kairi. Hajjo ta tashi ta na goge hawaye ta ce amen,dan Allah ina Mairo ta kawo Inna sauri na ke wlh,ai yanzu za ta dawo,Iyalle ta ba ta amsa,makota na aike ta,jin sallamar Mairo ta ce mata ga ta nan ma. Cikin sauri tace Mairo sinto min ita tafiya zan yi,ta sinto ta tana tambayar lfy? Ina Hajjo za ta? Ita dai ta yi ciki da diyar ta ta bar Kande na mata baya ni. Sai ga Hajjo ta fito goye da Inna,fantekar kayan Inna bisa kanta,ga Ghana must go a hannu,ta durkusa gaban Iyalle ta ce toh Iyalle a iya zaman mu idan na bata mi ki ki yafe ni,sai kuma Allah ya sada mu da alkhairin sa. Iyalle ta tada ita ta na fadin ni ce da neman yafiya Hajjo,a yayyafe mu. Hajjo tace la ba komai wlh dama bu ku bata min ba,Allah ya yafe ma na gaba daya. Gaba daya jikin su yayi sanyi,Mairo har da kuka,ita ko Hajjo yau ta ke sallah,da haka da haka su ka yi sallama Hajjo ta kama hanyar ta. Rashin Inna ya sa Hajjo maimakon ta je gidan su sai ta tafi gidan Indo,dan ko ta je gidan ba dadi za ta ji ba,sai ma kyara da tsangwama daga wajan Baba. A dakin girki ta tadda Indo,ganin ta da kaya niki niki ta kama ta sauke ma ta fantekar ta na fadin lfy kuwa uwar Inna? Hajjo ta na dariya ta ce Garbati dai ya sau ni! Kai kai kai amma ba dan saki abunda Allah ba ya so bane da na yi guda,kai amma na mi ki farin ciki,mu je daga ki fada min garin yaya. Ta dau fantekar su ka shige dakin Indo. Ko da Indo ta ji dalilin sakin sai cewa ta yi kan sa yayiwa ai,can da su gada. Ki kwantar da hankalin ki nan gida na za ki zauna,sai na gyara mi ki daki daya,idan Sani ya dawo sai mu je mu fadawa Baba. Dan murna Hajjo ta rungume Indo,ta ce na gode Allah ya saka da alkhairi,yan uwa dadi gare shi. Indo ta ce haba Hajjo ai yiwa kai ne. Ya Inna? Ta daina kukan dare? Hajjo ta sinto Inna da ta ke ta famar baccin ta,ta mikawa Indo ta ce gata ba ta daina ba,ita ta yi baccin ta da rana,da dare yayi ta hana ni sai dai a tashi a yi hira. Indo ta dara ta na kallan Inna,ta ce ayya Allah sarki ina ruwan Inna,Allah dai ya raya ma na ita,Hajjon ta ce amen amen. Da Sani ya dawo ya ji batun Hajjo,ya goyi bayan zaman ta a gida,ya kuma ce maza su je su fadawa Baba kar su yi laifi,dan haka Hajjo da Indo su ka kwashi kafa su ka je gun Baba. Be mu su tarbar mutunci ba,sai ma fadan da ya hau su da shi,wai ai ya ji batun sakin,me zai mu su yanzu da su ka zo su ka sa shi gaba? Tin wuri Hajjo ta je ta nemi afuwan mijin ta ya dawo da ita dan shi ba zai iya hidima da ita ba ya yi da wannan diyar ta ta ba,ka sayar da akuya ta dawo ta na cinyema dusa. Kai a kasa Indo ta ce dama Baba na zo ne neman alfarmar a bar Hajjo ta zauna gida na….yoo da shi ne ba ki yi bayani tin wuri ba? Baba ya katseta,ai ba sai ma kin tambaya ba,tai ta zama har mahadi ya bayyana,ni menene nawa a cikin tin da aljihuna ya kubuta! Jiki a sanyaye su ka ma sa sallama. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7:20pm, 5/18/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣6⃣ ya ce a sauka lfy,su ka fita,sam ba soyayyar Baba cikin ran Hajjo,bare yau ma da ya gama fita daga ranta. A soro suka gamu da Mudi,shi ya raka su hanya,Indo ta fada ma sa halin da ake ciki. Yayi bakin ciki da halayyar da Baba ke nunawa diyoyin sa mata,yay ta bawa Hajjo baki har su ka yi sallama. Gidan Indon Hajjo ta yi zamanta,har ta gama Idda Garbati be zo biko ba bare kuma batun kome,diyar sa kuma ta yi wata hudu,amma tsinke be taba siya mata ba. Da yammacin ranar lahadi Hajjo zaune cikin dakin da Indo ta ba ta,ta na yiwa Inna wasa,Indo ta shigo ta na umm su Hajjo ma su diya! Ta na dariya ta aje Inna ta ce wlh ki ga fa har zama ta ke….Inna ta yi luuuu za ta fadi Hajjo ta ruko ta da sauri ta na dariya. Indo ta ce Auta hankali! Maza ki karasa ma na yar Innar ta mu mu yi biyu babu. Duka dariya su ke. Duk da ba wani abu na daban ta ke ci ba,kwanciyar hankali ya sa ta canza ta yi kyau,gashi haihuwar da ta yi ya sa jikin ta yayi kyau,ta yi diri mai kyan gaske. Indo ta ce Sani ne ke kiran ki. Hajjo ta ce aw ya dawo? Ai ban sani ba da na ma sa barka da sauka,gani nan zuwa. Indo ta ce kar fa ki tsaya sirniki,So ya ke ya fita, Hajjo ta ce Indo ho toh mu je gaba daya,ta biyo ta dauke da Inna. A tsakar gida kan tabarma su ka tadda shi,hannun sa ruke da tasbaha. Hajjo ta zauna daga farkon tabarma yayinda ita kuma Indo ta zauna sosai bisa tabarma. Sannu da zuwa Babn Aisha,sunan da ta ke kiran sa kenan,da ke diyar Indo ta fari sunan ta Aisha,sunan Indon ta ci. Cikin sakin fuska ya amsa ma ta,su ka gaisa sosai. Ya kara da Hajjo za ki iya aikatau a cikin birnin kano? Ta na murna,abun nema ya samu kila za ta bar kumurya ko ta rage wasu bakin ciki da su ka sami wajan zama cikin zuciyar ta,ta ce wlh babu aikatau din da bazan iya ba. Shi kan shi Sani sai da ta bashi dariya bare kuma Indo,tace ka ji azarbabi,kya dai yi shiru ki ji karashen batun ko? Hajjo ta ce tam! Sani ya cigaba da fadin gidan da na ke musu direbanci ne,mai gidan ya jima da rasuwa,kusan shekara goma kenan ma muna tare,duk ‘ya’yan Hajiyar Maza ne su uku,biyu magidanta ne,sai kuma autan ta dan saurayi nan da wata hudu shima zai yi aure,kuma ba a kasar zai zauna ba shi ya sa ma su ka damu a samo ma ta yar aiki da za ta na debe ma ta kewa duk da de ba wani aiki ba ne a gidan ba yara. Baki washe Hajjo ta ce yasin zan yi! Ah ah toh ya za a yi da Inna? Tambayar Indon da ta katsewa Hajjo farin cikin ta kenan kafin Sani kuma ya dawo ma ta da farin cikin ta da ta jin amsar sa na dama sai da ya fadawa Hajiyar,ta ce ba komai indai na yaba da hankalin ta,na kawo ta sai ta ji nawa Hajjon ta ke so a matsayin albashin ta…ko nawa ne wlh ni zan yi! Caraf Hajjo ta amshe. Indo dai ba son tafiyar Hajjon ta ke ba,sai ta kara da za ta na biyo ka ne kullum kuna tafiya tare kuma? Sani ya ce ah ah su wacce za ta na kwana su ke so…ai ba komai sai na kwanan ma,yaushe za mu tafi? Ta na magana ne yayinda ta yunkura ta tashi,Sani ya ce duk sanda ki.ka shirya. Toh bari na fara shiri yanzu sai mu tafi gobe,ta tashi da sauri ta shige ciki. Indo ta ce toh fa,ka ga rawan jiki,toh Allah dai ya fisshe mu alkhairi. Sani ya tashi ya na fadin ameen,kar ki damu Indo,mutane ne ma su kirki,ba za ta sami matsala da su ba. Indo ta ce Allah ya sa,Sani ya amsa da ameen,sai na dawo,ta ce adawo lfy. Tin asubar fari Hajjo ta shirya tsaf ta shirya diyar ta,dan dakar ta iya bacci ma saboda zumudi da Allah Allah gari ya waye,wai Hajjo ce za ta shiga birnin kano,wayyo dadi abunda ta ke fadi cikin ran ta kenan. Da gari yayi haske sosai Indo ta kama mata karin kumallo dan Hajjo ta gagara fita ta dauka da kanta,sai da Indo ta tsaya kanta sannan ta ci,ita kawai a tafi a tafi. Indo ta bata kayan shafa,har da turaren shafawa su “aba rai dadi” da “danduwala” ta mata fada sosai,ta kula da kanta da kuma Inna,birnin kano girma gare shi,shi ake kira timbin giwa ko da me ka zo an fika,gwara ta bi hankali. Toh kawai ta ke cewa dan ba ma ta jin ta,ita dai kawai a tafi. Har mota Indo da ‘ya’yan ta su ka rako ta,suna ta daga ma ta hannu,baki washe ita ma ta ke daga musu,ta takure gidan baya Inna zaune bisa cinyarta…. su ka nufi birnin dabo,gari mai mata mai mota,gari ba kano ba dajin Allah! ☁☁🌞 ☁ ☁ ☁ ✈ ☁ 🚁 ☁ ☁ ☁ 🏬🏨🏫🏢🏤🏥🏦🏪 🌲 / l🚍 \🌳👭 🌳/ 🚘 l 🏃 \🌴 🌴/ l 🚔 \🌲 🌲/ 🚖 l \🌳 DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7 [16/10 21:46] .: 25, 9:38 AM] Salmah Ateeku: [2:41pm, 5/27/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣7⃣ Ko da su ka shiga garin baki Hajjo ta saki,idanu bude kamar za su fado ta ke kalle kalle,garin acike ya ke taf da jama’a,kowa da irin sa da irin salon shigar sa,ga motoci ga hayaniya,ga gidajen sama,kai kano sai ka ce duniyar ce gaba daya? Tambayar da take maimatawa cikin ranta kenan. Ita ko Inna tinda ta ji iskar mota ta noke jikin maman ta sai bacci. Hotoro G.R.A sunan unguwar da Sani ya shiga. A gaban Wani katan gida,mai dauke da ado da bishiyoyi na fure ya tsaya ya na danna hon,da sauri maigadin gidan ya bude gate,Sani ya karasa ciki. Dan al’ajabin kyauwun gidan ihu ne kawai Hajjo ba ta sa ba,tin da ta ke ba ta taba gani gida irin wannan ba,toh sai dai a kalandar da su Mudi ke kawo gida daga boko,wai amma yau ga ta ita ce cikin gidan. Da wannan tunani ta ji Sani ya tsaya ya na fadin Hajjo ga mu a kano,a sa takalmi a sauko ko? Cikin rawar jiki ta fara jijjiga Inna,ke Inna tashi ki ga aljannar duniya! Inna ta motsa ba tare da ta farka ba,hannun ta kamkame jikin Hajjo. Sani ya fito ya bude mata kofar yayin da ta sauko ta na mitar nauyin baccin Inna kamar na uban ta Garbati! Dariya Sani ya ke ma ta,ya taimaka ya fito ma ta da kayan ta da na Inna,ta saba Innar a baya ta sa zani ta daure. Sani a gaba hannu dauke da ghana must go din Hajjo,ita kuma biye da shi,ta daura fantekar kayan Inna bisa kanta su ka shige cikin gidan,tana mamakin yanda Sani ya san kan gidan dan lunguna da su ke ta kutsawa dan ta san kafin ta gane sai fa an kwala duk da Inna ta ce ta na da kan gane waje. Wani bangare su ka shiga,sai ga su tsaye cikin falo mai dauke da bangare biyu, Sani ya fara sallama,dan kallan kauye Hajjo har da tuntube da wani flower pot da ke aje gefe guda. Hankali dai!wata murya mai tarin nutsuwa da sanyi ta daki kunnen Hajjo,tini idanun Hajjo su ka shiga neman mai murya. Babban falo ne mai dauke da bangare biyu wanda gilashi fari ya raba,na fari an ma sa ado da fararen kujeru masu kyau da kayatarwa,ga lallausar carpet da ke shimfide kalar ganye a kasan kujerun,sai kuma dayan bangaran falon da ke dauke da wasu irin kujeru kanana sosai ga kuma wasu kanana tintin da ke watse amma cikin tsari,idan kana zaune cikin bangaran za ka iya ganin abun da ke faruwa a cikin dayan bangaran ba tare da na wancan bangaran ya lura ba. Dan haka har Hajjo ta gama kalle kallen ta ba ta ga kowa ba,sai da su ka fito. Dattijuwa ce wayayyiya fara sol,kakkaura mai kyauwun gaske,idanun ta sanye da farin gilashi ta fito,biye da ita danta ne mai kimanin shekara talatin aduniya,kamar shi daya da ita,hatta yanayin tsayin su daya,ba dogo ba ba kuma gajere ba,shima ya na da dan jiki,da ka gan shi ka ga magidanci. Dattijuwa ta na fara’a ta ce wa’alaikumul salam Malam Sani,yau ka so ka makara,ta bi Hajjo da kallo,gaban Hajjo ya fadi,ba shakka muryar ta ce wanda ta ji,kwarjini ta ma ta matuka,bare kuma danta da ke ma ta kallon kurilla. Sani ya durkusa yanda ya saba ya gaishe da Dattijuwar,bayan sun gama gaisawa su ka gaisa da dan na ta wanda sani ya kira da suna Jabir. Ganin haka Hajjo ma ta gaida su,sai a sannan Sani ke ma Hajiya bayanin dalilin makarar ta sa,ya tsaya tahowa da Hajjo ne…. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [2:54pm, 5/27/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣8⃣ Dattijuwar ta ce ah ku shigo daga ciki mana,abokiyar debe min kewar kenan? Jabir ya ce ban tari numfashin ka ba Mallam sani,amma wannan ai ta yi yarinta da yawa,wacce fa za ta taya Hajiya aiki fa aka ce,wannan ko ai ba ta wuce a yi renan ta ba itama! Kuma wai goyo na ke gani a bayan ta..Gaban Hajjo ya fadi,Malam Sani ya budi baki zai yi magana Hajiya ta katse shi da fadin kyale shi Mallam Sani,karaso ciki,ai na ce da ku zan iya zama na ni kadai na ku ka takura sai an samo min kuma ka fara sara tin kan su zauna,shigo abun ki yarinya. Hajiya ta wuce ta zauna kan doguwar kujera shi ma Jabir din kasa ya samu gaban ta ya zauna. Sani ya aje Ghana must go din Hajjo daga gefe,shi ma ya sami matsuguni,yayin da ita kuma Hajjo kici kici ta sauke fantekar da ke kanta kasa,sai kuwa Inna ta tsala kuka alalle Hajjo ba za ta zauna ba,itama Hajjo ji ta yi kamar ta tsala na ta kukan ganin yanda da ga Hajiyar har Jabir su ka zuba ma ta ido,ta ce wayyo ni Inna dan Allah ki taimaka min ki yi shiru! Jin haka sai Hajiya ta dara,ta ce sinto ta mana,ki ba ta ruwa ta sha kin san akwai zafi kila ma yunwa ta ke ji ki ba ta nono! Baki bude Jabir ya ke duban ta dan har yanzu be gama gasgata zatan shi na Inna diyar Hajjo ba ce,sai da ya ga ta sinto ta da rawar,ta sanya ta cikin mayafi ta fara ba ta nono. Ya ce kai jama’a wlh Hajiya diyar ta ce kuwa. Hajiyar dariya ta yi ta ce toh da diyar ka ce? Ta ce shekarar ki nawa? Ta tambayi Hajjo,Hajjo ta ce shekarata goma sha uku…..Jabir ya ce tashin hankali! Hajiya kuwa ko a jikin ta,ta ce Allah sarki,ni ma ina da shekara sha uku na haifi diya ta ta fari sai dai ba ta zauna ba,bayan shekara daya kuma na haifi Sabir yayan Jabir…ita dai Hajjo uhum kawai ta ke cewa ta na yake. Hajiya ta ce da Sani ai ba matsala Hajjon ta ma ta. Jabir ya ce Hajiya yarinya ce ga goyo,maimakon ta taya ki aiki ai sai dai ma ta saki,mai wannan yarinyar za ta iya fisabilillahi? Ta na gani za a ma ta biyu babu ba ta san sanda ta ce na iya ko wani aiki yasin! Ko aikin gidan su Garbati ma kaf ni na ke yi,Baban Aisha shi ne sheda ta ko? Ta dubi Sani idanun ta cike da magiyar ya sa baki. Sani ya ce kwarai kuwa,ai ba da ganan ba idan dai aiki ne Hajjo ba ta da san jiki…Hajiya ta ce bare ma ba wani aiki a gidan,ni ce fa dal sai Auta,shi ma din be fiya zama ba bare ma auren sa ya matso,to indai zan zauna da yar aiki toh Jabir da wannan diyar zan zauna,ta yi min ni dama dan ni ake yi ko? Jabir ya gyada kai tin da Hajiya ta dage,toh lalle hakan za a yi. Ya ce toh zan fadawa Sabir an samu,nawa za a ke biyan ta? Hajiya ta dubi Hajjo ta ce yarinya ya sunan ki ne? Hajjo ta ce Hajara,amma Hajjo ake kira na. Hajiya ta ce toh Hajjo nawa ki ke so a biya ki? Hajjo ta dubi Sani,dan ita ba ta ma san nawa za ta ce ba. Sani ya gyada ma ta kai,sannan ta ce ko nawa ne Hajiya zan karba. Hajiya ta ce ah ah gwara dai ki fada kar a kware ki Hajjo,kin san dai kwana za ki na yi,kuma duk wata za a ke baki kudin ki,kuma ni da kike ganina ban da matsala musammam idan ki na da tsafta,za ki ji dadin zama da ni. Hajjo ta ce Hajiya ni kam wlh ko nawa ne Allah sa albarka. Hajiya ta ce toh shikenan tin da kin ki ki fada,kin ga ko an kware ki ba laifin mu. Sani ya ce kwarai kuwa. Hajiya ta ce da Jabir sai su yanke nawa za su ke biyan ta,daga yau za ta fara aiki. Sani ya koma kan aikin shi,ita ko Hajjo dakin da za ta ke kwana Hajiya ta kai ta,daki ne mai hade da ban daki a ciki,ga wani sanyi mai dadin gaske da ke ratsa Hajjo wanda ta gaza gane sanyi daga ina ya ke busowa gashi dai zafi ake bare ta ce ta taga ne aka salima tagogin a rufe su ke. Hajjo tsaye ita da Inna tsakar dakin,wannan daki ai yayi a hada nawa da na Iyalle da na Baban Garbati! Wannan girma ai anyi asarar fili! Haka dai tai ta tabe tabe da kalle kalle,hatta bandakin abun kallo ya zame ma ta,ita kuwa Inna sai gwaran cin ta take. Ba a jima ba sai ga Hajiya ta dawo dauke da sinkin sabulun wanka,ta ce da Hajjo ta yi ta kuma yiwa Inna,sai ta fito ta ci abunci ta nuna ma mata gidan. Hajjo ta karba tare da ma ta godiya. Sai dai wankan kusan gagara yayi,da kyar ta samu ta yiwa Inna,ita kuwa sai dan kwaskwarima ta yi,dan gani ta ke da ta saki jikin a bandaki za ta ji ta a kasa,ta fito ta na mita an bi an lallaye ban daki da tangaran sai ka ce wajan hutawa! In dai ba ka mutu ba ka sha kallo….. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [3:09pm, 5/27/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 2⃣9⃣ Sati biyu Hajjo ta fara sabawa da rayuwar gidan,haka kuma sannu a hankali Hajiya ke nusar da ita yanayin yanda ya kamata ta kasance a matsayin ta na diya mace,uwa,kuma mai aiki,da ke Hajjon mai saurin dauka ce hakan ya sa da an gwada ma ta shikenan za ta dauka. Hajiya kuma ba ta da matsala,tausayin Hajjon ma ta ke ji,sai ta ke tuno ma ta sanda ita ma ta ke kamar ta,sai dai ita din da gatan ta ga kuma soyayyar miji amma duk da haka ta ji jiki bare kuma Hajjo ta take rayuwa daga ita sai diyar ta ta. Ga wata soyayya da ke kulluwa tsakanin Hajiya da Inna,da ke Hajiya ba ta taba samin diya mace ba,wacce ta haifa din ba ta zauna ba,kuma ta na sha’awa matuka,samin Inna kusa da ita sai ya sa take kaunar yarinyar,ta na yawan ma ta wasa,idan Hajjon ta na aiki gun Hajiyar ta ke barin Inna,sai ka ji suna ta dariya abun sha’awa. Da yamma Sani zai koma Kumurya,sai Hajiya ta ce ya aje Hajjo shagon da ake ma ta din ki a tarauni,in ya so sai ta hawo adaidaita ta dawo tin da Hajjon ta fara gane gari,Inna goye a baya,Hajiya ta ba ta naira dari ta ce idan ba za ta gane ba ta ce ya shigo da ita ta kwanan magi. A hanya Hajjo ta ke ta yiwa Sani tambayoyi,ta ce ‘ya’yan Hajiya uku,amma ita daya ta gani,ina sauran biyu? Sani ya na tuki ya ce ai babban dan na ta shi ne Sabir,a Abuja ya ke zaune da iyalin sa,matar shi daya da yara uku,suma duka maza ne, can ya ke aiki karkashin company da baban su mai rasuwa ya bari,shi mutum ne mai hakuri kwarai da kawaici,be fiya magana ba,da mahaifin su ya rasu bayan an raba mu su gado sai suka hada karfi da karfe su ka ci gaba da tafiyar da company din,karkashin jagorancin Sabir,duk da be yi wani karatu mai zurfi ba,a diploma ya tsaya. Hajjo ta ce menene diploma? Sani ya ce wani mataki ne na karatu na gaba da sakandiri. Hajjo ta ce ayyo. Shi kuma Jabir fa? Sani ya ce Jabir shi ne dan Hajiya na biyu,matar shi daya da yara biyu mata,na ukun kuma ko yau ko gobe. Mutum ne mai haba haba da surutu,likita ne a asibitin koyarwa na malam aminu kano. Hajjo ta kame baki likita? Kai gaskiya ya burge ni wlh. To waye autan kuma? Sani ya jinjina kai,yace wato sarkin kumbo da kwalisa kenan,ga kumbo,ga kyawu,ga jin kai,ga takama ga isa! Caf girman kai kenan? Hajjo ta tambaya cikin mamaki. Sani ya ce ah ah gaskiya Khalid be da girman kai,amma fa ya na ji da kan sa matuka,dan duk cikin yayun sa ba wanda ya kai sa nuna isa da tinkaho,akasali ma ko su ma yan uwan na sa kokawa su ke,ga tsafta ko zama a tabarma ba ya yi kar ta bata ma sa karin guga,ga kyamkyami,be sha ko cin abu acikin ko wace roba saboda yan da ake sarrafa su. Ina ga shekarun sa ishirin da shida a duniya,be dade da gama bautar kasa ba,ina wannan karatun na zanen gine gine? Ya ma ya ke da suna? Hajjo ta ce yo ni ina na sani? Daidai bakin shagon da zai sauke Hajjo ya faka,ya ce yauwa Ar-chi-tec-ture! Toh shi ya gama,auren sa be ma kai wata hudu ba yanzu…Hajjo na shirin fita daga motar,ta ce ya ban taba ganin shi ba shi ma? Sani ya ce ya na can Abuja ai,da ke shi ma karkashin company din na su ya ke aiki,na ji ma da an yi auran na sa ba a kasar za su zauna ba,can dayan bangaran company na su da ke a kasar landan zai yi aiki. Hajjo na jinjina kai ta fito tana fadin manya kenan,toh Allah ya sa a yi da mu. Dan Allah a gaida Indo da yara Allah ya kiyaye,Sani ya ce amen za su ji,ta dai kula da hanya,Allah ya tsare,ta ce amen,ya tafi ta shiga shago ta karbo din kin Hajiya. Ba ba tare da bata lokaci ba ta sami dan adaidai ta ya mai da ta gida. Ko da ta ce nawa za ta bashi,ya ce ta kawo naira hamsin,sai Hajjo ta kame baki,hansin fa Mallam? Yo ruwa ka hayar da ni? Yo toh ko ruwa ka hayar da ni alkur’an ban biyan hansin bare kuma nan da nan baki da hanci,da na sani ma silafowa na yi da kafa abuna,yasin sai dai na ba ka ishirin! Kut amma fa wannan yar kauyen ma ki na neman rigima,ya kashe adaidai ta ya fito,ya ce ke wlh na fiki kauyengi da gidadanci ki biya ni kudina ko na more ki! Hajjo ta dada gyara tsayuwa,da daure goyan bayan ta tamau,sannan ta daura hannu a kugu ta ce wa za ka more? Ni? Toh uban kuturu yayi kadan bare na makaho!shege ka fasa! Yasin ishirin zan ba ka,ka ga dari ne ma a hannu na sai ka miko min canji zan ba ka! Kan ka ce me? Rigima ta kaure tsakanin Hajjo da dan adaidai ta. Wata galleliyar mota ta zo,da alama gidan Hajiya ta ke san shiga,amma tsayuwar mai adaidaita a bakin gate ya hana shi,yayi horn amma ko a jikin sa,da dai ya gane rigima ya ke da yar yarinyar da ke tsaye ta ruke kugu sai tsiwa ta ke gaban sa,sai ya ja tsaki ya fito a hasale. Kai Mallam da Allah ka ja gefe kai yanzu ba ka ji kunyar sa’i sa da wannan yar tatsitsiyar yarinyar ba? Sai a sannan da ga Hajjon har abokin fadan na ta su ka san da tsayuwar sa,baki bude Hajjo ta ke kallan sa……Dogo ne,dogo sosai wane Garbati,fari ne amma irin wanda baki ya ratsa,fari mai duhu kamar na bakaken turawa haka,ya na da kyau matuka,ga hanci har baka,kan shi ya dan tara gashi baki wuluk,amma kadan irin dai na samarin zamani,be da kiba amma ya na da kafada irin mai kirar zakin nan. Amma ita Hajjo shigar shi ta fi burge ta,shiga ne na kanana kaya wanda su ka karbe shi matuka…ba fa wani kunya dan samari,wannan ba yarinya ba ce tin da ta san ta toye min hakki na,kowa dai ya san daga tarauni zuwa nan GRA hamsin ake biya,na fada ma ta ce wai ishirin za ta biya ni,ni kuwa wlh sai ta bani kudi na daidai ko na more ta!maganar dan adaidaita ya dawo da ita da ga kogin tunanin da ta fada. Tsaki ya ja ya sa hannu a aljihu ya fiddo da kudi naira dari biyu ya mikawa dan adaidaita ba tare da ya kalli Hajjon ba,ya ce gashi ka ruke har canji! Ya shige motar ya ja gefe ya faka. Mai adaidaita ya ce Allah ya cece ki yarinya,Hajjo tace yarinya na bayan uwar ta,kai dai Allah ya ceta da yau ka yi biyu babu! Suna musayan magana har ya fito ya shige gidan ba tare da Hajjo ta ankara ba. Mai adaidaita ya tada babur din sa ya na kiran Hajjo matsiyaciya,ta na kai ne matsiyaci! Sai da ya tafi sannan ita ma ta shige gida. DEFCATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7 [16/10 21:46] .: :49pm, 5/31/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 3⃣6⃣ Ranar aka yi dinnar,Hajjo da Dada da yara aka bari a gidan,washagari aka kai amarya gidan ta a court road. Bayan sati daya kuma jirgin su ya kyeta hazo. Bayan hayaniyar biki ya lafa,Hajjo ta je kumurya domin fadawa Indo maganar makarantar da za ta koma,Indo ta ce ta yi dabara Allah ya taimaka dai,ya za ta yi da Inna? Ta ce Hajiya ta ce ana barin ma ta ita,ta ce toh madallah. Bayan dawowar ta Jabir ya kai ta makarantar abokin sa,prestige gurls collage,duk da dai ba ta ci test din da aka ma ta ba aka samu aka makala ta a JS 1,Jabir ne ya biya kudin uniform da books din ta,da ke abokin sa ne,ya kuma ce Hajjo cousin din shi ce sai ya dauke ta on schlarship. Hajiya ta ji dadi kwarai,gashi makarantar kusa ce,dan haka Hajiya ta sa Hajjo ta yaye Inna indai makarantar ta ke so ta yi da gaske ga shi dama babu abun da ba ta ci kuma ta saba da Hajiyar,sai ta ke barin ta gun Hajiya,Inna na wata tara aka yaye ta. Kullum da tashi da asuba ba ta komawa bacci ta ke hawa kan aiki,kafin lokacin makaranta ta gama kome ta tiwa Inna wanka,sai ta je makarantar ta,2 na rana ana taso su ta dawo gidan Hajiya,da la’asar kuma ta je islamiyar da ke kusa da gidan Hajiya. Rayuwar makarantar na matukar bawa Hajjo wahala,Hajjo ba turanci,ba ta iya ba,ba kuma ta ji,so ko ya ta dan jagwalgwala sai ka ji dalibai sun dare suna ihu,gashi an hana hausa,in ka yi sai ka biya naira goma,tin Hajjo na biya ta ga ana shirin tatiketa abun ba na hankali ba ne ai kuwa sai ta dage da kwaba turancin ta,a rana be fi a karbi naira hamsin ba,shi ma din da kyar da sudin lodayi. In ka ji Hajjo na told me wen I say d hausa mana!!!!!! Toh fa an kama Hajjo ta na hausa an rubuta sunan ta,an zo an ce ta biya,da kuwa har dari biyu karbe ma ta ake,wato ta yi ya taru. Kullum in ta je gida tai ta gwarancin turancin ta ko Allah ya sa a daina karbe ma ta kudi. Sam ba wani alamar Hajjo ta yi aure,bare ta na da diya,tini ta saje da daliban,amma kauyencin Hajjo ya sa ta yi suna a makarantar,ko ina ka bi ka ji ana ina spoke the hausa,sunan da aka sa ma ta kenan. Da aka yi exam din first term Jabir ya zo ya karbar ma ta result,ba labari Hajjo ta dauke ajin,da ke ya san background din it was very poor,sai be damu ba,haka second nd third term ma. Ana shirin ma ta repeatn Jabir ya roki arziki da a barta,what is important shi ne kawai ta zo makarantar. Da su ka shiga JS2 sai Hajjo ta ba da mamaki,ta fara jin turanci sosai,kuma tsabar kar a karbi kudin ta ba ta jin kunyar kwaba turancin ta,ga ta gwana ce,kwaruwa ce wajan maths,kan ka ce mai sai ga Hajjo ta fito sahun goman farko,duka terms din. Jabir da Hajiya sun ji dadin kwazon Hajjo,da aka fara siyar da form din Junoir WEAC na science bord abokin Jabir ya ce a siya Hajjo ta gwada,da ke abun na Allah ne sai sai kuwa ta ci,ta sami Gurl science Garko. Murna gun Hajjo be musantuwa. Duk da JS 2 ta ke an gwada ne kawai a ga ya kwakwalwar ta ta take gashi kuma sun sauke alqurani a makarantar islamiya,su na shirin fara hadda da littafai na addini.da Jabir ya ga ta ci sai kawai ya ce kawai ta tafi abun ta. Lokacin Hajjo ta cika shekara goma shabiyar,Inna kuma an yi biyu,da Hajjo ta ga za ta makarantar kwana sai ta yanke hukunci mayar da Inna kumurya wajan Indo,Hajiya ta ce a bar ma ta ita,Hajjo ta ce ita ma za ta so haka,amma gaskiya ba za ta iya dorawa Hajiya dawainiya ba,sanda dai ta na prestige zaman Hajiya da Innar na dawainiya na awanni ne,yanzu kuwa shekaru ba wasa ba ne. Da haka din aka yanke hukuncin mayar da Inna kumurya. A wannan karan ne Khalid da Hauwa su ka sauka gida Nigeria domin yin hutun su na karshen shekara bayan sun shekara biyu a london. Murna gun Hajiya be musantuwa,dan da saukar su gidan Hajiyar su ka fara zuwa,sai dai har su ka tafi ba su hadu da Hajjo da Inna ba sun je Kumarya. Ana saura kwana hudu Hajjo ta tafi Garko,Jibril da Hajiya su ka ba ta kudi ta yi siyayya,Sani ya kai ta kasuwa,a gida wajan Hajiya. Hauwa da Khalid su ka zo gidan. Hauwa ta kara fari da kyau sosai, Tin da ta kyallara ido kan Inna ta ke ta bibiyar ta,dama tin usul ta na san yarinyar,gashi auren su 2years amma shiru ko batan wata ba ta taba yi ba,duk da dai shi Khalid be damu ba ya ce lokaci ne be yi ba,da yayi Allah zai kawo ma su albarka. Shima din dake Inna tashi ce,tin shigowar su ya ke makale da ita. Suna zaune tare da shi da Hajiya,Inna ta yi bacci kan cinyar sa. Hauwa ke tambayar Hajiya ina maman Inna kuwa? Tin da mu ka dawo ba mu hadu ba. Hajiya ta ce kai haba? Ai kuwa da kyar za ki gane ta idan ki ka ganta,Hajjo ta ta zama yar birni yar boko,ta ma tafi kasuwa siyo provisions za a shiga Ss1,ta sami admision. Hauwa ta ruke baki kai ya aka yi ta yi sauri haka? Ai ba ta dade da fara karatun ba na gani. Hajiya ta ce da ke she is naturally gifted,tsallake ta yi kamata yayi ta shiga JS3. Hauwa ta ce owk,ya za a yi da Inna? Gun ki za ta zauna? Hajiya ta ce haka na so,amma ta ce ba ta so ta daura min nauyi,za ta maida ita Kumurya wajan yayar ta. Budar bakin Hauwa sai cewa ta yi dan Allah Hajiya ni ta bani ita na tafi da ita ta na debe min kewa,ta kalli Khalid a marairaice ta ce ka sa baki a ba mu Inna. Shi ma Khalid din kamar ta shiga zuciyar sa ne,ya na zancen cikin zuciyar shi da za a ba shi Innar,ta na taya Hauwar sa rayuwa,dan ta na kadaici acan duk sanda ya tafi aiki. Ya ce eh Hajiya za mu so a mana wannan alfarmar,a roka mana dan Allah. Hajiya ta ce toh abun ne da kamar wuya,amma bari Hajjon ta dawo sai a mata maganar,ai kuna nan ma za ta dawo. Khalid ya tashi dauke da Inna,ya ce eh Hauwa na nan,ni yanzu zan fita ne,anjima na dawo na dauke ta. Hajiya ta ce adowo lfy,Hauwa ce ta raka shi su ka kwantar da Inna,bayan ya kwantar da ita ya jawo ta jikin sa,yayi kissing goshi ta tare da fadin worry nt baby-luv,ke ma very soon za ki haifa min mai kama da ke,so ko an hana mu Inna,ba fata na ke ba,kar ki damu owk? Hauwa ta murmusa ta ce owk Beb,Allah ya amsa. I love you big,ya yi hugn din ta tare da fadin I love you more. Hannun ta cikin na sa ta raka shi har mota. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7:23pm, 5/31/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 3⃣7⃣ Da Hajjo ta dawo ta tadda Hauwa cikin girmamawa ta gaishe ta,ita kan ta Hauwa ta yi mamakin yanda Hajjo ta canza she is realy transforming,ga kyau ga touch of wayewar da boko ya fara ba ta. Tare da Hajiyar Hauwa ta yi wa Hajjo zancen Inna,amma Hajiya ta ce kar ta ji nauyi,idan ba zai yiyu ba ta fada diyar ta ce,ba wanda ya taya ta wahalar kawo ta duniya. Hajjo ta ce toh su bari ta je Kumurya ta fadawa yayar ta,duk yanda su ka yi sai ta fada ma su. Amma har ran ta ba ta san a raba ta da diyar ta har zuwa wani kasar. Da haka su ka rabu washagari da safe Hajjo da Inna su ka hau motar haya sai gasu a Kumurya. Ita dai Indo zancen dadi ya ma ta,ta ce ke Hajjo wannan abu ai ba wanda za a ki ba ne,da ki aje diyar ki a wannan kauye ta tashi ba wani ilimin kirki da rayuwa mai inganci ai gwara ki dankata amana inda za ta sami rayuwa mai kyau da inganci,kin san dai mutanan nan mutane ne ma su kirki da aminci,wlh kawai ki yarda a tafi da ita…Salama alaikum! Sallama ce ta katse Indo,jin muryar mai sallamar tini Hajjo ta mi ke,ta suri Inna su ka buye bayan kofa. Sallamar aka kara dokawa, Indo ta amsa ta fito da sauri,a tsakar gida ta ci karo da Baba,ta durkusa da niyar gaishe shi,amma sai ya fara sirfo ma ta zagi,uwar ki! Uwar ki na ce Indo! Ina nan da rai na za ku tozarta ni? Indo ta ce me ya faru Baba? Ya ce ina Hajjo? Indo ta dan tsorata,tin tafiyar Hajjo be taba waiwayar ta ba sai yanzu,ko ya ji wani abu ne? Ba da ke na ke magana ba? Ya daka ma ta tsawa! Ta na kame kame tace Hajjo Baba ai ta na nan. Ungo nan! Ya ma ta dakuwa,ai na san komai, na ji lbryn kin turata birni,kin tura ta yo karuwanci ko? Auzubillahi minallahshaidanirrajim! Indo ta ce karuwanci fa Baba. Baki na kumfa ya ce ke ce shedaniyar ke da ki ka tura ta karuwanci,eh in ba haka ba waye na ku a kano?,dan haka na riga na sallama ta,sai dai kuma ki fada ma ta ta dawowa tsohon mijin ta Garbati da diyar sa! Dan jiya uban sa ya zo min da maganar,dan haka sai ki fadawa asararriya! Na ba ta daga yau zuwa rana eh na yau ta kawo diyar nan! Ya juya fuuuuu ya fice ya bar Indo cike da damuwu,ta ma kasa tashi. Jim kadan Hajjo ta fito goye da Inna ga jakarta makale,Indo ta tashi da sauri ta na tambayar yaya na gan ki haka? Rai bace Hajjo ta ce Kumurya zan bari ni da diya ta,ba kuma zan sake dawowa,dan wlh ko Baba be isa ya amshi diyar nan daga hannu na ba,bare Garbati! Indo ta ce ba a yi haka ba,dama ba za ki ba su ba,amma….ina fuuu Hajjo ta fice ta na sinbatu kamar wacce ta zare,har waje Indo ta bi ta ta na kiranta,amma ta ma ta banza,gani ta ke da ta tsaya za a kwace Inna. Sai da ta ganta a Kano ta fara nutsuwa,ta na isa gidan Hajiya ta ce da Hajiya ta fadawa Hauwa za su iya tafiya da Inna. Hajiya ta yi murna,ita ko Hauwa harda dan ihun ta. Hajjo dai duniya ce ta ma ta zafi,ta sha kukan ta a daki ta koshi har sai da Hajiya ta kama ta ta na kukan,ta ce me yayi zafi Hajjo,in ba ki so ai sai a fasa tafiya da Innar. Da ke Hajjo akwai zurfin ciki,gudun kar Hajiya ta goyi bayan Baba ta ce a mai da Inna sai ce ma ta yi ba wannan ba ne,kawai har ta fara kewar Inna ne,ga makarantar kwana da za ta shi ma din da ke ba ta saba ba ya na damunta,Hajiya ta ce awho,ai dole ki yi kyewa,tai ta bata baki har ta ware. Ta hadewa Inna kayan ta tsaf,amma sai Hauwa ta yi waya ta ce kar a damu da kayan Inna,ta nan ta na siya ma ta sababbi saboda sati biyu ya rage su koma. Hajjo ta yi godiya Hauwa ta ce ai ita ce da godiya. Jabir ne ya kai Hajjo Garko,har ta tafi ba su hadu da Khalid ba,sai dai sakon godiyar sa sa ta ji daga wajan Hauwa da ta zo ma ta sallama da godiya,ta kuma tafi da Innar. Daga uwar har diyar ba wanda be yi kuka ba,dan dai ita Innar ba ta ma san abunda ake nufi ba. Amma ita dai Hajjo ta yi mai isar ta,duk da dai ta san hannu mai kyau ta ke,da dai ta bawa Garbati diyar ta gwara ta bawa Hauwa. Sati biyu da tafiyar Hajjo su Khalid su ka tafi da Inna. Sannu a hankali Hajjo ta aje komai ta sa karatu gaba,dama ga kwakwalwa tini makaranta ta san da ita,duk quiz ne ba a fita sai da Hajjo,gashi ta dage da haddar alqur’ani,dalibai da malamai kowa na yin ta,ga ta sam ba wasa bare kuma sa tunanin maza ko san su cikin ranta. Kuma ba ta da kawaye saboda ba ta san kowa ya san tarihin rayuwar ta. Duk sanda aka yi hutu gidan Hajiya ta ke zama. Sanda ta kai Ss2 ne Jabir ke tsokanan ta ko dai za a sake tsallaken ne a shiga jami’a? Hajjo ta ce dan Allah ko ma ba za a yi tsallaken ba dan Allah ta na son gwada jarabawar. Jabir ya ce sai dai fa idan kin yi ki tafi kawai,dan na sa za ki ci wannan guruwar,MBBS din ko an sake shawara? Ta na dariya ta ce MBBS din dai,idan ka ga zan iya,in kuma ka ga ba zan iya ba sai ka ba ni shawara. Cikin jaddadawa ya ce ina ai da wannan kwakwalwar ta ki babu abunda ba za ki iya ba Hajjo? Hajjo ta ce kai kar ka sa kaina ya fashe,Jabir ya ce da ya fashe za mu tattara mu kwashi karama. Hajjo dai da ta ga zolayar Jabir ba mai karewa ba ce,sai kawai ta hada na ta ya na ta ta shige wajan Hajiya. Da yarda Allah Hajjo ta rubuta jamb ta ci sosai,dama MBBS ta cike,ta na cikin yin exam din ne su Hauwa su ka zo hutu,Inna ta cika shekara hudu Hajjo na shekara shabakwai. Sam ta ki zama gidan Hajiya ta kuma ki Hajjo sai dai Hauwa ko Khalid,da ke exam ya sha gaban Hajjo sai abun sam be dame ta. Ana gobe za su yi exam din maths ne,kan Hajjo yayi zafi ta dukufa ta na ta solving problems sai ga Hauwa ta shigo da sallamar ta, hannun ta ruke da na Inna. Hajjo ta dago ta na murmushi,ganin Inna sai farin ciki ya bayyana fuskar ta,ta ce wa’alaikumul salam Inna ta oyoyo ta tashi da sauri. Ganin Hajjon ta yo kan su,da sauri Inna ta noke jikin Hauwa ta na ummm Momma,Hauwa ta ce haba Neena! Maman ta ki za ki yiwa kiwa? Ganin yanda Innar ta ki ta sai ran ta ya sosa amma sai ta boye ta na murmushi ta koma ta yi zaman ta,ta ce ai ta manta da ni,shekara biyu ba wasa ba,Innar tawa Neena ta koma? Bakin gado Hauwan ta zauna,ta daga Inna da ta koma Neena a yanzu a yanzu ta dora kancinyar ta,ta ce wlh yaran neighbor ne ke kiran ta haka,da ke kin san turawa sun ka sa cewa Inna sai su ka maida shi Neenan. Hajjo ta yi yake,Allah sarki,cikin girmamawa yanda ta saba ta gaishe da Hauwa,Hauwan tai ta bata lbryn Inna,ita ko Hajjo da Allah sarki ta ke bin ta,cikin ranta ta tafasa ta ke,wai ita ce wata ke bawa lbryn diyar ta sai ka ce ita ta haife ta,toh an yi an gama karfe abar ta za ta yi,har wani Momma ta ke ce ma ta. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [16/10 21:47] .: /25, 9:44 AM] Salmah Ateeku: [7:34pm, 5/31/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 3⃣8⃣ Budar bakin Hauwa sai cewa ta yi Hajjo na gode kwarai,Allah ya saka mi ki da alkhairi,wlh ba karamin gurbi Neena ta cike a rayuwa ta ba,thanks to you da ki ka iya yarda na tafi da ita,ta sanadiyyar haka i knw wat it feels lyk to b a mother,to hold nd hug a little one dat cal u mother,idanun ta su ka ciko da kwalla,ta kara da ba dan Neena ba ina ga da duk wannan ba zan san su ba. Subhanallahi! Hajjo ta fada yayin da ta daura hannun ta kan na Hauwa,me zai sa ki ce haka? Ya kamar kin sare da ikon Allah? Ai Allah ne ke bayarwa,dan kin yi shekara hudu ba ki haihu ba be kamata ki fidda tsammani ba,ma su yin goma tukun su haihu su ce me? Kwallar da ya makale idanun Hauwa ne ya gangaro bisa kuncin ta,ta ce ba fidda rai na yi ba,kuma har gobe ina addua,sai dai mun je manya hosptals da dama a london ana duba mu,duk sun tabbatar ba zan iya samin ciki ba bare na haihu,matsalar kuma ta wa ce ba daga gun Khalid ba. Jikin Hajjo yayi san yi,ta tausayawa Hauwa,ko wace diya mace da kaddarar rayuwar ta,ita na ta kaddarar kenan,rashin haihuwa. Ta nisa tare da fadin kar ki damu,in da rai da rabo, Allah mai bayarwa shi zai ba ki. Ta na murmushi ta goge hawaye ta ce ameen Allah ya amsa,dan ma Khalid be da damuwa akan maganar,ya ce ba su dame shi ba,tin da Allah ya ba shi ni shikenan,ba maganar kara aure,ta kare ta na murmushi. Hajjo ta ce mashaAllahu,na ji mi ki dadi,Allah ya bar ku tare,ta ce ameen,ta dan yi shiru sannan ta ce ban sani ba ko za ki yarda na kara tafiya da Neena,kamar za ta hana,amma sai ta ga menene amfanin hanawar? Kar kishi da kyashi ya sa ta cuci diyar ta,dan gashi ta zama kamar diyar turawa dan kyau da kiba,gashi ita ma din fama ta ke da boko,dan haka sai ta ce me zai hana? Ke ma din ai kin zama maman ta,murna da farin ciki ya bayyana fuskar Hauwa,tai ta godiya har abun ya fara bawa Hajjo mamaki,ta tashi ta ce maza Neena zo mu tafi mu bar Mama ta yi karatu,ta ji ta na gani ta fita da noke jikin ta,ko daukar ta Inna ta ki bari ta yi. Hajjo na tsaka da jarabawa su Khalid su ka koma. Ta yi post UME ta ci aka bata admssion a BUK,foculty of medicen,za ta karanta MBBS,ta yi sa’a ta ci WAEC din ta,Jabir ya biya kudin registratoin,Hajjo ta zama yar Jami’a,ta waye ta goge kwarai,nan ta hadu da wata Aysha ana kiranta Ayush,su ka kulla amunta mai karfi. Tin da ta fara sau biyu kawai su Hauwa su ka zo hutu,shi ma din ba wani dadewa su ka yi ba,ta na makaranta ne ta ga kira international num ta wayar da Hajiya ta ba ta,ko da ta daga sai ta ci muryar Khalid,a dar dar ta gaisa da shi gani ta ke kamar zai ce ma ta wani abu ne ya sami Inna,ga mamakin ta sai ji ta yi ya ce ya na so ne ya sa Neena makaranta,amma be san surname din ta ba,Hajjo ta yi jim,har sai da Ayush da ke zaune kusa da ita ta fara tambaya lfy? Shi ko Khalid da ya ji shiru sai ya katse wayar a tunanin sa jin shi ne ba ta yi,ya ce ya kira anjima. Da Ayush ta damu Hajjo da tambaya,a karo na farko sai ta ba ta lbryn rayuwar ta gaba daya,Ayush har da zubda hawaye,ta ce lalle Hajiya da zuri’ar ta daban su ke,kin ga kuwa ni anawa shawarar Hajjo gwara ya sa ta da sunan shi,tin dadai a hannun shi ta ke yanzu. Shawarar Ayush din ta bi,da Khalid ya sake kira sai ta ce ya sa sunan shi,dama dai abunda ya ke so kenan,ya ji dadi sosai,har da yar fara’ar sa,wasa wasa dai Neena na kara zama tamkar diyar sa. Hajjo da Ayush na ta tare rai da rai,kuma kullum Ayush cikin ba ta lbryn wani cousn din ta da take so ta ke,shi ma Doctor ne,duka yan gidan su ma haka sun maida MBBS kamar gadon gidan su,dan san shi da ta ke ma shi ya sa ta ke course din,amma shi be ma san ta na yi ba,kuma ta ki fadawa Hajjon sunan shi,ita dai Hajjon abun mamaki ya ke ba ta dan tun da ta ke ba ta taba san wani da namiji ba,bare kuma irin na Ayush wanda ba a ma san ta na yu ba. tare su ka yi 3 yrz a Buk old sites (pre-clinicals),sai kuma su ka koma teaching hosptal na Amenu kano,sun yi 3years har sun shiga na hudu,housemanship su ke,shi ma din watanni kadan ya rage su gama. Sannan Hajjo na da shekara ishirin da da uku,diyar ta Inna kuwa na da daya. Tsabar kawacan Hajjo da Ayus ba wanda be san su tare ba,komai na su daya,haka ma group din su,da ke Ana raba whole Class into 2 groups first Lyk internal medicine Vs Surgery a level 4 and 6 While a level 5…into Paediatrics vs Obstetrics and Gynaecology (O&G) kuma a kowani department. Akwai sub speacialities….sai a ka qara raba su into no Of speacialities available Lyk into 5 or 6 haka Then sai suke rotating into kowannen su….every 2 or 3weeks. Kamar yanda su ka saba,yau ma tare su ke tafe,Hajjo na ma ta mitar wani young doctor da ke takura ma ta da kallo,sai dai ba su hadu ba,ita ta na mamakin me ya sa doctors ke da masifar san mata ne? Aysuh ta dara tare da fadin isn’t dat obvious? Irin wandannan docs din nay da basu yi aure da wuri ba…sun tsaya yin boko,ko toossing din babe ma basu iya ba….sai ta zo asibiti,kin ga kuwa dole su duba,Hajjo ta ce toh Allah dai ya sauwake! Ayush na dariya ta ce da Allah ni kuwa ki nuna min wannan Doc din na ki…ya Salam! Hajjo ta kau da kai,gashi nan wlh,daga idun Ayush wa za ta gani? Cousn din ta ne ma ashe Doc din da Hajjo ke magana akai. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [6:42pm, 6/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 3⃣9⃣ Baki ne,be fiya tsayi sosai ba,amma sai dai ba a kira shi gajera ba,ya na da hanci da manyan idanu,kuma da ka gansa ka ga bafulatanin mutum. Ya na murmushi ganin Ayush din tare da Hajjo,ya karaso gun su ya na fadin aminan juna,Doc Ayush ya ki ke ya kawar ki? Baki budi Hajjo ta ke kallan Ayush,ganin yanda ta ke ma sa murmushi ya kara ba ta tabbacin ta san shi,caf Allah da ya so ma ba zagin shi ta yi ba,da ta sha kunya,godewa Allah da ta ke nan,ta na ji Ayush ta amsa da Yaya Suraj,lfy lau,kawata ma haka,ya su Mama? Idanun sa kan Hajjo ya ce lfy lau,kawar ta ki ba ta magana ne? Hajjo ta yi yake ta ce ina gajiya? Ya na murmushi ya ce ko kefa,lfy lau,ya kokari? Ta ce Alhamdulillah. Ya mayar da kallan sa ga Ayush ya ce kanwata akwai maganar da na ke so mu yi,so zan zo na same ki a gida. Cikin jin dadi ta ce toh ya Suraj sai ka zo. Ya kalli Hajjo ya ce sai mun sake haduwa? Ta ce sai anjima,Ayush ta ce a gaida su Mama,ya ce za su ji,su ka! Wuce idanun sa kan Hajjo. Hajjo ta ce Ayush? Dama kin san shi? Ayush ta ce cousn dina ne fa,ina famly din su ne na ce mi ki ar ol doctors,Hajjo ta ce aw fmly din crush din ki? Ko dai shi ne ma? Ta yi saurin ce wa nooo ba shi ba ne,yayan sa ne. Hajjo ta ce toh Allah ya sa dai ayi da mu. Ayush ta ce shi da be ma san ina yi ba,toh amen dai. Maganar Suraj dai akan Hajjon ne,ya je ya sami Ayush ya ce da Allah ya za a yi shi wlh kawar ta ya ke so,nd da gaske ya ke. Duk da maganar ta ma ta ba zata,sai ta ce toh ba komai,za ta ma ta magana,ya kara da dan Allah ta taimaka,da gaske son Hajjo ya ke matuka. Washagari da Ayush ta yiwa Hajjo magana,sai ta ce ba wannan maganar,ba maganar maza ko so ko aure gaban ta…nan Ayush ta shiga ma ta nasiha,idan ta ce za ta yi haka ta sabawa mahaliccin ta,shi da ya halatta aure,da kuma manzo sallallahu’alihuwasallam da ya sunnata shi,haka kuma ta yi butulci. Da wannan Hajjo ta ce toh za ta yi kokari ta canza ra’ayi. Aysuh ta ce dan Allah for my sake dai ki bawa Suraj dama,wlh mutumin kirki ne,he is very differnt ko cikin fmly ma,he is nt jst a doctor,ya yi specialising a radiology,he is a great Radiologist. Cikin zolaya Hajjo ta ce ya kai Crush? Ayush ta murmusa ta ce He is exactly lyk him. Hajjo ta dara saboda ke Ayush,zan gwada ba shi chance. Ayush ta rungume ta ta na godiya,wayar ta ta dauka ta sawa Hajjo numbar Suraj din,ta ce dama shi tin jiya ta ba shi na Hajjon,Hajjo ta ce lalle,da kuma na ki fa? Ayush ta ce na san ba za ki ki ba ai. Wasa wasa soyayya ta fara nisa tsakanin Hajjo da Suraj,duk da kuwa Hajjon kara kawai ta ke ma sa,she is tryn to give him a chance. Su Hajjo sun gama housemanship,daf da za su fara service aka tura Suraj India wani course,tafe ya ke cikin mota tare da Hajjo, ya na ta ma ta surutu,lbryn dptment din su ya ke ta ba ta,yanda su ke gudanar da aikin su musammam wannan infertility test da su kewa mace mai matsalar haihuwa,ana kiran test din HYSTERO SELPHIGOGRAPHY(HSG),ya ci gaba da fadin abu ake sawa kamar pencil dan ya fi biro girma,saman sa kamar allura,kasa kuwa abu ne kamar screw,ana sa ruwan magani ciki,shi ake sawa mace,ta vagina,ya bi ta cervix,ya je ovary ya kutsa ta falloprain tube har zuwa uterus wato mahaifa. Idan ya shiga sai a murza ruwan maganin ya fita ya je both ovaries,idan akwai blockage as in wanda ya hana a sami ciki sai machine din mu radiograps ya dauka,idan blockage din kadan ne,ruwan maganin zai iya kau da shi,idan blockage din mai yawa ne,toh sai an yiwa mace surgery. Kai jama’a Hajjo ta dafe haba,diya mace na ganin ta kan ta! Suraj ya gyada kai,yes u can say dat again dan gaskiya duk macen da aka yiwa wannan sai ta yi ciwan mara kwarai,wasu ma har bleeding su ke,kai da wuya ma ayi ba a yi bleeding ba gaskiya. Hajjo ta saki ajiyar zuciya,to ko dan irin wannan ya kamata mata su dage su zama likitoci,da mace ta ke sakarwa namiji jiki yay ta jagwalgwalawa,a ma shiga hakkin addini! Dariya Suraj ya sa har da dan bingirewa,ya ce haba Doc Hajara,ya ki ke magana kamar ba ta mu ba? U knw better ai,kin san wani abu kuwa? Ta ce um um,ya ce yawan cin aikin dptment din mu deals wit issues lyk dat,wit females,amma duk sanda mu ke aiki Allah na dauke ma na sha’awa,wlh mantawa mu ke ma wai mace ce gaban mu,amma akwai abu biyu da we can’t help bt notice. Hajjo ta ce me kenan? Suraj ya gyada kai ya ce na fari shi ne kazanta,wlh Hajjo wa su matan ar too dirty abun har kunya ya ke bani,in ta mamaki shin wai ya maigidan su ya ke? Haka ya ke zama da su? Hw can a woman b dat dirty?,mace ta bude kafa sai ka ji wari na fita? Tsabar kazanta. Hajjo ta ce uhum,kunya ce ta kama ta,dan gaskiya wasu matan ko shaving ba su yi,dan ta taba jin wata nurse ta na ta mitar ta zo karbar haihuwar wata ta kasa banbance gashin baby ne ko gashin uwar baby ne da ya taru ya rufe ko ina!duk da ba a fiya so a yi shaving din tas ba,saboda shi ma gashin is a protection,ya na hana cuta shiga directly,so an fi so a yi saisaye,a dan bari kadan,as in KADAN dai,dan shi tsafta cikon musulin ci ne. Ta ce sai me kuma? Menene na biyun? Ya murmusa ya ce tsafta,wasu mata su na da tsafta kwarai,dole ka yi respectn din su. Dax y bazan iya auren ko wata mace ba sai doctor yar uwa ta,kin san doctors ar generally neat,saboda sun san yanda rashin tsaftar ke da matsala! Dax y dole na auri Hajjo,ke na ki tsaftar ma daban ya ke,Hajjo ta murmusa ta ce ta ya ka sani? Ya ce haba alamar karfi ai ya na ga mai kiba Hajjo. Ya kalle ta ya ce Hajjo kin dai ki bari na turo,kin ga da an yi gaisuwa ina dawowa sai a daura ma na aure. Murshi ta yi ta ce gwara ka dawo din sai a yi mai duka lokaci guda,cikin ranta kuwa tunanin yanda za ta fada ma sa wacece ita ta ke,tunda be san ta taba aure ba,bare a zo maganar ta na diya budurwa mai kimanin shekara goma sha uku….ko kuwa? Tambayar sa ta doki kunnen ta,cikin rashin gane abunda ya ke fada ta ce na’am? Suraj ya ce hmmm u mind is nt hear,me ki ke tunani? Ko kin fara missin dina ne tin kan a je ko ina? Murmushi ta yi,ta ce ina jin ka fa,ya ce in ki na ji na me na ce? Ta ce wannan ne ban ji ba,ya dara ya ce ba kya jin kenan Hajiya. Cewa na yi toh ana dawowa za a fara maganar auren,i can’t wait to b ur hero! Murmushi kawai ta ma sa. Ya ce da auren mu fa za a sha budiri,bikin Doc. Suraj da Doc Hajara! Hajjo ta ce eh sai mu yi ankon lapcoat ba…kut kin ma isa?! Cikin asibiti za a yi bikin da za mu sa coat? No ba wannan maganar. Hajjo ta ce ni kuwa shi zan sa,ka rubuta ka aje,ranar auren Doc Suraj ni Hajjo sai na sa lapcoat wajan shagali,gwara kowa ya san bikin na gida ne! Ya ce da an yi rigima,da haka ya sauke Hajjo gidan Jabir,da za ta fita ya ce da Allah ta gaida maigidan shi,wato Jabir,dan yanzu ya ma kai matsayin consultant,Hajjo ta ce zai ji. Sai da Suraj ya tafi da wata guda su Hajjo su ka shiga camp,ta yi sa’a kano aka bar ta,bayan sun fito aka yi postn din ta Abdullahi wase specialist hospital. Ayush kuma aka kai ta Murtala Muhammad specialist hosptal. Bautar kasa ta yi nisa kwarai,Hajjo na karbar allowee,rabi ta bari cikin account din ta,rabi kuma ta yi dan hidimar ta da shi na zirga zirgan kudin mota,sannan ta na yawan aikawa da Indo kudi,Kumuryan ne dai ta daukewa kafa,sai fa idan Allah ya kawo Indo kano ko kuma ta bawa Sani,haka kuma ta na yawan yiwa yaran Jibril hidima,yanzu yaran sa da Nabeela ta haifa sun kai shida,biyar mata,sai kuma Namiji shi ne karami. Hajjo zaune cikin Doctors a asibiti,dukkan nin su babu wanda be girmi Hajjo ba,kuma su na da aure,dattijiwar cikin su Doc Husaina yaran ta goma ma,haka sauran daga mai uku,sai huda sai mai daya. Kamar yanda su ka saba da sun zauna sai a fara maganar maza,aure,rashin mutuncin maza,maganin da’a,zancen manyan mata dai barkatai,dan ma su na saurarawa in dai Hajjo na waje saboda da dan jikin ta,duk da dai akwai ta structure mai bala’in kyau ganin ta su ke yarinya,dan ba wanda zai kalle ta ya ce ta taba aure bare kuma ace ta haihu. Sai kawai su ka yi zaton kirar ta ce haka. Yau din ma maganar su ke, da hira ta yi hira,Doc Husaina ta ce um um dai kan fanka,ku fa san abunda kuke fada ga Hajjo kar ku sa ta tsorata da aure. Su ka ce aw ai mun munta muna tare da yar budurwa,Hajjo cikin ranta ta ce yau dai bara na fadawa wannan matan wacece Hajjo, ta ce Anty Hussaina ni fa ba budurwa ba ce… DEDICATED to The Women OF Virtue💁👰🙋(group) [7:15pm, 6/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣0⃣ Gaba daya ido su ka zubo ma ta,Doc Hussaina ta ce garinyaya Hajara? Hajjo ta murmusa ta ce ai na taba aure har da diya ma na ke da, Ameena sunan ta. Ganin yanda fuskar su ta nuna ta gane ba su yarda ba,sai kuwa ta ba su lbryn rayuwar ta,babu wanda be yi kwallaba cikin su,Doc Hussaina ta ce sannu Hajara,sunnun ki Hajara,amma gaskiya ya kamata a dinki wannan tear din,kin yi sakaci da yawa,hakan zai iya ba ki matsala sosai,wai ma tsaya,shi wanda za ki aura,Suraj sunan sa ko?ya san da wannan maganar? Hajjo ta yi ajiyar zuciya ta ce wlh Anty Hussaina na kasa fada ma sa,har ya tafi,ya dai san matsayi na a gidan Hajiya. Gaba daya su ka ma ta ca,wannan na fadin kai ba ki kyauta ba,wannan na Hajara ina ake haka? Wata na ki gaggauta fada ma sa dan ku sami fahimtar juna. Doc Hussaina ta tashi,ta ce Hajara biyo ni office dina. Bin na ta tayi,su ka zauna suna fuskartar juna,Hajara? Doc Hussaina ta kira sunan ta,ta amsa da na’am,Doc Hussaina ta ce kin yi kuskuran rashin fadawa Suraj,menene dalilin ki amma? Hajjo ta ce wlh ni kai na na kasa gane dalili,ni dai kawai fada ma sa din ne ya min nauyi,shi ya sa ma da ya ce zai turo gaisuwa na ce ya dakata ta dawo,Anty Hussaina daga ina zan fara ne? Wajan wa zan tura shi dangin Baba na? Bare kuma Baba na da ya ce ma zaman kai na na ke,ya so raba ni da diya ta,sanadiyyar haka gashi yanzu bare ke ruke da diya ta,wlh ko Mama ba ta kira na bare ta yarda ma ta zauna guna idan su ka zo hutu,ta riga ta saba da mai rikon ta,ina ga har da haka ma ya sa suka rage zuwa hutu,ta gane abun na sosa min rai. Doc Hussaina ta gyada kai,ta ce ki manta da duk wannan,ki aje komai ki fuskanci rayuwar ki,ki yi kokari ki shedawa Suraj wacece ke,kar ki bari ya ji a baki wani,ba zai ji dadin abun ba. Hajjo ta ce ya na dawowa zan fada ma sa inshaAllahu. Doc Hussaina ta ce wannan kenan,sai zancen tear din ki,ya ki na Doctor za ki aikata aikin matan da ba su san darajar kan su ba? Ba su san ciwan kan su ba? Ya za ki zauna da tear for such a long tym?gaba daya iskar duniya ta gama shigar ki na tabbatar kin ma zama tukunyar iska da guguwa da yayin duniya,idan ma cuta ne haka zai sami wajan zama Kin san darajar wajan nan kuwa gare ki diya mace? Ke bari na aje mi ki girma da kunya na fada mi ki,wallahi ba kya bi na bashin rantsuwa Hajara,ko miji ne ya ji an sami dan sako-sako raina matar ya ke,ba kunya bare tsoran Allah sai a fara mi ki habaici da gutsiri tsoma,ni dinnan da ki ke gani na gama haihuwa,da na ga Oga na shirin fara kawo min rai ni zuwa na ke a kara ni a dinke ni tsaf!na yi jinya ta,sai ki ji dif dif da ni,nan kuma sai Oga ya fara min da’a,na yi haka ya kai sau buyi yanzu tinda na daina haihuwa,wai wani lallami na namiji duk dan me su ke? Dan wajan ne fa! Kunya ta lullube Hajjo,ta yi kasa da ido. Doc Hussaina ta ce ba zancen kunya fa ki dago ki kalle ni,am old enof to b your mother,ita diya mace da gyara aka san ta,kullum aji ki tsaf mana,bare da bakin ki ki ka bamu lbryn dalilin da ya sa auren ki ya mutu,gaskiya da sake sai kin gyara,so gobe ki zo da shirin ki,zan din ke mi ki tear dinnan,sai ki dan dauki hutu in ya healling kya dawo ki. Hajjo ta ce toh Anty Hussaina,kin ga sai na fadawa mijin yaya ta ki na gama min ya wuce da ni kumurya dan ba zan iya jinyar gidan Hajiya ba,Doc. Husaina ta ce toh Allah ya nuna mana. A haka su ka rabu. Hajjo na zuwa gida ta ke shedawa Hajiya gobe da yamma daga asibiti za ta wuce Kumurya,Hajiya ta ce lalle ziyara ta tashi kenan,gwara ana zumuncin ai,Allah ya kai mu,Sani za ki bi? Hajjo ta ce eh,idan ya zo da safe sai na sa kayan tafiyar cikin motar,kin ga da an tashi kafin ta tafi sai ya biyo ya dauke ni. Hajiya ta ce toh ba laifi,Allah ya nuna mana,ta ce amen amen. Ta kira Ayush ta fada ma ta,duk da dai kawancen na su ya ja baya sosai,ita kan ta Hajjo ta kasa gane dalili. Da fargaba Hajjo ta kwana,gani take kamar wani haihuwar za ta yi. Sai da ta jira Sani yazo ta fada ma sa plan din ta sannan ta tafi. Gaban ta na faduwa ta ke komai a asibitin,zuwan Doc Hussaina tini hankalin Hajjo ya gama tashi,ita kuwa sai tsokanar ta ke,maza maza ta tashi su shiga daki,yau ba aiki. Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki,ta bi Anty Hussaina,zani a gefe ta haye gado ta na jiran ta,bayan Doc Husaina ta shirya,hannu cikin hands gloves,ta ce oya oya gyara,Hajjo ta ce wayyo dan Allah ki dai na cewa na gyara,sai na ji kamar Garbati! Doc Husaina na dariya ta bude kafar Hajjo ta ce gwara dai ki tsaya! Kar ki bata min rai na! Sai a sannan ta gane tsabar tsokana ne irin na Doc Hussaina,sai kawai ta yi ma ta shiru,ta na ji ta mata allurar kashe zafi,sai gyada kai ta ke dan azaba duk da an ma ta allurar,dan kamar ba a mata ba,tin tana jurewa sai ta fara ihu,ta na wayyo,wayyo ni Hajjo,wayyo ni diya mace na cin kwakwa,ta na ganin tasko,yi min a hankali dan Allah Anty Hussaina! Wayyo! Doc Hussaina ta na aikin ta,ta ce kin ciki raki,pls ki yi shiru,ki bari na mi ki stiches dinnan yanda za ki ji dadin sa…Hajjo ta ce uhum,na ce tam! Da azaba tai azaba,jin yanda allurar ke shiga ya na fita ta fatar ta,ga wani dan ja da Doc Hussaina ke yi duk sanda ta zira ta fitar, kamar ta na dinke kwarya,sai Hajjo ta fara kamar fada fada,dallah Anty Hussaina ki min a hankali na ce! Haba mana!!wannan rashin imani har ina,Wayyo Inna ta! Yau ina ganin gwale gwale! Ta na yi ta na tsuke kafa Doc Hussaina na kara budewa ta na wlh zan kyale mi ki abun ki Hajara! Ta ce eh dan Allah ki kyale ni! Na ce ki kyale ni mana! Da haka ta lallaba ta dinke ta tas,ta samu ta kwantar da ita dan ta huta,jin ciwan ta ke har tsakiyar kwakwalwar ta. Bayan wasu awanni ne,ta dan nutsu Doc Hussaina ta ja kojera ta zauna gaban Hajjo,ta ce Hajara? Hajjo ta ce ummm,ta ce ke likita ce,kin san yanda za ki kula da kan ki,ba sai na fada mi ki ba,amma dai zan dan tuna mi ki,yau banda zirga zirga,in ki ka cika motsi mai karfi wlh dinkin lalacewa zai yi,sai an sake,ni kuma kin ga bana gajiya. Hajjo ta ce uhum. Doc Hussaina ta kara da zama cikin ruwan zafi Hajara,kar ki yi wasa da shi,pls don’t use dettol! I repeat my slf don’t use dettol,kin san hw powerful it is,ya yi karfi da yawa,gwara ki sa dan gishiri cikin ruwan kafin dinkin ya warke zare ya zare. Sai kuma bagaruwa,ai kin san shi ko? Hajjo ta gyada kai alamar eh,Doc Husaaina ta ce yauwa,ya na da kyau sosai,amma yafi kyau ga wacce ta haihu ko akawa dinki saboda karfin sa,in yayi yawa ya na sane mace,so u can use it for a week ki hada da ganyen magarya,ki tafasa idan ya huce as in yayi yanda za ki iya zama sai ki zauna har sai yayi sanyi sai ki fita,in ya so daga bisani ki na amfani da ganyen magarya shi kadai,twice a day,safe da yamma,sai kuma ki yi hannun riga da ruwan sanyi,kar ki sha mai sanyi karara in ya zama dole ki sha,ban da kuma kama ruwa da ruwan sanyi,kin gane ko? Hajjo ta gyada kai. Doc Hussaina ta kara da Allah ya bada lfy,bara na bar ki ki huta,ta bar Hajjo ta na tunanin rayuwar diya mace.. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [16/10 21:47] .: :29pm, 6/1/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣1⃣ Da yamma Sani ya zo tafiya da Hajjo,Doc Hussaina ta hada ma ta da wasu magunguna,ta ce za ta kira ta,Allah ya bata sauki. A daddafe Hajjo ta shiga gidan Indo,Indo sai sannu ta ke ma ta,shi kuwa sani gaba daya tausayin mata ne ya lullube shi. Sati daya Hajjo na yin yanda Doc Hussaina ta ce sai ga zare ya fita,amma fa ta ji jiki,idan ciwan ya tashi ma ta ji ta ke kamar ta yi hauka. Sati biyu ta sami sauki,a na ukun ta warke garau,ita kanta sai ta ji ta daban,ta fara jin ta cikakkiyar diya mace mai daraja. Su na waya da Suraj sosai,amma ko da wasa ta ki bari ya san ba ta da lfy. A sati na hudun ta komo kano,ran da ta je aiki kuwa sai tsokanan ta su Doc. Hussaina su ke,wai ya su ka ga har ta zama sisi ne,tafiya ta sake ana yanga,sai ma su gwada tafiyar ta sanda aka ma ta dinki,ita dai Hajjo ba ta da ta cewa. Ranar da ta koma gida Hajiya ke ma ta albishirin da dawowar su Khalid,ya dawo Nigeria gaba daya Suraj zai karbe shi,shi ya koma can,in ya so Khalid ya ke duba na nan din. Murna gun Hajjo kamar me,atlast Innar ta za ta dawo gida,dama dai ta na shirin cewa a dawo ma ta da diyar ta. Ranar da su Hajjo passin out,ta karbi certificate din ta na NYSC,Hajjo ta zama Doc Hajara,dama dai abun na Allah ne. ranar jirgin su Khalid ya sauka,amma dai gidan su su ka wuce ba su zo gidan Hajiya ba tukun,asibitin da ta yi service ne su ka riketa. Ita kuma Ayush AKTH ta sami na ta aikin. Suraj na ta ma ta mita,wai shi in da ya ke aiki nan za ta yi,da ya dawo za ta dawo AKTH itama,gwara matar shi na kusa da shi,ita ko da toh ta bi shi kawai. Ranar asabar Hajjo ba ta je aiki ba,ta na cikin kitchen ta na wanke wanke duk da dai yanzu ta tashi daga mai aikin Hajiya ta koma likita mai aikin gwamnati,amma hakan be sa ta daina yiwa Hajiya dukkan aikin da ya dace ba,ta zama kamar diya wajan ta,zancen albashi tin ta na secondry sch ta daina karba,tsakanin ta da Hajiya sai alkhairi. Atamfa ce a jikin ta,dinkin doguwar riga mai igiya a baya,ta kafo dankwali har gaban goshi,ga gashin nan dan tsut ko kamu daya be kai ba an ma sa jerry,gashin da ke kwance goshin ta wanda shi ne ke rufa ma ta asiri ya yi lublub a kwance abun sha’awa,sai ta yi kyau sosai duk da ba kwalliya ta yi ba. Ta dukufa ta na wanke wanke,kamar daga sama ta ke jiyo maganar mutane,ta dai san tabbas baki aka yi,kuma dama dai Jabir ya zo yana tare da Hajiya cikin dakin ta,dan haka sai ta cigaba da aikin ta. Jin gidan shiru Hauwa ta sami waje ta yi zaman ta a falo,Neena ta langwabe jikin maman ta a shagwabance, Khalid da ya kara girma da kyau,ya kara manyanta,ga shi zama cikin turawa rayuwar turai ta shiga jikin sa sosai. Ya kalle su ya ce ku ka ga yanda ku ka wani langwabe,ke Neena leka kitchen ki ga ko Hajiya na cen,na ji karar ruwa. Neena ta tashi,sanye ta ke cikin riga da wando,kai ba dankwali an faka gashi a kyeya,ga alamun girma sun fara bayyana a cikin ta,amma yanda Hauwa ke shagwaba ta ya sa ta tashi a sangarce,uwa ba kwaba. Kai tsaye kitchen din ta je,ta shiga ba tare da ta yi sallama ba,ganin Hajjo na wanke wanke sai ta tsaya kawai bakin kofa. Hajjo Ji ta yi kamar ba ita kadai ba ce ba,ta juyo su ka yi ido biyu da fuska mai kamar na ta sak,diyar ta kuma Innar ta. Inna? Inna ta ke ce? Wani irin farin ciki ya mamaye Hajjo,ta aje wanke wanke ta taho ta na Inna? Zo mana! Ina ita dai yarinya Neena ta san ana kiranta ba Inna ba,gashi kuma ba ta san Hajjo ba,ganin ta nufo ta,ta juya ta fice da sauri,ta kusa bige Khalid da ya biyo sahun ta,ganin yanda ta fito da sauri sai ya karasa kitchen din ya na sarkin kin mutane wa ki ka gani kar dai Hajiyar tawa ta ke gudu….ganin ta tsaye ya sa shi zuke maganar,ita ma kuma Hajjon tsayawa ta yi ta na kallan sa bakin bature ne wannan ko kuwa mai kama da shi,dan bakin bature dai da ta sani be kai haka manyan ta ba, be kuma kai haka kyau da kwarjini ba. ganin na ta ya ma sa bazata,be taba tunanin zai ga irin wannan fuskar ba bayan wanda ya sa ba gani,she is jst lyk his beloved one,lyk his Neena…shin wannan wacece? Kar dai maman Neena ce,Child abuse?tambayar da ya ke yi wa kan sa kenan cikin ran sa,he was soo confused,Uwar ce da ta kara girma ta rikida ko kuwa diyar ce ta girma ta zama uwar…..? Ji ya yi an taba kafadar sa ance ai sai dai diyar ta girma ta zama uwar,dan tin zuwan Child abuse gidan nan kamannin ta haka su ke ba ta canza,kawai dai ma su ido ke gani….hakan ya tabbatar ma sa a fili yayi maganar ba cikin ran sa ba,ya juyo ya na dariya,ya ce kwarai kuwa ma su ido da baki irin su Jabir ba,duka dariya su ke su ka rungume juna cikin musabaha. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 5:13 PM] Salmah Ateeku: [6:38pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣2⃣ Jabir na dariya ya ce da Hajjo kamar fa kin ruda kanin nawa,cikin girmamawa da kuma jin nauyin maganar Jabir ta gaida Khalid,ya amsa idanun sa kanta. Jabir ne ya janye shi ya na fadin wallahi child abuse din nan ta ka ce ka ma bar kokanto yaro! Ta na jin shi ya na wlh Jabir kada fa ka matsa min! Sai na fadawa Nabeela abunda ka fada min rannan! Shegen maza! Ta ciyo Jabir na zagen Khalid,ga dariyar su na tashi kamar su kadai ne a gidan. Hajjo ta saki ajiyar zuciya,damuwar da ke kwance cikin ranta ce ta taso,gaba daya ji ta ke ranta a dagule,ya za ta haifi diya ta na gudun ta? Su ma su rikon ta ba su sheda ma ta wacce mahaifiyar ta ba? Me ma su ke nufi ne? Kai lokaci ya yi da za a dawo ma ta da diyar ta gaskiya! Da wannan tunanin ta cigaba da wanke wanken ta,tsabar bacin rai ma ta kasa katsewa ta je su gaisa da Hauwa. Sai da ta gama tsaf. Can falo kuwa Hajiya zaune tare da su Khalid ana hirar ya bayan rabuwa,Jabir ya tafi gidan sa. Tin fitowar su hankalin sa ke kan hanyar fitowa daga kitchen,Allah Allah ya ke ya kara sa Hajjo a idon sa,ya ga baiwar Allah,kamar da diyar ta kamar an tsaga kara,kawai dai dan ita yar fara ce,ita kuma uwar wankan tarwada,da kuma ita Innar yarinya ce da sai ma ace yan biyu ne.bini bini Hajiya sai ta kalli Inna ta ce yarinya fa ta zama budurwa,yanzu wa zai kalle ta ya ce mahaifiyar ta ce ta haife ta,ai sai dai ayi zatan yaya da kanwa ne. Khalid ya ce wlh kuwa,ni kai na na yi mamaki kwarai da na ga uwar! Ita dai Hauwa da anyi maganar Hajjo gaban ta faduwa ya ke,duk da dai ta san Neenan ta ta ba diyar ta ba ce,amma ba ta ji za ta iya rabuwa da ita,shi ya sa ma ko zancen Hajjon ba ta ma ta,kunga karfin hali barawo da sallama. Hajjo ta fito fuskar ta dauke da murmushi,da Khalid ta fara hada ido saboda dama dai shi ne ya kasa ya tsare ya ke jiran tsammanin sake ganin ta. Ta yi saurin janye idanun ta da ga na shi gaban ta na faduwa,wajan Hauwa ta karasa ta na maraba sannun ku da zuwa,ita ko Inna da ta ga haka sai ta koma gefan Khalid. Hajiya ta ce aw ku ga yar butan uwa! Uwar ta ki ki ke gudu? Hauwa ta ce ina ruwan Neenan Mama,kin san ba ta san ta ba. Maganar ta yiwa Hajjo daci,amma sai kawai ta boye,ta ma dauke kai daga kan Innar. Bayan sun gaisa ta tashi ta ba su wuri,wanda hakan be yiwa Khalid dadi ba,ita kuwa Hauwa hakan daidai ya ma ta. Bayan tashin Hajjo, Hajiya ta bijiro mu su da maganar Inna,hankalin Hauwa ya tashi gudun kar Inna ta gane zancen da ake ta ce da ita ta Neena tashi ki je daki ki kwanta abun ki. Tana tafiya Hajiya ta ce kun dai san ya kamata ba sai an fada mu ku ba,amma na ga alamar ba ku ma shirin yin abunda ya kamata,kamata yayi ayau dinnan ku taho da komai na yarinyar nan ku damkata hannun mahaifiyar ta,ta mu ku kara ai. Idanun Hauwa yayi rau rau zai kawo ruwa,Khalid ya gyara zama,ya ce dama Hajiya za a yi hakan,dama so mu ke mu gama settle….ah ah! Hajiya ta katse shi,yarinyar nan fa alkunya ta ke mu ku,it is high time auta,ku dawo ma ta da diyar ta. Khalid ya sosa kyeya,idanun sa kan Hauwar shi,ganin yanda gaba daya ta sauya yanzu yanzu sai ta ba shi tausayi,dole ya nemo mu su mafita. Ya ce toh Hajiya ta,yanda ki ka ce haka za a yi,ta ma yi kokari ai,amma dan Allah ki ba mu zuwa sati na gaba sai mu dawo da ita din. Hajiya ta ce ko ku fa,Allah ya nuna mana,ya ce amen. Farin cikin Hauwa ya gushe,daurewa ta yi kawai har su ka gama wuni a gidan,amma kowa ya san ta na cikin damuwa. Suna komawa gidan su kuwa,ta samu ta kebe da Khalid sai kuka. Kuka sosai ya ma kasa rarrashin ta dan tuni ta riki ta shi,sai da kukan na ta ya tsagaita,kwance cikin sa ya ke ba ta baki,haba baby-luv,toh menene na kukan? Ta na ajiyar zuciya ta ce ya bazan yi kuka ba? Kasan matsala ta Khalid,kasan ba na haihuwa ba zan taba haihuwa ba ma wasu likotocin da ba su iya magana ba su ka ce….shhhhh ya toshe ma ta baki da dan yatsa,ya ce kema kin ce wanda ba su iya magana ba,ki sa Allah a ranki baby-luv,shi kadai ne mai iya bawa bawan sa kyauta sanda be yi zato ba,shi zai ba mu haihuwa…Hauwa ta ce haka ne,ban fidda tsammani ba duk da kowani indication ya nuna kishiyan haka,amma Beb idan aka dauke min Neena ban san inda zan sa rai na ba,ya zan yi da rayuwa ta,na riga na saba yarinyar ta shige jiki na.. shiru ya yi daga bisani ya ce ba yanda za mu yi,dole mu mayar ma ta da diyar ta,kar ki damu,Allah na sane da mu. Nan fa sai Hauwa ta kara fashewa da kuka,tin ya na rarrashi,har ya kyale ta,kusan kwana ta yi ta na kuka,wai za a raba ta da diyar da ke kiranta Momma. Washagari abun duniya ya ishi Khalid,shi ma din tafiyar Neena na damun shi,babu yanda zai yi ne kawai,da ga shi har matar ta shi babu mai walwala,zuciyar sa na sake sake kala kala,hez 37 yanzu,Hauwa 31,amma ko kwai be taba ajewa ba,shekaru na ja,tsufa da mutuwa na gabatowa,shin rayuwa za ta yiyu a haka kuwa? Da sam haihuwar ba ya gaban shi,sai yanzu da ya manyanta ya fara damun shi,duk da kuwa be taba nunawa baby-luv din ta shi ba. Da yamma ta yi sai ya wuce gidan Hajiya,ganin ta tare da Hajjo zaune cikin dakin Hajiyar sai abun ya bashi sha’awa,ita Hajiyar ma kenan da Allah ya ba ta haihuwa,dan dai kawai ba ta da diya mace ji soyayyar da ta kewa Hajjo da ta yi kusan rabin rayuwar ta a hannun ta,bare shi da be san dadin haihuwa ba,sai akan Neena,wacce tin ta na shekara biyu ta ke tare da shi. Hajjo sanye da doguwar riga baka,ta rufe kanta da mayafin rigar,daga gani fita za ta yi ko kuma daga fitar ta dawo,ganin sa ta yi saurin tashi za ta fita,Hajiya ta ce ina dawo ki zauna,kin ga shigowar Khalid za ki sami damar fita,zauna shima ya taya ni ai,Hajjo ta koma ta zauna a takure. Idanun Khalid kan ta,shi dai mamakin girma,kyau da wayewar ta ya ke,gaba daya ta canza kamar wacce makirin mata ya kyera. Ya dan kalli Hajiya ya gaishe ta,sannan Hajjon ma ta gaisheshi,yanda ta saba cikin girmamawa. Khalid ya ce Hajiya kamar ki na zan taya ki,me zan ta ya ki? Hajiya ta ce jin ta baki Hajjo,sam na ga alama ba zancen aure a gaban ta,ya kamata ta yarda tsayayye ya fito. Dim! Ya ji wani irin mummunar faduwar gaba,sai da ya koma ya dan jingina da bango…. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7:06pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYAMACE👭👭👭 4⃣3⃣ Ya gyara murya ya ce Hajiya ai gwara dai kar a ma ta shisshigi,tin da ba yarinya ba ce,auren nan ta yi na fari dama,kar a azalzale ta a jira na gari ya zo sai ta tsayar din. Hajiya ta ce ahaf,kar ka mai da mu baya kai kuma,wani na gari ya zo? Ai tuni Hajjo na da nagarin ta a hannu…da sauri ya daga ido ya kalli Hajjo,wani abu ne ya tsaya kamar kashi cikin ransa,well obviously mace kamar Hajjo ya kamata ace ta na da manema,plus shi ina ma ruwan sa ne? Tambayar da yayiwa zuciyar shi kenan! Ina ruwan ta da kaduwa akan maganar child abuse? A zahiri tambayar Hajiya ya yi waye shi na garin? Hajjo ta saci kallan sa ta wutsiyar ido,see dis man! Ina ruwan shi da ni da har zai na tambaya kan rayuwa ta! Ni fa shisshigi ne ban so,dan ya na ruke da Inna ta be zama uba na ba! Tafasar da zuciyar Hajjo ke yi kenan. Hajiya ba tare da ta kawo komai ba cikin ran ta,ta ce wani likita ne,Surajo,Jabir ma ya san shi,yaran arziki wlh. Ran sa idan yayi dubu ya baci,ya kasa gane mai ke ma sa dadi,wai ma ina ruwan sa ne! Toh Allah ya sa a yi da mu. Hajiya ta ce amen amen. Hajiya bari na tafi,dama gaishe ki na zo yi na yi da Jabir zan dauko sa daga asibiti,akwalar motar ta sa da ya kasa rage ciki ya sake ta kara samin matsala. Hajiya ta dara ta ce kamar a kunnan sa. Shi ma darawan yayi duk da de ba dadi ya ke ji ba,ya ce kin san dai gaskiya na fada. Zuciyar Hajiya daya ta ce in dai haka ne ka ragewa Hajjo hanya…..Hajjo kamar ta kurma ihu,sam ba ta san abunda zai hada ta da Khalid,da sauri ta ce ah ah Hajiya ba ma sai ya rage min ba sai na hau a daidaita sahu. Hajiya ta ce AKTH zai je,kin ga ina kundila ina AKTH,ai ya fi sauki ya sauke ki..dan kar na bata ma sa lokaci Jabir na jira Hajiya,Hajjo ta kara kan bayanin ta. Da ya fuskanci bin shi ne ba ta so,sai ya ce no ba bata lokaci,mu je na sauke ki kidin. Kamar ta yi kuka ta yiwa Hajiya sai ta dawo,Khalid ya ma ta sallama,su ka fito ya na gaba ta na biye da shi,sai watsawa bayan sa harara ta ke. Ko da su ka kai mota,ya bude ya shiga sai ta bude baya ta shiga ta rufe. Sai a sannan kamshin ta ya mamaye hancin sa,ya bi numfashin sa,kamshi ne mai dadin gaske ga sanyi,da ke ta na amfani da turaren the body shop(indian nyt jesmine) wanda Suraj ke yawan aiko ma ta da su,sai kuma wani hadadde kuma dadadden Humrah da Aunty Hussaina ta ba ta,so wani kamshi ta ke mai rikitarwa,kaji kamar ka janyo ta jikin ka ko ka samu kai ma ka shafa. Ya lumshe ido ya bude,gaskiya babu abunda ya kai kamshi dadi a duniya dadi,zaman Hajjon a baya ya sa ya ki tada motar,sun kai kusan minti goma a haka,shi dai be damu ba,as long as ya na jin kamshin nan,zaman is worth. Hajjon ce ta gaji,ta ce ko motar na da matsala ne?ya ce me ki gani? Ta ce na ga ba mu motsa ba. Ya gyada kai, Yes ta na da matsala,as long as u sitting der,ba za ta tashi ba. Cikin mamaki ta ce ikon Allah,me ya hada zama na a nan da kuma tashin mota? A hankali ya juyo suna fuskar tan juna,tini Hajjo ta daina numfashi na dan sakanni,ganin yanda mischievous idanun shi ke kallan ta,ta yi saurin nisar da na ta idon. Ya lura da yanayin da ta ke shiga duk sanda ya kalle ta,she catches her breath duk sanda ya kalle ta su ka hada ido,kamar yanda shi ma his hrt beat faster dan normal duk san da ya sa ta a ido. Ya na murmushi ya ce am nt a driver Hajiya…..ido a kasa ta ce nan ne wajan zama na a motar ka 11 years ago,u knw dat as well Alhaji… darawa yayi,indeed ba wai kamannin Hajjo ne kadai ya canza ba,hatta maganar ta ta sake,ta za ma brazen! Juyawa yayi ya na murmushi mischievously,ya ce yes u made ur point,noted,so dawo gaba in ki na so mu tafi,idan kuma kina san ki ta zama ne,i wil nt mind,cos i love ur scent,ya sunan turaren ne? Ta ma sa banza,ya dara tare da fadin shi ya kamata a kira a ba rai dadi,i soo much luv it. Ji ta yi kamar ta fasa fitar,sai dai sakon na Hajiya ne,kuma ba ta so Hijiyar ta ga ta ki bin maganar ta da ta fita ta hau dan sahu. Da wannan tunanin ta fito ta shiga gaban,kamshin na ta ya kara shigar Khalid har cikin ran sa,cikin zuciyar sa ya ce Astagafirullah! Allah ka yafe mana ni da wannan baiwa ta ka,dan gaskiya kamshin na ta ya ma sa,kamar ba shi ne mai sauke glass ko dauke numfashi da ta gifta shi. Hmmm duniya juyi juyi kwado ya fada ruwan zafi. Ganin ta dawo din,kuma be motsa ba,ta ce na dawo. Murmushi ya sakar ma ta,wacce ita kanta ba ta san na menene ba,yayinda ya kunna mota su ka fito su ka dauki hanya. Babu wanda ya sake magana har ya sauke ta,ta bishi da Allah ya tsare. Ya amsa amen. Sai da ta shiga gidan da ya kai ta sannan ya kunna mota ya tafi,ran sa cike da sake sake iri-iri ya karasa AKTH. Maimakon Jabir ya taho shi kadai sai ya taho da abokin aikin sa,Doc Ahmad,wai za su aje shi na’ibawa. Khalid na driving amma gaba daya hankalin sa ba ya wajen,kamar daga sama yaji Jabir ya ce wata kanwar ta wa ka ke so? Hajara?….kiiiiiiiiiiiii Khalid ya yi saurin ta ka birki,dan ya kusa bugawa wani jin inda maganar ta su ta dosa. Jabir dake zaune tare da shi a gaba ya daki kafadar sa ya na dan uban ka ka goga yar motar ta ka da ka ke ji da shi kamar kwai! Khalid yayi karfin hali ya murmusa gami da dagawa wanda ya kusa bugawa hannu,cikin ba da hakuri,ya ce ahaf tawa za ta siyi akwalar motar ka goma,ka ga ko dole na ji da ita! Jabir ya ce karya ne wlh,ya rush o karya ka ke! Gaba daya dari a su ke,Jabir na shirin cigabawa da maganar Doc Ahmad ya ce pls mu yi maganar Hajara,na kusa sauka,ya za a yi ne? Wlh shez exactly the womon of my dream,ga kyau,ga kwalliya irin na matan da su ka san ciwan kan su,ga sanin darajar mutane,ga tsafta…. o yes! Jabir ya katse shi,she is neat,exceptionally neat wlh,ga ga ga ga din Hajjo da yawa su ke Alhaji. Khalid dai ya baza kunne,ya na jira ya ga iya gudun ruwan su. Jin Doc Ahmad ya ce ka tabbata ba maganar kowa as in ba ta sasansan ta da kowa ba? Jabir ya ce etoh gaskiya.. kafin ya karasa Khalid ya saurin dakatar da shi ta hanyar tare maganar…gaskiya nauyin bayani ya ke ma,wato kai ma Jabir ka iya bugan cikin mutum,ka ma sa shiru ya na ta sakin layi,baki bude Jabir ya ke kallan Khalid,Khalid ba kunya bare shakka ya ce Doc Ahmad,na gode kwarai da yabon my wife to be da ka yi,amma an ba da ita. Jikin Doc Ahmad yayi sanyi,Jabir ya ce kut! A gidan ubanwa…… Jabir ka yi shiru kawai,ya dan kifta ma sa ido,ai Ahmad wil undstnd,kawai so ka ke na ji ana yaban Hajarar a gabana dax y,ryt? Jabir ya ma sa banza. Cikin jin kunya ya ce amma gaskiya Jabir ba ka kyauta ba,kullum na ta ma ka maganar yarinyar nan,ashe kanin ka ne zai aure ta ba ka fada min ba? Jabir ya ce kasan Allah Ahmadu….be yi da niya ba! Khalid ne ya kara katse shi,duk bakin Jabir sai gashi be da ta cewa. Doc Ahmad ya ce na gode Khalid,tsaya na sauka a nan. Khalid ya ce haba ai ba mu kai ga layin dan Hassan din ba,bari na karasa da kai ma na. Doc Ahmad ya ce kar ka damu,nan ya isa. Innocently Khalid ya faka,cike da burin kunya Doc Ahmad ya sauka,ko sallama be yiwa Jabir ba. Ya na fita Jabir ya fara sirfowa Khalid zagi,har da kun ga shegen maza! Gidan ubanwa ta zama ur wife to b? Kai wai haka ka dada lalacewa? Karya kuma Khalid? Ko a jikin sa ya ce karya kuma sai ka ce yaro Jabir? Jabir ya ce in ba karya ba har yau she ka dawo da za ka ce kun sasanta da yarinyar nan? Hankali kwance ya ce ni na ce ma da ita na sasanta? Toh da uban wa ka sasanta? Idanun sa kan hanya ya amsa da zuciya ta,yanzun nan na yanke shawara da zuciya ta dat i hav no choice buh making her my wife……ko da kuwa za a maimaita yakin badar! Dariya mai karfi Jabir ya saki,ya ce ko ba da zuciyar ka ba? Ga fili ga doki,ba ma yakin badar kadai ba,a ma yi na uhud!caf kai rigimar ma ka ma ba ta sallah wlh. Na ga dai ba wanda ya kai ka kyarar Hajjo,child abuse ma ka ke kiran ta,amma daga dowar ka ka ga ta zama very beautiful nd sophisticated woman har ka fara san ta? Cikin takama da dagawa ya ce har akwai wani beauty da sophistication da ya dara na ma tar sa na ke aure? Ta hada komai na diya ma ce,she got everyting na diya mace,Kasan ba maganar so,Hajara is nt even my type,kawai larula ce ta sa na ke considering auren na ta,Hajiya ta ce na mayar da Neena,hankalin wife dina ya tashi,plus am getting older kullum,at 37 ban da kids,so zan aure ta ne saboda abu biyu,na fari ka ga Neena za ta zauna guna,logically i wil remian her dad,na biyu kuma d woman wil bear my kids as many as i want…. hmmmm Jabir ya gyada kai,very selfish nd arrogant brother i have,ka san Allah? Kar ka sake ka matsawa yarinyar mutane saboda selfish interest din ka,ta na da wanda ta ke so,u better stay away from her. Khalid ya daga kafada,wannan na ka ra’ayin kenan,wat if shez interested? Bare na san she is,dole shi is cos ko wata mace burin ta ta sami miji kamar ni,ol women wants an outstanding man as a husby,kasan ma ta nawa ke sona ina mu su yabs bare kuma ni da baki na ce zan aure ta,God she should even b grtful,ai ina fada ma ta za ta hau murna,I tell u bro! Jabir ya murmusa,ya ce ba ko ba Hajjo ba? Ayi mu gani,.. Da haka su ka isa gidan Jabir,zai fita Khalid ya ce ya za a yi a min hanyar Hajara ne? Na ga da kai ake kama kafa….Jabir ya ce for ur imformation,yarinya na da correct man,a Doctor so kar ka bata lokacin ka!Khalid ya ya yi mika ya na mischievous murmurshi ya ce ko kai ne correct man din,d so called doctor sai ka saurara ka bar wajan bare kuma wani bare,Khalid ne fa kanin ka,taba neman mace na rasa ba! Sai dai ban nema ba! Jabir ya murmusa ya ce wannan karan ka ma rasa! Khalid ya ce no ka bani five month za ka ga Hajara a gida! Jabir ya na dariyar yanda Khalid ke da gadara,ya ce get lost! Ya na dariya Khalid ya tada motar shi,ya na a gaida uwar yan mata,Jabir ya daga ma sa hannu ya shige gidan sa. Khalid ya kama hanya da tunanin kudirin da zuciyar sa ta yanke,if realy goin to hav a second wife,den she should b Hajara. DEDICATED to The Women Of virtue💁👰🙋(group). Skip to content ummu-abdoul MENU Diya mace 2nd post Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17, 2016 ​[16/10 21:47] .: /25, 5:15 PM] Salmah Ateeku: [7:32pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣4⃣ Da zancen Hajjo cikin ran sa ya kwana,washagari Allah Allah ya ke yamma ta yi ya samu ya je gidan Hajiya ya ma ta zancen Hajjo ya ji ta bakin ta kafin ya yiwa Hajjon magana,dan ya san sai da yamman ake samun Hajjo a gida in dai ba weekend ba. La’asar sakaliya a gidan Hajiya ta ma sa,ya ko ci sa’a Hajjo ta dawo. Maganar ta sa ta yiwa Hajiya dadi,toh amma sai ba ta nuna ma sa sosai ba kar yayi taking advantage of it ya yi tunanin Hajiya za ta sa baki. Ta ce auta ba laifi idan za ka kara aure dan matar ka ba ta haihuwa,hakan ma dole ya faru tinda kowa ya na so ya ga zuri’ar sa ta cigaba from generation to generation,zabin ka na Hajjo shi ma ba laifi,amma ka same ta da kanka ku sasanta,dan ni na san Hajjo na da manemi,idan ta ga za ta aminta da kai,tin da waccan iyaye ba su shiga ba,fyn tsakanin ku,idan kuma ta ce ah ah,ban da takura,ka nemi wata. Ni dai fatan alkhairi mu ke,bazan sa baki ba sai Hajjo ta amince dan kanta dan sa baki na zai iya sawa ta yarda ko da kuwa ba ta so. Khalid ya ce Hajiya ta za ma ta so ai,am very sure of dat. Hajiya ta dara ai dama kai dai kam u ar olways full of urslf,toh Allah dai ya sa. Khalid ya ce amen. Hajiya ko za ki yi kiran Hajjon sai na sheda ma ta ko? Bara na jira ta a karamin falo,Hajiya ta ce toh bari na kira ta din. Hajjo kwance bisa gadan ta,ta gama waya da Suraj kenan ya fada ma ta wata daya ya rage ya dawo,sai sakar yanda za ta tarbe shi ta ke cikin ran ta,dan a zahiri ta fara sabawa da Suraj sosai ta damu da shi ba kamar da ba. Wayan da ke kan bedsyd din ta ne ya fara ringn,da ga kwance ta sa hannu ta dauka gami da karawa a kunnen ta,ta ce Hajiya na zo ne? Daga dayan bangaran Hajiya ta ce Khalid ne ke san magana da ke,ya na jiran ki karamin falo. Hajjo ta dan yi jim..Khalid? Ni kuma? Ta ce tam Hajiya,zan same shi yanzu. Ta aje wayar ta na tunanin me kuma ya faru? Ko ya dawo ma ta da Innar ta ta ne? Bari dai ta fita ta ji. Da ke ba kayan arziki ne a jikin ta ba,sai ta ja hijabin ta har kasa ta sanya,kai tsaye ta fito ba tare da ta damu da ta duba kamannin ta a madubi ba. Ta na shiga falon kamshin turaren shi ya daki hancin ta,ya harde kafa daya kan daya kan kujera,sanye da kanana kaya da ke matukar ma sa kyau. Ido su ka hada,ya sakar ma ta murmushi,ta ki maida ma sa da murmushin,sai ma sallama da ta ma sa,ta sami waje a kasa ta zauna gefe guda. Ya ce ya ki ka zauna a kasa? Dawo nan mana ya nuna kujerar da ke kusa da shi. Hajjo ta murmusa,dimpol ya bayya wanda ke kara ma ta kyau,no am owk nan ma. Ina wuni? Ya aiki? Ya amsa da lfy lau,ya na ki aiki? Ta ce Alhamdulillah. Sai kuma su ka yi shiru,Khalid ya zuba ma ta ido,kawai Neena ce zaune. Ya ce shez jst lyk you. Ta daga ma sa gira tare da fadin sorry? Ya ce diyar ki Neena,is precisely lyk you. Hajjo ta murmusa,ta ce na sani,is dat y u called me? To tell me am jst lyk her ko kuma wani abu ne ya same ta? Khalid ya dara,shi kawai mamaki ta ke bashi,child abuse ce haka ta ke iya kallan sa ido cikin ido ta bashi amsa daidai da ta shi,har wani sa’in ta watsa ma sa da yar magana? Kai gaskiya boko yayi,jami’a ba wasa ba ce. Ya ce no,ba ma saboda ita na ke neman ki ba,it is abt us,maganar mu ce ni da ke. Gaban Hajjo ya fadi,amma sai ta basar dan kar ya gane,ta ce us? Ni da kai? Hope all is well. Ya ce yes ol is well,na yanke shawarar auren ki ne a matsayin ki na mahaifiyar diyar da na ke so. A hankali ta daga ido ta kalle shi,maganar ta ma ta kama da tatsuniya,be yi mamakin ganin ta sa dariya ba,dariyar ta ta mai ban sha’awa,wushirta da dimpol din ta du su ka bayyana su ka kara kyawata kyan ta. tsayawa ya yi ya na duban ta kawai fuskar shi dauke da mischievous smile,dama ya sani,ya san she will celebrat idan ya ce zai aure ta,ko wace mace za ta yi,dama dai Jabir ya na nan ya gani da idanun sa. Ga mamakin sa da dariyar ta ta ta tsaya sai ya ga ta tashi ta na nufin juyawa ta fita,yayi zatan tsabar farin ciki ne ya sa za ta koma daki dan ta yi celebratn da kyau,ya ce wait,ba shi kenan ba ai Hajiya,wen za a fara maganar aure? Ta juyo ta na murmushi,Khalid? A karo na farko da ta kira sunan shi,wanda shi kan shi be lura da haka ba sai a yanzu,hakan kuma ya sa shi shiga wani yanayi na kasa gane shin wai ina matar nan ta dosa ne? Lokacin kuwa ta fahimtar da shi. Ta ci gaba da fadin wannan shi ake kira expensive joke,pls ina respect din ka,for d fact dat diya ta consider u a father,nd kai kuma ka yi taking responsbility din ta as if kai ne mahaifin ta,so i beg of u let us maintain dat,nxt tym in ka na da jest try someone else nt me,ta kare da murmushi. Gwiwar sa ta fara sanyi,wato shasha ma ta dauke shi ashe,hw dare her! Shi ma din tashi ya yi,ya tsaya gaban ta,ya ce expensive joke? Jest? Tin da mu ke na taba mi ki wasa ne Hajara? Hajjo ta ce Hajjo,kira ni da Hajjo ba Hajara ba pls,haka kowa ya ke kira na. Zan cen tin da mu ke babu,dan ba mu ta zama tare ba,daga nesa nesa dai jst lyk now,dax y na ce kar ka soma. Khalid ya ce ba wasa na ke ba toh,i mean it,marry me. Hajjo ta murmusa ta ce y should i of all people marry d mighty Khalid? Duk da ya san zolayar sa ta ke,ya gyara tsayuwa ya ce saboda Neena,nd ina so na sami yara nawa na kai na su zama tsatson su daya da Neena,kin san mata ta ba ta haihuwa,i want u to bear my kids. Hajjo ta dara,ta ce toh bazan aure ka ba. Cike da mamaki ya ce wannan amsa haka kiri kiri? Saboda me ya sa? Ta ce saboda you ar nt my type,i can’t even manege someone lyk you. Tsayawa yayi ya na kallanta,ya ma rasa amsar da zai ba ta har ta juya ta fice. Komawa yayi ya zauna,Hajjo ta ma sa bazata matuka,shin dama akwai macen da zai ce ya na so ya aura ta ki? Kai ko Hauwa da ta hadau ten over ten ba ta ma sa aji ba,bare kuma karan kada miya Hajjo. Ya saki ajiyar zuciya,obviously Hajjon da ya sani a da wato child abuse da wannan Hajjon ar two differant worlds! Rai bace ya tashi ba tare da ya yiwa Hajiya sallama ba ya bar gidan. Tin shigar ta daki ta haye gado ta yi kwanciyar ta,wai ita Khalid zai kalla ya ce zai aura tsabar ya yi niyyar ya wulakanta ta,shi kan shi ya fi ta kyau bare matar shi da Allah ya bawa baiwar kyau,mtws ta ja tsaki,in har wulakanci ne d toh wlh sai dai kar ta san kar,dan ita ba kowa ba ce,ba kuma ta isa a kira ta kowa ba ba za ta zauna a wulkantata ba. NO WAY! DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7:49pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣5⃣ Ganin Khalid ya tafi ba sallama Hajiya ta san ba a yi ta dadi ba,dan haka sai ta nuna kamar ba ta ma san zancen ba. Hakan ya sa Hajjo sakewa,ta ma mance da maganar ta da Khalid. Da ranar da ya kamata su dawo da Neena ya yi su ka ji shiru sai Hajiya ta fara fada,za ta yi kiran Khalid din ta ma sa tatas Hajjo ta ce wlh Hajiya da kin kyale su,ki bar su zuwa sanda zan yi aure ta dawo wajan nawa,tin da da nan din da can duk daya ne,Hajiya ta ce anya kuwa Hajjo? A biye yanda su ke so? Dama fa nufin na su kenan. Hajjo ta ce ba komai Hajiya,mai san na ka ai ya gama ma ka komai,tsakanina da su sai fatan alkhairi. Hajiya ta ce toh madallah. Ta kira wayar Khalid,ya na dagawa ya ce Hajiya yi hakuri,kin ji ni shiru Hauwa ce ba ta jin dadi na ce zan bari zuwa gobe…Hajiya ta ce toh ai abunda ku ke so ne ya faru,Hajjo ta ce ku kyale ta har zuwa auren ta sai ta dawo gurin maman ta. Saukar numfashin shi har sai da ya fito ta bangaran Hajiya,ya ce kai amma ta kyauta,zan fadawa Hauwar,a mana godiya,Hajiya ta kashe waya ta na fadawa Hajjo yanda Khalid ya hau murna. Murmushi kawai ta yi,ikon Allah wani diyoyi ma ta ya tsana,ga wani kuma ko diya macen be samu ba,sai kwalafacin ta wani ya ke,Allah mai yanda ya so. Ranar lahadi gidan Jabir Hajjo ta wuni,ta na can suna shan hira da Nabeela,ta zama kamar yayar ta,kamar yanda Jabir ya zama yayan ta. Suna zaune a falo sai ga Khalid ya aje Jabir,ya na mitar idan ba zai sake mota ba da ga yau ba zai sake dana shi a tasa motar ba diyar Jabir ta fito da gudu ta ba Baba Anty Hajjo ta siyo min choculate,ai kuwa sai Khalid ya ce ina ta ke Anty Hajjon? Ta ce ta na ciki ai,ta ce sai Baba ya dawo za ta tafi. Be yi niyar tsayawa ba saboda hadari da ya ga ya taso,amma jin haka sai ya faka ya fito,Jabir na fadin shegen maza,yanzun ai ga shi ka fito. Ya na murmushi ya ce my wife to b a gidan ka,dole na shiga. Diyar Jabir ta shiga da gudu ta na Mama ga Baba har da uncle Khalid! Jin haka gaban Hajjo ya fadi,tini ta nutsu ta ja mayafin ta ta rufe kan ta,Khalid? Ba ta yi niyar sake ganin shi ba,raban ta da shi tin ranar da ya zo ma ta da yashasshan zance,wlh da ta san zai zo da ba ta tsaya jiran Jabir ba….Nabeela ta na fadin yau Khalid a gidan nan,tin dawowar sa ban sa shi a ido ba,gwara ma dai Hauwa da Inna sun zo,babbar diyar Nabeela ta ce mama Neena ake cewa ba Inna ba. Nabeela ta ce aw Inna fa ta koma Neena,duk dariya su ka sa,sallamar Khalid da Jabir da shigowar su lokaci daya ne. Ya na shiga idanun sa su ka isa izuwa inda ta ke,be da buri da ya wuce ya kalle ta ya ga yanda ta ke reactn duk sanda ya san ya idanun sa cikin na ta,gashi d more ya ke ganin ta d more ta ke kara ma sa kyau,ganin ta ya yi cikin riga da wando na pakistan ja,mayafin yane bisa kanta gashi gashin goshin ta yayi lublub abun sha’awa ka yi zatan irin gashin nan ne na gaske. Kamar ta sani sai ta ki kallan ma in da ya ke,ta na murmushi ta ke yiwa Jabir sannu da zuwa,ya na yauwa Sannu my sister,ya na fama da yara da maman su,wata ruke da hannun sa na hagu,wata na dama,wata kafa,ga maman su ruge da jakar sa da ta karba,sauran yaran biye da su su ka shige ciki kowa na nashi surutun, aka bar Hajjo da Khalid a falon. Sai a sannan Hajjo ta daga ido ta kalle shi,ganin yanda hankalin sa gaba daya ya karkata ga inda su Jabir su ka shiga,ta ga yanayin da ya ke ciki,ta tabbata Jabir da yaransa ne su ka bashi sha’awa,rashin ‘ya’ya sam be da dadi,sai ta dan tausaya ma sa,amma na kankanin lokaci saboda ita ta shagala ta na kallan sa,har ya kama ta,sai ji ta yi yace am i dat handsum suger? Ta yi sauri kau da kai cikin jin kunya ta ce sannu da zuwa,ya aiki? Ya murmusa,yan da ya ga ta na kallan na sa ne ya ma sa dadi kwarai,ya ce hamdan. Jabir ya fito biye da Nabeela,sun hada yara da kayan dadi sun rabu da su a daki. Nan ya zauna tare da Khalid Nabeela ta kawo mu su abunci,Hajjo ta tashi za ta ba su wuri Jabir ya ce ta zauna abun ta,yay ta jan ta da hira,yanda ya ga ta sake da shi ya sosawa Khalid rai,wato shi ne dai ba ta so,ba ta ra’ayi,ko ya sa baki a zancen sai ka ji ta yi shiru,Nabeela ce ma mai kokarin sa shi cikin hirar. Sanda su ka gama cin abunci Hajjo ta fara shirin tafiya,Khalid ya ce dama dai gida za shi bari su tafi tare. Hajjo ta ce ah ah,ita ba gida za ta ba,Khalid ya ce ko ina za ta ba damu,he is free. Nabeela ta kalli Jabir da alamar tambaya irin wats up wit dem,ya daga kafada ya aje lyk i donno. Jabir ya gyara murya ya ce my sister gwara ya aje ki din,ga hadari kar ruwa ya taba ki. Da ke ta na jin maganar Jabir,ba mu su ta ce tam yaya na. Khalid ya kalle shi tare da fadin toh yayan ta da fatan xa a gyara ko a canza mota,Madam ki dena hawa motan sai ya sake wata. Nabeela ta sa dariya,Jabir da Hajjo kuwa ba wanda ya dara,sai ma Jabir da ke fadin na ki na canza din,ta dena hawa,diyoyi na sa hau. Da haka da haka ayi sallama, ya sanya Hajarar sa gaban mota,su ka dau hanya. Sai shan kam shi ta ke,shi kuwa zuciyar shi tas,ga iska da ke tashi,gari yayi baki,hadari ya hadu sai kugi yake. Ana yayyafi kadan kadan,kamshin ta da ya mamaye motar gami da yanda AC ke ratsa cikin ba karamin nishadi ya kara ma da ba. Idanun sa kan titi ya ce an gama jan ajin ko da saura? Ba tare da ta kalle shi ba ta ce ban gane ba. Ya ce har yanzu ajin ba a gama jan sa ba? Ar u still nt ready to obey ur hrt? Dan na san deep inside u ki na so ki aure ni,am every woman type,so don’t give dat clumsy excuse dat am ur type! Hajjo ta kalle shi tare da fadin nt every woman,nd mind you am nt in ur dat “every woman” Khalid ya ce big lie! Yayyafi ya karu sosai,ya kara da na sani Suger,ko ya ki ka so ki boye feelns din ki na sani,i can read u lyk a novel! U hav feelns for me,you hav crush on me. Rai bace Hajjo ta ce ka manta diabates ba Suger ba,i hav no feeln or wat so ever for you,so stop mistaking! Shiru ya ma ta,har ta na tunanin ya rasa ta cewa,sai kuma ya kallo ta ta hanyar danna idanun sa cikin na ta,yanayin fitar numfashin ta tini ya dan tsagaita,ya ce wat abt d way u catch ur breath wen i look at u? Ya saki murmushi mischievously tare da mai da idanun sa bisa titi,ya ce let it go Suger,ke ma kin san u lyk me! Rai bace,bakin cikin yanda da ta yi reactn ya sa ta fadin tsayar da motar ka! Fita zan yi! Cike da mamaki ya ce ki fita ki je ina kuma cikin ruwan nan? Ta ce da zama guri daya da kai gwara dukan ruwa,ka tsaya ko na bude na fita a haka. Ganin fuskar ta ba wasa,sai ya sauka gefe ya yi parkn. Ta yunkura za ta bude motar ya danna lock,wai ina zaki? Shin in kin fita ina za ki sami abun hawa cikin ruwan nan. Ta ce ina ruwan ka? Zan fita kuma zan sami abun hawa ba tare da bata lokaci ba,idan kuma ban samu ba zan taka daganan har hotoro GRA a kafa.. ya ce no way! A fusace idanun ta har spark su ke dan bacin rai ta ce way! Bude ka gani! A kasalance ya rangwadar da kai bisa kan kujerar sa,ya ce Suger….ta ce Hajjo! Ba suger sunana ba,kowa da Hajjo ya ke kira na,so ka kira ni Hajjo ko ma child abuse da ka saba kira ko ka yi shiru! Ya murmusa ya ce child abuse is no more,wannan zaune gabana is a strong woman! Khalid ba kowa ba ne,Khalid is unique dax y zai kira ki da sunan da ba kowa ke kiran ki da shi ba Suger! Ta ja hannun kofa,tare da fadin ka bude min. Ganin ta matsa sai ya bude ma ta kofar ya ga iyakan gudun ruwan ta. Ta ko sa kai ta fito,yayya fi ya zama ruwa,wani irin iska mai sanyi ya buso jikin ta,kayan ta ya fara bin jikin ta,ta ja daga jikin motar Khalid ta sami wata yar lemar ma su sayir da recharge cards ta kebe,amma duk da haka ruwan na taba ta. Daga mota ya ke kallan ta,he love d view,ta yi ma sa kyau kwarai,ba dan ya na tsoran kar ta kamu da sanyi ba da ya kyale ta yay ta kallan ta a haka. Ya yunkura zai fito kenan sai ya ga wata mota ta tsaya a gaban ta,an sauke glass din motar,abun da ya dada kular da shi yanda ya ga ta na ma mai motar murmushi mai kayatarwa! DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 5:16 PM] Salmah Ateeku: [10:56pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣6⃣ Ganin frnd din ta da ya dade da nace ma ta na yafuce shi,farin ciki ya lullube ta,a asibiti daya su ke aiki,amma shi a admin block ya ke aiki.Cikin jin dadin ganin sa Hajjo ta ce KB na ji dadin ganin ka wlh! KB ya dara tare da fadin maza shigo toh kar ruwa ya zane min ke. Dama tayin da ta ke jira kenan,dan ta fara jikewa sosai,ta yi saurin bude motar ta shige. A fusace Khalid ya fito daga ta shi motar,ya nufi motar KB amma ina KB be ma san da shi,tini ya karya kan mota ya haye kan kwalta abun sa. Rai bace ya bi motar da kallo,ruwa ne ke dukan sa amma sam be damu ba saboda zafin da kuna da ransa ke yi ya fi dukan ruwan. Sai da ya dau kusan minti biyar a tsaye,ya jike jagab,Hajjo sai dan waiwayen sa ta ke ta motar KB har sai da ya ce ko kin yi mantuwa ne? Ah ah,ta yi saurin ba shi amsa,mu je ba komai. A fusace ya juya ya koma motar shi,da juyawa zai yi kawai ya tafi gidan sa,amma kishin ganin Hajjo ta shiga motar wani,wanda ba mamaki ma ba ta san shi ba dan ta kuntata ma sa ta bishi ya sa zuciyar shi tafasa,a dole ya bi bayan su dan ya tabbatar ya sauke ta lfy. Har su ka kai kofar gida ba su san Khalid na biye da su ba,can gefe ya faka,ya na ji ana ta horn maigadi ya ki ya zo ya bude gate,shi ma ruwa ya buye shi,dan haka sai Hajjo da KB su ka tsaya shawara,ya na ta zauna a gama ruwan,ta na bari dai na shiga yanda ruwan nan yayi yawa Allah kadai ya san lokacin tsayawan sa. Khalid da ga na shi motar ya cika ya yi fam! Wai shin mai Hajjo ta ke nufi za ta zauna a motar wani kato! Ta na zaune motar wani cikin ruwan sama,sai shakar gamshin ta ya ke! Mtsw ya ja tsaki! Hakurin sa ya kare,ya yanke hukunci zuwa ya fito da ita da kan sa kenan sai ya ga ta bude mota ta fito,ta shige gida da sauri. Ajiyar zuciya ya saki tare da bin motar da kallo da ta zo shige shi ya na fadin Allah ya taimake ka kai dai,amma ka kuskura na kara ganin ka kusa da Suger ba za ka ji da dadi. Be shiga gidan Hajiyar ba ya tada motar shi cikin bacin rai da hanzari ya bar wajan. A hanya yayiwa Sani waya,ya ce da shi gobe kafin ya taho kano yayi jiran shi,zai shigo kumurya. Cike da mamaki Sani ya ce toh Allah ya kai mu. Ya amsa da amen. Yanda Hauwa ta ganshi jike rai a bace ta san ba lfy,ta yi kokarin jin musabbabin bacin ran na sa,ya ce da ita ta dan bar shi ya na so ya ji shi kadai,ta ce toh,Allah ya kyauta. Ta ja diyar ta ta bar shi ya ci kan sa,binibini sai ka ji ya ja tsaki,mtws! Ranar dai haka ya kwan da takaicin Hajjo wanda hakan shi ne karo na biyu. Washagari da sassafe sai ga Khalid a kumurya. A tsakar gida Sani ya sa ma sa kujerar da ya ke bawa bakin sa na albarma ya zauna. Bayan ya gaisa da Indo,ya ke ce ma ta ta fa dan so ta yi kama da Hajjo,dan dai ta fi Hajjon kyau,dadi har ran Indo,kyakkyawa kamar Khalid ya ce ta na da kyau. Zaman shi da Sani ya ke fada ma sa dalilin zuwan sa,so ya ke a kai shi gurin iyayen Hajara. Sani ya ce toh fa. Ai mahaifiyar Hajara Allah ya ma ta rasuwa shekara goma sha uku kenan. Khalid ya ce Allah sarki,Allah ya ji kanta,sunan ta Neena ta ci kenan shi ne Hajara ke kiran ta Inna. Mahaifin ta fa? Sani yayi jum. Khalid ya ce ya ka yi shiru ne? Sani ya ce ai abun ne,toh mahaifin ta na nan,gidan nan gaba ne ba nisa. Khalid ya ce toh mashaAllahu za ka iya raka ni gun sa? Sani ya yi jugum,kamar mai shawara. Khalid ya ce kar ka damu,tsakanin mu ne,ko matar ka ban so ta san za mu wajan na shi,sai nan gaba,da alkhairi na zo,kamar yanda na ma ka bayani a baya auren Hajara zan yi. Sani ya ce ba komai,sai na raka ka din. Sani ya ce da Indo su na zuwa,su ka fita ba su zame koina ba sai gidan su Hajjo. Gidan ya koke ya lalace kamar ba Jama’a ciki,wai kuma a haka Mudi ya yi aure ya aje matar shi ciki haka shi ma Ayuba shi ma da matar sa cikin gidan. A waje su ka tsaya,su ka tura yaro ya mu su sallama da Baba,Yaro na shiga ya fito ya ce ai ga Alhaji Mamman din nan soro sai nishi ya ke ina ga ba shi da lfy ne. Godiya su ka ma yaro,tare su ka kutsa cikin soron,sai kuwa ga Baban nan kwance a wulakance sai nishi ya ke,be ma san wa ke tsaye kan sa ba. Subhanallahi,tare su ka yi saurin durkusawa gaban Baba,Sani ya na fadin yaushe kuma haka ya faru? Ko da wasa ba mu ji rashin lfyar ba! Shi kuwa Khalid ran sa ne ya dada baci da al’amarin Hajjo,ya Baban ta mahaifi na nan kwance cikin wannan wulakantacciyar rayuwa ba gata,amma ita ko a jikin ta, ta na likita,haba wannan wata irin duniya ce haka! Ya kalli Sani ya ce bayan Hajjo da Indo bai da wasu ‘ya’ya ne? Ya ce akwai Mudi da Ayuba,nan su ke zaune da matan sa. Khalid ya leka ya sami yaro ya ce ya yi sallama da Mudi ko Ayuba,dan tin zuwan su ba wanda ya leko,da sun zo da wani mugun abu ne da tuni sun aiwatar. Yaro ya dawo ya ce ba sa nan,sai matan su. Khalid ya ce ace su su leko. Sai ga lantana matar Mudi ta leko da daurin kirji ta na mita wai waye maigida baya nan sa ya ce sai ya gan mu…Ganin Sani tare da wani dandasheshen namiji sai ta shanye maganar ta. Yanda ya ganta dukundukun,ga daurin kirji,Khalid ya ce disgusting! Ita ko sai ta fara hannu,hannun ku,ashe Sani ne,ai daga Mudi har Ayuban ba wanda ke gida,eh sun je samo mana na afawa! Khalid ya ce sun san da rashin lfyar mahaifin su? Lantana ta kalli inda Baba ke kwance ta ce sun shi na mana,kullum cikin ba shi jike jike su ke ai,Mudi ne ma ya kawo shi nan ya kwantar,dudu ma kwanan sa nan uku kwance ba,sai dai a tayar a kwantar. Rai bace Khalid ya ce Sani taimaka min mu sa wannan bawan Allah mota mu kai asibiti,wa’yan nan ba su san darajar iyayen su ba,da ga su har matan na su. Lantana ce yo ai dai mun ma sa iya kan kokarin mu mu dai,so ka ke mu sa zani da majanyi mu goya? Banza su ka ma ta,yayin da su ka kama Baba,sai zarnin fitsarin da yayi a kwance ya ke su sa shi mota. Sai da su ka biya gidan Sani,ganin halin da Baba ke ciki Indo ta girgiza,Khalid ya ce ya aka yi ba ta zuwa ganin sa har ya kai haka bai da lfy?Indo ta ce wlh ta na zuwa duk da ko ta je din fada ya ke ma ta wai ta na damun shi da yawan zuwa,ko kwana hudu da ya wuce ta je. Tare su ka dunguma su ka taho kano,Indo ta bar babbar yarta tare da yara. Su na zuwa kano AKTH su ka wuce,nan da nan aka kwantar da Baba emergency,darajar Jabir tuni likitoci su ka rufa kan Baba su na duba shi,abu na su. Khalid da Sani,da Indo su ka ja gefe,Har Khalid ya daga waya zai kira wayar Hajjo,sai ya ja tsaki ya kashe,an sha fada ma sa diya mace ta fi jin kan iyayen ta akan maza,amma sam ya ga bambamci gun Hajjo,hw comes? Hw can she be so cold to her biological father,ita ta yaya ta ke so na ta ‘ya’yan su ji kanta har su tausaya mana. Kai daga dowowar sa zuwa yanzu Hajjo ta tsaya ma sa a rai kan abubuwan ta da dama. Sani ya sallama,kar Hajiya ta ji shiru,ya ce kar ya fada ma ta sun kawo mara lfy,idan ya dawo zai ma ta maganar,gudun kar Hajiya ta ji irin abun da ya ke ji game da Hajjon. Da wuri ta samu ta bar asibiti,hudu a gida ta mata,ta yi saurin yin wanka ta shirya cikin english wears riga body hug ruwan goro,da kuma free skirt bski,sai ta daura bakar sweater da ke garin ana sanyin damina. KB ne ya dame ta zai zo tin da ya sauke ta jiya,ita kuma ganin kirkin da ya ma ta dan a ramawa kura aniyar ta sai ta yarda yau daya dai yazo. Ta na kallan kanta a madubi,ta dau humra ta na dan shafawa jikin mayafin da za ta yafa wayar ta ya fara kara,ta duba ta ga sunan KB sai ta aje humran ta daga,ya ce gashi cikin farfajiyar gidan. Ta ce toh ga ta nan fitowa. Ta kuma kalle kanta a madubi,ta yi kyau kamar diyar turawa,ta sanya takalmi ta je ta fadawa Hajiya za ta fita. DEDICATED to The women Of Women Of Virtue💁👰🙋(group) [1 [16/10 21:49] .: 1:15pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣7⃣ KB zaune kan motar shi ya na jiran fitowar Hajjo,wata mota ta shigo gidan,ta faka gefe guda. Ganin Khalid ya fito sai da ya sha jinin jikin shi duk da dai ba su taba haduwa ba,be kuma san wanene shi ba. Shi ma Khalid tin shigowar sa gidan ya gane KB,dan haka kai tsaye wajan shi ya je,ganin ya nufo shi KB ya sauko daga kan mota tare da mi ka ma sa hannun tare da fadin salama’alaikum,fuska murtuke ya amsa wa’alaikumul salam. Wajan wa ka zo ne? KB ya dan yi jim sannan ya ce wajan Doctor Hajara. Khalid ya ce a matsayin ka na wa? KB ya ce ban dai san kai wane ne ba,so dax y zan amsa ma ka,a matsayi na na friend din ta. Khalid ji yayi kamar ya buge bakin sa,ya ce matar tawa ce friend din ka? KB ya gyara tsayuwa,tare da fadin matar ka,wlh ban san ta na da aure ba,ba ta fada min ba,Khalid ya ce ba a daura ba ne,wata biyu ya rage dax y ina ga ba ta fada ma ba,so ka nemarwa kan ka arziki ka janye kafar ka daga gidan kuma da ga wajen mata ta. Jin ba a daura auren ba sai hankalin sa ya kwanta,ya ce ba damuwa,sure bazan sake zuwa ba. Khalid ya ce madallah. Ya juya ya na tafiyar nan ta shi cike da takama ya shige gida,KB ya ce ba shakka dan ma su gida,shi gidan ma ya ke shiga kai tsaye,bara na ja rayuwata na yi gefe guda! Be san gidan su Khalid din ba ne. Ya shige motar sa ya ya fita lokaci guda kuma Hajjon ta fito,sai gani korar motar ta yi,cike da mamaki ba ta ma san Khalid na tahowa ba ta ke fadin me zai sa kuma KB ya tafi,bari na dauko waya na kira shi. Da jin kamshin turaren sa da ankarewa da shi lokaci guda ne,ta daga kai ta kalle shi. Ya bi ta da kallo tin da ga sama har kasa,har sai da ta kasa sakewa. Fuska murtuke ya ce kar ki damu da ki kara kiran shi,na sallame shi har a bada ba zai sake dawowa gidan nan ba. Maganar ta bata ma ta rai matuka,har ta bude baki za ta yi magana,sai ta kuma ta fasa ta juya da niyyar komawa ciki,ya dada tsaida ta ta hanyar fadin yaushe raban ki da Baban ki? Dum maganar ta daki kunanta,ji ta yi komai ya tsaya ma ta cak na dan sakanni,sanna ta kara daga kafa ko taku uku ba ta yi ba ta ji ya sake fadin diya mace da jin kai aka san ta,musammam na iyayen ta,amma yanda na ki lamuran su ke kin sa ina kokon tan haka,ur father Hajara is very ill,shin ki na neman albarka kuwa?juyowa ta yi a hankali,dan bacin rai idanun ta har spark su ke,ta sake bude baki da niyyar magana,sai ta kasa. Yanda ya ga ta na kallan sa kamar kura ta ga nama,ga idanun nan na spark dan masifa sai ta ma sa kyau,ya ma kusa manta da bacin ran da ke tare da shi. Juyawa ta sake yi,dan gani ta ke magana be da amfani a yanayin da ta ke jin kanta,lalle zaman ta a gidan nan ya zo karshe! Da wannan kudiri cikin ranta ta shige ciki. Wato shirun da ta yiwa Khalid ya dada kona ma sa rai,shi tin da ya zo duniyar nan be taba ganin mace da ta ke bata ma sa rai kamar Hajjo ba,nd d more ta ke bata ma sa rai,d more he want to get close to her saboda shez so differant,an adventure for him. Rai bace shi ma ya shigo gidan,ganin Hajiya ba ta dukka falon sai ya wuce dakin ta. Ita kuwa Hajjo ta na shiga dakin ta sai ta fashe da kuka,kuka mai ban tausayi,ta tsani Khalid har ranta saboda ya ta kura ma ta,ya shiga rayuwar ta,tin da dai nan din gidan su ne hade na ta ya na ta za ta yi ta koma kumurya ta na doko sammako kullum zuwa aiki. Gashi jin rashin lfyar Baba ma ya sosa ma ta rai,ko me ke damun shi? Allah sarki Innar ta,sai mutuwar ta dawo ma ta. Ta na kuka ta fara hade yan kayan ta,kan kace mai ta hade kayan da za ta bukata tsaf,kannan magariba ta gabato,ta dauro alwala ta yi sallah. Ta na kwance bisa daddumar da ta yi sallah sai ga Hajiya ta shigo,ta ce Hajjo kar dai kin yi bacci? Hajjo ta tashi ta na murmushi,ta ce idanu na biyu Hajiya. Ganin yanda idanun Hajjon ya yi jajur Hajiya ta ce kuka ki ke ko Hajjo? Dazu Khalid ke fada min mahaifin ki ba lfy,na san shi ya sa ki damuwa,kar ki damu Allah zai ba shi lfy. Hajjo ta murmusa tare da fadin amen Hajiya,dama ina so na zo wajen ki,ina so na koma kumurya na dan wani lokaci. Lfy? An mi ki wani abu ne Hajjo? Ai gwara ki zauna tinda mahaifin na ki AKTH ya ke kwance. Hajjo ta ce Hajiya dama saboda yaran yayar tawa zan koma can din,dan ina ga ita za ta na kwana da Baba,ni kuma ina kwana da yaran ta saboda aiki sai na ke biyo Baban Aysha mu taho,Hajjo ta yi karya. Ba a san ran ta ba dan sam bayanin Hajjon be yi ma’ana ba,ta ce toh shikenan,amma dai za ki dawo ko? Nan din kamar gidan ku ne,an dade an saba,na dauke ki ne kamar diyar ciki na. Cikin jin dadin maganar Hajiya Hajjo ta ce na gode Hajiya,nan din gidan ne ai,zan dawo da Baba ya sami sauki. Hajiya ta ce toh Allah ya ba shi lfy. Hajjo ta ce amen. Nan su ka ci gaba da hirar su kamar yanda su ka saba kamar diya da uwa. Washagari Khalid ya ce AKTH billing office domin biyan bills din Baba,aka ce ai tin da sassafe aka yi settln bills din. Sai ya ce owk ba mamaki Jabir ne. Ko da ya yiwa Jabir maganar bayan ya duba Baba sun fito,sai Jabir ya ce shigowar sa kenan,be ma zauna ba. Sai Khalid ya ce ba mamaki daya daga cikin yaran sa maza ne. Indo ya kara tambaya,da ga ganin yanda ta amsa ya san ta san wanda ya biya din,tunanin sa ya tabbata,dan ce masa ta yi daya daga cikin yan uwa ne aka samu aka biya da sasafe. Khalid ya ce Allah sarki,wank mai neman albarka ne,Hajara kuwa ta zo ta duba shi? Indo ta ce tukunna dai amma za ta zo. Khalid ya ce toh Allah ya sa,sai ta ce abubuwa sun ma ta yawa, Hajaran sa ce halin ta sai ita. Uhum kawai Indo ta ce,ba dai a tone tone. Komawa gidan Hajiya da yayi ya tadda Hajjo ba ta nan ba karamin kunci ya shiga ba,har sai da Hauwa ta fara kokawa da al’amaran sa,tin da su ka dawo gida ya bi ya sukurkurce,idan ya na da damuwa ne ko kuma ta ma sa laifi ya fada ma ta,gani ta ke kamar zugo shi ake ma,sam ya rage ba su kulawar sa,ba ta san shikam hankalinsa na kan Hajjo ba,be da buri da ya wuce ta zama ta shi,so ya ke Neena ta zama ta shi,haka kuma ya sami ‘ya’yan sa na cikin sa. Amma lokacin fadawa Hauwa be yi ba,saboda haka sai ya ta bata kowani excuse da ya zo bakin sa. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 5:18 PM] Salmah Ateeku: [11:29pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣8⃣ Kwanan Baba biyu a AKTH ya fara gane mutane,Diabetes da hypertention ne su ka fara damkar sa. Bayan warwarewar sa be da magana da ya wuce na Hajjo,bini bini ya ce ko yaushe zan sa diya ta Hajjo a ido? Diya ta Hajjo kaza,diya ta Hajjo kaza,musammam da ya san waye Khalid,hakan ya na sosawa Khalid rai,ya kasa gane shin wai menene tsakanan diyar nan da mahaifinta ta har ta kasa zuwa ta duba shi. Sati daya yayi a AKTH ya sami sauki sosai,ya dage lalle shi fa a sallame shi,ya gaji da asibitin. Da aka duba aka ga zai iya tafiya din sai aka sallame shi din,ya na ta ciwa Khalid albarka. Mudi da yayi jinyar sa tare da taimakon Indo su ka hada na su ya na su su ka komo gida. Satin Hajjo biyu a kumurya,Sani ta ke biyowa,wani lokacin kuma ta hau motar haya,musammam idan za ta dawo. Sam zirga zirgar ba dadi dan haka kullum cikin zargin Khalid ta ke akan takurawa rayuwar ta. Tin da ta koma Kumurya be taba waiwayan ta ba bare ya kira ta waya,duk da tana kokarin kau da tunanin daga ran ta sai da ya dan dame ta,ta na dai yawan waya da Hajiya. Zancen Inna kuwa kullum ya na ranta,ta na so ta je ta ganta,amma ta na gudun abun da zai biyo bayan haka,dan haka ta yanke hukuncin yin aure da Suraj ya dawo diyar ta ta dawo kusa da ita. Allah ya dawo da Suraj,ya na Allah Allah ya ga Hajjon sa,ta ke fada ma sa ta na kumurya,ya ce garin mosoya ba ya nisa,washagarin ranar da ya dawo ya kama weekend,ya bakunci Kumurya. Duk yanda Hajjo ta so ta sawa ranta murna da doki ganin Suraj sai da ya gagara,amma ta yi kokarin ma sa kwaliyya,ta yi kyau matuka dan tin zaman su a soran gidan Indo Suraj ke yabata,ta ma sa kyau kwarai kamar ya dauke ta ya tafi da ita inji shi. Ita ko Hajjo sai kokarin ma sa hira ta ke,da ta so ma sa maganar rayuwar ta na baya,sai wani abu cikin ranta ya hana,har ta yanke shawarar bari sai ya sake dawowa wani karan ta ma sa. Zaman ta da Suraj lami sam ba wani chemistry,har so ta ke su hada ido da shi ko za ta ji yanda ta ke ji ta hada ido da Khalid,amma ina d combition din sam be hau ba. Zai tafi ta rakoshi bakin mota,ya dauko tsaraba jaka guda ya ba ta,ta karba ta na waiwaiwai wannan duk nawa ne? Ko lefe ka fara ragewa ne? Ya na dariya ya ce ai kin fi karfin wannan ma kin sani,lefe kuma ai sai kin ture gimbiya. Duka su ka yi dariya. Tsayuwar wata tsalleliyar mota da ta yi biyun ta Suraj ce ta ja hankalin su duka,ita dai Hajjo ba ta taba sanin mai mota irin wannan ba,so sai ba ta kawo wajan ta ma aka zo ba. Tin da ya shigo lungun gidan ya hangi Hajjo da wani ran sa ya baci. Ya zo duba Baba ne,ko gidan be iya karasawa ba ya biyo ya fara ganin Suger da yayi sati biyu be sa ta a ido ba.Ya dubi Neena da ke kwance a baya ta na sharar baccin ta,ya murmusa yayin da ya juya ya gyara ma ta kwanciya,ba shakka wannan karan da ita zai yi garkuwa ya harba wannan dan gajeran saurayin na Suger. Fitowa yayi cikin isa da shan kamshi,ganin sa gaban Hajjo ya fadi,shikenan ya biyo ta,Allah kadai ya san da me ya zo kuma yau. Shi kan shi Suraj sai da Khalid ya ma sa kwarjini saboda yanayin sa da cika ta kamala da Allah ya ma sa. Shekarunsa 37 amma yafi kama da dan 30 saboda baiwa da Allah ya ma sa sam baya tsufa. Sanye cikin farar shadda dinkin tazarce,abun ku da dogo sai ta ma sa kyau. Wajan na su ya karaso ya na kokarin sanya idanun sa cikin na Hajjo ga wani mischievous smile din nan da ya saba ma ta duk san da ya shiryo wata shiryayyiyar. Da sauri Hajjo ta yi kasa da na ta ido,hannu ya ba shi,gami da yin sallama. Suraj ya karba ya amsa da fara’ar sa. Ya kalli Hajjo ya ce Suger ya dai? Is dat a way to great d man you so much miss? Da sauri ta daga ido ta kalle shi,ya kashe ma ta ido daya,duk a kan idan Suraj,ya ce ban gane ba pls,Hajjo who is dis man? Hajjo ta ma rasa me za ta ce,kawai ta yanke hukuncin fadan gaskiya,ta ce shi ne autan Hajiya….kuma uban diyar ta Ameena!Khalid Ya ba da na shi gudun mawar. Ihu ne kawai Hajjo ba ta kurma ba,dan cikin ranta ihun ta ke,maganar Anty Hussaina ke ma ta ihu a kunne na “kar ki bari ya ji a bakin wani…”wanin ma kuma ya kasance Khalid shikenan yau Khalid zai cuce ta! Hajjo ta ce wasa ya ke,as in kar ka saurare shi,ina tuni zuciyar Suraj ta motsa,ya ce da Khalid i beg ur pardon! Wata diya ka ke magana akai? Khalid ya ce aw ba ta fada ma ba? Who exactly ar you? Hajjo ta ce Suraj pls kar ka saurare shi,ka bari ma yi maganar daga baya. Suraj ya ma ta banza,ya ce da Khalid sunana Doctor Suraj,wanda zai auri Hajjo nan ba da dadewa ba. Khalid ya murmusa tare da fadin nan ba da dadewa ba amma u don’t knw abt us? Ba ta fada ma ba? Me haka ya ke nufi Suger? Idanun Hajjo na spark ta ce Khalid don’t temper wit my future,i wil nt forgive you for dat! Worry not Suger,kawai ina taimako ne wajan fadawa saurayin ki abunda be sani ba,am aure be san da diyar mu ba! Rai bace da batun Khalid,Suraj ya ce pls ka fito baro baro ka fada min abunda ka ke so ka fada. Khalid ya na murmushi,ya nuna motar sa ya ce je ka duba bayan motar can,amma ka tabbatar diya ta ba ta tashi ba. Suraj ya juyo ya kalli Hajjo,ta girgiz kai ta ce ba gaskiya ba ne,kar ka je…ya juya ya nufi motar,ko da ya leka sai ga diya kwance ta na ta baccin ta,ya bude motar ya kalli fuskar Neena sosai,tamkar Hajjo ya ke kallo,dan dai wannan fara ce kuma yarinya ce shakaf da sai ya ce yar biyun Hajjo ce! Abun da ya zo ran sa shi ne kanwar Hajjo ce,duk da dai Hajjo ta fada ma sa ita ce auta,Allah kasa kanwarta ce addu’ar da yayi a fili kenan,Hajjo is too young to b her mother. Ji ya yi kamar ya tada Neena,sai kuma ya fasa ya dawo wajan su Hajjon da tuni idanun ta ya kawo ruwa. Hajjo ta ce let me explain plsssss Suraj. Khalid na gefe murmushi fal fuskar shi,yau dai kam tarkon da ya sa ta kam katan zaki ba kurciya ba. Suraj ya ce Hajjo,tambaya daya zan mi ki,ki kuma gaggauta fada min gaskiya,aaa ko ah ah,waccen diyar da ke kama da ke sak,diyar ki ce? Ya Allah ka sa ta ce ah ah! Kallan Hajjo ya ke kamar rayuwar sa depend on her answer. Hajjo ta yi kasa da ido,ji ta ke kamar kasa ya bude ta shige ciki,abun kadan da ya kamata ta fada ma sa tuntuni ya zama babba. Suraj ya ce ke na ke sauraro Hajjo! Murya a kasa ta ce eh Ameena diya ta ce… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [11:55pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 4⃣9⃣ Juyawa ya yi ba tare da sake furta komai ba ya shige motar sa. Hajjo na fadin dan Allah ka tsaya na ma ka bayani Suraj! Tuni ya figi motar sa ya tafi. Cikin tsana Hajjo ta ke kallan Khalid,ta ce dan me ya sa haka? Me na tsare ma? Me na taba ma ka da na cancanci wannan hukunci daga gare ka Khalid? Ya ce marry me,jst marry me suger! Ni na san da ‘ya’ya na cikin ki,kuma bazan bari ba sai inda karfi na ya kare,sai kin haifa min su Suger….kallon sa ta yi irin kallan da ake yiwa wanda su ka sami tabin hankali,ta ce Allah ta baka lfy! ta juya ta shige gida a fusace,ta na ji ya na kwalla ma ta kira ta ma sa banza,ta na shiga gida ta karasa daki da gudu sai ta fashe da kuka. Indo ta shigo da sauri ta na fadin lfy! Lfy Hajjo! Me ya faru! Cikin kuka Hajjo ta ce Indo Allah ya raba ni da Gatbati tin da dadewa amma yanzu ya hada ni da Khalid! Ya matsa min,ya isheni! Na tsane shi! Na tsane shi fiye da yanda na tsani Garbati tin da ya raba ni da Suraj.Kai gaskiya wannan bawan Allah ya yi lefi,amma zauna bar kukan,zauna ki bani lbry. Ba ta dena kuka ba har ta gama ba wa Indo labari tin daga sanda Khalid ya dawo har zuwa yau da ya raba ta da Suraj,me san ta dan soyayya ba dan ya na so ya aure ta saboda wani bukatar shi na daban kamar Khalid ba. Indo ta ce toh ki yarda ki aure shi mana Hajjo,menene a ciki tin da ya na kaunar diyar ki…bazan aure shi din ba,ni bazan taba auren mutum mai ji da kai da dagawa irin Khalid ba! Gwara ma kar na yi auren kwatata!!! Ba fa so na ya ke ba,kawai dan matar shi ba ta haihuwa zai aure ni,ga machine ta haihuwa ya samu ba! Ya aure ni ya hada ni da matar nan ta sa kamar balarabiya su ji dadin wulakanta ni,duk lalacewar rayuwa ta Indo na fi karfin wulakanci. Cikin tausayawa Indo ta ce yi shiru Hajjo,ki ta addu’a da istikara Allah ya zaba mi ki ma fi alkhairi. Hajjo ta ce babu alkhairi a tare da Khalid…kul Indo ta katse ta,ki dai yi addua na ce,zabin Allah ya shi ne zabi,Allah ya zaba mi ki. Hajjo ta ci gaba da kukan ta. Tin shigar Hajjo gida Khalid ya ja motar shi, shi ma ya je yayi abunda ya kawo shi,wato gaida Baba,har yau ma sai da ya tambaye shi Hajjo,Khalid ya yi mamakin ta na garin ma amma ba ta zo ta duba shi ba? Halin Hajjo sai ita. Da kyar Neena ta yarda Baba ya ruke hannun ta da ke Khalid tada ita yayi da su ka isa gidan dan Baba ya ga jikar ta sa. Ita ko Neena ce wa ta yi sam ba kakan ta ba ne,ita kakan ta na kano,wato mahaifin Hauwa,da shi ta saba, har cikin ranta tsoro Baba ya ke ba ta.Baba ya ce Allah sarki mai sunan ki mutuniyar kirki,ba dai ta cutar ba sai da a cuce ta,Allah ya ji kanta da rahama. Khalid ya amsa da amen. Neena ce ta matsa su tafi,dan haka ba dadewa su ka juyo abun su,zuciyatt sa cike da tunanin ko wani Hali Hajjo ta ke? Bayan ta sha kuka ta koshi ne ta yi kokarin kiran wayar Suraj,amma a kashe. Ta kira ta Ayush ta ba ta lbryn abunda ke faruwa,ta ce haba shi yasa Ya Suraj ke nema na,ya zo da magariba ba na nan,kar ki damu zan ma sa bayani inshaAllahu zai gane. Hajjo ta ce toh Allah ya sa. Su ka yi sallama. Sai a sannan ta bude jakar ta,Jewellery ne ma su kyan gaske Indian design,da kuma turare iri iri,sai kuma takalma da pakistans na gani na fada. Hajjo ta yi ajiyar zuciya ta re da fadin Allah sarki Suraj,Allah ya sa ka gane,amen. Suraj kuwa tin da ya je gidan su Ayus ba ta nan ya koma gida ya kasa zama,abun da ke daure ma sa kai shi ne ta yaya wannan za ta zama diyar Hajjo? Ai wannan ta yi rabin shekarun Hajjo,ta yi yarinta a ce ta na da diya kamar wannan,dama ba budurwa ba ce? Ta taba aure? Toh ma ta ce Khalid autan Hajiya ne,shin ta yaya ya zama mahaifin diyar Hajjo?me ya sa ba ta taba sanar da shi ba?da wannan tambayoyi ya sake komawa gidan su Ayush cikin daren,dan ba zai iya kwana ba su yi maganar ba. Ya ko ci sa’a ta na nan. Ta ji dadin ganin sa duk da ba dan ita ya zo ba,dan case din sa da Hajjon sa ne. Bayan zaman su yay ta jero ma ta tambayoyi,har dai ta banbance ma sa zare da abawa,ta bashi lbryn yanda aka yi Hajjo ta ke da diya kamar Neena,kuma Khalid ya kira kansa ne mahaifin Neena ba dan komai ba sai dan shi ne ke rukon Neena,kuma ya ke san auran Hajjo. Jikin sa ya yi sanyi ya ce amfanin bayani kenan in a relationshp,sam boye boye be da dadi,da ta fada min tuntuni da duk haka be faru ba,wai dan ta taba aure ba ya na nufin zan dai na san ta ba,I love her nd i wil olways love her. Ayush ta gyada kai ta na murmushi,duk da kuwa maganar ta dan taba zuciyar ta,ina ma ta ji wannan maganar da ga bakin wanda ta ke so,kuma ace da ita ya ke,da burin rayuwar ta ya cika. Bayan yayiwa yan gida sallama Ayush ta raka sa har mota,ya ce gobe zai koma ya sami Hajjo,amma kar ta fada ma ta,zai ma ta suprise visit ne. Ta na murmushi ta ce ka gaishe ta,su ka yi sallama ya tafi ta dawo gida zuciyar ta fal da san maso wani. Washagari Hajjo na asibiti Hajiya ta yi kiran wayar ta,ta ce idan ta tashi ta biyo gidan ta za su gidan kanwar Hajiya su ga wasu kayan kitchen da kanwar ta ta ta shigo da su. Da kamar ta ce da Hajiyar ba za ta sami damar zuwa ba,sai kuma ta guji bacin ran Hajiyar,dan ita ta tsaya tsayin daka Hajjo ta fara siyan kayan aure tin da ta fara daukan albashin ta,ta kuma sa Hajjo a dashi na daidai yanda Hajjon za ta iya. Duk wata shawara ita take bawa Hajjo ita take sa ta a hanya. ta amsa ma ta da toh,zan zo Hajiya. Bayan aje wayar ta ce ya Allah kar ka sa na hadu da wannan dan anacen har na je na tafi. Kayan kitchen din ko sun mata,dan har kwasar wasu ta yi,saboda ita ta gida ce aka ma ta ragi. Bayan dawowar su ta aje su dakin da ta ke taro. Ta ce Hajiya bara na kama hanyar na tafi kar dare ya yi. Hajiya ta ce jira ma na Sani ya dawo sai ku tafi tare. Hajjo ta ce ay na zaci ya tafi,bari na jira shi. Nan su ka zauna ita da Hajiya suna tadi,Hajjo na cin abunci. Har ta gama shiru shiru Sani be dawo ba. Sai Sallaman Khalid su ka ji,Shikenan gashi abun da na ke gudu ya zo! Hajjo ta fada cikin ranta. Ba kunya kamar babu lefin da yayiwa Hajjo ya raba ta kusa da ita ya zauna kusa da Hajiyar sa,bayan sun gaisa Hajjo ta daure ta gaishe shi,ya amsa,tare da fadin yar kumurya ta dawo kenan. Hajiya ta ce ba dawowa ta yi ba,Sani ta ke jira ya dawo su tafi,kuma na ji ma wayar sa a kashe. Khalid ya ce wani Sani kuma da ya tafi tin bayan la’asar? Hajiya ta ce haba dan Allah? Ya ce wlh,sai ma da ya biyo ta gida na da ke na neme sa. Hajiya ta ce Allah sarki na tsaida Hajjo,rashin sani. Kwayar idanun sa na rawa ya ke kallan Hajjo da tuni ta ji komai ya gama jagole ma ta,ga shi akwai wani file da za ta yi submitn gobe goben nan,kuma ta baro sa a gidan Indo. fuskar sa cike da murmushin mugunta ya ce Hajiya kar ki damu,dan dai nan da Kumurya ai sai na kai Hajjon ta ki. Da sauri ta daga ido ta kalle shi,ya kashe ma ta ido,ta ce Hajiya wlh na hakura zan kwana! Hajiya ta ce wa zai kawo mi ki file din da za ki yi submitn goben? Ta ce na kira Baban Aysha ya taho min da shi. Khalida ya sa hannu a aljihu ya fito da waya ya ce ga wayar Sani tare da ni,ya ji dadin girkin Hauwa ya manta kan kujera,abun da ya kawo ni gidan nam kenan na kawo ma sa na kuma mi ki sallama Hajiya,gome zan leka Abuja. Hajjo ta girgiza kai,ita dai kwanannan ba ta da sa’a kamar ta buge bakar karya da bakar mota. Hajiya ta ce Hajjo ba komai dare bai yi ba ai,ba a dade da kiran sallah ba,idan kun idda sallar magaribar sai a kai ki. Toh Hajiya,amsar ta kenan,ta tashi ta shige ciki,ta bar Hajiya na yiwa autan ta godiya na kai Hajjo da zai yi,fadi ya ke Hajiya ai yiwa kai ne… ni ma fa haka na gani,yiwa kai indeed. Tin da su ka dau hanya ba wanda ya yiwa wani magana,sai da su kusa isa Kumurya Khalid ya ce Suger? Ta ma sa banza,ya kara da Hajara? Ta daga ido ta kalle shi,ya murmusa ya ce ashe idanun ki biyu,na zaci kin yi bacci. Ta ce dama za ka yi shiru mu karasa kawai. Ai na mi ki shiru ne kar in zo na mi ki magana na kunna ki ki ce na tsaya ki sauka a dajin,amma tin da mun kusa shiga gari,i can open up! Ta ma sa shiru. Ya ce fushi ki ke wai dan na raba ki da wannan gajeran saurayin na ki? A hasale ta ce Suraj ba gajere ba ne! Khalid ya murmusa sannan ya ce well cikin dogayen maza irina gajere ne,cikin mata irin ku Suger ina ga shi ne za a kira shi dogo,kai kamar ma tsayin ku daya ma fa,shi dogo ke kuma doguwa! Hajjo ta watsa ma sa harara. Ya kara da kina da elegant man kamar Khalid ina mamakin me za ki yi da mutum laba laba kamar mace! Hajjo ta katse shi da fadin ban san cin fuska! He is my husby to be! Khalid ya dara,ya ce ba ku dace ba,you deserve someone lyk me. Hajjo ta ce no,u ar nt my type,plus ban san ka!! Dariya yayi mai kayatarwa,ya ce Suger Suger my dear innocent Suger! Ban da ke da abun ki ai ba maganar so mu ke ba,maganar making family mu ke,you don’t luv me nd i u,equation balanced,u love ur daughter nd i her,ina so na haihu nd u need a fmly,in dat case we both need each oda Suger… Hajjo ta murtuke fuska tare da fadin no ni ban bukatar fmly,in ma ina bukata din ba dai da kai ba,sai dai da Suraj…sun shigo kumurya,sun kama hanyar unguwar su Hajjo. Shiru Khalid yayi,daga bisani ya ce d more u try to push me away,d more find you interesting,you ar such an adventure in my lyf dat i can’t resist Suger,so get use to it. Banza ta ma sa,cikin ranta kuwa tafasa ta ke,ya maishe ta kamar toy da zai na having fun da,burin shi ya takura ta a kullum yaumin ya ji dadi,gashi Allah sai hada su ya ke. Ganin mota fake kofar gidan Indo ya sa ta sake kallan wajen da sauri. Ya salam! Suraj,motar Suraj ne,ai kuwa sai ta hango shi jin gine jikin motar. Ya dade yana jiran ta,ya kira ta ba ta daga ba,gashi waje da da nisa bare ya ce zai je ya dawo. Allah Allah ya ke ya sa ta a idan sa,tin bayan rabuwar su da Ayush ya ke shiraya abunda zai fada ma ta,son ta yake ji ya na ma sa ambaliya cikin ran sa,tin da ya ji lbryn ta ya ke tausayin ta,idan be auri Hajjo ba gani ya ke ya yi asara babba. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(gro . Skip to content ummu-abdoul MENU Diya mace 3rd Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17, 2016 ​[16/10 21:48] .: /25, 5:20 PM] Salmah Ateeku: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣0⃣ Ganin abun da ya dauke ma ta hankali zuciyar Khalid ta kada,ran sa ya fara baci,wato wannan be hakura ba kenan. Ya ja mota ya faka daga gefe,sai a sannan ta ji karar wayar ta,kafin ta dauka ta katse,ta dubu ashe Suraj ne,ya jima ya na kiranta ba ta ji ba,ya ma ta miss calls ba adadi. Daga ido ta yi ta kalli inda ya ke tsaye,wayar ruke a hannun sa. Ba shakka ya gane motar,motar jiya ce,kuma ya gane wanda ke zaune cikin motar tare da Hajjo,mutumin jiya da ta kira autan Hajiya ne,wato Khalid,dama dan tana tare da shi ne ta ki daga wayar sa?kishi da bakin ciki su ka taru su ka ma sa malulu kasan makogaro. Da sauri ta yunkura za ta bude mota ta na Suraj! Khalid ya sa lock tare da fadin idan ki na san kanki da arziki kar ki fita Hajara!ta juyo a fusace ta ce Khalid kar fa ka kai ni bango! Ka kusa kai ni bango! Idanun sa sun fara kadawa suna ja,lalle fadan rashin gaskiya. Rai bace ya ce ni dama a bangon na ke,ga shawara ta kar ki fita,idan kuma ki ka fita zaki sa na yi abunda daga ni har ke za mu yi danasani,i tell you! Rai bace ta ce zan fita,ka yi duk abunda ka ga dama,idan har abunda ka yi jiya be hana Suraj kara zuwa waje na ba,to babu abunda za ka yi ya hana shi,no way! Ya saki murmushi tare da fadin way! Yayinda ya bude motar,ya ce as u wish. Ai kuwa sai ta fita. Khalid ya girgiza kai tare da fadin dax it! Da ba ki fita ba Hajjo,wit d feelings am having ryt now,I don’t knw wat am capable of. Fitar ta ta karasa wajan Suraj ta na dan Allah ka yi hakuri,ban san za ka zo ba. Rai bace ya ce wayar ki fa? Me ya sa ba ki dagawa? Ta ce wlh ya na jaka ban san….ganin Khalid gefen ta,ya sanya hannun shi cikin na ta ya sa ta daskarewa,za ta fincike da karfi sai ta yi tuntube,da sauri ya dago ta ba tare da bari Suraj ya gane tuntuben ta yi ba,ya hada ta da jikin sa,ya yi hugn din ta kam a jikin shi. Daga ita Har Suraj ba wanda be yi mutuwar tsaye ba! Kwakwalwar ta daskare,ji ta yi kamar zuciyar ta ta daina bugawa…ta yunkura da niyar kwacewa,Khalid ya ruke ta kam,ya kalli Suraj ya ce she mine,stay away! Suraj ya gyada kai tare da fadin na gane,kar ka damu,ya juya zai shige motar shi,Khalid ya saki Hajjo ta daga hannu ta sauke kan kuncin shi,ji ka ke tas ko motsawa be yi ba. idanun ta na spark sanna ta bi bayan Suraj da tuni ya shige motar sa,ta ce Suraj dan Allah,dan Allah fito ka saurare ni! Duk da idanun sa sun yi jajur,sam ba ya gane komai sai ya murmusa,ya ce bazan iya ba Hajjo,idan har zai iya mi ki haka a gaba na,Allah ya kadai ya san me zai yi a bayan ido na,ni namiji ne mai kishin kan sa da abunda ya ke so,na barki lfy,wish you d best in lyf! Ya tada motar sa,ta na Suraj! Suraj! Suraj!! Ina hankalin ya yi gaba,ba ko waiwaye ta na ji na gani ya fita daga rayuwar ta. Ta juyo ga Khalid da ke jingine jikin ta sa motar,ta ce Khalid na tsane ka fiye da tunanin ka,na gode da gudunmawar da ka bani a matsayi na na diya mace! Ta juya za ta shige cike,ya biyo bayan ya da niyar dakatar da ita,amma ina ta shige da sauri. Ya yi aiken yara har ya gaji,gashi wayar Sani na wajan sa bare ya kira shi,dan ya san tabbas Sanin ba ya nan ne,da ya na nan aiken da ya ke ta mu su da tuni ya fito. Da wannan ya juya ya koma kano,ran sa shi ma ba dadi ganin halin da Hajjo ta shiga. Wata daya ba Suraj,duk yanda za ta yi ta ji daga gare shi ya yanke. Ta yi kokan har ta gaji,ita bakin cikin ta zubar ma ta da mutunci da Khalid ya yi a gaban Suraj,ya ma zai yi ya ma ta haka,Khalid da ko hannun ta be taba kokarin rukewa ba yayi hugn din ta gaban wanda ya ke san ta,ya ke so ya aure ta tsabar shi bai da adalci! Kamar Suraj din shi ma Khalid raban ta da shi wata daya kenan,ya raba ta da me san ta ba dole ya dauke wuta ba! Abunda Hajjo ke fadi kenan duk sanda ya zo ranta,gashi kuma ya na yawan zuwa din. Ta yanke shawarar yin aure da gaggawa ta karbe diyar ta ko Allah ya raba ta da Khalid ta huta. Bangaran Khalid kuwa karfin hali kawai ya ke,so dayawa ya kan dauki mota yayo hanyar kumurya sai ya kai rabi sai kuma ya sake shawara ya dawo. Ko hanya ba ta hada sa da asibiti ba sai ya san yanda yayi ya yi zagaye ya biyo ko Allah zai sa ya sa ya hadu da Hajjo. Har cikin ransa missing din ta ya ke,missing din kallan ta,kamshin ta da uwa uba fadan su. Wani sa’in shi kadai sai a ganshi ya ma murmushi har dariya ma,toh ya tuno wata rigimar ta sa da Hajjo,hatta randa ya fara ganin ta tana fada da dan adaidaita akan naira hamsin ya tuna dariya ya ke sosai,it appears dat Hajjo ta shiga rayuwar sa. Ba kuma mai yawan tado ma sa da Hajjo kamar Neena,da ta yi wani abu ko be yi niyar tuno Hajjo ba sai ya tuno ta,kan ka ce mai sai ga Khalid ya fara fita hayyacin sa,hankalin Hauwa ya fara tashi dan ta kasa gane me ke damun mijin na ta,har ta fara zargin ko rashin haihuwan ta ne,ita ma ta fara daga hankalin ta,ta zaunar da shi tai ta ma sa kuka,ya ce kar ta damu,ba komai amma ta ki ji,sai kawai ma ta kai korafi wajan Hajiya. Hajiya ta yi kiran sa,su ka sa shi a gaba ita da Jabir a lalle sai ya fada mu su damuwan shi,Hajiya ta ce ji fa har ya fada,ko wani abu Hauwan ta yi ma ne? Khalid ya girgiza kai ya ce lfy lau fa,ita dai ta damu kan ta,na fada ma ta ba damuwan ta ba ne! Jabir ya ce ya za ka ce damuwan ka ba zai zama na ta ba? Shez ur wife bro. Hajiya ta ce Khalid,na san da akwai da abun da ke da mun ka,hakan nan ba za ka fada ka ramr haka ba,let d cat out of d bag!ya kalli Jabir,ya ce Hajiya ya dan ba mu wuri…Jabir ya ce ku ji mara kunya,ba in da zani,Hajiya ta ce ka dan ba mu wurin ma na Jabir,Jabir ya ki motsawa,ya ce ai damuwar Khalid shi ma damuwar sa ce. Da dai su ka ga da gaske be motsawan,Hajiya ta ce Khalid ya yi hakuri ya kyale sa,ya fadi damuwar sa. Khalid ya dan sunkuyar da kai saboda nauyin abunda zai fita da ga bakin sa,ya ce Hajiya wlh kan maganar Hajara ne……wato wani irin dariya Jabir ya sheke da,har da mingirowa daga kan kujera!,ita kan ta Hajiyar daurewa ta yi ba ta yi na ta dariyar ba,ta fara yiwa Jabir fada ka ga yayan banza,menene abun dariya?.dole ya ce ka bashi wuri. Khalid ya murtuke fuska,dan ya san za a yi haka. Jabir na kwalla tsabar dariya ya ce Khalid yau kuma ina tunkaho da ji da kan na ka? Ina kuma takamar? Nan fa ce min kayi da ka fada ma ta murna za ta hau,ai ni da na ji shiru na zaci an gama magana,ashe kanina na nan ya na garuwa! Khalid ya ta shi a fusace zai fita,Hajiya ta dakatar da shi,ta ce dawo ka zauna,shi ya kamata ya fita,idan ba za ka bashi shawara ba ka tashi a sauka lfy. Da kyar ya iya daina dariyar. Hajiya ta ce ba na so na sa baki zancen nan na ku da Hajjo,shi ya sa ka ji na mu ku shiru,amma yanda za a yi yau ka sake komawa,ka gwada shawo kan ta,idan ba ta yarda ba,sai mu sa baki,ko Jabir? Ya na murmushin mugunta ya ce haka Hajiya,ka je ka lallabo child abuse din ka,ka kwantar da kai,ba wai ka je da gadara da jiji da kai yanda ka saba ba,kila ka shawo kan ta. Duk da dai ta shakiyanci ya ke maganar,shawarar ta yiwa Khalid,ya tashi da sauri ya na fadin yanzu hudu na san ta na kan hanyar komawa,bara na yi sauri na shirya na tafi,ya fita da sauri,ya na jiyo dariyar Jabir,shi abun ya ma sa dadi. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣1⃣ Har in da za ta sami mota Ayush ta sauke ta,ta na dada ba ta baki akan halin da ta ke ciki. Hajjo ta ce ba komai,ta so dai in ma rabuwa za ta yi da Suraj suyi na girma da arziki,ba irin wanda su ka yi yanzu ba. Ayush ta ce kar ta damu,a hankali zai gane. Su ka yi sallama,ta hau motar da zai kai ta kumurya. Da ke a tasha ta sauka sai da ta kara hawa wata motar,ta sauke ta a titi,ta tako dumin karasawa gidan Indo. Ta wuto ta wata majilasar yan zaman banza,suna ganin ta su ka fara maganar ta kamar yanda su ka saba duk sanda ta gifta ta wajan,wani ya ce ummmm ga fa iyayen boko,wa zai ce wannan diyar garin nan ce! Gaba daya sai saura su ka sa baki a ka sa Hajjo a faifai,cikin su har da Nuhu abokin Garbati,sam ba ta lura da shi ba. Takalmi ya sa bi bayan ta,ya ga gidan da ta shiga ya tabbatar Hajjon ce da gaske sannan ya juya da sauri sai gidan su Garbati. A kofar gida ya tadda shi,ya yi dakal dakal da shi,ga kazanta ga talauci,ga rashin haihuwa,ya yi aure auren har ya gaji amma shiru be sake samun haihuwa ba,sai ma mata da ya ke aure mai nakada ma sa na jaki duk sanda be kawo na cefane ba,Iyalle da Baba kadai ke iya cetan sa. Yanzun ma tunanin inda zai samu na dare ya ke Nuhu ya zo ya tadda shi. Bayan Hajjo ta yi wanka ta na cin abunci sai ga yaro ya zo ya ce wai ana sallama da Hajjo,ni kuma? Kai ka ce ba ta nan. Indo ta ce ba a haka Hajjo,ko lekawa ne ki yi mana ki ga wake sallamar,je ka ce ta na zuwa. Rai bace ta cire hannu daga abunci,tuwo ne miyar yauki,ta wanke hannu,ta yafa mayafi ta fito. Lekowar ta ta yi arba da Garbati da Nuhu. Cikin mamaki dan ta gane su sarai ta ke kallan su,shi kuwa Garbati sam be gane ta ba,zubewa kasa yayi ya na Hajiya ina wuni? Nuhu ya dan bige shi tare da fadin kai dallah tashi Hajjon ce fa,dallah Hajjo ce,gane ta ne ba ka yi ba! Garbati ya tashi da sauri ya na aw aw ashe!ya kalli Hajjo da kyau ya ce yasin ita ce,Hajjo ai kin zama kamar diyar yan birni shiya sa ban gane ki ba! Murmushin ta kaici ta saki,ta ce lfy? Garbati me ya kawo ka guna? Garbati ya ce eh na’am? Nuhu ya zingure shi. Sannan ya ce dama dai kin san saki daya na mi ki,na zo ne mu sasanta mu gyara auren mu ko kuwa ki bani diya ta……dariya Hajjo ta sa,har ta kusa kwarewa,Garbati ya ce yo menene abun dariyar? Kar fa ki bata min rai na! Ta na dariya ta ce ko ba ran ka ba? In yayi dubu toh zai dauwama a bace Garbati! Tin dosowar Khalid layin ya hangi Hajjo tsaye tare da wasu,har zai fara kunar rai sai ya ga wasu almajirai ne ma,ba shakka sadaka su ka zo nema,sai ya saki ran sa ya faka motar ya fito. Tin da Hajjo ta ke ba ta taba farin ciki da ganin Khalid ba sai yau,ya fito tas da shi cikin farar shadda ta sha bugu da guga,dinki boda an masa aikin sama da shudin zare,ga wani shudin hula da ta sha kari ya sanya ta a karkace,ga takalmin sa shudi,hunnun ruke da mukullin mota ya karaso wajan su Hajjo,tuni kamshin sa ya maye su,su kan su su Garbati sun kiyaya. Ta kasa dauke ido da ga kallan shi,ya ce Suger yanda ki ke kallo na…. kar ki damu i miss you more!ya kashe ma ta ido. Ta dauke kai ta na fadin in ba ka yi fariya ba ba sunan ka Khalid ba. Murmushi yayi tare da fadin na zo mi ki da magana mai muhimmanci yi sauri ki sallame su,taimako su ka zo nema gurin ki ko? Ya sa hannu a aljihu ya fito da dubunne farare kal ya ce nawa ku ke bukata bayin Allah? Ganin kudi makudai hannun Khalid tuni hankalin su ya tashi,Garbati ya ce eh na’am diya ta na zo karba,diyar ka? Khalid ya maimaita,ya kalli Hajjo ya ce Suger kin kuma fara ruke diyar mutane? Turo ma sa diyar ta sa ma na ya kama gaban sa,if u realy need a daughter dat much da kin fada min na kawo mi ki Neena. Hajjo ta murmusa tare da fadin ai Neena ya ke nufi! Khalid ya kalli Garbati ya ce kina nufin wannan local champion din is ur…..ex- husband ta karasa ma sa. Sai da yayi dariya mai isar sa,sannan ya ce amma Allah ya isan ki Suger. Ya mayarda kudin sa cikin aljihu,Nuhu ya hadiyi yawan bakin ciki ganin komwar kudin,Khalid ya ce kun ga wannan? Mata ta ce! Karo na farko da ya kira ta mata ta ba tare da ta musa ba. Ya kuma ce diyar da ka ke magana akai,tin shekara gomashabiyu da su ka shude ta zama diya ta. Ran da na sake ganin ku anan sai na sa an kama mun ku,an kulle am batar mun da ku! Abun ku da yan kauye tuni su ka tsorata,dama ga damin kudi sun gama gani hannun Khalid ba mamaki ma su ne masu kasar. Garbati ya ce ba ma sai an kai ga haka ba,bara mu tafi,ya ja Nuhu,su na dan yin gaba Nuhu ya fara sirfa ma sa masifa,wai ai gashi ya mu su asara,mai makon ya hakura su zauna a almajiran da Khalid ya yi zato,ko ya ce a ba shi wani abu ko a bashi diyar sa,yanda su ka yi za su fada. Shi ko Garbati ganin yanda Hajjo ta koma,ga kuma wanda ke kiran kansa mijin ta ne ya kashe ma sa jiki,wai yar Hajjon sa da ya sani a matsayin matar sa,Allah kenan! Allah kenan! Allah kenan! Abunda ya ke ta maimaitawa kenan. Bayan tafiyar su Hajjo ta ce me ya kawo ka mallam? Khalid ya murmusa ya ce is dat a way of sayin thank you? Ta ce thank you for wat? For saving u from dat local champoin u ar callin an ex-husby!Hajjo ta ce ko ba ka zo ba dama zai tafi,ya ce u ar glad am came Suger,admit it. Ta yi shiru. Da ya ga ba ta niyar magana ya ce magana za mu yi,za mu iya zama a soro? Kafin ta ba shi amsa ma har ya shiga,ta ce dan ma su gida! Ya ce na’am biyo shi ta yi ta ce no ba magana na yi ba. Murmushi kawai ya ma ta dan ya ji abunda ta ce saraj. Ta shige ciki dauko abun zama,ta ke fada ma Indo Khalid ne fa ya zo. Indo ta ce shi ne za ki zaunar da shi a soro? Cikin awaki,ki shigo da shi tsakar gida mana. Ta ce toh,ko dan darajar korar ma ta da Garbati da ya yi. Sai ta dauko tabarma duk da ta san ba ya zama kan tabar ma ta shimfila,sannan ta ce ya shigo ciki. Ya shigo sai ya ga tabarma,ta na jira ya ce ba zai zauna ba sai kuma ya ba ta mamaki ya zauna. Indo ta fito suna gaisawa sai ga Hajjo nan ta kawo ma sa ruwa a kofin roba,bayan ta san baya sha ko cin abunci a roba. Indo ta ce ya za ki kawo ma sa kofin roba ga na karfe Hajjo,ta na murmushin mugunta ta ke kallan sa,ta ce ya fi san na roba,ko Khalid? Shi ma murmushin yayi,ya san abunda ta ke yi,dan haka sai ma ya daga sha ya koshi ya aje sannan ya ce kwarai kuwa. Cike da mamaki Hajjon ta ke kallan sa. Sai ta kara da bara na kamasa abunci,na san shi da san miyar yauki. Ihu ne kawai Khalid be kurma ba,ba shakka Hajjo niyar ta ta kashe shi,duk abun da ta san ba yayi shi ta ke ma sa,wa ya sani ma ko guba za ta sa ma sa a abacin ya mutu ta huta,duk duniya idan akwai abuncin da ya tsana ya bi bayan miyar yauki. Ciki Indo ta koma ta na fadin saka ma sa mana,ki hado da yajin daddawa ma. Toh ta amsa cike da farin ciki. Ta kawo ma sa tuwon. Ga mamakin ta sai ya wanke hannu,ya dan ci kadan,dandai ya kunya ta ta,amma da kyar ya ke hadiya,har ya dan bata ma sa gaban riga. Bayan ya wanke hannu ya zauna ya ji zuciyar sa na tashi,ya ce dan Allah suger taimaka min da leman tsami,da har za ta hana shi,sai ta tausaya ma sa,ta dauko ta yanka ma sa,sai da ya dan sha kadan sannan ya samu nutsuwa,ya dago ya kalle ta,ya ce come here Suger,ya nuna kusa da shi. Ta harare shi ta ce Hajara ce ba diyar ka ba da za ka min irin kiran yara. Tashi yayi ya na murmushi,ya zo gaban ta,ya durkusa gwiwowi biyu a kasa,ya ce Hajara yau ga Maighty Khalid gaban ki,ya zo da kokan baran sa……baki bude ta tsaya ta na kallan sa. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 5:22 PM] Salmah Ateeku: [11:38pm, 6/10/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣2⃣ Hajara ki yi duba da soyayyar da mu kewa diya daya,diyar ki,kuma diya ta,ki amince na zama miji a gare ki dan cigaba da gina zuri’ar da za su kasance tsatso daya,idan ki ka ki aure na,za ki raba ni da diyar ki,ta riga ta shiga rayuwa ta,haihuwan ta ne kawai ban yi ba. Kuma za ki iya auren wanda kuma zai hana ki rukon ta,tin da uba aka sani da alhakin riko ‘yaya ba uwa ba,kin ga kenan mun yi biyu babu. Hajjo ta ce dan Allah ka tashi,kar wani ya gan ka haka na banu. Ya ce answer me first sai na tashi. Ta ce ba zan iya auren ka ba Khalid…saboda me ya sa? Saboda am nt ur type? I wil try to adjust to ur type,kawai ki fada min ya type din na ki ya ke. I promise to b good,zan yi respectn din ki untill my last breath,zan kuma so ‘ya’yan mu na ba su kulawa kamar uba na kwarai. Hajjo ta ce ba soyayya,ka san ba na san ka,ta ya za mu zauna? Khalid ya murmusa,ba soyayya,amma akwai respect,ba kya so na,i can do wit dat,ni ma wai san na ki na ke ba,amma ina san diyar ki Ameena zan kuma so yaran da za mu samu a gaba inshaAllah..duk da dai ita ta fara furta zancen rashin soyayyar sai da amsar ta shi ta ma ta daci,ita ta fada ne dan ta na san ji ya yake ji game da ita,ashe it is ol abt haihuwa da kuma diyar ta da ya ke so. Gashi ita har ran ta ta na jin sa,wanda kuma ke san na ta ya raba ta da shi. Yawun takaici ta hadiya dan jika makogaranta da ya bushe,ta ce ba ni kadai ba ce mace mai haihuwa a duniya,ka ne mi wata mana! Ya murmusa,ai nan gizon ke saka,ke zuciya ta ta zaba,ke ce zabin rai na,ba dan haka ba da ina tuni ma na yi watsi da zancen,i don’t go after gurls,gurls come after me,nd olryt u ar an exceptional. Babu yanda zan yi. Hajjo ta ce ka raba ni da mai sona,Khalid ya amsa da ba zai so diyar ki ba Hajara,dan haka be dace da ke ba! Ajiyar zuciya ta yi,sannan ta ce zan yi tunani a kai. Tunani akai? Kamar ni Khalid na zube gwiwowi na kasa na rokeki amma ki ce sai kin yi tunani?gaba daya kin taba tsarin rayuwa ta,har kin min gibi. Hajjo ta daga kafada ta sauke tare da fadin dax in za ka iya jira,idan kuma sauri ka ke sai ka sake saban lale. Tashi yayi ya na murmushi,ya ce ba sauri,amma ki sani da ga yau bazan sake bibiyan ki ba,da fatan za ki yi tunani da kyau,dan Allah ki yiwa sirika ta sallama,sai na zo maganar auren mu,ya zira takalmi,ya na murmushi ya fice,Hajjo ta bi bayan shi da kallo,kamar ta ce ya dawo ta yarda,dan ba wai yardan ne ba ta yi ba,ta na jin tsananin tsoran kishi da Hauwa,dan ta fita komai,bare uwa uba mai san auren na ta ba ma san ta ya ke ba.nan ta yi zaman ta sai da Indo ta fito ta same ta,ta yi nisa cikin tunani. Da ta matsa sai Hajjo ta fada ma ta damuwar ta ne sai ta fada ma ta yanda su ka yi da Khalid. Indo ta ce to menene na ki na kin yarda? Menene laifin Khalid,Hajjo kar fa ki yiwa kan ki asara! Mutum mai asali ga ilimi da komai na rayuwu? Ya na san ya aure ki,ya na kuma san diyar ki,ba kowani namiji za ki aura ba ya yarda ki zauna ma sa da agola ba,shi gashi saboda ita din ma ya dage ki aure shi,wani zancen ba ya san ki ki aje,ki ka iya zama da Garbati ma bare mutum kamar Khalid? Hajjo ta nisa tare da fadin ni fa kishi da matar shi ne bazan iya ba,ta fini komai,ni da ita ba gami. Indo ta ce Hajjo,ya fa san da matar ta shi ya dage sai ya aure ki,saboda kina da abunda ya ke bukata matar shi ba ta da shi,yar ki da kuma ‘ya’ya tsatson ki ya so,kin ga kuwa ba ta fi ki komai ba din kenan. Hajjo ta ce wulakanci ne ban so Indo. Indo ta ce ai kin fi karfin wulakanci Hajjo,bare ma Khalid ba zai wulakanta ki ba,a de bar shi da jin kai,amma ba wulakanci….Hajjo ta dara,ta ce aw ashe ke ma kin san halin nan na shi. Indon ma dariyar ta yi,ta ce waye be sani ba. Allah dai ya tabbatar da alkhairi,ki dai kara nazari Hajjo,ki kuma cire san zuciya ki zabi hanyar da zai fisshe ki. Hajjo ta ce amen amen,inshaAllahu,Allah ya sa mu dace. Ta amsa da amen. Da tunanin Hajjo khalid ya isa kano,shi kan shi ya kasa gane dalilin da ya sa ta mamaye zuciyar sa,gaba daya ta mamaye zuciyar sa,ji ya ke kamar ya kusa fara numfasa sunan ta tsabar yawan yanda ya ke tunanin ta a rana. Duk da haka ya ki yarda wai san Hajjon ya ke,shi a na shi daga Hauwa ba zai iya kara san kowace diya mace ba. Shigar shi gida be ga Hauwa da Neena a falo ba,kai tsaye bankaran Hauwa ya nufa,ya jiyo su a daki. Da shigar sa dakin kamshi da ya sani,ya ke balain so ya shaka,ya bi ta hanci ya shige har cikin zuciyar sa,be san sanda ya yi subul da baka ba ya ce ya na ke jin kamshi Suger? Hauwa da ke zaune kan gado ta na yiwa Neena kalaba,da tuni ta ankare da shigowar sa,ta amsa ma sa zuciya daya ta ce ba Suger ba ne,Humrah ne fa ya dade ajiye a kan dressing mirrow na Neena ta zubar garin tabe taben ta. A sannan ya gane kwaban da ya kusa tafkawa,yayi saurin bin ta ta hanyar yin kwana shi ma ya ce aw Humrah sunan turare? Kai amma yayi dadi,ki na da shi amma ba ki amfani da shi? Hauwa ta ce wlh be dame ni ba ne. Khalid ya karaso kusa da su,ya zauna tare da fadin ni ya dame ni,ki na amfani da shi daga yau. Hauwa ta dara,toh zan sa a kawo min wani,ina kasan kamshin humrah? Tambayar ta sa gaban sa ya fadi,ya na tuninin amsar da zai ba ta da gaggawa Neena ta ceto shi, Daga yanda ta ke a durkushe,ta ce sannu da zuwa Dady. Da sauri tare da maraba da gaisuwar ta ta ya amsa da yauwa sannu my beloved one. Ya kiriniya? Hauwa ta ce kasan ba kiriniya sai shagwaba. Ya na murmushi ya tashi gudun kar a koma maganar humrah,ya ce ki yi san ranki indai shagwaba ba ce,diyar Khalid ki ke. Neena ta ce yauwa Dady. Hauwa na dariya ta ce dama kai ka ke kara shagwaba ta. Ya ce ita diya tilo ya bazan shagwaba ta ba? Hauwa ta ce gaskiya fa. Ya ce in kun gama kwasame ni a bangare na. Hauwa ta amsa da toh. Ya fice ya na dirga sa’ar shi na yau,amma lokaci yayi da zai sanar da Hauwa kudirin sa akan Hajjo. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [11:50pm, 6/10/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣3⃣ Kusan sati daya kenan raban Hajjo da Khalid,kamar yanda ya ce ma ta din ya daina bibiyan ta,amsar ta ya ke jira. Da ya sanar da Hajiya da Jabir yanda ya yi da Hajjon amma be fada mu su har tsugunna ma ta ya yi ba gudun sharrin Jabir. Jabir ya ce ahaf,dama na fada mi ki Hajiya,jin kai irin na Khalid ba zai bari ya iya shawo kan ta ba,gashi kullum rama ya ke kamar kudin guzuri. Hajiya ta ce Jabir ai sai ka sa baki. Jabir ya ce toh Hajiya,gobe zan je na same ta inshaAllahu. Hajiya ta ce toh Allah ya kai mu. Ba karamin dadi ya ji ba jin Jabir zai sa baki,ya san Hajjo ta kusa shiga hannu kenan. Tattaunawar Hajjo da Jabir a asibiti Hajjo ta nuna amincewar ta kan auren Khalid. Jabir ya ji dadi matuka da yanda Hajjo ta ke ma sa,komai ya ke so ta yi,wuyan ta ya yi magana kamar yanka wuka haka ta ke aiwatar da shi. Ya ma ta alqawarin tsaya ma ta a komai kan auren,sannan kuma ta ba su sati biyu za su zo su nemi iyayen ta dan yanke maganar auren. Da kamar za ta fada ma sa tsakanin ta da Baba,sai ta ga ai kamar tonawa kan ta asiri ta ke,gwara su je da kan su,su ganewa idan su. Da wannan maganar su ka yi sallama. Cikin dalleliyar motar shi da ya sake ya nufi gidan Khalid. Bayan ya gama ma sa tsiya da Allah ya san ya alkhairi,Jabir ya ce albishirin ka? Khalid ya ce goro,bayan motar ka siyi private jet ko? Jabir ya make shi tare da fadin shegen maza,sai na siya ai,ka san da kudin. Khalid ya ce ni ko na san da su,ci ne dai kawai ba a yi. Jabir ya murmusa tare da fadin da kasan albishirin da zan ma ka da ba ka tsaya jan wannan shirmen da ka ke fada min ba…Khalid ya gyara tsayuwa,ya ce toh fadi na ji. Jabir ya ce na ga Hajjo yau. Cikin kaguwa ya ce dan Allah,ya ku ka yi? Jabir ya ce sai ka biya. Khalid ya ce kaiya! Dan Allah ka fada min mana,ban san wasa da irin wannan maganar,haba yaya na na kai na! Jabir na dariya ya ce na ji wannan social bribe din,toh ka shirya nan da sati biyu za mu kai gaisuwa da kuma sa ranar auren ka da Hajjo….baki Khalid ya bude kamar zai yi magana,sai kuma ya rufe,ya kara budewa ya na rufewa kusan sau uku,Jabir ya ce fadi ma na,Khalid ya ce Alhamdulillahi rabbi alamin!Jabir ya ce ko kai fa! Murna ce ta lullube Khalid,fiye da tunanin kuwa,gani ya ke ya haihu ma ya gama dan daga ganin Hajjo za ta yi kwayaye,baze bari ta yi fmly planing ba,yara za ta jero ma sa kamar bene. Ya ce Jabir wlh da na isa na ma ka kyauta da na ma ka,maganar da ka fada min ta yaye min rabin matsala ta. Jabir ya ce ka min mana,girman ka ne. Khalid ya ce ni din banza,me na isa na baka. Jabir na murmushi ya shige motar shi ya na fadin sauran mtsalar ta ka,ka yi saurin kau da shi,ka kuma tuna ma ta Allah ne ya bamu damar mu yi,kar ta yi jayayya da fadar Allah. Darawa Khalid ya yi,ba shakka Jabir ya san sa kwarai ya na iya karantar sa,ya ce madallah da wannan yaya nawa,na gode,Allah ya bar zumunci. Ya tada motar shi ya ce ameen dan rasulillahi,kar fa ka fara ma ta jiji da kan sosai,ka bari a daura kar ta ce ta fasa! Ya na dariya ya figi motar sa,Khalid na daga ma sa hannu,sannan ya juyu gida,ya fara tsara wasikar da zai karantowa uwar gida Hauwa. Kwance jikin shi,bayan ya gama nuna ma ta duk duniya ba diya mace kamar ita. Ya kira sunan ta,Hauwa?Jin ya kira ta ba tare da ya ce baby-luv din da ya saba fada ba musammam lokaci irin yanzu ta san da wani abu. Ta amsa da na’am. Ya ce kin san shekaran mu nawa da aure? Ta ce sha daya. Ya murmusa tare da fadin,ol those years da san ki ke kadai na ke kwana na ke tashi,haka ma har tsawan shekarun da Allah ya kindaya ma na,you ar d love of my lyf. Maganar ta sa tai ma ta dadi,ta dada kwanciya jikin sa,tare da fadin tell me more,ba ta san more din ba mai dadi ba ne. Sai da yayi shiru,sannan ya ce kin san dai Allah ba ya cutar da bayin sa,sai dai bawa ya cutar da kan sa,Hauwa ta ce haka ne. Ya ce kin san kuma kowa akwai kaddarar rayuwar sa..gaban ta ya fara faduwa,ta ce haka. Ya kara da kin san Allah na jin kunyar macen da be bawa haihuwa ba? Hauwa ta gyada kai,ta ce eh,ki tabbatar Allah na tare da ku,ya kuma san da ku,ku din ma mata masu daraja ne. Ya sake yin shiru,Hauwa ta ce ina jin ka. Ya ce Hauwa ki saurare ni da kyau dan Allah,wlh ban taba san kowace diya mace ba sai ke…zuciyar Hauwa ya fara kaduwa,ta ce dan Allah fada min,menene wai. Khalid ya nisa,ya ce aure n ke son na kara…….a razane ta dago daga jikin sa ta na kallan sa kamar wanda ya yi sabo,ta ce aure? Wasa ka ke ki Khalid! Aure fa? Kai ba da gaske ba ne! Yi shiru kawai mu kwanta mu yi bacci. Shi ma tashi yayi zaune gami da ruko hannun ta,ya ce ba wasa na ke ba,ba kuma ba dan ba na san ki ba ne….idanu cike da kwalla ta ce Khalid,me ka ke fada haka,ba ka san abunda ka ke fada ba! Ta ficge hannun ta,ya ce Hauwa ki saurare ni! Ta ce me za ka ce min? Ina jin ka! Ya ce Hauwa ki tausaya min,tsufa na ke,wlh duk yanda na so na hakura na kasa,ina san yara……sai ta fashe da kuka,ta na fadin dama na sani,dama na sani. Ka kasa hakuri? Dole ka kasa mana tunda ba kai ba ne da ralural ba! Bambamcin diya mace da namiji kenan,da kai ne da matsalar ka san haka zan hakura na zauna da kai ba ma me ji,amma yau dan ni ce gashi za ka tuzar ta ni….ya yi saurin rufe ma ta baki,ya ce haba Hauwa,kar ki manta bambamcin diya mace da namijin har da umarnin ubangiji da ya ce mu auri hudu,ko uku ko biyu har zuwa daya,manzo sallallahu alaihiwasallam be zauna da daya ba Hauwa,ya ce mu auri fiye da daya har zuwa hudu in har za mu iya adalci. Hauwa manzo sallallahu’alaihiwasallam ya ce mu hayayyafa dan mu zamo abun alfahari a gare shi ranar gobe kiyama,shin da wannan damar Hauwa na cigaba da ruyuwa yanda mu ke ki na gani na yiwa kai na adalci kenan? ‘Ya ‘ya na ai na ki ne Hauwa…ta na hawaye ta ce ni da ban haifa ba,ta yaya za su zamo nawa? Sanin kan ka ne Neenan da na ke gani kamar tawa ma an kusa raba ni da ita. Ya ruko hannun ta tare da fadin babu mai raba ki da ita,saboda na tabbatar da hakan ya sa na zabi na auri mahaifiyar ta…..dif Hauwa ta ji ta dai na ji,ta daga ido ta kalli fuskar Khalid da ke ma ta haske duk sanda ta daura idanun ta akai,yau sai gashi ya ma ta duhu dulum. Hauwa ba ta ji ba ta gani ta cire hannun ta daga na Khalid. Ta tashi za ta fita,shi ma din tashi yayi da sauri ya na Hauwa,Hauwa! Ina ba ta tsaya ba,ya bi bayan ta da sauri,ganin haka sai ma ta sa gudu,ya na biye da ita,ta yi saurin shiga bankaranta ta kulle. Sai ta zube kasa ta na kuka mai ban tausayi. Khalid yayi yayi ta bude ta ki,dan haka shi ma sai ya sami waje ya zauna daga jikin kofar,ya na jiyo kukan ta,ya rasa me ke ma sa dadi nan duniya. DEDICATED to The Women Of Virtue🙋👰💁(group) [16/10 21:54] .: :02am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣4⃣ Hajjo ma a na ta bangaran bacci nan ba ta yi ba. Tin da ta amince da auran Khalid ta kasa nutsuwa. Sai da ta dage da karatun alqur’ani,da kuma nafilfilu Allah ya sa hakan alkhairi ne. sannan ta samu idanun ta su ka rufe. Washagari da sassafe Hauwa ta tafi gidan su. Da ke iyayen ta na arziki ne sai su ka ma ta tatas,su ka zarge ta da san kanta,mutum ya iya zama da ita tsahon shekarunnan ba haihuwa,dan ya ce zai kara sai ta tada hankalin ta,ita ba mai ba shi shawarar ya kara ba ne! Yayyar Hauwa mai suna Zeena wacce bayan iyayen Hauwa sun gama ma ta fada ta zo,tare da kanan ta ne su ka ta zuga Hauwa,wai wlh ta bari ya auri yar aikin gidan su ta fado,duk matan da ke garin nan in ma kishi za su yi auro ma ta class din ta mana! Hauwa ta ce da ta ke mai aiki,yanzu fa doctor ce. Zeena ta ce sai me? Kowa dai ya san asalin ta,turan gini ran zane! Ke ce ma kin dau diya kin manne kamar ta ki! Yanzu kya gane kuran ki! Daya daga cikin kannan ta su ka ta ce Hajjon mummana ma da ita! Dayar ta ce ai kamar ta daya da Neena! Wlh kar ki kara kawo ma na yarinyar gidan nan. Ita kuwa Hauwa har lokacin jin Neena ta ke har ranta,dan haka ta ce ah ah fa,ba ruwan yarinya,ku dai taya ni bakin ciki amma kar ku kyarar min Neena! Hada baki su ka yi su ka ja tsaki. Mahaifiyar Hauwa ta shigo,da ke ta dan cinci maganar,ta ce maza ki biye mu su ki yi biyu babu,su zuga ki Neenan ma ki rasa,kin dai ji shawarar da mu ka baki! Hauwa ta ce uhum. Khalid da ya tashi ya ga Hauwa ba ta nan ya san za a yi haka. Sai cewa yayi da Neena maman na ta ta je gida ta yiwa dady sallama dan ba ya so ta gane ta yi abunda ba ta taba yi ba,wato yaji,shi zai kai ta makaranta,da ke Hauwa ke kai ta kulli yaumin,ko ya ce zai kai ta hanawa ta ke. Duk da hakan ya yiwa Neena wani iri,sai ta amsa da toh. Da ya sauke ta makarantar ya biya ta gidan su Hauwa. Iyayen ta su ka ce ta fito ta bi mijin ta,har da bashi hakuri,tare da mu su dan nasiha. A hanyar komawan su gida ba wanda ya ce da dan uwan sa kala. Sai da su ka shiga gida,Hauwa ta ce da Khalid me ya sa Hajjo? Me ya sa za ka zabi Hajjo maimakon wacce ta isa,na san yes isasshiya ce zan iya kira da sunan kishiya?yayi mamakin maganar na ta,dan shi zaman sa da Hauwa ya san mace ce wacce ba ruwanta da arziki ko rashin arzikin mutum,mace ce mai saukin kai,amma kishi na neman sauya ma ta hanya. Murmushi kawai yayi ya ce ki yi hakuri Hauwa. Zai wuce ta shagaban sa,ta ce me ya sa ita? San ta ka ke? Ya girgiza kai,alamar ah ah,ya ce ke kadai na ke so. Ta ce toh ka sake wata! Ya ce ba zan iya ba! Ta ce y her? Ya ce ita zuciya ta ta zaba,ki yi hakuri Hauwa. Yayi saurin shige ta ya shiga bangaran sa gudun ganin saukar hawayen ta. Nan ta zube ta na kuka,ta na fadin wlh san ta ya ke! Mayaudari! Makaryaci! Santa ya ke wlh!!!nan ta karaci kukan ta ta koshi. Jin Khalid shiru ta san ya bi ta kofar baya ya fice,ita ma ta lallaba ta shige dakin ta ta kwanta,tuni ta fita da ga hayyacin ta. Da azahar ta na tunanin Neena a makaranta dan ba ta ji za ta iya fita,sai ga ta ta shigo dakin sanye da kayan makarantar ta,da alama dawowar ta kenan. Ta ce Momma sannu da gida,ya ba ki zo dauka na ba sai dady? Ba ki da lfy? Ta zauna gaban ta kamar za ta shige cikin ta. Hauwa ta kau da kai ta na ban da lfy,Neena ta yi saurin ruko hannun ta,Dady ya kai ki asibiti? Cikin ranta cewa ta yi ai shi ne asibitin tinda shi ya daura min,azahiri kuma hawaye ne su ka fara zuba daga idanun ta,ganin haka Neena ta rude,tuni ta fara kuka ita ma,ta na pls Momma ki yi shiru na kira Dady mu je hosptal,bara na kira Uncle Jabir. Hauwa na hawaye ta ce rashin lfy na ba na hosptal ba ne Neena,ki min addua kawai dan na kusa zaucewa,aure Dadyn ki zai kara… a razane ta ce aure? Me ya sa? Ya dai na san mu? Hauwa ta ce ki tambaye shi da kan ki. Ai kuwa sai ta tashi fuuuuu ta fice,a falon sa ta tadda shi,ganin yanda ta shigo ga fuska shabe shabe da hawaye sai ya tsuke fuska,ya ce ya dai? Ta dan yi kasa da murya ta ce Dady wai za ka kara aure? Ya ce haka ne. Ta ce Dady saboda me ya sa? Ya ce kin yi kankanta,ba za ki fahimce ni ba yanzu. Ta ce ka dai na san mu ne? Ya ce na fi san ku akan kowa…ta ce plss Dady idan ka na san mu kar ka yi. Ba ta taba rokansa abu ya ki ba,amma wannan karan ta zo da maganar da ba wacce ta isa fadan ta ya amince idan ba Hajiyar sa ba. Ya ce ki yi hakuri Neena,it is for your own gud,dukkan ku,ina san ku,amma dole sai na yi. Idanun ta cike da kwalla,yayi mamakin yanda yar yarinya wai itama ta san ta ya wacce ta dauka mahaifiyar ta kishi,kai kishin mata daban ya ke. Juyawa ta yi za ta koma,sai kuma ta dawo ta ce wa za ka aura Dady? Ba tare da ya ji komai cikin ran sa ya ce Hajara ce wacce ake kira Hajjo,ta ce Anty Hajjo ta gidan Hajiya? Ya ce eh. Ta ce Momma ba ta so,Allah ya sa ka fasa Dady. Kallan ta ya ke kawai,Hajjo kawai a tsaye,da ta san matsayin Hajjo a rayuwar ta,da ta fi kowa farin ciki,amma a sannu za ta fahimta,har yanzu yarinya ce. Sai da ta fice,sannan ya koma ya kishingida. Ya shedawa Hajiya,har ta fadawa yayye da kannen Baban maza,su za su yi komai har sa rana da kai lefe,lokaci ya canja,ya fi san mazan su kai dan a rage bidi’a. Sati biyu su ka dauka kafin Sani ya mu su jagora zuwa wajan Baba,da ke dama Baban ya san Khalid sosai,sai gashi har da gayyato yayan sa da kuma Alhaji Baso baban Garbati,duk da kuwa ba wai warkewa yayi garau ba,jikin na sa na tashi lokaci lokaci,karfin hali ya ke kawai. Lokaci guda su ka bada kudin na gani ina so,ga kuma kayan sa rana da lefe,su ka ce wata uku su ke so a sa,ba mu su su Baba su ka amince,musamman yayan Baba da ya gaji da surutan jama’a wai kanin sa ya bar yarinya ta lalace ta zama yar boko ta ki aure. Lefe ma na gani na fada da Khalid ya hada cikin gaggawa su ka sauke su gaban su Baba. Su Baba sun yi mamakin yawan akwaitinan,ko da bakin su ka tafi bayan an basu tukwicin su daga kudin da su ka kawo bisa al’ada tuni magana ya fara zagaye gari,an kawo laifen birni gidan Alhaji Mamman,an sauke arziki gidan Alhaji Mamaman. Shiko Baba da ya san wacece Hajjo da irin rayuwar da ta yi a baya ya san kadan ma ya gani daga sakayyar alkhairi da Allah ke yiwa Hajjo. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 6:05 PM] Salmah Ateeku: [12:17am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣5⃣ Hajjo ta na zaune tsakar gida,ta cika ta yi fam,fashewa ne kawai ba ta yi ba. Sai ga Indo ta shigo ta na guda,wato ta gano kayan Hajjo kenan,har da takawa,ta na rai dai,rai dai,rai dai! Ina ma Inna ta na raye ta ga arzikin autar ta,Hajjo? Tin da na ke ban taba ganin kaya,kaya dai irin na akwatin lefan ki ba!anjiman nan ma Baba ya ce a zo a kwasa a kawo mi ki idan Sani ya sami lokaci. Ko a jikin ta,Hajjo ta ce hmmm. Indo ta kara da wata uku aka sanya ranar ma…..nan Hajjo ta fusata,ta ce na fasa auren na shi! Indo ta ce iyye? Hajjo ta ce eh na fasa! Indo ta na tafa hannu ta ce ku ga wacce ba a yiwa abun arziki dangin gidan maza! Akan wani dalili? Dan an sa rana wata uku? Hajjo ta ce haba Indo,ki na fa gani tun da na amince da auren mutumin nan be sa kafa ya tako ya zo gidan nan ba,ko waya ma be min ba,ba shawara ta ba komai an tashi an samin aure wata uku,na san Baba zai iya sa awa uku ma ba wata uku ba tinda dama ba kauna ta ya ke ba,amma shi ba sai ya tambayi shawara ta ba!! Indo ta ce gaskiya be kyauta ba,ai na zaci kun yi shawara ne,amma ki ma sa uziri be kai ga a fasa aure ba,ki yi kiran sa mana….Allah ya sauwake! Hajjo ta katse ta,wlh ba zan kira shi ba Indo! Indo ta ce toh sai ki yi hakuri tin da ke ma na ki jin kan ya hana ki neme shi,maganar fasa aure babu…ta na magana ta shige ciki ta bar Hajjo na ta faman kwafa. Khalid kuwa Hauwa ce ta ke gasa ma sa gurasa danya a hannu,gaba daya ta birkita shi,ta hana shi kwanciyar hankali,tashin hankalin yau da ban na gobe da ban. Har ya gwammaci zaman Abuja akan kano,ba dan ya na so ba sai dan ya ba ta lokaci ya yi nesa da ita ko ta huce. Idan ya zo kano shirye shiryen auren sa ya kai shi ko kuma ya leka site din sa ne,inda ake dankara ma sa hadadden gidan sa da ya yi designing da kwakwalwar sa dan zaman mata biyu. Hajjo na ransa kwarai,ya na son zuwa ya ganta,amma ba dama saboda abubuwa sun cude ma sa,gashi ya daga waya yay ta kiran ta,amma ba a dagawa,ashe wayar ta ta faduwa ta yi. Har ya yi fushi ya ce shi ma ya dai na kiran na ta,ta zo gidan sa sa na gaisawa gaba daya. In dan zai aika ma ta da sako Sani kawai ya ke bawa,idan aka kai ma ta ta ki karba,sai Sani da Indo sun ma ta ca ta ke hakura. Ana saura wata guda biki,su Doc Hussaina da yan uwanta likitoci aka kawowa Hajjo kayan gyara,su cikwaidi,zuman mata,tsumi har da turarukan tsugunno. Doc Hussaina ta ce matso nan ki ji diya ta,dan ni fa Hajara diya na ke da ke ba abokiyar aiki ba. Cikin jin kunya ta matsa kusa da ita,sauran matan ma matsowa su ka yi dan sun san Doc Hussaina ba da ga nan ba. Ta gyara murya ta ce Hajara kin shirya yin aure kin shirya zaman aure? Hajjo ta yi shiru,Doc Hussaina ta ce amsa min mana. Hajjo ta gyada kai alamar eh. Ta ce toh saurare ni da kyau,auren dai kin taba yi,amma ki sani wanda ki ka yi da da na yanzu ba daya ba ne,da bambamci,da ba ki san ciwan kan ki ba,yanzu kuwa kin san wacece ke,kuma kin san wa za ki aura,toh fa Hajara sai kin yi hakuri,dan hakuri shi ke zaunar da ko wace diya mace gidan mijin ta,Hajara da ba hakuri da aure dayawa tuni ya mutu,ki yi hakuri,ki toshe kunnuwan ki,ki kuma runtse idanun ki,ki sai ta harshen ki,ki ji ki ji,Hajara ki gani ki ki gani,kar ya hau ki hau,idan ya hau,shafawa zuciyar ki salama ta hanyar ambaton ubangiji,ki tuna Allah ki ke bautawa,ba wai dan shi wanda ya aje ki gidan na sa za ki yi ba,sai ki ga ke kin sauko,da iyaye ma sai an yi hakurin zama bare wani can da ya ganki da hakoran ki ras da wayan ki. Sauran su ka ce ba shakka. Doc Hussaina ta ce kin ga watannin farko na aure,nan su ke fara nuna isa,su a lalle sai sun gwada wannan ikon da Allah ya ba su kan mace tin da ta zama mallakin su,ke kuma daure ki gwada wannan sallamawar da Allah ya yassare mi ki,kwantar da kai,ba komai ba shi girman sa,girmama shi,yi ma sa ladabi da biyayya muddin be wuce gona da iri ba,kar ki yarda ki yi abunda zai rai na ki,duk da ba ke bace matar sa ta farko,dole da tambiyar uwar gida zai tafiyar da ke,da kin ga abunda be dace ba a musulunce da dabi’ance gyara ma sa a dabarance. Kar ki taba yarda wai kin zama daya da miji ki saki jiki,ki na zama anyhw,idan an yi abun dariya ki saki baki ki ta dariya kamar shashasha! Ah ah Hajara raini ya ke kawowa,wlh ba ko wani irin sakin jiki za ki yi da shi ba,kar ki yarda idea din an zama daya ta shiga ran ki,idan ki ka bari ya rai na ki kin shiga uku,ki yi yanda zai yi respectn din ki,ja girman ki ki ja ajin ki,yan da za ki yi reapectn din sa yayi respectn din ki,reapect beget respect. Uwar gidan sa gaba ta ke da ke,ko da kuwa kin girme ta,ita ma ba ta girmanta, tare ki ganta da mijin ta,kar ki yarda daidai da rana daya tunanin ki fitar da ita ya tsurga cikin zuciyar ki,ke ma diya mace,kuma ki na da diya diya mace,ki na da yan uwa,ba za ki so a yi mi ki ko na ki haka ba,ke ma ki yi adalci kar ki yiwa wata,amma fa kar ki yarda ta raina ki. Haka dangin miji,zama da su sai da dabara,zama da su iyawa ne,ki saki jiki a raina ki,ki ja jiki a ce kin ki su,toh sai dai ki ti kaffa kaffa da su,ko uwa tushe daya ku ke sai kin iya takun ki,bare ke zama ki ka taba yi sa su,da kin auri na su toh sun zama dangin miji,tsakanin ki da su kyautatawa,ki bude hannu,ba su,ke dai ba su,kyauta ta na raba ki da su,kar ki zura jiki,kar kuma ki janye jikin ki gaba daya,sama sama,sai wa kanki mutunci kar ki yarda a rai na ki. Tsakanin ki da facalolin ki mutunci,wacce ta ku ta zo daya sai ku yi,wacce ta ku ba ta zo daya ba ruwan ki da ita,kowa ya tsaya matsayin sa,I keep repeatn dis,kar ki yarda a raina ki,kar ki raina kowa. Ki zama mai tsafta,mai kula,mai tattali,mai boye sirri,Hajjo ki rufa sirrin mijin ki,ban da tona sirri,kin san duk abunda ya fita daga bakin ki zuwa kunnan wata ya tashi daga sirri,sirrin ma iri iri ne,akwai na dakin mijin ki,akwai na aljuhun shi,akwai kuma na tsakanin ku,akwai kuma na zamantakewa. Na zamantakewa ne mai wuyan boyewa,yau da gobe dole akwai randa za ki bukaci ki yi sharing abunda ke damun ki akan yanayin zaman auren na ku,ko da kuwa ba solution za a baki ba,ke dai ki fada ki sami sauki,wannan ba laifi idan kin sami wacce za ki yi sharing da ita,toh amma me? Ba kowa za ki fadawa ba,ban da ma iyaye,ke za ki manta,su ba sa mantawa,rukewa su ke a ransu,kawaye ba ko wacce kawa ba ce mai ruke sirri,wasu rashin ruke sirri ma a hilittar su ya ke musammam wacce ta fiya surutu,dan ko gawa za a wanka ba a yi a gaban mai surutu ko wanda ba na ka ba saboda kar ta ga wani abu suruta ya sa ta furta,dan uwa sai kin sami wacce ta ke very close da ke kuma kun saba sharing problems dinki,san samu ki sami mace wacce ta ke ta manyanta,cikin yan uwa ne kawayen mamanki ne,aunties ko ma maman kawar ki,idan kuma kawayen na ki ma akwai ta sirri wacce ki ka aminta da ita shi ma din ba laifi,dan ba a rasa na kwarai,kafin a same su ne aikin,inshaAllahu sai ki ga kin sami mafita asirin ki a rufe… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [16/10 22:03] .: 2:36am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣6⃣ Waje yayi shiru,Doc Hussaina ta kara da batun gyara,kin san dai ganyen magarya ko? Hajjo ta gyada kai. Doc Hussaina ta ce toh ki ruke shi,ya na da amfani matuka,musammam da aka hana amfani da soaps da kuma antibacteria,saboda any thing antibacteria is powerful,kuma ur private part is the most delicate part of ur body a matsayin ki na diya mace,wajan akwai flora wanda su ke da amfani,shi kuma antibacteria idan ki ka yi using ba ya iya bambamce tsakanin flora da bacteria,duka ya ke hadawa ya kashe,kin ga anyi ba a yi ba,haka kuma ya na sane mace yawan amfani da su,plus soap wari ma ya ke sawa. Shi ko ganyen magarya na tsaftace jiki kwarai,ya na hana warin gaba,ya na matsi,ya na maganin toilet infections, ya na kuma kara ni’ima,tin daga yanzu ki same she danye ko busasshe, ki fara daurayewa,sannan ki tafasa ki ta ce ki na tsarki da shi da dumin sa ba da sanyi ba. Haka farin almiski,dan kin ga shi ana ma kiransa miski Aisha,wanda ya samo asali daga wajan Nana Aysha Allah ya kara yarda da ita,duk san da ta gama period ta ke amfani da shi,ya na matsi kuma ya dauke wannan karni da gaifi na period. Kin ga ni duk juma’ar duniya na kan yi amfani da shi. Ni yara na da sun fara period na ke koya mu su amfani da ganyen magarya da miski badan komai ba sai dan period kadai kara budurwa ya ke,musamma idan ya na fita da yawan nan,tashi guda ka ji bulum ya sauka,gasu yawancin su suna shiga toilet na makaranta,akwai every possibility na kwasar toilet infection,so da sun gama sai na ba su ganyan magarya su kama ruwa sannan na ba su miski su shafa,ba wai sai sun zo aure ko sun yi ba. Daya daga cikin Docs din ta ce Anty Hussaina tin da kin ce period kadai ya na bude budurwa,ba laifi kenan budurwa ta yi amfani da abun matsai idan ta tashi aure? Doc Hussaina ta ce eh ba wai ba laifi ba ne,kamata ya yi ayi daidai ruwa daidai tsaki,kin ga lokacin mu dake at our tender age ake ma na aure,da yawa dakin mijin mu mu ke fara period,so idan aka tashi mana aure ba wani maganin matsi da mu ke bukata,amma yan matan mu na yanzu an yi period na kusan shekara da shekaru,ga daukan abu mai nauyi,ga tsallake tsallaken kwata mai girma dadai sauran su ya sa mu ke dan bawa yaran mu kayan matsi,shi ma din ba wai na matsi sosai ba,irin su ganyan magarya,ake tsarki da shi,da miski,dama kuma idan za ta yi gyaran jiki za ai mata dukkan da dirot ko farar kaya,wannan ma ya wadatar,ba a dinga tsugonno a wannan,a waccan, a shafa waccan,tusa waccan,garin neman gira a rasa ido,ku ga yarin ta matse gam kamar bango,wata dama a matsen ta ke sosai ba ta san kanta ta kara,sai daga baya a zo ana jinya,wasu har dinki ma,toh ina amfanin haka? In ma matsin sosai za ki yi gwara ki jira a kai ki ki san kan ki,ki gane irin ki sai ki yi matsin da hujja. Toh ga gudun mawata gare ki Hajara amarya. Doctors su ka ce ita kadai ko har mu? Doc Hussaina ta ce har ku da ma da ku ke gidajan ku za ku iya yi,amma yanzu da ita na ke magana ta,duk su ka sa dariya. Doc Hussaina ta ce ki na ji na Hajara? Hajara ta ce eh. Ta ce idan biki ya matso kusa sosai,kafin a fara sai ki sami kankanar ki wanda ki ka san za ki iya shayewa kwallo guda,sai ki yi sallah raka’a biyu nafila,ki fafaye saman kankanan,ki dan caccaki cikin yanda ruwan zai tsatso,sai ki karanta suratul Khafi,Maryam da Rahman ki tofa ciki,ruwan da ya tsotso na kankanan sai ki disa cikin turaren ki da ki ka ware dan amfanin ki ke kadai,kamar humrah,bayan ki tabbata ruwan kankanan ya zuba ciki sai ki aje kayan ki. Ki shanye kankanar ki tsaf ki koshi,turaren ki kuma ki na amfani da shi,inshaAllahu mijin ki zai girmama ki,ya martaba ki,yayi respect din ki,za kuma ki sami daukaka wajan sa wanda shi ake fata. Gaba daya kowa ya fara kai gaskiya ni ma zan yi,ni ma zan yi. Hajara ta ce na gode Anty Hussaina,Allah ya kara girma. Doc Hussaina ta ce amen. Allah ya bada zaman lfy. Hajiya ke neman ta ido rufe,da ta tashi daga aiki sai ta biya gidan ta. Hajiya ta na ta tsokanar ta wai Hajjo ta zama sirika. Wani nauyi da kunyar Hajiya ta ke ji sosai,ta ka sa sakin jiki su yi maganar auren da kuma sauran abunda Hajjo za ta bukata saboda kusan rabi tare su ka siya da Hajiya kafin ma Khalid ya dawo a fara maganar auren su. Da Hajiya ta ga dai Hajjo ta ka sa sakewa sai ta hada ta da kanwar ta,tare su ka cigaba da shirye shiryen biki,ba Jabir ba,har Hajiya sai da ta dunkula dukiya mai tsoka ta damkawa Hajjo dan shirye shiyen biki,ba shakka sun ma ta karamci kwarai. Gyara kam Hajjo na sha kwarai daga wajan Doc Hussaina,dake Doc Hussaina duniya ce. Hauwa kuwa sai da Khalid ya hada ta da Hajiya tai ma ta nasiha sosai sannan ta sauko. Ana sauran sati guda daurin aure ta tare saban gidan Khalid. Gidan ya hadu ya tsaru kamar gidan turawa,da ke ma su abu da abun su,abu na so Khalid bluiders of d world. Bangare uku ne,bangaren Khalid a sama,sai kuma katan falo a kasa wanda ya sada ban garan Hauwa da Hajjo matan na Khalid,sai kuma katan kitchen ma dauke da dining area,dakin Neena ma bangaran Hauwa ya ke,Gidan cike ya ke fal da kayan more rayuwa,gashi very spacious. Hatta bangaran Hajjo Shi ya zuba kaya,ya dai aika Sani ya tambaya ma ta colour din da ta ke so. Ranar juma’a aka daura auren Khalid da Hajara,Khalid ya biya sadakin sa dubu hamsin. Su Ayush ne amara,duk da ba wani bidi’a aka yi ba,daga wuni da aka yi a kumurya,sai walimar da aka yi gidan Hajiya sannan aka wuce da amarya akai Hajjo dakin ta. Kuka wajan Hajjo abun ba magana,rayuwa ta sake canzawa,ta shiga saban babi… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 6:06 PM] Salmah Ateeku: [12:56am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣7⃣ Hannu Hauwa aka damka amanar Hajjo,sai cika ta ke ta na batsewa ita da yan uwanta,habaici da guda kuwa yan uwan Hajjo sun sha. Ga wani ado da kyau da Hauwa ta yi kamar ita ta yi kanta dan kyau,sai a sannan Indo ta gane matsalar da Hajjo ke gujewa kan ta dan gaskiya Hauwa ta cika mace,su Doc Hussaina kuwa ba dan sun san wacece Hajjo ba sun kuma yarda da shirin da su ka ma ta da sai sun daura hannu a ka sun ce sun shiga uku. Bayan su Indo sun kara ma ta fada sai su ka watse,su ka bar Hajjo tsakiyar gadan ta ta na sharbar kuka. Ango Khalid ya shigo cikin shigar angwaye na alfarma,sai ma ya dada zama yaro kamar wanda ya yi auren fari.Hauwa zaune bangaran ta,ita ma yan uwanta sun watse,Neena na dakin ta ta yi bacci,Hauwa ta sake ado ta yi kyau kamar ita tai kanta ango Khalid ya shiga ya same ta. Shi kan shi kyan na ta ya ruda shi,ya janyo ta jikin sa ta zille ta na malam yaya ne,ba fa ni ba ce da kwanan ba yau! Ya dara tare da fadin an ma fara min gori kenan. Ta ce ya bazan ma ka ba gori ba tunda irin rayuwar da ka tsarawa kan ka kenan. Ya murmusa gami da sake janyo ta jikin,ya na hussssh,say no more. Ina Neena? Ta ce ta dade da kwanciya ita dai kam. Ya ce toh ki fito falo ki same mu,bari na kira kanwar ta ki. Da kamar za ta ce ba za ta zo ba,sai kuma ta ga kamar hakan zai sa Hajjon ta raina ta,ta ce toh ta na fitowa. Bangaran Hajjo ya shiga,ya tura komar a hankali,wani kamshi mai dadi ya daki hancin sa. Yayi sallama tare da shiga daki. Idanu ta daga ta kalle shi,wannan karan Khalid Khalid ne ke neman numfashi ba Hajjo ba,tsabar kyau da kwarjini irin na amare gaba daya ta sauya yanayin sa. An ma ta ado cikin farin leshi,ga farar lufaya an nada mata,ga gyaran jiki da ta sha wajan su Doc Hussaina fatar nan na ta wankan tarwada har wani sheki yake. Da kyar ya daure,ya na wani basarwa dan kar ta gane tarkon ta ta kama kurciya ya ce muna jiran ki falo amarya. Juyawa yayi ya fita ba tare da ya ji amsar ta ba. Falon kasa da yayi dan zaman iyalan na sa duka ya zauna. Hauwa ce ta riga fitowa,ta zauna kusa da shi suna dan hirarrakin su,sai ga Hajjo ta fito,idanun ta a kasa,fuskar ta rufe da mayafi ta zauna a na ta kujerar da ga gefe,Khalid ya ce ta so ta zauna kusa da shi kamar yanda Hauwa ta zauna,ma’ana su sa shi tsakiya. Ran Hauwa ya sosa da kishi,wato dai sai ya jera su,ya nuna ma ta matsayin su daya,bare ma fitowar Hajjo yanda ta ji tana kamshi kamar diyar shuwa ya sa zuciyar ta tsinkewa. Ba musu da ke gaban uwar gidan sa su ke sai ta tashi ta koma kusa da shi din. Ya mu su nasiha sosai da fatan za su hade kan su,ya kuma roki Hajjo da ta kara yiwa Hauwa kara akan Neena,tin da duk an zama daya,dan Allah ta karanta. Cikin ranta kuwa cewa ta ke indai kara ne kunzo wajan ta,ita ba matsala gare ta ba. Ya kare nasihar shi da addu’a. Hauwa ce ta fara tashi ta tafi,Khalid ya bi bayan ta. Ita ko Hajjo tashi ta yi ta koma na ta bangaran. Ta yi wanka fito daure da shawl dan yanda Khalid ya dade be fito ba sai ta dauka can zai kwana ta saki jikinta,ta zauna ta na shafa mai. Kamar da ga sama sallamar shi da shigowar sa lokacin guda ne… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) Advertisements SHARE THIS: TwitterFacebookGoogle RELATED Skip to content ummu-abdoul MENU Diya mace 4th Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17, 2016 ​14am, 6/11/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣8⃣ Da sauri Hajjo ta tashi,ta kuma koma ta zauna ta na jan shawl din kan gwiwar ta. Da ganin na ta da kuma yanda ya ga ta rude sai ya bashi dariya,dariyar ta sa ya bawa Hajjo haushi,dama kuma kule ta ke da shi. Ta yi saurin jan lufayan ta ta rufe jikin ta tana mallam menene za ka shigo min daki ba sallama! Ya na murmushi ya ce na yi sallama Suger,ta ce me ya sa ba ka tsaya na ba ka izinin shigowa ba kawai za ka shigo min?ya ce gida na ne,auren ki na ke. Ta cije leba gami da ka fita ka bar min daki,pls ka fita! Ya ce ni ki ke kora Hajara? A daren auren na mu na fari ki kore ni? Idanun ta kwalakwala,sai a sannan ta tuna fa ashe wai daren auren ta ne,ta tuno yanda na ta ta kasance da Garbati,tuni idanun ta ya rufe,ta ce eh kai na ke kora,pls ka fita. Duk da hakan be ma sa dadi ba,amma jin kai ya sa ya ki nunawa,sai ma murmushi da ya sakar ma ta,ya karasa cikin daki,gaban ta ya kara faduwa. Ya lura da hakan,sai da ya kai dab da ita,ta dada dunkulewa cikin mayafi,ya na murmushi ya aje ledar gaban ta yana fadin ga abunci,na san yunwa ki ke ji. Ya sunkuyo fuskar ta,Hajjo ta runtse ido,kumatun ta yayi kissin ya dago ya na dariyar yanda ta sankare,kana ya ce suger,Khalid is a gentle man,so ki sa a ranki ba zan taba kwana cikin dakin ki ba sai dai idan ke ki ka gayyace ni da kan ki. Ya juya ya fice. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta saki jikin ta. Cikin azama gudun kar ya dawo ta sanya rigar baccin ta iya gwiwa. Sai da ta nutsu sannan ta bude ledar da Khalid ya aje,kaza ce gashasshiya da fresh milk,ta ci ta koshi,sannan ta dan taka a tsakar dakin gudun bacin ciki,ta kwanta ta sha baccin ta dake dama ta tara gajiya. Sai da ta yi sati daya a gida ta koma kan aikin ta. Sam Khalid ba ya gaban ta bare kuma matar sa,kwana uku uku su ka raba kwanan duk da kuwa duk ranar kwanan Hajjo dakin sa ya ke kwana bisa ga alkawarin da yayiwa Hajjon,ita kuwa Hauwa da ta lura da haka,sai ta kara jin kan ta,wato da gaske dai ba san Hajjon ya ke ba tinda ya aje ta tamkar fanko ne kawai. idan ranar girkin Hajjo ne kafin ta fita ta ke musu brkfast da abuncin rana,da ke 7:30 ta ke fita,8 ta ke fara aiki. Da ta dawo 4 sai ta daura na dare. Kuma bisa al’adar su,tare a ke zama a ci abuncin kan dinig table da ke cikin kitchen din na su,nan Hajjo ta ke ganin kissa da kisisi na wajan Hauwa,ita abun har mamaki ya ke ba ga Neena na wajan ita ko kunya ba ta ji? Tai ta jan shi da hirar da be ma shafi Hajjo ba yanda za su ware,ita kuwa Hajjo ko a tafin kafarta,ita dai ta cika cikin ta tashi idan ma hadiye shi za ta yi tayi can ma ta.Khalid ya dame ta da korafin shi ba zai juri hawan adaidaitan ta ba,kullum wani gardi ya ke jin kamshin ta,dan haka lalle ta yi shirin koyar driving dan ba zai juri yay kai ta ya na dauko ta ba,haka kuma ba zai dau driver ba. Tsakanin ta da diyar ta nesa nesa,dan ita ganin ta take kishiyar uwa ba ma uwa ba,ita kuma Hajjon sai ta ke wa Hauwan kara,ta ke dauke kan ta daga kan Neenan. Randa ta cika sati biyu a gidan ta,bayan ta gama girki an zauna anci,sai ta tashi ta shige bangaran ta ta bawa Hauwa waje ta yi abunda ta ke so. Ta na shiga ciki Khalid shi ma ya tashi,ya sake kaya cikin sport wears din sa ya fita jogging. Wanka Hajjo ta yi,ta sanya rigar baccin ta pink mara hannu da nauyi,ga laushi iya gwiwa ta tsaya ma ta,ta kama kan ta da ya ke a tsefe ta rasa mai kitso,ta yi kalaba guda biyu,abun ku da kan ba gashi sai kuwa su ka tsaya gudil gudil da su kamar kaho. Ita kanta da ta kalli kanta a madubi sai da ta yi dariya,ta yi kama da yar yarinya sak. Ta ja kujerar karatun ta gaban table,ta kunna system ta fara sana’ar na ta,wato research. Bayan Khalid ya dawo,a tsakar dakin sa daga shi sai gajeran wando da shawl a rataye wuyar sa ya na shirin shiga yayi wanka,sai ya ji duk duniya idan be tsokano Hajjo ba ba zai ji dadi ba,dan yanzu ba wacce ya ke son zolaya kamar ita. Kawai sai ya fasa shiga na shi toilet din ya nufi bangaran na ta. Ta yi nisa cikin research,ba ta ankara ba ta ji an bude kofa,da sallamar sa da shigowar sa lokaci daya ne. Ta daga ido ta kalle shi,ganin yanayin shigar ta sa ta yi saurin yin kasa da ido. Murmushin nan na sa na tsokana ya sakar ma ta,tare da fadin nawa toilet din is faulty,i wil use urs in ba damuwa….ya na magana ya na nufar kofar bandakin,jin ta yi shiru ya juyo ya kalle ta,ya ga sam hankalin ta ma ba ya wajan sa,sai a sannan ya lura da kahon gashin ta biyu,ya ce like seriously Suger iyakan gashin ki kenan ko kuwa kin boye wani karkashin filon ki? Dagowa ta yi ta kalle shi,sai kuma ta tuna yanayin da ya ke ta kara saurin kau da kai,gaba daya magana ma ta kasa dan takaici da kuma takurar da shigowar sa ya sa ta. Ganin ta ma sa shiru ya shige ban daki ya rufo. Sai a sannan ta saki ajiyar zuciya. Kamar za ta koma falon ta,sai kuma ta fasa gudun kar yayi tunanin tsabar tsoran sa ya sa ta gudun. Amma gaba daya ta ma kasa gane komai,burin ta ya zo ya fita ko ta sami nutsuwa. Ile ko sai gashi ya fito daure da shawl,kirjin sa duk a waje ga ruwa na diga daga cikin sa,hannun shi ruke da dan karamin shawl din ta ya na goge kan sa. Da wayo ta saci kallan sa,su ka kusa hada ido ta yi sauri janye na ta ido. Ya na murmushi ya ce ba sai kin saci kallo na ba Suger,am ol urs,saki jikin ki u can stare as long as u want. Maganar ta sa sai ta bawa Hajjo haushi,ta yi karfin hali ta kalle shi ido cikin ido sannan ta ce ni Hajjo na saci kallan ka? Me zan kalla Khalid? U ar nt man enough for me…..sai da ta fada sannan ta yi dana sanin dan subul da baka da ta yi,da za ta iya shanye kalmomin ta na karshe da ta shanye ganin yanda idanun sa ke shining,fuskar sa dauke da mischievous smile ya nufo in da ta ke,dan tsoro kasa motsawa ta yi,kamar wacce aka sa igiya aka daure,har ya karasa kujerar da ta ke,ya sunkuyo da fuskar sa dabda na ta,Hajjo ta yi kasa da na ta idon gaban ta na dukan uku uku,ya sa hannu ya dago da haban ta ya na kokarin sanya kwayar idanun sa cikin ta,amma ta ki dagawa ta kalle,ta na jin saukar numfashin sa kan fuskar ta,ya ce maimaita abunda ki ka ce Hajara. Tsit ka ke jin Hajjo kamar wacce ruwa ya shanye,ya ce fadi na ji,who is nt man enough for u? Ta yi shiru,hannun sa bisa fuskar ta,ya fara wasa da yatsan sa kan lips din ta da yake kallo kamar mai nazari,kan ta ankara tuni ya mikar da ita ya hada da jikin sa ya fara kissing din ta. Da ke Hajjo ta ji saban abu,abun da sai dai ta gani ana yi a tv ta dauke kai ko kuma ta karanta a littafafai wai shi Khalid ke ma ta, ta fara kokarin zullewa har ta hakura ta dai na… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 6:12 PM] Salmah Ateeku: [11:30am, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 5⃣9⃣ Ya kusa shagala ya manta da inda ya ke haka ita ma Hajjo da ta shiga wani duniyar,da kyar ya iya yaki da zuciyar sa,ya dago ya na kallanta,idanun ta runtse tana numfashi a hankali,ya maida ta jikin sa,yayi hugn din ta sosai kamar za ta shige cikin sa,sai da ya sami nutsuwa,cikin rada ya ce mata dis is jst a kiss Suger,ba dan Khalid is a gentleman ba da na gwada mi ki ya Man ya ke,amma a sannu Suger,cikin kunnan ta ya rada ma ta am much more dan Man enough for all the women in d world Suger……ya janye jikin sa a hankali,sai da Hajjo ta yi saurin dafa table dan gani take ba za ta iya tsayuwa ba, shi kuwa ficewa yayi da sauri kafadar nan a tsaye dan jin kai. Da fitar shi ta yi saurin hayewa gado,ita dai kam ta shiga nau’i,bargo ta ja ta dukunkuna,abunda ya faru tsakanin ta da Khalid ya sa ta dai na gane komai,ya tsayar ma ta da duniyar cak. Shima wajan gugan na ta hakan ta ke,tin komawar sa daki ya kasa sukuni,he jst can’t blv Hajjo can b dis innocent yea Innocent nd sweet at thesame tym,sam da dukkan alamu yanda ta yi reactn ya san saban abu ne a wajan ta,hakan ya kara sa shi san more,he love every bit of it,He want her dan da kyar ya iya jurewa be koma ba,amma daran ranar sam bacci ya nema ya rasa,tunin Hajjo ne ya raya ma sa daren. Washagari ko karyawa ba ta yi ba ta gudu wajan aiki gudun haduwa da Khalid,dake ta yi sa’a ba girkin ta bane. Dab da la’asar bayan ta dawo daga aiki,ta yi wanka,sai ta fito babban falon su,nan ta tadda Neena a na game,ta ce Neena ba gaisuwa? Hankalin ta kan game tace ai ban gan ki ba Aunty,sannu da zuwa. Hajjo ta ce sannun ki,ta sami waje ta zauna,sai ga Hauwa ta fito daga kitchen ta ce Neena a tashi a yi shirin islamiya. Neena ta make kafada,ni wlh na gaji. Ga mamakin Hajjo sai ji ta yi Hauwa ta ce toh ai shikenan,ta cigaba da aikin ta. Har Hajjo za ta sa baki,sai kuma ta yi shiru,amma har ranta ba ta ji dadin abun ba. Ana kiran sallar la’asar,Hajjo ta tashi ta yi na ta,ta na zaune kan dadduma Hauwa ta sake shigowa ta ce da Neena a tashi a yi Sallah ma na. Idanun ta kan game ta ce sai an min game over Momma,Hauwa ta ce toh ai sai ki ta yi,ta shige kitchen. Ran Hajjo ya baci,ta ce ke aje game din nan ki je ki yi sallah. Ko kallan Hajjo ba ta yi ba bare ta aje game din,ta ce ai na ce sai an ce game over…..a fusace Hajjo ta tashi ta fizge handle din,tashi maza ki je ki yi sallah ko na sabar mi ki! Ta daka ma ta tsawa,a kideme Neena ta tashi,ta fashe da kuka da ke ba a saba ma ta tsawa ba,ko a jikin Hajjo dan ji take kamar ta make ka ta huta,ta ce dan iskanci ana mi ki magana ki na jin mutane sai kin gama game za ki yi sallah! Ki je islamiya kin ce kin gaji! Wlh ba zan juri wannan saken ba! Sai ga Hauwa ta shigo da sauri,ganin ta Neena ta karasa wajan ta da gudu ta na kuka,sai tambayar ta take lfy? Dukan ki ta yi? Kuka ya ci karfin Neena ta ka sa magana,sai Hauwa ta ce je ki dakin ki ina zuwa,sai kuwa ta shige bangaran Hauwa da gudu,ta na jiyo Hajjo na fadin ki tabbata kin yi sallah! Hauwa ta kalli Hajjo ta ce me ki ka ma ta? Kar dai dukan ta ki ka yi. Hajjo ta ce ban dake ta ba,amma kiris ya rage na dake ta,yarinyar is too spoiled,ya kamata a fara handling din ta wit iron hands. Hauwa ta ce ke kar ki nemi ki fada min magana! Me ki ke nufi? Ki na nufin ban iya tarbiya ba? Hajjo ta girgiza kai,ta ce ba haka na ke nufi ba,Hauwa ta ce haka ne mana,wato iko za ki nuna min,ban iya tarbiya ba muna sangantar mi ki da diya. Hajjo ta ce ba ki fahimce ni ba,gyara kayan ka ai ba zai zama sauke mu raba ba…ke tsaya matsayin ki! Hauwa ta daka ma ta tsawa,ta ce har ke kin isa ki fada min magana dan mijina ya auro ki,ki na ganin ba na haihuwa shi ki ke tunanin za ki iya min gori kan diyar ki……Hajjo dai tura ta kai bango,ita ma ta fusata ta ce eh an mi ki gorin,karya ne? Ba diyar tawa ba ce? Ko ke ki ka haifa min……karaf sai a kunnan Khalid da shigowar sa kenan ya tsinci maganar Hajjo,ran sa ya baci matuka. Ganin sa tsaye Hauwa ta juya ta shige bangaranta da gudu. Hajjo ta yi kasa da idanun ta,yanda ta ga idanun Khalid sun kada sun yi ja ya sa ta kokarin ma sa bayani….ya dakatar da ita ta hanyar fadin dama haka ki ke? Na zaci ke me rufa min asiri ce,amma ji yanda ki ke gorantawa mata ta? Ki da ki ke haihuwar ba Allah ne ya baki ba? Ko dabarar ki ce aka ce mi ki? Idanun Hajjo cike da kwalla ta ce ba haka ba ne,she pushed me to d extrem wall ne,dole na yi magana,ba zan iya jure ganin yanda Ameena ke tashi ba kwaba ba! Ba zan iya jure ganin ta na tashi kamar Baban ta ba,God shez becoming d personication of her biological father! Khalid ya cize lebe,ni ma gorin za a min? Na ji ba ni ne baban ta ba am so what? Hajjo ta ce me zan yi ku gane? Menene laifi dan na gyarwa diya ta tarbiya? Karya ne ba diyar tawa ba ce?yanda na san ciwan ta wlh ba zan sa ido ta tashi yanda ta ke yanzu ba,ba gata ba ne wannan,diya mace ce,uwa kuma za ta zama nan gaba…Hajara! Ya daka ma ta tsawa,enough of ur insult! Ita din da ki kewa gori ba taimaka mi ki ta ke ba?ki na da lokacin diyar ta ki ne?idan ki ka sa kafa ki ka bar gidan nan tin 8 ba ki dawowa sai 4,ina ki ke da lokacin kan ki bare na tarbiyar yara? Murya kasa kasa Hajjo ta ce no you ar mistaking,ku bani diya ta mana kuga ko zan gaza tarbiyartar da ita,ko bani ita ku ka ko za ta gaza samin lokaci na! Never underestimate d power of mother! Zan iya zama both! A responsible mother as well as a dedicating Doctor!Khalid ya daga kafada,Wuce ki bawa mata ta hakuri! Hajjo ta ce Khalid dan me ya sa? Dan me ya sa zan ba ta hakuri? Dan ni ba mutum ba ce ko dan ni ba a sona? Dan me ya sa? Me na mata da zan ba ta hakuri? Fuska murtuke ya ce a matsayi na na mijin ki na ce ki ba ta hakuri,it is an order! Rai bace,kwalla na shirin sauka ta makale,da sauri ta nufi bangaran Hauwa,ko da ta shiga dakin ta,ta ganta kwance,sai ta sake shawara,ta juyo za ta fita ashe Khalid na biye da ita,ya ce juya ki ba ta hakuri! Hajjo ta juya ta ce Hauwa Allah ya baki hakuri. Ta juyo tana kallan Khalid ido na spark din kwalla da bacin rai ta ce na bawa matar ta ka hakuri,ta fice da sauri. Shigewa dakin yayi,ya jawo Hauwan jikin shi ya na kara ba ta hakuri. Hajjo na shiga dakin ta sai ta fashe da kuka,sam ba za ta iya zaman gidan ba,dama ta san wulakanta ta Khalid ke da niyar yi shi ya sa ya auro ta. Tuni ta hada yan kayanta cikin karamar jaka,ta dau kudin mota,ta fito ba tare da kowa ya sani ba sai hanyar Kumurya. Sai da ya tabbatar Hauwa ta saki ranta,sai kuma hankalin sa ya koma ga Hajjo,ya fara ji kamar be kyauta ma ta ba tunda be ma ta uziri ba ya ji kanun zance,kawai tsintar ta yayi ta na gorantawa uwar gidan sa rashin haihuwa. Dakin Neena ya je,ya tambaye ta me ya faru ta yi kuka? Da ke yaro be fiya karya ba sai ta bashi lbrn yanda aka yi har kin zuwan ta islamiya da ma kin yin sallah. Jikin shi ya yi sanyi,ya tashi da sauri ya nufo bangaran Hajjo,amma me zai gani? Wayam babu Hajjo babu alamar ta,ya bi daki daki na bangaranta,har bandaki ya duba amma shiru,tuni ya rude,hankalin sa ya tashi. Da sauri ko takalmi be iya sawa ba ya fito wajan maigadi ya na tambayar ko ya ga fitowar amaryar sa? Maigadi ya ce kai be gani ba,in ma ta fita watakila sanda ya zaga bawali ta fita din….. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [16/10 21:48] .: :55am, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣0⃣ A kidime ya koma ciki,takalmin da ya sako ma hadin bauta ne be sani ba,tashin hankalin sa ina Hajjo za ta da yamma likis haka? Ko sallama be yiwa Hauwa ba ya figi motar sa dan bin sawun Hajjo. Ko da ta isa kumurya,idanun ta sun kumbura da kuka,sai tadda Indo ba ta nan sai yara,su ke fada ma ta wai Indo ta na gida dazu aka zo aka ce Baba ya kone. Nan tsakar gida ta saki jakar ta,bayan shekaru da dama sai ga ta ta dau hanyar gidan su,dan idan ba ta ga halin da Baba ya ke ciki ba hankalinta ba zai kwanta ba. Ganin yanda kofar gidan ya kwarabe sai da gaban ta ya fadi,bare da ta shiga gidan,kamar ba nan ne Innar ta ke rayuwa ciki ba da,gidan ya lalace,ya kazance. Muryar Indo ta ji ta na musayan magana da matan su Mudi,Indo na fadin wlh sam ba ku kyau ta ma na ba,amma ba laifin ku ba ne,laifin mazajen ku ne,idan ku be haife ku ba ai su ya haife su. Tare su ka ce eh mun ji din,yo ba shi ya ce a bashi garwashin ba,sai mu hana shi?ace mun yiwa siriki rowa? Muna fama da yara muna fama da tsoho,ai idan ba a gode mana ba ba a zage mu ba. Baba kwance gaba daya hannun sa na dama ya kone,yatsun duk sun durkushe,sai nishi ya ke dan azaba,bakin sa karkace daga alama barin jikin sa ya shanye. Hajjo ta yi sallama jiki sanyaye. Indo ta amsa ta na yauwa Hajjo gwara da Allah ya kawo ki,ji yanda Baba ya sanya hannun shi cikin garwashi ya kone dan Allah! Sai ta sa kuka…Matan Su Mudi su ka rude ganin Hajjo,dake sun santa tin kafin ta auri Garbati,tare su ka yi wasa,amma zaman kauye sun tsufe sun tsomare kamar ba sa’annin Hajjo ba. Su ka fara laha’ila Hajjo,Hajjon ce kuwa! Ko ta kan su ba ta yi ba,ta karasa wajan Baba da tin randa ya ce ta zauna wajan Indo ba ta kara sa shi a ido ba,gaba daya ya tsufe ya tsomare saboda cuta da rashin gata. Gaban shi ta zauna ta na hawaye. Jin ana Hajjo Hajjo! Idanun sa runtse sai yayi sauri ya bude ya na ina Hajjo? Ina diya ta Hajjo,ku hada ni da Hajjo na nemi gafarar ta! Indo ta ce yi magana Hajjo,taba shi ya jiyo ki! Hajjo ta sanya hannun ta cikin na Baba,ta kasa magana sai kuku. Tana kuka Indo na kuka. Su kuwa matan su Ayuba sai abun ya zama mu su na kallo. Sani Hajjo ta nema,su ka yi sa’a shigowar sa kumurya kenan,ya ce gashi nan tafe. kafin su iso Indo ke ba ta lbryn yanda aka yi Baba ya kone,wai cewa yayi a bashi garwashi zai yi turare,da ke Baban ba lfy gare shi ba,ya na cikin turaren ya yanki jiki ya fadi,sai hannu ya fada garwashi,gashi bangaran jikin sa ya shanye,ba daman ihu,baki ya karkace ko ya yi ihu ba mai ji bare a ka masa dauki,matan ‘ya’yan sa ba sa iya kula da shi,sai da babban dan Mudi ya gifta ta dakin ya ga Baban ya fasa ihu,shi ne fa aka zo aka cire hannun. Mudi da Ayuba sun dawo,sai mita su ke wai laifin Baba ne,shegen rigima na tsoho,ina shi ina turare! Abun mamaki da kudirar ubangiji a nan shine diyoyin matan na sa da ya guja ya ke kyama,ya ke kira da jidali su ke jin kan shi su ke tausayin shi,su kuma ‘ya’yan na sa maza da ya nunawa gata sam ba su damu da shi ba,shi ne ma ya zame mu su jidali su da matan su,sun ma daina kiran sa Baba sai rikitaccan tsoho. Jin yanda su ke wa Baban ran Hajjo ya baci,ta ce da Sani ya sa Baba a mota,su fara tsayawa a gida ta dan wanke konuwar in ya so sai wuce kano. Hakan ko aka yi,gidan Indo a tsakar gida aka yiwa Baba shimfida,Hajjo ta wanke konuwa ta ma sa dressing. Zaune gaban sa ta na ma sa fifita Sani ya ce bara ya samo mai ya kara a mota sai a tafi. Fitar shi ba da dadewa ba sai gashi ya dawo tare da Khalid. Jin muryar Khalid cikin gidan gaban Hajjo ya fadi,ta tashi da sauri ta shige ciki ba tare da ta ko daga ido ta kalle shi ba bare ma ta ga yanda ya ke a birkice. Daga ciki ita da Hajjo su ke jiwo maganar su,ya na ta jajanta jikin Baba,gashi ganin Hajjon kan sa ya ji dadi kwarai. Sani ne ya kwallawa Indo kira,ta fito su ka gaisa da Khalid,ba dan ta na fama da ciwan Baba ba da babu abunda zai hana ta dariya ganin Khalid ba yanda ta saba ganin sa ba,yau takalmin ma hadin bauta aka sako,lalle kanwar ta ta ruda shi,dake ta ba ta lbryn abun da ya faru. Khalid ya ma ta ya mai jiki,tare da fatan samin lfyar sa. Sani ya ce da Indo ta kawowa Khalid dadduma bara ya je ya karo mai. Khalid ya ce ka bari mana a tafi a tawa motar? Sani ya ce da ke har da su Mudi za a tafi,wajan ba isar mu zai yi ba. Khalid ya ce eh haka ne,toh a dawo lfy. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 6:13 PM] Salmah Ateeku: [12:01pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣1⃣ Daga can gefe ya na fuskantar inda Baba ke kwance ya zauna bisa dadduma. Indo ta zauna ita ma daga gefe,su na dan tattaunawa,Khalid ya kawo maganar Hajjo,ya ce wato Yaya ta(sunan da ya ke kiran Indo tin da ya auri Hajjo)na ji dadi kwarai da na ga Hajjo na kula da Baba,da har ina zargin ta da kin kula da lamarin sa da ma lfyar sa,ki ga sanda ya kwanta dinnan ko duba shi kin zuwa ta yi. Indo ta murmusa tare da fadin ai ina ga duk cikin mu babu wanda ke kula da Baba kamar ita,ka ga kwanciyar ta shi da ka ke magana a kai,eh kwanciyar da yayi ba ta je ta duba shi din ba,amma ita ta biya duka kudin asibitin,ina sanda ka zo ka ke tambaya ta wa ya biya kudi ka je biya aka ce an biya? Ai ita din ce ta biya. Khalid ya ruke baki tare da fadin ikon Allah,wani abun sai Hajara,a haka sai ka yi zatan ba ta damu ba! Indo ta ce ai haka take,ba mai gane halayyar Hajjo,ita dai kam wuyar sha’ani gare ta yanda ka san hawainiya haka ta ke rikida. Toh amma duk cikin mu babu wanda Baba ya yiwa ba daidai ba kamar Hajjo. Ta ba shi lbryn Hajjo tsaf,ba ta boye ma sa komai ba,gaba daya jikewa yayi da zufa,idanun sa sun yi jajur kwalla fal ciki,wani irin abu ya ke ji game da Hajjo,tausayi ga kuma abun da ya ke ji na game da ita da shi kan sa ya kasa ganewa. Shiru ya yi,ya ka sa magana dan ya rasa me zai ce yanda ya ke jin kan sa. Baba ne ya fara tari mai karfi,fitowar Hajjo da gudu da kuma tashin Indo da sauri lokaci guda ne,su ka yi kan sa,Hajjo ta tallafo kan sa hannun ta ruke da hannun sa mai konuwa,ita kuma Indo hannu bisa kirjin sa ta ke dan masa luf luf. Sha’awa su ka bawa Khalid,yanda su ka damu da mahaifin na su da yanda su ke ma sa sai dai diyoyin mata,ga mazan na shi can majalisa suna hirar su,wai suna jira Sani ya zo su tafi. Duk kiyayyar ta shi na diya mace gashi diyoyin na sa mata ne ke ji da shi,su ke ta hidama da shi,gaba daya soyayyar diya mace ta shiga zuciyar Khalid,gaskiya duk wanda be haihu ba abin tausayi ne,haka kuma duk wanda ya haihu din amma be sami diya mace ba toh be gama morewa. Idanun sa bisa Hajjo,sun samu tarin na Baba ya lafa,ta dauko ruwa ta na bashi da cokali saboda yanda bakin yayi. Hasken farin wata da na fitilar tsakar gidan ya haske fuskar ta,sai ta kara kyau da annuri,ji ya ke kamar ya tashi ya je yayi hugn din ta,kamar ya ruke ta gam ta shige har tsokar sa,kamar ya yi kissing din ta fiye da wanda yayi rannan…kamar kamar kamar…God i love dis woman! Abunda ya fada cikin ransa kenan ba tare da ya san ya fada ba a lokaci guda kuma ya ankare,ya fara tunanin so yace? Yes so ne,ya na san Hajara,ya kuma dade da fara san ta,soyayya da sabon da yayi da Hauwa ya sa ya kasa ganewa! Shi kadai ya ke murmushi idanun sa kan Hajjo,ta kwantar da Baba za ta koma ciki Indo ta ce kin ko gaisa da mijin ki? Wani irin kallo a marairaice na nuna rashin jin dadin maganar Indon ta yi ma ta. Shi kuwa Khalid cewa ya yi bar ta ta huta Yaya ta,ma gaisa anjima. Da amsar ta sa ta yi shigewar ta ta ciki. Sani ya dawo aka shirya tsaf aka sa Baba cikin motar Sani,Mudi ya zauna da shi a baya kan Baba bisa cinyar sa,Hajjo ta yi saurin shiga gaba. Khalid ya ce ta sauko a tashi za su tafi,ta ce wlh ba za ta shiga ta sa ba,aka yi aka yi ta fito ta bawa Indo wuri ta ki,da dai suka ga su ka biye ta Hajjo bata ma su lokaci za ta yi,sai aka hakura,Indon ta shiga bayan motar Khalid,Ayuba a gaba,Khalid sai kwafa ya ke bini bini. Su ka dau hanyar kano. Sai wajan goman dare su ka isa kano. Asibitin nasarawa su ka kai Baba da ke AKTH suna yajin aikin,ita ko Hajjo haka daidai ya ma ta,ga ta ga Baba ta fi kula da shi. Aka ba su daki V.I.P.,da ke baban Doc Hajara ne har riga rigan duba shi da kula da shi doctors din su ke,hakan ya burge Indo,cewa ta ke hmmmm ilimi dadi,kai ilimi yayi. Su kuwa Mudi da Ayuba sai kallo,wai Hajjo ce ke da matsayi haka har mutane ke dawainiya da Baba dan darajar ta? Shi ko gogan na Hajjo wato Khalid cikin takama ya ke jin kan sa,yes shine fa mijin Doc Hajarar nan,gwara kowa ya sani,kamar cingum ya like ma ta,ko ina ta yi biye da ita ya ke. . DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [12 [16/10 21:48] .: 13pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣2⃣ Kan kace mai har an duba Baba an daura shi kan medication. Sai fa rigimar kwana ta tashi tsakanin Indo da Hajjo,Indo ta ce Hajjo ta bi mijin ta ta tafi gida ita za ta kwana da Baba,Hajjo ta ce ba inda za ta sai dai Indo ta tafi,Mudi da Sani su ka sa baki,a dole su ka ce Hajjo ta tafi ta bar Indo tinda ita ce babba. Shi dai Khalid ya na gefe be tanka ba,amma har ga Allah ba zai so Hajjon ta kwana ba,zai fi so ya tafi da matar sa. Shi kuwa Ayuba cewa yayi toh kai Mudi kai za ka kwana ko? Dan ni ina da abun yi. Mudi ya ce sai na kwana din. Hajjo ta yiwa Indo da Mudi sallama rai bace baki zunbure Khalid ya tisa ta su ka tafi. Sai da su ka dau hanya ya ruko hannun ta,Hajjo ta yi saurin kokarin fizgewa,ya ruke gam,ya ce am sorry,am realy sorry Suger! Ta ma sa banza,ta ma ki kallan sa. Da ya ga haka sai ya yi shiru. Sai da su ka isa gida,bayan yayi parkin za ta fita ya ce diya mace kenan,duk abunda Baba ya mi ki,ki ka iya cire komai a ran ki,ki ka manta, ji yanda ki ka damu da shi Hajara,diya mace daban ta ke,Allah ya kara azurta ni da wata bayan Neena. Sai da ta bude motar ta sa kafar ta daya waje ta,sai ta juyo ta kalle shi ta ce na iya cire wanda ka min daga rai na,na manta bare na mahaifina da na ke tsatson shi? Shiru yayi har ta fice bai sake tankawa ba dan ta rufe bakin sa. Ta na shiga babban falo ta ga Hauwa na zaune,ta kafa ta tsare,sai cika ta ke ta na batsewa,yau girkin ta Khalid ya fice tare da amaryar sa har shadayan dare ba su dawo ba,ta kira ta kira wayar Khalid din be daga ba,ba ta san cikin aljihu ya aje wayar ba,ga shi a silent ta ke be sani ba. Sallama irin na dan Musulmi kawai Hajjo ta ma ta,ta shige na ta bangaran. Khalid na shigowa ta tare shi da masifa,inda ta ke shiga ba nan take fita ba,maimakon ya ba ta amsa,gudun kar rai ya baci kawai sai shi ma ya haye na shi bangaran,haka kusan sa Hauwa hauka yayi,gani ta ke Hajjo ta gama asirce Khalid,ya mutumin da ya gama lallaba ta dazu dazun nan,zai kuma shigo yanzu ya ma ta haka? Ba shakka akwai sa hannun malami! Sai kuwa ta shige na ta bangaran ita ma ta na rusa kuka. Washagari da duku duku gari ko haske be gama yi ba Hajjo ta shirya,ta fito za ta asibiti. Da ke Khalid ya san halin matar ta sa da wutar ciki tin da ya dawo daga sallar asuba ya zauna a babban falo ya na jiran tsammani. Ganin ta fito sai ya tashi,ya na Suger an fito? Ta kalle shi cikin girmamawa amma ba sakin fuska ta ce ina kwana? Ya ce lfy lau Suger,wuce mu tafi ko? Hauwa za ta yi brkfast zuwa anjima sai na kawo mu ku. Ita dai ba ta tambaye shi ba dan haka shiru ta ma sa,shi kuwa ko a jikin sa,shi mai laifi ne burin sa ya shawo kan Suger ya farantawa Suger ko ta huce. Sai da ya duba Baba sannan ya juya zai koma,ganin Hajjo ba ta da niyyar raka shi,ya ce Suger dan taka min mana. Gudun surutu da mitar Indo sai kuwa ta biyo sa din,su na fita ta ce ni fa yau ina da call,so kar ka yi expectn zan kwana a gida. Yayi jim ya ce toh yanzu ki na nufin tin 8 idan ki ka fara aiki ba za ki dawo gida ba ko kin ta shi? Ta ce ai kasan 4 na ke tashi,so daga 4 zan fara call din,sai kuma 8 na safe zan gama shi. Ya ce sannan ki dawo gida? Ta daga kafada ta sauke tare da fadin ya danganta. Kai ya gyada kawai tare da fadin Allah ya kyauta,sai na dawo. Ta ce a dawo lfy. Ya na tafe ya na tunanin Hajjo,shi fa a aikin Hajjo babu abunda ya tsana kamar wannan cal din na ta,dadin ta ma a wata be fi ta yi sau biyu ba,amma dai ya na tsaya ma sa a rai. Ko da gari ya waye sosai,wajan 10 sai gashi da Hauwa sun zo asibitin,wato sun aje Neena a makaranta. Ba su sami Hajjo ba ta tafi ta fara aiki,sai ya bar Hauwa wajan Indo,ya tafi office din Hajjo. Ga patience zauna akan layin ganin ta,ganin Khalid ba wanda bai bi shi da kallo ba,gaskiya ya hadu kwarai.kai tsaye ya kutsa,ya shige office din. Ta na duba wata tsohuwa Allah ma ya so ta gama da ita sai gashi tsakar office din. Ganin shi sai da gaban Hajjo ya fadi,dan duba tsohuwa ta ke amma ya na ranta,missing din shi ta ke sosai. Idanun sa kan Hajjo da ta wani basar kamar ba ta gan shi ba ya gaishe da tsohuwar tare da fadin Baba mata ta ta duba ki da kyau ko? Tsohuwa ta ce eh,ai akwai aiki,kai ne mijin ta? Cikin jin dadi an yabi Hajjo ya ce eh,tsohuwa ta ce kai amma ka yi sa’ar mata,Allah ya sa mu ku albarka. Ya na dariya ya ce ameen,amma dai Baba ai ita ta yi sa’a,dubanni fa kyakkyawa da ni? Tsohuwa ta ce eh wlh ga kyau ga ado,eh ta wannan dai ta yi sa’a,ya kashewa Hajjo ido,Hajjo ta yi rolling idanun ta,irin kai ka sani,ta ce iya za ki iya tafiya,sai a je a siyi magani Tsohuwa ta ce toh madallah. Ta tashi,tare da yiwa Khalid sallama ta fice. Tana fita ya zaga gaban Hajjo ya yi kissin kumatun ta tare da fadin u see Suger,har tsofaffi yabawa su ke da Khalid,you should b glad am urs….ta na ji wata za ta shigo tsohuwar na fadin ku dan dakata ya fito,mijin ta ne. Ajiyar zuciya Hajjo ta yi gami da fadin dan Allah Khalid ka tafi am too busy wlh,marasa lfy ke jira na fa. Ya ce ni ma mara lafiya ne,wani abu ya fito min a baki,da sauri Hajjo ta tashi ta na menene? Mu gani?daga zaune ya dan daga kai ya bude baki kamar mai nuna ma ta abu din. Hajjo ta dan matsa kusa da shi kamar ta na tsoran matsawa kusa sosai,ta ce ka ma kasa tsayawa na gani,ya ce matso kusa sosai za ki gani,ta na matsowa yayi saurin janyo ta,cikin zafin nama ya fara kissing din ta,ta na kokarin kwacewa ta kasa,dan kan sa ya sake ta,ta yi baya za ta fadi ya yi saurin ruko ta….. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 6:14 PM] Salmah Ateeku: [12:20pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣3⃣ Ta fizge hannun ta tana mayar da numfashi,ta ce nan office dina ne,ba gidan ka ba ne,ba dakin ka ba ne,pls kar ka jawo min mutane su shigo su raina ni mana!dan Allah tashi ka tafi. Ya daga kafada ya sauke tare da fadin ke fa mata ta ce,na fi bukatar ki fiye da kowa. Hajjo ta ce plss ka fita. Ya tashi ya na murmushi ya ce akwai abunci wajan Indo,ki daure idan kin sami dama ki ci. Tare na ke da Hauwa,ta na mi ki ya mai jiki. Ya juya ya fice. Sai da ta dau kusan minti goma zaune sannan nutsuwa ta dawo ma ta,ta cigaba da duba jama’a. Lokaci lokaci ta na zuwa ta na duba Baba,ranar har Hajiya sai da ta zo duba Baba,su Jabir,Nabila ne,Ayush hatta su Doc Hussaina sai da su ka shigo wajan sa,masinjoji da nurses ma ba a bar su a baya ba,kowa na zuwa duba baban Doc Hajara,sai dai ba a ji ba. Hajiya ce ta kai mu su abuncin rana,da za su tafi Nabeela ta ce ita za ta kawo na dare. Jikin Baba kuma ba laifi jikin na sa da sauki,ya na gane jama’a,ya ga yanda jama’a ke tururuwan zuwa duba shi,duk dan darajar diyar sa mace,diyar sa mace ce yau ta zama abun alfahiri ga jama’a,ta zama kamar tauraruwa kuma ya ke cin darajar ta,diyar da be san darajar ta ba,diyar sa Hajjo,ina ma matar sa Ameenutu na raye ta ga baiwa da daraja da yayiwa diyar su mace. Kai kawo na Khalid kuwa ba adadi,bini bini sai Hajjo ta ga ya zo ya duba su,har sai da ta ce ya huta haka da ta raka shi har mota bayan magrib. Ya ce toh gobe da sassafe zai dawo,ta ce Allah ya nuna mana. Su ka yi sallama suna missing juna gaba dayan su. Washagari da asuba bangaran Baba da ya shanye ya fara motsi,Hajjo ta tadda Mudi ya dan jinginar da shi ya sallaci asuba. Kujera ta ja gaban sa,ganin ta farin ciki ya bayyana fuskar Baba,ya ce Hajjo,Allah ya mi ku albarka ke da yar uwar ki,Allah ya sa diyar ki ta mi ki yanda ki ka min,Hajjo kin cika diya,da na san haka dadin diya mace ya ke da ban kyamace ku ba,da na yi addua’a Allah ya bani diya mace ba adadi,ki yafe min diya ta,na zalince ki yafe min diya ta. Hajjo na murmushi,idanun ta cike da kwalla ta ce ba komai Baba,ni ya kamata na nemi yafiyar ka,na kaurace ma tsawan shekaru,dan Allah Baba ka yafe ni. Ya na murmushi ya ce haba ai tsakani na da ku sai albarka,diyoyi na kun min komai,hakan zan yi kashi na yi fitsari a sitira yar uwar ki Indo ta sa hannu ta wanke,da kuwa matan yayyan ku sai dai su kyamace ni,su ka ma hana yaran su jikokin na zuwa waje na,na fada ma mazajen su sai suce na fiya korafi…..sai ya fashe da kuka,kunya ta kama Mudi,Indo da Hajjo su ka shiga rarrashin Baba,har su ka samu yayi shiru. Haka suna dan hira sama sama,Hajjo ta ce bara ta karasa aikin ta ta zo,ta tafi ta na murna Baba sauki ya samu. Wajan 7 ta koma wajan Baba,ya na ganin ta ya ce Hajjo kishi na ke ji,taimake ni da ruwa,ta dauko ruwan ta dan bashi ya sha,ya koma ya kwanta,Indo na murmushi ta ce din dazu yace ya na jin kishi fa,da na dauko zan bashi sai ya ce shi sai Hajjo ta zo. Hajjo ta ce Allah sarki ina ruwan Baba. Hannu ya daga kamar mai magana,Hajjo ta matsa kusa da shi sosai,sai cewa yayi Hajjo numfashi na neman ya gagare ni,numfashi na daukewa ya ke…ai kuwa sai ya fara gasping,gaba daya su ka rude,Indo ta ce Mudi kira likita kar mu rasa Baba,ta ma manta Hajjo likitan ce. Ita kuwa Hajjo jikin ta ne ya dau rawa,ta na san halin da Baba ya ke ciki,ba kan shi ta fara gani ba,ta sha gani marasa lfy na yi,ta kuma san karshen,dan haka sai ta juya ta fice da sauri sauri gudu gudu,a kofar da zai sada ta da waje ta yi karo da mutum har ta fadar ma sa da flask din hannun sa. Ya ruko ta,daga idan da za ta yi ashe Khalid ne,ya na menene Hajara? Me ya faru? Baba,Baba kawai ke fita daga bakin ta,ganin Mudi ya wuce su a guje,ga doctora har su hudu biye da shi sai sassarfa su ke dan karasawa ceton ran Baban Doc Hajara,Khalid ya gane me ke faruwa,ya janyo Hajjo jikin sa yayi hugn dinta ya na shafa bayan ta ya na fadin is owk,it is owk Hajara,yi masa addua!!!! DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [16/10 21:52] .: 2:33pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣4⃣ A kumurya aka yi zaman makokin Baba,can Hajjo ta tare. Ta ga jama’a an mata kara,ba wanda be je mata gaisuwa ba,hatta Hauwa sai da ta kai mahaifiyar ta da yan uwan ta,bare su Nabeela da Ayush. Ayush ke fada ma Hajjo Suraj na ma ta gaisuwa,ta ce a ma sa godiya,Allah ya bada lada. Amma fa duk abunda ake Hajjo ta ki tayi kuka kamar dai rasuwar Inna,abun na matukar bawa Indo da Khalid tsoro dan sun na zuci ta ke. Sai da aka yi bakwai Hajjo ta koma gidan ta. Da daddare zaune bisa gadon ta,ta hada kai da gwiwa,gaba daya ji take duniyar ma ta ishe ta. Khalid ya shigo ya zauna kusa da ita,ya ce Suger ya dai? Ta ce ba komai. Ya ce toh ki daure ki cire damuwa daga ranki,duk kan mai rai mamaci ne,mu ma ta mu ke jira. Har ran sa so ya ke ya kwana tare da ita dan ya debe ma ta kyewa dan ya san tin rasuwar Baba cikin mutane ta ke kwana,toh amma ba dama saboda he is man of his words,ya ce ba zai kwana dakin ta ba sai idan ita ta gayyace shi da kanta. Ya tashi tare da fadin bari na bar ki ki kwanta Suger,sai da safe. Ta ce toh. Sai da ya kai kofa ya ji ta kira sunan shi,ya juyo tare da fadin yes Suger? Ta yi kasa da ido ta ce dan Allah ka kwanta….ina nufin ka kwana dakin nan in ba damuwa…..ya san ba karamin abu zai sa Hajjo fadin haka ba,ya murmusa ya dawo ya zauna kusa da ita,ya ce ba dumuwa infact i wil love to. Ta ce amma fa a kasa za ka kwanta. Ta shi yayi ya na dariya,ya dau filo ya jefe kan carpet sannan ya ce duk da dai ban taba kwanan kasa ba,for you i wil nt mind. Ya kwanta sannan ya ce ki kwanta. Juyawa ta yi ta kwanta,gami da kashe wuta,amma sai bacci ya gagare ta,tai tajuyi,gaba daya wani irin tsoro ne ya addabe ta,burin ta taji mutum kusa da ita. Ko da ta tashi ta zauna tare da kunna wuta,ta ga Khalid be motsaba,ta tabbatar yayi bacci. Sai ta tashi a hankali,ta sauku kasa kan carpet inda ya ke kwance,itama ta kwanta bayan sa,ta juya ma sa baya kamar yanda shi ma ya juya ma ta,bayan ta jikin na sa,ta dai ji mutsin mutum kusa da ita,sai ta saki ajiyar zuciya,ta yi filo da tafikan hannun ta. Ko minta biyar ba ta yi da kwanciya ba ya jiyo ya sanya hannun sa ya zagayo ta jikin ta,har sai da ta firgita,ya ce shhhhh it is owk,babu abunda zan mi ki Hajara,jts relax owk? Ya janyo ta jikin sa,hannun sa zagaye da ita yayi hugn din ta,a sannnu a hankali Hajjo ta saki jikin ta. Sai kuma ta fashe da kuka. Kuka ta ke amma shi Khalid dadi ya ji,dan abunda su ke ta so ta yi kenan ta ki yi,tunda ta yi yanzu za su sami lfy kenan. Ya ta rarrashin ta kamar yar baby,har ta yi mai isar ta ta yi shiru. Khalid ya ce Hajara,ta ce ummm ya ce kiyi hakuri, ya ji ta yi shiru,ya cigaba da fadin pls ki yi hakuri kawai ki na ma Baba addua’a,owk? Ya ji shiru,yayi kissing wuyan ta,ta dan motsa kadan. Ya ce Hajara ina san ki! I love you soo much it is eating my hrt up. Ban san ya aka yi na fara san ki ba,ban kuma sanda na fara san ki ba,amma na san soyayyar ki na neman halaka ni Hajara,kin sauya min tunani kan abubuwa da dama,kin bude min ido,to see d world from every angle,u ar my bst half! Ya ce kin san me? Ya ji shiru,ya dan daga ya kalli fuskarta,sai ya ga ashe fa da iska ya ke magana,Hajjo kam tuni bacci ya kwashe ta,ya kara jin dadi ta sami bacci dan Indo ta ce ma sa ba ta bacci. Ya dada hugn dinta,ya karanto addua’ar bacci ya shafa ma ta da kan sa,sannan shima ya rufe na shi idon. Washagari tashi ta yi ta ganta in da su ka kwanta,Khalid ya tafi masallaci. Cikin azama ta yi sallah ta yi wanka,ta na kitchen ya dawo,amma ba su hadu hadu ba sai wajan brkfast. Shi ya sauke ta aiki,ranar ta koma aiki,nan ma sai gaisuwa ake ma ta. Da ta dawo duk da dai girkin ta ne sai ta tadda Hauwa ta shiga kitchen din ta ma ta,ta ji dadi sosai dan dama ta na ta tunanin girkin. Ta ma ta godiya,Hauwa ta ce ba komai ita da tawo jiya jiya,ga shi ba ta gama jin zafin rashi ba,ai amfanin zaman taren kenan. Can bayan isha’i ta yi wanka ta na shirin kwanciya sai ga Khalid. Ganin ta yi shirin bacci tsaf,ga ta ta yi kyau kamar ya dauka ya boye sai gaba daya ya fara rikicewa. Ya ce Suger tashi mu yi sallah. Ta na daga kwance cikin bargon da tinda ya shigo ba shiri ta kudunduna ciki ta ce wlh na yi sallah,ya ce nafila za mu yi,ta ce ai har shafa’i da wutiri ma na yi. Ya sosa kyeya,ya ce wannan daban ne za mu yi,pls tashi mana. Tana mita da zunbure zunburen baki ta tashi ta dauro alwala. Bisa dadduma ta tadda shi ya na jiranta. Ta daura zani ta hijab,Khalid ya ja su sallah raka biyu. Bayan sun idar,ya dafa kan Hajjo ya karanta adduar neman yarda da albarkar ubangiji. Tin daga sannan Hajjo ta gano inda ya nufa,tuni ta tsorata,ta fara neman hanyar zillewa. Ta yi saurin hayewa gadan ta ko Hijab din ba ta iya cirewa,shi ma din ya san abunda ta ke nufi,da ga zaune inda su ka yi sallah ya ce Suger yau a gado za mu yi bacci? Hajjo murya a kasa ta ce ah ah tafiya za ka yi,yau dakin ka za ka kwana….ya na dariya ya ce ai kuwa ba ki isa ba yarinya,ya tashi da nufin hawa gadon Hajjo ta tashi da sauri za ta sauko ta gudu,ai kuwa sai ya bi ta yayi caraf ya kamota,ta na magiya ya na dariya su ka dawo bisa gado. Kokarin da ta ke na kwacewa ya sa shi danne ta ya dan sakar ma ta nauyi,kwakkwaran motsi ma ya gagareta,sai ta sa kuka. Da ya ga haka ya dan daga ta,ya ce shhhh am nt going to hurt you,I love you,I jst love you my wife…fuska cike da hawaye ta tsaya ta na kallan sa,maganar ta sa tai ma ta bazata,ganin yanda ta ke kallan na sa ya sa shi gyada kai tare da fadin yes i mean it,ina matukar san ki Hajara,ba zan cuce ki ba,bazan zalince ki ba,I jst want to hold nd love you… DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 6:14 PM] Salmah Ateeku: [12:47pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣5⃣ Jin kalaman sa,yanda ya ke fada da yanda ya ke shigar ta ya sa hankalin ta ya kwanta,har ya iya cire ma ta hijabin ba ta lura ba,haka ma zani,ya rage sai kayan baccin ta,sannan ya ja ta jikin sa,ya cigaba da fada ma ta dadan kalame ma su kwantar da hankali har ya samu ta gama sakin jiki dashi,cikin dabara ya fara kissing din ta,ita kuwa Hajjo da ta ga ya sake salo sai ta koma shirin kwacewa,gaba daya tsoran abunda ya ke so take,ba ta ji dadin rayuwar ta na da ba gani take kamar maimaitawa za a yi duk da kuwa salon Garbati da na Khalid akwai bambamci,kamar duhu da haske ne. Shi kuwa Khalid ba ya ji ya ba ya gani,yayi lallami yayi lallami amma Hajjo ta ki amince ma sa,sai kawai ya bi san ransa amma ta lallami da lumana,cike da so da kulawa,a daren Hajjo ta tabbata matar Khalid. Manne da shi ta yi bacci,ba ita tashi ba sai da asuba,dan ta ma so ta makara. Ta duba gefanta ba Khalid,sai kuma abunda ya faru jiya ya dawo ma ta,yanda yay ta lallaba ta sannu a hankali,ba shakka shi dai kam Garbati ya tabbata bagidaje,ashe dai ita ba aure ta yi ba. Bayan ta yi wanka,ta idar da sallah sai ga Khalid ya dawo,ta yi saurin kasa da idon ta dan bala’in kunyar sa take ji. Ganin haka sai ma ya dauko ta cak ya aje bisa gado,ta ce ni fa ban komawa bacci,ya ce ni ina komawa,ai yau asabar ba aiki,pls ko ba za ki yi ba ki kwanta,ina son ki a kusa,I jst want to hold you,kan Hajjo ta tanka tuni ya janyo ta jikin sa,ya cire hijab din ta ya aje gefe. Kamar yanda ya ce din,he jst kissed nd hold her,kan kace me tuni bacci ya sake sace su. Sai wajen 8 Hajjo ta tashi,a hankali dan kar ta tada shi ta zame jikin ta. Ta shige toilet ta yiwo wanka,sauri sauri amma kuma a hankali ta shirya cikin kananan kaya rigar ruwan hoda da wando da ya bi jikin ta amma ba sosai ba shi kuma blue. Ta sanya wata yar hular ta,kafar ta sanye da takalmin ta flat ruwan hoda ta fito ta shiga kitchen. Nan ta tsaya tunanin abun dafawa dan ta makara,ba ta so ta bar Neena da yunwa. Dankali ta dauko Irish ta na barewa,kusan minti goma sha biyar kan aikin tana yi tana tunanin rayuwar da ta shiga jiya,saban rayuwa mai dadi,ta na yankawa ta ji anyi hugn din ta ta baya,har sai da ta dan tsorata. Fuskarshi ya kwantar bisa kafadar ta ya ce ni ne Suuuger,duk duniya ma wa ya isa ya tabaki in ba Khalid ba,yayi kissing wuyan ta,I love you suger…murmushi kawai ta yi,tare da fadin aiki na ke,pls ka kyale ni. Ya ba za ki ce you love me to ba? Thou na san you do. Murmushi Hajjo ta yi,dax Khalid for her. Ta ce toh tin da ka sani ba sai na fada ba,dan Allah ka sake ni kar fa Neena ko mamanta su shigo mu ji kunya…ya ce ba zan sake ki ba sai kin ce you love me too. Hajjo ta ce i love you tooo..kamar daga sama su ka ji muryar Hauwa na fadin amma dai kun san ba ku kadai ba ne? Akwai yarinya a gidan A rikece cikin jin kunya Hajjo ta cire jikan ta da ga jikin Khalid,shi kuwa Khalid ko a jikin sa ya juyo ya na kallan Hauwa da idanun ta tuni su ka kada,kishi kararara ya bayyana a idanun ta,ya ce ina manners din ki su ke Hauwa?ba kya iya sallama or atlest ki juya mana kawai ki tafi abun ki! Hauwa ta ce no kai zan tambaya ina manners din ka ya ke? Na zaci nan kitchen ne ba dakin ku ba da zan fara labewa ina sallama,dan kitchen is meant for everyone,har da diyar ku Neeena da ta zo neman brkfast ta gan ku yanda na ganku,ta zo ta fada min,am sure itama ba ta saba ganin haka cikin kitchen ba may b dax y ba ta mu ku sallamar ba,ta zo ta fita ba ku sani ba,musammam ma ni da kai ta tashi ta saba gani,d presence of a co-wife,b it her mother or watever is still unsual to her,be kamata ba,pls ake yin sara ana duban bakin gatari…ta juya ta fice,kunya da takaicin ya rufe Hajjo jin Neena ce ma ashe ta kai maganar..a fusace Khalid ya bi yanta,ba ta kai ga kaiwa falo ba ya janyo ta tare da fadin hw dare you za ki kunya ta ‘yar mutane haka,God Hauwa she is her daughter for crying out loud!ke zai mi ki dadi aka mi ki haka? Toh menene dan na yi hugn din ta? Ba mata ta bace!! Hawaye na zuba daga idanun ta,ba ta taba tunanin rana irin ta yau za ta tsirga cikin tarihin rayuwar ta ba,ta ga Khalid din ta da idanun ta jikin wata,kuma da bakin sa ya na tuna ma ta Neena ba diyar ta bace,gashi ya na jaddada mata cewa uwar Neenan is his wife. Ta ce yes ba diya ta bace,kuma matar ta ka ce Khalid dan Allah ka kyale ni na wuce. Sakin ta yayi,ta shige ciki da gudu,har zai bita sai kuma ya dakata ya buga hannun a iska tare da fadin ya salam! Hauwa za ta iya zarar da ni! Ita ko Hajjo kasa cigabawa ta yi da girkin gaba daya,sai da Khalid ya dawo ya ce da ita kar ta damu ya yi magana da Neena,so ba wai wani abu bane. Duk da haka da kyar ta gama brkfast din,amma ranar ba dadi zaman cin abunci,kowa yayi shiri,Khalid ne ya saki jikin sa ya na ta musu hira. Ita Hajjo kunyar Hauwa da diyar ta ce damuwan ta,ta san Hauwa dole ta san yanzu ita da Khalid ar intimate. Ita kuma Hauwa kishi ne damuwan ta,gaba daya ta tsani Hajjo,haka kuma ta fara jin dacin Neena cikin ranta. Ita ko Neena ta manta da komai,brkfst din ta kawai ta ke ci ta gama ta hau kan game,fargaban ta daya Hajjo za ta iya hana ta,ta ce sai dai ta taya ta aiki a kitchen,dax y sam ba ta san zaman Hajjo a gida,takura ne da ita,tai ta sa ta aiki. Soyayya tsakanin Hajjo da Khalid tai karfi,idan ba ya dakin ta Allah Allah ta ke ya dawo,idan kuma ya dawo ba ta san kwanakin ya kare. Haka shi ma Khalid,ya na jin ta har ransa ko dan kwanciyar hankalin da ya ke samu wajan ta,gaba daya Hauwa ta fara sauya hali,wanda haka ya ke taba daga Khalid din har Neena,hakan kuma ya sa ya ke kwalafacin Hajjo. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [1 [16/10 22:01] .: 12:54pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣6⃣ Mota Khalid ya siyowa Hajjo,ya kuma ware lokacin da ya ke koya mata,nan da nan ta iya da ke Hajjo komai idan za ta koya da gaske ta ke tsayawa ta koya.San da Hajjo ta cika wata hudu sai ga ta da tsintuwa,ta fara laulayi sosai. Ko da Khalid ya lura da hakan,ya kuma tabbatar da burin sa ne ya ciki tuni duniyar sa ta zama sabuwa,Hajiyar sa ya fara fadawa sannan su Jabir da Nabeela. Har gida su ka zo taya sa murna duk da dai suna taka tsantsan saboda Hauwa,shi ya sa ma Nabeela ba ta yawan zuwa wajan Hajjo sai dai Hajjon ta je. Tin da Hauwa ta san da cikin Hajjo gaba daya ta susuce,duniya ta mata zafi,duk da sam Hajjo na gudun duk abunda za ta yi wanda ta san zai motsa zuciyar Hauwa. Zama inda Hauwa ta ke ma dainawa ta yi saboda ta na yawan laulayi ba dadi kar Hauwa ta ga kamar da gangan ta ke,gashi ba ta iya girki,ba ta kuma ta san warin gas ko zaman dining area gagarar ta ya ke,sai dai ta yi zaman ta bangaran ta abun ta. Da fari Hauwa na jurar yi ma ta girki,daga bisani ta dai na,haka kawai ta na yiwa mace girki,ita kuma ta na kwana da miji! Nan ko nima na taya Hauwa kokawa,ba zai sabu ba bindiga a ruwa,ba za a maisheta yar aiki ba. Dan haka ranar girkin Hajjo sai dai a samo abunci gidan Hajiya da ke Hajiyar ba suruka ta ke da Hajjo ba,diya ta ke da ita,ran da ba aiki gidan Hajiyar ta ke zuwa ta wuni,musammam idan ranar girkin ta ne. Khalid na kaffa kaffa da Hajjo,ta sha kwararo ma sa amai a jiki,sai dai ya wanke,hakan kuma be hana shi sake kwantar da ita jikin sa ba,Hajjo dai ta zama yar gata. Wasa wasa,kuma kwanci tashi,da dadi ba dadi cikin Hajjo ya kai wata tara,yayi girma sosai wane na Neena,gashi ta kumbura kamar wacce aka hura,ya sake ma ta kamanni gaba daya,dama ba tsayi gare ta ba sosai sai ta zama kamar za ta kife idan tana tafiya saboda cikin rinjayar ta yake,Khalid yay ta tsokanar ta wai ta yi muni kamar a yanka a boye wukar. Hauwa kuwa tuni ta bata rawan ta da tsalla,gaba daya Khalid be jin dadin zama da ita,ta dau kishi da bakin ciki ta ji zugan ma su ziga hatta diyar ta ta Neena ta watsar,sam ta dai na nuna ma ta kulawa irin na uwa,hakan na damun yarinyar da Khalid da ma ita kan ta Hajjo,duk da haka Hajjo ba ta janye Neenan ba,ta barta tana addua Allah ya sa Hauwa ta farga ta san abunda ta ke,haka kuma ba ta ga laifin Hauwa ba,after ol ko wace diya mace ta shiga halin da Hauwa ke ciki sai abunda Allah ya yi. Sau dayawa sai ta ki zuwa dauko Neena,mussammam idan Khalid na Abuja,sai dai principal din su Neena ta kira shi ta ce ba a zo daukan ta ba,idan ya kira Hauwa sai ta ce ba ta jin dadi,sai ya kira Hajjo,ta bar aikin da ta ke ta dauko ta,sannan ta koma bakin aikin na ta. Hajjo na sane ta ki daukan hutu,tafi so sai daf da za ta haihu saboda ta samu ta na motsa jikin na ta sosai. Ranar da ta ke san zuwa aiki na karshe kafin ta fara hutun haihuwar na ta ranar Khalid shi ma ke shiring tafiya Abuja saboda wani meeting da za su yi. Tare su ka shirya da sassafe,ya sanya suit baki,yayi kyau sosai kamar dai bakin baturen na Hajjo,ita kan ta Hajjo ta na alfahari duk sanda ta tuna mijin ta ne. Team din su Hajjo na da wani discussion mai matukar muhimmanci,dan haka a gurguje ta shirya,by 8 za su fara. Tare su ka fito,su ka tadda Neena zaune a babban falo,Ta gaishe su,Khalid ya ce ya dai? Ina maman ta ki ba ta kai ki makaranta ba har yanzu? Za ki makara ai,ko ma na ce kin makara. Neena ta ce Momma ba ta tashi ba. Ba ta tashi ba?ba ki karya ba ma kenan!,aje briefcase din da ya ruko,kai tsaye bangaran Hauwa ya shiga,a daki zaune kan gadon ta ya tadda ta. Ta ce da shi barka da asuba. Da ga bakin kofa Ya ce yauwa Baby-luv,diyar ki fa ta dade da shiryawa,ke ta ke jira. Ta ce wata diyar tawa kenan?tambayar tata ta bashi mamaki,ya ji kamar an tsaya a baya san,da ya dan waigo sai ga Neena,ashe biyo shi ta yi. Wata diyar ta wa? Kamin shiru? Dawo da kallan sa yayi gare ta,sannan ya ce kina da wata diyar ne da ya wuce Neena? Juya ma sa baya ta yi ta fara ninke mayafi,ita sam ba ta lura tare ya ke da Neenan ba,ta ce no ban da wata diya,ko Neenan ma ba diya ta bace,ga uwar ta can Hajjo ta kai ta,ko na haife ta da zan na dawainiya da ita……? Ta juyo,sai a sannan ta yi ido biyu da Neena da ta karasa shigowa ta tsaya kusa da Khalid,idanun ta cike da hawaye. Baki bude cike da dana sani ta ce Khalid ba ka fada min ba…ban san tare ku ke ba…idanun sa jajur,ya murmusa ya ce no ba sai na fada mi ki ba,abunda ki ka yi kan ki kikayiwa Hauwa. Juyawa yayi ya fice a fusace. Hajjo da ke zaune falo sai ganin shi ta yi ya fito cikin bacin ran da ba ta taba ganin sa ciki ba,ko kallan in da ta ke be yi ba ya nufi bangaran sa. Tashi ta yi da kyar da niyar bin sa,sai ta jiyo muryar Hauwa na kira Neena! Neena! Ga mamakin ta sai ga Neenan ta fito a guje ta na kuka,za ta shige Hajjo,Hajjo ta janyo ta baya,hakan yayi daidai da fitowar Hauwa,ta yi turus ta tsaya,ita ma hawaye ne fal fuskar ta. Cike da bacin rai Hajjo ta tsawatarwa Neena,ta ce ina za ki? Ba ki jin Mahaifiyar ki na kiran ki!! Jikin Hauwa ya dada sanyi. Neena na kuka ta ce ki yi hakuri,amma ba mahaifiya ta ba ce,ke da ban dauka a matsayin uwa ba sai gashi ke ce uwa ta,ta fada ita ta fada da bakin ta…..a gajiye Hajjo ta saki Neena,maganar Neena ta gajiyar da ita kwarai. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 6:15 PM] Salmah Ateeku: [1:14pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣7⃣ Da gudu Neena ta shige bangaran Hajjo. Hajjo ta juya za ta bi ta,sai kuma ta tsaya,ta ma rasa ya za ta yi,Khalid za ta bi ko Neena? Gashi sai dada makara ta ke,ta juyo ta ce da Hauwa,Hauwa zan mi ki magana a matsayi na na diya mace,zan baki shawara a matsayin diya mace. Na san halin da ki ke ciki,amma karya ne na ce na san yanda ki ke ji,i undstnd ur situation,amma you pushing dem away,kina pushing mijin da ke son ki matuka,you pushing him to the wall,tura idan ta kai bango ba ta bullewa,you ar letn him go,d more u push him,d more he get close to me,nd am sorry to say dis the more i get to knw him well,d more i get to love him. Yanda ya ke san ki duk da kuntata mi shi da ki ke ya sa na san waye mijin ki,kuma na kara respectn din shi! Haka diyar ki,duk duniya ba wacce ta ke kira Momma,ta ke kira uwa sai ke,ba kuma wai dan ba na nan ba ne,ko ba na san ta,ina nan da rai na,ina kuma san ta,amma saboda compassion irin na diya mace,na runtse ido na,na danne zuciya ta,i let u guys b,ba ma sharing din ta na ke da ke ba,i overly let her b urs,ta na san ki wit oll passion na diya ga mahaifiyar ta,amma me u jst pushed her away. Wake up nd hold urslf,ko wani dan adam da kaddarar rayuwar sa Hauwa,bare kuma kina diya mace,it is part of ur destiny,jst take lyf d way it is,Allah be cutar da bawan sa,sai dai bawa ya cuci kansa…dan takaici Hauwa kasa magana ta yi,har Hajjo ta juya ta nufi bangaran ta,kai tsaye dakin ta ta nufa,jin shi a rufe ya tabbatar ma ta Neena na ciki,tai tai ta bude,amma ta ki,kukan ta kawai ta ke ji,sai kawai ta juyo,ta haye sama bangaran Khalid. Hauwa ma juyawa ta yi ta shige na ta bangaran cike da da na sani. Ya na tsaye hannu cikin aljuhu gaban window,idanun sa na kallan waje,gaba daya hankalin sa be wajan,ya ji an taba shi,ya saki ajiyar zuciya,duk da be juya ba ya san wacece. Ta ce am sorry,ka yi hakuri,undstnd her,try to undstnd,thou ba lalle ka fahimta sosai ba,diya mace ce kawai za ta gane,amma itama ba haka ta ke so ba,ba san ran ta bane,shez tyt,shez emotionally disturbed,Khalid ya ce ban taba canza ma ta ba,Allah shi ne sheda ta. Hajjo ta ce na sani,itama ba a san ranta ta canza ba,she need you! Juyowa yayi ya ruko hannun Hajjo,tare da fadin no i need you,i need you Hajara more dan ever….Hajjo ta girgiza kai,ta ce nd we need ur wife more,we need each other to survive,i need her Khalid,ita ce mahaifiyar diya ta,you need her,am a busy woman,dole za ta zama part of ur children’s lyf,nd she need us,we ar fmly. Khalid ya girgiza kai,ya ce na so Hauwa,ina san Hauwa ta kasa ganewa. Wani irin kishi ne ya tasowa Hajjo,ta yi saurin kauda shi,amma duk da haka Khalid sai da ga gani,ya saurin cewa don’t get me wrong Suger. Dariya Hajjo ta yi,ta ce haba worry nt,na fahimce ka,u ar tryn to make a point,bare kuma idan ba ka so Hauwa ba ai sai Allah ya tambaye ka. Hugn din ta yayi tare da fadin u ar ao diffrnt,ya ba zan so ki ba Hajara? Ta na murmushi ta ce nd i u. Maza ka je wajan diyar ka,ta rufe kanta a daki sai ka fito mu tafi na aje ka kar ka yi missing flight na samu ni ma na wuce hosptal. Hannun ta cikin na sa su ka fito,ya na fadin ya fasa zuwa Abujan yau,zai daga meetn din dan ya kula da Neena,tai tafiyar ta kawai. Hauwa kuwa gida ta tafi,ta na kuka ta fadawa Mahaifiyar ta abunda ya faru. Mahaifiyar ta ta ta ce ai ga irin ta,za ki yi biyu babu,kishiyar ta ki da ki ke tinkaho kin fita komai gashi ta zo ta fiki komai ai yanzu tsabar rashin hakuri,ita ki ka san menene na ta kaddarar rayuwar,kawai ganin ta ki ke amma ki ka san yanda rayuwar ta take? Ke kuma ga uwa ga uba,ga gata ga arziki,ga miji mai san ki so na gaske,ba ki haihu ba amma Allah ya baki soyayyar diyar wata,ki ka yi watsi damar ki. Ta na kuka ta ce yanzu ya zan yi? Ta ce ya za ki yi kuwa,ki je ki nemi yafiyar mijin ki,ku samu ku sasan ta. Da wannan kudirin Ta koma gidan ta. Da dadare Hajjo ta fito da niyar zuwa wajan Khalid,sai ga Hauwa ta ci ado mai kayatarwa,wasu irin kaya ta sa wanda su ka kama ta ma su jan hankalin mai kallo,ta yi kyau kamar yar tsana,itama din wajan Khalid din za ta,ganin Hajjo sai ta tsaya. Ganin yanda ta yi kyau sai da zuciyar Hajjo ta motsa,amma a zahiri murmushi ta yi,ta gyada ma ta kai alamar go ahead,ni bara na koma. Ita ma Hauwa murmushi ta sakar ma ta sannan ta haye bangaran Khalid. Zuciyar ta na bugawa Hajjo ta koma na ta bangaran. Dakin ta ta shiga ta na ambaton sunan Allah dan kishi ne ya tashi,raban shedan da ke zuciyar ta ya motsa. Khalid na zaune ya na Allah Allah ya gama hade papers din gaban sa ya je wajan Suger. Jin an bude kofa yayi zatan ita ce ya ce Suger Allah Allah na ke fa na gama na zo gare ki. Jin an yi shiru be kuma ji kamshin turaren na Hajjo ba sai ma na Hauwa ya sa shi dagowa,Hauwar ce gaban sa,God shez beautiful! Abunda ya fada kenan cikin ransa,ita kuwa karasowa gaban sa ta yi cikin yanga da kissa ganin yanda ya tsaya cak. Ta durkusa gaban sa tare da fadin dan Allah kamin afuwa,na kasance mace mara godiyar Allah,duk soyyayar da ka ke min amma nai ta saba ma ka,ka yafe min Khalid. Ganin be motsa ba,ta dago su ka hada ido,ta ga ya na murmushi,ya ce da gaske kike? Ta ce cross my hrt! Cikin jin dadi ya aje papers,ya ce come here baby-luv. Da sauri ta tashi ta shige jikin sa ta na kuka,ya ce shhhhhh is owk. Hajjo kwance bisa gadon ta,Ta ji an bude kofa,daga idon da za ta yi,ta ga Neena tsaye kofar dakin,ta ce zan iya shigowa? Hajjo ta tashi zaune tare da fadin shigo mana. Ga mamakin Hajjo sai ga ta ta shigo ta durkusa gaban ta,ta ce Mama,dan Allah zan iya kiran ki mama a matsayi na na diyar ki? Tashi Hajjo ta yi,ta tada ita su ka zauna bakin gado kamar yaya da kanwa,ta ce Ameena? Neena ta ce na’am,ta ce ko ba ki kirani mama ba ni mahaifiyar ki ce,wannan ba zai taba canzawa ba,zan fi so ki cigaba da kira na Antyn da ki ka saba,ki kuma kira dayar maman taki da Momma da ki ka saba,kar ki canza ma ta,ita ma maman ki ce,ta na san ki kwarai kamar yanda ni ma na ke san ki. Neena ta gyada kai tare da fadin na gode. Hajjo ta shafa kanta,nan fa hira ta bige,ta ma manta da Hauwa na wajan Khalid,hira har da dariya,ta na bata lbryn mai sunan ta,a haka har bacci ya dauke Neena,Hajjo ta gyra ma ta kwanciya,ta san Khalid na tare da Hauwa ana ta soyayya,sai kawai ta yi kwanciyar ta da diyar ta,a karo na farko kenan tin bayan da aka dauke ta ta na shekara biyu. DEDICA to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [16/10 22:05] .: [2:25pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣8⃣ Washagari cikin jin dadi aka karya,Khalid ya tafi Abuja,Hauwa ta kai diyar ta makaranta,Hajjo da ta daina fita ta yi kwanciyar ta a gida,rayuwa ta fada dadi. Da yamma bayan Hajjo ta gama waya da Indo,ta na tambayar yaya dai? Ba a motsa ba? Hajjo ta ce tukunna,ko yau ko gobe ta ke sa rai dan ta jin kab ta ba daidai ba,su ka kare da fatan alkahilairi,Indo ta ce suna nan suna jiran abun arziki dai. Aje wayar ta ke da wuya wani kiran ya shigo,kawar su ce Yusrah. Ta daga ta na Yusrah ashe ana tunawa da mu. Daga dayan bangaran ta ce haba ai kuna nan rai na,ni fa ance da ni an sake venue din walimar Aysuh da ke jiya ban sami daman zuwa ba,dan Allah taimaka ki fada min….cike da Mamaki Hajjo ta ce walima? Walimar me kuma Ayush ta ke? Kai Hajara! Yusrah ta fada daga dayan bangaran,ki na nufin ba ki san bikin Ayush ake ba? Ina amintar ta ku? Duniya da alkawari kuwa….? Ganin yanda Yusrah ta yi reactn Hajjo ta yi saurin yin kwana,ta ce no ban san da walimar bane,amma ma na san da biki,da ke na yi nauyi shi ya sa ta ke boye min. Yusrah ta ce yanzu na ji batu,bari na kira wata kawar ta mu na ji toh. Su ka yi sallama ta aje wayar. Hajjo ta dade ta na jinjina maganar,Ayush? Ayush kuwa? Ayush din ta? Ta dai san Ayush ta ja baya da ita,amma ba ta san abun ya kai ga haka ba. Kasa hakuri ta yi,tai ta gwada numbar Khalid ba ya shiga,kawai sai ta shirya,ta ce da Hauwa bari ta dan je ta dawo. Hauwa na be kamata ta fita ba a yanayin da ta ke ciki,ga kuma hadari na ta haduwa. Hajjo ta ce ba nisa za ta yi ba,kar ta damu garau ta ke. Kai tsaye gidan su Ayush ta je,ganin mutane a waje,ga motoci ya tabbatar ma ta amarya ake jira a tafi wajan walima. Gidan ta shiga tana tambayar Aysuh,wata kanwar ta ce ta gano Hajjo,ta ce laaa Anty Hajjo,ai ban gane ki ba da. Ita ta kai ta inda akewa Ayush make up,an gama ma ta kenan sai ga Hajjo gaban ta. Ta yi kyau sosai, Ganin ta Ayush ta ji wani iri,kunya ta rufe ta,ta ce da jama’ar wajan su dan ba ta wuri,kawayen su sai yiwa Hajjo biki su ke,wai bikin Ayush guda sai yau ta ke zuwa. Bayan kowa ya watse daga Hajjo sai Ayush,Hajjo ta ce Ayush,ina zumunci? Lefin me na mi ki haka? Bikin ki Ayush ki kasa fada min? Abun ya kai haka? Idanun ta sun yi rau,ta ce ban san da wani baki zan baki hakuri ba Hajara,ban san da wani ido zan kalle ki ba,ba yanda zan yi ne. Hajjon ma kwalla ne ya cika idanun ta,ta ce y? Saboda me ya sa? Kin fitar da ni daga cikin yan uwa da abokan arziki? Is dat y? Ayush ta girgiza kai. Hajjo ta ce den y? A sanyaye ta ce saboda mijin da na aura ne….Hajjo ta kasa fahimtar ta,ta ce kamar yaya mijin da ki ka aura? What bussiness do i hav wit him? Shi ya ce kar ki yi zumunci da kawar ki Hajara? Ta yi saurin cewa no ba haka bane! Wata yar budurwa ce ta leko ta ce Ayush tin dazu fa Su Ya Suraj su ka zo,ya ce ki fito! Ayush ta gyada ma ta kai. Kamar blow haka abun ya bugi Hajjo. Sai a sannan ta gane komai,hw can she blind? Ta kasa ganewa tintuni! Ta na murmushi ta ce Suraj? Suraj ki ka aura Aysuh? Dama shi ne Crush din na ki? Shi ne cousn din na ki da ki ke matukar so? Ayush ta gyada kai hawaye na zuba daga idanun ta. Hajjo ta ce oh my God!! Da na yi making mistake of my lfy! Ashe soyayyar Khalid ba karamar alkhairi bace a gareni!ta yi hugn din ta,tana mumu me ya sa baki fada min ba Ayush! Me ya sa. Ayush ta ce saboda ke kawata ce Hajjo,kuma ke ya ke so ba ni ba tym din,i can’t jst hurt you! Hajjo ta ce gwara kin yi hurtn kan ki Ayush? For you information,wallahi ban taba jin soyayyar Suraj cikin rai na ba,I was doing it for u mumu! It was all for ur sake!Duka su ka sa dariya,budurwar ce ta kara dawowa,kafin ta yi magana Hajjo ta ce gata nan,pls a yi hakuri. Ta ce da Ayush ina ne wajan bikin? Ayush ya ce ta yafe ma ta wlh ga hadari ga tsohon ciki! Hajjo ta ce wlh babu abunda ya isa ya hana ta zuwa auren Ayush da crush,so kawai ta fada ma ta,ta na fada ma ta,Hajjo ta taya ta share hawayen fuskarta,su ka fito. 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 6⃣9⃣ Tin shigar ta mota Aysuh ke kokarin gayawa angon na ta suna da babbar bakuwa,amma ina mitar ta ki fitowa da wuri ga hadari da ya ke ta ma ta ya ki bari ma ya ji,dan haka sai ta yi fushi ta ma sa banza. Sai da su ka shiga su ka zauna a dakin taron sannan Hajjo ta sami damar karasawa a na ta motar. Har ta fito sai ta tuno alkawarin da ta tabawa yiwa Suraj,ta ga lalle tin da Allah ya nuna ma ta ranar,dole ta cika,dan haka sai ta dauko ajiyayyar lapcoat din ta da ke cikin mota,ta sanya. Tin da ta shigo ya ke kallanta,ba komai ne ya ja hankalin sa ba sai lapcoat din da ya gani sanye jikin ta,haka ma dayawa daga cikin jama’ar wajan kallan ta su ke,mace mai tsohon cikin da ke rinjayar ta dan girma,ta na taku da kyar ga lapcoat ta daura,likitocin da su ka gane ta kuwa dariya kawai su ke,dax Doc Hajara for them,komai na ta da gaske ta ke yi. Suraj was lyk wacece wannan? Maganar sa da Hajjo ce ta fado ran sa,lapcoat? Sanya lapcoat ranar bikin sa? Mutum daya ce da wannan aiki! Ya juya ya kalli amaryar sa da alamar tambaya,murmushin da ke fuskar ta ya gasgata ma sa Hajjon ce ba kowa. Kai tsaye wajan ango da amarya ta nufa,ta isa gaban su Suraj ya dara tare da Fadin dax Hajjo for us! kin dai sa hankalin ki ya kwanta! Duka dariya su ka sa,da ke ya taba bawa Ayush lbryn sanda suna shawarar irin shigar da za su yi. Hajjo ta ce ana bikin Doctors ai ban yi adalci ba idan na kasa cika alkawari. Suraj ya gyada kai,ya ce yes,thank you for dat,amma you tooo heavy,ya kamata ki koma gida kar ki haihu wajan bikin doctors! Ayush ta ce menene ciki? Gwaggaro za mu aje mu karbi dam bebyn mu. Duka dariya suke,Hajjo ta tsaya tsakiyar su da tambatsatsen cikin ta aka mu su hoto,sannan ta mu su sallama da fatan alkhairi,zuciyar ta fari fat da annuri ta baro wajan. Tana shiga gida gaban ta ya fara faduwa,Khalid jingine jikin motar Hauwa,kallo daya za ka ma sa ka tabbatar da bacin ran da ke tattatare da shi,ya cika yayi fam dawowar Hajjo ya ke jira,tin dawowar sa da ya ga ba ta nan gaba daya hankalin sa ya gama tashi,gashi ba ta daga waya. Gefe ta faka,ta fito da fa’ar ta ta ce sannu da zuwa…bin ta yayi da kallo ya tabbatar da lfyn ta lau,fuska tsuke ya ce ke ce da sannu ke da ki ka fita bayan kin san na hana tsabar ba ki san ciwan kan ki ba! Nxt tym idan za ki fita ki aje min ciki na a gida sai ki je duk inda za ki! Ban mukullin motar! Rai ba dadi ta mi ka ma sa,tare da fadin ka yi hakuri! Banza ya ma ta,ya shige ciki ta na biye da shi,sai shunan sa ta ke da baki,ta na fadin masifaffe kawai! Da su ka shiga ciki ya juyo ya ce mekika ce? Ta ce ah ah ba magana na ke ba! Cikin takaici ya ce ina ma ki je? Ta ce wlh bikin Ayush ake,yace wacece Ayush? Ta ce kai Khalid kawar tawa ka man ta? Aysha? Ya ce cousn din tsohon saurayin ki? Ta ce yauwa Suraj din ma ta aura…WHAT bikin tsohon saurayin ki ka je! Hajjo ta ce Khalid! Ina ya hau ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba,gaba daya ya masife ta tsaf! Kafin ya haye bangaran sa,sai ga Hauwa ta fito ganin Hajjo tsaye ta kuma jiyo masifar Khalid din ta ce lfy kuwa Hajjo? Hajjo ta ce wannan masifaffan mijin na ki ne ke masifar rashin gaskiya. Hauwa ta ce ahh ran maza ya baci,aje a lallabo shi. Hajjo ta tabe baki ta ce caf bar ni na ji da kai na kin ji,can ma sa,sai dai ke ki lallabo shi din ba dai ni ba. Hauwa ta ce ah ah wane ni,ban shiga wannan fadan Hajjo. Hajjo ta ce toh ya je can ya karata,ina jin dan ciwo kadan,bari na je na kwanta ko zai lafa. DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) [7/25, 6:15 PM] Salmah Ateeku: [2:35pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 7⃣0⃣ Hauwa ta ce ko dai abun ne? Tana tafiya Hajjo ta ce ah ah,da saura dai,kawai ban jin dadi ne. Ta shige ciki Hauwa na ma ta sannu. Da aka zo cin dinner Hajjo ba ta fito ba,haka ma Khalid da ke fushi. Da ke Hauwa ta san haka sai su ka ci abuncin su ita da Neena. Sai da ta gama ta leka Hajjo,sai ta ga ta na bacci,ta kyale ta ba tare da ta tashe ta ba. Garin yayi baki matuka,hadari ya hadu sai walkiya,dan haka Hauwa da Neena ma da wuri su ka yi kwanciyar su. Cikin bacci ta ke jin ciwan na tsikarar ta sama sama,tin tana iya jurewa kamar a mafarki,abu ya zama unbearable har sai da ta farka,ta tashi zaune cikin zufa,sai da ciwan ya lafa sannan ,ta duba agogo ta ga karfe tara na dare. Tashi ta yi ta watsa ruwa,ta sanya wata rigar ta iyaka gwiwa,ta koma ta kwanta. Ciwan be kara motsa ma ta ba sai kusan wajan goma,one hour interval kenan,da ta ga haka ta tabbatar naguda ta ke,amma ta san da saura,za ta iya kaiwa ma zuwa asuba. Sai ta saki jikin ta ba ta kira Khalid ba,shi da ma ya ke fushi da ita ta ma kashe wutar dakin dan ta san ba shigowa zai yi ba. Haka ta yi zaman ta,tin tana kan gado sai ga ta ta sauko kasa,wato ya kara motsa ma ta kenan. Khalid kwance bisa gadan sa,ya na so ya kaurace Hajjo yau dai daya,amma abu na so ya gagare shi. Kamar wanda aka kira ya tashi da sauri,ya sauko sai gashi bakin kofar dakin Hajjo. Ya bude kofar a hankali,ganin wutar dakin a kashe ya san ta yi bacci,amma idanun sa na matukar san ganin ta duk da ita mai laifi ce. Dan haka sai ya shiga dakin,makunnin wuta ya danna,haske ya gauraya a dakin,ga mamakin sa gadan na ta ba kowa,ya na tunanin ko ta shiga bandaki,ya nufi bandaki da niyar kwankwasawa,sai ya hange ta can gefe,zaune dai dai bisa carpet,da sauri ya karasa wajan ta yana Suger ya dai? Ta na murmushi ta ce labour na fara. Ya ce ya salam! Ya ba ki kira ni ba! Bari na kira Hauwa mu tafi hsptal! Ta yi saurin ruko hannun shi ta ce da saura,pls ka dan barta tukunna,ina ga sai ma zuwa asuba zan haihu. Kallan ta yake kamar ma neman gaskiya daga fuskar ta,daga bisani ya ce tun yaushe ki ka fara jin ciwan? Ta ce tin dawowa ta gida. Ya ce da hadari Hajara,tin kafin ruwa ya sauka mu je asibiti. Ta ce blv me da saura Khalid. Sai da ya dan yi tunani,sannan shi ma ya zauna kusa da ita,ya janyo ta jikin sa. Bini bini sai yayi kissing kumatun ta,ko hannu ko wuyan ta. Can ya ce Hajara? Ta ce ummm ta yaya za mu gane kin kusa ne mu tafi? Ba ana gwadawa ba?ya ake yi?da me ake yi? Da ke ciwan ya lafa sosai,kamar ba ita ke yi ba,sai ta murmusa ce ita diya mace in tana labour abin da ake fara dubawa shine wannan hanyar da dan yake futowa aga yana budewa to in ya na budewa,budewar shine Cervical dilation ko Dilatation of cervix,sai a gwada hw many Cm ta ke,yatsa daya shine 2cm,biyu 4cm,uku 6cm,hudu 8cm, biyar kuma 10cm. Idan diya mace tana 2cm xata iya kaiwa 6hrs bata haihu ba, Idan taje 5 still she is on the way xata Iya taking 3hrs kafin ta haihu, It depends on multip ce ko primid, In primid ce xata dade saboda itace haihuwarta ta farko, In multipce baxa takai hrs din primid ba saboda tataba haihuwa,kamar ni kenan, Buh duk inda akaje 8 haihuwa taxo kusa xata iya haihuwa within 30mint, In kuma akace fully dilated dax 10cm tofa yanxu xa aga kan da. Khalid ya ce yaya kenan ke da ba wanda zai iya dubawa? Ta ce kar ka damu,na riga na kintati lokaci base on yanda ciwan ya ke tashi. Shiru su ka yi,daga bisani ya ce yaushe raban ki da abunci? Ta ce kafin na fita na ci. Ya ce kin dade,bari na samo mi ki,ta ce noo i can’t eat,bazan iya ba,ka dai bani black tea,shi zai iya keeping dina strong,ya ce owk ina zuwa ya fita jiki na rawa,sai gashi ya dawo dauke da flask din ruwan zafi,ya hada ma ta tea din,ya dawo ya dada jawo ta jikin sa,ta na sha suna dan hira. Tin suna jin saukar yayyafi sama sama,tuni ruwa ya tsuge kamar daga bakin kwarya,Khalid ya ce Allah ya taimake mu ruwan nan ya tsagaita san da za mu fita. Ta ce amen amen. Sai da ma ta manta shaf sannan ciwo ya dawo,mara ta fara juyawa,ta damki hannu Khalid, gaba daya ya kideme sai sannu Hajara,sannu sannu Hajara,me zan yi? Me zan mi ki na rage mi ki ciwo? Baki cize ta dafa bayan ta,ganin haka sai ya fara shafa ma ta bayan,sai sannu da surutai ya ke kamar shi ke jin ciwan ma. Can kuma kamar abun iska sai ciwo ya lafa,yayi hugn din ta gam daga zaune,ya na da ana daukewa da na dauke mi ki suger,I love you soo much! Ita dai uhum kawai ta ke cewa,ita ta san abunda ta ke ji. Haka su ka kusan raba dare,ciwo ya tashi ya lafa,tin yana after one hour,ya dawo 40mnts,30,25,20…..wajan uku da rabi sai fa abu yazo gangaganga,gashi ruwa ake sosai,ba karamin tashin hankali Khalid ya shiga ba. Da gudu ya taso Hauwa,tare su ka dawo kan Hajjo,gwara Hauwa atlest yayar ta Zeena ta taba haihuwa a gida dan haka ta na dan san kadan daga yanda za ta yi. Khalid ya kira wayar Jabir ba adadi amma saboda ruwa wayan be shiga,haka na matar sa. Gani ya ke laifin sa ne da yarda da maganar Hajjo,da sun tafi asibiti tuntuni da tuni hankalin su kwance. Carpet mai kamar leda Hauwa ta shimida gaban Hajjo,Khilid ya ce me ki ke yi haka? Asibiti fa za mu kai ta! Hauwa ta ce cikin ruwan nan? Kan mu karasa ta haihu,dubi kafar ta ka ga! Wani farin ruwa ne mai jini jini ya ga na bin kafar Hajjo,ta ce wannan zaki ne ke fita,daga shi sai faya,sai kuma kan da fa! Khalid ya ruko hannun Hajjo da ta ke ta nishi,ta na wayyo,wayyo,Hauwa ta ce addua Hajjo,summas sabila yassara! Summas sabila yassara! Caraf kuwa sai ta kama,tin tana fada a hankali,har ta fara fada da karfi. Idanun Khalid cike da kwalla,ya ce Hauwa ki taimaka min! I can’t bear this! Hauwa ta ce ka fita kawai Khalid,ya tashi zai fita,wani ihun da Hajjo ta yi sai gashi ya dawo da sauri ya na sannu! Sannu Hajara ra! Haka mata ke yi! Haka Hajiya ta ta yi? Hauwa Hajara ta jigata! Wanda be daraja uwar sa ba yayi asara! DEDICATED to The Women Of Virtue💁👰🙋(group) 5pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: 👭👭👭DIYA MACE👭👭👭 7⃣1⃣ Hauwa ta ce taimaka mu sa ta on her kneels,ga faya ta fashe,na kuma ji kan da, Ko da ya ga yanda Hajjo ke zufa,tana cize lebe kamar za ta gatsa,sai ya tashi a gigice ya na fadan i can’t take it,I can’t take dis! A guje ya fice ko takalmi be sanya ba,haka ya fita cikin ruwa ya tada mai gadi ya bude ma sa gate,sai gidan Jabir. Da fitar shi,Hauwa ta ce da Hajjo yi nishi,yi nishi Hajjo da yardar ubangiji! Hajjo ta ce dallah kyaleni! Ba zan yi ba! Ba zan iya ba! Wayyo Inna! Allah ka ji kan Inna ta! Wayyo Inna! Allah ka gafartawa Inna…wayyo summassabilayassara! Innalillahi! Wayyo Allah! Hauwa ta ce ga kan dan ki,yi nishi! Ai kuwa da yardar ubangiji wani karfi ya zowa Hajjo,ta nisa da karfi sai ga katan dan ta ya sullubo mai kama da Khalid sak,har tsayin! Tuni ya fara callara ihu Hauwa ta yi saurin riko shi,Allahu akbar Khalid ya yi da. dan murna hawaye wiwi ke zuba daga idanun Hauwa,ji take kamar ita ta haihu,ta aje yaro a gefe ta ce saura mabiyiya,sa hannu mai za ta ji? Cike da mamaki ta ce Hajjo..Hajara…wani kan ne! Ai kuwa sai Hajjo ta fashe da kuka,ta ce kumamawa?na baki wlh,dan Allah na baki,wlh bazan iya ba,bazan iya haifo shi ba! wayyo Inna ta!. Hauwa ta ce na gode,amma sai dai kimin addua ni ma na haihu dan bazan iya haifo na cikin ki ba,ke kadai za ki iya,yi nishi ya fito. Hajjo ta ce na mi ki,Allah ka sa Hauwa ta haihu,Allah ka sa ta haihu,Allah ka sa ta haifo har na ciki na! Hauwa ta murmusa,cikin lallabi ta ce Allah ya amsa,amma sai kinyi nishi,Hajjo ban yi nishin ba! Ke ki yi nishin mana! Dallah ki barni na ji da abunda ke damu n! Wayyo Inna,karfi na ya kare,Hauwa ta ce daure….da karfi duk da dai be kai wanda ta yi na fari ba,ta nisa,sai kuwa subul na biyun ya fito wanda be da bambamci da na farko! Ya na fitowa shi ma ya callara na shi kukan,tuni mabiyiyi ta biyo sa,ba kari sam ba ta karu ba,nan ta kwanta ta na mayar da numfashi,Hajjo mai kuka sai gashi ta na murmushi. Hauwa ta ce Khalid sak mu ka samu har su biyu,ya zan yi na yanke cibiyar? Daga kwance murya shake tana mayar da mumfashi Hajjo ta ce duba cikin waccan drawer akwai saban reza da zare,ki dauko. Jarirai na kuka Hauwa ta dauko,Hajjo ta ce awna da danyatsan ki na tsakiya,daidai tsayin za ki yanke,sai ki daure karshen da kyau,in be dauruba jini zai zo yana zuba tawajan. Yanda ta gwada ma ta,hakan ko Hauwa ta yi,ta nade su cikin shalw,ta ba ta daya ta bashi nono,sannan ta fara gyaran wajan. Kafin Hajjo ta shiga wanka sai da ta ba su nono dukkan su,sai dai wannan karan ma tana wannan ciwan cikin kamar na haihuwar Neena. Ruwa ya tsagaita sai yayyafi,da ke asuba ta yi ,an fara kiraye kirayen sallah,tana wanka Hauwa zaune da babies sai ga Khalid jike jagab,Jabir biye da shi,shi ma din ya jige amma ba sosai ba. Ganin jarire har biyu Khalid ya rikice,gashi jike ya ke ba damar dauka,hugn din Hauwa yayi, fadi ya ke dukwannan nawa ne? Alhamdulillah ka ga kyautar Allah,da ya tashi bani sai ya bani biyu!!! Jabir ya ce dama yanda cikin nan kamar tulu ya kumbura sis dina ai sai dai biyun!Ya Hajaran ta ke? Hauwa ta ce lfy lau,sai dai ciwan ciki,Jabir ya ce yea dama wasu na yi,PCM ya kamata a mata,da an yi mata allurar za ta sami sauki inshaAllahu,idan gari yayi haske sai kawai ku kai ta hosptal dan duba su da kyau,haihuwan gidan nan ban fiya san shi ba,gaskiya ka yi sakaci,Allah kuma ya kawo da sauki. Toh toh toh Doctor!ahhh ai bazan sake ba! Khalid ya fada cikin murna. Hauwa da Jabir dai uziri kawai su ka ma sa,Gaba daya a rude ya ke,ya kalli wannan sai ya dawo ya kalli wannan,ya daga waya ya kira Hajiya,ita ma Hajiya murnar gun ta kamar ta fito ta wayar,cewa ta yi gari na haske za su ganta. Masallaci su ka tafi,kafin su dawo Hajjo ta fito ta shirya tsaf. Hauwa ke ba ta lbryn kyautar da ta ma ta tin kan ya fito duniya,har da gwada maganar ta Hajjo. Dariya su ke sosai,har Khalid ya shigo,ya na mata murmushi cike da kauna,ya ma manta Hauwa na wajan ya jawo ta jikin sa,Hauwar ta shige bandaki ta wayance da wanke hannu,shikuwa Khalid hugn matar sa yayi gam,sannan ya bi fuskarta da kiss ta koina,ya na na gode maman yan biyu,na gode na gode. Jabir zai iya shigowa ya gan ki? Ta ce eh bissimillah. Sai da ya shigo da Jabir Hauwa ta fito. Cikin nuna kulawa su ka gaisa. Khalid ya dau babban dan sa,ya zauna kusa da Hajjo ya ce Suger da wani suna zan ma sa huduba? Ta kalli Jabir sannan ta ce sunan yaya na,ka ma sa da suna JABIR! Farin ciki da alfahari su ka bayyana fuskar Jabir,sai gyada kai ya ke. Khalid ya ce toh Khalid ya haifi Jabir kenan! Sai a yi din. Duka su ka sa dariya,yayiwa yaran huduba da Jabir,Jabir ya karbi takwarar sa,Khalid ya karbi na biyun,ya ce wannan fa? Sabir ne? Hajjo na dariya ta ce wannan kuma sai dai ka tambayi maman sa,baki bude Khalid ya ce wata maman ta sa kuma? Hajjo ta ce ga ta kusa da kai. Ya juya ya kalli Hauwa,sai murmushi ta ke,ya ce ta yaya ki ka zama maman shi? Hauwa ta ce tin kafin ya fito aka min kyautar sa ai,kai amma Hajjo daban ki ke,da gaske ni zan zaba ma sa suna? Hajjo ta gyada kai,Hauwa ta ce toh a sa sunan Baba na,Abbakar. Khalid ya gyada kai,ya ce madallah da Baba,ya ma sa huduba da sunan Baban Hauwa,shi ma ya ce da ya sani ya tsaya da kila ta haifi uku,shi ma ya sami na shi. Da wasa da dariya ya raka Jabir. Ya dawo ya tadda Hauwa da Neena wajan Hajjo,murna ya cika Neena,atlast! Ita ma ta na da kanne. Hauwa ce ta janye ta,su ka fita suna jin ta ta kira baban ta tana Baba an sami karuwa fa,na haifo takwarar ka! Sai murna ta ke! Khalid ya janyo Hajjo jikan sa,ya ce ba fa ko dayaushe za ki na ba su nono su ta tsotsa ba,daga ganin yaran nan tsotso za su yi! Hajjo ta ce toh idan ban ba su ba me zan yi da shi? Kayya! Me za ki yi da su? Ai nawa ne! Bazan barai su lalata min mata ba! Hajjo ta ce Ah wannan ai child abuse ne!! Ya ce eh na yarda,in kin ga dama ma kira ni Child abuse in dai kan wannan ne zan amsa! Duka dariya su ke,ya ce kara kara dai in dai kara ce sai DIYA MACE! Ya bazan so ki ba? I love you big. Ta ce hw big? Ya ce bigger nd larger than lyf. Ya fara kissing din ta,babies su ka callar kuka a tare,ya dago da sauri ya na nifa ba za a matsa min ba!kar fa a bata min rai na!! Hajjo na dariya ta ce me aka ce da maza?? Takura indai irin wannan yanzu ka fara gani! Ba dai ka zama Baba ba? Wlcm to d system……….!!!! “Every female is an angel Don’t west tym in selecting Unique,instead spend tym in Undstanding them……..” ALHAMDULILLAH Ta ku KHADIJA SIDI RAMADAN KAREEM:) For your comment nd correction txt me 07018583783 Advertisements SHARE THIS: TwitterFacebookGoogle RELATED