5/18/21, 11:41 PM - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more. 5/18/21, 11:43 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI NA🙆🏼‍♂️ 1️⃣ BISSMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI INA GODIYA GA ALLAH DA YA BANI DAMA DA IKON FARA WANAN LITTAFIN A CIKIN HIKIMA DA BASIRAN DA YA WADDATANI DASHI DA FATAN SAKON DA KE CIKI ZAI ISA GARE KU A CIKIN DAUKAKA DA FAHINTA YADDA NAKE BUKATA, , , , , WANAN LITTAFIN NA KUDI NE DON ALLAH KI SAYA KI SAURARI SAKON DAKE CIKI BA TARE DA CIN HAKKIN JUNA BA A TSAKANIN MU DARI UKU NE KACAL TA BANKI KO KATIN WAYA GA MASU SO ZASU IYA TUROWA TA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI KIRA LAYINA 080 36959257 KO 090 26937192 da fatan zamu fahinci juna daku kamar yadda Allah ya hadamu nagode. Yau garin ya tashi da matsanancin hadari sakamakon tsakiyan damana da muke ciki na wanan shekaran zaka iya cewa gari bai karasa wayewa ba a wanan lokacin. Don yanayin da garin ya nuna na damana a lokacin wanan yanayin bai hana mutanen garin yin zirga zirga haka a cikin sa ba don neman na yau da kullun. Hadiza ce tsaye yarinya karama da ita saidai tana da kaifin basiran da tunane don isowar mahaifiyar ta take jira wacce ta tafi birni tare da yan uwanta dubiya wata yar uwar su a can. Baya baida kadan don tafiyan ta wata matar kanin mahaifin su tazo ita ma daga lagos ta kawo masu tsaraba ciki har da ita hadizan ta samu da tan uwanta. Wanan dokin ne yasa hadiza fita a cikin wanan yanayin tana dakon isowar mahaifiyar ta ta zabga tagumi tana mai tsura ma hanya ido taga motar da zai iso garin su a cikin dauki. Wani dan uwansu ne ya biyo a cikin sauri yake yana ganin ta yake tambayan may take a nan a cikin wanan sanyin ita kadai. Tace mama nake jira sun tafi birni tun jiya ga matar baffa mu na birni tazo ta bani riga har yanzu mama bata dawo ba ni idan mama bata dawo ba yaya zanyi da rigar nan kowa ya saka nashi. Takaici ne ya kama mutumin ya hau yarinyar da fada yana fadin maza ki bace wurin nan ki koma gida duk inda ta tafi ai zata dawo riga kuma tunda an baki ai ba kwacewa za a yi ba. Simi simi ta juya zuwa gida don sanin ko waye a gare ta don baida wasa da yara shi a cikin yan uwa kaf sun san da zaman shi. A cikin sanda ta karasa shiga gidan don kada kakanta ta ganta don basu san fitan ta gidan ba a wanan lokacin. Kicibis sukayi da kakan da zata fita neman ta a kofar gidan don ta farga da yarinyar bata gida a lokacin. Tana rike da kwarya a hannun ta hannu daya tana gyara mayafin data dora a kanta tace suna arba tace haba kubura ina kika fita a wanan sanyin haka tun dazun nake neman ki ga uwar ki har yanzu basu dawo ba ni ban san irin wannan tafiyan ba na aje akai wani lokaci a garin mutane sunyi abinda ya kaisu sai su juyo su dawo gida kuma ba sai sun dora ma mutane lalura ba ai. Tace umma nima shine na fita ina jiranta don ga rigan ga da matar baffa ta bani ban mama bata dawo ba ta gani ni yanzu yaya zan yi ? Umma ta rike baki da mamaki tana kallon yarinyar tace kai kubura akwai ki da shirmay riga tunda an baki aiba kwacewa zatayi ba duk lokacin da Allah ya nufa uwar ki ta dawo ai gani zatayi ko ? Tace to umma kowa ya saka nashi ai amma ni har yanzu bata dawo ba balle in saka nawa a gani ko tace kai kin faye dumi da shiririta wallahi maza ki shiga daki ki dauki abincin ki kada yai sanyi in sha Allahu suna hanya tafe. Shiganta daki ke nan ba a jima ba taji dirin mota ya tsaya ta zabura ta leka a hankali tana sanda don bata son kakan nata ta ganta don kada ta hana ta fita. Ta kusa kofan fita taji muryan kakan na fadin ke! ke ! ke kubura tuni ta balla a guje ta fita wajen gidan don ganin ko mahaifiyar nata ne ta dawo a lokacin. Bata damu da masifan kakan nata ba akanta ita dai muradin ta uwar ta ta dawo taga sabon rigar yar kanti da aka zo mata dashi tsaraba ta saka a jikin ta. Sai dai kasshi ba su bane a wanan lokacin kai kallon ta tayi ga yanayin garin wanda wani sabon hadarine ake kara hadawa sai wallakiya ke haska ko ina a garin. Maimakon ta koma gida sai ta samu wuri ta zauna tana dakon mahaifiyar tata a lokacin tunda kakan tace suna gab da isowa insha Allahu. Bata jima da tsayi ba a gurin motar ta tsaya dauke da iyayyen nata mata tayi tsalle ta isa gurin motar tana leken cikin motar. Nan dai tayi arba da mahaifiyar nata dake kokarin fitowa a motar tun kan ta karasa sauka take ihun eh mama mama a cikin murna da dauki tana ganin ta diro take fadin mama matar Baffa na birni tazo ta kawo min riga da, , , , Buge bakin ta da uwar tayi tana fadin ke sai yaushe ne zakiyi hankali wai da wanan shiriritan naki haka ko sannu baki iyawa mutane ba zaki tare mu da bakin dumin ki da kika iya. Baya taja a cikin fushi tana turo baki uwar ce ta juyo tana fadin zoki daukan min kaya zuwa ciki da bakin surutun ki na banza ta turo baki ta dauki kayan da uwar ta nuna mata nata zuwa gidan su. Sai dai tana kawowa ta tuna da masifan kaka da zata tarar a ciki na hanata fita da tayi ta sa kai ta fita ba tare da taji gargadin ta ba ga kuma bakin ta da mahaifiyar ta buga don wautar ta da tace yayi yawa. Koda ta shiga umma bata tsaya bin ta kanta ba sai fadi take Alhamdullahi masu tafiya sun dawo lafiya ke nan. Uwar ta shigo goye da goyon kanwar ta a bayan ta da sallama a bakin ta aka shiga masu sannu da zuwa tare da gaidasu da dawowa. Sai lokacin umma ta farga da hadizan take fadin yar nema mara jin magana ga uwar taki ta dawo sai ki dauko rigar da kikewa dauki da mazari ki saka a daren nan in ga wanda zaki nunawa shi a garin nan a cikin dare. Ita dai Allah Allah take kada ta samu wani rankwashe a gurin kakan nasu kuma bayan na mahaifayar su da ta sha a waje duk wanan zumu din da take tunda taji umma tayi wanan maganan tasan ba za a barta yau ta saka kayan a jikin ta ba ke nan. Mahaifiyar nata tace wallahi umma ba hankali ne da yarinyar nan ba a waje ta samay ni ina fitowa ta tare ni da zancen kayan ashe bayan mu baki mukayi a gidan kuma ? Umma tace kin san halin kubura ai da wauta kamar wani zai kwace mata rigar ta dauki son abin duniya ta dora a ranta. Ai wanan yarinyar girma take tana cin kasa ko yaushe bata abin masu hankali ita, inji mahaifiyar nata tana fadin cikin takaicin diyan nata da take ji. Umma tace dazun su Aisha suka iso muna da abin arziki kin san su basu gajiya ko yaushe zasu zo da irin abin arzikin da zasu kawo muna. Wanan ma duk mun samu wanan tsaraban sai ita yar douki ta ishi mutane da magana kamar ita kadai akaiwa tafiyan. Ai Aisha akwai alheri mama ta kara fadi ni dai ina rakube a kofan dakn mu ina sauraren su duk raina a bace kan rashin yarda in saka sabon kayana inga yadda zai min kyau a jikina a lokacin. Don gani nake kamar gobe yayi nisa a gare ni kaya tun daga lagos ace kuma ba zan saka ba wai sai wani gobe can haka dai na hakkura dole. Karshe mama ta baje dan tsaraban data sawo muka lakumay a furin ta shiga ba umma labarin tafiyan nasu da wace suka je gaidawa din. Tun da safe hayaniya tsakar gidan su ne ya tada ita tashi tayi tana mustsike isanuwan ta tana sauraren muryan umma dake zazagawa iyayyen ta masifa. Kamar ba ita bace suka kwanta lafiya da maman nata a dare jiya wanan abin idan da sabo hadiza ta saba dashi a gidan su. Don tun bata san fada ba ta bude ido dashi yadda Umma kan tasa iyayyen ta mata tana masifa dasu a gidan kan dan abu kadan da bai taka kara ya karya ba a gurin mutum. Ta kashe kunne tana sauraren umma kakan su ta wajen uban su tana bala,i da iyayyen ta mata a gidan tana fadin. Don wulakanci da rainin hankali wanan dan kokon ne za a zubo min shine zan sha in koshi karshe kuma yaran ku su dawo su sha a gurina. Taji muryan mama tana fadin kiyi hakkuri umma kullun kokon ne ba yawa iyakar shi ke nan na dama muna don ba yawa ke da shi kawai kuka samu. Don ko yaran ban zubawa ba yanzu nake son in dan gwaba muna sauran tuwon daya rage da gutun raman dana shanya mu karya dashi ni da su. Tace ai haka zaki ce dama da anyi magana ki wani marairaice wake gata Allah kin sa min da a gaba kina ta wahalar dashi kullun ku ke nan cikin haihuwa a gidan nan baku san matse kafa ba ku ko irin dan abin nan na zamani da matan yanzu keyi ku ba a samu a gurin ku. Ko wace sai kirin tara diya wa mijin ta kullun suna fita suna nema kamar ba nema sukeyi ba basu da hutu idan sun kawo kuma ku cinye daku da diyan ku. Fitowa hadiza tayi ta tsaya a kofan dakin su tana sauraren fadan umma din na ba gaira ba dalili da takewa mahaifiyar ta da ta dawo a daren jiya din. Bata farga ba sai rankwashen kakan taji ya sauka a kanta tana fadin munafuka kin wani tsare ni da ido fiki fiki kina kallon bakina don rashin kunya. Baku da wani amfani sai naci daku da iyayyen ku sai dai in an kawo ku far ma abu da ci ku taru ku cinye shi a lokaci daya don fitina. Fitowan kanin mahaifin su daga daki yana fadin haba umma jiya fa saude ta dawo ai kamata yayi a jika mata kafin ta dawo ta samu sai ayi shi a wadatace yanzun dai wanan fadan da kikeyi ai ba ta da laifi ita. Ta juya gurin shi tana fadin to ubana sai kai min fadan abinda ya dace inyi din tunda ni ban san yakamata ba yanzu ai. Fitowan wan mahaifi mu daga nashi shiyan yake fadin umma ke da wa da safe haka ya karaso gaban umma din yana gaida ita da kwana. Yana fadin umma barka da kwana an tashi lafiya ban san kin fito ba ai sai yanzu danaji muryan ki a waje. Ai kasan na tashi tunda kaji murya na din ai kasan garau na tashi ke nan yayi yar dariya tare da fadin haka ne kuma umma muryan mama ne ke gaida Abba din da kwana. Ya juya gareta yana fadin saude an tashi lafiya ya gajiyan tafiyan ya kuka bar mai jikin kuma ta amsa a sanyaye da fadin da sauki yaya mun samu an sallamo ta daga asibiti tana gida. Umma ce ta katse su da fadin kayi ta kaunar uwarka ka fita zance na ai tunda duk ta hade ku gidan ta shanye baki daya. Kuna jina da safen nan ina masifa da ita shi wanan ya fito yana wani juya laifin a kaina kai kuma ka fito kana wani gaida ita. Kaga ke nan ta zama lami kanwata gare ku ta juya tana fadan ta dauko ma baba kwano tana nuna mai tare da fadin ka duba wanan dan kokon da Saude ta zuba min don Allah. Ita baga nemowa ba sai idan an nemo dafawa yazama rowa a gare ni baba yace haba umma ai naji abinda kabiru ya fada maki yanzu ina daki. Yace kiyi hakkuri da abinda kika samu kin san ko banza saude mijin ta baya gari ba wai abincin suke dashi ba kamar ko wa. Ki bari idan sauran sun dama a kawo maki nasu tayi mai wani kallo gami da jan tsuki tana fadin ai gara saude din har naga nata matan ku da suke saraki ko fitowa basuyi ba balle su dora wuta. Suna daki sun mike kafa sai idan an kawo min su turo yaran su karya a gurina idan na hana kuma aji dadin yin gulma na na hana jikokina abinci. Baba yace haba umma su sun isa ma su zage ki ko suyi gulman ki tunda su basu girka ba sun baki akan lokaci. Murya a sanyaye mama tace umma barin in dauko maki na wurin yushau don dama ke dashi kadai na sawa sai ku kara idan ya fito na diba mai gwaben yaci. Ta shige daki sai gata da kofin silver mai marfi dan madaidaici da take zubawa baba yushau kanin mahaifin mu abin karyawa a cikin sa ta kawo gaban umma din ta aje mata. Ta kalli kofin da fushi ta bude tana dan jujuya kokon dake cikin kofin tana fadin ji wanan wai shi za a ba mai karfi kamar yushau ya karya dashi da safen nan sai ra dauko wanda aka zuba mata din ta kara mai kofin ya taso kokon yai yawa ta rufe ta aje a gurin ta. Bata mika ma mama kofin ba baba kabiru ne yace umma ki mika sauran wa yaran su sha tunda basu samu ba in yaso ida saura sun dama a kawo maki sai ki, , , Bai kai karshe ba ta tare shi da fadin kabiru ka fita idona wallahi kafin in saba maka wanan kokon na matan ku da suke damawa ruwa ruwa kamar ruwan kasari ai sai ku da yaran ku. To kuma umma kike mata wanan masifan haka bayan kin san gaskiya idan ba girkin saude ba baki son na wani. Ta bishi da harara ya bar shiyan namu zuwa waje bai wani dade ba sai gashi ya shigo da tuwo irin na sayarwa dinnan ya kwala ba hadiza data gama sallah kira. Ta fito yace su dauka suje suci da kannen ta a dakin su ta karba tare da godiya don haka maman su ta koya masu yi din idan an basu abu komai kankantan shi suyi godiya. Umma hauwa itace mahaifiyar iyayyen mu maza ta haihu da yawa wasun su sun mutu tun suna yara sai iyayyen mu ne suka rage su kadai a raye su hudu maza mata biyu. Baba Sahabi baba gwago habiba gwago laure sai mahaifina da baba kabiru sai autan ta baba yushau da baiyi aure ba. Mahaifna shi ba mai zama a karkaran mu bane don yafi fita zuwa neman kudi sai ya kwashi watanni yake dawowa da dan abinda ya samo. Sai ditan kishiyan kakan mu da suma suna da yawa a dakin su don sun fi iyayyen mu yawa duk muna zaune ne a gida daya dasu sai wa yanda basu garin ne basu zaune a gidan. Auren zumunci iyayyen sukayi don hadin gidane da mahaifina da mahaifiyata diyan mace dana miji suke don haka umma ta zama gwagon maman mu ke nan. Amma wanan baisa mama ta samu ragwamay a gurin umma ba duk da zumuncin dake tsakanin su don Umma ta kasance mace ce mai fada da jinini ga saka ido sosai a gareta. Duk kusan haka take da matan baban nin nawa ko yaushe babu mai fari a gurin ta ita a ko yaushe kusan kanta ta sani fiye da kowa. Iyayye na kaf sunyi karatun zamani gaba dayan su sai matan ne basu samu yi ba don akidar mahaifin su ne mata basu karatun boko a gidan sa. Bai bari su wani tasa sai yai masu aure wanan dalilin ne yasa yanzu iyayye mu suka fara saka mu karatun boko mu dake tasowa a cikin su. Duk wanan fadan na umma tana kokari wurin hada kan diyan ta matsalan ta ya tsaya kawai iya sarakanta da diyan ta suke aure sai ko mu jikokin ta da bata faye wani wasan jika da kaka damu ba. Nice ta farko a gurin iyayyena sai kanwa ta da ake goyo yanzu iyayyena suka haifa hakan baisa umma ta wani jamu a jiki ba kamar yadda muke ganin wasu kakan ni sunawa jikokin su a wani gidajen. Sai dai duk da karancin shekaruna zan iya fahintar wani abin don na fahinci umma tana da dan nuna bambanci a tsakanin jikokin ta mu sanman jikon diyan ta mata da mu. Da kuma wasu dake zaune a gidan tare damu wana baya damuna tunda iyayye na suna nuna min gata a tsakanin su har ma da yan uwan mahaifina suna ina suka saka dani da yar kanwata shamsiya da maman mu take goyo. Tsakanina da shamsiya akwai yar tazaran haihuwa sosai don maman mu tana haihuwan diya maza suna mutuwa har sau uku sai akan shamsiya ne ta tsaya. Don yanzu shamsiya nada shekara uku a duniya da dan kai har yanzun kuma ba a kara samun wani rabon ba. Mahaifiyar mu muka biyo a kama don mahaufin mu fari ne sol dashi don umma ya kwaso gurin fari sabanin mu diyan shi da muke chaculate colour mu ba bakake ba kuma ba farare ba. Hanci da gashi ne kawai muka kwaso na iyayyen mu wanan kaman namu ne don duk jikon umma mun dan fita daban dashi umma ke zagin mu gurin fadan ta idan ta tashi cin mutuncin ta gare mu. Zaman karkara bawani sana,a ne akwai ba na zamani amma cikin hukuncin Allah haka mahaifiyar mu ke zama damu a cikin rufin asirin Allah kafin mahaifina yayo mata sako. Wanda sakon yana fadawa ne wani lokaci a hannun umma sai abinda taga dama tabawa mahaifiyar mu daga ciki sai dai idan sakon ya fada hannun baffa kabiru ne. Zai ba wa mama su a boye ba tare da ita umma ta sani ba ko wani ta dan yi muna lalurar mu a boye batare da wani faca ka ba na zamani. Kin san yadda uwa take fama da lalurar diya mace tun daga haihuwanta har zuwa tasowan ta don ba karamin lalura kega tayar da diya mace ba. Tun daga dankune kumshi zuwa kayan sakawa dasu pant da lalurar kayan kwaliya ga kitso da sauran su amma a haka mahaifiyar mu ke kula da alamuran mu a cikin yardan ubangiji. Batare da kowa ya fahinci halin da take ciki ba muke rayuwan sai ake ganin ai don mahaifin mu yana birni ne muke ko yaushe fes fes damu. ZAINAN IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:45 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI NA 🙆🏼‍♂️ 2️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA MARUBUCIYAR TAKARI FUREN JUJI TARKO SARAUTAR MATA A LOKACIN MUKE MARUCIN KAN DUTSE BAMU KADAI BANE BAHAGON RAYUWA MIJIN BUZUWA YANZUN KUMA NAZO MUKU DA KANIN AJALINA MAISON WANAN ZATA IYA TUNTUBANA TA LAYINA 080 36959257 KO 090 26937192 DON TURA KUDI DOMIN SAMUN LITATTAAFAINA AKAN KUDI DARI UKU KACAL ZAKI IYA TURAWA TA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK. NAGODE DA IRIN HALARCIN DA KUKE NUNA MUNA MU MARUBUTA ZO MU ZAUNA ZO MU SABA SAI HAKKURI A TSAKANIN MU DAKU, , , , , Ina lungun momy da tazo daga lagos ganin gida can muke tarewa idan sunzo muna kallon su ita da yaranta don komai nasu burge mu yakeyi. Muna ganin shi bakon yanayi a gurin mu ga abincin su mai dadi da suke dafawa suna bamu duk da a gurin zubawan dan diban muna akeyi sai yaran ta ne zamu ga anzubawa cike a plate ga ruwan leda suna ci. Wanan bai damun mu don muna samu muna ci ko yayane daga gare su ga baki yan birnin garin mu masu shigowa wirin ta a duk lokacin da take gari gidan mu baya rabuwa da mutane. Sai idan ta koma kafa ke daukewa na kawayen ta har bamu son ta koma idan tazo gaskiya matar ba laifi don tayi sosai. Saboda abinta bai rufe mata ido ba ita ko masu zuwa wurin ta basu tafiya hakana sai da dan abu da take basu. Misalin sha biyun rana mama ta leko shiyan bayan sun gaisa ne ta kirani wai inzo zata aike ni na biyo ta a baya muka fito daga shiyan. Wanka tayi mun tare da shirya ni tana karasa girkin da takeyi bayan na saka rigan da nake maitan sakawa a jikina fuskana yana dauke da murmushin jin dadi. Nima na fito yar birni irin yaran mama na lagos ina daukin fita in zaga sako da lungun gidan nami kowa yaga na saka rigar da babu irin shi a gidan sai naji muryan mama na fadin. Tana zuba miyan yakuwan da yaji kuli kuli a cikin sa tace yar kabiru dauki abincin nan ki kaiwa umma idan kin dawo ki kaiwa inna nata cewan kishiyar mama dake gidan a wani gefe. Nace to mama ina daki ina kara gyara make up din fuskana dakyau irin ta yaran kauye banyi saurin mikewa na fito kamar yadda take bukata ba. Muryan ta na karaji tana fadin yi maza mana ki fito kada abincin yai huce na amsa da to mama gani tafe na fito dakin da sauri na. Ban samay ta a gurin ba ta dan kewaya ban daki ina zuwa na dauki tuwon Inna na kaiwa umma itama umma bata nan na dawo na dauki na umma nakai wa inna. Tana ta faman saka ma mama albarka damu na fito ina murna don yaba kyau riigan jikina da tayi bayan albarkan da take saka muna din. Ina dawowa daga aiken ne na samu fitina a shiyan mu umma tana masifa da mama akan may ta saka mata abinci cikin kwanon da take sakawa inna yau. Son son nayi na fara rabe rabe donn jin abinda mama tace laifina ne don ta saka ina daki ban fito ba ta zaga ban daki na zo na dauki na inna na kai mata kamar yar kabiru za a ce bata san kwanon ki ba kuma inna. Tana fada tana kallon gurin da nake labe shiyasa umma juyowa gare ni tace munafuka yar bakin ciki da hassada abincin naku ne baki son inci da kikai min bukulu. Na kara bin bangon dana ja na tsaya a gurin ina sauraren maganan su umma tace sai ki koma ki karbo min abinci na don ba hakkin ta bane ai. Da sauri mama tace don Allah umma kiyi hakkkuri sai in zuba maki wani mu muci wanan din na wuri ki ta juya zuwa daki ta dauko sabin samira a cikin kayan ta tazo ta hada ma umma wani abinci. Har lokacin umma na tsaye tana zagina da rawqn kan da take fadin a gurin uwata na kwaso shi sallaman inna daidai ne da kawowa umma abincin da mama tayi a shiyan. Tana fadin ke kuma kawata nace ki jirani in zo sai kika gudu ingo wanan kya sai alwa don nayi niya yasa na biyo ki dashi ai umma bata ji nauyin fadin . Dama shiyasa ta dauki abincina takai maki gashi ta samu biyar din yin kwalama ai a gurin ki maketaciyan banza kawai. Sororo inna tayi tana salalami tare da tafa hannayen ta tace shirmay yara ne sai hakkuri bari na dauko maki Allah yasa ban saka hannu a ciki ba. Umma tace wa haba dai ai uwarta ta biyani da wani mama ce tayi saurin gyara zancen umna wurin inna tana fadin inna gidimin yar kabiru ne kawai fa ga naki kwanon ta sani sai ta dauki na umma takai maki. Sai hakkuri inna ta kara fada tana jawo hannu na zuwa cikin gidan namu ina dan turje mata tajani zuwa gurin mahaifiyana tana fadin kada ki duke ta don Allah halin kurciya ne irin na yarinta. Baba kabaru ne ya shigo hannun shi rike da ledan bacco baka ya nufu mama dashi yana fadin ga sakon ku yanzu ya iso gare ni daga mijin ki. Umma dake tsaye tana mai wani kallo tunda ya tunkari mamana da ledan tace to isashe sai kuma akace idan dana yayo sako ita zaka dankawa a hannun ta ko ? Yace umma wanan ba sakon ki bane kayan amfanin su ne ya turo mata dashi banga abinda zakiyi da omo da sabulu ba tunda naga mun sai maki shekaran jiya ai. Tace wai kabiru in tambaye ka kai ka haifar min dan ko ni ko ita ta haifa min shi wai daidai lokacin mama ta karaso da ledan ta kai dakin umma ta girke mata. Baba kabiru bai tankata ba ya shige gurin shi wurin iyalin shi ya barta tana jidalinta tayi ta gaji ta koma ta bude ledan kayan ta zazage shi saman tabarman ta. Tanz buda tana yamutse fuskan ta ta tsince abinda take so ta kwalawa mama dake zaune a inda ta idar da sallah kira da sauri mamata mike ta tafi. Dunguro ledan tayi tana fadin ga shinan na debi nawa saura kuma ki kwashe ki rabawa mutane don neman suna a gurin su ki dawo kina kiran baki dashi daga baya. Murmushi mama tayi ta duka ta dauki ledan tana fadin angode kin dai ji abinda na fada maki umma ta kara maimaita kalamin ta ga mama. Tana shigowa daki naga ta zazage kayan ta kura masu ido sai ta girgiza kanta ta juya bata kara kallon kayan ba ban iya debe dayan biyu idan ba zargi nakeyi ba kuka maman mu tayi wanda ban san ko kukan maye ba a lokacin. Jin umma ta fita unguwa sai da aka dan jima kadan tabani sabulu guda guda in rabawa mutanen gidan namu in kai ko wani shiya. Sai yan kadan daga cikin kayan muka tsira dashi bayan rabawa biyun da umma tayi har ma nata yafi namu yawa ta dauka. Wasu sun karba wasu basu karba ba sai da tasa na mayar ma wanda basu karba din ba sai dai suna tambayana halan umma bata gidan ne ? Ince masu eh ta fita zuwa wankan jarirai sai suce bari suje suyi godiya kafin ta dawo baba kabiru najin umma ta fita ya shigo ya mikawa mama kudi yana fadin sai da ta diba ko ? Dariya mama tayi mai tare da fadin bata debi wani abu mai yawa ba ai ya kalli sauran kayan dake zube tsakar dakin mu ya gyada kai. Yace kiyi hakkuri saude kin dai san halin gwagon naki ai tace ba komai ai hakkin ta take ci koba yayan ka nake aure ba ai zata iya cin abina don yarta nake. Muna tsakar gida da yan gidan mu muna ta raye raye duk mun cika shiya da surutu kasamcewa yau alhamis bamu shiga islamiya. Tun kan ta karaso mukaji muryan ta tana fadin kai kai wanan wani iya shege ne haka ku rasa wurin da zakuyi gada sai shiyana duk fadin gidan nan da wajen shi. Wace tazo fita farko ta kaiwa rankwashe akai duk sauran suka ja da baya don sanin halin ta suka kalli juna don idan da sabo sun saba da halin umma. Gaba dayan mu har ni muka sheko da gudu mukai cikin ta ta rasa wanda zata doka a cikin mu muka fice muna dariya. Ni ta azawa laifin da cewa ai zan dawo zata kamani idan na shigo tana fada kamar wace ta samu sa,anta damu. Mama dai sai tukin tuwon ta take bata ce komai ba ta gama ta gyara gurin har lokacin ban shigo ba ga magariba daya gabato sai da ta kaiwa inna abinci ta gargado ni muka dawo gurin mu. Kwanci tashi har bakin gidan mu lokacin komawan su yayi suka fara shirin tafiya dama hutu suka zo muna da ganin gida. Ashe mama da karfin hali tana nan tana tara abinda zata bata sai da taga umma ta fita ta dauki galon din data tara mata man shanu ta nufi gurin su dashi. Tayi mamaki tace keda mijin ki bai gari kikai wanan wahalan tace ai yiwa kaine don ke ma haka kike dawai niya damu ko yaushe. Tace wanan yayi yawa tace babu komai Allah ya kara sadamu da alherin sa washe gari suka juya suka barmu da kewan su. Haka dai rayuwan mu ke gudana a kauyen mu tare da umma da mama zama ne na kuntatawa a tsakanin su kamar ba jinin ta bace mama. An wayi gari shamsiya ta tashi da zazzabi mai karfi hakan ya dauke ma mama hankali ta shiga damuwa da tunanen yadda zatayi da yarinyar. Gashi tasan halin umma ba dama ta nufe ta idan kuma ta je gurin wani a gidan ya zamay mata fitina kuma dole haka ta tasa yar a gaba har lokacin da baba kabiru ya shigo ta fito tana fada mashi. Da sauri yace subbahanallahi ina yarinyar take ta shiga daki ta dauko ta jin maganan su yasa umma fitowa daga dakin ta tana fadin . Lalai saude kin kai munafuka yanzu da nace ki jikawa yarinyar ganye baki jiki mata ba ashe tun dazu ga kabiru mai kudin banza kina jiran shi yazo ki daura mashi nauyin da ba nasa ba ko. Haba umma wanan wani irin magana ne haka ina saude ko ba dan uwana take aure ba zan iya ma diyan ta abinda zan ma nawa ai don Allah dai umma ki daina haka. Yana magana yana kokarin fita da yarinyar bayan fitan su ne ta koma kan mama tana fada inda take shiga banan take fita ba. Mama dai bata tanka mata ba don ba sa,an yin ta bane koma sa,antane ita fitina ba abin yin ta bane da mutane shiyasa umma ke jin dadin kara cusguna mata duk cikjn sarakan nata. Don rashin hayaniyar ta da umma ke kira da duk munafunci ne hakan don ta yi gadon kili bibi daga wurin uwarta wai da haka uwarta ta watsa gidan dan uwanta. Duk da karancin shekaruna ina jin zafin irin abinda umma takewa mahaifiyata a gidan don abin yana ci mun rai kun san diya mace da tausayin uwar ta. Baba kabiru ya dawo gida da yarinya yana fadin kyanda ne ke damun ta an bata allurai da sauran maganunuwa umma dake dakin ta tayo zubur ta fito daga dakin ta tana fadin . Ba kaji ba gurin yayeyayen ta ta kwaso ma ya wanan bala,in yanzun ta bar mutane da wahala kashin kudi kai baba kabiru ya girgiza ya mikawa mama yar tare da mata bayanin maganin da yadda zasu yi amfani dashi. Mama tayi mai godiya ta karbi yar yana fadin Allah ya bata lafiya ya fita a tsakar gida ya tsaya suna magana da umma dake ta fada da mama. Yace umma ina saude ke zuwa kullun saude na gidan nan ba kamar sauran matan gidan nan take ba da ke yawan fita unguwa koda yaushe. Baku bari a fadi ai shiyasa take jin dadin maku makircin ta don kuna karba yanzu wanan kudin da kaje ka kaso wa yar nan da na gargajiya kazo aikai mata ai da kun amfana da kudin. Ranan dai umma tayi jinini sosai kan kai shamsiya chamest din da baba kabiru yayi kamar a aljihunta yayi wanan lalurar. Jikin yarinyar ya matsa sosai ana magani kamar ba ayi sai da takaisu ga kwanciya asibiti kafin ta samu sauki aka sallamo ta sai da umma tayi ta jininin kwanciya asibitin nan har ta gaji. Wai ni da wani zamu ji da fitinan umma ko da ciwon shamsiya mama nake kallo dake kwala tana shafa ma shamsiya magani. Ban san lokacin dana bude baki nace kai umma fada fada wallahi da sauri mama ta dago kai da fuskan ta dake shabe shabe da hawaye tace kul kul na kara jin wanan maganan a bakin ki. Da sauri na ja bakina nayi shiru don tsoron fushin mama a kaina na fice daga dakin simi simi dani zuwa waje na rakube don tsoro. Da kyar Allah ya taimaka shamsiya ta fara mayar da jikin ta a hankali sauki ya fara samuwa wa yar kanwa ta har ina daukan ta muna dan fita mama ta samu tayi aikin da zatayi. Zuwa makarantar kauye sai a hankali don sai munga daman zuwa muke zuwa idan kuma bamu ra,ayi umma tace a barmu karatun ya mace ai ba dole bane sai mace tayi karatun zamani. Nafi kowa son zuwa makaranta don haka tsana na da take ya karu a wurin ta sosai har da mahaifina data haifa takan hada tayi masu gori idan bakin halin nata ya tashi. Kowa a gari yasan halin umma da fitina don haka mutane ke kiyayan ta sai wanda Allah ya nufa ya fada tarkon ta ranan zai sheda fitinan ta. Tana matukar son matar baba kabiru da yaran shi duk daba wani dadin take samu ko biyaya a gurin matar ta baba kabiru ba. Yau mama wanki take yi don rashin lafiyan shamsiya ya hanata tayi muna wanki kwana biyu haka yasa mama tayi ranan kare girkin ta da ta saba gamawa a cikin lokaci. Umma na tashi daga barcin da ta dan yi na rana wanda a saman gira take yin shi don ko kaza ta gitta ko dogon motsi ta sani balle wani yazo yana magana da mahaifiya ta sai tace gulmanta suke yi. Ta fito daga daki tana gyara daurin dan kwalin kanta takai duban ta gurin girkin mama din tace wai ni ba a aiko min da abinci na bane yau ko ban samu bane don banda hakki a ciki. Mama ta dago daga duken da take tana fadin umma ban karasa bane yau wankin kayan yaran nan daya taru nake yi kwana biyu ban samu yin wanki ba don jikin shamsiyan. A,a dai inji umma don dai ba uwarki nake ba yasa zaki barni da yunwa har wanan lokaci da kinsan darajana da mutunci na ai ba zaki maida hankali gurin wankin kayan diyan ki ba ki barni da yunwa. Murya a sanyaye mamatace umma kiyi hakkuri iccen ne baya kamu sosai taja tsuki tace haka kuke ai matan yanzu da shegen kiuya gurin aiki. Kwala min kira tayi in zo in karbo mata goro wurin mai tiredan unguwar mu inda take saya sai da tayi min kashedi tare da dangwara ta mika min kudin goron. Illar ya jani ina fita na hadu da kawata hafsa an aketa tace in rakata idan mun dawo sai mu sayo goron mu kaiwa umma har naso na kiya don tuna halin umma . Sai dai jin gidan da zata yasa nace muje in rakata din don ina son zuwa gidan kanwar mahaufiyar hafsa gida ne daya fi ko wani gida a gari kkyau gashi idan munje bamu fitowa sai ta bamu wani abu da bazamu manta mun je gidan ba. Mun zauna harda cin abincin mu hankali a kwance kamar ba nice masifafiyar kakan mu ta aika ba tare da jan kunne kada in dade gurin aiken nata sai gashi duk gidajen dake makwabtaka damu umma ta shiga nema na ance ban shigo ba. Sai da muka gama kwadiyan mu muka tun karo gidane na tuna da zancen aiken umma gabana ne ya fadi na lalaba aljihuna naji gudin suna nan inda na aje su kudin da aka bamu ne na kara na sai mata goro manya guda uku na tunkaro gida da murna na. Ina sallama ta lalayo min wani uban ashar sai da na girgiza tazo kamani na gudu ta buge baba kabiru dake dakin shi ya fito yana asha subbanallahi umma ya akayi haka ya faru kuma. Ta mike da kyar tana fadin banda yar banzan nan da na aika tun dazun ta sayo min goro nan da shagon awali mai tireda ta tafi gantalin ta sai yanzu na ganta. Juyowa yayi gare ni inda nake tsaye ina kyarma cikin sanyin murya yace hadizatul kubura ina kika je da umma ta aike ki ne tun dazun. Dan kwala na fara kiu,kiu da idona ina kyarma a cikin inda inda nake fadin hafsa ne tace in rakata gidan mai kare an aike ta tana jin tsoro shine muka je tare. Baba yace watau kice baki jin tsoron karen ko hadizatu nayi narai narai da manyan idanuwana yace kinci abinci kai na gyada mai yayin da umna ke fadin ina fa taci tun kan muguwar uwata ta kare muna girki na aike ta fa. Haba umma may ye laifin saude a wanan magana don da zaki tona zuciyar saude da kinga rashin jin dadin abin da yarinyar nan tayi yanzu. Kiyi hakkuri umma tunda bata taba aikata hakan ba yau ne ta fara don Allah kiyi hakkuri kada ki dake ta. Wani kallo tayi wa baba din dake magana a cikin tsigan lalashi tace gidan uban wa kika ci abinci bakin ki haka duk maiko. Na dukar da kaina kasa ta kara daga murya tana tambayana da karfi da sauri na dan girgiza tare da fadin can ina nunawa da hannu. Oh kin fara yawon kwadayi gidajen mutane ki nuna wa duniya ubanki ya watsar daku a gari kuna gararanba kai kai haba umma wanan maganan haka ina yafito maki kuma haka ,? Dan naki ne yaje yawon gararanba ya watsar da iyalin shi da yawon gararan ba yake zai dawo muna da abin arziki idan ya tashi dawo haka. Umma idan wani ya fadi haka yaya zaki ji a matsayinki na mahaifiyar mu duk gari an san ida yake ansan kuma aikin da yakeyi a can. Jikin ta ne yai sanyi don itama din dai tuntuben harshe tayi wanan maganan ya fito saboda masifan ta har ta kai ga fadin hakan. Ta kama kamay kamay tana fadin bafa haka nake nufi ba yaya zan wa dana wanan kalamin da ita dai nake da wanan mai manyan udanuwan nake magana tana nunani inda nake tsaye. Ina aiken da tayi maki baba yake tambayana ledan dana dunkule na saka a aljihuna na ciro na mika mai ya karba ya mika mata ta karba tare da kutawa tana fadin yau kin kuru wallahi. Tana magana tana kallon goron nace na hada da kudin da hajiya ta bamu na sayo maki duka rufa min baki tace cikin tsawa na dan kara ja da baya. Umma har yanzu fadan bai kare bane duk da kudin da ta samo wurin rakiyan aiken ta nayi da zata ce ta cika min. Juyawa baba yayi gurina yana fadin ke kuma daga yau idan kin kara wuce wurin da aka aike ki sai na yanke maki kaunan ki gidan nan da sauri na daga kaina alaman naji ina kyarma yace shige shiyan ku maza sai da yaga na shige wurin mu ya ja ya wuce. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:45 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI NA 🙆🏼‍♂️ 3️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA MARUBUCIYAR TAKARI TARKO FUREN JUJI SARAUTAR MATA, ALOKACIN MUKE, MARUCIN KAN DUTSE, BAHAGO, BA MU KADAI BANE, MIJIN BUZUWA, DA KANIN AJALI. MAI SON NOVEL DINA ZATA IYA NEMA NA A WANAN LAYIN 080 36959257 KO 090 36938192 DON TURA KUDIN NOVEL ZAKI IYA TURAWA A WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KAN DARI UKU KO WANI LITTAFINA DON FADAKARWA DA NISHADI. NAGODE DA DAMAN KU DA KUKE BANI A KULUN ALLAH YA BADA IKON SHIGA DON JIN RAYUWAN WANAN BOYAR ALLAH. WACCE KEDA LABARI DA TAKE SON A HASKA MA YAN UWA MATA SU FARGA ZATA IYA NEMA NA TA WANAN LAYIN DAKE SAMA DON BANI LABARIN TA IN HASKA MATA SU FARGA., , , , Mama mace ce mai tsabta da tanadi yau ma kamar kulun tana tsakar gida tana gyaran guraren da take da ikon gyarawa har ma da wanda ba nata ba ta gyara idan gyaran ta ya tashi. Ta gama ta dora girki ba dai wani girki bane dan kullun ne tuwon masara ko na dawa sai wani lokaci jumma,a ake girka shikafa da wake muda nama sai idan sallah tazo ko Allah ya tsaga zamu ci . Ta kare komai akan lokaci tace zata kitso bayan muma ta sance muna kawonan mu daki ta rufo muka nufi gurin umma tayi mata sallama. Don gidan kitson namu a makwabtan mu ne ba wani nisa sosai a kofan shiga wurin umma taja ta tsaya tana mata sallama kamar ba zata amsa mata ba sai can tace a dawo lafiya. Kitson shuku akaiwa maman mu inda mu kuma akai muna zanen yawo na hannu ta biya kudin kitson muka dawo gida. Lokacin har anyi sallah azahar ko a gagauce mama tayi sallah don ta makara saboda kitson da aka tsaya mata. Sai da ta idar da sallah ta bamu abinci muka fara ci tare da ita muna tsaka dacin abincin ne mukaji muryan umma da itama shigowan ta gidan ke nan daga makwabta. Take fadin umma mun dawo tun dazun sai yanzun kuka shigo kamae kitson wata mai miji a kusa mama dai sai murmushi tayiwa umma din ta fara aikin ta na tsakar gida. Kafa dare yai mata kuma ya zama matsala gurin umma da bata raina laifi mutum gare ta gab da zata karasa aikin ne muka ji sallaman mahaifina da isowan shi ke nan garin sai shigo mashi da kaya akeyi wanda wanan karon yafi na kulkun zuwa da kaya masu yawa. Murna da farin ciki muka shiga yi na zuwan shi duk gidan in ka debe mama da take kawaici kada umma tace bata da kunyan idon su. Baza ka iya gane farin cikin mama ba duk yadda ka iya fahintar ta don kawaici irin na mutanen karkara da kawar da kai ga komai. Dakin umma ya fara shiga ya dade a gurin umma din don kayanshi da komai da komai da yazo dashi , yana dakin umma din son irin karfin da take dashi akan diyan ta. Kira ya kwalawa maman mu dake kara gyara dakin ta don taron baban mu da ya iso garin a bazata sai gata ta shigo da saurin ta . Ba tare daya kalli fuskan umma ba ko jin wani dar din ta irin da yace kwashe wanan kayan da yaran nan suka tara min a nan kikai daki mana. Dan darr mama tayi don jin abinda umma zata iya fadi a lokacin sai dai taji shiru bata ce kalla ba har ta duka ta fara kwashe kayan zuwa dakin mu. Sai dai fuska da umma ta bata gashi babu halin magana don yadda mahaufin namu yai mata kwarjini a idon ta sosai ya waye ya zama dan birni babu alaman kauyanci a tare dashi. Tana kallo ba yadda ta iya haka mama ta kwashe kayan kaf zuwa dakin mu karshe ya mike yabi bayan ta zuwa namu shiyan . Zaune muke inawa shamsiya wasa ya shigo na mike da murna ina taron shi yace a, a hadiza kina gidan nan dama baki fita ba shine ban gan ku ba ? Banji nauyi ko kunyan idon shi ko kurciyane sai bude baki nayi ina fadin idan naje umma zata kore ni ne baba na bashi amsa da hakan. Kai ya jijiga shigowan mama dakin dauke da ruwan sha a kofi da ta kawo mai ya samu yin shiru daga ni har baba din ta aje a gaban shi tana mai sannu da zuwa. Kiran da umma tayi min ne yasa na bar dakin da sauri zuwa amsa kiran nata da fadan nan nata ta tare ni wai na fado mata daki kamar an koro ni saboda gulma. Aikena tayi sayen goro na fita da sauri nan na samu daman fada ma kawayena da ma wasu da ba sa,a naba da naga suna mutunci da iyayyena ina fada masu zuwan mahaifina. Ko da na dawo na samu baba ya bude tsaraban shi ba abinda ya dauke min hankali kamar lemo da ayaba dana gani a cikin kayan anfitar daga cikin buhun da suke. Mama tana ta famsn kakasawa mutanen gida ina shigowa tace in dauka in kaiwa inna da sauri na shiga kawai inda take fada min sai godiya sukeyi zan kai na karshe ne umma ta dakatar dani da kuma kwala wa mama kira. Mama ta fito da sauri tana fadin gani umma tace yanzu dan tsaraban da mijin naki ya kawo ne mu tada komada kike kwashewa mutanen gidan saboda neman suna. Eh ai ki kwashe tunda ganin abin kiyi daga sama baki san wahalan da yayi ya sayo ba a can muryan mshaifina ne daya fito daga wanka yake fadin. Haba umma waye bare a gidan nan ina duk a yan uwana ta raba wanan abin dai don Allah ki bar yin haka mana umma kamata yayi ki godewa Allah daya bani halin sayowa ai. Baki umma ta tabe ta shiga gyara goron ta da ta mayar kamar abincin ta ta saka a baki ba tare da tace mai komai ba. Yan gidan mu sai shigowa suke gaida baba da masa godiyan tsaraba wanda hakan yake mashi dadi sosai mu kan muna cin abinci barci ya kwashe ni a gurin . Washe garine ya zauna da yan uwan shi da umma din yake fada masu zancen aikin daya samu na dan sanda sunyi farin ciki dajin wanan labarin sosai sai umma ta tuma ta kafe da ita bata yarda da wanan aikin ba. Baba kabiru ne yayi karfin halin yin magana tare da katse umma din yana fadin umma da wani ya fada min wanan zancen ba zan taba yarda ba. Sai gashi a gaba Allah ya nuna min akayi ashe wanan ba bin farin ciki bane a gurin ki garin nan kaf babu wanda ya fara wanan aikin sai tsatson ki ashe haka ya zama abin alfari a gare ki. May ye amfanin yin karatun da kika jajirce muyi Allah ya fara kawo muna mafita da bakin ki zaki fadi wanan maganan yanzu. Kamata yayi ki sa mai albarka da fatan alheri Allah ya tsare ya kare ya ba da sa,a ya kamata ki fada mashi. Umma da bakin ki fa kike kokarin fadin rashin aikin shi takamaimai a can yanzun Allah ya kawo mai mafita zaki kawo wani magana kuma umma. Jikin ta ne yayi sanyi tace idan haka ne Allah ya tsare ya bada sa, a kowa a gurin yace amin nan yake fada masu bai dawo ba sai da komai ya kammala a gare shi hae gidan da zai zauna sai da ya samu a can . Da sauri umma tace amma kai kadai zaka zauna a can din ko baba kabiru ne ya karba da fadin haba dai ai gara dai yaje da iyalin shi a kusa dashi zaifi mai sauki da kwanciyan hankali. Baba yushau yace nima dai haka naga yafi mai sauki kaga muna mun samu wurin zuwa a birni ke nan . Kai rufe muna baki da wanan shirmay yana nufin da saude duk da yaran zai tafi ke nan baba kabiru yace kwarai kuwa don ya kama inda zasu zauna ma a can tun kan yazo din. Don haka tare zasu tafi ke nan idan zai koma baba yushau tace kai amma naji dadin Wanan maganan don ko ba za a barni a nan ba nima kafan ku kafana. Da sauri umma tace babu inda zaka tafi shidai din da iyalin nasa Allah ya sa aje a sa,a yakai lafiya . Sai dai zanso ku barmin kubura a nan mu zauna tare wanan karon mahaifina ne yayi magana yace umma zan so mu tafi da ita don su samu karatun zamani mai kyau a can don rashin karatun da basu samu a nan yana damuna. Wanan mara makarin wani karatu zata gane ko sunje can kayi fatan Allah ya baka diya maza su samu ilimin kamar yadda kuma kuka samu. Kowa cikin iyayyen nawa maganan yayi mai zafi sai dai babu yadda zasuyi da mahaifiyar tasu baba kabiru ne ya murje ido yace dani mahaifa na zasu tafi. Tunda aka fadawa mama zancen tafiyan mu take jin dadi a ranta ta shiga sallaman yan uwa da bokan arziki suna mata fatan alheri da murnan fita cikin kangin umma da suke kallon tana gallaza ma rayuwan auren ta. Mama bata dauki wasu kaya ba sosai don baba ya hana yace ko can din basu da tabbas din zama za a iya daga su ko wani lokaci don haka aikin su ya gada kamad fulani suke su. Wanan shine fitar mu daga kauyen mu asalin garin mu na iyayyen mu ka shigo birni sai dai idan munje ziraya kuma. Mun isa birni kano unguwa madawari baba ya kama dan gida madaidaici mai dakuna biyu da falo sai kicin da makewayi, sai dan tsakae gidan ba wani mai girma ba sai dai duk an shafe shi da suminti kamar dakunan. Kauyawa muka zama a gidan don har kayan kallo a falin an shimfida ledan kasa a ko ina na gidan ga yan kayan aiki da baba ya sayawa mama na amfani irin na yan birni da alama bada itace zata dinga girki ba a garin. Murna fal a zuciyana muma mun zama yan birni ina kallon yadda baba ke koya wa mama yadda zatayi amfani da resho da karamin gas din da ke kitchen din. Satin biyu aka sani makaranta sai dai ta gwaunati ce amma duk da haka akwai banbanci sosai bisa ga karatun garin mu. Baba bai dauki wani lokaci yana kaini makarantar ba har na gane hanya don baida isashen lokacin da zai rika kaini ya dauko ni. Da yake mama ba karatun boko tayi ba sai hakan ya rage ma karatuna gudu don babu mai taimaka min a gida idan an bamu aikin gida muyi. Sai dai hakan bai hanani kokari ba don Allah ya bani kokari sosai na fahintar abu hakan ya jawo min farin jini ga malamai da yan ajin mu. Idan na dawo gida da yamma nake zuwa islamiyan uguwar mu gurin daukan karatu sai shidda na yamma ake tayar damu. Mama ma ta shiga wani islamiya a nan unguwar suje goma na safe su dawo da sha biyun rana wanan karatun da mama ta shiga ba karamin ci gaba ta samu ba sosai. Don ta fara koyon rayuwan yan birni tana fahintar zamantakewa da mutane zan iya cewa mun dai fito birni ne don a nan ma ba ganin mahaufi mu muke koda yaushe ba. Haka na dai yafi muna zaman can din da fitinan umma sai da muka share shekara daya a kano baba kabiru ya kawo muna ziyara. Ranan nayi murna sosai da ganin kanin mahaifina ya kawo muna ziyara na farko a gidan mu wanda tun tarewa mu kanon zance bamu taba yin bako ba a gidan mu. Sai faman rawan kai nake mai yana dariyan jin dadi da ganin yadda muka sauya a dan lokaci mama tayi kyauta kamar ba ita ba ga dan matashin cikin dake jikin ta daya fara tasawa yanzu. Yana fada ma mama zai dan kai sati daya a wurin mu mukai ta murna da zuwan shi sai dare baba ya dawo daga gurin aiki. Yana shigo ya samu da uwanshi yazo duk da yarinya nake a lokacin naji mamakin kalami mahaifin nawa a lokacin don cewan da yayiwa baba kabiru lafiya dai kazo kabiru ? Walwalan dake fuskan shi ta sauya yace lafiya kalau nazo in ganku ne kawai mu sada zimunci da kuma zancen siyasan da zan fara. Maganar baba ya girgiza mama don cewa yayi ashe kana da kudine da har zaka fara siyasa dashi ya danyi murmushi yana gyara zama yace. Ina dai da rufin asirin Allah dana yan uwa don ko ina noma da kiwo sai ko dan aikin da nakeyi yanzun kuma na sake. Baba baiyi magana ba ya mike ya shige daki ya dauki lokaci a dakin ya barshi nan suna hira da mama a dan falon mu. Ya fito ya samay su hiran gida da mutanen kauyen mu sukeyi haf barci ya dauke ni a gurin a falo baba kabiru ya kwana. Nidai washe gari na tafi makaranta na dawo na samu wai baba kabiru ya tafi nace mama ba yace sati zai muna ba tace dani kin san halin mahaifin ku ai haka yake kamar umma idan halin shi ya tashi. Ban san lokacin da hawaye ya fara zuba min ba don har ga Allah banji dadin wucewan da baba kabirun ba mutumin kirki mai kaunar mu da gaskiya. Ranan haka na wuni sokuku har zazzabi yaso kamani da wuri na kwanta tun kan baba ya dawo gida ya shigo yayi abinda zaiyi ya kai kallon shi a inda nake yana tambayan mama har nayi barci ne yau da wuri haka ? Mama tace fushi nake babana ya suce bamu yi sallama dashi ba ya ja tsuki tare da jawo kulan abincin shi gaban shi ya fara ci. Kuyi hakkuri yau ban da caji yanzu na samu na dan tubuta wanan . .. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:46 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 3️⃣ A cikin dare ba dinga jin kukan mama sama sama tana magana abinda ban taba jin ya faru da ita ba sai yau ban san abinda ya falkan dani daga barci ba a lokacin. Sauraren maganan mama da na sama tayi a lokacin shine dan uwanka yazo gurin ka don ka taimaka mai koda da shawara ne. Zaka rufe ido kayi mai cin mutunci irin wanan ka tuna kabiru shine jigon mu a lokacin da ka barmu gida banda wanda nake dafawa inji sanyi sai yan uwanka. Tsawan da baba ya daka yasa na runtse ido daga inda nake ina ci gaba da sauraren fadan da suke wanda akan zuwan baba kabiru ne gurin mu. Yace ke ki rufa min baki don ba kece ke nema min abinda nake nema din yan uwana ne ba naki ba don ba a canzawa tuwo suna. Tana dina a iyalina nake yin shi ban sa rai ga abin wani don haka kowa tashi ta fitar dashi duk da fadin hakan da baba yayi bai sa mama tayi shiru wurin nisan dashi nauyin zumucin ba. Taci gaba da fadin idan baka nuna wa diyan ka tan uwanka ba sai yaushe zasu fahinci muhinmancin zumunci icce fa tun yana danye ake lankwasa shi. Mudin ya bushe ba zai taba lankwasuwa ba sai dai ya karye don bushewan shi duk abinda kake yi suna hankalta dashi suke koyi. Idon baba suka kankance kalamin mama yana mashi zafi a ranshi yasa gaskiya mama ta fadi yasan bai kyautawa baba kabiru ba don yasan dan uwa ne na gari a gare shi . Lalai ya tafka kuskure sosai wanda bai dace ace yayi shi ba ga dan uwan shi yadda ya fito fili ya nuna ba zai taimaka mashi ba. Ni dai har na sake komawa barci ban san lokacin da suka kare fitinan ba a kan baba kabiru din wanda duk da yake ina da karancin shekaru na gane abinda mama ke son nuna ma mahaifin mu din. Tun wanan lokacin ba wani dan uwan mu da ya kara zuwa inda muke mu din kuma ba gida muke zuwa ba tunda muka baro gida. Tun ina kewan mutanen gidan mu har nazo na saba da rashin su a tare dani yanzu har kakata duk da fadan ta sai ya kasance ina kewan ta yanzu sosai. Washe gari ta fito kamar ba ita ba ni kaina ban nuna mata naji abinda ya wakana a tsakanin su ba a daren jiya din. Sai dai har wanan lokacin akwai damuwa a tare da ita sosai bata da yadda ta iya kasancewan mahaifin mu mutum ne mai riko sosai akan akidar shi da aikata duk wani abinda yayi niya idan har ya fada hakan yake nufi har a cikin ranshi. Aikin hada abin karyawa take tana hawaye hankalinta duk a tashe yake tasa mijin nata yana tafka kuskure a rayuwan shi. Sai dai babu yadda ta iya da wanan halin nashi na nuna son kai ga yan uwan shi yanzun ne ya kamata ace ya saka masu da abinda sukai masu a baya sai dai wannan mumunan halin nasa ya hana shi hango haka din yanzu. Hawaye ne masu dumi suka kara zubo mata a gurin gaskiya ce yanzu daci ne gare ta don wanan abin kunyan da mijin nata yaiwa dan uwanshi da wani ido zasu kalle shi dashi. Murya na ne ya katse ta ina fadin mama ki bar kuka ki kyale baba ai baba kabiru ba zaiyi fushi damu ba don yasan bamu ne da laifi ba laifin baba ne daya kore sa. Ta kai idon ta kaina tana nazarin magana na ni dai din duk da karanci na nice abokiyar firan ta a gidan don baba ba mai zama gida bane shi. Tace yi maza ki shirya kada ki makara kin tsaya fadin abinda ba a tambaye ki ba don iya surutun ki simi simi na koma falo ina saka sock a kafana don karasa shirin da nakeyi wanda yanzu ni ke taimaka ma mama da shara da sauran yan aiyukan gida. Nagama daidai lokacin da ta fito dauke da kulan abincina falon da wanda zan dan karya kafin in fita zuwa school din don duk saurin da nake mama bata bari in fita gida ban karya ba. Don munhinmanci da yin hakan ke dashi a cewan manya fita gida baka saka wani abu a baki ba yana kawo wa mutum rashin sa,a. Ina isa cikin makaranta na a buga muna assemble don haka ban makara ba duk da ganin da nake da farko na makara din. Muna shiga aji ne zazzabin dake damuna a daren jiya ya dawo min sabo duk kokarin danayi na kannewa dashi sai da ya kada ni a school din haka yasa jikina ya dauki kyarma har mutane suka gane hakan. Dole aka bugawa mahaifina waya akan yazo ya dauke ni don banda lafiya ba, a dauki lokaci ba baba ya iso school din akabashi ni muka tafi. Bai kaini gida ba ya tsaya dani wani asibiti na karbi allura da magani ya wuce dani gida mun samu gidan a rufe mama ta tafi islamiya wurin daukan darasi. Waya ya kirata do ya sai mata dan karamin nokia don kira idan baya gida sai gata tana gani na cikin yanayin ciwo tace. Kin dauki tafiyan baban ki kin sa a ranki kamar wata babban muta ga shi har ciwo ya kama ki yanzu. Baba dake jin mu kala bai ce ba ta bude gida muka shiga ya shimfide ni a falo ban dade ba barci ya dauke ni a gurin. Sai da mahaifina yaga na samu barci sosai yake tambayan mama abinda ya jawo min zazzabin da nakeyi. Mama bata bashi amsa ba don zuciyar ta dake tafasa a lokacin maimaita tambayan yasa ta bashi amsa da fadin don babanta kabiru daya wuce bata sani ba. Kukan tafiyan shi ya haddasa mata zazzabi tun jiya take fama dashi ai, magani na bata taji sauki a she bai tafi ba. Batare da ya tsaya jin karashin maganan ba ya fice daga gidan sai karan tayar da mashin din shi taji ya tafi. Wasa wasa na kwana biyu ina fama da jikin sai da nasha allurai na mike tare da fadan baba dayai min idan na kara saka abu haka a raina sai ya yanke min kauna. Na koma makaranta naci gaba da karatuna yayin da cikin jikin mama yake girma bata kai ga haihuwa ba akai muna transfer muka koma katsina. Acan mama ta haifi danta na miji mai kama da mahaifin mu sak aka saka mai suna wan mahaifin mu daya rasu muna kiranshi da baffa. Mun samu sauyin makaranta don da za,a saka Shamsiya makaranta boko sai ka maida mu guri daya makarantar yana da tsada sosai. Hakan yai ma mama dadi sosai don ita batayi boko ba tana da gurin taga mu mun samu ilimin zamani don mu samu na dogara da kan mu. School bus ke daukan mu ya dawo damu a can ne na fara kawa bayan kawayena su hafsa dana bari a kauyen mu. Baba ya shigo gida ranan da fara,ansa sabanin yadda yake shigo muna fuska a murde wanda mun saba da hakan yanzu. Tundai ni da nake yar fari a gurin a gurin duk abinda nayi ba daidai bane a gurin shi zai rufe ido yayi min fada sosai kan abu dan kankani. Sunan mama yake kira sauden ta don basu iya saya suna kamar yadda mazan birni sukewa matan su ba duk da wayewan da yayi yanzu. Daga kitchen ta amsa mai da gani baban shamsiya don itace ta biyu da bata kunyan kiran sunan ta ya taka har zuwa kofan kitchen din. Bata kai ga fitowa ba ya samai ta a gurin tana tsane hannun ta dake da ruwa yayin da ni kuma nake a kitchen din ina rufe abincin da ta zuba a kula. Daga cikin kitchen din na gaida shi da dawowa da sannu da dawowa baba ya amsa min da yauwa hadiza maman ta ina mamakin farin cikin mahaifina a yau. Yace yanzu ina offoce din mu na samu sakon ashe kabiru sun lashe zaben da akayi a gida yanzu ya zama kansilan garin mu. Ba mama ba har ni dake duke ina aikin ban san lokacin dana sake ihun murna ba duk da a lokacin ban san kan aikin da ake fadin baba ya samu ba. Yaci gaba da fadin zaki sha mamaki isan kinji wa yanda ya kara dasu ya kuma lashe zaben mama tace lalai abin farin ciki ya samay mu. Ta juya da fadin kaga abin Allah yafi gaban mamaki wa zaice zaici wanan zaben haka a sauwake tunda bayi ya saba yi ba can. Ya gama bata labari ya fita ya barta nan tana mamakin shi kamar bashine dan uwa yazo wurin shi neman shawara ya muzanta shi ba a lokacin. Abinka da dan uwa bayan kwana biyu sai ga baba kabiru ya kawo muna ziyara har inda muke gurin aikin su baba ya tafi inda suka dawo gida a tare. Mama na daki tana gyara baba ya shigo gidan yana fadin ina maman yara take ne yau kina da bako a gidan fa ta amsa da gani nan baban shamsiya. Yace yau kina da babba bako da ke da yara mama ta kalle shi cike da kulawa tace bako daga ina kuma yace kabir ne yazo gashi nan falo a zaune yana jin ki. Cikin mamaki mama ke dariyan jin dadin ganin na gida a karo na biyu da baro gidan mu tun zuwan Shi na baya da suka rabu da mahaifina babu dadi sai yau da ya sake dawowa da uwa ke nan . Ta fito falon a cikin fara, a don ta tare shi da zuwa yana zaune yaci shadda dan uban su ya sauya sosai a yadda ta san shi a da can baya. Nan suka kaure da hira da tambayan ya bayan rabo tana mashi murnan samun karuwa da yayi sun dan jima tana tambayan shi mutanen gida. Kafin ta koma ta hada girki lafiyayye da cafanen da baba ya fita ya sawo don kanin nashi da yazo inda baba kabiru ke falo zaune da baffa daya sake dashi kamar ya san shi. Mun dawo daga school muka samay shi nan na hau murna sai shamsiya ne da bata waye shi ba s taki zuwa wurin shi ta make gurin mama. Kiran da mama ta kwala min ne yasa na bar falon zuwa gurin ta kitchen inda take aikin abincin abinci na samu tana hada masu. Ta nuna min tire tace in hada abinsha a cikin dan karamin fridge din mu dake aiki a kitchen din na shiga hada kayan data umurce ni akan tire din tana gyara min. Lemu su zobo mai sanyi sai ruwan sha na leda shima dai mai sanyi sosai kofina na dauko na jera na dauka na kai masu a falon namu. Inda na samu suna magana akan umma nayi sallama suka amsa mun cike da fara,a a fuskokin su a gaban su na kawo na aje. Baba kabiru ne ya dube ni yace masha Allahu diyar tawa tayi wayo sosai wallahi ai umma bata gane ki idan ta ganki yanzu. Kunya naji na dan tsone kaina na dago ina fadin baba umma ta bar fada ne yanzu cikin yarinta zalla nake mashi tambayan. Mahaifina ne yayi min dakuwa a inda yake tare da fadin tabar ma furera fadan cewa yar shi watau gwagona shigowan mama bayana dauke da kayan abinci ne ya katse maganan. Sai da ta aje take fadin wai yaya ake magana baba yace wai tambaya take idan umma ta bar fada yanzu. Juyawa tayi tana fadin ga mara kunyan banza idan bata bar fada ba ke nan baki zuwa idan mun tashi tafiya da sauri nace wallahi ina zuwa mama suka sa min dariya. Muryan baba kabiru naji yana fadin idan kin gama aiki sai kije kiga mota dama ita nazo in nuna maku kusa min albarka. Mama ta fadada murmyshin ta tana murnan jin abinda yace din da sauri ta koma daki ta dauko hijja din ta zuwa waje inda muka mara mata baya zuwa ganin motar. Munyi murna sosai da ganin motar baba kabiru din sai albarka mama ke sakawa tana taya shi murna yana jin dadi har cikin ranshi. Sai lokacin ya sauke muna tsaraban da ya kawo muna abin kamar da gayya sai da babana ya sauke kai ya dago yana fadin kabiru may yasa kai muna haka. Yana dariya tare da fadin wanan ba komai bane ai nan dai baba ya rasa abinda zaice ya shiga yi mashi godiya. Sunyi hira sosai ranan kafin ya tafi masaukin daya sauka ya kwana a can din bai sauka a gidan mu ba kamar yadda ya saba. Sai washe garine da yazo ya karya yake fadin a ranan zai koma mama bata so jin hakan ba don ta dauka zai muna dan kwana biyu ne a nan. Da zai tafi ne baba yai mashi alkawarin muna nan tafe idan babban sallah yazo a gida yake so muyi sallah insha Allahu. Baba kabiru yace daka kyauta don umma ta damu da maganan ku idan kai ba zaka samu zuwa ba kabar iyalin ka suje suga gida hakana a gansu suma. Bai jima ba ya ba mama kudi ta g itama ya bata tayi mai godiya ya tafi ya barmu da kewan shi tare da kewan gida. Bayan komawan baba kabiru ne mama ta dinga tayarwa baba da hankali akan tafiyan namu don taga baida niyar zuwan namu kuma. Wanan dalilin yasa dole baba ya mayar da hankali gurin fara muna shirin tafiya gida don mu dubu su, suma su gane mu ba wani shiri baba yai muna na azo a gani ba. Amma haka mama tayi ta godiya ga abinda ya hada muna din inda suka aje magana idan mun fara isa zai zo shi daga baya sai mu dawo tare dashi. Bata ki ta hada kan mu munyi kumshi da kitso da duk wani gyara daya dace mace tayi idan zatai tafiya mun fito shar damu da kanshi ya kaimu tashan da zata sada mu da garin mu don indan munje ba wani wahala zamu kai kan mu gida. Sai bayan magariba muka isa garin sai ganin mu akayi daga sama ance mai hali baya barin halin sa don umma maimakon tayi murna da ganin mu sai cewa tayi haka kwatsam babu sanarwa da zuwan mu. Mama ta hade bacin ranta ga maganan umma din ta shiga gaida ita nan mutanen gidan namu suka shiga zuwa taron mu da zuwa suna nuna jin dadin ganin mu. Lokacin na dan kara tasawa ina aji biyar na primary don haka yan garin mu ke ganin na girma sosai a lokacin na isa budurwa a gurin su kowa yazo maganan girmana yake yi. Yadda matar baban mu na lagos suke zuwa ana kallon su muma haka muka koma a gurin yan garin mu don har zuwa ake kallon mu wai hausan mu daya canza yanzu. Mama sai faman raba dan tsaraban da tayo take yi masu wanda sai yanzu na fahinci hikimarta nayo wanan tsaraban har baba na fada da ita wai ta dauki kaya da yawa. Ashe da shirin ta tazo gida do fitar da kanta kunya mun samu baba kabiru ya auro wata mace a birni yar boko itace amaryan baba yanzu dake tashe a gidan. Munje gidan kakanin mu na fannin mahaifiyar mu mun gaida su mun wuni acan tare dasu suna nuna muna so da kauna irin na kakani. Satin mu daya da zuwa gida akai sallah baba na wanan shekaran mun shiga mun fita don ba laifi mahaifin mu ya muna dinkuna wanda zai fitar damu daban da mutane garin mu. Mun fita tare da yan uwana mun zaga gidajen yan uwa da abokan arziki duk gidan da muka je maganan tufafin jikina suke wanda a lokacin ban gane may suke nufi ba. Ranan sallah da dare mun fita wasa tunda sallah ne ba a hanamu fitan dare lokacin wasa ake irin na kauye maza da mata. Sai ga wasu sun zo inda muke zaune saman dan dakalin kofar gidan mu yan uwan mu ne don zuri,an mu daya dasu nan muka buge da wasa dasu sai daya daga ciki yake cewa wai yana so na. Maganan daya bata min wasana na ranan ke nan na shige gida ina kuka tare da fada ma umma nan umma ta fita da tujara ta zage shu tas har iyayyen shi. Tare da fadin da safe zataje har gida ta yiwa iyayyen shi kashedi kan wanan wasan banzan daya tsiro min dashi don ni ban san wanan ba kada su lalatani. Ashe tun shigowa ina kuka suka gudu daga kofan gidan don sun san dama umma na iya fitowa taci masu mutunci . Can daga baya suka labe suna sauraren fadan ta har taci ta sude ta koma ciki ni a lokacin har nayi barci ban san shigowan ta ba gidan. Washe gari ma da fitinan umma ta tashi sai da baba kabiru yai mata waigi kan maganan yace haba umma kurciyane fa yana ganin shima yana zuwa birni yana karatu. Don yace yana son ta ai ba ana nufin shine son ba ko dole taja bakin ta tayi shiru don taga ran baba kabiru din ya baci yanzun ko ko dan ka ne idan yana da hali tsoron saba mashi kake ji. Munyi hutu tun muna saka idon zuwan baba shiru baba bai zo ba har muka share wata da kwanaki shiru baba baizo ba. Tun mama na damuwa da rashin zuwan shi akan lokaci don karatun mu da zamu rasa don rashin zuwan shi zai iya kawo illa ga karatun namu da mukeyi a can. Sai dai shiru har wanan lokacin tun tana dan maneji da dan kudin dake hannun ta har komai ya fara yi muna tsaye sai dai baba kabiru yana yawan taimaka mata sosai ta fannin abin amfanin yau da kulun da abinda zamuci. Haka yasa damuwa ya rage a zuciyar mama din don dan abinda take samu na taimako a wurin dan uwan baba din a yanzu ba kamar da can baya ba. Dadai taga zaman ba mai karewa bane haka yasa ta dan fara sana, ar mata na cikin gida don rage zaman banza ga irin sana,an data ga anayi acan inda muka fito. Mu kan bamu da wani damuwa ganin yan uwa ta ko ina bai barmu mun shiga damuwa kamar yadda mama ta shiga ba sai dai wanan Jamilun yana matsa min har yanzu a rayuwana. Rana kasuwa garin zai dan sawo abu ya aiko mun dashi a boye umma bata sani ba don masu kawowan sun san halin umma har su zata iya yaga idan ta gani. Haka yasa a can wani lungu suke ajewa sai suzo su kirani idan na fito su bani sai in hau kuka suna dariya zasu cinye a gaba su koma suce sun bani na karba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:46 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 5️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Zaman gidan da mukayi baba kabiru ne yake tallabe damu da lalurorin mu bai taba nuna gajiya da abinda yake muna ba komai zai sayowa iyalin shi tare da namu ne. A hankali muka fara shakuwa da jamilu don gurin wasan mu daya ne dasu ba wani fin mu girma sukayi ba sosai dan abinda ya saka shakuwa a tsakanin mu shine. Karatu zamu zauna mu dinga fadar kalman turanci ina fasaara masu suna jin dadi ko in fada masu wani kallama yadda ake fadi da turanci. Ranan kwatsan sai ga mahaifin mu ya dira gari murnan ganin shi gurin mu ba,a magana ba laifi yazo ya nuna ma yan uwa da abokan arziki kauna a garin. Inda yake sheda ma umma da yan uwan shi samun sauyin wurin aiki ya samu yasa bamu ganshi da wuri ba don lokacin mun share kusan wata shidda a gida. Don haka tare dashi zamu tafi idan ya tashi tafiya haka yasa muka fara shiri inda ba wani shiri sosai mukayi ba don ba wani abin mama ke da shi ba da zata dauka anan. Satin shi biyu hutun daya samu ya kare don haka zamu koma jamil ya rubuta min wasika shifa da gaske yana so na ba wasa yake ba kada in manta da shi idan mun je. Ban dauki takardan dawani muhinmanci ba don haka na tura a kasan bage na kawai muka dauki hanya sai garin abuja inda can yanzu aka mayar da mahaifin mu. Kubuwa ya samu gida inda zamu zauna wani quaters ne da mai,aikata ke kamawa a cikin su ya samu ya kama daya muka tare a ciki. Kamar gidan da ya saba kamawa ne dakuna biyu sai falo da makeyi da kitchen sai karamin filin tsakar gida kin dai san yadda zaman bariki yake a birni. Satin mu biya muka shiga wani makaranta sai dai an mai dani baya ga karatuna don a katsina zan shiga primary five ne sai nan suka mayar dani primary four. Banda matsalan karatu don bawai na daga Allah ne don haka nake saurin haddatace duk abinda aka koya min da sauri a kaina. Ba laifi don mahaifin mu yana wadatar damu da abinci da sauran abubuwa sai dai fannin sutura ne bai faye muna tufafi ba akai sai sallah yake sai muna tufafi. Mama na zama da makwabtanta lafiya saboda rashin hayanitar ta don ita haka Allah yayi ta bata faye shiga jamma,a ba sosai. Don haka irin gulman bariki din nan da akeyi bata daga cikin masuyin don rashin hayaniyar ta tana gidan ta a ko wani lokaci. Idan kaga mahaifiyan mu bazakace itace matar mahaifin mu ba don idan baki manta ba na fada maki mahaifin mu farin mutum ne dan gaye sosai mai jin lokacin shi. Sabanin mahaifiyar mu da take baka yar kauye mara jiki ba wani kyau ne can da za a fada ba a kanta haka yasa matan bariki suke kawowa mahaifin mu hari kamar yadda sukewa maza idan sun shiga bariki. Ko baka da kudi zaka samu mata bila,adadi iya yadda kake so wanan bai dauke hankalin mahaifina gare su ba don ya tsaya ga iya iyalin shi. Akwai wata makwabcciyar mu ma,aikaciya ne da idan ta dawo aiki take shigowa gidan mu tana hira da maman mu daidai lokacin da tasan mahaifin mu yana dawowa a wurin aiki. Ashe ita mahaifina take kyarkyara a ranta ga kudi da take kashe mu idan taga abu zata sayo muna zata kaimu kitso har mama itace ta gwada mata gidan kitson mu. Sosai mama ta sake da wanan matar da sunan tana musulmane amma addini bai zauna a kanta ba sosai don mama tana yawan mata huduba sosai akan addinin ta. Shakuwa ce mai karfi a tsakanin su don har harkan da take da wasu maza takan fadawa mama idan mama taga rashin dacewa da abinda tayi takan mata nasiha akan abin. Ranan kanina baffa baida lafiya har yakai an kwantar dasu asibiti an basu gado yasa aka barmu gida daga mu sai mahaifin da idan ya dawo yake zama damu. Idan ya tafi aiki ko asibiti muke komawa mu kadai a gidan, kwana biyu da zaman su mama asibiti ranan matar da muke kiranta da anty sady ta shigo take tambayan mu har yanzu ba a sallamo mama daga asibiti ba nace eh ance sai an kara ma baffa jini kuma. Take tambayan mu a can mahaifin mu yake kwana nace a, a agida muke kwana tare dashi can mahaifin mu ya kusa dawowa gida daga asibiti sai ga anty sady ta kwankwasa gida na bude mata ta shigo. Nan ta zauna damu tana hira wanda ni hiran nata yayi min nauyi sosai amma haka muke ta hiran har barci ya dauke mu muka barta a zaune tana kallon tv. Can mahaifin mu ya dawo sai ya samu gida a bude da fushi ya shigo da zuman muna fada sai anty sady ya gani a zaune tana kallo munyi barci. Da mamaki yake kallon ta tace mashi sannu da zuwa ya mai jikin fa fuska daure yace da sauki don kallo daya yai mata ya kawar da kanshi gare ta saboda shegen kayan dake jikin ta rabin jikin ta duk a waje yake. Mikewa tayi ta dauko mai ruwa da abincin data girka ta aje a gaban shi yana zama ya dago yana kallon ta tana wani farr da idanu tana kada jikin ta ko ina rawa yakeyi. Wanan kuma daga ina ya tambaye ta tace nice na dafa don ka na dade ina son wanan daman da zan samu kebewa dakai in gwada maka irin yadda nake jinka a raina. Kina da hankali kuwa ya fada ta dago daga inda take zaune tazo inda yake cikin wani tako na yan iska tana kokarin ruguman shi. Cikin zafin rai ya dago ya wanka mata marin da sai data dafe kuncinta don zafi yace stupid idiout ki fice min daga gida banza kawai. Bata dadara ba ta kara yowa cikin shi zata kara rungumar shi tana fadin na kasa controling din kaina akanka ba komai naka nake bukata ba ka yarda dani kawai shine muradina. Mikewa yayi ya turata waje tare da wulgi da kayan abincin suka bare can ya rufo kofan gidan da karfi ya dawo yana mai sake tsuki. Ranan ta saka shi kwana a cikin bacin rai don har ya kwashe mu yakai mu dakin kwanan mu ya dawo ya kashe kayan wutan falon ya kwanta ranshi a bace yake. Da safe da muka tashi nayi gyaran falon mu da na saba yi duk safe kafin in wuce school ya hada muna breakfast da kanshi muka karya a gida muka je da wani. Mun dawo gida da yamma mun samu an sallamo su mama daga asibiti har ta gyara ko ina na gidan ya koma fes dashi badai tsabata ba a gurin mahaifiyar mu kan don bata son kazanta ko kadan. Wata makwaciyan mu ne ta shigo duba jikin baffa sun dan taba hira da mama a cikin hiran take fadawa mama tayi hankali da anty sady don bata yarda da ita ba. Don sun dawo cikin gari da mijin ta da dare sosai ta ganta ta fito gidan mu alhalin tasan mama din bata gida. Mama bata dauki wanan wani abu ba sai take ganin ai don dai mutuncin dake tsakanin su ne kawai yasa tazo gidan don duba yara. Kwana biyu sai ta dan lura baba baya son zancen anty sady sam ko ya dawo ya samay ta a gidan tana gaida shi baya amsa mata zai kama fushi har ta tsagu ta fita. Ranan ma haka ya kasance bayan fitanta muna falo dayaji firanta ya fito ya zauna a falon sai mama tace ban san abinda yasa kakewa matar nan haka ba yanzu idan ta shigo gidan nan. Wani tsawa ya daka mata tare da fadin ko ke idan baki fita harkanta ba sai na saba maki rai don ban son alakan ki da irin yan iskan matan nan don haka ki fita harkan ta. Kada in sake ganin takawo wani abu a gidan nan kin karba idan na ga haka zan saba maki sosai kinji na fada maki gaskiya. Baidai fito fili ya fada mata abinda ya faru a tsakanin su ba sai wanka da kamar jurwaye da yai mata kan anty sady kawai haka yasa mama shiga damuwa sosai a ranta yadda zata kakabe ta a jikin ta alhalin itace ke binta. Don gudun bacin ran mahaifin mu dole mama ta fara sakewa anty sady din ko ta shigo sai ta tsiri aikin karya da zai dauke mata hankali har ta gaji ta wuce don kanta. Da anty sady ta fahinci haka da kanta ta jaye a gidan sai dai can takan shigo jefi jefi neman wani abu ko tace tazo gaida mune. Shakaran mu biyu a madalla har mukai comman intrance na shiga secondary school na gama primary dina ke nan sai gaba zaman gida nake ban fita ko ina sai islamiya da muke zuwa wanda ke da dan nisa sosai da gidan mu. Ranan amaryan baba kabiru ta shigo abuja wurin yan uwanta sai gata a gidan mu muyi murna sosai da ganin ta itace ta farkon zuwa wurin mu a cikin yan uwan mu na gida. Kwanan ta biyu a wurin mu naji kamar kada ta wuce yarta ko yaushe tana gurina ina giyon ta ranan da zata tafi nayi kuka sosai da tafiyanta. Saboda ban raina abin kuka bayan tafiyan ta da kamar wata biyu na dawo daga islamiya na samu mama tana ta hada kayan mu da mamaki nake kallon ta ban hakkura ba na tambaye ta. Take fada min baba yace zamu tashi mu koma garki ne sai naji ba dadi a raina ko ina sai mun saba da mutane sai kuma mu tashi. Wurin tone tone nane na tono takardan da jamil ya bani da zan mu zo abuja din na dauka na bude karo na farko da kyat na iya karanta abinda ke cikin takardan wanda a lokacin na fara fahintar may yake nufi dani. Ranan haka na kwana karanta takardan a boye kada mahaifana su gani barci ne ya dauke da takardan a hannu na har baba ya shigo dakin mu ya samay ni dashi. Ya dauka ya karanta sai da kanshi ya daure don ganin takardan da yayi da alama kuma takardan ya dade don har ya fara canza launi don ajiya. Dukan da naji ne a cikin barci ya falkar dani a gigice uban wa ya aiko maki da takardan nan yace dani sai lokcin na tuna da zancen wani takarda . Cikin inda inda nake fadin baba baba Jamilu ne na gida ya bani shi da zamu zo shine shine sai yau na gani ban san may ya rubuta a takardan ba nima. Ina karantawa ne ban gane ba barci ya dauke ni idon shi yai ja yace koma ki kwanta ya fita falo wurin mama da takardan a hannun shi yana fada. Yana fadin yaya tayi sakaci dani haka har maza suka fara min wasika har nawa nake da zan fara samun wasikun maza haka. Rantsuwan duniya mama tayi mai akan takarda yai fadan shi ya kare ya fice sai da safe ne mama take min fada akan takardan na nuna mata ban san ko na may ye ba nima. Mun koma garki wanan gidan yafi duk gidajen da muka zauna a baya girma sosai ga gari muna gani komai da zamuyi a saukake mukeyin shi gurin. Nan ma mun hadu da abokan arziki da dama inda mama har tana sa,a a nan tana sa kankara yan sari na zuwa suna kwashewa. Naci makarantar bowari Abuja na kwana don haka boarding zan tafi karatun secondry dina sai faman shiri ake muna don tafiyan na can din. Ban dade ba na tafi karanta inda kowa yasan dan aji daya irin wahalan da yake fuskanta farkon zuwan shi makaranta haka nima nayi ta fuskantar wanan daga mutane . Mun dawo hutun farko ina ta dokin ganin mahaifana da yan uwa na a gida sai na samu mama da ciki kuma a jikin ta. Bandai yi magana ba sai binta da kallo da nakeyi idan ta gilma har ya kai ta tsargu tayi min magana tace ai kila in haihu kuna makaranta wanan karon. Nace lah mama kina da ciki ne dakuwa tayi min na kama dariya tace wanan manyatacen kallon da kike min na maiye shi in ba cikin kike kallo ba. Na kama dariya ta wuce ina ta murnan zamu kara yawa a gidan mu muma har hutu ya kare na koma mama bata haihu ba. Da mahaifina yazo min visting yake fada min haihuwan mama ta samu namiji har anyi suna ko nayi ta murna da dokin son ganin jaririn da mama ta haifa din. Sai da aka samu hutu muka je gida inda mahaina ne ke zuwa dauka na sai gashi na ganshi yazo da mota. A hanya ne yake fada min ai yasai mota bayana itace wanan din da nake gani nayi ta murna ina bin motar da kallo a cikin farin ciki. Mun isa gida inda na samu mama ta shiryawa dawowan nawa haka muke cikin son juna da kauna na karbi dan kanina dake kama da mahaifin mu sak wurin kama. Yaron ya shiga raina sosai a wanan hutun mahaifin mu yazo gida sai dai wanan karon shi kadai ya samu zuwa bada mu yace sai mun samu long voccation zamu tafi tare da mama. Yaje gida yayi masu abin arziki sai dai shi baba halin yahudawa gare shi kyautan shi sai sa, a mutum ke samu wanda ba a zata ba yake samun alherin sa da zai dawo ya dawo tare da umma don taga inda muke zaune. Mun ji dadin zuwan umma din mama ta kama ina aka saka da umma din cikin jin dadi da so da kauna hutun mu ya kare a nan nabar kakan mu na koma makaranta. Yanzu Alhamdullahi iyayyen mu sun samu walwala kamar a gariki arzikin baba yake ga karin girma da yake samu a gurin aikin shi haka yasa muke tasowa a cikin jin dadi sosai. Bamu da sauran damuwa ko kadan a tare damu komai a wadace mukeyin shi watan umma uku a wurin su ta koma gida dauke da abin arziki mai yawa. Wanda hakan ya faranta ma mama rai sosai ta koma gida cikin jin dadi ga abubuwan da baba ya saya mata a can mota guda ya dauka zai kaita har gida ba tare da kowa ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:46 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN A JALI 🙆🏼‍♂️ 5️6️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Yanzu zance alhamdullahi a gurin iyayyena don mahaifin mu ya samu ci gaban rayuwa sosai ya samu karin girma a gurin aikin shi. Baba kabiru ne a cikin yan uwa yakan dan leko mu lokaci lokaci har tsawon shekara uku bamu je gida ba rasuwan kani mahaifin mamane mun yi hutu a lokacin muka shirya zuwa gida. Alokavin mu hudu ne sai kannena guda uku mun tashi mu hudu ke nan wanan karon mahaifina ne ya kaimu gida da kan shi don muje ya samu gaisuwan shima don mai rasuwan yana kawu ne a wurin shi. Yasa shi zuwa don ba abu kadan ne ke kawo shi gida haka ba kai tsaye kwanan shi biyu ya koma tun mutane suna marmarin shi. Yana dawowa rayuwan gidan sai ta koma mashi wani iri sai dare sosai yake dawowa gidan da dan abinda zaici ya kwanta. Haka yaba matan dake son kai mai hari nuna kan su a gare shi yana watsar dasu don irin tarbiyan da suka samu tun daga gurin iyayye a gida. Muna gida mushiga nan mu fada can wurin ziyaran yan uwa ana ganin yan kanne na da basu sani ba don ni an fi bude ido dani a gida ni mutane suka sani sosai. Duk inda mukaje da dan abinda muke kai masu na fannin tsaaran ban da mahaifiyar mu ta dauko don yan uwa a gida. Mun samu baba kabiru da iyalin shi sun bar garin suna cikin birni a zaune don yanzu ya zama dan siyasa babba a jahar mu. Sai koma na jin dadi idan munzo gidan ya rage muna gidan ya koma ba dadi a gare mu don rashin kanin mahaifin na mu dake ina aka saka damu idan mun zo. Ya dai zo garin ya samay mu inda yai ma su mama alheri sosai bai kwana ba ya juya ya koma mama tayi mashi alkawarin zamu shigowa wirin su kafin mu koma. Wanan zuwan ne muka sake, kullewa da Jamil sosai nake dan tsayawa mu kebe a boye dashi ba tare da wani ya sani ba a gidan mu. Ba dai wani fira na iyaba a lokacin duk hiran na makaranta ne zamuyi kuma a tare da abokai na samu anyiwa wasu abokaina aure a gida. Hakan ke sa muna fakewa da zamu gidan su ziyara mu samu kebewa dasu a can sai mun dauki lokaci mu dawo gida. Ranan da rana ya baci muna ne umma ta rutsa mu a wurin da muke zama muyi hira dasu mun shagala muna tsakiyan hiran mu sai jin muryan ta mukayi kamar daga sama akan mu. Tana fadin muna fukan Allah ta,allah ya ya kama ku yau zuwa wurin Hannatu din ke nan da kukace zakuyi jikina yana rawa na dago da sauri ina neman hanyar guduwa. Tace kul kika fara kika daga daga wurin nan sai na bata maki rai yau kai kuma bari kaji daga yau daga rana mai kaman ta yau. Kada inji kada in kara ganin ka tsaya min da jika na bani ba irin gidan ku a zuri,ana har duniya ta kare mai na gaba yaci balle na baya ya lasa. Yanzu ba sai gobe ba gidan ku zanje in ma iyayyen ka iyayyaka dakai cikin zuria ta ke kuma wuce mu tafi mufuka banza da wofi kawai. Ta juya tare da fasa zuwa unguwar da zata tana gaba tana zagina Ainau da muke tare ta biyo ni ta juyo tace kul kika biyo mu sai na saba maki rai. Duk munafuncin nan kece mai kulla shi keda hafsa na sani ba yau ba kar nake kallon ku dama irin ranan nan nake jira gare ku. Banda lalacewa mai ya hada ki da wanan zurian marasa mutunci da tarbiya dama barewa bata gudu danta yai rarafe ai. Har muka kai gida tana saman bakin ta gurin fitina da tonon asiri wanda a lokacin ina jin kamar in magare ta ta bayan da nake binta don haushi. Lungin mu muna shiga take kwalawa maman mu kira ta fito da saurin don da jin kiran bana alheri bane an tabota ko wani abu ya faru. Mama na fitowa take fadin yanzu saude da sanin ki yar nan ke wanan iya shegen a gari haka yaron nan dana rabata dashi ashe suna tare har yanzu. Cikin mamaki mama tace umma wani yaro kuma tace dan gidan babbako mana shegen yaron nan mai son karyan tsiya. Karamin yaro ya dauki karya irin na ubanshi ya sawa kanshi tun yanzu gata nan can na tsura su wurin gidan wanzan sun labe suna zance da ita. Zance umma mama ta fadi a cikin mamaki tana mayar da kallon ta gurin da nake tsaye na sada kaina kasa da sauri don kunya da tsoron dake raina a lokacin. Ta juya tana fadin yanzu gidan su nayi gurin iyayyen shi ai mashi kashedi akan jikata bani ba irin zurian su a cikin kayana su sun sani dama. Umma kiyi hakkuri zan mata fada basai kinje ba muryan baba yusha,u dake dakin matar shi ne ya fito don jin abinda umma ke fadi. Tace kaidai barin je don da zafi zafi ake buga karfe kada yazo ya bata muna yarinya bamu sani ba don ba mutanen kwarai bane ka sani. Ya sake fadin umma yi hakkuri don mutuncin dake tsakanin mu dasu kinga duk gida ne nine ya kamata inje in tsawata mai tunda maganan mazane ai. Tace to shike nan tunda kace zaka amma duk na sake ganin haka ya zama dole in fada ma ubanki don yasan abinda kike zuwa nan kinayi. Da sauri nace don Allah umma kiyi hakkuri ba zan sake ba ko yanzu karatu ya tsayar dani ina koya masu shine kika samay mu tare a wurin ta daka min wani uwar harara sai da nasha jinin jikina don kallon da tayi min. Tsorona Allah tsorona ta fada ma mahaifin mu nasan dukan tsiya zansha kuma ya hanani zuwa gida idan mun tashi zuwa. Ranan duka nane mahaifiyata bata yi ba don ta nuna min iya bacin ranta itama sosai sai da na bata hakkuri sosai ta kyale ni sai dai ba wani sakin fuska a tsakanin mu. Haka har dare na nemi wuri na kwanta ba tare da naci abincin dare ba ranan ina tunane kala kala wanda duk haushin kakata umma nake ji a raina tunda itace ta hadani da mahaifiyata take wanan fushin dani haka. Ranan dai haka yazo min ba dadi tun wanan ranan ban kara fita ko ina ba koda yaushe ina gida da mahaifitya idan na fita sai dai idan naje wani lungu na gidan namu ne. Jamilu yabi duk hanyan da zaibi yaga mun hadu dashi amma abin ya gagara don kullun ina gida tare da mama da kanne na haka yasa yake turo min sako daga wurin su hafsa. Ban iya amsa mai don ina son in kiyayye kamar yadda mahaifiyata tayi mun kashedi a kanshi sosai na dauka kuma a raina. Anyi haka da sati biyu ne muka kai ma baba kabiru ziyara a local govenment din mu inda yake zaune da iyalin shi da matar shi ma,aikaciyar asibiti. Mun ji dadin zuwa wanan ziyaran don irin yadda baba kabiru yake nuna muna kulawanshi akan mu sosai wanda nina san mahaifin iya mu iyalin shi ne ya sani zai iya nuna muna hakan. Don ba damuwa yayi shi da nasu iyalin ba sam don ina yawan jin mama na mashi wanan korafin sosai idan dan abu ya hada su a gaban mu. Hakan bai sa ya canza halin shi sai ma cewan da yake shi ba haka nashi tsarin yake ba don kowa nasa yasani a yanzu idan bai muna tanadi ba wayake so yayi muna. Ire iten wanan maganan dai yana hadasu lokaci da dama don nasha jin suna wanan maganan wasa wasa sai da muka share kusan wata daya a gurin baba kabiru. Da zamu koma ma mahaifin mu shi yayowa waya kan ya samu a mota a dauki shata a dawo damu har abuja sai da muka koma gida mukai sallama da mutanen gida inda na dan samu kebewa a sace da jamil mukai sallama. Inda ya nuna min shifa da gaske yake maganan shi don haka in rike alkawarin mu idan munje can ni dai dariya nayi kawai ba tare dana nuna mashi wani alaman na yarda ba ko ban yarda da maganan shi ba. Wanan karon mun fi dauko kaya fiye da kullun idan zamu dawo wanda duk yawanci abin daga wurin baba kabiru ne ya fito don yin tsaraba dashi ga kayan daya dinka muna masu kyau dukkan mu har mahaifiyar mu. Mun sauka abuja lafiya sai washe gari ne mama ke nuna mashi kayan da dawainiyar da baba kabiru din yayi damu a wurin shi. Sai kallon kayan baba yayi yana fadin aiko kabiru yayi kokari sai dai idan yana hakan ai ba zai tara komai ba da mamaki mama ke kallin shi don jin furicin mahaifin mu din ta kasa hakkuri sai da tace mai. Wai kai wani irin mutum ne haka dan uwanka yai ma iyalinka abu haka na yabawa babu godiya sai wani magana can da bai dace ba haka , ? Murmushi kawai yayi tare da fadin ai dama idan zancen kabiru ne baki son a fadi a gaban ki ni gani nayi bai abinda ya dace a kanshi yasa na fadi wanan maganan. Ban dade ba na koma makaranta sai babane ya kaini da kansa don hutun dana kara yayi yawa bisa ga dokan makarantar mu sai da kyat suka karbe ni ma. A cikin wanan shekaran ne baba kabiru yakai mahaifiyar su saudiya ta sauke farali don itace ta fara kaiwa kafin shi ya tafi ya sauke nasa. Idan da son samu ne mahaifi yana da halin da zai kaita saudiya din sai dai baiyi dabaran hakan ba har Allah yaba baba kabiru ikon kaita ta sauke faralin. Muna ta daukin zamu je mu ganeta don muna dauka idan mutum yaje saudiya yana wani canzawa ne idan ya dawo. Ashe abin ba haka yake ba a fili ta aiko muna da tsaraban mu ta hannun wani mutumin garin mu daya gane gidan mu yake shigowa Abuja yin sana,an shi. Munyi murna sosai da ganin tsaraban zuwan da mahaifin mu yayi gaida umma ne yayi shawaran sayen fili don yai gina a garin da baba kabiru yake don nan ne local govenment din mu. Bai dawo ba sai da yaga komai ya kan kama na ginan ya dawo yabar baba kabiru da sauran aikin ginan gidan yadda yake son a tsara mashi ginan gidan. Akan ginan ne baba kabiru ya shigo Abuja wurin mahaifina munyi murna da ganin shi sai dai haduwan su baida dadi don bai koma ba sai da suka samu sabani sosai akan ginan da mahaifin mu. Don yace shi bai gane kan ginan ba don ba haka akai mashi lissafin komai ba kafin ya dawo wanan maganan ne ya tunzura baba kabiru din yai fushi ya fada ma mahaifin bakaken maganganu shima. Sai dai kafin ya dawo sai da mama tasan yadda tayi ta shirya tsakanin su dashi har ya hakkura ya karbi aikin akan zaici gaba da kula mashi da aikin a can. Washe gari ya juya ya koma sai da yai muna alheri sosai kafin ya tafi din muna ta murna da hakan shiyasa muke son zuwan shi ga kifi da sauran abin marmari dayazo muna dashi na tsaraba. Hutun mu ya kare na koma makaranta cike da kewan yan uwana dana bari a gida don sune abokan hiran nawa a gida tunda ba kawaye nakeyi ba ni. Karatuna ba wani matsala don baba yana alfahari dani sosai don bani cin na kasa da uku duk hutu don hakane ma nake samun kyauta daga gurin mahaifin namu. Matsalata daya da baba yawan ce mun banda wayo da yakeyi ko yaushe alhalin niko naga ina da wayau ai amma daga baba har mama abinda suke ce min ke nan danayi dan abu kadan yanzu zansha fada sosai a gurin su. Umma tazo ta kwana biyu a gurin mu lokacin na dawo gida na samay ta haka muka zauna a cikin tsangwama irin nata . Tsangwaman ta akainane da kanina baffa da yanzu ya tasa bai son zaman gida ko yaushe suna kwasa da baba akan fitan da yakeyi waje. Haka yasa itama zuwan ta ta karbe korafin da ta fita yanzu zata haushi da masifa ta bal,balleshi da masifa wai idan ya fita wanan garin da babu kai ba a gane gabas din shi don yawa. Ranan tare da da kanne na muka je bukin wani birthday sai ba a fara program din da wuri ba har muka kai dare muna can wurin wasan. Mahaifin mu ya dawo gida ya samu bamu nan nan ya hau mahaifiyar mu da fada don birthday din dan kawar tane muka je dan da kyat ya yarda mu tafi don umma ta saka baki yasa ya yarda muje din. Ya fita ya bimu a can ya samay mu ana sallaman mu don komawa gida sai gashi tun a gaban mai bukin ya fara bal,balan mu da fada tana bashi hakkuri. A mota ma mun shs fada sosai a furin shi inda duk laifin ani ya dora min don nice babba a cikin mu muna shigowa gidan umma ce ta tare ni da wani fadan kuma again har yafi na baba ma fadan nata. A cikin fadan take fadin da wanan wautar har kike son wanan yaron mai shegen wayau din da son banza da sauri baba yake tambayan ta wani yaro kuma umma. Ita hadiza din har take soyayya ban sani ba ni wai ma wani yaro ne take so din tace rabu da yar nema mara wayau kawai bata san sherin mutanen garin nan bane. Allah ya rufa muna asiri ya rabaku dasu kike son wanan dan banzan yaeon ya hure maki kunne wa yanda ke cikin garin ma mai suka zama har yanzu. Wani kallo nayi mata ta watso min dakuwa da hannun ta na noke kaina da sauri tace don na zage shi zaki min kallon banza ko ke gaki issasa ko ? Baba ya sake tambayan wani yaro ne wai take magana a kanshi tace bar yar nema ai na balbale ta babanta yushau kuma yaje yai mai iyaka da ita har gidan su. Don ubanshi yazo ya ban hakkuri har gida don yasan halina sarai ba kyalesu zanyi ba wurin mahaifiyana ya juya yana mata kallon tuhuma. Tayi saurin fadin ga umma nan ka tambaye ta idan da masaniyana haka ya faru din ta yi saurin kare kanta daga masifan shi. Kutawa yayi ya shige daki na koma na rakube a guri daya ina ganin kamar zai dauki matakine a kaina ranan. Umma duk abinta Allah yayi ta mace mai rikon ibada sosai dama ance mutum dan tara ne bai cika goma ba gata da yawan saka ma diyan ta albarka. Bata da sakaci da ibadan ta don ko yaushe a cikin lazimi take tana zikiri da sauran abin ibada daya dace mutum yayi a ganuwan shekaran shi ta karshe. Tun wanan ranan nake dari dari da mahaifina don ban san irin matakin da zai dauka a kaina kan maganan daya ji daga bakin umma din ba. Sai dai shiru har hutun mu ya kare muka koma makaranta na barsu a gida daya kaini tun a mota yake min fada mai kama da nasiha akan in mayar da hankalina ga karatuna sosai. Idan na gama zai kaini inyi kararun likita nan gaba kada in sa wasa in bata kurciyana ga banza har sai da nayi hawaye ba tare da ya sani ba. Lokacin vistinga da yayi ina saka idon zuwan yan gidan mu sai naga sabanin hakan sai babane yazo shi kadai wai sun tafi gida su. Banji dadin hakan ba amma sai na dake ina addu,an Allah ya dawo dasu lafiya ba karamin sayayya baba yai min ba a lokacin. Nasan duk cikin tsigar lalashine yasa yai min sayayya haka mai yawa bai jima a gurina ba ya wuce sai dana koma hostel ne nayi kukan tafiyan da sukayi wanan karon ba tare dani ba gida don ban san lokacin da zan tafi ba kuma. Mun dan jima wanan karon don candy da zamuyi na jinor waec sai da muka gama na dawo gida da kaina don yanzu ina da wayo na zan iya kai kaina gida da school din. Nayi murna da na samu sun dawo gida suna ta ban labarin gida da wuraren da sukaje ina son in tambaye su labarin Jamil babu daman in tambaya don mama dake falon tare damu. Da dare na ina shirin kwanciya baffa ya ban takarda wai inji Jamil yace ya kawo min tare da fadin bai bari kowa ya ga takardan ba ya boye min. Naji dadi sosai ga labarin shi da yake ban yace yanzu yana final year ne a inda yake karatun shi. Sai dana gama komai mun shige na fito da takardan na karanta gaisuwa ne tare da jaddada min irin kaunar da yake min din naji dadi sosai har cikin raina na samu wuri na boye takarda. Duk da takardan ya dade a wurin baffa kafin in dawo gida amma bai hana shi kamshin turaren daya zuba a jikin takardan ba daya rubuta. Na mayar da takardan abin dabe min kewa do duk dare idan zan kwanta zan dauko in karanta in mayar in nuke a inda nake adanawa kada wani ya gani a cikin iyayyena. Haka rayuwa ya dinga gudana muna jin dadi sosai a gurin mahaifan mu don duk wani abinjin dadi suna muna shi na nuna so da kauna gare mu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:49 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 7️⃣ ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI DA FATAN MUN WAYI GARI LAFIYA, YAN UWANA LITTAFIN KUDI NE MUJI TSORON SHIGA HAKKIN JUNAN MU DON ALLAH. MAI FAHINTA ZATA GANE MAI NAKE NUFI ALLAH YASA MU DACE YA KARE MU DAGA DUK WANI ABINKI DAGA SHERIN SHEDAN AMIN ALLAH TA BAMU WUNI MAI ALBARKA, , , Wanan dawowa gida ne danayi na samu mahaifina yana gina gida a garin abuja bayan wancan daya gina a garin mu wanda na samu yan gidan mu na ta dokin sabon gidan namu da zamu tare a ciki idan an kare ginan shi . Yau baba bai fita aiki don haka yana gida bai fito ba tun da safe sai mama ne takan fito jefi jefi ta duba aikin da mukeyi ni da kanwana dake secondry na jeka ka dawo don ita bata je bording school ba. Acewan mahaifin tayi karama sosai da zuwa makarantar kwana a shekaru ta gama yadda duniya ta koma yanzu babu yarda ta kowani fanni. Sai wuraren shadaya ya fito daga dakin kwanan shi muna falo muna kallo muka shiga gaidashi da kwana yana amsa muna tare da tambayan mu dalilin rashin zuwan mu islamiya yau. Nice na bashi amsa da fadin baba ka manta ance mu dinka uniform din makaranta idan bamu dinka ba kada muzo. Ya juya gurin mahaifiyar mu yana fadin may yasa baki tuna min ba na manta da zancen maganan uniform din nan gaba daya hankalina yana wurin aikin nan yanzu. Mama tace na tuna maka ai sai dai idan ka mantane amma ko shekaran jiya sai da na tuna ma ai kace kaji. Yace yana zama saman daya daga cikin kujerun falon yau insha Allahu idan na fita zan biya in saya maku ban son zancen rashin zuwa islamiya sam. Baffa ne yace da baba din baba idan zaka wurin ginan ka yau zakaje dani daga inda nake nace nima baba ina son zuwa inga wurun ban taba zuwa ba. Zanje daku yace amma ba yau ba don yau ba zan leka wurin akwai inda zan tafi idan na fita abinci yaci ya gama ya fita inda na mike na kwashe kayan na kai kitchen. Mama ne na gani zaune tayi shiru yasa na mayar da hankalina wuri ta tare da tambayanta abinda ya samay ta tace dani babu komai . Ashe aure mahaifin mu ya tarkato zai kara don yanzu ba zai iya zama da mahaifiyar mu ita kadai ba yana ganin yana a cikin lokacin shi. Kudi yana shigo mai ta ko ina akoda yaushe yadda mukaji labari wai wata yar uwarsu dake kaduna ne tayi mashi hanyar kanwar mijin ta zai aura. Aure rigirigi har yakai wani lokaci a dan zaman gidan da nakeyi baba ya kwashe mu har mama sai kaduna wai su sada zumunci da matar. Ran mama ya baci sai dai ba yadda ta iya don kalman zumunci daya fada zasuyi da yar uwarshi din yasa ta hade abinda ke ranta ta biye mashi akaje lafiya aka dawo lafiya. Ba a dauki wani lokaci ba muka ji labarin ashe har baba ya hade lefe kudi yaba wanan yar uwar tashi ta hada mashi lefe a can. Shine dalilin saurin ginan da yakeyi don ya samu kafin buki su tare da sabuwar amarya a ciki da yake mama mace ce mai hakkuri duk wanan abin bata yarda ta tada hankalin ta ba akan auren da zai kara din. Duk dako abin yana taba mata zuciya sosai sai take ganin kamar don yanzu ya samu ne yake son ya kara mata kishiya kamar yadda wasu maza da yawa keyiwa mace. Don wasu mazan sai su wahala da mace da zaran samu da yalwa yazo masu wanan matar da aka wahala da ita ta zama banza a gare su. A lokacin zasu fara neman wata wace zasu ji dadin rayuwa a morewa juna ke ko kin zama yar bi sai yadda akayi dake duk da tasan mahaifin mu yana kokari ta fannin kyautata ma iyalin shi din. Sai da fargaban ta shine bata san sauyin da hakan zai kawo a tsakanin su ba don anyi sau dayawa tana ganin yadda matar gida take komawa sai anyi dace da wace ta san Allah ake zaman lafiya yanzu. Duk wanan zancen auren da baba keda niyar karawa ba wanda ya sani a cikin yan uwan shi don haka bayan ya hada laifen shi ne. Yayi shirin zuwa gida don ya sanarwa umma da yan uwanshi zancen auren da yake son ya kara din nan bada jimawa ba. Umma ta nuna mai rashin jin dadin ta duk ko da yawan fitinan ta da mahaifiyar mu din anan kan umma ta nuna ma mahaifiyar mu gata don tas tayiwa mahaifin mu din. Sai da ya fadakar da ita abinda yake nufi da auren da yake son ya kara din sannan hankalin umma ya kwanta tayiwa mama nasiha ta kwantar da hankalinta indai tana raye bazata bari a cuta mata ba insha Allahu. Da haka hankalin mahaifiyar mu ya dan kara kwantawa don umma din data tsaya mata kan zancen tasan abinda ta fada haka yake don diyanta basu fi karfinta har lokacin. Da haka muka juyo muka dawo sai dai wanan tafiyan banji dasin shi ba don a cikin kwana biyu kawai da mukaje mukayi a gidan. Gashi ban samu ganin Jamil ba lokacin yana makaranta suna jerabawan karshe na fita secondry school ke nan Nikan damu da halin da nakan ga mahaifiyar mu a ciki na damuwa wanda nima yakan sani in damu a lokacin har nakan yi tunanen ko laifi mahaifiyar mu tayi mashi da zai kara aure kuma. Ranan dai sai da yakai na tambaye ta ko laifi mukayi wa baba zai kara aure mama ta dago ta kalle ni raci gaba da ninke kayan wankin da mukayi na kwaso muna a waje. Tace ba laifi mukai mashi ba ra,ayin shine kawai haka yanzu yaga lokaci yayi da zai kara ne don haka kibar wanan tunanen don ba naki bane a yanzu. Nan dai mukaci gaba da harkokin mu irin na yara ba tare dana kara bi ta kanta ba kuma, sai dai duk a cikin kwanakin haka nake ganin ta bata walwala idan na tambaye ta sai tace min ba komai. Na gama girkin rana tana daki na samay ta ina fada mata kai kawai ta gyada min har na juya zan tafi na juyo ina fadin in debo maki ne mama ? Tace bari idan na fito zanci kidai dibarwa kannen ki suci na amsa mata da to, na fice daga dakin ina kiran kanne na su zo suci abincin. Bayan na zuba masu ne sai sumaiya ta dawo tana fadin wai na zuba mata miya kadan sai ta kara nace ba zata kara ba. Muna cikin rikici da ita sai ga mahaifiyar mu fito daga daki tana fadin wai yaya haka ne mai ke faruwa daku ne wai ? A hasale nake mayar mata da abinda ke faruwa tsakanin mu kallo na tayi tana fadin yar kabiru ki zama mai hakkuri da kannen ki mana. Ki kara mata mana maye a ciki idan kin kara mata miyan ba akwai sauran miyan a cikin tukunyar ba, kara mata don Allah. Bayan na kara mata miyan na dawo na zauna ina hasalan dariyan da kaunan nawa take min muryan mamane yasa na dago kai ina kallon ta. Don cewa tayi keda zaki zama uwar su wata rana tun yanzu, kina nuna masu haka yaushe zasu girmama ki nan gaba kin riga da kin bari sun raina ki ko. Ki dinga binsu a hankali ki dauki girman ki gare su sai kiga sun koma jin tsoron ki suna daukan maganan ki da muhinmanci sosai ba raini a tsakanin ku. Nace nagode mama tace ba komai don Allah ki koyi hakkuri da yan uwanki don watan watarana kece dai babban su. Ta juya gurin da sumaiya ke cin abinci ta fara mata fada mai kamar nasiha ita ma ta nuna mata amfanin girmama na gaba gare ka. Ba tare da taci abincin ba ta mike don kiran sallah da ake zata je tayi sallah a lokacin na sake fadin mama abincin fa kada yai sanyi kuma ? Ta juyo a cikin yanayin rashin jin dadi tana fadin barin idar da sallah zan fito inci ta shige daki na bita da kallon tausayawa don na fara fahintar bata da lafiya ne. Sai dai tana daurewa kada mu fahinci halin da take ciki a lokacin abin yarinta sai ban mai da hankalina ba ga alamarin. Wasa wasa har yakai mama ga kwanciya asibiti ashe ciki ta samu yake mata wasa bai zauna ba shine take wanan wahalan haka. Ta sha jiki sosai da kyat ta sha wanan karon jikin bai gama warke mata ba na koma makaranta don jerabawan mu da ya fito sai dai na koma ba a dade ba don na dan jima ban koma ba akao hutu muka dawo gida . Abinda ya ban mamaki shine tunda na koma ba wanda ya lekoni a gidan mu har dan visting din da mahaifina yakan kawo mun na bazara wanan karon ba wanda ya leko ni . Sai dai ina shiga gida na samu tashin hankali don na samu mahaifiyata a cikin jin jiki sosai har yafi wanda tayi da farko wahala hankalin mahaifina yana a tashe shine dalilin rashin ganin shi da banyi ba. Wanan halin da mahaifiyar mu take ciki ya tayar muna da hankali sosai duk da yara kanana ne mu amma mun san mahaifiyar mu tana cikin wani hali mai muni a lokacin. Nafi kowa shiga tashin hankali a cikin mu don nafi sauran wayau don nice tunda na dawo na koma jinyar mama din don da makwabta da abokan arzikine ke jinyar ta. Dawowana sai komai ya dawo kaina nice girki nice kula da mahaifiyar mu din ga laluran kanne na wani lokaci nice maiyi masu wani abin. Da mahaifin mu yaga abin ba sauki sai na Allah dole ya buga waya yana sheda ma baba kabiru halin da mahaifiyata take ciki. Kwana biyu sai ga baba kabiru da umma da daya daga cikin matan shi sun iso garin hankalin su ya tashi sosai ganin yadda mama ta koma a dan kankanin lokacin. Sunyi jinyar ta a cikin ikon Allah zuwan su ta dan samu sauki sosai ta dan warke haka yasa na fara shirin komawa makaranta don an koma da dadewa . Saboda ciwon mama yasa ni ban koma ba do baba yaje ya daukan min permition a makaranta don kada aga na makara da yawa saboda suna daukan mataki sosai. Bayan tafiyana da sati daya Allah ya karbi ran mama ta tafi da cikin dake jikin ta su umma sun ga tashi hankali don mahaifin mu ya birkice masu shima gaba daya don mutuwan ya taba shi sosai. Abin mamaki a ranan ne kuma mahaifiyar Jamil ta rasu a can gida sai waya suka samu Allah yayi mata rasuwa itama da yammacin ranan a gida don ita ma tayi dan jiya sai dai ba a sa ran rashinta ba don zazzabi ne tayi na dan kwanaki yazo da ajali. Ina school ban san wainar da ake toyawa a gida don nasa ran mama taji sauki har su umma kila sun koma gida a lokacin. Ashe mama bata duniya ta tafi gurin da ba a dawo sai rabon a hadu gobe kiyama idan da rabon haduwa din gare mu Allah yasa mu cika dakyau da imanin ubangijin mu a ran mu Amin. Nasan wanan shafin zai taba zukatan makaranta da dama don akwai zafi irin wanan mutuwan ka rasa mahaifiya a lokacin da kafi kowa bukatan ta a duniya. Mama ta tafi tabar baba da nauyin rikon iyalin data bari shine kalman da mahaifin mu ke fada ko wani lokaci yana kuka da hawayen shi na rashinta a tare damu. Har sunje gida anyi zaman makoki sun kwana biyu a gida suka dawo duk banda labari saboda makaranta da ya boyeni a lokacin. Mahaifina ya kawo min ziyar sai dai duk da karancin shekaruna naga sauyi a tare dashi don ya ramay yayi baki sosai babu walwala a tare dashi. Cikin farin ciki da kaguwa na tambaye shi mahaifiyar mu yace taji sauki sosai tana gaishe ni umma fa na tambaya sun koma ne baba ? Yace umma nanan zaune gida zata kwana biyu a wurin mu kafin ta koma sai dai maman mu ta tafi gida a can zata haihu yace dani. Ina ta murna maman mu zata haihu ya bani abinda zai bani ya tafi bai dade a gurina ba kamar yana sauri ashe kuka ne yazo mashi a lokacin. Ina ta fadama abokaina mahaifiyata zata haihu zan gyaiyace buki suna ban address din su tare da layin wayan su idan ta haihu in fada masu. Har akai hutu baba yazo da kanshi ya dauke ni na isa gida da murna na ko zan samu mama ta haihu a lokacin. Sai dai ba mama a gidan sai umma da kanne na a gidan suma yanayin su ba dadi a yadda na samay su sai umma ce mai karfin halin taro na da zuwa. Ni a zatona tunda nace umma mama har yanzu tana gida bata haihu ba naga bata dawo ba sai cewa tayi da sauran lokaci zata dade a can kafin ta dawo. Na dauka idan ta haihy zamu tafi gida ayi bukin suna damu acan tana ganin ina murna ta shige daki tana kuka tunda nace Allah yasa mama ta haifi mace wanan karon. Maimakon in ga murna da doki a fuskan kanne na sai bata rai danaga sunayi idan na shiga daki su biyo ni sai umma ta kwala muna kira dole mu fito daga dakin. Ashe umma bata son su fada min halin da ake cikine sai washe garine bayan mun karya naga mahaifina bai fita aiki ba sai na dauka yana up ne aikin dare zai fita. Kira ya kwala min ina daki ina gyara na fito da sauri yake ce min tare da nuna min wuri in zauna bayan na samu wuri na zauna ne ya kira sunana. Na dago kai a hankali na amsa mashi da na,am baba yace magana zamuyi dake ina son ki fahince don ke musulmane ko. Na daga mashi kai a hankali yace kin san rayuwan mu a gurin Allah yake ko nace eh baba ya ce dakyau yace kin san ko yanzu ko anjima Allah zai iya kiranmu mu koma gare shi ko ? Sai lokacin na fara jin tashin hankali yana ziyara na don ban son ai min maganan mutuwa ko kadan sai naga umma tana share hawaye da gefen hijjab din ta. Baba yace kin san kin wuce kin bar mahaifiyar ki bata da lafiya ko da sauri na dago ina fadin eh baba nasani yace to hadiza hakkuri zamuyi don Allah daya bamu ita ya karbi abinshi . Baba nace da karfi sai kuma na koma fadin inna lillahi wa,inna alaihim rajiun sai naje su a gurin na somay masu ban san inda nake ba don halin da na shiga. Sai farfadowa nayi na ganni a hannun umma tana shafa min ruwa a fuskana budan baki na nace mama da karfi tayi saurin rufe min baki da hannun ta. Baba bai iya fadin komai ba don shima kuka yakeyi a lokacin ga kanne na da suke kuka wiwi a kaina suma. Umma rana naga taushi a gurin ta don ita ta koma tana lalashi kamar yadda mama zatayi min ta koma min makwafin mahaifiya a gareni. Banci ban sha don damuwan da nake ciki bazan iya fada ma mai karatu ba sai wanda ya taba shiga irin halin da nake ciki a lokacin yasan irin rayuwan dana riska a lokacin. Baba yana lalashin mu yana nan nan damu baya son yaga ran mu ya baci ko kadan sai dai duk wanan ban gani nidai muradina mahaifiyar mu ta dawo gare mu. Da kyat suka shawo kaina na fara dan walwala da kannena da nasiha da fada da komai hankalina ya fara kwantawa. Sai daga bayane nake jin labarin mutuwan mahaifiyar Jamil wurin kanne na na tausaya muna sosai dani dashi don irin halin da muka riski kan mu a ciki na rashin magaifiya da mukayi. A cikin wanan yanayi na bakin ciki ne hutun mu ya kare haka aka mayar dani school ba tare da na gama warwarewa ba. Wanan time din na dai koma school din ne ba don zan aiwatar da komai ba na fannin karatuna haka din ne kuwa don tunanen mahaifiyata ya hananu shakat a raina. Sannu a hankali na fara sakewa ina dan walwala a makaranta duk da ba wani yi nake kamar a baya don ba zan iya shafe rashin mahaifiya a zuciyana ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:49 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 8️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA FATAN ALHERI DA CIKAWA DA IMANI GARE KU MASOYANA ALLAH YA SA MU FI KARFIN ZUKATAN YABA MU IKON BAUTA MASHI, BAUTA TSARKAKAKIYA ALLAHU MA AMIN YA ALLLAH 👏👏👏👏 Wanan time din haka na kare shi babu dadin rayuwa a tare dani don sam hankali baya ga karatu don tunanen mahaifiya na da yai min yawa a raina. Na dawo gida na samu har lokacin umma tana gidan zaune da kanne na kamar kada in dawo sai umma ta tayar da hankalinta akan tana son zuwa gida ta duba su can. Wanan abin ya daga hankalin mahaifin mu sosai da ya rasa yadda zaiyi damu gashi hutu akeyi sai ya shirya har damu zata tafi muyi hutu a can. Da yake dogon zango ne muka fara murna zamu gida muga yan uwan mu sai dai ina gani kamar idan munje zanga mama acan a raina. Mun zama yan matasa yanzu don haka muka fito fes damu a gurin baba kabiru muka fara yadda zango da muka iso zamu dan kwana biyu a gurin shi kafin mu karasa gida. Matan shi suka shiga ina aka saka damu suna yi muna kokari mun fi sakewa da matar shi ta biyu a gurin ta muka sauka inda umma ta sauka gurin uwargidan shi. Bamu da wani damuwa dan zaman sati dayan da mukayi da iyalin shi sai dawainiya yake damu yana nuna diyan dan uwan shi ne mu tankar diyan cikin shi muma muke a gurin shi. Muka kare sati dayan mu muka wuce kauyen mu, yan uwa na ganin mu sai sharan hawaye sukeyi don tunawa da mahaifiyar mu da sukayi. Muma dai kukan muka dauka tundai ni dake da wayau a cikin mu nafi kowa shiga tashin hankali sai da kyat da fada da komai umma ta samu na dakatar da kukan da nake yi. Washe gari da rana muka shirya zuwa gidan kakannin mu na fanin mahaifiyar mu kai mata ziyara don muna jin dadin kasancewa da ita fiye da umma da take mahaifiyar mahaifinmu. A can ma mun taba kukan saidai da ta rarashe mu mukai hakkuri duk firan mu na ranan kan ciwon mama ne da yadda muke maraicin ta. Sai dare muka koma gida bayan tayi muna abinci mun ci mun dawo umma ta cika fam kan dadewan namu da mukayi a gidan kakan mu mahaifiyar maman mu din. Ba wanda ya tanka ta muka shige dakin mahaifiyar mu inda anan muka sauka tunda muka iso don dakin umma ba fili kaya sunyi yawa. Ina kokarin cire kayan jikina ne hafsa ta shigo tana rada min Jamil yana waje yana son ganina nace hafsa kin san ba abinda zai yuyu bane don yanzu umma ta gama muna fada munyi dare a gidan Auta don haka ake kiran kakan namu dashi. Kije kice yayi hakkuri tunda muna nan watarana zamu hadu ai wanan ranan bamu hadu ba dashi haka ya juya ya tafi . Ba tare da ya ganni ba sai dai banji dadin hakan ba don mun dade bamu hadu ba dashi ba zance ga ranan da muka hadu dashi last ba. Gama shiri nayi na samu wuri na kwanta har na fara barci nake jin umma tana kwala min kira daga kofan dakin ta na amsa a sanyaye tare da mikewa zuwa wurin ta ina fadin umma gani. Bazaku ci abinci bane har wanan lokacin baku dauka ba nace umma a koshe muke don mun ci abinci a gidan Auta kafin mu dawo gida. Salati ta saka tare da fadin yaran nan kun iya sai da hali yanzun zuwa kukayi kuka nuna mata muna barin ku da yunwa ko may ? Da sauri na dago ina girgiza kai tare da fadin ba hakana bane umma ba wanda ya nuna hakan a cikin mu wallahi rufa min baki munafukan banza kawai. Gobe in Allah ya kaimu zanje gidan inji abinda yasa ta girka maku abinci a gidan ta kallon mamaki nayiwa umma din kamar ta manta da Auta ma kakan mu ne kamar yadda take kakan mu itama. Nidai naja kafana na barta nan tana surfa muna zagi dani da kanne na akan zuwa gidan kakan mu ta uwa da mukayi muka kai dare. Washegari tun fitowan mu dakin na gaida umma ban kara fitowa ba ina dakin mama ina aikin tunane rayuwan mun yadda muka koma abin tausayi duk da dai bamu da tausayi don mahaifin mu yana tsaye a kan mu. Dama yan uwan shi kowa na nuna kulawan shi akan mu a matsayin su na yan uwan mahaifin mu din a gare mu. Saidai mu bamu ganin hakan da suke muna dan abu kadan zamu dauka don mahaifiyar mu bata da raine ake muna wani abin da bai dace ba. Yinin ranan haka nayi shi a dakin ba wani walwala a tare dani sai ma gyaran dakin da na tsiri yi tankar mahaifiyar mu tana nan a cikin sa ne kamar yadda naga tana yi idan munzo tare da ita garin. Sai yama lis na watsa ruwa a jikina kofan umma na dawo na zauna muna hira da yan uwana a gurin ta fito daga daki tana fadin kin ga dama kin fito ke nan don maganan da nayi maki jiya kike fan fushi haka yau. Nace ba haka na bane aikin dakin mu nayi don yayi kura da yawa sosai ta tace ke dai kika sani idan kin sa kanki a damuwa haka ma yan uwan ki ba zasu sake ba don basu ga kina walwala ba . Shiru nayi ina fadin a raina walwala ai ya kare a gurin mu umma tunda mun rasa mahaufiyar mu ko a duniya. Maganan ta ne ya dawo dani ga tunanen da nakeyi tana fadin idan ba zamu iyacin abincin da akayi ba a gidan mu dafa taliya muci da dare. Don mahaifin mu bai barmu munzo hakana ba garin sai da ya sawo muna duk wani cimar daya san muna amfani dashi a can muka zo dashi gida. Tambayan kanne na nayi idan zasu ci da sauri suka amsa min haka yasa na tashi don in dafa muna taliyan tunda suna son ci na sani dolene kawai yasa suke cin abincin gari. Mungama muka taru a gurin umma din nan mukaci taliyan sai dai itako kallo bai ishe ta ba tuwon ta da aka kawo muna taci. Bamu wani dade ba muka kwanta don dare yayi a lokacin sai dai ni ba barci ne nayi ba na dai kwanta ne ina tunanen duniya a lokacin. Tunda muka zo ko hanya bai hadani da jamilu ba har yakai satin mu daya da zuwa garin duk ko shima yana cikin garin a lokacin. Yau ya kama kasuwan kauyen mu ne kowa sai hada hadan sana,ar shi yakeyi don fita dashi gurin yan kasuwa in ka debe mu da bamu komai sai dai mu wanke mu saka don yanayin mu daya dan banbanta dana yan gari. Sai dai duk da haka ba,a barmu a baya ba don muma munyi kwalliya mun saka kaya masu kyau don muna da muradin shiga kasuwan mu dan zagaya. Saboda akwai kudi a hannun mu bayan wanda baba ya ba umma don lalurar mu na yau da kullun da wani matsala daka taso a gare mu a gidan. Kamar yadda tsoho keda naci a kudi haka ma yaro yake da kunata akan kudi don su sauran basu san baba ya bamu kudin ba a hannu na. Mun gama shiri muka sallami umma don abokai na da suka shigo don mu fita sai dai ni abinda ke ban mamaki shi su hafsa kawana ba karatun sukeyi ba kuma su ba aure sukayi ba har yanzu. Mun fita mun dan zaga abin marmari na sayo muna da kannen na don mun dade bamu ci ba a can mun juyo zamu dawo gidane muka hade da su jamil da kungiyar su. Ashe sun saka ido a kan mu suga fitowan mu take dan leken asirin su ya sheda masu mun fito garin muna zagawa a kasuwan sai gasu sun sha kwaliyan su zakace ba yan kauye bane su. Kallon juna mukayi na sada kaina kasa don kunya su a dole ga samarin da suka ga yan mata suka zo da guntun turancin su don su burge mu saboda mun fito birni musan sun iya turanci. Da sumaiya kawanta suke turancin sai kanne na maza da muke tare suke buga turanci dasu suna jin dadin yadda yaran ke amsa su. Na dago yana fadin baby ya kike ne kwana biyu bamu hadu ba ya mukaji da hakkurin rashin mama kuma sai lokacin naji wani iri a raina. Don haka nake da an min maganan mama hankalina sai ya tashi sosai mutuwan ya dawo min sabo a raina. Mun dan dade a gurin tsaye dasu suka rokeni da dare in basu lokaci su samay ni a gida mu kara gaisawa don nan ido yayi muna yawa akan mu. Na matsu in bar gurin haka yasa mukai sallama dasu muka wuce zuwa gida inda kannena maza suka bisu kamar yadda suka bukata suyi. Yalon da muka sayo kasuwa ne nake wankewa a bakin kwatan shiyan umma kanne na suka shigo da leda shake da abin motsa baki suna fadin cikin murna Jamil ne ya saya masu. Ina kokarin fadin su rage murya kada umma ta jiyo su sai ko gata tafito but daga dakin tana fada cikin hasala wani jamilun din badai na gidan babbaku ba danayi mashi iyaka daku ? Wanan yaron kamar jikan mayu da bakin naci haka na fada mai na mashi iyaka daku a garin nan Baffa kanina yace umma mu hadiza ne da za a hanamu fita gurin shi. Dakuwa tayi mai da hannu tana zagin shi tace dama zubin arnan da gare ka dan nema mara kunya ya juya zuwa dakin mu yana bata rai da zagin da tayi mashi din. Ko kafin in zo dakin na samu ya fitar da kayan yana ci fada na fara mai don may suka karbo mai kayan shi yanzu gashi sun sa umma fada damu haka. Yace idan ke baki ci ki barmu muci ai ba rokon shi mukayi ba ko tun ina jin haushi har na dauki gwangwanin maltina daya na bude ina kurbawa. Daidai lokacin umma ta dago labulen dakin tana fadin watau ma bakuji maganata ba ko in kuce kwadai ne ai wurin shi zaku mutu. An fada maku kauye ana haka ne a banza idan yasa maki asiri a ciki fa garin bakin kwadai ki bishi kamar karya kuwa. Dan maltinan dana fara sha ne nake kokarin amayarwa don abinda naji umma ta fadi don ina tsoron asiri kamar yadda umma din ta fada. Kanina yace humm, abin da a gaban mu ya sai muna wani magani zai sa a ciki kuma ni dai tsoron maganan umma ya kamani don haka naki cin komai a cikin kayan suka cinye shi tas suna santi. Kamar yadda mukai alkawari da su da dare sai gasu sun aiko inzo da yake mai wayau suka aiko sai umma bata san na fita ba har na dawo bata sani ba . Daddan kalaman shi gare ni sunyi tasiri sosai a raina tun daga wanan ranan muke haduwa duk dare ba tare da kowa ya san da haka ba cikin iyayyena har umma din. Sai ranan ne ta gane hakan aiko mun sha masifa dan gaba dayan mu ta hade tayi muna tas tare da alkawarin sai ta fada ma mahaifin mu wanan maganan. Tsoron kada ta fadi yasa na kama kaina kwana biyu don ina matukar tsoron mahaifin mu din tunda ya muna warning akan hakan da dadewa. Sai dai dadadan kalaman jamil suna min yawo har yanzu a zuciyana sun ki fita min a raina sai nake ganin duk duniya babu mai kaunata da yan uwana irin shi. Haka yasa alamarin shi yaki fita a raina sam hakana nake samun in dan kebe dashi mu danyi hira sama sama dashi ba tare da an fahunci hakan ba a gida. Don ita umma tana ganin na fita batun shi a yadda nake nunawa a gabanta gashi dogon hutu muka samu zamu share wurin wata biyu a gida kafin mu koma lokacin ana bada hutu yadda ya kamata ba irin yanzu ba don damana ne. Jamil dai dan kauye ne amma ya banbanta da mutanen kauyen mu wuein iya tsara kwaliyan shi da shigashin daban yake shi sai dai gajere ne baida wani tsayi sosai irin na wasu maza. Zan iya cewa ko mu dake abuja bamu fishi iya kwaliya ba don haka yake kamar mace wurin tsara ado da shiga kamar dan wasu manyan mutane can. Niko irin matan nan ne daba wani kyau gare ni ba can ina dai tsaka tsakiya ne kawai don banda abinda za a zuzuta a gare ni sai dai ilimin kawai da Allah ya bani. Baba kabiru ya kawo muna ziyara a dan zaman mu na kauyen da mukeyin hutun mu tare da wasu kayan da zamuyu amfani dashi irin sabulun wanka su omo da man shafi sai taliya da idomie daya zo muna dashi. Kwanan shi daya a tare damu ya koma tare da fadin idan lokacin komawan mu ya matso umma ta sheda mashi da wuri. Munji dadin kayan dama wanda mahaifin mu ya sai muna ya kusa karewa sai maneji mukeyi dasu kawai gashi bai kara bi ta kan mu ba tunda ya turo mu kauyen. Kanne na na yawan maganan shi akoda yaushe sai ince dasu aiki ne yayi mashi yawa sun san yadda aikin su yake. Hakan kan sa su manta da zancen don ko kadan ban bari su shiga damuwa a garin koda yaushe ina tare dasu sai mazab dakan dan fita yawo duk da muma ba wani shamaki akai muna da fita ba kowani lokaci. Ban san yadda akayi umma tasan da wanan zancen ba na ina kebewa da Jamil ranan ta haukace muna sosai tace ko mutuwa zanyi ba zan auri jamil ba wahal da kaina kawai nakeyi a banza. Kuma ko bayan ranta mukai aure dashi sai ta taso muna fatalwa ta hana mu zaman lafiya wanan zancen nata ne ya kara tsoratani. Sai ma na matsu mu koma abuja mu bar garin don samun salama a raina da saukin komai don fitinan ta ya isheni har muka kusa komawa schoool muka fara shirye shiryen komawa abuja. Duk da muna sa rai zamu koma da umma ne tunda ita ke zaune damu a can dama tun bayan rasuwan mama. Ashe abin ba haka yake ba don umma ta tace bazata koma wanan gari ba sai dai mahaifin mu ya barmu a nan mu zauna tare da ita din. Ranan sai ganin baba kabiru mukayi yazo garin sun dade daki da umma dasu baba yushau da baba musa suna tattaunawa akan zancen mu ne ashe. Bamu dai san yadda akayi ba baba kabiru ya fice da bacin rai yakai dare a garin mun dauka a nan zai kwana sai da yazo sallaman mune yake fada muna tare da wata gwagon mu zamu tafi don haka mu shirya nan da kwana uku zamu wuce. Bamu san matar ba da akace zamu tafi da ita mudai burin mu kawai muga mun koma Abujan gurin mahaifin mu ko ta halin kaka. Ranan tafiyan mu yazo motar da baba kabiru yayo muna shata zata kaimu har abuja ta iso muka shirya sai lokacin ne muka san matar da zamu koma Abuja da ita ta zauna damu a can. Muka dauki hanyan abuja cike da bacin ran rabuwa da yan uwa da abokan arziki da zamuyi a nan gida Allah ya sauke mu lafiya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:49 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 9️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA FATAN ALHERI DA CIKAWA DA IMANIN UBANGIJI A KARSHEN MU UBANGIJI YASA MUFI KARFIN ZUCIYAR MU AMIN 👏 TO ANCE KADA INJA ALLAH YA ISA BAI DACE BA, KUMA SAI KU MUNA ADALCI, KU DAINA FITAR MUNA DA NOVEL DON GIRMAN ALLAH, DON HAKA WACE TA FITAR KUMA KA GANI KA KARANTA SAI MU BARKU GA ALLAH SHIKE NAN SHI YASAN TSAKANIN MU DAKU, , , Bamu dade da dawowa daga gida ba sati daya na kara na koma school don na samu baba ya gama min shirin komawa makaranta. Nan na bar kanne na da gwagon mu da muka zo da ita na barsu ban gama fahintar yadda rayuwan ta yake da yadda zata zauna tare da yan uwana. Don hankalina sam bai kwanta da yanayi wanan matar ba don ina ganin zatayi fada don haka zata kwasa da kanne na a gida dana barsu tare. Ban yi wani nisan zango ba mahaifina yakawo min ziyar sai dai na kula ya danyi rama kadan da baki wanda na dauka duk yana cikin damuwa rashin mahaifiyar mu da yanayin da yake ganin mu a ciki na ban tausayi. Ga maganan auren shi tun bayan rasuwan mahaifiyar mu bamu kara jin magana ba a gidan itama kanta ta rage kiran shi kamar baya can. Ashe rikici suka yi da ita wai ba zata zauna ta dubu yaran shi ba shikuma ya yace ba zai iya rabuwa da yaran shi ba gaskiya. Shine rikicin da sukeyi a tsakanin su har ya kawo tsaikon auren mukaji shiru zuwa wanan lokacin don mun ki jinin matar tundai kauna ta summaiya bata kaunan ai maganan karin auren baba a gaban ta ko kadan. Yanzu zata kama zagi tana aibanta matar har wace ta hada auren zata zage ko a gaban waye duk da ba wani shekuru ke gare ta ba amma akwaita da tsananin kishin tsiya. Ita a dole tana taya mahaifiyar mu kishi tana fadin ai da baba baiyi zancen auren ta ba lafiya kalau maman mu ke haihuwanta. Wanan ke nan wanan time din mun dawo gida na samu kanne na sun rama sunyi baki raina ya baci da ganin hakan ko ban tambaya ba nasan zaman su da gwagon namu ne babu dadi. Mun samu kebewa da sune suke fada min ciwo sukai tayi har da kwanciya asibiti nayi masu sannu baba ma yai min bayanin irun ciwon da sukayi a bayana din sosai. Abin farko dana fara kula dashi wanan gwagon tamu sam jinin mu baizo daya da ita ba idan ina falo tana daki idan kuma daki nake ita tana falo don a dakin mu ta sauka. Ranan cikin dare ina barci na falka na ganta tsirara tsaye da wani kwarya a kaina wani irin ihu na yanka gashi mahaifin mu baya gida yana aikin dare ne ranan. Ihu na ne ya tayar da yan uwana a tsorace duk da basu san may ya faru ba suma suka shiga tsoron a lokacin. Ban iya fada ma kowa abinda ya faru ba ranan sai dai muna yar tsama da wanan matar da aka kira da gwagon mu mai zama damu. Sai ta so ta dora min tsangwama tana fadawa mahaifi mu wai ina mata rashin kunya nan zai kamani ya zage ni fes a kanta. Abinda bamu sani ba ashe matar manyace aka dauko aka kawota zama damu abuja cikin rashin sani wanan yawan ciwon da yan uwana ke fama dashi duk itace ummul,abasin ciwon su. Kwatsam sai ga umma ta dira abuja kamar daga sama tana zuwa matar tasha jinin jikin ta nan umma ta shiga yadda magana kamar haka. Mugu sai dai ya harari kayana ya barshi, idan yace zai taba kayana sai dai su tafi tare da maishi banci dan kowa ba babu mai zuwa ya taba min nawa. Idan mutum yace shi takaman shi sheri ne ya zo karshen sheri a rayuwan shi don asirin shi ya kusa tonowa a garin nan ire iren maganganun da umma kan zauna a falo tana sakewa ke nan. Idan baba yana gida zai tambayi umma wai da ita da waye take wanan magana haka sai tace mai ya barta ta fadi ai mashi yasan kanshi. Ranan dai gwagon ta tayar da hankali wai zata koma gida tunda umma tazo dama don babu kowa tare da mune baba kabiru ya roketa tazo. Batai wani kwanaki ba ta tafi ta barmu bayan baba yayi mata goma sha tara na arziki tana ta godiya aka sakata a mota da zai kaita jahan mu. Ranan ne umma ta zauna da baba tana fada mashi mugun halin gwagon namu da taji daga baya wanda hakan ne ya tayar mata hankali ta biyo mu. Mahaifin mu dariya yayi yana fadin may yasa kuke yarda da irin maganganun nan don Allah wanan duk camfine wallahi. Nan nake fada masu yadda na ganta ranan da bamu kara shiri da ita ba har ta tafi ke nan umma tace kaji ba aniyar kura ta bita ba a cikin kayana ba kan. Na koma school na bar gwagon mu a nan inda wanan zuwa da yar gurin baba musa tazo sai da mahaifina ya nuna rashin yardan shi akan zuwan da tayi da yarinyar da farko. Don shi bai ra,ayin rike dan wani a rayuwan shi yasa nashi ma bai yarda yan uwa suka dauka ba ina makaranta ne ciwo ya kama mahaifin mu lokacin mahaifitar mu tana da shekara biyu da rasuwa ke nan. Sai dai bai kwanta ba tsatsaye yake jiya muna samun hutun makaranta umma tace tunda yaji sauki gida zatazo damu mu kwana biyu. Mun dawo gidane muka barshi can sai kuma ya samu sauyin wurin aiki ya koma Niger state da aikin shi satin mu uku da zuwa gida ke nan ya samu wanan sauyin. Lokacin ne abubuwa suka taru sukai mai yawa dole yazo yayi reporting don kada ya samu matsala satin shi biyu a minna har ya samu gida inda zai zauna da iyalin shi sai kuma ciwo ya dawo mashi sabo. Da yan wuein aikin sukaga ba zasu iya ba aka tada mota a kawo shi gida wurin iyalin shi da yamma lis suka iso wurin baba kabiru dashi. Hankalin baba kabiru ya tashi sosai yadda yaga dan uwan shi ya koma a lokaci guda ciwon dai baiyi kama dana asibiti ba sam. Haka dai suka dauke shi zuwa asibiti suna hadawa dana gargajiya da farkon zuwan shi yana magana don har yana ma baba kabiru bayanin yadda yake jin jikin nasa a lokacin. Nan dai baba kabiru ya gane abin kamar sammune akai mashi hankali ta kara tashi sosai umma ta samu labarin ciwon nasa inda hankalin ta yayi matukar tashi da zancen. Washe gari ta shirya sai birni inda baba yake kwance a asibiti jikin ba sauki addua,a tayi mai ta dawo gida da yamma lis babu wani walwala a tare da ita ko kadan. Mun taru a dakin ta don son jin yaya jikin mahaifin namu da ta baro a can sai cewa tayi yace a gaida mu ya samu sauki sosai da taje . Munyi ta murnan jin hakan dama da zata tafi munce zamu tace mu bari idan ta dawo sai mu shirya mu zo mu duba shi da jiki don haka muka kasa kunnuwan mu don muji tace ga ranan da zamu mu duba mahaifin mu din kafin ya koma. Tunda tace damu ya samu lafiya ko banza mun san idan mun samu ganin shi zamu samu kudin kashi a gurin shi wanan shine burin yan kannena a lokacin sai lissafin abinda zasu saye da kudin sukeyi. Kwatsam muka wayi gari da mumunan labari kuma Allah yaiwa mahaifin mu rasuwa washe garin da dawowan umma daga wurin shi din . Ganin mutanen gidan mu nata kokekoke idan an ganmu sai a kama yan kamay kamay don kada mu gane nice na fara fahintar abinda ke wakana a gidan namu. Inda na tsura umma da taron mutane a dakin ta masu zuwa ta,aziya suna fadin ashe ba nisa tsakanin shi da matar shi don yanzu da rasuwanta shekara biyu ke nan tsakanin su. Duk da hankali bai gama shigana ba lokacin hakan bai hanani fahintar maganan da sukeyi ba ihun da na yanka daga inda nake ne ina fadin wayo baba, ya fargar dasu ina wurin tsaye . Kafin su taso zuwa inda nake na zube a somay kasa take sukayo kaina gaba dayan su sai fadin suke basu san da labarin rasuwan nasa bane dama ? Umma fadi take may zan gani haka kuma Allah ka dubeni da ido rahaman ka ya Allah tana fadi a cikin wani irin yanayi na tashin hankali ganin ana zuba min ruwa ban farfado ba yasa take wanan maganan hankali a tashe. Kururuwan da sukeyi ne ya dawo da hankalin mazan dake waje a cikin gidan hankali a tashe suka shigo don ganin abinda ke faruwa. Can kuma kanina wani ya tare shi yana fadin Allah sarki ashe kuma mahaifin ku shima ya rasu bayan mahaifiyar ku din. Da ya fara ihu daga van bai tsaya sauraren maganan shi ba yayo gida yana yanka ihu a cikin tashin hankali sai ya samu kuma ana fama danibin farfado daga suman da nayi. Daidai lokacin da ya shigone aka samu nayi dogon ajiyan zuciya sai fadi suke barka ta farfado yayo kaina yana kuka tare da fadin hadiza mun shiga uku ance baban mu ya rasu yau. Rungumay juna mukayi gaba dayan mu muna sake wani irin kuka na maraici a tsakanin mu da yan uwana duk tsawan da suke muna bama jin su a lokacin. Don haka dole aka kyale mu don abin kuka ya samay mu a lokacin ba mai iya hana mu yin kukan don suma kukan sukeyi a lokacin. Ranan dai muna a cikin tashin hankali da ba zan iya muku bayanin shi ba saboda halin da muke ciki ba wanda yai zancen cin abincin da ake kawo muna a ranan . Washegari ne baba kabiru ya iso da yan kayan da baban mu yayi jinya a wurin tare da yan kudaden da ya bari wanan ya kara tayar muna da hankali muka tabbatar da mahaifin namu ya rasu kuwa. Muna manne dashi yana kokarin ganin mun da sake sai magana yake bamu don mu dan sake jikin mu dasu. Sai dai ina nikan kamar kara tunzura ni ma sukeyi don ban iya ci ban iya sha a lokacin sai aikin kukan da nakeyi don tashin hankalin da nake ciki don na fi sauran fahintar halin da muka shiga a yanzu na rashin iyayyen mu din. Sai da baba kabiru ya nuna min bacin rashi sosai ga rashin kin cin komai da nakeyi ne yasa na dan daure nasha kunu a gaban shi kadan. Muna manne da umma wace yanzu nauyin mu ya koma kanta muna ganin ta komai namu a duniya duk da mahaifiyar maman mu tana nan da ranta a duniya. Sai dai ba sabawa mukayi sosai da ita ba don mun fi sabawa da umma don da ita muke zaune akoda yaushe. Wanan mutuwan ya tayar da hankalin mutane sosai a kauyen mu don yanzu ne mahaifin mu yake a ganuwan samun arzikin shi sosai a duniya. Sai kuma Allah yai nasa ikon akan shi ya raba mu dasu a daidai lokacin da mukafi kowa bukatan su daga shi har mahaifiyar mu a duniya. Kwanan baba kabiru uku bayan sadakan uku ne ya kebe damu yake fada muna shi zai koma zai tafi ya tattara kayan mu dake can abuja. Don yanzu zaman mu ya dawo nan ke nan da sauri nace baba karatun mu fa yace zamu duba wanan idan mun dawo sai mu san abinda za ayi akai. Abinda nake so daku shi ku kwantar da hankalin ku ku natsu ku rage wanan damuwan da kukeyi alabashin hakan zai sa muma hankalin mu ya kwanta mu samu natsuwan yin abinda ya dace a kan ku. Ya bar muna wanan kudin da yazo dashi yace muyi amfani dashi kafin ya dawo mukai mashi godiya ya tafi bayan ya gana da umma da yan uwan shi. A kwana na uku ne mukaga su baba yushau da baba musa sun shirya ashe tare zasu tafi abujan don ganin abinda mahaifin mu ya bari a can din. Har lokacin gani nake a raina kamar zamu koma Abuja ne ba a nan zamu zauna ba ban da wani sukuni a tare dani idan kaji muryana sai idan yan kannena ke wani abinda bai dace ba na tsawa ta masu. A rana ta bakwai da rasuwan mahaifin mu ina kwance saman gadon karfen umma dake dakin don yanzu gaba daya a dakinta na tare din tsoron dakin mu nake ji gaba daya. Yaro yazo yace wai Jamil yana sallama dani kamar banji yaron ba sai umma ne ta bashi amsa da fadin wanan mai bakin nacin kaje kace dashi ba zata zo ba. Summaiya ce tace haba umma ki bari taje su gaisa mana kila gaisuwa yazo yai muna kuma kin kore shi da fadan kin nan. Dakuwa ta sakar ma summaiya da hannun ta tana fadin ungo naki ni kike fadawa wai gaisuwa yazo yai maku kunfini rashi ne ni da dana ne ta rasu kuma nayi hakkuri da rashin shi. Sai mikewa nayi daga inda nake kwance ba tare danayi mata magana ba zan fita tace wai fitan zakiyi ko baya na hana. Umma ba dadewa zanyi ba gaisawa kawai zamuyi dashi in dawo na bata amsa na fice ban tsaya jin abinda zata fada min ba. Na samu ya juya zai tafi na kirashi ina fadin gani ya juyo fuskan shi ba yabo ba fallasa a cikin shi bayan mun gaisa ne suke fadin ashe kuma baba lokaci yayi. Idanuwana suka kawo hawaye nace muma haka wanan zancen yazo muna ashe iyakar mu dashi ke nan daya rakomu shiga mota da zamu zo nan. Sai hakkuri do mutum baya wuce lokacin shi kece babba idan yan uqan ki suna ganin ki a cikin damuwa suma ba zasu sake ba yace. Duk maganan da take kaina yana kasa ina hawaye a lokacin don ban iya kara furta komai saboda tunanen mahaifina da nakeyi a lokacin. Abokin nasa ne yace yanzu komawa zakuyi abujan ko may ake ciki tunda ance kuna da gida a can ai nace cikin muryan kuka ban sani ba sai dai babu alaman zamu koma can din . Don naji su baba kabiru sun tafi hada kayan mu dake can yanzun haka suna can basu dawo ba tun shekaran jiya suka tafi. Ajiyan zuciya naji jamil din ya sauke tare da fadin nima tunanen da nakeyi ke nan idan kun koma can dawa zaku zauna acan yanzu kuma. Muryan umma ne ta fito da tocilan ta tana haska muna tare da fadin kaikan wanan yaron idan kana maita sai ka cinye yan gaein nan a baki dayan su. Ke kuma munafuka maza ki shige tun ban bata maki rai ba a furin nan yanzu simi simi na wuce ta tare da fadin sai da safe ku na gode na barsu da ita a gurin. Bata shigo ba sai data dan dade dasu ban san dai yadda suka kwashe da ita ba don ko da ta shigo har na kwanta abina ta karashi fadan ta kala bance mata bani dai. Kuyi hakkuri da wanan yanzu muka dan samu wuta kuma har sun dauke muna ko wai gyara sukeyi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:49 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 🔟 ZAINAB IDRIS MAKAWA FATAN ALHERI GA YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA BAMU IKON CIKAWA DA IMANI A ZUKATAN MU YA BAMU IKON BAUTA MASHI BAUTA TSAKAKKIYA ALLAHUMA AMIN 👏👏👏👏 LITTAFINA NA KUDINE DON ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA YAR UWA DON GUDUN SHIGA HAKKIN JUNAN MU , , , , , Dawowan su baba kabiru daga abuja muna ta jiran muji wani bayani sai mukaji sheru ba suyi muna bayanin komai ba ga hutun makaranta ya kare ana shirin komawa a lokacin. Hakan ne ya kara tayar muna da hankali so sai ganin bamu san mafitan mu ba a wanan lokacin zamu koma ko ba zamu koma abujan ba mu dai gamu nan dai ne. Baba kabiru ya shigo garin ya samay mu yake fadin mu shirya muzo birmi don a san abin yi a kan karatun mu. Da muka tashi zuwa tare muka zo da wanan yarinyar da umma taje muna abuja da ita don itama yanzu daukan kanta take a cikin mu take. Itama ta zama yar abuja a cewan ta don haka take abubuwa irin na yan birini sosai don abinda take mu ko makamancin sa bamu iya yi ai. Gidan babs kabiru muka sauka mu biyar daga mu sai yan kayan mu wanda a lokacin ba wani kaya bane masu kyau don sun sha jiki sosai a gurin mu. Dakin anty amaryan baba kabiru muka sauka don ta fi sakin fuska a gida don haka ne da zaran mun shigo gidan muke sauka a wurin ta. Yau ma kamar kullun mun iso suna ta faman tausaya muna kan abinda ya samay mu din na rashin mahaifin mu da mukayi mun danyi kukan mu mukai shiru bayan an gabatar muna da abunci muka dan taba. Nan muka hade da yaran baba kabiru don yanzu shima yaran nasa sun tasa suna secondry schools su ma. Kwanan mu uku a gidan muna jin dadin zaman garin duk da baikai abuja ba amma yanayin garin yai muna a lokacin don yanzu bamu da zabi a rayuwan mu sai yadda akayi damu. Da safe ne bayan anty amarya ta shirya zata fita aiki take tambayan mu ko yanzu aji nawa muke na fada mata ss2 zan shiga kanwata kuma zata shiga jss 2 ne. Batace damu komai ba tayi muna sallama suka fita da yaranta zuwa makaranta gidan ya koma daga mu sai kananun yaran su sai uwar gidan baba Kabir da bata aiki ita amma tana sana,an dinki da sauran su. Mun yi wanka kamar yadda ta umurce dayi don ka,idan gidan ne idan gari ya waye za a sa ruwa zafi kowa yayi wanka tun safe wanda mu bamu saba da hanka ba can sai bayan azahar ko la,asar muke wanka don haka muka saba dashi. Kallon tashan mbc muke a dakin baba kabiru ya shigo dakin yana fadin yau yake son ya kai kannen mu ai masu interview a makarantar da yake son ya saka su a nan. Mukai ta murna da jin dadin don dama shine damuwan mu don muna ganin ba wanda zai damu da karatun mu anan. Sai gashi kanin mahaifin mu uba a gare mu yanzu don mun fi daukan shi a matsayin uba duk cikin iyayyen mu tunda dashi muka bude ido mu ga iyayyen mu suna hurdan arziki sosai. Shamsiya ne tace wai ana nufin anan zamu zauna ke nan ni dai nafi son mu koma abuja da zama da son samu ne gaskiya. Sai summaiya tace gurin wa zamu koma Abujan da kike magana yanzu ina dai baba ne kuma ya rasu shima yanzu. Ina jin su ban iya magana ba a lokacin don irin yadda nake jin mutuwan mahaifan mu sabo a zuciyana. Zuwa rana sai ga anty ta dawo tace zasu kai kannen mu makarantane yasa muka dawo a lokacin. Makarantar da yafi kudi sukaje inda akaiwa yaran gwaji sai dai basu ci ba don sun ce sai dai idan zasu mayar dasu baya ne hakan ya batawa baba rai yabar gurin dasu zuwa wani makaranta again a can suka dauke su a ajin da suke makarantar shima yana da kyau sosai. Kannen mu suka fara zuwa makaranta a satin sai mu muka rage a gidan ga wanan yarinyar duk irin kokarin da baba da iyalin shi su keyi a kan mu bata gani sai kushewa take wanda har na fara yarda da hakan. Ranan baba yazo yace za a kaimu makarantar kwana na nan garin dani da summaiya kanwata ita kuma shamsiya zata tsaya day don mahaifinta yace bazai iya lalurar makarantar kwana ba akanta. Shiri sosai baba kabiru yayi muna da shi da matar shi mun shirya aka kaimu naso ganin jamil muyi sallama kafin mu tafi sai dai hakan bai samu ba. Makarantar akwai dalibai sosai a cikin sa sai dai yanayin karatun mune ya dan banbanta dasu a nan ba laifi don dama ina da kokari sosai sai haka yasa nake ganewa banda wani matsala karatu na a nan. Munyi sabbin kawaye da ma wa yanda muke da zumunci dasu duk mun hade a nan din a dan lokaci kadan sunana yayi fice a makarantar sosai don kokarin da nake dashi din. A wurin abinci duk makarantar babu mai nuna muna abinci don baba kabiru yafi ma mahaifin mu yi muna provition mai yawa haka ya kara samu sake jiki sosai muna karatun mu hankali kwance. Lokacin da muka samu hutu muka koma gida mun samu yan uwan mu a cikin kula da tarairaya suke sai dai dawowan mu shamsiya ta fara aikin zugamu wai mu gudu mu koma gida. Don mun cewa baba muna son zuwa kauye ya hanamu haka yasa ta oawo muna wanan shawaran na guduwa daga wirin shi mu koma gida. Har naso yarda sai summaiya kanwata ta ban shawara da cewa gara da ita iyayyen ta suna a raye idan mun gudu daga wurin wanda muka samu yana tallafa muna ina zamu tafi. Kin dai san ita iyayyen ta suna a raye bata da matsala muko fa wanan shawaran ya dawo da hankalina na daina sauraren ta gaba daya. Don aiki muna aiki kamar wanki da gyaran daki duk da anty bata bari muyi shi mu kadai tare da ita mukeyi wanda kusan wankin duk na mu ne dana yan uwan mu don ita yaran ta hudune kawai. Sai dai wanan ne shamsiya take ganin ai duk wahalan duniya yana a kan mu ne yake karewa wanda ni a lokacin kanwata summaiya tafini zafin nama a gurin aikin. Iya kata in gyara daki shinr aikina rayuwan da ba tare da mahaifan ka kake yin sa ba sai ya zamo duk abinda ake ma baka ganin kokarin mai shi sai zargi da tsangwama ya shigo ciki. Hakan ne ke faruwa don yan uwan mu idan su zo daga kauye sun kan kebe damu suna tambayan mu irin rayuwan da muke ciki a nan din. Bamu kan boye masu komai mukan fada masu duk irin kokarin da akeyi damu a nan din sai su juya maganan da ana cutar mu ne ana cin amanan mu don wai da kudin mahaifin mu ai ake muna komai da ake muna na rayuwa. Tun ban daukan wanan maganan a raina har maganan ya fara tasiri a zuciyana wani hutu mun dawo ne muka samu an kawo kayan lefen da mahaifin mu yakai kaduna wai yanzu kayan ya zama na magada. Don haka suka dawo wa yan uwan mahaifin mu da kayan sai da muka kwana biyu da dawowa ne aka fitar muna da kayan baba kabiru ya kasa muna aka cire lwa umma nata kason a cikin kayan don ita ma tana da gadon kayan. Kurciya ke damun mu a lokacin sai murna muke mun samu kayan banza baba kabiru ya biya kudin dinki aka shiga dinka muna kayan bai dauki komai ba a ciki. Sai matar sa anty ne muka cirewa turmi daya da man shafi daga ciki sauran mu muka dinka abin mu muna sakawa mu a dole ga yan mata a lokacin ba abinda ya damay mu. Hura ma baba kabiru wutan da mukayi akan muna son zuwa kauye muyi hutu ne yasa ya barmu muka tafi kauyen wanda ni da biyu na tafi don ina son ganin jamil a lokacin wanda yanzu tsakanin mu sai wasika don bamu amfani da waya. Wanan zuwa kauyen da mukayi ne aka fara zuga mu kan iyayyen namu yan uwan mahaifin mu dake kula da alamarin mu tankar iyayyen mu na raye. Don suna iyakar kokarin su damu a lokacin wani dan wan mahaifin mu ne da mahaifin shi ya riga namu rasuwa ya fara tun kara na da maganan. Yace bayan mun gaisa ashe kun zo garin nace eh mun zo shekaran jiya sai yake cewa wai yaya zancen dukiyan ku ne har yanzu shiru. Nace wallahi bamu san komai ba akai don su baba ne ke da maganan a hannun su yake fadin ba naji ance an sai da motar marigayi din ba da gidan shi na Abuja . Wanan gidan da Alhaji kabiru ke ginawa yanzu ance da dukiyan ku ne yake gina sa ai maganan ya bani mamaki kwarai ban gaskanta maganan ba sai da jamil yazo muna hira ya kara fito min da wanan zancen na yarda. A lokacin naso in tayar da hankalina sosai na kebe da yan uwana ina fada masu halin da ake ciki sai baffa kanina ke fadin shima yaji wanan zancen sai dai ba yadda zamuyi yajzu don mu din ai kanana ne ga maganan . Amma an bashi shawara idan lokaci yayi ai dole za a fitar muna da dukiyan mu ne don haka mu bar zancen har mu tasa tukun na . Da wanan shawaran muka bar maganan iya mu don summaiya kanwa ta cewa tayi dani wai da nake magana kan dukiyan mahaifin mu ni ban ganin irin kokarin da kanin mahaifin namu yake damu ne. Maganan ta ya ban haushi sosai nake fadin kin ji nace baya kokari da mune ko kin ji na fadi wani abu ne mara kyau akan zancen. Maganan yaso ya zama muna fada a tsakanin mu sai da na taushi zuciyana don kada wani yaji mu muna magana akan zancen ai muna wani fassara na daban. Wanda ni zancen dukiyan ba wai ya damay ni bane sosai don maganganun mutane ne a kai har zancen ya fara tasiri a raina yanzu. Munyi hutun mu lafiya mun dawo inda bamuyi wani dadewa ba muka fara shirin komawa makaranta. A daren da zamu koma ne baba kabiru ya kiramu a falon shi yake fada muna sunyi shawara da yan uwan shi sun sayar da gidan mu na Abuja sun saya muna wani a nan garin don nan din yafi kusa da gida. Don haka yan haya ke cikin gidan za a dinga karban kudin haya ana muna abinda ya dace damu. Mukai mashi godiya bayan ya gama muna bayani ya fada muna zamu iya zuwa idan mun dawo muga gidan da ko yan uwan mu maza su tafi su gani. Wanan maganan ya kara kwantar muna da hankalin mu summaiya ke fadin kun gani nace daku abi sannu don ban sa baba zai iya muna hakan ba da ake fadi. Gashi mahaifin mu ashe duk takardun shi sunan baba kabiru ne a ciki sai nawa dana baffa daya saka magadan shi. Mun koma makaranta zuciyar mu ba wani zargi ko tunanen komai a ciki don yadda mutane ke zuzuta zancen kan mahaifin mu yabar dukiya mai yawa sai bamuyi tunanen a ina dukiyan yake ba wanda mu bamu san dashi ba. Bamuyi kuma la,akari da irin samun da baba kabiru yake yi ba don shi din yanzu shahararen dan siya sa ne da ake damawa dashi sosai. Ga kokarin da yake muna wanda mu bamu gani a lokacin don ma iyalin shi suna da hakuri da hangen nesa ne yasa basu damuwa da irin yadda yake gwada muna banbanci a tsakanin mu da nasa iyalan. Don kirikiri zai muna abu bai ma diyan cikin shi ba kuma basu damuwa da hakan da yake muna din sai dai duk da haka mutane masu hana ruwa gudu suna nuna muna ai cutar mu akeyi kawai. Matsin da shamsiya ke muna na mu gudu daga gidan na baba kabiru ne yayi yawa ganin bamu gudu ba yasa ranan muka wayi gari babu shamsiya ta tattara kayan ta ta gudu daga gidan baba kabiru din. Wanda hakan ya batawa baba rai sosai har yakai ga kiran wayan mahaifinta yana tambayan shi sai cewa yayi eh tana nan gida ai ta iso da yamman nan yace to ku barta a gurin ku don dai ni nasan gidana banda yunwar komai a tare dani. Maganan yaso hada zumunci fada don mahaifin nata na rufe ido ya goyi bayan yar shi ya mance da irin halarcin da akai muna din a gidan kanin nasa. A wani yammaci jamil ya kawo min ziyara yana saye a cikin dinkin shada da hula ya fito dan bahaushe shi sak sai dan glass din daya kafa a fuskan shi. Na fito na samay shi tsaye a waje yana jiran fitowa na lokacin yana gani na ya sakar min wani dan murmushi mai laushe yana a fuskan shi na jin dadin ganina a lokacin. Dadin ganin shi naji a lokacin ban san lokacin dana mayar mai da murmushin ba na karaso da sallama na gurin ina mashi sannu da zuwa. Ya amsa min da yar fara,a a fuskan shi tare da fadin gani dai na biyo ki don yanzu naga alaman kin samu wasu anan kin fara mantawa dani. Na dan ji zafin maganan a raina don ban ci wanan maganan ba a gare shi idan yayi duba ga yadda nake samun matsi a kan shi a gida akanshi gurin umma don tabi ta bata zancen shi ta ko ina. Gashi idan na tuna shi sai naji kamar nima in gudu yadda shamsiya ta gudu daga gidan baba kabiru din duk a kan shi. Sai dai ba zan iya yin hakan ga baba kabiru ba don ya nuna muna duk wani kauna daya dace a duniya dashi da matan shi. Naja dogon nunfashi tare da fadin wanan zaton kake mun kuma yanzu duk irin halaracin da nake nunawa akan ka yace. Kin san garin yafi namu matasa wayayu na sani ko wani ke son min yankan baya akan ki wanan dadewa da kika yi bamu hadu ba ya fara sani a shakun soyayyan mu. Murmushi nayi a raina ina kallon shi dayasan kewan shi na hanani sakat a raina da bai fada min wanan maganan ba tunanen sa yana hanani jin dadin zaman garin. Sai dai a fili nace bayan ajiyan zuciya ban yarda da uzurin ka ba jamil don da ka damu dani yadda kake fadin wani nisane a tsakanin mu da zai hanaka zuwa nan din kai. Yanisa yana murmushi yace kin san abu ga mara hali yanzun ma da kin san yarda nazo nan din dakin tausaya min. Nayi walwal da ido nace da fatan dai ba wani rikici ka jefa kanka ba don kazo nan din ya girgiza kai tare da fadin ko daya wallahi. Mun dauki lokaci har baba kabiru ya dawo ya samay mu a gurin na dauka zai min fada sai naga babu wani alaman baci rai a tare dashi dana shigo. Bayan tafiyan shi ne zuciyana ta shiga garari akan sa ashe duk yadda nake daukan shi a raina yafi hakan damuwa dani don irin dadan kalaman daya shimfida min ya tafi. Alhamdullahi na gama karatuna lafiya inda na samu kyautar jam daga hukumar makarantar da nake ciki mu uku muka samu wanan kyautar a shekaran. Zuwa lokacin tsakanina da jamil soyayya ne mai karfi wanda har lokacin umma na saman bakin ta akan bazan aure shi ba ko bayan ranta ne kuwa don ba zata hada zuria da irin gidan su ba. Ban damuwa da maganan ta don yanzu akai back din da ban tsoron ta na fahinci ita din kakace a wurina ba uwa ba sai dai akwai shakku da tsoron ta a raina. Don Allah kuyi hakkuri wanan ma da kyat na samu caji na dan rubuta shi don kuna raina da fatan zakuyi min afuwan kan hakan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:50 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 1️⃣1️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA Tunda na gama karatuna ina gida zaune sai dai ina gamawa summaiya tace ba zata koma boarding ba ita ma sai dai tayi jeka ka dawo a gida. Son da baba kabiru ke muna ne yasa bai mata fadan haka ba ya nema mata makarantar jeka ka dawo ta fara zuwa anan cikin garin. Gashi mun dinke sosai da jamil don yanzu shima a cikin gari yake zama gidan wani abokin aikin mahaifin shi don ya samu saukin kebewan mu a ko wani lokaci ya bukata. Da damana yayi zai koma gida ne muka kitsa akan nima in koma kauye na kwana biyu na yarda da hakan bayan tafiyan shi nima na tsiri son zuwa gida wurin umma kamar yadda nace a gida. Baba bai hanani ba don saukin kai irin nasa nan na shirya nayiwa kauye diran ba zata da farkon zuwa na naji rashin dadin garin don da yan uwana muka saba zuwa wanan karon kuma ni kadaice nazo. Sai daga baya na dan fara sake jikina a lokacin duk wata sa,a ta acikin dangin mu tayi aure nima don karatun da nake ne ba ai min ba na sani. Sannu a hankali na fara sajewa da su nan na yanke shawara na fara sana,a don kudin kashin da ke kokarin yi min tsaye a garin . Da taimakon yar mahaifiyar mu na samu jarin dana fara sana,a dashi a garin inda naje birni na saro kuloli da sauran kaya na bukatan mata. Sai dana kwana biyu a gurin yan uwana sai dai ban yarda na zo da kayan gidan baba kabiru an gani ba don kada yayi min fada kan hakan na gama masu kwana biyu tare da gama sayen duk wani abinda nake bukata na juya zuwa gida. Sai dai da farko naji kunyan yin talla don bantaba ba a rayuwana sai gani dauke da kaya buuuu a kaina ina shiga gidajen kauyokan mu dama ke waye ina tallatawa. Allah a cikin ikon sa yasa ma sana,an tawa albarka sai gashi dan lokaci kadan nayi suna sosai don bayan kuloli har turamay nake sayarwa kuma. Cikin dan lokaci kan kani nayi arziki da bai faduwa da wanan sana,an da nakeyi inda baba kabiru ya samu labari ya zo takanas ta kano har kauyen ya gana da umma akan barina da sukayi ina wanan ssna,an kamar mara gata a gari. Sai umma tace ni naga zan iya banda rashin gata abinda na zabawa kaina ke nan bai min magana ba ya koma da bacin rai don mahaifiyar su, ta hanashi yi min fada. Kudi na hada yakai dubu dari biyu jamil yazo gurina muna hira nake bashi labari yake fadin sai in samu wani sana an in dora a kai da riban nawa. Ya dan jima gurina muna hira daya koma gida ya kasa zaune ya kasa kwance yana tunanen wanan kudin dana bashi labarin na mallaka a yanzu. Washe gari bayan la,asar na dawo daga talla sai gashi nayi mamakin zuwan shi don ba lokacin zuwan shi bane kenan. Bayan mun gaisa ne yake fadin dama wani shawarane yazo min dashi shine dalilin ganin shi da nayi a wanan lokacin. Nace wani shawara ke nan yace eh gani yayi yanzu dai shi baida wani sana,an da yake yi mai zai hana shima ya fara sana,a da zaiyi saurin kawo muna kudi don mu samu mu fara shirin auren mu nan da dan lokaci kadan. Don ni gashi sana,an ya karbeni da farawa na tara wanan uban kudin idan mun hada hannu sai abin yayi auki mu kashe mu birne ba wanda yasan tsakanin mu. Nace ba tare da nayi wani tunane ba kana ganin haka zai fi muna yace kwarai kuwa don karuwan mune gaba daya. Nace yanzu kai may kake ganin zakayi wanda zamu samu karuwa haka da sauri ya gyara tsayuwa da kyau yace dani shawaran dana yanke shine in dinga shiga birni ina sayo mai na fetur da gas ina shigowa dashi nan kinga babu mai wanan sana,an ai anan ko ga kuma masaya na dayawa . Nace wanan shawaran yayi daidai gaskiya kaga a dan lokaci kankani zamu samu mu hada abinda muke so ke na yace shi ya gani shima. Batare da jin wani darrr ba nace ya je da dare idan yazo zan fito mai da kudin don yanzu idon mutane yayi yawa a kan mu. Ya gama min dadin bakin shi daya iya ya na shiga gida don jamil a gurin iya dadin baki baida tsara a kauyen mu nan da jin dadi na na shiga gida. Sai ga umma na gyaran gurin da take kiyon awakanta ta dago tana fadin yanzu muka gama maganan ki da babakin yushau nake fada mai riban da kika samu da sana,an ki . Shine ya kawo shawaran mai zai hana a sayo maki shanu a turke maki har lokacin da dabbobi zasuyi tsada a sayar nace ya bari ki shigo muyi shawara dake. Fuska na bata tare da fadin kash umma baki fada min wanan maganan da wuri ba yanzu fitan nan da nayi har na bada sakon a saro min kaya don ni ba zan samu zuwa ba wanan satin da kaina. Kuma gashi har mai sakon ya wuce ko fuska ta sauya tare da fadin Allah yasa haka shine alheri nace amin nayi saurin wuce guri don naga kamar bata yarda da magana ba a lokacin. Don idan zan sari kaya da kaina nake zuwa in sari duk abinda nake so in dawo don ko gidan baba kabiru sai inyi shiga goma ban leka su ba duk ko da cewa tan uwana suna gidan. Sai idan naga dama nakan dan leka su a gurguje in fito duk zuwa da zanyi sai anty tayi min korafin yadda na mayar da kaina wata gaja saboda da neman duniya ina karamar yarinya dani haka. Takan ce arziki na Allah ne ko nayi ko banyi ba idan lokacin arzikina yazo Allah zai bani ne gama mu da kudin mahaifin mu ake saka ran fitowan shi a ko wani lokaci zamu iya samun abin mu. Wanan fadan da takan min nakan ji zafin shi don ina fanin tana min hassada ga samun da taga inayi ne a yanzu ga zugin Jamil dake shiga kaina kan in raba yan uwana da can din ma gurin su anty din. Ga maganganun da wasu dangin mu yan hana ruwa gudu da sukan min kan dukiyan mahaifin mu wai su baba kabiru sun karbe sun cinye su da iyalin su. Maganan yanzu da nasan kudi sosai ya zauna min a raina sai nake ganin haka din ne don su ko yaushe yanzu a cikin wadatata suke don basu rashi sam. Dare yayi jamil yazo na fito da kudin zuwa gurin shi muna gaisawa yake fadin to yaya ina can ina Allah Allah kar gimbiyar tawa ta canza shawara don nasan idan umma ta sani zancen ta baci. Nayi murmushi tare da fadin ina zan bari umma ta san wanan zancen kaiko sai dai ina shiga dazun ta tare ni da zancen wai in kawo kudin a sawo min saniya da kudin. Da sauri yace sa may injin baki bata ba dai nace gasu tare dani yanzun haka ban yarda na bata ba don karya nayi mata kan cewa nabada sakon su a saro min kaya ai. Yayi wani irin shu,umin dariya tare da fadin da kyau ta wurina ita umma may tasani kan kudi yanzu su burin su ke nan idan mutum ya dan samu kudi ace wai yasai abin kiwo dashi. Nace ai ni ba zan yarda da wanan shawaran nata ba ga kudi ina ganin inda zamu samu karuwa wani zancen kiwo ake yanzu kuma da za a zo a girke a gida karshen tama ba wani riba a ciki. Na kawo kudin dana kulle a cikin bakin leda na mika mai yana rawan jiki ya karba tare da fadin gobe asubanci zanyi don in samu in dawo da wuri kin ga har rumfa na kafa dazun bayan rabuwan mu dake inda zan fara sana,an tawa. Bai dade ba yace zai tafi don ya samu barci issashe don asubancin da zaiyi a gobe din mukayi sallama dashi ya tafi na koma ciki cike da murnan wanan shawaran da jamil din ya kawo muna. Don ina ganin zai ma fini samun riba a yadda ake cinikin man fetur da gas a kauyu kan mu don masu noman rani dake amfani da injin da sauran abubuwan bukata don rashin wutan lantarki da muke dashi a garin. Washe gari sabo da murna ban fita talla ba barci na nayi sosai a gida sai zuwa sha daya da umma ta jini shiru ne ta leko dakin mu tana fadin. Yar kabiru yau nace ba fita tallan kayan ne ko hutu kikeyi ne haka na bude idona da kyar tare da fadin umma yau hutu nake yi don ba wasu kaya da yawa a tare dani sosai. Takai dubanta gurin da nake aje kayan tana fadin lalaikan kaya sun fada sosai wallahi kila zuwa gobe sakon ki ya iso ai kinga sai ki fita da tushe. Sai zuwa a zahar na fito na debi ruwa na watsa ma jikina na nemi abinda zanci don tun safe ban ci wani abin kirki a cikina ba don dauki da nakeyi jira kawai nakeyi inji ance ga jamil can ya bude rumfar shi ai. Sai dai har yamma banji komai ba yasa na dan fito na fita nabi ta wurin har lijacin ba jamil babu labarin shi a garin sai zuwa gab da magariba ne nake jin labari wai an tare jamil a hanya ko may ko may ban karasa jin maganan ba don faduwan da gabana yayi a lokacin. Fita nayi a gagauce don in tabbatar da zancen da nake ji nan nake ganin mutane gungu gungu kin san abu ga kauye basu iya samun magana ba. Yana kuka shabe shabe wai an tare shi a hanyan shi na zuwa birni sayan mai an kwace kudin an mashi dukan tsiya ko mashin din don sunga tsofo ne suka barshi dashi don ko sun dauka basu dauki komai ba don wahalanta. Jikina yayi sanyi nadai gode ma Allah da suka barmin shi da rai suka tsaya ga kudin kawai basu taba lafiyan shi ba sai dai ban yarda na nuna wani abinda zai kara tayar mashi da hankali ba a wanda yake ciki. Sai da dare muka samu kebewa dashi yake ban labarin abinda ya samay shi din inda hankalina yayi matukar tashi sosai na daiyi wa Allah godiya da ya dawo min dashi lafiya a lokacin. Satin shi daya sai gashi yazo min wai zai yi tafiya wani abokin baban shi yaji labarin abinda ya samay shi yace yazo ya taimaka mashi. Nayi murnan jin hakan sosai mukai sallama ya tafi akan washe gari zai tafi amsa kiran abokin mahaifin nasa a can birni. Abinda ban sani ba ashe kudina zai shiga birni yasha garalin shi dasu don abinda ya faru yana barin yankin kauyen mu da jarkokin daya dauka na sawo mai na bat da kama dayayi ya watsar dasu a hanya a cikin jeji. Ya shiga gari ya yi sayayan yadudukan shi na maza dasu takalma da sauran abin da yake da burin bukata a rayuwan shi. Sune ya koma ta karbi dinkunan shi ya karasa kashe kudin daya saura a hannun shi don rashin tausayi da imani da bai dashi. Nabi ruwa nabi iska na bi rana da sanyi na samo su rana daya jamil ya zo yaci amana ta ranan ko barci ban yi ba sai faman sakawa da kwancewa nake a raina. Ina kallon kayan sana,ata da dan abinda ya rage min a ciki wanda basu taka kara sin karya ba a lokacin wanan abin har zazzabin dole ya ja min sai da nayi jinya akan hakan. Bayan kamar sati uku ina dan bubugawa har tiren sana,an ya dan fara dagowa kaya ya fara samuwa min ga kuma kewan shi dake damuna a lokacin don tunda ya tafi ban samu labarin shi ba. Kwatsam sai gashi ya dawo garin kowa sai da ya girgiza da ganin canzawan da yayi a dan kankanin lokaci ya murje yayi kiba ga shiga ta alfarma da yakeyi kamar ba dan kauyen mu ba. Ban dai san inda umma taji rabarin ai nice na bashi kudin da yake karyan sun zube ba sai ji nayi tana fada tana fadin dama wanda baiji bari ba yaji hoho gashi yanzu ya fara nuna maki irin gidan su mayaudara. Na fada maki ki rabu da yaron nan ba dan arziki bane da yake ke mai taurin kan tsiya ne kika dauki kudi kika bashi ya shiga birni yasha garalin shi dashi. Yar nan kina arziki kuwa da wanan yaron da kika lakanta dama na fada maki ko mutuwa nayi sai na taso maku fatalwa idan kika ce wanan shegen yaron zaki nacewa. Yanzun dai ga magana ta nan ya fara fitowa fili ai ya yaudare ki ya raba ki da komai naki sai kamay kamay da ya barki kina yi a gari yanzu. Gabana ne ki faduwa don jin abinda umma take fada sai dai ni yace min abokin mahaifin shi ne ta bashi kudi ai yace ya sai kaya ya kuma koma karatu idan yana son ci gaba. Sai dai yaga ni banci gababa saboda shi ta yaya zai tafi ya barni a cikin wani hali ire iren dadin bakin da yai min ke nan lokacin daya dawo garin na gashi a cikin wadatan da ya dawo dashi. Na kasa hakkuri da dare daya zo sai dana fito mai da wanan maganan da umma tayi min ya dan yi shiru kafin ya hau fada yana fadin . Kai mutane basu son suga mutun ya samu karuwa yanzu, yazun kuma sherin da aka lakakamin ke nan shiyasa sai da na nunama baba sabo cewa ya bani kudin inzo in rage maki hasaran da mukayi. Amma ya nuna min ba haka ba yace in har kina sona tsakani da Allah aike ba zaki yarda da hakan ba a tsakanin mu. Jin wanan maganan ne yasa jikina yayi sanyi na kara yarda dashi hundred pacent naji ina son shi sosai a raina na watsar da maganan umma da na hau da farko. Yanzu bini bini Jamil sai yace yayi birni idan yaje sai ya share makonni a can yana sheke ayar shi kafin ya dawo gari duk wanan baisa naga laifin a raina ko kadan. Sai ma nake ganin na faso gari ai ina da saurayin da duk garin mu ba mai irin sa a garin kamar ni a yanzu mutane suna ganan min illar cutar da yake da buri a kaina wanda ni ban taba hango hakan ba. Gashi duk zuwan da zaiyi gurina sai ya fito min da zancen kudin mu na gado wanda ni ban kawo komai ga hakan sai ganin nuna damuwan shi ne da kulawa a kan mu yakeyi. Sannu a hankali mutanen dake ara min kudi ina bunkasa sana,a ta suka fara janye kudin su a gurina sai sana, an ya koma min gashi na yika nakeyi a yanzu. Ga kuma yan canjin da yake karbe min daga yace ya tashi bai da ko kobon da zai kashe sai ya kawo min wani lalura can ya aza min dole in lale kudin in bashi ya shige birni yaja garalin shi dasu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:53 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 1️⃣2️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA Wanan yawan maganan da umma ke ta yada min a gida tare da korafi ga kuma wanda na karbi kudin a hannun su na dan kara ina juyawa sun sakani a gaba akan in basu kudin su. Sai nayi shawaran zuwa birni gidan baba kabiru ko zan samu sauki a raina a ranan da nazo ban samu baba a gida yayi tafiya zuwa headquater jahar mu don halartan wani taro da zasuyi a can. Na samu taro na mutunci kamar yadda suka saba min idan nazo na kebe da kanne na ina tambayan lafiyan su da yanayin zaman su a gidan inda suka nuna min basu cikin wani damuwa. Da dare ne muna hira anty ta sako min zancen kudin dana ba wa jamil ya ce ya bace din take min fada akan hakan zafi naji sosai a raina da sukaji wanan maganan. Haka ya hasalani na rufe ido nayi mata tujaran da sai da ta kwanmace batayi min maganan ba don komawa nayi kamar wata zarara na dora hannu a kai na dinga yanka masu ihu a gida har makwabta sai da suka shigo tambayan ko lafiya. Ina fadin don anga iyayyen mu basu da raine ake muna wanan nuna bambanci haka komai nayi sai ace banyi daidai ba a rayuwana ranan dai ba karamin tujara nayiwa wanan matar mai kainan mu ba da zuciya daya akan dan maganan gyara kayan ka kawai da tayi min. Don duk abinda zai bata min jamil bani kaunan shi a lokacin a raina sai nake ganin zata iya tunzura baba kabiru wanda nake da hope akan shi zai aura min jamil mu zauna lafiya a lokacin. Sai daga baya ne naji kunyan abinda na aikata mata din don washe gari bata dauke ni da komai a ranta ba yadda na zata zata fita batun mu. Wanan abin da nayi mata ya dawo yana damuna har baba ya dawo na dauka zata fada mai sai banji yai min maganan komai ba. Har na gama kwanakin da zan masu don ban iya zama a inda babu masoyi na a lokacin na tattara na koma kauyen inda nake jin dadin rayuwa kowa na zuba min ido ina dauka sona suke a hakan da suke min. Zaman na kauye a lokacin dai gashi nan dai ne a gare ni don yanzu ban wani sana,an kwarai don duk ya cinye min jarin da nake dashi wanda ni a lokacin ban dauki hakan komai ba a rayuwa na. Zaman hakana ga maganganu suna zuwa wa baba kabiru a kaina don har ya kai yanzu ina zuwa dakin jamil muna hira a can wanda hakan a kauye wani abin magana ne sosai koma birni ne wace duk ta san kanta da mutuncin kanta ba zata aikata hakan ba. Haka yasa baba kabiru ya shiga nema min addmition na nursing school don kokarin da nake dashi burin shi shine mu zama wani abu a rayuwan mu da zamu iya rike kan mu a gaba. Alhamdullahi an sama min addimition din baba ya saya min komai da zan tafi inda ya aika min kwantsam in taso tafiya makarantana ya tashi. Hankalina ya tashi da jin wanan maganan don ban taba tsanmanin hakan ba don ni burina shine muyi aure da jamil ko zan huta da kalubalin rayuwan da nake fuskanta a yanzu. Sai ga zancen tafiya ya taso min inda jamil ya zugani sosai kan shi sam bai yarda da zancen zuwana makaranta ba ai idab son samu ne shi ya kamata da yake namiji ya tafi karo ilimi. Ganin ranshi ya baci sosai akan tafiyan hankalina ya daga sai dai babu yadda zanyi don dole in tafi din don ba zan iya musa ma iyayyena maza ba a lokacin. Ganin ban da mafita do ko ranan da zan tafi din da dare sai da muka kai ruwa rana dashi inda muka gama yanke sharawa na kamo hanya da safe zuwa birni. Na samu baba ya gama min sayayyan komai da zan bukata a karatuna har abinci da kayan girki komai ya saya min da na iso washe gari ne zamu tafi. Da dare washe gariin ne aka nemay ni aka rasa a gidan baba kabiru din inda hankalin su ya gama tashi sosai da nema na a garin sai dai babu labari na ko ina. Ran baba ya mugun baci ya buga gida ance banzo ba abin ya kara tayar mai da hankali sosai gashi nursing ba gurin wasa bane da za a dan daga min kafa . Basu ganni ba sai kwana biyu na dawo masu kamar wata gigitatta dani ina fama da matsanancin ciwon mara dake addabana. Gashi ban son in zauna a gurin da mutane suke zaune nafison in kebe gurin daya indinga tunanen halin rayuwan dana tsinci kaina. Anty tajini shiru tazo falo don ta dubani don kowa na cikin daki suna kallo wasu ma sunyi barci a lokacin halin tashin hankali ta samay ni ciki don ni ban san ta tsaya ba a kaina ina zaune sai buga kafa da rike mara da nakeyi ina ciza baki. Hankalin ta ya tashi da yanayin da ta riske ni din daki ta koma hankali a tashe tana fadawa kanwa ta summaiya da suke matukar dasawa da ita anya ba ciki yar uwarki ta zubar ba kuwa. Hankalin shamsiya yayi matukar tashi dajin zancen inda ta samay ni a falo hankali tashe tana tambayana may damuna na dai boye mata komai . Abinka da dan uwa take fada min abinda anty ta fada mata a kaina wanda jin hakan yayi matukar girgizani don ban sauka kowa ya fahinci halin da nake ciki ba. Ashe abin ba haka bane duk wata uwa ta gari tana saka ido akan yarta tasan duk takon da yarta ke takawa nan dai na hau fadan karya inda nake shiga ba nan nake fita ba sai da sumaiya ta taushe ni a kan zancen kada aji ace kuma wani abu. Ido kawai baba ya saka min don bai iya cewa dani komai ba sai idon da ya saka min a gidan sai dai banyi zaton bacin rashin yakai haka dani ba sai lokacin dana tashi komawa kauye yace ai na dawo nan ke nan don babu inda zan tafi kuma mutane suna zagin shi. Hankalina ya daga sosai da jin hakan na shiga jin haushin kowa har kannena takaicin su nake ji a raina kan wanan zancen. Dole ina ji ina gani zama na ya dawo a hannun baba kabiru na bar kauyen da sana,ata na dawo muka hade da yan uwa na wanda hakan yayi wa umma dadi a ranta sosai. Don tana ganin rabuwana da Jamil yazo ke nan a lokacin don taji komai ta kuma san halin da ake ciki sai dai zaman ta na kaka a gare ni ba yadda zatayi ne ga tsufan da ya kamata a lokacin . Zaman dai gashinan ba wani dadi har lokacin da yar uwata ta kare karatun ta muna zaune tare inda muna samun manema sai dai ni har lokacin ba wanda ya kwanta min a raina kamar Jamil dina. Kwatsam sai jamil shima ya tattaro ya dawo birni da zama gidan wanan abokin mahaifin nasa haka yai min dadi so sai a raina don masoyina da ke zaune yanzu a kusa dani. Tsagumi bai kare ba ga bakunan yan kauyen mu don har nan din ma basu barmu ba don maganan dayace koda yaushe shine su baba kabir sun cinye muna gadon kudin mu. Maganan bai yi zafi ba sai lokacin da dan kudin birnewan da gwaunati ke bayarwa na mahaifina da ya fito inda aka raba muna aka ware ma mahaifiyar shi nata. Nan mutane suka shiga tofa albarkacin bakin su wai kudin yafi haka yawa an dai san yadda akayi dasu ne inda mu kuma jin hakan ya fara daga muna hankali. Bamuyi kallon irin fadi tashin da baba kabiru yakeyi akan komai na mahaifin namu ya fito ba sai dai burin mu muji ina dukiyan iyayyen mu ya shiga. Wanda Jamil na daya daga cikin masu hasasa muna wuta akan hakan har takai zugan su ya shiga kawunan mu sosai mun fara dauka don haka muka tafi kauye muka samu umma kan muna son jin inda motar mahaifin mu da sauran dukiyan shi suke. Wanda hakan ba shawaran kowa bane sai nawa ni dake daukan zuga sai kanina Baffa da yanzu ya tasa shima burin shi na akan son jin komai don mun zugu da yawa a gurin mutane. Kakan mu batayi sanyi a gwiwa ba ta aika iyayyen mu maza suka zo ta tara su inda ta fito masu da maganan da muka zo mata dashi. Kai baba kabiru ya jijiga yana fadin Allahu akabar da yaran nan sun san komai akan dukiya da basuyi muna wanan fahintar ba sai dai yanzu a kira su muyi masu bayanin komai don suji su sani. Umma tasa a kiramu muka shigo idona ya bushe banjin nauyi kowa a cikin su a lokacin ni dai burina kawai in san inda dukiyan mu ya shiga don Jamil yace idan mun samu zamu iya rufawa kan mu asiri muyi aure da dukiyan. Ga wautana da rashin wayona da mahaifana suke kiramin kullun a lokacin da suke a raye sai nake ganin ai yin hakan shine daidai a gare mu. Baba kabiru ne ya fara da addua tare da fadin umma ta fada muna maganan da kuka samay ta dashi sai dai ina son ku sani mu bamu ci kwandala a cikin dukiyan mahaifin ku ba. Abinda bamu son ku sani yau ya zama dole gare ku ku sani don mahaifin ku ya mutu da bashin banki a tare dashi. Wanan nauyin ne muke ta kokarin ganin mun sauke a kanshi da abinda kuke hasashen mun ciye maku din nan dai ya shiga yi muna bayanin inda ya dora da fadin yanzu kuma Alhamdullahi don mun sauke mashi wanan nauyin a kan shi mun biya bankin bashin shi da kudin gida da motan da muka sayar nashi. Da fatan zaku fahince mu yanzu tsuru tsuru mukayi a dakin babu wanda ke iya magana a cikin mu lokacin ga nauyin da mukaje nasu kan kokarin da suke akan mahaifin mu din. Baba musa ya dora da fadin ban taba tsanmanin zakuyi wa wanan bawan Allah butulcin ba kabiru akan irin kokarin da yake a kan ku. Hakkuri muka shiga bashi muna fadin ya yafe muna munyi a kan kuskure da zufan mutaje ne don bamu san haka zancen yake ba ai. Muka mike simi simi don barin sakin don shi baba kabiru bai iya furta komai ba a lokacin sai baba yushau yace ai ba tafiya zakuyi ba. Ku zauna muka dawo a inda muke yace yanzu ku bakuji nauyi da kunya ba kan rikon da bawan Allah nan yake maku don mu din nan badon shi yana a cikin mu ba ina zamu shiga zuwa nemawa mahaifin ku dukiyan shi a kasan nan. Umma ne ta karbe da fadin duk wanan tsegumin yana gurin wanan mai shegen idanuwan kanana da kuke gani ba kowa ke zugata ba kuma sai wanan famfararen yaron da ta lakanta Jamil. Na fada maki ko mutuwa zakiyi sai dai ki mutu don ba zamu aura maki shi ba muddin ina raye sai dai ki mutu naji haushin wanan maganan da umma tayi a kaina a gaban iyayyena maza da suke da Alhakin daura min aure koda kuwa ace iyayyena suna raye ne sune dai din ma daura aure na a duniya. Ban iya cewa komai ba haka muka bar dakin a cikin bacin rai muna shiga daki kanwata sumaiya ta hauni da fada sosai tana fadin sai da tace muna kada muyi wanan maganan muka zo mukayi. Budan bakin Baffa sai cewa yayi da ita ke dole fa mubi ba ba,asin dukiyan mu don muna da gaskiyan mu yanzu ba cewa akayi wanan gidan da baba kabiru din yake ginawa ba yana cewa nasa ance da dukiyan mu ne yake gina sa ba. Don may zamuyi shiru akan abinda yake hakkin mune ba zamu tambaya ba tace yanzun da kuka tambaya ai kunji abinda bai muna dadin ji ba don ashe baba ya tafi da bashin banki ne tare dashi kuke wanan haukan. Bata bar baba kabiru ya dawo ba sai shiryawa tayi tana fadin ita binshi zatayi ba zata zauna ba don zaman kauyen ya isheta gaskiya. Dole muma muka shirya muka biyo shi birni har muka dawo bai nuna muna komai na bacin rai ba a tare da mu sai ma dan hiran da yake jan kanne dashi a motar. Gaskiya baba kabiru mutum ne da yasan hakkin rike maraya sosai don irin kokarin da yake ya yaki zuciyar shi a kan mu da kuma iyalan shi. Don bai taba yarda a kawo sukan mu a gurin shi koda ko mune bamu da gaskiya yanzun zai ma mashi fada sosai tare da fadakar dashi illan yin hakan gare mu. Mun dawo haka rayuwa ta ci gaba da tafiya muna inda yanzu shirin auren diyar baba kabiru mace ake yi wanda yaso ace nima a lokacin tunda ba karatu nake ba na samu wani tsayayye na tsayar ya hadamu tare yai muna aure. Sai dai banda Jamil ban kula kowa har yanzu gashi shi kuma jamil din baida ranan zancen auren mu din don bai aje ba bai ba wani ajiya ba. Dole haka aka fara gabatar da bukin yar uwata a gidan inda yan uwa da abokan arziki birni da kauye suka cika muna gida. Ayi lafiya an watse lafiya kowa ya koma gidan shi a cikin farin ciki zuwa lokacin baba kabiru ya karasa ginan shi muna shirin komawa ciki ke nan. Ranan laraba muka kwashe zuwa sabon gidan mu inda a nan dakin mu daban na yara da muke zama mu yan matan dakin anty amar mu biyar ne nata daya sai mu biyu da wata diyar baba yusha,u da mahaifiyar ta ta rasu a gurin haihu. Da suka je gaisuwa ta biyo anty muka tashi mu biyar sai kannen mu maza dake zaune da ita da nata biyu muka tashi mu takwas a gurin ta. Duk da wanan yawan rayuwan mu ba zaka ce ba itace ta haife mu ba don gaskiya babu banbanci a gurin ta da wanda ta haifa damu din haka muke rayuwan mu a cikin jin dadi. Don yanzu Allah yaiwa baba din budi sosai zaman mu gwanin ban sha,awa a gidan ana cikin haka ne umma ta kawo masu ziyara a garin. Munji dadin zuwan nata sosai inda muke zama gwanin ban sha,awa babu wani tsangwama a tare damu sai dan dan gulman mutane da ba a rasa ba dake zuwa yana dawowa a tsakani. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:53 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 1️⃣3️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA IMANI A ZUCIYA YAKE SANIN ALLAH DA IMANI DASHI YANA SA MUTUM TSIRA DAGA HALAKA AMMA FA SAI WANDA YA DAUKA DA GASKIYA YA KE KAI GA HAKAN UBANGIJI KA KARA MUNA IMANI A ZUKATAN KASA MU FI KARFIN ZUCIYAR MU, , , , JUMMA,ATUL HAIRAN YAN UWA MUSULMAI 👏👏👏👏👏👏 Zaman mu da umma a gidan baba kabiru ba tsangwama ko kadan yadda takewa kowa a cikin jikokin ta haka muma muke da ita har ina mamakin ta. A cikin wanan yanayin ne Jamil ya labartawa wani dan mutumin da yake zaune a gidan shi labarin mu dana mahaifin mu shima yaji yana ra,ayin kanwata summaiya ya samu wanan gara basan na mahaifin mu da jamil ke labarta mai zamu samu. Haka yayi dabaran daya hada sumaiya da wanan dan gidan da yake zaune dasu yazo gurin summaiya da sunan soyayya a gare ta. Sai dai shi wanan ba rago bane kamar jamil dina don yana matakin kare karatun digree din shi a lokacin. Batai wani na,am da shi ba a lokacin don ta gane manufa hakan a gareta don anty amarya ta hasko dabaran su a gare mu bata kuma boye muna ba ta fada muna kai tsaye abinda suke nufi damu din. Sai dai irin matsin da yaron keyi na zuwa wurin kanwar tawa tare da dadin bakin jamil yasa har take dan sauraron shi don yace da zuciya daya yake sonta a yadda yace mata din . Wai yana jin labarin ta yaji hankalin shi ya kwanta da ita sosai saboda tausayin mune yaji yana matukar son ta a ran shi don rashin mahaifan mu da mukayi. Sannu a hankali suka kulle dashi har ta fara samun kanta sai dai korafin anty a kan haka da tashin hankalin ta yasa tana dan ja da baya ga zancen shi. Tafini farin jini don tafini kira sosai don ni irin matan nan ne na fada maku tun baya ni kwalliya ma bai damay ni ba haka mukan ta kwasa da anty akan gyara irin na yan mata kullun muna zaune da daurin zani a gaba a gida wanda take mana masifa akan hakan idan tana gida idan ko ranan aiki ne tana gurin aikinta sai mu zauna hakana a gidan ba wani gyaran jiki. Don muna ganin ai ba inda muke zuwa banda gida gyaran may zamuyi itako anty yar gayece ta karshe gyara dai na matan zamani ba wanda bata iya ba. Hakama girki da gyaran muhallinta bata sakaci da wanan don idan mutum yana zaune da ita sai yaso ya ketaci kanshi a kan gyara idan kaji fadan ta damu akan rashin gyara ne da bamu yi don haka muka saba mu tun a can da muka taso. Dole ta kawo ido tasa muna hakana a yadda ta ganmu kamar wasu yan kauye damu ga yan uwanta daga Niger state suna yawan zuwa gurinta duk yan gayune su amma mu hakan duk bai damay mu ba. Wata rana umma ta tashi da ciwo mai tsanani a gidan wanda kowa na gidan hankalin shi ya tashi sosai da ciwon nata. Allah da ikon shi ana treating din ta ta samu lafiya sai kuma gudawa ya biyo bayan samun lafiyan nata nan ma hankalin iyayyen namu ya tashi sosai da ciwon na umma da takeyi. Kwana uku tana fama da wanan laluran ranan muna barci da dare anty ta tayar damu daga barcin tana fadin mu tashi mu ga halin da kakan mu ke ciki a lokacin. Abin gwanin ban tausayi mun falka mu samay ta a wani irin yanayi sai sambatun take faman yi haka anty tayi dubaran karantu mata kalman shada sai take amsawa daga inda take din gashi a lokacin baba yayi tafiya don ganin umma ta samu lafiya. Ba wani shirine tsakanin umma da anty amarya ba don bata ra,ayin ta ko kadan haka dai anty ke shanye halin umma har Allah yasa ta hayyayafa a gidan tare da baba kabiru din don shi yana son matar shi. Kiri kiri umma zata nuna bata son ta bata son diyan ta data haifa a gidan da baba kabiru din sai uwar gidan ta yar asalin kauyen namu itace mata a gurin umma. Idan baku manta ba na fada maki haka mahaifiyata ta sha wanan faman da umma lokacin da take zaune a kauye akan uwargidan na baba kabir da umma keji tankar itace ta haifa ta sa cikin ta a duniya. Don har mutane na fadin ba a banza ta barta ba kan wanan halin da take nunawa da diyan ta ma sune jikokin da umma tafi so a cikin jikoki gaba daya. Idan anty amarya taji sun shagala da zancen da bata ji daga inda muke a zaune sai ta fadi kalman shahada sai umna din ta karba daga cikin dakin mama din da take kwance. Hankalin umma yayi matukar tashi sosai ta mike ta fita zuwa makwabta a kwai wani tsoho da muke makwabtaka dashi da wani ba haushe a uguwar duk sauran yarbawa ne da iyamurai don sabon uguwane sosai gurin ba mai kula harkan wani a cikin unguwan. Tsohon yazo ya duba umma shima hankalin shi yayi matukar tashi sosai da ganin yanayin na umma dayayi yace yanzu dare ne babu yadda za a yi da an kaita asibiti. Baifi awa daya da fita ba anty amarya kuma bata fasa fadan kalman shahadan da take fadi ba a bakin ta Allah ya karbi ran umma take a wurin . Wani sabon tasgin hankali kuma a gare mu mun koma ba uwa ba uba babu kakan da muke dan rabawa muji sanyin rashin iyayyen mu a gurin ta. Haka muna kallo washe gari aka kawar da umma zuwa makwancinta ubangiji yasa sun huta da duk kan musulmin Allah da suka rigamu idan namu yazo mu cika da imanin ubanginjin mu Amin. Anyi zaman uku aka watse lafiya tare da jimamay rashin umma da mukayi lokacin bamu da kowa sai Allah sai baba kabir da matar shi anty da ta rikemu amana a hannun ta. Do muna ganin tafi muna duk yan uwa a gurin mu tunda ta zauna damu da zuciya daya sai muka kara mayar da ita uwa sosai a gare mu da muke da ita yanzu a duniya. Soyayyan mu da jamil yana nan duk da ba wani karuwa da nake samu a gurin shi a matsayin na wace zai aura sai dai zuciyata da gangan jikina ya yarda dashi dari bisa dari sosai. Itama sumaiya duk da farin jinin da take dashi na samari hankalinta yafi karkata akan wanan usman din da jamil ya hada ta dashi saboda karin kwarin gwiwan da nake bata . Wanda ita ma anty takan ce ai gara dashi din yafi mata jamil do shi yana da ilimi ana sa ran alheri a gare shi nan gaba don ilimin da yake dashi din. Ya gama ya jona karatun master din shi duk suna tare da summaiya din har lokacin dole kowa ya kawo ido ta zuba muna don babu daman magana sai mutane damu suce ai don basu suka haife mu bane suke muna hakan. Shinedalili su na saka muna ido a gidan ba tare da sun matsa muna ba sai dai yawan magana dake damun mahaifin mu din akan mu tundai ni na naki aure ya sa min ido yasa baba kabir din amincewa da jamil din yanzu. Sai dai kuma inda matsalan yake babu wani zancen auren shi a gidan su don bai da wani sana,a takamaimai da yake amma koda yaushe zaka ganshi fes dashi kamar dan wani gwauna ne don karya. Ban taba hango illan hakan da mutane ke gani ba akan Jamil din asalima ni dadin ganin shi hakan nake ji don ina ganin na haska a gari ai tunda ina da mutum kamar Jamil a tare dani. Ana cikin haka ne mahaifin jamil ya tattaro ya dawo birni da zama gaba daya da iyalan shi suna zaune a gidan da yayan jamil din ya gina don yana aikin soja ne shi. Yasa ya dankara gida a birni sai mahaifan nasu suka tare a ciki kanin shi kuma yai aure ya zauna tare da matar nasa a ciki baba kabir yana daukan shi wa a gurin shi sosai don alakan zamantakewan tare tun iyayye da kakanni a gida. Yaje ya samay shi akan zancen namu sai mahaifin nasa yake fadin shikan ina zai masa aure yanzu baida wani cikakken sana,a da yakeyi. Baba kabir ya dawo gida da bacin rai babu yadda zaiyi ya zuba min ido maganan ta zauna a kan hakan yace in fito da wani ya aura min tunda ga abinda mahaifan jamil din suka ce. Anan inda akai maganar na bar zancen ban kara bi ta kan zancen ba zai zo wuna mu sha hiran mu ya tafi har dai abin ya ishi baba ya nemi shawaran yan uwan shi akan zancen namu da jamil din. Baba musa yace idan ban fitar da wani ba ya aurani ga wanda yake so mana ai dole in zauna ko ban wa Allah tunda na zama abinda na zama a cikin dangi. Shi bai taba ganin yarinya mai taurin kai irina ba a rayunwan shi sanyi hali irin na baba kabir din ya sa ya daga min kafa ga zancen. Ina zaune gida ga masifa da kanne na a gidan ban bar diyan su sun sakata su wala yanzu za a ji mu dasu wanan abin yana yawan bakanta ran baba kabir sosai sai dai bai yarda yayi ko ayi muna abinda ran mu zai baci. Da abin ya ishe shine ya tayar da yan hayan gidan mu da aka saya muna daga baya ya shiga gyaran gidan gadan gadan sai da ya kusa gamawa ne yake fadin ya tsayar da ranan bukin mu da jamil. Ya samu iyayyen jamil ya sheda masu basuyi wani na,am da zancen ba sai dai a gaban shi matan mahaifin nashi sun nuna farin cikin su a gaban shi. Babu kuya mahaifin Jamil bayan kwana biyu ya aika yana neman baba kabir da shawara bai ki zuwa ba ya samu lokaci yaje gurin amsa kiran mahaifin Jamil din. Sai cewa yayi da baba yana nema alfarma akan maganan da yazo mai da ita yana son gidan da zamu zauna da jamil din a gyara masu dayan part din amaryan shi ta zauna a ciki don barin yara su kaidai haka bai da alfanu. Kawaici irin na baba kabir sai baiki hakan ba amma yayi mamaki da jin hakan daga gurin dattijon da ya iya taro shi da wanan maganan haka babu kunya babu tsoron Allah a cikin sa. Sai a lokacin ya kara hasko maganan mahaifiyar su umma sosai akan zurian su Jamil din da take fadi har ta kwanta damanta ba mutanen arziki bane su. Ya dawo gida da zancen nan matan shi suka shiga tofa albarkacin bakin su kan zancen don mai zai yardan masu da hakan yasan ai ba ni kadai bace da gadon gidan da za a mamaye ma yan uwana samun su a hana su don wasu. Fada baba yayi kan su bar zancen a dai samu ayi auren kowa ya hutu zaifi alfanu idan anyi hakkuri komai sai yazo ya wuce ai dole suka ja bakin su sukai shiru akan zancen. Ni dai duk hakan ina ganin ai ba illa bane a gareni don an taimaka masu da wurin zama ba zai zama abin magana ba kuma. Ga abin magana mutaje na gani babu halin a maganta don baba ya hana maganan sai dai ayi a bayan shi don bai ba da kafan yin hakan ba shi dai gurin shi ya sauke nauyin daya rataya namu a wuyan shi yanzu. Dole ba don anso ba kowa ya saka ma zancen auren nawa ido aga iya gudun mu da baba kabir din har iyayyen nasa da suka zo da wanan korafin . Sannun a hankali kamar yadda ko wace budurwa takan yi shiri bukin ta nima haka din ne a gurina sai dai mai karatu idan nace maki ko cibi ban aje ba na kaina duk ko da Sana,an danayi a baya kada kiyi mamaki. Amma haka baba kabiru ya fitar da makudan kudi ana mun sayayya yakuma ce a tambaye ni irin kayan da nake so na daki ai min anty ta ritsani sai cewa nayi ni roses nake so tace dani yanzu an bar yayin du ka crystal nan sun fito su ake yayi nace ni dai roses nake so a lokacin haka yasa ta shiga nema min roses din ta samo masu kyau da daukan ido aka saya min. Duk wani kaya na jin dadin amare sai da baba kabiru din ya saya min su don dai kawai ya fitar min da hakkina a kanshi nan aka fara kudindumin a cikin dangi kan zance shi dai baice da kowa kala ba kan bukin. Ance rana bata karya sai dai uwar diya tayi kunya don ranan buki yazo saura sati uku bukin mu da jamil iyayyen shi suka tare a gidan namu. Babu kunya ko nauyin hakan a tare dasu alai,alai abinsu a gidan namu na gado babu nauyi ko kunyan hakan a tare dasu udan anyi magana sai suce ai gidan diyan dan uwan su ne suka zauna ciki. Don dan su dake soja ya nuna masu bacin ranshi kan hakan da yake mahaifin nasu mutum ne mai bin ra,ayin matan shi sai bai ganin illan yin hakan don ita amaryan nasa burin ta tabar gidan dan kishiyar nata da take zaune a cikin sa a lokaci. Ni kuma na samu daurin gindi a gurin baba kabir ba wanda ya isa ya fada min gaskiya abinda ake kullawa kan hakan akwai illa a cikin sa. Gani raguwa inji anty yaya zama da sarakai zaiyi dadi irin yadda nake nan ban san ciwon kaina sai dai ance fadan dayafi karfin ka sai ido kawai. Haka yasa dole suka saka ido har saura yan kwanaki buki dangi suka fara halara gurin bukin inda a bangaren Jamil ma haka ne don dangin shi sun fara isowa gidan. Kai duniya wanda baida mafadi baiji dadin duniya ba wallahi don rawan kan da nake wai ni a dole ga amarya kowa na kallo na a hankade niko ban damu ba gurina kawai inga na malki mijina a hannu na a lokacin. In huta da zama gida cikin wahala da maraicin iyayye dake damuna ko yaushe don duk wanan gatan da kokarin baba kabiru a kan ni ban ganin hakan komai da ake muna ragaggene a gurina. Don nakan ce da mahaifana su na raye da abinda za ai min sai yafi hakan ai ga gulman dagi yan hana ruwa gudu da suke zugani wai ai da dukiyan mu ne baba kabiru yake mun komai. Wanda wauta da kurciya a lokacin ya hana ni hango gaskiyar maganan da zufan shi yake muna komai da yake yi din bada dukiyan mu bane don har lokacin komai na mahaifin mu bai fara fitowa ba. Har aka sakani a lallai babu wani motsi na al,ada daga gidan su Jamil da akewa amare irin kayan da ake kawowa din nan. An gulma ya fara tashi a tsakanin yan uwa da abokan arziki kan rashin wani motsi daga bangaren angon nawa inda shi jamil sai harkan yadda bukin namu zai kawatar yake a bangare shi. Sai ana saura kwana biyu ne daurin aure wata yar shi da suke uwa daya suka zo gidan mu anyi masu taro na mutunci sosai inda suka kebe da anty uwar amarya suna bada hakkurin rashin jin su da ba ayi ba din akan lokaci. Anty cikin fara,a take fadin ai babu komai duk gida ne damu dasu bata nuna masu komai a fuska sun dan zauna sai can dai a kunyace ta bude hijjabinta ta fito da yan turamay ko a leda tsiya bai bari sun saka su ba guda shidda wai gasu nan in fitan buki dasu daga baya idan sun samu hali ina gidan su zasu saya min. An karba da godiya da sa albarka sai dan shin kafa shima kwano biyar da suka gabatar mata wai a kara ayi hidimar buki dashi. Anty tace ai da baku wahal da kan ku ba don mahaifinta komai ya tanadar muna a nan sukace a daiyi hakuri a karba din Allah. Bayan tafiyan su ne ta fitar da kayan wa mutane nan kuma zance ya tashi karshe sai fita daga gidan nayi don ban iya sauraren maganan su. Dama baba ya saya min set din akwatuna da yan tufafin da yai min da zan saka aka kara zuba kayan da suka kawo a cikin akwatin. Shi dai baba sai fadin Allah dai ya bamu zaman lafiya ace gara da akayi albarkan auren ake nema ba kyalekyalin auren ba. Ga gida ya cika da yan uwa da abokan arziki ta ko ina a gidan don bukina kawai suka hallara wasu tsakani da Allah suka zo wasu kuma gulma aga karshen abin ne ya kawo su daga kauyen mu. Shiko gogan sai waya muke a tsakanin mu inda yake kara karfafa min yadda nake a rayuwan shi da irin taimakon da nayiwa rayuwan shi din. Anje an gyara min dakina komai tsone gwanin ban sha,awa dai kowa ya dawo yana yabawa irin kokarin da baba kabir din yayi don ba a ma maganan matan shi duk da suma sunyi iya kokarin su kan sha,anin. Party kan har kala biyu aka sha don jin dadin buki wanda ya shirya da abokan shi yan karya anci ansha an gwangwaje a gurin an dawo ana bada labarin komai. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:55 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 1️⃣4️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA LITTTAFIN KUDI NE IDAN KIN SAYE KIJI TSORON UBANGIJI KADA KI FITAR MIN DASHI DON AMANA NE A TSAKANIN MU KI GUJI NAUYIN AMANA A KANKI YAR UWA IDAN KIN GA MARA TSORON ALLAH TA FITAR KI GUJI SHIGA HAKKIN WANI YAR UWA DON NA BIKI DARI UKU AKAN NOVEL, , , , , , , , , , Duk wani abin al,ada na buki angama lafiya sai fatan Alheri ga auren mu da yan uwa da abokan arziki ke gabatarwa a gare ni. Abokan ango sun rako ango daki daya sha gyara sai kyali yake don katan alatun dayaji wanda a kauyen mu kaf idan da ca muke nabar tarihi a kauyen namu don haduwan dakin namu. Sai dai may bayan tafiyan abokan ango da kamar minti goma Jamil ya dawo daga rakiyan su yace hadizatul kubura yau dai Allah ya cika muna gurin mu akan jajircewan mu da juna. Ina dan murmushi na bude fuskana ina fadin bisa ga taimakon baba kabiru bawan Allah muka samu wanan cikan gurin namu da yake Allah yace ni matar kace jamil. Banda abinda zance da baba kabiru sai fatan Allah ya saka mashi da alheri yadda ya rike zumuci Allah ya bashi ladan zumunci kamar haka. Duk maganan da nakeyi jamil sai bin dakin da wani irin kallo yake wanda ba zan iya fassara shi a lokacin na burgewa ne ko na wani abu ba. Budan bakin shi bayan na gama magana sai cewa yayi dani amma dai ke har yanzu yarinya ce khadija wani kokari sukai maki a nan daki kamar na kauyawa. Da mamaki na juyo ina kallon shi ya ce eh duk irin dukiyan da mahaifin ku ya bari da wanda ya tara maku wanan abin zasuyi maki ga auren ki ? Yanzu dai ai kinga abinda nake fada maki ko da ina fada baki yarda yanzu don Allah wanan kayan yan kauyen tsohon yayi ya dace ace sunyi maki ? Tsaye nayi galala ina kallon shi don jin abinda yake fada a lokaci wanda ban san amsan da zan bashi ba kan maganan da yakeyi din. Yace eh na fada kuma gaskiya nake fadi da ke yar su ce wallahi ba zasuyi maki wanan wullakancin ba haka da komai na zamani zasu kawo muna. Amma da yake ke baki da wayau har wani addua kike kokarin zabga mashi irin haka ni har kunya naji da abokai na suka shigo suka samu dakin namu a haka. Yanzu jamil duk wanan uban kayan basuyi maka ba kake nufi yace wallahi basuyi min ba hadiza duk sake su zamuyi musai na zamani da ake yayi mu saka don abin kunya ne a gurina abokai na su zo suga dakin matana haka a wullakance bayan sun san yar gidan wanda na aura. Na fada maki ba son ku suke da zuciya daya ba kece baki yarda kin kasa fahinta na duk lokacin da nake fada maki sai ki dinga daukan magana kamar ina son hadaki dasu ne. To ai yanzu kin gani da idanuwan ki abinda sukai maki yar bare kike a gurin su kin fi nan gare su jima wani karamin tv da wasu kujeru na raini da suka saka maki a daki don Allah. Yar su da suka aurar haka kikaga sunyi mata ke baki tunanen haka da bakin ki ke fada min irin tsaruwan dakin hajara yadda suka gyara mata dakin. Kasa magana nayi sai tsayjn danayi galala ina kallon shi don yau na tabbatar mutum bai da kunya shi da ko pant ya kasa saya ya kawo min a matsayina na wace zai aura da kowa nasa ya kasa yi mai wani abin azo a gani a matsayin shi na dan su. Sannan iyayyena sunyi min abin arziki zai zo ya rena mamakon ya yaba da kokarin su a kaina da yake dan duniya ne sai yace koda yake ke har yanzun baki san komai ba ai. Don wallahi wanda suka sayar da gidan mahaifin ki a abuja ya fadi inda ba a karya kudin da aka sai wanan gidan naku zai iya sai maku ukun wanan ma don girman gidan mahaifin naku. Kuma kin san gida a abuja tsadane dashi nina dauka ya aje sauran kudin ne ai don laluran ku kawai wallahi nan hankalina ya daga sai dai ina tuna zancen baba kabir akan maganan baba na bashin da banki ke binshi sai nace niko ina ganin baba kabiru ba zai muna haka ba gaskiya. Ya bata rai sosai yana fadin ke may kika sani don Allah an barku a duhu ana cutan ku ya ja tsuki yana cire tufafin dake jikin shi fuska a daure. Idan akwai abinda naki baga jamil ya daure mun fuskan shi shima yasan da hakan yaune daren auren mu dashi duk da ba farkon kasancewar mu tare ke nan ba. Amma sai na koma fadin sun cuci kansu wallahi don mu basu cuce mu ba don amana muke a gare su dan uwansu ya haifa ya bar masu amana duk abinda sukayi mun barsu ga Allah. Wanan maganan da nayi yasa ya dan sassauta daure fuskan dayayi da farko don ya fara shawo kaina ke nan don duk takona ya sani kamar yunwar cikin shi. Mun raya dare mu kamar na sauran ango da amarya sai dai da safe kuma ya tashi yana cika yana batsewa duk a kan maganan dai dakin baiyi mashi ba. Ban fito ba sai da gari ya dan haska zuwa gaida iyayyen shi dake cikin gidan inda na zube daga kofan su ina gaida su da kwana ban san jamil yana dakin zaune ba tare da mahaifi nasa. Jin muryana mahaifin nasa yace in shigo daga ciki yana fadin ashe kuma haka mayaudaran ubannen ki sukai maki ya tabbata ke nan sun cinye maku gadon ku ko ? Nace baba basu cinye ba har yanzu kudin bai fito bane na baba yace sunciye mana waye bai san wanan maganan ba ya ta. Yanzun dai kuyi hakkuri da dan abinda suka kawo maku din tunda kin shigo cikin mu komai zaizo da sauki don ba zamu saka ido muga ana cutan ku ba haka ai. Nayi maki alkawarin zamu tsaya maki akan komai dake da yan uwan ki muddin muka samay ki a yadda muke son ki mai biyayya a gare mu. Nace insha Allahu baba mun gode yadai dan muna fadan zama tare da nusar dani akan saurin yarda da iyayyen nawa da nakeyi. Nayi godiya na bar sashen nasu don tsakanin mu dasu ba wani nisa bane kusan ma dakunan a hade suke sauran yan hayan da ba a tayar ba suna a dayan bangeren su uku. Ya ganin amarya suna ta zuwa daga gidan mu wasu kuma suna zuwa yi min sallama don komawa gidajen su an bude dayan buhun shimkafan da iyayyenba suka kawo na gara a gidan suna dafa ma yan uwan su da suka zo gurin buki. Sai dai abinda ke ban mamaki duk wanda yazo yana yaba kyawon dakin nawa in ka debe daidaikun yan uwan jamil dake tabe bakin su. Dangin mahaifiyar shi da suka zo buki a wurin su nake jin ashe su suka zo da turamay nan da aka kai gidan mu ke nan, nan iyayyen shi su basu kashe mai komai ba kenan. Ranan dai wuni nayi ina taron baki a gidan sai dai yakan shigo jefi jefi yana wani cika yana batsewa na rasa gane kan shi a gidan ga baki daya. Zaman sati dayan da mukayi kullun a cikin korafi yake akan shi shirin dakin bai mai ba har dai na hakkura na tambaye shi yanzu yaya kake son ayi ke nan yace yanzun kikai magana dai. Abinda nake so shine mu sayar da wanan kayan a sai wasu wanda ya dace damu a dakin ina ganin haka zaifi bada ma,ana sosai nace kana ganin haka zai yuyu tun ban kai wata daya da aure ba ace na sayar da kayan dakina. Baka ganin zasu ga na rena da abinda sukai min a baya yin hakan zai kawo wani rigima a tsakanin mu nan gaba a hasale ya furta ina ruwan su dake yanzu ina sun sauke nauyin su da ke kansu suke gani da wanan abin da sukai maki suna ganin burgewa ne a gurin su. Yanzu muke da ikon ki basu ba don nauyin ki ya dawo gare mu ke nan ba ruwan su da abinda zamuyi maki anan kuma yanzu. Nace to shike nan yace da kaina zan kai kayan nan can kauyen mahaifiyana a sayar muna dashi muzo mu cika kudi a sai maki na zamani wanda ake yayi. Nace idan kana ganin haka zaifi a kai a sayar din na kuma gode da kaunar da kake mun din dani da yan uwa na ya saki wani shu,umin murmushi a fuskan shi. Bai bar dakin ba nan ya zauna muna hiran yan uwan mahaifina na zage ina fadin karya da gaskiya ga irin rikon da suke muna a gidan baba kabiru din. Yana ta faman zugani ina hawa ina ganin gaskiya yake fada min don banda masoyi bayan shi a duniyan nan kaf baki daya. Washe gari ya bude kofan falona ta baya ashe tare da motar daukan kaya yake ina ji ina gani Jamil da wasu mutane suka kwashe kayan falon nan kaf suka fice dashi a gidan. Sai da yai kwana biyu bai dawo ba a cikin kwana na uku ne ya dawo garin fuska a daure ya shigo min ina jin muryan shi yana gaisawa da iyayyen shi bayan ya gama dasu ne ya shigo yana kara sha min kanshi. Ba daman in tambaye shi zancen kayan don banga fuskan haka ba a gurin shi abinda ban sani ba ashe ya fita yaje gidan wata dillaliya ya juye mata kayan ta bashi kudin shi ya biya bashin da ake bin shi na party bikin daya hada sai sutura na alfarma da turararuka daya kara saye. Sauran kuma ya hole da yan matan shi sai da kudin suka kare ya dawo gidan a lokacin shine yake cika yana batewa don kada inga fuska shi in tambaye shi yadda akayi da kudin kayan. Sai da yaga ban tambaye shi zancen kayan ba wanda ni a zahiri tsoron haka nake ji yasa ban tambaye shi ba amma zancen kaya yana a raina. Don ina jin kunyan mutane suna shigowa suna ganin dakin haka ba komai a cikin sa alhalin kowa gari yasan amin kayan daki na alfarma. Matsalan farko dana fara fuskanta shine akan ibada sam Jamil baya sallah ko wani iri da safe sai sha dayan rana zai tashi daga barcin jiya da muka kwanta yayi wanka ya shirya ba maganan yin sallah. Idan nayi mai magana sai ya hauni da fada yana fadin kin san ni bansan Allah ba sai kin koya min may zaki nuna min akan addini kin dai san na fiki sanin hakan. Ni da na tashi a gida cikin hausawa yan uwana kuma musulmai na san Al,Qurani nasan hadisi don haka bake zaki nuna min yin sallah ba inda yake shiga ba nan yake fita ba. Ni dai na samu gefen gado nayi tagumi ina kallon shi sai ruwan bala,i yake min kan kawai nace dashi ya tashi rana nayi yayi sallah. Har ta gaji ya mike ya dauki buta ya kurkure bakin sa ya dawo yana tambayana idan na gama abin karyawa in kawo mashi fita zaiyi. Na mike jiki ba karfi na fita na dauko mai kayar karyawan shi da na aje mai ya zauna sai da yayi kat ya fice daga gidan. Mikewa nayi na kwashe kaya raina ba dadi ina tunanen maganan umma a karo na farko a raina ashe abinda take hango min ke nan wanda na kaaa hangowa kaina shi. Tun ba,a je ko ina ba zaman ya fara ban tsoro da Jamil don babu wani dadin auren da zance naji wanda amare suke ji idan anyi aure a farkon aure. Ga tsoro shi da yake kokarin cusawa a zuciyana dan abu kadan zanyi yanzu ya hauni da fada na fitan arziki yana zagi iya son ranshi ni dai babu zancen wani amarci a gurina sam. Iyayyen shi kuma da muke zama dasu da akace wai zasu zauna ne don barin iya mu yara a gidan baiyi ba shine suka ga dacewan zaman mu tare dasu din. Ni dai banga wani amfanin su ba a gidan asalima kamar tsoron dan nasu suma suke ji don har su yakewa wanan tsare gidan nashi da yake min sai dan jefi jefi zakaji yana hira da mahaifin nasa. Ko idan yana min fada mahaifin nasa ya karbe ya goyi bayan dan nasa kirikiri yana fadin nice banda gaskiya banda mutunci. Sai dai idan sunga yana cikin dadin rai da nine nake samun sakewa dasu a gidan har zamu dan zauna muyi hira da matan amaryan baban nasa da muke zaune a tare. Duk wanan baya damu na nidai buri na inga munyi zaman lafiya a tsakanin mu dashi kamar na sauran ma,aurata don sam banda wani walwala balle har in dan fara cikan daki da akeyi idan anyi aure. Ranan da yan gidan mu suka zo gani na na rasa yadda zanyi akan rashin kayan dakin da babu dakina wanda akai min daga gida da Jamil ya sayar din. Suna shiga dakin maganan farko da sukai min shine anty hadiza ina kayan dakin ki nace ku zauna mana in fada maku komai a tsanake. Zama sukayi suna saurarona don jin abinda zance din bayan sun zauna ne muka gaisa nake fada masu sai da aka jera min kayan naga basu min kyau ba na bayar a hurhura min ne za a kawo min wani sati in Allah ya yarda. Badon sun yarda da magana ta ba don yarda naga suna min wani irin kallon na tuhuma a ransu sai da mukai hirane zasu tafi nake rokon su akan don Allah su rufa min asiri kada su fada a gida sai idan an kawo min kayan zanje in fada a gida. Sukai min alkawarin ba zasu fadi ba kuma hakan ne don naji shiru ya tabbatar min da basu fadi din ba a gida don banga kowa yazo min da maganan ba. Jin shirun yayi yawa ne kan kayan yasa ranan na tambaye shi labarin kayan fada ya fara yi abinda yasan ban so ke nan fada yana fadin idan ta ban ai zan kawo maki tunda kin nuna min banda iko a kan abinki yanzu. Da har zaki bude baki kina tambayana kayan ki kamar wanda baki yarda dashi ba ya fice yana fada kamar yadda ya saba yi idan zaiyi yaudaran nasa a gurina. Tun ranan da nai maganan kayan ya shiga fushi dani sai ya shigo fuska a murtuke yayi abinda zaiyi a dakin ya fice daga gidan idan ya gama. Da abin ya ishe gani ban iya gaba ba a rayuwana ranan dai na kudirta a raina zan mashi magana idan yashigo gidan don mu fahinci juna dashi. Dama ni tsoro na kada yan gidan mu su sanda wanan zancen a dauki mataki a kaina shine kawai damuwa na a lokacin. Can cikin dare ina barci ya shigo dakin ina jin motsin shi na bude idanuwa ina kallon shi filo ya dauka ba tare da yai min magana ba zai nufi falo dashi da sauran abinda yake bukata a dakin. Sannu da dawowa nayi mai bai amsa min ba sai kokarin fita yakeyi a dakin zuwa falo na mike na bishi falon yana kokarin kwanci a saman dogon kujera don kujera kawai ya bar min a dakin sai ledan kasa a lokacin. Zama nayi a dayan kujeran dake kusa dashi ina fadin haba my may ya faru da zafi haka kake fushi dani kan dan magana kankani. Ya juyo a fusace yana fadin oh baki ma san abinda kikai min ba ke nan har kina daukan maganan dan kankani a gurin ki ko ? Nace ni banga abindana fada mai zafi ba daga tambayan kaya sai ka hau fushi dani haka kawai yace eh tunda kin nuna min kayan ki kayan ki ne ni banda iko dasu ke nan. Na marairaice murya ina fadin ni ba haka nake nufi ba my ka sani wanan ba halina bane amma idan maganan ya bata maka rai kayi hakkuri don Allah. Sai hawaye ya zubo min wanda ban san ko na may ye ba a lokacin ya dago kai yana kallona tare da fadin mayye kuma na kuka yanzu daga magana. Nace naga maganan ya bata maka rai ne sosai don kawai na tambayi ba,asin kayan dakina daka kwashe da sunan hurhura min su. Yace baki yarda ba dani ke nan kika kasa hakkuri har kiga iya guduna a kan kayan na kara marairaicewa nace ni dama tsoro nake ji azo daga gida a samu babu kayan a dakin nan. Yace idan sun zo sunyi magana ki fada masu abinda na fada maki a baya, ina kin gane yanzu na gyada mai kai a hankali wanan ne yasa muka shirya ya bar fushin da yake yi din dani da farko. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:55 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️ 1️⃣5️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA A fanin girki ba iyawa nayi sosai ba ranan da suka sakar min girki da kaina don farkon zuwa uwar miji ke girkawa sai dana cika wata daya a gidan tace in karbi girki in dinga yi. Ranan tabara zalla a gurina don tun a gida muke kwasan rikici da anty akan girki sai kanwa tace mai yin girki da duk wani aiki daya shafi kitchen a gida don ni ba iyawa nayi ba ko nayi girki bai dadi. Anty kance dani sai nayi aure zan san illan yin hakan da nakeyi don cutar kaina nakeyi ince wai ban iya girki ba ni sai gashi yau maganan ta ya zama gaskiya a gare ni. Idea yazo min bayan na soya makarde na zunbuda maggi star ina jin uban mijina har da santin girkin yakeyi da aka kai mashi nace a raina nagode ma kafanin maggi star don sun fitar dani wanan kunyan. Tuwo dai ne ban iyaba ba musanman na gari ga uban mijina bai cin shinkafa da dare sai tuwo yake so ko wani abu mai nauyi haka. Sau biyu ina tuka tuwo yana ruwa ya sake don yadda nakeyi ashe ba haka akeyi ba don sai na kwaba garin da zantuka da ruwa nake tuka shi ban kuma bari talgi ya nuna nake tukawa sai tuwan ya sake baya kwana da safe ya sake sai dai a zubar. A nan muka fara samun matsala dasu sai uban mijin nawa ya hau zage zage ina ji shi har dakina yana fada akan ban iya tuka tuwo ba kamana. Dole uwar mijin nawa ta shiga koya min yadda zan tuka tuwon don barnan da nake ja masu din na hasaran garin kamar yadda sukace inayi masu. Shi dai zancen kayana yabi ruwa ke nan don babu halin in magana akan shi yanzu fada da gaba zai shiga tsakanina da Jamil din. Ina jin sarakuwa tana gulma da matan hayan gidan mu wai ban iya komai ba sai aukin kwanciya da miji suna min dariya. Ta dauka barci nake nan suka saka faifaina sukaci har suka gaji ina ji su ban kuma fito ba daga dakin har suka watse a gurin haka yasa na dauki niyar gyarawa da kaina. Da yamma na fito zan dora girki tace in jirata idan ruwa ya tafasa tazo ta duba min ruwa na tafasa nayi yadda ta koya min sai Allah ya taimake ni nayi a cikin sa,a don tuwon ya tuku da kyau baiyi ruwa ba. Ina gamawa na ta fito da taji shiru ta samu har na tuka tuwon har ta hau fada wai don may ban kirata tazo ta duba min ba. Shiko surkina da muke cewa malam yana ji ya fara fada tana bude tukunya taga tuwon yana tafasa ya tuku da kyau bata dai yi magana ba sai tabe baki da tayi ta juya ta tafi. Sauran yan hayan gidan sun kafa kujerun su a tsakar gida suna jiran suji yadda zamu kwashe da ita da ta fito sai sukaji ba ai magana ba haka yasa suka fara tashi daya bayan daya suna shigewa dakunan su mai zuwa yin aikin gabata kuma ta shiga yi. A kwaini da nauyin aiki idan na fara aiki daya sai ya kaini wani lokaci ban karasa ba yanzun ma wanke wanke na tattaro zanyi sarakuwa na tana fitowa ta hau fada wai wanke wanken da yakakata inyi da farko shije sai yanzu zanyi in sa masu abinci karnin kwano yana tashi zuciyar su ya kama tashi idan sun ci abincin. Na dai gama na kife ba tare dana ce da ita kanzil ba ga uban mijina daga daki yana karba mata don shi mutum ne da baya fita ko ina iyakan shi gida kullun sai dai akwashi da son cin dadi sosai. Don gaskiya fannin abinci baida wasa ko kadan muna cin mai lafiya mu sha mai lafiya sai mun koshi zaman nawa dasu dai da dadine ba dadi gamu nan dai ne zaune. Don ma ban cika shiga shirgin su ba idan na gama aiki ina cikin dakina sai ko idan yan uwa suka zo gurina zakaji murya na a gidan. Daga cikin matan hayan gida akwai wata jamila da jinin mu ya dan zo daya da ita itace ke fada min wata rana da muka dan kebe a gurin wanke wanke take ce min. Wanan sarakuwan bata son ki hadiza suruka haka komai kakeyi idon ta yana sama ni dai da nice ke bazan bari tasan komai nawa ba gaskiya ko dai don ba itace ta haifi mijin ki ba yasa take maki haka ne. Ni dai murmushi nayi mata tare da fadin kin san zama da manya sai hakkuri tunda suna koya muna gyara ne ai ban yarda na fadi wani maganan da zata kaini gaba ba a gaban ta. Fadin haka da wanan matar tayi yasa na shiga rufe sirina ga kowa dama shi kan shi Jamil din haka yake so bai son ina hurda da kowa bama a gidan kawai ba harda yan uwa na ga baki daya. Niko ina da dabi,an in nayi bako sai na cika mashi ciki ya koshi sosai kafin ya tafi sai hakan ya shiga bata ma uwar mijina rai kuma. Sai ta tsiru da dabian idan na gama girki itace wai zata raba wai ina sa masu nama kadan da kashi mijin ta bai iya ci wanda nake sa mashi din. Wanan dalilin yasa idan na gama girki sai in dauki tukunyar in kai mata itace zata raba ta diban muna namu sai dai arziki na daya Jamil ba mai zama gida bane yana cin abinci sai yamma yakan shigo ya dauki wanka ya fita kuma. Haka yasa abincin ke isana har in samu in ba yan kanne na dake zuwa wani lokaci wurina ga shi ta dauko min idan nayi baki zata shigo ta zauna a falona har sai hakin sun tafi zata bar dakin nawa. Wanan halin da take min yana damuna sosai sai dai banda halin yin magana don a cewan ta tana kulawa ne da bakin nawa ai ya kawo hakan . Wata rana yar shi ta haihu da dare da ya dawo gida yake ce min ina turamay nan da aka bani na aure nace suna cikin akwati yace in dauko mai turmi daya zai ara ne yaba yar uwar shi idan ya samu hali sai ya sai min wani. Da saurina na shiga daki na dauko mai wanda ban faye so ba daga ciki na kawo mai ya fita dakin dashi zuwa wurin iyayyen shi ya kai musu nashi gudun mawan na haihuwa da akai masu din suka shiga saka mai albarka. Tun ranan ban kara jin zancen turumin a bakin shi ba haka yai ta min wayo yana karbe turamen nan ban dinka ko daya ba daga cikin su saukina ma ina da kayan da baba yai min tun a gida dashi da anty amarya nayi fitan buki dashi. Ga matan hayan gidan ina gani da sallah tazo mazajen su suna saya masu kayan sallah niko ba wanda yai maganan nawa inda nasan da sanin iyayyen shi turamay na da yake karbewa a gidan sai banji sun min maganan dinki kayana ba sam ko tashin zancen babu a bakin su. Ashe ni ban sani ba idan ya fita da turmin sarakuwa ja da muke tare yake ba ta kadar mai dasu gidan dillalai abasu kudin suyi abinda suke so dashi. Hakanayi sallah da dan kamay kamay don babu tufafin kwarai a gare ni da zanyi firan sallah dashi haka dai wanan ya wuce kanne na sun zo suke min hira irin kayan da mijin yar uwana ya dinka mata yar wirin baba kabiru dake aure a kusa damu don babu da nisa sosai kusan duk unguwa daya muke har iyayuen namu sai dai akwai dan tazara damu dasu amma duk unguwa daya ne gidajen mu. Da sallah kan muci mun sha shi shan minerals a gurin mu ba wani aiki bane don duk dare yana shigowa da dan ledan shi gidan damu da iyayyen shi. Munje gidan gaida iyayyena da sallah mun fara shiga wurin iyayyena mata muka gaisa dasu ina kallon irin kallon da anty ke min sai dai batayi magana ba bayan kallon akai muna iso gurin baba kabiru. Mu kaje gaidashi a falon shi yayi murna da ganin mu ya tambayi iyayyen mu muka ce suna lafiya har zamu daga sai yake ce min dama yana son ganin mu. Muka koma muka zauna muna sauraren shi yace dani dama maganan aiki ne ya samu a lokal goverment yake son ji wa zai bawa aikin cikin mu niko mijina zai bawa aikin ? Har bakina na rawa don ban bari yakai aya ba nace abawa Jamil yace kina ganin haka yayi maki kada daga baya inzo inji wani magana nace na amince baba a bashi. Haka yasa aka buga offer na aiki da sunan Jamil din ya fara amsan albashin shi yan gidan mu kaf sun nuna min bakin ciki akan hakan danayi kowa sai fadan albarkacin bakin shi yakeyi kan hakan. Niko saima takaicin su da nake ji don may zasu hana in bawa mijina aikin da muka samu ni a ganina hakan zai kara muna dankon soyayya a tsakanin mu tunda har na sadaukar mai da aikin dana samu nawa. Idan wata yayi ya karbi kudin shi ban sani sai dai inga ya dinka sutura ya sai turare da sauran abubuwan bukatan shi da dan cafenen kwana biyu da yake sayowa muci. Gani ragga ya fara yi min sallama a jikina a lokacin sai dai ban daukan hakan wani abu don nasan ba karfi ne ga mijin nawa ba mahaifin shi kuma yayi ritaya yanzu daga aikin asibitin da yake na kauye mafarin tattarowan shi ke na ya dawo birni da zama a cewan shi. Sai dai shi yana kula iyalin shi don yana masu sutura sosai yana kuma basu suna ci da babban sallah yazo an kawo turamay a gidan uban mijin nawa yayiwa matan shi sayayya sosai lokacin ne na samu ya laba dani yake fadin in boye kada sauran sarakan shi su san da ya sai min zani din . Ina ta murna yace in kai a dinka min zai biya kudin dinkin sallah saura yan kwana ki ne Jamil ya shigo min da wasu wando da riga na wani material da aka dinka mai sulbi. Ina ta murna yan gidan mu na zuwa waini an min abin arziki da murna na na dauko kayan ina nuna masu sai cewa summaiya kanwa ta tayi a cikin tsuki . Yanzu ke wanan gwajon da aka gyara ne kike wa murna wana zanin kuma fa karami ne naji haushin maganan ta nan dai na hauta da fada sosai inda nake shiga ba nan nake fita ba. Sunje gida suke fada wa iyayyen mu mata sai cewa anty tayi shi Allah ya hore mashi ya sai mata ina laifin hakan ai ta samu kudai ku daina sa ido ga abinda bai shafe ku ba tsakanin miji da mata sai Allah. Sai cewa dayan tayi kamar kin sani anty don dakin ta tun auren ta da sati biyu da mukaje har yau babu komai a cikin sa duk an sayar wai za a canza mata wasu. Cikin dafe kirji anty tace wasu kaya kuke magana nata an sayar nan dai suka shiga fada mata abinda nace dasu anyi da kayan dakin nawa. Hankalin anty ya tashi sosai a lokacin take fadin an sayar fa da kayan kuka ce sukace idan karya ne taje gidan ta gani da idon ta. Batai nauyi a kafa ba sai gurin baba tana fada mashi shima baba da makmaki yake fadin sun sayar fa kuma malam bai fada min ba gashi duk jumma,a ina zuwa gaida shi da sallah. Ran baba ya baci sosai da wanan maganan dayaji ya danyi shiru na dan wani lokaci kafin ya furta ku kyaleta muga iya gudun ta kan wanan magana don dole wata rana magana ya taso ai. Ba haka anty taso ba taso baba ya barsu su tafi gidan su gani da kan su sai dai hakan bai samu ba dole taja bakin ta tayi shiru sai dai ta kwana da takaicin hakan a ranta. Gashi tunda aka kaini bata je dakin nawa ba saboda kawaici irin nasu don dauka na da takeyi tankar yar cikin ta tun wanan lokacin hurdan mu da anty yayi sanyi sosai. Duk da nasan laifin na a gurin su sai dai fushin ta dani yana damuna sosai da sallah ma yadda yan uwana da sauran masu kawo masu abincin sallah sukeyi nawa ya sha banbam dana saura don ba wani cika ido da yake masu ga komai nan dai a lalace a gurina. Sa,adatu diyar baba ta haihu akai suna inda baba yayi mata sha tara na arziki don shi baba mutum ne mai kula da hakkin iyalin shi gaskiya. Na dawo gida ina fadin irin abin arzikin da baba kabiru yayiwa kanwata da ta haihu sai sarakuwa na ke fadin nima inyi in samu ciki su dangwali arziki a cikin gatse. Gashi turmi turmi yayan mu yasa muna ni ban samu turmin da zan saka ba sai anty ne ta saya ta bani in bayar a lokacin amma da zan dawo sai da aka cika min leda babba da kayan buki. Zaman dai muna yinsa da dadi da wuya sai dai duk abinda suke min ina shanyewa ban fadi gidan mu don boye sirin gidan aure na. Jamil ya tsiro min da zuwa gida kauyen mu wai bukin dan uwan shi inda yace idan naje inyi sati hudu kuma kada in sauka a gurin dangi na sai gidan yan uwan shi. Nace zuwa bukin ne zanje in share har sati hudu a kauye har mutane su gaji dani kan hakan yace su yaga daman bani kuma su yake son inyi a gida idan naje. Dole haka na shirya na tafi ya danyi min dinki kala biyu na fitan buki muka je kauye aka sha buki lafiya bayan kowa ya watse ne aka ga ni banda niyar komawa gida. Sai suka tambaye ni nace sati hudu yace inyi idan nazo gidan sunyi mamakin jin hakan sai dai basuyi magana ba tunda gidane na zo ko nan din. Wasa wasa na share har sati shida bai zo ba gashi yace kada in dawo sai idan yazo ga zaman kauye ya ishe ni tun ana min abin arziki har aka koma gashi mun maki shegiya. A cikin satin na bakwai da zamu shiga ne yazo gaida wani mara lafiya a kauyen na fara shirin komawa tunda naga ya dira garin nan yace wai ba dani zai koma ba. Muka fara rikici dashi har abin ya kaimu ga saki daya naje na samu wan mahaifin mu da suka hada uba dashi da kuka na fada mai abinda Jamil yayi min. Nan dai aka kirashi akai mai fada sosai aka shirya mu ba tare da gida sun sani ba ya kuma ce ba tare dani zai koma ba sai dai idan ya koma da kwana biyu in koma. Hakan akayi ko da na dawo ina shan kamshi dashi kan sakin dayai min din ko may ya gani ya sauko da kan shi ya bar fushin da yake yi din dani. Ashe abinda ban sani ba bayan tafiyana Jamil mata yake daukowa ya kwana dasu har dakina ya bude ta baya inda iyayyen shi basu ganin abinda yakeyi don muna da kofan baya a cikin falon mu ba lalai ne su san abinda yakeyi a gidan ba. Kanne na duk sun san wanan labarin suna kallo na ne kawai an rasa wanda zai iya fada min don gudun tashin hankali sai dai su basu sani ba aikin gama ya gama ko in ma har saki suke gudu a gare ni. Don haushin cewa da nayi zan koma gida yasa shi ya sake ni a kauye don zan bata mai jin dadin shi da yake a nan din. Jamil yakai dan duniya sosai don har abokiyar ta gwaicin yar hayan gidan mu ashe wata yar duniya ita batai aure ba kamar yar uwarta ya samu suna shedan cin su a dakina da ita. Na dawo ina hura hanci wai ni ga mai miji suna kallona sara mai bisa ruwa duk da dawowan nawa bai rage shi da komai ba don sai ya raba dare a waje suna iya shegen su can da ita wai shi auren ta zaiyi a cewar shi kuji fa yan uwa. Na dawo ban dade ba Allah ya ban ciki dama a can kauye nasha maganin gargajiya na mara wai mara ne ke damuna sukace wai shiyasa har lokacin aure da shekara ban samu haihuwa ba. A fili ya nuna min farin cikin shi na samun cikin da mukayi sai dai a can kasan zuciyar shi ba haka yaso ba don yace shi bai shirya ma haihuwa ba yanzu. Daga yin aure ace wai an fara samun ciki mafarin a tara iyali ke nan da wuri tun muna da kurciyar mu ke nan zamu fara tara iyali. Nikan dadin samun cikin nakeyi sai faman planning nakeyi ni da yan uwa na dake tayani murna na gaskiya kan cikin da na samu din a yanzu. Lokacin da kanwata Saadatu ta samu ciki ta kusa haihuwa ta danyi tanadin ta takai gida don taimakawa iyayyen mu dashi duk da baba yayi fadan haka yace ta bar shi tayi laluran gaban ta ai itaka tana da hidimar da zatayi na kawayen ta. Sai dai ni ba wani labari kan hakan don ban aje ba ban ba wani ajiya ba ko turmin zanin da baba kabiru ya aiko min dashi da sallah yaso ya lalashe ni ya karbe sai dana nuna mashi hakan ba mai yuyuwa bane don tare da sauran yan uwana dake aure baba din ya saya muna kayan . Dole yana kallon abin kudi a wurina ya kyale ni ba yadda zaiyi yayi fushin shi ya gaji har ya sake don yasan na fishi gaskiya a kan zancen zanin. Iskanci ko yanzu baijin kunya a gabana zai dinga waya da yan mata suna hira da farko naso in sa mashi ido sai naga zanja wa kaina damuwa gurin kyale hakan. Ranan ina zaune wata ta kirashi ya dauka sun fara fira ke nan na wauce wayan daga hannun shi na fara dura mata ashar cikin dakiyar fuska ya dauka zanji tsoron shi dana saba ji ne ya fara daka min tsawa akan in bashi wayan har yana fadin you very stupid ki ban wayana nace. Nima tsawa ba daka mai take na birkice mashi a dakin yana gudun iyayyen shi suji ko daya daga cikin yan hayan mu suji. Girman shi ya zube a gurin su don idan zai shigo gida sai ya daure fuska kamar hadarin marance fuska ba annuri ko kadan. Zakace shine maigidan da muke cikin sa yadda yake basu doka da iko a gidan nasan badon baba yasa yan hayan ba da zai iya koran su ma. Ganin da gaske ina shirin tona mai asiri yasa ya sauko yana fadi amma ke baki da wayau dafa budurwan yayana sa,idu nake waya kin dauka ko budurwa tace. Da yake wawiya nake sai na yarda da maganan shi na miko mai wayan yayi saurin kashewa ya kuta ya fita daga dakin bai dawo gida ba sai da dare ya raba sosai ya dawo. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: ZIM Ina zaune ina kare mai kallo yana shirin fita da yamma don duk yamma haka yake wanan al,adan ya tsala ado a jikin shi ga kamshin turare mai tsada yana tashi. Sai daya gama shirin shi yana batun fita nace gida nake son zuwa in duba su yau kamar baiji abinda na fada ba ya kara dauko kwalban turaren shi ya kara fesa ma jikin shi yadda yake so. Bakajini bane na fadi daga inda nake zaune ina kallon shi cikin tagumi yace najiki mana sai dai ban san abinda zaki je yi gidan bane. Zuwa zanyi in gaida su kawai don nasan in ka fita ba lalai ne ka dawo da wuri ba yace ni na rasa ma may zance maki hadiza . Wai da kike dadin zaki ki duba su ina ko dazun naga shigowan Baffa gidan nan shekaran jiya kuma summaiya sun zo nan gurin ki. Nace su kadai ne a gidan halan yace ke kika damu dasu su basu damu dake ba ni dai da zaki bi shawarana ki hade kan uan uwanki kuzama tsintsiya daya madaurin ku daya ku hudu da zai fi maki alheri. Nace ban gane may kake nufi ba har yanzu yace eh bazaki gane ba muddin baki kwantar da hankalin ki yanzu kin fahinci magana na ba. Don yawan zuwa gidan nan da kike yi ko wani lokaci yana daya daga cikin daman da zasu samu su cinye maku kudin ku idan ya fito nan gaba. Wani kallo na watsa mashi tare da fadin kudin ina baba kabiru ne mai muna fafutukan fito dashi yace ko yanayi ai da wata manufa yake yin su don shima ya debi rabon shi daga ciki. Kara mai kallon mamaki nayi don jin furucin shi akan baba kabiru din yace yes waye bai san da dukiyan ku yake tunkaho ba a garin nan. Sai ku da har gobe baku wayau da zaku gane hakan sai idan sun gama maku barna zaki dawo kina fadin dama na fada maki kinki ji a baya. Ni fa ban fahinci inda maganan nan naka ya dosa ba har yanzu zama yayi a kusa dani don ya fahinci banda saurin zurmawa idan ya tsarani da magana. Yace ni abinda naga yafi maku shine kiyi kokari ku hade kai da yan uwan ki tun yanzu ta inda bakin ku zaizo daya a kasa gane tsakanin ku. Nace ai muna hakan ko yanzu wani shu,umin kallo yayi min tare da fadin ke har yanzu dai yarinya ce hadiza ana gabas kina yamma ni zan fita idan na samu lokaci zan maki bayani a tsanake. Daga haka yasa takalman shi ya fita kallon inda yaci abinci nayi naga ledan kazan daya shigo dashi da rana yaci yashe saman dan table din da muke cin abinci a falon namu. Naja tsuki tare da mikewa ina duba ledan kazan na samu ya rage dan guntu a ciki zama nayi na karasa cinye sauran tare da sude kasusuwan da bai karasa cinye tsokan su ba na gama na kwashe kayan na fita dasu. Gyaran daki nayi na fita gurin girki na don kada yamma yayi min don nasa a raina yau zan shiga gidan mu da dare. Da sallama na na shiga gidan namu inda na samu yan gidan mu a dakunan su suna kallo da murnan ganina kowa ya tare ni muka shiga gaisawa dasu. Sai da nabi da kunan matan baba na gaidasu na dawo dakin yan matan gidan mu na zauna muna hira sai tsokanana sukeyi wai ciki yasani muni. Anty ne ta shigo dakin ta zauna don ganina a cikin dakin tana fadin wai ke haka zaki haihu daki ba komai a cikin sa har yanzu hadiza. Ko kun gyara dakin naku ne yanzu muzo musha kallo mu kan tana fadi a cikin zolayata don takanyi wasa damu wani lokaci. Fadin haka yasa kanwata fadin wanan shegen macuci ai itace ya samu har ta yarda da hakan idan da nice wallahi sai ya fito min da kudin kayana wallahi. Take na daure fuska don jin ashar din data dura ma Jamil dina alhalin yanzu ya gama maganan alheri a kan mu. Sai anty ne tace kuna zagar mata miji a gaban ta yanzu kuna samun sabani a gidan nan bandai sake fuska ba har lokacin har ta gama dan hiran da mukeyi sama sama da ita a dakin ta fita. Can takira yarta dake dakin tare damu tayi mata wani abu lokacin na samu fadin yanzun ke da kanki kikewa Jamil haka idan wani yai min ashe ba zakiji haushin sa ba summaiya. Tace wallahi halin mijin nan naki yana ban haushi anty dubi yarda kika koma don Allah kamar wata bakauya dake don babu mai kallon ki ya dauka wai kin yi karatun boko. Nace to ki matsa kowa bada yadda Allah ke masa tsarin rayuwan sa ba ko kin naso ne in dawo wanan gidan ne kuma mu kama ganin laifin juna daku. Nan dai na nuna mata bacin raina akan abinda tayi min din har sai da ta bani hakkuri na sauka nace da ita ta samu lokaci ina son ganin ta ita kadai idan zata zo kuma ta zare jiki tazo ita kadai tace min taji. Ina shirin komawa baba ya dawo do yayi tafi ashe kwana biyu bai gidan yana dawowa muka fita muka gaida shi yake fadin a,a hadiza kin shigo ne ? To ya kuke ya mijin naki na amsa da suna lafiya suna gaida ku baba yace lafiya dai ko nace lafiya baba na daizo gaida ku ne kwana biyu ban shigo ba na duba ku. Yace cikin nuna jin dadin shi ga hakan mun ko gode naji dadin hakan sosai adaita hakkuri don Allah komai na duniya sai da hakkuri ake cin riba nace na gode baba daga inda nake tsugune. Har na mike ya sake fadin ina ganin kwanan nan zancen kudin ku zai tashi don munyi magana da wanan mutumin dake muna hanya kudin su fito a cikin jin dadi nace Allah ya nufa baba na kara mai godiya. Na fito ban dade kwarai ba don daren da yayi na yi masu sallama na nufi gida sai da yan gidan mu suka rakani har gida muna hira suka juya suka dawo gida. Har lokacin na sami Jamil bai dawo gida ba nima ban sa rai da zai dawo haka da wuri ba don sai dare yayi sosai yake shigowa gidan. Washe gari ya gama barcin shi karfe goma da wasu mintina ya bukaci ruwan wanka na kai mashi bandaki kafin ya fito na aje mai abin karyawan shi ko a inda na saba aje mai ina gyaran gida ne ya kwala min kira. Nazo yake fadin wa zai sha maki kunu haka babu sugar ko kosai nace yau baba bai sawo muna kosai bane kuma sugar ya kare tun jiya na fada maka. Ya ja tsaki tare da rufe kwanon kunun ya dan mayar da kan shi saman kujera fuska a daure nace jiya naje gida baba yana gaida kai ya mace wai kudin mu ya kusa fitowa. Wani irun dagowa yayi daga yadda yake kwance yana fadin saboda Allah nace wallahi ko jiya baba yake fada mi hakan da naje yace ashe mun kusa warkewa ke nan nace insha Allahu. Nan ya fara sake min hira a ciki sakin fuska inda yake shiga ba nan yake fita ba jin dadin hira yau yasa na sako mai zancen da anty tayi min. Take ya bata rai ya fara fada yana fadin ina ruwan ta da rayuwan mu ne nifa kwata kwata wanan matar batai min ba a rayuwana nasan duk wani cin amana da baba keyi da zuginta ne yakeyin shi. Nace niko banga hakan ba gaskiya don bata saka kanta a cikin maganan mu yace ke may kika sani so take kowa ya koma yadda take wai ita ta waye din nan . Ranan kan hirane zamzam dashi ba wani nuna bacin rai a tare dashi fitan da baiyi ba ke nan har mahaifin shi yana tambaya ko lafiya yake gida har yanzu. Yace lafiya yana dai hutawa ne a gida yau tun wanan ranan muke zamzam dashi kanwata tazo na danyi mata nasiha kamar yadda Jamil din ya lurar da mu muyi din. Bata ki ba sai dai cewan da tayi amma kada mu nuna yadda har za a fahince mu a gida tun daga wanan ranan muka dinke tam dani da yan uwana da muka fito ciki daya. Babu mai gane jan mu komai namu a hade mukeyin sa a gidan ga summaiya Allah ya dora ma anty sonta a rayuwan ta komai ta samu ko zatayi sai tace summaiya dai har yan uwanta suna sata gaba akan hakan da take nuna ma diyan cikin ta bata damu dasu ba sam. Bayan kamar sati uku dayaji shiru shi da kansa yace mu shirya muje mu gaida mutanen gidan namu nayi mamakin haka sai dai naja bakina nayi shiru tunda gidan mu zamu tafi. Mun samu baba a gidan ya tare mu a cikin fara,an nan nasa suka dan taba hira da Jamil din ina gefe ina jin su sai dan zungura na Jamil keyi akan inyi maganan kudin mu mana a gurin baba don ya gama kitsa min abinda zance tun a gida gamay da kudin da mukaji shiru. Can nace baba har yanzu dai wanan mutumin bai kira ba ko cikin mamakin wani mutumi nake nufi baba ya tambaye ni nace wanan mutumin da zancen kudin mu ke gurin shi baba. Baba yace wallahi har yanzu banji wani abu a guri sa ba amma dai barin kira shi muji yanzu komay ake ciki akan zancen nan ya daga waya tana ringing gab da ta katse ya dauka. Suka gaisa a cikin harshen turanci suke magana baba yace yaji shiru yace eh kasan abin da wuya amma dai insha Allahu ana sa ran fitowan shi a cikin wanan shekara din sai dai kasan ba duka yake fitowa ba za a kasa shi kamar kashi uku ne haka. Baba yace haka abin yake yace yadda tsarin namu yake ke nan ai dama sukayi sallama bayan baba yayi mashi godiya ya katse layin tare da dubo mu yace kunji ko. Abin sai kaman za a kama sai kuma aji shiru duk dai wani abinda suka bukata na riga dana gabatar masu dashi ko akan takardan nashi. Ya kare da fadin Allah dai ya jikan wani yai masa rahama muka ce amin don ni nama manta rabon da inwa mahaifina addua irin haka yanzu idan ba raina ne ya baci zan tuna dasu ba. Nan dai mukai wa baba sallama muka fito tare da yiwa sauran mutanen gida sallama ganin tare da shi muke yasa yau ban samu rakiyan yan gidan namu ba har gida. Tsuki yai ta ja har muka kawo gida yana dura ma wanda bai sani ba zagi wai sallon suci kudine yasa suka rike kudin har wanan lokacin ace mutum ya mutu har kusan shekara biyar kudin shi bai fito ba. Ni dai ina jin sa sai jefi jefi nake saka mai baki a zancen nasa sai kawai kwana biyu angulu ta koma gidan ta na tsamiya ya tayar da halin shi na yawon dare da yakeyi sosai. Nan dai nayi ta zaman hakkuri ban faye damuwa da halinsa ba sosai a cikin haka maganan kanwata da wanan mai nemanta usman magana tayi karfi sosai akai masu baiko a tsakanin su. Don yafi jamil dina hali ta ko ina bama za a hadasu ba kuma ya dan girmay ma Jamil din ga shekaru shi karatun shi yasa ma gaba sosai don gidan su suna karatu har nisa . Ba irin Jamil ba da yasa karyan duniya a gaba kuma a haka nake son abina kamar in hade shi ba dama wani dan gidan mu ya fadi maganan shi a gaba na koda kuwa mahaifan mu ne. Sai dadin hira yasa na kwashe na fada mashi abinda kace mai wani fa mai miji don a yadda mukai alkawari a tsakanin mu sai nake ganin ni kadai zai zauna dani har tsufa mutu ka raba takalmin kaza. Sai ya dibi kwanaki baya garin yana gurin yawon shi na banza zai dawo ga matsin daga wurun iyayyen shi dana fara fuskanta yanzu daga gare su tunda suka lura komai ya kare min danazo dashi daga gidan mu sai dan kamay kamay da nakeyi. Ina ganin yadda mata sa,anni na suke kwaliya gwanin ban sha,awa dasu niko babu hali sai kamay kamay idan buki ya kamani dole in tafi. Wani lokaci ina ji ina gani zanki zuwa bukin dangi daya dace ace na tafi don nasan yarda zan fito tsumai tsumai a gurin ina labe labe . Kowa tausayina yake ji ga abin magana ba halin a fada min gaskiya in kwashe in fada mashi ya tsiri yin gaba da mutum take zai nuna masu hakan. Shiya kowa ya kawo ido ya sa min dashi ana kallona don karya fure take bata yaya ni duk wanan bai damuna tunda dai muna zaune lafiya da mijina komai yayi. Idan yan uwana sun zo suna ban sha,awa yadda suke fita tsab dasu har ana kwatance dasu a gari saboda iya kwaliyan su da fita niko ganinan kullun a rabe a gida. Sai wani hali da yazo min yanzu dashi na ganin ya rabani da kowa daga cikin kawayena da mukayi makaranta a tare muna dan hurda dasu. Sai ya nuna min shifa bai son suna zuwa min gida duk yadda zanyi in kore su dole inyi don dai kawai a zauna lafiya dashi. A kwai wata kawata da tazo min muna zaune muna hira ya shigo suka gaisa dashi bayan ya shige ne take fadin hadiza dama mijin ki ke nan nace ina dariya kin san shi ne ? Tace uhumm gani nayi dai kamar na sanshi a wani guri ashe a unguwar su yana neman wata yarinya anan ta sanshi sai dai bata fada min ba sai bayan ta wuce ne ya hau fada dani. Wai shi bai son kwashe kwashen irin kawayen ga yan iska ya fa santa ba yarinyar kwarai bane sosai don haka kada ya kara ganin mu a tare kiri kiri ya hana wanan hurdan sai daga baya nake jin labari a gurin kawayen mu a inda ya santa yana gudun ta fada min komai inji. Sai dai abinda na kula dashi yana matukar son yaga kawaye yan karya sun zo min nan zai fara rawan jiki ya fita ya sayo kayan sha ya kawo muna. A zauna dashi ana hira da wasa da dariya har su wuce sai hakan ya fara kulle min kai don na rasa gane gabas din shi shida yace bai son kawaye sai inga idan wasu sunzo min yana rawan jiki wanan ke nan. Ina ji ina gani banda halin shan abu mai sayi a dakina sai na saya ga cikin dake gare ni yana sani shan abu mai sanyi sosai. Sai dai ban samu wani lokaci kuma banda canjin da zan saye a tare dani ga fridge dina Jamil ya hada dashi ya fitar yace wai karamine aka saya min. Haka yasa yanzun nake kama kama da wahalan sayen abin sanyi in jika makoshina dashi ko tausayin halin da nake ciki baiji ko kadan. A cikin haka har watan haihuwana ya kama inda na koma gida don haka aladan gidan mu yake haihuwan fari a koma gida a haihu a can. Shi da kanshi ya matsa min tun watan bai tsaya ba yake damuna wai yaushe ne zan koma gida ne har mahaifin shi ya kama mashi shima yana fafin haka kamar sun gaji dani a gidan ni da gidana. Haka dai na koma gida wurin haihuwa inda na dauki wasu satituka ban haihu ba ina zaune a gidan mu sai ya ga dama yake zuwa dubani a cikin sati sau daya. A cewan shi wa kada ace yayi rashin kunya idan yana zuwa nan ko yana sheke ayyan shine a gari kawai da yab mata tunda shi dan karyane. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: IZ Jamil zai dan zo ya dubani kacal yake zuwa a cikin sati a haka har haihuwa yazo min Allah ya sauke ni lafiya na haifi yar diya mace mai kama da mahaifinta sak. Murna wurin yan gidan mu ba,a cewa komai haka ma yan gidan su Jamil gwargwado sunzo sunyi barkan haihuwa su tare da farin ciki. Ba wani abinda suka kawo gidan mu wai don na haihu din do mahaifin shi har gida ta samu baba wai basu da halin kawo irin kayan da ake kawowa idan mace ta haihu a gida din nan. Baba yace ba dai an haihu lafiya ba shine dama abinda muke fata a gare ta wanan maganan ya kara masu kwarin gwiwa suna cewa wai baba ya rike zumunci dake tsakanin gidajen mu din biyu. Suna kwana hudu Jamil yazo gidan mu mun dade dashi muna sakawa da warwarewa a tsakanin mu karshe muka aje magana akan anty zai roka ta shige mai gaba ta samo mashi bashin turamay zani idan ya samu albashi ya rage mata taba mai kaya kudin ta. Na kira anty ta samay mu a daki muka fada mata shawara da muka yanke anty tayi shiru tana tunane muryan shi ne ya katse mata shirun yana dan wani kamay kamay. Ya kara kwantar da murya tare da fadin anty don Allah kada kiji komai da an samu kudi zan kawo maki kudin nan ko na samu wani hanya zan rage da yardan Allah. Don kin san da aure ban samu halin yin lefe ba shine nake son wanan karon in mata abinda mutane zasu gani su sheda nayi. Tace ba komai bari ta kira matar mai kaya sai aji turamay nawa nawa suke a gaban shi sai ya fadi wanda yake so. Yace har akwati da komai kada a wuce dubu hamsin gaba daya nan dai aka kira matar niko har da fadin haba anty ba zamu baki kunya ba ai nan fa gidan sarakunene. An shirya da matar inda tace ya zo su duba kayan ya yi ta ma anty godiya ya tafi ya karbo ya kaima iyayyen shi yana washe baki ala dole yayi abin kwarai da kanshi. A bangaren gidan mu duk abinda akewa yarinya idan ta haihu baba yayi min shi inda kuma baya su cincin da sauran kayan ciye ciye ya sa min turmi goma kamar yadda yayiwa yar gurin shi data haihu bai bambamta mu ba ko kadan. Harda set din jakkuna masu saukin kudi kuda biyu inda anty ma ta garje ta saka min kaya masu tsada nawa dana baby kowa sai yabawa yake da kayan. Yan uwa sun min fada sosai akan kayan kada in fara inbar kayan nan su lalace don ban san ciwon kaina ba suke fada duk wanda yayi min fada abinda yake fadi ke nan . Don na tashi da turakay har arba,in da wani abu ga wanan haihuwan yan uwa sun min kokari sosai ga haihuwan nan har sai da na rasa bakin godiya. Bayan an watse ne anty ta sa dani da kanne na mu zauna a ware masu tsada daga cikin kayan a jesu daban haka mukayi inda masu kyau da kudi sosai na samu sun kai guda goma sha takwas . Sauran duk suma duk atamfa ne sai dai ba masu tsada sosai ba irin da ake kaiwa buki inda duk na baba kabir da yai min manya ne. Dangi ko turmi dadaya sukai min don sunga baba kabiru yana tsaye da al,amarin mu sai suka sake mai komai kamar dukkan su ba yan uwan mahaifina bane fa baki dayan su. Don ni har abinda suke muna din yana matukar bani mamaki sosai sai kuma inyi tunane koshi baba kabir din don dukiyan mu yana hannun shi ne yake min haka din. Bayan kamar sati ne anty tace a dauko kayan nan akai dinkin su don in samu tufafin yin goyo don goyo sai da zani saboda goyo yana cin zani sosai. Banki ta nata ba duk da ina son in ba Jamil shawara akan hakan sai dai ba fuskan yin hakan a gare ni don na fahinci anty da serious take maganan ta. Ina kallo aka kira tela yazo har gida ya karbi dinkin kayan inda anty ta biya rabi ta sa mu kuma mu biya rabi din fitan rabin daga gurin jamil yayi wuya ashe don ina gida ne ya kyale ni. Nayi kiba sosai don jwgon yayi min kyau saboda ina samun hutu da kulawa sosai a zaman da nakeyi a gidan mu din. A kwana a tashi har mukai arba,in da kyat da boni don jamil duk ya matsu mu dawo kamar abin arziki har nima na fara kasa hakkuri da zaman gidan. Haka muka ga munyi arba,in a dadafe a gidan mahaifan nawa da zamu koma ne baba yayi muna sayayyan buhuhunan abinci gero masara shinkafa da su mangyda da kayan miya. Aka tarkata ni aka mayar dani gidan Jamil din dani da yar goyo na koda muka koma mun samu dakin kaca kaca ba gyara ko ina dole suka dan kama min muka dan gyara hakana kafin su tafi. Sarakuwa na sai murna take a gaban iyayyena da suka rakoni ta karbi yarinyar ta goyata tun suna gidan basu tafi ba kamar abin arziki. Jamil na gurin yawon shi koda muka dawo sai dare sosai ya dawo gidan yana fadin ashe da gaske yau zaku dawo din ? Kallon shi nayi da mamakin abinda yace din nace ba an aiko gidan mu a gyara min daki kafin in dawo yace shi ba wanda ya fada mai. Ya shiga daki ya na kallon kayan da muka dawo dashi ya wani ya tsune baki zai juya nake ce mai buhuhunan abinci suna sashen baba an aje da cewa mahaifin shi. Ya juyo da sauri cikin washe baki yana fadin har da abinci nace eh buhu uku ne sai kayan miya da sauran tarkace ya juya da sauri zuwa ganin kayan dana fada mai. Sai can gashi ya dawo yana washe baki tare da fadin shi baba bai san bamu cin masara bane da gero nace gero ai don kunu aka kawo min shi masara kuma don tuwo. Yace ba za mu sha kunnu a gidan nan ba don kin san bamu sha kunu ya fice yana murna ya dawo da leda a hannun shi kaza ce da zafin ta tare da abinsha ya shigo dashi. Mukaci muka kwanta tunda safe washe gari ya tashi ya fita sai gashi ya dawo da wani mutum a bayan shi ya sallama muna sai gani nayi kawai Jamil yana cicibo buhuhunan nan yana fita dasu waje gurin mutumin . Can sai gashi ya shigo yana washe baki yana murna da farin ciki sosai a fili na dauka zai ban wani abu a cikin kudi sai gani nayi ya soke abinshi ya fita. Ban kara ganin shi ba sai daren sosai ya shigo gidan yana wani daure fuskan shi ni dai ban tanka mashi ba na kama lamarin gabana. Ya gaji ya bari ya dawo ya sake da kanshi yana wani haba haba dani, niko kaina sai wani dadi nake ji a raina wai ni miji yana so na . Da rana tsaka sai gashi ya dawo a cikin fara,an shi yana kwala min kira nazo da sauri ina karbawa na amsa mai yana tsaye tsakiyan falon mu na samay shi yace dauko min kayan sunan nan naki in duba akwai abinda nake so a ciki. Kallon shi nayi galala nace wasu kaya ke nan yace cikin canza fuska turamay da kika samu da suna mana . Gaba nane naji ya buga gashi ban gama sululin wasu turamay na diyar kanwar mahaifiyar mu da ta kawo min dinkin su har na koma gida ban samu dinkawa ba na barsu a dakin namu. Ina gidan baba kabir ne ta aiko a karbar mata dinkin sai lokacin na tuna da turamay na tura summaiya kanwa ta ta kwaso min a dakina. Sai gata ta dawo tana fada min bata gansu ba a inda na aje su hankalina ya daga da yazo na tambaye shi sai cewa yayi shi bai gansu ba a dakin tun tafiya na. Wanan abin kusan yaso ya hada mu fada har da sister din mahaifiyar mu uwar yarinyar gashi ita kadai ce ta rage muna uwa da muke ganin dakin su daya da mahaifiyar mu. Amma ta rufe idon ta kan yar tace sai na biya turamay nan ni kuma na kasa dauka daga cikin turamay na in bata sai yanzu kuma shi gashi ya dawo min da zancen kayan dana samu din da haihuwa. Bai tsaya jin abinda zance ba ya fada daki ya fito da akwatunan zuwa falo ya fara budan su sai naga ya dago da sauri yana kallona tare da tambayana ina turamay suke ? Nace ai na fada ma mun kai dinkin su tun kan in dawo gidan ko sharan yan gidan mune hakan don sunce banda tufafi goyo kuma tufafi yake so sai. A hasale yace inji uban wa yace ki dinke wanan kayan masu uban yawa da tsada ki sa ma jikin ki kin ko san kudin kayan nan sai kallon shi nake a cikin mamaki na kasa magana ban iya furta mai komai ba. Ina kallo ya tattara sauran turamay bayan ya zabi guda biyar ya fita dasu da haka sai da ya jide kayan nan kaf ya fita dasu ya sayar. Idan nayi magana sai ya hauni da cin mutunci kamar zai duke ni idan mahaifin shi yaji mu sai yace idan ban rufawa mijina asiri ba wa zan rufawa duniyan nan. Haka dai rayuwan yake tafiya muna tun dawowana daga gidan na samu uwar mijina da muke zama da ita ta canza min sosai har gara lokacin da ban haihu ba din da dan dama. Yanzu ba nasiha a tsakanina da ita ga gori da take min akan gida dan abu kadan zatace idan don gidane nake son raina ta sai a fada masu kudin haya su biya ko su fita su bamu gidan mu. Ina dai hakkuri ban tanka ta duk fadan da zatayi har ta kare bana kulata sam sai idan ta huce ne zata dan dauki diyata ta dan wuni a gurin ta na dan wani lokaci. Wanan bai sa na canza daga abinda nake mata ba a matsayin ta na sarakuwa na a gurin su ina bata girman ta sosai da yin aikin dana san nawa ne inyi. Ranan dai ban san ko may ya hadasu fada ba da Jamil ya shigo yana jan tsaki har ya gaji ya kai ga fadin anzo an zauna zaman sa wa mutane ido ana faman takura muna. Wallahi daga yau idan tayi maki ki dinga ramawa ninace nasan bacin ran abinda tayi mai ne yasa ya fadi haka sai ban bi ta kan shi ba kan maganan tsakanin shi ne da ita wanan. Neman matan shi yanzu zanga zanga ne ya kara turani zuwa kauye wai inkai yarinya su gani don wasu da yawa basu santa ba tun kan ya karasa nake ce mai ni dai gaskiya idan yasan zanje ya barni can ne ba zan tafi ba. Wai ashe yaji haushin maganan sai gashi ya kaini kara wurin mahaifin shi ya kirani yai min fada sosai har yana fadin waini yanzu ya gane ina gudun zuwa kauyen mu ne don ina ganin nafisu. Mahaifin nasa yasa alla dole in shirya babu ko wani tsaraba dana tanadar masu na tafi kauye ganin gida tsomai tsomai dani ba laifi tunda nima garina ne yan uwa kuma suna jin tausayina ga maraici ga rashin dace da miji na gari da banyi a cewan su. Wanda ni hakan yana matukar ban haushi sosai don ni banga laifin Jamil ba ai ba gare shine rashi ya yanke cibi ba don ni dauka nake karfi ne baida yasa bai min abinda ya dace yayi na zaman shi miji a gare ni. Abinda ta dawo dani gari wanan karon bayan na shafe sati hudu da kwanaki masu kyau nayi baki duk na fige idan ka ganni bazakace na taba yin boko ba a rayuwana. Zancen kudin mu ne da ya taso yasa baba kabir aikwa in zo zamu tafi abuja muyi wani sgning a can shine dalilin dawowa na dawuri da bansan ranan dawowa na ba gidan. Ko da na dawo na samay su a cikin jin dadi don mahaifin shi ya samu kudin aikin shi da yai retaya ya fito sai dadi suke ci a gidan babu kama hannun yaro. Atm din shi ma yana a hannun Jamil ashe idan tsohon yace ya ciro mai dubu biyar sai yaje ya cire dubu hamsin ko arba,in yasha garalin shi dashi. Na dawo muna shirin zuwa abuja da baba kabir da kani na Baffa ne suka tashi da rikici a gidan da tsohon nashi ya tura wani kanin Jamil din ya ciro mai kudi aka samu saura dubu goma kacal a banki. Wanan abin ne ya kawo rikici tsakanin shi da mahaifin nasa sukai fada sosao ranan da dan son nasa haushin wanan abinda yaji yace duk zugin matar shi ce . Don itace mai zugashi a kanshi don ta tsane shi saboda ba ita ta haife shi ba niko ala dole sai naji zafin abin na shigar ma mijina fada. Har muka tafi abuja ban magana na kirki da ita ba wani abu bani hannu kawai muka sa a takarda muka juyo zuwa gida. Ina shigowa na samu Jamil ya gyara min daki ranan bai fita ko ina ba don dama muna ta wayan dashi ganin muna tare dasu baba ne yasa bai tambaye ni tun ina can ba zancen kudin namu. Ina dawowa ya tare ni da murnan shi har da karbar min jakka na ya karbi yarinya yayi mata wanka ya shirya ta sai da zzamu kwanta yake tambayana nayi mai bayani. Tsoki yaja ya bani baya bai kara magana sai safe ya tashi a cikin daure fuskan daya saba bai dade a gidan ba ya fice gaba daya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Tun wanan ranan da muka dawo daga Jamil har iyayyen shi ban kara gane kan su ba a gidan kowa zafi zafi yake dani a gidan har Jamil din kan shi ba wani maganan girma da arzikin dake hada mu dashi inji sanyi. Daki nake kwance da yar diyana anyi ruwan sama an dauke a lokacin misalin karfe goma na safe na ranan laraba hayaniya nake ji na mutanen gidan mu sama sama yasa na mike na fito don in ganewa idona abinda ke faruwa. Na samu data daga cikin matan hanyan gidan mu ne suke fitina sai dai ban san da wanda take fadan ba a lokacin maimakon in tsaya sauraren ta in gane kan maganan sai kawai na shiga aiki abina don lokacin dora girki na yayi kusa. Wanke wanke na tara don in yi sai da na hada kayan a gurin da muke zama mu wanke kayan mu na koma daki in dauko omo da zanyi amfani dashi gurin wanke kayan na fito naji matar na fadin mu za aiwa burgan aiki ana muna kurin ana da arziki babu kwarjini ga miji. Tambayan ta nayi wai yau waya taba ki ne haka da wanan sanyin haka ta wani kallo ni shekeke tare da fadin wai ke baki ma san da wanda nake fada ba ke nan ? Kai na girgiza mata ba tare da niyar yin hakan ba a gare ta take fadin amma ke kin kai yar rainin hankali wallahi to dake da mijin ki nake fada ba da kowa ba. A cikin mamaki nake fadin nidin nan kuma may mukai maki haka mai zafi da zaki tashi damu a rai haka da sanyin safiyan nan naga tun asuba dana fito hadari ya kora mu daki ban kara fitowa ba sai yanzu. Zaki ce hakan mana tunda kun san abinda kuka kulla min tun jiya din to bari kiji ni ba irin ki bane da miji ya mayar wata bi can don nasan ciwon kaina dana iyayyena da kuma darajan aure na. Tsaye nayi galala ina son jin inda wanan maganan nata ya nufa akan mu haka da take ta faman budan baki har makwabta zasu iya jin mu a lokacin. Ganin ban fahince ta ba ta buda baki tana fadin kina nufin baki san da zaman mijin ki ya fara jan baban Ahmed zuwa wurin shiririnta shi ba har tsakiyan dare jiya baban Ahmed bai dawo ba gidan nan. Ni ba yar rakiyan mata nake ba da zan saka ido wanan abin yana gudana a tsakanin su haka a zafafe nace wai ko kina da hankali maman Ahmed may ye nawa yanzu ni a cikin wanan zancen. Tace keko keda ruwa a wanan zancen don haka kiwa mijin ki kashedi akan mijina don zan debe kunyan da nake ji nasa in masa rashin mutunci yanzu a gidan nan idan bai fita harkata ba. Sale salin ya fara koya mai neman kannen da yan uwan matan gidan nan ke nan don shi ba abin kunya bane a gurin shi yin hakan. Nace na gane dai dani kike jin fada ba da baban Amira ba don shi bai gidan bai san kina yi ba ma san nan kuma yar uwar wace daga cikin mu kika ga baban Amira yana nema. Kafin ta bani amsa sai ga dayan ta fito daga daki tana fadin dama nasan dani kike wanan maganganun naki ai don ki fada mata mijin ta yana neman yar uwar tagwaici na ko. To ko taji may zatayi tunda shi yaje ba ita taje neman shi ba idona na ne naji ya rufe ga maganganun da suke yaba min dukkan su su biyu din a lokacin. Na rasa abinda zance kan zancen don raina yakai kololuwar baci da maganan su duk kokarin da nakeyi inga na kaice ma wani fitina dasu hakan bai yuyu ba sai da Jamil yayi sanadin hada ni fitina dasu a gidan nan . Kafin inyi yunkurin basu amsa sai ga sarakuwana ta fito daga dakin su tana fadin nasan dama wanan magana da kuke tun asuba da wata manufa kuke yin shi don ku tayar da zaune tsaye a gidan nan tsakanin yaran nan biyu ne. Idan ma ya nema mace nawa aka halasta wa namiji ya nema a rayuwan shi yayi idan ma har kun fada mata din taji za ta hanashi kara abinda Allah yace yayi ne ke da kike fadan yana jan mijin ki zai koya mai yawon banza daure shi yayi a kafan shi ko may ? Wanke wanke nakeyi ina jin raina yana min zafi nan dai sukai ta sa insa a tsakanin su ban iya tanka masu ba don mijina nane yaja min haka a gurin su din. Da ya kama kan shi da mutuncin shi kamar yadda sauran mazan gidan suka kama da duk wanan abin bai faru haka ba a yanzu har ana kokarin fada min magana a kan shi. Na gama na shiga daki sai naji ba zan iya zama ba na fakaici idon mutane na nufi gidan mu hankali a tashe dani na isa gidan kowa ya ganni yasan ba lafiya nake ba. Ban samu anty gida ba tana gurin aiki sai mama uwar gidan baba kabiru na sama a gidan da ita muka fara zancen abinda ke damuna kafin anty ta dawo daga gurin aiki da ta tafi. Muna kan zancen ne ta dawo ta samay ni a gidan da mamaki take kallona don tasan ban faye shigowa gidan haka da rana ba sai da dare nafi zuwa gaida su. Bayan mun gaisa ne take tambaya na ko lafiya a yadda ta samay ni naci kuka har na gaji nan mama ke fada mata abinda ke faruwa a gidan namu. Allah ya sauwaka tace min wanda ni ba haka naso naji daga gare su ba so nayi su goya min baya akan maganan sai kuma ba wace ta furta komai daga hakan sai cewa da sukayi a bari baban mu ya shigo gidan. Wanda ni naji haushin hakan sosai a raina don haka na dauka ko baba yazo shima abinda zai fada min ke nan bayan wanan. Na dora hannu a kai na fara rusa masu kuka a gidan cikin tashin hankali duk na daga masu hankali sosai a gidan ba, a fi minti talatin ba baba kabiru ya dawo gida. Tun daga kofa yake tambayan may ke faruwa ne a gidan nan dai anty ke fada mai maganan dana zo dashi gida kai ya gyada kawai tare da fadin abinda kowa ya guje maki ke nan tun farko. Kika nuna don bamu haife ki bane yasa bamu son abinda kike so din yanzu sai ki koma kiyi hakkuri zan ganshi in masa magana daga baya. Ba haka naso ji daga gurin baba kabiru din ba naso ya goya min baya ne akan maganan sai kuma ban samu haka din ba a gurin shi haka yasa na kara kargin kukana a lokacin. Anty tace hadiza wa zai furta wani kalami mara kyau akan mijin ki idan zuciyar ki tayi sanyi ki kwashe ki fada mai babu abinda zamuce sai hakkuri da zamu baki a yanzu. Raina ya kara baci sosai baba yace wanan yaron ba yaron kirki bane sam ni dake fita a garin nan nasan ko waye Jamil don bai aje kanshi a kusa ba. Baya hali irin na diyan tallakawa sai na diyan attajirai masu hali zaka dauka dan wani gwauna ne ko minister shi yaya ko mai wanan halin za a rabashi da neman mata. Tun farko abinda hajiya tayi maki duba ke nan a kanshi wanan na daya daga cikin abinda take maki gudu da halin su. Wani irin gululun bakin ciki ne ta ziyarci zuciyana a lokacin don may sai yanzu ake fada min abinda ni ba kasa hangowa kaina a baya aka rufeni ta baibai ina hauka. Muryan baba ne ke fadin yanzu shi da yaron arziki ne har zamu kai maki kaya ya kwashe ya sayar don baida kunya data idanu ga iyayyen shi a gida basu fada muna komai ba kan hakan. Tun wanan lokacin na raina halin shi dana mahaifin shi shine zaman da sukace zasu zo gidan su zauna daku don kada a barku ku yara zallah a gida babu babba a cikin ku din. Sai kuma ya koma bani hakkuri akan in koma in san hanyar da zan bullo mashi ya daina wanan halin daya tsiro min don rainin wayau ma a cikin gidan daya kanwar yar hayana yake nema kuma. Haka dai ya samu har na natsu na daina kukan fili da nakeyi sai na zuciya yanzu na koma yi ina maijin wani irin zafin Jamil din a raina ga wanan rainin wayau daya ja min gun yan hayan gida na. Duk zaman lafiyan da nakeyi dasu sai da yayi kokari ya zubar min da mutunci na a gare su ta hanyar neman yar uwarsu da yajeyi wanda nake ganin kasawa ne a hakan gare ni. Nan dai anty ta lalabani na koma daki na zauna aka kawo min abinci naci sai dai ban iya cin wani abin kirki ba duk da son abincin da nakeyi in ci a raina don tun safe ban samu na karya ba saboda ruwan saman da akai tayi da tun bayan sallah asuba din ranan. Bayan la,asar sai ga mama matar mahaifin shi ta biyo bayana tana fadin ita bata san ban gidan ba ta dauka ko ina daki na kwanta ne bayan da aka gama hayaniya da yan hanya aka lafa. Nan dai sukai ta magana kan hakan da matan baba inda suka nuna mata rashin dacewan hakan da yake min a gidan dake da mata da yawa. Ta samu ta bada hakkuri muka koma gida tare da ita kamar komai bai faru ba a baya har dare gogan bai leko gida ba sai dai ban sani ba ko ya shigo bayana don ban ga alaman hakan ba tunda banga ta canza tufafi ba . Daya shigo gidan kai tsaye abinci ya tambaya nace ban yi ba har da dan barazanan shi don may ba a girka abinci ba nima a hasale na bashi amsa da kaje gurin yan iskan da kuke watsewa su dafa maka ya juyo cikin mamaki yana kallo na . Kafin ya furta wani abu muryan mahaifin shi ne yake kiran shi yasa shi juyawa a hasale ya fice daga falon zuwa karba kiran mahaifin nasa. Ni dai ban san yadda akayi ba sai gashi ya dawo yana cicika yana fadin ni hussai zata dora wa sheri wai ke harda yarda da maganan ta. Wallahi sai sun bar gidan nan a cikin kwanan nan kuwa nace sherin may kai kadai ne namiji a gidan nan da ba a dorawa sauran sheri ba sai kai kadai da yake yasan baida gaskiya sai ya shiga yan kamay kamay yana fada har na fara yarda da abinda yake fadi din. Mun danyi zaman sama sama dashi na kwana biyu sai ranan naga ya dawo da wuri yana wani haba haba dani da yar goyona Amira . Abinda bai saba yi min ba ni kuma rashin wayau ya hanani gane halin shi da sai wani abin arziki zai faru dani yake min hakan da naga yanayi din zaiyi. Ashe sun hadu da kanina a waje yake fada mai ai mutumin nan ya kira baba yace mu sa rai a cikin sabon wata zamu samu kudin mu insha Allahu. Lokacin har na kashe yan kaya haihuwana da anty tasa aka dinka min dana haihu har sun fara shan ruwa sosai banda zanin shiga jama,a na kwarai a dakina. Sai daga bayane yake labarta min abinda ake ciki akan kudin yake fadin idan kudi sun zo sai mu gyara dakin mu muyi wanan muyi wancan. Ni dai kallon shi nakeyi sai da ya kare nace ni duk ba wanan ba indai samu abinyin sana,a daga ciki shine burina a yanzu don zama haka ba sana,a ya fara isata a gidan . Dan dadin bakin yace ki kwantar da hankalin ki sana,a ai kamar kinyi kin gama nima kaina sana, an nake son yi yanzu sosai don zaman nan haka ya isheni sosai. Yan matan gidan mu ne suka kawo min ziyara ashe suna kule da zancen neman kanwar yar hayan da naje masu da labari yayi ranan dai sai da sukayi shi ba dadi da matar gidan namu inda suka zage ta fes daga ita har yar uwan nata da take kurin yana nema din. Ya samu labari sai dai ban san a inda yaji labarin hakan ba nan yazo da cin mutunci wai shi nake son inwa tonon asiri da har zan gyato yan uwa suzo har gida suyi cin mutunci haka. Sai daga baya nake ji wata yar gidan dake haya take fada min wai matar mahaifin shi ne ta tare shi waje ta labarta mai komai daya faru. Wanan bai damay ni ba don cewa nayi idan da baiyi ba ai da hakan bai faru ba nima tan uwa sun kwatar min yanci ne a gurin su su san ba banza nake ba. Yayi fushin shi ya gaji ya sake hakan bai sa ya fasa halin shi ba kullu fes yake kamar wani mai zuwa office dashi haka zai dauki wanka ya fice daga gidan sai wani lokaci ya dawo. A cikin haka ne bukin kanwata Sumaiya ya kawo jiki ana ta shirin buki iyaka ta ido sai kamay kamay danakeyi do banda wani katabus a gurin sha,anin tunda banda shi. An nuna mata gata sosai don an mata abinda ko rabin shi ba ai min ba don komai nata yafi nawa tsada sosai suma gida mijin sun nuna nasu bajintan sosai don set din akwatuna ne da zanuwa ciki masu tsada sosai suka saka mata. Ana cikin harka bukin ne na dawo gida don daukan kayan dana manta na rista matar mahaifin Jamil mama suna gulma da yan hayan gidana inda suke shiga banan suke fita ba mama harda cewa wai ni din ba sa,an auren Jamil bace matsa mashi akayi ya aure ni. Nan kan idona ya rufe ranan na mayar mata da ansa sosai ga maganan ta inda ta shiga kamay kamay wai nayi mata kage da sheri ba abinda tace ke nan ba ita. Nan dai mukayishi ba dadi na dawo gidan mu ina labartawa yan uwana abinda mama din tayi min aiko suka shiga yaba bakar magana a kanta . Kowa da irin abinda yake fadi mai zafi don bacin rai can kuma gida jamil na dawowa ra samay shi da kukan munafunci wai nayi mata tono asiri don anga bata haihu da mahaifin su ba ake mata haka. Shiko Jamil ya daure min ko dana dawo yaki min magana nima na daure mai da safe na shirya zan tafi gidan mu ya hau bala,i wai na raina shi da iyayyen shi don naga basu da hali yasa nake masu wulakanci shi sai ya rabu dani ba komai bane a guri shi. Nima nayi zuciya ranan nace arabu din mana sai may ko shi ya samu ana gulman shi yadda na samu mama da yan haya suna gulma na dole ya dauki mataki. Yace ai shi ba haka ta fada mai ba nace ai ba zata fada ma gaskiya ba don tasan da kazo baka binkici zaka hauni da fada nan dai na kwashe yadda akayi na labarta mai komai. Yace ita mama din ke fadin hakan nace kwarai kuwa don da kunne na naji ba wani ne ya labarta min ba yace yayi kyau nan ya fice nima na rufe zuwa gidan mu wurin bukin yar uwata ta haihuwa. Anyi buki lafiya ankai amarya lafiya da na dawone naga canji sosai a gurin iyayyen mijina sai wata yar hayan ne take labarta min abinda ya faru a bayana tsakanin su da dan su. Inda tace Jamil din ya goyi bayana don anyi turke turke a gidan tun wanan lokaci ta fara tayar da hankalin ta a kan zama damu a gidan muka koma kamar kishiyoyi da ita kuma. Zaman kanwata da mijin ta kowa yana yabawa don zamane na mutunci sosai sukeyi ko ni din banda matsalan wurin abinci don muna cin maikyau mu sha mai kyau. Sai dai ta fannin sutura ne nake ganin ba daidai ba gare ni ga dakina ko macen data dade da aure ta bani lafiya har kunyan baki so zo min dakin nake ji sai in kama kamay kamay idan nayi baki. Shiko gogon haka bai damun shi kullun a cikin jiran kudin magaifin mu su fito yake a gyara daki dashi shine burin shi a kullun bai ko jin kunyan hakan. Neman mata kan sai ma abunda ya karu gare shi don yanzu baya kunya ko shayin kowa kai tsaye yake abinshi yadda yake son yi ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Ganin rashin dawowa gidan shi da wuri yana ci mun rai ga kuma abinda mahaifin shi yace da nakai kara yasa na sa ido gare shi. Yau ma da yamma yai wanka ya shirya ina zaune ina kallon shi yana ta faman feshe feshen jikin shi da turare har ya gama zai fita nake tambayan shi kudin cefane . Ko kallon banza ban samu ba a wurin shi yasa kai ya fice daga gidan wana abin ya karas min jin haushi da takaici ranan dai sai garin rogo muka sha nida diyana ga ciki a jikina kuma. Ina zaune ina kallo na dubi agogon dakin lokaci ya nuna sha biyu da rabi na dare tashi nayi na goya yar diyata a baya na sa hijjab dina. Banji tsoron dare ba haka na fice tunda gidan namu a bakin titin unguwan mu yake nasan ba zan rasa mutaje ba a lokacin a waje. Gidan hanyan da Ruth take na nufa don ba wani nisane a tsakanin mu ba don dama matan unguwan mu sun min kwatancen gidan har dakin da take zaune a ciki. Ina shiga dakuna ne birjit sai kida ke tashi da kallo a wasu dakunan na gida dagani kasan gidan da kabila suke zaune ne a cikin sa. Dakin na dosa inda cool music ke tashi ciki a hankali ban tsaya wata wata ba nayi nocking din kofan dakin da karfi ina duka iya karfina . Muryan Jamil ne daga ciki yake fadin who is there ? Na kara nockin iya karfina sai naji muryan ta tana fadin iam coming dan wani lokaci aka bude kofan tana dare da dan karamin towel iya cinyanta tayi daura gaba dashi. Budan kofan mukai arba da ita da sauri ta koma tayiwa kofan key yadda ba zan iya shiga ciki ba nan take na dinga dukan kofan ina zagi sukaki budewa daga ita har shi. Dukan kofan da nake da zagi ne ya jawo hankalin mazauna gidan suka fara fotowa daya bayan daua daga dakunan su suna tambaya lafiya. Sai zagi nake ina fadin husband snercher shame for you ina mata ihu idona ya rufe sai kallo na mutanen gidan keyi sin kasa min magana. Sai wani iyamiri daga shi sai dan gajeren wando ga katon ciki ne yazo wuri yana fadin madam kiyi hakkuri ki koma gida basu kyauta maki ba gaskiya amma kiyi hakkuri don Allah. Kin ga nan gidan haya ne yaran mu sunyi barci zaki iya tayar dasu daga barci gashi gobe suna da school yana kokarin jan hannu na na fisge hannun nawa daga rikon da yake son yi min. Na kokarin shi kaini wajen gidan ganin naki kula shi ya hada hannayen shi biyu guri daya yana fadin don Allah kiyi hakkuri ki koma gida ki jira mijin ki ya dawo sai kuyi ta can dashi tunda sunki bude kofan gidan. Kallon shi nayi ido jawur sai ya kara hada hannayen shi wuri daya tare da fadin don Allah a cikin hausan shi da bai zauna ba sosai a bakin shi. Ganin yana ta hada ni da Allah gasu su kuma sunki bude kofan yasa na juya na fara tafiya na fito daga gidan mutumin yana biye dani a baya yana bani hakkuri. Yace mun san basu kyauta ba muma muna magana don abin nasu yayi yawa sosai har muna tunanen yana da mata kuwa akace muna kece matar shi ai. Kiyi ma mijin ki nan fada sosai don Allah ko mu a gurin mu wanan abin kunya ne haka da sukeyi har sai da ya fitar dani a lungin gidan da sai yanzu nake jin tsoron wurin mutumin ya koma gida. Ni kuma na wuce zuwa gidana hankali a tashe kowa yayi barci a gidan haka na zauna kamar manya ina dakon jiran shi ya dawo. Karfe daya da wani abu ya shigo gidan yana wani muzurai da shan kamshi a fuskan shi yana shigowa na dora mugu azzalumi macuci ma,hainci kawai fita min daga daki kada ka goga min zunibin da ka kwaso a daki. Wani kallo ya watsa min yana kokarin shiga dakin na tare kofan da sauri ya bangaje ni na fadi ta bayana sai da kashina ya amsa min don yadda naje baya din. Ya shige abinshi na tashi da kyat na bishi ciki rikici sosai mukayi dashi har da saki ya bani a cikin daren nan kafin gari ya waye don ya zagu sosai a wurina. Da asuban farko ya fita gidan ashe gurin mahaifin shi yaje ya fada mai abinda ya faru a tsakanin mu inda ya nuna mai rashin gaskiyan shi kan abinda yayi min din . Ina zaune inda na idar da sallah sai lokacin nake jin ciwo a kwankwaso na a inda na buge din daya ture ni da dare yake min ciwo sai sallaman su naji har da matar baban shi sun shigo. Ban daga ba daga inda nake zaune anan suka samay ni muka gaisa dasu sai gashi ya shigo falon yana muzurai da idanuwan shi. Nan mahaifin ya fara bayani ya nuna ma kowan mu kuskuren shi ni dai laifina wai don may ban jirashi gida ba har ya dawo muyi abinda zamuyi dashi na bishi can. Budan bakina nace baba kai kace min na sheda abinda ake fadi din ne a kansu, baba danaje fa matar daga ita sai towel ta fito min dashi a gaba. Yace bake kika je mata gida ba koma yaya kika samay ta aike kika jawa kanki mugun gani na dauka wani fada sosai mahaifin nasa zai mashi sai ji nayi yana mashi fada akan sakin da yai min kawai. Inda ya kare zancen shi da fadin mu ruwa kan mu asiri mu boye maganan kada in bari gidan mu suji zancen sakin nan don nasan ba aure na da Jamil din suke so ba. Tun daga wanan ranan abubuwa suka kara jagulai muna don sai yayi min kamar basu haduwa da matar ashe sallon tako suka canza min don kada in gane suna tare da ita. Da zaran ya fita da safe yana gurin ta sai in yamma tayi zai dawo yayi wanka ya kara fita baya wuce sha daya zai dawo gida ya kwanta sai kuma gobe indan ya fita kuma. Cikin jikina yana ta kara girma a lokacin ga ba komai a hannun mu sai tunanen fitar da kai kunya da nake faman yi inda shima a bangaren shi haka din ne ke gudana wurin shi. Bai aje ba baiba wani ajiya ba sai ranan naga bai fita ba kamar yadda ya saba fita yawon shi na banza din har na gama abinda nakeyi na samay shi muka zauna muna hira dashi. Yake ce min wai yaya zancen filin mu na wani gari da mahaifin mu ya saya nace filin na nan baba yana kula muna dashi sai nan gaba za ai shawaran abinda za a yi da fili. Yace to may zai hana a sayar da fili in samu abinda zanyi na haihuwa da kudin shi yana ganin shine mafita a gare mu tunda dai naga shi baida shi ai. Nace wai wai nifa tsoro nake ji da kunya in tunkari baba da wanan zancen haka gaskiya a dai canza dabara zai fi nake gani. Da yake sarkin iya tsari ne nan ya zauna ya tsara min yadda zamuyi yace ai sai na fara neman hadin kan yan uwana tukun mun daidaita zan tukari baba da zancen fili. Haka dai na gaiyaci yan uwana kan suzo akwai maganan da zamuyi dasu a gidana ranan kaza da yake mukan hadu ba wanda ya sani mu dan tatauna dasu. Da farko sunki ban hadin kai kamar yadda naso sai daga baya ne da na sa masu kuka jikin su yayi sanyi suka yarda a sayar da filin don na fada masu abinda nake son inyi da kudin filin. Tunda wancan mai yawan baida ranan fitowa gare mu yanzu abinka ga dan uwa duk sai suka tausaya min suka fara fadin suma suna da abinda zasuyi idan kudin sun samu. Nan muka aje ranan da zamu samu baba kabiru da zancen filin kowa ya koma inda ya fito sai ranan da zamuje wa baba kabiru da zancen kuma. Jamil ya dawo yana tambaya na yadda mukayi dasu nace sun yarda nan ya hau yin dadin baki irin nasa har da fadin yadda kudin filin zai kai idan mun sayar din. Ya shiga tsara abinda zai saye na suna da wanda ni zanyi tun lokacin da yaji yan uwana sun yarda don ni yanzu ina kallon shi ya daina harkan bariki gani kadai ya dogara a gidan. Bukin yar uwanshi za ayi a kauye ya shiga min shiri wai yana son in fito wurin bukin dani da Amira yai muna dinki fita buki kala biyu duk da bamasu tsada bane niko sai rawan kai nake zan fasa taro da kayan idan naje. Ina ruwan dan baka saba ba nake ganin ai ba wanda zai kaini fita a gutin yadda yake dada kayan a gabana da yadda zasuyi min kyau. Mun samu baba da zancen fili baba yayi mamaki kwarai may zamuyi da kudi haka mukace muna dai son a sayar a bamu kudin mu ne lalura zamuyi. Yace mu bari zai tuntubi yan uwan shi idan sun yanke shawara zamuji daga baya abinda suka yanke. Kwana biyu na wuce wurin buki a kauye wanan karon ban dade kamar yadda yake turani in dade ba saboda zancen kudin da yasa ma rai din ya matsa akan in dawo. Tun da na dawo ya sani gaba haka nikuma na sa yan uwana a gaba muka tayarwa baba hankali akan fili baba musa yace wa baba kabiru a sayar kawai tunda matsin yayi yawa yaran nan idan ba munyi da gaske ba suna da ja sosai damu nan gaba. Haka dole aka sa fili kasuwa kan sayarwa shiko gogan kulun ya dawo tambaya yake yaya babu wani magana a bangaren babane har yanzu. Idan nace a,a sai yace ya gane mutanen nan cutan mu suke son yi idan ba haka ba fili ne za a ce yayi wuyan sayarwa a gari kaza. Shi idan basu samu mai saya ba shi zaije ya samo wanda zaisai fili a bamu kudin mu don ga lokaci yana karasowa na haihuwa na ni bani tunanen hakan shi idan na haihu baida yadda zaiyi gaskiya. Nikuma jin hakan sai na kara hasa ma yan uwana wuta muka matsama baba kan zancen fili mudai a sayar ko nawa ne a bamu kudin mu shine burin mu. Baba yace indon ta nasa ne a bari nan gaba fili zaifi kudi sosai don yanzu ba lokacin kudi bane ga mutane don damanane yanzu . Mukace mu dai a sayar duk wanan abin mu uku ne masu hasasa wutan komai shi karamin mu baya cewa komai sai yadda mukayi dashi. Da yake yana jin maganan mu shi dai bai cewa damu komai sai yace duk yadda muka yanke yayi mai don ko kudin farko da aka raba nasa Baffa ne ya kalalamay yaki bashi wai don kada ya halaka kudin. Ko dubu daya yake so dole sai baffa ya sani zai cire ga account din shi don Atm da komai nasa yana hannun baffa don bamu yarda da iyayyen mu ba saboda zugan su Jamil dake aiki a kan mu lokacin. Wani tsana da kiyayya ne ya fara shigowa tsakanin mu da yan uwan mu da farko muke daukan kan mu duk abu daya yanzu irin abinda suka ga muna nuna ma mahaisu sai tsana da rashin yarda ya fara shiga tsakanin mu dasu. Babu magana mai dadi haka ma su anty duk sun tsamay hannun su ga zancen mu yanzu a hankade suke kallon mu idan munje gidan. Haka yasa muma mukai shawaran daina zuwa gidan wurin su sai an dauki lokaci mai tsawo bamu taka gidaba da sunan zuwa gaida baba. Don shi baba kabir mutum ne mai wuyan sha,ani baka gane bacin ranshi a lokaci daya don bai nuna muna komai dake faruwa a tsakanin mu dashi sai dai su iyalin nasa. Anty ma tun abinda mukayi wa iyayyen mu maza muka rasa gane kanta ta daina muna komai sosai da take muna a baya yanzu ta rungumi diyan ta kawai. Duk da tana dan iya kokari wurin nuna muna ba komai amma mun ja baya ga al,amarin ta sosai yanzu haka dai ake zaman kadaran kadaham damu dasu. Ranan dai na samu baba da kuka ina fada mai ina cikin matukar bukatan kudi ne don haka don Allah a sayar da filin nan ko nawa ya samu. Ba a fi sati ba aka sayar da filin namu ina kwance gida baba ya aiko inzo yana neman mu Jamil yana jin haka yai zubur ya fito daga daki yana fadawa dan aiken yaje yace gani nan zuwa. Bayan fitan dan aiken yake fadin in tafi zai karasa min aiki na kafin in dawo don haka na shirya a gurguje na nufi gidan namu wurin kiran da baba kabiru ke muna. Ban dade da isa ba yan uwana suka hallara a gurin nan dai baba yai muna jawabin yadda filin ya kama inda za, a fitar da gadon mahaifiyar su sai a raba muna sauran. Idan akwai mu abinda muke ma bakin ciki shine ace za a raba gado a warewa mahaifiyar mahaifan mu gado tunda yanzun bata darai ai. Gani muke kuma da yadda Jamil ya lurar damu ai zalunci ne da ha,inci ake muna a hakan da komai za a ce wai a cire kason mahaifiyar su duk da bata raye wai a raba da ita don dai kawai su samu kason wani abu daga ciki. Yau ma kaman kullun bayan sun gama muna jawabi sai kanina baffa yace shi yana da magana wai duk da hajiya umma bata raye, may kesa ake cire mata nata kason ko yaushe idan anzo rabo. Kai baba kabiru ya girgiza yana murmushi yace yanzu kai baffa waye bare a cikin uban nan, nan naka , sai baba musa ya dakatar dashi da fadin ba wanan ba don na gane dan kason mahaifiyar mu da muke ci daga cikin arzikin su suke wa bakin ciki don yau kun fito fili kun baiyana muna manufa ku akan abinda kuke nufi. Baba kabiru ranshi ya baci sosai damu bai iya magana a gurin ba saboda bacin rai sai na koma tun a wurin ina jin nauyi da kunyan kanmu sosai na abinda mukaiwa baba kabiru da yan uwanshi sai dai murna da dokin samun kudi a lokacin bai bari mun rokeshi gafara ba. Kamar yadda muka saba idan mun saba mashi muke bashi hakkuri ya huce damu sai yau bamu samu yin haka gare shi ba don doukin samu kudi da mukeyi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Yau da gobe na Allah ne abinda muke jira tsawon shekaru sai gashi Allah ya nufa sun shigo gare mu nan hankali mutane ya dawo gare mu. Don suji yaya za ai rabon wanan kudin namu an kasa kudin gida uku muka fara samun kashin farko ranan jamil shi da kan shi ya shirya min yarinya don inyi sauri mu hadu a gidan baba kabiru inda aka bukaci muje har. Har kusa da gidan ya rakani yana fadin idan kinji ki maida hankali ki saurara da kyau don kada a samu matsala nace insha Allahu mukai sallama na yaju ya koma gida yana jiran dawowa na daga gidan mu din. Na samu su baba musa da baba yushau sun shigo garin inda na karasa ciki da sallama na ina gaida mutanen gidan namu da kwana. Aka ce ni ake jira in karasa ciki kafin yar uwata tazo an bude gurin da sallama tare da addua kamar yadda musulmai keyi idan sun hadu a gurin yin abu mai muhinmanci. Baba musa da yake babba ne ya fara magana yace to Alhamdullahi yau dai Allah ya nufa wanan kudin da aka dade ana jira sun fara shigowa gare mu. Sai dai zamu so muyi rabo kamar yadda addini ya umurta da ayi yadaiyi yan bayanan shi tare da fadin zasu cire kason umma mahaifiyar su a rabawa magadan ta kamar yadda addini yace. Nan kanina ya gyara zaman shi da kyau ya kuma dora da fadin zamu cirewa shi Alhaji kabiru kuma kudin shi daya sa na jigila tare da yin wahala kafin kudin nan su fito gare mu. Sai baba kabiru din yace ba zai karbi kudin duka ba tunda kudin namu bai gama shigowa ba lokacin tare da fadin zai kuma karbi iya wahalan shi rabine. Nan sukayi komai kamar yadda ya dace ayi kan tafarkin addinin musulunci aka fitarwa maza da kason su sai mu mata mu biyu . Ganin duk mun bata rai tunda baba musa ya fara magana yasa baba kabiru yin gyaran murya a gurin yace idan mun ga rabon da sukayi bai gamshe mu ba zasu iya kiran malamai ko alkalai suzo su raba muna da kansu idan haka zai gamsar damu din. Dakatar da rabon kudin baba musa yayi a lokacin da yaji abinda baba kabiru din ke fadi yace assha daga cikin mu nan wa zai cuce su suke gani idan mu masu hali ne ai ko kallon kudin nan da yake gadon mahaifiyar mu ne ba zamuyi ba. Nan dai muka dan fara kamay kamay alaman nuna haba dai baba aka raba kowa ya dunkule nasa muka fito idanuwan mu mirsisi nayi sallama da mutanen gidan mu muka bar gidan. Gaba dayan mu gidana muka hade dukkan mu nan kanina ya fara fada akan abinda su baba sukai mu nan dai kowan mu ya shiga fadan albarkacin bakin shi kan su baba din. Sai baffa ke fadin shi baba kabiru ne yafi bashi mamaki da wai ya karbi kudin da don yayi wahala ya nema muna hakkin ga gwaunati. Lokacin ko yana UG two ne baba ne mai daukan nauyin karatun shi a makarantar ga diyan shi a zaune bai kai su ba su amma duk wanan bamu gani ko kadan mu kudin mu dai muka sani mu. Sai Jamil da na samu yana dakon dawowa tun fitana yace yanzu kun fara gane mai nake fada maku din ke nan yanzu shi baiji kunyan fadin wai a bashi wanan kudin ba don Allah. Mun dai fadi magana a gurin duk wanda yazo muna a baki fadi mukeyi a lokacin don ran mu daya baci kan dan abinda iyayye mu suka dauka wanda iya hakkin su ne suka dauka. Nan mijin sumaiya yazo shima ya dan dora nasa zancen akarshe a ka yanke shawara Baffa kanina zai rubutawa baba takarda kan abinda sukai muna karshe su sumaiya suka dauki kudin su mukai sallama bayan mun cire wanda zamu rabawa dangin mu kaf daga cikin kudaden da kyat don kowa na fadin kudin sunyi yawa abinda nace a ware din abawa yan uwa da suka wahala damu. Daga cikin mu dan karamin mu ne kawai bai magana karshe ma da yaga irin shawaran da mazajen mu ke badawa yayi yawa ya mike tsam abinshi yace damu sai da safe. Nan na gano baya tare damu aiko muka haushi da fada shida bai ce damu komai ba ta fita abinshi yana fadin kudai bi sannu don kudi karewa zaiyi ya barmu da iyayyen mu daga haka ya fice abin shi ya barmu. Ina mamaki yanzu kwarai da kanwata tafini zakewa akan zancen kudin nan sosai sai daga baya na gane sherin mijin ta ne ya yi mata famfon shedan a zuciya itama ta kumbura fam da iyayyen namu. Tsakani da Jamil yanzu ko nan wani irin ladabi ya taso ga Jamil din gare ni sai nan nan yake yi dani da yar diyata na zama wata hajiya a guri shi da baya son ko kuda ya tabani a lokacin aka bude wani shafin sabon soyyaya sosai a tsakanin mu. Tun cikin dare muka fara kasafin kudin da abinda zamu saya da kudaden namu inda yasa na ware ma mahaifan shi nasu kason daga cikin kudin. Ni yar Dadi aure sai nace ya rike kudin a hannun shi gaba daya duk abinda za a yi sai ayi nan muka shiga facaka da kudi ba wanan, ba wancan, duk kuma yan uwan shi don ni nawa yan uwan ba wanda yazo kaman an tsayar dasu a lokacin daga zuwa gurina. Baka jin komai sai kamshin a shiyan mu na soyeye da dafe dafen kayan dani idan mun shige daki yana gida kowa yazo gurina ban fitowa sai dai mutum yayi sallama ya gaji ya tafi don bai bari in fito gurin mai shi. Ni da kaina naje gidan mu tare da kudin damu ka warewa yan uwan mu dubu sittin kacal da kyat da boni daga cikin kudaden namu. Banyi mamakin ganin canjin fuska ga kowa na gidan ba sai dai lokacin nima kaina na hayaki sai ban damu ba ashe da safe Jamil ya bayar da wanan takardan daya ce zai rubutawa baba kabir din. Shine sauyin fuskan dana gani a wurin yan gidan namu a lokacin jin sallama na yasa baba kabir fitowa ya kirani zuwa falon shi. Inda ya fara magana bayan kara gaisawan da mukayi yana fadin nasan da sanin ki jamil ya rubuto min takarda akan zancen kudin ku don haka na aika kowa yazo don kuji komai da kunnuwan ku. Ba a dauki lokaci ba naga su baba musa sun iso gidan kowa ranshi a bace damu yake lokacin sumaiya ma ta iso daga gidan mijin ta don unguwan su nada dan nisa da namu. Ran baba musa ya baci sosai nan sukai muna dala dala karshe suka nuna muna bacin ransu kan sun gane mazajen mu ne suka shiga cikin maganan kudin. Baba yusha,u yace yanzu kuko nauyi da kunyan wanan bawan Allah baku ji yadda kuka rufe ido kukai mai kan abin duniya shifa kudin gado sai wanda Allah ya nufa ya more zai more mai a duniya. Zaku iya rama mai irin dawai niyar da yayi dakune koma ince yakeyi dakune a duniya nan don dai mu kun san ba hali muke dashi ba da zamuyi maku. Cikin fushi baba kabiru yace in don kudin hakkina ne dana karba ya tashi ya mike ya dauko kudin yana fadin gasu na yafe ku kara da naku. Tunda kuna ganin na cuce ku ne na zallunce ku kuka na fara yi don nice babba kafin in magana kanin mu karami daddy ya mike yana fadin baba wallahi ni kan bada ni akai wanan shawaran ba ban ma san suyi wanan shawaran ba yana fadin haka ta mike ya fice daga fallon namu. Kuka nima nake ina nema gafaran baba kabir don hankalina ta tashi matuka yadda naga yana kuka akan mu sai abin ya daga min hankali sosai. Karshe dai muka bashi hakkuri muka fito rayu kan mu babu dadi kan rabon kudin inda kanina baffa da summaiya suka kyankyashe idanuwan su mirsisi basu kunyan kowa. Mun ba anty wani abu ba wani mai yawa bane don mun san ta wahala da rayuwan mu dubu ashirin muka bata baba ma haka sai uwar gidan ra goma da amaryan ta. Tace mu barshi ita kan ba zata karbi kudin mu ba gaskiya da kyat na samu na bar mata kudin a dakin ta na fito na tafi inda yaran baba kabir kaf suke muna kallon banza don mun taba masu mahaifin su. Sai gashi bayan sati biyu banda ko sisi a hannu na dama wurin shi koda na lalabo sai cewa yayi ai kudi sun kare babu komai a hannun shi kuma. Raina yayi matukar baci sosai da jin hakan ba yadda zanyi dole na kyale shi don banda yadda zanyi dashi kan hakan . Sai lokacin angulu ta fara komawa gidan ta na tsamiya kuma ya fara tayar da halin shi shikan ya samu ya yi dinkuna na alfarma daga cikin kudaden sosai ya sayi duk wani abinda yake da gurin saye din kafin kudin su shigo a hannun mu. Dan haka baida sauran takaici kuma yanzu nikan ko kyale da yar diyata bamu samu ba daga cikin kudaden na dai samu na sai wa kaina ledan daki da dutsen guga da wani tsohon tv na hannun don nagaji da shiga dakin yan hayan gidan mu kallo. Don Anty tasha min fada tana nuna min illar yin hakan da nakeyi na zuwa dakin yan gidan mu kallo wanda a lokacin ban daukan hakan a komai gare ni. Amma da take nuna min illar yin hakan sai naji abin ya fita mun a raina ko sunce an samo sabon kaset ban zuwa ko ina kallon ina dakina zaune. Shiyasa na matsa na sai wanan dan tv na hannu wanda ma bai kai nawa dana zo dashi gidan ba wanda baba kabiru suka saya min a lokacin aure na. Kowa taji zancen kudina sun kare sai yayi mamaki sosai don abin akwai mamaki gaskiya don ba a gani a dakina ba da jikina ba inda ya nuna na more ma kudin ko kadan. Muna a haka ne rikici na da uwar mijina yaki ci yaki karewa a tsakanin mu ga Jamil ya matsa min akan shifa zaman su a gidan damu ta ishe shi yanzu don suna hanashi walawa a gida. Haka yasa na fara daure mata fuska ina mata abinda ban mata a da can baya yanzu hankalin ta ya tashi har yakai ga taje ta nemi wani gida don su kama haya su koma ciki. Ina murna zamu rabu da kaya idan sun tashi wanda ban hango illan yin hakan da nai masu ba wanda da sunana suka tashi daga gidan bada sunan dan su Jamil ba. Don ni sukace ina masu wulakanci tunda ni yake izawa inyi mata rashin mutunci a fili shiko yana nokewa kamar bai sani ba. Yan uwana kaf sun dauke kafan su da gidan mu yanzu sun mayar da hankalin su gurin iyayye su sun ware mu inda muma muka kara dinkwa da junan mu a tsakanin mu. Jamil ya bamu shawara muyi dabara karbe kudade su Baffa dake hannun baba kabir da sunan ajiya kada azo a nema a samu babu su a cewan sa wai gwano baya jin warin kanshi ashe. Ni ga nawa tun ba akai ko ina ba duk ya halaka min su sai kamay kamay nake wa mutane da yan hayan gidan mu suka fahinci komai ya kare min sai habaici ya tashi tsakani na dasu. Wata daya da muke shiri ne take fada min gaskiya ta kebe dani tana fadin kinyi wauta hadiza may yakaiki bawa namiji kudi irin haka masu yawa. Na miji fa baida tabbas ko kadan baki gudun nan gaba ya karo maki kishiya da kudin naki may zaki fada nan dai tayi min nasiha sosai wanda yasa ni natsuwa. Ta nuna min abinda mukai wa kanin mahaifin mu mai kaunar mu bamuyi daidai ba wallahi gara inje in nemi gafaran shi kan abinda mukai mai mu koma daidai da iyalin shi dake fushi damu. Don ko wane ma haka ya faru dashi fushi zai dauka dakai tace da bakin ki kike fada min irin yadda yake nuna maku banbanci da iyalinshi har yau basu taba nuna jin zafin hakan ba don may zaku saka mai da hakan akan kudi ku ? Ta dai yi min nasihs sosai a matsayin ta na mai kaunata a gidan kuma ba laifi nayi kamar yadda tace din inyi don naje mun sasanta da yan gidan mu an fahinci juna don sun gane muna amfani ne da zugin mazajen mu. Don kanwata har ta fini daukan zugin mijin ta yanzu nake gani do ko ni banjin dadin ta bansan kuma irin yanayin da suke ciki da mijin ta ba a gidan su. Don ko naje ban gane komai haka nake juyowa in dawo don bata bari in fahinci komai sai dai na gane itama din duk abinda ya kwaso ni shiya kwaso ta yanzu don babu kudin a hannun ta kuma. Itama mijin ta ya kashe sunyi wani abinda kudin tunda kudin nata a hannun mijin nata suka gashi da daure fuska ga kowa bai sakin fuska balle ya bada kafa a fada mai wani magana. Har gara Jamil don shi yana dan wasa da yan uwana idan yaso yana kuma ziyaran iyayyena idan ya tashi yaso don kan shi yana yi. Ranan dai da talauci ya damay ni na shirya naje gidan wurin ta neman dan dubu daya in rike don lalurar yau da kullun don a takure nake ba walwala. Sai nake ganin ita ta dan rage da wani abu a gurin ta sai cewa tayi min wanan kudin fa kamar yadda nima nake fadin babu su itama gaskiya babu su a hannun ta yanzu don ko abinda zasu karya yau uwar mijin tane ta aiko masu dashi. Ban san lojacin da na bude baki nace sumaiyaay kikayi da kudi ki ba ni ansan mijina ne ya cinye min nawa naki fa ta hauni da fada tana daure fuska akan may zanzo in tasa ta gaba da tambaya kudi dai ne an bawa kowa hakkin sa ai. Ban dai gane komai ba haka na bar wurin ta don mijin ta da ya dawo yana wani daure fuska kamar yaji zancen mu da ita dama ya shigo yana shan kamshi daya ganni a gidan. Ban san dadin firan da ya kwashe wurin Jamil ba na kwashe zancen da mukayi da yar hayan gidan mu na fada mai ranan tun wanan lokacin ya matsa akan lalai sai na sallamay ta daga gidan din tana saka muna ido ga al,amuran mu dashi. Ban so haka ba don a wurin ta nake dan samun shawaran karuwa sai na rasa yadda zan mata magana kan matsin da yake min a kan su gashi shida mijin ta suna shiri sosai a gidan na gani. Amma haka yake matsa min a daki akan in kore su su bar gidan nan ko raina ya baci dashi banda yadda zanyi haka na daure na fara nuna mata wasu halaye na daban da ban saba nuna mata ba sai data ga haka ta fara jan jikin ta dani itama. Har ya kaimu da fara sa,insa a tsakanin mu in rufe ido in mata cin mutunci ala dole ni ga maigida sai fadi nake sufita su ba ni gidana tunda bada su aka sai muna ba. Takan ce ai nima saukin abin bani kadai ke da gidan ba namu na taro ne na algaje ni kadai sai munafukin miji dake yaudarana don banda wayo ya cinye min komai nawa tunda ina sakara yana fita yana neman mata da kudina. Wanan zancen ya bata min rai sosai nake jin zafi a raina kan abinda ta fada min sai ya bata min da Jamil din da ita a lokaci guda. Ko da ya shigo nan na haushi da sababi ina jidali kan zancen da maman Ahmed ta fada min nasa nake fadin idan har mata ya nema da kudina ba zan yafe mai ba. Wanan magana ya bata mashi rai sosai yasa ya kara fushi da mama Ahmed din kan yau ba gobe ba zasu tashi gidan sai da maigidan ta yaje gurin iyayye na akai muna magana na hakkura da zancen sai idan sun samu gida don mijin yana gina bai karasa ba lokacin. Wanan yasa muka dan samu saukin fitinan mu sai dai sama sama muka koma da ita a gidan ba wanan dogon shirin da mukeyi da ita. Ya koma ban wani dogon shiri da kowa a gidan yanzu don duk sun hada min kai ban gane masu nima ban shiga shirgin su dana yaran su kamar yadda mukeyi a baya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Ko dana koma gida na samu ya karasa min aikina kamar yadda yace zai mun din don har Amira na samu ya kimtsa min ita don bai bari na tafi da ita ba. Ina shigo jikin shi har rawa yake wurin tambayana to yaya zancen kudin ne komay ake neman mu dashi kudin dake a jikina na fitar ina nuna mai take ya washe baki yana fadin alhamdullahi. Allah ya rufa muna asiri dama ko barcin kirki ban samun yi kan rashin samun mafita da banyi ba yanzu kin ga Allah ya rufa muna asiri. Nan ya shiga lissafin irin karyan da zamuyi idan na haihu yake fadin in kawo kudin tun yanzu yakai na mai shagon da yake sayayya da na haihu daukowa kawai zamuyi a gurin shi. Ina kallo ya lissafa kudin da yake so ya kuma fitar da wanda zamu sai abinci har na suna idan na haihu din da za,a dafa gurin taron suna. Da kyat da boni na samu yabar min wanda zan dan rika a hannu na don lalurori irin na mata sai cewa yayi dani ba ga baba kabiru nan ba yasa zai min idan na haihu. Ni don sanin yadda muke da mutanen gidan mu yanzu sama sama yasa hankali bai kwanta da zasu yi min ba idan na haihu din ganin na na matsa mai ya firar da dubu talatin ya bani a cikin dubu dari tara da kyat ya mika min a hannu na wai sakaci gare ni kada in aje a wurina a kwashe. Nasan abin da yakewa shine ganin haihuwana na farko an min abinda ma bai zata zasuyi min ba ga kuma kanwa ta data haihu itama an mata sha tara na arziki ya gani. Ban san baida kunya ba sai da ya miko min kudin yana wani shan toka a fuskan shi tare da fadin ni ke nan naga kudi na daure fuska may zanyi dasu bayan baba kabiru yana muna komai idan mun haihu mafarin in koyi kashin kudi ke nan jifa. Baba kabiru da ya gama zagi yana batawa a gurin mu ne yake kuma tunanen zai muna abin arziki yanzu saboda son banza daya iya a rayuwan shi. Ni gani wawiya ta karshe ban koyi tunanen irin sakin da yake min ba a lokacin ni dai bukatana da tunane na dani kadai zai zauna ba wata mace da zaice zai kara aure nan gaba. Don sam bani irin wanan tunane a raina saboda son shi daya rufe min idanuwana a lokacin har mutane na fadin wai ko asiri yai min ne haka wana abin ga kowa don sanin halina an kawo ido ansa min dashi banda makwabi a rayuwa na. Don kowa yasan da ya fada min gaskiya zan kwashe in fada mai ya dora gaba da mutum har illa masha Allah. Yanzun kan muna da abinci ga kudi don shi Jamil mutum ne da bai ci ko wani irin nau,in abincin daya danganci tuwo a rayuwan shi sai dai dan taliya makaroni shimkafa da miya ko tea kamar ba haihuwa kauye ba shi. Sai daga kai nake wa mutanen gidan mu don komai ina dashi yanzu ban dan murya gun kowa don neman wani abu don tunda anty tai min fadan haka ga yan hayan gidana na daina tambayan su wani abu. Da yake ni sakarai ce sai wanan samun yasa ina daga masu kai har suka fahinci hakan gare ni kowa ya jaye min daga harkana sai ni dashi da yan uwan shi muke bushashan mu a gidan. Daka ji sallama yan uwanshi ne ba dai nawa ba yanzu zan hada masu delicious ko a sawo masu kayan sanyi susha su wuni suna cin dadi a gurin mu. Sati kaman uku da haka na haihu na kara haihuwar diya mace ba laifi don yan uwa da matan baba suna asibiti a tare damu har na haihu aka dawo dani gida. Tun yanda suka ga ni kaina da Jamil din muna masu kowa ya dauke kafan shi a gidan tun ranan matar mahaifin shi ce tazo ta zauna damu na satin da akeyi inda Jamil sai dadi yake cika mu dashi. Niko ban tunanen komai a raina don sai fadin ake yarinya tazo da goshin ta don muna cikin wadata inji yan uwan shi suke fadin haka gare mu. Ban wani damuwa ba na rashi ganin dangina basu tsayawa a gurina ni tunda ga dangi jamil sun tsaya min akan komai ai ya waddatar dani nake gani don haka ne ban nemi shawaran kowa ba. Da anty ta kara shigowa duba mu take kebewa dani irin yadda akeyi din nan tana tambayana mai muka shirya ma bukin don sunji shiru ban tuntube su ba har yanzu. Sai budan baki nayi nace kada su damu ai mun gama shirin komai da zamuyi tace kai madalla Allah ya raya muna bata dade ba ta fita . Sam ban kawo magana na wani katobara bane a lokacin don haka na shiga harkokina ba wani damuwa don ina ganin ai muna dashi. Summaiy kanwata ce tazo tana tambayana nake fada mata yadda mukayi da anty tace kai amma ke anty hadiza wai wata irin wawiyace haka don Allah. Anty ce zaki fadawa kun kun gama shirin komai da mijin ki kina ganin ke yanzu baki da bukatan komai a wuri su ke nan ? Nace may zamu bukata tunda muna da kudi a hannun mu yanzu tace to shike nan ita yanzu gida zata taji irin shirin da akeyi a gida don tasan yau ya kamata ace anyi su cicin da sauran su. Nace sai ta dawo ta fita zuwa gidan mu niko ban wani damuwa ba a raina don nasan zamu burge kowa da wanan haihuwa ko suyi ko kada suyi ban damu ba ni. Da ta shiga gida sai ganin gidan tayi wayau ba kowa anty ma tana dakin ta tana barcin ta a lokacin don tana up a wurin aiki. Bayan sun gaisa ne take tambayan ta ko akwai wani abinda za a yi a gidan sai take cewa ai mai haihuwa tace ta hutar damu don sun gama shirin komai. Tace a ina ta shirya anty har gashi gobe suna ni banga wani shiri da takeyi ba tace summaiya kin san shirin da sukayi ita da mijin ta ne ki sa masu ido aga ni mana. Abinka da dan uwa sai hankalin ta bai kwanta ba ta kara dawowa gidana tana fadin ita fa taje gidan mu bata ga wani shiri da akeyi ba a can yanzu idan mutane sun taru mai zan raba masu na buki ? Nan dai dabara ya fado min nace buta zan sayo sai alale da taliya da zan dafa kuma da dambu . Tace duk a ina za ai maki wanan aikin to nace a gidan yaya sani wanan Jamil din nan da suke kamar abokai wanda ya tilasta min kiran matan shi da anty. Wani tsoki taja tana fadin yanzu ke a can za ai maki aiki sai kace wace bata da gata a gari gaskiya bai kamata mu nuna wa baba kabiru da matan shi haka ba anty. Fada mukayi da ita sosai a gurin don ta fahinci ina haka ne don gyarawa Jamil dina rai kawai ban damu da abinda dangi zasu fada ba a kaina. Nan na fitar da kudi cikin wanda ya dan rage min na bashi ya sawo min buta sai gashi da kananin butoci kuma dozen uku ni da na bashi kudin dozen biyar yana fadin. Wai ya samu sun tashi shine ya sawo min wa yan nan nace ai ba zasu isheni ba yake fadin wai har wasu mutane zasu zo da zan saye da yawa don barnan kudi kawai. Dinki kala uku yai min duk a cikin kudina shiko ya dinka sun kai kala goma sha kamar shine mai haihuwan da zai fita bani ba. Washe gari a gidan su aka yanka katon ragon da ya sayo aka gyara sai dan hanjin da aka aiko min dashi wai sun raba a can suma zasuyi amdani dashi ne. Sannu sannu gida ya fara cika da mutanen arziki yan uwa da abokan arziki suka fara zuwa min suna gashi ba a kawo min abinda zan ba su ba. Yan uwana da suka zo tayani aikin suna daga gidan mu sai tambayana sukeyi mai zasu yi nake cewa ba wani aiki a can gidan su Jamil ake abinci. Koda za a kawo min sai ga taliya wani iri dashi ba mai kuma dan kadan kasan kula sai dana dafe kaina don takaici da bakin ciki ga alale shima kamar hakan aka kawo min din. Haka na aka raba ma wa yanda ke gidan a lokacin aka barni ina kamay kamay idan mutane sunzo mi don ba abinda zan basu anan. Yan uwana suka kwasa suka wuce gidan mu don a can suna nasu dahuwan don dangin mu da suka zo daga wurare anan suka sauka. Dama kuma a ka,ida hakan yake ga al,adan bahaushe yan uwan mai haihuwa zasu taru ne a gidan mahaifanta har zuwa wani lokaci kafin su zo gidan ta da dan abinda suka tanada don ta. Sai da sukaci suka sha a can suka dauko dan turamay dana samu wanan karon turmi hudu ne kawai daga gidan mu sai buhu biyu na abinci gero da masara da baba kabiru ya saka min. Aka nufo gidana dashi tun da naga haka naji raina ya baci dasu a zuciyata fadi nake aiko in haka ne zasu sha kunya don ni dama a shirye nake abina don haka. Nan gidan su Jamil suka shigo da akwatinan daya gabatar masu a ranan don ba wanda yai tsammanin haka daga gare mu. Sai wani washe baki nakeyi ina sallo ni adole mun faso gari muma sai fadi mutane ke yi basu taba ganin itin set din akwatinan ba a gurin. Da aka bude kuma sai da kowa ya kama baki don kyawon kayan dake cikin akwatinan danawa dana baby duk abin kallo ne a gurin. Aka kwasa zuwa gidan mahaifana kamar yadda akeyi a wuri mu sukai ta sa albarka suna fafin yarinya tazo da goshin ta inda yarinya taci sunan mahaifiyar Jamil data rasu watau maryam. Kayan basu dauki lokaci ba aka bayar aka dawo min dasu kamar dai yadda akeyi idan an haihu ga al,adan gidan mu idan ka haihu zaka cire wa mahaifiyar ka da mahaifin ka turmi ka basu su saka maka albarka. Amma haka nayi mirsisi na hana ma kowa wanan irin al,adan na hana masu ban basu komai ba nace nima na rama ai haka dai dan kudin da ake kawo min gudun mawa . Na fitar nake bayarwa ana sawo min biscuet da butan da nake rano ina ba mutane don wanda ya sawo min ko dangin shi bai isa ba lokacin. Na dai samu aka watse lafiya duk dan abinda na samu ya tafi gurin mutane sai dai ban damu ba don ni Jamil ya gama min komai tunda ya fitar dani a kunya. Na gyara dakina da taimakon yar uwana data kai har dare a gidan mu ta soya min nama tare da wasu aiyuka muka gyara ko ina na gidan . Muka gyara akwatin tsab har ta roke wani zani nace ta bari sai Jamil ya dawo naji kudin shi zan bata shi mijin ta yazo ya dauke ta suka tafi. Gidan ya rage sai ni da yan hayana wanda suke part din su Jamil ya dawo abinda ya fara tambayana shine ina naman da aka kawo na mike na dauko mashi. Ya karbi roban ya dan jujuya ya girgiza kai tare da fadin wanan naman za a bar muna duk rago dayan nan kato daya yanka sai wanan zamu ci. Nace gidan ku fa sun cire nasu ankai nawa kason gidan mu suma sun cire na iyayye kamar yadda akeyi baiga laifin wanda yan uwan shi sukaci ba sai wanda yan uwa na sukaci ya hashi haushi. Ya dan tsince tsoka daga ciki ya zauna yaci da drinks mai sanyi ya kora ya kwanta na dauki roban na duba babu komai sai kasusuwa suka rage. Dole haka na fara amfani dashi wa gida dashi nake muna girki ina watsawa a cikin abinci idan zanyi. Kwana biyu da suna tun da safe da yake ba sallah nakeyi ba ina barci ban ko tashi ba sai hayaniyar kattai naji suna fita da buhun abincin da baba kabiru ya aiko min na kunu da tuwo. Don shine abincin da mace da ta haihu ya kamata taci nasan shine dalilin da baba kabiru ya saka min su don samun sauki a gare ni. Sai gashi Jamil ashe ya sayar ya soke kudin shi bai min maganan komai ba ina kallon shi yana kallona ba dama inyi maganan komai ya hauni da fada kuma. Kafin kwana uku da suna duk Jamil ya zauna ya tsotse kasusuwan nan daya rage ya cinye komai dana tanada wa kaina don haihuwa na in samu inci in sha indan na haihu din. Ranan muna zaune dashi muna dan hira duk akan wa yanda suka zo min gun suna muke hira sai na jefo mai zancen ina son in danyi dinki daga cikin turamay nan daya saka min . Sai cewa yayi idan ya shirya kai mun dinki shi zai kai da kanshi don haka in saka mai ido kawai yace tun wanan lokacin ban kara mai magana ba ni kuma. Haihuwa na da sati biyu matar wani wanshi da suke zaune a gidan da wansu ya gina tare da mahaifiyar shi ta haihu . Tun haihuwa da kwana uku ya turani wai in je in kama masu aiki nace kada ka manta nima haihuwa nayi ai waya zo ya kama min aiki lokacin har ya tare haka a gurina cikin su. Yace ra,ayin shi ke nan shi don haka in shirya kawai in tafi in ba bacin ranshi nake son gani ba ba wanda ya sani haka na shirya na tafi ina mai jin kunya yadda zan tare wa mutane a gida nima da jego na haka. Da zan tafi yasa na dauki turmi daga cikin wanda na samu buki a gidan mu nakai wa mai jego cewan in ji shi nashi gudun mawan ke nan. Na Kai ba wani godiya suka karba a na wani yatsune baki don gaba dayan su ba sona sukeyi ba a gidan don karara ake nuna min bambamci ba boyo. Ina gidan har sati daya don ko bayan da akai suna sai da ya yasa na kara kwanaki a gidan kuma ranan dai da dare yaje ya dauko ni na dawo gida. Na samu dakin yayi kaca kaca kin san yarda daki keyi ida an kwana biyu ba,a cikin sa dole na zage na shiga gyaran dakin kamar yadda ya kamata sai dai sama sama nayi aikin ba ko ina na gyara ba lokacin. Sai waini faman daure fuska Jamil ke min wanda ban gane hakan ba a raina nace ai dole kai bakin ciki da dawowan mu tunda zamu hana ma jin dadin da yakeyi idan bamu nan. Ban bi ta kanshi ba sai da muka cika kwana uku da dawowa ne nace bari dai in gyara dakina da kyau don har lokacin banga ya koma min daidai ba a idona. Na shiga gyara inda na fara da falo ganin na gama da wuri yasa na shiga kuryan dakin don in gyara sharo nan kwakwalo nan har nakai wurin akwatuna na sai kawai naga sun biyo ni alaman dai babu komai a cikin sa ke nan. Ban san lokacin da na yarda tsintsiyan dake hannu na ba na shiga bude akwatunan na sama na bude wanda kayan baby na ke ciki babu komai a cikin sa hatta permpers din ciki an kwashe. Da sauri na jawo wanda kayan nawa ke cikin sa shima dai hakan na samay shi wayau ba komai a cikin sa hannun na dora akai na zurma ihu ni kadai a dakin. Ba wanda ya jini jiki na rawa da makyarkyata na fito falo na zauna ina tunane kala kala idanuwana suka birkici a lokaci guda. Sai wani zufa ke yanko min ta ko ina tunanen duniya na yishi a lokacin yafi a kirga a cikin dan lokaci kada ni kadai a daki ina jin hayaniyar matan gidan daga bangaren su. Sai nake jin dariyan su kamar dani sukeyin shi sun san abin da ya samay ni ne suke rahan su a cikin gida. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: WORLD Zaman mu ya koma lafiya da kowa a gidan sai kuma fitina ya taso tsakanina da Jamil akan yadda nake shiri da yan hayan mu yanzu. Yana fadin wai munafunci ne muke hadawa sai ya tsiri daure wa kowa fuska har ni da nake matar shi a gidan. Wanan karon fita zancem shi nayi ban yarda na dauki maganan shi da wani muhinmanci ba sosai kamar yadda nake dauka a baya. Yau tun safe nake wankin tufafin mu har nasa sai da na gama ke neman dutsen guga in goge kayan da suka bushe dutse yace in nemay sa a inda na aje. Duk dakin sai dana burkuce ina neman dutse ban ganshi ba haka na hakkura na nike kayan na saka a akwati hakana ba guga. Da dare daya dawo nake tambayan shi ko yaga min dutsen gugan mu sai ya hauni da fada wai na bashi ajiyan dutse ne da zan tambaye shi. Dole ina ji ina gani na danne zuciyana akan dutsen don duk mutanen gidan mu na tambaye su sunce basu ganshi ba. Sam a lokacin ban kawo shine ya dauki dutsen ba na dai sa a raina an sace min dutsen ne a dakina haka ba hakkura da zancen dutsen. Haka rayuwa namu ke tafiya a ba wani ci gaban da muke samu daga ko wani bangare namu daga ni har shi sai yan kamay kamay da mukeyi na rayuwa. Yayan shi da suke uba guda ya kara auren wata yar uwan maman shi haka yasa dole jamil yasa mu dinke da yarinyar don dole na kama hurda da ita nabar uwar gidan da muke yan uwa da ita tun a mahaifan mu. Gashi amaryan na bata shekara uku a makaranta don har na kare secondry tana jiniour class a makaranta dana kare secondary dina haka dole nake kiran ta da anty. Wanan ya jawo yan uwan haihuwana sun tasani a gaba da sheri idan ina kiranta da anty ga ba zaman lafiya tsakanin ta da kishiyar ta. Duk wani shawarana yana gurin ta shiko jamil da mijin ta ko yaushe tare suke kus,kus a tsakanin su yan kar kaunar da ban sani ba shine . Ashe Jamil yana zaune da wata matar da zata girmay min ga shekaru zata bani akalla shekara sha ga haihuwa ma,ana dai ta tsofe muna dagani har jamil a gurin haihuwa. Wanan matar ce suke soyayya da Jamil din sosai ashe har ta dauke mai hankali a gurin yawan neman matan da yakeyi a gari. Ya koma kamar wani dan dangana sanda ko mai zaman dadiro da ita a gari mutane sai zunden shi akeyi kan abinda suke aikatawa da wanan matar a cikin gari. Tun ban sani ba har ranan wata makwabciya ta da muke zaman mutunci sosai da ita Jamil din yana hanawa don bai son yaga kowa ya rabeni da sunan mutunci kamar yadda yake ga al,adan mata kowa nada wace nasu yazo daya suna sharing din idea din su na siri tare. Haka ne tsakani na da wanan matar nima tana sona da tsakani da Allah har a zuciyar ta don zamu kai age mate da ita haka zata shigo ta dan zauna a gurina mu yi hira saboda ita mijinta ba mazauni gari bane yana aiki a Abuja ne. Jamil na ganin haka ya fara matsa min shifa baison kwashe kwashen mutane bai son hakana sai dai ban yarda na nuna mata wani abuba ga hakan da yake min din na barshi a tsakanina da shi. Wata rana tazo gidan mu muna zaune muna hira take fadin ita dai zata fada min magana don tsakani da Allah ne take tare dani. Don ko nice naga abinda ke cuta mata tasan ba zanyi shiru ba ga hakan nace kwarai kuwa don ban kawo komai irin haka a raina ba lokacin. Sai ta fara min hannun ka mai sanda tana fadin in kama mijina don ita bata jin dadin yadda take ganina ko wani lokaci a shekarun mu bai dace ace ina zama ba kwalliya ba a gida haka yadda nake. Don mazan yanxu gyara suke so gun mace shike saka har su fita suna hangen wasu a waje da farko maganan nata ya dan soki zuciyana . Nake cewa a raina mai wanan matar take nufi danine wai har itace zata wani koya min in gyara idan wani gyara ne akwai wanda yafi anty iyashine tama raina min da wayau wallahi. Tace taji ana fadin wai mijina yana tare da wata mace mai zaman kanta a garin nan kuma a cikin unguwar nan namu shine take mamaki gashi da yarinya kamata a gida. May zai kai shi gurin irin wa yan nan matan masu zaman kan su yaro dashi a shekarun shi haka, gabana ne ya wani irin faduwa lokacin jin maganan data fada min din. Tace inyi kokari a matsayina na mace nima in gyara kaina in daina zama haka a cikin gida saboda mazajen mu yanzu basu da tabbas. Irin matan nan suna da yawa da suka shigo barki don kawai su ci mazanjen mutane su ba aure zasuyi ba dasu saboda cuta kawai. Ni dai har ta gama maganan ta tana fadin don Allah in boye ta don zancen akeyi a unguwa ta kara da fadin dama ba a cikin unguwa daya bane duk abinda namiji zaiyi dai baka gani ba. Kuma mutanen dake tare dakai ma basu gani ba balle su fadi, dariyan yake kawai nake mata amma ban ganin wuri saboda bacin rai. Sama sama muka karasa hiran mu ta koma gida don ta dora girki wa yaron ta don ita ma haihuwa daya tayi a lokacin. Idona ya rufe rana ko girki ban iya dorawa ba a ranan don bacin rai jiran shi kawai nake ya dawo muyi bala,i dashi kan wanan maganan . Don ranan duk naji ban wani wanan shegen son da nake mashi din nan sosai hakan nan saboda kishi da ke cina a raina. Kamar yasan ina jiran shi sai bai dawo ba har daya da wani abu na dare kafin ya dawo gidan munyi barci da yar diyata a lokacin naci maganan zuciyata har na gaji ni kadai a dakin. Ban samu magana dashi ba sai da asuba da yake ina da magana ranan fitina nane ya tayar damu da asuba inda nake shiga ba nan nake fita ba wurin bala,i dashi. Sai ya hau dan kamay kamay yana fada wai shi bai son shirmay waya fada min haka shi sai yayi karan mai shi don bata mai sunan da akayi. Haka muka kai wani lokaci muna ji dalin dashi kan sai na fada mai wanda yazo min da wanan maganan ko mu samu matsala a tsakanin mu. Har ta gaji ya fita daga gidan yana wani tuku buri a ran shi dani bayan fitan shi ne na dan fito don hada muna abin karyawa duk wanda ya ganni ranan yasan akwai abinda ke damuna a zuciyana. Don yadda na koma saboda masifa da muka sha dashi da safen maman Ahmed dai ce da muke dan dasawa sama sama take tambayana ko lafiya nake. Ban iya boye mata ba ranan sai da na gama magana na take fadin wai ashe naji take fadin maman Amira wa zai fada maki wanan maganan ki kwashe ki fada ma mijin ki mashi. Wanan maganan ai ya dade yana yawo a cikin unguwae nan gaskiya nan dai take kara fada min wani abinda kawata bata fada min ba akan maganan. Hankalina ya kara tashi da jin zancen satin mu biyu muna rikici dashi na dauka ya saduda ne ya daina don naga yayi sanyi sosai yana dawowa da wuri idan ya fita yanzu. Sai dai abinda ban sani ba hakan takone na mayaudaran maza da suka iya mu,amula da matan banza zuwa ga matan su na sunna. Kwanton bauna yayi min sun canza tako da wanan matar don yana ganin mutane sun saka masu ido yanzu. Sabon sallon da ya tsiro min dashi shine zai wuni gida dami da mu da rana a daidai lokacin da matar take fita gurin aiki don ma aikaciyar gwaunati ce ita. Sai ya wuni a gida yana barci sai ya kwantaci bayan la, asar zaiyi wanka ya fice gidan lokacin ta dawo daga wurin aiki ke nan. Ba zai dawo ba sai daya darabi ko biyun dare zai shigo ya kwanta a takure idan nayi magana sai yace min zafine yayi yawa yanzu yasa ya ke rage dare a gurin hiran su. A zatona ya rabu da wanan matar sai da wani watan azumi mijin ma kwabciyar mu yace tazo gurina in san mata attarudu don shi ya manta bai sawo ba. Amma yaga jamil ya sai kayan miya kila ya sayo da attarudun shi ina zaune ina jiran shi ya kawo min kayan miya wanan matar ta shigo. Tana tambaya na nace bai riga da ya iso gida ba a lokacin yau zanga jamil ya dawo gidan da kayan miya shiru har aikai maggariba ya dawo hannu a sake. Nake tambayan shi ina kayan miya shi nake jira ban karasa girki ba sai cewa yayi na bashi ajiyan kudin da zai sawo kayan miya ne ina ganin shi da safe ai haka ya fita gidan ba wani kudi a hamnun shi ko naga yana sana, a ne da zai samo kudi. Nace kayan miyan da aka ganka ka saya fa na waye shi nan ya fara fada wai ya gane dai yanzu ido aka saka mai a unguwar nan haka da yawa to baban shine ya aike shi ya sawo masu daya je gaida su. Jin haka hankalina ya dan kwanta har ina fadin aida ka fada mai baka da kudi muma ko zai sai muna yanzu ga shinkafa na dafa ba miyan da za,a ci kum, yace yanzu sai in san dabara ai. Ashe cefanan da aka ga yayi can gidan Ruth ya nufa dashi suka dafa a cewan ta yanzun ta musulunta tana son ta auri musulmi. Hakana rana muka ci abinci da mai har ya fara ci yace ba zai iya ba kada ya jawo mai ulcer ya sha ruwa ya fita zuwa gidan Ruth din yaci wanda ta dafa masu dashi. Sai dai ban kawo komai ba a raina tunda yace mahaifin shine ya aike shi saya na dauka bai da shine yasa bai sayo muna ba. Ban tsinke ba sai da sallah ya kwaso min gwanjon kaya da ta zauna ta gyara masu dinki dagani har yara ta bashi ya kawo muna wai kayan sallah mu ke nan. Da farko har ina munna na shirya zuwa gaida mutanen gidan mu anty na kallo na naga bacin rai karara a fuskan ta sai wata kanwata take ce min. Ke ko anty harda sallah baku gyara kowa na zuwa acan acan dashi ke sai ki zo muna haka ba dadin gani dake har yar ki don tunda yan kayan yarinyar da anty ta saya muna masu tsada na haihuwa sukayi mata kadan yanzu na koma mata yan kamay kamay. Don ban iya saya mata don banda shi gaba ban dashi baya sai dan abin da ya kawo muna muyi amfani dashi. Raina bace nace wa kanwar tawa wanan da na saka kika raina shine ya saya muna shi na sallahn mu ke nan daya sawo muna. Wanan ai mama ta mutu ne gwanjon lace din lagos aka gyara wani irin bacin rai naji da suke maganan nan dai na rufe ido naci masu mutunci yinin da banyi ba ke nan na fito na koma gida na cike da bacin rai. Tun da na tun karo gaban unguwar mu naga mutane suna kallo na haka na dage kai na wuce ban tsaya gaida kowa ba. Wai ashe sun shige ke nan dashi da ita na biyo gurin shine idon da mutane suka saka muna don gudun kada tsotsayi ya hada mu dasu a hanyan. Ba wanda ya iya fada min hakan sai wata tobashiyan shi data zo muna yawon sallah take tsokana na da fadin yanzu shi kuma mijin ki har lalacewan shi ya kai shi ga bin arna arniyar ma wace ta haifeshi. Har ya fito kerare yabi hanya da ita da uban ranan nan kowa yana kallon su bai ko jin kunyan idon mutane da nauyin su. Wani iri naji a raina yake na kama mata har dai na samu ta wuce bata gaji da zubawa ba raina yanaz bace. Fitan ta na shirya sai gidan da mahaifin shi yake naje da kuka na nakai masu maganan da nake ji a unguwa yana cewa karya da kazafi ake mashi. Sai da mahaifin nasa ya gama saurare na yace min ke kin tabbatar da hakan ko kin gane su da idanuwan ki haka dai yayi min magana ta baibai ta yadda ban gane komai da nake fadan akai. Abinda ban sani ba ashe tsohon yasan da wanan zancen har kayan sallah ta dinka mai da kayan azumi shine rashin kama min da bai yi din ba dana zo da zancen. Sai daga baya duk nake jiyo hakan a wurin mutane sai dai nasa a raina cewa tunda yace naga hakan da idanuna na hake sai na kama su din da idona. In da na na bar zancen a raina ba tare da na shedawa kowa zancen ba na koma normal life dina shima ya dauka na bar wanan zancen ne yaci gaba da harkokin shi kamar yadda yakeyi a baya. Har akai shagalin sallah aka gama ban kara fita ko ina da sunan zuwa unguwa ba ina gidana kumshe sai wanda ya tuna dani yazo gurina dubani a cikin yan uwa. Matsalan dake damun yan uwa na dani shine yarda da wanan zuwaira din danayi hundred pacent a raina don duk shawarana yana gurin ta duk da na girmay ta nisa ba kusa ba kuwa. Don ko sa,an kanwa ta summaiya batayi ba ga haihuwa amma haka muke mu,amula da ita duk shawarana yana gurinta wanda ni ban ganin laifin hakan da mukeyi da ita. Wanda hakan shi Jamil din ya kidanya min yana so dani adole in kirata da anty kuma mu kama mu,amula da juna kamar yan uwa. Ashe ban sani ba kuma yadda muke haka ya dauki wanan farkan tashi yakai gurin su suna mu,amula da ita tana masu abin arziki wanda ni nawa sun gama dashi ko an taru an cinye duka an barni da tunane. A cikin haka baba kabiru ya samo min aiki sure p da aka bude maimakon in bada nomber wayana sai Jamil yace in bada nasa don ni a lokacin banda waya a hannu na dole idan kudin sunzo zasu fada a wurin shi iyakata account dana bude da kaina kawai amma dole sai yaga alert ga wayan shi. Fitowan farko aka bamu na wata uku a jere tunda ya like min sai da aka ga bayan kudin dan abinda zance na tsira dashi shine kawai kudin da ya sai muna abinci dashi na gida naci wanan ne kawai ba zan ratse ban ci ba daga cikin kudin. Yanzu abin da dama sosai a tsakanin mu tunda ina samun yan kudade suna shigo min ta hannu na sai dai duk da hakan sunane don zaice nasa albashi yayi wani lalura dashi nawa zamuyi dan amfanin gida dashi saboda rashin tausayi. Don yasan da zaran ya bata rai hankalina tashi yakeyi sosai sai na bashi ATM ya ciro su za a zauna lafiya tsakanina dashi. Ga ido da yan gidan mu suka saka mi da yawan tambaya may nakeyi da kudina ne basu ga wani canji gurina ba ko a dakina da jikina. Duk da kowa ya san shine may karbe kudin yana min wayau don shikan wallahi yayi kiban shi bulbul dashi ga sutura kamar zai kashe shi na alfara da yake sakawa jikin shi sai kamshi idan yabar guri da zai bar mutane suna shaka. Na koma bagidajiyan dole saboda aure zaka rantse ban taba shiga boko nasan duniya ba idan ka ganni a cikin hakan na samu ciki na biyu a gidan shi. Kanwata ta haihu bayan ta share shekara a dakin ta ba haihuwa anyi shagalin suna lafiya mijin ta yai mata sha tara na arziki duk da naji yan gidan mu suna fadin itama da kudin ta mijin ta yake mata abu sai dai yafi nawa. Don su ana gani a jikin su da dakin su komai nasu acan acan yake ba kamar mu da muke a tauye ba nida yar diyata a gidan mijina. Rufin asirina guda shine aikin da baba ya samo min wanda bai hana inga laifin baba din a idona ba duk wanan abinda yake min duk da shima yana da nasa diyan da ya haifa suna bukatan haka a gare shi kuma. Amma ya rike mu fam yayi watsi da duk abinda mutane ke fadi a gamay dashi ya yi watsi da maganan kowa kan mu ya rungumay mu tsakani da Allah. Sai dai zugin Jamil a kanshi yana aiki a kaina don duk wanan kokarin da yake muna sai jamil din yace wai bai da hali bai taimaka muna don bai bamu kudi . Ko yace wai sun haye muna kudin gadon mu sun barmu muna wahala sun saka muna ido don basu suka haife mu ba idan da badon yana gudu mutane su gane ya cinye muna kudi ba ba abinda zai sa ma ya kula damu. Ire iren wanan maganan da yakeyi tun bai tasiri a zuciyar mu har ya fara nan zamu taru a gidana da yan uwan haihuwana mu kulla mu warware a tsakanin mu. Gashi kamar kudin uban shi ko da mahaifin shi ne ya mutu iya abinda zai iya ke nan a kan kudin mu gashi ban taba jin yana ma mahaifa addu,a ba a gaba na koda na rana daya ne. Karamin mu ne da aka samu kudin nan anty tasa ya sai tabarmi da butoci ya baya a masallatai sadaka mukan ta bimu har ta gaji bamu sai komai mun bada sadaka ba. Ni ina ma naga kudin tunda banda ta cewa alan kudin sai yadda akayi dani dasu yanzun ko ancinye an koma jin haushina. Ni dai ga wautana burina shine a zauna lafiya a tsakani na dashi na dauka yi hakan shine zai kara sa muna yarda da kauna a tsakani mu dashi. Ashe van san ba duka maza ne suka san hakan ba a rayuwan su don ba zance ba za, a rasa wanda keda rikon amana ba sam. Don girman Allah kuyi hakkuri ba laifina bane haka Allah ya tsara ma lamarina wallahi wallahi wutane bamu da har yanzu nakai caji wayata ta samu matsala dole yau sai da na sayi wata still bamu da wuta har yanzu don trasfomer din mune ya buga. 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Na samu wannan kawana dake makwabtan mu tasa mijin ta ya dauko muna manja da garin rogo a can inda yake da zai dawo. Ita nata zata aika dashi ne gidan su a sayar ni kuma tace in saida nawa a nan cikin unguwar mu din tabar min sai idan mun sayar zamu tura mai kudin ya kara sayo muna wani. Alhamdullahi don sana,ar ta karbu min a cikin unguwar tamu da farko da Jamil ya gani ya fara tambaya a ina na samo kudin da na sai wanan abin ? Ban so in fada mai ba amma danaga matsin yai yawa yana tambaya don zargina yake ko na samu wasu kudine naki fada mai don har bugun cikin baffa kanina yayi a waje bai ji komai ba. Dole na fada mai inda na samu kayan ina sayarwa din nan ya hau fada wai yarabani da wanan matar don ta fini wayewa shi bai son rikici da dauko magana. Na dai kyaleshi yayi fadan shi ya gaji ya sa mun ido mutane sai shigowa suke dare da rana suna fadin abasu manja ko gatin kwaki da sugar. Dadi dadi na hada kudin farko don a cikin sati biyu komai ya kare muka tura ya sake turo min da wani don ita ma an sayar mata da nata acan gida da ta kai. Wanan ma yayi saurin karewa da wuri don yanzu mutane sun sanda ina sayarwa kuma a cikin sauki na hada kudin mijin kawata cif da sunan washe gari in kai mata ta tura muna wurin mijin nata. Washe gari tun da safe Jamil ya fita kan zai tafi wani kauye yace min a can zai kwana don haka sai dana gaba duk aikin gida na shirya na nufi inda na aje kudin don in shiga in mika mata. Kudi yace dauke ni inda kika aje sai da na dafe kirji na nakai kasa don capert nake dagawa na aje ba wanda yasan inda nake aje kudi a dakin idan na hada su. Don gudun haka tunda nasan halin shi da kudi ni kadai a daki sai zufa ke karyo min a lokacin don nasan babu wanda zai dauki kudin nan sai Jamil din don ba mai shiga dakina har kurya. Ko baki nayi a falo nake ajesu basu shiga min daki, don kunyan dakin da nake ji ni kaina ban son wata mace yar uwana ta shiga min dakin. Don haka ban zargi kowa ya shigo min daki ba na rasa yadda zanyi a lokacin sai daukan diyana nayi na nufi gidan da mahaifi shi yake. Duk da nasan abu mawuci ne ya goyi bayan dan nasa a lokacin sai banda yadda zanyi dole in je gurin shi da wanan maganan. A gigice na isa gidan muka gaisa dasu sai na fashe da kuka na fara fada masu halin da ake ciki budan bakin mahaifin nashi tun ban karasa ba shine. Kina nufin Jamil ke nan yai maki sata ko wa da kika zo nan din ranan matar mahaifin nashi tayi min abin kwarai don kafin in magana tace . Haba malam idan bata zo nan ba ina kake son taje da wanan abin kunyan kai kullun danka bai laifi itace mai laifi haba a rika yin abu don Allah mana. Yarinyar ga dai tana iya kokarin ta wurin ganin ta kyautata mashi amma hakan bai isa ba sai an hada da dauke na mutane da ta dauko kuma yanzu mai kake son tace ma mai kudin do Allah. Ai sunan danka ne zai baci a unguwar tunda kowa yasa halin shi a gareta ido kawai mutane suka sa masu hakanan. Naji dadin wanan maganan har cikin raina don yau ta fadi alheri a gamay dani bayi son zuciyan da suka saba ba. Fada ya hau yi da ita amma bata barshi ba dole tsohon ya sauko tare da fadin nawa ne kudin na fada mai yana gyaran zama yace sai dai ayi raba daidai kije ki nemi saura ki cika masu kudin su. Ya kirga rabi kamar yadda yace din ya bani na fito ina share hawaye ina zan shiga cikin garin nan in samo rancen kudi in ba mutane kudin su. Ko dana koma yan gidan mu ke fadin matar tazo nema na sai da gaba na ya fadi lokacin haka na daure na shiga gidan ban boye mata komai ba na fada mata halin da nake ciki da kudin na bata rabin da mahaifin shi din ya bani. Na bata hakkuri kan zan nemo sauran in karkare mata in an kwana biyu hakkuri ta bani na fito ina hawaye gidan zuwa gidana. Bai dawo ba sai bayan kwana uku ya dawo in da ya samay ni zaune a cikin tagumi ban ko iya mai sannu da dawowa ba don zakace ba kauye ya fito ba da yace yaje. Shi sai wani fresh yake karawa ni ko ina figewa banda wani kumari a jikina ko kadan daka ganni, kasan damuwa ya samu gurin zama a zuciyana. Ganin yadda na fuske shima ya fuske ya shiga daki ko may yayi a ciki can ya fito yana fadin ke lafiya kuwa mutum ya dawo ko sannu da zuwa ba zaki mai ba. Wani kallo na watsa mashi tare da kawar da kaina daga kallon shi ina fadin azzalumi baiji dadi ba wallahi. Ka rasa wanda zaka yaudara sai matar ka ta gida mai dawainiya da yayan ka duk wani nauyi da hakkin ka ka rataya a kaina . Haka bai ishe kaba sai ka hada da kudin mutune ka kwashe ka tona min asiri a gari. Ya zaro ido yana fadin wa kika mayar barawon ki gida nan nace kai tas ya kwashe ni da mari sai da ba dafe wurin don zafi. Hakan bai sa na fasa magana ba nace ka kashe ni ka huta dama nasan mutuwa ta kake son ji macuci kawai azzalumi. Ba wanda zai shigo ya daukan min kudi dakin nan sai kai ba zan zargi kowa ba wallahi don kaine ka kwashe su . A harzuke yace an kwashe din kiyi abinda zakiyi in zaki iya wawiyar banza kawai kan wasu raggan kudin ki zaki dinga kirana da macuci can kudin da ko mota basu isheni shiga ba. Nace baka nayi da zakace kada in kiraka da macuci ya kara daga hannun zai mare ni na sa mai ihu sai ga yan hanyan gidan a sukwane sun shigo suna tambayan ko lafiya ? Ina kuka na fara fada masu abinda yai min don duk cin kudina da jamil keyi wanan din yafi bata min rai sosai wallahi. Don ya nuna min bai damu ba duk halin da zan shiga da mutane ni na sani ke nan shi ba damuwan shi bane hakan. Bayan sun gama ji ba mai shiga tsakanin miji da mata sai cewa sukayi inyi hakkuri in kyaleshi mu san yadda zamuyi kudin mutane ya fito. Haka suka dinga fita daya bayan daya suka barmu a dakin dagani sai shi ya shiga kuryan daki ya fito yana fadin wawiya da bata san ciwon kanta ba. Da kika fada masu kwatar maki zasuyi ko may ai na dauka zasu sa in biya ki ne dole ina kuka nace Allah dai zai kwatar min hakkina ba wani ba. Mu kai ta yada ma juna bakaken magana har ya gajibya fita daga gidan ya barni nan ina tukukin bakin ciki da na daman auren shi. Sai mutum daya ne cikin yan hayan mu ya iya mai magana kan abinda yakeyi din bai kyauta ba gaskiya kudi mutane ne fa ya dauka kuma ya sani yaya yake son inyi. Don Allah Jamil idan ka samu kudi kaba wanan yarinyar kudin ta don hakan zubar mutunci ne a gurin mace wallahi . Kaga dai duk cikin matan mu tafi kowa hakkuri yau gashi kakai har ta tona maka asiri a bainan jamma,a haka ai irin haka babu dadi. Jamil din yace ta dai tona ma kanta tunda bata da wayau don kawai na dauki kudin ta zatai min wanan tonon asirin haka a idon jamma, a. Mutumin ya sake fadin ai abin ne da cin rai jamil yace malam naga fa kana son shiga hurumin da ba naka ba gaskiya yace a, a niba haka na bane ina dai guje maka hakkin marainiya ne a kan ka. Kada ka manta matar ka marainiyar Allah ce ta gaskiya kowa kuma nan yasa tare kuke cin kudin gadon ta idan ya samu aiko kaga hakan tayi kokari wallahi. Don ba ko wace mace bace yanzu zaka samu haka nan yace kada ka fada min maganan banza Nasir ina ruwan ka ne da zancen mu wai da matana. Basuji dadin juna ba da mutumin nan kowa ya fadawa dan uwan shi bakaken magana ya kulla da wanan mutumin da yake gani wai ya raina mashi wayau shi. Tun wanan lokacin ya sa wana mutumin da matar shi agaba gidan da anyi abu zai fara fadin ba mutumin arziki bane dama ya kamata su tashi su bamu gida. Sai dai wanan karon baiyi nasaran haka ba kaina don ban bashi hadin kai yadda yaso ba yake min a baya kan yan hayan mu. Sannu a hankali na samu na biya kudin bashin da ake bina koshi da taimakon dan abin da nake samu a wurin baba kabiru aboye bai sani ba na biya. Don daya sanin karbe kudin zaiyi ba wani wuyan aiki bane a gurin shi don haka yanzu na fara boye mashi komai nawa nima saboda yanzu na fara fanhintar shi. Don a gaba shi maman jinior zata aiko batun kudin ko tazo da kanta yana ji bai cewa komai idan kuma na mashi magana sai yace idan ta samu zai bayar. Ko hakan da yake fadi don mahaifin shi wanan karon ya fita bayan shi yayi mashi fada sosai har ranshi ya baci shine yake fadin wai zai biya da baki don baida niyar biya din. Tun da yaji baba yace yana nema na yana daki kwance yaron yana fita zubur ya fito daga dakin yana tambaya ko lafiya baba ya aiko yans nema na ? Nace ban san ko may yake nema na dashi ba in dai na gama zanje in ji dalilin kiran yace ki tafi ni zan karasa sauran akin daya rage din. Ban ki nasa ba na gyara jikina na nufi gidan namu inda na samu baba na gida bai fita ba baya mun gaisa ne yake fada min zancen kudin mu ne ya taso bayan long proces da akayi yanzu ranan monday zamu je muyi signing din documents din a Abuja. Wani irin farin ciki ne ya turnuke min zuciya ta idan mai karatu bata manta ba na fada maki kudin an kasa su uku ne kadan kadan suke zuwa muna ke nan. Murna a gurina ba a cewa komai hakama dana koma gida da zumudi Jamil yake tambayana lafiya dai ko ? Ba bata lokaci na labarta mai abindake faruwa ya wani washe baki yana murna tare da fadin wai Allah dai ya jikan baba. Karo na farko danaji yayiwa mahaifina addu,a ke nan ita mahaifiyar mu ba a magana kanta. Nan wuyan talaucin da muka fito ne a ciki yasa yai wanan addua,an haka da bai ma san yazo mashi a baki ba a lokacin. Nan ya fara haba haba dani bai fita yawo sosai sai lokaci lokaci yakan dan fita ya dawo ana jiji dani da yarana lokacin har fita yake da yaran wurin fira kofan gida inda suke taruwa. Yanzu idan mun zauna baida magana sai na tsara yadda za,ayi idan kudi sun shigo hannun mu har da fadin zai fito dani gari don zai sai min babban waya irin na kowa ni da ko nokia banda shi. Sai yan uwa idan sunji haushi rashin wayana ya damay su zasu dan sai min yar nokia in rika bai kai wata daya a hannun na idan matsi ya kama mu in sayar in sai wani abin. Gashi nima bakina yasaba da dadi irin na jamil yanzu ba ko wani abinci nakan iya ci ba in ba yan kayan kwalama ba da sauran su. Ni dai ina jin shi yana ta tsara yadda yake so abin ya kasance wanan karon dariya nakan yi a raina kawai do ko da tsiya sai na gyara dakina wanan karon. Nagaji da rufe kofa da boye boye wa kawayena idan sun zo gidana har kunyar yadda dakina yake nakeji don ko na wata tsohuwa yafi shi dadin kallo. Ranan mondaya shi da kanshi ya rakani gidan baba kabiru tunda asuba don asubanci zamuyi mubar garin don mu isa da wurin during warking ahours. Sai dai bai yarda mutanen gidan mu sun gashi ba yana isa kofa saida yaga na shiga ya koma shi bai shiga ba lokacin. Nasan nasa wayau do kada aga zalaman shi a fili ne yasa ya boye hakan ya labe daga kofan gida yaki shiga daga ciki. Mun isa lafiya mun samu wanan kudin a yadda sukai muna bayani suna da yawa sosai don haka zai fi na farko dana baya yawa ke nan . Murna fal a zuciyana baki har kunne muka dawo gida da farin ciki zuciyar mu fara kal da jin wanan zancen. Na samu ya gyara daki ya dafa abinci ya jera min yana jiran dawowana kamar ance mai da kudin zamu dawo dayani daga zuwan mu. A gidana baba ya sauke ni suka tafi ina shiga na samu yana zaune yana jirana a cikin duhu duk da babu wuta a lokacin amma haka yake zaune kamar maye shi kadai a falon mu. Nan yai muna sannu da zuwa ya karbi goyo na yana tambayan ta ya hanya kamar yarinyar ta iya magana lokacin. Yace bari yai mata wanka don kada gajiyan hanya ya hanata barci shi yai mata wanka ya bata abinci taci ta kwanta tunda dama a gajiye muke. Ya fara tambayana yadda akayi ina labarta mashi yayi wani irin ihun murna tare da fadin kice zamu faso gari ke nan sosai wanan karon. Da yakw dan duniyan namiji ne bai barni na huta ba duk ko da gajiyan dana debo a hanya sai da ya kusanceni ranan . Don kawai ya kara gyara min rai niko ina jin dadi a raina ga miji na tatali na ana sona don sai ka dauka ya daina halinshi ne yanzu na bariki. Tun wanan ranan suka shiga yin meeting dashi da mijin kauwata wai idan kudi sun zo ga yadda zasuyi muna dashi . Zakace abin na Allah ne ake shiryawa lokacin don sunce bazasu yarda su baba kabiru suna muna wayau ba ko wani lokaci duk da fa su baba basu karban ko kwandala daga cikin kason mu din. Amma sun ce wai wayau suke muna kawai don sun dauke mu yara kanana suna yi muna yadda sukaga dama da hakkin mu . Muko mun hau munga ga masoyan mu na asali masu kaunar mu da zuciya daya don Jamil yana cewa. Da ke nan da baisan ciwon kan shi ba suke cinye kudin ba abin kwarai da mukeyi dashi yanzun kan tanadi sosai za a yi muna gaskiya. Fadin haka da yakeyi yasa na kara yarda dashi sosai don na dauka talaucin da muke ciki yasa yanzu yayi hankali ne. Mun dauka wani sati kudin zai fito a yadda aka nuna muna a can da mukaje abuja sai gashi shiru har mako uku ya share ba wani labari kuma na kudin . Nan dai ya shiga kuma sake magana yana fadin kila ma su baba ne da sherin su kudin an sako basu fada muna ba kai ba dai abinda bai fadi kan kudin. Har turani gida yayi in koma in tambayi baba cewa munji shiru baba dai yayi dariya yace hadiza banda abinki ko wancan karon ai haka akayi ko ? Sai lokacin da muka ji su kin san gwaunati ba ayi mata dole tunda ba abin mutum daya bane abu ne na taro kowa dake cikin system din jira yake yi kamar mu. Na dawo gida na fada mai abinda baba yace ya ja tsuki don takaicin da yake ji a lokacin yana fadin wanan shegen gwaunatin basu da tausayi wallahi. Yakan yi maganan kudin nan kusan sau uku ko hudu a wuni shi dai ina ganin lokacin damuwan shi bai wuce yaji ance kudi sun shigo muna ba shine nasa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU. 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Ranan dai ban iya aikata komai ba a gidan ko abinci ban dafa ba duk jikina ya mutu ina jiran shigowan jamil din gidan inji inda kayana suke. Wanda nasaye da hakkina na rufa mai asiri dashi na dawo yanzu ban samay su dakin ba kuma ai dole hankalina ya tashi sosai fiye da tsamani. Kamar yasan ina jiran shi sai ranan kuma bai shigo gida da wuri ba sai can cikin dare sosai ya dawo lokacin har barci ya fara sata na a inda nake zaune a falo. Jin karan bude kofan shi na mike zubur dani yace may ye haka ban bari ya rufe baki ba nace Jamil ina kayana suke don babu komai a cikin akwatunan ga baki daya dana bude. Yace cikin dakewa wasu kaya kuma nace kayan sunana da muka saye yace suna ciki mana ina ruwana da kayan ki tunda muka saya. Nace abar maganan wasa ina kayana suke yace wai bai sani ba yana kokarin shigewa daki na mike da sauri nasha gaban shi ido rufe na kara tambayan shi. Yace wai kina haukane ko may ko kin mai dani barawo ne da zaki tsare ni kina tambayana kayan ki ko kinga ina zama a gidan ne ni ? Hannu na dora a kai na fara zunduma mashi ihu a dakin ina fadin wallahi ban yarda ba don babu wanda zai shigo min daki bai bar alama ba. Ganin zan tayar da mutane gidan yasa yace ki bari zan maki bayani da safe don Allah yana fadin haka ya shige daki ya kwanta abinshi . Haka na kwana ina juyi duk tunane ya hanani barcin kirki washe gari ma da wuri na tashi don kada barci ya dauke ni ya gudu. Ina cikin aiki ya fito na bar abinda nakeyi nace Jamil ina sauraren ka yayi kamar bai jini ba yana kokarin ficewa dakin. Nayi sauylrin tarewa ina fadin wallahi ba inda zaka sai ka fada min ko inyi karan ka ya wani juyowa yana fadin ni zakiyi kara akan kayan ki hadiza ? Nace wallahi kuwa idan baka fada min inda kakai min kayana ba yau a gidan nan ganin da gaske nakeyi yasa shi fadin suna wurin dinki. Cikin zaro ido nace duka kake nufin kakai dinki turmi talatin da wani abu , yace bake kika ce a dinka ba shiyasa na kai dinki duka. Wani wawan ajiyan zuciya na sauke ina fadi yanzun naji magana dai sai dai har yanzu zuciyana bai yarda cewa duka kakai din ki ba gaskiya. Yace yanzu dai na gane abin hannun ki ya fara rufe maki ido da har kike son tayar min da hankali akan zanuwan banza naki ki jawo min mutane. Nace ai dole don kudin nan kaima kasan ban ci komai a cikin su ba don may ko ba zan tayar da hankalina ba akan su. Kowa ya sai abin kwarai da kudin shi sai nice zan banzatar da kudina a sakani a baki gashi dama mutane na fadin nice banda arziki cikin mu da an bani kudi ka cinye. Yace inji uban wa ke fadin haka ya wani gayayyako ni yana fadan karya har ya samu ya fice daga gidan dama abinda yake so ke nan ya samu hanya ya sulale ya fice. Ashe shi wayau shi daya kwashe kayan ace sata aka shigo akai min da bana nan shine hikima shi na turani gidan su in yi kwanaki acan. Sai kuma wani abinda ban sani ba mai ban mamaki da daure kai da lamarin Jamil shine ashe wai hayan kaya nan sukayo dashi da Ruth a shago. Sukayi alkawarin zai dawo masu dashi da zaran an gama suna danawa da na baby din ga baki daya har akwatinan gaba daya na hayane. To ina yakai min kudin da ya karbe a hannu na din daya karba wanda yasa na sayar da filin mu a wani gari daya matsa muna sai da muka sayar. Duk abinda nakeyi yin shi kawai nakeyi hankalina bai kwanta da zancen kayan ba don tun ranan da mukai maganan ya shiga wani tsare gida yana daure fuskan shi gare ni. Kyale shi nayi sau da aka cika sati biyu na kara tuntubanshi kan zancen dinki yace yaji kawai ya fita bayan kwana biyu mm a sake tambayan shi kuma. Ranan dai fada mukayi dashi sosai kan kayan inda nasha kuka na sosai don na fahinci babu dai kayan kwana kwana kawai yake min kan kayan. Washe gari tun da safe na shirya sai gidan mu gurin iyayyena inda na samu dama irin ranan da suke jira gare ni ke nan yazo. Sai da suka gama saurare na suka dora a inda na tsaya baba bai gida a lokacin sai da ya dawo ne anty ke fada mashi ina nan na zo gida mun samu rikici da Jamil. Yasa a kirani nazo ina kuka nake fada mai komai har na gama murmushi baba yayi tare da fadin ni dama ban shirya ma zuwan irin ranan nan bane a rayuwana. Ko ban san wanda na nace sai na aura din bane wai dama sin san abinda zai je ya dawo ke nan sai dai a lokacin da suke kokarin nuna min hakan ganin su nake a matsayin makiyana a gare ni. Ina kuka nace baba nayi nadaman auren Jamil a rayuwana don ya gama dani gaba daya a rayuwana wallahi. Baba yace hakuri zanyi in koma don ga zuria a tsakanin mu yanzu sai dai in koma inyi hakuri da halin mijina don su ba zasu taba kashe min aure ba in dawo ina kuka dasu daga baya. Naji haushin wanan maganan na baba gaskiya sai nake ganin don mahaifan mu basu da rai ne sukai min hakan. Kwanana uku a gida kafin Jamil yazo da yannan shi maza inda suja samu baba ya aika a kirani da su anty muka samay su a falon shi. Baba ya bukaci in fadi magana na nan dai na shiga jero magana yan uwan shi sai assha suke fadi tare da fadin su basu san komai ba a kan wanan abinda na fadi jamil din yana min. Ranan dai ya jishi ba dadi do a gurin yaso yai ma anty da ta zake tana kokarin kwatar min incina a gurin shi don shi baba yana sakaya wani abu don shima nashi ne. Nan dai anty tayi mashi tas ta zage shi sosai saida ya raina kan shi sosai a lokacin suka dai ba da hakkuri tace zai karbo dinkin idan tellan daya kaiwa ya dawo. Aka ba da hakkuri ban koma ranan ba sai washe gari inda anty ta saka ai min kitson kaina da kumshi ta bani kaya masu yawa . Irin su zanuwan gada da kayan aiki da tufafi masu yawa da dare suka mayar dani dakina mun samu bai gidan har suka tafi bai dawo ba. Sai dare can ya dawo bai kwanta ba yai min dadin bakin shi daya iya yana fadin ya dauka ni mai rufa mai asiri ne ba zanje gidan mu da wanan maganan ba. Lokacin ne yake ban hakkuri kan kayan nan dai babu su inyi hakkuri idan ya samu hali zai saya min wasu da yardan Allah ya kare cikin dadin baki da bani hakkuri. Haka na hakkura na shanye zancen kayan a raina na dogara ga dan albashin dake zuwa min wanda yanzu munyi wata uku ba a bamu ko sisi ba na aikin mu. Haka nake ta faman kama kama ina juya rayuwa a yadda yazo mi din sai daga baya nake jin gaskiyan maganan a makwabtan mu . Wurin wanan kawar tawa take fada min yadda zancen yake inda take fada min itama a gidan da taje kitso don kawar matar ce bata san suna tare ba take bata labari na. Inda take fadin maza suna cuta wallahi don abinda akai min din ko da bata sanni ba na bata tausayi sosai raina naji ya baci sosai kafin ta gama bani labarin a gidan ta. Inda nayi mata sallama na fito ban zamay ko don ko gida ban shiga ba sai gidan da mahaifin shi yake na samay su da kuka ina fada masu abinda naji a gari dan su yayi min don ni yanzu kunyan in koma gida da wanan maganan nakeji. Budan bakin mahaifin nasa sai fafin yayi ina da aiki idan zanyi amfani da jita jita a rayuwana su masu fadin haka kyashine da hassadan dan shi yasa suke kulla mai sheri. Don kawai su bata wa dan baidai goyi bayana ta ko ina na fito sai ya tare dan nasa ya kare shi haka na taso da bacin raina na dawo gida naci kuka na ba wanda zan fada ma wanan zancen na takaici ya saurare ni. Haka ya dawo gida ya samay ni yana wani cika yana batsewa don ma kada inga fuskan yi mai magana ban kula yadda ya dawo min ba. Na shiga fada mai duk wani kalma daya zo min a baki akan indan har maganan dabaji gaskiya ne na roki Allah ya dubi maraicina ya saka min a gare shi shi da Ruth da duk wani wanda ke da hannu a cikin cutana din da sukayi. Ruth kan itama bai barta ba don tatsanta yake sosai yayi mata alkawarin zai aure ta idan ta musulunta duk da kusan haihuwan shi da tayi . Amma haka munafukin yayi mata alkawarin aure a tsakanin su take bude mai bakin aljihun ta yake shagali shi dashi don iya yaudaran shi da karyan shi. Da farko yaje gun Ruth ne ya tatsi banza ya gudu sai ya hadu da yar duniya dama tana neman wanda zata kama sai ta daure shi har kafa baida daman dogon motsi ya gudu gareta. Don ta dade da asirice shi yaje cin banza banza ta ciyo shi ga masifana a gida da nake aza mai tunda nasan bai rabu da ruth din ba na sashi gaba da fitina. Har ya fito fili ya nuna min ban isa in rabashi da ita ba wallahi haka muke zaune bani na samu kaina ba dashi sai da kudin da muke bin gwaunati ya fito na wata hudu sannan ya nemi shiri dani don yaci kudina. Ya ko ci don nan ya kawo min kabali da ba,di bamu da kaza ya kamata mu sai kaza na amfanin mu shi nashi bana lalurar gida bane sai nawa idan sun zo ake sakawa a gaba a cinye anga banza. Niko ban gane shi ba har yanzu ina dauka sona yake tsakani da Allah sai nake sakar mashi komai idan yai min dadin bakin su na maza. Na ramay na lalace ni ragga diyana ragga duk mun bi mun kanjamay don wahala gashi dan aikin da nake kuri dashi an dakatar da yin shi yanzu. Sai abin ya taru yai min yawa sosai a kaina dole naje gida wurin anty don ta taimaka min tasa baki ga kanne na su bani dan wani abu in sai ko kura na ruwa dan kwabo ya dinga shigo min. Da kyat da boni anty ta yarda zata sa mun baki gare su duk ko da tasan abune mai wuya a banbare su kudin da nake so. Amma haka ta daure zatayi masu magana idan sun shigo shikan baffa tana tun karan shi da zancen yace ba zai bayar ba. Sai dan karamin mu ne da anty ta titsiye yace zai bani dubu goma tace bai yi ba don Allah su tausaya min idan basu koyi bani ba yanzu yaushe zasu koya. Haka dai har ta ciwo kanshi yace zai bani sha biyar lokacin daidai kudin baron ke nan nayi ta murna da ta fada min. Inda ta zaunar da kanne na tayi masu nasiha sosai mai ratsa jiki duniya ke nan wace Jamil ya cusa muna ra,ayi mu guje ta itace kuma yau na komawa ta taimake ni. Ba tare da tayi duban baya ba ga komai ta tausaya wa hali da nake ciki tasa ai min wani abu a tallafa ma rayuwana don Allah. Baron ruwan da na saye baiyi wani tasiri ba duka duka baifi wata ba na kadar dashi na fara sana,an kayan mata da dan kudin. Wai ni a gani na zaifi sana,an ruwa kawo min kudi a cikin lokaci kwana biyu muka turmushe kudin babu ko labarin su kuma. A cikin haka ne su maman Ahmed yan hayan gidan mu suka tashi don zaman mu yaki dadi dasu ga matsin jamil akan shi fa sai dai su bar muna gida. Do sune ke zugani ina wani abin don shi bai kaunar yaga nayi wayau a rayuwan shi yafi son ya gannin ko yaushe kamar wawiya yana juyani yadda yake so. Tashin su ba a dade ba aka sa wata amarya a dakin da suka tashi ciki amaryan matar abokin Jamil ne yasa muke kuma dan shiri da ita. Wanda hakan yasa na dan samu sauki wasu abubuwa a gidan yanzu don yana ganin yadda abokin nasa ke kula da matar shi. Sai dai abinda ba halin mutum ba bai iyayin kamar kowa don bai saba yin hakan ba tun farko ina dai zama zamana hakkuri dashi. Shiko yana holewar shi waje da matan banza yau ma kamar kullun na tashi babu ko sisi a hannuna ga yara na har sun fara min kukan yunwa. Na rasa yadda zanyi dasu a daki can dai dabara ya fado min wanka nayiwa yaran babu ko sabulu na shirya su muka nufi gidan mu dasu. Bayan mun gaisa ake tambayana inda na fito da sanyin safiyan nan nake cewa gida ganin yanayi na baisa sun matsa da dogon bincike a kaina ba sai abin karyawa aka gabatar min dashi. Na dan tsaya basarwa mama ta matsamin akan in dai karya din don ban samu anty a gida ba lokacin tana gurin aiki sai mama ne a gida kawai. Nan dai na fara labarta mata halin da muke ciki a gidan ina kuka tace in daina kuka nawa kaddaran auren ke nan yazo min a haka. Hadiza kina da hankali da ilimin ki zaki zauna kullun miji yana cutan ki kin kasa wayau ki fahinci abinda yake nufi dake. Fada sossi mama tayi min ban iya magana ba sai kukan da nakeyi har barci ya daukeni a gurin ban koma gida ba anan naci na safe dana rana har anty ta dawo daga aiki ta samay ni a gidan. Kallo daya taimin ta gane halin da nake ciki bayan ta idar da sallah la,asar ta fito ta samay mu nan dai ta shiga min nasiha inda duk laifin a kaina ta dora inda ta kare da fadin idan naga dama in koma in kara bashi kudin don yanzu ba abinda ma yarage ai. Na samu ta hada min abubuwa na koma gids na girka muna abinda zamuci da dare dani da yaya na sai gashi ya shigo dauke da dan leda a hannun shi. Lemon sha ne ya zauna ya bare ya min mikawa yayan shi bari ya shiga shan abinci sai da ya gama yayi gyatsa yana kaiwa kwance saman kujera ya mimike sallah na idar idar na jawo kullan abinci ina zubawa don in ci yace ina kika samu abinda kikai abinci ? Ban saurare shi ba saboda haushin shi da nakd ji a raina yaya nami zai fita tun safe bai damu da yasan iyalin shi sunci ko basu ci ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Kamar yadda Jamil ya damu da isowan kudina haka mijin yar uwata ya damu da zuwan su shima sai dai bai yarda ya nuna zalaman shi a fili ba kamar yadda nawa mijin ya nuna . Don ya fishi shekaru da ilimi da ma wayewa sosai don ni nawa mijin iya secondary ya tsaya shiko wanan har masters yayi a karatun boko. Wasa wasa har aka share wata uku ba labarin kudin sai abubuwa suka fara canzawa ga matsi da yai muna yawa na talauci . Mahaifin Jamil har gida yazo ya saka min magana wai sunji rigi rigi sakwat mana ance ga kudinan tafe sunji shiru kuma. Nace baba lokacin zuwan su ne baiyi ba tukun aida sun sunzo abinda bana mutum daya ba ai sai hakkuri kamar yadda kowa yayi. Allah karimun rahimun a ckin wata na hudu sai ga kiran baba wai kudi sun sauka muna a cikin dare ya kirani yana fada min haba kamar in jawo safiya a ranan. Don lokacin Jamil baya gari na kirashi ina fada mai ya yanka wani ihu a waya yana jin dadi kamar wanda ya biyo dare sai gashi koda goma tayi yana cikin garin. Ina tsaka ga gyara gida ya iso ina yana shiga daki yake fadin to yaya an raba ne nace har yanzu baba bai kirani ba yace kaji ko ? Kin ga halin yaudara ko in ba haka ba kudi sun zo araba aba kowa nasa mana an tsaya jan rai sallon ayi yaudara da aka saba kuma. Kallon shi nake da manaki yadda ya hakikance yana fada kan kudin da baida kaso a ciki koda yake shine mai kason nawa wanan zuzudin da yakeyi haka. Misalin sha daya ya kasa hakuri yana kwance a daki ya kwala min kira na amsa na shigo yake fadin kije gidan nan kiga abinda ake da idon ki zaifi gaskiya. Ke ma banda abinki an kiraki tun cikin dare an fada maki ba sai kiyi sakkon zuwa gidan ba amma kin tsaya kina shininiki irin wanda kika iya. Ba abu mai wuya bane gare su su rage yawan kudin kuma nace a a gaskiya yaya za a rage yawan su abinda ke rubuce. Sai fa baba yaba kowa waya munga yawan kudin ake fara rabawa yace ke dan Allah ja can ke may kika sani don Allah. Haka ya matsa min dole na shirya na tafi gida naje na samu baba baya gida lokacin don haka na tsaya jiran shi har ya dawo ban raba dayan biyu tunda na tambayi kani Baffa akace sun fita da baba nasan banki sukaje tare cire kudin. Komai na baba yana kokarin yaga ya fitar muna da hakkin mu amma huduban su Jamil yasa bamu ganin hakan da yake muna sai ma ganin laifin shi idan kudi sunzo da muke yi. Nan na zauna ranan ba ko sakin fuska suma yan gidan sai suka share ni suna harkokin su kamar ban gidan. Nakai kusan awa daya sai gasu sun baba sun dawo duk yayi zufa zufa dashi daya shigo, shima kani ya wani daure fuska a lokacin sai da gabana ya fadi na dauka ba kudin ne da sukaje banki ko kuma wani abin ya faru. Ashe tsare gidane na irin kada aga walenshi ai muna rainin wayau kamar yadda aka tsara mashi din yayi. Daga inda nake zaune naji hayaniyar su baba musa sun shigo ana bude masu falo ta baya na sauke ajiyan zuciya nasan kudi sun samu ke nan tunda suka zo. Araina nake zagin su ina fadin ko kunya basu ji da angansu an san abinda suka zo amsa ke nan wai suce suna cin gadon mahaifiyar su. Kanwata ta shigo da yar diyar ta suna gaisawa da mutanen gidan mu ana wasa da dariya da kowa sai lokacin naga wautana na gimtse masu danayi da farko. Nan naso saka baki sai wata kanwata diyan baba kabiru mara kunya tace a, a anty hadiza ke da kika shigo kina daure fuska yanzu zaki ce zaki mana magana kuma. In dai kudine karewa zasuyi mu zama daya kwana nawa ne ance ma mara mata gwauro raina ya baci sosai da maganan ta. Ina ganin tun kudin basu shiga hannuna ba tayi min baki aiko nan na hau bakina da fada da ita sai inda na tsaya jin muryana da baba yaji ya kirani tana fadin ashe ma na zo don da ya shigo bai lura dani ba. Nan muka mike muka nufi falo muka samay su kamar kullun baba musa ya bude da addua sai baba kabiru ya dora bayani kamar kullun tare da miko muna wqyan shi yana fadin. Ga sakon saukan su nan ga fitarwa yana miko muna wayan ga wautana har zan karbi wayan sai kanina baffa yace ai tare mukaje baba ba sai sun karbi wayan ka ba aci gaba dai kawai. Nan aka fitar da na mahaifiyar su sai aka fara kasafin namu kuma akayi lafiya aka kare kowa ya kama gaban shi don ko minti ashirin bamu kara a cikin gidan ba muka wuce. Gidana muka yadda zango kamar yadda muka saba yi idan mun fito wurin su baba din nan muka shiga kullawa da warwarewa a tsakanin mu. Muka gama shaci fadin mu da komai aka shiga kasafin abinda kowa zaiyi shidai karamin mu wanan karon ma cewa yayi duk yadda mukayi ya fita ya barmu nan. Kamar hadin baki sai ga Jamil da adam sun shigo gidan a tare da Ahmed mijin kanwata sai wani washe baki sukeyi. Nan mukai masu bayanin komai tare da fada masu yawan kudin da kowa ya samu da wanda aka fitar kason hajiya umma. Ahmed din yace yanzu abinda za ayi a cire kudi da zai isa kowa sayen uncomplet building a samu a saya kada kudin su lalace muna. Saura sai muyi lalurar mu dashi shawaran shi anyi na,am dashi sosai already dama ashe sun yanke hakan har sun cigiya muna ko an samu boyewa dai sukai muna kan hakan . Sukai muna sallama suka tafi haba shiko gogan nawa kamar jira yake su fita cikin tsare gida yace ina kudin naki nace suna ciki na boye. Ganin yana kallo na nasan abinda yake nufi yasa na mike na shiga na dauko mashi kudin na kawo mai ya karba yana juyawa tare da tambayan na tabbatar kudin sun kai yadda akace ? Nace sun kai mana ko a na gida sai da baffa ya sake kirga min yawan su yace to may kike ganin za a saye dasu yanzu in an cire wanda za a sai gidan da ba a kammala ba. Don dai data nice sai in ce kada asai wanan gina ki fara juya kudin har suyi tsoka daidai sayen gida ginane kinga sai ki zuba yan haya a ciki ko may kika gani ? Ya tambaye ni yana tsure ni da manyan idanuwan shi nace ni dai ayi yadda yan uwana sukace kada ya zamo na fita daban a cikin su bayan mun shirya yin hakan da su. Tun da yamman nan ya ware wasu kudi wai zai sayo abinci ya fita ban ganshi ba har dare ya dawo min babu kayan abincin wai sai gobe idan ya fita zai karbo. Washe gari ko sai ga kanwata da mijin ta sunzo sunce an samu kangon gida jamil da baffa suzo suje su gani idan yayi masu. Sun je sun duba kangaye nada dama sosai don gina da aka fara sun tasa sosai kuwa sukace sunyi masu sai Jamil ne yaso kawo rikici wai kangon yayi tsada ga yadda akace kudin shi. Nan dai Ahmed ya kara fahitar dashi har ya yarda a saye din aka saye bado yaso haka a ranshi ba ba dai yadda zaiyi ne. Bayan sun dawo sukai muna bayani har sauran kudi sun rage tun nan a gaban su muka fada masu shawaran da muka yake kan zamu gyara dakunan nmu ne. Jamil bai so haka ba yana ganin an takura mai da yawa mijin summaiya yace zai tambaya muna set din kujeru masu kyau mu saya zuwa gobe. An ko samu kijerun shi Jamil ya kawo shawara wai a na saka ties a falo na don shima kunyan azo aga dakin babu ledan kwarai yakeyi. Shawaran shi ya karbu a waje na da tan uwana sukace tunda zanyi gyara ya kamata a sa ties din a falon sai a bar dakin . Kamar wata amarya haka dakina ya koma ga ties ga tv plastma harda tauraron dan adam da fridge sabo ga su center kafet an saka a dakin. Duk da jamil yayi na kasa wurin sa ties di dakin ya kara kudi ga abubuwa da dama sosai amma haka aka gyara dakin . Duk ko da na bashi nasa kaso daga cikin kudin sai dai kuma bai hana shi yin na kasan ba a cikin dan abinda ya rage min din. Labarin baba kabir kuwa tunda ya bamu hakkin mu bai kara bi ta kan mu nasan don tsage rancin da muka nuna masu ne lokacin rabon kudin da Baffa yace wai dole ne sai an cire na mahaifiyar su . Sai kuma wanda baba ke bi a ciki na fafitikan neman muna kudin ya fito da yake kai cin hanci da sauran su wurin duk wanda ya dace ayiwa. Kuma gashi mun sani baiyi shi kadai sai da sanin mu idan za a yi don ko an lalubu mu kudin bamu dashi balle mu bayar din. Dole haka aka fitar mai da abin shi duk da ma bai cire na jigilan shi ba yace ya yafe muna su amma duk da haka sai da dan hakin shi ya tsone muna ido. Kada kukaga laifina masu karatu gama in kun tuna na fada maku sai da suka raba mu da kowa namu sai su mazajen namu da kannen mu biyu kawai muke shawaran mu. Do haka komai sukace sai muga ai sunyi daidai ba ba mu ganin rashin dacewan hakan a gare mu tunda yanzu su zama muna uwa da uban mu a yadda suke fadi ko yaushe. Don haka muka dauke su da zuciya daya ban ko tuna saura saki daya fa tsakani na da Jamil din duk da dai ban fadi a gidan mu ba kowa ya sani. Dakina yanzu har zuwa kallo akeyi koda yaushe tv na aiki a falon yan diyana suna zaune suna kallo basu zuwa dakin kowa na gidan da sunan kallo. Yanzu zamzam muke da Jamil baison ko kuda ya tabani ko diyana a gidan sai dai ban sani ba ashe har lokacin suna tare da Ruth farkan shi. Ba wanda zai iya fada min don ban iya boye mutum wurin magana shiyasa kowa ke tsoron fada min gaskiya koda an gani sai a kyale ni gashi wanan kawar tawa sun tashi tabi mijin ta can kasa ibo inda yake. Don da tana nan data fada min idan ta san da hakan ba zata boye min ba kamar yadda mutane suke boye min yanzu. Duk da na gyara daki yanzu tsiyan daya tsiro min shine sai yace bai iya kwanciya a dakin wai zafi yayi yawa a daki waje shi zai fita ya kwanta. Ashe in ya fita ya rufo mu ta baya wai kada barayi su shigo muna sai ya wuce gidan Ruth ya kwana sai asuba zai dawo gida idan yaga gari ya waye. Duk ban san wanan ba na dai dauka yawan jin zafin shi ne yasa bai iya kwana a cikin gida ashe munafuki dawata manufa yake min hakan. Ranan ko da na fito da dare sauro ya damay mu sai ban gashi ba wurin da yace yana kwanci din abin ya ban mamaki sosai a raina. Da safe daya shigo nake tambayan shi ina ya kwana an dauke wuta bamu da maganin sauro na fito da dare ban ganshi ba. Yace cikin dakewa ai wajen gida ya fita inda samarin unguwa ke kwanci da dare can yake kwana tare dasu sai ban kawo komai a raina ba danaji ya fadi hakan. Ranan ina zaune na gama girki da rana sai ga matan yayan shi din nan sun shigo gurina na tare su tare da basu ruwa da abincin dana gama. Sunci sun sha nake tambaya su ina suka fito suke ce min sun fito duba watace a cikin unguwan nan sai ban mai da hankali in san ko wacece suka zo gani ba . Wai ashe guri Ruth suka zo duba bata da lafiya sai bayan kwana biyu nake ji a gurin wata yar unguwan mu wai ta gansu ranan sunzo gaida Ruth tayi fama da zazzabi. Abin ya matukar bata mi rai naga yadda muke dasu wai ace sun zo duba farka miji na kuma gashi banda gidan zuwa sai nasu idan na tashi fita unguwa. Ban kyale su ba har gidan su na samay su suna faman yi min rantse rantse wai ba can suka fito ba ban wani tsaya ba na dawo gida. Wanan abin sai da ya hadamu fada da jamil yake cewa wai bakin kishi zai kashe ni idan banyi hankali ba nan dai muka kwasa dashi ranan sosai. Sai banda wani damuwa yanzu sosai don ban gama turmuje yan kudaden dake hannu na ba lokacin don haka yake bina a sannu. Mijin yar uwana ya samu aiki koyarwa a university da ke kano don haka ya tafi ya barta a nan inda take dan zuwa wurina tana debe min kewa a gidana. Nan take fadin ba zata yarda ya barta a garin mu ba bin shi zatayi idan ya samu wuri banga laifin ta ba, da take fadin hakan lokacin don zaman mace kusa da miji yafi. Sai dai ida bata samu anje da ita din ba tayi hakkuri zuwan shi biyu yana komawa inda suke daukan rikici dashi. Har dai ya yarda zai tafi da ita bayan iyayyen sun sa baki a cikin maganan nan ta fara shiri sai dai bamu fada a gida ba duk shirin da takeyi sai daga baya muka je tare muka fada masu batun tafiyan nata. Sun yi murna da farin ciki sosai don sam babu bakin ciki ga alamarin su damu sai nuna kulawa da kauna a gare mu. Wanan abin wani lokaci yana samu jin kunya har da muka fito muke maganan nan dai take fada min wallahi inbi yan uwa in daina bin zancen Jamil da yan uwanshi. Sosai taimin magana a cikin natsuwa yadda zan fahince ta na kuma fahinta da abinda take nufi don banyi sanyi a gwiwa ba na fara zuwa kai da kai ina ziyaran su. Tun kan Summaiya ta bar garin sai dai wani abu daya bata muna lamarin shine ita kanta summaiya tayi abinda har ni ya bata min rai da ita sosai. Don kaya dakin ta gaba daya har kujerun da muka canza ta sayar ba tare da ta fadi a gida ba bayan munce gyara muke son yi a gurin baba kabiru da iyalan shi. Don sun muna komai da akeyi a duniya nan gaskiya wanan abin da tayi ya bata ran mutanen gidan baba kabiru din sosai don ta fifita uwar mijin ta gare su. Kayan dakin nata ma karshe akace uwar mijin nata ke amfani dashi kin san abu ga mai kishiyoyi su suka kwarmata ma gidan mu wanan zancen. Ba yadda zasuyi damu dole sukai hakkuri suka bar zancen duk ko da ransu ya baci ga hakan da tayi masu din don sun fahinci dai bamu dauke su a maysayi iyayyen mu ba. Mun fi fifita mazan mu a kan su dole kowa yanzu ya kawo ido yasa muna aga iya gudun mu da mazajen namu da muka dauka uwa uba a gare mu. Sai bayan wucewan su magana ya fara tashi wai da kudin ta mijin ta ya nemi aikun daya samu wai wanan kangon da muka saye babu nata a halin yanzu. Waya na nema na kirata na fara mata korafi sai bata bari nakai ayya ba ta hau fada tana fadin wai ni a ina naji wana zancen wanan magana ba gaskiya bane duk wanda ya fada mun kuwa. Haka dai magana ke faman yawo kan mazajen mu sun cinye muna kudaden mu duk wanan maganan da ake fada baba kabiru baice damu kala ba kan zancen mazajen namu. Kuma ya hana iyali shi suyi muna magana don haka ne zancen bai daga sosai ba yadda wasu suka so cikin dangi a dauki mataki akan mu. Yakan ce kubar yaran nan inda kuka gansu idan masara taji wuta da kanta zatai kara ai ba sai an tambaye su ba duniyace. Don yanzu ana magana zasu ce kuna son ku kashe masu aure ne don baku kuka haifesu ba sai yan uwa suce kwarai kuwa Alhaji kabiru. ZAINAB IDRIS MAKAWA 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Kamar yadda Jamil ya damu da isowan kudina haka mijin yar uwata ya damu da zuwan su shima sai dai bai yarda ya nuna zalaman shi a fili ba kamar yadda nawa mijin ya nuna . Don ya fishi shekaru da ilimi da ma wayewa sosai don ni nawa mijin iya secondary ya tsaya shiko wanan har masters yayi a karatun boko. Wasa wasa har aka share wata uku ba labarin kudin sai abubuwa suka fara canzawa ga matsi da yai muna yawa na talauci . Mahaifin Jamil har gida yazo ya saka min magana wai sunji rigi rigi sakwat mana ance ga kudinan tafe sunji shiru kuma. Nace baba lokacin zuwan su ne baiyi ba tukun aida sun sunzo abinda bana mutum daya ba ai sai hakkuri kamar yadda kowa yayi. Allah karimun rahimun a ckin wata na hudu sai ga kiran baba wai kudi sun sauka muna a cikin dare ya kirani yana fada min haba kamar in jawo safiya a ranan. Don lokacin Jamil baya gari na kirashi ina fada mai ya yanka wani ihu a waya yana jin dadi kamar wanda ya biyo dare sai gashi koda goma tayi yana cikin garin. Ina tsaka ga gyara gida ya iso ina yana shiga daki yake fadin to yaya an raba ne nace har yanzu baba bai kirani ba yace kaji ko ? Kin ga halin yaudara ko in ba haka ba kudi sun zo araba aba kowa nasa mana an tsaya jan rai sallon ayi yaudara da aka saba kuma. Kallon shi nake da manaki yadda ya hakikance yana fada kan kudin da baida kaso a ciki koda yake shine mai kason nawa wanan zuzudin da yakeyi haka. Misalin sha daya ya kasa hakuri yana kwance a daki ya kwala min kira na amsa na shigo yake fadin kije gidan nan kiga abinda ake da idon ki zaifi gaskiya. Ke ma banda abinki an kiraki tun cikin dare an fada maki ba sai kiyi sakkon zuwa gidan ba amma kin tsaya kina shininiki irin wanda kika iya. Ba abu mai wuya bane gare su su rage yawan kudin kuma nace a a gaskiya yaya za a rage yawan su abinda ke rubuce. Sai fa baba yaba kowa waya munga yawan kudin ake fara rabawa yace ke dan Allah ja can ke may kika sani don Allah. Haka ya matsa min dole na shirya na tafi gida naje na samu baba baya gida lokacin don haka na tsaya jiran shi har ya dawo ban raba dayan biyu tunda na tambayi kani Baffa akace sun fita da baba nasan banki sukaje tare cire kudin. Komai na baba yana kokarin yaga ya fitar muna da hakkin mu amma huduban su Jamil yasa bamu ganin hakan da yake muna sai ma ganin laifin shi idan kudi sunzo da muke yi. Nan na zauna ranan ba ko sakin fuska suma yan gidan sai suka share ni suna harkokin su kamar ban gidan. Nakai kusan awa daya sai gasu sun baba sun dawo duk yayi zufa zufa dashi daya shigo, shima kani ya wani daure fuska a lokacin sai da gabana ya fadi na dauka ba kudin ne da sukaje banki ko kuma wani abin ya faru. Ashe tsare gidane na irin kada aga walenshi ai muna rainin wayau kamar yadda aka tsara mashi din yayi. Daga inda nake zaune naji hayaniyar su baba musa sun shigo ana bude masu falo ta baya na sauke ajiyan zuciya nasan kudi sun samu ke nan tunda suka zo. Araina nake zagin su ina fadin ko kunya basu ji da angansu an san abinda suka zo amsa ke nan wai suce suna cin gadon mahaifiyar su. Kanwata ta shigo da yar diyar ta suna gaisawa da mutanen gidan mu ana wasa da dariya da kowa sai lokacin naga wautana na gimtse masu danayi da farko. Nan naso saka baki sai wata kanwata diyan baba kabiru mara kunya tace a, a anty hadiza ke da kika shigo kina daure fuska yanzu zaki ce zaki mana magana kuma. In dai kudine karewa zasuyi mu zama daya kwana nawa ne ance ma mara mata gwauro raina ya baci sosai da maganan ta. Ina ganin tun kudin basu shiga hannuna ba tayi min baki aiko nan na hau bakina da fada da ita sai inda na tsaya jin muryana da baba yaji ya kirani tana fadin ashe ma na zo don da ya shigo bai lura dani ba. Nan muka mike muka nufi falo muka samay su kamar kullun baba musa ya bude da addua sai baba kabiru ya dora bayani kamar kullun tare da miko muna wqyan shi yana fadin. Ga sakon saukan su nan ga fitarwa yana miko muna wayan ga wautana har zan karbi wayan sai kanina baffa yace ai tare mukaje baba ba sai sun karbi wayan ka ba aci gaba dai kawai. Nan aka fitar da na mahaifiyar su sai aka fara kasafin namu kuma akayi lafiya aka kare kowa ya kama gaban shi don ko minti ashirin bamu kara a cikin gidan ba muka wuce. Gidana muka yadda zango kamar yadda muka saba yi idan mun fito wurin su baba din nan muka shiga kullawa da warwarewa a tsakanin mu. Muka gama shaci fadin mu da komai aka shiga kasafin abinda kowa zaiyi shidai karamin mu wanan karon ma cewa yayi duk yadda mukayi ya fita ya barmu nan. Kamar hadin baki sai ga Jamil da adam sun shigo gidan a tare da Ahmed mijin kanwata sai wani washe baki sukeyi. Nan mukai masu bayanin komai tare da fada masu yawan kudin da kowa ya samu da wanda aka fitar kason hajiya umma. Ahmed din yace yanzu abinda za ayi a cire kudi da zai isa kowa sayen uncomplet building a samu a saya kada kudin su lalace muna. Saura sai muyi lalurar mu dashi shawaran shi anyi na,am dashi sosai already dama ashe sun yanke hakan har sun cigiya muna ko an samu boyewa dai sukai muna kan hakan . Sukai muna sallama suka tafi haba shiko gogan nawa kamar jira yake su fita cikin tsare gida yace ina kudin naki nace suna ciki na boye. Ganin yana kallo na nasan abinda yake nufi yasa na mike na shiga na dauko mashi kudin na kawo mai ya karba yana juyawa tare da tambayan na tabbatar kudin sun kai yadda akace ? Nace sun kai mana ko a na gida sai da baffa ya sake kirga min yawan su yace to may kike ganin za a saye dasu yanzu in an cire wanda za a sai gidan da ba a kammala ba. Don dai data nice sai in ce kada asai wanan gina ki fara juya kudin har suyi tsoka daidai sayen gida ginane kinga sai ki zuba yan haya a ciki ko may kika gani ? Ya tambaye ni yana tsure ni da manyan idanuwan shi nace ni dai ayi yadda yan uwana sukace kada ya zamo na fita daban a cikin su bayan mun shirya yin hakan da su. Tun da yamman nan ya ware wasu kudi wai zai sayo abinci ya fita ban ganshi ba har dare ya dawo min babu kayan abincin wai sai gobe idan ya fita zai karbo. Washe gari ko sai ga kanwata da mijin ta sunzo sunce an samu kangon gida jamil da baffa suzo suje su gani idan yayi masu. Sun je sun duba kangaye nada dama sosai don gina da aka fara sun tasa sosai kuwa sukace sunyi masu sai Jamil ne yaso kawo rikici wai kangon yayi tsada ga yadda akace kudin shi. Nan dai Ahmed ya kara fahitar dashi har ya yarda a saye din aka saye bado yaso haka a ranshi ba ba dai yadda zaiyi ne. Bayan sun dawo sukai muna bayani har sauran kudi sun rage tun nan a gaban su muka fada masu shawaran da muka yake kan zamu gyara dakunan nmu ne. Jamil bai so haka ba yana ganin an takura mai da yawa mijin summaiya yace zai tambaya muna set din kujeru masu kyau mu saya zuwa gobe. An ko samu kijerun shi Jamil ya kawo shawara wai a na saka ties a falo na don shima kunyan azo aga dakin babu ledan kwarai yakeyi. Shawaran shi ya karbu a waje na da tan uwana sukace tunda zanyi gyara ya kamata a sa ties din a falon sai a bar dakin . Kamar wata amarya haka dakina ya koma ga ties ga tv plastma harda tauraron dan adam da fridge sabo ga su center kafet an saka a dakin. Duk da jamil yayi na kasa wurin sa ties di dakin ya kara kudi ga abubuwa da dama sosai amma haka aka gyara dakin . Duk ko da na bashi nasa kaso daga cikin kudin sai dai kuma bai hana shi yin na kasan ba a cikin dan abinda ya rage min din. Labarin baba kabir kuwa tunda ya bamu hakkin mu bai kara bi ta kan mu nasan don tsage rancin da muka nuna masu ne lokacin rabon kudin da Baffa yace wai dole ne sai an cire na mahaifiyar su . Sai kuma wanda baba ke bi a ciki na fafitikan neman muna kudin ya fito da yake kai cin hanci da sauran su wurin duk wanda ya dace ayiwa. Kuma gashi mun sani baiyi shi kadai sai da sanin mu idan za a yi don ko an lalubu mu kudin bamu dashi balle mu bayar din. Dole haka aka fitar mai da abin shi duk da ma bai cire na jigilan shi ba yace ya yafe muna su amma duk da haka sai da dan hakin shi ya tsone muna ido. Kada kukaga laifina masu karatu gama in kun tuna na fada maku sai da suka raba mu da kowa namu sai su mazajen namu da kannen mu biyu kawai muke shawaran mu. Do haka komai sukace sai muga ai sunyi daidai ba ba mu ganin rashin dacewan hakan a gare mu tunda yanzu su zama muna uwa da uban mu a yadda suke fadi ko yaushe. Don haka muka dauke su da zuciya daya ban ko tuna saura saki daya fa tsakani na da Jamil din duk da dai ban fadi a gidan mu ba kowa ya sani. Dakina yanzu har zuwa kallo akeyi koda yaushe tv na aiki a falon yan diyana suna zaune suna kallo basu zuwa dakin kowa na gidan da sunan kallo. Yanzu zamzam muke da Jamil baison ko kuda ya tabani ko diyana a gidan sai dai ban sani ba ashe har lokacin suna tare da Ruth farkan shi. Ba wanda zai iya fada min don ban iya boye mutum wurin magana shiyasa kowa ke tsoron fada min gaskiya koda an gani sai a kyale ni gashi wanan kawar tawa sun tashi tabi mijin ta can kasa ibo inda yake. Don da tana nan data fada min idan ta san da hakan ba zata boye min ba kamar yadda mutane suke boye min yanzu. Duk da na gyara daki yanzu tsiyan daya tsiro min shine sai yace bai iya kwanciya a dakin wai zafi yayi yawa a daki waje shi zai fita ya kwanta. Ashe in ya fita ya rufo mu ta baya wai kada barayi su shigo muna sai ya wuce gidan Ruth ya kwana sai asuba zai dawo gida idan yaga gari ya waye. Duk ban san wanan ba na dai dauka yawan jin zafin shi ne yasa bai iya kwana a cikin gida ashe munafuki dawata manufa yake min hakan. Ranan ko da na fito da dare sauro ya damay mu sai ban gashi ba wurin da yace yana kwanci din abin ya ban mamaki sosai a raina. Da safe daya shigo nake tambayan shi ina ya kwana an dauke wuta bamu da maganin sauro na fito da dare ban ganshi ba. Yace cikin dakewa ai wajen gida ya fita inda samarin unguwa ke kwanci da dare can yake kwana tare dasu sai ban kawo komai a raina ba danaji ya fadi hakan. Ranan ina zaune na gama girki da rana sai ga matan yayan shi din nan sun shigo gurina na tare su tare da basu ruwa da abincin dana gama. Sunci sun sha nake tambaya su ina suka fito suke ce min sun fito duba watace a cikin unguwan nan sai ban mai da hankali in san ko wacece suka zo gani ba . Wai ashe guri Ruth suka zo duba bata da lafiya sai bayan kwana biyu nake ji a gurin wata yar unguwan mu wai ta gansu ranan sunzo gaida Ruth tayi fama da zazzabi. Abin ya matukar bata mi rai naga yadda muke dasu wai ace sun zo duba farka miji na kuma gashi banda gidan zuwa sai nasu idan na tashi fita unguwa. Ban kyale su ba har gidan su na samay su suna faman yi min rantse rantse wai ba can suka fito ba ban wani tsaya ba na dawo gida. Wanan abin sai da ya hadamu fada da jamil yake cewa wai bakin kishi zai kashe ni idan banyi hankali ba nan dai muka kwasa dashi ranan sosai. Sai banda wani damuwa yanzu sosai don ban gama turmuje yan kudaden dake hannu na ba lokacin don haka yake bina a sannu. Mijin yar uwana ya samu aiki koyarwa a university da ke kano don haka ya tafi ya barta a nan inda take dan zuwa wurina tana debe min kewa a gidana. Nan take fadin ba zata yarda ya barta a garin mu ba bin shi zatayi idan ya samu wuri banga laifin ta ba, da take fadin hakan lokacin don zaman mace kusa da miji yafi. Sai dai ida bata samu anje da ita din ba tayi hakkuri zuwan shi biyu yana komawa inda suke daukan rikici dashi. Har dai ya yarda zai tafi da ita bayan iyayyen sun sa baki a cikin maganan nan ta fara shiri sai dai bamu fada a gida ba duk shirin da takeyi sai daga baya muka je tare muka fada masu batun tafiyan nata. Sun yi murna da farin ciki sosai don sam babu bakin ciki ga alamarin su damu sai nuna kulawa da kauna a gare mu. Wanan abin wani lokaci yana samu jin kunya har da muka fito muke maganan nan dai take fada min wallahi inbi yan uwa in daina bin zancen Jamil da yan uwanshi. Sosai taimin magana a cikin natsuwa yadda zan fahince ta na kuma fahinta da abinda take nufi don banyi sanyi a gwiwa ba na fara zuwa kai da kai ina ziyaran su. Tun kan Summaiya ta bar garin sai dai wani abu daya bata muna lamarin shine ita kanta summaiya tayi abinda har ni ya bata min rai da ita sosai. Don kaya dakin ta gaba daya har kujerun da muka canza ta sayar ba tare da ta fadi a gida ba bayan munce gyara muke son yi a gurin baba kabiru da iyalan shi. Don sun muna komai da akeyi a duniya nan gaskiya wanan abin da tayi ya bata ran mutanen gidan baba kabiru din sosai don ta fifita uwar mijin ta gare su. Kayan dakin nata ma karshe akace uwar mijin nata ke amfani dashi kin san abu ga mai kishiyoyi su suka kwarmata ma gidan mu wanan zancen. Ba yadda zasuyi damu dole sukai hakkuri suka bar zancen duk ko da ransu ya baci ga hakan da tayi masu din don sun fahinci dai bamu dauke su a maysayi iyayyen mu ba. Mun fi fifita mazan mu a kan su dole kowa yanzu ya kawo ido yasa muna aga iya gudun mu da mazajen namu da muka dauka uwa uba a gare mu. Sai bayan wucewan su magana ya fara tashi wai da kudin ta mijin ta ya nemi aikun daya samu wai wanan kangon da muka saye babu nata a halin yanzu. Waya na nema na kirata na fara mata korafi sai bata bari nakai ayya ba ta hau fada tana fadin wai ni a ina naji wana zancen wanan magana ba gaskiya bane duk wanda ya fada mun kuwa. Haka dai magana ke faman yawo kan mazajen mu sun cinye muna kudaden mu duk wanan maganan da ake fada baba kabiru baice damu kala ba kan zancen mazajen namu. Kuma ya hana iyali shi suyi muna magana don haka ne zancen bai daga sosai ba yadda wasu suka so cikin dangi a dauki mataki akan mu. Yakan ce kubar yaran nan inda kuka gansu idan masara taji wuta da kanta zatai kara ai ba sai an tambaye su ba duniyace. Don yanzu ana magana zasu ce kuna son ku kashe masu aure ne don baku kuka haifesu ba sai yan uwa suce kwarai kuwa Alhaji kabiru. ZAINAB IDRIS MAKAWA 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Na samu wannan kawana dake makwabtan mu tasa mijin ta ya dauko muna manja da garin rogo a can inda yake da zai dawo. Ita nata zata aika dashi ne gidan su a sayar ni kuma tace in saida nawa a nan cikin unguwar mu din tabar min sai idan mun sayar zamu tura mai kudin ya kara sayo muna wani. Alhamdullahi don sana,ar ta karbu min a cikin unguwar tamu da farko da Jamil ya gani ya fara tambaya a ina na samo kudin da na sai wanan abin ? Ban so in fada mai ba amma danaga matsin yai yawa yana tambaya don zargina yake ko na samu wasu kudine naki fada mai don har bugun cikin baffa kanina yayi a waje bai ji komai ba. Dole na fada mai inda na samu kayan ina sayarwa din nan ya hau fada wai yarabani da wanan matar don ta fini wayewa shi bai son rikici da dauko magana. Na dai kyaleshi yayi fadan shi ya gaji ya sa mun ido mutane sai shigowa suke dare da rana suna fadin abasu manja ko gatin kwaki da sugar. Dadi dadi na hada kudin farko don a cikin sati biyu komai ya kare muka tura ya sake turo min da wani don ita ma an sayar mata da nata acan gida da ta kai. Wanan ma yayi saurin karewa da wuri don yanzu mutane sun sanda ina sayarwa kuma a cikin sauki na hada kudin mijin kawata cif da sunan washe gari in kai mata ta tura muna wurin mijin nata. Washe gari tun da safe Jamil ya fita kan zai tafi wani kauye yace min a can zai kwana don haka sai dana gaba duk aikin gida na shirya na nufi inda na aje kudin don in shiga in mika mata. Kudi yace dauke ni inda kika aje sai da na dafe kirji na nakai kasa don capert nake dagawa na aje ba wanda yasan inda nake aje kudi a dakin idan na hada su. Don gudun haka tunda nasan halin shi da kudi ni kadai a daki sai zufa ke karyo min a lokacin don nasan babu wanda zai dauki kudin nan sai Jamil din don ba mai shiga dakina har kurya. Ko baki nayi a falo nake ajesu basu shiga min daki, don kunyan dakin da nake ji ni kaina ban son wata mace yar uwana ta shiga min dakin. Don haka ban zargi kowa ya shigo min daki ba na rasa yadda zanyi a lokacin sai daukan diyana nayi na nufi gidan da mahaifi shi yake. Duk da nasan abu mawuci ne ya goyi bayan dan nasa a lokacin sai banda yadda zanyi dole in je gurin shi da wanan maganan. A gigice na isa gidan muka gaisa dasu sai na fashe da kuka na fara fada masu halin da ake ciki budan bakin mahaifin nashi tun ban karasa ba shine. Kina nufin Jamil ke nan yai maki sata ko wa da kika zo nan din ranan matar mahaifin nashi tayi min abin kwarai don kafin in magana tace . Haba malam idan bata zo nan ba ina kake son taje da wanan abin kunyan kai kullun danka bai laifi itace mai laifi haba a rika yin abu don Allah mana. Yarinyar ga dai tana iya kokarin ta wurin ganin ta kyautata mashi amma hakan bai isa ba sai an hada da dauke na mutane da ta dauko kuma yanzu mai kake son tace ma mai kudin do Allah. Ai sunan danka ne zai baci a unguwar tunda kowa yasa halin shi a gareta ido kawai mutane suka sa masu hakanan. Naji dadin wanan maganan har cikin raina don yau ta fadi alheri a gamay dani bayi son zuciyan da suka saba ba. Fada ya hau yi da ita amma bata barshi ba dole tsohon ya sauko tare da fadin nawa ne kudin na fada mai yana gyaran zama yace sai dai ayi raba daidai kije ki nemi saura ki cika masu kudin su. Ya kirga rabi kamar yadda yace din ya bani na fito ina share hawaye ina zan shiga cikin garin nan in samo rancen kudi in ba mutane kudin su. Ko dana koma yan gidan mu ke fadin matar tazo nema na sai da gaba na ya fadi lokacin haka na daure na shiga gidan ban boye mata komai ba na fada mata halin da nake ciki da kudin na bata rabin da mahaifin shi din ya bani. Na bata hakkuri kan zan nemo sauran in karkare mata in an kwana biyu hakkuri ta bani na fito ina hawaye gidan zuwa gidana. Bai dawo ba sai bayan kwana uku ya dawo in da ya samay ni zaune a cikin tagumi ban ko iya mai sannu da dawowa ba don zakace ba kauye ya fito ba da yace yaje. Shi sai wani fresh yake karawa ni ko ina figewa banda wani kumari a jikina ko kadan daka ganni, kasan damuwa ya samu gurin zama a zuciyana. Ganin yadda na fuske shima ya fuske ya shiga daki ko may yayi a ciki can ya fito yana fadin ke lafiya kuwa mutum ya dawo ko sannu da zuwa ba zaki mai ba. Wani kallo na watsa mashi tare da kawar da kaina daga kallon shi ina fadin azzalumi baiji dadi ba wallahi. Ka rasa wanda zaka yaudara sai matar ka ta gida mai dawainiya da yayan ka duk wani nauyi da hakkin ka ka rataya a kaina . Haka bai ishe kaba sai ka hada da kudin mutune ka kwashe ka tona min asiri a gari. Ya zaro ido yana fadin wa kika mayar barawon ki gida nan nace kai tas ya kwashe ni da mari sai da ba dafe wurin don zafi. Hakan bai sa na fasa magana ba nace ka kashe ni ka huta dama nasan mutuwa ta kake son ji macuci kawai azzalumi. Ba wanda zai shigo ya daukan min kudi dakin nan sai kai ba zan zargi kowa ba wallahi don kaine ka kwashe su . A harzuke yace an kwashe din kiyi abinda zakiyi in zaki iya wawiyar banza kawai kan wasu raggan kudin ki zaki dinga kirana da macuci can kudin da ko mota basu isheni shiga ba. Nace baka nayi da zakace kada in kiraka da macuci ya kara daga hannun zai mare ni na sa mai ihu sai ga yan hanyan gidan a sukwane sun shigo suna tambayan ko lafiya ? Ina kuka na fara fada masu abinda yai min don duk cin kudina da jamil keyi wanan din yafi bata min rai sosai wallahi. Don ya nuna min bai damu ba duk halin da zan shiga da mutane ni na sani ke nan shi ba damuwan shi bane hakan. Bayan sun gama ji ba mai shiga tsakanin miji da mata sai cewa sukayi inyi hakkuri in kyaleshi mu san yadda zamuyi kudin mutane ya fito. Haka suka dinga fita daya bayan daya suka barmu a dakin dagani sai shi ya shiga kuryan daki ya fito yana fadin wawiya da bata san ciwon kanta ba. Da kika fada masu kwatar maki zasuyi ko may ai na dauka zasu sa in biya ki ne dole ina kuka nace Allah dai zai kwatar min hakkina ba wani ba. Mu kai ta yada ma juna bakaken magana har ya gajibya fita daga gidan ya barni nan ina tukukin bakin ciki da na daman auren shi. Sai mutum daya ne cikin yan hayan mu ya iya mai magana kan abinda yakeyi din bai kyauta ba gaskiya kudi mutane ne fa ya dauka kuma ya sani yaya yake son inyi. Don Allah Jamil idan ka samu kudi kaba wanan yarinyar kudin ta don hakan zubar mutunci ne a gurin mace wallahi . Kaga dai duk cikin matan mu tafi kowa hakkuri yau gashi kakai har ta tona maka asiri a bainan jamma,a haka ai irin haka babu dadi. Jamil din yace ta dai tona ma kanta tunda bata da wayau don kawai na dauki kudin ta zatai min wanan tonon asirin haka a idon jamma, a. Mutumin ya sake fadin ai abin ne da cin rai jamil yace malam naga fa kana son shiga hurumin da ba naka ba gaskiya yace a, a niba haka na bane ina dai guje maka hakkin marainiya ne a kan ka. Kada ka manta matar ka marainiyar Allah ce ta gaskiya kowa kuma nan yasa tare kuke cin kudin gadon ta idan ya samu aiko kaga hakan tayi kokari wallahi. Don ba ko wace mace bace yanzu zaka samu haka nan yace kada ka fada min maganan banza Nasir ina ruwan ka ne da zancen mu wai da matana. Basuji dadin juna ba da mutumin nan kowa ya fadawa dan uwan shi bakaken magana ya kulla da wanan mutumin da yake gani wai ya raina mashi wayau shi. Tun wanan lokacin ya sa wana mutumin da matar shi agaba gidan da anyi abu zai fara fadin ba mutumin arziki bane dama ya kamata su tashi su bamu gida. Sai dai wanan karon baiyi nasaran haka ba kaina don ban bashi hadin kai yadda yaso ba yake min a baya kan yan hayan mu. Sannu a hankali na samu na biya kudin bashin da ake bina koshi da taimakon dan abin da nake samu a wurin baba kabiru aboye bai sani ba na biya. Don daya sanin karbe kudin zaiyi ba wani wuyan aiki bane a gurin shi don haka yanzu na fara boye mashi komai nawa nima saboda yanzu na fara fanhintar shi. Don a gaba shi maman jinior zata aiko batun kudin ko tazo da kanta yana ji bai cewa komai idan kuma na mashi magana sai yace idan ta samu zai bayar. Ko hakan da yake fadi don mahaifin shi wanan karon ya fita bayan shi yayi mashi fada sosai har ranshi ya baci shine yake fadin wai zai biya da baki don baida niyar biya din. Tun da yaji baba yace yana nema na yana daki kwance yaron yana fita zubur ya fito daga dakin yana tambaya ko lafiya baba ya aiko yans nema na ? Nace ban san ko may yake nema na dashi ba in dai na gama zanje in ji dalilin kiran yace ki tafi ni zan karasa sauran akin daya rage din. Ban ki nasa ba na gyara jikina na nufi gidan namu inda na samu baba na gida bai fita ba baya mun gaisa ne yake fada min zancen kudin mu ne ya taso bayan long proces da akayi yanzu ranan monday zamu je muyi signing din documents din a Abuja. Wani irin farin ciki ne ya turnuke min zuciya ta idan mai karatu bata manta ba na fada maki kudin an kasa su uku ne kadan kadan suke zuwa muna ke nan. Murna a gurina ba a cewa komai hakama dana koma gida da zumudi Jamil yake tambayana lafiya dai ko ? Ba bata lokaci na labarta mai abindake faruwa ya wani washe baki yana murna tare da fadin wai Allah dai ya jikan baba. Karo na farko danaji yayiwa mahaifina addu,a ke nan ita mahaifiyar mu ba a magana kanta. Nan wuyan talaucin da muka fito ne a ciki yasa yai wanan addua,an haka da bai ma san yazo mashi a baki ba a lokacin. Nan ya fara haba haba dani bai fita yawo sosai sai lokaci lokaci yakan dan fita ya dawo ana jiji dani da yarana lokacin har fita yake da yaran wurin fira kofan gida inda suke taruwa. Yanzu idan mun zauna baida magana sai na tsara yadda za,ayi idan kudi sun shigo hannun mu har da fadin zai fito dani gari don zai sai min babban waya irin na kowa ni da ko nokia banda shi. Sai yan uwa idan sunji haushi rashin wayana ya damay su zasu dan sai min yar nokia in rika bai kai wata daya a hannun na idan matsi ya kama mu in sayar in sai wani abin. Gashi nima bakina yasaba da dadi irin na jamil yanzu ba ko wani abinci nakan iya ci ba in ba yan kayan kwalama ba da sauran su. Ni dai ina jin shi yana ta tsara yadda yake so abin ya kasance wanan karon dariya nakan yi a raina kawai do ko da tsiya sai na gyara dakina wanan karon. Nagaji da rufe kofa da boye boye wa kawayena idan sun zo gidana har kunyar yadda dakina yake nakeji don ko na wata tsohuwa yafi shi dadin kallo. Ranan mondaya shi da kanshi ya rakani gidan baba kabiru tunda asuba don asubanci zamuyi mubar garin don mu isa da wurin during warking ahours. Sai dai bai yarda mutanen gidan mu sun gashi ba yana isa kofa saida yaga na shiga ya koma shi bai shiga ba lokacin. Nasan nasa wayau do kada aga zalaman shi a fili ne yasa ya boye hakan ya labe daga kofan gida yaki shiga daga ciki. Mun isa lafiya mun samu wanan kudin a yadda sukai muna bayani suna da yawa sosai don haka zai fi na farko dana baya yawa ke nan . Murna fal a zuciyana baki har kunne muka dawo gida da farin ciki zuciyar mu fara kal da jin wanan zancen. Na samu ya gyara daki ya dafa abinci ya jera min yana jiran dawowana kamar ance mai da kudin zamu dawo dayani daga zuwan mu. A gidana baba ya sauke ni suka tafi ina shiga na samu yana zaune yana jirana a cikin duhu duk da babu wuta a lokacin amma haka yake zaune kamar maye shi kadai a falon mu. Nan yai muna sannu da zuwa ya karbi goyo na yana tambayan ta ya hanya kamar yarinyar ta iya magana lokacin. Yace bari yai mata wanka don kada gajiyan hanya ya hanata barci shi yai mata wanka ya bata abinci taci ta kwanta tunda dama a gajiye muke. Ya fara tambayana yadda akayi ina labarta mashi yayi wani irin ihun murna tare da fadin kice zamu faso gari ke nan sosai wanan karon. Da yakw dan duniyan namiji ne bai barni na huta ba duk ko da gajiyan dana debo a hanya sai da ya kusanceni ranan . Don kawai ya kara gyara min rai niko ina jin dadi a raina ga miji na tatali na ana sona don sai ka dauka ya daina halinshi ne yanzu na bariki. Tun wanan ranan suka shiga yin meeting dashi da mijin kauwata wai idan kudi sun zo ga yadda zasuyi muna dashi . Zakace abin na Allah ne ake shiryawa lokacin don sunce bazasu yarda su baba kabiru suna muna wayau ba ko wani lokaci duk da fa su baba basu karban ko kwandala daga cikin kason mu din. Amma sun ce wai wayau suke muna kawai don sun dauke mu yara kanana suna yi muna yadda sukaga dama da hakkin mu . Muko mun hau munga ga masoyan mu na asali masu kaunar mu da zuciya daya don Jamil yana cewa. Da ke nan da baisan ciwon kan shi ba suke cinye kudin ba abin kwarai da mukeyi dashi yanzun kan tanadi sosai za a yi muna gaskiya. Fadin haka da yakeyi yasa na kara yarda dashi sosai don na dauka talaucin da muke ciki yasa yanzu yayi hankali ne. Mun dauka wani sati kudin zai fito a yadda aka nuna muna a can da mukaje abuja sai gashi shiru har mako uku ya share ba wani labari kuma na kudin . Nan dai ya shiga kuma sake magana yana fadin kila ma su baba ne da sherin su kudin an sako basu fada muna ba kai ba dai abinda bai fadi kan kudin. Har turani gida yayi in koma in tambayi baba cewa munji shiru baba dai yayi dariya yace hadiza banda abinki ko wancan karon ai haka akayi ko ? Sai lokacin da muka ji su kin san gwaunati ba ayi mata dole tunda ba abin mutum daya bane abu ne na taro kowa dake cikin system din jira yake yi kamar mu. Na dawo gida na fada mai abinda baba yace ya ja tsuki don takaicin da yake ji a lokacin yana fadin wanan shegen gwaunatin basu da tausayi wallahi. Yakan yi maganan kudin nan kusan sau uku ko hudu a wuni shi dai ina ganin lokacin damuwan shi bai wuce yaji ance kudi sun shigo muna ba shine nasa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU. 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Tun barin kanwata garin ya koma min ba dadi ni kadai nake harkokina don na dada maki tun farko jamil ya rabani da duk wata kawa da nake da ita a baya. Haka kuma wa yanda ma a yanzu nakeyi baya bari muyi wani dogon hurda yake watse haduwan tamu a lokaci guda. Sannu a hankali ya fara sayar da dan mashin din dana saya kudi suna dan shigo min ta hanyan mashi din . Ni kadai naci kukana na share hawayena don ba wanda zan fadawa ya dube ni tunda kowa ya gama fahintar zaman mu da jamil din yanzu. Don ko mutum ya nuna min kulawa ya shigs zancen mu daga baya zan iya ba mutum kunya in barshi a ciki da jin nauyi don zan dawo mu shirya da jamil din ne daram. Wanan daliln yasa a yanzu ma ban san wanda zan kaiwa kuka na ya share min hawayena ba ta hanyar kiran jamil din yaji ba,asin zancen.. Har ya daukan mun mataki akan jamil din sai dai kassh babu mai iya kundun balun share min wanan hawayen nawa a lokaci daya. Wanan dalilin yasa dole na hakkure da zancen nayi kuka na ni kadai ba tare da sanin kowa ba sai dai yan gidan mu suna dauka mashin din yana nan har yanzu. Kanina Baffa na iya samu da maganan don yanzu ya tasa shima ranshi ya baci sosai da jin wanan maganan sai dai nasha fada a gurin shi sosai. Na koma kamar nice kanwarc shi ba ya ba shi ya tunkari jamil da zancen mashin din kai tsaye ba tare da wani jin tsoro ba kamar yadda saura suke tsoron shiga maganan mu. Sun buga sosai dashi don har ya kai su ga bacin rai sosai dashi inda ya fito fili ya nuna mashi yana cutawa rayuwana gaskiya. Sai jamil din ya nuna mai ai shi ke da ikon komai nawa tunda shi yake aure na ba wani ba idan ina dashi muci in shike da ma ci zamuyi a tare. Sai dai nayi zaton a yadda suka kwasa da Baffa din ba zai kara kallon kayana ba again sai dai ashe hali zanen dutse. Don mai hali akace baya barin halin sa muna haka ne kamar ya lafa baya duban kayana sai harkokin shi yake yi . Niko ina faman dan fadi tashi don kudi ya dan dinga shigo min tunda bai bani na kashi din koda ya sayar da abina kuwa. Gidan iyayyen shi naje ranan gaida mahaifin shi ban wani dade ba na dawo gida misalin daya saura ina shiga falona a cikin sauri ban kula da cewa fridge dina bai falon ba sai bayan na dora girki na dawo don in huta. Sai lokacin idona yakai gurin fridge din wayau na gani babu fridge babu dalilin shi a gurin . Allah yasa a zaune nake don bansan lokacin da nayi bayan kujeran ba da yai min mazaune da wuyana na jingine dashi. Sai dai na nemi kuka ko ihu na rasa a idona ko wani yaki zuwa a lokacin sai ajiyan zuciya nake faman saukewa don tashin hankalin da nake ciki. Ina cikin wanan halin sai gashi ya shigo gidan niki niki da kayan abinci kala kala a hannun shi yana faman washe baki . Ganina a wanan yanayin yasa ya sausauta fara,an da ya shigo gidan dashi yana tambayana ko lafiya ? Da kyat na iya budan baki nace mai Jamil ina fridge dina cikin wani irin murya mai kama da ta mai kuka ko tashin hankali. Bai bani amsa ba lokacin sai kokarin aje kayan abincin dake hannun shi da yakeyi ban damu da in san kayan ko damay damay ya sayo ba a lokacin. Jin shiru yasa na mike tsaye daga zaunen da nake ina sake tambayan shi ina fridge dina jamil amsa ya bani a takaice da fadin na fitar. Kakai ina na tambaye shi dagowa yayi ya juyo ya fuskance ni da kyau yace ya kike son muyi idan ban sayar ba na sayo muna abincin da zamuci . Ko haka zamu zauna da yunwa baya Allah ya hore muna abinda zamu sayar muci abinci dashi ba sai naje wurin wani ina tona ma kan mu asiri ba. Wani irin kallon mamaki nayi mai tare da fadin kana nufin ke nan da kayana haka zamu tabbata da cin komai nawa ko may ? Yace ciki daure fuska ko yau ma gorin naki ya tashi ne don kawai na sama ma kan mu mafita nace da abina din yace, Yace ke nan kina nufin abinki ba nawa bane ga yadda kikai maganan nan a yanzu. Nace ni ba haka nake nufi ba sai dai abin yayi yawa ne yanzun zakace wanan dan abin da ka shigo dashi shine iya kudin fridge din nawa ko may ? Ke nan kina ganin cutar ki zanyi ko may da kike fadin hakan ? Banda abin fada sai kawai na fice daga falon na barshi a ciki girki na fita na karasa har na gama na dawo na samay shi kwance saman tree seater yayi matangali da hannayen shi. Har na shigo na aje mai abinci bai dago kai ya kalle ni ba nima hakan dana aje fita nayi daga dakin . Har tsowon wani lokaci abinda nake ji a zuciya bai barni na bude ledojin da yashigo dasu dakin ba ya fito zuwa wurin randar ruwan mu yana deba da kanshi don zuwa yayi wanka. Ban tankashi ba don nasan fushi dani yake sai nima na share shi mu tafi a hakan da yake so din laifin ni akaiwa kuma yana kokarin ya juye shi a kaina. Ashe kamar yadda ya saba kirkiro min zuwa unguwa idan yana son zai cuta min haka ma wanan karon yayi min ya turani gaida mahaifin shi din don yaji dadin fita da fridge din gidan. Don yasa idan ina nan ba zan yarda ba don ina samun dan taro da sisi da fridge din ina rufawa kaina asiri shine yayi dabara turani in gaida mahaifin shi din. Don ya samu ya yaudare ni din ya kuma yaudara din sai dai ta annabawa yin hakkuri dashi yanzu. Mun kai sati biyu a hakan shi da kanshi ya gaji ya sauko daga motar fushin da ya shiga ya nemi shiri dani. Sai dai shirin nasa na yaudara ne ya yaudare ni idan mun shirya ya samu cutar da yai min daga baya kuma. Dadi dadi da muka shirya sai da yaja wani dan lokaci baiyi yaudaran nasa ba har ina dauka a raina don maganan da nayi mai ne yasa shi yin laushi. Sai dai matsalan neman matan shi abin gaba gaba yake sosai don yanzu bai boye min cewa suna tare da Ruth. Don jita jita nazo min kala kala akan alakan shi da ita wanda har na kasa danne hakurina a lokacin haka yasa na tayar mai da hankali kan zancen. Sannun a hankali ya nuna kamar ya daina harka da ita a yanzu hakan yai min dadi sannun a hankali na dan fara sana, a don dan kudi ya dinga shigo min na kashi. Sai dai banyi dace ba don shi muke har cefane dashi muci tare da yayana ko dashi ma din hakan yasa ina sana a kamar ba yi nake ba. Abin nawa ba karuwa sai ma rikicin dake shirin hawa kaina a lokacin don kudin mutane da nake hadawa a cikin sana, an tawa. Don da zaran yaga dan kudadeb sun taru zai san dabaran da yayi ya karbe su a hannu na sai yaga ba abinda ya saura zai daina tambayana kudi. Da zaran kuma yaga Allah ya rufa min asiri ta wani fannin zai kara dawowa ya lalabe ni ya karbi kudin da haka rikici da zaman gida ya fara gagarana a gida . Ko yaushe ina wajen neman wa kaina abin rufin asiri ga yarana sun fara tasawa yanzu ga ragga yana batun kashe mu a gida. Abinci kan duk inda zai shiga ya fita ya samo mai dan dadi yana yin shi don muna cin abinci lafiyayye ba laifi. Sai da ta fannin sutura ba kai muna kallo biyu ranka bai baci ba da mu don kamar wasu yan kauye muka koma dan da diyana. Don ko dinki zai muna sai sallah kuma ba wani abin kwarai zai dinka muna ba daga wando da riga sai wani shegen yadi da ban san inda yake samo su ba. Sai daga baya nake ji a gurin yan uwan mu wai ai Ruth ce ke zama ta dinka muna kayan mai kama da gwajo muna sakawa. Duk yadda na iya gaye zuwa gidan mu sai inji yan kanne na suna kushe ma kwalliyan da nayi din wanan abin yana matukar bankanta raina sosai. Har dai suka kai ga fada min gaskiya ranan naji bacin rai sosai a zuciyana jin wai farkan shi ce ke muna dinki ashe. Don ni cewa yake min wai wani telan shi ne ke dinka muna don dinkin yaran zaka ganshi kamar yar kanti na gaskiya don ta iya dinki sosai ba laifi. Na dawo gida na aza mashi jidali da zage zage sai da ya fice ya bar min gidan don haushi yana matukar mamakin yadda yan gidan mu ke saurin gane sirin shi a saukake. Wanan abin ya kara jawo kiyayya a tsakanin shi dasu inda anty ke yawan shan zagi a gurin shi komai yace wanan matar ai shu,umace ta kwarai. Bakajin kalamin dadi a bakin shi daya shafi yn gidan babana kabiru kullun sai aibanta su yake a bakin shi. Wani lokaci nakan ji haushin hakan wani lokacin kuma idan ni aka batawa zan biye mashi mu zage su a tare. Gashi dai ba damuwa sukayi da suzo gidan mu ba su sai can ba a rasa ba zaka ga sun zo gidan sai dan gurin anty ne karamin bai kwana uku shi bai zo gurina ba ya duba ni koda kuwa yana sauri ne. Wanan yasa namu yazo daya da yaron sosai don har shawara nakan yi dashi sosai har shi Jamil din ma yana sakewa yaron saboda yawan kawo muna ziyaran da yake akoda yaushe. A cikin hikima jamil yayi muna dabaran karban kudin yan hayan mu ya koma ta hannun shi. Wanda yasan cewa bani kadai keda hakkin kudin hayan ba amma bai hana shi karbewa ba idan an bayar da kudin shekara. Sai gashi wasa wasa Jamil sai canza yan hayan gidan ya keyi idan dan sabani ya hadasu da mutum yanzu zakaji ya fara korafin, korar mutum a gida. Sai ya zama dani da yan uwana sai abinda yace damu duk sunayi ne akan suna bashi girman shi ne hakan da sukeyi. Wanan dan uwan nawa shine nake dan samu yana ban shawara duk da kankantan shekarun shi kuma hakan yana mun dadi sosai. Don ina amfani da shawaran shi kuma ina ganin fa,idan hakan sosai ina kuma samun karuwa da walwala da hakan . Zan tura shi duk inda nake son abu zaije ya biya mun bukatana a cikin lokaci batare da bata rai ba. Ranan ina gida nazo gaida mutanen gidan mu sai ga kanin nawa ya shigo ganin a gida mun gaisa shine yake fada min ai yaga Jamil yanzu da carpet din dakina ko wurin wanki zai kai ne yake tambayana ? Gabana ne ya fadi don jin abinda ya fada min din ba tantama ko ba a fada ba nasan ya dauka zai sayar ke nan. Da yake gida nake sai ban nuna wani abu ba na aje zancen da fadin eh wanki yakai muna sai kuma godiya ga Allah ba kowa a gurin da yake fada min zance. Ban wani dade ba a gidan dole na shirya zuwa gida hankali a tashe na shiga falo na sai wayau. Ya kwashe carpet din ya fita dashi nasan sunana sorry don nayi bye bye da shi ke nan don ba dawowa gidan zai yi ba . Kamar yadda sauran suka fice babu dawowa gidan shima wanan din haka ya tafi har abadan ibada. Ban wani wahal da kaina gurin tambayan shi ba don nasan ko na tambaya din ma a banza ne. Haka ko ya shigo min gida yana wani cicika wai shi rako ke nan yake min abu daya nasan na fada shine ko mai mutum yayi shida Allah. Bai kula ni ba duk da yasan dashi nake ya mayar dani mahaukaciya mara hankali ga wani hali daya tsiro min dashi. Idan ya daka min tsawa sai na rude ko gabana ya dinga faduwa ba wani dadin rai a tsakani na dashi cikin wanan lokacin. Ga fita sai lokacin da yaga dama zai dawo gida don kan shi ba ruwan kowa da dan uwa sai idan yana da bukata na zai tayar dani a cikin dare ya biya bukatan shi a kaina. Idan ya gama kuma zai fice daga dakin yaje gurin kwanan shi ya kyale mu don kullun cikin kiran zafi yake a dakin mu shi bai iya kwana a ciki wai. Kowa a gari yana min kallon tausayi do abin ya daina ba mutane haushi sun koma tausayina yanzu kuma. Don sun san ba karamin cutamin yake yi ba babu dai yadda zan yi don an fahinci sona ya rinjayi nasa a raina. Nima kaina nasan ina son jamil fiye da komai arayuwa na don shi ma din da yake kokari nuna min haka ada can baya yanzu ya bari. Zama kawai yake dani na hakkuri da juriya a rayuwan shi don ba yadda zaiyi damu ko may oho ? Haka dai nake dauriyan yin hakkuri muna zaune da juna ba yabo ba fallasa a tsakani mu sai mutane ke jin haushin da takaicin zaman mu. Kuyi hakuri dani wanan labarin haka yazo min koni na matsu ya kare don takaicin dake cikin sa ga kuma matsalan da ya shigo na waya sai dai yanzu Alhamdullahi gaskiya. ZAINAB IDRIS MAKAWA 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Yanayi ya canza muna baki daya sai zaman kunci da zaman hakkuri ya rage min a gidan Jamil. Gashi ba wani jin dadin Jamil din nake ji ba ko kadan tsawa da hattara ne a tsakanin mu ko mai nayi banyi daidai ba a gurin shi. Hakana nake hakkuri da shi don son shi da nake ya rinjayi nasa a yanzu tunda ni tsakani da Allah nake son shi dama. Sabanin shi da nake ji mutane na fadin don kwadayi ya aureni ba matar sa bane ni don ko ganin mu kayi ba zaka taba dauka shine mijina ba a yarda. Don sai kace shine ya tashi a birni nice tashin kauye din yanzu don duk yanayina ya koma na tifical bakauya a baki daya. Tun Mutane sun jin haushi na har sun koma tausaya min na zama abin tausayi da kwatance a gari ga kowa da ya sanni a baya. Muna cikin wanan yanayin ne labarin barin garin Ruth wace ta musulunta yanzu ta koma maryam sunan mahaifiyar Jamil yazo min. Naji dadin samun wanan labarin sosai a raina don ko ba komai na samu salama a raina yanzu in huta da wani abun takaicin da yake min din. Ashe zance bai kare ba kwanton bauna yayi min sai gashi bayan kamar wata biyu da barin garin ta shima ya shirya wai gari zai bari zai koma Abuja ya fita nema. Sun shirya da wani abokin shi ya bashi labarin ana samu sosai idan mutum yana sana, a a can din. Shiri ya fara yi sosai don tafiya da yasa a ranshi nidai nawa ido ga tafiyan nashi don ban tada wani hankali na ba ga tafiya. Har ya gama ya sa rana ba tare da ya barmu da wani abin kirki ba da zai tafi don kukan babun da yakeyi ko yaushe yanzu tunda komai ya kare. Muna haka ne ya tafi ina jin dadi miji na ya tafi abuja neman kudi nasan yanzu zamu samu walwala mu sake don tsananin yayi yawa sosai. Acewan shi da yaje zai yo muna sako ya aiko muna da abinda zamu ci ni da yara ni kuma na yarda da hakan saboda yadda yake cika bakin shi da tafiya. Sai bayan tafiyan shi da kamar wata biyu shiru ba sako babu dalili ga dan kudin hayan da nake dan dogora dashi ya karbe yayi tafiyan shi wai da shi zai ja jari a can idan ya tafi. Haka na kama dan buga buga ina samun abinda zanci da yarana ba wanda zan nufa a cikin yan uwa don da na samu kin su nayi a baya. Don abin duniya da ya rufe min ido koda yake ba laifina bane idan nace zan ba wani abu yanzu zai bata rai yace shi may ya taba taimaka min dashi. Amma shi nasa suna ci har na kauye sai sunzo idan sunji na samu kudi a lokacin yanzu ko duk da baya nan sun san irin wahalan da mukeyi bai sa sun taimaka min ba. Bama wanda ke zuwa inda muke sai nice nakai dan je in ziyarce su wani lokacin haka zan dawo ba wanda zai ban komai a cikin su. Ranan nayi bakuwa tazo wurina dan abincin dana dafa na zubo mata tare da ruwan sha duk da ba mai sanyi bane na kawo mata. Na zubo ni da yarana kamar yadda muka saba zubawa idan zamuci mun yi nisa dacin abincin ne take fadin ashe maryam tabar garin nan ? Sam na mance da wata maryam nake tambaya wace maryam take magana tace Ruth mana data musulunta kan miji ki nace. Cikin bata rai wanan yar iskan har na manta da zancen ta yanzu ai na bata amsa cikin canza yanayin fuskana. Tace aini su matar wan mijin ki suka ban namaki don da sanin su ake komai suka munafunce ki dkn ko shirin tafiyan dasu akayi shi. Duk wani kayan da bata tafi dashi ba kuma su tabawa kyauta su kai wa yan na mutane ai basuyi ba ta kare zancen da fadi hakan. Raina naji ya baci sosai sai dai nayi dauriya danne zuciya muka dan zage su da mugu;hali su sai yamma ta bar gidana na rakata ta hau mashin. Ina dawowa gida hankalina ya daga sosai haka nake kamar zawo banda hakkuri ko kadan don haka ban iya kwana ba sai da naje gidan su mukayi tsiya dasu naji dan sanyi a raina. Sai dai sun karyata zancen wai kazafi akai masu wanan ba zancen gaskiya bane su ko gidan su maryam bata zuwa har ta bar gari. Haka yasa ni naji sanyi a raina har na basar da zancen don dama na kulla zan barsu har abada idan zancen ya zama gaskiya sai na samu ba haka zancen yake ba. Ashe sun boye min ne gaskiya ne dasu akai duk wani kulle kullen tafiyan ita maryam din. Ba dadi da dadi akoma sana,ata ta kayan mata ina kuma dan yin sana,an yara madara aya da sauran su a gida yara na shigowa suna saye. Sai da ya share wata hudu kafin kacar yayo min sakon dubu biyar mu sai abincin da zamuci. Jifa dubu biyar mai zai min nida yara da duk sun isa cin abinci yanzu haka na hakkura na karbi kudin muka sai dan abin bukatan mu dashi. A cikin hakan da muke ne na samu na dan sai tufafin dana dinka nida yarana karo na farko a rayuwana ke nan koshi bashi naci ina bada dan abin daya samu a hankali. Wanan yasa har ina da shiga jama, a yanzu tunda ina da dan nashiga mutane din da ko bukin dangi ya tashi duk yadda muke da mutum ba zai ganni ba. A cikin hakan kanwata suka zo ganin gida karo na farko tun tafiyan su kano da mijin ta da ya dauke ta suka tafi. Sai dai ba wanda yaji dadin gani yadda duk ta ramay ta kalmashe da gani itama dai zaman ana dai yin shine hakana. Sai dai ita tana da zurfin ciki sosai don bata fadawa kowa halin da take ciki a gidan ta duk da yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba gun mutane. Bata fada ba amma an fahinci hakan a gareta do a san halin da take ciki ba mai dadi bane don ba jiki mai kyau ba suturan kware a gareta sai dai ta dan darani ga hakan . Don tana dana canzawa gaskiya sosai sai dai ba wani na birgewa ba ne sosai hakan da za a gani asan miji yana kulla da ita . Abi mamaki shine duk mazaje namu sai kiba suke mulkawa a jikin su muko muna rama kamar ana diban mu kullun. Don ko shi mijin nata yadda nawa yayi kiba haka shima ya mulka kiban shi ga mota har ya saye na hawa da fara aikin shi . Shikan zaka gane shi ka gane da birni ne sosai ga wayewa a fuskan shi sai itace ta zama wata yar kunju da ita. Sai da muka samu kebewa ne da ita nake tambayan ta halin da suke ciki da mijin nata sai take fada min komai. Babu dai dadi sai dai ta dan dara nine kadan wurin samun walwala amma shima kusan mayau dari ne mijin nata don bai bari ta rike komai a hannun ta karshe kuma yace ba kudin kamar na Jamil dina. Kuka mukayi sosai muna ba juna magana kn halim da maza suka jefa mu a ciki sai da mu kayi sai da muka gaji muka ba kan mu hakku. Nace ta boye wanan zancen kada ta bari kowa yaji halin da take ciki a gidan ta tace ai ba zata iya fadi ba ko don anty . Tunda tun farko saida ta fada muna haka zasuyi muna bamu ji ba yanzu wa zamu tun kara da zancen. Duk da mun boye sai da anty ta gane muna a cikin wani hali tundai summaiya din don dai ni idan da sabo sun saba da nawa matsalan ko. Tare muka shigo gidan da kanwata bayan mun gaisa anty ke fadin anya Summaiya kina cikin dadin rai kuwa ? Dariya tayi na anty kawai tare da tambayan may ta gani halan tace yanayin ki ya nuna akwai abinda ke damun zuciyar ki gaskiya. Bata samu wani amsa kwarai ba ta bar zancen aka dauko wani hira sai dai hankalinta bai kwanta da ita ba. Don yawan kallon kanwar tawa da take yi akai akai yasa duk muka tsargu da zama tare da ita. Karshe tashi mukayi zuwa dakin yan matan gidan muka zauna ana hira mun kai har yamma a gidan kafin mu koma gidajen mu. A hanya muke maganan abinda yafaru tsakamin mu da anty har muka kai gidan mu muna magana daya akan matsalolin mu. Bayan kwana biyu ban san inda taji zance a gari ba wanda ni ma dake garin ban sani ba sai ita da tazo daga baya. Sai gata min hankali tashe tana tambayana wai Jamil wani gari yace min yake ? Cikin washe baki nake fadin yana abuja ai kila ma ya dawo kafin ku koma don yace kwanan nan zai leko gida. Ke kin yarda da cewan shi a Abuja yake zaune ne ta tambayane cikin son jin abinda zance mata din. Nace can yake don haka yace min da zai tafi sai naga tayi shiru taja bakin ta batai wani dadewa ba tace zata koma gida. Nace tun yanzu zaki koma barin dan dafa muna wani abu muci mana, kai ta girgiza min tare da fadin ita zata tafi. Don a gidan mahaifan mijin ta suka sauka don sun sake gidan da suke haya da farko. Rakiya nayi mata har ta samu abin hawa da zai kaita gida sai dai ina dawowa tunanen maganan ta ya hanani sukuni a raina. Da kyat na basar da maganan cikin zuciyana don kaina ya kulle da tambayan da tai min din wanda ban san dalilin ta na min wanan tambayan ba haka kan jamil din. Maganan yaso ya tsaya min a rai ko washe gari, sai dai na basar da zancen don ban san dalilin ta na tambayana ba dai. Yan tsunmakaran ta da na yaranta ta debo ta bamu mu kara duk da banda su hakana na amsa sai dai na raina kayan . Har fada mata nayi yanzun ke wanan raggadudan zaki bamu don Allah tace ai itama bata da wadattacen kaya da zata bamu wanda yafi wanan din. Bayan kwana biyu suka fara shiri komawa kano har lokacin Jamil bai dawo ba sai ana jibi zasu koma ne ya dira a garin. Abin mamaki ga wanda yaje nema ana sa ran zai dawo da abin arziki baje baje sai dai shi Jamil sabani haka na gani a gare shi. Don daga shi sai yar jakkar tafiya irin ta maza ya dawo garin babu komai a tare dashi. Sai na dauka kudi ya riko ya dawo dasu gidan don wahalan daukan kayan da zaiyi daga can . Sai dai har aka kwana aka wuni banji wani abu daga guri shi ba sai kwasan barcin da yake faman yi tun da yadawo a gida bai fita ba. Abinci lafiyayye na hada mai har da ciwo bashin kayan miya a makwabatar mu na hada mai abincin. Ya tashi daga barci ya nemi ruwan wanka nakai mai da soso da sabulu ya fito lokacin na gama abinci sai da ya shirya idan ya gama zai fita. Yar karamar yar mu ce tazo wurin shi tana fadin baba mai ka sawo muna can da zaka dawo shafa kan yarinyar yayi yana fadin.. Ka dai ba kinga babanki ya iso gida lafiya ba mamana da yanzu yan fashi sun kashe maki baba a ganya ai. Cikin faduwan gabx nace yan fashi kuma ban ya shiga rabtabo min karyan da ya shirya mi duk nabi na rude. Hankalina ya tashi yadda yake bamu labarin a cikin tashin hankali nan nayi muna barka da arziki da Allah ya tsirar muna dashi daga hannun yan fashi basu kashe shiba ko su illanta shi. Yana ganin karyan shi ya kamani yace zai tafi gidan mahaifan shi ya gaida su ya fada masu arzikin daya auna a hanya. Nace tunda dai rayuwan ka ya tsira ai mun gode ma Allah arziki kuma idan da rabon muyi mayi a gaba ai. Yaji dadin magana na yace wai da Allah yasa yazo gida da kudin nan da mun warke wallahi mun fita daga talaucin don ya samo kudi sosai acan. Nace ba rabon mu mare masu bane Allah ya kawo hakan nan nayi ta kwantar mai da hankali da dadden magana har ya samu ya fita daga gidan. Yana fita na nima na fita wurin yan hayan mu ina fada masu suyi min barka da arziki yan fashi Jamil ya hadu dasu a hanya sun kwace mai komai nasa da zai dawo. A gabana sun min jaje sosai da Allah ya kare gaba kuna sai dai ina basa baya sukace wawiya ya tsarata ta yarda. Nan dai suka zauna suna gulmana a gurin suna zagina kan irin watauna gurin miji daya tsara ni sai in yarda da karyan shi. Yinin rana duk wanda na gani sai ba bashi labarin mijina ya auna arziki da yan fashi a hanyar shi na dawowa gida. Komai basu barshi dashi rayuwan shi kawai ya tsira dashi a gurin su wasu suna yarda wasu kuma suna mn kallon shasha ban sani ba. Da yamma yar uwata tazo nake fada mata abinda ya faru da jamil din a hanya. Sai cewa naji tayi kai amma Jamil din nan bai ma ko iya karya ba wallahi da wani irin kallo mamaki na dago kai ina kallo ta. Ban bari ta karasa maganan ta ba na hauta da fada harda zagi inda nake shiga ba nan nake fita ba don raina ya baci sosai da kalamin ta. Tace Allah baki hakkuri anty nima rigima na ya kaini fafin haka ai ta mike tare da fadin zata karasa gidan baba kabiru tayi masu sallama. Ko kallon arziki bata samu ba a gurin balle a dawo lafiya yadda muka saba yi idan tazo gurina sai mu dade muna zuba hira dasu. Ba yar uwata ba a lokacin duk wanda yayi gigin tara ta ya fada min wanan magana wanke mai shi zanyi tas don idona da rufe. Sai kuma yadda na yarda da Jamil ya sa ban iya gano illar shi ta ko ina aka fito da zancen sukan shi a gabana. Don haka kowa yaja bakin shi yayi shiru tunda ban bari a fadi har wasu na zuwa gida yi min jaja suna muna barka da arziki. Niko sai rabbata masu labarin yadda abin ya faru nakeyi kamar a gaba hakan ya faru yadda nake bada labarin kamar yadda ya fada min. Kwana biyu muka fara dan ciye dan kudin dake hannu na ina dan juyawa ya fara karewa sai kama kama ya rage munayi. Gadai miji yaje nema amma haka ya dawo muna hannu rabbana babu ko ledan burudi ya dawo muna gida. ZAINAB IDRIS MAKAWA 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Ya gama yaudaran shi na yan fashi sun tare shi a hanya sun kwace komai ni kuma na gaji na sake yanzu. Baifi wata daya ba yace zai koma ya nade ya juya zuwa inda ya fito naci gaba da rayuwana a yadda na saba a baya. Ba wayan shi ba sako tunda ya tafi don haka fadi tashi ya taso ma rayuwana don nema wa kaina abinda zamu ci. Tunda ba zancen sutura bane yanzu gare ni sai dai na abinda zamu ci wa cikin mu kullun shine abin yi gare ni. Ina kallo yan uwa ba zuwa buki ni ba hali inje don ko nace zan tafi babu abinda zan sa a jiki babu wanda zan kai gudu mawa a guri bukin. Haka yasa na daina duk wani hurda da ya uwa na yanzu sai zagina ban so zumunci ban shiga dangi ga dai magana nan kala kala a kaina ba dadi anayi. Ni kuma ni nasan abinda nake ciki da miji na ba wai a cikin dadin rai nake ba gashi ya raba ni da kowa daga cikin yan uwana. Babu mau zuwa gurina da sunan zumunci kamar yadda nima ban zuwa gidajen nasu da sunan yin zumuci. Wahala yakai min wahala dole na nufi gidan mu dan samun mafita a kaina bayan an gama saurare na. Anty tace to hadiza ke ce da abin haushi duk abinda akai maku a baya baku gani ba an taimaka maki kin kwashe kin bashi. An maki fada kin kwashe kin fada mashi abinda kowa ya fada maki gamay yana kallon kowa a hankade don kin gama zubarwa yan uwanki da mutunci a gaban shi. Ina zaune ina hawaye banda bakin magana don duk abinda take fadi haka akayi babu karya a cikin shi. Muryan ta ne ya katse ni tana fadin ko yanzu aka taimaka maki kara bashi zakiyi don dawowa zaiyi ya lalabe ki ya kwashe abinda kika tara. Da sauri nace aa wallahi anty ai yanzu nayi wayau wallahi, tsuki taja bata bari naci gaba ba take fadin. Dama duk wanda ya danki na miji a matsiyin uba itako zata mutu maraya a duniya. Don namiji bai da tabbas baka daukan amana ka mikawa namiji hundred pacent kun nuna dan uwan mahaifin ku ya cuce ku yana cin amanan ku kan dan abinda aka bar maku a duniya. Idon ku ya rufe mazajen ku sun maku huduban shedan kun haye kunyibwa kowa cin mutunci duk mu nan kuna muna kallon mayaudaran ku . Abinda aka baku muke so muci daga gare ku hakan yasa kuka jaye daga wuri mu dama sun shirya hakan ne do su samu kafan yaudaran ku ba tare da kowa ya saka maku ido ba. Don ku zauna daga ku sai su suci karen su babu babbaka ko gashi sun kuma ci tunda wawaye kuke. Nasan ko waye jamil fiye da sanin ku na karanci wanan yaron tun yana karami nasa ko shi waye bake yake so ba hadiza tun farko abinku yake so. Ya kuma ci yanzu ma abinda baki sani ba shine ni zuciyana bai kwanta da wanan tafiyan daya ce yayi ba na zuwa wai neman kudi. Kaina na dago da sauri ina kallon ta da mamaki don ina tsoron kalamin anty don kamar mai baki take da wuya ta fadi bai faru ba. Da sauri na tare ta ina fadin wallahi anty yana abuja abokin shi ma da suke can tare ya fada muna tare suke. Na tare na hanata magana sai naga tayi murmushi tare da mikewa ta dauko dubu biyar tace shi zata iya bani a yanzu inyi hakkuri. Idan baba ya dawa zata fada mai halin da ake ciki don a samu abinda aka taimaka min dashi din ina kuka nayi mata godiya na koma gida. Ga dai anty tana nuna muna tankar ita ta haife mu amma mu har lokacin son mazajen mu ya rufe muna ido. Bamu yarda su sakamu a hanya da zaran an dauko zancen mazajen namu yanzun ne zamu nuna bacin ran mu gun mutum. Dama ita kadai ce mai fada muna gaskiya mu kyale ta itama din dai bata da zuciyane irin abinda muke mata tana shanyewa. Nayi iya bakin kokarina i bar fada mai zancen yan uwana akanshi sai dai dadin hira bai bari na daina ba do ban sani sanda za kwashe in fada mashi komai. Ba laifi baba ya dawo sai ga sako abinci harda kudi da sauran tarkace an kawo min naji dadin wanan sako don an samu banda komai a gidan dama. Ranan da naje godiya a gurin baba na samu anty ta dawo daga aiki take ce min hadiza zuciyana yana ban mijin ki yana tare da wanan matar daya musuluntar har yanzu. Ina dariya nace Anty ita da take nan jahar shi da yake abuja zaune ba tare suke ba gaskiya tace to Allah yasa . Ban dade ba na bar gidan don raina ya baci da zancen sosai sai hakkuri na shanye har zuwa lokacin da ya dawo garin. Wanan karon ba laifin irin yadda yake yi tun a waya yasa nasa zai dawo muna da abin arziki irin tambayan yara shi tsaraba da suke so ba kamar wancan karon ba da ya dawo da karya yan fashi. Na san da zuwa shi don haka nayi kwalliya kamar yadda mata keyi idan mijin su yayi tafiya zai dawo gida. Irin su kitso kumshi da gyaran daki da gida duk nayi shi kafin ya dawo daga tafiyan. A cikin dare ya sauka muna don haka ba kowa ne yasa da zuwan shi garin ba irin yadda ya shigo muna ana shigo da katon ghana most go yasa ni jin dadi a raina. Ga doya da manja da yashigo dashi duk da ba wani mai yawa bane sosai hakan dai yayi min dadi sai da nakai mai ruwa yayi wanka kafin ya bude jakkar bayan ya gama cin abinci. Kowan mu ya samu tsaraba dagani har yaran dadi ya kashe ni nan nake fadin dama ance mahakurci mawadaci da ace na dauki zuga da yanzu nine a ciki. Da sauri ya tambaya zuga akan may sai nayi shiru ban iya fada mai komai ba don na fara hankali da halin shi. Yanzu idan na furta mai sai ya sani a gaba dole na fada mai wanda ya fadi maganan yasa nayi shiru da bakina don ban son ince anty ce ke hasashe ba can yaje ba wai. Dadi dadi muke sai dadi muke ci kwana biyu har yan haya suna gulma idan ya kwanta bai tashi tun barcin dare sai karfe daya ko biyu na rana. Babu zancen sallah ga al,amarin shi don ko nayi mai magana ma bai sallah don haka na kawo ido na saka mai. Idan yayi wanka suna da wani daba a unguwar dake kallon titi ana suke zama har dare na dauka tafiyan da yayi ya sa ya canza rayuwan shi ne akan yawon banza. Ashe abin ba haka bane kudine baida ya kawo hakan ya dawo ya lafe min a gida niko ina ganin yadawo da kudade masu yawa yadda naga yana muna tunda neman kudi yaje. Ashe ban sani ba adashe yayi da albashin shi ya dan tara yadawo dasu yana muna karyan yaje nema a nan ba gaskiya bane. Mutane sun sani nice dai sakaran ban sani ba lokacin nake yarda da karyan shi idan ya sharara min sai in hau in zauna kan abinda ya fada min din. Haka muke zaman duk in yazo baifi yai wata daya ba ko sati uku ya koma inda ya fito da sunan neman kudi yake a abuja. Ana son fada min gaskiya sai dai ana gudun surutuna wajen shi injawa mutum magana akai yasa kowa yayi shiru da bakin shi aka zuba muna ido aga iya gudun mu. Sana,a kan ina dan yi don in samu kwabon kashi da diyana kar mu gani a gurin mutane musanman abinci do ban yarda suje daukan ido gurin yan hayan gidan mu. Wanan zuwa ya dade bai koma ba muna zaune dashi a gida tunda yazo yayi sallah tare damu yake zaune a gida. Bai komai sai dan buga buga a cikin gari mukeyi har ni don rufawa kan mu asiri a gari ba laifi tunda albashin shi yana zuwa duk wata. Dashi muke samu muna karyan ci bashin da yake turani in samo muna wani abin don bukatan mu na gida damu da yarad mu. Akwai wani lokaci da akai albashi ya nuna min ba kudi gashi yasa naciwo muna bashin shinkafa a guri makwaciyar mu har mudu goma. Gashi dajin anyi albashi ta fara aiko min da sako in bata kudin ta shi kuma ya nuna min ba kudin sai dai tayi hakkuri har wani wata. Cikin dare ina barci nake jin hayaniyar mace a kofan mu da sauri na mike ina saurare ashe bayeraban dake sai da kayan sanyi nasha ne a unguwar mu tazo bin bashi itama take wanan hayaniyar dashi haka. Ni dai ban kula ba don haka ban ma fito ba tunda ba maganata bace nima tawa ta isheni dashi ai. Sai da suka gama ya bata hakkuri bayan yayi mata alkawarin zai samu abinda ya rage mata bashin dashi. Da ya shigo gidan ne nake mashi magana kan abinda yake baida kyau tunda anyi biya ya biya mutane kudin su kawai zaifi. Fada ya hauni dashi waini zan koya mai abinda zaiyi ko may ko nafishi sanin duniyane inda yake shiga ba nan yake fita ba. Dole na kyaleshi na kwanta raina babu dadi ga wanan halin na Jamil ace mutum baya tsoron bashi har wurin mata yake cin bashi a waje. Fitina bai kare ba da safe ina shirin dora wutan abin karyawa sai ga mai kudin shikafa da kanta ta wai ala dole kudi ta take so a lokacin tunda anyi biya taji. Na rasa abinda zan ce mata ga matan gidan mu sunyi shiru da mazajen su suna sauraren mu don haka na fada daki na samay shi. Nasan ba barci yakeyi ba yadai lafe ne kwance nake fada mai mata mai shin kafane ta shigo ya ce yaya nake son yayi da ita shi. Daga waje kuma ina jin tana fadin ke nake jira fa don akwai inda zan tafi daga nan din ban samu kulawa daga gare shi ba dole na fito na bata hakkuri zan kawo mata zuwa anjima ta tafi. Ina aikin da nakeyi ina tunane a raina inda zan samo kudi in biyata tunda ni ta sani , har na gama ban samo mafita a raina. Ina gamawa nayi wanka na shirya lokacin shi har ya karya yayi sakkon fita daga gidan ya barni a zato shima neman kudin ya fita yi don mu biya bashin. Nima dai ban zauna ba fita nayi zuwa gidan yar uwata yar gurin baba kabir don bamu da nisa nida ita can naje na fada mata halin da nake ciki da kudin mutane. Sai da tayi min kwakwazon don may nasan halin mijina zan yarda in biye mashi inje ci mai bashi duk nassn ai ba biyana zaiyi ba . Da kyat da lalami ta aramin dubu biyar bayan nayi mata alkawarin zan biyata a cikin sati biyu abinka da dan uwa ganin yadda nake kuka ta tausaya min ta bani aro ban ko shiga gida ba da kudin naje nakaiwa matar kudin ta saura kuma nadan sayo abin bukatan gida dashi. Shiko bai shigo ba don yasan ba abinda zamu dafa da rana don haka bai damu ba ko yaya zanyi da yarana. Sai dare sosai ya shigo gidan yana wani cin magani dani nima ban kula shi ba hakana na kwanta na kyale shi. Ko tashin zancen kudin matar bai min ba ga kwanakin da na dauki alkawari wa yar uwata yana karasowa na bata kudin ta. Hankalina ya tashi sosai don haka na yanke shawaran zuwa gidan mu wurin anty don ta rokan min kanne na su bani wani abu in samu in biyata kudin ta. Da naje gidan kunya da nauyi ya hana in mata magana kamar yadda nayi niya sai ma itace taga damuwa a tare dani take tambayana ? Ko lafiya ta ganni a haka nake cewa ganinan dai anty sai kuma na fashe mata da kuka don ban san ta inda zan fara mata bayanin abinda ke tafe dani. Hakkuri ta shiga bani tana fadin hakkuri zakiyi hadiza matsalan mijin ki kin saba dashi nace cikin kuka anty bashi yasa naje naci yaki biya. Nan dai na kwashe komai na fada mata muna cikin magana ne sai ga kanni ya shigo dakin kallo daya yai min ya kawar da kan shi gareni. Don yanzu haushina suke ji suma ga shi sun gane Jamil yayi amfani damu mun saba da iyayyen mu masu kaunan mu tsakani da Allah. Don yanzu shekaru sun kora sun yi wayau fahintar wani abu daga iyayyen namu don haka suke jin haushi har dani baki daya. Anty ce ta iya mai magana akan abinda ke faruwa dani da Jamil din yace cikin tsaki anty bar wanan da kike gani ko yanzu ta samu kudi kara bashi zatayi wallahi. Ai tasan halin mijinta take biye mashi tasan mayaudari ne macuci tunda anyi daya anyi biyu yanzu jira yake na uku yazo ya cinye shike nan ya korata. Naji haushi maganan shi don ina neman abu a gurin su ban tsaya ya fada min maganan banza ba nan na haushi nima don ban son mutum yai min zancen mutuwan aure na ko kadan. Tunda nasan kowa hakkuri yake da auren shi kowa kuma da irin kaddaran da yake gani ga rayuwan shi ni da wanan na dogara na bashi amsa. Anty ce ta katse ni da fadin in bi a sannu tunda nema abu muke a hannun shi dole na sassauta harshena gareshi. Da kyat da sudin goshi ya yarda zai bani amma da sunan aro idan na samu zan biya shi abinshi sai bayan ya yarda ne ya kawo maganan kudin hayan da Jamil din ke cunyewa yanzu. Don lokaci ya kusa na biyan kudin yan hayan gidan mu don ba zasu yarda ina cinye kudi ko wani shekara ba da mijina mu kadai. Yace karshen shi ma ba nike cin kudin ba shine mai cinyewa ya kyale kowa ranan dai kanina ya fada min magana iya son ran shi sai da anty ta taushe ni. Na yace in tafi idan ya ciro kudin zai kawo min har gida da yamma ina komawa gida na samu Jamil yana cika yana batsewa wai na fita yawo na bar gida ba kowa. Kyaleshi nayi ban fada mai abinda naje yi ba don in har ya sani sai yasan yadda yayi yaci wani abu a cikin dubu goman da za a aramin din nan. Do haka naja bakina nayi shiru inda nayi sa, a koda kani yazo ya dan fita har ya bani kudin na boye bai gidan. Sai dai kafin ya tafi ya shigo ya samay mu muna hira ya zauna suka gaisa a cikin hiran ne yake tambayan wai yaushe ne sauran kudin mu zai fito har yanzu shiru. Amsan da Baffa di ya bashi ni kaina naji mamaki don cewa yayi dashi kudi tunda suna nan ko yaushe sukazo daidai ne. Don masu kudin ma basu damu kanar masu son cin banza ba ai yana fadi haka ya tashi yace zai tafi nayi mai sallama shi bai tanka shi ba. Yana fita Jamil din yace naga yanzu yaron nan yana son ya raina ni ko don yaga na damu da damuwan ku ne ko yana ganin yanzu ya kawo karfi ne shi ? Ni dai ban bashi amsa ba na share shi yaci gaba da fadin ni zai cewa masu son banza ke nan mune masu jira muci banza ke nan ko ? Ni abu ya damay ni ban tsaya bin ta nasa ba don tunanen maganan yaron kan kudin hayan da yayiwa anty ya damay ni a raina sosai . Tunda yace basu yafe min ba tunda ba ni kadai keda gadon kudin ba balle mijina yai ta karbewa yana ci shi kadai. Don haka wanan shekaran shi zai karbi kudin da kanshi gurin yan hayan nako san akwai tsiya da Jamil ke nan tunda ba kunya ke gare shi ba kan kudi da kowa yana ja tunda shi ya zama cima zaune. Ina samu kudin nan washe gari naje na kaiwa yar uwata kudin ta nan ta dorani ga sana,an da zanyi da sauran canji na daya rage min cikin dubu goman da akace an ara min ne. Na fara juyawa a hankali tunda banda komai ya karbe duk dan wanda nake juyawa a baya . Dan zaman ma da yake yanzu a gida sai ya gundure ni na kwammace ace ya fita din da yake yi yanzu zuwa wani gari neman kudi. Ko lalura zai rage min a gidan don na gane nisa da nisa dashi yanzu ya fiye min dadi da idan yana gari bai yi tafiya ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Sannu sanu zance ke zuwa min ban yarda akan jamil da dadiron shi wai basu rabu ba sun canza gari ne har yanzu ya tare da ita. Da farko wanan zancen ya tayar min da hankali sosai don har yangida mu naji zancen a gurin su sai ban yarda da su ba. Sai dai abinda ke daure min kai kuma shine yanzu zaman may yake a gida hakan ya kara ban kwarin gwiwan rashin yarda da zancen. Karshe dai na kasa hakkuri na tunkare shi da maganan da nake jin din a bakuna da yawa na mutane. Nan ya shiga fada yana zagi sai na fada mashi wanda ya fada min don kotu zai kai mai shi kara hankalina ya tashi yadda naga yana fadan nayi ta bashi hakkuri. Yace daga karshe idan na sake kawo mai wana magana ni zaiyi karan bata mai suna inyaso zan fitar da wanda ya fada min din. Hakan yasa na yarda dashi na basar da zancen duk wanda ya tare ni da maganan sai i nuna mai ba gaskiya bane wanan magana . Gani ban iya boyo ba don har gidan mu naje na fada masu yadda muka kwashe dashi din kan maganan. Nan sukai min caaa a kaina suna fadin yasan su suka fada yasa yace hakan da in kyale shi yai karan nasu daga wanan lokacin suka kara daukana shasha wace dai bata san abinda takeyi ba ma. Kowa ya kawo ido yasa mun a kan zancen ga gaskiya ana gani aka kyale ni dashi mu tafi a hakan . Kunci da talauci ya isheni babu sauran inda zan tafi in kai kukana kuma a tausaya min don ansa ko an bani shi zai karbe. Yasa yanzu babu sauran dan uwa da ke tausaya ma al, amarina kuma sai dai irin su baba kabir dana zama ma kamar dolen shi. Don abinda yake muna bai ko yiwa "ya"ya cikin shi gaskiya don yana matukar tausaya muna sosai a rayuwa . Ba dai yadda zaiyi ne mun riga da mun zabi mazajen mu dasu yasa suka saka muna ido sai dai taimakawa idan suna da halin yin hakan. Ga yanzu abin na baba kabir yaja baya sosai do yanayin da kowa na kasan nan ya shiga yanzu shima ba samu yake kamar can baya ba. Babu sauran abin kwarai da yarage min a daki sai kujerun dake falona kawai kula na kwarai da idan nayi baki ko na Jamil banda na fita kunya a gidana. Haka nake ta manejin rayuwa a wahalce don rashin da yai min katutu a gidana kamar ni kadai ce iyayyena suka fara mutuwa a duniya su barni. Yau ma ina kwance saman dogon kujeran falona tun safe nake aikin sakawa ina warwara a zuciyana don rashin samun mafita gashi ko kudin sayen garin kwaki banda shi. Balle shika ko wani abinci da zamu sarrafa a gidan. Shawara na yake a karshe in sayar da da gadona daya saura min a dakin wands shi kadai na saura dashi daga cikin kayan da akai min tun gida. Duk da ina fargaban hakan a raina amma kuma shine kawai mafita a gareni yanzu don in rufawa kaina asiri a gidana. Tunda ba kowa ke shiga min dakina ba dama iyakar bakona falo don ko banza ina jin kunyan a shigo aga dakin hakana ba katifan kwarai a dakin. Ya shigo nake fada mai shawaran dana yanke sai washe baki yayi yana fadin tuntuni naso in baki wanan shawaran ina gudun ki ce wani abu. Yanzu ki samu mai sayen gadon ne nace a,a dama kai nake jira ja shigo in fada ma idan ka yarda sai In nemi mai saye din. Yace kiyi ki shirya to ko za a samu ya shiga a lokaci nace ban samu abinda na dan dafa muna ba yau gaba daya ma ban karya ba tun safe. A, a ina ko da dari biyar barin baki ku samu abinda kukaci tunda ga kudi zasu dan shigo ya sa hannu a aljihu yana kumbiya kumbiyan ciro kudin kada in gani na tabe bakina tare da kawar da kai gefe daya. Ya ciro kudin yana miko min duk da lankwashe kudin da yayi alama ya nuna ba shi kadai bane a aljihun shi. Ni dai na karba tare da daukan hijjabina zan fita don samo muna abinda zamu sarrafa muci da rana don yanzun safiya ya wuce. Inda na barshi zaune nan na dawo na samay shi yana zaman jiran in dawo ina shigo yake ce min wai nace ai ya kamata a kwabe gadon kada tazo ta samay shi a kafe tace yana da wani bakasu kuma. Nace hakane kuma fa yanzun dai girki zan dora idan nagama sai in kwabe kafi in tafi yace bari dai in tayaki kwabewa zaifi sauki don in rage maki aiki. Na fita ya shiga aikin kwabe gadon kafin in gama hada abinci har ya gama ya fitar da gadkn wajen gidan ya jingine su. Arzikina daya ta kofan baya ya aje kayan gadon ba tare da yan haya gidana sun sani ba balle abin yazama abin magana. Bata na gama aikina muna zaune muna cin abinci yake fadin idan sauran kudin ku sunzo sai ki samu gado na zamani mai kyau na yayi ki saye. Ina mamakin Jamil ba wanan ne karo na farko da yake cika min baki kan kudin mu idan ya fito ba sai dai idon kufin sun fito kuma sai abi wani hanya dasu da ban sani ba. Na samu wata dillaliya mai saye tana sayarwa na kayan daki muka shirya da ita zata zo taga kayan sai tai mashi kudi idan zamu shirya. Kamar yadda tace din tazo taga gado tace kuma yayi mata nan muka fara cinikin kayan gado da ita. Dubu talatin ta saye da kyat ta karamin dubu uku sama nace ta kawo kudin an sayar mata take a gurin ta lale mun kudina ta bani ta fita neman wanda zai kwashe matasu Har aka fitar ba wanda ya sani a gidan shine rufin asirina saidai mai washe gari ina karyawa da safe sai gashi ya fito falon . Ya samu wuri ya zauna yana fuskanta na nasa yana da magana ke nan si kuwa bamu fi minti ralatin ba ya kawo zancen kudin. Yana fadin may kika yanke zaKiyi da kudin gadon nan dago kai nayi ina kallon shi nace. Sana,a nake son yi da wanan kudin ya gyara zama yans fadin sai nake ganin da zaki ban in fita garin nan zuwa wani gari da zaifi. Dago kai nayi tare da dakatar da abincin da nakeci ina kallon shi ya wani gyara zama yana fadin ko baki yarda dani bane . Abinda mutane ke fadi zaki dauka ni ba komai yasa nace hakan ba kinga ni wanan zaman da nake haka ya isheni. Gashi na saba yanzu da sana,a kinga in na fita na juya muna su ba,a san iya albarkan da zasu koma muna ba ai . Nan dai ya dinga kawo min dadin baki irin nasa yana tsarani har na yarda inda yace wanan karon ba Abuja zai tafi ba zai canza gurine. Zuwa bakin boarder ance sana yana daukuwa can sosai kamar may kin ga zama haka bazai yuyuba gare mu yanzu ga yaran nan suna tasawa. Amira na ina son idan na dawo mu sakata makarantar boko ta fara zuwa yakare tare da fadin ko may kikace ga shawarana. Dan shiru nayi ina nazarin sa sai naga maganar shi kuma gaskiyace idan ya fita din zaifi sana,an da zanyi a nan din samu. Sai na buda baki nace hakan za ayi sai kaje da kudin mu gani ko Allah zai sa muna albarka a cikin al,amarin. Wani shu,umin dariya yayi yana cabe yar karamar yar mu tare da fadin mamana babakin ya samu mafita ku tayani da addua, don ance addu,an yara tana kamu sosai. Tun ranan ya fara shiri kwana daya kawai yayi a tare dani ya kammala kudin shi ya bar garin ya barmu a cikin wani sabon wahala kuma. Sai da ya tafi naga wautana daga baya na yarda dashi danayi na bashi kudin yanzun gashi ya tafi ya barmu a cikin wahala nida yara. Nan sabon fadi tashi ya dawo min ina nema abinda zamu ci don ko na omo da sabulu ya ishe ni fama yanzu. Ance anbin duniya baya boyuwa koda ko kai kadai kayi shi ban san inda yan uwana sukaji wai na sayar da gado na ba. Sai ranan da na shiga wurin kanwata yar gurin baba kabiru muna ckin hira ta jefo min zance da cewa ke anty may ya kaiki sayar da gadon kwancin ki kiba namiji kudi yayi tafiya. Mutuwan zaune nayi don ban taba zaton wani yasan da wanan maganan ba sai ni sai shi muka sanda wanan maganan. Gashi yanzu magana ya fito fili har an sani wani irin bata rai nayi tare da faman rantsewa ni ban sayar da gado na bashi kudi ba. Nan dai ta dinga min nasiha akan namiji tana nuna min illolin dake cikin sakar, wa mijin bakin aljihun ka. Banji dadin da akaji wanan zancen ba dukda na nuna mata ba komai a haka ban bashi kudin bani. Dama mukan danje gurin ta mu cika cikin mu ne faman da abinci dagani har yaran sai mun koshi mu dan taba hira mu dawo gida. Amma yau wannan maganan data fito min dashi yasa naji raina ya baci da ita sosai ban ko tsaya yaran sun gama cin abinci ba nace da ita mu zamu tafi. Duk da ta gane nufina sai batai min magana ba a lokacin ta kyale ni na fice hakanan tunda ta fahinci rainane ya baci kan maganan da ta fito min dashi din. Niko damuwa da bakin cikina bai wuce ace yan gidan mu sun san da wanan maganan ba a gida tunda ko ita ta sani ke nan kowa ya gama sani a cikin dangin mu. Waima yaya akayi wanan maganan har ya fito fili akaji shi shine tambayan da nakewa kaina har na iso gida ina wanan tambayan a raina. Ga Jamil din tunda ya tafi wata biyu ke nan yanzu da tafiyan shi ko waya bai kiramu ba balle sakon shi ya iso gare mu. Gashi na dauke kafana ga kowa nawa don gudun wanan maganan kada in je inji takaici a raina don nasan nice banda gaskiya. Tunda munyi da anty cewa idan ya sake sayar min da wani abu da zafizafi in zo gida in fadi a dauki mataki a kan shi. Balle wanan din da dakaina na yanke shawaran sayarwa don sama wa kaina sallama sai ban mori kudin ba shi ya karbe abinshi ya tafi. Ga kuryan dakina ko dakin gwauro ya fishi dadin gani yanzu don babu komai a cikin shi sai tsohuwar katifana dake yashe a kasa da tsumakaran mu da ke gefe daya. Don hatta akwatunan auren da baba yayi min da gidan su Jamil basuyi min ba na sayar nayi lalura da kudin lokacin da naga ya sai min sabbi na haiwan karamar yata. Yanzu ko babu su tunda ya sace ya fita dasu basu dawo gidan ba har wanan lokacin, tundai ina saka damuwa a raina har yakai na hakkura na ci gaba da gudanar da rayuwana yadda na saba a baya cikin hakkuri. Mu ke nan ko yaushe cikin cin taliya ko garin kwaki don shinafi karfi a gidan yanzu. Duk da ba lalaifi indai shi zai sayo muna abinci abinda zamuci musan munci mai kyau yake sawo muna aci gaskiya.. Idan ina ba yan gida mu labari irin yadda nake baku yanzu sukan ce a cikin kudina muke cin dadin da yake sayo muna din ai. Ranan na gama abinda zanyi na kwanta barci da rana sai nayi mafalkin wai gashi tare sa wata mata da yaran su biyu wai nasa ne. Muna fada sosai dasu a cikin mafalki na falka daga barcin sai naga duk na jike da zufa jikina sai kyarma nakeyi kamar nayi fada a fili da wani. Nan na fara tunane a raina har tsawon wani lokaci ina zaune a gurin dana kwanta din ban iya tashi ba sai faman tunane nake kala kala a raina kan wanan mafalki da nayi dashi. Ina maimaitawa a cikin raina yara biyu fa a yadda na ganshi da yaran mace da namiji sai mafalkin yayi matukar tsaya mun a raina sosai. Da kyat na iya tashi na dan watsa ruwa a jikina sai ba samu na danji shakat a raina, sai dai na kasa cire zancen mafalkin a zuciya sai faman maimaita maganan nake har a fili kamar wata zautata dani. Bayan kwana biyu na fita zuwa gidan wanan kanwar tawa inda na samu aron waya na kirashi don abokin shi ya bamu lamban shi ranan. Kira biyu ya daga don baisan ko waye ya kirashi ba don nasan da yasan nice kila ba zai dauka ba ma ban sani ba. Yana dauka tare da fadin hello nace sallamu Alaikum baban Amira don haka yanzu nafi kiranshi dashi, yana jin muryana yace . Hadiza ce a ina kika samu layina wayan wa kika samu kika kirani dashi wani amsa zan bashi daga cikin don ko gaisawa bai bari munyi ba ya hauni da wanan tambayan haka a jere. Babu boyo nace na safiya ce kanwata yace kinje gidan ta ke nan ko nace eh yanzu nazo gidan ta don ta ara min waya in kiraka. Ya sauke ajiyan zuciya yana fadin to yaya gida ya yaran kunji kwana biyu shiru ko nace shiyasa ma na nemi layin ka don muji ko lafiya shiru haka ? Yace lafiya abubuwa ne suka dan cije min kwana biyu yasa ban kiraku ba ban turo maku sako ba har yanzu. Nace yanzu baba Amira don abubuwa sun tsaya sai ka kasa turo muna dan kudin da zamuci abinci dashi ka san fa baka barmu da komai ba ka tafi. Yace a hasale wanan wani irin magana ne haka ni ban fiki sanin halin da na barku a ciki bane gidan ke may yasa baki da fahinta ne wai hadiza ? Inda yake shiga ba nan yake fita ba idan da dane hakkuri zan bashi da yake fadan nan sai yaji har ya gama ban tanka shi ba sai da naji ya gama nace. Ni yanzu dai ka samu kudi ka turo min ko abinci mu samu mu saye ko ka turo min kudina idan ka samu mu sai abinci. Dan shiru yayi kamar mai nazarin magana na sai can naji muryan shi yana fadin naji zan turo idan na samu ya kashe wayan. Kallon juna mukayi dani da yar uwata kai kawai ta gyada tare da murmushi niko mamaki da takaici ya hanani magana. Hakkuri ta dinga bani inda ta hada min dan kayan abinci inzo dashi gida mu dan dafa da yara sai kwalla ya zubo min daga idona. Hawaye shar shar wani na bin wani a fuskana inda na kasa yin magana a lokacin saboda kunci da takaicin da ke cin zuciyata kamar ta fado min nake ji a lokacin. Na kasa fadin komai gare ta haka na mike zuwa gida sai Amira ne ta dauko dan kullin kayan da ta hadda min a cikin leda ta biyo bayana dashi zuwa gida. Ko da na shiga gida na dade zaune a falo na ina sakawa da kwancewa a zuciyata sai dai na rasa mafita a kan hakan. Ni, banga kudina, banga gadona, yanzun na tashi a tutar babu, ya yaudareni, ya cuce ni ya raba nida komai nawa na gado da wanda iyayyena dake raye sukai min na aure . Jamma,a ni haka tawa kaddaran tazo min da aure mayaudarin namiji wanda baida tausayi ko imani akan iyalin shi kanshi kawai ya sani a rayuwu. Nasan masu karatu duk kuna ganin laifi a wanan labarin sai dai ku sani Jamil ya yaudari mahaifin shi ya yaudari wasu maza yan uwan shi balle ni mace, macen ma kuma matar shi da yake ma kallon sakarai ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Yau da gabe muna zaman jiran kudin mu kin san yadda alamarin kudin suke yau zamu gansu gobe zasu fito shiru har wata uku da maganan da baba kabir yayi min yanzu babu labarin kudi. Ga bubuwa sun taru sun min yawa a kaina zuwa yanzun duk da Jamil din bai faye zama damu a gari ba yanzu. Sai yaje ya share wata uku hudu har shidda yanayi ba tare da mu ba a can na ramay nayi baki na lalace babu mai taimaka min a cikin dangina . Baba kabiru ne yanzu shima yana fama da kanshi baida karfi irin na da can baya da zai taimakamin dashi. Sai dai duk da halin da yake ciki ina dan samun kyautan dari biyar dubu daya idan Allah ya ciyar dani daga gareshi. A cikin rashin nan da yake fama yake kokarin ganin ya kwato muna hakkin mu da ya saura muna bin gwaunati a yanzu. Duk wani kokari don ganin kudin sun fito baba kabiru yana bin hakan da karfin shi da arzikon shi don dai ya sauke nauyin da dan uwanshi ya barshi a duniya. Wanan karon kan huduban Jamil a gurin mu bai samu karbuwa ba kamar yadda ya saba yi muna idan kudi zasu fito ya shiga hada muna meeting kenan da fada muna abinda zamuyi. Sai ya kasance wanan karo ba fuska a gurin kanne na ga baki daya nice zai samu ni din ma idan ya tambaya nakan ce dashi ban san komai ba har yanzu sai dai idan an kiramu din. Hakan bai mashi dadi a ranshi sai dai kuma baiyi fushi da zancen ba don yasan zai samu idan sun fito din nan gaba yasa bai fasa tuntuba na ba. A cikin hakan da muke ne yayi tafiya a cewar shi yake fadin ba zai dade ba idan ya tafi din sai bayan ya tafi ne na samu labarin da ya girgiza min rayuwana a gamay dashi. Don ba komai naji ba sai zancen zaman shi da wanan matar da suke zaman da ban san fassaran shi a gurina ba yanzu. Don wanda ya fada min din mijin wata yar uwatace ta jini shi driver motace da ake ma lakani da kanta na daukan kaya shima sun kai kaya garjn ne yaga jamil a can din. Sai dai yana ganin shi yace don Allah ya rufa mai asiri kada ya fada a gida ya ganshi a garin sai dai ya ki fadin yanayin daya ganshi a can din kawai ya furta Jamil mayaudari ne na kwarai. Kowa yasa halin da Jamil ke ciki da wata acan sai dai an rasa wanda zai iya fada min gaskiya a cikin su. Haka muka tafi da rayuwa ina shan bakar wahala a gidan aure na banda tsayayen da zai tsaya min tsaye kan alamarin. Ba komai ne ya jawo min haka ba sai sanin halina da kowa yayi na rashin fahintan da banda shi da kwanciyan hankali yasa kowa ya fita batuna yanzu. Don mutum zai iya zuwa mi da magana ba zan bari ya tadhi ba sai na bata mashi rai ina ganin kowa baiso zamana da Jamil din ne don suna kallo shi a mayaudari. Ni ko hakan na min haushi a raina sosai don may yan uwa zasu saka min miji a gaba da hattara da tsangwama shi kadai haka. Ni dai ko yaya yake tunda bai kini ba ina son abina hakana a wautana hakan shine zaman lafiyan da zamu dore a tare da yan diyan mu mu kadai. Ashe abin ba haka yake ba yadda kake so da wuya ka samu hakan a wuri namiji ban taba kawo wai zai iya kara aure ko hadani da wata ba a rayuwan mu. Sam bani wanan tunanen a raina ko kadan don gani nake haka zamu tabbata dani dashi sai yan diyan mu ba zai kara kallon wata mace ba, da sunan aure har kuma harsu haihu ma. Na mance da abinda sharia ya dorawa maza kan tara iyali rashin shiga mutane ya cutar dani sanin halin rayuwa na yauda kullun dake gudana ga al,umma yanzu. Ko gidan mu zan iya share watanni ban lekasu ba duk da kamar a unguwa daya muke zaune dasu ban damu da kowa ba suma basu damu dani ba tunda sunyi lurar dani ban fahinta ba. Idan do ta anty ce tu farko da ban auri Jamil ba don ta fada kuma ya tabbata hakan da ta fada gamay da mazajen namu. Rashin karfi ga al,amarin namu da bata dashi ne yasa ta saka muna ido kamar yadda kowa ke kallon mu yanzu kara zube don nakasa da muke dashi bamu daukan kowa a matsayin shi. Mu dai mazajen mu sune uwa uban mu da muka dogara dasu muke gani zasu tsaya muna ga komai duk mun ture kowa ga al,amarin mu har kanina Baffa haka baijin maganan kowa daga iyayyen mu din. Autan mu karamin mu ya kama dangin anty sosai ya mayar dasu yan uwan shi na jini suma haka yana zuwa gurin yan uwanta kamar dan ta haifa da cikin ta ya koma. Baka taba jin zancen shi kudin shi ma yana hannun baffa ko kwandala zai cire sai da yardan baffa din don tsamay kowa da mukayi cikin al,amarin mu. Suma din ido suka sa muna tunda sun gane muna zargin su da dukiyan mu da muke ganin ya ishemu rayuwan duniya ba mai yarda ya rabe mu muce abin mu yake so yaci. Duk da nasan ba kudin nake da shi ba bai sa na bi yan uwana na jini yadda ya kamata ba ina ganin duk basu son mu sai diyan su suke so kawai. Wanan ya kara ja muna bakin jini a cikin dangi ko ance abina ya tashi zakaga ana ja da baya ba mai kullawa sosai sai yan gidan baba kabir dana zama ma kamar dole su. Babu yadda zasuyi dani haka yaran su sune masu lekani jefi jefi don sun mafi zuwa wirina akan yar uwarsu don haka kuma idan sun zo zan saka su aiki ko in aike su suje min ko na tambaye su kudi su bani idan suna dashi duk da kanana ne sosai kuwa. Jamil ya dawo inda ya kwatanci biyan kudin yan hayan gidan mu yayi a lokacin ya dawo yasa su a gaba sai da suka bashi ba tare da sani na ba. Sai bayan ya karba ne yake fada min sun bashi kudin ya karba nan na nuna mashi kuskuren taba kudin da yake son yi don ba ni kadai keda kudin ba ya sani. Nan ya hau fada yana fadin ko bani kadai bane ai nike wahala da gidan da sauran su da dai naga yaki yarda da maganana na kawo ido na saka mai da kudin yayi yadda yake so dasu. Ba a sati biyu ba da ya karbi kidin sai ga kira daga wurin kanina Baffa yana tambayana lokacin biyan kudin yan hayan mu yayi fa. Nace sun biya sati biyu daya wuce ko yace kudin suna ina nayi shiru ba abinda zance dashi lokacin don ko banda su a gurina. Nan ya shiga fada sai abinda ya fito a bakin shi dadai naga fadan yayi yawa ne nake fada mai gaskiyan wanda ya karbi kudin bani bace. Nan ya kara hawa yana fada sosai yace ba zasu yarda ba dole in biya wanan kudin idan kudina sunzo na dauka wasa yake sai daga baya na ga da gaskiya yake maganan shi. Shiko gogan da ya shigo na fada mai sa tsaki yaja tare da fadin baida hankali shi yasan wahalan da akeyine kafin su biya kudin da zai fadi hakan. Bajima ba ya tattara ya koma dama kudin ya kawo shi garin ya karba kuma mai zai zauna yi kuma duk wanan tafiyan da yake da sunan yana zuwa neman kudi ne yake yin shi . Muna nan a haka kira yazo min daga wurin baba ban tafi ba na daga yar wayan da kanina dan wirin anty ya saya min nokia . Kafin ya saya min wayan sai da nasha kwakwazo kada in sayar da wayan nan don ba zai kara saya min ba idan na sayar yace. Shina samu ina amfani dashi don wayan yana min rana sosai yanzu na kira Jamil dashi ina fada mai baba na nema zan tafi. Yace lafiya ko nace dashi sai dai idan naje zanji abin da ake nemana dashi din yace sai na dawo zai kira na kashe wayan. Na samu baba a gida bai fita ba baya mun gaisa ne yake fada min mutanen nan sun kirashi zamu shiga sokoto ranan talata sgabiyu ga wata ke nan don haka in shirya tafiya don asuban ci zamuyi . Ina hanyan komawa gidana ne jamil din ya kirani yana tambayana idan naje nake fada mai abinda baba din yace dani a gamay da kiran da yayi min din. Yace okay kawai ya kashe wayan washe gari sai ganin shi nayi kwatsam ya fado min daki nayi mamakin ganin shi don bai sanar dani yana tafe ba a lokacin. Tafiyan dagani sai baba zamuyi shi don haka jamil din ya hau bakin shi da fadin in kula in sa ido idan muje don in gane abinda ke gudana acan. Yake fadin tafiyan da ake dani da Baffa yanzu don may za a cire shi idan ba wani manufa a cikin tafiyan kuma yanzu. Wanan maganan da Jamil yayi ya sake tunzura sauran yan uwana suka fara kananin magana kamar yadda Jamil din ke son yaga ya samu kan mu yana juyawa a hannun shi sai yadda yayi damu. Abin mamaki sai kuma gashi mun koma hannun Jamil din don muna gama waya dashi washe gari kwatsam sai gashi ya fado min da safe . Babu ko kunya don jin zamu samu kudi jamil din ya dawo gari babu shiri nan ya fara kule kule a tsakanin mu duk da rashin bashi fuska da basuyi sosai kamar farko. Yanzun dai ya samu yadda yake so haka yasa ya share wuri ya zauna yana jiran tsamani don baba yace kila da munje ance kudin zai fito ba da dadewa ba insha Allahu. Jin haka yasa jamil din ya mike kafa yana jiran saukan su don ya kwallafawa kudin rai sosai saboda halin da muke ciki a lokacin. Ranan da zamu tafi shida kanahi ya tashi ya dora min ruwan wanka don kada in makara na shirya ga abin karyawa daya sawo tunda dare ya aje min kamar wata basaraka dani can. Munyi tafiya lafiya munje hannu muka sa ga wasu takardu da aka gabatar muna inda matar ta yi min bayanin komai dala dala yadda zan gane komai da akeyi wurin. Bayan mun gama muka dawo a cikin dare don bamu kwana ba saboda sokoto ne zone din mu nan muka cika komai na karshe daga takardun mahaifin mu din na komai nasa. Tun a cikin daren nan da muka dawo ya sani gaba da tambaya nikan ban gane ba yasa nace mai ina ganin kudin milayan goma sha shiddane zasu fito muna. Ihu Jamil din yasa yace kin ga shike nan ai mun warke idan wanan kudi ya sauka muna kuma bamu ba sauran wahala kuma yanzu ai. Duk yan uwana muna murna da yawan kudin da zai fito muna din kamar yadda nace dasu ga abinda na gani a can cikin takardun da muka cika din a sokoto. Yau da gobe muna zaman jiran fitowan kudin kowa ya saka rai yana jiran saukan su a cikin ko wani lokaci da zamu jisu don an gama komai na fannin kudin da ya kamata ayi ko. Jin shiru har sati uku ya wuce yasa jamil din ya fara jan tsuki yana bakar magana kan rashin fitowan kudin akan lokaci ni dai ban tankashi ba iyakata ido dashi kawai. Ranan sai ga wayan baba da rana tsaka yana kirana ina waje ban sani ba ina aikin girki sai jamil ne ya dauki wayan a fitsaran ce ya amsa wa baba da fadin ina aiki idan na gama zan zo. Hakan daya fadi yaba su baba da duk suka hallara suna jirana mamaki hakkuri irin na baba ya shigo cikin gida yana fada ma matan shi abinda jamil din yace dasu a waya. Ran anty ya baci sosai don shi baba kabir da hakkurin shi cewa yayi a barshi wani lokaci su baba musa sai su dawo a raba kudin. A hasale anty tace ai kudin ba ni kadai ke da hakkin su ba don haka ta tayar da yaro yaje ya fada min da baki cewa nifa su baba ke jira duk sun hallara ko. Yaron da yazo yasamay ni ina kwashe abinci yake fada min yadda ran baba ya baci da amsan da Jamil din ya basu a waya ban tsaya jiran komai ba na fada daki na dauko hijjab dina yana kwance a dogon kujera falo yace min. Ina zaki kuma nace kiran dasu baba ke min don ance kowa yana nan yazo ni ake jira in zo ina fadin hakan na juya na fita tare da kanina daya zo kirana muka tafi. Tun shiga gidan naga bacin rai a fuskan su na nufi falo bayan mun gama gaisawa dasu ina shiga baba musa ya tare ni da fadin. An buga maki waya mijin ki yana fadin wai aiki kike wazai ci kudin naki bayan shi da zai fadawa mutane maganan banza a waya tunkan a haife shi matan mu suke aiki ai. Baba kabiru ne yaba baba musa hakkuri yabar maganan don fada yake min sosai kan Jamil din da bai ganin kowa da mutunci a cikin su yanzu. Baya baba kabiru yayi bayani sai aka fara gabatar da kudin wanda milayan hudu ne da dubu dari takwas bayan wanda aka cire dari uku akaba wa yanda sukai muna hidima acan sama. Ga yadda komai ya koma sai da hanya yanzu idan kana son abinka yazo hannun ka kuma baba bai yi hakkan ba sai da yardan mu dukan mu. Nan na fara ajiyan zuciya ina saukewa a fili don ba haka mukai tsamani ba bani kadai bace har kanina baffa a cikin halin da yake ke nan don bamuyi tsamanin ganin kudin a haka ba. Muryan baba ne yaci gaba da bayani kan kudin inda yace idan an hada kudin dana farko sun kama miliyan goma sha daya ke nan cif. Ya rufe da addua ga iyayyen mu da nasu mahaifiyar aka shafa sai dai har lokacin bamu a cikin hayacin mu ko kadan. Sai baba kabir ne ya farga da halin da muke ciki yake tambayan mu ko yaya akayi sai kanina Baffa ya kalle ni yace kiyi magana mana ke. Nace ni mai zance yanzu tunda haka aka bamu da sauri baba kabiru ya tambaya yace yaya akayi ne ko kudin basuyi maku bane? Baffa yace baba kudin nan fa miliyan goma sha shidda ne zasu zo muna ke ko ba haka kika gani ba a can kika sa hannu ? Na gyara zama ina fadin hakana na gani an rubuta da matar ta ban takarda da muka sa hannu. Innalillahi baba kabiru ya fara maimaitawa a hankali yana girgiza kanshi tare da dauko wayan shi yana bugawa lokaci guda cikin tashin hankali. Baffa kanina yace don may ba zakiyi bayanin abinda kika gani kika sa hannun ba a gaban kowa kina wani noke noke da kai kuma. Baba musa ne ya tambaya nawa ke kika saka hannu a ciki a can a takardan nace miliyan goma sha shidda ne na gani a rubuce na bashi amsa daidai lokacin da aka amsa kiran da baba kabir yayi ga wayan shi da ban san wanda ya kira a wayan ba lokacin. Anan kuma yana jin abinda na fada ya furta subbahanallahi hadiza kiji tsoron Allah ki fadi gaskiya nace. Wallahi baba shi nagani a rubuce ni ba wani ya fada min ba don har matar da ta bani takardan nasa hannu ta nuna min nagani. ZAINAN IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Jamil bai dawo ba sai da ya share wata shidda cif a can ko wanan dawowan don sallah karama daya gaba to ne yazo. Yadda ya tafi haka ya dawo min babu kudin gadona babu karuwa daga gare shi ni na tashi ga tutar babu ke nan yanzu. Duk cikin abinda yake min wanan sai yafi ci mun rai fiye da sauran don kudin gadon yafi tsaya min a rai. Ya dawo yana wani daure min fuska ko magana ya hadamu cikin tsawa zai mun magana da karfi yana daka min tsawa . Ganin haka yasa naja baya dashi sai dai ranan kanwata da sukazo gida sallah tazo gidan mu shine ya fito suna gaisawa da ita. Har ya jefoni a cikin zancen su harda fita ya sayo masu kayan sanyi na jika makoshi kamar wani na kirki dashi. Bai jima ba ya fita ya barmu gidan sai da ya fita take fadin kai mijin nan naki kamar wani na kirki idan yana wasu halaiya. Murmushi nayi bance da ita komai ba sai na dauko mata wani zance na daban wanda ya shafi hiran gidan mu sai muka shagala. Can lokacin sallah yayi ta mike ta fita don yin alwala ina Allah Allah ta tsaya iya falo kada tace zata shiga min kuryan dakina. Sai dai banyi sa,a ba don tana shigowa duk da na shimfida mata abin sallah a falo sai ta shige kuryan dakina direct don cire unders din ta. Kira naji ta kwala min daga dakin na dauka na wani abu ne sai na shiga tana cewa dani ina gadon ki anty ta tsare ni da idanuwan ta. Kasa amsa mata nayi lokacin take fadin yanzu har gadon kwsncin ku sai da wanan mayaudaron mijin naki yasa kika sayar wai may kika mayar da kanki for god sake ? Wallahi ban ganin laifin shi naki nake gani yanzu don kece mai bashi kwarin gwiwan yayi maki duk wani abinda yake maki.. Haka nazo nake jin wanan kangon da muka saya don gaba mu samu madogara wai ya sayar da naki ya tafi da kudin . Tsaye nake daga kofa ina sauraren ta ban san lokacin da na tafi baya ba suuuu zan fadi tayi saurin rike min hannu daga ciki. Falo ta fito dani tana fadin wai may ye haka ko dama baki da labarin ya sayar da kangon gidan da aka sai maki ne tana fadi tana kokarin zama a kusa dani lokacin. Wasu hawayen da sukaki tsayawa suke zubo min dafa idanuna lokaci guda na kasa controling din su in mata bayani. Taci gaba da fadi dama tunda nazo naji wanan zancen hankalina ya tashi gaki da yara mata a gaban ki yanzu kin san lalurar diya mace da kashin kudi ne komai na ya mace kudine tun tana yarinya. Duk bayanin da takeyi ban iya bata amsa ba ko daga kai in kalle ta banyi ba asalima na lula wani duniyan tunane ga baki daya. Sallah ta tayar har ta kare ina gurin a zaune ban iya dagawa ba waya ta dauko daga jakkar ta ta kira baffa kanina yazo ya samay mu agidan. Bai jima ba ya iso nan takw fada mai abinda ke faruwa dani numfasawa yayi tare da girgiza kanshi yace shike nan yana murmushi . Maimakon in ji haushin mai laifi Jamil sai haushin ya koma ga wanda baiji ba bai gani ba Baffa. Ban san lokacin da nace zakayi dariya mana tunda ba kai aka cuta ba yace nikan ai ya gama cutana wallahi . Sai dai ke ki zauna watarana sai ya sayar dake da yayan ki kuna zaune za a ce kuzo ku tafi ya sayar daku ya amshi kudin ku. Nikan yanzu wallahi kar nake kallon shi duk wani sallon yaudaran shi na sani tunkan ya min shi sai dai ke da yake tsarawa zai cuta amma bani ba. Ya mike har ya fara tafiya ya juyo yana dadin kuma bari kiji wallahi sai ya biya kudin wanan gidan daya sayar maki ko muyi sharia dashi wallahi . Yana fadin haka ya fice abinshi ya barmu zaune kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi zagi kan ranan ya sha,shi kwado kwado ba wurina ba wurin kanwata ba da tafini ma jin takaicin shi lokacin. Bai dawo gida ba har ta tafi kamar yasan muna jiran shi har ta tafi abinta sai dare sosai ya dawo ban jira ko ya zauna ba nace. Jamil may kake so da rayuwana ne wai Jamil may nai maka kake bina da cicin duduge na hakane ?. Ke ya fada cikin wani tsawa ya jiyo yana kallona tare da fadin wani irin magana kike fada min haka wai ? Na fada maka mayaudari kawai azzalumi na yarda da kai nabar kowa nawa saboda kai amma kazo ka cuce ni dan gidan da nake barazanar ina dashi don yaudara ashe ka sayar ban sani ba. Wani irin kallon mamaki yai min a lokaci guda yana mamakin yadda naji wanan maganan da yake ta boye min wata da watanni. Jin ban yi shiru ba yasa yace na sayar din idan ban sayar ba kina da kudin da zaki karasa ginashi ne komay. Ranan kaca kaca mukayi dashi har da dukana yayi kan abina saboda irin kalaman da nake fada mai masu daci duk abinda yazo min a baki fada mai nakeyi. Sai da yan hayan gidan mu suka rabamu a cikin daren nan abinda ba a taba yi muna ba wani yaji mu muna rikici irin haka. Asuban farko na nufi gidan iyayyen shi duk da yanzu ba shirin nan da mahaifin shi ke yi dashi irin baya can tunda ya yaudare shi kan kudi. Mahaifin shi ke nan balle ni haka dai na daure na tafi gidan nice na tayar dasu da barci ranan na shigo da kukana wiwi . Cikin tashin hankali suke tambayana ko wani abu ya samu dan nasu ne a cikin dare zama nayi nai masu bayanin komai dake faruwa. Sai tsuki mahaufin nashi yayi yana fadin wanan ai ba yanzu kuka fara ba ko don haka kije ki hakkuri ku shirya kan ku. Don ko biya akace yayi baida kudin biyan wanan gidan kin sani tunda ya mayar da kanshi mutumin banza a cikin yan uwa. Ban gane komai ba haka na juyo na dawo gida raina bace ina danasanin zuwa wurin mahaifan nasa. Ina dawowa gida na samu wani rikici a gida mu don kanina Baffa ne ya bugo sammako zuwa gidan mu ya samu Jamil din da tashin hankali kan maganan. Rikici sukayi sosai da kanina din kan sai ya biya wanab kudin shiko yana fadin ina ruwan Baffa din cikin magana mu. Shima ya rikice mai sunyi fitina sosai ranan tsakanin su sai da Jamil din yaje ya kira mijin kanwata suka zo tare aka hade nan tare aka aje magana yace zai biya idan ya samu kudi. Haka aka aje maganan rayuka dai basuyi dadi ba don Jamil din yan uwana sun bashi mamaki sosai ranan don basuyi mai ragowa ba. Haka dai muka hau sama muka fado yana ta faman fushi dani da kowa nawq da yazo min yawon sallah bai sakewa dasu koda sun gaida shi sai kace bashine mai laifin ba. Abinda ban sani ba shine jamil ya na zaman rayuwa can da wata yana yaudarana anan shine yake kwasan dukiyana yana karya dashi. Kanwata diyar baba kabir ke fada min wanan maganan da tazo gidan mu gaidani da sallah maimakon in kwantar da hankalina in fahinci may take nufi. Sai na tare ta da masifa kuma ina fadin yace wanan karya ake mai don yace duk wanda yaji yana wanan maganan sai yayi kotu da mau shi. Tace tau tau nayi shiru anty hadiza dama nima naga abindai tayi yawa ne yasa nace haka tana kokarin tashi tsaye tana saka hijabin ta a jiki. Haka ta tafi tana tsaron in kwashe in fada mashi bata san bamu cikin dadin raima dashi ba lokacin. Don bayan kanne na da muke ciki daya dasu lokacin ban yarda na fada wa wani wanan maganan dake cina ba kaf a cikin dangin mu. Waini ban son kowa yaji aimin dariya da gwai tunda naki uban mu na zabi mijina fiye dashi din yanzu ashe abin ba hala bane. Abin duniya baya boyuwa don kowa kallo na yake da maganan har baba kabir yasan da zancen sai da kangona da Jamil din yayi yanzu. Sai yanzu nake jin zafin aikina da baba kabir ya sama min nace aba Jamil ni yar dadi aure gashi yanzu dan wanda aka samo min ina dan samun rufin asiri an dakartar damu shekara biyu da wattani. Shine dalilin da nake cikin matse sosai ga sana, a ina son yi ba jari mai kwari da zanyi sana, ar dashi hakana. Sana,a sai da jari mai kwaro don idan baka da jari abin bai kai ko ina sai mutum ya cinye kwana biyu da farawa. Zaman jiran tsamani kawai muke na sauran kudin mu kullun ko zai fito mu dan samu sa,ida a gurin gashi shiru har yanzu ba labarin komai. Ashe ban sani ba mijin yar uwata ganin Jamil yaci bulus shima daya tashi sai ya sayar da kangayen kanne na gaba daya su uku ya sai mota dashi da mahaifin shi. Sai dai nasa akwai banbanci da nawa don da niyar idan ya samu sai ya sai masu wani nan gaba yayi haka kunga ke nan akwai banbanci sosai da nawa matsalan. Sai dai lokacin da kanina ya samu wanan labarin hankalin shi ya tashi yasa mijin nata a gaba dole ya samu kudi su sai dai saida ya bashi lokaci. Daya samu ya biya su nasu matar shi ce bamu san yadda suka kare da nata ba har yau don banji tai min maganan komai ba akan hakan. Haka yasa nasan cikin maza akwai mayaudara da dama sai sa, a abindai ke nan don wasu abin matan su bai ishe su kallo ba balle har su taba. Sai dai muka bamuyi dace da bagari ba gaskiya musanman ma ni da komai ci yake babu biyan bukata gare ni ko kadan banda riban kwana dashi da nake samu kawai. Nakan tuna maganan anty da takan fadi kafi auren mu da cewa sun hada bakine su aure mu do sun ga akwai ci cikin al,amarin mu nan gaba. Gashi ko maganan nata yana zama gaskiya akan mu yanzu muna ganin ishara kala kala daga mazajen namu. Muda kan bamuji dadin aure ba ko kadan wallahi musanman ma ni dai baka saye kobo a gidan miji sai dai ga wata na wanan bai kan damay ni. Nidai bukatana shine mu zauna lafiya dashi hakana tunda naji na gani ga auren shi sai dai hakan bai samu ba gare ni tundai yanzu da yasan banda komai da zai kadar nawa. Sai zaman ya koma kamar na dole yake dani don inda sabo na saba da zaran yaga banda komai ya shiga min wulakanci ke nan kala kala a rayuwan mu ina shanyewa ni kadai. Babu wanda zan iya fadaw don zurfin cikine ko may ye ban sani ba do ban iya fadawa kowa halin da nake ciki dashi waini may rike sirin aurena . Haka ma yar uwata take bakajin zancen ta a gurin kowa garama nawa ana gani ana fadi tunda a garin nake zaune tare da yan uwa. Ita ko ba, a ganin ta ma balle a fadi sai ita ke gani tana shanyewa gara ita idan tazo tana zama da anty da ta yarda da ita su zauna ta fada mata matsalan ta ta sama mata mafita nan take na yadda zarayi. Niko ko nazo na fada yanzun anty zatace ba ruwanta inje in hakkuri ko an fada min zuwa zanyi in fada ma mijina ya kama masu rashin kunya. Raina kan baci idan tace haka dani har nazo na daina fadi don ba anty ba duk wanda nakaiwa kukana haka ake ce min kada mutum yace wani abu in kwashe in fadawa mijina. Ranan ina gida da rana ina wanki sai ga baba ya aiko yana nemana wani tsale na daka ina murna don nasan baba baya nema na a banza saida dalili mai karfi. Kafana kawai na wanke na jawo kofana zuwa gida tare da dan aiken muka koma gida wurin kira baba din da yake min. Aikuwa zancen kudin mu ne baba ya nemo ni nan yake min bayanin mutanen sun kirashi akwai wasu takarda da zamu saka hannu a cikin shi kwanan nan don haka in zauna a cikin shiri ke nan . Nafi kowa murnan zuwan wanan kudin duk da kowanan mu a matse yake kan zancen kudin nan dama a cikin mu. Sai dai ni nawa yafi na kowa don ga Amira ta isa shiga makaranta mahaifin ta yace shi sai priravert zai sakata bai kaita na gwanati. Har kaita babban wan mu yace zaiyi wani makaranta dake kusa damu na gwaunati amma ya hana hakan. Wai sai lokacin da ya samu kudi zai kaita makarantar kudi irin na yayan masu shi karya da burgan aiki irin nasa. Wai isan baka isa irin na dan tallaka daya dauki duniya da fadi kamar jamil sam shi baison yin abin kananan mutane. Bai gida ko da baba ya kirani sai da ya dawo nake fada mai kiran da baba yai min din har ya fara fada yana huci wai na fita ban fada mai ba. Saida nace akan kudin mu ne kuma ka bani baki ko baka nan idan an kiranika ace udn in tafi. Sai naji yace yanzu akan kudin ne suka neme ki nace eh baba yace sun kira kudin zasu iya samuwa ko wani lokaci. Sai naga ya kai zaune yana fadin saboda Allah yausje ke nan nace yadai ce zasu samu ko wani lokaci daga yau za a iya kiran mu. Nan fira ya kaure a tsakani mu duk akan kudin da zasu zo muna ya fara sabon tsare tsaren shi ina kallon shi harda tsuki yana fadin. Sai dai tsiyan kudin naku kuma sai anjawa mutane rai dashi kafin ya fito mm nace ba dai in ya fito ba za a mu samu. Sai bude baki yayi yana fadin na matsune kudin suzo wallahi don a uzurce nake dasu dama na rasa inda zan samu kudi wallahi ina da lalura mai karfi a gabana. Nace idan ma kasarai ga kudin nan gara ka fitar don wallahi dakina zan gyara da sana, a wanan karo ba zan bawa kowa ba gaskiya. Fadin hakan danayi ya kalle ni da mamaki tare da fadi haka kikace nace haka din ne ma wallahi don ni zaman nan haka ya ishe ni. Wasa wasa daga fadin haka ya fara daure mun fuska yana wani sham kanshi dani tun ma kudin basu iso ba gare mu ke nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Wanda baba ya kira a waya ne yake ta faman magana a cikin wayan sai da baba ya tsnkayi muryan kamar daga sama mutumin na fadin hello hello ya karba shi da sauri tare da fadin. Hello mr Josua mun tashi lafiya ya iyalinka mutumin ya karba wa baba don wayan a handfree take a lokacin kowa najin mutumin a lokacin. Baba yace mr Josua dama akan maganan kudin yaran nan ne don Allah nawa ne kudin karshe da aka turo masu nan mutumin ya shiga yin bayani dala dala a waya yadda kudin suke a yadda zamu fahinta. Yana gama bayani yace ihope ba wani matsala aka samu ba dai ko baba yace yarinya tace abinda ta gani matar nan ta nuna mata miliyan goma sha shidda ne . Jesus mutumin ya furta da karfi lokaci guda tare da fafin ai duka kudin ma idan an hada bai kai haka ba sai kace kudin wani IG ko commitioner. Nan dai ya kara bayani baba yai mai godiya ya kashe wayan tare da fadin idan ma baku yarda ba ga nomban mutumin zaku iya kiranshi kuji karin bayani a gurin shi. Sai baffa yace ta yaya zataga abu a rubuce yanzu kuma ace ba hakana bane ? Innalillahi inji baba kabir Baffa nine kuma zan cuta maku yau kan kudin ku yace baba ba hakana bane don za a iya canza digit din kudin su rage babu abin da ba a iyawa gaskiya. Hawaye ke zuba daga idon baba kabiru na bacin rai kan maganan da mukayi yanzu a gaban kowa yace cikin wani murya mai ban tausayi ga mai saurare. Josua ko zaka iya hada ni da wanan matar da ta bamu takardu muka cika ranan Josua yace kwarai kuwa tana nan office din ta ai bara nakai mata wayan. Dan shiru ya biyo baya kafin ya kai ma matar wayan ta dauka muna ji ta dauka baba ya fara tambayan ta da fadin ko zaki duba muna takardan mu ji nawa muka saka hannu a kai. Ta duba tace miliyan shidda ne kamar yadda baba ya fada muna din nayi caraf nace ba naka sha shidda a waje farin rubutun kudin ba ? Dariya mai ban haushi sosai matar ta kwashe dashi sosai muna jin ta a waya tare da fadin amma ke kina da abin dariya fa. Luckly muna da komai anan a cikin computer mu muna reconding idan zaku iya zuwa kuzo ku duba da kan ku wanan lamban da kike magana. Shine serial nomba na kudin ku nan ta kara karanto min shi wanda shi din ne na gani a can sai nace bashine kika ce min kudin namu ba. Tace ke mahaukaciyar ina ne da za a baku wanan kudi haka mai uban yawa kiyi abu na masu hankali mana. Zaku iya zuwa ku duba komai na nan wurin mu a rubuce cikin computer mu kuzo ku duba shaaa ta katse wayan. Muryan baba musa ne ke fadin assha wanan hali a ina kuka samay shi ne haka kan kudi ku rufe ido kuciwa kowa mutunci wanan bawan Allah idan baku gode mashi ba bai kamata ku nuna mashi haka a fili ba. Baffa yace baba ba hakana bane shi sharian kudi idan yazo ds kowa kana iya yin sa ai mu abinda ta fada muna ne ta gani muka sa rai. Baba kabiru dai bai iya fadin komai ba lokacin sai hawayen da yake sharewa baba yushau yana bashi hakkuri kan maganan. Nan dai baba musa ya zage mu tas yasa mu bawa baba kabir di hakkuri wanda har muka gama ya kasa furta komai gare mu. Haka muka fito rai a bace don kudin ba suyi muna dadi ba kamar wa yanda suka sai da wani abu a kasuwa ba mahaifan su ne suka rasu ba. Gidana muka nufa da kudin kai tsaye inda muka samu Jamil yana jiran mu a kage dashi kamar yai tsuntsuwa ya bimu gidan baba din inda ake rabon kudin. Muna shiga yana ganin mi rai a bace yake fadin yaya akayi baffa ya ce kai rabu da mashiririciya kawai taje ta sa mutane a ciki kawai ashe ba haka na bane abin. Nan ya tare shi da fadin kai abi abin nan a hankali zaku gane gaskiya fa ba abinda ba a iyawa yanzu wallahi. Kana ganin ba hadin baki akayi a rage kudin ba a baku abinda bashi bane wai ma nawa ne suka baku wai ? Baffa yaja tsuki ya mike ba tare da ya fada mai komai ba ya fice daga gidan . Kallon mamaki Jamil ya bishi dashi har ya fice nan dai ya sakani gaba na fara mai bayanin shiririta cikin rashin fahinta. Yace kai ina ba za a yarda ba wallahi zanbi in gani har sai na gano gaskiyar wanan maganan sai kudin nan sun fito wallahi. Yace bari in nemi layin baba hamza wani dan uwan mahaifin mu dake aikin yan sanda shima a sokoto ne ya mike ya fita. Don zuwa nema layin baba namu dake sokoto ya fita bai dade ba ya dawo yana fadin na samo layin baba hamza barj in kira baffa yazo muji yadda za a yi. Ya zauna yana kiran layin baffa din har ya katse bai dauka ba ya ha tsuki ya kasa hakkuri ya kira layi wanan baban namu na sokoto can ya dauka. Kun san mutanen yanzu sai a hankali maimakon ya gyara zancen sai cewa yayi da Jamil tunda ta fadi haka ta ganine. Ni yanzu abinda zanyi shine zan nemo maku wayan wanan da aka saka gaba wurin fitowan kudin ku don muji gaskiyan maganan. Idan ya kama kuzo ne sai ku shirya kuzo ku samay ni nan sokoto muje office din da ake abin muji komai. Basu kashe waya ba suka shiga zagin su baba ina jin ban iya daukan matakain komai ba akai don nima a lokacin na hau sosai dasu a raina. Nan dai muka bar zancen iba batun tashi in fita naji yace to yaya ake ciki ne wai banji kince dani komai ba har yanzu mana ? Dakatawa nayi nace kamar na may fa yace a dake ba a baki kudin bane ko may nace ambani mana amma duka suna gurin baffa ai bai ba kowa nasa ba tukun. Kamar ya suna gurin Baffa kudin ke baki da laluran yi da kudine da zai rike maki kudi ko rainin wayau ne kuma yin hakan ? Nace suna dai guri shi ya rike baice dani komai ba har yanzu gaskiya yaja wani guntun tsuki ya mike yana fadin an sa muna da lalurar kudi zai wani rike kudi a hannun shi. Ko ya fiki sanin duniya ne da zai wani rike kudi a hannun shi yana karami gare ku kuma nidai tunda na fadi hakan ban kara mai magana ba. Sai dai nasan da wuya kudin nan su shiga hannun shi yadda aka saba don Baffa yasha alwashin shi zai rike namu din gaba daya dani da kanwata . Washe gari da muka tashi da wuri ranan Jamil din ya tashi yana tambayana ko baffa yazo a daren jiya wuri na ?. Nace tun fitan nan da yayi ba sake shigowa ba har yanzu ya ja tsukin da ya saba ja din kamar ko yaushe. Kafin karfe biya ya tambaye ni sau ba adadi ko Baffa din ya shigo nace bai shigo sai ya ja tsuki ya fita. Yinin ranan nan ya zauna a kofan gidan yana hira a camban yan unguwar wanda nasan zaman jiran Baffa yake ya bullo. Sai yamma lis Baffa din yazo gidan yana hango shi da kyat ya daure ya jira karasowan shi inda inda ya dan tsaya na wani lokaci har ya dan bada time kada aga gazawan shi. Tunda baffa din ya shigo muka gaisa nake tambayan shi ko yaga Jamil din a waje yake tambayan may zan mai idan na ganshi. Nake fadin kai yake jiran zuwan ka tundazun ai yaja tsuki yaci gaba da min bayanin abinda suka tsara da sauran yan uwana. Kan mu mata zamu bada dubu ashiri su maza dubu hamsin a rabawa yan uwa na birni dana kauye mazajen mu kuma dubu hamsim daga cikin kudaden mu . Sauran zai aje muna a gurin shi ya duba abinda ya dace asai muna dashi don gudun tabarbarewan kidin a hannun mu. Ban kai ga magana ba Jamil din ya shigo gidan yana fadin Baffa ka shigo ai dazun na kira layin ka bai shiga ba tunda safe nake gwada layin naka. Yace eh barci nake da safe na kashe wayana ne Jamil yace dama akan maganan kiran baba hamza ne don na samu layin nasa har na kirashi nayi mai bayani . Amma yace hakan ba gaskiya bane don hakama ba zai yuyuba tunda tagani a rubuce lalai an rage kudin nan ne anbi wani hanya dasu. Tsuki Baffa yaja tare da fadin kai wanan maganan a barshi kawai, don Allah, ba kamshin gaskiya ga maganan ta ko kadan . Jamil yace a, ba hakana bane kada kayi mamakin sai azo abincika kaga kudin sun fito daga baya don sun mayar da ita mace ce kawai wallahi ya kawo haka. Ni tun farko ban so aje da ita wanan tafiyan ba ita kadai haka, na riga da munyi magana da mutanen sun ce muna iya bi hakkin mu. Wani kallon kai din Baffa yaiwa Jamil tare da fadin da kudin wa zakuyi wanan hidiman haka yana fadin haka ya fice yana dariya. Ina zaune ina sauraren su, nan dai ya bi Baffa din zuwa waje sin dade suna magana dashi koda ya dawo naga fuskanshi a daure . Sai dai yana ga bakan shi na son abi kidinkidin din kudin da yake tunanen an lake muna a sokoto. Yana wanan maganan sai dai hankalin shi yana gun kaso na da baiji labarin shi ba har lokacin don haka a cikin dare ina barci ya tutseni ta hanyar tayar dani daga barci. Sai na fada mai ina kudina suke akan may ba a bani ba yadda aka saba bani nawa a hannu na da farko wanan karon aka hana min. Nace suna gun baffa duk kudin namu yana gurin shi ga baki daya ya rike ranan dai munyi fada sosai dashi kan kudin. Da safe kamar baffa ya san munyi wanan fitinar sai gashi ya sallama min da kudi daya lissafa min din zai bawa kowa ya fara fitar wa sai ga Jamil ya fito daga daki fuska a daure yana shan kanshi kamar wani Alhaji dashi. Sun gaisa da baffa a tsatsaye baffa ya kirgo kudin daya ware mai daga cikin kaso na dubu hamsin ya miko mai kallon kudin yayi shekeke tare da fadin wanan fa kudin may ye ? Shima cikin daure fuska ya bashi amsa da fadin kason kane daga cikin kudin matan ku dana cire makowanin ku. Kallon kudin yayi kamar ba zai karba sai kuma ya karba yana juya su a wullakance tare da fadin wanan ne kason nawa wanan karon? Eh su muka cire maku inji baffa shima ya kara bashi amsa a wullakance kamar yadda yai mashi magana shima. Yace kasan yadda mukai tsamanin kudin ba haka suka zo muna ba don haka ayi hakkuri da abinda aka gani kamar kowa. Ya juya inda nake yaci gaba da fadin sai kudin da za a rabawa mutane gasu nan naso nakai masu amma ina ganin banda lokacin yin hakan don zan koma wurin services dina wanan satin. Fita jamil yayi a dakin rai bace bai kara bi ta kan mu ba kuma ya fice gidan ga baki daya har muka gama maganan mu da baffa din. Ashe komawa yayi kofan gida wurin wani icce ya zauna yana hadiyan rai don bakin ciki da takaicin da ke diban shi a lokacin. Shi a ganin shi an mashi rainin wayau don may za a yanka mai abinda za a bashi daga cikin kaso na kuma don wullakanci. Ya dade gurin zaune yana sake sake a zuciyar shi har ya gaji ya mike ya shiga gari don kudin basu usan shi ko biyan bashin gari balle na can inda yake zuwa din. Cikin dare ya dawo har lokacin fuskan shi ba wani walwala a tare dashi sai bacin rai zalla da yake tare dashi. Muna zaune da yarana muna hira ya shigo falon ya samay mu a zaune muka gaida shi da dawowa gida. Ya amsa muna wani iri dashi ni dai ina zaune ina jiran jin abinda zai ce min din wuri ya samu ya zauna tare da bude abincin dake rufe nasa. Ya juyo yana kallo na da tambayan yaya naga miyar ba komai a cikin sa kuma ? Nace ba komai da zan saka ka fita baka dawo ba tu dazun kuma naga yamma bayi na dora hakana. Na bashi amsa ina kawar da kaina gefe daya yace naga alaman kun shiry yi min cin mutunci ke da yan uwanki a gidan nan . Kuna son mayar dani wanda bai san ciwon kanshi ba ko wani gara can dai kuke kokarin mayar dani ? Wanan ai wullakanci ne da rainin wayau ni ake gudu da kudin ki ko may yanzu don ban gane may kuke nufi dani ba haka ? Shiru nayi ina kallon shi yaci gaba da fadin don kun raina ni za a dauki wani dubu hamsin a bani anga mabukaci ko may ? Na kasa hakkuri da maganan da yake fadi din nace ni may ye nawa a cikin maganan nan tunda bani na tsara hakan ba. Idan bake kika tsara ba waya tsara hakan kudin su ne ko naki idan ba da yardan ki aikai hakan ba yaya zasuyi hakan da kudin ki ? To bari kiji ni ba zan yarda da wanan tsarin da aka fito dashi ba yanzu dole ne ki karbi kudin ki hannun baffa ki bani in juya su yadda muka saba. Nace ni wanan ba magana na bane ka samu baffa din kuyi magana dashi zaifi amma kazo ka samay ni kana fadin kai baka yarda va nima naga kudin nawa ne. Yace sai sun cire kudin su da kaci na haya aciki saura kuma kadan kadan zai dinga bani ina sayen abu dashi idan bukatan hakan ya taso min. Bai bari nakai aya ba yace a harzuke ida baki karbo kudin na ba wallahi sai rayuka su baci a gidan nan ni za a kawo wa raini hankalin banza ko wa ? Ya kare da fadin don rashin tausayi zakiyi wa yara abinci haka babu komai a ciki may ye amfanin kudin da kika samu yanzu yana fadin haka ya shige daki ya bar ni a gurin zaune. Wasa wasa ya tayar min da hankali sosai kan kudin ya hana mu zaman lafiya shi kuma ya kasa yiwa baffa maganan kufin da bakin sa sai ni yake turawa in mashi. Tun ina boyo har yakai na kira baffa din na fada mai halin da ake ciki akan kudin baffa yace idan yana son kudin ya nemay shi mana ai bani zaiwa magana ba. Kudin da baffa ya bani in kai wa yan uwana a kauye yasa ni gaba a kansu su da yake gani a kusa sai da ya kwaci dubu talatin a cikin su da fada da komai kuwa. Sai lissafin ya bace min yadda zan raba kudin wa mutane tu ina boyo har dai najewa anty da naganan bata so saka muna baki ha amma haka ta hakkura ta yi min bayani. Ta gane cewa Jamil ne ya karbe duk da na boye nace ban gane kan lissafin da baffa yai min bane. Da taimakon shawaran ta na samu na dan tsankwarawa mutane kudin abinda ya zama abin magana daga baya gareni ke nan. Don baffa yayi fada yayi jininin yadda nayi da kudin har ya gaji ya kyale ni hakana ga Jamil ya kasa hakkuri sai da suka zauna da baffa kan yana son a ra mai kudi daga cikin kudina ya juya. Baffan yaki ya bashi a cikin lalama sai ya shigo ya samay ni yayi min bambami ya fice kan zai iya sakina kan maganan nan don baiga amfanin aure na ba yanzu tunda zan iya samu in hana shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Mun kai wani lokaci ba zaman lafiya a tare damu a gidana ni da yar hayar nan sai da iyayyen ta suka zo suka shirya mu sama sama dai muke zaune da ita yanzu. Ranan naje gidan mu gaida su anty ke min fada don may na yarda da sherin mijina na biye mai akn zancen kudin da nasan ba gaskiya bane. Tace ke kin fi kowa sanin waye baban ku hadiza amma wai ace ki biye mai kun tafi sokoto binciken nawa ne kudin da aka turo mai ainihi a account naku ? Nauyi da kunya suka rufeni a lokaci daya don ban taba tsamanin zasuji wanan maganan ba sai gashi an tare ni dashi yanzu. Ta ci gaba da fadin wanan halin da kukeyi kunawa kanin mahaifin ku adalci ke nan ? Duk irin kokarin da yake daku may yasa baku gani kada fa ku zamo cikin irin marayun da basu da godiyan Allah nan gaba duk ko da irin tarbiyan da muka baku dan zaman da mukayi da ku. Kaina na dukar kasa don ban san abinda zance da ita ba kuma don dai bamu kyauta ba gaskiya nan dai na fara kamay kamay ina fadin . Anty kin san halin Jamil akan kudi idan yaji maganan kudi bai iya zama duk shi ya rikita wanan maganan haka wallahi. Tace don Allah ki bar wanan maganan banza idan ke baki nuna mashi cewa yana da right din tsoma baki a cikin maganan ku ba wane shi har yace zai soki mahaifin ki . Ranan dai naji nauyin kaina da kunya sosai don nice naba Jamil duk wani kafa nayin duk abinda yake so acikin maganan tamu. Amma idan ba haka ba ina shi ona zuwa wai bincike akan yadda kudin suke bayan iyakan shi ci idan an bani rabona ko yaushe in sun kare kuma in ga wullakanci. Ni kaina bansan ya tafi sokoto yana bincike akan kudin nan ba sai daga baya nake jin wai ya tafi sokoto ya bincika idan gaskiya haka aka ba da kudin kamar yadda baba ya fada an turo mai. Ina cikin wanan jimamay ne sai ga Jamil ya dawo a lokacin da banyi zaton dawowan shi ba garin. Ban san may yazo yi ba ni dai ranan ina waje koda na shigo na samu ya share dakina tas ya kwashe harda cinnakun da kiyashi yana zubawa a cikin leda. Tsaye nayi ina kallon shi da mamaki har ya gama abinda yake baice dani uffan ba yana kokarin fita daga dakin. Na iya bude bakina da kyat ina son in tambaye shi ina zai tafi da abinda ya kwasa a dakin sai hannu ya daga min alaman in bari ya dawo ya fice da saurin shi. Na bishi da kallon mamaki tare da daukan abinda zan dauka nabar dakin ba tare da wani damuwa da abinda naga yanayi din a dakin ba. Washe gari ya tattara yabar garin ya koma inda ya fito ba tare da bar muna komai ba da zamuyi amfani dashi kamar ba mutane yake bari gida ba ya tafi. Don yadda yake barin mu ya wuce bai aje muna komai na amfanin gida ba da ya kamata a jewa mace idan za ai tafiya da za, a dade ba,a dawo ba. Sannu sannu na fara aiki shikan shikafa ina sayar da tsakin buntun shikafan don samun abinda zan ci dani da yara na. Sana,an shika ya matukar karbe ni sosai ina zan dinga bin duk wani injin din nikan shimkafa ina bukin din butun shikafa idan sun fitar da mai kyau. Na fara a boye gidan mu da yan uwana ba wanda yasan ina wanan sana,an abu ga mara wayau ko dabara nan na fara ba mutane labarin irin amfanin da nake samu ta hanyar sana, an da nakeyi din. Baki na fadi takashi na fadi take ko mutane suka gane akaiwa sanan an ruuuuu kowa shi sai dai duk da hakan ina samu fiye da tsamanin mai karatu gaskiya. Alokacin na karkare komawa wata irin bagidajiya don baka saye na kwabo ka dauka daga ni har yarana dake a wahalce dasu. Saukin abin na samu zuwan kudin nan yasa min yarinyata babba makarantan ana biyan dubu uku da dari biyar niko sai yake hakori nake yarinya ta tana pravert school ai idan an tambaya. Gane sana,ata da kowa yayi bai hanani samun alheri daga ciki ba don ina samu gwargwado hali na sai yan tunkiya guda biyu na aika kauye a min kiwon su don kar Jamil ya gane ya batar dasu idan yazo. Abinci yanzu banda matsalan shi tunda kudi na zuwa min yadda ya dace sai dai tun ina boyo har na kai gidan mu sun gane ina wanan sana, an. Ba wanda yayi yunkurin hanani shikan shikafa da nake ina sayar da tsakin buntun daga cikin yan uwana tunda sun gane ina samu daga cikin sanaa,an . Sai fadi suke yadda nake wahala wata kila yanzun zan koyi tanadi in dinga boye kudi idan na samuwa jamil din. Ko ga yadda nake yawan nunawa mutane cewa ai yanzu nayi hankali na koyi darasi sosai na duniya. Sai mutum ya dauka lalle duniya ta koya min hankali sosai yanzu don na kare ga shikan butun shimkafa ina sayar ma masu karamin karfi irina ina samun alheri daga ciki nima. Da yake ban saba da aikin wahala irin haka ba sai abin ya fara fita mun rai duk da ina samu daga ciki ina rufawa kaina asiri da wanan sana,an shikan da nakeyi din. Yan uwana da saura abokan arziki suna ban shawaran in dan samu in dinka sutura ko yaya ne daga cikin dan abinda nake samu din daga sana, an. Sai dai kasssh ban saba ba don haka ban iya cire kudi in dinka wa kaina tufafi dashi sai dai muna ciwa ran mu mai dadi dani da yarana gaskiya. A haka nayi ta juya rayuwana har zuwa lokacin da Jamil ya waiwayo mu ya dawo gida bayan yaci zaman shi a garin da yake. Wanda izuwa yanzu kowa ya gama gane karyan da yake sharawa na zuwa neman kudin da yakeyi kamar yadda yake fadi idan zai tafi. Sai dai a wurina ne ban gane hakan ba saboda dan albashinshi da yakan tara ya dawo dashi mu cinye a cikin kwana biyu sai ya koma cin wanda na dan tanada muna nida yara anan. Tunda ta dawo nake boye mai wanan sana,an nawa da nakeyi yanzu ina samun rufin asiri ta wanan hanyan. Sai dai abin bai boyu min agareshi ba saboda mutane dake yawan zuwa tambayan ko akwai tsakin shimkafa din. Har dai na daure na fada mai abinda nake a bayan shi a zatona zaiyi fadan haka din. Don sana,an kaskantantu ne a gurin wasu da suke ganin shi aikin wahala ne da kaskantar da kai. Amma sai nayi mamakin jin baiyi fada ba illa fadin da yayi idan ana samu sai in rike sana,an da kyau in dinga yi. Nan naji dadi na shiga fada mai irin alherin da nake samu ta wanan sabon sana,an dana rike yanzu yana ta bugun cikina ta hayab nuna min jin dadin hakan da nakeyi. Sai da ya gama jin komai ya nuna kamar bai damu ba da yake ya iya sallon yaudara kala kala har yakai shike zuwa nema min butun shimkafa da kan shi. Hakan yasa na kara yarda dashi tunda ya nuna min kauna da yaudaran shi ashe kwanto yayi min a hakan. Sati biyu yazo min da dadin bakin ya samu kifi mai saukin kudi sosai da zai samu kudi ya saya zai samu karuwa sosai ba zai dade ba zai dawo ya kara saran wani. Ba tare sa wani shawara da zuciyana ko wani ba na yanke shawaran kulla kudade na tunda duk karuwan mune hakan nace ya bari zan hada in bashi sai mu gwada. Murmushin gefen fuska ya sakar min tare da shiga zuka min albarka da fatan alheri gamin da yabon halina na kirki a gare shi. Nan na fara fadi tashi har na hada mai dubu hamsin ya dukula ya tafi ya barni da fadi tashin hada wasu kudin kuma. Don na koma banda ko hari yanzu da zanjuya wurin sayen buhuhunan butun da nakeyi inzo in sheke su koma min tsakin shimkafa masu karamin karfi su saya a wurina su samu saukin sayen abinci a yadda kasa ta koma yanzu. Sai na tura kauye a sayar min da tumakan da na saya na turawa yar mahaifiyar mu a can a kiwata min su har su dan tasa in sayar. Sai ga sako yazo min wai ai tumakan sun dade da bacewa fada min daine basuyi ba amma zata kokarta ta saya mi wasu.. Jin haka hankalina ta kara tashi sosai gashi shi har wata biyu na neman rufewa bai dawo inda muke ba tunda ya tafi da sunan sati biyu kawai zaiyi a can. Gashi yanzu mutane sungane sana,an ana samu sosai gare shi mutane sun raja,a ga sayen shi don sauki da yake dashi a gurin jamma,a yanzu. Sai ya kasance butun yana wuyan samu gare mu haka zamuyi ta yawo a ckin rana muna neman shi don mu sarrafa wa masaya su samu su saya suma. Wahala yayi min yawa sosai a cikin haka na fahinci ina da shigan ciki a tare dani kuma sai abin ya zamo min sabo ga wahala ya taru yai min yawa lokaci daya. Haka nake ta fama da rayuwana ko yaushe don neman abinda zanci ba zancen yin sutura ko wani abu a gare ni kuma yanzu na karuwa. A haka ya dawo ya samay ni cikin wanan halin ba wani karuwa ko kadan daga gare shi sai buga bugan rayuwa da mukeyi a gidan yanzu har shi. Ba laifi duk da hakan da nake yan uwana diyan baba kabir suna kokarin su dani sosai don da matar nan yar haya ta matsa min da fitana a gida. Da taimakon yaran wurin baba kabiru na samu salama har ta bar gidan don suma kamar yadda ta tayar min da hankali haka sukazo suka tayar mata da hankali sosai. Sai data firgita ta tattara tabar muna gida ba shiri suka canza gida na samu yarbawa na saka a dakin ta sai dai Jamil din ya karyata matar akan wai sheri take mashi. Zaman da ya danyi tare damu na matsine sosai don banda halin tambayan shi komai na girki yanzu za a jimu yana cika yana batsewa. Sai in ya ga dama yake kawowa ayi in bai kawo ba dole inyi dabaran abinda zamu ci da yara don zama da yunwa bai yuyuwa gare mu. Dan sabon da nayi da rike kudi sai yanzu na koma wata kala can dani don rashin kudin dake shigo min a hannu na dana saba kwana biyu dayi ina taimakawa kaina dashi. Har yakai an fahinci halin da nake ciki don yawan ragga da ya baibaye ni har yarana bamu da sutura don ko na fita bamu dashi. Ni dai dama bukata muci musha tunda na saba da rashin sutura kamar yadda ya biyar dani a gidan shi tun shiga na ba zance ya kashe min kudi akan sutura ba ko yayane don duk wanda yake muna a cikin kudina ko jiki na yake yayabo muna su a wullakance. Ban baku labari ba can baya har maciji ya sare ni a gidan Allah ya taimaka yana garin lokacin da abin ya faru dani da kanwata tana gari sunzo a lokacin. Naga gata a wurin dangina kaf lokacin don sun nuna min suna kaunan mu don anty da kanta tazo gidan ta sa a toshe duk wani kafa dake gidan. Anan suke wuni tare dani da aka sallamoni daga asibiti ana hadawa dana gargajiya don kada ya taso min kamar yadda kace wai yana yi bayan duk shekara idan ya zagayo. Ba laifi lokacin ya nuna masu shi na miji na don ya tsaya ya kula dani sosai da fannin maganin da ake bayarwa anayi din . Kuma yana sayo min abinda zai gyara min jini na akai akai sai yabon shi ake tayi ana saka mai albarka kan namijin kokarin da yakeyi dani lokacin. Wanan dalili yasa na rike yan uwana yanzu sosai na fahinci mutum baiyi saida yan uwa shi na jini a rayuwan shi. Sabanin nida na rike yan uwan miji wanda hakan ke ba kowa nawa haushi irin yadda na ba yan uwan miji amana dari bisa dari na watsar da nawa sai wutin wahala nake nemo su. Yanzun ko na san dadin su sosai don ba a kwana a wuni basu shigo sun duba lafiyana ba duk da ba komai nake basu ba idan sunzo wurina din. A haka nake dan bubugawa ina samun rufin asiri a guri Allah muna ci muna sha nida ke dauko buhu goma sha bakwai har ashirin sai gashi na koma da kyat nake samun buhu daya in gyara a ciki zamuci na sayar da saura muyi lalurar mu dashi. Da Jamil ya fahinci ciki ne dani ya fasa tsiro min da wasu halaye wai shi haihuwana yayi yawa akan lokaci har yaushe da zan tara yara haka a gida. Wanan maganan ya tsaya min a rai naji na kara tsanar cikin da na samu yanzu dashi don nasan nike da wahala a karshe na cikin ke nan. Tunda dama ba komai yake tsinanawa idan na haihu din ba don nasan wanan tunane shima yake yasa ya fara aibanta cikin jikina din . Ya fara shirin komawa inda ya fito inda yake ta fadi tashin neman kudin motan da zai koma inda yace yake da zama. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Narasa inda zan sa kaina da rikicin Jamil akan kudin nan daya kwallafa ranshi gare su. Gashini bako ganin kudin nayi bawa a idona va do Baffa ya rike ya hanani komai daga cikin kudin. Gashi shi kuma Jamil har yana kirarin zai iya sakina idan na hanashi wana kudi do baiga amfnin zama dani va tunda zan iya samu in hanashi yanzu. Wai da sani na aikai komai na rike kudina a gidan mu don ai va haka aka saba yi ba a baya cn da yanzu za a kirkiro mai da wani sallon kanina ya rike kudina. Da abin ya ishe ni na aika akira min kanwata dake aure yar gurin baba kabir a kusa damu do ya hanani fita ko ina inga kowa nawa lokacj saboda baki rai da yakeyi dani a gida daga ni sai shi sai yan hayan mu dake gefe daya a gidan da ba wani shiri mm nake dasu ba sosai. Wanda duk sherin shi ne hakan ya hanani zaman lafiya da kowa a gidan don ba halin ya gano ina shiri da daya daga ciki matan gidan yanzu zai fara sukan mai shi har sai naji na tsaneta a raina. Mu bar shiri hankalin shi zai kwanta wasa wasa sai da yasa na kore duk hausawan dake gida suna haya ya zuba matan yare a gida sai bahausa daya ta saura muke zama da ita. Ko ita do tana matar abokin shine da suke shiri shi kuma mijin ba mazauni gari bane dama sai lokaci lokaci yake zuwa gurin iyalin shi yayi yan kwanaki ya koma. Abin da na kula dashi shine matar da muna zaman lafiya kasancewar mu hausawa a gidan dani da ita sai yanzu naga canjin fuska a gare ta kuma har da diyana. Abu kadan sai taso fada ya hada ni da ita sai dai ban biye mata nakan share ta idan naga tana jin fitina dani lokacin nakan fita batun ta sai ta sauka da kanta zamu shirya. Sai na fahinci na wanan lokacin yafi tsananta don magana take dashi a bakin ta da take son samun kafa ta fada min shi a cikin fada. Rashin kulata da banyi ba yasa ban ji ko may take da niyar fada min ba a lokacin wanan ke nan. Bayan kanwata tazo nake fada mata halin da muke ciki da jamil da abinda yake fada min a yanzu bata ko bari nakai ayaba ta karbe zancen da fadin shiko Jamil dai. Duk irin halarcin da kikai mashi da kudin ki da farko bai gani ba sai wanan da baida wani yawa kuma shine na karshe. Tace a fusace ki fita batun shi duk abinda zaiyi yaje yayi kawai kudi daine suna hannun baffa a yanzu bai iya kwatar su kuma. Watau shi ya saba cin banza yanzu ya sa rai a wayan nan yaga sunzo basu shiga hannun shi ba shine yake jin haushin akan hakan. Ki ma godewa Allah da akai dabaran yin hakan gareki don kila wanan a samu a sai maki abin kwarai dashi. Kinga ko ba zai so haka ba shi don yasan kece da karuwa a kan hakan da za ai maki din nan gaba, surutu take zubawa. Wanda ni ba haka naso daga gare taba don kiranta nayi ta ban shawaran yadda zan karbo kudina hannun baffa in bawa jamil nake so ba wanan dogon sharhin da take min ba a yanzu. Ta fahinci maganan bai mun dadi a raina yadda taga ina bata fuskana kamar zancen ya isheni ji hakana sai ta dawo fadin yanzun dai shawara ya rage gare ki . Idan kinga zaki karba ki bashi ne don kada ku samu matsala sai kiwa baffa magana ya baki ki bashi a zauna lafiya. Sai lokacin na iya magana tunda ta fara magana nace nima dai haka naga yafi sauki ya bani kudin in bashi a zauna lafiya idan ya kashe sai kwadan shi ya fada. Wani kallo tayi min tare da mikewa tana gyara goyon yarta dake bayan ta tare da fadin ni zan tafi Allah ya sauwa ka. Saurin tare ta nayi ina fadin yanzu in turo maki Baffa din gidan ki ki masa magana ko zai yarda ya bani kudin na fada cikin yanayin son ta taimakeni din. Tace ba matsala indai zai yarda ya bada kudin ai ta bafa cikin son ta bar gidana a gagauce don ko bata fada ba ranta ya baci dani sosai don bata samu hadin kai a gurina ba. Kamar yadda tace zata kira baffa din gidan ta haka ta aika yazo suka zauna sukai min tas kan rashin sanin ciwon kaina da banyi ba. Karshe dai baffa din yace ta barshi da Jamil din yasan hanyan da zai bullo mashi akan maganan kudin . Washe gari sai gashi ya sallama gidan namu da safe na tare shi a cikin daure fuska muka gaisa sama sama dashi yace dani bayan mun gama gaisawa. Naji sakon ki gurin anty sai dai ki sani na riga da nayi maki amfani da kudin ki kamar yadda nace zanyi Raina ya baci kafin ya gama magana nace kudin wai ko nawa nace kaban abina inyi yadda nake so da abina zaka kawo min wani magana yanzu kuma. Mikewa tsaye yayi yana fadin kiyi duk abinda zakiyi kudi dai ne na hana bazan bayar ba kiyi abinda zakiyi dake da mijin naki yana fadin haka ya fice daga gidan rai bace. Nima na bishi da zagi na fitan arziki har ya bace min a gidan na zauna ina huci sai ga jamil din ya fito daga daki don yana ciki kwace. Dama nasan da gaiyya akai min wanan abin don wanan ba shawaran baffa bane shi kadai da munafukar nan anty suka hada baki a karbe kudin nan. Suci, su rike zasu ga abinda zanyi nan gaba wallahi don kowa ai ya iya iskanci shi karami dashi zai kawowa mutane rainin wayo don ya raina mutane. In akwai abinda nake tsoro shine Jamil ya furta zai sakeni a duniyan nan don irin son da nake mashi a raina ba na wasa bane. Wanda mutane suke min kallon tababba ko mara wayo don ban san ciwon kaina ba dole na shirya zuwa gidan kanwata again don ta kara lalasan min Baffa din ya bani kudin in bashi . Don ban son iyayyen mu su san da wanan zancen ga kudin da aka bani in ba yan uwa daya karbe ya zama min fitina sai zargina da zagi yan uwa keyi kan an basu kudi na cinye. A gidan ta baffa yazo ya samay mu inda da kyat yace sai dai indan shi zai arawa Jamil din kudin shi inya yarda suyi aggrement a rubuce . Don kudina ya riga ya juya min su kamar yadda yace min da farko dole na yarda da wanan shawaran don nasan su suna da kudin ko nawane a hannun su. Da wanan shawaran na dawo gida sai zuwa hudu na yamma Jamil din ya shigo yana wani cicika dani na fada mai cikin daurewa abinda Baffa din ya ce min. Kamar maye don na dauka zaiyi fushi yace bai karba sai naji yace idan haka yaga zaiyi ai ba matsala . Shi a zato shi zai dai ci kudin ko ta halin kaka don haka ya dai samu su shigo hannun shi din shike nan yadai ci kudin ke nan. Ba musu ko wani zance yace sai baffa din yazo zuwa yamma ko sai gashi gidan mu nan suka zauna don tsaban iya makirci na Jamil ya nuna mai karmar bashine mai fushi da fada ba a kan kudin. Nan ya fara dadin baki wa baffa din yana fadin ba wani abu yasa nake son rike kudin nan ba sai don yanzu sana,an kifi yana tashi sosai daga nan zuwa kasan Niger nake son in dan juya in samu nima. Baffa ya katse shi da fadin zuwa yaushe zaka dawo min da kudin ke nan yace zuwa nan da wata hudu idan damana ya sauko kasuwa ya kwanta ke nan. Yace ba matsala yanzu a kawo takarda muyi shi a rubuce don gudun abinda kaje ya dawo nan gaba kaga kowa yasan munyi abu a cikin wayewan kai ke nan. Bai ki ba nan ya mile ya dauko biro da takarda sukayi shi a rubuce yace dari biyu ko da hamsim yake son a bashi. Baffa yace su dai tsaya a dari don shima yana son yin lalura da kudin ne nan gaba. Ranshi ya bata sosai don jin abinda Baffa din yace amma ba yadda zaiyi ya karbi dari din a rubuce kamar yadda yace zai bashi. Wanan ya kawo zaman lafiya a tsakanin mu yanzu kwana biyu da bashi kudin ya tattara ya bar garin ya tafi inda yake zuwa a cewar shi. Sai bayan tafiyan shi ne na samu sauki ga duk alamuran gabana Baffa ya samay ni gida yana fada min cewa kudina saura suna ban zai shiga kano ya saro muna kanani atamfofi mu sayar. Nayi murna kwarai da jin hakan inda bai kara kwanaki ba ya wuce zuwa kano komai daidai ya saya muna ya turo muna dashi. Nan na fara sana,a dadi dadi ana saye ana sayo min wasu idan na sayar na tura mai kudin sai ya turo min da wasu. Sana,an ya karbe ni sosai don dama haka nake da sana,a idan inayi sai ya karbe ni sai dai matsalan da aka samu daga baya shine. Tun tafiyan Jamil ba aike ba waya shiru kamar an aiki bawa garin su ga yara dole muci abinci na fara amfani da dan kudin dake a hannu na na turamay da nake sayarwa din. Sai kudin suka fara lalace min ga sana,a yanzu sai da bashi mutane sai su rike kudi kaita bi basu baka ba sai wani lokaci abaka su a lalace. Abin dai nawa sai ya koma min kamar mai bakin iyayye akai ba wani ci gaba kuma har yakai na kasa tura ma Baffa din da kudin da nake aikawa a sayo min yan turamay dashi. Kamar nawa matsalan itama sumaiya kanwata haka abin nata ya lalace sai dai ita ba a jin komai daga gareta don bata kusa da gida haka yasa ba a sanin halin da suke ciki da mijin ta can. Sai ni dake kusa ake sanin nawa din kowa ke magana sai dai ko may ye ita ta fini dama gaskiya sosai. Don ko ba komai ba aganin ta a gane don tana da yan suturorin ta na rufin asiri sai dai ba yanda mutum zaiyi tsamani bane. Sannu sannu abubuwa suka fara rikice min na rayuwa na ramay na lalace duk na fita cikin hayaci banda komai kuma kowa ya sani aka kawo ido aka samun a hakan nake rayuwa. Don an san ban son maganan da za a soki Jamil a gaba haka yasa haushina a rayukan yan uwa ya kara karuwa sai baba kabir me mai dan taimaka min wani lokaci can ba a rasa ba. Sai kuma anty daga dan muna hade hade idan naje gidan taga irin yanayin da nake ciki nida yara na idan zan dawo sai ta dan hada min abubuwa kamar yadda iyayye mata ke yiwa diyan su wani lokaci. Ranan kwatsan sai gashi da yammaci ya dawo min yanayin shi kawai na kalla nasan ba dawowan arziki yayi min ba a lokacin. Bayan ya huta yai wanka yaci abinci ya kwanta yayi barci da ya taso ne yake ban labarin wai tafiya bai mai dadi ba yasa muka jishi shiru haka. Don wanda suke sana, a tare ne ya gudu mai da kudi kasan mali da sunan zai tafi can ya saro masu kifi ashe gudu yayi da kudin sunje can kasan ance dasu baizo nan ba. Nan dai ya shiga bani labarin karya ina taya shi zagin mutumin tare da bashi hakkuri kan abinda ya samay shi din. Don sai ka rantse da Allah hakan daya tsara gaskiyane abin ya faru dashi ne a yadda ya tsara maganan nasa. Haka na koma nike laluran komai a gidan wahalce dani sai dai yayi wanka ya saka kaya ya feshe jikin shi da turare da komai ritse baya rasa su ya fice yawo sai dare zai dawo gida. Sai jefi jefi nake samu ya dan yo cefane a gidan duk wanan bai damuna idan dai zamu zauna lafiya a gidan dashi wanan bai damuna. Sai dai mutane suji min haushin abinda yake min din nikan ko a jikina waini mai zaman auren hakkuri sai dai ga nawa wautan banyi tsamanin mutane suna fahintar halin da muke ciki ba dashi. Na manta cewa yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba komai da kakeyi akan idon mutane yake ban san may ya hada shi da yar hayan nan bahausa ba. Sai ji nayi yana fadin ya kamata matar nan tabar gidan nan ita ma don halin ta baida kyau wallahi. Sai kuma bayan ya fita ita kuma naji tana jinini wai haka kawai mutum zai lalata mata yara don iskanci ta kyale shi. Nake tambayan da ita dawa ke fada kuma don muna dan shiri a lokacin takw ce min barni da dan iska ko waye ai yasan kanshi don wallahi sai na tona mashi asiri zai bari. Tun lokacin nasha jinin jikina da Jamil ne saboda shima yayi min maganan ta kan ta bargidan bata da hali mai kyau zata iya kashe mai yara saboda bakin halin ta ko ta illanta ni nikaina idan bai gari. Ai sai na dauki fushi da ita tun jin hakan da tace min nace bazatai ma mijina sheri in shirya da itaba niko. Har ya gama zaman garin da yake damu don bai dade ba yace zai koma don zaman gari ba nasa bane nan dai ya tafi ya barmu muna rikici da wanan matar. Rashin shi gida bai sa mun shirya da ita ba har wani lokaci ranan kan yar karamar ya ta mukai fada abunda take so ke nan ta fada min abinda ke ranta. Naji cewa wai Jamil yana kokarin bata mata yaranta yan mata dake gabanta bayan ya nemay ta ita bai samay ta ba ya koma ga yaranta. Wanan maganan da tai min ya bata min rai sosai don ban dauka Jamil din zai iya mata haka ba matar da ta haifi ganda gandan yan mata kamar ta mai Jamil din zai nema a gurin tayi kuma. Na hau fada nace sai ta bar min gida na tunda sherin ta yakai har ga mijina kuma yanzu. Yanzu tace ba zata tashi ba sai mijin ta ya dawo kuma ko ya dawo din sai kudin su na shakara ya kare zasu tashi min gida. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Tafiyan jamil yasa na samu sakata a zuciyana sosai duk da ya tafi bamu a cikin dadin rai dashi kan zancen cikin dake jikina din. Sai dai tafiyan nasa yasa na samu sakata ta hanyar da zanbi in dinga sana,ata ba a cikin takura ba ko tsangwama irin nasa. Don zan iya fita tun safe sai rana zan dawo ya danganta da lokacin da na samu buntun shinkafa din ga bakin wahalan yawon da nake sha wurin neman butu din. Na koma kamar wata sabuwar mahaukaciya dani don sana,a ba na tsabata bane ko gyaran jiki da mutum zai samu yayi. Sai dai duk wanan wahalan da nake zancen cikin jikina yana matukar damuna a raina sosai don nima ban so samu cikin a wanan lokacin ba ko kadan don wahalan da yai min yawa din. Ban samu zuwa gidan mu ba tunda akai karamar sallah don rashin walwalan da mutane basu a ciki don corona da aikawa mutane takunkumi dashi a ko ina a cikin kasan nan. Duk da hakan mu nan bai shafe mu sosai ba tunda ba alkarya muke ba kamar yadda yan alkarya suka wahala da wanan takunkumin . Ina shiga gidan mu ko gaisawa banyi da kowa ba anty dana samu a tsakar gida tana shan iska sai cewa tayi dama cikine dake ashe bamu sani ba ? Nan na fara irin halin mata idan wanda ya gane suna da ciki babbane gare su ina fadin ni wallahi banda komai a jikina. Sai cewa tayi wanan tunbi ne don samun lafiya da kikayi haka komay ga alama nan ya nuna ko ina kina da ciki kina wanan rantse rantsen haka ? Haka dai na shashantar da zancen ta kyale ni sai dai tun wanan lokacin haka duk wanda zan hadu dashi yake fada min ina da cikine zasu tambaye ni ? Amsa daya nake ba kowa ni banda komai sai abin ya fara damuna nima har wanan lokacin ba wani sako daga gurin Jamil tun lokacin da ya tafi. Ranan ina zaune sai ga kanina ya kawo min waya wai Jamil ne ke son magana dani a wayan shi. Na karba muka gaisa dashi inda ba wani gaisuwan dadi bane sai tambayan lafiyan mu dayayi zan fara korafi ya kashe wayan shi. Nabi wayan da kallon mamaki nasawa kanina dake waje zaune yana hira da abokin shi kira ya shigo na mika mai wayan shi. Yake ce min ke yanzu baki da ko wayan da mijin ki zai kiraki dashi don Allah ? Ni anty hadiza na rasa irin rayun kin nan idan kuma an baki mutun kwana biyu ba zai ga wayan ba inji kani dan wajen anty da ya kira ya bani waya yake wanan magana. Maimakon in fushi sai dariya nayi mai ina fadin kai yaro ne do Allah baka san komai ba yanzu yace ga waya zan baki idan ban ganki dashi ba wanan ne na karshe da zan baki.. Nan ya cire sim din karamar wayan shi ya miko min na hau murna da tsale ina mai godiya inda na dauko tsohon sim dina na saka. Ranan da farin ciki na kwana a raina don murnan samun wayan da nayi ba don komai ba sai don na samu abinda zan rika ji daga gun jamil din kawai tunda dama rashin waya nake gani baisa mu jin labarin juna din. Nakan kira ko ya kira sai dai duk da ba wani magana da zai farauta rai bane karshe ma ya fake da hira da yaran shi. A haka dai abubuwa suke tafiya cikin yakai wata hudu ga yanzu sana,a ya kwanta babu shinkafa don lokacin shi ya wuce. Ba kamar farkon kakan shi da muke samu sosai ba haka zan wuni ina bin injimomin gari ace ba aiki yanzu a gurin su. Ba zai wuce a wuni in samu dan rabin buhu ba in zo in sheke gaida wahalan rayuwa nan ya taru yayi min yawa a kaina. A haka ragga ya kara muna sallama dani da yarana bamu da sutiran shiga jama,a ko daya sai dai akance wai ban iya tanadi bane. Yo ina wani tanadin tunda wanda ma ake muna a cikin shekara din yanzu ko samu banyi ni kuma nemana na abinda zamu ci ne kada mu kwana da yunwa. Haka yasa ban shiga mutane ko abu ya samu yan uwa sai in share ban zuwa don dama ba kula yan uwa nakeyi ba. Ina ya Allah ranan kwatsan a cikin dare ina barci na shawo wahalan yawon neman butun da zan sheke ban samu ba can cikin barci na naji marana yana min wani irin ciwo . Koda na falka sai ganina nayi a cikin jini cikin jikina yana neman barewa don bakar wahalan da yai min yawa lokacin ina cikin wata na hudu da makwani dashi a jikina. Yar hayan gidan mu wata kabila ce ta taimaka min a cikin daren nan mukaje asibiti muna zuwa ya karasa fita daga jikina inda suka dan taimaka min da yan allurori don samun lafiya ta. Wanan matar itace tabiya komai da akai min akan cewa idan ya dawo zai biya don ta kirashi tun a gida kafin muzo asibiti din ta sheda mai halin da muke ciki zamu tafi asibiti. A asibiti ma ya kira take sheda mai abin ya fadi ana bani allura ne yace da ita ayi komai zai bata idan yazo tace ba komai ai ana tare. Mun dawo har na samu lafiya baizo kuma ba kira tunda ya kirani sau daya yaji lafiya ta bai kara kirana ba nima ban kirashi ba. Wahalolin rayuwa sun min yawa sosai don yanzu abinci yana neman gagara muna ni da yarana shi sutura ma ba,a zancen shi ai. Har yakai anyi sallah babba still bai zo ba bai aiko muna da abinci ba ko kudin da zamu saye ga mutane sai tambaya na sukeyi shi idan sun shigo wurina. Dole na fara shiga yan uwa hakana a kunyace ina neman abinda zamuci kada mu halaka duk da su basu nuna min komai akan kin su da nayi da farko din. Duk lokacin ana cikin tsananin harkan corna virus din nan dake yawo a kafafen yada labarai amma ni ta kaina nake da yarana a gari. Ganin halin da ya barni yasa ran kanina baffa ya baci don ya gama service yazo gida a lokacin nan ya fara matsa mashi akan yana bukatan kudin shi dake hannun shi. Zaiyi lalura dasu ne don haka ya aiko mashi da abinsa a cikin lokaci don lokacin da ya diba zai bada ya shige harda wata shidda ko. Tun ban san suna yar tsama da baffan ba har takai na sani nima baffan ya fara ganin laifina wai duk nice ai najawa kaina wullakanci a gun Jamil din. Ranan dai na gaji da safe na dauki waya na tura mai da text massage kamar haka. Jamil ko kare mutum ya bari aka ce mai ya samu matsala zai wawayo shi ya duba lafiyan shi. Balle dan mutum mai rai ka tuna ni marainiya ce banda uwa banda uba sai Allah da yan uwana dakai. Saukin abin Duk abinda mutum yayi Allah na ganin sa kuna can matan duniya suna rudin zuciyar ku ka jefar damu nan ka manta damu. Ina gamawa na tura masa bai bani amsa ba run ina duba wayata har na daina don bai turo min da amsa ba bai kuma kirani ba. Ni na dauka ba zai amsa min ba sai can dare misalin goma da rabi ya kirani sai Amira ta dauka tana gaida shi. Yake tambayan ina maman ku tace gata nan tana tambayan shi baba yaushe zaka zo yace yana nan tafe ki ba maman ku wayan. Ta miko min na karba da yi mashi sallama bai karba ba sai cewan da yayi kece kika turo min da sako ? Shiru nayi ban bashi amsa ba yace maman Amira kina jina nace eh yace na sake ki ma,ana sauran saki daya dake tsakani mu na yanke shi yau. Yana fadin haka ya kashe wayan shi ya barni a gurin sandare zuciyana tana famtsama da al,amarin shi ba abinda yazo min a rai sai maganan anty da tasha fada muna akan mazajen mu shine. Kuyi hankali da mazajen nan naku wallahi watarana zaku wayi gari sun baku baya indai namiji ne kun dauki rayuwan ku gaba daya kun ba mazajen ku amna kun manta da kowa naku. Kun maida su sune uwa sune uban ku duk kokarin da dangin mahaifan ku ke maku baku gani sai gani kuke kowa makiyin ku ne yanzu. Zasu iya sakin ku a lokacin da komai naku ya kare ko su kara aure abokiyar rayuwan jin dadi nan gaba bayan kun gaba batar da komai naku a kansu . Don haka wallahi ku gyara tun abu bai lalace maku ba gaba don mazan yanzu basu da tabbas a rayuwa wanan lokaci na ba maza amana gaba daya ya wuce ko. Idan anty tana wanan maganan mukan ji zafin ta ko muga tana muna baki ne sai muje gefe mu zage ta muce bakin da take muna ya koma kan diyan ta ba mu ba. Yau sai gashi maganan ta ya zama gaskiya a gare ni a lokaci guda nayi tunane kala kala a raina banda abokin kuka a dakin kuma hawaye bai zo min ba ko zan samu sauki a zuciyana. Murya yata amira ne ya dawo dani ga tunanen da nake a gurin tana fadin yanzu mama baba ya sakeki ina zamu koma ke nan kuma ? Sai lokacin hawayen da nake nema yazo min a lokaci daya na fara sakesu a fuskana nan muka taru dani dasu muna kuka a dakin ba mai bamu hakkuri. Don yanzu yara wayon su yafi shekarun su don sun fahinci abinda kalman sakin dayace yayi min yake nufi har suna tayani yin kukan da nakeyi. Na rasa yadda zanyi da raina kuma wa zan tunkara in fara fadawa sai gashi ya sake kiran wayan sai amira ce ta dauka tana fadin baba ka saki maman mu ne ? Yace Amira ba maman ki waya yarinyar tazo ta kara min wayan a kunne yake fadin sorry fa na saki karamin zawarci ko kiyi hakkuri yana gama fadin haka ya kashe wayan shi. Sai wani haushi shi na kara jin ya shigo min a zuciyana wai karag min zawarci ya manta da dinbin matsalon dake gabana wanda ban san da wanda zan fara ba a ciki yanzu. Don nasan na sabawa dangina da yan uwan mahaifan, dama duk wani wanda ke tare dani ada muna amfana da juna a can baya. Ba wanda yazo min a rai sai Baffa kanina a lokacin don haka na daga waya na kirashi a cikin daren lokacin sha daya da rabi na dare yayi. Yana dauka na fara mai kuka a kidimay yake tambayana abinda ke faruwa dani. Cikin muryan kuka nake fadin Baffa Jamil ya sake ni yanzu yace a cikin kidima shima yazo garin ne nace a a ta waya mukai magana dashi yace ya sakeni . Ya sake fadin garin yaya haka ya faru daku kuma nace wallahi daga magana ya furta ya sakeni sai cewa baffa din yayi to ai shike nan ya kashe waya. Na sake kiran shi duk da haushin kalamin shi da nake ji din a lokacin cewa da yayi ai shike nan nace zaka zo ne yanzu ? Yace ba inda zan zo yanzu dare yayi ki bari sai da safe zan shigo da Allah ya kaimu ya kashe wayan shi. Ranan a yadda naga dare haka naga rana a rayuwana in sakawa ina kwancewa ni kadai a dakina don yaran sun gaji da sharholiyan su sunyi barci abinsu ko. Kiran asuba nayi sallah ga batan basirana sai yafawa nayi zuwa gidan wanan dan uwan nasa da mukaci kudina a tare dasu nayi. Kafin inje shiya kirasu ya fada masu karya da gaskiya sun hau sai cewa sukayi ainina ja wa kaina da nayi hakkuri yadda kowa ke hakkuri aida ba haka ba. Na rasa abinda zance sabofa na fahinci bayan nasu suke haka na kwaso kafa na dawo gidana inda na samu kanina baffa yazo yana wanke ma yarana baki. Ina shiga ya kalleni fuska a murtuke yana fadin ke kuma ina kika fito tun da safen nan daga massalci na nufo gidan ki ban samay ki ba sai yara dake barci. Nace unguwa na tafi wani kallo ya watso min tare da fadin gidan malam kika tafi ke nan ko ? Cewa mahaifin jamil din kai tsaye na kyale shi tunda ya gano ni yanzu ni ba wanan ne a gabana ba nan dai na fara kawar da zancen tare da fadin wallahi baban Amira ya cuceni. Yace ya cuci kanshi don Allah zai saka maki dama mu ya samu wuri ya zauna tare da tambayana yadda abin ya faru haka. Ban boye mai komai ba na kwashe na fada mai duk yadda mukayi har sakin ya shiga tsakanin mu yace min takardun shi fa na karatu nace suna nan. Ok kin gane duk wani abu da kika san nasa ne ki hado min su ki bani wallahi idan bai ban kudina ba ba zan bashi ko allura ba a cikin su. Nan dai bayan mun gama magana na hado mai komai nasa harda yan tsumakaran shi na bashi na yadauka ya fita dasu akn cewa zamu hadu a gidan baba kabiru ansan yadda za a yi. A haka muka aje shawara dashi bayan fitan shi naji ba zan iya tsayawa yin wani abin karyawa ba can nasa yarana a gaba muka nufi gidan gaba daya. Sai ganin mu mutanen gidan sukayi da safe haka suna fadin ina muka fito haka ne da sassafen nan kuma ban iya masu magana ba na shige dakin anty. Na kasa magana sai da Baffa yaji muryana ya fito daga dakin su na samaein gidan yazo shike fada masu abinda ya faru dani . Sai duk suka saka salati a lokaci daya hankalin kowa ya tashi balle ma da na ce masu saki uku ne a tsakanin mu sai mamaki ya kamasu a lokacin . Suke tambayana garin yaya haka ya faru basu sani ba ko a lokaci daya yai min saki uku gaba daya haka ? Nan kowa ya shiga fadin abinda yazo mai a baki wanda a lokacin nake jin maganganun nasu kamar kari a jikina. Nadama ya fara zo min tare da dinbin dana sani a rayuwana wanda yanzu keya ce gareni don aikin gama ya gama ko wasu daga cikin su har da kuka sukayi don bacin rai. Anty ta nisa ta fara bani magana cikin kwanciyan hankali tare da jefa min kalaman da suka fara kwantar min da hankalina. Lokacin baba ya fita tace inje in rufe dakina in dawo lokacin baba din ya dawo gida sai a yanke shawaran abinda ya dace dani. Nace banda kwadon da zan kule dakina dashi tace ikon Allah ta mike ta dauko min kwason daki ta bani na tafi . Tun da na dawo gidan na rasa wani abin kwarai da zan dauka a dakin nawa don babu wani abin kwarai da zan iya tafiya dashi gida lokacin. Hakan dai na dan tsintsinto tsumakaran yarana don in sunyi wanka su samu na canzawa a gida kafin a yanke shawara akan mu a san yadda za ayi damu. Haka dai na rufo kofan na juya zuwa gida hankali a tashe dani don ko maganan karyawa ban da shi a lokacin don tsanin damuwan dake tare dani. A can gida kuma bayan fitana ne baba ya shigo ake fada mai abinda ke faruwa ashe a cikin dare a ciki ikon Allah baba ya samu wata dama na bada mutum biyu a nursing school . Sai ya kira layin Jamil din don yaji inda da hali sai jn tafi sai jamil di ke fada mai hali da muke ciki dashi sai dai bai fada mai ko saki nawa bane don baba ya kashe wayan tunda ya fada mai cewa ai mun rabu dashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU