[27/07 à 11:37] MRS SADAUKI 👑: *MAITAR IDO*👁️ 👁️👁️👁️👁️👁️ HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* 1-2 “ Gulbi ya zo” Laila ta faɗa ta na mai ajiye hullar gashin dokin da na bata ta sharce mini. “Za mu je mu yi wanka da zarar mun gama” Farida ta ɗora. “Ni dai ba zan je ba,ina da aiki sosai” na faɗa ina mai ci gaba da saƙa sabuwar hullar gashin doki. Duk suka matso kusa da ni kowacce da nata kalaman har suka ci galaba kaina na yarda ba tare da na san abin da ke jirana can gulbin ba. Na ce “ amma za ku taya ni sayar da abinci ” “Mun yarda” suka haɗa baki wurin faɗa . Sunana Sarah ,Laila da Farida ƙawayena dukkanmu ba za mu wuce shekara sha uku-uku ba.Muna da ra'ayi kusan duk ɗaya,ciki kuwa har son wasar ruwa ko ruwan sama ake yi sai mun san yadda muka yi muka fito muka yi wanka. Ƴar talakawa ce ni,boyi-boyi shi ne aikina ina taya wata mai gidan gyaran gashi aiki da kuma mai sayar da abinci aiki duk don na samu abin da za mu rufawa kanmu asiri ni da Kakata. Fitowa muka yi mu duka ukun na rufe salon ɗin kafin mu kama hanyar da za ta kai mu wajen magudanar ruwa.Tun a hanya muke ta zancen har muka iso,duk tsaye muka yi muna kallon yadda ruwan ke ta zubowa daga wani dogon tsauni su na cika makeken wurin da muke kira Gulbi . Tuni sun shige sun fara wanka,ƙafa ta ɗaya na saka da niyyar isa wurin su sai na ji kamar an riƙe ni. “Sarah ki shigo mana” shine abin da suke faɗa ,na amsa da “ tooo” ina mai ɗora ɗayar ƙafar tawa ta dama a can gaba. Dodon kunnena na ji ya tsira kamar wacce aka cakawa allura,kafin kuma na fara jin wani irin zafi daidai saitin zuciyata yayin da wani abu ke min yawo a maƙogoro kamar wacce ta ci yaji. Na ɗaga idona na kalli sararin samaniya sai na ga hadari baƙi ƙirin ya na haɗuwa ,ya na yo ƙasa kamar zai rubto cikin ruwan gulbin.Wani tsoro ne ya ziyarce ni nan take, kwacaaaa na faɗi rub da ciki cikin ruwan “Saraaaaah!” na ji muryar ƙawayena wacce ita ce ta ƙarshe daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai tashi na yi na gan ni kwance kan yamutsatsar katifar mu. A hankali na tashi zaune ina mai dafe gaban goshina da ke yi min mugun ciwo. “Kin tashi?” Kaka ta tambaye ni ta na tsure ni da ido. Na ce “ eh! Amma....” sai kuma na yi shiru. “Ki kwanta ki sake hutawa na san kin galabaita ” ta faɗa tare da miƙo min wata ƴar madaidaiciyar ƙwarya,na karɓa da niyyar shan ruwan da nake kyautata zaton magani ne sai kuma na tsaya cak ina kallon can ƙasan ƙwaryar da nake hango wasu halittu masu motsin rai. “Kaka mine ne nan kika bani?” na yi tambayar ina mai maido dubana gare ta. “Ruwan floris ne” ta bani amsa, floris wata itaciya ce mai warkar da dukkan wata cuta musamman wacce ta shafi mugaye,na sha jin masana na faɗar ta don ba zan manta har a cikin wani littafin Mrs Sadauki na RUHIN ALJAN na ta taɓa jin an yi amfani da ita.Sai dai sam wannan launin ruwan ba su yi kama da waɗanda aka yi siffanta na floris ɗin ba,duk da hakan dai bai hana ni na sha su ba. Ƙwaryar na ajiye ko minti biyar ba a yi ba na soma jin goshina na yin wata ƙara kamar irin ana son ɓara shi gida biyu.Dunƙulallar kwanyata ce ta fara motsi a cikin ƙoƙon kaina,yayin da hasken abin da ya faru da ni a cikin ruwan ya dawo min. Kifaye ne irin masu rabi mutum suka tarbe ni a ƙarƙashin ruwan ,tamkar wata sarauniya haka aka dinga yi mini wanka da wasu ruwa sannan aka shafa min wani abu cikin tafin ƙafa ,mundun wuyana wani matashin saurayi mai hatsabin kyawu ya cire ya saka a wuyansa kafin ya cillo ni gaɓar ruwa.Na ja wani dogon numfashi bayan na gama samun flashback ɗin da aka gama yi min,wuyana na shafa tabbas babu sarƙar munduwar (irin sarƙar nan da ake yi da kuɗi mai tambarin kan mutum....) Kaka ta matso kusa da ni ta na cewa “Sarah faɗa mini mi kika gani?” shiru na yi na ƙo bata amsa sai ma kwanciyata da na koma na juya mata baya. Ta yi wani “hum!” kafin ta fice,ganin haka yasa ni kuma na tashi da sauri na jawo wani tsohon akwatin ƙarfe da Kaka ke ajiyar shi shekara da shekaru don ko da na buɗe ido na ganta da abin ta sannan in ciwon mutum yayi ƙamari wasu na zuwa ta basu magani. Sosai na yi mamaki ganin tsofin hotuna waɗanda za su kai ɗaruruwan shekaru a cikin akwatin.A hankali nake dubawa har na zo kan wata sarauniyar kifaye,yanayin fuskarta kawai zai tabbatar ma ita ɗin muguwa ce.Abubuwan ban tsoro na ta ci karo da su waɗanda na cika kallo kuwa sai na ji idona sun yi wani zuuuuu! Kamar su na zuƙo wani abu.Jin kamar motsinta kawai sai na yi saurin na mayar da komai na tura akwatin. “Ku shigo” cewar Kaka alamun baƙi ta yi ,don dama jefi-jefi ta kan same su. “Sarah ki fita waje ina har mu gama” Kaka ta umarce ni. Fitar na yi kamar sauran lokutan da in ta samu ziyara haka za ta ce na fita ni kuma sai na yi amfani da wannan na je wurin wasa sai dai yau wani abu ya shiga kwanyata na son sanin shin mine ne Kaka ke yi da kullum take fiddo ni waje? Sai da na bari an ɗauki kamar minti biyar sannan na yi ƙoƙarin tashi daga inda nake saboda yadda zuciyata ke azalzala ta sai dai abun mamaki ji na yi ƙafafuna sun riƙe ba zan iya tashi ba kamar wacce ta samu shanyewar jiki.Ina nan cikin wannan hali har baƙin suka fito waɗanda suka kasance mata biyu ne uwa da kuma wata budurwa.Abun mamaki sai a lokacin ƙafafuwana suka saki,Kaka ta bini da wani kallo ta na mai jingina da lanlaga-langan ƙyauren ɗakinmu. “Tun yaushe kika fara jin wannan canjin?” ta jefo mini tambaya. Na miƙe tsaye ina cewa “wane irin canji?” “Na son ganin abin da nake yi” ta bani amsa kai tsaye.Na turo baki gaba na ce “to mine ne kike yi?” “Ki na son sani?” ta tambaye ni,na gyaɗa kai alamar eh tace “sai kin faɗa min mi ya faru da ke cikin ruwa” ban san ko mine ne dalili ba haka kawai na ji ina son ɓoye mata,na ce “babu komai ni da na faɗa ruwa ta ya za a yi na san abin da ya faru? Ki tambayi su Laila kawai” “To shikenan” Kaka ta faɗa amma tabbas a cikin ƙwayar idonta ina ganin ƙin yarda da zancena wanda kuma ban san dalili ba. Da dare bayan mun ci abincin Kaka ta soma yi mini gatana irin ta ababen tsoro,don ina son irin wannan labaran a haka na soma jin bacci kamar kullum sai dai na yau ya sha banban da sauran baccin da nake yi don kuwa idona a rufe suke amma ras nake ganin Kaka wacce take yi mini wasu abubuwa da na kasa gane su. Gashin kaji ne na ga ta maƙala bayan kunnuwan ta,ban gama mamakin dalilin yin haka ba har sai da na ga ta rikiɗe ta zama kaza sannan ta tashi sama.Maimakon ni da ke kwance cikin ɗaki na zamana a nan a'a duk inda Kaka ta nufa ina kallo,gidajen mutane ta dinga bi ta kasaye rufin ɗakinsu ban san dalilinta na yin haka ba sai da ta gaji da yawo kafin ta dawo ta gida.Siffarta ta ɗauka ta mutum daidai nan kuma baccin gaske ya ɗauke ni ban farka ba sai washegari,babu sallah babu salati haka na fita na yi fitsari na wanke ido.Wata irin yunwa nake ji,sai yanzu na nufi Kaka wacce ke zaune kan tabarmar kaba ta na zuba taba cikin leda.Tsaye na yi cak ina kallon ƙafafunta da suke sak irin na kaza,da sauri na ɗauke idona da na ga za ta ɗago kai. “ lafiya kika yi tsaye nan?” ta tambaye ni. “Yunwa nake ji,kuma kin san jiya ban je na taya Lantana sayar da abinci ba ballantana ta bani” na bata amsa,ko kafin ta ce wani abu Sailuba ta shigo gidanmu da sallama. Da sauri na gaishe ta,ita kuma ta shiga gaida Kaka kafin ta maido dubanta gare ni ta ce “jiya ba ki gama mini aiki ba kika rufe shago ina makullin yake?” Na waro ido kafin na fara lalubar riga ta ai kuwa na ci sa'a ya na ciki,na fiddo na bata ta karɓa kafin ta ce “mu je to ki ƙarasa” haka na bi bayanta muka tafi salon ɗin inda take yi wa mutane gyaran gashi da farce ,ta na yin kitso kuma da lalle. Tun da na ga mota a parker na san hajiyar birni ce ta zo,don haka duk muke kiranta.Duk bayan watan-wata take zuwa ta na sayen gashin mutane da ya zubo wurin gyara,ban san iya lokacin da suke tare da Sailuba ba amma dai na san wannan shine business ɗin su. Bayan Sailuba ta buɗe ɗan madaidaicin shagon ta ɗauko wata ƙatuwar leda ta zazzage duk gashin mutanen da aka tara, sai a lokacin Hajiya ta shigo ta karɓa ita kuma ta bata maƙudan kuɗi ta karɓe ta na godiya tare da cewa “hajiya sai kuma in kin sake dawowa”har mota ta yi mata rakiya kafin ta dawo sai fara'a take ta na ƙirga kuɗin.Karon farko da na ji ina son sanin dalilin business ɗin sayar da gashin mutane,na ce “anty wai don Allah mi hajiyar birni ke yi da gashi nan” “Ina na sani Sarah ? Ni dai ba ta bani kuɗina ba? Can ita ta sani in ma dai dafa shi za ta yi ta ci.Ɗauki tsintsiya ki share wurin kafin mutane su fara zuwa sannan ki ɗauki allon sanarwa ki fidda shi waje” ta na gama faɗa ta fice ta bar ni da tambayoyin da bani da amsar su sai dai na sha alwashin sai na binciko su..... *Gajeren labari ne*🌚 [27/07 à 12:52] MRS SADAUKI 👑: *MAITAR IDO*👁️ 👁️👁️👁️👁️👁️ HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* 3-4 Cikin sauri na share shagon na goge tile da kuma ƙaton bancin da aka jera mayuyuka na wanke gashi da kuma wanda ake shafa wa bayan an fiddo mutum daga tukunya. Zaune na yi na ɗauki hullar jiya da ban ida saƙawa ba,ina tsaka da yi sai ga anty Sailuba.Leda ta miƙo min ta dambu na karɓe na huda bakin ledar na soma ci ina shan ruwa har na gama. Ɗan ƙaramin rediyo anty Sailuba ta kunna muka fara shan kiɗa,wasu ƴan mata uku ne suka shigo ɗaya na santa ta na zuwa gyaran gashi, biyun kuma baƙin fuska ne. “Sannun ku da zuwa ku zauna,Sarah kawo musu ruwan sanyi Watsima sai yau aka dawo ina ta zuba ido shiru” anty Sailuba ta faɗa fuskar nan tata cike da fara'a don a haka take saye customer ɗinta. Kan kujera duk suka zauna yayin da Watsima ta biɗe kai ta na cewa “wallahi anty Sailuba gashina duk ya lalace dubi yadda ya koma,shi yasa na zo ki gyara min shi da kyau biki ake na ƙawarmu” Ruwan sanyin na miƙa wa kowacce leda ɗaya,kafin na zuba idona kan gashin Watsima da ya cicire a gaba sannan tsayinsa ya rage ba kamar wancan zuwan da ta yi ba. Anty Sailuba ta shiga tatataɓa gashin ta na cewa “ doli gashin ki ya lalace mana Watsima,ba ki zuwa saloon sai fa in za ku yi sabga da ace ki na zuwa akai-akai wallahi tsaf za ki ga ya miƙe yayi tsayi.Bari na nuna miki wani sabon man tado gashi,zan saka miki shi yanzu in na wanke miki kai in ki yayi miki kuma sai ki saya” ta faɗa tare da zuwa gaban table ɗin ta ɗauko wata ƴar kwalba ta miƙa wa Watsima kafin ta ce “ wannan ƙawayen ki ne?” “Eh su ne nake baki labari waɗanda na ce miki ƴan uku ake kiranmu ” ta bata amsa. Anty Sailuba ta ce “ Allah sarki ga shi kuwa har kun so ku yi kama da juna,su ba za a yi musu gyaran gashin ba?” Watsima ta kalle su kafin ta ce “ kun yi shiru sai kace wasu kurame ita wannan kitso za a yi mata ita kuma wai a ɗinka mata gashin doki ya haɗe da na ta” Anty Sailuba ta yi dariya kafin ta ce “ Sarah zo ki yi mata kitso ki aje hankali sosai kin ga yau ta fara zuwa ina son ayi mata wanda za ta jawo mana customers” ta ida zancen cikin raha. Wacce aka ce zan yi wa kitson ta ce “ wannan ƴar yarinya ? Na zata ke za ki yi min” sai ta ɓata rai. Anty Sailuba ta ce “ wai don a yi sauri ne na ce haka,amma in ni kike son duk ɗaya ne .Watsima ke zauna ta wanke miki gashin in ta gama miki sai ta ɗinka wa wannan gashin dokin” Ita Watsima ta san ni sarai,shi yasa ba ta yi gardama ba ta zauna na shiga wanke mata gashin nata.Bayan na tsane shi da towel sai na soma saka mata kwarkwaro daga nan ta shiga tukunyar busar da gashi. Na maido dubana ga wacce zan saka wa gashin dokin na ce “ kin zo da mèche ɗinki ko saya za ki yi?” “A'a saya zan yi ai ku na sayar wa ko?” ta tambaye ni,na bata amsa da “ eh bari na ɗauko ki zaɓa” kalolin na kawo mata bayan ta zaɓa ta koma ƙasa ni kuma na hau kujera na soma saƙa mata ita tsawon lokaci muna abu ɗaya don akwai wuya kafin na je na duba gashin Watsima tuni ya bushe kuwa.Na kashe casque ɗin ita kuma ta fito ta zauna kan kujera,mai na ɗauko da niyyar shafa mata sai kuma na ƙure gashin da ido. Wani haske na ga ya dalle gashin wanda kuma ina da tabbacin daga cikin idona yake,haka kawai na ji ina son gwada wani abu da ban san taƙamaimai mine ne ba.Can ƙasan zuciyata na raya ‘ gashi tsiro ka yi tsayi’ ai kuwa haka na ga ya ƙara tsayin na saki murmushi ni ɗaya zan sake ƙara gwadawa Watsima ta ce “ wai ba za ki gyara mini gashin ba ne na tashi?” da sauri na shiga shafa mata mai sannan na shace. Daga can anty Sailuba ta ce “ kin ga kuwa wallahi gashin ki har ya ƙara tsayi yanzu da kika shiga tukunya,mutane sun kasa ganewa ka wanke gashi gida ba ɗaya yake da ka zo saloon ba” Cike da murna ita ma Watsimar ke duba ƴar jelar gashinta da na ɗaure,ta ƙara tsayin ba ƙarya wanda kuma ni kaɗai na san wannan sirrin. “ A gaishe ki ƴar yarinyata aikin ki na kyau” anty Sailuba ta faɗa bayan na kammalawa ɗayar ita ma. Wacce ta ke yi wa kitson ta yamutsa fuska ta na kallona kafin ta ce “ ɗiyar taki dai ƙazama ce dubi jikinta kamar almajira da wani baƙi nata kamar zunubi” Anty Sailuba ce ta shigar min “ a'a yau dai ne ta tsaya da dauɗa shi ma don ba ta shirya ba na je na kirawo ta amma ta na da tsabta” Ta tuntsire da dariya ta na kallon kaina wanda yake ɗauke da kitso ƙire-ƙire saboda yadda banda gashi kafin ta ce “ da wani gashi nata kamar gammo! Ko da yake yawancin ƴaƴan masu salon suke babu gashi duk aci gwaigwai ne” Zuwa wannan matakin tuni raina ya ɓace amma ban ce komai ba sai gashinta da na ƙurawa ido, dogo ne mai santsi duk yadda aka yi ta gama iri da Fulani .A take kuma baƙin ciki ya kama ni ‘ Allah sa gashin naki duk ya zube’ na faɗa a zuci ina mai ci gaba da kallon gashin yayin da idona kuma sai vibration suke suna min wani zuuuu! “ Je ki yi wanka ki dawo kar ki biye mata,ni kam mine sunan ki?” anty Sailuba ta buge da tambayarta bayan ta umarce ni na je na yi wanka. “ Leemat” ta bata amsa nan ne na san sunan nata da haushinta kuma na fita na wuce gida. Ina shiga na tarar Kaka ba ta nan sai ɗaki da ta rufe shi ma ba kwaɗo,na buɗe na shiga.Jakar kayana na jawo don fiddo kayan da zan saka abun mamaki kuma sai na tarar da munduwa ɗina a sama .Cike da murna na ɗauke ta na mayar a wuyana,tsakar gida na fito na cika buta da ruwa na je na yi wanka da wani guntun sabulu .Ina fitowa na saka kayan da na fitar kafin na nufi gidan anty Hinda mai sayar da abinci.Ta na gani na ta haɗe rai na san fushi take da ni saboda jiya ban zo ba,na sosa ƙeya na ce “ ina kwana anty?” “Lafiya!” ta amsa mini da shi kafin ta ɗauko wani bokiti mai ɗauke da wasu ruwa kamar sauran wanka don har da sabulu-sabulu amma haka ta buɗe tukunyar mita ta juye su. Sai kuma na ga ta kalle ni a ɗan daburce kafin ta ce“am...yau ba ki je wurin Sailuba ba ne?” ni kuwa ganin ta saki ranta yasa na watsar da zancen ruwan dauɗar ta zuba a miya na ce “na je yanzu ma can zan koma,dama biyo wa na yi na baki haƙuri abin da yasa jiya ban zo ba ruwan Gulbi na faɗa sai bayan magarib na farfaɗo ” ta shiga tashin hankali sosai kafin ta ce “Allah tsare gaba,to in kin tafi don Allah ƙarfe biyu na ɗaya na buga wa ki wuce can inda muke sayar da abinci kin ga dai yau mai yawa na yi fiye da na kullum” da to na amsa mata kafin na koma saloon har an kusa ida mata kitson ,yanzu ma da na dawo sai da ta tsokane ni “aci gwaigwai an jiƙa dauɗa da sunan wanka” Anty Sailuba ta ce “Leemat ban son haka fa” dariya ta yi tare da ci gaba da yi min sharri,tsabar iskanci ma da za su tafi haka ta sa yatsa a fuskata ta na dirzawa ta na cewa “wallahi duk baƙin ta ne na zata ko dauɗa ce” na ture hannunta ina hararenta ta dungure min kai ta na sa tissu ta goge yatsanta ta ce “na shafo dauɗa” sai ta kai yatsan ga hanci ta na sunsuna wai wari nan fa suka shiga yi mini dariya,ni kuma kawai sai na fashe da kuka bayan tafiyar su ne anty Sailuba ke ce mini “ke wasa fa take yi miki kawai don a yi dariya” sai dai duk yadda ta so shawo kaina ƙin yarda na yi kawai dai na haɗe abin a zuci na kammala mata aikin da zan yi kafin na wuce wurin sayar da abincin. Yadda na ga dandazon mutane duk sun yaɓe anty Hinda sai abin ya bani mamaki don mun sha yin kwantai sai mun dawo da abinci gida yau kuma abun mamaki tururuwa saya ake.Ashe farkon mamakina ne ban ma ga komai ba,sai da na ƙarasa na soma taya ta sayarwa hatta yadda ake zuba abincin an rage awo amma haka muka sayar da shi tasss sai wanda ta zuba mini .Sai da na wanke robobin da aka ci abinci sannan na zauna na soma cin abincin hannu baka hannu akushi,daga nan gida na wuce amma har yanzu Kaka ba ta nan ganin haka na koma saloon ba ni na koma gida ba sai wajen taran dare. A zaune na tarar da Kaka ta na sauraren rediyo ,bayan na gaishe ta tare da tambayar inda ta je na samu wuri na zauna.Amma sai na ga Kaka ta ƙure cikina da ido,ban kai ga tambayar ta lafiya ba kuma na ji ya fara mirɗa mini.Maimakon in yi zawo a'a kumfa ne ya soma fito mini ta baki kamar akuyar da ta haɗi leda.Kaka ta yi ƙyaci kafin ta bani magani na sha nan na soma amai kamar zan amayar da hanjin cikina,“haba Hinda da ni kike zancen!” ta sake yin wani ƙyacin..... *Gajeren labari ne*🌚 [27/07 à 16:37] MRS SADAUKI 👑: *MAITAR IDO*👁️ 👁️👁️👁️👁️👁️ HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* *NB:* Maitar ido iri-iri ce akwai ta tsafi,akwai kuma wacce ake haifar mutum da ita irin tace wacce in mai ita ya kalli abu da ya burge shi ko akasin haka sai kuka abin ya lalace.Itaciyar bedi ta sha mutuwa silar Maitar ido,wasu sun san su na da ita wasu kuma ba su sani ba.In sha Allah a sannu zan faɗi alamominta da kuma yadda mutum zai yi rabu da ita. 5-6 Na sha baƙar azaba sosai kafin na samu aman ya tsaya,Kaka ta ce “je ki kwanta ” ban musa ba na haye katifa a gajiye,sai dai tuna abin da Leemat ta yi mini yasa na ji baƙin ciki ya rufe ni.Na yi ƙwafa kafin na ce “wai Kaka don Allah baƙin nan na wane ne na kwaso? Tsakanin Inna da Abba waye baƙi?” Abun mamaki tambayar tawa ce na ga ta razana Kaka,sai ta kasa bani amsa sai motsi take da baki ni kuma na ƙara jin haushi na ce “a gaskiya ko ma dai wane ne na biyo ya cuce ni,yau an wulaƙanta Ni an tozarta ni saboda kawai ni BAƘA CE(Sajida Nijar)” Kaka ta ce “mi ta yi miki? Sannan wane mataki kike son a ɗauka kanta?” Jin abin nema ya samu har da tashi na yi zaune ba tare da na san wannan ne farkon jefa rayuwata a cakwalkwalin ruɗani,na ce “so nake ta zama baƙa kamar dai ni,sannan gashin kanta wanda ta yi mini gori a ɓata shi ya zamana nawa ma ya fi nata kyau da tsayi” Kaka ta saki murmushi wanda a cikinsa na hango tsantsar farin ciki kafin tace “Sarah kin tabbata ki na son haka?” Ba tare da wani tunani ba na ce “eh sosai ma Kaka” Ta ce “kin shirya?” “A shirye nake ai” na faɗa ba tare da na san shirin mi Kaka ke nufi ba,ta ce “to babu damuwa yau za mu je ki ɓata rayuwarta da kan ki,don haka kwanta ki yi bacci tun kafin dare ya tsala ” Cike da murna na kwanta ina tunani ƙila acid za mu je mu watsa mata sannan mu datse gashinta,da haka bacci ya ɗauke ni.Na ɗauki lokaci mai tsayi a cikinsa kafin na ga Kaka na yi min irin wannan abun na jiya,wasu ruwa ne take yayafa min ta na yin wasu surkullen da ita kaɗai ta san ma'anar su.Abu guda na sani shine bacci nake,amma kuma abun mamaki sai na irina ta miƙe tsaye ta na tambayar Kaka “har lokacin tafiyar tamu yayi?” “Eh fito mu tafi jirgi na jiranmu” sai ta ja hannuna muka fito,ni kuwa sai ware ido nake na ga inda zan ga jirgi sai dai ina abin ya wuce tunanina.Turmi Kaka ta kada kwance hannuna na cikin nata muka shiga turmin nan kawai sai gani na yi ya tashi da mu sama.Da mamaki na tambaye ta “amma Kaka dama turmi ya na iya tashi sama?” Ba ta bani amsar tambayar da na yi mata sai bayani ta soma yi mini,“leƙa ƙasa ki ga yadda duniyar da muka baro take” na je na kama bakin turmin na leƙa sai na duk ga gidajen mutane nan da kuma ababen hawa,na waro ido ina mamaki na ce “ya na ga garin duk yayi duhu alhalin nan sama kuma hasken rana?” “Duniya biyu ce mabanbanta,daren can shine safiyar wannan duniyar.A sannu za ki saba za ki ji wannan ɓoyayyar duniyar ta fi waccan daɗi,tun tuni nake son kawo ki amma kika ƙi bani haɗin kai sai yau da zafin ɗaukar fansa ya ci galaba a kan ki” ina shirin yi mata wata tambayar ta ce “shuuut! Mun kawo Dutsen Muradi ki nutsu ki aiwatar da komai yadda ya kamata” Kan wani ƙaton dutse jirginmu na turmi ya sauka,yanzu ma Kaka ce ta kama hannuna muka fito “ ki faɗi abin da ya kawo ki mana kin yi wani tsaye” Kaka ta faɗa ta na kallona,“ to ai ni ban san ya zan yi ba” na faɗa ina ƙyafƙyaf da ido. “Sunan ta za ki kira ” “Leemat!” na faɗa cikin rawar murya,wani haske ne ya soma sauko wa daga sama mai gamar gajimare kafin ya tsaya a gabanmu,ta cikinsa nake hango Leemat a kwance jikin wani matashin saurayi sai shafar mata gashin da aka kitse yake. Maimakon muradin gashin ya zube kamar yadda na zo da niyyar,a'a sai na canza ƙudiri na kafe tsorayen da ido ina mai cewa “ ku zama macizai ta yadda saurayin kawai zai iya ganinsu” ko baki ban rufe ba kuwa tsorayen suka fara motsi kafin su zama macizai su na fiddo halshe.Saurayin ya fasa ihu tare da koma gefe ya na rawar sanyi tuni fitsari ya soma yi masa zuba,sai haƙuri yake bai wa Leemat kar ta cutar da shi ita kuma ta na tambayar mine ne gashin kanta yake yi mata nuni wanda yasa ta nufi madubi don dubawa sai dai kafin ta isa ne Kaka ke ce min “ da zarar ta isa ga madubin mutuwa za ta yi don shi mirror bai ƙarya ki yi saurin dakatar da ita” Take na ruɗe jin zan yi kashin kai na ce “ ta yaya Kaka? Ya zan tsayar da ita ?” kafin kuma ta bani amsa na ƙure ƙafar Leemat da ido nan take ta ɓangwale ta faɗi ƙasa timmm daidai nan kuma Kaka ta yi wani furuci komai ya tsaya cak ciki kuwa har da tsintar kaina kan katifa kuma numfashina ya dawo gangar jikina. A firgice na tashi ina dafe zuciya,sai kuma na yi saurin sauka na ɗauko ruwa na sha ina mai cewa “ na yi mummunan mafarki ” don ni duk a tunani mafarkin ne na yi ba gaske ba.Kan shimfiɗa na je kwanta,sai kuma na shiga tambayar to ina Kaka ta tafi cikin daren nan ƙila ko banɗaki.Ban kai ga samo amsa ba na ji wata uwar ƙara rudududuuu kamar ta sama za ta faɗo,tsoro ya kama ni na ƙanƙame jikina.Ina cikin wannan yanayi Kaka ta buɗo ɗaki ta shigo cakwal-cakwal da ƙafafunta na kaza,ido na murza na dai ga har yanzu ba su canza izuwa na mutane ba sai kuma na tuna tun jiya fa haka suke har lokacin da anty Sailuba ta zo ta ja ni muka tafi saloon. Na buɗe baki da niyyar tambayar ta “ Kaka wai...” amma sai ta katse ni ta hanyar cewa “ rufe mini baki tun da ke ba ƴar goyo ba ce,na taimaka miki don ɗaukar fansa shi ne kika baro ni can don ki nuna mini wuyan ki ya isa yanka ƙarfin ikonki(ƙarfin tsafi shine sai miyagu ke ɓoye shi su ce ƙarfin iko) ya ma fi nawa.Ina ce dai ni ce nan na raine ki tun ki na tsuman goyo,kuma ki sani daga yau na raba hanya da ke sai ki yi abin da kika ga dama tun da kin ishi kan ki.Sai dai ki sani tsohon kai ya fi sabon kai dafi ” ta na gama faɗa ta yi gaba ta nufi wani ɗan lungu da muke aje kaya.Wani ƙaton bindi na ga ya na yi mata reto kamar jela,duk ɓaɓatun da gama yi sam ban fahimci abin da take nufi ba don har zuwa yanzu duk na ɗauka mafarki ne na yi. Kayan jikinta ta canza sannan ta raɓa gefe na ta kwanta,hakan ya bani damar ganin salewar da gefen fuskarta yayi kamar wacce aka ƙona ga wuta. “Mi ya same ki kuma haka?” na yi tambayar ina shirin ɗora hannuna kan ciwon amma sai ta yi amfani da nata wurin buge ni tare da ɗora min yatsunta sak irin na mage don firgici har sai da na yi baya “ in kika kuskura kika taɓa ni zan yayage miki fuska” a tsorace na kai kaina na jingine ga bango. Ƙiri-ƙiri yau Kaka ta fito mini da ɓoyayyar siffarta,“ don Allah ki yi haƙuri ni ban mi na yi miki ba” na faɗa a tsorace ,“hum” ta yi wani ƙyaci kafin ta juya min baya ƙaton bindinta kuwa sai wani motsi yake kamar yadda mage ke yi. Muƙut! Na haɗiye wasu yawu kafin na ce “ wai Kaka wannan duk mine ne? Ƙafafuwan kaza ga kuma bindin mage a bayan ki?” Ba ta juyo ba ,amsa ta bani kai tsaye “ iya nawa kawai kika gani? Ke naki fa?” “Ni ai banda ƙafar kaza” “To ki duba wane kala gare ki” ta bani amsa . Furucinta yasa na tashi zaune don duba ƙafafuna sai dai mi zan gani? A madadin ƙafafu wani shabcecen bindi kifi ne tun daga wajen ƙuguna zuwa ƙasa na kifi ne.Ban san lokacin da na fasa wani uban ihu ba ina motsa bindin mai ɗauke da wasu ababe kamar mafarfeci. Ihun da na yi yayi daidai soma zubar ruwan sama masu mugun ƙarfi kafin ƙyaftawar ido ɗakinmu ya cika da ruwa.Hankalin Kaka a tashe ta soma tsalle-tsalle don kamar yadda mage ba ta son ruwa to ita ma haka take,ni kuwa maimakon ace na ji tsoron ruwan a'a sai na ji kamar ma na zo gidana ne .Ko kaɗan ban ji irin wannan yanayin ba na son fiddo kai waje,hasali ma wutsilniya na soma yi cikin ruwan ina yawo kamar wata ƴar ruwa.Munduwar wuyana ce ta soma fitar da wani haske mai ƙuna ,tsabar yadda hasken ke da ƙarfi har sai yasa na wani abu ya caki kwanyata da kuma daidai saitin zuciya ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai a washegari na tashi tuni kuma rana ta fito wantsar.Na yi miƙa na tashi zaune ina hamma,Kaka ta shigo ɗakin ta na mai cewa “sai yanzu kika ga damar dawowa?” Ban fahimci tambayarta ba hakan yasa na ce “Kaka ni da ke bacci ina kuma na je? Bari na yo fitsari na baki labarin mafarkin da na yi cabbb wai Allah na gode ma da mafarki ne” sai na sauka daga katifar na fita waje abun mamaki duk ruwa ne a kwance.Buta na ɗauka na raɓa ta inda babu ruwan na je na shiga banɗaki,ina fitowa na wanke fuska da ƙafafuwana sannan na koma ɗaki ina tambayar Kaka “wai ruwa aka yi jiya? Kuma ba lokacin damina ne ba” “Sarah kar ki raina mini hankali ki dinga yin abu kamar ba ki san mi kike yi ba,wuce dai ki tafi tun ɗazu Sailuba ke ta aikowa kiran ki” ficewa na yi na nufi saloon.Ina shiga na tarar da Leemat zaune a ƙasa yayin da kuma ƙawarta Watsima ke kwance kitson da aka yi mata jiya sai faman faɗin “washhh! Washhh” take yi yayin da ita kuma anty Sailuba ke ta masifa ta na cewa “ in ba abun ki ba Leemat daga saurayi ya ce kitson bai yi ba shikenan sai ki kwance?Allah duk da kin biya ni na ji zafi fa” “Anty Sailuba wallahi a rayuwata dama ban son kitso ,saboda na ci kuɗinsa ne na zo kika yi mini amma don wulaƙanci ba ki yadda ya fita daga ɗakin a guje ba kamar ya ga wata aljana” Watsima ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “In dai ya baki kuɗin iPhone ɗin ai shikenan ” “Ai ban yarda ma na raɓe shi ba sai da ya damƙa mini ita ga hannu,ta na can na baro ta a caji yanzu in gama wanke mini zan je na kunna ta na yi ta selfie ” Daga wannan ban sake sanin abin da suke tattauna wa ba sakamakon duniyar tunani da na lula ‘ kenan dama ba mafarki ne na yi ba a daren jiya?’ na tambayi kaina kafin kuma na yi wani makirin murmushi na ƙara cewa a zuci ‘ in dai haka ne kuwa Leemat ba zan bari ki yi selfie ɗin nan ba,wato za a yi mana burga da dogon gashi ’ Ina nan zaune ina ɗinka hulla aka gama kwance mata gashin,anty Sailuba ta wanke mata shi ta saka mata kwarkwaro sannan ta je ta zauna kan kujera aka ɗora mata tukunyar busar da gashi. Sai da na kwatanci gashin ya kusa bushewa kafin na ƙurawa tukunyar ido ina bata umarnin ta ja gashin Leemat ya shige can ciki ko minti biyu ba a yi ba kuwa tukunyar ta soma yin wata irin ƙara ta na fitar da haƙi haɗi da ƙauri. Hankali tashe anty Sailuba ta je za ta cire wayar lantarkin da ganga na kalli ƙawarta na ce ‘ɓangwale ki faɗi’ ji kake timmmm anty Sailuba ta faɗi tuni Leemat ta soma kuka haɗi da ƙoƙarin tashi amma ta kasa saboda yadda tukunyar ta riƙe gashin gam.Hayaƙin da ya soma fita na baiwa umarnin ya ƙara farashi ai kuwa shagon ya turniƙe da hayaƙi,Watsima sai tari take ta na cewa ta shiga uku ba ta ganin komai yayin da kuma anty Sailuba ke kukan ƙafarta.Sai a lokacin na miƙe na nufi Leemat,daidai gabanta na tsaya kafin na ƙuwara casque ido sai komai ya tsaya cak na jawo ta ina cewa “yi sauri ki tashi tun da an samu kin fito” Anty Sailuba da Watsima sai salati suke yi su na taɓa hannu ganin yadda gashin Leemat duk yayi wani iri kamar an kaɗa taliya ƴar murje.Kan kujera anty Sailuba ta zauna da Leemat wacce ke ta matsar ƙwallla,ɓarin mai aka yi mata iri-iri kafin a soma shatar gashin nan take ya soma zubewa ya na faɗuwa ƙasa sai ga Leemat da ƙwaiƙwayayen gashi.... [28/07 à 06:36] MRS SADAUKI 👑: *MAITAR IDO*👁️ 👁️👁️👁️👁️👁️ HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* 7-8 Wani irin daɗi yake ratsa ni ganin Leemat na kuka ta dalilina, wannan kuma bai rasa nasaba da MAITAR IDOna don duk wani mugu ya na jin daɗin mugunta musamman ga waɗanda suka taƙile shi. Leemat za ta kwashe gashinta don tafiya da shi amma anty Sailuba ta yi saurin hanata “ haba ke kuwa in kika tafi da shi a zai dinga tuna miki baƙin ciki,bari na baki mai ki dinga shafa wa gashin in sha Allah zai dawo normal” cike da siyasa anty Sailuba ta yi mata wayo ta karɓe gashin ta haɗa ta da mai ita kuma doluwar ta karɓa ba tare da ta san sayar da shi za a yi ba. Ko kuɗin gyaran gashin ba ta karɓa ba suka yi tafiyar su,ita kuwa anty Sailuba tamkar ma ta yi murna da hakan .Ƙaton gwangwanin da take ajiyar gashi ta buɗe ta zuba kafin ta juyo ta kalle ni ta tuntsire da dariya ta ce “ ikon Allah! Ki na ga fa jiya Leemat ta yi ta miki sharri yau ita ma gashinta ya koma irin naki ” Na saki murmushin ni ma kafin na ce “anty yunwa nake ji” “To acici ga abincin ki can tun ɗazu na ajiye miki shi” ta nuna mini da yatsanta na je na ɗauko. Zazafen tuwon shinkafa ne da miyar kuɓewa sai ƙamshi yake da alamu kuma girkin gida ne,ido kawai na ƙura ina kallon abincin wanda zuciyata ta shaida mini ‘an saka maganin mallaka’ da mamaki na ɗago na dubi anty Sailuba na ce “wai anty tuwon nan tun na yaushe ne?” Cike da masifa ta ce “babu ruwana da iskanci kamar ya na yaushe ne? Na sunan haihuwata.” “Daga tambaya?” “Ni na girka shi da kaina,kin samu ma na zuba miki sauran abincin mijina duk da uban kishin da nake da ” Anty Sailuba ta na da aure sai dai kusan shekara biyar ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba,ta na da mugun kishi sannan ta na son mijinta sosai kamar ta mutu.Duk in ta ji labarin yayi sabuwar budurwa haka za ta samo lambarta ko kuma ta je har gidansu yarinyar ta ci mata mutumci. A zuci na ce ‘shikenan Bilal ka shiga uku , Allah kaɗai ya san bayan maganin mallaka wane iri ake baka kuma’ a zahiri kuma cewa na yi “a'a gaskiya ba zan ci tuwon nan ba,yo ai in na yi hakan kamar na nuna raini ne a gare shi ” na kuwa rufe abincin. Anty Sailuba ta ƙure ni da ido kafin ta ce “ki ɗauka ki ci babu ruwana da shashanci” “Allah anty na ƙoshi ba zan ci wannan ba” na bata amsa don kuwa na san abu da magani ba zan cuci kaina ba. “Ke kika sani yi ta zama da yunwar don kan ki” ta faɗa tare da ficewa.Ina zaune ina tunanin ina zan samu abinci sai ga ƙawayena,da murna muka rungume juna kafin na ce “ ku shikenan tun ranar nan ba ku neme ni ba” Laila ta ce “ ke ɗin ce kin bamu tsoro sosai nitsewa kika yi cikin ruwa fa,hankali tashe muka je nemo masu ceto har sarkin ruwa fa sai da ya shiga neman wai a bai gan ki ba ” sai ta yi shiru hakan yasa Farida ci gaba da cewa “ amma Kaka na zuwa ta yi wasu bubuwa sai ganin ki muka yi gaɓar ruwa kamar wacce aka jefo,to shine fa duk muka ji tsoro saboda mutane na ta cece-kuce akan lamarin” “Don mi?” na yi tambayar,sai da suka kalli juna sannan Laila ta ce “ wai Kaka bokanya ce” na waro ido Farisa ta harare ni ta ce “ kamar ki ce ba ki yarda ba don dama tun tuni ana zarginta da hakan” Na haɗe rai na ce “ kun ga ban son wannan...” Laila ta katse ni “ to in ba boka ba wake bada magani? Kar ki manta in ciwo ya ta'azzara har gidanku ake zuwa karɓar magani” “Ni dai duk a bar wannan zancen yunwa nake ji” na faɗa don haka kawai na ji ban so a ci gaba. “ Ina da kuɗi mu je tashar kwaɗayi ” Farida ta faɗa ta na buɗe tafin hannunta kuɗi ne kuwa masu ɗan yawa,na ce “ ku je ku biyu ku sayo ni zan zauna nan kar anty Sailuba ta yi faɗa ” ba su musa ba suka fita ai kuwa ina nan zaune sai ga wata mata ta kawo ƴarta ƴar shekara goma a wanke mata gashi. Zaunar da ita na yi na soma wanke mata da sauri don haka kawai ban so ace ita ma ƴar mitsitsiyar nan an sayar da gashinta ga hajiyar birni.Sai dai duk saurin da nake a banza,ina daf da idawa anty Sailuba ta dawo idonta duk sun yi ja sosai.Sama-sama suka gaisa da Uwar yarinyar kafin ta samu wuri ta zauna ta na kallon yadda nake yin komai.Bayan na gama mata ta biya kuɗi suka tafi,gashin yarinyar nake son ceta sai dai na rasa ta ya zan yi haka. Anty Sailuba ta ɗauki masharcin da na shace mata kai ta shiga cire gashin da ya laƙe,ina ji ina gani ta jefa shi cikin gwangwani. Su Farida suka dawo,taliya ce suka sayo mini sai hanjin ligidi na karɓe na shiga ci yayin da anty kuma ta aike su . Haka muka yi ta samun customer har lokacin tafiya ta yayi gidan anty Hinda,ina zuwa sai na ga ta haɗe rai amma ban damu ba na shiga taya ta sayar da abincin yau ma dandanan muka sayar sai dai ko loma ɗaya ba ta bani ba. Na yi rau-rau da ido na ce “ anty ina nawa” “ Ni ai ba zan sake baki abinci ba,yau tun safe Kakar ki ita ta tashe ni daga bacci ta yi ta min masifa ta na zagina wai kar na sake baki abinci to wannan ma yasa na yanke shawarar sallamar ki” ta faɗa tare da ɗauko kuɗi ta miƙa mini. Na ƙi karɓa ina bata haƙuri amma ta ƙi haƙura har gidanta na bita,muna shiga ƴarta budurwa mai sunan Sharifa ta taso cike da wulaƙanci ta na cewa “ uwar mi kika zo yi gidanmu? Dama shi talaka bai iya samun wuri ba,ɗazu don rashin mutumci kika turo mana wannan tsohuwar Kakar taki ta zo ta yi wa mutane hauka.Duk alherin da muke yi muku ba ku gani ba har da wani cewa an zuba miki guba a abinci” Anty Hinda ta ce “ kin ga Sharifa zo ki ƙirga kuɗin nan mu ga ribar da muka samu” ta na hararena ta karɓi kuɗin da ke cikin wata roba ta koma gefe ta na ƙirgawa ta na masifa “ daga yau ni zan dinga taya uwata sayar da abinci sai ki tafi ba mu buƙata” da ta ga na ƙi gusawa ta juye kuɗin ƙasa tare da cika robar da ƙasari ta watsa min a fuska har sai na ji tsoro.Duk wannan bai ishe ta ba sai da ta wani ja ni ƙiiii ta cillo ni waje ,zuciyata ce ta soma tafasa yayin da duk illahin jikina nake jin ya ɗau zafi kamar garwashin wuta.Ni kaina ban san lokacin da na ɗauki hanyar Gulbi ba,kawai haka na ji a can ne kawai zan samu salama.Tun daga nesa da na fara hango ruwan sai nake jin kunnuwana na amsa kira, ina isa daidai gaɓarsu na yi tsaye ina kallon yadda suka soma yin zillo tuni munduwar wuyana ta fara motsi ta na ɗaukar wani haske.Ido biyu ba cikin bacci ba na soma jin tafin ƙafata na yi mini ƙaiƙayi,ko kafin ƙyaftawar ido na rikiɗe na zama Siren (sirène ) ina daga kwance gaɓar ruwa nake ƙarewa bindin nawa na kifi kallo sai motsi yake ya na fitar da haske.Kamar wata kifanya na yi tsalle na faɗa ruwan,ƙasa sosai nake nitsawa ina jin wani sanyi da daɗi na ratsa ni. Idona buɗe suke taram haka kuma sheɗa ta daidai take babu alamun gargada irin in mutum ya shiga ruwa.Ina tsaka da yawo cikin ruwan na soma jin dariya,na juya na soma bin inda sautin ke fitowa har na iso kusan wani dutse.Wata budurwa da saurayi na gani su na wasa haɗi da hirar masoya,su ma iri na ne rabi mutum rabi kifi.Budurwar na gani na ta nufo ni ta na cewa “ waooo! Princess” ƙyafƙyaf kawai na yi da ido ina kallonta har ta iso gare ni ta na shafa goshina wanda sai a yanzu na farga akwai wani tambari a jikinsa na haske. “ Ya aka yi kika zo wannan ƙasar? Ko wani aiki kika zo yi?” abun mamaki kasa magana na yi duk da kuwa na so buɗe baki,saurayin ne ya zo da sauri ya ja ta gefe ya na cewa “ Sarlah ya kike tsayuwa kusa da ita ko ba ki tambarin Masarautar Goma ne da ita ba?” haka suka tafi suka bar ni cike da mamaki. Sama-sama na soma yi har na fito gaɓar ruwan ,so nake na koma gida.Sai bayan na fito ne bindin ya ɓace na dawo da ƙafafun mutane,na saki murmushi ina jin wani daɗi yayin da kuma zuciyata ta yarda ta lamunce mini tabbas ina da wata baiwa ba daidai nake da sauran mutane ba. Ina zuwa gida na ga takalmin mutane a ƙofar ɗakinmu,ban nemi izini ba na shiga. Sai na tarar da wata mata a zaune yayin da Kaka kuma ke ta wasa da ɗiyan wuri ta na zayyano mata abubuwan da za su faru gobenta.Wato dibo Kaka take,macen ta yi godiya ta biya kuɗi irin sosai ɗin nan kafin ta fice.Na dubi Kaka wacce ke ta faman ƙirga kuɗi kamar ba ta gan ni ba,na yi gyaran murya na ce “Kaka...” ta yi saurin katse ni da “kin ga Sarah wuce ki bani wuri ban ƙaunar ganin ki,rainon ki bai yi mini rana ba sam.Ban ga amfanin zama da ke ba don haka ki kwashi inaki-inaki ki bar min gidana” Wata irin dariya na soma wacce sama ban lura da ruwan da suka fara ɓulɓulowa daga ƙasa ba har sai da suka kawo daidai wuyana.Tsit na yi ina kallon Kaka wacce ke ta ƙoƙarin fita daga ɗakin amma ta kasa,“za ki mayar da ruwan nan ƙarƙashin ƙasa ko sai sun kashe ni ” ta faɗa a tsorace ta na riƙe bango hakan kuma sai ya ƙara bani wata dariyar amma na gimtse munduwar wuyana na lalubo na riƙe ina yi wa ruwa magana da idona,a sannu a hankali suka yi ƙasa har suka ƙwafe. Da wani irin saurin Kaka ta cillo ni waje ta na mai cewa “ashe duk yadda nake tunani kin wuce nan,ke annoba ce ba zan iya zama da ke ba” Zuwa wannan lokacin na fahimci Kaka ba da wasa take ba,hakan yasa hankalina ya tashi na soma roƙonta “Kaka in kin kore ni ina zan je? Ke ce komai nawa ke kika raine ni ban san kowa ba sai ke” “Ban haɗa komai ba da ke wallahi tsintar ki na yi da tunanin za ki yi mini amfani a gaba ki gaje ni ashe musamman da na ga ki na ɗauke da *MAITAR IDO* ashe ban san bala'in naki ya wuce nan ba sai yau na ida ganewa Mamy Water ce ke ” Idona na zubar da ƙwalla nake kallon Kaka,tuni kuma ƙwaƙwalwata ta soma hargitse wa.Ana kiran sallar magrib haka Kaka ta jefo ni waje ni da jakar kayana ta kama gidanta ta rufe,kan dakali na zauna ina ta wasiƙar jaki har aka yi sallar isha'i.Ganin dare na ta ƙara yi na miƙe tsaye na soma tafiya,direct gidan anty Sailuba na nufa don ita ɗaya ce yanzu ta rage min wacce nake tunanin za ta zame mini bango.Da sallama na shiga gidan,tun kafin na ƙarasa nake jiyo sautin muryar mijinta Bilal ya na cewa “wallahi Sailuba ko mi za ki yi sai na ƙara aure,kuma goben nan zan je na yi wa Hajiya bayani ta samo min mata cikin danginta tun da ni ko na nema ba za ki bari ba” kai na kutsa na shiga ɗakin,anty Sailuba ta juyo ta na kallona a zuciye “uban mi kika zo yi kuma yanzu cikin dare?” ban bata amsa ba sai mijinta da na ƙure cikin ido ina mai taɓa munduwa ta ni kaina ban san dalilin yin haka ba. “My Lub Baby wane ni na yi miki kishiya don Allah ki kwantar da hankalin ki ina mugun son ki” Bilal ya faɗa ,ni kuma na saki murmushi ashe duk anty Sailuba ta ga komai.Hannuna ta ja muka fito waje kafin ta ce “ke mine ne kika yi wa mijina? Ko ke ma bokancin kike yi kamar Kaka” na girgiza kai na ce mata “a'a ina da MAITAR IDO ne mai sarrafa abin da duk nake so,kin ga gashin Leemat ma ni ce nan na mayar da shi yanzu kuma na juye tunanin mijin ki babu ke babu kishiya” anty Sailuba ta rungume ni ba tare da tunanin wannan ɗin fa abun gudu ne,ta ce “ina na za ki je?” bayani na yi mata kan cewa Kaka ta kore ni daga gidanta sai a lokacin kuma na ji hawaye ,ta goge mini su ta na cewa “sai ki zauna gidana” sai ta ja hannuna muka koma ciki..... Ga waɗanda suke son fara payment ƙofa a buɗe take 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 [29/07 à 09:28] MRS SADAUKI 👑: *MAITAR IDO* HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* 9-10 Ko da muka koma ciki mijinta bai falo alamun ya na can ƙurya ,anty Sailuba ta kai ni wani ɗaki ɗan madaidaici babu komai cikinsa sai dangin abinci.Ta je ta ɗauko tabarma da kuma wani ƙaton bargo ta shimfiɗa min,“ ki kwanta a nan zuwa gobe da safe in Allah ya kai mu za mu sake yin magana” kai na jinjina mata ta fice ta bar ni nan. Na haye shimfiɗar na kwanta ina tunanin furicin Kaka wai ba ta haɗa komai da ni ba tsintata ta yi.Na juya kwanci wani sashen zuciyata kuma na hasko min wulaƙanci da Sharifa ta yi min ƴar anty Hinda.Na lumshe ido ina mai kai hannu na riƙe munduwar wuyana,‘ ko ya ake yi mutum ya je wannan duniyar da Kaka ta kai ni ? ’ na tambayi kaina a zuci abun mamaki kuwa zuciyata ce ta soma yin nauyi kamar an ɗora dutse kafin in samo amsar tambayata .Cike da jin daɗi na yi bacci wannan daren,tun da asubah anty Sailuba ta shigo ɗakina “ tashi ki yi sallah” shine abin da ta faɗa ,duk da ban taɓa yin ta ba hakan bai hana ni miƙewa ba na fito.Ƙofar falo na ga a buɗe hakan yasa na fita,banɗaki na shiga har zan hau masai sai na tuna mafarkin da na yi a jiya an nuna mini yadda zan ɗauki fansa ta wajen su anty Hinda .Na fita na samo baƙar leda sannan na koma banɗaki,a cikinta na kasaye duk abin da ke cikina sannan na miƙe ina dariya ni ɗaya.Da ido na yi wa ledar umarni ta ƙulle kanta kafin kuma na aikata can gidan anty Hinda. Na fito na wanke jikina na koma ɗakina,gari na wayewa anty Sailuba ta sake shigowa tare da samun wuri ta zauna. Ta ɗan ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ da farko dai ina yi miki godiya game da abin da kika yi min jiya,na biyu kuma abin da zan ce miki babu kyau cutar da mutane ki bari” “ Shikenan ya bar zancen auren?” ita ce tambayar da na yi mata. Ta ce “ eh ya bari sai kuma ya ɓullo da wata matsalar wai za mu tashi daga nan mu koma can gidan da ɗan uwansa ya gina kin san nan haya muke” Na ce “ to ai hakan ba matsala ba ce kin ga kuɗin da yake biya na haya sai ku yi wani abu da su” Ta girgiza kai ta ce “ uwar mijina ƴar masifa ce ta bugawa a jarida,kuma kin ga ita ma a can take.Yanzu dai mu bar maganar nan zo ki yi mini wanki ki share gida da kuma wanke-wanke kin san halin Bilal shi ma wani sa'in bai da mutumci shi yasa kawai na ce masa ƴar aiki na ɗauke ki” Tashi na yi tsaye na ce “ babu matsala anty in dai zan zauna a nan ko ƴar aikin sai na zama” tulin kayanta da na mijinta na wanke ,na yi shara na yi wanke-wanke a ƙarshe na je na yi wanka sannan ta zuba mini waina da miya sosai na ci na ƙoshi.“ Ki shirya za mu je kasuwa abokan Bilal yau a nan za su ci abincin dare” Na ce “ kenan yau ba za mu buɗe shago ba?” “ Eh gaskiya tun da kaji za mu sayo sai kuma mun yi gyaran su” Da muka fito za mu tafiya kasuwa ta ƙofar gidan anty Hinda muka wuce,tun daga nesa na hango ledar kashin da na yi tanadi ta na nan tsaye kamar haure jira kawai take lokacin da na ƙa'ide ta faɗi ƙasa.Na yi murmushin mugunta har na matsu ƙarfe sha biyu ta yi,da muka shiga kasuwa kuwa na yi ta gamuwa da abubuwan mamaki waɗanda normal mutane ba su iya gani.Yawancin ƴan kasuwa duk su na da layar da za ta jawo musu customer su sayi kayansu ba tare da sanin ita fa wannan layar ta na ɗauke ne da aljanu su ne kesa mutane sayen kaya ko ba su shirya ba,wani abun ma bai da amfani sai ka je gida ka yi ta tunanin mi yasa ma ka saye shi da ka bar kuɗin ka. Kaji muka saye manya guda uku anty Sailuba ta miƙa min su na riƙe,daga nan muka wuce wurin ƴan yaji.Mun yi tsaye ta na cinikin nawa tiyar yaji,yayin da ni kuma idona ya sauka kan yaji wanda ake kira tsidagu irin ƴan mitsimitsi ɗin nan. “ In ɗauki guda?” na tambayi mai sayar da yajin yayi murmushi ya ce “ ɗauka mana” Cike da masifa anty Sailuba ta ce “ mi za ki yi da tsidagu kuma?” na ce “ kawai ya burge ni ne sai na ɗauki ƙwaya gudan.Haka dai muka yi ta zaga kasuwa har muka zo wajen ƴan sayar da nama,yadda na ga mata sun yi dandazo wajen wani alhalin duk ga ma su nama nan yasa na ji ina son ganin shi ɗin kuma wace irin laya yake amfani da ita.Kamar dole haka na duƙa ina kutsawa har na shigo gaba,sai dai kafin na miƙe tsaye sai idona ya sauka kan wasu ƙafafuwan jaki a tsaye daram,a hankali na miƙe sai na ga ashe mai sayar da naman ne .Ido huɗu muka haɗa da shi da farko ya ji tsoro kafin ya soma yi min magana da ido ba wai a bakinsa ba ballantana ace mutane za su ji. “ Mi kuma ya kawo macen Siren cikin mutane? Ko da yake ba abun mamaki ba in ka shigo kasuwa babu kalar jinsin da babu” Ni ma ta idon na mayar masa “ wane ne kai? Ya aka yi ƙafafunka suke na jaki?” “ Ki tambayi Anaba ita ai ta san ni ” Anaba sunan Kaka ne,jin furicinsa yasa na kai dubana ga naman da yake sayarwa duk babu ɗaya na ƙwarai mushe ne yake sayarwa in rago ya mutu ko saniya haka zai je ya ɗauko su inda aka jefar ya gyara shi ya zo ya na sayarwa ko da kuwa ya fara lalacewa shi zai san yadda yayi ya maida shi mai kyau a idon mutane irin shine kuma sai ka ga ka ci ka faɗi rashin lafiya. Ban ankara ba ashe har mutanen da ke zagaye da shi duk ya sallame su sai da na ji muryar anty Sailuba na cewa “ Sarah ke? Tun ɗazu fa nake yawon neman ki” sai kuma ta harari mai sayar da naman kafin ta ja hannuna mu wuce.Sai da muka yi nisa na tambaye ta “ amma anty mi yasa ba ki sayi namansa ba ? Na ga ya fi kowa arha” Ta ja baki ta ce “ arhar ce ke kai mutane ga hallaka,ni ma na taɓa saya lokacin da abokan Bilal za su zo amma abun mamaki suka ƙi ci wai naman nan da na saka ya lalace ko ban jin warinsa.A ƙarshe dai barina suka yi da shi sai ni da Bilal muka ci daren ranar kuwa muka dinga ƴar rige-rigen shiga banɗaki” na ƙyalƙyace da dariya kafin kuma na ce “ to anty mi yasa kuka ci alhalin an faɗa muku ya lalace?” Shiru ta yi ba ta bani amsa ba, wannan kuma yasa na lalubo amsar da kaina ‘ saboda ita da mijinta normal mutum ne!’ sai kuma zuciyata ta bada darammm ‘ to in haka ne su abokan Bilal waye ya sanar da su? Sai in kuwa su ma matsafan ne!’ duk a zuci na yi maganar har muka kai gida babu wanda ya ce komai. Mijin anty Sailuba ya karɓi kajin ya fita waje wani ya kama masa ya yanke,ni kuwa ƙatuwar tukunya na ɗora ta ruwan zafi .Sai da suka tafasa sannan na soma fige su yayin da anty Sailuba kuma ta ɗora girkin rana ,muna aiki muna hira har muka gama. Sai bayan mun ci abinci ne na kama mata ta tsaga cikin ta fiddo hanji ,su ma duk muka gyara su sannan ta wanke ta ɗora kan tukunya.Tafarnuwa ta miƙo min ita ma na gyara ,aikin da nake ganin mai sauƙi ne sannu-sannu sai ga shi ya ɗauki lokaci don bayan ta dafa kajin sai da ta soya su sannan ta ɗora miya bayan ta gama kuma ta tsumbula su ciki. #GIDAN ANTY HINDA Cike da iya yi Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka,ragowar ruwan kuma waɗanda duk sun yi farin sabulu ta kawo wa anty Hinda su ta juye cikin miya sai murna suke. Sharifa ta ce “Mama in muka ɗora da yin haka ai hajjin bana da mu za a yi” Ita ma Hindar ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “ai kuwa dai musamman yanzu da na rabu da jikar bokanya ” “Dama haushi take bani,yadda kullum cikin datti ko wanka ba ta yi” Hinda ta ce “miƙo min ƙatuwar muciya na motso miyar nan ” muciyar ta miƙo bayan ta motsa miyar ta sa murfi ta rufe kenan ai kuwa sai ganin leda suka kuwa daga sama ta faɗo kan tukunyar miyar kwacaaaa. Duk suka yi baya a tsorace su na zaro ido ganin kashi duk ya ɓata murfin tukunyar . Cike da ƙyanƙyami Hinda ta ɗauke murfin ta je ta wanke shi,Sharifa kuwa cewa ta yi “Allah ma dai yayi sa'a ba a ciki ya faɗa ba” “Ɗauko muzubi ku juye min miyata Allah kaɗai ya san abin da za a jefo min kuma nan gaba” cewar Hinda , Sharifa ta ɗauko ta dinga kwashe miyar dama ta dafu. Ita ma Hinda wankan ta yi kafin su ɗora abincin kan baro,almajiri ya tura masu shi inda suke sayarwa .Sharifa an ci wuyar kwalliya,mutane ne suka fara zuwa su na saye kamar kullum sai da Hinda ta buɗe baki ta na zage-zage “ ƴan hassada ƴan baƙin ciki,to sai ku je ku sake biyan wasu kuɗin wannan aikin bai yi ba.Ni za a yi wa turen aljanu daga ganin kasuwata ta bunƙasa” Customer ɗinta kuwa har da masu shigar mata,kafin kuma wurin yayi tsit babu wanda ya ƙara saya ga abinci jibge har bayan sallar Asar sai ƴar kallon-kallon suke ita da Sharifa. “ Na fa ji tsoro kar aje dai ɗin sun ƙara tafiya sun kai wasu kuɗin wurin Malam,dubi shiru babu masu saya” Sharifa ta turo baki ta ce “ ai ke ce da masifar tsiya tun da kin ga abun bai yi aiki ba ai sai ki yi shiru da bakin ki” “ Ƙirga kuɗin mu ga nawa aka samu” cewar Hinda . Sharifa ta ɗauki robar kuɗi,yaji ta gani tsidagu babu wani tunani ta ɗauke shi ta jefar kuɗin ta ƙirga ta na turo baki gaba saboda ko icce ba za su saya ba.Ta miƙa wa Hinda “ tsidagun mine ne kuma za ki aje min cikin kuɗi?” Hinda ta tambaya ta na mai ɗauka ita ma ta jefar a ƙasa. Sharifa ta ce “ na fa jefar da shi” “Ƙafafuwa gare shi ballantana ya sake tsalle ya shiga?” “Allah Mama na cire” “Kin ga tashi mu je gida kin ga duk wasu masu sayar da abinci sun sayar sai mu” “To wannan ɗin ya za mu yi da shi?” “Ko almajirai sai na rabawa ” Abincin suka mayar a baro suna gaba almajiri na bin su a baya har suka isa gida, Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka tun a cikin banɗaki ta ƙurma uban ihu ta na kiran Hinda . “ Ke lafiyar ki? Ko ƙadangaren ne yau ma ya sake faɗo miki?” Hinda ta tambaya, Sharifa ba ta amsa ba sai fitowa ta yi da ɗaurin ƙirji ta na soshe-soshe. “ Mama sosa mini ƙaiƙayi duk jikina ƙaiƙayi yake na shiga uku na lalace” haka take faman faɗa ,da farko Hinda ta ɗauka wasa ce sai da ta ga Sharifa na kuka har da majina sannan ta soma tayata, Sharifa ba ta samu sauƙin abun ba sai da jikinta ya bushe babu damshin ruwa.Tsabar wahala har sai ta rame,ta koma gefe ta na jan numfashi. Hinda kuwa alwala ta yi don yin sallah nan ita ma ƙaiƙayi yayi mata wuf duk inda ke da damshin ruwa.Soshe-soshen ta yi ita ma har sai alwalar ta bushe,suka kalli juna ita da Sharifa “ ina jin tsoro Sharifa kar ace tsidagun da muka ɗauka ne” “Shi ne mana Mama,kuma abin da na fahimta sai da ruwa suka taɓa mu ne muka ji ƙaiƙayin” Sharifa ta faɗa ,Hinda kuwa don gaskata maganar sai ta watsa ruwa a ƙafarta ai kuwa ƙaiƙayin ya sake dawowa sabo wannan karon Sharifa har sai da ta dara. # GIDAN BILAL Bayan sallar magrib anty Sailuba ta gama komai,an gyara ɗaki sai ƙamshi yake yayin da kuma aka jera kwanonin abinci kan table ɗinta mai kujeru huɗu.Sai da ta yi kwalliya sosai ta saka kaya masu kyau,abincina ta zuba mini kafin ta ce “ ki zauna ɗakin ki kar ki fito har sai baƙin nan sun tafi ” Na gyaɗa kai na ce “ to anty ” fita ta yi ni kuma na zauna na soma cin abincina,sai murmushi nake yadda na ji idona na wannan zuuuu ɗin na tabbata su anty Hinda ana can cikin uƙuba.Sosai nake jin daɗin mugunta a fili na ce “ ku da yin wanka kuma sai ta Allah,kuma sai kun dawo irina kun zama ƙazamai kun yi baƙi ƙirin” sai kuma na yi shiru jin muryoyi na tashi alamun baƙin ne suka zo. Ina jin su na zolayar anty Sailuba “ irin wannan kwalliyar matarmu ai sai ki sa mu kasa fita” “Ina ji fa saboda matarmu ba ta son tsufa shi yasa ta ƙi barin ta haihu” “ Ai kuwa dai in haka ne za mu kawo wata matar” “ Allah ina son haihuwa sosai zuwa dai ne ba ta yi ba” sai yanzu kawai anty Sailuba ta yi magana. “ Ba ki dai je neman ta ba” ɗaya daga cikinsu ya faɗa. Bilal mijin anty Sailuba ya ce “ yanzu dai mu fara cin abinci tukuna” Tsit falon ya ɗauka na wani lokaci kafin kuma wani irin gurnani ya ɗauki hankalina har na ji ina son leƙawa na ga su waye waɗannan baƙi.Labule na ɗan buɗe a hankali,su uku ne gami da mijin anty Sailuba su huɗu.Zaune suke su na cin abinci babu mai yin magana,amma ni kuma tambayata ita ce ‘to wannan sautin daga ina yake fitowa?’ ina shirin sauke labule daidai kuma lokacin ɗaya daga cikinsu ya ɗan tada kai tsabar tsoro har sai da na dafe zuciyata.Ido uku ne da shi,biyu irin na mutane ɗayan kuma can tsakiyar goshi ban ida shiga firgici ba sai da na ga wani abu na fitowa ta idon ya na cin abinci nan na fahimci shine ke fitar da gurnanin. Da sauri na saki labulen ina mai tambayar kaina ,“ina kuma Bilal ya kwaso matsafan nan?” shiru na yi sai yanzu na gane wato shi yasa anty tace suka ƙi cin abincin sai ita da mijinta suka ci saboda su idonsu uku ne biyu na nan duniyar ɗayan kuma na ɓoyayyar duniya. Tunani na soma yi mine ne dalinlinsu na abota da Bilal tabbas akwai wata a ƙasa,tunanin nawa ne ya tsaya cak jin ɗaya daga ciki ya na tambayar anty Sailuba “ni kam ku nawa ne cikin gidan nan? Ko kun samu ɗan hutu ne ?” Ba ta kai ga basa amsa ba shi ma wani ya ce “ƙamshin Gombowa ” “Tun shigowar mu na ji ƙazinin ɗan ƙabilar Gombo” A karo na biyu kenan da na ji kalmar sunan Gombo ɗin nan,a hankali na ƙara buɗe labule ina leƙo cikin rashin sa'a hasken idona ya sauka a rigar ɗaya daga cikinsu,raɗam ya fito kamar fitilar nan da aka yi yayi mai hasko hoton Obama.Ɗayan ne mai face da wanda hasken idonsa ya sauka kan rigarsa ya juyo baya,muka haɗa ido da shi ......... Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN ,ƴan Nijar kuma carte moov ko airtel ta 500f. NB:Daga lokacin da book ɗin nan ya zama complete 800 ne. 29 jully 2024 MRS SADAUKI ce 🌚 [29/07 à 09:31] MRS SADAUKI 👑: *IBRAHEEM* ```soldier man``` © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* #Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓 *Ƙirƙiraren labari ne,bai faru ba a gaske .Ban yarda a juya shi ko a mayar da shi audio doli sai da izinina* 1-2 A nutse nake sauraren mahaifiyata ido a lumshe,tun da ta fara nasihar nake daɗa jin nutsuwa na sake samun gurbi a zuciyata har sai da ta zo da furucinta na ƙarshe wanda yayi tsananin razana ni har ban san lokacin da na furta “mi kika ce Ammy?” na yi tambayar da tunanin ko kunnena ne bai jiye min daidai ba. “A yau an ɗaura aurenka da Maryama ina so ka riƙe amana zuwa gobe in sha Allah zan kawo ta da kaina” ta sake maimaita wa,shiru na yi ina jin wani yanayi marar misaltawa. “Ibraheemu haƙuri za ka yi, wannan ne kawai gatan da za mu yi wa Maryama don nuna soyayyarmu gare ta da kuma jadadda girman alƙawarin da na ɗaukar wa mahaifiyarta kafin ta bar duniya” yanzu ma dai shiru na yi ba don ban ji ba sai don abubuwa da dama da suka dinga gwaro a kwanyata. “Heemu ka na ji na kuwa?” “Na'am Ammy ina ji” na faɗa ina jan ajiyar zuciya,ita ma ajiyar zuciyar ta sauke kafin ta ce “ ina Daddyn ka?” “Ya fita tun jiya bai dawo ba” “Okay sai an jima ” “Ammyyy!” na faɗa da sauri,sai ta tsaya da ƙoƙarin kashewar ta ce “ ya aka yi yarona ina jin ka?” Kamar mai koyon magana na ce “ki bar ta nan wurin ki har zuwa wani lokaci ” “Saboda me?” “Kawai Ammy ” “Sai mun zo” ta faɗa tare da kashe kiran na furzar da huci ina jin duniyar na juya min.Screen ɗin wayar na ƙurawa ido ina kallon hotonmu wanda shine hoton ƙarshe da muka ɗauka tare da ɗan uwa kuma abokina. «Zo mu ɗauki hoto ina jin a jikina kamar ba zan fito daga wannan yaƙin ba»cewar Abakar ya na dariya,wacce ba ta kai ga gushe wa ba na yi amfani da wayata na ɗauke mu selfie.Hoton na shafa yayin da kuma muryarsa ke yi min amo a dodon kunne,da sauri na miƙe na nufi ɗakin motsa jiki na soma training.Na shafe kusan awa biyu kafin na fito na wuce bedroom wanka na yi na shirya cikin t-shirt ta soja da wandon kaki.Key ɗin mota na ɗauka kafin na sauko ƙasa inda ƴan aiki ke ta shawagi,su na gani na suka soma gaishe ni kamar kullum da kai kawai na amsa masu na fita zuwa harabar gidan. Inda motata ke parker na nufa direct, ɗaya daga cikin escort ɗin ne ya rugo ya na tambaya ta inda zan je.“ Ni kaɗai zan tafi babu buƙatar rakiya ko ba ga cikin kayan da nake ba?” “Sorry mai gida yalɓai ne ya bada umarnin duk inda za ka je mu yi ma rakiya” ya faɗa cike da girmamawa. “Yi tafiyar ka” na faɗa tare da shige wa ciki na yi wa motar key,wurin fita ma sai da sojawan da ke tsaron ƙofa suka ɓata min lokaci kafin su bar ni na fita. A hankali nake gudu ina duba yanayin garin da yadda al'amurra ke tafiya,a haka har na isa barikin soja.Daidai ɗakinmu na yi parking,na jima sosai kafin na fito ,key nasa na buɗe ƙofar na shiga a nan take duk wani tsohon tarihi ya dinga dawo min.Dakyar nake cira ƙafa ina takawa izuwa ciki,daidai akwatinsa na je na tsaya tare da buɗa shi na ciro kakinsa mai ɗauke da sunansa Abakar.Na rungume rigar ina jin ƙamshin jikinsa na ratsa hancina,karon farko da na ji idona sun cika da hawaye tun bayan dawowar mu daga yaƙin da ya zame mana shamaki ni da abokina. Sosai nake hawaye ina jin dutsen da ya jima da yin gini a zuciyata na motsawa haɗi da zubar da tururi . “Ibraheem!” ya kira sunana a dake,duk da na san ko wane ne bai sa na juyo ba har lokacin da nake jin takunsa na matso ni. “ Mi yasa ka fito alhalin na ce ka zauna gida? Shi ne kuma ka hana escort su take ma baya,mi yasa ba ka jin magana ta? In fa wani abu ya same ka?” Sai a lokacin na juyo muna facing juna,ban ce masa komai ba sai idona masu cike da baƙin ciki da zafin ɗaukar fansa na ƙura masa. “ Wannan zuciyar da kake ji da ita kar ka manta ni ka gado amma shine don tsageranci za ka ƙure ni da ido ka na kallo kamar sa'an ka.Abakar ya mutu ba shine sojan farko da ya taɓa rasa rayuwa ba a wurin yaƙi amma duk ka bi ka adabi mutane da hauka,shi Abakar ɗin wa ya fi ne da ba za a kashe shi b...” “Daddy???” na faɗa a zuciye kafin kuma na juya na mayar da rigar C cikin akwati na rufe na sungumi akwatin na fito,don yanzu shi ne kawai abin da ya rage min nasa. Bayan mota na saka shi,sam ban damu da tarin sojawan da suke tsaye ba waɗanda na san tare suke da mahaifina.Ko ɗakin ban koma na rufe ba na yi wa motar key,ina tafe ina tunanin ƙiyayyar da Daddy ya ɗorawa Abakar dare ɗaya wacce a can farko ba haka suke ba. Na ja wani huci ina mai danganta abin da don ya fito gari guda ne da mahaifiyata,a haka na isa gida can sama na haura da akwatin na ajiye shi bisa bed ɗina. Gaban mirror na je na yi tsaye na ƙurawa fuskata ido wacce ta ƙara yin ja don ɓacin rai,baƙar sumar kaina mai tarin yawa na hargitsa ina kai wa ƙaton ƙirjina duka ina mai yin wata hargowa kamar kumurcin zaki har manyan damatsana su na masu motsawa. Wayata ce ta ɗau ruri sai da ta yi na uku kafin na ciro ta na ɗauka haɗi da karawa a kunne. “Ka sauko ƙasa ina son yin magana da kai” shi ne abin da ya faɗa kafin ya kashe, toilet na shiga na wanke fuska ta kafin na sauka ɗin.A zaune na tarar da shi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya,shi ma sanye yake cikin na soja mai ɗauke da adon galolin yabo birjit.Kujera mai facing tasa na zauna ina mai sunne kai saboda sai yanzu ne na ji ban kyauta ba game da abin da na yi masa. “Ibraheem ka ɗago ka kalle ni” yayi furta cike da kulawa,ƙin ɗagowar na yi saboda kallon tsakiyar idon Daddy sai mutum ya shirya,na sha jin sojawa na faɗar su na shakkar kallon nasa wanda ni ma shaida ne ba a ko wane irin yanayi ba ne nake iya kallonsa. “Mine ne damuwar ka? Abakar?” Sai a lokacin na ɗago na dube shi,murya cike da rauni na ce “ Daddy shi ɗin abokina ne tun na ƙurciya ina mugun sonsa,tamkar yadda Wa ke son ƙanensa...” shiru na yi ina jan ajiyar zuciya. Daddy ya ce “ saboda mutuwarsa ce nake ganin rauni a idon ka? Ka gaji ne da aikin sojan na tsige ka?” Wani irin halbawa zuciyata ta yi,da sauri na ce “ haba Daddy ya za ka ce haka? In na bar aikin soja mi zan yi ?” Ya miƙe tsaye ya na cewa “to in ka na son ci gaba da zama a ciki,ka fidda Abakar a ranka ko sunansa kar na sake jin ka ambata” har ya kai bakin ƙofa kuma sai ya juyo muna kallon juna kafin ya ci gaba da cewa “zuwa an jima sabuwar mahaifiyar ka za ta tare ban son jin wata matsala ta fito daga gare ka” ya na gama faɗa ya fice. Tsakanin baƙin cikin sharaɗin da ya gindiya mini da kuma kishin Ammyna da nake yi jin zai kawo wata mace matsayin mata sai na rasa da wanne zan ji.Ɗaki na koma na kunna karatun Alkur'ani ina saurare,a haka bacci ya ɗauke sai wuraren sallar zuhur na farka.Na yi wanka haɗi da alwala na saka jallabiya na wuce masjid da ke nan cikin gidanmu,ni na ja su sallah bayan mu gama na zauna nan na ci gaba da lazumi ban fito ba sai bayan sallar Asar. “Babana yau mi za a girka ma na buɗa baki?” Granny ta tambaye ni,mahaifiyar Daddy ce a nan gidanmu take zaune tun kafin ma a naɗa shi komanda sojoji.Muna gane wa juna ni da ita don ni ɗaya ne kaɗai jikanta,kaf ƴaƴanta kuma tun su na jarirai suke mutuwa Daddy kawai ya tsaya. “Tsohuwa mai ran ƙarfe ina kika shige duk yau ban gan ki ba” na faɗa tare da nufar ta ina ta ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi. “Ina ɗakina,ai ba ka neme ni ba tun jiya ƙafar nan ta matsa min da ciwo” ta faɗa ta na nuna min ƙafar wacce ta ɗan kumbura. Kan capet na zauna na soma matsa mata ƙafar,cikin sigar zolaya na ce “ko sai an yanke ƙafar nan dai?” ta dungure min kai ta na mai cewa “ka ji min shashanci in an cire gobe da mi zan tarben amaryar ka?” Fuska na kwaɓe ina mai kallonta,ta sakar min murmushi ta ce “Ammyn ka ta kira ni ai ,t sanar da ni yadda kuka yi da ita.Ka na ji Babana ita wani sa'in rayuwa ita ke tsara mana yadda za mu yi,ba kowanne lokaci ba ne abin da mu muka tsara zai zamana daidai” sai kuma ta canza yanayin fuskarta kafin ta ci gaba da cewa “ka ɗauki misalin Daddynka mana,tun ya na yawo da ragga Maimuna ke sonsa kawai daga samun canjin rayuwa ya wulaƙanta ta ita kuma ta ɗauki abin da zafi mine ne na ɗaukar mataki maimakon ki bar wa Allah komai? ” Na ja numfashi na ce “Granny wai mi ya gama Ammy da Daddy faɗa har suke gaba haka? ” Ta shafi kaina ta ce,“Daddyn ka ya yi butulci,saboda amarya ya mari Ammyn ka da ta so nuna masa kuskuren yin haka ya lakaɗa mata na jaki a ƙarshe kuma ya danƙara mata saki.A ranar da za ta fita ta bugi ƙirji ta ce masa yadda ta fita daga gidansa,haka duk matar da zai auro za ta fita.Wai ka na da ma labarin yau wata amaryar zai kawo?” Granny ta buge da tambayata. Ni kuwa tun da na ji wulaƙanci da tozarcin da ya yi wa Ammyna na soma jin tsohon fushina na sake bijirowa.Na yunƙura zan tashi,Granny ta yi saurin mayar da ni ta na cewa “ina kuma za ka je? Faɗa min abin da za a yi ma na saka ƴan aiki yanzu nan” “Duk abin da kika zaɓa Granny ya yi” na faɗa tare da miƙe wa na haura sama.Ina shiga ɗakina na fahimci tabbas wani ya shigo ciki,to amma mi aka shigo yi? Kafin na kai ga lalubo amsa idona ya sauka kan bed sam babu akwatin da na ajiye. Waya na ɗauko na soma kiran Daddy amma bai ɗauka ba,na fito da sauri ina tambayar Granny “ba ki ga wanda ya shiga ɗakina ba?” “Lafiya mi ya faru?” “Akwatina aka ɗauke” na bata amsa kai tsaye. “Baturen nan ne dai ya ɗauko shi a gabana ya fita da shi” “Joy?” na tambaye ta ta ce “eh shi fa” na dafe kaina,Joy shi ne soja na hannun damar Daddyna.Da wannan takaicin na zauna zaman jiran shi,a nan falo na sha ruwa tare da taimakon Granny har na je na bayar da salloli na dawo babu ko motsin Joy.Mu na nan zaune ni da Granny,aka kawo amaryar Daddy wata ƴar ficiciya da ita ko kunyar aurenta bai ji ba. A gaban Granny aka kawo ta ,tun daga danginta har ita amaryar ƴan iya yi ne Granny ta yi musu Allah sa albarka kafin ta nuna musu sashen Daddy suka wuce da ita. Na dubi Granny cike da jin haushi na ce “yanzu wannan ce ya auro?” “Babu ruwan ka,dama ya ce na ja ma kunne akan haka.Duk gani yake saboda tsamin ranka matansa ke fita daga gidansa,sam ya ƙi yarda aikin Maimuna ne” Na ce “Granny ya za ki ce aikin Ammy ne?” “ A bar zancen to.Mi ka shirya wa goben?” Ban bata amsa ba sai kwanciya da na yi na ɗora kaina kan cinyarta,ta ce “sai son jiki kamar mage,ga ka dai ƙaroto amma da taɓi'a yara in ka karye ƙafar tawa ai shikenan” Na yi ɗan murmushi na ce “granny don Allah yi min addu'a na yi bacci ko zan huta da baƙin cikin nan da nake ji”haka kuwa aka yi ta soma yi min karatu,duk da ta na tsohuwa haka take fitar da harufa yadda ya kamata.Sosai nake jin daɗin karatun sai dai baccin ya ƙi samuwa,a ƙarshe ma ita ce ta soma yin gyangyaɗi a doli na miƙe na yi mata rakiya ɗakinta sannan na wuce nawa.A wannan daren ban rumtsa ba sam, system na ɗauka na soma yin binciken da y shafi aikina har aka kira sallar asubah bayan na dawo daga sallah na ɗora daga inda na tsaya.Wuraren ƙarfe tara na tashi na yi wanka na shirya cikin ƙanana kaya wando jean da rigarsa ,ko agogo ban saka ba na fita. [29/07 à 09:31] MRS SADAUKI 👑: *IBRAHEEM* ```soldier man``` © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* #Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓 3-4 Tun daga nesa nake ƙare musu kallo,sai kace wani ƙaramin yaro sai ririta amayar yake ya na bata abinci a baki ko kunya bai ji har da wani ɗora ta kan cinyarsa ita kuma uwar iya yi da rashin kunya ta na gyara masa hullar kansa. Na ɗauke kaina,har na ida sauko wa daga kan benen ban kalle su ba ina shirin zama kan kujera na ji Daddy na wata irin dariya mai cike da tsantsar farin ciki ya na cewa “Baby ba fa haka ake ɗora hullar ba,na faɗa miki kan zakin can gefe yake kallo” “Uhum!Umhum! Ni dai haka ta fi min kyau Baby” ta faɗa cikin wata shagwɓar da tasa na yi saurin ɗaga kai na kalle su ,aka kuwa ci sa'a shi ma Daddyn ya ɗago ya na kallon saitin da nake.Da ido na tsure shi da su rai ɓace,da sauri na ga ya sauke ta daga kan cinyarsa ya ɗora ta kan kujera.Ta taɓe baki ta na kallona,ashe kallon tsoro na yi mata a jiya tsohuwar yarinya ce ƙaramin jiki ne kawai da ita ta ci uban bleachin ta yi fayau. “Ibraheem ka fito?” Daddy ya tambaye ni,ban amsa ba na fasa zaman na wuce part ɗin Granny ina jin zuciyata na tururi.A zaune na tarar da ita ta na shafa maganin ciwon ƙafa,na zauna kusa da ita ina mai gaishe ta ciki-ciki. Ta amsa da “lafiya lau ka ci abinci ne?” na girgiza kai ta ci gaba da cewa “da kaina fa na zaɓi abin da za a dafa ganin jiya ba ka ci wani abin kirki ba” ban ce komai ba sai ƙafarta da na soma matsawa. “Babana ban son shirun nan,faɗa min mi aka yi?” “Daddy ne” na faɗa cike da takaici. “Mi yayi kuma?” “Shi da matarsa ne...” na cije leɓen ƙasa kafin na ci gaba da cewa “kamar wani ƙaramin yaro shine zai zo tsakiyar falo da girmansa da darajarsa ya na ba ƙaramar yarinya abinci a baki har da ɗora ta a cinya? Granny in ni ɗansa ne na kawar da kai su kuma ma'aikatan gidan nan fa?” “Don Allah fita batun su,bani makullin ɗakin ka zan sa a ƙara gyara shi kafin Ammyn ka su ƙaraso” Granny ta faɗa . Na ce “wato ke ma kin basa goyon baya ya ci gaba da yin haka?” Granny ta ce “to mi kake so na ce Babana? Duk tsiyarsa dai ai ba zai koma saurayi ba,ban makulli ka ji” “Wai yanzu gaske kawo ta Ammy za ta yi? Allah ni ban shirya wani zama da mata ba” na faɗa ina mai kwanciya kan lalausan capet ɗin. Granny ta ce “yau na ga abin da ya fi ƙarfina wai tsohuwar da ƙirgen dangi! Yanzu Babana kai ne ba ka shirya zama da mata ba? To halan so kake sai ka zama tuzuru sannan?” Na turo baki tare da lalubo key ɗin na miƙa mata na ce “ni dai wallahi inda ma wurin ki ta zauna” Ta na dariya ta miƙe tsaye ta ce “tun da ni aka aura ma ita ba.Tashi mu je ka ci abincin” “A kawo min nan ba zan sake fita na ga kayan takaici ba” “Ka ji wani zancen mutum da matarsa,kai ma ai ka kusa hutawa da zamana gwabranci can a yi wa kaji zabbi hira suke” ban sake cewa komai ba har ta fita,can sai ga ɗaya daga cikin ƴar aiki ta shigo da sallama ta kawo min abincin. Da kaina na zuba na ci sama-sama kafin na sha ruwa na haye katifar Granny,wani bacci ma na soma ji amma ina tunawa da Abakar ya bar duniya sai na ji ya fita idona.Da sauri na fito don tambayar Daddy inda yasa aka kai min akwatina sai kuma na tarar da shi a tsaye ya na kallon tv da ke manne a jikin bango. Zuciyata har wani tsalle take tsabar yadda allurar soja ta motsa,bresking New ne ake ƴan ta'adda sun kai hari a wani ƙaramin ƙauye da ke cikin Zamfara sun kwashe shanu da kuma wasu samarin garin. Daddy na kalla na ce “sai yaushe ne ƙasarmu za ta bar fuskantar ƙalubalen nan? Gagarar mutane ne suka yi ko rashin iya aikin jami'an tsaro ne?” kallona yayi ba tare da ya ce komai ba ya fita,da sauri na nufi matakalar da za ta sada ni da sashena.Bibiyu nake taka ta har na isa,ina shiga ɗakin na tarar da Granny da ƴan aiki su na ta gyaran falon direct bedroom na wuce nan ɗin ma akwai masu gyara shi.Falo na ce su koma na canza kayan jikina zuwa kakin soja,na saka takalmi da belt na ɗora hulla sannan na ɗauki baƙin gilashi na manna.Ƴar madaidaiciyar bindiga ta na ɗauko na soke a ƙugu kafin na fito,Granny ta tare ni ta na cewa “ina kuma za ka je?” “Wani ɗan aiki za mu yi ki sa min albarka ” “Allah tsare ya dawo da kai lafiya” Na amsa da “amen kafin na fito” Ina saukowa ƙasa na ji matar Daddy na waya “iyeee ke tsohon ɗan duniya ne inda kin ga yadda ya susuce jiya a kaina,na san tun da yake aure-aurensa bai taɓa samu mace haɗaɗiya kamar ni ba” Godiya na yi ga Allah da falon babu kowa masu tsaron gidan duk su na waje,da wannan takaicin na fito na ɗauki motata na bata huta. Sai da na hau kan titi sosai sannan na daidaita gudun motar na kira Ammy,har ta tsinke ba ta ɗauka ba sai a kira na biyu. “Ina kwana Ammy kin tashi lafiya?” na faɗa cike da kwantar da murya. “Lafiya lau alhamdullah! Ga mu a mota muna hanya ina ta bacci sai da Maryam ta tashe ni” cewar Ammy,na ɗan jan numfashi na ce “Ammy ni da na so na ce ku ɗan jira kar ku zo yau” “Saboda me?” “Ammy jiya fa Daddy ya kawo wata” na faɗa ina cije leɓena na ƙasa. Ta ce “ina ruwana da matarsa? Ai ni bai gabana ballantana wata can banza” “Zan sake kiran ki in na sauka Allah tsare hanya” na faɗa ,bayan ta yi min addu'o'in da ta saba na kashe.Ina isa can babban Barack na tarar da sojawa birjit duk sun yi uban layi,na san bai wuce umarnin Daddy ne ya na son tura su can inda abin ya faru. Mota na parker sannan na nufi hanyar da za ta sada ni da ofishinsa,duk da ya na mahaifina sannan kuma na kasance soja hakan bai hana masu tsaron ƙofar hana ni shiga ba. “Shi ne ya bada umarnin kar wanda ya shiga” “ Ku bar ni na ce akwai maganar da za mu yi” na faɗa a karo na biyu,amma suka ƙi nan fa muka hau rigimar da ina tunanin ita ta jawo hankalin mutanen ciki har aka buɗe ƙofar. Sergent Yakubu ne ya na ɗaya daga cikin waɗanda Daddy ke hulɗa da su ba a harakar aiki ba kaɗai,“ku bar shi ya shigo” ya faɗa ya na bani hanya don na wuce.Na yi musu kallon banza sannan na shige,a zaune na tarar da Daddy ya zube wasu duwatsu akan teburi alamu dabarun yaƙi yake shirya wa. “Daddy?” na furta ,shiru bai amsa ba na sake cewa “Daddy ina son zuwa don Allah ka sa a tafi da ni ” nan ma ɗin shiru yayi har sai da Sergent Yakubu ya ce “ shugaba za ka ce” “Ka dai barsa ya ɗauka nan a gida muke” Shiru na yi ina kallonsa,ya ɗago ya shi ma ya na kallon nawa kafin ya ce “ a gabana za ka tsaya da baƙin gilashi?” “Ka yi haƙuri yalaɓai ban iya kallon tsakiyar idonka ne shi yasa,amma ina neman alfarma don Allah ka tsara tafiyar nan da ni” “Captain IBRAHEEM Isa ba za ka je ba” ya faɗa tare da miƙe wa tsaye ya mayar da hankalinsa ga Sergent Yakubu ya ce “ daidai nan da nan za mu baza dakarun mu ta yadda za mu zagaye abokan hamayya,ka ga duk yadda aka yi dai mune da nasara in sha Allah saboda kowanne bango mun zagaye su” “In kuma aka yi rashin sa'a kafin su isa su ƴan ta'addan sun bar wurin?” Sergent Yakubu ya tambaya. Daddy ya ce “ har yanzu dai su na wajen kuma ba zata ce za mu yi musu ” “An bi didigi an gano inda suke?” na yi tambayar ni ma ina ƙara matsawa,Daddy ya ɗago a hassale ya ce “ wai mi kake jira ne? Ba na sallame ka ba?” “Don Allah Daddy ka bar ni na je” “Ba za ka je ba fitar min daga ofis ko na sa a zo a fitar da kai ta tsiya ” ya faɗa cikin tsawa ya na nuna min ƙofa. Amma abun ka da soja na dake na ce “ Yalaɓai mine ne amfanina kenan in har wata matsala za ta taso ba tare da na bai wa ƙasata kariya ba?” “ Sai ka ajiye aikin tun da ba ka ga amfaninsa ba,Sergent Yakubu biyo bayana” Daddy ya faɗa tare da kwashe duwatsun kan teburin ya nufi wani ɗaki da ke cikin ofishin.Haka na bi su da kallo har suka shige ina jin lokacin da aka murɗa key ta ciki,na ja ajiyar zuciya tare da zagayawa na zauna kan kujerar da Daddy ke zama .Kamar an mitsike ni na jawo ɗan ƙaramin aljihun table ɗin,wani ƙonanen agogo na gani na ɗauke shi ina dubawa a kallon farko na gane na Abakar ne don ga farkon sunansa nan da na mahaifinsa a jikin ƙarfen kamar yadda duk wani soja da za a bai wa ita ake masa haka.Mayar da ita na yi na soma bincike har na kai ga liste ɗin sunayen waɗanɗa suka mutu,a nan ne na gano ita gawar Abakar sam ba a ganta ba.Jikina har rawa yake wurin maida komai yadda yake kafin na fito,tuni sojawan har sun shiga motoci riƙe da bindigogi. Na je kusa da babban Sojan da ke kula da duk wani yaƙi ko tafiya in ta kama na ce “ a wacce mota zan shiga?” “ Banda sunan ka a jerin sunayen da Shugaba ya bani ikon na tura” ya bani amsa. “Saboda me?” “Ƙila don ba ka daɗe da dawowa daga mission ba” “Amma ya na ga har da waɗanda a tare muka dawo ɗin wasun su na ciki?” Ya dube ni da kyau ya ce “ mahaifin ka za ka tambaya ba ni ba” ya na gama faɗa yayi gaba ya bar ni nan.Ina ji ina gani motocin suka fita suka bar ni,ina cikin wannan takaicin Daddy ya aiko kira na.Ina shiga Sergent Yakubu ya fita ya bar mu,“zan saka wani aiki ne ka cike min takardun nan,sannan ka binciko min bayanai dangane da ƙauyukan nan” ya faɗa tare da miƙo min tulin takardu.Na karɓa har zan fita ya ce “zo ka zauna a nan ka yi” ban musa ba na ja kujera na soma cike takardun ,in jin idonsa a kaina amma na ƙi ɗagowa har sai da na ji muryarsa ya na cewa “Ammyn ka ta kira ni ...” sai kuma yayi shiru ya na kallona,na ce “mi ta ce ma?” “Za ta zo nan gida” Na ci gaba da abin da nake kafin na amsa masa da “eh na sani” “Zuwan nata ne ba na tunanin zai haifar ɗa mai ido,ka san halin ta ba ta ƙaunar zaman lafiya” “Shugaba wannan fa tsakanin ku ne bai kamata ka shigo da ni ciki ba” na faɗa ina mai kwashe takardun,na fita. Motata na shiga ban zarce ko ina ba sai ɗayar Compagnie ɗinmu inda a can wurin kwana yake.Ɗakin na buɗe,duk yadda na so kar na yi tunanin Abakar abu ya cuttura.Rabi da rabi na yi aikin,sallah kawai ke tsayar da ni sai dab da magrib na fito na nufi gida.Bayan na yi parking sai da na ɗan zauna na wani lokaci kafin na fito,da sallama na shiga falon idona ya sauka kan Ammy.Da sauri na je gabanta na gaishe ina mai gaishe ta,cike da fara'a ta amsa ta na tambaya ta ya aikin na amsa “Alhamdullah” Granny ta ce “baƙauyar amaryar ka ta zo,sai kuka take da rantse-rantse ita ba za ta haura saman bene ba” Shiru na yi ban ce komai ba,na miƙe na ce “Ammy zan je na yi wanka lokacin magrib ya gabato” “A fito lafiya” ta faɗa ,ni kuma na wuce na fara taka matakala kenan na ji muryar matar Daddy na cewa “Baby ga IBRAHEEM ɗin nan sai yanzu ya shigo,kaiii?” ta wani kira ni kamar ƙaramin yaro ko waigawa ban yi ba na idasa hayewa. Ina tura ƙofar falon wani ƙamshi ya ziyarce ni,na lumshe ido ina shaƙar ƙamshin kafin na wuce bedroom.Allah na gani sam ban lura da ita ba sai da na ji uban ihunta,“na shiga uku na lalace mugun abu soja na a gabana?” ido kawai na zuba mata duk uban ihun nan na zata tsoro ta ji wai ashe murna ce take ta ga soja .Rikitatun idona na zuba cikin nata,da sauri na ga ta je bayan labule ta ɓuya kafin ta fara leƙe ban ce mata komai ba na je gaban mirror na yi tsaye idona na ga sun yi ja sosai. “Je ki waje” na faɗa dakyar don so nake na canza kayan jikina . Da gudu ta fita ta na bangaje ƙofa, cire uniform ɗin na yi kafin na shiga toilet wanka na yi haɗi da alwala sannan na ɗauro towel daidai ƙuguna.Kan bed na tarar da ita ta zuba uban tagumi,muna haɗa ido ta ja blanket ta rufa ta na karkawa har gadon sai da ya dinga rawa ta ce “yi haƙuri....”cikin raunataciyar murya ta na mai fashewa da matsanancin kuka mai cin rai. Na rumtse ido,a duniya in akwai abin da na fi tsana to kuka ne shi yasa ma ban cika son yara ba .Ina shirin fara shafa mai na ji sai ƙara ƙaimi take wurin kukan,zuciya cunkushe na nufi bed na zauna tare da yaye blanket ɗin.Da sauri ta yi baya ta na curewa wuri guda,kamar mai koyon magana na ce “ mine ne?” shiru ta yi bata bani amsa ba,“ ban son kukan nan ki yi shiru” Cike da ƙurciya ta ce “ tsoro nake ji” “Tsoron me?” “Matakalar bene kuma ...kuma ni ban son nan wurin Ammy nake so kar ta tafi ta bar ni ban san kowa ba” ta bani amsa ta na shasheka kamar ranta zai fita. “Ni wane ne?” na jefo mata tambayar ba tare da ni kaina na shirya ba.Ta buɗe fuskarta ta tsure ni da manyan idonta,kafin ta ce “abokin Ya Abakar wanda azzalumai suka kasheee” shaaa kuma sai wasu hawayen tare da ɗaukar wani sanfarin kukan.Ji na yi tamkar ta taƙalo min wata masifa daga can ƙasan zuciyata,raɗaɗin rashin Abakar ɗin ya dawo min sabo dal kamar yanzu ne aka shaida min mutuwarsa.A duniya tun da nake ni ban taɓa rarrashi ba,don banda ƙanwa sannan cikin aikin soja na girma ta yadda zuciyata ba ta san soyayya ba in ka fidda ta iyayena da kuma abokina.Rasa yadda za a yi na rarrashe ta na,kamar wani mai jin tsoro haka na jawo ta jikina tare da ƙoƙarin haɗe dafin da nake ji a cikin maƙogorona don na samu na yi mata magana..... [29/07 à 09:31] MRS SADAUKI 👑: *IBRAHEEM* ```soldier man``` © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* #Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓 *YA Ubangiji rahama don ƙarfin ikonka ka wanzar da Zaman lafiya a ƙasata Nijar da Nigeria da ma duk sauran ƙasashen da ke fuskantar ƙalubalen rayuwar nan alfamar Manzon Rahama*👏🏻 5-6 “Yi shiru mana,ban son kukan nan Mary . Addu'armu ya fi buƙata a wannan lokacin,ki godewa Allah ɗan uwanki yayi mutuwar mazaje wacce ba kowa ne ke samun irin ta ba.Mutuwa a filin daga,domin kare ƙasarsa” na faɗa tare da ƙara janta jikina ina goge mata hawayen da suke ta faman yi mata zarya. Cikin muryar kuka ta ce “ abokin Yaya ina cikin damuwa na rashin ɗan uwana,amma Ammy ta ce da kai da shi duk ɗaya ne duk kulawar da yake min kai ma za ka iya kuma zan fi jin daɗin zama da kai fiye da in zauna wurin ta”ta yi maganar ta na faman cusa kanta a ƙirjina. Na ce “ eh gaskiya Ammy ta faɗa ,kin manta Abakar ƙanena ? Kin ga ke ma ƙanwata ce.Daga yau ban son ƙara ganinki ki na kuka,duk abin da kike so kuma ki sanar da ni” Ta gyaɗa kai tare da cewa “ Ammy ta ce za ka kai ni ƙaton kanti ka saya min kaya” Na ce “ eh sai in kin huta za mu je” “ Yaushe kenan?” “ Ko zuwa jibi haka” “ Ba gobe ba?” “ Za mu je goben to” na faɗa ina mai janye ta daga jikina tare da ƙoƙarin sauka daga bed ɗin,ta ce “ kenan kai ne mijina?” Dariya tambayar ta bani,na ce “ Mary shekarun ki nawa?” “Sha tara” ta bani amsa,na juyo ina kallon ta ban san mi yasa ba sai nake ji a raina ina son jan ta wasa na ce “ mai ƙarya dai ɗan wuta ne” Ta buɗe baki ta na murmushi,na kafe ta da ido ganin fara'ar nan yasa na ji daɗi . “ Na waɗa ma gaskiya ?”ta yi tambayar cikin Hausar ƙauyensu na Sokoto. Na yi murmushi na ce “ eh faɗa min” “Kai dai shekaruna Sha shida na” “Sha shida ne za ki ce” Ta turo baki ta ce “ ni wa ba zan iya yin Hausar ku ba,yawwa na ce ku nan kowa na da abun hawa na? Gari duk ko ina motoci na birjit awar an taso daga sallar idi ” Ban bata amsa ba na soma shafa mai da turare,ta madubi nake hango yadda take kallona.Na yi gyaran murya na ce “ ki je ki ci abinci” “ Ban jin yunwa” “To koma falo zan shirya” da “toh” ta amsa ta fice. Drower na buɗe na fiddo kayan da zan saka,ina tsaka da saka kayan kamar an ce in juya na hange ta ta na leƙe na.Muna haɗa ido ta tuntsire da dariya kafin ta gusa,na girgiza a zuci ina cewa ‘ yau na ga ikon Allah ’ bayan na gama na fita falon na tarar da ita a zaune ta ƙura wa ƙofar fitowa ido. Na ɗan haɗe rai na ce “ mi yasa kike leƙe na?” Ta sunne kai ƙila ta tsora ta da yanayin nawa,ta ce “ Ammy ta ce kar na ji kunyar ka kai mijina ne duk abin da za ka yi ni zan taya ka har saka kaya da wanka” Na waro ido ina mamakin ya kuma Ammy za ta faɗi haka,na ce “ shi ne sai ki leƙe ni ?” ta ɗago kai ta ce “ to mine ne in na yi hakan kai ai mijina ne” sai ta soma wasa da awarwaron hannunta na duwatsu. “ Na ji tashi mu sauka ƙasa” ta maƙe kafaɗa ta ce “ Allah tsoro naka ji” “Nake ji ake cewa” na gyara mata da sauri kafin na miƙar da ita tsaye ta na turjewa muka fito. “Kwarankwatse ba zan sauka ba” ta faɗa ta na shirin zubewa ƙasa ta riƙe ni gam. Na ce “ to waye ya hauda ke saman?” “Ammy ce da wata tsohuwa” “To na ji ki nutsu babu wuya fa ki kalli yadda zan yi” Ta ce “ Na wa san bene, kai hawar shi ta a ban yi saboda ina ganin jiri ” Cak na ɗauke ta na soma sauka da ita ƙasa,ido ta rumtse gam har muka sauka na aje ta ina mai cewa “ baƙauya” Ammy da Granny suka saka dariya ni kuma na fita zuwa masjid.Ina can aka kira sallah,bayan an gama na shigo ciki muka je muka ci abinci gaba ɗaya Granny ta miƙe ta nufi ɗakinta. Kusa da Ammy na dawo na zauna ji nake kamar kar lokacin ya shuɗe,“ Ammy yanzu tafiya za ki yi?” “Tambayata ce kake?” ta faɗa tare da kallona,na gyaɗa kai. Ta ce “ zuwa gobe in sha Allah zan koma” “Don Allah ki tsaya ko sati ɗaya ne ki yi” na faɗa . Ta ce “ a'a ba zan jure ba Heemu,ɗazu ai ka ga rainin hankali da matar Ubanka ta yi yadda take wani kiran ka da gadara so ta yi na tanka mata don kawai a yi faɗa ” Na ja numfashi na ce “ Ammy mi yasa ba za ki dawo nan da zama ba? Ban son ganin ku a rabe ke da Daddy ” Sai da ta kalli Maryam kafin ta ce “ jeki sama Maryam ” Ta ce “Ammy na dai je ɗakin waccan” “Okay tashi ki tafi” ta miƙe da saurinta ta na gyara hijabinta wanda tun da ta yi sallah ba ta cire ba. Bayan tafiyar ta ne Ammy ta dube ni da kyau ta ce “ faɗa mini matsalar ka” “Babu Ammy ni burina kawai ki dawo nan ɗin” ta girgiza kai ta ce “ na bar Daddynka har abada,tun ka na goye na bar gidansa bai taɓa tunanin dawo da ni ba sai ni ce zan sarkawa? Ya je yayi ta aure-aurensa wata rana sai ya auro aljana” “Ammy na sani Daddy yayi laifi amma hukuncin da kika ɗauka ne yayi tsauri sosai ” na faɗa cikin jimami ina tuno abin da Granny ta ce min game da mafarin rabuwar. Ammy ta yi wani murmushin wanda ka ganinsa ka san na takaici ne kafin ta ce “ tun bayan da na koma gida bai taɓa tako ƙafarsa ba sai da ka shekara goma a ranar da ya zo ya tafi da kai ya saka ka makarantar sojoji,ya nuna min iko ya maido ka gidansa da ace ya na ra'ayina ai a tare zai maido mu” idonta ne na ga sun cika da hawaye,da sauri na miƙe ina cewa “ kuka kuma Ammy? Don Allah a'a” sai na shiga goge mata su. Jiniya ce ta cika gidan alamun Daddy ya dawo,muna nan tare da Ammy amaryasa ta fito cikin murna.Daddy na shigo wa ta yi tsalle ta rungume shi ba tare da ko kunyar escort ɗinsa ba da suka yo masa rakiya. Raina ne na ji ya sosu musamman da na ji Daddy na cewa “ za ku iya tafiya yanzu lokacin iyalina ne” Ammy ta je ta miƙe na mayar da ita. “Muuuah! Muuuah!” kawai kake ji amaryasa na masa kiss wanda ina da tabbacin da gayya take yinsa ,shi kuwa Daddyn kamar wani soko yayi tsaye na yi imanin bai lura da mu ba da tabbas ba zai tsaya ba. “Mi kika girka min Bab...” sauran maganar ce ta laƙe a maƙoshinsa da muka haɗa ido da shi.Da sauri ya janye ta daga jikinsa “ jeki ɗaki ina zuwa” ya faɗa ita kuma ta harare ni kafin ta wuce. Daddy ya wani haɗe rai ya na mai ƙaraso wa inda muke,na taɓe baki tare da barin wurin na fita zuwa masjid. Daddy yayi gyaran murya ya ce “fatan kin sauka lafiya?” Ammy ta ce “ lafiya lau alhamdullah har ina shirin komawa ma” Ya shafi gefen wuyansa ya ce “ to madallah ” Ammy ta ƙure shi da ido ta na kallonsa kafin ta ce “Isah sai yaushe za ka sanin ciwon kan ka? Aure-auren naka har ya kai ka auro karuwa wacce ba ta san mutumcin kanta ba? A gaban ɗan cikin ka kake sumbatar mace? Ayir ɗinka wallahi ka bani mamaki ....” Daddy yayi saurin katse ta da “ don Allah Maimuna ban son tsiyar gumi.Ina ruwan ki da matata ? Wato kishi kike don kin gan kin koma tsohuwar akwala babu mashunshuni haushi ya kama ki kin ga na auri ƴar shilla?” Sam ba su ga zuwan Granny ba sai saukar marin da ta kifa wa Daddy,ya dafe kumci ya na kallonta “ Mama...” da sauri ta katse shi “ rufe mini baki! Wato kai ba ka ƙaunar zaman lafiya daga ta na faɗa maka gaskiya shikenan sai cibi ya zama ƙari?” “Wace gaskiya Mama ? Kawai banda ikon sakewa da matata?” “A gaban ɗanka? In shiriritar kuke so mi zai hana ku yi ta can sashen ku? Kai yanzu ba zubewar girman ka ba ce da matsayinka da ikonka a gan ka kana abin yara? Dubi gemunka farin gashi ne ya fara tsiro wa amma a haka kake rungumar ƙanƙanuwar yarinya a gaban ɗan cikin ka.Maimuna mu je,ke ma da naki laifin ban ma san mi ya tsayar da ke nan ba” Granny ta faɗa tare da jan hannun Ammy suka koma can ɗakinta. Maryam na zaune ta na karatun Alkur'ani,yanayin da ta ga Ammy ne yasa ta yi saurin rufewa ta nutsu sosai. “ Tashi ki koma sashen ku Maryam ki tabbatar kin yi wanka kin yi sallar isha'i kafin ki kwanta” cewar Ammy, Granny ta ce “a'a ki barta a nan har a jima” Ammy ta ce “ to ni zan ɗan kwanta ” dama fashin sallah take hakan yasa Granny ba ta ce komai ba.Karatun suka ci gaba da yi ita da Maryam inda ta yi kuskure sai ta gyara mata,Maryam ta ce “ ya aka yi kika iya karatu Kaka?” “To in ba abin ki ba ta ya ba zan iya ba tun da ba makarantar Boko na yi ba mai zurfi” “ Tun ki na yarinya kenan kika iya?” Ammy ta ce “ Maryam ba a tsare babba da tambayoyi” Granny ta ce “ a'a bar ta mana ita ma in ta tsufa haka jikokinta za su tsare ta da tambayoyi” Maryam ta ce “ ni dai gaskiya ban so na tsufa” Granny ta dinga dariya ta ce “ ai baƙin gashin nan a sannu zai koma fari sol” Maryam ta hau kukan sangarta. Ammy dai na jin su ba sake kula su ba,furicin Daddy sosai yayi mata tsaye a zuciya wai ta ƙi yin aure saboda babu mai sonta.Wasu hawayen takaici suka zubo mata a zuci ta ce ‘ in sha Allahu zan baka mamaki zan cire ka a rai na je na auri wani’ da wannan tunanin dai ta yi bacci. A can ɓangaren Daddy kuwa cike da jin haushi ya nufi ɗakin amarya Zainabu,a yadda ya tarar ta ci uban shiri cikin kananan kaya sai ya nemi fushin ya rasa.Ita ma cike da iya yi ta zo ta rungume shi suka gama shiriritarsu,kafin ta yi masa rakiya zuwa toilet yayi wanka .Sai da ta cika masa tumbinsa sannan ya je masjid ,ganin IBRAHEEM ne yau zai ja su sallar ya ji haushi sosai don ya matsu ya koma ciki wurin amarya . Cike da nutsuwa nake gabatar da sallar har muka kammala,kamar sauran lokuta a tare muke komawa gida ni da Daddy.Da sauri na miƙe na isa gare shi,ina son yi masa magana ne akan Ammy sai dai shi ya tari numfashina ya na mai cewa “ don Allah ka bar jan dogon karatu,wasu ba sa iya jurar tsayuwar nan ka yi ta karatu sai ka ce muna ƙiyamul laili?”yayi maganar ya na ɗaga ƙafa da alamu sauri yake. Na ce “ yaushe soja ya fara tsoron tsayuwa? Duk sojawa ne sun saba dama to ai ni ban ga wata damuwa ba don an ja dogon karatu.Aka yi tsayuwa akan lamarin duniya sai wurin bautar Ubangiji ne za mu samu rauni?” “To in fa mutum na da uzuri ? Irin hakan dai babu daɗi na faɗa ma” “ Daddy na ga alamun kamar ka na sauri ga shi kuma ina son yin magana da kai” na faɗa ina jan numfashi daidai nan muka iso ƙofar da za ta sada mu da babban falon gidan. “Ya ce ba yanzu ba ka bari zuwa gobe” “Amma Daddy...” shiru na yi sakamakon ganin amaryar ta sake fitowa cikin wata shiga ta riga da wando duk sun matse ta rabin mamarta duk a fili .Da sauri na kawar da kai ganin ta rungume mahaifina duk da kuwa ƙoƙarin hanata da ya so yi,“ Haba Zee ya za ki fito haka wuce gani nan zuwa” “ Ni dai... Ni dai Baby na ƙi wayon mu je ƙafarka ƙafata na sh....” sauran maganar ban ji abin da ta ce ba,na fi zaton Daddy ya toshe mata baki ne. “ To na ji na baka minti biyu” ta faɗa kafin kuma na ji ƙarar takalminta alamun ta tafi. “ Ibraheemu mi ka ce?” Daddy ya tambaye ni a ɗan daburce,sai yanzu na juyo na kalle shi da jajayen idona da suka rine tsabar ɓacin rai .A nan tsaye na barsa na wuce part ɗina, matakalar ma ban ganin ta da kyau. Ina shiga ɗakina direct bedroom na wuce na kwanta rairan ina kallon sama,zuciyata sai tuƙuƙi take. ‘ Wai mutumen da in za ka gansa sai ka yi fiye da sati guda ka na shan wuya,mutumen da in shugaban ƙasa zai fita sai ya bayar da izinin zai iya fita babu wata matsala,mutumen kowanne soja jininsa a akaifa yake in ya aiko kiran ka ko kuma in ransa ya ɓace shine waccar abar take cewa ta basa minti biyu?’ na yi wa kaina tambayar a zuci ina jin farashin ƙunci,baƙin ciki da takaicina su na ƙara yin sama. A daidai wannan gaɓar mutum ɗaya ne kacal ke saurin yin nasara kaina wurin sauke fushina,yanzu kuma ba ya tare da ni mutuwa ta yi mana yankan ƙauna.Haka na ci gaba da juyi a bed ina ta ƙoƙarin tunkuɗe lamarin amma abu ya cuttura,sama da awa biyar ina cikin hali guda.Dakyar na miƙe na je na shiga toilet,ko kayan jikina ban cire ba na sakarwa kaina shower.Ina nan daga tsaye na ji kukan Maryam,Ammy kuma na yi mata faɗan doli ta koyi hawa bene sannan ta jaddada mata nan ne ɗakinta kar ta saki ta kwana ɗakin Granny. Ina jin lokacin da ita Maryam ɗin ke cewa “ Ammy shikenan ba zan sake komawa bacci ba tun da kin tashe ni” Ammy ta ce “ ni ma ai don baccin ya sace ni ne amma ai sam da ba zan bari ki kwanta can ba,ki tabbatar kin yi wanka kin yi brush kafin ki kwanta” tsit kuma ban sake jin sautin muryoyinsu ba. Na ja ajiyar zuciya kafin na tuɓe na yi wankan soso da sabulu na fito ɗaure da towel a ƙugu ,ɗan ƙarami kuma ina tsane gashina. Zaune na tarar da ita ta buɗe trolly duk ta zubar da kayan da ke ciki sai wani turo baki gaba take,gaban dressing mirror na tsaya na yi shafe-shafe sannan na zaɓo kayan bacci masu riga mai sauka har ƙasa.Ina ganin lokacin da ta shiga toilet matse da kayan da za ta canza,da wannan ni ma na saka nawa kafin ta fito na je na haye bed bayan na kashe ƙwan lantarki sai na kunna fitilar bacci. Tunani na soma yi kan shuɗaɗiyar rayuwarmu ni da Abakar,«aboki don ba ka da ƙanwa ne da ka ji irin yadda nake ji,Maryam komai ce nawa.Farin cikinta ya fi min komai daɗi a duniya,aikin nan ma domin ita da Umma nake yinsa.Na ci burin yi wa Maryam kayan ɗaki na kece raini a matsayina na waliyinta maɗaurin aurenta» wannan na ɗaya daga cikin zantukan da yayi min game da Maryam. Yadda ta fado jikina ta bi ta kaina yasa ta katse min tunanin,“ ni wallahi sanyi naka ji ba don na yi wa Ammy alƙawarin ba,in na yi wankan nan shegiya nakai ” ta faɗa cikin mita tare da gyara kwanciyarta ta ja bargon da nake ciki ta rufa.Duk da ta rufa ɗin bai hana ta rawa sanyi ba,kamar wanda aka yi wa doli na ɗan matsa kaɗan sai gani kusa da ita sosai.A hankali na ɗan kwanta ta samanta na yi mata rumfa da ƙirjina,hannunta na ji gefen cikina ta sarkayo shi haɗi da riƙe wa gam ta ce “ ina jin sanyi sosai” Bargon na ida ja ya rufe mu har wajen kai,a hankali kuma na matsa fuskata kusan tata ta yadda muna jin numfashin juna.Ƙamshin turarenta ne ya sakar min wata kasala da na kusanci wuyanta,ban san lokacin da na saki wani gauron numfashi ba ina mai sake saka ta ƙirjina.Tuni Maryam ta fara mitsirniya,gefen wuyanta na soma aika ma sumba kafin na yi sa'ar lalubo bakinta na fara kissing.Sam ba ta yi ƙoƙarin hana ni ba da alamu ma ta na jin daɗin haka don sai ƙara riƙe ni take, wannan yanayin da na tsinci kaina sam ba zan iya faɗar yadda yake ba.Bugun zuciyata ne kawai ke ta tsananta ya na bada sauti na musamman,sama da minti talatin kafin na janye daga jikinta na koma gefe ina mayar da numfashi.Blanket ɗin na janye na maido shi iya ƙirji,idona a lumshe ina jin raina yayi ɗan sanyi ba kamar ɗazu ba.Na kai hannu na jawo ta na ɗora kanta kan ƙirjina yayin da kuma hannuna ke kan bayanta.Murya can ƙasan maƙoshi na ce “ kin bar jin sanyin ?” kamar wata munafuka ta ce min “ eh!” “ ok yi bacci” “ uhumm !” shiru duk muka yi ina ta mamakin kaina ,ɗaya ɓangaren kuma na sakawa Ammy da alkhairi da ta haɗa auren nan... [29/07 à 09:31] MRS SADAUKI 👑: *IBRAHEEM* ```soldier man``` © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* #Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓 7-8 Kiran sallar farin ne ya tashe ni daga dadaɗan baccin da nake.Ina ware ido na yi tozali da fuskar Maryam kwance kan ƙirjina sai baccinta take,moments ɗinmu na jiya ya dawo min na ɗan yi murmushi ina mamakin kaina .Janye ta na yi na nufi toilet na yi wanka,da na fito na shirya caf cikin jallabiya ruwan ƙasa .Sai da na yi nafiloli sannan na wuce masjid ,bayan mun gamo sallah na dawo gida har yanzu ba ta farka ba. Blanket ɗin na yaye ina mai kiran sunanta “ Mary ? Mary tashi ki yi sallah” ta ware idonta kaɗan kafin ta sake lumshe su har da gyara kwanciya ta ci gaba da baccinta.Na dafe goshi na ce “ Ammy kin kawo min aiki” ƙara tashe ta na yi,ta na gunguni ta tashi zaune ni kuma na fita na ɗauki key na je na buɗe mota na ɗauko takardun Daddy ya bani.Ina komawa bedroom na ga ta sake komawa bacci,raina ne na ji ya ɓace cikin ɗaga murya na ce “ keee! Tashi na ce har yanzu ba ki yi sallar ba ne ko me” A firgice ta tashi ta na kuka tare da zuba min manyan idonta,“ ba za ki wuce ba kenan?” na faɗa ina nufo ta da sauri ta ruga ta shige toilet ina jin ƙarar shower na tabbata wanka take.Falo na koma na soma yin aikina,wani iri nake ji na rasa gane mike damuna ma a yanzu. MARYAM Wani irin mugun tsoron Ibraheemu ne ya shige ta,duk yadda take da tsiwa sosai take shakkar idonsa.Ta na shiga wanka ta soma yi kamar yadda Ammy ta sanar da ita kullum kafin sallar asubah ta fara yin wanka ta yi kuma brush.Maclean ɗin da ta gani ta matsa ta wanke bakinta,soso ma da nasa ta yi amfani sannan ta fito ta saka rigar sallah ta gabatar.Bayan ta gama ta soma karatun Alkur'ani inda ta iya kafin ta zo wanda Granny ta yi mata,ganin ta na ta yin gargada yasa ta yi shiru kar ta yi saɓo. Miƙewa ta yi ta gyara shimfiɗar gadon ,ta fesa turare wanda tun jiya Ammy ta nuna mata ma'ajiyarsa.Toilet ma sai da ta je ta wanke ta sannan ta fito ta haye bed sai bacci. IBRAHEEM Ina nan zaune ina aiki kiran Ammy ya shigo wayata, Allah na gani abin da yasa ban je na gaishe su tun da asubah ba don kar ta yi min zancen tafiyarta ne. Kiran na ɗauka ko kafin na ce wani abu ta ce “ ka sauko ƙasa” sai kuma ta kashe. Na ja ajiyar zuciya ina jin wani yanayi kafin na miƙe,sai da na duba bedroom na ga Maryam ta koma bacci sannan na sauka. Ƴan aiki ke ta faman gyaran falo ana ƙara ƙawata shi ,haka na wuce sai gaishe ni suke.Sashen Granny na wuce da sallama a bakina,bayan na gaishe su ne na maida hankalina ga Ammy.Ta sakar min murmushi ta ce “ zan tafi Heemu sai in na dawo wajen suna” Da sauri na sauke idona ƙasa ina cewa “Ammy don Allah ki zauna” “ Mu je ka sauke ni na hau mota” Na ɗago a karo na biyu na kalle ta,sam babu alamun wasa kan fuskarta hakan yasa na dubi Granny na ce “ don Allah Granny ki sa baki mana” Ta ce “Baba tun da ta ce tafiya za ta yi na san babu wanda zai canza mata ra'ayi,haka halin Maimuna yake yadda ka san mutanen farko sai shegiyar kafiya ” Ba don na so ba haka na ɗauki ƙaramin trollynta muka fito,har mota Granny ta yi mata rakiya ta na mai cewa “ wancan tsohon ya ƙi fitowa haka za ki tafi ba ku yi ban kwana ba” Ammy ta ce “ bai komai Mama ai na yi abin da ya kawo ni” addu'a sosai Granny ta yi kafin mu wuce.Gidan Bus na kai ta don Ammy sam ba ta son doguwar tafiya cikin ƙananun motoci,har muka kai ta na yi min nasiha game da zaman aure da kuma jaddada min girman amana .Har ciki na yi mata rakiya,na kunna mata AC seat ɗinta kafin na fito.Ban baro wurin ba har sai da na ga motarsu ta tashi,ina isa gida lokacin ƙarfe takwas na safe ya buga.Sashen Daddy na duba alamun har yanzu su na ciki ba su fito ba,wani takaici ya rufe ni a haka na haye sama. ★A ɓangaren su Daddy kuwa ya na shiga Zeey ta cika bahon wanka ya shiga kamar wani ƙaramin yaro haka ta yi masa wanka.Daddy irin mazan nan ne masu budurwar zuciya sam bai ganin ya girma shi dai burinsa kawai ya ji shi jikin mace ,a kullum bai gajiya haka kuma bai kwanan banza.Yawan buƙatarsa na ɗaya daga cikin abin da yasa ya yi wa Ammy kishiya don an yi rashin sa'a ita ba kalarsa ba ce,auren kuma bai je ko ina ba ya mutu haka yake ta aure-aure har Allah ya kawo shi ga Zee wacce ta kasance bazawara ba ta taɓa haihuwa ba fitinarta yasa mijinta ya sake ta.Yanzu kuma da ta auri Daddy sai ta ga kamar tasu ta zo daidai duk da ta fi zaton ta fi shi juriya, wannan kuma har da don ita da sauran ƙarfinta ba ta yi shekarunsa ba. A wannan daren tamkar sallah haka su Daddy aka ta more aure,sai kace wasu karnai.Sallar asubah ma yau a ɗaki yayi ta,sai wuraren ƙarfe tara suka tashi suka yi wanka Zee ta taimaka masa ya shirya cikin kakinsa na sojoji ta ɗora masa hulla sannan suka fito falo. Jin ta yake kamar ƙwai ya na jin wata muguwar ƙaunarta,ba don komai ba sai don ta iya jure nauyin buƙatarsa. Kan dianing suka zauna,da sauri mai kula da lafiyarsa ya matso ya auna abincin da wata na'ura aka tabbatar normal yake ba komai sannan Zee ta zuba musu suka fara ci ta na masa hirar soyayya. “ In ka tafi zan yi kewar ka sosai Baby ”. “ Zan dawo ai kar ki damu,duk inda zan je ki na maƙale a birnin zuciyata ” Daddy ya faɗa ya na wani murmushi.Zee ta rausayar da kai ta ce “ banda kallon mata Baby don in ka ce za ka yi min kishiya zan kashe kaina” Da sauri ya ce “ haba don Allah bari yi min zancen mutuwa,na yi miki kishiya akan me? Sai in canzawa kika yi kika dinga min rowar kan ki” Ta yi wani fari da ido ta ce “ haba Baby in na yi wa rowa ribar mi zan ci? Ai ni taka ce” cike da murna Daddy ya kamo hannunta ya ce “ Baby kin ci kyautar mota ” Zeey ta yi wani irin ihu tare da rungume shi,daidai nan Granny ta fito a gaban idonta.Ta girgiza kai cike da masifa ta ce “ Allah wadaran naka ya lalace! Yanzu kai Isah mi na faɗa ma?” da sauri Zeey ta janye daga jikinsa ta duƙa har ƙasa ta ce “ ina kwana Mama?” Ba ta amsa ba sai ci gaba ta yi da cewa “ daga yau ku dinga zama can falon ku kuna cin abinci na soke fitowa nan,in kuma wallahi ka ci gaba zan bar ma gidan ka” Hankalin Daddy ya tashi don ya tsani fushin Granny,haƙuri ya soma bata kafin ya je ya kama hannunta ya zo ya zaunar da ita kan kujera.Da kansa ya zuba mata abincin cike da kulawa,ita kuwa Granny hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba. Ta saki murmushi ta ce “ Allah yi ma albarka ” “ Amen Mamana ki daɗe ki yi ƙarko,sai kin yi Hajiya Mama uwar shugaban sojoji kike doli a lalaɓa ki a sannu in ba haka ba a tayar da yaƙin duniya na uku” Daddy ke faɗa har da wani sunkuya wa ya na yi wa Granny kirari.Ranta fari ƙal ta kai hannu ta ɗora kan kafaɗar shi ta ce “tashi ya isa haka nan wuce ka tafi aiki kar ka makara” Sai da Daddy yayi kiran waya ya shaida fitowarsa kafin ya fita,masu take masa baya ne suka yi masa rakiya har motarsa kafin su fice. Zee kuwa kasa zama ta yi kawai ta miƙe ta bar Granny nan ta na cin abinci.Ɗaki ta wuce,akwatin da ta zuba kayan matanta ta buɗe ta zaɓi waɗanda za ta yi aiki da su na daren yau.Murmushi kan fuskarta ta soma jijiƙa su a gorar ruwa ta na girgiza wa,ita kaɗai ta san irin tanadin da ta yi wa Daddy.A fili ta ce “ ba dai lamarin nan kake so ba,yau zan fito ma da asalin maitata sai na gana ma baƙar wuya ” sai kuma ta kece da dariya. IBRAHEEMU Ina shiga ɗaki ko ta kan takardun ban bi ba na wuce bedroom, doguwar jallabiyar na cire na tsaya iya wandon cikin.Hasken ɗakin na kashe na raɓa gefen Maryam,wannan tiririn da zuciyata ke yi na baƙin cikin Daddy na can da wata baƙar amaryasa nake son na kashe. Abin da na lura shine kiss na yaye damuwa,ban taɓa sanin haka ba sai jiya da na yi wa Maryam shi.Bakina na ɗora kan lips ɗinta ,tun ina yi a hankali har na soma zaƙewa saboda abubuwan da nake ji su na ratsa ni.Zuciyata ce ta ƙara ƙarfin gudu jin Maryam na mayar min da martani,ba sai an faɗa min ba ita ma koyo take kamar dai ni tun da jiya ne muka fara sanin al'amarin.Kiss ɗin ne na ji bai isa na haɗa da romance,rigar jikinta na yi nasarar cire wa na soma sarrafa ta.Kuka ta soma yi min wannan yasa na mirgina baya ina mayar da numfashi,ta tashi zaune ta ɗauki rigarta ina kallonta na ga ta mayar da abar ta kafin ta dire daga bed ɗin.Sam ban yin ƙoƙarin hana ta ba sai ma haushin kaina da na ji,ƴar ƙanƙanuwa yarinya ta kwance min tunani abun takaicin kuma ƙanwar abokina.Na ja wani numfashi tare da ɗauko pilow na rungume.Shiru na yi ina tunanin kaina ‘ yaushe na samu wannan canji? Sanina dai sai lokacin damina kawai sha'awa ke damuna,ko kuma in an yi ƙololuwar sanyi’ sai kuma na ja tsuki a fili wani sashen zuciyata na bani amsar da ‘ ƙila don yanzu an yi maka aure ne an gama ka da mace ɗaki guda’ da sauri na miƙe na shiga toilet jin abin na sake yin gaba-gaba. Shower na sakar wa kaina,ina tsaka da wanka na soma jin wayata na ruri.Kiran Ammy ne don waƙarta ta musamman ce,a gaggauce na yi wankan na fito.Ina maida kiran amma ba a ɗauka,gabana ne ya shiga faɗuwa ina shirin aika wani saƙon text ɗinta ya shigo ``` Heemu ƴan ta'adda sun tare motarmu a hanya ba zan iya ɗaukar kira ba don tuni sun sauko mu ƙasa an fara lalubar wasu ma``` Ji na yi kamar an buga min wani ƙaton dutse a kai,da sauri na saka kakina na soja da bindigogi.Jikina har rawa yake,ko kallon inda Maryam take ban yi ba na fita da gudu-gudu.Ina cikin mota na kira Daddy na shaida masa amma yake min zancen banza wai kar na je na jira zai tura sojoji amma ina tuni na soma bibiyar layin Ammy na ƙure gudun mota. Tsawon lokaci ina sharara gudu kafin kira ya shigo da lambar Ammy,na ɗauka da mamakina sai na ji muryarta ce.“Sun yi tafiyarsu sun gudu! Sun bar mu lokaci guda bayan sun yi mana mugun duka Heemu ” na rumtse ido haɗi da jan wani dogon burki ina sauraren yadda Ammy ke rera kuka,dakyar na ce “ gani nan zuwa Ammy don Allah ki bar kuka ki na ɗaga mini hankali” “ Kar ka zo Heemu yanzu ai za mu tashi daga nan...” daidai nan kiran ya katse,a ta na'urar da na jona nake bibiyar Ammy na ga sun fara gusawa daga wurin alamun motar ta tafi.Amma duk da haka bai sa na koma ba,haka na ci gaba da gudun kusan a tare muka shiga gidan Bus ɗin ni da motarsu. Ko jira ban yi ba na nufi motar,ana buɗewa na shiga ciki na riƙo Ammy.Fuskarta ta yi ja sosai ga sawun yatsu nan kwance raɗau,haka na fiddo ta na kai ta motata ina jin haushin kaina.Asibiti na wuce da ita duk ƙoƙarin hana ni da ta yi a cewar ta lafiyarta lau kawai kanta ke ciwo,sai ga shi da muka je asibitin an ce jininta ya hau.Ƙarin ruwa suka saka mata,ina daga gefenta zaune ina saƙar zuci so nake yi na yi mat tambayoyi amma ina jiran har ta dawo hayyacinta. Kamar ta san abin da nake saƙawa a rai sai cewa ta yi “sun tafi da wasu daga cikinmu Heemu” Na dube ta da sauri,idonta na lumshewa take ci gaba da cewa “da dukkanmu za su tafi da mu sai ogansu ya samu kira bayan ya dawo daga wayar ne yake cewa a tafi da iya maza kawai a bar matan” “Da yayi wayar ba ki ji abin da ya ce ba?”na yi tambayar zuciyata na mugun bugawa,Ammy ta ce “ban ji ba,sai dai lokacin da ɗaya daga cikinsu yake tambayar ogan mi yasa ba za a tafi da mu duka ba sai ya ce umarnin Dagaci ne” Dagaci babban ɗan ta'adda ne shine shugaban duk wasu manyan-manyan ƴan daba don ƙungiyarsu guda ce. Shiru na yi ina wani tunani haɗi da zargin da ban son ya zama gaskiya ,sai dai duk yadda nake son tunkuɗe zargin abin ya cuttura sai ma wasu abubuwa da suka faru masu kamanceceniya da suka shiga dawo min. Ganin Ammy ta samu ta yi bacci na miƙe na fita waje na kira lambar Daddy,bugu biyu ya ɗauka kafin ya ce “ina jin ka” sam yanzu babu alamar tashin hankali ba kamar ɗazu da na sanar da shi an kama Ammy kuma gani a hanya zan je ƙwato ta. “Ya ake ciki ka aika sojojin ne?” na jefo masa tambayar ,shiru yayi bai ce komai ba har sai da na sake maimaita tambayar sannan ya ce “ka ga Abraheemu aiki nake ” ƙittt ya katse kiran.Na bi screen ɗin wayar da kallo ina juya maganar Daddyn.Karon farko da na tuna ina da wasu abokai na biyu bayan Abakar ,zama na yi na dinga gwada wayarsu babu wacce ta shiga sai ta mutum ɗaya ya na ɗaga wa ya ce “ya ne Soldier Man ya ƙarin haƙurinmu?” “Alhamdullah! Shamssudeen don Allah ina son ganin ka akwai aikin da nake son ka yi min” Ya ce “yanzu dai ina kan hanya mun je Katsina wani aiki sai gobe za mu koma Kano” Na ɗan nisa na ce “fatan kun yi nasara?” Ya ce “eh mun kama biyu daga cikin yaran Dagaci” Da sauri na ce “yaran Dagaci ka ce?” Ya ce “eh zuwa jibi za a wuce da su Abuja” Wani irin daɗi na ji ta faɗi gasasa kenan.Na ce “to kawai zan bari har ku ƙaraso Abujar ido da ido ma za mu fi fahimtar juna” nan muka yi sallama sai a lokacin kawai na je na yi sallolina,Ammy na farkawa na bata jus ta sha magani kafin mu wuce gidanta.....