[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ Ƙirƙiraren labari ne,ban yi shi don cin mutumci kowa ba.Duk wanda ya zo daidai da rayuwarsa to akasi aka samu. 1 #ƘASAR COTE D'IVOIRE #Babbar asibitin Abengourou A tsorace nake ƙara tushe kunnuwana ko zan samu sa'ar toshe ma'adanar sautina da ke zuƙo min wata murya mai cike da tashin hankali.Sai dai yaudarar kaina nake,domin kuwa toshe kunnen da na yi hakan bai canza zane ba .Na kai hannu da niyyar ɗaukar pilow ko shi Allah zai sa na dace,hasken ɗakin ne ya ɗauke ɗif wanda ya yi sanadiyar tsayawar na'urar da ke kore zafi. Ƙaiƙayi na fara ji yayin da sauro da zafi suka ce salama alaikum,shegiyar muryar nan mai shegen naci sai ƙara ƙaimi take wurin roƙon abin da ban san mi take so ba “ku cece ni ! Ku cece ni don Allah babu kowa ne?” Na ja tsuki bisanin na lalubo wayata na kunna fitila,duk abokan aikina baccinsu kawai suke a gajiye.Na miƙe tare da nufar ƙofa,na murɗa handle na fito ,ga mamakina ko ina na asibitin akwai hasken wuta sai ɗakinmu da kuma wani ɗakin da ke can gabashi wanda akwai ƴar tazara tsakani. Haka kawai na ji zuciyata na tunzura ni kan na je na duba tako ɗaya ,biyu,ina daɗa matsawa ina kuma daɗa jin sautin muryar nan mai neman taimako har na isa bakin ƙofar daidai nan hasken ɗakin ya dawo.Na kutsa kai,sai na tarar da nurse biyu da wani Dr a tsaye kan wata matashiyar budurwa ,gefe kuma wata jemamiyar tsohuwa ce zaune ta na kaɗa ƙafa. Duk kallonsu ya dawo kaina,ni ma su nake kallo ɗin. “Ayodele mi kike yi a nan? Babu aiki ne ɓangaren ku?” Dr ya tambaye ni,na buɗa baki da niyyar yin magana na tsinkayo wata murya kuma na ce min “Ayodele please ki taimaka min ban mutu ba!” Inda sautin ya fito na duba,sai yanzu na lura da idon budurwar rufe suke ruf kamar mai yin bacci.Da mamaki nake tambayar kaina ‘dama mai bacci ya na iya yin magana?’ “Ta rasu ne! Ƙoƙarin cire duk abubuwan da ke jikinta ne muke amma sun ƙi fita” Dr ya katse min tunani. “Amma yanzun nan fa ta min magana akan na taimaketa ba ta mutu ba” na faɗa . Duk kallon mamaki suka bi ni da shi,hakan yasa na ci gaba da cewa “tun ɗazu fa ita ta hana ni bacci kururuwar ta ce ta tashe ni” “Ayodeleee?” Dr ya kira ni da wani sauti,bisanin ya tambayi nurse ɗin “ku tun ɗazu da muke nan kun ji kururuwar ne?” duk kai suka girgiza alamun a'a. Sai ya maido kallonsa gare ni “to kin ji ta yiyu kunnuwanki ne ba su jiye miki daidai ba” “Mi sunanta?” ita ce tambayar da na yi,“Emeka” ɗaya daga cikin nurse ɗin ta ban amsa. A hankali na fara taka ƙafata sai dai kafin na isa ga Emekar tsohuwar nan ta taso tare da tsaya wa a gabana “ina za ki je? Mi za ki yi?” ta jero min tambayoyi haɗi da jifata da wani mugun kallo mai ratsa ɓargo da tsoka don sam bai da daɗi. Dakyar na fizgo numfashi tare da jarumtar kallonta cikin tsakiyar ido ,kawai sai na ga mugun razani a nata idon tare kuma da saurin ja ta bani wuri ba tare da na san dalilin yin haka ba. Kai ga Emeka na yi tsaye bisanin na kai hannu kan fuskarta na ce “Emeka ?” “Ayodele ta fa mutu,ya kike yi wa matatta magana kamar zautatta?” Dr ya tari numfashina.Ba tare da na dube shi ba na ce “ba ta mutu ba Dr ! Doguwar suma aka sa ta” “Wa ya sa ta doguwar suma? Nan fa asibiti ce kuma mun san aikinmu ” “Dr ita wacce ta saka ta suman ta san kan ta! Ina iyayenta suke?” na tambaya. “Daga ita sai Kakarta suka zo,kuma ga ta can ta fita” cewar nurse. Na ɗago kaina sai na ga tuni tsohuwar nan ba ta nan,wato abin da na fahimta ita ce Kakar Emeka. “Ayodele ki taimaka ki damƙa ni ga iyayena Kakata ba ta sona shi ne take son kashe ni,ta ɓoye ruhina cikin asusun ƙarfe ta lashi takobi ba za ta fiddo shi ba har abada” shiru na yi ina sauraren esprit ɗin Emeka da ke yi min magana ba tare da ni kaina na san shi ne ba. “Dr yanzu ma ba ga shi ta na yin magana ba?” “Mtsw! Ayodele fita! Fita na ce !” Dr ya yi min wata muguwar tsawa. Tako ɗaya na yi na tsaya,cikin fushi ya kuma cewa “kenan ba za ki fita ɗin ba?” Murya a raunane na ce “ba ka ga ta riƙe min hannu ba ne?” Duk ido suka waro Dr har da ɗora hannu a kai ya ce “wai Ayodele haukata ni kike son yi? Ku kun ga ta riƙe ta?” ya tambayi nurse suka girgiza kai. Da mamaki nake kallonsu bisanin na mayar da dubana ga Emeka wacce ta riƙe ni gam ta na girgiza kai idonta na shatatar da hawaye. “Ke kaɗai ke jin abin da nake cewa da kuma ganin abin da nake don Allah kar ki biye su” cewar Emeka . Cikin jin haushi Dr ya fizgo hannuna da niyyar fitar da ni da ƙarfin tsiya sai dai sam ya kasa sakamakon ɗayan hannun da ke riƙe da Emeka . “Dr ni fa na fara jin tsoro! Ina ga fa gaskiya ne! Dubi yadda hannunta ke jone kamar a rinƙe shi ɗin kuma ....kuma gadon kamar ya na motsa wa” nurse ta faɗa. Dr ya sake min hannu,ya ce “ba zan yi mamaki ba don Abeno cike take da ƴaƴan matsafa da Mayu....” bai rufe bakinsa ba Emeka ta fara shaƙuwa,da sauri duk suka nufeta tare da saita na'urar aiki a kanta. Ni kuwa ganin numfashinta ya dawo kawai sai na sulale na koma can ɓangaren mu.Kasa bacci na yi sai zaune da na yi na rabka uban tagumi ina tunanin abin da ya faru.Gadon bayana ne ya fara yin ƙaiƙayi,tare kuma da wata irin tsira wa tamkar ana nitsa wasu abubuwa gefe da gefen kafaɗuna. Dishi-dishi idona ya fara,ban san ya aka yi ba na tsinci kaina a wata duniya wacce na fi kyautata zaton ta mafarki ce. Wani ƙaton gida mai ɗauke da ɗakuna kashi-kashi,ruhina ya sallama.Babu wanda ya amsa min haka ba wanda ya ɗago ya dube ni sai tsohuwa wacce tun farkon shigowata na ji yaran gidan na ambaton sunanta da “Yaba” Mugun kallon nan mai cike da hassada,ƙyashi haɗi da baƙin ciki ta jefo min bisanin ta miƙe tsaye ta zo gare ni.“Mi kike so kuma yanzu?” “Abin da kika ɓoye!” na bata amsa. “Maganar ahali ce wannan bai shafe ki ba,kin dai yi naki ikon don haka ki....” ban bari ta dire ba na tari numfashinta da “ki bani cikin lumana ko kuma na ƙwata ta ƙarfin tsiya! Yin haka kuma babba asara ce gare ki domin duk abin da kika ɓoye zan fito da su ne” Tsoro ne na gani shimfiɗe ƙarara a fuskar Yaba,bisanin ta yi gaba ni kuma na take mata baya har cikin ɗakinta na laka wanda aka yi ma rufin kara. Ƙarƙashin gado ta duƙa ta fito da wani asusun ƙarfe tare da miƙo min shi,ban ɗauki lokaci ba wurin buɗe shi.Baƙin hayaƙi ya fito kamar fitar iska ya tashi sama,guntun ƙyallen atamfa na gani sai na ɗauke shi bisanin na aje asusun na fito. Daidai nan kuma na farka daga baccina,na dafe gefen goshina da yake sara min bisanin na buɗe idona taram .Da sauri na tashi ganin Emeka a tsaye ta na min murmushi. “Na gode sosai Ayodele,kin ceci rayuwata!” ta faɗa tare da ƙoƙarin karɓa wani abu daga hannuna da nake jin na jimƙe ba tare da na san mine ne ba sai da na kai dubana sai na ga ƙiren atamfar da na yi mafarki ne. Emeka ta ci gaba da cewa “wannan zanen ankon bikina ce,Inna Yaba ta yi amfani da shi don kashe ni saboda kawai zan auri bare wanda ba cikin danginmu ba.Na gode!” ta na gama faɗar haka ta fice ta bar ni sake da baki ina tunanin kar dai ace mafarkin da na yi gaskiya ne? ?????? MRS SADAUKI ce🌬️ [31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ 3 Cike da tashin hankali na fara jijiga Momah haɗi da kiran sunanta sai dai ko motsi ba ta yi ba.Idona tuni sun fara zubar da hawaye,na ruga a guje na nufi hanyar fita sai mu ka yi kiciɓis ni da A'ishah.Ita ta fara yin magana ta na cewa “Ayodele yarinyar nan fa an wuce da ita asibiti sai wani shure-shure take ta na kiran sunan ki” “Momah na ciki ta kasa tashi mu je ki taimaka min” na faɗa ina goge fuska da bayan hannu.Ciki mu ka koma , A'ishah ce ta yi azancin zuba wa Momah ruwan tulu masu masifar sanyi.Momoh ta ja ajiyar zuciya,idonta a rufe take yin wani Yare wanda ba Hausa ba haka ba French ba ne. Mu ka kalli juna ni da A'ishah,ban sani ba ko ita ma tunaninmu ya zo ɗaya wato Momah ko aljanu gare ta? Ciwon kai mai tsanani da ya fara farmakata ya addabe ni a lokaci guda na nemi wurin da zan kwanta don idona tuni sun fara lumshewa. A'isha ta riƙe ni ta na cewa “ina kuma za ki je alhalin mahaifiyar ki na cikin wannan hali?” ban bata amsa ba kawai da na janye hannuna tare da samun wuri na kwanta kan tabarma. Momah ta dawo daidai, A'ishah ta ce “ya jikin?” “Alhamdullah! Kin ga abin da ƙawar ki ta jindilo mini ko? Wancan baccin da take Allah kawai yasa masifar da zai haifar ” ba tare da A'isha ta san taƙamaimai abin da Momah ke nufi ba ta kalli inda Ayodele ke kwance har wani girgiza take ta na motsa baki kamar mai yin magana.Ba don ta so ba haka ta yi wa Momah sallama ta yi tafiyarta. Kwanta wa ta ke da wuya,wani hazo ya rufen ido.Tsofi huɗu na yi tozali da su ,dukkansu na san su zan iya shaida su duk da ban san gidajensu ba amma ina ganinsu a unguwa. “Mu za ki tona wa asiri? ” “Mine ne ruwan ki da mu?” “Ita Zeinab ɗin ƙanwar uwar ki ce?” “Ya kuke ɓata lokaci wurin tambayarta? Kawai mu shaƙe shegiya mu kashe ta” Kowacce daga cikin ta faɗa,ta ƙarshen abin da na lura ta na da zafi kuma tsafin maitarta ya fi na kowa ƙarfi shi yasa har take tunanin za ta iya ja da ni. “Ban zo nan don na haɗu da ku ba ku dinga kawo min shirme,ruhin Zeinab nake so ku saki cikin salama kafin na ƙwata ta ƙarfi.Dukkanin ku babu wacce ban san sirrin maitar ta ba,in kuka cika ni zan rusar daular ku” na faɗa cikin kakkausar murya,duk sai suka sheƙe da dariya. “Ke kuwa baiwar Allah miye na gudun ƴan uwanki Mayu?” “Hhhh! To wai mine yasa kika karɓi maita in kin san ba mugunta ne burin ki ba?” “Sannu mai son taimako al'umma,mu je mu yi farauta ke kuma ki zo ki karɓe.Kin san tun yaushe muke son naman Zeinab ? Tun ta na cikin tsumman goyo muke haƙonta sai yanzu da za mu sha romo za ki hana?” Idona ne suka fara yin zafi,a take na ji wani abu na cika su.Na zube su kan tsofin Mayun nan,duk sai na ga sun razana a take su ma suka faɗi wani ɗalasiman tsafi nan take suka rikiɗa suka zama macizai. Ko kaɗan ban son kashe rai,sai dai ɗaya daga cikinsu ta ja masu mutuwar kasko sakamakon shammata ta da ta yi ta cije ni a hannu.Bakina na buɗe na saki ihun azaba yayin da kuma idona ya fitar da wani tartatsin wuta duk sukama wuta su na ihu. Na ja wani dogon numfashi ina mai buɗe idona taram kan Momah wacce ke ta ƙoƙarin ɗaure min hannu da ƙyalle jini sai zuba yake. Mafarkin da na yi ne a yanzu ya dawo min tarau a kwanya,abin da na fahimta kawai ba irin sauran mafarkai ba ne da duk ƴan Adam ke yi nawa ya sha banban. “Tashi mu je na kai ki asibiti,jinin nan ba zai tsaya ba” cewar Momah ,ban tambaye ta komai ba na tashi.Takalmi kawai na saka a ƙafata muka fito waje,unguwar cike take da jama'a kowa mamaki shimfiɗe kan fuskarsa yayin da yake kallon makiran tsofin nan huɗu su na birgima a ƙasa tare da tona ma kansu asiri.Duk wanda suka taɓa kamawa sai da suka faɗa hatta Zeinab. Da sauri Momah ta ja hannuna muka bar wurin,taxi muka tara sai asibiti.“Mine ne ya same ta ?” cewar likita ,da mamaki na dubi Momah jin ta ce “sarar maciji ne” ‘To ta ya aka yi ta sani?’ na tambayi kaina a zuci. Allura yayi min tare da bani wasu magunguna , Momah ta biyasa bisanin mu fito. Tafiyar ƙasa kawai muke ta yi,sam ban ga alamun Momah na da niyyar tarar mana da abun hawa ba ga shi kuma na gaji. “Hum!” ta yi tare da dubana,na dube ta kawai.Sai kuma ta ja ta tsaya,bisanin ta ja ni zuwa gefe “zauna” ta faɗa tare da nuna min dakali.Na bi umarninta,wata tambaya ta jefo min da ban fahimce ta ba “mine ne haɗin ki da tsofin unguwa uhum? Duk yadda nake son liƙe ƙofofin nan sai da kika bi duk kika buɗe su ko? Ayodele rayuwar da kike so mu yi kenan kullum cikin sauya unguwa da ƙasashe?” “Momah ban fahimce ki ba...” ko rufe bakina ban yi ba ta zuba min yatsunta biyar bisanin ta yi zaman ƴan bori a ƙasa ta fashe da kuka.Na rumtse ido don sam ban son ganin zubar hawayenta ko ba komai ita ce gatana,ban san kowa ba daga ahalina sai ita kaɗai. Furucinta ya saka na ware idona kanta,“Ayodele ina roƙon ki daga yau kar ki sake shiga sabgar wani maye ko mayya,babu ruwan ki da su.Ki barsu su yi rayuwarsu,abu ɗaya na sani har abada babu wani daga cikinsu da zai samu zarrar kashe ki wannan ma da aka yi cikin rashin sanin ke wace ce suka yi miki illa” Bakina na samu da tambayarta “Momah wace ce ni ?” Ta min wani kallo bisanin ta miƙe ta kakaɓe jikinta,“tashi mu tafi ” ta umarce ni a doli na tashi ɗin.Sai a lokacin ta nema mana abun hawa muka isa gida,da labarin mutuwar tsofin nan huɗu muka ci karo yayin da Zeinab kuwa tuni ta samu lafiya ta dawo ras. A ranar nan ko abincin dare kasa ci na yi,magani kawai na kora da farau-farau sannan na kwanta bacci.Nan na yi mafarkin wani farin tsoho jawur da shi ya bayyana gare ni,bandejin da aka laulaya min a hannu ya warware bisanin ya saka min wasu ruwa masu masifar sanyi sai kuma yayi tafiyarsa. Washegari ko da na tashi hannuna ya warke kamar ma ban taɓa jin ciwo ba,cike da mamaki na fara ƙwala kiran sunan Momah ina mai fitowa waje “Momah dubi hannuna ya warke ” maimakon ta yi murna akasin haka na gani.Cikin tashin hankali take cewa “shikenan ashe su na biye da mu” “Su wa?” na jefo mata tambaya,“je ki yi wanka lokacin zuwa aiki ya kusa” Na turo baki cike da jin haushi,na cika bokiti na je na yi wanka.Bayan na shirya ne na lumshe idona,na fara yi wa abun bauta godiya kan lafiyar da ya bani bisanin na fito hannuna ɗauke da jaka. “Momah na tafi sai na dawo” “A dawo lafiya” shi ne abin da ta ce min. Sai da ina cikin taxi ne na fara duba wayata ,nan na ci karo da miss call ɗin A'isha da Fatima .Na saki murmushi,har cikin zuciyata nake son ƙawayena. A bakin asibiti na ci karo da su kamar kullum,Fatima na da babur ita ke ɗauko A'ishah tun da kusan unguwarsu ɗaya. Gaisa wa muka yi, A'ishah ta so yi min zancen abin da ya faru jiya sai dai ban bata fuska ba. Ta sauka daga mashin muka ƙarasa ciki,uwanda suka kwana nan suka sauka mu kuma mu ka hau aiki bayan mun ci abinci. Lokacin hutu mu na zaune ana hira A'ishah ta ce “Mansur ya matsa akan lalle aurenmu nan da 2weeks yake son shi,da Mama ta so masa bayanin kan lokacin ba ta gama haɗa min kayan ɗaki ba ya ce babu damuwa duk shi zai yi burinsa kawai a aura masa ni ” “Wayyo! Kin ji daɗin ki wallahi ina ma ace ni ce .Ya kamata mu je mu fitar da anko gobe in mun sauka daga aiki” cewar Fatimah. “Eh dama hakan na raina” hira sosai suke su biyu kamar sun manta da ni,don ko kaɗan ni ban da bakina ba saboda haka kawai na ji na tsani lamarin auren nan da ace ina da iko da babu shakka na hana shi. “Kin yi shiru tun ɗazu halan masoyin ɓoye ake tunani?” A'ishah ta tambaye ni cikin zolaya,na ɗan taɓe baki bisanin na miƙe na ce “ku dai tashi mu koma saura minti biyar” duk suka miƙe,nan mu ka ƙara hawa aiki sai lokacin sallah kawai suke tsayawa su yi ni kuwa da ban san taƙamaimai Addinina ba sai dai na zauna. Zuwa ƙarfe takwas na dare duk mun gaji saboda aikin likitanci sai jajirtace.Ɗakin baccinmu duk muka nufa,mu ka bar stagiaire irin sabbin likitocin da ake kawo wa asibitoci don koyon aiki sai in matsala ta yi tsanani ne sosai suke tayar da mu. A gajiya duk muka ɓingire bacci,babu ma kamar ni da nake jin kamar an min shegen duka. Ƙyalƙyal! Haka nake jin sautin dariya na ƙara yawaita,y wasu muryoyi ke tashi sama yayin da kuma shashekar kuka ke ƙara ƙaimi. Ba tare da na buɗe idona ba na tashi zaune,bisanin kuma na sauko daga bed.Ban buɗe ƙofa ba ita ta buɗe da kanta,wani haske ke yi min jagora ni kuma ina biye da shi kamar raƙumi da akala har na isa wani ɗaki. Tsit suka yi,sai wata murya da ke tambayar “wane ne? Ba za ka yi magana ba? Ka bar haske mu ” daidai nan hasken da ke min jagora ya ɓace hakan ya basu damar ganina mu ka yi gaba da gaba. “Kayiii! Mace a wannan lokacin? ” tako ɗaya na ƙara duk suka ja baya tare da ɓoye wa ƙarƙashin gadajen maras lafiya aka bar mai yi min magana. Abu guda na yi nasarar gane wa,shi a siffar mutum yake yayin da sauran kuma innuwarsu kawai ake gani. “Su wane ne ka gayyato mana a nan ana zaman lafiya?” na jefo masa tambayar . Muryarsa na ɗan rawa ya ce “abokaina ne! Umm.Sun zo ganina ne” Sai a yanzu na ƙare masa kallo,hannunsa na ɗauke da tiyon da ake yi wa mutum ƙarin ruwa. “Don sun zo ganin ka shi ne za su hana mutane bacci? Ce maku aka yi nan gidan caca ne? ” na sake faɗa cikin tsawa. Shiru ya ɗan yi bisanin ya ce “madam ke ɗaya ce kawai kika ji mu,amma normal mutum basa ji ” “Ka sallame su maza kar na sake ganinsu a nan har lokacin da za ka bar asibitin nan in kuma ba haka ba zan yi mugun saɓa maku” ko gama rufe baki ban yi ba ya ce “an gama ranki ya daɗe!” Har na juya zan koma sai kuma na tsaya tare da jefo masa tambaya “shashekar kukan wa nake ji a ɗazu?” Kame-kame ya fara,can cikin ikon Allah idona ya sauka kan wani ɗan yaro da ke kwance kan gado.Esprit ɗinsa na gani a ɗaure ana tsoratar da shi haka kawai,“wane ne yayi masa haka?” na yi tambayar tare da shaƙe mutumen wanda aƙalla zai kai shekar sittin . Cikin magagin wahala ya ce “abokina ne! Wallahi sai da na hana shi amma ya ƙiya” Yadda yake magana zan iya hangen wani koren abu daga cikin bakinsa,ban san da me na yi amfani ba na ciro shi daga bakinsa bisanin na je na saki yaron nan da suke cutar wa sai kuma na koma ɗaki. Ina kwanciya kan bed sai na ji nutsuwata ta dawo daidai saɓanin a ɗazu da nake jin kamar mu biyu ne a cikin gangar jikina. Washegari Da na tashi na yi zaton mafarki ne na yi wannan yasa ban bai wa abun muhimmanci ba.Ɗakunan maras lafiya mu ka fara shiga mu na duba su,na zo daidai gadon wannan mutumen na jiya da dare na ji muryarsa ya na cewa “madam don Allah ki taimaka ki bani kambuna” Da mugun mamaki na dube shi na ce “mi kake magana a kai? Ko wani abu yake ma ciwo ne?” Ya waro ido ya ce “kambun maitata da kika karɓe a daren jiya ” Ras gabana ya faɗi,a fili na furta “kenan ba mafarki ne na yi ba?” “Ki ban abina don Allah na yi miki alƙawari har na fita daga nan ba zan ƙara cutar da kowa ba” ya sake faɗa a karo na biyu,wani baƙin ciki ne ya turnuƙe ni nan take.“Wato ka ma taɓa cutar da wasu kenan?” Muryarsa na ɗan rawa ya ce “wallahi yara biyu ne kawai na shanye ma jini bayan su babu wanda na cutar” Na lumshe ido,nan take abun da yake kira da kambun maita ya bayyana gare ni daga nan inda nake zan iya hango shi cikin jakata wacce ke can ɗakin baccinmu. ‘Duk wanda ya kashe shi ma a kashe shi,don haka kai ma dole ka bi su’ na faɗa a zuci ina mai juya wa zan fita hargaginsa ya tsayar da ni na juyo. Duk hankalin kowa ya koma kansa,nishi kawai yake ya na zarar ido. A'isha ta nufe shi ta fara dubasa,kafin wani lokaci ya ce ga garinku nan ya mutu. Wani kallo na ga ta na jifata da shi na tuhuma,sai kuma ta fita babu jima wa suka shigo ita da Dr . Rubuce-rubuce aka yi bisanin a sanar da ƴan uwansa suka fita da shi. Har muka sauka daga aiki A'ishah ba ta bar min kallon nan ba,tuni na tsargu.Ko da na je gida hankalina kasa kwanciya yayi,haka na wuni sukuku Momah ta yi tambayar duniya amma na ce da ita babu komai. Da dare bayan duniya ta yi tsit na buɗe jakata na ciro kambun maitar nan,wata ƴar ƙaramar halitta ce mai rai sai motsi take.Sai da na ƙura idona da kyau sannan na fahimci Kunkuru ne,hannuna na rawa na ɗauko shi nan take ya ɗauki wani irin haske kamar an kunna ƙwan lantarki. Muryar Momah na ji daga sama ta na mai cewa “kambun wane ne?” na juyo a razane ina kallon ta,sai dai abin da ya fi ɗaga min hankali shi ne iya muryar ce kawai ke ta Momah amma fuskarta ta canza ..... [31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ 2 Har aka fara kiran asallatu ban rumtsa ba,ina ta saƙa da warwara don gano ainahin abin da ke faruwa da ni sai dai ga banza wai an tsikari kakkausa. Ƙarfe biyar na asubahi abokan aikina suka tashi don gabatar da sallah.Har suka ida ina nan zaune ina reto da ƙafafuna, A'ishah ta dube ni cike da kulawa ta ce “Ayodele lafiyar ki kuwa?” “Ƙalau nake!” na bata amsa. “Mi ya samu fuskar ki duk ta yi ja?” ta sake tambayata,ban bata amsa ba sai wata nauyayyar ajiyar zuciya da na sauke. Fatima da ke jan casbi kusa da ita ta ce “ƙila mafarkin da ta saba yi ne yau ma ya sake zuwar mata” Na ɗan harareta na ce “don ban da aikin yi sai mafarkin ɓoyayyen masoyi ko?” duk suka yi dariya bisanin A'ishah ta ce “Ya kamata dai ki tashi ki wanke fuskar ki tun da ba sallah za ki yi ba” Na dube ta na ce “lokacin da nake tawa ibadar ki na ina ne?” Ta taɓe baki ta ce “ibadar da kike yi marar alƙibila? Ke fa kan ki ba ki san wane ne kike bauta ma ba” “Ubangiji nake bauta! Kuma na yi imani da shi,kamar yadda kuke bautar naku da ba ku taɓa gani ba” na bata amsa. Fatima ta ce “don Allah ku bar zancen Addini! Mu je mu ida aikinmu mu kama gabanmu” Hakan kuwa aka yi,bayan na wanke fuskata mu ka shiga fara duba maras lafiya ƙarfe tara na buga wa duk mu ka sauka daga aiki. Kasancewar banda abun hawa yasa na zo bakin titi,dakyar na samu taxi ita ma wata tsohuwa ce.Gidan baya na zauna,mutum uku na taras a ciki hakan yasa duk mu ka matse. “Mtsw ! ” ta kusa da ni ta ja tsaki a karo na uku,na kasa haƙuri na ce “ya dai?” Kamar jira take in tanka ta ce “ah toh! Gari yanzu ya lalace ko ina ka je sai ka ji ana zancen Mayu ! Abun baƙin ciki har da yara ƙanana suke kama wa” Ni kuwa na ce “kuma wallahi in kika bincika kaso casa'in na Mayun garin nan tsofi ne....” ban rufe baki ba motar ta yi wani ƙuuu! Ta tsaya. “To shikenan kun yi sara da mutum sama sai ku fito!” shi ne abin da mai taxi ɗin ya faɗa ya na mai jan tsuki,sai kuma ya fita. Ƴan dube-dube ya yi bisanin ya umarci kowa ya fito,duk mu ka sauka sai wani tsoho da ke gaba mai cin goro bakinsa duk yayi ja. “Ka yi haƙuri ba su san da kai ciki ba ne shi yasa har suka tsokane ka” mai taxi ya faɗa cikin wata irin murya mai rauni. Kamar wani sarki tsohon nan ya fito tare da tsirtar da yawu abun mamaki sai suka zuba ga jikina da kuma na matar da muke hirar. Dariyar shaƙiyanci ya fara bisanin ya ce “halan ku baƙi ne a Abengourou? Na ce ku baƙi ne?” kamar wasu ƴaƴansa haka yake mana ihu,tuni wannan matar ta zube ƙasa ta na basa haƙuri. Raina ne na ji ya ƙara ɓaci,zuciyata ta kawo min wuya.Ban san mi ya shiga kaina ba kawai dai na samu bakina da furta “dara ta ci gida !” sai tsohon ya ɗago da ƙarfi ya na kallona,jikinsa har rawa yake wurin ƙetara wa bakin kwalta ya karɓo ruwan leda ya zo ya fara wanke daidai inda ya tsirta min yawunsa masu ɗauke da jan goro. Na lumshe ido ina jin zuciyata na ɗan doka wa tare da ƙoƙarin yaƙarta akan tafarfasa da take. Cikin taxi mu ka koma don kuwa ta tashi,fafur tsohon nan ya ƙi shiga direba sai magiya yake. Har za mu tafi na ce “ita kuma wannan da ka riƙe?” Jikinsa na rawa ya ɓallo goro ya bata,na dubeta na yi mata alama da ta karɓa hannunta na rawa ta amsa tare da kai goron baki,mai taxi yayi mata key. Mun ɗan tafi kaɗan matar ta fara aman baƙin wani abu kamar ranta zai fita,a dole duk mu ka sauka daga taxi ɗin na tari wata sai gida. “Washhh! Na gaji” shi ne abin da na furta ina mai zube wa kan tabarmar kaba wacce Momah ke zaune ta na gyaran wake. Wani kallo take bi na da shi wanda yasa na tsargu na ce “Momah ya dai ?” Sai ta ja wata doguwar ajiyar zuciya ta ce “wa kika tsokana a saman hanya?” “Da aka yi mi fa?” na tambayeta. “Idon ki na ga sun canza launi” ta ban amsa. Na yi ƴar dariya tare da canza zancen “babu ruwan ƙanƙara masu sanyi?” “Babu sai dai ki sha na tulu,ɗiyar Asabe ta rasu duk can aka saye ƙanƙarar ” “Wace daga ciki?” “Zeinab mana! Ai kin san dama ta jima babu lafiya” Na dafe ƙirji na ce “tun yaushe a ba ta da lafiya? Ban sani ba” “Eh to ba a fi sati ba! Don a gida aka yi jinyar ta ba kowa ya san da rashin lafiyar ba” Jiki babu ƙwari na miƙe don sosai mutuwar ta dake ni a kaf faɗin unguwarmu gidansu kawai nake shiga.Ina tafiya sai na ji kamar ana take min baya na waigo sai dai ban ga kowa ba.Ɗaki na shiga na cire kaya,ɗaurin ƙirji na yi na fito na yi wanka. Bayan na gama na zuba kunu a roba na fara sha kenan wayata ta ɗau ringing,na ɗauka ban kai ga magana ba na ji muryar A'ishah na ce min “Albishirin ki?An kawo kuɗin aurena yanzu haka har an tsayar da ranar buki?” cike da murna na shiga tambayarta “da gaske? A'isha kar fa a ce ƙarya kike min” “Allah gaske ne! Ki zo Please ” Na ja dogon numfashi na ce “sai dai zuwa gobe tun da yau akwai inda zan je” “Ke dalla wacce magana kuma kike? Ko ma ina za ki je ki jingine tafiyar kawai ki zo nan kin ga fa Fatimah nan” Jin haka yasa na ce “ok gani nan zuwa!” sai ta kashe ,ni kuma na miƙe na je na saka kaya ko mai ban shafa ba na fito na sanar da Momah. “Masha Allah! Ki dai dawo da wuri kin ga zan shiga gidan mutuwa zuwa biyar na marice” “To Momah!” na amsa tare da fitowa waje.Cak na tsaya ina kallon yadda unguwar ta ɗauki wani duhu har wani hayaƙi ke tashi.Cike da mamaki sai na ga na ƙofar gidansu Zeinab ya fi yawa,a fili na furta “to! Mi kuma ke faruwa?” kiran A'ishah da ya shigo shi yasa na watsar na nufi bakin titi na samu abun hawa sai gidansu. Ai kuwa gaskiya ne an kawo lefen ,ina shiga na ta gani mutane masu zuwa yin barka.Bayan na gaishe da Mamarta na wuce ɗakinta,nan mu ka ta yin ihun murna tare da tsara yadda bikin zai kasance.Bayan mun ci abinci ne na yi tambaya “ A'isha wai wane ne za ki aura?” “Cousin ɗina ne! Dama kin san tun farko ya nuna ya na sona sai kuma abun ya watse tun da ya tafi Lagos to ya dawo shi ne fa aka kawo lefe” ta ban amsa cike da murna. “Aikin mi yake na ga lefen Masha Allah kamar matar gwamna” cewar Fatimah,na karɓe zancen da “ai kuwa dai! Ko bra da pant kawai abun kallo ne uwa uba sarƙoƙin da na gani har da na zinare” “Na faɗa maku Lagos ya je wurin diga ya samo kuɗi sosai yanzu haka ya fara kasuwanci!” A'ishah ta faɗa . “Fatimah saura ke! Ki cewa Nasir ya fito kawai mu sha biki!” na faɗa cikin zolaya,ta kai min dundu a baya ta ce “ Allah kiyaye min ni Dr nake so” Duk muka fiddo ido waje , A'ishah ta ce “wannan masifaffen? Tabbb! Ayodele kin san kuwa ɗazu da na wuce ta gaban su na ji ya na bai wa Dr Jameela labarin ki wai kin ceci wata su sun yi zaton ta mutu” Wani irin ras na ji,yayin da kaina ya sara kamar zai tsage.Ba don ace na yi ƙarya ba da zan iya cewa har mahudanar jinina ta sauya tsarin gudu. Dakyar na iya cewa “bacci ma nake ji bari na kwanta kafin a jima na tafi gida” “Munafuka yanzu da kika ga lokacin sallah yayi ko?” Na dubi Fatimah da idona da nake jin tamkar ana yi min masanye bisanin na lumshe su ba tare da na bata amsa ba.Ina jin lokacin da ta ci gaba da cewa “ A'isha ni kuwa lamarin Ayodele na ban tsoro idonta wani sa'in sai su koma kamar na damusa ” Duniyar da na lula wacce take kusan zahiri ba mafarki ba yasa ban sake jin hirarsu ba. Ranar da Momah ta zo min da zancen za mu tashi daga unguwar da muke zuwa wannan da muke ciki,ba zan manta a ranar da mu ka dira sai da na kwana da ciwo ƙafa mai tsanani.Maƙociyarmu Asabe ce take shaida mana unguwar Mayu sun yawaita duk da har yanzu ba a san su wane ne ba amma mu tashi tsaye wurin addu'o'i.Na sha daga bisanin na warke,abu guda da kuma ba zan manta ba kusan tsofin unguwarmu ba na shiri da su. A cikin baccin nan na ja wata ajiyar zuciya ganin Zeinab ta nufo ni idonta shaɓe-shaɓe da hawaye,bayanta kuma tsofin unguwarmu ne ke biye da ita ko wacce daga cikinsu da wuƙa a hannunta. “Ayodele? Ayodele? Lafiyar ki?” na ji muryar A'ishah wacce ta tashe ni daga bacci,na buɗe ido dakyar bisanin na lumshe su Zeinab ta sake bayyana gare ni sai dai nacin A'ishah ya saka na tashi daga baccin ba don na so ba. “Haba sai ki tsora mutum! Haka kike bacci dama? Ninshari ne wannan kamar kururuwar damusa a cikin daji” ta faɗi haka ta na mai kallona. “Ina Fatimah ?” shi ne abin da na tambaye ta. “Ta tafi gida mana,tashi mu je don Allah ki yi min rakiya daga can sai mu wuce gidan ku” . Toilet na shiga na wanke fuskata sannan muka wuce gun tela,bayan sun gama tattauna komai muka samu taxi zuwa gidanmu. Rana tsaka ne wantsar,duk an yi gudu ba za a wuce ƙarfe uku ba. “Ayodele sallar gawa ce ake yi wai ” cewar A'isha don ta riga ni fita daga taxi,na ziro ƙafata kenan idona yayi tozali da gawar Zeinab wacce maza suka sa a gaba su na sallata. Gadan-gadan na nufe wurin, A'ishah ta riƙe hannuna daga baya ta na cewa “ina za ki kuma?” na fizge hannuna na je na yi tsaye kusa da makara ina mai ɗaga hannu na ce “ku dakata! Ba ta mutu ba ga ta a zaune ta na faman kuka” Farin likafanin da aka rufeta na yaye daidai fuskarta,ni kaina ban san mine ne na faɗa ba ko kuma na yi sai Zeinab ta tashi zaune daram da ƙugunta “Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allahu Akbar!” maza suka fara yin kabbara kafin wani lokaci har labari ya kai cikin gida. Sam ban ga tawowar Momah ba sai ganinta na yi a gabana cikin ɓacin rai ta fizgo ni mu ka fito dandazon jama'a,ƙiiii take ja na zuwa gidanmu har mu ka shiga. Daidai tsakiyar gida ta wani tura ni na faɗi ƙasa,cikin ɓacin rai take cewa “wannan wace irin masifa ce? Gadon tsiya,gadon jaraba! Ayodeleeee!” sai kuma ta yi shiru ta na mai dafe saitin zuciyarta,da azama na miƙe ina mai tare ta don kar ta faɗi sai inaaaa tuni Momah ta rinjaye ni ta faɗi ƙasa warwas.... [31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ *Na ji wasu na ta tambaya wai free book ne? To paid ne! Sannan wannan ba gajeren labari ba ne irin su BOKANYA,MACIJIN CIKI da sauransu da nake yi iya page 20 .Duk wacce ke ra'ayin book ɗin MUTUWARE za ta iya yi min magana kai tsaye ta WhatsApp domin biyan kuɗin karatunta* +22795045822 Page 4 Fuskar Momah sak ta tsohuwa irin uwanda sun ga jiya da yau.Tuni tsoro yayi min dabaibayi ya ɗaure min zuciya,cikin wata irin murya wacce ba tata ba take shaida min “wannan halittar da ke hannunki ta na da matuƙar haɗari ki yi gaggawa mayar masu ita kayar su.Kin san kuwa mi ake kira da Kambun Kunkuru? Maita ce mai shegen naci masu ita za ki ga ko mutuwa suka yi sun dinga yin fatalwa kenan domin son duniya ba zai taɓa gushe wa ba daga zuciyarsa” Momah na gama faɗar haka kamar ƙyaftawar ido ainahin fuskarta ta dawo normal. Wani numfashi na ga ta ja ta na mai kafe ni da ido,da sauri na mayar da Kunkurun cikin jaka ina mai cewa “Momah ke ce?” Maimakon ta ban amsa sai kawai ta fashe da kuka,hankalina ya ƙara tashi na shiga tambayarta can ta tsagaita da kukan tare da yi min umarni na je na kwanta. Ban musa ba na kwanta sai dai fa ko kaɗan babu ɗigon bacci a idona.Tunani kawai nake,zuwa yanzu na fahimci akwai wani ƁOYAYYEN SIRRI(MRS SADAUKI) da Momah ke ɓoye min sai dai ban san shi ba. Kamar wacce take karantar zuciyata na ji saukar furucinta “Ayodele ban ɓoye miki tarihin ki ba don wani abu ba,sai don kiyaye ki daga mumunar ƙaddarar da mahaifin ki ke son ɗora ki a kai” Da sauri na yunƙura na tashi zaune na ce “Momah don Allah ki faɗa min wane ne mahaifina? Sannan ya na raye?” “Da ransa duk da na fi shekara ashirin da baro ƙasarmu ta gado,amma ina ji a jikina bai mutu ba” “Mine ne dalilin ki na guduwa to?” “Zan faɗa miki sai ranar da kika cika shekara ashirin da biyu cicif” “Nan da wata biyu kenan?” na faɗa don birthday ɗina ya kusa.Ta jinjina min kai alamar tabbatar wa,cike da farin ciki na kwana. Washegari da zan tafi makaranta Momah ta jadadda min kan cewa na mayar da Kunkurun nan inda na ɗauko shi “to” kawai na ce mata ba wai don ina da niyyar yin haka ba. Da na fito waje a ƙofar gida na yi rame daidai inda ruwa ke kwanta wa na saka Kambun Kunkuru na mayar da ƙasa,ina ganin yadda yake kallona da manyan idonsa amma Allah na gani ba zan barsa ba ya cutar da mutane. Ko da na isa asibiti na tarar ana ta ɗaga ankon bikin A'isha ,ban ware kaina ba na shiga duba wa tare da tambayar inda suka fiddota. Muna tsaka da aiki A'isha ta zo kusa da ni ta ce “Ayodele kin tuna mutumen da ya mutu jiya?” duk da na fahimci wanda take nufi bai hana ni neman ƙarin haske ba “wane fa?” “Wanda kafin mu sauka ya mutu,gadonsa kusa da na yaron nan mai cutar sikila” “Oh! Na gane shi” “Hum! In faɗa miki an sake maido shi asibiti” “Bai mutu ba?” na tambayeta da sauri,har sai da ta min wani kallo bisanin ta ce “ya mutu! ” Na sauke ajiyar zuciya,ita kuma ta ci gaba da cewa “sai dai fa gawarsa ta ƙi shiga kabari ” A'ishah ta faɗa cikin wani yanayi. Dukkan nutsuwata na bata tare da tambayarta “ban gane ba? To ya su ka yi da gawar?” “Sun maido ta mana! Ta na can MUTUWARE cikin sanyi”ta ban amsa. “Can shi ya sani! Mugun halinsa ne yasa Ubangiji ya nuna masa ishara” na faɗa zan ci gaba da aikin cika takardu don mun ɗan tsaya hutu ne . “Amma Ayodele na tambaye ki mana” “Ina jin ki” na faɗa ba tare da na dube ta ba. Ta ce “mine ne haɗin ki da shi?” na ɗago na zuba mata na mujiya sai na ga ta ɗan rikice da sauri ta ce “ah! Ina nufin mi ya haɗa ku,jiya da ina ƙoƙarin taimakonsa na ji ya na cewa ki yi masa rai kar ki muzanta ni ban shirya zuwa ɓoyayyar duniya ba” “Sai kuma ya ce miki da ni yake?” “Sunan ki na ji ya faɗa” “To ki je ki tambayesa” na faɗa cikin fushi tare da tashi na barta ma wurin. Wunin ranar haka muka yi aiki sam babu walwala har Fatimah sai da ta lura kamar mun samu saɓani.Ta yi tambayar duk muka ce mata ba komai,wurin cin abinci ma haka A'isha ke ta min kallon ƙasa-ƙasa ban san mi take zargi a kaina ba har mu ka zo kwanciya. Addu'o'i na ga ta na ta yi na neman tsari,sannan alamu sun nuna a tsorace take don motsi kaɗan sai ta zabura.Kasa haƙuri na yi na ce “ A'ishah ina son yin magana da ke” Fatimah ta kalla wacce ta sharar bacci bisanin ta ce min “to” Na saki wani murmushi sannan na ce “ki na tunanin ko wani na gani zai cutar da ke zan bari ballantana ni da kaina na cuce ki? Ban san zargin mi kike yi a kaina ba,amma ki sani ruhin Ayodele tsarkake ne .Burinsa kullum ya kawar da mugunta da masu yin ta,na san abin da ya faru a unguwarmu da kuma na mutumen nan sun saka miki shakku a kaina” Ta ja wani dogon numfashi sannan ta ce “wallahi ni lamarin ki ne ya fara bani tsoro,abubuwa kike kamar ƴar autar aljan.Idonki fa har canza kala suke,kuma ba zan ɓoye miki ba wallahi na fara jin tsoron ki” Na ƙyalƙyace da dariya na ce “wallahi ba muguwa ba ce ni ! Kuma ban san mike faruwa da ni ba.Abu guda nake so ki saka a ran ki shi ne Ayodele amanar A'isha ce” Wani gamsashen murmushi ta sakar min ta ce “har na ji zuciyata wasai,yanzu kam zan yi bacci cikin aminci” Sai da mu ka ɗan yi hira bisanin ta ɓingire bacci,na dube su cike da so da ƙauna irin ta jini. Ina shirin yin kwanciya na ji an kira sunana “Ayodele?” na waiga ban ga kowa ba,sai na yi tunanin ko kunnena ne bai ji min daidai ba.Sai dai da mamakina haka aka sake kira a karo na biyu,kawai sai na fito. Ci gaba da kiran sunan nawa aka yi,inda sautin ke fito wa na dinga bin direction ina ta tafiya har na ɓullo wata kwana.Nan na yi kiciɓis da allon sanarwa,sunan *GIDAN GAWA* ne ɓaro-ɓaro da manyan baƙi,a ƙasa kuma hoton gawa ne naɗe cikin farin likafani. Waige-waige na fara ,har zan koma na ƙara jin sautin sunana,muryar ya ta namiji ce ba mace ba.Ɗakunan da aka tanada don ajiyar gawa na nufi na mazan,ƙofar da kanta ta buɗe hakan yasa na kutsa kai. Ƙyalƙyal ! Aka kece da dariya,da sauri na fara dube-dube don tantance shin cikin wane akwatin ne ake dariya. “Ga ni nan” na ji ya faɗa a bayana,na juya na yi tozali da mutumen da A'ishah ke ban labari an maido gawarsa. Ido cikin ido muke kallon juna da shi,bisanin na ce “lafiya ka kira ni izuwa nan?” “Kambuna nake so ki ban” “Ba zan bayar ba doli ka mutu kamar sauran da ka kashe” “Ki bani cikin lalama ko kuma na gayyato miki shugabanmu” “Au! Har shugaba gare ku? Na tambaye ka mi yasa kuke son yin mugunta? Don me ba za ku zauna cikin duniya normal ba kamar kowa?” “Saboda duniyar ɓoye ta matsafa ta fi daɗi,za ka sha jini ka yi ta siddabaru ka na tsoratar da mutane cike da nishaɗi ” Hira ya fara yi min ta yadda suke kama kurwar mutum da kuma yadda suke yi in su na son bai wa mutum tsoro,hakan ya shagaltar da ni sosai sam ban fargaba sai mugayen esprit na ga duk sun cika ɗakin. Ruhika ne na maras imani,wasu ma daga maƙabarta suka zo nan don taimakon ɗan uwansu.Kewaye ni suka yi,ba na ganin fuskokinsu.Wasunsu tamkar innuwa,wasu kamar dunƙulalen baƙin hayaƙi,wasu kuma cikin siffar fatalwa ne da farin likafaninsu. “Auwushhh tangarrsinn,mahulujaaa.An yarhihum khaaaaa!” shi ne furicin da na samu bakina ya na furta wa,duk a tsorace suka ja ba shi kuwa tuni ya koma cikin akwatinsa.Idona na rufe na ci gaba da yin wani Yare ina yarfa hannu,a take wani haske duk ya game ɗakin wanda rufe wa idona bai hana ni ganin halin da suke ciki ba. Tuni duk suka tsere suka bar ni da shi,akwatin da yake ciki na ɗora hannuna akai ya fara ihu ya na “cewa ki yi haƙuri zan tafi wallahi na yi miki alƙawari gobe zan bar gidan gawar nan zan je na kwanta kabar....” bai ida kai furucinsa ba wani haske ya fito daga bakina ya daki goshinsa tsit ya mutu a yanzu kuma na tabbata ko fatalwar ba zai iya yi ba. Kaina yayi mugun sarawa,na dawo garas da sauri na fito waje sai kuma na ci karo da mai gadin wurin.“Wace ce ke?” ya jefo min tambaya,murya na ɗan rawa na ce “dama... Dama!” Sai ya saki murmushi ya ce “yi tafiyar ki” ban san dalilin shi na yin haka ba amma sosai na ji,domin muddin maganar ta yi nisa ya tara min mutane dole a ɗora min Ayar tambayar mi ya kawo ni gidan gawa a wannan tsohon daren. Ko da na koma ɗaki sai da na yi tunani bisanin bacci ɓarawo ya ɗauke ni. Washegari bayan duk mun kimtsa na ga A'isha sai murna take,ban yi ƙasa da gwiwa ba na tambaye ta “wai farin cikin na mine?” “Mansur zai zo ɗaukata,kin ga daga nan sai mu aje ki gida” ta ban amsa. “Au haba? Fatimah ba ta zo da babur ba?” “Ya samu matsala a jiya hanyar mu ta fiddo anko sai ta barsa wurin mai gyara” Mu na tsaka da hira aka kirata,cike da murmushi ta ɗauka bisanin ta aje wayar ta ce “har ma ya iso mu je” Sai da muka fito ne muka haɗe da Fatimah wacce ke zaune ta na shan love.Bakin ƙofar asibitin muka fita ,idona ya sauka kan wata ƙatuwar mota baƙa wuluk mai taya a baya. A'isha ta buɗe mana gidan baya muka shiga ni da Fatimah yayin da ita kuma ta shiga gidan gaba. “Baby ga ƙawayena da nake baka labari ka rage masu hanya” cewar A'isha . “A gaishe ku fatan duk ku na lafiya?” ya faɗa cikin muryarsa irin ta siraran maza ,duk muka amsa da lafiya lau. Ya dubi A'isha ya ce “ya maganar zuwa gidan abinci kenan?” “Mu je mana ai su ma za su ji daɗi,ko ya kuka ce ƙawayena?” Fatimah kawai ta amsa mata,ni kuwa na lula duniyar tunanin ta yaya ya samu kuɗi har haka cikin ƙanƙanen lokaci in dai yadda A'isha ta bamu labari ne Lagos ne ya je to tabbas akwai lauje cikin naɗi. Ina cikin wannan tunanin har muka isa , restaurant ce ta sai wane da wane don ni ban ma san da zamanta ba. Yadda aka tarbe mu kawai ya isa mu gane Mansur sananne ne a wurin. Shi ya zaɓi abin da za a kawo ma A'ishah yayin da ya nemi mu zaɓa da kanmu,amma sai A'ishar ta nuna masa ko wurin aiki cikin plate ɗaya muke cin abinci don haka nan ɗin ma ba za a ware mu ba. Shiru yayi ya na ɗan tunani,bisanin ya bai wa serveur ɗin umarni kan yayi yadda ta ce.Lafiyayen abinci ne,haka muka fara ci hankali kwance ba tare da wani tunani ba shi kuwa Mansur duk ya zama wani iri. Tamkar wacce aka sa ƙugiya ana ƙoƙarin zaƙulo hanjin cikinta haka na fara ji cikina na min ciwo,da sauri na fidda hannuna na ce na ƙoshi. Na tashi tare da tambayar masu kula da wurin ina ne toilet,aka nuna min na shiga.Amai na ta kwarara wa kamar raina zai fita,tsabar azaba har wata zufa ke tsatsafo min ina buɗe ƙofar toilet na yi kiciɓis da saurayin A'ishah.... [31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ Page 5 Na yi tunanin ko banɗakin zai shiga hakan yasa na ɗan yi saurin ja baya na basa wuri.Amma da mamakina sai na ga yayi tsaye ƙiƙam hakan yasa na ɗago na dube shi. Kamar mai son tantance wani abu haka yake kallona bisanin ya ce min “fatan dai lafiya?” “Alhamdullah!” na amsa masa a takaice “okay!” ya faɗa tare da koma wa baya yayi tafiyar shi.Na bi shi da kallon mamaki bisanin na take masa baya,ina zuwa sai na tarar ya zauna kujerata wacce na tashi kawai sai na yi tsaye. “Ki zauna mana” ya faɗa cike da kulawa,ban sani ba ko bai lura ba ne ya zauna a nan ɗin oho amma dai haka kawai na ji ban ra'ayin zama inda ya tashi . “Ke ma ki zauna mana ga kujera nan,ki yi tsaye kamar wata soja?”cewar A'ishah,ganin haka yasa na zagaya zan zauna kan kujerarsa ba don na so ba don haka kawai nake jin akwai makircin da ya shirya,cikin ikon Allah wayata ta ɗau ringing,ina duba wa sai na ga sunan Momah . Ina ɗaga wa ta ce “a ina kika tsaya har yanzu ba ki zo gida ba?” “Momah gani nan zuwa yanzun nan” na faɗa cikin rawar murya. “Ki na ina na ce?” “Tare da su A'isha Momah ” na faɗa tare da mayar da wayar a hand free ta yadda za su ji abin da Momar za ta ce sai kuma na yi masu alama da su yi magana,sai dai kafin su kai ga yi Momah ta ce “ki dai yi sauri ki dawo gida sam jikina na bani babu hairan a ind....” ban bari ta kai Aya ba na kashe kiran ina muzurai “zan tafi sai gobe in mun haɗe”shi ne abin da na iya furta wa bisanin na yi tafiyata ba tare da na jira cewar su ba. Bayan na fito daga restaurant ɗin sai na yi tsaye turus,don rasa ta ina zan bi na yi.Tamkar an sauya hanyar, lokacin da muna cikin mota lafiyayyar kwalta ce saɓanin yanzu da na tsinci kaina cikin jeji. Wurin babu gida ko ɗaya sai ciyayi,da na waiga ma hatta restaurant ɗin babu ta ɓace ma ganina.A nan take na fara jin tsoro duk da ni ɗin ba ma'abuciyarsa ba ce,tafiya na fara ba tare da na san inda nake jefa ƙafata ba har na isa wurin da hanya ta tsage ta rabu biyu.Wata irin ƙishirwa nake ji a cikin mintin da bai gaza goma ba,maƙoshina ya bushe ƙamas. Idona suka fara ɗaukar caji,na lumshe su a hankali kuma bakina ya fara fitar da sautin wani Yare.Ban buɗe idona ba sai da na ji ƙarar motoci da zantukan mutane. A bakin titi na tsinci kaina, Allah ya taimake ni na hangi wani gu ana sayar da ruwan leda na tsallaka na sayi leda huɗu a nan tsaye na shanye su.Na ja ajiyar zuciya kamar wacce aka dawo ma da ruhi haka na ji,daga nan na tari taxi sai gida. A can restaurant kuwa sosai hankalin Mansur ya tashi,muryar Momah tamkar busar sarewa haka ta ratsa dodon kunnen shi.Ya so ya tsayar da Ayodele saboda hatsarin da ke da wurin,amma da ya tuna zuciyarsa ba ta aminta da lamarinta ba sai ya ƙyaleta tare da yaƙinin sai dai a yi labarin wata amma ba dai ita ba. Bayan sun gama cin abinci ya ɗauki su a mota,sai da ya fara ajiye Fatimah sannan ya kai A'ishah. “Wai wace ce ita? Wato abinci mai magani ba zai taɓa zama a cikinta ba shi yasa ta amayar da shi.Na tsane ki! Ita kuma uwarta ta wace ce? Ya aka yi har ta san na shirya plan akan ɗiyarta?” ya jero ma kansa tambayoyin ya na mai bugun sitiyarin mota a haka har ya isa tankaɗeɗen gidansa wanda ya ji komai na more rayuwa.Sai da yayi wanka ya sha madara mai sanyi sannan ya kira A'isha suka yi ta hirar soyayya a ƙarshe ya tambaye ta “ya labarin ƙawar ki?” “Wace daga ciki?” “Wannan mai siffar Inyamurai” ya bata amsa,ta yi dariya ta ce “don dai ta na da jar fata ne sosai amma ai ba ta kama da Inyamure ” “Fatan ta je gida lafiya?” “Wallahi ba mu yi waya ba” “To ki kira ta mana,sam ban yi kirki ba da ban bata ko da kuɗin taxi ba ne” “Jira na kirata to” cewar A'isha ta na mai kashe kiran,Mansur ya lumshe ido ya na jin zuciyarsa na ɗan dokawa burinsa guda A'isha ta kira ta ce masa ta mutu. AYODELE Ina isa gida Momah ta wani jawo ni a jikinta ta rungume bisanin ta fara duduba ni kamar wacce ke neman ko na samu wata illa ne. “Daga yau kar na sake jin kin tafi yawo kin ji ko? ” “To Momah ” na amsa. “Ayodele ke ɗin ta daban ce,dole ki dinga taka tsantsan duk da ina da yaƙinin ababen bauta ba su taɓa bari a cutar da ke ba,domin su na tare da ke a ko ina amma ki dinga kulawa ba ko ina ba ne ake zuwa” Momah ta sake faɗa ta na mai kallona cikin ido.Kai kawai na jinjina mata bisanin na wuce ɗaki,kaya na cire na yi ɗaurin ƙirji na je na yi wanka . Ina tsaka da cin dambun shinkafa da Moma ta girka kiran A'ishah ya shigo,gabana sai da ya faɗi a take duk abin da ya faru da ni ya dawo kaina,hakan yasa har kiran ya katse ban ɗauka ba . Lokacin da na biyu ya shigo kuma a daidai nan maƙociyarmu Asabe ta shigo ta na rangaɗa sallama. Na amsa mu na gaisa wa,Momah ma ta fito .Godiya ta zo ta na ta faɗa mana yadda lamarin ya kasance da Zeinab nan muka yi ta hira kan Mayu da illolinsu.Sai bayan ta fita ne na duba wayata ,har zan maida kira kuma sai na fasa na tsunduma zancen zuci ‘tabbas da walakin goro cikin miya! In babu rame mi ya kawo zancen shi? Mine ne na biyana har toilet? Babu shakka akwai abin da ya saka a abincinmu,to shi kuma restaurant ɗin da ya zama kamar ɓatan wata? Hummm! Zan nutsu,na ankare komai sai na gano gaskiyar lamarin’ Abincin ma sai ya fita raina,tashi na yi na fiddo fararen rigunan da nake saka wa na likitanci na wanke su tasss bisanin na kwanta ina yin bacci don jiya mun sha aiki sosai. Tamkar a mafarki na ga wasu mutane masu fararen kaya sun zagaye ni,idona sun min nauyin da ba zan iya ware su duka ba amma tabbas ina iya ganin abin da ke gabana.Kaina na ji an fara shafa wa yayin da sauran kuma ke yin hira cikin wani Yare wanda in ba zan manta ba shi ne na taɓa ji Momah ta yi.Cikin wannan yanayi na lula duniyar mafarki,yau ma kamar kullum sanye yake cikin kayan ƴaƴan sarakuna ya saka kayan yaƙi,daidai ƙugunsa kubai ne mai ɗauke da takobinsa.Gefensa kuma masu tsaron lafiyarsa ne a tsaye cikin shirin yaƙi akan duk wanda ya kawo masu farmaki.Murmushi yake sakar min ya na kallona daga nesa, cikin izzar da ban san yaushe na same ta ba na fara takawa izuwa inda yake muna facing juna.Da sauri na lumshe ido sa'ilin da ya tsaka ɗan yatsansa manuni ya dangwala min jininsa a goshi a nan take wani sanyi ya luluɓe ni yayin da kuma nake jin shigar wasu lamurran da ba zan iya fassara su ba su na ratsa ɓargo da tsokar jikina. “Ayodele? Ayo....” a kasalance na buɗe idona na zube su kan Momah wacce ke faman jijigata da kiran sunana. Ta sakiya wata nauyayyar ajiyar zuciya bisanin ta ce “daga yau kar na sake ganin kin yi bacci a daidai lokacin da tartatsin rana ke tsakiya ban so” Dakyar na iya buɗa baki na ce “don me?” “Lokacin babu wata albarka a cikinsa ,bacci ya haramta ga al'ummar Victoria Falls ” Da mugun sauri na ce “su waye kuma al'ummar Victoria Falls ? A wacce ƙasa ce? Mine ne haɗi na da su?” Da mamakina sai na ga Momah ta rikice,abin da na lura ma kamar suɓutar baki ce ta yi.“Ki na ji Ayodele mu bar wannan maganar,ke dai kawai ki kiyaye abin da na ce.Am...na ce ... Ki taso na koyar da ke saƙar hannu” duk a rikice take,ni kuwa na zuba mata ido.Lokacin baya babu yadda ban yi da ita kan takoya min saƙar hannu ba ta ƙiya,amma yau sai gashi yau take son koyar da ni. Fuskata na wanke,na gyara zama ta fara nuna min yadda ake fara aza zaren farko na Foundation ɗin sannan a fara zarga wa gabanin ta miƙo min ƙarafan saƙar. Abu guda ya ban mamaki yadda na iya tafiya da takun saƙar kamar wacce tun can farko na taɓa koyon ta ,Momah na daga gefe ta ƙure ni da ido .Ko shakka babu ta zurfa sosai cikin tunani duba da yadda na yi mata magana sam ba ta ji ba.Ganin haka yasa na je na fara cika bokiti da ruwa,“oh! Har kin gaji?” na tsinkayo muryarta, murmushi kawai na sakar mata bisanin na ɗauki bokitin ruwan. Ina kai soso fuskata na ji wani irin uban raɗaɗi tamkar na zuba barkono ,da sauri na wanke na fito direct ɗaki na shiga na ɗauki madubi.Ɗigon ja na gani a goshina mai ɗauke da wani ƙaramin tauraro.Shiru na yi ina daɗa kallonsa,“Momah???” na ƙwala kiranta ,ta na shigo wa na ce, “Dubi wannan abun mine ne? Zafi yake min” Cike da kula wa ta ce min “ki jira har ranar da kika cika shekaru ashirin da biyu duk zan yi miki bayani” Na turo baki gaba na ce “ni dai ki faɗa min yanzu” “Ke ban fa son sakarci ,wai haihuwata ma kika yi da za ki tsare ni da tambayoyi ? To ban sani ba” ta na gama faɗa ta shige ƙurya ɗaki. Yadda na matsa wa kaina sanin mine ne har Allah yasa na tuna da mafarkin da na yi,wato na masoyin ɓoye.Har ban san lokacin da na saki murmushi ba,cike da nishaɗi na shirya cikin riga da wando na fita ƙofar gida. FATIMAH Tun lokacin da ta ci abincin da Mansur ya saya masu a restaurant take jin wani mugun sauyi a jikinta.Tamkar wacce ba da lafiya haka ta samu wuri ta kwanta,wani irin tsoro da shakkar saurayin ƙawarta take ji ba tare da ta san dalili ba.Ummarta har tambayarta ta yi abin da ke damunta amma ta ce babu komai.Ta rufe kanta cikin ɗaki kawai ,domin wani irin son kaɗaici ne ya zo mata.Wayarta ta ɗauka ta tura ma Nasir saurayin ta text ,duk da ba ta son shi haka ta ji ra'ayin kula shi.Da wannan ta ɗan rage faɗuwar gaban da take ji,har ta samu ta ɗan saki jiki. A can ɓangaren A'ishah kuwa haka ta kira Mansur ta shaida masa ta yi ta kiran Ayodele amma ba ta ɗauka ba.Har ƙasan ransa ya ji mugun daɗi don dama ya na tabbacin fatalen da ke kan hanya kawai sun isa su kasheta da tsoro. Washegari A asibiti duk muka haɗu,ko kaɗan ban yi ma A'ishah maganar kiranta da ban ɗauka ba hasali ma ban so wata doguwar hira ta haɗa mu. Ina ƙoƙarin saka wa wata mata tiyon fitsari A'ishah ta matso kusa da ni,ta ce “jiya Mansur na tambayar ki” sai na yi shiru kamar ban ji ta ba,ta sake maimaita min sai na ce “ki jira har mu fita mana,ki duba sauran patients ko akwai wanda ba a yi masa aiki ba ” na yi tunanin na rabu da ita kenan amma mu na fito wa ta sake tara ta da zancen “jiya sai da ya tambaye ni ,sam bai ji daɗi da bai baki kuɗin taxi ba” Na ce “ba komai ana tare,ki tuna min don Allah zan baki kuɗin anko sai ki sayo min” “Ok to babu matsala,amma Mansur ya ce min abokansa sun shirya party kin ga ya zama dole a sake fitar da wata ankon ” “ A'ishah yanzu fa babu kuɗi ba lallai kowa ya iya sayen har anko biyu ba” “Zan yi masa magana to,ƙila su abokan su saya maku” “Hum!” kawai na yi,bisanin na ce “wai ita Fatimah ba za ta zo ta kama aiki ba ne?” “Kanta ke ciwo ta na can baya wurin ƙofar emergency ” Da sauri na kewaya ta bayan na sameta a kwance kamar ba likita ba.“Fatimah?” na kira sunanta,ta buɗe ido dakyar ta dube ni ai ban san lokacin da na yi zaune ba na ɗauko kanta na ɗora a cinyata. “Mine ne taƙamaimai abin da ke damun ki?” Murya na ɗan sarƙe wa ta ce “ A'ishah ce sai hirar mijin da za ta aura take yi min,ni kuma wallahi mugun tsoronsa nake ji.Ban so ko kaɗan ana kiran sunansa” shiru na yi na ɗan wani lokaci bisanin na ce “yaushe kika fara jin tsoron nasa?” “Jiya” “Bayan kun dawo daga restaurant ko kuma kafin mu je?” “Bayan mun dawo” ta ban amsa ta na wani irin tari,na lumshe ido ‘ tabbas zargina ya zama gaskiya.Saurayin A'ishah ba mutumen kirki ba ne,to amma wace iri ce ɓoyayyar fuskarsa? Ban sani ba!’ na faɗa a zuci tare kuma da tunanin mafita. Can dubara ta faɗo min na ce “Fatimah a Addinin ku ba a sanar da ku yadda ake karye asiri ba?” “Mi ya kawo zancen Addini kuma?” cewar Fatimah don na santa sarai,ba tun yau take guje duk hirar da za ta kawo banbancin Addinai ba. “Ke dai ki ban amsa” na sake faɗa,ta ce “eh an sanar da mu mana,gaba ɗaya Alkur'ani waraka ce akan dukkan ko wace matsala” Ta na gama faɗa min na ce “ok jira ni” sai na sauke kanta kamar yadda na tarar da shi tun farko bisanin na koma can ciki.Direct office ɗin Dr Haleema na nufa,mace ce mai matsayi babba sannan ma'abociyar Addini ga ta kuma da sauƙin kai ba ta hantarar na ƙasa da ita. A zaune na tarar da ita ta na duba wasu takardu ,da murmushi ta dube ni ta na mai cewa “Ayodele dama ke ce ke buga ƙofa? To zauna” Na zauna tare da gaisheta bayan ta amsa na ce “Dr don Allah a Musulunce wane abu ne ina nufin addu'a ko kuma magani wanda yake saurin kare asirin da mutum ya ci” Cike da kulawa ta ce “sanamaki! Ganye ne mai matuƙar amfani wurin kare tasirin asirin da mutum ya ci ,in an tafasa shi sai a yi addu'a cikinsa a sha” “A ina zan same shi don Allah?” “Wurin masu sayar da ganye ko kuma Islamique center,mike damun ki Ayodele?” “Babu komai Dr na gode,jira ina dawo wa” Ina fito wa daga office ɗinta na je na shiga ɗakinmu inda na aje jakkata,kuɗi na ɗauko sannan na fita bakin hanya.Na samu mai taxi na yi masa bayanin inda zai kai ni,wata cibiyar sayar da maganin musulunci ya kai ni.A can na sayo sanamiki mai kantin ya haɗo min da zuma,sannan na dawo asibiti. Tun daga nesa nake hangen Dr Jaleel ya na masifa,ina zuwa ya ce “daga ina kike? Wa ya baki izinin fita?” “Ka yi haƙuri matsala ce ta ujila ” na furta ina mai sunne kai domin yin ladabi. “Su majinyatan da kika bari fa? In wata matsala ta faru ki sani a bakin aikin ki” nan ya shiga yin min masifa kamar wata ƴarsa kafin yayi gaba. Office ɗin Dr Haleema na sake komawa na nuna mata ,“Ayodele ki faɗa min abin da ke faruwa mana sannan ba ko wane lokaci ba fa ake shansa” “Dr Fatimah ce babu lafiya,kuma na tabbata sihiri ne ke ɗawainiya da ita ki taimaka min ki yi min addu'o'in ciki na bata ta sha don ta galabaita sosai” shiru ta yi,bisanin kuma ta ɗauko moɗar ƙarfe wacce take dafa Lipton a ciki, da ita ta yi amfani wurin tafasa Sanamakin bayan nan ta zuba zuma ta shiga yin karatu ciki.Na yi mata godiya na karɓa,inda na bar Fatimah nan na same ta.Dakyar ta iya tashi zaune ta yi Bismillah ta sha,a nan take zufa ta karye mata.Sai ta fara sauke ajiyar zuciya bisanin ta ce “Ayodele cikina na murɗawa toilet zan shiga ” da sauri ta miƙe,na take mata baya har muka isa banɗakin da aka tanada don likitoci. A wannan wunin tun ina ƙirga adadin da Fatimah ta kewaya har lissafi ya ɓace min, zawayi kawai take mai ɗan uban wari don ko ni da ke tsaye bakin toilet ɗin ina jin warinsa.A ƙarshe dai har ni sai da na shiga toilet ɗin don ta galabaita sosai,idonta tuni sun faɗa ta yi zuru.Ganin an ɗauki sama da minti ashirin ba ta samu wata murɗawar cikin ba,na taimaka mata ta yi wanka sannan mu ka fito.A ɗakinmu ta kwanta,sai a lokacin A'ishah ta san da ciwon yayi tsanani.Ƙarin ruwa na saka mata,bayan ta sha lemu exotic baiwar Allah sai bacci. A'isha ta tsaya tare da ita ni kuma na fita na hau aiki don kusan ban yi komai ba.Sai ƙarfe tara na dare na nufi ɗakinmu,duk bacci suke.Na taɓa wuyan Fatimah na ji babu zazzaɓi ,na je na haye gado sai bacci. “Yaanhun! Uhun ! Uhun!” shashekar kuka ta tashe ni daga bacci,na lalubo wayata na duba.Ƙarfe biyu ta gota,na ja tsuki tare da fita na nufi MUTUWARE don tuni ruhina ya lamunta da lamarin da ke faruwa da ni. Ɓangaren mata na shiga inda ake aje gawa,kwaɗon kawai na taɓa ya buɗe kansa na ja ƙofar na shiga sanyi AC ya ratsa ni sosai bisanin na yi tozali da wata sabuwar gawa don ko wanka ba yi mata ba.Mu na haɗa ido da ita ta bar kukan,a gajiye nake hakan yasa nake jin haushin tashe ni daga baccin da ta yi. “Sai ki tashi ki faɗa min abin da yasa kika jawo ni izuwa nan” na faɗa ina waige-waige don neman wurin da zan zauna,sai dai ban farga ba na ji wani hannu ya jawo ni da mugun ƙarfi na yi baya tare da faɗa wa cikin akwatin mutuwa..... My book is only 500 duk mai son biyan kuɗin karatunta za ta iya tuntuɓata kai tsaye ta WhatsApp +22795045822 sai na bata account ɗin da za ta saka kuɗin. [31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ *Promo:* mai ra'ayi zai iya biyan 400 kafin na gama free page a maimakon 500,wacce ta shirya biyan kuɗin karatunta za ta iya min magana kai tsaye ta WhatsApp +22795045822 sai na bata account ɗin da za ta tura na gode! Page 6 Kiciniyar fita daga cikin akwatin gawar na fara sai dai ga mamakina wata gawar na gani a tsaye kan ƙafafunta ta na ƙoƙarin danna ni ciki.Da dukkan alamu akwatinta ne,cikin wata irin murya ta maso duniya take cewa “ki zauna madadina don Allah na ga ke lamarin duniya bai sha maki kai ba,ban shirya zuwa can mazaunar fatale da ruhika ba” Idona na ware sosai kan matar, datijuwa ce a ƙalla ta kai shekara hamsin da ɗoriya fara ce tasss sai tsagen fuskarta na kurmawanci da ya fito raɗo-raɗo. Tabon goshina ne na fara jin ya na motsi,kamar almara sai gani na fito daga cikin akwatin na tsaya kan ƙafafuna. Gawa ta fashe da kuka,cikin tsawa na ce “je ki koma makwancin ki,wato lokacin da malamai ke yi muku wa'azi kar ku biye ma ruɗin duniya ku na yawon dare amma kuka yi kunnen uwar shegu da su kuke fita cikin dare farautar bayin Allah.Yanzu kuma da zanzaro ya tonon gidan Rina gari ya kwaɓe miki za ki neman ki dawo duniyarmu?” Idonta na zubar da hawaye ta shiga akwati ta kwanta wani haske ya fita daga goshina ya daketa tsit kake ji har esprit ɗin nata ya bar motsi,na maido dubana ga ɗayar wacce ke shashekar kuka na zuba mata Mayun idona masu masifar kaifi na ce “ ke kuma ina jin ki” Cikin kuka ta fara yi min bayani “wannan da kike gani mahaifiyata ce,ta ja ni izuwa wani ƙauye ne don yin shagali ita da ƙawayenta a can suka nemi da ta bada jinina su sha da ta ƙiya ne hanyarmu ta dawowa mu ka yi hatsari.Kin ga ban mutu ba sun ɗaure ni da azargagi ne,shirinsu shi ne in an kai ni maƙabarta su je su haƙo ni su tsotsen jini” A ɗan takaitaccen bayaninta na fahimci mahaifiyarta ta na cikin wata ƙungiyar Mayu ce masu shan jini,sannan duk shekara su na gudanar da bikin ƙara danƙon zumunci inda a dole wata za ta bayar da kyautar jini daga cikin ahalinta,kamar ɗa,jika ko ƙane. Kallon tsaf na yi mata,sai yanzu na lura da goshinta da gefen bakinta duk a fashe suke alamun buguwa.Tunani na fara ta inda zan taimakonta,sai dai na kasa samun mafita don ban san fuskokin masu son kaita ƙasa ba. “Ki taimaka min kar ki bari a kai ni maƙabarta da raina ban mutu ba sun juyar da hankulan mutane ne kawai ake min kallon gawa ” muryarta ta katse min tunani. Na ja dogon numfashi bisanin na ce “ki na ji na,a halin yanzu banda mafita amma na yi miki alƙawari zan cece ki ko bayan an haƙa miki kabari ne an saka ki ci to zan zo gare ki” Fararen idonta ta zuba min uwanda sam ba su da ɗigon baƙin ciki,na jinjina mata kai alamar tabbatar wa kan ƙudirina.Ban sani ba ko ta yarda da ni ɗari bisa ɗari,amma a sannu na ga ruhinta da ke dabaibaye da wasu Kambu ya ɗan samu salama. Sai da na shafi fuskarta bisanin na fito,direct ɗakinmu na wuce sai na tarar da Fatimah a zaune. “Kin tashi? Ya jikin naki?” na tambayeta. “Da sauƙi alhamdullah! Na gode sosai Ayodele,haƙiƙa ke ƴar baiwa ce.Da ace musulma ce ke da tabbas ba ƙaramin gudumuwa za ki bayar ba” Na sakar mata murmushi na ce “duk Ubangiji muke bauta ! Banbanci kaɗan ne,sannan shi ke tsara komai iyakacinmu mu yi aiki da baiwar da ya bamu amma komai daga Ubangiji yake” “Zance na hikima! Anya kuwa ruhinki ba na Musulunci ba ne gangar jikin kaɗai ke ta Yahudawa?” Fatimah ta faɗa,dariya na yi na canza zancen “ai yanzu dai kin bar jin tsoron komai ko?” Ta ja tsuki tare da cewa “shi ɗin banza Allah na tsane shi ,amma yanzu ban ji shakkar shi .Wai daga ina kike ko an kawo sabbin patients ?” Na ja ajiyar zuciya domin tambayarta sai ta tuna min da danbarwar da na baro a can MUTUWARE.“Ki koma ki kwanta don kin galabaita sosai ,ni ma baccin nake ji akwai aikin da nake son yi cikin bacci” na faɗa tare da kwanta wa kan gado,Fatimah ta waro ido bisanin ta ce “kin san kuwa a jiya ne ko yaushe da kika yi bacci gidansu A'ishah wallahi sai da kika bani tsoro don ba zan ɓoye miki ba shi ne dalilin da yasa na sulala zuwa gida” Na lumshe ido ba tare da na bai wa abin da take faɗa muhimmanci ba,nan take bacci ya ɗauke.Duk a mafarki aka nuna min maƙabartar da za a rufe wannan baiwar Allah,da kuma duk abin da zai faru da yadda zan kuɓutar da ita. Washegari muka hau aikin safe bisanin mu sauka,tuni Fatimah ta yi tafiyarta A'ishah kuwa a gabana ta kira Mansur kan ya zo ya ɗauke ta.Na taɓe baki don na lura har wani rawar kai take wanda yawancin amare ko kuma wanda za su auri mai kuɗi suke yi. Kafin ya zo ne na samu tsure A'isha da ido na ce “bayan Mansur ya dawo daga Lagos halan kasuwanci ya fara?” shiru ta yi bisanin ta ce “wallahi ban sani ba,kin san in mutum ya je neman kuɗi da zarar ya dawo to fa hutu ne kawai yake,ina ga shi ma bai komi” “To in kuɗin suka ƙare fa? Ke dai ki tambaye shi ƙila ya na kasuwanci ya ɓoye miki ne” na faɗa cikin son jawo ra'ayinta,don zuciyata ta fara aminta kan na rusar maganar auren nan . “Wallahi ba zan iya ba,ƙwarjini yake yi min ba zan iya tambayarsa ba.Kin san kuwa yadda nake jin mugun tsoron Mansur? Wallahi yau da ya zo ɗaukata kasa kallon ƙwayar idonsa na yi” “Hum! Wai dama ki na sonsa ko kuwa yanzu ne da ya zama mai kuɗi kike ra'ayin shi?” “Sosai kuwa! Dama rashin kuɗi yasa ba a bari muka yi aure ba.Abbana ya ce sai na ida karatu duk don kar ran Mama ya ɓace kin ɗan Yayarta ne” Kai kawai na jinjina ina tunanin wani babban al'amari,bisanin na ce mata “okay ni zan tafi in ya zo ki gaishe shi” “Ki jira mana sai ya sauke ki gida” “A'a na gode!” A'ishah ta riƙe ni ta na cewa “ wallahi babu inda za ki je dole mu aje ki gida” Muna cikin wannan yanayi motar Mansur ta tsaya,fito wa yayi.Sanye yake da baƙaƙen suit idonsa manne da baƙin gilashi,cike da ƙasaita ya iso kusa da mu. A inda yake tsaye zan iya hango tsantsar mamaki kan fuskarsa,wanda tuni na fahimci na gani na a raye ne.“sannu angonmu” na faɗa cikin raha,sai ya ɗan daburce ya na mai cewa “oh! Na shagala da kallon amaryata ne shi yasa,fatan ki na lafiya?” “Garas nake!” na basa amsa ina mai kallon tsakiyar idonsa don tuni ya cire gilashin,ya kawar da kai ɓangaren A'ishah ya na mai cewa “amarya ba kya laifi! Mu je ko? ” ga mamakina kamar raƙumi da akala haka A'ishar ta bi bayansa ko kallona ba ta yi ballantana zancen yi min sallama ko kuwa ta yi maganar sauke ni a gida da ta ce. Na rumtse ido tsabar takaici,ganin Mansur ya ci taya ƙura ta tashi duk ta baɗe ni.A hankali na buɗe su tare da bin motar da idon har ta ɓace ma ganina,jiki a matuƙar sanyayye na je na tsaya bakin hanya.Tsabar yadda ruhina yayi baƙi har ban san lokacin da na tsayar da wata farar mota ba madadin taxi,sai da na ji muryarsa ya na cewa “hanya zan rage miki?” Cike da masifa na buɗa baki na ce “aka ce ma banda kuɗi ko na yi ma kama da irin ƴan iskan ƴan matan nan?” Ya waro ido ya ce “keee! To ce miki aka yi motata taxi ce?” Sai a lokacin na farga da mota ce,na yi baya ina cewa “ka yi haƙuri ” “Na ƙi ɗin dole ki shigo na kai gida” Zan kuma ƙara yaɓa masa magana sai na ga yayi min ƙwarjini don babban mutum ne mai cike da kamala zai kai shekara arba'in da biyar.Na haɗe yawu na ce “na gode” amma fafur ya ƙi tafiya ya nace a ƙarshe dai na yarda na shiga. Mu na tafe ya mayar da volume ɗinsa,ƙira'a ce ke tashi ana karatun Alkur'ani.Ban san mi ya shige ni ba,amma sauraren sautin ya saka na fara jin sanyi a raina .“Wace unguwa za mu je” “Unguwar ƴan tsofi” na basa amsa don haka ake kiran unguwarmu.Ya ci gaba da driving,ni kuwa sai sauke ajiyar zuciya nake ina jin nutsuwa na daɗa ratsa ni har mu ka isa layinmu.A ƙofar gida ya sauke ni,na masa godiya ina mai ficewa. A'ISHA Yanayin kallon da Mansur yayi mata ya saka duk wata gaɓa ta jikinta ta yi sanyi.Tamkar za ta shiɗe haka ta ji,ga wani tsoronsa da shakkarsa da ta ji sun ƙara dirar mata.Allah na gani sam ta manta da Ayodele na kusa da ita,hakan yasa ta bi bayan Mansur da take jin ko yanka kanta ya ce ta yi to babu shakka za ta yi tsabar biyayya. Su na shiga mota ya kamo tafin hannunta,cikin salon yaudara yake mata magana “na tsani arniyar can mi ma sunanta?” “Ayodele” ta furzo lafazin dakyar.Ya ci gaba da cewa “yawwa! Daga yau ina so ki nisanta kan ki da ita,kar na sake ganin ku na ƙawancen na yanke shi kowa yayi harakar gabansa ki na ji na ko?” A'isha ta jinjina kai ta ce “in sha Allah ko magana ban sake yi mata” “Yawwa my Ayush! Kar ki sake ce mata ko kanzil! Ki goge lambarta daga wayar ki kafin nan ki tabbatar kin yi blocking nata” “Yanzun nan kuwa Oga!” A'isha ta faɗa tare da fiddo waya ta aiwatar da duk abin da ya ce.Ya saki hannunta,ya na canza akalar motarsa zuwa restaurant ɗin jiya. A'isha na zaune Mansur ke cewa “gishiri bai kama kaza ba yadda nake so,ka san a jiya wasu sun ci da rabonta shi yasa na kawota yau ta yadda komai zai tafi daidai” Wanda zai kawo abincin ya ce “an gama ranka shi daɗe!” can ya tafi ya kawo,tsabar mugunta ta Mansur shi ya dinga bata abincin da Allah kawai ya san adadin tsafin da aka yi masa,ita kuwa sai ci take.Bayan ta gama ya kaita gida zuciyarsa fal farin ciki,“na tsane ki Ayodele! Daga yau dai na yi ma takalme tubkar hanci” ya faɗa a bayyane ya na wata irin dariya. FATIMAH Tunanin kar Mansur ya tarar da ita ya saka ta yi tafiyarta tun da wuri.Addu'a neman tsari take kar Allah ya sake haɗa ta da shi,duk da ta na jin cutar da ya bata ta ci duk ta zawayeta amma hakan bai hanata jin normal tsoro a kansa ba tun da shi ɗin mugu ne.Ta na zuwa gida ta samu tuni ƙanenta ya karɓo mata babur ɗinta daga wurin gyara,sosai ta ji daɗin haka don ta na tunanin ta kaucewa shiga motar mugun saurayin A'ishah. AYODELE Ina shiga gida na tarar da Momah zaune kan tabarma ga wani akwati a gabanta ,ta na gani na da sauri ta rufe shi ta shige ɗaki,na bi bayanta sai na ga ta tura shi ƙarƙashin gado. Ban damu ba don ko magana ban yi mata ba,kayan jikina kawai na canza na fito.Jikina na bani kan na je maƙabarta hakan yasa na fito na samu wata taxi na masa kwantace da inda zai kai ni.Kamar dai yadda na gani cikin mafarki tun daga hanyar da aka bi da ni har izuwa maƙabartar. Daga nesa na yi tsaye,mutane sai bisa suke ido kawai nake bazawa ko Allah yasa na ga kabarin wannan baiwar Allah. Wani ihu ya ja hankalina,da sauri na juya ɓangaren haguna,sai na ga ashe akwai wasu kaburbura ma ta nan.Idona ya sauka kan gawarta,mugayen tsofin nan kuwa jira suke a rufeta su far mata.Ban buɗe bakina na yi magana ba,amma tabbas na kira su izuwa gare ni.Duk da alamun tsoro a fuskarsu yayin da kuma suke ƴar kallon-kallon,ban basu isasshen lokaci ba na dirar masu ko kuma na ce esprit ɗina ya shiga yin faɗa da su har na ci nasara a kansu duk suka gudu. Daidai nan na dawo cikin hayyacina,wasu daga cikin mutanen da ke ƙoƙarin turbuɗeta suka ja baya su na kiran “wallahi da ranta” ina jin haka na yo baya na yi tafiyata. Lokacin da na iso gida na Momah na banɗaki ta na wanka,hakan yasa na yi saurin shiga ɗaki na jawo akwatin ina buɗe wa na yi arba da wani hoto da yasa kaina yayi bala'in sarawa ya na daɗa juyawa...... Iya page 10 zan yi a free,ki yi amfani da wannan damar ki biya 400 kafin na gama free page in kin shirya ki min magana +22795045822 [31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ *Masu maganar gari babu kuɗi na hauda farashin littafi daga 300 zuwa 500, na faɗa maku wannan ba gajere ne ba.Amma tun da kun ce 300 ɗin za ku biya mu je a haka amma ni ba zan yi dogon labari ba sai na mayar da shi gajere*🤷🏻‍♀️ Wacce ta shirya yin payment za ta iya tuntuɓata kai tsaye ta WhatsApp +22795045822 Page 7 A cikin hoton zan iya gane Momah duk da ƙarancin shekarunta a lokacin,hannunta riƙe da baby girl an yi wa gashinta wani tozo daga gaba,gefenta kuma wani gawurtacen namiji ne dattijo amma ka na ganinsa ka ga jarumi. Duk cikin hoton yanayin shigarsu ce ta fi ɗaukar min hankali,ba kaya ba ne irin wannan da muke saka wa ba.A'a nasu kamar fata ce aka sarrafa aka mayar da su kayan,su ma ɗin iya cinya ne a saman riga kuma wata rabaja ce kamar zaren kwakwa. Kaina banda sarawa babu abin da yake,daga bayana na ji taku da sauri na mayar da hoton cikin akwati ina ƙoƙarin mayar wa. “Ayodele mi kike a nan?” Da sauri na miƙe na ce “babu komai Momah ” kallon tuhuma ta fara yi min amma na share tare da fito wa tsakar gida,zuciyata fal fargaba ‘wannan shi ne mahaifina? Wace ƙasa ce wannan ke shiga kamar ta arna? Sai yaushe Momah za ta kai ni gare shi? Ina son mahaifina’ duk a zuci na yi maganar kafin na zauna na kishingiɗa ga katanga.Wasu hawaye masu mugun ɗumi ne suka shiga sintiri a kumatuna, “na fita zuwa kasuwa sai na dawo” na ji muryar Momah ,na buɗe ido ina kallonta sarai ta ga ina hawaye amma ba ta tambaye ni ba ta fice. Ko mi ta tuna oho,sai ga ta kuma ta dawo “tashi mu tafi tare ” na miƙe na ɗauko kallabina na saka takalmi,sai da na wanke fuska sannan na fito.Momah ta rufe ɗaki da gida mu ka wuce kasuwa,tun da mu ka shiga nake jin tsikar jikina na tashi. Ina nan tsaye na ga wata yarinya na jaye da wani tsoho irin masu Bara a kasuwa,sai cewa take “a bamu sadaka saboda Allah da Annabi ” kafe su na yi da ido sun tsaya gaban wata mace mai sayar da busasar zogale. Cike da azama na yi tako ɗaya zuwa biyu na damƙe hannunsa,cike da mamaki yake kallona idonsa da suke a rufe ƙarya ce ba makahon gaskiya ba ne. “Mine ne za ka yi? Kan mi za ka saka hannunka cikin kwagirinta na kuɗi?” na tambaye shi,duk sai ya rikice ya ce “ki yi min rai ƴata,doli ce ta saka nake wannan ɗabi'ar ” “Kake damfarar mutane ba! A yadda kake duk wanda ya ganka zai ji tausayin ka amma ka yi amfani da maganin rufa ido ka na cutar bayin Allah ” Hawaye na ga su na zuba a idonsa ya ce “saboda na ciyar da iyalina ne amma ba da son raina nake hakan ba,amma na yi miki alƙawari daga yau ban sake wa” Na sakar masa hannu,abu guda da na fahimta kaf uwanda ke kusanmu babu wanda ya gani ko ya ji tattaunawar mu.Dube-dube na fara can na hango Momah da ɗan saurina na ƙarasa gun ta. Mun yi gaba kaɗan wani yaro ya faɗi gabana,cike da tausayi na miƙar da shi ina mai tambayarsa “mi kake ma kuka?” da hannu ya yi min nuni ya na magana amma ba ta fita saboda yadda kukan ya ci ƙarfinsa,hannunsa na ja mu ka shiga tafiya direction ɗin da yake nuna wa har mu ka isa wurin wani mutum. Na buɗe baki zan ƙara tambayarsa kawai idona ya sauka kan ƴar ƙaramar baro mai ɗauke da doya. Cikin dake wa na dubi mai sayar da doyar na ce “mi ka yi masa yake kuka?”banza yayi da ni hakan ya ban haushi na yi kururuwa duk mutane hankalinsu ya dawo kanmu wasu tuni sun zo su na tambayar lafiya. “Faɗa masu abin da ya faru” na cewa yaron,cikin ikon Allah yayi bayani yadda kowa ya ji “mu na tafiya ne ni da twin ɗina sai wannan mutumen ya kira mu ya ce mu zo mu karɓi chocolat sai ni na ƙi zuwa Amra ta je ta karɓa shine ta zama doya” “Laaaaha'ilah! ” duk kusan mutanen suka faɗa,amma mai doya ƙiri-ƙiri ya ƙaryata yaron ya ce “ka ji zai ƙulla min sharrin duniya,tun yaushe nake sana'ar sayar da doya a nan an taɓa kama ni ne? To nuna min ƴar uwar taka wacce na mayar” Cike da yarinta yaron ya je ya nuna ɗaya da ke can ƙasa,shi kuma mai doyar ya ɗauki wuƙa ya yanka. Da hannu na shiga taɓi na ce “a gaishe ka sarkin macuta na duniya,wato masanya ka yi to yanka wannan mu gani” na faɗa tare da nuna doyar da idona ƴar ƙaramar yarinya ce ƴar shekara huɗu.Muƙut ya haɗiye wasu yawu,cikin tsawa na ce “ka yanka aka ce ko kuma na kira ma ƴan sanda” Ya ƙanƙance ido zai yi magana amma mutane ba su basa dama ba saboda hantarar shi da suka fara kan ya yanka ko kuma su kashe shi.Hannunsa na rawa yasa wuƙa zai yanka na ce “ba nan ba” sai dai tuni ya yi wulish ya yanka nan jini ya fara tsirta.Kawai sai ya fashe da kuka,wani ya kira ƴan sanda a nan cikin kasuwa ya mayar da ita mutum wurin da ya yanka kuma kusan idonta ne. Ɗan kwalina na keta na ɗaure mata gun,ƴan sanda suka cabke shi kafin ƴan sanda su tafi da su suma don doli sai an kira iyayensu. Neman duniya na yi wa Momah amma ban ganta ba ,a doli na dawo gida. Bakin ƙofa na zauna ina zaman jiranta,kamar wacce aka mitsika na je na buɗe ramen da na saka Kambun Kunkuru.Har yanzu da ransa,sai dai ya ɗan gaji ya kuma ƙara girma.Na kuma mayar da shi a karo na biyu na rufe,ina nan zaune taxi ta tsaya .Momah ta fito,har muka sa kaya cikin gida ba ta ce min uffan wato fushi take da ni. “Mom...” “Yi min shiru! Wato ke ba za ki taɓa ganin abu ki yi shiru ba ko? Kaf kasuwa zancen ki ake ,ko kin yi tunanin ban san abin da kika yi ba? Na san yanzu zancen ya zo har nan unguwar shikenan sai a dinga kasa mu a faifai ana tallarmu duk irin gargaɗin da na yi miki amma kika yi fatali da shi kin kyauta!” ta na gama ta shige ɗaki. Duk jikina ne yayi sanyi,a fili na furta “in sha Allah daga yau ba zan sake shiga sabgar kowa ba,ko da kuwa ace ni ce za su cutar zan yi shiru su kashe ni ” Kamar yadda Momah ta yi hasashe kuwa hakan ce ta faru,zancen Ayodele ya cika unguwar tuni ma wasu sun fara zarginta da mayya.Dama ba su gama tantama akan al'amarin ceton Zeinab da ta yi ba.Yau kuma ta ceto yarinyar da aka mayar doya,tambayarsu ita ce inda a ce ba ta da ido uku ta ya aka yi har take fahimtar abubuwan da ke ɓoye wanda normal mutum bai gani? Wannan al'amari ya ƙara tunzura sauran Mayun da ke unguwar,tare da ɗaukar alwashin sai sun tozarta ta a bainar nasi. ★Washegari Yau juma'a ce,da baƙin cikin abin da A'isha ta min jiya na kwana duk tun a jiyar na yi ƙoƙarin kiranta na wanke ta tasss amma ban same ta ba. Ina isa asibiti na tarar da ita bakin ƙofa a tsaye jikin mota sai uban murmushi take zuba wa,da alamu sallamar Mansur ce za ta yi wanda shi kuma yake a zaune ya fiddo ƙafarsa ɗaya waje. Na danne zuciyata na ce masu “sannun ku da hira” in dai ganye bedi na magana to su ma sun tanka ni,tunani na yi ba su ji ba sai na yi tsaye na ce “duk soyayyar ce haka?” Mansur kawai ya dube ni shi ma bai yi magana ba ,ita kuwa A'isha ko waiwaye . Ganin irin cin kashin da suka yi min ya saka na shige cikin asibiti,na ja ƙyaci ina mai cewa “ai za ki zo ki tarar da ni ” “Ayodele lafiya kike magana ke ɗaya” cewar Fatimah,na ce “ A'ishah ce wai don ta na gaban saurayi ta yi banza da ni ” “Kai haba? Ni kuwa sai da mu ka gaisa har da shi Mansur ɗin” “Hum!” kawai na iya yi bisanin na je na aje jaka na saka farar rigar likitoci. Sai da mu ka yi nisa cikin aiki sannan A'ishah ta shigo,ina jin lokacin da Dr Jaleel ke yi mata faɗa kan ta zo lati sai haƙuri take basa. Cikin sigar wasa na zo daf da ita ina mai cewa “na zata har shi Dr Jaleel ɗin banza za ki yi da shi,ko da yake yanzu masoyin naki bai nan” wani kallo ta yi min ba tare da ta ce komai ba. Ni ma na kama gabana,ko lokacin cin abinci haka A'isha ta ware kanta duk yadda Fatimah ta so ta ja ra'ayinta amma ta ƙiya. Tun daga wannan rana mu ka fara takon saƙa da ita,tun mutane ba su gane ba har suka fahimta.Dr Haleema har zaunar da mu ta yi ta yi mana nasiha amma a banza ,haka zan yi ma A'ishah magana ita kuma ta basar.In muna zaune cikin jama'a sai ta bai wa kowa hannu in ta zo gare ni sai ta tsallake,tun ina yi mata uzuri har ni ma na aro rigar rashin mutumci na yaɓa ma kaina don dama can ni masifaffiya ce ta ajin farko. Yau saura kwana uku bikin ta,ina ji ta na bai wa Fatimah labari “Oga dai ya matsu a yi aurenmu,kin san a baya ya sha wuya sosai wurin soyayyata yanzu lokaci yayi da zai cika burinsa” Fatimah ta ce “ai ke ma ga shi sai zumuɗi kike,na matsu mu miƙa ki gidan Mansur ko hankalinmu ya kwanta” “Ai fa dai na matsu wallahi ” “Ayodele kin ji yaran zamani ko?” Fatimah ta sako sunana,ina jin lokacin da A'ishah ta ja tsuki. Ina cika takardu na ajiye na kalle ta na ce “da wa kike?” shiru ta yi ba ta ban amsa,na miƙe a hassale Fatimah ta sha gabana ta na cewa “don Allah ki yi haƙuri! Kin ga dai ba ta ce da ke take ba” “To da uban wa take?” “Ba ta dai ce ke ba, A'ishah don Allah tashi ki yi tafiyar ki tun da lokacin tashi yayi” cewar Fatimah,kamar jira take ta ɗauki jakarta ta fice. Sosai Fatimah ta yi ta danna zuciyata tare da roƙona kan na je bikinta na nuna mata ba komai ba ce duniya,bisanin ita ma ta tafi. Sai da na gama cika takardu sannan na fito. “Ƴan mata?” Da mamaki nake kallon shi na ce “kai ne?” “Eh wallahi na zo wurin abokina,ashe wannan asibitin kike aiki ?” “Eh! Wurin wa ka zo?” “Dr Jaleel mana,kin san abokina ne yanzu haka shi nake jira za mu wuce gidana” “Ok yayi” “Ba ki faɗa min sunan ki ba,tun ranar nan dai da na rage miki hanya na ji kin burge ni” karon farko da na taɓa jin haka daga namiji,sai abun ya ban dariya ban kai ga magana ba Dr Jaleel ya fito hakan yasa na yi tafiyata. Tun daga nesa nake tsinkayen yadda mutane suka yi dandazo a ƙofar gidanmu.Gabana tuni ya fara dakan uku-uku,ina iso wa wasu suka fara faɗin “Ga ta nan!” can kusan ƙyauren gidanmu na ga Momah a rakuɓe idonta sun yi ja jawur,kallon mutane kuwa tuni ya dawo kaina...... [31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ *Har yanzu ƙofa a buɗe take,za ki iya biyan 400 domin shiga vip group wacce ta shirya biyan kuɗin karatunta za ta iya tuntuɓata kai tsaye ta WhatsApp* +22795045822 Page 9 A lokacin da na juyo na fuskance shi,a sa'ilin ne kuma na tantance fuskarsa duk da ƙarancin haske da ke wurin.Fuskarsa baƙa ƙirin ce mai ɗauke da ƙwalayen idanuwa babu komai sai gurbinsu da ya bai wa jini damar gangaro wa kan lamutsatsun kumatunsa. Zuciyata ta fara rawa,hankalina ya tashi farashin tsorona ya ninku ainun ina ta ƙoƙarin cira ƙafata sai dai bai bani damar ba domin kuwa tamkar an dasa ni haka nake a tsaye ƙiƙam. “Mi bil'adama yake a duniyarmu?” ita ce tambayarsa. Gabana ya ƙara bada wani sautin rasss,tsabar firgici ban san lokacin da na furta “Ayodele yau kin ɗebo ruwan dafa kan ki” “Ayodele? Ayodele?” ya maimaita sunan har sau biyu cike da mamaki,bisanin ya ci gaba da cewa “ƴar sarki Lassey?” A daidai wannan gaɓa samaniya ta ɗauki wani irin rugugi da kuma wata irin walƙiya. Da sauri na lumshe ido jin saukar ruwan sama,wanda suka zame min tamkar wankewar tsoron da ya aure ni.Ji na nake kamar ina kan gajiyar izzata wacce nake juya gawa tare da yin magana da su ba tare da na ji tsoro ba. Na ji saukar hannunsa akan kafaɗa a karo na biyu,“barka da zuwa duniyar ababen bauta,haƙiƙa ƙarfin ruhinki da nacinsa ya jawo ki izuwa nan.Zo ki yi ziyara gun dangin kakannin ki” Na ware idona,a yanzu kam ban san mi ya shige ni ba sam ba na jin tsoronsa haka fuskarsa ma ba na ganin muninta. Tamkar raƙumi da akala ya yi min jagora izuwa tsakiyar maƙabartar wacce take maƙil da kaburbura. Wasu sanaye ya shiga ambato dukkanninsu babu ɗaya na musulmi,kamar almara sai na fara ganinsu su na fito wa daga cikin kabarinsu su na yin zaune. Gabatar min da su ya fara ɗai baya ɗayan har aka kawo kan wani tsoho ya nuna min shi da hannu ya ce “kin ga wannan shi ne kakan ki Sarki Octbar,shi ya haifi mahaifin ki Sarki Lassey,waccan kuma da kike gani Yayar baban ki ce sunanta Déborah bayan ta sauka daga mulki mahaifin ki ya hau.Je ki gare su na san za su baki saƙo ,bayan nan sai na kai ki gun ababen bauta” Gun wanda ya kira da Kakana na je na yi tsayi,hannuna ya kama bai yi magana ba sai jimƙe shi kawai da yayi.Tamkar yadda ake turan abu a xender haka na fara jin sabbin abubuwa na ratsa jijiyoyin hannuna su na shiga magudanar jinina wanda don dole na lumshe ido. Ya na sake min hannu ya shige ƙarƙashin ƙasa,“ungo wannan zoben ki saka shi,na san komai daren daɗewa za ki je Victoria Falls duk da mahaifiyar ki ba ta so.In kin je ki gaishe min da ƙanena ” Déborah ta faɗa ta na saka min wani tsobe a yatsana manuniya na hagun. “Mu je” na ji muryarsa, “André kar ka kaita ko ina ka mayar da ita duniya,a halin yanzu akwai tazara mai ƙarfi ita da karagar mulkinta.In lokaci yayi ababen bauta su za su neme ta da kansu,amma mi zai hana ka nuna mata ababen tarihin shahararrun matsafa da kuma yadda suke wanzar da tsafin?” Sai da ya dube ni da kyau bisanin ya jinjina kansa , Déborah ta ɓace ma ganina a kuma daidai wannan lokaci na tsinci kaina cikin wani hatsabibin daji.Na fara waige-waige,wani irin “wuhummm! Zummm!” nake jin ma'adanar sautina na zuƙo min ai kuwa na toshe kunne,ashe hakan shi ake kiran ainahin ga wofi wai harare cikin duhu don hakan da na yi bai canza zane ba. “Haƙuri za ki yi da sannu za ki saba”cewar André ,bisanin ya shiga nuna min wasu itatuwa wanda suka fi ɗaukar hankalina su ne wanda suke jere su uku an yi masu ado na penti masu nuni da kalolin tsafi da asiri (mai son ƙarin bayani ya nemi littafina na ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI) Mun yi yawo sosai sai bayanin abubuwa yake min,cikin haka ne na shagala sai ji na yi na yi baya.“Kar ki bi ta nan...” yayi saurin faɗa sai dai tuni na ɗora ƙafata ɗaya wacce nake jin kamar a garwashin wuta take.Tsabar azaba ban san lokacin da na fasa ihu ba,kaina ya juya daga nan ban sake sanin abin da ya faru ba. “Ayodele keee ?” muryar Momah ta daki kunnena,na ja ajiyar zuciya tare da buɗe idona dakyar da suka min nauyi. “Lafiya kika kwana a titi? Wato ƙofar gida shi ya fiye miki kan ki kwanta a ciki?” Momah ce ke faɗa rai ɓace. Kallon wurin da nake na yi,eh a dai ƙofar gidan ne nake zafin rana na haske ni.Dakyar na yunƙura na tashi tsaye,ƙafata ta dama ce na ji ta riƙe “washhh! Wayyooo Momah ” na faɗa hawaye na min shatata. Abun ka ga uwa tuni ta haɗiye ɓacin ran ta fara taimaka min,dakyar na shiga gida kuka wiwi nake rera wa ita kuma ta na tambayata abubuwan da na yi jiya.Sam ban iya tuna wa ba,to ina ma na ga nutsuwar da zan tuna ɗin. Jiƙe-jiƙen magani ta yi ta bani na yi wanka,babu laifi na ɗan ji dama musamman da ta saka min maganin massage abokini ta min tausa.Wunin ranar dai na dawo ƴar lelen Momah kamar can farko,duk fushin da take da ni ta janye. “Allah sa dai ba jan magana ki ka je ki ka sake yi ba! Na sha faɗa miki ba komai ne mutum yake magana ba,haka ba kullum ya zama dole sai ka yi taimako ba.Amma ba ki ji,kunnen ƙashi ne da ke ! Duba ta dalilin ki inda mu ka dawo,da ace kin zauna ɗam da duk hakan ba ta faru ba” Sama-sama nake jin furucinta don tuni na lula duniyar tunani,wanda ba na komai ba ne sai na mutumen nan mai suna André duk abubuwan da suka faru kuma suka dawo min daram a kwanya sai dai ban san ya aka yi na tsinci kaina ƙofar gida ba. Na ja a jiyar zuciya ‘ta yi yu kuma mafarki ne na yi’ na faɗa a zuci bisanin na lalubo wayata,na kunnata saƙonnin Fatimah da kiranta ne barkatai na yi ta cin karo da su. Kiranta na yi,har sai da ta yi ajiyar zuciya wacce nake kyautata zato ta murna ce. “Wallahi duk kin tashi hankalina,kin kashe waya na je gidan ku kuma kun tashi har wasu sun shiga” cewar Fatimah. “Yi haƙuri ƙawata tashin ne ya zo cikin wani yanayi,ya aiki kuma ku na ta zuwa?” “Ina ta dai zuwa! A'isha yau wajen kwana nawa rabonta da aiki,kin san kuwa Dr Jaleel ya karɓi lambar ki wurina” “Hum! Wasa dai kike,kuma sai kika basa?” “To ya zan yi?” ta faɗa cikin tausayi,tuni na fahimceta don na daɗe da sanin Fatimah na mugun son Dr Jaleel. “Oh! Na gane yanzu haka abokinsa ya tambaye shi,ban faɗa miki ba wani ya rage min hanya kwanaki har ya ce na burge shi wai” Fatimah ta saki ranta,ta ce “wai ne ma? Don Allah Ayodele ki yarda ki fara soyayya a yi mutum kamar jikar almutsutsai” Shiru na yi ,tunanina ya koma duniyar da na je jiya sai na ce mata kawai “Fatimah zan sake kiran ki” ƙittt! Na kashe kiran. So nake na tantance shin wai mafarki na yi ko kuwa gaske ne,ina ta tunanin hanyar da zan bi na gaskata cikin ɗaga murya na ce “Lassey!” Ji kake kwacaaaa Momah ta saki kwandon kwanoni da ta gama wanke wa,dama da gangan na yi don na ga réaction ɗinta. Da sauri kuma ta shiga kwashe su jikinta har rawa yake,na kuma furta “Lassey fa?” sai na yi tamkar waya nake,ina ankare da Momah a wannan karon ma sai da ta zabura.Na saki murmushi na ce “to Allah kyauta sai an jima” Duk motsin Momah a wannan ranar kan idona,ta yi wani irin sanyi liƙis abinci ma dai ban ga lokacin da ta ci shi ba.Sai na ji ta ban tausayi,kusa da ita na ƙarasa ina ɗingishi.Na kwanta tare da ɗora kaina kan cinyarta na ce “Momah gobe zan koma aiki” “Allah kai mu” shi ne abin da ta faɗa ta na cire hullar kaina,“sabon kitso za a yi min?” “Eh na gwara na rufa ma kan naki asiri je ɗauko mai da tsinke da kuma mashaci” Hakan kuwa aka yi, Momah na min kitso ina ji lokaci zuwa lokaci ta na ajiyar zuciya haɗi da “hum” can ta kasa haƙuri ta ce “Ayodele ɗazu ke da wa kuke wa?” “Fatimah ce” “Na yi tunanin musulma ce fa,sai kuma na ji ki na ambaton sunan mahaifinta irin na Kirista” Na gane sarai da Momah wayo take son yi min don ta ji gaskiyar lamarin,amma da yake ni ma hatsabibiyar kaina ce sai ce mata na yi “wane suna kuma?” “Wai ina A'isha ? Har an yi bikin?” Momah ta canza zance,na lumshe ido na ce “bacci nake ji” na yi hakan ne don ɓoye mata abin da ya faru tsakanina da A'isha don za mu iya shirya wa ko da yaushe ,amma in na sanar da Momah ta yi yu ta riƙe abun a rai. ★MANSUR Ya na fita daga gida ya wuce can gidan ogansu,bayan ya gaishe shi ne ya gayyace shi can tamtsetsen falonsa mai ɗauke da hatsabiben aljannu.Ka na ganin wurin za ka gane babu rahama,saboda komai na ciki baƙi ne wuluk hatta da capet da labulaye da kujeru. Bayan sun zauna sun nutsu ogan ya fara bayani “Mansur ƙarshen watan April za ka kawo sacrifice ɗinka,budurcin mata huɗu,sai zuciyar jinjirin yaro sabuwar haihuwa” Hankali tashe Mansur ya ce “oga a ina zan samu jinjiri? Su ƴan matan ba matsala ba ne saboda ina da gumbar susa,ga shi kuma watan Valentin Day ne ba za su wuya ba amma oga saboda Allah....” “Noooo! Bar kira min sunan shi cikin falo! Wa ya faɗa maka muna buƙatar rahama a nan da za ka kira abun bauta ?” Mansur ya kalli ogan nasu da kyau,ƙaton Arne ne mai yaƙi da Musulunci abin da ya fahimta bai son jin sunan Allah tsabar taɓe wa. “Sorry oga! Amma please a duba min a ina zan samu jinjiri?” “Wannan ba matsalata ba ce,sannan abu na gaba ba za ka yi wanka ba sai ka tara janaba sau talatin da tara” ogan ya faɗa cikin bagwariyar Hausar shi. Mansur ya waro ido,dama yau ɗin ya ƙi yin wanka da Sallah ne a bisa sharaɗin ogansu. “A dai duba oga! Yanzu haka ji na nake duk a takure da ban yi wanka ba” “To maganar kake so sai kuma ka je ka yi wankan ka ga abin da zai faru da kai! Tashi ka bani wuri” Da mugun sauri Mansur ya fito,a kan hanya sai tunani yake kan mafita cikin haka kiran Momynsa ya shigo “Allo Momy?” “Na ce sai yaushe za ka zo ka ɗauke ni ne tun jiya na haɗa kayana” ta faɗa daga can ɓangaren. “Gani nan zuwa Momy ” sai ya kashe kiran ya je can gidan mahaifansa. Bayan sun gaisa ta basa fura ya sha sannan ya ɗauki tulin kayanta ya saka bayan mota,wasu ma a gidan baya ya zuba su.Ta shiga gaba suka wuce gida,ya na parker mota A'ishah ta fito da ɗan gudunta irin na sabbin amaren nan amma sai ta tsaya cak ganin Mansur ya zagaya baya na fiddo kaya ,Momy kuwa hannunta riƙe da uwar jaka sai ka ce mai biki. Wani zungureren bido ta fiddo ta shiga yayafa ruwan da ke ciki a tsakar gida ta na yi ta na yin wasu surkullenta. Babu shiri A'isha ta koma ɗaki jikinta na rawa,babu sallama duk suka shigo.Rasa mi za ta ce ta yi kawai ta yi tsaye su na ƴar kallon-kallon,“laaa! A'isha ko ba ki gane ni ba ? Ni ce Mairo Yayar Tani uwarki kin wani yi tsaye kin tare hanya ko ba ki so na zo ba ni da gidan ɗana ” “Momy ai zuwan ne na ga kamar ba na lafiya ba har da kayan jiki sai ka ce wacce za ta dawo nan da zama?” ba ta rufe baki ba Mansur ya zube mata yatsunsa biyar tare da ɗora mata kwandon masifa. Momy ta yi murmushi ta ce “yaro man kaza! Wato A'isha duk wulaƙanci da ku ka yi mana ke da uban ki duk kin manta? Bai da kuɗin aure ƴata karatu za ta yi ba zan sayar da Akuya ba ta dawo gida ta na ci min darni ba” Momy ta kwaikwayi muryar Abban A'isha . Mansur ya ɗora da nasa furicin “daga rana irin ta yau doli ki yi duk abin da Momah ta saka ki saɓanin haka ki saka a ran ki kin ƙulla aure da ƙunci” ya na gama faɗa ya nufi ɓangaren da dama tun can na Momy ne,ita kuma ta take masa baya. A'isha ta faɗi gwaram ta yi zaman ƴan bori ta na jin wani matsanancin tashin hankali.... [31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ Ba kusan a mayar da labari gajere amma kuma ba kusan biya daidai hum! MUTUWARE book ɗin kuɗi ne 300 normal group,vip kuma 500 ba zan rage ko tamma ba ki zaɓi wanda kike so wacce ta san ba ta shirya ba don Allah kar ta min magana.Ki tuntuɓe Ni kai tsaye ta WhatsApp domin biyan kuɗin karatunki +22795045822 Page 8 Da sauri na nufi Momah ina mai tambayar ta “mi ya faru? Lafiya kike kuka?” ba ta kai ga bani amsa ba na ji an wani jawo ni ta baya ,dakyar na iya miƙe wa kan ƙafafuna na juyo ina fuskantar shi.Namiji ne dattijo wanda ya ba shekara saba'in baya ,shi ne ya jawo ni yayin da sauran tsofin da suka haɗa maza da mata suka yo gaba. “Yau dai asirin ki ya tonu,shegiyar yarinya ashe mayya ce ke shi ne kika fake da sunan ceto kike.Wancan Kambun maitar da kika rufe shi muke so ki tono kafin Sarkin Mayu ya ƙara so ” ya faɗa ya na mai yin nuni da inda na rufe Kambun Kunkuru. Banda haske babu abin da wurin yake ,wanda a bayyane yake kowa na ganinsa har da normal mutane.A daidai wannan lokaci ba zan iya yin wani dogon tunani ba ballantana na samo mafita ,duk ma ba wannan ba halin da Momah ke ciki shi ya fi ɗagan hankali. Tsofin unguwarmu sai zagi ne suke a gaban jama'a, miyagun kalamai wanda duk mai zuciya ba zai iya jura ba.Sosai na yi mamakin dalilin da yasa ban ji sarawar kai ba ,saɓanin sauran lokuta da nake harzuƙa na ɗauki ɓoyayyar fuskata. A na haka har Sarkin Mayu ya iso,sosai na yi mamaki ganin mutumen nan da muka taɓa haɗuwa cikin taxi.Bayani suka fara yi masa,shi kuma yayi kamar bai taɓa gani na ba tare da umarta ta “je ki haƙo abin da kika ɓoye” Sai a lokacin na juya na dubi Momah,jiki a sanyayye na duƙa na buɗe ramen tare da ciron Kambun Kunkuru.Haskensa ya ƙara yawaita kan lokacin da yake cikin ƙasa,Sarkin Mayu ya karɓe shi ya na cewa “kin ji kunya ƴar ƙanƙanuwar yarinya da ke amma kin zama muguwa mayya kawai” da mugun sauri na rumtse ido ina jin hawaye na min zuba. Mutane ne suka fara suratai akan sai mun tashi mun bar masu unguwa,zagi kam ya fi cika buhu babu kalar baƙar maganar da ba a faɗa wa Momah.Ita kuka ni kuka,Sarkin Mayu ya ƙara ɗaukar magana inda yake cewa “na baku nan da awa ɗaya kacal ku tashi ku bar nan ko kuma na sa a ƙone ku da ranku” Jama'a suka ɗau ihu,da mugun sauri Momah ta shiga gida na take mata baya.A ɗaki na tarar da ita ta na gangamar kaya,rasa abin da zan ce mata na yi kawai sai na faɗa jikinta ina kuka. “Kukan mi kike? Ina ce ke kika saya mana wulaƙancin da kuɗin ki,tun ranar da kika zo da abin nan sai da na ce ki mayar mai shi abinsa amma kika yi kunnen uwar shegu da ni” ta ida faɗa ta na mai ture ni na yi baya. Daga inda nake ina jiyo hargowar mutane sai juya suke mana cikin gida tare da zaginmu.Cikin ƙanƙanen lokaci Momah ta haɗa kayanmu,dakyar da siɗin goshi muka samu mu ka isa bakin hanya.Ɗaiɗaikun mutane ne kawai ke tausaya mana,ciki kuwa har da Asabe don a gidanta ma Momah ta kai ajiyar sauran kaya. A wannan wunin mu ka bazama neman haya sai dai kamar abun tsiya ba mu samu ba,sai a wata unguwa mai ƙarancin mutane kamar za a fita gari shi ma ɗaki ne ciki guda.A haka dai mu ka share mu ka zauna bayan Momah ta kwaso sauran kayanmu. ★ Komai na ta tafiya cikin tsari, musamman bikin da ya kasance tuwona maina ne.Amayar da angon duk ƴan uwa ne,sosai abun ya tafi cikin tsari. A'ishah sai rawar kai take,abokanta kuwa duk sun haɗu wurin kanmu . Fatimah kuwa sai ƙoƙarin kiran Ayodele take a waya saboda rabonta da ita wajen kwana biyu wayarta ma ba ta shiga,cikin wannan zullumi dai ta yi shagalin bikin. Ranar ɗaurin aure tamkar babu gobe haka aka yi abun hauka musamman ɓangaren Mansur da yake taƙama da Nera.Motocin ɗaukar amarya kaf ɗinsu babu tsohuwa sun jeru rasss sai wacce ranka ya yi ma za ka shiga.A haka aka miƙa A'isha tamfatsetsen gidan mai kama da aljannar duniya,duk yadda ta so Fatimah ta tsaya fafur ta ƙi don dama kan babur ɗinta ta je ko kaɗan ba ta saki jiki da abokan Mansur ba don ƴan magana kan ce sai hali ya zo ɗaya ake abota. Bayan kowa ya watse Mansur ya shigo tare da abokansa.Kallo ɗaya za ka yi wa gizner jikinsu ka ga Nera ce ke magana,suratansu suka fara ita dai A'ishah ta na rakuɓe sai da suka matsa mata ne ta ɗan ɗage mayafinta.Amanar abokinsu suka bata bisanin yayi masu rakiya ya dawo shi ɗaya. “Ki sauko mu ci abinci mana” ya faɗa ya na mai jawo hannunta,cike da mamaki A'isha ta bisa har suka baje kan capet.Ta sha ji daga abokaina abu na farko da ake yi in an kai amarya sallah ce domin nuna godiya ga Ubangiji,amma sai ta yi masa uzuri da tunanin ko yunwa yake ji shi yasa.Ba ta kai ƙarshen mamakinta ba sai bayan da suka cika tumbinansu Mansur ya fara aika mata saƙonnin soyayya har ya kai da ya kusanceta,ko Bismillah ba ta ji yayi ba ballantana wai addu'a. Washegari Tsabar gajiya da ta yi ya saka ta rasa sallar asubah,hasken rana ne ya daki fuskarta ya sa ta yunƙura ta tashi zaune ta na kallon window.Gefenta kuwa Mansur ne ke ta sharar baccinsa,ta kai hannu ta na jijiga shi “Ogana ka tashi ka kai ni toilet ka min wanka please ba zan iya tashi ba” a shagwaɓe take fitar da harufan har ta ci nasarar tayar da shi. Ya buɗe idonsa ya zuba mata su ,iya kallon da watsa mata kaɗai sai da gabanta ya faɗi. “Mine ne?” “Wanka za min ” “Can a gidanku wa ke yi miki?” Ras gaban A'isha ya faɗi jin furucinsa sun yi hannun riga da wanda ya sha faɗa mata satin aurensu. Dakyar ta ƙoƙarta ta je ta yi wanka ta zo ta gabatar da sallah.Ta na nan zauna har Mansur ya tashi daga bacci,direct wurin drower ya wuce ya fitar da kaya masu kyau ya saka. “Ka manta ba ka yi wanka ba fa ” ta faɗa ganin bilhaƙi yake shirin,“uban waye ya faɗa miki manta wa na yi?” Mansur ya faɗa a zafafe ya na kallonta. “Ka yi haƙuri ”shi ne kawai abin da ta iya furta wa. “Ki tashi ki ɗora min breakfast!” ya faɗa ya na mai fesa turare. “To” ta amsa tare da tashi.Tsabar takaici sai da ta zubar da hawaye ,amma a haka ta haɗa masa frite da gasashen kifi don ta ga kusan akwai komai. Kan table ɗin cin abinci ta ajiye bisanin ta wuce bedroom,waya ta tarar da shi ya na yi sai magana yake cikin ladabi.Da ace mahaifinsa na da rai da to babu shakka za ta ce da shi ne yake waya. Bayan ya gama ne ya zo ya rungume ta tare da cewa “har kin gama?” kai ta jinjina masa,“ok mu je” Falo suka koma a tare suka ci abincin, Mansur na yi mata hirar soyayya hakan ya kuma ƙulle mata kai. “Zan tafi wurin aiki,tun ɗazu shugaba ke jirana” ya faɗa tare da miƙe wa tsaye. “Aiki kuma? A cikin satin aurenmu?” “To sai aka yi mi? Kin ga ban so sakarci sai na dawo” ya na gama faɗa ya fice. A'isha ta zube kan salon ta na jin wata irin damuwa na dabaibaye ta,tun kafin aje ko ina auren Mansur ya fice mata a rai.“Babu wankan janaba ballantana a yi maganar sallah anya kuwa na auru? Mine ne ma ya hana shi ko fuska da baki ya wanke?” ta furta hawayen takaici na zubo mata bisanin ta ɓingire bacci. Hayaniyar ƙawayenta ce ta tashe ta,sosai ta yi murnar zuwan su.Sauran kazar jiya ta ɗauko masu kafin a hau hira da girke-girke cike da nishaɗin ƙawarsu ta auri mai kuɗi kowacce ta sasaɓe zane ta ci abubuwa na kayan daɗi ta ƙoshi da za a tafi gida kuwa har da yin tsaraba. AYODELE Tun da muka dawo sabon gida Momah ke fushi da ni mai tsanani ,duk uban haƙuri da magiyar da na ta yi mata kanzil ba ta ce min ba.Hakan ya jefa raunatacen ruhina a cakwakiyar matsala,na bar cin abinci kan ƙa'ida,na kashe wayata aiki ma sam na bar zuwa.Amma hakan bai sa Momah ta tausaya min ba. Kamar kullum wuraren ƙarfe takwas na dare na fito ƙofar gida na yi zaune,unguwar tsit take ko tsuntsu babu. Wani mutum na ga ya bi ya wuce ta gaban ya nufi wani ɗan gangare,na bi bayansa da kallo kawai ina mamakinsa don yau kusan sau uku kenan da ina ganinsa. Zuciyata ce ta raya min na bi bayansa,kamar aikaka haka na miƙe har da haɗa wa da gudu na take masa baya.Mun yi tafiya mai ƴar nisa bisanin na tsaya,domin ya kai wurin da ke da tsananin duhu ba zan iya shiga ba. Idona ne ya sauka ga allon sanarwa mai ɗauke da sunan MAƘABARTA,gabana ya bada ras! ‘Ko shakka babu irin mutanen nan ne masu haƙo kabari don yi aikin asiri ko tsafi’ na faɗa a zuci ina mai ƙara ɗan yin gaba ina ɗigirgire ko Allah ya sa na hango wani abu.Daga bayana na ji an dafa kafaɗa,da mugun sauri na juyo muka haɗa ido a take hanjin cikina suka hautsana...... Ban jin daɗin jikina ina barar addu'ar ku🙏🏻 [31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️ GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️ Love and Horror story ```MRS SADAUKI💫✍🏻``` Dedicted to Ameera Adam FCWA ☀️ _________________________ To alhamdullah wannan ce page ɗin ƙarshe ta kyauta,don haka duk mai son ci gaba da karatu zai biya kuɗinsa na karatu 500 ta wannan account 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank kafin na saka shi group sai a turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 Last free page 10 A'isha na nan zaune cikin halin ƙaƙanikayi Momy ta fito Mansur na bayanta.Kan salon ta hakimce ta sune ta tare da cewa “ A'isha ruwan gidan ma ba za a bani ba sai na roƙa ko kuwa ban isa ba ne?” “Haba Momy ya za ki ce haka? Ai ko ban auren Mansur ke ɗin uwa ce gare ni domin ciki guda kuka fito ke da Mamana ” cewar A'isha ta na mai tashi da sauri har jikinta ke yin rawa ta nufi kitchen. Drinks da abinci ta haɗo mata,ta dire su a gaban Momy sai bayan ta zuba mata komai ne ta tashi ta shige bedroom.Matsanacin kuka ya kubce mata,ta faɗa kan gado ta rusa shi cincin ƙarfinta. Mansur ya shigo,“ A'isha?” ya faɗa cikin sanyin murya kamar ba shi ne ya ga ma yi mata tsawa ba. Ba ta daina kukan ba ballantana ta kula shi,ya isa gare ta ya na mai jawo ta jikinsa ya shiga aikin rarrashi amma ta ƙi yin shiru .Sai da Mansur ya kai ruwa rana sannan ya shawo kanta,ashe shi ma da walakin wai goro a miya.Buƙatarsa ce ta kawo shi,kuma ko da ya samu abin da yake so ya bar ta nan. Cike da baƙin ciki A'ishah ta isa toilet,abu ya tare mata goma da gomiya tara. Kamar wata zararriya ta shiga dukan ruwa ta na cewa “da me zan ji? Wace rayuwa na tsoma kaina ni A'isha? Wayyo Allahna!” sai ta ƙanƙame dukkan jikinta jin tamkar ana kallonta . Ƙoƙarin fita daga bawon wankan ta fara,sai dai tamkar wacce aka jone fatar jikinta da bawon haka ta ji ta liƙe gam.Cincin ƙarfinta ta buga wani uban ihu wanda ya karaɗe duka gidan,sai dai ko motsin wucewar ɓera ba ta ji ba ballantana Mansur ko Momy su kawo mata agaji. Dakyar ta ci nasarar fiddo ƙafafunta waje,sai ta ga su yin wani ja ƙau jawur babu kyawun gani kamar jan nama.Hankalin A'isha bai ida tashi ba sai lokacin da Allah ya bata iko ta tashi kan ƙafafuwanta.Kaf shap ɗinta ya zube kamar an zuba sukari a ruwa,jikinta ne ya ɗauki wani irin rawa ganin ƙugunta kamar muciya saɓanin da can farko da take turbakallah. Towel ta saka ta fito da mugun sauri,bayan Momy ta gani ta na mai fita daga ɗakinta ba tare da ta san mi ya kawo ta ba. Bakin ƙaton madubi ta tsaya ta na kallon kanta,sai kuma ta ganta normal ba ta san lokacin da ta saki ajiyar zuciya ba.“Ashe gizau ne ban canza ba” ta furta cikin murna bisanin ta shafa mai da turare,ta saka kaya sai kuma ta fito falo. Turus ta yi ta na kallon Momy na yayafa ruwa a duk wata kusurwa ɗaki,ba abin da ya fi bata mamaki irin sunanta da na Mansur da ta ji ta na ambato. “In kin gama gulmar sai ki je ki yi abin da za ki yi” cewar Mamy ba tare da ta juyo ba. ‘Ko ya aka yi ta san na fito?’ A'isha ta tambayi kanta bisanin ta wuce kitchen.Girki ta ɗora ,bisanin ta dawo falo ta ɗauki wayarta.Fatimah ta kira,cikin sa'a ta same ta tamkar rariya haka A'isha ta buɗe baki ta na ba Fatimah labarin abin da ya faru da wanda ma ke kan faruwa ba tare da ta san babban kuskure ta aikata ba. Da dare Mansur na dawo wa ya shiga ɗakin Momy,bayan ya gaisheta ne take ce masa “ɗazu matarka ta kira wata mai suna Fatimah ban san ya suke ba,amma kaf sirrin gidanka ta sanar da ita na mu'amalar ka da ita .Hum! Ni kuwa cewa ta yi jarababiyar tsohuwa ko amarci ba ku gama ci ba na zo na tare muku a gida” Ran Mansur ne yayi bala'in ɓaci ,ya tashi da sauri ya fita.Ya na shiga ɗakin ya tarar da A'isha ta zanzare ta ci uban ado,tuni ya manta abin da ma ya kawo shi ya je ya rungumeta. Gabanta ne ya faɗi lokacin da Mansur ke ƙoƙarin yi mata kiss saboda wani uban wari da bakinsa ke yi,warin hammatarsa kuwa ko bunsuru albarka .Amma a haka ta daure suka raya sunnah,cike da kula wa ya dube ta ya ce “daga yau kar na sake jin kin fitar da sirrina ,ko Momy ba ta faɗa min ba zan gane wa” A'ishah dai ba ta ce komai ba ,zai lokacin da zai mayar da kaya ta ce masa “don Allah ka je ka yi wanka” “Ba zan yi ba” ya bata amsa a takaice. “Ko brush ka yi” Mansur yayi saurin juyo wa ya na ƙare mata kallo cikin ido,‘ko dai maganin da na bata har ya karye ne da har ta ke iya faɗa min magana kai tsaye babu ɗigon tsoro?’ ya yi wa kansa tambayar a zuci. “Ka yi haƙuri don Allah ” ta faɗa a ɗan daburce bisanin ta shiga toilet ta yi wanka. Ɓangaren Momy kuwa shiru har yanzu ba ta ji ihun A'ishah ba ,ta yi zaton shegen duka Mansur zai lakaɗa mata.Ganin haƙar ta ba ta cimma ruwa ba yasa ta tashi ta rufe ƙofa da key,kayan jikinta ta cire ta ɗaura wani jan ƙyalle a ƙugu. A cikin jakkar kayanta ta fiddo wata ƙaramar tukunyar laka mai ɗauke da layu da sauran abubuwan shirka sai kuma wani bokitin roba fari mai ɗauke da korayen ruwa,nan ta fara yin surkulle a nan take hayaƙi ya turniƙe ɗakin ba ka jin komai sai hucin narkeken kwaɗo da kukansa. Ta ɗauki lokaci da dama bisanin ta tsaya,murmushin mugunta ɗauke a fuskarta ta ce “ A'isha tun da ki ka yi sanadin shigar ɗana ƙungiyar asiri wallahi ke ma sai na gulala miki,sai kin gwammaci kiɗi da rawarki.Da ni da ke shege ka fasa” ta gama faɗar haka ta buɗe bokitin nan fa kwaɗon nan ya yi tsalle ya fito kamar mai jira. Shegun idonsa tulu-tulu sai faman juya su yake ya na ƙoto.Ba tare da jin tsoro ba Momy ta shafi kansa ta na mai cewa “na wakilta ka a matsayin mai ɗaukar fansata,ina so ka fitini A'isha cikin mafarki da kuma zahiri ka zame mata hawainiya ka na sauya kala kamar yadda aka bani Kambunka” ta na zowa daidai nan ta furta wasu surkulle a take ya ɓace bai bayyana ko ina ba sai a ɗakin A'isha. Ta na zaune kan gado kunnenta maƙale da waya ta na cewa “wallahi Fatimah in faɗa miki har yanzu ma Mansur ya ƙi yin wanka,ban san dalili ba in kuma na yi magana ya yi fushi” Can ɓangaren Fatimah ta ce “to ke kamar ba mace ba,ki rasa dubarar da za ta sa yayi wankan? Kawai ki bari sai ya na kwance ki cika bokiti da ruwa ki zuba masa ai doli ya yi wankan ” “Katifata ta jiƙe?” “Ai ta na da leda” “Ok to zan jarraba na gani” sun yi hira sosai bisanin ta kashe kiran, lokacin ƙarfe takwas na dare bai gota ba. A'isha ta sauko ƙafarta ƙasa da niyyar zuwa toilet sai ta ji wani bala'in sanyi tamkar ƙanƙara,“innalillahi!” ta fusrta da mugun sauri a take kuma ta ji normal . Toilet ta shiga ,ta hau WC kenan ta fara jin kukan kwaɗo ta saki ihu ta fito a guje sai kuma ta ci karo da Mansur ya shigo. Ko tambayarta bai yi ba lafiya take ihu ya zube kan bed,saboda ya gaji sosai ya sha yawo a gari ko zai samu ƴan mata huɗun da aka buƙata sai dai ko guda bai samu ba. Baccin da ya fara da ninshari ya saka A'isha da ke can takure saurin dubansa,shawarar Fatimah ce ta zo mata a kai.Da mugun sauri ta fita waje ta ciko bokiti da ruwa ta malala masa a jiki.Hargowar da ya yi ya saka A'isha sakin bokitin ta na mai dafe ƙirji. ★AYODELE Duk yadda na so in danne muradina akan sanin tarihina kasa wa na yi.Bayan mun gama cin abincin dare na ce “Momah wai mine ne sunan Abbana? Na ga ko lokacin da na yi makaranta Ayodele kawai ake kira na” shirun da ta yi ya saka ni ci gaba da cewa “ko dai shegiya ce ni banda uba?” “Da ubanki Ayodele! Jarumi mai zubar da maza ko a fagen yaƙin wasa.Ke ɗin sauraniya ce ɗaya tamkar dubu,a kaf cikin ƴaƴansa maza da mata,manya da ƙanana ke ce ƴar baiwa” Momah ta faɗa wanda a ƙarshe sai da ta saki murmushi. “To ya na ina? Mi yasa ba mu rayu a tare ba?” “Don na tseratar da ke daga uƙubar da ababen bauta ke shirin tsoma ki yasa na gudo” ta bani amsa ta na mai kallon cikin idona, ta ci gaba da cewa “ko da na ji kin ambaci sunan Lassey na fahimci lokaci ya yi da za ki san tarihin ki,sai dai fa ba komai zan sanar da ke a yau ba sauran sai ranar birthday ɗin ki” Cike da jin daɗi na matso, Momah ta saki murmushi wanda a cikinsa ina iya hango tsantsar farin ciki wanda ban san mi ya wanzar da shi ba sai dai na fi alaƙanta shi ƙila ta na son mahaifina irin sosai ɗin nan. Sai da ta jawo ni jikinta kamar wata ƙaramar yarinyar,kaina na kan cinyarta hannunta kuma na shafa ƙananun kitson da ta yi min. Momah ta ce “kamar yadda na shaida miki ke sarauniya ce to mahaifin ki shi ne Sarkin Victoria Falls inda ya gaji sarautar ne a hannun Yayarsa na manta sunanta ” Da mugun sauri na ce “ Déborah ” ambaton sunan ya saka ƙwan lantarkin ɗakinmu fashe wa ji kake ɗuuuu. Momah ta zabura ta miƙe tsaye,“wa ya faɗa miki sunanta? Wa ya ce miki ana ambaton sunanta a ko ina? Da na ce miki na manta a tunanin ki gaske manta war na yi?” Momah ke faɗa cikin wata irin murya wacce ba ita na santa da ita ba,idonta kuwa wani irin haske suke fitar wa kamar an kunna glov har wani canza kala suke. Jikina ne ya ɗauki rawa ainun, musamman da ƙofofin gidanmu suka fara yin wata irin buga wa su rufe kansu su buɗe ji kake faaa-faaa! Rufin ɗakinmu kuwa kamar zai kware har ɗaga wa sama yake,wata da ban manta inda na ɗora ta ba na lalubo tare da ƙoƙarin kunna fitila ita ma ta yi bindiga ta fashe har ɗiyan hanjinta da garin batirinta na ji a hannuna. Tashin hankali,gobarar gemu Momah ta canza Yare ta shiga suratai.In ba gizau idona ke min ba wasu fararen siffofi ne ke faman shigo wa ɗakinmu tamkar duniyar fatale......... A nan kawo ƙarshen free page,duk wacce ke so ta biya 500 ta akwatin nan 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki tura shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 MRS SADAUKI NIJAR 🇳🇪