[17/04 à 16:40] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Page 1 Duk illahirin Musulmin Nijar sai hada-hadar jajibirin ƙaramar sallah suke,ƴan mata sai kitso da lalle suke yayin da ni kuma zuciyata take cike da tsoro, fargaba da zullumi suka raunata ruhina wanda ba komai ya haifar da haka ba sai baƙin alƙawarin da na ɗaukar wa Saurayina wanda duk duniya babu wanda nake so sama da shi.Ido na rumtse gam ina addu'ar da ba za ta guje ba,don in ba yau ba ne gobe sai ya tabbata. A karo na biyu Mama ta jefo min tambayar “ke Sharifa ba za ki je ƙumshin ba?” yanayin yadda ta min maganar a tsawace ya saka ni saurin buɗe idon tare da miƙewa daga kwancen da nake,raunatacen maƙoshina mai cike da ƙishi na daidaita kafin na ce “Mama babu tabbas fa ganin wata a yau! ” Sosai Mama ta ƙure ni da idonta masu matuƙar razana ni,“Sharifa mine ne ke damun ki ? Yau ke ce kike gudun kwalliyar sallah?” Na sunkuyar da kaina zuciyata na ɗan bugawa ,domin muddin na ci gaba da kallon idon Mama tabbas za ta fahimci wani abu. “Tambayar ki nake! Ko Fahad ya ce bai son ki?” Furucinta har ya fi damuwar da ke damuna zama tashin hankali a wurina,tuni idona suka ciko da ƙwalla ban san na lokacin da na furta “gwara na ga mutuwata da wannan ranar,Mama Fahad shi ne rayuwata in babu shi babu ni ” Tsuki ta ja ta na amsa sallamar Papa da ya shigo ,a bayansa kuma yaransa ne ɗauke da ledodi. Kallo ɗaya na yi masa na sunne kai ina wasa da yatsuna,“wa ya taɓa ki?” Papa ya faɗa,ba tare da na kalle shi ba na ce “ba komai !” “Mi kika yi mata take kuka? ” “Ƙumshi kawai na ce ta je ta yi fa ”Mama ta faɗa don kare kanta,don duk yadda take da tsanani a kanmu Papa na yi mata katsalandan don bai son ana takura mu. “Tun da ba ta so ai shikenan mine ne na takura ta?” Saurin barin wurin na yi na koma can ɗakina,tun kafin na isa nake jin tsuwar wayata ta na ringing ɗin waƙar *Zan rayu da kai zan mutu da kai* iya Fahad kawai na sawa shi na musamman. Wayar na cire daga caji ,a nan wani kiran ya kuma shigowa hannu na rawa na ɗaga .Ina jin lokacin da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce “babyna ina kika aje wayar ki? Sama da kira goma fa na yi ko ki na salon ne ana ƙawata min ke?” Kamar ya na ganina na girgiza kai tare da cewa “a'a ban je ba” “Kamar ya ba ki je ba? ” “Had ba fa lalle gobe sallah ba,yau duk ban jin daɗin jikina ” na furta murya na ɗan rawa don na fahimci kamar ransa ya ɓace wanda kuma hakan barazana ce gare ni. “Sharifa ban son iskanci da rainin hankali,wato ba ki son cika alkawarin da kika yi min shi ne za ki kawo wani banzan tunanin ki .Tun da aka haife ki kin taɓa ganin inda aka yi azumi talatin?” “Had wallahi ba haka nak...” saurin katse ni yayi ta hanyar cewa “ya isa haka Malama! Dama na san ba sona kike ba shi yasa kika ƙi bari mu zama abu ɗaya! ” “Innalillihi! Had ni ce ban son ka? ” “Eh mana Rifa! In ba haka ba miye a ciki don kin bani kan ki? Ni fa zan aure ki ba wani ba kuma na faɗa miki zan saka kwararon roba gudun shigar ciki” Shaaa! Haka hawaye ke min shatata a kumatu,Allah ne shaida ta ina mahaukacin son Fahad wanda shi kuma ko rabinsa bai yi min.Inda kuma aka samu akasi mugun tsoronsa da nake ji,yadda nake shakkarsa ko Mama albarka. “Za a ga wata a yau in sha Allah! Ki je a yi miki ƙunshi kin san ai ya na burge ni sosai.Ina so gobe na sha yatsun ki fiye da na kullum.Babyna don Allah ki cika min muradina wallahi ke ɗaya nake so nake kuma sha'awa ke ma ai shaida ce” Fahad ke faɗa cikin zaƙin muryarsa mai kamar busar sarewa. Ban iya cewa komai ba sai kuka marar sauti,ya ci gaba da cewa “babyna har fa na samo mana inda za mu huta,ɗaki mai kyau har da AC dakyar abokina ya ban auro duk don ina son nuna miki irin yadda nake maitar son ki” Furucinsa na ƙarshe yasa na ɗan ji sanyi ,kamar wacce aka yi wa dole na tambaye shi “Had da gaske ka na sona sosai?” sai da yayi murmushi mai sauti sannan ya ce min “fiye da so!” nan fuskata ta cika da annuri kan kace wani abu mun fake da hirar soyayya wacce babu wani abun albarka a ciki sai yadda za mu kasance a gobe. Bayan ya kashe wayar ne na nufi toilet cike don yi ɗahara saboda yanayin da na tsinci kaina.Bayan na fito na shirya tsab na fito domin zuwa gun ƙunshi,kuɗi Mama ta bani kafin direba ya kai ni. Ko da na isa gidan cike yake da jama'a,ta na ganina ta miƙe ta zo ta rungume ni ta na ihu tare da cewa “na zata ba za ki zo ba” Na ɗan ture ta ina hararen ta na ce “kar ki wani nuna kin damu tun da ban ga kin kira ni ba” “Hankalina ne ya ɗauku! Zauna in na ida ma wannan sai na yi miki ” ta faɗa tare da jawo min kujera,a haka muke yin hira ta tsokana.Har ta zo ta soma yi min wanda iya yatsun hannu ne dama nake yi wa lalle a ƙafa kuwa daidai suwu ne ake yi wa kwalliya amma duk da haka da zan tafiya sai da na aje mata kuɗi wanda ita kanta Ramlah ɗin ba ta sani ba. A cikin wannan wunin tunanina ya rabu biyu,na ganin wata da kuma abin da zai faru a gobe.A cikin wannan zullumin muka sha ruwa har muka tafi sallah muka dawo,kamar marar lafiya haka na kwanta a doguwar kujera na ƙurawa tv ido ina jiran jin labaru.Yayuna maza kuwa sai ciye-ciye suke su na hira da Mama,ina jin su suna tambayar Lafiya yau Auta ta kasa cin komai amma Mama ta share su. Ana sanarwa an ga wata na ji duk illahirin hankalina ya tashi,sam na kasa ɓoye damuwata har sai da na fiddota fili “innalillahi shikenan gobe sallah!” “Ka ji min zancen banza! Ganin watan ne ke innalillahi? ” Ya Mustapha ya tambaya a tsawace wanda shigowarsa kenan,na yunƙura na tashi hakan yayi daidai da shigowar kiran Fahad.Hannu na rawa na ɗaga kiran, “Ya tabbata gobe sallah!” shi ne abin da Fahad ɗin ya faɗa cike da murna wacce nake da yaƙinin ba wai don saboda sallah ba ne sai kawai don zai karɓi budurcina ne a goben kamar yadda na masa alƙawari. A sanyayye na furta “ni ma yanzu nake gani a télé Sahel ” “Lafiya na ji duk kin yi sanyi ?” “Gajiya ce kawai,azumin yau ya ɗan wahalar da ni kuma na fita na yi ƙunshi” na furta tare da ɓoye masa damuwata don gudun ɓacin ransa. “Gobe da ƙarfe nawa za ki zo?” ya tambaye ni cike,“zan zo kar ka damu” na furta cikin salon kwantar masa da hankali da basa tabbaci .Mun yi hira sosai kafin ya min sallama,waigowar ga da zan yi sai na ga kamar innuwar mutum ta yi saurin barin ƙofar ɗakina.Na basar tare da shiga toilet na sakarwa sumar kaina da ke tsefe ruwa,sai faman lumshe ido nake ina nazarin ‘anya zan amince na bayar da kyautar abu mafi muhimmanci a rayuwata? Shin in ma na yarda Mama za ta iya ganewa? ’ sai kuma na cije leɓena na ƙasa kafin na ɗauro towel na fito. Mama na tarar zaune bakin gadona hannunta riƙe da wata sarƙa mai shegen kyau sai juya ta take. “Zo nan ki gwada na gani in za ta yi miki ” na ji furucinta daga sama ,kusa da ita na matsa tare da karɓa na duƙa na ɗaura sarƙar ƙafar na saka ta tsakiyar biyun srkoƙin da ke ƙafar haguna.Wani abu mai kamar shock ɗin lantarki na ji ya ɗan kama ni,sai kuma na ji kamar ƙafar ta yi min nauyi amma duk da haka bai hana ni bayyana murnata ba ganin farar ƙafar tawa ta ƙara yin kyau . “Na gode Mama!” na furta ina shafa sarƙar,ba tare da ta ce komai ba ta tashi ta fita na bi bayanta da kallo ina tambayar zuci ‘ lafiya mike damun Mama?’ ba yau ba ne ta fara bani kyauta irin wannan ba,hasali ma duk ita ta bani sarƙoƙin da ke ƙafata kasancewar saka ta ya zama kamar al'adarmu ce Buzaye. A gaggauce na shirya cikin rigar bacci na haye bed,lambar Anty Maimuna Yayata wacce na bi ma na kira bayan mun gaisa na marairaice murya na ce “anty don Allah ki kira Mama ki ce ki na so na zo na taya ki aikin abincin sallah,wallahi duk Ya Mustapha ya takura ni ina tsoron ya dake ni ” “Ai kuwa dama ina da niyyar yin haka sai dai sanin halin ki na ƙiwa shi yasa ban roƙi alfarmar ba” ta faɗa ta na dariya,ni ma dariyar na yi kafin na kashe . Ina nan kwance ina tunani har bacci ya ɗauke ni,sai sallar asubah da na tashi.Ina zaune kan tapis Mama ta shigo,ko gaishe ta ban yi ba saboda ta wani haɗe fuska ta ce “ki tashi ki shirya direba zai kai ki gidan Maimuna ” “Wajen mi kuma yau sallah?” na yi tambayar ina ɓoye murna ta kamar ba ni na shirya plan ɗin ba. “Sharifa umarni na baki in kin je kin ga abin da za ki yi ɗin” ta na gama faɗa ta fice . Har da tsallen murna na yi kafin na shirya cikin wasu arnan ƙanana kaya sai na saka doguwar riga sama.Ɗinkin sallana na saka a leda kafin na fito ina kumbure-kumbure irin ban son zuwa,haka na yi wa Mama sallama bayan ta kawo ni bakin mota ta shaidawa direba in da zai kai ni. Gidan baya na zauna na hakimce tare da tsara text na tura wa Fahad,ina ɗago idona suka sarƙe da na Mubashar direbana.Na tamke fuska ba tare da na ce masa uffan ba,a haka dai ya kai ni har ƙofar gidan Anty Maimuna,da na fita daga mota ƙin tafiya yayi hakan na ja tsuki ƙasa-ƙasa tare da tura ƙofa na shiga na yi tsaye ban fito ba sai da na ji ƙarar mota. Bayan layi na nufa inda muka aje magana da Fahad zai tsaya jirana,ai kuwa ya na zaune kan tsohon mashin roba-roba.Ina haɗa ido da shi na ji sanyi ya ratsa ni,da ya sakar min makirin murmushinsa kuwa ji na yi kamar na some don daɗi .A shagwaɓe na ƙarasa shi kuma ya wani jawo ni kaina ya bugu da ƙirjinsa,“babyna!” ya furta cikin wani salon tayar da hankali ya na jan numfashi,ban kai ga amsawa ba ya fara shafa yatsuna da suka sha lalle. “Zo ki hau yau ke za ki tuƙa mu ” ya furta ya na daɗa jawo ni,da murna na hau babur ɗin ya na bayana na lula da mu a direction ɗin da yake nuna min.Hannuwansa biyu sarkaye da cikina,haɓarsa kan kafaɗata haka nake tuƙin ba tare da mun ishi kowa kallo ba kasancewar muna cikin babban birnin Niamey har muka isa wani haɗaɗen gida.Fahad ya saka babur ɗin ciki ni kuma ina take masa baya har cikin falon ɗakin,tun a nan wasa ya fara zalamarsa ta fito ƙarara musamman da na cire abayar sama . Rawa ta kai rawa har muka zube kan doguwar kujera,a yadda na ga Fahad ya fita hayyacinsa na gansa kuma a zahiri babu sutura jikinsa ya tado min tsohuwar fargaba da tsoron da na binne tun gida ........ [18/04 à 09:34] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Page 2 Yadda Fahad ya raba mu kaf da suturar jikinmu yasa na sadaukar na miƙa wuya ,na rumtse ido ina jin wani baƙin ciki na taso min a ƙahon zuciya.Jira kawai nake na ji azaba ta ratsa ni kamar yadda nake ji ƙawayena na faɗa da zafi sex ɗin farin sai dai shurun da na ji yasa na buɗe idona.Fahad na gani a zaune ya kafe jikina da ido kawai,na ɗan yunƙura na tashi zaune ban kai ga tambayarsa ba na ga jini duk ya ɓata gun da na kwanta. “Jinin mine ne?” na tambaya a ɗan tsorace,sai a lokacin ya kafe ni da mayun idonsa masu saka zuciyata rauni. “Dama kin san ki na period ba ki faɗa min ba umhum?” ita ce tambayar da yayi min. Na girgiza kai cike da tsoronsa na ce “ a'a sai fa sha biyu ga wata nake yi ko ka manta?” “To mi ya kawo shi tara ga wata iyeee?” ya min wata tsawa da tasa duk na firgice har na kasa basa amsa,ya ci gaba da cewa “wato magani kika sha ko?” “A'a wallahi Had ban sha komai ba sai dai in stress ce ta sa ya zo lokacinsa bai yi ba” na faɗa cikin rawar jiki muryata na rawa. Wani wawan mari ya ɗauke ni da shi kafin ya ce “kenan baƙin cikin kasancewa da junanmu kike? Sharifa ba ki sona! Yanzu na gane da ba ki sona yayi na gode” ya na gama faɗa ya dire ya nufi wata ƙofa ya shiga can sai na ji ƙarar ruwa alamun wanka yake yi. Hankalina ne yayi mugun tashi ganin irin fushin da yayi har da ikirarin wai ban sonsa,wanda a duniya in akwai kalmar da na tsana bayan wannan take.Cikin fitar hayyaci na miƙe na bi bayansa, tsaye yake shower na ta shatatar ruwa a kansa,amma farin sanin da na yi masa har na fahimci idonsa ma zubar ruwan suke a haka ya watso min su sun ja kamar nunannen tumatur.Kamar wacce ta zauce na taka gun shi,abin da na yi sam ban yi tunanin zan iya taɓa jikin nasa ba ma amma sai ya wani kwaɓe min hannu ya tura ni na yi tangal-tangal zan faɗa ga madubi yayi saurin caɓko hannuna ya haɗe ni da ƙirjinsa a tare muka saki ajiyar zuciya. “Had ina son ka don Allah kar ka sake furta haka! Zo ka yi a hakan!” na furta cikin gwanjin kuka ina mai matse damatsan shi irin na ƴan dambe. Muryarsa na ɗan rawa ya ce “ko na yi ba zan samu yadda nake so ba babyna!” yadda numfashinsa ke fita ma kawai ya tabbatar min ya na cikin tsananin buƙata. Ban da abin cewa kawai sai na shige jikinsa na yi lamo,da ƴan dubarun da muka saba samar wa kanmu nutsuwa a duk lokacin da muka haɗe club muka yi a nan toilet kafin mu fito. Sai da na goge inda jinin ya ɓata sannan na yi ƙunzugu da kallabina,a haka muka fito ya mayar da ni gidan anty Maimuna.Ina shirin sauka daga babur motar gidanmu na tsayawa,ta glass muka haɗa ido da Mubashar direbanmu wanda ban san uwar mi ya dawo yi ba. “Had ka tafi” na furta zuciyata na ɗan bugawa yayin da sam na kasa ɗauke idona kan Mubashar wanda alamu yayi suman zaune daga cikin mota. Fahad ya kamo tsintsiyar hannuna ya ce “wane ne wancan ɗin?” “Sabon direban gidanmu ne ” na basa amsa ba tare da na maido dubana kansa ba. “Shi ne kuma duk kika firgice haka? Ko akwai wani abu tsakanin ku?” Sai a lokacin na kalle shi,na ce “Allah kiyaye min baƙauyen? Mi zan yi da shi?” “To tsoron mi kike?” “Kar ya je ya faɗa wa Mama ya ce ya ganmu tare” “Ki gargaɗe shi mana ai ƙasan ki yake,ki masa barazana in ya faɗa za ki sa Papa ya kore shi” Fahad ya faɗa ya na wani mirza yatsuna. Na saki murmushi na ce “ina son ka nawa! Je ka kawai sai mun yi waya” Ya sakar min murmushi ya na mai tuƙa babur ɗinsa,sai a lokacin Mubashar ya fito hannunsa riƙe da leda wacce ita ɗin ta kasance tawa wacce na saka kayan sallana. Ya zo gabana ya tsaya ƙiƙam kamar wani soja,dogo ne irin sosai don ya fi Fahad zati da faɗin ƙirji damatsa kawai Fahad ɗin zai nuna masa shi ma don ya na ɗaukar ƙarfe ne ya na sport kuma. Ledar da ya miƙo min na karɓa,har na juya zan tafi na ji maganar shi daga sama “daga ina kuke? Wane ne wancan ɗin? Ina kallabinki yake kika bar gashin ki a buɗe ya na shan iska?” Takaicin da ya rufe ni a matsayinsa na ƙasƙantace mai aiki gidanmu yasa ni juyo cikin fushi na ce “daga gidan ubank....” ɓarin makauniyar da na ji ne ya hana ni ƙarasa abin da na so faɗa ɗin. Azaba da raɗaɗin marin yasa na kai hannu na dafe kumcin da ya mara ina mai fashewa da kuka.Dakyar na iya buɗe idona da na ji yanayin ganinsu ya ragu,don buji-buji ma nake ganinsa sai hucinsa da kunnuwana ke jiyo min. Ya nuna min yatsa ya ce “duk ranar da wannan ƙazamin bakin naki yayi gigin zagina sai na zubar miki da haƙora!” ya na gama faɗa yayi tafiyarsa ya bar ni shaye da mamakinsa.Wai yau ni ce Mubashar ya mara,sai da motar ta ɓace ma ganina sannan na duƙa na ɗauki ledar da ta faɗi na je na shiga gidan anty. Wanke fuskata na yi da pampon tsakar gida kafin na shiga ciki,daga kitchen ta amsa sallamar da na yi mata .Ni kuwa ɗakin da nake shiga a duk lokacin da na zo gidan na nufa, toilet na shiga na yi wanka bayan na fito ne na je kitchen na gaishe ta tare da roƙonta ta bani auduga. “Je ki ɗauko a ɗakina,kin san Chéri tun jiya aka kira shi a Company tsabar iskanci wai mission za su je” anty Maimuna ta faɗa ta na juya tukunyar miya. Na yi ƴar dariya na ce “ai duk wacce ta auri soja ba ta more aure ba,ina dalili ba za ku sha love ba” Dundu ta min a baya ta ce “ba ki san fa'idar auren soja ba yarinya shi yasa” “Mi haɗi na da soja dama a bar ni da Had ɗina ɗan Ball ” na faɗa tare da ficewa na je na ɗauko na kimtsa kaina,sai kuma na koma na kama wa anty aikin. MUBASHAR Tun ranar farko da ya zo gidan ya ƙyallara ido ya ga Sharifa ya ji Allah ya jarabce shi da muguwar kaunar ta ,sai dai abu guda ya lura da shi kanta na rawa ba ta tsoron kowa gidan daga babban yayansu sai Mama.Hakan kuma ya samo asali ne daga Papa wanda shi ne ke sangarta ta duk abin da take so shi za a yi sam bai son ana takura ta. Duk abin da Sharifa ke yi Mubashar na ankare da ita, ya sani sarai ta na zuwa gidan rawa don ya sha bin ta a ɓoye amma abun na basa mamaki yadda Papa bai ɗauki hakan wata matsala ba tun da a gabansa take fita ɗin. Yau lokacin da Mama ta sanar da shi zai kai ta gidan anty Maimuna tun da safen nan sam sai ya ji hankalinsa bai kwanta ba.Wannan yasa ya tsaya sai da ya tabbatar ta shiga gidan sannan ya dawo,a saman hanya ne ya lura ta manta ledarta bai yi saurin komawa ba ya bari ne sai an ɗauki lokaci ya je ya kai mata ashe rabon ya je ya ga abin takaici. Madubin idonsa babu abin da suka nuna masa sai fuskar Fahad wanda babu abin da ya fi shi da shi na dangin kyau sai hasken fata.Mubashar ya bugi sitiyarin mota ya na jin wani baƙin ciki na daɗa rufe shi,a haka har ya isa gida.Dakyar yayi wanka ya shirya cikin farar shadda wacce Papa ne ya basa ita sabuwa dal a leda,bai saka hulla ba haka ya fito ya zauna zaman jiran mai gidan nasa wanda a tare za su je sallar idi. Papa ya fito cikin shirinsa sai baza ƙamshi yake,fuskarsa cike da annuri ya ce “mu je ko?” Miƙewa Mubashar ɗin yayi ya shiga ya zauna mazaunin direba,Papa na gefensa tun da suka ɗauki hanya suke kabbara har suka isa.Bayan sun dawo kuwa har falo Papa ya ja shi suka je don cin abinci amma fafur Mubashar ya ƙi sai zubo masa nasa aka yi ya je ɗakinsa,ba don an haramta yin azumi ranar sallah ba to da tabbas azumi ya miƙe da shi tsabar yadda zuciyarsa ke cike da ƙunci.Kishin Sharifa kuwa ya rufe masa ido musamman yadda ta bar sumarta ta buzaye a buɗe sai kaɗawa take,ya rumtse ido a can ƙasan zuciyarsa ya ce ‘ Allah kaɗai ya san iyakar mazan da suka gan ta a haka ɗin’ A can bangaren Fahad kuwa ya na isa gida da kashin awaki ya fara cin karo da shi wanda ƙanwarsa ke ta faman tattara shi wuri guda.Ya ja tsuki,don a kullum ya na takaicin kasancewar shi ɗan nan gidan ya so ace gidan masu kuɗi aka haife shi.Ɗakinsa ya wuce wanda ko ƙyaure bai da sai labulen wani koɗaɗen yadi,maimakon ya fara shirin zuwa sallar idi kamar yadda kowanne matashi musulmi yake a'a kawai sai yayi kwanciyarsa kan cakusasar katifa ya ɓingire baccin da bai yi ba a jiya ya na tunanin yadda zai yaga mutumci Sharifa.Ba shi ya farka ba sai ƙarfe ɗayan yara,ko wanka bai yi ba ya je ya buɗe tukunyar da ke kan murhu dafa duka ya gani ta macaroni ya ja tsuki ya ce “tsabar baƙin ciki ko nama babu sunan wai nan sallah ake yi” Mahaifinsa wanda ke can gefe ya na sauraren rediyo ya ce “saboda ba ka kawo ba shi yasa ba a saka ba” Fahad ya taɓe baki kawai har zai zuba abincin ya ci ,Umma mahaifiyarsa ta ce “ka ga wani abinci nan da aka kawo gidan maƙwabta zo ka ci jar miya ce da naman kaza” Fahad ya washe baki ya je ya karɓa,ba wanke hannu ko Bismillah ya shiga kwasar girki.Can ƙasan zuciyarsa kuwa cewa yake ‘yo in ba don ina son saya wa kaina mutumci wurin babyna ba ai da gidansu zan je na ci ɗuwawun kaji har sai na gaji! ’ sai kuma ya ja tsuki a fili. Umma ta ce “lafiyar ka kuwa?” “Wallahi Umma wani banza ne kawai ya firgita min Sharifa ” Umma ta washe baki ta ce “wai ni kam sai yaushe za ka kawo min ita na gan ta? Ko za ta zo ta gaishe ni ga sallar nan?” Fahad ya ƙyalƙyace da dariya ya ce “haba Umma a wannan gidan ne zan gayyaci Sharifa? Kin san kuwa waye mahaifinta? Shararren mai kuɗi ne fa irin manyan buzayen nan ne wanda Nera ta kwanta” “To in ba da abun ka ba Fahad mi yake? Ai ba a canza wa tuwo suna,ka sani in ta zo ta taimaka mana da kuɗin da za mu gyara gidanmu?” “Umma har yanzu fa ɗaliba ce ba ta gama karatu ba,ina za ta samu kuɗi?” “Mahaifinta za ta yi wa magana mana” “Hum! ” shi kawai Fahad ya yi,don duk yadda suka kwashe shekara biyu suna soyayya ko da wasa bai taɓa nuna wa Sharifa ya na son dalar ta ba,gani yake tsoronsa da take ji duk zai zube in ta fara basa kuɗi.Sannan yanayin yadda yake shigar tsadadun kaya ko ita ba za ta yi tunanin talaucinsu ya kai har haka ba. Ya na gama cin abincin ya je ya ɗibi ruwa ga randa ya je yayi wanka,shiri yayi mai kyau ya fesa turare bai zarce ko ina ba sai majalissar su ta ƴan zaman banza,a sha shayi a zagi mutane masu wucewa da hirar ƴan mata da duk wani dangin shiririta. SHARIFA A gidan Anty Maimuna na yi wunin sallah mun ci mun sha mun yi hotuna ni da ita,lokacin da mijinta ya zo shi da wani abokinsa suka zo mai suna Ali mai mayen kallo da makirin murmushi.Duk yadda na so guje masa amma sai da ya karɓi lambata kafin su tafi. Bayan sallar magrib muka yi waya da Mama ta sanar da ni Mubashar na kan hanya zai zo ya ɗauke ni.Haka kawai na ji zuciyata na buga wa,ina nan zaune kuwa sai ga shi ya shigo da sallama kasancewar dama ya san Anty Maimuna in ta je gida shi ke maido ta nan ɗin. A mutumce suke gaisawa tare da yi wa juna barka da Sallah kafin mu ɗunguma mu fito,ban sani ba hira ce ta yi daɗi ko me kawai dai na samu kaina da buɗe gidan gaba na zauna sam ban farga ba har sai da ya soma tuƙi na ji numfashinmu na garwaya. A hankali na ɗan saci kallonsa,tuƙi yake a hankali kamar bai son yin gudu sai bin ƙira'a Sudais yake yi.Wayarsa ta ɗau ruri wacce ya jona da motar, ya ɗaga ba tare da ya cire ta a bluetooth ɗin ba. “Assalamu aleykum yaron albarka” na ji muryar wata mata ta furta. Sai da ya saki murmushi mai sauti kafin ya amsa a shagwaɓe,ni abun ma dariya ya ban. “Wa'aleykum Salam Ya Ammy kin wuni lafiya?” “Alhamdullah! Lafiya lau ɗazu mun tafi gidan gaisu ne na zo na tarar da wani kiran naka.Am... muna magana ka ce ka samu matar aure ,fatan dai mai tarbiyya ce Malama kamar dai kai,ta iya girkin gargajiya ne irin miyar kuɓewa da ta ganye?” Wani murmushin ya kuma yi ya na mai kallona sai muka haɗa ido,ba tare da ya janyen idonsa kaina ba ya ce “Ammy ina tuƙi in na sauka zan kira ki” ƙittt ya kashe. Haka kawai na ji haushi da ban ji amsar da ya bata ba,sai kuma na taɓe baki kafin na mayar da hankalina kan hanya a haka har muka isa gida ina shirin fita ya rufe ƙofofin duka..... [19/04 à 13:33] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Page 3 “Wane iskanci ne wannan?” na furta a harzuƙe ina kallonsa raina a ɓace,akwai haske hakan yasa na ga lokacin da annurin fuskarsa ya ɗauke ya maye gurbinsa da haɗe rai.Muƙut! Na haɗiye wasu yawu,amma da yake ina da ƙarfin hali da ji da kai sai cewa na yi “ kar fa ka manta a karkashin innuwata kake aiki?” “Sai aka yi me?” ya tambaya a dake. “Sai ka girmama ni ” na basa amsa haɗi da murguɗa baki. “Kin manta abin da na faɗa miki ɗazu ko sai mun je gun Mama na sake jaddada miki?” “Yi haƙuri don Allah ka ji Mubshar!” na yi saurin faɗa cikin rawar murya. Ya saki wani makirin murmushi ya ce “ki kiyaye ni bari ganin ki na auta zan ɓaɓalla ki ne kuma ba za a min komai ba tun da amanar ki aka ban ” “To na ji ka buɗe na fita” “Yawwa kuma abu na gaba kar na sake jin ƙazamin bakin ki ya ambaci tsarkaken sunana” Idona ne ya ciko da ƙwalla na ce “ni ce ƙazama?” Bai bani amsa ba sai motar da ya buɗe ya fice ya bar ni nan zaune,dakyar na iya fiddo ƙafafuwana waje na ja su zuwa babban falonmu.Ina shiga da Ya Mustapha na fara cin karo ya sha shiri kamar wani ango,har zan wuce na ji muryarsa “keee?” Jiki na ɓari na dawo na yi tsaye gabansa “Yaya ina wuni?” Bai amsa ba sai umarni da ya bani,“je ki gyara fruits su na kitchen ki saka su a frigo su yi sanyi kafin na dawo,sannan ki nutsu in kika kuskura kika yi min ɗan banzan shirmen ki jikin ki zai faɗa miki ” Yadda yake maganar cike da iko ya ƙara tunzura zuciyata,tuni wani baƙin cikin ya rufe ni.Ido na tsiyayar ruwa na wuce kitchen ɗin.Wata uwar leda ce cike da kayan marmari haka na zauna na gyara su na saka a frigo kamar yadda ya ce ɗin kafin na wuce ɗakina.Kan bed na haye na fashe da kuka,na ɗauki lokaci mai tsayi kafin na bai wa kaina haƙuri na tashi na yi wanka.Ina tsaka da shafa mai Mama ta shigo,“Sharifa zo ki gaida antyn ki ga ta nan a falo ” ta furta fuskarta cike da annuri. Na turo baki gaba na ce “ai dama na san ita ce za ta zo tun da ya jido fruits sai ka ce ɗiyar gwal sai wani jiji da kai yake ” Mama ta min tsawa “zan ci mutumci ki! Babban yayan naku kike faɗa ma haka? Maza ki saka kaya ki fito” ta na gama faɗa ta fice ,a gagguce na kimtsa na fita falon. A hakimce na gan ta a zaune ta wani sunne kai su na hira da Mama shi kuma gogan ya kafe ta da ido ya na sakin murmushi. Sanin halinsa yasa na daure na yi sallama,kafin na gaishe ta “anty Nafi ina wuni?” Sai a lokacin ta ɗago fuskarta wacce ke ɗauke da simple make-up ta yi kyau sosai duk da ta na baƙar mace,“lafiya lau my lil sis fatan kin yi sallah lafiya?” “Lafiya lau ya gida?” na faɗa ina ƙirƙiro murmushin dole don ni Allah na gani ba ta kwanta min ba tun farkon kawo ta gidanmu ,lokacin da aka kai lefe kamar na yi hauka haka na ji. “Alhamdullah!” ta amsa a taƙaice ta na satar Ya Mustapha da wani mayen kallon love. Na taɓe baki ina shirin tafiya na ji Mama na cewa “ki kawo mata ruwa mana Auta ” ‘ Hum! Dama na sani yau zan koma ƴar aikinta har sai ta tafi kuma!’ na faɗa a zuci na nufin kitchen.Ƙaton tray na ɗauka na jera jus da kofi biyu sannan na ɗauki wanda ake saka fruits na jera su tuni sun yi sanyi kuwa. ‘Tsabar iskanci saboda mutum guda aka sayo duk wannan abun mtws ! Shegiya mayuwanci ƴar talakawa yanzu ta buɗe hanji ta yi ta ci’ shi ne abin da nake faɗa a zuci har na iso falon sam ban lura da Mubashar tsabar yadda idona ya rufe da takaici kawai sai ji na yi na yi tuntuɓe ashe ƙafarsa ce.Nan wani abun mamaki ya faru duk abubuwan da ke kan tray ɗin suka yi sama amma kamar almara sai suka dawo suka zauna a trayn ba tare da sun zube ba. Na ja wata ajiyar zuciya,sai a sannan na lura ma kan cinyarsa nake zaune dirshen .A kunyace na miƙe na je na ajiye tray ɗin kan table,kusa da Mama na zauna wacce na lura kamar duk falon ita kaɗai ta lura da abin da ya faru. “Zan koma yalaɓai sai kun fito” Mubashar ya faɗa ya na mai miƙewa,Mama ta ce “kar ka yi nisa dai ka san na ce za mu je wani wuri” “To Hajiya ! ” ya amsa tare da ficewa. Mama ta kama hannuna ta ce “auta mu je” miƙewa na yi muka basu wuri.Ya Mustapha kuwa kamar jira yake haka ya miƙe ya koma kusa da Nafi ya soma ciyar da su ya na yi mata hirar soyayya har suka ƙoshi,an ɗauki lokaci mai tsayi mu kuma kafin mu dawo falon hannuna riƙe da ledar da Mama ta jibgo wa anty Nafi kaya. Har bakin mota na yi mata rakiya sai godiya take zuba wa Mama kafin ta ce “Auta sai yaushe za ki je gidanmu?” Na ɗan murmusa kawai,Ya Mustapha ya zuba min ido hakan yasa na dubi Mama wacce ke tsaye sai cewa ta yi “zan sa Mubashar ya kai ta jibi sai ta yi miki wuni” A haka sai suka tafi,na yi tunanin ciki za mu koma amma sai na ji Mama na cewa “za mu je ki yi shopping Auta ” sai kuma ta soma kiran sunan Mubashar,babu jimawa ya fito ya na kaɗa key ɗin mota kamar tasa. Gidan baya muka zauna,mai gadi ya buɗe get yayin da shi kuma ya cinna hancin motar waje.Sai da muka hau kan titi sannan ta sanar da shi Mall ɗin da za mu je,da muka isa har zai zauna cikin mota amma Mama ta ce mu shiga tare.Turarruka ne na zaɓa,sai pant da bra yayin da ita kuma Mama ke ta zaɓar min wasu kayan daban ga mamakina wai har da hijabai abin da bai sha min kai ba muddin ba sallah zan yi ba. Mubashar ne ya ɗauko su ya kawo su mota bayan an biya,sai hira Mama ke jansa da ita wacce ta kasance ta ƙauyensu ce da kuma Ammynsa.A nan ne na tsinci cewa shi ɗin malami ne yayi makaranta can Borno zaman tsangaya,don har haddar Alkur'ani gare shi a kai kuma hakan ta faru ne saboda burin mahaifiyarsa ne wacce ke can zaune yanki Tilabery. Shiru kawai na yi ina nazarin abin da ya faru ɗazu wanda tabbas bai da maraba da tsafi,a zuci na raya ‘kenan malamin tsibo ne ko me?’ sai kuma na ji tsoronsa ya kama ni don a duniya ina tsoron lamarin tsafi ko asiri.Muna isa gida na fice ko kayan ban ɗauka ba,direct sashena na shige ina mai kiran layin Fahad amma ga mamakina sai ji na yi ya na kan layi wato waya yake. Sama da minti talatin ina fafutukar nemansa amma sai hirarsa yake alhalin ina da tabbacin ya na ganin kirana.Tuni zuciyata ta tsinke na rungume matashin kai sai hawaye shaaa,tun ba yau ba na san da cewa Fahad na da ƴan mata dayawa yawanci su suke bibiyar shi wanda na san bai rasa asali da yadda Allah ya yi masa baiwar kyawu.Amma duk da haka ni ta musamman ce soyayyar da yake min ta sha banban da ta sauran. “Sharifa ga kayan ki nan daga gobe ina son ki fara saka su,kar na ƙara ganin ki cikin matsatsun kaya sannan duk inda za ki je dole Mubashar ne zai kai ki” furicin Mama shi ya ida ruguza laɓuɓuwar zuciyata mai cike da rauni,mai son kuka an jefe shi da kashin awaki mai zai yi? Kawai sai na fashe da kuka wiwi. Ina jin lokacin da Mama ta hau gado ta jawo ni jikinta,“Autana ki na ji na? Duk abin da nake min ƙauna ce,kuma kowacce uwa haka ya dace ta yi wa ƴarta ta bata kariya.Na ji duk wayar da kika yi da Fahad a jiya,ki sani shi ɗin ba masoyin ki ba ne shekara biyu kenan ku na soyayya an ce ya kawo sadaki ya ƙi ina ce dai ki na ganin duk yadda Papan ku ke son ki sai da ya ɗau matakin hana shi zuwa nan gidan.Duk wanda yake sonka auren ka yake yi ba ya dinga ɗaukar ki ba ku na yawon club-club ba” Duk da irin ƙuncin da nake ji sam ba zan iya sauraren ana ɓata Fahad ba,hakan yasa na yi saurin cewa “A'a Mama kar ki ce haka wallahi zan iya rantsuwa da Alkur'ani Fahad na mugun sona,maganar aure kuma lokaci ne dole mu jira shi” Mama ta ɗago haɓata,ido cikin ido muke kallon juna kafin ta ce min “ki na son Fahad?” na gyaɗa mata kai na ce “fiye da kalmar so” “Kin tabbata ya na son ki zai aure ki ko?” “Eh Mama!” “To ki ce ina son ganinsa gobe!” ta na gama faɗa ta kwantar da ni kamar wata ƙaramar yarinya kafin ta fice,na bi bayanta da kallo kafin na ƙoƙarta na rubuta wa Fahad saƙo sai kuma na kashe wayana. MAMA Ta na fita ta wuce ɗakin Papa wanda bai jima da dawowa ba,jiki a sanyayye ta zo ta zauna. Ya ɗan dube ta ya ce “ya dai?” “Akan auta ne!” Mama ta faɗa dakyar. “Ina jin ki” “Alhaji na ce mi zai hana ka sassauta lamarin nan ka ce Fahad ya kawo duk abin da Allah ya sawwaƙe masa ka aura masa ita hankalin kowa ya kwanta” Papa ya ɗaure fuska ya ce “duka nawa Autar take? 22years ne fa? Sai na yi mata aure ko karatu ba ta gama ba kuma da wancan yaron?” Mama ta ce “in an yi auren....” yayi saurin katse ta da “ba za a yi ba!” Cikin jimami Mama ta fito daga ɗakin ta koma nata ta fara saffa da marwa,tun ranar da ta ɗora idonta kan Mubashar ta gamsu da nutsuwar shi, abu na gaba kuma shi ne yadda ya bata laƙanin yadda za ta tsare mutumci ƴarta.Ta ja wani dogon numfashi ta ce “rashin uwa ke sa a yi uwar ɗaki! Da dai in bari Fahad ya ɓata miki rayuwa gwara na bai wa Mubashar auren ki kowa ya huta” daren nan sam Mama ba ta rumtsa ba sai da ta samo wa kanta mafita,ta kira babban Yayanta Sheik Mohammed ta sanar da shi burinta. Washegari Wuraren ƙarfe goma na safe ina kwance kan gado Mama ta shigo cikin shirin fita,dakyar na buɗe baki na gaishe ta. “Zan fita ki shiga kitchen ki ɗora girki” Na ɗan shagwaɓe fuska na ce “Mama don me Saude ba za ta yi ba?” “Ke nake so ki yi! ” ta na gama faɗa ta fice.Toilet na shiga na yi wanka na kimtsa kafin na fita falo,babu kowa sai ƙaton tv da ke ta magana shi ɗaya.Table na nufa na haɗa tea na sha kafin na wuce kitchen,tuni Saude ta fara gyaran kayan miya da taimakon ta na yi komai. A ɓangaren Mama kuwa ta dai ce Mubashar ya kai ta wani wuri ba tare da ta yi masa bayani ba har suka isa. A tare suka shiga har babban falon kamar yadda ta buƙata,su na ta gaisawa da mutanen gidan kafin Sheikh Muhammad ya fito cikin shigarsa ta kamala dogo ne fari tasss ya ɗora gemunsa ka na ganinsa ka ga ahali sunnah. Bayan sun gaisa ne Mama ta ce “wannan ne dama nake yi maka zance a jiya,ya na hadda alƙur'ani sai dai na Warshi ne irin na ƴan allo to Yaya ina son ya koma kamar dai kai haka a koya masa karatun litattafan Musulunci ” “Ai duk ɗaya ne karatun Warshi da Habsi,amma in sha Allah za mu yi abin da ya dace.Ya sunan ka?” cewar Sheikh Mohammed. Mubashar da sai yanzu ne ya san dalilin zuwan nasu wato gata Mama za ta yi masa kenan ya basa amsa da “Mubashar ne sunana” Nan ya fara yi masa tambayoyi game da makarantar da yayi,kamar yadda ya shaida wa Mama haka ya maimaita yanzun ma ba tare da ya ɓoye komai ba. “A Borno na yi karatu,a can ne kuma aka koyar da mu wasu laƙanin,wanda da farko muna dai taya malaminmu ne in an kawo masa aikin tsibo daga haka yayi ta koyar da mu amma ban taɓa gwada wa ba sai sau ɗaya a can Tilabery da wani ya ce ya na son wata na masa aiki kuma ya ci.A ranar da ya zo yi min godiya ne Ammyna ta fahimci al'amarin da ke faruwa shine ta ƙone duk kayan aikin sannan ta hane ni da juya ilimina domin sana'a, wannan dalilin yasa ma na fito neman aiki har Allah ya haɗa ni da Hajiya Mama” Sheikh Muhammad ya jinjina kai bayan ya gama sauraren shi kafin ya ce “Allah yafe mana baki ɗaya ka ci gaba da yin istigfar.Gobe za ka fara zuwa makarantarmu ban sani ba ko ka taɓa jin ana cewa Imam Malik ba? To sunanta kenan.Makaranta ce mai koyi da sunnah da kaucewa duk wani abu da ya saɓa ma koyarwar manzonmu” sosai Sheikh Mohammed yayi masa bayani yadda zai fahimta,kasancewar Mubashar bai da girman kai haka ya tsaya ya saurare shi. Da za su koma haka ya basa wasu littattafan,a hanya ya na zuba wa Mama godiya har da yin kukan farin ciki.Su na isa gida Mama ta wuce can ciki,shi kuma Mubashar ƙarƙashin innuwar mangoro da ke tsakar gidan ya je ya zauna tare da danna kiran Ammy. Bayan sun gaisa ta ce “jiya ina ta jira ka maido shiru,ba ka bani amsa ba na ce yarinyar....” yayi saurin katse ta ya na mai cewa “Ammy akwai abun murnar da nake son sanar da ke fa” “Wanda ya fi wannan?” ta tambaya. “Eh Ammy! Hajiyar da suka ɗauke ni aiki ce ta biya min makaranta irin ta ƴan gayu,gobe zan fara” nan ya yi mata bayani,sai ga Ammy ta na kukan murna “Alhamdullah! Allah na gode ma dama ya ce in ka yarda da shi zai maka ni'ima ta inda ba ka zato.Ka bani lambar Hajiyar na kira na yi mata godiya, Mubashar ka je hankali ka yi karatu Imam Malik duk Nijar babu makarantar da kai ta,domin har Larabawa ke da kwai cikin masu karantarwar” “In sha Allah Ammy! Zan sake kiran ki” sai ya kashe tare da nufar ɗakinsa.Ɗan ƙaramin akwatinsa na ƙarfe ya buɗe ya zaro wata sarƙa wacce suke shige da wacce ya bai wa Ammy a shekaran jiya.Sai da ya ɗan juya ta kafin yayi Bismillah ya buɗe lular tsakiya,garin magani ne a ciki wanda Allah kaɗai ya san surkullen da aka yi masa. “Daga yau ba zan sake yin imani da duk wani abu da ya shafi abu kamar haka ba” ya furta tare da sauke ajiyar zuciya sai ya je ya ƙone su daga ƙarshe. FAHAD Abokansa suka haɗa wasa a wani gidan gona ,sanin Sharifa ta na cikin period kuma ba zai samun yadda yake so ba yasa shi fara kiran ƴan matansa uwanda sun fi goma a haka yayi ta nema har ya samu wacce ta yarda su je su watse ɗin.Lokacin da Sharifa ke ta gwada kiransa shi kam bai da lokacinta ,sai dai ya na da niyyar kiranta a gobe . A gajiye ya buɗe idonsa saboda sam bai rumtsa ba ya samu ƴar mutane ya na ta hole wa da ita,tun dare har asubah abu ɗaya suke. Fahad ya jawo wayarsa da ke can gefe ya duba,saƙon Sharifa ya gani «Had gobe ka zo gida Mama na son ganin ka,da dukkan alamu lokacin aurenmu ne ya zo» ya na gama karanta saƙon ya ida ture budurwa da ke kan ƙirjinsa ta na sharar bacci.Kayan jikinsa ya fara nema a cikin kayan da ke zube na abokan shiriritar tasa.Ya na gama kimtsa wa ya fice ko ta kanta bai bi ba,babur ɗinsa ya hau ya na tafe ya na gwada kiran lambar sharifa amma ba ta shiga a haka har ya isa unguwarsu inda ya tarar da cincirindon mutane a ƙofar gidansu.Bai kai ga tambaya ba ya hangi motar ƴan sanda ga Umma a zaune ta na sharar ƙwalla..... [21/04 à 09:07] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Page 4 Da azama Fahad ya nufi motar ƴan sandar,sai dai kafin yayi magana ya ji muryar Nana na cewa “yawwa Maman ga shi nan ya zo” inda sautin ya fito ya duba,sai yayi tozali da Nana hannunta riƙe da jinjirin yaro sabuwar haihuwa.Gabansa ne ya faɗi ras ,ya haɗiye wasu yawun tsoro kafin ya ce “ uwar mi kike nema a gidanmu?” Mahaifiyarta ce ta basa amsa da “uwar abin da ka shuka ta zo miƙa ma tsiyar ka.Ke miƙa masa shegen ɗansa,miƙa masa na ce!” ta ƙarashe faɗa cikin ƙaraji hakan ya janyo hankalin dukkan mutanen da ba su hankalta ba. Umma ta fito daga mota ta na kallon Fahad wanda ya rungume jaririn,sai rarraba ido yake ya rasa mi zai cewa Ummar.Nana da mahaifiyarta kuwa tuni sun bar gun su da motar ƴan sanda,“ka kyauta kuma na gode” cewar Umma ta na mai shigewa cikin gidansu na laka. Cike da kunyar jama'a Fahad ya ratsa su ya bi bayan Umma,bai taɓa tunanin akwai ranar tonon asirinsa ba sai yau. “Umma don Allah ki yi haƙuri wallahi tsautsayi ne kuma ba ni ɗaya ba na kusance ta...” ko kafin ya dire zancensa Umma ta zuba masa yatsunta biyar kan kunci . “Ban son jin komai! Ka san tun yaushe ake neman ka? Tun jiya zuwan da suka yi ya fi cikon casbi,duk tunanin su na ɓoye ka ne shi yasa yau suka zo da motar ƴan sanda ta yadda asirinmu zai tonu ana zunɗenmu a unguwa.Dama ka san ba aurenta ba za ka yi shi ne har da wani bani labarin ta?” Fahad ya ajiye jaririn da sai baccinsa yake kafin ya ce “wannan fa ba Sharifa ba ce! Dama ƴar iska ce kawai don ban son tsiyar gumi shi yasa na karɓi yaron nan amma ki bar ta da ni take zancen” Umma ta jefe shi da kallon masheƙan aya ta ce “ko makaho ya dubi jaririn nan ya san ɗan ka ne,abin da nake so da kai dai shi ne ka bar yawon banza ka san ciwon kanka don na ji labarin jiya wasa kuka shirya shi yasa ma ba ka kwana gida ba” “Umma ni fa ban son yaron nan...” bai ƙarasa faɗa ba sai ga abokinsa Kb ya shigo gidan hankalin tashe don ko sallama bai yi ba . “Abokina yanzu aka kira ni aka ce babu lafiya,na zo kuma na ga kamar hankalin ka kwance ” cewa Kb. Umma ta yi caraf ta ce “eh mi zai sa ya tada hankalinsa tun da ita ƙaddara ta san ɗakin kowa ,kuma ai ba gare shi farau ba ballantana ya ƙare kansa” daidai nan jinjirin ya fara canyara kuka,Kb sam bai damu da zantukan Umma ba don tun ba yau ba ya san da ba ta son taren shi da ɗanta Fahad sai dai babu yadda zai yi Allah ya haɗa jinin su. Fahad ya girgiza kai kawai kafin ya buɗe ɗakinsa ya ce wa kb ya wuce ciki,yayin da Umma ta ɗauki ɗan ta na ririga shi “Fahad ya kamata fa ka nemo madarar da za a basa ya sha” “Banda ko sisi aljihuna ki ara min in na samu sai na baki” ya bata amsa. Kb ya ce “akwai a wurina bari na je na siyo” sai ya fasa shiga ɗakin ya fice . Fahad ya dubi mahaifiyarsa ya ce “ Umma don Allah ki bar nuna zallar ƙiyayyar ki ga Kabiru shi ɗin...” “Ya isa haka! Wuce ka yi wanka dubi yadda fuskarka take a yamutse” Umma ta faɗa ta na bai wa jaririn ruwa. Bokiti ya cika da ruwa ya je yayi wankan,ya na fitowa shi kuma Kb na shigo wa. Madarar gwangwani ce sai biberon inda za a dinga kaɗa madarar,sai da ya nuna wa Umma yadda ake haɗa wa sannan ya wuce ɗakin abokin nasa. “Fahad ka ga abin da nake guje maka ko? Wannan rayuwar da ka ɗaukar wa kan ka sam ba ta da tabbas” Kb ya faɗa cikin rashin jin daɗi. Fahad ya ja numfashi kawai,sai da ya gama shirya wa cikin ƙananan kaya sannan ya ce “sau ɗayan wahala ne kawai ka ji abokina” “A'a tun ba yau ba kuke tare da Nana ni a tawa shawarar kawai ka aure ta” “Allah tsare ni da auren ƴar iska!” cewar Fahad ya na haɗe rai. Kb ya murmusa ya ce “to kai mine ne?” “Irin ka ne ni ko ka zata ban san ku na holewa kai da Ramlah ba?” “Ita ɗin wacce zan aura ce kar ka manta haka.Kuma babu abin da ya shiga tsakanina da ita,ranar nan ma da ka gan ta ɗakina wani dalilin ne ƙwaƙwara ya kawo ta” Sai da Fahad ya sheƙe da dariya ya ce “to a faɗa wa kaji zabi hira suke! Ka ga tashi mu je ka yi min rakiya gidansu Sharifa” “Ba zan je ba! Ni ma gidan tawa amaryar zan je!” “Okay!" Ya faɗa ya na mai maƙe kafaɗu.A tare suka fito,Umma sai wanka aka yi wa baby Kb yayi mata sallama maimakon ta amsa sai cewa ta yi “saura kayan sawa na baby ” bai ce da ita komai ba ya zo ya ja motarsa ya wuce gidansu Ramlah wacce ke can ta na jiransa tun ɗazu . Sai da ya shiga ya gaida iyayenta sannan ya fito ya zauna cikin mota,jim kaɗan ta fito cikin adonta.Yadda ta haɗe rai alamun ta yi fushi yasa shi cewa “sorry Hajiyata ba gani na zo ba?” Ramlah kamar za ta yi kuka ta ce “saboda Allah mi ya tsayar da kai?” “Fahad ne mana” “Ka ce ciwon kan ka” Ramlah ta faɗa ta na taɓe baki. Kamar suɓul da baka Kb ya ce “ai kuwa yau ma ya kwaso jan aiki,wata yarinya ya yi wa ciki yanzu har ta haihu yau ta kawo masa ɗansa” Ramlah ta dafe ƙirji “ciki?” ta faɗa da ƙarfi sai a lokacin Kb ya tuna ya yi katoɓara musamman da ya san ita ɗin ƙawar Sharifa ce. Cikin son kawar da zancen ya ce “wane gida za mu fara zuwa?” “Duk inda ka kai mu” Ramlah ta faɗa ta na fiddo wayarta ta na dadana wa a haka suka fara ziyar dangi da abokon arziki inda a ƙarshe ta ce ya kai ta gidan su Sharifa. #Gidan Papa Muna gama girki ni da Saude muka jera kan table ɗin cin abinci.Wanka na je na sake yi sannan na kunna wayata,saƙon Fahad ya ta gwada kirana aka turo min na lumshe ido ina jin wani irin sanyi na ratsa ni wanda ba komai ya janyo haka ba sai don ganin Fahad ya damu da ni tun da har ya gwada kirana sama da goma sai kuma na wata baƙuwar lamba marar suna. Simple kwalliya na yi kafin na feshe jikina da turare na fito falo,tuni Yayuna Munir da Sharif sun fito su na ma cin abinci. Na turo baki gaba na ce “ba a ko jira har na fara ci shine kuka zuba” “Ke wa?” muryar Ya Mustapha ta katse ni wanda shi ma ya fito cikin shirinsa sai baza ƙamshi yake . “Yaya wasa fa nake!" Na faɗa cike da shakku. “Su ɗin sa'anin ki ne?” na girgiza kai idona na cikowa da ƙwalla. “Na sake jin banzan shirmen nan ki ga ikon Allah.Mi yasa kika kashe wayar ki ne? Ali ya ce yayi ta kiran ki bai samu ba” sai a lokacin na ɗago na dube shi,wato tuni shi ma sun gulmata masa abokin mijin anty Maimuna na sona. “Wayar ce ta mutu sai yanzu na caza ” “Yau zai zo sai ki shirya tarbarsa,sannan ki aje hankali ki nutsu da kyau da zarar kun fahimci juna zan basa auren ki” Tamkar saukar guduma haka na ji furucinsa,babu tsoro sam a idona na kafe shi da su na ce “shi kuma Fahad ɗin fa?” Ya Mustapha ya ɗaga hannu da niyyar mari na amma Papa ya dakatar da shi.Da gudu na koma ɗakina ina kuka,ban ma san lokacin da Mama ta dawo ba. Ina cike da ƙuncin nan ƙawata Ramlah ta shigo,“ke lafiyar ki?” shi ne abin da ta faɗa ta na buga bayana.Na tashi zaune ina dubanta da kumburarun idona,ban wani ɓata lokaci ba na koro mata bayani tun da ni da ita ba mu ɓoye wa juna sirrinmu.Maimakon na ga damuwa kan fuskarta sai akasin haka,“ai wallahi gwara ki cire Fahad a ran ki don sam ba ku dace ba,kin ga fa yanzu Kb ke faɗa min ya yi wa wata ciki an kawo masa baby.Yanzu irin wannan mijin za ki aura?” “Ban gane ba ki yi min gwari-gwari!” na faɗa don sam ban fahimce ta ba,sai da Ramlah ta sake maimaita min sannan na gane. Nan wani sabon kukan ya kubce min,maimakon ta rarrashe ni a'a kawai sai ta yi ta ɓata Fahad ana cikin haka ne kiransa ya shigo.Sanin shi ɗaya ke da irin wannan ringing ɗin yasa na ɗaga kiran ko screen ban kalla ba,“ga ni a ƙofar gidan naku mai gadi ya hana ni shiga” jin muryarsa cikin damuwa sai na ji tawa damuwar na barazanar ɓacewa.Ko kallabi ban tsaya sakawa ba na dire daga bed na fice,a tsakar gida na gamu da Mubashar ina jin ya na tambayata ina zan je ƙafata babu takalmi kuma ba mayafi amma na yi masa banza. Ina isa bakin get mai gadi ya tare ni ya na cewa “hajiya umarni Oga Mustapha ya bayar kan cewa kar na saki na bari ki fita, sannan wancan ma ya ce kar a bar shi ya shigo” “Ja ka bani wuri in ba so kake na mare ka ba” na faɗa ba tare da na duba yawan shekarunsa ba,da na ga bai da niyyar ja na yi wani ƙuuu doli ya kauce min na fita. Fahad na ganina ya sauko daga kan mashin ya nufo ni,ya buɗe baki zai yi magana na wanke shi da mari sai kuma na cakumi kwalar rigarsa ina jijiga shi.Cikin kuka na soma magana “ Had mi na yi maka ne har haka? Don mi? Akan wani dalili za ka je ka yi wa wata ciki ta haifa ma ka ɗa? Ni mi na kashe maka ne? Mi yasa ba ka yi min cikin ba madadin ta? Ka san yadda nake mahaukacin sonka kuwa? Ka san yadda soyayyar ka da kishin ka ke azalzalar zuciyata?” cikin fitar hayyaci nake maganar kafin kuma na shige jikinsa ina wani sabon kuka. Daga baya na ji an wani fizgo ni,babu zato babu tsammani na ji gau tuni na soma gani dishi-dishi ko kafin na koma normal na ji saukar muryarsa mai kamar aradu “tun da kin haukace ai sai ki je yayi miki ciki,banza wacce ba ta san ciwon kanta ba wuce maza gida” ya ƙarashe faɗa ya na wani hankaɗa ni saura ƙiris kaina ya bugi ƙaton get Allah ya min sa'a Ramlah ta yi saurin taro ni. Mama wacce hayaniyar su ta fiddo ta waje ta yi tsaye ta na kallon ikon Allah yadda Mubashar ya kama Fahad sai jibgarsa yake kamar wanda Allah ya kawo. “Mama ki na gani ya na dukansa,ki masa magana kar ya ji masa ciwo” na faɗa ina mai zubewa ƙasa cikin gwanjin kuka,duk yadda Fahad ke mayar da martani da kuma ƙoƙarin kare kansa Mubashar ya fi ƙarfinsa. Mai gadi ne ya shiga tsakaninsu,Mama kuma ta sa baki sannan kawai ya rabu da shi.Idon Mubashar sun kaɗa sun yi ja kamar garwashin wuta,haka ya zubo min su ya na huci babu shiri na miƙe na nufi ciki ko ta kan Fahad ban bi ba. A tsakar ɗaki na zauna dirshen,hawayen ma ji na yi sun ɗauke.Na rasa jimamen wane takaici zan yi,na cikin da Fahad ya yi wa wata ba ni ba ko kuwa na Mubashar wanda ya zaƙe a lamarin da bai shafe shi ba. “Cabbb! Wai da gaske wancan direban gidan ku ne? Ko dai shi ma Soja ne Ya Mustapha yake yi wa aiki ?” Ramlah ta faɗa lokacin da ta shigo,kanzil ban ce mata ba.Ta ci gaba da cewa “ba don an yi mana baiko da Kb ba ai da na shigar da takarduna” Ganin za ta ƙara min takaici yasa na shige toilet,ruwa na sakarwa kaina ba tare da na cire kaya ba.Tsawon lokaci ina a tsaye idona a lumshe sai hoton abin da ya faru,na kashe pampo na fito daidai nan na ji kaina ya sara ban sake sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsince ni a gadon asibiti. Da Mubashar na fara yin tozali fuskarsa cike da yanayi na tausayi da rashin jin daɗi,“Kin tashi?” na ji muryar Mama kusa da ni sai a lokacin na karkato kaina saitin inda take zaune . “Bari na kira likita” cewar shi ya na mai fita,daidai nan Ya Mustapha da kuma Ali suka shigo..... [24/04 à 09:02] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Page 5 Cikin second uku na ƙara ƙarewa Ali kallo, kyakkyawan namiji ne son kowa don bai da makusa amma sam ni dai bai min ba. “Ya jikin naki?” muryarsa ta ƙatse min tunani,ban iya buɗe baki ba sai idona na ɗan juya sai na ga ya saki murmushi kamar a mafarki sai jin na yi ya shafi gefen fuskata,ƙurrr idon Mubashar kanmu wanda ya dawo shi da docter tuni yanayinsa ya canza zan iya hango tsantsar takaici a ƙwayar idonsa. Dr ya zo kai gare ni ya fara min tambayoyi abin da nake ji yanzu,na girgiza masa kai kawai alamun ban jin komai.Sai kawai ya fita,Ya Mustapha ne ya tambayi ba'asi Mama ta ce “a bar zancen kawai tun da dai mun samu ta farfaɗo ” “Shi kuma ɗan banzan yaron can fa? Haka kuka bar shi ya tafi? ” Sai da Mama ta kalle ni kafin ta ce “am... Alamu dai sun nuna kamar Mubashar ya ji masa ciwo a hannu shi ne...shi ne na ce ya biyo mu asibitin a dubasa shi ma” Wannan karon Ali ne yayi magana “dole na ɗauki mataki akai! Amma yanzu dai ba wannan ne gabana ba,fatana ta warware tun da ina son a gama komai na aurenmu tun da mission zan zan je Kamaru” Da mamaki a fuskar Mama,amma sai ta shanye shi sanin Ali abokin Mustapha ne gun aikinsu guda. Mubashar dai ne ɗan faɗi ba a sa ka ba ya ce “wane aure kuma?” Sai a lokacin Ali ya juyo ya dube shi,sai kuma ya maida dubansa ga Ya Mustapha ya ce “abokina ba ka yi masu bayani ba?” “Mu je sergent na kirana ” Ya Mustapha ɗin ya faɗa ya na mai duba wayarsa,Ali ya fiddo kuɗi ya ajiye gefen kaina suka fice Mubashar ya bisa da mugun kallo kafin ya maido hankalinsa kaina. “Mi kike ji yanzu?” ya jefo min tambayar a dake,ban basa amsa ba sai harara da turo baki gaba. “Ba ta jin komai ,ƙila da ƙarin ruwan sun ida gida za mu je” Mama ta faɗa ta na murmushi, Mubashar ya sauke ajiyar zuciya ya na mai ci gaba da kallona,tsabar takaici na lumshe ido ina tunanin Fahad ɗina ina tsoron Ya Mustapha da baƙin abokinsa Ali su yi masa wani abun.Tuna irin dukan da Mubashar yayi masa ya saka na ƙara jin ɗaci a raina har ban san lokacin da na ce “Mugu!” sai kuma na fashe da kuka wiwi. “Ke lafiyar ki?” Mama ta yi saurin tambaya ta. Cikin kuka na ce “Mama ina son ganin Had don Allah a kai ni ɗakinsa” “Tuni an sallame an ɗora shi malama don haka ki nutsu bai asibitin nan” Mubashar ya faɗa ya na mai ƙaraso wa kusa da ni ya riƙe min hannun da aka saka wa ƙarin ruwa,cike da takaicinsa na kai bakina na gantsara masa cizo. Tamkar wata mahaukaciya haka na dinga cizon duk inda na samu a jikinsa hatta ƙirjinsa,duk yadda ya so kuma na tsaya na nutsu kamar yadda na lura amma na ƙi ba sa haɗin kai har sai da na cire robar ƙarin ruwan. Duk wani saurin ƙarfina na tattara na ture shi baya,cikin rashin sa'a kuma ni ma sai na biyo shi na faɗi kan ƙirjinsa kaina ya bugu da kansa.Mubashar kuwa da mugun sauri ya rumtse ido jin azaba ta ratsa kwanyayarsa don buguwa yayi da ƙarfen gado. Na yunƙura dakyar na tashi zaune kan ruwan cikinsa,“aiii!” ya saki ƙara da sauri na dire na zauna ƙasa ina kallon yadda goshinsa ke zubar da jini.Mama da likita suka shigo a tare hankali tashe,sai yanzu na lura ashe Mama ta fita. “Innalillahi ta jima ciwo ko? Likita duba min kwanyarta kar ace ta taɓu” Mama ta faɗa ta na mai nufar Mubashar wanda tuni ya tashi zaune. “Ni lafiyata lau kuma gida nake son zuwa” na furta cikin kuka. Sai da aka yi wa goshinsa bandeji ni ma likita ya duba ni kafin mu dawo gida.A falo na zube ina ta zuba wa Papa shagwaɓa sai dai ba ta je ko ina ba na ji ya na jadadda maganar Ya Mustapha “Yayan ki ya ce min abokinsa na son ki kuma da aure don haka zan baku dama ta biyu ke da Fahad ko ya kawo kuɗin auren ki ko kuma shi Ali ɗin ya kawo.Za a ɗaura aure in Allah ya so bayan kin gama karatu sai ki tare” “Papa Ya Mustapha ya hana Had ya shigo gidan nan fa,ɗazu ma sai da suka yi ta yin rikici da mai gadi” na faɗa kamar zan yi kuka. Papa ya ce “zan yi wa mai gadin magana” Tashi na yi na koma ɗaki,na kira Fahad bugu biyu ya ɗaga “Had don Allah ka yi haƙuri abin da ya faru,Papa kuma ya ce na sanar da kai ya amince da aurenmu don haka ka kawo duk abin da kafi ƙarfi a ɗaura mana aure in na gama karatu kuma sai in tare” “Ban shirya aure yanzu ba! A ƙara min lokaci ni da kaina zan tsara yadda auren zai kasance ba ƴan gidanku ba” ya na gama faɗa min haka ƙittt ya yanke kiran.Wani takaici ne ya rufe ni,ban san mine ne Fahad ke taƙama da shi ba duk wata hanyar tsiranmu sai ya daƙile ta na yi tunanin zai yi murna da hakan amma girman kansa da gadarar shi sun sa ya watsa min ƙasa a ido .Karon farko kenan da na ji na tsani soyayyarmu,tun ba yau ba na fahimci na fi sonsa fiye da yadda yake sona.Na ja wata ajiyar zuciya ina jin wani abu na min yawo a jiki yayin da kuma zuciyata ke raya min wani matakin da na tabbatar zan cutu amma ƙila hakan ne kawai zai sa Fahad ya shiga hankalinsa . FAHAD Ba ƙaramar jibga ya samu daga hannun Mubashar ba, wannan yasa ya kasa tuƙa babur ɗinsa.Ana cikin haka ne kuma Ramlah ta rugo da gudu ta na sanar da su Sharifa ta suma,duk a tare suka dugunzuma har da shi.Wurin ciciɓar ta ne ma ya fahimci kamar ya goce a hannu don har sai da ya saki ƙara,Mama ce ta basa umarnin ya biyo bayansu hakan yasa a asibiti aka duba hannun nasa bai wani jima ba kuma ya kira Kb ya zo ya ɗauke shi.Babur ɗinsa ma ya na can gidansu Sharifa, lokacin da ya zo ba ƙaramin tashin hankali Umma ta shiga ba.Ga jaririn da suka maƙala wa sunan Jamilu mai shegen kuka ne duk sai Umma ta ida rikicewa.Tambayar duniya ta yi wa Fahad amma ya ƙi sanar da ita gaskiya,a doli ta haƙura ta dai shimfiɗa masa tabarma tare da nemo masa lemu mai sayin.A gabanta ya ɗauki kiran Sharifa a yanzu,ya na kashe wa ya dubi Umma ya ce “ina son na yi kuɗi ko don na nuna wa iyayen Sharifa ba su suka baiwa kansu ba.Kin ji wani rainin hankali wai su za su tsara yadda aurenmu zai kasance,to na ƙi na je ɗin kuma wallahi sai sun san ni suka wulaƙanta” Umma ta ce “a'a kar ka yi haka! Tun da dai ku na son junan ku ai shi ne abu mafi muhimmanci...” ya tari numfashinta ya na mai cewa “wallahi tallahi ba su ga komai ba sai yanzu ma ne zai fara wahalar da Sharifa,sai sun yi da na sani sun zo su na bani haƙuri” “Mi za ka yi mata?” Umma ta tambaya da tsoro a fuskarta. “Kwantar da hankalin ki ban yi mata komai,kawai zan daina ɗaukar kiran ta kuma ni ma ba zan kira ta ba na san ba za ta juri haka ba” Sai a lokacin Umma ta samu natsuwa. A can bangaren Mubashar kuwa da zarar ya lumshe ido hoton Ali yake gani ya na shafa kumatun Sharifa.Ya ja dogon tsaki a fili ya na jin tsanar gayen,sai kuma ya saki murmushi tuna yadda moments ɗinsu ya kasance.Ya kai hannu ya shafi wurin da ya ji ciwo,wanda ba don ya rasa control ɗinsa ba lokacin da jikinsu ya haɗu da na Sharifa ba to da tabbas ba za ta iya ture shi ba.Da wannan tunanin ya ɗan samu sassauci ya na mai roƙon Allah ya nuna masa ranar da zai mallake ta. ★★★ Rana zafi innuwa ƙuna,duk yadda na yi ƙoƙarin share FAHAD na kasa kullum cikin tura masa saƙon soyayya da magiya akan ya zo mu yi aure nake amma a wofi an tsikari kakkausa.Ko kaɗan bai nuna ya ga ma kirana ballantana na san ran zai ɗauka,gefe guda kuma Ali sai baje min kolin na sa salon soyayyar yake.Kullum cikin bazata yake min, kyaututtuka tun ban nuna komai har na fara jin daɗinsu.A duk in ya samu sarari ya kan zo gida mu yi hira,ko kuma ya je can makarantarmu in lokacin shan iska yayi wani sa'in restaurant muke zuwa mu ci abinci in banda ra'ayin ya kawo min komai.A sannu a hankali muka fara shaƙuwa da shi har ta kai in bai zo ba zan ɗauki waya na kira na ji dalili,amma hakan bai sauya son FAHAD a zuciyata ba ya na nan daram. Muna tsaye ni da Ali ya na bani labarin lokacin da su na sabbi a aikin soja ya ce“ ina faɗa miki Habibaty mun ci kwakwa,abinci fa da zafinsa muke ci kuma ba zaune ake yi ba a'a muna motsa jiki in mutum ya kawo daidai farantin abincin ne ya damtsa ya ci” Na ƙyalƙyale da dariya na ce “ai kuwa ni ba zan iya aikin soja ba,to ya kake yi ka ƙoshi?” “Ke da na ga fa za a ƙwaren kawai na dinga zuba abincin a aljihu” ai kuwa nan ma dariya na ƙara yi ɗagowar ga da zan yi muka haɗa ido da Mubashar wanda a yanzu na ɗauke shi tamkar Yayana tsabar yadda Mama ta jawo shi a jiki ,don hatta abinci ma tare da ahalin gida yake ci sam ba za ka ɗauka bare ne ba don tuni an kawo ma wani sabon direba shi bai aikin komai sai zuwa Imam Malik in ya dawo ne yake koya min karatu . A take nutsuwa ta zo min,murya na ɗan rawa na ce “Ya Mubshar!” ba mu da tazara sosai na san ya ji abin da na ce,kawai sai gani na yi ya lumshe ido kafin kuma ya buɗe su ya ƙure ni da su kafin ya soma takowa har ya iso sallama a bakinsa ya miƙa wa Ali hannu suka yi musafaha tare da gaisuwa. “Babu karatu ne?” ya tambaye ni bayan ya dubi agogon hannunsa,tabbas na san da an shiga aji amma na ƙi faɗawa Ali don ban so ya tafi saboda in ya na min hira ina mantawa da damuwa ta. “Eh! A'a ban sani ba” na faɗa a ɗan rikice,Mubashar ya shafi gemunsa wanda a yanzu yake samun gyara kuma ya ƙara fito da kyawunsa sosai. “An kira ni ne an ce ba ki shiga aji ba ko zan san dalili?” ya sake watso min wata tambayar,sai na ɗan saci kallon Ali wanda da dukkan alamu bai ji daɗi ba. “Yanzu zan shiga” na faɗa da sauri ina juyawa saboda yadda Mubashar ɗin ya kafe ni da mayun idonsa,ina tafe ƙafafuna na harɗewa kamar zan faɗi har yanzu ina jin idonsa a jikina. Bayan tafiyar Sharifa, Mubashar ya ɗan yi gyaran murya ya ce “don Allah ka bar zuwa nan saboda hakan zai taɓa karatunta da ƙimar ta musamman in ka dubi kayan jikin ka” Ali ya dubi kansa,kakin soja ne yake sanye da su .Ya ɗan haɗe rai ya ce “mi kayan nawa suka yi ?” “Ba su yi komai ba” Mubashar ya faɗa kafin ya shiga cikin makarantar ya bar Ali nan tsaye shaye da mamaki.Direct ajin su ya wuce ya tabbatar ta shiga kafin ya je ya zauna zaman jiran ta,da ya ga lokacin tashi ya kusa ya kira sabon direban ya tabbatar masa ma tuni ya na kan hanya. Cours ake amma sam hankalina ya kasa nutsuwa,ina tsoron faɗan Ya Mubashar ɗin wanda a yanzu ya kasance malamina mai koya min karatun Addini.Ana gama darasi na fito ina raba ido don yadda zuciyata ke bugawar nan ya tabbatar min ya na nan bai tafi ba. “Ga ni a nan!” na ji muryarsa a bayana,na ɗan zabura tare da juyowa muka haɗa ido.Muƙur na haɗe yawu kafin na ce “ashe ba ka tafi ba?” “Um! Ba ki so gani na ba ko?” “A'a ni ban ce ba” “Tun yaushe Ali ya zo nan?” Sai da na sunne kai kafin na ce “bai jima da tafiya ba” “Ki ɗago ki ban amsa” Ƙin ɗagowa na yi saboda na san muddin na yi masa ƙarya zai gane in dai muna kallon juna ne,zip ɗin jaka ta na zuge na ciro waya ina ƙoƙarin kiran direba amma ya fige ta hakan yasa na ɗago.A take tsoronsa ya rufe ni ganin idonsa sun yi ja,murya na ɗan rawa na ce “Zan kira direba ne” “Ga shi a can ya na jiranmu” sai kuma ya soma tafiya,na take masa baya har muka isa ina kallonsa ya miƙawa direban kuɗi ya ce “ka shiga taxi” sai kuma ya karɓi key ya buɗe mota ya zauna. Jikina ne ya ɗauki rawa,rabon da na hau tuƙinsa an fi wata uku amma banda zaɓi haka na je na zauna a gaba ya figi motar kamar zai tashi sama maimakon ya ɗauki hanyar gida sai kawai na ga ya ɗauki wata.Tuni idona suka ciko da ƙwalla amma ban ce komai ba,kamar yadda shi ma yayi shirun sai hucin da yake fitowa daga ƙasan zuciyarsa.Mun yi tafiya mai ɗan nisa kafin mu isa wani wurin mai ɗauke da itace dayawa,a hankali yayi parking ya fita ya zagayo ya buɗe min.Na fito dakyar,duk ko ina innuwa ce ya nuna min wani dutse ya ce “zauna!” ban musa ba na zauna ɗin. Murya a ɗan dake ya ce “kin san abin da yasa na kawo ki nan?” Na girgiza kai,ya dafe saitin zuciyarsa ya ce “don na baki wani labari ne mai kama da naki wanda ya shuɗe wasu shekaru.Labarin wani kamilin saurayi da wata budurwa ƴar talakawa ” Ƙurrr na yi masa da ido ina kallonsa kawai,yayin da shi kuma ya ci gaba da cewa “wani saurayi ne suke haukan son juna shi da wata budurwa kullum su na tare in ta na makaranta haka yake bin bayanta,in an aike ta shi ne ɗan rakiya.Iyayenta da iyayensa sam ba sam ba son ganinsu a tare amma suka nace suka biye wa zuciyoyinsu.Ana haka ne shi saurayin mahaifinsa ya shirya masa zuwa ƙasar waje domin yin karatu,hankali tashe ya je kira budurwar ya sanar da ita haka ta kwaso jiki ta zo gidansu kasancewar dama Yayan ƙawarta ne saurayin yasa ta shigo gidan babu wata matsala sai kawai ta yi tsinke ɗakinsa” ya na kawowa nan sai ya tsaya ya na wani lumshe ido,“mugun son da take masa ya rinjaye ta har ta amince da shi yayi sanadiyar rabata da mutumcin ta.Sai bayan komai ya lafa ne suka farga,haka ya taimaka mata dai ta kimtsa ba tare da sanin ashe a wannan daren Allah ya ƙaddarar rabo ya shiga” “Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un ! Cikin shege?” kallona yayi kawai,“tashi mu tafi!” na miƙe da sauri na bi bayansa ina mai cewa “to ya aka yi gaba?” bai ban amsa ba har muka shiga mota. Kallonsa kawai nake har muka isa gida,da zan fita na ce “Ya Mubshar ka faɗa min mi ya faru mana” “Sai in an jima zan sanar da ke ,yanzu makaranta an koma akwai jarabawar da zan yi” Na turo baki kafin na fice,shi kuma ya ja motar ya tsaya bakin get sai da direba ya shiga kafin su wuce. Ina shiga ciki na zube falo ina faman yi wa Mama ƙorafin na gaji. “An dai kusa yin auren ki na ga ta rakin kin gaji can ai doli ki girka abinci da kuma aikin gida” cewar Mama. “Ni dai ban shirya ba sai..” ban kai ƙarshe ba Mama ta ce “in an jima iyayen Ali za su zo ki tashi ki tafi gidan Antyn ki” Tamkar aradu haka na ji,ko kafin na yi wa Mama tambaya tuni ta tashi.Ni ma ba shiri na wuce ɗakina sai a lokacin na tuna kuma wayata na ga hannun Mubshar.Toilet na faɗa na yi wanka, zuciyata sai matsanancin bugawa take a haka na fito na yi sallah na shirya cikin riga doguwa da hijabinta .Ƴar ƙaramar jaka na ɗauka na fito na yi wa Mama sallama,maimakon na je gidan anty ɗin kawai na cewa mai taxi ya kai ni Imam Malik. Bayan na biya shi ne na shiga daga ciki,sai kuma na rasa wane ɓangare zan bi tsabar girmanta ina nan ina shawagi a ciki har aka fito sallar Asar nan na ware ido ko Allah yasa na ga Mubshar ɗin sai dai abun takaici duk mazan jallabiya fara ce da su.Tuni idona ya fara kawo ruwa,kamar daga sama na ji an ce “ Ifa ” har ban san lokacin da murmushi ya suɓuce min don shi kaɗai ke kirana a haka. Ina ɗan waigawa idonmu ya sarƙe cikin na juna,ban taɓa yi masa kallon ƙure ba sai yau dogo ne sosai mai faɗin ƙirji.Ya na da doguwar fuska da dogon hanci,idonsa madadaidaita ne ba su fiya girma ba,bakinsa na ɗauke da laɓa masu kauri baƙaƙe wanda sajensa ya ƙara masa kyawu.Ban san ya iso gare ni ba sai da na ji ya busa min iskan bakinsa,na lumshe ido hakan ya baiwa ƙwallar da ta ciko idona damar saukowa kan kumatuna.Tattausan hannunsa na ji cikin nawa ya na mai cewa “zo nan!” haɗi da jawo ni gefe,sai a lokacin na buɗe ido. “Mubashar wace ce wannan?” a tare muka juya sai na ga ashe Yayan Mama ne sheik Mohammed. Gaishe shi na yi sai na ji ya ce “Kamar Sharifa nake gani” Na ce masa “ni ce!” sai na ga ya kalli hannunmu da ke cikin na juna,sai a lokacin Mubashar ya sake ni. Sheikh Muhammed yayi tafiyarsa ya na mai cewa “lokacin sallah yayi ta je ɓangaren mata ta yi alwala,in an gama kuma ina son ganin ka a office ɗina” Na ja wata wawiyar ajiyar zuciya ina saƙa wani abu a raina wanda ban sani ba ko idona ne ba su gane min daidai ba.... [26/04 à 09:57] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Page 6 Ɓangaren mata Mubshar ya kai ni ya na mai yi min magana cikin taushin murya “ki nutsu ki yi sallah in kin gama ki jira ni a nan cikin masjid zan zo na neme ki kar ki je ko ina kin ji ko?” Tsakiyar idonsa na kalla ina mai jinjina masa kai,kamar wata ƙaramar yarinya da ya juya zai tafi na tsayar da shi .“Ya Mub...shar don Allah kar ka jima ban san kowa ba a nan” ya sakar min murmushi kafin ya tafi .Toilet na shiga na ɗauro alwala sannan na shiga masjid ɗin mai cike da mata duk sun sha manyan hijabai har ƙasa.Na shiga sahu na yi tsaye har aka tada sallar,bayan an gama da ɗaiɗaya duk suka fita na yi saura ni ɗaya kawai sai faman zuba wa ƙofa ido nake ina jiran shigowar shi. An ɗauki lokaci mai ɗan tsayi kafin ya shigo,da mugun sauri na miƙe wani irin abu nake ji kamar ƙaramin yaro mai neman rarrashin uwa.Wannan yasa saura ƙiris na faɗa jikinsa yayi saurin tare ni da dukkan hannuwansa,murya a sanyayye ya ce “mu je na kai ki gida” Idona ya ciko da ƙwalla,ba haka na so ba ! Na yi tunanin zai tambaye ni dalilin zuwana a nan ɗin amma haka na bi bayansa har muka isa parking special.Wata haɗaɗiyar mota Benz na ga ya buɗe min gidan gaba,haka na shiga na zauna kafin shi ma ya shiga ya tuƙa mu. “Ya jikin ki?” na ji ya furta ƙasan maƙoshi kamar ba shi ne yayi maganar ba sai yanzu na tuna ma da kaina na ciwo.Murya na ɗan rawa na ce “babu sauƙi!” ƙuuuu ya ja ya tsaya,da idonsa ya kafe ni kafin ya ce “mine ne ainahin abin da ke damun ki?” kuka na fashe masa da shi kafin na ce “aure za su min Yayaaaa!” Bai ce komai ba sai ya ci gaba da tuƙi,sai da ya ɗauki lokaci kafin ya ce “ba ki na son shi ba ?” “A'a ni kawai burge ni yake yi, amma zuciyata Fah....” ko kafin na ida ya buga min tsawa “ya isa! Kar na sake jin kin furta sunansa domin ba mutumin kirki ba ne bai son ki” “Ya na sona kawai dai bai da kuɗi ne,ina da tabbacin in ya samu kuɗi sai ya fi faranta min rai da su fiye da kowa” na furta ina jin wani abu na tsira min a zuciya. “Saboda ki faɗa min ki na son shi ne kika zo wurina?” “A'a gidan anty Maimuna za ka kai ni kuma ka ban wayata ” “Ba zan bayar ba!” ya furta hankali kwance daga nan bai sake furta komai ba har muka isa ƙofar gidan,sai a lokacin na tambaye shi “motar wace ce wannan?” Ya ban amsa kai tsaye “ta Sheikh ce” “Mine ne ya faɗa maka to? Wace magana kuka yi da ya ce ya na son ganin ka?” “In ji tsoron Allah in girmama wacce nake so kar na yi amfani da so wurin cutar da ita,sai kuma ya ce na mayar da ke gida” ya bani amsar ya na kallona,na ɗan haɗiye yawu kafin na ce “Ya Mubshar har yanzu ba ka taɓa nuna min budurwar ka ba ko a hoto ne” Ya ce “mine ne amfanin nuna wa mutum kansa?” “Ban gane ba?” “Wuce ki shiga ciki muna da darasi zan koma makaranta” “Amma Yaya don Allah ka sanar da ni ya budurwar nan ta yi bayan ta gano ta na ɗauke da ciki?” “Ƙawarta ta fara sanar ma,ta bata shawarar a zubar ta ƙi.A ƙarshe dai tun ta na ɓoyo har iyayenta suka sani,ba su jinkirta zuwa gidan su saurayin ba amma fafur suka ƙi amincewa da zancen suka ce ƙazafi ne ta yi wa ɗansu tun da kowa ya san ustaz ne” “Kenan cikin ta zubar?” “A'a barin gidan iyayenta ta yi ta je can wani gari ta raini cikinta har ta haifu” “To amma ya labarin su har yanzu su na raye ita da ɗanta?”na tambaya ina jin tausayin su,sai da ya yi min wani kallo mai wuyar fassarawa kafin ya ce “ga yaron da aka haifa zaune tare da ke!” kallon ban gane ba na fara binsa da shi kafin na waro ido na ce “wai kai? Kai ne aka haifa? Ka na nufin labarin Ammy ka ban?” Bai bani amsa ba kawai dai ya jingina ga kujera haɗi da lumshe ido,daga inda nake ina jin yadda zuciyarsa ke mugun bugawa.Cikin wata irin murya ya ce “ wannan dalilin yasa nake jin takaici in na ga budurwa na haukan saurayi musamman irin FAHAD wanda kullum burinsa ya kusance ki.Ifa na rantse da Allah da ace na yi dogon karatun boko da tabbas zan fito alƙalin mata ne,duk wanda na samu da laifi kwatankwacin hakan da Allah kawai ya san hukuncin da zan yi masa” “Ka yi haƙuri!” na furta dakyar,ya buɗe idonsa ya watso min su kamar daga sama ya jefo min tambayar “ki na sona?” ji na yi kamar ya buga min guduma,ban basa amsa ba kawai na ɓalle murfin mota na fita da gudu na shiga gidan ina jin wani iri a jikina. MUBASHAR Ya bi bayanta da kallo ya na jin wani irin takaicin kansa ,da ya kasa riƙe sirrin zucinsa har ya sanar da ita ya na sonta.Dakyar ya iya jan mota ya koma makaranta,ya na isa ya wuce aji don ya san tuni Sheikh Muhammad na ciki. Murya kamar ta maras lafiya yayi sallama a bakin ƙofar aji, Sheikh ya juyo ya dube shi kafin ya amsa tare da basa izinin shigowa.Mubashar ya je ya zauna mazauninsa,sam hankalinsa bai wurin ballantana har ya fahimci abin da ake a haka har aka gama darasin.Ya miƙe ya nufi Sheikh da ke zaune ya na duba system ɗinsa,“ga key ɗin motar” ya faɗa cikin sanyi. “Ka riƙe shi gun ka” Sheikh ya basa amsa ba tare da ya ɗago ya dube shi ba. “Na kai gida?” “Ka tafi da ita ka dinga hawa” ya faɗa wannan karon ya na mai ɗagowa ya kalle shi,da sauri Mubashar ɗin ya sunne kai. “Lafiya ? ” “Alhamdullah!” ya faɗa domin ɓoye sirrinsa. “Okay ka tafi” “Na gode” ya faɗa kafin ya fice,yau dai ga shi an basa mota special don ya dinga hawa amma sam bai jin murna.Dakyar ya isa gida,nan ya ƙara tarar da wani sabon tashin hankalin yadda mutane suka cika tsakar gidan ga kuma akwatina jere ras. “Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un !” Mubashar ya motsa laɓansa,kasa fita yayi daga cikin mota haka ya zauna ya na kallon yadda komai ke wakana.Can mata suka fito daga ɗaki su na rangaɗa buɗa wacce ta kusa tarwatsa zuciyarsa, Mubashar ba shi ya fito daga cikin mota ba sai da ƴan kawo lefe suka watse.Ya na fitowa kuma ana kiran sallar magrib.Sashensa ya nufa ya je ya yi wanka ko zai ji sanyi kafin ya ɗaura alwala ya wuce masjid,bayan an gama sallah ne ya wuce can ciki ya gaishe da su Mama. Papa ne ya sanar da shi zancen kawo lefen,ya yi jarumtar yaɓo murmushi a fuskarsa ya yi doguwar addu'a kafin ya miƙe zai tafi Mama ta tsayar da shi “ka zauna ka ci abinci tukuna,yau ya aka yi kuka taso da wuri na zata sai an yi sallar isha'i za ka dawo” “Dama ina tsayawa ne don ƙara bibiyar abin da aka yi mana” ya bata amsa,Mama ta ce “au! Shi yasa zo zauna na zuba mana” “A'a ban jin yunwa! Yanzu ma fita nake son yi” “Ok in ka dawo sai ka ci” Da haka Mubashar ya fita,mota ya shiga ya duba yawan petur ya ga kusan ma tankin cike yake.Kawai ya ɗauki hanyar Tilabery,gudu kawai yake shaɗaɗawa sai ya ɗauki wajen awa uku kafin ya isa. Ammy na kwance ta na jan casbi yayin da Fadila ke yi mata matsa ƙafa kawai sai jin tsayuwar mota suka yi.Babu jimawa kuma Mubashar ya shigo,gaban Ammy ya zube wacce tuni ta tashi zaune kasancewar akwai hasken lantarki ta gane shi. “Subahanallah! Yaron kirki mine ne haka?” bai iya cewa komai ba kawai ya kwanta ya ɗora kansa kan cinyarta kafin ya ɗora hannunsa saitin zuciyarsa ya na fitar da wani huci. “Fadila ɗebo min ruwa masu sanyi a randa ” cewar Ammy,ta yi saurin miƙe wa hankali tashe ta ciko moɗa ta kawo Ammy ta karɓa ta yi tofi ciki kafin ta soma yayafa masa su a jiki a ƙarshe ta buɗe bakinsa ta fara basa ya na sha.Ajiyar zuciya kawai yake saukewa,“ɗauko min fanka ki kunna” Ammy ta ƙara faɗa,Fadila ta sake miƙewa ta je ta ɗauko ta kunna.Iska mai sanyi ya soma fita,Mubashar ya lumshe ido kawai tun ya na jin muryar Ammynsa na yi masa addu'o'i har bacci ya ɗauke shi. A daren dai babu wanda ya rumtsa,Fadila baiwar Allah sai faman zubar da hawaye take yayin da Ammy ke ta jan casbi.Wuraren ƙarfe biyun dare Mubashar ya farka,sai da yayi ɗan jimmm kafin ya fahimci inda yake.Ya tashi zaune kafin kuma ya miƙe ya je yayi alwala,sallar isha'i yayi sannan ya zo gaban Ammy ya ce “ina wuni Ammy na same ku lafiya?” “Alhamdullah! Tashi ga shimfiɗa can ka shiga ka kwanta” ta nuna masa gidan sauro wanda tuni an ɗaura shi,bai musa ba ya je ya shige.Lamo yayi ya na tunanin yanzu Sharifa aure za ta yi ta bar shi? Ita kuwa Ammy jan Fadila ta yi su ma suka je suka kwanta. A can Niamey kuwa sai dare ne Sheikh Muhammad ya samu labarin zancen kawo lefen Sharifa.Hankalinsa in yayi dubu to ya watse,duk yadda ya so kiran Mubashar kuma wayar ba ta shiga.Da ya kira Mama kuma ta tabbatar masa tun da ya fita bai dawo ba,tsohon hawan jininsa ne ya ji ya na son tashi.Tasbihi kawai yake yi amma ya kasa nutsuwa,matarsa Hajiya Balkis tambayar duniya ta yi masa amma ya ƙi sanar da ita damuwarsa.Ya jingina jikin kujera ya na roƙon Allah a zuci ‘ Ya Rabb kar ka jarabce ni da abin da ba zan iya ɗauka ba,a baya na rasa farin cikina ina tsaka da maraici ka jefo min gudan jinina tsokata wanda nake jin ko cinaka ban so ya cije shi ballantana wani abu ya same shi.Allah ka tausaya min ka tsare Mubashar a duk inda yake,ka sassauta masa wannan jarabawar’ haka yayi ta yi sanfarorin addu'o'i har garin Allah ya waye. Ƙarfe bakwai na safe Hajiya Balkis ta shaida masa zuwan Mama,ya bada izinin ta shigo. Ta shigo ta zauna gabansa,ta rasa ta ina za ta soma faɗa wa Yayan nata har yanzu fa Mubashar bai dawo ba don bai kwana gidan ba. “Amma ai kin san ya na son Sharifa ko? Shi ne kika yarda wani ya kawo sadakinsa har aka ɗaura auren duk a jiya....” Sheikh Muhammad ya faɗa ya na jan zuciyarsa da ke barazanar faso ƙirjinsa ta faɗo,Mama da ba ta fahimci abin da yake nufi ba kawai ta zuba masa ido. “Karo na biyu kin ruguza farin cikina! Kin kasa kulawa da amanar da na damƙa miki kin kyauta Aghaisha!” ya faɗa ya na ɗan yin tari haɗi da dafe ƙirji. “Yaya wallahi ban taɓa sanin Mubashar na son Sharifa ba! Sannan tun kafin na gano ɗan Hawa Kulu ne na ƙudirta a raina zan aura masa Sharifa. A ranar da na je ɗakinsa zan nemi ra'ayinsa akan auren a ranar ne kuma na ga hotunan Hawa Kulu, wannan dalilin yasa na ɓoye saboda muddin ya san ni ce silar barin mahaifiyarsa garin nan zai iya tsana ta ma” “Wannan duk ba hujja ba ce Aghaisha,a ranar da kika sanar da ni ina ce dai a tare muka yi alƙawarin nema masa duk wani farin cikin rayuwa ta yadda ko da ya san mu ahalinsa ne ba zai guje mu ba,amma yanzu mi kika yi? Farin cikinsa wacce nake hango ita ce nutsuwar shi kika ɗauka kika bai wa wani bare” Cikin kuka Mama ta girgiza kai ta na mai cewa “ wallahi ba da sa hannuna aka yi auren nan ba ,komai Mustapha ya tsara shi da mahaifinsa kuma...” da sauri katse ta ya na cewa “ya isa haka! Ki tashi ki tafi ban son jin komai da ace ki na son Mubashar ɗin ya aure ta ai kin sanar da ni zancen kawo lefen amma kika ƙi har sai da aka ɗaura” sai kawai Sheikh Muhammad ya soma tari jini ya soma zubo wa ta bakinsa,hankali tashe Mama ta fita ta sanar nan yaran da suke karatu gidansa suka zo suka ciciɓe shi aka kai shi asibiti. Cikin ikon Allah dai aka samu aka daidaita igiyar numfashinsa,sai dai an hana kowa shiga ɗakin da yake.Mama kuwa sai gwada kiran Mubashar take amma wayar a kashe ,haka ta yi ta yi har Allah yasa ta same shi bayan ya kunna wayar.Cikin kuka ta sanar da shi Sheikh bai da lafiya,ya kuma shaida mata zai zo. A bangaren Ammy ba ta takura Mubashar ba sai ya faɗa mata abin da yake faruwa ba.Kawai dai ta yi masa nasiha mai ratsa jiki,wanda a ƙarshe ya sanar da ita budurwar da yake tsananin so ce aka aurar.Murmushi kawai ta yi nasu na manya ba don wai ba ta ji ɗacin haka ba a'a sai don basa ƙwarin gwiwa tare da nuna masa ba komai ne da kake so ba kake samu.“Dama haka lamarin Allah yake,sai ka so abu wanda shi ɗin ba alkhairi ne gare ka ba in ka yi dace Allah na sonka sai ya kuɓutar da kai daga sharrinsa.Ka yi haƙuri Allah zai baka wacce ta fi ta” Ammy ta faɗa ta na kallon Fadila, Mubashar ma haka ya na shirin magana ne kiran Mama ya shigo ta sanar da shi zancen rashin lafiyar Sheikh. Da sauri ya miƙe ya ce “Ammy zan koma sai in mun yi waya” har bakin motar suka yi masa rakiya ,ya sosa ƙeya ya ce “sai dai ban kawo muku komai ba” Ammy ta ce “ai ba mu buƙatar koman ,kwanaki ma an fidda zakka an kawo mana duk kayan abinci kuɗin da ka aiko kuma su na nan ko dala ban kashe ba har ina cewa ko na sayo ma Akuya a kiyaya ma” Mubashar ya ɗan saki murmushi kawai,nan dai yayi musu sallama kafin ya ɗauki hanyar komawa Niamey. SHARIFA Furucin Mubashar abu ne da ban yi tunani ba,ko kaɗan ban taɓa kawo hakan a raina ba wannan yasa kawai na gudu na barsa.Da na shiga ciki kuwa kuka kawai nake yi,anty Maimuna ta yi tunanin na murna hakan yasa ta yi ta buɗa ta na min waƙar amare.Sai da na gaji don kaina sannan na daina,sallah kawai na iya yi amma sam na kasa cin abinci.A gidanta na kwana da tunanin Mubashar,da safe yunwa ta tayar da ni na je na ɗora ruwan zafi na haɗa Lipton da citta da menthe na sha.Ina nan zaune falo Anty Maimuna ta fito ta na sanar da ni Sheikh bai da lafiya,kuma Mubashar bai kwana gida ba. “Wa ya faɗa miki bai kwana gida ba?” na tambaya hankali tashe. “Mama ce! Zo mu haɗa abincin da za mu kai daga asibitin sai mu wuce gida na ga lefe” Na ja tsuki na ce “wai lefe!” anty Maimuna ta saki baki ta na kallona,na ce “ni fa ban shirya aure ba gaskiya karatu ne gabana ” “Sai ki je ki sanar da Papa,ko kuma bari na kira Ya Mustapha sai ki faɗa masa” ta na gama faɗa ta wuce kitchen,ni kuwa ɗakinta na wuce na ɗauko wayarta kiran lambar Mubashar na yi ta yi amma ya ƙi ɗagawa.Ina nan kwance ina saƙe-saƙe har anty Maimuna ta zo ta sanar da ni na je na shirya .Wanka na yi ta fiddo min doguwar riga fara sol na saka ,hijabin na wurgar na ce “ki ban kallabin rigar mana” “Ki na matar auren?” “Don Allah Anty ki ban” Ta miƙo min na ɗora shi a kai,sannan muka fita ita ke ɗauke da ƙaramin basket ɗin abincin har muka je bakin titi muka samu taxi. Tun da muka ɗauki hanyar asibitin gabana ke wani irin bugawa,har muka isa.Muna shiga ciki na tsaya cak ina kallonsa ya na mai fitowa daga cikin mota ,anty Maimuna ce ta kira sunansa sai ya juya muka haɗa ido da shi.Ban sani ba ko idona ne amma gani na yi kamar ya rame,ban taɓa ganinsa da uwannan kayan na jikinsa ba duk da ba wasu tsadadi ne ba amma ni dai ya min kyau . Iskan da ya fara kaɗawa ne ya sa na lumshe idona,sam ban damu ba da kallabina da ya sauka daga kaina ba duk da ina jin gashina na taɓa min fuska alamun iska na kaɗa shi. “Sai ki buɗe idon don ya tafi” na ji muryar Anty Maimuna,ai kuwa ina buɗe wa babu Mubshar.Takaici na ji,a haka muka ƙarasa ciki inda muka tarar da danginmu an dubiya sai dai fa shi Sheikh ɗin an ɓoye shi. Ina ƙoƙarin wuce wa don samun wurin zama na take ƙafarsa,wajen na yi sauri na janye sulɓi ya kwashe ni na faɗi ƙasa na buge baki na saki ƙara ina mai ɗagowa na kalli Mubshar da ya ƙi tare ni har na faɗi....... *Jummah Mubarak*😶‍🌫 [28/04 à 10:15] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Page 7 A kunyace na miƙe ina shafar inda na buge ɗin ko zan ga jini amma babu komai.Kowa yayi min sannu amma banda shi,gefen anty na zauna ina satar kallonsa sai wani ƙara haɗe rai yake ya na haɗiyar yawun da ban san ko na mene ba kawai dai ina ganin maƙogoronsa na motsawa.Ya juyo muka haɗa ido sai kuma ya ƙi kauce wa kallona ni ma haka na yi masa ƙur,yadda ya kafe bakina yasa na shafa gun sai na ji ya ɗan kumbura.Na shagwaɓe fuska kamar zan yi kuka ina mai ci gaba da kallonsa,ya kawar da kai gefe.Ana cikin haka ne kawai muka ga an turo Sheikh Muhammad bisa gadon maras lafiya an nufi wani ɗakin da shi duk sai muka tashi muka bi bayan su. Idonsa biyu sai kllonmu yake ɗaya bayan ɗaya,Mubashar ne ya matsa kusan kansa ya na cewa “Sheikh ya jiki?” bai basa amsa ba sai hannunsa da ya kamo ya na ɗan matsa shi.Mubashar ya buɗe baki zai yi magana Sheikh ya tari numfashinsa “alhamdullah ai na samu lafiya! Ya kake ? Ina ka tafi na yi ta kiran wayar ka amma ba ka ɗauka ba ka sa duk hankalina ya tashi?” yadda Sheikh ke magana cike da kulawa yasa tsikar jikin Mubashar tashi sai yake jin ina ma ace wannan ɗin mahaifinsa ne? Rana ɗaya tak da bai ji ɗuriyarsa ba ya ɗaga hankali amma shi mahaifinsa bai taɓa ma nemansa ba duk tsawon rayuwarsa. Sheikh ya katse masa tunanin da yake ya ce “ kar ka sake yin nisa da ni ! Kai ne na fi jin farin ciki in ina tare da kai kaf cikin yarana ” Mubashar ya lumshe ido,sanin duk yaran da Sheikh ɗin ke magana ba biologique ƴaƴansa ba kawai zumuncin musulunci ne . “In sha Allah Dadd...am Sheikh ” Mubashar ya furta a rarrabe,saura ƙiris ya kira shi da Daddy amma sai kuma ya canza . Sheikh ya ɗan murmusa ya ce “ya ammyn naka ta na lafiya ko?” Ya jinjina kai ya ce “lafiyarta lau” Da taimakon Mubashar ya tashi zaune sai a lokacin ya fara amsa gaisuwarmu amma banda ta Mama,ina lura kuma da ita sai ta sunne kai. Hajiya Balkis ce ta shigo sai baza ƙamshi take,direct kusan mijinta ta je ta zauna ta na mai tambayarsa jikinsa ya amsa sama-sama kafin ya dubi Mubashar ya ce “ina son jus!” da to ya amsa kafin ya fita ni ma na take masa baya ina kiran sunansa amma yayi banza da ni haka na koma a kunyace. A nan bakin asibiti Mubashar ya siyo jus ɗin ya dawo,anty Maimuna ce ta bayar da kofi aka tsiyaya masa ya sha bayan nan ya lumshe ido kafin ya ce “Mubashar kira min likita ya zo ya sallame ni ” “Wane irin a kira likita ka ga kuwa halin da aka ɗauko ka? Kawai ka bari har ka ƙara samun lafiya” cewar Hajiya Balkis wanda hakan ne ya tsayar da Mubashar, Sheikh ya dube shi kallo irin mi ka tsaya jira shi kuma ya ce “da dai ka ƙara haƙuri zuwa an yamma” “To Allah kai mu” Da rana abincin da muka kawo ne aka zuba aka ci,wanda ni sam na kasa ma tantance daɗinsa saboda yadda Mubashar ke wani hura min hanci sai shan ƙamshi yake.Bayan sallar azahar ne muka wuce gida ni da anty Maimuna,a hanya take tambaya abin da ya haɗa mu da Mubashar amma na ƙi bata amsa.Da muka isa gida haka ta yi ta duba kayan da ke ciki ta na yabawa ni dai ina gefe ina kallonta haɗi da tunanin wai yanzu gaske na zama matar Ali. A can asibiti kuwa yamma na yi likita ya sallame Sheikh Muhammad bayan an yi masa gwaji an ga jikin nasa yayi sauƙi sosai. A mota Mubashar ne ke tuƙi, Sheikh na zaune gefensa a can baya kuma Mama ce da Hajiya Balkis hira suke kan zancen lefen Sharifa da aka kawo ita Hajiya Balkisun ce ke sanar da Mama ai Ali ɗan ƙawarta ne da dalilin da ya hana ta zuwa wurin kawo lefen. “Amma Sharifa ta yi dacen miji don Ali babu ruwansa da ƴan mata duk kuwa kuɗinsa” Mama dai ba ta ce komai ba sai murmushin yaƙe,“amma ba da ita zai tafi ba ko? Ko da yake na ji uwarsa na cewa a bari sai Sharifar ta gama karatu ban sani ba ko Ali ya yarda”yadda Hajiya Balkis ta ƙure Mama da ido yasa a doli ta bata amsa da “juma'a mai zuwa za ta tare don ba wani babban...” maganar ce ta yanke sakamakon sakin mota da Mubashar yayi ya na ta ƙoƙarin danne burki amma ya kasa sai da Sheikh ya taimaka masa.Cak motar ta tsaya, Mubashar ya ja wani dogon numfashi kamar ransa zai fita kafin ya aro jarumta ya lalubo nutsuwa ƙira'a ya saka ya ƙure volume kafin ya ci gaba da tuƙin. Sheikh ya juya ya kalli Mama kafin ya maido dubansa kan titi,lokaci zuwa lokaci kuma ya na ankare da Mubashar har suka isa gida.Da taimakonsa Sheikh ya isa har ɗakinsa,Mubashar zai fita amma ya tsayar da shi ya na mai cewa “ka je ka yi wanka wani zai zo ku tafi wani gun ” “To bari na je gida” Sheikh ya rumtse ido tuna har yanzu fa Mubashar gidan Mama yake da zama,“ok ka yi sauri ” Mubashar na fitowa Mama ta miƙe suka fita ,shi ya tuƙa ta har gida amma babu wanda ya cewa wani komai. Wanka yayi ya shirya kafin ya koma can gidan Sheikh ɗin,tuni mutumin da za su tare ɗin ya zo. “Ina katin ɗan ƙasar ka yake?” mutumin ya tambaya, Mubashar ya fiddo ya nuna masa sai suka yi wa Sheikh sallama suka fito. Shi ke tuƙi Mubashar na gefen shi,sai nasiha yake yi masa har suka isa inda ake paspo ba su wani ɓata lokaci ba aka yi wa Mubashar duk abin da ya dace kafin a sanar da shi nan da kwana biyu ya dawo ya karɓa. Mutumin ya maido shi gida,sai a lokacin Mubashar ya samu lokacin yin tunanin da bai yi ba .Yadda Sharifa ta bugu ba ƙaramin zafi yayi masa ba amma sanin ta haramta gare shi yasa bai yi yunƙurin tare ta ba.Hawaye suka ciko idonsa ji yake kamar yanzu ne Mama ke cewa juma'a mai zuwa za a kai Sharifa gidan wani ƙato namiji wanda ba shi ba.Rurin wayarsa ne yasa shi dawowa hayyacinsa,Ammy ce da sauri ya ɗaga . “Ina ta jira ka kira ni amma shiru,ya ne ka sauka lafiya ya mai jikin?” “Da sauƙi Ammy,har ma mun dawo gida” “To ka bani shi na yi masa ya jiki” “To kashe in na shiga bangaren shi sai na kira ki”cewar Mubashar kafin ya fito daga ƙarƙashin innuwar mangoro ya wuce ciki. A zaune ya tarar da Sheikh a falo ya na duba wasu takardu,cikin girmamawa ya sanar da shi Ammy na son magana da shi. Sai da yayi ɗan jimmm kafin ya amince, Mubashar ya kira bayan Ammy ta ɗaga ne ya miƙa masa,“assalamu aleykum ustaz ya gida ya ƙarfin jikin?” sai da Sheikh ya lumshe ido saboda jin muryar da ya jima ya na jin ƙishirwar ta ,“Alhamdullah jiki yayi sauƙi na gode sosai ” ya furta muryarsa na rawa. Ammy ta ce “ni ke da godiya Alhaji , Allah ƙaro afuwa yasa kaffara ne” ya amsa da “amen Ya Rabb na gode!" Kafin ta miƙa wa Mubashar wayar ba don ya gaji da muryar ba a'a sai don jin wani yanayi wanda ya tunatar da shi ashe har yanzu namiji ne shi. “Ka tsaya ina son yi magana da kai” Sheikh ya tsayar da Mubashar da ke ƙoƙarin fita “ammy zan kira ki daga baya” bayan ya kashe kiran ya saka wayar aljihu sai ya zo ya zauna gabansa. “Ina son fitar da kai waje domin ci gaban karatun ka wace ƙasa kake son zuwa?” Sheikh ya tambaye shi . “Duk wacce ka zaɓa ta yi” “Zaɓin ka shi ne nawa” Sheikh ɗin ya faɗa ya na tsure shi da ido kafin kuma ya turo masa takarda mai zanen ƙasashen duniya. Idon Mubashar suka ciko da hawaye,wai yau shi ne ake neman zaɓinsa domin zuwa wani gun da mota ba ta zuwa sai jirgi kamar ba shi ne almajirin nan ba wanda yake kwana bakin titi. “Daddy ka zaɓa min” ya furta muryarsa na rawa, Sheikh ya saki wani murmushi mai sauti ya na jin zuciyarsa fara sol Mubashar ne farkon wanda ya kira shi da sunan Uba duk da Sheikh yaransa ke kiran shi. Ya sauka daga kujera ya rungume shi ya na bubuga bayansa “ya isa haka! Yi shiru zan zaɓa ma ai dama haƙi ne na Uba ya aika ɗansa wurin da ya dace da shi” Hajiya Balkis da ta fito daga kitchen tun ɗazu ta taɓe bakinta kawai kafin ta wuce ɗakinta baƙin ciki fal zuciyarta . Tsawon lokaci Sheikh ya sake shi suka koma zancen karatu ya na yi masa tambayoyi shi kuma ya na basa amsa. FAHAD Ji yake matakin da ya ɗauka shi ne daidai,duk da kuwa ya na cutuwa da rashin Sharifa.Iya romance kawai ke shiga tsakaninsu amma ya fi samun nutsuwa da ita kan sauran ƴan matansa da suke sheƙe ayarsu. Sannu a hankali soyayyar shegen ɗansa ke ratsa zuciyarsa,har yau ba a yanka masa rago ba sunansa dai Jamilu.Kusan kullum ya na fita aiki don samo kuɗin sayen madara,babur ɗinsa kuwa tuni ya aika abokinsa Kb ya ɗauko masa shi a gidan su Sharifa. Yau ya na zaune a gida ya na hutawa kwatsam Kb ya aiko masa hoton Sharifa da Ali ga akwatinan aure a tsakiya.Zumbur ya miƙe zuciyarsa na bugun tara-tara,ya mirza ido ya fi sau goma don tabbatar da ko idon ne nasa ke masa gizau amma tabbas Sharifar dai ce .Sam bai taɓa tunanin ko saurayi ta saurara ba ballantana ta kai su da zancen aure. Karon farko kenan da ya kira ta tun bayan da uban dukan da ya sha,sai da ya jera kira wajen bakwai kafin a ɗaga,FAHAD dama tuni zuciyarsa ta yi rauni kawai sai ya fashe da kuka ya na cewa “Rifa dama akwai ranar da za ki manta soyayya ta har ki amince da auren wani? Wallahi duk duniyar nan babu wanda ya fi son ki sama da ni har su munafukan iyayen naki masu hure miki kunne ki na ji na ko? Don Allah kar ki amince na san tabbas auren doli ne za su miki ni kuma da na bar sauraren ki shine kika amince,to ki yi haƙuri ki fito mu gudu mu....” Mubashar da zuciyarsa ke tafarfasa ya yi saurin katse shi “kai banza ka cika min kunnuwa da shirmen ka,alamu sun nuna ka manta dukan da na yi maka har yasa ka buɗe ƙazamin bakin ka kake wani cewa ta fito ku tsere to tsaya na faɗa maka billahil azim ko ka yi saurin cire wannan banzan tunanin daga kan ka ko kuma haɗuwa ta da kai hummmm” sai kawai kashe kiran. Fahad ya kalli wayar ya na ƙara jin wani tashin hankalin,hoton ya sake dubawa ya ga dai ba na Mubashar ba ne wannan soja ne. Babu shiri ya fito ya zuri takalmi kamar wani mahaukaci haka ya ɗau mashin ya nufi gidan su Sharifa.Yayi niyyar ko kirɓin gumba za a yi masa sai ya je,ya na shiga layin ya ga motocin sojawa su ma duk sayen suke da kakin soja wanda babu tantama abokan angon ne.Gefe guda kuma ƙawayen amarya ne kowacce ta ci ado,can ya hango Ramlah wacce yake jin haushinta don ya san babu ta yadda za a yi ace ba ta san an kawo kuɗin auren Sharifa ba ga dukkan alamu ma har an fara shagalin biki. SHARIFA Tamkar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka na koma,duk wani shirye-shirye ƴan gida kawai ke yinsa.Mama ma sam ba ta wani damu da ta yi min gyara ba, babu abin da take ban na sha ballantana gyaran fata.Yau muna ranar Alhamis wacce ita ce jajibir ɗin ranar tarewa wata,anty Maimuna tun safe ta zo ta shafa min dilka a dukkan jikina haka ta dinga haɗa min kayan gyaran fata ina wanka za ta yi min wani.Tuni na yi fresh na yi kyau,da na dubi kaina ga madubi sai da na ji takaicin ina ma gidan Fahad ne za a kai ni ba na Ali ba? Wuraren ƙarfe biyar na maraice duk ƙawayena suka hallara gidanmu don sai yau ne kawai za su yi réunion su da abokan ango wanda a bakin anty Maimuna ne nake samun labarin shi ma zai shigo gari. Ina nan zaune cikin dangin Mama da suka zo tun daga Agadas sai ga Ya Mustapha ya shigo,gaishe su yayi kafin ya mayar da hankalinsa kaina ya ce “ki fita zuwa lambu Ali na son ganin ki” kai kawai na jinjina masa amma banda niyyar miƙewa. Tun da aka kawo lefe ba mu yi magana da shi ba,don Ya Mubashar ya ƙi ban wayata hasali ma ya bar barin hanyarmu ta haɗu da na sanar da Mama kuma ta yi kamar ba ta ji ba dole na barsa da ita. “Ke ba magana nake yi miki ba?” ya Mustapha ya daka min tsawa,da sauri na miƙe ina gyara zaman sahari na da ke barazanar kwancewa na nufi ƙofa da sauri. Ina ƙoƙarin bin hanyar da za ta kai ni lambu na kai masa karo na yi baya zan faɗi ya jawo ni na faɗa kan ƙirjinsa.Iya ƙamshin jikinsa kawai na ji na fahimci wane ne,ban san lokacin da na fashe da kuka ba na ce “Ya Mubshar shi ne kake fushi da ƙanwar ka a lokacin da ta fi buƙatar ka.Kai fa malamina ne babu abin da ka koya min na dangane da zaman aure ko da yake ba son shi nake ba” na ida furicin ina mai ɗan ja da baya don na ji tun ɗazu yake kiciniyar raba ni da jikinsa. Cikin idonsa na kalla wanda suka yi zurfi suka faɗa,ya motsa baki dakyar ya ce “Mijin ki na jiran ki” sai kuma ya kauce ya bar ni nan tsaye ,ban gusa ba sai da ya ɓace wa ganina juyowar ga da zan yi na ga Ali tsaye cikin kakin soja ya harɗe hannuwansa.A tunanina ko ya gan ni jikin Mubashar ne sai na ji kunya na sunne kai,“amarya babu lalle?” na ji muryarsa daga sama. Na ɗago na dube shi,sai ya sakar min murmushi ya ce “kin yi kyau ma sha Allah,ganin ki kawai ya sa na ji duk fushin da nake yi da ke ya ɓace” sai ya zo kuma yayi hugging ɗina ya na son sumbatata na kauce ai kuwa ya riƙe ni gam ganin in na yi wasa kissing ɗin nawa zai yi kawai na ɓoye fuskata cikin ƙirjinsa ina ce masa “ban so! Ban so!” bai kula ni ba sai kuma na ji wani sabon salo hannunsa kan fatar cikina.Kuka na fashe masa da shi sai ya sake ni,“ina wayar ki kullum ina kiran ki ba ki ɗagawa?” ya tambaye ni. Na turo baki na ce “ta na hannun shi” “Wa?” “Ya Mubshar!” “Mubashar ɗin ne ya koma Mubshar?” Na gyaɗa masa kai ya ce “ok koma ciki zan fita waje su na jirana” “Har yanzu ba su tafi ba?” “Eh! Amma an kama wurin da za su tattauna ɗin abin da aka tsayar kenan sai su faɗa miki ” na jinjina kai kawai . Sai da ya kawo ni har bakin ƙofar shiga falo sannan ya fice. Abun mamaki Mubashar na tarar a zaune cikin dangina sai jansa suke da hira duk da alamu sun nuna shi fa ya matsu ya tafi.Muka haɗa ido da shi na ga ya na ƙare min kallo,can kuma ya miƙe ya fice na bisa da kallo ina juyowa kuma muka haɗa ido da Mama.Ɗakina na wuce na bar gun,na ma rasa abin da ke damuna.Sai can cikin dare ƙawayena suka dawo da uban kaya niƙi-niƙi ,dogayen riguna ne iri ɗaya duk suka sayo uwanda za su saka a gobe kan amarya,kuɗin da aka basu suka nuna min Ramlah ce babbar ƙawa wannan ya saka komai na hannunta. A can bangaren Mubashar kuwa shi dai haka yake jin ahalin Mama tamkar danginsa yanayin yadda suka ja shi a jiki kamar sun san shi kuma suka nuna ma soyayya ƙarara.Ya lumshe ido a karo na barkatai ya na ƙara shaƙar ƙamshin SHARIFA da har yanzu bai bar jikinsa.Ya na nan zaune saƙo ya shigo wayarta,ya duba ya gani hankalinsa ya tashi ganin lambar FAHAD ce ....... Ga masu son fara payment 500 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ku turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 [29/04 à 13:12] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Page 8 Jikin Mubashar har rawa yake yi lokacin da ya karanta saƙon.A zuciye ya fara neman layin FAHAD ɗin,ya na ɗaga wa ya fara mayar masa da martani “in ka fasa zuwa sace ta daga tsaye uwarka ta haife ka,zo ka ɗauke ta tun yau ba sai gobe ba” ƙittt ya kashe kiran kwanyarsa na mugun sarawa,wato ya fahimci muddin budurwa ta yi rashin dace da saurayin albarka to tabbas rayuwarta na cikin kwata.A daren sam bai rumtsa ba,da zullumi biyu ya kwana ya rasa wacce yake so ga kuma wani banza na son jefa ta cikin matsala. Washegari tun asuba ake ta hidima ,Mubashar na dai ta dauriya amma sam ya kasa nutsuwa.Sheikh ma ya zo saboda mahaifiyarsa Mami da ta matsa har yanzu ba ta gansa ba,Mama ta sanar da ita Mubashar ɗan Sheikh ne amma ko kaɗan ba ta yi kuskuren shaida mata wai ya na son Sharifa ba so take abun kar yayi nisa musamman da ta hango mugun son Mubashar a idonta kasancewar shine ɗa tilo gun Sheikh. Iyayen ango sun zo domin ƙara jadadda godiya,ambaton sunan Ali kawai ana jona shi da na Sharifa tafasa zuciyar Mubashar yake. A hankali ya matsa kusa da Sheikh ya ce “Daddy yanzu za a iya samun jirgin da zai tashi?” Bai basa amsa ba sai kawai jansa da yayi suka nufi mota,hakan kuma ba ƙaramin daɗi ya yi wa Mubashar ɗin ba.Direba ne ke jansu su kuma su na baya,ya lumshe ido ya na hango fuskar Sharifa wacce ta sha ado da kayan kwalliya na zinare tamkar wata matar indiya.Waya Sheikh ke yi amma bai tsinci komai a ciki ba,ya dai ji mota ta tsaya sai ya ga suna cikin filin jirgi.Dama komai na cikin mota tun daga paspo har ticket,Mubashar yayi tunanin shi ɗaya zai tafi sai da aka zo shiga jirgin ne ya ga Sheikh ma ashe zai bisa. A wannan gaɓar ne yake jin wata irin soyayya da ƙaunar Sheikh na ƙara huda ɓargon jikinsa.Ya sa hannunsa cikin nasa ya ce “na gode sosai Daddy ka bani kulawa wacce ko mahaifina ne kai sai haka” murmushi kawai Sheikh yayi gudun kar ya buɗa baki zuciyarsa ta rufe. Daga nan cikin jirgi Mubashar ya rubuta wa Ali text kamar haka «ina taya ka murnar mallakar ƙaddara mafi daraja a duniya ta,don Allah ka riƙe Ifa amana kar ka cutar da ita sannan ka jona mata tsaro na musamman ta yadda FAHAD ba zai ƙara shiga rayuwarta ba.Ka kula sosai yayi ikirarin zai sace ta a yau wurin kan amarya, wannan dalilin ne yasa ma na ƙi bata wayarta» Da ya aika saƙon sai ya nuna masa ya ƙi zuwa,hasali ma layin ya sauka sai alamar jirgi✈️ a zuci ya ce ‘ashe har yanzu baƙauye ne ni wato in ana cikin jirgi sauka komai yake’ sai kuma ya miƙe zai fita Sheikh ya tsayar da shi “ina za ka je?” “Zan tura saƙo mai muhimmanci ne” ya basa amsa tare da fita,sai da ya tabbatar saƙon ya tafi sannan ya koma ciki. SHARIFA Dukkan amare su na farin ciki ne a irin wannan babbar rana wacce ƴan magana kan kira ranar farin ciki! Sai dai ni akasin haka ne a wurina.Baƙin ciki ,tsoro da fargaba sun yi wa zuciyata ƙawanya.Duk hidimar biki da ake yi sam ba ta gabana,lokacin da aka fitar da ni domin gaishe da iyayen Ali ji na yi kamar na zage su ko ƙila Allah yasa ya sake ni.A ɗan nesa da ni na hango fuskar Mubashar wacce ba sai an faɗa ba ka na gani ka san bai cikin farin ciki.Da tunanin mike damunsa na wuni,ana tsaka da cin biki kuma labari ya riske mu wai ya tafi Misira wurin karatu babu sallama ba komai. Da dare aka shirya ni kamar kowacce amarya,bayan na sha nasiha ƙanwar Mama da kuma wasu daga cikin dangin Papa suka ja ni izuwa waje. Yadda aka baza sojoji ta ko ina kai ka ce juyin mulki ne za a yi,ina kuka ina ƙari aka shigar da ni motar. Aka ce ko an yaudari kowa banda zuciyar da ta kamu da soyayya,a hankali na soma buɗe mayafin da rufe min fuska saboda ƙamshin turaren FAHAD da na ji ya cika motar amma sai dai sam ba shi ne a mazaunin direban ba.Ƙofofin hancina na buɗe ina shaƙo ƙamshi tabbas dai nasa ne,a zuci na soma magana ‘ Allah sarki masoyina yau zan tafi gidan wani wanda ba kai,lamarin da bai taɓa zo min ko a afarki ba ballantana na yi tunanin haka.Fahad ka cutar da mu duk laifin ka ne yasa hakan ta faru,kai kuma Ali tsakanina da kai Allah ya isa ka raba ni da farin cikina ’ sai na fashe da kuka. A haka dai aka miƙa ni gidana da ke can unguwar plateau,irin uwar dukiyar da Papa ya zuba min kai kace ƴar minista ce ni amma sam duk munin su nake gani saboda ban auri wanda zuciyata ke so ba. Lokacin da kowa ya watse ƙarfe ukun dare ta gota,irin rakiyar nan da ake yi wa ango sam Ali bai same ta ba shi ɗaya kawai ya zo. Duk yadda yake ƙoƙarin ɓoye damuwarsa sai da na san akwai matsala,ban tambaye shi ba na dai bi umarninsa ne na je na yi alwala.Bayan ya ja mu sallah ya gabatar da abin da ya shigo da shi,da hannunsa yake bani ni kuma sai imagination nake in na ganin FAHAD ne a gabana wannan ya saka na saki jiki na ci na ƙoshi muka sha madara. Wani salon soyayya irin na FAHAD da Ali ke yi min ya ƙara shagaltar da ni na ji na yarda kawai da Fahad nake tare.Ban dawo hayyacina ba sai da na ji ya na ƙoƙarin raba ni da budurcina,“a'a Had ban so kar ka yi wannan!” na faɗa ina jan numfashi. Ali ya kunna ƙwan fitilar da tun farkon hawan mu gado ya kashe,tsoro ne ya kama ni ganin yadda ya ɓata zanen gadon da ke shimfiɗe.Abu ko shiga bai yi ba wai amma ya samu nutsuwa,abin da ya fi ban mamaki kamar ma ya ji daɗin haka.Na dire daga kan bed na wuce toilet,shower na sakarwa kaina ina jin sanyin ruwan na ratsa ni. A can bangaren Ali kuwa lokacin da yayi niyyar kusantar Sharifa ji yayi duk wani desir ɗinsa ya tawo gaba ɗaya kafin ƙyaftawar ido.In ya ce bai ji daɗi ba to yayi ƙarya,amma sosai yayi mamakin yadda ko shigar ta bai yi ba amma abun ya zube.Ya ɗan ja ajiyar zuciya a fili ya furta “ƙila don ita matar aurena ce ba kamar sauran matan ba” sai kuma ya saki murmushi ya sauka ya cire zanen ya shiga toilet. Da sauri na juyo jin an buɗe ƙofa,jikina na soma rufe wa ina kallonsa.Ali kuwa ji yayi kamar numfashinsa zai ɗauke ganin ainahin surar Sharifa a cikin ƙwan lantarki,ɗazu ma ya kashe ne saboda kar ta yi zargin ko ya san mace kafin ta. Wata irin muguwar buƙatuwa ce ya ji ta na bijiro masa haɗi da game duk illahirin jikinsa sai dai kash ya na isa kusa da ita ya ji wani irin sanyi ya rufe shi. Tun da na ga Ali na nufo ni na rumtse ido gam,ina jiran in ji ya fara wasa da jikina na ji tsit hakan yasa na buɗe ido.Gabana ya faɗi ganin mugun al'amari,ban gama ma fita daga wancan mamakin ba kuma yanzu ga wani ya ƙara shayar da ni. A zuci na ce ‘ko dai bai da lafiya ne?’ sai kuma kawai na jawo towel na ɗaura tare da fice wa. Ali kuwa wannan karon ya ji tsoro sosai,sai ya fara tunanin kar dai ace cikin matan da yake holewa da su ne wata ta yi masa asiri amma kuma sai wata zuciyar ta rarrashe shi ta ce masa ‘ ta yiyu dai don Sharifa matar ka ce ta sunnah ka ƙara gwada wa ka gani’ a haka dai yayi wanka ya jefa zanen gadon a mashine ya wanke. Tun da na fito na rataya doguwar rigar na haye doguwar kujerar da ke nan gefen gado sai bacci. Ina tsaka da hutawa ta ya tashe ni lokacin sallah asubah yayi,haka na miƙe na je na yi alwala na zo na gabatar. Sanyin AC na ƙara sannan na haye bed wanda na ga tunu Ali ya sake masa shimfiɗa,yadda ya zo ya wani jawo ni ƙirjinsa yasa na buɗe ido tarau.Kamar wani tsohon maye haka ya dinga bibiya ta, wannan karon da yayi yunƙurin kusantata sai jini ya ɓalle min a dole ya haƙura. Cikin jin haushi na wuce toilet na haɗa ruwan zafi na gasa jikina,abun mamaki jinin ya ɗauke.Ina fitowa na shirya cikin riga da zane na atamfa na fito falo ina ta tunani iri-iri,ina nan na ji ana buga ƙofa na je na buɗe Ramlah ce tsaye hannunta riƙe da basket. Murya ƙasa-ƙasa ta ce “na zo ɗaukar zanen gado ne” Na ƙyaƙyace da dariya na ce “ango ya wanke abinsa sai in ni za ki gasa ” Ita ma dariyar ta yi ta na mai shigowa ta ce “inda an karɓe budurcin ai ba zan gan ki a nan ba” “Hum! Mi kika kawo mana?” “Ni ma ban sani ba,Mama dai ta ce na zo na kawo kin san can na kwana” “Ok buɗe ki zuba mana bari na kira Ali” “Ke fa ba ki da mutumci da sunansa za ki kira shi?” “Eh mana ko FAHAD ai ɗan guntile sunan ne na yi”ina faɗar haka fuskar Ramlah ta canza kafin ta ce “hum! Ai jiya ya sha na jaki tun da taurin kansa yayi yawa” “Ban gane ba?” “Ina fa za ki gane jiya ki na ta kuka ai ba za ki sanin abin da ya faru ba,duk fa uban sojojin nan haka FAHAD ya ratsa ya shiga motar da za ta ɗauke ki hum wai sace ki zai yi don ƙarfin hali har da saka kakin soja ko gidan uban wa ya same su oho” Tun da ta fara zuba na kafe ta da ido,saitin zuciyata na dafe da nake jin ya na tsarga min.Idona kuwa tuni sun fara tsiyaya, sama-sama nake jin muryar Ali ya na banbami ya na cewa wa ya ce Ramlah ta sanar da ni. Da na buɗe ido ne na ji ni tsudum cikin ruwa sai na fahimci ashe suma na yi,fashe wa na yi da kuka haɗi da ɗora borin sai an kai ni gun FAHAD . Cikin zuciya irin tasu ta sojoji Ali ya ce “wane FAHAD ɗin? Ba ki da hankali ne ina matsayin mijin ki shi ne za ki kira min sunan wani banza” Idona sun rufe har ban san lokacin da na ce “wallahi Had ba banza ba ne shi ɗin *SAURAYINA* ne kuma shi nake s....” ban dire zancen ba Ali ya zuba min yatsunsa biyar har sai da na ga taurari na gilma min. Ya sa kai ya fita,ni ma na miƙe na take masa baya na buɗe murya sosai na ce “ don Allah kar ku cutar da shi,ba laifinsa ba ne laifin son da yake min ne” Cak Ali ya tsaya tare da juyo wa ,a hankali kuma na ga ya soma takowa ya zo gare ni. “Ki na son na bar shi ya tafi kar a sake dukansa?”ya tambaye ni,na gyaɗa masa kai ya ce “ok je ki sako hijabin ki ” ban musa ba na koma ɗaki har tuntuɓe nake yi na je na ɗauko ko ta kan Ramlah ban bi ba wacce ke faman goge ɗaki. A mota Ali ya ɗauke ni ,bayan mun sharara gudu muka isa Company ɗin su.Ina biye da shi har muka isa wani part mai duhu,da fitilar wayarsa ya haska nan na hango Fahad yashe a ƙasa ya na fitar da numfashi dakyar in aka ce ya sha duka to mai sauƙi ne sai dai ƙirɓar gumba. Tako ɗaya kawai na yi Ali ya riƙe ni,ya ce “zan sa a bar shi yayi tafiyarsa amma ki sani ko ke ko shi duk wanda ya sake tunanin ɗayanku zan sa a yi masa dukan da ko uwar da ta haife shi ba za ta gane shi ba” Ina kuka ina ƙari haka nake kallon yadda ƙananan sojawa ke yi FAHAD wanka da ruwa sai jan rai yake,dakyar ya iya tashi ya na gwalar ido Ali ya kunna ampoule ɗakin ya gauraye da haske mun haɗa ido ya rairafo ya kama ƙafafuna..... *Yayana Laminou Gonda ina kawo gaisuwa*🌚 My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [01/05 à 09:30] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Page 9 Ban san lokacin da na zube kan gwiwaina ba,ina shirin jawo FAHAD jikina Ali ya wani ciro ni sama kafin ya soma tafiya da mu da ƙarfi.Waiwayen FAHAD nake wanda yake ta kallona da kumbararun idonsa uwanda suka kusa rufe wa saboda uban dukan da ya sha,sai a bakin mota Ali ya dire ni da kansa ya shigar da ni ciki ina ta kuka a haka muka koma gida. Ko ciki bai shiga ba ya ƙara fita,ina shiga falo na tarar da Ramlah ta rabka uban tagumi.Jikinta na faɗa na shiga koro mata bayani masu taɓa zuciya dangane da halin da na tarar da Fahad,rarrashina kawai take ta na kwantar min da hankali amma sam na kasa yin haƙurin wannan lamari.A nan ta wuni sai yamma ta yi tafiyar ta bayan ta min girki da gyaran gida,dakyar na aro jarumta na je na yi wanka na saka doguwar riga ta less.Mai kawai na shafa sai turare,kusan mirror na yi tsaye ina ƙarewa halittar da Allah ya min kallo.Ina da tsayi amma ba sosai can ba,ban da ƙiba kuma ba za a kira ni ramamiya ba,tsayin hanci dogon hanci da manyan idona wanda gashinsu da na gira ta su ne suka ƙara masu kyau baƙaƙe wuluk kamar doguwar sumar kaina wacce take har gadon baya.Laɓana sirara ne sun ɗan canza kala su ba jajaye ba su ba pink ba,ina da albarkar Fulani da lafafen ciki hakan yasa shap ɗina ya fita kamar coca cola. Tunanin Mubshar ne ya faɗo min a daidai kuma wannan lokacin na ji ƙafata na min wani irin ƙaiƙayi.Da sauri na je bakin bed na zauna ina sosa gun,ina shirin cire sarƙoƙin Ali ya shigo da sallama kawai sai na fasa cirewa ina mai tashi tsaye ban amsa ba na zuba masa na mujiya. Ya je kusan drower ya fara rage kayan jikinsa,ni dai ina tsaye ina kallon murɗaɗen jikinsa wanda ka na gani kasan ya na ɗaukar ƙarfe . Toilet ya wuce yayi wanka ya fito,a inda ya bar ni ko motsi ban yi ba. “Ki zo ki shafa min mai” ya faɗa ya na wani zama gefen gado. “Ban zo don shafa maka mai ba” na samu kaina da furta wa ina mai kafe shi da ido haɗi da jifarsa da kallon tsana. “Ki zo ki shafa min,ba zaɓi ba ne umarni ne” ya sake faɗa ya na haɗe rai. Na taɓe baki na ce “in kuma ba haka ba?ko ni ma dukan nawa za ka yi kamar yadda ka yi wa SAURAYINA? ” Shiru yayi ya na kallona kafin yayi ƙyaci ya miƙe,a gabana ya shirya ko kunya babu har da wani sakin towel.A zuci na furta ‘girman banza! Duk da hakan dai Had ya fi ka kuzari’ sai kuma na saki murmushi. “Na yi kyau ne?” ya jefo min tambayar.Na ja tsuki ina shirin yin magana amma ya ƙi ban dama dukkan laɓana biyu ya haɗe ya matse tare da murɗe su,sai da na ji zafin har tsakar raina. Hawaye suka fara zubo min,Ali ya wani fincike ni muka yi falo.“Ki zuba mana abinci” ya faɗa ya na mai zauna wa,babu shiri na zuba abincin jikina har rawa yake.Tsabar mugunta haka ya tursasa min na ci,bayan mun gama cin abinci ya fita ko minti biyu ba a yi ba sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da kwalin maganin ƙarfin maza.Iya hoton jikin kwalin kawai yasa gabana yayi wata mummunar faɗuwa,tsoronsa kuwa tuni ya fara kaɗa hantar cikina.Muƙut na haɗiye wasu yawu ina kallon ya na juye maganin a kofi kafin ya zuba ruwa ya shanye.Jajayen idonsa da suka sauya kala ya zuba min,da mugun sauri na miƙe tsaye cikin tsabar yadda na firgice yasa na yi tuntuɓe na faɗa jikinsa.Ali ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya wacce ta ƙara fallasa sirrinsa,na rumtse ido jin ya na zuge zip ɗin riga ta.Duk yadda na so ƙwatar kaina kasa wa na yi,sai abubuwa yake min wanda sam ban jin daɗin su sai ma ƙara ƙaimin tashin hankalina suke. A nan kan kujera Ali yake ta ƙoƙarin fanshe sadakinsa,amma a banza sai wahalar yake.Can ya tsaya,ya jawo wayar shi kamar wani likita haka ya shiga duba ni.Na rumtse ido cike da takaici kafin na haɗe cinyoyina,saɓa ta yayi bai dire ni ko ina ba sai kan bed.Da ƙarfin tsiya ya sake dubana ni kuma sai hawayen takaici nake kafin furucinsa ya jawo hankalina,“ Sharifa dama ba ki lafiya? Ni nan ban ga komai ba” Sai a lokacin na buɗe ido,yadda ya wani kafe jikina da ido yasa na jawo zanen gado na rufa kafin na tashi zaune.Dubansa ya maido kan fuskata kamar wani maye,na turo baki na ce “mi?” “Ba ki ji abin da na ce ? Babu komai a wurin kamar ma ba a hallici gun ba” “To ai shikenan sai ka haƙura” na faɗa ina mai ƙoƙarin sauka amma ya tsayar da ni “ki samar min da nutsuwa to kafin gobe na kai ki asibiti ” Baki kawai na saki ina kallonsa,ya ƙara furta “please!” Na ce “ni ban san ya zan yi ba” “Bari na nuna miki ” ya furta da sauri ya na matso wa guna,sai dai fa sam ba zan yi ƙazantar da yake so ba.Ali ya yi iya yinsa amma wallahi na ƙi buɗe bakina,da ya gaji da roƙona ya tsiro wani sabon salon daban ya samu nutsuwa. Cike da ƙyanƙyami na shiga toilet na wanke ƙirjina da ya ɓace,Allah ya isa wacce na jero masa ta fi cikon casbi.Ina jinsa ya na murɗa handle amma na ƙi buɗe wa dama na san a rina shi yasa na kulle ƙofar da key.Bayan na tsarkake kaina na fito,sai a lokacin shi ya shiga.Kayan bacci na saka na cire zanen gadon na jefar na shimfiɗa sabo na haye tare da lumshe ido.Hoton fuskar Mubshar ya sake faɗo min ,sai kuma na ji tamkar ana matse min ƙafa na yunƙura zan tashi na ji Ali bayana ya na mai rungumo ni.Hasken ɗaki ya kashe ya fara lalube na,bakinsa ya ɗora kan nawa ai kuwa na gantsara masa cizo ba shiri ya sake ni.Bai ce komai ba,tun ina jiransa har bacci ya ɗauke ni. Washegari Bayan mun yi sallar asubah haka ya sake yunƙurin nema na,cikin takaici na ce “Wai Ali ka manta banda lafiya ne?” Ya sauke wani huci kafin ya ce “na sani ina dai son samun nutsuwa ne kafin mu je asibiti” “To ban so ka ƙyale ni ko kuma wallahi na tsere na bar ma gidan ka,ni ban son takura ” “Ok ki sha min” “Ko Had da nake so ban yi wa haka ba” ina gama faɗa na dire daga bed ɗin,baccin ma ya fita raina. Falo na je na zauna na kunna sunnah tv,karatun Alkur'ani ne ake hakan yasa na soma jin wani sanyi na ratsa ni kamar wacce ke da cutar sandarewar jiki.Idona suka fara lumshe wa,buji-buji nake ganin mai yin karatun wanda ban sani ba ko idona ne ke nuna min alarama Afif ɗin na kama da Mubshar. Tun ina jin karatun har na tsunduma duniyar mafarki,wanda farawar shi kawai na gan ni kwance babu sutura gefena kuma Mubshar ne shi ma haka.Romance ɗina yake ya na min abin da ban ma san ana yin su ba kafin ya soma kusantata.Tamkar a zahiri haka nake jin lamarin,yadda Ali ya min tsawa haɗi da jawo ni ƙasa na faɗi yasa na buɗe idona da suka min nauyi. Na kalle shi a kasalance sai huci yake sauke wa,“tsabar iskanci kin guji mijin ki na aure shine kika zo nan falo ki na mafarkin Mubashar uwar mi ce yake miki kike min ihu cikin gida?” tun da Ali ya soma magana na kafe shi da ido,yayin da mafarkin da na yi kuma ya dawo min daram a kai. A hankali na lumshe ido ina jin zuciyata na dokawa da ƙarfi,“tashi ki shirya mu je asibiti” na ƙara jin Ali ya faɗa,ba tare da na buɗe ido ba na ce “to amma don Allah ka kira min Ramlah” Shirun da na ji yasa na buɗe ido,ya na tsaye ya na kallona.Saurin tashi na yi na wuce bedrom, toilet na shiga na ƙara tsarkaka kafin na zo na shirya .Ko da na fita na tarar da shi a zaune ya na cin abinci sai ƙamshi ke tashi,ina shirin tambayarsa ina ya samu abinci sai ga Ramlah ta fito daga kitchen. “Kin fito? Tun ɗazu na zo Ali ya ce ki na wanka,abinci ne Mama ta ce na kawo” Ramlah ta faɗa ta na ajiye gorar ruwa da kofi kusan Ali. “Ashe ki na hanya ,ya kike ya Mama ɗin ta na lafiya?” “Lafiyar ta lau.Sai yau fa zan koma gida,don haka sai an jima sauri nake” “Ki jira mu fita tare” na faɗa tare da buɗe kwanon abincin na ce “ zo mu ci ko?” “A'a na ci a gida ” Plate na samo na zuba couscous ɗin da miya na ci na ƙoshi,bayan duk mun gama ne muka fito.Ina gaba Ramlah na baya,Ali na tuƙi sai wani iya yi yake ya na kamo hannuna.Duk da akwai nisa amma sai da ya kai Ramlah gidansu,da za ta sauka kuma ya bata kuɗi masu yawa.Daga nan asibiti muka wuce,bayan yayi musu bayani aka haɗa mu da likitar mata ta duba ni ta kuma tabbatar da lafiyata lau ƙila rashin kwantar da hankalina ne da ban yi ba saboda tsoro yasa bai ga hanyar ba . Godiya Ali yayi mata kafin mu baro asibitin,a kan hanya ya saya min sabuwar waya sannan ya je gidan layi aka min copy nawa . Sosai na yi murna ina ta zuba masa godiya. ★MISIRA Jirgin su Sheikh ya sauka lafiya,kasancewar sananne ne tun a nan wasu ke ta masa gaisuwar girma.Su na nan zaune aka zo aka ɗauke su,a hanya Mubashar ke ƙarewa garin kallo yadda ya haɗu sosai.A haka suka sauka masaukinsu,wani ɗan madaidaicin gida ne mai shuke-shuke.Sheikh ya nuna wa Mubashar part ɗin da zai zauna,ya wuce ciki sanyin ƙamshi ne ya tarbe shi har sai da ya lumshe ido.Babu ce kawai a babu a ɗakin, toilet ya wuce yayi wanka ya na fito wa ya ga kaya ajiye kan bed.Ɗauka yayi ya saka kafin ya fito falo,Sheikh ya sakar masa murmushi ya ce “yanzu nake shirin cewa Khalid ya kira ka” Mubashar ya saki murmushi kawai,Khalid shi ne matashin da ya je ya ɗauko su Balarabe ne bai jin Hausa sai English. Shayi ya zauna suka sha kafin a gabatar masu da wani kalar abinci mai shegen daɗi.Mubashar sai ƙoƙarin watsar da tunanin Sharifa yake,haka shi ma Sheikh sai jansa yake da hira.Bayan sun dawo daga sallar isha'i ne duk kowa ya shiga part ɗinsa domin hutawa. Mubashar ya jawo wayar Sharifa,sai yau ne kawai ya binciki abin da ke ciki.Sosai hankalinsa ya tashi ganin irin ƙazaman kalaman da suka yi masaya ita da Fahad.Ya shiga gallery yadda ya ga hotunan su manne da juna saura ƙiris zuciyarsa ta buga ,wasu ma a gidan rawa aka ɗauke su .Idonsa ya kaɗa yayi ja ganin Sharifa zaune raɗam kan cinyar ƙato, addu'a ya soma yi ya na karanto sunayen Allah a haka bacci ya ɗauke shi.Ba shi ya farka ba sai ƙarfe ukun dare,ya je yayi wanka da alwala ya zo ya tada sallar nafila kusan rabin addu'o'in da yayi duk Sharifa ya yi wa su. Da ya ji ana kiran sallar asubahi ya fito, Sheikh ya fito sai suka dugunzuma suka wuce masjid. Bayan sun dawo suka yi karatu,kafin Sheikh ya umarce shi ya je ya shirya za su fita. Bayan Mubashar yayi wanka Khalid ya kawo masa kayan da zai saka,cikin halshen larabci suka gaisa a nan ya sanar masa breakfast na jiransa. MUBASHAR ya fito cikin irin shigar larabawa, Sheikh ya ƙure shi da ido ya na murmushi haɗi da yi masa addu'a a can ƙasan zuciyarsa .Abinci suka ci su uku kafin Khalid ya tuƙa su zuwa University ta karatun Alkur'ani ta ƙasar.Sheikh ya rubuta sunan Mubashar sannan aka zagaya da shi ya ga ɓangarorin wurin ,daga nan shopping suka wuce. Yadda aka kashe uwayen kuɗi yasa Mubashar kasa cewa komai sai hawayen farin ciki,kamar wani ƙaramin yaro haka yayi tsaye gaban Sheikh wanda shi kuma ya tallabe kumatunsa ha na murmushi ya ce “ka fi kyau haka my son,in ka na shagwaɓar nan sai ka dinga tuna min lokacin ina saurayi kamar ka.In kuma na ga ka na murna sai na ji takaicin yadda ban yi ma hidima tun ka na ɗan ƙanƙanen ka sai da ka girma” Mubashar ya shige cikin ƙirjin Sheikh,soyayyar mahaifi da ya rasa ce yake jin ta na huda fatarsa ta na shiga jijiyoyinsa.Son mahaifi yake yi wa Sheikh,murya na ɗan rawa ya ce “Daddy Allah saka ma da gidan Aljannar firdausi! Ya yafe ma zunuban ka ya luluɓe ka da rahamarsa” “Amen!” Sheikh ya furta ya na ƙoƙarin mayar da kukan da ke shirin kubce masa. Khalid da ke tsaye ya na kallonsu shi ma sai da ya goge ƙwalla duk da bai san abin da suke cewa ba. ★A can bangaren FAHAD kuwa tuni sojawa sun sake shi,cikin su ne wani ya basa 10mill ya kuwa karɓe.Da ya isa gida Umma ta gasa masa jiki ,juyin duniya kuma ya ƙi faɗa mata dalilin da yasa aka duke shi don ya na tsoron kar ya sanar da ita azo ta tsani Sharifa wacce bai san ma mugun sonta ya fi sha'awar da yake yi mata yawa ba.Ya lashi takobin ko zai rasa ransa sai ya raba Sharifa da gidan Ali shi kuma ya aure ta....... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,DM +22795045822 [03/05 à 09:18] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻 LoVe and HoRrOr story💔☠️ ```MRS SADAUKI```✍🏻 Dedicated to Autar Manya👑 *FCWA*☀️ ____________________________________________________________________________________________________ Last free page 10 Sama da shekara ɗaya yanzu da aurena amma ko sau ɗaya Ali bai kusance ni ba duk da kuwa ya na gwada sa'ar shi sai kafin ya cimma burinsa lamari ke kwaɓe wa.Abu guda na sa a raina kawai bai da lafiya ne dama,kuma sosai na ji daɗin haka don normal nake karatuna wanda tuni mun gama Finally year rantsar da mu kawai ya yi saura. A gurguje nake tafiya kasancewar motar gidana ta lalace ba direba ne ya kawo ni ba.Kasuwa na je na yi dukkan siyayyar abin da zan buƙata a taron karrama ɗalibai da za a yi gobe,ina jin tun ɗazu wayata na ringing amma ban fiddo ta ba saboda kar a ƙwace. Na ja tsuki na ce “yanzu haka Ramlah ce ita da komai na ƙauyawa tak....” magana ta ce ta tsaya sakamakon wata dalleliyar mota da ta kusa kaɗe ni.Na yi ɗan baya da sauri ina zagin matuƙin kafin na yi gaba,abun mamaki har na yi nisa ni na ga motar na bin bayana na tsaya cak.Motar ta zo daidai gabana ta yi parking,kafin a hankali a sauke baƙaƙen maduban,ido cikin ido muke kallon juna.Ban san lokacin da na saki ledodin hannuwana ba sam,jikina tuni ya ɗau rawa zuciyata kuma ta soma buga wa da mugun ƙarfi kamar za ta faɗo.Na lumshe ido ganinsa a tsaye a gabana,ya sha wasu mayun suit baƙaƙe sai baza ƙamshi yake. “Rifa!” ya kira sunana cikin wani yanayi mai tattare da ma'anoni dayawa,na buɗe idona wanda tuni suka ciko da ƙwalla. “Na yi kewar ki” ya furta ya na kallona tsakiyar ido.Murya na ɗan rawa na ce “Had! Kai ne? Ko kuwa mafarkin da na saba yi ne? Don Allah ka faɗa min ba bacci ba nake” “Ni ne da kaina my Rifa ” ya bani tabbaci kawai sai na faɗa jikinsa na saki wani marayan kuka,ina jin yadda zuciyar FAHAD ke wani irin mugun buga wa da ƙarfi . Ya ja numfashi ya ce “mu je ki shiga mota kin ga mutane sun fara kallonmu” sai ya ni kamar wata ƙaramar yarinya ya zagaya da ni can ɓangaren ya zaunar da ni a gaba.Ina kallonsa ya kwashe ledodina yasa gidan baya kafin ya shigo ya zauna,ido kawai na tsura masa yadda yayi wani mugun kyawu kamar Balarabe fatar jikinsa har wani ƙyalli take baƙar sumar kansa da ta gemu da sajensa kuwa kamar Karaan. Muna tafe ina ƙare masa kallo,sanyi ac motarsa ma kaɗai ya isa ya nuna ma ya na cikin jin daɗi.Har muka kai wani tantatsetsen gida bai ce min uffan ba sai aukin murmushi,mai gadi ya buɗe ya na wani rusuna masa shi kuma ya Parker motar cikin jerin motocin da ke ajiye sun fi kala biyar. Da kansa ya buɗe min ,ƙafafuwa tuni sun yi sanyi dakyar na iya fiddo su waje ai kuwa tsayuwa ta gagare ni.Cak ya sungume ni ba tare da na yi zato ba,da sauri na lanƙame wuyansa da hannuna hakan ya ƙara wa fuskokinmu kusanci har ina iya jiyo ƙamshin man da ya shafa a sajensa. Tafiya ya soma da mu har muka isa bakin wata ƙofa mai kyau,da kanta ta buɗe ya shigar da mu ya aje ni kan luntsuma-luntsuman kujerun da ke zube a falon. “Barka da zuwa gidan ki” ya furta ya na murmushi kafin ya ƙwala kiran sunan “Sulvi? Sulvi?” da gudu wata matashiyar budurwa ta fito ka na ganinta ka ga inyamura,da Yaren French yayi mata magana ta amsa kafin ta wuce babu jima wa ta dawo da tray hannunta ta aje a gabana. Na kasa cewa komai sai kallon uwar dukiyar da aka zuba nake,ina son tambayar FAHAD gidansa ne ko kuwa na uban gidansa ne amma dai na yi shiru. Hijabin jikina ya cire ya na mai zama kusa da ni,da kansa ya zuba min jus na sha haka ma kayan marmari kafin ya ce “taso mu wuce ciki” babu muso haka na bi bayansa muka hau ƙaton benen da zai sada mu a sama mai ɗakuna sama da biyar. Wani shock na ji lokacin da muka bi ta wani ɗakin mai jar ƙofa,sai da na ji kamar an zuba min ruwan ƙanƙara yayin da kuma sarƙa ƙafata na ji ta na matse ni. Idona na ji kamar za su rufe,na yi saurin kamo hannun FAHAD na riƙe gam.Murmushi kawai ya yi min ,wani ɗaki muka shiga mai kayan ado komai na rayuwa akwai. Da shigar mu ya umarce ni da na cire duk kayan jikina ko pant bai son gani,tamkar wacce ya rufe wa baki ko gardama ban yi ba na bi umarninsa duk da ba yau ne muka saba keɓe wa ba amma lokutan baya shi ke cire min sutura ai. Kallona kawai yake yi ya na lumshe ido,ni kuwa duk sai na ji babu daɗi.Ya tako gabana yasa hannu ya cire shushu ɗin da na ƙulle gashina,ai kuwa ya baje kan kafaɗuna. “Za mu je mu yi wanka” ya ƙara furta min cikin kunne,yadda sautin ya fita ya saka ni saurin lumshe ido.Fahad ya ɗauke ni bai dire ni ba sai cikin ƙaton bahon wanka,shi ma ya cire suturar shi ya shigo ya soma yi mana wanka mai haɗe da romance.Yadda yake kissing ɗina ya sha banban da na Ali,ban sani ba ko ƙila don shi ne nake so nake jin komai normal.Samar da minti talatin muka ɗauka a ciki kafin ya fitar mu muka koma kuma wajen shower,ina gaba shi kuma ya na rungume da ni a baya.A cikin kunnena ya dinga jero min baitocin soyayya masu ratsa ɓargon zuciya,yadda yayi kukan kewata,abin da rashina kusa da shi ya haifar masa. “Rifa ina mutuwar son ki,babban burina shi ne na mallake ki a matsayin mata.Ki san yadda za ki yi ki rabu da Ali ki zo mu yi aure mu ji daɗin rayuwarmu kin ji?” ya tambaye ni ya kuma hana min damar yin magana sakamakon bakinmu da ya haɗe. Niyyar kansa ya dawo da mu kan bed ɗinsa ya zuba min salo iri-iri na soyayya .Duk da bai kusance ni ba a yadda ya kula da ni kawai mun gamsu,sosai kuma na yi mamakin yadda ko ƙaƙarin yin sex ɗin bai yi ba. Da muka ƙara shiga Toilet abu guda na lura da shi,FAHAD bai yi wankan tsarki ba ni kawai na yi muka fito shi da sabulu yayi. Wani wuri ya buɗe sai ga akwtina sun fi goma,dukkansu manya ne.Ya buɗe ɗaya daga ciki ya zaɓo min wasu kaya riga da wando irin na tura wa ya ce na saka ya na son ganina cikin su,na yi murmushi tare da karɓa na ce “yaushe ka saye su?” “Sun ɗan jima! Ko na buɗe miki sauran akwatinan ki gani? Kayan lefen ki nake haɗa wa” ya bani amsa tare da taimaka min na sa kayan ai kuwa tamkar wata baturiya haka na fito. Ɗaya bayan ɗaya haka FAHAD ya buɗe min duk na ga komai,sosai na ji daɗi ina jin ƙaunarsa na ƙara haɓaka.Falo muka wuce,Sulvi ta kawo mana abinci ya fi iri goma ina zaune raɗam kan cinyar shi ita kuma ta na sanar da shi sunayen abincin. “Zuba min shinkafa da miyar biri,babyna ke mi kike so?” Da mamaki na dube shi na ce “biri kuma? Yaushe aka halitta mana cin Biri kuma?” Wani kallo ya min wanda ban san na mine ne ba kawai sai na ji ma kamar na manta tambayar da na yi. “Zuba mata acake da kifi” ya ba Sulvi umarni,plate biyu ta ɗauka ta zuba wa kowa nasa sai a lokacin na zauna kan kujera.Bayan mun gama ne na ce masa ina son zuwa gida,na saka hijabina muka fito. A hanya ne yake ce min “na yi tunanin nan za ki zauna sai dare ki koma amma da alamu duk kin damu ki zo baƙin gidan nan” Na ce “gobe ake karrama mu a makaranta shi yasa” “Ok amma gobe a gidana za ki kwana” Na yi shiru ban ce komai ba,“ko ba za ki zo ba?” ya tambaye tare da min shegen kallonsa wanda ban san yaushe ya koye shi ba amma sam bai da daɗi sai nake ganin ma kamar idonsa su na canza wa. Na haɗiye yawu na ce “zan zo” “Tun da kin yi alƙawari na yarda,in ma ba ki zo ba da kaina zan shigo har gidan na ɗauke ki” ni dai ban ce komai ba har ya kawo ƙofar gidana,sai da ya min kiss kafin na fice. Ina shiga na tarar da Ramlah ta cika ta yi fam kamar za ta fashe,na ƙyalƙyace da dariya na ce “fushin na mine?” “Ban sani ba tun ɗazu kin samu wuri kin yi zaman ,daga ina kike ma wai?” ta tambaye ni ta na wani kallona,sai da na ja ajiyar zuciya na ce “zan faɗa miki ba yanzu ba” sai kawai na wuce bedroom.Kan gado na haye bayan na cire hijabi,na lumshe ido ina tuna moments ɗinmu. “Ina kika samu uwannan kayan?” na ji muryar Ramlah daga bayana.Da sauri na tashi zaune muna kallon juna,tambayar ta sake maimaita wa ni kuma ba tare da wani ɓoye mata ba na ce “Had ya saya min” “Wane Had ɗin?” “Fahad mana” “Yaushe suka dawo Nijar?” “Wallahi ban sani ba ni ma yau dai na haɗu da shi kasuwa” Ramlah za ta yi magana kenan ,Ali ya shigo bakinsa ɗauke da sallama da sauri ta fita yayin da shi kuma ya tsure ni da ido.Sanin halinsa ba ƙaramin aikinsa ba ne ya nuna min na jaki ba yasa na kawar da kaina,“daga ina kike? ” “Kasuwa na tafi”na basa amsa . “Mi kika siyo? ” “Kayan da zan sa gobe ko?” “Su na ina?” ya watso min tambaya. Na yi shiru ina tunani ,tabbas na bar su a motar FAHAD. “Ba ki ji abin da na ce ba?” ya daka min tsawa ya na ƙara matso wa,bakina na rawa na ce “su na cikin drower” tare da nuna masa da yatsa. Ali ya je ya buɗe drower nan take ledodi suka faɗo,ya ɗauko su tare da buɗe wa ya na duba wa haɗi da karanta reçu/ receip .Ni kuwa mamaki ne ya kusan kashe ni ganin kayan da na bari a mota ga su kuma a ɗakina.Ya mayar da kayan ya fice,na ja wata wawiyar ajiyar zuciya ina mai cewa “to ya aka yi suka zo nan?” sai kuma na soma tunanin ko na shigo da su ne,ganin zan sawa kaina ciwo kawai na share na soma baccin gajiya. Ali kuwa ya na fita direct kitchen ya wuce inda yake jin motsin Ramlah.Wani irin finciko ta yayi ya ce “daga yau in na sake jin banzan shirmen ki wallahi ni da ke ne.Kin san aikin da nake yi ne kika taso ni ? Kawai saboda banzan kishin ki a dole so kike mu yi faɗa ni da matata” Ramlah ta fincike hannunta ta ce“oh matar ka ce? Shi ne ta kasa yi ma komai ina ce ni nake sauƙe duk buƙatun ka sama da shekara ɗaya.Ka na ji Ali wallahi na gaji kawai ka aure ni ko kuma na tona ma asiri” Ramlah ta faɗa ta na jin wata irin da na sani,saboda cin amanar ƙawar ta da take yi ita da mijin ta wanda ba komai ya jawo hakan ba sai yadda SHARIFAr ke bata labarin sirrin aurenta sannan kuma da kwaɗayi da hassadar ƙawarta ta auri wanda ya fi masoyinta Kb.Tun lokacin auren Sharifa bai wuce wata biyu ba Ramlah ke shige da fice har sai da ta ja hankalin Ali,ta yi hakan ne don cin kuɗinsa tun da Sharifa ta tabbatar mata ya na da muguwar sha'awa sai dai fa ko kafin akai ga yin sex komai ke lalace wa.Ta zata za ta ci bulus sai kogo ya juye da Mujiya Ali ya karɓe budurcinta ta mummunar hanya,ta yi kuka har ta gaji a ƙarshe kuma ta shafe idonta da toka suka dinga holewar su kai kace wasu ma'aurata har da ɗaukar maganin tsarin iyali.Burin ta guda a yanzu shi ne Ali ya aureta,shi kuma ya tabbatar mata har abada ba za a yi cin amana da shi ba sai dai in bai auren Sharifa, wannan hujjar ta saka Ramlah a doli sai ta samo laifin da zai sa Ali ya saki Sharifa har wani ta samu wanda zai dinga bin bayan Sharifa duk inda za ta je. Ali ya dubi Ramlah,kallo irin na ba ki da hankali kafin ya ce “na aure ki? Mi za ki min wanda yanzu ba ki min ba? Ki na ji na ko? Ki buɗe kunnuwan ki babu aure tsakaninmu” ya na gama faɗa ya ficewar shi. FAHAD Tun bayan haɗuwarsa da Sharifa yayi dubarar haɗa wani plan kanta ,na kula da duk wani motsin ta da abin da ya shafe ta.Ya na tsaka da driving ya ji ledodi na motsi daga bayansa,kallonsu kawai yayi ya fahimci abin da ke faruwa.Umarni kawai ya basu ya na mai furta wata kalma kawai suka ɓace suka kai kansu cikin drower Sharifa. Cike da annushuwa ya isa gida,tun bayan rabuwarsa da ita bai taɓa samun nutsuwa ba sai yau kuma da idonsa suka sake tozali da ita. Ya na isa gida ya hau bene,bai tsaya ko ina ba sai bakin ƙofar da ta sha banban da kowacce ƙofofin da ke jere,don ita hatta pentin ta daban yake . Bayan ya buɗe ta na ya soma shiga da baya-baya har zo tsakiyar ɗakin wanda tsabar duhunsa ba ka iya ganin komai amma a haka FAHAD yake yin wani yare.Kyandirori ne suka kawo jar wuta kamar jini,hakan ya ɗan haskaka ɗakin wanda komai nasa ja ne in ka cire baƙin capet ɗin da ke shimfiɗe a duk illahirin wurin. Gumki da ke tsaye ƙiƙam FAHAD ya je ya yi wa sujuda kafin ya tashi ya yanka yatsansa ya kai bakin shi.Kamar wani mutum mai rai haka ya dinga zuƙar jininsa na tsawon minti biyu kafin ya saki yatsan,a nutse FAHAD ya soma yin magana “Gourou ka cika min alƙawari,na samu masoyiyyata silar shiga ta ƙungiyar asiri.Ka faɗa min wane irin tukuici zan yi ma domin nuna godiya ta gare ka?” Kamar daga sama gumkin ya buɗa baki ya ce “ita nake so! Sharifa nake so ka kawo min ita ina son shan jinin ta!”. Ƙarshen free page ! *Ya aka yi FAHAD har ya shiga ƙungiyar asiri? Ta wacce hanya ce? Shin zai kai bayar da Sharifa ɗin? Mine ne makomar Ramlah? Shin ina labarin MUBASHAR ?* Mu haɗe a PAID GROOP duk za ku mu ji ainahin abin da ya faru shekara ɗaya da ta wuce,sannan za mu ji yadda gourou gumkin da FAHAD ke yi wa tsafi za su kaya. Mai son shiga group only 500 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,ko kuma katin MTN na 500 .Ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f,sai ku tura shaidar biya ta WhatsApp +22795045822. Ga account nan kawai ki yi payment ki turo min evidence haka ma masu turo kati,wacce ta san ba ta da niyyar biya ta yi wa Allah kar ta min magana na gode! MRS SADAUKI Nijar 🇳🇪