[1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 1 Zaune take a matsakaicin falonta kan kujera mai zaman mutum ɗaya, inda take tsefe gashin kanta wanda ya rage saura guda ɗaya rak ta gama tsifar. Sai da ta karasa, ta taje sannan ta fito daga falon ta nufi bedroom ɗinta wanda yake jere da falon da yake irin ɗakunan nan ne da ake yi wa lakabi da mu koma aji. Tsaye ta yi gaban mudubi tana karewa kanta kallo, fara ce tas sai dai tana da matsakaicin tsawo doguwar fuskarta mai yalwataccen gashin gira manyan idanunta da suke ɗauke da zara-zaran gashin ido, hancin ta irin wanda ake yi wa lakabi da tamkar biro, gashin kanta baki wuluk wanda ya zuba har bayan kafaɗarta. Cikakkiyar halittar da take da ita daga sama har kasa wacce kowace mace za ta so a ce ta mallaki hakan, wannan kyawun halitta da Allah ya mata shi ya sa kawayenta suke mata kirari da MATAR MANYA amma sai dai kash! An samu akasin lissafi domin kuwa buri da mafarkinta bai cika ba a nata ganin kenan da kuma ganin wasu daga cikin kawayenta. Kasancewar ta auri mutumin da take ganin ba shi da sunan da ya dace a kira shi illa mai na sama ya ci bare ya ba na kasa ba. "Wannan ita ce kaddarata, sai dai na tabbata ba zan dawwama a hakan ba, dole na samarwa kaina mafita ko ba jima ko ba daɗe sai mafarkina na MATAR MANYA, ya cika domin ba zan lamunci zama da kaddararran auren kafinta ba" Ta furta a fili tana kara karewa cikakkiyar halittar da take da ita kallo wacce tana ganin har yanzu dai ruwa bai karewa ɗan kada ba akwai sauran rina a kaba. Wani uban tsaki ta ja lokacin da ta hango hoton ABBAS ta cikin mudubin wanda yake jingine a gefen gado, tana jin wani haushi da takaici tabbas ba shi ne mafarki da burinta ba, shi ɗin da mai gadin gidanta ya dace sai ga shi kaddara ta haɗa aure a tsakaninsu, hakorinta ta saka ta dantse leɓanta na sama tana mai kankance idanu janyo ribon ɗinta da yake kan madubin ta yi ta haɗa gashin wuri ɗaya ta yi parking ɗinsa, dakyar ta samu ta haɗa wuri guda saboda tsawo da kuma cikarsa. Fitowa tsakar gidan ta yi ta rasa ma mai yake mata daɗi saboda kugin yunwar da cikinta yake, kicin ta karasa ta buɗe ragowar sauran tuwon jiya wanda kasancewar ba shi da yawa ABBAS ya hakura ya ce ita ta ɗumama ta ci gawayi ta kunna ta saka tuwon cikin miya ta ɗora. Karan wayarta da take ta ruri a falo ya sa ta taho kafin ta zo kiran ya katse har ta juya saboda idan ta ɗauko wayar ma hakan ba shi da amfani saboda bata da kati bare ta bi kiran, shigowar wani kiran ne ya dakatar da ita ta koma ta ɗauki wayar EESHART shi ne sunan da yake yawo a kan wayar. "Wai ina kika shiga ne kawata na miki sako saman whatsapp na ga bakya online yanzu ina kiranki ma shiru" "Data ce ta kare mini" Ta ce tamkar ta saki kuka. "Kai innalillahi gaskiya SALIMAH kin saka kan ki cikin wani hali ke yanzu data ma sai take gagararki, kamar dai ke kika rako mata duniya to shi kuma kiran da kika ki ɗauka fa?". "Ina kicin ina ɗumama tuwo... "Tuwo!?" Ta ce tamkar ta faɗi wani mugun abu. Shiru ta yi saboda takaici ya gama cika mata zuciya. "Dama abubuwan da ƴar aiki ta dafa mini wanda nake son na ci, na ɗauka a hoto na turo miki, yam balls, chicken pepper, wainar kwai sai shayin da na saka aka juye madarar gwangwani ta ruwa uku don ruwa ma kaɗan aka zuba" Ta ce jin ta yi shiru SALIMAH a take yawunta ya tsinke ta ji dama ita ce a cikin daular da kawar tata take. "Ai tun da kika zaɓi zama cikin talauci kin dinga ganin takaici kenan, ni fa sai a wajenki ne nake jin sunan tuwo, don rabona da na saka shi a bakina tun ina gidanmu shi ma kin sanni sai na ga dama nake ci" ."To wai ya zan yi ne EESHART kin san dai bani da ikon sakin kaina shi kuma ABBAS yadda kika san da igiyar aurena aka halicce shi ya ce muddin yana numfashi ba zai taɓa sakina ba kin san irin mutuwar da ya yi a kan sona... "Yo dama ya za a yi ya yarda ya saki mace kamarki, bayan ya samu tsuntsu daga sama gasasshe ai ya sani idan ya rabu da ke ba zai samu kamar ke ta aure shi ba, bayan ya san sa'a ya taka amma ki cigaba da gwadawa shi aure ai rai ne da shi daga wa'adinsa ya cika dole a rabu ko ba a so" "Haba EESHART kina ganin shekara biyar kenan ina fama amma bai sake ni ba". "Ki dai cigaba da gwadawa domin da gwado jirgin sama ya tashi" Da to ta amsa mata suka yi sallama bayan ta ce za ta saka mata datar da kati. Da tunanin mafita ta ajiye wayar tana jinjina ranar da za ta dace ABBAS ya furta mata kalmar saki ko da a cikin baccinsa ne ko da suɓutar baki ne don ta fita ta auri miji na kece raini ta rayu a gidan hutu wannan shi ne mafarkinta wanda marigayin Babanta ya yi fatali da shi a cewarsa ABBAS ne da ya dace da ita shi ne mai kaunarta da gaskiya duk runtsi duk wuya sai ga shi bayan auren Baban ya mutu kuma ABBAS ya ki sakinta har yau. Kicin ta koma tsabar tuno abin da kawarta za ta ci da kafa ta yi ball da karamar tukunyar tuwon da ta ɗora ya kuwa kife a kasa ta juya falon ta dawo kuɗin da ABBAS ya bata ta ba almajirinta ya auno shinkafa da kayan miya a yi abincin rana shi ta zari dubu ɗaya ta fita ta buɗe kofar gidan nasu wanda yake gidan haya ba mallakin ABBAS ɗin bane. Tana buɗe kofar idanunta ya sauka a kan gidan makocinsu Alhaji ALI wanda gidan yana kallon gidan nata, iya ganinka gida ne da aka kashewa dukiya don kuwa gida ne aljannar duniya gida ne da take mafarkin samu irin gidan nan ko da mutum bai rayu a ciki ba in har yana sa hangen na sama da shi tare da raina matsayin da Allah ya ajiye shi to kuwa zai so ko sau ɗaya ne tak ya shiga gidan ya kashe kwarkwatar idanunsa. Ta yi nisa a zancen zuci ta shagala da kallon gidan bata ankara ba sai gani ta yi an wangale get ɗin gidan motar da aka buɗe get ɗin don ita ce ta fito kallon yadda motar ta haɗu tare da yin shekin sabunta ne ya ɗauki hankalinta bayan sauran da take hangowa daga cikin get ɗin wanda suke fake wasu a lulluɓe wasu a buɗe. Alhaji ALI da yake bayan motar direbansa yana jansa ne ya yi gam da katar da ganin SALIMAH cike da mamaki yake ganin kyawunta da kuma kira da Allah ya mata kyakkyawa ce ajin karshe, tsantsar mamaki ne ya kama shi ganin cewar mace kamar wannan tana rayuwa a kaskantaccen gida kamar wannan domin yanayin shigarta ko ɗankwali babu ga rigar jikinta da ta kama ilahirin jikin nata hakan ya nuna matar gidan ce ba wai zuwa ta yi ba. Tsabar kallonta da yake har sai da ya sauke glass ɗin motar, ido huɗu SALIMAH ta yi da shi da yake bakin glass ne baka ganin na ciki amma na ciki yana ganinka ita kuma kyan motar take karewa kallo tana kiyasta ranar da za ta shiga mota kamar wannan. Ganin sun haɗa ido sai kawai ta diririce ta shiga ɗagawa almajirin da ta gani yana bara a wani gidan da yake gefen gidanta hannu alamar ya zo, hakan ya yi daidai da saita hancin motar da direban ya yi a inda suka saka gaba. Har waiwayenta Alhaji ALI yake har sai da suka ɓace daga layin sannan ya daina waiwaye. Karan rufe get ɗin ne ya saka ta sauke ajiyar zuciya tare da maida hankalinta kan almajirin ta ce. "Je ka wurin mai biredin wancan ka siyo mini bidredi na ɗari uku kwai guda biyu madarar sachet guda ɗaya" Robarsa ya bata ya tafi ta dawo ta ajiye robar jim kaɗan ya shigo da sallama. "Kwan ɗari biyu da hamsin-hamsin madara kuma ɗari da saba'in" Ya ce yana mika mata ledar da canjin naira talatin ɗin. "Rike canjin" ,Kawai ta ce ta juya ya ce Allah karɓa ya ɗauki robar tasa ya juya ya fita, ko amsa masa bata yi ba ta wuce kicin ɗin saboda yunwar da take kwakular ƴaƴan hanjinta ta dafa ruwan zafi ta soya kwan ta dawo ta haɗa shayi ta zauna ta ci ta koshi. Sai lokacin ta ji dama-dama a kan kwaɗayin da EESHART ta tada mata. Tana nan tana danne danne a waya ta shiga nan group ɗin a whatsapp ta fita saboda datar da EESHART ta turo mata, wani group na bussines ta shiga inda admin ɗin ta turo hotunan lesuna da dogayen rigunan abaya, wata mata da user name ɗinta aka rubuta matar mai kumbar susa ita ce ta zaɓi lesuna guda uku dogayen riguna guda biyu ta ce a mata total a tura mata acc no ta private ko ragi bata nema ba kusan dubu ɗari uku. "Kuɗi sun yi a rayuwa" Ta ce tana kallon lesunan tana hango yadda da ita ce ta same su ba karamin kyau za ta yi a ciki ba amma ina bata da ko irinsa guda ɗaya ma dama ko kayan lefe bai mata ba Babanta ya ce ABBAS ya kawo kuɗin da ya sawwaka ai aure albarkarsa ake nema kuma aure yana kawo arziki. Yanzu shekara biyar da auren amma babu wani ci gaba sai ma ci baya gabaɗaya talauci ya musu kaka gida ga tsadar rayuwa rashin isassun sutura ya sa ko biki da suna bata son zuwa idan ta je sai ta ga ta raina kanta musamman in ta ga kawayenta sun yi shiga ta kece raini ita kuwa daga atamfa leda sai leshin mama ta mutu irin na legas ɗin nan da ake sayarwa na hannu. Saboda haushi bata san ma lokacin da ta fito daga bussines group ɗin ba, wajen status ta je nan ma ta shiga ganin hotunan da aka ɗaɗɗora a status wanda na jikin hotunan suke sanye cikin shiga ta alfarma wasu an musu make up gashi nan dai amma duk ciki bata ga wacce ta mallaki ko da rabin kyanta ne ko kirar halittarta. Wani hoton wata mata da ta gani a status ɗin wata kawarta matar tana zaune a kayataccen falonta da yaranta guda uku da alama yarinya ɗaya ce ake yi wa murnar zagayowar ranar haihuwar ta domin ga cake nan da lemuka. "Gida na alfarma shi ne rayuwa" Ta ce a fili tana sauka daga whatsapp ɗin ma baki ɗaya ta ajiye wayar tana sauke idanunta a nata falon wanda sai ta ga tamkar a kufai take. "Ga doya da kwai" Ta jiyo wata tana tallah. Kiranta ta yi ta saya ta dubu ɗayar ragowar kuɗin abincin ranar da yake doyar ɗari bibbiyu ce ta zauna ta ci ta yi sallah ta kwanta bacci ya yi awon gaba da ita. ABBAS tun da ya baro gida ya nufi ƴan kafintoci inda yake aikin kafinta haka ya wuni yana aiki, ko da ya ji kewar matarsa SALIMAH ya yi ta kiranta a waya amma bata ɗauka ba haka ya gaji da kira ya hakura. Bai karya ba ya fita saboda tuwon kaɗan ne ko dubu biyun da ya bar mata ma rantowa ya yi haka ya wuni bai ci komai ba sai karfe biyar ya baro kafintocin. Tun da ya doso gidan gabansa yake faɗuwa duk da hakan ya san yana faruwa da shi amma sai yake jin kamar na yau ya fi kullum hannu ya saka a aljihu ya fito da kuɗin ladan aikinsa da aka biya shi dubu uku da ɗari takwas, mayar da su ya yi yana son gano ko kuɗin za su isa ya famshi kansa a wajenta duk da ya ranci kuɗi da safe don ba ya so ta zauna babu abinci, a duniya da SALIMAH ta rasa abu gwara shi ya rasa ko ta halin kaka yana iya bakin kokarinsa don ganin ya faranta mata amma bata ganin hakan kullum gazawarsa take gani kullum burinta ya sawwake mata auransa amma ba zai iya sakinta ba sakinta babbar barazana ce ga rayuwarsa gani yake ba zai iya rayuwa a wannan duniyar matsawar ba tare da ita ba, amma ita sheɗan da muggan kawayenta suna mata huɗubar banza ta ganin sun kawo karshen zaman sa da ita. Da sallama ya shigo gidan amma shiru ba a amsa ba, dama ya saba da hakan amma kuma rashin amsa sallamar ba zai sa ya daina yi ba saboda wajabcin sallamar da kuma ladan da ake samu idan an yi sallamar. Buhunsa mai ɗauke da kayan kwale-kwalensa ya ajiye a inda yake ajiyewa kicin ya nufa domin samarwa cikinsa da yake ta kugi abin da zai sa a ciki sai dai tun kan ya karasa kicin ɗin yake hango tamkar dai babu wasu alamu na an ɗora wani abu, hakan ce kuwa ta tabbata da ya karasa domin idanu huɗu da ya yi da tuwon safen da ya sadaukar shi ga SALIMAH shi ya ɗauki na annabawa. Wani ɓacin rai ne ya ziyarce shi shaiɗan ya azalzala zuciyarsa yana jin wani tukuki inda ya haɗu da ɓacin ran da yunwar ta haifar. Amma yaki ya yi da zuciyarsa wajen dannewa ya nufi falon. Tana zaune a kasan ledar tsakar ɗakin tana yin magana da alama voice take yi sai da ya jira ta kammala ya dube ta ya ce "Haba SALIMAH yanzu in fita tun safe in dawo amma babu abin da kika dafa, kuma tuwon da na hakura na bar miki kika zubar da shi a kasa yanzu a halin da mutane suke ciki na tsadar rayuwar nan wasu ma suna kwana da yunwa, wasu suna mutuwa da yunwa wasu dusar awara suke ci ke har da wanda suke sakawa ruwan ɗanwake suga suna sha amma ke... "Kai ABBAS dakata! Ba fa haifata ka yi ba da za kake mini magana faɗa-faɗa" "Haba SALIMAH mene ne na faɗan a nan daga faɗar gaskiya sai cibi ya zama kari... "Bana son jin komai yanzu don ban yi girki ba za kake wani maimaita mini magana ai hukunta ni ya dace ka yi, sannan batun tuwo,tuwo,tuwo kana maimaitawa tamkar ka samu karatu mene ne don na zubar da tuwon bana ci sai kawai in ci kuma su masu kwana da yunwar ai su suka so dama rayuwa ai hawa-hawa ce tun da ba ni na hana su neman abin da za su ci ba, wasu ma basu san mene ne wani tuwo a rayuwarsu ba daga nama sai kayan daɗi irin rayuwar da nake mafarkin yi, irin burin da na ci ka zo ka mini shigar sauri ni ba tsararka bace ni ba sa'ar aurenka ba ce ba ajinka ba ce ni ABBAS sau nawa kake so in maimaita maka cewa na tsaneka ka sake ni in je in auri wanda yake daidai da tsarin rayuwata, inda zan huta wani nawa ma ya huta wallahi wallahi wallahi ba zan taɓa kashe yarintata a wannan kaskantacciyar rayuwar talaucin ba!" Yadda take maganar cikin hargowa da ɗaga sauti ya sa gabaɗaya ya rasa bakin magana, ta saba masa hakan a kullum wani lokacin ma tsakar dare yana bacci take tada shi da wannan masifar da zancen saki ya sha faɗa mata babu kyau mace take neman saki a wajen miji ba tare da wani kwakkwaran dalili ba na cutarwa ko makamancin su amma kururuwar shaiɗan ba ta bari ta fuskanci komai sai ta ce ita kuwa take da hujja domin kuwa cutar da ita ake yi, saboda wata sabuwar rayuwar take so ba wannan ba. Sai dai yau maganganun nata sun masa zafi da yawa wani ciwo yake ji a zuciyarsa musamman saitin kirjinsa daga hagu inda zuciyarsa take dashe a wajen tabbas in bai yi wasa ba SALIMAH tana dab da saka masa ciwon zuciya don hawan jini tuni ya haɗu da shi. "SALIMAH" Ya faɗa da sanyin murya yana jin yadda kwalla ta taru a idanunsa, ga wani nauyi da yake ji a zuciyarsa tamkar an ajiye dutse a wajen. ."Sunan da ubana ya dasa mini" Ta ce tana rike da kugu tana wani jijjiga jiki. ."Na sani dama, amma don Allah ki bar zuciyata ta huta ina kaunarki SALIMAH na yi yaki da zuciyata a kan in sawwake miki ko don na ga hakan shi ne farin cikin ki, amma ba zan iya ba SALIMAH, wallahi ba zan iya rabuwa da ke ba, ba zan juri rashin ki ba rasa ki tamkar rasa duk wani walwala da farinciki na ne duk da ina tare da ke ɗin ma baki bar ni na samu hakan ba amma dai da babu gwara babu daɗi ko da a ce za kike yankar naman jikina a kullum na yarda na rayu da ke na zan iya rasa komai saboda ke na aminta a hana ni komai in za a barni da ke... "Ai kuwa wallahi ka kama RUƁAƁƁIYAR IGIYA don wacce kake so ɗin baka gabanta kuma ni zan iya yin komai don na rabu da kai kuma tun da kai babu zuciya a kirjinka zan cigaba da zame maka ciwon ido har ranar da wa'adin aurena zai cika ka sauwake mini, duniya ban taɓa ganin marar zuciya ba sai kai ABBAS ni dai ina jin sai na fara rokon Allah ya ɗauki ranka ka mutu in auri wani... "Zan fi so hakan ya kasance ni na fi son na mutu ke ki rayu, na fi so indai bana duniyar ki auri kowa ma na san tun da bana raye hakan ba zai yi wani sanadi a gareni ba, idan har kika haifa mini ɗa wanda zai zama na bar tsatson ki a duniya wanda zai ke mini addu'a SALIMAH burina ya cika" "Albishinka ce goro ABBAS kalli nan" Ta ce tana ɗaga hannun rigarta farin fatar dantsen hannunta ya bayyana. "Wannan tsinken hana haihuwa ne na saka tun ana gobe ɗaurin aurena da kai na je na saka na shekara uku! Kuma bayan wa'adin shekarun sun cika na je aka cire aka mayar mini da wani na shekara ukun yanzu shekararsa biyu yana karasa shekara ɗaya zan cire in maida wani, ko shekara dubu zan yi a gidanka sai na yi ta sakawa, ku tarayyar auratayyar ma ai ka san ba da haɗin kaina kake yi ba, kai kanka ka san wata rana maganin bacci kake zuba mini a abun sha wanda bacci mai nauyi zai ɗauke ni har ka gama uzurinka ban sani ba, saboda baka gabana uzurin auratayya da kai ma bana kaunar yi, kuma ina son ka san wani abu ni dama ba zan haifi yara a gidan talauci ba rainon madara rarrafen kafet da tiles nake so ba rainon tuwo rarrafen ledar tsakar ɗaki ba" Tun da ta fara maganar hawaye suke ambaliya a idanunsa, wani ɗaci yake ji a zuciyarsa tabbas SALIMAH ita ce kaddararsa da Allah ya ɗora masa masifaffan sonta yana hakuri da duk abubuwa da cin kashin da take masa, sai dai an zo gaɓar da ba zai jure ba an zo wajen da bai ji zai iya ba dole ya yi hukunci dole ya ɗau mataki a kan wannan mummunan laifin da ta aikata masa tana ikirarin shi juya ne ta sanya yake bin asibitoci yana biyan kuɗin gwaji ana tabbatar masa da lafiya yake ashe dai ga miciji amma yana abin ja. Bai san lokacin da hannunsa ya ɗauki hanyar fuskar SALIMAH ba sai gani ya yi ya wanke kyakkyawar fuskarta da wani wawan marin da sai da ta ga gilmawar taurari. MAMAN AFRAH 09013181851 [1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ka/ki ya yi daidai da labarin ki to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah ya saka da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 2 Cike da tsananin mamaki take duban ABBAS jin yatsun sa biyar a fuskarta. Bakinta take son motsawa amma ta kasa buɗewa bare har ta haɗa haruffan da za su zama kalaman da za ta furta. Shi kuma ABBAS sai a sannan ya gane katoɓarar da ya yi. 'Ai ni wallahi ba a yi ɗa namijin da zai kai hannunsa jikina ba, duk ranar da giggiwar namiji ta saka ya dake ni wallahi yana sauke hannunsa ina ɗaga nawa, kuma daga ranar ya daki aurensa wallahi don ko kai ne autan maza na bar ka bari na har abada ma kuwa' Maganar wata mata ta faɗo mata a rai wata rana a gidan biki tana tsaye take jiyo maganar wasu mata guda uku da suke jajantawa wai kawarsu mijinta ya mata shegen duka. A ranar da SALIMAH ta ji tattaunarwar su take kiyasta to ita wane tsautsayin ne zai sa namiji ya kai hannu jikinta ita bata yi kalar matan da za a duka a gidan aure ba, to kuwa tabbas shi ma da ya daki auren nasa bare kuma ita dama da take neman makala wato ABBAS lallai yau mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki. Sai da ta shammace shi ta ɗaga nata hannun ta sauke masa a fuska. Al'ajabi ne ya hana shi yinkurin komai don bai taɓa zaton SALIMAH za ta iya dukansa ba duk da shi ne ya fara taɓa lafiyarta amma dai abin akwai mamaki. "SALIMAH ni kika mara?" "An mare ka who are you?" Ta ce cikin halin ko in kula. "Kuma idan har ka haifu ɗan halal ba shege ba a cikin iyayanka to ka sawwake mini" "Na sake ki saki ɗaya SALIMAH" "Ayyiriri yiriiii" Karan guɗar da ta saki ne ya dawo da shi hayyacinsa tare da ankara da abin da ya yi. Sai dai kalmomin da ta yi amfani da su wajen karɓar sakin ne sun zafafa sun rura masa wuta a zuciya, sai dai ba zai ce bai shiga ruɗani da tashin hankali ba na kalmar sakin da ya furta mata wacce ta fito daga bakinsa tamkar an fisgo ta. Yaraf ya zube a kan gwiwoyinsa don ya san SALIMAH ta suɓuce masa suɓucewa ta har abada kuwa, sai dai ya ɗauki na annabawa amma da wuya ta yarda ta dawo gare shi domin abin da take nema ne shekara da shekaru ya samu. "Innalillahi wa inna alaihi raji'un" Ya faɗi hakan a fili sai dai kafin ya ankara har ta fita daga ɗakin ya san kuwa zancen gizo ba ya wuce na koki ma'ana zuwa za ta yi ta haɗa kayanta. Daɓas ya zauna ya haɗa kansa da gwiwa yana jin yadda gabansa yake bugawa gabaɗaya ya rasa ma wane tunani zai yi shi yunwar da yake ji ma bai san ta inda ta bi ba saboda wani ciwon ya danne wani zafin rabuwa da masoyi ya fi gaban wasa. SALIMAH kuwa wani irin daɗi da farin ciki take ji, ji take tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha, har da wata rawa ta taka a ɗakin kayanta ta shiga haɗawa a wata babbar jaka sai da ta cika ta taf da sauran kayan amfanin da za ta bukata, kafin a zo kwasar kaya, rigar jikinta ta sauya ta yafo mayafi ta ɗakko jakar ta fito a kofar falon ta ajiye jakar ta shigo falon domin ɗaukan waya, jin shigowar ta ya tashi tamkar an tsikare shi yana jin da na sanin abin da ya yi. Cajar wayarta ta ɗauka da kuma wayarta kallo ɗaya ya mata ya gane tsantsar farin cikin da take ciki. "ABBAS saduwar alkairi Allah haɗa kowa da rabonsa yau ka biya ni" Ba ta jira cewarsa ba ta bankaɗa labulen ta fita ta ɗauki jakar sai ga shi kamar an watso shi duk ya firgice sai ma ta so ta ji tausayinsa amma dai ganin bahaushe ya ce so, so ne amma son kai ya fi sai ta ji ta fi tausayawa kanta a kan shi. "SALIMAH don girman Allah ki yi hakuri" "Wa? Ai in ka ganni a lahira kai ni aka yi" Daga haka bata jira cewarsa na ta juya ta fice, zaunawa ya yi a kasa yana jin zuciyarsa tana suya tabbas in akwai abin da yake kaddararsa kuma jarabawarsa to bai wuce son SALIMAH ba, akwai lokacin da ta yi yaji ta ki dawowa ba tare da wani dalili ba dama mahaifiyarta ma ba kaunar auren take ba Babanta ne mai son auren kuma ya mutu. Tsawon sati biyu ta yi bata gidan amma sai da ya kwanta jinya hatta aikin kafinta ba ya fita, wata rana idan ya je gidansu SALIMAH aka ki kula shi kan maganar bikon sai ya zauna a kofar gidan ya wuni sallah ce kawai take tashin sa daga wurin idan ya yi ya dawo saboda kawai jurewa ya yi ta yi amma ya san ya azabtu da rashinta. Wasu hawaye ne masu zafi suke masa ambaliya a fuska tabbas ba kowa zai gane irin hali da raɗaɗin da yake ciki ba sai wanda yake cikin halin da yake ko wanda ya taɓa shiga irin halin. 'A kullum addu'a ta shi ne in rayu a duniya ɗaya da SALIMAH duk duniyar da babu SALIMAH sai in ji tamkar dai makabarta ce, amma yau kaddara ta gifta kaddara wacce take rubutacciya don in ba kaddara ba ba na jin akwai ranar da ni da bakina zan furta kalmar saki ga SALIMAH amma rubutacciyar kaddara wacce ba ta goguwa domin irin wannan kaddarar ita ce ake kira kaddara wacce ta riga fata, na san wasu za su ji haushina wani ya ji kamar ya hau ni da duka wani kuwa zai ga ai so ba hauka bane sai dai kash! Bai san irin ɗinbin so da kaunar SALIMAH da suke dankare a tawa zuciyar ba ni ban taɓa cin karo da irin son da nake yi wa SALIMAH ba, ko da kuwa a labari ne son da nake mata ya fita da ban ya fi karfin zuciyata, da ce SALIMAH za ta bukaci in ɗaye fatar jikina in bata babu wani dalili da zai sa in kasa ko da za a saka bakin bindiga a kaina a ce in sake ta ko a harbe ni, to tabbas ba zan furta mata kalmar saki ba amma yau tsautsayi wanda ba ya wuce ranar sa ya sa giyar fusata da gajen hakurin ɓacin rai da kasa jure kalamanta uwa uba shaiɗan mai amfani da dama idan mutum na cikin ɓacin rai ya ci galaba a kaina' Ya furta a zuciyarsa yana haɗa kai da gwiwa ji yake duniya ta masa kunci tabbas yana cikin matsatsi. "Don Allah ki dawo gare ni SALIMAH" Ya furta a fili da karfi har jijiyar wuyansa tana bayyana raɗo-raɗo, yana mai fashewa da kukan tausayin kansa. *SALIMAH* Cikin wani farin ciki ta fito daga gidan kofar gidan ma a buɗe ta bar ta ko darajar rufewa bata samu ba, ji take tamkar ta taka rawa ji take rabon da ta ji ta cikin annashuwa tun ranar da aka ɗaura mata aure da ABBAS, tun daga wannan rana ta tsinci kanta cikin wani yanayi tun daga wannan rana wani abu ya tokare mata makoshi abin nan da ya tokare ta bata taɓa jin ya gushe daga wurin ba sai yau da ABBAS ya furta mata kalmar saki abin dai tana jin sa kamar almara sannan kuma sai take jin tamkar a mafarki. Duk da soyayya suka yi da ABBAS ɗin sai dai ita ta kauna ce shi ne saboda kyau da yake da shi duk cikin maneman ta babu wanda yake da kyansa, kuma babu wanda ya haɗa duk abin da take bukata daga ɗa namiji kamar ABBAS su dai sauran kuɗi da manyan motoci da gidaje za su faɗa masa shi kuma Allah ya mallaka masa komai da mace za ta so ga ɗa namiji matsalarsa ɗaya cikas ɗinsa ɗaya mugun talaucin da ya kanannaɗe shi ya masa dabaibayi. Manyan alhazan da take kulawa masu hannu da shuni suna kashe mata kuɗaɗe jikinta suke so, don sun sha zuwa mata da kalmar ɓatanci amma ta ki bada haɗin kai, shi kuma ABBAS kaunarta yake da gaskiya wannan dalilin ganin yana jumuri da jure duk wani abu da za ta masa kuma nutsatstsan matashi mai girmama na gaba, uwa uba ibada da tarbiya hakan ya sa mahaifinta ya dakatar da kowa daga zuwa wurinta ya ce ABBAS zai aura mata. Ta yi kukan bakin ciki tun daga ranar ta ji ta tsani ABBAS kyansa da take gani ya koma mata muni domin ta fi kaunar kuɗi da morewar rayuwar duniya a kansa. Kamar kumbo kamar katanta yadda abin nan yake a wajen SALIMAH haka yake a wajen mahaifiyarta, bakin su ɗaya ita ma duniyar ce a gabanta, don duk abin da mahaifin SALIMAH zai faɗa mata a kan rayuwar duniya da bin duniya a sannu da dai nasihu masu bin sassan jiki da shiga zuciya, yana tufka ne mahaifiyarta tana warwara abin da zai faɗa mata da ban wanda za ta faɗa mata da ban, idan ya biya mata karatun ta nutsu sai mahaifiyarta ta goge hardar. Har ya bar duniya bayan auren da watanni uku a sannan ne ruwa ya karewa ɗan kada domin kuwa sun bi duk hanyar da za su bi wulakanci kala-kala a kan ABBAS ya sake ta amma ya ki yau dai ga shi buri ya cika. Tafiya ta fara yi tana rike niki-niki da jakar kayanta, sai murmushi take, sai sannan kiran kawarta EESHART ya faɗo mata da sauri ta kamo sunanta ta danna mata kira ringin ɗaya biyu wayar ta yi ta ɗauka. "Hlo kawata... "Albishirinki ce goro" Ta katse mata maganar tana dariya. "Goro fari tassss" Ta ce cikin zakuwa da son sanin dalilin shigar kawar tata cikin wannan farin ciki, saboda bata yi wani tunanin komai ba. "ABBAS ya rangaɗa mini saki EESHART yau ya warware wannan doguwar igiyar kaddarar da tsofaffin nan da shedu suka taru suka talaulaye ni da ita" Ta ce hakoranta talatin da biyu a waje. Alhaji ALI da suka shawo kwanar layin yana waya, da ita ya fara tozali ganin dariyarta sai ya saka shi cikin wani yanayi har ya shagala da kallonta har suka zo saitin ta yana kare mata kallo tabbas ya shaidata ita ce dai ta safen nan da ya gani lokacin da suka fita. "Eh, dariya, kyakkyawa" Ya ce a wayar saboda gabaɗaya ya ma sha'afa da abin da suke magana a kai. Daga ɗaya ɓangaren aka katse shi da mai yake nufi sai sannan ya dawo hayyacinsa don hatta direban sai da ya gane cewa Alhajin ya yi suɓutar baki, dariya ce ta so kwace masa amma gudun yi laifi sai ya danne, don ya lura da wacce yake kallo yana ganinsa ta madubi. "Ke SALIMAH bana son wasa wallahi ai ko za ki yi wasa da komai ban da wasa da sakin ABBAS don na san wannan ɗan a nace ɗin ba zai sake ki ba" "Wallahi kawata da gaske nake da bakinsa ya furta kin ganni har na haɗo kayana na baro masa agwajan gidansa, kin ga shi ma ya huta da da biyan kuɗin haya" Wani ihu EESHART ta saka don ta rasa ma ina za ta ajiye wanna magana mai daɗi. ."Barka kawata na taya ki murna Allah mana tsari da auren masu dattin hula ƴaƴan malam shehu to ina dalilin auren talaka " ."Wallahi kuwa ai yanzu sai na zaɓa na darje" "Hahaha wallahi kuwa kawata kina lokaci" Ta ce tare daɗa fashewa da dariya. "Bari in na je gida ma yi waya so nake in je in yi wa Umma albishir ita ma ta ɗanɗani wannan farin ciki" Da to ta amsa mata tana mai kashe wayar sosai take ji da EESHART yadda take kaunarta tana bata shawarwarin yadda za ta kuɓuta daga auren ABBAS ta yi auren da za ta ji daɗi ta huta, sai dai bata san cewa ba turba mai kyau ba ce haka ba kuma hanya mai ɓullewa ba ce illa iyaka RUƁAƁƁIYAR IGIYA ce. Alhaji ALI kashe wayar ma ya yi don ba ya so yake kwariɓi a waya, sai ya ga gwara ya bari idan ya zauna ya nutsu ya yi wayar. Raja'a ya yi da kallon SALIMAH da take waya har aka buɗe get ɗin bai sani ba sai da direban ya durfafi cikin gidan sannan ya dawo hayyacinsa. Ganinta yake tamkar ba bahaushiya ba sai ka ce wacce take ɗaya daga cikin ukun nan, larabawa turawa ko indiyawa saboda yanayin farin fatarta kamar ba na africa ba. Napep ta hanga ta ɗaga masa hannu tahowa ya yi sai da ya zo saitin ta ya ja birki. Jakar ta saka a cikin napep ɗin, tana shirin shiga kamar an ce ta ɗago kanta ai kuwa ta hango ABBAS ya fito daga gidan tamkar zararre kafarsa ko takalmi babu uwa uba fuskarsa da hawaye, da sauri ta yi saurin shigewa napep ɗin. "Malam ja da sauri mu tafi kar wancan ya karaso na ga ya yi kama da mahaukaci kar ya warce ni ya mini duka" Ta ce tana hango yadda ABBAS ɗin ya rugo da gudu zai zo wajensu ganin da ya yi ta shige. So yake ya zo ya gwada sa'arsa ko za a dace duk da ya san da wuya wai gurguwa da auren nesa. Mai napep kuwa kallon tsoro ya jefi ABBAS ɗin da shi duk da bai masa kama da mahaukaci ba ko ta yanayin shigarsa, sai dai dole ya bi umarninta tun da aikin kuɗi zai yi. A guje ya fisgi napep ɗin suka tafi. Cak! ABBAS ya tsaya bai san ma ya ɗaga hannaye biyu ya ɗora a kansa ba tamkar wanda aka yi wa mutuwa. SALIMAH wata ajiyar zuciya ta sauke ganin bai cim musu ba domin ita a halin da ake ciki yanzu ko hanya ba ta son haɗawa da ABBAS ɗin don an yi mai gabaɗaya haihuwa har hanji. A kofar gidansu aka ajiye ta, gidan kasa ne aka shafe shi da jar kasa, cewa ta yi ya jira ta ta ɗauki jakar ta shige cikin gida. Umma da take zaune a kan kujera tana goga ɗanyar kuɓewa ganin shigowar SALIMAH da sallama tana rike da jaka riki-riki bata san lokacin da ta cillar da magogin kuɓewar ba, tare da kuɓewa guda ɗaya da take rike a hannunta tana gogawa tsaye ta mike tana kallon fuskar SALIMAH mai cike da alamar farin ciki hakan ne ma ya sa ko sallama ta kasa amsawa. "Allah ubangiji ya sa ba ya ji bane" Ta faɗa tana kallonta don ta tsani yaji ma ta fi son ta ji kalmar saki duk da ta san mawuyaci ne a yi sakin amma dai ganin yanayin SALIMAH ya sa ta ji tana son jin karin bayani. Cilli SALIMAH ta yi da jakar hannunta, ta karasa da gudu ta kankame Umma cike da farin ciki. ."Umma ABBAS ya sake ni" Ta ce tana kara kankame mahaifiyar tata da karfi. "Ke SALIMAH kin san dai bana wasa da ke" Ta ce lokacin da ta ciro SALIMAH daga jikinta tana kallonta ido cikin ido. "Wallahi Umma ya sake ni saki ɗaya" Ta ce tana ta murna da nuna farin ciki.. "Ayyyyyiririr yiriiiiii" Umma ta rike hanci tare da kwarara guɗa. "SALIMAH anya yana cikin hankalinsa kuwa ya sake ki, ko dai wani abu kika bashi ya sha ya bugu kika tambaye shi sakin?" Umma ta ce tana jinjina yadda aka yi hakan ya afku. "Rass yake babu wani buguwa dawowarsa kenan ma daga... ."Assalamu alaikum" Wani yaro ya shigo da sallam. Amsa masa Umma ta yi tana masa kallon rashin sani. "Wai in ji mai adaidaita sahu a bashi kuɗinsa" Ya ce yana ja ya tsaya. "Lah ka ga na manta ma da shi, Umma kawo ɗari huɗu a bashi" Cewar SALIMAH. "To zo ka karɓa" Ta ce tana mika masa ya karɓa ta fita. "Oh wai kuɗin adaidaita ma sai kin zo gida baki da kuɗi, yau dai Allah ya yanke miki wannan wahala, mai za a yi da wahala na san yanzu manyan mutane masu faɗa a ji sai kin zaɓa kin darje" Umma ta ce tana dafa kafaɗar SALIMAH. "Wallahi kuwa Umma na san layi za suke yi da motoci a kofar gidan nan kowa yana burin ya mallake ni" Ta ce tana rungume Umma tana jin wani daɗi domin ta rasa gurbin da za ta ajiye farin cikin da take ciki. Saboda har ta fara hango ta a kayataccen gida na alfarma tana cin duniyarta da tsinke. "Ai babu wanda zai yi tozali da wannan kyakkyawar halittar taki, ya yarda ki suɓuce masa, shi ya sa nake jin takaici da mahaifinki ya aura miki fukara'u bayan na san na haifi babban jari farar mace alkyabbar mata" Umma ta ce, dariya suka saki a tare. *ABBAS* Tamkar mahaukaci sabon kamu haka ya juyo ya dawo gidan, yana shigowa ya ji wani kunci a ransa kamar zararre haka yake jin sa sai ya ji ba zai iya jure zama a cikin gidan ba, ganin SALIMAH bata nan kuma ya san cewa ba wai unguwa ta je ba gidansu ta tafi a matsayin ya sake ta. Bedroom ɗin ya shiga da niyyar ya sauya kayan jikinsa amma da ya shiga sai ma ya rasa mai zai yi a cikin ɗakin, fitowa ya yi ya shiga falon ya ɗakko mukulli ya kama hanyar waje sai a sannan ya tuna babu takalmi a kafarsa, dawowa ya yi ya saka takalman ya fita ya rufe gidan. Tafiya ya fara yi amma sai yake ji tamkar kafafunsa ba za su yi jumurin ɗaukan gangar jikinsa ba, saboda yadda kafafun nasa suka yi sanyi ba ma kafafun ba hatta jikin nasa ma sanyi karai ya yi kawai dai yana saka kafafun ne ba tare da sanin ina ma yake jefa su ba, ga wata juwa da take faman ɗaukansa. Machine ya tsayar ya faɗa masa inda zai kai shi a daidai kofar gidan da ya masa nuni ya ajiye shi ya bashi kuɗinsa. Da sallama ya shiga gidan Mama da fitowarta kenan daga banɗaki tana rike da buta ta ga ABBAS ya shigo da sallama amsa masa ta cikin sanyin murya, ganinsa ba yadda yake, idanunsa jajur kai gabaɗaya a matsayinta na uwa mahaifiya a gare shi tana ganinsa ta san yana cikin matukar damuwa tana ganinsa ta san gabaɗaya ba ya cikin hayyacinsa. Butar hannunta ta ajiye tana nutar falo ya bi bayanta zaunawa ta yi a kujera yana shigowa ɗakin wani kukan ya taho masa irin kukan da mai yinsa yake yi idan ya ga mai rarrashin sa. Da sauri ya karasa gabanta ya durkusa gwiyoyinsa a kasa tare da kifa kansa a kan cinyarta ya fashe da kuka. 09013181851 [1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 4 *ABBAS* Dakatawa Mama ta yi bata hana shi kukan ba, duk da sautin kukan nasa yana taɓa mata zuciya, ta san cewa ba karamin abu bane zai sa ABBAS ɗin kuka haka ba kamar wani mace, kasancewarsa mai hakuri da juriya haɗe da kawar da kai sai dai ta san kukan nasa ba ya rasa nasaba da SALIMAH domin ta san ita kaɗai ce matsalarsa, ita kaɗai ce damuwarsa, ya ɗauki son wacce ba ta son shi ya saka a ransa ko kaɗan SALIMAH ba ta tausayinsa bare ta ji tausayin halin da yake ciki na soyayyarta burinsa kullum ya faranta mata, amma bata gani ta raina duk kokarinsa a kanta shi kuma kullum faɗi tashin sa SALIMAH ce duk da Mama ta san yana matukar kokarin ganin ya kyautata wa Mamar matsayinta na mahaifiya a gare shi sai dai ganin irin jarabawar da ya haɗu da ita na matar da ya aura sai take yafe wasu abubuwan tun da bata rasa komai ba kanin mahaifin ABBAS ɗin bai rage ta da komai ba tun bayan mutuwar mahaifin ABBAS yake ɗawainiya da su har yau bai daina ba kuma bai gajiya ba. Sai da ta ji kukan nashi ya tsagaita, ta tabbatar ko ma mene ne yanzu zuciyarsa ta yi sanyi, saboda duk idanun da suka zubar da hawaye to mai idanun yana samun salama a zuciyarsa. Jin yana ajiyar zuciyar sai ta saka hannunta wanda tun da ya kifa kansa a cinyarta ta ɗora hannun a bayansa, fara buga masa bayan ta shiga yi a hankali sai da ta tabbatar ya samu nutsuwa daga ɗimuwar da ta gan shi a ciki sannan ta saka hannun ta duka biyu ta ɗago shi. Sosai ta ji rauni a zuciyarta ganin yadda idanunsa suka yi wani irin ja hatta fuskarsa da saman hancinsa duk sun yi ja saboda kukan da ya yi, kasancewarsa mai farar fata. Ba ma wannan ne ya ɗaga mata hankali ba sai ganin ya yi wani irin zuru-zuru idanun duk sun faɗa, kuma ko jiya ya je gidan nata domin rana bata taɓa fitowa ta faɗa bai je ya ga Mama ba yana kaunar mahaifiyarsa ita ma tana kaunarsa kasancewar sa ɗa ɗaya tilo a wajenta. "ABBAS mene ne?" Ta tambaye shi cikin sanyi da tausasa murya. Idanunsa ya runtse wasu hawayen suka zubo sosai ta ji hakan ya taɓa ta, ta rasa SALIMAH wace irin mace ce da bata tausayin mijinta kullum yana cikin damuwa sai dai ta ɗauki hakan a matsayin jarabawar da Allah ya jarabci ABBAS ɗin da ita tana masa fatan Allah ya bashi ikon cin jarabawar. Idanunsa take kallo wanda ya rufe su hawayen suna surnanowa. "Na sha faɗa maka kake rike sirrinka, su iyali da kake gani sirri ne, daɗi ko wuya ba a son a ke jin kansu sai in abin ne ya yi yawa sai a faɗa domin sulhu da kawo maslaha" Ta ce cikin murya mai kama tana masa nasiha, duk da ta san ABBAS yana da dauriya da zurfin ciki sai dai wani lokacin kasancewar ta na mahaifiya gare shi ba sai ya furta cewa yana cikin damuwa ba kallo ɗaya take masa ta fahimci halin da yake ciki, duk da cewar halin da gidan ABBAS ɗin yake ciki abu ne bayyananne wanda kowa ma ya sani sai dai wanda bai taɓa taka kafarsa a gidan ABBAS ɗin ba. "Ka cigaba da hakuri wata rana sai labari, wata rana masu bada labarin ma babu kowa, shi zaman duniya ɗan hakuri ne duk abin da aka yi hakuri da shi zai wuce wata rana kamar ba a yi ba" "Mama" Ya ce bakinsa yana rawa don har ya fara jin sanyi alamar zazzaɓi zai rufe shi, ga shi yana so ya faɗa mata cewa ya saki SALIMAH amma kuma bakin nasa ya masa nauyi. "Na'am ABBAS" "Na, na, na" Ya ce yana ta faman maimaitawa tamkar wani mai in'inna. "Mai ka yi ABBAS? Ni mahaifiyarka ce da baka da kamata a faɗin duniya ina so ka sani da a ce SALIMAH ce take maka wannan kaunar da kake mata, ai dai ka san kana matukar kaunarta, kaunar da kai kan ka baka san iyakarta ba to da ita ce take maka kauna ko da ta fi wacce kake mata to ina so ka sani da bata kai ni kaunarka ba" Idanunsa da suke rufe ya buɗe har sai da gaban Mama ya faɗi ganin irin mugun jan da suka yi. ."Tabbas da bata kai ni kaunarka ba, ai a duniya babu wanda ya kai uwa kaunar ɗanta, na maka misali da kaunar da kake mata ne don ka gane, uwa-uwa ce kaunar uwa da ban take, shi ya sa ma aka ce a yi wa uwa biyayya sai da aka nanata sau uku sannan aka ce a bi uba amma sau ɗaya aka ambaci uba. Saboda kaunar uwa da ban take ɗanta tun yana cikinta bata gan shi ba take kaunarsa, jin sa take har cikin ranta, yadda take shan wahala rainon cikin da haihuwar da kuma shayarwa rainon yaro har ya girma shi ya sa ubangaji maɗaukakin sarki ya ambata a littafinsa mai tsarki, cewa wahala ce a kan wahala. Shi ya sa uwa kaunar ɗanta bata taɓa gushewa a zuciyarta sai dai ta ki wani hali nasa in yana aikatawa sannan kuma kullum a yaro yake a wurinta bata ganin girmansa" "Haka ne Mama" ABBAS ya ce cikin sanyin murya yana jaddada cewa in har duk wannan kaunar da yake yi wa SALIMAH yana jin zai iya sadaukar da komai ita ta samu zai iya sadaukar da numfashin sa ita ta rayu, amma kuma Mama ta ce ko dai kaunar ta fi haka to kaunar uwa ta wuce nan wannan ya sa ya ji jikinsa ya yi sanyi. ."Faɗa mini mene ne ka yi?" "Na saki SALIMAH" Ya ce wani kuka yana taho masa sai da ya dantse bakinsa ne kuka mai sauti bai fito ba sai hawaye kawai. Wani irin bugawa da karfi zuciyar Mama ta yi. Sosai ta ji tashin hankali tun da ta san tabbas zai shiga matukar damuwa da rashin SALIMAH abu ne mawuyaci SALIMAH ta karɓi bikonsa ba ta ma jin hakan zai iyu musamman da yake daga mahaifiyar SALIMAH har SALIMAH burinsu bai wuce karɓar takardar sakin ba, dama mahaifinta ne zai iya yin komai to shi kuma mai yanke kauna ta ɗauke shi wato mutuwa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!" Ta shiga maimaitawa har sau uku, shi dai yana ambata mata ya yi sakin sai ya yi saurin maida kansa ya kifa a cinyarta, ita ma ganin zai kifa kan nasa sai ta sake shi daga rikon da ta masa tun lokacin da ta ɗago shi. Shiru ta yi na ɗan lokaci gabaɗaya tausayinsa ya mamaye mata zuciya, da a ce tana da ikon cire masa son SALIMAH daga zuciyarsa da tuni ta cire masa ya huta. "ABBAS garin yaya haka ta faru? Baka san cewa saki shi ne halataccen abun da ubangaji ba ya so ba? Baka san cewa a duk lokacin da aka yi saki sai al'arshin ubangiji ya girgiza ba? Mai ya sa ka yi wannan ɗanyan aikin bayan ka san kai ne za ka cutu ba ita ba, ita dama wannan damar take nema kuma ita ce cikar burinsu ita da mahaifiyarta. Sau nawa suna tako gidan nan su mini ɗiban albarka da cin mutunci a kan sai na saka ka sake ta, amma saboda son da na san kana mata nake shanyewa in jure, mai ya sa ka yi haka babu shawarata?" "Mama, ni ma ban san na furta ba zuciya ce ta ɗauke ni da ɓacin rai, haushi da takaici sai da na furta kalmar sakin sannan na gane wautar da na yi" "To ai dama shi shaiɗan har abada burinsa kenan burinsa ya shiga tsakanin ma'aurata burinsa ba ya cika sai ya ga ya raba aure, kai shi fa duk wani abu mai kyau gaba yake da shi" . "Haka Allah, ya kaddara dama can rubutacciyar kaddara ce, a rubuce yake cewa a wannan rana igiyar aurenku za ta datse, a wannan rana zamanta a gidanka zai yanke sai dai wani rabon kuma in akwai shi za ta dawo" Mama ta ce bayan ya gama faɗa mata yadda abin ya faru. "Ba za ta taɓa dawowa ba Mama ni na sani" Ya ce har lokacin kansa kife a cinyarta. "Ka kwantar da hankalinka ka yi addu'a ni ma in taya ka Allah zaɓa abin da ya fi alkairi" Ta ce tana ɗago fuskarsa ta share masa hayawayen, tare da masa faɗa sosai a kan sanyawa mace hannu sosai ta nuna masa illar yin hakan ta umarce shi da duk runtsi duk wuya kar ya kara dukan mace, sannan ta masa nasiha mai ratsa jiki a kan yadda da kaddara kyakkyawa da kuma mummuna. Har sai da aka kira magriba tana ta masa nasihar sai da ta ga ya samu nutsuwa, ta saka masa albarka da fatan wanyewa lafiya, sannan ta ce ya je ya tafi masallaci ita ma ta yi alwala ta yi tata sallar. Sai da ya yi sallar ishsha'i ya dawo gidan, nan ta zuba masa abinci amma ya ki ci duk da akwai yunwa a tare da shi amma shi ba ya jin yunwar zafin rashin SALIMAH ya danne komai. A tsakiya Mama ta saka abincin ta ɗauka a cokali ta nufi bakinsa tare da ce masa ya yi Bismillah, Bismillar ya yi ta shiga bashi a baki, sai ya samu kansa da kin mata musu haka take bashi abincin a baki ita ma tana ci har suka cinye ta karo musu, suka kara cinyewa sannan ta mika masa ruwa shi ma a baki. "Haba Mama aikin ai ya miki yawa ruwan ma sai kin bani a baki" Ya ce yana dariya har hakoransa suka bayyana. Ita ma dariyar ta yi ta ce "Ai gwara in karasa laifina, na bada abinci ma bare ruwa" Haka ya buɗe baki suna rike da kofin a tare har sai da ya ɗago kansa alamar ya koshi sannan ta shanye sauran. "Mama saura nawan kika shanye?" "Ai uwa ba ta jin tsantsanin ɗanta" Sosai suka ringa hira cikin farin ciki tana ta jan shi da hira tana bashi labarai don ta kawar masa da damuwa, domin ya ce ba zai koma gidansa ba a nan zai kwana. Ɗakinsa na da ta shiga ta share masa, katifarsa ce a ciki sai sallaya da qur'ani. Tana dawowa ta ga ya yi nisa a cikin tunani da haka ta ce ya tafi ɗakin ya kwanta, a can ma zuwa ta yi ta zauna har sai da ta ji ya yi ɗiff alamar bacci ya ɗauke shi ta fito ta tafi nata ɗakin. ABBAS kuwa dama ba bacci ya yi ba ya yi hakan ne don ta je ta kwanta ta huta kuma idan ta ga ya yi baccin za ta rage damuwa amma idanunsa biyu. Wayarsa ya zaro daga aljihu ya kamo sunan SALIMAH "Duniyata" Shi ne sunan da ya yi saved da ɗaya lambarta, ya daɗe yana kallon sunan amma sai ya kasa kira domin tsoron abin da zai biyo baya, watakila ta ki ɗauka ko kuma ta ɗauka ta faɗa masa maganar da za ta tada masa mikin damuwar da ya ji ya kwanta masa. Har wajen karfe biyun dare idanunsa biyu, fitowa ta yi ya yi alwala domin zuwa ya yi nafila haske ya hango a ɗakin Mama ya san ita ma kuma sallar take don tun yana yaro haka ya ga suna tashi da Babansa suna nafilar dare idan ya falka bacci, kuma ko yanzu ma ya ga inda ta yi alwala da butar a wajen. Sai da aka kira asuba sannan ya tashi daga kan sallayar ya tafi masallaci bai dawo ba sai da gari ya yi haske sosai ya ji damuwar ta ragu. Da ya dawo ma bai kwanta ba sai ya ɗauki qur'ani ya shiga karantawa cikin kira'arsa ta Ahmad Sulaiman wanda tun suna islamiya ƴan ajin su suke cewa suna son kira'arsa ko malamin su idan ya zo karɓat harda sai ya yi ta saka ABBAS maimaitawa in ya gama bashi hardar ya ce ya kara maimaitawa ba don akwai kuskure a cikin karatun ba sai domin daɗin kira'arsa. Shi kuma tun yana karami Mama take kunna karatun Ahmad Sulaiman ɗin sai ya taso da son zama kamar shi, kullum in ta kunna sai ya ce. "Mama ina son zama wannan malamin idan na girma, ina so in iya karatu irin nasa" Sai ya zamana ko surorin kasa da take koya masa sai ya ce sai ta masa kira'ar malamin haka take koya masa da kira'ar shi ma yana yi wannan ne mafarin koyon kira'ar idan yana yi tamkar Ahmad Sulaiman ɗin ne yake ga ba wa kowane harafi hakkinsa, shi dama yaro yana tashi ne da abin da ya ga mahaifiyarsa tana yi, idan mai kyau ne haka zai ke yi in akasin haka ne ma koya zai yi saboda yara sun fi ɗaukan abin da suke gani ana yi fiye da wanda ake koya musu ko ake umartarsu su yi. Ɗumamen tuwo suka ci amma kuma sai ya ki tafiya wajen aikin kafinta ya ce zai ɗan huta zuwa kwana biyu. Ita ma Mama bata takura masa ba saboda ta san saboda damuwar da yake ciki ne kuma dama ciwo ɗan lokaci guda ne sauki sai a hankali, bare kuma cuta ta so. Da yamma ya tafi gidan nasa ɗauko kayan sawa saboda ko da ya yi wanka na jikinsa ya maimaita. Tun da mai machine ɗin ya ajiye ji a kofar gidan sai gabansa yake faɗuwa dakyar ya samu karfin gwiwar tunkarar kofar gidan ya buɗe yana ta karanto addu'a a ransa domin yana dosar cikin gidan sai ya ji komai ya dawo masa sabo fil. Tamkar ba a taɓa halittar SALIMAH ba haka ya ga gidan. Bedroom ɗin ya dosa ya shiga yana ganin kofar dirowar kayanta a buɗe ko rufewa bata yi ba jiyan duk ga kayanta nan a ciki saurin ɗauke idanunsa ya yi daga kallon kayan nata, jin wani abu ya tsarga masa a kirjinsa kan mudubin ya kalla ganin kayanta duk suna nan sai ya ji kuka yana son taso masa. Bakin gadon ya karasa ya zauna ya sunkuyar da kansa yana jin yadda sonta yake kona masa zuciya. "Ya Allah kai ne kake jarabtar bayinka a kan komai, kai ka jarabce ni da son wannan baiwa taka wacce ita bata sona ya rabbi don tsarkin mulkinka, domin buwayarka don karfin ikon ka Allah, ka kawo mini mafita ta alkairi ka yaye mini damuwata na san babu abin da ya gagare ka, kai kake iko da kowa kai kake juya lamura ya rabb ka juya al"amurana zuwa abin da ya fi alkairi kar ka barni da son zuciyata ya Allah" Ya ce a zuciyarsa yana jin hawaye suna taruwa sai dai bai bari sun zubo masa ba ya ya ɗago tare da ɗaga hannuwansa sama ya ce. ."Rabbi inni lima anzalta ilayya min kairin fakir, la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin, subhanallahi wa bi handihi subhanallahil azim, Allah hakika baka mayar da addu'ar bayinka, ko dai ka amsa a lokacin, ko ka sanya addu'ar ta kare musu wata musiba da ta tunkarosu, ko dai ka sauya musu da abin da ya fi wanda suka nema alkairi a gare su ko ka jinkirta musu Allah ka sa jinkirin tawa addu'ar ya zama alkairi, Allah ka kawo mini ranar da zan yi farin ciki saɓanin damuwar nan da nake ciki" Ya kai karshen addu'ar bayan ya karanto sunayen Allah 99 ya shafa addu'ar tare da goge idanunsa. Dirowar kayansa ya buɗe ya ɗauki kayan ya saka a jaka ya fito daga ɗakin da sauri tamkar wanda aka ce ya yi mantuwa a waje, cikin sauri ya fita daga gidan ya rufe kofar don ba ya so ko kaɗan wani abu ya tsikari zuciyarsa a cikin gidan game da SALIMAH. Washe gari ABBAS jin ya kasa jure rashin SALIMAH gabaɗaya ba ya samun ishashshan bacci, ko kaɗan ba ya cikin walwala ko kafintocin ba ya iya zuwa ji yake gabaɗaya duniyar ta masa kunci. FAROUQ ya kira a waya yake faɗa masa cewa ya saki SALIMAH, maimakon da ya gama faɗa masa yadda abubuwan suka wakana sai cewa ya yi. ."Alhamdulillahi, Allah na gode maka" "Haba FAROUQ ya ina faɗa maka ina cikin matsala amma sai ka nuna farin ciki kana hamdala". "To ai dole na yi hamdala wannan abin a taya ka murna ne, haba ABBAS mace ka zama tamkar bawanta amma ba ta kaunarka ko kaɗan ta mayar da kai tamkar baka sam mai kake ba. Ai sakin SALIMAH shi ne kwanciyar hankalinka ka daure kawai don farko ne amma komai zai wuce tamkar ba a yi ba" Ya ce cikin halin ko in kula. ."To wallahi na san zaman da zan yi da kai" "Yo wane zama kuwa za ka yi da ni in ba wanda ya fi na baya tsawo ba" "Wai mai ya sa ka cika ɗaukan abu da wasa, ina faɗa maka bani da sukuni ko aiki bana iya zuwa zuciyata bata da nutsuwa ko na kawar da komai a raina sai tunaninta ya hana kwanyata sakat" "Saboda ka sake ta ka daina zuwa wurin neman halalinka? na faɗa maka ka jure Allah zai baka wacce ta fi ta wacce za ta kaunace ka tun da ba ita kaɗai ce mai kyau ba" "Sanin kan ka ne ba kyan SALIMAH ne ya ruɗe ni ba kawai kauna ce domin Allah da a ce SALIMAH fuskarta za ta yi dameji ta samu nakasa a jikinta wallahi daidai kwayar zarra son ta ba zai ragu a zuciyata ba". "Wannan abu ne da ka sha biya mini shi da karatu ne ma da tuni na haddace, yanzu mai kake so in maka" "Please FAROUQ ka zo gobe ka rakani bikonta ko Allah zai sa ta tausaya mini ta dawo" Ya ce cikin marairaicewa. "Taɓ amma kai dai ka cika marar zuciya mace ta sa hannu ta mareka har kake marmarin dawowa da ita to ba zan maka baki ba nan gaba za ta iya saka bulala ta zane ka, kuma ina so ka sani SALIMAH ba ta tausayinka kuma ba na jin za ta taɓa tausaya maka, yadda ma take burin samun rabuwa da kai ba na jin za ta yarda ta dawo" "Fata na gari lamiri". "Haka ne ka jira ni gobe da bayan isha'i sai mu je ka gwada sa'arka" "Na gode abokina". "Tun yanzu kake gode mini ka bari sai mun dawo da ita" Ya ce cike da shekiyanci yana kyakkyalewa da dariya ya kashe wayar. Shi sosai ya ji daɗin sakin ko ba komai abokinsa zai samu nutsuwar ruhi in ta fita daga rayuwarsa. ABBAS kuwa wayar da suka yi sai ya ji nauyi ya ragu a zuciyarsa duk da ba shi da tabbacin dawowarta amma ya dace ta bibiyeta ko ba za ta dawo yanzu ba zai tsumayi zuwanta wata rana. Ko da ya faɗawa Mama bata yi yinkurin hana shi ba, duk da ta san ba lallai ne ta dawo ba amma sai ta ga ba a kwacewa yaro garma hakan ya sa ta masa fatan nasara. Kwana ya yi yana sallah yana addu'ar Allah ya ɗora shi a kan SALIMAH da Ummarta. Ko wunin ranar ma bakinsa ba ya rabuwa da ambaton Allah har da sadaka ya yj duk na neman dacewa a wurin bikon. Da la'asar ya yi wanka ya saka wani yadinsa fari wanda yake ga ya fi kowanne sabunta a cikin kayansa, madarar turare ya shafa ya saka hula, sai murmushi yake yana jin daɗin zai yi kwalli da wacce ya fi kauna. Duk da a gefe ɗaya yana ta jin fargaba tamkar amarya a daren farko. Hula ya saka sosai ya yi kyau kasancewarsa fari dogo mai doguwar fuska wacce ta kawatu da dogon hancinsa da yake har wajen baki, karamin pink ɗin bakinsa wanda yake tamkar ya saka jambaki, hakoransa da suke a jere reras tamkar masara gashin kansa wanda yake baki wulik a kwance tamkar na larabawa, kwancaccan gashin girarsa da zara-zaran gashin idanu, idanunsa da suke farare tas kamar madara haɗe da bakar kwayar idanun da ko kallonka yake sai ka ga tamkar kallon love yake maka,kakkarfa ne kuma fafffaɗa, ba shi da makusa ko ta ina a tare da shi ga uwa uba mahaddacin qur'ani za a iya kiransa da ya haɗa komai kuma bai rasa ba komai. Tun da ya durkusa raka'ar karshe ta nafilar da ya yi bayan an idar da sallar ishsha'i addu'ar neman dacewa ya yi ta yi bayan kafin ya fito ya sanar da Mama a kan ta masa addu'a SALIMAH ta amince ta dawo da to ta amsa masa. Ko da ya fito daga masallacin a kofar gidan Mama ya samu machine ɗin FAROUQ roba-roba tun da dama ya faɗa masa ya kauro gidan Mama a can zai same shi. A kofar gidan suka ci karo da FAROUQ da ya fito bayan ya gaishe da Mama ta ce ya duba ABBAS ɗin a waje bai dawo daga masallaci ba. "Kai mutumina irin wannan kyau haka kamar dai angon da zai je ɗaurin aurensa" FAROUQ ya ce cike da tsokana. "Yo mene ne bambanci ni duba mini ma na yi kyau ko in koma in sauya kaya?". "Eh koma ka sake har fatarka ma sai ka sake , tun da wacce za mu je wajen nata ai za ta yaba ko" FAROUQ ya ce cike da gatse. ."Ka ji ka da wani abu za ta yaba mana". "Allah sa" Daga haka suka hau machine ɗin suka kama hanyar gidan su SALIMAH da yake unguwar badarawa. A kofar gidan suka faka machine ɗin nasu suka samu yaro domin ya kira musu ita, ABBAS ko magana ya daina sai sunayen Allah kawai yake jerowa gabansa yana faɗuwa. "Assalamu alaikum, wai ana magana da SALIMAH" Cewar yaron da ya shigo. Maimakon Umma ta amsa masa, sai ta carara guɗa. SALIMAH da take ɗakin jin Umma tana guda sai ta bazamo da gundunta domin ta san ruwa ba ya tsami banza ma'ana Umma ba za ta yi guɗa ba sai da dalili mai karfi. "Mene ne Umma?" "Sai ni uwar kyakkyawa shi ya sa aka ce ƴa mace kyakkyawa jari ce, musamman kyakkyawa idan ana neman aurenta ka wanki gara idan ta yi aure ma kai ka kasa kayanka ka siyar" Umma ta ce tana darawa. "Wallahi Umma kin kara saka ni a duhu" "Ke goshi kika yi ƴar nan, tun baki yi idda ba har an fara zuwa zawarci kai na san dai bana kakarmu ta yanke saka" "Wayyo daɗi Umma na kusa fara kashe kala" . "Ai kaloli ma za ki kashe ɗiyar nan Allah ya mini gyaɗar dogo na kusa daina zaman gaban murhu ina toya kosai da koko" Ta ce tana mikawa SALIMAH hannu suka tafa kamar wasu kawaye. "Kula ki leka sai ki musu bayanin cewa su jira kaɗan kwanakin iddarki su cika, su zo su hau layi, don wallahi wannan karon sai kin zaɓa kin darje Allah jikan Malam wannan karon zaɓe ba nasa bane bare ya miki zaɓen tumun dare ya zaɓa miki ahlil fukara'u" "To Umma bari na ɗakko mayafi, ai ni na matsu na gama iddar nan ko na fara wankar kuɗaɗen zawarawa in sake kayan sawa na kece raini" "Ko ni uwaki ai sai kin sake mini sabon zubi saboda in zawarawan naki za su shigo mu gaisa kar su ganni a tsumma" Cewar Umma tana dariya. "Ai dole ki ɗaura manyan lasa-lasai. "Kai yaro in ji wa ko ba faɗi sunansa ba" Umma ta ce tana murmushi don kunnuwanta so suke kawai su ji an ce Alhaji wane ne, amma sai dai kash an samu akasin lissafi don cewa ya yi. "Wai in ji ABBAS..." Ku biyo ni don jin ya za ta kaya...😍🥹. 09013181851 [1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 3 *SALIMAH* Sai da ta yi sallar ishsha'i sannan batun EESHART ya faɗo mata, ta yi mamaki matuka na ganin bata kira ta ba wayar ta ɗakko ta duba bata ga miss call ba. Shiru ta yi tana ta mamaki a ranta duk tunaninta EESHART ɗin za ta yi ta kiranta suna labarta abin da ya faru tun da dai bata gama bata labari ba ta ce ta bari za su yi waya idan ta je gida. Kawar da tunanin ta yi, ta buɗe data ta hau whatsapp, sakonnin da suke ta rige-rigen shigowa ne ta jira suka gama shigowa, dubawa ta yi ko za ta ga EESHART ta mata magana amma ta ga tun maganar da suka yi lokacin tana gidan ABBAS amma ko ɗigon magana bata mata ba, bayan ta saba ko yaushe suna tare a online idan ta mata magana ta ga bata nan ta kira ta idan bata da data ta saka mata amma dai yau ta rasa dalilin hakan sai dai ta mata uzuri a kan ko wani babban dalili ne ya mantar da ita farin cikin da take, cikar burinta wato sakin da ABBAS ya mata a yau ɗin. Ganin tana online sai ta kara shan ruwan mamaki amma bata dogara da mamakin da ta shayar da ita ba ta je ta mata magana. Hi ta ce mata amma shiru-shiru sama da minti goma bata ma buɗe sakon ba bare ta mata replay. Kara mata magana ta yi cewa kawata ya na jiki shiru, sama da minti biyar bata buɗe ba abin ya yi wa SALIMAH ciwo amma dai sai ta dake har lokacin tana jiran ta fara ji daga gare ta duk da tana ganin nata online, bayan ta saba tana hawowa wani lokacin idan ita EESHART ta bar mata sako sai ta kara cewa ina ganin ki online fa matar manya. Basarwa ta yi ta fara scrolling ganin sakonnin group ɗin kawayen su da suka buɗe message yana ta shigowa, sai ta shiga group ɗin nan ta ga sun baja kolin hira har da EESHART ɗin yawanci hira ce ake ta zaman takewar auratayya kowacce tana bada labarin mijinta da kulawar da yake bata da yake duk yawanci matan aure ne sai ƴanmata kalilan. Taggin ɗin EESHART ta yi ta ce na ajiye miki sako a pc kawata na ga baki duba ba har yanzu. Ok kawai ta ce suka cigaba da hirarsu. Jim kaɗan ta duba amma ta ga EESHART bata duba ba har dai ta fara tunanin ko wani laifi ta mata amma iya tunaninta bata gano komai ba. Ta kasa duba sakon kowa kawai sai dawuwuri take abin da EESHART ta mata ya tsaye mata a rai. Sunan kawarta ta kamo BASEERA wacce har ta manta rabon da su yi magana saboda ita BASEERA tana faɗa mata gaskiya tana nuna mata ta yi hakuri ta zauna a ɗakinta tun da ABBAS yana son ta kuma yana kyautata mata, shi arziki na Allah ne in da rabo wata rana sai ta ga ya yi arzikin. Wannan ne ya sa kullum suke faɗa da ita saboda tana ganin ita ma bakin cikin ta fito ta auri mai kuɗi take mata tun da ita ma BASEERA talakan take aure sai dai shi mijinta ya fi ABBAS rufin asiri. Sallama ta mata amma sai ta ga ba ta oline datar ta kashe ta sauka ma daga whatsapp ɗin. "Ki zubo tuwo ki ci SALIMAH, ɗazu na ce mu ci ɗazu kika ce sai an jima idan ya huce ba za ki ji daɗinsa ba" Umma ta ce tana tattare kwanuka. Da to ta amsa mata tana zuwa ta zubo kaɗan amma tana sakawa a baki sai ta ji ɗanɗanon dai sai a hankali ba kamar miyarta ba ta saka ishashshan magi duk tsiya kuma dole ABBAS ɗin ya kawo. "Umma ki bani magi na kara lami na ji miyar" "Haba SALIMAH to ya kike so ki ji ni da na gama ci yanzu ban ji wani lami ba, amma ga gishiri nan ki kara saboda maggi dai kin san tsada yake ni kuwa da ba wanda zai kawo mini gare ni ba komai ni nake siya da sana'ar da nake yi" "Ai kin kusa hutawa don har mai girki zan ɗaukar miki idan na auri attajiri" Dariya ta yi ta bata maggin guda ɗaya ta saka sannan ta ji dama-dama. Sai da ta gama bayan sun kwanta Umma a saman gado ita tana katifa a kasa, wayar ta ɗakko ta sake hawa whatsapp amma har lokacin babu sakon EESHART. Sai dai BASEERA ta amsa mata sallama har tana tambayarta lafiyarta. "BASEERA yau dai ABBAS ya yanke igiyar aurenmu na huta da alakakai" "Subahanallah! Yanzu sai da kika yi yadda kika yi kika kashe aurenki, darajarki da kimarki ɗakin mijinki, wannan rayuwar da ake ciki a irin dagulallan zamanin mai cike da ruɗu samun miji managarci ma wahala yake, maimakon ki rufawa kan ki asiri ki rabu da tunanin ruɗin duniya mijin ki yana son ki yana kyautata miki sai abin da kike so yake yi ki juya shi kamar waina a tanda, mai mace take nema da ya wuce abin da kika samu? Wasu fa malamai da bokaye suke bi don su samu waɗannan abubuwan amma ke ba boka ba malam Allah ya mallaka miki, amma shi ne kika yi watsi da ni'imar Allah, kina bin gurguwar shawarar zuciyarki da ta kawaye suna ɗora ki a keken ɓera, ke baki san RUƁAƁƁIYAR IGIYA kike kamawa ba... "Dakata! BASEERA wai ce miki na yi na gama aure a duniya ne? ". "Baki ce mini ba amma dai ai auren mai kuɗi ne da kike kwaɗayin yi ya sa kika raina naki mijin, shin wai ke baki san cewa kuɗi ba su ne rayuwa ba, kuɗi ba su ne farin ciki ba, to wallahi mafi yawan wanda suke cikin daula wasu basu da kwanciyar hankali, ga komai sun samu gida mai kyau mota su hau wacce suke so kuɗin su yi facaka, ga sutura sai wacce suke so ga ƴan aiki nan bila adadin suna musu hidima su ci mai kyau su kwanta mai kyau, amma da za ki duba rayuwar gidan cike take da tarin matsaloli da kalubale, wata da za a bata zaɓi in dai za ta auri talakan da za ta samu kwanciyar hankali to ta gwammace ta bar daular da take ciki. Wata mijin ma ba shi da lokacin ta wata ta yi hannun riga da farin ciki abubuwa dai barkatai ga su nan ke idan ana cin ɓaure ba a tona cikinsa, amma ke ki raina taki ni'imar kike hangen na sama da ke? Idan mutum yana son ya gane ni'imar da Allah ya masa to kar ya dubi na sama da shi ya dubi na kasa da shi, shi inda mutum yake buri da kwaɗayin samu ai hangen dala ba shiga birni bane, akwai abubuwa barkatai da baki ba zai iya faɗinsu ba" Gabaɗaya ran SALIMAH ya gama ɓaci kwata-kwata wannan dogon lissafin da BASEERA take mata shi ne ya sa take raba hanya da ita, shi ne dalilin da ya sa ko magana bata san faɗa mata ita kullum nasiha tamkar malamin da ya hau minbarin wa,azi sai ka ce ita ce mikiya mai hangen nesa. "Fakyakul kairan auli yasmut" Shi ne abin da SALIMAH ta tura mata bayan ta gama jin dogon voice ɗin. Haushi ma ya sa ta kashe datar ta sauka, tun da har lokacin ita EESHART bata mata replay ba, dama a rashin uwa ne ake uwar ɗaki, da a ce EESHART ta mata magana sun cigaba da tattaunawa da babu abin da zai sa ta taɓo ustaziyar wannan wato BASEERA dama EESHART ɗin ce tasu ta zo ɗaya don ko wasu daga cikin kawayenta haushin ta suke ji a kan yadda ta auri kyakkyawan miji managarci mai cikar haiba da kamala yake son ta da nuna kulawarsa a gare ta wannan ya sa wasu duk suka janye jiki daga gare ta don kowacce so take dama a ce ita ce ta samu wannan damar. Suna ganin sun auri ɗan dukununu ga baki ga bakar zuciya amma ita ta samu fari mai farar aniya da kyakkyawar zuciya. *WASHE GARI* Tun da asuba da Umma ta idar da sallah ta hura wuta ta ɗora katuwar tukunyar ruwan koko. Ita kuma SALIMAH tana idar da sallah ta koma ta kwanta. "Ke SALIMAH tashi kike iza wutar kokon nan idan ya tafasa ki dama, zan tafi in kai markaɗen kosan nan" Umma ta ce tana ɗaɗa mata duka a kafa. Ɗif ta yi tana jin wani ɓacin rai in akwai abin da ta tsana a duniya bai wuce a ce an hana ta bacci ba, da a gidanta ne idan ta kwanta ko mene ne sai dai ABBAS ya hakura da tambaya saboda kar ya tashe ta sai ta yi bacci son ranta take tashi amma ga shi tun da farar safiya Umma za ta ɗaga mata hankalo. Wani dukan ta sakar mata a kafa tana cewa. "Wallahi kar fa in tafi ki koma bacci, ki tashi gari ya waye tangararai ana jimawa masu siyan kokon za su fara zuwa" Ba don ta so ba ta tashi tana murtsuke ido ta fito tsakar gidan ta wanke fuskarta, kujera ta ɗakko ta zauna tana iza wutar ga uban hayaki duk ya turnuke da yake iccen ɗanye ne. Haka ta cigaba da fifitawa idanunta yana ruwa, ita rabon da ta fifita wuta ma ta manta tun yajin da ta yi ta zo gida sai ko idan ta zo gida Umma ta ce ta iza wuta, duk talaucin ABBAS da take gani amma da gawayi take girki bai taɓa siyan ita ce ba, sai dai da sallar layya in ya saya ma kuwa shi yake suyar don cewa take ita bata son zuwa wurin hayaki. Sai da ta dama kokon ya sha iska ta masa gasara sannan Umma ta shigo lokacin har an fara shigowa siyan koko, ita ta zauna tana zuba musu kokon tana ɗaura sugar, ita kuma Umma ta ɗora kasko ta fara soya kosan. Sai da kokon ya kare ta ɗauki wanda ta zuba a karamin kofi ta sa sugar ta zuba kosan a plate, ɗaki ta shiga tana ci. Bayan ta gama ta share gidan ta hau wanke-wanke wanda a gidanta duk da ba wasu kwanuka ba ne sai da ta matsawa ABBAS ya ɗauka mata mai shara da wanke -wanke. Da yamma ta shirya ta yi wa Umma sallama a kan za ta je gidan EESHART. "Ni ban ji kuna waya ba ma tun da kika zo, ku da kun saba kamar saurayi da budurwa ko yaushe kuna waya" "Ba ta jin daɗi ne wayar ma bata fiya amfani da ita ba" SALIMAH ta samu kanta da sharara karya. "Subhanallah, Allah sawake ki ce ina mata sannu" Umma ta ce tana jimantawa. Da to ta amsa ta fito ta kama hanyar gidan EESHART a kafa ga shi da nisa sai dai bata da kuɗin hawa napep kuma ba ta son tambayar Umma don yanzu za ta fara mata lissafi, kuma ma da ta san bata da kuɗi ai sai ta bata ba sai ta tambaya ba tun da jiyan ma ta san da ta zo a wajenta ta karɓi kuɗin napep ɗin. Tun da take tafiya ake mata magana amma sai ta ce tana da aure ganin bata gama idda ba kuma ma dai masu tsayar da ita ɗin dai dama a mota suke tsayawa ita kuma duka motocin burinta ya fi karfin su, dama da a ce ta samu wanda ya mallaki tsadaddiyar mota da ta sanar da shi auranta ya mutu sai ta bashi lambar wayarta idan ta yi idda sai ya shiga sahu. A gajiye tikis ta karasa gidan EESHART saboda sanin da da mai gadin ya yi bata wani sha wahala wajen shiga gidan ba. Ƴar aikin EESHART ɗin ce ta mata iso zuwa falon ta kawo mata lemo da ruwa da kofi, bayan ta sanar da EESHART ɗin zuwan SALIMAH. Shiru-shiru tana zaune sama da minti ashirin amma babu alamar EESHART ɗin za ta fito. "Kin ce mata ni ce kuwa?" SALIMAH ta tambayi ƴar aikin tana kallonta. ."Eh na faɗa mata" "Ko wani abun take yi?" "A kwance take tana danna waya" Sosai mamaki ya cika SALIMAH sai ta ma rasa wane kalar tunani za ta yi, tana ta tunanin manufar kawar tata amma bata gane komai ba. "Je ki kara tuna mata ce ina jiranta" Ta kara faɗa mata ganin zamanta ma wajen sau huɗu ta kira ta amma bata ɗauka ba. Da to ta amsa mata ta koma ɗakin sai ga ta ta fito jikinta sanyi kalau, da alama amsar da aka bata ce bata mata daɗi ba da alama ma ko koro ta EESHART ɗin ta yi amma kuma sai ta kirkiri murmushin yake ta ce mata tana zuwa ta fita daga falon. Sai da aka ɗauki kimanin minti biyar sai ga EESHART ɗin ta fito sanye take cikin dakakkiyar shadda da alama ma yau ta fara saka shaddar ta sha ɗaukin ɗankwali ta fito tana wani takun kasaita. Ko irin murnar da take nunawa idan ta zo gidanta yau bata nuna ba, zama ta yi tana mata magana ba yabo ba fallasa. "Haba EESHART wai mai yake damunki ne, tun jiya nake miki magana a whtsapp amma shiru har a group na sanar miki na ajiye miki sako amma baki buɗe ba bare ki mini replay". "Ayya kin ga mantawa na yi ya kike ina Umma, don ba a ce miki ina mijinki ABBAS ba tun da yanzu bazawara ce ke baki da aure" Sasai ta yi mamakin kalamanta jin kamar ma har da gori take mata wai ta zama bazawara duk da ba son ABBAS take ba amma sai ta ji wani iri wani banbarakwai wai namiji da suna hajara. "Haba EESHART mu da dama burinmu kenan samun sakin to don ya sake ni na zama bazawara ai ba wani aibu bane, ba ma wannan ba duk kiran da na miki yanzu amma baki ɗaga ba zamana a nan ma kusan minti talatin amma kin yi ɓatan dabo a cikin gidan" "Ayya sorry fa ina can tare da baby nah ya saka ina masa tausa, kin san matar aure" Ta ce tana mata wani kallo mai haɗe da murmushin da ta kasa gane inda ya dosa ko dalilin yin sa. Ɗan jim kaɗan ta yi tana nazarin maganganunta, da kuma maganganun ƴar aikin EESHART ɗin da ta ce tana kwance tana danna waya kuma ita kuma ta ce tana wurin miji har da faɗa mata abin da take yi a wajen miji. "Kai kawata kina wuta wallahi" Ta ce tana dariya don kawar da maganar da EESHART ɗin ta yi da wacce ƴar aikin ta yi don kar ta ba kanta wahala, tun da ma ba daga ɗakin mijin ta fito ba. "Ke ko" Ta ce tana ɗan darawa. "Wai ni ko maganar sakin da aka yi mini jiya baki mini ba, kuma ko ki tuntuɓe ni" "Ki mini uzuri abubuwa ne suka sha min... "Aysha wai mai ya sa bakya jin magana ne, ba na ce in na ajiye abu a daina canja mini waje ba? amma saboda raini sai an taɓa" Mijin EESHART Alhaji Yusuf da ya sakko daga saman bene bai gama sakkowa ba ya faɗa cikin hargowa. Ɗan diriricewa ta yi saboda ganin SALIMAH tun da bata fiya zuwa gidan idan mijinta yana nan ba idan kuma ta same shi ma to wata rana har ta tafi bai fito ba. Maimakon ta bashi amsa jiki yana rawa kamar yadda ta saba, sai ta tashi cikin kissa da kisisina tana son ta tabbatarwa SALIMAH irin abubuwan da take faɗa mata na tattalinta da mijin nata yake yi, don tana nuna cewa ita ta haɗa komai ga miji mai kuɗi ga kulawar miji. Tana ɗan wani murmusawa ta fara hawa step ɗin shi kuma gabaɗaya ya kufula da abin da ta yi saboda dama ransa a ɓace karuwarsa ta gama masa rashin mutunci kuma ya je ɗaukan agogonsa ya ga agogunan basa lokar agogunan. "Baby n... Maganar tata ta katse ne sanadin marin da ya ɗauke ta da shi, a fusace ya shiga nuna ta da yatsa. "Mahaukaciyar banza da wofi, ina miki magana kika watsa yin maganata kamar wani sa'anki" Ya ce a fusace yana nuna ta da yatsa. Sosai abin ya ba wa SALIMAH mamaki sannan ta shiga ruɗani ganin marin da aka ɗauke da kawarta ba da wani kwakkwaran dalili ba, sannan aka bi ta da bakaken maganganu. A take maganganun da BASEERA ta mata jiya suka faɗo mata, ta shiga jimanta wa a ranta ashe dai wasu masu kuɗin suna shuka rashin mutunci, tun da ga shi dai EESHART ɗin bata rasa komai ba na morewar rayuwa ita za ta tabbatar da hakan don ko cima sai abin da take so take ci haka za ta tura mata hoton abinci kala-kala sannan suturarta ma in ka gani tamkar za ta buɗe shago komai wadatacce amma kuma ga wani abu da ban wanda iya zamansu da shakuwarsu da EESHART bata taɓa faɗa mata hakan ba, sai ta nuna bata da matsalar komai. Yanayin yadda ta yi lokacin da ya mare ta ɗin alamu sun nuna cewar ba wannan bane karo na farko. Ita kuwa ABBAS in ban da jiya ko yatsa bai taɓa kaiwa jikinta ba, jiyan ma ta san tsinken hana haihuwar da ta saka ne ya kona masa rai tun da ta san yadda yake da son yara, sai kuma maganganun da ta fusata shi da su amma in ban da wannan tsawon shekara biyar ABBAS ko harararta bai taɓa yi ba duk abin ta masa shanyewa yake ya nuna komai ba komai bane. EESHART kuwa dama ta saba idan da sabo sai dai yau bata ji daɗin hakan ba da aka mata a gaban SALIMAH shi dama mijin nata babu abin da ya dame shi a gaban ƴan aiki na sai ya kai mata hannu shi dama wuyarta abu ya bashi haushi yanzu zai ɗauke mutum da mari. "Ka yi hakuri Alhaji ɗaya lokar na saka maka" Ta ce cikin sanyin murya idanunta yana cikowa da kwallar zafin marin. "Hakurinki na banza da wofi, uban wa ya ce ki canja mini ma'ajji? Sakarar banza da wofi" Ya ce yana doka tsaki ya haye saman ya bar ta rike da kumatu. Jiki ba kwari ta dawo tana wayancewa, duk da ta ji haushi kuma ya tsinka ta amma hakan ba zai sa ta rasa abin faɗa ba. " SALIMAH kin ga baby ko da alama ransa ɓace yake yau amma ba komai na san ana jimawa zai durkusa ya bani hakuri" Ta ce tana sakin murmushin yake tare da danne ɓacin ranta duk da dama mari ba wani bakon abu bane a wurinta. "Durkusawa fa kika ce EESHART? To ko jiya gama baki labari ne ban yi ba ni da ABBAS ya tsinke ni da mari a take na ɗaga hannu na rama, sannan na bishi da bakaken maganganun da suka fusata shi ya sawwake mini amma ke ba wani babban abu ba ya mare ki amma kin kasa kataɓus, dama haka masu kuɗin suke?" Diriricewa ta yi ta ma rasa abin cewa nan ta kawar da maganar tare da shigo da hirar babban rashin da ABBAS ya yi da ya da ya rabu da ita tabbas za ta auri attajiri nan ta ci gaba da ɗota ta a RUƁAƁƁIYAR IGIYA ita kuma tana hawa. Sai da ta yi magriba sannan suka ci abinci don ko da Alhaji Yusuf ɗin mijin EESHART ya sakko zai fita sai buɗaɗa kamshi yake watakila ita dai SALIMAH ba ta raba ɗayan biyu zance zai je duba da yanayin shigar da ya yi. Ko da SALIMAH ta gaishe shi a ciki ya amsa ita kuma EESHART cikin kalmashe murya ta ce masa. "A dawo lafiya" Amma ya ba bango ajiyarta. Sallama ta mata ta bata kama hanyar gida, da ta saba in ta zo tana bata dubu biyu ta ce ta hau napep amma yau ko naira biyar bata ba ta ba, tana zuwa gida ta yi sallar isha'i ta kwanta tana ɗan charting yau dai EESHART ta kula ta sun yi magana ba kamar jiya ba amma da alama har yanzu tana jin kunyar abin da ya faru. Wannan karon mmn afrah ba dariya za ta baku ba, labarin yana ɗauke da sarkakiya, cin amana, butulci soyayya mai zafin maraici labari ne da zai taɓo mana ɓangarori da dama. Ba zan warware muku komai na labarin ba ku dai ku yi jumurin bina har karshe mu warware tufkar a tare a nan ne za ku gane mai ya sa aka sanyawa labarin RUƁAƁƁIYAR IGIYA. 09013181851 *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 5 "ABBAS" Suka haɗa baki wajen faɗa cike da mamaki, wani takaici ne ya turnuke SALIMAH ita a halin da ake ciki ko sunansa bata so ta ji an ambata. "Umma kin ga ɗan nacin nan ya zo ko? Har kina cewa tun da ya ji ciwon abin da na masa har ya iya furta sakin ya rabu da ni kenan, ina ganin na yadda kwallon mangwaro kuda ya daina addabata ashe dai na fahimci abin a baibai" SALIMAH ta ce tamkar ta yi kuka. Shi yaro yana gama faɗa musu sunan mai kiran ya juya ya tafi ya je ya cewa su ABBAS ɗin tana zuwa. "SALIMAH idan baki yi da gaske ba wannan ɗan anacen sai ya hana ki rawar gaban hantsi, domin zai hana ki cin duniyarki da tsinken tsire, dole ki tashi haikan ki je ki tauna tsakuwa don aya ta ji tsaro. Idan har kika masa sakwa-sakwa ya samu dama wallahi zai kore miki duk wani bazawari da zai zo wajenki da sunan so, idan baki sani ba ki sani, idan bacci kike ki farka duk wata bazawara da ta fito daga gidan aure to idan har tsohon mijinta zai ke diddiftu a kofar gidan su to babu mai cigaba da zuwa wajenta kowa zai ke ganin gidan tsohon mijin za ta koma ko da kuwa ita bata da niyyar hakan, shikenan zai sa ki yi biyu babu gwara ki fita a yi ta a watse" Umma ta ce cikin hargagi saboda gabaɗaya ta ɗauka wani Alhaji ne mai faɗa a ji ya zo ashe dai wancan ahalul fukara'un ne da bai ajiye ba bai ba wani ajiya ba. SALIMAH da ta cika ta yi fam gabaɗaya kuɗubar mahaifiyarta ta shiga kunnuwanta da kwakwalwarta, ta kara gane irin rusa mata burin da ABBAS zai yi in dai yana zuwa hakan ya sa ta ci alwashin taka masa birki. "Wallahi Umma bai isa ba, na rantse da Allah ba zan lamunci wannan abin ba, wannan talakan ya ga makwacina da yawa wane shegen ne ya ce masa ni SALIMAH zan taɓa komawa gidansa wallahi ko a mafarki na ga na doshi cikin gidan ABBAS zan kwaɗawa kaina mugun marin da zai sa na farka daga mugun bakin mafarkin komawa gidan talauci" Ta ce a fusace don har ta fi Ummar ma fusata saboda sai yanzu ne ma Ummar ta haska mata wani duhun ta ga haske. Buguzum-buguzum ta shige ɗaki sai ga ta ta fito da mayafi sakale a kafaɗa, wani karanin bokiti ta ɗauka ta nufi wajen gasarar kokon Umma wanda ruwan saman gasarar yake da tsami irin na ruwan tsari, tsiyaya ta yi sai da ta cika bokitin fal, ta nufi hanyar fita. "Kar ki masa da sauki kin ji na faɗa miki" Umma ta ce amma SALIMAH ko amsa bata samu damar ba wa Umma ba, saboda yadda take jin tukukin bakin cikin jin ABBAS a kofar gidansu.. Tsaye ta same su, FAROUQ jingine da machine yayin da ABBAS yake tsaye yana rungume da hannunsa a kirjinsa, wurin gabaɗaya ya kaure da kamshin turare musamman na ABBAS da ya fi yawa da daɗin kamshi. Da yake dama kofar gidan yake fuskanta tun da yaron ya ce tana zuwa sai ya ji daɗi a ransa ko ba komai zai ganta don bai ma yi zaton za ta fito ba, don lokacin da ta yi yaji sai dai ya gaji da tsayuwa ya tafi ko ta cewa ɗan aiken ba za ta zo ba shi kuma ba shi da damar shiga gidan nasu yadda suke tsaki da tsakuwa shi da Umma tun da bata kaunarsa.. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke hangota da ya yi ta fito, a duniya ba ya ganin kowace mace sai SALIMAH ya ɗauke ta tamkar sarauniyar mata kasancewarta sarauniyar zuciyarsa, ganinta yake tamkar ɗawisu jin ta yake tamkar numfashinsa, rayuwarsa haɗe yake da ita saboda kaunar da yake mata. Bai lura tana ɗauke da wani abu a hannunta ba, ya shagala da kallon fuskarta ta cikin hasken farin wata da ya haske duniya. Tunani yake a ransa ya aka yi ya ɗaga hannu ya mari wannan fuskar da take da matukar daraja a wajensa. "Waye yake kirana a cikin ku?" Ta tambaya cike da rainin hankali ko arzikin yin sallama basu samu ba. FAROUQ da dama a kufule yake na shanyar da aka musu suke tsaye zaman jiranta jin kalaman rainin hankalin da ta yi ya mayar mata da martani. "Waye kike ganin zai zo wajenki a cikinmu? Ni dai ban miki kama da wanda zai zo wajenki ba ko cikin mafarkin ki" "Haba FAROUQ kai da ka rakoni sasanci bai kamata ka mayar da martani haka ba, a kalla sai ka ce mata ABBAS ne" "To kai in ba tambayar rainin hankali ba ai ta san waye ya zo wajen nata ko yaron da ka aika ai ABBAS ya ce yana kiranta, kuma abin haushin kai baka fahimci ko darajar ta mana sallama bamu samu ba?" "Wa ya gayyatoku da har zai muku sallama? Ku kuka ɗakko kafafunku masu kama da na kwaɗo kuka zo, to bari ku ji in faɗa muku bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane iya gani iya kyalewa ni yanzu na maka nisa kwatankwacin nisan da yake tsakanin sama da kasa, sau nawa zan faɗa maka ABBAS na tsane ka! Na tsani mai kaunarka, bana son duk wani abu da ya danganceka, mai ya sa baka da zuciya mai ya sa ka bari kare ya cinye maka zuciya? Mai ya sa kai kawai hangena kake baka ganin mugun talaucin da kake ciki wanda ya maka kamun kazar kuku, ka rubuta ka ajiye na barka har abada yadda na fito daga gidanka da sunan matarka na fito fitowa ta har abada ko gawata na ji an saka a gidanka idan da hali zan yunkura in fito daga ciki" Tun da ta fara maganganun yake kallonta duk da yana jin ciwo a zuciyarsa amma kuma a wani sashen na zuciyarsa ya kasa ganin abin da take yi laifi ne, bai san mai ya sa ba ba ya ganin laifin SALIMAH ko abu ta masa zai ji haushi amma na ɗan lokaci ne daga abin ya gushe zai ji ba ya ganin laifinta sai dai wani ya ga laifin nata ko wani ya jiye masa ciwon abin da take masa shi kansa bai san mai ya sa ba, illa iyaka ya san so ne, son da yake mata ne ya lulluɓe laifinta. "Kar ki ce haka SALIMAH ki tausaya mini, ba zan iya rayuwa ba sai da ke, da wane amon murya kike so na faɗa miki ina son ki ki yarda? Da wane martani kike so in fahimtar da ke irin son ki da kaunarki da nake yi ki yarda? SALIMAH ni kaina ban taɓa ji ko a labari akwai irin son da nake miki ba Allah ne shaidata bayan mahaifana ba na kaunar wata halitta sai ke. Da a ce ɗan adam yana iya tsaga kirjinsa ya nuna so a yarda da shi da na buɗe miki kirjina da kin duba cikin zuciyata ki ga yadda son ki ya cika zuciyata ko da ba za ki so ni ba idan kin gani za ki yarda da ɗimbin makahon son da nake miki wallahi ba na ji, ba na gani, bana gane rashin ki masifa ne a wajena sai kin yi nesa da ni, na yarda na amince ki koma gidana ki mini duk azabar da za ki gasa mini na yarda ki mini fiye da abubuwan da kike mini, zan ɗauki komai zan jure komai in har zan rayu da ke a inuwa ɗaya, wallahi, wallahi, wallahi ba zan taɓa butulcewa ba, ba zan taɓa haɗa ki da wata mace ba idan kika dawo gare ni ba zan taɓa miki kishiya ba ke kaɗai za ki rayu ki yi yadda kike so da ni, ni naki ne zuciyata taki ce SALIMAH" Ya kai karshen maganar rauninsa yana bayyana a cikin nuryarsa. Wani uban tsaki ta doka, wanda ya sa hawayen da suke makale a kwarmin idansa gangarowa, wannan tsakin ya tabbatar da maganganunsa tamar busar sarewa ya yi wato sun shiga ta kunnenta na hagu sun bi ta kunnen dama ko alamar tasiri kalamansa basu yi ba. FAROUQ wani tausayin abokin nasa ya kara kama shi, ko shi da yake namiji maganganun ABBAS sun shige shi amma ita SALIMAH da ake yi wa kalaman sannan ita ce mace kuma an san mata da tausayi kuma zuciyarsu tana da rauni a kalla ko da bata amince za ta koma ba ta masa wata kalma mai taushi. "SALIMAH" Ya furta a daidai lokacin da ya durkusa gwiwoyinsa a kasa yana durkushe a gabanta, bai yi la'akari da farin yadin jikinsa ba shi damuwarsa ma duk so da yake mata bata gaskata shi ba ya ma gabanta kwata-kwata. "Ya kike so a yi, mai kike so in yi ko kina so in ɗayo miki fatar jikina ki yarda, ko akwai wani ɓangare na jikina ko koda ta kike so zan iya bari a cire guda ɗaya ko da kare kika ce a dasawa zan yarda ko da hakan zai zama siyar mutuwata ai a dalilin so ne son ma naki SALIMAH... "Kai ya isa haka ABBAS mai ya sa kake kalami a inda ba za a tausaya maka ba? Wannan da kake gani ko ranka za ka cira ka bata ba za ta yarda ba kai alamunta sun nuna ko mutuwa za ka yi ba za ta tausaya maka ba, na lura mugun tsanar da ta yi maka ba iya kai take wa ba talaucin da kake ciki ne bata so da a ce kana da ɗimbin dukiya ba sai ka ka roke ta ba, dukiya ce kawai a ranta duniya ce kawai a gabanta ka daina ɓata gishirinka a dahuwar kaho, ka zo mu tafi ka roki Allah ya cire maka son ta ka samu mai kaunarka ka yi sabuwar rayuwa ka manta da ita... ."Ita nake kauna FAROUQ" . Wani haushin su ne da ya turnuke SALIMAH ya sa ta kasa magana sun mayar da abu tamkar a wasan kwaikwayo ko littafin hausa, sai wani kalaman soyayya yake tamkar wani romeo, ita fa ko kalmar so bata damu sosai a furta mata ba ta fi damuwa ta ji dumus wato masu gidan rana, kuɗi da ake kira kare kukan ka, kuɗi aljannar duniya mai kuɗi ya huta sai yake shagalinsa. . FAROUQ kuwa jin furucin da abokin nasa ya yi sai ya juya musu baya, don ya gaji da ganin abubuwan takaicin da ABBAS yake a kan so ana wulakanta shi. SALIMAH kuwa ganinsa durkushe a gabanta sai wata tsanarsa take tsarga mata zuciya musamman in ta tuno da maganar Umma cewa zuwansa wajenta barazana ne ga zuwan manyan Alhazan zawarawan ta, zuwansa zai zama shamaki ga cikar burinta hakan ya sa ta ji gwara ta masa hukunci. "Dan Allah SALIMAH... Maganar ABBAS ta makale ne a daidai lokacin da SALIMAH ta ɗaga bokitin ruwan tsarin nan ta sheka masa tun daga saman hular kansa, har bayansa jigilif ya jike, FAROUQ da sauri ga juyo jin zubar ruwa sannan jin wurin ya ɗumame da wari, ya san kafin SALIMAH ta fito kamshi wurin yake amma tun da ta zo yake jin wani wari tunaninsa ko kwata ake kwashewa a wani wajen amma yanzu kuma sai ya ji warina dab da su hakan ya sa ya gane cewa ruwan wannan ne dama yake warin wanda ko kaɗan bai kawo a ransa cewa ruwa ne ma a bokintin hannunta ba. "Wannan kaɗan kenan daga abubuwan da za ka fuskanta matukar ka ci gaba da zuwa kofar gidanmu, ba za ka hana ni rawar gaban hantsi ba, nan gaba zan iya watsa maka tafashashshan ruwan zafi ka ga idan fatar jikinka ta silsilge ka hakura da zuwa in kuma baka daddara ba akwai wasu abubuwan da na tanadar maka har sai ka janye kafarka ta fukara'u a kofar gidan nan" Lokacin da ta wasa masa ruwan sai ya ji wani sanyi ne da ruwan tamkar ruwan randa ko na firji, ga wani wari da ruwan yake har fuskarsa ruwan ya wanke, jikinsa jigilif babu inda ruwan bai taɓa ba a take wani kaikayi ya fara masa sallama a fatarsa. Duk wannan batutuwan da take masa ba ya ma fahimta, tsaye ya mike yana kallon kwayar idanunta bai ga salama ko tausayi ko rangwame daga idanunta ba. Laɓensa na kasa ya cije da hakoransa an kai gaɓar da bakinsa ya kasa furta komai da a ce wani ne ya masa haka ba SALIMAH ba da sai ya gwammace kiɗa da karatu. "Ke wace irin wawiya ce, mai ya sa kika ɗauki ɗan adam ba a bakin komai ba, kike wulakanta ɗan adam, bayan ubangijinmu ma ya faɗa a littafinsa mai tsarki cewa ( Wakakadi karramana bani adama,,, hakika mun karrama ɗan adam)" FAROUQ ya faɗa a kufule yana jin tamkar ya hau ta da duka. "Yanzu zan nuna maka wawiya ce ni" Ta ce tana juyawa wajen kwatar gidansu inda aka yi wa makwararan wanke-wanke hanya ruwan yake taruwa a kwatar simintin da aka yi bokitin ta saka ta kwalfo ruwan ta nufo su a wanna lokacin su duka za ta watsawa don shi ma abokin hakan ya zama izna gare shi nan gaba ba zai sake yarda ya rako shi ba. Tana ɗagawa za ta fara shekawa ABBAS FAROUQ ya yi saurin ɗaga hannu zai wanka mata mari, cikin sauri ABBAS ya saka hannu ya rike masa hannun nasa, ba wai don abin da ta yi bata cancanci mari ba sai dai ba ya so a taɓa lafiyarta gani yake da a mare ta gwara shi a mare shi zai fi jin saukin abin a ransa. ."Da ka bar shi ya mararwa kansa bala'i wallahi sai na saka an kulleka har igiya ta yi saura, ba kai kaɗai abin zai shafa ba har danginka, kuma in kara gani wani ya zo wajen na" Ta ce tana nuna FAROUQ da yatsa tare da shekar da ruwan kwatar a waje ta yi jifa da bokitin ta juya abin ta tana dab da shigewa gidan ABBAS ya ce "SALIMAH" Tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba. "Idan har hakan zai sa ki farinciki na yarda na amince ba zan sake zuwa ba na zaɓi na rayu da kuncin rashinki ke ki yi farin ciki" ."Hahahaha wa ya faɗa maka barno gabas take, ai in ka ji mutum yana cewa ba zai iya ba bai kama shi bane ka ji uwar bari" Ta ce a zuciyarta wani daɗi yana baibayeta ganin ta yi galaba a kansa ashe akwai barazanar da za ta masa ya kyale ta. A fili kuma sai ta ce "Naka ya rage ABBAS za ka iya cigaba da zuwa ni kuma ba zan gaji da maka hukunci ba, kuma gobe za mu zo mu kwashe kayanmu daga wannan gidan kaima ka huta da biyan kuɗin haya" Tana gama faɗa ta juya. "Za ki yi da na sani wata rana, za ki dawo ga ABBAS a lokacin da ya miki nisan da sai dai ki hango keyarsa daga nesa, yadda kika wulakanta shi na tabbatar Allah ba zai barki haka ba, yadda kika raina matsayi da samunsa na tabbatar akwai lokaci yana zuwa ki rubuta ki ajiye za ki ce dama FAROUQ ya faɗa mini indai auren mai kuɗi ne, auren jari, auren da ba don Allah ba ga wurin nan wasu masu kuɗin suna da kirki da duk kyawawan abubuwa tun da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba amma ke saboda abin da kika yi wa ABBAS sai Allah ya jarabce ki! " FAROUQ ya ce cikin ɗaga murya dama da ta juya ba tafiya ta yi ba sai da ta gama ji tsaf. Dogon tsaki ta ja ta ce. ."Bakin ka ya sari kashi, kuma mugun fatanka ya koma maka, babu abin da zan gani, sai dai ya kare a kan ka" Bata jira cewarsu ba ta shige gida. Har ta ɓace wa ganin ABBAS amma bai ɗauke idanunsa daga wurin ba tamkar dai zai ganta haka ya kurawa wajen ido. A hankali FAROUQ ya yi taku ɗaya biyu ya dafa kafaɗarsa ya ce ."Abokina" Ya ce cikin tausayawa ABBAS ɗin. Ya san ba laifinsa bane so abu ne da yake cikin zuciya idanu ba ya ganinsa bare hannu ya taɓa shi. ABBAS kawai juyowa ya yi ya rungume FAROUQ duk da jikinsa a jike kuma yana warin ruwan tsarin da ta watsa masa amma bai ji tsantsani ba, yana jin irin yadda kirjinsa yake bugu da sauri da sauri. ."Ka yi hakuri ka ji, idan so cuta ne hakuri magani ne" Kai kawai ABBAS ya gyaɗa masa saboda ya ma rasa bakin magana ba ya gane komai kuma ba ya fahimtar komai. Da lallashi FAROUQ ya saka suka hau machine ɗin suka tafi. Da sallama suka shiga gidan Mama inda ta shiga kallon yadda ABBAS ɗin yake a jike. "SALIMAH ce ko?" Mama ta jefa musu tambayar don ta san ita ce kaɗai za ta aikata wannan aikin. Shi dai ABBAS bai ce komai ba, FAROUQ ne ya bata amsa amma bai faɗa mata yadda suka yi ba ya dai ce mata ta ce ba a ta koma ba gobe za su zo su ɗauki kaya. "Allah kawo su lafiya, ya sa haka ne ya fi alkairi' Mama ta ce tana jin ciwon wulakanta mata ɗa da SALIMAH take. ABBAS ɗakinsa ya shiga ya kwanta rubda ciki, jinsa yake tamkar ba shi da lafiya, ga jikinsa ma ya ɗau zafi jin sa yake tamkar a wata duniya ta da ban. "ABBAS baka jin yadda kake warin ruwan nan?" "Ba na jin warin abu ɗaya na sani ina jin kamshi" "Kamshi fa ka ce?" FAROUQ ya tambaya da mamaki. "Ai tun da SALIMAH ce ta watsa mini ba zan ji warinsa ba, kuma zuciyata bata ganin laifinta sannan kuma har abada ba zan daina sonta ba" Ya ce har lokacin yana nan kwance rubda ciki. "To majnun na Laila ai sai ka tashi ka je ka yi wanka ka cire jikakken kayan nan, ni na tafi sai da safe" Bai jira cewarsa ba ya fita daga ɗakin ya wa Mama sallama ya tafi. Mamar ce ta shiga ɗakin take masa nasiha dakyar ta shawo kansa ya yi wankan ga zazzaɓi mai zafi ya rufe shi magani ta bashi ta rufe shi sai numfarfashi yake. Washe gari da yamma Mama tana waje makwarara ta rike ABBAS ɗin da yake ta kelaya amai, da yake da zazzaɓin ya kwana ga ciwon kai mai tsanani hakan ya sa da safe ta kira FAROUQ suka je asibiti magunguna allurori da drip aka rubuto masa, wani abokin su FAROUQ ya kira ya zo gida ya saka masa drip ɗin bayan ya masa allurorin. Bayan an cire ne kuma ya ce zai yi amai Mama ta fito da shi da yake yanzu su kaɗai ne a gidan FAROUQ ya tafi. Bayan ya gama aman ne ya zauna a kan wani ɗan dakali da yake tsakar gidan, Mama sai kallonsa take da tausayawa, suna cikin wannan halin ne suka tsinkayi muryar ana sallama. "SALIMAH ce Mama" ABBAS ya ce yana tashi tsaye yana faɗa jin muryar SALIMAH tana ɗaya daga cikin masu sallamar duk da bai ganta ba amma ba zai kasa gane muryarta ba amon muryarta yana ɗaya daga cikin sautuka masu muhimmanci a rayuwarsa. Mama hannu ya kai ta rike shi ganin yana karkarwa kuma duk ya ruɗe ga jikinsa ba karfi, sallamar ta amsa tana jin wani ɗaci a ranta jin ya ce SALIMAH ce. Cikin gidan suka shigo, su biyu ne, ita da wata kawarta ƴar unguwarsu wacce kusan shekara uku da mutuwar aurenta, ita ma bata yi auren ba har yanzu. Suna wani gani-gani suka shigo gidan su duka suna taunar cingam tana kas-kas cike da rashin kamun kai mayafin nan sakale a kafaɗunsu ko arzikin yafawa bai samu ba. "Mamar ABBAS ya kike?" SALIMAH ta ce cike da shekiyanci. Shi kuwa garau ya mata da idanu yana kallonta har ba ya son ya kiftawa ya zama tamkar wani zararre, gani yake tamkar yau ne rana ta karshe da zai sake ganinta a rayuwarsa tun da ya yarda ba zai sake zuwa gidansu ba ita kuma ba za ta dawo ba. "Ina lafiya" Mama ta bata amsa cike da gatsali kamar yadda ta yi don Mama ji take ta tsani yarinyar nan yanzu ma bata so ta shigo mata gida ba za ta fama wa ABBAS mikin ciwon sonta da ta tabbatar ko jinyar nan da ya kwanta ita ce sila. "Mukullin akurkin kajin can za a bamu za mu kwashe kayanmu" Kawar tata mai suna RUKY ta faɗa tana yi wa Mama kallon up and down. Ko kala Mama bata ce ba ta ja ABBAS yana togewa amma a haka ta nufi ɗakinsa da shi, sai waiwayenta yake, Mama tana zaunar da shi ya yunkura zai tashi wata harara ta zabga masa da ta sa ya koma ya kwanta a katifar dama ba karfin jikinsa yake ji ba. Mukullin ta ɗauka ya fita daga kofar ɗakin ta tsaya ta jefa musu ta koma ɗakin ABBAS yana jin lokacin da suka fice idanunsa a rufe yana jin yadda bugun zuciyarsa yake bugawa sosai. Da motar ɗaukan kaya suka je da maza uku suka kwashe kayan tas don sauran kayan ABBAS ma a nan aka watsar masa su suna bi ta kai suna wucewa, hatta ledar tsakar ɗakin sai da suka naɗe kayan nasa a dandamalin kasa suka ajiye, da suka gama suka rufe musu gidan. Motar kayan tana biye da napep ɗin da su SALIMAH suke ciki, a kofar gidan Mama suka tsaya, ita da RUKY dai suka shiga da sallama suna wani yatsina. Mama da ta fito daga ɗakin ABBAS jin sallamarsu bayan ta amsa sallamar kafin ta yi magana SALIMAH ta cillo mukullin suka juya suka fice daga gidan. Sosai Mama ta jinjina rashin tarbiya da rashin girmama na gaba tabbas in ba kaddara ba ma babu abin da zai sa ABBAS ya auri SALIMAH don ko hanya basu haɗa ba ya bata rata a komai na daga nagartar tarbiya. ABBAS da yake cikin bargon da Mama ta rufe shi yana jin karan dirin tsayuwar motar da shigowar su cikin gidan da kuma fitarsu, sannan ya ji lokacin da motar da napep ɗin suka tashi idanunsa kawai ya runtse yana jin wani zafi a ruhinsa. SALIMAH basu yi masauki ba sai a ƴan kafintoci, in da ABBAS yake aiki saboda rashin mutunci wai a can za ta siyar da kayan haka suka je aka sauke kaya aka yi ciniki aka biya su, gida suka karasa ta sauke tarkace da sauran kayan kicin ɗinta ta sallami masu motar da napep ɗin bayan an shigar mata da kayan gida. Dubu biyar ta ba RUKY a cikin kuɗin sauran kuma ta ba Umma ta ajiye bayan ta ɗauki dubu ashirin don har kujerun ta siyar. "Yo ajiyar mai za a yi ke da idan kika fara samun kuɗin sai mun rasa yadda za mu yi da su, ai kawai mu yi cefanen kayan daɗi mi fara wankin ciki tun yanzu, ki ɗauki wani abun ki yi ɗinkunan kafin na kece raini ya zo wato na zawarawa" Cewar Umma. 09013181851 KU MATSO DOMIN JIN DADDAƊAN LABARI 💃💃💃💃💃💃💃💃 . ZAN CIKAWA KOWANE MUTUM ƊAYA DUBU GOMA 1OK Shin kin taɓa jin labarin 52U? Yadda mutane suke register da cin moriyarsa, da dala 21 ake yi $21 kimanin 35k. Duk wacce za ta yi register a team ɗina zan cika mata dubu goma 1OK ta kawo 25k sannan duk wata zan ke bata 15k tsawon wata 3 idan acc ɗinta ya cika wata shida zai buɗe sai ta cigaba da kwashe kuɗaɗenta. Mutum 2O nake nema kar ku bari damar nan ta wuce ku ki mini magana a PC 09013181851 [1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 6 *ZARIYA* *Unguwar Gwalagwaji* Kwance take a kan tsohuwar tabarmar wacce ta shimfiɗa musu zannuwa guda biyu, SABEER wanda ya ɗora kansa a jikinta duk ya takura saboda fitsarin da ya yi ɗan yalolon zanin da ta rufe su ta cire daga jikinta ta rufa masa, a haka bacci ya yi awon gaba da ita kasancewar ayyukan da ta yi ta gaji. Hajiya Rayyanatu wacce ta nufo ɗakin nasu da sanyin safiya ɗauke da ruwa a jug ta shigo ɗakin tana jan wani tsaki tare da toshe hanci, ruwan ta ɗaga ta sheke musu a jikinsu a gigice suka falka SABEER yana sakin kuka da sauri ta ja shi jikinta ta rungume shi tare da jijjiga shi alamar rarrashi duk da yake in da sabo ya ci a ce sun saba don kullum ruwan shi ne abin da ake tashin su da shi daga bacci sai dai hakan ya ki zama sabo kasancewar mai bacci ba ya son a zuba masa ruwa hakan yana zuwar wa mutum a bazata kuma duk wanda yake da ikon tsawatarwa kan cewa kar a zuba masa ruwa ko da ba a bacci bane zai tsawatar amma a inda yake da iko ba kamar su ba da basu da kataɓus maraici ne silar komai mutuwa mai yankan kauna da yanke jin daɗin duniya a lokacin da ba a zata ba, kuma ba a tsammata ba mai raba ɗa da mahaifi ta musu shigar sauri ta yanke musu rayuwa da mahaifansu a lokacin da suka fi bukatarsu a lokacin da suka sakankance suna rayuwar da basu kawo rabuwa da juna ba. Sai dai shi tsari na ɗan adam da ban yake tsarin ubangiji na da ban yake, a lokacin da kake lissafin sherakara goma za ka yi kaza kai baka san cewa saura minti goma ka bar duniyar ba Allah ya bar wa kansa sanin wannan ya ɓoye shi ga ɗan adam sai dai zama koyaushe cikin shirin da sakawa a rai cewa ko da yaushe mutuwa na iya riskarka shi zai sa ka yi duk wani abu wanda zai kusanta ka ga aljanna, ka nesanci wanda zai kai ka ya zuwa wuta!. "Ki tashi ki tafi ki haɗu da ƴan aiki kin zo kin kwanta gari har ya waye ko har yanzu dakikiyar kwakwalwarki tana miki tunanin rayuwarki ta baya ne? To nan ba da gidan ubanku bane gidan kanen ubanku ne, uban naku yana can cikin kasa a rufe" Hajiya Rayyanatu ta ce tana aika musu kallon mugun tsana. Kallon ta Hauwa'u( Hawwa) Ta yi tana jin zafin kalamanta bata san irin zafin da take ji ba idan aka sosa mata mikin mutuwar mahaifanta wanda mutuwa ta ɗauke musu su a rana ɗaya a lokaci guda ba tare da ciwon komai ba sai kaddara da karar kwana. "Ai Aunty Hawwa ta ce Ummie da Abbie za su buɗe kasar su dawo mu koma gidanmu ko Aunty Hawwa" SABEER ya ce yana karkarwar sanyi. Kai kawai Hawwa ta gyaɗa masa tausayinsu yana kara shiga zuciyarta har gwara ita yanzu shekarunta sha takwas, iyayanta sun rasu tana da shekara sha shida, shi kuma SABEER shekara bakwai lokacin yana ɗan shekara biyar suka rasu amma kasancewarsa yaro mai wayo da rashin mantuwa har yanzu bai manta komai ba. "Kai dalla rufewa mutane baki uban waye ya ce maka idan an mutu ana dawowa duk wanda ya mutu ba zai taɓa dawowa ba, su ma suna can sun tafi kenan" Da kuka ya fashe yana kifa kansa a kirjin Hawwa ita ma Hawwa hawayen take tana jin kukansa har kasan ranta tana kuma jin haushin maganganun Hajiya Rayyanatu wacce ta kasance matar kanin mahaifinsu. "Za su dawo mu koma gidanmu" Ya ce cikin kuka, Hajiyar ce ta karasa gabansu ta saka jug ɗin hannunta ta kai masa bugu ai kuwa Hawwa ta saka hannu ta kare dukan da ta kawo ita aka same ta a hannu, ganin haka sai Hajiyar ta juya akalar dukan zuwa gareta ta rangaɗa masa jug ɗin a ka da karfi. Bata ce komai ba kuma bata yi yunkurin komai illa iyaka ta sunkuyar da kanta kasa hawaye suna malala daga idanunta tana tunanin ranar da za su bar gidan nan su fita daga ukubar da ake musu da gallazawa. "Idan kika kara minti biyar baki fito ba wallahi sai kin gwammace kiɗa da karatu shegiya mai farin fatar zabiya, wannan farin naki na maita ne gadon tsiya gayyar na ayya gayyar tsiya" Ta ce tana juyawa ta fita daga ɗakin. Hannu SABEER ya saka yana share mata hawaye n. "Aunty Hawwa ki yi hakuri daga Ummie da Abie idan sun dawo za mu bar musu gidansu mu koma gidanmu ko? Inda muke kwana a saman bed, har Ummie take ce miki Hawwa in kara gani kin ce a ɗakin SABEER za ki kwana shi ɗakin naki dafawa za ki yi ki ci? Muke cin abinci mai daɗi direba ya kai mu makaranta ya dawo da mu Abie ya ka kaimu wurin wasa da gidan zoo" Ya ce har yana murmushi tunowa da ya yi da rayuwarsu lokacin iyayansu suna raye. Rungume shi ta yi tana tuno abin da ya ce Ummie tana cewa ɗin har jiyo sautin maganar ta yi yadda take mata faɗan cikin wasa saboda tsokana irin ta Hawwa sai ta je ta kwanta a ɗakin SABEER yana tashi ya ganta a kan gadonsa tana bacci sai ya ringa kuka wai ta zo masa ɗakin bayan fitsarin kwance ma yake. Da sauri ta tashi tana kama SABEER ɗin suka fito suka nufi bayin wanda yake na ƴan aikin gidan ne, dama a ɓangaren ƴan aiki aka basu ɗaki. Ruwan ɗumi ta karɓa a wajen Baba Sadiya mai aiki dattijuwa mai sanin ya kamata sosai take tausaya wa yaran ganin yadda masu gidan suka mayar da su tamkar ba ƴaƴan zumunsu ba, har yau tana mamakin yadda duniya ta lalace wasu daga cikin mutanen cikinta suka ɗauki duniyar tamkar matabbata, yadda suka ɗauke ta wuyarta mutum ya mutu yanzu komai zai canja daga fari zuwa baki wani idanunsa ne mashi daga babu idanunsa shikenan komai an dainawa ƴaƴansa dama na ganin ido ne ake. Wani ko a kwnce yake ba ya iya komai amma albarkacin numfashin da yake da idanunsa da suke kiftawa sai ki ga ƴaƴansa basu tagayyara ba amma daga ranar da aka ce ya bar duniya sai komai ya sauya wani duk abin da yake maka na kyautatawa daga ranar ya daina wani ko magana mai daɗi ba zai kara maka ba. Wanka ta masa ta je Baba Sadiya ta lakuta mata man shafawa ta shafa masa ta saka masa kayan makaranta wanda makarantar gwamnati ce aka saka shi bayan gabaɗaya yaran gidan a makarantun kuɗi suke amma shi a makarantar gwamnati yake. Lokacin iyayansu suna raye Abie ne yake biyan kuɗin makarantar har ƴaƴan kanin mahaifin nasu, makaranta ce mai tsada da sai wane da wance ne suke, duka a makaranta ɗaya suke kuma shi yake biya ba don kanin nasa bashi da hali ba sai don zumunci Allah, don hatta gidan kanin nasa shi ya gina shi ya bashi. Direban gidan Abie shi yake kai su makarantar tare ya ɗakko su ya kai su gida sai ya wuce da su Hawwa gidansu. Amma su Abie suna mutuwa Alhaji Bukhari ya cire su daga makarantar ya mayar da su ta gwamnati kuma a kafa suke zuwa su dawo a kafa suna gani za a ɗauki ƴan gidan a mota su kuwa kafarsu ce take aiki haka Hawwa take goyon SABEER a bayanta idan ya gaji da yake makarantar da nisa da gidan, har ta karasa secondry scul dama tana aji huɗu iyayan nasu suka rasu, yanzu kuma da ta kammala sai take raka SABEER ɗin ta dawo in an tashi ta je ta taho da shi. Kasancewar dama ba sallah take ba, shi bayan ta shirya shi ta saka shi ya yi alwala ya yi sallah. A ɗakin ta bar shi ta tafi kicin inda masu aikin suke hada-hadar haɗa kayan karin kumallo, haɗuwa ta yi da su suka cigaba da yi tare don tun da ta dawo gidan komai na aikace-aikacen da ita ake yi jin daɗinta ɗaya Ummie ta koya mata girki da aikace-aikace, duk da kasancewar mahaifinta mai tarin dukiya amma Ummie bata bar su kara zube ba tarbiya da sanin ya kamata girmama na gaba. Duk da gatan da suke da shi amma tana fahimtar da su rayuwa. Sai da aka gama haɗawa ta fara kwasa tana kai wa kan dinning ɗin tana jerawa lokacin har takwas ta kusa ga shi tana so ta tafi kai SABEER makaranta kullum yana faɗa mata in ya je class ɗin su sai an masa bulalar makara kullum shi ne na karshen zuwa class, sai dai babu yadda za ta yi tun da ba za a kai shi a mota ba sannan ita ba za a bar ta ta tafi ta raka shi da wuri ba, dole sai an yi karin kumallo an gama karin kumallon da ko a hannu basu isa an basu sun ci ba sai dai su ci abincin ƴan aiki da yake na ƴan aiki da ban na masu gida ma da ban. ."Wane shegen ne zai zuba abincin da kika gama jerawa za ki tafi Yaya Umar ya ce yana mata wani kallo" .."Ban gama kawo wa ba " Ta ce cikin muryarta mai sanyi. "Kai mene ne na tuna mata baka bari ta yi kuskuren jikinta ya faɗa mata" Alhaji ya ce yana aika mata harara ya tsani yaran ba don yana so ya yi kakagida da sama da faɗi da dukiyar da ubansu ya bari ba da babu dalilin da zai sa ya karɓi rukonsu da ko za suke yawo suna bara ba zai rike su ba!. "Ai Baba yarinyar nan mugun taurin kai ne da ita wai jiya na dawo da dare na ce ta zo ɗakina ta mini taɗi wai taki har ni take faɗawa wai babu kyau namiji da mace su keɓe kamar dai wani saɓon Allah na ce zan yi" Ya faɗa yana kallon Hawwa da take zuzzuba musu abincin tana ajiyewa kowa a gabansa. "Ai kai ne da jarabar naci ni ban ga abin so a wannan figaggiyar yarinyar ba ka nemi wayyayyi wacce take da cikakken gata amma sai ka kare a mai karatu iya sakandire marainiya da bata da wani gata" Hajiya ta ce tana taɓe baki. "Ai na faɗa masa ya ki ji ga ƴaƴan abokaina nan, amma ya ce sai ita tun da ita ya ce zai aura zan aura masa don in nuna masa indai ina raye ba zai taɓa rasa abu ba, in ya so idan ya samu mata sai ya aura ko uku ne ya rufe kofa" Baba ya faɗa. "Kai ma Yaya da wani abu wallahi ni fa yadda na tsani Hawwa bana jin akwai wani abu da zai haɗa ni da ita sai dai in aiki za ta mini, yarinyar nan ta fini kyau ta fini ilimi ga kokari kamar masifa ko lokacin muna makaranta ita take ɗaukan first position a class ɗin ni in yi na karshe wannan mataccen uban nasu ya ringa mini faɗan wai in dage in ke kokari yanyanyanyan ya ringa wata nasihar sa da ba shigata take ba illa mugun haushin sa da nake ji ita ma uwar tasu Ummie take ko Ummita bata da abu misali sai mu yi koyi da Hawwa... "Ya isa Lawisa! Wasa ya yi wasa ban da tsikarin uwar miji, duk abin da za ki faɗa ji faɗa iya kaina sa SABEER bana so ki taɓo mini iyayena da suke kwance a cikin kasa" Hawwa ta ce cikin ɓacin rai idanunta suna ciko da kwalla. "To mene ne saura idan an yi zancen matacce? Ai arahar kunu ta banza ce idan babu gaya a ciki, yanzu baku da gata da galihu don haka abin da kuka yi a gidan nan mai kyau shi zai sa ku samu abinci saboda abubuwan da iyayanku suka yi na kyautatawa ya wuce babu shi mun ɗakko ku ne gidan nan ku yi mana hidima ku samu abinci, in kun yi da kyau za ku ga da kyau! Kuma ko Umar da yake cewa zai aure ki ba wai ƴanci za ki samu ba illa iyaka bauta ce da musgunawa ki zama baiwarsa. Kanta ta sunkuyar ta ci gaba da zuba musu abincin hawaye suna sintiri a kumatun ta, a duniya ta tsani ta ji ana faɗawa iyayanta maganganu, sannan ta ki jinin ta ji ana cewa za a aura mata Yaya Umar mutumin da bai san komai ba sai shaye-shaye kullum ya zo gida idanunsa jawur in ya dawo da dare a buge amma saboda ita ba su suka haife ta ba sai a aura mata shi, ita yanzu aure ma ba ya gabanta karatu take so amma tun da ta kammala karatun ga takardun sakandiren nan amma kuma an ki a sama mata adimishan ta cigaba da karatu in ta yi magana a ce wai ta gama karatu iya sakandiren ma ya isa saboda ba sa kaunar ta yi zurfi a karatu har ta zo ta samu aiki ta zama wani abu shi ya sa don su dakusar da rayuwarta za su aura mata Yaya Umar wanda shi ko secondryn bai gama ba ya watsar da karatun wai dama ana karatu ne don a samu aiki ana yin aiki ne don a samu kuɗi to su kuma dukiya gata nan har sun ci sun tada kai. Sallah wannan bai damu ya yi ba shin ta aure shi ta ce ta auri wa?" Fitowa ta yi bayan ta gama haɗa musu ta nufi wajen Baba Sadiya ta karɓo abincin SABEER wanda koko ne da kosai. "SABEER ba ya son kokon nan ya fi son shayi kullum in na masa dole ya sha sai ya yi amansa" Hawwa ta ce cikin sanyin murya. "Ki yi hakuri Hauwa'u da a ce da yadda za a yi in ke zuba masa shayin da ko na iya lipton ne da na zuba masa, to bani da wannan damar, da ina da ita hatta dankalin turawan nan da wainar kwai sai na zuba masa Hauwa'u to kin san dai tsari da dokar gidan nan matsawar aka yi hakan ko a ɓoye ne sai ka fuskanci hukunci ko ka rasa aikin ma baki ɗaya' "Na sani Baba Sadiya abubuwan ne suke damuna, ni na san babu na san hakuri amma SABEER yaro ne kullum sai ya yi mitar abinci sai ya yi mitar makaranta da zuwa makaranta a kafa sai ya yi mitar kwanciya a kasa a ɗakin wancan kuma in dai zai yi sai ya sako maganar su Ummie a ciki sai ya tuno cewa da a gidanmu ne da an yi kaza da kaza ya kasa mantawa ni kuma hakan yana tada mini mikin damuwar da muke ciki yana tada mini rashin da muka yi wanda ba za mu mayar da gurbin ba har abada!" "Ita dama rayuwa tana canjawa mutum a lokacin da bai yi zato ba, to ya za a yi da lamarin ubangiji haka Allah ya tsara, wata rana sai labari duk abin da mutum ya yi hakuri wata ran zai zama tarihi" "Haka ne" Hawwa ta faɗa tana danne kukanta. "Ki yi hakuri ke ma girma ne ya same ki wanda baki yi zato ba, haka za ji bi komai a sannu su kuma Allah ganar da su". "Amin Baba na gode da kulawarki gare mu".. "Babu komai Hauwa'u karamcin mahaifiyarki gare ni ba zan taɓa mantawa ba mace mai kirki da girmama ɗan adam kowa nata ne abin hannunta bai rufe mata ido ba, ɗimbin dukiyar da suke da shi bai saka nata girman kai ko kyamatar talaka ba, ki je ki bashi abincin ku tafi ungo wannan ɗari biyun ko hau adaidaita sahu, idan kin kai shi sai ki dawo a kafa, wannan kuma man shafawar ne na lakuta muku kuke shafawa in aka biya mu kuɗin aiki zan saya muku naku tun da nakun ya kare" Hannu biyu ta saka ta karɓa tana godiya yanzu duk duniya Baba Sadiya ce kaɗai mai kaunarsu mai taimaka musu duk da taimakon ma a ɓoye ake yi saboda kar masu gidan su ankara wani abu ya biyo baya. Dakyar ta samu ya kukkurɓi kokon jin ya ce zai yi amai ta kyale shi kosan ya ci kaɗan yana ta cewa da a gidansu ne da an yi kaza da Ummie ta haɗa masa kaza ita dai tana ta cewa sun kusa dawowa. "Aunty Hawwa kullum fa sai Hajiya ta ce sun tafi kenan" "Wasa take yi" Ta ce tana jin zafin furucin da Hajiyar take musu tun da ga shi ya shiga kwakwalwar yaron ya zauna daram. Hannunsa ta kamo suka fito suna zuwa get ɗin ga motoci nan guda shida a ajiye ga direbobi nan zaune suna jiran umarni. "Aunty Hawwa ki ce direba ya kai mu mun makarafa" "SABEER, SABEER, SABEER sau nawa na kira ka?" "Uku to ka daina cewa mu hau motacin nan daga su Ummie sun dawo za mu koma gidanmu sai mun zaɓi wacce za mu hau" Ta ce tana sakar masa murmushi tare da lakato hancinsa dariya ya kyalkyale yana kankame ta suka cigaba da da hira suna darawa su kaɗai ne farin cikin junansu. Har suka samu napep ɗin ɗan arziki a ɗari da hamsin ya kai su sai ta siya masa biskit na hamsin ɗin yana ta murna. A da SABEER bai damu da biskit ba saboda gasu nan kala-kala- da wafera da cakulet lemuka iri -iri a store in aka saka masa cikin lunch box ɗinsa wata rana ma haka zai dawo bai ci ba, amma rayuwa kenan yanzu sai ya yi wata ma bai ci ba. Tana dawowa Hajiya ta tisa ta da masifa wai ta je ta daɗe ko yawon banza take tafiya, haka ta yi ta gasa mata maganganu ta shiga aiyukan gidan duk da akwai isassun masu aiki amma don a musguna mata ita ake sakawa rabi da kwatar aikin gidan. "Ki je ki gyara ɗakin Umar saboda raini kullum sai ki gyara ko ina ban da ɗakinsa ki gyarawa kowa nasa ɗakin amma ban da shi" Hajiya da take zaune a kan kujera ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya ta ce tana aika mata harara. Da to ta amsa tana daukan kayan gyaran ta nufi ɗakin nasa ta tsani zuwa ɗakin Yaya Umar kasancewar shi namiji kuma mashayi. Tana tura kofar wari ya mata sallama wannan warin da take ji gwara warin kashi a kansa. Kolon amai ne ya sa ta fitowa daga ɗakin tana danne bakinta da tafin hannunta Hajiya da take zaune ganin wulgawarta da ta fito daga part ɗin Umar sai kuwa ta taso cike da masifa son a zaton ta gyaran ne ta yi ha,inci bai gyaru ba ta fito. Duk kiran da take mata bata amsa ba kasancewar aman ya taho can ciki ta wuce ɓangarensu na ma'aikata ta je makwarara ta ringa kela amai cikinta yana kullewa kasancewar babu wani abinci a cikin sai da gama ta wanke fuskarta ta gyara wajen ta dawo nan ta samu Hajiya ko ta bakinta ba ta saurara ba illa iyaka ta ce ta raina mata wayo tana ji tana kiranta ta kyale ta sai yanzu ta zo a shelake. Hakuri ta shiga bata duk da bata san takamaiman laifinta ba amma haka ta kama kunnenta ta murɗe sai da ta kusa sakin fitsari sannan ta kyale ta ganin ta jigata. Umarni ta mata a kan ta koma ta kara gyara ɗakin Umar ɗin ira Hawwa bata samu damar cewa komai ba tun da ba saurarenta za a yi ba. Ɗankwalinta ta since ta ɗaure hancinta ta shiga ɗakin duk kayansa a kasa haka ta tattare ta kintsa su a waje guda hango wasu kwalabe reras a kasan gadon karambani ya sa ta yin kallon kwakwaf ai kuwa ta yi tozali da kwalaben giya. Sosai jikinta ya shiga karkarwa tana mamakin shi dai Yaya Umar duk wani abu na saɓo yana yi bayan shan kwaya, yana shan giya ga neman mata wace mace ce za ta yarda ta aure shi? In ba wacce bata san ciwon kanta ba, ko iyayanta mararsa sanin darajar ƴar su ba, amma ita saboda maraici da rashin sanin ya kamata da kuma rashin tsoron Allah za a aura mata ɗan shaye-shaye. Da a ce ƴar su ce ba za su taɓa yarda su aura mata shi ba. 09013181851 [1/5, 8:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 7 *SALIMAH* Kwance take a barandar kofar ɗaki tana charting da EESHART yanzu kam ta sakar suna hulɗarsu kamar da, sai dai ita a ɓangaren EESHART dama abij da ya da ta fara yi wa SALIMAH wulakanci lokacin da aka yi sakin saboda kuduri da burinta ne ya cika a fili tana kaunar SALIMAH kamar me amma a zuciyarta ta tsane ta hassada take mata musanman da take zaune a gidan aurenta lafiya bata san matsaloli da kalubaken da mata suke fuskanta a gidanjen aurensu ba. Duk da dama aure ɗan hakuri kuma hanya ce ta samu aljanna ita kuma aljanna ba za a same ta a haka ba dama an kewaye aljanna da abubuwan da zuciya bata so, kuma an lulluɓe wuta da abin da zuciya take so. Ma'ana duk wani abu wanda yake saɓon Allah ne sai aka ce sai mutum ya bar shi zai shiga aljanna, haka ma duk wani abu da zuciya take so sai aka hani mutum aikatawa sai hakan ya zama mukullin shiga aljanna. Misali idan mace ta yi hakuri ta jure a gidan aure ta yi biyayya ga mijinta to za ta shiga aljanna sai dai wannan biyayyar ita ce mai wahala wata tana gani mijim ya tauye ta ne bayan kuma Allah ne ya yi umarni da hakan. Idan kuma ta bijire hakan zai sa ta shiga wuta Allah kiyaye. Har sai da ta ga ta kashe mata auren sannan hankalinta ya kwanta ko kyautata mata da take yi a gidan auren, saka kati da data bata kuɗi da sauransu din ta kara saka mata kwaɗayi da burin auren mai kuɗi ne ta kashe auren saboda ta san da wahala ta samu miji mai hakuri mai sonta wanda ya haɗa komai kamar ABBAS. Ganin kar SALIMAH ta yi saurin harbo jirginta tun lokaci bai kure mata ba ta koma gidan ABBAS ɗin shi ya sa ta sauya shawara a kan bin komai a sannu har sai ta yi wani auren duk da ta san yanzu burin auren mai kuɗin ya zauna a zuciyarta daram ta yadda duk runtsi duk wuya ba za ta koma gidan ABBAS ɗin ba. Sallamar BASEERA ce ta katse mata dariyar da take kyalkyalawa, EESHART tana bata labarin wani littafi mai ban dariya da ta karanta na maman afrah mai suna ƳAN ADAIDAITA SAHU har tana ce mata tsabar dariya sai da ta tuntsuro daga kan kujera, tamkar ita take karantawa haka ta ji labarin ya bata dariya tana cikin wannan halin ne BASEERA ta yi sallama. Amsa mata ta yi tana mai haɗe rai tamkar ba ita ce take dariya yanzu ba. Karasowa ta yi ta zauna tana murmushi dama ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya. "Hajiya SALIMAH ikon Allah kamar kin ga makiyiyarki?" Ta ce tana murmushi har lokaci. "Mai kika gani?" "Mene ne ma ban gani ba, kin ga yadda kika ɓara rai?" Majewa ta yi ba tare da ta amsa mata ba. "Ina wuni, ni in gaishe ki tun da ni ban samu arzikin a gaishe ni ba" "Yo katin gayyata na aika miki da zan gaishe ki? Ke babu mai yin magana da ke cikin daɗin rai sai ki hau wa'azi tamkar ke kika fi kowa sanin dai dai da sanin ya kamata" "Allah sarki kawata, ita dama ai gaskiya ciwi ne da ita kuma tana da ɗaci amma ki saki ranki yau ba wannan ne ya kawo ni ba dama na ga na miki magana saman whatsapp baki buɗe ba na kira ki ya fi a kirga bakya ɗaukan kirana, sgi ne na ce bati na zo in ji laifina tun da ni ba za a je inda nake ba" Sakin fuskarta ta yi, ta ce "To ai ke ɗin ce daga nasiha sai wa'azi kin ga kuwa ai ba kullum akw kwana a gado ba" "Haka ne" "Yanzu ya kike, kuma ina kika baro mini baby da babanta?" "Ina lafiya, baby tana gidanmu a can take yau tun safe, shi kuma Habib kalbi yanzu ya ajiye ni" "Inyeee ka ga tattabaru masoyan asali in ka ga wata ka ga zarah ni na kasa sanin yaushe ne soyayyar nan za ta tsufa don kullum sai hauhawa take tamkar an zubaaa fulawa yis" Ta ce tana dariya. "Ke ko, wa ya faɗa miki soyayya tana tsufa ai sai dai masu yin ta su tsufa, kuma a gidan aure in dai miji zai samu abin da yake so daga gare ki, na daga biyayya kuma kina girmama shi, sanna uwa uba tsafta da kwalliya gyara jikin ki matsayinki na ƴa mace idan na ce gyara kowace macs ta san mai nake nufi to matsawar kika kiyaye wannan duk taurin kan namiji za ki samu salama da sasaauci za ki samu zaman lafiya shi namiji yana da son girma da son a girmama shi, sannan gyaran jikin ki ko yaushe ya jiki yadda ya kamata domin mu'amalar auratayya ita ce aure duk wanda ba ya samun biyan bukata kuwa wannan ne mafarin gurɓacewar zaman lafiyarsa a tare da abokin zamansa, wai ina Umma kin sa sai zuba nake ban tambaye ta ba". "Ta je asibiti dubiya, kuma wannan dogon jawabin naki zai fi kyau ga wanda yake tare da mijin da yake so yake kauna, idan fa aka ce babu so to babu magana duk wani abu ba zai samu ba, idan na yi sabon aure na auri zaɓina zan zo kike biya mini karatuttukan nan" Ta ce tana dariya, ita ma dariyar ta yi shiru ya ɗan biyo baya. "Ga ruwa" Ta ce lokacin da ta ɗakko mata pure water ta mika mata, karɓa ta yi tana fasawa ta sha kaɗan ta ajiye. "Ni yanzu na matsu in gama idda ko na fara famtamawa na zaɓa na darje" Ta ce tana kallon BASEERA. Murmushi mg ciwo BASEERA ta yi tana kallonta da tausayawa ta san SALIMAH ta yi rashin miji mai kaunarta da gaskiya kauna wacce babu algus duk da bata mata fatan wani abun a nan gama amma dai ta san ba za ta taɓa samun kamar ABBAS ba sai dai wani lulluɓi mai cike da duhu ya mata shamaki da ganin hakan, duniyar ce w gabanta tana mamakin ma yadda ita ko mutuwa ba ta wani damuwa da tunaninta ko a cikin zance da wuya ki ji ta sako mutuwa. "Zaɓa da darjewa ai ba shi ne nagartar ba, wani zaɓin ba ka gane zaɓen tumun dare ka yi sai in ka je cikin gidan auren" "Ban gane ba mai kike so ki ce mini?" "Hmmm! SALIMAH kenan, shi fa samun nagartaccen miji dace ne kin san shi namiji ba kamar kwarya bane da za ki ce sai kin kwankwasa kin gane shi, kuma baka gane waye mutum har sai ka zauna da shi ko da kuwa cikin kawaye ne zama ne yake sa ka fahimci halayyar mutum idan zama ya yi zama, kin san hangen dala ba shiga birni ne ba bari na yi shiru kar na cika ki da surutu tun da kin ce ni wa'azi da nasihata sun yi yawa" "A'a ni fa a kan ABBAS ne bana son ki dame ni amma in dai a kan zawarawa ne idan akwai hanyoyin da zan gane wa zan aura ki fahimtar da ni duk da ni ban damu da kasancewar mutum na kirki ba bukatata in samu inda zan huta in ci uban naira har ta yi kukan dole" "To ai tun da tunanin da burinki ya sha bamban ba sai na mata lokacina ba, in dai mai kuɗi ne ai ana iya gane shi a kallon farko dama nagarta ce nake magana ke kuma ba ita bace a tsarinki, kenan ke ko buri da fatan ki zaɓawa yaranki uba nagari bakya yi sai mai kuɗi kawai?" Sosai SALIMAH ta kyalkyale da dariya, hae tana rike ciki, mamaki BASEERA take yi don a cikin maganganunta ba ta ga wanda ta yi da har zai bada dariya kamar yadda ta ga tana yi ba. Kallonta take har sai da ta tsagaita sannan ta ce "Wai don Allah BASEERA sai yaushe za ki waye? Har yanzu idan kika yi wani furucin sai in ji tamkar a cikin tukunyar yake, baki san yanzu ka ya waye ba an samu cigaba ta ɓangarori da dama, shin an faɗa miki a banza nake son na yi aure a daula?" Ta yi maganar tana kafe ta da ido alamar tambaya. "Sai kin faɗa na ji ai ba zan sani ba tun da ina cikin duhun kai da rashin wayewa kaina yana rufe a tukunya" Ta ce cike da gatse, amma da yake ita SALIMAH dukan iska ce bata gane magana BASEERA ta faɗa mata ba. Murmusawa ta yi ta ɗaga hannunta ta ɗora a kafaɗar BASEERA ta ce "Yanzu da jike gani duniya ta lalace, idan kana da kuɗi kai ne mutumin kirki a idanun mutane ko da kuwa ka fi kowa rashin mutunci da halayen kyama, yanzu ba a duba wani hali kake da shi illa iyaka ana duba mai kake da shi mai ka tara? In har kana da kuɗi a gidanku kai ne babba ko da kuwa kai ne autan gidan, in kana da kuɗi ko shawara sai an jira ka zo za a yanke idan kuwa ka ce ga yadda za a yi babu mai canjawa. In aure ka je nema ko da an san duka kake wa matarka ta gidan ko kuma kana wulakantata to fa ba za a ga wannan ba ko wani ya yi yunkurin faɗar aibinka to cewa za a yi bakin ciki yake, yanzu akwai kawayenmu wanda muka taso tare tun da suka yi aure a gidan daula shikenan ko a hanya muka haɗu kallon arziki ba ma samu, a takaice ko biki kika je ko suna kina dosowa kafin ki karaso zugar matan da suke wurin za su shiga karewa suturarki kallo tun daga tsakiyar kan ki har yatsan kafarki sai an kalla daga nan za a gane wacece ke idan aka ga kin gaza ta ko ina kina karasowa idan akwai wanda kika sani za su ɗauke kai, idan kuwa sutura kika saka ta kece raini kina zuwa za a washe baki kowa yana kokarin miki magana wannan ne manyan dalilan da suke ci mini tuwo a kwarya, su ne suke sa burina yake karuwa ina so in ci mai kyau in kwanta mai kyau ni soyayya baya dame ni ba ko kasancewar miji na gari, kuma ƴaƴa ma idan suka taso suka ga talaka ka zaɓa musu sai suke ganin abubuwan more rayuwa wajen wasu amma in ka zaɓa musu attajiri ɗif za ki ji kowa yana ji da su a dangi" Tun da ta fara dogon jawabin nan kallonta kawai take tana tunanin sabo da wannan ne ta kira ta kanta yana tukunya tabbas idan haka ne kuwa ta kama RUƁAƁƁIYAR IGIYA. "Duk wannan ba gaskiya banr idan kuwa gaskiya ne ya keɓantu ga wanda suke da gajeran tunani da rashin tauhidi, ai zama na gari ya fi komai a rayuwa, kuɗi suna karewa talauci ya baibaye mai su sai ki ga ya zama tamkar ba shi ne mai kuɗin nan ba da yake ta facaka, shi ma talaka arziki yana zuwar masa sai ki ga Allah ya azurtashi tamar bai taɓa neman taro da kwabo ya rasa ba, ƴaƴa kuma uba na gari da shi ake ado, idan har dukiya gare shi yana da hali marar kyau wata rana sai an goranta musu wata rana sai sun tuhumi mahaifiyarsu da maganar ko tambayar da za ta nemi amsar basu ta rasa" "Ba za ji gane ba, shi ya sa na ce a duhu kike". "Ko kuma ke ce a duhun ba". "Ni a haske nake kuma ni idan na tashi sai na auri mai dukiyar da koginta ba zai taɓa kafewa ba kin ga na yi ban kwana da talauci, ke ni fa saboda ba na son haihuwa gidan talauci ka taso babu ta baibayeka kai da yaran da uban ko asibiti za a kai yaro ana cewa ku je asibitin sai ki kawo katin idan na yi buga-buga na samo sai a saya maganin, in kin tambaya kuɗin cefane a ce babu a duniya na tsani kalmar babu nama kuwa daga sallar layya sai wata layyar ina dalili" "Allah shirye ki ya ganar da ke". "Ai kuwa ba zan gane ba, ke dai ce nake so ki gane bari sai na yi aure zan kara fahimtar da ke, shi ya sa na saka inplan a gidan ABBAS kar na haihuwa abubuwa su caɓe mutumin da ko gidan kansa ba shi da shi, sai aikin kafinta ni karatun da ya yi ma ban ga amfaninsa ba wai mai digiri amma ya ajiye takardu saboda ba aiki yana fama da kusa da katako" Ta ce tana yatsina fuska da taɓe baki. "Allah zai bashi" Ta ce cike da takaici don ba za ta iya cigaba da tattaunawa da SALIMAH ba saboda ta yi nisa ba ta jin kira in ban da toshewar basira har ta saka inpan lallai abin mai girma ne ba karamin gaba take yi da talauci ba tana mantawa Allah ne yake azurtawa kuma shi yake talautawa. Bata wani kara jimawa ba ta mata sallama za ta tafi saboda takaici, har kofar gida ta rako ta suka yi sallama ta tafi tana shirin shiga gida sai ga RUKY tare suka shiga gidan suna tattaunawa. "Wallahi RUKU har alla-alla nake na kammala iddar nan ko na fara tara zawara wa in ke kashe kala, don ni da na samu mai kumbar susa ba zan tsaya kallon ruwa kwaɗo ya mini kafa ba" "To ai ba a nan gizo yake sakar ba SALIMAH, zuwan zawarawa ba shi ne auren ba, bare ke da kike da kyau da kirar nan ai sai an miki layi sai dai... "Kamar ya? Dama ai na san abu mai kyau shi yake siyar da kansa a kasuwa, amma sai dai mai?" SALIMAH ta yi saurin katse mata magana. "Abin da nake so ki sani na gari sun yi karanci, yanzu za ki ga tarin zawarawa amma ba da aure suke zuwa ba" "Da mai suke zuwa to?" "Don a yi soyayya kawai" "To ba amfanin soyayya aure ba". "Hmmm! A baya kenan amma a wannan zamani akalar ta canja, kalilan ne masu zuwa da auren kuma wahala suke, daga namiji ya zo rimi-rimi sai ki ji ya fito fili ya faɗa miki holewa ce ta kawo shi, ku kunya ma ba sa ji ke wani fa sai ki ji ya kama miki hannu ba da izininki ba in kika masa magana zai ce ai ba komai bane, saboda yanzu zina ma ba ɗauke ta a bakin komai ba ado aka ɗauke ta duniya ta lalace kuma ta zo karshe" .."Ikon Allah, to amma sun san matan da suke wa ko?" "Kamar ya ai abin ya zama ruwam dare gama duniya, sai ko ga babban mutum yana baza babbar riga a girme zai haife ki amma ya zo miki da magana ta banza" "Sai ka zaɓi wanda basu da irin halayyar nan, kin san a duniya na tsani zina na tsani mai yinta ko abin da zai kusanta ni da ita" ."To kuwa ki shirya saboda haɗuwa ɗaya biyu za ki ji ya anbata miki so yake ku keɓe, ko ya ce yana so ku je hotel ku huta". . "Haba dai wasa ma ai wargi yake ai bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane" . "SALIMAH duniyar nan fa da kika sani shekaru biyar baya kafin ki yi aure ba ita ba ce a halin yanzu, duniya ta lalace wallahi, yadda bakya zato yanzu tsawon shekara uku da aurena ya mutu ina gida amma har yau na kasa samun tsayayye, kowa ya zo ba da maganar aure zai zo ba, yanzu ƴanmata ma gasu nan duk suna zaune a gida amma miji ya kasa samuwa bare bazawara, na bari SANUSI tsohon mijina ya suɓuce mini yanzu na zo ina da na sani da son komawa gidansa amma shi kuma yanzu ba ta ni yake ba ya samu wata ya aura" "Kowa da farin jininsa bari ki ga in yi idda zan baki mamaki" "Hmmm! Kin kasa fahimtata ina nuna miki maza za suke miki tururuwa amma ba da aure ba ko maganar aure kika yi wa mutum sai ya janye kafarsa, idan suna zuwar miki da hulewa kika nuna ke ba haka ba da kaɗan-kaɗan za su dare su barki" "Ki zuba ido kawai BASEERA kin san dai irin tarin farin jinin da na yi ina budurwa yanzu sai na kere" Ta ce tana wani murmushi. ."Wallahi da za ki ji shawarata da baki bari kin yi idda ba tun kina da sauran dama ki koma ɗakin ki, ba za ki gane mai nake nufi ba sai kin fara zawarcin" "Allah mini tsari kuma za mu ɓata idan kina mini maganar komawa gidan ABBAS" Ta ce tana jan wani tsaki. "Shikena SALIMAH tun da haka kika ce amma akwai ranar da za ki tuna da wannan tattaunawar" "Wai ya maganar Alhaji ma'ilu naki?" Ta jefa mata maganar don son kawai da wancan maganar. Shiru BASEERA ta yi tana tuno yadda suka rabu jiya baran-baran saboda kawai suna hira a mota sai ji ta yi ya rungume ta dakyar ta kwaci kanta, bayan shi kaɗai ne take ganin ta samu mai tsoron Allah ashe dai shi ma lumbu-lumbu ne wutar kaikayi, wannan dalilin ne ya sa ta zo don ta bayyanawa SALIMAH cewa ta rasa wanda za ta zaɓa ta aura amma ta ki fahimta ita yanzu damuwarta ta samu wanda zai aure ta amma abu ya gagara. Ga shi ita mace sai ta jira an ce ana son ta ba wai ita ce za ta je ta zaɓa ba ta ce tana so. Ita gabaɗaya sai yanzu ta gane aure ba karamar sutura ba ce ga mace sai yanzu da ta fito don takaici sai a mayar da mace kamar karya kowa ma sai ya zo ya ce yana sonta, kare da doki wani ma sa'an kanenka ne za a ce yana sallama da kai kana fita ka ga yaro a tsaye wai sonka yake tabbas akwai takaici da kalubale a rayuwar zawarci. "Ko bai zo ba jiyan na ga muna nan a tare ya kira ki yana zuwa" "Ya zo amma na sallame shi" "Ke ko saboda mai bayan kin tsayar da shi" "Saboda shi ma kamar sauran yake abin da yake kawo sauran shi ma shi ne ya kawo shi, kwantan ɓauna ya yi shi ya sa bai fahimta ba, duk na sallami kowa na rike shi ashe dai RUƁAƁƁIYAR IGIYA na kama" "Ikon Allah to Allah kawo miki wani" Shiru ta yi bata ce komai ba. "Ba za ki amsa da amin ba" "Wallahi SALIMAH na rasa wane kalar tunani zan yi, a zatona idan na yi idda ba zan wuce wata biyu ban yi aure ba, amma kin ga har shekara uku na rasa mai aurena kullum jiya i yau, ga yarana ba bar su gidan ubansu kullum idan suka zo wurina sai na zubar da hawaye saboda sun yi baki sun rame ko kaɗan ba sa cikin farin ciki ko walwala matar ubansu ta sako su a gaba basu da ƴanci uban nasu ma bai damu da su ba. Kin san mata nu ne natsalar kan mu da kan mu, idan kika samu yara gidan ubansu don kin aure shi maimakon ki rike su da amana amma sai ki ɗau tsana ki ɗora musu kike kishi da su kina gana musu azaba na yi da na sanin fitowa daga gidan aurena ga shi na yi saki na dafe a kan karamin abu na kasa hakuri har sai da na ga na kashe auren yanzu abin yana damuna na yarda duk wanda bai godewa ni'imar Allah ba zai godewa azabarsa, yanzu ina so in koma in rike yarana amma bani da wannan damar" Ajiyar zuciya SALIMAH ta sauke jin abubuwan da RUKY ta zayyano mata, duk da bata wani ji maganar ta shige ta ba amma dai ta ji babu daɗi amma tunaninta ya bata cewa RUKY don ba ta kai ta kyau da diri bane ta kasa samun tsayayye amma ita tana ganin babu mai kawo mata wargi a nata zawarcin. 09013181851 [1/5, 8:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 8 *ABBAS* Ya sha yaki da zuciyarsa kafin ya samu zafin so da na rabuwa da SALIMAH ya sassautu a zuciyarsa haka ya danne ya hakura ba don ya so ba sai don haka Allah ya tsara masa kaddararsa kuma bai isa ya guje mata ba. Sai da Mama ta dage da addu'a da nasiha sannan ta samu ya dawo hayyacinsa, addu'a sallar dare da karatun qur'ani wanda ya kasance magani kuma waraka ga dukkan komai, a hankali nutsuwa ta saukar masa a ruhinsa har ma ya ji son na SALIMAH ya kwanta masa a zuciya tun da yanzu sai ya wuni ma bai fi ta faɗo masa sau ɗaya a zuciya ba kuma ko da ta faɗo masa yana kokarin kawar da tunaninta a zuciyarsa, da kuma nesanta kansa da yake sa zaman kaɗaici domin zaman kaɗaici yana sa mutum yake tafiya tunani. Gabaɗaya kayansa na gidan ya kwashe su ya kaura gidan Mama, dama yanzu kuɗin hayar ma ya kare, ganin ya dawo daidai sai ya ɗaura ɗamarar komawa bakin aikinsa, tare da kudurtar zai yi aiki tukuru tun da yanzu babu wani mai ɗaga masa hankali ba kamar a baya ba idan zai tafi aiki ta ɗaga masa hankali haka idan ya dawo yana wurin aikin zuciyarsa bata huta ba. Sai dai kash! Duk buri da kudurin da ya ci na yin aiki sai da ya je wurin ya tarar da abin da ya karya masa zuciya, wato kayan gadon da SALIMAH ta je wurin ta siyar, da kujerun ko kallon wurin ya yi sai ya ji wani rauni a zuciyarsa, musamman idan ya kalli kujerun sai take masa gizo yana hangota zaune a kan kujera kamar yadda yake samun ta idan ya shigo gida. Ko mudubin ya kalla hangota yake tsaye tana gyaran gashi kasancewarta ma'abociyar gyara gashinta. Da farko ya yanke shawarar canja sana'a sai da FAROUQ ya hau kansa da faɗan yana nuna masa ita tana can ta manta da shi amma shi yana nan yana wani maganar fasa sana'arsa saboda kawai ya ga kayan ɗakinta, ita kuwa dama SALIMAH da gayya ta yi hakan saboda tsabar rashin tausayi. Irin furucin da FAROUQ ya yi ta amfani da su hakan ya saka ya dake zuciyarsa sai ya zo wurin ya tafi ma amma bai ko kalli kayan ba har aka zo gaɓar da ko ya kalli kayan ba ya jin komai, har dai Allah ya kawo wanda suka siye kayan ma ko a jikinsa ma lokacin don yanzu kam ya fara aniya da ɗamarar haka rami ya binne duk wani son SALIMAH da yake addabar zuciyarsa. Aiki yake tukuru a rana sai ya yi aikin dubu goma kasancewar yanzu ba shi da wata damuwa sai wacce ba a rasa ba, saɓanin da idan ya zo hankakinsa yana gida idan ta kira ta a waya ba za ta ɗaga ba idan ya dawo gidan ma babu kwanciyar hankali wannan dalilin ya sa yanzu ya kara gane cewa ka samu mace ta gari mai sonka wacce za ta faranta maka shi ne samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. *HAWWA* Kwana biyu a tsakani da faruwar abin na ganin kwalabe giya a ɗakin Yaya Umar sai ga shi ya shigo gida da gabannin magrina a buge ya sha giya ya yi tatul. Sosai Hajiya ta shiga tashin hankali tana kuka wiwi kamar matar marigayi. "Na shiga uku yanzu Umar abin naka har ya kai ga shan giya? Ni duk tunanina ɗan kodin nw kawai kake afawa ashe har da giya da kwaya wannan wace irin rayuwa ka sa kan ka?" Ta ce tana rusa kuka ganin ya kwanta male-male a tsakiyar falon yana ta wani surutai cikin muryar bugaggu ga kuma kwaya nan da tje jimke a hannunsa. "Ke ma in za ki sha kwayar ai sai ki karɓa ni ba hana ki zan yi ba, akwai ma giyar a ɗakina a kasan gado sai ki ɗakko ko da kwalba goma kike so" Ya ce cikin muryar maye yana mika mata kwayar. Jin furucinsa na cewa akwai kwaya a gidan sai hankalinta ya kara tashi, ko ta kan kwayar da yake miko mata bata bi ba ta yi hanyar ɗakinsa a kiɗime cikin tashin hankali tana zuwa ta ga ɗakin a rufe a 360 ta dawo duk ta fita hayyacinta wannan ahi ake kira tashin hankali wanda ba a saka nasa rana da lokaci. Cikin kukan ta da ta kasa rikewa ta kama wandon Umar ɗin ta saka hannunta a aljihinsa za ta ɗakko mukullin ɗakin nasa. "Wai waye yake saka mini hannu a aljihu zai mini sata, to wallahi zan sa kulawa(Ƴan sanda) Su kama mutum" Ya ce yana mika hannu ya dafe hannun Hajiya da yake aljihu za ta ɗakko mukulli. "Ubanka ne, na ce ubanka ne, sakaran banza da baka san inda yake maka ciwo ba" Ta ce lokacin da ta saka ɗaya hannunta ta ɗaka masa duka a hannun da ya danne hannunta da yake cikin aljihu. Yana ɗauke hannun ta zaro mukullin da kuma wasu kula-kulai da wani abu da ta kasa gane mene ne, sai dai mai, tana fitowa da hannun ta ga mugun abin da ya kusa tarwatsa zuciyarta, condom ne da kuma sarkarta da ɗan kunne na gwal da suka he dubai ta siyo wacce ko sakawa bata yi ba. Hannu ta ɗora a kanta ta shiga runtuma ihu tana ambaton ta shiga uku. Zaman dirshan ɗin da ta yi a wajen tana rasgar kuka tamkar an mata mutuwa, cikin kukan ta tafi da rarrafe ta ɗauki wayarta da take kan kujera da dokawa Alhaji kira, sai dai har ta tsinke bai ɗaga ba, kiransa ta yi a karo na biyu ringing ɗaya biyu ya ɗaga, kuka kawai take ta kasa cewa komai, Alhaji jin kukanta ya shiga tashin hankali don ya ɗauka ma mutuwa aka yi. Ganin ta ki cewa komai sai ya kashe wayar yna yi wa direbansa umarni a kan ya yi sauri akwai matsala a gida, abokin sa da suke tare a bayan motar ya shiga tambayarsa amma sai ya ce shi ma bai san mene ne ba. A kiɗime suka shigo gidan Baban a gaba abokinsa yana biye da shi suna sauri tamkar su kifa, tun da suka doso gidan suke jiyo ihun kukanta, falon suka nufa suna zuwa suka ganta zaune dirshan tana kuka. Baba rasa bakin magana ya yi don ahi tsabar tashin hankali da rikicewa ko lura bai yi da Umar da yake yashe a falon ba amma shi abokin Baban ya gan shi. "Yawwa kulawa kun iso ku mini ram da wannan ɓarauniyar ta sace mini makudan daloli a aljihu" Maganar Umar ce ta ankarar da Baba. "Hajiya wai mene ne kike kuka kika tada mini hankali?". . ."Yanzu Alhaji baka ga abin da ya saka ni kuka ba?" ."Ina yake?" Ya tambaya cikin rashin fahimta. "Wai har tambaya ma kake? Kana ganin Umar a buge" Wani dogon tsaki ya ja kafin ya ce .."Wai a kan wannan ne kike kukan in ce dai kin daɗe da sanin yana shaye-shaye to mai zai ɗaga miki hankali ne har kika ɗaga mini nawa hankakin" "Giya ce fa ya sha" "Giya???" Ya tambaya hankali tashe yana rarraba ido. "Giya ya sha, kuma ya ce akwai ta a ɗakinsa ko kwalba nawa ake so akwai a kasan gado, zan je in ɗakko na ga ɗakin a rufe shi ne na dawo zan ɗauki mukulli a aljihunsa, ina saka hannu na samu sarka da ɗankunne na wanda na siyo a dubai kimanin miliyan uku ya ɗauka, yanzu Umar mashayin giya kuma ɓarawo " Ta ce tana rushewa da kuka. Gabaɗaya gumi ya jika Alhaji. "Kai kuna tsaye gaban manya kowa ya kama kunnensa dole a ladabtar da ku... Kafin Umar ɗin ya kai karshe maganar Baba ya karasa gabansa ya ɗaga hannu ya wanke shi da mari, da sauri abokinsa Alhaji Khamis ya rike shi yana ba shi baki. Sosai hankalin iyayan ya tashi amma sun manta cewa su ne suka bar kashi tun ran kwasa, domin tun ran gini ran zane. Sun sangarta ƴaƴa babu kwaɓa babu tsawatarwa komai suka yi daidai ne da wayewa sai yanzu da abubuwa suka caɓe ne suka gane wautar da suka yi. Karasawa ya yi ya zauna a kujera yana ta faman huci basu san ta ina za su fara ba don lokaci ya kure musu ita tarbiya tana farawa ne daga gida duk abin da yaro ya yi ka tsawatarsa masa, ka nusar da shi itace tun yana ɗanye ake tankwara shi idan ya bushe a tarki lankwasawa karyewa zai yi. Duk abin da ya zo ya yi da farko ka yi shiru to nan gaba ma zai kara yi da kaɗan da kaɗan sai abu yake yin gaba kafin ka ankara sai ka ga abu ya girmama ta yadda lokacin gyarawa zai gagare ka. Addu'a ita ce babban makami wajen tarbiyantar da yara, sannan kuma saka idanu a lamuransu tun suna kankana, ku lura su waye abokan su kuma su waye kawayensu nusar da su zama a class kusa da yara masu jin magana a aji ba masu wasa da rashin kulawa da karatu ba, waɗanda ko a islamiya suke bayar da harda. Umar kuwa zaune ya tashi yana ta kelaya aman giya a falon Hajiya kuwa tana sharɓar kuka ta tafi ɗakin nasa tana buɗewa a kiɗime ta karasa kasan gadon gabanta yana tsananta bugu tana tsoran abin da za ta gani. Tana lekawa kuwa ta yi ido biyu da kwalaben giya tamkar dai shagon siyar da giyar zai buɗe saboda yawansu wasu sun kwalaben ne babu giya wasu kuwa giyar ce a ciki. Sosai ta yi mamakin yadda giya mai yawan wannan take zaune a gidanta amma bata sani ba ta fara tunanin sakacinta ne ya haifar da hakan da a ce tana saka ido a al'amuransa to ko bai daina duka ba zai rage amma ta bar shi sakakaka tamkar dabbobin da aka yi asakon su. Tana kuka tana fito da kwalaben sai da ta fitar duka sannan ta ɗakko guda biyu ta nufo falon lokacin Alhaji Khamis ya ba Baba baki ya zauna sai dai ganin Umar ba karamin bakij ciki da takaici ba yake kara masa. Haka ta karaso tsakiyar falon idanun nan nata jawur tamkar ta kwana tana kukan. "Kika ishi mutane da cewa ana shan giya ashe kema kina sha" Umar ya ce yana ɗaga idanu yana kallon Hajiya da take ji tamkar ta hau shi da duka. "Wai da gaske akwai a ɗakin kenan?" Baba ya ce yana tashi tsaye yana kallon kwalaben da mamaki. "Sun fi kwalba talatin" Ta ce cike da takaici. "Bani in yi kurɓa ɗaya" Umar ya ce don har lokacin a buge yake, a kufule Hajiya ta karasa ya wanka masa mari wanda ya sa sai da ya tuntura daga zaunen da yake. "Kara masa shege tsinanne... "A'uzubillahi haba Alhaji Bukhari ya haka, da bakin ka kake tsinewa ɗanka? Shin baka san baki shi yake kara kangarar da yaro ba? Akwai lokutan karɓar addu'a idan mutum ya yi tana karɓuwa ko lokacin da mala'iku za su ce amin. Shi ya sa ake son iyaye su rika saka linzami a harshensu suke yin furucin mai daɗi ga yaransu ko da kuwa yaran sun ɓata musu rai su yi kokarin danne zuciyarsu su faɗi kalma mai daɗi, ko da karamin yaro ne idan ya yi laifi kar ka ce masa shege ɗan iska, ko munafuki da sauransu, ka yi kokarin cewa Allah maka albarka Allah sa wannan abin da kake yarinta ce, amma furuci mai muni shi yake kara kangarar da yaro maimakon al'amura suke baya sai suke yin gaba bayan kuma duk halin da suka shiga mu ne dai a ciki" Alhaji Khamis ya katsewa Alhaji Bukhari maganar. Dantse bakinsa ya yi yana jin yadda zuciyarsa take zafi so yake ya furzar da maganar ko ya ji sassauci amma kuma an taka masa birki da mummunan furuci. Wani ashar Hajiya ta yi wa Umar mai maiko... "Hajiya Rayyanatu ana ga yaki kina ga kura, ana hana wani maganar ke kina yi" "Wallahi Alhaji Khamis yaron ne sai da haka kullum daga an hana shi sata sai ya koma sane" "Kin ji fa, wai a nan fa kina nufin daga kin hana shi wannam sai ya koma wancan amma maimakon ki faɗi hakan sai kika ce daga an hana shi sata sai ya koma sane, shin sata abu ne mai kyau? Ko sane yana da kyau? Amma kina danganta ɗanki da shi ko zagi da iyaye suke yi wa yaransu tun suna kanana ba tarbiya ba ce saboda yara suna harda a kwakwalwarsu, sai kun ki yaro ya yi zagi sai ku kama shi ku duka kuna ikirarin ba kun hana shi yin zagi ba bayan kuma ku kuna yi kenan idan ba abu bane mai kyau mai ya sa kuke yi? In dai ana bada tarbiya sai an kiyaye da wasu abubuwan sosai saboda yara sun fi ɗaukan abin da ake yi a aikace fiye da wanda ake koya musu" Ya ce yana kallonta daga ita har Alhaji sai suka yi ɗif domin su basu san duk wannan abubuwam da yake faɗa ba saboda su dama ba wani damuwa suka yi da tarbiyar ba. "Ai komai ya zo karshe a gobe zan ɗaura maka aure domin ka sani ma, babu fashi ko ka san annabi ya faku ba, idan ka ga kana da iyali ka hankalta" Baba ya ce yana nuna shi da yatsa. "Kuma wannan shawara ce mai kyau aure yana sa nutsuwa da hankalta musamman in aka yi dace da yarinyar kwarai, sai dai ba a nan gizo yake sakar ba, shin a ina za ka samu matar? Ka san dai abokin kura guza kuma na san kalar zaren kalar yadin, ma'ana ba za a samu wata mace budurwarsa mai nagarta ba don babu nutsatstsiyar da za ta kula shi, kuma in ba ta kirki ba ce maimakon ya shiryu sai dani ya kara shiga dawa wato lamura su kara taɓarɓarewa" Cewar Alhaji Khamis. "Akwai matar da yake so kuma nutsatstsiya ce" Alhaji Bukhari ya faɗa. "Ikon Allah!" Ya ce da mamaki don ya san dai wace ce za ta yarfa da haka, kafin ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula na kankanin lokaci sai ji ya yi Alhaji ya ɗaga waya yana ta kiran mutane yana cewa akwai ɗaurin auren ɗansa da za a yi gobe karfe goma sha ɗaya na safe, haka ya ringa kiran jama'a yana gamawa ya shiga kwalawa Hawwa kira. "Hauwa'u! Hauwa'u!! Hauwa'u!!!" HAWWA da take ɗakin tana ɗinke wa SABEER rigar islamiyarsa da ta yage da zare da allura ta daɗe tana ta yi kasancewar bata iya ba, ita hatta keken ɗinki ma bata taɓa ganin yadda ake ɗinki da shi ba sai dai in an ɗinko musu kaya ta saka kawai wata rana ma in ɗinkin bai yi mata ba ta ce Ummie ta bayar da kayan saboda gata da suke da shi amma sai ga shi yanzu rayuwa ta juya musu maraici ya sa har tana iya ɗinki da allura da zare, ga kayan duk sun tsufa sun koɗe ko ɗan aikin gidansu ba zai saka kayan da suka yi mugun tsufa haka ba, amma sai ga shi abin da suka fi karfinsa ya fi karfinsu dama yawanci gata na iyaye ne daga ranar da ka rasa su a duniya daga lokacin za ka fahimci girma da darajarsu babu wanda zai gane hakan sai maraya wanda ya rasa uwa ko uba ko ma ya rasa su gabaɗaya. Ko da za ka samu dukkanin gata a bayan ransu to ganinsu kaɗai ma rahma ne, daga lokacin da mutuwa ta yi yankan kauna a tsakaninku za ka gane girma da ɗacin maraici!. Yar aikin da ta shigo ɗakin da sauri take faɗa mata ta jiyo Baba yana kwala mata kira, da sauri ta yi jifa da riga da zare da allurar hannunta, don ta san yanzu za a ce ta yi laifi a hukunta ta ita kuma bata ji ba saboda hankalinta yana a kan SABEER suna hira suna ta kyalkyalar dariya saboda su biyu ne farin cikin junansu. Fitowa ta yi da sauri ta nufi sashen Baban ta shiga da sallama, tana shiga ta samu gefe a kasan tiles ta durkusa gwiyoyinta a kasa cikin ladabi ta ce. "Ga ni Baba" "Gobr da karfe sha ɗaya za a ɗaura auranku da Umar.... Idanu ta ɗago tana kallonsa gabanta yana bugawa da karfi, hatta jin ta sai da ya ɗauke na wasu sakkani don kunnen nan nata dummm ya yi. "Alhaji ƴar aiki za ka aurawa Umar?" Alhaji Khamis ya tambaya yana kallon HAWWA wacce kayan jikinta suka tsufa hatta hijabin jikinta wuyan ya yi yawa ga shi daga gefe da yaga yadda daga gani dutsin guga ne ya kona. HAWWA jin an ce mata ƴar aiki sai da idanunta suka kawo ruwa duk da bata da bambanci da ƴan aikin, hatta kayan jikinta har gwara na wasu ƴan aikin, ita mutumin ma kallon sani take yi wa fuskarsa. "Ƴar gidan Yaya ce marigayi" "Wai HAWWA ce wannan?" Ya tambaya da mamaki. "Ita ce" Hajiya ta ce, shi kuwa Umar lokacin ma bacci ya ɗauke shi yana yashe a tsakiyar falon don tun mangyarin da Hajiya ta masa sai ya kwanta duk kafafunsa a cikin aman da ya yi. "Amma Alhaji Bukhari baka kyauta ba, yanzu ƴar zumun naka ce ka bari haka a wulakance? Yanzu da shi ne zai bar tsatsonka su wulakanta idan baka raye?" Ya tambaya cike da mamaki "Dakata! Alhaji Khamis kar ka ɗora mini jakar tsaba kaji su bini, kar ku ka sa duniya ta zage ni ya zan ɗakko yaran su biyu in rike su cin su shan su sutura da karatunsu duk in ɗauki nauyi amma kake mini wata magana a karshe don in kara dankon zumunci ma ɗauki ɗana sukutum zan aura mata" Murmushin takaici ya yi mai ciwo kafin ya ce "A ina rufin asirin yake? Wannan ne gata, kalli suturar da take jikin yarinyar nan kamar wata almajira yanayin jikinta da na nutsuwarta bai yi kama da na wanda yake cikin farin ciki ba sannan maganar aura mata Umar kuma ai ita za a zalunta tun da duk wanda yake da dogon tunani ba zai ɗauki ƴa mai kamala da hankali kamar HAWWA ya aurawa mashayin giya ba d... "Ya isa haka Alhaji Khamis! Wasa ya yi wasa ban da tsinkarin uwar miji, idan magana za ka faɗawa mutane da tada tarzoma haɗe da tada zaune tsaye to mun gode ka je umma ta gaishe da aisha" Hajiya Rayyanatu ta ce rai a matukar ɓace. "Na ji kuma zan fita muku a gida amma ina so ku sani zalunci ba abu ne mai kyau ba, kuma cin dukiyar maraya haramun ne domin Allah maɗaukaki ya faɗa a littafinsa mai tsarki cewa, kada ku ci dukiyar maraya da zalunci, a wani wajen kuma ya ce hakika masu cin dukiyar maraya da zalunci ba komai suke ci ba a cikin su, illa wuta, kuma za su shiga cikin wutar sa'ira. Domin na sam tabbas kun hau dukiyar marayu kun yi kaka gida, saboda dukiyar da mahaifansu suka bari basu ba hatta ƴaƴa da jikokinsu sai sun mora, amma tun ba a je ko ina ba tun ana shekara biyu da mutuwarsu ga shi nan suturar kirki ta gagari ƴaƴansu suna rayuwa kaskantacciya, yanzu da iyayansu za su dawo duniya mai za ku ce musu? Tabbas duniya ta zo karshe zumunci ya ki daɗi amana ta yi karanci amma a juriya zuwa tafi wata rana tulu zai fashe! Na bar ku lafiya" Ya ce yana juyawa ya fice. Daga Baban har Hajiyar ransu ne ya yi matukar ɓaci don kalamnsa basu shige su ba illa haushin sa da takaici. Haushi ne ya sa Hajiya Rayyanatu ɗaga kafa ta hamɓare Umar da ya yi shame-shame don asara yana sakin munshari. Jin an masa kafa ya tashi zaune a kiɗime yana rarraba idanu kamar shege a rabon gado. [1/5, 8:58 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 9 "Sai ka tashi malalacin banza gobe ɗaurin aurenka amma maganar auren kana yashe kamar kayan wanki" Ta ce tana harararsa ganin ya saki wata uwar hamma. "To a kai ni ɗakin amaryar tawa mana" Ya ce yana kallonta da lunsassun bugaggun idanunsa. "Hajiya ki kyale wannan ba a hayyacinsa yake ba, da yana cikin hankalinsa da yanzu yana cikin farin cikin murnar auren nan" "To Alhaji" "Yanzu dai ita wannan ki binciko mata kaya a cikin kayan Lawisa wanda za ta saka goben' "Wallahi ba za a ɗauko a kayanta ba wannan yarinyar da ta tsani a taɓa mata komai nata, kana gani yanzu kamar ita ce uwata ko raga mini bata yi ina faɗa tana faɗa" "To ki ɗakko mata marar ɗinkawa a kayanki sai a bada ɗinki" "Nawa ai sun fi karfin ajinta amma zan san yadda za a yi" "Don Allah Baba ka taimaka mini ni bana son a mini aure karatu nake so na yi" HAWWA ta ce tana hawaye. "Matsayinki na mai rangwamen gata wato marainiya, har kina da zaɓin kan ki? To ai karatun secondry ma sa kika yi ya ishe ki son ko yo zurfi a karatu shi mijinki da bai san ko bihim ba ki zo kina goranta masa to ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa" Cewar Baba. Sai da suka gama faɗar abin da za su faɗa suka ce ta tafi, dama ba shawarar ta ake nema ba umarni ne, haka ta tashi ta fito ta nufi ɗakin Baba Sadiya tana zuwa Baba da take linke kaya ta je ta faɗa jikinta tare da fashewa da kuka sosai Baba ta ji abin ya taɓa ta lallashinta ta shiga yi har sai da kukan ya tsagaita, sannan Babar ta shiga tambayarta dalilin kukan nata, nan ta shiga labarta mata abin da ya faru, sosai ta tausaya mata kuma take jinjina rashin imani da tausayi na mutanen gidan uwa uba rashin amana. "Baba ki bani wannan zoben da na baki ajiya" "Hauwa'u shi kaɗai fa ya rage miki mai ya za ki karɓa suna ganinsa a hannunki za su kwace" "Guduwa zan yi Baba, barin gidan nan zan yi ba zan zauna a rusa mini burina na karatun likita ba, burina na taimakawa al'umma mararsa lafiya, burin da tun ban san inda yake mini ciwo ba yake damfare a zuciyata" "Haba Hauwa'u ina za ki dosa a halin yanzu?" "Kaduna zan je Baba wurin yayan Ummiena da aka hana ya tafi da ni, kuma da kunnena na taɓa jin Hajiya tana waya tana cewa wurin malamai ta je aka masa mantau, wai ba zai kara tunowa da mu ba bare har ya zo neman mu, sai dai makarin abun shi ne idan ya yi ido huɗu da mu tun da ta san mu ba za su bari mu je gare shi ba" Ta ce cikin sanyin murya sosai Baba ta jimanta maganar tana kallon HAWWA sannan tana jinjina rashin imani na su Hajiya Rayyanatu. "Kar ki damu zan baki ko ni ba zan so ki auri wannan yaron ba da shi kansa bai san kansa ba, amma wani hanzari ba gudu ba ta yaya za ku bar gidan nan bayan gobe ne ɗaurin auren kar ki tafi da igiya a kan ki' "A daren yau za mu gudu Baba, ba zan bari igiyar aurensa ta ratayu a wuyana ba, ni dai ki taimaka mini Baba ki je kasuwa ki sayar mini da zoben ki bani kuɗin mu samu kuɗin mota " Shiri Baba Sadiya ta yi tana nazarin maganar tana son gano matsalar da za a iya samu idan aka aikata hakan ko aka san da saka hannunta a guduwar yaran sai dai irin halaccin da mahaifiyarsu ta mata da kirkin ta gare ta ba za ta bar ƴaƴanta su tozarta ba daidai gwargwado za ta yi iya yinta kuma ta shirya tunkarar kowane ƙalubale a kan hakan. "Don Allah Baba" Muryar HAWWA ta katse mata tunanin. "Hauwa'u dama zan je kasuwa siyayya da Hajiya ta aike ni sai na tafi da zoben na sayar miki na kawo miki kuɗin" Sosai HAWWA ta shiga mata godiya domin har ta hango sun bar gidan ta tsallake auren mashayi. Ɗakin nasu ta koma ta samu SABEER zaune ya jingina da bango yana gyangyaɗi a zaune ga rigar da take ɗinke ɓasa nan lokacin da aka kira ta a kan cinyarsa. Kai ta jijjiga cike da tausayin kansu da tausayin kaninta kasancewarsa karami wanda maraici ya masa dirar mikiya tabbas mutuwa tana da yankan kauna in ba haka ba mai zai raba uwa da ɗa ko kuma mai zai raba iyaye da ƴaƴa sai mutuwa, domin mutuwa ba ta duban girma ko kankantar wanda za ta raba da iyayan. A hankali ta samu wuri ta zauna a kusa da shi, tare da janyo shi ta ɗora shi a kan cinyarta, tana karewa fuskarsa kallo tana tuno yadda mahaifansu suke kaunarsu tare da lulawa duniyar tunanin ranar da ba za ta taɓa mantawa a rayuwarta ba, ranar da ya kasance rubutu a kan dutse wanda ba zai taɓa goguwa ba, ba rubutu a kan ruwa ba wanda zai gogu. A ranar wata juma'a da yamma, HAWWA ta ce tana son zuwa gidan kawarta ziyarar juma'a ai kuwa SABEER ya ce sai ya bi ta, sai da Ummie ta saka baki sannan ta yarda za su tafi tare, lokacin da za su fita Ummie tana cikin kicin tana girki, a hanyar fita suka haɗu da Abbie zai shigo gidan. "Sai ina kuma ƴaƴan Ummie?" Ya tambaye su yana murmushi mai nuna so da kaunar ƴaƴan nasa. "Abbie Aunty HAWWA ce za ta je gidan kawarta ziyara shi ne zan raka ta" SABEER ya ce yana rungume Abbie. "To kai da ba kawarka ba ya za a yi ka je?" Ya ce yana dariya saboda ya san yanzu HAWWA za ta ce wani abu. "Sai da na ce fa ba zai bini ba amma Ummie ta ce sai ya bini" Ta ce tana kumbura baki. "To ke da ɗan uwanki ai sai ku je dama ai na ga tare kuke uzurinku ko my HAWWA" Ya ce yana kama hannunta. "Ai ni ma yawo nake son zuwa tun da yau babu islamiya ga shi na saka babbar riga da hula" Ya ce yana yi wa HAWWA gwalo. Sai da ya lallaɓata sannan ya kama hannunsu ɗaya a hannunsa na dama ɗaya a hagu shi yana tsakiya, ya raka su har wurin mota suka zaɓi wacce za su fita suka shiga direba ya ja suna ɗagawa Abbie hannu yana ɗaga musu har aka fita da su daga get ɗin sannan ya juya ya nufi cikin gidan. Basu san mai ya faru ba sai dab da magriba direba ya zo a kiɗime ya ce su zo su tafi gida in ji Ummie sosai HAWWA ta yi mamaki don ta ce za ta kira shi a waya in sun gama amma kuma ga shi bata kira shi ba ya zo kuma ga shi duk ta gan shi a rikice, ko da ta tambaye shi dalilin rashin nutsuwarsa sai ya ce mata waya aka masa daga garinsu mahaifiyarsa ba lafiya. Ko da ya ɗakko su maimakon ya nufi gidansu sai ta ga ya nufi gidan kanin mahaifinta, da ta tambaye shi sai ya ce wai Ammie ce ta ce ya karɓo mata sako. Tun kan su karaso gidan ta hangi yadda jama'a suka yi dandazo a kofar gidan, sosai ta ji faɗuwar gaba ganin mutanen babu alama ta abin farin ciki ko abu mai daɗi ne ya tara su, sannan ta san dai da ɗaurin aure ne ko makamancinsa da za ta sani saboda shakuwar Abbie da ta kaninsa Baba ta wuce a ce an yi wani taro ko da kuwa na wani ne da ban ba tare da Abbie ya sani ba. Ta shiga tashin hankali da ta gane mutuwa aka yi tun da lokacin Baba da Hajiya Rayyanatu so da kauna marar algus suke nuna musu kamar su haɗiye su. Don bata taɓa kawowa cewa mahaifanta bane. Tashin hankalin da ta tarar na gawar mahaifan nasu ya haifar mata da suman da sai da ta kwanta asibiti, ganin su kwance babu kyan gani yadda tukunyar gas ta yi bindiga suka kone har da wasu daga cikin ma'aikatan gidan. Hannu ta saka ta sharenhawayen da suka gangaro mata tana jin tamkar yau abin ya faru. A ɓoye Baba ta kawo mata kuɗin zobe kulle.a bakar leda dubu ɗari biyu da hamsin da yake zoben da girmansa. Dubu ɗari ta ba Baba wanda dakyar ta karɓa shi ma saboda HAWWA ta nuna mata kuɗin ya musi yawa. Da za su kwanta Baba ta musu sallama saboda gudun kar ta fiya zama tare da su zargi zai shiga idan aka neme su aka rasa. Tana jin babu daɗi rabuwar da za su yi. Tsakiyar dare wajen karfe biyu HAWWA ta tashi ta ɗauki ruwan da ta ajiye a kofi ta zuba a hannunta ta shafawa SABEER a fuska yana warewa ta shiga raɗa masa cewa za su tafi saboda dama ta faɗa masa cewa za su gudu Kaduna gidan Baffa Nasiru. Yanzu murna yake don haka kuɗin ta saka a wata karamar jaka marar nauyi da Baba Sadiya ta bata ta ce ta saka, sai da ta goye shi a bayanta ta rataya jakar a wuyanta ta tsaya ta yi ta addu'a a kan Allah sa su fita ba tare da wani ya gan su ba. Dama tuni ta zari mukullin kofar da za ta sada ta da get ɗin gidan haka ta fito cikin sanɗa ta fara lallaɓawa har suka zo kofar gabanta yana ta faɗuwa ta saka mukullin ta buɗe a hankali ta fita ta ja kofar wurin mai gadi ta nufa da yake sharara bacci da munshari tana zuwa ta shiga dube-dube cikin ikon Allah sai ta ga mukullin a cikin hularsa ta ga mukullin ta lallaɓa ta ɗauka ta buɗe get ɗin suka fita cikin sanɗa ta ja musu get ɗin. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ganin sun kuɓuto daga gidan, sai dai inda gizo yake sakar tana fatan su samu mafaka kafin da asuba su nufi tashar motar. A wani kango suka samu mafaka inda suka yi addu'a suka shiga saboda gujewa abu mai cutarwa. A nan suka karasa kwanan da asubar tun gari bai yi haske ba suka fito wannan karon hannun SABEER ta kama suka kama hanyar tashar. Sai da suka kusa sannan suka samu napep kai su suka yi sallah ganin mota za ta tashi suka shiga motar ta tashi duka lokacin shida da rabi, sai da ta ga sun ɗaili hanya sannan ta sauke ajiyar zuciya tana rungume da SABEER wanda bacci ya yi awon gaba da shi kasancewar jiya basu samu wani bacci ba. *SALIMAH* Da tsananin murna da farin ciki wanda bashi da kwatankwaci ko misaltuwa da lokacin fa kwanakin iddarta suka cika, domin a wannan lokacin ne take ji ba ya ita domin ta samu cikakken ƴanci, ƴanci wanda take jin tamkar na wanda yake gidan yari ya samu fitowa daga ciki. A ganinta a yanzu ne take ganin tama da damar da za ta dama wacce ta daɗe tana jiran zuwanta a inda za ta ci karenta babu babbaka. Don tun da ya sayi kaya ta yi ɗinkuna na kece raini ɗinkuna na fita taro take jin kanta yana hayaki take jin kanta daidai da kowace shegiya da take jin ta samu dama. Kayan da suka janyo mata farin jini haɗe da kwarjini, kayayyakin da take shiga ta kece raini wacce ta kara fitowa da aji da mugun kyan da take da shi wanda a da take ganin talauci ya yi wa mutane shamaki da ganin kyan nawa kasancewar tana gidan ABBAS babu kayan da za ta yi tinkaho matsayinta na babbar yarinya amma yanzu tana ganin buri da mafarkin ta zai cika na zama matar manya. Tun da ta yi idda ta fara ba mazan da suka yi mata caaa suna son samun dama a wajenta kasancewar bata yi idda ba sai ta ɗan dakatar da su amma tana kammalawa sai ta shiga rangaɗa musu kira ta wayar salula da yake tana karɓar lambobinsu. Hakan ya sa lokaci kankani ta sha kwana kamar yadda ta yi tsammani. Manyan mutane ne masu hannu da shuni suka fara rububin aurenta wannan ne ya sa ta karyata maganar BASEERA, da kuma RUKY don yanzu dai ga maza nan kowa yana so ta bashi dama ya dama, kowa yana bayyana mata irin tsantsar son da yake mata tare da koɗa irin baiwar kyawun da Allah ya mata. Wannan ya sa kanta ya fashe take ta jin takaici da ta kare a gidan talauci bayan ga rayuwar da ta dace da ita duk da tana ganin lokaci bai kure mata ba. "RUKY kin ga abin da nake faɗa miki ko, zawarci ya danganta da irin kyau da aji da kuma iya kamun ludayin bazawarar yanzu dai idanunki sun gane miki dama bahaushe ya ce gani ya kori ji, kina gani har gajiya nake da amsa kiran maza a wayata kuma kaf cikinsu babu na jefarwa kowanne yana takama da dukiya yana kuma ji da kansa, kowanne yana nuna mini so da kauna da kulawa ga su wayayyun maza ba kamar wancan fakirin da na baro gidansa ba ga bakin talauci ga kansa kife a cikin kwarya ba ma tukunya ba" "SALIMAH ba za ki gane bane, ai fa haka suke fitowa a farkon zawarci ai kamar budurwa ce da za ki ga farkon fara budurcinta za ki ga maza gasu nan manema kamar me amma da kaɗan-kaɗan za su watse sai wanda yake da gaske da aure yake sonta shi ne zai tsaya. To zawarci ma haka yake farko ga mazan nan kamar jamfa a jos amma tafiya in ta yi tafiya za su zame su barka wani dama rage dare yake zuwa kuma ABBAS ai wayayyan mutum ne ke ce baki bashi damar nuna miki kulawa ba da kin ba shi da sai ya mayar da ke sarauniyar mata" "Hahahaha ni nawa ba irin na kowa bane, yadda nake mai kyan nan babu mai yarda na kufce masa, kuma ki daina kira mini sunan mutumin nan don muna iya yin uwar watsi da ke yanzu" Ta ce tana wani yatsina irin na wanda duniya ta ɗaga, ko kaɗan ba ta tunanin akwai ranar da duniya za ta nanata da kasa don ta ga yanzu tana murza kambunta yadda take so. "Allah baki hakuri kawata kin san ni ruwa ya karewa ɗan kada shi ya sa nake ganin kamar kowa ma haka ne" "Ban da kowar wake, ki bi sannu ki dangwali arziki ki bar shi nan, ni nawa zawarcin mai lasisi ne, kuma arzikin auren da zan yi sunansa kogi mai gudana wanda ruwansa ba ya taɓa kafewa" Ta ce tana saka hannu a jakarta pink wacce ta yi macin da leshin jikinta mai ratsin pink da takalmi da mayafinta. Dubu ashirin ta lissafa ta ba RUKY godiya ta mata tana ta mamakin yadda zawarawa suke wa SALIMAH ɓarin kuɗi tamkar basu san ciwonsa ba. "Kina lokaci!" "Faɗi ki kara RUKY ban rasa komai ba ga iphone 16 ga keypad hr biyu ga android nan kina dai ganin hannun Umma ita ma tana rike wayar dubu ɗari biyu da ashirin ai mu kam mun yi ban kwana da talauci" "Na ga Umma ita ma yanzu ba kowa take kulawa ba, ranar nan yarinya ƴar makotanmu ta je siyan koko da kosai da sassafe amma ta yi ta buga gidan ba a buɗe ba wai sai ma karan jannareto da take ji har safe ba a kashe ba" "RUKY kenan ai mu da sana'a sai dai mu ga ana yi, kina dai ganin yadda aka gyara mana gida kai gaskiya kuɗi ya yi a rayuwa mai kuɗi bai kwana da haushin kowa ba" "Wai yanzu a cikin mutum ukun nan da kike ji da su duk cikin zawarawan ki, Alhaji Tahir, Alhaji Mubarak, Alhaji Abdullahi wanne za ki aura? Kowanne dai ji yake da ke kuma burinsa ya zama gwani wato zakaran gwajin dafi" "Lokaci zai nuna" Ta ce tana jin kanta saboda ta san a halin yanzu ita allurar ruwa ce mai rabo ne zai ɗauka. *BAYAN WATA GUDA* Tafe suke a mota ita da Alhaji Tahir da ya zo suka je ya mata siyayya, suna hirar soyayya abin su, saboda ta nunawa ABBAS cewa ga irin matsayin da ta taka yanzu ta saka Alhaji Tahir ɗin ya biyo ta wajen kafintocin da ABBAS yake aiki wai za ta saya kujerar yar tsugunno irin ta tsakar gida, wai Umma ce ta ce ta siyo mata kuma kawai don ta kuntatawa ABBAS ne ta san in ya ganta hankalinsa zai tashi, shi kuwa Alhaji Tahir ya amsa mata da "Ranki ya daɗe tauraruwar mata an gama ai sai yadda kika ce za a yi, matsayinki ya fi haka" Ya ce yana wani koɗa ta, wani murmushi ta yi wanda ya kara bayyana kyan ta, a daidai wajen ya gangara gefen hanya ya faka motar har yana cewa ta zauna ya fita ya siyo da yake bai san manufarta ba sai ta nuna masa ai Ummar akwai kalar wacce take so. Fita ya yi daga motar ya kewaya zai buɗe mata don ko yaushe shi yake buɗe mata ta shiga haka idan za ta fita ma. Sosai ta ki daɗi domin kuwa tarkonta ya kama, hango ABBAS yana ta yanka katako sai gumi yake ga shi inda suka tsaya saitinsa ne dole idan za ta fito zai ganta. Zagayowa Alhaji Tahir ya yi ya buɗe mata kofar fararen kafafunta ta ziro wanda suke sanye cikin goldin ɗin takalmi, a adaidai lokacin wayar ABBAS ta yi kara ya fito da ita daga aljihu zai amsa kiran, a hankali ta fito sanye take cikin doguwar rigar bakar atamfa mai goldin, ta sha ɗaurin ɗankwali mayafinta yana yafe a kafaɗarta da yake yau yafawa ta yi ba kamar kullum da take sakalawa a gefen kafaɗa ba ta yi bala'in kyau laɓɓanta sai shekin lip stick ɗin da ta shafa suke. Yana danne ok ya kara wayar a kunne kamar an ce ya ɗago kansa sai ya hangi fitowar SALIMAH daga mota wani mutumi yana rike da murfin kofar da ta fito ɗin, sai wani kare mata kallo yake yana washe baki kamar tsoho ya ga budurwa ita kuma tana masa wani murmushi da shi kansa ABBAS a iya sanin da ya mata na matsayin matarsa tsawon shekara biyar bai taɓa ganin ta yi irinsa ba murmushi ne mai cike da ma'anoni da dama murmushi ne da yake nuna tsantsar so da kauna da nuna kulawa ga wanda ake yi wa shi. "Ko don ba ta so na shi ya sa bata taɓa yi a gabana ba" Ya ce a zuciyarsa kirjinsa yana bugawa amma kaɗan ba wani sosai ba ambaton Allah da ya fara yi a zuciyarsa shi ya sa ya ji nutsuwarsa ta daidaita, a hankali ya ɗauke idanunsa daga kallonta ya yi tamkar bai san fa zamanta a wajen ba tamkar babu wata halitta SALIMAH haka ya nuna yana magana a wayarsa wanda ba da kowa yake wayar ba sai Mama har da dariya yake wacce ta bayyana hakoransa. SALIMAH gefe ta matsa Alhajin ya rufe kofar. Duk da a jike take da kuɗi ko ɗazu ya mata transper na dubu ɗari biyar sannan da suka je shagon siyayyar ya bata dubu ɗari kuma duk kayan da ya ɗauka shi ya biya kuɗin amma yanzu ya fito da 50k ya miƙa mata ta karɓa. Tana taku ɗai-ɗai suna masu jerawa duk gurin kafintocin cike yake da ma'aikatan kowa yana ɓangarensa yana aiki amma sai ta tsallake wajen kowa ta nufi wajen ABBAS saboda cim ma manufarta domin ta fara zargin kamar bai gane ta ba tun da ta hangi lokacin da ya kalleta har kamar ma sun haɗa ido sai dai ta ga bata zame masa TV ba don ta san da ya gane ta zai saka gaba yana kallo tamkar ta samu TV musamman da aka ɗauki tsawon lokaci bai saka ta a idanunsa ba tun ranar da suka je da FAROUQ. Gabansa suka karasa tana wani yauki da jijki da kai ita ala dole tana son bayyana masa ta fi karfin talaka tana son kara tabbatar masa matar manya don da manyan ta dace. "Sannu da aiki fa " Alhaji Tahir ya ce yana murmusawa. "Yawwa Alhajin Allah barkan ku da zuwa" ABBAS ya ce cikin sakin fuskan. "Barkan ku dai?" SALIMAH ta maimaita a zuciyarta tana mamaki don ABBAS ya shayar da ita mamaki sai dai tana zargin bai gane ta ba watakila ko saboda hutu ya ratsa ta sosai, amma dai a nata zaton ko wae irin canji ta samu bata zaci zai kasa gane ta ba. Satar kallonsa ta yi a nan ta ga abin mamaki ya kara fari ya yi kiba duk tunaninta za ta gan shi ya kare kamar hatsin guzuri amma sai ta ga saɓanin haka. "Yawwa kujera muke so" Alhaji ya faɗa. "Wace iri kuke so Hajiya" ABBAS ya tambaya yana kallon SALIMAH da duk ta sha jinin jikinta tun da ta zo don ta tada masa hankali sai ta ga ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa. "Eh kujerar za...za... zama " "Haba Hajiya ke da za ki faɗi wace iri ai kowace kujera ta zama ce" Ya ce yana dariya. Duk ta diririce ji take tamkar ta ce ABBAS baka gane ni ba sai dai babu amfanin hakan. "Ta zaman tsakar gida" Alhaji ya faɗa yana dariya, ɗakko musu ya yi ta ce guda biyu suke so, ya ce kowacce dubu biyu. Dubu ashirin ta lissafa daga cikin 50k ɗin da Alhajin ya bata yanzu, ta mika masa. Karɓa ya yi tare da ɗaukan kujerun ya bi bayansu da su da yake idan aka zo siyan kayan in za a saka a mota su suke kaiwa costomer mota. Alhajin ya buɗe masa ya saka a baya, Alhajin ya buɗe mata ta shiga ta zauna, ABBAS kuwa tsayawa ya yi daga gefe ya irgi kuɗinsa dubu huɗu ya zo gaban kofar da ta shiga ta zauna Alhajin yana kokarin rufewa ABBAS ya mika kuɗin ya ɗora mata a cinya yana mai cewa "Hajiya kin yi mantuwa kuɗin sun zarta kimar wanda za ki biya" Ya ce yana mata murmushin gefen baki. Baki sake take kallonsa wato ma ba zai karɓi bajintar da ta masa ba, dama ba don tausayinsa ta bashi kuɗin ba sai don ta nuna masa a halin da ake ciki yanzu wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa, duk da ta san ta biya masa wannan karatun da baki amma sai ta ga dacewar yanzu ta biya masa shi a aikace. "No ka bar shi ka kara cefane" "Lah ki bar shi godiya nake" Ya ce ba tare da ya jira cewarta ba ya juya ya bar ta baki sake ga takaici shi kuwa Alhaji bai kawo komai ba saboda ya san akwai mutanen da suke basa son a musu kyauta ko an musu sai su ki karɓa bai san cewa ABBAS ɗin tsohon mijin SALIMAH ne da ta guda saboda talaucinsa.... *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 10 *HAJIYA RAYYANATU* Tun da magriba ta tara Baba Sadiya da sauran ma'aikatan ta faɗa musu gobe HAWWA amarya ce don haka kar su jira ta shiga kicin su gabatar da break fast ɗin. Sun amsa mata inda kowa a zuciyarsa ya yi mamakin kalaminta ganin babu wani shiri a tare da HAWWA da zai nuna cewa ita ɗin amarya ce. Saboda haka ko da safe babu wanda ya lura da cewa HAWWA da SABEER basa gidan in banda Baba Sadiya da ta san sun bi dare sun gudu. Hajiya Rayyanatu ce zaune a kujera a falonta ta harɗe ɗaya kan ɗaya sai Lawisa da take latsa waya, ɗaya daga cikin ma'aikatan ce ta shigo cikin ladabi take sanar da Hajiyar cewa HAWWA bata gidan daga ita har SABEER ɗin. Da farko ta ɗan ji wani irin don bata zaci cewa guduwa suka yi ba sai da aka duba gidan kaf aka ce basa nan sannan kuma daga sassafe har zuwa yanzu da ake karfe tara mai gadi ya ce bai ga fitarsu daga gidan ba. Ko da aka bincika cewa komai nasu yana ɗakin sai ta kuduri cewar ko ma ina ta tafi za su dawo ne su same ta. Wajen goma da rabi Baba ya fito daga ɓangarensa sanye cikin babbar riga shi dama gogan Umar yana get ya sha shaddar nan sai sheƙi take ya kafa hula sai kamshi yake shi a dole za a tafi masallacin unguwar a ɗaura masa aure, saboda haka Hajiya bata ma san sun fita ba saboda ma kayan amarya da ta bayar aka ɗinka yana ajiye a kan kujera a falo dama atamfa ce leda (Atamfa roba) Wacce ba cotton ba aka yi doguwar riga wata binjimemiya tamkar buhu wai a cewar Hajiya atamfa leda ta fi kwari kuma ɗinkin a mata maje gaba wanda za ta daɗe tana mora. Wata makociyarsu ce da Hajiya Rayyanatu da mata waya ta sanar da ita ɗaurin auren ta zagayo don ta ce musu auren za a ɗaura a gaba za a yi shagalin biki. Sosai ta shiga yaba ɗinkin amaryar a maimakon ta faɗa mata gaskiya cewar atamfar da ɗinkin basu dace da amarya ba amma sai ta shiga yabawa tana sam barka. "Ni fa a yau ban saka yarinyar nan a idona ba" Hajiya Raytanatu ta ce tana kallon makociyarta. "To ina suka je da duku duku ɗan mai gidana yake ce mini ya ganta ita da ƙaninta a tasha" Da mamaki Hajiya ta kalleta ta ce "Tasha kuma wace irin tasha" "Tashar hawa mota ai ya je kai abokin mai gidana da za hau mota da ya dawo yake faɗa mini ya gansu kasancewar jiya da kika kirani muna tare sai nake faɗa musu aurenta za a ɗaura yau shi ne da ya dawo yake ce mini ya ga amaryar da nake ce musu za a ɗaura mata aure" Ta kai karshen maganar tana fito da wayarta ta yi danne -danne ta kara a kunne. "Ni wa ka ce mini ka gani a tasha da safe" Nan ya mata bayani Hajiya Rayyanatu da kunnenta ta ji da yake a handsfee ta saka wayar. Wayarta ta ɗauka ta dokawa Baba kira, Baba da yake tsakiyar taro sai baza malun-malun yake wani maroƙi yana binsa yana ta masa kirarin uban amarya uban ango. Vibration ɗin da wayarsa da take cikin aljihu ta ɗauka hakan ya ankarar da shi ana kiransa fito da ita ya yi ya kara a kunnen nasa yana ɗagawa wasu abokansa hannu yana ta doka murmushi, Umar ango sai washe baki yake jin kaɗan ta gyara hula abinka da ba a saba sakawa ba. "Alhaji wallahi kar a ɗaura auren nan, shegiyar yarinyar nan ashe bata kwana a gida ba ta ɗauke wannan zololon ƙanin nata sum je tasha sun hau mota sun gudu" Har ta gama bayanin bai ce uffan ba ya yi mutuwar tsaye yana hango Umar da yake ta gaisawa da mutane kamar abin arziƙi. "To" Kawai ya ce wani gumi yana karyo masa ya shiga ƙarewa yawan bataliyar mutanen da ya tara domin halartar auren babban ɗansa, da kuma ƴar ɗan uwansa da ya gama yayatawa cewa suna kaunar junansu kamar su cinye juna. Hakan ya sa aka yi ta masa sam barka mutane suna ƙara ganin girmansa na ganin ya riƙe ƴar zumunsa har zai aurar da ita don wasu basu san halayyar Umar ɗin ba sun ɗauka mutumin arziƙi ne. 'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un' Ya ce yana sauke wayar daga kunnensa yana kallon jama'a yana ganin ga ƙoshi ga kwanan yunwa ba ya so a ɗaura auren bayan bai san inda ta tafi ba kuma bai san ranar da za ta dawo ba kuma bai san lokacin da za ta dawo ba sannan bai san mai zai faɗawa mutane a fasa ɗaurin auren ba. Hukunci ɗaya kawai ya yanke shi ne ya faɗi a ƙasa wannan ne kaɗai zai sa a fasa ɗaura auren. Wayar ya ƙara mayarwa kunne da gangan sai kawai ya fata ambaton subhanallahi, kawai sai ya yanke jiki ta faɗi a take jama'a suna hayya-hayya aka yi kansa amma ya saki jiki har da ɗauke numfashi kinkimarsa aka yi aka saka a mota, nan fa wuri ya kacame da hayaniya wasu suna a ɗaura tun da an taru wasu suna cewa ya za a yi a ɗaura auren shugaban ɗaurin aure rai a hannun Allah, da haka mutane suka watse Umar zaman dirshan ya yi a ƙasa yana sharɓar kuka shi a dole ba zai tafi ba sai an dawo an taru an ɗaura masa auren wai Babansa baƙin ciki yake masa shi ya sa ya faɗi ana shirin mayar da shi ango dakyar direban gidansu ya lallaɓa shi ya shiga mota don ya mayar da shi gida don da alama shaye-shayen ya fata taɓa masa ƙwaƙwalwa. *ABBAS* Tun lokacin da ya hango SALIMAH da bazawarinta sarai ya gane ta amma kuma abin ban mamakin shi ne bai ji ya shiga tashin hankalin da yake tunanin zai shiga ba idan ya ganta, sannan ko a ransa bai ji wani kishi na ya ganta da wani namiji wanda a baya yake ganin idan har ya ganta da wani sai abin da ba a rasa ba ita kanta SALIMAH bai wani ji damuwa da ita ba, a baya ko wuri ta ziyarta in yana wajen sai jikinsa ya bashi, amma saɓanin yau bai ji komai ba illa iyaka ganin ba zatan da ya mata da farko ya so ruɗa shi amma sa ya shiga ambaton Allah sai ya ji ya saitu. Abin da SALIMAH bata sani ba ya gane don ta nuna masa matsayin da take takawa a yanzu ta je wurin sai dai ya lura har yau bata gama gane waye shi ba, a duniya abin wani abi tsone masa ido ba ko da a ce bashi da naira biyar ta kansa idan wani yana da miliyan ɗari ba zai damu ba ya san Allah ne ya ba wancan shi ma kuma ba ya cire rai daga rahmar ubangiji domin Allah ne yake azurtawa. Talaucinsa bai koya masa kyashi ko hassada da son kai wa matsayin wani da Allah ya yi wa arziki yake ji dama shi ne. *HAWWA* Tun da suka ɗauki hanya hankalinta ya kwanta ganin ta kuɓuta daga wannan kaddararran auren da ake son lakaba mata auren wanda bai sam kansa ba kuma bai san darajar ɗan adam ba, ba za ta taɓa yarda ya aure shi a matsayin uban ƴaƴanta ba don ba ta ga zai zame musu garkuwa ba. Kallon SABEER take da yake kwance a jikinta yana baccinsa tana tunanin rayuwa kenan yanzu ita yake gani madadin mahaifiya tana son ta faranta masa kuma ba ta so ya yi kunci ko bakin ciki a rayuwa amma ta san matsawar suna gidan Baba Bukhari to tabbas za su rayu a ƙunci saboda rashin amana. A tasha aka sauke su lokacin SABEER ya falka amma bai ware daga baccin ba, goyonsa ta yi ta tsaya ta saya masa pure water jin yana cewa zai sha ruwa duk da ta san yunwa yake ji tun da bai ci abinci ba. Napep ta tare musu suka kama hanyar gidan Baffa Nasiru a kofar gidan aka sauke su ta bawa mai napep kuɗin ta kama hannun SABEER suna shirin shiga gidan ta hango Baffa. "SABEER ka ga Baffan can" Ta ce cike da farin cikin ganin ɗan uwan mahaifiyar tasu mai kama da Ummien kamar an tsaga kara. Dariya shi ma ya yi yana ɗan tsalle alamar murna kasancewar yana matukar kaunarsu. SABEER hannunsa ya kwace daga rikon da ta masa ya nufi wurin Baffa da yake tsaye a wajen amma shi da yake hankalinsa ba a wurin yake ba sai bai gan su ba, bai ankara ba ya ji an rungume shi ta baya cike da mamaki ya juyo don a tunaninsa ma cikin wasu yaran ne saboda shi mutum ne na yara. "Baffa!" SABEER ya ce yana kara kankame shi don tun bayan mutuwar mahaifiyarsu tsawon shekara biyun bai sanya shi a ido ba, sannan a halin yanzu bayan HAWWA sai Baba Sadiya ne kawai wanda ya san masu kaunarsa sai yanzu da ya yi ido biyu da Baffa. Yaro kenan duk ƙanƙantarsa ya san mai ƙaunarsa ko da zare masa idanu kake wannan abin yana ƙwaƙwalwarsa ba zai manta da shi domin yaro ba ya mantuwa. "SABEER kai ne" Baffa ya faɗa yana kama hannuwan yaron duka biyu yana kallonsa tamkar yau ya fara arba da fuskarsa. Washe bakinsa ya yi ya ce "Ni ne Baffa ga can Aunty HAWWA" Ya ce yana nuno ya da yatsa, ɗago kai Baffa ya yi ya ganta tsaye tana murmushi. Idanunsa ne suka kawo ƙwallah ya daka hannu ya goge wacce ta gangaro ganin mutane a wajen sai ya kama hannun SABEER ɗin, wurin HAWWA suka ƙarasa, yana zuwa ita ma ta rungume shi don ganin kamannin mahaifiyarta a fuskarsa ya sa ta ga tamkar mahaifiyarsu ce. "Hauwa kulu" Ya ce muryarsa tana rawa yana matukar kaunar yaran yana jin kaunar har cikin zuciyarsa tun da mahaifansu suka rasu ya nemi Alhaji Bukhari da ya bar masa yaran ya tafi da su Kaduna su zauna a hannunsa amma fafur ya ƙi wai dangin uba su ne suka fi cancanta da su riƙe ƴaƴa kuma ma a yadda ya fuskanta dukiya ce kawai a gaban Alhaji Bukhari har sai da Baffa ya ce shi ya amince a bashi yaran ba tare da an bashi ko da tsinke bane daga cikin dukiyarsu don shi dama tsoron cin dukiyar maraya yake, yana tsoron ranar da Allah zai tashi shi ya tambaye shi yadda ya ci shi hatta bashi tsoron cinsa yake, saɓanin wasu mutanen da basu ɗauki cin bashi a komai ba, suna mantawa da ranar karshe, suna mantawa da ranar sakamako suna mantawa da hisabi. Bayanta ya bubbuga tare da janye ta daga jikinsa ganin a kofar gida ne hannunta ya kama yana rike da su suka kama hanyar kofar gidan. "Baffa ga kuɗin kayan can da aka siyar ɗazu" ABBAS da ya zo zai ba Baffa kuɗin ciniki ya faɗa yana ɗan sunkuyowa ya mika masa da hannu biyu. "Ka ajiye a wurinka ABBAS zan shiga gida ne in na fito ma yi maganar" Cewar Baffa yana ɓoye fuskarsa da ruwan hawaye ya taru a kwarmin idanun, yana so ya tuna dalilin da ya sa ya manta da ƴaƴan ƴar uwarsa, yana so ya tuna dalilin da ya sa ba ya zuwa ya gan su amma ya kasa tuna komai shi ba don ya gan su ba ma, ko a ƙwaƙwalwarsa ba ya tuno su. Ba tare da ya ƙara ko da bi ta kan ABBAS ɗin ba ya juya yana rike da hannayensu suka shiga cikin gidan. ABBAS har suka ɓacewa ganinsa yana tsaye a wurin riƙe da kuɗin a hannunsa bai taɓa ganin uban gidan nasa a yanayin makamancin wannan ba sai dai lokacin da ƴar uwarsa ta mutu a Zariya da ya dawo duk ya zama wani iri amma yanzu ya rasa wane yara ne da zuwansu a sauya shi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Da sanyin jiki ya juya ya koma wurin aikinsa ya san sai dai Usman ya musu rashin kyautawa kasancewarsa ɗan abokin Baffan da yake riƙewa sai ya yi ta musu ɗagawa da rainin hankali amma shi Baffa ya ɗauke su tamkar ƴaƴan da ya haifa. Suna shiga gidan da sallama da take hura wuta ta ɗago tana amsa sallamar cike da mamaki. "SABEER, Hauwa'u" Ta ce tana kallonsu, da gudu SABEER ya je ya rungume ta yana ta murna kasancewarta mace ta gari wajen Baffa kuma tana kaunar ƴaƴan ƴar uwarsa kamar yadda shi ma yake kaunarsu kasancewar ma su basu taɓa haihuwa ba sai ƴaƴan abokinsa kuma amininsa da ya mutu Malam Ashiru yake rikon ƴaƴansa guda biyu mace da na miji Usman da Amrah. "Ina ka shige Alhaji SABEER " Ta tambaya tana kama hannunsa suka nufi baranda inda tabarma take a shimfiɗe.Lale marhabin da zuwanku ƴaƴana" Ta ce tana ta murma ta zauna tare da zaunar da SABEER a kan cinyarsa. "Hauwa'u" "Na'am Goggo" "Ina can gidan Baba, kuma a ɗakin da muke kwana babu gado babu katifa, kuma babu abinci mai daɗi, kuma yageggen kaya nake sakawa" Ya ce yana kallonta, sosai Baffa ya ji maganar ta taɓa shi dama ya san a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ya san dama Alhaji Bukhari ba zai iya riƙe amanar yaran nan ba shi kuma ya rasa mai ya sa ya manta da lamuransu duk da ganinsu da ya yi yau ya sanya shi fara zargin wani abu a kan mantuwar ta tsawon shekaru biyu ba tare da ya waiwayesu ba sai dai ba ya son zurfafa tunani domin an ce zato zunubi ko da ya zama gaskiya. An kawo musu abinci da ruwan sha, SABEER zagewa ya yi yana ta cin abincin saɓanin HAWWA da ta ci kaɗan saboda duk gajiya ta gama ratsa jikinta. "Hauwa'u ya aka yi tsawon lokacin nan baki zo nan ba? Kin san mahaifiyarki mai yawan zumunci ce kuma tana zuwa da ku ke mai ya sa baki zo sada zumuncin ba tun da kika ga ni Allah bai bani iko ba? " Baffa ya tambaye ta yana kallonta tana wasa da yatsunta shi SABEER ya samu abin wasa yana ta uzurinsa. "Baffa babu dama shi ya sa bamu zo ba, babu wanda zai barmu" Ta ce tana tuna wayar da ta ji Hajiya ta yi a kan an mantar da shi su. SALIMAH Har suka iso kofar gidansu ran SALIMAH a matukar ɓace da abin da ABBAS ya mata a ganinta ya watsa mata ƙasa a ido a yadda ta san ya mutu a kan soyayyarta a nata zaton ko ƙasa ta bashi zai rusuna ya karɓa da hannu bibiyu, amma wai ita SALIMAH ya nuna tamkar Allah bai yi ruwanta a wajen ba. "Sarauniyar mata ina so mu tsayar da magana nan da sati guda a ɗaura mana aure li tare gimbiya sarauniya mai mulkin zuciyata" Muryar Alhaji Tahir ta katse mata tunani. Wani mugun daɗi ne ya baibayeta jin maganar da ya zo danita duk da ba shi kaɗai bane maneminta zawarawa gasu nan kamar jamfa a jos amma maganar auren da ya zo mata da ita ya yi sara a kan gaɓa, tana ganin kamar dai ABBAS ya mata abin da ya mata ne saboda yana ganin tana zawarci ne ya raina mata hankali amma za ta nuna masa kallon kitse yake wa rogo sai ta je har wajen kafintocin da yake taƙama da shi ta kai masa katin ɗaurin aurenta in zuciya zai haɗiya ma ya mutu ko ma dai ya yi mushe... https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 11 Hajiya Rayyanatu da bata san shirin Baba ba ko kaɗan bata san mai yake wakana a can ɗin ba tun lokacin da ya kashe mata waya, suna zance da maƙociyarta tana ta nuna cewa iya yarinyar ai kanta ta yi wa da ta gudu don su gaba ta kai su gobarar titi. Da yake ita da ita ɗin sammakal jirgi ɗaya ne ya ɗakko su sai take nuna mata ta hutar da su Hajiyar wahala. Ita dai fatan ta Allah sa kar a ɗaura auren a wannan halin ne suna ta dariya abin su da alama duniyar ta musu daɗi don a ganin Hajiyar da tafiyar HAWWA da zamanta duk uwar ubansu ɗaya, idan ma ɓaya suka yi su je dan kansu, ita dai fatan ta kar a ɗaura auren a bar mata ɗa da igiyar wata matar galihu in ban da ma suna son ya shiryu ai shi ba sa'an auren HAWWA bane domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Kukan da Umar yake ta faman rafkawa tamkar wanda ake zare masa rai shi ne ya katse musu nishaɗin da suke ciki, dama su kaɗai ne a falon da yake bata ɗauki auren da muhimmanci ba ko gayyata bata yi ba ita ma Lawisa tana sama abinta. A kiɗime Hajiya ta tashi ta fito daga falon maƙociyarta tana take mata baya saboda abin ya ɗaure mata kai ya san dai matsawar an ɗaura aure babu abin da zai sa Umar yake faman yage baki yana kuka da kururuwa tamkar uwarsa ta bar duniya, amma dai ta fi son tabbayar da gaskiyar lamari saboda masu iya magana sun ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗin ji. Suna fitowa suka yi ido huɗu da Umar da yake tamkar mahaukaci sabon kamu ya cire babbar rigarsa ya yi ɗamara da ita a ƙugu ma'ana ya ɗaure a ƙugunsa ga hular nan ta kalli arewa masu gabas uwa uba fuskar nan sharɓar da hawaye har da majina yana kuka haiƙan direban yana rirriƙe shi, shi kuma yana fisgewa tamkar za a saka mahaukaci a turu. "Baƙin ciki yake mini wayyo na shiga uku na lalace" Ya ce yana rusar kuka duk ya cika gidan da kururuwa abin da ya ɗauki hankalin ma'aikatan gidan suka fara fitowa daga ciki domin an ce gani ya kori ji sai dai suna zuwa da suka ga angon ranar a rikice sai suka sha jinin jikinsu. "Duk wanda ya kara minti biyu a wurin nan a bakin aikinsa" Cewar Hajiya a ƙufule tana jin haushin su kowa ya ya dare ya koma ciki suke ƙusƙus ban da Baba Sadiya da ta shige ɗaki ta tuntsure da dariya don ta san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi ma'ana kukan nashi da haukar da yake ba ya rasa nasaba da tafiyar HAWWA. "Wallahi Hauwa'u ta maka nisa yaro dama ba sa'arka bace ƙaddara ce wacce ta riga fata ta kusan giftawa a tsakaninku kuma Allah ya kare yarinyar kirki, ai Hauwa'u da nagartaccen miji ta dace ba kai ba sangartacce" Ta faɗa a fili tana zaumawa ta cigaba da abinnda take yi. "Wai kukan uban me yake?" Hajiya ta faɗa tana zare ido ranta in ya yi dubu ya ɓaci. "Auren ne ba a ɗaura ba taron ma ya watse shi ne yake kuka yana cewa wai Alhaji ne ya masa baƙinciki" Direban ya faɗa dariya tana neman kufce masa ya danne ganin gabaɗaya abubuwa sun caɓe sai ka ce wata dirama ake yi. "To sai mai don ba a ɗaura ba aikin banza da wofi yarinyar da ta gudu yawon ta zubar ko a gida bata kwana ba ai dama ruwa ba sa'an kwando bane, kuma ko da an ɗaura ma ƙarshen alewa ƙasa!" "Ta gudu?" Umar ya faɗa a kiɗime tare da yin kukan kura ya fisge riƙon da direban ya masa sai ga direba wancakar an jefar da shi gefe, yana kwace kansa ya zura a guje ya yi hanyar ficewa daga gidan, hularsa ta yi tsalle ta bar kansa. "Wallahi wani abu ya same shi ka kuka da kanka ragon banza da wofi ka yarda ya jefar da kai gefe kamar wani kayan wanki in baka dawo da shi yanzun nan ba a bakin aikin ka" Hajiya ta ce tana zabga wa direban harara. Mikewa ya yi tare da cire takalmansa ya marawa Umar baya, jin za a yanke masa hanyar cin abinsa. Daga nan su Hajiyar suna iya jiyo maganar Umar da ƙarfi yana cewa. "Sai na bi HAWWA yawon ta zubar" Faɗa yake tamkar zararre. "Hajiya amma yaron nan yana shaye-shaye ko?" Maƙociyar Hajiya ta tambaya ganin abin da yake ya wuce misali. "Ah bushe-bushe yake ba shaye-shaye ba" Hajiya da maganar ta mata ciwo ta faɗa tana aika mata harara da jajayen idanunta da takaici ya sa suka yi ja. An ɗauki kamar minti goma suna tsaye da ita da maƙociyar cirko-cirko ita dai maƙociyar bata ƙara cewa uffan ba ganin daga tambaya cibi ya zama ƙari. Riƙe take da tsantsa sai huci take ta rasa mai ya sa take ta kiran Baba bai ɗauki waya ba, ta ma rasa takamaimai mai ya sa bai dawo gidan ba tin da an fasa ɗaurin auren, ya barta da ganin tashin hankalin da Umar yake duk zai janyo hankulan jama'a su gane halin da ake ciki. Suna nan tsaye sai ga Lawisa ta sakko daga sama riƙe da glass cup mai ɗauke da lemo a ciki. "Hajiyancy uwar amarya da ango" Ta ce tana ƴar dariya don ita bata san mai yake faruwa ba. "Ubanki ne angon?" "Mai ya yi zafi shi ba wuta ba Hajjaku mutanen saudi arabiya" Ta ce cikin wasa tana kurɓar lemon hannunta. Shigowar mai gadin gidan da direba da wasu ƙartan samari guda biyu sun iyo wa Umar cali-cali sai zufa suke na tseren wahalar gudun da suka sha a titi yadda ya hau kwalta yana zabgar gudu yana kiran sunan HAWWA daƙyar suka cim masa ana hayya-hayya aka kamo shi. "Ango ranar ɗaurin auren ka sha ka yi tatul" Lawisa ta ce tana juyawa ta shige falo don bata iya ganin wannan kayan takaicin ganin ya fusge-fusge yana ambaton HAWWA sai ta ɗauka a buge yake bata san duk zafin so bane. Ɗakinsa ta ce su kai shi su saka cike da takaici ana saka shi a ɗakin ta kulle da mukullin tana jin yadda yake dukan ƙofar, ita kanta ta fara zargin ko dai kafin ya fita ɗaurin auren ya sha ƙwayar ko dai akwai wata a jikinsa wacce bata sake shi ba don lamarin abin mamaki ne da al'ajabi. Tana fitowa za ta nufi ɓangarenta ta samu samarin nan biyu da suka taimakawa mai gadi da direba aka shigo da Umar suna tsaye. Hatara ta wurga musu ta ce 'Tsayuwar mai kuke ko ganin ƙwaƙwaf?" "Sallama muke jira" "Sallamar uban me, saboda kun kamo Umar ɗin ne har sai an biya ku? Sai ka ce wanda kuka kamo raƙumi ko doki?" Sumi-sumi suka fice suna jan Allah ya isa a zukatansu su dama sun ɗauka za a basu wani abu shi ya sa suka zage suna zabgar gudu har aka ci nasarar kamo shi aka kawo shi gida. Falo ta koma duk tanta a jagule maƙociyar tata ce take bata baki, waya ta ɗauka ta dokawa direban nan ta ce ya zo ba a ɗauki minti uku ba sai ga shi ya shigo. "Wai Alhaji a masallacin can wajen ɗaurin auren kuka baro shi? Ina ta kiran wayarsa a kashe" "Alhaji fa yana asibiti... "Yanzu fisabilillahi maimakon ya zo gida ana buƙayarsa ya wuce dubiya asibiti" Ta katse shi ba tare da ya kai aya ba. "Jiki ya yanke ya faɗi a wajen ɗaurin auren fa aka kwashe shi aka tafi da shi asibiti bai san ma a wanda yake kanshi ba, shi ne taron ya watse ba a ɗaura auren ba" "Ya faɗai innalillahi wa inna ilaihi raji'un yanzu tsakani da Allah ka san Alhaji yana can asibitin amma baka faɗa mini ba ka barni gaho a nan ina aikin banza da wofi har da wani cewa aka kwashe shi ba za ka ce aka taimaka masa ba" Ta ce lokacin da ta miƙe tsaye daga zaunen da take tamkar ta kai masa duka shi da ba shi ya kai zomon ba rataya aka bashi. "To fa! Iko sai rabbani su Baba ko dai lokaci ya yi" Lawisa ta ce cikin halin ko in kula. Wani dundu Hajiya ta sakar mata a baya har sai da ta gantsare. "Shegiya marar tarbiyaina zaman zamana za ki jaza mini takaba to a bakin ki" Ta ce tana nufar hanyar fita ɗankwali yana neman faɗuwa duk ta rikice. Ita da maƙociyar tata suka shiga motar direban ya ja suka nufi asibitin don Lawisa ko a jikinta wai an tsikari kakkausa sai ma haushin dukan da Hajiya ta mata tana jin ba don ba don ba da sai ta rama dukan amma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe!. A harabar asibitin ya tsayar da motar tun kafin ya gama fakin Hajiya ta fito hankali tashe maƙociyarta ta bi bayanta hango wasu abokan Alhajin a tsaye cirko-cirko daga can ɗan nesa da su wurinsu ta nufa hankali tashe tana tambayar ya jikin nasa ko dai mutuwa ya yi nan suka shiga bata haƙuri da kwantar mata da hankali a kan cewa yana nan da rai kawai dai ruɗani ne ya saka ya suma amma basu san ruɗanin mene ne yana waya dai ya yanke jiki ya faɗi. Ganin tana kuka wiwi hankalinta a tashe likita ya bata damar ta shiga ta gan shi ko hankalinta ya kwanta ganin tana nuna ko dai mutuwa ya yi aka ɓoye mata. Ita kaɗai likitan ya ba umarni ta shiga ita maƙociyarta sai ta tsaya, shi dama direban yana can gefe don dama a wajen ɗaurin auren ya ji suna faɗar sunan asibitin da za a kai Alhaji. A rikice ta shiga ɗakin da yake tana ta faman share hawaye, Baba da ya ji shigowarta idanu ya ƙyallara ya ga ita kaɗai ce amma bai buɗe ba saboda kar ya je wani ya biyo bayanta a gane gafar zaren da ya shirya. Tana zuwa ta dafa jikinsa tana kuka. "Hajiya!" Ya kira sunanta a hankali yana buɗe idanunsa tarwai mamki take ganinsa raɗai tamkar dai lafiyarsa ƙalau. "Ki kwantar da hankalinki lafiyata ƙalau na yi haka ne don a fasa ɗaura auren kin san in ban yi wannan dabarar ba babu wanda zai fahimce ni idan na ce kar a ɗaura auren" Ya ce cikin raɗa-raɗa yana sakar mata murmushi, ido ta ƙyafita masa tana sakin nata murmushin tare da ɗaga hannunta tana jinjina masa da babban ɗan yatsanta ganin abin bajintar da ya yi. A hakan likitan ya ƙwanƙwasa ƙofa ƙofa da sauri Alhaji ya koma ya kwanta lifet tare da rufe idanu ita kuma ta ba likitan umarnin shigowa tare da cigaba da ɗan share hawayen munafurci!. *HAWWA* Bayan sun gama tattaunawa da Baffa suka shiga hirar yaushe gamo tana ta bashi labarin irin halin da suka kasance na rayuwa a gidan ƙanin mahaifinsu, sosai ya tausaya musu yana Allah wadarai da halin wasu mutanen da suke gallazawa maraya, bayan sun san cewa duk wanda ya raini maraya ya faranta masa zai zauna a aljanna da ma'aikin Allah kafaɗa da kafaɗa yadda manzo S.A.W ya kwatanta kusancinsa da shi, kamar kusancin yatsun hannu. Amma shi wannan ga cin amanar marayu ga kuma cin amanar zumunci duk yadda aka yi ta nuna girman zumunci da lada da matsayin da wanda ya sada shi yake da shi amma shi ya yi watsi da hakan. Goggo Salame ruwan wanka ta haɗa ta yi wa SABEER wanka ta shafa masa mai sai ta bashi kayansa ya mayar. Sannan ta haɗawa HAWWA ma ta ce ta yi wankan, kafin HAWWA ta fito ta shiga ɗakin Amrah ta ɗakko wata doguwar riga ta atamfa ta ajiyewa HAWWA da yake kusan sa'annu suke sai dai Amrah ta girmi HAWWA amma da kaɗan. Bayan ta fito Goggo Salame ta bita ɗakin ta nuna mata rigar. "Ki saka rigar nan kin ga sai ku zauna a nan ɗakin ke da ƴar uwarki Amrah" Gaban HAWWA ne ya bada sautin didim jin sunan da Goggo ta ambata saboda ta san basa ga miciji da Amrah gabaɗaya ma bata san mai ta mata ba ta tsaneta tun lokacin Ummie tana raye idan suka zo sai Amrah ta yi ta harararta ko take faɗa mata magana bare kuma yanzu a ce ta saka rigarta ba ma wannan ne damuwarta ba wai da aka ce su zauna a ɗaki ɗaya. "To Goggo amma da kin bar mata kayanta sai na mayar da ma jikina tun da Baffa ya ce za a siyo mana kaya" HAWWA ta ce cikin sanyin murya don ta san muddin ta saka kayan sai Amrah ta mata wulaƙanci idan ta zo ita kuma duk abin da za a wulaƙan tata ko mene ne gwara ta haƙura da shi. "To shikenan " Goggo ta ce ita ma dama ƙarfin hali ne ɓarawo da sallama domin ta san Amrah bata da kunya ko kaɗan ita ma ba raga mata take yi ba dama an ce riƙon ɗan wani sai mai haƙuri, ko kaɗan Amrah ba ta ganin maraicinta kuma bata ɗaukan Baffa da Goggo da muhimmanci da kuma godewa ɗawainiya da su da suke yi duk da suna yi domin Allah na sai dai wani lokacin sai take ganin kamar ita mahaifiyar su Amrah ɗin ce take zuga su da yake ita tana raye tana aure a wani gidan bayan mutuwar mahaifinsu. Fita Goggo ta yi daga ɗakin ita kuma ta shafa mai ta mayar da kayanta ta fito,, lokacin Baffa ya fita, nan ta karɓi girkin da Goggo take ta ƙarasa dafawa dama wake da shinkafa ne bayan ta tace ta mayar da shi ruwan ya tsotse sai ta ɗora miyar tana gamawa tana cikin kashe wutar sai ga Amrah ta shigo gidan da sallama tana wani shan ƙamshi, HAWWA ce ta amsa mata da kallo ta bi HAWWA daƙyar ta gane ta saboda kayan jikinta da suke ƙasƙantattu sannan lokacin a sunkuye take tana kashe wuta. "Sannu da ƙoƙari Hauwa'u Allah ya baki masu yi miki" Goggo ta ce tana kallon HAWWA tabbas HAWWA ta samu tarbiya ta san girman na gaba da tausayawa komai nata a nutse tabbas Goggo ta san tarbiya ce kawai iyaye za su ba ƴaƴansu ita ce har bayan ransu ba za su taɓe ba domin tarbiya ita ce mutum. "To in ji mai tallar totuwa yau kuma marayu ne suka kawo mana ziyara wato an tuna da dangi an zo kenan... "Amrah ke mai ya sa har kullum tunaninki na ƙananan yara ne yanzu mene ne na ambaton marayu ne, ba sai kin faɗa ba kowa ya san hakan ai amma maimaitawar bata fa wani amfani" Goggo ta katse wa Amrah zancen. "Yo ƙarya na yi ba marayun bane Goggo kuma ai ba ni na kashe musu iyayan ba" Ta ce cike da fitsara tana shigewa ɗaki, HAWWA shiru ta yi bata ce komai ba don in da sabo ta saba ita yanzu abubuwan da aka mata bayan mutuwar iyayanta sun ƙara ankarar da ita rayuwar duniya. "Wane mai ƙarfin halin ne ya taɓa mini mai waye ma ya shigo mini ɗaki babu izinina?" Ta fito ta tsaya riƙe da ƙugu. "HAWWA ce ta shafa man kuma ni na ce ta shafa sannan wannan ɗakin naku ne ku biyu yanzu ita ma a ciki za take zama, kuma ba ziyara suka zo ba" "Ah to hakan ma ya yi" Ta ce cikin gatse ta kuya ta koma ɗaki dama tun da safe ta fita wai ta tafi gidan babarta sai yanzu ta dawo babu tsiyar da take tsinanawa sai lokacin abinci ta zauna ta cika cikinta, sannan halinsu ɗaya kuma bakinsu ɗaya da Usman yayanta idan Baffa yana nan su ringa nuna su mutanen kirki ne amma idan a bayan idanunsa ne ƴan iskan kan su ne. Ɗaki ta koma tana ji ana cewa ta fito su ci abinci da yake Goggo haɗa musu ta yi da HAWWA amma ta ce tana zuwa kuma ta ƙi fitowa. SABEER kuwa ya ce sai Baffa ya dawo za su tare. Sai da Baffa ya masallaci aka idar da sallah ya sannan ya shigo gidan, har lokacin HAWWA tana zaune da abincin a gefe sai ma ta ɗauki murfi ta rufe tun da ita zaƙaƙura Amrah ta ƙi fitowa ita ma Goggo ya yi alwala ta shiga ɗaki ta yo sallaj ya rage sai Amrah a kan baranda sai kuma SABEER yana wasa. Jin sallamar Baffa SABEER ya tafi ta gudu tana masa oyoyo hannunsa Baffa ya riƙo suka ƙaraso cikin gidan. Amrah da take kwance tana danna waya jin shigowar Baffa sai gata ta yi wuff ta fito daga ɗakin ta zauna ko kunya tana washe baki ta ce "Yi haƙuri ƴar ƙanwata sallah na yi kina ta jirana ko?" Ta ce tana janyo abincin ta saka a gabansu tana kallon HAWWA da murmushi a fuskarsa sosai HAWWA ta yi mutuwar zaune ganin abin da Amrah ta yi amma sai ta danne mamakinta tana sakin murmushin ita ma a zuciyarta tana mamakin irin kissa da kisisina na Amrah tana tunanin lallai idan aka ce Amrah kishiyarka ce ka shiga uku. Sosai Baffa ya ji daɗin ganin Amrah da HAWWA suna tare wannan ya ƙara sakawa ya ji daɗi a ransa. Abincin suka shiga ci, ko nisa basu yi da fara ci ba Usman ya yi sallama ya shigo riƙe da ledar salad da ya taho fa shi, ƙurrrrr ya kafe HAWWA da idanu yana kallon yadda ta ƙara kyau da kuma girma farin fatarta ya sa ya hangi ƙanwarsa Amrah ta ƙara baƙi, dama baƙa ce sai faɗin fuskar da wani hancinta kamar gajeran wando. Wani irin daɗi ya ji a ransa don dama sun haɗu da Baffa a waje yake sanar masa da zuwansu ya daɗe yana jin son HAWWA ransa sai dai sanin ba sa'arsa bace wato iyayanta masu akwai ne sai ya ja bakinsa ya yi shiru amma yanzu tun da dai ga ta a matsayin marainiya kuma ta zo zama sannan uwa uba Baffa ne auwalin aurenta to shi fa ya ga matar aure. "Yaya sannu da zuwa" HAWWA ta ce ganin ya ƙura mata idanu. Amsa mata ya yi yana murmushin yaƙe don sai yanzu ya gane katoɓarar da ya yi. Amrah ganin da Baffa a zaune sai ta tashi ta karɓa salad ɗin ta je ya shiga yankawa ta saka gishiri ta wanke tas ta zuba a mataci ta tsakura musu ita da HAWWA. "Ƴar ƙanwata kina so in zuba mana, in kuma bakya cinsa ni ma ba zan ci ba abin da kike so shi nake so" Ta ce tana murmushi dakyar HAWWA ta samu damar bata amsa saboda gabaɗaya ta shallake mata tunani. "SABEER ko da ni za ka ci abincin ?" Usman ya tambaya. "Ni dai da Baffa zan ci" Ya ce yana noƙe kafaɗa saboda bai manta ba lokacin suna zuwa da Ummiensa sai yake harararsa idan ba kowa a wajen ko yake zare masa idanu yana hantararsa yaro babu mantuwa. Da daddare bayan Goggo ta ɗakkowa HAWWA katifar da za ta kwanta ta bata ta SABEER ƙarama irin ta ƴan makarantar kwana, da yake da wuri ya yi bacci sai ta kai shi ta kwantar bayan ta saka leda ta masa shimfiɗa. Sai da suka sha hira kowa ya shiga ɗaki a lokacin ne HAWWA ta ga ikon Allah don Amrah tuni ta sauya fuska ta fara mata tijara. "Ba an lallaɓo cin arziƙi ba kar fa a zo a takurawa rayuwata, an zo kalen dangi da can baku san da Baffan ba sai da ruwa ya ƙarewa ɗan kada? Kun taɓa kun ji maraici babu daɗi ko? To bari ki ji in faɗa miki ki sani bauta kika zo yi gidan nan wankina share ɗakin nan ke komai ke za kike mini kar ki ga an haɗa mu ɗaki ɗaya ki zata ɗaya muke to ki sani baki da galihu" Ta faɗa cikin wani iko da izza. Wani ruwa ne ya taru a idanunta ganin ba a rabu da bukar ba za a haifi habu tana ganin sun baro ƙangin rayuwa a Zariya sun taho Kaduna ashe dai a nan ɗin ma ba za ta sauya zani ba. Da wutsiyar ido ta kalli inda SABEER yake a kwance tana jin tausayinta saboda muddin Amrah za ta hana ta rawar gaban hantsi to shi ma ba zai samu sakewa ba tun da ta ga hatta Goggo ma ba raga mata take yi ba sai Baffa yana nan shi kuma namiji ba ɗan zaman gidan bane koyaushe. Shirun da ta yi ta ɗan yi nazari cewa dole ta ɗauki mataki dole ta tauna tsakuwa aya ta ji tsoro dole sai ta zagine dantse za ta ƙwata musu ƴanci ita da ɗan uwanta maraici ba hauka bane ai maraya kuma yana da dama da ƴancin da zai rama koma mene ne in ba haka ba sai ya zama ahi da kashi basu da maraba wajen ƙyama. "Amrah!!! Ina so ki sani duk wani maraya ba shi ya zaɓarwa kansa maraici ba Allah ne ya ƙaddara masa. Sannan kuma da kike batun kalen dangi ai mu munfi ƙarfin kalen dangi tun da uwa ɗaya uba ɗaya ba wasa bane mu ƴaƴan ƙanwar Baffa ne kin ga ba za a kira mu ƴan kalen dangi ba, ku da kuke ƴaƴan abokinsa ku ne za a kira da masu kalen dangi, kuma maraici tun da ku ɗin ma ubanku ya mutu su waye ku in ba marayun ba? Kuma ke baki isa in miki wanki ba ko da kuwa wankin pant ne bare na kaya, duk wani hayaƙi da kan ki yake ina so ki sani nawa ya wuta yake yi" Amrah da ta zaɓi take cin ƙaniyar Amrah a gefe a gaban su Baffa kuma ta mata walai-walai kamar yadda take wa mutane dama masu iya magana sun ce idan ka je gari ka ga kowa da jela to ko ta tsummace kaima ka ɗaura dole sai ta yi mata zabu-zabu ta yi maganin rashin mutuncin da ta mayar da shi abin yi. Amrah sosai ta sha mamaki jin kalaman HAWWA saboda a iya saninta da HAWWA tana da haƙuri da kawar da kai kuma tana girmama na gaba ko da kuwa da kwana ɗaya tak! Ya girme ta amma yau ta shayar da ita ruwan mamaki sai dai ba za ta bada kai bori ya hau ba dole ta nunawa HAWWA cewa barazanarta babu abin da ta mata. Dakewa ta yi tana mai yin taku ɗaya biyu ta zo gaban HAWWA. "Ke sa'ar yinki ce ni?" Ta tambaya tana sanya idanunta cikin na HAWWA amma sai ta ga ko gezau HAWWA bata yi ba, hakan ya sa ta fara tunanin to ko dai bayan mutuwar iyayanta ta samu wasu wanda suka koya mata rashin mutunci suka wanke ta. Hannu ta ɗaga don ba za ta juri raini ba wai har tana cewa su ne ƴan kalen dangi, fuskar HAWWA ta nufa ta sakar mata marin bazata, a gefen hagu kafin HAWWA ta dawo daga duniyar mamakin da ta shayar da ita ta ɗaga hannun za ta bata marin a karo na biyu. A fusace HAWWA ta kaiwa hannun Amrah damƙa, tana mai sa ɗaya hannun ta wanke fuskarta hagu da dama da mari tare da wujijjiga ta, ta yi wurgi da ita a tsakiyar ɗaki... *SALIMAH* Da wani irin farinciki ta juyo tana kallonsa tamkar wanda ya mata albashir da kujerar hajj. Ta ji daɗin wannan kalami na shi don haka babu wani dogon tunani ta amince da auren a sati guda. "Amma da sharaɗin za ka mini lefe na kece raini, lefen da za a daɗe a unguwarmu ana maganarsa domin kaya nake so na ɗaukan magana kaya wanda suka amsa sunansu kaya" Ta ce tana kallonsa wata ƴar dariya ya yi irin tasu ta mantya yana mai juyowa kocakwam yana kallonta ya ce. "Haba gimbiya ai faɗa ma ɓata baki ne ni ganinki nake baki da bambanci da budurwa kin fi wata budurwar ma lefe zan miki na gani na faɗa kar fa ki manta da Alhaji Tahir kike magana bana tsoron kuɗi kuma bana jin komai don na kashe kuɗi dama masu iya magana sun ce da kuɗi da miciji dukakaninsu maganinsu kashewa! Bare kuma a kan tauraruwata wacce nake jin mallakarta ya fiye mini mallakar wani ƙaton zinare" Ya faɗa yana kashe mata ido, wani gingiringim kanta ya yi ya mata nauyi tamkar an ɗora mata dutse domin ya fasa mata kai sai yanzu ne take ƙara jin daɗin mutuwar aurenta ga shi tana sabuwar rayuwa bare kuma idan ta je gidansa ta zama mallakinsa tabbas wataƙila ta kan naira za take bi tana wucewa a lokacin ne za ta taka wanda take so. "Shi ya sa nake jin ka fiye mini dubu dukkaninsu ina musu kallon taron yuyuyu, kai ne na zaɓa kuma kai zan ci gaba da zaɓa" Ta ce tana jin tamkar ta haɗiye shi saboda so don ita sai da ta ji baya jin ciwon kashe mata kuɗi ne ma ta ji tana ƙaunarsa saboda ita duk wanda zai bata kuɗi shi ne nata. Nan suka zauna suna tsara yadda komai zai kasance daga nan suka yi sallama ta kwaso siyayyar da ya mata tana fitowa ta samu Alhaji Abdullahi tsaye a gaban motarsa. "Big girl, sun buga sun barki babban goro sai magogin ƙarfe" Ya ce yana washe baki da ƙare mata kallo tamkar idanunsa za su fito a jikinta bayanta ta waiwaya ta ga Alhaji Tahir ya ja motarsa ya tafi sai lokacin ma ta tuna bata ɗauki kujerun ba. Juyo kallonta ta yi gare shi tana aika masa harara saboda wani message na banza da ta ga ya tura mata a waya ɗazu hakan ya nuna mata mu'amalar banza ta kawo shi gare ta ba aure ba don haka gwara ma ta auri wanda ya nuna zai aure ta kuma ta tabbata za ta samu abubuwan da take buƙata na daga dukiya da yin duk yadda ta so na facaka da kuɗi. "Kin amincr mu tafi hotel ɗin awanni biyu sun yi yawa zan dawo da ke ba kwana za ki yi ba, na miki alƙawarin maƙudan kuɗi" Wani tsaki ta je ta masa kallon sheƙeƙe ta ce "Allah tsari gatarina da saran shuka ka je ka nemi daidai ya kai ni kam mun yi hannun riga da zina da kuma mazinaci!. Tana faɗa ta juya ta bar shi baki sake yana mamakin ta a yadda ya santa lashe money bai taɓa zaton za ta ƙyamaci zina ba. Jiki ba ƙwari ya shiga motarsa ya bar wajen. Tana shiga gida ta shiga labartawa Umma yadda suka yi da Alhaji Tahir sosai ta carara guɗa tana tashi tsaye ta taka rawa ta juya ta koma ta zauna ta ce. "Kai Allah na gode maka da ka bani ƴa mai goshi mai farin jini kin ga abin da nake faɗa miki ko da yanzu kina can gidan talauci ahlil fuƙara'u Allah baku mu samu" "Bari Ummata ta kaina yau ni ABBAS zai wa tashin balagar tsintsaye" Ta ce tana kwashe komai ta faɗa mata. "Baƙin ciki ne yake cinsa ya gane ki sarai ko ni uwarki ba zai manta da ni ba bare ke, so ya yi ki zauna a ƙarƙashinsa baƙin talauci ya miki kanta" Nan suka shiga tattaunawa yadda komai zai kasance don shagali za a yi. Bayan ta kwanta ta taɓo EESHART a whatsapp ta shiga labarta mata yadda suka yi da Alhaji Tahir. Sosai ta ji baƙin cikin za ta yi aure don ita a yadda ta taya ta ta kashe aurenta so ta yi ra yi ta yawo a kwararo a ƙarshe ta ƙi auruwa amma yanzum ma ta san dai ba za ta samu kamar ABBAS ba shi ne jin daɗinta. Nana ta shiga labarta mata yadda za su tsara komai. Ko RUKY da BASEERA bata kira ta faɗa musu ba dama har gwara RUKY ita BASEERA ƴar bayan a koma gidan ABBAS ce sabon auren ba zai mata daɗi ba. Washe gari Alhaji Tahir ya kira ta ya ce su shirya su je siyan lefe waya ta yi wa EESHART dama mijinta ba ya gari ta kwaso ta taho ita ma RUKY da ta zo ta yi mamakin yadda aka yi SALIMAH ta samu miji hakan ya sa ta fara tunanin ko dai maganar SALIMAH ta tabbata da take cewa kyawawa basa kwantai. Yana zuwa ya kwashe su da motoci biyu ya zo ɗaya direba ne kawai a ciki ɗaya shi haka suka tafi sai dare suka dawo akwati dozin kaya na gani na faɗa babu abin da babu hatta manyan sarƙar gwal da ɗankunne da warwaro set uku ne a ciki, hassada sosai EESHART ta ji a ranta amma ta danne ita ma RUKY tana jin ina ma ita ce. Tun da aka ringa shiga da akwatuna Umma take murna tana carara guɗa tana ta fama ƴarta ta yi gashi ƴarta ta kerewa sa'a ita a rayuwa ƴa ɗaya ta haifa amma ta zame mata babban jari. Sosai suka rungumi juna ita da SALIMAH suna murna kamar wasu ƙawaye, Umma bata zauce ba sai da aka fara buɗe kaya ta ga tamkar za a buɗe shago. Da daddare ya kira ta a waya yana shawarta ta a kan cewa gidanta da ban za a ware mata ko kuwa za ta zauna da matansa. "Haba Alhaji ai kawai ka kwatsamu tun da ka ce kowacce da ɓangarenta, in ka ware ni ai ba za su san suna da kishiya ba gwara dai in je mu jera su ga ruwan kyau yana zuba don su san cewa ni ba kishiyarsu bace shugabarsu ce saboda ba za su iya kishi da ni ba basu da abubuwan fa za su yi kishi da SALIMAH" Sosai yake yi wa maganganunta dariya daga ƙarshe ya ce babu komai kuma za a saka komai na buƙata ba sai sun kai ko da tsinke ba. A motar EESHART da ta zo gidansu suka ɗauki katin ɗaurin aure suka yi wa kafintocin su ABBAS tsinke. Zaune yake yana danna carbi ya ga mota ta tsaya a saitinsa da yake baƙin gilashi ne kuma dai bai ɓatawa kansa lokaci wajen sanin waye mamallakin motar ba. Jim kaɗan sai aka buɗe ƙofofin biyu, ba zato ba tsammani ya ga EESHART da SALIMAH sun fito. Mamaki ya yi amma sai ya ɓoye mamakinsa suna doso inda yake bugun zuciyarsa yana ƙaruwa sai dai ambaton Allah ya sa ya ji nutsuwa ta saukar masa. "Malam ABBAS ya kake ya ƙwale-ƙwale" SALIMAH ta ce tana wani murmushin gefen baki hakan ya tabbatar masa da wata manufa suka zo don ko ranar nan ya yi mamakin dalilin zuwanta na siyan kujera sai dai ya kasa gano dalilin da ya sa take bibiyarsa. EESHART kuwa kallo ɗaya ta masa ta kauda kai gefe tana wani yatsina da taɓe baki. "Lafiya Alhamdulillahi, ƙwale-ƙwale ga shi nan an fito tun da shi ne hanyar cin abincin kuma bamu raina wa ubangiji hakan da ya bamu ba, a koyaushe mu masu godiya ne a gare shi dama ya ce fazkuruni azkurkum washkuruni wala takfurun, wato ku ambace ni zan ambace ku, kuma ku gode mini kada ku kafice mini" "Allahu akbar!" EESHART ta ce . "Yo ai ba sai ka fassara mana ayar ba mu ma ba jahilai bane" SALIMAH da ganin bai wani damu da kasancewarta a wajen ba tamkar dai ba shi ne yake cewa in babu ita ba zai iya rayuwa ba ashe dai zai rayun tun da ga shi yana lafiya babu alamar damuwa a tattare da shi harnya samu bakin magana yana faɗa musu baƙar magana wai yana godiya da matsayin da ubangiji ya ajiye shi kenan su ne basa godiya?. "Ki bashi mu wuce" EESHART ta ce tana kallonta, jakar ta buɗe ta ɗakko katin da yake gidanda mai kwalliyar ƙyari-ƙyari ta miƙa masa. Karɓa ya yi ya fito da katin ya shiga karantawa yana murmushi har haƙoransa suka bayyana. "Inyeee SALIMAH amarya ma sha Allah, Allah sanya albarka ya sa abokin zama ne kuma abokin arziƙin k... Ba ta jira ya ƙarasa maganar ba fuuuu ta tafi cikin baƙin ciki EESHART ta mara mata baya sun ga abin da basu yi zato ba. Shi ABBAS da ya fisu ma ko ɗago kai bai yi ba ya kafa idanu a kan katin yana murmushi a mugun guje EESHART ta ja motar don suna kallonsa ta gilas babu abin da ya dame shi da auren nata har ma ƙara karantawa yake yana murmushi sun ɗauka zai yaga ya shiga kuka yana roƙon ta koma gidansa. ABBAS kuwa ya ji babu daɗi da za su buɗa zuciyarsa da sun ga yadda ta yi baƙi amma ya danne hakan ne don kar ya ba haƙarsu ruwa. Suna jan motar ya yaga katin yana mai raya wa a zuciyarsa cewa haka Allah ya ƙaddara kuma shi bai isa ya canja ƙaddara ba. Ta saya dai zannuwan gadon MAMAN AFRAH masu kyau da inganci wanda basa kuɗewa kuma basa yin gashi, da turarukan wuta, da humra masu musulmin ƙamshi, sai kuma sahihin maganin sanyi da kuma kazar sababi da aka dafa mata sai daka da original man ayu mai buƙata ga lambar MAMAN AFRAH 09013181851. Ta sha tsumi ta tsumu an sha ƙunshi da gyaran gashi gyaran fata kuwa tamkar fatar jarirai haka fatarta ta dawo sai sheƙi take ga laushi. An sha biki an kashe kuɗi an gayyaci masu hali an watsar da talakawa ta shiga ta fita kaya har da wanda bata saka ba daga cikin na fitar biki haka ma uwar amarya Umma. Da daddare motoci guda talatin ne suka layu a layin gidan su SALIMAH wata motar ma mutum biyu ne ko ɗaya a ciki saboda motoci sun wadata!. Motar amarya sabuwa ce dal sai sheƙin sabunta take haka aka tafi kai amarya da ta sha ado ta yafa mayafi sai farin ciki ya hana ta sukuni. A ƙogar wani tangamemen gida tamkar unguwa guda motocinsu suka yi masauki aka wangale tangamemen get ɗin motoci suka fara shiga a laye duk yawansu amma sai da suka shige gidan duka. Part ɗin ta aka nuna musu mai gadin ne ya nuna nan ƴan kai amarya suka nufa suna sharara guɗa, ta cikin mayafi take ƙarewa gidan kallo aljannar duniya don gidan ya fi na EESHART nesa ba kusa ba. A bakin gado aka mata masauki ana ta yaba tsaruwar gidan da kayan alfarmar da aka zuba mata. Nana dai masu kawo amarya suka mata sallama suka kama gabansu masu motoci suka ɗauke su ciki har da BASEERA kuwa ta rage daga ita sai EESHART da RUKY. Tun suna jiran ango ya zo a yi siyan baki har suka fara gajiya ga shi SALIMAH ta kira wayarsa ya fi sau shurin masaƙi a rufe duka layikansa. Mai gadi RUKY ta je ta tambayo ya ce ai Alhajin tun da ya fita da safe bai shigo ba hakan ya sa ta yi tunanin ko yana tare da abokansa. Ganin goma da rabi sai EESHART ta ce ita za ta tafi da yake da motar ta ta zo sai ita ma RUKY ta ce bari ta bita ta rage mata hanya, haka suka mata sallama suka tafi amarya duk ido ya raina fata babu ango ga an zambaɗi magunguna da kazar sababi. Bayan tafiyarsu ta haura sama ta shiga ƙarewa gidan kallo ta sama, amma gidan shiru sai hasken ƙwayaye da take gani daga kowane ɓangaren guda biyu inda ta yi tunanin nan ne ɓangaren matan nasa sai kuma wani guda ɗaya da yake duhu dilim babu haske ta yi hasashen ɓangarensa ne tun da ba ya nan shi ya sa ba fitilu. Ƙasan ta dawo wai kar ya dawo ya ga bata nan ga tana jin yunwa bata ci abinci ba a cewarta sai an kawo kayan maƙulashen amarya. Bakin gadon ta koma ta zauna tare da lulluɓa mayafinta ta zauna zaman jiran ango a haka gyangyaɗi ya fara ɗaukanta tun tana gyangyaɗawa har ɗaurin ɗankwalin ya kama gabansa jingina ta yi da allon gadon bacci ya ɗauke ta tana cikin baccin ta falka duba wayarta ta yi ta ga karfe uku da rabi na dare. Sosai ta yi mamaki ganin ta kusa kwana a zaune duk ma ba wannan ba ina ango yake ya aka yi bai zo ba kuma mai ya sa wayarsa a kashe? Waɗannan su ne himilin tambayoyij da suke ƙumshe a zuciyar sabuwar amarya SALIMAH... Na rubutu yau🤦‍♀️ 10 readmore wayyo ni😫 MAMAN AFRAH 09013181851 https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 12 Sai da yamma aka sallamo Baba daga asibiti abokansa wanda suke asibitin sun yi murna sosai don a yadda ya yanke jiki ya faɗi wasu basu tsammaci zai tashi ba tare da ya samu matsalar shanyewar ɓarin jiki ba. Ko da aka dawo da shi gida mutane suka ringa tururuwar zuwa duba shi, Umar kuwa sai da aka ɗura masa maganin bacci aka samu salama gabaɗaya ya haukace musu shi sai an nemo masa matarsa sai an ɗaura musu aure. Sai da daddare Baba da Hajiya suka samu keɓewa inda ya shiga labarta mata yadda abubuwa suka kasance wato yadda ya shammaci mutane ya faɗi wanwar don dakatar da ɗaurin auren. "Ai wallahi Alhaji na tsorata sosai, duk tunanina faɗuwar gaske" "Hahaha babu wani gaske kuma babu wanda ya gane shiri na ko shi likitan ina jin dukan iska ne bai san aikinsa ba domin cewa yake ɓacin rai ne ya kawo hakan ko ubansa ne ya ɓata mini ran oho" Ya ce yana fashewa da dariya ita ma Hajiya dariyar ta yi ta ce. "Ai wallaho ta yi wa kanta kuma ta yi wa arziƙo dundu na tabbata har ta mutu ba za a samu wani mai ɗan maiƙo ya aure ta ba" Hajiya ta ce tana dariya. "Rabu fa sakarya ni ai na ji daɗin hakan, dama saboda jama'a kar a ce na karɓi dukiyarsu na kore su amma ai da tuni sun daɗe da barin gidan nan, kuma da a ce na san idan za a mata auren guduwa za su yi da tun bayan bakwai ɗin ubansu zan tarki ɗaura auren kin ga da tuni wani batun ake ba wannan ba amma yanzu ma ta kwana gidan sauƙi lokaci bai ƙure ba abu ɗaya na sani mun jefar da ƙwallon mangwaro mun huta da ƙuda su je can su gaishe da na gaba" Cewar Baba yana kishingiɗa. "Yo dama mana ai sun taimake mu sun taimaki kansu, dama in sun zauna ma za su rayu cikin uƙuba ne!." Hajiya ta ce. "Yanzu dai babu mai cewa ni na kore su za a ji da ƙafafunsu suka gudu, kuma babu mai ɗarsa zargin wahala ce ta kore su tun da ga shi ƙarewar adalci ma ɗan cikina zan aura mata, batun dukiyarsu kuwa yanzu ne zan kwanta a kan dukiyar na ci karena babu babbaka duk da dama babu abin da ya hanani wadaƙa da dukiyar, to wa ma zai tuhume ni ai dai duk duniya kowa ya sani ni kaɗai ne ɗan uwan ubansu kin ga kuwa babu mai cin gadonsu sai ni" "Gado kuma Alhaji mutuwa suka yi?" "Yo sai sun mutu duk wanda ba a san inda ya dosa ba ba a san inda zai je ba, kuma ba a san inda yake ba shi da matacce duk ɗaya! Ni nan zan tara mutane a yi musu sadakar uku da sadakar bakwai ke har da ta arba'in ma, idan shekara ta zagayo in musu sadakar cikon shekara don tabbatarwa da mutane sun mutu! Zan ce ruwa suka faɗa ya tafi da su ko gawarsu bamu samu gani ba" "Allah dai ya biya Alhajina, shi ya sa kake ƙara shiga raina kan yin kane-kane kwakwalwarka tana ja" Hajiya ta ce tana ɗora kanta a kafaɗarsa. "Musamman a kan kuɗi!" Ya ce yana farawa tare da lakato hancinta. "Inda ƙara volume, kin ga ana labarai kuma ga shi ana nuno mota ta kama da wuta" Alhaji ya ce yana maida hankalinsa ga TV. "A safiyar yau ne wata mota sharon ta samu ibtila'in kamawa da wuta, motar dai ta haya ce ta ɗakko mutane daga garin Zariya za ta ke Kano, motar tana ɗauke da mutane da har yanzu ba a tantance yawansu ba, babu wanda ya tsira gabaɗaya ta ƙone ƙurmus" Mai karanto labaran ya gama faɗa. "Allahu akbar! Rai baƙon duniya HAWWA da SABEER lokaci ya yi" Hajiya ta ce tana murmushin jin daɗi. "Allah jiƙan musulmi yara sa'i ya yi" Baba ya ce yana kallon TV amma babu wani jimami a tare da fuskokinsu. "Dama lokaci ne ya kira su ko uban me za su je yi a Kano ai shikenan" "Kin ga ni yanzu na samu abin faɗa zan tara mutane in faɗa musu jiya yarinyar nan ta ɗauki ƙaninta sun tafi Kano sun yi haɗari mota ta kama da wuta sun mutu" "Shikenan ƙurunƙus" Hajiya ta ce tana tafa hannu. Washe gari tun da aka yi sallar asuba Baba ya sa aka sanar d mutuwar a masallaci mutane suna ya masa gaisuwa gari yana wayewa aka shimfiɗa tabarmi aka zauna zaman makoki Umar kuwa sai da ya yi ƙaramar hauka. Kowa ya yi jimami har da Baba Sadiya amma a zuciyarta ta san hakan ba gaskiya bane tun da ba gawarsu aka gani ba kuma ma ta san ba Kano suka tafi ba Kaduna suka tafi. *HAWWA* Amrah ta sha ruwan mamakin abin da ta mata kuma ya sha jinin jikinta ganin HAWWA ta zama fitsararriya, sai dai ta dangana hakan da rayuwar gidan da suke zaune bayan mutuwar mahaifansu. "Ni kika mara kika hankaɗe HAWWA" ",Ni tawa fuskar ba fuska ba ce kenan, to ki dawo hayyacin ki ba zan taɓa saurara miki ba matsawar baki saurara mini ba" "Haka kika ce?" Ta ce tana tashi tsaye tana aikawa HAWWA harara. "Eh" "Mu zuba mu gani!" Amrah ta ce tana yin ƙwafa. Washe gari haka HAWWA ta shiga gyara gidan tas ta share ta yi wanke-wanke. Ruwan zafin shayi ta dafa ta yi wainar fulawa haka aka zauna Goggo ta zubawa kowa Usman sai yaba daɗin wainar yake don shi ko biredin bai ci wainar kawai ya ci da shayin da ya sha kayan ƙamshi. "Usman" "Na'am Baffa" "Zan ba HAWWA kuɗi ka kai ta za ta sayo kayan SABEER da nata sai ku biya ta kai ɗinki sannan ta siyo da dogayen riguna kafin a hankali sai ake saya musu, da kaɗan-kaɗan shi ma SABEER ɗin a yanko masa yadi da shadda duk sai ku bada ɗinkin" Wani daɗi Usman ya ji a ransa jin zai fita da abar ƙaunarsa. "To Baffa" Ya ce har ya kasa ɓoye farin cikinsa. HAWWA ma ta ji daɗin abin da Baffa ya yi murna wajen SABEER kuwa ba a magana sai tsalle yake wai zai sa kaya mai kyau tun da Abbie da Ummie suka mutu tsohon kaya yake sakawa kuma yaggagu sai dai HAWWA ta ɗinke masa da zare da allura. Tausayinsa ne ya kama Baffa da Goggo Amrah kuwa Allah ya ƙara ta yi a zuciyarta. Godiya HAWWA ta yi wa Baffa amma ya dakatar da ita ya ce ai shi Babbanta ne babu godiya a tsakaninsu. "Mun gode Baffa saura ka saka mu a makaranta" SABEER ya ce yana dariya. "Babu godiya SABEER kuma zan saka ku a makaranta kai duk wani abu da kuke buƙata da ɗawainiya da ku zan muku daidai gwargwadon samuna, ban yi alƙawarin yi muku gata kamar na mahaifanku ba kasancewarku ƴan gata kuma mahaifanku suna da dukiya amma ni ma zan yi iyar iyawata" Ya ce yana kama SABEER ya jingina shi a jikinsa. Idanun HAWWA ne ya ciko da ƙwalla, tana tuno irin rayuwar da suka yi a gidan Baba, babu tausayawa babu tausasawa babu ja a jiki tamkar wanda basu da wata alaƙa da su amma ga shi Baffa yana nuna musu su ɗin ma suna da gata yana nuna musu cewa marayu ma ƴaƴa ne saɓanin inda ake nuna musu maraya bashi da wani tun da iyayansa basa raye ya rasa komai. "Baffa in bi su mu siyo?"SABEER ya katse mata tunani. "A'a SABEER yanzu zan fita ƙofar gida wajen aiki an jima idan sun kawo maka kayan sai a ɗauko riga da wando a maka wanka sai ka fito wajen ka ga yadda kayan jikin ka suke kunya zan ji a ce ka fita waje da ƙasƙantattu haka" Ya faɗa yana shafan kansa. Tsalle ya yi yana ta murna. Hijabi HAWWA ta saka ta fito daga ɗaki. "Amrah ɗakko mata hijabi mana dogo wanda zai rufe mata kayan jikinta" Baffa ya ce yana kallon yadda hijabin jikinya ya tsufa ya yaƙune yana ta tunanin wai ƴar gidan ƴar uwarsa ce wannan da kayan kamar almajira rayuwa kenan duk yadda ka kai ga samun gata don iyayanka suna raye ne amma da zarar ƙasa ta rufe idanunsu sai dai ka sa ido ka yi kallo saboda ba kowa bane bayan ransu zai mayar da kai mutum wani ma dama yana maka abubuwa ne saboda idanun mahaifanka da zarar sun gusa sai dai ka ga ana yi. Cike da ladabi da biyayya ta amsa wa Baffan ta shige ɗaki a ranta tana ƙunƙune ba don Baffa bane ko ana ha maza ha mata babu wanda ya isa ya juya ta. Hijabin ta ɗakko mata ta karɓa ta cire na jikinta tana murmushi ta ce "Ya mini kyau Aunty Amrah" Wani takaici ne ya turnuƙe Amrah ganin yadda hijabin jalbab ɗin ya yi wa HAWWA mugun kyau tamkar dama don ita aka yi kalar yadin ash. Murmushin yaƙe ta saki ta ce "Ai kuwa dai ya karɓe ki ƙanwata kin fito fes abinki" "Ni ma zan sayo irinsu idan muka je kasuwar" Ta faɗa tana murmushi tana kuma fakar idanun su Baffa ta taɓewa Amrah baki, sosai Amrah ta ji tamkar ta tashi ta hau HAWWA da duka. Ita kuwa Goggo bata kawo komai a ranta ba kasancewar ta san HAWWA har zuciyarta take magana saɓanin Amrah da take abu cikin kissa saboda ganin Baffa yana wajen bata san cewa ita ma HAWWA ta fara yi wa Amrar abinda take ganin za ta ƙwatawa kansu ƴanci ba ita da ɗan uwanta. Sallama HAWWA ta musu ta bi bayan Usman Goggo tana musu a dawo lafiya SABEER yana ɗaga mata hannu har da bata saƙon sweet Amrah kuwa dama tuni ta cikawa rigarta iska ta shige ɗaki. "Wannan yarinyar ta zo gidan nan don ta kashe mini kasuwa, bana jin akwai wani ɗa namiji da yana ganin tsinanniyar yarinyar nan zai zo gare ni har ya iya furta mini kalmar so? Ga ta haɗaɗɗiya ga kyau ga addini ga nutsuwa ta fi ni komai gaskiya sai na tashi tsaye a kan yarinyar nan in ban lallashi ziciyata ba sai na kwaɓe mata kyakkyawar fuskar nan tata da asid ya ƙone fuskar ta dawo abin tsoro" Amrah ta ce a zuciyarta tana jin tsanar HAWWA a ranta musamman da Baffa ya bata kuɗin sayayyar nan sai ta ki kenan yanzu ta zama tamkar kishiyarta za a ke musu abu tare bare ma da ta ji HAWWA tana cewa za ta saya irin hijabinta wato gasa ma za ta tsaya yi da ita. "Don ma dai mazan basa gabana ina kula su ne don nake tatiƙe musu aljihu, ga wanda zuciyata can ta mutu a kansa wato kyakkyawan matashi wanda yake ji da lokaci son kowa ƙin wanda bai samu ba haƙiƙa in na mallaki ABBAS a matsayin miji kuma na dace yana matuƙar ƙaunata to ni fa na kasa na sayar" Ta ce tana yin juyi a katifarta tare da kamo hotonsa wanda ta ɗauke shi yana jingine a jikin banci ba tare da ya sani ba. "Yaushe ne zan furta maka kalmar so, kalmar nan da ta daɗe tana yawo da addabar zuciyata, son ka wanda na kamu da shi tun ban san mene ne so ba, ma yi matuƙar baƙinciki a shekaru biyar da suka wuce lokacin da sanarwar ɗaurin aurenka ta same ni na yi baƙin ciki na yi kuka na shiga damuwa ganin za ka auri wata ba ni ba sai dai yanzu ina cikin tsananin farin ciki jin ka rabu da matarka sai dai ba a nan gizo yake saƙar ba shin za ka so ni? Har ka yarda mu yi aure mu rayu a inuwa ɗaya? A duk ranar da na furta kalmar so a gare ka kuma ka aminci sai na zubar da ruwa a ƙasa na sunkuya na kafa bakina na shanye shi tas" Ta ce tana shafa hoton nasa tana jin wani shauƙi na soyayya tana sawa a ranta a wannan gaɓar dole za ta yi iya yinta don ganin ta cim ma burinta muradinta ya tabbata na zama matar ABBAS. HAWWA a waje ta samu mashin ɗin Yaya Usman ya ajiye shi, shi kuma yana can tsaye yana magana faɗa-faɗa. " ABBAS to ni na ce ka ba Baffa kuɗin cinikin jiyan a kan mai za ka bashi, ai ka san dai ni ne magajinsa a kafintocin nan kuma komai a hannuna yake mai ya sa kai ba za ka bayar da komai ba gare ni kai wa ka fi? Shegen shishshigi da neman wuri don Baffa yake ganin riƙon amanarka dama kullum yana yabonka so dai kake ya ɗauki matsayina ya baka to wallahi baka isa ba matsayina ya fi ƙarfin takawar ƙafarka" Ya ce yana haki wasu daga gefe suna ta bashi baki amma tamkar zuga shi suke. "Haba Usman mene ne na ɗaga jikiyoyin wuyan ni fa kuɗin nan ba cin su na yi ba kuma ba nawa bane laifi ne don na ba Baffa, kuma ka saka ranka a inuwa ni ba zan taɓa karɓe matsayinka ba kana matsayin ɗan mai wurin nan baki ɗaya mu ai cin arziƙi muka zo" "Uban waye da ya ce ka isa ka karɓe matsayinaa munafukin banza da wofi... "Dakata! Usman wasa ya yi wasa amma ban da tsikarin uwar miji, ka mini komai ka ce mini komai amma ba zan ɗauko cin mutunci ba na tsani a kirani munafuki domin ba na munafurci saboda munfukin ko a cikin wuta yana ƙasan kafiri saboda girman munafurci don haka ka kiyaye bana son a kira ni munafuki ko a zagi iyayena saboda iyaye su ne gaba da komai iyaye su ne jigon kowa duk wanda ya rasa su ya yi kuka don haka na san muhimmancin su bana so a zagar mini su" "Sosai HAWWA ta ji abin da Yaya Usman ya yi wa wanda ya kira da suna ABBAS ya taɓa mata zuciya, saboda bata ga laifin da ya yi ba kuma jiya a gabanta ta ga ya kawowa Baffa kuɗin ya ce ga cinikin amma Baffan ma bai karɓa ba bata sani ba ko bayan ya fita ba ya bashi, yadda ABBAS ɗin ya nuna iyayansa suna da muhimmanci abin ya burge ta sosai saboda ko ita a duniya ta ƙi jinin a zage ta ko a wulaƙanta mata iyaye tun suna raye bare yanzu da basa duniyar sai take jin abin ya ƙara shiga zuciyarta ya zauna daram! Sakarai ne zai kasa sanin muhimmancin iyaye, uwa ita take ɗaukan ciki ta raina ta sha wahala, ya zo ta sha wuya a naƙuda har ta haihu ba a nan abin ya tsaya ba ta shayar ta ba ƴaƴa kulawa har su girma aiyuka uwa suna da yawa haka uba komai shi ne ciyarwa shayarwa tufatarwa ɗaukan nauyin karatu duk mahaifi ne komai in babu sai dai a faɗa masa, tabbas wanda bai san muhimmancin iyaye ba ko bai ɗauke su bakin komai ba ya yi babbar asara. Cikin sanyin jiki ta fara taka ƙafarta a hankali ta nufi wajensu, Yaya Usman bai lura da ita ba idanunsa sun rufe sai masifa yake shi ya tsani ABBAS ya ba Baffa kuɗi saboda ya fi so kuɗaɗe su biyo ta hannunsa ya ci karensa babu babbaka ya ba Baffa abin da ya samu, shi kuma Baffa ba ya tuhumarsa ko da kuwa kuɗin bai kai yadda ya tsammata ba kasancewar Yaya Usman yana nunawa Baffa shi mutumin kirki ne don ya yarda da shi amma a bayan idanunsa shi kura ne lulluɓe da fatar akuya. Fuskar wanda aka kira da suna ABBAS ta kalla cikin sanyin zazzaƙar muryarta mai daɗin amo a kunnen mai sauraro ta ce "Ka yi hakuri" Ta faɗa tana haɗe hannuwanta biyu wuri guda, saboda yadda ta ga yana magana cikin nutsuwa da kuma nuna abin da aka faɗa masa ya masa ciwo musamman zagin sai ta ji tamkar ita aka zaga sannan sai kuma da aka kira shi munafuki ya musanta hakan har yana nuna ƙyamar munafurcin yana kuma ambata makomar munafukin sai ta ji ya burge ta tana son mutum wanda ya san darajar kansa a rayuwa. Ƙurrr ya ɗago wannan kyawawan fararen idanunsa masu kallo tamkar na soyayya ya zuba mata su tare da son gaskata cewa shi ɗin take ba haƙuri a bisa laifin da ba ita ta masa ba, shin mai ya ja hankalinta har ta so bada haƙurin?. Yaya Usman kuwa maganarta ce ta ankarar da shi zuwanta wanda fitar furucin daga bakinta ya zuwa kunnuwansa sai ya ji tamkar an zuba masa dalma, wani turnuƙuƙin kishi ya yi wa zuciyarsa dabaibaiyi, yana hasko nan gaba kaɗan za ta zama matarsa kuma mallakinsa tabbas ba zai so ba kuma ba zai lamunci ta yi wa wani ɗa namiji magana ba bare har wani namijin ya mata. Yana da kishi matuƙa a nashi tsari da halayya tun yana ƙarami ya ƙi jinin su yi abu iri ɗaya da wani sabo da kishi irin nasa bare kuma yanzu da ya girma ya mallaki hankalin kansa kishin ma a kan wacce yake muradin ta zama mata kuma uwar ƴaƴansa. Wata irin tsanar ABBAS ce ta shiga zuciyarsa ta yi masauki, a ƙufule ya ɗago ya kalle ta ya ce "Wa kike ba haƙuri a tsakaninmu" HAWWA da har lokacin hannuwanta suke a haɗe ta lunshe kyawawan idanunta ta buɗe a hankali ta ce "Haba Yaya da wannan nake mana ai kai ne ka masa laifi jifansa da ka yi da kalma marar daɗi, bayan laifinsa bai kai matakin hukuncin da ka ɗauka ba wato zagi... "Ya ishe ki HAWWA, yaushe na zama sa'anki za har za ki nemi nuna mini abin da ya dace in yi... Fitowar Baffa daga gida ne ya dakatar da Yaya Usman daga dokin zuciyar da ya hau cikin iya kissa da wayincewa ya saki murmushi tare da dafa kafaɗar ABBAS ya ce "Ina son riƙon amanarka ABBAS baka yadda ka ci ko da ƙwandala ba in har ta kasance ba mallakin ka ba ce ka cigaba da tsayuwa a kan turbarka lallai duk wanda hulɗa ta haɗa ka da shi ba zai so ka suɓuce masa ba" Ya ce yana dariya har haƙoransa suka bayyana. ABBAS ma murmushin ƙarfin halin ya saki don inda sabo ma saba da halin Yaya Usman na nuna halin rashin kirki a bayan idon Baffa amma a gaban idanunsa babu wanda ya kai shi kirki da girmama mutanen da suke ƙarƙashin su. Cikin halin dattako Baffa ya ƙaraso gabansu fuskarsa cike da alamar abin da ya gani ya faranta masa ya zo, miƙa hannu ya yi ya dafa ABBAS da hannun dama hagun ɗin kuma ya dafa Yaya Usman ya ce "Haƙiƙa ina alfahri da dukan ku, kamar yadda kake yabon ABBAS kai ma haka kake ɗana haƙiƙa na yi sa'a da samunku a matsayin jigon jingina wanda a zamanin nan ba kowa bane za ka ɗora shi a kan kasuwanci na harkar kuɗi kuma ya riƙe amana ba tare da ya cuce ka, tabbad kuna ƙyamatar cin haramun wanda haka ya dace kowane musulmi ya yi" Su duka murmushi suke daga ABBAS har Yaya Usman, ban da HAWWA da take tsaye sake da baki tana mamakin abin da Yaya Usman ya yi lokaci guda ya sawaya tamkar hawainiya daga tafiya irin ta ƙosasshen zaki zuwa tafiyar hawainiya wato yana cikin faɗa da tada jijiyoyin wuya sai kuma ya yi sanyi ƙalau tamkar ƙanƙara. Kallon fuskar ABBAS ta yi tana son gane wani abu wato dalilin da ya sa shi ma ya sakar da maganar ya goyawa Yaya Usman baya, wato ya bi yarima ake shan kiɗa maimakon ta ga ya cigaba da nuna ɓacin rai kamar yadda yake sai ya sakar shi ma ya nuna babu abin da yake faruwa kuma hatta sauran mutanen da suke wajen babu wanda ya tofa wani abu makamancin wannan. Suna haɗa ido sai ta ga ya faɗaɗa murmushinsa tare da ɗan rausayar da kai yana son nuna mata hakan ba komai bane, ganin dai tana ta masa kallon mamaki sai ya kanne mata ido ɗaya da sauri ta juya har tana harɗewa ta bar wajen wanda hakan sai da ya sa dariya ta kusa suɓucewa ABBAS ɗin ganin ta tsorata kuma ta ɗauki kashe idon da ya yi a matsayin wani abu wanda shi kuma ya yi hakan ne don ya ƙara nuna mata komai normal kar ta damu. "Hauwa'u" Baffa ya kira ta. "Na'am Baffa " Ta ce tana juyowa duk ta duburburce. "Ku je ku dawo ko SABEER yana can yana jiran dawowarku ya matsu a masa wanka" Da to ta amsa sakin kafaɗar su ABBAS ɗin Baffan ya yi Yaya Usman yana murmushi ya juya ya nufi wajen machine ɗin, Baffa wajen kujerarsa ya wuce ya zauna ABBAS kuma ya cigaba da buga hannun drower a jiki. Yaya Usman sai da ya tada machine ɗin HAWWA ta hau suka zo giftawa ta gaban ABBAS wani kallo Yaya Usman ya aika masa irin na da ni kake zancen. ABBAS kuwa kallo ɗaya ya musu ya ɗauke kansa ya cigaba da abin da yake amma ko ba komai ya ji daɗin abin da HAWWA ta masa a ƙalla dai gata yarinya amma tunaninta ya fi na Yaya Usman ɗin ta fi shi hangen nesa da sanin darajar ɗan adam, karon farko da ya ji wata mace ta burge shi bayan SALIMAH amma ba da so ba, burgewa kawai. *SALIMAH* Tun karon farko da ta farka babu wani bacci da ya yi nasarar ɗaukanta ko da kuwa ɓarawo ne, saƙa da warwara su ne abin da ta fi yi ta rasa wane za ta ɗauka daga cikin saƙar jakin da zuciyarta take mata. Ga shi kiran duniyar nan ta yi wa Alhaji Tahir amma wayarsa a kashe, ga shi da tsakar daren nan bata so ta kira kowa haka ta ɗauki na annabawa har aka faramkiran assalatu, cike da takaici ta sakko daga kan gadon tana duba iya haɗuwa da tsaruwarsa haɗe da lallausan bedsheet da ta yi oder wajen Maman Afrah amma a ce wai ita kaɗai ta kwana a kan gadon babu ango? Ita ɗin ma da ta kwana a kai babu wani bacci mai daɗi tunani bai bar zuciyarta ta huta ba. Wucewa ta zo yi ta gaban madubi kallon kanta ya yi a ciki sai da ta ba kanta da kanta tausayi yadda fuskarta ta sha make up amma duk ya caɓe a banza ango bai gani ba ɗaurin ɗankwalin da mai ɗaurin ɗankwali ta ɓata lokaci wajen tsantsara mata shi amma ya tashi a banzar bazara, a ce wai ko kayan bacci bata saka ba da leshin zuwa gidan mijin ta kwana ba ma wannan ba a ce tana amarya amma ko kazar amarci babu haka ta kwana da yunwa. "To ina angon ma mai kawo kazar bare ita kazar?" Wani sashe na zuciyarta ya jefo mata tambayar da ita kanta bata san amsarta ba. Ganin eye lashes ɗin guda ɗaya ya farƙale ya mayar da ita kamar aljana haka ta saka hannu ta cisge ko zafin cirewa bata ji ba ta yi cilli da shi ta bar gaban madubin saboda kallon kanta a madubi yana ƙara ɗago mata da ɓacin rai. Tana tafiya a tangamememan falonta tana kallon haɗuwa da kayan alatun da aka kashe kamar ba gobe, tunanin ranar farkonta a gidan ABBAS ya faɗo mata, a ranar sai da ƙawayenta suka yanka masa kuɗi mai tsoka ya bayar matsayin siyan baki duk da talaucinsa ya shigo da kaza da lemuka daidai ƙarfinsa yana ta nan -nan da ita yana lallashinta ba ya ma ganin kyara da nuna masa tsanar da take yi, amma sai ga shi yau an mata wulaƙanci iya wulaƙanci am bar ta babu ango abin takaicin ma bai ce mata ga uzurinsa ba sai ka ce wata marar galihu ai ƴan magana suka ce wai amarya ko ta kyankyaso ce ana riɗin ta. Da wannan takaicin ta ƙarasa bayin tana ganin yadda ya gaji da haɗuwa alwala ta yi ta fito ta yi sallah tana jin ƙugin cikinta haɗe da ciwon marar magungunan da ta bankamawa kanta. Hannu ta sanya ta dafe goshinta tana jin tamkar ta rushe da kuka amma sai ta dake ta tashi ta bar sallayar a wajen ko arziƙin linkewa bata samu ba. Ganin shida da rabi sai ta nufi saman bene ta je windown ta tsaya tana ƙara ƙarewa gidan kallo, tabbas gida ya amsa sunansa gida musamman yauzu da yake da safiya ce ba dare ba sai ta ga ta fi ƙarewa komai kallo yadda ya kamata. A yadda gidan yake bata taɓa zato za ta zama ɗaya daga cikin wanda za su zauna a matsayin matar gidan ba ita ko a ƴar aiki bata taɓa zaton zuwa gida irin wannan ba amma sai ga ta a matsayin matar gidan. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana sakin labulen ta bar wajen, har ta juya za ta tafi ta dawo ta ƙara taɓa labulen tana ƙara jin ƙwari da nagartarsa . 'Lallai labulen nan yana da inganci tabbas maman afrah kayanta suna da kyau' Ta ce a zuciyarta tana barin wajen ta shiga ƙarewa ko ina kallo ganin bata gane wasu abubuwan saboda yunwa sai ta sakko ƙasa tana tunanin inda za ta samu abinci, ƙofar da take tunanin nan ne kicin ta nufa ta shiga komai tamkar a ƙasashen ƙetare murmushi ta saki ta fito ta nufi inda take tunanin nan ne a matsayin store tana buɗewa ta ga kayan abinci lodi guda katan ɗin indomie ta buɗe ta ɗakko guda biyu ta fito ta dawo kicin ta kunna gas ta ɗora ruwa yana tafasa ta zuba indomie ɗin, haka ta dafa ta da gishirin ta ta juye a plate. Har za ta ɗakki ƙwai ta soya sai ta ji tana jin jiri ba za ta iya soyawa ba haka ta kashe gas ɗin ta fito daga kicin ɗin a falo ta zauna a ƙasan capet ko kan dining bata yi tunanin hawa ba saboda yunwa uwa uba babu ango bare ake bata a baki ita ma tana mayar da martani. Har sha ɗaya a safe amma babu ango babu dalilinsa kuma har lokacin ta kira duka layilansa a kashe hatta whatsappa ma da ta duba shi ba ya hawa, ita kuma bata son faɗawa kowa a mata dariya Umma ta so faɗawa amma kuma ta kasa saboda bata son saka mahaifiyarta a damuwa tun da ita kaɗai ta rage mata. Saboda ta san duk wanda ya ji abin zai ji wani bambarakwai. Kiran Ummar ta yi don su gaisa ringin ɗaya biyu Umma ta ɗaga cike da zumuɗi. "SALIMAH amarya" Ta ce bakinta har kunne tana samun wuri ta zauna saboda a yi maganar a nutse ta san akwai labarin yadda ta ga gidan nata. "Na'am Umma ina kwana" "Lafiya ƙalau ya kwana baƙunci" "Alhamdulillahi" "Oh kuma maimakon ki buɗe baki tiryan-tiryan ki hau bani labarin gidan ƴan gayu sai kike wani jan aji SALIMAH ko angon bai fita ba dama ai na san yanzu ba kasafai zai ke fita ba shi da ya ajiye amarya, ai jiya ƴan kai amarya har sai da na gaji da labarin yadda ake faɗa mini gida ya ƙawatu" Umma ta ce tana dariya. "Umma ai abin sai wanda ya gani" Ta ce cikin ƙarfin hali don kaɗan kuka ya ƙwace mata gani ita angon ma ko ƙeyarsa bata gani ba. Nan dau suka taɓa hira suka yi sallama ta yi jigum bata son faɗawa kowa. Wasa-wasa har kwana biyu babu ango kuma babu wanda ya zo ya ce mata wani abu daga cikin kishiyoyin nata tana so ta je ta tambaye su ko ina mai gidan amma rana tsoron raini kuma hakan ma tamkar zubar da ajinta ne a ce tana amarya bata san inda ango yake ba sai ta je ta tambayi kishiyoyi. Sawunta biyu wajen mai gadi amma yana tabbatar mata cewa tun ranar ɗaurin auren Alhajin bai zo gida ba. Haka za ta koma jiki babu ƙwari a kwana na uku ne ta dokawa RUKY kira ta ce ta zo tana son ganinta da yamma kuwa sai ga ta ta zo, amma sai ta kasa faɗa mata ganin tana ta yaba kyan da ta ƙara amma ta ce ta ga ta ɗan rame amma hakan ba ya rasa nasaba da shan amarci da ake yi. "Kai SALIMAH kin samu duniya saura ƙiyama kai Allah ya saka mu a damshinku" Ta ce tana kai lomar jalof ɗin taliya. Murmushin yaƙe da ya fi kuka ciwo ta yi ta ce "Abin ba a cewa komai" "Wai ya kyan magungunan na da kika babbaka?" "Suna da mugun kyau kuwa" Ta samu kanta da kwararo ƙarta tun da ita mijin ma bata gani ba bare ta tabbatar da kyan magungunan. "Kai ai kuwa in zan yi aure irin su zan saya" "Ai kuwa" Ta ce tana damƙe baki jin mararta ta murɗa mata. Hannu ta kai ta dafe wajen tana yamutsa fuska, ta san tarin kwamacalar magungunan da ta sha ne suke tambayarta. "Inyeee amarsu ko dai har ango ya yi ajiye ne? In k,uma priod ne zai zo gaskiya kar ya zo ya kawo cikas ana tsaka da cin duniya da tsinken tsire" Ta ce tana ɗaga ruwan roba ta kwankwaɗa. Murmushi kawai ta yi. "Ai dai kin cire inplan ɗin nan shi ya sa wataƙila ciki ne ya shiga, kin san ai dama an ce inplan wankin mara yake shi ya sa ana cire shi ake samun ciki" Ta ce tana tuno ranar da ta raka ta asibiti aka cire mata saboda kar ta haihuwa a gidan ABBAS ta saka shi dama. "To sai dai abin da gogan nawa ya ce" Ta ce rana ƴar dariyar da bata wuce leɓenta ba. Haka suka sha zancen su kafin ta mata sallama ta tafi. Da daddare ta watsa ruwa ta saka doguwar rigar bacci tana kwance ta yi nisa cikin tunani tana tuna yadda duniya ta juya mata baya lokaci guda, dama mace farin cikinta da walwalarta yana damfare ne a wajen mijinta da ta rasa hakan sai ta ji duk ta rasa mai yake damunta. Ƙaran wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula banza ta yi da wayar har ta gama ringin ta katse, a karo na biyu wani kiran ya sake shigowa wani gajeran tsaki ta yi tare da miƙa hannu ta ɗakko wayar tana rayawa a ranta ko waye sai ta sauke ɓacin ranta a kansa, sai dai mai? Tana duba fuskar wayar ta yi tozali da suna angon nata yana wayo a kan screen ɗin wayar idanunta ta ƙara warewa ta tabbatar da shi ɗin ne da sauri ta tashi zaune ta danna ok tare da kara wayar a kunnenta, tana jin wasu tambayoyin da ta shirya domin yi masa su suna bijiro mata, ina yake tsawon kwanaki uku, mai ya sa wayarsa a rufe kuma mene ne dalilin wofantar da ita a matsayinta na sabuwar amaryar da ya ce ta fiye masa budurwa a matsayinta na bazawara... *Gabaɗaya littafin RUƁAƁƁIYAR IGIYA book 1 za ku karanta a free wato kyauta, idan mun gama book 1 za mu yi book 2 wanda shi kuma zai kasance paid book wato littafin kuɗi, wanda yake da hali kuma yake da buƙata* . NGD maman afrah🥰 09013181851 [1/11, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 13 *ABBAS* Tun da HAWWA ta bashi haƙurin nan ya kasa mantawa da abin da ta masa, domin wannan abin da ta yi ya nuna ta san kima da muhimmancin ɗan adam wanda ba kowa ne ya san hakan ba bare har ya bada haƙurin laifin da ba shi ne ya yi ba, galibin mutane ko da a ce su suka maka laifi to baka isa su ce ka yi haƙuri ba. Wasu suna ganin hakan ci baya ne yayin da wasu suke ganin wanda za su ba haƙurin bai isa su furta masa kalmar haƙurin ba kuma ba komai ne yake saka hakan ba illa girman kai. HAWWA ya furta hakan a fili yana son sanin dalilin da ya sa bata zama mai girman kai da ɗagawa ba irin na wasu ƴan matan zamanin da aka fi samu yawanci idan suna daidai shekarunta ake samun su da gigiwa rawar kai da kuma raini amma kuma sam ita yanayinta ya nuna ba haka bane. "ABBAS yarinyar nan ta baka haƙuri ne kasancewar Yayanta ne ya maka laifin ba don wani abu ba" Wani sashe na zuciyarsa ya kissima masa hakan. Iska ya fesar daga bakinsa yana mai son mantarwa da duk batun ta dama kawai ta burge shi ne sannan haƙurin da ta bashi ya wanke masa kaso mafi yawa daga cikin ɓacin ran da Yaya Usman ɗin ya saka shi ba tare da wani ƙwaƙƙwaran laifi ba bayan yana ganin za su yi sa'anni da Yaya Usman ɗin tun da a ƙalla shi ma ba zai wuce shekaru 30 ba. Juyi ya yi tare da miƙa hannu ya janyo katin ɗaurin auren SALIMAH wanda suka kai masa ita da EESHART fito da shi ya yi yana ƙare masa kallo musamman wurin sunanta da na angon nata da kuma date ɗin ɗaurin auren ma'ana ranar da aka ɗaura. Shiru ya yi yana ta tunanin shikenan SALIMAH ta yi aure ta bar shi ta auri zaɓin ranta mai kuɗi kamar yadda take da buri shi ta bar shi saboda talauci da halin babu. Motsi ya ji da sauri ya tura katin ƙasan latifarsa ya kwanta lif. Mama da sallama ta shigo ɗakin yana daga kwancen ya amsa mata wuri ta samu ta zauna ta ce "ABBAS" "Na'am Mama" Ya ce yana tashi zaune amma ya kasa haɗa ido da ita saboda ba ya so ta gane halin da yake ciki ya san kuwa kallo ɗaya za ta masa ta gane. "Mai yake damunka kwana biyun nan? Kai da ka daina saka kan ka ciki damuwa amma yanzu kake so ka mayar da kan ka ruwa? " Ta jefa masa tambayar tana tsare shi da ido. "Mam... "SALIMAH ce ko?" Ta katse masa hanzarin kiran sunanta da ya fara. Idanunsa ya ɗago ya sauke a kan fuskarta yana jinjina yadda aka yi ta gane damuwarsa bayan ya san ya sanar da ita cewa shi yanzu ko tuna SALIMAH ba ya yi amma kuma shi kansa bai san ya aka yi daga ranar da ta damƙa masa katin ɗaurin auren sai kawai ya ji ya fiya tunaninta tabbas so ba ƙarya bane kuma ba ya fita ya bar zuciya sai dai ya lafa. "Na ce SALIMAH ce ?" Kansa ya sunkuyar don ba zai iya mata ƙarya cewa ba ita ba ce. "To kuwa ka sani haramun kake aikatawa ABBAS tun da yanzu ta zama mallakin wani dole ka yi yaƙi da zuciyarka na ganin ka ƙauracewa tunaninta " 'Mama ya aka yi kika sani?" "Ai na ga katin ɗaurin auren tun ranar da ka shigo da shi a hannunka na lura kana cikin damuwa shi ne da ka tafi masallaci na buɗe na gani, kuma na san babu mai yin wannan ɗanyan aikin sai SALIMAH wato ta ɗakko ƙafa ta kai maka katin ka karɓa ka ga yanzu burinta ya cika ta mayar da kai tuwa wato cikin damuwa" Ɗagowa ya yi yana kallon Mama a gefe ɗaya yana raya cewa kenan SALIMAH da biyu ta bashi katin ɗaurin aurenta shi duk a tunaninsa don kawai ya gani ne amma in haka ne ba ƙaramar ƙiyayya take masa ba. Hannu ya kai ƙasan katifa ya zaro katin ya yayyaga shi tare da masa gutsin-gutsin. " Da ya fiye maka dai tana can ta buɗe babin sabuwar rayuwa ta barka da dakon so ita kuma cikin walwala da jin daɗi da kuma daula, ya kama ta kaima ka fitar da matar aure ka yi aurenka hakan zai sa damuwar da kake da ita ta ragu ko da ba duka ni na rasa ma ya aka yi ka koma ruwa" Shiru ya yi . "Da kai nake magana fa ABBAS" "Mama ni ina zan samu wata matar aure ni ai na gama aure a duniya!" "Baka isa ba ABBAS" Mama ta yi maganar a zafafe cikin hargowa. Shi kansa sai da ya tsorata da yadda ta masa maganar har ya rasa abin cewa. "Saboda wata wacce bata damu da kai ba babu yadda za a yi ka ƙi yin aure' "To Mama ki yafe mini Allah huci zuciyarki, ni kawai ina ganin na gama so a rayuwata ba zan ƙara soyayya ba matan ma tsoronsu nake" "Sai ka yi aure ABBAS ai a duniya ba a taɓa zama ɗaya kuma duk lalacewar zamani ba a rasa na kirki tuni idan ka saka tunaninta a kwandon shara za ka samu wacce kake so take sonka kai har ma ku zo ku yi rayuwa ka ji tamkar baka taɓa sanin wata SALIMAH ba" Jin ta kawai yake amma ya san da wuya kuma zai yi wahala hakan ya kasance. "Tun da kana ganin kai ka gama zaɓin mace a duniya, to ni zan zama maka matar kuma ba zan maka zaɓen tumun dare ba, don aure kam babu fashi sannan ba gudu ba ja da baya!" Tana gama zuwa nan a maganarta ta tashi fuuuu ta bar ɗakin don tana ganin in har bata zage dantse ba to tunani zai yi tafiyar ruwa da hankali da tunanin ABBAS!. "Da kallo ya bi ta tamkar wani sakarai, ji yake gabaɗaya Mama ta hargitsa masa tunani da lissafi, shi da a son samunsa ne ba zai ƙara yin aure ba gwara ya ringa azumi saboda ya yi wa mata kuɗin goro tun daga kan SALIMAH ya san dai an ce zuciyar mace( SADIYA ABDULRAZAƘ) Tana da tausayi da rauni amma dai ban da ta SALIMAH. Da a ce SALIMAH tana da tausayi da bata guke shi saboda talauci ba amma ya fawwalawa Allah komai kuma ya sa a ransa zai karɓi zaɓin mahaifiyarsa da hannu bibiyu wataƙila ya dace wataƙila ya samu mai share masa hawaye wataƙila ba maye gurbi ba har ma sai ta fi SALIMAH matsayi a wajensa sai dai shin wace ce wannan? Wace mai baiwa da sa'ar ce za ta tsinci dami a kale?!. *SALIMAH* Hannunta har rawa yake wajen riƙon wayar da ta kara a kunne, zuciyarta tana azalzalarta a kan tambayoyin da suke ƙunshe a birnin zuciyarta wanda take tunanin ta inda za ta fara jero masa su, don ba za ta iya jira har sai ya dawo gida ba ko ma a ina yake dole ta fallasa masa asirin zuciyarta na ɓacin ran da ta ƙunsa kuma ta yi dakonsa tsawon kwanaki uku ragas. A ƙufule ta yi niyyar zayyano masa laifinsa don ta ji ko zai yi ƙarfin halin kare kansa? Domin ta yi alƙawarin sai dai a yi duk wacce za a yi amma ba za ta saurara ko ta lallashin zuciyarta ta bi abin a sannu ba. Sai dai me? Kalaman da Alhaji Tahir ya feso mata su ne suka sa ta guntse nata da ta guntso za ta amayar masa. "Ki zo ɓangarena yanzun nan bana son ɓata lokaci, minti biyar kacal na baki!." Yana gama faɗar hakan ƙit ya kashe wayar ba tare da ya jira cewar ta ba, dama ya yi maganar ne bisa bada umarni ba wai neman shawara ba. Da kallo ta bi wayar bakinta a sake tamkar yawu zai zubo mamaki al'ajabi game da mutuwar zaune su ne suka taru suka saka ƙasusuwan da suke ilahirin jikin SALIMAH yin mutuwar kasko. Zuciyarta tana harzuƙata a kan cewa ya raina mata wayo game da rainin hankali gabaɗaya ma ya raina mata ajawali ita ɗin SALIMAH da maza suke buri da fatan su mallaka don su same ta yake neman buɗaɗa mata ƙasa a idanu? Ita SALIMAH da yake kaffa-kaffa da ɓacin ranta yake rawar ƙafafu a neman aurenta ita zai wa haka, ita SALIMAH da take bada umarni a gidan ABBAS kuma ABBAS ya bi ba tare da musu ko gajiyawa ba kuma ko da ita ce ta yi laifi sai dai a bi abin da take so amma yau ita aka yi wa laifi kuma ake bata umarni cikin halin ko in kula wato an dake ta an hanata kuka. Bayan umarnin da aka bata na zuwa ɓangaren wai har da iyakance mata lokaci, a matsayinta na sabuwar amaryar da bata tare da ango ba bare ta yi tunanin har an ci moriyar ganga ne za a yada korenta. Wani ƙunci ne da takaici ya cika mata zuciya wai ita ce ma za ta je part ɗinsa tana ganin wannan raini zai ja mata a wajen abokan zamanta wanda tsawon kwanaki ukun nan babu wacce ta yi tozali da ita. "Kawai ki je a yi wacce za a yi tun da dai haka ya zaɓa ke kuwa kar ki raga masa a gaban uban kowa ki faɗi abin da yake ranki" Wani ɓangare na zuciyarta ya bata wannan shawarar. Ƙafafinta ta sakko daga kan gadon ta ɗauki takalmi plat ta saka tare da ɗora hijabi a kan rigar baccin jikinta. Ƙofar ta buɗe ta fito tana takawa tana jin yadda zuciyarta take zugi har wani ruwan hawaye yana taruwa a idanunta bayan hannunta ta sa ta goge wanda ya gangaro tana tafiya tana ƙarewa girma da ƙawatuwar tankameme kuma tamfatsetsen gida mai laƙabi da aljannar duniya sai dai ga ta a cikin gidan amma kuma a iya kwanani uku kacal ranta yana suyar da ta manta tsawon lokacin da ta ɗauka ranta bai ɓaci haka ba. 'Dama matan masu kuɗi ne suna shiga ɓacin rai? Ai ni na ɗauka basu san wani kalma mai suna damuwa ko ɓacin rai ba, a nawa zaton talaka shi ne mai damuwa saboda talauci ashe dai kowa yana da damuwa ko dai a kaina ne hakan ya faru?' Ta tambayi hakan a zuciyarta lokacin da ta zo tangamemiyar haɗaɗɗiyar ƙofar da za ta sada ta da falon Alhajin don part ɗin ya fita da ban da sauran duka ukun iri ɗaya ne amma ban da nashi da zubin ginin ma ya sja bamban da sauran. Idanu ta runtse tana damƙe fatar bakinta da haƙoranta, so take ta danne ɓacin ranta ta yi ƴar kissa ko yaya ne amma ina! Sai ta ji ba za ta iya ba dole ta nuna masa kuskurensa wai ita ce ma za ta je turakarsa ai ko da a ce a can za su kwana to ya ci a ce shi zai zo ɓangarenta da kansa sannan ya faɗa mata dalilinsa na ɓatan dabin da ya yi tsawon kwanaki uku tare da lallashinta da bata haƙuri in ya so idan ta haƙura sai ya kamo hannunta cikin so da ƙauna in ma bai mata ɗaukan jarirai ba yadda indiyawa suke yi wa mata. Dakewa ta yi ta tura ƙofar wani sanyin ac da ƙamshin turare ya buɗaɗe mata hanci, shagala ta yi da kallon girma da ƙawatuwar falon har ta manta da yin sallama yayin shiga. Ƙofar ta mayar ta rufe tana ganin ta zama baƙauyiya sai ta raina nata ɓangaren duk haɗuwarsa domin wannan ya dame shi ya shanye a komai. Ɗago kai ta yi sai ta yi tozali da Alhaji Tahir zaune a kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya fuskarsa tamkar kumurcin miciji babu alamar walwala kai za a iya alaƙanta yanayin da tamkar wanda bai san sunan wani abu dariya ba bare kuma a ce ya taɓa yin ta. Ko kallo bata ishe sa ba ai kuwa ta taho fuuu a fusace don ta zo ta ji amsoshin tambayarsa don gani take buƙatarsa ce ta tashi sai yanzu ya san da ta saboda zai nemi haƙƙinsa a wajenta. Tahowar da ta yi tana ƙoƙarin ƙarasowa wajensa da yake da ɗan tazara tsakanin ƙofar da ta shigo da kuma inda yake tsakiyar falon a zaune kasancewar falon yana da girma sosai. "Ki samu wuri ki zauna ban baki damar furta ko da uffan ba!" Ya ce babu alamun wasa a furucinsa. Kallo ɗaya ta ƙara masa ta ga ba wajen wargi bane yadda ya haɗe rai sai ta sha jinin jikinta. Kanta ta samu da bin umarninsa ba tare da ta san dalilin yin hakan ba wuri ta samu ta ɗosana mazaunanta tana jiran ta ji mai zai ce. Sai dai hankalinsa ya mayar wajen danna waya da alama ya ba bango ajiyarta!. Kallon fuskarsa take wani irin muni da baƙi ta ga ya yi ga wani bajajjan hancinsa kunnuwansa tamkar na zomo. Tabbas kuɗi sun rufe mata muninsa har ta kai bata san mugun mummuna bane shi sai yazu yanayinsa ma sai ya ga kamar wani yare amma ba na hausa ba. Ƙaran buɗe ƙofa ne ya dakatar da ita daga kallon munin angon nata, ƙaran takalmi ƙwas-ƙwas da ake takawa shi ne ya tunatar da ita mace ce ta shigo, waiwayawa ta yi abin da ta gani ne ya so zautar da ita ganin wata kyakkyawar mata gashinta har baya yadda take tafiya ƙugunta yana juyawa a cikin siket ɗin jikinta shi ne abin kallo sosai nesa ba kusa ba ta ɗara SALIMAH a komai hatta mazaunanta sun san an yi dirarriyar mace, ko kallo SALIMAH bata isheta ba ta cire takalmanta tate da tako lallausan kafet ɗin ta ƙarasa har gaban Alhaji ta durƙusa ta ce "Barka da dare shugaba, fatan an dawo lafiya" Ta ce tana mai sadda kanta ƙasa. Baki ta saki SALIMAH tana kallonta da mamaki ko ɗagowa bai yi ba sai hannu da ya ɗaga mata idanunsa suna bisa waya, tashi ta yi ta koma ta samu wuri ta zauna. 'Kenan ma sun san baya nan a daren amarcina har sai yau ya dawo lallai mutumin nan ya bar mini abin gori' Ta ce a zuciyarta tana mamakin durƙusawar matar wani ƙaran ƙofar ne ya ƙara katsewa SALIMAH tunani wata baƙar mata ce ƙatuwa ita ma ta shigo ta yi yadda ta farkon ta yi ita ma hannu ya ɗaga mata ta tashi ta zauna a mazauninta. "SALIMAH waɗannan su ne abokan zamanki" Ya ce ba tare da ya kalle ta ba" Ita bata samu damar amsa masa ba sai ya ajiye wayarsa ya yi gyaran murya tare da cewa. "Na tara ku ne a nan domin na sanar da ku gobe za a ɗaura mini aure zan rufe ƙofa ma'ana zan cike mace ta huɗu...!!!!" [1/11, 7:55 PM] MOM MASHKUR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 14 *HAWWA* Siyayyar da suka yi kaya sun yi kyau sosai Yaya Usman sai wani shishshige mata yake yi, yana so ya fara fahimtar da ita akwai ɓoyayyan sirri a zuciyarsa sai dai ba wai da baki yake son faɗa mata ba so yake ya fara nuna mata a aikace ta yadda za ta fara fahimta da kanta, ma'ana zai ke yin abu wanda za ta fara gane ya mutu a kan soyayyarta duk da yau ya ji haushi sosai abin da ta yi wa ABBAS amma kuma ganinsa gata ga shi sai ya wanke duk wata damuwarsa. Sun biya shago ta bayar da ɗinkinta amma na SABEER sun bayar sai Yaya Usman ya ce zai kawo shi su gwada shi, da yake shagon ɗinkin akwai masu yin na zama da masu yin na mata. Baffa ya yi murnar ganin kayan, SABEER kuwa sai murna yake an siyo masa kaya, bawan Allah cewa yake "Na huta da saka tsohon kaya yagagge" Wanka HAWWA ta masa aka saka masa ɗaya daga cikin kayan sai murna yake yana farin ciki. Baffa ma daɗi ya ji a ransa ganin ya faranta zuciyar maraya. Kuɗin zoben nan HAWWA ta ɗakko ta ba Baffa tare da masa bayanin kuɗin zoben ta ne Baba Sadiya ta sayar mata, suka yi kuɗin motar ta sanar da shi ta ba Baba Sadiyar wani abu daga ciki. "Wannan kuɗin ai naki ne Hauwa'u zan mayar da wanda kuka ɗauka kuka yi kuɗin motar sai a juya miki sauran" Ya ce yana kallon kuɗin wanda shi ne kaɗai ya yi saura daga cikin maƙudan kuɗaɗe da ƙadarorin da suke da shi, mararsa tsoron Allah sun cinye kuɗin ba tare da tunanin makomarsu ko azabar da Allah zai musu a kan cin dukiyar marayun ba. Islamiyar unguwar da Amrah take zuwa nan aka karɓowa HAWWA form za a saka ta, har an bata hijabin ɗinkakke da suke siyarwa tare da form ɗin, har ƙasa hijabin. A wayar Baffa ta saka lambar Baba Sadiya da ta haddace ta kira ta da daddare cikin raɗa ta ce. "Baba Sadiya" Da sauri Baba Sadiya ta tashi zaune daga kwancen da take cikin farin ciki ta ce "Ɗiyata!" "Na'am Baba" "Baba babu kowa a kusa da ke?" "Babu kowa duk suna waje ni ma ban daɗe da shigowa ɗakin ba" Nan suka gaisa cikin tsananin farin cikin jin muryar juna. Baba take tambayar yadda suka je Kadunar nan take faɗa mata lafiya suka je, ta shiga bata labarin yadda suka samu sauyin da suka, samu sosai ta ji daɗi da farin cikin daddaɗan labarin tana son yaran tamkar ƴaƴan cikinta tana son ta ga sun samu rayuwa mai inganci sun yi farinciki, abin da ya gagari ƙanin mahaifinsu ya basu kulawar da ta dace ko don maraicin su. HAWWA ta tambaye ta yadda suka yi da suka fuskanci basa nan, Baba bata ɓoye mata komai ba da ya faru har sanarwar mutuwar su ta hanyar haɗarin da mota ta ƙone da zaman makokin da aka yi. HAWWA har da kuka tana mamakin duniyar nan da take sabuwa dal a wajen wasu mutanen, da basa ganin ƙarshen ta ya zo ga tsoron Allah ya yi ƙaranci a zukatan wasu ta yadda suka yi watsi da zumunci har a ce ƴaƴan ɗan uwanka uwa ɗaya uba ɗaya amma ka ci amanarsu har ka sanar da barin su duniya ba tare da ka tabbatar da sun mutun ko suna raye ba. Lallashin ta Baba Sadiya ta shiga yi har ta samu ta yi shiru, ita HAWWA ba komai take tunowa ba sai yadda Baba ya nuna musu soyayya da ƙauna lokacin iyayansu suna raye, hatta Hajiya Rayyanatu ta nuna musu ƙauna tamkar ƴaƴan cikinta ashe dai so ne na ganin ido so ne da zai gushe ya juya zuwa ƙiyayya a bayan ƙasa ta rufe idanun iyayan nasu. "Baba takarduna suna nan?" "Haba Hauwa'u ai takardunki suna nan na ɓoye miki su, yadda na sanki da son ilimi ina zan yi wasa da takardunki" "Dama Baffa ne zai sama mini admission shi ne nake so ki kai tasha ki saka mini a mota wannan lambar da na kira ki ita za su kwafa idan sun kawo su kira sai a je a karɓa a basu kuɗin motar" Sosai Baba ta ji daɗin maganar ta san yadda HAWWA take da son karatu amma iyayan riƙonta suka daƙushe mata ba don komai ba sai don su tauye su a ko ina suna son nuna maraya bashi da galihu. Sun yi sallama cike da kewar juna kasancewar an saba ana tare kullum. Sai da ta yi kuka mai isarta ta ta share don ta ji ciwon zaman makokinsu da aka yi bayan suna raye, kenan da ba wurin Baffa bama suka nufa wata uwa duniyar suka nufa shikenan ba za su neme su ba, tun da har sun tabbatarwa da duniya mutuwarsu kai duniya ina za ki damu?!. Fitowa ta yi daga ɗakin ta kai wa Baffa wayar ta faɗa masa yadda suka yi da Baba Sadiyar a kan takardun, sai dai ganin yanayinta ya sauya sai da Baffan ya tambaye ta, wani kuka ne ya ƙwace mata lokacin da take bashi labarin shi ma sai da ya yi hawaye Goggo kuwa kasa tsayar da nata hawayen ta yi saboda abin ya yi matuƙar ɗaure musu kai, lallai su Alhaji Bukhari sun ci dubu sai ceto. Haƙuri ya bata tare da nuna mata cewar gwara ma hakan don wannan zai basu damar rayuwa babu fargabar za su neme su bare su katse musu walwala da jin daɗin da suka samu bayan dawowarsu Kadunar Amrah yau ma wunin gidan Mamansu ta yi tun zuwanta ta ce da yamma za ta aike ta gidan ƙawarta da suke islamiya ɗaya, da yammar kuwa ta bata saƙon turaren wutar da za ta kai mata. Sanye take da hijabi iya gwiwarta ta nufi gidan kamar yadda ta kwatanta, sallama ta yi bayan an amsa ta shiga zaune ta samu Mamar ABBAS a kan tabarma tana yankan farce, ladabin kunamar nan dai da take a idanun wanda ta ga dama shi ta yi wa Mama domin har ƙasa ta durƙusa ta gaishe ta amsa mata Mama ta yi tun bata san daga inda take ba ta ji yarinyar ta kwanta mata a rai. Bayan ta ce ta zauna a tabarmar dakyar ta zauna daga gefen baranda alamar ba za ta haɗa wurin zama da babba ba, sosai hakan ya ƙara burge Mama. "Ga shi in ji Mamata ta ce na kawo miki" Ta ce tana miƙa mata da hannu biyu. "Lah wai yarinyar wajen Habiba ce? Amrah ko?" Gyaɗa mata kai ta yi tana murmushi haɗe da wasa da yatsun hannunta. "Ah ma sha Allah" Ta ce tana jinjina tarbiyar yarinyar. Ko ruwa da Mama ta kawo mata ƙin sha ta yi, da za ta tafi Mama ta ce ta miƙa mata saƙon godiya tare da bata ɗari biyar ta hau napep duk da ba wani nisa bane tsakanin amma ta ƙi karɓa hakan ya ƙara saka wa ta ji yarinyar ta ƙara kwanta mata. Tashin da ta yi za ta tafi abin da idanunta suka mata tozali da shi, sai da ta kusa kasa shaƙar numfashi. 'ABBAS' Ta ce a zuciyarta hango hotonsa kafe a ɗakin Mama, dakyar ta saisaita kanta don kar Mama ta gane. "Yes! Tsuntsu daga saman gasashshe lallai na samu wurin kamun ƙafa, wannan mutumin mai taurin tan tsiya da nuna mace bata dame shi ba Allah ya kawo mini sassauƙar hanya" Ta ce a zuciyarta lokacin da ta fito daga gidan. *SALIMAH* Wata irin bugawa zuciyar SALIMAH ta yi fat-fat jiri ya fara ɗibanta duk da a zaune take, gabaɗaya tangameman falon ya shiga juya mata tamkar jirgin sama yana shawagi a sarararin samaniya, jikinta ya ɗauki rawa tamkar mazari cikin zafin nama ta fusgi jikinta ta fara ƙoƙarin raba shi da kan kukerar duk da tana jin yadda sagaggun ƙafafunta suke barazanar gaza ɗaukan gangar jikinta, saboda mugun kashe ta da mamaki da Alhaji Tahir ya yi. Duk da ta ci nasarar tsayawar a kan ƙafafunta amma karkarwa suke mata, za ta iya cewa tun da ta baƙunci duniya ba a taɓa mata abin da ya bata mamaki ba ya daki ƙwaƙwalwarta lokaci guda lissafi ya rikice mata ya ƙwace mata ba, sama da wannan furucin na Alhaji Tahir. Gabaɗaya sai ta ji kalaman da ya furta sun dame tare da shanye laifukan da take taƙamar ya mata, na rashin zuwa gare ta tun daga ranar farkon da aka mata masauki a gidansa kawo yau da ta cika kwanaki uku!. A nata ra'ayi da tunanin wannan ne laifi mafi muni da ya mata wanda take ganin ba zai ƙara mata wani makamancinsa ba, sani ne bai yi ba a duniya tana da mugun kishi ta tsani kishiya, kai ko sunan kishiya aka ambata ɗaci take ji a zuciyarta!. Abin da ya sa ma ta yarda za ta aure shi bayan yana da mata har biyu saboda amanna da ta yi da kyau da zubin halittar da Allah ya mata, a nata bahagon tunanin tana ganin babu wani gida da za ta saka ƙafarta da sunan zaman aure idan har da mace a gidan face matar ta zama sorry, ta sakar mata akalar mijin. Ganin za ta zama tauraruwa mai haske a gidansa da yadda yake nuna so da ƙaunarsa gare ta wannan dalilin ne ya sa take ganin in ta shiga gidansa matansa ba za su zame mata kishiyoyi ba sai dai su zama tamkar bayi a wajen sarauniyai!!!. Niyyarta ta gallaza musu ta ci karenta babu babbaka a ƙarshe duk wacce ta gaji da gashin ƙumar cikin gidan ta cikawa bujenta iska. Sai dai kash! Yau ta gane akwai bambanci tsakanin aya da tsakuwa ashe dai kallon haddirin nesa ne ya sa ta yi wanka da kashi, tabbas kallon kitse take wa rogo. A yau ɗaya ta gane karin maganar da bahaushe yake cewa gaba da gabanta aljani ya taka wuta. Bata taɓa zaton duk kyan da take taƙama da shi ba za ta samu wacce ta fi ta ɗari bisa ɗari a cikin gidan Alhaji Tahir ba, kyan da shi ne makamin da ya sa ta kashe aurenta don tana ganin kyan nata zai sa ta samu mai kuɗi inda za ta yi amfani da zallar son ta ci duniyarta da tsinken tsire. Sai ga shi matarsa da ta fara shigowa ta kere ta a komai ko ɗayar ma ta fi ta komai haske kawai za SALIMAR za ta faɗa mata, domin irin matan nan ne da ake wa laƙabi da black beauty. Idanunta tamkar za su faɗo take kallonsa wanda shi ɗin ma ita yake kallo da mamakin ganin ruɗewarta a ƙanƙanuwar maganar da ya yi, wacce bata fi kalmomi ƙalilan ba, taku ɗaya biyu ta yi za ta ƙarasa gabansa saboda yadda take jin zuciyarta tana azalzalarta dole ta tauna tsakuwa ko aya ta ji tsoro dole ta ankarar da shi mummunan kuskure zai yi don idanunta a rufe suke basa tsoron ta mutu ko ta yi rai. "Alhaji Tahir! Haka muka yi da kai? Ni SALIMAH za ka ci wa mutunci ka wulaƙanta a idanun duniya sa... "Da na miki me?" Ya tari numfashin ta har yana ƙanƙance ido ɗaya saboda shayar da shi giyar mamakin kalamanta. "Tambaya kake ko neman sani? Idan ka manta in tuna maka yau kwanana uku kacal a cikin gidanka ko wulginka ban gani ba, a matsayina na amaryar da ka yi wa furucin kalmar so da ƙauna ba wacce aka laƙaba maka auren dole da ita ba, amma kake ikirarin gobe za a ɗaura maka wani auren? Ni kuma a wane matsayi ka ajiye kenan? To bari ka ji ni SALIMAH ba zan lamunci raini ba kuma ina so ka sani shi rashin mutunci biki ne idan ka mini ramawa zan yi don wallahi! Wallahi!! Ba zan ɗaga maka ƙafa ba" A fusace ya miƙe tsaye cikin zafin nama yana nuna ta yatsa ya ce "SALIMAH ki sani nan ba wajen warginki bane, idan kin saba duk wani abu da kike taƙama da yinsa to ki sani shi fa bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri!. Da kike ikirarin duk abin da kike faɗa yanzu shin sakin ki na yi? To ko sakin ki na yi baki da hurumin tuhumata tun da ni nake aurenki ba ke kike aurena ba. Aure kuma babu fashi ki kalle su mai suka rasa? Kyau ko diri? Duk wani abu da ƴa mace za ta yi taƙama da shi kowaccensu tana da shi amma na auro ki" Ya ce yana nuna mata matansa da suke zaune, samun kanta ta yi da waiwayawa ta kalle su kamar mai son tabbatarwa da maganar tasa. Farar ganin SALIMAH ta juyo har da gyara kafaɗar rigarta irin ta kalle ta da kyau, baƙar kuma sai ta gyara ɗaurin ɗankwalinta wanda ya kasance ture ka ga tsiya ya sake iyowa gaban goshinta, wani mugun haushin matan nasa da tsanarsu ne suka dirar mata a zuciya. "Ka san suna da komai amma ka auro ni" "In kin manta in tuna miki ko lokacin da kika yi kuri da kyau wata rana da muna magana, in za ki lura ai ban yi magana ba kawai dariya na yi saboda na san mai na ajiye a cikin gidan" "Ba wannan ba Alhaji dole ka fasa maganar aurenka, tun da su wannan na san da zaman su da wacce kake ƙoƙarin ba ƙofar shigowa nake, idan ma har ya zama dole za ka yi sai dai idan na gama cin amarcina!" "Baki isa ba SALIMAH ni bai mace bata juyani, kuma ina so ki sani a gobe idan an ɗaura aure a goben amarya za ta tare, sannan bakin kwananta ne don naki ya wuce a ƙa'ida ita dama bazawara kwanaki uku ne nata kacal!!!. Kuma kin cinye naki domin kuwa sun wuce gobe kwanankin amarya ne in suka ƙare sai na uwar gida, sannan na mai ɗakin tsakiya daga ita kuma a sannan ne aka zagayo kan ki ina fatan kin fahimta!" Ya faɗa babu ko alamar wasa don yadda ma yake magana ko walwala babu a fuskarsa yana yi ne cikin hargowa tamkar zai kai mata duka. Ɗif ta yi tamkar ruwa ya ci ta, ashe wulaƙaci ba shi da daɗi? Ashe akwai damuwa a nuna maka baka isa ba a inda kake ganin ka isa har ka yi yawa? Ashe abu ne mai cin rai a nuna maka kai ba kowa bane a inda kake ganin ka isa, yau ita SALIMAH za a yi wa tonon silili ina dirin jikinta da yake ɗaukan hankalin maza? Ko shi Alhaji Tahir makaho ne? Amma in makaho ne ya aka yi ya ga diri da kyan nata har suka ruɗe shi ya aure ta, yanzu duk kyan da ya zame mata jari take ganin za ta juya namiji kamar sitiyarin mota amma wai ake nuna mata kwananta ya wuce, wai ake tabbatar mata kwananta uku ne na bazawara bayan shi da kanshi ya sanar da ita ta fiye masa budurwa, kuma kwana ukun ma ba a mata shi ba, tunaninta sai sun kwashe wata uku currr suna cin amarci ba tare da ya waiwayi kwanan sauran matan nasa ba sai ga shi ko saninta bai yi ba a matsayin mace yana ambaton kwanakin sun wuce sai kuma sun zagayo, wannan shi ne ƙalubale babba a wajen ƴa mace mijinta ya nuna mata raya sunnar aure da ita ba bakin komai bane don hakan ya nuna Alhaji Tahir ba ya mararin sanin wace ce ita a cikin mata shu ya sa ya ce kwananta ya wuce. "Ka ha'ince ni wallahi" Ta ce wani kuka yana neman ƙwace mata. "Na ha'ince ki ko kika ha'inci kan ki? Auren nera kika yi kuma ga ki ga nairar, ki kalli Khadija da kyau " Ya faɗa yana nuna baƙar matarsa. "Ita ce uwar gidana, kuma mahaifinta mai kuɗin gaske ne, haka ma Aina'u" Ya ce yana nuna farar da yatsa. "Ita ma mahaifinta mai mugun kuɗi ne, zan iya cewa babu wacce ta aure ni saboda dukiyata, kuma a ranar da Khadija ta tare washe gari aka ɗaura aurena da Aina'u kuma a ranar aka kawo ta babu wacce ta yi musu da magana ta kuma har yau tsawon shekara goma da auren mu babu wacce ta ƙetara umarni na sai ke? Ke da ba ƴar kowan kowa ba ke da na auro a duhun talauci na fito da ke hasken arziƙi bari ki ji daga bakin abokanan zamanki ku faɗa mata doka ta" Ya ce yana kallonsu. "Ba a musayar zance da kai" Khadija uwar gida ta faɗa. "Ba saɓa magana ko karya dokar ka" Aina'u mai ɗakin tsakiya ta ce. "To dawo nutsuwarki idan za ki ci arziƙi ki ci ki idan kuma za ki koma ƙangin talauci to dama daga shi kika zo, sai dai ki sani fita daga gidan nan akwai haɗari, haɗarin da ba za ki so jin wane iri bane" Hawaye ne suka fara sintiri a kumatun ta jin ya mata gorin arziƙi wai har yana cewa ta zo daga ƙangin talauci, wato su sauran matansa ƴaƴan masu da shi, ita kuma talaka, idanunta ta ɗaga ta sauke a kan fuskarsa da take haɗe kamar ta mayunwacin zaki, fuskar da take ganin ta fi kowacce fuskar muni a duniya yau, tana jin yadda zazzafar kalmar da ya jefe ta da ita ta talauci tana kai kawo a birnin zuciyarta. "Haka ABBAS yake ji idan na ambace shi talaka ahalil fuƙara'u? Ashe dai kalmar talauci a dangantaka da ita ta sigar cin mutunci baka jin daɗi ko da kuwa kai talakan ne tun da ba kai ka ƙaddarawa kan ka ba, a karon farko da ta gane cewa ABBAS yana jin ƙuna a ransa, dama baka sanin munin abu ko kyansa idan kana yi sai ranar da aka maka. "Talauci?" Ta tambaya tamkar an fisgo maganar daga bakinta. "Eh, kuma na faɗa saboda kuɗi kika aure ni, ki kalli tazarar da take tsakanin farin fatarki da baƙar fatata, ki kalli ratar da kyan da kike da shi da munin halittata, ki dubi tsawon shekaruna da suka ɗara naki, a ƙiyasi a haihuwar kaji na kusa haifar ki SALIMAH ki hasko ni a idanun zuciyarki ina sanye da rigar talauci shin za ki yarda ki aure ni? " "Kenan kuɗina su suka lulluɓe muni, shekaruna, da duk wani abu da za ki ga gazawata" Ya ɗora ba tare da ya jira cewarta ba "Ki koma wajen zamanki aure babu fashi ki saurara ki ji dokokin gidan nan wanda su ne abu mafi a'ala a gare ki don saɓa su ba ƙaramin barazana bane a gare ki" Ya ce yana komawa ya zauna yana aika mata wani kallon mai cike da ma'anoni da dama amma ba masu kyau ba don tuni ya gane ba don Allah ta aure shi ba, duk da shi ɗin ma hakan take a wajensa sai dai shi ya aure ta don cim ma wata ɓoyayyar manufa( Littafin MAIMUNA IYAM) manufar da shi kaɗai ya santa kuma saboda cikar burinsa. Durƙushewa ta yi a wajen, ba don bin umarninsa na cewa ta koma mazauninta ta zauna ba, sai don ƙafafunta sun kasa jumurin ɗaukan gangar jikinta, gabaɗaya ta rasa a wace kalar duniya take, shin a duniyar mafarki take ko kuwa a duniyar zahiriyya. Alhaji Tahir bai bi ta kan ta ba illa iyaka ya ɗora maganarsa da cewa. "Abu na farko saƙo ne da yake damfare da ke ma'ana ina nufin ke ce baƙuwa a gidan nan dole ki san dokokina tun da su abokan zamanki tuni sun daɗe da sani, jajayen idanunta ta ɗaga tana kallonsa garau da ita tamkar wata sakarya ta rasa ma'aunin da za ta ajiye duk abubuwan da yake faɗa mata. "Dokar ta farko ki sani part ɗina ba a shigarsa matsawar bana nan, ki kiyaye da wannan babban al'amari ne karya dokar nan babu ke babu part ɗina sai in har ni ina ciki!" Kallon tuhuma ta shiga jifansa da shi a wannan karon tana ganin an zo gaɓar da aka shallake tunaninta. A iya saninta ta yaya za a ce mace an saka mata dokar shiga ɓangaren mijinta sai in yana ciki sai ka ce wani marar gaskiya. "Sannan abu na biyu a saman akwai ɗakuna guda uku a jere wannan ɗakuna in har ina part ɗin don kin shiga babu laifi sai dai akwai wani ɗaki daga gabas shi kaɗai a ware a gefe guda, ko a jikin bangon ɗakin daga saman ƙofa an rubuta ƊAKIN ALHAJI TAHIR, to wannan ɗakin ni kaɗai ne mamallakinsa ni kaɗai ne nake shiga babu wani mahluƙi da zai taɓa shiga, ko ya taɓa shiga ina gargaɗinki a kan kar gigiwa ko rawar kan ki ya sa ki shiga rufaffan ɗakin wannn" Ya ce yana nuna ta da yatsa alamar kashedi, ita gabaɗaya a sanyata a tsaka mai wuya yanzu kam mugun tsoron Alhajin ne ya ɗarsu a zuciyarta a gefe ɗaya tana tuhumar anya yana da gaskiya? Idan har yana da gaskiya mene ne dalili lo hujjarsa na cewa kar a shiga ɓangarensa sai yana ciki kuma kar a shiga wani ɗaki guda ɗaya tal da ya keɓance shin mai zai faru idan an shiga? Take ta yawo da tambayoyin a zuciyarta tambayoyin da bata da wanda zai amsa mata su shi wanda zai amsa mata ba shi da salamar da jinƙai irin na mijin da za a faɗa masa abu. "Sannan ki sani ba a haihuwa a gidana!!! Wannan wani ɓoyayyan sirri ne, kuma ba don ana tsarin hana haihuwa ba wato palaning sai dai wannan ni na san dalilan da ba na bayyanawa kuma duk son ki da haihuwa ba za ki haihu ba kuma babu wanda zai haihu" Dumm kunnuwanta suka yi, nan ta shiga tunano inplan ɗin da ta saka har sau biyu a gidan ABBAS don kar ta haihu a gidan talauci yanzu ta cire ta zo gidan kuɗin da nufin ta buɗe mahaifa ta yi ta barbaɗa ƴaƴa in son samu ne ma ƴaƴan maza don su ci gado mai tsoka. Sai dai kash! Kenan babu haihuwar ƴaƴa masu rarrafen cafet to zaman mai za a yi babu haihuwa a aure? Ga ya ce babu fita daga gidan ma shin wane irin bahagon gida ta shigo, wane irin ƙangin rayuwa ta kawo kanta?. "Ga mukullin part ɗin nan wannan naki ne idan ranar bakin ki ta zo za ki yi amfani da shi wajen buɗe babbar ƙofar part ɗin ta farko don a rufe take" Ya ce yana jefa mata wani mukulli ƙwaya ɗaya jal kamar rai. Kallon mukullin take da idanunta da hawaye ya mata shamaki da ganin mukullin raɗau, hannu ta kai ta ɗauka. "Za ku iya tafiya " Ya ce cikin bada umarni. "Godiya muke Allah tsare ka ya kawo amarya lafiya" Hajiya Khadija da Hajiya Aina'u suka haɗa baki wajen faɗa cike da ladabi. SALIMAH samun kanta ta yi da kasa furta komai ta tashi tsaye jiki babu ƙwari wannan ita ce rana ta farko da ta ji ta tuna zamanta a cikin gidan ABBAS zama ne wanda ta yi cikin kwanciyar hankali kulawa tare da nuna soyayyarsa gare ta duk da tana wofantar da komai nasa amma bai taɓa gajiyawa ba!. "Yawwa na manta" Hajiya Aina'u da take tsaye ta miƙa hannu za ta buɗe handle ɗin ƙofar ta dakata tare da juyowa, ita ma Hajiya Khadija dakatarwa ta yi suna masu juyowa a tare suka dawo tare da komawa suka zauna. SALIMAH amarya ma ko a ce amarya mai barin gado ita ma sai ta dawo wannan karon ma a cafet ta zauna. "SALIMAH" Ya kira sunanta ba tare da ta amsa ba ta ɗago kai tana kallonsa don zuwa yanzu magana ma wahala take mata "Ba da ke nake magana ba?" Ya tambaya a zafafe. "Na'am" "Idan kin koma part ɗinki ki zaɓa ko sama ko ƙasa ki ɗauki ɗaya ki bar wa ƙanwarki amarya mai jiran gado ɗaya gidanta na yi niyyar ware mata kasancewar nan ɗin iya part uku ne sai nawa to amma sai ta ce mini ita a nan gidan take so ta zauna tare da ku ƴan uwanta don haka ki ɗauki ɗaya tun da ke ce ƙarama a cikinsu kuma sama ko ƙasa kaɗai ma ya ishe mutum rayuwa akwai isassun faluka da ɗakuna da kicin da bayi da komai na buƙata " Tun da ya fara maganar take kuka wannan karon ta kasa hana kanta zubar hawayen bata ma so ta dakatar da hawayen saboda so take ta zubar da su ko ta samu sauƙin raɗaɗin abin da aka mata!!!... FREE BOOKS RAYUWAR MARYAMU GIDAN MIJINA ƳAN UBANCI MAI FARAR ƘAFA SANADIN KISHIYA NE ALAƘAR YARINTA. PAID BOOKS ƳAR ƘANWATA 500 BEELAL BOOK 1 free book 2 paid 500 ƳAR ZAMAN WANKA 500 ƘARA'IN INNA DELU 500 JALLI JOGA 600 UNGOZOMA 700 ƳAN ADAIDAITA SAHU 500 MAMAN AFRAH 09013181851 *RUƁAƁƁIYAR IGIYA* NA MAMAN AFRAH ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. *END OF BOOK 1* PAGE 15 *ALHAJI BUKHARI* Rayuwa ta yi musu daɗi tun bayan da aka gama zaman makokin su HAWWA bayan suna raye, amma su da basu tabbatar ba babu wani ko ɗar a zuciyarsu don ko inda aka yi haɗarin basu je ba bare wajen ƴan sandan da suka yi binciken yadda abin ya afku ma'ana ko ba komai ai sa ji yaya ne tun da ba ɗan mutum ba ko akuyar da kake kiwo ce ka bi bayanta ka ji kadin abin dabba ma kenan bare ɗan mutum, ko don ba ƴaƴan su bane da ƴaƴansu ne da har yanzu tabon mutuwar bai bar zukatansu ba kuma ba zai bari ba har abada don ma dai su suke kiɗa da rawarsu su HAWWA suna can cikin ƙoshin lafiya. Zaune suke a falo suna taɓa hira Hajiya Baba sai Lawisa da take zaune tana cin meet pie ga dambun nama a gefe. Yaya Umar ne ya shigo babu ko sallama don dama su basu yi wa ƴaƴansu tarbiyar yin sallama ba tun da dama yaro sai kana koya masa ne zai koya ko da shigowa ya yi bai yi sallama ba sai ka ce ya koma ya yi sallama, idan ya yi ka amsa sai ka ce ya shigo yau da gobe har zai zamana ba ya iya shiga wuri ba tare da ya yi sallama ba ita tarbiya sai an dage an jajirce. "Baba kuɗi nake so" Ya ce yana yin kalar tausayi. "Kamar nawa kake so?" "Baba duka fa shekaran jiya ka tura masa miliyan biyu amma yau za ka ƙara masa gaskiya ni ma sai an ƙara mini" Lawisa ta ce tana zunɓura baki. "To mene ne na ɗaga jijiyoyin wuya kuɗi akwai su mu ma facakar mu muke yi dama dukiyar marigaya ne wato ɗan uwana da matarsa da suka bar kadarori da kuɗaɗe sai aka ba marigaya su HAWWA ƴaƴansu to su ma sun riga mu gidan gaskiya kuma basu da masu cin gadonsu sai mu kun ga kuwa dole mu fantama, baki ga ko shi Umar da yake ikirarin yana son ta ba yanzu ko zancenta ba ya yi shegen yaro ya samu duniya!" Baba ya ce yana dariya. "Ni ma fa ba son gaskiya bane kawai dai ina son in san wace ce ita to ita ba yarda za ta yi mu ke ba wai ita mai tsoron Allah, mu ma ai muna tsoronsa istigfari muke, da a ce dama an yi auren ma da na gama samun komai zan sake saki uku" Umar ya ce yana fashewa da dariya. Saboda sakarci yanzu ba a ɗauki zina a bakin komai ba zina ta zama ado wayewa iskanci kala-kala ba a tuno ranar mutuwa da kwanciyar kabari azabar kabari nauyin ƙasa kai makomar ma gaba ki ɗaya ita mutuwar da ba sallama take yi ba yama daga cikin hikimar ubangiji ɓoye mana sanin ranar mutuwar mu mai ya kamata mu yi? Istigfari da sanya tsoronsa a zukatanmu ma'ana mu aikata alkairi ko don gobenmu. Idan kana ganin shi mai gafara ne za ka aikata saɓo da gangan ka nemi gafararsa shin kana da tabbacin idan kana aikata saɓon ba za a ɗauki ranka a lokacin ba idan ka je ka ce mai?. "Wannan yaron ya san ta kan tsiya" Hajiya ta ce tana kallonsa tana dariya. "Ke ma kuwa to ba mu muka haife sa ba ai dole ya san ta kan tsiya" Baba ya ce yana ɗaukan wayarsa. Yanzu kuɗin nan da suke wadaƙa da shi sun ma daina ganin laifin shaye-shaye da laifukan da Umar yake aikatawa munin abin da yake ya ɓaci hatta Lawisa mu'amala take da maza amma saboda suna cikin iyaye masu sakaci da saka wayewa a gaba babu abin da suka fuskanta, duk wasu kadarori na su HAWWA sun sayar sun zuba a kasuwanci suna cin wasu. "Yeee sai Baba" Lawisa da ta ga shigowar miliyan biyu ta ce tana tashi ta je ta rungume Baba, shi kuma sai cewa yake "Ai babu ku babu talauci yara dole in ke cika muku aljihu don ni ma nawa a cike yake" "Yihuhuuuu" Yaya Umar ya ce yana murna ganin na shi transper da Baba ya masa sun shigo. "Kai kuɗin shan ice cream ɗin kuke yi wa ihu, ai ba wasu kuɗi bane wannan na zuwa wajen shaƙatawa da abokai da ƙawayenku ne don kar ake raina muku hankali yanzu akwai wasu kuɗi da za su shigo na kamfani da na saka a kasuwa za ku sha mamakin kyautar da zan muku" Baba ya ce yana fasa musu kai. "Kai mutuwar wani tashin wani, rabon wani shi yake kashe wani, yanzu duk rabonmu ne ya kashe masu kuɗaɗen nan amma su lokacin suna raye basa wannan wadaƙar komai a sannu cikin nutsuwa da taimakon talakawa da gina masallatai da gidan marayu duk da suna yi wa ƴaƴansu gata amma basa iya mallaka musu ƙaramin kuɗi to a duniya in ɗanka bai ci ba waye zai ci" Hajiya ta ce tana taɓe baki. "Ƙauyanci dai da rashin wayewa ai kuɗi da miciji maganinsu a kashe kawai t... ƙaran wayarsa ya katse masa maganar da yake ganin abokin kasuwancin sa ne wanda ya kwashe maƙudan kuɗaɗe ya tura masa zai taho musu da kaya a jirgin ruwa, ya sanar masa jirgin ya taho ma nan da kwana biyu zai iso da kayan. "A yi shiru zan yi waya kun san harkar arziƙi wallahi Alhaji Lawal cewa ya yi muddin kayan nan suka zo muka siyar to ni fa na sha kwana, don sai an shigar da ni sahun gaba na waɗanda suke da muhaukacin kuɗi a Nigeri'a " Ya ce yana kallon Hajiya da sauran yara. "Ka wayyo mun kusa daina zaman ƙasar baƙaƙen fata" Hajiya ta ce tana wani murmushi. Hannu ya ɗaga mata ganin kiran zai katse ya ɗaga ya kara a kunne. "Alhaji Bukhari akwai matsala fa" Aka faɗa daga ɗaya ɓangaren. "Wace irin matsala, haba Alhaji Lawal na tsani a ambaci matsala a ko ina bare a wajenka kayan ne ba za su samu zuwa ba sai nan da kwana uku a maimakob biyu?" "Ba wannan bane Alhaji Bukhari" Alhaji Lawal ya ce hankali tashe. Wani irin warɓar da Lawisa da ta jingina da jikinsa ya yi gabaɗaya gumi ya karyo masa tsaye ya tashi don jin wannan abu da aka kira da suna matsala, yana ganin ba zai iya fuskanta ko sauraronta a zaune ba shi ya sa ya miƙe tsaye. Hajiya ma tsaye ta miƙe tana kallonsa a kiɗime don ta san babu lafiya, Lawisa da Yaya Usman sai zare ido suke suna son sanin mai za a faɗa wa Baban nasu da duk ya rikice haka. "Na shiga uku!!! Na lalace, wayyo jama'a... Cewar Baba da ƙarfi tamkar zai fasa gidan da ƙara yadda ya yi maganar gabaɗaya sai da gidan ya amsa, jif ya yanke jiki ya faɗi wayar da ban shi da ban. Hankali tashe su duka ukun suka yi kansa, suna faman jijjiga shi amma ko motsi ba ya yi lumfashinsa ma ya ɗauke cak!. *HAWWA* Rayuwa ta yi musu daɗi hankali ya kwanta, SABEER an sanya shi a makarantar boko da islamiya private school Baffa ya saka shi sai dai ba wata mai tsada ba dai dai ƙarfinsa amma makarantar tana da kyau sosai, Yaya Usman yake kai shi yana ɗakko shi. HAWWA tun da Baba Sadiya ta sako mata takardunta a mota aka kawo ita ma aka sama mata tata makarantar ita mai napep yake kai ta ƙarfe bakwai da rabi ya dawo da ita ƙarfe biyu da rabi ita ma private ce ta mayar da hankali don ganin burinta na zama ma'aikaciyar jinya ya cika. Yau ma kamar kullum ta tashi ta yi shirinta tsaf bayan ta ci abinci. Wayarta ta ɗauka ƙirar infinix da Baffa ya saya mata ganin bakwai da minti ashirin da biyar ta fito daga ɗakin lokacin Amrah tana ta shaƙar bacci ko karyawa bata yi ba da yake iya takardun ta na secondry basu yi kyau ba kuma ta gyara ma amma duk bata ci ba kasancewar bata da mayar da hankali kuma ma Baffa ne mai matsa mata a kan karatun ita a nata burin ta fi son a yi mata aure amma bata son wani karatu ko secondry ɗin ma dakyar ta ƙarasa. "Malamar asibiti mai tabarau" Baffa ya ce yana kallonta da murmushi a saman fuskarsa. "Ni dai ba za take mini allura ba Baffa bata iya ba fa kar a je in zama gurgu" SABEER ya ce yana saka littafi da pencil ɗinsa a jakarsa da ya gama home work. "To ban da abinka SABEER ai koya za ta yi, a makarantar ake koya wa ko su wanda ka ga suna allurar ai karatu ne da suka yi ya sa suka iya babu wanda aka haifa da iyawa" Baffa ya ce yana dafa kansa. "Ni dai soja nake son zama Baffa, in aka bani bindiga in harbe Baba Bukhari da Hajiya da Yaya Umar da Aunty Lawisa" "Ikon Allah kai dama don ka harbe mutane za ka zama soja?" Goggo ta tambaye shi. "Eh da lokacin kafin su Ummiena su mutu lawyer nake ce mata zan zama in na girma, amma yanzu na fasa soja zan zama" "To mai ya sa kake so ka harbe su iyayanka ne da ƴan uwanka" Baffa ya faɗa. "Bama jin daɗi a gidansu fa Baffa kayanmu a yage kamar mu ne almajirai, suke ta saka Aunty HAWWA aiki wata rana su mare ta kuma basa bamu abincin da suke ci, ga shi mu tafi school a ƙafa ga nisa in na gaji Aunty ta goye ni kuma fa akwai motoci masu yawa a gidan amma mu ba a barmu mu hau" Ya ƙarasa faɗa kamar zai yi kuka. Kallon kallo aka shiga yi da Baffa da Goggo suna jinjina ƙwaƙwalwar yaro da bata mantuwa ko ka masa alheri ko saɓanin haka yana sane da kai. "Ka yi haƙuri ka ji yaron kirki yanzu ba ga shi ka bar gidan ba Allah yana son masu haƙuri da masu yafiya" Baffa ya ce yana rataya masa jakarsa a bayansa tare da shafa kansa. Shiru ya yi bai yi magana ba. "SABEER zo mu tafi" Yaya Usman da ya shigo ya ce. Yanzu ya sakarwa SABEER sosai yake jansa a jiki don ya ƙara samun fili a zuciyar HAWWA da zai gina soyayyarsa. Yana ɗaga musu hannu suka fita. Ita ma sallama ta musu ta fita don ta san yanzu mai napep ɗinta ya zo. Sanye take cikin riga da wandon farare tass babu sirki a jiki, rigar tana da ɗan tsayi iyakarta cinyarta sai ƙaramin hijabi da bai kai cibiyarta ba, ƙafarta cikin farar socks da baƙin ƙafa ciki, jakarta baƙa rataye a bayanta sai wayarta a hannunta. Tun bayan fitowar su SABEER yake kallon ƙofar yana jiran fitowarta bai san mai ya sa ba kuma bai san dalili ba yarinyar tana matuƙar birge shi halayenta kyawawa ladabi da biyayyarta uwa uba girmama ta gaba da ita ya jima bai ga mai halayya da sanyin hali irinta ba. Sautin ƙira'ar karatun ta da ya ji ranar da Baffa ya bashi kaya ya kai cikin gidan, sosai ya ji daɗin karatun tana ba kowane harafi haƙƙinsa, tun daga ranar ya ji ya bata matsayi na musamman, tun daga ranar ya ji yana son ganinta wanna dalilin ya sa yake yin sakkon zuwa wajen aiki don ya sanyata a idanunsa, saboda sai ya ji idanunsa sun kasa jure jiran har sai ta dawo daga school zai ganta, idan ya koma gida tunaninta ya yi ta yi masa kai kawo a zuciya. Fitowarta daga gidan ne ya tsananta bugun zuciyarsa ya ƙaru dakyar ya saisaita kansa yana ɗan satar kallonta farin siririn gilashin da ta sanya ya ƙawata fuskarta tare da ƙara bayyana dogon hamcinta da yake kwance a kan kyakkyawar doguwar fuskarta. Ko kaɗan bata lura da shi ba, hankalinta ya yi school bata son malamin da zai shiga da safen nan ya hana ta shiga kawai haka yake yi idan har ya riga ka shiga da minti biyu to ba za ka shiga ba. Ta yi mamakin ganin mai napep ɗin bai zo shi da kullum a wajen take samun sa, lambarsa ta binciko a cikin wayarta ta shiga doka masa kira sai dai a kashe wayar, fuska ta marairaice tamkar za ta yi kuka, hakan da ta yi sai da ABBAS da yake dakon kallonta ya ji abin ya daki zuciyarsa, da a ce za a masa tambayar waye baya son ya gani cikin damuwa to bayan Mamarsa HAWWA zai ce, amma shi bai yarda wai so bane tun da ya yi ittifaƙin ya daina soyayya daga kan SALIMAH ba zai ƙara son wata mace ba da sunan soyayya wannan yanayi da alamomin da suke farmakar zuciyarsa game da HAWWA ya ƙaryata zuciyarsa da kuma FAROUQ ya ce kawai kyawawan halayenta ne kawai suke birge shi har yake jin ta tamkar ƙanwarsa. Yanzu idan suka zauna da FROUQ ba shi da magana sai ta HAWWA ta gaishe ni da safe da yamma da za ta je islamiyya ma ta gaishe ni ta yi kaza ta yi kaza amma in ya ce ya kamu da sonta sai ya ce ba haka bane. Kallonta yake har ba ya son ƙiftawa, ganin narai-narai da ta yi da fuskar sai da ya ji tamkar ya je ya tambaye ta damuwarta duk da yanayinta ya nuna masa mai napep take jira. Wata ajiyar zuciya ya sauke ɗagowar da ya ƙara yi sai kuwa suka yi ido huɗu da ita, da sauri ya sadda kansa yana danna waya duk sai kunya ta kama shi. Ita kuma sai lokacin ta gan shi, cikin takun ta mai tattare nutsuwa ta tako zuwa wajensa. Subhanallahi kawai yake ambata don tana tunkaro shi bugun zuciyarsa yana ƙaruwa. "Yaya ABBAS" Har tsakiyar zuciyarsa ya ji sunan sai yake ji a duk lokacin da ta kira shi tamkar duniya babu wanda ya fi iya kiran sunansa ya yi daɗi sama da HAWWA. "Na'am ƙanwata har an fito" Ya ce yana ƙarfin halin kallon fuskarsa wani abu ya fusge shi, wanda ba don yana ƙaryata kansa a kan ba zai so wata bayan SALIMAH ba da sai ya ce so ne ya fusge shi, ji ya yi dama a ce ta tsaya a haka kawai yake kallon fuskarta ba ya jin zai taɓa gajiya amma fa a hakan ma wai matsayin ƙanwarsa. "Na fito Yaya amma ban ga mai napep ɗin ma kuma wayarsa a kashe ko ka ga zuwansa tafiya ya yi?" Tamkar kar ta tsaya da magana sosai yake jin kalamai da sanyin murya yadda take magana yana shiga dodon kunnensa tare da ratsa ɓargo kai hatta ƙasusuwansa bai bari ba, ji yake tamkar muryarta ma tana gudana a jikin jijiyoyin jikinsa. Yadda ta langaɓar da kai tana yin tamkar ta yi kuka sai ya ji tamkar ya zama tsuntsu ya sunkuce ta ya kai ta school ɗina minti ƙalilan don kar ya ga alamar damuwa shimfiɗe a fuskarsa. "Ki yi haƙuri mana, ba sai kin shiga damuwa ba, ban gan shi ba amma na yi mamakin rashin zuwansa" Ya samu kansa da bata haƙurin laifin da ba shi ya mata ba sai don kawai ba ya son ta damu, sannan ƙoƙarinsa na faranta mata don ko shi a ranar da ta fara bashi haƙuri da Yaya Usman yana faɗa masa maganganu haƙiƙa ya ji sanyi a ransa. Shiru ta yi ganin kiran ƙawarta Afrah ya shigo wayarta, ɗagawa ta yi. "Wai ya baki taho ba har yanzu? Sai an hana ki shiga" " "Mai napep ɗin ne bai zo ba amma bari na samu wani ko machine sai na taho" Wani abu ne ya caki zuciyar ABBAS jin wai za ta hau machine sai ya ji wani abu kawai ba ya son ganin ta hau bayan machine ɗin wani namiji har gwara napep a kan machine, kafin ya ce wani abu sai ga Baffa ya fito. "Hauwa'u baki tafi ba dama?" "Bai zo ba Baffa ga shi ina neman makara kuma layin nan da safe abin hawa wahala yake" Wannan maganar ta yi dai dai fa zuwan FAROUQ abokin ABBAS da yake ta kiran ABBAS a waya zai tura masa lambar wani abokinsu da yake nema da gaggawa amma bai ɗaga ba ya je gida Mama ta ce masa ya tafi wurin aiki shi ne ya biyo shi. ABBAS kuwa wayarsa a silent take ya ga kiran FAROUQ na farko kafin ya ɗaga HAWWA ta zo sai ya sha'afa da kiran wani FAROUQ kasancewar wayar bata ƙara shi ya sa bai sake tunanin kiran yana shigowa ba bare har ya bi kira. Tun kan ya ƙaraso ya hangi ABBAS ɗin HAWWA tsaye daga gefe a gabansa, shi dariya ce ma ta kufce masa saboda ya tabbata ABBAS ya kamu da son yarinyar amma ya ƙi yarda da haka, ya ƙyale shi sai son ya gama masa dabaibayi yadda a lokacin bai isa ya yi musu ba. Baffa barka da safiya" ABBAS da FAROUQ suka haɗa baki wajen faɗa. Amsa musu ya yi sai kuma ya ce. "FARUQU idan ban ɗora maka nauyi ba don Allah miƙa Hauwa'u makaranta mai adaidaita sahunta bai zo ba(SHIN KIN KARANTA LITTAFINA ƳAN ADAIDAITA SAHU? IDAN BAKI KARANTA BA AN BARKI A BAYA DOMIN NA ƊATA LOKACI SOSAI WAJEN ƘAYATA LABARIN IYA ANSAI DA JABIRU SUN TAKA MUHIMMIYAR RAWA A LABARIN DA NAIRA 500 KACAL ZA KI SHA KARATU). Kafin FAROUQ ya ba Baffa amsa ABBAS ya yi karaf ya ce. "Babu wani ɗora nauyi Baffa ai sai a miƙa ta bari na karɓi mukullin sai na miƙa ta" Shi kansa ABBAS bai san maganar ta fito ba ji ya yi tamkar an fusge ta. Sosai Baffa ya ji daɗin cewa zai kai ta, ita ma sai fuskarta ta washe jin za a kai ta ba tare da ta makara ba. FAROUQ sosai ya yi ƙarfin halin danne dariyarsa don ya gane kishi ne ya sarƙe ABBAS shi ya sa ya ce shi zai kai ta da alama ba ya son ta hau bayan machine ɗin kowa. "Bani mukullin" Ya faɗa cikin majewa don ya ga FAROUQ ɗin yana satar kallon Baffa da HAWWA yana masa wani murmushin na gano ka. Shi kuma abin da ya sa ya maje ya san har kullum dai zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi wato FAROUQ yana zarginsa da kamuwa soyayyar HAWWA wanda har yanzu yake ƙaryatawa. Tada machine ɗin ya yi ta hau suka fara tafiya Baffa yana ɗaga mata hannu tare da fatan dawowa lafiya ita ma hannun ta ɗaga masa daga nan suka tafi FAROUQ kuma ya shiga bincikar wayar ABBAS zai ɗauki lambar kafin ya dawo masa da machine ɗin ya wuce gida. Tuƙi ne yake yi mai cike da nutsuwa, ƙamshin turarensa da nata yana dakar masa hanci, yadda suke tare a machine ɗin sai yake rawa a zuciyarsa ina ma su cigaba da kasancewa a haka, daɗin da yake ji a ransa sai ya ji tamkar bai taɓa riskar kansa a cikin irin hakan ba. "Mai ya sa bakya sa niƙabi idan za ki je school?" ABBAS ya tsinci kansa da tambayar da shi kansa bai san ya yi ba. "Niƙabi kuma Yaya?" "Au ashe ba islamiya ba ce " Ya ce cikin wayancewa yana tuhumar kansa dalilin da ya sa ya yi tambayar ma. A dai dai titin da za su tsallaka wanda zai sada su da school ɗin su HAWWA suka hango Yaya Usman ya taho, ganin HAWWA a bayan machine ABBAS yana ja ransa in ya yi dubu ya ɓaci shi a haka nan ma ya tsani ABBAS amma shi ne don gigiwa ya ɗakko masa abar ƙaunarsa a machine, wacce yake fata da burin mallaka a matsayin mata kuma uwar ƴaƴa. A fusace ya taho har yana neman karawa wani mai napep, shi kuma ABBAS sai a lokacin ya gan shi haka ma HAWWA. "ABBAS kai ABBAS" Ya shiga ƙwala masa kira tun kan ya ƙaraso. Ɗan dakatawa ABBAS ya yi tare da gangarawa gefen titi ya tsaya, shi ma Yaya Usman ɗin gangarawa ya yi inda suke ya sauka daga nasa machine ɗin ya tunkari ABBAS rai a mugun ɓace sosai a fusace yake ta yadda ABBAS yake mamakin dalilin tsayar da su da kuma dalilin ɓacin ransa. HAWWA jikinta ne ya ɗauki mazari don ta san yadda yake a fusacen nan dakyar ne in ba rashin mutunci zai yi wa ABBAS ba sosai ta ji damuwa ta sarƙe ta lokaci guda don bata son abin da za a ɓatawa ABBAS rai kamar yadda ta lura shi ma yanzu ba ya son a ɓata mata... *SALIMAH* Yana kai wa inda nan ne ta san ya kai ƙarshen magan kai kawai ta ɗaga masa ta tashi da ɗan gudu tana tashe bakinta jin kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata, ƙofar ta buɗe ta fice takalmanta ma a hannu ta riƙo su, shi kuwa Alhaji kafaɗa ya ɗaga alamar can ta matse mata, sauran matan sallama suka masa suka kama gabansu. Baram ta banka ƙofar da za ta sada ta da falon nata jifa ta yi da takalman a falon tana kallon tangameman falon da ya gaji da haɗuwa da tsaruwa amma wai ake mata batun zai zama mallakin wata a gobe, bayan ƴan uwa da abokan arziƙi nan suka kawo ta ƙawaye duk sun san nata ne amma saboda cin fuska za a ce wai ta bar wa wata bayan ta san yana da halin da ko gida ɗari zai iya siyawa amarya amma saboda kwamacala zai ce a part ɗaya za su zauna shin wane irin miji ta aura? Fiiii ta hau sama ta je ta shiga ƙarewa ko ina kallo tana kuka wiwi tabbas akwai tashin hankali a kalamansa da dokokinsa amma duk abu ne wanda a duhu yake ba wani zai gani ba sai dai in ita ta faɗa wannan batun zaɓar ɗaki kuwa dole duk wanda ya zo sai ya gane tun da dole za a ga amarya ba ma wannan ba wa za ya faɗawa za a mata kishiya? Bayan ta yi wa mutane kurin cewa daga ita Alhaji Tahir ya rufe ƙofa ita ce ta gaban mota ita ce ta shiga taro amma kwatsam a ce a kwana uku rak wannan matsayin ya zagwanye? Ƙasan ta sake sakkowa kamar wata mahaukaciya sabon kamu duk ta zauce ta firgice ita gabaɗaya ta ruɗe da rabon part ɗin nan da aka ce da yake duniyar ce a gabata ita dokokinsa za ta iya fatali da su amma batun part ɗin nan tamkar cewa ya yi ta raba ranta biyu ne ta bada rabi, part ɗin da ko Ummarta bata zo ta gani ba amma za a raba a ba wata bayan su sauran matan gidan kowacce gashin kanta za ta ci. "Ko dai hannu aka saka mini? Ko dai shiga tsakanina aka yi da shi' Wani sashe na zuciyarta ya jefa mata tambaya. "Waye zai shiga tsakaninku kawai butulci ne irin ma maza shi dama namiji ai butulu ne a wani ƙaulin ba ɗan goyon baya ba" Wani ɓangaren na zuciyarta ya sake saƙa mata hakan. Baki ta damƙe tana jin ruwan hawayenta yana biyowa ta bakinta yana sauka haɓarta wai ita SALIMAH ce yau namiji ya saka ta zubar da hawaye a cikin kwanakin cin amarcin ta amarcin da bai ciwu bama, ba ma wannan ba yau ne kwanan nata na uku zai cika amma mai zai yi da daren nata na yau wanda ya rage ƙwaya ɗaya tal? Ko dai ita ce ba ya son kasancewa tare da ita ta rasa kalar tunanin da za ta yi hakan ya sa take zaune tamkar mutuntumi ko gunki ta daɗe a wajen ita kanta bata san iya awannin da ta kwashe a wajen ba a ƙatshe ta lallaɓa ta koma bedroom ɗin da yake ƙasa inda aka ajiye ta jiya ta zame ta kwanta ba wai don ta rintsa ba sai don duniya ta rasa mai za ta yi ta ji daɗi a ranta. Ta yanke hukuncin ta zaɓi ƙasa saboda idan ta zaɓi sama duk wanda ya zo zai gane an raba part ɗin ta biyu tun da dole za su ga amaryar a nan kuma dole a jefa mata ayar tambaya. Tamkar taɓi-taɓi haka take kwance garau har aka faran assalatu dakyar ta lallaɓa ta tashi tana jin wani zafi a jikinta kamar zazzaɓi, alwala ta yi ta yi sallah sallar da ita kanta tana karatun sallah amma bata san mai take karantawa ba saboda tunani ya cunkushe mata ƙwaƙwalwa maimakon ta mayar da hankali ga sallaar ta yi addu'ar neman mafita amma haka ta sallame ta tashi ta koma makwancinta. Wayarta ta ɗakko iphone 16 ɗin tana ƙarewa wayar kallo tana tuna android ɗinta ta gidan ABBAS wacce bashi ya ci ya saya mata don ya faranta ranta shi kuma yake riƙe keypad amma bata gode masa ba a raine ta karɓa ga shi yanzu tana fa wayar da ake yayi sai dai kash! Cukurkuɗaɗɗun al'amuran da suka taru suka yi wa rayuwarta ƙawanya sun disashe duk wani walwalarta. Sunan Umma ta kamo tana son kiranta ta sanar mata matsalolin da suka kunno kai a sabon gidan auren da suka ci buri amma tana tsoron ran Ummar ya ɓaci saboda tana ƙaunar Ummarta a duniya ota kaɗai ta rage mata tate suka kasawa su tsare amma kuma dole ne ta faɗa mata tun da ita ce mahaifiyarta kuma ƴan magana sun ce abin da babba ya hango yaro ba zai hango ba ganin ƙarfe shi sai kuwa ta doka mata kira. Umma da bayan ta idar da sallah ta zubo ruwan zafi a plask ta haɗa kakkauran shayi da ya ji madara da milo tana zaune tana haɗawa da biredi tana lumshe ido ga ƙaran jannareton da wani matashi yake zuwa ana tada mata gida sabo ga plasma tangamemiya abun sai wanda ya gani, kiran da ya shigo wayarta ne ya sa ta tashi ta ɗakko ganin SALIMAH sai murmushi ya suɓuce mata. "Yarinya mai goshin arziƙi auren mai kuɗi da daɗi duk rayuwarmu ta sauya, bare yanzu in kika bararraje ai duniya sabuwa mu gaba ta kaimu gobarar titi" Shi ne furucin Umma bayan SALIMAH ta danne kukan da ya taho mata ta yi sallama, shiru ta yi tana tuna wannan zancen bai tabbata ba. "Umma mun kama RUƁAƁƁIYAR IGIYA" Ta ce tana fashewa da kuka. "SALIMAH RUƁAƁƁIYAR IGIYAR uban me wai?" Ta tambaya tana dangwarar da kofin shayi ya tuntsure, don a tunaninta SALIMAH ta jaza musu salalan tsiya ne wato ta saka ya sake ta. "Umma aure za a ɗaura masa yau" "Aure dai da na sani SALIMAH shi Alhaji Tahir ɗin ne zai miki kiahiya bayan na cikin gidan da kika tarar?" Kwashe komai ta yi ta faɗa mata amma banda dokokinsa da maganar haihuwa. "Sakaran banza to ta Allah ba tashi ba da ya ƙi saninki ƴa mace kansa ya yi wa ai ya yi wa arziƙi dundu kuma zai dawo ya same ki ai kujera ce ke ko don ya zauna zai neme ki da tsohuwar zuma ake magani" Ta ce tana jin ciwon abin da aka yi wa ƴarta. "Yanzu ni ban san ya zan yi ba ko na faɗawa su EESHART da RUKY su zo dannar kirji?" "Hauka kike SALIMAH son a saka ki a bakin duniya, yadda muka cika baki muna daga ke ba ƙari ya samu mace kyakkyawa kuma yanzu a ji labari ya sauya to wallahi da fita waje ma sai ta gagaremu daga ni har ke, bakin ki alekum ki zauna ke kaɗai wani ma bai san an yi ba, shi kuma abin da ya yi ya je don kansa, saboda wallahi ba don mai kuɗi ne ba da a ce ABBAS ne ahalil fuƙara'u ba zan raga masa ba sai na wanke shi tas" "Ai shi ABBAS cewa ya yi ba zai mini kishiya ba " Ta ce cikin sanyin murya tana tuna yadda yake roƙon ta zauna da shi ba zai taɓa haɗa ta wata ƴa mace ba amma ga shi a kwana uku da aure ranar na huɗu za a danƙara mata kishiya. Haka suka zanta da Umma suka yi sallama Umma sai ashat take luƙawa tana tsinewa Alhaji Tahir. Nan ta kwanta bata tashi ba, yau ko yunwar ma bata ji, wajen ƙarfe takwas ta ji an turo ƙofar falo tana jin ƙaran sauran ƙofofin ɗakuna ana buɗewa ana rufewa wannan ya nuna mata cewa Alhaji Tahir ne ya zo nemanta shi ne yake duba ɗakunan ko zai ganta amma ganin bata nan bai kuma buɗe inda take ciki ba ya koma falon ƙasan ya zauna a kujera ya kame yana danna waya. "SALIMAH" Ya ƙwala mata kira, sai da ya yi sau uku don ya ɗauka tana sama ma shi kuma ba ya son ya hau saman, fitowa ta yi ba tare da ta amsa ba, sanye yake da blue shaddar sabuwa dal sai sheƙi take ya sha babbar riga da hula ga agogo takalmansa suna ƙafarsa gabaɗaya falon ya buɗaɗe da ƙamshin turarensa. Sau ɗaya ya ɗago ya ganta da rigar bacci idanun nan jeme-jeme tana aika masa kallon tsana ta ƙaraso ta zauna a wata kujerar da ban. "Kin tashi lafiya? Tsakanin sama da ƙasan wanne kika ɗauka? Zan fita ƙarfe goma za a ɗaura auren" "Ƙasa" Shi ne kawai abin da ta ce. "To ita amarya ASEEYA sai ta ɗau saman" Ya ce yana tashi tare da gyara babbar rigarsa ya fita, da harara ta bi bayan nasa tana maimaita sunan amaryar a zuciyarta. Wai "ASEEYA" Ko daɗi babu. Haka ta wuni suƙuƙu babu walwala yau ko charting ɗin ma ta kasa yi bata ganr komai zuciyarta kawai zafi take ashe haka mata suke ji in za a musu kishiya? Har gwara wasu sun ɗauki shekaru amma ita fa kwana uku a kwana ukun ko da ango bata tare ba. Bayan ta idar da sallar isha'i tana falon a zaune ta doka uban tagumi tana jiran zuwan ƴan kawo amarya, ƙaran buɗe get ne ya sa gabanta mummunan faɗuwa don ta ɗauka ƴan kawo amaryar ne amma abin mamaki ƙaaran shigowar mota ɗaya ta jiyo sai aka rufe get ɗin wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana fatan Allah sa ba a ɗaura auren ba, don a tunaninta Alhaji ne ya shigo gidan. Tsayuwar motar ta ji tare da buɗe ƙofa da rufewa sau biyu, tana ta saƙa da warwara ba ɗauki wani lokaci ba ta ji an turo ƙofar falo ido ta zubawa ƙofar, abin da ta gani ne ya so zautar da ita babu shiri sai gata a tsaye a kan ƙafafunta, Alhaji Tahir ne goye da wata zankaɗeɗiyar budurwa wacce fuskarta take a lulluɓe irin ta amare. "SALIMAH rufe ƙofar amarya na goyo wai bata son a zo kawota a taru ni kaɗai na je na ɗakkota kuma shi ne wai ba za ta taka da ƙafarta ba sai na goye ta kin ji rigima irin ta amare ko" Ya ce bakinsa washe kamar gonar auduga yadda dai yake washe mata baki lokacin tana gidansu amma zuwanta gidansa ya sa dariyarsa ta yi ɓatan dabo sai yanzu da yake cike da shauƙin ya goyo amarya. "Aunty SALIMAH ina wuni" Ta ji wata siririyar muryar amaryar da take bayan Alhaji ta faɗa. Basu jira cewarta ba kawai ya doshi matakala suka bar ta a tsaye tamkar an dasa ta a wajen, da kallo ta bi su sai da suka gama hayewa ta hango amaryar ta ɗaga mayafi ta mata gwalo ta rufe fuskar tare da ɗago mata hannu alamar bye-bye. Suna ɓacewa ganinta ta durƙushe a wajen ta saki kuka marar sauti, ta fara rarrafawa ta shige ɗakinta ko ƙofar falon da ya ce ta rufe bata rufe ba, a ƙasan cafet ta kwanta ta kamo sunan Umma ta rangaɗa mata kira. "Allah sa an fasa ba a ɗaura ba" Shi ne abin da Umma ta ce. "Umma an ɗaura shi fa ya ɗakko amarya goye da ita ya shigo falona, suka haye sama" "Shegu aniyarsu ta bi su, marar riƙe alƙawari na mamajon banza na mamajon wofi" Umma ta shiga surfa faɗa tana kumfar baki ita kuma SALIMAH kawai kuka take. *BAYAN KWANA GOMA* Alhaji da amarya sai da suka kwashe sati guda suna cin amarci, ta sha ganin takaici tsantsa da bariki, tana zaune a falo za su sakko hannunsu maƙale da juna, amaryar budurwa ce kuma tana da nata kyan daidai gwargwado, sai dai kissarta kaɗai ta isa saka kishiya kuka, kissa take irin ƴar ƙasan nan don hatta zaman falon ƙasa sai da ya gagari SALIMAH saboda gani takaici sai bedroom ta mayar wurin zamanta. Kwanakin amarya suna ƙarewa ya yi tafiya wai zai yi sati guda, dama ko da amarya tana nan ma saboda riɗi a ɓangaren suke basa tafiya nasa ɓangaren kuma SALIMAH ta lura kullum sai ya fita da dare tsakiyar dare amma bata san ina yake zuwa ba. Ganin yau kwanasa uku da tafiya kuma ya ce sati guda zai yi ta saka a ranta yau sai ta ziyarci part ɗin Alhaji Tahir, kawai so take ta ga uwar abin da ya saka a ɗakin ya ce ba a shiga wataƙila ma amaryar zai bar wa. Sai da ta bari sawu ya ɗauke babu motsin kowa sha ɗaya da rabi ta ɗakko mukullin da ya bata guda ɗayan nan da ya ce za take amfani da shi ranar bakinta. Har ta ƙaraso part ɗin tana waige-waige na rashin gaskiya, hannunta yana karkarwa ta saka mukullin ta buɗe ta shiga ta rufe ƙofar ba tare da ta saka mukulli ba. Da fitilar wayarta ta haska kasancewar ɓangaren duhu ƙarin, direct sama ta hau duk da bata taɓa hawa ba gabanta yana faɗuwa saboda ya ce kar a shiga amma ita sai ta ga ƙwal uwar daka. Gabas ta yi kamar yadda ya ce tana xuwa ta ga ɗakin, ta haska ta ga sunansa da ya faɗa a rubuce hannunta tsabar karkarwa har wayar neman suɓucewa take amma a haka ta murɗa handle ɗin cikin sa'a ƙofar ta buɗe alamar babu mukulli da sauri ta kutsa kai ciki don ƙarfin hali har da mayar da ƙofar ta rufe. Ɗakin ya fi kama da a kira shi ɗakin duhu don duk hasken fitilar hannunta ta waya sai ta ga tamkar an dushashe hasken bata gani sosai. Abubuwa da ta gani ne suka kusa tarwatsa ƙwaƙwalwa da zuciyarta, ƙwarangwal ɗin uban jikin mutane, ƙwarangwal ɗin ƙoƙon kan mutane, wasu jajayen kaya a rarrataye ga wasu ƙwarya masu ɗauke da wani abu ja tana haskawa ta ga jini ne a ƙwaraken. Zuciyarta tamkar za ta fasa ƙirjinta ta fito yanzu ta gane dalilin hana shiga ɗakin, wani abu ta gani jikinsa duka glass ne tana haskwa ta ga jarirai guda biyu suna wutsil-wutsil sai da ta toshe bakinta ganin bata saki ihu ba, tana cikin wannan halin ta ji ƙaran buɗe get ɗin gidan bata kawo komai ba duk da ta ji shigowar mota ta san Alhaji ba ya gari sai dai ko Khadija ko Aina'u don ASEEYA tuni ta haye sama ta san bata fita ba tana nan. Ita dai bata san ya aka yi ba amma ta ji an buɗe ƙofar part ɗin Alhaji sai gabanta ya yanke ya faɗi tashin hankalinta ya ninku, Alhaji Tahir da ɗaukan wani muhimmin abu a ɗakin sirrinsa ya dawo da shi, bai san ƙofar part ɗin a buɗe ba don da ya saka mukulli ya buɗe sai ya murɗa ta buɗu ya shigo, sama ya haye don ɗaukan abin da ya kawo shi. Yana dab da shiga ɗakin wayarsa ta ɗau ƙara, ya ɗaga. "Oga babu wani abu da ƙungiya za ta nema ban bada shi ba ko mene ne kuwa, ai in dai dodo ya faɗin jinin wanda zai sha a shirye nake na bayar kar ka manta fa uwar da ta kawo ni duniya ma na sadaukar da ita ga ƙungiya dodon tsafin ya yi awon gaba da jininta ta bar duniya ban ga wanda zan gagara bayarwa ba ai in dai a kan kuɗi ne to ba gudu ba ja da baya" SALIMAH tun da ta ji an hayo sama ta shiga wani tsoron da tashin hankalin da ya fi na da, musamman da aka tunkaro ɗakin da take ciki, ƙaran wayar ya sa ta kusa zauncewa saboda ta san ringtone ɗin Alhaji Tahir ne bata gama sanin tashin hankali ba saka masa rana ba sai da ta ji maganar da yake yi. Jikinta muguwar karkarwa yake fitsarin da ya cika mata mara ne ya kufce yana bin ƙafafunta. "Surukata? Wacce daga ciki ka san an bada jinin babar Hajiya Khadija fa, au babar ta ukun na gane babar SALIMAH kenan?" Wani bugawa ƙirjinta ya yi da ƙarfi nan take duniyar ta shiga juya mata jin ana maganar sadaukar da jini uwar da ita kaɗai ta rage mata, karkarwar hannunta ce ta saka wayarta kuɓucewa wayar ta faɗa kan wani kofin glass da yake ajiye a wurin cike da jini a take kofin ma ya fashe, wannan ƙaran ne ya daki kunnuwan Alhaji Tahir hakan ya ankarar da shi akwai wani mai ƙararran kwanan a cikin ɗakin... *A NAN NA KAWO MUKU ƘARSHEN BOOK 1 WANDA YA KASANCE FREE MAI SON JIN YADDA ZA TA KAYA A LABARIN, MAI AKA SANAR DA ALHAJI BUKHARI HAR YA FAƊI BABU RAI? WANE SAKAMAKO ZA SU FUSKANTA A RAYUWARSU? MAI USMAN ZAI YI WA ABBAS? SHIN SOYAYYA TANA ƘULLUWA TSAKANIN ABBAS DA HAWWA? WA ZAI AURI ABBAS HAWWA KO AMRAH? YAYA USMAN FA? YA ZA TA KAYA DA SALIMAH??? DA WASU TARIN AMSOSHIN TAMBAYOYIN SUNA CIKIN BOOK 2 WANDA ZA A BIYA NAIRA 500 KACAL AMMA GA WANDA ZA SU BIYA DAGA YAU LAHDI 12/12025 ZUWA 14/1/2025 ZA SU BIYA NAIRA 400 DAGA NAN ZAI KOMA 500* *ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHEDAR BIYA TA 09013181851* *NGD SOSAI TAKU MAMAN AFRAH ALƘALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME* 🥰