*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 1* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ABUJA *T* sarin unguwar tamkar a Turai, unguwa ce wadda ƙaramin mai kuɗi ba zai taɓa iya mallakar muhalli a cikinta ba, shahararrun masu kuɗi waɗanda su ka ci su ka tada kai irin manyan ‘yan siyasa, ƙusoshin gwamnati, ministoci, ‘yan majalissu, sanatoci. Su ne su ka yi sansani a cikin wannan unguwar. Cikin unguwar da kewayenta ba za ka taɓa ganin ƙasa ba, ƙamshin unguwar kaɗai ma ya fita daban. Manyan gidaje masu ɗauke da wasu irin manyan get, su suka fi yawa a nan. Kai kan ka kana dosar unguwar za ka san ka zo unguwar masu gidan rana, ta yadda tun daga nesa za ka hangi sojoji suna ta faman safa da marwa ɗauke da bindigoginsu, kamar masu shirin fita yaƙi. Ko kaɗan babu mabuƙaci a cikin wannan unguwa, za ka gane hakan ne ta yadda za ka dinga ganin kaji a abin shara waɗanda su ka yi funfuna. Shiru-shirun unguwar ya fi komai daɗaɗa wa ‘yan cikinta. Idan kai kaɗai ne a gidanka sai ka mutu har ka ruɓe babu wanda zai sani. Akasari ‘yan cikin unguwar kansu kawai suka sani, babu wanda ya damu da shiga harkar wani. Ba kowane maƙoci ne ya taɓa ganin maƙocinsa ba, saboda kowanne gida garƙame ya ke da get, tsakanin get ɗin ma zuwa gidan sai an yi tafiya mai nisa, wanda ko da yanka ka za a yi in maƙogoronka zai tsago saboda ihu, babu wanda zai ji ka. Akasarinsu ba su san me ake nufi da talauci ba, ba su san me ake nufi da sanyi ko zafi ba. Kullum suna cikin A.C, ba a taɓa ɗauke wuta wuta a wannn unguwar, duk da suna amfani da sola, shirun unguwar tamkar ba a duniya ba, in ka ji hayaniya sai ta motoci. Wannan kenan. Yana zaune a babban sitroom idanunsa a kan akwatun talabijin, yadda ya ga talakawa na kukan farin ciki, tare da sanya masa albarka ya dinga jin tsigar jikinsa na tashi. Burinsa kullum ya ga ya sanya talakawa farin ciki, hakan ne kaɗai ke sanya shi nishaɗi. Daga can bayansa Hajiya Khadija ce wadda ya ke kira da Ummi, motsinta ya jiyo ya yi saurin miƙewa ya ƙarasa gare ta. Zai yi magana ta riga shi. “Ka kalli yadda talakawa ke farin ciki, zuciyarsu fari ƙal! Deedat ɗina, kai ma Allah ya faranta maka”. Ya riƙo hannunta. “Ummina, duk ke ce. Komai na zama ke ce sila, ke ce ki ka ɗora ni a wannan turba. Na gode miki ƙwarai da gaske Ummina”. Ya kwantar da kai a kafaɗarta. Ta shafa gashin kansa. “Allah ya yi maka albarka”. Komawa su ka yi suka zauna, tare da sake mai da hankali a kan akwatun talabijin. Daidai lokacin da wasu matasa ke roƙon ya fito ya tsaya takarar kujerar gwamna. Ummi ta dube shi, “Ko bayan raina ban amince ka tsaya takarar siyasa ba, ban ƙi ka yi ja-gaba gurin cicciɓa na gari ba har ya kai ga gaci kamar yadda ka ke yi, amma siyasa? Sam ban lamunta ba”. Yana murmushi, “Ki kwantar da hankalinki, ɗanki ba shi da wannan ra’ayin, burina da man a kada wannan gwamnan, kuma na ji daɗi da ya faɗi tun a primary election, na san gaba ma ba zai taɓa cin nasara ba”. Ummi ta dinga kallonsa cike da wani irin tausayinsa. “Ummina, kina tuna baya ko? Ka da ki damu, da izinin Allah sai mun ga bayan wannan gwamnan”. Ta dinga kaɗa kai. “Ka bi a hankali, ka dinga sassautawa…” Kuka ne ke ƙoƙarin ƙwace mata, da sauri ta bar gurin. *** *** *** Gaba ɗaya ‘yan jam’iyyar hankalinsu a tashe ya ke, cikin kakkausar murya Injiniya Usain ya ke magana. “Ba mu san me ye dangantakanka da shi ba, mun sani ka sanshi, kai ne kaɗan ka san ta in da za mu gane waye shi, amma ka qi ba mu haske, yaro qarami yana faman shigar mana hanci da qudundune. Ka gaya mana sa, ko mu ɓatar da shege”. Dr. Munir ya furzar da huci mai zafi, wani irin miki ne ke taso masa. “Na kasa tantance shi ɗin waye kun fi kowa sanin in da ya ke yadda bami, shu’umi ne shi tamkar aljani”. Ya sauke ajiyar zuciya, “Mu dai mu tsananta bincike”. Ahmad Deedat kwance a kan wani faffaɗan gado lulluɓe da wani lallausar bargo ruwan damusa. Idanunsa a lumshe shi ba bacci ba, ba kuma ido biyu ba, muryar Sudais cikin rairo Suratul Mulk ne ke tashi a hankali. Ya so ma jin rurin wayarsa. Muskutawa ya yi cikin gyara kwanciyarsa ba shi da alamar kai wa wayar agaji har ta katse. Ba a ɗauki wani lokaci ba ta sake ɗaukar ruri. Ya ja tsaki ya miƙe zaune, ya dubi windo yana kallon in da sojoji ke faman shawagi. Ya ja tsaki, “Idan mutuwa ta zo ba za ku hana ta ɗauke ni ba”. ya ce a ransa. Ya miƙa hannu zai ɗauki wayar, ta sake katsewa. Ya maida kai ga kallon agogon da ke manne a jikin bango. aƙarfe shida na safe. “AAZEEN!” ya faɗa a ransa. Da sauri ya sake ɗaukar wayar ya shiga jujjuya ta a hannunsa. “Yau akwai rigima kenan”. Ya sake ayyanawa a ransa. Ya yi murmushi, daidai lokacin ya sake jin rurin wayar, ya yi saurin amsawa tare da karawa a kunne. “Me ya sa ba za ka ɗaga min waya ba”. ɗasasshiyar muryarta ta ratsa kunnensa, muryar da ya fi ƙauna fiye da kowacce murya, muryar da ta fi kowacce murya burge shi. Haka kawai sau tari ya ke kewar muryar, bai san dalili ba idan bai ji muryar ba ya kan ji tamkar ya yi missing ɗin wani abu mai muhimmanci. Ta ci gaba da faɗa, “Jiya na kira ba ka yi picking ba, yau ma ba ka da niyya”. Ta wani taƙƙaƙare. Shi kuma sai murmushi ya ke yi, acting ɗinta na burge shi. “Au ina ta magana ka ƙyale ni ko?” Ya ƙunshe dariya a ciki. “Ki yi haƙuri ƙanwata, ba zan sake ba”. Duk da bai san wace ce ita ba, amma ya gama karantar halayyarta, akwai ƙuruciya a tare da ita, haka ne ya sanya ya ke biye mata. “Au? Ka ci gaba da shirun ko?” “Kin ga ai na ga bai kamata ina katse ki a magana ba…” “To gaya min”. “Ba ni da lafiya ne shi ne na sha maganin bacci, wannan shi ne dalilin da ya hana in ji kiran wayar taki”. Tausayinsa ta ji sosai har zuciyarta. “Oh! I’m sorry, me ya sa ba ka sanar da ni ba?” Ya fahimci akwai alamun ruɗewa a cikin maganarta. “Ta ya ya zan sanar da ke? Kin mance dokar da ki ka saka min na cewar kada na kira, kuma da tuni sai dai ki ji na mutu, kin ga da a ce ma ina kiranki da yanzu na sanar da ke”. “Sannu, yanzu me ke yi maka ciwo?” Ya ce, “Ciki da zazzaɓi”. Ta zaro ido kamar yana a gabanta. “Tab! An fa ce ba a son namiji ya yi ciwon ciki”. “Ai na ji sauƙi, na je kyamis…” Ta katse shi a zabure, “Kana son mutuwa ne? Kada ka sake zuwa kyamis, asibiti za ka je a duba ka. Shi kyamis zuwa ake sayen magani, ko karɓar taimakon gaggawa. Yanzu ka shirya ka je ka ji. Bara na turo maka kuɗi, sai ka je…” Zai yi magana ya ji ta katse wayar. Yana zaune a dinning room yana kallon inda Ummi da masu aikinta Dije da Dela suna ta sintiri daga kicin zuwa dinning room. In ka ga yadda ta yi kwalliya sai ka rantse wani gagarumin bikin ko taro za ta je, komai nata abin burgewa, ba ta yadda wani ya yi ma Deedat girki da duk abin da zai kai bakinsa, ba ta da yarda a kan Deedat. Ba ta lamunce kowa ya shige masa in ya wuce Salim da Sulaiman. Ita ke tsara masa komai tun yana yaro burinta ya zamo mutumin da za ta yi alfahari da shi, duk wani mai ƴyamarsa ya yi alfahari da shi ta koya masa dabaru, da duk wani salo, ga shi yanzu ya girma, Allah ya amsa mata dukkan addu’o’inta, ko yanzu ta koma ga Ubangiji ba za ta yi baƙin ciki ba. Abin da kawai ya rage mata shi ne, ya yi aure ta ga jikanta. Ummi ce ke wannan tunanin a taƙaice, kawai Deedat ya zuba mata ido, da alama ta yi nisa. Ya shafi gefen fuskarta. Ta yi firgigi tare da sauke ajiyar zuciya. “Ummina, me ke damunki ne?” Ta taɓe baki haɗe da ɗaga kafaɗa. “Me ko zai dame ni bayan ga ni ga ka?” Ya yi murmushi, ya ɗan kurɓi shayi. Da sauri ya ajiye kofin saboda zafinsa. “Oh God! Sannu”. “Shi ke nan Ummi… da ma ina son zan je gurin Kabir, kuma…” “Ya isa, ban amince ba”. “Don Allah Ummi ki bar ni, babu abin da zai same ni”. “Idan ka je ba da yawuna ba, in kuma ka ƙi ji ga hanya”. Ya lura da yadda ranta ya ɓaci. Ya miƙe ya ƙarasa gabanta, ya dire a kan gwiwoyinsa. “Afuwan, ba zan sake ɗaga maganar ba”. Ta ɗan saki fuska, ta sa hannunta biyu ta tallafi haɓarsa. “Ka tabbata?” Ya jinjina kai. “That’s good! Na mance ban gaya maka ba, jibi Nabila za su dawo, Hajiya *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 2 3 4* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *B* an taba ganin mutum irinsa ba, ina da tambayoyin da zan yi masa bila adadin, ban san me ye ribarsa na tuna in boye kansa ba”. “Rangida na fi tunanin asalinsa talaka ne, kai ni gani nake ma kamar babu shi, kawai ana son yawo da hankalin mutane”. “No Dad, na ji a majiya mai qarfi akwai shi, duba ka ga yadda yake sakar wa Malaman addini miliyoyin kudi duk wata, sauka ko musabaqar alqur’ani da za a yi sai ya kashe miliyoyi. Na fi tunanin qila aljani ne. In ba aljani ba, waye zai yi abin da yake yi? Duk wani mai kudii yana so idan ya yi abin bajinta a san ya yi. Yana son duk inda ya sanya qafarsa ana girmama shi”. “Dad su ma wadan da suke program din nan ba su sanshi ba kenan?” Nurat ta tambaya. “Haka na ji ana cewa”. Aazeen ta ce, “To me ye amfanin abin da suke yi?” “Saboda suna son ya san taimakon da yake yi, saqo na isa gare su”. “Mtsew! Ji wani shashanci”. Alhaji Usman ya ci gaba da fadin, “Wannan da zai fito ya zama dan siyasa ba zai wani sha wuya ba, don abin ma da yake yi zai zamo kamar kamfen ne”. “Dad bana ji an ce ba shi da aure ba, kuma mara aure ba ya tsayawa takarar neman gwamna?” “Wannan ai mai sauqi ne, daga ya amice cikin lokaci qanqani zai iya yin aurensa”. “Dad idan na kwanta ina mafarkin ya zama mijina. Dad ina ma zan ganshi ko da sau daya ne?” “To Dad ta yaya taimakonsa ke isa hannun mutane?” Nurat ta sake tambaya. “Ya kan kintaci duk lokacin da yake da buqata ya je inda yake buqata, bayan kiran assalatu yake isar da zakkarsa ko sadaka, sai dai ka ji an dan qwanqwasa maka qofa. Kana budewa za ka ci karo da abin da yake rabonka, duk nacinka ba za ka ga kowa ba. Da yawa an sha yin dako sai kun gama hada target da inda za ku ganshi, sai kawai ya sauya yanayin lokutan rabon babu zato babu tsammani ka ke ganin kayan arziqi, kama buhun shinkafa, taliya, kudi, sutura da sauransu. Ba qananan kudi yake badawa ba, kudi ne wanda zai ishe ka ka ja jari, wanda in ka yi dace ka yi sallama da talauci. Dadin dadawa yana da asibitoci, makarantu wadanda an gina su ne kawai saboda talakawa”. “Tab! Ka ce shi kawai don taimako aka halicce shi?” Aazeen ta fada. “kila ma na sanshi”. Alhaji Usman ya yi dariya, “Babu mamaki don an ce yana nan yana mu’amala da mutane ba tare da sun sanshi din ba ne”. “Gaskiya wannan batan basira ne, shi ke nan ya dauki kansa kamar kowa, ba ya son idan ya shiga guri a dinga nuna shi ana b shi girma? Shi sam bai damu da ya yi suna ba Dad? Wadannan abubuwan fa su ne jin dadin, kamar ni in na shiga guri za ka ga yadda ake girmama ni, ina taka duk wanda na so”. “Yaya Aazeen wannan riya kenan fa, kuma duk mutumin da yake riya ladansa iya nan kawai za ta tsaya. Sai dai mutane su yabe shi. Shi ya ji dadi gurin Ubangiji komai fanko yake”. Ta ja tsaki, “Ai kin ji irinta. Dad shi ya sa na qi amincewa da makarantun nan, islamiyya tahfiz, makarantar magriba ko yaushe ba ta da hutu tana zuwa ana zura mata al’adun mutan da. Ta sauke abin da aka ce an fi buqata, wato alqur’ani mai girma, amma har yanzu ta qi ta haqura”. “Ke ma da a ce kina zuwa duk za ki watsar da wadannan shirmen da ki ke yi”. Hajiya Rahma ta fada. “Hum Ammi kenan, da girmana da komai kawai sai na je na zauna ana koyar da ni salon kowa ya raina ni? Ita dai da ta ga za ta iya sai ta je ta qara ta”. “Da Allah malama rufa mana baki”. Ammi ta ce da ita. A take ta ji haushi, Alhaji Usman ya dubi hajiya Rahma. “Ba kya kyautawa”. “To yanzu me na yi ne?” Bai ce da ita komai ba ya miqe ya rufa wa Aazeen baya. A lokacin da kowa ke bacci, a lokacin ta ke sake sabon zama a gindin akwatun talabijin, a nan ne ta ke cashe mata kallon. Qarfe goma sha biyu tana zaune a sitroom dinta ta dora qafa daya kan daya, lokaci-lokaci ta kan dauki tea ta kurba. Rimot ta dauka tana canza tashoshi. Ta ji dadin film din da ta ga ana yi. Ta ajiye rimote gaba daya hankalinta ya karkata daidai lokacin da aka nuno jarumin da budurwarsa rungume da juna suna yi wa juna wani irin wasa, yadda jarumin yake ba ta wani hot kisses tare da sake rungume ta tsam-tsam cikin wani irin salo, ji ta yi gaba daya hankalinta na neman fita a jikinta. “Wayyo! Tana son wannan rayuwa, su kam Turawa sune suka zo duniya a sa’a, sukan yi duk abin da suka so a gaban kowa ba su da shamaki da duk wata rayuwa da holewa. Ta lumshe ido tare da kwantar da kai a allon kujera tana saukar da numfshi, ina ma a Turan aka halicce ta? Ba za ta iya jurewa ba. ta zaro waya ta shiga lalubar wata lamba. Ringin daya aka dauka daga dayan bangaren aka ce, “Ya na ji muryarki haka? Me ke faruwa?” “Komi ma ya faru. Ya za a yi ka zo gare ni?” “Ke ba ki da hankali? Idan na zo in ce me? Ba ki ga dare ya yi ba? ki lallaba zuwa gobe, amman gaya min duk me ya janyo hakan”. Ta ja tsaki hade da katse wayar. Ta yi lamo cikin wani irin shauqi, shi ne kawai yake dan kwantanta yadda ta ke so, shi ne yake fahimtar feeling dinta, shi ma din tana tunanin don ya yi karatu a Turai ne. “Mtsew!” haka ake ta faman son ta yi aure, to ta auri me? Babu abin da auren bahaushe ke haifarwa sai bacin rai. Su dai burinsu idan suka tashi da safe Allah-Allah suke yi su wuce gurin neman kudi, idan suka tashi a kasuwar su wuce majalisar gulma, wanda su abokan nasu ke dora musu wani tunanin ko layin rashin mutunci. A nan suke koyon tsumulmula, suke koyon son mata. A nan ake cusa musu ra’ayin su kara aure, ba za su tashi dawowa gida ba sai matar ta yi bacci, yaransa sun yi bacci. Kai wani ma saboda tsabar kwarewa da yawon majalisa yaransa ba su gama sanin waye shi ba, wani fannin in matar ba ta samu damar yin bacci ba, daga ta yi musu sannu da zuwa a ciki za su amsa suna faman cika da batsewa, wai kada ta raina su, za su baka abinci idan ba masu ci a waje ba ne, da zarar sun dirka a ciki sai kwanciya, sai dai ka ji yana jan minshari, shi ke nan ke an mayar da ke dutse kin zamo mai zaman ‘ya’yanki. “Ammina ta kasa gane inda na dosa ita dai kullum na fitar da mijin aure, ba zan taba biye mata ba. Mijin da zan yi rayuwa da shi dan gaske ne, wanda zai ba ni hakkina a duk lokacin da na buqata. Ai ni da na ga mijin da zai iya ina ganewa, har yanzu ban ganshi ba”. Tana matuqar son namiji wanda ya kai qololuwa gurin haduwa, kyawun, suffa da na aljihu, shahararren mai kudi shi ne burinta, don haka a kullum ta ke mafarkin kasancewa da Ahmad Deedat. Tana ji a ranta kamar shi din ajiyarta ne. Kiraye-kirayen sallah ne ya katse mata tunani. Mikewa ta yi hade da kashe kayan kallon ta nufi dakin Ammi, wadda da alamun kiran sallar bai ratsa ta ba. Ta shiga dukan filon da Ammin ke kwance a kai. A firgice ta bude ido, tana tunanin ta makara. Jin alamun za a tada sallar a masallaci ta yi, da sauri ta miqe har tana ture Aazeen. “Haba Ammi, ki bi a hankali mana, ba fa ce miki aka yi tashin alkiyama za a yi ba”. Ba ta bi ta kanta ba ta fice abinta. Aazeen ta koma bedroom dinta ta mike a gado, tuni bacci ya yi awon gaba da ita. karfe goma da rabi sun hallara a dinning room, Alhaji Usman ya dubi Hajiya Rahma, “Ya dai?” “Me ka gani?” “Na ga kamar kina da damuwa”. Ta kada kai, “Ko daya”. Nurat ko littafi ne a hannunta tana dubawa. “Nurat ki aje littafin nan ki ja abinci duk kin daga hankali, in dai ba kya cin abinci zan fa hana ki”. Ta ajiye alqur’anin a gefe tana cin abincin. Tana leka surar da ke a bude. Aazeen ce ta fito cikin kayan bacci manne da waya a kunne. Da alama waya ta ke amsawa, gaba daya ita suke bi da kallo. Bathroom ta nufa. “Ran gida me ya samu bathroom dinki?” “Ina ganin kamar rariyar ce ta toshe”. “Ok”. Ta shige bathroom din. Mintina biyar ta diba a ciki ta fito da kayanta a jike sharkaf! Wai nan alwala ta daura. Ammi ta cika fal da takaici, kokarin zama ta ke a dinning. “Kin ga ki fara sitirta jikinki, idan ki ka yi sallah sai ki yi break ”. “Tab! Ammi, sallah ba zai yiwu cikin wannan yanayin ba, kin ga kuwa yadda nake jin yunwa?” Kokarin zuba dankali ta ke a plate. “Magana fa nake yi”. In ji Ammi. “Oh my Mom, please ki kyale ni”. “Haba Rahma ke kuwa ki kyale ta mana, ai shi ci shi ne gaba da komai”. Dole ta yi shiru tana jin zuciyarta duk a jagule. Ta sani tun farko shi ne masomin rusa tarbiyyar Aazeen, yadda yake yi din ne ya sanya ta ke tuhumarsa da abubuwa iri-iri. Ta sani wannan ba shi ne so ba, me ya sa ita Nurat bai ba ta irin wannan tarbiyyar ba? Shin a cikinsu waye ya fi so kenan? Yana nuna ma Aazeen duk wata gata da soyayya, ba ya son bacin ranta. Ita kuma Nurat tsangwama, da kyara. Yana shigowa gida sai ya fara tambayar ta yi sallah? Ta je islamiyya da ire-iren wadannan tambayoyin. Shin wa ke nan yake kauna? “Dankali kawai na gani, ban ga farfesun da na ce ladidi ta yi min ba?” “Kira ta, kila karasawa ne ba ta yi ba, ai babu wanda zai ketare umarninki Rangida”. Ta bude murya baki daya cikin kwala mata kira. A sukwane ta karaso tare da durkusawa a gabanta. Ta watsa mata harara. “Ina kayan karyawata?” “Yanzun nan na hattama, bari na kawo miki”. Da sauri ta yi waje, sai ga ta da kayan karyawar ta jere a gabanta. Janye plate din Ammi ta yi a gabanta. “Kada ki taba komai a nan ba tare da kin je kin sauya kayan jikinki ba”. “Haba Ammi, kashe ni za ki yi? Na ce da ke yunwa nake ji. Ni kam gaskiya a’a”. Ai kuwa ta shiga yi mata fada, takaici kamar Aazeen za ta mutu. Baqin cikinta wai Ammi ta yi mata fada a gaban mai aiki. Juyin duniyar nan ba ta mike ba, ta bude farfesun a qufule, cikin neman wanda za ta huce a kansa. Ta dubi Ladidi. “Cewa na yi ki saka min curry? Uban waye ya sa ki? Kawai ba ki yi shawara da ni ba kin yi abin da ki ke so ko?” A sanyaye, “Ki yi haquri, na ga ai kullum ina yi miki amfani da shi”. “Shut up! Ina magana kina yi?” Gaba xaya ta dauki plate din farfesun ta watsa mata a fuska. Wata gigitacciyar qara Ladidi ta saka. Da gudu Nurat ta mike tare da rungume ta a jiki. Ladidi na ta ihu tamkar wadda ake kokarin zare mata rai. Da taimakon Nurat suka nufi famfo. “Man kana ganin abin da Aazeen ta aikata ko?” Hajiya Rahma ta fada tana kallon Alhaji Usman. “Ita ta ja ma kanta. Ya kamata ta dinga kiyaye matakan aikinta, tunda ba kyauta ta ke aikin ba”. “Dad, ina son gaya maka. su Zee fa na tafe”. Aazeen ta fada ba tare da ta nuna nadama a abin da ta aikata ba. Gaba daya ma sun mance da ita Hajiya Rahmar, hirarsu suka shiga na yadda za su sauki bakin nata. Miqewa ta yi cike da takaici, har lokacin tana jin ihun kukan Ladidi, Nurat na faman ba ta haquri. A can shashin masu aiki, Ladidi ta yi matashi da cinyar Nurat ta dage sai bushe mata idanu ta ke faman yi, hankalinta a tashe, yadda idanun suka kumbure sun yi jajir da kyar ta ke motsa su. Hawaye sai faman tsinkowa suke daga idanun. Cikin muryar kuka. “Ladidi sannu, za ki warke. Yana yi miki zafi? Sannu”. Ta rude matuqa, jikinta sai bari yake, zuciyarta fal haushin Aazeen. Karin bakin cikinta shi ne na halin ko’inkular da akai wa Ladidi akalla ya kamata su zo su duba halin da Ladidi ke ciki, yanzu ya za ta yi idan Ladidin ta makance? “Nurat ina son dora girki”. Cikin tausayawa, “Haba ta ya ya za ki iya wani girki? Ki bari ni zan yi kokari in ga na yi”. “A’a Nurat, ki rufa min asiri”. “Kada ki damu babu wanda zai fahimci haka. Ina zuwa… amma dai akwai duk abin da zan bukata ko?” Ladidi ta jinjina kai. “Ok, yanzu ki kwanta ki huta kafin ki tashi na gama kin ji”. “Na gode Nurat”. Ta bi Nurat da kallo tana jin qaunarta a ranta. Halayyarta daban da na iyayenta, kamar yadda ta lura kowa na gidan bai damu da damuwar wani ba, sun dauki rayuwarsu tamkar na turawa, musamman Aazeen wadda duka dabi’unta irin na ubanta ne. Ita kam Hajiya Rahma babu wanda ya fahimci inda ta sa gaba, ba za a dai a kira ta mara kirki ba, kodayake ba lallai a fahimci wace ita ba, saboda ba ta cika shiga shirgin mutane ba, sabanin Nurat wadda ba ta wuce shekaru sha bakwai ba, yarinya mai mutumci da shiga rai, wadda ba ta xauki kanta da zafi ba, ba ta da wahalar sha’ani, kunyarta shi ke kara mata daraja a idanun jama’a, don hakan ya zame mata tamkar wani ado. Tazarar da ke tsakanin kicin da dakunan da ke gidan ya sanya babu wanda ya lura da kai-komonta. Wanke-wanke ta fara yi, ta ci uwar damara. Bayan ta gama ta shiga dogon tunanin abin da za ta dafa wanda ba zai ba ta wahala ba. taliya ta ayyana a ranta, amma ta ya ya za ta sarrafa kayan miya? Ita ba ta taba kwatanta shiga kicin don sarrafa wani girki ba. Komawa ta yi dakin Ladidi, don ta gaya mata yadda za ta yi. Bacci ta ke yi lakadan, har da su minshari. Murmushi ta yi ta koma ta shiga tunanin yadda za ta yi. Tunawa ta yi da tana da littafin girki, da sauri ta nufi ma’ajiyar littattafanta. KADARAR KITCHEN wanda Bilkisu Salisu Funtua ta rubuta ta nemi guri ta zauna, tare da dubo abin da ta ke son dafawa. Ta mayar da littafin ma’ajiyarsa, ta koma kicin ta debo kayan miya ta wanke, ta soma yanka albasa. Ji ta yi wuqa ta shige hannunta, ta kwalla kara tare da sakin wukar yadda ta ga jini na zuba ne ya sanya ta rudewa. A sukwane Zaruk ya dano kicin din ya kai hannu zai riko hannunta. Da sauri ta maida hannun baya cikin tsananin tsoro. “Ki bari in gani, ba ki ga jini ne ke zuba ba?” Ta yi saurin maida hawayen da ke qoqarin silalo mata. “Kada ka damu, kawai jinin ne, amma ai babu zafi”. “Oh God! Wai ke me ma ya kawo ki kicin? Wa ya aike ki?” Ta fara in’ina, ya daure fuska. “Na ce da ke waye ya aiko ki kicin?” Za ta yi magana ya mike a fusace zai fita. “Don Allah ka yi haquri, zan gaya maka. Ka dawo don Allah Yaya Zaruk”. Ya koma ya zauna cikin kafe ta da idanunshi. “Ke nake ji”. “Ladidi ba ta da lafiya shi ne nake taya ta”. Ya sake xaure fuska. “Ita din ce ta ce ki taya ta?” Cikin rawar murya, “A’a, to gaya min”. Dole ta zabi ta ba shi labarin yadda abin ya faru. Ya ja tsaki ya janyo mata kujera. “Maza zauna”. Ba ta da zabi dole ta bi umarninsa. Komawa ta yi ta zauna, nade hannun rigarsa ya yi ya shiga aiki tukuru. Ta dinga kunshe dariya a ciki, ga mamakinta Zaruk ya iya komi. Ya dube ta a sakarce, “Nurat, fito ki yi dariyarki a bayyane”. Ta dabarbarce, “Da gaske Yaya Zaruk ba dariya nake yi ba”. Jalof din taliya ya yi, sai plaintain da ya soya farfesun kifi. Ya diba a cokali ya mika mata. Ya yi mata alama da ta yi testing. Ta karba tana dandanawa. Ya kafe ta da ido. “Ya ki ka ji?” “Yaya Zaruk, ashe ka iya girki?” Ya harare ta, “je ki yi maza ki shirya dinning ko?” “An gama Yayana”. Da sauri ta yi abin da ya ce. Bayan ta gama shirya komai ya ce da ita, zai je ya siya ma Ladidi magani. Yana fita ta shiga wanka. Zaruk ta hango da Hajiya Rahma zaune suna cin abinci, ta sakar masa murmushi. Karasawa ta yi ta zauna. Ba a jima ba Alhaji Usman suka shigo da Aazeen rike da ledoji a hannu, su ma joining suka yi zaman cin abincin. “Yau Rangida babu korafi, da alama abincin ya yi dadi”. Nurat ta dubi Zaruk ya sakar mata murmushi. “No Dad, kawai dai ina jin yunwa ne”. “Da ma ai ke ba a taba iya miki”. Hajiya Rahma ta ce da ita. “Ladidi ta cancanci tukwici kenan?” In ji Zaruk yana kallon Nurat, ya faki idonsu a hankali ya dinga motsa baki yana nufin zai fada. Ta yi saurin kada kai tana rokonsa. Mikewa ya yi tsaye. “Ni zan wuce Ammi, a yi wa kuku godiya sosai”. Ya fada yana murmushi. ABUJA “Ummi ya kamata ki saba, na yi tafiya zuwa qasashen waje bila’adadin, na zaga duniya komai bai same ni ba, nan zuwa Kano tafiyar mintina ne, da zarar jirginmu ya sauka shi kenan an wuce gurin. Ko kina tsoro ne kada jirgi ya fado da dan lelenki?” Deedat ya fada yana kokarin tallafo kuncinta da hannayensa biyu. Ta sauke ajiyar zuciya cikin damuwa. “Ba haka ba ne, kawai dai ina tsintar kaina cikin rudu duk lokacin da ka ambata cewar za ka Kano. Bana samun nutsuwa, ban san me ya sa haka ba”. Ya yi murmushi cikin kokarin kwarara mata gwiwa. “No, Ummina kada ki mance kirarina, in ka san ni ni ne, in ba ka sanni ba, ba ni ba ne. Ummina. Kowa ya san ba ni ba ne, kin ji sam ba ni ba ne babu wanda ya san ni, kuma ma ban da ke da abinki addu’arki fa na tare da ni, ba zan mutu YAUTAR ZUCIYA PAGE 2 3 4 NA BILKISU H MUHD Ban taba ganin mutum irinsa ba, ina da tambayoyin da zan yi masa bila adadin, ban san me ye ribarsa na tuna in boye kansa ba”. “Rangida na fi tunanin asalinsa talaka ne, kai ni gani nake ma kamar babu shi, kawai ana son yawo da hankalin mutane”. “No Dad, na ji a majiya mai qarfi akwai shi, duba ka ga yadda yake sakar wa Malaman addini miliyoyin kudi duk wata, sauka ko musabaqar alqur’ani da za a yi sai ya kashe miliyoyi. Na fi tunanin qila aljani ne. In ba aljani ba, waye zai yi abin da yake yi? Duk wani mai kudii yana so idan ya yi abin bajinta a san ya yi. Yana son duk inda ya sanya qafarsa ana girmama shi”. “Dad su ma wadan da suke program din nan ba su sanshi ba kenan?” Nurat ta tambaya. “Haka na ji ana cewa”. Aazeen ta ce, “To me ye amfanin abin da suke yi?” “Saboda suna son ya san taimakon da yake yi, saqo na isa gare su”. “Mtsew! Ji wani shashanci”. Alhaji Usman ya ci gaba da fadin, “Wannan da zai fito ya zama dan siyasa ba zai wani sha wuya ba, don abin ma da yake yi zai zamo kamar kamfen ne”. “Dad bana ji an ce ba shi da aure ba, kuma mara aure ba ya tsayawa takarar neman gwamna?” “Wannan ai mai sauqi ne, daga ya amice cikin lokaci qanqani zai iya yin aurensa”. “Dad idan na kwanta ina mafarkin ya zama mijina. Dad ina ma zan ganshi ko da sau daya ne?” “To Dad ta yaya taimakonsa ke isa hannun mutane?” Nurat ta sake tambaya. “Ya kan kintaci duk lokacin da yake da buqata ya je inda yake buqata, bayan kiran assalatu yake isar da zakkarsa ko sadaka, sai dai ka ji an dan qwanqwasa maka qofa. Kana budewa za ka ci karo da abin da yake rabonka, duk nacinka ba za ka ga kowa ba. Da yawa an sha yin dako sai kun gama hada target da inda za ku ganshi, sai kawai ya sauya yanayin lokutan rabon babu zato babu tsammani ka ke ganin kayan arziqi, kama buhun shinkafa, taliya, kudi, sutura da sauransu. Ba qananan kudi yake badawa ba, kudi ne wanda zai ishe ka ka ja jari, wanda in ka yi dace ka yi sallama da talauci. Dadin dadawa yana da asibitoci, makarantu wadanda an gina su ne kawai saboda talakawa”. “Tab! Ka ce shi kawai don taimako aka halicce shi?” Aazeen ta fada. “kila ma na sanshi”. Alhaji Usman ya yi dariya, “Babu mamaki don an ce yana nan yana mu’amala da mutane ba tare da sun sanshi din ba ne”. “Gaskiya wannan batan basira ne, shi ke nan ya dauki kansa kamar kowa, ba ya son idan ya shiga guri a dinga nuna shi ana b shi girma? Shi sam bai damu da ya yi suna ba Dad? Wadannan abubuwan fa su ne jin dadin, kamar ni in na shiga guri za ka ga yadda ake girmama ni, ina taka duk wanda na so”. “Yaya Aazeen wannan riya kenan fa, kuma duk mutumin da yake riya ladansa iya nan kawai za ta tsaya. Sai dai mutane su yabe shi. Shi ya ji dadi gurin Ubangiji komai fanko yake”. Ta ja tsaki, “Ai kin ji irinta. Dad shi ya sa na qi amincewa da makarantun nan, islamiyya tahfiz, makarantar magriba ko yaushe ba ta da hutu tana zuwa ana zura mata al’adun mutan da. Ta sauke abin da aka ce an fi buqata, wato alqur’ani mai girma, amma har yanzu ta qi ta haqura”. “Ke ma da a ce kina zuwa duk za ki watsar da wadannan shirmen da ki ke yi”. Hajiya Rahma ta fada. “Hum Ammi kenan, da girmana da komai kawai sai na je na zauna ana koyar da ni salon kowa ya raina ni? Ita dai da ta ga za ta iya sai ta je ta qara ta”. “Da Allah malama rufa mana baki”. Ammi ta ce da ita. A take ta ji haushi, Alhaji Usman ya dubi hajiya Rahma. “Ba kya kyautawa”. “To yanzu me na yi ne?” Bai ce da ita komai ba ya miqe ya rufa wa Aazeen baya. A lokacin da kowa ke bacci, a lokacin ta ke sake sabon zama a gindin akwatun talabijin, a nan ne ta ke cashe mata kallon. Qarfe goma sha biyu tana zaune a sitroom dinta ta dora qafa daya kan daya, lokaci-lokaci ta kan dauki tea ta kurba. Rimot ta dauka tana canza tashoshi. Ta ji dadin film din da ta ga ana yi. Ta ajiye rimote gaba daya hankalinta ya karkata daidai lokacin da aka nuno jarumin da budurwarsa rungume da juna suna yi wa juna wani irin wasa, yadda jarumin yake ba ta wani hot kisses tare da sake rungume ta tsam-tsam cikin wani irin salo, ji ta yi gaba daya hankalinta na neman fita a jikinta. “Wayyo! Tana son wannan rayuwa, su kam Turawa sune suka zo duniya a sa’a, sukan yi duk abin da suka so a gaban kowa ba su da shamaki da duk wata rayuwa da holewa. Ta lumshe ido tare da kwantar da kai a allon kujera tana saukar da numfshi, ina ma a Turan aka halicce ta? Ba za ta iya jurewa ba. ta zaro waya ta shiga lalubar wata lamba. Ringin daya aka dauka daga dayan bangaren aka ce, “Ya na ji muryarki haka? Me ke faruwa?” “Komi ma ya faru. Ya za a yi ka zo gare ni?” “Ke ba ki da hankali? Idan na zo in ce me? Ba ki ga dare ya yi ba? ki lallaba zuwa gobe, amman gaya min duk me ya janyo hakan”. Ta ja tsaki hade da katse wayar. Ta yi lamo cikin wani irin shauqi, shi ne kawai yake dan kwantanta yadda ta ke so, shi ne yake fahimtar feeling dinta, shi ma din tana tunanin don ya yi karatu a Turai ne. “Mtsew!” haka ake ta faman son ta yi aure, to ta auri me? Babu abin da auren bahaushe ke haifarwa sai bacin rai. Su dai burinsu idan suka tashi da safe Allah-Allah suke yi su wuce gurin neman kudi, idan suka tashi a kasuwar su wuce majalisar gulma, wanda su abokan nasu ke dora musu wani tunanin ko layin rashin mutunci. A nan suke koyon tsumulmula, suke koyon son mata. A nan ake cusa musu ra’ayin su kara aure, ba za su tashi dawowa gida ba sai matar ta yi bacci, yaransa sun yi bacci. Kai wani ma saboda tsabar kwarewa da yawon majalisa yaransa ba su gama sanin waye shi ba, wani fannin in matar ba ta samu damar yin bacci ba, daga ta yi musu sannu da zuwa a ciki za su amsa suna faman cika da batsewa, wai kada ta raina su, za su baka abinci idan ba masu ci a waje ba ne, da zarar sun dirka a ciki sai kwanciya, sai dai ka ji yana jan minshari, shi ke nan ke an mayar da ke dutse kin zamo mai zaman ‘ya’yanki. “Ammina ta kasa gane inda na dosa ita dai kullum na fitar da mijin aure, ba zan taba biye mata ba. Mijin da zan yi rayuwa da shi dan gaske ne, wanda zai ba ni hakkina a duk lokacin da na buqata. Ai ni da na ga mijin da zai iya ina ganewa, har yanzu ban ganshi ba”. Tana matuqar son namiji wanda ya kai qololuwa gurin haduwa, kyawun, suffa da na aljihu, shahararren mai kudi shi ne burinta, don haka a kullum ta ke mafarkin kasancewa da Ahmad Deedat. Tana ji a ranta kamar shi din ajiyarta ne. Kiraye-kirayen sallah ne ya katse mata tunani. Mikewa ta yi hade da kashe kayan kallon ta nufi dakin Ammi, wadda da alamun kiran sallar bai ratsa ta ba. Ta shiga dukan filon da Ammin ke kwance a kai. A firgice ta bude ido, tana tunanin ta makara. Jin alamun za a tada sallar a masallaci ta yi, da sauri ta miqe har tana ture Aazeen. “Haba Ammi, ki bi a hankali mana, ba fa ce miki aka yi tashin alkiyama za a yi ba”. Ba ta bi ta kanta ba ta fice abinta. Aazeen ta koma bedroom dinta ta mike a gado, tuni bacci ya yi awon gaba da ita. karfe goma da rabi sun hallara a dinning room, Alhaji Usman ya dubi Hajiya Rahma, “Ya dai?” “Me ka gani?” “Na ga kamar kina da damuwa”. Ta kada kai, “Ko daya”. Nurat ko littafi ne a hannunta tana dubawa. “Nurat ki aje littafin nan ki ja abinci duk kin daga hankali, in dai ba kya cin abinci zan fa hana ki”. Ta ajiye alqur’anin a gefe tana cin abincin. Tana leka surar da ke a bude. Aazeen ce ta fito cikin kayan bacci manne da waya a kunne. Da alama waya ta ke amsawa, gaba daya ita suke bi da kallo. Bathroom ta nufa. “Ran gida me ya samu bathroom dinki?” “Ina ganin kamar rariyar ce ta toshe”. “Ok”. Ta shige bathroom din. Mintina biyar ta diba a ciki ta fito da kayanta a jike sharkaf! Wai nan alwala ta daura. Ammi ta cika fal da takaici, kokarin zama ta ke a dinning. “Kin ga ki fara sitirta jikinki, idan ki ka yi sallah sai ki yi break ”. “Tab! Ammi, sallah ba zai yiwu cikin wannan yanayin ba, kin ga kuwa yadda nake jin yunwa?” Kokarin zuba dankali ta ke a plate. “Magana fa nake yi”. In ji Ammi. “Oh my Mom, please ki kyale ni”. “Haba Rahma ke kuwa ki kyale ta mana, ai shi ci shi ne gaba da komai”. Dole ta yi shiru tana jin zuciyarta duk a jagule. Ta sani tun farko shi ne masomin rusa tarbiyyar Aazeen, yadda yake yi din ne ya sanya ta ke tuhumarsa da abubuwa iri-iri. Ta sani wannan ba shi ne so ba, me ya sa ita Nurat bai ba ta irin wannan tarbiyyar ba? Shin a cikinsu waye ya fi so kenan? Yana nuna ma Aazeen duk wata gata da soyayya, ba ya son bacin ranta. Ita kuma Nurat tsangwama, da kyara. Yana shigowa gida sai ya fara tambayar ta yi sallah? Ta je islamiyya da ire-iren wadannan tambayoyin. Shin wa ke nan yake kauna? “Dankali kawai na gani, ban ga farfesun da na ce ladidi ta yi min ba?” “Kira ta, kila karasawa ne ba ta yi ba, ai babu wanda zai ketare umarninki Rangida”. Ta bude murya baki daya cikin kwala mata kira. A sukwane ta karaso tare da durkusawa a gabanta. Ta watsa mata harara. “Ina kayan karyawata?” “Yanzun nan na hattama, bari na kawo miki”. Da sauri ta yi waje, sai ga ta da kayan karyawar ta jere a gabanta. Janye plate din Ammi ta yi a gabanta. “Kada ki taba komai a nan ba tare da kin je kin sauya kayan jikinki ba”. “Haba Ammi, kashe ni za ki yi? Na ce da ke yunwa nake ji. Ni kam gaskiya a’a”. Ai kuwa ta shiga yi mata fada, takaici kamar Aazeen za ta mutu. Baqin cikinta wai Ammi ta yi mata fada a gaban mai aiki. Juyin duniyar nan ba ta mike ba, ta bude farfesun a qufule, cikin neman wanda za ta huce a kansa. Ta dubi Ladidi. “Cewa na yi ki saka min curry? Uban waye ya sa ki? Kawai ba ki yi shawara da ni ba kin yi abin da ki ke so ko?” A sanyaye, “Ki yi haquri, na ga ai kullum ina yi miki amfani da shi”. “Shut up! Ina magana kina yi?” Gaba xaya ta dauki plate din farfesun ta watsa mata a fuska. Wata gigitacciyar qara Ladidi ta saka. Da gudu Nurat ta mike tare da rungume ta a jiki. Ladidi na ta ihu tamkar wadda ake kokarin zare mata rai. Da taimakon Nurat suka nufi famfo. “Man kana ganin abin da Aazeen ta aikata ko?” Hajiya Rahma ta fada tana kallon Alhaji Usman. “Ita ta ja ma kanta. Ya kamata ta dinga kiyaye matakan aikinta, tunda ba kyauta ta ke aikin ba”. “Dad, ina son gaya maka. su Zee fa na tafe”. Aazeen ta fada ba tare da ta nuna nadama a abin da ta aikata ba. Gaba daya ma sun mance da ita Hajiya Rahmar, hirarsu suka shiga na yadda za su sauki bakin nata. Miqewa ta yi cike da takaici, har lokacin tana jin ihun kukan Ladidi, Nurat na faman ba ta haquri. A can shashin masu aiki, Ladidi ta yi matashi da cinyar Nurat ta dage sai bushe mata idanu ta ke faman yi, hankalinta a tashe, yadda idanun suka kumbure sun yi jajir da kyar ta ke motsa su. Hawaye sai faman tsinkowa suke daga idanun. Cikin muryar kuka. “Ladidi sannu, za ki warke. Yana yi miki zafi? Sannu”. Ta rude matuqa, jikinta sai bari yake, zuciyarta fal haushin Aazeen. Karin bakin cikinta shi ne na halin ko’inkular da akai wa Ladidi akalla ya kamata su zo su duba halin da Ladidi ke ciki, yanzu ya za ta yi idan Ladidin ta makance? “Nurat ina son dora girki”. Cikin tausayawa, “Haba ta ya ya za ki iya wani girki? Ki bari ni zan yi kokari in ga na yi”. “A’a Nurat, ki rufa min asiri”. “Kada ki damu babu wanda zai fahimci haka. Ina zuwa… amma dai akwai duk abin da zan bukata ko?” Ladidi ta jinjina kai. “Ok, yanzu ki kwanta ki huta kafin ki tashi na gama kin ji”. “Na gode Nurat”. Ta bi Nurat da kallo tana jin qaunarta a ranta. Halayyarta daban da na iyayenta, kamar yadda ta lura kowa na gidan bai damu da damuwar wani ba, sun dauki rayuwarsu tamkar na turawa, musamman Aazeen wadda duka dabi’unta irin na ubanta ne. Ita kam Hajiya Rahma babu wanda ya fahimci inda ta sa gaba, ba za a dai a kira ta mara kirki ba, kodayake ba lallai a fahimci wace ita ba, saboda ba ta cika shiga shirgin mutane ba, sabanin Nurat wadda ba ta wuce shekaru sha bakwai ba, yarinya mai mutumci da shiga rai, wadda ba ta xauki kanta da zafi ba, ba ta da wahalar sha’ani, kunyarta shi ke kara mata daraja a idanun jama’a, don hakan ya zame mata tamkar wani ado. Tazarar da ke tsakanin kicin da dakunan da ke gidan ya sanya babu wanda ya lura da kai-komonta. Wanke-wanke ta fara yi, ta ci uwar damara. Bayan ta gama ta shiga dogon tunanin abin da za ta dafa wanda ba zai ba ta wahala ba. taliya ta ayyana a ranta, amma ta ya ya za ta sarrafa kayan miya? Ita ba ta taba kwatanta shiga kicin don sarrafa wani girki ba. Komawa ta yi dakin Ladidi, don ta gaya mata yadda za ta yi. Bacci ta ke yi lakadan, har da su minshari. Murmushi ta yi ta koma ta shiga tunanin yadda za ta yi. Tunawa ta yi da tana da littafin girki, da sauri ta nufi ma’ajiyar littattafanta. KADARAR KITCHEN wanda Bilkisu Salisu Funtua ta rubuta ta nemi guri ta zauna, tare da dubo abin da ta ke son dafawa. Ta mayar da littafin ma’ajiyarsa, ta koma kicin ta debo kayan miya ta wanke, ta soma yanka albasa. Ji ta yi wuqa ta shige hannunta, ta kwalla kara tare da sakin wukar yadda ta ga jini na zuba ne ya sanya ta rudewa. A sukwane Zaruk ya dano kicin din ya kai hannu zai riko hannunta. Da sauri ta maida hannun baya cikin tsananin tsoro. “Ki bari in gani, ba ki ga jini ne ke zuba ba?” Ta yi saurin maida hawayen da ke qoqarin silalo mata. “Kada ka damu, kawai jinin ne, amma ai babu zafi”. “Oh God! Wai ke me ma ya kawo ki kicin? Wa ya aike ki?” Ta fara in’ina, ya daure fuska. “Na ce da ke waye ya aiko ki kicin?” Za ta yi magana ya mike a fusace zai fita. “Don Allah ka yi haquri, zan gaya maka. Ka dawo don Allah Yaya Zaruk”. Ya koma ya zauna cikin kafe ta da idanunshi. “Ke nake ji”. “Ladidi ba ta da lafiya shi ne nake taya ta”. Ya sake xaure fuska. “Ita din ce ta ce ki taya ta?” Cikin rawar murya, “A’a, to gaya min”. Dole ta zabi ta ba shi labarin yadda abin ya faru. Ya ja tsaki ya janyo mata kujera. “Maza zauna”. Ba ta da zabi dole ta bi umarninsa. Komawa ta yi ta zauna, nade hannun rigarsa ya yi ya shiga aiki tukuru. Ta dinga kunshe dariya a ciki, ga mamakinta Zaruk ya iya komi. Ya dube ta a sakarce, “Nurat, fito ki yi dariyarki a bayyane”. Ta dabarbarce, “Da gaske Yaya Zaruk ba dariya nake yi ba”. Jalof din taliya ya yi, sai plaintain da ya soya farfesun kifi. Ya diba a cokali ya mika mata. Ya yi mata alama da ta yi testing. Ta karba tana dandanawa. Ya kafe ta da ido. “Ya ki ka ji?” “Yaya Zaruk, ashe ka iya girki?” Ya harare ta, “je ki yi maza ki shirya dinning ko?” “An gama Yayana”. Da sauri ta yi abin da ya ce. Bayan ta gama shirya komai ya ce da ita, zai je ya siya ma Ladidi magani. Yana fita ta shiga wanka. Zaruk ta hango da Hajiya Rahma zaune suna cin abinci, ta sakar masa murmushi. Karasawa ta yi ta zauna. Ba a jima ba Alhaji Usman suka shigo da Aazeen rike da ledoji a hannu, su ma joining suka yi zaman cin abincin. “Yau Rangida babu korafi, da alama abincin ya yi dadi”. Nurat ta dubi Zaruk ya sakar mata murmushi. “No Dad, kawai dai ina jin yunwa ne”. “Da ma ai ke ba a taba iya miki”. Hajiya Rahma ta ce da ita. “Ladidi ta cancanci tukwici kenan?” In ji Zaruk yana kallon Nurat, ya faki idonsu a hankali ya dinga motsa baki yana nufin zai fada. Ta yi saurin kada kai tana rokonsa. Mikewa ya yi tsaye. “Ni zan wuce Ammi, a yi wa kuku godiya sosai”. Ya fada yana murmushi. ABUJA “Ummi ya kamata ki saba, na yi tafiya zuwa qasashen waje bila’adadin, na zaga duniya komai bai same ni ba, nan zuwa Kano tafiyar mintina ne, da zarar jirginmu ya sauka shi kenan an wuce gurin. Ko kina tsoro ne kada jirgi ya fado da dan lelenki?” Deedat ya fada yana kokarin tallafo kuncinta da hannayensa biyu. Ta sauke ajiyar zuciya cikin damu “Ba haka ba ne, kawai dai ina tsintar kaina cikin rudu duk lokacin da ka ambata cewar za ka Kano. Bana samun nutsuwa, ban san me ya sa haka ba”. Ya yi murmushi cikin kokarin kwarara mata gwiwa. “No, Ummina kada ki mance kirarina, in ka san ni ni ne, in ba ka sanni ba, ba ni ba ne. Ummina. Kowa ya san ba ni ba ne, kin ji sam ba ni ba ne babu wanda ya san ni, kuma ma ban da ke da abinki addu’arki fa na tare da ni, ba zan mutu *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 5 6* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *“N* o, Ummina kada ki mance kirarina, in ka san ni ni ne, in ba ka sanni ba, ba ni ba ne. Ba ni ba ne Ummina. Kowa ya san ba ni ba ne, kin ji sam ba ni ba ne babu wanda ya san ni, kuma ma ban da ke da abinki addu’arki fa na tare da ni, ba zan mutu ta hanyar da ki ke tunani ba, a kan gadonki zan mutu, a kan kafafunki, yanzu ki yi min addu’a zan tafi kwana bakwai kacal zan yi ai kamar yau ne ko Tawan?” Ta dinga murmushi a gefe daya kuma idanunta na fidda kwalla ta shafa sumarsa. “Ka kula da kanka yarona, Allah ya yi maka albarka”. Gaba daya suka dunguma har zuwa get inda ya shiga mota zuwa airport, ba ta bar get ba har sai da motar ta bace ma ganinta, ta juyo gida cike da kewarsa. Hango shi ta yi zaune ya dora kafa daya kan daya yana kada su. Gabanta ne ya yi wani irin bugawa, ta shiga maimaita innalillahi… Ya mike ya karaso gabanta yana tintsira dariya. “Ya yi babar mai kudi, babar Richman da kyau”. Ya sake tintsirewa da dariya. “Da alama kina cike da kewarsa, kina tsoron kada ya mutu ko? To ai da saura, domin har yanzu ba wanda ya san shi ne da zarar an fahimci waye shi ina tabbatar miki ko awa daya ba zai kara ba, ni ne kuma zan tona masa asiri, ni din nan ni ne ajalinsa. Yanzu ki shiga ki debo min rabona in tafi, na sani ke ma saboda wannan din ki ke nuna mishi cewar kin fi kowa kaunar…” Kyakkyawan marin da ta wanke shi da shi ne ya sanya shi kasa karasa maganarsa. daki ta shiga, sai ga ta da bandir din ‘yan dubu-dubu guda biyu. Cikin muryar kuka ta soma magana, “Bana son ka kara minti daya a gidan nan, ka bace min da gani”. Ya karbi kudin ya cilla su sama ya cafe, ya sumbaci kudin. “Kin fanshi kanki, sai gani na biyu”. Durkushewa ta yi ta dora kai a kujera, ta rushe da wani irin kuka. KANO Gida ne madaidaici ba za a kira shi na masu kudi ba, daga waje gidan bai wani hadu ba, a cikin gidan duniyar ta ke, don duk wani abin more rayuwa an tanade shi a ciki. Mutane biyu ne ke kula da gidan wadanda suke amintattunsa ne, su ne ke kula da komai na gidan. Tunda ya shigo Kano bai iso gidan ba sai da ya je ya gama duk wasu harkokinsa, sannan ya nufi gidan. A harabar gidan ya yi parking. Idris ya yi saurin karasowa ya bude masa murfin motar cikin yi mishi sannu da zuwa. “Ya na ganka kai daya Ina Adamu?” “Ya fita karba wa Madam take away”. “Madan? Wacce?” “Nabila”. “Nabila kuma, yaushe ta zo?” “Tun dazu”. Nan da nan yanayinshi ya sauya, bai sake bi ta kan Idris ba ya yi gaba. Ya yi arba da ita ta fito daga wanka daure da tawul. Ya yi saurin kawar da kai. Ya sake tamke fuska. “Ke ba kya jin kunyar abin da ki ke aikatawa ko?” Ta yi dariya, “Saboda na ganka in fita da gudu in dauko hijabi in yaba ko ya ya Deedat? To ma me zan boye maka? Ka yi min wanka, ka sanya min kaya, Yayana mijina. To me ya rage?” “Wannan abubuwan duk sun faru ne lokacin da kina karama, yanzu kin girma, ya kamata ki kiyaye”. Ya shige bed room. Ta yatsina fuska, “karamin abu kana son maida shi babba”. Yana zaune a kan gado da laptop a gabansa yana tura wa abokan kasuwancinsa sako ta mail dinsa. Ta shigo sanye da wasu fitinannun kaya, sai faman karairaya ta ke. Ta zauna a kusa da shi. “Na tsorata da rashin dawowarka, har na soma tunanin yadda zan iya kwana a gidan nan ni kadai”. Ya rufe laptop dinsa ya kallo ta. “Wannan ya zamo zuwanki na farko da na karshe a gidan nan, muddin ki ka kara tako kafarki gidan nan wallahi sai kin yi da na sanin zuwanki. Kuma yanzun nan ki shirya na kai ki gidan Salim, gobe ki wuce gida”. Kuka ta saka masa. “Yanzu saboda na zo ne duk ka ke gaya min ba dadi? Mene ne laifina? Sati na biyu ban sanya ka a idona ba, na dawo gida a do kance a ka ce ka taho, ba zan iya kwana guda ba tare da na ganka ba shi ya saka na biyo ka, kuma ai Mom ta san da zuwana, kowa ya san gurinka na taho”. “Okey su su Mom sun san gaskiya suka take? Ina ganin hakan bai dace ba”. “Ai su ma sun san abin da ya dace, amincewa da kai da suka yi ne ya sanya su barina na taho”. “Idan sun amince min ke kuma fa? Shin ba su san ke din fitinanniya ba ce?” “Yaya Deedat ka san abin da ka ke cewa kuwa?” Mikewa ya yi zai fita, ta yi saurin shan gabansa. “Ko ma me ce ce ni ai mijina na yi mawa, aure ne kawai ba a daura ba, akwai baikonka a kaina. A wata ruwayar ma tamkar ka aure ni ne…” “Shi ya sa ki ke ta bibiya ta? Ai don an yi baiko bai zamo lallai a ce ni ne mijinki ba”. “Hakan ba zai taba yiwuwa ba. Allah ma ba zai sa haka ba, na sani ina da rayuwa mai tsawo a gaba inda ba kai ne mijina ba, ba zan yi tsawon rai ba. Don kai Allah ya halicce ni, dole ne sai mun yi aure”. Ta kuma sanyaya murya. “Ka gaya min me ya sa ba ka damu da ni ba? duk lokacin da na yi maka maganar aure, sai ka nemi kashe min jiki. Zancenka kullum ba ya wuce aure nufin Allah ne, aure lokaci ne. ta bangaren iyaye ma cewa ka ke yi a kara maka lokaci, me ya sa ba ka jin tausayina? Me ye laifina? Ina son ka sani rayuwata ta ginu ne da soyayyarka, ban san me ake nufi da soyayya ba sai a dalilinka. Kai ne nutsuwa ta, idan ba ka son na ci gaba da bibiyarka ka amince a daura aure ko da ba a tare ba, zan iya jiranka zuwa duk lokacin da za ka gama shirinka”. “Dadina da ke ba kya rabo da shirme. Kin cika shirme. Ba ni da lokacin tsayawa jin wannan maganganun naki, ni ban san me ye so ba, bana son kuma na sanshi. Zan yi aure kawai don cika umarnin Allah da Manzonmu. Ke ma haka nake so ki saka a ranki, sai ki samu sassauci a ranki. Kada ki kara yi min wani zancen so, don ba burge ni za ki yi ba, maimakon haka ma sai matsala da za ki kara ma kanki”. kokarin barin gurin yake yi, da sauri ta riqe shi kamkam da qarfin da bai san tana da shi ba. “Nabila, me ki ke nufi da hakan?” Ya fada cikin kausasshiyar murya. “Yaya Deedat, ni mace ce mai tsananin bukata, na kai kololuwa. Idan ba ka bari an yi auren nan ba, zan iya aikata komai. Ka tausaya min don Allah”. Da karfi ya watsar da ita gefe ta zube a kan carpet, tana faman maida numfashi. “Yaya Deedat karya ka ke yi, burga ka ke yi. Na sani kai namiji ne mai girman kai, amma akwai mutanen da suka fi ka girman kai, sai dai ba su nunawa a irin wannan lokacin, ko shi sarki idan aka zo wannan gabar sauke rawaninsa yake yi. Da farko na san ba za ka ce ba ni da kyau ba, na san kuma ina da kirar da duk wani namiji zai so ya mallake ni. Zan fi yarda da cewar sona ne ba ka yi sam! Bana kuma burge ka, to ina son ka sani, idan ba ka bari an yi auren nan cikin wannan lokutan ba zan samu hanyar da zan sama wa kaina mafita, kuma dole ka aure ni, ni ajiyarka ce”. Ta mike a fusace ta fita. Ya koma ya zauna a kan gado, maganganunta ne suke dawo masa. “Ummina, ban yi ma Ummina adalci ba”. Da sauri ya mike, kokarin ficewa daga gidan ta ke. Da gudu ya cimmata ya damko hannunta ta shiga kiciniyar kwacewa. Tsawar da ya daka mata ne ya sa ta shiga taitayinta. Bai saki hannunta ba har sai da suka dangana ga falo. Ya zaunar da ita, ya kasa zama sai faman kai-komo yake, ya koma ya dire gwiwoyinsa a gabanta yana son rarrashinta. Tausayinta yake ji musamman yadda idanunta suka tattasa saboda tsabar kuka. Ta ya ma zai iya wanke mata zuciya. Ya lura Nabila babu abin da ta ke bukata irin tarayya da soyayya, ga shi bai iya ba, ya zai yi da ita? Ya dan cije lebe. “Oh God! Nabila bana son cutar da rayuwarki shi ya sa nake ta jan lokaci, ke mace ce wadda ba za ki iya rayuwa ba tare da mijinki na nuna miki soyayya ba, ni duk irin wannan abubuwan ban sansu ba. Ban taso a gaban iyayena na ga hakan ba, na taso cikin tsangwama da qyama, Ummina ba ta tare da Babana, ni ban iya ba ban san ya zan yi ba”. Duk sai ya dinga ba ta tausayi, kalaminsa sun taba mata zuciya, abin da ya tsana dai shi ta yi, ta dora hannunta a kan nashi. “Yaya Deedat na fahimce ka, ka daina tuno da abubuwan da suka wuce, ni zan iya zama da kai, zan koya maka yadda za ka kula da ni, zan rayu da kai a yadda ka ke. Kada ka damu ni ina sonka”. “No, Nabila kina buqatar miji jarumi wanda zai dinga kulawa da ke. Na ji mutane na cewa ci da sha ba shi kadai ake bukata cikin rayuwar aure ba. ana bukatar kulawa, kin ga ni kuma ban da isasshen lokaci, asalima ni ba mazauni ba ne yadda al’amuranki suka nuna kin fi son ko da yaushe kina tare da mijinki”. “Sai dai ko rayuwa da ni ne ba ka son yi, amma ni zan rayu da kai a hakan’. “No Nabila, akwai abin da ya rage da nake son gaya miki. Amma sai na komo gida, wannan shi ne zai zamo maganarmu ta karshe da ke, idan ki ka amince za a iya yin bikin a duk lokacin da ki ka shirya kin ji?” “Me ya sa ba za mu yi maganar yanzu ba?” “Dare ya riga ya yi, ina jin barci saboda gobe da wuri zan fita, ki bari kwana biyar kacal zan yi, ina komawa gida zan gaya miki”. Washegari da sassafe ya sallame ta bayan sun gama karin kumallo. ANNUR INTERNATIONAL SCHOOL makaranta ce wadda ke tashe, ta yi ma makarantu da yawa zarra, sam babu ragon Malamai, duk cikin malaman makarantar da yawancinsu a waje suka yi karatunsu, haka yawancin xaliban ciki Deedat na daukar nauyinsu su fita karatu waje, kudin makarantar bai cika tsada ba, sai dai duk da haka masu hannu da shuni suna barin tsadaddun makarantu su kawo su wannan, saboda karatun da ake yi a cikinta. Wannan makaranta sunanta ya kewaye gida da waje, ba wani ne mamallakin Annur International School ba face Ahmad Deedat. karfe bakwai da rabi Deedat ya isa makarantar kamar yadda Maigadi ya sani, shi din abokin principal ne, gurinsa yake zuwa don haka yana yin parking din Lipan maigadi ya karasa gare shi yana yi masa sannu da zuwa. “Ai kuwa Principal yanzun nan ya fita, sai dai na san ba nisa ya yi ba”. Maigadi ya fada. “Okey bari na jira shi”. “Ko a kawo maka abin zama?” “A’a kada ka damu”. Ya koma bakin aikinsa, shi kuma Deedat ya koma gindin wata bishiya ya tsaya yana kallon daliban da ke shigowa. Hankalinsa ya kai ga Nurat wadda ke ta faman sauri hade da waiwaye, abin da ya ja hankalinsa ke nan, ya san duban abin da ta ke waiwaye. Idanunsa suka kai ga wasu samari. Da alama ita suke bi. “Na gaya maka in dai Nurat ce kun yi kun gama ba ‘yar hannu ba ce. Ita muguwar bagidajiya ce, sam ba ta waye ba saboda gidadanci, ko ‘yar kwalliyar nan ba ta yi”. “Na ce ku sanya min ido duk gidadancinta sai na wayar da ita, zan ba ku mamaki, ni ne fa, kwana uku kawai za ku ba ni duk abin da ta ke takama da shi sai na sauke mata shi, na yi alkawari sai na sauya mata tunani”. Gaba daya suka sa shewa. Ya kasa gaskata abin da iska ya debo wa kunnuwansa. Ras! Ras!! Ya ji gabansa na bugawa, hankalinsa ya yi mugun tashi. Yana son gano yaran sai dai ya kasa tantance su. Tuni suka bace ma ganinsa, daga can nesa ya sake hangensu sun sha gabanta yana kallo ta ja da baya, ta kuma fada wani ajin, su kuma suka dauki wata hanyar. “Ta ya ya aka samu irin wadannan yaran a cikin makarantar nan? Wannan babban kuskure ne, ba za mu laminci haka ba, duk inda yaran nan suke dole ne a zakulo su, ba za su bata mana sunan makaranta ba. Ba zai yiwu ba, wannan ba abu ne wanda za a bari ya wuce ba”. Duk yadda suke da Principal, wato Zaid bai iya daga masa kafa ba. hankalin Zaid ya yi matukar tashi. “Dole ne za mu nemo su, za mu je ajin da yarinyar ta shiga, hakan zai taimaka mu gano su”. Karfe goma sha daya aka fito break, haka ne ya ba wa Deedat da Principal damar zaga ajujuwan don ganin abubuwan da suke buqatar gyara ko sakewa. A can aji Nurat na zaune tana nazarin littafinta na English, Faisal Nura da Abdul suka kutso kai cikin ajin. Ba ta yi aune ba ji ta yi kawai an wafce littafin, a tsorace ta dago kai lokacin da ta lura da su ne jikinta ya hau bari. “Ke ba ki ji ba, magana fa ake yi miki’. Tamkar ba da ita suke ba, hakan ne ya sa su gaba daya suka katange ta, babu ta inda za ta iya guduwa. Faisal ya sa hannu yana shafar kuncinta, kawai ta naxe hannayenta cikin hijabi ta kuma runtse ido, kwalla suka soma tsinkawa a idanunta. “Me ye a hannun naki da ki ke boyewa?” Abdul ya fada. “Ni kuma sai na sumbaci hannun”. In ji Faisal. “Don Allah ku yi hakuri”. Hakan bai sa sun fasa kudirinsu ba, Faisal ya kai hannu ya damko hannunta. Ta qwalla ihun kuka, daidai lokacin Principal da Deedat suka kunno kai. Da sauri ya saki hannun, gaba daya suka yi tsuru-tsuru. Wata uwar tsawa Principal ya daka musu, ta sake rushewa da kuka, Principal ya yi matukar tsorata a yadda ya ga kamannin Deedat sun sauya. “Ina iyakacin kokarina ban san ta ya ya ake samun irin haka ba. ban taba cin karo da wannan matsalar ba, dole ne ku cancanci hukunci mai tsauri. Sai kun gwammace ba ku taba yin makaranta ba”. Deedat hankalinsa na ga Nurat, tabbas ita ce yarinyar dazu, duk ya ji tausayinta. Principal ya kira Displine master a waya, ba a wuce minti biyu ba sai ga shi. Ya umarce shi da ya yi ofis da su ya yi musu horon da ba a taba yi wa wani dalibi ba. daga nan ya sanar da assambly din gaggawa. A nan ma a hukunta su, daga nan a kore su ga iyayensu, kora na har abada. su faisal sun cika samari amma hakan bai hana su kokawa ba, tare da ban haquri, musamman yadda suka rigaya suka san muguntar Displine master a lafiya ma yana mugunta ballantana wannan ganga-gangan laifin. Yau ne karo na farko da suka taba yin da na sani a irin kura-kuran da suke tafkawa, shi kam deedat duk hakan bai burge shi ba, ya fusata sosai, inda ya danganta laifin ga Principal. Fuu! Ya yi waje, da sauri ya rufa masa baya cike da zullumi. Can cikin ofis Deedat ya rikicewa Principal, ta inda yake tuhumarsa. Rantsuwa ya dinga yi yana yi masa magiya da ban hakuri, gaba daya ya gama jikewa sharkaf da gumi. “Dole ne ka zamo jajirtacce, na tsorata da al’amarin nan, idan ita yarinyar ta sanar wa da iyayenta da me za mu kare kanmu? Wannan sakacin zai iya janyowa a rufe makarantar baki daya, ka sani rufewar ba zai dame ni ba, kamar yadda talakawan da suke mora za su dame ni”. Cikin muryar lallashi Principal ke fadin, “Zan sanya idanu, hakan ba zai sake faruwa ba”. Malama Aisha ce ta turo kai, inda ya umarce ta da ta kira Nurat. Shi kam Deedat ya shiga kai-komo, al’amarin ya gigita shi. Shesshekar Nurat ya tabbatar masa da sun karaso. “Principal me ke faruwa da Nurat haka, na ga yarinyar ta shiga rudani da yawa”. Principal ya dubi Nurat. “Ko dai sun yi miki wani abin ne bayan abin da idanunmu suka gane mana?” Fir! Ta ki magana. “Ita ya kamata ta jata ta tambaye ta”. Deedat ya fada, kamar ya san halinta, Nurat akwai kunya. Principal ya dan ja ta gefe ya shaida mata abin da ya faru. Malama Aisha ta nufi ofis dinsu da ita, inda ta dinga tambayarta cikin dubara. Da kyar ta iya budar baki cikin shesshekar kuka. “Ammina ta ce duk lokacin da na bari namiji ya taba mini hannu, ciki zan samu, in…” Daidai lokacin Principal da Deedat suka kutso kai cikin ofis din nata. Deedat ya kasa jurewa shi ya sa ya azalzali da a biyo sahu. Ganinsu ya sa Nurat tsuke baki. “Ke nake saurare Nurat, ba komai ki yi magana kin ji”. Kawai Nurat ta yi kasa da kanta. *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 7* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *D* eedat ya kasa jurewa shi ya sa ya azalzali da a biyo sahu. Ganinsu ya sa Nurat tsuke baki. “Ke nake saurare Nurat, ba komai ki yi magana kin ji”. Kawai Nurat ta yi qasa da kanta. “Ummi ta ce, duk lokacin da na bari namiji ya tava min hannu zan samu ciki in haifi shege, idan na haifi shege mutuwa za ta yi, kuma su… su… sun tavan hannu…” Ta qarasa cikin saka gursheqen kuka. Deedat ya harba cikin tunani, gaba xaya jikinsa ya hau tsuma, wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa tare da wani irin abu wanda ya kasa tantance ko me ye. “Amma wannan zancen banza ne ta ya za a xora ki a kan wan…” Deedat ya yi saurin dakatar da Malama Aisha, “Haka ne, Ammi ta yi gaskiya, ai na ga hannunsu bai tava naki ba sosai, yanzu za mu je asibiti in har da cikin za su gaya mana. Ki daina kuka kin ji ko”. “Ina jin tsoro, za ta gane hakan ta faru, bana son na samu shege kowa zai tsane ni, bana son samun xan da ba shi da tsarki”. Ba ya son jin kalamanta, da sauri ya yi waje, idanuwa sun sake rinewa, “Za mu je asibiti”. Ya faxa lokacin da ya bar ofis xin. A can harabar makarantar Doctor Salim amininsa ya kira inda a taqaice ya ba shi labarin abin da ke faruwa, tare da sanar da shi ga shi nan tafe, yana kuma son a yi mata duk abin da zai sa ta samu nutsuwa. Ya yi saurin katse wayar daidai lokacin da Principal ya yi parking xin mota a gabanshi. A can baya ya hangi Nurat gidan gaba ya shiga, yana gano yadda hawaye suke faman tsinkowa daga idanun Nurat. Ya yi saurin kawar da ido, yayin da gabansa ya dinga dukan uku-uku, yarinya ce qarama, sai dai akwai ta da kwarjini. Lokaci-lokaci ya dinga satar kallonta har suka isa asibitin. Abin da ya bai wa Nurat mamaki, yadda sunan makarantar da na asibitin suka zamo xaya. Dr. Samir sun tsara komai da Nurse kafin su qaraso, sirinji ya xauka ya yi umarnin da ta miqo hannunta zai xauki jini domin gwaji. Nan fa idanunta suka yo waje, ji ta ke kamar ta sa gudu, sai ga wasu sababbin hawayen. Dr. Samir babu wani abin da za a yi, maimakon xaukar jinin?” Deedat ya faxa. “Dole dai sai dai jinin”. Babu yadda ta iya haka ta runtse ido, ya shiga shirin zuqo jinin, inda Deedat ya xauko wayarsa a fakaice ya shiga xaukarta ta yadda babu mai lura da abin da yake yi. Bayan an gama Nurse ta yi wani xaki da jinin, sun zauna sai ga sakamako ta shigo da shi. Ta miqa wa Dr. Salim, ya duba cikin gintse dariya a ciki, saboda yadda ya ga alamun tsoro qarara a idanun Nurat, sai da ya xan yi ‘yan rubuce-rubuce sannan ya sake xago kai cikin dubanta. Idanun nan sun yi luhu-luhu saboda kuka, tana jin kamar ta matsi bakinsa ya yi magana, Deedat kam yana iya jin bugun zuciyarta na tsananta, da yake shi ne a kusa da ita. “Ina taya ki murna xalibar kirki, ba ki da matsala”. Cike da farin ciki ta sake wani irin murmushi, dukan kumatunta suka lotsa. Wani irin wushirya mai xaukar hankali suka bayyana. Da sauri Deedat ya shiga xaukarta. “Doctor na gode”. Ta ce. Ya miqa mata ambulan, “Doctor na bar maka”. Ya yi murmushi. “Ki dai tafi da shi”. Ta karva. “Abu na gaba ina son kada wannan maganar ta fita ko a gida kada ki faxa kin ji ko?” “Insha Allahu babu wanda zai ji”. Cikin farin xiki ta ke magana. Deedat ya shiga duniyar tunani, yana tunanin a inda ya san wannan muryar, sai dai duk iya yinsa haka ya haqura. Sai da Principal ya sanya ta a mota aka maida ita makaranta, sannan ya dawo ofis xin Dr. Samir inda kowa ke faxin albarkacin bakinsa a kan al’amarin Nurat. “Hakan na da kyau, ban yi tunanin akwai irin waxannan iyaye ba. babu wadda ta burge ni sai mahaifiyarta wacce ta xora ta a wannan turba”. In ji Salim. Principal ya karve zancen, “Cikin class mate xinta ita ce mafi qanqantar shekaru, ga su nan ganxama-ganxama amma babu wadda ta kai ta qoqari. Qwaqwalwarta tamkar computer, irinsu ake ma laqabi da gifted. Na daxe ban ga yarinya kamarta ba, yadda xalibai da malamai ke qaunarta bai sa ta giggiwa ba, gaba xayanta ma tsoro ne da ita, ba ta shiga cikin mutane sosai. Ba qaramin abu ne zai sa ka ji bakinta a class ba, kullum ka ganta wala’Allah a makaranta ko a gida cikin hijabinta zumbulele kamar mai shirin tafiya masallaci. Su kansu malamai mata in sun zauna hirarta suke babu wanda ya tava kawo qararta’. Haka ya yi ta bada labarinta, har sai da Deedat ya ji a cikin zuciyarsa babu masaqar tsinke, bai tava jin yadda yake ji game da ita ba a kan wata mace ba, shin me hakan ke nufi? Me ke shirin faruwa da shi? “Ammi ta ce duk lokacin da na bari namiji ya tava min hannu zan samu cikin shege, idan na samu cikin shege mutuwa za ta yi”. Sautin muryarta ya dinga yi masa kuwwa a kunne, ya shiga kai-komo, gaba xaya ya kasa samun nutsuwa. Bathroom ya shiga, gaba xayansa ya shige cikin shaya yana jin ko hakan zai saukar masa da nutsuwa. Babu abin da ya ragu, sai ma rikicewa da ya qara yi. Doguwar riga ya saka jallabiya mai yankakken hannu, ya yi zaman dirshan a kan carpet, kuka yake yi kamar qaramin yaro. Ya riqe kai yana juyawa cikin tafin hannunsa. “Sun cutar da ni, sun cuce ni”. Wani irin zazzavi mai zafi ya rufe shi har haqoransa na gwaruwa, barci ya sace shi. A can cikin baccin nasa babu abin da yake gani sai fuskar Nurat. Tana zaune a farfajiyar gidan riqe da littafi a hannu tana karatu. Harxe hannu a qirji yana kallonta yana murmushi, bai qi ya tabbata a haka cikin kallon kyakkyawar fuskarta ba. Jikinta ne ya ba ta akwai mutum tsaye a kanta, ta xan xago kai suka yi ido biyu. Ta yi saurin kawar da kai tare da faxin, “Zauna mana”. Ta nuna masa kujera. “Ban ji shigowarka ba”. Yana murmushi, “kina zaune har na zo na shige na yi ciki, kin ga ke kam idan kina karatu ba kya ji ba kya gani”. “Yaya Zaruk mun fa kusa fara jarabawa, ina son in karvi kyaututtuka a gurin Dad da Ammi, har ma da Yayata’. Ya tafa hannu, “Da kyau yarinya mai wayo. To ki qara da tawa, zan yi miki kyautar da babu wanda zai yi miki irinta”. Ta yi murmushi, cikin satar kallonsa. “To, yanzu xan gaya mini kalar kyautar”. “No, ki dai bari zan ba ki mamaki”. “Allah ya nuna mana lokacin”. Ta xan yi shiru tana tunanin wani abu. “Wannan yarinya akwai magana a bakinki”. “Yaya Zaruk inda a ce kowa zai riqe kyautarsa a yi mini alqawarin auren Yaya Aazeen, zan fi jin daxin haka fiye da komai”. “Har yanzu ba ki bar wannan zancen ba? na ce da ke shi aure lokaci ne da zarar lokacin ya zo komai zai zamo labari”. “Amma Yaya Zaruk Yayata ba ta rasa masoya ba, girman kanta ne ya rasa masoyan nata su tarke ta. Ka sani kuma ba ta da kirki kamar ba ‘yar gidan nan ba”. “Ki bar ni da ita, ni ne nan zan yi mata miji, kuma ko ba ta so zan sa ta aure…” Zumbur! Kamar wadda aka tsikara, “Yayana!” “Na’am, qanwas?” Ta gyara zama cikin muryar raxa, “Ashe kenan za ka iya taimaka mini na yi wa Yaya Aazeen miji?” “Kina nufin ke za ki samo mata wanda za ta aura? To ta ya ya?” “Mun haxu da shi ne ta sanadiyyar sava lamba, sau tari ina karvar wayar Yaya Aazeen na yi game ko na kira qawayena. Rannan na karvi wayar na sanya lambar qawata Hasina, ina kira aka xauki wayar, maimakon in ji muryarta sai na ji muryar namiji. Da farko na zaci yayanta ne, na ce da shi ina neman Hasina, sai ya ce ba ta nan. Hasina qawata ce sosai, sun tashi sun koma Lagos, na daxe ina neman layinta tun daga ranar na dinga bibiyar layin mutumin, ya iya magana, ba shi da wulaqanci, yana da tsananin haquri”. Kawai Zaruk ya dinga binta da kallo. “Mutumin da ba ki sani ba, ta ya ya ki ka iya xorar da halayyarsa?” “Saboda a lokacin da na fahimci raina min hankali yake yi raina ya vaci, na kasa tanqwara zuciyata, na yi ta jifarsa da magana”. Zaruk ya watsa mata harara. “Ke xin har wani iya magana ki ka yi? Yaushe ne ma ki ka koyi magana?” “Allah da gaske nake yi, ita magana zuwa ta ke yi. Ya ci gaba da haxiye duk wasu kalamaina, sannu a hankali muka fara sabawa da shi, idan ban kira shi ba na kan dinga jin kamar na rasa wani abu muhimmi. Bana son a ce zumuncinmu ya sha ruwa, ina ji a jikina yayata za ta so shi da zarar sun haxu sai dai idan na tuna ba shi ne irin mijin da ta ke mafarkin samu ba, ina jin tsoro, domin na fahimci shi xin ba wani mai qarfi ba ne”. *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 8* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *G* aba xaya ta dage sai zuba ta ke yi, tunda suke da ita bai tava sanin tana da magana haka ba, maganganunta yana jin zubarsu tamkar yayyafin wuta. Kullum idan ya yi magana sai a ce masa nawa ta ke? Ga shi ya yi sake har son wani ya shige ta. Ya sauke ajiyar zuciya. “To ta ya ya za ki haxa wannan soyayyar?” “Ina son tafiyata da shi ta sauya salo”. “Ban fahimta ba”. “Na ce da shi sunana Aazeen, ina amfani da komai na Yayata a zuwan ni xin Aazeen ce, hakan ya yi?” Kawai jinjina mata kai yake yi. “Amma ya ya Zaruk ka san me? Ya qi cewa yana sona, ina son in tursasa masa furta hakan”. “To idan ya qi fa?” “Yanzu Yaya Zaruk koya min za ka yi”. Ji ya yi kamar ya tsinka mata mari, dole ya danne zuciyarsa, murya sama-sama, ‘Ke xin fa mace ce”. Da sauri ta katse shi, “No, cewa za ka yi ita xin fa mace ce”. Tilas ya bi yadda ta ke so. “Ok, na ji ita xin fa mace ce, duk inda mace ta ke ana son ta darajja kanta, ki ci gaba da bi da shi a hankali, zai yi yadda ki ke so xin. Amma ya kamata ki ba ni lambarsa…” Da sauri ta katse shi, “No, ba yanzu ba, idan komai ya yi daidai kai kanka sai ka fi samun qwarin gwiwar kiransa”. Miqewa ya yi, “Ok, ba matsala”. Ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, wannan yanayi da ya shiga ya kamata ta iya fahimta, sai dai ko kaxan ba ta kawo komai ba, asalima daxi ta ke ji tana ganin kamar ya ba ta qwarin gwiwa ne. A wannan dare Zaruk ya kasa bacci, yana ta juye-juye a gado, son Nurat kullum qaruwa yake yi a ransa, musamman yanzu da komai nata ya bayyana. Nurat yarinya ce mai sanyin hali da son mutane, tana da shiga rai, tana da surutu amma ga waxanda ta saba da su, domin sam ba ta da saurin sabo, idan ta ga dama sai ka rantse ba ta magana saboda yanayinta mai sanyi ne. Akwai ta da tsoro, xaya daga cikin abin da ta tsana shi ne mu’amala da maza, duk yadda suke da namiji ta kan yi xari-xari da shi. Nurat mai kyau ce, sai dai ba kowa ke gane hakan ba, dalilin kwalliya ba ta dame ta ba, ba ta saka xamammun kaya kullum cikin hijabi, ko da a gida ne in ta yi wanka ko hoda ba ta damu da ta saka ba, ballantana kwalli. Ba za a kira ta da baqa ba, ba kuma za a ce da ita fara tas ba, idan ta tsaya a kusa da baqin mutum lokaci xaya za ka iya ce mata fara, sai dai idan ta tsaya a kusa da fari. Kalarta na xaukar hankali, ita ba golden ba, ita ba choculate ba, abin da ya fi komai xaukar hankali a tare da ita shi ne diri, duk yadda ake son mace ta kai, tana da wushirya, muryarta a xan xashe ta ke, damvareren baqin da ke kwance a goshinta, wanda ake wa laqabi da tabon sallah ya yi matuqar qara mata kwarjini da kyau. Idanunta manya farare qwal, gashin girarta a haxe da xan uwansa. Abin da Nurat ta fi so a rayuwarta shi ne, Aazeen, tana matuqar qaunar ‘yar uwar tata. Ya miqe zaune, “Kina qaunar Yayarki, da ita za mu yaqe ki. Aazeen tawa ce, sai yadda na tsara mata”. *** *** *** “Yaya Aazeen ana kiranki a waya fa”. Sai da ta maimaita faxa kusan sau uku, sannan Aazeen ta yi firgigt. “Mtsew! Qyale su”. “Yaya Aazeen ba ki da lafiya ne?” “Ina cikin damuwa ne kawai Nurat, tunanina da hankali gaba xaya sun koma ga mutumin nan, ina ji a jikina tamkar zai kusanto ni. Ina ji tamkar shi ne mijina, ban san shi ba amma kullum sai ya zo min cikin mafarkina. Wannan karon ne kaxai wani abun ke neman fin qarfina, amma ban tava neman abu na rasa ba, sai ya zamo mallakina ko da hakan zai zamo sanadiyyar rasa komai nawa”. “Yaya Aazeen komai naki fa ki ka ce?” “Eh mana, ban da abinki idan na rasa komai shi ne zai dawo min da ninkinsa. Ba ki san matsayinsa ba ne, har ma fa ya fi shugaban qasa kuxi”. “To idan bai zama yadda ki ke so ba fa?” “Kin ga Nurat, muddin yana da kuxi ko ya dai yake zan yi maleji, ai ba xaure shi zan yi a qafa ina yawo da shi ba”. “To idan ki ka samu wanda ki ke so ba”. Ta kai mata dukan wasa, “Allah ba zai sa in kamu da soyayyar wani ba, wannan zuciyar ba ta san so ba sai jin daxi da holewa, gwara ma idan na samu mai kyau na dinga kare yawa in mayar da shi fulawa kawai”. “Yayata kina son mai kyau’. “Eh mana, shi ya sa nake matuqar sonki”. Nurat ta yi dariya. “Yanzu idan ki ka haxu da mai kyau za ki so shi?” “Mai zai hana?” Wani daxi ya kama Nurat, tabbas haqanta zai cimma ruwa, ta fara samun yadda za ta villowa lamarin, ba za ta bari shaquwa da Adamu ya tashi a banza ba, sai sun zamo xaya. Ji ta yi an zunguro ta. Ido biyu ta yi da Aazeen, Aazeen ta kanne mata ido xaya. “Tunanin me ki ke yi? Gaya min, ko kin kamu ne?” Ta yi murmushi, “Haba ‘yar maniniyata, kawai kina maganar maikyau na tuna da wani, ni ban ma tava ganin mai kyawunsa ba, za ku dace da shi”. Tsaki Aazeen ta ja daidai lokacin wayarta ta sake xaukar ruri, ta miqe tana faxin, “Ke kin cika shirme’. Xaki ta shige. Zuciyarsa tamkar ta faso qirji, son Nurat na neman halaka shi ta ina zai fara? Ya zai yi? Da sauri ya fito a xakinsa. Zainab matar yayansa na zaune a babban sitroom riqe da waya a hannu tana game. Kawai ya zube a kujera, ta xan dube shi, yadda yake ta faman huci. “Man, waye ya tava mana kai?” Kansa a qasa bai ce da ita komai ba, za ta sake yin magana ya yi saurin katse ta. “Ban san haka nake sonta ba, ta yi tasiri a zuciyata, ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba. lokaci ya yi da zan tinkari su Papa da maganar kada na mutu”. ‘Duk ita kaxai? Wace wannan haka?” Ya furzar da huci. “Nurat! Ina sonta, ina matuqar sonta. Ina jinta tamkar numfashina, ina jinta a can qarqashin zuciyata’. Ta yi murmushi cikin sigar wasa ta dungure mishi kai. “Da Allah can, sunan wacce ka ke ihun ita ce ruhinka ka mance Aazeen za ka ce”. “Oh God! Kina tunanin mantuwa na yi? Nurat wadda na xebi shekaru ina dakon sonta, Nurat ita xin dai nake nufi”. Ido buxe ta ke dubansa. “Allah ba zai yi ma Nurat haka ba”. A zahiri ta yi murmushi, “Haba dai, me za ka yi da wannan ‘yar mutsilar yarinyar da ba ta gama sanin ciwon kanta ba? Aazeen xin dai. Aazeen ita ce wadda za ku yi matching, gogaggiya kamar kai. Amma Nurat is too younger…” “Stop Aunt! Kawai ki fito ki ce ni xin ban cancanci zama mijinta ba, saboda ni ban da kirki, ni ba na qwarai ba ne. To ina son ki sani zan sauya, zan iya yin komai a kan in mallake ta”. Ta karyar da murya, “No, ba fa nufina kenan ba. Wai ni ina son in ce qarama ce ita”. Tsaki ya ja ya miqe yana jin iya ci gaba da tsayuwa a gurinta zai iya marinta. Juyowa ya yi ya dube ta da idanun nan jajir, haka ne ya sa ta shiga hankalinta. Ya tarar wayarsa na faman ruri, lambar Aazeen ya gani, da sauri ya xauka. Muryar Nurat xin ce ta ratsa kunnuwansa, wata irin ajiyar zuciya ya sauke. “Yaya Zaruk”. Ta kira sunansa a can vangarenta, ta kuma rasa da me za ta fara, don haka ta yi shiru. Ya katse shirun da faxin, “Gaya min, kina son ganina ne?” Ya faxa yana mai roqon Allah ya sanya ita ma ta jarabtu da sonsa. “Nurat, gaya mini kada ki damu, kin ji?” “Um-um… da man ce maka zan yi ina son kiran Adamu jiya mun fara hira da Yaya Aazeen, sai nake jin kamar zan dace, za ta iya amincewa”. Ya cije leve, ji ya yi kamar wani tsini ya soke shi. Da qyar ya danne zuciyarsa. “Ya kamata ki fara shawo kanta kafin ki jajibo shi”. “Ai na ce da kai ta fara amincewa”. “To shi kenan, ki bari gobe in na zo sai mu ga ya za mu yi”. Ta yi murmushi mai sauti. Ba ta sake jiran me zai ce ba ta yi saurin katse wayar. Ciki ya yi da wayar ya riqe kai yana faman huci. “Zan nemo shi, ba zan amince ba. zan yi wani abu a kai, bana tsoron duk abin da zai faru. I don’t care, zan gaya ma Papana dole ne in tabbatar da za ki zamo tawa, kina wasa da rayuwa ta, ba zan tava amincewa da wannan ba, kullum ana raina min hankali da faxin ke xin qarama ce, da zarar na taso sai a danqwafe ni, an bar zuciyata da masifa, shekara da shekaru ina azabtuwa. Wallahi na yi alqawari ko kallonki wani ya yi da zummar so sai na vatar da shi, bana tsoro, ba zan xaga qafa ba, dole ne ki zamo tawa. Ni ne kaxai na san muhimmancinki ba zan yarda ba, ina! Haka ba za ta tava yiwuwa ba, kai xin ma sai na gano ko kai waye na sani duk da ba ka santa ba da zarar ka xora ido a kanta ba za ka barta ba”. Ya ci gaba da sambatunsa kamar wani tavavve ko qaramin yaro. Idan ta tuno hirarsu da Aazeen duk sai daxi ya kamata, yanzu ta ina za ta fara? Ta yi shiru cikin tunani. Ta yi murmushi, me ya sa ta damu da yawa? Me ya sa zuciyarta ta nace da son haxa dangantaka da Adamu? Ta gyara zamanta, “Qila shi ne sanadin gyaruwarta, sai kun haxu zai gane wace ke na sani, ba zai guje ki ba a lokacin da ya san halayyarki, don haka nake son in kama zuciyarsa da zummar ke ce, kuma ai ni ma mace ce, zan iya har ma sai na jira Yaya Zaruk ya koyar da ni, mutumin da yake ta faman ja min rai? Zan ba shi mamaki, sai dai kawai ya ji ana yi”. Ta miqe tsaye ta shiga zaryar yadda za a yi ta sato wayar Aazeen. Da sauri ta yi sitroom inda ta riski Aazeen zaune sanye da wasu maqalallun kaya, ta xora qafa xaya kan xaya cikin duba novel book. “Yayata, ko za ki ba ni wayarki zan kira Aisha?” Ba ta yi magana ba, kawai ta yi mata nuni da wayar. Da sauri ta xauka ta koma xaki. Sai da ta kulle ta murxa key ta koma ta zauna a kan gado. “Ke ce kuwa?” “Mai ka gani?” “Ba ki saba kira a irin wannan lokacin ba shi ya sa nake jin kamar ba ke ba ce”. “Ni kaina ban san lokacin da na kira ba, kawai ina wasa da wayar na ga kawai hannuna ya kai ga lambarka’. “Amma kuma kin tava ce min ba ki yi saving ba…” “Uhum”. Kawai ta yi. “Lallai na qara matsayi, na ji daxin haka qanwata”. “Ai da ma kana da matsayi”. “Ok, yanzu ba ni labari”. Ta xan yi jim kamar ba ta kan wayar. *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 9* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *L* abari sai dai kai, ni da kullum ke kulle a cikin gida… amma dai yanzu gaya min yaushe zan ganka?” Ya yi ajiyar zuciya, “Saura qiris na zo, to amma idan na zo gurin wa zan ce na zo in na tura kiranki, ke kuma wa za ki ce ya zo?” Ta yi shiru. “Sai ki ce abokinki ne?” “Kai ai namiji ne, ba zai yiwu ba’. “Ok, to za ki ce saurayinki ne ya zo?” Nan ma ba ta iya magana ba. qoqarin share caftar ya yi, ta yi saurin dawo da zancen. “Da gaske ni xin budurwarka ce, kana sona kenan?” Ya yi murmushi yana jin daxin yadda yake zolayarta. “Ina sonki mana”. Da sauri ta katse wayar ta yi ciki da shi. Ta yi rigingine a gado haxi da runtse ido kawai, kunyar kanta ta ke ji. Ji ta ke yi kamar ta aikata babban zunubi, amma a can qarqashin zuciyarta wani irin nishaxi ta ke ji, ko me hakan ke nufi? *** *** *** “Ji yadda duk ki ka tada hankali kamar wadda ki ka aiki jaririya, wai ke ba kya ganin yadda hadari ya haxo, ga gari ya yi baqiqirin? Ni ba abin da ke tayar min da hankali irin iskar da ke tasowa, kin san Nurat da tsoro, na sani duk inda ta ke tana cikin ruxu. Na kira Hajiya Fati ta ce tun xazu ta fita a gidan, sai yanzu nake jin haushin rashin waya a hannunta, da sai mu kira ta”. Shewa Aazeen ta yi ta qaraso gaban Amminta tare da rungumo ta ta vaya. “Dube ki don Allah, inda a ce ni ce da yanzu kina nan hankalinki a kwance, da yanzu ma kina bacci, amma dai ki kwantar da hankalinki ‘yarki na da wayo, za ta dawo lafiya kin ji Amminmu, kuma na yi miki alqawari da kaina zan siya mata waya”. Daga can vangaren Nurat hankalinta ya yi qololuwar tashi, musamman yadda ta ji ana ta tsawa gaba xaya a qanqame ta ke tafiya, cikin sharar qwalla duk motar da ta tsayar kko kallonta ba su yi. Tasowar iska ya tsananta sanadiyyar haka aka xauke wuta, gari ya soma duhu, jama’a sai gudu ake. Cikin lokaci qanqani ruwan sama mai qarfi ya sauko haxi da walqiya. A hankali yake tafiya saboda kada ya haifarwa kansa matsala, lokaci xaya ya dallaro fitila ya yi arba da fuskar Nurat. Dam! Ya ji gabansa ya buga, sauran qiris ya saki sitiyari. Ya sake rage gudu, ya san rasa mota ta yi a daidai gabanta ya yi parking, bai fito ba bai kuma kashe motar ba, tunaninsa za ta doso shi don neman taimako, maimakon haka gani ya yi tana neman kwasa da gudu, haka ne ya sa ya tada motar. Gabanta ya sha ya sake tsayawa, ta yi saurin kauce wa motar. Bai sake mamaki ba in ya yi la’akari a abin da ya faru a makaranta, dole ya yanke shawarar yi mata magana. Kashe motar ya yi ya fito cikin sauri ya qarasa ya sha gabanta. Ta tsaya qyam kanta a qasa, jikinta na rawa. “Ki shigo mota in kai ki”. Ta yi saurin kaxa kai cikin tunanin inda ta san wannan muryar. A hankali ta xago kaiza ta saci kallonsa, aka yi sa;a gari ya haska da walqiya idanunsu suka gauraya da juna. Gaba xaya Deedat ya kixime wani irin bugawa gabansa ke yi, shin wace irin yarinya ce wannan wadda yake jin abin da bai tava ji ga wata mace ba a yayin da ya xora ido a kanta, ko da kuwa a hoto ne tana yi masa kwarjini, ji yake yi ma kamar yana tsoronta, ita ma xin ta gane shi. Abokin Principal xin sune sai dai haka ba zai sa ta shiga motarsa ba, ko da hakan na nufin za ta kwana tana tafe a qasa ne. Ya sanyaya murya, “Ke fa xalibar abokina ce, na san kin gane ni, ba zan cutar da ke ba”. “Ka yi haquri na gode”. Yadda ya lura da ita ya sani ba za ta tava shiga ba, ga dare na daxa yi, ya xan kausasa murya wai ko da za ta ji tsoro. ‘Ki shiga na ce!” Ta raunana murya kamar za ta rushe da kuka. “Allah ba zan shiga ba”. Takaici ya sanya ya shige motar, ya murxa key, amman ya kasa tafiya. Wayarsa ya xauko ya shiga kiran xaya daga cikin masu adaidaita sahunsa tare da yi masa kwatancen inda ta ke. Bai bar gurin ba, har sai da ya tabbatar an xauke ta tukunna ya samu nutsuwa. *** *** *** “Ammi ga ‘yar mitsilanki nan ta dawo ba a cinye ta ba”. “Za ki ci gidanku, ce miki na yi ba za ta dawo ba?” Aazeen tana dariya, “Kin ga wannan Umman taki gaba xaya ta sukurkurce kamar ce mata aka yi an sace ki”. “Ai ko ba don wani abokin Principal ya yi gadina ba da yanzu na sume a gurin, don ba kowa a gurin, ya yi ta nacin in shiga motar ya kawo ni, na qi shiga, har sai da na samu adaidaita”. “Kin yi daidai”. “Ammi, haka ne daidai? Inda ba ta samu abin hawa ba fa?” “Na ma san Allah ba zai sa hakan ta faru ba”. Yana gaisawa da Hajiya Rahma idanunsa na yawo, yana tsammanin ganin Nurat. Ya numfasa, “Ba kowa a gidan ne sai ke kaxai?” “Mutuniyarka na xaki bacci ta ke yi, ba ta da lafiya, ita kuma Aazeen na shashenta”. Ya miqe, “Bari in je mu gaisa”. “To”. Ta ce da shi. Ta miqe a doguwar kujera tana jin kixa. Ta faxaxa fara’arta, “Yanzu nake shirin kiranka”. “Kirana? Kina da magana kenan?” Ta kaxa kai, ‘Kawai kewarka na ke yi”. “Sai ga ni na zo ba, amma ni ma tawa ce ta kawo ni’. Ta miqe zaune cingam ta xauka a kan table ta vare tare da cillawa a baki, ta tauna, ta yi qwai haxe da yin qas-qas ta koma ta tattara hankalinta kanshi. “Ina sauraronka”. Ya zauna kusa da ita, ya marairace kamar mai shirin yin kuka. “Na kasa jurewa, ba zan iya ba”. Ta bi shi da kallo, ‘Wai me ke faruwa?” “Ina son Nurat, lokaci ya yi da zan furta mata. Rashin furtawa a wanan lokaci zai iya haifar da komai”. Tuntsirewa ta yi da dariya, har da qyaqyatawa. Ya qulu sosai, miqewa ya yi zai fita, ta sha gabansa ta kama hannunsa ta zaunar da shi. “Afuwan, mu yi magana, amma ranka ya daxe ka rasa wadda za ka zava ta zame maka mata sai qwaila, kuma ma wacce ba ta waye ba? kuma wai har ma ka dubi idanuna ka ce kana son qanwata? To wai ma gaya min da me na rage ka?” Ya watsa mata harara, “Ok, haka ki ke son na yi ta zama babu aure ko?” “Why not, yanzun da me na rage ka ko kana son ka ce ni xin na gundire ka?” “Kin ga Rangida wannan daban ne, kin san kamalar mutum shi ne aure ko?” “Na ji wannan, amma me ya sa ba za ka samu gogaggiya irinka ba? Ka san Nurat qarama ce ba za ka samu yadda ka ke so daga gare ta ba”. “Kin ga Rangida kada ki ce kishi ki ke da ita?” Ta ja wani dogon tsaki. “Matar arziqi ma ban yi kishi da su ba sai wannan? Kawai dai ina tsoron alaqarka da ita kada ka laluve mini ita’. “Kin ga ki ajiye zancen wasa ju tausaya mini ki gaya min ya zan yi, ta ina zan fara?” Ta lakuce masa hanci, “Dube shi don Allah ko kunyata ba ya ji. Ka ga shawarata ka bi a hankali, muddin ka kuskura gurin furta mata kalmar so, kai da ita, kun soma wasan vuya kenan in ma ba ka yi sa’a ba kun qulla gaba kenan don haka ka bi a sannu cikin dabara za ka fahimtar da ita a aikace”. Ya miqe ya shiga zarya. “Nurat, ban ga damar canza ta ba ne yarinyar bagidajiya ce amma ka ban lokaci, da sannu zan fahimtar da ita abin da duniya take ci….” “Ban amince ba”. Ya yi saurin katse ta cikin gigita, “Ni rayuwarta ta yi min a haka nake son rayuwa da ita”. Ya koma ya zauna cike da tsananin tsoro “Come down, abokina, kana tsoro ko, amman ba ka tabbatar ita din matarka ba ce ballantana ka…” Turo qofar da a ka yi ne ya katse daga maganar da take son yi, sanye ta ke da zumbulelen hijab, Aazeen ta saci kallon Zaruk cikin muryar raxa. “Haka xin yayi maka ko?” Ya xan lumshe ido ya buxe alamar hakan ya yi masa. “Yaya Zaruk sannu da zuwa”. “Yauwa qanwa ta gwara da Allah ya kawo ki, daman ya dame ni da surutu”. Shigar jikinta ya sanya Nurat jin kunyar Zaruk, three quater a jikinta na wando, sai riga plat, kan nan ya sha attach, ta lura da yadda Zaruk ke faman satar kallonta. Yana ji tamkar ya bi ta. “Ya Zaruk me ya sa ba ka yi mata faxa na ga kamar tana jin maganarka”. Ya maida kallonsa gare ta, “A kan me fa? “A kan me? Ba ka ganin yadda ta ari al’adar da ta sava wa addininmu na islama?” “Kada ki damu da hakan, ra’ayinta ne haka, wataran za ta daina da zarar ta shiga daga ciki shi kenan komai zai sauya, kamar ba a yi ba, kin ji?” A hankali ta rausayar da kai. “Haka ne Yaya Zaruk, Allah ya nuna mana lokacin”. Wani mayen kallo ya dinga bin ta da shi har sai da ta tsargu. Ya yi murmushi, “Ba kya son kallo da yawa ko? Ki yi haquri qanwata, kina da kyau da yawa. Ban gajiya da kallonki, da ma a ce mu dauwama a haka”. Ta xan murmusa, “Yaya Zaruk ka iya zolaya”. Ya sake riqe hava cikin kallonta. “Murmushi na yi miki kyau, ina ma kada ki daina?” “Yau ka zo ne musamman don ka tsokane ni ko? Ka san wani abu?” Haka kawai ya ji zuciyarsa ta buga. “Sai kin faxa”. “Ammina tana son Yayata ta yi aure, na ga kai ma ka faxa idan ta yi aure za ta daina duk waxannan abubuwan shi ya sa nake ta neman taimakonka”. “Shi ya sa na ce ki ba ni lambar mutumin nan”. Ya katse ta da faxin haja. “Na san yadda zan bi in daidaita komai”. “Ba ka sani ba, komai ya daidaita har na zurmo shi da bakinsa ya furta cewar yana sona”. Lokaci xaya ya firgice duk walwalar fuskarsa ta dusashe, cikin shaqaqqiyar murya ya soma magana, “Kina son ki ce kin zubar da qimarki gurin roqonshi ya so ki ko? Nurat kin hauka ce? Me ya sa ki ka fitini kanki da yawa a kan wannan? Ki gaya min ki ke sonsa ko? Ki gaya min gaskiya”. Ta tsorata da sauyawarshi. “Yaya Zaruk ni in ce ina sonsa? Wace irin magana ka ke yi haka?” “Shiru! Na ce ki rufe min baki, ni za ki raina ma hankali? Ni za ki yi wa haka?” *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 10* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *A* zahiri ta gama tsorata ba ta tava ganinshi cikin irin wannan yanayin ba, gani ta yi ya miqe a zafafe ya fice ya turo qofa da qarfi har sai da ta firgita, kawai ta bi shi da kallo, ta rasa me hakan ke nufi. Ta sauke ajiyar zuciya, a sanyaye ta miqe ta yi waje. A harabar gidan ta samu Ammi zaune tana alwala, Aazeen na qoqarin ficewa. “A’a sai yanzu ki ka bar Ya Zaruk ya tafi?” Aazeen ta faxa. Nurat ta xaure fuska. Aazeen ta maida kallonta ga Ammi tana faxin, “Ammi da alamun tuwona maina za mu yi”. “Ammi kina jinta ko? Wallahi za ta sa na daina kula shi”. “Me ya yi zafi? Allah ya ba ki haquri, ai shi xin Yayanki ne”. ammi ta ce tana murmushi. “To ai Ammi shi ma babu abin da zai yi da qwaila”. “Eh xin na ji”. Nurat ta faxa a qufule kamar za ta yi kuka. Binshi kawai ta ke da kallo, yadda ta ga yana faman dudduba ko’ina na gidan. “Yallavai lafiya kuwa?” “Ina duba ta inda zan fara ne”. “Me za ka fara?” “Rangida za ta yi manyan baqi daga Jos, tana buqatar a yi wa gidan kwaskwarima”. Ta jinjina kai cike da takaici. Ya janyo kujera kusa da ita ya zauna, ta dube shi cikin sanyin murya, ya fahimci haka, “Da magana ne?” “Ina ganin bai dace a ce ‘yar da muka haifa ta dinga tsara mana abin da za mu yi ba, hatta da girki sai wanda ta ke so ake yi? Ya kamata ka yi nazari watarana fa gidan wani za ta je, za ta iya rayuwa da kishiya ko uwar miji, kana ganin za su xauki wannan? Waye zai iya zama da ita da wannan xabi’un? Ya kamata ka duba ka koma ka sauke ta daga wannan layin ya kamata Aazeen ta san rayuwa, sangartar nata ya yi yawa, rayuwa na iya juyawa a kowane lokaci bana fata, amma…” Ya yi saurin katse ta, “Ba za ta tava ganin duhu a rayuwarta idan kina tunanin gidan aurenta ne, su kansu mazan yanzu har da iyayen nasu duniya suke bi, idan za ta ce mijinta ya durqusa ta hau bayansa ina rantse miki sai ya durqusa”. “Shi kenan”. Ta ce da shi, ta koma ta tsuke baki. “Kin yi shiru, ba gaskiya na faxa ba ne?” “A naka ra’ayin ka yi daidai amma don ya kamata a qalla mu koya mata mu’amala yadda za ta jeranto wa wanda ya girme mata magana”. “Okey, gaya mini wa ya tava kawo qararta? A kunnena ina jin yadda ake yaba mata, ba ta tava yin ba daidai ba”. Ta miqe cikin qoqarin barin gurin, ta xan dube shi a qufule. “A ganinka ba…” Kan ya kai ga magana ta yi saurin barin gurin. *** *** *** Da murnarta ta danno kai hotel xin har zuwa xakin da yake, yana tsaye ya juya baya da gudu ta rungumo shi ta baya, ta daxe a haka ba tare da ya tanka mata ba. Ta sake shi ta zagayo gabansa, fuskar nan ta gani a xaure. “Why?” Ya kamo hannunta suka zauna. Ya xauki tsawon lokaci kafin ya yi magana, gaba xaya ta gama kafe shi da ido, cikin son ji daga gare shi. Ya furzar da wani huci. “Ke ce ki ka lalata komai”. Cike da mamaki ta dube shi. “Ni kuma? Da na yi me?” A qufule ya zayyane mata komai, hankalinta ya yi matuqar tashi. Ta miqe a zuciya, “Zan yi maganinta. Wallahi sai ta gane kurenta”. Ta nufi hanyar fita, ya yi saurin janyonta ta zube a jikinsa, za ta yi magana ya danna harshensa cikin bakinta. Sun daxe a haka, cikin wani irin salo ya janye harshen nasa, sai dai tana manne a jikinsa. “Ina son mu bi komai a hankali kamar yada ki ka ce yarinya ce za mu bi da ita ta dabara. Ina so ki samu bayanin komai daga bakinta, ina son ki yi mata wayo har ki samo mana lambarsa, inyaso sai ki bar min ragowar aikin, ni na san yadda zan ji da komai”. “Okey, to shi kenan, ni zan tafi”. Ya sake qanqame ta. “me ki ke nufi, haka za ki tafi ki bar ni?” “Na ga kai ma ya ba wannan ce ta kawo ka ba”. Ya sanyaya murya cikin salon yaudara. “Kin sani duk yanayin da nake ciki da zarar na ji ki a jikina na kan ji sanyi, bana iya jure rashinki, don Allah kada ki yi min xangwalilliya”. Ta daddage ta tankaxa shi, “Ba za ka samu komai ba yau ko da na amince da kai babu abin da zan xorar, ni kuma ba zan yi abin da zai daxa dama wani ni na kasa nishaxantuwa ba”. Ta miqe yana magana ta yi saurin ficewa a xakin. Tun daga harabar gidan ta ke faman qwalla mata kira, ba ta ji motsinta ba har ta ratsa sitroom inda ta ga Ammi zaune a kan darduma da alamun sallah ta idar. Ba tare da ta ce komai ba, kodayake matar da ba ta yi sallama ba me za ta iya cewa? Kawao ta bi ta da kallo gurin nema mata shiriya. A can xaki ta tarar da Nurat tana gyaran littattafanta, ba ta saba ganinta cikin wannan yanayin ba, don haka duk ta gama tsorata. Zama ta yi a kan kujera ta xora qafa xaya kan xaya tana faman haxa su, wannan shi ne alamarta duk lokacin da ranta yake a vace haka ne ya sa Nurat ta qara kiximewa, ba qaramin abu ne yake sanya ta haka ba. gabanta ya shiga bugawa tsawon mintina uku kamar ba za ta yi magana ba, sai faman huci ta ke. “Ki gaya min ina son sani da wa ki ke yin waya a cikin waya xina?” Ta ji tambayar ba-zata, tsananin ruxewa ta yi, ji ta yi tamkar numfashinta zai xauke. “Wayyo Allah”. Ta ce a zuciyarta. Wata irin tsawa Aazeen ta daka mata. “ke nake sauraro ki yi min bayani, ko ke kurma ce?” “Um-um…Aa’, um daman… da man… ba…ba…” “Wannan wace irin magana ki ke yi haka, munafuka? Za ki buxe baki ko sai na yi miki xankaren duka? Shegiya lumbu-lumbu wutar qaiqayi, da an yi magana Ammi ta ce ke qarama ce, ko ke ustaziyya ce, nan kam ke baqar shaixaniya ce, wallahi in ba ki gaya min gaskiya ba yau sai kin raina kanki”. Ba ta san sa’adda ta sa kuka ba, cikin shessheka, “Ni ban aikata komai ba, ban yi komai ba”. “To gaya min yadda aka yi ki ke bin maza a cikin wayata, har kina amfani da sunana ki yi min magana”. Ta ce cikin xaga murya. ‘Wayyo Allah na shiga uku Yayata kada ki yi mini mummunan fahimta. Kada ki zarge ni, don Allah ba zan aikata ba daidai ba, ki yarda da ni”. “Idan kina son in rufa miki asiri, ki buxe baki ki gaya min gaskiya, in ba haka ba sai kin gane shayi ruwa ne”. Hankalin Nurat ya sake tashi, duk lalacewar Aazeen hakan bai sa Nurat ta raina ta ba, Amminsu ta koyar da ita yadda za ta girmamata. Tana tsoron Aazeen ba ta ajiye mata kara ta tsallake, tana matuqar tsoron vacin ranta. Waxannan abubuwa su ke qara dasa wa Aazeen qaunarta, haka ne ya sa ba ta cika takura ta ba, wani fannin tana sane ta ke biye mata su yi ta shirme, duk kuwa da cewar ta bata shekaru takwas. “Wato soyayya ki ke yi ko? Gaya min me ki ka sani game da so?” Ta shiga rantse-rantsen cewar ba haka ba ne. “Ba soyayya ki ke ba, me ki ke yi?” Gaba xaya ta rasa kalmar da za ta kare kanta da shi. “Okey, to me ki ke yi?” “Da gaske nake Yaya, ban san me ki ke nufi ba, ban san me soyayyar ba. Ban tava ganinsa ba, ban san yadda ake yi ba, ki yarda da ni kawai dai na saba da shi ne saboda ke…” Ta qarasa zancen cikin shaqaqqiyar murya mai tattare da tsoro cikin kallon Aazeen xin. “Okey, wato kina nufin ke ce za ki aurar da ni kenan?” Ta shiga sintiri, ta koma ta tsaya. “Oh ni yanzu kin gama zubda min mutunci kenan?” Ta kai mata hauri da qafa. Jikin Nurat na krayma. “Ki yi haquri, na tuba ba zan sake ba”. “Sai kin gaya min ta yadda ki ka sanshi, idan ki ka yi min qarya sai na gaya wa Ammi na ke wadda kullum ke yi miki kallon yarinya mara wayo”. Ta sake kiximewa, cikin sarqewar murya ta soma magana. “Na saba da shi ne ta dalilin mistake xin lambar Anisa qawata wadda suka koma Lagos, ta ba ni lambarta shi ne kiran ya shiga wayarsa. Hakan ne ya sa muka saba da shi a dalilin ya ce shi yayanta ne. Na kan kira shi akai-akai ina tambayarsa labarinta, a haka muka saba, sai daga baya ya ce da ni bai ma santa ba. Yana da kirki haka ya sa muka ci gaba da gaisawa…” “To me ya sa lokacin da ya ce da ke bai santa ba ki ka ci gaba da bibiyarshi? Kuma na duba na ga kaf ke ce kaxai ki ke kiranshi, tabbacin shi talakan talas ne?” *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 11* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *T* a runtse ido ta buxe, wasu zafafan hawaye suka sulalo kan kuncinta. “Ban san dalilin da ya sa na ci gaba da kiranshi ba, kuma ban sanshi ba, bai tava ganina ba, sau xaya na tura masa da hotonki ta facebook…” “What? Oh ni! Na shiga uku, ki ce duk kin gama tallata ni, shin Nurat kin gaji da ni? Kin tsane ni ko shi ya sa ki ke son na bar gida ko?” “Ba haka ba ne, ki yi haquri. Ina sonki, kada ki yi min mummunar fahimta, na tuba”. ‘To bari ki ji, daga yau kada in sake ganin wayata a hannunki”. Ta yi waje tana faman huci. Nurat ta kwanta lamo tana maida numfashi, gaba xaya ta dinga jin haushin kanta. Me ya sa ta aikata haka ba ta yi tunani ba? Ba za ta sake ba, ta daina! Daga yau ta tsinke alaqa da Adamu, babu ita babu shi, sai dai a kan kanta ta qaryata kanta, tana ji ba za ta iya ba. “Dole ma in iya”. Ta faxa a fili, “Ai daman ban sanshi ba, dole ne na cire shi a rayuwarmu”. Qarfe goma sha biyu da rabi na dare tana faman juye-juye a kan gado, tana faman qasa da warwara, ta miqe zaune ta rafka tagumi. “Ko da mutuwa aka yi sabo ake wa kuka, na saba da kai sosai, na xauka komai zai zo da sauqi ashe ba haka yake ba? ina ji kamar na rasa abu mai muhimmanci a rayuwa ta, to idan ya daina jina ya zai yi? Na tabbata zai yi kewata, to ya zan yi?” Ta miqe tsaye zumbur. “Kai ba zan iya ba, ba zan iya tsinke wannan alaqar ba, duk me hakan ke nufi? Ba kya jin kunya, to inda a ce Yaya Aazeen ta amince haka za ki ji kenan?” Zuciyarta ke raya mata hakan ta cije leve a bayyane kamar wata tavavviya, ta buxi aki, “Ba don ni nake yi ba, babu shi a raina, kawai ina qaunar kasancewarsu da Yayata. Ina jin tausayinsa, na yi masa alqawarin Yayata za ta kasance da shi ko da kuwa me ye zai faru sai na cika wannan alqawarin, ta ya ya?” Zuciyarta ta tambaye ta, “Yaya Zaruk! Shi ne ya faxo mata a rai, da sauri ta yi waje. Lokacin da ta isa qofar xakin Ammi sai ta shiga sanxa, a hankali ta buxe qofar. Ta yi sa’a Ammi na xakin Dad, ta hangi wayarta a kan gado. Ta xauka wuf! Ta yi waje kamar mara gaskiya. A can cikin xaki ta murxa key tare da lalubo lambar Zaruk. Shi ma Zaruk tunanin Nurat ya hana shi sukuni, ya ji wayarsa na ruri. Waye zai kira shi a irin wannan lokacin? Kamar ba zai xaga wayar ba, ya dai miqa hannu ya xaga. Lambar Ammi ya gani, cike da mamaki ya kara a kunne. Muryar Nurat ta ratsa kunnensa, ya saki ajiyar zuciya. “Me ya hana ki bacci?” Kai tsaye ya tambaya. A gaggauce ta soma faxin, “Yayata ta juyan baya, ta qi amincewa da Adamu, ban san ya zan yi ba”. “Wayyo Allah”. Ya ce a ransa kamar zai yi kuka. ‘Nurat me ya sa ba za ki mance wannan mutumin bab? Aazeen ba ta rasa komai ba, don me ya sa za ki tsananta? Tunda ta nuna ba ta so ki haqura, muddin kuma ba ke ce ki ke son nasa ba”. “Yaya Zaruk me ya sa za ka ce haka?” “A’a to, in ba haka ba, tunda ba ta ra’ayi kurum ki haqura’. Za ta yi magana ya katse ta. “Kin ga, in har ba haka ba ne, ki yi min alqawarin za ki fita harkarsa”. Ta raunana murya. “Ba zan iya ba, na riga na yi mishi alqawarin zan aure shi…” “What? Kin san me ki ke cewa? Nurat mutumin nan ko dai aljani ne? za ki aure shi fa ki ka ce?” “Ina nufin za ta aure shi”. “Saboda ita xin kaza ce, ko saboda ‘yarki ce, ke ce ki ke da ikon aurar da ita? Me ta tsare miki haka?” Ya faxa cikin xaga murya. “Haba Yaya Zaruk, in ba ka fahimci ni ba, bana ganin akwai wanda zai iya fahimtata kuma”. ‘Ba zan tava fahimtar taki ba har abada, mahaukaciya kawai. Yanzu ki gaya mini za ki fita a rayuwarsa ko kuwa?” Ya soma qular da ita, xuf! Ta katse wayar. Ya yi cilli da wayar yana jin zuciyarsa tamkar ta faso qirjinsa, ga dare ya yi ballantana ya yi wani abu a kai. Tuni ya janyo kwalin taba ya kunna ya shiga zuqa, ya kusan shanye kwali guda ba tare da ya samu wata nutsuwa ba. yana jin tamkar an tsawaita daren, idanuwan nan sun yi jajir ko kaxan bai runtsa ba, kan safe ya yi wani zuru-zuru. Ita kam Nurat a safiyar tunda sassafe ta shirya tsaf don tafiya makaranta. Hajiya Rahma da Alhaji Usman zaune suna karyawa ta fito. “Da wuri haka?” Dad ya tambaya. “Yau muna da test”. “Amma dai kin karya ko?” “Ammi bana jin yunwa”. Ba ta tsaya sake jin komai ba, za ta fice, Aazeen ta fito ita ma cikin shirinta. “Bari na sauke ta, ni ma yau fitar wuri zan yi, muna da manyan baqi a ofis”. A gidan baya Nurat ta zauna, hakan na nufin Nurat xin na fushi da ita ta fara tuqi babu wanda ya kula wani har zuwa get xin makarantar. Kusan tare suka yi parking da Deedat, bai sauka a kan Vespansa ba ya hangi Nurat na qoqarin fitowa a mota. Gabansa ya yi wani mugun bugawa. Da sauri ya maida ido ga motar don ganin wanda ya kawo ta, duk da bai ganta tartar ba ksancewar gilas xin motar ba mai haske ba ce. Ya shiga tunanin inda ya santa. Vacewa ganinta da ya yi ya sanya ya gaza tuno komai, zai maida kallonsa ga Nurat ita ma ta vace wa ganinsa. Ina tsantsar qaunarta ina sonta, ita kaxai na tava so a rayuwa ta, ina ji tamkar ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba, kafe shi principal ya yi da ido cikin mamaki, har yana ji kamar ba Deedat xinsa ba ne. Deedat mai kunya da aji ya kan yi haquri a kan abin da yake so, ya danne. Tabbas al’amarin yana girmama, gane abin da yake qauna abu ne mai wahala. Sai ga shi yau ya dubi qwayar idonsa ya furta masa yana son xalibarsa. Abin da kansa ya haramta, ya dubi Deedat cikin sauke ajiyar zuciya. “Ina jin komai tamkar cikin mafarki, amma ina zuwa”. Qarasowa ya yi qofa ya murxa key ya dawo ya zauna. Deedat ya dube shi, wani irin duba, duban da ya sanya Principal ya sake gaskata abin da bakinsa ke furtawa. “Xalibarka ta kasa goguwa a zuciyata, ban tava sanin haka soyayya ta ke ba, yarinya ce qarama wadda ba tsarata ba, amma zuciyata ta kasa sukuni da sonta. Ban tava cin karo da abin da nake matuqar qauna ba irinta. Ka gaya min ya zan yi? In ka yi la’akari da waye ni, za ka tabbatar da cewar lalacewa ta zo min, wannan shi ne jarrabawa ta. Allah ya jarrabe ni da abin da ba zan tava samu ba, ita xin…” “No, kada ka ce haka”. Principal ya yi saurin katse shi. “Babu mahalukin da za ka so alaqa da shi irin wannan, ya ce zai guje maka ko da kuwa bai sa matsayinka ba, kwarjininka da kalaman da ke shimfixe a fuskarka kaxai zai sa ka samu komai da kowa, ballantana idan aka gane waye kai”. “Abin da bana so kenan, ina son samun macen da za ta so ni don Allah ba don komai nawa ba. Ina son samun soyayyar gaskiya”. Principal ya dafa kafaxarsa cikin xan bubbuga shi. “Da yardar Allah za ka samu abin da ka ke so”. “Ina zuwa”. Wayarsa ya xauko ya shiga laluben wata lamba. “Malam isma’il ka bai wa Nurat littattafan nan ta kawo min yanzu”. Shi kam Deedat ya maida kai ga wayarsa yana tura saqonni. Bai fahimci abin da principal ke qoqarin yi ba. “Assalamu alaikum”. Wani irin bugawa gabansa ya yi, da sauri ya xago kai idanunsu suka gauraya. Ta xauke kai, shi ma komawa ya yi yana satar kallonta. Ta durqusa cikin girmama ta gaishe su. Ta aje littattafan a kan tebur. “In ji Malam isma’il”. Miqewa ta yi za ta fita. “Am.. xan dawo in xan sa ki aiki kafin na dawo, ki duba ki ware min books xin kowane aji a cikin waxanda ki ka kawo da na gurin nan, ina zuwa” Ya miqe cikin sauri, “Deedat ba ni minti biyar ina zuwa”. Ba tare d ya jira me Deedat zai ce ba ya yi saurin ficewa. Ita kam ta duqufa ware littattafai, hakan ne ya ba shi damar qare mata kallo. “Kina buqatar in taya ki ne?” Bai san sanda wannan furucin ya kufce a bakinsa ba. Ta xan xago kai cikin dubansa. “Na gode na ma kusan gamawa”. Ya shiga tunanin ta ya ya zai taqalo hira tsakaninsa da ita. Ya nufasa. “Kafin malam ya kira ki ya ba ni labarin kina da qoqari sosai qanwata”. Ta yi murmushi. “Ko ba haka ba ne?” “Ya dai faxa ne, amma akwai waxanda suka fi ni”. Ya dinga jin wani irin nishaxi mara isaltuwa. “Ya sunanki qanwata?” Ta xan dube shi a kaikaice. “Sunana qanwata”. Ta faxa cikin murmushihar kumatunta nalotsawa. “Kin amince ki zamoqanwata?” “Eh mana ai da ma kai xin Yayana ne”. “Na gode da wannan matsayin”. *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 12* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *M* amakin yadda ta biye mishi yake yi. Ita xin ma haka ne, tana mamakin yadda ta kasa share shi, yau shi ne karo na farko da ta saki jiki da mutumin da ba ta san waye ba. babu alamun shashanci a tare da shi, ba mutum ne wanda za a iya rainawa ba. yana burge ta da yawa, da alama mutumin kirki ne, kuma ma ai shi xin babba ne, ba za ta iya biris da shi ba. Miqewa ta yi. “Ya na ga kin miqe?” “Na gama”. “Ai cewa ya yi ki jira shi, ko dai ni ne na cika ki da surutu?” Murmushi kawai ta yi. “To bari in jira shi”. Zamanta ya yi daidai da shigowar Principal, “Kada dai kin gama?” “Eh tun xazu”. “Okey sannunki”. Ta yi saurin nufar qofar ficewa. “Qanwata babu sallama?” Tsoro ya kamata, ba ta iya cewa komai ba ta yi saurin ficewa. *** *** *** “Haba Malam a kan yarinya qarama ka ke neman lahanta rayuwarka? Tunda na shigo ka ke faman xaxxakar sigari, ba ka san wannan hayaqin matsala ne a lafiyarka ba?” “Faisal zuciyata ta kasa samun nutsuwa, ina ma zan san inda wannan xan iskan ya ke? Ban tava kisa ba,amma da na soma a kansa. Ya zo ya rusa min komai, wani abin takaici wai ba ta sanshi ba ma, ina ga idan tasanshi?” “Zaruk sam rayuwa ba za ta yi daidai da ita ba, yarinyar da ta ke ‘yar qauye sam ba ta da wayewa, yarinyar da kwalliya ma ba ta dame ta ba, idan ka ce ita ce za ka aura za ka zamo kullum cikin jin kunya, don ba za ta fidda ka jin kunyar abokai ba, tunda ba ka rigaya ka furta mata ba ka nemi Aazeen ita ce daidai da kai”. “Kana son ka ce in zavi Aazeen ta zamo uwar ‘ya’yana? Anya kana kishina kuwa? Ta ya ya za ka ba ni shawarar haka alhalin ka riga ka san ita xin wace ce? To bari ka ji, ni na tsani mazinaciya, na tsani ‘yar iska. Ba zan tava rayuwa da tantiriyar mace mai wayewa irin Aazeen ba, na fison na auri matar da ba zata zo wucewa wani namiji ya dube ta yana tuna abin da suka aikata da ita ba. Na fi son na auri macen da ko hannunta wani xa namiji bai tava riqewa ba. Na fi son mai nutsuwa da kamun kai irin Nurat, ina ganin ita ce ta fi kowacce mace halin qwarai”. Faisal baki buxe yake kallonsa cike da mamaki, ya koma ya tuntsire da dariya. “Oho da kyau, wato kana son ka ce Allah za ka yi ma wayo ko? To bari ka ji, shi Ubangiji ba haka Yake ba, ita xin ta gama kauwama kanta tana tsare mutuncinta, sa’annan sai Ubangiji ya yi mata tukwici da samun miji qasurgumi kamarka? A’a ranka ya daxe ba wannan zancen, lallava kawai ka qarasa rayuwarka da Aazeen xin dai… kai ba ma wannan ba, ita xin Aazeen ta ya ya za ta iya barin ka yi wannan kwamacalar?” Ya kai ma kafaxar Zaruk duka. “Ka ga Malam, kawai dai ka sake tunani”. Da qarfi Zaruk ya daki table xin da ke gabansu har sai da Faisal ya firgita. “Allah ya tsine ma duk mutumin da ke qoqarin shiga tsakanina da Nurat ko da bai furta ba”. Ya faxa yana huci da zaro ido. Faisal ya xaga kafaxa cikin yanayin ko a jikinsa. “Ni dai na ga ka makance ne shi ya sa nake son dawo da kai kan hanya. Ka gama bin yawon matanka, sannan ka ce kana qyamarsu?” Ya faxa daidai lokacin da Zaruk ya bar gurin. “Kana tunanin za ka kuvuta daga faxin Ubangiji ne, alhalin har yanzu ba ka tuba ba? kama ta dini tujani”. Gidan ya cika da ife-ifen Aazeen da qawayenta, gaba xaya suka qanqame ta. Kallo xaya za ka yi mata ka tabbatar tana ji da qawayen nata fiye da yadda Dad xinsu ya sake mata komi na xakinsu an yo musu odar abin da za su dinga ci, an samo ‘yar aiki daga wani hotel wanda za ta dinga kula da abincinsu zuwa lokacin da za su tafi. Suna zaune a dinning room, hira suke yi na yaushe gamo tare da gaya mata yadda suka yi kewarta. Zainab wadda suke kira Zee ita ce wadda halayyarsu ta zo xaya da Aazeen, tantiriya ce ba a haife ta da xigon kunya ba, ba ta da tsoro, haka ibada ba ta dame ta ba. Ba ta da burin da ya wuce kullum ta ganta ga ta ga namiji. Sai Mima, ita kuma tana son harkar qawance, tana xaukar kowa da muhimmanci fiye da uwar da ta haife ta, duk rayuwarta tana qarewa a yi ma qawaye hidima. Hakan ne ya sa ta jefa kanta a harkar less. Sai Tina, ita xin arniya ce, ba ta da addini. Ita kuma sun fi kusanci da Mima saboda kusan harkarsu xaya, don haka ba su tava rabuwa. Minal ita ce mai sauqin hali a cikinsu, ita dai bar ta da shaixanci, ga tsananin yaudara. Kyakkyawa ce ta gaske, kyawunta ya zame mata kadara, iyayenta talakawa ne tuvus, ita ce komai nasu. Kyawunta ke burge Aazeen, don haka ta ja ta jikinta, Minal na da kirki, datausayi. Tanada son taimako, ga ta da shiga rai. Ammi ta fito daga sashenta cikin nuna farin cikinta. Minal ta dube ta, “Our Momcy ko?” Hankalinsu ya karkata gare ta. Wani irin gaisuwa suke mata, kawai yaqe Ammi ke yi. Cikin nuna musu shariya bata ji daxin mu’amalar yarinyarta dasu ba, shigarsu gaba xaya tamkar ba yaran musulmi ba. Daga gaisuwar nan ci gaba suka yi da harkokinsu. Zee ce ta kunna music a wayarta suka hau rawa daga zaune, Ammi ta kaxa kai kawai ta koma ciki. Nurat ta shigo sanye dakayan makaranta, ganin fuskar Aazeen a sake ya ba tadamar qarasowa ta tsugunna tana gaida baqi. “Nurat ce ta girma haka?” Minal ta faxa yayin da ta kai hannu ta xago ta daga tsugunnen. “Masha Allah, ka ga yadda yarinyar nan ta qara girma, ta yi kyau na ban mamaki”. In ji Mima. “Zauna mu ci abinci kin ji”. Gaba xaya Nurat ta gama shige musu rai. “Qanwata ba kya magana, ko don ba ki sanmu ba”. Zee ta faxa. “Rabonmu da ganinki tun kina ‘yar mitsitsiya, lokacin da ku ka je da Dad xinku visiting”. Tina ta karve zancen, “Yanzu ga yadda ta cika har tana son ta fi sister Aazeen nonuwa”. Aazeen ta xaure fuska tamau cikin duban Nurat, “Ke je ki xaki”. Sum-sum ta miqe, Mima ta kai mata duka. “Ji ki da Allah, sai wani muzurai ki ke”. “Na lura yarinyar akwai ta da kunya”. Wannan kalmar ce ta tuno mata da layin da Amminsu ta xorata na cewa, in ta bari namiji ya riqe mata hannu za ta samu ciki, gaba xaya suka kwashe da dariya. “Ki ce an cusa kan yarinya a ta kunta ba za ta ji daxin rayuwarta ba, ita xin zubin hakan ce”. In ji Aazeen. Suka sake sheqewa da dariya. “Haka ya fi mata”. Minal ta faxa. Horn xin motar Alhaji Usman suka ji da gudu, Aazeen ta miqe kanta kan ya fita har ya cimma gurin. Gaba xaya ta qanqame shi, shi kuma sai washe baki yake. “Baqin namu har sun qaraso kenan?” “Sannu Dad, da fatan mun same ku lafiya?” A xaya daga cikin kujerun gurin ya zauna. Hira suke da shi sosai. “Wai ina Amminku ne?” Aazeen ta yatsina baki, “Tunda ta leqo suka gaisa ta shige ciki ba ta sake leqowa ba”. “Bari in qarasa na gani”. Yana barin gurin suka shiga yaba masa. Da alama Dad ya fi yi da ke, amma fa ya burge mu, wayayye da shi. Dole ki fantama yarinya, ashe xaurin gindi ki ka samu tun daga tushe?” Zee ta faxa. Suka saka wani ihun shewa, haxi da tafawa. *** *** *** “Ke kullum burinki ki qasqantar da Aazeen, ina amfanin haka? Kun yi baqi kin wani shigo ciki kin kwanta, kina son nuna musu cewar ba ki damu da ita ba kenan ko?” Banza ta masa tamkar ba da ita yake ba, idanunta a rufe. ‘Na sani kina jina, da ke fa nake”. Ganin ta qi motsawa ya daka mata duka. Ta buxe ido a qufule. “Ina magana kin maishe ni sha-ka-tafi, wai shin ba baqi ku ka yi ba ne?” Ta miqe zaune. “Kana son ne in je na zauna a cikinsu kamar yadda kai xin ka yi?” Ya saki baki yana kallonta. “Kada dai a ce kishi ki ke yi da ‘ya’yan cikinki?” “Uhum, Yallavai kenan. Ashe da na daxe da qarewa, ai ni inda sabo na saba da irin haka, ina da aikin yi”. Ta miqe za ta barshi a gurin. Ya wani figo ta ta zube a qasa. “Ni za ki raina wa hankali, ina magana za ki fita? Yaushe ki ka dawo haka?” “Komai koya xan Adam yake yi”. Mamaki ya sake kashe shi, yana ji kamar ba Rahmarsa ba ce. “Ni ki ke gaya ma magana?” Ta tave baki, kallonsa ta ke a tsakiyar ido, babu shakka a tare da ita. “Kana mamaki ko? Muddin waxannan qananun ‘yan barikin ba su bar gidan nan yau ba, zan ba ka mamaki”. Yadda ta yi xin ya xaga masa hankali, ya kasa zaune ya kasa tsaye. *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 13* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *Y* adda ta yi xin ya xaga masa hankali, ya kasa zaune ya kasa tsaye. “Tabbas ni xin kaina ina ji a jikina irin wannan tashin hankali da ya shiga da walakin, kamar yana tsoron wani abu. Da sauri ya rufa mata baya, kai tsaye sashen su Aazeen ya yi. Bai ji motsinta a nan ba, haka ne ya sa ya nufi vangarenta, inda ya tadda ta zaune a tsakiyar gado tana faman kuka. Gaba xaya ya gama karaya, dole ya sassauta yana ganin wannan karon tsaurinsa ba zai sa ta biyu ba, dole ne sai ya haxa da lallami. Ya haye gadon tare da raunana murya. “Kin kasa fahimtar dalilin biye mata xin da nake yi, a tunani na yadda nake mata xin zai sanya ki yaba mini, sai na ga savanin hakan, in ban biye ma yaran nan ba ya ki ke so su yi? Su ne komai namu, idan ba mu biye musu ba waye za su je gurinsa da lamarinsu ya biye musu? Ki fahimce ni mana, ki duba ki gani Aazeen ta wuce munzalin da za mu takure ta. Ta mallaki hankalin kanta, ta san fari ta san baqi, ba za ta aikata abin da zai cutar da rayuwarta ba, kawai abin da za mu yi shi ne addu’a, lallavawa za mu yi su tafi inyaso sai mu kiyayi gaba kin ji”. Binsa ta ke yi kawai da kallo cike da mamakin yadda soyayyar ‘yarsa ta rufe masa idanu, har ya kasa tantance fari da baqi. “Ji yadda duk ya bi ya ruxe, sai faman zuba yake”. Hannu ya kai yana share mata qwalla. “Ki yi haquri kin ji”. Dole ta dinga xaga kai alamar ta haqura. Labarin da Aazeen ke ba su ya yi matuqar sanya su nishaxi, ita xin kanta cikin nishaxi ta ke ba su labarin. Minal na dariya, “Bai kamata ki yi ma Nurat haka ba, ki karvi zavinta, Hajiya ta. Sau tari abin da ake xauka wasa yakan dawo abin burgewa…” “Babu mamaki wani alheri ne ya tunkaro ki”. Zee ta katse ta da faxin haka. “Hajiya ta ki nemi ganinsa, ke ma za ki yaba. Hajiya alheri na tunkaro ki kina wasarere?” Aazeen ta kai mata duka. “Rufa min baki, alheri ko shirme?” “Ku tsaya duk ku ji”. In ji Tina. “Idan da ni ce ita, biye mata zan yi. Bai kamata a ce kin gwale ta ba, musamman yarinya irin Nurat”. “Tabbas haka ya kamata ta yi”. Minal ta ce. “Ok, kuna son ku ce in biye ma shirmenta kenan ko? Ok, zan yi yadda ku ka ce, ko ba komai na yi sabon kamu. Allah ya sa xan harka ne”. “Good aminiyar, ashe kin gane karatun namu?”. A wannan daren kwana suka yi cur a gindin talabijin suna faman kallon tashar fim xin da addininmu ya haramta mana gani. Abin da ya jawo Mima da Tina suka kasa xaga wa juna aka keve suka yi gefe suna biya ma kansu buqata. Ita kam Zee chating ta shiga yi da saurayinta, Minal da Aazeen hira suke yi, a haka suka kwana zur sai da aka fara kiraye-kirayen sallah, Aazeen ta xauki filo ta koma gefen su Tina. “Ni ban ga tsiyar da za ki tsinta a wannan harka ba sai wahala”. Ta ja tsaki ta yi waje tana faan haxa hanya saboda tsananin baccin da ta ke ji. Sashen Ammi ta nufa domin tashinta. A kan dardua ta riske ta a zaune ta xaga hannu tana kai kukanta ga Ubangiji. “Na kasa samun nutsuwa, farin cikin rayuwata na fushi da ni”. Nurat ta dube ta don gaskata abin da kunnuwanta ke jiyo mata. Aazeen ta dafe kuncin Nurat da hannu biyu ta xago fuskarta. “Ko ba haka ba ne qanwar?” Nurat ta yi murmushi, har kumatunta na lotsawa. “Okey yanzu na amince da zavin abar qaunata, shi ke nan?” Nurat ta buga tsalle. “Yayata da gaske ki ke yi?” “Eh ana”. Ta rasa inda za ta tsoma ranta saboda tsananin farin ciki. “Saura kawai na ganshi. Allah ya sa dai qanwata ta iya zave”. Cike da farin ciki, “Yayata, dole a ya yi miki. Ya dace da ke. Na gode yaya Aazeen”. “No, kafin ki yi min godiya, ki fara jin sharaxina. Akwai wanda nake son aure ke ma kin san da wannan shi ne burina. Ina son ya zamo mallakina yana da kuxi, ni kuma ina matuqar qaunar kuxi, bana son haxa hanya da talauci muddin na haxu da mutumin nan zan janye naki mijin da ki ka yi min,saidaiidan ke ki aure shi”. Har ta sa Nurat dariya. “Yaya ni aure kuma? Hmm har kin sa na ji kunya. To amma shi wancan xin idan bai ce yana sonki ba fa?” Dariya ta dinga yi har da tafa hannu, ta tsagaita dariyarta cikin duban Nurat. “Ke a tunaninki har akwai namijin da zai iya cewa ban yi ishi ba? Ki ma daina wannan tunanin, ni na yarda da kaina, kodayake ba za ki fahimci abin da nake nufi ba. Za mu fita da su Zee idan mun dawo za ki haxa ni da shi, kin ji?” Ta miqe ta yi waje. Nurat ta yi ajiyar zuciya, wani irin farin ciki ya ci gaba da lulluve mata zuciya. *** *** *** “Ba ka isa ka ce za ka juya wa Nabila baya ba, wannan karon dole ne a yi wannan aure inyaso kabarta a gidan nan, ka sani kullum ina jin nauyin mutanen nan, karo na uku kenan mahaifinta na yi mini maganar yaushe za a saka ranar auren nan, don haka yau ba za ka bar gidan nan ba sai ka sanar da ni. Ba ka san cewar cikar kamalar xan Adam shi ne aure ba?” Miqewa ya yi tsaye, tare da juya mata baya. “Ummita, kin sani ba ni da wata kamala, don Allah ki yi haquri ki qyale wannan maganar”. Da sauri ta zago gabansa, a can qarqashin zuciyarta ji ta ke yi tamkar ta sa kuka da kalamansa mai narkar mata da zuciya. A zahiri kuma ta xaure fuska, “Na sani kada ka yaudare ni na san dalilin janye-janyen nan naka. Ita Nabila ai ko ma ya ta ke bai kamata ka duba haka ba, karamcin iyayenta gare mu za ka duba ko da kuwa a ce tana zaman kanta ne”. Ya sanyaya murya, “Ummita, idan na ce zan aure ta ba kya ganin abin zai yi min yawa haka? Rayuwata da ta yarana za ta qara lalacewa, abin da ya faru a kaina ba ni na xora wa kaina ba, sai dai ba zan so a ce ni ina ganin kuskure in take saboda kawai wata alaqa. Don girman Allah Ummita ki qyale ni, ba zan iya ba, ba kya ajiye min kara na tsallake sai dai wannan karon ki yi min afuwa”. Yana gama faxin haka ya juya zai fita. Kuka ne ya qwace mata, ta durqusa kamar qaramar yarinya, dole ya juyo a ruxe ya qarasa gare ta. Xago ta ya yi yana goge mata qwalla. “No Ummita, don Allah kada ki yi min haka, kin san matsayin hawayenki kuwa a gurina? Shin kina son na lalace?” Da sauri ta girgiza kai. Ya jawo hannunta ya zaunar da ita, ya koma ya buxe firij ya tsiyayi ruwan Faro a glass cup, da kansa ya ba ta a baki. Ta sha ya ajiye kofin. “An yi an gama Ummita, ki bari na haxu yau da Nabila sai mu yanke hukunci, kin ji ko?” Daxi ya kama ta. “Allah ya yi maka albarka Babana, Allah ba zai tozarta ka ba insha Allah”. Tsararren qaton hall xin da kallo xaya za ka yi masa ka yi tunanin fada ce ta shugaban qasa. Gurin ya yi matuqar tsaruwa, kujerun gurin ma kaxai abin kallo ne, yadda jama’a suka zazzauna a kan kujerun kaxai abin burgewa ne. Hall xin ya yi shiru, sai sautin muryar Ahmad Deedat ne kawai ke tashi. Sanye yake da wasu fitinannun qananan kaya, wanda ya bi ya kwanta a fatarshi. Fuskar nan sai sheqin annuri ta ke. Ya wani qara kyau. Ya xan dakata da maganarsa lokacin da ya hangi wayarsa na wuta alamar ana kira. Qanwata ya gani a kan fuskar wayar. Mamaki ya ke yi, Aazeen a wannan lokaci? Lafiya kuwa? Dole ne ya xaga wayar ya nemi su ba shi minti biyu, ya koma farfajiyar kamfanin wayar a kunne. ‘Kana can ka mance da ni ko?” Muryarta ta ratsa dodon kunnensa. “Da a ce ba ki kira ni yanzu ba da jimawa kaxan ni zan kira ki”. Ta yi dariya har yana jin sautin dariyar. “Ka ji ka da qoqari, ina za ka samu katin?” “Xazun na saka xari biyu na kira Kakata, akwai bonus”. “Na ji ka ce za ka kira ni, kana nufin kana kewata kenan?” “Sosai ma kuwa”. ‘Okey, gaya min yaushe za ka zo?” Ras! Gabanshi ya buga. ‘Har kin shirya ganina?” “Eh mana, sosai ma”. Ji ya yi an qwalla mata kira. Xuf! Ya ji wayar ta katse. Ya yi murmushi, “Ba mu tava yin sallama da ke ba”. Ya faxa a bayyane cikin murmushi. *** *** *** “Ba wani yanayi a soyayya, so kamar rayuwa ne, ba kowane lokaci ba ne ake samun sauqi kuma ba kowane lokaci ake samun farin ciki ba. Ya kamata ka koyi sona, tunda ina nan a raye bana jin zan iya rabuwa da kai Yaya Deedat. Kai ne numfashina na sani ba wata damuwa ka yi da ni ba, da zan iya da tuni na cire ka a raina. Sai dai ina ji a jikina wataran za ka so ni, zan iya jure komai a kanka. Na amince zan rayu da kai a ba ka sona xin”. Kalamanta sun karyar masa da zuciya. Duk sai ta ba shi tausayi. “Nabila ban ce bana sonki ba, xabi’unki kawai za ki sauya”. “To ka gaya min, me ye aibuna? Me nake yi wanda ba daidai ba?” Ya ja wani xan qaramin tsaki, matsalarta kenan ba ta amince da ba ta yin daidai, xabi’unta tana xaukarsu abin burgewa. “To shi kenan, tunda kina ganin komai daidai ne babu matsala, yanzu ki gaya ma su Papa, wata biyu na xiba”. Ta yi sororo. “Yaya Deedat, wata biyu ba ma sati biyu ba?” Ya ce, “Akwai tafiyar da zan yi, zan kai kusan hakan idan na dawo sai a yi bikin. Ni zan wuce”. Ta matso kusa da shi, matsalarsa kenan, sam bai iya soyayya ba, yadda ka san mutumin da. “Yaya Deedat shin ba ka xokina ne? Ya kamata a yi bikin nan kafin ka tafi inyaso sai mu tafi tare, please”. “Ba zai yiwu ba, idan hakan bai yi miki ba kin iya neman wani”. ‘Uhm Yaya Deedat, ka sani ba ni da mijin da ya wuce ka. Ina son ka sani ko da za ka kai shekaru goma ina nan daram babu inda zan xaga, kawai dai ka sa a ranka duk bala’i ba ka da matar da ta wuce ni”. Ya yi wani murmushi mai ciwo. “Allah ko? To sai ki ci gaba da jira”. Murmushi ta yi, ta sani gaba xaya Deedat ba ya sonta, bai tsara rayuwarsa da ita ba, kuma dole ne ya aure ta, ba za ta bari wata shegiya ta rave shi ba, ba ta fatan ganinshi da wata ko da ba shi da komai, ballantana hamshaqi kamarsa, ko za ta mutu babu aure za ta jira shi. Ta sani haramtaccen abu ne ya yi aure ba tare da ya aure ta ba. Ta sani dama yake nema da zarar ta ji haushi ta ce za ta auri wani zai auri wadda yake so, don haka za ta jira shi. Ta qarasa gabanshi inda suke iya jin hucin juna. ‘Zan jira ka ko da hakan zai kai mu da tsofewa, na yi alqawari ba ni da miji face kai, in ka je ka yi shekara ba ka dawo ba Mr. Man”. Ta yi murmushi, a gurin ta barshi. Takaici kamar zai rufe ta da duka. “Dole ne fa ka yi yadda iyayenka ke so, kai ma ka sani tuntuni ita xin zamanka ta ke yi, ba ka da hujjar da za ka guje mata”. “Mtss! Salim ka sani bai tava sonta ba, ta ya ya zaman aure ya yiwu a haka?” “Nawa aka yi Yaya? Iyayenmu na da suka yi ba su tava zaven mace a kan kansu ba, kai wasu ma ba za su tava sanin wace matarsu ba sai ranar da suka tare”. ‘Ok, na ji wannan, amma kuma ba ka tunanin ita xin Nabila wace ce ita ba?” “Wannan ba hujja ba ce, a koyaushe xan Adam na iya sauyawa, ballantana Nabila wadda da zarar ka aure ta soyayyarka na iya sauya ta, in fa ka aure ta za ku kasance ne tare, in ma ba ku kasance tare ba kana datse ta a gida zama za ta yi”. Deedat ya furzar da wani huci mai zafi, kalaman Salim ba su zame masa hujja ba. ya sani babu wanda zai iya fahimtarsa, babu wanda zai hangi abin da shi yake hange. “Kawai ka lallava ku rabu da Ummi lafiya”. Salim ya katse shi da faxin haka. Bai dai ce masa komai ba, ya soko wata maganar, ba ya son ci gaba da maganar Nabila. Gaba xaya rayuwar gidan ta sauya, gida ya koma tamkar ba na musulmi ba, kixe-kixe da raye-raye shi ne abin yi. A kullum cikin kawo maza suke, da Hajiya Rahma ta yi magana sai Aazeen ta ce abokansu ne daga ofis xinta, tana tsoro, don haka kusan kullum ta ke nemar wa Nurat inda za ta tura ta ta wuni. Tana jin tsoron kada idanunta su dinga ganin irin waxannan abubuwan. Haka a wannan lokacin ta qara qaimi gurin kai kukanta ga Ubangiji a kan Aazeen, babu abin da ba ta ayyanawa a kan Aazeen. Tuni ta gama sallama cewar ita xin tana bin maza ne, don haka ma babu aure a gabanta. Yau kam ta gama kai wa qololuwa, ko qawayenta ko ita ba za ta ci gaba da zama da su ba alhalin ba su da niyyar komawa, sun ma miqe qafa, don haka ko da ya dawo ba ta doshi turakarsa ba, ba ta kuma kai mishi abinci ba. Ya dinga kiranta a waya ta yi biris! Ya turo text nan ma babu amsa. Ya qulu sosai har wani huci ya dinga yi. A zafafe ya miqe ya nufi shashinta, ya afka ciki. Tana zaune a kan sallaya yana huci. “Ban san sa’adda raini ya shiga tsakanina da ke ba, ina so ki sani ba zan xauki wannan wulaqancin ba, ba zan tava ba. In ban da rashin mutunci ta ya za a yi in dawo ban tarar da abinci ba, in kira wayarki ki qi xauka, wannan ai iskanci ne”. Har ta shafa addu’a ta cire hijabi tare da ninke darduma ta ajiye a gefe, ta koma bakin gado ta zauna ba tare da ta tanka mishi ba, hakan ya sake qular da shi, hannu ya xaga ya kifa mata mari. Dafe da kunci ta dube shi da ido fal qwalla. *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *Free page 14* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *D* afe da kunci ta dube shi da ido fal qwalla. “A kan me za ka mare ni?” Ya sake xaga hannu zai qara mata, ta yi saurin kaucewa ta dube shi a tsakiyar ido, yayin da qwalla ta gama lulluve mata ido. “Akwai Allah”. Ya bi ta ya shaqo ta. “Ki gaya min abin da ki ke nufi”. ‘Ni ka cika ni na ce”. Ta daddage ta qwaci kanta da qyar tana haki. “Wallahi muddin waxannan yaran ba su bar gidan nan ba, ba za mu tava zama lafiya ba”. ‘Zancen banza, an gaya miki su irinki ne? su xin suna da gurin zuwa, ke kam idan na kora ki ba ki da gurin zuwa, su da gatansu, ke ko fa? Ba ki da gatan, ke xin korarriya ce, mujiya ce wadda ki ke da danvareren tabo har a gurin Allah, ke xin…” “Ya isa! Ya ishe ka haka! Ka fara tunanin makomarka kafin ka hangi tawa. Wannan fuffukar da ka ke yi a da kenan, yanzu kar nake kallonka, na san ta yadda zan bi in wanke kaina. Na san yadda zan yi shari’a ta xaure ka, ita xin kanta na san yadda zan bi ta dinga ganin baqinka saboda ni ce mahaifiyarta. Sanin kanka ne uwa ta fi uba soyuwa a gurin zuciyar yaransu”. Ya saki wata dariyar takaici. “Ni a gurina Aazeen na yi nisa! Yadda nake da Aazeen ko cewa na yi ta kashe ki na yi imanin za ta bi umarnina, kuma wallahi idan ba ki bi a sannu ba sai kin yi kuka da idanunki, sai kin zamo qasqantacciya a gurin yaranki. Sai na yi miki lambar da za ki zame musu tamkar java, mara mutuncin banza. Qarqari kuma ki ce ba za ki ba ni abin da nake so daga gare ki ba, ki je ki riqe, kawai ina zuwa ne saboda in fita haqqinki, abin naki da kike rowarsa ba ya qara ta da komai, kawai maleji nake”. Ya yi waje, ya rufe qofar da qarfi har sai da ta firgita. “Wayyo Allah, na shiga uku!” Ta zube a qasa tana wani irin kuka. ‘Ni na ja wa kaina, kaico! Na sani hakan za ta faru. Usman tuntuni na gama sanin waye kai, sai dai soyayyarka ce ta makantar da ni. Usman ban tava ganin mara imani irinka ba, Ubangiji ka kashe ni in har mutuwa ta za ta zamo alheri a gare ni”. Wunin ranar ba ta iya fita ko da sitroom ba. A haka Aazeen ta riske ta, hankalinta ya yi matuqar tashi, duk shaixancinta tana son mahaifiyarta, ba ta son abin da zai xaga mata hankali. Da gudu ta tsugunna a gabanta. “Ammina, waye ya tava ki? Ammi kalli yadda ki ka komo wuni xaya, gaya min, Dad ne ko?” Ta kaxa kai. “To me ke damunki? Don Allah ki faxa min kin ji”. “Na ce da ke babu komai, kawai kaina ne ke yi min ciwo”. “No Ammi, ban amince ba, tunda qawayena suka zo ki ka kasa sukuni. Za su tafi, zan sallame su, ko kuma na maida su hotel, hakan ya yi miki?” Ba ta kula ta ba, kawai binta ta ke yi da ido har ta gama surutunta ta fice, tsananin tausayinta ta ke ji. Ta gama ba su labarin abin da ta fahimta ga Amminta. “Tab! Lallai Ammi tana da matsala”. In ji Tina. “To ai shi ke nan, sai ki yi irin rayuwar da ta ke so xin, saboda na ga kamar kin shiga damuwa”. Zee ta karvi zancen, “Yanzu ke hakan ne zai sauya ki? Kin ga Hajiyata kawai injoy your life”. Mima ta ce, “Ita wannan Ammin a haka kamar wayayyiya. Duk ta maida kanta wata ‘yarqauye, ba ta da aiki sai riqe carbi, ga kyakkyawar qanwarki na qoqarin kwaikwayarta, qauyancinta ya sanya an kasa gane ita xin mai kyau ce. Wai shin ma idan ba ki more rayuwarki a lokacin quruciya ba, yaushe ake son ki more shi? Sai lokaci da ta zamo yagwalgwal?” In ji Zee. Gaba xaya suka xau shewa. “Kun ga ku daina wannan zancen kuna kada min da gaba, babu abin da na tsana irin in ji an ambaci tsufa, a hakan ma nauyin shekaruna na ke ji, don haka nake roqon in mutu kafin tsufa”. “Shi ne aminiyas, kawai ki huta”. Minal ta ce da ita. “Amman da har Ammi na son karya min zuciya, na ji tausayinta yau”. “Okey, shi kenan sai ki koma zumbula hijbi, riqe carbi, zama a kan darduma takura kai”. Suka sake kwashewa da dariya. “A duk lokacin da ta sanya karatun alqur’ani na kan ji duk na takura”. Tina ta faxa, “Ban sakewa wallahi. Ki yi mata magana”. ‘No Tina, don’t cross your limit. Ki rufe bakinki haka kada ki wuce gona da iri”. Minal ta katse ta da faxin haka. Tuni ta shiga taitayinta. *** *** *** “Ba aiki ya kamata ki yi ba, hutawa za ki yi, ki bar ni da wannan uwar qwiyar”. “Babu komai Anty, kin ga idan na saka hannu sai mu fi saurin gamawa”. “Okey, shi ke nan tunda kin dage. Ga kaya can na xauko miki ki saka, kada ki vata na jikinki”. “To Anti”. Nurat ta faxa. Ta koma xaki ta sauya kaya. Kayan sun yi mata xas tamkar nata. Ba ta xaura xankwali ba, ta gyara tufkar gashinta ta fito. Kicin ta nufa inda ta samu Anti Aisha da qanwarta Yusra. Anti Aisha ta bi ta da kallo, ba ta tava ganin Nurat ba sai yau, amma jinta ta ke yi kamar wadda suka shekara da ita. Wani irin qaunarta ce ta xarsu a zuciyarta. Ta sauke ajiyar zuciya. “Kawai ki tafi da kayan, da ma ban tava saka su ba, tunani nake yi kamar sun yi min kaxan shi ya sa tuntuni na qi sakawa”. Yusra ta ce, “Wallahi kin yi kyau”. “Yanzu ki ci gaba da aikin, zan je na yi wanka, na san suna hanya kada su zo ban shirya ba. Oga ya yi min kashedin in yi kyau sosai, kada Ogansa ya raina shi”. “Wai Yaya Aisha waye wannan xin?” Yusra ta tambaya tana kallonta. ‘Shi xin na musamman ne. Takensa shi ne, in k sanshi shi ne, idan ba ka sanshi ba, to ba shi ba ne”. “Okey, to me hakan ke nufi?” “Ni kaina ban sani ba, a bakin Ogana nake jin wannan kirarin, na dai san mutum ne mai kirki. Da bazarsa muke rawa, ban tava ganin mutum irinsa ba, ya fi kowa kirki…” Ringin xin wayarta ne ya katse ta. Ta zaro ido. “Kada dai sun iso?” Jiki na rawa ta xaga wayar. “Da fatan kun gama shirya komai?” Deeni ya tambaya ta xaya vangaren. Ta ce, “Sauran qiris”. ‘Okey, shi ke nan. Mu ma ga mu nan mun nufo gidan, abu mafi muhimmnci ki bar su Yusra su qarasa aikin ki je ki yi wanka”. “An gama ranka ya daxe”. Da gudu ta fice ta nufi bathroom. “Tunda ki ka ga Yayata na wannan rawar qafar ba qaramin kuxi za ta shaqa ba, Deeni yana da son abin duniya, na tabbata ba qaramin samu yake a gindin wannan baqon ba. shi fa mijin Yaya idan ya raina ma qura ko kallo ba ka ishe shi ba. Yana da girman kai, ya fi mu’amala da manyan mutane…” “Kin ga Yusra ki bar wannan gulmar mu yi qoqarin gama aikin nan tukunna’. Sun gama komai, suna jidar kayan abincin zuwa dinning room, Aisha na can xaki tana shirya kanta, Nurat ta xauko jug na glass ta nufi dinning room. Ita kuma Yusra na moping xin kicin. Nurat ta duqufa tana shirya dinning table suka kutso kai. Sallama suka yi gaba xaya su ukun idanunsu a kanta, ba su tava ganin kyakkyawar halitta irinta ba. Zo ka ga kunya da tashin hankali, qam! Ta qame a gurin. “Subhanallahi! Ya Allah, na shiga uku, ta ya ya zan iya ficewa?” Ba ta iya amsa sallamarsu ba. Shi kam Deedat gabansa ne ya shiga bugawa. “Ba kya jin ana sallama?” Deeni ya faxa. “Amin”. Ta ce a taqaice. Da qyar ta ke xaga qafafunta ko gabanta ba ta gani saboda kunya. Juyawar da ta yi Salim da Deedat suka dubi juna. Da sauri ya voye kansa da wani irin sonta da ya shiga naso a dukkan sassan jikinsa. Ita xin ma duk da ba ta waye da ko su waye ba, ai hijabinta kawai ta xauka ta yi waje ba tare da ta yi sallama da su Yusra ba. Aisha ta fita daga xaki cikin qayatacciyar shigar da ta sanya ma Deeni nutsuwa. Bayan sun zazzauna, Deeni ya dube ta. ‘Waccan baquwar muka yi?” “Ni ma yau na fara ganinta, qawar Yusra ce. Yarinyar kirki ba ruwanta, komai nata abin burgewa ne”. ‘Yaya ban ga Nurat ba fa, ina ta shiga?” Yusra da ke qoqarin shigowa ta tambaya. “Ki duba”. Ta ce, “Ba ta nan, daga can nake”. “To ina ta yi?” In ji Aisha. “Shi ya sa ban so ta fio diining ba, ba ta son mutane. Ina zuwa”. Aisha ta ce. Xaki ta koma, inda ta tarar da kayan ta zube a kan gado ta dawo gurinsu. “Wallahi ko tafiya ta yi, hijabinta kurum ta xauka ko kayan nata ba ta canza ba”. Yusra ta yi murmushi, “Da alamar kacivus ku ka yi da ita cikin rashin sani kuma babu hijabi a jikinta ko?” Da sauri deeni ya kaxa kai. “Tab! Yaya ai ko ke da ganin Nurat Usman a gidanki za ki rina, ita xin wata iri ce, kunyarta ta yi mata yawa, ai wannan xin ustaziyya ce, ni fa na yi mamakin da ta amince ta sanya wannan riga da wandon, Nana ta ce min, ko a gidansu ba ta zama babu hijabi, idan ma ba a yi sa’a ba ko gidansu Nanan ba za ta koma ba, qarshenta ma tana can tana kuka”. “To ke ba ki san gidansu ba?” “Ina zan sani, ni da ba ‘yar gari ba? Ni ma yau darajar Nanar ba ta nan ne ya sa ta shigo gidanmu. Ni kuma na rakito ta nan”. Salim kam hankalinsa gaba xaya ya dawo kan Deedat, tsantsar sonta ya dinga hange a idanunsa. Tabbas wannan xin ce ta dace da rayuwar Deedat, ita ce macen da yake mafarkin mallaka. Da alamun an tada mishi mikin da ke kwance a zuciyarsa. Gaisuwar Aisha ce ta katse masa tunani. Hira suka shiga yi tsakaninsu ban da Deedat, ba su wani damu da hakan ba sanin cewar shi xin ba mai son magana ba ne. Tashin hankalinsu xaya, ya qi cin abinci sai lemo kawai da ya sha. Qarshe ma miqewa ya yi. Suka bi shi da kallo. “Sai ina?” Deeni ya tambaya. “Ku ba ni minti goma zan dawo”. Bai jira amsarsu ba ya yi waje. Duk inda yake tunanin zai ganta ya duba babu alamarta, dole ya koma gidan duk hankalinsa a tashe. Yana son zama da Yusra domin tambayar inda ta ke, to amman yana jin wani irin nauyi, ba zai iya tsayawa yana taxin budurwa da ita ba, yana jin hakan bai dace ba, ko ba ma haka ba, hakan ba girmansa ba ne. Sai bayan magriba suka bar gidan, inda Salim ya ajiye ma Aisha dubu xari biyu gen-gen, ya bai wa Yusra dubu hamsin. Farin ciki a gurinsu tamkar za su shixe. Bayan fitarsu Yusra ta dubi Aisha. “Kin ga Nurat ta yi ma kanta, da tuni ta samu kuxaxen nan”. “Amma dai ko ‘yar dubu goma kin ba ta?” “Tab! Wai ma, wa ya ce ta tafi? Ko sisi ba zan ba ta ba”. “Shi ke nan zan ba ki dubu goma ki ba ta”. “Wannan kam in ki ka ba ni zan ba ta”. Aisha ta kai mata duka. “Mara mutunci”. *** *** *** Ta rungume shi ta baya, “Daddy kana sona da yawa, ba ni da tamkarka. Ina yinka wallahi ka fidda ni kunyar qawayena, zan nuna musu taka kyautar’. Ya mirgino da ita gabansa yana murmushi. “Rangida zan iya yin komai domin farin cikinki. Ba ma haka na so ba”. “Dad taho mu je ku yi sallama da su, suna xaki”. Ta janyo hannunsa. Hajiya Rahma ta kawar da kai ba ta ma san suna yi ba, ita dai ko ba komai ta rabu da qaya. Nurat ce ta shigo, ta bi ta da kallo. “Ina kayanki?” “Ammi na yi kyau ko? Kwata na faxa shi ne na saka kayan qawata, maqociyarsu ce, ina Yayata?” “Tana can xaki ita da qawayenta’. “Okey, bari in je na ci abinci, yunwa nake ji”. Ta yi waje, ta bi ta da kallo. “Aazeen ina ma za ki zama kamar Nurat?” Ta kaxa kai kawai. Washegari da sassafe su Zee suka wuce, ranar Hajiya rahma ji ta yi kamar an sauke mata dutsen dala daga kanta. Alhaji Usman ne ya shigo sitroom yana faman cika da batsewa. Ta yi kamar ba ta ganshi ba, ya zauna xaya daga cikin kujerun. “Sun tafi hankalinki ya kwanta, ban ce zan auri xaya daga cikinsu ba. Da sun ci gaba da zama ina jin sai kin qone su. Ni ban tava jin uwar da ke kishi da yaranta ba, ita kanta Aazeen kishi ki ke da ita, ko wata kyautar na yi mata sai kin nuna damuwarki. Wallahi sam ba ki da tunani”. Ba ta so tanka mishi ba, sai dai a wannan gavar ba ta jin za ta iya yin shiru. “Ko a tarihi ban tava jin inda aka ce ga wata uwa can na baqin ciki da abin da uba ya yi ma xiyarta ba, ballantana Aazeen wadda nake jinta tamkar numfashina. Aazeen na fara samu a duniya, ina sonta fiye da komai, duk son da za ka yi mata ba za ka fi ni ba. Don haka nake kiyaye duk abin da zai rusa mata tarbiyya, idan za ka siyi duk abin da ke duniyar nan ka ba ta zan fi kowa farin ciki, amma ka dinga yin abin da addininmu ya halatta”. *💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞* *NA* *BILKISU H.MUHAMMAD* _(Matar Auwalu By fos zage)_ *last Free page 15* *_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_* *Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa* *1. IZZATU* *2. MULKIN MALLAKA* *3. KAUNA CE* *4. DACEWA* *5. RASHIN RABO* *6.TARAIRAYA* *7. JINI BIYU* *8. AKWAI BAMBANCI* *9. TSALAR KAUNA* *10. YA YI SAKE* *11. ILLAR SABO* *12. SO DA SANKARA* *13. RASHIN RABO* *14. WATA RAYUWA* *15. HUBBAN SHADIDAN* *16. BAKIN K'AZAFI* *17. MATSALAR KAUNA* *18. KYAN KUSKURE* *19. WA YAFI SONTA?* *20. GABA DA SO* _NOW_ *KYAUTA ZUCIYA* ```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah``` *_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_* *_2277439558 UBA Bank_* Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* *“T* unda dai su xin sun tafi komai ya wuce ko?” Ya faxa yana qoqarin matsawa jikinta. “Ki yi haquri, taso mu je ciki zan nuna miki wani abu”. Shi kanshi ya yi mamakin yadda yake faman kimtsa kansa kamar wani mace, wankan shadda ya yi gizna, ash colour, hularsa ma ash, hatta takalminsa ash ne, ya feshe jiki da turare ya fito sitroom cikin qoqarin gyara link xin hannun rigarsa. Maryam zaune tana kallon talabijin. “Wow, qaramin maigidan ka fa yi kyau, sai ina?” Ya yi murmushi, “Matar Yaya yau zan tunkari mutuniyar. Yau zan yi mata zuwa na musamman”. “Okey, kana son ka ce iyanzu ta san komai kenan?” “Ke dai kawai ki yi min addu’a, ki bari sai na dawo mun yi maganar”. Ya xauki key xin mota ya yi waje. Ta bi shi da kallo cikin tave baki. Da alamar Hajiya rahma ba ta nan, hakan ya yi masa daxi, kai tsaye ya doshi vangaren Nurat. Tana kwance a gado, bacci ta ke lakadan, iskan fanka na faman watsi da gashin kanta. Gabansa ne ya faxi, ya wani irin bugawa wani abu ya tsarga masa tun daga tsakiyar kai har zuwa yatsunsa. Duk yadda yake zana halittarta ta wuce nan, ashe dai bai ga komai ba? Wani irin sha’awarta ya dinga shigarsa, zuciyarsa ta dinga ingiza shi da ya afka mata. Ya yi tattaki zuwa gabanta, ya xan ranqwafa a kanta, wani qamshi ya shaqa nan ya qara fitinuwa. Hannu ya kai zai xauke gashin da ya zubo fuskarta, ya ga ta xan motsa. Tsam! Ya qame a tsaye, can ta qara nutsuwa cikin baccinta haka ya ba shi damar tattare gashinta yamaida shi baya. Ya xan matso da kansa daf da fuskarta zai sumbaci xan mininin bakinta. A karo na biyu ta sake motsawa, ya tuna idan ta farka ta ganshi akwai matsala. Da sauri ya fice daga xakin cike da tsananin so da sha’awarta, sai kuma ya jira ta a gurin Aazeen. A daidai wannan okacin ta fito daga bathroom, bai san sa’ar da ya afka mata ba. sun gama shagalta da juna, gaba xaya sun mance a inda suke, hankainsu ya fita a jikinsu, shi kam Zaruk ji yake yi kamar tare yake da Nurat, surarta ce ta dinga yi masa gizo. Daga vangaren Nurat firgigit ta farka, ta dinga ji a jikinta tamkar wani abu ya faru da ita. Ta miqe zaune, qamshin turaren Zaruk ta shaqa. Dam! Gabanta ya buga, da sauri ta dubi jikinta, riga ce a jikinta iya gwiwa mai xan siririn hannu. Ta miqe cikin sauri, hijabi ta xauko ta xora a kai ta shiga bathroom ta wanke baki. Al’adarta ce ko da baccin minti goma ta yi ba ta iya fuskantar kowa sai ta goge baki, ta xauraye fuska. Ficewa ta yi daga xakin, kai tsaye sashen Aazeen ta nufa, duk takun da ta yi yana daidai da bugun zuciyarta. Haka kawai ta dinga jin wani tsoro na ziyartar zuciyar tata. Daf da za ta kutsa kai ciki ta dinga jin wasu irin surutai marasa kan gado, ta xan yi turus! Abu ya qi qarewa kawai sai ta tura kai ciki da qarfi. Gabanta ya buga, kanta ya yi wani irin sarawa yana kuma juyawa, jikinta ya hau vari. Ta yi saurin runtse idanunta ta kasa aminta da abin da ke gabanta, me ya sanya ta yi irin wannan mafarkin? Me ke faruwa da ita? Idan bacci ta ke Ubangiji Ya gaggauta farkar da ita. Ta buxe idanunta, har yanzu suna nan, wayyo Allah ba mafarki ta ke yi ba, “Allahumma ajirni fi masibati…” Ta shiga maimaitawa cikin zuciyarta. Kunyar kanta ce ta kamata, ta juya cikin matsanancin kukan da ke son qwace mata, gudu-gudu, sauri-sauri ta nufi xakinta inda ta zube a qasa. Wani irin azababben kuka ya qace mata, wani irin tsanar Zaruk ta dinga xarsuwa a zuciyarta. Tana ji a ranta ba ta tava tsanar wata halitta kamarsa ba. Yaya Zaruk mutumin da ta ke matuqar ganin mutuncinsa wanda magana ba ta cika damunsa ba, idan yana magana wani lokacin tamkar wani limami. Ta runtse idanu, kuka ya sake qwace mata, ‘Babu kama Yaya Zaruk babu kama, waye ya san tsawon lokacin da suke aikata hakan?” Hirarsu da Fa’iza qawarta ta faxo mata, “In dai riqe hannu ne ashe da kowa ya samu ciki, da shegu sun cika duniya. Ke da Allah can tsokanarki Amminki ta ke yi, kawai tana tsoratar da ke ne kawai, ba kya ganin ‘yan Indiya har rungume juna suke yi da namiji, to su me ya sa ba su tava samun cikin ba? ‘Yan matan zamanin nan iyayen shan minti duk me ya sa ba su samun ciki?” Nurat ta ce, “ko ma me ye ni dole ne in kiyaye, mahaifiyata ce yadda uwa ta ke da girma zai iya yiwuwa idan aka riqe hannun nawa in iya samun ciki”. Ta dawo daga duniyar tunani, lokaci guda abin da ta gani ya dinga dawo mata. “Yayata kin ci amanar Ammina, Zaruk na tsane ka, ba zan yafe maka ba”. Taqarqarewa ta yi ta turar da shi, ya zube gefe yana faman ajiye numfashi. “Kai wai ka mance a inda muke ne, ba ka tsoron wani ya ganmu?” Da sauri ta janyo rigar ta saka. Ya dube ta da lumsassun idanunsa, “Aazeen, ina son Nurat, ki taimake ni kada in rasa ta”. Ta xaure fuska tamau. “Ba ka tava ganewa furta mata wani kalaman so zai iya nesanta mu da juna. Ka bari da zarar ta zana jarabawa sai ka yi duka xaya xauka”. ‘Ba zan iya ba, ba zan tava amincewa ba. wannan karon dole ne kowa ya sani. Na gaji, ina zuwa”. Ya ce da ita ya miqe. Ta bi shi kawai da kallo. Nurat ta gaji da kuka, idanun nan sun yi jawur har wani tasawa suka yi. Takun tahowa ta ji, ta yi saurin kifa kai cikin filo, ga mamakinta muryar Zaruk ta ji a kanta. ‘Nurat, tashi za ki yi, ina son za mu yi wata magana da ke. Na zo ne kawai don ke, na san kina jina’. Ji ta ke yi kamar ya watsa mata garwashi. Ya kaxa ya raya ko motsawa ta qi yi. Ya koma yi mata magiya tamkar dutse haka ta koma mishi, kamar zai yi kuka, tilas ya bar mata xakin, takaici bai sa ya bi ta kan Aazeen ba. *** *** *** “Sam-sam sonka ne ba ta yi, ta gane inda ka dosa shi ya sa ta xauki wannan matakin”. “Ba zai tava yiwuwa ba akwai alaqa mai qarfi tsakanina mahaifina da nata, in na ga dama sai dai kawai ta ga an xaura aure. To amma don in fita haqqinta ne ya sanya na shaida mata. Amma ita xin ma…” “Zaruk kenan, kada ka mance kamar yadda Dad ke qaunarka ita ma haka nata ke qaunarta. Ina ba ka shawara in ka ga ba ta ra’ayinka ka haqura ga mata nan da yawa?” “Matar Yaya idan na qyale ta mutuwa zan yi, ni kaina ban san yadda nake sonta ba, wallahi dole sai na aure ta duk bala’i sai na mallake ta”. “Uhum Zaruk kenan, shi kenan Allah ya ba ka sa’a, Ubangiji ya zava mana abin da ya fi alkhairi”. “Daga baya kenan, ni kam ko babu alkhairin zan aure ta, sai fa na auri Nurat. Shekara kusan goma ina gadinta, lokaci xaya na faxo? Ina! Allah ba zai xora mini wannan ba, ba zai tava xora min ba’. “Shi ke nan”. A can bedroom xinsa sambatu ya yi ta yi tamkar mahaukaci. Ya sha sigari babu adadi duk ba ta gamshe shi ba, ya buxe firij ya xauki kwalbar giyar da rabonshi da ya sha ya fi wata uku, tun lokacin da ya yi ma Dad xinshi alqawari, bai ma san akwai ragowa a firij xin ba sai da ya hange ta. Kafa kai ya yi bai sauke kwalbar ba sai da ya ga babu komai a ciki, ya kwanta rigingine, Nurat ce ke masa gizo. Ya miqe tsaye yana sanxa wai zai kamo ta. Haka ya yi ta yi, daga qarshe ya yi wani irin wawar faxuwa, har sai da ya faxa kan kwalbar ta fashe ta yi masa wata muguwar yanka a gefen fuska da qirji, jini ya valle. Daidai lokacin Alhaji Aminu ya turo qofa, duk warin giya ya cika xakin, ga xansa kwance cikin jini yana faman amai. A sukwane ya qarasa gare shi ya janyo shi kan cinya yana jijjiga shi. Sunan Nurat kawai yake faman kira, a ruxe ya kira likitansa a waya tare da yi mishi bayanin abin da ke faruwa. “Zaruk ashe qarya ka yi min, da man yaudara ta ka yi ka ce ka daina? Me ya sa?” Qoqarin qwacewa ya dinga yi daga jikinsa yana kiran sunan Nurat. Kuka Alhaji Aminu ya saka, yadda ya ga jini ya tsananta zuba. Likita ne ya turo qofa. Shi kanshi hankalinsa ya tashi. Ya dubi Alhaji Aminu, “Garin ya ya hakan ta faru?” “Ban sani ba, kawai na xai ji yana ta ambatar wata Nurat”. Likita ya sauke ajiyar zuciya. “Ko wacce tana da alaqa da shigarsa wannan yanayin”. Allura ya yi masa ya yi dressing xin raunikan, ya kuma xora masa da allurar bacci, kafin wani lokaci bacci mai qarfi ya yi awon gaba da shi”. Hajiya Amina da Maryam sun dawo daga gidan suna, suka riski mummunan labari. “Da na san abin da zai aikata ma kansa da ban barshi shi kaxai ba”. A nan ta kwashe labarin komai ta shaida musu. “Ban da abin Zaruk ya sani dole ma ya aure ta ko da ba ta so, da ita da Baban nata duk a hannun Alhajina suke shi ne fa qarfin arziqin ba ko wannan uwar girman kai ya ce yana so dole ne ta amince, balle ita Nurat baiwar Allah, yarinyar da babu sa wa ba fitarwa”. Yana zaune a tsakiyar gado ko a jikinsa halin da ya ganshi a ciki, ya sani hakan zai xaga ma Dad hankali, ba zai bari ya rasa Nurat ba, sigarinsa ma ya ke faman zuqa. Hajiya Amina da Alhaji Aminu suka shigo xakin daidai lokacin wutar sigarin ta cimma hannunsa. Da gudu Alhaji Aminu ya zare tabar a hannunsa ya cillar a qasa haxi da mitsike ta a qasa. Suka zauna a gefe, gaba xaya yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa, ya yi ramar wuni xaya. Ya raunana murya, “Haba Zaruk har kana da damuwar da ka ke tunanin ba zan iya magance maka ba? Maryam ta gaya min komai kai ma da gangan ka tada hankali, ka sani ni da Alhaji Usman mun zamo xaya babu abin da ba zai iya mallaka min ba”. “Daddy, Nurat ba za ta so ni ba, ta daina kula ni, ba zan iya rayuwa babu ita ba, ina tsananin sonta, da ita kaxai nake son rayuwa, ka taimaka kada ta guje mini”. “Ya isa haka, na ji za ka auri Nurat, amma sai in na ga ka raba kanka da waxannan mugayen xabi’un, domin babu uban da zai so ka zama surikinsa in har ba ka daina ba, zan fita a harkarka…” “Ban da ma abin Zaruk, ai ita xin taka ce, ko da ba ta so dole ma ta so ka, ka kwantar da hankalinka in ba haka ba za ka kashe rayuwarka a banza, kana ji kana gani wani nan zai aure ta”. “Mommy na yi muku alqawarin na daina har abada, ku yi haquri”. Suna zaune a falo dukkansu, kallon suke yi, hankalin Alhaji Usman ya karkata ga Nuratm ya fahimci kamar akwai abin da ke damunta. Kallon ta ke yi amma tunaninta na wani guri. “Nurat wai me yake damunki?” Ta tilasta wa kanta sakin murmushi, wato yaqe. “Dad me ka gani? Lafiya ta qalau”. “Tunda na dawo na ganta a haka, na tambaya ta ce kanta ne ke ciwo”. Hajiya rahma ta faxa. “Ai na sha magani, ya daina ciwo”. Aazeen ta xan dube ta, ta kawar da kai, don idan tana kallon program xin Ahmad ba ta son abin da zai katse ta, tana tunanin kamar za ta samu hasken inda za ta same shi. Wayar Alhaji Usman ta shiga ruri, ya xaga. ‘Subhanallahi, yaushe? Okey za mu shigo gobe, Allah ya ba shi lafiya”. Gaba xaya hankalinsu ya koma kansa. Ya ajiye wayar cikin dubansu. “Lafiya kuwa?” Hajiya Rahma ta tambaya. “Wai Zaruk ne ya yi hatsari”. Aazeen ta ji wani shook, “Daddy xazun fa ya bar gidan nan?” Ta iya yuwuwa ko a hanyar komawarsa ne ya gamu da tsautsayi”. Duk ta gigice. “Dad yana asibiti ne?” “A’a yana gida”. “Allah Sarki Zaruk”. Ta wutsiyar ido Nurat ke duban Aazeen, ji ta ke yi kamar ta shaqe ta, ta ja tsaki a zuciyarta, dole ta damu tunda abokin fasiqancinta ne. ‘Idan Allah ya kai mu gobe, sai ku je gaba xaya”. “Ni dai ba za ni ba, gobe wuni za mu yi a school”. “Qarya ki ke yi, ba ki isa ba, wallahi sai kin je, mara mutunci”. Yadda ta hayayyaqo mata ne ya sanya ta tsuke baki. *** *** *** Alhaji Usman ya nuna farin cikinsa sosai, “Ban da abinka Alhaji Aminu, kai fa me iya xaukar Nurat ne ka bada aurenta, ballantana yarona ne mai sonta”. “Eh na na sani, amma duk da haka ina son ka ji ra’ayin Nurat”. “Kada ka damu, ban da lalacewar zamani, auren fari iyaye ne ke sama wa ‘yarsu miji. In dai Nurat ce kada ya damu an gama, kawai bari zai yi ta qarasa karatu, lokacin ta qara tasawa, don ita xin har yanzu akwai quruciya a tattare da ita, shekara sha shida”. “Gaskiya ne”. Duk wannan hirar a ofis xin Alhaji Aminu ake yinta. ‘Yanzu ya jikin nasa?” “Da sauqi”. “Yanzu na barsu sun tafi duba shi dukkansu”. Sun zube a sitroom, ita kam Aazeen har ta isa xakin Zaruk, Hajiya Rahma suna gaisawa da Hajiya Amina da tambayar yadda mai jiki ya qara ji, hankalin Hajiya Amina na ga Nurat, tana mamakin me Zaruk zai yi da wannan tatsitsiyar yarinyar, ina ma a ce ta xan fi haka? Babu matar da ba za ta so Nurat ta zame mata suruka ba, duk xabi’unta abin so ne, kunya, biyayya, kawaici da ibada. Nan-nan ta dinga yi da ita, ta so su xan tattauna maganar da Hajiya Rahma sai dai ta ga alamar kamar ita xin ba ta san komai a kan zancen ba. “Ya aka yi na ganki ke xaya?” Cike da jimami ta ke dubansa. “Dukkanmu muka zo, to ina ki ka baro Nurat?” “Tana can sitroom”. Ya xan yi shiru, zuwa wani loakci ya koma ya numfasa, “Aazeen, na karaya, kamar Nurat ba za ta so ni ba”. Ta xan murmusa, “Ka daina shakka Zaruk, babu macen da za ta ganka ba ta yi fatan ta mallake ka ba”. “Ki gaya min me zan yi ta so ni?” Lakuce masa hanci ta yi. “Dube shi don Allah, duk qaramar yarinya ta gama rikita shi’. “Don ba ki san yadda nake ji ba ne”. “Ta ya za a yi na ji? Kai ma ka ne ka xora ma kanka,. Babbar soyayyata ita ce in gan ni da kuxi. Duk lokacin da na ga account xina ya soma qasa a nan za ka ga tashin hankalina”. “ba za ki gane ba, yanzu dai ya za a yi ki iya turo min ita?” “Korata ka ke son yi kenan ko? Shi kenan bari na turo maka ita”. Ta miqe ta yi waje. “Wai ke ba dubiya ki ka zo ba ne, kin wani kime a nan?” Ta xaure fuska, har kullum gani ta ke duk lokacin da suka kevance da Zaruk xin abin da ta gani shi ne suke yi. “Tare za mu shiga da Ammina”. “Tashi ki shiga, ga ni nan”. Ta miqe cike da damuwa, ko kaxan ba ta son ganin fuskarsa, kullum qara tsanarsa ta ke. Ta daxe tsaye a bakin qofar, sai da ta ji motsi kamar za a taho ta yi saurin ture qofar ta shiga haxe da sallama. Yana kwance dafe da gurin ciwonsa, a daidai wannan lokacin zogin ciwon ya addabe shi. Kasa qarasawa ta yi ta tsaya a xan nesa da shi, ko son kallonsa ba ta yi. Yunqurawa ya yi ya miqe zaune cikin dubanta. “Qanwata ga kujera ki zauna mana”. Ta yi yadda ya ce kanta a qasa. “Sannu, ina wuni? Ya jiki?” Duk ta faxa a lokaci xaya. “Sai ki ka ji mummunan labari ko?” Qala ba ta ce masa ba. “Yau babu makaranta? Ammi tana sitroom?” Haka ya yi ta soki burutsunsa ya qosa da yanayinta, ya kafe ta da ido. “Qanwata kin canza, gaya min me ya sa ki yin shiru?” Nan ma babu amsa, tilas ya tsuke baki cike da tunani barkatai. Ya zai yi ta fahimci yana sonta? Ya zai yi ta fahimci ita ce farin cikinsa? Zumbur ya ga ta miqe, kasa magana ya yi kawai ya bi ta da ido. Me ya sa ta daina sakin jiki da shi a daidai lokacin da ya fi buqatar haka? Me yake faruwa haka? “Ya Allah ka nuna mini hanyar da za ta fahimci ita kaxai nake so”. Ya ayyana a zuciyarsa. “Nurat tafiya za ki yi?” “Sallah zan yi”. Ba ta jira jin me zai sake cewa ba ta yi saurin ficewa. Bayan ta idar da sallah tana sani ta miqe a kan doguwar kujera da faxin kanta ne ke ciwo. Ba su bar gidan ba, sai bayan sallar magriba. *** *** *** Alhaji Usman ya shigo gidan cike da farin ciki. “Daddy ta samu kenan?” “Rangida ina cike da farin ciki, burina kullum zumuncinmu ya xore da Alhaji Aminu. Yanzu kam za mu zama xaya, don ko har zuri’a za mu haxa, kin ga kenan zai sake sakin jiki, babu maganar qyashi a tsakaninmu”. Hankalin Ammi ya tattara a kansa, tana son jin inda ya dosa. “Daddy ka vatar da ni, sam ban gane ba”. Ya numfasa, “Ina Nurat?” “Tunda muka dawo ta ke kwance”. Aazeen ta faxa. “To lafiya kuwa?” “Kanta ne ke ciwo, amma ta sha magani tun a gidan su Zaruk”. “Ok, to shi ke nan Allah ya sauwaqe”. “Dad ina jinka”. “Mutuminki Zaruk ashe duk wannan abin wai Nurat yake so?” Aazeen ta yi tsalle ta dire, har tana guxa. “Dad dole ka yi farin ciki”. “Allah dai ya sa Nurat ta amince da shi”. Ammi ta faxa tana kawar da kai. “Duk wani abu da na tsara a gidan nan ke ce ke rusawa, an gaya miki ina son jin ra’ayinta ne? to bari ki ji, ko tana so ko ba ta so Zaruk shi ne mijinta. Ni ne na haifi Nurat ba ita ta haife ni ba, ina da ikon ba ta duk wanda na yi ra’ayi kin gane?” Ya tashi ya shige sashensa ransa a matuqar vace. Duk jikinta ya yi sanyi, ta yi da ta sanin ba ta yi magana ba. “Ammi, Daddy yana da gaskiya fa. Ai ita Nurat ba ta da wani ra’ayi, kawai ki sanya masa ido, don ni ban ga aibun Yaya Zaruk ba, sai dai in ke xin ce ba kya son ta aure shi’. Ita ma ficewa ta yi ta barta zaune a gurin qiqam kamar an dasa ta. Tun daga farko har qarshe Nurat ta ji hirar tasu. Kifa kai ta yi a filo tana faman gursheqen kuka. A haka Ammi ta riske ta, zama ta yi a gefenta, ta ma rasa ta ina za ta fara. Ita kanta ba ta so hakan ba, ba wai don ba ta qaunar aurensu ba, sai dai tana ganin nawa Nurat xin ta ke da za a yi zancen aurar da ita yanzu? Ban da ma ta fara makaranta da wuri bai fi a ce tana J.S 3 ba. Hannu ta sa tana shafa bayanta. “Me ye na kuka Nurat? Fata za mu yi Allah ya sa haka ne ya fi alkhairi. Shi xin mutumin kirki ne, Yaya yake a gare ki”. Ta xago kai idanunta na tsiyayar da qwalla. “Ammi ki taimake ni, wallahi bana son auren nan. Ammi, Dad har ya gaji da ni ne da zai aurar da ni? Me ya sa ba za a yi wa Yaya Aazeen ba? ta fi ni girma, ta gama karatu. Ta fi ni cancanta, don Allah ki taimake ni ki fahimtar da shi”. Ta kai hannu tana share mata qwallan. “Shi ke nan, zan yi hakan. Amma sai na ga kin cire damuwa a ranki kin ji. Yanzu tashi ki je ki yi wanka ki ci abinci”. Ta miqe ta yi waje, Ammi ta bi ta da kallo, gaba xaya tausayinta ta ke ji. Babu kunya ya saka wa Abbansa rigimar ba zai iya jira zuwa wani lokaci ba. Alhaji Aminu mamakin Zaruk yake yi. “Ka shaida mini tun tana qanqanuwarta ka ke sonta, ka duba ka ga shekarun da ka xiba, don ka jira shekara xaya ai ba zai cutar da kai da komai ba…” “Abbana ba zan iya ba. ina sonta kamar raina, ba zan iya ba. Ji nake kamar zan mace, Dad ina son na yi rayuwa da ita kafin in mutu. Don Allah ka saka baki na sani muddin ka ce ba ka amince ta qarasa karatunta a gidansu ba zai amince. Abba kai ne fa komai nasa, da taimakonka yake samun komai’. Xaga masa hannu ya yi. “Kada in sake jin makamancin wannan zancen a bakinka”. “To Dad na ji, ba zan sake ba. amma ka duba, na amince ta qarasa karatun a gidana”. “Oh God, shin Zaruk ba ka san a gaban wa ka ke magana ba? ina kunyarka ta ke ne? ni ba zan yi musu dole ba, idan auren ka matsu da shi ka nemi wata cikin sati biyu zan aura maka ita. Amma ba za ka sanya ni in takura bayin Allah a kan son ranka ba”. Ya miqe a fusace ya yi waje. Zaruk ya miqe ya shiga sintiri, wani irin son Nurat na ratsa dukkan sassan jikinsa. Fuu! Ya yi waje da nufin ya koma gurin Abban nasa ya sanya masa kuka, qila ya gane abin da yake ji. Sai dai yana sa kai ya ji tashin motarsa, ya juya a zabure zai koma ciki suka yi arba da Ummansa. Kallonsa ta ke a tsorace. “Ciwon ne ya motsa?” “Umma, Abba ne, ba ya son farin cikina”. Kamo hannunshi ta yi, ba su zame ko’ina ba sai sitroom,. Ta zaunar da shi a kan kujera, ta soma magana cikin kafe shi da ido. “Tunda ka furta kana son Nurat, ba ta da miji sai kai. Me ya sa ba za ka kwantar da hankalinka ba?” “Oh Umma, me ya sa ba kwa ganewa? Nurat mace ce, kuma mai matuqar kyau. Tana da xabi’u masu kyau, a yanzu haka tana da masu sonta da yawa, wataran za su hure mata kunne, za ta juya min baya… Umma ta ma fara yanzu haka Nurat ta daina kula ni, ba ta son ganina. Ina ganin qiyayyata kwance a fuskarta…” “Ka ga Zaruk, kai ma ka riga ka sani aurenka da ita tilas ne, ko da tana so ko ba ta so. Na sani mahaifinka ya fi ka son wannan auren shi ya sa nake son ka nutsu”. “Zan yi haka, amman sai dai ta dawo gidan nan, inyaso ni sai na dinga kai ta makaranta”. “Haba Zaruk, ina ka tava ganin an yi haka? Gaskiya ba zai yiwu ba”. Ya miqe a fusace. “Umma, ke ma ba za ki fahimce ni ba ko? Shi ke nan”. Ya juya ya koma ciki. Aazeen tunda ake wannan abu ba ta xora ido a kan Nurat ba, kwana uku kenan ba ta zama a gida saboda binciken inda za ta samu Ahmad Deedat. Kuxi ta ke ta faman kashewa har da masu bincike a yanar gizo, wasu ma qarya suke yi mata da cewar sun sanshi don kawai su karvi kuxi. Duk kuxin kuma da ta ke kashewa ko a jikinta, kullum gani ta ke yi wataran za ta fanshe, ba ta fidda tsammanin cewar shi xin zai zamo nata ba. Yau qarfe huxu ta dawo gida, kai tsaye ta faxa bathroom ta yi wanka, riga da wando ta saka marasa nauyi, ta miqe a kan gado, ta janyo waya. Wasu rubutukan batsa ta ke karantawa, lokaci xaya ta ji kewar Zaruk, tunda ya qwallafa rikicin son Nurat ba shi da lokacinta, ita xin in ba shi ba ba ta tava ganewa, ya xora ta a kan salon da ba ta iya haqurcewa da shi, dole ne ta yi wani abu a kan lamarin nan ko don ya samu nutsuwa. Za ta je ta samu Nurat, za ta yi mata wayo. Ta shigo xakin, a bakin gado ta same ta a zaune tana ta fushi. Ta zo ta zauna a kusa da ita ta sa hannu ta kamo nata, ta kira sunanta. Ba ta amsa ba sai ma kawar da fuska da ta yi, ta soma magana. “Qanwata kin ba ni kunya, anya kuwa Nurat xina ce kuwa? Ni dai na san tawa Nurat xin mai biyayya ba ta tsallake abin da family xinta suka gindaya mata, amma yanzu duk ta sauya, me ya sa?” Ta saki hannun nata ta kamo havarta. “Gaya min ko akwai wani a cikin zuciyarki?” Da sauri Nurat ta kaxa kai, da ido taf qwalla. “Kullum kina yi min wa’azi ta ya ya mai dokar bacci zai vuge da gyangyaxi? Kin ga ke fa saukakkiya ce ga hadda a kanki, duk wasu littattafan addini suna kanki, kin kuma san hukuncin mutumin da bai bi iyayenshi ba, kin san irinku Allah ya fi kama ku da hujja”. Wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta, lallai wannan ‘yar rainin hankali ce. Ta faxa a ranta. “Ni bana sonsa. Ban tava sonsa ba”. Ta kai hannu fuskarta tana share mata qwalla. “Kin ga in dai wannan ne ta zo gidan sauqi. Ke da ma ba ki san me ye so ba? Babu kowa a zuciyarki, zai koya miki yadda za ki so shi kin ji”. Ta kama kumatunta ta ja. “Yauwa qanwata, small”. Maimakon murmushin sai ta rushe da wani sabon kukan, cikin shesshekar kuka, “Yaya Aazeen ai kin fi ni buqatar aure, amma ni me na yi wa Dad da yake son xauke ni a gidan nan? Ni ba zan iya ba”. “Ni ma ina son ki yi aure ba Dad kaxai ba Nurat, ina qaunarki, ina tsoro kada ki riski kanki a rayuwa irin wadda nake ciki. Yadda Ammi ta ba ki tarbiyya ina son ki xora duk inda ki ka shiga a yi alfahari da ke…” “Yaya shi xin ai ba na gari ba ne”. Ta katse ta da faxin haka. “Wa ya gaya miki?” Ta tambaya cikin faxuwar gaba. Shiru Nurat ta yi. “Ni kam ban ga aibunsa ba, Zaruk xan asali, ga shi mai kyau. Za ki yi alfahari da shi”. Zumbur ta miqe tsaye. “Da an yi magana ki ce kyau, shi kyau ba abu ne mai xorewa ba, ai ba a tava gama wa xan Adam halitta har sai ya koma ga Ubangijinsa. Halayyar Yaya Zaruk nan gaba zai iya tsintarsa a kowane yanayi, ina da yaqini Allah ba zai xora qaddarar aurensa ba domin an tsarkake kaina”. Ya dace a ce Aazeen ta gano inda Nurat ta dosa a maganganunta, sai dai ba ta gane komai ba. Miqewa ta yi. “Shi ke nan, ni ma idan ki ka amince da Zaruk zai auri wannan Adamun zan yi duk yadda ki ke so, me ki ka ce? Ba kin ce kin yi masa alqawari ba?” A hankali ta jinjina kai. “Zauna, kirawo min shi, ina son ya zo in ganshi”. Ta dube ta don gaskata abin da ta ke faxi. “Yayata da gaske ki ke yi?” “Mamaki zan ba ki. Zan yi komai don xorar da farin cikin qanwata”. Take suka shiga kiran layinsa, sai dai an yi rashin sa’a wayar tasa na kashe. Daxi ne ya kama Nurat, a tunaninta wayo za ta yi wa Aazeen, ta sani in ta ganshi za ta iya sonsa, yayin da ita ma Aazeen ke murmushin mugunta, tana jin cewar dabararta ta yi. Sun tsayar cewar duk lokacin da ya kunna wayarsa za su kira shi. Hankalin Alhaji Usman ya kai qololuwa gurin tashi a kan abin da Alhaji Aminu ya zo masa da shi a kan Nurat, ya sani rashin amincewarsa zai iya haifar da komai, yana tausayin Nurat, ya sani kawai son rai zai nuna, bai dace a ce ya aurar da ita nan kusa ba. Alhaji Aminu yana da kirki, ya taka rawar gani a rayuwarsa, shi ne ya koya mishi yadda zai dinga juya kuxi, shi ya fito da shi a idon duniya har aka sanshi. Alhaji Aminu ya fi qarfin komai a gurinsa, akwai kunya in har ya juya wa buqatarsa baya, ya yi masa halacci da yawa. Yanzu ne lokacin da ya kamata ya rama masa, don haka ya qudiri niyar kyautatawa Nurat ko don ya shawo kanta, don haka yau bai dawo gida ba sai da ya yi mata siyayyar kayan kwalliya, kayan sawa har da sabuwar waya. Lokacin da Hajiya Rahma ta shigo xakin, ya lura da yadda ta rame, tausayinta ya kama shi. Ya kai hannu ya janyo ta jikinsa, yana son Rahma tamkar ransa, in ban da fitina irin ta zamani mutumin da yake da kamar Rahma ya gama samun arziqin duniya, sautari in yana baqanta mata rai ya kan ji ya tsani kansa. Ta nuna mishi qololuwar so, ta rabu da komai da kowa saboda shi. Me ya sa shaixan ke hilatarsa haka? Sakin baki ta yi tana dubansa, ya xan numfasa, idanunsa a kanta. “Kin tsane ni ko?” Da sauri ta kaxa kai. “Me ya sa zan tsani mijina uban yarana?” Ya sauke ajiyar zuciya. “Na sani ban kyauta muku ba ke da Nurat, ni kaina na shiga tsaka mai wuya ne, babu abin da Alhaji Usman zai iya nema in hana shi, idan na juya mishi baya ma duniya za ta zage ni, danginsa za su yi mishi dariya. Kuma ni ban ga aibun shi Zaruk xin ba”. Idanunta fal qwalla. “Ai ni ban ce komai ba, Nurat ‘yarka ce, ka fi kowa iko da ita. Ina fatan Allah ya sa haka ne ya fi alheri”. Ya sake shiga jikinta yana zargin kansa da abubuwa da dama. “Yauwa Rahmar Allah, haka nake so. Yanzu ki turo min ita”. Ta miqe jiki a sanyaye, yadda ta samu suna hira da Aazeen har da dariya ya sanya ta xan ji sanyi a ranta. “Alhaji na kiranki”. Ta ce da ita. Tunda ta zauna yake ta rarrashi, amma zuciyar nan tamkar rodi, musamman da ta fahimci yadda yake qoqarin sai ya cusa mata son Zaruk ta qarfin tsiya. Ta yadda yake ta faman yabon Zaruk, yana kururuta dacen da ta yi, da faxin jaruntarsa, son mutanensa ga addini da taimakon marasa qarfi. Ya xora da cewar, “Ki fidda ni kunya, ban tava neman abu a gurinki ba Nurat, yau na zo da qoqon barata, kada ki zubar min da mutuncina, ki rufa min asiri”. Ba ta ji daxin yadda Dad ke roqonta ba, tamkar zai yi kuka. “Dad na amince, na yarda Dad. Ka daina roqona, kai mahaifina ne, za ka iya yin duk yadda ka so da ni. Zan aure shi ka bada aurena a duk lokacin da ka so, ba zan musa ba”. Daxi ya kama shi, ya sani an wuce gurin, ya gama sanin ‘yarsa kaifi xaya ce ba ta magana biyu, yadda ka san babbar mace. Yaqe ta ke yi yadda ta ga mahaifin nata na ta rawar jiki, yadda ya nuna farin cikinsa idanunta ke qoqarin zubda qwalla. Cikin dabara ta goge su ta sani zai iya tilasta mata ta aure shi, amma ba za a tilasta mata ta so shi ba. shi kenan ba ita babu wani farin ciki a duniyar nan? Ta katse tunaninta a daidai lokacin da ya nuna mata kayayyakin da ya siya mata. Ya xauko waya ya miqa mata, da cajinta full har ma an xora layi a kai. Yadda ya santa da son waya tun tana qaramarta, ya yi zaton za ta nuna farin ciki, karva kawai ta yi kamar ba ta so, haka ne ya tabbatar masa cewar ba ta son Zaruk. “Na saka miki lambata da ta Amminku, ki tashi ki je, Allah ya yi miki albarka”. Ta kwashi kayan ta yi waje. *** *** *** Rashin ganin Ummita a bakin get ya sanya gabanshi bugawa. Ba ta qin tsayawa tarbarsa, duk lokacin da zai dawo daga tafiya sai in har ya yi mata laifi ko da ba ta da lafiya yana ce mata ga shi nan ya kusa qarasowa ta ke cin dako a bakin get, duk ruwa duk sanyi, duk iska. Maigadi ya yi saurin buxe mishi murfin mota. ‘Sannu da dawowa yallavai”. “Yauwa Adamu, yau kuma lafiya ban ga Ummina ba?” “Lafiya qalau”. Mamai ya qara kama shi. “Adamu gaya min gaskiya”. “Da gaske nake Yallavai, yanzu haka daga cikin gida nake”. “Ok”. Ya ce. Buxe mishi but ya yi ya tafi ya barshi a gurin yana fara jidar kaya. Ko da ya isa ciki bai ga alamar an shirya zuwansa ba, savanin da da ya shigo zai dinga jin qamshin girkin tarbarsa, an cika teburi da kayan abinci kala-kala, yau ga shi wayam! Jikinsa ya yi sanyi, cikin rashin kuzari ya nufi xakinta. Tana zaune a kujerar roba, da asuwaki a hannu, fuskar nan a kirne. Ya zauna a sanyaye. “Ummita, yunwa nake ji, ban ga kin shirya min komai ba, bayan kin riga kin sani duk lokacin da zan dawo gida bana iya karyawa a ko’ina”. Ta ajiye asuwakin cikin sake xaure fuska. “Daga yanzu na daina, kuma kai nake jira yau zan bar gidan nan”. Bai san lokacin da ya dire gwiwoyinsa a gabanta ba, ya lura babu alamar wasa a maganarta. “Ummita me na yi? Gaya min, ba zan jure fushinki ba. Kada ki yi min haka”. “Da gaske nake yi, yau zan bar maka gida, ai ni ban san haka kuxi ke sanya izza ba, ban san haka kuxi ke sanyawa a daina girmama na gaba ba”. “Wayyo Ummita, ya isa haka. Yi sauri ki gaya min abin da ki ke so na yi, in gaggauta yi”. “Ka fi kowa sanin abin da nake so’. “Ummita a tunanina ina yin duk abin da ki ke so, ki ka umarce ni tun ina qarami. Kin tarbiyyantar da ni, kin nuna min yadda zan kyautata wa marasa qarfi, rayuwata gaba xaya ta tafi ne a taimakon miskinai. Na kan ajiye buqatata na yi tasu Ummita, arziqina gaba xaya ya zamo ba nawa ba, na gina asibitoci saboda talaka ya ji sauqi. Na gina makarantu saboda su. Na gina rayuwar mutane da dama duk domin su ma su ji cewar mutane ne, kin ce in voye kaina saboda kada yabon jama’a ya haifar min da girman kai duka na yi. Yanzu me ye ya rage? Me ye ban yi ba?” Ya qarasa maganar a raunane. “Duka ka zubar da ladarka. Auren Nabila shi ne ya fiye min dukkan komai, wallahi idan Nabila ta mutu ta sanadiyyarka iyayenta da ni ba za mu yafe maka ba”. A ruxe ya ce, “Tana ina? Me ke faruwa da ita?” “Tana asibiti babu yadda ta ke. Wallahi kai kam Babana ba ka da imani, me ye laifin Nabila?” Ya kamo hannunta ya riqe. “Ki yi haquri komai zai yi daidai, bari in je asibitin idan na dawo za mu yi magana”. “Ka ga na gaji da qarairayinka babu abin da zan ji daga gare ka, na gaya maka ba za ka same ni ba”. “No kada ki yi min haka, na yi miki alqawari za mu sasanta ki ba ni lokaci in dawo ko kuma in zauna mu gama magana sai in tafi”. “Shi ke nan, je ka zan jirayi dawowarka”. Receiption xin cike dangin Nabila ganinsa ya sanya kowa miqewa, don nuna girmamawa a gare shi. Haka ya dinga miqa hannu ga masu qoqarin durqusa masa. Wani abin takaici har da tsoffi, arziqi kan sanya rashin gane masoyin qwarai. Abdul babban yayanta yana nan zaune sai faman cika da batsewa yake, yana kallon Babansu na zungurinsa a kan ya je ya kwashi gaisuwa da kansa ya qarasa ya miqa masa hannu. Da qyar Abdul ya miqa nasa, nuna masa xakin da ta ke suka yi. Likitoci biyu tsaye a kanta, xaya na qoqarin xora mata drip. Ganinsa ya sa su ma suka gaggauwa abin da suke yi, bayan sun gaisa duka suka yi waje, da alamar ba ta ji shigowarsa ba, qamshin turarensa ta shaqa. Ba ta tava jin irin wannan qamshin a jikin kowa ba in ba shi ba. Tana qoqarin juyowa muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. Ji ta yi tamkar a mafarki, qoqarin miqewa ta yi. “No Nabila, ki bi a hankali, kin ga ba ki da lafiya, kin ji?” Wani irin daxi ya kama ta, ta dinga jin kamar ta rungume shi. “Yaya Deedat ka dawo?” Ya jinjina kai, tausayinta ya dinga shigarshi ganin yadda ta rame, idanunta sun faxa loko. “Qanwata me ke damunki haka?” Idanunta fal qwalla ta ji kamar ya yi mata fami. “Yaya Abdul ya ce na haqura da kai ba aurena za ka yi ba, ba ka sona, da gaske yake yi kai ka ce da shi ba ka sona?” “In ji wa ya ce miki bana sonki? Kin tava jin mutum ya qi qanwarsa?” “Yayana na gode, kuma ina sonka. Ban taba son wani abu kamarka ba. Ina matuqar sonka, yanzu ka dawo ne mu yi aure ko?” Ta tambaya cikin tsira mishi ido. “Yaya Deedat ba haka ba ne?” Ta faxa daidai lokacin da ta xora hannunta a kan nashi. “Kin ga ki bari ki qara samun sauqi sai mu yi maganar, kin ji?” “Ba zan warke ba, ba zan tava warkewa ba in har Allah zai nuna min ranar da za ka qi aurena gwara ya xauki raina, ba zan jure ganinka alhalin ba ka zamo nawa ba”. Cikin dabara ya zare hannunsa daga cikin nata. Ta sani qoqarin ficewa yake yi. Ta yi saurin zare drip xin da ke hannunta, sai ga jini. Ya yi gaggawar gutsuro auduga ya danne gurin jinin ba tare da ya xauke hannun nasa ba. Haka ya fi komai yi mata daxi, sai ta ji ina ma su dauwama a haka? Tsananin kallon da ta ke yi masa, har ya qufula ba ya son mace mara kunya. Duk macen da ke tsura wa namiji ido haka, yana yi mata kallon mara kamun kai. Lokaci xaya ya ji yana jin haushinta, daga vangarenta ji ta ke yi tana qara sonsa. Tana jin ya fi kowa idan ta tuno da shi ko da ba ya nan nishaxi ta ke ji. Ko kallonta ya yi sai tsigar jikinta ta tashi. “Yaya Deedat bana son wannan shirun, don Allah ka ce wani abu”. Ganin jinin hannunta ya tsagaita ya sanya shi xauke hannunsa. “Tafiya zan yi Nabila, zan dawo kin ji”. “Ba za ka tafi ba, ka gaya mini yaushe ne za a yi auren nan, ka ga kowa fushi yake yi da kai. Kowa haushinka ya ke ji, Ummita, Yaya Abdul, Ummata da kowa”. Ya yi saurin katse ta. “Ba zan tsallake lokacina ba, duk kun mance da cewar shi aure lokaci ne, da zarar Allah ya kawo lokacin komai sai ya zamo labari”. Kalamansa sun fusatata, ta dinga jin kamar ya gama raina mata hankali. Idanunta suka juya. “Da haka ka ke fakewa”. Cikin xaga murya ta dinga magana, ta ci gaba da faxin, “Komai sai ka ce Allah, ni na gaji! Na gaji da wannan qarairayin naka”. Yana son yin magana ta qi ba shi dama. ‘Ba zan saurare ka ba, komai ya zo qarshe, ka fita ka je, na haqura, inyaso in mutu’. Tausayinta ya sake mamaye zuciyarsa, yana cikin yanayin da ta ke ciki. Yadda yake ji ya ninka nata, inda zai iya da ya haqura da ita, sai dai halayyarta ya sanya shi yake qyamarta, ya so ya aure ta duk da cewar bai tava jin sonta ba, amma gurvataccen halinta ba su barshi ba. yana son ya yi aure, ya hayayyafa yana son yaransa su kasance a qarqashin uwa ta gari. Auren Nabila zai rusa masa dukkan mafarkinsa, yana da burin auren mace xaya, muddin ya auri Nabila yana da tabbacin tilas nan gaba sai ya sake aure. Zai auri Nabila ne alhalin ya auri wata, zai aure ta ne da sharaxin ba zai haihu da ita ba, abin da ya san ko a mafarki ba zai yiwu ba. TURQASHI! Mu je ga littafi na biyu don jin yadda wannan gumurun za ta kasance. Yanzu aka soma labarin ma. *_wanan shine karshan littafi na daya Kuma karshan free page duk Mai son cigaban shi zata iya tu tubata a Kan number da nabada da Kuma account din da suke sama karku manta kudin karatu 300 ce kacal_* Taku har kullum. Bilkisu H. Muhd.