[9/15, 2:47 PM] Asmau: ZUCIYAR MUTUM……. …….BIRNIN SA…… 2 Yau yana ofis ayyuka sun kacame masa, sakatariyarshi ta sanar da shi yana da baquwa. Ya dube ta ya ce, “kin ganni dai damn too busy...... ba zan iya ganin kowa ba, tana iya dawowa gobe idan ta matsu”. Ta fita ta shaidawa baquwa. Ta sake dawowa ta sanar da shi cewa, “Ta ce kwarai take son ganin ka a yau”. Ya yi mamaki don kuwa bai fiye yin baki mata ba. Ba tare da ya tambayi ko wace ce ba ya yi mata umarnin ta shigo da ita. Farida Alqasim, ta bayyana a ofishin, cikin kwalliyar ‘cotton lace’ fari sol mai ban sha’awa. Ta yane kanta da dan share-sharen gyale kalar adon leshin jikinta. Duk inda ake neman kyakkyawar mace choculate colour to Farida ta kai, har ta so ta wuce. Tana taku dai-dai cikin tsinin takalminta. Lumsassun idanunshi ya sanya mata har ta yiwa kanta matsuguni a kujerar da ke fuskantar shi. Dan siririn bakinta dauke da lallausar murmushi a sanda take zama. Ta ce, “Kana mamakin ganina ko?” Ya lumshe ido ya bude ya ce, “Dole in yi mamaki, ashe talaka na ganin ku?” Dariya ta yi, “Abdulhakim ke nan, long time!” Ya ce, “Farida-Farida-Farida! Ya ya a kai kika tuna dani?” Ta ce, “Mance mutum irinka ba abu ne mai sauki ba”. Hararar ta ya yi, amma sai ta dauka irin kallon da yake mata a baya ne. Sun dade suna kallon juna, kowanne da abin da yake tunawa. Shi yana tuna dacin soyayyarta daya dandana ya gode Allah. Ita kuma tana tuna lokuta mafi muhimmanci a gareta, wato lokacin tarayyarsu tun a jami’ar Nsukka. Ta tabbata mahaifinta ya cuceta, tunda gata nan tana ta bokon banda Alhazan birni har yanzu ba wani kwakkwaran mashinshini. Ko da yake ba mashinshinin ne babu ba, nagartacce na kwarai kamar Abdulhakim ne babu, duk sai Suger Daddies irin wadanda Babanta ke so ta aura kenan. Wanda shi ma a yanzu ya zo yana nadama. Ya so ya nemi Abdulhakim don ya ba shi hakuri inda ya ji daga majiya mai tushe cewa tun a lokacin ya yi aure da ‘yar aminin mahaifinsa. Haduwarshi da Farida ta faro ne a jami’ar Ahmadu Bello, suna karanta kwas daya. Sai dai yana gaba da ita da shekaru biyu. Ita kadai ce mace cikin masu yin wannan course din a ajinsu. Don haka Abdulhakim ya ga karfin halinta, kuma ta birge shi. Don yana son mutum mai karfin zuciya a karatu mai wahala . Sun fara gaisawa ne ta dalilin abokinshi Nura Sule, wanda ya kasance aboki ga yayan ita Farida Mohammed Alqasim. Cikin dan lokaci soyayyar junansu ta kamasu, musamman da ta fara neman shi da ya fahimtar da ita abubuwan da suka shige mata duhu. Ta gane Abdulhakim qwaro ne a kan fanninsa da ya yiwa sauran ‘yan ajinsu fintinkau saboda dinbin fasaha da basirar da Allah ya bashi. Lokacin da Abdulhakim ya kammala karatu, Farida tana shekararta ta uku, duk da haka basu rabu ba suna tare a waya kullum, sannan in ta zo week end gida Kaduna da yake ‘yan Kaduna ne yana zuwa har ta koma. Daga baya ne su Farida suka koma Abuja, lokacin da babanta ya samu hayewa kujerar Senator na Southern Kaduna. Har zuwa lokacin da Farida ta kare karatu, ta gabatarwa da iyayenta Abdulhakim a matsayin mijin da ta zaba. Budar bakin mahaifinta sai cewa ya yi, “Mene matsayin ubanshi?” Ta ce, “Alkali ne”. Ya ce, “Shi kuma yaron aikin me yake?” Ta ce, “Bai dade da samun aiki da ‘Julius Barger’ ba”. Senator Alqasim ya yi tsaki ya ce, “Kin gane ko Farida? Bana son ki da auren kananan mutane, ke kadai ce ‘ya mace cikin ‘ya’yana, ina sonki da auren da za ki huta ba in daure akuyar ta dawo tana ci min danga ba. Don haka ba zan karbi maganar wannan yaron ba, ki ci gaba da karatunki har Allah ya kawo miki daidai ke”. Farida ta rasa inda za ta sa kanta, don hakika tana son Abdulhakim dinta, shi din take so ba wai abin hannunshi ba. Ta yi kuka ta yi roqon duniya amma Sanata Alqasim ya ki. Don haka da aka kawo kayan auren Abdulhakim a take ya juyar dasu da abinsu, wanda kuma hakan ya fusata Alkali Khalil Ribadu, ya nemawa Abdulhakim aurena. Duk abubuwan da suka biyo baya kun ji su. Masoya kam Farida ta gansu kala-kala, sai dai duk ba irin wadanda take so ba. Sai zabin babanta wanda ita kuma ta ki yarda. Ta fara karatun masters a jami’ar Ahmadu Bello, a halin yanzu ta kammala sai rubutun project take. Mahaifin Farida shi da kanshi ya zauna ya yi tunani ya gane bai kyauta ba, ya yarda Farida ba za ta taba son kowa ba bayan Abdulhakim Ribadu. Rashin aurenta ya dame shi. Don auren da yayi mata da abokinsa bata dade ba ta kashe auren ta fito. Don haka ne ya soma neman inda zai ga Abdulhakim, a lokacin aka sanar da shi ba ya kasar yana Beirut kuma ya yi aure. Ya yi kiran Farida ya ce ya amince mata ta nemi Abdulhakim su sasanta in har ya amince zai aure ta, ko da a ta biyu ne ya amince. Farida ta rasa inda za ta sa kanta don farin ciki, gani take kamar har ta auri Abdulhakim ta gama, don ta san Abdulhakim din ba zai taba iya daina sonta ba, ko da kuwa a ce mata goma ya aura kuwa, balle mace daya. Don haka ne yau tayo tattaki har Lagos ta cimma shi a ofis. Abdulhakim ya canza, ya kara gigita ta. Ofishinsa kadai abin kallo ne, balle shi mamallakin ofishin, wanda ya yi wani irin lallausan kyau hade da murjewa tabbacin ilimi da naira sun zauna da gindinsu. Yana sanye da baqaqen ‘suit’ wadanda ya matse wuyansa da ruwan tokar tie mai santsi, kafafunshi cikin bakin rufaffen cover kirar Italy ya tara lallausar suma a kanshi. Idan ka yi mishi kallo daya ba za ka so ka dauke idonka ba. Haduwarshi ta kai inda kowacce lafiyayyar diya mace ke buri duk kyau, nasaba da iliminta. Har ta ji ta raina kanta. Da duk abinda take taqama da shi. Sai dai hakan ba ya nufin za ta kasa isar da saqon da ya taso da ita gari ya gari tun daga Abuja har Lagos. Da ganin shi ka ga daya daga cikin ‘yan gatan ma’aikatan ‘Julius Berger’ tsantsa. Wadanda ke daga gaba-gaba, ake kuma matukar ji da su. Ganin ta yi shiru tana tunani sai ya kawar da shirun ta hanyar cewa, “Ya ya Farida meye labari? Ya ya Mohammed? Kuma ya ya maigidanki?” Ta daga fararen idanunta ta kalle shi, amma ta kasa jurewa, sabida yadda gabadaya Abdulhakim din ya canza mata, da tsabar kwarjinin da yayi mata, babu wannan lallausar kallon da yake yi mata a da cikin fararen kwayan idanunsa. Gwiwoyinta suka yi sanyi, ta sunkuyar da kai idanunta cike da qwalla, ta samu kanta da yanka karya ba tare data shirya ba. “Ban yi aure ba”. Cikin mamaki ya dube ta amma sai ya boye mamakin nashi. Ta kara da cewa, “Mohammed ya yi aure yana N.N.P.C na nan Lagos, a hidansa na sauka, shi ma yana tambayarka, ya yi takaicin rashin aurenmu. A yau na zo ne Abdul musamman don in baka hakuri, in kuma isar da saqon Daddyna na cewa ya gane ya yi kuskure mu dawo da soyayyarmu, don tunda aka yi haka ban kara sauraren kowanne namiji ba. Ka yi hakuri Abdul, Daddy ya yi nadama ka yi hakuri mu yi aure......”. Sai hawaye sharr-sharr. Bai katseta ba har sai da ta gama. Sai dai zuciyarshi ta sosu da kukan da take yi, ba ya son ganin mace na kuka, musamman a dalilinsa. Ya ciri tissue guda uku ya mika mata, ya ce, “Share hawayen”. Ta karba tana sharewa. A ranshi yana fadin rashin aurena da ke Farida rahama ne a gareni, alheri ne mai dimbin yawa, don hakan ne ya yi sanadin da na samu matar Abdulhakim wanda har yau ban qosa da tarin kuruciyarta ba. Ya bude murya sosai ya ce, “Farida kina da labarin na yi aure?” Ta daga kai ba tare da ta hada ido da shi ba. Ya ce, “To kin shirya zama da talaka mai mata ne?” Furucin ya taba zuciyarta sosai, don haka ba ta ba shi amsa ba. Ya kura ma hoton matar Abdulhakim dake cikin wani dan kyakkyawan frame ido dake kan teburin shi, sai murmushi take cikin uniform dinta. Shi ma murmushin ya yi mata kamar tana kallon shi, rabon shi da ita yau kwanaki biyar, yana tunanin nan ba da jimawa ba zai canza akalar rayuwarsu zuwa irin ta kowadanne ma’aurata na hakika, don in bai manta ba Abbanta ya gaya mishi watan Aprilu mai kamawa Sakinah za ta cika shekaru goma sha biyar. Wanda shi ne target point dinsa na mika mata akalar rayuwar shi. To kuma sai ga Faridah, wadda har gobe akwai birbishin sonta a zuciyarshi, don tana burge shi saboda hazaqa da jarumtakarta a fannin karatu. Tana ba shi sha’awa don ta san kanta, ta san yadda za ta nuna mashi soyayya mai tsabta ba ta sakarci ba, wai don ta yi zurfin karatu. A kamile take, cike da aji da sanyin zuciya, yadda ya san ba zai sha wahalar lankwasa ta ba duk tarin ilmin ta. Ganin ta yi shiru ya sake cewa, “Ina da mata Farida. Shekaru biyu da rabi kenan da aurenmu. Na dauki al’amari na dake a qaddara ban kullaci kowa ba. I hold nothing against you dear....... balle kuma Babanki wanda ke da iko da damar zaba miki mijin da ya dace dake. Zan iya auren ki a matsayin mace ta biyu Farida, domin har gobe ina sonki. Sai dai bana jin iyayena za su kuma yin murna da maganar ki, domin mahaifina ranshi ya baci sosai. Don haka ki bani lokaci in yi tunani, ki yarda har gobe ban daina tuna ki ba, da lokutanmu na baya”. Ta yi ajiyar zuciya mai karfi irin ta samun salama a zuci, ruhi da gangar jiki. Ko da wannan ta tsira ta gode, ta yarda Abdulhakim bai manta da ita da soyayyarta ba. Ta ce, “Kamar kwanaki nawa zan baka? Don am eager in san matsayina”. Ya yi murmushi sosai yana tunanin yadda za su kwashe da Matar-Abdulhakim in ya ce zai kara aure, don ta sha fadi mishi ba ta so tunda kananan shekarunta, balle yanzu da ta fara mallakar hankalin kanta. Ya ce, “Ki bani kwanaki bakwai, insha Allahu za ki ji komai, in yin yin, in barin barin. Ki gai da Mohammed”. Suka yi musayar lambar waya ya rakota har inda ta adana motarta. Ya dade tsaye a wurin yana tunani, daga baya ya koma ofis. Ganin tunanin ya dame shi ya tattara komai ya yi gida. Don ya kasa hattama aikin. Tausayin Farida fal ranshi, ya kuma yarda da soyayyar da take yi mishi ne ta hanata aure har zuwa wannan lokacin. Ya yi wanka ya zuba shirt da wandon DKNY ya kwanta cikin resting dake falonshi, Kukun shi Alfa na shirya mishi abinci a tebir. Shi kuma yana ta ansa call a wayoyinshi. Ya yi kiran Abdallah ya ce, “Ko za ka iya zuwa nan Lagos muyi wata shawara?” Ya ce, “Gaskiya bani da sararin aiki, mu hadu dai next week a gida. In ce ko lafiya?” “Lafiya sai alheri, sai mun hadu dai”. Yana kashe wayar kirana na shigowa, ya kashe ya kirani da tashi wayar. “Ya ya aka yi matas?’ Murmushi na yi kamar yadda na tabbatar shi ma murmushin yake yi. “Za ka zo Friday?” “A’a, sai upper week”. Kamar na yi kuka, na ce, “Amma me ya sa Mijin-Sakinah?” “Common matas! Aiyuka ne sunyi yawa, ki yi hakuri, ki yi min uzuri kin ji babyna?” Na kyalkyale da dariya, “Nice ma babynka?” Ya ce, “Ke baby ce man kamar teddy, ko in siyo miki teddy ne? Jiya na gansu bula-bula a wani boutique”. Na ce, “Don Allah ina so”. Ya ce, “Na yi alqawari zan kawo teddy”. Ranar yau na dawo gida dauke da matsananciyar yunwa, abin haushi na samu Sabuwa ba ta nan ta barwa mai gadinmu Buzu sallahun wai ta je can gidanmu duba jikin Yaya Suwaiba. Na cillar da jakar na tube socks da sandal suma na yi wurgi dasu na fada kicin. Na bude firji duk lemukan sun kare, sai ruwa mai sanyi na daddaka. Na soma tunanin abin da zan dafa wanda ba zai dauki lokaci ba. Don haka na dauko Indomie guda biyu na soma soyawa tare da kwai. Ban ji takun mutum ba sai wani abu mai laushi na ji yana zungurina. A razane na juyo na yi arba da dindimemiyar ‘teddy bear pink’ mai shegen kyau. Na yi tsalle na rungume shi, shi ma ya makaleni muna kyalkyala dariya. Na ce, “Amma ka yi min bazata mijin sakina, kai da ka ce sai upper week?” Ya rausayar da kai yana ta kallona da wani irin sassanyan murmushi a fuskarsa, ya ce, “To ya zan yi? Tunanin Sakinata ya hanani aikin, dole in zo in ganta in ina son kwanciyar hankalina”. Dukkanmu bamu ankara ba, sai kauri muka ji yana tashi a gidan. Da gudu na yi kan girkina, na tadda Indomie na da kwai sun kone qurmus. Shi kansa frying-fan din ya yi bakikkirin. Kamar inyi kuka don haushi, sai kuwa ga kukan ya zo, amma ba mai sauti ba. Na kashe gass din na sauke ina share hawaye. Tsaye ya yi a bakin kofar ya ce, “Kukan na mene ne?” Na ce, “Bayan girkin da na sha wahala na yi ya kone?” Dariya ya yi, ya karaso ya kama hannuna ya rike cikin nasa. “Konewar girkin laifin wanene? Cewa nake laifi na ne? Sai yaushe za ki girma ne matar Abdulhakim? Ki daina yin abubuwa irin na su Nazir mana? Da abin da ya isa, da wanda bai isa ba ki dinga zubar min da tears dina”. Ya fada yana share min hawayen da hankicinsa. “Kada ki yi fushi, ki dafa wani, nima ki dafa dani ina jin yunwa”. Na ce, “To”. Cikin minti ashirin na kammala muka zauna a tsakiyar falo ba bisa tebir ba, ya nado taliyar a fork (cokali mai yatsu) ya ce, “Bude bakin”. Na bude ya saka mini na cinye, ya sake kawo min wata lomar na karba, sai nima na debo da nawa cokalin na ba shi. Yana murmushi ya amsa. Haka muka ci abincin har muka qoshi. Na kwashe kayan na kai kicin. Ya yi kwance cikin doguwar leather da suka yiwa dakin kawanya ya ce, “ Bani labari me da me ya faru in my absence this week?” Na ce, “Abubuwa da yawa, munje ‘quizz’ Queen Amina College Kaduna da motar makaranta, kuma school dinmu ne ta dau kofin”. Ya ce, “Weldone! A kan me aka yi quizz din?” Na ce, “Wadanne abubuwa ne idan anyi eradicating dinsu (kau da su) Nigeria za ta samu ci gaba tsakanin rashin adalcin shuwagabannin mu da hauhawar farashin man fetur?” Ya gyara kishingidarsa sosai yana dubana, “To ku wanne bangare kuka kare?” Na ce, “Muna bayan hauhawar farashin man fetur”. Ya kalle ni sosai ya ce, “Ni kuwa sai na ga adalcin shuwagabannin mu garemu ya fi komai, tunda ba sai ana cikin kwanciyar hankali za a sayi man fetur din ba?” Na yi murmushi na ce, “Haka ne. Sai dai ka san quiz ba ‘reality’ ke ba da makin ba, a’ah, hujjoji kwarara da points din da ka kawo sune”. Ya sunkuyo gabana yace, “….Give me a kiss Sakinah….!”. Na rufe fuska ina murmushi, na kuma zura daki da gudu. Ya biyoni dakin ya ga ina zaro lokas da alama neman wani abu nake. Ya ce, “Me kike nema?” Na ce, “Report card dina”. Na ciro na mika mishi. Ya karba ya duba ya bude min hannunshi, da sassarfa na tafi, sai kuma na kara da gudu-gudu na shige, ya mayar ya rungume yana shafa kwantaccen gashin kaina yana lumshe idanu. Ya ce, “Sakinah har tsaho kin kara......” Jin sautin shi da yanayin jikinshi ya sauya sai na yi kokarin zamewa amma na kasa, ya soma kissing dina passionately. Ji na yi nima numfashina yau yana canzawa, yanayin jikina shima na sauyawa, numfashina ya soma fita da sauri da sauri. Zan janye, ya ce, “A’a, Sakinah….. kada ki yimin hakan……?’ Dole na yi hakuri ya cigaba da abin da yake yi. Ganin muna shirin shiga wani ‘limit’ ya janye jikinsa da karfi ya jingina da kofa yana regaining consciousness. Gaba daya a firgice nake, don hakika na tsorata da al’amuran Mijin-Sakinah a yau. Na dauka cinye ni zai yi yadda yake bina da sumba ta ko’ina tamkar namijin Zakin da yunwa ta koro. Saida ya samu nutsuwa ya ce (cikin wata irin lallausar murya), “Ki yi hakuri, ban sani bane Sakina.... kwanta a gadonki, ki huta, ba zan yi abin da baki so ba, kin yi hakurin?” Na daga kai. “To kwanta ki huta”. “Ai lokacin barci bai yi ba”. “To zo ki yi min tausa?” Na ce, “To”. Ya ce, “To bari in yi wanka in zo”. Kafin ya fito wankan na fiddo mishi riga da wandon barci masu laushi, na feshe su da turaren ‘dior’ (Mid-Night Poison). Ya fito daure da tawul iya kugunshi, na yi saurin kawar da kaina, sakamakon ganin wasu nannadaddun muscles da kwantaccen bakin gashi a kan kirjinshi. Kwarjininshi da zatinshi ya cika dakin. Na daga kai ina duban Abdulhakim, ina kallon kyautar da Allah ya bani, wani irin abu na tsirgawa yau a zuciyata da gangar jiki na wanda ban taba ji ba. Tsigar jikina na tashi. Ya yi saurin sanya kayanshi yana cewa, “Wannan kallo haka Sakinah?’ Kunya ta kamani, na fice dakin da gudu. Na kwaso manyan teddyn da ya kawo min na yi dakina dasu, na jajjerasu a kan gadona ina ta murmushi. Shigowa ya yi ya tsaya a kanmu ni da teddyn, ya ce, “Baki ce kin gode ba”. Cike da kunya na ce, “Ai kaima ka san na gode”. Ya ce, “A’a, ni ban san kin gode ba, tunda baki bude baki kin gaya min ba ya ya za ai in sani? Tunda kuwa ni ba Allahn musuru bane?” Na ce, “To godiya nake Mijin-Sakinah”. Ya ce, “To, shirya fita zamu yi”. Na ce, “Zuwa ina?” Ya ce, “Saloon, bana son ganin wannan gashin a cukurkude himili guda, na fi so in ganshi a kwance yana qyalli kamar na Larabawa”. Na yi dariya na ce, “To fita in shirya”. Ya ce, “Na fita, kada a ce na yi iskanci”. Na kyalkyale da dariya, “Allah na tuba ba zan kara fadi ba”. Ya ce, “Ki ma kara din mana, in gayawa Abba da Hajiya”. Na hangame baki nace “yanzu Allah sai ka gaya musu?” Yace “in kina haufi ki sake fada ki gani”. Wani saloon ne mai kyau ya kaini na mutanen Lebanon, aka wanke min kan ya sha gyara, fuskata ta fito sumul ta yi kyau sosai. Na ji wata iska mai dadi na ratsa kaina, tabbas ba abin da ya kai gyara dadi. Daga nan cikin wani boutique muka shiga ya ce in dauki duk abin da nake so. Kada in damu da yawan kudin dake jiki. Na debi English wears masu kyau da kayan shafa na ‘MAKARI’ da turaruka uku muka fito bayan mun biya. Maimakon mu tafi gida sai na ga ya canza hanya ya dauki kwanar gidanmu. Murna ta kama ni sai dariya nake. Mami ba ta nan taje ta’aziyyar Baffanta a Bidda. Gidan daga Abba sai Yaya Suwaiba, ta shiga hidima damu kamar ta goyamu, sannan ta yi mana iso falon Abba. Fuskar Abbana kadai ka kalla za ka gane tsantsar farin cikin da yake ciki da ganinmu. Na kwaso turarukan da na siya na bashi. Ya yi ta godiya. Yaya Suwaiba ma na ba ta turmin super ita da Mami, na kuma yi mata ya jiki don Sabuwa ta gaya min ba ta da lafiya. Muka kebe ni da Abba bayan fitar Mijin-Sakinah. Ya dube ni da kallon kauna irin ta mahaifi ya ce, “Babu matsala Sakinah?” Na ce, “Babu Abba”. Na yi shiru ina tauna maganar da nake so in yi mishi. Ya lura ina son yin magana amma na yi shiru. Ya ce, “Kika ce mun babu matsala, gata kuma a fuskarki kin kasa furtawa”. Na ce, “Abba har yanzu baka samu adireshin Maman nawa ba?” Ya dan yi shiru sannan ya ce, “Shekaran jiya na dawo daga Qatar na kuma samu labarin suna cikin garin, amma ban samu adires din gidansu ba. Ina nan ina bincike kada ki damu insha Allah za ki rungumi mahaifiyarki kamar kowa ba da jimawa ba”. Na wani irin lumshe ido wani farin ciki na ratsa dukkan kofofin jiki na. Ya kawo kudi masu dama ya bani. Abdulhakim kuma ya sauke sayayyar da ya yi musu na dankali da doya mai yawa.Muka nufo gida, zuciyata cike da kaunar Abbana mai sona da son farin cikina. [9/15, 2:47 PM] Asmau: WashegariAbdulhakim ya yi shirin komawa Lagos, amma ya ce min zai biya ta Kaduna wajen Abdallah. Gidan ya rage daga ni sai Sabuwa, sai dai Hajiya tana shigowa jefi-jefi don ta ji ko muna bukatar wani abu. Abdulhakim Ribadu a ofishin Abdallah Ribadu, dake cikin kamfanin tauraron dan adam na DSTV suna shan coffee. Abdallah ya ce, “Satin ne ba za ka iya bari ya zagayo ba sai ka biyoni?” Ya ce, “Ya ya zan yi Abdallah? Aure nake so na kara”. Abdallah ya tsura mishi ido ya ce, “Aure? Wane irin aure kuma dan uwa?” Ya rausayar da kai ya ce, “Da Farida!”. Abdallah ya yi shiru kamar ruwa ya cinye shi, kafin daga bisani ya ce, “Ita Sakinah har yanzu baka son ta?” Da sauri ya girgiza kai, “Ita ce wadda nake so kuwa”. Ya ce, “To mai zai sa ka raba hankalinka? Ga mata ta kwarai Allah ya baka, ka bar ganinta yarinya karama, nan da shekaru uku za ka sha mamakin ta. Ita Faridar ba ta yi aure ba har yanzu?” Ya ce, “Ba ta yi ba”. Ya ce, “Me ya hanata?” Ya ce, “Soyayyar da ke cikin zuciyarta”. Abdallah ya ce, “Ni dai in za ka bi shawarata ka hakura da Sakinar da Allah ya baka, duk abubuwan da ake nema a lafiyayyar mace Allah ya halittata dasu polygamy bai dace da kai ba, musamman kai da ba mazauni ba”. Ya ce, “Abdallah akwai matsala ne Abdallah, Sakinah yarinya ce har yanzu, ina da bukatar aure na sosai, ban so ka ji ba, amma har yau rainon Sakinah kawai nakeyi ba zan iya dora mata lalurata yanzu ba”. Da mamaki Abdallah ya dube shi, “Kana nufin har zuwa wannan lokacin haka kuke zaune?” Ya ce, “Kusan haka, she is too young Abdallah. Ina jin tausayinta. Ko jinin haila ba ta fara ba har yau, ina tsoron kada ta yi ciki ta zo haihuwa ta samu matsala”. Abdallah ya yi shiru yana tunani, can ya ce, “Tunda ba ta fara haila ba ai ba yadda za a yi ta yi ciki”. Ya ce, “A’a, Abdallah kashin kugunta bai yi kwari ba, ina tsoron abin da ka-je-ya-zo”. Abdallah ya dade yana tunani sosai ya ce, “Hakan ma tserar da kai ne daga zina. Ina bayanka. Amma ka ji tsoron Allah ka rike amanar Sakinah, don mutum ce har mutum duk da kananan shekarunta”. Ya ce, “Kada ka ji komai akan Sakinah na yarda da kaina na yarda da soyayyar da nake yi mata. Ni yanzu fargabata yadda zan bullo ma Daddy da Hajiya su karbi zancen ne”. Abdallah ya ce, “Da wannan ma, amma mu fara da addu’a kafin mu tunkare su. Nima na daidaita da Safina yayar Sakinah, ka ga sai a hada lokaci daya. Yanzu abin da za a yi, mu durfafi addu’a tsayin sati daya kai ma kuma ka yi Istikhara kafin lokacin, idan ka ji ranka ya kwanta da auren, to akwai alheri a ciki, idan babu za ka ji baka so. Mu hadu a gida next week din”. Da wannan Abdulhakim ya wuce Lagos, ya kuma kashe wayoyinsa don kada Farida ta kira shi gabanin kammala addu’arshi. Addu’a ya ke sosai dare da rana ya amince ma zuciyarshi auren Farida. Tun can yana son Farida, sai dai ba irin wanda yake yiwa Sakinah a halin yanzu ba. Son Sakinah har cikin kashi da bargo yake, sabanin son Farida wanda iyakacinsa zuciya. Zullumin shi daya yadda zai tunkari Daddy da Hajiya, amma wani bangaren na zuciyarshi na ba shi karfin gwiwa na baza su ki ya raya sunnar ma’aiki ba. Ranar juma’a ya iso Abuja bayan sallar magariba, Abdallah ya riga shi isowa. Daddy ya jasu suka bishi jam’i a masallaci. Bayan sun dawo sallah tare suka ci abinci a falo a dining din Hajiya Laila. Da suka kammala Abdallah ya dubi Daddy yana murmushi. Ya ce, “Ya ya aka yi ne Abdallah? Na ga bakinka yana motsi. Ya ya zancen Safinar kun daidaita in ce ko?’ Ya ce, “Babu matsala Daddy ta karbe ni hannu bibbiyu. Sai dai muna so a hada ne”. Ya ce, “Me za a hada?” Ya sunkuyar da kai, shi ma Abdulhakim kan ya sunkuyar. Daddy ya ce, “Tambayarku nake me za a hada kun yi min shiru?’ Abdallah ya yi ta maza ya ce, “Dama zancen Farida ne Daddy, yarinyar da Abdulhakim ya so a baya. To iyayenta sun gane kurensu har ita Farida ta samu Abdulhakim sun sasanta........”. Hajiya Laila ta katse shi gabannin idasa babatunsa, “Kai Abdallah fita idona, bana son zancen banza, bayan an gama wulaqanta shi din ‘yar tasu ta yi kwantai shi ne zai koma mata don rashin zuciya? Tukunna Sakinah nawa take da za a yi mata kishiya? Ko ubansa bai yi mata biyu ba sai shi?” Daddy ya yi murmushi ya ce, “Ai ina so hanani kika yi. Na kuma tabbatar Sakinah ba za ta hana mijinta raya sunnar ma’aiki ba kamar yadda kika hanani. Ai ya fiki sanin da zaman Sakinar, in dai zai yi adalci a tsakaninsu shi ne abin bukata. A da kam na dauki zafi da al’amarin, amma yanzu na sauke don ba a shisshigi cikin al’amarin Ubangiji. Don haka kuje ku ci gaba da shirye-shiryen ku mun amince, Allah ya sa hakan ya zamo alheri a gareka. Sai dai ina nanata maka zan juri komai amma ban da wulaqanta Sakinah, domin ita din amana ce a hannuna, kar a danne mata hakki don anga tana da karancin shekaru. Ku tashi kuje, Allah ya yi muku albarka da kuka zabi raya sunnar ma’aiki ba zinace-zinacen zamani ba”. Hajiya tana so ta yi magana Daddy ya daga mata hannu, “Idan ba za ki sanya albarka ba, to ki yi shiru. Ba a jayayya a sha’anin aure, ba ki san rabon dake cikinshi ba, sai ki mutu kuma a zo ayi a zo ana cewa da kina nan da ba za a yi ba”. Ta mai da bakinta ta yi shiru, amma ranta ya yi mummunan baci, amma ta hadiye bacin ranta. Tunda Daddy ya ruga ya daddaure ta da jijiyoyin jikinta. **** Na baje litattafaina a falo ina ta ayyukan makaranta (assignment), Sabuwa na gefe tana kallon talabijin. Sanye nake da doguwar riga kirar Dammam, na tattare tulin gashin kaina na nade a tsakiyar kaina cikin ‘bound’ lokacin da Mijin-Sakina ya shigo. Bakina bude ina murmushi from ear to ear, ya ce, “Rufe bakin kada sauro ya fada”. Na kyalkyale da dariya na ce, “Don Allah da gaske sauro yana fadawa bakin mutane?” Ya ce, “Quda ma yana fadawa ba sauro ba, idan an hangame bakin kamar yadda kika hangame din nan”. Ya isa ga dining yana bubbudewa, qamshin mushroom ya doki hancinsa yana murmushi, ya ce, “Hmm! Duk wannan delicious ni kadai?” Na ce, “Sai ka kira Abdallah ya taya ka”. Ya ce, “Ke rabu da shi, zuwa zai yi yasa ni gaba da surutu na rasa inda yake koyon surutu”. Na ce, “Don Allah ka kira shi, hira zamu yi”. Ya fiddo wayarshi ya kira Abdallah, cikin mintuna biyar ya iso. Sabuwa tuni ta yi dakinta tun shigowar Mijin-Sakinah. Yana shigowa ya sa dariya ganin yadda na baje litattafai a kasa, ya ce, “Uwargidan Abdulhakim kuma kanwata, Safina na gaishe ki”. Cikin mamaki na ce, “A ina ka san Yaya Safinar?” Ya ce, “Rannan da ta zo miki hira na ganta gidannan lokacin Abdulhakim yana Beirut, yanzu zancen da nake miki tuni mun daidaita har su Daddy sun sani”. Mamaki ya isheni, na ce, “Can gidanmu ka bita?’ Dariya ya sake yi, ya ce, “Ya ya ba zan bita ba? Rai ya ga abin da yake so sai ya bari ya kubce masa a banza?” Na girgiza kai na ce, “To ina labarin Safiyyah?” Ya ce, “Ita fa ni ke son ta amma ba ita ba, kanwar abokina ce amma ba halinsu daya ba. Ya kuma gaya min kwanan nan anyi mata baiko, don haka na hakura da Safiyyah na koma Safinah. Sai ki tayamu da addu’a”. Na ce, “Allah shi tabbatar da alheri”. Ya isa ga dining shi ma yana budewa, ya ce, “Gaskiya kina shagwaba Abdulhakim da yawa Sakinah”. Mu duka muka murmusa. Mijin-Sakinah ya ce, “Ai na gaya miki surutun zai zo ya cika mu da shi kika ce in kira shi”. Bayan sun gama suka nufi masallaci tare, ni da Sabuwa muka gyara komai. Tana kicin tana wanke-wanke ina ci gaba da assignment dina. Can na tuna Yaya Safinah ta ce kullum Abdulhakim ya zo in sake wanka in yi kwalliya ko da ban dade da yin wankan ba. Na tattara komai na mayar jakata na nufi shower na yi wanka sosai da bath foam din ‘FA’ na wanke gashina da pert-plus, na dauro tawul na fito na jona dryer ina busar da gashina. Ya turo kofar ya shigo cikin ruwan tokar (pjs) ya zuba hannuwanshi a baya ya jingina da kofar yana kallona da fararen idanunshi da suka yi kasa sosai. Kafin in yi wani reaction dani da dirayar ya hada ya rungume mu, runguma mai karfi kamar zai balla ni. Bansan lokacin da na wancakalar da dryer din ba nace “zaka karya ni mijin Sakeenah”, ya rufe bakina da nashi ya soma kissing cikin wani irin salo mai dimautarwa, daga can kasan maqoshinsa yake Magana. “.......Yarinyar nan kina so ki hallaka ni …”. Kararrawar da ake ta dannawa ne ta qwace ni a hannun Abdulhakim, don Sabuwa ba ta nan ta shiga kai wa Hajiya abinci.Ya dade kafin ya saita kansa. Yana tausayina, amma ya tabbata yana qwarar kansa, don duk wasu surori na danyar budurwa awannan lokacin sun gama bayyana a tareda ni, duk da haka ya zabi ya ci gaba da tausayin nawa, shi yayi ta kwarar kansa. Na budewa Sabuwa kofa ta shigo, ta ce, “Na dade ko?” Hajiya ce ta tsare ni da hira”. Ban ce mata komai ba don a firgice nake da al’amarin Mijin-Sakinah, iyakar tsorata na tsorata dashi yau, don haka ban koma dakin ba. Sabuwa na bi dakinta tana ta yi min hirar wai Yaya Suwaiba ciki gareta. Na kwanta a kafitarta tun tana hirar ita kadai har ta gaji ta yi shiru. An gama labaran tara ta ga bani da niyyar tashi. Ta ce, “Kinga tashi ki tafi kin baro maigidan shi kadai ke sai yaushe za ki yi wayo ne?” Kamar zan yi kuka na ce, “Ni wallahi a nan zan kwana”. Ta kama baki ta ce, “Saboda mene?” Na yi shiru. Abinki da babba tuni ta je gano. Sai ta yi murmushi ta tausasa murya ta ce, “Ban da abinki Sakinah, yanzu mata duk kankantarsu sun daina gudun mijinsu, kanana ma na qauye basa gudun miji balle ke ‘yar birni da wayonki. Ba ki san lada mai yawa ake samu ba?” Na ce, “Lada kuma?” Ta ce, “Eh, lada mai yawa har da ‘ya’ya, ba kya son ki haifi Da mai kyau kamarki kina goyawa kina cillashi kina cafewa?” Na kyalkyale da dariya na ce, “Wallahi ina so Sabuwa”. Ta ce, “In haka ne maza tashi ki koma wajen mijinki, duk abin da ya saki kiyi, kada kiyi musu kada ki ji tsoro. Wuyar ba ta kisa, da tana kisa da bamu kawo yau ba, kin ganmu nan mun ci dubu sai ceto, haihuwa goma kuma gani da raina da lafiyata har mai rabawa ta raba”. Na ce, “Mijinki ya rasu ne?” Nan da nan idanunta suka kawo ruwa, ta ce, “Yau shekarar Malam Salihu biyar a karkashin kasa, yarinya tashi ki je ki rungume mijinki ku ci lokacinku, ku moribund kuruciyarku in yau mune gobe ba mu bane. Wannan shi ne auren, in baki sani ba in gaya miki. In har ba kina so mijinki ya rage sonki bane, in bai zo wajenki ba wajen wa zai je? Ko kina so ya fada cikin mummunar hanya?” Na ce, “Wace irin mummunar hanya kuma Sabuwa?” Ta ce, “Neman mata mana”. Na ce, “Su da ba matansa ba sai ya je yana neman su, to suje ina?” Haushi ya kama Sabuwa, ta ce, “Yanzu kina nufin baki san me ake nufi da neman mata ba?” Na ce, “Na gane yanzu”. Ta ce, “To tashi muje in rakaki tun Abdulhakim bai yi fushi dani ba”. Har kofar dakina ta rakoni, sannan ta juya. Na murda kofar dakina ba ya ciki, na nufi nashi dakin. Yana kwance tsakiyar makeken gadonshi da ‘yar redio a hannunshi yana sauraron labaran B.B.C. Bai yi min magana ba har na zauna daidai kafafunshi, bai aje rediyonsa ba. Na ce, “Sabuwa ta ce in zo mu samo baby”. Bai san sanda dariya ta kubuce masa ba, ya ce, “Ya ya zamu yi mu samo babyn?” Na ce cikin tabe baki, “Nima ban sani ba”. Ya kamo hannuna ya rike cikin nasa, sannan ya rungumoni a hankali yana sumbatana. Ya ce, “Kada ki damu zan koya miki yadda ake samo baby, amma ba yanzu ba sai kin kara girma, yanzu abokiyar zama zan kawo miki mai kirki ko ba kya so?” Na ce, “Ba ga Sabuwa ba muna zamanmu tare?” Ya yi murmushi ya tausasa murya ya ce, “A’a, ita wannan aurenta zan yi........” Na fincike hannuna na mike tsaye nace cikin muryar kuka, “Me na yi maka ni din ABDULHAKIM da ka daina sona?” Ban saurari amsar da zai bani ba na juya ina kuka na yi dakina. Murmushi ya yi, ya yi cilli da rediyon ya biyoni. Na tura kofa zan sa key ya sa karfi wajen turo kofar ciki, to karfin ba daya ba. Ya turo da karfi saura kadan in fadi, ya zagayeni da hannayenshi a jikin kofar yadda bani da hanyar wucewa. Ya ce, “Ni din Sakinah? Ni yau kike yiwa bore don na ce zan yi aure? Auren da ba abin da zai shafa daga soyayyar da nake yi miki? Ni na ce miki na daina son ki?”. Na share idona da tafukana na ce, “In ba daina sona ka yi ba me ya sa za ka yi auren?” Ya ce, “Zan yi aure ne saboda TAUSAYINKI”. “Ni marainiya ce da za ka ji tausayina?” “Ke ba marainiya ba ce, ba za ki iya da lalurata ba Sakinah! Wanda shi ne jigon auren. Ni kuma ba zan iya jurewa ba, ba tare da na nemi alternative ba. Sakinah ina son ki son da ban taba yiwa komi a rayuwata ba, in kika dauke Hajiya da Daddy. Zan yi aure don amfaninmu duka ba don na daina sonki ba. Ina so kashinki ya yi kwari kamin in dora miki hidimar aure, dalilina ke nan”. “Ni kuwa meye wannan lalurar taka da kake tunanin ba zan iya ba? Ka fada min ko ta mece ce ni kuma na yi alqawarin zan yi maka ko da hakan shi ne abu na karshe da zan gabatar a rayuwata...........in dai za ka fasa yin auren, na yi alqawari zan yi maka...”. Da sauri ya rungume ni, “Da gaske kin amince Sakinah in dora miki nauyin kirjina?” “Na amince Mijin-Sakinah.......sai dai don Allah idan na mutu, ka nemi Mamana ka ce da ita INA SONTA……!!!’ Yadda ya rike ni cikin rawar jiki da gigicewa na raina wautata. Cikin wata irin dakusasshiyar murya ya ce, “Balle ma ba za ki mutu ba, sai Mamanki ta goya ‘ya’yanmu”. Bai lura da rashin tausayin da ya yi min ba, sai da ya nemi numfashina ya rasa. Har asuba ban gama wartsakewa ba. Har wankan shi ne ya yi mini, sannan ya gaya min yadda zan yi wankan sallah. Na yi yadda ya ce, ya nado ni a tawul ya kwantar a resting chair ya bani paracetamol. Ya kuma kwashe shimfidar ya wanke da kansa, ya ci gaba da bani treatment kamar wani likita har gari ya waye. Ya mai dani dakina sannan ya durqusa a kan gwiwoyinsa, yana kallona da murmushin da ban taba ganin yayi irinshi ba, domin murmushi ne daya fito daga karkashin zuciya, ba daga fatar baki ba. Sannan murmushine mai bayyanar da halin da ZUCIYAR MUTUM ke ciki., ya ce, “Allah ya yi miki albarka Sakinah! Sakinah na gode Allah ya yi miki albarka!”. Kunya ba ta barni na amsa ba, na rufe fuskata da tafukana ina murmushi. **** Kwananshi biyu ya koma Lagos, zuciyarshi fal da so da kaunar matarsa. Har yake jin bazai iya auren Farida ba, dama a rashin uwa ne akayi uwar daki, duk wata barakar da tasa shi tunanin yin auren matar shi ta tosheta. Sai dai yayi don son rai kawai amma ba don wani abu daban ba. A wani bangaren kuma yana tunanin yadda zai tunkari Faridar, ba zai iya keta idonta yace da ita baya son taba. Da gaske Sakinah ba ta son kishiya, yarinya da ita amma ta san kishi a ‘yan shekarunta da yake rainawa. Sannan ita ma Farida yana sonta, don ita ce first love din shi, tana da wasu qualities da yake so a diya mace. Kamar kamun kai, nutsuwa da wadataccen ilimi. Sannan yana son kasancewa da mace a kusa da shi a nan Lagos, tunda ba zai raba Sakinah da karatunta ba. Wadannan tunanikan su suka taru suka dagula mishi lissafi. Yana zaune a ofis ya bude wayoyinshi, text din Farida ne ya fara shigowa kafin na sauran mutane. Ya kira Abdallah yake gaya mishi Sakinah fa ba ta son kishiya, ta yarda ko mutuwa ne ta yi a kan turbar auren in dai zai janye niyyarshi na kara auren. Abdallah ya ce, “To ban da abinka wace mace ce take son kishiya? Ba burina a quntatawa kanwata ba, sai dai ina so kaima ka samu peace of mind, don na tabbata kana son Farida. In ka dawo sai ka sa Abbanta ya yi mata nasiha tana jin maganarsa sosai. Wannan ba wani abu bane, wace ce za ta buga kirji ta ce ayi mata kishiya don tana so?” Ya dade yana tauna maganar Abdallah, kafin ya amsawa Farida cewa Daddy ya amince ya aure ta. Farin ciki a wajen Farida kamar ta yi ya ya. Zuwan shi gidansu uku suna shirye-shiryen auren, sai dai Farida ta tsorata da yadda duk wata magana ta Abdulhakim daya-biyu, to zai ambato sunan Sakinah. Ba ta tashi kara rikicewa ba sai da suka fara saye-sayen da zai zuba mata a lefe, ta ga komai biyu yake saye, in ta yi magana ya ce daya na Sakinah ne ba tare da ya damu da reaction dinta ba. Ta cika ta yi fam, amma ita da take lallabawa ta samu ya aure ta, ta samu din ai fushin fari ba nata bane. Da yake mace ce mai wayayyen kai, sai ta biye mishi, har tana tambayarshi size din kafar Sakinah, ya ce, (38) ita kuma nata (40). Lefe sosai na gani a ba da labari suka hada, wanda ya lashe miliyan uku cif! Da ya tashi tahowa a karshen satin ya taho dasu ya kaima Hajiya na Farida don a samu masu kaiwa, don tuni Daddy da mahaifin Farida sun yanke magana an sanya daurin auren watanni uku cif!. Babu yadda Hajiya za ta yi, ta nemi Jama’arta don su kai. Ciki har da Mami, Mami ta tambayi Hajiya dalilin kara auren na Abdulhakim. Hajiya ta ce, “Watakila ba haka yarinyar nan da iyayenta suka barshi ba, amma mai mace kamar Sakinah me zai nemo a jikin wata diya mace?” Mami ta ce, “Baki lura bane Hajiya Lailah, Sakinah fa sai yanzu ta soma kirgen dangi. Ga dukkan alamu bai samun gamsuwa a jikinta ne”. Hajiya ta ce, “To ba zai yi hakuri ba? Hakurin da zai yi ai ba zai kai wanda ya yi a baya ba”. Mami ta ce, “Rabu da ‘ya’yan zamani Hajiya Laila, ai ba irin mutanen da bane da za su iya zubawa matansu ido har tsayin shekaru ba”. “Hajiya Lailai ta jinjina kai ta ce, “Allah ya kyauta”. Ina kicin ina hada salad don tuni Abdulhakim ya yi min waya cewa yana bisa hanyar Abuja. Sadi da Uche wanda yanzu ya koma gidan Hajiya suka soma shigo da akwatuna ko in ce irin jakunkunan nan na zamani da ake kai lefe a cikinsu. Ban fito ba sai da na kammala ayyukana, snanan na soma fito dasu bisa dining, nan na yi arba da akwatunan wanda ke tabbatar min Mijin-Sakina ya iso. Na fada toilet na yi wanka na shirya cikin wani tattausan leshi ruwan zuma mai yarfen qananun duwarwatsu kala-kala, na feshe jikina da turarena na din-din-din wato Azzaro Visit, na feshe gashina da turaren gashi mai sanyin qamshi, sannan na taje na matse shi da bound kalar leshin jikina. Ban daura dankwali ba. Juyawa nake a gaban mudubi ina kallon kaina, ko da inda bai yi ba a canza? Wani juyi da na yi sai na hango dan Alkali Ribadu cikin mudubin yana murmushin nan nasa mai ban sha’awa, cikin farin yadin filtex mai santsi, dinkin Mohammed. Kamar kullum yau ma hannuwanshi ya bude mini, maimakon in tafi da sauri kamar yadda na saba a da, sai na sarqe hannayena a baya na runtse idona, kunya kamar in yi ya ya. Sai ji na yi ya sureni ya yi sama dani, sannan ya cillani tsakiyar gadona yana cewa, “Tallafeni Sakinah….. da bukata na zo mai yawa.......” [9/15, 2:47 PM] Asmau: An ci soyayya, so bege da kauna an gaji, wannan karon ban ji wuyar ba sai dan abinda ba’a rasa ba. Kankame muke da juna kamar masu tsoron kada wani iftila’i ya ratsa a tsakaninmu. Zuwa yanzu na san mene ne auren, na san wane ne mijina Abdulhakim Khalil Ribadu? Idan maza sun yi dubu na san da kyar a samu uku kwarara masu nagartar nawa mijin. Sannan ko cikin laluben rufa- ido zan tsame mijina a cikinsu. Mutum ne da ya san ciwon kansa kwarai, ya kuma san mutuncin dan adam duk lalacewarsa, ko daga yadda yake mutunta Sabuwa ya ba ta girma. Ya kuma kaunaci duk ahalina ko wanda ya shafeni. Mutum ne da ya san soyayya mai tsayawa matarsa a qoqon rai. Bar ta kyawun halitta, Abdulhakim is classique da kowacce diya mace da ta san ciwon kanta za ta yiwa kanta burin mallakarshi. Zuwa yanzu soyayyar mijina Abdulhakim ta gama ratsa kowacce jijiya mai gudanar da jini a jikina, ta ratsa kashi da bargo. Ta yi kwance cikin tsoka da fatar jikina. Wani mahaukacin so nake mishi wanda ni kaina ban san iyakarshi ba. Kamar ya san tunanin da nake yi, ya sake rungume ni, runguma mai karfi. Ya ci gaba da rikitani da wasu irin hot-kisses har na fita hayyacina. Saida dukkannin mu muka samu nutsuwa. Amma bai sakeni daga kyakkyawar rungumar da yayimin ba. Sannan ne ya ce, “Zan yi miki laifi Sakinah, Sakinah zan kara AURE. Ba don kin gaza dani ba ta kowanne fanni, duk da karancin shekarunki. Allah ya yi miki baiwarwaki da dama wadanda ke kanki ba ki sansu ba. Na yaba da kokarin ki…. na kuma yaba da jarumtakarki........ Sai dai Sakinah ina son zama da mace kusa dani a inda nake zaune, ga shi bana so in rabaki da karatunki yadda kike jin dadinsa. (Shi akan kansa bayan ya fada yasan wannan dalilin bai isa hujja ba). Zan auri Farida mu zauna a Lagos kafin in samu transfer. Ita ce wacce na ce miki na so in aura a baya Allah bai yi ba. Zan samu goyon bayanki Sakinah? Ina neman alfarmar ki. Idan baki amince ba wallahi zan bari, idan kin amince na yi alqawarin zamowa mai adalci a tsakaninku.....”. Tunda ya soma maganar kallon shi nake babu ko kiftawa har ya gama, wani abu ne dunqulalle ya zo ya tokare ni a kirjina, ina so in yi kuka amma kukan ya ki zuwa. Da kyar na samu sautin dana ke ta tattarawa ya fito daga bakina, “Ni kuma sai ka sallameni! Don ban ga sauran amfani na ba, kana nufin yadda muke dinnan haka zaka yi da wata matar ni ina gefe? Kuma ita ma ta samu ‘ya’ya da kai, nima ta dinga yiwa ‘ya’yana irin azabar da Mami ke min? Wataran ka sake ni a dalilin ta? Ka daina ganina yarinya haka, na san wace ce KISHIYA!” Murmushi ya yi irin na maza, a lokacin da suka fahimci matansu na kishin su, wanda baya sawa kuma baya hanawa kan abinda suka yi niyya, yana shafa kwantacciyar sumar kanshi, ganin yadda idanuwana suka juye ina amayar da dukkan radadin kishin da ke zuciyata. Ya kama hannuna na fizge na mike zan fita, ya sha gabana ya sanyani a kwana, ya zagaye ni da hannuwan shi babu hanyar wucewa. Na sulale kasa na zauna dirshan bisa kilishi, zuciyata na wani irin tafasa. Sai yanzu ne na samu hawaye masu zafi da radadi suka zubo. Shi ma bina ya yi ya zauna dabas a kasa, ya tara hannu ya taro hawayen ya ce, “Haba Sakinah! Matar nan fa ba cinye miki ni za tai ba. Ba wani abu za ta cira a jikina ba, babu abin da za ta gutsira na soyayyata a gareki. Karewa ma mijinki za ta taimaka ta zauna da shi a inda ba shi da kowa. Ko kin fi son in dinga kula ‘yam matan Lagos masu bin maza har ofishinsu da in auro miki ta kirki?” Na kai yatsuna na toshe kunnuwana ina kuka sosai, na ce, “Bana sonka..........bana sonka! Bana son ka! Ta je na bar mata. Ba abinda zaka fada in yarda har yanzu kana so na. Amma ni ka mai dani gidan Abbana, na yarda Mamin ta yi ta dukana tana sani aikatau din in har akan haka ne aka yi min auren, da dai in hada miji da wata. In kuma ka ki mai dani wallahi zan kashe kaina da wuqa ka huta tunda yanzu baka sona........”. Rigimar ke nan har tsayin kwana biyu, ga shi a gobe zai koma Lagos. Duk yadda ya so in saurare shi in ji hukuncin da ya yanke na ki. Duk wata kyakkyawar alaqa dake tsakaninmu na janye ta. Akwatunan da ya kawo min wai na fadar kishiya kananzir na zuba musu na qyasta ashana zan qona ya dauke ni da wani wawan mari sai da na ga wuta. Ya kwace ashanar ya kwashe su ya maida dakin shi, ya fita sallar magariba bai tashi dawowa ba sai tare da Abbana da Daddy. Na fada jikin Abba ina kuka. Ya ce, “Ni dagani tun ban zane ki ba, sakarar banza shashasha!”. Daddy ya ce, “Taho nan Sakinah, tunda ba kya so ba za a yi ba”. Cikin haushi mai tsanani Abba ya ce, “In kin kashe auren saboda rashin hankali sai ki nemi wani uban ba ni ba, ni mata nawa kika ga na aura a kan idonki? Mahaifiyar ki ba ta dau kishiya a bakin komai ba sai ‘yar’uwa, abokiyar shawara. Don haka wannan kishin dabbacin ban san inda kika samo abinki ba, sai ki koma wajen wadanda suka koya miki ki kuma nemi gidan zuwa ba gidana ba”. Daddy ya ce, “Haba M.T? Lallashinta ya kamata ayi ba a kara tunzura ta ba. Zo nan Sakinah, ki gaya min duk abin da ba kya so”. Na ja shesshekar kuka na ce, “Bayan ita ma idan ta zo sonta zai rinqa yi har su haifi ‘ya’ya ni ban haihu ba”. Gaba dayansu suka bushe da dariya har Abdulhakim da ya yi zugumm! Sai da ya murmusa. Daddy ya ce, “To ke nan yanzu haihuwa ce ba kya so ta yi?” Na ce, “Eh, kuma ya ce wai tafiya zai yi da ita Lagos ni su barni ina yi musu gadin gida”. Daddy ya ce, “To ayi miki transfer mana ki bisu can ma ai akwai makarantu Sakinah?”. Na share hawaye na ce, “Ni ba zan rabu da Nadiya ba, ina son makarantar mu sosai”. Abba ya ce, “To shi ke nan za a gaya mata kada ta haihu idan ta zo. Amma ita ma za ki sota kamar Nadiya? Kinga Auntynki ce”. Na ce, “Au, babba zai auro don ta dinga turmushe ni tana duka idan ba ya nan?” Daddy ya ce, “Ita ta isa ta taba ki ‘yar lelena? Bayan ma ba garin ku daya ba”. Haka suka sani gaba suna ta lallashi, in bullo ta nan su toshe can har na yarda na hakura ya yi auren. Daddy ya ce, “To kayanki fa na fadar kishiya ai za ki karba ko?” Na daga mishi kai. Ya ce, “To Allah ya yi miki albarka, duk abin da ya yi miki ba daidai ba ki zo har gida ki same ni ko ki yi min waya in zo, in ta kama in zane shi wallahi sai na zane shi, shi da matar tasa”. Na yi dariya da hawaye jabe-jabe na ce, “Duka Daddy?” In affirmation ya ce, “Kwarai kuwa, duk girman nan nasa wallahi zan zane shi in dai a kanki ne”. Na ce, “Balle ma ba sai ka doke shi ba, ai ya yi girma da duka”. Daddy ya ce, “Bai yi ba, sai idan bai yi miki laifin ba”. Da haka suka lallaba ni suka tafi, ya bisu don ya taka musu. Ina kallon yadda yake satar kallona a kasan idanunshi yana murmushi. Ya rakasu ya dawo, ina zaune inda suka barni ban tashi ba, ya zauna opposite dina watau ya kara bayanshi a bayana. “Yau kwana biyu ba a bani abinci ba saboda KISHI. Hanjin cikina duk ya kanannade, wannan mai sauki ne idan aka kwatanta shi da babban abincin da ba’a bani ba don kawai na ce zan yi aure. Shin ba sunnar ma’aiki zan raya ba? Mene ne laifi a cikin yin aure?’ Ya juyo ya kuma juyo dani muka fuskanci juna. Hawayen da nake tattali kada su zubo sune suka zubo, yasa hannu yana taro su akan tafukansa. Cikin karyayyar murya ya ce, “Me ya yi zafi Sakinah? Na ce in ba kya so zan bari........” “Bayan ka riga ka hadani da su Abba, ni ban gaya musu marin da ka yi min ba sai kai ne mai bakin kai kara ta don kai ne dan gata?” Ya yi murmushi ya ce, “Ai marina mai hujja ne, almubazzaranci za ki yi na hanaki, ko su suka ji abin da kika yi niyya sai sun mare ki. Sakinah haka kike da kishi? Kada ki qona min matata fa?” Na cika na yi fam! Na mike na barshi a wurin ya biyoni yana cewa, “Ana sona ne, in ba haka ba ai ba za a yi min haka ba”. Biki ya matso, tun ana i gobe kamu lokacin Abdulhakim yana Lagos na hada kayan da zan yi amfani dasu a karamar jaka na shiga na yiwa Hajiya sallama na tafi gidanmu, na shige cikin ‘yammatan Safinah. Sabuwa kadai na baro a gidan, harka da jama’a da kujiba-kujiba yasa na mance da damuwata, na mance cewa nima ana yi min bikin kishiya ne. Mun kebe ni da Yaya Safina ta ce, “Wai da gaske Abdulhakim aure zai kara?” Na ce mata, “Eh”. Ta ce, “Kin fa sa jikina ya yi sanyi, domin Abdulhakim da Abdallah bakinsu daya, shawarar su daya”. Na ce, “Wallahi kuwa, don shi ma Abdallah ai ya so wata ita ta kishi kamar Faridan”. Ta ce, “Tab! In nice wallahi za a yi bala’i, don ba zan yarda ba”. Na ce, “Sai ki mutu ai, kuma sai ya yi. Ba abin da ban yi ba, ba boren da ban yi ba, ai bai fasa ba. Na yi kukan na yi fushin, na yi haukan sai mari da na sha, sannan ba’a fasa ba”. A nan harabar gidanmu aka shirya yin kamun, an qawata wurin sosai. Safinah ta yi kyan har ta gaji. Tana cikin runfarta, ta kishingida da tuntu mu kuma da sauran kawayenta mun sha anko muna gefe da gefenta wasu a bayanta. ‘Yan kamu suka iso aka yi kamun mai ban sha’awa na mata zalla. Washegari karfe takwas na dare motocin angwaye suka zo diban mutane zuwa wajen dinner. Sai da aka kwashe kowa tsaf ya rage daga ni sai amarya da wata qawarta Hamida Sajoh. Na yi saurin kashe wayata kada Abdallah ko Abdulhakim su nemeni na gudu dakin Yaya Suwaiba wadda ke fama da tirtsetsen ciki na haihuwa yau ko gobe, na yi can quryar dakinta na yi kwance abina. Ko Safinah ba ta san inda na shiga ba”. Yaya Suwaiba ta shigo dakin tana cewa, “Au ashe kina nan? Kika bar mijinki yana ta neman ki? Ga shi kin sha ankonki kin yi kyau, sai dai kuma kin bata gwaggwaron. Sai ki tashi ki je yana waje har su Safinah ke suke jira”. Nasa kuka na ce, “Ni wallahi ba zani ba, ya je can ya dauki matarshi”. Ta yi dariya ta ce, “Oh! Ni ‘yasu. Sakinah ban san yaushe kika koyi wannan kishin ba. To ita ba a dadinta ba kin bar mata mijin ke kin hakura”. Na ce, “Eh, na ji, su karata can ba inda za ni”. Ban ankara ba sai jin sallamar Mijin-Sakinah na yi a falon Yaya Suwaiba”. Ta ce, “Gara dai ka zo da kanka don ta ce ba inda za ta”. Kai tsaye ya shigo dakin ya sha wata jiqakkiyar farar excellencior mai maiqo da yarari, wadda a qalla ta bai wa naira dubu casa’in baya. Qamshinsa da kwarjininsa sun cika dakin. Haiba da kamalarshi sun cika idanun kowa. Ya dauki Gwaggwaron yana gyara lanqwashewar da ya yi ya kifa min a kaina. Ya ce, “Tashi ki taka da kafafunki ko in sungume ki wallahi....”. Kunya ta kama Yaya Suwaiba ta fita ta bar mana dakin. Na balla mai harara sannan na yi saurin tashi don na san kadan da aikinsa. Cikin motar Abdulhakim (SL 360) Abdallah ne da Safina a baya, wani abokinsu ya dauki Hamida, na shiga gaba Abdulhakim ke tukin. Wayar Farida ta shigo, ban dai ji me ta ce da shi ba ya ce, “Bana son mita, gamu nan?” Ya dan juyo ya dubi Abdallah ya ce, “Ba sai mun je gidansu Farida ba tana can already”. Abdallah bai yi magana ba, hirar shi yake da amaryarshi. Ina jinsu tana cewa, “Ka gayyato Safiyyah?” Ya yi dariya ya ce, “Ta yi aure”. Harabar Hotel din na (Rock-View) cike take da motoci na zamani danqam! Haka al’umma danqam. Su Safina ne a gaba rike da hannun junansu mu kuma muna biye dasu. ‘Yammatan Safina suka taho suna take mata baya. Tun daga nesa Farida Alqasim ta zuba min ido ta cikin medicated glass dinta, tana mamakin yadda aka yi Abdulhakim ya auri kankanuwar yarinya haka wadda ko nonuwan kirki babu a kirjinta. Sai dai da ganina ka ga (half caste) watau ruwa biyu. Ta ci gaba da kallona kamar mai son karanta ta. Ba ta karanci komai ba, sai zallar kuruciya da rashin fara’a. Fuskata a dinke tsaf, amma ba karamin kyau na yi ba. Musamman sanda idanuwa da attention din kowa ya dawo kanmu, masu vedio na yi masu camera na yi. Har muka zauna a kujerun da aka tanada domin mu. Ina gefen daman Abdulhakim, Farida na gefen hagu, ta kama hannun Abdulhakim na hagu ta rike cikin nata. Tana murmushi ta ce, “Sakinah ba gaisuwa?” Sai sannan ne na juyo na dube ta, kyakkyawa ce sosai hasken fata da yawan gashi kawai zan nuna mata. Sai dai ta kusa sa’ar Abdul din, tunda shi yana (32) tana (27). A raina na ce, “Ki qwacen mijin sannan ki ce in gaishe ki?” Ganin ban ba ta amsa ba sai ta dauke kanta tana sauraron Hamida Sajoh wadda ke ba da tarihin Safinah. Ta gama sannan tata qawar ta tashi ta ba da nata tarishin. A nan na ji wai har masters ta yi. Na ce, “Tsohuwa kawai, ashe kwantan ‘yammata aka kwaso mini, Allah ya isa!” Ashe Abdulhakim ya ji Allah ya isan. Dariya ta kama shi ya hanata fita saboda masu vedio. Ya sunkuyo daidai kunnena wani irin lafiyayyen qamshi na tashi a jikinsa da bakinsa, ya ce, “Da bai isa ba ya yi dan dama da kabewa?” Harara na manna mishi sannan muka kyalkyale da dariya daga ni har shi. Haushi ya kama Farida, amma ba ta yi magana ba. Sai dai za ka iya karantar kishin a kwayar idonta. Karfe goma na dare aka tashi daga taron. Wannan karon Safinah motar Abdallah ta bi, ina kokarin guduwa in shige motar da su Hamida suka shiga caraf! Ya damqo ni ya fizgo hannuna muka nufi tashi motar. Tuni Farida ta kame a gaba tun kan mu karaso. Na ce, “Lallai yau za ayi ta”. Ya ce, “Da aka yi ya ya?” Na ce, “A gaban mota na saba zama yau kuma ba zan canza ba”. Ya yi dariya ya ce, “Sakinah-Sakinah! My Queen my princess........I love you girl!!” Daidai sanda muka karaso jikin motar ya bude gaban, ya ce, “Fito Farida ki koma baya”. Ta daure fuska sosai ta gyara zaman gilashinta a idanunta ba ta motsa ba. Can kuma ko me ta tuna? Ta fito ta koma bayan. Na yi mata gwalo a qeyarta ba tare da ta sani ba. Ita muka fara saukewa a gidansu. Daga ganin gate din kadai za ka san naira ta zauna da duwawunta a wannan gida. Ya fita ya taka mata har kofar reception dinsu, suka yi ‘yar magana sannan ta shige, shi kuma ya juyo. Ganin ya dauko hanyar gidanshi na ce, “Ni fa gidanmu za ka kaini, duk kayana suna can sai an gama biki zan komo”. Bai kula ni ba har na yi mitata na gama. Saura kadan in fashe da kuka lokacin da muka shigo gate, na ce, “Yanzu don Allah da gaske ba za ka mai dani gidan bikin ba?” Ya ce, “Ba za ki ba, za ki fito ko in sunkuce ki?’ Ganin yana nade hannun riga na balle murfin motar na fice fuuu! Uwa guguwa. Ya yi dariya ya kwaso wayoyinshi ya fito ya rufe motar. Kishin Sakinah har tsoro yake ba shi. Ina wanka lokacin da ya shigo, na yi saurin kammalawa na fito don na san kadan da aikinsa ya shigo toilet din. Shi ma wankan ya yi, na zuba hijabi na soma sallar isha’i da ban yi ba. Shi ma sallar ya yi sannan muka kwanta. Yana ta lallashina, ya ce. “Don Allah Sakinah ki sassauta min. In kina nuna min fushinki za ki sa in zamo mara adalci in tashi ranar alkiyama da rubabben barin jiki. Kina son hakan?” Na girgiza kai. “To ki rage wannan kishin bana so, idan kina so mu shirya”. Na ce, “To”. Ya janyo ni yana cewa, “Matso nan ki gani in daga miki kofar shiga Aljannah”. Washegari aka yi daurin aure, Safina da Abdallah, Abdulhakim da Farida. Daga nan angwayen suka wuce walima ta maza zallah. A cikin gida kuma a kowanne bangare na amaren yinin biki suke. Ban kara tsinkewa da al’amarin ba sai da na ga an bude daya flat din dake jikin namu an fara sauke kaya, na tabbatar dai da gaske Mijin-Sakinah ya tashi daga mijin Sakina ya zama mijin Sakinah Da Farida. Na karbi hakan a matsayin abin da Allah ya rubutawa Abdulhakim wanda bawa bai isa ya kankare shi ba. Da daddare Hajiya ta aiko Sabuwa ta yi kirana in je can gidansu a karbi amayar a can. Zuwa yanzu na koyawa zuciyata dauriya da tawakkali. Muna can falon Hajiya wanda ke cike taf da jama’arta da matan abokan Daddy. Safinah aka fara kawowa, nan gidan Hajiya aka sauke ta kafin baki su watse su wuce Kaduna. Sannan aka kawo Farida. Bayan jama’a sun watse Daddy ya shigo ya hadamu mu duka biyun ya yi mana nasihar hakuri a zama da juna da yin biyayya ga mijin aurenmu don samun mafificiyar rayuwa a duniya da lahira. Hajiya da kanta ta rakamu har gida. Ta raka kowacce sashinta, sannan ta yi mana addu’a ta tafi. Tafiyarta da wajen awa daya na yi wanka na yi shirin barci, amma barcin ya gagara duk juyin da na yi Abdulhakim nake gani rungume da Farida. Na shige toilet na yi kukana mai isata. A karshe na yi tunanin ban isa in haramta abin da Allah ya halasta ba. Sannan Abdulhakim din bai rageni da komai ba, sai ma wata sabuwar kauna da a kullum take kara habaka kamar ya mai dani cikin kirjinsa saboda kauna da soyayya. Da wannan na rarrashi zuciyata na kwanta rigingine a gadona ina karatun addu’o’in littafin HISNUL MUSLIM. Tareda duba littattafaina na makaranta. [9/15, 8:18 PM] Asmau: A hankali ya murda kofar ya shigo, ya zauna daidai kafafuna, qamshin masifaffen turarenshi (Aqua D’gio) na dukan hancina. Ya dora hannu akan yatsun kafata yana ja a hankali. Na samu kaina da rashin son daga ido in dubi Abdulhakim, domin son da nake mishi ya ragu, yayi rauni, yana nema ma ya rikide zuwa tsana mai tsanani, ga shi na yiwa kaina alqawarin na daina nuna mishi fushina tun ranar da ya tunatar dani illar hakan a gare shi. Sai na sauke littafin a hankali ina kallonsa. Ba tare da na ce dashi komi ba. Ya ce, “Ki yafe ni idan na yi miki ba daidai ba, ki yafe ni idan na yi wani abu wanda ya bata miki rai.... ki....” Nayi saurin kai yatsuna na rufe mishi baki, “Ni baka yi min komai ba, nice ma zan baka hakuri a kan abin da na yi jiya wajen shiga mota. Ita ma amarya ka ba ta hakuri......” Farin ciki ya bayyana a fuskarsa, don bai zaci hakan daga gareni ba, musamman a daidai wannan lokacin da kowacce mace ke azabtuwa da shi. Ya kama hannuna muka mike tsaye, ya ce, “Abinci nake so zan samu?” “Akwai, Hajiya ta aiko dashi tun dazu”. “To dauko muje wajen Farida”. Na nufi kicin na fiddo abincin cikin kwandon abinci, ya karba ya wuce gaba na sanyo hijabi kan kayan barcin da ke jikina na cimma shi muka isa side din Farida. Shi ya fara shiga kafin in bi bayanshi. Tana kishingide tana waya tana dariya. Shigowarmu tasa ta kashe wayar ta yi fara’a sosai ta mike ta karbi kwandon hannunshi ta aza a dining na falonta. Ina kallon ta ina tazbihi ga sarkin halitta, ashe akwai mata masu kyau haka a duniya ban sani ba? Na ji tausayin kaina, ko da yake Abdulhakim ya ce wai nima ina da kyau? Oho! Da kanta ta yi serving kowannenmu, duk inda ta motsa tattausan qamshin Estee-Lauder ke tashi. Maimakon ta ci wanda ta zuba, sai ta sanya cokalinta cikin plate din Mijin-Sakinah. Bai yi magana ba, da haka aka kare cin abincin. Ya dubi Farida sosai ya mai da fuskarshi ya dinke. Ya ce, “Farida ga matata Sakinah, lafiya muke zaune ba don ta yi min wani laifi bane ko ta gaza dani ta wani bangare yasa na aure ki ba. Na aure ki ne don ina sonki kamar yadda nake sonta. Bamu taba samun rashin fahimta ba a tsayin zamanmu na shekaru uku, ina fatan shigowarki cikin rayuwarmu ba zai canza komai ba. A girme dai kin girme ta, kin fita hankali, don haka ki rike ta kamar kanwarki. Alfarma ce nake nema, zan samu Farida?” Ta dube ni sosai cikin ido, Allah kadai ya san abin da take saqawa a ranta. Ba tare da ta ce komai ba. Ganin ba ta da abin cewa sai ya juyo gareni ya ce, “Sakinah ga nan Farida, ita ma matata ce kamar ke, na aure ta don ina sonta, ba don mu quntata miki ba. Idan ta girme ki a shekaru, kin girme ta a aure. Don haka ke ce uwargidana a duniya da lahira. Ki zauna lafiya da ita, duk da ba tare za ku zauna ba. Ki rike girman da na baki, kada ki yi wasa da shi. Tashi ki je ki kwanta, Allah ya bamu alheri”. Tun kan ya idasa rufe bakinsa na mike, don bana son wannan kallon qurillar da matarshi ke yi mini. Abin da ban sani ba shi ne kowa ya firgita da kowa. Sai dai kuma Hausawa sun ce ‘ZUCIYAR MUTUM.......BIRNIN SA’. Don haka ban san abin da Farida ke saqawa a tata zuciyar ba. Duk da wannan kyawun nata, da gayun nata ban ji gwiwata ta yi sanyi ba har in ji tsoron da zan sallama mata Abdulhakim Ribadu. Kowacce ta murza irin kambunta in yaso mai sa’a ta kwace. A wannan daren idan na ce na yi barci babu shakka na fadi karya, sanda na tashi da safe idanuwana sunyi luhu-luhu na rashin barci. A haka na yi wanka na sanya uniform. Ina daura sandal na fata a kafata Abdulhakim ya turo kofar ya shigo. Ya zuba wani farin yadi caftan mai yarari da rashin kauri, ta yadda har ana iya hango vest din da ke jikinshi. Na ci gaba da daura igiyar takalmina ba tare da na dago na dube shi ba, don bana son ganinsa. Ya zauna gefena, sai na ji shi ma yana qamshin (Estee-Lauder) maimakon kamshin jikinsa na tun fil azal. Na finciki jakata zan wuce ya rike hannun jakar, na ja ya ja bai cika ba sai na sakar mishi. Hawayen da nake tattali suka shimfido a kundukukina. Cikin sassanyar murya ya ce, “Me ya yi zafi haka Sakinah? Ki yiwa Allah idan laifi na yi miki ki yi hakuri, gaya min me na yi miki ya saki kuka?” Na zumbura baki tareda sharce wasu matsiyatan hawaye na ce, “Ni ka bani jakata zan makara, kuma John yana jirana a waje”. Ya ce, “Ai na sallame shi, ni da kaina zan kai ki. Amma sai kin yi kalaci ko yaya tukunna”. “Ni ba zan ci ba”. “To ki sha ruwan tea kadai, ina zuwa”. Ya fita wajen Sabuwa ya hado tea din da coconut-cake guda uku a kan dan tangaran ya dawo. Da lallashi da ban baki na karba na sha, amma ban daina zubar da hawaye ba. Sai da na shanye sannan muka fito, muna tafe a mota ya damu ya ji abin da ya sanyani kuka da sassafen nan. Da ya isheni da naci na bude baki na furta mishi abin da bai yi tsammani ba....... “……Ba kai bane ka fesa Estee -Lauder!”. Ya kama baki, sannan ya yi dariya, ya kwaikwayi muryata shima ya ce. “Ni Abdulhakim na fesa Estee-Lauder.....!” Ganin ya maida abin wasa sai nayi fuska, na fuske suntum. Shima nan da nan ya zama ‘serious’ ya shiga taitayin sa, yace. “…..Fesa min ta yi, ba ni na fesa ba. Tunda kuma ba kya so ba zan kuma bari ta fesa min ba”. Na kara kuluwa kamar in fashe don bakin ciki. Na ce, “Ka ga tada motar nan mu tafi na makara”. Don na lura idan na ce irin wadannan kananan abubuwan zan dinga sanyawa a raina suna damuna nice zan kamu da hawan jini a banza. Da muka tashi ma shi da Faridan suka zo dauka ta, duk da a ranar za su wuce Lagos. Allah sarki, sai ta fito daga gaban mota tun kafin in karaso ta koma baya. Ni kuma na ce ba zan shiga gaban ba ta dawo wajenta ta zauna. Ba ta yi musu ba ta koma gaban, shi dai bai ce komi ba. Kafin mu iso Abdallah ya rigamu isowa, domin shi zai kaisu filin jirgi. Ya bani wasu kaya cikin leda wai in ji Safina akwai wasiqa a ciki. Ina zaune gefen gado ina duba wasiqar Safinah ya shigo, ya zuba sabuwar shiga na shadda deep-blue.Da ganinshi kaga ango sosai sai zuba qamshi da sheki yake. Ya ce, “Zamu tafi Sakinah sai upper week, me zan samu ne?” Na kawas da kai ganin yadda ya yi kyau da yawa, ban taba ganin mutum mai kyau da sigar Abdulhakim ba. Wani takaici na cina a zucci. Da kyar na ce, “Allah ya kiyaye hanya”. Ba tare dana dago ba. Ya ce, “Ba zan samu komai ba?” Kai tsaye na ce, “Ba za ka samu ba!”. Yayi murmushi cikin damuwa ya ce, “Not even your smile?” Na hade girar sama da ta kasa na yi banza da shi. Ya bude baki zai kara magana, na yi kicin-kicin da fuska. Ya ga ba alamun wargi, sai ya yi murmushi ya sosa kai ya ja tsumman rayuwarshi yai gaba. Bayan tafiyar su na ci gaba da zuwa makaranta ta, bani da lokacin wasu tunaninnika balle tunanin su ya dame ni, musamman da muka soma jarabawar shiga aji shida. Safinah ta gama, sai ni da Nadiya wadda take a SS1, yayin da ni kuma nake shirin shiga ajin karshe. Mijin-Sakinah yana kirana a waya yana jin lafiyarmu. Ita ma Faridar ta kira sau biyu wai mu gaisa. Mun gaisa din amma daga jin muryarta ka san tursasata aka yi. Nima ban kara cewa komai ba bayan gaisuwar. Sati biyu da tafiyarsu na soma wani irin azababben ciwon mara, kwanana biyu a kwance ina murqususu ba tare dana bari Sabuwa ta gane ba, don ban fito falon ba. Ina can bed room dina ina juyi ina salati. Ban ji karar bude kofa ba sai tausasan hannun Abdulhakim a kafaduna, ko iya bude idona bana yi saboda azaba. Ganin yadda nake kankameshi kamar mai shirin haifo da ya sunkuce ni, kafin ya kai bakin kofa jini ya balle, har da guda-guda. Ciwon kuma ya lafa. A take na ce, “Sauke ni, wani abu yana zubowa”. Ya yi toilet dani ya dire ni cikin kwami ya kwance min zanin, sai ga jini na ta shatata. Daga ni har shi duk mun rude mun firgice mun rasa abin yi. Da sauri ya fita ya aika Sabuwa ta siyo always pad, cikin dan lokaci ta kawo. Ya ce, “Kin iya amfani da ita?” Na girgiza kai alamar “A’a. Ya fita ya kira Sabuwa, ita ta taimaka min na yi wanka na yi qunzugun. Ya dawo muka fita sai asibiti. Likita ya dubani sosai, ya ce “Kada ku damu menstruation ne ta fara”. Ya rubuta min qwayoyin da za su taimaka mini muka fito. Abdulhakim cike da tunanin Sakinah ta girma, daga yanzu zuwa kowanne lokaci za ta iya daukar ciki. Don haka ya shiga damuwa sosai, amma da ya yi tunanin ta cika shekaru sha biyar sai bai damu sosai ba. Shi da ya zo da qishin Sakinah, haka ya hakura ya bige da jinya, saboda yadda na firgita da wannan sabon al’amari da ya same ni. Na yi zaton wani ciwo ne Allah ya dora mini, yana lallashina yana nuna min ba wani abu bane, abu ne da kowacce mace ke yinsa. Har ya koma jinin bai dauke ba. Wannan tafiyar da Mijin-Sakinah ya yi har aka kwana goma bai neme ni a waya ba, nima ban damu ba saboda karatunmu ya yi zafi. Wani satin ya shude babu Abdulhakim babu wayarshi. Tun bana damuwa har na soma damuwa. A satin Abdallah ya zo, ya kawo min cheque din kudi wai in ji Abdulhakim. Kamar in yi shiru sai kuma na daure na ce, “Yau satinshi hudu ke nan bai zo ba”. Abdallah ya ce, “Lafiyarsu lau, don last week na je Lagos din, kin san yanayin aikin nasu ba wuri daya suke zaune ba, kuma na ji yana cewa zai je Akure yin wani aiki wanda zai dauke shi lokaci mai tsawo”. Kamar in ce waya fa? Na ga babu amfanin tambayar, sai na yi shiru. Wasa-wasa sai da Mijin-Sakinah ya shafe watanni hudu bai zo ba, sai dai bai fasa turo Abdallah ya kawo min kudi ba. Shi kadai ya san me yake gayawa Daddy har bai damu da zuwan nashi ba. Hajiya ce dai ba ta yarda ba, ta kira shi ta ce, “Duk abin da yake ya bari ya zo gida ta gaji da uzurirrikan sa”. Da ya tashi zuwan sai ga shi da Farida, lokacin muna tsaka da shirye-shiryen jarrabawar fita. Watanni bakwai cif ban sa Abdulhakim a idona ba. Ina study room ina nazarin litattafaina ya yi sallama a kofar studyn Farida na bayanshi, muna hada ido ta kasheni da murmushi wanda da gani za ka san na gayya ne. Na rufe littafin ina yi mishi sannu da zuwa cike da karfin zuciya kada Farida ta ga weakness dina. Nima murmushin na yi mata cikin nuna ban gane irin murmushin da ta yi min ba. Na ce, “Ga shi ban san za ku zo ba, bamu sanya sanwa daku ba”. Ta ce, “Ba wani abu zamu iya jira har a dafa tunda ba a yunwace muke ba, bamu dade da cin abinci ba”. Dakinshi ya shige ya barmu a falon. Ta ci gaba da yi min wannan mugun murmushin nata, na fara tsorata da sha’anin matar nan, don ba ta yi min kama da mutane masu dauke da alheri ba. Na soma karanto duk addu’o’in tsarin da suka zo bakina, na tashi na bar mata falon. Ganin haka ita ma ta koma sashenta. Da daddare mun kammala hada abinci ni da sabuwa, Abdulhakim ya shigo kai tsaye ya wuce sassan Farida. Ko a fuska Abdulhakim ya sauya, kai yadda yake nunawa ma kamar bai sanni ba. Ya sosa zuciyata, ga tsoron matarsa a gefe. Na tambaye shi inda za a shirya abinci ya ce ba tare da walwala ba, “Ki kai sassan Farida”. Da taimakon Sabuwa muka jera abincin a dining din Farida. Sabuwa ta fita, ni kuma na zauna cikin kujerun falonta ina jiransu. Sai na jiyo shesshekar kukan Farida, irin kukan nan da ake kira kukan kissa. Tana cewa a hankali......... “Ni dai don Allah kada ka bari ta dau ciki, ka yi min alfarma in fara haihuwa tare da kai. Bana so ‘ya’yana su samu ‘yan ‘uba........don na tashi cikin ‘yan ubanci na san rashin dadinsa. Plz Hakim ka rike alqawarinmu da ka ce ni kadai zan haihu tare da kai.......” Da alama ya tsaya ne yana lallashinta, ya ce, “Na ji na yi wannan alqawarin, sai dai kuma kina nufin ba zan kusanci matata bane ita ma in ba ta hakkinta mai yawa da yake a kaina? Watanni bakwai tunda na aureki bana tare da ita, kin hanani zuwa, na zama makaryacin karfi da yaji ga iyayena. Yanzu kuma da muka zo ki ce ba za ki ba ta girki ba? Kada ki manta ita ma ‘yar adam ce kamar ki. Don kin ganta yarinya karama sai ki dinga ribatata mu zalunce ta? Wata bakwai fa, haba Farida!” Cikin sassanyar murya ta ce, “Ni ban ce kada ka kusance ta ba, tunda akwai contraceptions kamar kwararon roba da loops ka kaita a sanya mata.....” Da gudu na yi daki bana ganin abin da yake gabana. Lallai gaskiyar Hausawa da suka ce ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA. Idan wani ne ya gaya min Abdulhakim zai taba yi min haka ba zan taba yarda ba, sai ga shi Allah ya yarda kunnuwana sun jiye min, don ya san bani da hakkinsu. Allah abin tsoro, mutum ma abin tsoro ne. Soyayya KARYA ce a yau na kalubalanci duk masu yarda da ita. Na yi kukana ya isheni na gode Allah. Ba abin da zuciyata ba ta kimsa mini ba a a daidai wannan lokacin. Wanda ya ce ba zai haihu da kai ba, shi ne kuma yake ikirarin yana kaunar ka. To wace irin kauna? Ko dai yaudara? Lokaci daya na ji Mijin-Sakinah ya sire mini, duk wata soyayya da kaunar da nake yi mishi na nemesu na rasa. Wata zuciyar ta ce, “Hada kayanki ki yi tafiyarki gidan ubanki”. Wata kuma ta ce, “A’a, in kin je ki ce me? Baki da hujjar da Abba da Daddy za su yarda dake, ki ce labe kika yi musu ko ya ya? Ke za a bawa laifi. Zuba musu ido ki ga kamun ludayin su tukunna. Shin da gaske ne zai aiwatar da abin da matarshi ke so a kanki? Ko zai dubi soyayya, kauna da amana? Jin takun tahowarshi yana tahowa na yi saurin gyara kwanciyata na rufe ido kamar ina barci, ya dade tsaye a kaina yana mamakin kansa. Ya kama kanshi da hannuwanshi biyu. Ya ce, “Me ke damuna ne? ……TSORON FARIDAH?” Ya kai hannu ya ja babban dan yatsana na kafa na bude jajayen idanuna a kanshi, wanda ya yi zaton barci ne ya mai dasu hakan. Mun dade muna kallon juna, kallon da babu so da kauna a kwayar idon kowannenmu. Ya yi karfin halin cewa. “Ya za ki kai abinci ba ki zama mu fito mu ci tare?” Na kawar da idona a kansa, “A qoshe nake, shi ne dalili”. Bai ce komi ba ya juya yana cewa, “Ki shirya yanzu asibiti zamu je”. Na bishi da kallon mamaki da tsoro, tare da kara sarewa da al’amarin Da-Namiji. Na amince lokaci ya zo da zan koma gidan Mami, in koma cikin rayuwata ta baya, ta da mara ‘yanci ya fiye min da in zauna da mayaudarin masoyi. Sai dai na qudurce ni da aure hai-hata-hai-hata. Ina shiryawa ina kuka wanda ba zai sa ba, ba kuma zai hana ba. Na qudurce a raina in na fita gidan nan a yau na fita ke nan har illa masha Allahu. Na dauki daya cikin jakunkunana na zuba duk abubuwan da zan bukata, na yankewa zuciyata rabuwa ta har abada da Mijin-Sakinah, ina maraba da duk irin rayuwar da zan tsinci kaina a gaba. Har jikin mota Farida ta rakamu, kamar ta hadiye Abdulhakim don tsatsiba. “Plz Hakim kar ka dade ka san zamu je dinar Iman karfe takwas”. Ya ce, “Ina sane ba zan dade ba”. Ta juyo kaina tana murmushin nan nata, “To Sakinah sai kun dawo”. Ban kalle ta ba, sannan ban amsa ba. Ya yi mamakin ganin na bude but na jefa katuwar jaka. Ya ce, “Ina za ki da wannan jakar?” Na ce, “Ina so in mun gama da asibitin ne mu biya gida in kai wa Nadiya kayanta ne a ciki”. [9/15, 8:18 PM] Asmau: **** Dawowar shi kenan daga sallar juma’a ya shigo falon Farida babu kowa, Sabuwa ta koma gidan Hajiya tun bayan tafiyar Sakinah. Ya duba dining babu wani abincin kirki da aka ajiye, sai wata dankararriyar taliyar Indomie fara sol. Ya yi tsaki ya rufe, matsalar Farida ke nan, shegiyar kiwa da lalaci. Ba ya jin wannan farar taliyar za ta iya quenching wannan gigitacciyar yunwa da yake ji. Don tun safe haka ya fita ya barta tana barci ko karin kumallo ba ta ba shi ba. Sannan Hajiya ta ce kada ya sake ya kara zuwa wajenta neman abinci, ta kuma gargadi masu aikinta kada wanda ya ba shi, ya je ya soya Faridar ya cinye, amma babu ruwanta. Ya shiga kicin ya bude firij babu komi ciki, sai doyin rubabben nama, ga tulin wanke-wanke ba a yi ba. A store din da ke cikin kicin din kayan miya ne fal da potatoes duk sun rube, sai wari suke. Cike da bakin ciki ya nufo dakin Farida don ya sauke mata bala’in da ke cin zuciyarshi, ya dora hannu akan marikin kofar dakinta ke nan ya jiyo dariyarta, da alama ba ita kadai ba ce. Ta ce, “Duk magungunan da na karba na yi amfani dasu yadda ya dace, zancen nan da nake miki Mama, yanzu ba ta gidan nan, shi kansa bai san inda take ba. Kuma ya tabbatar min ta tafi ke nan, don ta bi mahaifiyarta kasar su. Aikin na Bakin-Kogi ya fi na dan Tsubura’u, don na ga yakini, tunda na hada na zuba mishi a juicy shi ke nan bai kara tunata ba tsayin watannin nan, sai da uwar ta bude mishi wuta. Duk da haka ya ce sai dai in tare zamu je, amma in ba haka ba to ba zai zo ba. Ni kuma gudun bacin ran iyayen ya sa na ce da shi ya yi hakuri mu zo don na lura ba tun yau ba Hajiyar ba ta sona, Balarabiyar take so. Sannan na hana shi haihuwa da ita kuma ya amince, har ya kaita an sa mata abin hana daukar ciki da yake yarinya ce ba ta san komai ba. Ni yanzu hankalina kwance yake ya tsumma a randa, don haka na fasa fitowa in komawa Alh. Garba, don ba zai shayar dani soyayyar da Abdulhakim ke shayar dani ba. Saidai ya bani kudi. In kuma don naira ne ga inda nairar ta zauna da gindinta nan. Ada kam ban san yaya aljihun Abdulhakim yake ba, shi ya sa naki aurensa na yarda da auren Alh. Garba......” Ji ya yi numfashinsa na shidewa, ya juya baya ya jingina da kofar don ta dauki nauyin gangar jikinshi. Uwar ta ce, “Kina nufin bai san kin taba aure ba? Kada fa watarana ya binciko liki ya balle?” Ta ce, “Ni mahaukaciyar ina ce zan gaya mishi na taba auren? Ai duniyar nan Mama yanzu kawai ZUCIYAR MUTUM..........BIRNIN SA, wallahi da ya ji da ba zai aure ni ba yadda yake da masifaffen kishin nan. Dinki na je aka yi min kuma bai gane ba, don har yau bai taba tada zancen ba. Yanzu abin da ya rage min shi ne, ina jiran aikin da na bakin kogi yake hadamin wanda zai bita da takardarta har dakin uwarta..........” Sai ya bude kofar, hawaye na tsiyaya daga idanunsa ya ce, “Kafin in bita da takardar har dakin uwarta.......ke ga taki a gaban taki uwar. Ki je ki komawa mai kudi tsohon mijinki, amma ni bani da kudin da kike zato. Ni ma’aikaci ne kawai wanda zai iya ciyar da Sakinah kadai, ki je na sake ki saki uku! Ko a yanzu haila kike, babu jinina a tare da ke. Cutar da kika yi min kika kika rabani da mai kaunata kika hadani da iyayena ki je na yafe miki”. Ya juya ya fita ya barsu tsuru-tsuru an rasa mai karfin gwiwar yin wani motsin kirki a tsakaninsu. Ya dawo da takarda cikin ambulan ya dora mata a kan cinya ya juya ya fita yana cewa. “Ina da bukatar muhallina, don haka na baki kwana daya ko allurarki kada in gani a gidana. Idan hakan ta faru to za ki kwashe su a waje. Na gaya miki na kara gaya miki, kwana daya rak na baki ki bani muhallina”. Ya fita yana hawaye ya nufi gidan Hajiya. Yadda ya shigo ma Hajiya Laila sai da gabanta ya fadi. Ya zauna cikin kujera idanuwanshi jazur, jijiyoyin kansa sun fito rado-rado, ya dafe kanshi da hannuwa bibbiyu hawayenshi na zuba. Ta ce, “Kai lafiya? Ko wani ya mutu?” Ya girgiza kai, ya ce, “Ki yafeni Hajiya......tabbas duk wanda ya ki bin mahaifiyarshi yana tare da nadama......” Ya kwashe duk abin da kunnuwanshi suka jiye mishi tsakanin Farida da mahaifiyarta ya fada mata. Da kuma matakin da ya dauka. Ta ce, “Kash! Ka yi mummunan saki wanda Allah ba ya so. Sannan saurin saki ba dabi’a ce mai kyau ba. Ni din nan ba abin da ban yiwa mahaifinka ba,don kada ya kara aure, don haka don anyi maka ba zai zamo abin mamaki ba, tunda an ce duk abin da ka yi, sai an yi maka, ko a yiwa naka. Amma yanzu na gane kuskurena, na tuba ga Allah na nemi afuwar mahaifinka, kuma ya yi afuwa a gareni. Sannan don ta taba yin aure ai ba wani abu bane, tunda ba cikin shege ta yi ba. Sannan akasarin mata da suke bin wannan hanyar don soyayyar da suke yiwa mazajensu ne ta yadda har basa son wata ta rabe su......” Ya girgiza kai ya ce, “Duk soyayyar da aka ginata bisa karya da yaudara Hajiya ba soyayyar gaskiya ba ce, don wanda ke son wani da sharri, shi da alheri, to zuciyarshi ba mai kyau ba ce. Farida ta sire min Hajiya, don ba sona take ba, kanta kawai take so da amfanin kanta. Ba zan kuma amince mata ba, domin a da na yarda da ita, nayi mata shaidar alheri, amma ashe ZUCIYAR MUTUM….BIRNIN SA! Ba zan kuma iya ci gaba da zama da ita ba. Ina da kishi Hajiya, ba zan iya sake hada jiki da sauran wani ba. Ta je ta koma gidan mijinta, dama tausayinta ne ya ribace ni da tunanin soyayyar da take yi min ce ta hanata yin aure. Don haka tunda ita mayaudariya ce, to ta je ta ci gaba da yaudarar wasu ba ni ba”. Hajiya ta girgiza kai ta ce, “Allah shi kyauta”. Ya ci gaba da zama bai tashi ba, yana so Hajiya ta yi mishi zancen Sakinah, amma ba ta yi ba. Ya kara sunkuyar da kai ya ce, “Don Allah Hajiya ki taimake ni ku dawo min da Sakinah........Daddy da Abban Sakinah sun ki saurarata. Wallahi Hajiya bani da wani nufi a kan Sakinah sai na soyayya, amana da alheri........illa na samu kaina cikin gudun bacin ran Farida da tsoronta. Hajiya a yanzu Allah ya yaye min, ji nake kamar an sauke min wasu kaya masu nauyi daga kaina”. Hararar shi Hajiya ta yi, kafin ta yi murmushi ta ce, “Sanda kuke kulla mata mugun nufi kai da matar da kake son ka tuna dani? Sai yanzu da ta kwabe maka za ka san dani? To babu ruwana, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Cewa nake ka san inda take, sai ka je can ka nemo ta”. Kamar ya yi kuka ya ce, “Don Allah don Annabi Hajiya ki yi hakuri, kuskure ne babu wanda ya wuce shi. Na kuma amsa cewa na yi kuskuren, na tuba na bi Allah na biki...........don Allah Hajiyata”. Abin ki da UWA, nan da nan zuciyarta ta soma sanyi, ganin Abdulhakim yau yana yi mata kuka da girmanshi da komai, abin da ba ta taba gani ba a girmansa. Sannan Abdulhakim din shi kadai Allah ya bata duk fadin duniyar nan, kaunar da ta ke mishi ba kadan ba ce. Sai dai ya bata mata rai ba kadan ba, tunda ya batawa Sakinarta. Ya sauka daga kujerar ya kama kafafunta yana kuka sosai. Ba ta san sanda ta kai hannunta tana share mai hawaye ba. Ta ce, “Ya isa haka Abdulhakim, Sakinah da Abbanta basa nan suna kasar Libya wajen mahaifiyarta. Ban san kuma ranar da za su dawo ba, ka je ka nemi afuwar Daddy in ya ga dama sai ya baka adires ka same su a can ko ya rakaka tunda ya san inda suke”. Ranshi ya yi sanyi, tunda a qalla Hajiya ta yafe mishi. Sai dai yana tsoron karon shi da Daddy. Kwanan shi uku yana bin Daddy da magiya da ban hakuri kamin ya samu Daddyn ya sauko, amma ya yi masa fada sosai, ya kuma hada da nasiha. Sannan shi ma bai ji dadin sakin rashin tausayi da ya yiwa Farida ba. Duk Abdulhakim ya karba ya kuma ba da hakuri, sannan ne Daddyn ya ce ya soma yi musu shirin tafiya kasar Libya. **** Kwananmu bakwai a Libya, Abbana da Sakinah kullum suna tare, tsumin tsohuwar soyayya na tashi. Daga karshe suka sasanta kansu, na cewa sun yarda za su kara zama karkashin inuwar aure a karo na biyu. Sai dai ta ce ba za ta kuma zama da Lami ba, ya amince kuma zai ware mata gidanta daban, ya kuma dauki alqawarin rike mata ‘ya’yanta Tananni da Mus’ab su zauna tare da ita. Ya yi waya da Kawu Tasi’u ya sa shi ya yi musu shirin tahowa kasar Libya shi da Baffa Sule zai aiko musu da tikiti. Ranar litinin suka iso Libya, washegari aka mai da auren Abbana da mahaifiyata a masallacin da ke maqwabtaka dasu. A ranar ne kuma Abdulhakim da Daddyn shi suka iso Tripoli, suka samu walimar daurin auren. Karramawa ta musamman Gaddafi ya yiwa su Daddy jin cewa surukinshi ne. Abba da Daddy suka zaunar da shi suna ta nasiha, wani zubin su hada da fada. Duk Mijin-Sakinah ya amsa cewa ya yi laifi. Sakinah kawai yake so in dai za su ba shi a karo na biyu, to zai jure duk wani punishment da za su ba shi. Waya ta samu Abba cewa Mami babu lafiya ta samu ciwon iska, yanzu haka tana Psychiatrist na National Hospital. Nan aka soma shirin tahowa. Ranar juma’a muka sauka a filin jirgin saman Abuja, kai tsaye asibitin muka wuce. Abun babu kyawun gani, Mami sai addu’a domin hauka tuburan take tana tonawa kanta asiri tana cizgar gashin kanta, na gabanta dana hammatarta, na duk irin abubuwan da ta yiwa matan da Daddy yake aure yana saki, da abubuwan da ta yiwa Sakinah. Sakinah ta kama hannunta ta ce, “Na yafe miki Lami duniya da lahira na yafe miki”. Amma ba ta fasa surutanta ba. Sai likitocin sun zurmuqa mata allura sannan ake samu ta yi barci. Hajiya Laila ita ma ta dinga kuka tana cewa, “Da ban tuba ba nima da na san makomata ke nan, Alhaji ka yafe mini, duk tare muke yin komai, ko mata dari kake so ka aura wallahi na amince maka”. Dariya ta kama Daddy, ya ce, “A’a, ki bar casa’in da shidan na bar miki, guda ukun dai zan kara tambadaddu masu ja da abin da Allah ya halarta”. Kwanan Mami goma sha hudu sannan ta samu sauki, suka sallame ta da magungunan da za ta dinga sha. Gaba daya Mami ta yi sanyi, tana ji kuma tana ganin Sakinah da M.T Liman matsayin mata da miji a karo na biyu. Ta yi ladaf ta zama kamar idan ka sanya mata yatsa a baka ba za ta ciza ba. Gidan da Abba ya sayawa Mamana yana nan a Kubuwa, kwanan su Uncle Gadaffi uku a Abuja suka koma Libya. Babu abin da babu a gidan na jin dadin rayuwa. Duk yadda Abdulhakim ya yi don ya ganni a wannan dan tsukin bai samu ba, Mamana ta boye ni, tana ta gyareni, gyara irin na Larabawan asali. Jikina ya yi kyau, zuciyata sarai. Da kanta ta kaini asibiti aka cire min loops din. Sati hudu ke nan rabona da Mijin-Sakinah, ni kaina na san na yi kewarsa, yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Na yi kewar soyayya da kyautayinsa, na kuma tabbata ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba. Kwance nake a cinyar Mamana tana gyara min gashina da man (Bergamot), sallamar Abdallah ta tsinkayi kunnuwanmu, Abdulhakim na bayansa, wasu irin zaratan matasa masu kwarjini na daukar hankali, ilhama da cikar zati. Mijin-Sakinah ya rame fiye da tsammanina, ya riga ya ganni, don haka babu damar gudu. Ko da damar gudun ba zan iya gudun ba, don kwarjinin shi ya cika ko ina. Na tashi daga kwanciyar da na yi, na nemi dankwalina na daura. Tunda suka shigo Tananni ta zura daki da gudu saboda yadda tun a Libya Abdulhakim ke tsokanarta da kiranta “Zaujatee”. Wato matarsa. Sakinah ta shiga marhaban dasu, cikin dan lokaci an cikasu da cima kala-kala. Mijin Sakinah kokari yake mu hada idanu amma na ki. Abba ya yi sallama ya shigo yana murmushi, ya ce, “Manyan baki garemu a gidan? Da kun yi zamanku yau zamu kawo muku matarku. Ke Sakinah dauko mayafinki ku tafi bana son wata tashin-tashina, komai ya wuce Allah ya baku hakurin zama da juna”. Idanuna suka cicciko zan yi kuka, Abba ya ce, “A’a, kar ki yarda mu yi haka dake Sakinah. Shi auren baki dayansa jigonsa shi ne hakuri, Abdulhakim ya yi laifi, amma ya gane da kansa bai kyauta ba, ki zamo mai afuwa ga wanda ya saba miki, amma bana son kullaci da sanya abu a rai fiye da kima, maza tashi kuje Allah ya yi muku albarka”. Har mota suka rakomu ina ta kuka, Mamana rungume dani tana lallashina. Tunanina shi ne yadda zan ci gaba da rayuwa da Farida, tunda na gane ba ta sona da alheri. Abdulhakim na tuki yana murmushi, Abdallah sai zuba min hira yake, amma na ki in kula shi. Ya ce, “Haba Sakinah, dan wannan abu da bai kai ya kawo ba sai ki zo ki gayawa Abba? Maimakon ki neme ni ki gaya mini mu ci mu binne abinmu ba tare da kowa ya ji ba. Na raina wayonki, nan gaba kar ki sake yin haka, wannan rashin wayo ne, kin ji na gaya miki”. Ko amsa ban ba shi ba ya gaji da babatunshi ya yi shiru. Abdulhakim bai tofa mana ba, tukin shi yake cikin kwarewa da sukuni. Gidan Hajiya muka fara shiga don ta san na dawo, Hajiya kamar ta goyani saboda lallashi da nuna kauna. Sabuwa bakinta har kunne, tana “sannu da zuwa uwar dakina”. Daddy kansa sannu da zuwa yake min. Abdallah ya wuce gidanshi, mu kuma muka nufo namu gidan. Sabuwa ta sa mukulli ta bude, ko ina fes kamar ba a je ko ina ba. Sabuwa na ba da baya ya sunkuce ni yana juyi dani a tsakar falon yana cewa, “Yarinyar nan kin wana ni da yawa…..”. Daga nan muka rankaya ga dakin barcin mu, cikin wata irin soyayyah mai wuyar bayyanawa. Gyaran Mamana yayi aiki sosai, lallai ‘gata’ sai uwar data haifeka. Babban goro sai magogin karfe….(sunan littafin TAKORI mai zuwa). Duk yadda Abdulhakim zai yi ya wanke laifinsa cikin hikima da soyayya ya sani. Na ji babu abin da nake so nake kuma kishi a wannan duniyar irin mijina Abdulhakim Khalil Ribadu. Daya tamkar da dubu, abin alfaharina, farin cikin rayuwata. Bani da zabi ban da nima in mallaka mishi soyayyata mu raya daren cikin farantawa juna rai. Na kalubalanci kaina da tunanina na baya cewa zan iya rayuwa babu Abdulhakim a cikinta. Kwana uku kwarara Abdulhakim bai je ofis ba, amarci sosai muke gudanarwa wanda a baya bamu taba yi ba. Na sha mamaki da har kwana uku ban ga Farida ba, ban ji ya yi zancenta ba. Ni kuma ban tambaye shi ba. Sabuwa ke kyankyasa min tana jin Abdulhakim ya saki Farida, don taga sanda ake kwashe kayanta. Na dade ina tunanin al’amarin, daga baya na watsar na shiga harkokina. Shi da kansa yake gaya min Farida tana gidansu, sun rabu. Bayan wannan bai kara komi a kai ba. Na ji tausayin Farida, domin dai duk wacce ta yi rashin gwarzon miji irin Mijin-Sakina, dole a jajanta mata. Sannan ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne. Sati hudun da na yi ba tare da Abdulhakim ba, ni kadai na san irin halin da na shiga. Na yi mana addu’a dukkanmu cewa, Allah ya sa hakan shi ne alherinmu. Jarrabawarmu ta fito, daidai sanda Abdulhakim zai tafi qaro karatu (in-service) zuwa jami’ar (Waterloo, Canada).Ya yi cuku-cukun da nima na samu gurbi a can, inda zan yi karatu a kan tsimi da tanadi, wanda aka fi sani da tattalin arzikin kasa (economics). Ranar litinin jirginmu ya daga zuwa kasar Canada, birnin ‘Vancouver’. Rayuwa ta mika mana cike da ci gaba da budi ta kowanne bangare. Da albarkar iyaye lullube da mu. A Canada na haifi Abdulhakim (Daddy), Ibrahim Khalil, da Mukhtar. Iyayenmu kullum cikin sanya mana albarka suke, kuma albarkar muke ta gani har gobe, don kuwa kullum cikin ni’imomin Ubangiji muke. Tabbas duk wanda ya yi biyayya ga iyayenshi zai ga da kyau a rayuwarshi ta duniya da lahira. Masha Allahu la-quwwata illa billah! Maman Safah da Marwah ce ... [9/15, 8:18 PM] Asmau: Cikin halin ko in kula ya ta da motar muka hau kan titi. Ina daga waje inda ya ce in jira shi ya shiga wajen likitan, suka yi magana ya fito ya yi kirana. Ban yi musu ba na bishi da yadda ya ce. Likitan ya ce in kwanta, na dubi Abdulhakim kallo na al’ajabi, tsoro da mamaki. Ya yi saurin sunkuyar da kansa bayan ya daure fuska sosai alamun ba wasa. Ina ji ina gani aka zurmika min wani abu. Sannan likitan ya shiga yi min bayanin wai bleeding zai dan qaru a lokacin menstruation. Muka fito daga ofishin ina kuka. Shi ma Abdulhakim ya sha jinin jikinsa, don na lura ya yi cooling, nadama baro-baro ta bayyana a fuskarsa. Muna tafe ya daure ya ce, “Me aka yi na kuka? Don kawai an duba mahaifarki ko ta isa daukar ciki?” Kallon da na yi masa na rainin hankalin ya isa! Shi ya sanya ya shiga taitayinsa. Ya kuma tabbatar Sakinar da, da yake treating ‘yar karamar yarinya ba ita ce yanzu ba. Jikinshi ya ba shi ko dai Sakinah ta san loops ne aka luntsuma mata? Ya yi ta maza ya ce, “Idan baki daina kukan ba, to sai a fasa zuwa gidan Abban”. Jin haka na yi shiru ina share hawayena. Har muka zo gidanmu babu wanda ya kara magana. Ya ajiye mu ni da jakata ya ce, “Idan sun dawo daga dinar da zasu je shi da Farida zai dawo ya dauke ni. Na ce, “To”. Na bishi da kallo a sanda ya tada motar, domin na tabbata kallon karshe nake mishi. Na daga hannu ina share hawaye wanda ke fita tun daga karkashin zuciyata. Ilyas ne ya fito, yana ganina ya sunkuci jaka yana yi min oyoyo! Duk al’ummar gidan suna falon Abba, kowa ya shiga murnar zuwana, musamman Yaya Suwaiba. Na yi iyakar kokarin da zan yi don boye damuwar da ke tattare dani. Nadiya ta taho da gudu ta rungume ni muka zube bisa carpet, Mami ta ce, “Wani irin rashin hankali ne haka Nadiya? Karyata za ki yi?” Ta ce, “Mami sister ta dade ba ta zo ba”. Na ce, “To ai gani yau na zo”. Aka ci gaba da hira har kowa ya zame ya barni da Abba, don sun lura cikin damuwa nake ina bukatar kadaicewa da Abbana. Abba ya dube ni sosai yana nazarina, ya ce, “Goben nan nake sa ran zuwa gidan ki in sanar dake labari mai dadi......” Kafin Abba ya sanar dani albishir din nasa kuka ya kece mini, na yi ta yi ba qaqqautawa. Hankalin Abba in ya yi dubu to ya tashi. Ya ce, “Me ya faru Sakinah? Fada mini ko mene ne? Na ce me ya faru? Ko Abdulhakim din ya sake ki ne?” Na girgiza kai, “Ko daya Abba! Illa na gane Abdulhakim ba kaunata yake yi ba. Ya so ni ne kafin ya samu matar da yake so. Abba ka karba min takardar saki a matsayinka na Alkali mai kare hakkin dan adam”. Na kwashe komi na alqawarin da na ji yana yiwa Farida, na cewa da ita kadai zai haihu, ni ba zai haihu dani ba. Don kar ‘ya’yan matarshi su samu ‘yan uba. Da kuma abin da ya kaini asibiti yanzun nan aka saka mini. Abba ya yi shiru kamar ruwa ya cishi, can kuma muryar shi ta yi sanyi ya ce, “Yanzu akwai abin a jikinki?” Na daga mishi kai. Ya ci gaba da yin shiru, Allah kadai ya san irin bacin ran da ya shiga. Can ya ce, “Ke me ya sa kika labe musu? Kin san labe babu kyau ko?” Na ce, “Wallahi Abba ba labewa na yi ba, zama na yi ina jiransu su fito mu ci abinci Allah ya nufeni da ji. Duk da haka ban yarda ba sai da ya kaini aka sa min. Sannan gaba daya ya sauya mini tunda ya yi aure, tamkar bai taba sani na ba”. Ya ce, “Ni wannan bai dame ni ba, amma maganar a hanaki haihuwa saboda wata ba zan yarda da ita ba. Tashi ki tafi dakin Nadiya zan nemi Ribadu gobe, amma ki kama bakinki ban yarda ki yi zancen nan da kowa ba”. Sallamar Abdulhakim ta isa kunnuwanmu, ganina gaban Abba ina kuka duk ya sha jinin jikinsa. A sanyaye jiki babu nauyi ya durkusa yana gai da Abba. Abba ya amsa mishi fuska a sake, wannan ne ya ba shi kwarin gwiwar da ya iya zama a falon. Abba ya ce, “Yaushe za ka koma Lagos?” Ya ce, “Ai na samu transfer zuwa nan Branch dinmu na Abuja, don haka ba zan koma ba”. Abba ya ce, “Allah ya yi jagora, amma Sakinah zan dan riketa kwana biyu. Ya ya babu damuwa?” Ya dago fararen idanunshi ya dube ni ya yi hanzarin sunkuyar da kansa, cikin sarkewar murya ya ce, “Babu komai Abba”. Ya ce, “To Allah ya bamu alheri, a gai da Farida”. Haka ya taso ya fito daga falon kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Bayan ya fita nima na yiwa Abba sallama na nufi dakin Nadiya, zuciyata na suyar da ban san dalilinta ba. Shi ma Abban cikin tunani na barshi, ko kadan bai ji dadin abin da Abdulhakim ya yi ba. Sannan ba ya so aurena ya mutu a kan ‘yar wannan matsalar. Don haka a daren ya kira Alkali Ribadu ya ce ya zo gobe yana son ganinsa. Da yake Mami ce da girki ta shigo cikin kwalliya tana ce da Abba, “Lafiya Sakinah za ta kwana a nan?” Ya daure fuska ya ce, “Lafiya qalau sai alkairi”. Jin haka ta mai da bakinta ta rufe suka shiga wata hirar daban. Washegari ya kama lahadi. Tun karfe goma na safe Alkali Ribadu na cikin gidanmu, Abba ya kwashe komai ya gaya mishi. Ya yi shiru sai zufa ke keto mishi ta al’ajabi da mamaki, sannan da kunyar amininshi da ta baibaye shi. Ya fiddo waya ya kira Abdulhakim ya ce ya same shi yanzun nan a gidanmu. Cikin mintuna ashirin ya iso, sai walainiya yake cikin danyen farin boyel. Kai da ganinsa ka ga matashi mai jini a jika wanda ke cikin lokacinsa, yake kuma jiqe cikin rabar naira. Abba ne ya amsa mishi sallama, amma Daddy bai amsa ba sai kallon mamaki da ya bishi da shi. Ya gai da Abba ya gai da Daddy, tun bai idasa rufe bakinshi ba ya ce, “Wane asibiti ka kai Sakinah aka sa mata abin hana haihuwa?’ Abdulhakim ya dago ya dubi mahaifinsa wanda idonsa ke cike taf da qwalla. Ya yi shiru bai yi magana ba. Daddy ya ci gaba da cewa, “Tunda baka son hada zuri’a damu sai ka sallame mu ka zauna da wadda kake so ta haifa maka zuria.......” A razane ya dago ya dubi mahaifinsa cikin mamakin yadda a kai hirarsu shi da matarshi a daki ta fito waje har su Daddy suka ji. Nadama sosai ta bayyana a fuskar shi, amma idanun Daddy sun rufe da bacin rai, ya dauki takarda da biro ya mika masa. “Ina son takardar Sakinah yanzun nan.....” Ya soma kuka yana bai wa Daddy hakuri da duk iya kalmar da zai iya. Ya ce, “Yanzun nan zamu je a cire, ni kaina ban san abin da ke faruwa da zuciyata ba kwanan nan Daddy. Ina cikin tsoron matata Farida, na fada ne kawai don in kwantar mata da hankali amma ba don haka abin yake har karkashin zuciyata ba. Ina neman addu’arku a kan Allah ya sa na fi karfin gidana na kasance mai adalci a tsakaninsu......” Amma ina! Ran Alqalan ya yi matukar baci, sun ce takarda kawai suke so, babu ruwansu da duk wani halin da yake ciki a kan matarshi. Wanda ya ja ruwa shi ruwa kan doka, amma Sakinah ta gama aurensa. Ya ce, “Har abada Daddy ba zan taba sakin Sakinah ba ko bindiga za a dora mini”. Daddy ya ce, “To ka je ka yi ta rikon igiyar aure amma Sakinah ta gama zama da kai, Allah ya ba ta mai kaunarta da zuri’ar da za ta fito daga jikinta. Maganar za ka kaita a cire mata abin da ka kaita aka sa mata, muma mun san hanyar asibiti, zamu kaita a cire”. Ya ce, “Ku yi min alfarma Daddy in ga Sakinah in ba ta hakuri, wallahi komai ya wuce”. Daddy ya ce, “Ba za a yi ba. Ta riga ta kubce maka, kuma da sannu za ta zama mallakin waninka”. A ranshi ya ce, “Ba sai in na sake ta ba?” A ranar duka mutum hudun wato Daddy, M.T Liman, ni Sakinah da Abdulhakim babu wanda ya yi kwanan dadin rai. Washegari Abba ya yi kiran Daddy ya ce zai wuce da Sakinah Libya don an gaya mishi mahaifiyar Sakinah ta koma Tripoli bayan rasuwar mijin da take aure a Qatar din Masar. Daddy ya ce, “Na ji dadin hakan, ko don a horar da Abdulhakim na wani dan lokaci. Sai kun dawo, Allah ya ba da sa’a”. Cikin kwanaki uku Abba ya gama min duk cuku-cukun pasport da visa. Ranar juma’a muka daga zuwa Tripoli, babban birnin kasar Libya. *** Agidan wani abokin Abba da suka yi karatu tare muka sauka, yana aiki da Nigerian Embassy Tripoli Libya. Sunan shi Abulkhair da matarshi Radhiyyah. Mutanen Katsina ne usul, amma Larabci a bakinsu kamar haifaffun kasar Libya. Kwanan Abba uku suna bincike sosai shi da Abulkhair da wani abokinsu Balarabe Ridhwan, wanda yake sanar da shi labarin Sakinah suka samo gidan. Gidan gini ne irin na Larabawan Libya na red bricks (jan dutse). Flat mai hawa biyu, sai korran furanni masu ban sha’awa da suka yanyame gidan tun daga kasa har sama. An kuma tabbatar musu Sakinah tana gidan tare da mahaifiyarta da ‘ya’yanta biyu, da kuma Yayanta Gaddafi da na shi iyalin. Tunda Abba ya bani labarin ya ce kuma gobe zamu je jikina yake rawa da karkarwa. Abba ya lura da halin da nake ciki, ya yi murmushi ya ce, “Relax Sakinah....... your mother is nice……. Qaddara ta rabamu, amma muna matukar kaunar junanmu”. Sanye nake da abayat kirar Abu-Dhabi na nade kaina da bakin mayafi. Kafata cikin takalmi mai tudu sosai shi ma baki samfurin C.K, watau dan gidan Calvin Klien. Hannuna cikin na Radhiyyah lokacin da Abulkhair ke danna kararrawar shiga cikin gidan. Wata yarinya Balarabiya ‘yar kimanin shekaru goma, ta zo ta bude kofar. Kallo daya na yi mata na dauka photocopy na ne a lokacin da nake shekaru goma. Ita ma yarinyar kallona take cikin tsoro da mamaki, kafin ta juya da gudu cikin gidan. Dukkan mu aka rasa mai fara shiga, can anjima sai wani magidanci ya fito dan kimanin shekaru arba’in da biyu. Yana ganin Abba ya bude baki ya ce, “Mukhtar!” Sannan ya rungume Abba,a lokacinne ya hango ni a rabe a bayan Abba. Ya cika Abba ya kamo hannuna har cikin gidan yana ta qwala kira, “Sakinah! Sakinah!!” Daga kicin ta leqo, doguwar rigar jeans ce a jikinta, ta daura apron (rigar girki) a kai. Gashin kanta jibgi guda nade cikin tafkeken ribbon. A zahiri shekarunta talatin da takwas amma a idaniyarka ba za ta fice shekaru ashirin da tara ba. Na rabe a bayanshi ina kallon Barabiyar da aka kira Mamana Sakinah. A haife dai ba za ka ce ta haife ni ba, zai fi kyau a kirata da yayata ba mahaifiya ba. Na kasa kifta idanuna daga kanta, kamar yadda ita ma ta kasa dauke ido a kaina. Ta dauka mafarki ne cikin irin mafarke-mafarken ta, na dauka hoton zuciya ne wanda nake kwana da yini ina gani. Kafin ka ce meye wannan hawaye ya kece mini. Sannan wani irin nitsattsen so da kauna na UWA- MAHAIFIYA (maternal love) ya shiga ratsa zuciyata, wanda ke rike dani din wato yayanta (Gaddafi) ya ja hannuna har inda take. Maimakon ta yi magana sai ta saki ludayin dake hannunta ta yi daki da gudu ta rufo kofa. Ni kuma sai na durqushe a nan ina kuka. Ya ya to ba zan yi kuka ba? Tunda mahaifiyar tawa da kullum nake kwana da wuni da burin ganin ta ba ta yi farin ciki da ganina ba? Wata dattijuwa Balarabiya sol ta fito daga wani daki dake cikin tafkeken kayataccen falon. Gaddafi ya yi mata magana cikin harshensu, na dai ji ya ambaci sunan Abba da nawa, bayan haka ban fahimci komai cikin bayanin da yake yi mata ba. Don ko ta’al ban sani ba. Ta taho da sauri ta kama kafaduna ta mikar dani tsaye, sannan ta rungumeni a kirjinta. Hawaye suka kara kece mani, karo na farko da na ji feeling din cewa nima cikakkiyar mutum ce mai cikakken asali da nasaba, sannan gani rungume a kirjin mahaifiyar uwata. Ko da wannan na tsira na gode Allah ko Sakinah ba ta yi farin ciki da zuwana ba. Ya fita ya shigo da su Abba, Abulkhair da Ridhwan. Da shi da dattijuwar nan da na ji yana kira Khala suka shiga hidimar sauke ababan jiqa maqoshi masu sanyi. Sannan yarinyar nan da ta bude kofa ta shimfida ledar cin abinci suka soma fiddo nau’in abinci kala daban-daban a ‘yan kananan tangaraye kamar dama sun san da zuwanmu. Ko da yake lokacin cin abincin rana ne a can kasar. Gaddafi ya hau saman bene wato flat din dake samansu suka dawo tare da wata Balarabiyar mai kimanin shekaru ashirin da tara, tana dauke da baby ga wani yaron karami na binsu a baya. Nan na gane matarshi ce da ‘ya’yansu. Ta iso gareni da sauri ta jani cikin jikinta tana ta magana da Larabci wanda bana fahimta. Sai Abba ne yake mata bayani duk suka zagayeni suna murna, kamar su lashe ni. Ta yi kiran yarinyar da ta bude kofa da muka zo ta hada hannuna da nata. Sai ga wani yaron shi ma da gani ba tambaya ka ga dan gidan, don shi ma muna kama sosai. Sai dai ban san dan waye ba tsakanin Sakinah mahaifiyata da yayanta Gaddafi. Su Abba suna ta cin abincinsu suna hira, wadda ban san me suke cewa ba. Gaddafi ya yi bugun duniyar nan amma Sakinah ta ki bude kofa. Sai ya dauko safayan mukulli ya bude, nan ya tadda ita ta hada kanta da gwiwa tana rasgar kuka. Ya zauna dirshen a gabanta yana yi mata magana cikin sanyin rai, sannan ya fito ya yi kirana, ya kama hannuna da nata ya hada sannan ya fita. Ta tsagaita da kukan da ta ke yi tana kallona, har zuwa lokacin ni ban daina kuka ba. Ta kai hannunta kan kafaduna tana jijjiga ni, sannan ta rungume ni sosai a kirjinta, dukkanin mu muka saki wata nannauyar ajiyar zuciya. Ga mamakina sai na ji ta ce, “Ajinki nawa a makaranta?” Hausar tata ba ta fita sosai. Na ce, “Na gama muna jiran sakamako ne”. Ta koma Turanci don Hausar ta gagara, ta ce, “Ina su Zainaba, ina yayarki Safinah?” Cikin farin cikin jin ta yi yaren da zan iya na ce, “Su Zainaba suna ‘Yan Leman, Safina ma anyi mata aure”. Ta ce, “Ke kuma fa?” Na sunkuyar da kaina kasa cikin kunya ban amsa ba, nan ta gane nima anyi min auren. Ta ce, “Baki da baby?” Na daga mata kai. “Ya ya sunan mijinki?” A takaice na ce, “Abdulhakim”. Ta ce, “Yana ina yanzu bai biyo ku ba?” Nan da nan hawaye suka cika idona, na ce, “Mun samu sabani ne”. Cikin damuwa da kulawa ta ce, “Wane irin sabani ne? Amma dai bai sake ki ba ko?” Na ce, “Bai sakeni ba, amma ina so ya sakeni”. Ta ce, “Kul! Sakin aure ba shi da dadi. Duk lalacewar mijin fari shi ne miji, tunda shi kika sani, shi kika san halinsa. Kinga na rabu da babanki ba don raina ya so ba, sai don abubuwan tsoro da nake gani cikin barcina. Ana tsoratar dani da cewa in rabu da shi ko a sabauta ni. Don haka Babanki kotu na mayar mai da sadakinshi, Alkali ya sanya ya bani takardata. Na so in taho dake amma ya hanani, ya dauke ki ya bawa Lami. Don haka na sanya ma raina hakuri na taho ba tare da ke ba, don na amince idan ke rayayyah ce, Allah zai raya ki har ki neme ni da kafafunki. Ga ranar yau Allah ya kawo. Babanki mutumin kirki ne, don a tsayin zamana da shi na wasu ‘yan shekaru bai taba bata min rai ba. Na dauki auranmu a matsayin rubutacciyar qaddara daga Allah da kuma rabon haihuwarki. Bayan na gama iddah na ci gaba da karatu, watarana Allah ya hadani da marigayin mijina Uthman. Haifaffen Libya ne, matukin jirgin sama a Qatar. Muka yi aure muka koma Masar, na dauke mahaifiyata da Yayana don bazan iya zama a wata kasa basu ba, a can na haifi Tananni waccan yarinyar mai kama dake, da dan’uwanta Mus’ab. Na samu aiki a babbar kotun Qatar, yau shekaru uku ke nan da rasuwar Uthman bayan gajeriyar jinya. Muka hado komai namu muka dawo kasarmu ta gado, bana tashi daga inda na yi sallah tsawon shekaru goma sha biyar ban yi miki addu’a ba Sakinah. Ban bai wa Ubangijina amanarki ba. Sannan ina roqon shi ya sada fuskokinmu da alheri, ga shi yau Allah ya kawo min ke. Bani labarin rayuwarki gaba daya kada ki rufe min komai. Ban ga Abdulhakim ba, amma na ji zuciyata tana kaunarsa. Yadda ya yarda ya auri yarinya karama kamar ki.......” Na yi murmushi ina tuna rayuwarmu ta baya da Abdulhakim. Gaskiya ne Abdulhakim ba masoyin yadawa bane. Sai dai Farida ta rugurguza komai, ta murqushe soyayyar da nake yi mishi. Ta murkushe wadda yake yimin. Na dago idona da suka canza launi na ce, “Zan baki labarin rayuwata gaba daya, amma zan yi sallah in ci abinci. Sannan ina neman alfarmar ki GAISA DA ABBANA ba don ya isa ba, sai don albarkacin soyayya da kaunar da ya wanzar da rayuwarshi yana yi miki. Kullum ya budi baki alheri yake fada game da ke. Kullum sai ya ce min ‘my mother is a nice person”. Murmushi ta yi kawai. Ta nuna min kofar toilet, sannan ta zuba abayat ta fita falo. Ta gaisa da Abba, Abulkhair da Ridhwan, sannan ta shiga hidimar dafa musu na’a’na’a. Cikin dan lokaci ta kammala, ta zubawa kowannen su a qanqanin kofi ta mika mishi fuskarta na cikin niqab. Da suka kammala suka mike za su tafi, gabanta na faduwa kada su ce za su tafi dani. Kamar Abba ya san abin da take saqawa a zuciyarta. Ya ce, “Sakinah za ta zauna nan kafin mu warware wasu ‘yan matsaloli a kanta. A qalla za ta yi watanni uku, zan dawo in mai da ita dakin mijinta idan mun sulhunta su”. Ta ce, “Aiwa!” Suka hada ido suka yi murmushi, wanda ya tado da tsohuwar soyayya. Cikinsu babu wanda zuciyarshi ba ta buga ba. Ya fita yana waiwayonta, ita ma ba ta motsa daga inda take ba, sai da ta ji tashin motarsu tukunna. Na yi wanka na dauro alwala na fito, na canza kaya na yi shigarmu ta Hausawa, wato atamfa super blue riga, zani da kallabinsu. Juyawar nan da zan yi na ga ‘yar kanwata tana lekena ta taga, na yi mata murmushi sai ta falla da gudu. Na yi dariya daidai lokacin da ta murda kofar dakin ta shigo niki-niki da qaton ‘tray’, na yi hanzarin karbarta. Ta ce, “Ke da wa kike dariya?” Na nuna mata Tananni da ke lekena ta kasan labule. Ita ma ta yi dariya ta ce, “Ba ta da sakewa da mutane, amma ke ta ce min tana sonki ya sunanki? Na ce mata Sakinah. Sai ta ce sunan ku daya ke nan? Na ce mata eh. Ta ce a ina na samo ki? Na ce mata a wata kasa mai nisa, ke yayarta ce”. Duk muka yi dariya. Ta sake fita don ta kawo abin sha, wato na’a-na’a, ni kuma na tada sallah. Da na idar tare muka ci abincin duk gidan har da Amal matar Gaddafi. Tananni da Mus’ab da kakarmu Khala, kowannensu da irin kulawar da yake nuna mini. Uncle dina Gaddafi ya shigo da Inab da Tuffah fal leda ya miko mini. Ban taba cin abinci mai dadin wanda na ci yau ba. Balarabe daban ne ta fannin kwarewa wajen girka abinci. A nan Gaddafi ya gabatar min da kowa da matsayinshi gareni. Ya ce cikin watan nan nake sa ran zuwa Najeriya in nemi Mukhtar in ganki, sai gaki Allah ya kawo ki. Mu dangin mahaifiyarki muna baki hakurin rashin neman ki har tsawon wannan lokacin. Kin san komai ka yi nufi sai Allah ya nufa, shekaru goma sha uku ke nan, wallahi Sakinah kullum kina ranmu”. Na yi murmushi na ce, “Nima kullum zancen da nake yiwa Abbana ke nan, yana cewa lokaci zai zo da Allah zai sadani daku”. Dare ya yi, misalin karfe goma sha biyu na dare, lokacin da kowanne dan adam ke nemawa haqarqarinshi mahuta. Amma ban da mu, Sakinah da Sakinah, kwance muke a gado daya kowacce da pillow a karkashin hannunta. Na soma ba ta labarin rayuwata a hannun Mami, tun daga kuruciya har girma. Auren da Abba ya yi min ina da shekaru sha biyu don kwatar min ‘yanci daga hannun Mami, da rayuwata da Mijin-Sakinah, Abdulhakim Khalil Ribadu. Na nuna mata hoton Abdulhakim cikin wayata yana cikin suit na ma’aikatan Julisu Berger ya cacume ni muna dariya. Ta dade tana kallon hoton kafin ta ajiye. Na ci gaba da gaya mata alqawarin da na ji ya yiwa matarsa na cewa ba ta yarda ya haihu dani ba don kar a yiwa ‘ya’yanta ‘yan uba, da kaini da ya yi aka zurmuqa min loopscikin umarninta, da matakin da na dauka na gayawa Abba. Shi kuma ya ce zai nemi Daddy. To har muka taho ban san hukuncin da suka yanke a kan al’amarin ba. Shiru ta yi na lokaci mai tsaho, can ta ce, “Me ya sa kika gayawa Babanki? Me yasa shi baki fito fili kin gaya mishi kin san abin da suke ciki ba? Daga nan ki ba shi dama ya baki uzurin kare kansa? Uzuri sau saba’in Allah ya ce ki yi masa kafin ki kama shi da laifi. Kishiyarki wayo ta fiki, ba matsayi a zuciyar miji ba. Kinga dai ba ta taba nuna miki ba ta sonki ba, amma a zahiri ba ta sonki. Sannan akwai sihiri irin naku na Hausawa da ake yi don a raba mace da mijinta, kamar wanda Lami take yi a baya. Ji na yi na tsani Abban ki, gara in ga mutuwata da in ganshi. Amma soyayya ta gaskiya ba ta taba gushewa. Shi sihiri ko Annabi (S.A.W) anyi masa, kuma ya cishi balle Abdulhakim. Maganin hakan shi ne, mikewa tsaye da addu’a da neman kariyar Allah. Shi sihirin yana tasiri amma abune na dan taqaitaccen lokaci, sai dai idan za ka dauwama a cikin aikata shi, amma ko ba dade ko bajima yana da karshe. Kada ki kara sama ranki wai za ki bar masoyin kwarai irin Abdulhakim saboda wata can. Kar in kara jin wannan furucin. Aure da Abdulhakim yanzu kuka fara har zuwa ranar da muka daina numfashi”.