ƘARA'IN INNA DELU 💄💄💄💄 NA MAMAN AFRAH FCW💛 Page 1⃣➡2⃣ Zaune suke kowa yana jiran tsammani, sai dai kiran da mahaifiyar tasu ta musu ta tara su, su duka abin ya basu mamaki, dan ta ƙi furta musu komai wai har sai ƙanwarsu Maryam ta ƙaraso, wacce Inna ta kira ta a kan ta zo da gaggawa lallai akwai muhimmiyar magana da za su yi.Sallamar Maryam ita ta sanya kowa ɗagowa yana kallonta. " Lale marhabin da autata, sannu autayye sannu da zuwa auta jaja manya, auta kin fi na fari, kin mabiyin na fari" Cewar Inna Delu tana tafa hannu har da rausaya kai. Abba da Baba sakin fuska suka yi ganin zuwan ƙanwar tasu wacce mahaifiyarsu da su kansu ke matuƙar ƙaunarta kasancewarta ƙanwarsu kuma autarsu Cikin murmusawa Maryam ta ƙaraso falon ta samu wuri ta zauna. "A'a dawo kusa da ni ki zauna, ina mijin nawa" Cewar Inna tana washe baki. "Ya tafi makaranta jarabawa suke" Ta faɗa tana samun wuri ta zauna ta gaishe da yayun nata da kuma Inna. Bayan an gaisa shiru ya ɗan biyo baya kafin Inna ta yi gyaran murya ta fara magana kamar haka. "Dama na tara ku ne a kan in sanar da ku abin da ke raina, kun san an ce mai zurfin ido da wuri yake fara kuka, kun san dai yau da kammala takabar mutuwar mahaifinku sati biyu, Allah jiƙan Malam ya sa kwanciya hutu ce Allah dai ya sa bai sha kulkin walakiru ba" Ta kai ƙarshen maganar tana sakin kuka. "Haba Inna yanzu fa Malam babu abin da yake buƙata sama da addu'a amma kike zancen kulki" Cewar Abba cikin ɓacin rai. "Haba Sa'adu ni ba mugun fata nake masa ba kawai dai na san aradu ya sha cinye kaji da zabbin mutane bashi, Allah ka ɓoyi muryata ba da niyyar tone-tone na yi ba, amma mahaifinku ya ƙi jinin biyan bashi, kuma na ce zamanin annabi idan mutum ya mutu in ana binsa bashi ko gawarsa ma'aikin Allah ba ya sallata, ka ga kuwa bashi musiba ne amma mahaifinku ba ya son biya ka san shi da son nama kamar maye, ko ni nan akwai lokacin da ya karɓi wata kaza, kazar nan ina sonta saboda tana min ƙwai mai yawa amma tana cikin kwancinta ya karɓa ya yanke aka masa dabgenta, tasha kalwa amma banda kai da ƙwabri babu abin da na ci a kazar nan ya lamushe, da na san ba biya na xai yi aradun Allah da cinyoyin da ƙirji zan ci innkai masa sauran, yo har ya koma ga Allah bai b... "Inna dan Allah ki bar tone-tonen nan ko ke mai biyawa Baba Malam bashi ne , kuma ma duk sai da muka tabbatar mun biya masa bashi" Cewar Baba Umar yana kallonta. "Allah sarki to na yi shiru, ai da baku wahal da kan ku ba wajen biya masa bashi yo mutumin da ya daɗe da zama ƙasa da kun bani kuɗin na sayi agwagi na yi kiwo, yo shi in azabar ce ma ai an masa... Kallon da Maryam ta mata irin na bain da kike bakya kyautawa shi ya hana ta ƙarasa maganar. "Uhm in ji mai ciwon haƙori kai da bakin ka bawa a hanaka magana, idan ma aka so raina maka hankali a ce shiriftun tsufa ne" Cewar Inna tana taɓe baki. Ta ɗora da cewa "Dama cewa na yi tunda na kammala takabar har na ƙara zaman kwanaki goma sha huɗu ina jimamin mutuwar Malam, a haka ma na danne na cije na kuma yi ta maza, amma da a ce ba a takaba dama tun washe garin kwana bakwai za a ɗaura mini aurena yo ai wanda ya mutu ya mutu kenan, amma da yake akwai ɓurɓushin takabarsa shi yasa na haƙura yo ai ko dan tumunin takaba na masa takaba, tunda yanzu na kammala takaba kuma zaman haka ya ishe ni, kar in ja muku gori a ke cewa uwarku bata da aure, kuma ake lissafa uwarku a cikin zawarawan unguwa shi ne na ce AURE zan yi... Gabaɗaya suka ɗago da mamaki a fuskarsu suna kallonta kowa bakinsa a sake "Aure Inna?" Suka haɗa baki wurin faɗa. "Kai ɗiyan nan ku maida mamakin da na baku, aure mana ko baku ji mai na ce ba, kuke maimaitawa kamar wanda nake biya muku karatun allo, haba ɗiyan nan aure fa na ce sunnar ma'aiki, ko akwai wanda zai ja da sunnar ma'aikin Allah" Ta faɗa tana rausayar da kai ganin kamar dai za a sha fama da su. "Inna kin san kuwa mai kike faɗa, aure fa kika ce, yanzu shekara saba'in mai kuma ya rage miki sama da ki tsaya ki yi ibadar sallah da salatin annabi... "Ungo nan Sa'adu" Cewar Inna tana watsa masa yatsunta biyar alamar daƙuwa da sauri ya sunkuyar da kansa ƙasa "Yau na ga abin da ya turewa buzu naɗi, ni Delu yanzu Sa'adu ni kake cewa ban san abin da nake faɗa ba, wato ga mahaukaciya mai taɓin hankali, wato shekara saba'in mai ya rage mini sai sallah da salatin annabi yo ce maka aka yi bana yinsu ai ko auren ma ibada ce mai zaman kanta Allah na tuba da in zauna in mutu bazawara ai gwara in mutu a ɗakin mijina ko ruwan wanka da na alwala nake kai masa bayi mai na manta, ai ya fi dai a ce zaune nake ba miji, kai in taƙaita muku wallahi ko tsarkin kashi ya ce in masa tatas zan wanke masa mazaunansa yo ai duk a cikin soyayya da ibada ne, bare ma ku ne kuke mini kallon na tsufa, amma ni nan da kuke gani wallahi da saurana babu abin da ba zan iya ba a gidan aure, daga sama har ƙasa ban tsufa ba yo Allah na tuba ai ni irin matan nan ne da ake kira DAKI BARI... "Haba Inna me yasa kike haka dan Allah mu fa ƴaƴanki ne me ya kawo maganar daki bari kamar wata atamfa" "Yo Maryama da bakina ba ɗinke min aka yi ba a hana ni faɗar gaskiya ko ku ƴaƴana ne ai ina da ƴancin faɗar abin da ke raina, gani na yi ana mini kallon na yi tsufan da bani da mamora, har kya yi maganar atamfa ma wacce shekara uku ta mutu, amma ni nan shekarata hamsun da bakwai ina gidan ubanku amma yanzu nake son ƙara aure kin ga luwa ubanku ya daka ya bari Jauro ma zai ɗora daga inda ya tsaya, dan ni na san kamar yadda ƴar shekara ashirin za ta moru a wurin miji a gidan aurenta ta kowane ɓangare haka ni ma zan moru, aradun Allah Maryama ku yarda dani da saurana, zamzam nake wallahi abin da na sani makusa a jikina wallahi ɗiyar nan mashaya ce (Nono) Amma mafitar ɗa (HQ), yana nan tsut a tsuke kamar ba ni na haifeku ba, mashayar ce dai ni kaina na san akwai matsala yo dama nono ba kwalifi gareshi (quality) Abu ne ya jagule yanyi jalele kamar alalar gero, duk ya tauye ya yamutse amma Allah na tuba mai gyara ya bari har mafitar ɗan ma sai a nemi abin gyara yo na san dai kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan kwano, tuni Maryam kina rakani kasuwar kayan gyara muka samo maida tsohuwa yarinya na gyara ko ina daga na shiga ɗakin mijin kirif za ki ji an rufe bakinsa yp gyara mai ya bari komai yana so gyara, yo ango ɗiɗif zai yi, ya ji abu zamzam" Cewar Inna tana murmushin tare da ɗan kauda kai tana ɗan sussunkuyarwa ita ala dole ta ɗan ji kunyar furucin da ta yi. "INNA!!!" Cewar Maryam da takaici ya hana ta magana ga kunyar yayunta Abba da Baba da suke zaune, jin nauyin maganar Inna ya sanya sun yi ɗif kamar ruwa ya ci su. "Allahu akbar kabiran wallahi Maryama sai yanzu na ankara, duk sai na ji kunyar ku ta baibaiyeni, yo kin san ni ƴar gaskiya ce kuma an ce in zaka faɗi faɗi gaskiya, kuma dai da na ga auren nan ba haramun bane, kuma kuna kawo ƙauli da ba a di kinga sai na zage dantse na muku biyani yadda zaku fahimta, kin ga kuwa dole na yi iya yina na fahimtar da ku da akwai mamora a tare da ni, kuma dai kun ga ni ma zan so in ƙara muku ƴan ƙanne tun da ku uku rak na haifa bare ke, ke kaɗai ce mace kina buƙatar abokiyar shawara, tun da auren nan ma'aikin Allah S.A .W ya ce mu yi aure dan mu hayayyafa domin ya yi alfahri da mu" "Wai Inna me kike nufi ne?" Maryam ta tambaya kamar za ta yi kuka. "Ka ji ja'irar yarinya, da hausa fa nake magana sai wani hanya -hanya kuke kuna kaucewa to tun da haka kuke so bari na muku gwari-gwari a harshen hausa da aure kowa ya san mai ake nufi da shi tun da kaf ɗinku babu wanda bai san auren lanjane na yi da mahaifinku ba, dan auren marigayin ubanku sunansa kaɗan ya fi zawarci, kun san dai Jauro shi ne zaɓina.... "Inna" Cewar Umar fuskarsa na nuni da tsantsar jin haushin abin da Innar ke faɗa. "Na'am Umaru faɗi ina jinka, dan wallahi faɗarka ba faɗar annabi bace tuni zan saka ƙafata na yi fatali da kai da maganarka matsawar dai ba baya za ka goya mini in yi abin da raina ke buri ba, yo ƙarya zan muku abu da auren dole ne aka laƙaba mini uban naku tun yana almajirci bai zama Malam ɗin ba" Ta faɗa tana kallonsa ido cikin ido dan kar ma ya yi zaton za ta ji kunyarsa ta ɗan fari ta fasa kudurinta na auren ƙara'i "Inna a kan maganar wai auren nan da kike faɗa haba dan Allah... "Kai Umaru sa idanunka cikin nawa da kyau aure na ya fi ƙarfin wai, dan wallahi ko budurwa dal a leda ba za ta cewa aure na wai ba, dan aurena dai dai yake da nata na saurayi da budurwa wataƙila ma nawa ya fi armashi da moruwa ko dan saboda tsohuwar zumar soyayyar da nake yiwa wanda zan aura ɗin, soyayya ce mai ruwa-ruwa wacce ta daɗe tana iyo a cikin gogin raina, duk ta bi ta sanya mini rauni a zuciya kunsan so da raunana zuciyar mai yinsa duk girman mutum sai ya so ya mayar masa da zuciyarsa ɗanya sharaf kamar ta jaririn da ya sunkuto daga mahaifar uwarsa yanzu... "Inna!!!" Cewar Sa'adu da ya miƙe tsaye kamar an tsikareshi yadda furucin Innar ke masa dirar mikiya a kunnuwansa shi kansa bai sa ya tashi ba sai ganinsa ya yi a tsaye cankarkar. "Sa'aduuuu" Ita ma ta faɗa tana miƙewa tsaye har zaninta na kuncewa ta kama ta ɗaureshi gamgam. "Inna maganar auren nan ki daina yi dan Allah ko daɗin ji ma babu yanzu dan Allah a ce daga gama takaba da sati biyu sai ki ce wai aure za ki yi, mahaifinmu ko shekara bai yi ba a ƙasa amma dan Allah Inna da girmanki a ce wai kina maganar ƙara aure. "HHHH na dawo in ji ɗan yawon duniya yo Umaru cewa za ka yi marigayin ubanku kuke tayawa kishi bayan yana can rufe a cikin ƙasa,Allah na tuba a nunawa na ringingine farin wata, yo kalle ni da kyau ka gani dangargar nake ji na kamar saurayi sabon balaga, amma kowa dama da kiwon da ya karɓeshi maƙocin mai akuya ya sayi kura, ni babu ni babu Malam Lawwali mahaifinku, mutuwa ce ya mutu tsakaninmu kuwa takaba ce ko a musulunci idan na gama takaba ko da kwana ɗaya ne zan iya yin aure, babu inda addini ya haramta kuma addini ba ruwansa da tsufana, ko akwai wanda zai faɗa mini inda aka haramta auren tsohuwa???" Ta jefa musu tambayar tana tsatstsare su da ido. Babu wanda ya tanka dan sun rasa bakin magana. "Kun gani, baku da amsa to tunda ba faɗin Allah bane ba na ma'aikinsa ba babu wanda zai taka mini birki duk cikin ku, in banda ma sabo da yi gawa da gatsine ina za a haɗa wanda ke doron duniya da kuma wanda ke can ƙasa a ƙumshe ya gama zagwanyewa... "Inna fata nagari lamiri" "To na ji ubana Umaru in kuma duka zaka saka to aiki Maryama ta samo maka kirfo(Bulala ko madoki)" "Ni ba haka bane amma gaskiya ki janye maganar aure dan duk wanda ma ya ji maganar nan mu za a zaga a ce mu ne ƴaƴanki muna gani... "Yo a faɗa mana zagi kuma a zageku tun da dai zagi baya fitowa a jiki,duk da an ce ba a ƙin ta mutane wai an ce wa ɓarawo ya gudu, amma ni dai na san duk wanda ma ya zage ku ya ɗauki alhakinku dan ni ce mai aure, sai ka ce wanda na ce zan fara karuwanci, to aure dai kuma babu wanda ya isa ya taka mini birki duk duniya sai dai in ni Delu bana numfashi" Ta faɗa tana bugar ƙirjinta. "Haba Inna wai shin mai kike so mu miki? Mai kika nema kika rasa da zaki mana wannan abin dan Allah " Maryam ta faɗa tana sakin kuka. "Maryama goge hawayenki kar ki yi asarar zubar da su, dan indai dan in saduda ne in ji tausayinki to ba zan ji ba tun da ni ma baku ji tausayina na luguden da zuciyata take yi ba, kullum bugawa take tana kiran Jauro, Jauro, wallahi auren ƙara'i dai tsakani na da jauro babu fashi har sai na ji an ce alfatiya, sannan hankalina zai kwanta duk wanda kuma ya ce zai hana ga wurin nan dan ta yaro kyau take bata ƙarko!" "INNA zan biya miki umara idan kika fasa auren nan" Sa'adu ya faɗa da ƙarfin gwiwarsa dan sai yanzu ma ya tuna lagom mahaifiyar tasu, dan tana mutuwar son zuwa makka duk da ta je ta koma. "Yanzu dai na je hajj ita ce farilla, umara kuwa zuwana ya fi a ƙirga to ko ban taɓa zuwa umara ba gwara in auri Jauro wataƙila ya mini tukuici da amarcin darenmu na farko ya biya mini umarar " Ta faɗa tana ɗan darawa Da sauri Sa'adu ya zauna daɓas jiki ba ƙwari dan yana ganin mahaifiyar tasu ta yi nisa ba lallai ta ji kira ba! 🤚😃🤚😃🤚😃🤚 ƘARA'IN INNA DELU 💄💄💄💄 NA MAMAN AFRAH ƘARA'IN INNA DELU 💄💄💄💄 NA MAMAN AFRAH FCW💛 Page3⃣➡4⃣ "Inna kamar yadda kike da haƙƙi a kan mu, na mu miki abin da kike so mu ma fa muna da haƙƙi a kan ki, dan haka daga cikin haƙƙoƙinmu da ke kan ki, kar ki zubar mana da mutuncinmu tare da ja mana zagi a gari" Cewar Baba Umar yana ɓata rai tare da kauda kai gefe. "Au Allah, Umaru to tsakanin haƙƙin uwa da haƙƙin ɗa wanne ya fi ƙarfi, ba cewa aka yi a yiwa uwa biyayya har sai da Allah ya faɗa sau uku kafin ma a ce a bi uba kuma sau ɗaya Allah ya faɗa, to ka ga ba a haɗa ni da ubanka Malam ba ma a wajen yi mana biyayya bare kuma a haɗa ni da kai, kuma idan maganar zagi ce an daɗe ba a zage ku ba amma ku sani aure wallahi tallahi babu fashi sai an ɗaura shi, sai dai ɗan baƙinciki ya mutu arqur'ani kwa" Ta faɗa tana tafa hannu a cinya tare da komawa mazauninta ta zauna tana hararar Maryam da ke ta sharar ƙwallah. "Ke matsa daga kusa dani uwar ƴan arahar hawaye, dan uwaki za ta ƙara aurar sabon miji ki samu wani uban ki huta da maraici shi ne kika zauna kina kuka kamar dai an ce na mutu, ko kuma an ce ke za a yiwa kishiyar" Inna ta faɗa tana taɓe baki.Maryam kuwa kamar Inna ta zuga ta sai kawai ta ƙara volume ɗin kukanta. "Affafadaran to wallahi sai ko in kin koma gidanki mijinki ya yi aikin lallashi, ko in kin je ya ga idanunki luhu-luhu ya tambayeki dalilin kukan, kin ga sai ki ji daɗin ce masa Inna ce ta samu bazawari son kowa ƙin wanda bai samu ba za ta galla aure shi ne kike kuka kin ga sai ya ce baƙinciki kike mini" Ta faɗa tana miƙa hannu ta ɗauki ledar goranta a kan kujerar ta since ta ɗauki ɗaya ta mayar ta ƙulle ta ɓalgata ta shiga taunawa hankali kwance. "Inna!" "Umaru" "Inna ki janye maganar auren nan" Ya faɗa cikin ɓacin rai da murya mai kamar yana bata umarni. "Iko sai rabbani Umaru ni kake aikowa saƙon harara, kamar wata kishiyar uwarka, to na gode, amma ba bansan harara ba sai dio ya faɗu, kuma in ce dai ka fitar da ni daga matsayin uwarka, shi yasa kake wannan muzuran har kana bani uwarni kamar kai ne uwar ni ce ɗan, to wallahi ko ubanka Lawwali, zai dawo daga lahira bai isa in fasa auren nan ba bare kai cacakurukuci cikon banci, banda ma rashin tunani ni da aka mini auren dole da ubanku na haƙura na zauna da shi shekara da shekaru da ƙiyayyarsa a zuciyata kuma yanzu dan ya margaya(mutu) Sai a hanani rawar gaban hantsi" "Inna ba na son maganar auren nan gaskiya matsawar dai mu ne ƴaƴanki to dole ki haƙura" Baba ya faɗa yana kallonta, shi dai Abba tun da ya zauna bai kuma magana ba. "Umaru, biyani nono na da na shayar da kai, aradun Allah gwara na sheƙa masa ruwa na yi kindirmo(Nono) tun da ni kake so na maka biyayya ba wai kai bane za ka mini biyayya ba" "Ni ba haka nake nufi ba" "Yo in ba haka kake nufi ba menene ba dai ni bace kake rainawa har muke faɗi in faɗa, to ni kuwa ni ce ƙofar shigarka aljanna, ka ga wannan ƙafartawa mai faso da kaushi kana ganinta kamar kofaton doki wallahi ita zan ɗaga ka shiga aljanna" Ta faɗa tana ɗage ƙafarta ta nuna masa. Gabaɗaya sun kasa gane ta inda za su ɓullowa Innar kowa sai ya zuba mata ido tana ta taunar goro abinta, zuwa can, Abba Sa'adu ya zamo daga kan kujera ya nufi wajen Inna da rarrafe, shi ma Baba Umar sakkowa ya yi ya nufi wanjenta gwiwarsa a ƙasa yana rarrafe, Maryam ma ganin haka sai ta sakko daga kujera ta durƙusa a kan gwiwoyinta. Su duka kuka suka saka mata kamar ƙananan yara, Inna kuwa baki sake take kallonsu dan ko a jikinta kukan da suke ita dai aurenta na ƙara'i babu abin da zai sanya ta fasa. Ai Inna ma sai gani suka yi bidik ta sakko ƙasan ta durƙusa kamar yadda suka yi gabaɗaya sai kowa ya tsayar da kukan da yake suka shiga kallonta. Fashewa ta yi da wani irin kuka mai jiniya wanda ya fi nasu su duka ukun, tun da ta ɓare bakinta bata rufe ba kuka kawai take zabgawa kamar wanda aka bata umarni. Yin nan take babu ƙaƙƙautawa sun rasa ma bakin magana. "Inna menene" Maryam ta yi ƙarfin halin jefa mata tambayar cikin shaƙeƙƙiyar muryarra da bata fita sosai saboda kukan da ta yi. Maimakon Inna ta bata amsa sai kawai ta ƙara gudu da kuma ƙaran kukan nata.Tun suna lallashinta har suka yi shiru gabaɗaya tausayinta ya kama su dan su duk tunaninsu ko iyayenta ta tuna take kukan, falon ya yi tsit baka jin komai sai kukanta zuwa can. "Dan Allah Inna ki daina kukan nan baki ji ba yadda duk kika karya mana zuciya, su kaka babu abin da suke buƙata sama da addu'a" Cewar Baba yana kallon Inna da tausayawa. "Ba batun mutuwa bane ɗan nan, duk da an ce ana bikin duniya ake na ƙiyama amma yau dai iya duniyar ne" "Ikon Allah, ba su kaka kika tuna ba dama" Abba ya jefa mata tambayar. "Allah sarki Inna Baba Malam ta tuna ai dama ko ba komai akwai sabo sa... Wani kallo da Inna ta bi Maryam da shi, shi ne abin da ya hanata ƙarasa maganar. "Waye Malam kuma, in ce dai yanzu aka ambaci uwata da ubana na ce ba su nake yiwa kuka ba, kuma sai ki ce wani Malam" Ta faɗa tana ƙara rushewa da kukan. "Dan Allah to Inna ki faɗa mana tun da duk abubuwan da muke zato ba su bane" Baba ya faɗa yana kallonta har lokacin su duka ukun sun akan gwiwoyinsu ciki kuwa har da Inna da ke da rasgar kuka. "To ku yi shiru zan faɗa, tun da kun takurani" "Allah sarki Inna" Suka faɗa a zuciyarsu suna jin wani daɗi dan duk tunninsu cewa za ta yi ta haƙura da auren tun da suna kuka shi yasa take kuka dan ta fasa auren. "Faɗi mana Inna" Cewar Maryam tana washe haƙora dan ita tafi su Abba shiga damuwa dan ta san matsawar dai Inna ta yi auren na to fa dangin mijinta sai sun rinƙa goranta mata a kan uwarta mai budurwar zuciya, shi kansa mijin nata ta san wataran zai iya mata gori. "Zan faɗa ɗiyar nan" Cewar Inna tana ɗan kauda kai gefe tana ɗan murmushi. "Dama, dama, dama" "Dama me Inna" Cewar Abba haƙoransa a buɗe dan shi ma ya gama jango jirgin Inna cewa za ta yi ta fasa auren. "Kai wallahi sai zan faɗa sai kuma in ji kunya ta rufe ni" Ta faɗa tana ɗan kallon ƴaƴan nata. "Inna mu fa ƴaƴanki ne babu wata kunya" Baba ya ce shi ma yana ƴar dariya, tarw da kannewa ƴan uwansa ido dan ya san mahaifiyarsu ta fasa aure take son cewa. "I LOBIYU (I LOVE U) Ta faɗa tana rufe fuskarta da hannunta. Wani daɗi ne ya ziyarce su jin abin da ta faɗa, dan sun ɗauka ma sai ta ce tana son nasu sannan ta ce ta janye maganar auren. "Wallahi kukan daɗi nake ɗiyan nan, duk lokacin da na tuna kalamar I LOBIYU (I LOVE U) Sai in ji wani daɗi da farinciki marar misaltuwa" "Allah sarki Inna" Suka haɗa baki wajen faɗa. "Wallahi ƴaƴan nan wannan kalma ce da Jauro ya faɗa mini tun ina budurwa, kalmar nan ce kullum ke kwaɗaitar da ni zuwa ga aurensa domin ina da yaƙinin zai rinƙa faɗa mini ita idan mun yi aure, dan safe da yamma zan ce masa yake faɗa mini saboda yadda take faranta mini rai, shi yasa nake kwaɗayin aurensa dan idan zai faɗi kalmar nan har wani gunna yake mata yadda za ta ƙara garɗi a bakinsa zuwa cikin kunnuwana, wallahi ya fi ubanku iya soyayya nesa ba ma kusa ba, ka san shi ubanku ban da Deluna babu wani abu da ya iya na jan hankalin mace, sai shigen son raya sunna kamar ɗan taure gashi babu wani armashi a gabatar da sunnar tashi, shi yasa kawai zama da shi alal larurati, yo ya zanyi tun da ya zame mini ƙarfen ƙafa, kullum sai dai yake rubutu yana bani wai dan ya zaunar dani a gidansa bai san ba tun da bai iya soyayya ba shi da sakainar kashi ɗaya suke a wuri... Tunda ta fara wannan bayanin sai suka yi ɗif kamar babu kowa a falon, su duka banda lazimi babu abinda suke dan sun gama fahimtar lamarin Inna addu'a ce kawai za ta musu maganinsa. Haka suka tashi daga durƙuson da suka yi dan sun lura babu wani amfanin yin hakan, da haka suka mata sallamar za su je masallacin la'asar ita ma bata bi ta kansu ba sai dai ta sa nya a ranta ko ana ha maza ha mata aurenta da Jauro bbu fashi. Maryam ma haka ta tashi ta tafi ɓangaren matan gidan dan bata ma jin za ta cigaba da zama Inna tana ta maimaita zancen da bashi da kai bate ƙafa. *DA LA'ASAR LIS* Inna tana zaune a falo ta ɗora ƙafarta ɗaya kan ɗaya sai farantin kankana irin mai jan nan kuma mai yashi tana sha tana lunshe ido saboda zaƙi ga kuma sanyi da kankanar ta ɗauka. "Allah sarki Jaurona da kana kusa da a baki zan ke baka irin na turawa, shi yasa na ƙosa mu yi auren nan dan mu yi ƘARA'I babu kama hannun yaro, amma dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama yaran nan suna neman kawo mana cikas sabo... Sallamar Abba, Baba, da kuma abokansu tun na yarinta wanda suke a ƙauyensu kafin yanzu su ma a Kanon suke zaune da iyalansu amma ƙauyensu ɗaya da su Inna, ita ma Maryam dama a hannun su Abba ta taso a Kano ta yi karatun ta da ta kammala fa samu miji sai aka mata aurenta, yanzu haka suna da ɗa ɗan shekara takwas. Baki washe Inna ta amsa tana kallonsu, dan ita a ranta har ta gama ƙiyasta za ta faɗawa abokan nasu ƙudurinta na son yin aure da ƴaƴan nata ke son hana ta duk da ta nuna musu basu isa ba amma tana ganin idan abokan nasu sun faɗa musu ko su sa ji maganarsu tun da suna mata ganin ta tsufa, su sa banbance da sauran ta. "Marhababin da su Rabilu sannunku da zuwa" Cewar Inna tana washe baki har kunne dan ta hango burinta na dab da cika tun da su Rabilu sun zo to tabbas faɗuwa ta zo dai dai da zama. Bayan sun zazzauna suka shiga gaishe da Inna ta amsa musu tana musu faɗan basa son zumunci wai rabon da ta gansu tun da suka je yi mata gaisuwar Malam. Haka sai suka ɗan kare kansu a kan aiyuka ne suka musu yawa. Bayan shiru ya ɗan gifta Inna tana raya ta inda za ta fara sai kawai ta ji Kamal ya fara gyaran murya ya fara magana. "Inna dama mun zo ne a kan wata muhimmiyar magana, da su Umar suka same mu da ita, a kan mu zo ko Allah zai sa a sasanta mu shawo kan lamarin" Ya faɗa cikin ladabi yana kallon Inna wanda tun da ya farw magana ta wani yatsina fuska tare da mere baki tana kallonsa dan tun kan ya kai aya ta gama harbo jirginsa ta ƙyaleshi ne kawai ya ƙarasa dan kar ta katse masa hanzari. "Haka ne Inna ai maganar aure ma bai taso ba, haƙuri za ki yi tunda kin ga yanzu Baba Malam ko cikon shekara ba a masa ba, babu zancen cikon shekara tun da ko wata biyar bai ƙarasa ba, kai koda ma a ce ya yi shekaru goma ne da rasuwa bai kamata a ce kin yi wani auren ba tun da kin riga kin manyanta, bare kuma a ce ko jimawa baki yi da kammala takaba ba wannan sai ya zama abin faɗa a wurin jama'a kuma ko ba komai ko dan ƴaƴanki ai kya janye maganar auren nan" Rabilu ya kai ƙarshen maganar a dai dai lokacin da Maryam ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama, amsa mata suka yi ta gaishe da su Rabilun ta nemi wuri ta zauna tana jin wani daɗi a ranta dan ta san dai magana ta ƙare tun da dai Inna ta ga abokan su Abba. Tun da Rabilu ya ɗora daga inda Kamal ɗin ya tsaya Inna ta yi tagumi da ɗaya hannunta ɗayan kuma tana riƙe da gutsuren kankanarta da ta riƙe mamaki ma ya hanata magana. Ganin da suka yi ta kifa uban tagumi duk tunaninsu maganar da aka yi ce ta shigeta har sun fara tunanin tsuntsunsu ya kama tarko. Sai da Rabilu ya kai aya Inna ta ɗauke hannunta daga tagumin da ta yi, ta kai kankanarta ta saka a bakinta har da lunshe ido, sai da ta tauna ta haɗiye abinta ta suɗe yatsunta ta maida kallonta gare su ta ce "Kamalu, Rabilu, kun gama jawabin naku, in ce dai duk a kan magana ɗaya kuka kwaso ƙafa kuka zo nan?" Kallon kallo aka shiga tsakanin su Baba da su Rabilu ita dai tun da ta jefa ayar tambaya bata sake cewa komai ba. "Bani amsa mana" Ta faɗa tana ɗan muskuwata a kan kujera. "Eh Inna" Cewar Rabilu jiki ba ƙwari dan bai ga alamar akwai sauƙi a tattare da Inna ba. "To duk cikinku babu wanda ya isa ya dakatar da ni, wato su sun kasa shawo kaina shi ne suka je sula taho daku, ku kuma kuka ɗakko ƙafa ya sillen kara, kai kana tura ƙeya kamar gafiya ta so shiga rami" Ta faɗa tana kallon Kamal da ya sunkuyar da kai tsabar ba ar da Inna ta masa. "Kai kuma ka ɗauki fuska kamar farantin tallar kukar kaɗi, kana ɗaga dogon wuyanka mai kama da mariƙin lema "Unbrella) Tambayar da zan muku uwaku Talatu bayan mutuwar ubanku aure nawa ta ƙara?" Ta faɗa tana tsare su da ido, babu wanda ya tanka mata dan haka sai ta ɗora da cewa "Tunda ba za ka bani amsa ba, dan na ga ba niyya ango ya kwana da wando, tun da kun ƙi magana kun ƙunshe baki kamar amaryar da bata kai budurci gidan miji ba, bari ni in baku amsar, Talatu bayan mutuwar ubanku sai da ta yi aure-aure, sai da ta ƙara aure uku rigis, fir taƙi zama a gidan mijin da ta aura na farko bayan mutuwar uban naku, taƙi zama ne kuwa dan bashi da kataɓus a wajen gabatar da sunna. Bayan ta fito daga gidansa ta sake sabon aure amma saboda mijin baya gamsheta(Gamsar da ita) Ta fito dan cewa ta yi shi da lagwanin fitila babu banbanci yo cewa fa ta yi abar tasa ce jalele kamar hanjin ɗan tsako. Sai a gidan mijin na uku ne ta zauna har yau tana can dan cewa ta yi zama daram ita da shi mutukaraba takalmin kaza yo ai a can ne ta samu abin da take so me ya hana ku hanata lokacin da take aure-auren ? Shi ne dan rashin ta ido ni kuka zo za ku mini sagegeduwa wato in ƙare a gantale ba aure, na zo a sadaka in koma a alakoro, to wallahi haka ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa dan aurena da Jauro kamar an ɗaura taminjau" Ta faɗa tana binsu su duka da kallo. "Dan Allah Inna ba dan mu ba" Baba ya faɗa kamar zai yi kuka. "Kai rufe mini baki, ba waɗannn ka ɗakko ba kana ganin kamar su za su saka ni abin da ban yi niyya ba, to duk cikinku babu wanda ya isa ya tauye mini haƙƙi, ni babu wanda na hana ya ƙara aure a cikin ku ko mata huɗu kuke so babu mai hana ku, amma duk wanda ya ce ni zai hana rawar gaban hantsi, to mu zuba shege ka fasa ɗan halak sai yanka, kuma duk wanda ya ƙara yunƙurin hana ni aure sai na saka ya saki matarsa ya zauna a gauro ya ji idan zama haka ba aure da daɗi" Ta faɗa tana miƙa hannu ta ɗauki kankan ɗaya ta kai bakinta har ruwan na gangarowa daga bakin nata ta saka harshe ta suɗe. Tun da ta yi maganaar sakin matansu sai duk suka shiga taitayinsu, babu wansa ya ƙara magana. "Ke ma kuma in sak naki mijin ya sake ki sai ki dawo mu zauna a tare" Ta faɗa tana kallon Maryam da gabanta ya buga jin furucin Inna na saki. Haka sai su Rabilu suka yiwa Inna sallama suka fice sumi-sumi su da su Abba, Maryam kuma bedroom ɗin Inna ta kwanra tana jiran mijinta ya zo ya ɗauketa su tafi, dan sun yi magana ya ce zai zo bayan magriba saboda ta gaji da abubuwan nan da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa, dan har alla alla take a gama maganar kafin mijin nata ya zo dan bata so ko ɓurɓushin maganar ya tarar a barta da abin kunya. Inna kuwa ko ta kanta bata bi ba dan ta yi alƙawarin babu wanda za ta saurarawa matsawar dai babu wanda zai goyi bayanta. BAYAN MAGRIBA Zaune suke a falo su uku Inna tana kan sallaya ta miƙe ƙafafunta tana jan carbi dan tun da ta idar da sallar magariba bata tashi daga wurin ba. Sai Maryam da Amna da suke cin abinci a falon suna hira abinsu, bayan sun kammmala Amna ta kwashe kwanukan ta kai kicin ya cewa Maryam "Aunty bari in je zan yi karatu" "To my Amna a yi karatu da yawa, sai yaushe za ki je gidan nawa kuma?" "Sai dai idan na samu lokaci dan yanzu makarantar boko da islamiya babu hutu amma zan zo" "To Allah taimaka ya baku sa'a sai kin zo ɗin ina zuba ido" Cewar Maryam tana kallon ƴar wan nata. Fita Amna ta yi wanda hakan ya yi dai dai da shigowar mijin Aunty Maryam ɗin sa sallama cikin ɗan sakin fuska Inna ta amsa masa saboda ta san ko ba komai idan zai tafi yana bata kuɗi sababbi Inna kuwa akwai son sabon kuɗi dan wano lokacin ma sai ta yi ta ajiyarsu kamar wanda za ta rataya a wuya wai bata son kashe sabon kuɗi ƘARA'IN INNA DELU 💄💄💄💄 NA MAMAN AFRAH FCW Page5⃣➡6⃣ Ƙarasowa ya yi ya zauna Inna tana ta washe baki tare da masa marhabin. Bayan ya gaisheta take tambayarsa ɗan gidan Maryam ɗin yake sanar da ita ai daga makaranta gidan mahaifiyrsa ya wuce. 'Yo ke ko ruwa bakya kawo masa ba kika zauna kina wani zumu-zumu da baki kamar shazumamu ya samu sikari" Cewar Inna da ta lura da ɓacin ran da maryam ɗin ke yi tun shigowar mijin nata ita dai ta san dalilinta ma yin hakan. Ruwan ta tafi ta ɗakko masa a plate ta kawo masa tare da masa sanju da zuwa cikin sakin fuska ya amsa yana ɗaukan ruwan ya tilla ya sha ya mayar da ledar kan plate ɗin da yake pure water ne. "Wannan matar taka ta koyi mugun hali wallahi" "Mugun hali kuma Inna?" "Eh mana kai vaka lura sa muzuran da take ba tun shigowarka ai ko idanunta ka kalla za ka ga sun yi luhu-luhu, to kuka ne ta yi ta garƙawa kamar da ranar sa ubanta Malam ya bar duniya" "Subhanallahi mai ya yi zafi Inna" Ya tambaya da mamaki. "Maza Maryama ki yi ta hararata amma wallahi harararki ba za fa hana ni faɗin abin da ke raina ba" Cewar Inna tana wani gatsina fuska. Jin haka Maryam ta tashi fa sauri ta shige ɗaki dan ta san yun da Inna za ta fara magana babu mai taka mata birki sai ta ida amma dai ta san yau abin kunya ne ta gama ja mata a wajen mijinta "Inna idan laifi ta miki ai sai ki ja mata kunne... "Yi shiru ɗan nan bakinka alekum, ai ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wajen faɗa maka komai da komai ba in yaso ko addu'a ce sai ka taya ni a kan Allah ya mini mafita ya ganar da yaran nan gaskiya gaskiya ce ƙarya kuma ɓata ce" Ta katse shi tana rattabo bayaninta. "Yarinyar nan Maryama da ƴan uwanta ne suke son yin kisan kai... "Subhanallahi, kisan kai fa Inna amma dai na tattabara ko?" "Kai dallah ja can, ana maka maganar mutane kana ɓaganar tsuntsaye, to bari na maka gwari-gwari dan na tuna kisan zuciyoyi ya kamata in ce" "Inna ban fahimta, sai ƙara ɓatar da ni kike, kin ce kisan kai kin ce na zuciya... "Na gama shiryawa" Cewar Maryam da ta ɗakko jakarta ta fito daga ɗaki dan duk abin da ake faɗa tana jin su. "To uwa gwadaga babu inda zai je sai na gama faɗa masa abin da ke raina wato shi ne kika ɗakko wata shegiyar jakarki mai kama da zabirar aski, wai kin gama to sai dai ki jira shi ya gama shi ma" "Haba Inna "Ta faɗa taa zunɓura baki tare da komawa ɗaki dan ta ga mijin nata ya saki baki cikin rashin fahimtar takamaiman abin da ke faruwa. 'Ɗan nan ina kai ka, kana jina, Maryma da Yayunta su ne suke so su daƙushe zuciyoyi guda biyu haka kawai fa dan na ce zan yi aure, saboda son tauye mimi haƙƙi da kuma neman dalili suke so su dakatar dani wai na tsufa, dan na tarasu na sanar musu tunda na kammala takaba in yi aure, ni ma in huta idan da rabon haihuwa ma ba sai a yiwa mai ɗakin naka ƙanwa ko ƙani ba, to fir suka ƙi yo daɗi ta musu ake lissafani cikin zawarawa bayan ga ƴan matan nan da zawarawa sun rasa mazajen aure amma ni Allah ya bani mijina a hannu amma dan kawai su shiga haƙƙina sai su ce babu maganar aure wai sai dai in zauna in ke sallah da salatin annabi kaar da can ba na yi. Ai gwara dai in mutu a ɗakin aurena, in banda ƙoƙari faɗawa mijin baya tariya, meye a ido banda ruwa, abu lami ba ɗaci ba, banda ma ɗaukan alhaki ɗanka ya hanaka sunnar ma'aiki, to shi ne na ce ko kai za ka mini WALI (Alwali) Cewar Inna tana kafe sirikin nata da ido dan shi tun daga lokacin da ta ambaci aure ya saki baki yake kallonfa dan har ta gama leɓɓansa bash haɗu ba suna nan a buɗe. "Kai ko kaima mijin ta ce ne, yo ya za a yi in zaunar da kai ina faɗa maka magana sai ka saki baki sharam ya layar mai tafiya kana kallona, ko baka fahimci inda maganar ta dosa bane na maka gwari-gwari" "Eh Inna haka ne dama ai" "Sammani anya kuwa cikin hayyacinka kake ko dai ka farw shaye-shaye ne, ya xa a yi in taƙarƙare in zabgo maka bayanai rututu amma ka kasa bani gamshashshiyar amsa sai ka ce wai eh Inna haka ne" Ta faɗa tana mere baki tate da maimaita abin da ya faɗa ta hanyar kwaikwayar muryartasa. "Ko ɗaya Inna babu abin fa nake sha" "A'a yo ni ai ban ga alamar hakan ba, yo wannan ai ba shawara bace ba kuma mafita bace ka bani Allah na tuba wannan magana taka akwai ya babu kakar wajen uba, ina so in ji ka zage kana rattabo bayanai sai kwai ka ɓige da eh Inna haka ne, tashi ku je Allah bamu alheri dan na ga kai da matartaka halinku ɗaya bakwa son ƙaruwata tun da kuwa haka ne sai ko ka ga katin gayyata dan aure babu fashi ko ana ha maza ha mata. Sammani kamar jira yake ya miƙe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa, dan shi gabaɗaya yadda kansa ya ɗaure da maganar Innar idan da a ce mahaifiyarsa ce ta zo da wannan maganar ai sai dai ya zauna ya yi ta girka kuka saboda bai san mafita ba a ce mace tsofai-tsofai da ke kina maganar ƙara aure daga mutuwar mijinki. Haka dai ya sanya hannu a aljihu ya ɗakko rafar ƴan ɗari biyu ya ajiye mata a gabanta ya ce "Gashi Inna kya sayi goro" "Ikon Allah yo kai kuma Sammani a yi haka, har da kuɗin goro kamar yadda aka saba ai da ka barshi a haɗu a gaba tunda ga abu nan ya taho kar wahalar ta yi yawa" "Menene ya taho" "Yo har ka tambaya ma kai da yanzu na gama baka labarin zan yi aure ai ko dan saboda haɗa gudunmuwa da ka bat na goron a haɗu a gudunmuwar fan wallahi biki zan karɓa babu babbba ba yaro ba ɗa ba siriki... Kafin ta kai aya Maryam ta daɗe da ficewa saboda takaici. "To Inna ai duk ba zai gagara ba" Cewar Sammani cikin ɗan jin nauyi. "Allahu akbar kabiran to ai shikenan Allah nuna mana dama da na ga ba wani lokaci za a ɗauka ba" Shi dai ba sake cewa komai ba ya saka kai ya fice Da dare Inna ta sanya aka kira mata mamar Amna da Mamar Abubakar, bayan sun zo sun gaisheta cikin girmamawa ta kalle su a shelaƙe ta ce "Na kirawo ku ne dan in sanar da ku abin da baku sani ba, idan ma ku ne kuke sonnshiga tsakani na da ƴaƴana to ku sani watan komawarku gidajen iyayenku wato ƙauye za ta ɗauke ku" Cikin rashin fahimta suke bin Inna da kallo wacce ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana musu kallon ɗai - ɗai "Inna mai ya yi zafi kuma shi ba wuta ba" "Kwa santa munfukan banza, wato kuna can ɗakunanku kun ƙule da mazajenku hankalu kwance ni ina nan a matsayin mai muku gadi yo Allah na tuba in ba dai dama su Umaru sun so su ja mini raini ba ya za a yi ina zaune da sirikai gida ɗaya amma a ce ina mazaunin bazawara kuma na ce zan yi aure suke neman hana ni, to tunda haka ne kowane ɗan banza zan sanya ya saki tasa matar su ma su zauna a gwauraye idan zaman haka da daɗi" Tunda ta fara zuba suka saku baki cike da mamaki suke kallonta, dan sai ma yanzu suka fahimci inda maganar tata ta dosa. "Inna wallahi bamu san da wannan maganar bama babu wanda ya faɗa mana Allah ne shaidarmu, mu ya za a yi mu hana sunnar ma'aiki abin da Allah ya halatta miki duk wanda zai hana ki ai bai so zaman lafiya ba" Suka haɗa baku wajen faɗa cikin girmamawa dan sun san kaɗan daga aikin nata ta sanya a mayar da su ƙauyen ko a a sake su baki ɗaya. "Allah sarki ƴaƴan nan ku yafe mini wallahi duk zatona da haɗin bakinku" "Wallahi babu Inna ai ciwon ƴa mace na ƴa mace ne kowace mace za ta so ta muti a ɗakin mijinta" "Kai Allah sarki daman an ce mace ita ta san damuwar ƴar uwarta mace, da a ce ku ne na haifa da tuni an ɗaura mini auren ba za ku mini gardama ba amma wannan yarinya Maryama kai kamar kwakwa taƙi fir sai kuka take kamar matar marigayi, amma na san abin da zan yi ku tashi ku tafi Allah muku albarka" Ta faɗa tana share hawayen takaici. "Amin Inna" Suka haɗa baki waje faɗa suka mata sallama suka tafi WASHE GARI Tunda garin Allah ya waye take ta saƙa da warwara tana son ta samu mafita dan dole auren take so a ɗaura mata. Sai da yamma ta fito lokacin babu kowa a waje ta fito tana ta waige-waige kamar marar gaskiya mai gadin ma yana bayi ta sulale ta bar gidan, titi ta tsallaka abinta tana ta saƙa abin da za ta faɗa idan ta je. Masallacin juma'ar wanda yake unguwar ta nufa tana zuwa ta samu mutane a ƙofar daga can gefe zazzaune a bishiya suna hira, wurinsu ta nufa ta musu sallama suka amsa mata. "Dan Allah limamin masallacin nan nake nema" Ta faɗa tana kallon matasan da su ma ita suke kallo. "Gashi can shi ne wanda yake fitowa daga cikin masallacin" Ɗaya daga cikinsu ya bata amsa. Nufar mutumin ta yi wanda zai kai Abba a shekaru rike yake da carbi a hannunsa sai ganin Inna ya yi ta nufoshi tana zuwa ta ce "Gafar malam wajenka na zo" "Ikon Allah to sannu iya ina saurarenki" "Wallahi mijina ne Allah ya masa cikawa ... "Allahu akbar kabiran Iya abinci kike buƙata" Ya katse ta,cike da tausayawa duk da bata yi kama da mai jin yunwa ba "Haba ɗan nan wane irin abinci ana maganar babban abinci, aure ne nake so shi ne ƴaƴana suka hana ni, na ce bari na kawo maka sadakin ka ɗaura mini tunda ba haramun bane" Ta faɗa tana share hawaye tare da saka hannu a aljihun ɗan tofinta ta zaro kuɗi. "Aure iya" "Yo aure mana ɗan nan ku ma da kuke malaman kana tantama da maganar auren bare kuma wanda ba malamai ba" "Ba haka bane Iya" "To karɓi nan, ka kirawo matasan can na zaune su zo ku haɗu ku ɗaura mana aure" "Ina angon" "Yana can ƙauyenmu, yo ai yana so na ba sai yana nan ba duk abinda na zartar daidai ne" "Iya ki riƙe kuɗinki mu je gidan ƴaƴan naki sai a musu nasiha su barki ki yi auren" "To ba a ƙi ta mutum ba" Haka suka ta shiga gaba yana binta ashe dai ya san gidan ya yi mamakin ganin gidan Alhaji Umar da Alhaji Sa'adu ne ashe mahaifiyarsu ce mai son yin aure tsofe-tsofe da ita. Haka aka sha ɗauki ba daɗi da liman da su Abba da Hajiya Inna suna ta kawo hujjoji ita kuma tana ta sharar hawaye ta dage a kan za ta gudu ta shiga yawon duniya idan ba a ɗaura mata aure da Jauro ba a haka dai suka amince ba dan sun so ba sai dan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ta dage a kan sai a gidan nan za ta zauna ita da Jauron haka suka amince ba dan ransu ya so ba. Bayan an daidaita da Jauro ya yi matuƙar jin daɗin zaman da za su yi a birnin Kano dan haka ya xe zai siyar da komai nasa dan su dawo nan da zaa ko Kande da ta tada ɓasa hankalin ba zai tafi ya barta ba Inna ta saka an bata inda za ta zauna a cikin gidan. Dan haka aka tsayar da ranar ɗaurin aure Inna ta saka Shattu ta gayyato mata ƴan ƙauyensu dan su zo su sha bidiri. Page 7⃣➡8⃣ RANAR ƊAURIN AURE Zaune take a kan kujera mai mazaunin mutum biyu, sanye take da atamfa ja wacce aka yiwa kwalliyar manyan ganye koraye, riga da zani sai ɗankwalin atamfar da ta tufka uban gwaggwaro irin nasu na tsoffi, hannayenta sanye da awarwaraye ƙafar nan ta sha jan ƙunshi dagwal har wajen ƙwaurinta. Kwalli ta rambaɗa da janbaki kai har ma da jagira ta zana abinta jagirar tamkar wanda aka zana da muciya gashi ya haɗu da yamutsatstsiyar fuska. Shattu aminiyarta ce a kusa da ita, ita ma irin kayan Inna Delun ne a jikinta sai washe baki suke kamar wanda ka yiwa albishir da tafiya aikin hajj bana. Mata ne cike a ɗakin ƴan ƙauyukan su, suna zazzaune a falon suna ta cin abinci wasu tuwon shinkafa da taushe sai rangaɗa hira suke ana yi ana suɗe hannu, da alama ma dai akwai abin da ke faruwa na fari ciki. "Wai ni Shattu har yanzu auren nan bai ɗauru ba, tun daɗewa aka tafi amma har zuwa yanzu ban ga ana shigowa da goro da alawa ba bare in tabbatar da zamana matar Jauro, karfa a yi mini sakiyar da ba ruwa, dan wallahi kwarankwatsa dubu matuƙar su Sa'adu rufata suka yi ba ɗaurin aure aka tafi ba, to a yau ɗin nan ba sai gobe ba zan ɗagawa kowannensu nono, tsinuwa kwa sai na tabbatar sun gama tsinuwa zan daina ja musu ita, ace na tara jama'a dan taya ni murna amma an shanya mu kamar wasu kaya a igiyar shanya"Inna Delu ta faɗa cikin raɗa dan kar mutane su fuskanci me ke faruwa, jikinta babu ƙwari dan duk ta gama sarewa daga samun cikar burinta. "Haba Delu me yasa kike da gajen haƙuri ne? Ai duk gaggawar asara ta jira samu ko, sai ki bari ki ga gudun ruwan yaran nan amma ba wai kike ikirarin ɗaiɗaita musu rayuwa ba ta hanyar ambata musu tsinuwa bayan kin tursasa musu su aurar da ke, ai duk lalacewar naka nake ne, kuma naka sai naka daɗin zama sai bare, sannan ma ba da ni ba gaɗa a hurumi, in goyi bayanki da tsinewa ƴaƴan cikin ki yo Allah na tuba kika tsinewa su Umaru ina muka kama kuma" Cewar Shattu cikin ƙarfin hali dan ita ma gabaɗaya ta sare da ɗaurin auren aminiyar tata. "Haba Shattu bakya tausayina yanzu a ce shekarata 70 amma sai yanzu zan yi auren soyayya, amma ina shirin rasa maƙwallaton zuciyata kuma marurun raina Jauro kina wata magana, na lura yaran nan kishin mataccen ubansu suke" Cewar Inna tana fakar idanun ƴan ɗakin ta share hawayen da ya taru a idanunta "Ki dauri ki jure Delu, dan rabon kwaɗo ba ya hawa sama kuma duk nisan dare ai gari zai waye, in har kuna da rabon aure to za a ɗaura in kuma babu to sai... "Bakin ki ya sari ɗanyen kashi Shattu, ai rabon aure ma kamar an yi an gama... "Aure ya ɗauru, tsakanin Aisha (Delu) Tare da Jabiru (Jauro) A kan sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba" Maganar da wani maroƙi da ya shiga faɗa a lasifika "An ɗaura, an ɗaura na zama matar Jauro Allah na gode ma" Cewar Inna Delu da ta tashi tsaye ta fara taka rawa tana waƙa, ita ma Shattun tsaye ta tashi suka shiga taka rawar a tare gabaɗaya falon ya karaɗe da guɗa kowa ƙoƙarin tofa albarkacin bakinsa yake na guɗar dan duk ɗakin kowa ya san cewa Delu tana mutuwer son Jauro haka shi ma yana ƙaunarta. Shattu ce ta ɗakko ƴar pos ɗinta ta buɗe ta ɗakko ƴan biyar-biyar sabbi dal ta shiga liƙawa aminiyar tata tana yi tana cewa "Alƙawari ya cika amarya, alƙawari ya cika amarya, in angonki ya shigo amarya ki yi masa fifita, amarya ki bashi ruwa ya sha, amarya alƙawari ya cika amarya" Tana yi tana mata liƙi ita kuma Imma Delu sai rawa take tana juyi, gabaɗaya matan falo ma tashi suka yi, suka haɗu da Inna ana ta rawa ana ranbaɗa guɗa ko hannu basu wanke ba da suke cin abinci. Inna! Inna!! Inna!!!" Cewar Abubakar cikin ɗaga murya rai a ɓace yana wani muzurai da cin magani sai wani harare-harare yake yana musu kallon ɗaya saura kwata. Cikin kiɗima Inna da Shattu kai har ma da ƴan ɗakin da ke ife-ife da guɗa suka dakata kowa ya maida hanklinsa kan Abubakar ɗin da ya shigo kamar an koro shi. "Habubakar kar dai ka ce mini maroƙin nan ƙarya yake ba a ɗaura ba ya karaɗe gida da sanarwa? Idan kuwa har ƙarya yake to wallahi sai na ɗaureshi daga shi har danginsa har sai igiya ta yi saura, a kan ɗaga mini hankali da ya yi" Cewar Inna cikin tashin hankali, burinta kawai Abubakar ɗin ya bata amsa bata ma lura da manyan ledojin hannunsa. "Oho miki, gashi in ji Abba" Ya faɗa yana dangwarar mata ƙatuwar ledar goro, alewa, da kuma dibono wacce Abba (Sa'adu) Ya bashi ya kawo mata saboda ta ce matsawar ba a sayi goro da alewa da dabino an raba a wurin ɗaurin aure ba sai ran kowa ya ɓaci. Juyawar da Abubakar zai yi aikuwa Inna taku ɗaya biyu ta yi fisgoshi, ji kake ƙiii ta maido dashi baya ta hanyar riƙo wuyan rigar jikinsa, sai da ta kawo shi gabanta sannan ta damƙe wuyan rigar da hannu ɗaya, ɗaya hannun ta dunƙule ta dage ƙarfinta na tuwo ta duma masa dundu a baya sai da ta masa dundu kifi uku sannan ta ce "Ko ubanka Sa'adu ya yi kaɗan ya yiwa goron ɗaurin aurena da Jauro wannan dangwararwar yo Allah na tuba ba gwara ka ce Inna kwanta a ƙasa ba idan na kwanta ka fisgi ƙafata riiii har sai ka dangana ni da ƙofar gida, ai sai ya fi mini sauƙi a kan yadda na ji da ka yiwa goro da alewar ɗaurin aurenmu da Jauro riƙon sakainar kashi tare da dangwarar da su kamar an maka dole" Ta faɗa tana sakin rigarsa da ta riƙe wanda wurin gabaɗaya ya cukurkuɗe kamar an fito da rigar daga bakin kura. Wani takaici ne ya rufe Abubakar ganin abin da kakarsa mahaifiyar ubansa ta masa a cikin mutane, dama ransa a matuƙar ɓace yake na auren da ta yi, dan abin kunya tsofe-tsofe da ita duk ta yi yaba amma wai za ta yi auren ƘARA'I. Wani irin kumburo baki ya yi yana wani huhhura hanci ya juya yana wani fisfisga ya fice daga falon. "Au ko da na ji, she dai an ɗaura wallahi har gabana ya faɗi" Cewar Shattu tana buɗa ledojin. "Rabu dashi ɗan kan uwa, an ɗauremu ni da Jauro, mugun hali ne irin na uwarsa, baƙinciki suke da auren sun fi so na zo mutuwa ana cewa matar marigayi ce haka kawai ai gwara a ce ka mutu da mijinka duk da ba a san gawar fari ba" Ta faɗa suna ɗaukar ledojin shiga rabawa mutanen da suke falon, dan dama duk daga ƙauyensu suke Shattu ta gayyato mata su, haka suka shiga rabawa mutane bakin Inna dan dama duk tsofaffi ne bakin Inna har kunne yau dai burinta ya cika, ɗaki ta shiga ta ɗakko wata shadda ƴar ubansu ta saka ta cakara ɗaurin ɗankwali har ta yi gwaggwaro ta koma ta ware ta ɗauki wani kofi a cikin ɗakin ɗan ƙarami da shi ta ɗora a tsakiyar kan nata tare da ɗaura ɗankwalin a kan kofin mudubi ta kalla aikuwa ɗaurin ya mata yadda take so. "Ai gwara dai yau ɗaya in yi ƘARA'I in yi ɗaurin ɗankwali irin na yaran ƙauyenmu da suke wanda ake cewa a cuci maza"Cewar Inna tana dubawa ta ga ya yi kamar yadda yaran ke yi. Ƙaramar lokar mudubin ɗakin ta janyo ta ɗakko fanfas na yara guda biyu, jimƙe ɗaya ta yi ta ɗaga bireziyarta ta saka fanfas ɗaya a ƙasan nonon nata sai ta maida nonon ya zamana shi ne a akan fanfas ɗin ɗayan ma haka ta masa tun da ta zubawa jikinta da fuskarta ido a mudubi take ta faman doka murmushi, walwala ta kasa barin fuskarta. "Taɓ lallai na yi maida tsohuwa yarinya ni Delu ai za mu kwashi ƙara'i ta faɗa tana washe bakinta har haƙorin makkarta ya bayyana. Hanyar fitowa daga ɗakin ta yi domin ta san yanzu Jauro yana dab da zuwa, tana fitowa hakan ya yi dai dai da wata uwar guɗa da Shattu ƙawarta ta carara ba komai ya kawo guɗar ba kuwa sai shigowar Jauro falon shi da abokinsa Mati. Tunda ya shigo yake wuwulga ido ya ga ta inda zai ga Delunsa. "Shattu ina amaryar take?" Ya faɗa yana washe bakinsa. "Baka gane ni ba" Cewar Inna Delu tana wani farrr da ido ita ala dole amarya. "De, De,Delu" Ya faɗa idanunsa a waje baki sake yana nuna ta da yatsansa. Kowa ma na falon maida kallonsa ya yi kan Inna Delu ganin ɗaurin ɗankwali mai acuci gashi fanfas ɗin da ta saka ya ɗago da nonon nata sai suka hayo ƙirji hakan ya sanya ta zama kamar yarinyar mace dan sosai fandas ɗin ya yi ɗoɗar a cikin shaddar. "Wallahi Delu kin fiye mini Kande sau miliyan" Cewar Jauro yana kallonta baki sake. "Ai baka haɗa bama Jauro" Cewar Mati yana ƙarewa Inna Delu kallo a ransa yana rayawa ina ma a ce shi ne ya yi wannan dacen tsuntsu daga sama gashasshshe, dan ya matuƙar so a ce shi ne musamman ma da ya ji wai a binnin a wannan ƙerarran gidan Jauron zai zauna da Delun dan ɗaurewa ƙarya tsantsa ma har da ɓangaren da zai saka matarsa Kande dan Kanden ta tada badaƙala cewar ba zai tafi binni ya barta a ƙauye ba ita kuma Inna da yake so take yi tana ganin mijinta kullum sai ta saka aka gyarawa Kande wani ɗaki ciki ɗaya daga can gefe yake.Ita kuma Kanden saboda son zaman binni take gani ba za ta yi saki na dafe ba gwara dai ta zo ko a akurkin kaji ne ta zauna. "Kai jama'a wallahi na tsinci dami a kala" Ya faɗa yana shafo farin gashin gemunsa. "Ai yau sai ka biya mu kwalliyar nan Jauro ango" Cewar Shattu tana washe bakinta wanda ta tauna goro. Baki ya washe ya ce "Ai in kin ji biya ma ɗaya kenan, kar ki samu damuwa aminiyar amarya sha kuruminki, kwantar da hankalinki kamar kin kashe ɗan mutum, ko kamar tsumma a randa" Ya faɗa har lokacin idanunsa a kan amaryarsa. Nan aka shiga gaisawa da mutanen ƙauye da suka zo domin ɗaurin aure, da la'asar suka koma garinsu dan Inna ta ce sai nan da sati guda za su zo shagalin biki dan yanzu aure kawai aka ɗaura dan hankalinta da na Jauro ya kwanta. Da daddare bayan sallar isha'i Inna ta aika aka kirawo mata Abba Sa'adu da Baba Umar a kan tana son magana da su, cikin bin umarninta suka taho a tare sa sallama suka shiga lokacin ta ɗaga waya za ta kara a kunne, sai da ta msa sallamar tasu ya musu izinin shiga sannan ta kara wayar a kunne "Alo Jaurona ango" Ta faɗa tana wani murmushi tare da kashe murya kamar wata ƙaramar budurwa. Daga ɗaya ɓangaren Jauro ya ce "Amarya, amarya, amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" Cewar Jauro yana waya dariya da sautin dariya ya karaɗe kunnuwan Abba da Baba, da yake bolum ɗin wayar a ƙure yake ana iya jiyo maganar tasa. "Angona kenan bada kan ka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, ina ƙaunarka Jaurona" "Ai kin zama mallakina yanzu Deluwa maƙwallaton zuciyata" Gabaɗaya Abba da Baba kai kawai suka sunkuyar saboda tsabar kunyar da ta ziyarce su a ce uwarsu mahaifiyarsu ta yi sabon aure yau kuma tana wayar soyayya har da kalamai kamar wata farin shiga, ƙaramar yarinya ko nauyinsu bata ji. "Ka zo ɓangarena za a yi magana kan shagalin bikinmu" Ta faɗa tana ƙara kashe muryarta har da wani lanƙwasa muryar kamar wani lauje. "Yanzu kuwa" Ya faɗa yana kashe wayar ya taso zai taho. Ajiye wayar ta yi har lokacin murmushi bai bar yamutsatstsiyar fuskarta wacce tun tuni tsufa ya yiwa kamun kazar kuku. Dakyar ta iya dakayar da murmushin, ta kalli ɗiyan nata ta ce bari Baban naku ya ƙaraso dan na fi so a yi maganar shagulgulan bikin namu a gabansa ko yana da wani tsare-tsaren shi ma" Baki sake ƴaƴan nata suke kallonta fuskarsu fal mamaki. "Umaru, Sa'adu wai ko bakwa son albarkar iyaye ne, ya ina maganar abin da zai saka ni farinciki kuna wani kauce kauce kamar wacce ta faɗi saɓon Allah, aure ne fa ba haramun ba sunnar ma'aiki" Ta faɗa tana kama haɓa cike da mamaki dan ita har ga Allah a kan gaskiyarta take. Da sallama Jauro ya shigo wanda hakan ne ya katse musu maganar, amsa masa ta yi ya ƙaraso zai zauna a kujera mai zaman mutum ɗaya. "Haba Jaurona matso kusan iyalinka mana ka zauna a nesa da ni" Cewar Inna da ke zaune kan kujera mai zaman mutum biyu, su Umar suna ƙasa daga gabanta, haka ya ƙaraso yana wani washe baki yana wani baza babbar riga kamar wanda ke baza buhu a kasuwar barkono. Kusa da ita ya zauna suka zauna da ita dab da juna da ido ya kafe ta yana mata wani kallon soyayya dan ya kasa ɗauke idanunsa daga kan ɗaurin ɗankwalin acuci mazan da ta yi sosai ta masa kyau. "Barka da dare" Umar da Sa'adu suka faɗa, wanda hakan ne ya dawo da shi daga hayyacinsa daga kallon da yake yiwa uwarsu, amma bai ɗauke idanun daga kallonta ba, amsawa ya yi ba tare da ya kallesu ba har lokacin yana kallon Inna Delu. "Kallon fa" Ta faɗa tana rufe fuska da tafukan hannayenta alamun kunya. "Wallahi bana gajiya da kallonki Deluna, sosai ɗaurin nan ya miki kyau ya ɗauru sosai kamar an ɗaure itace da igiya ɗaurin ya zauna daram ga wani ɗan tozo da ya yi irin na yara, sai kika dawo mini ɗanya sharaf kamar kina budurwa sai yau nake ƙara jin haushi da ba ni na aureki ba, na so a ce ni ne nan na buɗe ki a leda lokacin kina sabuwa dadal, amma Allah bai yi ba sai yau da kike da shekara saba'in" Ya faɗa haƙoransa washe gabaɗaya talatin da biyun a waje. ƘARA'IN INNA DELU 💄💄💄💄💄 NA MAMAN AFRAH FCW 💛 Pag 9⃣➡🔟 Wani daɗi ne ya lulluɓe Inna Delu jin irin yabon da angon nata ke mata, ƙuri ta masa da ido tana kallon fuskar nan tasa mai yalwar furfurar gashin baki da saje. Dai dai nan Shattu wacce ita kaɗai ce bata tafi ba saboda ita ce aminiyar Delu wai sai bayan shagali za ta tafi, shigowa ta yi ganin kallon da Delun ke jifan Jauro da shi sai kuwa ta carara wata uwar guɗa, guɗar da ta carara ce ta sanya Delun sanya hannu ta rufe ido. "Ikon Allah ga zara ga wata" Ta faɗa lokacin da ta shigo tare da ƙarasowa ta tsaya fuskarta da fara'a "Wallahi Shattu ke dai bari garin daɗi ba kusa da wai kyankyaso ya leƙa masai ai ni ma tun shigowata nan gabaɗaya aminiyar taki ta kunce mini notin kaina ita kaɗai nake gani duk ta susutani da wani kallo wanda ko kwatarsa Kande bata iya ba, yo ina ma Kande ta iya kallon soyayya babu abin da ta iya idan tana kallona wani lokacin har cewa nake me na miki Kande? Ko na miki laifi ne? Sai ta ce me ka gani? In ce na ga kina hararata, sai ta ce ba harara bace kallon soyayya ne, to haka dai zan yi yaƙe amma ba wai dan na gamsu ba dan kawai gani zaki yi tana zare ido kamar wacce tsakuwa ta faɗawa ido can kuma sai ki ga ta gwale idon sai kuma ta runtse, da sauri nake nufarta in ce kawo in bushe miki idon naki in wani abu ne ya faɗa miki a ciki, sai ta ce ka jika Jsuro da wani abu duk a cikin kallon soyayyar fa ake har yanzu" Ya faɗa yana tuntsurewa da dariya har da ƙyaƙyatawa da ya tuno irin yadda matarsa take masa kallon soyayya bata iya ba. "Taɓ ashe kana shan kallo"Shattu ta faɗa tana ƙilƙilewa da dariya. "Ba ni da zara ido ba, gata da ƙwal ƙwalan ido kamar ƴaƴan carabke" Cewar Jauro har lokacin yana dariya. "Amma ya na ga aminiyar tawa tana rufe ido?" "Rabu da ita Shattu wai kunya ce take ji irin ta sabuwar amarya, wacce amare ke ji, ni zan cire wannan kunyar gabaɗaya, dan duk wayon amarya sai an sha man ta" Ya faɗa yana wani ƙallare ido ɗaya shi a dole ɗan duniya "Aikuwa dai gwara ka cire kunyar nan" "To ko in fara rage hanya yanzu" Ya faɗa yana ƙoƙarin kamo hannun Inna Delu. "Ashsha, gyara kintsi da kyau ango"Cewar Shattu tana masa nuni da Abba da Baba da suke zaune a ƙasan capet kamar an dasa su kowanne kansa a kasa saboda tssbar jin nauyi da kunyar maganganun da su Jauron ke yi. "La'ilaha illalahu muhammaddur rasuslullah S.A.W, an yi abin kunya yau wallahi Shattu na ma manta da yaran nan suna zaune, kin san dai ni idan Deluna tana wuri mantawa nake da kaina ma bare kuma wani" Ya faɗa hannunsa a haɓarsa. "Haba angona ai wannan ba abin kunya bane ka san ai su ma ba yara bane, tun da har sun hayayyafa kuma waye cikinsu bai san soyayya ba wa ma ya san irin ƴar muryar da suke yiwa nasu matan, kuma ai dama an fi so ƴaƴa suke ganin iyaye na soyayya ba wai ƙiyyya ba dan yara tsanar uban da baya son uwarsu suke kuma suna jin haushin uwar da take uzzurawa ubansu sun fi so su ga ana zaman lafiya da nuna ƙauna ko ba haka bane Umaru" Cewar Inna Delu tana ƴar dariya kaɗan. "Haka ne Inna" Cewar Baba Umar kamar ya yi kuka. "Yawwa ɗan albarka, kai kuma fa Sa'adu ko ba haka bane?" Ta faɗa tana kallon Sa'adu da ya sunkuyar da kai ƙasa kamar zai kifa dan takaici. Shiru bai bata amsa ba. "Ba tambayarka ba nake Sa'adu ka watsa yina, kamar shara a bola" "Allah baki haƙuri Inna, haka ne" Ya faɗa cikin ɗacin rai. "Allah sarki uwa da ɗa kenan ashe kuwa maganar taki haka ne Delu, gaskiya babu wanda ya fi uwa fahimtar halin da ƴaƴanta ke ciki" Cewar Jauro yana washe baki. "Yo ai su ma murna suke sun yi sabon uba ka ga basu da maraici kenan, shi yasa na ce mu zauna a nan ɗin kusa da su ko ba komai ma ke ɗauke musu kewa, kuma idan suna ganinka za suke mantawa da mutuwar mahaifinsu" Cewar Inna tana kallon fuskar Jauro dan ita tafi ƙaunar gemun fuskarsa fiye da komai yadda ya tashi ɗin nan ziyat ya fi tafiya da ita. "Amarya mai daɗin tuwo amarya mai maganar siga" Cewar Jauro yana ƙara gyara zamansa, idanunsa kafe a kan Inna Delu. "Allah gamu gareka ɓarawo a hannun mata" Cewar Abba a zuciyarsa dan ji yake kamar ya zura da gudu. "Allah mun gode maka haƙiƙa baka ɗorawa bawa abin da ba zai iya ba" Baba ya faɗa a ransa. "Kuna birgeni wallahi haƙiƙa kun matuƙar dacewa da juna, na so kun auri junanku tin a samartaka, sai dai Malam Lawwali ya muku shigar sauri" Cewar Shattu tana neman wuri ta zauna. "Ke dai bari Shattu ai tuna baya shi ne roƙo" Cewar Jauro yana ɗan jijjiga kai, dan idan ya tuna Malam ne ya fara sanin Inna Delunsa a matsayin mace sai ya ji ransa na ƙuna amma babu yadda zai yi dan ƙaddara ta riga fata. "Haka ne Shattu ya za a yi da ƙaddara, ai banda tuna baya wai gyartai ya ci sarauta" Cewar Inna Delu tana jin haushi a ranta. "To ai yanzu kun auri junanku sai ku yi koma menene dan wuri bai ƙure muku ba" Shattu ta faɗa tana dariyarsu ta tsofaffi. "Ai fa za ku gani, dan za a kashe arnan soyayya har ma dana ƙaunayya"Jauro ya faɗa yana jifan Inna Delu da wani kallo. Hannu ta sanya ta ɗan rufe fuskarta tana murmushi. "Allah nuna mana" "Amin, ai idan aminiyar nan taki ta rufe fuskar nan tata baki ji ba yadda nake ji, ba ƙaramin tsumani take ba sosai nake ganinta kamar budurwa ɗanya sharaf, ƴar shekara sha biyar" Cewar Jauro yana dariya, gabaɗaya Inna Delu da Shattun ma dariyar suka sanya, hatta Abba da Baba sun ɗan murmusa a ransu amma murmushin na takaici ba wai na jin daɗi ba. "Inna ko mu tafi ma yi maganar da safe" Cewar Umar yana wani ɗan ɓata rai dan ya ga abin nasu ba na ƙare bane gwara su basu wuri sa fi sakewa su yi maganar duk da yanzun ma ba wai sun fasa maganar bane kuma ko sakaya wa basa yi. "Oh ni Delu, na ga ikon Allah faɗa da mai gari ranar sallah, yo Allah na tuba banda ƙarfin hali ɓarawo da sallama, yanzu Umaru in kirawo ka wato ba za ka iya jira in gama abin da nake ba shi ne har ka ƙagauta kana so ka tafi ka yi uzurinka da ya fi nawa, ko soyayyar da sabon uban naka yake nuna mini kke baƙinciki? Wato kana taya ubanka marigayi kishi ko, Yo in ba baƙinciki ba menene a ciki ɗan ƘARA'IN da zan yi a sauran rayuwata shi kake yiwa baƙinciki in ka yi haƙuri dai nawa ma ya rage mini a rayuwar, tunda dai wanda zai je sama ya taka leda ai ya ci ƙarfin tafiya, ni da nake da shekaru saba'in aikuwa idan da saura ma kaɗan ne, kai idan ka tafi ɓangaren naka wa ya san me za ka yi wato kana sauri ka tafi wajen matar so, waccen ƙeƙashashshiyar matar da ciyar da ita da hana ta abinci babu banbanci abu kullum a rame kamar raƙumin dawa, kullum jikinta jiya i yau, sai shegen ɗaga kai kamar ƙadangaruwa da haɗe rai fuskar nan kamar faten wake, tana tafiya tana tura baki yadda kika san bakin jaɓa" Tun da Inna ta fara faɗa babu wanda ya tanka daga Abba har Baba kowa kai ya cigaba da sunkuyar da kansa. "Ƙyale shi aminiya tun da dai kin auri Jauro yau kar ki bari wani abu ya ɓata miki rai ko ki yi ɓacin rai a ranar farincikin ki, ranar da kika daɗe kina dakon ta, ranar da muka daɗe muna jiran zuwanta ranar da ta zama rana mai matuƙar tarihi a cikin rayuwarku ke da angonki" Cewar Shattu da ta taso daga mazauninta ta zo gaban Inna Delu ta dafa kafaɗarta. Wani daɗi ne ya rufe zuciyar Inna a take ta washe baki kamar gonar auduga ta ce "Haka ne aminiyata ta gaban goshi, ai dama komai nisan dare gari zai waye kuma duk nisan jifa ƙasa zai dawo, sannan matar mutum kabarinsa, ban taɓa tunanin nesa za ta zo kusa ba, na daina faɗar abin da zai sosa raina ko kaɗan a ranar nan abin alfaharina" "Yawwa ko ke fa, ai ni da kina faɗan ma kawai kallonki nake Deluna dan sai na ga babu banbanci da dariyarki da ɓacin ranki kowanne kyau kike a ciki, kin san ke kyakkyawa ce" Cewar Jauro yana kallonta "Bari zuga ni Jaurona ai ni kaina na san da hakan tun da har ka ce kana sona ina budurwa yadda lokacin ka yi tashen kyau kamar amita bacas (Aminta bacha) Na indiya yanzu ma har na tsufa amma kana nan a kan bakar ka to na tabbata ina da kyau na nunawa sa'a" "Ai har gobe ke ce tauraruwata Delu, ko Kande kawai ƙaddara ce da bin umarnin iyaye ya sa na aure ta, amma wallahi ba da niyyar na ci amanarki ba, dan ko yanzu sai in iya ƙidaye miki sau nawa na taɓa zuwa wajenta a matsayin miji, tafi kawo kanta kin ga ni kuma ai ba na ce a'a ba ko dan in sauke nauyinta kar in shiga haƙƙinta take mini kallon ragon namiji shi yasa nake ɗan yarda amma kaɗan-kaɗan ba da yawa ba, wallahi Delu kwarankwatsa dubu bana wuce awa bakwai ina yin sunna da Kande" Jauro ya kai maganar yana sakin kuka dan shi sai yake ga kamar Delu za ta ce kusantar Kanden ma cin amana ne. "Awa bakwai fa ka ce Jauro" Cewar Inna tana dafe ƙirji. "Haka na ce Delu, idan kuma ƙarya nake miki Allah yafe mini, wataran ne ma daga farkon dare muke kaiwa asuba, kin ga kuwa wannan ai duk ba wani abu bane ko?" Ya faɗa cikin karya murya yana karkarta kai shi a dole ta yarda dashi. "Awa goma da wani abu Jauro, sai ka ce wani bunsuru, yo Allah na tuba in ba ɗan taure ba waye zai yi sama da awa goma yana gabatar da sunna" Cewar Shattu cikin ɓacin rai da taya aminiyarta kishi. "Aradun Allah saisa-saisa nake yi Shattu" Ya faɗa yana share hawaye dan shi har ga Allah gani yake kamar ma ya ɗakko ruwan dafa kansa ne Delun za ta ce ta fasa, shikenan zai rasa zaman birni ya ga samu zai ga rashi, sannan zai mutu da son ta a ransa. "Rabu da shi Shattu yo ko ɗan taure ne yake awoyin nan ai a sara masa ba wajen kaifin ba, haƙiƙa ka ci amana ta Jauro, kake daɗewa haka kana sunna kenan baka da lokacin tunani na ma, ni ina can a gidan Malam ko yaushe ina tunaninka, ko Malam ɗin ne ya kawo kansa wataran hana shi kaina nake dan sai in ke ganin kamar amanarka zan ci ashe kai kana can kana kashe arnan soyayya, kana kwashe awoyi da mace yo Allah na tuba ai duk ka gama lale komai da komai babu sauran abin da zan samu, ko wani sauran abin da zan mora, har nake zumuɗin cin amarci... Tana cikin faɗa tana kuka, bata ankara ba sai hango wulgawar Abba da Baba ta yi sun fice dan ko ganin tashin su bata yi ba ficewarsu kawai ta gani. Umaru, Sa'adu" Ta faɗa tana ware murya dan su dawo. Amma ko alamarsu bata gani ba. "Shattu bisu ki kirawo mini su, ki ce wallahi idan basu dawo ba zan yi abar" Ta faɗa tana kallon aminiyar tata da gabaɗaya ita ma ranta a jagule yake da maganar Jauro. "Ki bar maganar yin abar ke baki da aiki sai anbaton za ki yi abar, to meye ribarki in kika tsinewa ƴaƴanki?" Cewar Shattu tana kallonta. "Ke ce miki aka yi Delun mahaukata ce ni, ai ba wai yin tsinuwar zan yi ba ina faɗa ne dan in samu cikar burina kin san tsinuwar ce kaɗai zan ambata a mini abin da nake so a zauna lafiya" Cewar Inna cikin raɗa dan kar su Abban ko suna kusa su jiyo ta. "Yawwa ko da na ji" Bari in bi bayansu" Shattu ta faɗa tana ficewa da sauri dan kar kowannen su ya shige ɓangarensa. Tana fita Jauro ya matsa kusa da Inna ya kamo hannunta ta ƙwace, ganin za ta ɓata masa lokaci ya haɗa duka hannun biyu ya riƙe ya shiga aikin lallashi tana ta zunɓura baki ta ce "Haka kurum ka je kana cin amanar soyayya ta" "Haba Delu fara kyakkyawa wallahi kina raina, kuma da kike maganar ba na tunaninki, wani lokacin ko ina kan masai(Toilet) Ina kashi sai in ji tunaninki ya hana ni sakat, ke ko sallah nake ma tunaninki nake" "Ka ce ɓata sallarka kake" "A'a ba haka bane ai ina cewa a'uzubillahi minashshaiɗanir rajimmm, in kori shaiɗan ɗin kawai dai ina so ki san irin yadda kika yi kane-kane a raina, ke ni fa akwai lokacin da Harɗon rugarmu ya aika a kirawo ni wai dabobina sun shiga gonarsa, tun da na doshi fadar tasa kawai sai na ga ya koma mini ke sak, kawai ke na gani a kan kujerar mulkin dan haka tun da na kalleshi sai nake sakin murmushin ƙaunayya aikuwa ya harzuƙa, ina zama yake faɗa kamar ya cinyeni ɗanye, ni kuwa tun da na sunkuyar da kai tunaninki kawai nake, dan haka faɗan da yake mini ma amon muryarki nake ji kina mimi kalaman soyayya dan haka ko da ya saurara da faɗan ya ce da kai fa nake Jauro ka ƙyaleni ai ina ɗago kaina ban san lokacin da na ce ina jinki Deluna" Gabaɗaya Inna ta tuntsure da wata irin dariya sai ƙyaƙyatawa take ita ala dole Jauro yana tuna ta duk daɗi ya cika ta. ƘARA'IN INNA DELU 💄💄💄💄 NA MAMAN AFRAH FCW💛 Page 1⃣1⃣➡1⃣2⃣ Abba ne ya yi gyaran murya ya fara magana kamar haka, dan ya ga abin na su Inna ya wuce gona da iri nema suke su ɗakko musu magana su ɗakko musu ruwan dafa kansu. "Hana Inna wannan abu fa ba mai yiwuwa bane, saboda abin da zai iyu shi ake faɗa ta yaya ma haka zai faru a ce wai mu kama ɗakin taron shagali ai sai duniya ta zage... "Idan fa ban yi da gaske ba, ba zan taɓa samun abin da nake so ba gwara dai in tauna tsakuwa ko aya ta ji tsoro" Cewar Inna Delu a zuciyarta a fili kuma sai ta ce "Yanzu Sa'adu ni kake faɗi in faɗa dani, ni kake cewa ba mai yiwuwa bane, haka zan tare a ɗakin sabon uban naka babu wani shagali kamar wacce ta yi auren ƙiyayya, yo in ba auren ƙiyayya ba a ina aka taɓa biki lami shataf babu wani ɗanɗano, ai ko auren ubanka Malam duk da ba son sa nake ba sai da aka ɗakko masu gurmi" Ta katse masa maganar tana kaiwa ƙarshen maganar tare da fashewa da wani kuka mai sauti kamar an kunna jiniya, tana fara kukan Jauro ya yi saurin ruƙo hannunta yake bata baki amma ko saurara wa da kukan bata yi ba ganin haka shi ma sai ya ɓare baki ya saki nasa kukan yana ƙwalawa da ƙarfi har wani jan birki yake sai kuma ya ci gaba. Shattu ma bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ƙarasa wajensu tana basu baki "Haba amarya da ango ya da kuka kuma a ranar farincikin ku, ranar da kuka yi shekaru sama da hamsin kuna mafarkin samunta" "Barmu mu yi kayanmu Shattu ɗan yanzu ni ka haifeshi baka haifi halinshi ba, in banda zamani mai sa wani ya ƙi uwarsa ya so wasu, zamani mai sanya ɗa ya baƙantawa uwarsa rai ya farantawa uwar matarsa rai, ta yaya za a ce kamar ni in haifi yaran na su girma su mallaki hanklin kansu amma su ƙi mini abun da zai sa ni farinciki" Cewar Inna tana goge hawayen takaici. Ganin haka sai Jauro ya miƙa goshinsa ya haɗa da goshin Inna a haka suke kukan kamar wasu tsuntsaye. "Muke kukan a haka Bebi in gwara duk runtsi duk wuya mu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya" Ya faɗa yana ƙara sautin kukansa. Shattu ma ganin haka sai kawai ta mara musu baya dan ita ma tana ganin ba a barta a baya ba wani irin kukan tsoffi ta saki irin mai sanya ciwon kai lokaci guda. Sun cika ɗakin da koke -koke kamar gidan mutuwa, baka jin komai sai sautin kukansu babu mai lallashin wani. Idan Inna ta bada sautin "Yiiiiii" Sai Jauro ya bada sautin Yeeeee" Ita kuma Shattu nata sauti "Yeyiye-yiye" Kamar wata agwagwa haka suke kukan suna jan hanci. Abba da Baba kawai kansu suka sunkuyar hannuwansu dafe da kansu. "Ya Allah ka bamu ikon cin jarabawar nan" Cewar Abba a zuciyarsa. "Kai ji nake dama bana ƙasar nan Inna ta yi aure da wataƙila ba zan ji takaici kamar haka ba" Cewar Baba a zuciyarsa yana jin wani damshi a fuskarsa hannu ya kai ya shafo ashe dai hawaye ne suke gangaro masa. "Bari dai in tashi mu san inda dare ya mana yaran nan in basu ga da gaske nake ba babu abin da za su yarda su mana" Inna ta faɗa a ranta tana mai tashi ta nufi ɗakin har lokacin tana kuka mai sauti, su ma su Shattu basu bari ba an ma rasa sautin kukan wa za a saurara kamar wasu yara. Ƙaran akwatunan da Inna ta ɗakko guda biyu su ne suka dakatar da kowa aka shiga kallonta har masu kukan ma ɗiff suka yi dan dama kukan sheƙiyanci ne. A kanta ta ɗora akwatin ɗaya yadda kika san irin inyamuran nan na Lagos masu ɗora daro a ka haka ta koma, tana janye da ɗaya akwatin a hannunta "Kai wannan mata da shegen abu take kin ga ni ban samu shagalin biki ba za ta jaza mini komawa ruga bayan na yi sallama da zaman can" Cewar Jauro da bai san ma lokacin da kukan munafurcin da yake yi ya tsaya ba, banda faɗuwa babu abin da gabansa ke yi. "Kin mini dai dai gwara ki tarki tafiya ko sa saduda su sakko" Cewar Shattu a ranta. Cikin hanzari Jauro ya tashi ya karɓi akwatin kan Inna ya sauke ta ƙasa sannan ya koma ya zauna yana share hawaye, amma a baɗini hawayen baƙincikin barin binni ne dan ya ga Delu da gaske take tun da har ta ɗakko akwati. "Ku taso mu tafi mu bar musu gidansu" Cewar Inna tana saurin dafe kanta jin ɗaurin ɗankwalin na neman faɗuwa. Wani zillo gaban Jauro ya yi jin maganar da ta ratsa kunensa a kiɗime ya ɗago yana kallon amaryar tasa ji yake kamar ya ce su haƙura da shagalin su tare a haka amma kuma ya ga babu fuska a wajen Inna. "Ni dama a shirye nake aminiyata dan dai nan da garinmu ko a ƙafarmu ma isa daga yanzu zuwa sulusun dare kan gari ya waye" Cewar Shattu da ta ɗauki akwati ɗaya. "Bebi taso ka ɗauki ɗayar" "Ga samu ga rashi wayyo ni Jauro duk na ɗaga dabbobina da shanaye da gonaki na siyar yanzu idan na koma gorin jama,a ma ya ishe ni" Cewar Jauro a zuciyarsa yana tuna washe garin ranar da Inna ta dawo binni aka ɗakko shi har za a ɗaura aure aka fasa shi ne da ya koma ya siyar da duka kadarorinsa. "Ina zamu???" Cewar Jauro har lokacin yana zaune a kujera dan ko maganar tafiyar ma baya ƙaunar ji. "Ka taso mana, baka gani yanzu dare ne kuma akwai gidan casu a garin nan akwai kwalob (Club) Akwai gidan karuwa kai sai inda muka zaɓa sai mu je mu yi casunmu in yaso daga can sai mu koma rugarku mu yi rayuwar aurenmu a can tun da nan an gagara kama mana gida a sirri ai sai mu je inda ƴan iskan duniya suke in yaso tunda su suna gudun maganar, a ce sun kamawa uwarsu ɗakin taro an yi shagali ai a ce an ga uwarsu a gidan rawa " Cewar Inna tana saurin ƙara dafe kanta jin kofin da ta yi acuci zai gangaro aikuwa dai an yi rashin sa'a dan ya faɗo ji kake ƙwal, ya faɗowa Abba a tsakiyar kansa da babu hula. Wani kallon mamaki suka bi Inna da shi, ganin kofin da ya faɗo daga cikin ɗankwalinta, shi Abba ba ta faɗo masa da ya yi ba yake kawai ta yadda aka yi uwarsa tsofai-tsofai ta saka kofin yake dan sun fahimci babu makawa acuci maza ta yi. "Haɓɓasa aminiyar gaskiya ne ba a bori sa sanyin jiki ai gwara ki gwangwaje ki yi ƙara'in ki" Shattu ta faɗa tana kallon Inna. "Acuci maza ne, kuma babu wanda na cuta dan mijina na yi kuma ya yaba ɗaurin ɗankwalin" Inna ta faɗa tana juyawa ta kalli Jauro ta ce "Ko baka yaba ɗaurin ba Bebi" Wani takaici ne ya turnuƙe zuciyar Jauro dan shi gabaɗaya hankalinsa ya ɗugunzuma ga tafiyar da ta ce za su yi cikin ƙarfin hali ya daure ya ce "Eh ya miki kyau" "Yawwa Bauti (Beauty) Jaurona ko a maida kofin cikin ɗankwalin?" "Barshi kawai ai a haka ma kin yi kyau" Ya faɗa yana jin tamkar ya hau Inna da duka dan ya lura shirin tafiyar da take ba wasa a ciki. "To kun dai ji daga bakin uban naku wanda aka yi ɗaurin dominsa" Ta faɗa tana gyara ɗaurin ɗankwalin ba tare da ta ɗauki kofin ba ta , juya abinta Shattu na bin bayanta da akwatin, ganin haka ne Jauro ya yi ta maza ya tashi ya ɗauki ɗaya akwatin yana jin babu daɗi a ransa, suna dab da fita daga falon Baba ya ce "Ku dakata Inna mun ji za a muku duk abin da kuke so a kan dai ko je gidan rawa" Ya faɗa kamar ya saki kuka. "Eh mun amince" Abba ma ya faɗa ba dan ransa ya so ba. "Kayyasa in ka ji ana ba zan iya ba to bai samu mutum ba" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce "A'a ku barshi kawai" "Dan Allah Inna ki yi haƙuri" Abba ya faɗa cikin sanyin murya yana tsaye a gabansu. "Ke ko Delu ki haƙura mana kuma babu kyau dai fushin uwa a kan ɗanta kuma Allah ma yana son mai haƙuri" ,Jauro ya faɗa yana wani karyar da kai fuskar nan tashi duk hawaye shaɓe-shaɓe "Haba Delu ki yi haƙuri mana" Shattu ma ta sanya baki. Dakyar aka shawo kan Inna ta aminci suka dawo da akwatunan nan kowa ya zauna Inna Delu ta ce "Ni dama ba wai wani abun a zo a gani na ce ku yi ba ƴaƴan nan, yanzu kuɗi nake so ku bani gobe masu ɗan gwaɓi da direba a kai mu kasuwa mu siyo ƴan kayayyakin amarci sannan kuma ranar tariyar a kirawo mai kwalliyar amare (make up) Ta mini kwalliyar in fito rangaɗaɗau a amaryata, sai kuma a ɗauki motoci a kai jama'a can a ɗauki me kiɗa (DJ) A kai shikenan fa daga wannan" Ta faɗa tana kallon Abba da Baba da suka rasa bakin magana. "To Inna za a miki duk abin da kike buƙata, idan har kika fasa tafiya" Baba da Abba suka haɗa baki wajen faɗa. "Yawwa ƴaƴan nan ko da na ji ubangiji ya libga muku albarka ku wanye da duniya lafiya" Cewar Inna tana washe baki, Abba ya fito da 100k ya bata haka ma Baba shi ma 100k ya bata na siyayyar da ta ce za ta je haka suka rinƙa jero musu godiya da sanya musu albarka su dai haka suka amsa amma ba dan ransu ya so ba. Washe gari tun da sanyin safiya Inna ta aika aka kira mata Lantana mai aiki, haka suka sanya ta a gaba wai za ta raka su siyayya, cikin zumuɗi Lantana ta yarda, da yamma haka suka ɗumguma Inna, Shattu da Lantana a baya Jauro da direba a gaba haka direba ya ɗau hanya Lantana ita ce mai faɗa kusu inda zai kai su suna cikin tafiya su Inna sai aikin washe baki suke. "Tsaya, tsaya direba" Cewar Inna da ƙarfi tamkar wanda ta hango wani mugun abu ya tunkaro su da sauri direban ya taka birki ya ɗan gangara gefen titi yana tambaya ko lafiya. "Haba ɗan nan aiulafiya ce ta fito da mu kalli can wancan shagon na tsallake nake so ka kaimu kalli wata mata can ta saka kayan indiyawa ni ma irin nata nake so, Lantana ce ta fashe da dariya ta ce "Inna wannan fa mutunmutumi ne ba mutum ba kayan siyarwa ne aka saka mata dan masu siye su ga yadda kayan yake yi a jikin mutum" "Allahu akbar kabiran lallai komai yana binni wallahi, gaskiya Delu idan kika saka kayan nan har sai na kusa suma" Cewar Jauro yana kallon Inna Delu da bakinta ke buɗe kamar gonar auduga. "Ai Bebi yau kaya sai mun siyo har dana banza dan kaima sai ka gaji da zaɓar naka" Cewar Inna tana kallon Jauro. "Direba yi aikin ka kawai" Cewar Shattu tana ƴar dariya. Haka direban ya gangara ya je ya samu wajen parking ya ajiye motar su kuma suka fita su duka suka barshi a motar yana mamakin halin tsofaffin nan. Ƙaton shago ne wanda ya haɗa komai da komai kayan mata kananan kaya dogayen riguna babu abin babu na maza da mata. Tun da suka shiga kallo ya koma sama. Hular gashi, rigar amare gown, pakistan, dogayen riguna, rigunan bacci da rigunan bacci wanda basu kai ƙasa ba, bireziya mai ƙoƙo, sarƙa da ɗankunne takalmi mai tudu pos ta amare. Su ne kayan da Inna ta ɗakko Lantana na taya ta zaɓe. Wandunan jeans, shirts, combos, glases pacing cap , wanduna tiri kwata, su ne kayan da aka zaɓarwa Jauro, sai murna yake zai dawo yaro ɗanye sharaf, shagon aski suka shiga aka yiwa Jauro askin zamani na samari Daga nan kasuwar ƴan kayan maganun mata suka je suka kwaso kayan mata na amare wai za a ci amarci Jauro kwa sai washe baki yake zai kwashi ganima. Haka suka dawo gida niƙi-niƙi da kaya. Tun da suka fito suna tsaye ana fiddo kayan sai ga Abubakar kallo ɗaya ya musu ya ɗauke kai. "Kai fitsararren yaron nan baka da kunya kana ganin kakanninka amma ka ɗauke kai sai ka ce ka ga wasu bare, to wallahi ka shiga taitayinka, zo ɗauke mana kayan kanshiga da su" Cewar Inna cikin faɗa-faɗa dan ta lura Abubakar ɗin ba ya son cigabanta kwata-kwata yana ta zumɓura baki ya ɗauki ledojin ita ma Lantana ta ɗauki wasu suka shige ɓangaren Inna domin zuwa su ƙara kashe kwarkwatar idanunsu. Bayan kwana huɗu Yau ta kama alhamis ita ce ranar da za a yi shagalin bikin Inna da Jauro dan haka juma'a kuma za ta tare dan haka yau gabaɗaya wanda suka gayyato daga ƙauye sun hallara tun safe sai hada hadar ake yi masu kiɗan ƙwarya da aka ɗakko su sai aikin kiɗa suke masu rawa na yi su dai masu gidan wato sirikan Inna duk suna ɓangarensu abin duniya ya ishe su saboda abin da surukarsu ke yi hatta Abba da Baba tunda suka fita da safe basu dawo gidan ba sai dai sun bawa Inna komai da za a buƙata hatta hall da dj babu abin da baa ɗakko ba sun ajiye motoci da direbobi dan kawai su faranta mata, Amna ma gidan su ƙawarta ta tafi dan haushi da yake yanzu suna hutun makaranta ne. Misalin ƙarfe biyu da rabi mai kwalliya ta zo da kayan kwalliyarta haka ta zauna jiran fitowar amarya a ɓangaren Inna a falon sai mutane da kowa je sabgar gabansa. Inna ce ta fito daga ƙuryar ɗakinta (Bedroom) Hannunta riƙe da leda, mai ɗauke da kayan da za ta yi amfani da su. "Ƴar nan ina fatan dai kin ƙware wajen yin ƙyalin(kwalliya) Nan na zamani dan ranar nan a TV na ga ana yiwa wata amarya baki ga yadda jagirar ta zanu ba raɗau kamar ka sace amaryar ka zangaya da gudu" Cewar Inna tana kallon yarinyar. "Kar ki damu Iya in sha Allah idan na gama zaki yaba kwalliyar da zan yiwa jikarki" Mai kwalliya ta faɗa tana dariya, dan ita tunaninta amaryar da za ta yiwa kwalliyar jikar Inna ce . "Wace magana kike kuma wace jikartawa, ai Namna (Amna) Baƙinciki take da auren nan ko zama bata yi a gidan ba bare har a mata kwalliya" Cewar Inna dan ita tunninta mai kwalliyar tana nufin ifan ta yiwa Amna ne. "Auren dole ne kenan" Cewar mai kwalliya dan ita kwai yadda Inna ke magana ne ya matuƙar birgeta dan tana son hulɗa da tsoffi ko ba komai ka sha dariya abinka. "Ke wai maganar me kike ana maganar auren ƘARA'I na soyayya kina maganar dole, kula ki gama mini dan kar mu ɓata lokaci na ji an ce kwalliyar akwai ɗaukan lokaci" "Wai Iya mai za a miki tukunna?" "Yau ni na ga ikon Allah ɓatan nono a ƙirjin budurwa, ban da kudura ya za a yi a ɗakko ki ki mini kwalliya amma kina mini wani tambyar rainin wayo" "Ita ce fa amaryar kuma ita aka ɗakkoki domin ki yiwa kwallyar" Cewar Lantana da shigowarta kenan, da sauri mai kwalliya ta tashi tana kallon Inna da mamaki dan ta lura cikin maganar da Lantana ta yi babu wasa ko ƙarya a ciki. "Ita za a yiwa make up?" "Ni na ga ƙarfin hali ɓarawo da sallama ke dai ba aikin kuɗi kike ba to ina ruwanki ko bango aka ɗakko ki ki yiwa ai kuɗinki dai kika sani" Cewar Inna tana kallon yarinyar dan ranta har ya ɓaci. "Haba Iya yanzu tsofai-tsofai da ke zamki ce a yiwa fuskarki kwalliya wannan abu duk a yamutse kamar k... "Ke! Idan ba za ki yi ba ki kama gabanki u nemi wata" Inna ta faɗa tana harararta, mai kwalliya dai ganin da gaske Inna za ta yiwa sai kawai ta zauna ta shiga fitar da kayan kwalliyarta sai da ta gama tsaf ta kama fuskar Inna ta fente ta tass kamar budurwar amarya, dan har gashin gira aka askewa Inna da za a zana jagira wajen kwalliyar baki kwa sun ɓata lokaci saboda yadda bakin nata yake guluf na tsofaffi haka aka buɗe ledar Inna aka ɗakko wedding gown ɗin da suka siyo aka zige zip ɗin ta sanyata mai kwalliya ta rangaɗa mata ɗauri mai fanka sannanta sanya mata komai sai ga Inna ta fito a amaryarta. Haka dai ta saka takalminta da yamma aka zo za a tafi ɗakin da aka kama har da wasu kayan Inna da Jauro suka tafi dan canjawa. A bayan mota aka sanya su motoci huɗu ne suka tafi cike da mutane, ana zuwa ɗakin taron aka tarar da wasu mutanen a can ga kuma wurin zaman amarya da ango ya sha decoration yinƙurawa ya yi ya fito sanye yake da shaddarsa fara ƙal ta sha aiki sai Inna ma ta fito daga ɗaya ƙofar gabaɗaya sai kallo ya koma kansu... ƘARA'IN INNA DELU 💄💄💄💄 NA MAMAN AFRAH FCW💛 Page 1⃣3⃣➡1⃣4⃣ Da yake ba wani tsaro aka saka a wurin ba duk mutanen gari sun shigo kallo musamman samari, yadda wurin ya tsaru kowa ya ɗauka zai ga amarya budurwa ango saurayi amma suna fitowa aka fara tozali da wata uwar furfura da ta yiwa Jauro ƙawanya a fuska ga wani aski da aka masa na zamani aka aske wani wurin wani wurin aka bar masa gashi sai ya zama kamar irin fataken nan wanda suka daɗe suna yawo basu samu gari a kusa ba. Inna na fitowa daga motar da yake rigar tata doguwa ce ta mata yawa ko ƙafar baka hangowa da takalminta mai tudu gashi kuma yadin satin ne aka yi ɗinkin da shi sai aka ɗora net aka sosai rigar ta mata yawa, tana fitowa kowa ya saki baki yana kallonsu banda ƴan ƙauyensu da dama sun san su waye amarya da angon. Shattu ce riƙe da wani bokiti da aka zuba ganyen maina irin wanda ya yi yellow ɗin nan tana watsa musu a matsayin furanni dan Inna ta ce babu wani abu da ba za a musu ba sai dai ko idan mantawa suka yi da shi. Tana watsa musu tana carara guda duk da mc ya ƙure kiɗa baka jin komai amma bata daina guɗar ba, Jauro ne ya riƙe hannunta irin yadda amarya da ango suke yi, matakala ce a wurin suna zuwa sun hau ɗaya biyu suna shirin hawa ta ukun rigar Inna ta taɗe ta aikuwa ta zame ta tafi za ta faɗi, da sauri Jauro ya tareta ashe shi ma rigar ta maƙalo da ƙafarsa aikuwa suka tafi a tare suka tiƙu da ƙasa ji kake tim sun faɗi ai gabaɗaya samarin nan da suka ziyarci wurin ba gayyata suka ɗauki wani uban ihu kamar an ci ball a gidan kallon ƙwallo. Gabaɗaya wurin ya kaure da ihu wasu har fito suke, da yake da suka faɗin Jauro ne a ƙasa ita kuma sai ta faɗa da rubda ciki a kansa, duk sai kunya ta rufe su, Shattu bokitin ganyen mainar da take watsawa a matsayin furanni ta ajiye tana sakin wani salati ta nufe su cikin azama tana faɗin. "Ya subhanallahi, amarya da ango an sha ƙasa, yo dama ku da za ku shigo cikin mutane ai bakwa fito ba tare da kun sha lahaula ba, ko maganin baki saboda kallo, yadda kuka yi kyan nan ai sai ido ya kama ku kar fa ku manta duk taron nan saboda ku aka yi kuma kowa ƙoƙarinsa ya ganku wasu har ɗaɗɗage suke dan su hangi amarya da ango" Ta faɗa tana ƙarasawa wurinsu ta ce "Sannu Delu sannu Jauro ai sai ku tashi ku karkaɗe jikinku domin ƙasa ba sirikar kowa bace da za ku ji kunyarta"Cewar Shattu tana miƙa hannu za ta ɗaga Delu dan yanzu ta gangara ƙasa daga kan Jauron, gashi taƙi tashi sai Shattun ta ce "Ki tashi mana ku ƙarasa kan kujerunku na amare" "Haba Shattu kin ji ƙirjina kuwa... "Wane irin na ji ƙirjinki kuwa ke da kika faɗi ai ke za ki ji a jikinki dama" Shattu ta faɗa rai ɓace dan ta fi so Innar ta tashi saboda yadda idanu suka musu caaa "Haba ina dalili dama ai laifin Lantana ne da bata saka an rage mini tsawon rigar nan ba ta barni ina yawo a ciki zulum-zulum kamar limamin masallacin juma'a zai yi kuɗuba... "Wai Delu ki tashi mana banda ma ɗan adam ke da Allah ya taimake ki kika faɗa a kan Jauro da kan dakalin nan kika faɗa ai da kin ji a jikin ki" Cewar Shattu tana kama tsantsa ganin Delu ta ƙi tashi. "Ke kike ganin na faɗa kan Jauro, amma ni na san inda na faɗa, yadda na bugu a ƙirjinsa ankan ƙashin haƙarƙarinsa baki ji ba kamar wanda na faɗa kan duwatsun wuta, har sai da na gwammace a kan dakalin na faɗa, yo ƙirjinsa babu tsoka ko ƙwaya sai ƙashi kamar ƙashin kan saniya, yadda kika san baya cin abinci" Cewar Inna tana kai hannu fuskarta ta shiga cire ganyayen mainan da suka lilliƙe mata a fuska wanda Shattu ke watsawa a matsayin furanni, da yake zafi ake fuskar nan ta yi jargaf da gumi fawundation ɗin da aka mata kwalliya da ita duk ta haɗu da gumi ya gangaro har bakinta jagirar ta haɗe da ƴar uwarta fuskar nan ta miki kamar an shafa mata jan ɓurjin bulo, tana cikin cire mainan da yake yanzu a zaune take dakaka shi kuma gogan har yanzu bai tashi ba dan shi kaɗai ya san irin azabar da yake ji, tana cire maina sai wani ƙwaro ya hau fuskar aikuwa ta sanya hannu ta dakeshi daga fuskar ta da sanya hannu ta murtsuke fuskar dan ji ta yi kamar ƙwaron ya cije ta a fuskar duk wanda ya kalli amarya sai ya yi kamar ya shiɗe saboda dariya sosai foundation ɗin ta mata kaca-kaca da fuskar. "Delu kin ganki kuwa" Shattu ta faɗa tana tuntsurewa da dariya, banza ta yiwa Shattu dan ita bata ma san kwalliyar ta caɓe ba, gabaɗaya ma jin jikinta take kamar an sheƙa mata ruwa saboda gumi ga zafi da kuma nauyin rigar. "Kamani Delu, ɗago ni, ki taya ni in tashi wallahi allon bayana kamar zai rabe a biyu, wannan wane irin daɓe (ploring) Ne suka yiwa wurin nan wallahi yadda kika san ƙarfe wajen ya daɓu sosai sun samu ma'aikatan gini wanda basu da ha'inci da kuma yashi na kirki marar algus da ƙasa, simintin da suka yi amfani ma da alama irin mai luwai-luwai ɗin nan ne. Tunda ya fara magana Inna da ke zaune take jifansa da wata ƙatuwar harara, ita takaicinta ma ɗaya yadda ta ji ƙirjinsa babu komai banda tarin ƙasusuwa, wani kishi ne ya turnuƙeta dan tana ji a ranta cewa duk Kande ta lale tsokar wajen shi yasa ta ji saura ƙashi, baƙincikinta ɗaya shi ne babu abin da za ta samu a wajen na amarci. "Kai wannan mutum akwai ayar tambaya a kan ka wallahi ka ce wai Kande kana ɗan yin sunna da ita saisa -saisa amma gashi duk ta lale tsokar jikinka sai ƙashi wato ma kullum a nan take aaɗora kanta" Cewar Inna a ranta wani kishi na turnuƙeta a gefe ɗaya kuma wata ƙwalla na cika idanunta a fili kuma ta ce "Zaka tashi da kan ka ka kama hannun nawa irin yadda ake yiwa amaren mu ƙarasa kujerar zaman namu ko kuma zaka tsaya jiran gawon shanu ne har sai na ɗaga ka, to in kuwa haka ne wallahi iska na yawo da mai kayan kara dan ko yatsanka ba zan kama ka tashi ba, banda ragwanta mai makon da zan faɗin daka taro ni ka mini irin ɗaukan da namiji ba indiye ke yiwa ba indiya wato ɗaukan jarirai kar ka bari na kufce daga hannunka yadda za a tafa mana amma shi ne kai ka faɗi ni ɗin ma na faɗi gashi nan maimakon a mana tafi ihu ake mana, zaka bar mini abin gori son a je a baiwa Kande labari take goranta mini" Cewar Inna har lokacin bata daina jifansa da harara ba. "Haba Delu bakya ganin mutane suna kallomu, a bainan nasi fa muke in banda ma ƙaran kiɗan nan ai da sai kowa ya ji abin da kike cewa... "Yo su ji mana abin kunya ai ni gaba na bashi ba baya ba, tunda dai suka ga faɗuwarmu mai kuma ya rage, ai komai aka yi da jaki sai ya ci kara in banda ma abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma zaginsa ake, ta yaya za a ce amarya da ango sun sha ƙasa, musamma ma ni amarya, ai amarya ko ta buzuzu ce sunanta amarya a wajen ango" Ta faɗa tana ƙara sharɓuno fuskar zuwa lokacin fuska ta kwaɓe kwaɓ kamar wanda aka yiwa bango flasta da kashi. Jin maganganun Inna Jauro ya yi ta maza ya miƙe zaune, kamar wanda aka janyoshi ya sake komawa ya kwanta lifet, dakyar dai ya tashi zaune yana yatsina fuska alamar shi kaɗai ya san abin da ya ji. "Kai Bebi na doku a ƙasan nan yadda kika san ba faɗuwa na yi ba, kamar wanda muke dambe aka samu wanda ya fi ƙarfina ya ɗaga ni sama ya niƙa ni da ƙasa wallahi haka na ji" Ya faɗa, yana ƙoƙarin miƙewa dakyar a dai dai nan ne Lantana da ta koma gida domin ɗakkowa amarya gwaggwaron da za ta yi amfani da shi in za ta canja kaya da magriba ta dawo cikin sauri ta nufi wurin suka kama Inna ita da Shattu suka ɗaga ta tsaye hakan ya yi dai dai da tashin Jauro tsaye aikuwa ya miƙa hannu zai kama hannun Inna ta janye tana ɓata rai. "Na gano ki aradun Allah na gano ki Delu wannan ihun ne da ake mana yake ɓata miki rai amma yanzu zan sa a mana tafi" Cewar Jauro yana matsawa saitin fuskar Inna ya miƙa dogon bakinsa mai kamar na jaɓa, wanda yake da adon gemu fari fat, ya kaiwa Inna wani kiss a kunci, yadda ya buɗe bakin ba ƙaramin wuri bakin ya ci ba a wajen yin kiss ɗin dan sosai ba kuma haɗe kuncin ma baki ɗaya d yake ƙaton baki ne da shi, yana mata kiss ɗin wanda sai da aka yi kamar a haɗo da fatar kuncin dan Inna har haƙoransa ta ji sun gatso fatar amma saboda yadda ya shammace ta da kuma tafin da wurin ya ɗauka shi ne abin da ya bala'in birgeta. ..ƘARA'IN INNA DELU 💄💄💄💄 NA MAMAN AFRAH FCW💛 Page 1⃣5⃣➡1⃣6⃣ Yana ɗago fuskarsa wajen ya ƙara kacamewa da ihu da tafi, ihu amma irin ma an burge mutane, kowa gemun ango yake bi da kallo dan ya koma kala biyu sama fari na furfura ƙasan kuma na foundation dan kiss ɗin da ya yiwa amarya Delu gabaɗaya ya gogo foundation a ƙasan gemu, hatta bakinsa da ya doɓara wajen yin kiss ɗin kamar akuya ta ci dusa dan foundation ɗin ce da ta haɗu da gumi ya danɓarota. Shi kuwa Jauro da bai san abin da ake yiwa dariya ba tunaninsa duk kiss ɗin da ya yi ne ya burgesu, dan haka sai ya shiga washe baki. "Aikin banza ashe ma abu ƙanƙane zan yi ku daina ihun ku koma yi mana tafi, da kun ɗauka indiyawa ne kaɗai suka iya hiss (kiss) Da nuna soyayya ga mace to ni ma da nake rugage gashi nan na yi abin da na caje muku ƙwalƙwalwa, ai dama da rashin kira karen bebe ya ɓata kuɓa da rashin tayi ake barin araha" Cewar Jauro a zuciyarsa. Inna ma ganin abin da ango ya mata ya ɗau hankalin jama'ar wurin dan ta lura mutanen gari ma sai ƙara tuttulowa suke kamar wanda ake faɗa musu su zo dan yanzu gabaɗaya hall ɗin ya cika maƙil. Ganin haka ya sanya Inna ita ma ta nufi fuskar Jauro dan ya mayar masa da martani aikuwa sai da ta doɓara masa bakinta a wuri uku goshi, kan hanci da kuma kunci. Wani uba ihu da tafi ne ya karaɗe wajen wasu ar da tsalle suke, samari da ƴanmata duk sun fito da wayarsu suna ɗaukan hoto wasu video, su kuma nago da amarya sai daɗi ya cika su ganin kowa son ɗaukan hotonsu yake. Samari kuwa gani suke sun samu comedy dan wasu videon ma a status za su ɗora wasu kuwa a facebuk wasu a wasu kafar sadarwar dan wanda basu gani ba su ga wannan abu mai kama da almara. Yadda ake ihu abin har ya so basu mamaki sai dai basu san ba fuskar jauro ce ta bada wani irin abin dariya, dan duk inda Inna ra masa kiss wuraren nan guda uku goshi hanci da kunci sai ya yi abin powder fuskar ya fito a wuraren sai duskar ta zama kamar yadda ake yiwa mota idan za a sake mata fenti a saka mata farin abu yi tabbare tabbataren nan, haka fuskar ta yi da foundation sosai ya koma kamar wanda zai je tashe na iya duba-duba sammadara wanda ake da watan azumi. Lantana ma ta haɗe da ƴan tafi da ihu bata lura da yadda fuskar ango ta koma ba, bare kuma Shattu da ke ta aikin watsa ganye kamar wanda aka ce da ganyen ne auren zai ɗauru. Wani daɗi ne yake baibaye Inna da Jauro idan suka ga wulgawar yellown ganyen mainan nan hakan ba ƙaramin faranta musu rai yake ba sannan suna ƙara tabbatar da cewa su amare ne. MC ne ya fara magana bayan an kashe kiɗan da ya karaɗe wajen. "Amarya da ango muna muku barka da zuwa wannan waje, sannan muna baku haƙuri a kan faɗuwar da kuka yi wacce sanadinta ya haifar da wata salon soyayya da kuka gabatar mai ɗinbin tarihi a rayuwar aurenku da duk wanda ke wajen nan ya ga yadda kuka nunawa duniya irin yadda kuke son junanku" MC ya kai ƙarshen maganar yana cewa "Dan Allah a tafa musu" A take wajen ya karaɗe da tafi da kuma ihu. Sosai zugar nan da aka yiwa amarya da ango ta shiga kunnuwansu shi kuma MC ya yi hakan ne dan ya fasa musu kai amma a zuciyarsa cewa yake "Allah wadaran naka ya lalace cewar jakin dawa da ya ga an laftawa jakin gida kaya, banda budurwar zuciya mai sa raƙuma ta auri ɗan tsako ya za a yi tsofai-tsofai da ku, amma ku zo ku kama hall dan shagalin bikin ku, ai Allah raba bawa da wahala wai gwauro a teburin mai shayi" Ya faɗa a ransa a fili kuma ya ce Dan haka yanzu amarya da ango za su ƙarasa wajen zaman su, su zauna dan mu fara gabatar da abin da ya taramu" Ya kai ƙarshen maganar yana ƙarewa wanda ke zaune kallo wanda duk yawanci ƴan ƙauye ne kuma tsofaffi sai matasan mata haka dan duk samari da ƴan matan ƴan cikin gari ne kumabya tabbatar kallon ƙwaƙwaf ne ya kawo su ba wai gayyatarsu aka yi ba. Hannun dama Jauro ya kai ya riƙo ƙugun Inna tare da riƙe hannunta da ɗaya hannun nasa kamar yadda jiya da dare ya ga wani actor ya yiwa budurwarsa a film ɗin india. A haka suka nufi kujerar tasu, Shattu na aikin watsa musu ganyen maina. "Wai bauti (Beauty) Ka ɗauke ni mana yadda indiyawa ke yi " Cewar Inna ƙasa-ƙasa. "A'a Bebi kinsan dai yadda muka sha ƙasa ɗazu kuma lokacin ma da ƙafafunmu muke tafiya shegiyar rigar nan ta taɗe mu bare kuma a ce na ɗaga ki to wallahi yanzu dai muka ƙara shan ƙasa sai kuma yadda hali ya yi" Shi ma Jauro ya bata amsa a hankali, yadda suke maganar raɗa-raɗa sai ya ƙara baiwa mutane dariya su ala dole ango da amarya a haka suka ƙarasa suka zauna. Kande da Karime da ke laɓe a cikin wani ɗaki suna hango duk abin da ke faruwa, gabaɗaya kishi ya baibaiye musu zuciya Karime mahaifiyar Kande uwar gidan Jauro ita ce ta kalli Kande ta ce "Maza ɗauki kwanan shan manjan nan tun da sun zauna yanzu ne dai dai aiwatar da abin da a dace tsaffin banza da basa jin kunya" Ta faɗa tana ƙara ƙyallara idonta ɗaya da yake ido ɗaya gareta. Jan hanci Kande ta yi yare da sanya hannu ta share hawayenta ta ce "Gaskiya Jauro ya iya cin amana ji yadda ya riƙo ta yana zubar mini da mutunci a idon mutanen ƙauye da rugagenmu " Ta kai ƙarshen maganar tana sakin kukan takaici da na kishi. "Ki haƙuri ai sai inda ƙarfinmu ya ƙare yanzu dai ki je ki yi abin da n saka ki" Cewar mahaifiyarta. Haka ta fito ta nufi wajen da ya karaɗe da kiɗa wasu har sun fita suna cashewa Kande na zuwa bata yi wata-wata ba ta faki idanun mutane da yake kowa idanunsa na kan masu rawa ne amarya da ango kuma ana zaune da cake a gabansu da lemuka amma in ka kalli fuskar Inna yadda take shaining ɗin foundation ga gumin nan yana ta kwaranyowa shi kuma ango da dabbaren fuskar kashe uku a fuskarsa ga wacce ta mayar masa da gemu kala biyu. Ta bayan kujerarsu Kande ta zo ta ɗaga kwanon sha mai cike da manja ta shiga kwaranyawa a kan ango da amarya tun daga kansu har uban jikinsu bata dakata ba sai da ta juye musu shi tas... Su Jauro an saki baki an maida hankali kan kiɗa ana kallon masu rawa da juyi basu zata ba basu tsammata ba sai suka fara jin zubar wani abu a jikinsu yana gangarowa har fuskarsu. Inna Delu ce ta juya bayanta dan ganin wanda ke musu wannan aika aikan amma sai ta ga wayam babu kowa, juyawa ta yi ga masoyinta abin ƙaunarta Jauro aikuwa ta yi mugun gani domin kuwa manjan ne ya masa sharkaf tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi babu abin da ya so baiwa Inna Delu dariya irin yadda manjan ke zubowa ta gemun Jauron, gurbin idanunsa ne kaɗai ake gani a fuskarsa inda ba manja. "Badaƙalar nan lallai yau zan nuna wa wanda ya mana wannan aiki wacece ni, tabbas dama a san mutum a san sana'arsa in ya bari a san ya daina, domin kuwa inda ba ƙasa nan ake gardamar kokawa" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuwa sai ta kalli Jauro da ya washe bakinsa gemun nan nasa har lokacin yana ɗigar manjan amma wai ita yake yiwa dariya kuma duk abin da ake babu wanda ya lura da abin da aka yiwa ango da amarya dan kowa hankalinsa ya karkata ga rawar da ake a wurin. Deluna kin ganki kuwa, kin ga yadda kika koma kamar jemage ya faɗo daga sama" Cewar Jauro cikin sigar wasa. "Yo ba gwara ni kamar jemage ya faɗo daga sama ba wallahi idan ka ga yadda ka koma kamar an tsamo ɓera daga ruwa" Ta faɗa tana tashi tsaye dan ta ji haushin maganarsa duk da wasa ya faɗa. Tashin amarya tsaye shi ya sanar da mutane halin da ake ciki kowa ɗaɗɗage yake ya hango amarya da ango dan ya tabbatar da ka ce na cen da ake, ita kuwa Delu bata damu da kallon da ake musu ba kawai so take ta ga wanda ya musu wannan ɗanyen aikin. Iya ganinta bata ga kowa ba shi ma Jauro haka ya tashi yana dubawa amma ba a ga kowa ba Shattu ce ta kamo hanya daga mazauninta dan zuwa wurin aminiyarta amma kafin ta ƙarasa sai ganin Inna ta yi a fusace ta nufi wajen MC rigar nan sai rinjayarta take rana neman faɗuwa. Inna na zuwa wajen MC ta warce lasifikar hannunsa shi kuwa saka mata ya yi dan kar ta goga masa manja ta taƙaita shi. "Lallai yau na gane shayi ruwa ne, banda mutane baku da tsoron Allah ku da kuka zo cin arziƙi amma wadatar biki tsarki da romo shi ne har aka samu wani ɗan kan uwan da ya lalata mana kwalliyarmu saboda baƙinciki, to inason wanda ya yi wannan aiki ya sani an yi ba a yi bane wai rufe ƙofa da ɓarawo, in ma baƙinciki mutum yake to sai dai ya mutu mutu dan ni da Bebi Jauro mutuƙaraba takalmin kaza, kuma masu cewa tsoho da tsohuwa to ni banga tsofan Jaurona ba ganinsa make kamar saurayi ɗan shekaru ashirin, yo ai guntun gatarinka ya fi sari ka bani kuma... Maganar Inna ta tsaya ne sanadin ganin wani saurayi mai ƙarfin hali, wanda ya zo har gabanta y tsaya yana mata video dan shi daga can inda yake videon ba ya ɗaukuwa shi yasa ya zo gabanta dan yau ya yi alƙawari duk wata lfr sadarwa sai ya ɗorata yadda ta yi jargaf da manjan nan, ko kwalliyar da aka mata ba a gani manja ya rufe ta ruf. Kallo Inna ta ƙare masa ta ganshi sanye yake da garar riga irin mai farin nan tass sai baƙin wando, cikin sanɗa da ƙarasa gabansa shi kuma ya maida hankali cikin wayar dan da ya fara ganin tana matsowa a a cikin wayar sai ya ganta kamar aljana kuma bai yi zaton wurinsa ta nufa ba ya ɗauka ta kammala jawabin ne za ta bar wajen. Inna Delu na ƙarasowa ta miƙa hannu cikin zafin nama ta damƙo wuyan rigar saurayin nan, saurayi na ɗaukan video sai ji ya yi an rafkoshi kamar wanda ɗan sanda ya kama ɓarawo, ɗago kan da zai yi aikuwa ya sauke su a kan Inna Delu da manjan nan sharkaf sai ɗiga take kamar wacce ta yi noman kwakwar manja. Wani takaici ne ya lulluɓeshi ganin hannunta da manja amma ta kama masa riga, rigar ma fara, wani irin zabura ya yi zai fara mata rashin kunya, Inna kuwa hannu ta kai ta damƙo hannayensa ta haɗa wuri ɗaya ta damƙe dama ɗan siriri da shi kamar sandar rake, bakinsa dai ya buɗa zai fara magana aikuwa Inna ta saki ɗaya hannun nasa ta gwabje masa baki ta janyoshi ta wanka masa mari sannan ta kai masa kyawawan ranƙwashi guda uku. "Allah ya isa n... Ai kafin ya ƙarasa Inna ta janyoshi jikinta ta rungume sai da ta tabbatar rigarsa fara ta gama samun manja har fuskarsa marabarsu da Innar yanzu kaɗan ne dan shi ma kamar wanda ya shafa shuni amma na manja. Ihu aka ɗauka a wajen wanda har ya fi na lokacin faɗuwa da kiss ɗin su Inna... Wani takaici ne ya turnuƙe saurayin ganin irin cakumar da Inna ta yiwa rigarsa, domin kuwa ta yiwa rigar wani irin ɗiban karan mahaukaciya. " Zamani kenan mura ta tadda kwaɗo wallahi sai kin san wanda kika yiwa wannan riƙon kamar kin samu wuyan saniya, wallahi sai kin banbance tsakanin kiɗa da karatu" Cewar saurayin a ransa yana ƙiyasta irin cin mutuncin da zai yiwa Inna domin huce takaicin haushin abin da ta masa za ta sanya duk inda ya yi ake nuna shi. Hannu ya sanya ya rungomo Inna, wani irin zare ido Inna ta yi dan duk tunaninta faɗe zai mata "Wallahi sai na kai amarcina gidan mijina dan yanzu layin Jauro ne, na Malam ya wuce kai kuwa baka isa ka sha zuma ta ba" Cewar Inna tana ƙoƙarin ƙwatar kanta. Kafin ta gama tantancewa sai ji ta yi ya sakata daga rungumar da ya mata ya finciki ɗaurin ɗankwalinta haɗe da hular gashin da aka saka mata, sai ga kan Inna a bainan nasi, gabaɗaya kan a ƙwaiƙwaye yake babu ma kitso saboda kan ba zai kitsu ba, duk ya zube, dan dama ƙawarta Shattu ke haɗawa da tsumma tana mata zanen hausa shi ne yanzu aka sayi hula za a yi ƙara'in biki da ita.Yana yin jifa da hula da ɗan kwalinya kama wuyan rigarta sai da ya daidaici saitin ƙirjinta ya kama ya yaga rigar har wajen saitin cibiyarta, tana ƙoƙarin kare wurin saurayin nan ya yi ido biyu da bireziyarta da ke shaƙe da fanfas ɗin yara, da alama ciko ta yi kuma cikon daban nonon da ban, dan haka ai bai yi wata-wata ba ya sa hannu ya fisgi hannun bireziyar duka biyu sai kuwa ta cire sai ga fanfas suna faɗowa kamar ƙwallon mangwaro na faɗowa daga bishiya, dan guda huɗu ne ragas ko ina biyu ta saka dan cikon ya yi tudu. Inna kuwa ganin fanfas a ƙasa a zube kuma jin wurin ya ɗauki ihu har da amsa kuwwa sannan sai ta ji nonuwan nata na reto kamar lilon wasan yara domin ya fito daga bireziya babu mafakar fakewa dan haka bata yi wata-wata ba ta durƙushe hannunta riƙe gam a ƙirjinta. Jauro daga inda yake ganin abin da ke faruwa sai kuwa ya yi wani tsalle kamar jakican sai gashi ya yi dirar mikiya a gaban wasu ƙarafe da ake ajiyewa a wajen daga can gefe, guda ɗaya ya warto ya taho rai a matuƙar ɓace dan shi ba komai bane ya ɓata masa rai irin yadda saurayin nan ya rungume Inna tare da kai hannunsa jikin bireziyarta wannan ne ya tada masa wani kishi marar misali Saurayin nan ganin irin yadda Jauro ya taho a matuƙar fusace kamar kumurcin maciji hakan ya sanya ya bawa kansa shawarar cika wandonsa da iska dan idan ya tsaya bafulatanin nan ya far masa sai ya kwanta asibiti in ma bai kai shi kushewa ba. Da mugun gudu ya bar wajen Inna yana haɗawa da tsalle, haka ma Jauro ya mara masa baya ɗauke da ƙarfen, a ransa yana raya wa a ransa cewa ba zai yiwu ba kura da aiki gardi da shan bugu. Yadda suka zuba a na kare kamar ibro ya biyo ƙulu Allah jkn rai, haka suka falfala kamar sun ci ƙafar kare. Wurin kuwa ya karaɗe da ihu MC kuwa sai cewa yake "Jama'a a yi haƙuri wuri fa ya hargitse an samu wani saurayi ya kaiwa amarya farmaki, dan haka ango ya fusata ya ga ba zai iya haƙuri ba bare ya jure ya bi bayan saurayin sai yadda hali ya yi" Samarin nan kuwa sai cewa suke "Sai ka cimmasa ango ya za a yi kai baka ga amaryarka ba, shi ya gane maka, har da rungumeta ya yi kamar shi ne angon" Haka suke faɗa suna ihu, dan su zuga Jauro dan ko tarkar riƙe masa saurayin babu wanda ya yi niyyar yi dan dama sun fi so su ga yadda wasan zai kasance dan su sha dariya. Sai faman keta gudu suke Jauro da saurayin nan, dan saurayin na fita ya sha wata uwar kwana bai bi kan titi ba sai ya keta wata unguwa shi kuwa Jauro ya take masa baya dan Jauro tun daga ƙofar wajen taron ya sille takalmansa dan ba ya jin gudun zai yiwu da takalmi, ga farar rigar nan da ta sha manja fuskar nan ban da idanunsa a fuskar babu inda manjan bai taɓa ba amma a haka yake zabga gudun famfalaƙi sai ƙara haɗa gumi yake. Saurayin nan kuwa sai waiwaye yake idan ya hango tazarar da ya bawa Jauron sai ya ƙilƙili da dariya amma dan ƙarfin hali Jauro ba ya ganin tazarar da ya bashi kawai burinsa ya same shi ya kwantar da shi da ƙarfen nan. "Wallahi ba zai yiwu ba aradun Allah, ina zan yarda mai ɗakko katifar amarya da ban mai morarta ma da ban" Ya faɗa a ransa yana ƙara wuyar gudu dan ya ga ya ɗan fara taddo saurayin duk da duk inda suka gifta sai kallonsu ake. Sai da suka kusa zuwa wani wuri inda akwai taron jama'a saurayin ya rage zabga gudun sai da ya bari Jauro ya kusa ƙarasowa sai ya ware murya ya ce "Ihu mahaukaci jama'a duka yake kun ga da ya damƙe ni yadda ya ɓata mini riga da manjan jikinsa, ai mutane na jin furucinsa sai kowa ya fara guduwa wasu suna shiga gida suna rufewa dan ganin yanayin jikin Jauro ga manja a jikinsa da fuskarsa ga babu takalmi ga ya riƙo ƙarfe kowa sai ya fara ta kansa a ƙarshe dai ya ma rasa inda saurayin ya yi dan ya ɓace masa ga mutane sai kiransa suke mahaukaci ba wanda ke sauraronsa bare ya faɗa musu lafiyarsa ƙalaw. Daga ƙarshe dai ya zo wucewa zai koma wajen taron, ta wani ƙaramin lungu sai ji ya yi, ƙum an sakar masa wani ƙaton bokitin fanti a kansa, daga saman wata katanga yana ɗagowa ya yi ido huɗu da saurayin nan shi da wani abokinsa, kan ka ce kwabo sun diro daga katangar kamar wasu birrai sun sheƙa a guje, haka ya yi ta danƙara musu Allah ya isa, har da ɗan kukansa ya matse a hanya dan kansa har ya yi wani ƙaton ƙullutu a tsakiyar kan nasa. A hanyar dawo wa yana tafiya amma wani ƙululun baƙincikin kishin abin da aka yiwa Delunsa na runguma da taɓa bireziyarta, da kuma bokitin fantin da ya sha a tsakiyar kai duk su ne suka haɗe masa goma da ashirin . "Gaskiya mutanen birni basu da kara, yanzu wannan da a ce a rugarmu ne abin nan ya faru da kowa sanda zai ɗakko a bi kwarton nan da ya rungume mini amarya, amma a nan sai ihu suke babu wanda ya yi kataɓus bare ya taimaka mini, sai ni kaɗai gashi a ƙarshe sun rafka mini bokiti kamar wanda aka aiko su duk da akwai gashin furfura a kaina amma sai da bokitin ya mini illa" Cewar Jauro a ransa lokacin da ya taho a hanya har wani ƙwallar takaici ne ya taru a idanunsa dan ba a taɓa ce masa ko da taɓi-taɓi ba amma yanzu gashi an kira shi mahaukaci sanadin ƘARA'IN aurensa da Delu. A haka ya ƙaraso bakin get ɗin inda ya watsar da takalmansa, a hannu ya ɗauka dan haushi ma ya hana shi ya saka a ƙafarsa. ƘARA'IN INNA DELU Page 1⃣7⃣➡1⃣8⃣ A fusace ya shigo wurin yana shigowa ya yi wurgi da ƙarfen hannunsa rai a matuƙar ɓace. Yana shigowa idanunsa suka sauka a tsakiyar kan furfurar amaryarsa kan nan kawai yake hangowa tana daga durƙushe Shattu da Lantana suna ta faman ta tashi amma kunyar yadda rigarta ke a ɓarke ga babu bireziya dan hannun ɗaya bireziyar ma ya maƙale a jikin ɗankunnenta, ga ihun da wajen ya karaɗe wurin ranta in ya yi dubu ya ɓaci yadda gashin kanta da ta san ko kitson kirki babu a jiki dama hular gashin da aka saka ita ce rufin asirin kan sai kuma saurayin nan ya cire mata dan ya kunyata ta a gaban jama'a. "Ya Allah kai ka san karatun kurma, ranar ƘARA'IN nan da na ci buri a rayuwata, tun da aka ɗaura auren nan ko barcin kirki bana yi sabo da ɗoki amma a ce yau tun daga farkon shigowarmu muka sha ƙasa ni da ango na anya ba hannu aka saka mini ba, wani ɗan hana ruwa gudu, wato sa'idinawa wanda ana ruwa suna irgawa" Cewar Inna a ranta zuciyarta na ƙuna. "Jama'a ku kauce, ku jaye ga ango nan da ƙarfin gwiwarsa ya dawo daga filin dagar ya je ya ɗauki fansa ya dawo" Cewar MC a lasifika. "Ka ji ɗan jaraba, in banda dai neman magana fansar me na ɗauka in banda jikina da ya faɗa mini, kan nan nawa kamar na ɗauki duron kananzir, ai ba dan ba dan ba da na ce wannan ƙara'i ban ji daɗinsa ba" Ya faɗa a ransa lokacin da ya ƙaraso wajen yana aikawa MC wata muguwar harara kamar dai shi ya ce ya bi bayan saurayin. "Ɗan tsoho ƙyamus-ƙyamus ba ni na ce ka yi auren ƙara'i ba kuma ba ni na saka ka bin saurayin nan ba, ka ga kuwa ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Ya faɗa a ransa yana saki wata ɓoyayyar dariya. Cikin hanzari Jauro ya nufi inda su Shattun da Inna da Lantanar suke. Su Kande da Karima kuwa sun daɗe da cikawa rigarsu iska dan tun lokacin da ta watsa manjan ta shige ƙasan kujerun da ke wajen shi sa ba a ganta ba, bayan hankalin mutane ya koma wajen Inna da saurayin sai ta fito suka silale suka fice daga wajen, daga nan kuwa garinsu suka koma dan dama Jauro ya ce sai ranar da amarya za ta tare za ta dawo gidan da zama. Yana zuwa Shattun cikin sanyin murya ta ce "Yawwa ango, ka ganta nan sai fama muke da ita ta ƙi tashi" Wani haushin Shattu ne ya cikawa Jauro ciki da ta kirashi da suna ango, dan shi a yadda jikinsa yake a damule da manja kai da cillukutu ko abokin ango bai ci a ce an kira shi ba bare ango, gashi ji ya yi kamar ya zabgawa Shattu da Lantana mari da suka bar Delunsa a wajen ai da ko cicciɓarta sun yi sun kaita wani ɗaki. Hannu kawai ya miƙa ba tare da ya ce uffan ba, Delu da ke durƙushe kanta a ƙasa sai ji ta yi an sure ta an yi sama da ita, sosai ta tsorata dan tunaninta wani ne cikin samarin wurin a sure ta gabaɗaya zai gudu da ita ya mata fyaɗe, dan sosai ta tsorata da lamarin abin da saurayin nan ya mata, sannan bata zaci Jauro zai iya ɗaukanta ba. Tana ɗan ɗago fuska ta sauketa a kan fuskar angon nata da ta sha manja abinta sharkaf, kamar daron da ake siyar da manjan wani tausayin kansu ne ya kama Inna Delu ganin halin da suka tsinci kansu a ciki a yau da ta kasance ranar farinciki. "Bebi in ce dai ka sumar da shi da ƙarfen nan?" Cewar Inna tana kallonsa. Ai maganar nan da Inna ta faɗa Jauro ji ya yi wani kishi ya ƙara taso masa gashi ba ya so ya faɗa mata gaskiya ta ga ragwantarsa dan haka sai ya ce "Ai na masa illa, ma dakyar mutane suka ƙwace shi, yana can lange-lange aka tafi da shi asibiti" Ya faɗa yana kallon gefe dan kar ta gano ƙaryar da ya sheƙa mata. Wani daɗi ne ya baibaye Inna jin an ɗau mata fansa hakan ya sanya ta ƙara jin ƙaunar Jauro a ranta. "Lallai na auri miji na nunawa sa'a" Ta faɗa a zuciyarta tana jinjina jaruntarsa. Tun da ya ɗakko Inna Delu mutane suke ra binsu da kallo samari da ƴan mata kuwa sai ihu suke ganin ango ya yiwa amarya ɗaukan jarirai, hakan ya sa wurin ya ƙara kacamewa da ife-ife shi kuwa bai bi ta kan koa b duk da nauyi yake ji da ya ɗauki Inna kamar wanda ya ɗauki buhun gero, dan dakyar yake ɗaga ƙafafunsa ƙarfin hali ne kawai yake. Ɗakin da aka ajiye musu kayan da za su canja da magriba saboda ƙayatarwa to yanzu kuma tun da komai ya kwaɓe musu dole yanzu su canja kaya tun da kayan sun ɓaci da manja. Suna shiga ɗakin Jauro ya nufi wata kujera mai zaman mutum ɗaya da ke ajiye yana zuwa jaɓar ya saki Inna a kan kujerar ashe kujerar tsohuwar kujera ce dan haka Inna ji kawai ta yi ta ɓurma ciki, kafin raɗaɗin faɗawar ya gama ratsa t sai ji ta yi mazaunanta sun yi karo da wata ƙusa wani uban ihu ta saki wanda ya saka Jauro da ke sunkuye ya ɗago dan tun da y jaɓar da ita a kan kujerar ya sunkuya saboda ƙagewa da bayansa ya yi na gudun da ya tiƙa da kuma ɗaukan da ya yiwa Inna. "Wayyo ni Delu yau dai ina ganin sauyawar kalolin rayuwa kamar wacce iyaye suka jeki ka gani, in banda jafa'i da neman rarrabuwar sassan jikin mutane ya za ayi a ajiye wannan ƙazamar kujerar mai jiki duk ƙusoshi " Ta faɗa tana ƙoƙarin kai hannu wajen mazaunan nata tare da sakin wani kuka. "Haba Delu wai me yasa kike haka ke ba damar a yi abu sai ki ɓare baki ki fara kuka kamar matar marigayi, saboda ke ga mai arahar hawaye" "Au haka ma zaka ce Jauro, bayan ka jefa ni kan ruɓaɓɓiyar kujerar nan na faɗa a kan ƙosa" "Wato Jauro gatse-gatse ko sakayawa babu, ko kan ƙaya tsidau na jefa ki ai kya gode mini domin kuwa na yi namijin ƙoƙari da na ɗakko ki a hannu na, tun daga filin can har nan, hannu na da kafaɗata kamar an sara mini da gatari saboda tsabar ƙagewa da suka yi" "Na faɗa Jauro, kamar wani wanda na yi saɓon Allah dan na faɗi sunanka shin da soyayya ma tana bari masoyi ya ji nauyin masoyi, baka ga yadda turawa ke ɗaukan matansu ba" "Ashsha Allah baki haƙuri Bebi" Ya faɗa dan kawo ƙarshen maganar. Banza ta masa tare da taɓe baki, tashi ta yi dakyar daga kan kujerar ta shiga bayi ta wanke fuskar tas ta fito ta cire kayan ta sanya wanda Lantana ta kawo musu, shi ma ya shiga bayin ya gyara jikinsa tare da canja kayan nasa sai gasu sun fito a amarya da angon su. Hannunta ya kama suka fito suna sakarwa juna murmushi gabaɗaya wuri ya ruɗe da fitowarsu haka suka ƙarasa wajen teburinsu. "Yanzu amarya da ango za su yanka cake" MC ya faɗa. Cikin washe baki suka tashi Jauro sai washe baki yake jin zaa yanka cake dan gabaɗaya yawun bakinsa ya tsinke. Haka suka kama hannu a tare suka yanka cake ɗin. "Ango zai fara bawa amarya a baki sai ita ma ta bashi" Cewar MC. Jauro hannu ya kai ya ɗakko cake ɗin da ya gutsuro da wuƙa, ya nufi bakin Inna da take wani ɗan sunkuyar da kai alamar kunya irin ta amare, dakyar da ta buɗe bakin aikuwa ya saka mata, a take aka ɗauki ihu da tafi. Inna tunda cake ɗin ya isa bakinta ta ji wani irin ɗaci da tsami a lokaci guda haɗe d warin kananzir, amma haka ta daure ta ɗan runtse ido yadda mutane ba zasu lura ba ta haɗiye ba tare da ko taunawa ta yi ba ita kaɗai ta san bala'in da ke cikin cake ɗin wanda ya ziyarceta amma kuma bata ya aka yi haka ta faru ba. "Amarya sai gareki ke ma za ki bawa angon naki cikin shauƙi na soyayya" Inna da ta yi nisa wajen tunanin ya aka yi haka ta kasance ta tsinkayi muryar MC yana magana. Inna cikin rashin kuzari ta yanko cake ɗin ta ɗauka a hannunta, tunda ta fara yankowa yawun Jauro ya cigaba da tsinkewa sai haɗiyewa yake wani yawun na ƙara taruwa, bare da ya ga ta ɗakko a hannunta ai har wani dillo harshe gake, sai dai yadda Inna ta birgeshi ƙato ta yanko ya san dai duk faɗin bakinsa dole wanda ta yanko ya cika masa baki. Inna kuwa tunaninta ɗaya kar fa ta saka masa a baki ya kunyata ta, dan ta san dai akwai gwarama matsawar Jauro ya ji ɗanɗanon cake ɗin gashi tana so ta masa bayanin kar ya kunyata ta amma kuma idanun jama'a a kansu, sannan tana so ta masa raɗa a kunne sai dai ta ga gabaɗaya hankalinsa a kan cake ɗin yake sai wani raba ido yake yana washe baki. "Haba Delu ƙur'ani kika yi jinkirin saka mini cake ɗin nan a bakina sai dai jama'a su ga yawu yana dalalowa daga bakina saboda gabaɗaya yawuna ya tsinke ƙiris yake jira ya zubo" Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma sai ya shiga ɗan kannewa Inna ido ɗaya yana mata alamar ta sama. Hannu ta ɗaga a hankali tana so ta saka masa a bakin nasa har dai ya yi ƙarfin halin cewa "Wannan ɗaukan alhaki da yawa yake Delu mai magana (MC) A dodon magana (Lasifika) Yana cewa in baki na yi saurin baki amma ni kike jirgani" Ya ƙarasa faɗa cikin raɗa-raɗa. Ta ji shi sarai amma sai ta masa banza. "Bebi ka ce azumi kake" Ta faɗa masa ita ma cikin raɗa dan ta lura in ta zauna masa bayanin abubuwan da ke cikin cake ɗin ba ganewa za ta yi ba. "Azumi fa kika ce Delu yo wane shegen ne zai yarda azumi nake, yo ni rabona sa azumi tin wancan shekarar, ko azumi nake saboda ket (Cake)Ɗin nan aradu na karya shi katsak sai dai in yi istigfari" Ya faɗa yana aikwa Inna wata harara dan ya lura kamar baƙinciki take ya ci cake ɗin. "Amarya ke ake jira fa domin kowa yana son ganin kalar taki soyayyar" Cewar MC ganin amarya ta yi jinkirin bada cake. Wani irin gyaɗa kai Jauro ya yi irin na kin dai ji ai ɗin nan. Inna kuwa wani kallo ta masa tare da ɗan danne gefen leɓenta ta saki wani murmushin yaƙe. Wani irin hangame baki Jauro ya yi ganin za a saka masa cake aikuwa Inna tana zuwa bakin ta tura cake ɗin cikin bakin nasa tare da ƙara zungura shi da hannunta. Jauro kuwa da ya buɗe baki jin dirar wani tsatstsaman abu mai shegen ɗaci da wani warin kananzir sun baibaye masa baki, wani irin yamutsa fuska ya yi tare da zaro idanu dan gabaɗaya abun ya haɗe masa baki. "Haɗiye mana Bebi" Cewar Inna tana sanya hannu ta haɗe masa leɓɓan bakin. Wani amai ne ya yunƙuro masa amma ganin Inna riƙe da leɓunansa ga idanun mutane a kansu dan kowa ya yi zaton duj cikin salon soyayya ne haka ya daure ya haɗiye dakyar yana neman yin amai aikuwa aka shiga tafa masa. "Kai jama'a da kun san mai na ƙunsa a bakin nan nawa na haɗiya da baku tafa mini ba" Cewar Jauro a zuciyarsa kamar ya yi kuka. Duk abin nan da ake Amna tana laɓe daga wani wuri tana kallonsu, dan ita ce ta je kicin ɗin Inna inda aka ajiye cake ɗin ta jiƙa bula lemo, ta yi amfani da sabon sirinji wajen zuba wa a jikin cake ɗin, ta jiƙa filajin mai yawa gabaɗaya ta ɗore a cikin cake ɗin daga ƙarshe ta ɗura kananzir duk da sirinji. Bayan ta je gidan su ƙawarta shi ne ta biyo ta wajen partyn na Inna domin ganin ya za ta kaya. "Ba dai kin ce sai kin yi aure ba duk da iyayenmu sun hana ki kaɗan ma kika gani" Cewar Amna a zuciyarta. Haka dai aka gama taro aka watse motoci suka maida su Inna gida. Washe gari da yake a ranar ne za ta tare da yamma suka tafi gidan wata mai maganin mata duk da wanda Inna tasha wanda suka siyo daga kasuwa amma sai da ta ce Lantana ta raka ta dan tana so ta rikirkita ango haka suka je da Shattu da Inna da Lantana direba ya kai su. Cicciɓi aka dafawa Inna ta cinye, da ƴan shila aka ƙara mata da maganin matsi har da na gyaran nono, haka suka cake kuɗin mai kayan suka bata tun a mota Inna take ta sakin wani murmushi, Shattu ce ta gaji ta ɗan matsa kusa da kunnenta ta ce "Wai ni kam Delu dariyar me kike?" "Hmmm bari dai ke ai na fara tunano yadda ango zai rule saboda na sha gyara, kinsan Allah Shattu a gidan mai maganin nan da na shiga bayi fitsari tsabar matsin da aka mini ko yatsa bai shiga wurin nan ba, aradu ina jin Jauro sai ya ɗauka da budurwa yake tare, dan yanzu ma ɗan tofina jargaf yake ya jiƙe yadda kika san ƙorama haka na koma" Cewar Inna tana ƴar dariya yadda direba da Lantana da suke gaba ba za su ji ba. Hannu Shattu ta bata suka tafa suna sakin wata dariya irin tasu ta tsofaffi da su kaɗai suka san ma'anarta. Dab da magriba wata mota golf da Kande ta iyo shatar ta tun daga garinsu aka ɗakko mata kayanta, ita da wata budurwa ƴar ƙawarta mai suna Balaraba suka taho motar ce ta ƙaraso gidan aka ƙarasa da ita ɓangaren da aka ce za ta zauna dan Jauron ne ma ya raka ta sai kuma aka saka almajirai suka kwashe kayan. *DARE* *JAURO* Sanye yake da shadda mai babbar riga hannunsa riƙe da kedoji guda biyu, haka ya je ɗakin Kande da ke zaune ita da Balaraba suna zumɓure-zumɓuren baki, da sallama ya shiga amma babu wanda ya amsa sai dai abin da ya lura da shi tun shigarsa Balaraba ke satar kallonsa tana masa wani kallo da ya kasa gane na menene. Haka dai ya ajiye musu ƙaramar leda mai tanƙwashen kifi ɗaya rak ya musu sallama babu wanda ya tanka masa ya fito ya nufi ɓangaren amarya Delu dan Inna ta ce babu wani wanda zai haɗa ta da wata kishiya ya musu kashedi dan haka ma bai tarka ba. Yana shiga falon da sallama Shattu ce da ke cikin ɗakin ta amsa masa, suka masa iso a kan ya ƙarasa cikin bedroom ɗin haka ya ƙarasa ya same su Inna zaune a bakin gado lulluɓe da mayafi kanta a sunkuye, ƙafar nn da hannu ta sha ƙunshi, Shattu da Lantana sun saka ta a tsakiya. Cinikin baki aka yi ya biya Shattu da Lantana suka musu sallama suka tafi ɓagaren su Lantana. Bayan fitarsu ango ya miƙe ya cire babbar riga ya matsa yana yiwa amarya daɗin baki ya buɗe fuskar. "Allahu akbar, lallai Allah ya yi halitta a nan kin ganki kuwa Delu duk duniya babu wata mace da ta fiki kyau da matsayi a wurina" "Har Baba Asabe?" Cewar Inna tana wani fari da ido. "Haba Bebi idan ana dara ai fidda uwa ake, ya za a yi ki haɗa kanki da uwata" "Allah huci zuciyarka ai na ji ka ce duk duniya yo ai na ɗauka har ita" Banza ya mata yana jin babu daɗi a ransa, amma babu yadda ya iya tunda dai yau yana so ya kwashi ganimar amarya. Hannun Inna ya kamo ta janye da sauri. "Haba Bebi ya haka kuma? Bayan na biya sadaki" "Ka biya sadaki ko dai an biya maka, wallahi kana taɓa ni na ji wani yammm " "Duk ɗaya ne ai tun da dai mijinki nake, yo ai yammm ɗin da kika ji alamar lafiyarmu ƙalaw ne " "Haba Jauro ai tun ranar aure aka gwadamu aka ce babu mai ƙanjamau" "Ba wannan lafiyar ba, lafiyar gabatar d sunnar aure" Hannu ta sanya ta rufe idanunta alamar kunya, haka dai ya kama hannunta suka zauna a ƙasan ɗakin, har sun zauna Jauro ya ce su cire kayansu dan kar su yi ƙarnin kifi. "Ki...ki...kifi fa ka ce?" "Eh mana kifin amarci" "Haba Bebi yanzu tsakaninka da Allah kifi ne a matsayin kazar amarya duk yadda muka ci burin ranar nn" Ta faɗa tana zumɓura baki. Haƙuri ya shiga bata haka suka cire kaya ita sai ta saka rigar bacci mai ƙaramin hannu shi kuma ya zauna da gaeran wando kawai. A baki yake bata tana bashi sun yi nisa wurin cin kifin suna korawa da lemon kwalbar da ya sako guda biyu sai kawai Inna ta haɗiyi ƙaya lemon ta sha amma ƙaya ta ƙi gaba ta ƙi baya, tun abin kamar wasa ya koma ba na wasa ba, ganin Inna riƙe da maƙogwaro tana ta ƙolon amai, hakan ua sanya Jauro cewa "Bari dai in je ɓangaren su Umaru ko za a samu gayan tuwo ki samu ki haɗiya ƙayar ta wuce" Yana faɗa bai jira cewar Inna ba ya fita da sauri dan gabaɗaya ma a ruɗe yake. Haka ya ƙarasa ɓangaren Baba daga shi sai gajeran wando tiɓi-tiɓi dan wandon ya kama shi, yana zuwa ya shiga doka ƙofar da uban ƙarfi Baba da matarsa har sun kwanta suka ji ana ta bugun ƙofa kamar za a ɓalla, haushi ya sanya Baban ƙin tasowa ya buɗe dan gabaɗaya zuciyarsa a dagule take haushin wai yau mahaifiyarsa ke tarewa sai wani rawar ƙafa take wai ita amarya wannan abun shi ke ci masa tuwo a ƙwarya. Matarce ta tashi tana wani yamutsa fuska ta sauko ƙasa dan a sama ma suke.Tana zuwa bata tambayi waye ba ta buɗe ƙofar Jauro da ke jiran a buɗe ƙofar yana ganin an buɗe sai kawai ya afka ciki, ita kuma bata tsaya ta tantance waye ba dan kallan tsoro ta masa tunaninta ma ko wani kwarton ne dan ganinshi tuɓe sai gajeran wando bai ƙarami ɗaga mata hankali ya yi ba. A sukwane ta juya tana sakin ihu kwarto, ta haura sama dan step bibbiyu take tsallakewa tsabar a ruɗe take. Jauro kuwa haushinta ma ya ji dan haka ko ta kanta bai bi ba sai ya nufi kicin zai dubo tuwon san shi amaryarsa ce a gabansa ba zai tsaya dogon surutu ba ya je ya rasa ta. Baba kuwa jin ihun matarsa da kuma kiran kwarto da take sai ya tashi ya ɗakko wata sanda wadda ya tanada saboda irin ranar nan dan haka kafin ta shigo ɗakin ma ya fito da gudu ɗauke da sanda, a bakin ƙofa suka yi kiciɓis ta shige ɗakin da gudu a ruɗe alamar a tsorace take, tana shiga shi kuma ya iyo ƙasan a sukwane, yana sakkowa falon ƙasan ya hango Jauro ya bashi baya ya nufi ƙofar fita, ganinshi da gajeran wando ya tabbatar masa da kwartancin ya zo, dan haka cikin sanɗa ya lallaɓa ya saukewa Jauro sanda a gadon baya, sai ga Jauro ya zube a reran hannunsa riƙe da gayan tuwon da ya ɗakko a kicin zai kai wa Inna taimakon gaggawa. Zubewar Jauro ta yi daidai da saukar idon Baba a akan fuskar Jauro idanu ya zaro ganin mijin mahaifiyarsa kuma angon wannan rana. "Baba Jauro" Ya faɗa cikin tashin hankali yana jefar da sandar ya nufe shi, hakan ya yi dai dai da sakkowar matar Baban daga sama tana ɗari-ɗari. "Alhamdulillah dear ka rafka masa sandar" Ta faɗa tana ƙarasowa inda aka baje Jauro. Banza Baba ya mata dan ya san yau sai ta Allah tunda ya rafke angon mahaifiyarsa tunanin da yake a gefe guda ma shin mai ya kawo shi ɗakin. "Lah ashe bayan kwartanci har da satar tuwo ya zo" Ta ce lokacin da ta ƙaraso wajen idanunta a kan tuwon da ya faɗi daga hannunsa. "Mijin Inna ne fa" Ya faɗa yana fito da wayarsa daga aljihunsa ya shiga kiran Abba. Haɓa ta dafe tana jinjina abin a ranta yanzu haka za su rayu da waɗannan tsofaffin a gida ɗaya suna abu kamar yara ƙanana a ce har da gajeran wando zai shigo musu sashen su. "Ka zo ɓangarena yanzu" Haka Baba ya cewa Abba lokacin da ya ɗauki wayar dan shi ma yana kwance bacci ya kasa ɗaukansa abin duniya duk ya ishe sa. Yana zuwa ya ga abin da ke faruwa ruwa aka ɗakko aka shiga sheƙa masa ya farfarɗo yana cewa "Bebi dama ba za mu rayu tare ba, a daten farkonmu ashe zan mutu ko amarcin bamu fara ci ba" Ya faɗa yana sumbatu, su kuwa kowa jinin jikinsa ya sha. Sai da ya dawo hayyacinsa suka masa kama-kama suka nufi sashen Inna dashi sun doshi ɓangaren Innar sai ga Inna ta fito tana ɗan tari tare da cewa "Bebi Jauro ina kake ko... Ganin su Baba ɗauke da Jauro ya dakatar da Inna daga maganar da take ta shiga rafka salati yare da sakin kuka, tana ta tambayar mai ya same shi basu tanka mata ba dan so suke su je su ajiye shi dan nauyi ma kaɗai ya ishe su Page 1⃣9⃣➡2⃣0⃣ Tun daga bakin ƙofar take rafka uban kuka wai an kashe mata ango, babu wanda ya tanka ta har suka shigo falon aka kwantar da shi a kan kujera. "Wayyo masoyi wayo ya maka wannan aika-aikan, wane ɗan baƙincikin ne wanda yake so ya shiga tsakanin amare da amarci" Cewar Inna tana rushewa da kuka. "Wayyo bayana Delu, ai kawai in faɗa miki na ɗakko gayan tuwon nan kawai sai ji na yi an yi sama dani, ni dai ban san ya aka yi ba sai gani na na yi zube ana yayyafa mini ruwa, aradu na ɗauka mutuwa na yi ake mini wankan gawa da ruwan ashe dai ina nan da raina" Ya faɗa cikin ƙasa da murya irin na mai jin jiki yana sakin kuka a hankali. "Ƴan abin da malam ya hana faɗa waye cikinku ya masa wannan aikin" Ta faɗa tana kallon Baba da Abba. "Inna santsin tiles ne ya kwashe shi" Abba ya faɗa. "Wallahi Delu ƙarya ne har ihun kwarto fa aka mini a kan na je ɗaukan gayan tuw... "Waye ya maka ihun kwarton" Ta katse shi a zafafe dan har kishi ya yiwa zuciyarta dirar mikiya. 'Matar wannan yaro Umaru... "Allah na tuba ka mini aikin gafara yanzu mai za a je wa kwartanci wannan mata a ƙeƙashe ko ina ba mamora yo ai ko Umaru ina ga haƙuri yake da ita" Cewar Inna tana harare-harare. "Wai ta ganni da gajeran wando" "Yo ai ka gama zubar mini da ɗanyen mutunci Jauro, yanzu haka ka fita tsirara da ɗan kanfai ka bari matar ɗana ta gama gane mini sirrina son ka ja mini raini, ai ni ɗazu ma ƙayar nan ce ta hana ni maka magana, kuma kana fita sai na samu tsoka na mulmule na haɗiye sai ji kake mudik ƙayar ta wuce " "Ni fa ban bari ta gane ni ba, dan baya ma na juya mata na tafi ɗaukan tuwo... "Rufe mini baki, da banda dai tagayyara ya za a yi ka kawo wa amarya kifi sai kace wata amaryar kyankyaso maimakon ka samo mini ƙatuwar zabuwa in ci in nare har in yi guntun wanda su Shattu za su ci da safe, dama Shattu sai faɗi take in ajiye musu kazar amarya amma dan ka jawo mini gori ka kawo wani bushashsshan kifinka mai zaƙo-zaƙon ƙaya ta maƙale mini a maƙoshi... "Inna bari mu je sai da safe" Cewar Baba ganin maganar bata shafeta ba "Umma ta gaida Aisha tun da kun gama gane Babanku da ɗan kanfai" Ta faɗa tana jifansu da harara babu wanda ya tanka mata suka fice sumi-sumi. "Wayyo bayana samo ruwan ɗumi ki mini gashi" Ya faɗa yana mere baki. Wata uwar harara Inna ta jefa masa baki sake sannan ta ce. 'A'a Jauro bana son wani ɓoye-boye in ka san babu wani bayani a tare da kai ba sai ka biyo mini ta bayan gida ba, amma in ba son ka sanya na fara tunanin makomar amarcina na yau ba kai da zaka tashi ka zage domin taryar amarya a baje basirar tunanin sarrafa komai da komai a yi gagarumin yaƙi a kashe arna amma dan lalaci kake maganar ruwan ɗumi ai na ɗauka ni ce zan buƙaci ruwan ɗumi amma ba dai kai ba" "Ikon Allah na kwance ya faɗi yanzu ashe Delu har ni zaki fara tunanin babu abin da zan iya taɓukawa a daren amarci sai kace wani sauna kira mana shashasha in ka ga sakarai ku taho tare, in ma ba dan wannan tsautsayin ba ai da yanzu muna filin daga, ni nan jarumin jarumai ne awa bakwai nake kwashewa a gabatar da sunna ga Kande ma bare kuma ke ai sai yadda hali ya yi sai na ga abin da ya turewa buzu naɗi" Wani irin washe baki Inna ta yi, jin za a sha amarci, dan har ta fara sarewa cewar babu shan amarci a daren yau. Haka ta tashi ta samo ruwan ɗumi ta ɗan gargasa masa inda aka doka sandar kafin ya ɗan ware yana zaunawa dakyar, bayan yanji ɗan dama-dama ya tashi suka koma ƙuryar ɗaki, har suna shirin kwanciya Inna ta tuna bata rufe ƙofa ba dan haka ta fita domin ta rufe, tana fita Jauro ya tashi da sauri ya ɗakko wata leda a ajjihun rigarsa da sauri ya buɗe ya lakuci maganin ya shafa a jikinsa (Al'aurarsa) Maganin ƙarfin maza ne da tada shu'umar sha'awa da sauri ya maida ya koma kan gado ya kwanta. Inna tana gama rufewa ya dawo ɗakin ta kashe fitila ta ƙarasa kan gadon, can sun ɗan yi nisa ana shirin cin amarci sai kawai suka fara jin wani sauti ana cewa "Delu, Deluna taho mana Delu" Muryar Malam marigayi mijin Inna ita ce ta karaɗe falon Inna wanda suke jin sautin har cikin ƙuryar ɗakin da suke. Wani irin zabura Jauro ya yi tare da ƙara ƙanƙame Inna, cikin razana da gushewar hankali haɗe da tsoro Inna ta sanya hannu biyu ta hankaɗa Jauro dan jin wani irin tsoro take "Angon naki kije turewa a daren amarci, haba Delu ya za a yi ina shirin haƙar rijiya (Gabatar da sunna) Amma kike neman kawo mini cikas" "Haba Jauro baka jin muryar fatalwar Malam duk ta karaɗe ɗakin wani irin cin amarci ana zaune ƙalaw ai indai amarci ne na haƙura ko so kake in ci amarci fatalwa ta tafi dani yanzu, ai wallahi wannan Malam an yi kudurarre, yanzu ba ya duniyar ma sai ya haramta mini more rayuwata duk irin burin da na ci a kan ranar nan amma sai da ... "Delu ina kallonki ke da sabon mijin naki, ashe dai dan dole sai da kuka yi aure,to cin amarci dai haramun giya a gidan liman, babu wani amarci da za ku ci in kuma kuka ƙi ji to tabbas bakwa ƙi gani ba, dan haka Ku taso ku bar ɗakin nan yanzun nan in ba haka ba yanzu za ku ganku a maƙabarta" Abubakar da ke ƙasan kujera wanda tun fitar Inna da ta bi bayan Jauro da ya tafi ɗaukan tuwo ta shigo ɗakin ya shige ƙasan kujera shi ne yake magana a cikin kofin silba ya toshe hancinsa ɗaya yake muryar Malam, dan ya ci alwashin babu wani amarci da za su ci. Ai jin ya ce su bar ɗakin ai a sukwane suka fara rige-rigen sakkowa daga kan gadon koww jikinsa na karkarwa. Inna ce ma ta yi ƙarfin halin saka wani zurmemen hijabi amma ko ɗan tofinta baya jikinta "Da rarrafe za ku fito" Jin haka ya sanya Jauro sauri zubewa rigijib a ƙasa har sai da ya ji raɗaɗi a gwiwoyinsa amma haka ya daure dan shi yanzu da za a ce ya bar garin Kano ma gabaɗaya babu abin da zai sanya ya zauna dan ya tsorata sosai. Haka suka rarrafo Jauro a gaba Inna tana binsa a baya,Jauro tsirara yake dan tsabar tsoro ko gajeran wandon bai saka ba Inna da ke bayansa tana hango sandar girmansa daga vaya da yake da rarrafe suke tafiyar. "Wa ya ga jelani, wannan abu carai-carai kamar ɗan wada ya je ci rani" Cewar Inna zuciyarta ganin sandar girman angon nata tana reto. "Jauro wato dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama sai da ka auri matata ko?" Suka tsinkayo muryar Abubakar da yake magana a matsayin Malam. "A mini afuwa ranka ya daɗe, na tuba na bi Allah da manzonsa a yafe mini, ai ni in ka ganni a lahira kaini aka yi Delu ce ta matsa mini aka yi auren amma ba a son raina ba" Cewar Jauro da ke duƙe yana rarrafawa yana sakin nishi kamar wani raƙumin da ya kwaso gajiya. "Allahu akbar kabiran wallahi Jauro ka ji tsoron Allah, ni ce ma na matsa maka ni Delu barni in mutu maza su kai ni ba mata ba. "Ku rufe mini baki, kai kuma ka koma cikin sauri ka saka wando" Cewar Abubakar da ke kallonsu dan ƙasab kujerar da ɗan faɗi kuma kofin silbar ƙarami ne sai dai su Inna ruɗewa ta hana su gane cewa ga daga inda maganar take. Wani salati Jauro ya ɗauka a ransa dan ya ma manta da zancen wani wando hannu ya kai da sauri gabansa aikuwa ya ji shi timɓir haihuwar gyatumarsa da sauri ya yi kwana, dan dama kwana ba sai mota ba, ɗakin ya nufa ya sako gajeran wandon. ya dawo suka cigaba da tafiya domin barin falon suna zuwa Inna ta miƙe tana karkarwa ta buɗe musu ƙofar suka zangaya a guje, suna fitowa Jauro ya nufi hanyar ɓangaren Kande cikin sauri Inna ta janyo wandon nasa ƙiii sai gashi a gabanta "Wallahi baka isa ka kai mata kwanana ba" Ta faɗa tana haƙi. "Haba Delu ni yanzu da nake neman mafakar fakewa kwanan me zan kai mata ni da zan samu in ɓoya saboda fatalwa amma ke kin sa kishi a ranki"Banza ta masa ta nufi ɓangaren Abba ya bi bayanta sauri suke kamar su cu da ka har suna neman tuntuɓe. Da ƙarfi suka shiga bugawa Abba ne ya zo ya buɗe bayan ya tambaya Inna ta tabbatar masa da su ne, yana buɗewa suka shigo a kiɗime suna zare ido dan har sai da Jauro ya buge Abba ba tare da ya lura ba. "Lafiya Inna?" z "Ina fa lafiya ubanku ta iyo fatalwa ya zo ya hana mu cin amarci saboda mugun hali da baƙin kishi" Cewar Inna da ta kama ƙofar ta rufe har da sanya mukulli. "Umma ta gaida Aisha tun da kun gama gane Babanku da ɗan kanfai" Ta faɗa tana jifansu da harara babu wanda ya tanka mata suka fice sumi-sumi. "Wayyo bayana samo ruwan ɗumi ki mini gashi" Ya faɗa yana mere baki. Wata uwar harara Inna ta jefa masa baki sake sannan ta ce. 'A'a Jauro bana son wani ɓoye-boye in ka san babu wani bayani a tare da kai ba sai ka biyo mini ta bayan gida ba, amma in ba son ka sanya na fara tunanin makomar amarcina na yau ba kai da zaka tashi ka zage domin taryar amarya a baje basirar tunanin sarrafa komai da komai a yi gagarumin yaƙi a kashe arna amma dan lalaci kake maganar ruwan ɗumi ai na ɗauka ni ce zan buƙaci ruwan ɗumi amma ba dai kai ba" "Ikon Allah na kwance ya faɗi yanzu ashe Delu har ni zaki fara tunanin babu abin da zan iya taɓukawa a daren amarci sai kace wani sauna kira mana shashasha in ka ga sakarai ku taho tare, in ma ba dan wannan tsautsayin ba ai da yanzu muna filin daga, ni nan jarumin jarumai ne awa bakwai nake kwashewa a gabatar da sunna ga Kande ma bare kuma ke ai sai yadda hali ya yi sai na ga abin da ya turewa buzu naɗi" Wani irin washe baki Inna ta yi, jin za a sha amarci, dan har ta fara sarewa cewar babu shan amarci a daren yau. Haka ta tashi ta samo ruwan ɗumi ta ɗan gargasa masa inda aka doka sandar kafin ya ɗan ware yana zaunawa dakyar, bayan yanji ɗan dama-dama ya tashi suka koma ƙuryar ɗaki, har suna shirin kwanciya Inna ta tuna bata rufe ƙofa ba dan haka ta fita domin ta rufe, tana fita Jauro ya tashi da sauri ya ɗakko wata leda a ajjihun rigarsa da sauri ya buɗe ya lakuci maganin ya shafa a jikinsa (Al'aurarsa) Maganin ƙarfin maza ne da tada shu'umar sha'awa da sauri ya maida ya koma kan gado ya kwanta. Inna tana gama rufewa ya dawo ɗakin ta kashe fitila ta ƙarasa kan gadon, can sun ɗan yi nisa ana shirin cin amarci sai kawai suka fara jin wani sauti ana cewa "Delu, Deluna taho mana Delu" Muryar Malam marigayi mijin Inna ita ce ta karaɗe falon Inna wanda suke jin sautin har cikin ƙuryar ɗakin da suke. Wani irin zabura Jauro ya yi tare da ƙara ƙanƙame Inna, cikin razana da gushewar hankali haɗe da tsoro Inna ta sanya hannu biyu ta hankaɗa Jauro dan jin wani irin tsoro take "Angon naki kije turewa a daren amarci, haba Delu ya za a yi ina shirin haƙar rijiya (Gabatar da sunna) Amma kike neman kawo mini cikas" "Haba Jauro baka jin muryar fatalwar Malam duk ta karaɗe ɗakin wani irin cin amarci ana zaune ƙalaw ai indai amarci ne na haƙura ko so kake in ci amarci fatalwa ta tafi dani yanzu, ai wallahi wannan Malam an yi kudurarre, yanzu ba ya duniyar ma sai ya haramta mini more rayuwata duk irin burin da na ci a kan ranar nan amma sai da ... "Delu ina kallonki ke da sabon mijin naki, ashe dai dan dole sai da kuka yi aure,to cin amarci dai haramun giya a gidan liman, babu wani amarci da za ku ci in kuma kuka ƙi ji to tabbas bakwa ƙi gani ba, dan haka Ku taso ku bar ɗakin nan yanzun nan in ba haka ba yanzu za ku ganku a maƙabarta" Abubakar da ke ƙasan kujera wanda tun fitar Inna da ta bi bayan Jauro da ya tafi ɗaukan tuwo ta shigo ɗakin ya shige ƙasan kujera shi ne yake magana a cikin kofin silba ya toshe hancinsa ɗaya yake muryar Malam, dan ya ci alwashin babu wani amarci da za su ci. Ai jin ya ce su bar ɗakin ai a sukwane suka fara rige-rigen sakkowa daga kan gadon koww jikinsa na karkarwa. Inna ce ma ta yi ƙarfin halin saka wani zurmemen hijabi amma ko ɗan tofinta baya jikinta "Da rarrafe za ku fito" Jin haka ya sanya Jauro sauri zubewa rigijib a ƙasa har sai da ya ji raɗaɗi a gwiwoyinsa amma haka ya daure dan shi yanzu da za a ce ya bar garin Kano ma gabaɗaya babu abin da zai sanya ya zauna dan ya tsorata sosai. Haka suka rarrafo Jauro a gaba Inna tana binsa a baya,Jauro tsirara yake dan tsabar tsoro ko gajeran wandon bai saka ba Inna da ke bayansa tana hango sandar girmansa daga vaya da yake da rarrafe suke tafiyar. "Wa ya ga jelani, wannan abu carai-carai kamar ɗan wada ya je ci rani" Cewar Inna zuciyarta ganin sandar girman angon nata tana reto. "Jauro wato dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama sai da ka auri matata ko?" Suka tsinkayo muryar Abubakar da yake magana a matsayin Malam. "A mini afuwa ranka ya daɗe, na tuba na bi Allah da manzonsa a yafe mini, ai ni in ka ganni a lahira kaini aka yi Delu ce ta matsa mini aka yi auren amma ba a son raina ba" Cewar Jauro da ke duƙe yana rarrafawa yana sakin nishi kamar wani raƙumin da ya kwaso gajiya. "Allahu akbar kabiran wallahi Jauro ka ji tsoron Allah, ni ce ma na matsa maka ni Delu barni in mutu maza su kai ni ba mata ba. "Ku rufe mini baki, kai kuma ka koma cikin sauri ka saka wando" Cewar Abubakar da ke kallonsu dan ƙasab kujerar da ɗan faɗi kuma kofin silbar ƙarami ne sai dai su Inna ruɗewa ta hana su gane cewa ga daga inda maganar take. Wani salati Jauro ya ɗauka a ransa dan ya ma manta da zancen wani wando hannu ya kai da sauri gabansa aikuwa ya ji shi timɓir haihuwar gyatumarsa da sauri ya yi kwana, dan dama kwana ba sai mota ba, ɗakin ya nufa ya sako gajeran wandon. ya dawo suka cigaba da tafiya domin barin falon suna zuwa Inna ta miƙe tana karkarwa ta buɗe musu ƙofar suka zangaya a guje, suna fitowa Jauro ya nufi hanyar ɓangaren Kande cikin sauri Inna ta janyo wandon nasa ƙiii sai gashi a gabanta "Wallahi baka isa ka kai mata kwanana ba" Ta faɗa tana haƙi. "Haba Delu ni yanzu da nake neman mafakar fakewa kwanan me zan kai mata ni da zan samu in ɓoya saboda fatalwa amma ke kin sa kishi a ranki"Banza ta masa ta nufi ɓangaren Abba ya bi bayanta sauri suke kamar su cu da ka har suna neman tuntuɓe. Da ƙarfi suka shiga bugawa Abba ne ya zo ya buɗe bayan ya tambaya Inna ta tabbatar masa da su ne, yana buɗewa suka shigo a kiɗime suna zare ido dan har sai da Jauro ya buge Abba ba tare da ya lura ba. "Lafiya Inna?" "Ina da lafiya ubanku ta iyo fatalwa ya zo ya hana mu cin amarci saboda mugun hali da baƙin kishi" Cewar Inna da ta kama ƙofar ta rufe har da sanya mukulli. Da sakekken baki Abba ya buta tsabar mamaki, yana dana sani a kan auren da Innar ta yi gashi ko kwana ɗaya ba a yi ba amma tana ta kawo musu matsala daga matsalar da ta faru ɗazu yanzu ma ga wata ta kunno kai. "Haba Inna wace irin magana ce wannan kin taɓa gani wanda ya mutu ya dawo? " "Ka jini da ja'irin yaro to ƙarya zan maka? Na ce ƙarya zan maka, mutumin da yanzu ya furtumo mu daga ɓangarena, shi sabon ubanka ma tsirara haihuwar gyatumarsa ya taho amma ya maidashi ya sako ɗan kamfai (Wando) Da ba dan haka ba da yanzu tsirara za ka ganshi" Da ido Abba ya bi Jauro aikuwa ya sauke idanunsa kan wandon Jauro wanda , gabansa ya tashi saboda maganin da ya sha, dan shi yanzu maganin ya gama bin jikinsa gashi kuma ba damar gabatar da sunna tun da an koro su shi da amaryar. "Haba Bebi yanzu dan Allah meye haka, ka bar jikinka (Gabanka) Na tashi sama kamar wani doki yana hamimiya, haka kawai ka bar abu zalolo ya tashi sai harbin iska yake" Cewar Inna da ita ma ta sauke nata idanunsa a kan wandon Jauro. Wata irin kunya ce fa rufe Jauro har ya kai hannu da sauri ya dafe wurin dan shi kaɗai ma ya san abin da yake ji saboda maganin fa ya sha shi kaɗai ya san hali da masifar da yake ciki. "Yau dai na ga avin da ya fi ƙarfina, a ce wai mijin mahaifiyarka yana tsaye a gabanka da gajeran wanda jikinsa na tashi wannan wace irin rayuwa ce" Cewar Abba a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce "Inna dan Allah mu je in taka ku ɓangarenku" Ya faɗa yana kallonsu dan ya ga su ko a jikinsu. "Ikon Allah na zaune ya faɗi, Sa'adu ni kake kallon tsabar idona kake faɗa mini mu tafi ɓangarena sai kace wanda suka zo da mugun abu in faɗa maka fatalawar ubanka Malam tana can ɓangarena amma ka ce wai mu zo ka raka mu dama ai ba kai ka rako mu nan ɗin ba" "Allah baki haƙuri Inna" Banza ta masa idanunta a kan Jauro da ke ta wani harhaɗe ƙafafu dan yanzu maganin nan ya fara tsuma shi. "Wai kuwa Bebi in fitsari kake ji ai ya kamata ka je ka yi, dan, amma ya za a yi ka rinƙa haɗe ƙafafu kamar ƴan sanda za su sarawa shugabansu" Jauro kwa ko kaɗan ya kasa furta komai dan gabaɗaya mararsa tsinkonsa take sai wani zate ido yake ya rasa yadda zai yi. "Bebi a bamu ɗaki a nan mana sai mu yi kwanciyarmu kin san da can da nan duk ɗaya ne" "Haba ya za a yi mu kwana a nan sai dai a je a kori fatalwar mu koma ɗakinmu ai l ɗakin mutum sirrinsa" "Inna bari in je in gani" Cewar Abba yana kama hanya ya buɗe ƙofar ya fita ba tare da ya jira cewarsu ba. Yana zuwa ya shiga ya duba ko ina amma babu kowa dan Abubakar suna fita ya fice dan dama burinsa ya tsorata su, kuma ya san tun da suka fita to ba za su wuce ɓangaren Baba ko Abba ba. Haka Abba ya shigo ɓangaren bai ga kowa ba har ƙuryar ɗakin ya leƙa ya fito ya koma ya kirawo su Innar dakyar suka koma sai da suka tabbatat babu komai suka shiga dan a zatonsu fatalwar ta tafi. Bayan sun tabbatar babu kowa Abba ya musu sallama ya tafi. Suka shiga ɗaki abinsu. *WASHE GARI* Tun kan na shiga ɗakin Inna nake jiyo sautin kukanta sai yi take tana face hanci, ina shigowa na yi tozali da Inna kwance reran magashiyan tana kuka abinta ahi kwa gogan yana gefe ya ɗora kan Inna a kan cinyarsa sai aikin lallashi yake a kan ta yi haƙuri ta daina kuka. "Haba Jauro yanzu tsakani da Allah baka dubi tsufana ba ka haike mini kamar wata budurwar amarya" "Haba Delu ki yi haƙuri mana, duka-duka awa takwas ne fa na yi amma gobe tin daga farkon dare har asubahi irin wannan gyara da kika sha aradun Allah ko Kande lokacin amarcin budurci bata kai ki ba" Wani irin washe baki Inna ta yi jin an yabe ta, amma kuma wani raɗaɗi da ya ziyarce ta sai ya hanata darawa sosai. A hankali ya kama hannunta ta tashi zaune tana ɗan ciccije baki, kamar an ce ta leƙa ƙasanta aikuwa ta shiga rafka salati tamkar ta ga kwarata turmi da taɓarya. "Haba Deluna zunzurutun maƙwallaton zuciyata, ai wallahi kin fiye mini mata dubu d... "Haba wace irin Delunka ashe haka ka mini rata-rata, ka kekketa ni, kamar wata takarda" Ta faɗa tana sakin wani marayan kuka "Haba Bebi amarci ne fa yanzu ma aka fara ai, ni tsakani na da ke babu abin da zan ce sai addu'ar shiga aljanna" "Yo ba dole ka ce haka ba bayan ja gama dani yanzu Allah na tuba ko tafiya zan taka da ƙafafuna ai na san tatata zan rinƙa yi ni ba wata ƴar shayi ba amma a haɗa ni da tafiya ƙafafu a gwagwgwale" Ta faɗa a ranta a fili kuma ta ce "Wannan Lanatana an yi shegiyar yarinya kudurarriya, ita ta kai ni gidan mai maganin mata gashi ta janyo mini shan wahala" "Haba Bebi ni kwa ai na ji daɗin abin da ta yi ai ƴar albarka ce yarinya ai ta gyara aure" Ya faɗa yana washe baki, wata harara Inna ta jefa masa dan yanzu wani haushinsa take ji tana ganin ta yaya za ta zo tana tafiyar tatata a gaban ƴaƴa da jikoki har ma da sirikanta. "Allah maimaita mana Allah ƙara maimaita mana mummunai" Ya faɗa da sigar waƙa yana wani rausaya kai kamar wani ƙadangaren da ya samu kedar manja. Banza ta masa ta shiga ƙoƙarin tashi tsaye tana wani ciccije baki. Ai Inna na duro da ƙafafunta daga kan gadon, ta tashi tsaye sai gata tana sakin wani ihu mai haɗe da kuka a lokaci guda dan ƙafafunta karkarwa suka shiga yi gabaɗaya ta kasa tsayawa da ƙafarta saboda azaba. Da sauri ta koma ta zauna a karkace ta gwale ƙafafu ta ɗauki muhuci ta shiga fifitawa ai wani raɗaɗi da ya ziyarceta saboda yadda iskar ta shiga sai ga Inna na sakin wani hawaye wani na bin wani. "Sannu Bebi" Ya faɗa yana kanne mata ido. Kanta ta ɗauke duk abin duniya ya isheta. "Allah raba bawa da wahala wai gwauro a teburin mai shayi, in ba tsautsayin takaba ba auren shiɗaɗɗe ina ni ina wannan aiki fisabilillahi ni ƴasu da wane idon zan kalli Umaru da Sa'adu a ce a daren farkon amarcina an farkeni kamar wata ɗanyar kaza ko ma in ce kamar wani tsohon buhun siminti" Cewar Inna a zuciyarta taa sauke idanunta a kan Jauro. "Tashi in raka ki bayin " Ya faɗa yana kama hannunta dakyar ta tashi ya shiga kafaɗarta. Taku ɗaya biyu ta yi Jauro bai ankara ba sai ji ya yi ta sakar masa wani uban dundu a bayansa fa sauri ya dakata yana kallonta da mamaki fuskar nn tata sharkaf da hawaye. "Haba Dulu wai duk amarcin kike yiwa wannan raɓetun da hawaye kamar wata ƴar shekaru sha uku, to aradu a daren farkonmu da Kande cewa take ja mu je direba kar ka tsaya direba amma banda tuƙin ganganci, amma ke ba da waƙa ba lokacin ana aiki sai bayan an gama ki zo ki rinƙa raki har da su duka kamar wanda na saɓi Allah" Wani haushi da kishi ne suka turnuƙe Inna dan a duniya ta tsani ya yabi Kanden nan bare a ɓangaren aiwatar da sunna dan haka cikin zafin nama ta janye jikinta daga gareshi za ta tafi bayin da kanta aikuwa tana ɗaga ƙafar sai ta zauna a ƙasa ta karkace. "Wannan dai ragwanta ce aradun Allah Delu" "Ka manta kakar ragwanta ce, yanzun nan na ji kamar an tsala ni da reza ko adda tsabar raɗaɗi da azaba, amma kana kiran ragwanta mutumin nan jiya ko tausayin tsufana baka yi ba ka rinƙa haƙa rijiya da mugun ƙarfi kamar ka samu shebir, haka na daure sai da ka mini fata-fata, yo ina dalili ina ɗan mafari za a kassara mini mafitar ɗa, wannan ai gamganci ne haihuwa da damina, kana tuƙi baka san hanya ba kawai sai ji nake wani garrrrr, gugurummm, buuuuu, haka kawai ka maidani kamar wata kwalta ina dalili ai ni dai cin amarcin nan bai mini rana ba wallahi yo abin da ka yi ne ya fi ƙarfin hankali da na sani wallahi haka na yi zamana salam-salam babu wani gyara bare matsi, ni ce harda su maida tsohuwa yarinya, ni ce cicciɓi kai babu wani abu da na raga masa na amate dan duk mu damu ƘARAI mai tsayawa a zuciya amma gashi ka maidani kamar wacce aka fiddo daga injin markaɗen kayan miya, ai wallahi ka wuce gona da iri yo ina zan iya tafiya da ƙafata yau ai sai ka kirawo mini Shattu da Lantana dan na san yau dai sai an mini rubdugu" Cikin sauri ya ɗakko riga ya saka mata ya ɗakko tiri kwata wando na jeans ya saka tare da t-shirt ya zo ya gifta ta gabanta zai kirawo mata su Shattu aikuwa giftawar da ya yi duk da halin da Inna ke ciki sai da ta ji ya birgeta kayan da ya saka dan ɗaya daga cikin wanda suka siyo ne. Sauri yake har ya je ya kirawo su, lokacin ma har wajen ƙarfe takwas da rabi, suna tafiya suka haɗu da Abba da Baba suna tsaye suna magana. Da kallo suka bi su Jauro wani takaici na cika musu rai na kayan da Jauron ya saka amma babu yadda suka iya haka suka durƙusa suka gaishe shi, shi kuwa Jauro har da wani saka hannu a aljihu yake wani ƙwambo. "Baba Shattu lafiya dai na ga kuna sauri" Baba ya tambaya dan bai kawo komai ba. "Yaro man kaza na yiwa uwaka aika-aika" Jauro ya faɗa a ransa a fili kuma ya ce "Gyatumarku ce ba lafiya tana nan magashiyan tana neman ɗauki na ce dai bari na samo mata ƴa uwanta mata su suka san yadda kan abin yake" "Mai ya sameta?" "Yo ɗan nan kake bincike, amarya ce fa kuma ka san amarya ko ta buzuzu ce sai an... "Haba Baba Shattu" Lantana ta katse Shattu dake ƙoƙarin sakin layi, dan su Baba basu ma gama gane abin da take nufi ba. "Ke dai wannan ƴa da shegen sanabe kike yo waye bare a ciki na ga uwarsu ce ita ai damuwarta damuwarsu ce mu je ke in ga halin da take ciki" Ta faɗa tana ɗan faɗansu na tsofaffi ta wuce ba tare da ta jira cewar su Baba ba, Lantana da Jauro suka mara mata baya. "Allah kyauta" Cewar Abba da Baba da suka haɗa baki wajen faɗa duk da basu fuskanci inda maganar ta dosa ba. Shattu da Lantana suna shiga suka gant sharaf a tsakar ɗaki dama shi Jauro bai shigo ba a falo ya zauna yana jira su yi abinda za su yi. "Delu mai zan gani haka?" Shattu ta faɗa da mamaki a fuskarta "Kai Shattu mi ƴasu wannan al'amari da wuya yake abu ji kake gigigi kaar haɗarin mota wallahi ko darena na farko da Malam ya karɓi budurci ba a yi wannan badaƙalar ba, yo turnuƙun da aka sha ba na wasa bane , Wallahi Lantana ba dan zuciyar musulunci ba a shekara ma ba zan bar kwashe mata sulusin albarka ba, wallahi Shattu da za kinga matantaka ta da kin ga tsiyar da Jauro ya tafka mini, yo ya mini fata-fata kamar ya samu tsohuwar besfa sai da ya mayar da ni kamar an daddatsani da gatari ba ma wuƙa ba" Cewar Inna tana riƙe da haɓarta. "Haba Delu yo ke garin ya haa ta faru, mu da muna can muna jiran in an ci amarci mu zo mu ci ragowar kazar da safe, sai jin bugun ƙofa muka yi tun da sanyin safiya ina buɗewa sai ga ango afujajan wai mu zo kina buƙatar taimakon gaggawa, na ce masa ka yi aiki ne ya ce ai aika-aika ma ya yi, ke ma ai bakya bari ya miki lugude ba kamar wata gumbar sadaka" "Haba Shattu dan rashin imani ma haka zaki ce, yo banda dai neman sababi irin naki ya za a yi a haɗa ƙarfin namiji da mace, yo da idan aka maƙureki ko motsin kirki kin isa ki yi, yo ji za ki yi kamar jirgin sama ya danne mota, babu wani kataɓus da za ki iya yi, haba kamar dai baki taɓa auren ba Shattu" "Yo ko na taɓa aure yanzu mai zan adar abu da ya wuce kamar shuɗewar lokacin bazara, wannan bayani ai sai ke da kika yi ƘARA'I jiya" "Hummm ni na san abin da na ji jiya ni na san abin da ya ziyarce ni aradu bana ko tantama Jauro ya kwankwaɗi maganin ƙarfi dan ƙarfin nan na jiya ba nashi bane ƙarfi kamar marashin doki, ai da jin ƙarfin ka san ba na tsoho bane" "Yo kema baki zauna hakan ba ai ɗure- ɗurenki da kika yi kaɗai ya isa ki zautar da ɗan tahalikin nan" ."To dan na yi ɗure-ɗure sai aka ce ya mini fyaɗe yo meye marabar dambe da faɗa ai wallahi mai maganin matan nn da ta dafa mini cicciɓi na cicciɓe mata albarka kanta ya fi cikin kwando dan idan da sauran albarka ma a kanta to bai fi cikin cokali ba dan wallahi ta cuceni ni kaina ban san iyakar cutar da ta mini ba, in ba rashin imani da tausayi ba ta yaya za ta bai wa tsohuwa abinda zai zama ajalinta, kawai ta saka in ke tafiyar tata ta ni ba ƴar kaciya ba cinyoyin nan nawa kamar an karairaya mini ƙasusuwan saboda tsabar suke sagewa yo ina dalili wannan amarci ko wahala ai daga yau mi da Jauro haihata-haihata mun yi hannun riga, da rana dai ma yi waricinmu ido na ganin ido amma waricin na hira ba wani abu ba dare kwa na yi zai kwana a falo ni in ɗaka yo aradu sai dai mu raba jaha... "Haba Delu ke da kije da kishiya ko kin manta da Kande ne, maimakon ki ɗaura ɗamarar ƙwace mijinki ta hanyar rattaba sunna sak ba gajiyawa amma daga yi rana ɗaya ki sare kina maganganu masu sakin layi kina nuna gajiyawarki zai raina ki bayan kin san da bakinsa ya ce awa bakwai yake kwashewa yana sunna da Kande" Shattu ta katse mata maganar. "Ke dallah rufe mini baki kar ki yi saɓo ma yo wace kishiya kuma, ƙyaleni da maganar sunnar nan yo shegiya ce ni zan yi kishi da aikata sunna, sai kace wacce uwata ta ce jeki kya gani, zan zauna ake rugurguzata kamar wata ƙanzon tuwo, to indai kin ganni a lahira kaini aka yi amma ba da ƙafata na je ba" "Da Allah kar ki bani kunya ya kike neman bada mata Delu, kina ga dai yau ɗaya yadda ya susuce sai rawar ƙafa yake a kan ki, ba saboda komai bane kuwa sai dan canjin da ya ji amma kina neman ɓata rawarki da tsalle" "Allah wadaran naka ya lalace yo ina ruwana da rawar ƙafarsa ai ko rawar ɗuwawu zai yi babu abin da ya shafi Delu, babu abin da zai shalle ni kuwa, da kike maganar zan bauar da mata to wallahi na bayar da mata kyauta kuwa indai a kan wannan doguwar sunnar ne da ake gabatarwa babu ƙaƙƙautawa kamar kamar sallar tarawihi' "Ikon Allah na kwance ya faɗu ke kwa Delu ina soyayar da kike ikirari kina yiwa wannan bawan Allahn tun ta budurta?" "Na bi soyayya da gudu dan gwafar ubanta, yo ina dalili indai a kan wannan abin ne na jiya na yafe wannan ai wahala ce ba soyayya ba, ina laifin ma a yi abu saisa-saisa Shattu amma abu yake tahowa ruuuuuu kamar tasowar guguwa babu tsayawa sai kace za a yi tashin duniya, kamar ana yaƙin duniya na uku, yadda tsohon nan ya mini rata-rata wannan ko likitocin da suke ɗinke mata idan sun ƙaru a haihuwa wallahi sun yi kaɗan su ɗinke ni kin dai ga yadda suke ɗinke su kamar wasu ƙwarake, ni yanzu yadda na yi wayam ɗin nan a ɓarɓarke sai ko a samo allurar makaffi da zaren buhu a ɗinke ni, in ban ɗinku ba sai dai a ɗora ni a kan keken ɗinki a ɗinke ni yadda ake ɗinke zanen atamfa, in ban ɗinku ba aradu Shattu sai ko a barni a haka in tafi har kabari a ɓarke, kai wannan ƘARA'I bai mini rana ba Shattu" Ta faɗa tana sakin kuka hannayenta bibbiyu a kumatun ta, ta yi tagumi kamar wacce aka faɗawa saƙon mutuwa. A NAN FREE PAGE YA KARE Mai son ji har karshen labari ya biya 500 ta faiza Abubakar 9030283375 opay a tuntubeni ta 09013181851