[11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ................ *JA'JIRTACCE* .............. *1* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla ✍ Bismillahirrahmanirraheem! Dasunan Allah mai rahma mai jinqai, Alhamdulillah! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (s,w,a) dayasake bani ikon rubuto muku wannan sabon labari mai suna *JA'JIRTACCE* *Matashiya* "Wani karamin kauyene mai suna kasa,wasa. Wand yake cikin babban birnin jihar sokoto, can a wani dan karamin gida danagani kofarshi a wangale shiyasaka nakutsa kaina da sallam tareda fatan samo maku abinda kuke nema." Wata matashiyar mace ce na hango kwance akan wata yagaggiyar taburma da kallo daya nagano tana cikin mawuyacin hali na jinya, duk dacewa jikinta yana lullube cikin zannuwa har guda biyu amma sai kyarma take tana kar-karwa kamar maxari habarta na rawa hakoranta na had`uwa da yan'uwansu. Zagayeda ita wasu kana'nan yara ne guda biyu, mace da namiji, namijin zaikai shekaru gomasha uku zuwa sha hud`u, macen kuwa bazata wuce shekaru takwas ba, kuka suke sosai kamar ransu zaifita, mai d`an wayon shine mai faman yimata sannu had`eda yimata fifita da wani farantin roba mai fad`i, cikin tsananin dakewa da juriya ta rintse ido ta kira sunan yaron dakyar ta iya har had`a kalmomin sunan shi Am..mar ya amsa dasauri na'am Ummana saida ta nisa dakyar sannan ta koma yinkurin had`a wata maganar Ammar ga qanwarka tafad`a lokacinda tad`auko hannun karamar kanwar tashi ta had`a da nashi. Ga Safeena nan Ammar nasani zaka kula da ita kamar ina raye zaka riketa fiyeda kanka, Ammar ka kulada Feenah kariketa kamar yanda kasaba, yarona inaji ajikina nima zan tafi, zanyi nisa daku Ammar, saidai nayi imanin cewa wanda zai d`aukeni shizai tsaya muku, Allah yana tare daku Ammar,yaron data ke kira da Ammar yafashe da kuka a'a Umma dan Allah kibari Umma narokeki karki tafi karki tafi kibarmu Umma na kina kallo Abba yatafi yabarmu, yabarmu ba kowa sai ke, umma inkika tafi ba'ba Larai zata kashemin qanwa kinsani Umma kullum saita hantareta tana cemata yar'tsintuwa shegiya idan naji haushi nayi magana su yaya Lodo sumin duka, agabanki kenan Umma, yaki ke gani ranarda babu idonki? Umma kashemu zasuyi wlh kashemu zasuyi Ummana yakoma fashewa da kuka, wasu za'fafan hawayene suka silalo daga idon Umma ta tattaro duka ragowar karfin da ya rage mata ta rungumo yaran nata, tsananin tausayin su yakamata musamman Feenah wadda har yau batasan inda ahlinta yakeba. Tamatse ragowar kwallar dake idon ta cikin yanayin jin jiki tace Ammar yau zan gaya maka gaskiya, gaskiyarda saninta yazama wajibi a gareka a matsayin ka na wanda zan barwa rikon Safeenah! Ammar yakoma kankame uwar yanaji kamar ya ciro ciwon jikinta ya jefar, duk da yanada yaranta amma yaro ne mai kaifin tunani da saurin fahimta, inajinki Umma na amma dan Allah karki mutu dan Allah kitsaya damu kinji Umma ke kad`ai ce.........dasauri ta toshe bakin d`an nata tace a'a Ammar karka soma karka yarda Allah shine gatan kowa da kowa Allah shine mafi kusanci daku fiyeda ni dakuka sani ka saurareni d`ana..... Abinda yaya Larai take fad`a akan Feenah gaskiya ne tabbas kanwarka yar'tsintuwa ce saidai hakan bai tabbatar da ita shegiya bace, kai kodama hakan din ne meye laifin yarinya? Ka saurareni da kunnen basira kaji tarihin Safeenah da inda muka sameta bata jira cewarshi ba ta fara bashi labarin kamar haka: **************************** "Ranar laraba itace ranarda d`aukacin jama'ar garin kasa'wasa da masu makwabtaka da ita suke cin kasuwar garin wannan ne yasaka mutane daga kowane yanki suke fitowa domin kawo hajar su, to hakan ne ta kasance dani da kuma mahaifin ka a lokacin kana da shekaru shida a duniya, munje kai kayan mafifitai damuke sakawa ne wanda duk ranar kasuwa muke kaiwa domin samun abin sakawa bakin salati, kasancewarmu masu karamin karfi, lfy kalau mukaci kasuwa muka fito a hanyar mu ta dawowa ne muka sami feenah a gefen gwanakin bayan gari tana kanannade a cikin wani zani mai kyau da sheki wanda ban taba ganin irinshiba a wuyanta ansaka mata wata lafiyayyar sarka wadda bansan asalin ta mene ne ba amma na tabbata bata banza bace ta musamman ce wadda tunanina dakuma ilimina baikai na ganota ba, tanata tsala kuka ga rana data daketa muryarta harta disashe, abban ka shiya daukota cikeda tausayi mukazo da ita gida, bayan sallar magariba muka gabatar da ita gamai anguwa yasaka akayita cigiya tsawon sati daya, amma ba,a sami wani dayace yanada wata alaka da jinjirar ba. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *2* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Umma taja numfashi dakyar sannan taci gaba - "to shine mai anguwa yace mu kawo yarinyar zai bayar da ita a kaita birni gidan da ake renon yaran da ake tsintuwa kamarta, ana cemishi gidan marayu, nan fa hankalina yayi mummunan tashi magana ta gaskiya a d`an zaman da mukayi da yarinyar na tsawon sati d`aya ta shiga raina ba kad`anba. kodan bantaba haifa mace bane? Oho komadai ya'yane sai naji bana son rabuwa da Safeena yarinyar da nasaka mata suna da kaina a ranar da ta cika sati daya a hannun mu, dafari naso na share na mikata amma sainaji nakasa jurewa, kai tsaye na tunkari abban ka da maganar yayimin izni in karbi rikon yarinya Safeenah domin cigaba da rainonta, budar bakin mahaifinka yace " a'a maryama badai ki reneta ba, cewa zakiyi mu cigaba da rainonta, naji dadi sosai da yanda yabani goyon baya dama banyi tunanin samun matsala ta gefenshiba domin shi mutum ne mai saurin fahimta, kyan hali dakuma tausayi. bamusha wata wahala wajan samun amincewar mai anguwa ba kasancewar mune mutanenda suka tsinto yarinyar, ban sami matsala da kowa ba sai yayata,abokiyar zamana Karai wadda dama ba zaman lafiya muke da ita ba saukin abinma ni bana dakata ta'ta, shiyasa lamura suke mana sauki. domin ita irin matan nan ce masu zafin kishi da jiyewa, sautari ni nake tare abban ku idan yayi niyyar rabuwa da ita domin munanan halayen larai sun wuce tunanika shi kuma abban ku mutum ne wanda bayason rigima da tashin hankali shiyasa basu cika jituwa da ita dakuma ya'yanta ba. hakadai rayuwa tacigaba da tafi mana, da madarar shanu na shayarda safeenah harxuwa lokacin yayenta, nida abbanka muna rayuwar mutinci da mutinta juna yana kula da mu sosai yarike Feenah tamkar yarda ya haifa da cikinsa ko kadan baitaba nuna mata wani banbanci daku ba, amatsayi na na marikiyarta kuma matarshi inajin dadin hakan sosai. amma ita abokiyar zamana kusan ba abinda ta tsana a gidan nan samada ta bude idon ta taga Feenah bansan meyasaka ba, ko kai dana haifa bata hantararka kamar yanda take yiwa yarinyar nan sau tari duk wani duka dazata saka yayunka suyi maka saboda Feena ne domin kaiba kamar ni bane baka iya kyalewa idan aka ci zarafin yarinyar wanda nikaina bayanda na iyane banason fitina ko kad`an hakan yana damuna sosai yana bakanta raina domin a ganina idan Feena ta kasance cikin takura a karkashin rikona kamar nice na takura mata, amma yazanyi abinda nima ban wuce amin ba? Babu abinda yafi damuna fiyeda barinku nan Ammar, amma nasan Allah yafini, gatan shi gareku yafi dorewar rayuwata tare da ku. ta fasheda kuka sosai, hankalin yaran yakara tashi suma suka koma fashewa da kuka. Ta yunkura ta d`aga fatarinta wata ma'ajiya ta mutanen kauye, taciro wata sarka nad`e acikin wata leda ga dukkan alamu sarkar tasha ajiya ba kad`an ba, tace d`ana wannan itace sarkar damuka samu a wuyan kanwarka Safeenah ka riketa da muhimmanci ka tabbatar ka hannunta ta gareta a lokacin da zata mallaki hankalinta ba mamaki wannan sarkar ta taimaka mata wajen gano asalin iyayen ta iyayenta wata rana. Wannan shine labari akan Safeenah ina fata zaka cigaba da rike ta yanda ka saba. kuyi hakuri da rayuwa a duk yanda ta kasance a gareku, rayuwa dakake gani bata dorewa kamar yanda ita kuma wahala komin yawanta bata kisa. Takarasa maganarta had`eda sauke ajiyar zuciya mai nauyi Ahankali Ammar ya d`ago da idanunshi dasuka rine suka canza kala daga fari zuwa jaaa! Alamar yasha kuka harya gode Allah domin tunda Umma tafara maganar kuka yakeyi kamar me, yakafe Umma da ido ko kiftawa babu irin kallonda bai taba yimata irinshi ba tunda yazo duniya, ko'kari yake na saita zuciyar shi ya rarrashe ta ta karbi maganar da Umma tagaya mishi domin yasan Umma bazata taba gaya Mishi karya ba, tabbas uwa uwa ce yau da ace ba Umma ce mai bashi wannan labarin ba da sam bazai yarda ba bayan haka ma bazasu rabu lfy damai bada labarin ba, ya sharce hawayen idonshi sannan ya maida kallonshi ga Safeenah wadda ke makale jikin Umma tana sauraron su sai dai babu wayon gane inda maganar ta dosa. Allah sarki tausayi da kaunar kanwar tashi suka bai baye shi ya d`agota daga jikin Umma ya rungume ta sai kawai ya fashe da kuka, ita ma Feenah kukan takeyi ganin yayan ta nayin kuka. Farin cikine ya lullube Umma dan tasan ko ba rayuwar ta Ammar zai kula da yar'amar ta Safeenah ta yarda da d`an ta d`ari bisa d`ari, wani ni'imtaccen murmushi ne ya wanzu akan fuskarta dad`i ya lullube zuciyar ta, a hankali tafara motsa lebenta tana yiwa yaran fatan samun rayuwa mai albarka da kariyar Allah sanan daga bisani tarufe da karanto kalmar shahada ruf. bakinta ya rufe lokaci daya, fuskarta d`aukeda murmushi. Su Ammar sun dad`e a hakan kafin daga karshe ya sake kanwar ta shi ya koma kan umma yana mata sannu, yadauki farantin robar nan yacigaba dayi mata fifita Sallamar ba'ba Uwale suka ji ta shigo gidan kai tsaye kofar Umman su ta nufa ba'ba Larai na daga kofar ta tana ganin ta amma ko sallamar da tayi bata amsa ba saima harara da tsaki data bita dasu, ba'ba Uwale kam ko ajikinta dan tariga ta saba da wannan kasancewar ta aminiyar Umman Ammar. Shida Feenah duka suka gaisheta ta amsa cikin sakin fuska ta karasa gaban kawar tata tana gaisheta saitaji shuru ta kura mata ido ba alama ko motsi a tattareda ita, cikin tsoro da firgici tayi gaggawar kai hannunta kan kirjin umman taji shiru ba motsi takoma cirewa tamayar kan hancinta ta kara yatsanta dai dai kofar hancin amma shiru takeji ba numfashi, ta daga hannun ta ta saki sai taga yakoma ragob! Innalillahi wa inna ilaihi raji,un Allahu akbar! Allahu akbar! dasauri tad`ibi ruwan karamar randar sha dake kusada Umman ta shafeta, sannan taja zanin dake rufeda jikinta ta rufe mata fuskarta. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *3* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Ammar yabi ba'ba Uwale da kallon ma'maki fuskar shi da alamar tambayoyi shi atunanin shi Umma bacci tayi sai dai kabbara da sala'lamin ba'ba sun tsorata shi cikin firgici ya kalli ba'ba hawayen da ya gani a fuskarta sun koma rudar dashi da sauri yamatsa ga mahaifiyar tashi yana ko'karin yaye rufinda aka mata ba'ba Uwale tayi gaggawar riko'shi tana sharar kolla Ammar ya fashe da kuka "me hakan yake nufi ba'ba? Me ya sami Umma na? Dan Allah kibari in gan ta" Ba'ba ta kasa rike kukan da ke bijiro mata sai kawai ta rungume Ammar ta fashe da kuka wiwi, "Umman ka ta tafi Ammar yau maryama ta tafi ta barmu da kewar ta ta har abada, sai dai hakuri Amar tariga tayi nisa damu." ta koma fashewa da kuka Ammar ya kankame ta nashiga uku Umma ta mutu? Yadafe kai ya kwarara uban ihu yazube kasa sumamme, abinda yajawo hankalin ba'ba Larai kenan tayo kansu a d`an tsorace ganin umma a rufe Uwale na zubawa amar ruwa yasa ta rafka salati Maryama ta mutu ne? Ta tambaya ido waje ba'ba Uwale bata kulata ba saida taga farfadowar Amar sannan taja hannunshi dana Feenah ta fita dasu sukabar ba'ba Larai nan tana sambatu akan gawar Umma. Amar sai waiwayen gawar yake har suka fita gidan saidai tunda ya farfad`o daga sumar dayayi bai koma zubarda hawayeba yarasa abinda ke masa dad`i jin kansa yake kamar matacce yanaso yayi kuka amma ya gagara yanaso yayi maganar Ummar shi amma ya gagara yin ko d`aya. Gidan ta ta kaisu ta zaunar dasu sannan ta sanarwa mijinta da labarin rasuuwar Umma malam bawa shima yaji mutuwar bama kad`an ba da hanzari yafita ya sanarwa limamin garin da mai anguwa nan take mazan garin suka had`u aka suturta gawar Umma aka kaita makwancinta, ta bakunci gidanta na gaskiya. Allah sarki rayuwa kenan Umma kam ta shud`e rayuwar yara ta dawo abar tausayi ba'ba Lrai ta d`an yi sanyi na kwanaki ukun rasuwar Umma Yau kwana bakwai kenan da faruwar lamarin Amar yadawo abin tausayi yazama wani iri gaba d`aya ya canza baya magana baya walwala hatta abincin da ake tsakura musu bai damu dashi ba, ga matsi da takurar dayakesha daga Feenah kullum cikin kuka take tana tambayarshi ina Umma, gaba daya sun rame sun lalace idan ta dameshi da tambayar sai ya fashe da kuka ganin hakan itama saita fara lokaci mai tsayi suke d`auka suna kukan bamai rarrashin wani, wani lokacin sai bacci ya dauke Feenah sannan Ba'ba Uwale tana iya ko'karinta wajen kula dasu wani d`an abinci da fura duk ita take basu dukda Amar baci yakeba sai in Feenah ta saka mishi kuka yake daurewa yadan tsakura kad`an. Haka sukaci gaba da rayuwa cikin kunci da damuwa kafin sati biyu wata sabuwar wahala ta bud`e musu...............wani sabon salon shafi na zalinci da cin amana ba'ba Larai da ya'yanta suka bud`e musu kullum sai Amar yayi wanki na ba'ba dana yaranta katti guda biyu shine zuwa kiwo da ban ruwan dabbobi shine d`iban ruwan gidan da shara da kankanta gida basubarshi hakaba duk sati sai sun turashi kasuwa yayi dako ya kawo musu kud`i, ita kuwa Feenah bata da aikin daya wuce talla sau uku take daukar awara a rana da safe da rana da daddare dandali take kaiwa. Ga yunwa ga detti yara duk sun haukace kai kace ya'yan bayine gabad`aya garin bawanda bai yiwa ba'ba Larai tofin Allah tsine ba sai dai ita ba damuwarta mutane ba, a yanzu jitake ba abinda zai dakatar da ita gayin arziki da wayannan marayun yaran tunda nata ya'yan ba amfanarta suke ba, kyakkyawar yarinya Safeenah ta kod`e tadawo kazama futuk hatta hasken fatarta yafara dishewa gashin kanta da Umma ke gyara duk sati a yanzu sai tayi watanni ko bud`a kan ba ayiba tun bayan rasuwar Umma sau uku suka shiga gidan ba'ba Uwale ana karshen ne yaya lado ya kama su yayi musu lilis kamar zai kashe su tareda gargad`i mai tsoratarwa shiyasa basu koma shigaba. sai itace take zagayo wa da kanta tazo tabasu abinci ko abinsha ta fita. Rayuwar yara dai abar tausayi basuda kowa sai Allah duk inda suka bi nuna su ake suna bawa kowa tausayi, sai dai ba wanda ya isa ya taimakesu saboda gudun masifar ba'ba Larai *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *4* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Wata ranar laraba da daddare kamar kullum Feenah tadawo daga tallan dare, Amar yana zaune a kofar gidan yana jiran dawowarta ya tareta da murna kamar kullum suka shiga gidan, ta kaiwa ba'ba kud`i da bokitin awaran ta, ta fito suka koma d`akin baccinsu wato d`akin ummansu, Amar ya hankad`a gado ya d`auko dafaffen dankalin daya siyo mata daga kasuwa ya bata, takalleshi cikeda so da kulawa tace "yaya muci tare mana nasan kaima bakaci komai ba", yai murmushi tareda kama kumatun ta yace "saboda ke nakawo ni nariga nakoshi ya d`ebo dankalin da hannu ya nufi bakinta tayi saurin d`auke fuska tasha mur alamar tayi fushi amar ya komayin murmushi akarona biyu dan yariga yasan halin yar kanwar ta shi, tsakiyarsu ya ajiye ledar dankalin yabud`eta suka faraciyarda junansu cikin farin ciki sunayiwa juna murmushi. kamar daga sama sukaji an banko kofar d`akin dakarfi aka shigo. Tare suka d`ago kai dan ganin mai shigowa yaya Lado ne yashigo. buge acikin yanayin maye , Amar yayi saurin mikewa ya boye kanwarshi a bayanshi Feenah wadda tuni jikinta yahau kyarma da karkarwa dan a rayuwar ta babu wanda take tsoro samada yaya Lado domin duk wani zalinci nashi a kanta yake karewa Lado ya tangad`a taga taga kamar zai fad`i ya hankad`e Amar gefe yaron yafad`i Sannan ya zaburo da sauri yakoma tare gaban Lado dan ya gane nufinshi na son isa ga Safeena ya cutar da ita. "Dan Allah yaya kayi hakuri metayi maka ne? Yaya dan Allah kayi hakuri ni kadakeni a madadinta dan Allah. Yayi folding hannayen shi yana rokon Lado, wani mahaukacin mari yakife shi dashi saida yafad`i a razane Safeena ta kwalla uban ihu tayi kan yayan ta ta d`agoshi cikin kuka take tambayarshi bakaji ciwo bako? Kafin yayi wani yunkuri na bata amsa saiji yayi an finciketa an jefar kanta ya daki bango ta kwalla kara tadafe kan nan take jini yafara fita daga gurin yanabin hannun nata. ai kuwa sai ta kara sautin kuka da ihu ta hau yin birgima a kasa Amar ya tsorata matuka da ganin jini daga jikin tilon yar'uwarsa wadda koda kuda bayaso ya tabata da nufin cutarwa zuciyar shi ta gama rufewa yashiga tunanin abinda zaiyiwa Lado a matsayin hukunci akan abinda ya aikata, Lado kuwa inda Feena take ya nufa da nufin jibgarta sai dai kafin ya isa gareta Amar ya rarumo wani katon tire na karfe dake ajiye a d`akin ya daka tsalle ya tallawa Lado shi a ka, habawo nanfa kato ya ware baki yasaki uban ihu ya dafe gurin yashiga lalube da kaiwa iska duka, jini kuwa ya balle daga goshin shi sai hargowa yake. Amar ya gama rikicewa da rud`ewa, babbar amina dake ajiye a kuryar d`akin ya bud`e ya d`auko wani kullin keda ya cusa a aljihun wandon shi. daga can yajiyo muryar ba'ba Larai tana fad`in me nake ji haka? Kai Lado meya sameka? ga dukkan alamu fitowa takeyi daga d`akin ta nanfa Amar ya tashi Safeena yaja hannun ta suka fita d`akin da gudu ba'ba Larai sai inuwarsu ta gani sun fice fit ga kukan d`anta da ihunsa sun cika gidan " ku la'anannu me kukayiwa Lado? ta karasa d`akin da sauri halin data ganshi ya sakata kuka taja hannun sa zuwa tsakar gidan ta shiga wanke masa jinin kafin ta barbad`a mishi dakakkiyar bagaruwa maganin tsayar da jini da kashe zogi Amar kuwa yana fita gidan ba'ba Uwale ya nufa ya buga kofar yakai sau biyar amma ba'a bud`e ba dama yasan sun isa yin bacci, jin ana fitowa daga gidansu yasa ya koma jan hannun Kanwar shi suka kama hanyar fita daga cikin kauyen da gudu. Hanyar kasuwa suka d`auka duk da cewa darene sosai amma hakan bai hana suka sami mutane a kasuwar ba keburori ne masu loda kayan amfani da aka siya amotoci za'a kaisi birnin kano, cikin alamar maganar kurame Amar ya umarci Feena da tayi shiru dasand`a ya lallaba yana janye da hannun ta dakyar ya d`agata ya jefata a babbar motar kafin shima ya kama ya hau wani lungu suka samu inda aka rage d`an fili a mitar suka tsuguna, sunaji aka sallami masu lodi aka tashi motar tafara tafiya. Cikin duhun daren Amar yayiwa yan tsirarrun gidaje da d`akunan garin su kallon bankwana batareda yasan inda zasu ba shidai yasan duk inda zasu gwara su tafi su rayu, dan ya tabbatar wannan fasa kan daya yiwa Lado ba makawa idan yakama su zai iya kashe su duka. Cikin wannan halin ne ya lura da kanwarshi na kyarmar sanyi ga wajan da taji ciwo duk jinin ya bata mata gefen fuska, da sauri ya janyota kusa da shi ya yaga habar rigarshi ya fara goge mata jinin duka sannan ya koma yago wani kyallen ya d`aure mata kan. Yajata zuwa jikinshi ya rungume ta cikeda tausayin rayuwar su a nan ne yaji jikinta zau da zafi alamar zazzabi zai kamata nanfa hankalin shi ya kara tashi *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *5* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ "Feenah gurin yana miki ciwo ne?" Ya tambayeta cikin inna-inna ta yanayin fargaba. Feenah ta gyad`a mishi kai ba tareda tayi magana ba dan ita kad`ai tasan azabar zogin da wajan yake mata, musamman daya d`aura mata kyallen rigar nan kasancewar rigar tana da detti sosai. "Wayyo Allah kanwa ta Allah ya baki lfy sannu kinji,". Ya fad`a yana bubbuga bayan ta alamar rarrashi. Wasu za'fafan hawaye suka silalo daga idonshi, tunawa yakeyi da lokacin da Umma tana raye, baisan lokacin da yafara sambatu ba, "kin gani ko Umma na, saida nace karki tafi, karki barmu da wad`ancan azzaluman Umma ki kalli yanda suka maida miki mu, yan gayun yaranki sun dawo yan daud`a, d`an dako da yar'talla haka suka maida miki mu Umma, yau gashi ma sun rabomu da gidan Umma bansan inda zamu ba" sai kuma ya fashe da kuka kafin ya cigaba da cewa "kalli halin da suka jefa miki yar'amanar ki, sun illata miki Safeenarki Umma meyasa kika zabi tafiya akan zama damu?" Ya koma fashewa da kuka ya kara kankame Feenah domin yasan Umma bazata taba amsa mishiba. Safeenar ce cikin yanayin zazzabi take tambayar shi "Yaya gurin Umma zamu je? Yaya dama kasan inda Umma take shine tun da can baka kaini ba? Sai itama ta fara kuka. Ganin hakan yasaka ya tsayar da nashi kukan ya shiga rarrshin ta dan kar zazzabin ya karayi mata karfi, haka yayi ta bubbuga bayan ta yana mata wakar dasukeyi a islamiyyarsu da suke zuwa kafin rasuwar Umma, wakar "IYAYE NA NE GATANA", Safeenah na son wakar sosai shiyasa suka haddace ta, a duk lokacin da suke cikin damuwa sukan rerata tare ko kuma idan Safeenar tana kuka sai Amar yayita rera mata wakar har sai tayi bacci. Yanzun ma kuwa hakan akayi yanayi yana zubda hawaye, tun tana ajiyar zuciya mai nauyi har bacci yayi awon gaba da ita, a hankali shima ya d`an zame ya kwanta, ya gyara mata kwanciya a gefen jikin sa ya shiga tunanin koya rayuwar shi data kanwar shi zata kasan ce nan gaba? Bai sami lokacin yin wani dogon tunanin ba dan shima baccin ne ya d`auke shi, Ba'ba Larai da kanta ta biyo bayan yaran cikin daren nan tadinga neman su ko wanne lungu da sako na kauyen zuciyarta cikeda mugun nufi akan su, sai dai bata gansu ba. tayi kofa ta koma gida, a ran ta cewa take duk inda suka shiga ai zasu dawo haka ta koma gida tana ta faman sababi da la'antar Amar da Safeenah, Lado na kwance yayi wani shame-shame a taburma abin dariya kan nan nashi ya kumbura yayi suntum dakyar yake numfashi, shima dai rayawa yake yi a ran sa duk ranar da ya warke ciwon nan ba abinda bazai iya yiwa yaran nan ba. (Nikuwa Nasmat nace daga baya kenan lolz) Amar da Safeenah sunyi bacci sosai domin kuwa basu suka farkaba sai wuraren karfe goma na safiyar Al'kamis. Amar ne ya fara farkawa fuskar kanwar shi yafara kallo kafin komai, wurin da kanta ya bugun ya d`anyi kunburi kad`an a hankali ya zameta daga jikinshi sai yashiga mamaki ganin har yanzu motar tafiya take yi, yasan dai tun daren jiya ta tashi gashi har gari ya waye rana ta haska ko ina, to ko ina wannan motar zataje? Ya tambayi kansa tambayar da bashida amsar ta kawai dai abinda yasani shine koma inane zataje to gurin yanada nisa sosai. Yana cikin saka da warwara Feenah ta farka ahankaki ta fara bud`e idonta bata diresu ko inaba sai kan fuskar yayan ta shima dai ita yake kallo suka sakewa junan su murmushi. Ta yunkura zata tashi Amar ya taimaka mata ta hanyar tallabota da hannayen sa duka biyu, suka fuskanci juna yace sannu Feenah ya kikejin gurin yanzu? Ta koma sake mishi wani murmushin a karo na biyu tace naji sauki yaya, ya kai hannu ya taba jikin ta sai baiji irin zafin da yayi mata jiya ba Alhamdu lillah ya fad`a yana kallon ta. Yaya, ta kira sunan shi na'am kanwa ta, ya amsa yana kallon ta cike da kulawa. kafin ta fad`i abinda ke bakinta sai sukaji motar ta shiga wani guri mai yawan mutane anata hayaniya Da sauri Amar ya mike ya leko ta bayan motar dan ganin inda suka shigo. ikon Allah wani babban birni ya gani guda sukutum yana cike da mutane sai hada-hada ake da kai komo, da sauri ya juyo ya riko hannun kanwar tasa ya mikar da ita "zoki gani kanwa ta" mamaki da al'ajabi suka mamaye ta "nan kuma ina ne yaya? Anan Umma take? Ta jero mishi tambayoyin a d`okance. Murmushi yayi mata a madadin amsoshin tambayoyin ta ya safa kanta nan wata duniyar ce kanwa ta, ki kalla ki gani komai nasu daban yake da inda muka fito. Feenah tabi wurin da kallo cikeda mamaki yaya wai ina zamu je ne? Inda Allah ya kai mu Feenah ni kaina bansan inda zamuje ba. Hawaye suka silali daga idon shi dai-dai da tsayuwar motar a tsakiyar kasuwar dawanau, tuni kasuwar ta fara cika da masu kawo kaya kowa sabgar gabansa yakeyi hakan yasa babu wanda ya lura da fitowar yaran daga cikin motar da tsayuwarta ya sakko da kanwarshi sannan shima ya diro ya kama hannun ta suka bar gun suka nausa cikin kasuwar ba tareda sanin inda suke ko inda suka nufa ba. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *6* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Tafiya sukayi mai tsawo wadda ta rabasu da kasuwar ta sada su da wata babbar anguwa mai d`auke da manyan gidaje da shaguna a gefen titi, nan ne Safeenah ta fara gazawa yunwa take ji da kishrwa ga azababben ciwon da kanta yake mata. Tirjewa tayi ta tsaya Amar ya kalle ta da alamar tambaya, cikin yanayin gajiya tace "yaya ni na gaji kuma Wlh yunwa da kishi nake ji". nan da nan tausayin kanwar tashi ya kama shi. cikin tausasa murya yace "kiyi hakuri Feena anan bansan abinda zanyi in sami kud`i ko abinci ba, amma saboda cika alkawarin danayiwa Umma na kula da ke ba abinda bazan iya ba". Yana kaiwa nan ya kama hannun ta suka nufi wani babban shago dake gaban su. Suna zuwa yayi sallama, ba Wanda ya kulasu a haka yafara rokonsu "dan Allah bayin Allah Ku taimaka mana da sadakan abinda zamu ci saboda Allah" wani gaye dake tsaye akofar shagon ya d`aga mishi hannu yace "yi hakuri ka kara gaba" Amar yayi shiru yana kallon biredi dake ajiye a kan teburan su. Gayan nan ya daka mishi tsawa "zaka bar nan kosai na mangare ka, sha'shashu kawai banga amfanin iyayen Ku ba indai bazasu iya cida Ku ba" Amar yayi kasa da kansa lokaci d`aya wasu zafafan hawaye suka gangaro kan kumatun sa. Yaja hannun kanwar shi suka nufi shagon gabada wannan. Hajiya Yusra dake tsaye cikin babban shagon tabi bayan su da kallo, yanda tagan su a hargitse kayan jikin su a yayyage sai suka bata tausayi ga uban raunin dake kan karamar yarinyar, ta tabbatar koda sunada iyaye to marasa karfi ne domin kuwa babu wata Uwa dazata iya kallon ya'yan ta cikin wannan dettin ta barsu dashi sai dai in batada halin gyara musu. A shago na gaban ma basu sami komai ba haka aka Kore su, dama mazauna wajan sun fara gajiya da yawan mabarata musamman kananan yara wayanda ya kamata ace suna makaranta. A ganin mutanen iyaye irin wayan nan yaran sun maida rayuwar ya'yan su tamkar jarin kasuwanci su suke turasu kasuwanni da tashoshi, har ma da madakar motoci. Haka Amar ya ding a bin shagunan d`aya bayan d`aya yana baran abinci wa kanwar shi, amma abin kamar had`in baki duk inda suka je korar su akeyi ana hantar su tareda fad`ar bakaken maganganu akan iyayen su abinda yake tilastawa Amar zubda hawaye kenan. Ji yayi Feena ta tsaya ga tafiyar da sukeyi da nufin zuwa wani shagon ya juyo da sauri ya kalle ta Feena lafiya? Hawaye ya gani yana zuba a kan kumatun ta tace "yaya dan Allah ka daina rokon su ni na daina jin yunwa dan Allah yaya" ka karashe maganar da kuka mai sauti. Shima kukan ne ya subuce mishi suka dinga kuka ba mai rarrashi ya jata jikinshi ya rungumeta a lokacin ne yaji zafin jakin ta ya tsananta da sauri ya janye jikinshi daga cikin nata "Safeenah me yake domin ki? Kan ne yake miki ciwo? A razane yake mata wayannan tambayoyin shiru tayi bata ce dashi komai ba yaja hannun ta suka nufi karkashin wata baranda wadda ba kowa acikin ta ya zaunar da ita agefe shima ya zauna ya fuskance ta. Kanwata ya fad`a yana taba kumatun ta da bayan hannun shi ta amsa dakyar a lokacin jikinta yafi kowane lokaci zafi. Yace "kan ne yake miki ciwo?" Tace "eh" "sannu kinji" yace mata ta gyad`a kai gawaye nabin kumatun ta. nan da nan jikinta ya fara kyarma ta zame daga zaunen da take ta kwanta a kasa. Nan fa hankalin Amar ya kara tashi baisan sanda ya fashe da kuka ba, ya d`auki kanta ya d`ora a cinyarshi ya fara sambatu. "Dan Allah Safeenah karki min haka, kin sani ke kad`ai kika rage min Abba ya tafi Umma ma ta bishi yanzu Feena idan kika bisu nikuma dawa zan rayu?, Dan Allah kitsaya ki rayu da d`an'uwanki". Ya koma fashewa da kuka "Hajiya Yusra dake tsaye a Kansu itama kalaman Amar sun sakata kuka, ta share hawayen dake fuskar ta ta tsuguna gaban yaran tace "sannu yaro", Amar ya d`ago a d`an tsorace ya zuba mata ido, murmushi tayi mishi tace me ya sami kanwar taka ne?" Saida ya kalli Safeenar sannan yace "kanta ne ya bugu tun jiya ya saka mata zazzabi gashi kuma tanajin yunwa da kishirwa, dan Allah ki taimake ni da abinci inbata kar ta mutu" wasu hawayen suka koma zubo masa Hajiyar ta kara nutsewa cikin tausayin su takai farin hannun ta ta taba jikin yarinyar zafin da taji ya tsorata ta, zazzabi ne mai karfi yake addabar ta. da sauri ta d`ago tace da Amar "zan taimake ku yanzu kuwa" ta saka hannu cikin handbag d`inta ta ciro dalleliyar wayarta tayi searching wata number tayi dialling, ringing biyu aka d`aga da harshen turanci yayi magana da wanda ta kira d`in wanda nake kyautata zatan direban ta ne, misalin gun da take tayi mishi. ba jimawa sai gashi da wata irin had`ad`d`iyar mota doguwa mai kofofi shida a kowane bangare, da gudu ya fito ya bud`e mata motar ganin ta nufo ta d`auke da karamar yarinya, Amar na biye da ita a baya *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *7* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Tana zuwa ta saka yarinyar, sannan ta juyo ta kama hannun yaron shima ta saka shi itama ta shiga driver ya rufe ya koma mazaunin sa ya tayar saida ya hau titi sosai sannan ta gaya mishi asibiti zai kai su, Emanuel ya kad`a kan motar ya d`orata a hanyar asibitin da ake kula da lafiyar su Hajiyar. Hajiya Yusra tajawo Safeenah ta sakata jikinta sosai ta rungumeta duk yawan dettin dake jikin ta, da kuma rashin sanin inda yaran suka fito bai dameta ba, yanayin yarinyar kawai take kallo dan zazzabin nata kara tsananta yake yi. Haka ma Amar duk tsari da daular dake tattare da motar Hajiya bai d`auki hankalin shi ga barin kallon kanwar shi ba, hannun shi na rike da nata duk kuwa da cewa tana rungume a cinyar Hajiyar, motar kuwa mota ce wadda bai taba ganin irinta ba. Motar Hajiya Yusra cikinta ya kasance tamkar wani karamin falo, kujerun ta suna zagaye da wani d`an karamin table na glass ba a jere kujerun suke ba kamar kujerun motocin daya taba gani. A farfajiyar asibitin drivern ya nemi guri yayi parking ya koma fitowa da gudu ya bud`e mata kofar ta fito d`auke da yarinyar a hannu tayi cikin asibitin yaron yana biye da ita da sauri-sauri gudu-gudu suke tafiyar. Da shigar su nurses suka karbi yarinya suka shigar da ita. Ita kuma Hajiya sai ta nufi office d`in likitar su Dr.Batul, Amar kam wayanda suka d`auki Feena yabi aka kwantar da ita a gadon asibitin suka fara bata taimakon gaggawa wannan raggan dake d`aure da kanta suka kwance suka shiga wanke raunin. Suna cikin yi Hajiya ta shigo tareda likita Dr Batul ta duba yarinyar ta d`aura mata drip sannan ta rubuta mata magunguna ta bawa Norse d`aya tace "taje ta karbo su yanzu su bata". Ta juya taja hannun Hajiya suka koma office d`inta Dr. ta kalli kawar ta Yusra tace "ke kuwa ina kika samo wayannan ditty?" Hajiya tayi murmushi tace Wlh a hanya na same su suna bukatar taimako ne shiyasa na taimake su" tayi shiru tana kallon yanayin fuskar kawar ta'ta. Batul ta yatsina fuska tace "to ai da kud`i kika bawa iyayen su su kaita asibiti ba sai kin bawa kanki aiki ba" Ta sauke numfashi tace "bana tunanin suna tare da iyayen su, but ban tabbatar ba nidai su kad`ai na gani" Tace "hmm Allah dai ya agajeji da zuciyar kin nan, ta cika tausayi kar wata rana a d`ana miki tarko da abin tausayin" Yusra ma murmushin tayi tace "Allah ma ba zai bari ba kawa ta, yanzu gaya min wane hali yarinyar take ciki?" Tace "batada wata matsala wannan buguwar da kanta yayi ne kawai sai yunwa data addabeta, amma da zarar ruwan suka shiga jikin ta zataji saukinta kafin taci abinci" Hajiya Yusra ta dafe kanta "Oh Allah ya bata lafiya", ta mike tana fad`in "bari in tashi in bawa d`an'uwanta abincin tun shima bai fad`imin ba in boni" ta fice da sauri Dr. tabi bayanta da kallo tana murmushi a ranta tace "Yusra bazata canza ba. Zaune ta sami Amar a kan gadon da Safeenah take kai, nurses sun fita bayan sun bata magunguna har tayi bacci yana rike da hannunta wanda aka d`aurawa Karin ruwan, ya zuba mata ido yana hawaye. Ita kuwa baccinta take hani'an bai d`auke kansa daga kallon dayake mata ba, ya dai amsa sallamar Hajiyar. Kasa da shi ta zauna tace "Alhamdulillah likita tace da zarar ta farka shikenan kayi hakuri ka daina kuka kanwar ka bazata mutu ba kaji" ya gyad`a mata kai Emanuel yayi nocking door aka bashi iznin shiga ya shigo sai da ya tsuguna har kasa sannan ya mikawa Hajiyar wata leda d`auke da abinci take a way gidan biyu da robar ruwa data lemuka bibbiyu ta karba sannan ya mike ya fita. Ta bud`e ta fiddo takeaway d`aya da roban ruwa da lemu ta ajiye a gabanahi ta bude abincin masha Allah pride rice ce wadda taji Corry da kayan vegetables ga wata lafceciyar cinyar kaza an kifa akan abincin. tace "kaci abinci kafin kanwar ka ta farka itama ga nata nan" Yaron yabi plet d`in abincin da kallo har cikin zuciyar shi yana son abincin tabbas yanajin yunwa bama kad`an ba sai dai Sam ba zai iya cin abinci ba Feena ba. Ya d`auke kanshi daga kallon abincin ya mayar da ganinshi ga yar'uwar shi, cikin tausasa murya yace wa Hajiyar "nagode amma bazan iya cin abinci babu ita ba *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *9* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Dr. ce taja hannun Yusra suka fice tana cewa yaran "muna zuwa" kai tsaye office d`inta suka nufa. Bayan sun zauna ta kalli kawar ta'ta tace "kawata nima fa yaran nan sun fara burge ni, shin kin sami jin wani labari game da su?" Hajiya Yusra ta muskuta ta gyara zamanta fuskarta d`auke da mayalwaci murmushi tace "naji komai game da su kawata su d`in marayu ne kuma daga kauye suka zo wahala ce ta fiddo su, nan ta bayyana mata duk yanda Amar ya gaya mata ta, daga karshe tace "in takaice miki labari dai yanzu nima na sami ya'ya Allah ya bani masu d`ebemin kewa" tana fad`in hakan kwalla suka cicciko daga idon ta, taja gefen gyalenta ta share hawayen. Dr.Batul ta d`an harare ta kinga matsalarki Yusra dan Allah ki daure ki manta baya ki fuskanci gaban rayuwar ki, kisani abinda ya faru akan ki rubutacciyar kaddara ce kuma jarrabawa ga rayuwar ki data Alhajin duka kiyi hakuri kinji kawata". Hajiya Yusra taja numfashi cikin kuka mai sauti da rawar murya tace "nasani Batul kawai tunani nayi da ya'ta tana nan da yanzu itama ta girma, ba mamaki ma da takai wannan yarinyar" tausayin ta ya kara lullube Dr. Tace "hakane Yusra a wannan shekarar ne yarki zata cika shekaru takwas ko a mace ko a raye" itama dai hawayen ne suka silalo mata domin tausayin kawar ta'ta da tuna baya da sukayi. Shiru ta ratsa office d`in na wasu yan dakiku Dr. ce ta kauda shirun da cewa "bari muje mugani ko sun kammala cin abincin", sai da ta tashi sannan ta mikar da kawar ta'ta tsaye tissue ta yago daga kan table d`inta ta shere mata hawayen fuskar ta, sannan taja hannun ta suka fice daga office d`in tana cewa "ki aika yaron can ya siyo musu Kayan sakawa akwai a wajen asibitin nan zan saka ayi musu wanka su canza kafin Ku tafi gida". Hakan kuwa akayi kafin su shiga d`akin ta kira Emanuel tace "yaje ya siyo kayan sakawa kwatancin na yaran nan da muka zo dasu na mace da namiji" duk da harshen turanci take masa maganar ya amsa da "yes maa" ya juya ya fice da sauri Koda suka shiga d`akin sai suka tarar Safeenah tana ta tari Amar ne keta faman bubbuga kanta yana hura mata iskar bakin shi a ka, da sauri Hajiya Yusra ta isa gare su ta kama yarinyar tana girgizata "Amar meya sami Safeenah?" Yusra ce tayi wannan maganar cikin kid`ima da rud`ewa. Yana zubda hawaye ya nuna mata robar lemun cock data basu yace "wan can abin tasha shine ta kware ta dinga tari" Dr tayi murmushi ta kalli Safeenah wadda zuwa lokacin tarin ya lafa mata tace "ayya rashin sabo ne inaga da karfi kika zuki lemun, sannu kinji" Safeenah ta gyad`a kai kawai dan bakaramin zafin abin taji a makogoro da kwakwalwar ta ba. Duk abin nan da taji kuwa bai hanata d`aukar robar ta karashe sauran daya rage na saboda taji dad`in abin sosai. Sai dai wannan karon a hankali ta dinga kurba har ta shanye shi Tass dai-dai da shigowar nurses d`in da Dr ta kira. Da shigowar su tayi musu umarni da suyiwa yaran nan wanka yanzu. Ai kuwa ba bata lokaci d`ayar ta ja hannun Safeenah tana mata yan wasanni tashige toilet d`in d`akin da ita, sai da ta cire mata kaya sannan ta kara tsinkewa da yawan dettin dake jikin yarinyar "ya Rabbi" ta fad`a tana kallon fuskar Feena wadda ita kanta fuskar a dankare take da tarin dettin balle kuma uwa uba wato kan yarinyar wanda duk ya cukurkud`e ya cure guri d`aya sai kace abinda aka sakawa ruwan gam kan tarin dattin dake cikin shi, ai nurse kam kasa jurewa tayi sai da ta leko d`akin ta umarci yar'uwar ta data kawo mata wani sabulu mai karfi da man wanke kai *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *8* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Hajiya Yusra ta kurawa yaron ido cike da mamakin kalaman sa, sai kuma taji tausayin shi ya kama ta, wannan wane irin So ne yake yiwa kanwar shi? ta maida kallon ta ga Safeenar wadda har yanzu bacci takeyi baccin da ba wanda yasan lokacin da zata farka tamatsa daf da Amar ta dafa kafad`arshi ta sanyaya muryar ta tace "yaro ka daure kaci abinci ba abinda zai sami kanwar ka data farka itama zan bata nata kaji" sai a lokacin ya daga kai ya kalli Hajiyar yace "kiyi hakuri Umma tunda muka taso haka muke ban taba cin abinci babu ita ba haka itama tare muke cin komai randa bamusamu ba muyi hakuri, rashin lafiyar ta bazaisa in karya wannan dokar ba zan jira ta na kowane lokaci indai har zata farka" ya karasa maganar lokacin da wasu sababbin hawaye suka gangaro daga idon shi. Tausayi al'ajabi da sonjin labarin yaran suka dirarwa Hajiya Yusra lokaci d`aya ta rungume Amar itama hawaye na bin kuncin ta tace "yaro gaya min sunan ka da kuma wani abu gameda Ku Wato labarin Ku hakika zan taimake Ku da duk abinda nake da shi" ta raba jikin ta da nashi ta zuba mishi ido tana sauraren ji daga gareshi. Shiru yayi na lokaci mai tsayi wanda har sai da Hajiyar ta fara cire rai da zaiyi magana can ya sunkuyar da kansa kasa yace "Suna na Amar, kanwa ta kuma Safeenah, daga kauye muka zo kuma mu marayu ne Abba da Ummar mu duka sun rasu a hannun Ba'ba Larai muke kishiyar Mahaifiyar mu........************************** Nan dai Amar ya kwashe kaf Abinda ya sani ya gaya mata har dalilin daya rabo su da gida da yadda suka tsinci Kansu nan bai boye mata komai ba sai labarin asalin Safeenah Wanda yayiwa kansa alkawarin bayan shi ba wanda zai koma sani, domin guje mata tsana da hantara irin wadda ba'ba Larai tayi mata zai ci gaba da kasancewa Yayan ta Uwa d`aya Uba d`aya Hawaye ne sharkab a kan fuskar Hajiya Yusra wasu na ture wasu hakika labarin rayuwar yara biyun ya girgizata ya kuma kara nunka tausayin da take musu a ran ta, Rayuwa kenan ita a nasu gidan neman haihuwar suke ruwa jallo amma ta ga'gare su ga wasu Allah ya basu suna neman hallakawa. Sake rungume Amar tayi a karo na biyu wannan karon kukan ta hadda sauti cikin kukan tace "Allah yajikan Mahaifiyar Ku Amar, hakika kuna cikin garari da matsin Rayuwa amma inaso daga yau kai da kanwar ka kudaina kallon kanku a matsayin marayu" Amar ya d`ago da sauri ya kalli fuskar Hajiyar ta gyad`a mishi kai "eh daga yau Ku ba marayu bane kunada Uwa kuma kunada Uba, Amar nice Ummar Ku Abban Ku kuma yana gida" Amar ya kalleta zuciyar shi cike da farin ciki damashi tunda ta d`auko su yaji hankalin shi ya kwanta da ita. har ya bud`i baki zaiyi magana sukaji an ce "Umma?" Tare suka juya ga mai maganar Safeenah ce wadda tun d`azu ta farka tana kallon su kuma tana sauraren su. Cikin sakin fuska Hajiya Yusra tace mata "eh Umma, zaki yarda ki d`auke ni a matsayin Umman ki?" Feena ta washe baki"eh Umma" dad`i ya lullube Hajiya Yusra ta shafi fuskar Safeenah tace "na gode ya'ta, ya kike jin jikin naki?" Amar ma goshin ta ya dafa yace "ya kikeji yamzu?" Murmushi tayi musu tace "dad`i nakeji sosai yau nasami Umma, yanzu ba abinda yake min ciwo" sai kuma ta marairaice fuska tace "sai dai har yanzu inajin yunwa" ta kalli Hajiya Yusra tace "Umma zaki dinga bamu abinci?" Hajiyar tayi murmushi tace "duk irin wanda kike so kuwa" Safeenah taji dad`in maganar ta kara fad`ad`a murmushin ta tace "na gode Umma" Da waya Hajiya Yusra ta kira kawar ta Dr Batul ta shaida mata farkawar yarinyar, ba jimawa kuwa ta shigo ta cire mata Karin ruwan sannan ne Hajiya taja hannun su duka biyun takai su toilet ta wanke musu hannayen su suka fito tare. Wani Capet Dr ta bata ta shimfid`a musu tsakiyar d`akin suka zauna, ta bud`e musu abincin nan da tasa aka siyo musu ba musu suka fara ci fuskokin su cikeda annuri da murnar samun abinda suke so, lafiyayyen abinci wanda basu taba koda ganin irin sa ba. Sai dai hakan bai sa su sauri ko ribibin cin abincin ba, a hankali suke ci dukda da hannu suke cin abincin bai hana tabashi a baki ya bata ba Haka Hajiya da Dr. suka saka su gaba suna kallo cike da mamakin irin kaunar da suke wa junan su, Hajiya Yusra a ranta ta jinjinawa duk Uwar data haifi yaran nan, dan had`a kan yara da koya musu son juna haka ba karamin Abu bane *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:43 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *10* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Nurse d`in ta amsa da "OK" ta fita d`aukowa ba jimawa ta dawo da duka kayan da ta bukata ta kai mata toilet d`in, da taimakon yar'uwar ta'ta ta samu suka wanke kan yarinyar ya fita fess sannan suka mata wanka suka fito da ita. A lokacin Dr da Hajiya Yusra basa d`akin sun fita zaga marasa lafiya Yusra ta basu sadaka tunda Allah ya kawo ta, a kan gado suka sauke Safeenah bayan sun nannad`e ta da towel. Suka kama hannun Amar shima suka shiga dashi, daga sosai sukayi dashi akan ya cire Kayan sa a mishi wankan Sam ya ki yarda su tube shi yace musu "ni bazaku min wanka ba nariga na girma ai ni nake yin wanka da kaina a gida, harma in yiwa kanwa ta". Dakyar da rarrashi suka samu ya bari suka tobe shi suka mar wanka wanda shi d`in ma ba karamin datti aka kankara daga jikin shi ba kanshi ma yasha wanki da man da suka wanke na Safeenah domin shi d`in ma gashi ne curkus a kan nashi ba gyara ba aski. Suka gama suka fito dashi a lokacin Feena har ta fara gyangyad`i wani irin dad`i na iskar duniya dataji yana shigarta ta ko'ina ita kanta yarinyar tasan wanka rahma ne kuma ta yarda da hakan Suka shafe su da lafiyayyun mayuka lotions sannan suka saka musu sababbin Kayan da aka siyo musu. Masha Allah Kayan d`ass a jikin su kamar abinda aka gwada, kananan kaya ne yan kanti, Kayan sun masifar yi musu kyau barimma Safeenah da take fara suka kama gashin kanta suka shafe shi da mayukan kai nan take kan ya d`au Kelli da sheki. Yarinyar ta burge nurses d`in ashe kyakkyawa ce boye a cikin detti haka suka dinga fad`a da harshen turanci d`ayar ta ciro wani tafkeken ribbon dake kanta kasancewar guda biyu ta saka. Ta d`aurewa Feena kai da shi haske da sirrin kyawunta suka kara bayyana ba make-up ba komai gashi da wanka d`aya ta bayyana yar gayu mai kyau da yalwar Gashin kai dana ido hakama gashin girarr ta baki ne sid`ik kwantacce. Amar ya zuba mata ido ko kiftawa bayayi ganin Safeenar shi yake kamar wadda aka canza lokaci d`aya ta sauya ko lokacin da Umma ta nan tana yi musu wanka Feena batayi kyaun haka ba. Ita kanta Feena daban take jin kanta wani irin dad`i ne ya lullube ta data kalli yayan nata yayi matukar kyau kamar ba Amar mai dako ba, duk da kasancewar shi baki sai dai shi black beauty ne tare suka yi taku d`ad`d`aya suka isa ga junan su sannan cikin had`a baki wajen cewa junan su "kinyi mutukar kyau kanwa ta" "kayi mutukar kyau yaya na" sai kuma sukayi dariya jin sun fad`i Abu d`aya, nurses d`in ma dariya suka yi. Aka turo kofar aka ahigo Hajiya Yusra ce da Dr.Batul suka dawo *wacce ce Hajiya Yusra?* Hajiya Yusra matashiyar mace ce yar kimanin shekaru talatin da hud`u a duniya. Farar mace ce doguwa mai dara-daran ido farare kal kamar madara kyakkyawar gaske ce mai murzajjen jiki da lafiyayyar fata, kana ganin ta kaga girman a.c, hutu da Naira, Mata ta biyu kuma abar So ga Alhaji Tijjani Wakkala. sanan ne ne kuma fitacce a ciki da wajen kasar nan, shahararren d`an kasuwa ne kuma d`an siyasa Masu fad`a aji a majalisar Tarayya. Asalin ta yar kasar saudiyya ce a wani zuwa da Alhaji Tijjani yayi can a lokacin aikin hajji anan kusada masaukin su anan gidan su Yusra yake, gani d`aya yayi mata yaji ta kwanta masa a rai gashi kuma a lokacin iyayen shi na raye kuma sun matsa masa akan ya karo aure domin tun lokacin da ya auri matar shi ta fari hajiya Ummu ko batan wata basu taba yi ba samada shekaru sha'uku, wannan ne yasaka iyayen su ke fata da burin ya kara aure dan acewar su ba mamaki matsalar daga matar tashi ne. To Allah dai bai tabbatar ba sai a lokacin da yaga Yusra dayake lokacin ma da iyayen shi yazo bayan kammala aikin hajji yasa suka nema mishi Auren ta. Iyayen ta mutanen kirki Masu son mutane suka karbesu hannu bibbiyu kuma suka bashi Auren ta, basubar kasar ba sai da aka d`aura Auren aka danka mishi matar shi suka dawo Nigeria tare da rakiyar yayun ta maza biyu da kanwar Umman ta. Kwatsam sai Hajiya Ummu taga Alhaji ya dawo da Amarya balarabiya ai kuwa sai da hankalin kowa ya tashi a gidan ta dinga hauka da zage-zage bata bar kowa ba. Amma ya ta iya da ikon Allah dole ta hakura ta rungumi kaddara, Amma tasha jinya har asibiti sai da ta kwanta saboda Karin Auren *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:44 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *11* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Ta yarda Auren Hajiya Yusra da Alhajin ta kaddara ce amma tace "har abada bazata taba d`aukar Yusra a abokiyar zama ba sai dai kishiya, kishiyar ma abar ki. Haka dai Alhaji ya tursasata zama da Yusra dole sai dai ba zaman lafiya kullum cikin cemini-cemini da neman fitina take dayake ita Yusrar ba fitinanniya bace bata kula ta gashi kuma a lokacin batajin Hausa dayawa mugayen maganganun da Hahiyar ke jifanta dasu batasan me take cewa ba sai dai wad`an da ta fad`a da harshen turanci dan itama hogaggiyar yar'boko ce kuma yar'siyasa ma'aikaciyar gwamnati. Haka Rayuwa ta tafi musu cikin yanayi na zaman doya da manja. Hahiya Yusra bata ciki watanni uku a gidan ba Allah ya bata ciki ai kuwa nan hankalin Hajiya Ummu yayi masifar tashi, duniya tayi mata zafi tace ina wuta ta fad`a? Haukacewa ne kawai batayi ba. Alhaji da iyayenshi kuwa farin ciki ne mara misaltuwa ya mamaye zukatan su abinda ko a mafarki nemanshi yake yau gashi Allah ya bashi murna ya hau yi da ririta Yusra wadda ita abin har kunya yake bata Yayi bari da dukiya bayin Allah sunsha sadaka a dalilin samun wannan cikin a gidan Wakkala ma tawakkali ga Allah Rabbi, kirarin Alhaji Tijjani Wakkala kenan. Haka sukayita renon cikin cikin marari da tsantsan so da kauna a lokacin Alhaji Tijjani ya d`auki son duniya ya d`orawa amaryar shi da abinda ke cikin ta, Wanda a bangaren Hajiya Ummu babu abinda ta tsana a duniya sama da su, neman hanya take wadda zata samu ta hallaka su kota halin ka'ka amma bata samu ba. Bakin cikin duniya ya ishe ta Iya mahaifiyar Alhaji da kanta ta tare gidan domin kulada Yusra da cikin ta sai nan-nan ake da ita har Allah yasa cikin ya isa haihuwa ranar wata assabar biyu ga watan August na wan nan shekarar Yusra ta haifo santaleliyar yar'ta mai d`iban kama da ita tubarkalla haka duk Wanda yayi arba da jinjirar ke fad`i Kwanaki uku da haihuwar yarinyar iyayen Yusra da yan'uwa na saudiyya suka iso ga sanin Alhaji na kusa dana nesa sun fara hallara gida ya fara ciki ya kacame da yan'uwa da abokan arziki masu zuwa ganin baby. Hakan yasa aka warewa yarinyar d`aki d`aya na musamman saboda hayaniyar mutane mutum uku ne ke kula da ita mata duka Yan aikin gidan Amma dayake ance mai son abinka ya fika dabara sai da Hajiya Ummu ta kulla tuggun da ta saka wata shakikiyar kawarta Eysha ta sato mata babyn tace "Eysha wannan ita ce abar danafi tsana a rayuwata domin duk sauran Masu sauki ne, ki tafi da ita nesa da garin kano sannan ki kashe ta ki jefar da gawarta karnuka su cinye" Eysha rikakkiyar karuwa ce yar maye amma hakan bai makanta zuciyar ta da har xara iya yin kisa ba, ta amsawa Hajiya Ummu da "to" ta fice da yarinyar a sace. Kasan cewar mutane Yan barka da sukayi yawa a gidan yasa tsaro yayi rauni a gidan ba Wanda ake bincike Bata zame ko'ina ba sai tasha ta hau motar sokoto da Tatar ana jiran mutum d`aya, da suka iso sokoton ma sai da ta nemi motar wani kauye ta hau domin sirranta abinda tayi nufin aikatawa. Saida taga motar takai wani karamin jeji inda ba yawan mutane sai dai tana hangen wani karamin kauye daga nesa tasa motar ta ajiye ta a gurin. Sai da motar tayi nisa har ta bacewa ganinta sannan ta ajiye yarinyar a gefen hanya. take ta gaggauta barin gurin ta kama hanya taje wata kasuwa ta hau motar kano ta koma A gidan Alhaji Tijjani kuwa hankula ne suka tashi a lokacin da aka tabbatar da batan jinjirar da aka haifawa Wakkala babu inda ba'a bincika ba amma bata gidan haka ya tabbatar musu da cewa d`aukar ta akayi Alhajin da Hajiya duk a sume aka kaisu asibiti. Babu irin cigiya da binciken da ba'ayi ba amma ba'a gano yarinyar ba tun daga wannan ranar bakin ciki da damuwa suka dankare zukatan masoyan biyu duk wani mai kaunar su sai da ya tausaya musu a ranar bakin ciki ya kashe mahaifiyar Alhaji saboda tanada hawan jini mijinta farin dattijo ya kwanta jinya. Hajiya Ummu dad`i kamar ta zuba ruwa kasa tasha miliyan Goma tabawa kawar ta Eysha sannan ta bazama duniyar bokaye gurin neman asirin da zai hana Alhajin sake haihuwa har abada. Allah ko ya amsa musu dan tun daga wannan jinjirar Hajiya Yusra bata koma yin koda batan wata ba, idan sukaje asibiti sai ace lafiyar su lau lokaci ne bayyi ba Daga baya mahaifin ahi ma Allah yayi masa rasuwa shi kuwa Alhaji Wakkala Allah ya jarrabeshi da masifar son yara kamar me Gashi shi kad`ai ne baida wa ba kani balle ya ga ya'yansu yaji dad`i. Hakan yasa Hajiya Ummu ta d`auko d`an yayarta Mubarak tana rikon shi Wannan kenan *cigaban labari* Dam! Gaban Yusra yai mummunan fad`uwa a lokacin da idonta ya sauka ga Safeenah *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *12* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Ji tayi kamar taga wani Abu da ta taba sani a baya, kamar photo haka ta tsaya a kofar idon ta kir akan yarinyar tabbas tasan fuskar nan inji wani sashe na zuciyar ta. "Eh kin Santa mana tun bayan wasu awanni da kika fara ganin ta" Zuciyar ta ta tabbatar mata inda tasan yarinyar, sannan tacigaba da kawo mata dalilai da hujjoji Wato lokacin da kika fara ganin ta kyau da hasken fuskar basu fita haka ba shiyasa yanzun kika ganta kamar wata sabuwa. Wannan duk bayani ne na zuciyar Hajiya Yusra wanda ta koro mata a dalilin sarkakiya da ta shiga na tunanin ta taba sanin fuskar Safeenah. Tamayar da kofa ta rufe sannan ta karasa shigowa. Sai a lokacin yaran suka sanda shigowar ta'ta gaba d`aya suka kalle ta fuskokin su d`auke da murmushi, itama dai murmushin take ta isa gare su ta shafa kawunan su tace "yarana kunga yadda kuka canza?, kai masha Allah gaskiya kunyi kyau" sunji dad`in yanda ta yaba kyan na su dan su Kansu sunajin kan su daban. Suka kara fad`ad`a fara'ar su dai-dai nan Dr. Ta shigo hannun ta rike da wasu files da Jaka tace "yi hakuri na tsaya had`a kayana ne," ta fad`a idon ta akan Yusra "Bakomai kawata, ya kika ga yara na?" Sai a lokacin idon ta yakai garesu "wow! Masha Allah gaskiya na tayaki murna Yusra" Dr.Batul ce mai wannan maganar fuskar ta d`aukeda murmushi ta koma cewa " to ko dai zamuyi raba dai-dai ne?" Ta fad`a cikeda tsokana Yusra ta harare ta kafin taja hannun yaran ta nufi kofa tana cewa "to sarki had`ama babu naki a nan, yar rainin hankali su kuma yaranki hud`u ki kaisu INA?" Dr. tayi dariya "to sarki rowwa na bar miki Allah ya taya ki riko" tana maganar tana binsu a baya tare suka fito farfajiyar Asibitin suna tafe suna hira yaran na rike a hannun Yusra inda sukayi sallama kowacce ta nufi inda motar ta take, har zasu shiga Amar yayi wata irin zabura kamar wanda aka tsikara "Innalillahi" ya fad`a yana laluben aljihun wandon sa ganin ba wandon shi bane ya tuna masa an cire mishi wan can a lokacin da za'ai mishi wanka. da karfi ya kwace hannun shi daga cikin na hajiyar ya juya da gudu ya koma d`akin da suka fito. da sauri Hajiya tabi bayan shi tana tambaya "Amar lafiya? Ina zaka?" Inaa ko juyowa baiyi ba, dole tabi bayan shi tana rike da Feena dake ta faman Jan hannun ta da nufin suma suyi gudun su same shi. Toilet d`in d`akin ya fad`a yana dube-dube amma me? Baiga Kayan da aka cire musu ba, ba nashi ba na Feena ya koma fitowa da gudu zai bar d`akin a kofar suka ci karo da su Hajiya harma da Dr. "Kai Amar lafiya, me ka ke nema?" Hajiyar ce mai wannan tambayar "Umma kaya na wanda aka cire min su nake nema" ya fad`a lokacin da kwalla suka cicciko masa ido. Hajiyar tayi ajiyar zuciya tace "banda abinka Amar ai ka gama da wannan Kayan zo mu tafi sababbin kaya zan saya muku masu yawa" ta karashe maganar tareda mika hannun ta zata riko nashi. Yai baya yana girgiza mata kai "a'a Umma akwai wani Abu mai muhimmanci a cikin wannan kayan dan Allah suna ina?" Ya yi tambayar a lokacin da hawaye suka fara gangarowa bisa kumatun shi "haba Amar meye abun?, kayan nan fa an riga an saka su a shara". "Shara" ya fad`a ido waje "wane sharar?" "Dan Allah wane shara?, Ku taimaka Ku nunamin sharar Alkawari na d`aukawa Umma'na gashi zai karye, Ku taimake ni amanar Umma ce." duk wayannan maganganun cikin kuka Amar yake yin su, Al'amarin da yabawa su Yusra da Dr. mamaki to meye a kayan da yaron yake yiwa kuka haka? Dr. ce ta dafa kafad`ar shi tace "to ya isa Amar bari inkira nurses d`in in tambaye su inda suka kai kayan" Tana rufe bakin ta sukaji an turo kofar d`aya daga cikin nurses d`in nan ce sai da ta rusina ta gaishe su baki na ruwa tace "Hajiya wani muhimmin Abu na gani a cikin Kayan yaran nan, lokacin da naje jefarwa ya fad`o" tana maganar ne tana kallon Hajiya Yusra *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *13* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ "Wai Alhamdulillah, to gashi ma an gani, kawo nan, mun gode fa" duk Hajiya Yusra ce mai wannan maganar cikin fara'a da jin dad`in bayyanar abin duk da batasan asalin mene ne ba, sai dai ta san samun shi d`in shine kwanciyar hankalin su baki d`aya, duba ga yadda yaron ya d`aga hankalin shi akan shi Norse ta mike tareda mikowa hajiya karamin abin dake d`aure a cikin leda, wuf ! Amar ya damke ledar yana fad`in "mun gode sosai Allah ya saka miki da alkhair" sai da ya bawa Hajiyar dariya, nurse d`in ma sai da ta dara sannan ta juya ta fice. ya kanannad`e abun ya cusa a aljihun wandon shi, sannan Hajiyar ta kama hannun shi suka tafi. Dr. Tace "Yusra wannan yaron naki akwai rigima yanzu haka abun wasa ne yake yiwa rigima haka" hajiyar tace "bar shi ya yi ai rayuwar yaran kenan" suka yi dariya a nan suka yi sallama kowacce ta nufi motar ta suka shiga. Wata kebabbiyar anguwa aka shiga dasu wadda bata cika yawan mutane ba, tituna ne layi-layi sai maka-makan didaje na Masu kud`i babu alamar karamin gida ko ginin talakawa a anguwar. A kofar wani gidan suka faka driver yayi horn wani jibgegen inyamuri ya bud`e musu gate tare da rusunawa yana mika gaisuwa ga Hajiyar. A filin parking ya tsayar da motar sanna ya fito da sauri ya bud`e musu kofar suma suka fito. nan fa Amar da Safeenah suka koma asalin su na kauyawa, suka hau kallace-kallace da waige-waige. Sun kasa tantance wannan wane irin gida ne wanda ko a mafarki basu taba ganin irin shi ba Murmushi tayi ta kama hannayen su suka shige ciki zuciyar ta cike da farin ciki wanda ita kanta batasan na meye da meye ba, domin a ganin ta farin cikin da take ji a ranta ya zarce na samun yaran kawai, ji take kamar ta cike wani gurbi ta data rasa a rayuwar ta. "Salamu Alaikum" tayi sallama a falon gidan na su wanda yake a had`e Wato (general falo) Alhaji Tijjani (wakkala) dake zaune a falon ya mike a d`okance ya taro ta "wa Alaikissalam, mata ta, where have you been?" Ya fad`a tared marairaice fuska "kin tada hankali na, tun d`azu nake neman wayar ki sai tayita ringing ba'a d`agawa" tace "oh (habibi) Wlh ban lura ba nasaka wayar silent ne, saboda ina asibiti" "asibiti kuma?" Ya fad`a a tsorace yana kallon ta "me ya same ki?" (Hhhh) tayi dariya sanah ta bashi ransa "ba abinda yasame ni sai alkhairi, yarinya ta na kai asibiti" cike da mamaki ya kalle ta "yarinyar ki kuma?" Ya tambaya cikeda neman karin bayani. Tace "eh gata nan" ta bashi amsa tana nuna Safeenah dake makale a gefen ta. Sai a lokacin ya lura da yara biyu dake bayan ta, idon shi kyar akan Feena sai ji yayi wani Abu ya taso daga kasan kirjin shi ya soki zuciyar shi cusss *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *14* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Hannun shi ya saka ya d`an tura Yusra gefe d`aya ya kurawa yarinyar ido na lokaci mai tsawo. Yusra dake gefe itama saida taji wani Abu, tausayin mijin ta ya kama ta, ko shakka babu tasan tunanin su ne yazo d`aya Wato yana yiwa Safeenah kallon batacciyar yar'su ne. a ganin su da tana raye tare da su da yanzu ta kai sa'ar wannan yarinyar ko ma ta fita Ya tsuguna gaban Feena ya zuba mata ido tare da kamo duka hannayen ta biyu ya rike su gam. "Kyakkyawar yarinya" ya fad`a yana kara karewa fuskar ta kallo "Yusra ina kika samo yara haka? Ko yaran wacce ce a cikin kawayen naki?" Lallausan murmushi ne ya wanzu a kan kyakkyawar fuskar ta, ta matso kusa dashi ta kama hannun yaran taja su zuwa kan lafiyayyun kujerun dake zagaye da falon tana fad`in "ka cika sauri habibi zo ka zauna in maka bayani" yabi bayan ta da ido kafin ya mike shima ya nufi kan kujerar dake makoftaka da ta'ta ya zauna, har yanzu bai d`auke idon shi daga gare ta ba bayani yake son ji game da yaran dasuka matukar burge shi kuma suka shiga ran shi farat d`aya Yara kam sam hankalin su baya kan su, tuni sunyi nisa da abinda suke na raba ido suna karewa kayan alatun dake falon kallo, ji suke kamar wata duniya ce ta daban ta wasu jinsi suka zo sabanin waccan da suka baro ta karkara. Murmushi ta komayi tana kallon fuskar mijin nata yanda ya kagu yaji inda ta samo yara, addu'a ta fara yi a ran ta Allah yasa ya karbi uzurin ta wato ya yarda da kudurin ta na rikon yaran da take so suyi. Sannan tace "Habibi wayan nan yara da kake gani sakon Allah ne zuwa gareni, domin Allah shi kad`ai ne yasan yanda nake azabtuwa da yawan tunani da damuwa na rashin haihuwa tun daga kan yarinyar mu da aka sace har yau abin baibar zuciya ta ba," tayi shiru tana goge kwalla. Kafin taci gaba -"a hanya ta ta dawowa na had`u da su cikin mawuyacin hali suna neman taimako na taimaka musu," sannan na nemi sanin iyayen su domin sanin inda zan kai su ko wayanda zan nema na hannun ta su gare su. sai suka gayamin su bakin ne daga kauye suka zo kuma su marayu ne" nan dai Yusra ta kwashe labarin su Feena kamar yadda Amar ya gaya mata ta nawa Alhaji Shi kan shi sai da jikin shi yayi sanyi sosai da jin labarin yaran da irin matsi da takurar da suka sha a wannan shekarun na su daya kamata ace suna samun gata da kulawa ta iyaye, tareda koyarwar addini ba dai talla da dako ba. Ya sauke numfashi ya fuskanci matar tashi yace "Yusra zamu taimaki yaran nan kamar yadda kika kudirta a ranki zan zame musu Uba muddin kika zame musu Uwa" Murmushin jin dad`i ne ya subuce mata, tace na gode sosai Habibi Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, idan munada rabo muma Allah ya bamu namu masu Albarka." Ya amsa da "Ameen Yusra" tajuya ga yaran wayanda ke can kan plasma t'v suna shafawa suna kallon kan su a ciki kasancewar a kashe yake. "Amar", ta kira sunan a hankali "kuzo ga Abba" ta fad`a fuskar ta a sake. Yaran suka zo gaban ta suka tsaya suna kallon Alhajin "lah Umma wannan shine Abban mu da kika ce yana gida?" tace "eh shine wannan kuje ya saka muku Albarka" suka kalli junan su Amar ya sakewa Feena murmushi sannan ya kama hannun ta suka je har gaban Abba suka tsuguna "sannu Abba" suka fad`a tare Alhaji Wakkala ya d`agosu tare ya mikar dasu sannan ya nuna musu gefen shi yana cewa "a nan zaku zauna kusa da Abba kunji yara na" Amar ya amsa da "to Abba" domin Safeenah kam har tayi tsalle ta haye kujerar, Amar da Abban suka kalle ta. Alhaji ya koma fad`awa tunani Wanda shi kan sa baisan na meye ba, kawai dai kallon fuskar yarinyar yana saka shi tunani *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *15* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ Amar kuwa dad`i da farin ciki ne suka lullube shi, yau ga Safeenar shi tana farin ciki, gasu a sabuwar duniya inda yake kyautata zaton rayuwar su zata haska da iznin Allah Karar takun takalmi sukaji tana sakkowa daga saman bene cikin takon nan nata na nuna isa da kasaita ta iso gaban Alhajin cikin shirin ta na fita office hannun rike da jaka da key d`in mota, Sai faman shan kamshi take tana yatsina. "Zan fita" ta fad`a tana yage baki tana tauna cingam. Alhaji Wakkala ya sauke numfashi yace "Wai sabida Allah Ummu sai yaushe zaki canza? Tun wayewar garin nan fa wannan shine ganin farko kika yimin amma ace sam ba zaki iya gaida ni ba sai dai Zaki fita ko?" Ta had`e fuska tareda juya mishi baya "inaga baka so a gaishe ka bane shiyasa ban gaida kai ba, Dani da kai wa Allah ya ce yaje yaga lafiyar wani idan gari ya waye?, duk yau kafarka ta leka d`aki na? To kamar yanda bazaka canza ba haka nima bazan taba canzawa ba" taja dogon tsaki tayi ficewar ta. tabar Alhaji da Hajiya Yusra da kallon inda tabi Haka yara ma suka bita da kallon mamaki. Safeenah ce tazo gaban sabuwar Ummar su ta tsaya fuskar ta cike da damuwa tace "Umma wannan fa wacce ce?, naga tana da fad`a sosai amma dai nazata dake mu ba ko?" ta karashe maganar cikin marairaice fuska. Hajiya ta shafi kanta "ba abinda zatayi muku Feena kuzo mu karasa d`aki" tarika hannayen su suka haye saman bene tana cewa Alhajin "ina dawowa Habibi, bari in kaisu masaukin su". yaran kuwa sai d`ari-d`ari suke da hawa saman saboda tsoro abinka da ba' saba ba A can saman da suka nufa sashe uku ne da wasu bangarori guda biyu, sashe na bangaren dama shine na Hajiya Yusra, na hagun shine na Hajiya Ummu, sai wanda akayi shi tsakiyar su Wanda shine sashen Alhaji. Kai tsaye sashen ta tanufa da su, yara suka tsinci kansu a wani wuri da zasu iya kira da Aljannar duniya. Sanyin A.C da wani lallausan kamshi ne suka yi musu maraba. Bada labari ko fad`ar kayatuwar sahen kamar bata lokaci ne dan sai in shafe shafuka masu yawan gaske garin yin hakan readers imaging. Sashen babban ne mai d`auke da d`akunan bacci biyar falo uku, d`akunan baccin Hajiya Yusra biyu ne da falo d`aya, sai na batacciyar babyn su d`aya mai had`e da falo Wanda har yau yake kebe a matsayin nata, duk wasu kaya da aka saya mata na barka da wayanda yan'uwa da abokan arziki suka kawo mata suna nan ajiye a d`akin, a cikin shi suke gudanar da birthday d`in haihuwar ta wanda suke yi duk shekara. Bayan shi akwai d`akunan baki guda biyu had`e da falo d`aya. direct d`akin ta ta nufa da su har kan gadon ta ta zaunar da su. Yara sai raba ido sukeyi suna mamakin ikon Allah Wata yar kararrawa ta danna wadda kai tsaye take kai sakon nema ga Masu aikin ta dake can kasa, ba jimawa kuwa sai ga wata dattijuwa ta shigo d`akin da sallamar ta Hajiya ta amsa mata fuska a sake. Sai da dattijiluwar ta rusuna tace "Hajiya gani kina bukatar wani Abu ne?" "Eh Iya dan Allah yara nake so ki turomin Yan'mata wayanda kika yarda da hankalin su guda biyu" ta d`an numfasa wanda ya bawa wadda ta kira da Iya damar cewa "to Hajiya kamar masu me kenan?" Tace "wayanda zasu iya kula da yara, su dinga yi musu wanka da kula da abincin su" tace wannan ba matsala, yara muka samu Uwar d`aki na?". Tayi tambayar tana kallon yaran dake zaune gefen hajiyar sunyi shiru suna sauraren su. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *16* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ "Eh yara na ne ana zasu ci gaba da zama tare damu" ta bata amsa a takaice. "Allah sarki kyawawan yara, ai da gani nasan wayannan irin larabawa ne". Iya ce mai maganar idon ta a kan Safeenah tana mata murmushi Feena ma murmuahin ta mayar mata. Ta juya ta fice. Iya ita ce shugabar ma'aikatan gidan baki d`aya, ita take kula da su kuma take ba su umarnin aiki na kowanne sashe na gidan wanda gaba d`aya san-sanin su a kasa yake, sai aiki ko bukatar wani abu ta taso ake kiran su. kamar mintuna biyar sai ga Iya ta dawo da yara wasu yan'mata guda biyu, wayanda basufi shejaru 16 to 18 ba dukkan su suka zube bisa guiwoyin su suka gaida Hajiyar ta amsa sannan ta kare musu kallo ba laifi ta yaba da tsabtar jikin su ta kalli Iya tace "nagode Iya zaki iya tafiya" itama dai godiyar tayi sannan tajuya ta fita. Hajiya ta kalli yan'matan "sannunku yara ya Sunan Ku?" d`aya ce ta bata amsa"suna na Aysha, wannan kuma Laure" Hajiya tace "Madalla Aysha yaran nan nake so Ku dinga kula da su, yanzu shi kad`ai ne aikin Ku a gidan nan, yimusu wanka da kula da abincin su kuyi ko'karin ba su duk abinda suka ce suna so" tayi shiru na dakiku kad`an yaran kuwa na tsugune suna jiran umarnin ta "Kuje d`akunan bakin nan Ku gyara kowanne ya zamana kowaccen ku ta d`auki d`aki d`aya da kuma yaro d`aya, kubar min su nan zamu shiga gari, kuje ku fara gyaran d`akunan duk abinda babu kumin magana". Suka amsa da to suka mike cikin ladabi suka fita. Da kanta ta shiga kitchen ta had`owa yaran abinci chicken Pepe soup ne da tuwan sakwara miyar agushi, ta kawo ta ajiye musu a dining table ta koma ta had`o musu kalolin drinks ta kawo duk tq jere sannan ta shiga d`akin ta fito dasu ta zaunar dasu bisa table d`in ta basu abincin sai da ta tabbatar sun fara ci sannan ta mike ta koma kasa inda ta baro mijin ta, ganin baya falon yasa ta koma dawowa saman a d`akin shi ta same shi yayi zurfi wajan kallon photon jaririyar yar'su da aka sace musu, ko sallamar datayi baiji ba balle ya amsa mata. Akalla takai mintuna uku a kan sa amma Sam bai San da shigowar ta ba, sai da ta kai hannu ta rufe fuskar photon sannan ya Ankara da shigowar ta nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da komawa yayi rigingine kan resting chair da yake zaune a kai. Ta zuba mishi narkakkun idanun ta masu kawar mishi da damuwa cikin tausasa murya tace "Habibi Y? Me yasa kake ko'karin illata kan ka ne? Shin ka manta da shawarwarin da likita ya baka?" Alhajin yayi kasa da kan sa zuciyar shi cike da damuwa yace "ban manta ba Yusra, amma ya zanyi? I have no choice my wife, dole in yi tunani ya zama dole in tuna da gudan jini na". Ya juyar da kan sa gefe idon shi na fitar da hawaye, tausayin mijin nata ya kama ta tasan dole ne domin ita kan ta hakuri take yi, amma ya zasuyi? Basuda abin yi wanda ya wuce hakuri, amma a zahirin gaskiya ita kam yau Allah ya rage mata damuwar dake addabar zukatan na su, ta dalilin samun yara biyun nan sosai ta sami sassauci a zuciyar ta. Itama dai hawayen ne ya zubo mata sai da ta share sannan ta zauna bakin gadon shi ta zuba mishi ido ina so ka saurare ni Habibi. Yarda da kaddara wajibi ne ga kowane musulmi ita kuma kaddara suna ta tara akwai mai kyau wadda zatayi sanadin haska rayuwar d`an Adam, kuma akwai akasin ta wadda Kusan ita ce ta same mu Habibi meyasa ba zamu karbeta hannu bibbiyu mu godewa Allah ba?" -"ka duba kagani yarinya d`aya muka rasa gaahi Allah ya bamu yaran har guda biyu, shin duk da hakan bai can-canci mu gode masa ba?" Ya d`ago kai ya kalle ta "yara fa kika ce Yusra shin ke a tunanin ki d`an wani zai iya maye gurbin wannan yarinyar a rai na?" *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:47 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *17* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad Yar'mutan Arkilla✍ "Never", ya fad`a yana kad`a kan shi, hankali na ya kwanta da yaran sosai, sai dai kin san bazasu iya maye min gurbin (baby) ba, Sunan da suke kiranta da shi kenan idan zasuyi maganar ta. Yusra ta sauke numfashi tare da sunkuyar da kanta kasa, tunani ta shiga yi tabbas maganar mijin ta gaskiya ne, soyayyar d`a da iyayen sa ta daban ce wadda babu mai iya samun irin ta sai dai shi d`an A sanyaye ta koma kallon photon yarinyar dake sanye da wasu jajayen kaya na sanyi masu had`e da hula kayan sun mata kyau sosai. Kyakkyawar fuskar nan ta'ta tayi fess da ita. A ran ta ta koma rayawa "ko tana raye ko ta mutu? Allahu a'alamu" idanun ta suka kawo kwalla a lokacin da wani sashe na zuciyar ta yace "ai duk wanda ya sace ta badan karbar kud`in fansa ba kin san kashe ta zai yi, ba zai bar ta a raye ba." Yusra ta kankame mijin ta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, kukan da yazame mata jiki a duk lokacin da tayi irin wannan tunanin. Alhaji Tijjani na matukar tausayawa matar tashi fiye da shi kan shi, domin yasan duk yanda ya kai ga son yar'tasu bai kai gareta ba ita da tayi d`awainiyar cikin ta da kuma nakudar haihuwar ta. Ya kwantar da murya ya shiga rarrashin ta, lokaci mai tsayi ta d`auka kafin tayi shiru. muryar ta can kasa tace mishi "dama ina so mu fita da yaran nan in siyo musu Kayan sakawa da na amfanin gida harma da kayan wasa". Yayi murmushi yace "an gaishe ki Maman yara, wannan ba komai amma kid`an huta tukunna" yayi maganar yana gyara mata kwanciya akan gadon. Mintuna kad`an bacci yayi awon gaba da ita, murmushi ya koma yi sannan yaja mayafi ya rufe mata jikin ta ya mike a hankali ya fice daga d`akin Kai tsaye d`akin ta ya nufa inda ya Tatar da yaran sun gama cin abinci sun baje kasan Capet suna wasanni. Da ganin shi suka nutsu suka zauna guri d`aya Amar ya kalle shi cikin girmamawa yace "barka da shigowa Abba" jin haka yasa Feena ita ma ta kwaikwaye shi "barka da shigowa Abba" ya amsa da "yawwa yaran Abba" ya kama hannun Amar "my boy kuzo muje mu sha ice cream sannan a siyo muka kayan wasa dana sakawa ko?" kafin Amar yayi magana Feena tayi tsalle ta rike d'aya hannun Abba "yawwa Abba nima zani" ya shafi kyakkyawar fuskar ta yace "dama tafiyar taku ce yarinyar Abba" ta falle baki tana dariya dad'i kaman me ji take kamar yau ta fara zuwa duniya tun bayan da Allah ya amshi ran Umma Feena bata taba yin farin cikin irin na yau ba. hakan ba karamin faranta wa Amar yayi ba sai yaji ya kara son Alhajin da Hajiya fuskokin su cike da annuri ya rika hannayen su suka fita a parking space ya tarar da drivern dake kai Mubarak (yaron da hajiya Ummu ke riko) makaranta ya yana jiran sa, da gudu Mubarak d'in ya fito daga cikin gidan ya makale Dady kamar yadda yake Kiran shi Dady ya saki hannun Amar ya shafa kan Mubarak yana cewa "yaka ke yaro na, ka tashi lafiya". "lfy kalau Dady fatan kaima" "am good, za'aje school ko?" "eh" inji Mubarak hankalin shi akan su Safeenah domin sai a lokacin ya lura da su. "Dady su waye wad'an nan?" Yaron ya tambaya yana kallon su yaran "Mamyn ka ne yau suka zo, kaga ka sami abokai ko?" yaron ya yatsina fuska "Dady ni bana so kawai suyi tafiyar su, ni ko a school banida aboki" yayi maganar da yananyin bacin rai Alhj Wakkala yayi murmushi "kayi sauri ka tafi karka makara" bai koma cewa komai ba ya nufi motar da ake d'aukar shi da ita yana waigen su Amar ranshi a bace. Alhj yaja hannayen su ya nufi motar shi inda driver yariga ya shiga yana jiran su. zuciyar shi cike da mamakin karamin yaro Mubarak amma hjy Ummu ta bata shi da kin mutane, su basa son kowa sai kan su. ya jinjina kai a zuciyar shi yace Allah ya kyauta. *Yar'mutan Arkilla*✍ [11/26/2017, 6:48 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *18* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Nasmatu Muhammad (Yar'mutan Arkilla)✍ FOLLOWING US AS: ---- Like us page. Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION ---- Check us blogger. Zamaniwriters.blogspot.com ---- Email us your comment and reports. Zamaniwritersassociation@gmail.com ---- (Ali ishor supermarket) can ya shiga da su wurinda kasaitattun mutane ke baje kolin siyayyar kayan su dana yaran su, nan ne ya basu dama ta su zabi duk abinda suke da bukata yana biye dasu a baya yaran suna matukar burge shi. musamman Feena wadda yake kallon ta kamar wadda ya taba sani a fuska. Ya lura kusan basu san komai ba a wurin saboda haka kyale su da siyayyar bata lokaci ne, da kan sa ya shiga zabar musu kayan sakawa iri-iri kayan wasanni da na amfanin su kamar su brush, macline da dai sauran su. Sai da ya kammala had'a nasu kakkaf sannan ya shiga had'owa batacciyar yar'su nata. Hakan kuwa abu ne da yariga ya zame musu al'ada dashi da Yusra duk lokacin da suka ga wani abu na wasan yara daya burge su sai sun saya mata, a d'akin ta suke tara kayan duk tsawon shekarun nan ya gama jibga kayan suka je gurin biyan kud'in, inda makudan kud'in da ya cire ya bayar suka kusa tsorata Amar da Safeenah daga nan da aka saka musu kayan a mota basu tsaya ko ina ba sai gurin wasan yara wannan Umarnin Alhj ne. Ya fito da yaran suka shiga ciki, driver kuwa ya gyara parking a inda zai jira fitowar su. Babban gurin wasa ne kuma sananne a garin Kano gurin ya kasance kayatacce inda aka tanadi kayan wasar yara iri dabam-daban, nan fa yara suka fara sakewa tun suna d'ari-d'ari da Alhjn har suka saki jikin su sunata wasanni yana taya su sosai yayi amfani da hikima wajen jan su a jiki domin yana so ya riki yaran ne kamar yadda matar sa tace, yana so ya zame musu Uba makusanci mai kula dasu mai yawan fara'a da walwala gare su. Sun manta da komai sai wasanni suke Alhjn yana bin su kamar zai kama su, su kuwa suna zillewa haka sukayi ta shiga cikin kyawawan fulawoyo masu ado na jajayen furanni ma'abota faranta rai na yara da na manya. Ba iya yaran kad'ai ba hatta Alhjn kanshi yau yana cikin farin ciki wanda ya dad'e bai ji irin sa ba. ya yarda da tunanin zuciyar shi na cewa "hakika yaran nan alkhairi ne a gare su, da shi da matar sa". domin ko ba komai zasu rage musu damuwa da bakin ciki na zama shiru babu yara. zasu rage musu kewar baby dake jefa zukatan su cikin tawaya da kunci. basu suka koma gida ba sai misalin sha biyu na rana yara da Alhj suka fito sunata dariya. abin yabawa ma'aikatan gidan dake zaune a farfajiyar gidan mamaki suka bisu da kallo zukatan su cike da mamakin wannan canjin na uban gidan su. Har zuwa lokacin Yusra bata tashi bacci ba koda suka shiga gidan yayi shiru ba motsin kowa kasancewar Hjy Ummu ta fita aiki, Mubarak ya tafi School ga kuma Mamyn su na bacci. Sai Laure da Aysha yaran da zasu cigaba da kula da Amar da Feena suna ta goge-goge a sababbin d'akunan da aka basu dan zama da yaran, su Alhj ya kira ya hannunta musu duka siyayyar yaran yace su had'a kayan kowanne a kaishi mazaunin sa sannan su yiwa yaran wanka kafin ya fito yana gama basu Umarnin hakan ya wuce yana yiwa yaran murmushi suma abinda suka bishi da shi kenan zukatan su fari kal sunajin kan su kamar ba a duniya suke ba Aysha ta kama hannun Feena tana cewa "ni zan rika kula dake daga yau, ya sunan ki?" "Safeenah" ta bata amsa Laure ta kalli Amar "kaifa fine boy?" Yace "suna na Amar"kowacce ta kama hannun d'aya suka nufi d'akunan su masu had'e da falo d'aya amma d'akunan daban-daban ne kofofin su suna kallon juna suka shiga dasu a falon suka tsaya suka rarraba kayan Aysha ta kwashe na Feena Laure kuma ta d'auki na Amar suka shige d'akunan kowa da nashi Amar da Feena basu fahimci komai a lokacin ba a zaton su dan za'ayi musu wanka ne yasa aka shiga dasu gurare dabam-daban bayan anyowa Feena wanka Aysha ta shafe mata jikin ta da mayukan jiki masu kyau da santsi tayi mata make-up dai-dai iyawar ta bayan ta taje mata lallausan gashin ta ta tufke mata shi da band mai kauri. doguwar riga ta saka mata baka mai dogayen hannu rigar ta shiga da yanayin jikin yarinyar sosai, tayi kyau kamar yar'tsana a cikin kayan da suka zo da su Aysha ta d'auko mata cocolet babba ta bata Feenah tace "ba wannan nake so ba" Aysha yace "to wanne kike so kanwata?" da sauri ta kalle ta "kiyi hakuri kar ki koma kirana da wannan sunan" Aysha ta kalle ta da mamaki "me yasa Safeena?" ta d'an bata rai "saboda yayana kad'ai yake kirana da hakan, kuma nafi jin dad'in shi a bakin shi karki koma fad'a nidai ki ce min Feena kinji yaya" Aysha tayi murmushi domin yadda yarinyar take magana cike da yaranta tace "to nima kar ki koma cemin yaya" "meyasa" Feena ta tambaye ta tana kallon fuskar ta "saboda yayi kama da wanda kike gayawa yayan ki" ta karadhe tana dariya Feena tace "to mezan ce miki?" "Anty" aysha ta fad'a tana shafa kan yarinyar mai wayau da saurin shiga rai. "to yanzu gaya min me ki ke so Feena?". tace "wannan mai sanyin na cikin ko'ko kuma hadda kankara gareshi, ni sunan shi ne ban sani ba". Aysha tayi dariya sosai kafin tace "na gane, inaga ice-cream kike so, zo mu tafi". ta kama hannun ta suka fita a falo sukayi kicibis da Laure ta fito da Amar cikin shirin wasu kayan kanti masu kama da jamfa sun masa cif-cif dai-dai jikin sa *Yar'mutan arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *19* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Na Nasmatu Muhammad (Yar'mutan Arkilla)✍ FOLLOWING US AS: ---- Like us page. Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION ---- Check us blogger. Zamaniwriters.blogspot.com ---- Email us your comment and reports. Zamaniwritersassociation@gmail.com ---- *Soyayya rayuwa ce, mutane kuma rahma ne, kauna Abu ce mai muhimmanci da tsayuwa a rai. Samun wayannan abubuwa a had'e kuwa sai mai tsananin rabo da kyakkyawar sa'a 😊, Oh! Allah gaskiya ni mai mutukar sa'a ce domin na had'a duka wad'annan abubuwa daga gareku masoya na😍* *ina da mutane ga so da kauna da suke nuna min a bayyane kuma a aikace, INA yin Ku sosai masoya nah!*😍😘 Yana ganinta ya sake mata murmushi itama ta mayar mishi suka karasa inda suke tsaye ya kama kumatun ta "kinyi kyau kanwata". dad'i sosai taji a ranta kafin itama tayi tsalle ta lakuto hancin sa "kayi kyau sosai yayana". Yace "to naji amma ai bankai Feena ba". Su Aysha suka yi murmshi tace "to kizo muje in baki abunda kika ce, ko kin fasa?". "a'a ban fasa ba, yaya zo muje musha wannan abin da Abba ya siyo mana". Ba musu yabi ta inda taja hannun shi suka nufi falo Aysha da Laure na bin su abaya , yaran suna birge su. Acan suka baje bisa capet kowannen su rike da robar ice-cream yana sha. Sunayi sana taba kallon TV wanda yake bakon al'amari a gare su kasancewar kaf kauyen su basu taba ganin irin shi ko mai kama da shi ba. A hakan momyn A haka Hjy Yusra ta fito ta same su, itama dai ta canza shiga tayi wanka ta caba ado naji da fad'a sai tashin kamshi take suna ganin ta suka fara fara'a musamman Feena da ta mike ta taro momyn tana fad'in "momy kinga muma an mana wani wankan hadda kaya aka sauya mana". Yusra tayi murmushi tace "gud hakan yayi kyau baby nah, kinyi kyau kuwa". Feena ta saki murmushi lokacin da Yusra ta ja hannun ta suka zauna kan kujera d'aya tace "momy to baki ce yaya yayi kyau ba". Yusra tayi dariya lokacin datake kallon Amar tace "ni na isa? Kayi matukar kyau yayan Feena nah". Amar ma murmushi yayi kafin yace komai Feena ta karbe da "kema fa kinyi kyau momy nah". Yusra ta zubawa yarinyar ido ganin yadda murmushin ta da yanayin maganar ta sak kamar na wata da ta sani sosai ta sakawa zuciyar ta kaimi wajen tunani da son gano shin da wacce fuska ce Feena take mata kama? Tabbas tana kama da wata da ta sani to amma wacece? Muryar Abba taji a gefenta yana fad'in "Yusra wannan kallon haka karki cinye min kyawun yarinya". firgigi ta dawo daga nisan tunanin da tayi ta maida kallon ta gareshi wanda taga ashema har ya zauna a kusa da ita amma ita sam bata san da zuwan shi ba tayi murmushi "Habibi ai yar'taka ne tayi kyau yau, a ina suka sami sababbin kaya?". Amar dake makake a gefen Dady yayi karaf yace "ai Abba ne ya siyo mana masu yawa ne ni da kanwata, kuma harda gun wasanni muka je". Sosai Yusra taji dad'in lamarin ta maida kallonta ga mijin nata tace "oh my Habibi gaskiya bansan taya zan gode maka ba, ina sonka da yawa Alhjna". Abban yayi dariya mai sauti "nima haka matata farin cikina, ki sani indai har hakan zai faranta miki rai to zan cigaba da rikon su Amar tamkar ya'yan da na haifa da cikina". "ina godiya Allah ya saka maka da alkhairi miji na". Ya mayar mata da martanin murmushin da tayi mishi kafin yace "to ku tashi muje muci abinci ko". Tace "yadda kace". Cikin salo da kashe ido tayi maganar ya faki idanun yara dasuke can suna badali da ice-cream ya manna mata kissa a gefen farar fuskar ta sannan ya mike ya kama hannun Amar itama mikewar tayi taja hannun Feena suka nufi danning aria, a dai-dai tsakiyar falon sukayi kicibis da Hjy Ummu dawowar ta kenan daga aiki. Turus tayi ganin sabon al'amari a gidan nasu. Hjy Yusra da Alhj kam sam basu lura da yadda ta d'auki abin ba suka tare ta da murmushi as usual "sannu da dawowa aunty". Yusra ta fad'a tana kallon Hjy Ummu bata amsa mata ba saima wani wulakantaccen kallo da tabita da shi daga ita har Alhjn, amma me gabanta ne yayi mummunar fad'uwa lokacinda idonta suka sauka kan yarinya Feena take taji tsoro da wata irin fargaba sun mamaye zuciyar ta a ranta kuwa tambaya take wacce ce wannan mai kama da Yusra? Domin ita kam da kallo d'aya ta hango yawan kamanni da yarinyar take yi da Yusra *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *20* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ FOLLOWING US AS: ---- Like us page. Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION ---- Check us blogger. Zamaniwriters.blogspot.com ---- Email us your comment and reports. Zamaniwritersassociation@gmail.com ---- *Rayuwar makaranta dad'i banison tuna baya 😰 , never ever forget you guys. (Asiya Isah & Sumayya Isah) har yau ana tare* 🤝😘 Cikin matsanancin tashin hankali ta zaburi gabban jikin ta, a sukwane ta isa bangarenta. Mijin da matar harma da yaran suka bita da kallo sai dai kowa da abinda yake sakawa aransa domin kuwa yaran kallon mamaki suke mata had'eda tsoro su kuwa iyayen ko ajikin su domin kuwa inda sabo ya isa su saba da irin halayyarta. Suka girgiza kai suka wuce danning abinsu. Tashin hankalin Hjy Ummu sai kara ninkuwa yake, mayafinta kawai ta jefar akan gadon ta ajiye jakar hannun ta tashiga warwareta domin fiddo wayar ta. Tana cirowa ta saka kiran wata number data lalubo a makance. Takuwa ci sa'ar samun number dukda a tsorace da hakan takira domin Eysha bahaguwar yar'bariki ce bata cika barin waya a kunne ba. Ringing biyu ana uku aka d'aga da "hello, uwargida agidan wakkala kinci naki kinci na dangi, Ummu kinci dubu sai ceto, yau kin tuna da tsohuwar kawarki?". Tayi tambayar da yanayin wasa domin kuwa ta dad'e rabonda taji wayar Ummun indai ba ita takirata dakanta domin su gaisaba. Babu wasa ko sonjin wani dogon surutu a tattare da ita yau, hakan yasa ta takawa Eysha birki, cikin wani yanayi na tsoro ta fara maganar da murya kasa-kasa wadda ta tabbatar ko a d'akin mutum yake bazai tabajin metake cewa ba. "Eysha, magana nake so muyi dake, akan wnnan aikin da kikamin a shekarun baya na yar'gidan nan". Wani irin dumm! Eysha taji tamkar anbuga guduma a kirjin ta domin tsawon rayuwarta duk da zinace-zinacen da take bata taba jin nauyi da bakin cikin suba kamar yadda take jin na wannan mummunan aikin data aikata ba, tun bayanda ta aikata abin yazo yayi sanadiyyar rayukan tsofaffi guda biyu iyayen Alhj, takuma jefa Alhj da Hjy Yusra cikin mawutacin hali sai ta tsinci kanta dajin haushin kanta, na biyewa Ummu su aikata wannan mummunan laifin abinda koda wasa ba aikin mutum bane domin kuwa raba d'a da Uwa sai Allah. Ayanzu Eysha tayi matukar nadama akan abinda ta aikata. Shirun da Hajyn taji ne yasa ta sakeyin magana "Eysha kina jina kuwa?". "ina jinki hjy menene" Eysha ta fad'a tareda danne takaicin ta da takeji. "dama tambayar ki zanyi kawata, wai dan Allah kin kuwa kashe yarinyar nan kamar yadda mukayi alkawari dake?". Sai taji tambayar a wani bambarakwai takaici da tsanar halin bakar kawar tata suka sake cikata amma saita danne ta wayance da fad'in "wannan kuma wace irin Tambaya ce Ummu?". Tayi maganar cikin bacin rai alamar antabo ta. Shiru ne ya ratsa daga kowanne bangare wani tunani ne ya zowa hjy Ummu wanda yasa tai Allah wadai da saurin bakin da tayi nayiwa Aminiyarta wannan tambayar, amma dayake an dad'e a bariki sai ta wayance da fad'in "kiyi hakuri kawata, na kwanta baccin rana ne nayi mafarki da yarinyar shiyasaka duk na tsorata". "na fahimce ki amma karki koma tunkarata da irin wannan banzan tambayar, nice fa Eysha saikace baki san waye ni ba". "Afwan kawata abar maganar, y kike?". Eysha tayi hanzarin katse wayar domin ta kara gamsar da kawarta cewa ta bata mata rai da wannan tambayar tata. Hjy Ummu ta kalli wayar ta sauke numfashi tace "fushinki ai mai sauki ne nasan 200k zasu hutar dake, amma kasancewar yarinyar nan a raye zai iya sawa na rasa rayuwata". A wurin tayiwa Eysha transfer na (200,000) sannan ta ajiye wayar ta fad'a bayi zuciyar ta na kara bata tabbaci akan tunanin da yazo mata daga baya, wato wad'an nan yaran dai ya'yan d'an'uwantan nan ne na saudiya (yayan hjy Yusra take nufi) tasan bazai wuce hutu aka kawo suba, Domin kuwa babu yadda za'ayi Alhj yaga batacciyar yar'shi ta bayyana sannan farin cikin sa ya tsaya iya haka inaaaaa, ai da ace hakan d'inne da tuni gidan yagama cika da batsewa da mutane domin bazasu iya boye farin cikin su ba. Wanka tayo ta fito cikin kankanin lokaci tagama shirin ta cikin wata arabian gown ta feshe jikinta da turaruka ta nufi falon domin kara samun tabbacin daga ina yaran suka zo, kuma su waye su? *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *21* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* *Alhamdulillah hakika Allah shine abin godiya, kusha sha'anin Ku ZAMANAWA lokacin kune Yan baiwa, tauraruwar Ku na haskawa nikuwa Nasmat burina ya cika, ⭐⭐⭐⭐⭐ a yau kune Shining stars a online writers. Ya Allah Kaine maiyi kuma Kaine mai isarwa ya Allah ka kara d'aukaka ZAMANI WRITERS* 🙏 _______________________________ Da murmuhin ta ta isa gare su, sam basuyi mamakin hakan ba domin sanin da qukayi mata na tsayin shekaru haka take yanzu-yanzu ne ta sauya. tayi sallama suka amsa, ta zauna kan kujerar dake kusada ta alhjn a gefen hagu. Amar da Feena kam mikewa sukayi domin suna jin tsoron hjyr, dama sun gama cin abinci hira kawai sukeyi da sababbin iyayen nasu.. Ya kama hannun kanwar sa suka koma tsakiyar falon hjy Ummu ta bisu da kallo ta kasan ido, ganin yadda gashin kab yarinyar yayi tsayi har wucu tsakar bayanta ya kara tabbatarwa hjy Ummu tabbas wad'annan irin sai dai larabawan. A hankali ta kalli Yusra "me aka girka yau?". Cikin sakin fuska ta amsa mata "priderice ce sai farfesun kifi dana kayan ciki, akwai had'in fruitsalad" tayi murmushi irin na naji d'in nan, saka min duka dai-dai ciki na". Tayi murmushi ta mike tayi seaving hjyr kamar yadda ta bukata Alhj dai baice komai ba sai ido dayake bin su dashi, a zuciyar shi ko yana yaba kyawun rayuwa da halayyar Yusra, da ace ba haka take ba da gidan shi ya zama dandamalin masifa, domin ya lura wasu abubuwan dagangan Ummu take mata su domin neman taki yi, a tashi hankalin gida. ta fara cin abincin cikin d'asashi da yanga abin ya bashi dariya "Uwargida ran gida, hjy Ummu kina sha'anin ki wlh". Yayi maganar yana murmushi dama neman hanyar magana take "Uhum to me kuma Ummu tayi?". "a'a ni na isa infad'i laifin manya?". Alhjn yafad'a cikin dariya "Hmmm ana min abubuwa a gidan nan idan nayi magana kuma ace Ummu ta cika mita, idan nayi shiru kuma ace na nuna halin ko in kula". Ya komayi murmushi a karo na biyu "tofa yau kuma me akayiwa sarautar mata?". Ta yatsina fuska "sarauta dai, uhum". Sai kuma tayi shiru "to ko ba haka bane?". "Alhj kenan, abufa ake yi amma sam ni ban cancanci a gayamin ba, yanzu sabida Allah yara fa na gani a gidan, amma a cikin ku ba wanda ya gayamin su waye, balle insan daga ina suke, idan nayi magana kuma kai da kanka zakace na cika magana". Alhjn yai murmushi yace "to ai jiya suka iso kekuma kina busy da ayyukan ki, ni yaushe ma naga fuskar ki dazan tsaya yimiki wani bayanin?". Ya fad'a cike da tsokana murmushi kawai tayi Alhjn ya d'ora da cewa "yaran Yusra ne, nan zasu cigaba da zama da mu insha Allahu". Wani irin dukan kirji taji, dukda zuwa yanzu ta tabbatar yaran yan'uwan Yusra ne aka kawo mata daga kasar su, amma miye na wani anan zasu zauna? Ta tambaya a zuciyar ta. A fili kuma tace "Oho dama nikam naga kama domin da gani d'aya za'a gano irin larabawan ne". Yusra da tunda suka fara maganar batace komaiba tayi murmushin jin dad'in yabon da tayiwa yaran nata. Alhjn ma murmushi yayi ya mike yana fad'in "nizan fita daga can zan lalubo musu malamin lesson su fara d'aukar darasi kafin asaka su a makarantar". Wani haushi ya koma tirnike hjy Ummu. Yusra kuwa dad'ine ya lullubeta tashiga yiwa mijin nata addu'a da fatan Alkhairi har yabar falon hjy Ummun bata koma cewa komai ba . *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *22* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Mike tayi cikin bacin rai ta ture kujerar da take kai ta nufi d'akin ta. Yusra ta bita da kallon mamaki kamar ba ita ake taba hira da ita yanzu ba. Kai kawai ta girgiza tare da cewa "Allah ya baki lfy" Itana dai mikewar tayi ta koma tsakiyar falo inda yaran suke suna wasa da sababbin kayan wasar da Dady ya siyo musu. ta zauna a cikin su sukaci gaba da wasar tare tanajin dad'i sosai yadda yaran suka saki jiki da ita bama kamar Feena ba wadda kallonta kad'ai saita jefata cikin farin ciki haka kuma wani lokacin har mamaki take wane irin so ne Amar yake yiwa kanwarsa Feena, sau tari idan da manya aguri yaran sukayi abu sai sun basu mamaki domin irin kulawar uwa da uba yake bata Sam bai had'a Feena da komai ba yana sonta kamar rayuwar sa zahiri da bad'inin shi. hakan na kara sakawa hjy Yusra soyayyar yaran ji take dama ya'yanta ne su, da tayi farin ciki da irin son da sukewa junan su. Haka itana Safeenar bata kaunar tayi wani abu da zai batawa yayan nata rai basa rabuwa ko kad'an inba lokacin bacci yayi ba. Nan ma dakyar da fama suka Saba kwana daban-daban, tare suke cin abici a plat d'aya da spon d'aya wani lokacin ma sai dai yabata a baki ko kuma ta bashi. yaran suna burge kowa. Yau ta kama laraba ranar da Amar da Safeena suka cika sati d'aya a gidan sun saba da yanayin gidan da mutanen cikin sa sun gama gane halayyar kowa. Kuma suna taka tsan-tsan da abinda zai had'asu da kowa a gidan musamman hjy Ummu wadda suke kira da mama, dakuma yaron ta Mubarak wad'anda suka lura har nema suke su musu laifi su hayyako musu da masifa. Tsakanin su da Umman su Yusra da Dady kuwa sai godiya, domin suna nuna musu so da kauna iyaka. Sati d'aya malamin lesson yayi yana koyar dasu ya gano yaran sunada ko'kari da kwazon karatu ya gayawa Dady a saka su a primary kawai. Hakan kuwa aka yi a (Iman international schools) aka saka su. Inda suke samun kulawa daga malaman makarantar sabida darajar wanda yakawo su ga kuma lesson da ake musu a gida. Ga islamiyya da suke zuwa akowane yammaci. Masha Allah rayuwar yara dai ta haska, kullum ka gansu tsab-tsab da su. motar su ta kansu aka ware musu duk inda zasu ita ake kaisu da ita farin ciki da canjin rayuwa ya bayyana karara ajikin yaran cikin sati uku kacal sai gasu sunyi kyau sun Kara haske ga wata ni'ima da Allah ya basu ta yalwar jiki dukkan su sun kara kiba sun mulmule. abin dai gwanin sha'awa sai dai ace tubarkalla yara kam sun sami gata duk yadda hjy Ummu da yaron wajenta suka kai ga son su shiga rayuwar yaran su takura musu sun gagara saboda yaran basa shiga sabgar su, haka Allah yayi su basu da kwaramniya ko kad'an Haka rayuwa ta rika tafiya satittika suna ture watanni watanni, yau Amar da Safeena watannin su uku a gidan alhaji Tijjani wakkala a yau ne kuma suka ga antashi da shirye-shiryen biki a gidan nasu sai kawata gida ake ana mishi decorations, musamman d'akin nan da tunda suka shigo gidan basu taba ganin an bad'eshi ba. (d'akin baby, batacciyar yar' hjy Yusra, kuma ya d'aya tilo ga Alhj Tijjani wakkala) d'akin yasha gyara da Kayan kawace gurare da turaruka gaba d'aya gidan ya d'auki haske da sheki ko ina ka gifta sai kaci karo da turaren wuta irin na larabawan asali kayan sakawa kuwa na musamman aka siyo wa yaran yan saiti Kala d'aya dasu da Mubarak haka iyayen suka yi ado na alfarma. a d'akin kowa ya hallara inda aka tanadi kujeru da shimgid'u na alfarma. Karfe Tara dai-dai mutanen Saudiyya suka iso Ummin hjy Yusra da Yayan ta da kuma matar yayan ta, Tareda rakiyar manyan malaman nan guda biyu kamar yadda suka saba a kowace shekara..... *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *23* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* _MARUCI MAKARANCI, HAKA MAGANAR TAKE 👌🏼 wannan shafin naka ne kai kad'ai *Autan writers, 'KING BOY ISAH'* kai d'in na daban ne kamar yanda rubutun ka ma ya bambanta, gabadai-gabadai *Autan Mu* Nasmat tana yin ka sosai da sosai😍 ka huta na waje na, ana tare matuka 🤝_ Da guda hjy Yusra ta isa ga mahaifiyar ta ta rungumeta, itama ummyn sakin jakar hannun ta tayi ta rungume Yusra yar'ta mace d'aya da Allah ya bata. Sai kuma su duka biyun suka fashe da kuka mai tsanani da tsuma zuciya, ganin Ummy ta biyewa Yusra suna ta rusar kuka yasa yayan ta ya matso gare su ya d'ago ta cikin harshen larabci yake maganar yace "kiyi hakuri kanwata Allah babu inda baya yin ikon sa, ba mamaki yarinyar nan bata mutu ba domin kuwa ni ban taba jin hakan ajikina ba" Yusra ta kankame shi lokacinda kukan ta ya kara tsanan ta itama dai da larabcin take mishi magana "a'a d'an'uwa na ni kam inaga baby bata raye, domin na tabbabar duk wayanda suka saceta ba dan kud'i suka d'auke ta ba, da tuni sunyi magana an basu kud'in" matar yayan ta ta d'agota itama dai hawayen take yi tace "yar'uwa Yusrah kiyi hakuri ki dogara ga Allah shikad'ai ya barwa kansa sani akan batan wannan yarinyar, yau tsawon shekaru takwas kenan muna had'uwa anan saboda ita ki sani addu'oin mu bazasu tafi a banzaba muddin yar'ki tana raye na tabbata Allah zai bayyana miki ita" sosai taji sanyi a ran ta da jin maganganun Raudah matar yayan ta. suna cikin wannan halin ne Alhj Tijjani ya sauko daga kan bene da alama daga d'akin sa yake. ya caba ado da wata dakakkiyar shadda bakin sa har kunne farin cikin sa na ganin sirikan sa ya kasa boyuwa. mutanen da suka d'auke shi tamkar d'an cikin su. da hanzari ya karaso garesu ya zube kasa yana kwasar gaisuwa gaban Ummy. farar dattijuwar tasa hannayen ta ta d'aga shi ta mikar dashi tsaye suka gaisa cikin girmamawa da mutinta juna sannan daga bisani ya juya ya gaisa da shaihunan malaman da suka zo daga Saudia wad'anda duk shekara sai sun zo a irin wannan ranar domin yin addu'oi ga batacciyar yar'su Baby. A taice dai yau ne ranar da suke bikin zagayowar shekarar haihuwar ta wanda suke yi a kowace shekara. sannan a bangare d'aya a yi saukar alkur'ani da yanka tareda karanto manyan addu'oi akan idan tana raye Allah ya bayyana musu ita ya dawo musu da yar'su cikin salama, in kuwa ta rigamu gidan gaskiya to Allah ya jikanta da rahmar sa yakuma bawa iyayen ta hakurin jure rashinta in da rabon wata haihuwar a gaba Allah ya basu wasu masu albarka. to yau ma dai kamar kowanne lokaci masaukin su aka fara kai su suka huta sannan aka gabatar musu da abinci da abin sha na musamman da aka tanada domin su. Sukaci, suka sha Sannan sukayi wanka kowannen su ya sauya kaya sannan ne dukan su suka d'unguma zuwa d'akin Baby, inda suka tarar an gama tsara komai kamar dai yadda aka saba. Duk wannan hidindimu da hayaniyar da ake hjy Ummu ko lekowa batayi ba, tana can d'akinta tai d'ai-d'ai akan gadon ta tana murmushi a ranta cewa take "hakika iska na wahalar da mai kayan kara, wlh ita kam baza'ayi wannan wahalar da ita ba ta gaji da yiwa matacciya hidima" hatta zuwan su Ummy duk a kunnen ta kawai kin tasowa tayi. Daga karshe ma tashi tayi ta yi wanka ta shirya cikin shirinta na suwa offices ta fice bayan ta tura Mubarak makaranta. da shigar su d'akin suka fara cin karo da manya-manyan hotunan Baby na jarantaka da aka manna ajikin kowane bango dake d'akin sai tarin kayan wasan ta a gefe d'aya, ga kuma rafkeken gadon ta na jarirai flowers kota ina turarukan wuta kuwa tamkar ana gasar fitar da kamshi ne. gefe d'aya kuma wani irin katon cake ne wanda ya kusa tsayin mutum ajikin shi an rubuta da manyan haruffa 'HAPPY BIRTHDAY BABY' wani sabon kukan ne ya subucewa Ummy mahaifiyar hjy Yusra, ta fungume yar ta'ta ta fara rera kukan Yusra ma kukan take kai kowa a d'akin saida ya koka, hatta malaman sai da suka zubda hawaye domin tausayin wayannan iyalan da sukaji. Alhj Tijjani sai sharar kwalla yake yana rarrashin matar shi cake d'in aka fara nufa domin dama haka suke yi sai anyi murnar hauhuwarta sannan daga bisani a rufe da saukar alkur'ani da addu'oi gabad'ayan su suka zagaye Birthday cake d'in wanda akowace shekara hjy Yusra ce mai yanka shi. harta hure wutar tana shirin yankawa lokaci guda ta tuna da Safeenah sabuwar yar'ta wadda ta ajiye a gurbin baby, sai ta tsaya cak tana kallon mijin nata wanda ya zuba mata ido cikin tausayawa. "ina Feenah?". Ta tambaye shi cikin rawar murya da sheshshekar kuka. shi kan shi sai a lokacin ya tuna da yaran da hanzari ya nufi kofar da zummar fita sai dai kafin yakai ga fitar aka turo kofa dukkan su sai suka maida hankalin su ga kofar dan ganin mai shigowa. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *24* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Safeenah ce da Amar suna rike da hannun juna cikin wata irin shiga ta alfarma doguwar riga ce a jikin ta fara kal kamar dai irin weading gown d'inan amma karama dai-dai jikin ta kanta yasha gyara an tufke gashin waje d'aya tareda d'aure mata shi da white band babba hatta sarka da yan kunnen ta farare ne haka takalmin kafar ta ma yarin ya dai ta fito tamkar yar gold sai kyalli da walwali sirrin kyawunta ya kara bayyana haka shima Amar suite ne farare kal ajikin sa wanda aka siyo mishi iri d'aya dashi da mubarak. kayan sun zauna d'as a jikin sa kamar dan shi aka yi su, rigar cikin su ja ce haka neck d'in da wuyan hannun shi ma duka ja ne takalmin kafar shi ma jajaye ne. Sai zuba kamshi suke gaba d'aya mutanen dake d'akin suka zubawa yaran ido domin kasancewar su bakin fuska a gare su. Ummy kuwa kallon sani take yiwa Safeenah, inda zuciyar ta ta shiga dukan ukuk-uku kwakwalwar ta na son tunano wani abu gameda yarinyar amma ta gagara sai dai kam ba makawa yarinyar tayi mata kama da yar'ta Yusra, ganin Alhj ya tsuguna ya rungumi yaran yasa sukayi tunanin ko yaran dangin sa ne. shi kanshi alhj baisan lokacin da yayi hakan d'in ba, kawai ganin Feenah yayi tamkar wata flower abar so, ya kuwa rungumeta na tsayin lokaci ji yake ina ma ace yar sa ce baby ta girma haka kuma ake shagalin Birthday d'inta da ita. Ganin bashida niyyar sakin ta yasa Yusra ta karaso gare su ta kama hannun Amar da Feena taja su zuwa inda Birthday cake d'in yake ta bawa Feenah wukar tana fad'in "na manta da na sami sabuwar yarinya, daga yanzu zuwa kowane lokaci Safeenah ita zata rika wakiltar baby" da harshen larabci tayi maganar wanda yanzu Alh Tijjani ma yanaji sosai da mamaki Ummy ta kalleta "wacce ce wannan?" Tai murmushi "zanyi muku bayani daga baya" safeena kam tsaye tayi da wukar a hannu tana karewa wad'annan fararen mutanen kallo kasancewar su baki a gareta haka Amar ma Yusra da kanta ta kama hannun Feena ta danna wukar a cake d'in gaba d'aya suka d'auka _"Happy Birthday to you, happy Birthday baby!_" nan ne Raudah matar yayan Yusra tayita d'aukar su hotuna da phone d'inta haka dai aka yi murnar harma da su jijjiga lemuna ana watsawa sama aka gama aka dawo kan shimfid'u inda aka tanadi Alkur'ani irin na d'ibar nan mai peces Yusra ta kira Aysha mai kula da Feena tace ta tafi da yaran ciki. Taja su suka tafi suko suka fara karatu dukkan su kowa ya d'ibi dai-dai gwargwadon iyawar shi. Feena da Amar dai bin Aysha kawai sukayi amma zukatan su basu so barin guri ba, duk da cewa basusan bikin wa akeyi ba. Haka a d'akin ma suka saka su Aysha gaba da tambayoyi wai bikin wa ake? Dayake Aysha mai saukin kai ce ita ce ta basu labari tun daga haihuwar baby yar' Yusra har zuwa bacewarta da kuma shekarun da aka d'auka ana gudanar da wannan bikin shekaru takwas kenan. Dukda kasancewar su kananun yara hakan bai hanasu nuna tausayawar su ga Uwar rainon su Yusra ba. Safeena hadda kwalla. Wunin ranar kacokam a d'akin baby suka yishi dasu da bakin nasu, saidai ayi salla a koma aiki (wato karatun Alkur'ani) duk da cewa suna yi da gaske ne amma sai wuraren karfe goma sha biyun dare sannan suka isar nan kowannan su ya mike suka fara jera nafilfili na tsawon awa d'aya misalin karfe d'ayan dare suka tsayar da sallar sannan suka hau karanto manya-manyan addu'oi suka shiga rokon Allah ya kyawawan sunayen sa tsarkaka akan ya bayyana musu wannan yarinyar indai tana raye Allah ya dawo da ita ga mahimaifiyar ta, inko bata raye Allah yai rahma ga ruhin ta kuma ya bawa iyayenta hakuri da juriyar rashin ta. in suna da sauran rabon haihuwa Allah ya basu wasu masu albarka. Haka suka ci daren kaf acikin su ba wanda ya rintsa har sukayi sallar asuba sannan ne aka fiddo tarkacen kayan abinci da ragowar cake d'innan aka tsabtace d'akin kamar ba cikin sa akayi shagalin ba. sannan suka rufo d'akin. baki suka koma masaukin su,Yusra da Alh kuwa suka koma d'akunan su. Duk wannan abin da akeyi zuciyar Ummy ta kasa nutsuwa, sai kai'kawo take akan yarinyar data gani Safeenah Allah-Allah take gari ya waye taji Shin wacce ce wannan Yarinyar mai d'iban kamannin yar'ta Yusra, me kuma yasa suka bata matsayin jikar ta?. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:53 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *25* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* *Ba anan ta tsaya ba, Ku ɗin wani sashe ne na rayuwar Nasmat.* 1, *Queen haucy* 2, *Beauty Queen* 3, *Queen Yar'mama* *Those are the triple QUEENS of ZAMANI WRITERS* love all😍😘 Bacci ne mai nauyi ya ɗauke dukkan su, basu suka farka ba sai karfe goma. Nan ma hayaniyar yara ce ta taso su. Rigima ce ta shiga tsakanin Mubarak na wajen hjy Ummu da Safeena karo na farko da suka fara faɗa tun zuwan su gidan, duk da cewa yana shiga sabgar su su ɗin ne dai basa biye mishi. Yanzun ma bazata iya hakura bane. Domin yar'babyn ta ce ya kwace, ita kuma yadda take son ta bazata iya bar masa ba. Sai ta saka kuka shikuwa Amar yana zuwa ya kwace mata abarta ya mayar mata, nan ne fa Mabarak ya nemi yayi faɗa da Amar ɗin dama shi yake nema, shi ya fara kai masa duka shi kuwa ya rama karfi ba ɗaya ba sai ga Mubarak ya hangame baki yana kuka. Kusan tare suka iso da hjy Ummu wadda ta fito a hassle jin kukan Mubarak data yi, turus tayi ganin duka iyayen sun sauko kuma ta gane faɗa yaran suke yi Amar da Mubarak shiya sai shi kuka. Salati ta fara yi tana rafka hannaye "me zan gani a gidan nan?, ai wlh baku isa ba kuzo ku sami yaro a gida sannan ku takura shi?, ina ai baza ba sa6u ba wlh" ta isa gun ta rika hannun Mubarak "wanene ne ya dake ka eye?". cikin kukan da shagwa6a ya nuna Amar da yatsan sa. Ai kuwa bata jira komai ba ta nufi inda Amar yake da nufin ta dake shi. Hjy Yusra da Alh dake gefe tsaye mamaki ya cika su Lallai son kai irin na Ummu ya buwaya, haka kurum ba tambayar ba'asi ba komai sai ka yanke hukunci a faɗan yara?. Abu kaɗan ya rage ta isa ga Amar d'in, Alh ya dakatar da ita da cewa "kar ki kusakura ki ta6a yaron nan Ummu". wani mugun kallo ta wurgawa Alhjn "kamar ya kar na ta6a shi, shugaban rashin adalci?". Tayi maganar tana kallon inda yake. Bai damu da kallo da kuma maganar da tayi mishi ba. Ya share ta, ya kalli Amar yace kai mene ne ya had'a ku?". Amar ya koro masa bayanin abinda ya faru duka. Ya juya ga Mubarak yace "Abinda ya faɗa gaskiya ne?". ba kunya yace "eh" Alh ya kalli Ummu dake tsaye tana cin ranta yace "to kin ji dai sarkin fushi, Mubarak shine yafara bugun Amar, kuma shine mara gaskiya sai ki kiyaye gaba kirika bincike kafin ki yanke hukunci". bai jira me zata ce ba ya kama hannun Amar da Feena Yusra ta rufa musu baya suka koma sahen su. Haka suka bar hjy Ummu tana ta bambami. Alh ya yiwa yaran nasiha akan su daina faɗa su ɗauki Mubarak tamkar ɗan'uwan su. Suka amsa da "to Abba". "good Allah muku Albarka". Nan suka bar su falon su kuma suka koma ɗaki domin shiryowa su fito kasancewar tashin su kenan. Ba jimawa suka fito tsaf-tsaf dasu suka ja yaran duka suka tafi gaisa baki ɗakin Ummyn ta suka fara. Bayan sunyi nocking aka basu iznin shiga suka shiga da sallama, a lokacin Ummy na zaune a kan sallaya tana jan carbi, suka shiga har kasa suka rusuna suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a sa sakin fuska. Idon ta akan yaran ta kasa jurewa sam bazata iya danne abinda take ji gameda yarinyar ba tace da harshen larabci "Yusra wannan yaran fa, yaran waye?". Yusra tayi murmushi batare da bata lokaci ba ta kwashe duk yadda ta sami yaran ta gayawa Ummyn ta. Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar Ummy, ta cika da al'ajabi Ummy sam ta kasa 6oye abinda ke ranta tace "ikon Allah kenan idan aka gan su kamar ya'yan ku, musamman wannan yarinyar dan wlh har kamanni take yi dake Yusra". Maganar ta Ummy ta fama wa Yusra wani tabo dake kan kirjinta ta kuwa kafe Safeenah da ido ko kiftawa batayi "tabbas abinda Ummy ta faɗa gaskiya ne, domin kuwa ta daɗe tana kallon yarinyar na mata kama da wata fuska amma sai yau ta fahimta. Ashe da ita Feena take kama..." *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:53 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *26* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* A cikin farin ciki nake sadaukar da wannan kawataccen shafin gareka *80k*, domin ka cancanta saboda ɗinbin ko'kari da ɗawainiyar ka garemu *ZAMANI WRITERS* basa raina alkhairi. Allah ya bar tare. muna godiya irin sosai da sosai ɗin nan. 🤝 "ikon Allah kenan" cewar Alh dan yanzu ya tabbatar hakan ɗin ne tabbas suna da kama da yarinyar. A ranshi yace ba mamaki kamannin ta da matar tashi ne yasa yake matukar son yarinyar Lura da yayi matar shi ta shiga wani hali na zuzurfan tunani ne yasa ya ɗan girgiza ta tareda ambaton sunan ta a hankali "Yusra" cikin nutsuwa ta juyo da fararen idin ta gareshi waɗanda hawaye suka soma fitowa daga cikin su. "pls Yusra dont" ya kara faɗa cikin raunin murya da tausayi domin ya hango tunanin ta da inda ta dosa. yasan tunani take akan yar'su Baby tanaji a ranta dama itace wannan. Ummy ma dai jurewa ne kawai take domin ita ɗin ma ji take inama jikar ta ce wannan saboda haka ne ta kasa furta komai Alh ya mike yana cewa Ummy a huta lfy zai fita. Murmushin yake ta masa tareda addu'ar Allah kare ya fice Yusra ma ta bishi a baya da sauri yaran suka mike dan bin Momyn su wajan rakiyar Abba amma sai Feena taji an riko mata hannu Dasauri ta juyo idon ta ya sauka akan na Ummy data rike hannun nata duk da cewa ita yarinya ce saida taji wani sauyi a tattare da ita. Ta zubawa dattijuwar ido tana Murmushi domin wani irin son matar da taji ya shigeta a lokaci ɗaya taji tana kaunar Ummy har cikin ranta Ummy ta zaunar da ita bisa cinyar ta har yanzu Murmushin ne a fuskarta. Cikin wargazajjiyar hausarta tace "baza ku tsaya ku tayani hira ba?" Amar yace "zamu raka Abba ne, muna dawo wa. Zo mu tafi kanwata". Yayi maganar yana kama hannun ta abin mamaki sai yaga Feena ta zame hannun ta tana faɗin "a'a yaya zan taya Ummy hira kai kaje ka raka Abba". Tsananin mamaki hana Amar magana yayi domin tunda suke da Safeenah bata taba gujewa umarnin sa ba, bata taba son wani abu sabanin wanda yake so ba bai taba cewa ga abu tace a'a ba sai yau. Bai koma cewa komai ba ya juya ya fice cike da al'ajabi bai kara tsinkewa ba sai sanda yaga har yakai ga barin falon bata fito ta biyo shi ba. Feena kam sakin jikinta tayi sosai tana zubawa Ummy hira haka itama ta biye mata duk da ba gane wata hausar tata take ba, amma tana jin daɗin hira da ita jinta take har cikin ki'kon ranta sonta take ji wanda ko jikokinta ya'yan yayan Yusra bata jin son su kamar yadda take jin na yar'rikon yar'ta yarinya Feena. To tun daga wannan ranar wata irin soyayya da shakuwa ta ɗinke tsakanin Ummy da Safeenah kullum suna tare dare da rana tun abin na damun Amar har yazo shima ya saba saboda Tsananin son da yakewa farin cikin kanwarshi. Satin su biyu a Nigeria suka kimtsa suka koma kasar su zuciyar Ummy cike da kewar Safeenah sabanin sauran lokuta da idan suka zo take komawa da tausayin yar'ta Yusra. Haka Safeenah ma tasha kuka ita a dole sai dai Ummy ta tafi da ita dakyar aka riketa suka tafi da zazzabi ta wunin a ranar. Hankalin Amar yayi masifar tashi shi kan shi yasha kuka yanata rokon Momyn su akan ta bari Ummy ta tafi da su. Wasge garin ranar suka fara zuwa makaranta bayan an kammala musu komai daya dace a IMAN INTERNATIONAL SCHOOLS primary 1 aka saka Feena inda Amar ya sami 3 saboda girman shi. Ai kuwa sun fara karatu cikin nasara da sa'a sam basu sha wata wahala ba kasancewar sun jima suna ɗaukan lesson a gida. Rayuwar su gidan Alh Wakkala tamkar farin wata ne a cikin duhun dare basuda wata matsala ko damuwa iyayen na nuna musu soyayya iyaka kulawar uwa suke samu daga Hjy Yusra kamar yadda Alh Wakkala ya maye musu gurbin Uba. Haka lokuta suka cigaba da shuɗewa wasu na ture wasu suna waya da video call sosai da Ummy haka duk shekara suka ziyarci bikin birthday na Baby kamar yadda ya gabata a farko haka ya cigaba da kasancewa Safeenah ta cigaba da maye gurbin Baby a ranar birthday tun bata san me ake yiba har ta fara fahimta a ranta tana jinjinawa soyayyar da waɗannan iyayen suke yiwa batacciyar yarinyar tasu. Tana tausaya musu matuka tareda taya su addu'ar Allah ya banana musu ita a duk likacin da tayi salla bayan ta yiwa Umman ta addu'ar neman rahama kamar yadda malamin islamiyyar su ya koyar da ita. ************************************* *Bayan shekaru shida* Shagali na samu anayi sosai a gidan Alh Wakkala murnar kammala makarantar primary ta Safeenah. An kawata gidan ta kowanne fanni musamman bangaren garden ɗin gidan wanda a can aka shirya gudanar da gagarumin bikin Duk inda ka kyalla idon ka manyan mata ne kawayen Hjy Yusra cikin shiga ta alfarma itama dai ba karya ta caba ado na musamman sai hidima take da baki duk inda ta gifta haske da kyalkyalin zinarin dake sanye a wuya da hannayen ta ke walwali Komai ya gama tsaruwa su Ummy kawai ake jiran isowar su sai uwar gayyar wadda take can ana tsantsara mata kwalliya. Amar sai kaikawo yake ya rasa abin yi fitowar ta kawai yake jira domin a yau ba wanda ya kai shi farin ciki Feenanshi ta kammala primary zata zo makarantar su su cigaba da zuwa tare domin shi tuni ya bar bangaren primary yana secondary js2. Inda rayuwar can ta zame mishi tamkar dole tsawon awannin da yake batare da ita ba jin kanshi yake tamkar a ɗaɗɗaure yake Yana cikin zariyar ne ta fito cikin wata kiriyar doguwar riga wadda aka ɗinka ta da wani yadi mai shara-shara rigar tabi jikinta cif-cif ga adon stones kota ina a jikin rigar takalmin kamata ma green ne hils masu tudu sai sarka da warwaro na ɗanyen gold da aka zuba mata bakin gashin nan nata yasha gyara sai shaki da walwali yake Lokacin da ta gama fitowa farfajiyar filin yayi dai-dai da ɗago kanta fuskarta ɗauke da farin ciki mara misaltuwa "masha Allah" iyakan abinda bakina ya iya furtawa kenan saboda tsananin kyau da kwarjinin da Safeenah tayi min sai naga ma kamar sauya min ita aka yi da wata balarabiyar kyakkyawar yarinyar yar shekaru goma sha huɗu wadda makerin budurci ya fara kerawa wato duk wata sura ta ya'mace ta fara bayyana a jikin Safeenah Babu yadda za'ayi mutum ya iya yi mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa ko waye shi kuwa fans bansan yazan kwatanta muku wannan budurwar ba amma gaskiya Safeenah ta gama haɗewa Shi kanshi Amar bai taba ganin kyawun Safeenah ya bayyana kamar na yau ba. Sam ya gagara raba idon sa da kallon ta Murmushi kawai ya tsinci kansa da yi tareda tunkarar ta da hanzari cikin takunnan nasa na babban yaro. Murmushinta ta kara faɗaɗawa ta nufe shi da zummar rungume shi yayanta Amar wanda tafi so akan komai da kowa a a cikin mutanen wannan duniyar nan Abin da ya rage su haɗu kalilan ne hakan yasa Feena ta ware hannayen ta duka tareda lumshe idonta, Kyakkyawar runguma taji an yi mata tareda manna mata kiss a wuyan ta cikin wani yanayi wanda ya rungume ta ya matsi kuibinta sai a Lokacin hancinta ya bambance mata kamshin turaren Amar da na wanda taji ya rungume ta Da sauri ta buɗe kwayar idon ta tareda zuba su akan sa cikeda tsantsar mamaki *Ya Mubbarak* ta faɗa tana ko'karin raba jikinta da nashi *Afwan my fans, nasan ban kyauta ba dana tsayar da rubutu ba tareda sanar muku ba. Ku sani Nasmat batada burin batawa kowa da niyya kumin afwa hakan ya faru ne bisa wasu dalilai na sirri masoyana Kuna raina much love to you guys* 😍😘 *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/27/2017, 4:57 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *27* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Mubarak ya sake mata wani lallausan murmushi, wanda bai ta6a yi mata irinsa ba tunda Allah ya haɗa zaman su a gidan. Mamaki ya kara turnuke ta dai-dai lokacin da Amar ya karaso gaban su, su duka biyun ba wanda yayi magana sai dai kallon-kallo da suke wa junansu Mubarak yana yi mata wani kallo ne wanda ta rasa dame zata fassara shi, ita kuwa kallon mamaki da tantama take masa a ranta tana kissima abubuwanda bata tunanin kasancewarsu tsakanin ta da shi. Duk tarin farin cikin dake cike da zuciyar Amar ya kau, sai ya tsinci kanshi cikin bakin ciki da jin haushin yadda Mubarak ya rungumi kanwar tashi kodan basuda jituwa dashi-dashi ne oho. Bai jira komai ba ya kama hannun ta, ya jata zuwa wani gefe na 6angaren garden, duk wannan abin da ake yi babu wanda idonsa ya kai garesu saboda abin ya faru ne a kofar shiga main Palo na gidan, su kuwa mutanen da suka halarci bikin suna can tsakiyar gurin kowa da abinda yake yi. A kan wata kujerar roba ya zaunar da ita ba tareda yace mata komai ba, shima ya zauna yana kallon ɗaya gefen ranshi a 6ace. Kirjinta ne ya hau dukan uku-uku badan komai ba sai dan tarin 6acin rai da ta hango a cikin kwayar idon yayan nata. Lokaci mai tsawo ba wanda yayi magana a cikin su, hankalin Safeenah ya koma tashi "me ya 6ata ran Yaya Amar haka?" ta tambayi kanta Shi kuwa Amar zuciyar shi ce ta kasa nutsuwa "me wannan yake nufi?, a lokacin da Feena ta fito ta nufo shi da murmushi ya ɗauka gunshi ta nufo ashe ba shi ta nufo ba, dama akwai wata alaka ta jituwa tsakanin ta da Mubarak amma take nuna kamar ba ruwanta da shi?". Sai kuma yaji haushin ta ya kama shi ya kara kama shi, cika yayi bam kamar zai fashe, yayin da yake dukan teburin dake tsakiyar su a hankali da hannunsa daya dunkule. Feena ta kasa jurewa zafin da zuciyar ta take mata na ganin fushin yayanta, abokin tafiyar da rayuwar ta. Tafin hannunta ta ɗora akan nashi dake kan table ɗin a hankali ta kira Sunan shi, "Yaya, wai meke faruwa ne ni ban gane makaba waye ya 6ata maka rai, nima kake neman 6ata nawa bayan kasan yau Ranar farin ciki ce a garemu baki ɗaya?. Nasan ka fiye da kowa, kar kayi tunanin wani shiri ne tsakani na da Ya Mubarak, wlh ko magana baya yi min in ba ta faɗa ko hantara ba, ni kaina ina cike da maimakin abinda ya faru yanzu kuma yaya wlh na ɗauka kaina shiyasa na rike shi". Ta karashe zancen tana share hawaye domin ganin yadda ɗan'uwan nata ya ɗauki zafi. Ya yarda da Feena da kuma kalamanta, amma abinda Mubarak ya aikata ya kasa gogewa a zuciya da kuma kwayar idon shi, ganin zai rushe farin cikin da ta daɗe tana gidana ma wannan Ranar yasa ya kakaro murmushi yana faɗin "shikenan ai my Feena, ya wuce amma ki kiyaye domin Mubarak da Mamanshi mugaye ne, a koda yaushe basuda burin da ya wuce su cutar da mu, karki yarda wata alaka ta shiga tsakanin ki da shi kinji kanwata?". Ya faɗa yana share mata halayen data fara yi, yace "karki yarda ki 6ata adonki, bakiga yadda kika yi kyau ba". "Allah yaya?, wlh kaima kayi kyau sosai". Ta faɗa cikin sakin fuska da murmushi Amar ya ciro wayarsa ya fara ɗaukar su hoto suna ta dariya 6angaren Mubarak kuwa daɗi ne ya lullu6e shi ganin yadda ran abokin faɗan shi Amar ya 6aci, koba komai ya sami hanyar da zai rika tusa mishi bakin ciki kamar yadda shima yake ji idan ya ga yadda Dady yake nan-nan da shi. Tofa🤔 *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/27/2017, 4:57 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *28* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Suna cikin ɗaukar hotunan ne suka ji shigowar motoci a gidan, hakan ne ya tabbatar musu da isowar Ummy Mahaifiyar Hjy Yusra. Da gudu Feena ta nufi inda aka faka motocin tana tsallen murna, Amar yabita da kallo kafin daga bisani shima ya bi bayan ta, amma shi kam ba gudu yake ba (uhum Amar fa an girma lolz) . Ummy na fitowa suka rungume juna itada Feena, kowanne su na bayyana irin farin cikin da yake ciki na ganin juna. Dai-dai nan Hjy Yusra da Amar suka karasa gurin har kasa ta zube ta gaida Mahaifiyar tata, Amar ma haka ya gaisheta, Ummy ta ɗagota tana murmushi "Yusra na same ku lafiya?". Izuwa yanzu bakin Ummy yaji hausa sosai "lafiya lau Alhamdulillahi Ummyna ya hanya?". Haka dai suka shiga gaishe-gaishe wannan karon Ummy ita kaɗai ta zo sai kayan tsarabar ta. Saboda karancin lokaci ko hutawa Ummy bata yi ba aka fara gudanar da bikin, inda mutane suka fara cike table ɗin dake gaban Feena da kyaututtuka, gaba ɗayan su kawayen Hjy Yusra ne. Sai ɗaukar hotuna ake ana ajiye gifts, daɗi takeji kamar me, haka taro ya watse bayan anci ansha kuma an nishaɗantu. Bayan sallar magariba ne suka hallara a babban falon gidan bayan kowa yayi wanka yayi salla, yau wani sakalci Feena take ji saboda ganin Ummy da tayi, kwance take bisa carpet ta ɗora kanta bisa cinyar Ummy tana zuba shagwa6a, wai taron nan duk ya gajiyar da ita. Ita kuwa Ummy sai sannu take mata, haɗe matsa mata kafafuwanta. Momy Yusra Dady da Amar duka sun zama yan'kallo, a 6angare ɗaya kuma suna jin daɗin yadda Ummyn take tarairayar Feena tana nuna mata so. Dady yai murmushi kana yayi maganar cikeda tsokana, "Ummy karfa ta karya miki kafa" da sauri Feena ta ɗago "kai Dady dan Allah ka bari, ni ina naga nauyin da zan karya wannan tsohuwar da Kuka riga kuka ginata da beta". Itama dai da tsokanar tayi magana dan sun saba irin wannan da Dad, yanzu sun saba sosai wasa sukeyi tsakanin su da Iyayen, kai ka ce a gidan aka haife su. Ummy tace "Ke, lallaima Feena baki ganki bane kin girma fa". Ta shagwa6e fuska "amma ai ban yi girman da na wuce hawa cinyarki ba ko?". Su duka sukayi dariya, Dady ya kawar da zance a lokacin da ya zura hannun shi aljihu ya ciro wani makulli sabo fill, ya kira ta da cikakken sunanta "Safeenah" "na'am Dady" ta amsa tareda tashi zaune tana kallon Dadyn, yace "ga yar karamar Kyautata a gare ku keda yayanki, wannan makullin motor ku ne kwananta biyu da zuwa, tana nan ajiye a parking space wadda kukaga an lullu6eta ɗin nan, kyauta ce dana baku. Amar yarona ka girma na yarda da nutsuwa da kyan hankalin ka, zan sa Ilu ya koya maka tuki sai kufara kai kanku makaranta, kaga nan gaba kaida Feena zaku rika tafiya". Safeena ta daka uban tsalle "Wayyo Allah daɗi, kai Dady amma wlh ka gama min komai, Allah dai ya biya ka da Aljannarsa maɗaukakiya". Dady ya amsa da "ameen ameen". Amar ya kara matsawa dai-dai da kafafuwan Dady ya rusuna, yana daɗa yi mishi godiya, Dady ya shafa kansa "bakomai yarona kai dai ka dage da karatu ka kuma ɗore da kyawawan halayenka dana sanka da su, Allah yayi muku albarka". "Ameen Dady". Suka amsa a tare. Wannan kyautar ta Alh bakaramin faranta ran Momy Yusra tayi ba, ta daɗe tana yi mishi godiya Ummy na taya ta, yace "haba wannan ai yiwa kai ne, yara namu ne ga baki ɗaya" Ummy ma kwance Jakarta tayi, inda ta ciro tata kyautar a cikin wani ɗan karamin box ta buɗe Wata dankariyar sarka ce mai matukar kyau da sheki sai walwali take tana ɗaukar ido, wannan ko ba'a faɗa ba sun san zinari ne. Ta ciro ta tana kallon inda Safeenah take, "zo nan". Ummy tayi maganar a takaice Feena ta baro gaban Dady ta dawo inda Ummy ta tsuguna zuciyarta cike da farin ciki, Ummy ta kwance sarkar nan ta ɗaurawa Feena a wuya, sannan ta ciro ɗan kunnen ta saka mata bayan ta cire wanda ke sanye a kunnenta. Feena ta kalli yadda sarkar ta kwanta a wuyanta, da sauri ta rungume Ummy tana yi mata godiya. Iyayen kuwa bakaramin fami ganin wannan sarkar yayi musu ba, sai dukan su sukayi shiru suna tuna wancan lokacin kamar dai haka, haka Ummy ta sakawa Baby sarkar nan da hannun ta. Amar kanshi bin sarkar yayi da kallo zuciyar shi naso ta zargi wani abu. Murna da farin ciki sun cika Feena ta rarrafa gaban Momy Yusra tana faɗin "Momy kalla, kalli sarkar da Ummy ta siyo min", Bakina sam yaki rufuwa saboda murna, amma ga maimakin ta sai taji Yusra batace komai ba, hasali ma gaba ɗaya yanayin ta ya sauya. Ganin yaran zasu fahimci wani abu, Dady yayi saurin dafata "ya dai Yusra?". Ya kalli Amar yace "kuje, kuce Ilu ya nuna muku sabuwar motar ku". Suka mike suka fita cike da murna, a lokacin ne kuma Yusra ta sami damar fashewa da kuka. Amar kuwa suna fita ya kama hannun Feena zuwa ɗakinshi a madadin inda suka nufa, zuciyar shi cike da tantama, so yake yaje ya tabbatar domin wannan sarkar da Ummy ta sakawa Feena a wuya tayi matukar kama da wadda Ummanshi ta bashi kafin rasuwar ta. Wadda tace masa da ita aka tsinci Safeenah, kuma ta umarce shi da ya rike sarkar da aminci, ya kula da ita sosai domin tabbas sarkar ta musamman ce, dukda batasan takamaiman matsayin sarkar ba, amma tunda take bata ta6a ganin sarka mai kyau kamar ta ba. kuma tana tunanin ko da ita za'a iya gano asalin Safeenah. Wardrobe ɗinsa ya buɗe, kana ya sunkuya can kasanta ya ɗauko ɗaurin ledar ya fara kwancewa yana kallon Safeenah, wadda har yanzu bata sami damar yi mishi magana ko tambayar abinda hakan yake nufi ba. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/28/2017, 9:59 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *29* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Bayan ya sami nasarar kwance kullin ledar ne ya zaro sarkar dake cikin ta, naɗe a cikin wata takarda. Safeenah kanta data kalli sarkar saida ta koma kallon ta wuyan ta, wadda Ummy ta saka mata yanzun nan. "Yayana wannan fa?" a ina ka samu?" Baisamu nutsuwar bata amsa ba har saida ya karaso gabanta, yasa hannunsa ya ɗago sarkar da aka sa matan yana kare mata kallo, domin tantance bambancinta da wannan wadda Ummansa ta bashi. Ya kuwa gano bambancin domin wannan tata ta jaranta karma ce, kuma zagayayya kamar sifar kwallo. Bayan wannan ma da rubutun larabci a jikinta wanda a yanzu zai iya karantawa, (Marhaba) haka aka tubuta ajikin wancan karamar. Sa6anin wannan da aka rubuta Sunan Safeenah da manyan haruffa na larabci. Ya kara duban sarkokin ya cika da mamaki, ganin duk irin daɗewar da wannan karamar tayi haskenta da shekinta suna nan kamar na wannan wadda aka bawa Feena yanzu. Hakan ya daɗa tabbabar wa Amar cewa lallai maganar Ummanshi ta tabbata akan cewa wannan sarkar ta musamman ce. Ya rumtse idonshi tareda damke sarkar a tafin hannunshi, yana tunano maganganun Ummanshi akan Safeenah, "Abinda yaya Larai take faɗa akan Safeenah gaskiya ne Amar, tabbas ita yar'tsintuwa ce. Sai dai hakan bai isa yasa akirata da shegiya ba, kai inma hakan ɗin ne meye laifin yarinya?". Maganar ta dawo raɗau a kunnen sa, tamkar a lokacin take gaya mishi ita. "Babu Umma, wlh bata da laifi" ya faɗa cikin rauni kamar mai shirin fashewa da kuka Safeenah ce yaji ta dafa kafaɗarshi tana faɗin "Yaya, wacce ce batada laifin?" Da sauri ya juyo ya kalleta, a lokacin idon shi sun fara kawo kwalla. Ganin zata gane kuka yake, yasa yayi saurin rungume ta dai-dai lokacin da halayen ke fitowa daga idonsa. Tausayin rayuwar Feena ya kara lullu6eshi. A wani 6angaren na zuciyarshi kuma godewa Allah yake daɗa yi, akan taimakon da yayi musu ya inganta rayuwarsu ta hanyar haɗa su da waɗanan bayin nashi Momy Yusra da Dadynsu Alh Wakkala. Cikin dabara ya kai hannunshi bisa kumatunsa ya goge hawayen fuskarshi, domin yasan da zarar ta gani yanzu itama zata saka kukan. A sannan ne ya raba jikinshi da nata ya ɗagota suka fuskanci juna. "Kanwata Feena kinsan ina kaunar ki, Umma ma tana sonki sosai, ita ce ta bayar da wannan tace na baki, kuma tace taki ce tun kina jinjira". Ya faɗa yana nuna mata sarkar, lallausan murmushin nan nata ta sake mishi, alamun farin ciki ne suka bayyana karara a fuskarta. Ta kar6i sarkar "Allah sarki Ummana, ina kaunar ki Umma. Allah ya kai rahma kabarinki". Da sauri ta fara kiciniyar cire sarkar da Ummy ta saka mata domin maye gurbin ta da wannan wadda Umma ta bayar a ajiye mata. "a'a kanwata, kar kiyi haka". Amar ya yayi maganar yana janye hannuta ga barin abinda take ko'karin yi. "me yasa?". Ta tambaye shi fuskarta cike da damuwa. "Feena Umma tamu ce a kowane lokaci zamu iya amfani da abinda ta bamu, waɗannan bayin Allah kuma sune suka ɗauke mu a matsayin nasu, irin Soyayya da kulawar da suke nuna mana ko a gurin Iyaye sunada wahalar samu Safeenah. "Kiyi hakuri da wannan ta Umma har zuwa wani lokacin, yanzu ki zauna da ta Ummy idan kika cireta sam bazata ji daɗi ba". Shiru tayi na ɗan lokaci tana nazarin kalaman sa, tabbas abinda ya faɗa gaskiya ne. "Shikenan Yaya, amma zuwa yaushe zan saka ta Ummana?". Tayi tambayar cikin sanyin jiki, da alama hakura kawai tayi amma tana muradin sarkar. Yai murmushi "bafa ta Umma bace, taki ce". Ta kalle shi "to ai itace ta bani". Shiru kawai yayi dan bazai iya gaya mata yanda abin yake ba. Hannu ya zira ya kar6i sarkar ya maida ta cikin takardar nan ya ninketa, sannan ya saka a leda ya maidata inda ya ɗauko ta. Ya juyo ya kama hannunta suka fice. Direct compound ɗin gidan suka nufa inda ake ajiye motocin gidan, Feena ce mai kwallawa Ilu direban gidan nasu kira. Cike da murna da farin ciki. Da hanzarin sa ya taso yana faɗin "Uwar ɗaki fita zamu yi?" Sunan da duka ma'aikatan gidan suke Kiran ta da shi kenan. "A'a Ilu, Dady ne yace ka nuna mana sabuwar motar da tazo jiya tamu ce, mu aka siyawa". Tayi maganar da yanayin nan nata na yaranta. Ilu ya hangame baki yana kallon Amar "gaskiya na taya ku murna domin ko Alhaji bai ta6a hawa motar da takai kuɗi da kyawun wannan ba". Ya karashe maganar lokacin da yake yayewa motar rufin da akaimata. "wow" Safeenah ta faɗa cikin kwalalo ido waje. Amar kansa ya jinjinawa kyau da girman motar daɗi ne ya lullu6e zukatan matasan biyu. Tayi tsalle ta rungume yayanta "wayyo Allah yaya, daɗi zai kashe ni". Tare suka karasa gaban motor key ɗin ta saka ta buɗe kofar ta shiga shima ta buɗe mishi 6angaren driver ya shiga ya zauna yana karewa cikin motar kallo. Wannan karon kasa 6oyewa yayi, hawayen farin cikin da suka gangaro daga idanun shi. Feena tayi saurin kai hannunta ta share mishi. "Meye haka kuma yaya?, me ya saka ka Kuka?". Shiru yayi na wasu dakiku yana kissima yadda rayuwa take tafiya da tsare-tsaren ta. "Kinga rayuwa ko kanwata?, kinga yadda abubuwa suka canza daga tsanani zuwa daɗi ko?, shin ke baki ji wani iri ba Safeenah?". Ita ɗinma hawayen ne shar a fuskarta. "na gani yaya wannan duka ikon Allah ne, shi ne mai maida zafi sanyi ya kuma juyar da sanyi ya koma zafi, babu abinda ya gagari Ubangiji haka malamin islamiyyar mu yake gaya mana". Ta matsa daf da shi ta kwantar da kanta bisa kafaɗarshi "haka Allah ya tsara mana tamu rayuwar Yayana, mu godewa Allah dan na tabbatar wannan shi ne Alkhairi akan zaman mu kauye". Ya share mata hawayen yana faɗin "Allah ya jikan Umma yayi mata rahma". tace "ameen ya Allah". Makullin ta mika masa ungo yaya tayar mu tafi, Dady fa bai san mun iya mota ba" tayi maganar tana dariya. Amar ya kare mata kallo daga ita sai kayan jikinta riga da siket, ko ɗankwali batada shi balle mayafi. Ya harare ta "waye zai fita dake haka?". *Yar'muta Arkilla* ✍ [11/29/2017, 10:01 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*......... *30* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Shigar jikinta ta kalla cikin shagwa6a "kai Yaya Allah wani lokacin ka fiya takura, yanzu meye illar fita na haka?". "hmm bazaki gane ba Feena, idan baki koya yanzu ba to yaushe kike so ki koyi suturta jikinki idan zaki fita?". Tayi shiru tana zun6oro baki. Yai murmushi sannan ya buɗe murfin motar ya fito, ya zagayo ta gefen ta dan ya lura da abinda take son yi wato fushi. Ya buɗe kofar gefen ta ya janyo hannunta, ba musu ta fito maimakon ya ja hannun nata su tafi sai ma ya janyo ta ya kwantar da ita a gefen jikin shi suka nufi cikin gidan, suna tafe tana dire-diren kafa tana tittirjewa tareda guna-guni. Shi dai ba abinda yake sai lallashi da ban baki. Ilu da Mudi mai gadi kuwa me zasuyi inba dariya ba domin su sun saba ganin irin wannan shagwa6ar ta Uwarɗakin su ba adadi, tana juyowa suka gimtse dariyar, suka cigaba da hirar da suke. Amar kamar yayi dariya haka dai ya lalla6ata suka shiga gidan, haka wajen saka mata hijabi ma yasha fama, dan a cewar ta karamin mayafi take son yafawa, dakyar da lallashi dai ya samu ta yarda ta sako ɗaya daga cikin hijabanta. Ya kalli fuskarta wadda ta haɗe ta guri ɗaya, ta cakuɗe kamar mai shirin fashewa da kuka. "Haba dan Allah Feena, so kike kisa ni kuka?". Yayi maganar kamar da gaske shima kukan zai yi, da sauri ta harare shi "wlh kar kayi Kuka, kaji na rantse ko?". Yayi dariya saboda yadda tayi maganar "to naji bazan yi ba, amma kema ki daina wannan fushin da kike Allah sai kika ɗebe kyawu kamar ba ke bace". Tayi saurin kallon shi "da gaske?". "da gaske kuwa, zo ki gani". Ya kama hannunta ya kai ta gaban madubin ɗakin nata "kalla". Ya nuna mata madubin ta kuwa duba, sai taga ashe da gaske ne sam batayi kyau da fushin ba. Sai ta fara murmushi. "Lah! Yaya kalli nayi kyau sosai da nayi murmushi". ta faɗa tana dariya. "Sosai ma kuwa, ai ke ɗin kyakkyawar gaske ce, kawai kiyi ta murmushi, kiga yadda kyawunki zai daɗa yin yawa". Tafukan hannayenta ta saka ta rufe fuskarta wai kunya taji, Amar yayi dariya a ranshi yana jinjina yadda yake tsintar kansa cikin farin ciki idan yaga kawar tashi tana murmushi ko dariya. Haka suka fito suna ta kyalkyala dariya, suka shiga motar, Mudi ne ya buɗe musu gate suka fice cikin farin ciki, yana ɗaga musu hannu. Ma'akatan dake zaune a harabar gidan suka bisu da kallon sha'awa, yaran sun yi a rayuwa suna burge kowa. Ummy ta kalli yar'ta Yusra da fuskarta tayi sharkaf da hawaye tace "kiyi hakuri Yusra, nasan abinda kike tunawa, kuma ni kaina inajin wannan zafin. Amma ki sani wlh har ga Allah yaran nan da kike gani rahma ne a gare mu". Ta tsaiga tana duban yar'tata da surikin ta, kafin ta cigaba "ni kaina da kike gani har yau ina jin zafi da kunan rashin haihuwar ki da kuma 6atan yariyar nan Baby, amma abin mamaki sai zuwan bakin yaran nan ya rage kusan kaso arba'in a cikin ɗari na tarin damuwar. Kuma nasan kema dole taki ta rugu dukda zamomar ki Uwa, kodai har yanzu kina fushi da ikon Allah ne dukda kyautar ta ya koma yi miki?". Yusra ta share hawayen ta, ta ɗago kai ta kalli Ummy cikin sanyin murya tace "Ummy bawai ina fushi da ikon Allah bane, wallahi ko ɗaya. Tsakani na da Allah sai godiya, bisa kyaututtuka da ya wanzar da rahmarsa da yayi gareni". Ta ɗan yi shiru kafin ta ɗora da cewa "ya'mace na rasa kwaya ɗaya jal, yau gashi na wayi gari da ya'ya biyu mace da namiji. Duk da cewa su ba ya'yana bane amma na tabbatar zasu min rana koma ince suna kan yimim ɗin, suna cire min kewa suna saka ni farin ciki, duk abinda nake so shi suke yi, koda wasa basa kusantar abinda bana so. Ummy nifa ganin sarkar nan ne ya saka ni kuka, in baki manta ba irinta kika sa aka yowa Baby a lokacin da aka haife ta. Ranar da kuka diro Nigeria a ranar kika saka mata ita, haka kuma a ranar aka ɗauke yarinyar". Sai ta fashe da kuka mai tsanani "ɗa' na jini daban ne Ummy, soyayyar da nake ji ina yiwa Baby ta daban ce abinda na tuna ya saka ni Kuka kenan". Ta faɗa cikin kuka. Tausayin ta ya kara kama Ummy da Alh Tijjani, wanda su dukan su hawayen suke yi, jin bazai iya kallon Yusrar shi tana wannan kukan ba yasa ya tashi tsaye yayi taku zuwa kujerar da take kai itama ya mikar da ita. Sannan ya kama hannunta suka fice daga ɗakin. Ummy ta bi bayan su da kallo, sai bayan fitar su ta kai hannu ta share nata zafafan hawayen. Ita kanta kukan take domin rashin Baby ba nasu bane su kadai, hadda ita ya shafi zuciyarta. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/25/2017, 3:09 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *31* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Yau kam Amar da Safeenah sun kasa kididdige adadin farin cikin da suke ji a zukatan su, yawo sukayi sosai a cikin garin Kano (ta dabo tumbin giwa) sun zaga guraren hutu da shakatawa bila adadin. Daga karshe suka juya akalar sabuwar motor tasu zuwa Gida cike da farin ciki. Karfe ɗaya saura suka shiga gidan, dai-dai lokacin da shi kuma Dady yake shirin fita, cike da mamaki ya bisu da kallo har Amar ya daidaitawa motar tsayuwa ya fito, Feena ma fitowar tayi hannunta rike da robar ice cream babba. "Lah Dady fita zaka yi?" ta tambaye shi baki a washe, kai da ganin ta kasan tana cikin farin ciki. Bai amsa mata ba, sai dai hankalinsa na gareta, na lura kallon da yake mata na nazari da kididdiga ne, Alh Tijjani ya gamsu da gulmar da zuciyarsa ke yawan kawo masa ya yarda ɗari bisa ɗari Feena tayi kama da matarsa Yusra bama kaɗan ba, musamman yanzu da yariyar ta fara girma sai kamanninta da Hjy Yusra suka kara bayyana. Amar ne ya katsewa Alh tunani da cewa "barka da fitowa Dady" ya faɗi hakan ne bayan ya rusuna gaban sa. "Yauwa barka dai Amar, dama ka iya tuki ban sani ba, yaushe ka koya?". Kafin ya amsa tambayar tayi caraf "hhhh Dady ai tun yana primary 6 Ilu yake koya mishi mota, nima fa yanzu na fara iyawa". Ta karkare da dariyar nan tata mai ɗaukar hankali. "Kai gaskiya na yaba, madalla da aikin Ilu, naji daɗi sosai, sai ku shiga ciki Momyn ku tana ta neman ku". "Shikenan Dady, a dawo lafiya". Suka faɗa a tare, ya amsa musu yana murmushi, sannan ya shige mota driver ya ja suka fita. Amar yayi gaba ta ruwa masa baya tana ta zuba mishi surutun ta,suka yi sallama a falon. "Amar ina Kuka tafi?" Momy Yusra ta tambaya tana kallon su. Saida suka kalli juna sannan Feena tayi zaraf "kai Momy shine kika 6ata rai kamar 6ata muka yi?" da sauri Hjy Yusra ta ɗago manyan idonta ta sauke su a kan Feena, zuciyarta na mata wani zafi da raɗaɗi wanda kalaman Feena suka haifar mata. "Ke! Feena are you mad?, did you ever know what you are saying?, pls live this room live me alone". ta faɗa a tsawace irin tsawar da bata ta6a yi musu ba, saida ta dafe kirkira kafin ta nuna musu hanyar ɗakunansu alamar su wuce. Feena ta fashe da kuka ta ruga ta fice da gudu ta nufi ɗakin ta, hankali tashe Amar ya ruga mata baya. Hjy Yusra kuwa komawa tayi ta zube kan kujerar dake kusa da ita tana maida numfashi, yayinda zuciyarta ke mata Kuna, kalaman Safeenah na neman fasa kwanyar kanta. Da sauri ta mike ta shiga ɗakin ta, toilet ta wuce kai tsaye ta sakarwa kanta ruwa tareda lumshe fararen idonta da sukayi jajur tana tuna halin da ta shiga ɗazu da bata ga su Amar da kanwarsa Safeenah ba. Wato bayan da Dady gama rarrashin ta ne, sai taji tana son ganin Feena kafin tayi bacci, hannunta ta kai ta danna kararrawar kiran sashen ma'aikatan gidan, mintuna kaɗan Iya ta bayyana a ɗakin, nan tasa Iya ta kira mata Feena a waje ko a sashen su, ta amsa da "to" ta fita. Jimawa kaɗan ta dawo nan take shaidawa Hjyr cewa Amar da Feena basa gidan. Nan da nan hankalita ya tashi, ta mike da kanta ta fito saida ta zaga duka 6angarorin gidan amma bata gansu ba, tun tana yi da karfinta har sassan jikinta suka sanyaye saboda turawa da yadda tayi irin wannan zagayen na nema lokacin da baby ta 6ata. Sai daga bisani Ilu da Mudi suke gaya mata ai sun fita da sabuwar motarsu, sannan ne ta sami nutsuwa nan ma ba sosai ba, zuciyarta na ta zarya da zullumin kar wani abu ya same su, sai gashi kuma Feena tazo tana sinfonia kansu da kalmar da ba zata ta6a mantawa da ita ba, wato *6ata*. Towel ta ɗauro ta fito bayan ta tabbabar ruwan sun gama ratsa jikinta, doguwar riga ta zira bayan ta gama tsane jikinta. Ta koma ta baje bisa lallausan gadonta, tana tuna yadda Feena ta bar falonta da gudu tana kuka saboda yadda ta mata magana, sai taji bata kyauta ba, saboda yariyar bata San komai dangane da abinda ke ranta ba. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/25/2017, 5:33 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *32* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Bangaren Feena kuwa Da zuwa ɗakinta sai ta afka bisa lallausan gadonta tana karawa kukanta sauti, Amar da ke biye da bayanta duk nutsuwarsa ta fara kwacewa, dan duk fad'in duniya babu abinda ya tsana bisa yaga Feenar sa cikin halin damuwa balle ma ta kaita ga kuka tana zubda gwalagwalan hawayenta. Gefen gadon ya zauna dai-dai kanta, shiru yayi na lokaci mai tsayi yana kallon ta, yayin da sautin kukan nata ke masa yawo a zuci yana ji kamar kankarar kirjinsa ake da wuka ko wani abu mai kaifi. "Feena, ya kira Sunan lokacin da ya kai hannunsa bisa kanta, "dan Allah kiyi shiru kanwata da gaske kukan ki ciwo yake min a nan". Ya faɗa yana nuna kirjinsa da ɗaya hannunsa, Safeenah juyar da kanta gefe tana sheshshekar kuka "Feena pls" ya koma faɗa a tausashe, "kanwata zaki sakani a wani hali, ki sani Momy batai miki tsawa dan tsana ko jin haushin ki ba, hasali ma tayi miki tsawa ne dan tana kaunar ki tsakanin ta Da Allah". Dara-daran idon nan nata ta ɗago ta sauke su fes a kan sa, tana nazarin abinda ya fito bakin sa. "me kake so kace min? Did I do something wrong da za'ayimin tsawa a kai?". "for her understand u do Feena". Tashi tayi ta zauna da kyau tana kallon shi "meye wannan abin, me nayiwa Momy da zata min tsawa yaya?". Cikin tausayin ta da kuma jinjinawa yarantar ta yasa hannu ya goge mata hawaye yana faɗin "me yasa bakya son faɗa Feena?". Ta yatsina fuska "ni kawai bana so ne, ai waɗanda aka tsana ne kawai ake yiwa faɗa". Ta karashe maganar cikeda yaranta "hmm Feena ho, to bari kiji in gaya miki duk wanda kika ga ana yi mishi faɗa akan abinda bai dace ba to shine asalin wanda ake so, kuma wannan shine mai gata... Ya cigaba da cewa "Momy tana son mu sosai ta damu da rayuwar mu, adalcinta ne yasa ta dai-daita soyayyar da take mana da wadda takewa yar'da ta haifa, Momy tayi miki tsawa ne saboda maganar *6ata* da kika danganta da mu, kin san meyasa?". Ta girgiza kai tana kallon sa, murmushi yayi mata kafin yace "saboda kaunar da take mana bata so mu *6ata* ta rasa mu kamar yadda ta rasa yar'ta Baby". Shiru ya ratsa ɗakin Amar ya zubawa kanwarsa ido, yana kallon yadda ta dage tana nazarin maganganun sa, "lallai Feena akwai kuruciya" ya ayyana a ransa A hankali ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga ciki, idanuwanta kyar akan su, sannan ta tako cikin sanyain jiki ta isa garesu. Hjy Yusra kenan wadda ta kasa jure zogin da cuciyarta ke yi mata akan halin 6acin ran da ta jefa Feena ciki, dukkanin su ita suke kallo cikeda tausayin ta har Safeenar domin zuwa yanzu ta fahimci dalilin Hjyr na yi mata tsawa. Da sauri ta mike ta rungume Momyn itama sai ta rungume ta, kusan a tare suka sauke numfashi mai kunshe da abubuwa daban-daban, "Momy pls forgive me, I don't really understand how it's feel, I know it's hurt, and I know you are doing all this for us just because you love us, you are different Momy na, we love you too". Duk wannan maganganun tayi su ne tana kankame da Momy, wadda take jin kalaman yarinyar kamar ana yafawa zuciyarta ruwan sanyi, soyayyar ta Da kaunar ta na data ninkuwa a ranta cikin sautin kuka ta fara magana. "Thank God you understand me Feena, I don't want to lose you as I lose her, kiyi ko'kari ki fahimce ni ina matukar kaunar ku keda yayanki, Kun kasance min tamkar ya'yan cikina". Hawaye ne suka gangaro daga idon Amar, tausayin baiwar Allah nan ya lullu6e shi, sosai kalamanta suka kara narkar da zuciyar matasa, a 6angare ɗaya kuma soyayyar da suke mata ta kara ha6aka. Nan da nan Feena ta warware su duka suka ɗunguma sashen da Ummy ta sauka, a nan aka ci dare ana hira kafin daga bisani suka yi mata sallama suka fita, Amar ya nufi ɗakin sa Feena da Momy kuwa ɗakinta suka wuce dan yau Hjy Babba ce da girki a can Dady yake, (Hjyr Mubarak kenan Hjy Ummu). Dama duk ranar girkin ta Feena a ɗakin Momy take kwana, wannan ne ya kara musu shakuwa da kusanci, domin a can ma wata sabuwar hirar suke kullawa su yita yi har sai Feena tayi bacci, sannan Momy ta mata addu'a ta rufe ta da blanket itama ta kwanta daf da ita. Haka rayuwa tayi gaba da tafiya cikin farin ciki da annashuwa, inda lokaci ya ke ta kwararawa, watanni biyu Feena tayi tana hutar kafin daga bisani results ɗin su ya fito, jarrabawa tayi kyau Alhamdulillah, Safeenah Wakkala taci exam 100%. Ba jimawa aka kammala mata komai ta koma fannin Secondary duk a cikin Makarantar, wai a ranar Amar ji yayi tamkar an maklakar masa duka garin Kano saboda murna, da yawan ɗalibai da Malamai sun yita mamaki, yadda nutsatstsen yaron ya sauya a wuni ɗaya da zuwan wata yarinya, suka yita ce-ce kace kafin su san takamaiman matsayin Safeenah a gurin Amar Wakkala, gwarzo kuma jarumi ɗalibi na farko wajen ko'karin cin jarrabawa, sai dai tarin miskilanci da kyale mutane. Tunda ya fara zuwa school ɗin bai yi aboki ba, dukda tarin sa'anninsa masu neman cusa kansu gare shi, shi kam sam baya saurarar su. Baya magana da kowa inba ta kama dole ba, sai gashi yau sun gashi da wata yarinya tanata juya shi, kamar remote control, haka yake bin duk wani umarninta, haka a filin makaranta lokacin break, suka kafa dandalin wasar su gefe, daga ita sai shi suke wasan ball abinda bai ta6a yi ba koda da maza yan'uwansa balle da mace. Sai gaba ɗaya hankulan ɗaliban suka dawo kansu, bayan burgewa akwai alamun mamaki karara a fuskar ɗaliban. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/25/2017, 7:30 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *33* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Haka suka cigaba da tafiyar da rayuwar su a makarantar ganin sha'awa, suna burge kowa a school ɗin tun ba'a san su waye ba har ɗalibai da malaman suka fahimci yaya da kanwa ne, sun gane hakan ne a lokacin taron Yara da Iyayensu wanda hukumar gudanarwar makarantar ta shirya, inda suka ga Iyayen Amar sune Iyayen Feena wato dai Iyayensu ɗaya. To da haka dai sukayi ta mulmula rayuwa tana mulmula su, kwanci tashi, da daɗi da ba daɗi Momy da Dady na iya ko'karin su wajen kula da yaran da faranta musu, 6angaren Hjy Ummu kuwa zaman nan nasu na doya da manja yana nan itada abokiyar zamanta Yusra, wadda sam bata kulata, bata shiga sabgar ta, hasalima kullum cikin gargaɗin su Feena take akan su yiwa Hjy biyayya kamar yadda suke mata, Mubarak kuma su rike shi a matsayin ɗan'uwa. Ita kuwa Hjy Ummu a kullum cikin jin zafi da takaicin Yusra take, tareda hura wutar gaba tsakanin yaron wajenta Mubarak da su Amar, kullum nuna mishi take Dady yafi son su akan sa shi da suka zo suka samu a gidan, hatta motar da aka saya musu saida shima aka siya masa iri ɗaya kala ce kawai ta bambanta, amma saida tayita zugashi akan wai ta su Feena tafi tashi kyawu. Rayuwa kenan mai hali baya canjawa, ta sakanta yaronta Mubarak ta nuna mishi jin daɗin duniya tun bai tauna ba balle ya haɗa, yaro ɗan 22years yasa yayi shaye-shaye, ya nemi mata, ya saci kuɗin Dady idan ya gani, kasancewar yana gaban su a karatu yanzu haka yana jami'a matakin farko, Sam babu jituwa tsakanin sa da Amar domin ko wannen su kallon tsana yake yiwa ɗan'uwan sa, dambe suke yi sosai, domin wasu lokutan ma idan yana neman Amar da rigima ta kan Safeenah yake farawa wadda yasan muddin ya ta6ata to dole Amar zai kula shi. Yau ranar girkin Hjy Babba ne, saboda haka bayan sun kammala hira Hjy Yusra da Feena suka nufi ɗakinta, Amar kuma ya nufi nasa ɗakin. Bayan yar hirar da suke yi a ɗakin sai ta kwanta tayi shiru tana nazarin sabon al'anarin da take ji a jikinta yau, tax juyin duniyar nan tana neman bacci ya ɗauke ta amma bata samu ba, zogi da raɗaɗin da take ji a mararta sai kara yawa yake yi, tun tana iya jurewa har ta fara kuka kasa-kasa. Momy Yusra dake gefenta tayi zaraf ta tashi zaune, Safeenah? Lafiyar ki kuwa? me yake damun ki?". Ta jero mata tambayoyin lokacin da take ɗago ta, ta mikar da ita zaune tana nazarin fuskar ta, wadda duk ta kumbura kana idanunta sukayi jajir. "Safeenah lfy? What's wrong with you?" cikin kukan ta nunawa Momy mararta da yatsa, alamar a nan take jin ciwon, hankalin Momy yayi matukar tashi, da sauri ta mike tsaye tareda mikar da Safeenah da nufin ta kaita asibiti. Abinda ta gani a jikin bedsheet ɗinta ne ya ganar da ita matsalar Feena, sai jikinta yayi sanyi, hankalinta ya ɗan kwanta. Feena kam idonta a rufe sai Kuka take tana gimtse fuska, lebenta har ja yayi saboda cizon da take masa. Jin Momy ta tashe ta tsaye kuma tayi shiru yasa ta buɗe idonta ta sauke su kan Momy, fuska a marairaice tace "Momy marata, wlh ciwo take min sosai, ganin kan Momy na kallon gadon yasa itama tayi can da idonta, ai kuwa karaf suka sauka akan jinin da ya fara fitar mata a jiki har ya 6atawa Momy zanin gado, cikin rashin fahimta ta kalli Momy "na shiga uku na yau me zan gani, Momy mutuwa zanyi?, yan'ciki na ne suka fashe ko me wlh ina zubar da jini". Sai kuma ta fashe da Kuka ta kankame Momy, kuka take sosai tana jerowa Momy tambayoyi waɗanda Momy ta rasa yadda zata amsa mata su. A madadin haka sai ta kama hannun ta suka shiga toilet ta cire mata kayan jikin ta, sannan ta tsabtace mata shi ta nayi tana mata sannu, ita kuwa ta gama tsurewa, gaba ɗaya tunanin ta ya bata yan'cikinta ne suka fashe kuma babu makawa mutuwa za'ayi, wannan tunanin yana cikin abinda ya hanata tsagaita kukan da take. Sabon pad da pant Hjy ta ɗauko ta haɗa mata, da kanta ta manna mata always ɗin a jikin pant sannan ta bata tace ta saka, ba musu ta kar6a ta saka, sai dai har yanzu bata daina kukan ba. Hjy Yusra kuwa banda rarrashinta ba abinda take, saida ta tabbatar ta kimtsa ta Da wasu kayan sannan ta riko hannunta zuwa ɗakin ta yake bedsheet ɗinanan ta shimfiɗa wani, ta zaunar da Feena gefen gadon sannan ita kuma ta koma toilet, ta kama zanin gadon nan dai-dai inda ya 6aci ta wanke shi tas, abinda bata ta6a yi ba a rayuwar ta, sannan ta dawo ta zauna gefen Feena wadda har yanzu Kuka take, tana ganin ta ta fara rokon ta akan ta barta ta tafi gun Yayanta ta ganshi kafin ta mutu. Momy ta tattara nutsuwarta ta fuskanci Safeenah, tace "Feena ina son ki saurare ni da kunnen basira, kuma kiyi amfani da duk wani abu da zan gaya miki". Safeenah tayi zuru tana kallon Momy, cikin yanayin damuwa da tashin hankali. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 8:10 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *34* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Cikin sanyi da lalkausar murya, ta fara yiwa Safeenah bayanin wannan hali da ta tsinci kanta a ciki, ta tabbatar mata da cewa al'ada ta fara (haila) wato menstruation a turance, sosai ta wayar mata kai akan messes, kuma ta fahimta domin an jima ana yi musu bayanin lalurar a islamiyya, tasan abubuwa da yawa akan sa, kamar barin salla da mai lalurar zai yi har zuwa ranar da zai yanke, da yadda zai tsabtace jikinsa ya koma salla a lokacin da ya yanke, da nisantar ta6a alkur'ani mai tsarki da dai sauran su. Sai taji kunyar Momy ta kama ta, ta rufe fuska da tafukan hannayen ta, na gane Momy Malaman makarantar mu suna yawan gaya mana wannan abin da hukunce-hukuncen sa, kuma duka na sani in Allah ya yarda zan zamo mai kiyayewa. Momy taji daɗin yadda yarinyar ta fahimta, tayi murmushi tana faɗin gud girl, dare sosai suka kai suna hira Momy na kara wayar mata kai akan abinda ya shafi al'ada, ta tabbatar mata da dole ne mai wannan abin ya zama cikakken mai tsabta, baya ga wanna ta nusar da ita abubuwa masu yawan gaske, daga karshe ta rufe da nasihohi masu sanyi da ratsa jiki. Duka dai Safeenah ta fahimce ta, magunguna Momy ta haɗo mata tasha sannan ta kwanta bayan tayi filo da cinyar Momy dake kwance, wai a haka zatafi jin daɗin kwanciya, Momy dai bata ce komai ba, saima shafa kanta da ta shiga yi, a hankali kuwa bacci yayi kasa da ita. Saida ta tabbatar tayi baccin sannan ta ɗaga ta ta gyara mata kwanciyar ta, ta rufe ta Da mayafi, sannan itama ta kwanta tana mai cigaba da kallon fuskar Safeenah, fuskar da tafi soyuwa a cikin zuciyarta. Washe gari suka tashi kamar yadda suka saba, da asuba kenan Momy ta ɗauro alwala ta tashi salla, Feena kuwa toilet ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi tayi wanka, ta fito lokacin Momy ta idar da salla tana addu'a, hakan yasa Feena ta fara tsane jikin ta tukunna, sannan ta fara shafa lafiyayyun lotions ɗin su, bayan ta kammala ne ta ɗauko wata doguwar riga ta saka, kasancewar da yawa kayan ta a ɗakin suke, sai da Momy ta shafa addu'a sannan ta tashi, ta ninke sallaya ta mayar, a wardrobe ɗin ta koma ɗaukowa Feena wani sabon pad da wani pant ta bata, ita ta koya mata yadda zata rika haɗa su, ta kuwa iya duk da tana jin kunyar Momy sosai. Lafiyar gado ta koma bi ta lafe saida gari ya waye, sannan ta farka a lokacin Momy ta fita kitchen, ganin haka yasa ta shige toilet wani wankan ta kuma yi sannan ta fito ta shirya, cikin wata atamfa super yar' asali, kalar light green, ɗinkin riga da sket, kayan sun mata kyawu matuka, ta taje lafiyayyen gashin kanta, ya kwanta ya luf-luf, ta ɗaure shi da ribbon kalar kayan jikinta, ta naɗa ɗankwalin tayi kyakkyawan ɗauri ɗan yayi, yarinya ta fito fes da ita. Suna zaune a kan dinning suna cin abinci, Momy da Amar wanda duk hankalin shi na kan kanwarsa, wadda tun ɗazu yaso yaje ya taso ta Momy tace ya barta tukunna tunda bata jin daɗin jikin ta, sai yayi duk hankalin sa ya tashi, abincin ma sakawa kawai yake ba tareda gane takamaiman ɗanɗanon sa ba. Momy ta lura da yadda yake kimsa abincin tamkar wanda aka yiwa dole, sai ta basar ta kyale shi, domin tasan damuwar sa Feena ce. Tare suka juyo lokacin da suka jiyo takun takalmin ta, tana sakkowa daga kan benen, Amar kam kasa hakura yayi, da sauri mike yayo kanta, "Safeenah kanwata, ya jikin naki?". Yayi maganar lokacin da ya riko hannunta, murmushin nan nata ta sake mishi, kafin tace "lau nake Yayana, fatan kaima haka, barka da safiya". Ta shafi kumatun ta yana faɗin, "na shiga uku Momy, Feena ta fara 6oye min damuwar ta, kinga wai bata gaya min batada lafiya ba". Momy tayi dariya tana cewa "nima ai ba gaya maka nayi ba kawai dai cewa nayi karka taso ta saboda bata jin daɗi". Ajiyar zuciya ta saki jin Momy bata gayawa yayan nata abinda ya faru da ita a daren jiya ba, "bana son damuwar ka ne Yayana, tunda na riga naji sauki to miye na gaya maka?". "Shikenan amma kin tabbata kin ji sauki ko?". Ta gyaɗa kai "sosai ma kuwa, kaikam zo mu ci abinci". Ta kama hannun sa suka isa gun dinning, ta ja mishi kujera shima ya janyo mata suka zauna fuskoki da zukatan su tas da farinciki. Momy kam nata ido ne, domin ta riga ta saba, tunda take a duniyar nan bata ta6a ganin soyayyar yaya da kanwa kamar irin ta su Feena da Amar ba. Sai a lokacin ya ware, ya saki jiki ya ci abincin sosai, haka itama, sai watanni suke da labarun raha, Yusra kam banda dariya ba abinda take, haka Dady ya fito ya same su, sosai zuciyarsa tayi fari, soyayyar yaran ta kara samun muhalli a rayuwar sa, domin ya yarda a yanzu yaran sune farin cikin Matarsa da shi kan shi ma. Tare suka mike suka taro shi, Amar ya kar6i jakar shi Feena kuma ta riko hannun shi suna mishi ina kwana, ya amsa cikin fara'ar nan tashi da sakin fuska, idon sa akan Matarsa yace "Maman yara, a nata hira ko?" "barka da safiya, an tashi lafiya". Ta gaishe shi kicin fara'a, ya amsa mata cikeda jin daɗi, Mubarak dake bayan shi sai hararar Hjyr da yaranta yake, Dady ya kalle shi "boy ba zaka gaida Maman ka ba?", ya kara tamke fuska, ya kalle ta kasa-kasa "ina kwana" Yusra tayi murmushi "lafiya lau Mubarak, ka tashi lafiya?" bai koma tanka mata ba ya fice daga falon yayi waje. Dady ya girgiza kai, ya kalli Yusra "ki kara hakuri da halayyar Ummu da yaron nan Mubarak, dan Allah Yusra kar ki yarda kisa wata damuwar a ranki kinyi?". Yana gama faɗin haka ya juya "ni Na fita" "a dawo lafiya Alh, Ubangiji Allah ya tsare ka, ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah ya bada sa'a da rabo mai albarka ". "ameen Yusra nagode da addu'a Allah ya albarkaci rayuwar ki da ta yaran ki". Ya fice yaran suka rufa masa baya dan yi masa rakiya. Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah. Rayuwa ta nisa lokuta sun shuɗe, abubuwa da yawa sun faru, an rasa da yawa kuma an sami da yawa, Amar da Safeenah an girma, ya kammala secondary har ya sami gurbin karatu a jami'a, Safeenah ma ta kammala secondary tana jiran sakamakon jarrabawa. Suna sami kulawa sosai, sam basu ta6a tunanin samun irin wannan gatan ba a rayuwar su, sau da yawa sukan ke6e wasu lokuta domin yin addu'oi ga Iyayen rokon su Alh Wakkala da Hjy Yusra, alkhairin waɗannan mutanen a gare su abu ne mai wahalar samu a wannan rayuwar *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 9:59 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *35* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Safeenah yan'mata jarrabawa ta fito harma an sama mata gurbin karatu a jami'ar bayero inda Amar yake level 1, yau itace rana ta farko da zata fara shiga jami'a, ta riga kowa farkawa a gidan, tunda tayi salla ta nufi kitchen, ta samu ma'aikatan nata kiciniyar harhaɗa break, ta saka hannun ta suka cigaba da aikin tare, kamar yadda Momy Yusra take yi. Shida da rabi Yusra ta iso kitchen, sosai try mamakin ganin Feena da yadda ta zage take aiki, "Feena dear, ya akayi yau kika rigani tashi?" murmushi tayi tareda juyowa ta kalli Momy, tana sosa kyeya "uhum, ba komai Momyna kin san yau ne zan fara zuwa school, kuma da lecture karfe takwas zan fara, shiyasa na tashi da wuri". Dariya sosai Momy tayi "Feena ho, yarinya ta ba dai zumuɗi ba, to kawo aikin maza kije ki fara shiri dan nasan yau wankan ma na musamman za'ayi". Kunya ce ta kama ta, sumi-sumi ta ra6a Momy ta wuce, ta shiga ɗakinta kai tsaye toilet ta nufa, ta haɗa ruwan ɗumi ta shige cikin su, mintuna goma tayi tana wankan sannan ta fito, tabbas maganar Momy tayi fari domin yau komai na musamman tayi, bayan kwalliyar ma takai mintuna talatin tana canje-canjen kaya duk wanda ta saka sai taga kamar basu mata kyau ba ta cire, haka Momy ta shigo ta same ta duk ta cika gadonta da kaya, "ikon Allah". Momy ta faɗa tana kallon Safeenah, "wannan kuma miye Feena?" "yauwa Momy pls zo ki taya ni za6a, na rasa kalar kayan da zan saka, pls Mom". Momy tayi murmushi "lallai yau naga yar jami'a, Feena tun ba'a shiga ba?" tayi dariya ta rufe fuskar ta da tafukan hannunta "Momy bazaki gane ba, kin san ina bin yaya wasu lokutan, wlh baki gani ba yadda yan'jami'a suke kure wanka". "To naji zo ki gani" ta kama hannun ta ta zaunar da ita tukunna, sannan ta shiga duba kayan dake baje bisa gadon, can ta hango wani swiesless red colour, mai kananan flowers, masu kalar milk ta ɗauko shi ta bata, "ki saka wannan na tabbatar zai amshi jikinki". Ta kar6a da sauri tana godiya, "thanks Mom" ta manna mata kiss a kumatu, Yusra tayi dariya tana girgiza kai. Da kanta ta ninke ragowar kayan da Feena ta fitar ta mayar dasu cikin wardrobe ta rufe, ta bar ta nan tana saka kaya. Saida suka kusa kammala break sannan ta fito, cikin takun nan nata na kasaita ta sakko daga upstairs, tare suka maida hankalin su gareta, Amar da Momy kenan, suka zuba mata ido kamar yau suka fara ganin ta, saida ita iso inda suke sannan suka iya ɗauke mata ido, kowannen su da abinda yake ji a ransa. Ita dai Yusra kallon tsaf takewa Feena dan ganin yau ta fito ita sak, a lokacin da take budurwa kamar haka take ba ba wani bambanci. Shi kuwa Amar kallon da yake mata na daban ne dan tunda take ado bata ta6a yin wanda ya fitar da ita kamar wannan ba, kayan sun kama jikinta sosai sannan sun bayyana kuruciyar ta ainun, tsayayyar budurwa yar shekaru ashirin cif-cif, fuskar nan tata ta shimfiɗu da rantsattsiyar kwalliyar ta, kayan jikinta ɗinkin doguwar riga ne fited gown sai takalmi da hand bag ɗinta milk colour haka siririn mayafinta ma, ɗaurin ɗankwalin ya zauna ɗan tamkar anan aka halicce shi. Ji yayi sassan jikin sa sun yi sanyi, zuciyar sa ta dugunzuma, ya rasa gane gabanta dangane da kwalliyar Safeenah, shin daɗin ganinta yaji ko akasin hakan?. Ita ce ta katse masa tuna ni da zankaɗeɗiyar muryar ta, tana faɗin "badai har Dady ya fita ba?". "hmm Feena manya, kin kuwa san lokacin da kika 6ata kina shiri?". Momy ta tambaye ta, sai taji kunya ta kama ta. Amar kam bai sami damar yin magana ba sam ya kasa gano yanayin da yake ciki. Zungurar shi tayi bayan ta zauna, tana faɗin "barka da safiya Yaya" "yauwa barka dai Feena kin tashi lafiya?" tayi murmushi "lafiya lau, amma Yaya baka ce nayi kyau ba" tayi maganar tana zun6uro baki, "ni na isa, ai dama jira nake ki zauna in tambaya any ba canjin fuska kika yi ba?" yayi maganar yana murmushi. Momy ta ka6i maganar sosai kuwa Amar ni kaina ina tantama, yau sai naga fuskar kamar tawa. Dukkan su suka yi dariya Sama-sama tayi break ɗin, cike da zumuɗin zuwa makarantar tana yi suna mata dariya, da haka har ta kammala ta kira Uwani mai dafa musu abinci tace ta kawo mata abinda suka yi, ba jimawa ta dawo ɗauke da leda babba a hannunta ta bawa Safeenah, ta kar6a tayi godiya suka mike, suka yiwa Momy sallama suka fita, ta bisu da kallo cike da sha'awa. Tafe suke tana zuba masa hira da tambayoyi, waɗanda ya kasa amsa mata ko ɗaya, saboda tsantsar takaicin da ya tsinci kansa daji gameda shigar da tayi, shi kansa ya kasa gane kansa yau ne rana ta farko da ya fara jin ciwon kar wasu su kalleta, saboda tsantsar kyawun da tayi, musamman a sanin da ya yiwa jami'a akwai da yawa waɗanda basuda aiki sai kallon kyawawa irinta, wasun ma har da tanka musu suke. Dogon tsaki ya ja lokacin ya dai-daita tsayuwar motar a harabar makarantar, da sauri ta kalle shi "Yaya lafiya?" saida yayi ko'karin dai-daita nutduwar sa sannan ya kakaro wani murmushi da bai wuce le6en shi ba, yace "ba komai, wani malami na tuna ɗan tsurku ne, shi zai ɗauke mu anjima". Tayi dariya "lallai Yaya an zama yan gari, a malaman ma har da yan tsurku". Bai tanka mata ba, sai dai dariyar yaken da yayi mata, suka buɗe kifofin motar suka fito, fuskokin su ɗauke da yalwataccen murmushi, ita dai Safeenah murmushin farin ciki take da murnar ranar ta ta farko a jami'a, shi kuwa Amar yana yi ne dan karta gano halin damuwar da yake ciki. Haka suka tsatsa cikin makarantar hannayen su sarke da na juna, suna tafe tana zuba shiko yana binta da murmushi. Sannu a hankali yan'matan dake kai koma a tsakiyar makarantar suka fara maida hankalin su akan kyawawan matasan, yayinda da yawa daga cikin su suka raina kansu, suka kuma tabbatar da dalilin Amar na rashin sake fuska gare su. Wata ɗaya daga cikin tawagar kawayen Jidda tace "wai zankaɗi, wanda yake da wannan santaleliyar budurwar dama yaushe zai tsaya ta kan mu. Jidda wata department met ɗinsa dake zaune da kawayen nata, ta kura musu ido, zuciyarta na tafarfasa, nan take tsanar Safeenah ta tsargu a cikin zuciyarta, ji tayi kamar ta tashi taje ta shake yarinyar har sai ta mutu. Tofa🤔 Wace ce Jidda?, me kuma Feena ta kashe mata da shigowar ta jami'a?. Ku biyo ni domin jin dalilin, yanzu ne wasar zata fara 😎. *Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/27/2017, 8:10 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *36* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Har kofar ɗakin karatun su ya raka ta tareda, bayan ya nuna mata inda zata same shi idan ta fito. Duk zumuɗin da take saida ya kau, lokacin da taga Amar zai tafi ya bar ta, shiru tayi tana kallon shi kafin kace me sai hawaye shar a fuskar ta. Nan da nan hanklin sa ya tashi, ya kama hannunta suka kauce daga kofar ajin saboda masu shiga, "haba Feena, haba mana kanwata, so kika karatun yau ya wuce ni?". Ta girgiza kai alamar a'a, yace "to in haka ne meyasa kike kuka dan zan tafi"? Cikin shagwa6a da yaranta ta fara magana" Yaya ni bana so ka barni ne, bansan kowa a nan ba, nidai zan bika naku ajin". Kusan dariya maganar ta'ta ta bashi, sai ya daure yace "Feena manya, ta ya zaki bini ajin mu bacin kema ga naku ajin nan, kuma fa zaman na ɗan lokaci ne da zarar kuka gama wannan lecture ai muna tare ko". Yayi maganar da sigar rarrashi. "To shikenan ka tafi karka makara, da zarar na fito zan same ka acan" "yauwa Feena na, sai mun fito ko" ya faɗa yana share mata hawaye da handkerchief ɗan dake hannun sa, saida ya manna mata kiss a gashi sannan ya kama hannunta ya shigar da ita cikin class ɗin, a kujerar gaba ya zaunar da ita kusa da wata ɗaliba, sannan ya juya ya fice yana yi mata murmushi. Ta bishi da kallo sai da ya kurewa ganin ta, sannan ta sauke numfashi ta kira kanta bisa table. Amar kuwa yana fita ya nufi department ɗin su, sauri-sauri yake tafiyar saboda lokaci baya so ya haɗu da fushin fitinannen Malamin nan nasu. Abu kaɗan ya rage ya kaureta saboda yadda ta tari gaban shi bada sanin sa ba, yaja ya tsaya yana kare mata kallo cikeda mamaki. Duk da yau ya fara ganin ta hakan bai hana shi gano tana cikin 6acin rai ba, ya tambayi kansa a ran sa yace "wannan kuma me na mata?" Jidda kuwa sai cika take tana batsewa akan dalilin da bai sani ba, "Ke lafiya, kika zo kika tare min hanya?" yayi mata tambayar a tsawace. Amma ga mamakin sa sai ta tintsire da dariya a madadin amsa tambayar shi, abinda ya kara harzuka Amar kenan. Ya canza hanya zuwa gefen ta ya cigaba da tafiya "dakata Amar" yaji ta faɗa cikin tsawa, sai yaji yana son sanin dalilin da yasa ta tsayar da ɗin, cak! yaja ya tsaya ba tareda ya juyo ba, hakan bai dame ta ba, ta fara magana cikin 6acin rai, "yau shekara ɗaya kenan ido na yana kan ka, tun randa na fara ganin ka naji ina kaunar ka, ina ta fara da soyayyar ka tsayin lokacin nan, ganin baka kula ko wacce mace yasa nake shayin tunkarar ka, amma yau sai gashi ka bayyana da wata mace a gabana, wannan yana nufin kana soyayya, kana kula mata, amma sai ka nuna kamar baka San komai ba" Tayi shiru sannan tayi taku ta isa gaban sa, Amar wanda yayi tsaye tamkar wanda aka dasa kallon ta yaci gaba da yi ba tareda ya iya ɗaga harshe ya mata magana ba, Jidda ta sauke numfashi sannan ta kwantar da murya lokacin da hawaye suka fara bin kuncin ta. "Amar ina son ka, ina maka son da ban ta6a yiwa wani irin sa ba, a baya na zata baka kula ko wacce mace ashe hauka nake kana da wacce kake so, kar ka yi min haka Amar, idan ka su6ucemin zan rasa rai na, shekara ɗaya nayi ina renon son ka, na roke ka karka nisanta tsakanina da kai". Ta karashe maganar cikin kuka tareda durkushewa gaban sa, hanklin sa ya kara tashi, ganin yadda mutane ke kallon su yasa dole ya sassauta zuciyar sa, yace "naji, duk naji abinda kika faɗa, amma dan Allah ki tashi kinga mutane sai kallon ki suke, ba a haka ya kamata muyi maganar ba". Jidda ta tashi tsaye tana sharar kwalla, ta kalle shi "ya kake so nayi?, haka zan cigaba da zama muddin baka saurare ni ba". Yayi ajiyar zuciya sannan ya kwatanta mata inda zasu zauna bayan lecture, yace ta same shi can. A kan haka suka raba zuciyar sa cunkus da mamaki da kuma tsoron abinda ke shirin faruwa da shi... *Yar'mutan Arkilla* ✍ [12/6/2017, 5:40 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *37* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* A ɗakin karatun ma haka ya kasance sama-sama yake jin abinda ake yi. Har aka kammala kwakwalwar sa bata ɗauki komai ba. (Allah sarki Amar) To haka ma 6angaren karatun su Feena ɗaliban sun yaba sosai da irin son da wannan da ya kawo ta yake mata, a tunanin su Amar saurayin ta ne. Maryam wadda ke zaune a kusa da ita, ita ce ta fara yi mata magana "sannu frnd suna na Maryam Muktar, da fatan zamu zama abokai". Murmushi kawai ta mata ba tareda tace komai ba ta koma kifa kanta da table. bata koma ɗagowa ba sai lokacin da ta ji shigowar Malamin da zai ɗauke su lacture. Mintuna biyar da zaman shi sai gata ta iso, Feena ita ce wadda ta fara zuwa bayan fitar Malamin su. Amar na zaune yana nazarin abin yi, saka yake yana warwarewa tunda yake bai ta6a Soyayya ba, yau da rana tsaka wannan ta bijiro masa da ita. Tambayar kansa yake anya kuwa zai iya?, to inma zai iya ta ina zai fara?". Yana cikin wannan yanayin ne ya ji an rufe masa ido ta baya, kamshin turaren da yaji ne ya tabbatar masa Safeenah ce. Dan haka yasa nashi hannayen ya janyo ta, ya zagayo da ita gaban sa kana yayi ko'karin danne damuwarsa yana faɗin "barka da fitowa yar' jami'a". dariya tayi sosai saboda yadda yayi maganar. "Allah yaya yau ina cikin farin ciki". "Naga alama ai" ya faɗa yana murmushi. Duk wannan abin da suke yi akan idon Jidda, tana kallon su kasancewar itama fitowar ta kenan daga class, ta nufo inda ya kwatanta matan. Tun daga nesa idanuwanta suka yi tozali da tauraron nata, duk da cewa babu wata fara'a ko murmushi akan fuskar tashi ita ganin kyanshi take tamkar sabon wata tsayuwar yau. Sai murmushi take, tana ji a ranta ta sami shiga ganin yadda ya bawa ganawa da ita muhimmanci har ma ya rigata zuwa wajen. Ganin Feena tayi kamar wadda aka jeho daga sama ta nufi inda Amar ɗin yake zaune. Hakan ne yasa dole taja ta tsaya tana kare musu kallo, a take zuciyar ta ta ɗauki zafi, wani kululun bakin ciki ya tokare mata a makogwaro, "dama ya kira ta nan ne dan ya ci mata mutunci?". Ta tambayi kanta, tambayar da batada amsar ta Ta kasa karasawa gurin, ta kuma kasa juyawa ta koma cikin Makaranta. A gaban idon ta Feena ta fito musu da kayan abinci, a plate ɗaya ta zuba musu, dambun nama ne wanda yaji haɗi yasha kaya, sai robar ruwa ɗaya da ta lemun fanta, nan ma kofi ɗaya ta dire a tsakiyar su. Abinda ya daɗa tunzura zuciyar Jidda kenan. Wato komai ma ɗaya suke amfani da shi. Ta jinjina lamarin a ranta, tareda kissimawa tana so ta tantance irin soyayyar dake tsakanin su. Can taji zuciyarta na gargaɗin ta akan ta hakura da wannan guy ɗin, tunda har ta ga da wadda yake so kuma ta tabbata wannan ta fita da komai da ɗa namiji zai so a jikin mace, Sai dai ita ta girme ta da shekaru wata zuciyar ta ce mata "a kul karki yarda ki sadaukar da soyayyar ki saboda wata macen, kamata yayi ki dage kema ki nemi soyayyar sa kamar yadda ta nema ta samu. Namiji ai tsamiya ne ki tsotsa ki bani in tsotsa. Hannun ta tasa ta share zafafan hawayen da suka fara jerin gwano bisa kumatunta. Igiyar so na janta, zuciyarta na dad'a yin nutso a tafkin kaunar sa. Saida ta danni zuciyarta sosai sannan ta iya takawa ta isa inda suke zaune. Dakyar harshenta ya iya dai-daita kalmomin Sallamar da tayi musu. Tare suka amsa Sallamar kamar yadda suka ɗago kai tare suna rige-rigen ganin wadda ke musu Sallamar. Wani irin faɗuwar gaba ne ya riske shi a sakamakon ganin wadda ke tsaye a gaban sa. Feena kuwa murmushi ta koma saki ganin bakuwar fuskar da bata sani ba, "sannun ku da hutawa, Amar gunka na zo". Ta faɗa kanta na kasa tana ko'karin danne damuwar ta. "Bismilla zauna" ya faɗa yana nuna mata wani 6angare na lallausar grass carpet ɗinda yake zaune akai. Zuba mishi ido tayi tana mishi kallon tuhuma, ganin duk yadda ta kai ga dannar fusatacciyar zuciyar ta Amar yana son yaga ya kular da ita. "inba haka ba Akan me zata ce tana son magana da shi sannan yace wai ta zauna a nan, yana nufin a gaban budurwar sa zasu yi maganar?" ta koma tambayar kanta. A fusace ta ɗago kai tareda zarewa bakinta sakatar da tasa masa tace... *Yar'mutan Arkilla* ✍ [12/8/2017, 7:41 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *38* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ ........... *JA'JIRTACCE*....... *25* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* "Haba Amar wai wane irin wulakanci kake so ka min ne?". Yadda tayi maganar a fusace ya bawa Safeenah da shi kanshi Amar ɗin mamaki. Bata tsaya nan ba ta cigaba "ka kuwa san hukuncin wulakanta ɗan Adam, anya kuwa kasan irin nauyin da zuciyata take ɗauke da shi akan ka?". Amar ina son ka naji ko a gabanta zan faɗa ina son ka zan iya faɗe a gaban kowa ina kaunar ka, wlh idan ka cutar da ni Allah bazai barka ba" sai ta fashe da Kuka. Kuka take sosai zuciyarta na mata raɗaɗi. Amar kam ya narke gaba ɗaya jikinsa ya sanyaye, ya kasa koda kwakwaran motsi ne balle ya iya ce mata wani abu. Safeenah ce tayi karfin halin mikewa tsaye, cikin sanyin jiki ta nufo inda take. Domin zuwa yanzu ta fahimci inda maganganun bakuwar tasu suka nufa, duk da cewa bata ta6a jin labarinta a bakin yayanta ba ta lura da akwai alakar Soyayya tsakanin su. Sai wani abin dariyar da ta lura budurwar yayan nata ta ɗauka ita ɗin Sonta yake yi ko kuma itama budurwarsa ce. "Haba mana Auntyna me yayi zafi haka?, dan Allah zauna" ta kama hannun ta ta zaunar da ita bisa carpet ɗinda suke kai Jidda sai sharar kwalla take kanta na kasa tana tunanin mafita ga wannan kaddarar da Ubangiji ya saukar mata ta son maso wani. "Yaya kaɗan bamu waje mana, ina son mu ke6e nida Auntyna". Tayi maganar tana kallon sa mikewa yayi ba tareda yace komai ba yayi gaba ya bar su a gurin ya tafi a makauce domin ko harbeshi za'ayi bai san abinda yake tunanowa ba a lokacin kawai dai yaji zuciyarsa cike da tunanuka. Kusan mintuna da tashin sa su duka ba wadda tayi magana lokaci mai tsayi can Feena ta nisa tace "kiyi hakuri zan miki shishshigi akan abinda ya shafi rayuwar ki, da fatan hakan bazai zama laifi ba?" jin bata ce mata komai ba yasa ta cigaba da magana "kafin mu tsunduma cikin maganar mu zan sanar miki da abinda na lura baki sani ba. Bata jira cewar ta ba ta ɗora wancan da kike gani ba saurayi na bane kamar yadda zuciyar ki ta baki, shi Yayana ne". Da sauri Jidda ta ɗago suka yi ido biyu da Feena wadda ita ma ita take kallo. Murmushi tayi sannan ta gyaɗa mata kai alamar tabbabarwa. Daɗin wannan furucin ya lullu6eta, farin ciki mara misaltuwa ya ziyarci zuciyarta. A 6angare ɗaya kuma kunya ce ta lullu6eta ta kara kasa da kanta tana Murmushi. Safeenah tace cikin zumuɗin son jin kokof "Ke budurwar shi ce?" Jidda ta kaɗa mata kai alamar "a'a. Mamaki ya kama Feena kuma bata 6oye ba tace" to amma naji kina maganar kina son sa". Nan Jidda ta warwarewa Feena komai akan irin son da takewa yayanta Amar da tsayin lokacin da ta ɗauka tana yi mishi shi. Allah sarki Feena gwanar tausayi hadda yar kwalla ta rarrashi Jidda ta bata hakuri tareda tabbabar mata cewa insha Allah zata shawo mata kan Amar zai so ta kamar yadda take kaunar sa. Sosai taji daɗin alkawarin da Feena ta mata nan da nan ta saki jiki da ita suka hau hira da dariya har ma tana cin abincin nasu da Safeenah ta saka ta ci dole. A haka ta ciro wayarta ta saka kiran layinsa, ringing biyu a na uku ya ɗaga wayar bata bari yayi magana ba tace "kazo mun gama maganar" yayi mamaki sosai yadda yazo ya same su sun baje sunata hira da wadda ta zo tana ta kuka, "hmm Feena hoo" ya faɗa a zuciyarsa cikeda mamakin me ta gaya mata wanda ya faranta mata haka. Zaman sa keda wuya Jidda ta mike ta ɗauki jakar ta ta tafi tana murmushi, ya bita da kallon mamaki ita kuwa Feena dariya take kyalkyalawa. Saida ta kurewa ganinsa sannan ya juyo ga Feena "ke me kika bata ne naga duk haukar tata ta kwanta har tana murmushi" ta kwashe da dariya hadda kwanciya saida ta ɗora kanta bisa cinyoyinsa sannan ta fara magana "abinda take so na bata yaya" ya bata da kallon mamaki "abinda take so?" ya tambaya yana kallon fuskarta. "eh mana kasan me Jidda sunan ta kuma tanada kirki, ta tsinci kanta cikin sarkakiyar so da kaunar ka. Ni kuma a matsayin kaunar ka na yi mata alkawarin samun ka, a takaice dai na gaya mata kaima zaka so ta. Dan Allah yaya ka tausaya mata ka so ta, kasan shi so mummunan akasin sa shine ka nemi wanda kake yiwa shi ka rasa". Ido kawai ya zuba mata yana kallon yanda le6enta yake motsawa, kwakwalwarsa na jinjina lamarin "yaushe Feena ta San wani abu so har tasan yadda ake ji idan aka kama da shi?". Kallon da yake mata ne ya tabbar mata da tunani yake, ta hura masa iskar bakinta a fuskarshi. Firgigit ya dawo daga dogon tunanin tareda sauke nannauyan ajiyar zuciya. "Me yasa kika gaya mata hakan nan, shin kina da tabbacin zan so ta ne da kika mata alkawari bayan kin san girma da darajar alkawari?" yayi mata tambayoyin ne yana kallon cikin kwayar idonta, domin kan cinyarsa kanta yake ita ɗin ma shi take kallo. Tambayoyin da ya mata ne suka haddasar mata da mutuwar jiki, tunaninta ya sarke ta kalle shi duba na nutsuwa tace "saboda na yarda da kai, nasan zaka so ta saboda ni, Jidda tana cikin wani hali na soyayyar ka idan bata sami so daga gareka ba zata iya samun matsala" Kamar wanda aka data haka ya kame kam idonsa akan ta, anya kuwa Feena tasan matsala ta so, anya tasan asalin abinda ke zuciyarsa, ta yaya zata kyautar da zuciyar da ba tata ba?. Akan me zata ɗora shi akan hanyar da bansan ta ba?"... *Yar'mutan Arkilla* ✍ [12/8/2017, 9:10 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: .......... *JA'JIRTACCE*....... *39* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍ *FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* Hannayensa ya saka ya tashe ta zaune, suka fuskanci juna a kwayar idanun shi ta fahimci babu wasa a tattare da shi. "Feena". Ya kira sunan ta da murya mai sanyi da rauni wadda bata ta6a jin shi da irinta ba. Bata iya amsawa ba sai dai kanta da ta ɗaga tana kallon yanayinsa bai damu da rashin amsawarta ba ya fara magana... "ban ta6a yin Soyayya ba kin sani, ban san yadda take ko yadda ake yin ta ba, ban ta6a jin so na wata ya'mace a zuciyata ba sai na Umma da ke!" ya nuna ta da yatsa sannan ya ɗora "sai kuma Mommyn mu (Yusra). Yau kin zo min da maganar na so wata" da sauri ta ɗago ta kalle shi jin muryar shi ta canza, tsoro ne ya lullu6eta ganin yadda yanayinsa ya sauya idanun shi suka kaɗa suka canza launi daga fari zuwa ja... Hankalinta ne ya tashi, hawaye suka fara bin kuncinta Sam bata ji daɗin ganin halin da ta jefa yayanta ba. Maganar sa ce ta katse mata tunani "zan so ta Safeenah, zan so wannan budurwar da naji kin kira da Jidda. Amma kamar yanda kika faɗa zan so ta saboda ke ne". Yanayin yadda yake magana kaɗai ya isa ya ya baka tausayi. Kuka ne ya kwace mata ganin ta tilasta yayanta yin abinda bai yi niyya ba, ta saka shi yin abinda bai ta6a yi ko tunanin yi ba. "Yaya ta faɗa a raunane sannan ta rungume shi ta kara fashewa da kuka. "kayi hakuri Yayana na shiga hurumin da ba nawa ba, kuskure na ne dana manta kai kake ikon zuciyar ka ba ni b... Hannun sa yasa ya toshe mata baki bai barta ta karasa faɗar abinda ke bakinta ba. Feena ni ɗin nan naki ne, karki ta6a tunanin da akwai abinda zaki ce kina so inyi kuma ban yi shi ba, muhimmancin ki da darajar gare ni sun wuce nan Kanwata". ya kara kankame ta jikinsa dukkanin su kuka suke yi, lokaci mai tsayi suka ɗauka a haka kafin su saki juna ita kam kasa jure zaman tayi ta koma ta kwanta. Shi kuwa Amar zaune yake yana kallon yanayinta duk tayi sanyi kamar wadda zazza6i ya kama. Sai ya fara jin haushin kansa da bai amince kai tsaye ba gashi ya saka Kanwar shi kuka. Rarrashinta ya shiga yi yana bata baki, tareda nuna mata abinda zai yi fa ba komai bane kuma shima yana son Jidda ɗin sosai tunda kanwar shi ta yarda da ita. Haka dai yayi ta lalla6a ta har zuwa lokacin komawarta lecture yayi ya koma raka ta har kan sit ɗinta yana rike da hannunta zaunar da ita sannan ya fito ya koma gurin nan ya zauna zaman jiran fitowar ta domin shi baida wata lecture sai gobe. ************************************ Tun daga wannan Ranar Soyayya ta fara kulluwa tsakanin Jidda da Amar, a School kullum suna tare su Uku haka zaka gan su Koda yaushe cikin farin ciki da nishaɗi. Sau biyu tana zuwa gidan su a matsayin kawar Safeenah a can ta kara samun tabbacin su ɗin Yaya da Kanwa ne. Domin a lokuta da yawa tana tsintar kanta da zargin alakar Amar da Safeenah, a cewar ta shakuwar tayi yawa soyayyar da yake nuna mata ta zarce wadda kowane wa yake nunawa kanwar sa. Sau tari danne zuciyar ta take, idan suna wani abu a gabanta kallon masoya take musu. Masoyan ma na musamman waɗanda suke da wahalar samu a wannan lokacin da shi da ita ko wanne yana iya ko'karin sa wajen nunawa ɗan'uwan sa so da kulawa. To haka dai suka yi ta mulmula rayuwa lokaci na tafiya safina an shekara har da ɗorin watanni jami'a tana level 2. Amar da Jidda suna final year. I zuwa yanzu ya fara son Jidda sosai kamar yadda take son sa, Iyayen su ma sun san da maganar har an sanar da sun kammala karatun su za'a musu Aure. Jidda sai jiji da kai ake a Makaranta ta sami cikar burinta Amar ya zama nata ita kaɗai. Feena an kare rawar kai rayuwar Makaranta ta fara mata zafi, GA karatu ga katuwar katangar da take gani ta shiga tsakaninta da Yayanta a School koda sun fito sai su ke6e da Jidda su yita hira abinsu su kyale ta zaune ita kaɗai. Wannan wani sabon salo ne da Jidda ta kirkira na nesanta Amar da Feena a Makaranta, sai take nuna masa bai kamata suna hirar Soyayya a gabanta ba kar su shiga hakkinta kuma ma bazasu sami sakewa da kyau su bayayyawa juna Soyayya ba. Haka suke mata kullum tun abin baya damunta har ta fara shiga damuwa. Yau ma kamar kullum zaune take bisa carpet ɗinsu a garden ɗin School inda suka saba zama. Ta zuba musu ido ko kiftawa bata yi daga inda take tana hango su sai zuba hira suke suna dariya. "Safeenah Y?" ta tambayi kanta "me yasa kika ɗauki farin cikin ki kika kyautar ga wata? Me yasa kika yarda da mace akan gudan jinin ki?, me yasa???" Sai kawai ta fashe da kuka... To fah🤔 Fans ku taya ni ganin wannan drama 🤣 *Yar'mutan Arkilla* ✍ [12/12/2017, 9:46 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *40* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ We are here to educate motivate and entertain our readers. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ Amar da Jidda kam suna can suna kwasar love, sam basu san halin da take ciki ba. Zumbur ta mike ta ɗebi jakar ta, Allah yasa key na motar su yana hannunta. Da gudu ta ratsa cikin makarantar kamar wacce aka yiwa mutuwa kuka take sosai har ta isa parking space da remote ta fara buɗe lock na motar sannan ta buɗe ta shiga. Hannun ta bai wani faɗa da tukin ba dan bata maida hankali ba, sam bata ta6a tuka mota ita kaɗai ba. Haka ta figeta ta tafi cikin kunan rai. Ikon Allah ne kaɗai ya kai ta Gida a motar ma tafe take tana kuka. Wani mahaukacin horn da ta saki gaba ɗaya layin saida ya ɗauka, da gudu Mudi ya buɗe kofar bayan ya tabbabar motar gidan ce. Kamar zata tashi sama haka ta shiga gidan gurin tsayuwa ne birki yaki mata, a yadda ta zo haka ta kauru da wata sabuwar motar Dady dake ajiye a gurin. Sai ji kake gau... Da gudu Momy Yusra ta fito itada ma'aikatan suka yi rige-rigen isa gareta, hankali tashe suka buɗe motar "innalillahi! wa inna ilaihi raji'un" abinda Momy ta faɗa kenan cikin kuka ganin Safeenah kife akan sitiyarin motar bata ko matsawa. Jikinta har 6ari yake ta fara kiciniyar ɗago ta, "ku taimaka min Feena zata mutu" Momy ta faɗa cikin kuka, Iya ce ta kama mata ita suka sakata a wata motar. Ilu ya ja su sai asibiti har suka isa Momy bata daina Kuka ba, tana rungume da Feena wadda take ji tamkar ta tashe ta. Da isar su nurses suka taresu, akan kujerar nan ta marasa lafiya suka ɗora ta suka gungura ta zuwa cikin asibitin. Ba jira aka shigar da ita emergency word, likitoci biyu ne suka hau kanta dressing suka fara yi mata inda kanta ya fashe gurinda ta bugu. Sannan suka hau aikin ceto rayuwar ta. Momy sai Kuka take Iya na Rarrashinta, ko mayafi babu a kanta daga ita sai kayan jikinta sai ɗankwalin kanta. Haka tana so ta kira Dady ta sanar masa amma bata zo da waya ba. 6angaren Amar kuwa time ɗin shiga lecture ne yayi suka juyo suka dawo inda suka bar Feena sai basu ganta ba, daga nan hankalinsa ya fara tashi. Tare suka nufi department ɗin su dan ganin ko ta koma class ne. Can ma wayam babuta babu dalilin ta. Da sauri ya nufi inda suka yi parking motar su kamar zai tashi sama. Duk yadda Jidda taso su jera sai da ya bata rata dan yadda yake tafiyar bada wasa bane. Wani irin bugu yaji zuciyarsa tayi tamkar an doka masa guduma a kirji, sakamakon ganin babu motarsu a inda yayi parking. Bisa dole ya kai hannu Ya dafe saitin zuciyarsa saboda yadda yake ji kamar zata faso kirjin ta fito. Ya tabbatar ba lafiya ba, dole akwai wani abu domin Feenarsa bata ta6a yi masa haka ba. Dai-dai lokacin Jidda ta iso inda yake, ganin yanayin sa ne ya ɗan dakusar da ita ga korafin da taso ta yi mishi na ya barta baya. Bangare ɗaya kuma haushi ne ya lullu6eta ganin yadda karamar yarinya ke juya mata saurayi. Wani irin tsaki taja kamar zata tsinke harshenta, lokacin da taga ya ciro waya yana searching number ta tabbatar ita zai nema. "Hmm lallai Amar yanzu a kan kanwar taka kake duk wannan damuwar?, ai ba cewa aka yi wani abu ya same ta ba, kawai fa dan taga ka damu da ita ne yasa take duk wannan abun duk inda ta tafi ai zata dawo ne. Dan Allah zo mu tafi." Amar dake nema layin Feena, wayar har ta gama ringing ta yanke ba'a d'aga wa. Sai yaji saukar kalaman Jidda tamkar tana yi masa feshin tafasashshen ruwa a kirji. "Ke! Ya daka mata tsawa, tareda ɗaga hannunsa sama kamar zai daketa sai kuma ya sauke tareda furzar da wata iska mai zafi. Ya nuna ta da yatsa yace cikin tsananin fushi da 6acin rai "wacce ce ke da har kika isa ki shiga tsakani na da kanwata, Kim kuwa San wace ce Safeenah?, tabbas baki sani ba da bazaki fara tunkarata da magana irin wannan ba. To ina miki kashedi na karshe akan aibata kanwata ko faɗar wani abu da bai dace ba a kanta. In ba haka ba... " bai karasa ba ya juya a fusace ya kama hanyar ficewa daga School ɗin da kafa. Tamkar wadda aka dasa haka ta sandare, zuciya da kwakwalwarta sun cika sun batse da mamakin Amar. Fargaba da tsoro suka koma kama ta." Wannan wace irin Soyayya yake wa Safeenah?" ta san ba wanda zai amsa mata wannan tambayar. Wasu siraran hawaye suka fara zariya a kumatunta, tana son Amar duk tsanani tana ji a ranta zata iya jure komai domin shi. Amma wannan ya gagare ta, ta kasa hakura da kakkarfar alakar dake tsakanin shi da kanwarsa. Komai yayi mata zata iya shanyewa amma idan ta ga yadda yake rawar jiki da Feena yana faranta mata sai taji ta kasa jurewa duk da tasan matsayinta gare shi na kanwa ne. Kuka mai karfi ya kwace mata. Amar yana fita gate ɗin makarantar ya tari mai mashin ya hau bayan ya kwatanta masa inda zai kai shi. Karo na farko daya fara hawa mashin a rayuwarsa. Har wani jiri yake ji yana ɗiban sa daga sama, da sauri ya kulle idon sa gam, bai koma buɗe su ba sai da yaji mai mashin ɗin yana cewa "ranka ya daɗe mun zo layin... *follow us on this details :* ---- *like our facebook page :* ↓↓ *Fb.me/zamaniwritersassociation* ---- *check our blog's* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *your comments and reports are highly welcome on this email address:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com* *Nasmat* ✍ [12/15/2017, 7:34 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *41* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ We are here to educate motivate and entertain our readers. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ Ai kuwa gwara da yayi mishi maganar domin mai babur ɗin ya ɗan wuce gate ɗin gidansu kaɗan. Da sauri ya umarce shi da ya ajiye shi nan, hakan kuwa aka yi ya tsayar da babur ɗin shi kuma ya sauka yana kallon gate ɗin gidansu bugun zuciyarsa na kara tsananta. Gudar ɗari biyar ya ciro daga aljihunsa ya bawa mai babur, bai tsaya jiran canji ko jin wani abu ba ya juya ya tunkari kofar gidan. Mai babur kam sai washe baki yayi yabi shi da addu'ar "na gode Allah ya saka da alkhairi" da isar sa bakin gate ɗin ya fara bugawa yana haɗawa da kiran sunan mai gadin wato Mudi. Jin muryar Amar ce yasa ya buɗe kofar cike da jimami, tun kafin ya shiga yake tambayar Mai gadin "Feena tana ciki kuwa?" alamun tashin hankali karara a fuskar shi, kamar wanda yasan abinda ya faru. Amma tambayar da yayi ta nuna baisan komai game da hatsarin da ta samu a cikin gidan ba. "Mudi" ya kira Sunan yana girgiza shi domin ya lura kamar wani tunanin yake. Mudi yai firgigit! Ya dawo hayyacinsa "baka ji tambaya ta bane?" Amar ya koma tambayar sa fuska cike da damuwa. Mudi ya nisa yana cewa "to ka shigo daga ciki mana in yasa sai kaji komai a nutse." "ya kalle shi kallon tuhuma kafin yace "me ya faru da kanwata?" yayi tambayar ne saboda ganin damuwa da jimami karara a fuskar Mudi. Ya kaɗa kai yana share kwallar da ta gangaro masa a kumatu. Sannan ya dubi Amar ya ce "kayi hakuri Amar komai mukaddari ne daga Allah, ban san me ya tashi hankalin kanwarka ba sai dai na ganta ta shigo cikin matsananciyar damuwa. Tunda nake ban ta6a ganin Uwar ɗaki a yanayi irin wannan ba. Yadda take tuka motar ma ya bayyana karara cewa tana cikin damuwa ne... " Mudi ya kwashe duk yadda abin ya faru ya gaya wa Amar, daga karshe ya sanar masa suna Asibiti. Tunda ya fara maganar Amar bai koma iya ɗaga harshensa da sunan yayi magana ba, haka bayan ya gama gaya masan ma bai ce komai ba ya juya yana layi, yana dafa bango. Da sauri Mudi ya kai masa agaji ta hanyar riko gefen kafaɗarsa domin a yadda yake ya tabbata idan ya bar shi kasa wanwar zai zube. Amar ya fizge hannunsa daga rikon da Mudi yai masa, kana ya wuce cikin gidan. Kai tsaye inda motar tasu take ya nufa. Dama a buɗe take yana zuwa ya faɗa cikin ta yai mata key. Dai-dai nan Mudi ya isa gare shi yana faɗin "a'a Amar, bai kamata kayi tuki a wannan yanayin ba, ka dube kafa..." "buɗe min gate." Amar ya buɗi bakin sa dakyar ya cewa Mudi. Mudi yayi jugum kamar ba zai motsa ba yana jinjina abin a ransa "kar fa azo ayi faɗuwar guzuma" yace a ransa ya na kallon Amar da yanayinsa. Ɗago kai yayi cikin wani yanayi ya koma maimaita abinda ya faɗa "buɗe min gate nace." sauyin da Mudi ya gani a idon Amar yafi komai tsorata shi, domin idon sun kaɗe sun canja kala daga fari zuwa ja, wasu igiyoyin jini suka rarratsa a cikin kwayar idon na shi. Babu shiri ko neman karin bayani Mudi ya nufi gate da saurin sa tun mummunan abu bai faru ba. Domin a yadda yaga Amar zai iya yin ɗaya a cikin biyu idan ya dakatar da shi, ko dai ya 6alla kofar ya fita ko kuma shima ya faɗar masa a nan. Domin su ganau ne ba jiyau ba, dangane da irin Soyayyar dake gudana tsakanin Yaya da kanwar. Yana ɗaga gate ɗin Amar ya figi motar nan ya cilla kanta waje, ji kake kiiiiiii... Karar murɗe sitiyari domin yin kwana a ɗora motar bisa titi. Mudi ya dafe kai yana faɗin "ya Allah ka kare wannan bawan naka ka kai shi inda ya nufa lafiya" (to nima dai Nasmat addu'ar da na yiwa Amar kenan). A Asibiti kuwa cikin mintuna talatin Likitocin nan suka sami nasarar ce to rayuwar Safeenah. Bayan numfashinta ya dawo dai-dai suka ɗora mata drip da allurar bacci saboda jikinta ya saki kwarinsa ya dawo. Hankalin Momy da ɗan kwanta, tana zaune gefen gadon hannunta rike da na Feena tana kara karanto mata wasu addu'oi tana tofa mata a jiki. *Nasmat* ✍ [12/16/2017, 10:15 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *42* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ We are here to educate motivate and entertain our readers. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ Cikin matsanancin tashin hankali ya isa asbitin. Kai tsaye office ɗin babban likitan ya nufa domin shine family doctor ɗin su. Dr. Kamal na zaune yana nazarin wasu takardu na resold ɗin gwajin wani majinyaci, sai ji yayi an banko kofarshi an shigo ba tareda neman izni ba. Ya ɗago kai da sauri a ɗan razane. Amar ya gani tsaye a gabansa yana sauke manya-manyan numfashi hatta sallama da ta wajabta bai yi tunanin yi ga likitan ba balle gaisuwa. "Dr. Wane hali kanwata take ciki?" tamayar da ya jefa masa kenan bayan ya isa gaban teburin likitan ya ɗora hannayensa duka biyu akai sannan ya zubawa Dr. Ido yana jiran yaji ta bakin sa. Dr. Kamal ya san komai gameda soyayyar yaya da kanwar nan, domin shine likitansu. Ba tun yau ba ya saba ganin ire-iren hakan daga kowanen su idan ɗan'uwan sa bashi da lafiya. Wannan yasa ya mike daga kan kujerar sa ya zagayo inda Amar yake tsaye yana hawa da sauka na numfashi wato yana jan iska yana feshewa cikin matsananciyar damuwa. Likitan ya dafa kafaɗarsa ya fara rarrashin sa yana kwantar masa da hankali, tareda tabbatar masa ba wani ciwo taji sosai ba. Duk wannan jawabin na likita ai sawa Amar nutsuwa ba daga karshe ya kama hannunsa ya kai shi har ɗakin da suka kwantar da Feena. Har lokacin da suka shiga Momy na nan a inda take zaune, hannunta rike da na Feena idanunta sun yi ja sosai alamar kuka tayi ba kaɗan ba. Likitan yayi sallama Amar kuwa da sauri ya isa ga kanwarsa dake mike akan gadon kamar matacciya. Feena! Ya kira sunanta da karfi bayan yayi zaman dirshan bisa gadon yana kokarin tallbo ta zuwa jikinshi. Da sauri likita ya dakatar da shi a ɗan tsawace yace "kai Amar, baka gani da karin ruwa a jikinta ne?" Amar ya dubi hannun Feena wanda aka ɗaura mata karin ruwan hawaye tam a idonsa ya koma maida kallonsa ga likita yace "ya zan yi Dr. Ina son jingina ta a jikina, ina son na ra6eta Dr. Bazan iya kallonta nesa da ni a wannan yanayin ba." tausayin shi ya kama Momy da likitan Momy ce ta mike a hankali ta ɗaga kan Safeenah ta ɗora bisa cinyarsa, hannun ta da take rike ta mika masa ya kama hannun ya rike shi gam hawaye na ci gaba da gudana a kumatunsa. Momy ma kukan take tausayin kanta da Amar take ji idan suka rasa Feena ta kasa tantance ida da shi wa zai fi shan wuya. Likita kuwa jikinsa ne yayi sanyi likis ganin inda soyayyar yan'uwantaka ta gaskiya da gaskiya take, ya kurawa Amar ido lokacin da aka ɗora masa ita a ciyarsa ya lura ya sami salama ga abinda yake ji a zuciyarsa domin yadda yake sauke ajiyan zuciya manya-manya tamkar wanda yayi gudu na kilo meters. Ya rumtse ido yana nazari "shin shima da yanada kanwa zai so ta haka?" (tabbas wannan abin tambaya ne likita, inma dai na tambaye ku readers shin zaku iya son kannenku kamar yadda Amar yake son Feena ta ciki da wane? Ina jiran amsoshinku). Dr. Kamal kam juyowa yayi ya fice daga ɗakin yana sharar kwalla, 6angare ɗaya kuma yana jin rayuwar yaran na ta6a zuciyarsa. Karfe huɗu na yammacin Feena ta farka, a lokaci an jima da cire mata ribar karin ruwan nan. A hankali ta fara buɗe idanunta, da fari dishi-dishi take gani kafin daga bisani ganina ya dawo Momy ta fara tozali da ita zaune gefen gadon da take kai wanda har yanzu bata tantance na ina bane, tana kokarin tashi taji an yi gaggawar ɗago ta cikin azama ya manta ta a kirjinsa "Alhamdulillah Momy kanwata ta tashi, Feena ta dawo hayyacinta." sosai ta gane Yayana ne mai maganar da sauri ta ture shi tana ja da baya har ta jingina da jikin Momy. Domin ta tuna komai ba abinda ta manta dangane da abinda ya faru. Momy ta rungume ta cikin farin ciki tace "Alhamdulillah my Feena, ya jikin naki?" sai a lokacin ta fahimci cewa a asibiti suke. Kanta taji ya tsuke kamar a ɗaure yake ta kai hannu tana shafawa ta tabbata ɗauri ne akan ta "kenan ciwo taji?" ta tambayi kanta "Feena" ya kira sunan ta a raunane cikin mutuwar jiki da tsoro na ganin yadda tayi mishi. Bata ɗago kai ba kamar yadda bata amsa masa ba. Sai a lokacin Momy take tambayar su. "me yasa kika yi wasa da rayuwarki Feena, me ya kai ki yin tuki bayan kin tabbatar hannunki bai faɗa ba?" a madadin ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka tareda kara kankame Momy a jikinta,wani irin kuna take ji a rayuwarta. Ganin hakan yasa Momy juyowa ga Amar wanda yake a sandare cikin wani yanayi. "Amar ina hankalinka yake da har zaka bar Safeenah ta ɗauko mota bayan ka tabbatar bata kware ba, yanzu da ace a hanya ne wani mummunan hatsari ya auku ya zamu yi?" ya rasa taya zai fara yiwa Momy bayani domin shi kan shi bai san dalilinta na yin hakan ba. "wlh Momy ban sani ba, ni kaina sai neman ta nayi na rasa shi yasa na dawo gida hankali tashe." ya juya gareta yana shirin janyo ta jikinsa yana faɗin "me yasa kika yi haka kanwata, waya ta6a min ke?" Da karfi ta kwace jikinta ta koma cikin jikin Momy tareda tsananta kukanta. Iya da Momy sai rarrashin ta suke Amar kuwa wani sabon tashin hankalin ne ya same shi domin tunda yake Safeenah bata ta6a yi masa kwatankwacin hakan ba. "Ace da kansa yana junta tana kwarewa?" Momy ma dai mamakin ne ya kamata domin ganin sabon lamarin da bata ta6a gani ba. Ta kalli Iya tace "iya ki je gurin Dr. Kice ya zo yarinya ta farka." dattijuwar ta amsa da "to" ta tashi ta fita. A hankali Momy ta ɗaga Feena a jikinta ta gyara mata zamanta tana kallon ta sai Kuka take taki tayi shuru haka Amar ma ganin ya yi ta yi mata magana ta kyale shi, ga kuma fisgewar da take idan ya rikota kawai sai shima ya fashe da kuka. Momy Yusra hankalinka ya tashi ta rasa wa zata rarrasa a cikin su duk wanda ta yiwa magana ba ya shiru sai Kuka suke kamar wasu kananan yara. *Nasmat* ✍ [12/16/2017, 11:19 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *43* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ We are here to educate motivate and entertain our readers. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ "Wai meye haka ne?" ta faɗa a tsawace cikin ɗaga murya da nuna 6acin rai. Sannan ta ci gaba da magana "haukata ni kuke so kuyi, akan me zaku saka ni gaba Kuna kuka y, me aka yi muku." ganin 6acin ran Momy yasa duk suka yi tsit! Shiru ne ya ratsa ɗakin na wasu dakiku babu wanda yayi yunkurin yin magana a cikin su kowa da abinda yake sakawa a ransa. Suna cikin wannan halin likita ya shigo tareda Iya da Dady wanda zuwansa kenan. Sun yi mamakin ganin sa tunda ba gaya masa suka yi ba, shine ya gaya mata ai da dawowar shi Mudi ya gaya masa, yayi takaitacciyar maganar ne idonshi akan Feena. "sannu Safeenah" da kai ta amsa masa domin yadda take ji ba zata iya magana ba, likitan ya duba ta tareda yi mata yan'tambayoyi shima dai bai sami amsar ko ɗaya ba. Momy ta bashi hakuri ta gaya masa fushin Amar ne ya shafe shi domin ta lura shine ya ta6a Feena." likita yayi murmushi bayan yan gajerun rubuce-rubuce ya bawa Dady takardar yana cewa "magungunan da zata bukata ne, a saya mata su Allah ya baki lafiya Feena." ya karkare yana mata murmushi yayi musu sallama ya fita. "Dady ya ce to ai sai ku tashi mu tafi." ganin yanayin Amar yasa Momy tace bata yarda tayi tuki ba sai dai driver ya kai mishi motar gida sannan shima ya dawo ya ɗauki tashi motar. Su kuma zasu tafi a motar Dady. Nan fa aka shiga wata sabuwar drama, domin Feena karuwa tayi kai da fata ba zata shiga mota ɗaya da Amar ba. Tun Iyayen na ɗaukar abin wasa har suka tabbata da gaske take, tun Dady na rarrashin ta har ya dawo ya 6ata rai ya tubure mata da faɗa abinda bai ta6a yi mata ba, ita kuwa sai kara fashewa da kuku tayi tana buga kafarta da kasa bisa dole ta buɗe bayan motar ta shiga inda ta tarar da Amar yana ta kuka domin shi tuni ya daɗe da shiga. Dady ya zaga ya shiga mazaunin driver bayan ya buɗewa Momy gidan gaba ta shiga. Ya tashi motar ranshi a 6ace suka kama hanyar gida. Ba Amar ba ba Feena ba duk sun cika motar da koke-koke ba daɗin ji sai tashin hankali. Basu koma ce musu komai ba suka dukkan su suka kyale su. Da isar su gidan kamar jira take da tsayar motar ta falle kofar ta fita da gudu ta shige gidan kai tsaye ɗakinta ta nufa ta faɗa bisa gadonta ta koma rushewa da wani sabon kukan Har ga Allah kukan da taga Yayanta yana yi ciwo yake mata sai dai bazata iya saurarar shi ba tunda har yafi son wata a kanta, bayan da ita kaɗai yake kula da ita. Amar kuwa dakyar ya fito daga motar yana matsar kwalla ya wuce ciki kaman baya son ɗaga kafarsa. Iyayen suka bishi da kallon tausayi, sannan suma suka rufa masa baya da shigar shi ɗakinsa ya nufa, shima dai kwanciyar yayi yana mai cigaba da kuka tareda zurfafa tunanin neman dalili ko laifin da yayiwa Feena da har bata son ganin sa. Nan da nan zazza6i ya rufe shi kafin kace me jikinsa ya fara makyarkyata, dakyar ya iya jan blanket ya rufe jikinsa da yake jin saukar sanyi kamar wanda ake zubawa ruwan sanyi a jiki. Kamar mintuna goma da kwanciyar sa Momy ta turo kofar ɗakin ta shigo da sallama. Sam baya iya amsa mata domin yana nan rufe da mayafin jikinsa sai kyarma yake yana karkarwa. Gabanta yayi mummunar faɗuwa da sauri-sauri gudu-gudu ta isa gare shi tana kiran sunansa "Amar! Amar! Me ya same ka?" cikin in-ina da rawar murya yace "Banida lafiya Momy, Feena ta tsane ni sam bata son ganina bata bukatar zama kusa da ni, karshena ne kawai yazo Momy na san mutuwa zan yi." da sauri ta rufe bakinsa da tafin hannunta ta fashe da kuka sannan ta juya da gudu ta fice daga ɗakin. Amar yaja numfashi dakyar ya furzar muryarshi na rawa yake sambatu "kar ki yi min haka kanwata, zan mutu koda ba kiyi kewata ba ni zanyi kewar ki koda ba kiyi kukan rashi na ba ni zan yi kukan rashin ki. Ina kaunar ki Safeenah kin riga kin zama gudun jini na idan babu Ke jinin zai daina gudana, dan Allah ki zo gareni zo amanar Ummata." yana cikin wannan halin ne suka shigo ɗakin Momy da Dady harma da Safeenar wadda Momy taje ta gaya mata ga Yayanta can zai mutu saboda rashin kula shin da tayi. Da gudu ta faɗa jikin sa tana kuka "Yaya dan Allah ka tashi, idan ka tafi nima zan bika ka tashi Yayana wlh na bari bazan koma ba." zumbur ya mike jin wadda ke magana kuma take kan shi. Bai jira komai ba ya yakice bargon ya rungume ta. Suka kankame juna suna maida numfashi domin kowannen su yaji a jikinsa, sun tabbatar wa kansu cewa ɗaya ba zai iya rayuwa babu ɗaya ba. Kuka take sosai tana ta6a kumatunsa "Yaya zazza6i ne ya kama ka? Momy dan Allah ki bashi maganin zazza6i." Dady ya girgiza kai ya juya yana faɗin idan yasha maganin ke da shi Ku same ni ɗaki ina son ganin ku." Momy kuwa juyawa tayi ta fita dan ɗauko masa magani har zuwa lokacin suna nan rungume da junan su sun kasa rabewa ji suke kamar in suka rabu ba zasu koma haɗuwa ba. Cikin hakan nan yake raɗa mata "dan Allah kar ki koma gudana kinji kanwata." "bazan koma ba yaya, wlh bazan koma ba bana so wani abu ya same ka." "Dakin kyautawa kanki, ɗaga shi yasha magani." Momy ce mai maganar cikin murmushi... *Nasmat* ✍ [1/7, 8:05 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *44* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ 📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION 📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com A hankali Feena ta sake shi suka dai-daita zamansu bisa gadon, ta kar6i maganin daga hannun Momy ta ba shi. Ba musu ya kar6a ya sha, dama maganin a 6alle yake. "Sannu yaya." ta faɗa tana kallon fuskarshi. Murmushi yayi mata sannan ya mike yana karasa yaye mayafin da ya rufu da shi, ya kama hannunta itama ya mikar da ita bayan ya sauko daga kan gadon yana faɗin "muje muji kiran Dady ko?" Momy ta riga su ficewa daga ɗakin itan ma ɗakin Dady ta nufa suka rufa mata baya. Zaune yake yana nazari akan wannan sabon lamarin da basu ta6a gani ba, tunda yaran suke basu ta6a samun sa6ani makamancin wannan ba, kome ya haddasa hakan?. Dai-dai nan yaji sallamar matarshi Yusra ya amsa sallamar tareda ɗago kansa. Ganin yaran a bayanta yasa ya 6oye murmushinsa, ya ɗan haɗa fuska tareda juyar da kansa gefe. Abinda yasa yaran suka kara shan jinin jikinsu kenan, domin tunda suke basu ta6a ganin wannan sauyin a tattare da shi ba. Haka suka karasa jiki a sanyaye suka zauna gefen shi akan carpet, kawunan su sunkuye a kasa. Momy kuwa a kujerar dake gefen daman shi ta zauna. Amar ne yayi karfin halin cewa "Dady gamu mun zo." yayi maganar ne dan ganin Dadyn yayi kamar bai san da shigowar tasu ba. Ya gyaɗa kai yana faɗin "na ganku" ya tattara kallonsa ya mayar kan Feena babu wasa ko alamar ta ya ce "ina son sanin dalilin da yasa kika baro Amar kika ɗauko mota ke kaɗai kuma cikin tashin hankali me ya faru, me aka yo miki?" Safeenah tai narai-narai da ido sai hawaye ta riga tasan Dady ta kuma san yadda ya tsani a mishi karya kanta na sunkuye a kasa ta fara share kwalla "kayi hakuri Dady bazan sake ba." idonsa a kanta yace "amsar tambayar da nayi miki kenan?" "a'a Dady" "to tambayar ce batada amsa kika maye gurbin ta da wannan?" tayi shiru shima bai koma cewa komai ba sai ido da ya tsare ta da su. Amar ma ita yake kallo domin har yanzu baisan dalilin da yasa ta aikata hakan ba bai kuma san dalilinta na yin fushi da shi ba, tabbas yaji daɗin wannan tambayar kuma shima yana so yaji amsar da zata bayar. Momy ma ita take kallo cikin ina-ina ta fara magana "dama..dama shine..." Nan ta kwashe duk abinda ya sanyata fushin ta gaya musu. Dady da Momy kamar zasu yi dariya musamman a kalmar ta ta karshe inda take cewa "tun daga ranar idan aka fito baya kula ni sosai sai dai su ke6e shida Jidda su yi ta hira ni kuma su bar ni ni kaɗai." Dady ya kalle ta dariya kunshe a bakinsa yace "wannan shine dalilin da kika tashi kashe kanki a kan sa?" ta gyaɗa kai tana share kwalla. Dady yau shiru yana nazarin halin kurciya irin na Safeenah. Shi kuwa Amar tuni ya shiga wata sabuwar damuwar zullumi da tsoro suka baibaye shi, cewa yake a zuciyarshi "kar fa in zamo sila na tarwatsa 'amanar Ummana', babu shakka ban kyauta ba." a fili kuwa hawaye ne sharkaf a kan fuskar shi ya tashi daga zaunen da yake ya tsuguna a gabanta suna kallon juna. Ganin yadda take Kuka ya kara razana shi sai yaji gaba ɗaya ya tsani Jidda a lokaci ɗaya ta fita rayuwarshi. Yasa hannayensa ya tallabo kumatunta ta ɗago kanta tana kallon shi sannan ya fara magana "ki yi hakuri Feena tabbas nayi kuskure sam ban kyauta miki ba, amma dan Allah ki yafe min kanwata. Idan nayi miki laifi ki yi mini kowane irin hukunci amma pls kar ki koma yunkurin hallaka kanki, koda duka na zaki yi ki dake ni ke ki min komai ma amma dan Allah karki yi abinda zai shafi rayuwarki. Feena ke amana ta ce dan Allah kar ki koma cutar da kan ki a kaina Umma bazata ji daɗi ba kin ji Feena na." yana maganar hawaye na bin kuncin sa "daga wannan ranar na bar Jidda har abada babu ni babu ita, zan ci gaba da baki kulawa kin ji kanwata." kalaman Amar suka sun ratsa zuciyarta tausayinshi ya lullu6e ta ta fashe da kuka ta rungume shi tana faɗin "na gode yayana, nasan ba zaka koma yin nisa da ni ba." Momy ce ta gyara zama cike da mamakin wannan kuruciyar wato shi ɗin ma yarantar bata gama fitar sa ba. Ta kalli Dady wanda shima mamaki ne fall zuciyarshi. "Wannan wane irin hauka kenan Amar?, yanzu saboda bata so kayi nisa da ita yasa zaka bar budurwar taka? Me hakan yake nufi?." Amar ya ɗago da jajayen idonsa yace "ba haka bane Momy Jidda tana da laifi sosai kusan ma ince kamar da gan-gan take saka ni yin wasu abubuwa dan kanwata taji haushi. Sau tari sai ta nuna tana jin haushin yadda nake kula da Feena wanda nikam bazan ɗauka ba." "kenan bazaka koma son wata mace ba?" Dady ne ya wurgo masa wannan tambayar. "yai murmushi zan so mana Dady, sai dai bazan koma amincewa da wata macen ba har sai ta amince da Feena a matsayin kanwa ta kuma so ta kamar yadda nake son ta, taso abinda take so ta kuma guji abinda bata so. Wannan shi ne doka akan duk wata macen da zan koma so nan gaba." Yana kaiwa nan a zancensa ya muke tsaye hannunsa rike da na kanwarsa suka fice. Dady da Momy kam kasa magana suka yi ko shakka babu sun san abinda ya faɗa shi yake nufi kuma zai aikata. *Nasmat* ✍ [1/10, 1:57 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *45* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ 📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION 📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com "Amar!" aka dakatar da shi a ɗan tsawa ce. Jin muryar Dady yasa ya juyo tareda dawowa ya tsuguna a gabansa Feena ma hakan tayi kasancewar hannunta na rike a nashi. Dukkan su shiru suka yi suna sauraren abinda zai fito daga bakinsa. "Abinda kake shirin aikatawa kuskure ne, ko ba dan kai ba saboda ita. Shin baka san daga yanzu zuwa kowane lokaci ba wani zai aure ta?, taya kake tunanin zata zauna da shi a inda babu kai in har tun yanzu baka koyar da ita ba?. Kai yaro ne Amar Safeenah da kake gani bakuwa ce a gidan wani zata rayu ba zamu dauwama da ita ba. Ko kuma kai a tunanin ka da akwai wata macen da zata amince maka da waɗannan sharuɗɗan daka gindaya akan kanwarka?." Amar yayi shiru jikinsa yayi sanyi kalau musamman da ya ji maganar wata rana za'a aurar da Feena wanda tabbas ya san haka ne. Hawaye suka fara bin kuncisa "na sani Dady na san zata za'a aurar da ita kuma in Allah ya yarda zata zauna musamman idan muka aurar da ita ga wanda take so. Da sauri ta ɗago kai ganin yayanta na kuka itama sai ta fara kukan "a'a Dady ni ba zan yi aure ba, anan zan ci gaba da zama da ku da kuma yayana zan rika taya Momy da matar yaya aikin gida." Momy ce ta kalle su ta girgiza kai kafin tace ku tashi ku tafi. Suka mike suka fice kowannen su na sharar kwalla. Hjiy Yusra ta kalli mijinta tace "habibi wlh ni tunda nake ban ta6a ganin yan'uwan da suke son junan su kamar Amar da Feena ba. Rayuwarsu tana burge ni amma yanzu sun fara bani tausayi." Alhj ya kalle ta da mamaki "tausayi kuma?" ya tambaya "eh" ta bashi amsa a takaice tana share kwalla a idonta. "babu wanda yasan sirrin yaran nan sama da ni, nice na rene su ni nasan komai game da su, ko shakka babu lokaci yayi da dukakkanin su zasu sha bakar wahala." Dady ya kalle ta da sauri "wannan wace irin magana ce Yusra?" "maganar gaskiya ce Alhj sai dai kawai mu taya su da addu'a amma muddin aka aurar da ɗayan su za'a sha fama musamman ita Feena da take mace ɗaukar ta za'a yi a kai ta wani guri." Alhj ya sauke numfashi domin ya gano inda maganar matar tasa ta nufa abinda ta faɗa gaskiya ne sai dai su dage da addu'ar neman sauki daga Allah. Amar da Feena kam suna fita garden suka nufa a can suka baje suna ja'jantawa juna abinda ya faru, yana bata hakuri tana bashi yana mata alkawura itama tana mishi wanda duk dai akan kula da ita ne da kuma yin duk abinda take so. Haka rayuwarsu ta ci gaba da gudana. Kamar yada ya kudurta a ransa tun daga ranar ya bar Jidda da shirginta tayi waya tayi aike tayi zuwa da kanta duk a banza. Karshen ta ma har gurin Momy ta zo kamun kafa amma ba'a dace ba Momyn kanta hakuri ta bata dan bata san yadda zata yi ta tilasta Amar ya so ta ba. Bisa dole ta bar shi ba dan ranta na so ba. Tun daga lokacin ya fara gwagwarmaya da rayuwa, ga karatu ga takurar da Dady yake masa akan lallai ya fito da mata ya masa aure domin su a ganin su kasancewar shi da Safeenah a koda yaushe shi ne ya hana ita ma ta samu saurayi ko mijin aure. Sai dai abinda basu sani ba shi ne ko a school masoyanta ba zasu kirgu ba. Ita ɗin ce dai bata basu fuska balle su sami damar furta mata abinda ke ran su. Hujjarta kuwa ita ce bata son aure tunda ta ji ance idan aka aurar da ita ɗaukar ta za'a yi a kai ta gidan wani har ma ana cewa zata rabu da kowa harda yayanta wannan kenan. Duk wata budurwar da ya fara nema da zarar ya je da Feena ya gabatar da ita da kuma dokokinsa akan ta sai lamarin ya lallace, wasu yan'matan har bakaken maganganu suke ya6a masa. Haka zaka gansu kullum indai aka je da Feena gun budurwa to da Kuka take dawowa. Abin yana damun ta sosai ganin yayan nata ya gagara samun macen da zata so shi ta so kanwarsa. Momy kam nata ido ne, domin bata san wani abin yi da wuce addu'a ba. (ni kuwa Nasmat cewa nayi "kuruci dangin hauka" lolz) ************************************* Yau gidan Alhj Tijjani Wakkala an tashi cikin farin ciki da kuma jimami domin safiyar yau ta kama ranar zagayowar shekarar haihuwar 6atacciyar yar su wato (Baby). Bikin da basu ta6a tsallake shekara ba'a yi shi ba. Sai Shirye-shirye suke an gama gyare gidan tsab. Momy da Dady su tafi ɗauko Ummy da yan rakiyar ta airport. Amar kuwa yana can da masu decoration suna karasa gyara ɗakin na Baby inda ake gudanar da birthdayn. Feena kuwa tuni ta gama shirin ta cikin haɗaɗɗiyar gwon ɗinta red color gashi nan yasha gyara an tufke shi guri ɗaya an ɗaure shi da wani tafkeken band shima red ne haka takalmin dake kafarta da pos dinta ma red color ne. Budurwar ta fito shar da ita, a hankali ta taka zuwa gaban mudubi kai kace ɗanyen fure ne ke rausayawa. Tsayuwa tayi tana karewa kanta kallo kafin daga bisani ta saki wani lallausan murmushi, ita kanta ta San ta haɗu. Cikin zumuɗi ta juya ta nufi ɗakin yayanta, ta shiga da sanɗa tana waige-waige kamar 6arauniya ta buɗe wardrobe ɗinsa sannan ta tsuguna can kasa ta lalubo ɗaurin sarka nan da yace Umma ta bata ita. Wani irin daɗi da farin ciki ne suka lullu6e ta a lokacin da idonta suka yi arba da rantsatstsiyar sarkar zinarin, mai tsananin haske da sheki. Hannunta har rawa yake gurin sakawa tun kan yayanta ya gani tana tsoro kar ya hana ta sakawa. Sai da ta gama saka sarkar sannan ta matsa gaban madubinsa ta kalli kanta, duk da cewa sarkar ta ɗan matse wuyanta hakan bai hana bayyanar kyawun da sarkar tayi mata ba. Ta zauna ɗas! Sai taji tunda take saka sarka ma bata ta6a saka wadda ta ka6e ta kamar wannan ba. Ta ɗora hannunta bisa sarkar tareda lumshe idonta, a fili ta shiga kwararowa Ummanta addu'ar neman rahmar Allah da jin kansa. "Ameen ya Allahu" ta ji an amsa addu'arta a bayan ta. Da sauri ta buɗe idonta. Karf! Ta sauke su a nashi, Amar ne jingine da kofar ɗakin ya harɗe hannayensa fuskarsa ɗauke da murmushi. "Kin yi kyau kanwata." ya faɗa a sanyaye. Murmushin ta mayar masa tana kallon sarkar tace "kayi hakuri Yayana naga kamar baka so in saka kyautar Umma." da sauri ya girgiza kai "ni na isa?, wannan fa ba kyauta Umma ta baki ba, taki ce ta kanki inji Umma." ta kalle shi cikin rashin fahimta. Da sauri ya dawo hayyacinsa ya kuma fahimci su6ul da bakan da yayi. Sai yayi hanzarin kawar da maganar da cewa "zan shiga wanka, fiddo min kayan da zan saka." ya shige bayin da sauri. *Nasmat* ✍ [1/10, 5:30 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *46* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ 📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION 📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com Murmushi tayi tana kallon kofar toilet ɗin kafin ta girgiza kai ta nufi wardrobe. Kayan da zai saka yau sababbi ne na musamman suka siyo kamar yadda suke yi a kowace shekara. Tana cikin fesawa kayan turare ne taji tsayuwar motoci a harabar gidan na su, hakan ne ya tabbatar mata da isowar bakinsu. Wato Ummy da tawagarta. Da gudu ta fice daga ɗakin ta nufi harabar gidan tana tsalle da ihun murna zataga yar tsohuwa Ummy kamar yadda take kiran ta, dattijuwar da take ji da kaunarta har cikin ranta. Ummy ma ta kagu taga Safeenarta hakan yasa ta saki fara'a a lokacin da ta hango ta ta nufo inda suke da murna. Ummy ta saki hannun jikinta Sagir ta rungume Feena cike da farin cikin ganin ta. "Oh wannan yar' haka kika kara nauyi? To sake ni kar ki yadda ni." inji Ummy cikin raha da wasa. Feena tayi dariya tana ko'karin raba jikinta da na Ummy tana faɗin "naci beta ne, kin san fa Momy da Dady ba karamin daɗi suke bani ba..." ciwon da taji a wuyanta ne ya hana ta karasa maganar cikin daɗi, sai ta karashe da faɗin "...wash!" tana rike wuyanta. Ummy tayi gaggawar rike ta a jikinta dan kar ta ji ciwo saboda sarkar wuyanta ce ta makale a jikin babban mayafin na Ummy. A hankali ta fara ko'karin cire sarkar Safeenah na aikin wash! Wash! sai dai cikin rashin sa'a sarkar ta tsinke kat! "Innalillahi! Wa inna ilaihiraji'un." Feena ta faɗa da karfi cikin kwalalo ido waje, kafin ta ɗora hannu aka ta fashe da kuka. Abinda ta bawa su Dady matukar mamaki. Ta tsuguna ta ɗauki rabin sarkar da ya faɗi kasa ta fara ko'karin haɗa su tana sharar kwalla tana faɗin "shikenan sarkar da Umma ta bani, yau na fara sakawa gashi ta tsinke." Momy ta sauke numfashi tana faɗin Allah ya shirye ki Feena wlh kin tsorata ni wacce irin sarka ce wannan?" a sanyaye ta Mike tana nuna musu sarkar da yadda ta zama. Tana sharar hawayen tana cigaba da cewa "ban ta6a sakawa ba sai yau tunda nake" Ummy da Momy suka kaiwa sarkar cafka a lokaci ɗaya ko waccen su ta zari rabin suka kura mata ido suna nazarin sarkar da abinda suke so su gano game da ita. Kamar haɗin baki tare suka ɗago kai idanunsu kan Feena, gaba ɗaya jikinsu rawa yake yana karkarwa bakunansu na motsi amma duk sun gagara furta komai. Al'amarinda ya jefa Dady da Feena da matar yayan Mommyn cikin ruɗani. Dady ya matsa kusa da su ganin hawaye sun wanke fuskokin uwa da yar', yace Ummy lafiya kuwa me ya faru ne?" Ummy ta kasa magana tamkar wadda aka zukewa jini haka ta silale zata zube kasa sarakuwarta tayi gaggawar riko ta tana faɗin "subhanallahi Ummy" Alhj ya kara ruɗewa yace ta shiga ciki da ita. Momy Yusra ta fashe da kuka ta kara kankame ragowar sarkar dake hannunta ta fuskanci Safeenah bakinta na rawa hannayenta na karkarwa ta buɗi bakin dakyar tana faɗin "Feena! A ina kika samu sarkar nan, wacce ce Umman da ta baki wannan sarkar?" tsoro da firgici suka kara kama Safeenah ga tashin hankali da ta ga iyayen nasu sun shiga. Ta gagara magana ita kanta jikinta kyarma yake. Momy duk ta ruɗe ta fita hayyacinta ta koma baya ta cakumo rigar Dady tana girgiza shi "habibi sarkar Baby ce, sarkar da Ummy ta sa aka buga mata a lokacin haihuwarta." Dady ya zamo ido yana kallon Yusra cike da tantama bakinsa ya kasa furta komai. "wlh ita ce habibi, dan Allah ka tambayi Feena ta gaya mana inda ta samu." Wani sabon kuka ya su6uce mata. Dady ya nufi Feena dake gefe ta zubawa sarautar Allah ido. Ya kama hannayenta duka biyu ya rike a nashi "ya'ta Safeenah ki taimake mu ki gaya mana ina kika sami wannan sarkar?" ganin hawayen Dady ya kara tashin hankalinta. Haka sauran manyan malaman nan biyu suma hawayen suke ganin halinda Yusra da Alhj suka shiga suka isa gaban Feena babban ne ya fara mata magana "haba yar nan ki yi magana mana, ki taimaka ki gaya musu inda kika same ta sarkar tasu ce ta yar'su ce data 6ata." Tirkashi! Nan fa ɗimuwa da kiɗima suka kara kama ta. Ta fara ja da baya tana girgiza kai, zasu sa zuciyarta ta buga akan abinda batada masaniya a kai. Kanta har wani juyi yake ta juya da gudu ta koma cikin gidan tana kwalla wa yayanta kira. A falo suka yi kici6is da shi yana tsaye a kan Ummy dake kuka kamar ranta zai fita tana rokon shi ya gaya mata inda suka sami sarkar nan da ke wuyan Safeenah. Tana zuwa ta rungume shi cikin tsananin kuka ta fara magana "yaya dan Allah ka gaya musu sarka ta ce da Umma ta bani, suna nunawa kamar sun San sarkar har suna cewa sarkar Baby ce yaya pls ka yiwa Dady da Momy bayani." dai-dai nan su Dady da suka biyo bayan Feena suka shigo, fuskar kowannen su sharkaf da hawaye. Suka saka Amar gaba wanda hankalinshi ya gama tashi zuciyarshi ta shiga kai komo. Bakinsa na son magana amma ya rasa me zai furta, su Dady suna son sanin gaskiya game da sarkar ta yaya zai iya furtawa a gaban Feena ya gaya musu cewa ita ɗin yar'tsintuwa ce? Yana cikin wannan halin ne yaji an tsuguna an kama kafafun shi, ruwan hawayenta na kwaranya bisa takalminsa. Cikin matsanancin tashin hankali ya yi gaggawar ɗago ta da hannayensa ya fashe da kuka yana faɗin "a'a Momy daraja da kimar ki sun wuce hakan, kin fi karfin komai a gurina Momy zan gaya miki zan sanar daku abinda ban ta6a sanarwa kowaba, abinda na sirranta yau zai bayyana. Na tabbatar kunada alaka da labarin nan." ya sulale ya zube kasa a inda yake tsaye haka Feena ma domin tana manne da shi, ji yake tamkar an zare masa duk wata laka dake jikinsa. Gaba ɗaya suka zuba masa ido cike da kaguwa ta jin abinda zai faɗa gameda sarkar Baby... *Nasmat* ✍ [1/10, 7:41 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *47* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ 📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION 📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com Feena ta yi zurum tana yiwa Amar wani kallo wanda bata ta6a yi masa ba dan a zamnta da shi bata ta6a ganin yana shar6ar kuka haka ba. "Wannan sarkar ta Feena ce. Kamar yadda Ummata ta sanar mini." yayi shiru yana jan numfashi kafin ya cigaba... "Feena ba Kanwata bace kamar yadda kuke tsammani." alamun mamaki karasa suka bayyana a fuskokin ilahirin mutanen dake wajen musamman Safeenah wadda ta kara gwale ido numfashinta na zariya kamar zai kwace ya fice daga gangar jikinta. Babu wanda ya sami damar yin magana saboda tsananin mamaki hakan yasa Amar cigaba da magana. "Kamar yadda Ummana ta gaya min tsintar Feena suka yi a gefen hanya ita da Abbana, a lokacin Feena na jinjira wadda bata wuce yan kwanaki da haihuwa ba... ****************************** Kaf Amar ya kwashe labarin rayuwar su da Safeenah a kauye har barowar su gida ya gaya masu har izuwa lokacin da Momy ta gansu ta taimake su ta ɗauko su. Ya ɗora da cewa "na cigaba da kasancewa yayan Safeenah ne saboda guje mata tsangwama da kyara bana so a koma ce mata yar tsintuwa balle har a kwatanta ta da shegiya. Dama Umma ta faɗa cewa ba mamaki wannan sarkar ta zamo silar gano asalin iyayen Safeenah, Allah ya jikan ki Umma yau ga iyayen Feenarki sun bayyana, Allah ya faranta iyayen yar' amanarki Umma." Ya ɗago manyan idanunsa da suka sha kuka ya kalli su Dady da Momy harma da Ummy yadda suka yi jage-jage da kuka yace "in dai wannan sarkar yar' ku ce to ba makawa Safeenah ita ce yar' ku Baby." Dady da Momy a tare suka tankwashe kafa suka yi sujjadu shakur, suna Kuka suna rera kirari ga Ubangijin talikai gagara misali suna godiya ga Allah tareda kara sallamawa karfin iko da adalcin Ubangiji ga bayinsa masu gaskiya. Ummy ma ba'a barta baya ba saida ta ɗaga hannayenta sama ta godewa Allah. Dady ya juya ga Safeenah wadda tunda Amar ya fara bada labari a kanta take sandare tamkar gangar jikin da babu rai a cikinta. Janyo ta yayi ya rungume ta tsam yana sauke numfashi yana cewa "lale marhabin da bayyanar ki gareni Safeenah, ya' ta gudan jini na Baby muna kaunar ki. Rahamar Ubangiji taje ga kabarin uwar da ta rene ki Allah ya jikan wannan baiwar tashi yasa aljanna ta zamo makomar ta." "ameen" inji Amar yana matse kwalla. Yau kam duk wani lungu da sako na zuciyarsa a cike yake tam da farin ciki, ga Safeenah ga asalin iyayenta. Ba shakka ya taya ta murna na kasancewarta ya' daga tsatson Momy da Dady nagartattun mutane waɗanda suka san darajar ɗan adam, suka san mutunci mutane waɗanda basu ɗauki abin duniya a bakin komai ba. Feena kam shiru take a jikin Dady wanda tunda ta fara girma baya ra6ata da jikinsa har yanzu bazata iya rarrabe halin da take ciki da mafarki ba, jira kawai take ta farka. Momy ta janyo guiwar ta ta haɗa Safeenah da Dady duka ta rungume su wani irin sanyi da daɗi ne ya ratsa zuciyarta ta lumshe idonta hawayen farin ciki na cigaba da kwaranya. Tace "Allah bai sanar da ni gaibi ba amma tsananin kamar da nake yi da Safeenah na matukar bani mamaki, na daɗe ina nazarin abin a raina haka kawai sai inji kamar ku ɗin ya'ya na ne waɗanda na haifa da cikina." Dady ya kar6e da cewa "Allah shi ya barwa kansa sanin dalilin raba mu da ke, gashi ya dawo mana dake mun rene ki da hannunmu, godiya ga Allah da ya bamu ikon tarbiyantar dake bisa turba ta gari. Ya Allah kai ne kayi wannan shirin Allah mun gode maka." Aunty Sumayya matar uncle Al'ameen ta share hawaye ta kara saita wayar hannunta wadda tunda aka fara badakalar take ɗaukar su video. Ummy ta muskuta cikin tsananin farin ciki tace ku sako min jika ta nima in rungume ta." suka yi murmushi cike da jin daɗi suka sake Safeenah, Ummy ta ware hannayenta tana murmushi tace "zo nan jika ta." ba yadda ta iya haka ta tafi ta rungumi Ummy. kamar dai hoto haka aka rika sarrafata sai dai har yanzu ta kasa furta koda kalma ɗaya. Zuwa yanzu ta gama tabbatarwa kanta cewa ba mafarki take ba, wannan al'amarin na zahiri ne. A duk sanda ta kai dubanta ga Amar sai ya sake mata murmushi, kawai sai ta fashe da kuka al'amarinda ya bawa dukan su mamaki. Da sauri Amar ya matsa daf da ita ya riko hannunta a'a kanwata yau ba ranar kuka bace godiya zaki yiwa Allah da ya bayyana miki asalin iyayenki na gaskiya. Ki godewa Allah Feena iyayenki na son ki ki kalli yadda suke tafiyar da rayuwa cike da so da begen ki dukda bakya tareda su, kullum addu'oi suke a gare ki. Zukatansu na cike da jimamin 6atan ki. Ashe kina tare da su a kowace shekara ke kike wakiltar Baby a wannan bikin na zagayowar shekarar haihuwar ta she ke ce ita. Ashe sunanki kike amsawa, ashe bikin ki ake Safeenah ki godewa Allah iyayenki mutanen kirki ne Masu zuciyar taimakon marasa gata da badan haka ba da baki dawo garesu cikin sauki haka ba." Ta juya da sauri ta rungume shi tana kara tsananta kukanta cikin kukan ta fara magana "yaya dama kasan ba uwa ɗaya uba ɗaya suka haife mu ba amma baka ta6a gaya min ba? Yaya kai ɗin na daban ne ban ta6a jin cewa kai ba jini na bane soyayyar uwa da uba da yan'uwa duka ka haɗa kake bani. Yaya banida bakin godiya gareka ka sadaukar da abubuwa da yawa saboda ni, saboda farin cikina. Ka bar abubuwa da yawa saboda ni duk da cewa kana son su. Ka kwana da yunwa ka bani abinci. Ka nuna min so da gata tun bamu san kanmu ba. Yayana kai ɗin *JA'JIRTACCE* ne wannan sunan shi yafi dacewa da kai. Nasan ba zaka ta6a yi min karya ba, yaya na kar6i Momy da Dady a matsayin iyayena na gaskiya amma hakan ba zai shafewa Umma matsayinta na uwa a gare ni ba. Duk da cewa inda kuruciya a lokacin nasan iya wahala da bakin cikin da Umma take ji idan ba'ba Larai na zagi da hantara ta, sau tari Umma har kuka take yi. Ina son ki Umma Allah ya kai rahma kabarinki." gaba ɗaya suka amsa da ameen. Jikin kowa a gurin sai da ya yi sanyi babu shakka su kan su shaida ne akan abubuwan da ta faɗa gameda shi. Amar ya cancanci sunan da ta bashi na *JA'JIRTACCE* Kamar daga sama suka ji muryar Hajiya Ummu tana faɗin "wlh karya ne, wannan ba yar' ka bace yar' ka ta daɗe da mutuwa wlh karya suke baka da wata ya' a duniya." Ta jima a gurin tana sauraron maganganun da suke akan Feena taji komai har labarin da Amar ya bayar na rayuwarsu ta baya. Wata irin ɗimuwa da tashin hankali ne suka kusan zautar da ita bata san sanda ta fara sambatun ba. Nan fa aka hau kallon-kallo tsakani Dady da Momy kafin ya juya ga Hajiya Ummu yace... *Nasmat* ✍ [1/11, 8:03 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *48* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ 📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION 📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com "Ummu, me kika sani akan ya' ta da har zaki yanke hukunci karaf ɗaya kice ta mutu?" nan fa Hajiya Ummu ta hau so she-so she da kora kunya da hauka tana faɗin "to shekara nawa da 6atan yarinya babu ta babu labarin ta sai yau da rana tsaka ace wai Safeenah ce ita?, haba ni wlh inba yau ba ma ban ta6a sanin tsinto yaran nan kuka yi ba." Alhj Wakkala yayi murmushi "wannan ne hujjar ki?" tace "eh" tana damke cikinta dake mata wani irin juyi. Ya kar6o tsinkakkiyar sarkar nan daga hannun Momy Yusra ya ɗaga mata yana faɗin "to mu kuma ga tamu hujjar, na san dai zaki iya gane wannan sarkar ko?" Hajiya Ummu ta waro idanu dan babu shakka ba zata iya manta wannan sarkar ba, muhummiyar kyauta ta farko da yar' ta fara samu kenan. "gareta aka samu wannan?" ta tambaya a matukar tsorace tana ja baya. Alhj ya tabbatar mata da hakan. Bata koma cewa komai ba ta juya da gudu ta nufi ɗakinta cikin maysanancin tashin hankali. Nan dai Alhj da Hajiya Yusra Ummy da Aunty Sumayya haɗa da Amar da Safeenah suka kasance cikin farin ciki da annashuwa. Nan da nan ya shiga kiran yan'uwa da manya-manyan abokansa da kusa da na nesa yana shaida musu Allah ya bayyana 6atacciyar yar'sa Baby. Haka Ummy ma ta kira Saudiya ta shaida musu wannan daddaɗan labari na bayyanar jikarta yar wajen Yusra. Kafin kace me gidan ya fara cika da yan'uwa masoya da makota duk wanda yazo yaji labarin sai al'ajabi ya cika shi, sai dai kaji kowa na faɗin "ikon Allah kenan sun reni yar' su da kan su." Bikin birthday kam ya tashi daga karamin biki ya koma gagarumi. Hatta cake saida aka koma yin order wani abinda da masu da shi cikin kankanin lokaci aka kawo. Gaba ɗaya farfajiyar gidan aka yiwa sabon tsari dan yawan jama'a ɗakinta ba zai ɗauka ba. Ansha addu'a manyan malaman nan sun jima suna jero wa Allah (s. w. a) kirari suna yabo da godiya gare shi. Haka iyayen da bakin nasu. Amar da Safeenah sun zama tamkar wasu taurari a wannan taron idon kowa a kan ta, ita kuma tana makale da shi. Ana cikin taron bikin ne wata yar'aikin gidan ta fito da gudu kanta a fashe jini yana zuba, ta dafe gurin tana haki tana kiran "Hajiya! Hajiya!. Ta faɗa jikin Hajiya Yusra. Abinda ya ja hankalin kowa zuwa gare su kenan aka rufu a kan ta ana tambayar abinda ya same ta. Bata jita komai ba ta fara koro musu bayani cikin mawuyacin hali kamar kaha : "Hajiya babba ce naji tana waya cikin tashin hankali tana tambayar wata da ban san ko wacce ce ba, tana cewa ashe dama bata kashe yar' nan taka data bata aikin kashewa ba?, Ashe sace yar' kawai tayi ba tareda ta kashe ta ba kuma ta kar6ar mata kuɗi har miliyan gama?. To shine ni kuma na tsorata da jin hakan na fara salati, dan dama bata san ina ɗakin ba. Shikenan tana gani na ta fara duka na cikin firgici tana cewa gwara ta kashe ni akan na tona mata asiri shine ta yi min haka dakyar na ku6ita na taho nan." ta karashe maganar a wahale tana dafe kai jama'ar dake wajen suka ɗauki salati da salami cikin alhini da matukar mamakin jin wannan maganar. Alhj da Hajiya Yusra kamar sun sandare Ummy ta fara girgiza kai tana faɗin "tabbas hausawa sun yi gaskiya da suke cewa 'makashinka yana jikin ka'." kafin wani ya furta wani abu yar aikin nan ta nisa tana ambaton Sunan Allah rayuwarta ta fice. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abinda ɗaukacin mutanen dake gurin suka shiga ambatawa kenan. Dai-dai nan kuma Hajiya Ummu ta fito da gudu da iccen mofa a hannunta tana muzurai... Amma halin da ta tsinci ma'aikaciyar tata Zainab ya tsorata ta matuka. Hajiya Yusra ta zubo ruwan gorar dake ajiye a gurin ta shafe Zainab. Ai kuwa Hajiya Ummu na ganin haka ta juya da gudu ta nufi kofar gate dan ficewa daga gidan domin ta tabbatar dubunta ta gama cika yau. Cikin tsawa da ɗaga murya Dady ya bawa security umarnin su rikita. Ai kuwa kamar jira suke suka riko ta suka nufo inda mutanen suke da ita. Da sauri Dady ya ɗaga musu hannu alamar dakatarwa yana cewa "kar ku zo min da ita nan, ku ajiye min ita can ɗakin mai gadi kafin nayi waya ma'aikata su zo su tafi da ita. Bana bukatar sake ganin ta a rayuwa na tsane ta. Na tsane ki Ummu kuma kije na sawuwaka miki na yanke igiyar aure dake tsakani na da ke kuma cutar mu da kika yi Allah ya isa ba zamu ta6a yafe miki ba. Babu shakka ko yanzu Allah (s.w.a) ya nuna miki karfin ikon sa da kuma ɗinbin adalcinsa ga waɗanda aka zalinta." Hajiya Ummu ta dafe kai ta fara rurin kuka da tirje-tirje. Nadama da dana sani ne fall a zuciyarta, da tasan irin wannan ranar zata zo mata da bata aikata abinda ta aikata ba. Amma inaa azal ta rigaya babu sauran gyara... *Nasmat* ✍ [1/11, 10:17 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*....... *49* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ 📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION 📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com Cikin tsananin 6acin rai Dady ya kaɗe rigarsa ya shiga cikin gida yana danna wayar hannunsa bisa dukkan alamu yan' sandan yake nema. Babu shakka wannan ranar ta yau tazo musu da abubuwan al'ajabi daban-daban na farin ciki da na bakin ciki harma da na ban mamaki. Wai ace Hajiya Ummu ce da kanta zata saka a sace masa yar guda gudar yar' sa harma da cewa a kashe ta. Taron mazajen da suke wajen ne suka taimakawa yan sanda wajen basu cikakken bayani akan abinda ya faru matan kuwa tuni suka watse. Tsananin tsoro da al'ajabi ya kama Amar da Feena su kam basu ta6a tsammanin rashin imanin Hajiya babba ya kai har haka ba. Washe gari da safe aka dawo da gawar Zainab bayan an kammala bincike a kan ta aka suturta ta aka kai ta makwancinta. Hajiya Ummu kuwa tana can a hannusu labarin aika-aikarta ya gama zama gari abinka da an ta6o masu da shi har gidajen TV aka rika yaɗawa, danginta kuwa ruɗani suka shiga Mubbarak ma tun daren jiya ya tattare ya bar gidan ya koma gidan iyayensa. Ma'aikatan gidan na cikin alhinin rashin yar'uwarsu Zainab haka iyayenta ma da labari ya riske su hankali tashe suka iso Kano. Bayan sati Uku komai ya lafa al'amura sun fara zama dai-dai gidan ya dawo ramin kura (daga ita sai ya'yanta) wato daga Momy sai yaranta Amar da Feena da kuma Dadyn su da kuma bakinsu Ummy da Aunty Sumayya da malaman nan. Allah sarki rayuwa kenan Safeenah sai take jinta tamkar wata sabuwa tana jin Momy kamar wata Bakuwar ta haka Ummy ma ita yadda suke tarairayarta suna kara saka ta a jiki har kunya yake bata. Shi kuwa Amar farin ciki ne ya lullu6e ruhinsa Safeenah mafi soyuwar zuciyarsa ta sami cikakken gata wanda baida tawaya. Sati uku su Ummy suka yi cikin farin ciki da daɗin rai kamar kar su tafi amma da yake ya zama dole haka suka shirya suka yi sallama suka koma cike da farin ciki na wannan gagarumin lamari da tsarin Allah. Safeenah hadda kukanta kamar dai yadda ta saba idan zata rabu da Ummy, to balle ma yanzu da suka fi shakuwa da juna domin kasa rabewa take yi tsakanin soyayyar da Momy ke nuna mata da wadda Ummyn ke mata. Bayan sati ɗaya da tafiyar su Ummy ne aka kara buɗe sabon shafin rayuwar farin ciki a gidan. Dady da Momy ji suke kamar su haɗiye Safeenah a yan kwanakin nan Sam basa iya yin nisa da ita, musamman Momy sau tari sai dai ta zuba mata ido hawayen farin ciki na bin kuncinta. Haka Amar ma basu ware shi ba, duk wata soyayya da zasu nuna wa Feena shima da tashi saboda Amar mutum ne wanda daraja da kimar sa bazasu ta6a barin idonsu ba. Iyayensu ne suka rike musu yar'su suka reneta cikin aminci, bayan mutuwar su kuma shi ya maye gurbin ya zame mata gata a lokacin da bata da shi. Hutu ya kare suka koma school sai dai a kwana biyun Dady ya lura Feena bata son zuwa makarantar koda zasu tafi sai ta murtuke fuska ta fita tana fushi. Yau ma gaba ɗaya ki tayi tace ita ba zata je ba. Ya daɗe yana nazarin ta, tana kishingiɗe bisa kujera sai hura hanci take tana hararar Amar dake tsaye a kanta yana magiyar ta tashi su tafi ta ki. A hankali ya kira sunanta "Safeenah" ta amsa kanta na kallon inda yake "na'am Dady" "me yasa ba zaki je makaranta ba?" maimakon ta ba shi amsa sai hawaye suka fara bin kuncinta tana sharewa. Mamaki ya kama Momy Amar harma da Dady. Momy Yusra ta kalle ta cikeda fargaba "Feena baki da lafiya ne?" ta girgiza kai "lafiya na kalau Momy, kawai ni ba zani school ɗin bane." Amar ya kara tsurewa dan ya san laifin nasa ne ya jangwalo rigima. "saboda me?" Dady ya tambaya yana kallonta. Sai ta daina share hawayen ta fashe da kuka. Cikin kukan ta fara magana "Dady yaya ne fa ya yi sabuwar budurwa mai shegen nacin tsaya, ko bai neme ta ba sai tazo muna hirar mu ta addabemu da shegen surutu sai iya yi baka gani ba fa har nunawa take yi tafi ni son shi." Ta karashe zancen tareda saka wani sabon kukan. Maganar Safeenah ta bawa dukkan su dariya banda Amar da yasha jinin jikinsa dan yasan tashi dariyar zata fi ta kowa yi mata ciwo. Iyayen suka kalli juna suka yi murmushi. Amar kuwa tsugunawa yayi gabanta ya marairaice murya "yanzu Feena wannan dalilin ne yasa zaki daina zuwa makaranta? Wa yace miki ni zan yarda da akwai wadda ta fiki so na a duniya?, wlh babu ita ni kam na san kin fi kowa so na a duniyar nan Safeenah." Ta murguɗa baki ta juya masa baya "amma ai baka ta6a gaya mata haka ba, sai wani ji da kanta take in ta ganka." Amar ya kunshe dariyar da ta ciko bakin sa yace "in ji wa? Allah a gabanta ma zan faɗa. Zo mu tafi, a gabanki zan sanar mata hakan." ya kama hannunta ya mikar da ita yana bata mayafi dan tuni ya ɗauko mata jakar litattafanta. Har suka fita iyayen basu koma cewa komai ba. Bayan tafiyar su ne Dady ya kalli Momy yace "alhamdulillahi Yusra kinga hakar zata cimma ruwa, babu shakka tunanin ki ya zo dai-dai." dariya ta yi tana faɗin ai dama na gaya maka Allah ya saukake komai. Har zai yi magana wayar hannunsa tayi kara alamar shigowar kira ya ɗaga da sallama yana murmushi tareda sallama. "Allah ya taimaki Alhj wannan aikin da ka bayar komai ya kammala an riga an canza komai kamar yadda ka bukata." sai da mai maganar ya kai aya sannan Alhjn ya fara magana "masha Allahu malam sabo, Allah ya saka da alkhairi insha Allahu gobe da sassafe zan shigo na gani in ya so bikin buɗewar ya kasance ranar litinin." a haka suka yi sallama ya kashe wayar yana daɗa godiya. Bayan ya kammala ne yake gaya mata wannan kamfanin nashi na buga atamfofi ne yasa aka gyara tareda sauya masa sabon tsari sai ta shirya domin ranar da za'a buɗe shi gagarumin biki za'a yi. Momy tayi murmushi "kaji habibi bikin ma hadda wani gagarumi?" ya mike yana faɗin sosai ma kuwa domin kudurina a ranar na musamman ne. Ni zan fita." "to Allah ya kiyaye ya dawo da kai lafiya, Allah kuma ya kai mu jibin mu sha biki." ta faɗa da tsokana. Bai ce komai ba ya fice yana dariya. Momy bata san yadda suka kare a makaranta ba ta dai ga Safeenah an dawo ana ta kyalkyala dariya kamar ba ita ta fita tana sharar kwalla ba. Ranar monday ta zo inda Dady ya sa aka shirya gagarumin taro a harabar wannan kamfanin nashi. Misalin karfe tara da rabo kowa ya hallara a farfajiyar katafaren kamfanin wanda yasha gyara da sababbin tsare-tsare ya koma kamar sabon guri. Bayan manyan malamai sun buɗe taro da addu'a aka fara gabatar da abinda ya tara su a gurin wato buɗe kamfanin. Inda aka fara da zuge wani babban kyalle wanda aka rufe allon dake ɗauke da sunan kamfanin a jiki. Ai kuwa sai ga sunani ya bayyana raɗau cikin tsarin rubutu mai kyau da ɗaukar hankali. Ga sunan kamar haka : *JA'JIRTACCE WAX & MATERIALS LIMITED.* Tsananin mamaki ya kama Hajiya Yusra da yaranta musamman Amar domin a sanin shi wannan shine sunan da kanwarsa ta bashi. Bai kara tsinkewa ba sai da Dady ya kama hannunsa ya fara jawabi tareda damka masa takardun kamfanin a gaban waɗannan dubban mutanen. Ya kuma shaida musu ya mallakawa Amar wannan kamfanin daga yau kamfanin ya zama mallakinsa halak malak. Aka hau tafi da haska su da camera. Tsabar farin ciki Safeenah sakin hannun Momy tayi ta tafi da gudu ta rungume mahaifinta tana hawayen farin ciki, tareda taya yayanta godiya. Haka Amar ma rungume Dady yayi yana hawaye dan nuna farin cikin sa ga wannan dankariyar kyautar da bai ta6a tsammani ba. Abokan Dady da manyan yan' kasuwa da suka halarci bikin suka rika taya shi murna. Haka taro ya watse suka koma gida cike da murna. *Nasmat* ✍ [1/12, 11:06 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ........... *JA'JIRTACCE*... *50* last page ... *The end😇* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © Yar'mutan Arkilla✍ ____________ 📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION 📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com Rayuwa kenan. Hausawa suka ce kwanci tashi asarar mai rai. Haka rayuwa ta ɗore musu cikin farin ciki da nishaɗi kankanin ta na saudiya kuwa kullum suna manne a waya, sun maida zuwa saudiya kamar shiga kasuwa domin bayan kowane sati biyu sai sun je suyi weekend can sannan su dawo. Feena tasan da yawa dangin mahaifiyarta kuma suna zumunci sosai. Alhamdulillah yau Amar ya kammala karatunsa cikin sa'a da nasara resold yayi kyau inda ya cinye komai 100%. Ya zama kwararren masani akan harkokin kasuwanci da kuma fannin na'ura mai kwakwalwa wato computer. Gagarumar walima Dady ya haɗa masa suka sha shagali da addu'oi. A cikin satin kuma ya fara aiki a sabon kamfaninsa wanda dama akwai komai na dangane da kayan aiki ma'aikata ma tuni aka nema sai kira kawai aka yi kowa ya fito. Masha Allah kamfani ya fara aiki da sa'a kuwa domin abubuwa sai ha6aka suke yi. Amar yana aiki tukuru yarinya yake jin kansa tamkar wani daban saboda sauye-sauyen da ya samu a jiki da ma rayuwarsa duka. Feena kuwa maraici ne ya fara shigar ta a Gida da makaranta rayuwa babu Amar ba daɗi, har gara ma na gidan ta zuwa har can ta same shi har ma ta taya shi wasu ayyukan amma a makaranta shiru ne gata bata da wata kawa balle saurayi ba wanda yake ra6ar ta. A daddafe ta samu ta kammala ragowar shekara ɗaya da ta rage mata. Kasancewar cos ɗaya suka karanta abin ba wahala. Kafin fitowar takardunta kullum tare suke fita da Amar office har Dady da Momy suka fara faɗa wai zata je ta hana shi aiki da surutun ta. Shine ya gaya musu ai aiki take taya shi kuma takardunta na fitowa zai bata babban aiki yadda bazata yi nisa da shi ba. A cewarsa office ɗinta na nan yana jiran ta. Dady yace "to da kyau ku ci gaba da tarawa kan ku aiki, Amar kullum ina gaya maka ka bar Safeenah ta saba da nisantar ka ka ki, shin idan tayi aure ya zaka yi?" Amar ya sunkuyar da kansa kasa sai hawaye bai iya cewa komai ba ya tashi ya fice. Wunin ranar kam haka ya kare masa tamkar wanda aka zarewa laka, izuwa yanzu ya kasa tantance wane irin so ne yake yiwa Feena wanda idan ya ji an yi maganar aurenta sai hankalisa ya tashi ya nemi nutsuwarsa ya rasa. Magana ta gaskiya ya kasa gane komai. Da dare misalin karfe takwas da rabi bayan sun kammala cin abinci ne Dady ya kira su zuwa ɗakinsa gaba ɗayan su harda Momy. Da suka je ɗin ma ya ɗauki lokaci mai tsayi kafin yayi maganar da ban san yadda yaran zasu ɗauke ta ba. Can bayan shirun ya fara da kiran sunayensu a sanyaye "Amar da Safeenah" suka amsa a tare suna nazarin yanayinsa. Ya fara maganar cikin waswasi na samun nasara ko akasin hakan "ba komai yasa na kira ku nan ba sai dan sanar da ku wani al'amari da na lura har yau ku kun kasa sanin shi da kan ku, ko in ce kun San shi amma kun kasa gano shi." ya takaita yana kallon fuskokinsu. Sai da suka kalli juna sannan suka kalli Dady cikin rashin fahimta, sai ya yi musu murmushi sannan ya ci gaba da magana. "lokaci yayi da ya kamata ace kowannen ku ya mallaki muhallin sa na rayuwa, wato ya kamata ace yanzu dukkan ku kuna da aure" tare suka waro ido suka kalli Dady fuskokinsu cike da damuwa. Amar ya maida kansa kasa Safeenah kuwa kukan shagwa6a ta saka tana tirje kafa "Dady wlh ba zan yi auren nan ba, ba ku kuka ce idan nayi aure ɗauka ta za'a yi a tafi dani wani gidan ba? Shikenan an raba ni da ku an kuma raba ni da yayana. Wlh bazan yi ba." ta faɗa cike da hakikancewa tana matse kwalla. Momy tayi murmushi tace "kenan kina nufin har abada ke ba zaki yi aure ba?" ta gyaɗa kai alamar eh. "Koda ace yayan naki za'a aura miki ba zaki yi ba?" Dady ne ya watso mata wannan tambayar da tasa dukkan su ɗagowa suka zuba masa ido da alama maganar ta zo musu a bai-bai. Yayi murmushi sannan yace "mu yara bane kamar ku, mun riga mun fahimci matsalar ku mun kuma san maganin ta dan ba zamu tabbata daku babu aure ba kuma Allah bai haramta auren a tsakanin ku ba. Ni da Momynku mun yanke hukuncin haɗa ku aure domin hakan shi kaɗai ne mafita ga ɗorewar rayuwar ku cikin farin ciki." daga Safeenan har Amar sai suka ji kamar Dady yayi sa6o domin su a ganin su ai babu aure tsakanin su dan basu ta6a kawowa ba ko a mafarki. Wani irin nauyi ne ya sauka bisa kirji da kawunansu. Babu wanda ya iya furta komai amma harta Allah jin maganar suke kamar ma haramun aka faɗa. "Dady" Feena ta ambata cikin nauyin baki "Safeenah" shima ya kira sunanta a madadin amsa kiranta "Dady yayana ne fa" tace tana kallon iyayen nata. "To Safeenah yayanki uwa ɗaya ce ta haife ku ko uba ɗaya?" Sai a lokacin tunanin Feena da Amar ya harbo musu wanna "ai kuwa tabbas da akwai aure tsakanin su amma taya zai kasance? Ta yaya zai kalli idon Safeenah ya furta mata kalmar soyayya? " Amar ne mai wannan tunanin cikin zuciyarsa. Ita kuwa Feena farin ciki ne ya lullu6e ta ciki da waje wanda har saida ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta. A ranta take kissimawa shikenan yaya Amar ya zama nata, yanzu babu wata macen da zata koma ra6arsa sai ita. Ta saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta tana murmushi, al'amarin da ya faranta ran iyayen nasu kenan domin hakan ya tabbatar musu cewa tana so kuma ta amince. Shi kuwa Amar tsananin mamaki ne ya kama shi "me hakan yake nufi? Kenan Safeenah ta yarda da aure tsakanin ta da shi? Ko dai bata fahimci abinda ake nufi ba?". Can ya tsinkayo muryar Dady yana cewa "yauwa yar albarka dama nasan zaki so yayanki kamar yadda kike faɗa kin fi kowa son sa a duniya to yau gashi nan zai zama mallakin ki duka." ta mike da gudu tana dariya ta fice daga ɗakin. Momy tace "ja'ira ai wannan tata kuruciyar ta daban ce, dama haka take so ya daina kula kowa sai ita kaɗai." Alhjn ma dariyar yayi yace "ai gaskiyar ta gwara ta rike yayanta da kanta." Amar kam ko motsin kirki ya kasa yi ya rasa gane yanayin da yake ciki shin farin ciki ne ko kuma kunyar su Dady? "Amar" Dady ya kira sunan sa. "Na'am Dady." Ya amsa dakyar. "har yanzu baka ce komai ba, shin ka kar6i kanwar ka a matsayin mata ko ko kana da wani za6in daban?" ya tsagaita yana kallon sa. Jin bai ce komai ba yasa ya ci gaba da magana "Amar nifa ba zan maka dole ga auren Safeenah ba, kuma dan baka aure ta ba sam bazan zarge ka da wani laifi ko kuskure ba domin ni nan shaida ne a kan son da kake yiwa Safeenah ko ni da na haife ta ba zan kaika son ta a aikace ba sai dai ko na faɗa a baki." Kunya da nauyin Dady suka lullu6e Amar hakika shi kansa yasan ko yace baya son Feena karya yake, sai dai son da yake mata bashida alaka da aure ko soyayya dan a yadda yake jin son ta a ransa ma ya zarce irin son da saurayi zai yiwa budurwa ko matar da zai aura. "to amma tunda har Safeenah ta nuna ta amince zata aure shi ta yaya shi zai ki?". Kan sa na sunkuye a kasa yace "ba haka bane Dady wlh ina kaunar Safeenah son da ya zarce wanda saurayi zai yiwa budurwa ko matar da zai aura. Soyayyar aure ce ban ta6a yi mata ba ban kuma ta6a kallonta da wani nau'in so wanda ya zarce na wa da kanwarsa ba. Amma hakan ba zai sa naki auren Feena ba tana so na ina sonta nida ita mun fi kowa kusanci da sanin halayyar juna, ko dan gudun abinda zai faru da ni idan aka aurar da Safeenah ga wani zan aureta. Dan na tabbata Allah ne kaɗai ya san yanda zan zama ranar da kanwata tayi nisa dani. Dady nida Safeenah muna kaunar junan mu nasan so ba zai gagara ba. Mun gode da zurfin tunanin ku akan rayuwar mu Allah ya saka da mafificin alkhairinsa amin." Dady ya sauke numfashi yana kara yaba hankali da nutsuwar Amar. Yace "haka muke son ji Amar tashi ka tafi Allah yayi muku albarka" ya amsa da "ameen" Momy ma addu'ar ta bishi da ita zuciyarta kal da farin ciki Amar kam dakyar ya iya mikewa ya fita dan a lokaci ɗaya yaji kunyar waɗannan karmtaccin mutanen ta lullu6e shi. To fa wani sabon al'amari tun daga ranar da aka yi wannan maganar Safeenah ta shiga yin baya-baya da Amar bawai na ki ba a'a yanzu wata irin kunyarsa take ji, idan yana guri sai ta noke babu yawan surutun nan ba tsalle da direwa a jikinsa. Shi kan sa nauyin yi mata magana yake yi idan yana kallonta. Amma abin mamaki sai suka maida rayuwarsu cikin waya wato a waya zai kirata su rakashe da hira kamar ba su ɗin ba, wasu lokuta ma harda taɗin soyayya suke ta6awa. Dady da Momy kam ba jan lokaci Shirye-shiryen biki suka fara, daga Safeenar har shi ido ne nasu dan su Momy ne suke yin komai tun daga kan haɗa lehe har zuwa sauran kashe-kashen kuɗin da ake basu nemi komai a hannun Amar ba duk kuwa da cewa yanzu ya fara zama babban attajiri domin kamfani yana juyawa akwai kasuwa riba tana shigowa sosai. Ba'afi wata ɗaya da yin maganar ba suka ga an kawo iv an saka ranar biki a sati biyu masu zuwa. Farin ciki a zuciyar Safeenah ba'a magana haka Amar ɗin ma duk da baya nunawa. A ranar larabawan saudiya suka sauka garin Kano wannan karon hadda Malam Mahmud mahaifin Hajiya Yusra wanda kafarsa bata ta6a takowa Nigeria ba, a cewarsa sai ya shedi ɗaurin auren jikarsa, farin ciki ya cika Hajiya Yusra domin tunda aka auro ta kafarsa bata ta6a zuwa gidan ba balle ya zauna yau gashi taci albarkar haihuwa mahaifinta ya zo gidanta har zai zauna na sati biyu. Su Aunty Sumayya sune iyayen Amarya na kurkusa ita da wata kawarta da suka zo tare ne suka dage da gyara Amarya ta ciki da waje. Gida ya ɗauki baki harda dangin Dady na nesa duk sun fara zuwa, kullum cikin tarbar baki ake. Abu kamar wasa ranakun sai sauri suke kamar abinda ake turawa. Yau ne sati biyun da aka ɗiba suka cika, kuma yau ne dubbban ja'a suka shaidi ɗaurin auren zaratan masoyan Safeenah Tijjani (wakkala) da yayanta Amar Abubakar. ɗaurin auren da ya bar tarihi a cikin garin Kano a ranar gaba ɗaya gidajen TV da suke Kano aikin da suka wuni yi kenan na nuna wannan bikin da shahararriyar walimar da abokan Dady suka shiryawa amarya da ango. Hajiya Yusra da nata kawayen ma ba'a barsu baya ba. Biki kam yayi biki duk da ba wata bidi'a na party ko wani shagali amma sai da ka kwana uku ana jera walima a ko wace rana da Malaman da zasu yi. A kwana na ukun ne kuma amarya zata tare a rantsatstsen gidansu da Dady ya gama shirya musu komai na jin daɗin rayuwa a cikin sa. Gidan a bayan layinsu ne babu nisa da gidan Dan haka karfe takwas na daren aka kaita gidan mijinta bugun zuciyarta Amar. Ranar kam munga amarya wadda ba rakiyar kawaye domin bata da kawa ko guda ɗaya, haka yan kai amaryar suka barta ita kaɗai kamar mayya kafin shigowar angon. Shi kam ya samu rakiyar abokan aikin shi da yaran sa na kamfani, sune suka rako shi kuma suka musu addu'ar neman zaman lafiya da kariya daga sharrin sheɗan sannan suka yi sallama suka tafi. Sam taba zama irin amaren nan masu nuna tsoron mazajen su a ranar da suka tare gidajen su ba, domin ta san nata angon amintacce ne. Tayi amanna cewar Amar ba zai ta6a cutar da ita ba. Bayan kwana biyu su Ummy yan biki suka yi shirin komawa kasarsu, har gidan su je ita da Malam suka kara yiwa yaran nasiha tareda kara nusar da su gameda aure da manufofinsa. Sannan suka yi musu sallama suka tafi. Babu shakka dukkan su sun ji daɗin wannan faɗakarwa ta Malam da matarsa domin a da suna ganin kamar bazasu iya zaman da ake kira na aure da junan su ba, a tunaninsu tunda an ɗaura ai shikenan sun sami lasisin zama guri ɗaya na har abada ba wai sai sun yi wasu abubuwan ba. Amma zuwan Malam ya tunatar da su aure fa ba abin wasa bane ibada ne Shi kuma abinda suke ko'karin kaucewa sunna ne na Ma'aiki (s.a.w) a domin hakan ne kowannen su ya shirya tsab domin kar6ar ɗan'uwansa a matsayin abokin zamantakewar aure. Yau sati uku da yin auren Alhamdulillah Amarya da ango sun zama ɗaya. Farin ciki da jin daɗin su ya kara nunkuwa Ganin darajar juna da mutunta juna ya karu a tsakanin su, ko wannen su ko'kari yake ya nunawa ɗan'uwansa irin son da yake masa. Sai a lokacin suka yarda kuma suka gane cewa Dady da Momy gata suka yi musu da basu bari suka rabu ba. Sai godewa Allah suke da kuma iyayensu da sukayi wannan tunanin na haɗa su aure. A yanzu sun yarda kasancewar su ma'aurata shine hanya mikakka ta ɗorewar rayuwarsu a tare har abada. Safeenah ta yarda Amar shine rayuwarta, kamar yadda shima yake ji a ransa babu mace kamar Feena a wannan duniyar yana kaunar ta ta ciki da waje yana jinta tamkar kurjin da ya fito ma mutum bisa zuciya. Kimanin watanni bakwai da auren ciki ya bayyana a jikin Safeenah wanda ko Amar bai san da shi ba har saida ya ganshi ya fara girma. Allah sarki Momy da Dady harda hawayen farin ciki suka yi da labari yaje musu cewa Safeenah nada ciki wata biyar. Amar kam nan ya kara sukurkurcewa ya zama bawan Safeenah in tari zata yi idonsa na kanta kullum cikin bautawa bukatun cikin nata yake kasancewar cikin yazo mata da laulayi ga yawan kwaɗayi yau wannan gobe wancan. A nan ne ta kara yarda da Amar ya cika *JA'JIRTACCE* domin duk abin nan bai ta6a nuna gajiyawa da bukatun ta ko kasawa duk kuwa da cewa aikin office na taruwar masa ta dalilin tsayawar da yake yi da ita yana bata kulawa ita da cikin ta. Amma ko sau ɗaya bai ta6a korafi ba. Rayuwa kenan. Ranar wata litinim da sassafe ciwon nakuda ya sallamowa Safeenah. Nan fa aka ga tashin hankalin *JA'JIRTACCE* domin ko a asibiti da suka je kasa barin ɗakin haihuwar yayi duk da cewa tareda Momy suka tafi amma Amar ya kasa fita ya bar Safeenah cikin wannan halin duk kuwa da rokon da likitoci suke masa akan ya fita sam yaki dole suka hakura suka kyale shi suka koma kan mara lafiya. Da taimakon Allah da na likitocin Safeenah ta haifo yaranta biyu tagwaye mace da namiji a gaban Amar bayan tasha bakar wahala. Nan da nan kukansa ya tsaya farin ciki ya maye gurbin damuwar ganin yaran da uwar duka suna cikin koshin lafiya. Allah sarki Safeenah tausayin iyaye mata ne ya kara cika ta musamman yadda taji azabar haihuwa sai ta kara jinjinawa Momy da jarumtar ta da bata haɗiyi zuciya ta mutuba a lokacin da ta gama wahalar haihuwarta kuma aka sace ta. Da wannan take tausayawa ya'yan da basa tausayin iyayensu ba kuma sa yi musu biyayya kamar yadda addini ya tanada. (nima dai Nasmat nace ya'ya mu kula musan su waye iyaye kuma muyi ko'karin kyautata musu. Allah yasa mu dace.) Nan da nan labarin haihuwar Feena ya karaɗe dangi na kusa da na nesa suka sani. Tsakanin Amar da su Dady bansan wanda yafi wani murna da wannan haihuwar ba. Yara kam an kasa kwantar da su koda yaushe suna sungume ga Momy da Amar lokacin salla da bacci ne kawai yake raba su. Idan Momy ta kaɗaitu ita kaɗai har kuka take yi, tana kara sallamawa lamarin Ubangiji. Wai yau ita ce da jikoki ya'yan yar'ta. Haka Dady ma abinda ba'a cewa komai Kwanakin su uku a asibiti aka sallame su suka koma gida. Kai tsaye gidan Dady aka wuce da su, inda zata fi samun kulawa ta manya. Washe gari Ummy ta iso ita kaɗai cike da zumuɗin ganin ya'yan jikarta. Suka haɗu ita da Momy gurin kula da Feena wajen gasa mata jikinta da wankan jego, sai kuma faman da ake yi da ita wajen shayar da yaran wai bata so tana jin ciwo. Haka zasu yi ta lallai6a ta har ta yarda ta bawa yaran abincinsu. Amar kuwa ya zama daddawar ɗaya, kullum yana nan like da su hatta gurin aikin ya daina zuwa ɗakinsa dake gidan ya gyara ya tare a ciki. Tun Ummy na masa tsaya har ta gaji da kanta ta kyale shi bacci ne kawai yake raba shi da Safeenah da yaransu hatta abinci tare suke ci a ɗakin da take. Tun ana gobe daren suna baki suka fara zuwa ciki kuwa harda Aunty Sumayya da maigidanta Uncle. Wannan karon basu zo da yara ba Malam ma bai sami zuwa ba saboda gabatowar watan azumi suna Shirye-shiryen taron sa. Sai video calla da sue yi da shi yana ganin kyawawan yaran masu kama da iyayensu. Ranar suna ta zo inda yara suka ci sunayen su na Hassan da Husaina ba'a canza masu wani ba. Alhamdulillah biki yayi biki dabbobin da aka yanka a wannan sunan ba zasu irguba domin kuwa Dady ji yayi kamar ya tashi gidan gonarsa duka, dan dama yana da takaicin yankan da bai yiwa mahaifiyarsu ba a lokacin haihuwarta sakamakon sace ta da aka yi. Allah sarki Dady ya hana Amar yin komai hatta kayan Feena da jinjiranta duk shi yasa aka haɗo musu. Bayan kwanaki uku da sunan yan biki suka watse su Ummy ma duk sun tafi. Sai da Dady yayi da gaske sannan Amar ya fara zuwa office nan ma baya kai lokacin tashi sai dai yaje ya duba yadda al'amura ke tafiya ya dawo dai-dai lokacin da ya tabbatar Dady ya fita. Ita dai Momy nata ido ne domin tasan ikon Allah ne kaɗai ya isa raba tsakanin Amar da tilon yar' tasu Safeenah. Watanni biyu cif Feena tayi a gidan iyayenta aka ce za'a maida ta gidan ta wannan karon Momy da kanta ta ɗebe kunyar yar fari ta gyara yar'ta. Amar kuwa duk wani abin amfani dake gidansu sai da ya fidda shi ya canza wani hatta kayan sakawa wasu sababbin aka zuba da sabon tsari. ɗaki na musamman aka ware wa twins inda aka zuba musu kyawawan gadajen baccin jarirai da sef da kuma tulin kayan wasa iri daban-daban. Hmm wani abu sai mai hali. Ranar tarewar kuwa kamar ranar biki haka kawayen Momy suka zo da kyaututtukan su Feena da ya'yan ta saune kuma suka maida ta gidanta bayan an kara yi mata nasiha aka kara mata masu aiki mutum biyu waɗanda zasu taya ta renon yan'biyu. Wani sabon shafin soyayya ne aka buɗe a gidan ma'auratan wanda ya kusa nunka na farko da suka yi. Ya'yan su sun zama taurarin su ababen so da kaunar su. Tuni Amar ya tashi daga yayana ya koma *JA'JIRTACCE* a bakin Safeenah inda ita kuma take amsa sunan kanwata har kwanan gobe. 6angaren addu'a kuma basa mantuwa da Umma da Abbansu kullum addu'a suke Allah ya jikan Umma da Abba Allah kuma ya kara haskaka rayuwarsu da farin ciki. Nima Nasmat nace ameen ya Allahu, fatan alkhairi ga ilahirin rayuwar Safeenah da *JA'JIRTACCEN* yayanta harma da yaransu baki ɗaya. Fatan alkhairi gare ku masoya makaranta wannan littafi a duk inda kuke. Alhamdulillah a nan na kawo karshen wannan labari mai ɗauke da sakonni bila adadin da fatan masu karatu sun amfana. Yar'mutan Arkilla na godiya bisa goyon bayan ku da juriyar bibiyar littafin ta. Kaunar da kuke nuna min a koda yaushe ita take kara min kwarin guiwa ina kaunar ku pans ɗina 😘 Kungiya ta abar fahari na *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ɗaya tamkar da dubu bazan daina alfahari da ku ba ɗaukacin Mambobi na wannan Kungiyar Allah ta'ala ya ji6anci al'amuran mu baki ɗaya. Yan'uwa abokan aiki takwarorin mu na sauran kungiyoyin Marubuta fatan alkhairi gare ku duka. *ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION* *PEN WRITERS ASSOCIATION* *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *UNIQUE WRITERS ASSOCIATION* *FIKRA WRITERS ASSOCIATION* *AMINCI WRITERS ASSOCIATION* *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* Kai har ma da kungiyoyin da ban samu ambata sunayen su ba ina musu fatan alkhairi da fatan samun nasara ga Marubuci a duk inda yake na cikin kungiyoyin da ma masu zaman kan su. Ku huta yan baiwa ana matukar tare 🤝 *Da wannan kuma nake cewa sai ku tare ni a sabon novel ɗina na gaba mai suna 'MARUBUCI ZAN RAYU DA KAI' littafin da nake Kyautata zaton zai faɗakar ya wa'azantar har ma nishaɗantar da ku masu sha'awar karatu da kuma bibiyar litattafai na. Alhamdulillah! Na gode! Na gode!! Na gode!!! *Nasmat* ✍