[11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writings by; Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam 📚✍🏽 Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Ina yi wa Allah godiya da ya bani ikon kammala littafina mai suna DA MAI RAI AKE RIKICIN DUNIYA Littafi ne da ya yi duba akan ƙanne, iyaye da irin yadda suke shigo-shigo ba zurfi na ji daɗin yadda littafin ya samu karɓuwa. Labari guda uku basira uku mahanga uku labarin ba iri ɗaya bane ko wani labari mahangar shi daban don haka ku shirya a sannu zaku gane In da labarin ya dosa a wata mahangar Yanzu ma muna tafe da wani littafi mai suna WATA MAHANGAR ku buɗe kunnen ku zaku sha labari tare da faɗakar wa daga garemu littafi ne da zai haɗa marubuta guda uku, zamani uku, da tunani guda uku. Ina ma'abota karance- karance ku matso kusa don zaman jiran fitowar wannan littafi na marubuta Amina maaji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam. Paid book 400 Kai tsaye zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984 Doka bamu yadda a juya mana labari ta kowace fuska ba yin hakan saɓa doka ce garemu duk mai matsala ko labarin yayi dai dai da rayuwar wasu mafita da gyara a ke nema duk da labarin a cikin kashi ɗari kashi sittin gaskiya ne ,ba munyi dan cin zarafi ko sawa wasu sunji sun tsani soyayya ba kowa da irin tashi ƙaddaran kai tsaye kakira_ kikira ɗaya daga cikin marubutan littafin mungode . LAMBA TA ƊAYA So shine ya ruguza min dukkanin tunanina ya ruguza min dukkanin ƙofofin daƙile wani gurbi na soyayya so ya yi min mungun saran maciji da son JB gara na sha guba lokaci ɗaya na bar duniya ashe maza sun daɗe suna yi mana lahani mai kama da ukuba na shiga garari tare da shiga tsaka mai wuya na tattara dukkan yarda da amana na bawa JB ashe mungu ne azzalumi, kuma mayaudari. ina rokon Allah da ya sakawa duk wacce ta faɗa irin tarkon da na faɗa wannan shine da na sanin da na fara yi na amsa tayin JB .da na barshi ya shiga cikin gararin rayuwa da tashin hankalin na godewa Allah da yasa ba a kan soyayyar shi na fara tsintar kaina da soyayya mai ruɗani ba sai in ce a cikin soyayya ni ce ban dace ba don an cutar dani .anyi mun lahani an sa natsani soyayya gaba ɗaya aguna bata da amfani don tayi mun illa a dalilin so narasa wasu abubuwa masu mahimmanci agareni. Saboda soyayyar da muka yi da sauran ya sha banban da na JB duk da ƙaracin shekarun shi sai da ya yi min wayo yaci zarafina girma na bai amfane ni da komai ba sai cizon yatsa. so bai yi min adalci ba yasa na ruguza irin tarbiyyar da iyayena suka ɗaura ni akai Allah ka saka min. A wani safiyar asabar ne ina cikin zama na na hau yanar gizo misalin ƙarfe bakwai da rabi na safe 7:30am don ganin wani wainar ake toyawa na hau shafin sada zumunta wato wajen da ya haɗa mutane daban-daban wato facebook duk da a yanzu kasuwar shi ta kwanta yanzu yayin TikTok ake yi yawanci yan mata da samari nanne wajen samun nishaɗin su .amma hakan bai dame ni ba don duk in da kayi sabo to nan ne hanyar farin cikin ka. ba da kowa nake mutunci ba bana yawan posting amma mutane da yawa sukan yi min magana kuma muyi mutunci da mutunta junanmu har ma da girmama wa a tsakanin mu. Wani naga ya yi min magana ganin sunan yasa na amsa don kuwa sunan mahaifinmu iri ɗaya da shi mun gaisa sosai sannan na mutunta shi kwana biyu da faruwan hakan ranar Laraba ina zaune misalin ƙarfe tara na safe 9am naga wani baƙon number ya Kira ni da kamar ba zan ɗauka ba kawai wani tunani nayi na ɗauka can! sai naji ya yi sallama ta ɓangaren shi na amsa "kin san da waye kike magana?"cewa nayi gaskiya ban sani ba . "JB ne kin gane ni" waye haka kenan?" wanda sunan mahaifinmu iri ɗaya "na gane amma waye ya baka number ta kuma waye ya baka izinin kira na? "Ki yi haƙuri babu wanda ya bani kawai nine na samu ki yi haƙuri don Allah "shikenan yaya na ba komai na gode Ka ci darajar suna "godiya nake sosai gimbiya ta sarauniyar raina. Murmushi nayi don gaskiya ya yi matuƙar bani dariya da Hausar shi irin ta Barebari. Bayan mun gaisa shikenan ban ƙara jin labarin shi ko da na minti ɗaya ba a ranan haka ban sa komai a raina ba don ni ba komai a raina sannan nasan mutunci ne yasa ya ƙira ni ban san in da ya samu number ta ba tunda ni wajen shekaru hudu ban yi soyayya ba naso ganin hoton shi amma ba shi bane a kan dpn shi na Whatsapp ba, bayan Kwana biyu naji ya yi min magana ya ƙira ni da sunan da ni kaina muddin a ka kira ni da sunan bana jin daɗin shi wato a kira ni da baby, a dama bai yi min amfani ba balle yanzu. "Me yasa zaka Kira ni da wani sunan da gara guba ma da shi? '' subhanallahi! me yasa kika ce haka?"e babu wani suna da zai burge ni indai ta shafi soyayya ce "ki yi haƙuri nima da soyayya na zo miki sannan da maganar aure". Aure kuma? "bana jin soyayya a raina ka bar ni inyi rayuwa ta ba tare da wani ɓangare na jiki na ya samu matsala ba, don kuwa maza duk halinku ɗaya duk da sunan ku daban ne, amma hali kam duk ɗaya ne,"ka yi haƙuri na daina soyayya"ki taimaka mun ki karɓi tayin soyayya ta ba zan taɓa gudun ki ba zan kula dake da baki dukkan kulawa daga gare ni". dogon numfashi naja saboda abun ya dame ni wallahi ko kalmar so bana son ji ko kaɗan saboda yana matuƙar ɗaga min hankali ba na kaɗan ba, na rasa dalili, a ranar ya kira ni yafi sau goma yace min sai mun yi video call ni kuma na kafe, bani da ra'ayin shi tunda ni ba ma'abociyar yin shi bane da safe ina buɗe waya ta da saƙon shi zan fara cin karo tun bana yarda har na fara sakin jiki da shi in ya kira mu zage mu yi ta hira da shi sosai A nan ne nake sanar mishi nifa ba yarinya bace ya kamata ya gane nayi mishi bayanin yadda shekaru na shima ya gayamun na shi duk da ba a nan gizo ke saƙar ba don na ba shi shekaru kusan biyar ma'ana na girme shi kalman da yace min "wallahi shekaru ba za su taɓa ruguza mana soyayyar mu ba ko dai su hana mu auren junanmu ba. ''tura min hoton ki' don Allah' ba musu na tura mishi shima ya turamun nashi tabbas yaro ne sosai don wani zubin a hoton kaya ne ke sawa a ganshi kamar mai yawan shekaru da yawa tun daga nan muka yarda da juna har muka amince da juna ya yi min dukkan bayani a cikin Borno yake ni kuma cikin Damaturu nake ban ɓoye masa komai ba kamar na ƙara masa wutar so na a ranshi amma na sanar masa da irin lalurar da nake fama da ita na ciwon zuciya ya yi min fatan samun sauƙi. Akwai wani ranar da ya tambaye ni me ya raba ni da tsofin samari na a yadda ya ganni bazai iyu a ce banida samari ba . Numfashi naja sosai " Na farko mun rabu ne sakamakon shaye-shaye na biyu mun rabu saboda na kama shi yana soyayya da ƙanwata a ɓoye na uku saura sati biyu auren shi ban sani ba sai na ƙarshe Muhammad wanda har in koma ga wanda ya halicce ni ba zan samu madadin shi ba " Muhammad ya So ni ya ƙauna ce ni, in kuwa abubuwa zai yi wan da ya shafi jin daɗi tabbas baya barina a baya koda sutura ce ko da shadda zai ɗin ka to kala ɗaya zai ɗinka mana in anyi musu albashi zuwa yake garin mu muyi kusan kashe kuɗin in zai koma yabar min kuɗin kashewa . kasancewar jinyar mu ta ciwon iri ɗaya ce ba ya ɓata min rai, bai taɓa gaya min abun da zan ji raina ya ɓaci ba yakan baro garinsu don kulawa da tawa lafiyar, mahaifiyar shi da sauran danginsa, suna mutunta ni a ganin su, haɗuwa dani yasa ya samu sauƙi don baya yawan kwanciya rashin lafiya a kan da, su biyu iyayen su suka haifa duk da suna da kuɗi amma baya garesu ni yake so yakan iya baro garin su yazo guna ya kama hotel don ya kula dani a gidan mu muke wuni Gani yake yi kamar za a sace ni ko wani ya kwace mishi ni shekarun mu uku da shi an yi mana baiko kenan komai na akwati tare muka siya ina makaranta zaije department ɗin mu ya jirani na samu gata sosai, ban taɓa jin wani abu zai raba mu ba, ashe muna namu ne Allah na nashi wannan rana ta zame min wani ɓangare na jiki na da duk lokacin da na tuna sai na zubar da hawaye . Kuka ne ya kuɓuce min sosai nai ta kuka na gagara daina kukan har yakai ga JB ya tambaye ni ki dai na kuka me ya samu Muhammed? tuna min da ya yi shine ji nake kamar zuciya ta zata fashe don fargaba da ruɗani . "JB Muhammad ya rasu ciwon ciki ne sanadi ciwon zuciya bata zama ajalin sa ba duk da ita ce jinyar sa sanadin rabuwar mu ,ta har abadan don ranar Laraba shine ranar da Muhammad ya amsa kiran mahaliccin sa ,wajen misalin ƙarfe takwas ya kira ni mun sha hira sosai da shi wani kalmar da ta tasar min hankali da ya gayamun "yau ba kya son mu yi hira ki kasan ko mutuwa zan yi? "ya Muhammad to sai me Allah ya jiƙan ka" ya dame ni da surutu gashi bacci nake ji yana yi min magana kamar wasiyya wajen ƙarfe tara yace min cikin shi na ciwo nace yasha magani yace babu nace ya kira maman shi yace ba kati a wayarsa dole na kira ta nace babanta cikin shi ciwo yake yi mishi a aika mishi magani zai sha ta bayar a ka kai mishi bayan wasu lokutan na kira shi don tabbatar da ya sha maganin, a daren mun yi hira sosai sai cewa ya yi "muddin nabar duniya ban yarda a ɗauki kayana a bawa Kowa ba don kayan auren mu da sunan ki na siya bada wata ba sannan ban san wa zai riƙemin ke amana ba ,ba lalle bane wanda zai soki ya kulamun da ke yadda ya kamata ke macece mai sauƙin kai naso mu rayu tare mu gina rayuwa kash zanyi tafiya gari mai nisa wanda ba lalle ne ki zoba ko da kinzo .a matar wani zaki zo in sha Allahu in dai baki cenza hali ba zaki samu mai irin halina ."kai dai Allah ya baka lafiya "Amin ya rabbi". Har sha ɗaya kafin nayi bacci na barshi jin waya ta na ƙara neman agaji shine ya farkar da ni"ya Muhammad ka kwanta kayi bacci mana kaji "shikenan zan kwanta amma muddin kika ga ban tashi da wuri ba ki tasar dani kinji da to na bishi saboda bacci da nakeji sosai . Washe gari Shine ke zuwa ya tasar da iyayen shi sallah amma sunji shiru har kusan goma na safe aka aiki yaro yaje ya dubo shi yace yana bacci, "bacci kuma kodai bai samu yayi bacci da dare ba in ji mahaifiyar shi kabar shi zuwa anjima sai ka tasar da shi, yayan shi ne ya shigo don tambayar shi a na neman shi a office a kwai signature (saka hannu) ɗin da zai yi " ba shida lafiya kaje zan gaya mishi' in ji mahaifiyar shi da sauri ta wuce ɓangaren shi ta dinga kira babana ka tashi mana ayya kayi sallah kuwa jin shiru bai motsa ba ashe rai yayi halin shi ɗaga hannun shi ta yi ta duba saitin zuciyarshi ashe zuciyar ba lalle ne tayi aiki ba, ba a son yaushe ya rasu ba, addu'a ta yi mishi tare da hawayen da suka biyo kuncinta masu zafi yana ta zuba, ta gagara fitowa daga ɗakin ana cikin haka ne ya yi daidai da lokacin dana ke kiran wayar . Mum ce ta ɗaga a take zuciyata ta tsinke jin kalmar haƙuri da take bani da kuma yi min nasiha, sunana ta kira Nusaiba nasihar da tayi min shine ya tabbatar min akwai babban matsala sosai . Sai da taga na samu nutsuwa kafin ta gaya min rasuwar Muhammad na shiga fargaba tare da ruɗani, a lokacin muka haɗa kayan mu sai Bauchi mutane da ke zuwa yawanci a ni ake yiwa ta'aziyya, na rame sosai, so bala'i ne! akwai wata kalma da mom ta gaya min , akan in yi haƙuri Allah zai bani wani a madadin shi kwanan mu shida kafin muka dawo nasha wahala muna dawowa na kwanta jinya kamar ba zan yi rai ba don har aman jini nake yi sai da nayi wata biyu a asibiti kafin na dawo dai dai na sha fama da addu'a na fara mantawa . "Ka ji waye mahaƙurci wanda yayi so tsakani da Allah babu algus a cikin ta ko". jikin shi yayi sanyi sosai haka ya daure ban taɓa jin labarin da ya tarwatsa tunani na ba, hakika na tausaya miki, Allah ya mishi rahama kin bani tausayi labarin akwai tausayi a cikin ta Allah ya bamu ikon yin gyara kuskuren mu Amin ya rabbi "Nusaiba zan riƙe ki tamkar jinina zan nuna miki gata sosai in sha Allahu zan kwatanta irin abun da Muhammad yake miki koda bai kai nashi ba kisa a ranki kin samu miji shekara huɗu da kika yi ba tare da soyayyar wani a ranki ba rabona ne ya tsaida ke daga kula kowa 'ki bani zuciyar ki zan mallaka miki ruhina da tawa zuciyar ". Godiya nayi mi shi na kamu da son JB a kwanaki kaɗan a raina saboda kulawa da yake nuna min har jina nake na tafi wata duniyar sauran rayuwa ko, in ce na buɗe wata rayuwa mai tare da jindadi, JB ya So ni ya ƙauna ce ni sannan yana kulawa da ni amma ba zan taɓa haɗa soyayyar Muhammad da ta JB ba don shi Muhammad so mai tsafta yake min don ko ya tsana bai taɓa riƙewa ba. JB kuwa sai yasa in tura mishi suran jiki na in naƙi turawa ya yi fushi sosai ya daina kula ni duk da yawan shekaru na soyayyar JB ta yi min kamu amma abun da na lura da shi shine. Suran jiki na yake so amma son bata da yawa gare shi son da nake mishi yafi nashi yawa nayi tafiya ya ce dole sai na tura mishi hoton ƙirjina naƙi kasancewar ina gidan biki shine yayi min fushi ya daina kula ni, duk hankalina ya tashi ba na kaɗan ba gashi na kamu da son shi wanda, raba mu zai yi mun illa tabbas . Wajen sati ɗaya bai kula ni ba can dai na shiga fargaba sai da natura mishi' kafin yayi murmushi muka shirya... Takun farko [11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR MARUBUTAN JAHAR YOBE Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam 📚✍🏽 Paid book 400 zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068758984 LAMBA NA BIYU *Masu karatu ku shirya wajen yin comments da sharhi marubuta guda uku zamani uku tunani uku karku sake ayi babu ku ,zaku sha karatu cikin aminci fatan alkairi gareku*. Yanzu kenan na fuskanci bana ranshi wata ɗaya muka yi da shi wanda bai nemi komai daga gare ni ba yawan tura mishi hotuna na da nake yi cikin kaya masu daraja wanda kaman doka ne ya bani zan tura mishi guda uku a kowace rana da farko ya nuna min shi na Allah ne don baya son yawan sa gyalen da nake yi ko fita zan yi tabbas kamar mijina sai na tambaye shi . a bu ɗaya na ɓoye mishi aiki da nakeyi amma shi kanshi ganin walwalan da nakeyi sannan ban taɓa roƙon shi ko mai ba ,bashida arzikin da zan roƙeshi ko mai wannan, ya samo a saline da irin kulawa dana ke samu daga iyaye na.yace kar in jima nace to, in kuwa ya kai awa ɗaya zai ta kira na ya dame ni in koma gida ya zo mun a kan shi na Allah ne tunda nake ban taɓa soyayya marar tsafta da kishin kaina kamar na JB ba, samarin da nayi duk sun girme Ni daga wanda ya bani shekara biyar sai shida Muhammad shekara biyar ya bani.a haka ban taɓa kallon shi a zahiri ba har muka yi kusan wata biyu. Kamar wani ubana, ni nake fara kiran shi in ce mishi ina kwana mu gaisa baya aiki shago ne da shi na siyar da kayan ɗinki, ƙarfe tara yake fita na safe ni kuma muddin na tashi to tabbas zan tashe shi wajen kiran number shi dole ya tashi har zai ce min . "wato ke in kin tashi sai kin tashe ni ko me zan yi miki ne kike yawan tashi na? "In kuwa baka son in tashe ka to ya zama dole ka rufe wayarka amma yau ina son muyi magana ". A kan me kenan! A haka ya yarda muka yi ta charting ina tambayar shi "don Allah ka gaya min baka taɓa soyayya bane sai a kaina naga kana yawan zumuɗi na sosai a ranka ? Numfashi ya ja kamun ya fara yi mun magana kamar haka "nayi soyayya a baya wanda na so faɗawa cikin tashin hankali na so ta sosai,tunda muke da ita nine na fi damuwa da ita akan ita, yar unguwar muce sunan ta A'isha da farko ta So ni daga baya kuwa ta shiga yi min wulaƙanci in ban kira ta ba ba zata taɓa kira na ba in kuwa ta kira ni wani maganar ce kawai zata gaya min daga baya wulaƙancin yayi yawa na haƙura". Amma yanzu kam ba kwa tare ko don gaskiya ni kishi ne dani? amsa ya bani da basa tare amma yana ganin status in ta ɗaura shima haka, "haba Noor ina so ka goge number ta daga wayarka don tunda bata son ka ni kam ina son ka, ya tabbatar min da ya goge sannan ya tura min number ta nace me zan yi da shi? anan ne na gane tabbas soyayya da yaro yarintar zai yi ta maka na nunawa JB tsantsar soyayya nasan zan samu matsala a gun iyayena don koda giya suka sha ba zasu taɓa yarda in auri yaron nan da sa'an ƙanina na uku ba amma babu ruwa na don shi nake so shine mahadin dukkan rayuwa ta, suna muka sawa junan mu Noor shi kuma Hayat tsabagen kunyar shi da nake ji ban taba kiran shi da sunan shi ba nasan duk wata soyayya da ba'a gina ta ta fuska mai kyau ba an dinga samun matsala farkon abun da ya ɓata mun rai kullum nine ke yawar kiran shi amma shi sai ya wuni bai Kira ni ba ina zaune naje gidan ƙawata kenan nayi' mishi' sallama ya amsa a WhatsApp bayan mun gaisa shine nace mi shi kai kullum nine ke yawan kiran ka amma ba komai kamar daman jira yake yi ya fara gaya min magana . Ke nifa ba za ki takura min ba taya kinsan ina da shago sannan mutane zasu zo siyan kaya a guna in ƙi kulasu in biye Miki mu yi hira nifa kina takura min gaskiya wato ke dai burinki, kiji murya ta ko, gaskiya ki canja tunani " duk yasa jikina yayi sanyi a hanyar dawowa gida ne na kira shi nayi mishi' tas . Ina da zuciya in raina ya ɓaci nayi mishi magana "Kaci sa'a don na kira ka don na cire ka cikin samari ka sani in na jure maka mai ƙarancin shekaru ba zata jure ba sannan ya kake mai da ni kamar wata marar gata sai kace soyayyar dole . ka sani banyi banzan da wani bazai ganni da daraja ba yawan faranta maka da nake yi baya bayyana maka na rasa masu sona ba kaji da kyau . Yaga raina ya ɓaci yayi shiru ko kulani bai yi ba kwana uku na daina yi mishi magana don in karɓawa kaina yanci tun daga nan ban ƙara shiga wani ruɗani na rashin mutuncin saba. Naƙara da cewa muddin kawuce kwana uku baka zo in da nake ba wallahi ka nemi wata bani ba sannan in har kana tunanin ba zaka zo guna ba saboda mahaifiyar ka bata gari ka zauna sai ta dawo kace an bar maka kannen ka nono suke Sha ne da zaka gaya min haka bance karka bi umarnin iyayen ka ba amma ka sani ni ban gina rayuwata ta haka ba da to kawai ya bini . Naji ya ce ikon Allah ! Kwana uku yayi yawa tsakanin mu kawai naji ya Kirani gobe yana kan hanya da safe na yi mishi girki na daddafa wasu abubuwan nau'ikan abinci a lokacin da na ganshi sai da nace Allah ya tsinewa soyayya yau kuma nan ya kawo ni ? siriri ne sosai bashi da jiki sai tsawo kaman dogon karfe a nan hankalina ya tafi don in ba soyayya ba babu abun da zai sa na kula JB don ƙaunar da nake yi mishi ne ya jawo haka tabbas haka muka ta surutu da shi don yadda ya ganni a hoto a zahiri nafi haka kyau a ranar na tsinci kaina cikin farin ciki kunya nake ji na cewa iyaye na wannan saurayi nane daman bance zaizo ba ganin shi suka yi na kuma ce da iyayena ƙanin kawata ne. zai wuce Gashua . Dare yayi kusan ƙarfe tara i yaye na sun yarda dani,sun yaba da hankali na da tarbiyyar da suka bani basu kawo komai a ransu ba a daren soyayya ta ɗebo mu muka aikata alfasha ban baro ɗakin ba sai da nayi wanka kafin kusan goma da rabi na fito naci azaba sosai amma shi kuma ko a jikin shi babu ruwan shi naga farin ciki a tattare da shi na wuce ɗakina dake cikin gida bacci ne ya gagara ɗauka na. ganin hoton mu nake yi a ido na yau ba kuɗi ba ba komai na rasa budurci na na tsawon shekaru talatin da uku a duniya saboda so a washe gari da safe nine naje ta shin shi yayi Sallah bayan yayi Sallah ya jawoni jikin shi nayi rumfa da ƙirjinsa, a safen muka ƙara kasancewa da junan mu. Tare muka shiga wanka dani da shi kamar wasu ma'aurata, idan na tuna yanzu wannan yaron shine yayi min abun da manya ma ba su samu dama a kaina ba sai takaici ya dame ni, abun haushin ma Naira ɗari biyu ne ya hada su da kanne na don baizo da komai ba daga shi sai kayan jikin shi kawai yazo da shi . Wajajen ƙarfe biyu yace zai koma gida, ya koma garinsu tunda ya tafi daman wayar shi ta ɓaci a hanyar zuwa kwana biyar bai Kirani ba, lokacin da ya Kira ni maza mutanan mu wasu kam kalar halin su irin nasaran su ce a rayuwa kwata-kwata JB bai dace da tsarin rayuwa ta ba sai sajen sane irin wanda na ke so amma na miji kamar bishiya. "Saunawa kika Kira ni?" Abun ya bani haushi bai ma tambayi ya lafiya ta ba amma yake tambayar sau nawa na kira shi tsabagen takaici shiru kawai nayi narasa abun faɗa kawai a haka muka ci gaba da gudanar da soyayyarmu ba tare da mun yi nadama ba, a duk lokacin da muka kasance tare sai naga wani sabon soyayya a gun JB . Mungu ne maƙaryaci ɗan sharri ne azzalumi har gidan mu yazo ya keta min haddi don so ko cuta Allah ka saka min sakayya na har a bada Allah kasa yadda zan auri wani ba tare da na kai mishi daraja taba kasa shima kar ya auri kamila. A karon nan kuma son da yake min yafi wanda nake yi mishi ya fara fita a raina sosai wani rana kawai mahaifina ya Kira ni akan cewa zai yi min miji akwai wanda zai ba dani a shi amma na ƙi amincewa ga mutumin babba ne ga kuɗi ga ilimi amma naƙi shi, kiran JB nayi nace akwai babbar matsala sosai tambaya ta yayi. "matsala a kan me kenan ki gaya min mata ta"? a na so a haɗa ni aure da wani ina ji JB yace ''babbar magana!'' daga nan zuga ni yayi yace kar na yarda nace to na amince ni kai kadai nake so Saide kuma kash! namiji munafiki ne na nunawa a jarida amma masu hali irin na JB. Maza sun daɗe suna cutar da mu sun daɗe suna jefa mu cikin ukuba da tashin hankali zance maza lawurjen wandonsu mutum ɗaya ne mai ɗinka wa wallahi wasu mazan ba su da maƙiya sama da mu a tattare da muma haka. Ina cikin zama na rana ɗaya an rabani da kima na da kuma daraja ta da martaba na hawaye Masu zafi da ciwo ne ke zuɓa daga ido na' ni kai na abun tsoro ye bani ina wayo na da nake tinƙaho da shi. So mungune wannan kalman shine ya ruguza wa ,wasu lissafi wannan lafazin shike bawa sheɗan daɗin zuga mu ,ina ma nayi zamana a haka . [11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR MARUBUTAN JAHAR YOBE Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA UKU *Labarin Nusaiba abun dubawa ne ina yan mata labarin Nusaiba da JB ya,isa kugane maza halin su duk ɗaya ne amma a kwai kaɗan na kirki a* *cikin su Allah ka shiga lamarin Nusaiba ka dafa mata kabata juriya* *kasakawa duk macen da ,a ka cutar da ita ta fannin soyayya.* *Maza maza halin ku sai wanda ya halicce ku* A duk lokacin da nake cikin farin ciki tabbas ina jin daɗi sosai nafi bawa JB lokaci na fiye da komai haka zai ce in baya komai ki hau online a kwai magana mai daɗi bana video call amma dole, saida na fara. JB ne ya kira ni wato irinsu JB halin su daban ne bana raba ɗaya cikin biyu soyayyar da JB yayi soyayya ce wanda har da na yarinta a cikin ta ba ya hangen nesa ko kaɗan ina cikin farin ciki in har zan ga ya Kira ni kamar an yi min kyautar dubu goma in nace zanje kitso sai ya ce yafi son gashi na a haka . Watarana JB ya yi min magana "ki yi haƙuri don Allah " Me yasa kake ba ni haƙuri me ya faru ne? "a gaskiya ba zan cutar da ke ba iyayena sunce sun zaɓa min mata sannan yarinyar tun ban kai haka ba take so na nasan auren mu dake ba lalle ne ya kasance ba muddin haka ya kasance me zance miki don Allah ki fahimce ni sannan in kin samu wani kiyi auren ki kar ki jira ni don jira na gaibu ne har ga Allah, a lokacin da yake gaya min tamkar an watsa min ruwan zafi. Me yasa ba ka sanar dani ba sai da ka bari son ka yayi min illa kafin nan? me yasa sai da ka bari muka samu matsala kafin zaka sanar dani ka janye maganar auren mu? me yasa kayi min haka? Daman yaudara ce ta shigo da kai cikin rayuwa ta? Ka cuce ni Allah kuma zai yi min Sakayya ta hanyar da ba ka yi zato ba amma ka sani ban cutar da kai ba muddin akwai wanda ya cutar da wani Allah ya bi mishi kadun shi wallahi zan barka ne kayi aure amma muddin nasa wani abu a raina har ka mutu ba za ka yi aure ba. A lokacin da yaga saƙon ranshi ya sosu kalmar ''Hmm'' kawai ya rubuta min ni kuwa kamar zuga ni a keyi na fara magana "da na san kai mayaudari ne da ban baka kaina ba amma muddin kace tukunyan wani ba za ta- tafasa ba haƙiƙa naka ko zafi ba zai yi ba sannan ka sani ba lalle bane ka auri kamila, raina ya ɓaci na gaya mishi magana sannan nace mishi mu zuba mu gani. A ranar ciwon zuciya ta ya tashi nasha wahala don alluran da aka yi min masu tsada ne da su, magani, kuwa an siya min ya kai na dubu talatin duk dangi na suna tausaya min muddin ciwo na ya tashi to kowa sai ya tausaya min, naga rayuwa sati nayi ina kwance a asibiti saboda numfashi na rabewa yake yi nayi da na sanin haɗuwa da JB don ya ɗaga min hankali sosai. Rufe waya ta nayi saboda nasan babu wata alaƙa da zai shiga tsakanin mu da JB tunda ya furta a yadda na fuskanci JB ƙarya yake yi ya yi hakan ne kawai don ya guje min, babu ra'ayin aure a tattare da shi kawai ya samu mafita ne kawai na barshi da Allah babu wanda yasan me ya haɗa mu tunda daman gidan mu basu san da shi ba sun ɗauka kawai ciwo na ne ya tashi sun bani kulawa sosai a tunanin yan gidan mu ban ƙara sa wani a raina ba tunda Muhammad ya rasu mahaifina har ya shiga ruɗani da fargaba yadda ya je ya duba ni. Ina zaune naga anyi min magana a kan cewa in yi haƙuri don Allah komai ya wuce "JB bana ƙara soyayya a cikin rayuwa ta ni ban san daɗin soyayya ba wahalar ta na sani, Muhammad bai taɓa sani damuwa ba, yakan girmama buƙata ta wallahi na rasa me sona na har abadan don haka bana jin wani zai ƙara samun gurbi ta soyayya a tattare dani . Sai ce mun yayi "Ko da na dawo gare ki "? Koda ka dawo gare ni ba zan yi soyayya ba don babu komai cikin ta sai azaba amma na gode wa Allah yanzu fa idan kayi la'akari soyayyar da ka nuna min na lokaci ne ƙalilan don haka mu bar maganar zai fi ko dai me ka gani? "Ki yafe min ban san za ki jefa rayuwar ki cikin tashin hankali ba amma ina neman afuwa ki yafe min ". Jiki na ne yayi sanyi nace babu damuwa komai ya wuce Allah ya rufa asiri muka dawo kamar ba muyi komai ba bayan yayi min alƙawari zai shawo kan iyayen shi sai naji sanyi a raina sosai in banda so. JB banda sana'ar da yake yi wanda kudin sana'ar in an haɗa shi bazai kai miliyan ɗaya ba amma yanzu yana yaron shi wani zama za muyi da shi kenan don a yadda yake koda ance ya kawo kuɗin aure na wallahi ba shida shi dubu hudu ne ya shiga tsakanin mu kati kuwa ban taɓa ganin shi a waya ta da zumar shi ya sanya min ba. wannan soyayyar da shi da babu duk ɗaya ne . Lokacin da muka yi faɗa har zance ya turo account no na tura mishi kuɗin shi amma kawai nayi haƙuri da yawa a cikinmu mu ne mu ke janyo wa samari suke raina mu ba don komai ba sai don yawan yarda da muke yi da su da sauri ba mu kiwaci hankalin su ba muke basu saurin yarda su kuma yan yarima a sha kiɗa ne maza gaskiya basu da imani su cutar da mu ko don sun ga su ba ta yadda za'ayi a gane sun banzatar da kan sune duk yawan rashin mutuncin su basa nadama Allah ya ɗaura su a kan mu . shiyasa suke haka amma na tabbata a kan ƙannen su za'a rama mana ko kan ƴaƴan su azzalumai. A kullum ina nadama sosai sannan na roƙi Allah ya yafe min Allah da kan shi ya ce zinar ma kada mu kusance ta yau gashi son wanda zai walaƙanta ni ya janyo min na rasa komai nawa nayi hawaye a duk lokacin da nake kuka babu wanda nake gaya mishi damuwa ta don bashi da magani . Idan mun shirya haka za mu yi ta marmarin juna kamar ba za mu ƙara faɗa ba ashe kan faɗa ya na gaban mu, na fuskanci tunda muka haɗu, ciwo na ya cika tashi ba don komai ba sai matsalar JB amma kuma ni Nusaiba nayi da na sanin JB don ya zame min ƙarfen ƙafa wannan shine a sanadin ƙadddara ko dai ince a haka ƙaddara ta yazo min, ni Nusaiba wallahi so mugun abu ne ina tsintar kaina cikin jin daɗi don JB ya iya kalamai masu ratsa zuciya shine baiwar da Allah yayi mishi zan jure amma ba a nan gizo ke saƙar ba bana iya jurewa na minti talatin ba tare da naji muryar shi ba, abun walaƙancin ma shine zan kira sai yayi sau uku kafin ya ɗauka koda ya ɗauka to wata ƙaryar zai min ina ganin shi a online amma zai iya ce min ya dade bai hauba. Tambayar shi nayi me yasa baya daukar waya wannan baya kyautawa sannan wannan cin zali ne bana kaɗan ba yana dubawa daya gani bai bani amsa ba naga yayi blocking ɗina a facebook da Whatsapp da telegram har ya cire photon sa akan dp duk na duba babu komai nace to naso gaya mishi magana amma kawai na ɗaure JB mungu ne azzalumi mayaudari, yafi son iyayena su dinga kashe kuɗi a kan jinya ta babu ruwan shi a nawa tunanin ban yi mishi magana mai zafi ba. Da na cancanci kyautar fushi daga gareshi walaƙancin ne ya tashi kawai irin nashi Allah ya shiga lamarina ya sakamun to kowa ce hanya yabimin hakki na ,maza a duk lokacin da ka yadda da namiji tashin farko zai baka kunya ne bana kaɗan ba JB yagama da rayuwa ta. [11/5, 11:20] Maman Khairat: *WATA MAHANGAR* Story and writing by *Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam* LAMBA TA HUDU Lumshe idanuna na yi a karo na barkatai ina cije leɓɓana da matuƙar ƙarfi. Tare da sakin sakekken ajiyar zuciya, idanuna tar na buɗe a bisa rufin ɗakin da ya zama shamaki tsakani na da sararin samaniya. A hankali nake jin ɗumin hawayen da nake jin sauƙar su a bisa fatar fuskata da ta sha gyara da dilkar amare tayi fes da ita. Duk inda ruwan hawayen ya bi ji nake tamkar ana watsa mini garwashin wuta, duk yanda naso danne kukan da ke ƙoƙarin suɓuce mini sai da lamarin ya ci tura. Cikin sauri na zaro kallabin dake kaina na tura cikin bakina, a ƙoƙarin hana sautin kukan fita. Ɗakin cike yake maƙil da ƙawayena da suke jiran wayewar garin gobe domin gabatar da dinner ɗin bikina. Jibi kuwa warhaka na zama matar aure na zama mallakin yaya Sufyan kuma halaliyarsa. Babu shiri sautin kukan ya karaɗe dukkan ɗakin da duhun daren ya mamaye ko ina, muryar Sakina babbar aminiyata ya ratsa ƙofofin kunnuwana. Ta kunna fitilar ɗakin take haske ya gauraye ko'ina, ta nufo ni tare da jeranta mini tambayar lafiya wani na bin wani, kwantar da kaina kawai nayi a kan kafaɗarta ina cigaba da kukan tausayin kaina da yanda zanen ƙaddarata take ƙoƙarin rufe shafukan farin cikin rayuwata. "Ke Surayya wai lafiya kuwa?, ko fasawa yaya Sufyan ɗin ya yi?". Ban iya furta mata ko kalma ɗaya ba domin nauyin da bakina ya yi mini, na gaza samun yawun da zan sarrafa. Ina jin ina ma fasawan ya yi da sai nafi zama cikin kwanciyar hankali da samun nutsuwar ruhi fiye da halin da nake ciki yanzu. Miƙewar da tayi tana faɗin"bari na ƙira Hajiya don tabbas akwai matsala". Ya San ya ni jin wani kuzarin da ban san ina dashi ba a wannan lokacin ya sauƙar mini, na riƙe hannunta gam cikin nawa. Har yanzu hawaye yana zuba daga idona na cira kaina tare da watsa idanuna akan fuskarta da razani ya bayyana ɓaro ɓaro. Sai da nayi kokawa da numfashina da yake sarƙewa kafin na sama zarafin faɗin babu buƙatar ki ƙira Hajiya. Ina iya jin ajiyar zuciyar da ta saka kana ta zauna cikin sanyin jiki tana fuskan tana ta soma faɗin "to menene matsalarki?, kamar ba ke bace kike cikin walwala awannin da suka gabata. Ina wannan annurin fuskarta kin?". Shuru nayi mata ba tare da na ce da ita ko kanzil ba, hakan mai hana ta ɗaurawa da"kowa ya shaida yanda yaya Sufyan yake tsananin sonki, da hakan yake bada tabbacin zai kula dake". Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauƙe ina jin wani ɗaci yana gauraye mini dukkan kusurwa bakina domin ba a nan gizo ke saƙar ba. Komawa nayi na kwanta lamau saboda ɗaɗɗakun mutanen da suka fara tashi, ina jin suna faɗin wai Sakina ta kwantar da hankalinta. Dukkan wata amarya tana tsintar kanta a irin wannan yanayin na damuwa da fargaba matuƙar bikinta ya gabato. Wata irin ƙaddara ce take ƙoƙarin yin diran mikiya a rayuwata a wannan lokacin?. Me yasa Suraj zai bayyana a cikin rayuwata a dai dai wannan gaɓar?, waye zan tunkara da batun kuma ya fahimci ni ba tare da ya yi mini kallon bututu ba?. A take zuciyata ta sanar da ni ko Hajiya da ta kasance uwar ta haife ni ba lalle bane ta fahimci ni. Amma tabbas dole nayi yaƙin nemawa kaina yanci da farin ciki na har abada a gidan aurena. Haka na ƙarar da dare ina tufka da warwara cikin raina, ƙiran sallan farko na assalatu kuwa tamkar a kunnuwana ladanin ya ƙwala. Wayata ta soma ruri ko ban duba ba na san yaya Sufyan ne domin ko wacce rana dai dai irin wannan lokacin yake ƙira na na tashi nayi sallah. Jawo wayar nayi na tsura mata ido ina jin wani raɗaɗi a cikin raina, na rasa dalilin da ya hana ni ɗaga ƙiran kamar yanda na kasa katsewa. Sai da ya ƙira a karo na biyu sannan na ɗaga. Ban amsa sallaman da ya yi ba balle gaisuwar a taƙaice na furta na tashi. Ban jira amsar da zai bani ba na gimtse ƙiran tare da ajiye ta gefe guda, tunin aka fara tashi don gabatar da salla hayaniya ya ɗauki gabaɗaya gidan. Sai da na jira duk suka gama ɗauro alwalan sannan na ɗauki wayata da na sanya a airplane mode don ƙar yaya Sufyan ya ƙara ƙira na na shiga banɗakin. Na mayar da ƙofar na rufe sannan na buɗe ruwa yana zuba. Zaman dirshan nayi tallafe da kuncina sannu a hankali hawaye suka fara tsere a bisa fuskata, na shiga manhajar whatsapp ɗin wayata na latsa saƙon muryan da Suraj ya turo mini na fara saurara. Cikin kuka da muryan dake bayyanar da tsantsar nadamar guje mini da ya yi, yake bayyana mini cewar ya dawo gare ni dawowa ta har abada. Tare da alƙawarin kasancewa tare da ni har izuwa ranar da numfashi zai yi bankwana da gangar jikinsa. A bayyane na furta me yasa me yasa Suraj?, me yasa za ka bayyana a wannan lokacin da kwanaki biyu kaɗai suka rage na zama mallakin wani?. Me yasa ka guje mini a lokacin da nake tsananin buƙatar ka a kusa da ni?. Waye zan tunkara na sanar dashi cewar soyayyata na tsawon shekaru uku ya dawo?. Rashin Suraj ya sanya ni amsar tayin soyayyar yaya Sufyan kasancewar sa ɗan uwana, amma babu wani namijin da zan gwada soyayyarsa da ta Suraj a cikin zuciyata. Ko yaushe zuciyata cikin yi masa uzuri take akan laifin da ya aikata mini, shi kaɗai nake da tabbacin zan iya zaman aure na mutu ka raba dashi. Sai da na saurara ya fi sau goma sannan na cire airplane mode ɗin da na sanya. Saƙon yaya Sufyan na fara karo dashi yana tambayar na yi salla da kuma fatan na tashi lafiya haɗe da tuna mini adadin awannin da ya rage a ɗaura auren mu. Share saƙon nayi na kunna data na mayarwa Suraj da amsa akan ina so mu haɗu da yammacin yau, hoton dake bisa DP ɗin sa na tsurawa ido domin sunana ne aka rubuta da manyan harrufa da ƙaton hoton zuciya a ƙasa. Ban damu da inda ya sama lambata ba na soma shafa hoton wasu sabbin hawayen suna bin kuncina, ina takaicin rashin kula shi da nayi tun lokacin da aka fara yi mini magana da lambar ina sharewa da rashin mayar da amsa, har sai da ya sanar da ni wanene a ƙurarren lokacin da aski ya zo gaban goshi. Na rasa mafita da madafa sai dai tabbas ba zan taɓa yin gangancin rasa Suraj ba tunda har ya kawo kansa cike da nadama. Da wata mahangar iyayena zasu dubi lamarin?. Tsam na miƙe har zuciyata nake jin zan iya ɗaukar duk wani abin da zai je ya dawo matuƙar zan mallaki Suraj, sai da na wanke fuskana sannan nayi alwalan na fito cikin sanyin jiki. Duk da ban ɗago kaina na kalli kowa ba tabbas jikina ya bani tabbacin cewar duk ni suke kallo. Hijabi na zura na tada kabbara sosai nake godewa ubangijina da ya dawo mini da Suraj gabannin a kai ni cikin gidan wani. Gaisawa muka shiga yi da ƙawayena suna ta yi mini tsiya da faɗin amarya gobe da yardan Allah, taɓe baki nayi na haye gado nayi kwanciyata na kunna data ko Suraj ya maido mini da amsa amma shuru. Tagwayen ajiyar zuciya na saka ina matse wayar a jikina ban san sanda bacci ya yi nasarar ɗauka ta ba sai ji nayi kamar a mafarki Sakina tana tashi na tare da ƙiran sunana. A hankali na buɗe idona sannan na tashi na zauna ina kallon ta. "Hajiya ce ta ce a tashe ki kiyi wanka rana tayi". Sai a sannan na lura da hasken ranar da yake shigowa ta tagar ɗakin, na ƙara yin wata miƙa sannan na sauƙo na nufi banɗaki. Wanka nayi na fito na shirya cikin doguwar rigar atamfar da ta bi jikina ga farin fatar hannu da ƙafata da aka yiwa zanen jan lalle ya fito ya yi ɗas dashi. Ban tsaya ɗaura kallabi ba nayi lulluɓi da gyale na fice sashin Hajiya, ina ta cin karo da jama'ar da suka cika gidan. Cike na iske falon Hajiya ana shigowa da abin karin kumallo na tsuguna na gaishe su sannan na wuce cikin ɗakinta. Tana zaune da ƙanwarta ɗaya tilo da muke ƙira da Mami sai yayyena mata biyu Anty Sadiya da Anty Suwaiba, da alama tattaunawa suke yi na katse musu hanzari. Suka haɗe baki wajen amsa sallamar da na shigo da ita har na zauna suna bi na da kallon dake bayyanar da tsantsar ƙaunar su da babu algus a cikinta gare ni. Ɗaya bayan ɗaya na gaishe su suka amsa cikin sakin fuska kafin Hajiya ta ce"na ga har ƙarfe goma ba ki fito ba na ce Sakina taje ta ƙira min ke, lafiya kike kuwa?". Kaina kawai na ɗaga mata alamar e kafin Anty Suwaiba ta ce"ku shirye ke da ƙawayenki mai baƙin lalle tana tafe da ƙarfe sha biyun rana, sannan Sufyan ya ƙira ni wai na baki waya yana ƙiran naki bakya ɗagawa. Ki ƙira shi zaku yi magana". Take naji raina ya tunzura ko sunansa bana ƙaunar a ambata kusa dani yanzu, da kalmar to na amsa mata dashi na miƙe na fice. Sanda na dawo na tarar an shigo da abin karin daƙin, su Sakina suna ci suna hirar yanda taron dinnern da za a gudanar ƙarfe huɗu zai kasance. Gefe na samu na zauna duk abin duniya ya ishe ni wayata na ɗauka na tarar da missed call ɗin yaya Sufyan rigis ban bi ta kan su ba na kunna data kai tsaye na wuce whatsapp ɗina amma har yanzu Suraj bai maido mini da amsa ba. Zancen da wata ƙawata da muke da bambamcin addini Sonia ta fara mini ya dawo dani cikin hayyacina. "Lafiya kuwa kika zauna kika yi shuru?, ga abinci ki sauƙo mana". Dariyar dole na ƙirƙira na dasawa fuskata na ce lafiya ƙalau. Na sauƙo na fara cin abincin ba don ina jin yunwar ko don ina jin daɗin abincin a bisa harshena ba, sai don tabbatar da furucin lafiya ƙalau ɗin da na furta. Ina gama tura abincin na haye gado shaf na manta da batun ƙiran yaya Sufyan, sai da sha biyu ta gota mai lallen ta iso na ce a fara yi wa su Sonia ni sai nayi salla tukunna. Ban tashi daga kan sallayan da na sallame sallan ba na tisa wayata a gabana, ban san sanda hawaye suka fara zarya a tsakanin kuncina da tudun wuyana ba. Sai da naji hannun Sakina bisa kafaɗata. Kamar mai raɗa take faɗin"wai me yake faruwa ne Surayya? kuka fa kike yi". Hannunta dake dafe da kafaɗata na riƙo na tashi na taja ta muka fice daga ɗakin. Can cikin lambu na dakata na zube akan kujerun simintin dake jere da juna a wajen. "Kin bar ni cikin duhu don Allah ki sanar dani meke faruwa. Kar ki bari zargin zuciyata ya tabbata". Ba tare da na ɗago kaina ba na ce wani zargi kike yi?, sai da yi ɗan jim kafin ta ce"cutar ƙanjamau kike ɗauke dashi ko kuma ciki?". Girgiza mata kaina nayi ina zuƙe majinar kukan da ya zo mini kafin na furta da hakan ne sai nafi samun kwanciyar hankali ma. Matso ni ta kuma yi tare da sausauta amon muryarta ta ce"to menene?". Wayata na buɗe na shiga tarin saƙon Suraj na nuna mata, cikin rawar jiki ta karɓa tana bi sannu a hankali har ta ƙare. Ta kafe ni ido ta ce"amma kin bani mamaki da kika azawa kanki damuwar wanda bai san darajarki ba balle kimarki. Kin manta yanda ya rabu dake bayan ya dasa bishiyar soyayyarsa da ta yi rassa a cikin ranki?, kin manta halin da ya jefa rayuwarki a ciki?. Kin manta sanda kike bibiyarsa yake wulaƙanta ki?, shin kin manta lokacin da mahaifinki ya sauƙar da duk wani matsayinsa ya ƙira Suraj har cikin gidan nan. Yake roƙonsa da ya aure ki saboda halin da kika shiga amma ya shafawa idanunsa toka ya ce ya gama soyayya dake ko da kyauta aka ba shi ke?". Sai da ta numfasa ta cigaba"wallahi tun wuri ki farka daga wannan baccin da kike yi Suraj bai dace dake ba. Ta ko'ina kin yi masa fintinkau, har akwai wani kalmar yaudaran da zai zo miki dashi ya sama matsuguni a cikin zuciyarki?. Ko da Allah bai musanya miki da yaya Sufyan ba wallahi bana goyon bayan ki komawa masa, kiyi blocking ɗin sa sannan ki sanya yaya Sufyan ya canja miki layi. Wallahi tsantsar yaudara ce kawai irin na jinsin maza yazo miki da ita amma babu wani soyayyarki a cikin zuciyarsa". A hankali na zame hannuna daga tagumin da na zabga na ce kar ki ce haka domin Allah ne kaɗai masanin sirrin zuciya. Harara ta watsa mini alamar ta fara fusata ta ce"kar ki zama butulu ki tuna yanda bawan Allahn nan Sufyan ya sadaukar da farin cikinsa don inganta naki, ki tuna yanda ya yi juriya wajen samun soyayyarki. Wallahi matuƙar kika fifita Suraj akan yaya Sufyan za ki ƙarar da rayuwarki ne cikin tafkin nadama, yaudaran ki yake wasa yake so ya yi da hankalinki ki nutsu kiyi tinani". Ƙatuwar ajiyar zuciya na saka komai ya dagule mini, na fahimci Sakina ba zata fahimta yanda nake ji a raina ba don haka nayi mata shuru. Hannuna duka ta riƙo ta sanya cikin nata cikin kwantar da murya ta ce"ba za ki taɓa da na sanin auren yaya Sufyan ba na tabbatar miki da haka". Da sauri na ce amma ai zan yi dana sanin zuwa gidansa da soyayyar wani a raina. Take ta sakar mini hannaye tana kallo na fuskarta ɗauke da maɗaukakiyar mamaki. [11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writen By Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA BIYAR "Surayya kina nufin za ki iya juyawa yaya Sufyan baya kenan? da kuwa kin tabbatarwa mutane cewar bakya cikin hankalinki. Me ki kike nufi?". Ba tare da wani dogon tinani ba idona a cikin nata na ce abin da kunnenki suka jiyo miki shi na faɗa, ai na san ba ki da lalurar da ta shafi ji. Bayyanannen ajiyar zuciya ta saka tana ƙara matso ni sai da matso dab da ni ta soma furta"kar kiyi wannan gangancin wai shin ina ilminki ne? ina wayewar ki tayi ƙaura ta tare?. Yanzu ke har sai an zaunar dake ana biya miki karatun yaudaran maza. Ai nayi tunanin abinda Suraj ya aika a gare ki kaɗai ya isa ya sa ki zama malama mai bada ilmi a wannan fannin, babu wanda zai saurare ki da wannan zancen a duk danginki". Hannu na ɗaga mata alamar ta dakata mini hakan nan idanu taf da ƙwalla nake faɗin shikenan idan mutum ya aikata laifi kuma ya yi nadama ba za a yafe masa ba?. Ko Allah muna yi masa laifi kuma ya yafe mana. Kai tsaye zantukan suke fitowa daga ƙalbina domin ina jin zan iya kare Suraj a gaban ko wani mahaluki ciki har da iyayena, duk da tun bayan rabuwar mu ban ƙara sanya shi a idanuna ba. Rurin da wayata ta soma yi da maganar da Sakina ta soma suka dirar mini a kunne a tare. Ajiye mini wayar tayi akan cinyata tare da cewa"gashi nan yana ƙiran ki sai ki ɗauka ki sanar dashi cewar hasken tauraron soyayyar da kike masa ya dishashe, yayin da na Suraj yanzu take haska ko'ina". Hawayen da suka ciko mini ido suka zubo a fuskar wayar sai da ƙiran ya kusa tsinkewa na ɗaga tare da karawa a kunnena. Ina iya jiyo ajiyar zuciya da ya sauƙe yana faɗin kalmar alhamdulillah wani na bin wani kafin ya ce"ina kika shiga yau gabaɗaya ban ji muryarki ba?, duk da na ƙira Anty Suwaiba ta tabbatar mini da lafiyarki ƙalau amma na gaza samun kwanciyar hankali". Sai da na dai daita nutsuwata kana na ce dashi ina lafiya ƙalau kawai na bar wayar a ciki ne. Hamdala ya kuma yi haɗi da faɗin"ina son ganin ki anjima zan zo kafin lokacin dinner ɗin". Da sauri na tari numfashinsa da a'a mai lalle tazo yanzu za ta fara yi mini ka bari kawai mu haɗu a can. Sai da ya ɗan yi shuru kaɗan na ɗago ido ina satar kallon Sakina naga ta maida hankalinta gefe guda. Muryarshi ya ratsa kunnuwana"to shikenan ki kula mini da amanar kanki da na ba ki", kaina na ɗaga kamar ina gabansa sannan na ce ina sha Allah. Kit na kashe wayar ina maida numfashi tamkar wacce tayi gudun ceto rai, na saka ran Sakina za ta cigaba daga inda ta tsaya sai na ga saɓanin hashashena domin tsuke bakinta tayi. Sai ni na furta a raunana don Allah wannan ya sama sirri tsakanina dake bana son kowa ji. Ba tare da ta kalle ni ba ta furta"ke zan yi wa wannan roƙon Allah ya saka ki iya riƙe abin, don naga gabaɗaya ki zuzuce". Tana ƙare faɗin hakan ta miƙe ta bar ni zaune a wajen tashin ta ya yi dai dai da isowar yaya Sa'eed wajen ya zauna kusa dani sai da ya ƙare mini kallon tsaf kafin ya ce"meye amaryar gobe take yi a nan?". Ɗago kaina nayi cike da shagwaɓa na ce yaya Sa'eed, ban ƙarisa ba sakamakon dakatar dani da ya yi ta hanyar ɗaura yatsansa a bisa leɓensa yana faɗin"shiiiit bana son jin komai tashi ki shiga ciki ki gama shirye shiryen ki". Bani da zaɓi face bin umarninsa haka na miƙe jikina babu kuzari tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri na koma ciki. Sanda na isa an ganawa kowa Sakina ake yiwa ana gamawa aka fara ɗanɗasa min nawa cikin ƙanƙanin lokaci aka gama. Wasu danginmu suka shigo tare da su Anty Suwaiba suna ta yaba tsarin lallen nawan da bai cika yawa ba suna ɗauka na a hoto. Kafin ƙarfe uku kowa ya fara shirin zuwa dinner gidan ya ƙara cika da mutane babu masaka tsinke. Sai na gabatar da sallan asr mai kwalliyar da Anty Safiya da suke tagwaye da yaya Sufyan ta aiko ta musamman don ni ta fara tsantsara mini kwalliya, dukkan wasu tufafi da zan sanya a bikin ita ta samar mini dasu. Ina jin mai kwalliyar suna taɗi da Sakina tana labarta mata yanda Anty Safiya ta buɗe bakin jakarta a kaina don ganin na fita daban. Mahaifin yaya Sufyan da mahaifina wa da ƙani suke duk wanda ya san su ya san irin yanda suke so, ƙauna da kuma kulawa da junan su. Su kaɗai iyayen su suka haifa jinkirin haihuwar da mahaifiyar su yaya Sufyan ta samo, ya sanya Abba damƙa musu yaya Sa'eed tun yana shekara ɗaya da haihuwa wanda ya ci sunan mahaifin su yaya Sufyan. Sai da ya cika shekara ɗaya da rabi sannan Allah ya azurta su da haihuwar yaya Sufyan da Anty Safiya yayin da yaya Sufyan ya ci sunan Abban mu, basu cika watanni uku a duniya ba Hajiya ta haifo Anty Suwaiba tazaran shekaru uku ne tsakanin su da Anty Sadiya da take tsaran Sultan gambon su yaya Sufyan. Tun daga haihuwar Anty Sadiya Hajiya ta sama matsala har likitoci suka bayyana da wuya mahaifarta ta kuma ɗaukar wani cikin. Kafin Anty Sadiya ta rufa shekara biyu Allah ya ƙaddara kasantuwa ta a cikin cikin Hajiya. Haihuwar da ya zo mata da matsalar da ta sanya aka cire mahaifarta gabaɗaya. "Wallahi ke kam kin yi dacen iyayen miji da kuma miji irin wannan zallar ƙaunar". Zancen da kunnuwa suka tsinkayo mini mai kwalliyar ta furta kenan, da ya yi nasarar dawo da ni daga tafkin tunanin da nake ninƙaya a cikinsa. Dai dai sanda take miƙo mini madubi ina duban fuskata da kwalliya ya zauna a fuskar sosai. Tunin ta fara ɗauka na hoto doguwar rigar ta zauna sosai a jikina mai launin ja haka nan ma ɗaurin dake kaina da dogon mayafina ya kasance ja. Ƙiran Anty Safiya ya shigo wayata na ɗauka da sauri bamu tsaya dogon gaisuwa ba ta sanar da ni idan mu shirya ni da ƙawayena mu fito. Takalmin mai tsini na sanya na riƙe ƙaramar jakata a hannu, Sakina da Sonia sune a gefe dama da haguna a ƙofar fita muka yi kiciɓus da Anty Suwaiba da Anty Sadiya suka zuba mini idona suna faɗin kalmar masha Allah. Tunin motoci sun fara iso suna kwasar mutane izuwa wajen dinnern. Mota ɗaya muka shiga da Sakina da har yanzu bata ce dani komai ba nima na share ta. Hankalina gabaɗaya yana ga wayata da har yanzu ban cire rai da samun amsa daga Suraj ba, har motan taja burki a bakin tafkeken hall ɗin sai da aka ɗauki kusan mintinan uku kafin Anty Safiya da Anty Suwaiba suka ƙariso wajen suka buɗe motar. Tare da umartan Sakina ta sanar da ƙawayen mu su kammala waje guda domin su zasu fara shiga, ta fita domin aiwatar da hakan. Ƙawaye da abokan ango ne suka fara shiga a jere a layi guda biyu kwalliyan wajen ya kasance ja da fari kalan shirgar da muka yi. 'ya'yan su Anty Suwaiba, Anty Sadiya da Anty Safiya aka sanya a gaban mu suna tafe suna watsa wasu furanni akan lallausan shinfiɗar dake wajen. Tsananta bugun zuciyata ya yi dai dai da tashin ƙidar waƙar Ali Jita mai taken sadaki da ya karaɗe hall ɗin, ƙamshin turaren yaya Sufyan da suka baƙunci hancina shi ya tabbatar mini da kasancewar sa dab da ni. Na yi saurin rusunar da ƙwayoyin idanuna da suka cika taf da ƙwalla ƙasa, a hankali muke takawa masu hoto da naɗar video suna yi har muka isa ga inda aka tanada domin mu. Ya matso dab da ni har ina iya jiyo bugun zuciyarsa. A kunnena ya raɗa mini"kin yi kyau matuƙa Gimbiyata, amma menene ya kawar da wannan annurin da baya rabo da kyakkyawar fuskarki?". Sai da na haɗiye wani yawun da ƙyar kafin na sama damar furta kawai yanayin ne bana jin daɗinsa, hayaniya komai kaɗan ɗin sa ka san ciwon kai yake sa ni. Sai da ya ƙara yalwanta fuskarsa da annuri sannan ya ce"to ko dai in yiwa su Abba magana akwai daren yau a ɗaura a cikin gida, saboda amaryar bata son hayaniya". Harara na watsa masa ina ƙara damƙe fuskata. Ji nake yi tamkar na sanya hannu a kai na ta kurma ihu ko zan ji sauƙin zogin nake jin yana sukar zuciyata. Mami ce ta buɗe taron da addu'a sannan aka fara gabatar da abinda ya kamata komai an yi shi cikin tsari. Duk mahalalta taron fuskokin su a watse da tsantsar farin cikin da ya gaza ɓoya. Lokacin da Momma mahaifiyar yaya Sufyan take gabatar da addu'ar samun dawamamme farin cikin a cikin auren mu sai da hawaye suka zuba daga idaniyata, wani kunya da nauyinta suna ƙara narkar da raunanniyar zuciyata da don Suraj ya gama yi mata illa. Na sama kyaututtuka daga gare ta da kuma wasu dangina. Ƙarfe bakwai aka tashi domin su Abba sun yi gargaɗi kai wa dare, duk yanda yaya Sufyan yaso mu keɓe bijirewa nayi. Raina a jagule nake fige kallabin kaina ina firawa akan gadon ban damu da kallon da mutanen ɗakin suke yi mini ba domin basu bane a gabana. Muradina bai wuce samun amsa daga Suraj ba kafin wayewar gobe da ɗimbun jama'a zasu shaida ɗaurin aurena. A tare Anty Suwaiba da Anty Sadiya suka shigo ɗakin dukkan su idanunsu a kaina, suka ce ga su Sakina su jira a falo zasu tattauna da ni. Sai da suka gama ficewa gabaɗaya sannan Anty Sadiya ta kamo hannuna ta zaunar da ni ta zauna kusa da ni. "Me yake damun ki ne? kowa sai maganar yanda kika canja wajen dinner yake yi. Ko akwai wata matsalar ne?". Kaina na jijjija mata alamar a'a ta sauƙe numfashi haɗi da faɗin" ba ki da waɗanda suka fi mu bayan su Hajiya a duniyar nan Surayya don haka ki sanar damu". Tsinta kaina nayi da faɗin babu wata matsala wacce ni dai na san da ita a yanzu, kawai inna tuna zan yi nisa da Hajiya ne nake jin wani iri. A tare suka sauƙe ajiyar zuciya kafin Anty Suwaiba ta hau yi mini nasiha da nusar da ni cewar hakan normal ne mafi yawan amare suna fuskantar irin wannan yanayin. Sun daɗe suna kwantar mini da hankali kafin suka fice, wanka nayi sannan nayi alwala sanda na fito na tarar su Sakina su ma suna tasu sallar. Akan sallayar na zauna ina kirari ga ubangijina tare da addu'ar ya zaɓa mini abin da yafi zama alkhairi a gare ni, jikina babu kuzari na shafa addu'ar raina cike da fargaba. Sai bayan sallan isha'i muka sama keɓewa da Sakina wani kallon da na kasa fahimtar inda ta dosa ta kafe ni dashi kafin ta ce da ni"kin kyauta abinda kika yi kenan?". Cike da rashin fahimta na gwalalo ido tare da cewa me nayi?, Ta tsirtar da siririyar tsaki kana ta ce"duk kin bi kin haɗe rai a wajen dinner ɗin nan kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta". Zazzafan iska mai ɗumi na fesar daga bakina na ce na rasa yanda zan yi ne Sakina wallahi komai ya yi mini zafi. "Ai dole ki rasa yanda za ki yi tunda kina ƙoƙarin ɗaukar dala ba gammo. Ki nutsu ki san inda yake miki ciwo tun kafin ruwa ya ƙarewa ɗan kada. Soyayyar gaskiya bata taɓa gushewa sannan masoyi na gaske baya taɓa juyawa masoyinsa baya cikin ko wani hali na rayuwa. Yaudara ce ta dawo da Suraj cikin rayuwarki a yanzu, da za ki nutsu da kema kin hango hakan. Meye amfanin soyayya da mayaudari marar tausayi?, wataƙila ma sam babu tsarin aurenki a cikin zuciyansa". Daga nan ban ƙara fahimtar abin da ta ɗaura dashi ba sai dai ganin leɓɓanta suna matsawa da hakan ya bani tabbacin maganar ta cigaba yi. Sai bitar zantukan nake yi, tabbas so masifa ya zama a gare ni. Ko da naje kwanciya ƙiran yaya Sufyan ya shigo wayata na katse na tura masa saƙo da uzurin kaina ciwo yake mini ba zan iya maganar ba, daƙiƙu biyu tsakani ya dawo mini da amsa cike da kulawa gami da tausayawa cikin kalamansa yake yi mini addu'ar samun lafiya. Wayar na ƙurawa ido ƙirjina yana dakan lugudai, sam bacci ya gagari idanuna na kunna data na ziyarci whatsapp. Take na wartsake na tashi zaune ina mirtsike idona don tabbatar da sahihacin abin da nayi tozali dashi. Cikin rawar jiki na buɗe saƙon da Suraj ya maido mini shi. "Ki yi haƙuri sai yanzu naga saƙonki ina can wajen fafutukan yanda zan haɗa abin da zan mallake ki. Bana son samun sauƙi, taimakon wani ko kuma rangwame wajen samun ki. Zan yi aiki tuƙuru don na mallake ki na samar miki da farin ciki marar yankewa". Kamar wacce aka tsigarawa allurar dawakai haka na diro daga kan gadon na nufi banɗaki a harzance. Ruwa na buɗe yana zuba domin kar aji sautin kukan da ya ƙwace mini, bayan soyayyar Suraj da ta yi babakere tare da zaman dirshan a cikin zuciyata tausayinsa da ya ƙara mamaye ta. Take naji ya goge mini dukkan haddar da Sakina ta gama tisa mini game dashi. Hannuna yana rawa na rubuta gobe ɗaurin aurena Suraj gobe na zama mallakin wani ba kai ba. Ina gama turawa na sulale ƙasa na zauna saboda bijirewan ƙafafuna da nuna gajiyawar su da ɗaukar nauyin gangar jikina. Son Suraj yana ƙara bin ko'ina a cikin jikina tabbas so bai yi mini adalci ba. Da ina da iko da na zaro zuciyata na wanke komai na cikinta na sanya soyayyar yaya Sufyan kaɗai na mayar da ita. Sai dai kash bani da wannan ikon, haka nan na tsinta kaina da yin addu'ar Allah ya ɗauki raina kafin wayewar gari gobe domin yanda nake ji gwara na mutu akan a ɗaura aurena da wani saɓanin Suraj. [11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writings by Amina maaji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA SHIDA Zaku sanya kuɗin ku ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan no 08068748984 Muhammad ya kasance namiji ne matashi mai kamala da natsuwa son kowa ƙin wacce ta rasa, tsayayye ne mai irin zubin jarumai ɗin nan amma a fuska yana kama da larabawa sakamakon kasancewar sa bafulatani ne, ba laifi kam a wajen kyau nan ma ba kafar baya ba ne domin sai de ace Tubarkallah Masha Allah! Domin dukkan wata ni'ima Allah ya wadata shi da ita ga hakuri da kuma riƙon amana sannan kuma tsayayye ne wajen lamurran addini ba ya wasa wajen ibada. Duk irin wannan baiwa da Allah ya masa sai de kuma shi mutum ne mai saurin fushi shiyasa baya fiye shiga lamurran da basu shafe shi ba saboda gudun raini. Iyayensa sun kasance mutane ne da zama ya ɗauke su ya kai su jihar Borno a sakamakon mahaifinsa ma'aikacin gwamnati ne aiki ne yasa iyayensa tarewa da zama zuwa can, shiyasa dukkanin ƴan gidansu sai al'adun su ya fara canja wa zuwa na Barebari a sakamakon zama da su amma su asalin su Fulani ne na jihar Adamawa. Muhammad sun kasance su biyar ne a wajen iyayensu yayun sa mutum biyu maza da kuma ƙannensa biyu shima mata idan da shi su biyar kenan wato shine ɗan tsakiya shiyasa sai ya zama a gidan kowa nasa ne kuma yana girmama kowa ba tare da tawaya ba ko kuma fifiko ba amma da akwai autarsu mai suna Maimuna amma yakan kiranta da Mimi sakamakon tsokalar ta da yawa take mafi yawan lokuta suna wani abu kamar gwaigunan talabijin wato Tom da Jerry amma kuma favorite ta shi ce duk da wasu lokutan suna ɗan dana rikici idan sunan Muhammad ɗin ya motsa. Ranar sa ta farko a jami'ar Maiduguri wato UNIMAID ita ce ranar da ta zama masa silar ta shi baƙar ƙaddarar duk da ɗan Adam ba ya wuce kaddara amma a WATA MAHANGAR kuwa jarabawa ce domin kowane mutum da irin ta shi jarabawar a faculty na science sashen ne mai girma domin departments din da suke wannan faculty suna da yawan gaske amma sai de kuma shi yana department na Laboratory ne domin shi tun yana yaro yake da burin zama ma'aikacin binciken cututtukan dake cikin jini. Zuwansa bakin department nasu ya duba jadawalin shiga aji ɗaukar darasi yaga sauransu wasu mintinan da basu wuce goma ba nan take ya wuce izuwa ɗakin ɗaukar darasi domin jiran malamin da zai karanta da su. Bayan sun gama ɗaukar darasi kowa yana fita daga cikin dakin shima ya mike tsaye kenan wata kyakkyawar budurwa su biyu suka masa sallama. ''don Allah idan ba za ka damu ba suna na Khairat, ina so da ka bani lambar wayar ka domin idan bamu da darasi muna yin bitar karatu a tare domin na lura da kai kana da fahimtar abinda ake koya mana fiye da sauran daliban ajin'' tana mai yin murmushi. ''babu komai ai amma cewar na fi kowa fahimtar ki janye wannan maganar'' cikin zolaya ya furta hakan dukkanin su suka tuntsire da dariya haka suka yi musayar lambar waya suka rabu da nufin sai washe gari saboda sun gama ɗaukar darasi na wannan ranar. Khairat ba ta da wani aboki da ya wuce Muhammad kamar yadda Hausawa sukan ce ''idan kaga wata a gefe za ka ga zara'' to haka suke a kodayaushe don kowa kallon soyayya da juna ake musu suke yi amma su kuwa a nasu bangaren ba haka bane musamman ma shi Muhammad. A kwana a tashi alaƙar da ke tsakaninsu ta fara barin iya makaranta kaɗai don ko sun dawo gida basu da aiki sai waya da kuma yin bidiyo call a tare da juna, a takaice dai shaƙuwa ta shiga tsakaninsu. Muhammad yana gida a wata ranar hutun karshen mako sai Khairat ta kira shi a bidiyo call tana sanar da shi cewa ta yi kewar shi don ba ta gana da shi na wuni ɗaya ba yana tsaka da mata dariya sai yaji ta bayansa an fizge wayar da ke hannunsa ''la...l..a..la! ya Muhammad dama Aunty tamu ce kake ɓoye mana ita idan za kayi waya sai ka ɓuya duk don kar mu ganta to yau Allah ya to ni asirinka sai na nuna wa Mama ta gani'' ''don Allah ki yi haƙuri kar ki yi haka so kike ki zubar min da girma na ne a wajen Mama"? Mimi kuwa tayi biris da shi kamar ba da ita yake ba sai ma cewa da take ''kyakkyawar Aunty ta ina kwana"? Kin ga ya Muhammad da wani ɓoye mana ke duk don kar mu san ki cikin shagwaɓa take maganar Khairat me take kuwa ban da dariya domin jin yadda Muhammad yake ta magiya da bada haƙuri a autarsu domin ita Khairat duk ta san ƴan uwansa a hoto domin duk abinda ya shafi rayuwar sa da ƴan uwansa duk ta sani nan dai ta lallaɓa auta da alkawarin cewa za ta zo musu takanas ta Kano don ta zo gaishe da Mama amma yanzu kam ta yi haƙuri kar ta aikata abinda ta yi niyya. Mimi tace zan haƙura amma ki zama shaida sai ya Muhammad ya siya min rake mai zaƙi zan haƙura don idan bai yi ba zan fasa taya! ''e, na yarda zan siya miki mai zaƙi ma kuwa wanda har sai kunnenki ya fadi ƙasa don daɗi'' yana mai durkusawa na rokon da ta ba shi wayar Mimi tace ikon Allah! Yau su yaya har da durkuso! Tana taɓe baki ta mika masa wayar ta yi cikin gida tana dariya ta bar shi yana wayarsa. Can bayan irin sakaliyar la'asar ana zazzaune a cikin falo ana kallo sai a kalli Maimuna ta kalli ya Muhammad ta yi gyaran murya da sun haɗa ido sai ta tuntsire da dariya shi kuwa sai ya haɗa rai don abun nasu har ta kai ga Mama tace da su kai abun naku lafiya kalau kuwa bana son iskanci fa me kuka ƙulla na munafurci da yake cin ku? Sai Muhammad ya yi caraf! Yace Mama ba komai kawai Mimi ce ta raina ni kuma laifi na ne! Yana mai jijjiga kai ai kuwa Mimi tace Mama ba....ya yi saurin tasowa da gudu zuwa wajen ta ya rufe mata baki da hannu ke me yasa ba kya jin magana ne? Ba mun gama magana ba? ''ikon Allah! Idan ta yi tsami ma ji'' shine maganar da Mama ta yi. Wasa gaske soyayya mai ƙarfi ta kullu tsakanin Khairat da Muhammad inda shi Muhammad yana ta tsara rayuwa a tare da Khairat da zarar sun kammala karatu amma kuma Saide kash! Ba a nan gizo ke saƙar ba domin kuwa Khairat kura ce da fatar akuya domin a nata ɓangaren bata taɓa mafarkin ta yi rayuwar aure da Muhammad ba domin ita ta kasance mace ce mai kwaɗayi da son abun duniya don ita shazumami ce duk inda zaƙi yake tana bi ta lasa wanda shi Muhammad kwata-kwata bai san da asalin boyayyar fuskar Khairat ba wanda a nasa zaton mace ce mai kamun kai amma ba haka bane domin da akwai watarana da suna zaune sai ta rike hannunsa yace da ita ta bari haramun ne mutum ya taba wacce ba muharramar sa ba nan ta rinƙa ce masa dama ashe bai waye ba? Maganganu marasa daɗi dai suka bayyana daga wajen ta daga nan Muhammad ya fara ƙokonto a kan wace ce Khairat? Kwatsam! Yana tafiya a cikin makaranta watarana a bayan wasu samari sai yaji suna hirar ai yarinyar ana ganin ta a otel tana yawa da maza wannan maganar ta tayar da hankalin Muhammad sosai don kwana ya yi yana bibiyar maganar a ransa wanda daga ƙarshe tsintar kansa ya yi a gadon asibiti nan ne ya fahimci cewa ba shi da lafiya ne. A ɗayan bangaren kuwa likita ya sanar da iyayen Muhammad da su kula da rayuwarsa domin tana cikin hatsari a sakamakon ya kamu da ciwon zuciya kuma Sa'a aka ci da zuciyar bata buga ba amma dai su kula sosai wajen kiyaye duk wani abu da zai bakanta masa rai ko kuma zai jefa shi cikin tunani. Ita kuwa Khairat ko a jikinta domin Muhammad ya rayu ko kar ya rayu ba damuwar ta ba ce domin ita ta cimma nata muradun a tattara da shi don haka ba ta da bukatar shi. Wannan ita ce rayuwar Muhammad kafin ya fara soyayya da Nusaiba. [11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR MARUBUTAN JAHAR YOBE Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Kai tsaye zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 400 FCMB sai shedar biya ta wannan no 08068748984 LAMBA TA BAKWAI Wace ce khairat ?. Khairat mace ce wacce ta taso tun yarintar ta ba tare da mahaifiyarta ba dukkan wani irin gata da ɗa yake samu da kuma kulawa ta tarbiyya duk ta rasa su sakamakon mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙarama, ta tashi a gaban matar ubanta wacce take gallazawa rayuwarta ba ta bata kulawa da kuma lura da tarbiyyarta ballantana har ta damu don wajen tsare mata mutunci, yaro tamkar dabba yake idan ba a kwaɓarsa idan ya yi abu ba daidai ba domin shi bai san mene ne abu mai kyau da maras kyau ba, Khairat ta tashi cikin abokai maza tun a matakin firamare har zuwa matakin ƙaramar sakandare je-ka ka dawo ba ta da abokan wasa da kuma hulɗa sai maza saboda ita wacce take hannunta ba damuwar ta ba ce da Khairat ta zama mutumiyar kirki ko akasin haka domin ita bata taɓa haihuwa ba. Aikin cikin gida kuwa duk min wahalarsa haka Khairat ita ce za ta yi shi, a kwana a tashi Khairat ta kammala karatunta na matakin je-ka ka dawo za ta kara matsawa zuwa mataki na gaba wato sakandare wanda daga shi sai kwaleji ko kuma jami'a, nan uwar goyonta ta matsa akan ala-tilas sai an kai Khairat makarantar kwana ta mata domin ta yi karatu a can wanda a ɓoyayyen manufar ta kuma shine Khairat ta bar mata gidan domin ta sakata ta wala iya ma'ishinta. Rayuwa haka ta ci gaba a Khairat a wurin da babu kowa nata sai abokan karatun ta wuri ne da ƙaddara ke zaɓa wa mutum rayuwarsa ta silar aboki ko kuma ƙawar da aka haɗu da su a cikin makarantar idan har abokai sun zama na gari hakika mutum ya yi dace idan kuma aka yi rashin Sa'a aka haɗu da gurbatattun abokai shikenan rayuwa kuma daga nan takan lalace kamar yadda mai littafin Ta'ilimi yace ''ɗabi'a naso take'' ma'ana dai dabi'u kamar mai ne da ya zube a kasa sannu a hankali yake matsawa zuwa ga wani abun haka rayuwar Khairat ta ci gaba da gudana a makaranta tare da wasu wayayyun ƙawaye waɗanda suka sauya mata rayuwa daga wacce take izuwa ƴar maɗigo wanda tun tana yi a tsorace har ta zo ita ma ta zama goggagiya a harkar ta tara ƙawayen banza sosai a rayuwarta waɗanda duk babu nagari a cikinsu ballantana a samu wacce za tace da ita ''mu ji tsoron Allah'' Kwanci tashi Khairat tana a ajin ƙarshe na gama karatun Sakandire abu kamar wasa a kama ta ita da wasu ƙawayenta suna aikata maasha'ar da suke yi wanda har ya yi sanadiyar da aka nemi mahaifinta don za a kore ta daga makarantar kuma haka aka yi domin jarabawar karshe ba a makarantar ta rubuta ba wata makarantar mahaifinta ya nema mata na je-ka ka dawo domin yana kallon motsin ta amma hakan duk ba ta sauya zani ba domin kuwa maza ne suka fara mata cincirindon zuwa wajen ta kuma duk tarin iska babu nagari wanda zai iya aurenta kowa da tasa manufar domin sun fahimci Khairat ta cika kwaɗayi da son abun duniya wannan ya bawa mazaje dama da yawa wajen cimma muradun su a kanta. Khairat ba ta mu'amala da mutum matukar ba za ta amfana da shi ba domin ta riga da ta zama kaska raɓi mai jini cikin kankanin lokaci ta sauya tsarin halittar ta daga baƙa zuwa fara ta hanyar shafe-shafen mayukan sanja launin fata. Khairat mace ce son kowa ƙin wacce ya rasa dirarriya ce ga ta kuma da kyawun ta Tubarkallah! Amma kuma kyawun ɗan maciji ne ga kyau ga illa. Tun a farkon haɗuwar ta da Muhammad ta fahimci cewa bata taɓa haɗuwa da ɗa namiji kamili wanda yake son ta tsakaninsa da Allah ba kamar shi kuma shi kaɗai ne a tarihin rayuwarta yake iya gaya mata gaskiya duk min ɗacin ta hakika ta so Muhammad so na gaske amma sai dai kuma kwata-kwata baya a tsarin samarin da take mafarkin mallaka domin shi ba namiji mai ƙarya ba ne ko kaɗan ga shi ita kuma da rayuwar karya ta taso shiyasa mu'amalar ta da Muhammad ba ta yi tsawo da rai ba sakamakon dabi'un ta da ta nuna wajen bibiyar malamai na banza a cikin makaranta. Ita ba damuwarta ba ce tun safe ta fito daga gidansu kuma ba za ta koma har dare da sunan an je makaranta sannan irin manyan wayoyin hannu da ta ke rikewa nan ne za su bawa mutum mamaki domin ba aikin komai take ba amma take rike irin wadannan wayoyin. Watarana Muhammad suna zaune a cikin aji shi da Khairat da abokinsa da kuma ƙawar Khairat ita ma sai ƙawar Khairat tace ƙawata ba fata nake miki ba amma idan har kika rasa Muhammad ba ki aure shi ba to gaskiya ba za ki taba samun kamarsa don haka ki riƙe shi hannu bibbiyu Khairat ta kalli Muhammad ta sunkuyar da kai ƙasa yayin da Muhammad yace wallahi Khairat ba za ta aure ni ba! Cikin mamaki ƙawar Khairat tace amma mai yasa ka faɗar hakan? Ko ƙawa tace ta gaya maka hakan? Muhammad ya yi murmushi kana yace a'a ai ita ƙawar ki ce ku je duk lokacin da kuka zauna ki tambaye ta me yasa na yi wannan maganar tabbas za ta ba ki amsa domin ita ta sani amma ni kam ba za ki ji amsar daga baki na ba nan dai Khairat ta yi kokarin canja hirar domin kwata-kwata hirar ba ta mata daɗi ba. Mata su na kuskure da yawa a rayuwa da sunan soyayya kana suna jefa rayukansu cikin haɗari duk da sunan soyayya wanda daga baya kuma suke zagin namiji da munanan kalamai wanda asali ba sa duba na su laifin ai Bahaushe yace sai bango Ya tsage ƙadangare ke samun mafaka kuma hakane domin kuwa duk macen da ta kama kanta ta fi ƙarfin wulaƙanci da kaskanci a wajen namiji kuma duk macen da namiji yayi amfani da rauninta wajen cutar da ita to lallai ba ta da wayo kuma ba ta cika cikakkiyar mace ba domin mace ita ce ke da wayo da hikimar juya tunani da halin namiji koma wane ne shi, amma rashin sanin matsayi naki shi zai haifar da duk wani tozarci da namiji zai miki. Da mata suna da wayo da na basu wani sirri game da halayyar maza. Duk namiji mai zaman majalisa ba mijin aure ba ne, duk namijin da ya cika kula-kulen mata ba mijin aure ba ne amma ta ya ya ake gane mijin aure? ''kalamansa!" Cikin hirar ku nan za ki fahimci wane irin mutum kike tarayya da shi. [11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki 400 a wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan no 08068748984 LAMBA TA TAKWAS Haka na sha kuka na batare da wani ko wata sun rarrashe niba .a karan nan ko bani da zuciya zan ta kawa JB burki . Duk lokacin da mukayi faɗa da JB tabbas in ka ganni zaka san da muwa da tararradi sunyi mun yawa .da far gaban rasa JB .a na cikin wannan matsalar sai ga kiran mahaifiyar Muhammad tazo zai gaishe ni,a kan rashin lafiyar da nayi tsara ba da yawa ta kawo mun irin wanda marasa lafiya suke nema, tun bayan rasuwar Muhammad. a duk lokacin da mum zata ji banida lafiya ko dai wani ,abu ya sameni in ban gan taba' zan ga hannun ta a wannan karon sai na tsinci kai na da jin kunyar mum sai nake ganin kamar zata gane meya shiga tsakanina da wani bayan ɗan ta ban taɓa tsan manin har akwai wani wanda zan so ba bayan Muhammad ba.sai gashi ƙaddara tasa nafara mantawa da shi ,a ƙarshe har da cin amanar shi. Mum sannu da zuwa ya hanya na warke da baki zo ba wallahi a saran kuɗin mota ne ai naga mun gaisa a waya ,uwata kamar yadda take kirana na don Muhammad mai sunan baban tane "ba zan iya jure ganin ki ,kina kwance nikuma in zauna cikin tararraɗin rashin dubo ki ba ,nayi Wa babana alƙawari cewa zan kula da ke ,da,a kwai ɗina da babu na zanyi iya kar ƙoƙari na in sha Allahu". "Na gode mum Allah yasa ka ya biya ku da gidan Aljanna . "Amin uwata" Ina son ki kwantar da hankalin ki,uwa ta kiyi aure in kin samu wanda ya kwanta ,miki a rai dan Allah wallahi zan so ganin ki,a cikin gidan ki"mum ba zan taɓa samun wanda zai so ni kamar yadda ya ke so na ba."nasani amma bake ganin Allah ya ɗauke shine dan keba matar shi ba haba uwata nasan ki da sani kar,sheɗan ya hanaki samun lada kitina aure fa,ibada ne ". maganganu masu ratsa jiki tatayi mun ,har nace mata a kwai wanda na keso ,a barno yake tayi mana fatan alkairi dan nakira JB baima ɗauka ba ƙarfe biyu direba ya zo ɗaukar ta,a bun da ta kawo mun naji daɗi sosai Allah sarki mum tana ji dani ina ma ace ni sirikar ta ne ina son mum macece mai kulawa da ɗan adam . tinawa nayi da lokacin da suka ɗauko a kwatin da muka siya da Muhammad suka kawo mun wai shine ya bar wasiyya a kan a bani na nuna bazan karɓa ba ,har kuka sai da tayi ganin babbar mace na kuka shine na karɓi wasu daga ciki ,ita ma na bata nace ta ɗin ka haƙiƙa mum tana sona ita uwa ce tagari wallahi haɗuwa da JB shine babban matsala ta a rayuwa ta. cen sai da ya tashi daga shago goma da kwata kafun ya Kirani "daman maman Muhammad ne tazo duba ni shine nace ko zaku gaisa ,ta ce in gaishe ka"ayya bana kusa da wayar ne tatafi ne? e tatafi Allah sarki ki gaishe ta sosai amma na daɗe banga soyayya irin taku ba gaskiya abun yana burgeni sosai da kulawan da suke nuna miki ina jin daɗin hakan ta,iyu ke rabo nane shiyasa yabar duniyan. Noor kenan ai ita soyayyar gaskiya a na gina ta 'tahanyar da ta dace ne in kaga haka su ,ai zuciyar su ɗaya ne in da wasu ne a yadda nice ƙarshen waya da shi kafun ya rasu bincike sai ya ,hau kai na amma daya ke su ba jahilai bane basa jayayya da ikon Allah . a haka muka ta hira da shi kamar bai gayamun magana a kan yarinyar da za,a ba shi ba in kana so kaga JB ya rikice tou ko banida lafiya ko dai in ce zanje asibiti dan in duba lafiya na tou a rana zai ta kirana zai ce mun ya jiki wato tsabagen da muwa ,watarana sai in ga zuciya na ya dai na aiki dai dai kamar na sauran muta ne. Kwana kusan uku shine ke fara ta shina ya ce mun ya jiki kin sha magani ,ina ne kemiki ciwo ki daure ki sha magani mana ba nason rasaki Hayat zan shiga cikin da muwa,muta wasa da shi har in ta zo ,layan shi . "In kuma kaji na mutu fa"? "dole na zan haƙura dan babu yadda zan yi dan mutuwa da rayuwa duk ta Allah ce "a kwai wani ranan da bakina ya suɓuce nace mishi in ya Muhammad kafun in rufe bakina naji ya ce mun " nifa zancen wannan Muhammad ɗin ya,ishe ni, taya mutum ya mutu ma,bazai barki ki huta ba taya zanji daɗi amma nikuma kullum ki dameni da wani zancen Muhammad ,in kinsan za ki damu meyasa kika barshi ya tafi baki tsai da shiba. Sai naga fishi a tare da shi sosai ranshi ya baçi"haba JB yanzu ka rasa da wama zakayi kishi sai ya Muhammad amma gaskiya a kwai alamar tambaya a tare da kai wani irin kishi ne a tattare da kai ". Iska ya fesar irin yadda yawancin maza in ransu ya baci, haka sukeyi yi ya zame musu al,ada . "Ikon Allah" A take nima na nemo nawa ɓacin ran sosai jina shiru yata, magana sai da yayi baki uku kafun nayi magana ina jin ka"me yasa kika nuna ranki ya ɓaci ?"JB " yau kuma suna na kike kira tsirara haka? . "Zan kira sunan ka wanda ma ,a ka yanka maka ragon suna da shi ,ya kake so nayi kai baka bani kulawa yadda nake so ba sannan iyayen ka sunce aure zasuyi maka yanzu ƙaddara ban aure ka ba ,so kake ka rabani da kowa nawa kenan ko dai da kai kaɗai zan rayu bayan ku maza bakuda tabbas". Karki ga laifi na Hayat nake ganin wannan sirikar taki kaman kama,ƙafa take yi a yaron ta ɗayan in ba haƙa ba taya daga jinya tace zata zo a haka ma sai ta kawo miki wasu a'bubun . masifan JB ya,ishe nika she waya ta nayi ga ba ɗaya yata nema a rufe na rasa meye matsalan shi ga ba ɗaya, mutum kullum bashida alƙibila wannan rayuwar tafara gundura na . kwana nayi ban buɗe wayar ba da ƙaramin waya ta nayi amfani wanda bashi da ma number,zan so in gina sabuwar rayuwa wanda ko da bana tare da JB ba zan taɓa samun matsala ba in kuwa zanyi aiki da basira da tunanina yaro ƙarami duk ya rikita mun lissafi ai kuwa naga soyayyar yarintar kuwa. JB ya kasance mutum ne mai son kan shi ba shida mara ba da baƙin maciji ya kasance shi a shanane halayyar JB babu wanda zanyi alfahari da shi koma yaya ne don yazama mungu. aikin fishi kuwa shine zance yazama mishi al,ada Allah wadaran sayayyar JB yayiwa so mummunan fahimta da,ace zan ,iya komar da kai na baya to da na cenza wa JB .ina buɗe waya ta kiran shi yana shigo wa bayan na ɗauka"meyasa kika kashe wayar ki ? Shiru nayi don banida amsar da zan bashi kawai ya hauni da masifa" don kin ga na damu da kene shiya sa kike yi mun walaƙanci" ko tanka mishi banyi ba na barshi sai da ya huce kafun na sanar da shi gobe ƙarfe tara zanje asibiti yayi mun fatan alkairi nace to na gode wunin ranan yawanci in ,ina online zan ganshi bai yi mun magana ba nima ban yi mishi ,ba in natina wanda iyayena suka zaɓa mun na bijire musu a kan wanda bai san ma,ina yi ba sai abun ya bani mamaki .daman a kwai ranan da iyayena zasuce in yi abu in ce a'a don soyayya kenan , washegari ƙarfe tara na safe a asibiti yayi mun doctor Ibrahim Sulaiman bayan dubani da yayi sannan har zan fita daga officer ɗin shi naji ya kira sunana "Nusaiba juyowa nayi na tabbatar da shi yake kirana bawai wani ba,na,amsa "ki dawo a kwai a,bun da nake son gaya miki sai cewa nayi to na dawo na zauna bayan shiru da ya biyo baya sai naji yayi gyaran murya "dan Allah kibani lokacin ki ina son muyi magana mai mahimmanci "ba komai doctor ina jin ka kafaɗi koma meye ne " wallahi ina mungun tausayin ki ,a kan irin halin da kike shiga idan ciwon ki ya tashi,ki bani zuciyar ki ki,amince mun ina son ki da aure zan kula da ke tunda nine likitan ki halayyar ki ba ƙaramin burgeni sukeyi ba kiyi mun wannan alfarman dan Allah kina burgeni nasan wasu bazasu so,su auri mai jinya irin naki ba dan jinyar tanada hatsari nikuma a hakan na ke sonki . Doctor kayi haƙuri na gode da soyayya ban,iya soyayya guda biyu ba a lokaci ɗaya saboda yanayin da nake ciki sannan nayi mishi alƙawari bazanci amanar shiba zan kula da soyayyar shi a gareni doctor ina jin nauyin ka amma kayi haƙuri dan girman Allah ka taima kamun karka ƙara wannan maganar pls doctor... [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Kai tsaye zaki sanya kuɗin ki ta wannan asusun 400 Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan no 08068748984 LAMBA NA TARA *Ni kai na labarin yana taɓa zuciya ta dan haushin Nusaiba nake ji wallahi abu kamar dole haba so hauka ne* Na ɗauke ka a matsayin yayana ne.sannan malami na abu na ƙarshe kafiye mun ,mutane miliyan a guna sannan kai wani jigo ne ga rayuwa ta,da a,ce babu wani wanda nake so tabbas ka cancanci kyautar da bata da iya ka agareni. "babu komai daman nasan ba lalle ne ki yadda da ƙudiri na ba .da kinsan yadda na damu dake sannan nadaɗe ,da,daƙon sonki a rayuwa ta wallahi a yadda na sanki ke macece mai tausayi ki kan,iya sadaukar da farin cikin ki saboda wasu ke ba matar walaƙanta wa bane kiyi mun uzuri bazan dai na son ki ba har lokacin da zaki wai-wayo gareni ina miki fatan alkairi "ka yafe mun doctor soyayyar JB tayi mun kamun da bana ,iya control ɗin kai na "nine wanda ya dace da ke Nusaiba ki, karɓi tayin da nayi miki kar kibar wani da bai san amfanin ki a duniya ba ya walaƙanta ki". Ganin hawaye na zuba daga idon doctor sai naji kunya sosai narasa yadda a,kayi ban damu da kowa ba nidai farin cikin JB nake so dayawan mutane masu daraja wanda, suke da tarin matsayi a gareni a dalilin JB duk na watsar dasu ganin na shiga tinani sai jin muryan shi nayi . Tashi in kaiki gida! a razane na ɗago fuska ta wanda ta cika da damuwa ko ban faɗi damuwar ba duk wanda ya kalle ni zai gane hakan a tattare dani Fita nayi daga cikin officer ɗin har na manta waya na a cikin officer ɗin shi ina tsaye sai naji yace "ga cen motar muje" da to na bishi doctor mutum ne mai wasa da,dariya mai barkonci yana sa kowa farin ciki a yau na kasa karɓan uzurin shi don saboda soyayyar JB tayi mun kamun zaren leda wayyo ni,tun da muka shiga mota babu wanda yayi magana a ɗan uwan shi kowa da abun da yake saƙawa a ranshi jinayi ya tsaya ,ɗago ido na nayi sai muka haɗa ido da shi naji ya ce"zan sai abu ne kiyi haƙuri "siyayya yayi ganin shi nayi da leɗa a hannun shi buɗe marfin motar yayi "a yi mun afuwa Nusaiba na daɗe ko kiyi haƙuri kinji ". "Ba ko mai doctor" Min tina kaɗan ne ya kai mu unguwar mu,bayan ya tsaya a ƙofar gidan mu,nayi ƙoƙarin fitowa daga motar "ga wannan ga kuma magunguna ban sanki da ƙin shan magani ba dan Allah karki dinga barin da muwa yanayi Miki yawa sannan ki ɗauka bamu taɓa yin magana da ta shafi soyayya ba dan Allah ki tausaya mun dan nasan in kin tashi shan wahala har dani don nasan kinsan irin wahalar da kike sha kinji in sha Allahu irin wannan haƙurin naki zanyi Miki takwara ko zata biyo halin ki .in kuma ta biyo irin jinya ta fa?" ai shima zanyi iya ƙoƙari na koda bata warke ba za dai ta samu sauƙi a ranta". Sallama mukayi tare dayi mishi godiya sosai na shige gida babu kowa a tsakar gida dan halayyar mutanan gidan mune basa zama,a tsakar gida kowa yana ɗaƙin sa cin karo nayi da Ibrahim ɗan yayan Hajiya"ya Ibrahim yau she kazo ya barno ?" lafiya Nusaiba ya jikin dafa yanzu zanje in ɗauko ki Hajiya tace kinje ganin likita nifa wannan jinyar daga zaran an aura mun ke shikenan kin san ance farin ciki ciwon zuciya yake ɓuƙata ko. Sauri nakeyi gashi ya dameni da yawan surutu ledar hannu na ya riƙe muka ƙarisa cikin gida har ɗakina ya kai mun kayana ya fice dan bani sarari ya na fita naji hawayen da na maƙale ya zubo mun a fuska na .naji tausayin doctor duk mutanan da zan samu gata a wajen su, basu ne zuciya ta take soba nasaka zuciya na cikin ruɗani da far gaba da tashin hankali wallahi ina nadama wato JB shine ƙaddarata a rayuwa na gashi tun safe bai Kirani ba na hau Whatsapp na duba shima shiru nayi mishi sallama sai da yayi kusan minti talatin ga shi yana online amma bai amsa ba cen naƙara ce mishi na dawo naga a lamar ya buɗe ce mun yayi ya jiki nace da sauƙi "kiyi haƙuri yau mutane sunyi mun yawa a shago ne shiyasa ban samu damar kiran kiba amma ki yafe mun sai naji fishin ,da nakeyi da shi na janye da sauri,ban ɓoye mishi yadda mukayi da doctor ba. komai na gaya mishi sai dai na ɓoye a bun da zai saka shi ɓacin rai abun takaici sai ce mun yayi"nagode da soyayyar da kike nuna mun amma ina so kisani manyan masu kuɗi da manyan yan kasuwa suna nunawa suna sonki, kina da farin jini da amana da alkunya baza kirasa wanda ya fini komai ba, amma narasa dalilin ƙin amincewar ki nifa kinga abun da iyayena suka ce kar,in ɓata miki lokaci ban aure ki ba kiyi kuka dani wataran"a jiki na nakeji kai mijina ne zan zauna da kai koda baka da komai sannan koda ciyawa ,zamuci ba matsala"Nusaiba mudai samu ƙudin waya ki ɗaɗi babu wanda yake son wahala. Amma meyasa daga zaran munyi faɗa kake dawowa rayuwa ta ,ya kamata mu dinga mantawa da juna zaifi mana "nasan kina sona sannan kin nuna mun son da ko wanda zan aura bana tinanin zan samu wannan gatan daga gareta ,kefa soyayya da ke duniya ne Nusaiba kin shayar dani wani zuma mai daɗin gaske amma kiyi haƙuri ki yafe mun a kullum ce miki nakeyi in kin samu miji kiyi ƙoƙarin ki manta dani ,a rayuwar ki kiyi, auren ki. Maganganun baya yake ta maimai tamun amma ido na ya rufe in gane baya sona yaudara ce kawai ke damun JB a duk lokacin da zai nemi in tura mishi surar jiki na kalaman shi daban ne agareni bana son fishin JB haka zan tura mishi matsalan ɗaya ce a duk lokacin da natura mishi bana iya samun nutsuwa a rai na.,haka Ibrahim yayi sallama na ajiye wayar Ibrahim ɗan uwa nane yazama tamkar jinina ɗaukar shi nake a matsayin yayana Abubakar shiyasa bana sa komai a rai na barin shi kawai nakeyi"kina charting ne?e ya hanya ina fatan ka,kawo mun Farana yana gun Hajiya na,isa in zo garin nan batare da na kawo miki fara ba ya jikin "da sauƙi sosai " inna tace a gaishe ki"ina amsa wa". Sai kusan mangari ba kafun ya fita daga ɗaki na Ibrahim duk lokacin da yazo ɗaki na to ɗaga mun, labulai zai yi sama duk wanda zai wuce yana kallon mu,ko kulashi banayi . Kwanan sa uku bai iya shawo kai na ba duk wani hanya da zai bi dan mallakar nawa zuciyar a banza ne don nawa zuciyar gaba ɗaya na miƙawa JB ban taɓa tsan manin zan so wani ba bayan Muhammad sai gashi nasamu wani amma yazo mun a wata mahangar.iyayen mu so ,suke su haɗamu aure da shi amma zuciya ta bata sonshi babban ma,aikaci ne ,a CBN a cikin barno amma bañsan a wani ɓangare ya keba a salin su Ibrahim Usman Garba yan damaturu ne aiki ne yakai mahaifin shi cikin garin barno a cen duk a ka haife su su bakwai a ka haifa shine na farko maza hudu mata uku sannan a cikin zuriyar mu ,shine jika na farko a ɓangaren mahaifiya ta daga mahaifin shi sai Hajiya na yana da kuɗi sosai ga kyau ga ilimin boko da na,addini amma duk wannan basu bane a gaba na da,a ce shine yafara sona kafun JB zan so shi so mafi inganci a duk lokacin da yazo shike ƙaramun karatu kafun ya tafi duka sai na bashi hadda .ranshi ya ɓaci ne ya tafi da wuri sati biyu yake yi ma na in yazo ga miskili ne bana kaɗan ba irin su doctor da Ibrahim da Alhaji Sani sune zan iya nunawa duniya ga zaɓi na ,amma in har na nuna JB sai na samu wanda zai wanke ni da mari . Washe gari Tun safe nake kiran JB bai ɗauka ba nata kiran shi shiru nayi mishi magana shiru tura mishi saƙo shiru,har dare shima shiru sai danayi kwana biyu baya ɗaukar waya ta ina zaune nace bari na jarraba cikin ikon Allah ya ɗauka tambayan shi nayi lafiya kuwa ina ta kiran ka shiru ? a bun da ya ce mun "karki ƙara kiran number nan don an riga da an karɓe wayar Babana ya karɓa yanzu ma dabara nayi mishi ya bani ki bari sai komai ya lafa zan kira ki. Tinani nadin gayi me ya faru ko dai iyayen shi sunga wani ,abu a wayar shine kodai wani matsalan ne.daure wa nayi na ƙiyi mishi magana sai da yayi kwana biyu kafun yayi mun magana shiru nayi yata sharara mun ƙarya wai duk a kan auren shine iyayen shi suke fishi da shi kar,in ta kira ya gaya mun magana in ya ɗauka .babu abun da nace sai Allah ya rufa asiri nasan ƙarya ne a yaran zamanin nan a ce iyaye zasu karɓe maka waya kamar ɗan secondary school nasan ya shirya mun ƙarya ne kawai walakanci ne yake damun shi . Yanayi na ya cenza ,abun haushi yake bani .da ina yawan kiran shi ,amma yanzu missed call ɗaya zanyi mishi nam ma sai da yayi ƙorafi da,ina yawan kiran shi zai ga missed call goma biyar amma yanzu kaman wani maye guda ɗaya in ba zan kira shi ba in haƙura da kiran kawai. na rasa dalili ina da zuciya amma ta ɓangaren JB nazama lusura ta,ajin gaske har mamakin kaina nakeyi na daina yi mishi magana sai in yayi mun daya ke shi tinanin shi irin na yaran ce ko ganewa bai yi ba ko yayi mun magana ta Whatsapp bana kula shi daman nice ke yawan kiran shi sau uku a rana ko sau hudu nakan bashi lokaci na muta hira ko zuciya irin na sauran mazan nan babu .ina cikin zamana a ɗaki yaya na Abubakar ya shigo na gaishe shi ce mun yayi Abban mu yana kirana yana falon ƙasa cemishi nayi ina zuwa jin kiran Abba sai da zuciya ta ya,tsinke ban san mezanje in tarar ba da sauri na sanya hijabi na ,nanufi ɓangaren Abba bakina ɗauke da sallama ganin yanayin mahaifina ya ɗaga mun hankali bana kaɗan ba gaishe shi nayi ya amsa hannun shi ɗauke da jarida bayan shiru da ya biyo baya sai jinayi yayi gyaran murya"Nusaiba bafa zan zuba miki ido kina abun da zuciyar ki take so ba me Ibrahim yayi Miki kikayi mishi korar kare mekike nufi Muhammad ya riga mu gidan gaskiya in da kece kika mutu wallahi aure zai yi muddin kuwa ya samu matar da take kulawa da shi mantawa zai yi dake haba Nusaiba to ke wakike so tunda bake son Alhaji Sani bake son Ibrahim kigaya mun sannan kice mishi na bashi kwana goma sha biyar . Juyawa yayi yaci gaba da karatun jaridar dake hannun shi ban taɓa riskar kaina a tashin hankali ba irin ranan na ɗinga maima tawa kwana sha biyar a take zufa ta karyo ,mun ya zanyi kaina a sunkuye yake tun da naje falon Abba zanyi magana ya ɗaga mun hannu "ki tashi ki fice mun daganan sannan nasan halin ki yanzu zakije ne kita tunani sannan ni kai na,ban taɓa ganin ki da kowa ba tun bayan rasuwar Muhammad " Jan ƙafana nayi nawuce cikin ɗakina ina zuwa hijabi na nacire na rushe da kuka ya zanyi nima zanso in yi auren kodan shekaruna da suka ja ina yiwa JB mungun so ga duk abun da yayi mun bana ganin laifin shi taya zan fuskan ce shi bayan shima, yana da nashi matsalan duk da ƙarya shi ya keyi mun haka nata tinani har bacci yayi awun gaba dani sai kusan ƙarfe biyar na yamma na tashi jikina duk yayi nauyi . Yau da wuri JB ya tashi ban san kome ya faru ba nidai ya ce mun yana gida hirar ma sama sama ,mukayi yayi mun sallama.abun mamaki da safe da na hau Whatsapp naga har ƙarfe uku bai rufe datar shi ba sannan ya ɗaura status ƙarfe ɗaya na dare . JB munafikin na miji ne sannan ya cika son kanshi dayawa bai damu da damuwar wani ba nashi ya sani . [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR MARUBUTAN JAHAR YOBE Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam 📚✍🏽 *Wasu mazan musamman samarin zamanin nan har ma da matan sai a hankali basuda imani sun ɗauka babu gida babba ne ko sun ɗauka babu wani shari,a da zata biyo bayan zalinci ina tausaya miki Nusaiba Allah ka shiryar da mu badan halin muba so makaho ne bashi da ido* ```Muna godiya sosai da karɓuwar littafin nan wata mahangar ina yawan samun kira dayawa da ɓangarori da dama da kuma addu,a garemu mu samman yan mata da samari mungode sosai zan sanya number ɗayan marubucin in an Kirani bai shiga ,ba a kira shi ``` LAMBA NA GOMA Ikon Allah ! mamaki ne ya kamani taya JB ya nuna mun bacci yake ji a she ƙarya ne ba baccin yake ji ba ,ban biyo ta kanshi ba naci gaba da aiki na ko in kula shi .har ƙarfe biyu na rana kafun naga yayi mun magana nima sai da naja lokaci kafun na mayar mishi da amsa ya bani haushi daman duk lokacin da zamuyi hira shiyake nuna wa bacci yake ji nikuma ganin tun safe yake aiki a shago sai in tausaya mishi in ce ya kwanta kawai shagon JB bawani abun kirki gare shiba dan nagani in har muna video call a hakan ko yau she fatan alheri nakeyi mishi maza . !maza !! Ya lura da yanayi na yaga raina ya ɓaci shine yayi mun magana ya ,yaga raina a ɓace ce mishi nayi ba komai ya hauni da masifa wai nafara yawan tinani so nake ciwo na yatashi bana tausayin irin kuɗin da ake kashewa ne ko uffan bance ba na barshi har ce mun yayi inyi bacci ko kaɗan ne zaifi .nace to na gagara baccin tinanin matsalar da yake bani ce tafara gundura na. ni ma,abociyar son kasance wa ita kaɗai ce sai in wuni ina ɗaki in ta karanta jarida. a ranan yana tashi daga shago ya Kirani bayan mun gaisa sai ce mun yayi ɗazu naga ranki a ɓace to meyafaru mata na ki gayamun ɗan Allah karki barni a cikin duhu ko dai har yanzu a kan maganar Alhaji Sani ne? Nunawa nayi ba shi bane tambayan shi nayi jiya da yau she yayi bacci "na gane fishin ki dan kinga lokacin da na sauƙa kiyi haƙuri wallahi babu wanda nake so fiye da ke sannan ban taɓa soyayya da wata ba bayan ke da A'isha to meye na ɓacin ran ina bacci ne naji baccin ya,ishe ni shine na kunna data na naso in tashe ki amma nayi tinanin kina bacci banaso in katse miki jin daɗin ki haba mata na kece fa wanda nake tattalin ki. a ranan sai da yasani farin ciki muka ta faranta wa junan mu rai da kalamai masu daɗi daga ƙarshe ya fake da cewa ina kayan sa ,nayi mamaki daya ke tambayan ina kayan sa a she yana tambayan abubuwan jiki nane murmushi nayi nace suna gaishe ka wani murmushi yayi mun daga ƙarshe sai cewa yayi ɗauka mun hoton su in gansu mu gaisa ina neman su . Ko kulashi banyi ba na kashe waya ta kawai na kwanta nayi bacci washe gari ban buɗe wayar da wuri ba sai ƙarfe goma na safe naga yayi mun magana ta Whatsapp a kan cewa "jiya muna magana najiki shiru ?"nima Hajiya nane ta karɓe wayar dan taga menakeyi "me yasa kin kasa yadda dani a kan babana ya karɓe mun waya ta kwanaki "tsiya nifa ba haka nake nufi ba baka yadda ba kenan" tun ranan kullum sai kin gayamun magana a kan mekenan babu yadda a tsakanin mu kina zargina wannan ya nuna koda munyi aure zargi zai shiga tsakanin mu kenan. Zargi ! "In har munka sance mata da mijin kenan ko,ka manta zaɓin iyayen naka ne karfa ka manta auren mu bamai iyuwa bane nida kai taya zaka gayamun abun da zai faranta mun rai bayan kasan ba haka bane meyasa kake son wasa da hankali na nifa macece mai rauni " yaga bashida abun faɗa sai yafake da cewa "ina zuwa minti goma ". a jiye wayar nayi na nufi ɓangaren mahaifiya ta baki na ɗauke da sallama ƙanwata Hibba ce ta amsa shigowa nayi nasamu guna zauna mahaifiya tane da tazame mun kamar Sirika zan iya cewa sirikar ce tunda ni, mai sunan umma ce maman Abba na "yau kuma ziyaran safe ,muka samu ne ? Murmushi nayi nace e Hajiya haɗa shayi nayi nasha na ƙarya daman nasame su ,suna karyawa shiru nayi ta ga yanayin da nake tambaya ta tayi "lafiya kuwa Nusaiba meyafaru "? babu komai Hajiya kawai ina son kasancewa a cikin kune shine nazo gareku karkiji komai babu komai. Hibba ce tada meni da surutu ita da Fatima har da Aliyu sai naji sun ishe nida surutu Aliyu ne yayi magana"Anty Nusaiba ranan nashiga ɗakin ki zan baki kati Abba yace in baki nasamu kina kuka shine nadawo da shi bana son katse miki kukan ki ban san ko zai sakaki farin ciki ko dai yasa damuwar taragu ba shi yasa" Aliyu kenan bani Katina shine banyiwa Abba godiya ba haba da Kabani .kallon mahaifiya tanayi,ita ma nitake kallo nasan ta karanci meke da muna a kan fuska ta batayi mun magana ba nima haka iyayen mu basu cika jawo mu,a jiki ba koda muna da matsala a wasu zamu faɗa wa ko dai a ƙawayen mu ,damuwa sai tayi mana yawa fiye da komai koda wani abu yana damun mu ba lalle ne su tambaye muba. iyayen yanzu kuwa yaran su sun zame musu tamkar ƙawaye koda kaya ne zasuyi anko kamar ƙawaye shine banbancin mu da yaran yanzu. nada sunfi kunya yaran yanzu suna kan cinyar iyayen su zasu amsa wayar samarin su ganin su,abun burgewa ce agaresu . Ganin zama daƙin Hajiya bazai kaini ko ina ba tashi nayi nashiga kitchen a ranan nine na ɗaura mana abincin rana tun da nabar ɗakina ban koma ba sai da na kammala komai kafun nayi alwala na shiga ɗakin danyin sallah na daɗe a kan sallaya ina zaune waya tane tafara ya neman agaji tashi nayi na ɗauko nacire daga key ina buɗe wa naga missed call goma ganin kiran JB guda takwas da sauri nabi ta kanshi bayan nayi sallama ya amsa sai ce mun yayi ina kikabar wayar ki tun ɗazu ina ta kiranki ko dai kintafi kina cin amana ta ne bansani ba,a nawa tinanin ban taɓa jin kin anbaci sunan wani ba. ce mishi nayi niban iya cin amana ba in kaga an samu matsala daga gareka ne bada gani ba "nagaya maka a tsari na bana haɗa soyayya guda biyu a lokaci ɗaya kaima ya na,iya da fitinar ka balle kun haɗu ku biyu kitchen na shiga_shiyasa kaji shiru ban tafi da waya ta ba . Hira mukayi cen nace lokacin da kazo ka samun number mama na gwada jiya wanine ya ɗauka kodai ka cenza number ne ba shi kasamun ba."wani irin magana kike yi haka Hayat taya zan saka miki number da ba ,dai dai ba mekike nufi kenan kin gwada kuwa dan naduba shine nasa miki. " da mutumin da na kira da wanda na rage wasu nombobin na saka wasu na gwada nakira wata ce tana Kaduna duk nayi recoding din na tura mishi ya turo mun da number iri ɗaya dana guna nasan ƙarya ne kawai yayi haka ne dan kar wataran in kirata in wani abu ya faru bana son jayayya kawai barin shi nayi da halin shi. Ban ƙarayi mishi zancen wani abu da ya shafi mahaifiyar shi ba tunda naga in har naci gaba da magana zamu samu babban matsala na rage yawan kiran shi da nakeyi ,badan komai ba sai don in samu sauƙi a zuciya ta a hakan zan iya cewa Ma sha Allah .ganin nayi kwana biyu ban fita ba shirya wa nayi kusan ƙarfe biyar zanje in duba ƙawata maman Sadiq tambayan JB nayi ce mun yayi kar in kai mangari ba in dawo da wuri da to na bishi . naje munata hira da,ita har ƙarfe bakwai na dare ko sallah bamuyi ba ganin kar in tsaya Sallah dare yayi sallama mukayi ,na dawo gida ina zuwa alwala nayi sai da nayi sallah kafun na kira JB yana ɗauka sheda mishi nayi kaina ciwo yake yi sannu ya ce mun tambaya na yayi yaushe nadawo cemishi nayi kusan ƙarfe takwas ya dinga masifa banace karki kai mangari ba ,ba gashi kin dawo da ciwon kai zaki dameni surutu yatayi haƙuri na bashi na sha magani na kwanta. Ƙwana biyu ina kwance ciwon kai ya takura mun ko waya bana,iya ɗauka wayar ma,a hannun Aliyu yake a she JB ya kira shi kuma Aliyu ya ɗauka jin muryan shi yaɗinga yiwa Aliyu masifa . Ina bacci a ka kawo mun wayar tashina Aliyu yayi ya bani ya juya shima bai ce an Kirani ba ranshi ya ɓaci sai ƙarfe goma na dare kafun ya Kirani ,ko sallama bai yi ba ya dinga masifa "a waye kika bada wayar ki yayi mun rashin kunya ko dai a saurayin ki ne wannan cin mutunci ne taya zaki ɗauki waya kibawa wani". Ka tsaya mana ya kake yi mun masifa kamar wani wanda zai dokeni ka tsaya in yi maka magana ka gagara tsayuwa jinayi ya kashe wayar nace zancen banza daman an daɗe ba,ayi faɗa da kai ba ,daga ciwon kai tsintar kai na ,nayi a asibiti an samun dirif juyawa nayi naga guda biyu sun ƙare a lama ya nuna na daɗe a asibiti na uku ne a jiki na a she tun da na kwanta numfashi na yafara sarƙewa ciwo na ya tashi cewa nayi Hajiya ta bani waya ta miƙa mun tayi . Buɗewa nayi cin karo nayi da saƙon JB "kin zaɓi farin cikin mutane da nawa kina ganin kin rufa mun asiri kin soni, ina yaro ƙarami to nima haka ban kula yara sa,annun aure na ba natsaya kulaki ,kema haka manyan masu kuɗi suna sonki kinƙi su ,dan Allah mu haƙura da juna zaifi kawai bana so ki rasa ranki ta dalili na nasan yanzu a kwance kike bakida lafiya ina yi miki fatan alkairi . Jinayi hawaye suna bin ƙunci na ba kalaman JB ne suke damu na,ba yawan damuwa da nayi da shi gani nake in babu shi ba zan ,iya rayuwa ba sau daya wa yawan nunawa samari tsantsan so har su gane son da muke yi musu yafi nasu yawa to nanne hanyar basu daman cin zarafin mu,ko dan na daɗe ban yi soyayya ba sai a kanshi ban sani ba ace masoyin gaskiya ba zai ganni a kwance ya cimun mutunci ba. juyawar da zanyi muka haɗa ido hudu da doctor Ibrahim Sulaiman.... [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA GOMA SHA DAYA Na sha jin ana cewar zuciya tana son mai kyautata mata sai dai na rasa wacce irin zuciya ce a cikin tawa ƙirjin. Da ta kasa amsar yaya Sufyan a matsayin masoyi. Dafe kaina nayi da nake jin kamar zai tarwatse gida biyu don ciwon da yake mini, zuciyata tana harbawa da sauri da sauri. Sai da aka ɗauki mintina biyu kafin ya maido mini da amsa da kalmar innalilahi wa inna ilahir raji'un, sannan ya yi mini saƙon murya da farko na zargi kunnuwa da rashin jiyo mini abin da yake faɗi. Sai da na ƙara saurara a karo na biyu na tabbatar da cewa kuka yake yi bilhaƙƙi, yana shaida mini ba zai iya aiwatar da komai a rayuwarsa ba tare da ina kusa dashi ba ko guje mini da ya yi a baya ya zabga babban da na-sa-ni. Take na ji jikina ya ƙara yin la'asar idanuna ya daina gano mini komai sai baƙin duhu. Rayuwar da muka yi da Suraj ya fara dawo mini sabo fil. Ya kasance malamin mu lokacin muna aji uku a babban sakandiri. Yana ɗaya daga cikin malaman da suka kasance abin tsoro ga ɗalibai, baya dariya ko bisa kuskure yayin da yake koyarwa sannan ba ya ƙarban uzuri balle ɗaga ƙafa. Darasin lissafi yake mana na fi kowa tsoronsa a kaf ajin mu hakan ya sanya ko darasin da yake koyar damu bana fahimta, duk gwajin da ya yi mana sai na faɗi domin ko sahun waɗanda suka haye maki biyar bana kai wa. Hakan ya sanya shi tsaurarawa da sanya ido a kaina fiye da kowa, ko sunansa naji an ambata zuciyata sai ta tsinke balle tozali da fuskarsa da babu rahama a tattare da ita. Tun da ya shigo bugun ƙirjina ya tsananta saboda fargaban kar sunana ya faɗo cikin waɗanda basu haye gwajin da yake mana a duk lokacin da ya kammala darasi ba. Sakina dake zaune kusa da ni ta riƙe hannuna saboda rawar da jikina ya ɗauka kamar mazari, zubar hawayen idanuna ya yi dai dai da sanda ya ƙwala ƙiran sunana. Na ƙara daburcewa. Tsawar da ya daka mini ya tursasa mini runtsun idanuna da har yanzu yake tsiyayar da ƙwalla tamkar burɗaɗɗen famfo. Kaina a ƙasa na iso gabansa na zube akan gwiwoyina, bai ce da ni komai ba sai ma cigaba da ƙiran waɗanda basu haye ba yake yi. Sai da duk suka fito ya ce"ku je ku zauna yau nayi muku alfarmata da ba kullum ake yin katari da shi ba". Abin da ya tokare mini ƙirji ne naji ya wuce na miƙe da sauri zan wuce, ya dakatar dani da faɗin"Madam ban da ke". Na koma da baya duk suka koma suka zauna ban da ni. Bai ce dani uffan ba har sai da ya ƙare darasin tsaf ya bada aikin gida, sannan ya dube Ni fuskarsa tamkar magribar ɗinya haɗi da furta"ke kuma za ki zauna a nan har sai wani malamin ya shigo". Yana dasa aya nan ya fice kukan na cigaba da shi saboda sanyin da duk gaɓoɓin ƙafata ya yi, Sakina ce ke ta jeranta mini sannu wani na bin wani. Shigowar Malam Saminu ya sanya ni jin wani sanyi ya ziyarci sashin ruhina. Ko gaisuwar da 'yan ajin suka miƙe suke yi masa bai amsa ba ya fara da tambaya ta me nake yi a wajen. Na sanar dashi bai ce komai ba illa jijjiga kansa da ya yi ya fice ransa a matuƙar ɓace. Kafin lokacin tashi zazzaɓi mai zafi ya rufe Ni ko da na isa gida ban iya assala komai ba face kwanciya. Hawayen takaici ne suke gudu a bisa fuskata na rasa dalilin tsanar malam Suraj gare ni da yake yi mini hakan, kamar daga sama naje jin muryar yaya Sufyan da ya sanya ni saurin tashi na fita. Zaune na iske sa da yaya Sa'eed da kuma Hajiya. Ciki ciki nayi sallama kafin na yiwa kaina mazauni. Yaya Sa'eed ya hararo ni tare da faɗin"kafurai kika tarar a wajen shi yasa kika adana sallamarki ko?". Da sauri na zaro ido na ce "wallahi nayi" . Taɓe baki ya yi yana mayar da kansa tare da mayar da hankalinsa a wayarsa da yake latsawa, idona na zube a bisa fuskar yaya Sufyan ina yi masa sannu da zuwa. Fuskarsa tamkar gonar auduga ya amsa mini yana ɗaurawa da"kaga autar Hajiya da Momma". Sunkuyar da kaina nayi ina murza zoben dake saƙale a hannu, ban ɗago ba naji ya cigaba da cewa"ki rabu da Sa'eed yau sai an yi masa uzuri shi kaɗai ya san abin da yake ji". Ya ƙare maganar yana kashe mini ido ɗaya dai dai sanda na ɗago kaina, ƙunshe dariyata nayi da ido nayi masa alamar me ya faru?. Kafin ya yi wata magana yaya Sa'eed ya tare shi da faɗin " wallahi na gaya maka ka kiyaye ni fa bana son raini Sufyan". "To yaya babba meye kuma nayi?, naga dai bani na kar zomon nan ba rataya aka bani". A kufule yaya Sa'eed ya kallo Hajiya da ta maida hankalinta ga TV ya ce" ki yi wa yaron nan kashedi bana son raini ni fa". "Ba ruwana da sha'anin ku". Ƙasa nayi da kaina ina dariya don yanda yaya Sa'eed ya yi kici kici da fuska a dole baya son raini, Anty Sadiya ta shigo da tray tana ajiye wa a dinning tare da furtawa Hajiya cewar komai ya kammala. Sannu tayi mata sannan ta iso ta zauna tana tambayar yaya Sufyan abin da ke faru, ɗage kafaɗa ya yi alamar me sa ni ba yana mata nuni da yaya Sa'eed. Har muka wuce dinning area ɗin babu wanda ya ce ƙalla, tare da Anty Sadiya da lokacin ita ce bata yi aure ba muka yi serving ɗin kowa. Kasancewar ranar Abba baya gari. Muna haɗa ido da yaya Sufyan nake jin wani sabon dariya yana zuwar mini dole na danne shi don gudun ɓacin rai yaya Sa'eed. Gyaran murya yaya Sufyan ya yi, yana kallon yaya Sa'eed da yake juya cokalin kawai a cikin abincin ya ce"malam ka ci abinci da don wallahi yunwa ba ta da hankali, kuma ba ƙanwar su Abba ba c...". Bai ƙarisa ba sakamakon cokalin da ya jefa masa ya kauce da sauri yana dariya. Tsam ya tashi yana huci"Hajiya na gaya miki yaron nan ya gama raina ni, gidan Momma zan koma". Yana gamawa ya fice daga falon gabaɗaya. Duk dariya muka tuntsire dashi ni kam har da riƙe ciki Hajiya ke tambayan yaya Sufyan abin da ya faru. "Wata yarinya yake so tun da daɗewa ya kasa faɗa mata. Sun daɗe suna alaƙa a matsayin aboka ashe shi ba haka ya ɗauka ba, sai da yau da na raka shi wajen ta muka iske ta da wani da ya tambayi wanene sai take sanar damu cewar wanda zata aura ne. Shine fa duk ya birkice yake ta wannan ƙuncin, bayan shi ya tsaya ganin ruwa kwaɗo ya yi masa ƙafa". Jijjiga kansa kawai Hajiya tayi ta cigaba da cin abincinta, ni da Anty Sadiya kuwa sai da muka ji ƙwaƙwaf don har hotonta ya nuna mana 'yar guntuwa da ita a gefensa. Na sha dariya sai da na ji cikina ya fara ƙullewa sannan na tsagaita. Muna gamawa na haɗe kwanukan na kai kicin, nake naji cikina ya bada sautin ƙululu tunawa da nayi da aikin gidan da malam Suraj ya bayar da ban yi ba. Na fita da sauri zan wuce na yi kiciɓus da yaya Sufyan ya tsare ni da ido kafin ya furta"meye kika birkice haka?". Take ƙwalla ya ciko mini koramar idona, muryarta tana rawa na furta"aikin gida aka bamu kuma ban iya ba". Taƙaitaccen murmushi ya yi"to shikenan ki je ki jira ni na kaiwa Sa'eed abinci, sai nazo na taya ki ko?". Kaina na ɗaga masa cike da jin daɗi, na ware idona akan fuskarsa da har yanzu yake sakin murmushi na ce"baka taɓa fushi da yaya Sa'eed ". Rausayar da kai ya yi yana shafi ƙeyarsa kana ya ce"shima baya iya fushi da ni na gudun lokaci, na tabbatar yanzu yana can yana tunanina". Murmushi kawai na yi na matsa na bashi waje ni kuma na fita izuwa ɗaki. Sai da na yi wanka na yi sallan isha'i sannan na ɗauko takardan ina ƙara dubawa, a saki sakekken ajiyar zuciya gani na saka gane komai a ciki. Ina ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan fuskarsa yaya Sufyan da yake tsaye a ƙofar ɗakin ya naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa. Na kwaɓe fuska na ce"kai fa nake ta jira". Ya saki murmushin da ya zamo ɗabi'arsa kana ya tako a hankali ya zauna a ƙasa a gabana. Na yi saurin dirowa daga kan kujera da nake na dawo ƙasa nima na zauna, dariya kawai ya yi ya jijjiga kansa ya umarce ni da na miƙo masa takardan na miƙa masa da rawar jiki. Ya karɓa yana dubawa sai ya ya kalla sosai sannan ya ce na miƙa masa biro na bashi, ya fara solving ɗin tambayoyin sai da ya gama tas ya ɗaura mini takardan a bisa cinya. Cike da tsantsar farin ciki na zari takardar ina kallo na mai da idona gare shi na furta"na gode sosai ka ceci rayuwata". "Na gode sosai ka ceci rayuwata". Ya furta cikin kwaikwayon muryata na yi kasa da kaina ina yin dariya, ya miƙe tare da faɗin"bari na wuce gobe ina da class ɗin safe". Nima tashi tsaye na yi"kuna ƙoƙari fa bi kam gani nake kamar ba zan iya koyarwa ba". Ya galla mini harara"ai kuwa koyarwa ba ƙaramin aiki bane sai dai lecturing da sauƙi. Mafi yawan lokuta guiding ɗin su kawai za ka yi". Jinjina kaina na yi alamar gamsuwa da zancen na san, na rako shi har wajen motarsa ina masa addu'ar sauƙa lafiya da saƙon gaisuwata ga Momma. Washe gari na tashi cikin nishaɗi haka na tafi makaranta, darasi ɗaya muka yi na biyun kuwa Malam Suraj ya shigo. Tsit ajin ya ɗauki shuru tamkar babu wani halitta mai motsi a cikinsa. Ya ce a haɗa masa aikin gidan da ya bayar da zumuɗina na ciro nawa daga cikin jaka na miƙa. A ajin ya zauna yana makawa har ya gama ya fara ƙiran waɗanda basu haye maki biyar ba, kamar daga sama na ji ya ambaci sunana. Cikina ya bada ƙarar ƙululu na miƙe tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki na fita. Bulala uku uku aka yi mana muka dawo muka zauna, tunda na kifa kaina akan benci ina kuka har ya gama darasin ya fice ban ɗago ba. Sai da aka tashi tara sannan na fito na wanke fuskana, Sakina ta zauna kusa da ni tana faɗin"don Allah ki daina wannan kuka tun ɗazu fa kike yin sa". Ban kula ta don yanda nake jin wani zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin rufe ni. Ta dafa kaɗata"ki yi haƙuri don Allah". Sai a lokacin na yi ƙarfin halin faɗin"ke fa ki haye maki biyar kuma wanda na yi kika kwafa, kawai ni ɗin ya tsane ni me nayi masa?". "Bai tsane ki ba hasalima sonki ne ya yi masa da har ya rasa ta yanda zai fara sanar dake. Takaicin ba zai iya tunkarar ki da zancen ba ya sanya shi yi miki waɗannan abubuwan". Tare muka waiga ni da Sakina don ganin mai maganar, Sabira 'yar ajinmu ce tsaye a bayan mu kafin ta tako ta zauna akan dakalin ƙofar ajin da muke zaune a kai. "Ke Sabira ke kuma yaya aka yi kika san duk wannan, shi ya faɗa miki?". Ta yi mana wani kallon da na gaza gane abinda take nufi kafin ta furta"ba shi ya faɗa mini ba amma kowa dake cikin makarantar nan ya san da wannan abunda na faɗa muku yanzu. Malam Suraj son Surayya take yi so mai tsananin gaske, a cikin biyu nan dole akwai dalilin da ya sanya shi yake nuna kamar ya tsane ta a fili. Ko dai yana tunanin ba zai iya samun soyayyarta ba bisa wasu dalilai nashi na karan kan shi, ko kuma ya na tsoron ya sanar da ita ta ƙi amsar sa hakan ta jawo masa raina daga sauran ɗalibai". Duk shuru muka muna nazarin zantukan bayan daki-daki. Ta katse mana hanzari ta hanyar cewar" kun taɓa lura da cewar duk ranar da ya shigo aji bai ganta ba baya taɓa samun nutsuwa?. Kuma ranar komai cikin sanyin jiki zai aiwatar dashi saɓani in tana cikin ajin. Kullum sai ya ƙira sunanki cikin waɗanda basu haye makin ɗin da yake buƙata a gwajin da yake mana ba, don kawai ya gan ki ko kin yi dai dai fa sai ya ƙira sunanki don kawai ya sama nutsuwa a ransa ya kuma tabbatar da kasantuwarki cikin ajin". Ƙarƙafan ajiyar zuciya na sauƙe ina zabga tagumi da hannu bibbiyu, kaina gabaɗaya ya kulle na rasa ta inda zan fara tantance zantukan na Sabira na yi musu rankaɗe da rairaya na ware aya na watsar da tsakuwa. "Maganarki abun dubawa ne tabbas, da akwai alamar ambayar akan abubuwan nan da Malam Suraj yake aikewa. Amma ta yaya zamu tabbatar da abinda kika faɗa". Sai da ta gyara zaman ta kana ta ce"lokaci ne zai tabbatar da hakan amma ina da tabbacin malam Suraj yana son Surayya. Kuma dole komai daren daɗewa zai furta hakan a gare ta domin ba zai taɓa iya riƙe abin a ransa ba, sannan ko ba ki amshi tayin soyayyar sa ba sai sama nutsuwa domin ta furzar da abinda yake sukar ransa har yake masa zogi a cikin zuciya". Tsam na miƙe tsaye ina cewa"don Allah ku daina wannan hashashen domin ba zai taɓa zama gaskiya ba". Ina dasa aya a nan na koma cikin aji na zauna, sai dai na gaza samun nutsuwa har aka tashi ban dawo dai dai ba. Kwana nayi da tunanin abin a raina ina kwantanta girman bayyanannen tsanar da yake nuni mini a zahiri, babu yanda za'a yi a ce wai akwai soyayyata ko da misƙala zarratin a cikin zuciyarsa. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA GOMA SHA BIYU Tsanar da Malam Suraj yake gwada mini kullum ƙara ƙaruwa yake yi, ko yaushe ina cikin waɗanda suka faɗi a gwajinsa. Hatta 'yan uwansa ragowar malamai zai da suka fahimci hakan . Bana taɓa samun nutsuwa idan yana cikin aji haka nan bana taɓa fahimtar darasinsa, sai dai bayan fitar da Sakina ta koyar da ni ƙalilun abubuwan da ta fahimta. Domin zafi da tsananinsa ya sanya ba kowa yake fahimtar darasinsa ba. A haka lokaci ya cigaba da tafiya, rayuwa ta na juyawa har aka yi bikin Anty Sadiya lokacin muna hutun ƙarshen zangon karatu. Muna komawa babu ɗadewa muka zana jarabawar jamb. Koda aka sake sakamako ina ɗaya daga cikin waɗanda suka ci maki mafi yawa a kaf makarantarmu. Da shugaban makarantar ya gabatar da mu a gaban assembly tare da shawarar raguwar sauran ɗalibai da su yi koyi da mu su zamo jajirtattu kuma masu mai da hankali akan harkan karatun su. Ina sauƙa daga izuwa wajen da sauran ɗaliban suke tsaye na ci karo da Malam Suraj yana nufi wajen. Da hanzari na rusunar da idanuna ƙasa saboda wani kallon da ya jefo mini yana ɗaure fuska tamau tamkar magribar ɗinya. Har aka gama assembly ɗin ba ni da nutsuwa muka koma aji, muna tsaka da gudanar da darasin kusa da na ƙarshe a ranar. Wata yarinya daga ajin bayan mu ta nema izni ta shigo ta na cewar"wai Surayya ta je inji Malam Suraj". Take na annurin dake fuskana ya kau zuciyata ta shiga dakan lugudan tara-tara sau tara. Muka haɗa ido da Sakina ta jinjina mini kai alamar na tashi na je, a sanyaye na miƙe ina taka ƙafata a hankali har na isa cikin ofishin malamai na shi ne na biyu daga gefen hagu. Na kai hannu da nufin bubbugawa na ji saurin janyewa, ina runtse idanuna da ƙarfin gaske. Ina karanta duk wani addu'ar da ya fara zuwar mini a rai har na sama nutsuwa a cikin raina. Na ɗaga hannu zan buda aka buɗe ƙofar. Idanunmu suka sarƙafe a cikin na juna babu shiri na kawar da nawa gefe ina ƙoƙarin danne ruwan da nake jin yana ƙoƙarin zubawa daga koramar idanuna. "Sai yanzu za ki zo?". Ya furta a zafafe na jijjiga kaina da sauri alamar a'a. Ya sa ki tsaki yana juyawa ciki na taka a hankali raina cike maƙil da tsoro na bi bayansa. Na daɗe a tsaye ba tare da ya ce da ni komai ba, sai ma mayar da hankalinsa da ya yi ga making ɗin wasu takardun dake gabansa. Jin ƙafafunsa sun fara rawa su na alamta mini gajiyarwar su na ɗaukar nauyin gangar jikina ya sanya ni cira kai na kalle shi. "Malam muna darasi ne na fito". Sai da na cire rai da samun amsarsa kana ya furta mini"na fi ki sanin hakan ai". Ban kuma cewa komai ba wasu hawaye suka gangaro izuwa kan kuncina. "Na ji wai ance kina ɗaya daga cikin waɗanda suka fi kowa cin jarabawar jamb a makarantar nan ko?". "E". "Ya yi kyau keep up ruwa good work". A sanyaye na furta"na gode". Shuru ya kuma karaɗe ofishin sai can ya ya ce"ki fice min daga ofishin". Da hanzarina na fita na jawo ƙofar na rufe, sai da na koma cikin aji na sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi ina dafe ƙirjina. Haka har muka fara zana jarabawar waec da neco, yaya Sufyan ya cika mini alƙawarin da ya yi mini na cewar matuƙar na yi ƙoƙari a jarabawar jamb zai saya mini waya. Sauranmu kwanaki biyar mun kammala jarabawar aka ce mu je ofishin Malam Suraj domin cike abubuwan da za a sanya mana a cikin photo album. Tare da Sakina da kuma Sabira muka je duk da ni ce gaba dasu a layi amma ya ce na jira sai kowa ya gama sannan ni na yi, haka na zauna sai da kowa ya gama sannan ya ba ni na nawa lambar waya, adireshi da wasu abubuwan. Ina fitowa na iske su tsaye suna jiran fitowata Sakina ta na riƙe da jakata. Ina isa na dafe kaina ina faɗin"wash". Maimakon na tsinci tausayina wahalar da na sha a fuskar Sabira sai ma dariya ta tuntsire dashi tana cewar"Surayyan Malam Suraj". Tunin na wartsake ina jefan ta da harara"Allah ya kiyaye wallahi". "Ke dai ina raba ki wallahi yarinya, ki yarda ko kar ki yarda da bawan Allahn nan son ki yake yi. Shin ba ki lura tunda muka fara jarabawar nan ya ƙara shiga cikin wani hali ba?. Kin san dalili?". A tare muka jijjiga mata kai ni da Sakina, ta gyara tsayiwarta kana ta ɗaura da"saboda mun kusa kammala makaranta, zai dai na ganin ki zai daina jin muryarki. Ta wani ɓangaren kuma cire yake da tsoron kar ya rasa damar sa gabaɗaya akan ki". Taɓe baki na yi ina karɓar jakata na rataya a kafaɗata, muka fara tafiya zamu fice daga cikin makarantar kasancewar duk an fara watsewa daman iya mu da muke zana jarabawar ce muka zo. "Na fara yarda da zantukanki Sabira wataƙila duk abinda kike faɗa ya kasance gaskiya". Ban tanka musu ba na yi kunne uwar shegu har muka isa bakin gate. Bamu yi jiran mintuna goma ƙwarara ba yaya Sufyan ya iso domin ɗaukar mu. Dai-dai sanda Malam Suraj yake fitowa daga cikin makarantar a bisa kuskure idanuna suka gano mini gefen da yake, ban ƙara gigin ƙars kai idanuna wajen ma muka shige cikin motar. Sabira aka fara sauƙewa sannan Sakina muka yi sallama cike da son juna. Gidan Momma na ce ya kai ni, ya kallo ni fuskarsa kamar gonar auduga ya ce"an gama ranki ya daɗe". Murmushi na saka"yaushe zaka koya mini mota?". Ya ɗan zaro ido a lokacin da yake karya kwanar da zata sada shi da unguwar kafin ya furta"so kike Hajiya da Momma su yi min tarin dangi ko?". "Me yasa to?". "Su ce zan tsorita musu ɗiya ma, kin san da har yanzu basa yarda su shiga motana. Kullum ƙorafin su wai na cika gudu". Dariya na saka saboda yanda ya yi maganar har muka isa ban daina ba. Yana gama daidaita parking na fito da guduna na shiga sashin Momma. Shi kuma ya koma makaranta. Nan na wuni sai bayan sallan magrib ya mai da ya ni gida, bai tafi ba sai ƙarfe goman dare na rako shi har jikin motarsa. Sai da na hana shirin kwanciya tsaf na tuna da wayata, na tashi na ɗauko ta a cikin kayana da nake ajiye ta. Na kunna sannan na koma na kwanta ina latsawa. Whatsapp na shigo domin tambayar yaya Sufyan ya isa gida lafiya, na ci karo da saƙo da wani baƙuwar lambar an yi mini sallama cikakkiyar. Ban amsa ba sai da na turawa yaya Sufyan saƙon babu jimawa ya maido mini da amsa. Haka muka cigaba da yiwa juna saƙo har dare kusan sha ɗaya ya yi ya ce na kwanta. Washe garin ranar bayan mun fito tara, wannan yarinyar jiyan ta ƙara dawowa tare da isar mini da saƙon Malam Suraj yana ƙira na. Cikina ya ƙululu muka haɗa ido da Sakina, ta jinjina mini kanka tana ɗaurawa da"ba komai tashi mu je". Tare da ita muka je ofishin yau su biyu ne a ciki shi da Malam Saminu muka haɗe baki wajen yi musu sallama, shi kaɗai ya amsa mana amma shi gogan ko ɗaga ido bai ya mana kallon arziki ba ya cigaba da latsa wayar dake hannunsa. "Surayya Sufyan". Malam Saminu ya furta na amsa masa ina sunkuyar da kaina ƙasa. "Ko da bayan kun gama nan ki cigaba da maida hankali ga karatunki kamar yanda kika saba, in sha Allah za ki yi nasara". Kaina na jinjina masa ina cewa"in sha Allah ". "Kuma ce maka yi cewar lalle ne in ta gama nan ɗin ta cigaba, wataƙila aure zata yi don jiya har ƙofar makarantar nan saurayi yazo ya ɗauke su". "Saurayi kuma?". Malam Saminu ya furta yana bin mu da kallon mamakin da ya wanzu a fuskarsa. Ban iya furta masa ko kalma ɗaya ba illa Sakina da ta ce"wannan wanda ta dauke mu jiya yayanta ne, kuma mafi yawan lokuta shi yake zuwa ɗaukar ta". "Yauwa sai yanzu na ji batu". Sai a lokacin ya ajiye wayar dake hannunsa ya kafe mu da ido"so yanzu kenan auren ne ko kuma karatun?". "A burina da na Iyayena karatun ne wannan tsarinmu, amma ba mu san yanda Allah ya tsara mana ba. Kuma a ko yaushe zaɓinsa shine daidai". "Madalla! a ko yaushe maganar hankali ta na fitowa ne daga nagartaccen mutum. Shiyasa a ko yaushe nake girmama kaifin basirarsa". Furucin Malam Saminu yana tafa mini, a suƙure na ce"na gode". Malam Suraj ya buga uban tsarkin da ya sanya hankulanmu komawa gare shi. Dosara wayar ya yi ya gabansa yana ɓallawa Malam Saminu harara"aikin banza ko meye wani sabon abu cikin kalamanta da ya burge ka har kake yabonta haka oho?. Kar ka ce min ba ka taɓa jin wani ya yi irin wannan maganar da ta faɗa ba?". Yana kai aya ya miƙe tare da shigewa cikin banɗakin dake cikin ofishin ya maida ƙofar ya rufe da ƙarfin da ya tursasa mini matse idanuna. Murmushi kawai Malam Saminu ya yi ya ce mu koma ajinmu. Sakina ta riƙo hannuna"ke wallahi yau na gaskaka zancen da Sabira take fada mana, shin ba ki hangi tsantsar kishi a cikin idanunsa ba sa'ilin da Malam Saminu yake yabon ki?". "Ban gani ba komai ba zan taba gani ba, kuma da kuke ikirarin cewar kuna gani akwai don kun canfa abun ne". Haka har muka gama rubuta jarabawar kullum na shiga what's app ɗin sai na tarar da an ƙara yi mini sallama da wannan lambar, duk da kuwa bana amsawa saboda kashedin da yaya Sufyan ya yi mini akan takan tsantsan da mutanen yanan gizo. Mun yi walima mun kuma yi ƙwarya ƙwarya party muka cashe da ƙawayen mu. Raina fari ƙal ji nake tamkar babu wanda ya kai ni murnar wannan gamawan da muka yi, domin ko banza na rabu da ganin tsanar Malam Suraj a gare ni. Ranar da muka y partyn a cikin makaranta, malamai da sauran ɗalibai duk suka taya mu murna. Ban sanya Malam Suraj a idanuna ba domin ko wulgawarsa sai ɗaya ban gani ba. A bakin wasu nake jin cewar bai zo makarantar ba a ranar. Tunda muka yi candy na koma gidan Momma da zama. Yaya Sufyan da Yaya Sa'eed suka tafi ƙarin karatu kasashen ƙetare. Watarana tsautsayi da rabon tafka da ba sa ni ya sanya ni shiga saƙon da ake turo mini da wannan lambar domin na kwana biyu ban duba ba. Murnar kammala makaranta aka yi mini tare da fatan alkhairi da addu'a sosai. Haka kawai na tsinci kaina da amsa addu'ar da kalmar amin a bayyane, sannan ya mayar da martanin cewar na gode da manyan baƙaƙe. Ban tashi daga wajen ba aka maido mini da amsa. Tsoro ya kama ni na tambayi da mace nake magana ko namiji?. Emojis dariya aka turo mini haɗi da cewar na kwantar da hankalina shi mai sona ne kuma sona ya yi tasirin da ba zai taɓa iya cutar da ni ba. Na faɗa wasi-wasi ban ja batun da tsayi na na yi bulokin ɗin layin. Sai dai hakan bai hana ni ganin an ƙara turo mini makamancin saƙon da ake turo mini a baya ba, ko wacce safiya da saƙonsa nake fara cinkaro kana nan kafin na kwanta bacci sai ya turo mini. Tun daga lokacin da ya mayar masa da martani ban ƙara kula sa ba, sai dai nakan buɗe duk wani saƙon da yake turo mini na karanta wani lokacin na yi dariya wani lokacin kuma takaici ya ishe ni. Sai da aka ɗebi tsawon makonnai uku babu ranar da ya taɓa fashin turo mini wannan saƙonnin. Har ya zama na riƙe lokacin da yake turawa da na ga lokacin ya yi komai nake yi zan bari na shiga what'sapp ɗina ina jira. Da ya turo zan tsinci kaina ina sakin murmushin da ban san ina yi ba ina gama karantawa zan ajiye wayar. A haka yi kwana uku ban ga saƙonsa ko ɗaya ba, tun bana mayar da hankali har na fara shiga damuwar rashin ji daga gare sa. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki ta 400 wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan no 08068748984 LAMBA NA GOMA SHA HUDA ________Murmushi naga yayi mun ya fara ta kowa in da gado na yake a hankali idon shi a kai na ƙura mun ido yayi bakin shi yana son furta wasu a bubuwan amma irin yadda na haɗe rai bai bashi daman magana ba sai da ya jima a kai na kafun naji yace"ya jikin naki dafatan kin fara samun lafiya in baki dage ba da kulawa da kanki da bawa zuciyar ki hutu ta samu sauƙi ba zan tura ki barno a cen zaki dinga kallon likita yanzu me yasaki kuka ?. Kallon shi nakeyi bana son wata kalma daga gareshi ko da ta farin ciki ne don zuciya ta tafara rashin yadda da wasu mazan na gagara sai ta kaina sannan nayi hawayen ya daina gangarowa daga ƙunci na amma hawayen ba,daga ido na yake zuba ba daga zuciya ta ce ban ,isa in hana shi zuba ba ko yaya ne . natafi duniyar tinani a karo na biyu kenan da naji zuciya ta tafara ƙarye wa daga samun JB in kuwa halaccin da nayi Wa JB bai sa yayi mun uzuri ba lalle so bai samu matsugu ni a gareni ba . Jin doctor nayi ya fara magana "me yasa kike son jefa kanki cikin tashin hankali meyasa kike son ki kasa jurewa a kan ƙaddaran ki, soyayya ,itace ke sawa zuciya matsaloli masu tarin yawa ,a da zuciyar ki bata samu raunin da yanzu yake samu ba ,na tambaye ki ,kin fara soyayya ne a lokacin da ,a ka kawo ki na duba ki kin ce a'a to yanzu nagane wannan wanda yake saki damu wa,amma bashi da yan uwa ko bashi da ƙanwa ko dai a zuriyar su babu mai irin jinyar ki . "Wa Yagaya maka a irin wannan matsalar nake yin kuka kawai dai bansan yaushe ,a ka kawo ni nan ba shine kawai na shiga damuwa a kai " ƙarya bata da ce da fuskar ki ba wannan ya nuna wanda ya fara sanya ki damuwa a lamu ya nuna maƙaryaci ne zai koya miki a bun da ba ɗabi,ar ki ba ce ". So yake ya ƙureni ga shi ya zauna yaƙi tafiya sai ɗan na wayar shi yake yi cen wayar tafara neman ,a gaji sanya wayar yayi a kunnen shi jinayi yace ganinan zuwa bani minti goma tashi yayi yace zai je asibiti yana zuwa zaije General hospital an kawo wata mara lafiya an nemi jijiyar ta dan a sanya mata drip ba,a samu ba in taya shi da addu,a Allah yasa yayi nasara dan ance tana shan wahala . da to na bishi Allah ya bata lafiya Amin ya ce mun ya fice kafun ya fita ya cire mun drip ɗin don ya ƙare . Hajiya ce ta shigo da su Inna mahaifiyar Ibrahim "sannu uwa ta Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne Ibrahim yace a gaishe ki ɗazu ya kira waya kina bacci bamu tashe kiba duk ya shiga da muwa a jhkan halin da kike "ayya inna ina ji da shi nima ko aure yayi matar shi bata kaini son shi ba "ke ce matar Ibrahim in har ina raye babu wanda zakiaura sama da shi yana sonki ga shi ɗan uwan ki ne, zai kula da ke to meye abun sai kinje wani gidan ko ba haka ba Lubabatu . Hajiya ta ce tace e inna yafi kam Allah dai ya nuna mana lokacin kawai musha biki mu huta wayaga miskilai guda biyu suna ta maganar su ,ko in kulasu na kashe waya ta tun da nakaranta saƙon JB bana son ya Kirani gara kawai in fara mantawa da shi Inna ce ta miƙo mun wayar ta wai ga Ibrahim amsa nayi muka fara gaisawa "ya jikin ki sannu Allah ya baki lafiya duk na rikice bana gari naje Abuja zan dawo gobe zaki ganni bazan wuce barno ba a nan zan tsaya Allah ya baki lafiya don Allah ki daina sanya kanki cikin damuwa baki san halin da nake shiga ba shiya sa ki tausaya mun . duk naji wayar ta gundire ni ba muyi sallama ba na miƙawa Inna wayar ta abinci a ka sanya mun nací ƙadan na kwanta zuciya na kamar an ɗaura mun ɗutsi mai nauyin gaske jama,a sai zuwa suke tayi asibiti sai ya zama kaman gidan biki maman Sadiq ne tazo duba ni"ƙawata kamar kinyi kwana goma kina jinya kina bani tausayi gaskiya baban su yace in gaishe ki "ina amsa wa,jikin da sauƙi gobe za,a sallame mu, da safe duk asibitin ta,ishe ni nagaji. "ki bari kisamu sauƙi in kinje gidan ma kwanciyar ce sai tinanin banza" ,munata hira sai kusan mangari ta ,tafi naji daɗi sosai don tabani abun dariya,ni kaina in natino sai in yi dariya ƙarfe tara na dare doctor ya shigo duba ni . "Ya jikin ki da fatan yanzu kam babu komai allura ce saura guda biyu Barole sannan I v ne zakuyi haƙuri zuwa gobe ko jibi zamu sallame ku"ba komai Allah ya kaimu . "Amin ya rabbi ". Bansan yaushe ya tafi ba don nayi bacci farkawar da zanyi a raza ne na farka,wani mummunan mafarki nayi da JB ya ɗaga mun hankali addu,a nayi na kwanta nayi bacci cikin ikon Allah baccin ya sake ɗauƙa na mafarki na sake yi da Muhammad yana roƙo na kar,in bari JB ya cuceni bai dace dani ba ya koya mun abubuwan da bai sanni da shi ba addu,a yatayi mun mafarki da Muhammad ya tasar mun da hankali sosai na sha kuka ban taɓa mafarki da Muhammad ba a she daman abun da yake gayamun na cewa in nací amanar shi zai ɗinga fito mun a fatalwa da gaske ne ,kenan hawaye Masu zafi ne suka zubo daga ido na ,na gagara mantawa da mafarkin duk wanda ya ƙara kallo na yasan a kwai babban damuwa a tattare dani. buɗe waya ta nayi na rubuta wa doctor saƙo a kan yayi haƙuri ya sallame mu, yaje in ya samu lokaci yayi mun Alluran a gida . Sallamar mu,sukayi na dawo gida ,a nan ma yan unguwar mu suka ta tururuwa wajen zuwa duba ni daga na rufe ido ,na Muhammad nake gani yana roƙona kar ,in bari a ci zarafina . A darán Ibrahim ya sauƙa bai wuce barno ba a damaturu ya tsaya ban san ya zo ba sai washe gari naga ya shigo duba ni ,banyi mamaki ba . "Yau she kazo"? "Wajajen ƙarfe goma kina bacci ya jikin da sauƙi ko ɗan naga ,alama kin sha jiki sosai ,ki daina yawan sa tinani a ranki don Allah wallahi ko da baki aure ni ba ki ɗauke ni a matsayin abokin ki, zaki samu ilimi mai tarin yawa daga gareni ko yaya ne bana son ki shiga wani hali "tinawa nayi da maganar Abba na cewa ya bani kwana sha biyar gashi har yau banga kiran JB ba muna tare da Ibrahim nace ya miƙa mun waya ta zan buɗe "meyasa kika kashe wayar ki bake tinanin a kiraki a gun aiki ne ko dai wani abu mai mahimmanci haba Nusaiba"?. Buɗe wayar nayi a take nashiga Whatsapp cin karo nayi da saƙon mutane da yawa har da wani number a na roƙona da in buɗe waya ta a kwai matsala nagama karanta wa kenan saƙon JB ya shigo a kan inyi haƙuri zai, gaya mun magana koda a ce zagin shi zan yi in yi mishi afuwa in kula shi haƙuri yata bani ,a kan in har na yadda zan ganshi gobe ya shiga wani hali. Amsar da na bashi "kayi hakuri JB baka dace da rayuwa taba nasan Kanada rauni sannan nayi maka halacci ka saka mun da tsiya bani da lokacin ka koda, mutuwa zakayi bazance karƙa mutu ba nasan zaka tarar da abun da ka shuka yau she kafara soyayya da har kake ganin nakai matsayin wanda zaka walaƙanta bari kaji nagama da babin ka . Ibrahim ne yayi mun magana "kin barni sai latse latsen waya kike yi ko dai kuna magana da saurayin ki,ne in barki ki huta don ke nazo garin nan meyasa kike walaƙanta nine haba Nusaiba kiji tausayi na ,mana Abba ya ce in zo akwai magana Allah yasa ba cewa, zai yi yafasa aura mun ke ba . Ikon Allah ! Ibrahim sirrin zuciya tane bayyana maka wanda nake so koda a, ce bana sonka bazan nuna maka JB ba don rainani zakayi murmushi nayi sai kusan azahar yafita daga ɗakin yana fita na rushe da kuka damuwa tayi mun yawa bayan la,asar sai ga doctor yazo yi mun allura har falon Abba ya ,shiga Ibrahim yana gefe yana kallo neman Jijiyar tawa wahala gareta waje biyu ya bula sai jin muryan Ibrahim nayi"malam ko dan kaga ba jikin ka bane baka san yana mata zafi ba kayi a hankali dan Allah . Ko kula shi bai yi ba yaci gaba da aikin shi ya gama ya fice ko sallama bai yi mun ba sai naji wani iri a raina yanzu kenan ranshi ya ɓaci kenan . "Ya Ibrahim meyasa kayi mishi haka doctor nane kodai baka gane shi ba ? Nagane shi mana "Kuna da matsala baza ki gane abun da na lura da likitan nan ba sonki yake yi bakiga kallon da yake yi miki ba shiya sa ". Ficewa nayi na barshi a falon na tafi ɗaki waya ta na ɗauka sai ga kiran JB a dai dai lokacin Ibrahim ya shigo naga ya karbi wayar ya sanya shi ,a kunnen shi sannan ya tsare ni da ido.... [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR MARUBUTAN JAHAR YOBE Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Kai tsaye ki sanya kuɗin ki ta wannan asusun 400 Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984 LAMBA NA SHA BIYAR ____________Bansan me yace ba sai jinayi yace ga wayar ki "me yasa zaka karɓi waya ta ya Ibrahim me hakan yake nufi kenan"? Kiyi haƙuri Nusaiba bana son ki shiga wani hali amma kisani bazan jure cin fuska daga kowa ce fanni a gareki ba zuciyar ki ,ta dagule kin cenza ya kamata ki hango wata mahangar in ba haka ba ,muddin kika zurfafa soyayya zakiyi naɗama waye wannan wanda ya kiraki nasan shi shine yayi mun pop na gida na shida wasu yayun shi ɗan barno ne mai ya haɗaki da wannan yaron ? Ikon Allah ya haka! Ka tsare ni to babu komai mun saba ne shiya sa kai na bincike ka, dawa kuke waya ne ko dai duk matan da kake, da number su ,ina takura maka "nifa ba wai ina tuhumar ki da sai kingaya mun ko shi waye ba naji yayi wasu kalamai wanda sai wani alaƙa ta soyayya ce keda hakkin furta wannan kalamai . Zan fita mekike so in kawo Miki gobe zan koma tunda naga kin warke in kuma ina takura miki zan baki lokaci kisani zan nemi yaron nan inji wani matsayi kike da shi, a gun shi "me yasa kake haka ne wallahi girman ka zai zube a ƙasa ya kamata ka gane hakan nasan kana da ,alaƙa da shi tunda ya maka aiki ,kirane ya shigo wayar ya Ibrahim da sauri ya ɗauka naji yace to "Abba yana kiranki wai kije amma yace in rakoki". Bansan hanya bane ko dai banida ƙafa kaje kayan ka zanje hijabi na ɗauka na nufi hanyar fita ya bini ya nace mun Ibrahim takura ne da shi duk ya gundire ni .da sallama na shiga Abba na ya amsa Hajiya na gefen shi "uwata yaufa saura kwana takwas a kan maganar da mukayi a razane na ɗago fuska ta,na daɗe ban ɗ'ago ba shiru nayi sai da naji muryan Abba ya ƙara magana. "ba dake nake ba wa kike so ne kigaya mishi yazo gobe ina son ganin shi in kuwa ya wuce gobe bakida miji fiye da Ibrahim ga shi nan shi ɗan uwan ki ne, zai kula da ke a kowa ni hali kika shiga sannan zai yi tattalin ki, zai baki kulawa". "Abba nifa ya Ibrahim a matsayin yayana na ɗauke shi ban taɓa sawa a zuciya ta,wani alakar soyayya zai shiga tsakanin muba ni auren nema ya fice mun daga raina amma kayi haƙuri Abba . Kina nufin bake son shi ne ko dai yaya? Shiru ne ya biyo baya babu macen da zata ga ya Ibrahim tace bata son shi sai dai mara rabo amma mai hankali dole zata ɗau ya Ibrahim yabar JB kodan halin shi ,na gagara magana tashi nayi nace to Abba daga mun hannu yayi ki zauna waya ce miki mun gama ina son a kwanakin da yarage ki kawo mun wanda kike so , sannan muddin kika sanya kanki damuwa ko dai jawowa kanki tashin hankali zan baki mamaki bakida mijin da yakai Ibrahim sannan kisawa ranki da shi zaki zauna zama na har abadan kawai dan saurayin ki ya mutu shikenan kice bazaki kula wani, ba wayon ki ne ya haɗaki da shi kodai ikon Allah ne ya haɗaku. Ido na ya cika da hawaye jiran zubowar su nake haɗa idon da zanyi,da ya Ibrahim naga hawayen sun gangaro jijjiga mun kai yayi ,alama karnayi kuka"Abba bana son a takura mata tawajen tilastata a kan sai ta aure ni tunda batada ra,ayi a barta kawai zaifi wallahi ba nason ganin ta cikin da muwa babu wanda baya tausaya mata sai mara imani". Ba komai a hankali zata gane tunda nake gani a kwai wanda take so a ranta amma taƙi bayyana shi ,mujira kwana kin da suka rage . Lokacin da nabar gun Abba ban ɗaga hankali na ba ,shiru kawai nayi waya ta naɗauko na kira JB sai da natara mishi missed call uku ,a na huɗun ya ɗauƙa ,sanar da shi nayi a kwai matsala gaskiya babba makuwa a na son haɗani da wani ɗan yayan Hajiya sannan saura kwana ki takwas . "banji mekike cewa ba"? Ko mai nagaya mishi "kiyi haƙuri har yanzu ban shawo kan iyayena game da auren muba kawai so suke su zaɓa mun ita sunyi shiru a kan maganar banji daga bakin suba wallahi ina son ki a lokacin da na zo miki banzo da yaudara ba manufa mai kyau ce a tattare da ni"banga alamar hakan ba JB kawai dai baka sona ne shikenan duk yadda kayi dai dai ne, nasan zan kai kaina ne in da ba,a damu dani ba iyayen ka basa sona tunda mahaifin ka da kanshi ya karɓe maka wayar ka sannan kace karna kira zai gaya mun magana sosai. "Me yasa bake mantuwa ne,naga abun nan ya wuce meye na dawo da shi kuma a yanzu da muke shirin iskar wata mahangar agun iyayen ki.shikenan nagode Na gagara gaya mishi Abba na yana son ganin shi gobe zan bari ya Ibrahim ya tafi babbar da damuwa ta ya zan nuna JB a matsayin wanda nake so bansan wani ƙaddaran ne ta haɗani da JB ba gashi kuwa ,komai yana son tarwatsa mun zuciya na tarasa waza ta zaɓa a cikin su Doctor ko dai ya Ibrahim ko wanne yayi mun halacci har dare ina ta tararraɗin gayawa JB ganin shi nayi yana online rubuta mishi nayi Abba yace yana son ganin ka gobe in ka shirya kazo kuyi magana . A jiye wayar nayi na nufi ɓangaren Hajiya bayan mun gaisa a cen nasamu ya Ibrahim suna ta hira yara sai cin abun da ya kawo musu,sukeyi sannu da zuwa nayi mishi abinci naje na debo nafara ci naga ya sauƙo ya sa hannu daka mishi harara nayi ko,a jikin sa bada ledar hannun shi yayi ciki da kaya a Aliyu ya kai mun ɗaki na ,bafa yunwar yake jiba gulma ce kawai yake damun shi "Hajiya zanje barno in yi kwana biyu agun Inna da sauri ya Ibrahim ya ɗago . "Da gaske kike yi "? Ina ruwan ka ba yanzu ba sai ka tafi zanje kowa yayi tafiyan shi nasan hanya "ai kuwa baza dai ki hau motar kasuwa ba sai dai in zo in ɗauke ki ,kinga kin huta abun ki ,jinayi Hajiya tayi magana"tunda zai tafi gobe ki shirya ku tafi tare mana ba yafi ba sai kiyi sati ki,dawo ". Hakan ma yafi sati biyu za'tayi kafun ta warke sosai a dole Hajiya tasani nace zamu tafi gobe naga farin ciki agun ya Ibrahim don Fatima tace zata bini mutafi tare tashi nayi na nufi ɗaki na shiga wanka,nayi ban tsaya duba waya taɓa sai da nagama kafun na ɗauko , wayar Whatsapp na shiga naga JB ya rubuto mun bashida kuɗin mota amma in ya samu zan ganshi in yi haƙuri don Allah ,ba shi amsa nayi yanzu mahaifina yana kiranka a ce bakada kuɗin da zaka zo kuyi magana ayya JB abun ka akwai Allah a cikin ta kuwa ba komai ka zauna karma kazo duk wanda ta raɓeka ita da takaici yanzu tafara ganin baƙin ciki tunda ita ta,ɗauka wa,kanta tashin hankali ne kawai. Jawo ledar da ya Ibrahim ya kawo mun nayi a,bubuwa ne masu tarin yawa ya kashe kuɗi sosai ,dama a ce wannan daga gun JB yake amma shi ,tsiya ce da shi ina son ganin JB yayi mun kyauta ko na meye ne zanji daɗi a rayuwa ta ,kirana yayi a waya na ɗauka "meya sa zakiyi fushi babu ɓoye _boye tsakanin mu ,bani da shi naje nayi sari ne shiyasa in kina da shi kitura mun zan baki in nasamu naje gun mama yanzu ma tace babu kiyi haƙuri karkiyi fishi kinji". Ko magana ban yi ba na kashe wayar nací gaba da abun da nakeyi a ranar ya Ibrahim bai shigo yayi mun sai da safe ba nata jira shiru har ƙarfe sha biyu sai naga ya tura mun sako , kiyi haƙuri kaina ciwo yake yi sosai shiyasa ban shigo ba sai da safe ki ,kula da kanki banda tinani sannan ki shirya da wuri mutafi ... [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA GOMA SHA UKU Tun ina danne abun a cikin zuciyata har lamarin ya soma fin ƙarfina, ba ni da aiki sai danna wayata da zaman jiran saƙo daga gare sa. Na yi yunƙurin mayar masa da amsa amma wata zuciyar ta na yi mini gargaɗi, cikin wannan halin aka shafe satikai uku. Har wani zazzaɓi ne na ji yana son rufe ni. Juyi kawai nake yi akan gadon ina sauƙe ajiyar zuciya ban san sanda hawaye ya soma kwaranyo daga koramar idanuna ba. Haka na ƙarar da rabin daren ina saƙa da warwara a cikin raina, tare da tunanin waye wannan wanda yake neman yin tasiri a cikin zuciyata. Ranar na tashi da matuƙar ciwon kai Momma ta kasa zaune ta kasa tsaye duk motsin da na yi sai ta yi mini sannu, tare da tambayar me ke damuna. Ganin yanda duk ta ruɗe ya tursasa mini daurewa na ce da ita babu inda yake yi mini ciwo, amma ba ta yarda ba sai da ta ƙira likita ya ƙara mini ruwa ta kuma gargaɗe akan kar na sanar da Hajiya hankalinta ya tashe. Da ƙyar nake buɗe idanuna da nake jin sun yi mini wani nauyin gaske, na dafe kaina da na jin sauƙinsa fiye da ɗazu kafin a sanya alluran bacci cikin ƙarin ruwan da ya fara aiki a jikina. Ajiyar zuciya nake sauƙewa a kai a kai tamkar wacce ta yi gudun ceton rai, haka na cigaba da kwanciya na jawo wayata dake ajiye akan drawer ɗin dake gefen gadon na kai ziyara a shafina na whatsapp. Take na ji wani ƙarfi da kuzarin da ban san ina dashi a wannan lokacin ya zo mini, zumbur na tashi ba zauna ba tare da na mai da hankali ga zafin da na ji ya ratsa ni daga hannun da aka maƙala mini ƙarin ruwan ba. Sai da na mirtsike idanuna domin son tabbatar da sahihancin abinda suke hasko mini, tabbas saƙonsa ne ya shigo cikin wayata. Jikina har rawa yake yi na shiga saƙon sai da na karanta aƙalla sau bakwai sannan na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya, ina rungume wayar a ƙirjina ina lumshe shanyayyun idanuna. Ban san dalilin da ya sanya ni jin wani sanyi yana ratsa shashin ruhina ba, haka nan nake ji na tamkar wacce aka yi wa bushara da shiga gidan aljanna. Jin ƙarar shigowar wani saƙon cikin wayar ya sa ni saurin buɗe lumshashshun idanuna na duba. Shi ne ya kuma yi mini wani saƙon. Yana tambayar a tsawon kwanakin nan shin ban yi kewarsa ba?. Domin shi duk wani bugun da zuciyansa za ta yi sai na faɗo a ransa. Tsintar kaina kawai na yi ina sakin wani ƙayataccen murmushin da yake fitowa kai tsaye tun daga ƙasa ƙalbina. Ban san sanda ya shigo ba balle zaman da ya yi kusa da ni sai ji na yi kamar daga sama an wafce wayar dake hannuna. Na zabura tare da ɗauko kaina domin ganin wanda ya aikata hakan a gare ni, ya katse mini farin ciki da annashuwan da nake ciki. Gabana ya faɗi ganin Sultan ya miƙe tsaye da wayar yana ƙoƙarin duba abinda nake kallo. Na marairaice tamkar mai shirin yin kuka"Don Allah yaya Sultan ka ba ni wayata wani abun mai muhimmanci nake dubawa". "Nima wannan abun mai muhimmanci nake son gani da har ya ɗauke hankalinki, ko motsin shigowa ba ki ji ba". Da sauri na fige ƙarin ruwan zan tashi na karɓa wayata, kallon da ya kafe ni da shi ya sanya ni komawa na zauna ina sunkuyar da kaina ƙasa. "Wani irin abu ne wannan da bakya son kowa ya gani?. Shin muhimmancin abun har ya ɗara muhimmancin lafiyarki?. Na lura kwana biyun nan gabaɗaya hankalinki yana kan wayar nan, kin ga ki nutsu har ki ɗaura rayuwarki gabaɗaya akan waya domin sharrin dake tattare da ita ya fi alfanunta". Yana dasa aya ya ajiye mini wayar a kusa ni ya juya ya fice, ban damu da ko ransa ya ɓaci ko akasinn hakan ba. Yana fita na ɗauki wayar ina Allah-Allah ya sa na tarar dashi a online bai sauƙa ba, domin yau na yi ɗamaran mayar masa da amsar duk wani magana da ya yi mini. A ina ya san ni?. Waya bashi lambar wayata?. Sannan me yake so daga gare ni?. Su ne jerin gwanon tambayoyin da na fara watsa masa. Daki-daki ya ba ni amsar da suka ƙara narƙa da zuciyata cikin son ganin wanene shi a zahiri. "Kar ka sake yi mini magana, matuƙar ba zaka bayyana kanka a fili na ganka ba". Na karanta abin da na rubuta a zahiri kana na tura masa, ya dawo mini da amsa cikin faɗin"zan bayyana a gare ki nan ba daɗewa ba. Amma sai na tabbatar da cewar na kafu a cikin zuciyarki, ta yanda ko a wani hali na bayyana a gare ki ba za ki juya min bayana". Bayyanannen ajiyar zuciya na sauƙe na ƙurawa fuskar wayar kallo, jin ana ƙoƙarin turo ƙofar ɗakin ya sa ni saurin ajiye wayar a gefe ina kafe ƙofar da ido. Ta nufo Ni da hanzari ta cire mini ƙarin ruwan tana faɗin"kina zaune drip ɗin ya ƙare yana tara jikinki, tunanin meye kike yi?". Sai a lokacin na lura da ƙarewar ƙarin ruwan na sadda kai ƙasa don bani da kalaman da zan yi amfani da su wajen kare kaina musamman da ta tsare ni da idanunta. Sai da ta zauna a kusa da ni sannan ta furta"yanzu me yake damun ki?". "Babu inda yake yi mini ciwo, ciwon kai ne daman kuma shima ya daina". Ta kai hannunta ta tallafo haɓata "Allah ya ƙara sauƙi". Na ƙirƙiro murmushi dole na dasa a fuskata"Amin ya Allah ". Ta ce na je na yi wanka na yi salla sannan na fito na ci abinci nasha magani, yanda ta faɗa haka na yi na iske su a falo ni kaɗai suke jira. Na saci kallon Sultan na ga babu yake kallo ba hankalinsa gabaɗaya yana kan na'ura mai ƙwaƙwalwar dake yake latsawa cike da ƙorewa a gabansa. Tare muka ci abincin na gyara wajen, Momma tana tashi ta shiga ɗakinta nima na miƙe zan tashi. Maganar da Sultan ya furta ya sanya ni dakatawa. "To za ki je ki kama sana'ar danna wayar ko?". "Da Sakina fa muke magana akan karatunmu?". Ya ɗago kansa ya yi mini kallo ɗaya"kai tsaye ƙarya ki ke faɗa". Na buɗe baki zan kuma yin wani maganan ya ɗaga mini hannu alamar na dakata. "Yanzun ma ƙaryar za ki ƙara faɗa ki dai nutsu kuma kin san abinda ya dace domin yanzu ke ba yarinya ba ce. Wuce ki ba ni waje". Na haɗe rai na fice daga falon izuwa ɗakin kwanana. Na haye gado na cigaba da chat ɗina. Sabo tirke wawa kafin a rufa watanni biyu tunin wani shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu ga mutumin da ban san wanene ba. Sai dai tabbas kalamansa sun yi tasiri wajen karkato da hankalina izuwa gare shi har na fara sauraronsa. Na taɓa yi masa tambayar ko dai ya kasance ɗaya daga cikin marubuta saboda yanda yake tsarawa, jeranta da kimtsa zance daki daki. Babu wanda ya san ina soyayya ko Sakina ban sanarwa ba, na yunƙuce a raina cewar sai na gan shi a zahiri sannan zan sanar da ita. Wata ranar na ce dashi zan je wankin kai ya tambaye ni a ina ne Allah ya sa kusa ne don ba ya son na wahala. Na sanar dashi ya ce kusa da unguwar su ne, ya nema da inda na gana na tura masa saƙo zai zo. Ina saka da tsallen farin ciki Sakina ta turo ƙofar ɗakin tare da sallama, ta sa ki baki sakake tana bina da kallo. Sai da na yi na gaji sannan na faɗa kan gado ina maida numfashi. "Ke in ce dai lafiyarki ko?". "Lafiyarce ta kawo haka". Na bata amsa ina tashi zaune na kashe mata ido ɗaya, na tashi na shiga ɓandaki ina jin ta tana faɗin"ikon Allah". A gaggauce na yi wanka na shirya cikin shirgar riga da siket ɗin kamfala. Duk da hijabi zan sanya sai da na kashe ɗaurin kallabina, har muka yi wa Momma sallama Sakina ba ta daina mamakina ba. Yaya Sultan ne ya kai mu kuma shi zai ɗauko mu kamar yanda Momma ta faɗa. Da ya ajiye mu ya juya akan in mun kammala mu ƙira shi. A ni aka fara yi sannan Sakina, ana gama mini na zaro wayata daga jakata na tura masa saƙon na gama. Mintuna kaɗan tsakani ya dawo mini da amsar na yi haƙuri ya ɗan fita amma yanzu zai dawo na ɗan jira. Na mayar masa da amsar Allah ya kawo shi lafiya. Aka gamawa Sakina shuru ban ji ya turo mini saƙo ba. Ina jinta tana faɗin wai na ƙira yaya Sultan na shaida masa mun gama na yi kunnen uwar shegu da ita. Muka yi sallan zuhr a nan shagon don da ta matsa mini cewa na yi na ƙira ba ta shiga. Ta ce na bada ta ƙira da kanta don na ga alamar bata yarda da ni ba ƙarara akan fuskarta. Dole ba danna ƙiran na sanya a amsa-kuwwa na galla mata harara"gashi sai ki yi magana". Na ji wani daɗi ya lulluɓe ni da na ji yana faɗa mata wani uzuri ya riƙe shi ba zai sama damar zuwa ɗaukar mu ba, mu nema drop ɗin daidaita kawai ya kai mu gida. Haka muka fito bakin titi riƙe da wayata da nake jiran saƙonsa. Duk zumuɗin da nake yi ya koma ciki, na ji ni kamar wacce mutuwa ta ɗauke mata wani jigo na rayuwata. Sai da Sakina ta taɓo ni kafin na dawo duniyar zahiri daga na tunanin da na faɗa. "Tunanin me kike yi haka tun ɗazu ina ta miki magana shuru?". "Babu". Sai da ta ƙare mini kallo"to ga adaidaitan in kin gama tunanin zai ki shigo mu tafi, hadiri ne yake tasowa". Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina kuma waiwagawa, har na gama cire rai zan shiga adaidaitan na ji muryar wani yaro a bayana. "Gashi in ji wancan mutumin a ba ki". Na ƙura masa ido daga shi har farar fefan da yake miƙo mini"ina yake?". "Yana ba ni ya tafi". Na karɓa cikin rawar jiki na tusa ta a jakata, na shiga. Har muka isa gida ban ce komai ba. Na zauna a bakin gado ina dafe da kaina. "Me kike ɓoyewa ne Surayya?. Tun safe kika dasa zarginki a cikin raina tabbas akwai wani abun da bakya son na sa ni. Waye wanda ya aiko a ba ki wannan takardan?. Sannan me yake ƙunshe a cikin ta". "Ban san shi ba ban san shi ba Sakina. Ban san wanene ba". "Kamar ya?". Na ɗaga kaina"kamar yanda kika ji na faɗa". Ba tare da bakina ya yi shawara da zuciyata ba na ji ya hau feɗe mata biri har wutsiya. Jakata ta fizgo ta ɗauko takardar ta fara karantawa a bayyane. "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya azurta ni da idanun da nake iya ganin kyakkyawa kamar ki. Ba zan iya ƙarisowa inda kike ba amma ki sa ni a ko yaushe ke ce abun tunawa a gare ni, ko a farke ko a cikin bacci. Zan bayyana a gare ki nan ba da daɗewa ba". Muka haɗa ido ƙirjina yana gudun famfalaƙi..... [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA GOMA SHA BAKWAI "Surayya lalle ba ki da hankali wallahi kina dab da haukacewa matuƙar kika cigaba da biyewa wannan mutumin da ya kasa bayyana kansa a gare ki, wai yaushe ma kika canja har haka ne?" A jere ta watso mini tambayar, na sauƙe gigitaccen ajiyar zuciya ina lumshe idanuna saboda sarawar da kaina yake yi mini tamkar zai rabe gida biyu. Ta dafa kafaɗata"da zan ba ki shawara ki ɗauka to ki gaugauta cike shi daga cikin rayuwarki domin na ga kema kin ɗaukake shi. Ni tsoro na ma kar ya cutar dake wallahi". Ban ce da ita ko kanzil ba har ta yi ta gama tana haɗawa da nasiha da nusarta da ni illar abinda na ke aikatawa. Har ta bar gidan kalamanta suna yi mini zarya a cikin kwanyata. Ranar ban iya runtsawa ba gabaɗaya. Tabbas zantukan Sakina suna kan gwadaben gaskiya sai dai aikata su zai zango mawuyacin abu a gare ni. Na ƙara buƙatar ina don mu haɗu a zahiri ko kuma ya daina kula ni, ya dunga kawo mini wasu uzurruka. Na daina kula shi ba wasu kwanaki sai dai ina jinyar zuciyata na share shin da nake yi. A wani yamma ya turo mini saƙo akan ya aminci mu haɗu amma don Allah na yi masa alƙawarin ba zan taɓa rabuwa dashi ba idan na yi tozali dashi. Ba tare da wani dogon tunani ba na yarda da hakan. Ranar da zamu haɗu tun da asubahi na ƙira zaSakina na sanar da ita tazo muka je tare. A gidan wani cin abinci muka zauna muna jiran shi. "Anya kuwa bawan Allahn nan ba jirga mu ya yi ba?". Na sa ki ajiyar zuciya"shi fa ya bamu wannan adireshin, na tabbatar da cewar zai zo". Ina rufe bakina saƙonsa ya shigo cikin wayata domin ba mu taɓa yin waya dashi ba. Yana sanar da ni cewar ya iso na sanar dashi ta inda muke, ban yi sanya ba na turo masa da amsa. Babu ɓata lokaci ya maido mini da amsar cewar gashi a wajen yana ma hango mu na ɗago kaina. Idanuna suka hango mini abunda ya hautsina tunanina tare da damalmala lissafina, tsam na miƙe tsaye jikina yana rawa. Sakina ta kafe ni da ido tare da tambayar lafiya kuwa?. Na kasa sanar da ita illa nuni da nayi mata da hannu ga malam Suraj ɗin da yake nufo inda muke. Ya murza shadda da karin hula fuskarsa ɗauke da fara'ar da ban taɓa ganin makamanciyarta a bisa fuskarsa ba. "Me ya kawo wannan kuma nan wajen?". Na yarfa hannuna alamar ban sa ni ba, ina ɗaukar jaka da nufin barin wajen. Na ji ya ƙira sunana cak na tsaya na lumshe idanuna da ya ciko da ƙwalla. Ina jin ƙarar taku har aka iso gabana"ni ne wanda kika daɗe kina muraɗin gani Surayya, ga ni yau tsaye a gabanki buɗe idonki ki ganni". "Kai ne waye?". Muka haɗe baki wajen furtawa ni da Sakina a gigice ina ƙura masa ido, ya yi ƙasa da kansa sannan ya ɗauro"ni ne wanda kike magana dashi a whatsapp, sannan ni ne wanda zaku haɗu dashi a yau a daidai wannan lokacin a kuma wannan wajen". Take na ji wani zazzaɓi ya rufe ni na dafe kaina ina karanto kalmar innalillahi wa inna ilaihir raji'u. "Malam anya ka san abinda bakinka yake furtawa kuwa?. Shin ka san su waye tsaye a gabanka?. Ko wani abun ka sha wanda ya gusar maka da hankali?". "Duk abinda nake faɗa daga zuciyana suke fitowa kai tsaye, kuma ras nake domin ina cikin cikakken hankali da nutsuwata. Sonta ne kawai ya rufe min ido bana ganin kowa sai ita ko yaushe ita ce a cikin tunanina". "Wallahi na tabbatar da ba ka cikin hayyacinka, shi ne zaka ɓoye kanka tsawon wannan lokacin ka ƙi bayyana kanka a gare ta sai yanzu. Ina ganin girmanka a idanuna don haka ka ja kimarka Malam, daga yau ka rabu da Surayya ka daina tura mata saƙonni ka fita daga cikin rayuwarta. Ka bar ta ta huta haka nan ya isa haka basajan da kake yi kana yawo da hankalinta". Ta na dasa aya a nan ta fige hannuna zamu fice daga wajen ya yi saurin shan gabanmu. Tun kafin ya ce wani abu na yi saurin fizge hannuna daga cikin na Sakina na fice da sauri saboda hankula mutanen wajen da ya fara dawowa gare mu. Sakina ta fito muka hau adaidaita muka tafi, tsabar rashin hankalin da nake ciki ko motsi mai ƙarfi na kasa yi har muka isa gidansu, ta sallame mai adaidaitan tare da riƙo hannuna domin na gaza sarrafa jikina muka shiga ciki. Kaina a ƙasa na gaishe da iyayenta da muke iske a tare, kana muka shige ɗakinta ina shiga na zube akan gado ina rero kukan da nake jin ciwonsa har cikin zuciyata. Sai da aka ɗauki wasu mintoti kafin ta ce da ni"ba kuka za ki yi ba ɗaga hannu za ki yi ki godewa Allah ya sa kika gano shi tun kafin abubuwa su yi nisa, sai ki yi wa kanku faɗa da karatun ta nutsu ki san inda duniya ta nausa. Ki sa ni ba ko wacce mu'amala ba ce ake zurfafawa". "Na ƙure tunanina na gaza gano manufarsa na aikata hakan a gare ni, wallahi zuciyata bugawa take yi da ƙarfi". Ta matso ta ɗago kaina"mugunta ce kawai babu wata soyayya, kar ki ƙara maimaita wani kuskuren na barin kalamansa su yi tasiri a gare ki". "Sai da ya bari na yi sabo dashi zuciyata ta kamu da soyayyarsa, wallahi in da ban ga saƙonsa ba ko bacci bana iya yi Sakina". Ware idanunta ta yi a kaina cike da mamaki nake faɗin"malam Suraj ɗin?". Na sadda kaina ƙasa domin sirrin zuciya sai mai ita, ni kaɗai na san ƙangin da nake ciki. Tun tana lallashina har na soma bata haushi ta ƙyale ni. Sai yamma na baro gidan. Kullum cikin tunani nake na koma tamkar marar lafiyar da ta yi jinyar shekara. Komai cikin sanyan jiki nake aiwatar dashi na daina kula shi na kuma daina buɗe saƙonsa gaba ɗaya. Sai ya koma ƙiran wayata hakan ya sanya ni barinta kullum a kashe. Na rame na kuma yi baƙi kullum sai Momma ta tambaya me ke damuna, na ce da ita babu babu tambaya da matsawar da ba ta yi mini ba akan na sanar da ita abinda ke damuna amma na nuna mata ba komai. A haka har muka sama gurbin karatu a jami'ar da Yaya Sufyan da Yaya Sa'eed suke koyarwa, muka fara zuwa. Ba na taɓa mance wani daren ranar alhamis da ba ɗebo gajiyar makaranta ga shi ranar na yi azumi haka na dawo na yi luguf. Har bacci ya fara ɗauka ta na ji wayata na ruri na buɗe idona ina lumshewa. Har ƙiran ya katse ban tashi na ɗauka ba, aka ƙara ƙira a karo na biyu na yi tsaki tare da lalumo wayar ban tsaya duba mai ƙiran ba na kara a kunnena. "Ke ce Surayya?". Cikin magagin baccin da bai gama barin idona ba na ce "ni ce". "Suraj ne ya bada lambarki ya ce a ƙira ki". Duk da mutum ɗaya jal na sani mai irin sunan a rayuwata, amma sai na tsinci kaina da tambayar"wani Suraj ɗin?". "Suraj masoyinki gashi nan kwance magashiyan rai a hannun Allah, tun yana tafiya da jinyar a jikin shi har ya kai matakin da ta kai shi ƙasa. Tun dare jiya aka kawo shi asibiti baya cikin hayyacinsa sai yanzu ya farka, likitoci sun shaida mana cewar zuciyarsa ce ta kumbura za ta iya bugawa a ko wani lokaci daga yanzu, sunanki kawai yake ƙira don Allah ki taimaka mana ki ceci rayuwarsa". Take na ji kaina yana juyawa, baccin da ke idona ya wartsake na tashi na zauna hawaye yana bin kuncina. Ba zan iya jurar jin raguwar maganganun ba don haka na datse ƙiran ina fashewa da wani matsanancin kuka, sosai nake kukan sai da na ji numfashina yana cushewa waje guda sannan na tsagaita. Na danna ƙiran layin da ya ƙira ni dashi ringing ɗaya ya ɗauka, na ce ya ba wa Suraj ɗin wayar. Ya ce da ni ba zai iya amsa ba sai dai ya sanya masa a kunnensa. A hankali yake maganar muryarsa sam ba ta fita, babu abinda yake faɗa illa roƙona da na furta ina sonta koda sau ɗaya ne kafin Allah ya ɗauki rayuwarsa. Wani kifiyar tausayinsa ta yi tsalle ta dira a zuciyata tare da tarwatsa ta into pieces. Haƙuri kawai na ke iya bashi da kuma yi masa addu'ar samun lafiya daga wajen Allah. Ban mu sallama ba sai da ƙaninsa Sani kamar yanda ya sanar da ni sunansa, ya ba ni adireshin asibitin da suke na yi masa alƙawarin gobe ina sha Allah kafin na wuce makaranta zan tsaya na duba jikin nasan. Har alfijir ya keto ban tsunra sai saƙe saƙe nake yi cikin raina da nazarin maganganun malam Suraj, shin daman tsana ta na rikiɗewa ta koma soyayya? Daman haka soyayya take shigewa cikin zuciya ta yi bankan-bankan ba tare da sanin mai ita ba. A bayyane na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina wargaza gashin kaina da na tufke shi ta baya. A gaggauce na yi wanka na shirya ko abinci ban tsaya ci ba na ce da Momma na yi latti kuma malamin zai iya hana ni shiga, addu'ar fatan alkhairiin da ta saba yi mini kullum ta raka ni dashi na fice. Sai da na shiga cikin asibitin na danna ƙiran wayar Sani kamar jira yake yi ya yi caraf ya ɗaga, na sanar dashi ga ni a cikin asibitin na yi masa kwatancen inda nake. Ya fito tun kafin ya iso na ga tsantsar kamarsa da malam Suraj da hakan ya ba ni tabbacin cewar jininsa ce. Na lura da wani irin kallon da yake yi mini da ya sanya ni tsarguwa da kaina, shi ya yi mini jagora har cikin ɗakin yana kwance ga ƙarin jinin da aka yi masa da ya kusa ƙarewa, fuskarsa ya yi wata 'yar rama. Yana ganina ya tashi zaune na ƙarisa cikin ɗakin ina jan ƙafata da ƙyar, bai damu da ƙarin jinin dake jikinsa ba ya sauƙo ƙasa ya zube akan gwiwoyinsa yana roƙon na yafe masa a cewarsa duk abinda ya aikata son da yake yi mini ne sila. Na sha kuka kafin na baro asibitin koda nake makaranta ban fahimci komai ba. Sai da muka fito na cewa Sakina za ta raka ni asibiti dubiya dubu ɗayan dake cikin jakata na yi amfani da ita wajen sayan lemo da raguwar kayan zuwa duba marar lafiya. Muna shiga ɗakin ta yi turus tana kallo na, na yi saurin ɗauke nawa ido ina ƙarisa shiga. Na gaishe shi tare da yi masa yaya jiki ya amsa mini da alhamdulillah. Sakina da ta ƙi ƙarisowa cikin ɗakin ya ƙurawa ido yana ba ta haƙuri cikin tausasan lafuza da nuna tsantsar nadamar abinda ya aikata a bayyane, yanda yake furzo zancen daki-daki ya isa karyar da zuciyar ko wanene. Tun daga lokacin na soma sauraronsa da kuma ɗaga wayarsa idan ya ƙira ni, malam Suraj mai nuna mini tsantsar tsana sai gashi yau shi ne ya zamo masoyin da ba ya son ganina cikin ko wacce irin damuwa komai ƙanƙantarta. Sau tari na kan lura da Sakina ba a son ranta nake ɗaga wayarsa ba sai dai kawai babu yanda ta iya, amma hakan bai hana ta yi mini kashedi da jan kunne akan na bi a hankali ba kuma na dunga yin ta-ka-tsantsan. Shaƙuwa ya ƙara shiga tsakaninmu mai ƙarfi kullum sai ya je makarantar mu, ba ma iya yin awa biyu ba tare da mun ji muryar juna ba, ko yaushe shi ne a tunanina. Ya canja matuƙa daga malam Suraj ɗin da na sa ni a da, domin na yanzu mutum ne mai tsananin kulawa da ƙoƙarin kiyaye duk wani abun da zai sanya raina ya sosu. Ya iya tsara zancen da zai tsaye imanin ko waye da kalamai. A lokacin Momma ta fahimci cewar ina kula wani ba tare da sanin su sosai ta yi mini faɗa da nasiha, tare da umartata da na sanar dashi ya gabatar da kansa ga Abbanmu. Tun a ranar na sanar dashi sai dai na ga yana kwacewa maganar, sai da aka jera sati biyu ina masa maganar amma yana bani wasu uzurruka a cewar yana tsoron kar iyayena su hana sa aurena domin kasancewarsa talaka. Ranar da ya amsa mini cewar zai zo na yi matuƙar murna domin ko makaranta ban je ba, na sanarwa Momma ta faɗawa Abba na sha faɗa a wajen sosai. Da yazo na yi masa jagora har cikin falon Abba suka gaisha, sannan Momma ta ce na basu waje zasu tattauna. Haka nan kawai na ji zuciyata ta kasa nutsuwa da abinda zasu tattauna har na je ɗaki na dawo na leɓe a ƙofar falon ina sauraron abinda suke faɗa. Tambayoyin asali da sana'arsa Abba ya yi masa duk ya amsa masa su, sannan ya tambaye shi shin ko ya shirya yin aure a yanzu, domin ba zasu laminta ya cigaba da kula ni ahalin bai shirya yin aure ba. Amsar da ya ba shi shi ya goge mini yadda tas tare da ƙarar da ruwar kaina, na ƙara gaskata wannan karin maganar"namiji ba ɗan goyo da zani bane". "Ranka ya daɗe ta kasance ɗalibata a makarantar sakandiri, rashin fahimtar da ta yi min na cewar ina da zafi ya ɗarsa da tsorona a cikin ranta, shiyasa na yi amfani da wannan damar wajen goge hakan daga cikin ranta. Ban so ta da soyayya ba duk abinda na yi na aikata shi ne a matsayin shiri, ba zan yi mamaki ba idan ita ta ɗauki hakan a matsayin soyayya amma ni kam ba haka bane daga nawa ɓangaren". Take na ji numfashina yana hawa da sauƙa, na kasa sarrafa kaina, na yi baya lu na faɗi ƙasa sumammiya. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA GOMA SHA TAKWAS Ban san iya adadin kwanakin da na ɗaba ina cikin halin da ban san waye a tsaye a kaina ba balle halin da nake ciki. A firgici na buɗe idona bayan tsawon lokacin da na kwashe a sume. Rarraba idanuna na shiga yi ina ƙarewa ɗakin kallo, Anty Sadiya da Sakina su kenan zaune a cikin ɗakin ganin na duɓe ido ya sanya su isowa gare ni da sauri suna jeranta mini sannu wani na bin wani. Kafin Anty Sadiya ta yi wa Sakina wani maganar da ban fahimci abinda take faɗa ba ta fice babu jimawa ta dawo tare da likita ya duba ni tare da yin wasu 'yan rubuce rubuce. Ranar haka na wuni ba magana sai dai bin mutum da kallo, so nake yi wani daga cikin ya ƙaryata mini zancen da kunnuwana suka ji ye mini Suraj yana furtawa su Abba babu kunya balle nauyin ganin idonsu cewar duk soyayyar da muke yi shi a wasa ya ɗauki hakan. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u". Shi ne kalmar da ya yi nasara fara fita daga bakina, ina dafe kaina da nake jin tamkar ana buga mini guduma saboda tsananin sarawa da yake yi mini. Sai da na yi kwanaci uku cur a asibitin sannan aka sallame ni muka koma gida, na ƙara faɗawa cikin matsanancin fargaba da tunani domin babu wanda ya yi mini maganar Suraj a iya zaman da muka yi a asibiti ko da wasa. Anty Suwaiba ce ta fara yi mini faɗa har da ɗauke ni da marin da ya sanya ni dafe kuncina saboda zafin da na ji ya ratsa ni. "Mahaukaciyar ina ce ke da za ki biye saurayin da bai taɓa gabatar da kansa a gaban iyayenki ba har ki faɗa soyayyar mai zurfi haka. Sakina ta sanar da mu komai yanda kuka fara har zuwa yanzu. Ashe ba ki da hankali bamu sani ba, kafin mu yi aure a cikin mu akwai wacce kika taɓa ganin tana kula wani ba tare da sanin gida ba?. To gashi za ki je ki ɗaurawa kanki wani ciwon a banza akan wanda bai dauƙi rayuwarki da muhimmanci ba, da ki rayu da ki mace duk ɗaya ne a gare sa domin bashi da asara ko kaɗan". Hawaye shaɓe-shaɓe a fuskata na furta"ku yi haƙuri Anty amma wallahi Malam Suraj yana so na kuma ya ɗauke ni da muhimmanci fiye da komai a rayuwarsa". Wani kallo ta watsa mini cike da takaici take faɗin"ai ɗaukar ki da muhimmancin ne ya sanya ya kalli tsabar idon iyayenki ya furta musu cewar babu soyayyarki a cikin ransa kawai ke ce kika ɗauka a hakan". Take na ji na wartsake na janye hannuna da har yanzu yake dafe da kuncina. Na gwalo idanuna waje"ashe ba kunnuwa bane suka yi ji mini ba daidai ba, wallahi soyayya muke yi dashi wataƙil kwarjini Abba ya yi masa shiyasa ya furta haka". Jijjiga kanta ta yi"ƙwarai ya faɗa kuma ki saurari hukuncin da su Abba za su zartar akan ki, tun wuri ki rabu da wannan yaron". Tana dasa aya a nan ta fice daga ɗakin ta bar ni da yin zaman 'yan bori dirshan a ƙasa saboda rawar da ƙafafuna suke yi. Tagumi na zabga ina nazari zantukanta, na yi tunanin zan tarar da ƙiran malam Suraj rigis a cikin wayata idan muka dawo daga asibiti sai dai ko sau ɗaya bai ƙira ni ba, bai kuma ajiye mini saƙo ba. Daren jiya na ƙira shi sau babu adadi amma wayar a rufe take. Da hanzari na tashi ina jin jiri yana ɗauka ta na ɗauki wayata na tura masa saƙo akan idan ya kunna wayarsa ya ƙira ni akwai maganar da zamu mai muhimmanci. Haka na kwana na wuni cikin faɗuwar gaba kowa ya canja mini an kuma ƙara sanya ido sosai a kaina, ko wani motsin na yi sai an ji ba'asi. Na yi mamakin rashin zuwar Sakina gidan tun bayan sallamo ni daga asibiti kuma na ƙira wayarta bata ɗauka. Tunda Hajiya ta haifo ni nayi wayo ban taɓa ganin ɓacin ran Abbanmu da Abban su yaya Sufyan ba sai a wannan lokacin na ci faɗa tamkar za su yi aron baki da kuma barazanar ƙwace wayata da hana ni fito ko nan da can, Momma ita ke ta bada haƙuri da roƙo mini sausauci amma Hajiya ma kawar da kanta ta yi. A ƙarshe an yi mini gargaɗi mai ratsa cikin akan na fita daga harkan Suraj idan kuma aure nake so na sanar da su, a nema mini miji na yi auren su daina ɓata ƙudinsu a harkan karatuna tunda bashi bane a gabana. Na ci kuka tamkar raina zai fita na rasa inda zan tsoma raina na ji sanyi, babban tashin hankalina bai wuce rashin samun Suraj a waya ba. Na yi imani da kalama ɗaya idan ya faɗa mini zai warware duk saƙar da su Abba suka yi mini game dashi . Ban taɓa sanin so ya kan zama cuta ba sai ya da faru akan kaina. Ban taɓa tunanin so ya kan ɗaɗɗata mutum ya fitar dashi a cikin hankalinsa ba sai da na ga misali akan kaina. Ban taɓa zaton so ya kan raunana zuciya ba sai yanzu da yake neman tarwatsa mini tawa zuciyar. Na yi wani mungun rama da baƙi, ko makaranta na je bani da aiki sai tunani da ƙiran layin Suraj wanda bana gajiya da ce mini da ake yi a kashe ko sau nawa ne. Na rasa abokin shawara domin Sakina ma ta fita daga harkata gabaɗaya, gaisuwa ce kawai take shiga tsakanin mu da ita. Gani nake yi tamkar a cikin mafarki komai suke faruwa. Na kasa jurewa na kasa daurewa kamar yanda na gaza lallashin zuciya da take tafasa. Watarana zuciyata ta kitsa mini da na je makaranta ko zan sama malam Suraj haka na ɗebi kafa bayan na fito daga gida da shirin wucewa makaranta domin zana gwaji. Dashi na fara yin tozali ina cilla ƙafata a filin makarantar na sauƙe bayyanannen ajiyar zuciya ganin sa da na yi cikin ƙoshin lafiya ƙadai ya samarwa zuciyata lafiya, salama da nutsuwa. Na sa ki jakata a ƙasa tamkar mahaukaciyar na nufi wajensa da sauri kamar zan kife akan hancina. Ya juyo ya watsa mini wani kallon da ya tursasa mini tsayawa na yi turus. "Ka sanya ni cikin tunani da damuwa matuƙa, ka bar zuciyata cikin fargaba da zulumin anya kana lafiya kuwa. Ka daina kula ni na daina samun ka a waya duk na shiga damuwa da tashin hankali". Amsar da ya ba ni cikin gatse ya sanya juwa fara kwasa ta, tsabar idona da babu komai sai zallar ƙaunarsa ya kalla ya ce da ni"Malama me ye haka za ki ɗebo ƙafa ki biyo ni har cikin makaranta gaban ɗalibaina?. Salon kawai ki jawo min raini a wajen su wanda kema shaida ce bana son sa kuma bana ɗaukarsa". Numfashina ya na hawa da sauƙa na ce"malam Suraj ni ce fa, Surayya ce ko dai baka gane ni bane?". Ya buga mini tsawa" na gane ki in Surayyan ce sai me ye?. Malama ki ɓace min daga gani, in ma ikirarinki cewar na ce ina son ki ne za ki yi amfani da hakan ki zubar mini da mutunci gaban ɗalibaina to yanzu na janye. Domin na farka daga baccin da nake yi da yake haddasa min yin mafarkin mallakar ki, na gano iyayenki ba zasu taɓa bani aurenki ba". Ɗaga hannuna na yi sama ina faɗin"na rantse da girman Allah malam Suraj iyayena zasu baka aurena ko da kuwa ace kai ka yanke wa talauci cibiya. Basa daga cikin irin waɗannan mutanen masu raina ƙarfin na ƙasa da su, don Allah kar ka ce za ka guje ni bayan sai da ka sanya igiyoyin sonka ka ɗaure mini raina dasu, wallahi zan sha baƙar wahala". Tsaki mai dogon zango ya buga mini zai bar wajen na yi saurin riƙe rigarsa ya fincike. Ya fara tafiya ina bin sa a baya tare da yi masa roƙo da magiya ban damu da inda nake ba balle raguwar ɗalibai da suka yi mini farin sani suke bi na da na mujiya. Ban yi aune ba juyarwa da zai yi kawai na ji ya ɗauke ni da wani gigitaccen marin da sai na idanuna suka hango mini gilmawar baƙin duhu. "Kashegin ƙarshe zan yi miki ƙi fita a harkata idan kin cika 'yar sunna a cikin iyayenki". Na buɗe baki da nufin bashi amsa idanuna suka sauƙa akan fuskar shugaban makarantar da Malam Saminu da suke kallon da dukkan alamo sun daɗe tsaye a wajen. Wani tsaki ya kuma dokawa ya juya ya ɗauki hanyar ficewa daga makarantar, na sunkuyar da kaina ƙasa ina hawaye, in ban da so me zai haɗa ni da malam Suraj har ya yi mini wannan cin mutuncin a bainar nasi kuma na kasa ganin laifinsa. Ofishinsa Shugaban makarantar ya ƙira ni tare da tambayata abinda ke faruwa, ban yi ƙwauron baki ba na feɗe masa biri har wutsiya tare da roƙonsa ya ba wa Malam Suraj haƙuri har ya rabu da ni. Kwantar mini da hankali ya yi sosai sannan ya ce na je gida tare da yi mini gargaɗin cewar kar na ƙara yin kuskuren bin saurayi inda yake. Makaranta na wuce lokacin har sun fito daga gwajin, ina isa wajen hall ɗin na yanke jiki na faɗi sai buɗe ido na yi na gan ni kwance a asibiti ma'aikatan jinya tsaye a kaina. Tun su Momma da Hajiya da raguwar 'yan uwana suna yi mini faɗa da jin takaicin abinda na aikata har suka koma jin tausayina domin ko maƙiyina ne ya ganni dole ya yi mini ƙwalla. Sai da Abban su yaya Sufyan ya tabbatar mini da cewar zai nema Suraj su zauna dashi sannan na ɗan dawo cikin hayyacina, bayan ya zo gidan mu da ƙyar da suɗin goshi ya bayyanawa su Abba cewar ko kyauta aka ba shi aure na ya yafe domin a cewar wai bani da kamun kan da yake buƙata daga wajen mace. Na yi jinya tamkar ba zan cigaba da rayuwa ba, sai da na koma kamar mahaukaciya ba ni da aiki sai sumbatu ganin halin da nake ciki shi ke sanya su Abba ƙara tuntuɓar Suraj amma yana maimaita musu zance ɗaya. A lokacin yaya Sufyan da Yaya Sa'eed suka dawo bayan kammala karatun su na shekara biyu. Suka tarar da ni cikin wannan yanayin sun yi baƙin ciki matuƙa da kuma tausaya mini. Ko makaranta bana iya zuwa dole na yi dipparing domin ba ni da nutsuwar yin komai. Bayan dawowar su da wata biyu yaya Sa'eed ya yi aure, ni kuma Anty Suwaiba ta ɗauke ni na kuma gidanta da zama sai da na yi watanni tara cur bana garin sannan na ciwon zuciyata ya soma warkewa. Yaya Sufyan ya sadaukar da lokacinsa wajen ba ni kulawa har na soma dawowa dai dai. Ya hana ni na yi kaɗaici ya zamo abokin a gare ni kuma bangon da zan jingina a duk lokacin da nake tangal tangal. Ya wadata ni da komai kullum cikin rarrashin zuciyata yake yi. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA TA GOMA SHA TARA Sai da aka ƙarar da zangon karatu cur bana nan ko jarabawa ban sama damar zanawa ba. Sai da daga bayan na dawo garin bayan na gama ciwon raunin dake ke cikin zuciyata da kullum yake ɗanye. Yaya Sufyan ya sanar da su Abba yana so na sun yi matuƙar farin ciki. Abbanmu har da kukan sa don murna domin a cewar sa tun bayan faruwar wannan lamarin kullum cikin fargaba yake, bai san wanda zan kuma faɗawa soyayya dashi ba don ya fahimci cewar ina da rauni sosai, idan ba a yi dace da na ƙwarai ba sai ya yi amfani da hakan ya cutar da ni. Ba a nema jin daga gare ni ba balle tambaya ra'ayina ina son shi ko akasin hakan duk ba a bani damar faɗin hakan. Gadan gadan aka fara shirin biki dole na lallashi zuciyata ta ƙarfi da yaji na tusa Yaya Sufyan a cikinta, ba don komai saboda farin cikin iyayena da kuma irin halaccin da yaya Sufyan ya yi a gare ni a lokacin da nake cikin tsanani. Babu wanda ya damu da me nake ji a cikin raina, kowa gwaɗa mini kyawawan halayyansa kawai yake yi da yi mini don albarka. Momma ta ƙara ninka soyayyar da take gwada mini sai nan da nan take yi da ni. Na canza layi na kuma goge duk wani abun da zai sanya ni tunawa da malam Suraj haka nan na dage da kai kuka ga Allah. Na koma makaranta na cigaba da karatuna bayan na ƙara kwasa-kwasan da na yi diparing ɗin su kafin na zo na jona su Sakina da a lokacin su na aji biyu a jami'ar. Tabbas Yaya Sufyan ya cika cikakken masoyin da samun irin sa a Wannan zamani sai an tona, sai kuma mai da ce gami da sa'a. Babu shakka ya nuna mini tsantsar soyayya kuma tsaftacceyi, soyayyar da yake bani 'yanci na faɗi ra'ayina akan komai. Na sha jin ana cewar maza ba sa karɓan laifin su balle har su ba da haƙuri, amma yaya Sufyan ya sha bambam da da yawan mazaje. Ya kan karɓa laifinsa da ma wanda ba nashi ba na kuma bada haƙuri, haƙurin da ya amsa sunan sa ba irin na izgilanci ba. Ɓat hotunan abubuwan da suka wakana masu motsi suka ɓacewa ganina, na dafe kaina da nake jin tamkar zai rabe izuwa gida biyu tsabar sarawar da yake yi mini. Na matse jikina wajen guda wasu hawayen masu ɗumi suna fareti akan kuncina tare da zarewa izuwa tudun wuyata. Na saki bayyananniyar ajiyar zuciya tare da buɗe rinannun idanuna na zubawa wayata. Har yanzun bai ajiye mini wani saƙon ba kuma ya ga rubutun gobe ɗaurin aurena da aika masa. Figigi na dawo hayyacina tare da ɗauke idona daga kan wayar jin ana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin. Muryar Sakina ce na ji tana ƙiran sunana tare da ɗaurawa"lafiya kuwa?. Kina ji na?". Sai da fesar da zazzafan iska daga bakina na ce"lafiya ƙalau". Na miƙe akan ƙafafuna da suke rawa na isa ga famfon da na buɗe yana zubar da ruwa na wanke fuskata sannan na ɗauro alawala na riƙo wayata na fito. Tana tsaye a ƙofar banɗakin ta ba ni hanya na wuce har na shimfiɗa sallaya ba ta ce da ni komai ba. Wutar ɗakin yana kunne ɗaiɗaikun ƙawayenmu suna bacci yayin da masu wayar dare da samarin su kuwa suke ta fama. Raka'ar farko kawai na iya yin ta a tsaye amma na biyu a zaune na yi shi saboda juwan dake shammatar ƙafafuna. A zuciyata na yi addu'ar domin na gaza samun haɗin kai daga bakina wajen furzo da zancen dake cikina. Sakina ta zo ta zauna a gabana tare da kafe ni da ido"Surayya wai lafiya kike kuwa?". Na yi mata kallo ɗaya na ɗauke kaina gefe"ga alama kuwa kin ga ni". Ta jijjiga kanta"duk alamomin da suka bayyana a gare ki ba na mai lafiya bane, don Allah ki sanar da ni me ke faru". Sai na yi ɗan jim kafin na ce"ki taya ni da addu'a kawai Allah ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar". Ina dasa aya nan na miƙe tare da zage hijabin kaina na je na kwanta sai dai gabaɗaya bacci ya gagari idanuna, duk motsin da zan yi sai na duba wayata ko zan ga saƙon Suraj amma shuru tamkar an shuka dusa. Har aka ƙiran sallan assalatu idanuna ƙar wani zazzaɓi mai zafi ya rufe ni, sai na sha magani sannan na ji ɗan ƙarfi a jikina. Wanka ma da ƙyar na yi shi na fito fuskata a kumbure bayan na gama cin kukana a cikin banɗakin tare da ƙara aikawa Suraj saƙon cewar ƙarfe goman safiyar yau za a ɗaura aurena. Shadda na saka ɗinkin doguwar rigar da ya bi jikina aka ɗaura mini kallabin da ya zauna a kaina ya yi mini ɗas. Sashin Hajiya aka kai ni na gaishe da ita da kuma ƙawenta da sauran dangi. Yaƙe kawai nake yi amma ni kaɗai na san zafin da nake ji a cikin raina da balbalin wutar raɗaɗin da nake ji a cikin raina. Ƙarfi da yaji Sakina ta raba ni da wayata a cewar ta wai ita take ɗauke mini hankali don haka za ta ajiye ta a wajen ta. A masallacin da ke jikin gidan mu za a ɗaura auren, ina zaune bayan na canja shiga ana gyara mini kwalliyar fuskata. Na ji sanarwar an ɗaura aurena da yaya Sufyan. Kwatankwacin yanda gero ke tashi yayin casarsa a cikin turmi ya yi tsalle haka zuciyata ta yi tsalle. Da hakan ya sanya ni numfashina sarƙafe babu shiri na ɓarke da wani matsanancin tari mai ƙarfi. Duk sannu suke jeranta mini wani na bin wani tare da ba ni ruwa, kafa kaina na yi na soma shan ruwan babu ƙwauƙwatawa sai da na shan tas sannan na koma sakin ajiyar zuciya tare da dafe kaina. "Lafiya kuwa Surayyan?". Kaina kawai na iya ɗaga mata mai kwalliyar ta cigaba yi mini, ana ɗaura mini kallabi Sakina ta sanya mini wayata a kunnena kafin na tambaye waye ne. Muryarsa yaya Sufyan cikin tsantsar farin ciki da annashuwa yana faɗin"alhamdulillah an ɗaura yau dai kin zama mallakina Surayya. Mun zama ma'aurata wallahi na rasa yana zan falsata miki farin cikin da nake ciki a yau. Zan tabbatar miki da cewar ba ki yi zaɓen tunin dare ba zan wadaci da dukkanin abinda mace take da buƙata daga wajen ɗan miji." Ihu da shewan da 'yan ɗakin suka saka a tare suna hasko ni da kemarurin wayoyinsu, shi ya ankarar da ni cewar wayar a amsa-kuwwa take duk abinda yake faɗa suna yi. Shima dariyar ya yi"ku shirya zamu shigo da abokinsa". Daga haka ya kashe wayar kwatattun hawayen da suka ciko mini idanuna suka zubo. Duk a zaton su hawayen farin ciki ne da murnar ganin wannan ranar amma ni a gare ni abun ba haka yake ba. Mun sha hotuna da dangi da abokan arziki, shigowar yaya Sufyan ya abokansa ya sanya wata tsohuwa sakin goɗa ana shelantawa ga ango ga ango. Hotuna aka yi mana dashi sosai da kuma abokansa a kunnena yake yi mini raɗar cewar shiga ta da kwalliyata sun burge ni. Sadda kaina ƙasa kawai na yi ban ce dashi komai ba. Sai da aka yi sallan magrib aka kai ni wajen su Abba suka yi mini nasiha sosai mai ratsa jiki da haifar da nutsuwa a dukkan sassan jiki. Haka nan ma Hajiya da kuma su Anty Suwaiba sai sauran dangi da suke ta yi mini fatan alkhairi da addu'ar samun zaman lafiya a cikin auren mu. Tamkar wacce aka ciro daga cikin ruwan sanyi za a tsoma ta cika wuta haka nake jin kaina yayin da aka fito da ni za a sanya ni cikin mota. Kuka nake yi bil haƙƙi da dukkan ƙarfina amma haka aka ɓamɓare ni daga jikin Hajiya aka sanya ni a cikin motar. Har muka isa gidan ban tsagaita daga sakin hawayen da nake yi, Sakina da Anty Sadiya suka tsaye a gefen hagu da damana. Suka umarce ni da na shiga da addu'a da kuma ƙafar dama. Har cikin uwar ɗaka suka shiga da ni tare da ɗaura ni akan gadon da Abban su yaya Sufyan ya saya mini. Nasiha suka ƙara yi mini sosai tare da nusar da ni cewar na bi wa mijina biyayya akan dukkan komai matuƙar komai ɗin bai kaucewa komai daga cikin tsarin Allah da dokokinsa ba. Alfarmar Anty Sadiya na nema akan ta bamu waje ina son ganawa da Sakina, kasancewar mai fahimta da sauƙin hali ba ta kawo komai a ranta ba ta tashi ta koma falo wajen su Anty Suwaiba da raguwar dangi da ƙawayena. "Don Allah me yake damun ki?, shin kin gani cewar yaya Sufyan yana da wani mummunan hali ne da yake ɓoyewa ko kuma menene?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a sannan na yaye laffayar dake kaina na ce"maganar Suraj ne". Na yi mini wani kallo fuskarta ɗauke da mamaki ta ke faɗin"Suraj kuma?. Na yi tunanin su mun gama wannan maganar dake. Don Allah ne yasa kike son ɗaurawa kanki damuwar wanda bai damu dake bane. Wanda ya yi fatali dake a lokacin da kike tsananin buƙatarsa. Wallahi Surayya ina guje miki faɗawa cikin fushin Allah domin yanzu fa ke matar aure ce ". "Son gujewa kaina ɗaukar zunubi shiyasa tun farko na zuciyata ta ke yi mini huɗubar na ce na fasa wannan aur.....". Kafin na ƙarisa ta yi saurin kai takufan hannunta ta rufe mini bakina"kar ki ƙara faɗin hakan kuskure ne, na roƙo ki don Allah kar ki sake ki yi maganar nan da wani ba don ni ba ki duba ko don soyayyar da yaya Sufyan yake yi miki shi da iyayensa ki manta da Suraj". Tamkar ta ɗaba mini mashi haka na ji zafin zancenta na ƙarshe na kasa cewa komai, har izuwa lokacin da Anty Sadiya ta dawo cikin ɗakin tare da cewar na gyara ga ango nan da abokansa zasu shigo. A falo muka zauna muka ƙara yi mana nasihohi tare da damƙa amanata gare shi, abokansa suka biya kuɗin sayan bakin sannan aka buɗe mini fuskata. Duk suka watse domin su Abba sun ce babu kwana a gidan amarya. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani LAMBA NA ASHIRIN DA ƊAYA Kai tsaye zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun 400 Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta nombobin 08068748984 Kai na ciwo yake yi mun ba na kaɗan ba haka na daure ba na son kwanciya nasan ya Ibrahim zai shiga wani hali sosai. Anty Nusaiba ina son gaya miki wani magana amma bansan ya zaki ɗauki maganar ba sannan ina jin tsoron ya Ibrahim daga ya ganmu tare sai yace muna takura miki"karki da mu zo muyi maganar amma lafiya kuwa meyafaru?. Ya kuke da wanda muka je shagon shi siyan kayan ɗinki ,a ina kika sanshi ya alaƙar ku ya ke da shi saurayin ƙawata ne Aisha Salisu Sharif sunyi soyayya da shi ,ada ya sota ,ita ma tayi mishi wani kalan soyayya a kanshi tafara soyayya wani abu da yake zuwa mata da shi wanda ta gagara gane hakan kullum sai yace sai ta tura mishi sufffan jikin ta,tun bata yadda tafara tura mishi gashi ba halayyar ta ba ce unguwar su ɗaya da shi nikuma tare mukayi secondary school da ita aminiya tane bata boye mun komai a haka. sukayi shekara ɗaya da rabi da shi wannan shine aikin shi yanzu basa tare da shi sun rabu taga zuciyar shi babu Allah kinga gemun nan duk ta banza ne ,rana ɗaya in iskancin ya tashi ajiye ta yake matsalan a lokacin da yake neman ta ko shagon ba shida shi abubuwa dayawa a kanshi wani rana da ya tura mata photon jikin shi,a lokacin ƙanin ta ya ɗauki wayar kaman za,a kashe ta,a gida sai dai fuskar shi bai fito ba da,a sirin shi ya tonu mungu ne fuska biyu ne gare shi wallahi Allah sai ya sakawa Aisha na tsane shi gashi ya yaro ne sai zuciyar banza . Numfashi na ja,yanzu wannan shine halayyar JB kenan shine yamun ƙarya tarabu da shi a she shine mungun Allah ya bimiki hakkin ki ya saka miki Aisha mata yawancin yadda da,amana da suke yi da saurin yadda da mutum shine babban kuskuren da sukeyi"ba komai laifi yayi shiyasa na nuna mishi ni nafishi wayo "ko dai kuɗin ki ya ƙarɓa ne bai biya kiba?"aa ba kuɗi bane abun da, nake so da ke shine don Allah karki gayawa ƙawarki munje shagon shi zaki rakani gidan su Aishan da yamma muje mu gaisa da iyayen ta bakince ke ƙawar ta bace zamuje ki shirya anjima kinji . Duk yadda Aisha tayi tasan meke tsakanin mu da JB ban bata wani ƙofa ba illah kawai nuna mata nayi zan taimake shi da yamma muka shirya muka je gidan su Aishan yarinyar kekkewa da ita gata da fara,a sai Aishan ne ta nunani ga Anty na ku gaisa ƙaragaishe ni tayi "ni kuwa A'isha ya labarin ɗan iskan nan ne JB ya nanan makuwa?"ya nanan , bani da lokacin shi yaje duniya ce wanda bai zoba ma tana jiran shi ,ƙarya ce kawai yanzu in ance ya turo kuɗin gaisuwa gidan su budurwa ba shida shi abun da JB yayi mun har yanzu mama fishi take da ni duk da nace bansan wanda ya turo ba . Allah ya kyau ta ! Bari mutafi duk abun da tafaɗa nayi recoding da zamu tafi har ɗaukan photo mukayi saboda tina ranan kash JB wannan in shine halin ka ,baka samu hali mai kyau ba in sha Allah macen banza ne zata zama matar ka yaudara da cin amanar soyayya sun zama ruwan dare naji takaicin yadda iyayen A'isha sukayi mata shi kuma ko a jikin shi gashi ta rufa mishi asiri taƙi bayyana siffofin shi ina son in ga ina kuka amma hawayen yaƙi zuba ban san dalili ba . Muna zuwa ƙofar gida muka tarar da ya Ibrahim tsayawa nayi a kusa da shi a jikin mota shi kuma yana ta danna wayar shi "kunje unguwa ne "? e munje unguwa gobe ki shirya zamuje gun likitan ki shirya da wuri ya tura miki number baki kira ba sai da nakira meyasa kike wasa da lafiyar ki ne haba Nusy ? "Ina so ka bani labarin rayuwar ku da Fiddausi nasan ka yaudare ta ne kawai nasan kufa maza kuɗin ne sai a hankali" ba wani labarin da zan baki ina ruwan ki ,ne ke kin fi son abun da zai ɗaga miki hankali kenan bazan bayar ba ki shiga gida maza karsu kalle mun ke kinga sai kallon ki suke tayi . Numfashi naja nayi kamar bada ni yake ba . Ina ganin JB yana ta kirana ko ɗauka banyi ba haɗa ido nayi da shi ya Ibrahim naga ya wani daka mun harara kira ne ya shigo wayar tawa mum Muhammad ce ta Kirani bayan mungaisa "ya gida ina su Hajiya daman yayan kune matar shi ta haihu yau suna an samu Muhammad shine nace bari na gaya miki ".murna nayi tare da yiwa yaron addu,a Allah yasa ya biyo halin mai sunan shi na sanar mata bana gari amma ina dawowa zanzo in Sha Allah nayi godiya sai na tsinci kai na da farin ciki Allah sarki nima akwai takwara n ka a ciki na Muhammad ina son halayyar ka sosai Buɗe Whatsapp nayi naga an tura mun hoton yaron take na ɗaura a status mutane da yawa, suka buɗe har da JB . Suka tayiwa yaron addu,a Allah ya raya shi ya sha addu,a wasu cewa suke har yana kama da mai sunan shi rayuwa kenan. Buɗe saƙon JB nayi Yau she kika zo barno ya,akayi kika gane unguwar mu,ya akayi kikasan shago na wannan ya nuna kinsan ko mai agareni kenan ko kula shi banyi ba tun daga ranan JB ya daina wannan rawan kan irin na yan bana bakwai . Photon mu nasa nida Aisha shine na uku da yagani ya ta,kira na sosai yakira yafi sau a shirin ko,in kula shi yayi mun magana ƙarshe har da muryan kuka karkisa nima nawa zuciyar ta fashe me ya haɗaki da Aisha meye a laƙar ku,da ita ? rubuta mishi nayi yar uwa ta ce.. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR MARUBUTAN JAHAR YOBE Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki 400 ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984 LAMBA NA A SHIRIN Ya zama dole in bishi tunda Hajiya ta sa baki ga shi mai sunan mahaifin ta ne bata ganin laifin shi ko kaɗan . bana son tafiya da ya Ibrahim gudu ne da shi ba ka,isa kayi mishi magana ba kamar zuga shi kake yi ,ga yadda hanyar take shiru nayi na shirya mana kayan mu ,nida Fatima ƙarfe goma muka bar damaturu mun kama hanyar barno ban gayawa Inna ina hanya ba sai dai ta ganni . In da zuciya ta zata ,amince da ta zaɓi mutumin da yake da kima da daraja agun kowa kash sai dai ita so duk ba ruwan ta da wannan,ina mamakin yadda ya Ibrahim yake nuna mun kulawa fiye da kanshi a lokacin da Muhammad ya rasu tamkar ɗan uwan shi tare muka wuce bauchi da shi sunyi sabo da mutune agun zaman makokin Muhammad . Muhammad yana da zafin kishi, amma ban taɓa ganin ya nuna wa ya Ibrahim ba . Tinani natayi da yawa a cikin motar shi kuma ƙaratu ya kunna yana taji Fatima tayi bacci a cikin tunanin da nakeyi har na tino in da zamuje bauchi da Muhammad muka tsaya a darazo yace mu tsaya mu gaisa da wata batada lafiya haɗe rai nayi nace wata kuma ni bazan jeba ya je ina cikin mota lokacin da muka je duba mara lafiyan a she na miji ne zolaya ta yake yi nikuwa kishi ya rufe mun ido wajen samun lada. Babban mutum ne a she sunan shi TY wajen aikin su ɗaya naji kunya da yazo ya sameni a cikin mota ya gaishe ni abun da naji ,yace"Madam kin ɗauka wata ne ko shiyasa kikaƙi zuwa a hakan ma nagode sosai Allah ya bar zumunci na gode ". A bubuwan masu matuƙar rikitarwa da ruɗani da zullumi Muhammad ya bar mun suna dayawa a rayuwa ta a kan alkairi zan ta, tina shi irin su JB ko da mutuwa sukayi babu abu mafi daraja da zan tina shi da shi sai jin maganar ya Ibrahim nayi yace "in kin shiga kicewa Inna na wuce gun aiki wannan key ɗin ɗaki nane ki share mun ɗan Allah ga kayan nan ku shiga da shi ".mai shara kamayar,dani ?ba zanyi ba in kadawo zakayi kayan ka ,kana da ƙanne kawani sani aiki sai kace wata matar ka kama hannun Fatima nayi muka ƙarisa ciki Inna nata rar tana tsaye ganina da tayi tace oyoyo uwata kece tafe babu waya kuma ?. e Inna nice bazata zanyi miki shiyasa kika ganni . Sannun da zuwa shiga ciki nayi na huta nací abinci nayi sallah har bacci ya ɗauke ni banga kiran JB ba tun safe a waya ta sannan bance ina garin suba akwai abun da nake son shirya mishi zan bashi mamaki kuwa sai ƙarfe takwas na dare ya Ibrahim ya shigo bayan na bada key ɗin ɗakin na shi a gyara mishi abun ka da mai tsafta komai a gyare ya ke kawai dai in da sabo ne an saba . Sai kusan mangari ba kafun ya dawo duk muna falo muna ta shan hira yau sai naji damuwar da nake ciki a cikin kashi ɗari hamsin ya bar raina . "Inna kiyi mun afuwa nawuce gun aiki ban shigo ba sauri nakeyi shiya sa ki yafe mun kinji" babu komai karka da mu hakan ma yayi tunda ka,kawo mun uwata kana kulawa da ita sosai ina godiya Allah yayi albarka . "Amin ya rabbi ". Washe gari da safe Misalin ƙarfe goma na safe 10am bayan ya Ibrahim ya fita wajen aiki nima na shirya hijabin nan me rufe fuska da ko,ina na sanya na rufe fuska ta , yadda ko kasan ni ba lalle ne ka gane niba na ɗauki Aisha nace muje ta rakani unguwa amma karta faɗa fa tace to unguwar su JB na nufa ban tsaya shan wahala ba na tambayi shagon shi da zumar nazo siyan kayan ɗinki na samu shagon bada waya ta nayi a Aisha ta yadda zata ɗauka mun photo in naje shagon na samu wasu yara sunzo siyan zare da zip nikuma rubuta wa nayi da naje na ba,shi ya faɗa mun kuɗin na ba shi naga ya rame sosai ya ƙara duhu tsayin nan dai tana nan bai damu da yasan ko wa ye ba sana,ar shi yasa a gaba na duba shagon sosai abun duk ya bani mamaki bayan taho wata daga shagon karɓan wayar nayi Aisha ta burgeni har wajen da nake ba shi kuɗi sai da ta ɗauka da lokacin da yake bani kayan da nasiya munji ma,a unguwar kafun muka tafi har gidan su ,sai da a ka nuna mun nagani . Sai naji sanyi a raina da bansan da bansan da wa nake tare ba ina, gudun wani abu kar ya faru batare da nasan komai a tattare da shi ba wasu na samu lokacin da zan shiga shagon suna bakin shagon ɗayan na gane shi wani abokin shine bansan ya ,suke ba a hoton da ya tura mun har da shi tabbas shima yaron ne JB yana cika ido abokin shi kuwa asalin yaron ne dan ga,a lama suna tashan rake a bakin shagon oh ni Nusaiba. Soyayya nan ta jefo ni cikin ya rannan bayan mun dawo gida ne na buɗe waya ta don muna hanya na kashe wayar ina buɗe wa yana kira yayi muka gaisa "kiyi haƙuri na samu kuɗin gobe zanzo "ka zauna kayan ka, bance ka nemi kuɗi a ro saboda nawa buƙatan ba baka da shi sannan koda kaje gun Abba ba shida amfani don ga abun da iyayen ka suka ce ko dai wata manufar kake da shi kuma. "Me yasa kike haka ne kinsan abun da Allah zai yi ya,kamata ki gane masoyi ba ya taɓa zama maƙiyi a rayuwa . Har kana da bakin magana JB a she son kanka yayi yawa wallahi muddin ka ce tukunyan wani ba zai tafasa ba naka ko zafi bazai yi ba . Nuna mishi nayi bana gari nayi tafiya amma in zaizo yayi mun magana in gaya wa Abba "wani kalan zuwa zanyi bayan bake nan kibari sai kin dawo kafun na shirya sai in je da to na bishi banyi musu ba amma a jiki na nakeji bazai jeba kawai ya faɗa ne . Nayi kwana uku a barno babu komai JB yayi blocking ɗina a Whatapp ban bita, kan shi ba na ci gaba da,abun da nake yi duk wani abu na shi a waya ta duk na goge su wani hoto da wasu a ,bubuwa wanda suke a laƙa da soyayyar mu duk na fitar da su daga raina nagoge ban bar komai ba nagoge a nawa tinanin ban gaya mishi magana mai zafi ba da takai ya mun irin wannan tijaran ba .har zai rufeni daga ko mai na shi ayya JB yana da hankali kuwa ga shi yayi karatu da, ace bai yi karatu tuba zance a kwai rashin ilimi a tattare da shi . Ta howa ta barno yayi mun rana in da a damaturu nake yanzu ina ɗaki duk tunani ya dameni nan kuwa ina cikin yan uwa na ,babu abun da basa mun tun ranan da muka je ban ƙara sa ya Ibrahim a ido na ba ,da wuri yake fita yau dai takama Jumma,a naga Aisha sai washe baki ta ketayi "Lafiya kuwa indo sai wani fara,a kike tayi"? "Anty Nusaiba yau na tashi bani da kuɗi ga shi yau ne ya Ibrahim yake mana rabo na kuɗi ko wani jumma,a,kinga kuwa dole in yi murna da kasance war wannan ranan " gaskiyar ki kice mutumin ya nason lada kenan miƙomun jakata in fara baki kafun ya tashi daga bacci miƙo mun jakar tayi na ɗauki dubu goma na bata tsalle tayi tariƙeni sai murna take tayi tun da ga cen naga ya Ibrahim yana ta. hararan ta "ki cika ta so kike ki karya ta baki ga ita ba lafiya ne da ,ita ba haba Aisha ina ganin ki kamar mai hankali ",kayi haƙuri ba zan ƙara ba zan kiyaye ". Ya dai fi miki kyau ki kiyaye zaifi ƙariso wa in da nake yayi "Madam a nema mun abun da zanci yunwa na keji gaskiya ko dai in yi miki kuka" kayi kayan ka meyasa kake son ka dinga bani wahala ne ina huta wana zaka takura mun . na haƙura zan wuni haka tunda yau babu in da zanje sannan da yamma ki shirya zaki rakani unguwa kinji abincin shi na kawo mishi kaɗan yaci yace ya ƙoshi . Da yamma misalin ƙarfe hudu muka fita unguwa hanyar unguwar su JB naga ya nufa har kusan bakin shagon shi ,da yake motar ba lalle ne ka gane waye a cikin taba fita yayi suka ɗan matsa ya fara yi mishi magana a kan yana so a sa,pop a ɗakin baƙi yau she zasuyi ban san me suka yi ba kawai kallon JB nake tayi hawaye kuma daga zuciya na , yake zubo wa bada ga ido na ba ban san me hakan ya ke nufi ba ya Ibrahim so yake yace ya fahimci a kwai soyayya ,a tsakanin mu ,shine zai yi mishi haka ko dai cin mutunci zai yi mishi ya na so ya ce yaron bai kai ya Soni ba ko yaya ina kuka ina tinani har ya Ibrahim ya ƙariso bai kula da yanayin da nake ciki ba jan motar yayi . Ina zamuje ko dai in kaiki gidan abokina ku gaisa matar sa tana sonki kullum labarin ki ,take yi "ba na so mu wuce gida shine kaje ka jima gun waye ma ,kazo ne? "baki gane shi bane ko yaya yaron da ya kiraki ne fa a ,waya shine akwai aikin da zai yi mun "ya Ibrahim kenan yau she ka koyi cin zarafin mutane ,yau she zaka ɗauki talaka a kan matsayin ku ɗaya kayi hakan ne dan Kaci mishi mutunci ko dai ka ɓata mishi rai na gaya maka babu komai a tsakanin mu, mutunci ne sannan girman ka zai zube nidai na gaya maka dole sai shine zai yi maka aikin ka nemi wasu,mana taya zaka zo ka ɗauke ni ka ,kaini gunshi wallahi muddin ka nuna mishi ka sanni bazai ƙarbi kuɗin aikin ba sannan zai yi maka biyayya don nima daraja wa ne da karamci tsakanin mu. "Ba komai Nusaiba baki san meke zuciya na ba naso in kyautata mishi ne ta,wani hanyar amma tunda kin ce hakan zan kiyaye bazan bari ya gane ke mata na bace kin yadda bana son ganin ki cikin ɓacin rai banajin daɗi gaskiya ". Naƙi zuwa gidan abokin na shi siyayya yayi da yawa muka wuce gida muna zuwa a na kiran sallah masallaci ya wuce nima alwala nayi na shige ɗaki don gabatar da sallah. JB fuska biyu gareshi ya cutar da zuciyar da ta,amince da shi ya koma kaman na Allah na sha kuka a kan soyayyar JB na shiga ruɗani da farga bar rasa shi yanzu ko da za,ace ya turo gidan mu ba shida komai na shi ga ƙaryar da yayi mun na cewa a na son haɗa shi da yar uwar shi ,maganganu masu zafi a tare da kalaman shi a kwai ranan da nakira shi cewa yayi in ba kida abun faɗa zan ka she waya ta ina kuka ina cewa zan yi magana . Kamar yadda wasu ke faɗa soyayya da babbar mace a kwai riba da amfani mafi tsoka a tarayyar. shi JB yayi faɗuwar da bazai da woba ba yaruguza duk wata, kima da daraja da yake fama da shi wai har ni JB zai kalla ya ce yanzu babu ruwa a idon ki meyake nufi kenan.... [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki 400 ta wannan a asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984 LAMBA NA ASHIRIN DA UKU Bana son jin komai daga bakin ki Nusaiba kyi duk abun da ya dace kisani shi masoyi yafi maƙiyi wallahi ko da Muhammad zai dawo duniya zai yi alfahari da irin son da nake miki yau aure nane ya zame miki illa haba Nusaiba meye babu a jiki na wanda ba keson in raɓe ki mena tare miki. Shin na cencenci ki watsar dani mutune da dama suna son kasance wadani yau kin sameni a ,araha shine kike walaƙan ni, na tabbata hakkin yan matan da suke sona nikuma zuciya ta ke take so shine ƙaddarata . Ya Ibrahim kayi hakuri wallahi nayi nayi in ko yawa zuciya ta son ka abu ya gagara ban san ya zanyi ba ka yafe mun zan zauna da kai koda zuciya ta bata tare da kai zan baka farin ciki ". Ki a da na kalaman ki zai yi miki amfani wataran tunda yanzu zuciyar ki guduna takeyi"ban gane gudun ka take yi ba haba ya Ibrahim meyayi zafi haka ya kamata ka fahimce ni ". babu wani abu da zanji daga gareki kin gama magana me kuma ya rage yanzu Nusaiba. na soki na ƙauna ce ki karki bari zuciya ta taraya mun wani abu wanda ba ta da ce da naki rayuwar ba meyasa baki da tausayi ki duba irin ƙaunar ki da nake yi na hana kai na ci sabo da naki rayuwar na hana kaina jin daɗi dan kiji daɗi, kash a she taki , zuciyar bata tare da ni ko kaɗan zan barki bari na har abada sannan ki sawa zuciyar ki bazan yi aure kwana kusa ba koda an tambaye ki dalili ki ce baki sani ba .zan dai na zuwa garin nan da man dan ke nake zuwa ga shi kinyi mun nisan da bazaki ji kira na ba . tabbas a kwai wani a ranki na tabbata in ba haka ba bata yadda za,ayi kice bake sona kije kiyi tinani sosai bana son a walaƙan ta mun ke ko babu komai ke yar uwa ta ce nasan baza ki cenza ni daga suffan ɗan uwan ki ba Nusaiba . A guje na ƙarisa ɗaki hawaye masu zafi ne suka zubo daga ƙunci na ya zanyi ya kamata jama,a su fahimce ni son JB yayi mun kamun zaren leda bana iya jin zan ya gashi nayi kuka sosai har bacci ya ɗauke ni bayan na farka ne na tambayi Aliyu ina ya Ibrahim yace mun ya tafi jijjiga kai nayi ina cikin tsayuwa ina karanta wasiƙar jaki sai jin muryan Hajiya nayi "Nusaiba har kinyi waye War da zaki ce bake son Ibrahim me ya tare miki a she ke baki da hankali in kuwa kika ce Ibrahim bai yi miki ba duk duniya ban ga wanda zaki ce kina so ba ya gaya mun a kwai wanda kike so ki gaya mana waye ne ɗan wani gari ne ɗan waye shi? "Hajiya ba na son kowa kawai soyayyar ce yanzu bata raina jina ke kaman shima Ibrahim ɗin mutuwa zaiyi shine dalili na "da yake ranshi a hannun ki yake ba to ki sani ko dai ki auri Ibrahim ko ki dai na kirana da sunan mahaifiyar ki tunda ban cencenci alfarma a gare ki ba sannan na dai na tausayin ki ko da mutuwa zakiyi ki nemi wanda zai yi miki jinya na zare hannun na daga komai naki da sauri na ƙarisa gun Hajiya na kama hannun ta ture ni tayi sai da na faɗi ƙasa na shiga ɗaki na kira ya Ibrahim yaƙi ɗauka na tura mishi saƙo yaƙi da womun da amsa na rasa me ke yi mun ɗadi duniyar tayi mun zafi da wanne zanji matsalan ya Ibrahim ko dai dana JB ga saƙon da Doctor ya tura mun nace wa yana kan bakan shi ya fasa barina ya na tare dani kar in barshi ya shiga wani hali oh ni Nusaiba ya zanyi wani mahangar zan duba a cikin su . Kwana uku nayi ko da na gaishe da Hajiya ko amsa wa bata yi sai na dai na zuwa in da take gudun kar fishin yayi yawa ina zaune misalin ƙarfe sha ɗaya na safe kiran JB ya shigo waya ta ɗauka nayi nayi shiru yayi sallama na amsa sai jinayi yace ganinan a ƙofar get ɗin ku ,duk da ina son ganin JB a karon nan kuma sai naji nafi kowa tsanar shi "me ya kawo ka gidan mu bana son in ƙara ganin fuskar ka, ka jefa ni akuba ka touzartani katafi ba na son ganin ka ". Da gaske ba ke son gani na Nusaiba! e ba na son ganin ka ,katafi ina cikin matsala kar ka ƙara jefani a wani "ba zan tafi ba ko da kwana zanyi tun da nazo sai na ganki ". Daukar hijabi na nayi nafita haƙiƙa shine naga ya rame yafita ta hayya cin shi shigo wa nayi da shi na kai shi ɗakin baƙi naje nakawo mishi ruwa da abinci na zauna nayi shiru ko magana ban yi ba ya sha ruwan "yau na tabbata nafice miki daga rai bake son ganina ko kaɗan ko kiyi haƙuri don Allah laifi nane"muddin kana son na haƙura to ka gayamun abu guda uku kuma ya kasance duk gaskiya ce zata fito daga bakin ka ,da gaske ne ranan mahaifin ka ya karɓi wayar ka ko dai ƙarya ne shin ya maganar auren ka da gaske ne ko dai shima ? Shiru yayi ya ɗau lokaci kafun yayi mun magana "kiyi mun afuwa wallahi ƙarya nake yi a lokacin kin dameni da kira ne abu na biyu kuwa maganar auren naga yayi shiru gaskiya ba da gaske bane na shiga rayuwar kine don wata manufa da ban sai gashi Allah yayi miki sakayya ta wani hanyar nasan ke macece mai kirkin gaske sannan ke mai afuwa ne na kamu da son ki sosai a raina wallahi rasa ki tamkar rasa wani ɓangare ne na jiki na ki yafe mun don Allah . dogon numfashi naja "JB nasan tun ba yau ba kai maƙarya cine kai mungu ne gashi karaba ni da martaba na shekara talatin da uku ina killace kai na daga zina sai gashi rana ɗaya ka karabani da komai nawa ka yaudari Aisha ka sa iyayen ta sun tsane ta kasa rashin yadda a tsakanin su wallahi ba zan yafe maka ba ka cuceni koda son ka zai zama ajali na na barka kunna mishi hiran da mukayi da A'isha nayi wannan duk laifin kane ga kuma hoton da muka ɗauka nayi bincike a kanka naga kai ɗin fuska uku gareka ni yanzu an mun miji ɗan uwa nane ba ta yadda zan yi in bijire musu ko da ban son shi ba auren ka babban matsala zai zame mun ina da kudin da zan buɗe maka shago ko dai baka wani jari dan murufawa juna a Siri sai dai kash kazo a wata mahangar bazan iya rayuwa da maƙarya ci ba ban son gaba in na baka dukiya ta mezaka ce mun ba . Hawaye yatayi kuka yake yi kamar ranshi zai fita "wallahi Nusaiba bazakiyi aure ki barni ba kina sona har yanzu don ke ba maƙaryaci bace kamar nizan kashe kashe ki in kashe wanda zaki aura ki zaɓi ɗaya ko soyayya dani ko mutuwar mu wanne kika zaɓa a ciki . Na zaɓi mutuwa da sake tarayya da kai JB Allah ya tsinewa soyayya JB in dai haka soyayyar take meyasa mutane dayawa basuyi mun illar da kayi mun ba meyasa mutane masu daraja naƙisu sabo da kai kafice mana daga gida tarayya ta da kai bata amfane ni da komai ba sai dana sani,na tashi zan bar ɗakin ya riƙe mun hijabi juyowa nayina ɗauke shi da mari gudu biyu .. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki ta 400 wannan asusun Amina maaji account no 4271914914 FCMB sai shedar biya wannan no 08068748984 LAMBA NA ASHIRIN DA BIYU _________Yar uwar ki kuma taya kenan mekike nufi ne don Allah yau she kika cenza daga mai gaskiya kika dawo mai bincike? JB Wannan ba shine abun da zakayi mun magana a kai ba kafara tsarkake zuciyar ka da niya mai kyau kana yaron ka a farkon soyayyar ka ,kasa yaudara da cin mutunci da nuna ,isa kai waye JB yau she kazo duniya waye a tattare da kai dame kake gadara nasaba ko dai kima ko daraja ko kuɗi ko kyau ni har ka,isa ka yaudare ni wallahi tunda na rigaka fitowa duniya dole akwai abun da nasani wanda kai baka sanshi ba. yaushe balagar ka tafara tasiri ina son in gaya maka kafita ta harka ta in ba haka ba zan baka mamaki . a lokacin da narubuta mishi natura mishi yasha ruwan jikin shi ya tsorita da kalamai na sosai a,bubuwan duk sunyi mishi yawa sosai zafi biyu duk a lokaci ɗaya "kiyi haƙuri don Allah wallahi rufe ki danayi ba yana nufin kinyi mun wani abu bane kawai raina ne ya ɓaci yarinyar da a kecewa za,bani ita ce aka ,kawo ta barno wai Musa ba da,ita shine duk abun ya dameni ina kaunar ki,nasan kinyi mun halacci wanda a nasabar ki kinfi ƙarfi na amma kika amince da soyayya da ni har na yaudare ki, ki yafe mun don Allah zan kiyaye zuciya ta ke, take kauna kece wanda zan zauna dake batare da naji ciwon abun da kikayi mun ba kamar yadda,kika faɗa so halitta ne nima na kamu da ƙaunar ki ,ina neman afuwan ki ". Duk ƙarya ce irin na shi nasan waye JB har ga Allah soyayyar shi ta fice mun daga rai ban,iya walaƙanci ba ban kuma tashi naga a nayi ba amma JB ya bani haushi ,narasa dalilin zubar hawaye na tausayi ko dai takaici ne yasani kuka babu wanda ya gane ina kuka abincin dare ko ci banyi ba. Ibrahim yana da wani kunya a duk lokacin da mahaifin shi yake gari ko kulani sosai bayayi mahaifin shi mutum ne mai sauƙin kai duk da mahaifina yana da zafi sosai da safe muka shirya muka nufi asibiti bamu sha wahala ba muka samu doctor Salisu ya karɓe mu hannu biyu bayan tambayoyin da yayi mun da yadda nake ji,in raina ya ɓaci komai nagaya mishi ban ɓoye komai ba yace in raina ya ɓaci wani yanayi nake tsintar kai na bashi amsa nayi da cewa hajijiya shine abu na farko da zan fara ji sai zuciya na za'tayi zafi kamar an zuba ruwan zafi,bugun zuciyar zai ɗingayi a kai a kai shine abun da nake ji wataran kuma ƙafana zai ɗau zafi sosai . "karki damu sannan shawaran da zan baki karkisa tinani dayawa a ranki karkuma ki dinga barin zuciyar ki ,tana tsinkewa ko dai wani abu mai ƙara ki gujewa hakan sannan kidinga kulawa da kanki banda hayaniya da kuma tinani Allah ya baki lafiya". "Amin ya rabbi ". Magani ya rubuta yace a je a siyo a kawo mishi amma yanzu yake so ya nuna mun yadda zansha maganin ya Ibrahim ne yaje ya siyo ya dawo ya nuna mun yadda zan yi amfani da shi munyi mishi godiya sosai a kwai shi da kirki gaskiya in da a ce haka likitoti suke wallahi da babu wanda zai ƙi zuwa asibiti muna iso wa gida naji ya Ibrahim yayi mun magana "kije ki huta sannan kicewa A'isha don Allah karta dameki,da surutu. Shida kanshi ya je ya kawo mana abinci tare mukaci munata hira "Nusaiba gobe muje kiga gidan namu mana in bai yi miki ba sai mu cenza tsarin gidan ko mekika gani "haba komai yayi ba ka nuna mun a waya ba ba sai naje ba Allah ya sanya alkairi. Ki ɗaure kije mana ai zaifi keda kanki ko yaya ne zamu rayu a ciki tare da yaran mu ,muba su kulawa in sha Allahu baki da mijin da yafini kinga jibi zaki koma "haka ne Allah ya kaimu goben yasa muna da rai . Amin Mata na Murmushi nayi wato shifa jiyake har an bashi ni,shi yasa yake ta wani shiri kallon shi nakeyi na zuba mishi ido ne kawai . Washegari Muka je na duba gidan ya tsaru sosai gaskiya gida ne wanda,duk ma,abocin rayuwa a gidan sai dai yace Alhamdulillah don komai yazo haƙiƙa Ibrahim ya na sona son da bazan kwatanta shi da komai ba ya nuna mun ƙauna fiye da komai daɗi yake ji "me kike so a ƙara kinga wancan ɗakin shine na baƙi mata ga cen na maza kuma sai kuma mekike so a yi bayan wannan ?. Ba komai yayi Allah yasa rai ya mora Amin nagode Shirin tafiya damaturu nake yi don komawa gun aiki in an haɗa da rashin lafiyar da nayi zatakai kusan sati biyu ranan jumma,a zan dawo wani irin tsara ba da Ibrahim ya siyamun kamar bada kuɗi ya siya ba ya kashe kuɗi ina mamakin yadda Ibrahim yake faranta mun abun yana sani da muwa ƙarfa shima in zo in rasa shi a kaɗan har nafara koyawa zuciya ta son shi Daddy shima ya siya mun tsara ba tare da bani kuɗi masu yawan gaske a na gobe zan tafi unguwar su JB naje nayi siyayya mai yawa nace a kaiwa maman shi nabawa yara nace sukai in an tambaye su ,suce wata ce daga damaturu ,tace su kawo na sallame su kafun su fitoh na wuce nikuma. Ya Ibrahim ne ya kawo mu har gida hakiƙa nayi kewar su Inna sosai musamman Aisha jin ta nake tamkar wata ƙawata tana da saurin fahimtar abu daga ne matsalan mutum a tattare da shi Hajiya tayi kewa ta duk da bawa ni hira mukeyi da ita ba naga farin ciki a tattare da fuskokin ,yaran gidan mu,abun duk ya ɗaure mun kai bayan Abba na ya dawo naje dan yi mishi sannu da zuwa "Abba ya gida "lafiya uwata kindawo sannu da zuwa sai kuma kukaji an gama komai da Ibrahim ko Allah ya miki albarka bazan taɓa zaɓa miki abun da zai cutar da ke ba in sha Allahu Ibrahim sai ma yafi Muhammad sonki zai kula da ke koda bayan bana reye zai baki duk wani jin daɗi karki da mu ,amma baza mu zuba miki ido kina abun da ranki ya ke so ba munba ki kwanaki har ya shuɗe banji kince ko mai ba shirun ki ya tabbatar mun da baki da kowa a ƙasa shiyasa kikayi shi". Na shiga ruɗa ni da far gaba na rikice yanzu kenan JB baza muyi zaman aure da shi ba kenan shikenan a nan soyayyar ta tsaya kenan ya zanyi dole in yi duk yadda zan yi ban san me yasa nagagara sa son ya Ibrahim a raina hawaye ne ya ta kwaran ya daga ido na juyo wa Abba yayi "a kwai matsala ne uwa ta ? girgiza kaina nayi tashi nayi na nufi ɗaƙi na a she ya Ibrahim duk ya na jin mu ,shiru yayi ya biyo nI zai yi magana na ɗaga mishi hannu . Bana son jin komai daga gareka bayan duk kai ne ka tarwatsa komai Meya sa ya Ibrahim baka sanar da niba bayan kasan ko mai don Allah ka koma barno gobe in zuciya ta tasamu nutsuwa zan kira ka don Allah ka tafi jin muryan Hajiya nayi "don ubanki babu in da zaije meyasa kike haka yau Ibrahim ɗinne kike kora daga gidan ku don baki da kirki kisani in kin walaƙanta Ibrahim ba shi kika walaƙanta ba nine sannan nasan babu ,abun da kika sa ,a ranki tun muna tausayin,ki yanzu mun dawo daga rakiyar ki sannan in an yi auren ki kashe shi mutumiyar ban za kawai ke uban wa ,kika fi waya gaya miki ana haka . Shiru ya Ibrahim yayi jin mu kawai ya keyi "Hajiya a bita a hankali don Allah kar ciwon ta ya tashi yanzu an ba mu dokoki wajen kulawa da lafiyan ta,kuyi haƙuri zai wuce wataran . Duk kansu ficewa sukayi daga ɗakin waya ta na ɗauko naga mutane da yawa sun Kirani har da JB ko kiran shi banyi ba ina riƙe da wayar naga ya sake kira ɗauka nayi "don Allah ki ɗaure ki dawo yadda kike don ina cutuwa yau she kika je barno ko gaya mun ba kiyi ba ? Jiya na dawo sati na biyu a cen lafiya kuwa kake tambaya na me ya faru dole ne in zanyi tafiya sai na gaya maka me ya faru . An kai saƙo gidan mu, sannan an ce daga damaturu yaran kuma sunce wata ce na tabbata kece don yanzu ko mai nawa kin sani shi yasa amma hidimar tayi yawa ga nawa har da na iyaye na sun gode wallahi da,ina nan babu wanda zai karba . Fa shewa da kuka nayi yanzu shikenan hankalin ka, ya kwanta kenan zan yi aure kamar yadda ka faɗa a baya in na samu miji in yi aure jiran ka gaibu ne zan yi tunda haka ,kace sannan wanda zan aura ya haɗa duk wani abu da nake buƙata hankali nasaba kima daraja babu ,abun da bai haɗa ba daman na gaya maka wataran zakaji abun da zai tarwa tsa,maka tunani . Jinayi ya ce na shiga uku Nusaiba wallahi ba zakiyi aure ki barni ina waje ba ban shirya rabuwa da ke ba ko da rai na zaifi ta,ki tausaya mun karki gujeni wallahi na dai na duk abun da nake yi kiyi mun afuwa kuka ya keyi kamar an aiko mishi da mutuwa . Ikon Allah Yau JB ne ke kuka ina gadaran ina rashin mutunci ,ina jiji da kanshi tabbas in naga ba,ayi auren nan ba to ɗayan mu ya mutu, taya zan yi rayuwa da mutumin da babu son shi a raina amma zan yi ko da zan mutu koda shine zai zama,abu mafi muni a gareni ban taɓa ganin fishin Hajiya ba sai a kan auren Ibrahim ya JB zai yi ya zai yi rayuwa ba tare da niba ban son wani hali yake ba a yanzu na nafi son yaga mata suna da mutunci kar ya mana kuɗin goro nafi so ko da rabuwa mukayi yaga wasu matan da mutunci yau sanadin ƙadddara ya raba mu. Jinayi ya Ibrahim ya kira sunana "Nusy kiyi haƙuri karki zargeni wajen an gama ko mai dani wallahi bansan ko mai ba ,ni ce mun a kayi in ci gaba da shiri wallahi bansan ko mai ba tunda bake ƙauna na zanyi nesa da ke har sai kin koyi sona kafun zan bari a yi auren in kuma kika ce bake suna zan tayaki neman wanda kike so don naga a lama a kwai wani a ranki ". Zanyi magana ya dakatar dani [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki ta 400 wannan asusun Amina maaji Accounts no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan ta wannan number no 08068748984 LAMBA NA ASHIRIN DA HUƊU Kowa ya watse aka bar mu mu kaɗai. Duk wani lallashi, lallami gami da kwantar da muryar da ya yi wajen ban haƙuri bai sanya ni tsagaita da kukan da nake yi da dukkan ƙarfina ba. Cikin zuciyata ji nake yi tamkar ana sanya tsinin bakin mashi ana caccaka mini saboda tsananin azabar zogin da yake yi mini. "Duk wannan kukan na menene Surayya? Don Allah ki yi haƙuri ya isa hakan nan, kar ki jawa kanki wani ciwon na daban". Yanda ya yi maganar kaɗai ya isa ya bayyanar da irin tsananin damuwa da tashin hankalin dake tattare a dunƙule a cikin ƙirjinsa. Ya zube akan gwiwoyinsa a gaba tare da haɗe dukkan hannayensa biyu waje guda alamar roƙo"ko don ni don Allah ki yi haƙuri ku tsagaita wannan kukan, wallahi duk wani ɗigon ruwan hawayen da ya zuba daga idonki. Ji nake yi tamkar tafashashshen ruwan dalma ake watsa min". Na ɗago rinannun idanuna na zube su akan fuskarsa da ya yi kalan tausayi, ya ɗaga mini kansa alamar tabbatar mini da gaskiyar kalaman da ya furta. A bayyane na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina tausayin kaina da kuma hashashen irin rayuwar da zan yi a cikin gidan sa da soyayyar wani a cikin raina. Dole na tsagaita don ganin irin damuwar da ya shiga, ya yi ta zabga mini addu'o'i da alƙawarin ƙawata rayuwata da farin ciki da jin daɗi. Washe gari kafin na tashi na iske ya kammala komai, wanka kawai na yi na shirya don gabaɗaya bana jin daɗin jikina. Ya yi mana karin kumallo na ɗan cakala bisa takura mini da ya yi da marairaicewa. Na zauna a falon shi kuma ya shiga yin wanka, ina ƙarewa tsarin falon kallo. Ya ƙawatu sosai domin irin design ɗin da ya turo mini na zaɓa shi aka yi kwabo da kwabo babu abinda aka canja. Sai a lokacin na tuna da wayata da rabo na da ita tun ranar jiya, na tashi na koma ɗaki ina duba inda Sakina ta ajiye mini ita. A cikin jakata na same ta na ɗauka na kunna, take saƙonni suka fara shigo da jerin ƙiraye ƙiraye da suka zama missed call ana bani bayanan su ta saƙo. Ƙira bakwai rigis Suraj ya yi ga kuma saƙonsa da na latsa kansa na buɗe jikina yana rawa. ```"Na san ni har yanzu mai laifi ne a wajen ki. Amma na roƙe ki da girman wanda yake yi mana ruwa da ƙanƙara kar ji ba wa ko wani ɗa namiji damar kusantar ki Surayya. Wallahi ba zan iya jurewa domin zuciyata zata iya bugawa ki riƙe min amanar kanki, ko ba daɗe ko ba ji ma sai na cika alƙawarin da na yiwa kaina na auren ki".``` Take na ji gabaɗaya jikina ya soma rawa tamkar wacce ake jonawa wutar lantarki, zuffa ya fara tsatstsafowa daga jikina. Ganin ina gab da faɗuwa ya sanya ni yin zaman dirshan a ƙasa dafe da kaina da nake jin tamkar zai rabe gida biyu saboda tsananin sarawan da yake yi mini kwatankwacin irin bugun da maƙeri yake yiwa ƙarfe. Na tsurawa saƙon kallon ina ƙara karantawa wasu hawaye suna zarya a bisa a kuncina. Tabbas so bai yi mini adalci ba domin ni a gare ni masifa da bala'i ya zame saɓanin wasu da yake zamowa silar farin ciki da annuri akan fuskokinsu. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u!". Na furta a bayyane ina cije leɓena tare da lumshe idanuna, me ye mafita a gare ni? A ko yaushe Suraj zuciyata take hango mini a mahangar dacewa da ni ta kowacce fuska. Jin kamar za a shigo ɗakin ya sa ni saurin miƙewa na mayar da wayar ciki jakar da na ɗauko ta, na nufi banɗaki na wanke fuskana na fito. Yana tsaye jikin ƙofar ɗakin ya haɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa tare da zubo mini idanu. Har na iso gabansa ni yake na yarfa hannuna a fuskar tare da ɗage masa idona ɗaya alamar lafiya. Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana gyara tsayiwarsa"godewa kawai nake yi da ya mallaka min ke a matsayi mata, wallahi Surayya ina son ki irin son da babu wasu kalmomin da zasu wadatar wajen furta miki girman su ba. Na yi alƙawarin gusar miki da duk damuwarki ta hanyar ƙawata duniyarki da farin ciki marar yankewa". Tun da ya fara maganar na yi ƙasa da kaina ban ɗago sai da na ji hannunsa a jikina. Ya tallafo fuskana idanunmu suka sarƙafe cikin na juna, tabbas na hangi tausayi da tsantsar soyayyata a cikin idanunsa sai dai soyayyar Suraj ta yi rassa a cikin zuciyata da tuge ta dai-dai yake da datse mini numfashina a duniya. Ban ankara ba na ji hannunsa ya zame zuwa saman kafaɗata, da sauri na ture ina ɗan ja da baya. Ya nufo inda nake gadan gadan ya jawo ni jikinsa yana shafa fuskata. Roƙon da Suraj ya yi mini akan na riƙe masa amanar kaina kar ba ba wa ko wani ɗa namiji damar kusanta ta, ya fara dawo mini cikin kwanyata tiryan tiryan. Take na fara kiciniyar raba jikina da nashi, ya riƙe ni gam na kasa ƙwacan kaina. Dole na sadadu ina sakin hawayen takaicin da ya turnuƙe mini raina. Ya ɗago kaina yana kallon fuskana da hawaye ya gama ɓata shi"lafiya? Wannan kukan fa na menene?". Ban iya cewa dashi komai ba, ba samu na zame jikina daga nashi, na koma gefe ina sakin wasu sabbin hawayen. "Don Allah ki sanar da ni wai me yake faruwa ne?". Na shiga saƙe saƙen abinda zan faɗa masa domin ba kaɗan ba ya yi matuƙar kiɗimewa. Ganin yana matsowa inda nake kuma na tabbatar inda ya iso ni dole sai ya taɓa ni abinda na tsana kenan a yanzu fiye da komai. Na yi saurin faɗin"tsoro nake ji". "Tsoron meye?". "Tsoron gidan ba zan iya zama a cikinsa ni ɗaya ba". Ya yi dariya"to ai ba ke ɗaya za ki zauna ba. Ba ga ni ba tare zamu zauna" . Na yi masa shuru da akan ya bashi damar ɗaurawa"ki daina damuwa za ki saba kin ji? Kema makaranta nan da ɗan kwanaki za ki fara fita, zamu fita tare mu kuma ce dawo tare kin ga ba ke ɗaya za ki zauna ba". Kaina kawai na sama damar ɗaga masa muka fito falo, gabaɗaya a takure nake domin ya kasa motsawa ko nan da can daga inda nake zaune. Sai wajajen ƙarfe goma sha ɗaya su Anty Safiya, ƙawayena da sauran dangi suka zo. Na ji daɗin zuwan su ba don komai sai don gajiyan da nayi dashi. Tare muka wuni dasu har sai magrib ba sannan suka tafi bayan su ƙara yi mini nasiha da bani wasu shawarwarin da zai taimaki duk wasu ma'aurata. Wajen gudanar da zamantakewar aurensu ciki lafiya baka lafiya, sai dai a gare ni abun ya sha bambam domin idan ya shiga ta wannan kunnen babu ɓata lokaci yake ficewa ta ɗayan. Sosai Sakina ta yi ta kwantar mini da hankali da karanto min tari kyawawan halayyan yaya Sufyan da ni gabaɗaya yanzu bana ganin su. Ban sanar da ita komai game da saƙon da Suraj ta aiko mini ba, domin a wannan karon na zaɓi na kashi a cikina ko da kuwa ba zai yi mini maganin yunwa ba . [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA NA ASHIRIN DA BIYAR Har na cika sati guda cif a cikin gidan Suraj bai taɓa kuskurewa wata rana ɗaya bai turo mini saƙon ba. Tsaf nake karanta su sannan na zauna na yi zaman haddan su daki-daki a cikin kwanyata. Tun da aka kawo ni cikin gidan bamu taɓa kwana ɗaki ɗaya da yaya Sufyan ba balle mu haɗa shimfiɗa. Yana ɗakinsa ina nawa, domin na roƙi alfarmar masa kan cewar ban saba kwana da mutum ba ko a gida shima ya san hakan, kuma yanzu bani da tsarki don haka sai na sama tsarki sannan zan sanar dashi. Bai nuna mini komai a fuskarsa ba amma na san tabbas sai ya yi jinyar zuciyarsa. Kafin na tashi ya kammala karin kumallo tsaf wanka kawai zan yi na ci, ya shirya ya fice makaranta idan yana da lecture ɗin safe da zai yi, idan kuwa babu sam baya gusawa daga inda nake. Zaune muke a falo a zahiri idanuna suna akan akwatin talabijin ɗin da yake aiki, amma a baɗili na yi zurfi cikin tafkin tunanin da na faɗa. "Madam lafiya?". Ya faɗa yana ɗage mini ido ɗaya, na yi gefe da kaina"lafiya ƙalau". "Sati za ki fara fita makaranta, zan kai ki sannan kuma na ɗauko ki. Za ki zame min garkuwa ga 'yan matan da suke kawo min hari". Na yi saurin kallonsa ya sakar mini da laulansan murmushi, na taɓe baki game da faɗin"har wani hari 'yan mata suke kawo maka?". "Ƙwarai kuwa kuma har da ƙawayenki na cikin makarantar". Na gwalalo idanuna waje"tab ai kuwa iska yana wahalar da mai kayan kara". Murmushi mai sauti ya saka kafin ya furta"ke ko irin kishin nan na mata akan mazajen su bakya yi?". Cike da ƙosawa da jin zantukan sa na ce"akan me zan yi kishi akan kan, bayan na san ka ɗin mijin mace huɗu ne. Ai abunda ake so shi ake kishinsa kai kuwa na sa.....". Tun kafin na ƙarisa dire zancen da na ɗauko, ya dakatar da ni ta hanyar ɗaura yatsarsa akan leɓena yana faɗin"shit!. Ko da addini ya bani damar auren mata huɗu, to ni ɗin mijinki ne ke kaɗai daga ke na rufe ƙofa. Wallahi ba zan taɓa haɗa soyayyarki da na wata ba a cikin zuciyata ke kaɗai ce kuma da ke kaɗai zan rayu". Na kasa cewa komai illa ƙasa da kaina da na yi, kunyar ɗagowa na haɗa ido dashi nake yi saboda takaicin zancen da na furta da nake yi. Tabbas baki ba zai gajiya wajen furta cewar yaya Sufyan ya fita daban a cikin ragowar jinsinsa maza ba, ya daɗe yana nuna mini tsantsar soyayyar da babu tsirki a cikin ta. Yana nuna mini kulawa matuƙar da ban zan iya butulce masa ba. Sai dai haƙiƙa na ƙara yarda cewar duk wanda ya yi nisa a soyayya bata jin ƙirji domin tamkar kifiyar ajali ce da tsilke baya tare ta. "Ka yi haƙuri". Ya sa hannunsa ya tallafo haɓata"ba ki aikata min laifin komai ba 'yan matana". Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya da nufin furta maganar dake baki, ya tari numfashina tare da sauya akalan zancen gabaɗaya ya koma wani daban. Na yi artabu da zuciya ta hanyar amfani da ƙarfi wajen tusa soyayya yaya Sufyan a cikin ta, amma a banza wai an muntsine kakkaura. Ina son na ga nima ina nuna masa kulawa, taraiyaya da kuma soyayya kamar yanda yake nuna mini amma bana iya yin hakan. Da zaran na yi ƙudurin kyautata masa sai na tuna da Suraj da kuma roƙon da ya yi mini, bai damu da auren da na yi ba shi dai kawai burinsa na riƙe masa mutuncina. Tare da tabbatar mini cewar zai cika alƙawarin mallaka ta komai daren daɗewa. Bani da aiki da zaran yaya Sufyan ya fita face ɗaukar wayata ina karanta saƙon Suraj, duk da ban taɓa mayar masa da amsa ba amma kalamansa suna yin tasiri da cikin jikina. Ina jin ɗumin hawayen da suka bin kuncina, ban yi wani yunƙurin kawar da su ba domin a yanzu fitar su ne kawai ke samar mini da nutsuwa a sashin ruhina. "Surayya". Na ji an furta kalmar sunana tare da fizge wayar dake hannuna. Na ɗago kaina da sauri cike da zaƙuwar son ganin wanda ya aikata hakan a gare ni. Sakina ce tsaye a kaina ta tsura mini idanu. Ban damu da yanayin fuskarta ba kamar yanda ban ji ɗar da ganin ta ba na ce"me ye haka? Ba ni wayata malama". Na ƙarkare zancen ina miƙewa tsaye. "Me ye haka? Daman abinda kike aikatawa kenan da auren ki Surayya?". Ban tanka mata ba na miƙa hannuna na kuma cewa"ba ni wayata". "Ba zan bayar ba, ba zan bayar ba. Har sai kin sanar da ni yaushe kika yi wannan lalacewar?. Ina hankali da tunaninki suka yi ƙaura suka tare da kike aikata wannan jahilcin da aurenk?". Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina koma na zauna daga inda na tashi, na fashe da wani matsanancin kuka mai taɓa zuciya da kai tsaye yake fitowa daga ƙasan raina. Sai da ta zauna kusa da ni kana ta cigaba da"sai yaushe za ki mance da Suraj? Sai yaushe za ki bambamce tsakanin masoyin ƙwarai da kuma wanda yake buƙatar a lokacin da yake nashi buƙatatun suka taso? . Sai yaushe za ki gane cewar Allah ya yi miki babbar kyauta da ya mallaka miki mutum irin yaya Sufyan, wallahi Surayya na rantse miki har da Sarkin da bashi da abokin tarayya, wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. A zamanin da muke cikinsa yanzu ire-iren su yaya Sufyan ƙalilan ne sukar rage, kuma ke kin sama ɗaya daga cikin su amma kuma nema yin wasa da damar ki". Shuru na yi mata hakan ya bata damar cigaba da faɗin"yanzu ke fa matar aure ce kin san hukuncin macen da take da aure kuma tana tunanin wani a cikin ranta. Ki cire Suraj a cikin ranki ki sanya yaya Sufyan wallahi na tabbatar miki sai ya maida ke sauraniya a dukkan nahiya". "Abinda nake ƙoƙarin yi kenan Sakina". "Ba ki ɗauko hanyar yin hakan ba sam. Da kin ƙudurce a cikin ranki za ki hakan da ba zo na iske ki kin kafa waya a gaba kina karanta banzayen saƙonninsa masu cike da kalaman ƙarya da yaudara ki na kuka ba. Allah ya gani na yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na jawo ki daga faɗawa halakan da kike son jefa kanki". Wasu hawayen masu zafi suka kwaranyo mini"ba za ki gane bane. Ba za ki gane yanda nake ji a cikin raina bane. A tunaninki a son raina nake yi wannan abun?. Ko kina tunanin nima bana son na yi rayuwar aure kamar ko wacce mace cikin kwanciyar hankali da mijinta da son farantawa juna?". Sai da na numfasa na ɗaura da"nima da akwai zuciya a cikin ƙirjina, ni na da mutum ce mai 'yancin zaɓar abinda nake ganin ya dace da rayuwata. An tauye mini haƙƙina ta hanyar fifita dacewar yaya Sufyan da ni ba tare da koda da rana ɗaya an tuntunɓe da suna jin ta bakina ko ina son shi ko akasin hakan ba". Na lura ta fara fusata domin zance kaɗan wani lokacin yake sanya ta tunzura, a lokuta da dama na fita haƙuri da kawar da kai ga wasu abubuwan. "An tauye miki haƙƙi fa kika ce?. Sai yanzu na tabbatar da cewar lalle Surayya ba ki da hankali wallahi kin zauce. Ba zan ƙara yi magana akan wannan lamarin ba ki yi duk abinda kike ganin ya dace Allah ya ba ki sa'a. Amma ina tabbatar miki da cewar idan kika yi ganganci kika rasa yaya Sufyan za ki nadama mai tarin yawa a rayuwarki". A kufule na ce"ko yaushe zancen ki idan na rasa shi zan yi nadama zan yi nadama. Shin ko sau ɗaya ba ki taɓa yin tunanin jin yanda nake ji a cikin raina ba?. Zafi da zogi nake ji suna sukar zuciyata. Na zaɓi na rasa komai da kowa akan wannan lamarin, in yaso ke sai ki auri yaya Sufyan ɗin tunda a idanunki babu mutumin kirki a kaf duniyar nan kamar sa". Duk muka miƙe tsaye ni da ita muna kallon juna, har yanzu hawaye yana zuba daga idona. Na bude baki da nufin cigaba da amayar da zancen da yake kartan zuciyata, na hangi yaya Sufyan tsaye a ƙofar falon ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa tare da kafe mu da idanu. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA NA ASHIRIN DA SHIDA Ina wani irin huci na juya na shige ɗaki tare da murza key a ƙofar, na bar su tsaye a wajen. Ba damuwata yaya Sufyan ya ji ya abinda na furta ba domin ba shi ne a gabana ba a halin yanzu. Ina shiga na zube akan gado ina sakin wani gigitaccen kuka mai matuƙar ƙarfi, ina yi ina taune naman bakina tamkar ba jikina ba. Sosai da na yi kukan sai da na ji jikina gabaɗaya ya mutu ga wani zazzaɓin da ya rufe ni sannan na tsagaita. Ba domin na ci sauƙin zogin da nake ji a cikin zuciyata ba. A hankali kunnuwana suke jiyo mini ana bubbuga ƙofar ɗakin tare da ƙiran sunana. Jin muryan yaya Sufyan ne ya sanya ni tsintar kaina cikin faɗuwar gaban da ban san dalilinsa. Na san ko takardan saki ya damƙa mini ba ni da damuwa, to amma menene dalilin tsintar kaina a cikin wannan yanayi?. Take zuciyata da take bugawa a raunane ta bani amsa da faɗin Surayya wani fuskar ya fi ƙarfin mari. "Don Allah ki buɗe ƙofar nan na roƙe ki". Ya furta muryarsa a sanyaye, ko motsawa daga inda nake kwance ban yi ba. Ya cigaba da faɗin"ina son magana ki taimaka ki buɗe ƙofar nan". Shuru na yi tamkar bana jin abinda yake faɗi. Ina da tabbacin idan ba ni na tashi na buɗe ƙofar ba babu ta yanda zai iya shigowa ɗakin. Irin ƙofar da idan aka rufe ta ta cikin to ba za a iya buɗe ta ta waje ba. "Surayyaaaa". Ya furta kalmar sunan cikin wani irin muryar da sam ban san ya mallake ta ba. Wani yar na ji a jikina da hakan ya tilasta mini runtse idanuna da ƙarfi wasu hawaye suna gangarowa daga koramar idanuna. Babu irin magiya da roƙon da bai yi gare ni ba, ƙiran wayata kuwa ya yi yafi a irga amma na kasa cewa dashi komai. Haka har aka yi ƙiran sallan zuhr na miƙe ina jin wani jiri ya ɗeba ta na shiga banɗaki na yi alwala, a zaune na yi sallan saboda rashin ƙarfin da nake ji bani dashi ba. Na kasa furta komai yayin da na ɗaga hannayena sama, illa hawayen da nake yi. Na tabbatar da cewar ubangijina shi kaɗai ka san irin radaɗin da nake ji a cikin ƙalbina kuma shi kaɗai zai iya kawo mini sauƙi da mafita daga tsaka mai wuyar da na faɗa ba. Ina shafa addu'ar na ji yaya Sufyan yana buga ƙofar, yanda ya kwantar da murya ya sa naji kifiyar tausayinta ta caki ƙirjina. Ina tafiya ina dafe bango hakan na miƙe na buɗe masa ƙofar. Ban yarda na ga inda yake ba na juya ya yi saurin riƙo ni na faɗa jikinsa. "Me yake faru? Me yake faruwa Surayya ki sanar da ni. Sakina ta tafi bata ce min komai ba". Ya ƙare zancen yana jijjiga na matse idanuna gam. Cikin sarƙafewa harshe na furta"babu abinda ya faru face abinda ka ji". "Me ye kike nufi?". Sai a lokacin na yi nasarar kwace kaina daga riƙon da ya yi mini, na koma cikin ɗakin na zauna a ƙasa dirshan. Ya tako ya zauna a gabana kamar mai ɗaukar karatu ya kafe ni da ido"tun kuna ƙanana ku ke tare da Sakina, babu wanda bai san ku a matsayi ƙawaye ba daga danginmu har na ta, kowa ya shaida irin yanda kuke kulawa da juna da ɗaukar matsala da damuwar ɗaya tamkar ta ɗayan. Na yi mamakin ganin kuna cacar baki da ita a yau me ya faru?". Na ɗago idanuna da suka kumbura tsimtim na ce"kana nufin bata sanar da kai komai ba har ta bar cikin gidan nan?". "Ƙwarai kuwa". Na sauƙe ɓoyayyiyar ajiyar zuciya tare da faɗawan tunanin dalilin da ya hana Sakina sanar dashi komai duk da fusatan da tayi game da lamarin. Sautin muryarsa da suka yi dirar mikiya a na'urar jiyo mini sauti ya katse mini zancen zucin da nake yi. "Me yake faruwa? Don na yi imanin ba ƙaramin abu bane zai sanya ku mayarwa irin wannan martanin da zafafan kalamai ". Na kasa cewa komai sai da ya ƙara maimaita tambayar a karo na biyu. Haka siddan na tsinci kaina da sakin wasu hawayen da na kasa tantance dalilin zubar su. Shin na halaccin da Sakina ta yi mini wajen ganin ta ƙara zuba ƙasa a ramin da na haƙa na ɓoye sirrina bane, ko kuma na takaicin ƙaryar da zuciyata take shirya mini ne na gaza ganewa. Cikin rawar murya na furta"zuciyata ce ta kasa daurewa na kuma gaza jure zantukan da take yi mini a kanka. Na ga take taken ta kamar sonka take yi domin kullum cikin yi mini zancenka take yi da kuma yabon kyawawan halayenka tare da addu'ar Allah ya mallaka mata miji irin ka. Ko yau ma da tazo zancen ta yi mini kenan na kasa daurewa har ka shigo ka ji ina furta mata idan sonka take yi ta aure ka tunda a idanunta babu mutumin kirki a kaf duniya nan kamar k....". Tun kafin na dire zancen ya katse ni"innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Surayya kika faɗa mata haka"?. Na gyaɗa masa kaina, ya cigaba da cewa"Sakina ta wuce haka a wajen ki, na tabbatar tana ɗaya daga cikin masoyanki masu ƙaunar ganin farin cikinki. Ta taimaka min sosai wajen samun soyayyarki bana tunanin idan tana yi min kallo so zata yi min wannan taimako. Surayya idan hankali ya gushe hankali ake sawa a nemo shi, shi harshe bashi da ƙashi amma yana da dafi sosai". Sosai na fashe da wani irin kuka har jikina rawa yake yi. "Subhallahi lafiya?". "Kai ma kenan goyan bayan ta kake yi?". Na faɗa ina ƙoƙarin miƙewa jirin da yake walagigi da na ya dawo da ni na zauna. Ya riƙo hannuna na fizge. "Ba ina goyan bayan ta bane face ina sanar dake gaskiyar da idanunki suka makance suka kasa gano miki su. Kin san ina sonki wallahi ba zan taɓa fifita wata 'ya mace akan ki ba ki yi haƙuri kin ji?". Banza na yi dashi, rashin kula shin da nayi bai sanya shi dakatawa daga furta mini kalaman ban haƙuri ba tamkar shi ya aikata mini laifin. Bai tsagaita ba har da ya yi nasarar sanya zuciyata da take tafasa lafawa. A karo na farko a rayuwarta da na roƙo Allah idan son Suraj ba alkhairi bane a gare ni Allah ya cire mini shi har daga zuciyata gabaɗaya. Ban taɓan jin tausayin yaya Sufyan ba kamar yau domin da farko na yi tunanin cewar ya ji duk tattaunawar da muka yi da Sakina ashe har yanzu lalume yake yi a cikin duhu. Har na fara fita makaranta ban nema Sakina ba kamar yanda ita ma bata nema ni, sannu kawai shi yake shiga tsakanina da ita ko mun haɗu a cikin makarantar. Duk wasu abubuwan da muke yi tare bamu daina ba magana ce dai kawai bana yi, hakan ya sanya mutane da yawa basu gano taskaron da ya gifta a tsakanin amintar mu ba. Wata ranar asabar bayan yaya Sufyan ya dawo daga lecture ɗin ƙarfe goma sha ɗayan da yake dashi ya ce na shirya zamu je gidan su Sakina. Direwa na yi akan babu inda za ni tun ita ma har yanzu ba ta tako tazo inda nake ba to ban ga dalilin da zai na kwashe ƙafafuna nake inda take ba. Sai da na ya nuna mini ɓacin ran da ban taɓa gani akan fuskarsa ba sannan na shirya muka je. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984 LAMBA TA ASHIRIN DA BAKWAI Yau Nusaiba ni kika mara sabo da kin tsane ni kaicun wannan ranan nasan nayi miki laifi ki yafe mun don girman Allah zan gyara kuskure na kiyi mun afuwa . "Wallahi JB muddin baka fita daga rayuwa ta ba zan baka mamaki sannan kace zaka kashe mu ,duk kan mu sannan ka kashe kanka ina jiran wannan ranan fisge hijabi na nayi nafice ko wai-wayo wa banyi ba haka na nufi ɗaki na na kwanta ina fitar da numfashi mai wahala jin wani yanayi sai da gaba na ya faɗi nayi ƙoƙarin dai dai ta numfashi na amma ina bazan iya ba ido na yafara juyawa baki na yafara kumfa bugun numfashi na da sauri yake yi tsintar kaina nayi a asibiti a lokacin kwana na uku ina kwance wanda duk wani masoyi na ya fidda ran zan rayu duba wa nayi naga banga Hajiya ba sai ƙanwar Abba na takaici duk ya cika ni yanzu daman da gaske Hajiya take yi wani likita ne da ban ba doctor Ibrahim ba shima yanzu fushi yake dani kenan. Jin wani yayi mun magana "kin tashi sannu Allah ya baki lafiya irin wannan rashin lafiyar taki sai wanda zai,iya fatan mudai Allah ya baki lafiya tambaya na ina ne yake mun ciwo nace babu Anty mariya ce ta matso in da nake tayi mun sannu da jiki na amsa "Anty ina Hajiya ban ganta ba ?"kiyi haƙuri tayi fushi da ke a kan hakan ne ma suka samu matsala da Abban ki muma kan mu bamu ji daɗin hakan ba Allah ya baki lafiya ". Kuka nakeyi sosai Anty mariya tabani haƙuri "amma taya Hajiya tana fushi da ni zan samu sauƙi a zuciya ta ya zanyi yadda na keji sai nake ganin kamar ba zan rayu ba fatana Hajiya ta yafe mun wallahi zan auri ya Ibrahim sannan zan zauna da shi ko dani nawa farin cikin zai dirƙushe ina son ganin Abba na don Allah a kira mun shi zamuyi magana jikin Anty mariya yayi sanyi kiran Abba tayi juyowar da zatayi ganin ina aman jini numfashi na ina ta kokuwa da shi ban ƙara sanin in da hankalina ya ke ba Sai da nayi kwana hudu kafun na dawo hankalina karan nan har Abba na ya fitar da tsan mani zan rayu narame sati ɗaya nayi ina kwance kamar wata nayi ,karan nan Hajiya tazo duba ni amma an ce mun bata jima ba na gaya wa Abba a daura auren kawai ko da ina Asibiti da ya tambayi ya Ibrahim ya ce a dakata a bari sai na warke nasan fushi yayi don bai Kirani ba sannan bai zo ba sai da Abba na ya ce ya na son ganin shi kafun ya zo shi yaje du bani a asibiti ko minti talatin bai yi ba ya dawo . Zuciya ta a tunku she take matsaloli sunyi mun yawa in na tina irin ƙaryan da JB yayi mun ji nake kamar in haɗiye rai na duniya yanzu ba yadda masoyi yaci amanar masoyiyar shi ƙawa taci amanar ƙawar ta duniya ke nan a ranan da za,a sallame ni a ranan ya Ibrahim ya bar damaturu . Lokacin da zamu bar asibitin a lokacin naga doctor in badan na gan shi sannan mun haɗa ido hudu ba bai yi niyar ƙariso wa ba kunya yaji ya kari so "ya jikin har an sallame ku kenan ? "e doctor daman kana nan na ɗauka ba kanan ne shiya sa Allah sarki "Nusaiba ba na son in ƙarasa bata miki rai shine nace doctor Garba ya duba ki . Kayi fushi dai kawai taya zakace baza ka duba ni ba tunda ka gaji nima bazamu ƙara zuwa asibitin nan ba wani zamu koma kallon da yake mun kallo ne na wasu abubuwa da ban nasan waye doctor tunda yace har sun samu saɓani da matar shi a kaina haƙiƙa so mungun abu ne na tabbata da son da doctor ya ke mun da na ya Ibrahim shine asalin so amma in a kace JB yazo a wata mahangar don son shi ya zame mun illa ya cutar ni sallama yayi man ko kallo na ba yason yi jan motar mu,mukayi muka bar asibitin . Sati na ɗaya da warke wa,ina kwance naga sai kirana a ke da wani number naƙi dauƙa cen wani zuciyar ta bani umarni da in ɗauka na ɗauƙa bayan sallama da nayi a gigice a ka amsa "a kwai wani ne yayi hatsari a mota duka yan cikin motar Allah ya musu rasuwa sai shi ƙadai ne ya rage a hanyar su ta zuwa Biu wayar shi babu kati shine muka kiraki don number ki ne yafi yawa wajen kiranki ". A gigice nace malam ka gaya mun sunan shi da number wayar yace mun bai san ya zai yi ba ba kati a wayar gaya mishi wasu number da zai sa number mai shi zai fito a lokacin da yake gaya mun number na gigice ba kowa bane illa JB sake kiran mutumin nayi nace ya duba zai ga an rubuta my mum ya kira yace mun baya shiga ,na rasa wazan kira A'isha na kira nace bata da number abokin JB ko dai na yan gidan su tace bata da shi amma bari taje shagon shi ko zata,ga wani a shagon nace tayi sauri don babu nisa tsakanin su. [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam LAMBA NA ASHIRIN DA TAKWAS Jiran kiran Aisha nakeyi ina ta zullumi sai naga kiranta ya shigo waya ta da sauri na ɗauƙa take sanar mun babu kowa a shagon ita kuma tana tsoron ta gayawa wani tunda babu komai a tsakaninsu yanzu tambayar ta nayi wata gani a bakin shagon tace wani makwabcin shine mai sai da magani nace ta bashi wayar sanar da shi nayi sannan nace ya faɗa a gidan su an kira number mahaifiyar shi a kashe ya ce to . Godiya nayi a Aisha da irin taimakon da tayi mun har zan kashe wayar naji tace "Anty in tambaye ki daman tunda kin sanshi ne ya alaƙar ku take da shi ne naga kin damu wallahi in zanga JB mota yabi ta kanshi wucewa zanyi ". Haba Aisha Musulmi ne don uwanki ki yafe mi shi babu komai a tsakanin mu sai mutunci lokacin da nazo gidan ku, ina son sani wani abu ne game da shi karki damu ba komai Allah ya bashi lafiya shiru tayi banji tace Amin ba mukayi sallama . Mutumin na kira nace ya jikin nasu yake sanar dani an kawo su damaturu suna TH in zo suna neman taimako tunda babu wanda ya sani gashi wayar shima ta mutu tashin hankali ba,a sa mishi rana da sauri na canja kaya na nace a Hajiya zan fita wani ne bashida lafiya zanje duba shi kafun yan uwan shi suzo,fatan samun sauƙi tayi mun na fita a lokacin da na ƙarisa da sauri na kira wanda ya Kirani yamun kwatance na tausaya mishi sosai yaji ciwo a hannu da fuska da ƙafar shi cikin ci ya bugu bai san waye a kanshi ba A'isha ne ta Kirani wai zata bada number na a yan uwan shi sunzo karɓa nace ta basu duk wani abu da ake buƙata duk na siya komai tinanin wanda zai kwana ,a gunshi nakeyi narasa wani ma,aikaci nagani yana shirin tafiya gida daga ganin ya gama aikin shi na yau naji yana sallama da sauran ma,aikatan shan gaban shi nayi "malam don Allah ina son muyi magana tun da nazo na yaba da hankalin ka ina da mara lafiya ne sannan yan uwan shi yan barno ne basu,iso ba ina son wanda zai kwana tare da shi zan biya shi nima gobe zanzo ƙarfe bakwai Kozaka taimaka mun ku kwana zan baka 10k". Karki damu ba komai zan zauna da shi amma zanje gida in dawo Zangaya wa iyayena kiyi haƙuri ba nisa yanzu zan dawo in sha Allahu "shikenan ina jiran ka sai ka dawo zan tafi " Bai jima ba ya dawo na ɗauki kuɗin shi na ba shi da wasu kuɗin kar za,a buƙaci wani abu bayan bananan komai sai da na tanadar kafun na tafi gida ina shiga gida Abba na shigowa sannu da zuwa nayi mishi na na shiga ciki numfashi naja rayuwar nan babu komai a cikin ta sai rudun duniya duk abun da JB yayi mun yanzu Allah yasa ni zan taimake shi duniya kenan tausayi yake bani yanzu babu wani so a zuciya ta har ƙarfe tara na dare yaron da yake kulawa da shi ya Kirani a kan ya farka nace ya gaishe shi gashi na taho da wayar shi zansa mishi chargi Ƙarfe sha ɗaya na kunna wayar na dare kira yata shigowa kiran mahaifiyar shine ya shigo da bazan ɗauka ba na ɗauka bayan mun gaisa da taji murya ta ta ,tambaye ni, ina mai wayar bayani nayi mata tayi mun godiya a kan ƙanin shi da yayan shi zasu shigo gobe da safe nace to bana son kashe wayar karsu sa wani abu a ransu na barshi a kunne da safe nida kaina na shiga kitchen na haɗa komai da mota na nafita bana son wani abu ya biyo baya ƙarfe bakwai ina bakin get . Ɓangaren in da suke na nufa na samu yana kwance idon shi a rufe godiya nayi wa, Usman ya bani kuɗin yace ba,a buƙaci komai ba bai san anjima ba ko zasu buƙaci wani abu godiya nayi mishi sosai nace muje in kaishi gida yace ba komai in barshi babu nisa tsakanin su zai wuce kawai fita nayi daga ɗakin har nafice bai farka ba naje siyo wasu abu ne nadawo zama nayi a kujerar gefen gadon sai cen ya farka ganina a kusa da shi duk ya firgita zare ido yayi tambayan shi nayi ya jikin ya amsa kiran mahaifin shine ya shigo wayar shi nuna mishi nayi yace in ɗauka kwatance nayi musu sannan na tashi naje don shigowa da su . Kanin shi da yaga halin da yake ciki sai ya fashe da kuka mahaifin shi ya tausaya mishi dana ga yan uwan shi sunzo sai na fice daga ɗakin na shiga cikin mota na zauna nasha ruwa fita nayi don ƙara duba shi tun da na shigo ya zuba mun ido da wani kumburarren fuska mahaifin shine yayi mun godiya da hidimar da nayi musu nace ga abinci suci tunda jikin da sauƙi sosai godiya yayi mun sallama nayi musu nafice zan dawo gida ina fita muka haɗu da doctor Ibrahim muka gaisa "lafiya kuwa ? e lafiya nazo duba mara lafiya ne jiya sunyi hatsari a hanyar biu wani kallo yayi mun "muje na duba shi haka na ƙara komawa ya duba shi tare da tambayan ya jikin shi . Bayan mun fito naga bakin shi yana ta motsi ",ya jikin ki kema don kema mara lafiyar ce?"ka damu da lafiya ta ne yanzu tunda kace bazaka ƙara duba niba da sauƙi sosai . Allah ya baki lafiya kizo na kaiki "na gode da mota nazo "ya batun magana na kuma Nusaiba ina kan baka na har yanzu ban fidda ran zamuyi aure ba ki karɓi tayi na mana "babu komai a zuciya ta doctor kayi haƙuri bana son jefa ka cikin wani hali nasan yadda so yake "babu ruwan ki da halin da zan shiga tunda bake tausayi na kibarni kawai zaifi. Ikon Allah ! naga ya ɗau zafi na tafi daga gun na barshi shiga mota nayi amma na kasa jan motar duk mutuwar Muhammad ne ya jawo mun komai da yanzu ina gidan shi ƙaddaran haɗuwa da JB bata shigo ba da ya Ibrahim zaici gaba da ɗauka na a matsayin ƙanwar shi doctor zaici gaba da kallona a matsayin mara lafiya na daɗe kafun na tafi . Tun daga ranan ban ƙara zuwa asibiti ba amma kullum sau uku zan aika musu da abinci yan uwan shi sunzo duba shi suka tambaye ni mahaifin shi yace sauɗaya ya ganni amma bai san ko lafiya ba ga dai number na su Kirani ina zaune naga kira ya shigo ɗauka nayi jin mahaifiyar JB ce sai da gaba na ya faɗi "lafiya kuwa kin daina zuwa asibiti ko dai laifi a kayi miki ne "ba banajin daɗi ne shiyasa ya jikin na shi Allah ya bashi lafiya . Ta buƙaci in mata kwatancen unguwar mu nayi musu Hajiya ce ta ,karɓe su hannu biyu naji daɗin zuwan su "yauwa Nusaiba kardai kece kika bada saƙo a kawo mun ranan a barno ? Shiru nayi tayi mun godiya sosai tace a lama tagani tagane hakan nida kaina na mayar da su asibitin na duba JB nayi mishi sannu da jiki yace da sauƙi" naji duk kan hidimar da kikayi mun nagode sosai nasan kin daina zuwa asibiti ne don bake son ganina kin tsaneni bake son tarayya ta dake kefa macece wanda babu wanda tarayya zai haɗaku ya watsar da ke ki yafe mun yanzu kam komai ya ƙare Allah yasa ta dalilin hatsarin nan zaki san iyayena suma su sanki zan bayya na musu ke nake so [11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR MARUBUTAN JAHAR YOBE Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki 400 ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984 LAMBA NA GOMA SHA SHIDA Bana son tafiya da ya Ibrahim gudu ne da shi gashi ba ka,isa kayi mishi magana ba kamar zuga shi kake yi ,ga yadda hanyar take shiru nayi na shirya mana kayan mu ,nida Fatima ƙarfe goma muka bar damaturu mun kama hanyar barno ban gayawa Inna ina hanya ba sai dai ta ganni . In da ace zuciya ta zata ,a mince min da ta zaɓi mutumin da yake da kima da daraja agun kowa ina mamakin yadda ya Ibrahim yake nuna mun kulawa fiye da kanshi a lokacin da Muhammad ya rasu tamkar ɗan uwan shi tare muka wuce bauchi da shi sunyi sabo da mutune agun zaman makokin Muhammad . Muhammad yana da zafin kishi, amma ban taɓa ganin ya nuna wa ya Ibrahim ba . Tinani natayi da yawa a cikin motar shi kuma ƙaratu ya kunna yana taji Fatima tayi bacci a cikin tunanin da nakeyi har na tino in da zamuje bauchi da Muhammad muka tsaya a darazo yace mu tsaya mu gaisa da wata batada lafiya haɗe rai nayi nace wata kuma ni bazan jeba ya je ina cikin mota lokacin da muka je duba mara lafiyan a she na miji ne zolaya ta yake yi nikuwa kishi ya rufe mun ido wajen samun lada. Babban mutum ne a she sunan shi TY wajen aikin su ɗaya naji kunya da yazo ya sameni a cikin mota ya gaishe ni abun da naji ,ya faɗs"Madam kin ɗauka wata ne ko shiyasa kikaƙi zuwa a hakan ma nagode sosai Allah ya bar zumunci na gode ". Abubuwan da Muhammad ya bar mun suna dayawa a rayuwa ta a kan alkairi zan ta, tina shi irin su JB ko da mutuwa sukayi babu abu mafi daraja da zan tina shi da shi sai jin maganar ya Ibrahim nayi yace "in kin shiga kicewa Inna na wuce gun aiki wannan key ɗin ɗaki nane ki share mun ɗan Allah ga kayan nan ku shiga da shi ".mai shara kamayar,dani ba zanyi ba in kadawo zakayi kayan ka ,kana da ƙanne kawani sani aiki sai kace wata matar ka kama hannun Fatima nayi muka ƙarisa ciki Inna nata rar tana tsaye ganina da tayi tace oyoyo uwata kece tafe babu waya kuma ?. e Inna nice bazata zanyi miki shiyasa kika ganni . Sannun da zuwa shiga ciki nayi na huta nací abinci nayi sallah har bacci ya ɗauke ni banga kiran JB ba tun safe a waya ta sannan bance ina garin suba akwai abun da nake son shirya mishi zan bashi mamaki kuwa sai ƙarfe takwas ya Ibrahim ya shigo bayan na bada key ɗin ɗakin na shi a gyara mishi abun ka da mai tsafta komai a gyare ya ke kawai dai in da sabo ne an saba . Sai kusan mangari ba kafun ya dawo duk muna falo muna ta shan hira yau sai naji damuwar da nake ciki a cikin kashi ɗari hamsin ta bar raina . "Inna kiyi mun afuwa nawuce gun aiki ban shigo ba sauri nakeyi shiya sa ki yafe mun kinji" babu komai karka da mu hakan ma yayi tunda ka,kawo mun uwata kana kulawa da ita sosai ina godiya Allah yayi albarka . "Amin ya rabbi ". Washe gari da safe Misalin ƙarfe goma na safe bayan ya Ibrahim ya fita wajen aiki nima na shirya na rufe fuska ta ,ta yadda ko kasan ni ba lalle ne ka gane niba na ɗauki A'isha nace muje ta rakani unguwa amma karta faɗa fa tace to unguwar su JB na nufa ban tsaya shan wahala ba na tambayi shagon shi da zumar nazo siyan kayan ɗinki na samu shagon bada waya ta nayi a A'isha ta yadda zata ɗauka mun photo in naje shagon na samu wasu yara sunzo siyan zare da zip nikuma rubuta wa nayi da naje na ba,shi ya faɗa mun kuɗin na ba shi naga ya rame sosai ya ƙara duhu tsayin nan dai tana nan bai damu da yasan ko wa ye ba sana,ar shi yasa a gaba na duba shagon sosai abun duk ya bani mamaki bayan taho wata daga shagon karɓan wayar nayi A'isha ta burgeni har wajen da nake ba shi kuɗi sai da ta ɗauka da lokacin da yake bani kayan da nasiya munji ma,kafun muka tafi daga unguwar har gidan su ,sai da a ka nuna mun nagani . Sai naji sanyi a raina bansan da wanake tare ba ina, gudun wani abu kar ya faru batare da nasan komai a tattare da shi ba wasu na samu suna bakin shagon ɗayan na gane shi wani abokin shine bansan ya ,suke ba a hoton da ya tura mun har da shi tabbas shima yaron ne JB yana cika ido abokin shi kuwa asalin yaron ne dan ga,a lama suna tashan rake a bakin shagon oh ni Nusaiba. Bayan mun dawo gida ne na buɗe waya ta don muna hanya na kashe ina buɗe wa yana kira muka gaisa sosai"kiyi haƙuri na samu kuɗin gobe zanje "ka zauna kayan ka, bance ka nemi kuɗi a ro saboda nawa buƙatan ba baka da shi sannan koda kaje gun Abba ba shida amfani don ga abun da iyayen ka suka ce . "Me yasa kike haka ne kinsan abun da Allah zai yi ya,kamata ki gane masoyi ba ya taɓa zama maƙiyi a rayuwa . Nuna mishi nayi bana gari nayi tafiya amma in zaizo yayi mun magana in gaya mishi "wani kalan zuwa zanyi bayan bake nan kibari sai kin dawo kafun na shirya sai in je da to na bishi banyi musu ba amma a jiki na nakeji bazai jeba kawai ya faɗa ne . Nayi kwana uku a barno babu komai JB yayi blocking ɗina a Whatspp ban bita, kan shi ba na ci gaba da,abun da nake yi duk wani abu na shi a waya ta duk na goge su wani photon da wasu abubuwa wanda suke a laƙa da soyayyar mu duk na fitar da su daga raina nagoge ban bar komai ba nagoge a nawa tinanin ban gaya mishi magana mai zafi ba da takai ya mun irin wannan tijaran ba .har zai rufeni daga ko mai na shi ayya JB yana da hankali kuwa ga shi yayi karatu da, ace bai yi karatu tuba zance a kwai rashin ilimi a tattare da shi . Ta howa ta barno yayi mun rana in da a damaturu nake yanzu ina ɗaki duk tunani ya dameni nan kuwa ina cikin yan uwa na ,babu abun da basa mun tun ranan da muka je ban ƙara sa ya Ibrahim a ido na ba ,da wuri yake fita yau dai takama Jumma,a naga A'isha sai washe baki ta ketayi "Lafiya kuwa indo sai wani fara,a kike tayi"? "Anty Nusaiba yau na tashi bani da kuɗi ga shi yau ne ya Ibrahim yake mana rabo na kuɗi ko wani jumma,kinga kuwa dole in yi murna da kasance war wannan ranan " gaskiyar ki kice mutumin ya nason lada kenan miƙomun jakata in fara baki kafun ya tashi daga bacci miƙo mun jakar tayi na ɗauki dubu goma na bata tsalle tayi tariƙeni sai murna take tayi tun da ga cen naga ya Ibrahim yana ta hararan ta "ki cika ta so kike ki karya ta baki ga ita ba lafiya ne da ,ita ba haba A'isha ina ganin ki kamar mai hankali ",kayi haƙuri ba zan ƙara ba zan kiyaye " Ya dai fi miki kyau ki kiyaye zaifi ƙariso wa in da nake yayi "Madam a nema mun abun da zanci yunwa na keji gaskiya ko dai in yi miki kuka" kayi kayan ka meyasa kake son ka dinga bani wahala ne ina huta wana zaka takura mun . na haƙura zan wuni haka tunda yau babu in da zanje sannan da yamma ki shirya zaki rakani unguwa kinji da to na bishi abincin shi na kawo mishi kaɗan yaci yace ya ƙoshi Da yamma misalin ƙarfe hudu muka fita unguwar su JB naga ya nufa har kusan bakin shagon shi ,da yake motar ba lalle ne ka gane waye a cikin taba fita yayi suka ɗan matsa ya fara yi mishi magana a kan yana so a sa,pop a ɗakin baƙi yau she zasuyi ban san me suka yi ba kawai kallon JB nake tayi hawaye kuma daga zuciya na ,take zubo wa bada ga ido na ba ban san me hakan ya ke nufi ba ya Ibrahim so yake yace ya fahimci a kwai soyayya ,a tsakanin mu ,shine zai yi mishi haka ko dai cin mutunci zai yi mishi ya na so ya ce yaron bai kai ya Soni ba ko yaya ina kuka ina tinani har ya Ibrahim ya ƙariso bai kula da yanayin da nake ciki ba jan motar yayi . Ina zamuje ko dai in kaiki gidan abokina ku gaisa matar sa tana sonki kullum labarin ki ,take yi "ba na so mu wuce gida shine kaje ka jima gun waye ma ,kazo ne? "baki gane shi bane ko yaya yaron da ya kiraki ne fa a ,waya shine akwai aikin da zai yi mun "ya Ibrahim kenan yau she ka koyi cin zarafin mutane ,yau she zaka ɗauki talaka a kan matsayin ku ɗaya kayi hakan ne dan Kaci mishi mutunci ko dai ka ɓata mishi rai na gaya maka babu komai a tsakanin mu, mutunci ne sannan girman ka zai zube nida na gaya maka dole sai shine zai yi maka aikin ka nemi wasu,mana taya zaka zo ka ɗauke ni ka ,kaini gunshi wallahi muddin ka nuna mishi ka sanni bazai ƙarbi kuɗin aikin ba sannan zai yi maka biyayya don nima daraja wa ne da karamci tsakanin mu. "Ba komai Nusaiba baki san meke zuciya na ba naso in kyautata mishi ne ta,wani hanyar amma tunda kin ce hakan zan kiyaye bazan bari ya gane ke mata na bace kin yadda bana son ganin ki cikin ɓacin rai banajin daɗi gaskiya ". Naƙi zuwa gidan abokin na shi siyayya yayi da yawa muka wuce gida muna zuwa a na kiran sallah masallaci ya wuce nima alwala nayi na shige ɗaki don gabatar da sallah. [11/4, 21:47] Maman Khairat: * [11/5, 21:39] Maman Khairat: WATA MAHANGAR Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam Zaki sanya kuɗin ki ɗari huɗu 400 ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984 Laifin daɗi ƙarewa a nan muka kawo ƙarshen labarin JB a cikin littafi na ɗaya duk mesón ci gaba ya biya kuɗi kafun ya karanta sannan ya duba number waya kafun ya mana magana gudun kar a samu matsala littafi na biyu yana nan tafe. Wani darasi kuka ɗauka ,a labarin JB ? Wani a bu kuka koya a labarin JB Wa kuka fi so tsakanin JB da Nusaiba? Wa yafi burge ku tsakanin JB Ya Ibrahim doctor?. LAMBA NA ASHIRIN DA TARA __________Karma ka fara wannan gangancin JB aure tsakanin mu da kai ka,ajiye shi gefe yadda baka bayyana musu a farko nikake so ba rashin yin maganar ka shine ya jawo maka komai koda na rasa mijin aure bana jin zan zauna da mayaudari sannan maƙaryaci kasani da na soka yanzu gara na haƙura da auran. tsanar ka tafi yawa a gareni bana son kallon fuskar ka ka barshi a zuciyar ka bayyana musu koni waye ce hakan zai rage maka kima da daraja a tsakanin ka da iyayen ka. sanin kanka ne natsani ƙarya da yaudara sannan kai mungu ne JB . "Karkiyi mun haka kibarni inji da,azabar rabuwa da ke kawai ina son ki sani nafi kowa sonki " ka gyara kalaman ka don babu komai a idon ka sai tsanata da yaudara da haƙinci ". tafiya na farayi ko wai _wayo wa banyi ba da muryar shi wanda ba fitowa take ba yata kirana sosai ko wai wayo wa banyi ba gida na wuce Hajiya ta tambaye ni ya maijikin nace da sauƙi "yauwa mahaifiyar yaron tananan ko dai ta koma in kuwa bata tafiba zanje in dubo ta kawai don kartaga rashin zumunci ,agaremu shiru kawai nayi cen taƙara tambaya na ko munyi waya da Ibrahim nace mata bamuyi ba ce mun tayi gobe yana hanya zaizo wani abu ne nace Allah ya kaimu na shige ɗakina . Washe gari da kaina na shiga kitchen na haɗa wasu JB abinci na bayar a direban mu ya kai musu na ɗaura wanda ya Ibrahim zaici in ya iso tun sha ɗaya na gama nayi wanka na shiga ɗaki na dau jarida a hannuna ina ta aikin karatu yau ta kama asabar Abba na yana gida tashi nayi dana ga azahar yayi nayi sallah na kwanta sai ƙarfe hudu na tashi daga bacci yunwa naji nafito ina tafiya nací karo da mutum a gabana ɗaga idon da zanyi naga ya Ibrahim ya ƙuramun ido sosai "yaushe ka zo ?tun ƙarfe sha ɗaya na shigo gidan "shine baka nemeni ba meyasa haka? "bana son in raɓi in da kike taya zan nemeki kice na takura miki a duk yadda kika zo a haka zan biki yadda kike so Nusaiba ". Kaci abinci kuwa? Nací tun da nazo meye na tambaya na kin damu da rayuwa nane don Allah kibarni karki ɓatamun rai don Allah "nasan baka Ciba kafaɗa ne kawai kaida cin abinci bai da meka ba taya zakace Kaci abinci don Allah ka daina faɗa tun safe na dafa maka abun da kafi so "waya gayyace ki bana so ki cinye na ƙoshi ". Jan rigar shi nayi na kaishi ɗaki na wuce kitchen na ɗauko abincin na kawo,naje na ɗauko ruwa nazuba mana abincin har nafara ci banga yana da niya ba danna wayar shi kawai bata rai nayi nací gaba da cin abinci na aiko Fatima Abba yayi a kan ya na son ganin mu nace mishi zanzo kafun nabar cin abinci naga ya jawo ya fara ci loma uku yayi sai gashi ya tashi ɓangaren Abba ya nufa bayan ya shiga na bishi a baya da sallama dukkan mu,muka shiga waje na samu muka gaisa da Abba naji yace ya mai jikin nace da sauƙi sosai . "Ibrahim ina son zan yanke lokacin auren ku da Nusaiba nan da wata ɗaya nasan ka gama shiri in baka gama ba to ka bari in taje gidan ka zaka ƙarisa komai a ,hankali". Da Sauri na ɗago Aure Aure kuma Abba! e auren bake sone ko dai ke baki shirya ba ku tashi kubani waje muddin kuka furta wasu magana zan bata muku rai in bakwa son junan ku ,in kunje ku kashe kanku . Kallon ya Ibrahim nayi shima kallona ya keyi ya zuba mun ido duk tausayi na ya kama shi ya rasa ya zai yi muddin zan samu farin ciki ya haƙura da auren har abadan duk kanmu hawaye mukeyi mun gagara tashi daga wajen kowa yasan ma,anar kukan shi na ya Ibrahim tausayi nane ya sashi kuka nikuwa bañsan ya zan yi ba bana son tarayya ta da shi in badan ba zan so in auri JB ko don shine mutum na farko da yasan daraja ta zanso mu zauna tare da shi ina son nunawa JB shi ba komai bane taya zan auri ya Ibrahim bayan nasan ni fanko ce nasan ɗan uwana ne zai rufa mun asiri amma in har kuma yana da zafin kishi fa . Kiyi haƙuri ba na son Abba yayi fushi da mu ki taimake mu ,mugama da iyayen mu lafiya, ki shirya muje asibiti don ance kina da mara lafiya "ba zanje ba kuje kayan ku nafasa zuwan "Hajiya ne fa tace ki shirya zan kaiku don Allah kar ki bari wasu mutane su gane bama son junan mu ki taimake ni don Allah musamman Hajiya . Bayan nayi sallar mangari ba muka tafi asibiti har da Hajiya da Aliyu da Hibba da Fatima da mahaifiyar JB muka fara haduwa nikuma na ƙarisa cikin ɗakin nabar ya Ibrahim yana waya da ganina ya tashi "daman zakizo na ɗauka kinyi fushi shiyasa don Allah ki shigo rayuwa ta mugina rayuwa mai ɗaɗi ina son kisawa ranki ruwan sanyi ni nakine wallahi ina ƙaunar ki zan baki duk wata kulawa zan kula da lafiyar ki zan tarairayi duk wani matsalan ki". Ƙarya kake yi baka cencenci haka ba daga gareni bana son ka har Hajiya tazo ta duba shi B banga ya Ibrahim ba kardai har yanzu waya yake yi Allah yasa baiga in da na shigo ba kafun JB ya gama kalaman shi wanda a zuciya daɗi kalaman suke mun a zahiri kuwa baƙin ciki nake yi sosai ina son in nuna mishi kuskuren shine ta yadda ko da munrabu zai mutunta, mata yan uwana ba zai walaƙanta suba musamman ya samu wanda yake so duk ƙarya ce irin ta maza mayaudara, kalman su guba ne a garemu yakan dagula mana duk wata kafa ta ɓangaren numfashin mu ,maza yawancin su da kalma ɗaya suke yaudaran mu. "Kin yi shiru Hayat kiyimun magana so kike in mutu ne ki duba yadda numfashi take yi mun wahala hawaye ne suka ta gangarowa na gagara tsayar da su daga ido na gara na barshi ko zanji sauƙi a bakin gadon na kifa kaina shikuma yana riƙe da gyale na muna ta kuka sosai "yau guduna kike yi nayi laifi kin gagara haƙura kiyi haƙuri don girman Allah so kike kiyi rayuwa da wani , ki yafe mun kinsan gatan da Allah yayi mun bai ɗauki raina ba a lokacin da muka yi hatsari don in gyara kuskuren da na aikata nacutar da ku keda A'isha musamman ke nabar miki tabon da har ki koma ga Allah bazaki manta dani ba ki tausaya mun karki auri wani "ka gyara kalaman ka wanda zan aura yafi ƙarfin wani a gareni don ɗan uwa na ne, sannan yafika sona da tattalin rayuwa ta na rasa Muhammad a duniya wallahi ko kai ka mutu bazan shiga damuwa ba mai amfani a gareni ma narasa balle kai ko wani abu bazan jiba ina son in fige gyale na ,daga hannun shi na gagara duk wanda ya ganmu zai san mu ,masoya ne in da,ace ɗakin da aka bashi ba shi kaɗai bane mai haɗe da mutane ,ne da mun zama yan kallo zamu bawa duk wanda ya kalle mu tausayi babu wanda zai rarrashe mu ko dai wani ya fahimci halin da muke ciki a wani ɓangaren kuma ina tausayin ya Ibrahim sosai " yanzu Nusaiba kenan kanki zaki bawa wani ina alkawarin da muka yi na cewa zamu kasance da juna ko daɗi ko akasin haka riƙe hannu,na yayi kamar za,a gudu dani ɗago kaina nayi ga hannun shi riƙe da hannuna banƙaɗo ƙofar da a kayi juyawa mukayi don ganin waye ne da ,a lama wanda ya bankaɗo ƙofar ya jima yana tsaye .. Tammat Gareku masu karatu shin waye ya shigo ɗakin ? Shin auren Ibrahim da Nusaiba zai,iyu kuwa ? Ya Hajiya da Abba zasuji in sunji labarin soyayyar JB da Nusaiba gashi yaro mara aji Tsakanin doctor da Ibrahim da JB waye zai lashe wannan gasar Duk kan amsoshin ku yana cikin littafi na biyu ki biya kudin ki kisha karatu. WATA MAHANGAR* ©️ Amina Ma'aji Ahmad Toshiba Maimuna Tijjani Iyam LAMBA NA TALATIN Bisa tursasawar yaya Sufyan muka je gidan su Sakina da son raina ba babu ina da za ni. Domin na yi wa kaina alƙawarin ba ta hutu kafin mu daidaita kamar yanda ita ma take share ni. Mahaifiyarta muka iske a falo muka gaishe ta, ta amsa mana fuskarta tamkar gonar auduga tsabar farin ciki ta rasa inda za ta sanya mu, sai nan da nan take yi damu. "Masha Allah! Allah ya ƙara haɗa kanku ya albarkaci aurenku". "Amin". Muka haɗa baki wajen amsawa dashi kafin yaya Sufyan ya furta"ina Sakina fa tun shigowar mu ban gan ta ba". "Tana ciki yau ta tashi ba ta jin daɗin jikin ta ne, bari a ƙira muku ita". Ta ƙare zancen tana miƙewa dai-dai sanda na haɗo kaina muka haɗa ido da shi. Ta cikin idonsa na fahimci saƙon da yake son aika mini bai wuce irin tarban karamcin da mahaifiyar Sakina ta yi mana ba. Ban bari ya ja da nisa ba na kawar da ido lokacin da sallamar Sakina take ratsa ƙofofin kunnuwana. Kujerar dake kallona wanda na zauna ta yi wa kanta mazauni tare da gaishe damu cikin jumla guda ɗaya. A sanyaye na amsa tare da yiwa bakina linzami. "Na kawo ta mun ba ki haƙuri akan abinda ya faru a tsakaninku. Da ke har ita ranku ya ɓaci da ku ka mayarwa juna martani a zafafe, ba domin ɗaya daga cikin ya manta matsayin ɗayan a gare shi sai don rufewan da idanunku suka yi". Daga haka ya dakata tare da sausauta amon muryarsa kana ya ɗaura da"dukkanku ku yi haƙuri a zamantakewa dole wataran a saɓawa juna domin ko harshe da haƙori ma suna saɓawa. Komai ya wuce ku dawo tamkar yanda kuke a da don Allah ". Take na ji gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalai tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Kalamansa sun bi dukkan sassan jikina sun ɗaure shi tamau. Na kasa cewa komai sai Sakina ce ta furta"la ni kam wallahi ba komai tun lokacin da abin ya faru ma na manta shi. Ban riƙe Surayya a cikin raina ba kawai dai na bata lokaci ne ta huce daga dokin zuciyar da ta hau". "To Gimbiya kin ji dai da kunnenki ko? Sai ke ma ki zubar da makaman yaƙinki". Ya furta yana kafe ni da idanu, sai da ya furzar da zazzafan iska daga baki kafin na sama sararin faɗin"nima komai ya wuce a wajena ki yi haƙuri da kalaman da na furta miki a cikin fushi". Da walwataccen murmushi akan fuskarta ta ce"ke ma ina mai ba ki haƙuri". Murmushi nima na sakar mata, muka haɗa ido da yaya Sufyan shima fuskarsa ɗauke da murmushin da ya ƙara fitowa da kyawun sukakkiyar fuskar da sumarsa suka kwanta luf a saman haɓarsa"to Alhamdulillah! Allah ya ƙara haɗa kanku. Zan bar ki a nan sai zuwa anjima na dawo da ɗauke ki". Kaina kawai na gyaɗa masa Sakina ta ƙira Hajiyarta suka yi sallama. Ina ankare da ita ta ke yi mini alama akan na tashi na raka shi na yi kunne uwar shegu da ita. Ɗakinta muka koma na yaye mayafin kaina na ajiye shi a gefe guda. Ta dire mini kofin ruwa a gabana na bi ta da kallo yayin da take koma gaban madubi tana gyara ɗaurin kallabinta. Sakakken ajiyar zuciya na sauƙe haɗi da faɗin"me yasa kika zaɓi ki rufa mini asiri a wajen yaya Sufyan?". Sai da ta gama tsaf ta juyo"idan ba ku canza hali ba ko ban sanar dashi ba wataran da idanunsa zai ga ni". Na cije leɓena domin na san magana ta karta mini. Sai da na jim kafin na ce"hmm Sakina kenan na lura ba za ki taɓa ganewa ba. Na gode da halaccin da kika nuna min". A hankali ta tako ta iso gabana ta tsaya"zan gane Surayya ke ce kawai idanunkin ya makance akan wani banzan da sam bai damu dake ba. Idan ya damu dake me yasa bai tunkari iyayenki an yi maganar aurenku ba? Me yasa zai laɓe ta bayan fege yana farmaƙan ki ba tare da ya bayyana kansa ga kowa ba?. Uhmm a wancan lokacin na zo wucewa gidanku na sanar da Hajiyarku halin da ake ciki. Amma tunin da na yi ki gargaɗe ni akan fita daga abinda ya shafe ki sai nima na shafawa kaina lafiya". Ta ka aya tana ɗage kafaɗarta alamar babu abinda ya sha mata kai. Musgutawa na yi ina ɗaura idanuna akan ta"shikenan na janye duk kalaman da na yi a baya yanzu ki ba ni shawara". Ba ta ce da ni komai ba sai da ta zauna kusa da ni tana fuskantana sosai"babu shawaran da zan ba ki face wanda na ba ki a baya kika sanya ƙafa kika shure su. Ki maida hankalinki wajen neman aljannarki ta hanyar farantawa mijinki. Ki cire ƙaddararren soyayyar Suraj daga cikin ranki ko kema za ki sama sallamar rai da ruhi". Sai da na haɗi wani miyau mai ɗaci kafin na ce da ita"shikenan in sha Allah zan yi ƙoƙarin yin hakan". "Da kin ga alfanun hakan a gare ki kuwa ba ɗan kaɗan ba". Mun tattauna sosai da ita ta inda ta dunga bani shawarwarin yanda zan sanya Yaya Sufyan a cikin raina. Har wasu addu'o'i ta ba ni ta ce na dunga yi a cewar ta wai ba ta yarda Suraj haka banza ya bar ni ba. Sai bayan sallan Asr yaya Sufyan ya zo ya ɗauke ni muka tafi cike da sanyawar albarkan majaifiyar Sakina. A cikin kwanakin nan na yi ƙoƙarin ganin na yi duk wani mai yiyuwa wajen ganin na samarwa yaya Sufyan matsuguni a cikin zuciyata amma lamarin ya garare ni wankin hula yana neman kai ni dare. Dukkanin wani kyautatawa ina yi masa haka nan duk wani saƙon da Suraj zai turo mini sai dai na karanta na shafe amma ba na mayar masa da amsa. Na rungume mijina da kuma aurena hannu bibiyu ina bautar Ubangiji, kullum soyayyar da yaya Sufyan yake nuna mini hauhawa take yi kwatankwacin yanda farashin man fetur ke hawa a ƙasata. Bai da burin da ya wuce kyautata mini da yin silar wanzuwar annuri akan fuskata. Mun shirya da Sakina mun dawo tamkar yanda kowa ya san mu. A na cikin haka Sultan ya nuna yana sonta, ni kam na yi murna sosai tare da yin mata gargaɗin har ta ja wa ɗan uwana aji akwai ta bada kai bori ya hau. Suraj ya zame mini ƙadangaren bakin tulu na bar shi ya lalata ruwa na kashe shi na fasa tulu. Har yanzun bai daina bibiyata da nuna mini soyayyarsa a gare ni. Bana mance wani yammaci da ya aiko mini da saƙon murya ta wasof. Yana yi mini roƙo da magiya akan ko sau ɗaya ne na dawo masa da amsar tarin maganganun da ya yi mini. Babu kalmar da ta sanya mini a raina kamar ƙayar kifi a maƙwoƙwaro kamar faɗin da ya yi ya yarda ko da auren wani a kaina shi dai kawai na amshi soyayyarsa. Na ci kuka tamkar raina zai fita a lokacin na goge dukkan lambarsa daga wayata. Duk da har yanzu soyayyarsa tana nan a cikin zuciyata amma ba zan iya aikata abinda yake so daga gare ni ba a wannan lokacin. Ba zan iya cin amanar aurena, mijina da kuma iyayena ba. Na gwammace na kashe auren na fito kana mu yi soyayyar amma ba dai ina cikin gidan wani ba. Duk wata hanyar da zai iya turo mini da saƙon na bi na toshe ta ko ƙirana aka yi da baƙuwar lamba bana ɗagawa. Wani ranar da ba zan taɓa mancewa da ita ba a cikin tarihin rayuwata saboda muninta da kuma zama sanadin datsewar igiyoyin farin cikin rayuwata. Na dawo daga makaranta na shiga kitchen domin ɗaura girki a lokacin yaya Sufyan ya fita masallaci, wayata dake kan firiji ta yi ruri alamar shigowar saƙo ban bi ta kan ta ba sai da na gama yanda albasan da nake yi sannan na ɗauko ta. Baƙuwar lambar ce na shiga saƙon da sauri. "Ki fito ina ƙofar gidanki idan kuma kin yi biris da zancena, babu shakka zan shigo har cikin gidan na sanar da mijinki abinda ke tsakanin mu". Mutuwar tsaye na yi bayan na gama karanta saƙon tare da dulmiyawa kogin tunanin wanene wannan?. Kafin na kai ga cimma amsar aka ƙara turo wani saƙon sunan da na ga an rubuta da manyan harrufa suka sanya hancin cikina haɗawa, na maimaita sunan a bayyane. "Su-su-su-suraj". Kamar mahaukaciya sabon kamu haka na fito daga kitchen na ɗauko mayafina na banko ƙofar falon na fito waje. Rarraba ido na soma yi akan shimfiɗanɗan titin dake ƙofar gidan, na yi turus saboda ganin yaya Sufyan da Suraj suna tsaye suna gaisa. Wani jiri ya soma deɓe na, na ƙara ware girman idona akan su daidai sanda duk suka juyo suna kallona. Suraj yana jifa na da wani shu'umin kallo.