*JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW Page 1️⃣➡️2️⃣ Inna da Lami ne suka fito daga ɗaki cikin sanɗa, kallon ƙofar Yaya Lado suka yi wacce take hanyar ƙofar gida ganin ya ɗan karo ta saboda sanyin ruwan saman da aka wuni ana yi, dan yana dawo wa daga masallacin ishsha'i ya shige ɗaki. Hakan ya basu ƙwarin gwiwar yin bayan gidan dan ba zai yi wu su bi ta ƙofar gida ba kasancewar ɗakin Yaya Ladon a hanyar fita daga gidan yake. Lami ta taka duron da suka kifa ta haura katangar, ta dira wajen santsi na barazanar warɓar da ita ta daddage bata faɗi ba, Inna ma cikin ƙarfin hali ta taka ta hau duron tana damƙe baki da haƙoranta ƙafafunta na karkarwa ta ɗane katangar, tare da maƙalƙale katangar wacce take a jiƙe da ruwan sama, tamkar wutar lantarki ta kama mutum haka Inna da damƙe katangar hannayenta da ƙirjinta suna kan katangar ƙafafunta da fa miƙa waje za ta dira sai reto suke basu dira ƙasa ba. Hannu Lami ta sanya ta riƙo cikin Inna daga bayanta ta taimakawa Innar ta sakko. Babu batun jira wai an ɗaurawa karya zani haka suka fara surfa sauri tamkar za su ci da ka, duk da caɓalin ruwan amma a haka suke bi suna kewaye caɓali. Tun da suka fara tafiya Inna take sufa a laka, dan daga ta ga Lami ta tsallake waje sai ita ma ta ce fafur ta wajen za ta bi dan haka kuwa sai su shiga kokawa da caɓalin laka, ƴar tafiyar da suka yi a hanyar faɗuwar Inna a laka ta yi bakwai jikin nan nata sharkaf yake da ruwa da laka sai tsiyaya take tamkar yaro ya saki fitsari a tsaye. Dan wani wuri da ya yi caɓali da yawa tana taka wa takalminta silifas ya ce bai ga ta fitowa ba haka Inna ta shiga jan katanar takalmin amma babu yadda ta iya ta sille su ta barsu a wajen Lami tana mata dariya dan ta ce ba za ta tsaya ciro takalmi ba su ɓata lokaci. A haka suka ƙaraso wani gida mai ƙatuwar kwata, wanda yake kusa da gidan Malam Ashiru daga hagu. Lami ta daddage ta tsallake kwalbatin Inna tana zuwa sai da ta ɗora ƙafarta ta dama za ta tsallaka ya zamana ƙafafun duk sun tale kwatar na tsakanin ƙafafun Inna Uwani, tana son tsallakawa ta yi taga-taga aikuwa santsi ya ja ƙafar Inna da babu takalmi ta tafi suuuuuu ji kake tunjum Inna ta kamo kifi. Dariya ce ta ƙwacewa Lami da ta waiwayo dan har ta yi gaba, ganin Inna kwance cikin ruwan saman da ya cika kwatar maƙil, sa kan kake hangowa tana ƙifƙifta idanun tana tamkar wacce kishiya ta kama ta da satar kwanan ɗakin miji, duka uban jikin ya lume sai kan kawai kake hangowa tana rangaɗa shi tamkar tsohon najadu ya ji kalangu. Dakyar Lami ta taimaka wa Inna ta fito, kayan nan sun yi jargwaf sai rawar ɗari take kasancewar kishi kumollan mata sai Inna bata damu da jiƙewar ba haka Lami ta cigaba da tafiya cikin sassarfa, Inna kuwa sai take tafiya a hankali. "Haba Inna maimakon kike gudu-gudu sauri-sauri tafiyar larabawa amma kin tsaya a baya kina tafiyar kamar ƙwai ya fashe miki a ciki" "Haba Lami ya kike so in yi da raina ne, wannan sauri da kike ina dalili ina ɗan mafari duk ƙwaurina ya gaji, kina gani tafiya kaɗan sai santsi ya niƙa ni da ƙasa, ga jikin tsufa amma sai daɗa saurin muke sai kace wanda za mu tashi sama" "To shikenan ki yi ta tafiya a hankali, wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho! Ke da za a kaiwa amarya yanzu, amma duk ƙoƙarin da nake miki bakya gani" "Yi haƙuri ƴar jikallena Lamisa, na sani amma tun da kina ganin bana sauri bari in ɗaga ƙafa... Kafin Inna ta kai ƙarshen maganar santsin lakar ruwa ya ɗauketa sai da ta yi gaba ta dawo baya ji kake timmm ta rafku da ƙasa, wani ƙara ta saki a wahalce ta ce "Wayyo kwankwasona, duk faɗuwar nan da nake ji nake tamkar an sa inji za a murɗe mini kwankwaso, haka kawai in je in karye a banza Malam ya ji daɗin cin amarcin a... Bata ƙarasa ba Lami ta katse ta da jaraba "Wai Inna so kike Malam ya shiga ɗakin Duduwa, kin ga idan ya shiga sai mu koma gida kin ga mun zo a sadaka za mu koma a alakoro, bayan kin san ke da kika yi yaji wajen sati uku bakya nan babu wanda ya yi bikonki na taimake ki zan mayar da ke ɗakin ki na miki alƙawarin kazar amarcin da Malam zai kai wa Duduwa ke za ki cinye amma kike sanya tafiya kaɗan sai ki zube a cikin laka tamkar tsohon ginin da ruwa ya duka to ƙur'anin Allah ba a bori da sanyin jiki" Tana gama faɗar haka ta cigaba da tafiya. Haka Inna ta daure ta tashi ta bi bayan Lami duk da ta lura yarinyar tana sauri ga wani uban duhu dan ma da hasken farin wata sai dai wani lokacin yana shiga cikin gajimare amma haka suka ƙaraso, gidan Malam Ashiru mai almajirai suka nufa inda nan ne gidan Innar shi ne ta yi yaji dan Malam zai auri ƙawarta Duduwa daga can bayan gidan suka tsaya. "Inna kalli dangan karan da aka sake sabo dal taɓɗi lallai sai kin yi da gaske in ba haka ba sunanki soriye ba ma sore (Sorry) Ba a gidan nan" Cewar Lami tana ƙarewa sabon dangan kallo ta farin wata. Wata ajiyar zuciya Inna ta sauke tana jin zuciyarta na suya, ga faɗuwar da ta yi har lokacin kwankwasonta kamar ba a jikinta ba yake, hannu ta sanya ta goge hawayen kishin da ya gangaro mata tare da jan hanci ta ce "Ɓalle shege mu wuce ai wallahi Ashirulle ya ɗakko ruwan tafasa kansa" "Inna sabon dangan karan za a ɓalle?" "I mana ai dama ƙarsheb tika tiki tik" Lami bata yi wata -wata ba ta saka wani murɗigegen icce ta shiga buga dangan, sai da ta musu kofa (Ƙofar ficewa) Sannan ta shige, duk tana karcewa da karan amma dan kudura sai da ta shige. "Duƙa Inna, ki shigo a hankali, yi dibara kar ki je ki buge ƙoƙon baya" Ta faɗa cikin raɗa. Haka Inna ta daddage ta kutso ta cikin karan amma tana zuwa saitin ƙugunta ya maƙale. Haka Lami ta kama hannayen Inna ta shiga janyota tamkar ta samu gugan rizabuwa. Inna kwa faɗi take "Haba Lamisa jani sannu a hankali mana tsautsayin gaban auren Malam kar in mutu in bar Malam, yo kar ki girgiɗe mini kwankwaso bikiji ba idan kika fisgi hannun nan nawa tamkar birin da aka ɗaure a ƙugu har wani garrrr nake ji wallahi ba dai azaba ba... Wata irin fisga da Lami ta yi wa Inna hakan ya sanya Inna damƙe bakinta dan tana buɗe bakin ihu ne zai fito asirinsu ya tonu. "Lami kwarankwatsa dubu mazaunai na za su huje a banza" Cewar Inna tana sakin kuka. "Wai Inna mene ne hakan? " Lami ta faɗa cikin tsiwa. "Lamisa wallahi wata zarɓeɓiyar ƙaya ce ta shige mini ɓarin ɗuwawuna na dama, kuma ki duba har ɗankwalina ma ya maƙale haɗe da beɗon kitsona (Jelar kitso)" Da sauri Lami ta duba ta cire ɗankwalin kitson kuwa dakyar ya ciro Inna tana kukan azaba marar sauti dan kar a ji su.Ƙayar ma dakyar ta fita dan Inna har wani ƙara ta saki jin tamkar za a cire gefen ɗuwawun. Kafin Innar ta dawo hayyacinta Lami ta samu nasarar fisgota daga tsakiyar dangan karan sai gata kwacar yashe a gefe guda tana maida numfashin wahala. "Wannan wadaƙa da kwankwasona yake sha yau Allah dai ya sa kaffara ce amma na ga ta kaina ni na ga jalala auren karuwa ba sadaki" Inna ta faɗa tana mirginawa ta tashi zaune tana riƙe da ƙugunta da hannu biyu sai murza wajen ƙayar take tamkar wacce likita ya yi wa allura ya ya ce ta murza. Ganin Lami ta yi adungure da shala sai gata tsaye daram a kan ƙafafunta dan da ta janyo Innar faɗuwa ƙasa ta yi, hakan ya sanya Inna tuntsurewa da dariya ƙasa-ƙasa amma kuma wata wawiyar guɗa da wata tsohuwa ta rangaɗa ɗaya daga cikin ƙawayen amarya ita ce ta sanya ƙirjin Inna ya bada wani dammmm wata uwar harara ta aikawa yankin da take jiyo tashin ƙaran guɗar. "Inna a duƙe fa za mu tafi kar a ganmu kuma kar ki tsaya tsegumi ki ce za ki hango ɗakin amaryar ko ƴan kawo amaryar aje a ganmu" "Haba Lami yo ni ina ma na ga nutsuwar kallonsu ina ta kaina ai ni burina bai wuce in ga Ashirulle a ɗakina ba ya kawo kazar nan da rabona da in ci tun ta amarci shekara saba,in ina ga har da ɗoriya" "Inna wai yau ba Malam ɗin ba Malam Ashirun sai Ashirulle kamar wata atamfa" "Ke rabu da ni namiji ɗan jakar uba n, ba ɗan goyo bane in da sunan shantu ma zan kirawo shi ƙyaleni, ke Allah ko da sunan garken dabobi na kira shi aradu sunan ya dace da shi" A haka suka shiga tafiya a dudduƙe tamkar masu ƙusumbi a baya. Har suka isa kewayen Inna da ke can ƙarshen gidan. Babu mukulli dan haka suka rasa yadda za su yi. "Lami shiga ta taga(Window) Ki ɗakko mukullin a cikin samirar da nake ajiyewa kin san da na tashi tafiya yaji ban tafi da mukulli ba shine shi kuma mai gidan ya kulle wato ma ko lissafin dawowata ba ya yi wai shi nan mai amarya" Lami bata tanka wa Inna ba haka ta kama windown ta haye har tana karcewa da langa-langan jiki haka ta dira ta ɗakko mukullin ta buɗe suka shige cikin ɗaki. Da sauri Lami ta kunce harshen zaninta ta ɗakko wani ɗan magani a ƙulle, kwanon sha ta ɗakko ta ɗauki wani allo mai rubutu a jiki ta zuba ruwa ta wanke allon maganin ta zuba a ciki ta gwauraya, ta juye a ƙaramin kofi. Inna tana kallonta bata ce mata komai ba dan ta san hatsabibancin Lami babu wanda ta bari kuma ta san duk abin da ta saka gaba sai ta ga bayansa dan haka Inna bata taka mata birki domin ita ma tana taimakonta. Ficewa ta yi riƙe da kofin da ta zuba rubutun ɓangaren amaryar ta nufa mata tsofaffi suna ta hayaniya. Wata tsohuwa da ke carara guɗa ta ɗan yafito gyalenta ta ce "Wai ga wannan rubutun in ji Malam a bawa amaryarsa, na taryar ango ne ta sha" Karɓa tsohuwar ta yi ta shige ɗakin ta kaiwa amarya Duduwa a take aka ba amarya sai da Lami ta tabbatar sun ba amarya Duduwa dan ƴar tsohuwa ta kwankwaɗe magani wata tana a bincika a tabbatar Malam ɗin ne ya aiko aka gwasileta ana cewa waye zai iya aikin Malamai. Bayan ƴan kawo amarya sun watse aka bar amarya zaune a bakin gado, dan tun kan su tafi take jin jikinta duk ya saki babu ƙarfi duk idanunta sun mata nauyi. Iya Duduwa ta hangame baki tana wata doguwar hamma Lami da ke laɓe a gefen window tana kallonta a take ta fara gyangyaɗi tun tana yin a zaunen har ta dawo tana yin wanda dai ta gyangyaɗa goshinta ya kusa kaiwa kan cinyarta, a haka gwaggwaron nata na ɗankwalin kanta ya ɓingire daga kan baka hango komai a kan sai kitson zanen hausa wanda har da ɗan gaba aka mata an saka tsakiya(beat) Gyangyaɗin da take sai kusa tuntsurawa sai ta dawo ta zauna har dai ta tuntsuro daga kan gadon timmm ta faɗo ƙasan ɗakin amma cikin bacci mai nauyi bata san ma ta yi ba, a ƙasan ta kwanta ta yi ɗai-ɗai ta shiga sakin munshari tamkar an shaƙewa rago wuya. Lami hannu ta shiga ɗaga wa Inna da ke can tsaye tana jiran umarni daga Lami, cikin sauri ta taho dan lokacin har ta saka wasu kayan ta shafa turare dan Malam ya tabbatar amaryarsa ce Dududuwa Inna tana zuwa suka shiga ɗakin amarya Duduwa, Lami ta kama haƙarƙarin Duduwa ta ɗagota ta kama hannayenta daga baya, baki sake take kallon Inna da ke bin ɗakin da kallo tana taɓe baki. "Allah suturu buƙui in ji kishiyar mai doro, kuma haka tara dai in ji kishiyar mai mageduwa" Cewar Inna tana hararar an kayan da aka jera wa amarya wanda tsofaffi ne kuma dama Innar ta san su a gidan mijin Duduwar na baya dan su suka jera mata, dan tun kayanta ne na auren fari, kafin mijin ya mutu yanzu shekaru bakwai. Wata uwar harara da Lamin ta dokawa Inna ita ta ankarar da Innar da sauri ta kama ƙafafun Duduwa bayan ta sakar mata mugun ranƙwashi a wannan kan fa makitsiyar ta gama taltale shi sai ƙyalli yake Duduwa da ke bacci magashiyan ta saki jiki tamkar gawa, Lami ma hannu ta saka ta dungurewa Duduwar rantalelen goshinta haka suka cicciɓota suka fito da ita daga ɗakin, Inna da ke riƙe da ƙafaffun duduwa sai faman doka mata harara take haka suka ƙarasa ɗakin Innar Inna ta saki ƙafafun Duduwa ji kake jaɓak ta zube kamar kayan wanki, sannan Inna ta zaune Dududuwa. "Maciya amana da kika aure mini mijina, daga ke har shi kun ci amana wallahi, ai Ashirullen ya fi kowa ya ɗauki fuska kamar ta tsulan biri" Cewar Inna tana tashi daga kan Duduwar ta ƙara zaunawa jaɓar sai da ta yi haka sau uku ta saka hannu ta sakar mata wani uban ɗaɗe a mazaunai. Lami banda dariya babu abin da take. "Kishi kumallon mata Inna, yanzu mai mazaunanta suka miki?" "Ke rabu da ni yo wa ya sani ma ko mazaunan nata ya gani ya ƙyasa, ke baki san namiji ba kina dai ganin mazaunan nan nata masu kama da fantalo to wallahi sai ya ɗauki hankalinsa ai wallahi Ashiru ya ci amanata" Inna ta faɗa tana share hawayen takaici. " Yo Inna ta yaya zai gani shi da ba gani yake ba Rabu da su Inna daga shi har ita sai mun gasa musu aya a hannu "Haba Inna kar fa Malam ya shigo ya same mu ki kama ta mana daman ke da za ki kamata kika je kika saka ledoji kika ƙulle hannaye kamar wanda za ki kama wani mushen arne" "Yo ba gwara mushen arne ba Lami kar ki manta fa jikin kishiya zan kama haka kawai in je in kama jaraba, a hakan ma sai faman harararta da nake idanuna har ciwo suke saboda zarosun da nake" "Wa ya ga ban san ana yi ba kunu a maƙota ita da take bacci, kuma ma kr dai aminiyarki duk garin nan waye bai san ki da Duduwa ba, ku zauna a ɗakin nan naki kuke hira kuna tafa wa abinku amma yau har kike ƙyanƙyamin taɓa jikinta sai ka ce wata mai cutar kuturta" "Humm Lamisa ai da kika ce to tun da tsoho bai ji kuyar hawa jaki ba ai jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, yanzu ai dole in ji ƙyanƙyaminta tun da yanzu turaka ɗaya za mu ke shiga ni da ita, yo kama-kama za muke yi da ita (Sharing ɗin miji) Inna ta faɗa tana kauda kai gefe. Haka dai suka kama ta ƙiiii rabin jikin da mazaunanta suna janƙasa, ƙasan gado suka ɗaɗɗauke fantekoki suka samu buhun hatsi suka saka amaryar Malam a ciki kai kaɗai suka bari a wajen buhun suka tura ta ƙasan gado. Ɗakin Innar suka mayar suka kulle kamar ma ba a buɗe ba. Ɗakin amarya suka koma Inna ta zauna a bakin gado, tamkar ita ce amaryar. "Sai Innata, ai indai ina raye ba za ki yi maraici ba, kuma ba za ki yi kuja va dole na share miki hawaye" Lami ta faɗa tana dafa kafaɗar Inna da murmushi ya kasa barin fuskarta. "Na sani Lami ai shi ya sa nake alfahri da ke, ga shi yanzu kin share min hawayena, mun saka sabuwar amarya a buhun hatsi ni kuma na maye gurbinta dama duk wanda ya ce tukunyar wani ba za ta tafasa ba tashi ko zafi ba za ta yi ba, yanzu saura kazar amarci" "Ita ma ke za ki ci" Malam Ashiru suna tsaye da abokinsa Malam Liman suna ɗan taɓa hira amma Malam Ashiru kunnensa yana ƙofar gidansa yana so ƴan kai amarya su watse ya je gun Duduwarsa masoyiyarsa, duk da ba gani yake ba amma kuma yana ankare. "Kai Malam Ashiru wannan kazar amaryar da ƙamshi take wallahi ƙamshinta duk ya cika mini hanci da cikina" "Aikuwa Malam Liman haka za ka ɗau na annabawa kake haɗiyar miyau dan kazar nan ko ƙafa ba zan iya baka ba, ka san dai ta amarya ce ni ma rabona da cin gashin kaza tun ta amarcina da Uwani wannan ma kuɗin larabar da nake karɓa wajen almajiraina, na tara na laraba takwas shi ne na siyo mu yi Allah kaimu" Allah kaimu kuma?" "Allah kaimu mana, ina nufin Allah kaimu lokacin da zan kuma yin wata amaryar in siyo kazar a ci da ni" *JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW Page 3️⃣➡️4️⃣ "Taɓ gaskiya dai Malam Ashiru kana taro aradu da ka, yanzu a nan gaba har kana ganin za ka iya ƙaro wata matar? Bayan yanzu wutar da za ta kunnu gidanka baka tanadi ruwan kashe ta ba, ka aurowa Uwani ƙawarta Dududuwa aikuwa ka ɗakko ruwan dafa kan ka, ka san dai dukansu ba kanwar lasa bane" Wata dariya Malam Ashiru ya yi ya ce "Malam Liman ai da kake ganin mata kawai ka barsu, ni yanzu dai gabaɗaya hankalina yana kan kazar nan da kuma maryata dan ni ba na ta wata Uwani dan yau za mu daki amarci ni da Dududuwalle dan ko amarcin da kansa sai ya yi kukan dole dan ba ƙaramar gurza zan masa ba, kafin dai in je bikon Uwani ta dawo gidan mun mori amarcinmu san kowa ƙin wanda ya rasa. Malam Ashiru ya faɗa yana hango irin yadda zai kwashi ganima "Taɓ lallai akwai ƙura wai ɗan dako ya hango ayarin udawa" "Bari in shiga daga cikin tun da na ji matan nan sun daina hayaniya da alama duk sun fice kar fa in bar amarya tana jiran ango " "Uwaniiiii" Malam Liman ya faɗa cike da tsokana. "Hahhhh ka ce dai tauraruwa mai wutsiya jinta ba alkairi bane, tun da ni ba ganinta nake ba bare na ce ganinta ba alkairi bane" Cewar Malam Ashiru yana ƙanƙame ledar kazarsa ya shiga dogara sandarsa da ke masa jagora ya bar Malam Liman na ta dariya. Ya zo dai dai inda zai shiga gida daga gefe almajiransa ne suke zazzaune a kan wani dogon icce wanda suke zauna wa idan an yi ruwa su yi karatu, ƙaran sautin karatunsu ya ji ya ce "Kai kowa ya karanta ƙulhuwallahu ƙafa uku Allah kaini wajen amarya a sa,a sai kuma kowa ya tafi ya kwanta yau ba ranar karatu bace kar ku hana sabuwar amarya bacci" Haka suka bi umarnin Malam ɗin bayan sun karanta ya sallame su suka ɗuru a shagunan da suke kwana. Yana fara tafiya suka shiga leƙensa Binsa da kallo ya suka yi, ganin ya yi gaba yana gyara riƙon ledar kazar kamar wanda za a ƙwace masa. Haka ya shiga zauren gidan ya maƙale ledar a hamatarsa ya tura ƙofar gidan cikin lalume ya garƙama uwar sakata ya janyo wani ƙaton dutse ya ƙara tokare ƙofar ya ce "Kar tsakar dare kishi ya hana Uwani bacci ta tarki zuwa gidan nan to ahir ɗinki Uwani yau dai da sabuwar amarya zan yi amarci" Ya faɗa yana dogara sandarsa ya shiga gidan bakin nan nasa har kunne. "Inna kar ki kuskura ko da wasa ki yi magana kin san dai ni ina da baiwar yin kowace murya dan haka ni zan yi muryar Duduwa ke kuma kina daga gefe a matsayin Duduwa" Lami ta faɗa cikin raɗa. Inna Uwani da ke zaune bakin gado sai ƙamshin madarar turare take ana zaune a bakin gado ta gyaɗa wa Lami kai ganin Malam Ashiru ya taho ɗakin. "Assalamu alaikum amarya fara mai farar aniya" Malam da ya bankaɗo labulen ɗakin ya faɗa yana wani lashe baki kamar tsohon maye fuskarnan kamar gonar auduga, wata uwar harara da Inna ta doka masa tamkar idanunta za su faɗo ƙasa wani kishi ne ya tsarga mata a take ta tashi a zuciye ta je za ta bangaza shi ya hantsila, da sauri Lami ta je ta shiga tsakani sai sannan Inna ta lura da katoɓarar da kishi ya kusa sanya wa ta yi, da hanzari ta koma ta zauna. "Wa alaikumus salamu, angona ka sha ƙamshi" Cewar Lami da ta yi murya sak Duduwa wani daɗi ne ya ratsa zuciyar Malam ya sako sandar tasa ya shigo yana ta faman washe bakinsa mai wani uban wawulon da babu haƙori a wurin, Inna kuwa har lokacin tana aika masa saƙon harara. "Ikon Allah, sannu da zuwa gidan mijinki na alheri na ji daɗi da na kasa zawarawanki a ina zan zauna" "Ai kai ɗin ne ko laraba wa sai sun sara maka wajen kyau da iya tsara mace, zauna a nan ga kujera nan" Cewar Lami. Har lokacin bakinsa ya ƙi rufuwa shi kaɗai ya san daɗin da yake ji a ransa ga kaza ga kuma amarya yau sai ya zaɓa ya darje. Hannu ya kai yana laluma kujerar da ke gaban gadon irin ta robar nan, sai da ya dafa ta sannan ya ajiye sandarsa har lokacin ledar kazar tana maƙale a hannunsa. A zuciyarsa kuwa sai haɗiyar yawu yake yi. Inna sai da ta bari ya juya zai zauna ta ɗan matsar da kujerar a hankali ba tare da wani ƙara ba, aikuwa Malam da ya tafi da ƙarfin jiki ya zauna jaɓak a ƙasa ya wutsila ya yi wanwar a tsakar ɗakin, shi a gefe ledar kazar ma a gefe ya ji zafin faɗuwar amma saboda shegen kwaɗayi da sauri ya tashi zaune ya shiga lalumen ledar amma abin ammaki bai taɓo ledar ba, ledar kuwa tana hannun Lami sai da ta ɗauki wata ƙatuwar cinya sannan ta ajiye a ƙasa ta ce "Wayyo angona sai da na ji faɗuwar nan taka har maƙwallaton zuciyata, ashe baka ƙarasa kan kujarar ba" Ta faɗa cikin muryar tausayi. Malam kuwa bai samu damar amsawa ba dan burinsa kawai ya ji ya damƙo ledar kazarsa ko hankalinsa zai kwanta, sai da ya ji ya lalimo ledar ya ɗauka da sauri, ya damƙe yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya kai ledar wajem hancinsa ya shinshina ya tabbayar da ledar kazar ce sai ya shiga washe baki dan ya wayance tare da ƙoƙarin tashi zaune dan a laluman ledar bai sani ba har rubda ciki ya yi yake tafiya a tsakiyar ɗakin da jan ciki, shi ne cikin wayancewa ya miƙe yana haɗiyar wani miyau da ya taru a bakinsa dan yana ɗaukan ledar ya ji yawunsa ya tsinke, dan bashi da burin da ya wuce ya ji tsokar naman nan a bakinsa dan tsoro yake kar ya falka ya ga ma mafarki yake bai ci ba, ya fi so ko da zai falka daga bacci to ya samu ya ci kazar a mafarkin amma ba ya ma fatan haka ta kasance. "Malam ya na ga duk ka ruɗe" "Lah ba komai Duduwata" Ya faɗa yana tashi tsaye riƙe da ledar. "To dawo bakin gadon kuda da ni ba sai ka hau kan kujearar ba" Lami ta faɗa cikin wayancewa. Tsabar zumuɗi bai ɗauki sandar ba haka ya miƙe dan zalama ledar kazar ce kawai a hannunsa, yana shirin zama a kan gadon a gaban gadon, ya taka wani ɗankunne mai tsinin barima wataƙila ɗaya daga cikin ƴan kawo amarya suka jefar a tashin sani, zafin zugin ɗankunnen da ya gama shigewa cikin ƙafar tasa, sai ya saki ledar kazar ya zame zai zauna yana riƙe da ƙafar ji kake ƙum, ya buga fuskarsa a jikin katakon gadon wanda har ya sa laɓɓan bakinsa suka bugu da jikin katakon tsabar gigicewa. Lami ta yi wa Inna nuni da ta taimaka masa da sauri Inna ta kama shi sai Lami ta zo daga wajen take magana. "Wayyo sannu, ni dai yau ko dai tsakaninmu da marcinmu aka shiga yanzu a ce tun da ka shigo ɗakin nan kake faɗuwa kamar ginin ƙasar da ya shekara arba'in babu yaɓe" Malam hannunsa ya janye daga na Inna ya shiga lalume. "Ina ledar kazar nan kwa Duduwa" Da sauri Lami ta miƙa wa Inna ledar bayan ta ɗauki wata ƙatuwar tsoka ta saka abakinta dan ta ɗazu ma cinye wa ta yi. "Ga ta nan Malam" Cewar Lami cikin muryar Duduwa ita kuma Inna ta miƙa masa, bayan ta zare masa ɗankunnan daga ƙafar haka dai ya damƙe ledar kazar yana jin zugin laɓɓansa ya tashi ya ƙarasa ya zauna a kan gadon da taimakon Inna, da duk tunaninsa amaryarsa Duduwa ce bai san ba ita tana can cikin buhu a ƙasan gadon ɗakin Inna Uwani. Zaman da ya yi sai ga shi ya miƙe tsayi da sauri yana yin wurgi da ledar kazar, tsabar ganin yadda ya yi daga Inna har Lami dariya suke kawai marar sauti dan Lami har da kwanciya a ƙasa tana kallon yadda Malam ya yi hajaran majaran shiga aljannar alƙali. "Wiiii, yiiii wuuuu" Kawai yake yi yana wani sambatu sai zagaya ɗakin yake riƙe da mazaunansa, a haka ya ƙarasa jikin bango ya jingina bayansa yana sakin kuka. Lami dakyar ta tsayar da dariyarta dan har da hawaye ta yi muryar Duduwa ta saki kukan kissa ta ce "Ni ya zan yi ko dai wani ne ya jefeka, wanda ba ya son ganin mun ci amarcin nan tun da ka shigo ɗakin nan nake ganinka cikin ƙaƙanika yi, kamar ba jarumi ba" "Yi shiru Duduwalle, wallahi abin ne ya zo mini bagatatan samun biyan kuɗin hajjin kishiya, in banda da'ira cuta bayan rai ya za a yi a samu allura a kan gadon amaryar da ta tare yanzu... "Allura Malam?" "Allura ce yanzu hakan tana cikin mazaunaina ta yi luntsum a cikin tsoka" Inna kawai kwanta wa ta yi a kan gadon tsabar dariyar da ke cinta dan sai da ta rufe bakinta da hannunta dan kar sautin ya fito, saboda furucin Malam sai ya tuna mata da halin da ta shiga ɗazu a tsakanin dangan kara da ƙaya ta shige mata cikin mazaunai, banda Lami ta cire mata da bata san inda za ta saka ranta ba kuma har yanzu wurin ciwo yake dan ɓarin mazaunan nata ma wanda ƙayar ta shiga bata bashi ƙarfi idan tana zaune saboda ba ya zaunuwa, bare kuma shi da allura ƙarfe ce har ta fi ƙaya zafi. "Bari in taimaka maka" Cewar Lami tana yi wa Inna signa, Inna ta taso daga gadon tana danne dariyarta ganin Malam ɗin sai gaba yake yana baya tamkar mazari, ga hawaye sai fitowa suke daga makancaccan idanunsa. Dakyar ta samu ya juyo mata bayan aikuwa ta saka hannuna cikin wandon a saitin inda allurar take dan dama Lami ce ta soka allurar a wajen dan kar ya zargi komai shi ya sa aka ce ya zauna a kan kujera dan ta san dole zai ce zai dawo kan gadon kusa da ita. "Wallahi duk kunya nake ji, a ce amarya da ni saukar yanzu tsal ɗin nan a gidanka amma na saka hannu a wandonka ai abin da kunya faɗa da mai gari ranar sallah" Lami ta faɗa da muryar Duduwa. "Kayya Duduwa ai ana bikin duniya ake na ƙiyama wa ya ce miki ana batun kunya a nan wurin ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, kula ki zara hannun ki cire mini allurar, ke da za a yi mai ɗungurugum ( Mu,amalar auratayya) Mene ne dan kin saka hannu a wandon ango" Inna tana ɗan danne dariyarta ta taɓa wajen allurar ta danna ta shige duka sai ɗan tsinin da bai gama shigewa ba, hannu ta saka cike da mugunta ta danna allurar ciki aikuwa Malam ya yi wani uban tsalle ya zandama ihu tare da sakin wani marayan kuka ya ƙanƙame Inna, irin yadda yara suke ƙanƙame mutum in ya riƙe su za a musu allura. "Ai bari ba shegiya bace da ubanta, ai da alheri uwar kishiya ta hau kura" Cewar Inna a zuciyarta. "Sannu Malam ban san a nan allurar take ba" Cewar Lami da ta lura da abin da Inna ta yi masa. Malam kuwa bai samu damar magana ba sai kai ya gyaɗa kamar ƙadangare haka Inna ta matse gefen mazaunin nasa daga cikin wandon Lami kwa ko ta kansu bata bi ba ta juya musu baya, har sai da Inna ta yi dibarar fito da allurar bayan ta gana masa azabar haushinsa da take ji na kishiyar da ya mata. Hannunsa ta kamo ta zaunar da shi a bakin gadon tana bashi haƙuri a kan wata ƙila ƴan kawo amarya ne wata ta ajiye allurar bata sani ba. "Duduwa amarya ina ledar kazar nan?" Cewar Malam bayan ya ji shi a zaune. Wata harara Inna ta aika masa tare da ɗakko ledar kazar ta dangwara masa a kan cinyarsa. Aikuwa ko haushin ɗora masa a cinya bai ji ba domin kirarin da ake yi wa amare na amarya bata laifi. Hannunsa har karkarwa yake wajen buɗe ledar ya kai hannu yana ɗan tatttaɓa naman, hannun ya saka a baki ya suɗe aikuwa da sauri ba shiri ya saka harshensa ya shiga lashewa saboda wani raɗaɗin yajin kazar da ya luntuma hannu a kan yajin shi ne ya taɓa bakinsa da ya buge ɗazau dan gabaɗaya bakin ya yi tozo ya kumbura dan Malam ɗin har ya sauya kama. "Kai ta yaya zan ci naman nan duk burin da na ci a kansa ga shi na ƙare da kumburarren baki, haka kawai baki ya mini zuntuntum sai ka ce tozon raƙumi" Ya faɗa a ransa yana daurewa bai ce komai ba saboda kar amarya ta ɗauke shi ragon namiji dan kar ta cigaba da ɗaukansa kamar ba jarumi ba. Hannu Inna ta miƙa cikin ledar za ta ɗauki naman dan ita ma yawu ya taru a bakinta dan har ɗisa ma sai da ya yi saboda son ta ji naman a bakinta an daɗe ba haɗu da gasasshiyar kaza ba shekaru aru-aru, wai shekara dubu annabi lada in ji bahaushe. Ai kafin ta ɗauka Malam ya yi saurin dafe mata hannu sai da ya riƙo hannun nata, ya sa hannunsa ya taɓa tafin hannun nata ya ji bata ɗauki naman ba, sai ya ɗauke shi daga kan ledar kazar ya dangana mata hannun da jikinta ya ce "Haba amarya ai bana son ki yi aiki ki wahalar mini da kan ki" "Ai ba wahala bace a cin nama ina aiki" Lami ta faɗa Inna kuwa sai harararsa take. "A hannu zan ke danƙa miki amaryata" Ya faɗa yana ɗan jan ledar gabansa. Wata ƙatuwar tsoka ya ɗakko, Inna kuwa da sauri ta miƙa hannu dan ƙarfin hali kaɗan ya rage ta ce masa ga hannun nawa tun da ba gani yake ba, sai dai idanun nashi a buɗe suke kasancewar makantar daga baya ta same shi, amma kuma tunawa da ta yi cewa Lami ce take maganar Duduwa sai ta yi shiru ta dakata ta ga iya gudun ruwansa. *JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW Page5️⃣➡️6️⃣ Sai da ya duƙunƙune tsokar a wuri ɗaya, ya dunƙuleta a hannunsa sannan ya nufi bakinsa da ita amma cikin rashin sa'a naman ya yi girma kasancewar fatar bakin a kumbure take dan yajin jikin naman ma da ya taɓa wajen kumburin da sauri ya janye naman ya lashe wurin yana jan iska dan zafin yajin ya ragu a wajen kumburin. Amma dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama haka Malam ya saka ɗaya hannun nasa ya ɗaga laɓɓan dan ya ci alwashin naman nan duka zai tura a baki haka ya danna tsokar nan ta cika bakin ga kumburin leɓan sai bakin ya koma kamar shantu, ya yi wani zototo, Malam na kiciniya da wajen wawulonsa da babu haƙori wajen tauna naman wani uban raɗaɗin zafin yajin da ya shiga kumburin ashe ya ɗan fashe wajen wani zabura da ya yi babu shiri ya tofo naman yana damƙe wa a hannunsa na hagu. Kallon kallo aka shiga tsakanin Inna da Lami ganin Malam yana tanɗar baki a take suka fara dariya marar sauti. Kafin ya gama jin raɗaɗin yajin Inna ta yi saɗaf-saɗaf ta ɗakko haƙarƙari ta yaga a bakinta ta miƙa wa Lami sauran. "Amarya ungo nan ni wannan laɓɓan nawa ba zasu barni in ci da daɗin rai ba sai dai ko in ke ci da gutsure-gutsure" Ya faɗa kamar ya yi kuka, ya miƙa wa Inna wani da ya ɗakko ɗin yana cewa "Ai soyayya ruwan zuma buɗe bakin in baki" Ya faɗa yana miƙa hannu ya shafo bakin Inna sannan ya miƙa naman Inna kuwa ta buɗe bakin ya saka mata aikuwa cikin mugunta ta haɗa da yatsunsa guda biyu ta gantsara masa cizo ai da sauri ya warce hannunsa yana danne zafin cizon da ta kafa masa haƙoranta masu tsini dan kar ta ga ragwantarsa. "Malam ɗina cizon so ne fa na maka, ina sonka" Lami ta faɗa da muryar Duduwa. "Aikuwa na tsinci shi har cikin zuciyata ni ma ina sonki Dududuwa" Malam ya faɗa kamar zai yi kuja amma ya, ya iya da abin da ya fi ƙarfinsa ai dama faɗan da ya fi ƙarfinka maida shi wasa dan babu yadda zai yi amma tabbas ya sha azaba a cizon, wuri uku kenan suke masa raɗaɗi, mazaunansa, inda allura ta shige masa, bakinsa inda ya kumbura ga kuma yatsunsa biyu da yake jin dafin haƙorin amarya a jiki, dan ƙafarsa bata masa ciwo inda ya taka ɗankunne. Inna tana gama taune nama da ta haɗiye, ido Lami ta ƙifta mata dan dama komai a shirye suka yi, dan haka Inna ta miƙa hannu ta maƙalo wuyan Malam da hannu biyu, Malam jin hannun amarya a wuyansa dai ya ɗauka soyayya ce za a nuna masa dan haka bai san lokacin da ya manta da duka ciwukan da suke damunsa ba wani irin washe baki ya yi dan ya san an zo kan gaɓa wato cin amarci, don a ganinsa tun da kaza ya ƙi ciyiwa da daɗi rai ai gwara ya ci amarcin kar ya yi biyu babu. Dan haka cikin zumuɗi ya saki naman hannunsa wanda ya saka a baki ya fiddo ya damƙe a hannun hagu amma duk da ya shirya kwasar ganima da romon so da ƙauna hakan bai sa ya manta da ledar kazar amarci ba hannu ya sanya ya janyota aikuwa Inna ta saka hannu ɗaya za ta ɗauke ledar hannun nata ɗaya kuma yana wuyan nasa. Janyewa ya yi ba tare da ya ce komai ba ita ma ta ƙyaleshi ta mayar da hannun wuyan nasa. "Ina sonki Duduwalleta, duk duniya babu macen da ta kaiki, sauran duk muna mata ne ke kaɗai ce mace sabo... Kafin ya kai ƙarshen maganar Inna ta fara ƙoƙarin aiwatar da abin da za ta masa dan kirarin da ya yi wa Duduwa wani haushi da kishi ya turnuƙeta hakan ya sa bata yi wata-wata ba ta miƙa bakinta kan bakin Malam. Shi kuwa gogan tunaninsa kiss za a masa na soyayya dan haka a ransa yake raya cewa an zo wajen. Bai zata ba bai tsammata ba sai ji ya yi Inna ta haɗe kumburarrun laɓɓansa ta damƙe a nata bakin. Ƙafafu ya shiga haurawa tamkar wanda yake gangarar mutuwa. Bakinta da abin yajin naman da ta ci dan haka abin sai ya haɗe wa Malam biyu wai shege da hauka. Tun da ta damƙi laɓɓan Malam take ta faman tsotsa ta ƙi saka wa Malam wani raɗaɗi da zugi ne suka ratsa bakinsa har ƙwaƙwalwarsa yake ji dan haka ya shiga tura Inna amma Inna ta yi ƙememe ta ƙi sakinsa dan haka sai ya shiga zullo yana haura ƙafa tamkar wanda ake cire wa rai dan shi kaɗai ya san azabar da yake sha. Inna da take masa abin da mugunta musamman da ya ce wai Duduwa cw mace su sauran suna mata ne bayan ita kaɗai ce matarsa tun auren saurayi da budurwa tun kan Allah ya saukar masa da makantar da ya samu daga ciwon ido, soyayya da kula wa kai har da alƙawarin ba zai mata kishiya ba amma sai yanzu tsofai-tsofai da su zai auro mata ƙawarta aminiyarta Duduwa, Duduwar da cacakurukuci cikon banci ce amma har yake ikirarin ita ce mace. Kishi ya saka Inna ta ƙara damƙe laɓɓan har da ɗan gatsawa da haƙori. Azaba ta saka Malam sakin fitsarin wuya sai da Inna ta tabbatar ya wahaltu tare da jigata sannan ta saki laɓɓan aikuwa Lami ta taƙarƙare cikin muryar Duduwa ta ce "I lobiyu wujiga-wujiga Malam" Malam da bai gama jin raɗaɗin ba wani irin haushin amaryar tashi ya ji dan shi dai bai ga kyan wuri a kunnen jaki ba dan ko kusa wannan abin da aka masa bai yi kama da soyayyya ba soyayyar ma wujiga-wujiga. Amma gudun kar ran amarya ya ɓaci tun da an ce amarya bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida dan haka ya mayar da ƙwallarsa ya ce "Na gani Dududuwa, nikwa na ga ƙauna muraran gata kina nuna mini" Ya faɗa amma cikin ƙarfin hali dan shi kaɗai ya san abin da ya ji a kiss ɗin da ta masa. Inna kuwa kallon bakin Malam ta yi sai ta ga ya ƙara tsini a kan da kumburin ya ƙaru tamkar an hura balo wata dariya ce ta kusa ƙwace mata amma sai ta danne Lami ce ta kashe murya cikin kwaikwayon muryar Duduwa ta ce "Bari in ƙara maka na san ka ji daɗin abin dan da ganinka har ka shiga yanayi irin yanayin da angwaye suke shiga ranar da suka tare da amarensu na shauƙin ƙauna" Lami na gama faɗar haka Inna ta ƙara miƙa hannu ta cafko wuyan Malam, ai Inna bata ankara ba sai ganin Malam ta yi zumɓur ya miƙe tsaye kamar an tsikare shi. "Lafiya angona ina za ka je kai da muke tsaka a filin soyayya kafin mu tsunduma kogin ƙaunayya" Sai lokacin ma Malam ya gane wautar da ya yi ta tashin tsaye, dan haka cikin wayancewa ya koma ya zauna yana sakin wani murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo ya ce "Ni dai ba sai kin sake mini irin wannan ba bakya ganin yadda bakina ya koma kamar na zomo kar gobe almajiraina suke kallon bakin suna mini dariya kin san yara da sheƙiyanci bare kuma ni ba gani nake ba" Kallon bakin nasa Inna ta yi aikuwa ta ga ya koma kamar na zomon dan har ya fi na zomon ma tsawo. "To mu ci naman" Lami ta faɗa cikin muryar Duduwa. 'To ya ce dan shi kwata-kwata ma ba ya gane cewar wacce ke kusa da shi ba ita ce ke magana ba duk da ita ma Lamin a kusa take da su amma sanin daga shi sai amarya a gidan kuma bai taɓa tunanin ko a mafarki Inna da Lami za su masa wannan ƙanƙanci ba. Haka yake zaune zugum kamar an ajiye turmi dan naman ma sai ƙaran taunar Inna yake ji dan shi babu halin ci ga yawunsa banda tsinkewa da taruwa a bakinsa babu abinda yake sai dai ya haɗiye dan babu yadda zai yi naman kazar da tun ba yau ba yake saƙa yadda zai masa cin wulaƙanci dan a yau tun koko da ya sha da safe shi ma dakyar ya sha kokon dan tun da ya fara kissima ɗanɗanon kazar a bakinsa yana tunano yadda zai ji zauzau a bakinsa to fa duk wani abu da zai sa a bakinsa sai ya ji lami shataɓ amma kuma ga shi yanzu babu yadda zai yi ya ci naman cikinsa sai kira ciroma yake dan babu komai a ciki sai yunwa. "Kai angona amma ɗan garki mai nama ya iya gashi, kazar nan dan daɗi kamar kunne na zai tsinke" Ya ji muryar Lami a matsayin ta Duduwa ta daki majiyar sautinsa wani takaici ne ya baibaye shi, dan shi ina zai adar da baccin makaho tun da ba cin naman ya yi ba, banda guda ɗayan nan da ya danna zai masa cin mun daɗe bamu haɗu ba amma abu ya ƙi da daɗi sai fito da shi ya yi wanda shi bai san ma inda ya faɗi ba dan yana riƙe a hannunsa amma azabar da ta ziyarce shi lokacin da Inna ta yi wa laɓansa kamun gugan mai janyo ruwa a rijiya hakan ya saka bai ma san ya jefar da shi ba. Inna kuwa abinsu bajau ita da jikarta, idan ta ɗau naman ɗaya sai ta miƙa wa Lami ɗaya, a haka suka ci suka ƙoshi dan kazar ƙatuwa ce dan haka sun ci nama sun more abinsu ai da suka cinye tas Inna ta zuba ƙasusuwan a cikin ledar. "Amarya idan kin ci ki ɗaure sauran ki bani ledar in saka a fanteka zuwa tsakiyar dare idan na falka in bakin nawa ya sassauta mini sai in ji dan baki ji yadda cikina ke kiran ciroma ba sai ƙara dake ƙululu-ƙuluuuuu, idan kuma bai sace ba da safe sai in ci dan jinsa nake ya yi wani luhuhu kamar an busa balan-balan" Malam da duk takaicin yadda taunar Inna fa cika masa kunne ya faɗa dan kar ta je ta yi wa naman cin mugunta ta rage masa kaɗan. "Allahu akbar kabiran, Allah sarki angona, na Duduwa bada kanka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, ai ni da na ga bakinka a kumbure na ɗauka ba za ka iya ci ba dan gabaɗaya na gama yi wa naman nan aiki sai dai idan ka siyo mana na gobe idan kana da rabo bakin ya sace sai ka ci... "Duduwa! Kika ce kin cinye naman duka ina nan zaune gaho kika cinye sai ka ce wanda kike zuba wa buhu ba a ciki ba, to wa ya ce miki naman kaza koko da ƙosai ne da za ki tunanin gobe ma kawo wa zan yi yo idan dai ba fara zan sa almajirai su kamo miki ba idan sun je gona yin ciyawa su kawo ki silala a siyo ko majan murtala (20) Ki soya da lan manda(Gishiri) Ki maida yawun bakinki ina na ga wani kuɗin kaza kin san rabon da na ci naman gashashshiyar kaza to aradu tun ranar da aka kawo Uwani gidan nan tun ta amarci shekaru saba'in da ɗori" Cewar Malam da ya harzuƙa wani takaici da haushin amaryar tasa ya turnuƙe shi jin wai ta cinye naman har tana ikirarin gobe zai samo bayan wannan ma kuɗin larabar da yake karɓa a wajen almajirai ne yake tarawa ya suyo naman da shi. *JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW Page7️⃣➡️8️⃣ "Fara fa ka ce Malam?" "Haka na ce" "Ikon Allah na zaune ya faɗi, yanzu amaryar taka ce sai ka ce wata amaryar alade za ka ce a kamo mini fara, farar ma wai in soya da manjan murtala (20) Kuka ba ma in saka yaji ba sai ka ce wai in sa manda(Gishiri) Sai ka ce wata tsohuwar mayya" "Yo da ban, matar da kike hallaka kazar amarci a lokaci ƙanƙani ki ƴar kunyar nan ta amare babu da yanga da suke yi sai kawai ki cinye" Ya faɗa a ransa a fili kuma sai ya ce "Yo ai kin san yanzu rayuwarce sai a hankali Duduwa, komai tsada yake in ma ba ni ba mai ƙarfin hali ɓarawo da sallama waye zai kai wa amarya kaza a wannan zamanin mulkin Tinubuyya ( Tinubu) Mulkin da ake ganin har gwara Bahariyya sau dubu, to yanzu ko saurayi ne ya auri budurwa kifi yake kai mata a matsayin kazar amarci" "Kifi fa ka ce Malam?" "Kifi mana, yo kifin ma ba ta samu ba ina laifi wai bikin ƙanwar kishiya ka bada jaka guda (200) To wajan masu tuyar kifi angwaye ke zuwa su bada kuɗi a naɗe musu kifi sadin tanƙwashe biyu,sai su siyo gurasa ta sha ƙuli-ƙuli da albasa to idan suka riƙo ledar ƙawayen amarya ba za su ji ƙarnin kifi ba bare su yi wa ƙawarsu amarya gorin ba a kaoo kaza va dan ƙamshin ƙaragon gurasar nan sai su ji tamkar ƙamshin kaza, idan suka tafi sai ango ya buɗe su ci kayansu babu wanda ya sani sai ya ce bakinta alekum ko ƙawaye sun zo neman sauran kazar amarci ta ce mage ta ɗauke" "Taɓ" Lamu ta faɗa da muryar Duduwa. Hannu ya miƙa ya warto ledar hannun Inna ya shiga buɗawa yana lalume aikuwa banda ƙasusuwa babu abin da ya ci karo da su a cikin ledar dan ƙasusuwan ma duk yawu ne a jiki alamar an gama tsotse su. Haka ya saki ledar ta faɗo daga kan gadon yana jin wani takaici da haushi kamar ya yi kuka, yana tunano yadda ya yi ta saka rai a naman amma ga shi ko tsoka ɗaya bai haɗiya ba, ya tuno yadda abokinsa Malam Liman ya yi ta haɗiyar yawu saboda ƙamshin kazar amma ya hana shi ashe dai shi ma ba zai ci ba. "Wallahi sai na yi Allah kaimu" Ya faɗa yana sakkowa daga kan gadon ya shiga lalumen ƙasa. Inna da Lami da ido suka bi shi suna son ganin abin d yake so ya yi. Aikuwa haƙarsa ta cimma ruwa domin kuwa ya yi nasarar ɗora tafin hannunsa a kan ƙatuwar tsokar da ta faɗi a hannunsa wacce ya saka a baki taƙi ciyiwa. Haka ya ɗakkota yana ta faman faɗin. "Allah na gode maka ashe dai da rabona ai dama rabon kwaɗo ba ya hawa sama" Ya faɗa yana tasowa riƙe da naman ya zauna a kan gadon ya ce "Riƙe mini nan amarya idan na kwanta ki miƙo mini dan yau ko ana ha maza ha mata sai na ci naman nan" Ya faɗa yana miƙa wa Inna ta karɓa. Inna da Lami sai ganin suka yi ya kwanta a kan gadon ya yi reran ya miƙo hannu ya ce amarya ta bashi naman Inna ta bashi aikuwa ya shiga cira tsokar nan sai da ya cira ta gida uku yana daga kwancen. Ɗaya bayan ɗaya ya shiga jefa wa cikin hanga-mamman bakinsa da ya buɗe duk da yana jin raɗaɗi amma ya sha alwashin sai ya ci naman. Haka ya dinga saka wa cikin dibara yana cinyewa dan wani ma idan ya jefa haɗiye wa yake ba tare da ya tauna ba. Sai da ya cinye duka ya tashi zaune yana lamushe baki yana suɗe kumburarran bakinsa da yaji ya ɗan taɓa. Sai lokacin ya ji ɗan dama-dama a ransa amma da ransa ƙuna yake na rashin cin naman duk da kaɗan ya ci ba haka aka so ba ƙanin miji ya fi mijin kyau amma dai wanda za shi sama ya taka leda haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya. Bayan ya ya tashi daga zaunen da yake, ya miƙe tsaye yana wani baza babbar rigarsa, aka cire huta tare da rigar gabaɗaya kusa da Inna ya matsa yana rattabo mata kalaman soyayya duk zatonsa Duduwarsa ce amaryarsa. Lami ganin haka sai ta fice daga ɗakin, Malam Ashiru haka ya shiga gabatar da sunna da Inna sai da ya ci amarcinsa son ransa. Haka suka fito da shi da Inna za su je bayi yin wanka sai yabon Duduwa yake yana kushe Inna Uwani bai san cewa da Innar yake tare ba dama ƴan magana sun ce rashin sani ta fi dare duhu. Dama Inna da Lami sun gama shirya yadda komai zai kasance dan Lami ta ce Inna za ta tafi gida ita kuma za ta yi muryar da za ta tsorata Malam dan Lami babu muryar da bata iya yi. Dan haka sai ta cewa Inna ta tafi ita za ta biyo bayanta idan ta gama abin da za ta yi. Malam suna fitowa sai Inna ta sakar masa sandarsa da ta ɗauki wani takalminta ɗan madina a ƙofar ɗakinta ta lallaɓa ta fita ta kafar da suka shigo sai dai wannan karon bata sha wuya wajen fita ba. "Amaryata ina kika yi wai, ai yau take sallah gaskiya na ji daɗi da kika aure ni Duduwalleta" Ya faɗa yana wani washe baki har kunne amma kuma sai ya ji shiru can sai ya ji wata murya mai abin tsoro ta ce "Mu ne mutanen ɓoye mun ɗauke amaryarka mun tafi da ita kogon aljannu" Lami da ta maida muryarta ta ƙaton namiji ta faɗa tana daga can gefe idanunta a kan Malam. Malam sakin sandar hannunsa ya yi, a take jikinda ya ɗauki karkarwa, ƙafafunsa suke neman kasa ɗaukan gangar jikinsa wani fitsari da ya matse shi yana so idan sun je bayin zai yi a take ya shiga bin ƙafafunsa lokaci ɗaya ya yi jargaf da shi dan dama ya cire wancan wandon da ya yi fitsari a ciki yanzu ma wannan ɗin ya jiƙe kamar an sheƙa masa ruwa. Hannu ya fara bazawa alamar lalume tun da ba gani yake ba kuma ya saki sandar tasa da ta kasance ƴa jagorarsa, gabas ya yi sai ya dawo ya yi yamma, hallaw ya yi arewa ya rasa ma ina zai yi duk ya ruɗe. "Muna so ka fito da jelar biri a mazaunanka dan mun ga kamarku ɗaya da gwaggwon biri in ba haka ba yanzu za ka ji ka yi sama kana tashi kamar tattabara" Muryar nan mai ban tsoro ta katse Malam. Tsabar ruɗanin da ya shiga sai kawai ya shiga zagaya inda yake tsaye tamkar dai yadda ake ɗawafi. "Ya Allah ka fito mini da jela jela zankaɗeɗiya" Faɗa yake cikin muryar kuka dan shi gabaɗaya ma ya sare tun da an ce an ɗauke Duduwa kuma shi kaɗai ne a gidan yau ai sai ta Allah. "Dakata!" Aka katse shi da muguwar tsawa, ita kanta Lamin sai ta danne dariyarta ganin irin halin da Malam ɗin ya shiga. Malam kuwa da sauri ya ƙame a waje ɗaya tamkar soja haka ya dakata da abin da yake yi cikin bin umarni dan yadda yake jin muryar a kusa da shi ya san komai zai iya faruwa da shi. "Tun da baka fito da jele ba ka fito da cikin wata tara a jikinka" Da hanzari Malam ya saka hannu biyu ya dafe cikinsa, yana jin wani iri a ransa in har aka ce ya fitar da cikin wata tara a jikinsa aikuwa an tashe shi tsaye domin kuwa shi dama tsigi tsila ne babu ko ƙibar kirki a jikinsa bare a yi zancen timbi har ta kai ga samun cikin wata tara, shi da ko tafiya yake tamkar iska za ta kwashe shi ta watsar haka yake. "Fiddo ciki ko ƙusumbi" "Hasbunallahu wa ni'imal wakil ni Ashiru na ga ta kaina yau, Allag gamu gareka ɓarawo a hannun mata" Cewar Malam yana karkarwa dan maganar cikin nan da ta ƙusumbi ba ƙaramin dulmiyar da tunanin Malam ya yi ba a take ya ɗauke hannayensa daga kan cikinsa ya miƙa ƙeyarsa ya taɓo bayansa inda ƙusumbi yake fitowa nan take ya hango shi a idanun zuciyarsa yadda zai koma kamar aljani matsawar aka fito masa da ƙusumbi ya san ba ƙaramin aikin aljani bane ya fitar masa da ƙusumbin. Da sauri ya zube gwiyoyinsa a cikin caɓalin ruwan nan na sama ya haɗe hannuwa ya fara roƙo da ban haƙuri. Lami kuwa a hankali ta matsa kusa da Malam ta miƙa hannu ta dafa bayansa saitin inda ƙusumbi ke fitowa mutum. Wani irin ɗauke wuta Malam ya yi cike da bala'in tsoro a take ya ji ya fara kokawa da numfashinsa dan ji ya yi tamkar za a ɗauki ransa ne. "Yau na ga ikon Allah ɓatan nono a ƙirjin budurwa ni Ashiru ni ne yau a daren amarcina da Duduwa durƙushe a ƙasa cikin ruwa aljani yana dafe da bayana ya Allah ka sanya kar ya fitar mini da ƙusumbi jama'ar gari suke guduna" Ya faɗa a ransa hawaye suna ambaliya a fuskarsa. "Za mu sanya maka sharaɗi" "To, to, to, ku faɗa ko mene ne zan muku amma kar ku mini cikin wata tata ko ƙusumbi ku taimake ni k... "Ba ma son yawan magana" Ɗiff Malam ya yi yana danne kukan da ya taho masa. "Ko da wasa idan amaryarka ta faɗa maka magana dangane da daren yau ka ce to dan za ta iya iyuwa ba da ita kuka zauna ba da ɗata daga cikin jinsinmu ne dan ita mun ɗauketa kar fa ta nuna maka bata san da wani zance ba ka yi musu" Lami ta faɗa cikin muryar da take tsorata Malam ɗin da yake tunanin aljannu ne a tsakiyar daren nan, dan ta yi hakan ne dan kar Duduwa ta ce ba ita ta ci nama ba ya zargi wani abu duk da ta san tunaninsa ba zai taɓa bashi su ne suka zo suka masa wannan ƙanƙanci ba. "An gama" Ya faɗa yana wani gyaɗa kai da sauri da sauri. "Za mu barka amma da cewa na yi zan fito maka da ciki na wata tata da ƙusumbi lokaci guda in barka a haka sai kuma in motse kan ka ya koma kamar na ƴan ruwa in mayar maka da ƙafafu kamar zabirar wanzan, kan ka kuwa sulsul zwi dawo wa ya ga sulluwaye" "A mini rai tuba nake" "Ka tashi ka kama gabanka" Lami ta faɗa da muryar tana ɗauke hannunta daga bayansa sai kuma ta saka ƙafa ta dungure shi. Ai a gigice Malam ya tashi yana karanto salatin annabi kafin ya kai sai ya kamo alamnashrah duk ya duburburce sai miƙa hannu yake yana lalume abinka da makaho ba gani yake aba. Caɓal-caɓal kake ji Malam yana faɗa wa cikin guntayen ruwan da yake tsakar gidan tsabar gigicewa hanyar kijin talo-talonsa da yake kiwo ya nufa wanda tun la'asar ɗin fari ya sa aka rufe su duk dan riɗin zuwan amarya bayan ba a rufe su sai da magariba. Yana zuwa bum-bum kake ji yana ta gwaruwa da jikin langa-langan kejin can dai ya samu ya ɗora hannunsa a kan ƙofar kejin, duk tunaninsa ƙofar ɗaki ce amma bai san wane ɗaki bane dan shi tunaninsa ko wane ɗaki ne ma ya je burinsa kawai ya ceci ransa daga aljannun nan kar su masa cikin wata tara ko su fito masa da ƙusumbi. Ga sun ce za su mayar masa da kansa irin na ƴan ruwa ya san kuwa kan ƴan ruwa tamkar ƙwarya ko tulu haka yake, bare ma sun ce kan nasa taltal za su masa ai kawai aljani sak dan ya san idan suka mayar da shi haka to daga ranar sai dai ya tashi daga suna Malam Ashiru ya koma Malam Ifritu. Lami tana can gefe tana dariya har da riƙe ciki har wani sunkuya wa take saboda yadda dariyar ke cin ƙarfinta amma marar sauti take yi. "Hahahahhhhahh" Ta saki wata ƙatuwar dariyar da ta saka Malam tsabar ruɗewa har amsa kuwwa ya ji tana masa. A take ya ja ƙofar kejin wacce tana da ɗan faɗi dama kasancewar talo-talon na da ɗan girma. Yana cin nasarar buɗewa sai kawai ya afka cikin kejin ji kake burum ya shige ciki amma kuma rabin uban jikin ne ya shige kasancewar cikin babu wani space sosai. Yana shige talo-talon suka tsorata a take suka fara karo da juna suna neman wurin gudu dan duk ya hargitsasu. Fat,fat,fat kake ji ƙaran gwaruwar junansu. Malam kuwa yana jin yadda suke gwaruwa shi da ba gani yake ba sai ya ƙara tsorata kasancewar an ce dabbobi suna ganin aljannu sai ya yi tunanin aljannu ne suka biyo shi, shi ya sa da suka gan su suka tsorata, wannan ya sa ya ƙara tsorata dan ya san tabbas abinda ya tsorata dabba to ina kuma ga mutum. *JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW *JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW Page9️⃣➡️🔟 Ƙara kaimi Malam ya yi wajen totsuwa dan so yake ya ji shi ya shige cikin ayarin talo-talon ko ba komai ai ya yi ɓadda kama a cikinsu idan aljannun sun ƙaraso ya samu rangwame. Totsuwar da ya fara yi wani cikin kijin yana so ya shige duka jikinsa aikuwa wani talo-talo ya cako bakin Malam wani zafi Malam ya ji a bakin nasa da yake a kumbure har lokacin kafin ya gama jin raɗaɗin wani talo-talon ma ya cako hancinsa sai kawai Malam ta saki kukan takaici kuka mai sauti ma kuwa saboda yana tunano wai shi Malam Ashiru mai almajirai da mutane suke girmama wa almajirai suna jiran ya bada umarni su aiwatar wai shi ne yau a cikin kejin talo-talo har talo-talon suna cakon bakinsa da hancinsa. Kukan da ya saki hakan ya yi dai dai fa zuwan Lami wajen aikuwa ta daddage ta ɗaga hannu ta daki jikin langa-langan. "Wayyo ni Malam Ashiru na ga ta kaina, wbin ya mini yawa shege da hauka ashe dai kejin talo-talon da na shigo a zatona ɗaki ne, kuma da na gane keji ne tunanina na tsira ashe dai akwai ya babu ne kakar wajen uba, an yi ba a yi ba juyin fatar fara" Ya faɗa a zuciyarsa yana sakin kukan takaici yana jin ina ma dai zai ɓace ɓat domin ya tsira daga tsoron aljannun nan da ya cika masa zuciya. Ƙara buga kejin Lami ta yi ai sai kawai Malam ya iyo baya ya fito daga kejin dan ya gane babu mafita gwara ya nemi wata mafakar. Yana fitowa ya yi taga-taga zai faɗi bugun da Lami ta yi wanda ya fi na farko shi ne ya saka Malam ya bazama da ɗan gudu-gudu cikin sa'a sai ya faɗa kewayen Inna Uwani lalamen ƙofa ya fara aikuwa ya ji ta rufe da ɗan kwaɗo. Sai lokacin ma ya tuno ashe fa Innar bata nan dan haka sai ya shiga lalamen windown cikin ikon Allah ya samu dama takalmansa tuni ya warɓar da su wajen gudun famfalaƙin ceton ransa daga aljannu . Yana jin ya ɗora hannunsa a windown sai ya fara kiciniyar hawa aikuwa ya ɗane ya maƙalƙale buuuummmmm ɗin da ya ji na ƙaran kejin da Lami ta taɓa dan so take ya samu mafaka dan gidan Yaya Lado take so ta tafi ta ba Inna labari. Ƙaran nan ya sanya Malam hayewa windown bai ti wata-wata ba ya hantsila aikuwa da ka ya je, yana faɗawa da ka sai ya kwanta lifet a inda ya faɗa ya yi rubda ciki cikin faɗuwar da gabansa yake dufdufduf ya fara magana "Innahu min sulaimana, wa innahu bismillahir rahmarnir rahiiiim, Alamnashra lakasadarak, tabbat yada abilahabin watabbu, maaa agnee anhu maluhu wama kasab, wadduhee, wal laili iza saje, inna a'a ɗaina kalkausar" Haka Malam ya shiga rattabowa idan ya fara wata kafin ya ƙarasa sai ya sake ta ya kama wata surar idan ya yi aya ɗaya, biyu sai ya saketa yana cikin wannan halin na rayuwa ko mutuwa Lami ta zo ta buga ƙofar Innar dan ta san dole zai nemi mafaka, kuma dai mafakar ta san ba za ta wuce ƙasan gado ba dama kuma so take ya je wajen amaryarsa Duduwa da ke ƙasan gadon a cikin buhu idan ta falka sai ya yi tunanin aljannu ne suka kaita ƙasan gadon tun da dai ya san shi ma ta window ya shiga ɗakin domin ƙofar a rufe take bare ya yi wani tunanin da ban duk da ta san ko wace irin ƙwaƙwalwa gareshi ba zai taɓa gano abin da suka shirya ba sai dai in su suka faɗa da bakinsu. Malam cikin ƙarfin hali da rashin ƙarfin jiki dan duk jikinsa ya mutu saboda tsoro haka ya ƙuƙuta ya fara jan ciki yana tafiya da baya da baya, a haka ya ƙarasa wajen gadon na Inna sai wani nishi yake sakarwa tamkar wanda aka shaƙewa maƙoshi. Ƙafafun ya miƙa ƙasan gadon sai ya shige yana ta faman faɗar . "Lahaula wala ƙuwwata" A haka ya shige har kansa lifet ya kwanta tamkar babu rai a jikinsa yana ji a ransa bai taɓa shiga tashin hankali wanda ya gigitashi sama da na yau ba. *INNA UWANI* Tun da ta fito daga kafar karan dangan gidan Malam take jin ta a sama sai wani shauƙi take tana ta saka wa Lami albarka irin yadda ta ringa faɗi tashi har burinta ya cika dan tana ganin dai ga shi ta shiga gidan Malam salin alin ta fito ta kuma ci naman kazar amarcin Duduwa sannan kuma ta murƙushe amaryar a cikin buhun hatsi. "Allah ka yafe mini ai wallahi na yi hakan ne saboda auren cin amanar da aka yi mini tana aminiyata ta san sirrina amma ta aure mini miji, shi ma kuma dan rashin ta ido yana so ya nuna mini iyakata da kuma halinsu na maza ya manta da babina ina can na yi yaji sati ɗai-ɗai har uku amma ko ta kaina bai bi ba yana nan zai kwashi ganimar amarci da Duduwa, aikuwa baka kwashi amarci da sabuwar amaryarka Duduwa ba ka kwashi ganimar amarci da matarka Uwani" Inna ta faɗa tana sakin wata bazawarar dariya haɗe da wata gyatsa da take jin gabaɗaya cikinta a cike yake dam-dam. Tana cikin tafiya ta ji ta yi wata uwar sufa a cikin laka tagar-tagar ta yi za ta faɗi dakar ta yi nasarar tsayawa a kan ƙafafunta eata ajiyar zuciya ta sauke ganin bata kai ƙasa ba. Ƙafafunta ta zare daga cikin takalman nata da suka maƙale a cikin lakar ta saka hannu ta saka ta ɗauki takalman tana yin gaba abinta dan ita yanzu jinta take warai babu wata damuwa sai annashuwa. Cigaba ta yi da tafiya ko tsoro bata ji sai ma waƙar soriye da take rerawa har wani ɗan rausaya wa take yi, dan har tsaya wa take tana rawar ittigi a hanya idan ta yi, ta ƙara yi sai kuma ta cigaba da tafiya abin ta dan wani nishaɗi take ji wanda bashi da misali. "Mai akori kura tsaya a nan in hau ka kaini gida" Wani matashi da ya shawo kwanar da Inna take yana tafiya yana haɗa hanya ya faɗa cikin muryarsa da ya sha ya bugu. Inna kuwa tsaya wa ta yi ganin ya sha gabanta ta shiga waiwaye ko za ta ga akori kurar amma sai ta ga wayam babu kowa sai su kaɗai daga ita sai shi dan farin watan da ya haske duniya daga sararin samaniya shi ne hasken da suke amfani da shi wajen ganin juna dan daga ita har shi babu mai fitila dan basu ɗakko ba ita da Lami suna sauri a haka suka taho. Ƙoƙarin kewaye shi ta shiga yi dan ta tafi abinta fan ta ga babu mutane kar ya je ya libga mata shegen duka a zo ana A'i ina indo. Shi ma cikin rashin kuzarinsa ya ƙara tare gefen da Innar ta yi za ta wuce. "Haba kai kuwa jikana bani hanya mana in wuce in tafi ka tare ni a tsohon daren nan" "Ke!Tsohuwa waye jikan naki, kuma da kike batun tarewa ai ni cewa na yi ki tsaya in hau akori kurar ki kaini gida" Galala baki sake Inna take kallonsa wai jin ita ce za ta ɗauke shi a akori kurar sai dai kuma a take ta kawar da tunanin hakan duba da yadda yake a buge ta san kuwa shaye-shaye babu abinda ba zai saka ba tun da ba a hayyacinsa yake ba to dole ƙwaƙwalwarsa ,a ta nuna masa ƙarya. "Ni fa a ƙafata nake tafiya ko gare-garen wasan yara babu a hannuna bare wata akori kura" "Billahil lazi huwar rahmanu tsohuwa sai kin ɗauke ni, a kan me ga abin hawa zan tafi a ƙafa" "Oh ni Uwani na dawo in ji ɗan yawon duniya ni ce abin hawan? TO ƙur'ani ni kaɗai ce singil fakitin buɗe magananka da kyau ɗan nan, ko dai ka yi makuwa ne?" "Kin manta makau na yi ba makuwa ba, to yasin babu mai rabani da ke yanzun nan zan miki filla-filla yankan naman layya, ko in miki sala-sala" "A'ubillahi haba kai kuwa ɗan nan sala-sala sai ka ce wata lemon fata" "Kin ɗauki abin wasa, to ba wai duka zan miki ba aradu kalacin dare zan yi da ke dan wallahi yanzun nan zan kwaɓe in yi zigidir a nan in gurji amarci... "La'ilaha ilallahu, muhammadur rasulullahi, S.A.W yanzu ɗan nan dan ka kwashe kayanka daga gaban ma'aiki tsofai -tsofai da ni za ka gurjeni sai ka ce wata rigar da ta yi dauɗa?" "To shikenan kar ki sunkuya in hau bayanki bari ki ga aiki da cikawa" Ya faɗa cikin muryar buguwa yana kama wando. Ai da sauri Inna ta saki takalman hannunta ta zube a ƙasa gwiwa bibiyu ta duƙa irin yadda yara ke yin wasan doki, aikuwa saurayin nan bai yi wata-wata ba ya ɗaga ƙafa ya haye bayan Inna. Inna da ta ji tamkar an ɗora mata dakon tirela ta danne kukan da yake son fito mata. "Ja mu je, bari in sa giya" Ya faɗa yana karkaɗa ƙafafunsa a jikin Inna irin yadda masu hawa jaki suke kaɗa wa jaki ƙafafu idan suna tafiya a kansa, giyar kwa da ya ce zai saka sai da ya daidaici kunnenta ya kama ya murɗa tare da lanƙwasa wa har sai da ta saki ɗan ƙaran azaba aikuwa Inna jin azabar da ake gana mata sai ta fara jan ƙafafun tana rarrafa wa dakyar saboda nauyin saurayin. A haka suke tafiya shi kwa sai ƴar waƙa yake ya yi wa Inna sandan-dan a baya. "Da wane shegen ya fito da ke a tsohon daren nan?" "Daga gidana nake ɗiyata ce aka ce tana naƙuda ni kuma gozoma ce shi ne zan je can" Ta samu kanta da sharara masan ƙarya dan ta san muddun ta faɗi abin da ya fito da ita to tabbas zai iya mata tonon silili. Shiru ya yi bai ce komai ba a haka take tafiya dakyar ga santsin laka da yake jan gwiwarta da tafin hannunta ga nauyinsa a haka take bi ta cikin lan sauran ruwan da suke taru a hanya duk da zuwa lokacin ma ruwan duk ya janye ya shanye. Bai tanka mata ba sai dai ya cigaba da buga ƙafafun har wani is-is-is yake cewa irin yadda ake kiran tattabaru. Sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa ya kalli wata bishiyar kuka da k gefen hanya ya ce "Ga gidana can a can za ki ajiye ni" "Ina ne?" "Gashi can ai logon kukar can nan ne ƙofar shiga gidana" Wani sautin ƙululuuuuu cikin Inna ya bada a take jikinta ya shiga karkarwa lokaci guda kuma ta fara fitar da wata iskar tusa a jere a jere tamkar wata bodara. Dan ta san dai babu wani wanda zai ce gidansa a kogon kuka in ba aljani ba, a nan take ta fara tunanin kenan aljani ne a bayanta, amma haka ta daure ba ta ce komai ba amma har wata gudawa ta ji tana neman ƙwace mata. Ɓuuwwwt sautin tusar Inna ya daki kunnen saurayin. 'Mene ne haka tusa kuma?" "A yi haƙuri yallaɓai mai gidan kogo wallahi ba da sanina na yi ba suɓuce mini ya yi ban san lokacin da ta sufce mini ba" "Duk kin sa dakarun rundunar aljannun da suke biye da mu a kan ababen hawansu suna buɗe baki za su haɗiye ki saboda kin ɓata ransu" Ɓiiiɓiɓiiiit Wata tusar ta samu nasarar fitowa wata kan wata. Ga kuka marar sauti da Inna take gabaɗaya sai ta ji duniyar ta mata ƙunci tana da na sanin fitowa daga gidan Yayanta da tana can babu abin da zai da ta ɗauki aljani a gadon bayanta har rundunar aljannu suke binsu a baya. Sai ta ji dama bata je gidan mijin nata ba ta yi haƙuri ta jure. "Ki riƙe tusarki kar ki ƙara yi wa mutane tusa a nan in ba haka ba za ki ga kin ɓace ɓat ko kuma a rufe miki ɗuwawu babu ke babu wata tusa bare kuma kashi sai dai ki ga ana yi" Ya faɗa cikin muryar ƴan shaye-shaye dan har lokacin a buge yake. *JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW Page 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣ Jin ya ce za a rufe mata ɗuwawu ta daina tusar ma bare wani kashi, da sauri ta ɗauke hannunta ɗaya daga dafe ƙasa da ta yi. Miƙa hannun ta yi bayanta daitin ƙofar da tusar ke fitowa ta saka tafin hannun nata ta toshe ƙofar dan ta san idan har aka ce ta daina tusa da kashi ai babu lafiya yo ina za ta saka ranta a ce ka daina tusa da kashi ai ta san to kuwa akwai gagarumar matsala bare kuma a ce aljannu ne za su toshe maka ɗuwawu to a ina ma za a gansu bare a ce su buɗe to tabbas dole ta yi iya yinta dan ganin ta yi yaƙi da usjar tusar da take fitowa tana ƙoƙarin mata shamaki da yin kashi ma gabaɗaya wanda ta san ko likitoci ba lallai su iya ɓarke toshiyar da aljannun za su yi sai dai ta haƙura da yin tusa da kashi, idan kuwa haka ta kasance to tabbas ko abinci sai dai ta haƙura da ci tun da babu inda za a kasayar da shi. " Yallaɓsi ai ita tusar da kanta ta yi kaɗan ta ci ƙarya ta kwana da yunwa ta ƙara ƙetara umarninka tajawarka lafiya ai na done kafar da tusar takw fitowa babu yadda ma za a yi ta kufce ta fito. "Da dai ya fi tsohuwa mai rangwangwan, ga ki da tsoron jinsin aljannu kamar farar kura amma kuma kina fitowa tsakiyar dare lokacun da rundunar mu suke fitowa dan zuwa gidan biki da zuwa kasuwa ku kuma lokacin bil adama duk kuna bacci amma saboda kankanba kika fito, to yanzu da ke za mu shiga kogon kukar nan a yi shagalin bikin ɗan ƙundalo da ke" Ɓiriɓiiiiiit Ƙaran wata tusar da iskarta ta zarce a kan hannun da Inna ta toshe ta fito abinta sariri dan ƙaran har ya fi na sauran tusosin da ta ɓurɓurka ɗazu. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, amma ke kuwa tusa mai ya kai ki wannan ɗanyan aiki an ce ki daina fitowa su yallaɓai basa son jinki amma kika fito gaba yo ai sai ki bari idan na koma gidan Yaya Lado na shiga ɗaki sai ki yi ta keto hazo kina fitowa haba amma dan jan jafa'i za ki... "Ai kin zo kenan a nan za a sama miji a haɗa shagalin bikinki da na ɗan ƙundalo a kai ki can birnin sin" "Wallahi matar aure ce ni, Uwani ce matar Malam Ashiru mai almajirai na unguwar tudun tsira" Cewar Inna tana sakin kuka mai sauti. "Yanzu kuma za ki samu cigaba ki auri Sarkin aljannu kin ga kin tashi daga matar bil adama Malam za ki koma matar mutanen ɓoye a mutanen ɓoyen ma. " Wayyo Allah ni Uwani yau cuta ta ɗakko cuta akuya ta ɗakko akwatin miciji, dan Allah ku mini rai ku barni a jinsina wallahi ina da jikata marainiya bata da uwa bata da uba Lami ni kaɗai take da ni" "To kin ci sa'a amma yanzu za ki mana adungure bakwai kafin ki tafi" Ya faɗa yana sauka daga bayan Innar. Wani irin sagewa bayan Inna ya yi har ƙara ta ji ƙashin bayanta ya yi. "An gama indai adungure ce amma a caɓalin nan zan yi?" "To ko na kwanta ki yi a kaina?" "Ni shegiya Uwani wace ni, ƙaryata ta sha ƙarya" Ta faɗa tana wani bashi girma. Bai ce komai ba dan har lokacin ma ya kasa tsayuwa da ƙafafunsa dan kayan mayen basu saka shi ba. "Tashi ki duddungura" "Yanzu kwa" Ta faɗa tana tashi tsaye duk ƙafafunta a sage suke, tashin da ta yi ganin saurayin tsaye a gabanta sai ƙirjinta ya cigaba da lugude dan babu yadda za ta yi amma da tuni ta ari na kare(Ta gudu) Amma sanin duk gudun da bil adama zai yi ba zai tserewa aljani ba sai ta daure ta tsaya duk da ita ma tsayuwar tata bata da banbanci da tsayuwar saurayin domin kuwa ita ma tangal-tangal ɗin take saboda karkarwar tsoro da ƙafafunta suke yi, ga zaninta da je barazanar kuncewa sai ɗaurawa take amma sai kuncewa yake yaa neman sumɓulewa daga tsantsar tata amma saboda gudun yin tsirara gaban aljannu sai ta kama zanin daga tsantsa ta ƙanƙame. "Tsohuwa za ki iya fara wa" "To,to,to, ta ina zan fara?" "Tambayata ma kike?" "Ni kaza, ba haka nake nufi ba ina nufi daga kaina zan fara adunguren ko kuma da mazaunaina zai zan fara" Wata dariya saurayin ya saki jin abinda ta faɗa dan har ya hango yadda za ta yi adungure ta mazaunai. "Ki yi daga mazaunan, amma ba wai a nan za ki tsaya ba kuna dungurawa kina tafiya daga kin yi bakwa sau ki tashi ki tafi da ƙafafunki kuma ko da wasa kar ki kuskura ki ce za ki waiwayo" "An gama ranka shi daɗe na gode" Ta faɗa tana koma wa ta zauna tana tunanin ta inda za ta fara adungure fa mazaunan bata ma san dalilin da ya sa ta tambaya ko daga mazaunai za ta yi ba sai dai ta san hakan bai rasa nasaba da tsoron da kuma gudun yin ba dai dai ba dan duk a ruɗe take. Haka ta fara dungurawa amma dakyar ta yi ɗaya saboda wahala amma ya za ta yi a haka ta cigaba da tafiya shi kuma yana tsaye yana kallonta, tana ta dungurawa tamkar kunkuru haka Inna ta koma sai da ya ga ta yi biyar ya fashe da wata dariya da ta sa Inna ta fara dungura wa kafin ta ɗago ta sake juya mazaunan ta dungura ba ƙaramar wahala take sha ba da a ce ba a ce ba aljannu bane suka saka ta ba da babu yadda za a yi ta iya yin ko sau ɗaya ne. Yana gama dariyar ya fara waiwayen wajen kogon kukar jin wani ɗan motsi daga wajen cikin hanzari ya bar wajen dan shi ma a tsorace yake da wajen kuma rass yake ba wai a buge yake ba kawai tantiranci ne dan ya tsorata tsohuwar dan ya san dai babu wani abin kirki da zai sa ta fito tsakiyar daren nan ba. Shi ma daga yawo yake suka je wani ƙauye kallon wasa da samari ke gabatarwa shi ne da suka dawo abokin nasa ya ajiye shi a hanya ya tafi a machine ɗin dan dare ya yi yana shirin yin hanyar gidansu ya hango Inna tana tahowa tana waƙa shi ne ya fara maganar ƴan shaye-shaye. Inna kuwa tana ta dungurawa har ta yi bakwai amma saboda tsabagen ruɗewa bata ma san ta yi bakwai ɗin ba, dan haka bata dakata da adunguren mazaunan ba har sai da ta yi goma sha uku lokacin ta gama jigata dan haka sai kawai ta kwanta a tsakiyar hanyar dan ƙarfinta ya ƙare. Amma tsoro da fargabar kar aljannu su biyota su mata aure da jinsin su, su kaita birnin sin haka ta tashi zaune ta cigaba da jan ɗuwawu a ƙasa har Allah ya kaita gidan Yaya Lado amma kasancewar ba da saninsa suka fita ba dan in ya sani ma sai ya musu faɗa hakan ya sa ba za ta bi ta ƙofar gidan ba wajen shiga cikin gidan bare ma ƙofar a rufe take da sakata daga ciki. Lallaɓawa ta yi ta je inda suka hauro ɗazu ta katanga dan dama an ce ta inda aka hau ta nan ake sauka ha Inna ta kama katangar nan tana ƙi-ƙi-ƙiƙitun hawa amma cikin rashin sa'a ta kasa hawa da yake a hayowa ma sai da suka taka duro bare ɓa sai da Lami ta taimka mata ta samu ta sakko dan haka yanzu kuwa babu duro kuma babu Lami bare ta ciccigata. "Yauwa na ga ta kaina, kaza garen tone-tonenta ta tono wuƙar yankanta, yanzu ni Uwani ina zan saka kaina babu kowa a hanyar nan hallaw idan mutanen ɓoyen nan suka biyo ta hanyar nan haka za su ci mutuncina in banda tambaɗa ma kai da ɗuwawunka a ce ba za ka yi tusa ba sai abu ya zama jidali, haka kawai Allah ya halasta yin abu amma su haramta yin tusa haka kawai a ce wai za a toshe mini ƙofar fitowar kashi wannan jalala da na gani yau ai tafi gaban wasa, ga shi ban san lokacin zuwan lami ba bare ta taimaka mini tana can suna artabu da Malam ko ya aka ƙare" Ta kai ƙarshen maganar tana sakin dariyar mugunta tunowa da ta yi da yadda bakin Malam ya koma suntumeme. Sai da dariyar ta tsagaita sannan ta tashi ta shiga riƙetun hawa katangar dan ta san muddin aljannun nan suka kamata a wajen nan in har suka dawo suka tarar da ita to kashinta ya bushe. Katangar ta kama da hannun biyu ta ɗare sai dai ƙafafunta da take son hayowa da su daga ta ɗare su jikin katangar suke zamewa saboda ruwan da ya jiƙata. Amma dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama Inna bata daina yunƙurin hawa ba dan ta san bata da mafitar da ta wuce wannan. Tana cikin hakan ta kusa hawar da ƙafar tata kawai sai inda ta kama ƙasar jikin katangar ta ɓantale gabaɗaya Inna ta iyo baya idanunta duka biyu a zare tamkar za su faɗo sai ga Inna kwacar a ƙasa hannunta duka biyu riƙe da ƙasar da ta guntule daga jikin katangar saboda ruwan da aka yi katangar ta jiƙu sosai in da har wani ɓangare na katangar duk ya zagwanye. "Wayyo ni Uwani matar Malam Ashiru kakar Lamisa, ya Allah ka raba bawa da wahala wai gwauro a teburin mai shayi" Ta faɗa tana jin tamkar ta yi ta rasgar kuka da ƙarfinta yadda jama'a za su ji su kawo mata ɗauki. Sai dai kash babu damar hakan domin kuwa sakin kukanta da ƙarfi tamkar tonuwar asirinta ne dan ta tabbata muddun maganar abinda suka yi wa Malam da Duduwa ya koma kunnen Malam to tamkar ta saka kuɗinta ne ta sayi takardar sakinta da domin ta san dai babu fashi wai tusar asubar fari ga gauro dan farilla ne tusa a masallaci sai Malam ya yanke igiyar da ke tsakaninsu in ma bai yanke duka ukun ba ita kwa ina za ta kai wannan abin kunyar dan ta san har jikokin Lami ba za su tsallake gorin abinda suka yi ba idan har asirinsu ya tonu to ta shigegen dan lafinta za a gani tun da Lami yarinya ce. "Inna! Mai kike yi a nan har yanzu baki shiga gida ba?" Cewar Lami tana kama hannun Inna ta ɗaga ta daga kwancen da take tana kallonta cike da mamakin ganin duk ta fita hayyacinta ga kayan jikinta jargaf da ruwa da ƙasa. "Ke dai bari Lami labarin mai mugun tsawo ne ke dai tun da kika tarar da ni da rai kawai mu yi mu bar wajen nan dan idan aka zo aka ganmu zai zama mun yi tufka da warwara kuma abin da muka yi zai zama fallasa auren bashi" Cewar Inna tana kallon Lami da take haƙi da alama ita ma gudu ta yi kodai mugun sauri. Haka Lami ta kama Inna ta ciccigata tana cewa "Wallahi Inna ki riƙe gagam kuɓa kar ki saki nauyinki domin katangar nan ta jiƙu da ruwa sosai karki je ki zuba mata nauyinki ta je ta faɗi ta rufta da ke in shiga uku" "Ai ban bata nauyi ba Lami na riƙe kayana, ke dai taimako ki cicciɓani in dira wannan abin da kike jihadi ne" Haka aka cicciga Inna ta haye ta taka duron da yake wurin dan dama a wajen suka barshi sai da ta ganta tsaye a kan ƙafafunta duk da gwiwoyinta na mata raɗaɗi saboda duk sun ɗan sassale a rarrafen da ta yi na yi wa saurayin nan doki. "Kula maza Lami mace mai kamar maza kwarin ne babu an buga an barki Lami jikar Uwani bada kanki a sare ki je gida ki ce ya faɗi" Ta faɗa tana kallon Lami da ta yi wa katangar Yaya Lado hawan ƙawara dan ita ko da ta hayo bata hau kan duro ɗin ba ta dira a ƙasa. Tana wani hura hanci ita ala dole kirarin da Inna ta mata ya shigeta. Sai da suka gyara duron kamar yadda yake sannan cikin sanɗa suka lallaɓa suka shige ɗakin nasu bayan sun ƙarewa ɗakin Yaya Lado kallo suka ga yana nan yadda yake alamar bacci ya yi masa kamun kazar kuku dan babu alamar ma ya fito daga ɗakin har suka dawo. Ɗakin rufo suna shiga Inna ta kunna fitila tana kunna wa suka shiga taka rawa suna kwaso shoki na cikar burinsu da suka yi wa kazar amarcin Duduwa kankat. *JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW Page1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣ "Inna wai kuwa kin ga yadda Malam duk ya diririce har da shiga akurkin talo-talo kin san Allah Inna sai na ga ya saje da su sosai na gan shi kamar jimina" Lami ta faɗa tana dariya har da riƙe ciki itama Innar dariyar take cike da mugunta. Sai da Lami ta bata karkaf yanda komai ya wakana har yadda ta fito ta yi dibara ta rufe kafar dangan ya koma tamkar ba a huda shi ba. "Ai kin min dai dai Lami kuma kin haifu aradun Allah ai maganin ɓeran daji sai ɓeran birni, kuma Duduwa ya kamata ta ƙara rabbatarwa duk wanda ya ci tuwo da Uwani to alal haƙiƙa miya ya sha, miyar ma miyar kuka tsalala marar kauri wacce ita kanta kukar kaɗin bata ishi miyar ba. Da in banda ɗan adam ma butulu ina Duduwa ina auren mijina a tunanina ko wata Duduwa ta ga za ta ci amanata ta hana ashe dai gaskiyar ƴan magana da suka ce makashinka yana tare da kai, kuma Allah ya bayyana mini Duduwa baƙar fura ce ana gama ta mai gida na mutuwa, yo banda ma duniya ba amana da gaskiya ai aradu Duduwa ta mayar da ni ƙaramar danga mai daɗin tsallaka, amma ba komai mu je zuwa wai mahaukaci ya hau kura" Inna ta faɗa cike da takaicin abinda Duduwar ta mata dn tana ganin ma ko me ta yi wa Duduwa bata huce ba dan gani take duk abinda ta mata bata rama ba. "Barta Inna ai za ta gane shayi ruwa ne , dan dama duj wanda kika ga ya yaga rigarsa to tabbas ya san inda zare ke tsada! Dan sai ta ɗanɗani kuɗarta a gidan nan daga ita har wanda ta kawo ta gidan, yanzu dai suna can ƙasan gado ko ya wasan zai kaya Allahu a'alamu, ai alƙur'an karambanin akuya ya sa ta leƙa ɗakin kura" Cewar Lami suna tuntsurewa da dariya har da yafawa abinsu. "Ah Lamisa yau na tari aradu da ka, ai yau na ga bin umarni waiwayen makaho, ni na ga balbalalin bala'i muraran wai ganin kama ruwan siriki! wai ni Uwani ni ce na ɗauki aljani a bayan nan nawa ni da tun da uwata Laure ta haifeni ko gamo ban taɓa yi ba amma sai gashi yau aljani ya buɗe mini ido, abin takaicin ma bai wuce da yake cewa wai ni ce mai akori kura dan ya rainani wai ni za a toshewa mafitar kashi, kuma ko in yi yaya, wai har da cewa za a ɗaura mini aure yo da ubansa za a ɗau... Hannun da Lami ta saka ta rufe mata baki shi ne dalilin da ya hana fitowar ragowar maganar tata. Lami kuwa sai wani kallon saman ɗakin take tana wani kallon ko ina na ɗakin tamkar wacce ta yi wa sarki ƙarya aka kama ta. "Ke dalla ja can, rabu da ni in faɗi son raina meye na rufe mini baki kamar wanda zan faɗi saɓo" Inna da ta saka hannu ta fincike hannun Lami daga bakinta ta faɗa tana hararar Lami dan so Inna take Lami ta barta ta kai ayar labarin da take bata. 'Inna, labarin aljannu fa kike, kin manta su suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba, da kike wannan maganar to idan kika ga yanzu ya tsago bangon ɗakin nan ya shigo fa ya za ki yi d... Ai Inna bata bar Lami ta ƙarasa maganar ba ta shiga zazzare idanu dan sai a lokacin ma ta lura da ɓaran-ɓaramar da ta yi nan take ta ja bargo ta lafta a jikinta ta rufa har kanta tana karanto ayatul kutsiyyu. Lami dariya take wa Inna ganin harta tsorata tabbas Inna kura ce ga tsoro ga ban tsoro. Lami dai ta samu cire kayanta ta canja Inna kuwa ko motsi ta kasa bare a yi zancen tashi a canja kaya, juyin duniyar nan Lami ta yi da ita a kan ta tashi ta cire kayan amma Inna fafur ta ƙi ta kwanta da jiƙaƙƙen kayan tana ta faman karanto ƙulaƙuzai har bacci ya yi awon gaba da ita. *MALAM* Tun da ya shige ƙasan gadon nan ko motsi ba ya yi saboda yadda ya tsorata, a haka yake tamkar wani matacce shi dai ba bacci yake ba amma fa banda numfashi babu abin da yake aiki a jikinsa, numfashin ma kaɗan-kaɗan yake yi gudun jar ya saki numfashin duka aljannu su ce ta yi laifi. *DUDUWA* Ita dai bata san ma wainar da ake toyawa ba, saboda baccin nan da aka sakata na dolen doliya sai da gari ya yi haske shaaaa sannan ta ɗan fara motsi Malam da ke ƙasan gadon jin ƙusur-ƙusur sai ya ƙara shiga tashin hankali wanda ƴan magana suke yi wa kirari da wanda ba a sa masa rana. Haka ya daddage yana addu'a har wani yawu yana zubowa daga bakin saboda ba ya iya rufe bakin dan wani lokacin ma ta baki yake ƙarasa numfshinsa. Duduwa da ta ɗan fara falkawa sai ta ji ta a ƙudundune hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ba ya yi ba. "Allahu akbar kabiran, Allah ka sa na zo a sa'a Allah ka rabani da macijan kabari wayyo ni Duduwa ai da na san ma sa'ina ya yi da ban yi auren cin amana ba ashe ma kwanakina sun zo gargara ban sani ba gashi ko amarcin ban ci ba mala'ikan mutuwa ya ɗakko raina, shikenan na barwa Uwani Malam ɗinta wayyo ni Allah" Cewar Duduwa a zuciyarta jin ƙafafunta da uban jikinta ƙunshe cikin buhun hatsi duk a tunaninta mutuwa ta yi aka saka ta cikin likafaninta. Amma kuma abinda ya bata mamaki bai wuce yadda take jin hucin numfashinta ba yana fita da yake kuma ƙasan gadon da ɗan duhu duk da gari ya fara waye wa sai bata ganin hasken a ƙasan gadon. Idanunta ta buɗe warai sai ta ga suna juyawa har ma tana ɗan hango alamar haske daga ɗan nesa da ita. Motsawa ta shiga yi sai kuma ta ji kasarsar ɗin buhun da take ciki ko kusa bai yi kama da laushin likafani ba gashi dai har hannayenta a ciki suke cikin ɗaurewar kai ta shiga kiciniyar fitowa da hannayenta har dai ta fito da su har lokacin tana mamaki ƙafafunta ta fitar tana daga kwancen ta yunƙura za ta tashi zaune amma sai ta ji ƙum ta buge kai da yake ƙasan gadon ba zai isa ta tashi zaune ba. Malam kuwa tun sanda ya ji motsi a kusa da shi sai ya yi saranda yana daga kwancen nan rubda ciki ya cigaba da jin motsin nan a kusa da shi kusan ma dab da shi dan haka sai tsoro ya ƙara cika shi dan zatonsa aljannun nan ne dai suka dawo duk da ya san zuwa lokacin gari ya fara wayewa duk da ba gani yake ba dan a kan kunnensa ladanin masallacin kusa da gidansa ya rangaɗa kiran sallah, kuma yana jin lokacin da abokinsa Malam Liman ya ja sallar, shi da kullum shi ne a sahun farko wataran ma shi yake yin ladanci amma yau ga shi ko alwala bai samu yi ba bare sallah kai jikinsa ma ba a tsarkake yake ba, banda uban fitsarin da ya sha jabgawa wani kan wani dan ko a ƙasan gadon ma yadda ƙirjinsa ke bugawa haka fitsari ke ƙwace masa yana fita da kaɗan-kaɗan dan bashi da ƙarfin hana fitsarin fitowa dan ya yi fitsarin a ƙasan gadon ma sama da sau bakwai har mamaki yake yi yadda yake fitsarin tamkar wanda ya haɗiyi famfo amma hakan bai bashi ƙarfin gwiwar daina jin tsoro ba dan shi ba gani yake ba idan aljannun ne a kusa da shi. Sai da ta lura sosai sai ta ga alamar mutum a kusa da ita ƙafa ta miƙa ta ɗan shureshi. Malam da ke tsaka mai wuya yana cikin halin ƙaƙanikayi jin an zungureshi sai ya yi zaton aljannun nan ne dan haka sai jikinsa ya ɗauki wata irin karkarwa a take haƙoransa suka shiga haɗuwa kafkafkaf. Duduwa ma ganin hakan sai tsoro ya dirar mata dan ta kasa gane a ina take. Amma dan ƙarfin hali sai ta ƙara miƙa hannu ta taɓo mutumin. Malam jin saukar abu kamar hannu a wajen saitin mararsa inda ya yi rufda cikin sai ƙirjinsa ya shig lugude tsoro ya ƙara mamaye shi. "Wayyo Allah lallai aljannun nan basu da imani yanzu kaf a jikina su rasa inda suke son tsigewa sai mafitsarata ni da na yi sabon aure ban sani ba ko Allah zai sa in samu rabon haihuwa da Duduwa" Malam ya faɗa a zuciyarsa wani kuka marar sauti yana ƙwace masa amma haka ya danne zan kar ya saki kuka su masa abinda ya fi haka duk da dai ya san zai yi wahala su cire masa mafitsari ya cigaba da rayuwa, dan shi duk tunaninsa Duduwa da ta ɗora masa hannun nan aljannu ne suke so su cire masa mafitsara tun da in ba mafitsara za su cire ba mai ya kai hannunsu saitin mararsa. Duduwa kwa jin jikin mutumin da ta taɓa yana motsi kamar karkarwa dan ƙarfin hali bata ɗauke hannun ba sai ta ɗan shafa dan ta tabbatar dai motsin yake. "Kar ku tsinke abin kasafin nan dan Allah, ku mini rai in kuka cire mini kun taƙaitani na daina amsa sunan namiji sai dai, a kirani tsaka-tsakiya dan ba a kirani da mata maza ba ma" Ya faɗa a ransa yana jin kamar ya zabga ihu amma ba hali. Duduwa kuwa jin karkarwar mutumin da ta taɓa sai tsoro ya dirar mata kan cewa kar dai ba mutum bane aljani ne ya yi likimo yake son lokaci guda ya far mata dan haka sai ita ma jikin nata ya shiga karkarwar dan sai yanzu ma ta ƙara tabbatar da cewar in ba aljani ba waye zai saka ta a buhu. Cikin sanɗa ta janye hannunt a hankali tana son ta lallaɓa ta bar wajen tun kashinta bai bushe ba. Malam ma jin an janye hannun da ake taɓa shi sai ya fara tunanin barin ƙasan gadon tun da dai ya tabbatar zuwa yanzu gari ya waye dan haka sai ya fita ko inu ne ya kurma a kawo masa ɗauki in ya so dai ya bar gidan nasa gabaɗaya ma ya bar wa aljannhn su je su ƙarata idan ma kukar bulukiya za su kawo gidan su ajiye a kan ya zauna yana kallo su tsige masa mafitsara su barshi da cizon yatsa. Duduwa karkartawa ta yi ta bi ta wajen ƙafar gadon ta fara ƙoƙarin fitowa daga ƙasan gadon da jan ciki sai yanzu take ƙara tabbatarwa aikin jinnu ne amma in ba haka ba wa zai kawo ta ƙasan gado ya saka ta a buhu. A hankali a hankali ta shiga jan ciki tana son ceton ranta. Malam ma jan cikin ya fara yana son fitowa daga ƙasan gadon lifliflif yake yana yi a hankali kuma a tsorace tamkar yadda sojoji suke yi a daji idan suna son kama wasu suke tafiya da jan ciki riƙe da bindiga haka Malam yake yana ta ja Lahaula wala ƙuwwata a zuciyarsa. Duduwa ma da take da idanun ganin runtsewa ta yi dan zuwa lokacin ta tsorata sosai tana tsoro ta buɗe idanun ta yi arba da ganin fuskar aljani muraran. Ta samu nasarar fitowa shi ma haka shi makaho ita ido a rufe dn haka suna fitowa sai motsin kowannensu yake ƙara firgita kowanne dan kowa yana tunanin da aljani yake tare . Duduwa ta kwallaso daga ɗaya ɓarin gadon shi ma ya kawo tsakiyar ɗakin aikuwa gummm goshinansu suka haɗu tamkar yadda raguna suke karo da ƙahonsu idan suna faɗa haka goshin amarya Duduwa da ango Malam Ashiru mai almajirai suka haɗu. Gwaruwar goshinan nasu ya ɗaukewa kowa numfashin na wucin gadi kafin ƙirjin kowanne ya fara bugawa da sauri da sauri tsabar ruɗu da tsoron fa kowannensu ya shiga dan kowanne ya ɗauka gware ya yi da aljani ƙurrrrrr ƙaran fitar tusar Duduwa ta doki majiyar sautin Malam, boootttt ita ma Duduwa ta ji ƙaran fitowar tusar angon nata Malam mai almajirai kafin kowa ya gama mamakin ƙaran da ya tusar da ya ji sai suka ɗan fara ƙoƙarin tsrewa juna shi yana so ya tserewa aljani ita ma a nata ɓangaren haka ne, ƙafarsa ce ta taɓo ƙafar Duduwa cikin halin da kiwanne yake na gudun famfalaƙin ceton rai haɗuwar ƙafafunsu ya ƙara dagula lissafinsu a inda babu shiri fitsari ya ƙwacewa kowannesu. Lemar fitsarin Duduwa ta isa ga ƙafar Malam da yake lokacin da suka tsorata juna kowa kwana ya yi jin lemar a ƙafarsa kuma ya ji dai abin gangarowa ya yi ba wai nashi babe sai ya yi zaton yawun aljani ne dan an ce wani yawun aljanin kamar fetur yake idan aljani ya tsarta maka kama wa da wuta kake. ƙurrrrrr ƙaran fitar tusar Duduwa ta doki majiyar sautin Malam, boootttt ita ma Duduwa ta ji ƙaran fitowar tusar angon nata Malam mai almajirai kafin kowa ya gama mamakin ƙaran da ya tusar da ya ji sai suka ɗan fara ƙoƙarin tsrewa juna shi yana so ya tserewa aljani ita ma a nata ɓangaren haka ne, ƙafarsa ce ta taɓo ƙafar Duduwa cikin halin da kiwanne yake na gudun famfalaƙin ceton rai haɗuwar ƙafafunsu ya ƙara dagula lissafinsu a inda babu shiri fitsari ya ƙwacewa kowannesu. Lemar fitsarin Duduwa ta isa ga ƙafar Malam da yake lokacin da suka tsorata juna kowa kwana ya yi jin lemar a ƙafarsa kuma ya ji dai abin gangarowa ya yi ba wai nashi babe sai ya yi zaton yawun aljani ne dan an ce wani yawun aljanin kamar fetur yake idan aljani ya tsarta maka kama wa da wuta kake.dakowanne ta karaɗe "Allahumma ajirni minan nari fid duniya wal akira" Malam da ya yi niyyar faɗar addu'ar a zuciya amma tsabar tashin hankalin da ya mamaye masa zuciya bai san ta fito fili, dan duk tunaninsa aljanin da ya yi niyyar cire masa mafitsara ne ganin zai gudu shi ne ya ce bari ya masa mai kankat ma'ana ya ƙone shi da yawunsa ƙurmus sai ya ga ƙafar guduwa. Duduwa da jin muryar angonta Malam yana neman tsari da wuta a duniya da kuma lahira, sai ta ji abin ya kwana gidan sauƙi tun da ba ita kaɗai bace a wajen har da wanda take ganin zai iya cetonta hakan ya sa cikin ɗan jin daɗin da bai taka kara ya karya ba ta ce. "Malam" Saboda ta san shu'umancin aljani zai iya yin muryar Malam ɗin ma. Malam da ke cikin halin ƙaƙanika yi jin muryar amaryarsa ta daren jiya sai ya ji ɗan sauƙi cikin zaƙuwa ya ware murya ya ce "Duduwaaaa!" Idanunta ta buɗe aikuwa ta sauke su a kan angonta da ke yashe a tsakar ɗaki rubda ciki sharkaf cikin lema duk da ita ma a jiƙen take amma dai ta san ya fita jiƙewa dan har da wani wajen da ya yi jurwayin bushe da kuma sabuwar lema a gefe ɗaya wani zarnin fitsari da na ɗoyi kamar kashi ya ziyarci hancin amarya wanda da duk ruɗu da tashin hankali bai bari ta shaƙa ba. Dan lokacin gari ya waye tangararai. "Na'am angona ya na ganka haka tashi zaune ni ce ka ga ashe safiya ce" Ai jin haka sai ga Malam wancakal ya yi wani juyi sai gashi a zaune yana zauna wa kuwa ya jishi ya zaune wani abu latsotso wanda hakan ya tabbatar masa da kashi ne ya jabga a wando. Da sauri suka rungume juna Malam ya yi wa Duduwa wata ƙanƙama tamkar zai mayar da ita cikinsa saboda tsabar farinciki jin akwai mai cetonsa a kusa duk da bai san ya aka yi suka kasance a wuri ɗaya ba amma dai ya san hakan ba zai rasa nasaba da addu'ar da ya yi ba shi ne Allah ya sa aljanin ya kawo masa Duduwarsa da suka ɗauke masa ita. JALLI JOGA NA MAMAN AFRAH FCW Page 1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣ Duduwa jin warin ya fara cika mata ciki sai ta fara janye jikinta tana ɗan murmushin yaƙe duk da ta san angon nata ba zai gani ba amma kuma zai ji sautin. "Sannu Malam wai ya aka yi muka zo nan ne?" "Ke dai bari amarya ai wallahi kawai a bar kaza cikin gashinta hakan zai fi amma bala'i iya bala'i tashin hankali iya ƙololuwa na shige shi sai dai in ce kar Allah ya maimaita amma sauran bayani bakya ji mutuwar sarki a bakina ba a bar maganar kawai" Duduwa da maganganunsa suka ɗaure mata kai amma kuma ita ma ganin bata san hawa ba bata san sauka ba, aka kawo ta bata ma san yadda aka yi ta zo ɗakin ba sai ta danganta hakan ga mutanen ɓoye tun da abinda har Malam yake tsoron bada labari to ba ƙaramin abu bane. "Malam kashi ne fa janɓar a wandon sabuwar shaddar ɗaurin auren nan taka" "Kayya Duduwa ai ba kashi ba abinda ya fi kashi ma za a tarar a wandon nan nawa dan wallahi ko kashin hanjina aka ce na yi ba zan yi mamaki ba sai dai tun da babu abinda ruwa ya bari ai shikenan. Haka suka fito daga ɗakin ta window kamar wasu tattabaru, Duduwa ganin daga ɗakin Inna Uwani suka fito hakan bai bata mamaki ba dan ta san aljani babu abin da ba zai iya ba. Kallon sawun ƙafar Malam ta yi inda aka sha artabu, mamaki duk ya cika ta, take ta dariya a zuciyarta. Wanka suka yi suka yi sallah, da Malam har da wankan tsarki ya yi na angoncewar da ya yi a daren jiya da Inna Uwani wacce ya yi zaton da maarya Duduwa yake tare, Malam dai har lokacin jikinsa sanyi ƙalaw tun da ya idar da sallar yake jan carbi. Bayan ya gama Duduwa ta ce "Oh Malam ni dai jiya ina ta jiran shigowarka bayan fitar ƴan kawo amarya ban san lokacin da baccin gajiya ya kwasheni ba, kuma ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai ɗazun nan kai abubuwan mamaki basa ƙarewa, Allah na ɗauka ma daga bacci wa'adina ya cika". Dummm gaban Malam ya buga jin wai bata san ma ya shigo ba a take ga fara tunanin to da wa suka ci kaza? Ko ma ya ce wacece ta ci kazar dan shi da tsoka ɗaya jal ya tsira ita ɗinma sai da ya dage ya samu ya ci saboda kumburar da bakinsa ya yi suntum. Cikin sauri Malam ya tashi zaune daga rungishen da ya yi babu shiri sai gashi a zaune yana wani malushe baki. "Ikon Allah da'ira cuta bayan rai! Wai Duduwa duk kazar nan da kika ci kika taune ƙashin kamar ba sabuwar amarya ba har kike cewa ban shigo ba kika yi bacci?" Malam ya tambaya yana fuskantar saitin inda yake jin Duduwa tana zaune daga gefensa. "Kaza kuma Malam! Ni ai ko takarda ban gani ba bare a yi zancen kaza... "Jar ubancan, boko kayan arna wai ustaz ya samu carry over (C.O), To wallahi ina sane wai karuwa ta taka matar aure kin san nawa na siyo kazar nan ko kin san faɗi tashin da na yi na haɗa kuɗin kazar? To ƙur'ani kuɗin larabar almajiraina ne na haɗa na laraba takwas, ke in taƙaice miki wani almajirin ma ko ya biya rufe ido nake in ce bai bayar ba duk dan in samu in fita kunyar ki, naira na gogar naira sai da na bada jaka goma sha biyu da rabi (2500) Aka bani kazar nan amma ki ce baki ci ba, haba Duduwa ɗan musulmi fa da rangwame aka san shi" "Haba Malam ƙarya zan maka da kake ta wannan haƙilun, to ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo babu yadda zan yi in amsa laifin da ba nawa ba kaza ce dai ban ci kuma ko sama da ƙasa za su haɗe sai an nemo mini kaza ta dan babu yadda za a yi in tare a gidan miji dan an raina ni a bar mini abin gori har da goruba a wurin kishiy da mutanen gari dole ko ka so ko ka ƙi ka sake siyo mini kaza ko ma in ce dole ka siyo dan ba na ce sakewa ba dan ni ban ga wata kaza va da har ake ƙulla mini sharrin na ci" Duduwa ta faɗa har da tafa cinya. Tun da ta fara magana Malam ya saki baki ya layar mai tafiya tsabar mamaki ma ya rasa bakin magana sai dai tunowa da ya yi da maganar aljani jiya a kan kar ya fiya bincike shi ya sa ba zai matsa da tambayarta ba wataƙila ma ko aljana suka kawo ta ci kazar ko ma ba dai ba haka bane shi ba gani yake ba amma ba zai kasa shaida muryar Duduwa ba ko daga bacci aka tada shi. Uwa uba ya san Duduwa ba kanwar lasa bace dan za ta tada masa zaune tsaye ne a kan kazar nan domin ba ta barin ta kwana shi ya sa ma tasu ta zo ɗaya da Uwani suke ƙawance dan duk halinsu ɗaya ne. "Dan Allah ki mini afuwa wallahi babu wani kuɗi a hannu na, sai dai in yi shahada in kama guda ɗaya daga cikin wanda suke kwanci a akurki wanda nake kiwonsu ki fige ki yi dahuwar kalwa shi ma dan na kai zuciya nesa zan iya taɓa kazar nan... "Kar ka ma fara! Wato ga Duduwa ƙaramar katanga mai daɗin tsallaka, ni za a nuna wa sabon salo gemu a kafaɗa, wato ga sakarya zan karɓi kazar akurki mai kwanci in yi dahuwar kalwa to ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa yadda ka kawo wa Uwani kaza gasasshiya ta amarci wacce ake kai wa kowace amarya a cikin ƙauyen nan haka za a nemo kaza gashin ɗan garki in ci in yi shanak amma ba dahuwar kalwa ba saboda ga amarya marar galihu!" Wani marayan kuka Malam ya saki jin irin ruwan da Duduwa take ƙoƙarin ɓallo masa shi ina ya ga kuɗin kaza gasasshiya. Kuka yake bil haƙƙi dan ya san muddun bai samo kuɗin kazar nan ya siyo ba to shigowa gidan nan ma sai ya gagare shi dan shi yanzu gabaɗaya ma ruɗu ya shige shi tun da ta ce bata ci kaza ba to da wa ya gurji amarcin? Tunowa da aljani ya hana dogon bincike kuma yana tsoron su bayyana sai ya ce "Dan Allah Duduwa ki ɗaga mini ƙafa zuwa lokacin rani idan aka samu amfanin gona na siyar sai in siya miki ko budurwar kaza ce. "Akwai ruguntsumi kenan wai mai sabuwar haihuwa ta ci karo da mai naƙuda! Wallahi ba za a wuce yau ba sai ka kawo mini kaza ta" Tun da ta faɗi wannan maganar bai sake cewa komai ba dan ya san babu yadda za a yi ya haƙura amma abin dubawar bai san inda zai samo ko da rancen kuɗi ba tun da ko kuɗin sadakinta da ya bayar bashi ya ciwo amma yanzu gashi tana son ta sake ɓallo masa ruwa. *INNA UWANI* Tun da ta yi wankan tsarkake jikinta da asubar farin, wankan amarcin da ta ci ba nata ba, suka yi sallar asuba bata koma ta kwanta ba tana zaune a kan sallaya ta saka gabanta gabas ita kaɗai ta san abin da yake damunta. Lami kuwa tun da ta yi sallah ta koma ta kwanta, bacci ya fara ɗibanta ta ji sautin kuka Inna da take ta gursheƙen kuka da sauri ta tashi kallon Innar take da tausayawa tana raya wa a ranta ya zama dole ra samo maganin matsakar Innarta dan bata son ta ganta cikin damuwa ko ɓacin rai. Da sauri ta tashi ta je wajenta ta zauna ta dafa kafaɗarta a maimako Innar ta yi shiru sai kawai ta ɗora kanta a kan Lami ta fashe da wani kukan mai cin rai. "Haba Inna ki yi shiru dan Allah ba na son ganin kukan nan naki" Ta faɗa cikin muryar kuka ita ma tana neman yin kuka. "Ba dole na yi kuka ba Lami irin abin da aka mini a duniyar nan, yanzu a ce Duduwa ta rasa amanar wa za ta ci sai amanata ina ƙawarta aminiyarta tun ra yarinta kawo tsufa amma kuma sai yanzu za ta ci amanata" "To Inna ki yi haƙuri mana kowa fa ya yi na gari kansa kowa ya yi da kyau kansa kuma duk wanda ya ɓata ya sani wanda ya gyara ma ya sani, ki barta da halinta kawai" "Haka ne amma ki ga shi ma Malam yadda ya rufe idanu ya manta da ni, haka kawai in ji a gari cewar zai auri Duduwa kuma abin ya tabbata amma dan rashin adalci da rashin ta ido a ce ba zan nuna ɓacin raina ba shi ne zai ci mini mutunci wai aure ba fashi kamar yadda aka auro ni ita ma haka zai aurota kawai dan yana son nuna mini iyakata, shi ne na dako yaji ya ƙullo na taho gida yau sati uku da kwana ɗaya amma ko ya biyo ni bare ya yi bikona hakan ya nuna baya buƙatata yana can zai ci amarci da amaryarsa wato an ci moriyar ganga an yada korenta" "Inna! Ki manta da su, indai gidan Malam ne a yau ba sai gobe ba za ki koma ko da biko ko ba biko sai na mayar da ke dan kin zama ƙadangaren bakin tulu, ba zai iyu ki bar mata Malam ki bar mata gida ba dole mu koma a ci gaba da gashi babu gudu babu ja da baya" "Lami dama ana yi a ce mace ta yi yaji amma miji ko dangin miji ko abokinsa bai zo ba ta koma?" "Haba Inna ai ko ba a yi a kan ki za a fara, shi ya sa a rayuwa ake so kullum ake fito da sabbin abubuwa ba wai abubuwan da aka saba da su ba ko su zo ko kar su zo ya rage nasu! Matar da aka saka ita ce bata kome sai miji ya ce ya mayar da ita matar da ta yi yaji kwa har yanzu akwai dama a hannunta Inna, ke ce uwata ke ce ubana, mahaifina ya rasu tun kan in zo duniya, mahaifiyata ta mutu a wajen haihuwa ta wacce ta zame miki tilo da kika haifa a duniya, ke ce komai nawa ba kya bari na yi baƙinciki kuma ban san mene ne maraici ba dan haka ni ma sai inda ƙarfina ya ƙare wajen ganin farincikin ki". "Yanzu ya za a yi wajen komawar kenan? Kin san dai Yaya ba zai bari in koma ba in dai ba a zo biko ba bare ma dama shi haushina yake ji da na taho ya fi so ma in zauna a gidan ko na gane shayi ruwa ne, ni kuma saboda kar Duduwa take firirita cewar ina gida na bar mata mijin shi sa nake son na koma" "Wannan duk ba komai bane Inna ki bar komai a hannuna, kin manta yau ne lahdi Kaka Lado zai yi tafiya garin nan mai nisa gaisuwar Babar abokinsa kuma ya ce kwana biyu zai yi saboda sai an kwana a hanya, to idan ya tafi za yi komai" "Tabbas an yi haka yau ne zai tafi ni ai na manta kwata-kwata Allah miki albarka Lamisa ya jiƙan gyatumarki da tsohonki" "Amin Inna" "Yo da banda abin Yaya a ce wai dan ka tsufa ka kwashe shekaru aru-aru a gidan aure wai baka yi yaji ba sai yake kiran wani tsofai-tsofai da ni sao ka ce wata jakar zabira" Dariya suka saka daga ita har Lamin dan Inna har ta ji saƙayau jin za ta koma ta san kuwa sai yadda hali ya yi. Wajen ƙarfe tara Yaya Lado ya musu sallama ya tafi suka masa fatan sauka lafiya duk da shi ma ba wata lafiyar kirki ce da shi ba gashi kuma jikin tsufa dan dama su kaɗai iyayensu suka haifa shi da Inna yanzu kuma sun daɗe da rasuwa. Yaya Lado na tafiya Lami ta fasa asusunta ko Inna bata faɗa wa ba, haka ta tafi kasuwar garinsu ta siyo robar ɗaure-ɗaure mai uban yawa tare da tsakiya (beat) Sai dogayen wanduna kala huɗu da wasu body hug guda biyu, sai wani kamfacecen kambas irin na ƴan ball second hand ta siyo da wata damɓareriyar sarƙa da ɗankunne. Wata doguwar rigar buba ta leshi irin gwajon nan na Lagos ta siyo mai fankaɗeɗan ɗankwali. Daga nan gidan su tsigi-tsila mai kitso ta wuce ta je ta tarar tana yi wa wata kitso bata gama mata ba amma jin Lami ta ce za ta biya ta kuɗi masu tsoka ya sa tsigi-tsila ta saka wa matar kai ta biyo Lami. Suna zuwa Lami ta jibgewa tsigi-tsila robar ɗaure-ɗauren ta ce ta yi wa Inna ɗaure-ɗaure na ɗiban magana haka Inna ta washe baki tana murna tun da take ma ba a taɓa mata ɗaure-ɗaure ba ko da tana budurwa ma amma saboda ta turawa Duduwa haushi ta yarda tsigi-tsila ta kama kan nan ta fara tamke mata shi kaar yadda Lami ta nuna wai tsawon ƙarin gashin da za a yi sai ya zo gadon baya kamar gashin ƴan indiya. Sai da aka jibgewa Inna robar nan a kanta yaraf-yaraf kamar wata ƴar bori, aka zo aka bi ɗaure-ɗauren da beat (Tsakiya) Sai da aka gama tsaf aka sharɓa mata wata uwar fulawar baƙin lalle kamar an goga dayis duk ta kwaɓe amma Inna kamar an tsomata a aljanna sai faman sheƙawa Lami da tsigi-tsila albarka take dan ta kira ɗaure-ɗauren nata da fulawar da suna da Duduwa tagumi. Da la'asar lis ayarin ƴan mata da masu waƙe wanda suke yi in za a kai marya da Lami ta gayyato su suka yi wa gidan Yaya Lado tsinke. Inna tana ɗaki ta sha wanka an kyankyatsa leshi wuyan nan sanye da damfareriyar sarka sai walwali take kan nan da ya sha ɗaure-ɗaure da ƙarin roba yaraf-yaraf sai bin bayanta yake banda wanda aka yi wo shi ya yi gaba tsawonsa har wajen cibiyarta ko idanunta sai ta janye robar take ganin mutane. Kambas ɗin nan an ɗaure maɗautin taminjau ga wata uwar jagira da Lami ta gyara mata ɗaurin ɗankwalin aka yi shi wani gwaggwaro haka Lami ta sinyo jakin Yaya Lado daga jigon da ake ɗaure shi Inna ta hau aka ɗora kullin kayan Inna a gaba wasu kayan kuma wasu suka ɗauka. Tunda suka fito mawaƙiyar take waƙa sauran ƴan matan suna amshi, haka suka keto ta cikin garin kowa yana kallon ikon Allah abin da ba a taɓa yi ba a garin dan sun sa budurwa ake ɗorawa a doki a kaita gidan miji amma bazawara ko ƙaramar bazawara ce inda ta taɓa aure to ta girmi zuwa gidan miji a doki amma sai ga shi tsohuwa tukuf har da furfura an ɗakkota a kan jaki kuma ma ba wai sabon aure ba komen yaji, yajin ma da ba a je biko ba har da masu waƙar amarya da kuma masu amshi bugu da ƙari ma kitson kanta kaɗai ma abin kallo ne. Mata da yara sai turuwar fitowa suke suna kallon ikon Allah, wata bazawara da Lami ta gayyato ta ita kuma daga an yi tafiya ɗaya biyu sai ta carara wata uwar guɗa. A haka suka yi wa gidan Malam Ashiru tsinke. Malam da Duduwa da ke tsaye a ƙofar ɗaki yana so ya shiga amma ta hana shi dan ta ce idan jar babu kaza ko inda take kar ya kuskura ya tunkaro shi kuma ya je ya buga ya buga amma bai samo ko rancen biyar ba. Ana cikin wannan dambarwar suka fara jiyo waƙa da guɗa sun doso cikin gidan gabaɗaya saranda suka yi kowanensu yana so ya tabbatar da abin da kunnesa yake ji yo wa jin dai gidan aka doso sai suka fara tunanin ko dai ƴan kai amaya ne suka yi ɓatan kai. "Iye shama arayye, shama ayye ruwa lilo iyeee ayye shama ayye ruwa lilo shama arayye" "Iye kece amarya, ko wacce jani talau bayanki take iyee ayye shama ayye ruwa lilo shama arayye" Wannan waƙar ita ce wacce aka shigo ana faman yi ga guɗa tamkar mai guɗar za ta tsinke hancinta. Inna kuwa da ke daman jaki da ƙullin kayanta sai langi take irin na ƴan mata da suke yi a kan doki, idan ta yi girgiza sai ta tafi da baya kamar za ta kwanta sai ta yi langi a haka aka shigo da ita cikin gidan. Galala Duduwa ta saki baki tana kallon abin mamakin da ya kusa kasheta a tsaye dan mutuwar tsaye ta yi. "Mai nake ji ne haka a gidan nan, Duduwa ba kya faɗa musu ba sun yi ɓatan kai nan ba gidan da za su kawo amaryar bane?" "Yo wane irin ba gidan bane Malam tayani gani wai makaho ya so gulma" "Wato makaho ne marar galihu da za a ce ya so gulma ba dole ya ce a taya shi gani ba tun da bashi da idon ganin, kuma da kike cewa in tayaki gani da wane idon zan gani" "Malam Uwani ce fa ake yi wa wannan waƙen da guɗa tana saman jakin Yayanta Lado" "Uwani kuma a saman jaki?" Ai tsabar mamaki ma Duduwa ta kasa magana binsu kawai take da kallo babu abin da ya fi tafiya da hankalinta irin lashin jikin Inna da kuma ɗaure-ɗauren robar da ta ga ya mayar da Innar tamkar wata tauraruwa ga wata damfareriyar sarƙa ita gabaɗaya kayan jikin Innar ma bata san su ba duk iya ƙawancensu bata santa ba da su. Ganin kambas ɗin ƙafar Inna da zanen fulawar hannunta sai ta ji tamkar ta kurma ihu ko ita amaryar jiya bata yi wannan kyan ba, hannu ta kai da sauri ta shafo gashi gaban goshinta da bai taka kara ya karya ba da aka mata zanen hausa aka saka tsakiya dan duk a turawa Inna haushi sai ga shi ita an mata ɗan yayi wanda tsawonsa ya kai cibiyarta daga baya kuwa har gadon baya. *JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW Page 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣ Ƴan kawo Uwani kuwa sashen Inna suka nufa, dan tamkar basu san da halittar Malam da Duduwa a cikin gidan ba haka suka watsa yinsu. Suna dab da shiga sashen na Inna Lami ta saka hannu ta gyarawa Inna robar da ta kwanta a gadon bayanta tamkar ƙadangare ya samu bango, har wani ƙara bazasu Lami ta yi ai hakan da ta yi sai Duduwa ta ji kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda ta tabbatar idan Malam ya kai hannunsa ya taɓa ɗaure-ɗauren nan sunanta soriye. Idanunta kafe a kanu har suka shige Inna kuwa har wani daɗa gyaran zaman rigar leshin nata take. Suna shigewa kewayen Inna Duduwa da ta saki wani kuka mai kama da na jakin dawa ra zube zaune a ƙasan ta yi zaman ƴan bori. "Ni dama dan a ci mini mutunci aka auroni ko kazar amarci ba a siya mini ba son a jawo mini gori a gari" Wannan kalaman nata su suka dawo da Malam daga duniyar tunanin da ya lula dan shi gabaɗaya dawowar Inna ɗaga masa hankali ya yi tun da dai ya san ita ma yanzu sai ta ce sai ya basu kaza ita da jikarta dan ya san halinsu hatta Lami ya san taƙidarancinta sai dai sun sa shi a tsakiya bai ma san ya zai yi ba da wannan rikicin. Jin maganar Duduwa sai hankalinsa ya ƙara tashi dan ya san dai ko ƙuli-ƙulin kubura za a yi da shi ba san inda zai samu wata kaza ba gasasshiya ba. "Mamaye luba ayya mamaye luba waya-waya. Mun kawo amaryarmu, mun kawota da langinta ta sha kwalliyar gashi waya-waya. Mun kawo amaryarmu mun ajiye ta a can ɗaki kai ango ka nemo kazar amaryar, mun fa faɗa da waƙenmu dan ma kar ka haɗa ta da jani talau wacce ko ƙafar kaza bata gani ba" Haka ƴan matan da suka rako Inna suke faɗa da waƙe dan Lami bayan ta sallamesu ta faɗa musu idan za su fita su fita da waƙar nan. Haka suka fice suna maimaitawa har wani ɗaga muryar suke ganin Duduwa ta yi zaman ƴan bori a cikin ƙasa har da masu mata dariya da gwalo dan kowa ya san auren cin amana ta yi dan kaf garin babu wanda bai san amintakarsu da Inna ba. Suna fita ta saki wani marayan kukan da ya san hantar cikin Malam hautsinawa dan shi tun ba a zo mawar gumurzun ba har ya shiga tsoron abubuwan da ka iya zuwa su zo dan ya san dai tabbas akwai badaƙala. "Wayyo shikenan an sani a bakin duniya, ashe kowa ma ya san ba a kawo mini kaza ba tun da ƴan waƙe suka fara waƙa da ni na san tuni zance zai bazama a gari shikenan ake nuna ni idan na fita wataran ma fitar ta gagareni" Ta faɗa tana kuka. Malam jin kukan nata yana ƙaruww sai ya fara matsawa kuda da ita dan ya bata baki dan idan ba bakin ba, ba ya jin akwai yadda zaa yi kazar nan ta samu. Lalume ya fara yana son ya taɓo ta Duduwa da ta zare idanu tana aikawa Malam wata harara ganin yana lalumenta aikuwa bata aikara ba sai jin yatsunsa ta yi luntsun a cikin idanunta dan shi har ga Allah so yake ya taɓo ta kuma da yake ba gani yake ba bai ma san ina yake shirin kai hannun ba sai da ya shi ta zunduma wani uban ihu tana kiran wayyo ya tsole mini ido zai nakasta mini idona mu zama ɗaya da shi" Sai sannan Malam ɗin ya farga da abinda ya yi. "Ashsha Duduwa ba da sani na yi ba" "Yo dama ina za ka sani kana baƙinciki ni ina gani kai baka gani shi ne ka sarƙama mini wannan kantoman hannun naka mai farata kamar na muzuru" Ɗiiff Malam ya yi ya san dai duk tana abubuwan nan ne saboda ka shi kuwa sai dai in tsirensa za ta yi amma bashi da kaza bashi da dalilinta. Inna da ke tsaye a kewayanta tana kallon duk abinda ke faruwa dariyar ƙeta kawai take har da riƙe ciki dan sosai suka mata kama da ƴan film ɗin Hausa. Lami da ke ta faman share ɗakin Innar ta ɗagawa Inna hannu alamar ya ake ciki. A hankali Innar ta faɗa mata tana zuwa bata gama ganin diramar ba. Bayan Lami ta kammala gyaran ɗakin ta dawo suka haɗu da Inna suna leƙen su Malam lokacin Duduwa ta fito daga ɗakinta ɗauke da wani ƙullin himilin kaya wai tafiya gida za ta yi yaji a kan kazar amarci. Malam da ke riƙe gagam da mayafin Duduwa yana haɗa ta da Allah a kan ta yi haƙuri kar ta tafi yaji tana amaryar daren jiya. Banza ta masa tana cigaba da tafiya riƙe mayafin da ya yi ƙaƙam kuma da yake ta fishi ƙiba shi kuma ɗan tsololo ne tana cigaba da tafiya sai gashi ƙiiii tana jansa dan ta rinjayeshi amma dan ƙarfin hali ya ƙi ya sakata saboda ya san muddin ta kufce masa ba lallai ya kamata ba bare ya hanata tafiya tun da ba gani yake ba. Ko da a ce laɓewa ta yi a wajen haka zai wuce ya barta tun da makaho ne. Tun daga ƙofar ɗakinta take janyo shi dan gabaɗaya ma ya janye mata mayafin sai kaɗan ne a kafaɗarta wanda ta dafe da hannu. Malam sai gashi wacakar a ƙasa riƙe da mayafin aikuwa Duduwa ko ta kansa bata bi ba ta cigaba da tafiya haka take jansa ƙasa suna zuwa ƙarshen tudun barandar ƙofar ɗakin nata aikuwa Malam ya ci da ka, dan bai ma san ina suke ba duk ya rikice mayafinkwa yana riƙe a hannunsa ya ƙi saka wa dan ƙarfin hali ya riƙe ƙamƙam da hannu biyu tamkar wanda aka ce za a ƙwace masa sai faman haki yake tamkar wanda ya yi tseran gudu. Yana tuntsurowa daga tudun barandar Duduwa ta dage iya ƙarfinta ta fisgi mayafinta aikuwa ya ƙara wuntsilawa ya ci da ka dan ita ko tausayinsa bata ji tun da tana ganin ya zubar mata da kima bai kawo mata kazar amarci ba tun da ga shi har maganar ta fita idan bashi ya faɗa ba wa ya saa ba a kawo kaza ba. Su Inna kuwa dariya har da hawaye dan su ma ko tausayin Malam ɗin basu ji ba dan dama duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka. Itama kuma Duduwar son banza ya sa ta aureshi dama kuma duk wanda ya ce zai hau motar kwaɗayi to kuwa a tashar wulaƙanci za ta sauke shi. Yana wuntsila wa cikin ƙarfin hali ya miƙe zinbet kamar ba shi ya niƙu da ƙasa ba ya hantsila. Raruma ya shiga kaiwa wajen dan burinsa kawai ya wawuro Duduwa ya hanata tafiya tana ƙoƙari shiga zauren fita daga gidan kuwa cikin ikon Allah ya ki mata cafka ya kamata, hannu biyu ya sa ya ruƙumƙumeta dan dan ko ana ha maza ha mata ba zai saka ta ba. Ƙiiii take jansa ƙafafun nan nasa suna tuzuwa a cikin ƙasa da yake zauren ruwa ba ya shiga akwai rairayi a ciki ƙafafun nan nasa suka yi butu-butu a cikin ƙasa tamkar wanda ya je ya wuni aikin siminti. "Malam sakani" "Haba Duduwa ya za a yi in saka ki, ki tafi ki tona mini asiri" "Yo ba gwara in tona maka asirin ba ashe ba daɗi ni kuma ka tona mini" "Ki mini afuwa yanzu zan fita na miki alaƙawarin da kaza zan dawo miki gidan nan duk runtsi duk wuya" Ya faɗa har lokacin yana riƙe da tsantsarta da ya yi wa kamun kazar kuka dan babu wanda zai sa shi ya barta ta tafi ko mai za a yi. Haka ya lallaɓata ta yarda za ta koma amma da sharaɗin matsawar bai kawo kaza ba komin dare za ta tafi. Haka ta dawo da ƙullin kayanta duk abinda suka tattauna a kunnen Lami dan suna shiga zauren ta lallaɓo ta zo ta laɓe suna shirin fitowa kuwa fa koma kewayen Inna ta zayyane mata komai. "Gashin yau nake so ba na son kwananniya, mai ɗumi wacce bara ƙone ba wajen gashin?" Ta faɗa lokacin da Malam ya tashi tsaye riƙe da hularsa yana daidaita ta. "Yo ban da zaƙiya ko moshe kika samu ma in kawo mana amma har wani zaɓe kike" Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma ya ce "Ayya amarya bakya laifi wa ya isa ya baki kwananniyar kaza ai ƙaryarsa ta sha ƙarya" Wani irin washe baki ta yi jin ana koɗata haka ta rako shi ƙofar ɗaki ta koma ciki. Tahowa ya yi yana dogara sanda ransa in ya yi dubu ya ɓaci dan ya san ruwan dafa kansa ya ɗakko in dii ba wajen masu gashin zai je ya sato ba ina zai samu kuɗin siyan kaza a wannan halin da ake ciki na... "Malam" Cewar Lami da ta zo wajen ta katse masa tunanin da yake idanunta kafe a kan hularsa da ya saka ta a baibai, kuma bayan a baibai ya saka hallaw ta kalli arewa maso gabas kallo ɗaya za ka masa sai ka yi da gaske in dariya bata ƙwace maka ba. "Na'am Lami" Ya faɗa yana sakin murmushin yaƙe gabansa na wani irin bugawa dan ya san Lami tauraruwa ce mai wutsiya ganinta ba alkairi bane. "Inna ce ta ce tana maka magana" "Ƙulululuuuuuu" Cikin Malam ya bada wani sauti dan shi mugun jin nauyin Inna yake ji saboda auren cin amanar da ya yi da aminiyarta ga shi ta tafi yaji sati uku amma bai je biko ba ta dawo da kanta bai je ɗakin ba gudun kar ya ɓatawa amarya rai sai kuma gashi yanzu ta aiko masa saƙon kira. "To, to, to Lamisa shalelen Innarta" Ya faɗa yana daddogara sandarsa ya nufi hanyar kewayen Innar. "Salama alekum, uwar gida ran gida, uwar gida shalele an buga an barki gaba salamu baya salamun barka da dawowa ta hannun damar Malam kowacce mace bayan Uwani take bi" Ya kai ƙarshen kirarin nasa yana wani jinjina hannu. "Shege sama wai kura ta hangi biri, lallai namiji barkono ne sai an tauna za a san yajinsa, a gabana fa jiya kake yabon amaryarka kana kusheni baka san da ni kake tare ba amma kuma yanzu ka zo kana yabona kana cewa ni ce sama da kowace mace lallai Ashirulle ka zama munafikin mata" Inna ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce "Wayyo Malam na ji daɗin kirarin nan naka Allah barmu tare" Ta faɗa tana danne zuciyarta dan haushinsa take ji amma kuma ba za ta ba wa marar ɗa kunya ba "Ai matsayinki ya kai dole a yaba miki" Ya faɗa yana washe baki. "To godiya nake, na ce kuma sai ka ji dawowata banbarakwai" "Kai Uwaniyo ke da gidanki wane irin banbarakwai kuma ai kin birgeni har da su guɗa da waƙe irin na yaran amare kika dawo a kan jaki abin ya birgeni" "Ai sai ka ji yadda na sha gyara ma taɓa kaina ka ji" Inna ta kama hannun Malam ta ɗora a gadon bayanta ɗaya hannun nasa kuma ta ɗora daga gaban goshinta inda robar ta zuba yaraf-yaraf. "Uwani waiiiii wai-wai-wai in ji ciroki, wai Uwanin ce ko kuma indiya na je ziyara" Ya faɗa yana taƙarƙarewa yana ta murza robar har neman wareta yake, ya kamo wajen tsakiya ya shiga jijjijgawa suna ƙara kacaf-kacaf. "Ni ce mana kuma hannayen nan zanen fulawa ni Tsigi-tsila ce ma ta mini ga sarƙa da sabon leshi" Ya faɗa tana ɗora hannunsa kan sarƙar aikuwa ya shiga santi yana cewa "Kuma aradun Allah Uwani har wani ƙamshi na ji kina yi tamkar na kai ziyara garin shuwa arab" Wani daɗi ya cika Inna jin an zo kan gaɓa. "Ai duk dan kai na yi shi ne na ce sai ka biya tukuici" "Yo faɗi mana Allah na tuba ko shi tukuicin ya ganni ai guduwa zai yi mai aka yi aka yi wani tukuici wanne daga ciki kike so bado zan siyo miki a kasuwa ko kanya ko magarya? Ke idan ma aduwa kika ce kina so kwano guda zan auno miki Uwaniyota" Ya faɗa yana washe baki yana kuma jiran Inna ta zaɓi ɗaya daga cikin abubuwan da ya lissafo. "Babu ko ɗaya" "To zaɓi da kan ki ko a ina yake sai an nemo" Ya faɗa yana wani bada faɗi dan shi tunaninsa abin da Innar za ta zaɓa ba zai wuce kayan naira ɗari ba zuwa da hamsin kuma ya ga dai ita ma kuɗi ta kashe ta masa gayu ga kuma daɗin da yake ji ganin ta saki jiki da shi bata masa jidali ba a kan auren nasa. "Cewa na yi dama... "Haba ki faɗa mana ai kawai ki bar wani kame-kame" "Na ce tun da ni ma amarya ce to ina so ka kawo mini gasasshiyar... "Masara ko Uwani" Malam da yake tsoron abinda za ta ce ya yi saurin cewa gasasshiyar masara dan kar ta ɓallo masa ruwa dan in ta ce kaza ai ta kashe shi. "Kaza dai ko" "Ka???" "Za" Ta ƙarasa masa ji ya yi kamar ta doka masa guduma lokaci guda ya ɗauke wuta kitsan robar ma ya daina shafawa. "Malam ya ka daina taɓa ɗaure-ɗauren. "Haba Uwani ɗarme-ɗarmen me(Ɗaure-ɗaure) Haka kawai z ki tada zaune tsaye in lalifin ma ki ce gashin masara zan kawo" "Wato banda cin amanar da ka mini har kazar ma tafi ƙarfin in ci amma ai jiya an ce manyan zabbi ka kawo wa amarya har guda biyu amma ni saboda kuka ce mai daɗin hawa ka nuna ba zan samu ba" "A'a abin bai kai nan ba bari in fita in ga yadda za a yi" Ya faɗa kamar zai yi kuka. "Yawwa masoyina Malamina abin ƙau... "Bari in je in dawo" Ya faɗa yana ɗaukan sandarsa ya dogaro ya fito daga ɗakin yana jin kamar an tsoma shi a ruwan zafi yau ake yinta ashe mata biyu matsala ne yanzu kowacce ta murza kambunta ya ma rasa wane kalar tunani zai yi ina zai samo kaji har biyu gasassu a wannan zamani da masarar tuwo ma wahalar samu take yi wa talaka. Yana fita Lami ta shigo suka tafa ita da Inna tare da fashewa da dariya. Yana cikin tafiya ya kusa kaiwa zaure ya ji motsin Duduwa tana ƙoƙarin fitowa daga ɗakinta da sauri ya tura sandarsa har yana neman ha tsilawa Allah ya taimakeshi bata gan shi ba da yanzu sai yadda hali ya yi. *JALLI JOGA* NA MAMAN AFRAH FCW Page1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣ Duk damuwa da da na sani sun baibayeshi ganin wai yau shi ne yake gujewa Duduwa saboda gudun bala'inta ya san idan ta san daga ɗaki Inna yake to sai ta yi kamar ta haɗiye shi ɗanye. Wasu hawayen tausayin kansa ne suka gangaro masa ya saka hannu ya share, yana ji ina ma bai auri Duduwa ba, gashi ba a je ko ina ba har sun fara haɗa masa kitumurmura. "Ni dai wanan mata sun zame mini JALLI JOGA" Ya faɗa a zuciyarsa yana tunano lokacin da yana da idanu ya san fuskar Duduwar ba wani kyau ne da ita ba haka ma Uwanin amma kuma sai shegen iyayi da baƙin jidali. Haka dai ya yanke shawarar fita daga gidan dan har lokacin yana cikin zauren gidan, dan ya je ya samarwa kansa mafita dan lokaci tafiya yake. Tura sandar ya fara ya buɗe ƙofar ya shiga shi dai ya ji shi kamar bai fito ƙofar gidan ba amma haka ya bi sandar tasa tana masa jagoranci sai lokacin ya ji ya shaƙi iskar waje alamar ya fita kenan. Tuntuɓen da ya yi da wani dutse har ya kusa faɗuwa shi ne abin da ya bashi mamaki dan ya san dai a bakin ƙofar gidansa babu wani dutse kuma ma abinda ya ɗaure masa kai bai wuce yadda ya ji bai ji hayaniyar mutane ba da ya fito. "Malam dama baka tafi ba" Muryar Lami ta katse masa tunani. Da sauri ya sunkuya ya taɓa dutsen da ya yi tuntuɓe aikuwa zarginsa ya zama gaskiya domin dutse ƙofar ɗakinsa ne wanda yake daga can gefen ƙofar ɗakin da yake zama a ka ya yi alwala. Wani tausayin kansa ne ya kama shi jin wai tsabar damuwar da tashin hankalin JALLI JOGAR matansa da suka saka ya nemo gasassun kaji har biyu a wannan zamani na Tinubuyya (Mulkin Tinubu) Abin har ya kai ya shiga ɗakinsa ya ƙofar zaure da aka yi dan shigar baƙin turakar tasa ya fito ta ƙofar tsakar gida amma bai gane a ina yake ba. "Yanzu zan tafi Lami" Ya faɗa kamar zai yi kuka yana saurin juyawa ya koma cikin ɗakin nasa da sauri-sauri gudun kar ta je ta faɗa wa Inna cewar yana nan ta tada masa zaune tsaye ko kuma ita Duduwa ta fito ta ganshi ta sako shi a gaba da jarabar za ta tafi gida. "Wata shari'ar sai a lahira" Ya faɗa a zuciyarsa tunowa da ya yi duk abubuwan nan mutanen ɓoye ne suka janyo masa da suka haɗa shi da matar da ta cinye kazar tas da yanzu lamarin aljannu bai shigo sabgar ba ai da ina yana cikin matsala ma kaɗan ce bata wuce matsalar Inna. "Barka da fitowa Malam, ina wuni Malam" Su ne abubuwan da suka yi wa kunnuwansa tsinke lokacin da ya fito daga gida da almajiransa ke gaishe da shi kai kawai ya shiga gyaɗa musu dan shi yanzu ba gaisuwarsu bace a gabansa dan haka sai ya shiga cewa. "Garzali, Garzali" "Na'am Malam gani" Cewar wani matashin almajiri da ya zo ya tsugunna a gaban Malam da yake tsaye. "Garzali ka je akurkin kaji, ka kamo ɗan tsako guda biyu, na wannan kazar da ta haihu, ka yanka su ka gyara tas ka soka a tinken gashinku da kuke gashi da sallar layya idan kun samu sadakar nama, ka haɗa wuta maza -maza ka musu gashi ga fam goma, murtala(20) Ka siyo mandan 10 (Gishiri) Barkono dakakke na goma ka barbaɗa ka yi sauri ka gasa" Malam ya kai ƙarshen maganar yana jin wani ɗaci a ransa na yan tsakin da za a kama masa har biyu inda barsu za a yi ai za su girma ya siyar ya samu kuɗi amma yanzu tun da Inna ta matsa a kan tana son kaza dole a a kama a gasa ba dan ransa ya so ba ita kuma Duduwa ya fita ya ga yadda hali zai yi. "Malam ƴan tsaki kuma? Ko dai talo-talo?" Dammm Gaban Malam ya buga jin Garzali ya ambaci talo-talo yo shi idan har ya ce a kamo talo-talo biyu a yanka to ai tabbatar ranar cutar ajali ce ta kama shi dan kar ya mutu ya bari zai je a yanka masa ya ci. "Talo-talo Garzali ashe baka da hankali ina maka ganin mai tunani ashe kallon kitse nake wa rogo yanzu talo-talo zan ce a kamo har biyu a yanka? Sai ka ce wanda nake gargarar mutuwa to ai sai dai gani na yi ina dab da barin duniya zan ce a yanka ko ba zan iya taunawa ba saboda cutar ajali sai in ce a soye raƙas a nuƙo a inji a jiƙa da ruwa ake mini ɗura in san dai na ci amma ina nan da raina kaima da gangan kake to da ka ji na ambaci keji? Akurki fa na ce" Ya kai ƙarshen maganar yana ɗaga sandarsa dan haushi zai ƙwaɗawa Garzali da sauri Garzalin ya goce ya koma ɗaga gefen ya tsugunna ya ce "Malam ni tunanina ko sabo da sabbin amare za a kamo talo-talon a yanka shi ya sa na tambaya" "A ina sabbin amaren?" "Iya Duduwa da Inna Uwani mana, jiya an kawo Iya Duduwa ɗazu kuma muna nan aka wuce da Inna Uwani a kan jaki ana waƙa ana rafka guɗa tana langi to duk tunanina wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar walima za a shirya musu" "Garzali na bi sabbin amaren da gudu babu takalmi haka kawai dan ka jaza mini yo a kan me ma" "A mini afuwa Malam, dana ƴab tsakin da ka yi magana ne na ga ko isa yanka basu yi ba jairirai ne fa tun da yaushe ma uwarsu ta tashi daga kwancinsu ko yayesu ba a yi ba bana ji ma sun cika sati biyu da haihuwa fa" "Ma,aifa ce (Mahaifa) Ƙarewa jarirai to ko a cikin ma'aifar kazar na ce a fito da su a yanka ina ruwanka, ƴan tsakin da har suna iya faɗin iya-iya(Ciyat-ciyat da ƴan tsakin ke yi) mutane bakwa mutuwar tsakar ɗakinku" "Allah huci zuciyar Malam bari na je na aiwatar yanzu" Ya faɗa yana kallon ashirin ɗin da Malam ya bashi ta gishiri da yaji. "Yawwa ko kai fa suyar ta yi daɗi" "To Malam" Juyawa Malam ɗin ya yi yana sauke wata ajiyar zuciya jin ya samu mafita ɗaya saura ɗaya tun da ya san dai Inna ba sani za ta yi ya siyowa Duduwa kazar ba in ya samo kenan bare har ta ji haushin ƴan sakin da za a gasa mata duk da ya san ƴan tsakin cinyarsu ma vata fi yatsan jariri ɗan mutum ba dan yara ne. Tun da ya tafi yake jin faɗuwar gaba dan ya san dai ɗan Garki ba zai taɓa bashi ko da kai da ƙafa bane idan bai bashi kuɗi ba bare kuma kaza haka ya tafi yana ta taraddadin yanda abin zai kasance. A haka ya je wurin ɗan Garki mai gashin kaza ya samu wuri ya zauna sai da mutane suka ɗan watse ya shiga gabatarwa da ɗan Garki bayanin abin da ya kawo shi wato ya bashi bashin kaza idan aka gama amfanin gona zai kawo asa kuɗinsa amma fir ya ce wallahi ba zai bayar ba Malam ya yi ta magiya ya hana shi ƙarshe dai ya ce sai Malam ya kawo masa wani abu wanda zai riƙe a wajensa matsayin jingina duk ranar da Malam ya kawo asa kuɗi sai ya bashi abin. Haka Malam ya baro wajen ɗan Garki yana ta saƙe-saƙe dan shi bai san ma mai zai kai masa a matsayin jingina ba dan ba a bada ɗan mutum jingina da ɗaya zai ɗauka cikin almajiransa ya bashi yake masa aiki idan ya kai kuɗin sai almajirin ya dawo wajensa. Gida ya koma ko cikin gidan bai shiga ba gudun matsala ta ƙofar zaure ya shiga ɗakinsa kayansa ya ɗakko sabbi wanda yake saka wa idan za shi ɗaurin aure ko dai wani taro nasu na Malamai idan an gayyaceshi. Haka ya ɗakko shaddodin nan yana ji kamar ya yi kuka ya saka a kedar biba ya fito ya koma wajen ɗan Garki ko da ya je suna masallacin magriba haka ya zauna riƙe da ledar dan shi ko alwala bai samu ya yi ba bare a yi zancen sallah. Ɗan Garki ganin kaya masu kyau sun sha gugar almajiran Malam sai ya karɓa ya saka wa Malam kaza a leda da ɗuminta ta sha mai shanak sai ƙashi take, a kan idanun Lami aka saka wa Malam kaza a leda kuma ganin idanunta guda ɗaya aka saka masa dama daga siyen rogo take Inna ta aiketa wajan ta siyo rogo mai ƴar dama da zafinsa. Tana kallon Malam ya karɓi ledar kaza ya ƙanƙame yana ta faman godiya. Ta kama hanya ta tafi gida ba tare da ta yi wa Malam magana ba. Malam kuwa hanya ya kamo yana ta murna ransa fari ƙal zai kwashi garar amarci yau dan ya huta da jarabar Duduwa da ta ce za ta bar gidan a kan kaza. Yana zuwa ya karɓi ƴan tsakin da ya saka Garzali ya gasa, dan Garzali ya gasa har ya saka a baƙar leda dan shi kansa Garzali idan ya kalli ƴan tsakin dariya ce take kama shi dan ko girman tsuntsuwa basu yi ba ko da ya je akurkin ma dakyar kazar ta bari ya kama ƴaƴan nata tana ta cakon hannunsa. Malam yana karɓar ledar ƴan tsakin sai ya ji ta shafal bbu nauyi kamar ma ba a saka komai a ciki ba. "Garzali ledar ƴan tsakin da na ce ka gasa fa na ce ja bani ba ledar ƙosai ba" "Malam su ne dai a ciki" "Kuma guda biyun ne ko dai ɗaya ne ai na ji ledar shafal kamar babu komai a ciki" "Biyu ne Malam" "To, to, to, ina sauran mandan (Gishirin da yajin?)" "Duk suna cikin ledar Malam" "Ikon Allah duk a cikin ledar amma bata yi ɗan nauyi ba to ai shikenan da babu ai gwara ba daɗi sa maida mugun yawu" Ya faɗa yana saka kai zai shiga cikin gidan dai dai nan Lami da ta gama jin komai ta sawo kai za ta fito. "Sannu da dawowa Malam" "Yauwa sannu Lami, ungo wannan ledar ki kaiwa Innarki ki ce har sauran manda da yajin ta riƙe gasu nan da zafinsu ni sallah zan yi ne shi ya sa" Ya faɗa yana miƙa mata ledar ƴan tsakin yana kuma ɓoye ledar kaza dan kar ta gani ta faɗa ya san Lami da shegen gulma bai san cewa ba a gabanta aka saka masa kazar a leda. Karɓa ta yi ta koma cikin gidan amma bata shiga ba tana ganinsa ya shige ɗakinsa ta ƙofar soro, yana shigewa ta fito waje ta faki idanun mutane ta saka ledar ƴan tsakin a cikin kwata. "Wato ga mayu, yo in ba maita ba waye zai ci naman jinjirin ɗan tsako dan bamu da galihu ita kuma ishashshiya da mai za a kai mata kaza" Cewar Lami a ranta cikin tsiwa ta koma cikin gidan ta je ta ɗakko ledar zazzafan rogon da ta siyo musu yana turiri, lokacin Inna tana bayi bata san ma mai ake yi ba zauren ta dawo tana kallon Malam ya fita ya yi alwala a tsakar gida amma ledar kazae tana hannunsa da zai yi alwala ma a cinya ya ɗora ta matse ƙafafunsa. Malam kuwa duk gudun kar aljannu su ɗauke kazar ya shiga uku shi ya sa ya ƙi ajiyeta kuma abinda ya sa bai kai wa Duduwa ba ba ya so ya kai mata ya fito yin sallah ta je ta ci ƙarfin naman shi bai ci ba. Dan haka da ya gama alwala ya zo ya lalumi dardumarsa ya shimfiɗa har lokacin ledar tana maƙale a hannunsa. "Allah ka yafe mini ban yi sallah a sahu ba ban yi ta a kan lokaci dama haka yau da safe ma na yi sallah ban je masallaci ba" Ya faɗa a fili. Lami da ke tsaye ta ga Malam ya janyo wani wandonsa ya nemi waje ya zauna ita da take tunanin sallah zai tada kallonsa take cikin mamaki, lawurjen wandon(Tazuge) Ya shiga zarewa daga jikin wandon sai da ya ciro sai ta ga ya ƙulla tazugen a ƙafarsa, bayan ya ƙulla ya janyo ledar kazar ya ƙulla a jikin tazugen ƙafarrasa. Sai da ya nannaga ƙullin ya ji ya ƙulli taminjau a fili ya ce "Wallahi sai ko a haɗa da ni da kazar a ɗauke" Ya faɗa yana saka hannu ya rufe bakinsa saboda tunawa da ya yi da ɓaran-ɓararmar da ya yi ashe fa aljannu yake cewa su haɗa har da shi a kan su ɗauki kazar. Gabas ya fuskanta ya fara tada iƙama har ya kammala iƙamar zai tada sallah sai kuma ya sunkuya ya ƙara taɓo ledar kazar ya ji tana nan sannan sai ya juya ya tada sallaar ya shiga karatun sallah. Sai da ta ga ya yi ruku'u ta lallaɓo ta shigo ɗakin riƙe da ledar rogon abinka da ba gani yake ba bare ya ganta idan ya sunkuya haka ta lallaɓa ta kama tazugen jikin ledar kazar ta since ta ɗauki ledar rogon ta ƙulla a jikin tazugen ta tashi saɗaf-saɗaf ta bar ɗakin ta tafi ta kai musu ita da Inna suka rufe ɗaki suka shiga watandar kazar amarya Duduwa suna ci suna santi Inna na saka wa Lami albarka. Bayan ya sallame sallar ko azkar bai yi ba bare addu'a ya kai hannunsa ya taɓo ledar da tunaninsa ta kazar ce jin ɗumin rogon sai ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya dan shi ko addu,a ma ba zai tsaya yi ba burinsa bai wuce ya kai kazar nan ya damƙata a hannun amaryar Duduwa ba ya huta da fargaba da kuma masifarta. Ƙafarsa ya since daga jikin tazugen ya since ledar rogon ma da tunninsa kaza ce ya ajiye tazugen ya ɗauki ledar ya lalumi sandarsa ya fito yana wani washe baki kamar gonar auduga cikin sanɗa ya shigo tsakar gidan gudun kar Inna ta ji shigowarsa ta fito ta masa zancen ƴan tsakin da ya aika mata aikuwa cikin nasara ya samu ya shige ɗakin Duduwa da ko sallama bai yi ba gudun kar a jiyo muryarsa sai da ya shiga tsakar ɗakin sannan ya buɗe murya har da wani zaƙaƙa muryar shi ala dole ya shigo da ledar kaza. Duduwa ganin shi da baƙar leda kuma yana washe baki sannan ko a sallamarsa ta lura da ƙwarin gwiwarsa ya shigo sai ta ji wani irin daɗi ua ratsata tare da dabaibayeta dan hakan yana nuni tare da tabbtar mata yau akwai asuwaki da gasasshiyar kaza. Malam tashi ya yi yana rawar ƙafa ya je ya bankawa ƙofar gida sakata ya dawo yana zuwa lokacin an fara kiran sallar ishsha'i sai kawai suka yi sallar tare da amaryarsa. Bayan sun idar da sallah Duduwa har da rungume Malam tana jin daɗi a ranta dan ya gama mata komai kuma ya fitar da ita kunya da gorin jama'a. Shi kwa gogan sai wani washe baki yake Duduwa tashi ta yi ta je ta banka ƙofar ɗaki da ƙarfi dan Inna ta jiyo haushi ya hanata bacci dan ta san amarci za su ɓarza ita da Malam ga gasasshiyar kaza a gefe. Bayan ta dawo ta ɗakko sabon plate daga cikin loka ta kawo ta ajiye. "Baka ji ba ji nake kamar in goya ka in zaga garin nan da kai dan daɗi" Ta faɗa tana ƴar dariyarsu ta masoya. *INNA* Tatas suka cinye kazar suka sha ruwa abinsu tate da yi wa Allah godiya. "Taɓ Inna wallahi har hangowa nake irin badaƙalar da za a sha da Malam da Duduwa matuƙar ta ga rogo ne a ledar nan akwai badaƙala! Dan sai ta kusa murɗewa Malam kai kina ji fa dan ƙarfin hali har ƙofa suka rufe wato mu an haɗa su da jariran ƴan tsaki ai dama haka ne" Lami ta faɗa tana dariya. "Ai na san halin Duduwa babu sauƙi sai an yi yaƙin duniya na uku a gidan nan idan ta gano haka" Inna ma ta faɗa tana dariyar. *Duduwa* Tun da ta kawo masa farantin take haɗiyar yawu dan yau Allah ne kaɗai ya san irin cin ƙetar da za ta yi wa kazar nan saboda an daɗe ba a haɗu ba. "Taɓa kai da ba gani kake ba ai sai yadda hali ya yi dan lallaɓawa zan ke ina sunkutar narkekiyar tsoka in barka da ƙasusuwa" Ta faɗa a ranta tana dariyar ƙeta a zuciyarta dan har ta hango yadda wasan zai kaya domin kuwa mai kaza ne zai tashi da kai da ƙafa. "Kam bala'iiiii Ashiruuuu wannan gardin fa da ka juye a faranti wace shegiyar ce za ta ci?" Cewar Duduwa tana zaro idanu ganin Malam ya ɗaga baƙar ledar ya juye a farantin ta yi ido huɗu da dafaffan rogo mai gari sai tururi yake. A nan na kawo ƙarshen free pages wanda yake buƙatar cigaban har ƙarshe ya tuntuɓe ni a whatsapp ta wannn number 09013181851