*ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* https://chat.whatsapp.com/J0qrgC0rXNQ57u50VzeewR FREE PAGE 1 Girma da nauyin cikin da ke jikinta kamar an kifa ƙwarya, bai hanata gudun da take yi na ceton rai ba. Gudu take zabgawa saboda miyagun hallitun da ta yi tozali da su, masu kawo mata farmaki da zimmar cafkar tsohon cikin da ya yi tsini tamkar zai fashe. Zuwanta bakin wata bishiyar kuka mai duhun gaske ya bata damar tsugunnawa cikin haki, saboda ji take kamar bayanta zai ɓalle gida biyu saboda azaba, ajiyar zuciya take saukewa akai-akai kamar wacce ta shekara tana matsanancin gudu a tsakiyar rani. Dafe bayanta ta yi wani irin azabar ciwon baya da mara ya sarƙeta kamar ana tsaga marar tata da kaifaffiyar aska. Sannu a hankali ta waiga bayanta don ganin mummunar halittar da ke bibiyarta kamar yanda inuwar mutum take bibiyarsa. Kukan jarirai ne ya fara yi mata amsa kuwwa kamar saukar aradu a tsakiyar ka! Ta ko ina take jin sautin kukan na su kamar kunnuwanta za su tawatse. Kuka haɗe da dariya ne suke ta shi a cikin dajin, zuwa can ta hango inuwar wata hallita na tunkaro ta, matsananciyar guguwa ce ke tashi bishiyoyi na kaɗawa da ƙarfa yanda kasan za su jijjigo daga jikin jijiyoyinsu. Cikin wani irin gwamamman yare ta riski muryar inuwar tana cewa, "Sai kin halaka ke da abin da yake cikinki, kin zama halakakkiya keda tsiron da ke cikinki." Ba ta yi aune ba ta fara jin abu na bin ƙafarta zuu! A daidai lokacin da ta ji wani irin nishi ya taso mata. Durƙushewa ta yi a wurin tana murƙususu, nan take wani irin kukan Jarirai mai haɗe da kukan Jaki ya fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dajin tamkar zai tsage gida biyu. Sannu a hankali Jarirai suka fara rarrafowa suna zageta kamar ana zagaye wainar gero. Duk da halin da take ciki bai hanata yunƙurin tashi domin tseratar da rayuwarta ba, amma ina! Haihuwa ta tunkarota gadan-gadan nan take jaririn ya faɗo. Sannu a hankali ya rinƙa bin duk wurin da jini ya zuba yana lasa shi da sauran 'yan uwansa Jarirai, tamkar waɗanɗa suke da'irar ƙungiyar asiri. Raihan da ke durƙushe da sauri ta zabura kamar wacce aka ɗanawa ruwan dalma, tana yunƙurin tashi nan take mabiyiya ta faɗo. Kamar yanda Kura take ƙishirwar nama haka suka afkawa Mabiyyar kafin wani lokaci tuni suka gama da ita. Kamar haɗin baki haka suka waiwayi wurin da take tsaye, tamkar 'ya'yan Birrai haka suka fara tsalle suna ɗane jikinta har Allah ya basu nasarar hawa jikinta. Lokaci ɗaya suka fara lasar jikinta, ihu take kurmawa kamar zautacciya amma babu ɗaya daga cikinsu da ya yi alamun dakatawa. Daga can ƙafarta ta hango Jaririn da ya fito daga jikinta yana bin jinin ƙafarta yana lasa. A haukace ta ƙwalla ƙara tana ambatar sunan Mahaifiyarta kamar wacce ake zare wa rai. Firgigit ta farka daga bacci tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta ci gasar tseren gudu, jikinta rawa yake kamar mazari, ta haɗa gumi sharkaf kamar wacce take gaban maƙera. "Barka da tashi ranki shi daɗe." Ba ta yi aune ba ta ji kalaman Mama Uwani a tsakiyar kanta. Da sauri ta ɗago ta kalle ta har lokacin jikinta rawa yake, sai da ta jingina da bangon gadon ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Yauwa Mama Uwani." "Kina buƙatar wani abu?" Girgiza mata kai ta yi tana murza idanu, hamma ta yi haɗe da miƙa sannan ta dubi Mama Uwani tana faɗin, "Mama Uwani ki haɗa min Tea kafin na fito." Cike da girmamawa Mama Uwani ya russuna tana faɗin, "An gama shalelen Uwani, gabanki gata bayanki gata. Duk abin da kika faɗa haka za a yi uwar ɗakina." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin, Raihan miƙewa ta yi tana ɗan waƙe-waƙenta sannan ta faɗa toilet don ɗaura alwalar sallar asuba. Sai dai rana ta buɗe sosai wacce take nuni da gari ya waye tangararan don ƙarfe tara har da kwata a lokacin. Sai dai har lokacin mafarkin da ta yi bai gama sakin jikinta, wani abin da ya bata mamaki bai wuce zuwan period ɗin ta ba alhalin ba lokacin zuwansa ba ne. Mama Uwani tana fita bayan Raihan ta shiga toilet wata baƙar mage ce ta ratso daga bangon kusurwar ɗakin, idanunta jawur suke kamar gauta ga ƙarshen jelarta wani tafkeken kan maciji ne ban da sheƙi babu abin da yake yi. Kalle-kalle ta fara yi tana shine-shine sannan ta fara girgiza cikin wani irin yanayi, lokaci ɗaya ta fara rikiɗa zuwa kaloli daban-daban. Sai da ta rikiɗa zuwa kaloli sama da goma sannan ta dawo kalarta ta farko, ta buga tsalle zuwa kan gadon da Raihan ta tashi wanda har ya ɗan fara ɓaci da jini. Tana hawa kai ta fara lasa sai da ta siɗe shi tas sannan ta sauko cikin takun ƙasaita tana kalle-kalle, a hankali ta taka zuwa kan mudubin Raihan da ke cike da kayan shafe-shafe da turarruka kala-kala. Girgiza ta yi lokaci ɗaya ta rike zuwa wata mummunar hallita mai siffar dorinar ruwa da ranƙwalelen ƙaho a goshinta, a hankali ta fara zuƙe mayuka da tururrukan da ke cikin kwalabe da robobinsu, nan take komai ya zama wayam babu komai a ciki. Wani irin ruwa ta shiga ɗurawa mai yauƙi sai da ta gama cika su sannan ta hura iska suka dawo tamkar mayuka da turarrrukan da ke ciki da farko. Mama Uwani ce ta tunkaro ƙofar da sauri wannan hallitar ta sake rikiɗewa zuwa mage wannan karon jelar rabuwa ta yi gida biyu dukkansu ɗauke da kan maciji. Tana jin alamun buɗe ƙofa da sauri ta ratse ta jikin bango ta ɓace daga ɗakin, sai dai takaicinta ɗaya da bata samu ta ƙarasa cimma abin da yake tafe da ita ba. Mama Uwani jere kayan abincin Raihan ta fara yi, a daidai lokacin Raihan ta fito ɗaure da towel. Da murmushi Mama Uwani ta riƙo hannunta tana faɗin, "Ƴar gatan Uwani me kike buƙata bayan wannan?" Ɗan yamutsa fuska ta yi ta ce, "Babu." Mama Uwani cikin wani yanayi ta fara bin ɗakin da kallo, Raihan ta ɗan ja guntun tsaki tana faɗin, "Mama Uwani ki bani wuri bana buƙatar hayaniya." Mama Uwani ba don ta so ba ta juya jiki a sanyaye ta fice daga ɗakin tana waige, fitarta ke da wuya Mommy na kawo kai tana ganin Mama Uwani ta ce, "Uwani yarinyar ta tashi kuwa?" Mama Uwani cikin ladabi ta ce, "Ta tashi hajiya yanzu na kai mata abin kari." Mommy bata tanka mata ba ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, Raihan na gaban mudubi za ta fara shafa mai. Mummy ta kira sunanta tana ci gaba da cewa, "Raihan ba dai yanzu kika ta shi kika yi sallaha ba?" Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Haba Mommy wai me kika mayar da ni, ni ba sallah ma zan yi ba period ɗina ya dawo." Fuska ɗauke da damuwa Mommy ta ce, "Period kuma, ina ce yau ko sati biyu ba ki da gamawa ba." Cikin rashin damuwa ta gyaɗa kai tana ci gaba da shafa mai, juyawa Mommy ta yi ta fi ce tana faɗin, "Gaskiya idan ya ci gaba da yi miki wasa dole mu je mu ga likita." Raihan ta tura baki gaba ƙasa-ƙasa da murya tana faɗin, "Kawai don period ɗina ya dawo sai ace sai na je wani Hospital ana zaune ƙalau." Turo ƙofar da aka yi ne ya sa Raihan waigawa a lokacin ta fesa turare tana saka wata doguwar rigar bacci, Mama Uwani ce ta sake shiga hannu ɗauke da kunun gyaɗa ta ajiye, Raihan na ganin haka ta saki murmushi mai sauti ta ce, "Mama Uwani dama kin yi kunu shi ne baki kawo min ba, ai kuwa da na cika cikina sai kin kwashe min tass kin ɗura min kunun nan." Ta ƙarasa magana tana zame towel ɗin jikinta don ita Raihan bata kunyar ko a gaban waye ta cire kayanta ko ta sauya wasu. Mama Uwani na ganin haka ta fice daga ɗakin, Raihan na cikin saka kaya ta ji kanta na sara mara lokaci ɗaya jini ya fara bin ƙafarta ga wani irin raɗaɗi da jikinta yake yi ta ko'ina, nan take ta yanke jiki ta faɗi a wurin. Wani irin hayaƙi ne ya fara zirarowa ta jikin ƙofa har sai da ya zo gaban Raihan da ke kwance jini ya fara malala daga jikinta, lokaci ɗaya hayaƙin ya rikiɗa zuwa siffar mutum. Kallon kan mudubin Raihan ya yi yana girgiza kai cike da baƙin ciki, ɗaya bayan ɗaya ya fara zuƙewa mayuwan ciki da yake ganinsu da kalar ruwan nan mai yauƙi, kusurwa bangon ɗakin ya kalla ya ce, "Tabbas ba aikin kowa ba ne sai naki Mugaza, na lura kin fara wuce makaɗi da rawa amma ranki sai ya yi mummunan ɓaci." Tun bai rufe baki ba magen nan ta sake ɓullowa ta bango, har sai da ta zo gabansa ta yi girgiza cikin surar wata matashiyar budurwa ta ce, "Ka ga laifina don na nakasta mai shirin tarwatsa farincikina? Ko kana tsammanin zan zura ido ka ɗauko mini kishiya alhalin ka san wannan haramtacciyar al'ada ce a zuri'armu. Wani abin takaici ma ka rasa wacce za ka aura sai bil'adam salon ka ja mini abin kunya cikin ahalina, wallahi ba zan lamunci haka ba kuma wannan somin taɓu ne ka zuba ido ka gani." Tana gama maganar ta sake rikiɗa zuwa mage ta ɓace daga ɗakin, cike da takaici ya kalli gadon Raihan sai kawai ya fara kiran sunan Hidaya. Sai da ya kira sau uku sannan wata matashiyar budurwa ta ratso ta ƙarƙashin ƙasa mai zubin siffar Raihan babu abin da ya bambamta su har kayan jikinta. Wurin abincin Raihan ya nuna mata ya ce, "Ki maye gurbinta kuma bana buƙatar a samu matsala idan ba haka ba har abada ke da biyan buƙatar ƙudurinki." Idanunta ne suka ciko da ƙwallah ta ce, "Wuskarbat min kalsusbima wakfit karmu linkasbu muzrabatu fisgatmuha warmi Jalkisu Mu'az." (Don Allah karka yi mini haka, ka san duk duniya babu wanda nake ƙauna kamar Yarima Mu'az.) Ɗaukan Raihan ya yi da ke kwance ya saɓa a kafaɗa sannan ya kalli jabun Raihan da ke tsaye ya ce, "Dole ki ɗauki ɗabi'a irin ta Raihan hatta yare dole ki ci gaba da irin yarenta ba namu da muka saba yi ba. Na gaya miki idan aka samu matsala ke da Yarima Mu'az har abada." Yana gama maganar ya daki tsakar ɗakin nan take ƙasar wurin ta dare ya faɗa ciki hannunsa ɗauke da Raihan suna shigewa ƙasar wurin ta haɗe ta shafe kamar wani abu bai taɓa faruwa a wurin ba. SHARE HILIS🌚 Daga yau za ki iya turo kuɗinki don karki bari ayi babu ke🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ Ummou Aslam Bint Adam🌚 *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* FREE PAGE 2 https://chat.whatsapp.com/J0qrgC0rXNQ57u50VzeewR A hankali Jabun Raihan ta fara bin ɗakin da kallon, miƙewa ta yi ta fara buɗe drowers ɗin kayan Raihan sai kuma ta bi hotunan ɗakin Raihan da ke maƙale a jikin bango tana kallo ɗaya bayan ɗaya, tana jin motsi ta koma wurin kayan abincin ta zauna. Kallon abincin take don sam bai burgeta ba cikin zuciyarta take mamakin irin abincin bil'adam don ita bata ga abin daɗi a ciki ba. Goggo ce ta turo ƙofar tana faɗin, "Rehanu! Ke Rehanu wai ina kika shiga ne tun jiya ban ji wulgawarki ba, yarinya sai iya shege don kin ga na damu da ke." Turus ta yi tana kallon Jabun Raihan da ke cin abinci tana yamutsa fuska, daƙuwa ta yi mata da hannu tana faɗin, "Kin ci ƙaniyarki Rehanu dama kina jina kika yi shiru to kin wulaƙanta uwarki Abu. Meye wannan ɗin kike ci kina yamutsa fuska kamar abinci?" Jabun Raihan a daƙile ta ce, "Gashi kuwa kin gani." Goggo ta shiga ɗakin ta yi tsaye a kan Raihan tana faɗin, "Oho dai kowa ya raina uwar wani tashi ya raina, wallahi duk maganar da kika gaya min uwarki da Ubanki kika gayawa." A fusace ta ɗago tana duban Goggo da ke tsaye tana zazzaga ruwan masifa, farantan gabanta ta kalla tana motsa baki lokaci ɗaya ta cinye abincin ciki sai kwanukan, tana kallon Goggo kamar wacce ta basu umarni sai farantan suka yi tsalle zuwa gaban Goggo, wuƙar da Mama Uwani ta haɗowa Raihan don ta riƙa yankar farfesun ƙafar sa ce ta yi tsaye a daidai fuskar Goggo saitin idonta tana wani juyi, kamar za ta tsokane mata ido. Jabun Raihan ta kalli Goggo fuska ba walwala tana cewa, "Kika sake zagar mini iyaye sai na tsokane idonki, ke da sake gani har abada. Wannan kwanukan kuwa sai na basu umarni su yi ta ranƙwale miki kai har sai sun illataki." Goggo daskarewa ta yi a wurin, tuni fitsari ya jiƙe mata zani gumi sai yanko mata yake ta ko'ina. Tun Jabun Raihan bata gama magana ba, Goggo ta juya da gudu tana ƙawalawa Mahaifiyar Raihan kira, sai dai yadda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ya sa ta fice da rarrafe zanin jikinta kuwa tuni ya samu mutsuguni a bakin ƙofa. Tana fita Jabun Raihan ta miƙe tana kaiwa da kawowa don gabaɗaya zaman wurin ya gundureta, abin da ya sa ta bi umarnin Huzaifa don biyan tata buƙatar amma ba don haka ba babu yadda za a yi ta amince da rayuwa cikin siffar bil'adam. Huzaifa bai tsaya ko'ina ba sai cikin wani ƙasurgumin daji mai ɗauke da jajayen furanni, da jajayen ƙoramu. Komai na wurin ja ne hatta ciyayin da suke wurin, sai waɗansu korayen kifaye da su kaɗai ne suka bambamta da jajayen abubuwan da ke wurin. Kan wani jan dutse ya kaita ya kwantar da ita nan take ya fara gyara mata jikinta, kafin wani lokaci tuni ya gyara mata jikinta ya ɗauko wani ƙaramin jariri da ke kwance cikin wata ƙorama mai ɗauke da siffar kunkuru, sai dai kansa ɗauke yake da kawuna huɗu kowanne da surarsa. Akwai kai mai siffar jaki, agwagwa, mage da mai siffar kifi, a kowanne kai akwai manya kahunhuna guda biyu, daga jelar hallitar ɗauke take da tafkeken kan maciji. Yana zuwa ya ɗora shi a gefenta sannan ya ɗaga hannunta ya tura shi ƙarƙashin jikinta kamar yadda uwa take rungume jaririnta. Nesa da su ya koma yana sakin murmushin farinciki a fili ya fara faɗin, "Na jima ina burin haka ban samu dama ba domin gudin abin da zai ɓata miki rai, sai dai a wannan karon dole na ɗau wannan matakin domin haka ne kaɗai sai tseratar da ke daga kaidin Mugaza, idan ba haka ba duk yadda za ta yi sai ta halaka min ku. Ni kuma ba zan juri rabuwa da ke ba wanda ya nemi raba ni da ku zan iya hallaka shi ko wanene, ko da kuwa Mahaifina ne Jingas." Yana gama magana ya ɗaga dutsen da Raihan take kwance da jaririnta, naɗe su ya yi cikin wani kogon dutse sannan ya hura wani kogi da korayen kifayen nan suke ciki, nan take ruwan ya dare Huzaifa ya jefa su ciki ya sake hura ruwan ya haɗe gabaɗaya. Mommy na daga falo ta fara jiyo muryar Goggo na ƙwala mata kira, da sauri ta nufi wurin da ta ji muryar Goggo tana zuwa ta yi turus ganin Goggo na rarrafe daga ita sai ɗan fatari. Da sauri ta sunkuya tana faɗin, "Goggo lafiya kuwa ko ƙafar ce ta motsa?" Tun bata rufe baki ba Goggo ta ci gaba da faɗin, "Abu ki dubi Allah da ma'aiki ka mayar da ni Albasu wallahi na yafe zaman gidanki, ki maida ni Albasu na mutu cikin aminci tun bata tsaface ni a gidan nan ba." Goggo na maganar hawaye da majina na zuba, a gefe ɗaya fitsari ne ke zuba don Goggo ta yi fitsari daga ɗakin Raihan zuwa babban falo ya kai sau uku. A ɗan tsorace Mommy ta waiga tana faɗin, "Goggo lafiya kuwa wace ce ta zama matsafiya?" Goggo ta fyace majina da gefen zaninta ta ce, "Wa kuwa kika sani idan ba Rehanu ba. Wallahi yadda na ga tana tsafi ido biyu na ga Annabi haka..." Tun bata ƙarasa maganar ba Mommy ta fara waige tana katseta da sauri cikin ƙasa-ƙasa da murya. "Goggo don Allah ki daina faɗin haka wallahi Alhaji yana gida kar ya ji abin da kike faɗa, kin san fa baya kawaici a kan yarinyar nan Raihan." Tana rufe baki Inno ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Allah ya tonu asirinku, ashe gulmar Ɗana kuke da jikalleta to ahir ɗinku wallahi ke Zinaru ki yi ta kanki arziƙi kika zo ci ba zan miki baƙin ciki ba, gida dai gidan Ɗana ne ba a isa a sawa jikata ido." Goggo takaici ya sake cikata tana ganin kamar gori Inno take yi mata, don haka a zafafe ta ce, "Allah ya sa ni na haifi Abulle har ɗan naki ya aura, magana ce na gama ta yau za a mayar da ni Albasu don wannan sheɗaniyar jikar taki ba za ta sayar da kaina ina ji ina gani ba." Inno na jin haka ta yi zaman ƴan bori daɓar sai kawai ta fashe da kuka, da sauri Mommy ta koma wurinta tana rarrashinta amma fir taƙi yin shiru. Suna nan zaune Alhaji Abdallah ya sauko cikin dakakkiyar shadda ruwan toka da hula baƙa, kayan ba ƙaramin kyau suka yi masa ba. Tun kafin ya ƙaraso Mommy ta fisge ɗankwalinta ta rufawa Goggo, yana ƙarasowa ya ce, "Lafiya dai Inno mai yake faruwa?" Inno na jin haka ta rushe da kuka tana faɗin, "Audullahi ka dubi irin sitirar da ka yi wa Zinaru ita da ƴarta amma da yake sun samu wuri wai cin naman ka suke da ƴarka ɗaya tilo a gidan duniya. Don Allah ko don darajar haihuwa Abulle ai da ɗagawa yarinyar nan ƙafa ina dalili tana uwarta tana cin namanta?" Goggo ta ƙanƙance ido cikin masifa ta ce: "Audullahi wallahi tun wuri ka san halin da kake ciki, kwarankwatsa dubi Rehanu ta shiga ƙungiyar asiri." Kamar wanda aka zagi iyayensa haka Alhaji ya ɓata fuska sai da ya haɗiyi yawu mai ɗaci ya ce, "Goggo kin san wa kike faɗa kuwa? Raihan ɗina ce ta shiga ƙungiyar asiri?" "Ƙarya na yi maka kenan Audullahi?" Goggo ta tambaye shi tana ɗage kai gefe. Shiru ya yi don ya san idan ya buɗe baki a kan Raihan za a iya samun matsala shi kuma yana ganin girman Mahaifiyar matarsa, ba zai so wani abu ya haɗa su ta sanadiyyar Raihan ba. Ganin haka ya sa Mommy ta riƙo hannun Goggo tana cewa, "Goggo ta so mu je ɗaki don Allah." Inno na ganin haka ta fashe da kuka tana faɗin: "Allah ya fini sanin dalilin da ya sa bai bani ƴa mace ba, amma ya yi mini komai da ya bani Audullahi da ban haihu ba sai na rasa mai kaini ɗaki nima." Tana gama maganar ta kalli Alhaji ta ci gaba da cewa, "Audullahi nima ka kaini ɗaki ba sai an goranta min ba, kuma wallahi aure za ka ƙara don ba za ka zauna da macen da bata ganin mutumcina ba." Daddy na shirin yin magana suka ji Raihan ta turo ƙofa ta fito fuskarta murtuk babu fara'a, da sauri Goggo ta fara ja baya tana leƙenta. Daddy na ganinta ya saki murmushi ya rungumota yana faɗin, "Barka da fitowa habibtyn daddy." ƙarasowa wurin ta yi ta ce, "Daddy ba dai fita za ka yi ba?" riƙo hannunta ya yi ya ce, "Yanzu ma kuwa don na gama komai." Fisge hannunta ta yi ta koma kan kujera tana faɗin, "Na faɗa maka gaskiya za ka yarda?" Murmushi ya yi ya ƙarasa wurinta ya ce, "Faɗi babyna." "Ka haƙura da fita da baƙar mota idan ba haka ba za a samu matsala." Mommy ta kalle ta tana faɗin, "Raihan me ya sa bakinki baya furta alheri ne? Ke kin san gaibu ne da za ki yanke masa wannan hukuncin." Goggo da ke gefe tana son yin magana tsoro ya hanata. Daddy ya gyara zaman agogonsa yana faɗin, "Baby sai abin da kika ce da wacce kike son da ita." Daga wurin da take ta ce, "Kowacce ka yi niyyar fita da ita amma ban da baƙar." Daga haka sallama ya yi musu Mommy ta wuce raka shi, Raihan na ganin haka ta ƙarasa gaban Goggo ta tsugunna a wurinta tana faɗin, "Wallahi na kuma jin kin danganta ni da ƙungiyar asiri Allah za ki yi mamakina, sai na kaiki Daulatul Jinnul nariy na azabtar da ke." Inno da ke gefe ta karɓe zancen da faɗin, "Wallahi kema kya gaya mata ai ni wallahi ban yafe wannan ƙazafin da ta yi miki ba. Ni dai wannan larabcin da kika yi ne ban san me kika faɗa ba, amma idan za ki tafi da ita don Allah ki kaini na ga yadda Zinaru za ta yabawa aya zaƙinta." Raihan bata bi ta kansu ba ta wuce kan dianning table, saboda yadda yunwa take sasaƙar cikinta don abincin da ta ci babu in da yaje mata. Tana zama ta fara buɗe kulolin da ke wurin nan take ta fara tasa kulolin a gaba, ɗaya bayan ɗaya tana cinyewa, kuloli huɗu ne a wurin amma da zaman ta ko minti biyar bata yi ba ta cinye abincin ciki gabaɗaya, tare da shanye shayin da ke cikin fulas ɗin ta kora da ruwa sannan ta dawo falo ta zauna. Lokacin da ta dawo tuni su Inno sun wuce sashensu don haka basu lura da abin da Jabun Raihan ta aiwatar ba. Sanyin da yake busawa a wurin ne ya doki gangar jikinta wanda ya sa ta buɗe idanunta a hankali tana ƙarewa wurin kallo, cikin rashin ƙwarin jiki ta miƙe zaune har lokacin kallon wurin take yi da tsananin mamaki. A hankali wannan jaririyar hallitar ta fara matsowa har sai da ta hau cinyar Raihan, zamanta a cinyarta ya sa ta lura da wurin a zabure ta miƙe tana ƙwalla ƙara haɗe da ja da baya zafin buguwar ya sa hallitar yin can gefe wanda yake nuni da jin zafin da ta yi. Waige-waige ta fara yi tana ambatar sunan mahaifiyarta, kamar daga sama ta riski muryar Mommynta tana faɗin, "Ga ni nan zuwa Raihan." Tafiya ta fara yi daga wurin da ta fara jin sautin muryar, ta wani lungu ta hango Mommynta ta fito cikin doguwar rigar shadda tana sakar mata murmushi, kallo ɗaya ta yi mata ta ji gabanta ya yu mummunan faɗuwa. Dafa Raihan ta yi tana faɗin, "Kin tashi Raihan?" Kuka Raihan ta fashe da shi tana faɗin, "Mommy ina ne nan menene wancan abin?" Ta ƙarasa maganar tana nuna wurin da wannan hallitar take rarrafowa a hankali, Mommy ta kalli wurin tana murmushi ta ce, "Taho mu je ki rabu da wancen abin." Har sun fara tafiya Mommy ta kalli Raihan ta ce, "Amma duk wanda zai ce miki ki bishi kar kije wurinsa cutar da ke zai yi ni ce mahaifiyarki babu abin da zan yi miki." Har lokacin Raihan a tsorace take don haka ta kalli yanayin wurin ta ce, "Amma mommy ya aka yi muka zo nan?" A ɗan tsawace ta ce mata: "Za ki taho ko tambaya ta za ki tsaya yi." Ba musu Raihan ta bi bayan wacce take gani da siffar Mommynta, har sun kusa fita sai gani ta yi Daddynta ya diro da ƙarfin gaske yana faɗin, "Raihan." Da sauri ta waiga wurinsa tana shirin yin magana mai ɗauke da siffar Mommynta ta fara fisgar hannunta tana faɗin, "Karki saurare shi wuce mu je." Da sauri ya ƙaraso wurin rai a ɓace ya fisgi hannun Raihan sannan ya dubi Mai ɗauke da siffar Mommy yana faɗin, "Mugaza ki shiga taitayinki fa, na gaya miki ki fita harkar yarinyar nan ba na son na hukuntaki a kanta amma wallahi idan kika illatata sai na baki mamaki." Lokaci ɗaya ta rikiɗa zuwa wata mummunar hallita mai ɗauke da siffar ƙadangare sai dai kawunanta goma kowanne ɗauke yake da wasu irin manyan harsuna masu kama da kaifin takobi. Da gudu Raihan ta rungume mai ɗauke da siffar mahaifinta tana wani irin kuka tare da faɗin, "Daddy tsoro nake ji." Ilahirin jikinta ban da rawa babu abin da yake yi, rumgume ta ya yi tsam a jikinsa yana shafa bayanta cikin wata irin soyayyarta da take fisgarsa, don karta fahimci wani abu ya sa ya iya riƙe kansa ba tare da kusanceta ba. Wannan abin ba ƙaramin ɓata ran Mugaza ya yi ba, a shammace ta kaiwa Raihan cafka da ɗaya daga cikin harshenta a ƙafa, da sauri Huzaifa ya janyeta amma sai da harshen nata ya samu ƙafarta. Wata uwar ƙara ta ƙwalla sannan ta faɗa jikin Huzaifa wanda yake nuna suma ta yi. Wata irin mahaukaciyar dariya Mugaza ta fara ƙyaƙyatawa lokaci ɗaya ta murtuke fuska tana faɗin, "Ki je ki da wannan damuwar zan baki rata kafin na sake waiwayo ki." Tana gama maganar ta ɓace daga wurin. Cike da tausayi Huzaifa da ke ɗauke siffar Daddy ya shimfiɗar da Raihan, a daidai wannan lokacin jaririn hallitar nan ya ƙaraso wurin ya kwantar da kansa a jikinta. Hannu biyu Huzaifa ya sa ya ɗago jaririn idanunsa ɗauke da ƙwallah ya ce, "Mahaifiyarka na fuskantar ƙalubalen rayuwa, amma daga yanzu zan tsaya mata tsayin daka don kare martaba da ƙimarta." Yana gama maganar ya sake ɗora mata shi a kanta yana motsa baki, lokaci ɗaya jaririn hallitar ya ɓace. Yana ganin ɓacewarsa ya kalli Raihan da ke kwance ya ce, "Daga yau za ka kasance tare da Mahaifiyarka ko baby komai za ka riƙa ankarar da ni kamar yadda ka ankarar da ni kafin Mugaza ta cimma ƙuduri a kanta." Share hilis🌚 Ummou Aslam Bint Adam🌚 *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* FREE PAGE 3 Mommy na shigowa ta nufi wurin dianning sai da ta zauna sannan ta kalli wurin da Raihan take zaune ta ce, "Mama Uwani ta ce min kin yi breakfast ko?" Jabun Raihan da ke zaune a kan kujera ta ce, "Eh na yi ɗazu." Mommy na juyawa ta buɗe kular abinci sai ta ga wayam, sake buɗe ɗayar kular ita ma babu komai; haka ta riƙa buɗe kulolin abincin amma sai taunannun ƙashi a ɗan tsorace ta tashi tana faɗin, "Waye ya cinye abincin nan Mama Uwani?" Cikin rashin damuwa Raihan ta ce, "Yanzu na cinye su." A ɗan tsorace mommy ta ce, "Gabaɗaya abincin ke kika cinye har fa da abincin rana na ajiye mana." Raihan ta miƙe ta nufi ɗakinta tana faɗin, "Wanda Mama Uwani ta kaimin bai ishe ni ba shi ya sa." Mommy sororo ta yi jikinta a sanyaye tana bin bayan Raihan da kallo. Jabun Raihan na shiga ɗaki ta ji Huzaifa na ƙwala mata kira, ta kusurwar bango ta wuce cike da ɗoki don zamanta a cikin gidan jin ta take kamar a kabari take. Huzaifa da ke tsaye a gaban Raihan ya dubi Jabun Raihan ya ce, "Mugaza ta yi mata rauni zan mayar da ita ga mahaifanta amma zan ci gaba da bata kulawa kamar yadda na kwashe dubban shekaru ina tsaye a kanta. Ki je na sallame ki idan da yuwar wani lokacin na buƙace ki za ki ji ni." Cike da farinciki jabun Raihan ta rikiɗe zuwa siffar wani ƙaton tsuntsu mai ɗauke da manyan fuka-fukai ta ɓace daga wurin, daga wurin da yake ya ɗauki Raihan ya ɗora ta akan gadonta sannan ya ɓace daga wurin. Bayan shigar jabun Raihan ɗaki ta fara kiran Mama Uwani, cike da girmamawa ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Ga ni hajiya." Mommy ta kalli kulolin kan dianning ta ce, "Mama Uwani yau mun wayi gari da wani abin almara, dubi kulolin nan wai Raihan ta cinye." Da mamaki Mama Uwani ta zaro idanu ta ce, "Hajiya duka ita Uwarɗakin nawa ce ta cinye?" Mommy ta taɓe baki ta ce, "Dama ke ba ta laifi a wurinki ai, yanzu a sake dafa wani abincin bari na haɗa cornflakes." Mama Uwani ta fara tattara kwanukan tana faɗin, "Hajiy ai kowanne laifi kika ɗauko cewa kike ita ce, ni kuma uwarɗakina bata laifi." Tana gama maganar ta kwashe kwanukan ta wuce kitchen da su. Raihan ba ita ta farka sai bayan azahar, a hankali ta buɗe idonta da suka yi mata nauyi dum! Tana ƙarewa ɗakin nata kallo. Lumshe idonta ta yi saboda yadda ta ji kanta yana sara mata kamar zai tarwatse, yunƙurawa ta yi zata tashi zaune ta ji jikinta ya yi mata wani irin tsami, ƙafarta ta hagu ta ji ta yi mata sanyi kamar ba a jikinta take ba. Da ƙyar ta samu ta fara dafa bango tana jan ƙafar tata da take jin ta yi mata nauyi kamar gungumen icce, tana zuwa falo ta fara yamutsa fuska tana bin ko'ina da kallo, a gefe ɗaya kuma ta fara wani shinshine-shinshine a haukace kamar mahaukaciya sabon kamu, da rarrafe ta fara watsi da kayan fallon cikin wani irin yanayi tana wani irin ƙaraji da gurnani kamar zakanyar da take tsaka da farauta. Ƙarar fashewar kayan ne ya fito da Mommy daga ɗaki a tsorace tana bin wurin da kallo, tana shirin yin magana su Goggo suma suka turo ƙofa suka fito don ganin abin da yake faruwa. Gilas ɗin center table da ta fasa ta fara ɗauka tana wurga musu tana faɗin, "Waye ya ɗauke min ɗana, ɗana ne wallahi duk wanda ya taɓa min shi sai na kashe shi." Inno da Goggo na ganin haka da rarrafe suka juya cikin ɗaki a tsorace, suna shiga suka bankawa ƙofarsu sakata jiki na rawa. Mommy jiki na karkarwa ta ce, "Raihan lafiyarki kuwa?" Raihan ta sake wurgawa Mommy wata kwalba da sauri ta sa hannu ta kare, kwalbar ta yanketa a hannu jini ya fara zuba, jin ƙarnin jinin mommy ya sa ta fara wurga mata wani mugun kallo tana lasar baki. Ta ci gaba da surutai ba fasali, Mama uwani ta shigo a tsorace tana kallon abin da yake faruwa. Hanyar kitchen ta nufa tana zuwa a haukace ta fisgo wata ƙatuwar roba wacce take ciki da ɗanyan kifi, tana zuwa falo ta rungumeta da hannuwa biyu tana sauke ajiyar zuciya. Mommy na shiga ɗaki hankali a tashe ta ɗau waya ta fara kiran Daddy, ba a jima ba ya ɗauka ko jiran cewarsa bata yi ba ta fara faɗin, "Alhaji muna cikin tashin hankali, da alama ciwon Raihan na shekarun baya ne ya dawo sabo don Allah ka yi maza ka zo." Amsa mata ya yi sannan suka yi sallama ya katse wayar a gaggauce, Mommy na daga wurin da take a ɗaki tana jiyo ƙarara fashe-fashen kayan da Raihan take yi. Bayan wani lokaci shiru ne ya biyo baya, jin shirin ya sa Mommy ta miƙe a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin. A falo ta hango Raihan zaune rungume da ɗanyun kifi, gabaɗaya ta ɓata jikinta da falon da ruwan kifi ban da ƙarninsa babu abin da yake tashi. Daddy ne ya turo ƙofa ya shigo yana gaba Dr Hamza na biye da shi, sai dai ganin yanayin falon ya sa ya fahimci wannan ciwon nata har ya ninka na baya. Jin sallamar Daddy ya sa ta ɗago da jajayen idanunta tana yi masa wani irin kallo, a haukace ta zaburo kansu tana faɗin, "Kar wanda ya taɓa mini ɗana jinina ne ba zan laminta a raba ni da shi ba." Tana rufe baki ta wurgowa Daddy wata kwalba saura kaɗan ta same shi a fuska ya kauce, Daddy ne ya fara kiran Yunusa mai gadi yana zuwa suka shiga kiciniyar riƙe Raihan sai da ƙyar suka samu nasarar riƙeta Likita ya yi mata allurar bacci, a take bacci ya ɗauketa ta faɗi gefe. Kan kujera suka ɗorata Likitan ya fita yana yi wa Daddy bayani. "Wato Alhaji da alama ciwon yarinyar nan ya dawo sabo, domin idan har abin da mahaifiyarta ta faɗa ne za mu iya cewa ya ninku a kan na da, saboda a da tana surutai kawai idan abin ya tashi, amma a wannan karon tana nuna kifi a matsayin ɗan cikinta. Akwai issue mai girma a game da lamarin ciwonta, za mu yi bincike mai zurfi a kai, sannan kar a riƙa wasa da magungunanta ta riƙa sha akai-akai." Jikin Daddy a sanyaye ya miƙawa Dr Hamza hannu yana faɗin, "Na gode sosai Dr don Allah a yi wani abu kai, ka san ina matuƙar son Raihan ba zan iya jure rashinta." Dr Hamza ya jinjina kai ya ce, "Insha Allah Alhaji kuma a ci gaba da addu'a everything will be successfully." Daga haka suka yi sallama da Likita. Yana komawa ciki tuni ma'aikatan gidan suka shiga hada-hadar gyaran falon, kusa da ita ya je ya zauna ya zura mata ido, hannu ya ɗora a kan goshinta zuciyarsa babu daɗi ya ce, "Wish you quick recovery dear, me ya sa al'amuranki basa zuwa da sauƙi why? Allah ya baki lafiya my baby." Mommy na ƙarasowa wurin ta dubi Alhaji cikin damuwa ta ce, "Habibi ni kam wata shawara gare ni." Bai furta mata komai ba ya ɗago yana kallonta ya yi mata alamar yana sauraronta. Jingina ta yi da bango ta ce, "Gani nake yi mai zai hana ciwon yarinyar nan a haɗa shi da na islamic chemist ko akwai shafar aljanu a ciki..." Tun bata dire zancenta ya buga mata tsawa da cewar, "Ba na son na ƙara jin kin danganta min Raihan da wani jinsin bayan bil'adam, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci. Me ye wani islamic chemist malaman da kaje wurinsu sai dai su fara yi maka turare da hayaƙi, da sun samu wuri za su fara yi maka maula. Idan ba za ki taya ni mu nema mata magani ba don Allah ki cire hannunki daga cikin maganar, ni kaɗai na isa na nema mata lafiya." Ran mommy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, amma babu yadda ta iya haka ta ja bakinta ta tsuke don ta san akan wannan maganar sai su haura sama su faɗo. Daddy ne ya cicciɓi Raihan zai kaita ɗaki da sauri Mommy ta nuna masa ɗakinta tana faɗin, "Ka kaita Toilet ɗina zan gyara mata jikinta a can sai ta kwanta." Bai tanka mata ba ya wuce ya kaita ɗakin Mommy don har lokacin fushi yake yi. Mommy da kanta ta gyara Raihan ta kwantar da ita a kan gadonta, zama ta yi a gefe tana kallon ƴartata cike da tausayawa. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla, ta sharce ƙwallah ta furta, "Wannan ita ce kalar tamu ƙaddarar, Allah ya baki lafiya Raihan." Raihan ta jima tana bacci sai bayan wani lokaci sannan ta tashi, ɗingisawa ta ci gaba da yi har ta fito zuwa falo. A lokacin an gyara falon sai ƙamshin turare yake. A zaune ta hango Mommy Mama Uwani na zaune a ƙasa tana matsawa Mommy ƙafa, cike da farinciki Mama Uwani ta ce, "Uwar ɗakina kin tashi?" Kafin Raihan ta yi magana Mommy ta furta, "Barka da tashi My Princess." A ɗingishe ta ƙaraso wurin cikin damuwa mommy ta ce, "Me ya samu ƙafar taki?" Raihan ta yamutsa fuska ta ce, "Wallahi haka kawai na ta yi min nauyi. Mommy kamar mun je wani wurin ko? Ko dai mafarki na yi ne?" Mommy a tunaninta lokacin da ciwon Raihan ya tashi take nufi, ita kuma Raihan tana son tuna zuwanta Duniyar su Huzaifa amma kanta ya yi nauyi ta manta. Mama Uwani ta kafeta da ido sannan ta ce, "Uwar ɗakina sannu kin ji, ai ke kin zama ƙadagaren bakin tulu a karki a kar tulu a barki ki ɓata ruwa." Raihan ta ce, "Yauwa Mama Uwani, don Allah haɗo min ruwan tea." Ta yi maganar cikin jin daɗin kanbabawar da Mama Uwani ta yi mata, Nan take Mama Uwani ta tashi ta nufi hanyar kitchen. A hankali Goggo ta turo ƙofa ta fito falo, don tun lokacin da ciwon Raihan ya tashi da suka shige ɗaki babu wacce ta fito a cikinsu, kallo ɗaya za ka yi wa Goggo ka tabbatar da tsoro ya mamaye zuciyarta amma sai ta dake ta fara yashe baki tana faɗin, "Rehanu hutawa ake yi." Raihan ta taɓe baki ta ce, "Ni kam ko karatu ne wallahi Goggo ya ci ki haddace sunana, kullin sai na ce miki ba sunana Rehanu ba amma ina miyar kuka ta toshe ko'ina." Mommy ta ɓata fuska ta ce, "Gidanku Raihan." Goggo da ta lura Raihan ta dawo cikin hayyacinta, ta yi mata daƙuwa ta ce, "Gata a zaune ita kika gayawa haka." Goggo ta nemi wuri ta zauna tana faɗin, "Abu kunna mini wannan shirin da suke na ƙasashen labarawa ko idanuna sa ƙara ƙarfi." Inno ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Allah ya sani ba za mu kalli masu jajayen kunne ba, ni dai ki kai mini shirinsu wannan yaron Adamu zango da Ali Nuhu, ki saka mana sangaya mu kallah." Mama Uwani ce ta ƙaraso da kofin shayi ta taimakawa Raihan suka wuce ɗaki, don ƙafarta sosai ta yi mata nauyi ɗingisawa take yi. Shigar su ɗaki keda wuya, Mama Hasiya ƙanwar Daddy ta yi sallama cikin falon. Fara'a ɗauke a fuskarta ta shiga cikin falon. Mommy da murmushi ta tarbi Mama Hasiya tana faɗin, "Mai gidan da ba awo ba cefane, ba waya ba labari." Mama Hasiya ta zame mayafin jikinta tana faɗin, "Mutum da gidansa wacce waya zai yi." Mommy ta saki murmushi tana faɗin, "Barka da zuwa wai da yamman nan kike tafe." Mama Hasiya ta ajiye jakar hannunta tana faɗin, "Wallahi dole ce ta kawo ni, kin san Hubbi ya yi tafiya ƙafar Dubai to sun yi waya da DR John wai yau zai shigo gari so kin san matsalar hospital ɗin Dr John idan kana son ganinsa sai dare." Mommy ta sauya fuska cikin yanayin damuwa ta ce, "Allah ya sa a dace wai wancen karon ba ya ce ƙasa da six months komai zai iya faruwa ba? Ya ce za ki iya samu ciki a kowanne lokaci." Mama Hasiya ta jinjina kai ta ce, "To kin ga dai shiru, lamarin rashin haihuwar nan ba ƙaramin damuna yake yi ba. Tun hubbi bai fara damuwa ba yanzu na fuskanci abin ya fara damunsa, shekara sama da goma sha biyar ba haihuwa an ya ina da rabon ganin ƙwaina a duniya kuwa?" Mama Hasiya ta yi maganar idanunta na cikowa da ƙwallah. Cikin sigar lallashi Mommy ta dubi Mama Hasiya tana faɗin, "Komai kika ga ya faru da bawa da sanin Allah, ba a nan take ba. Komai fa lokaci ne mutane da dama akwai waɗanda suka fiki daɗewa kuma Allah ya kawo musu mafita, mu ci gaba da addu'a komai ya yi farko zai yi ƙarshe." Mama Uwani ta ƙaraso cikin falon fuskarta ɗauke da fara'a tana faɗin, "Hajiya barka da zuwa." Bayan sun gaisa ta fara kawo mata kayan ciye-ciye da shaye-shaye bata jima da barin wurin ba su Inno suka fito falo, nan take suka ci gaba da hira. Mama Hasiya ƙanwar Daddy ce uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, tana auren wani hamshaƙin ɗan kasuwa a unguwar Hotoro. Sun shafe shekara goma sha biyar da auren saurayi da budurwa, sai dai Allah bai basu haihuwa ba duk wannan tsahon shekarun, sun yi yawon ƙasashe amma duk ba a dace ba har sai da suka fara ganin wani likita Dr John, ta taɓa samun ciki ta yi ɓari har sau biyu daga haka ko ɓatan wata bata sake yi ba, don haka ta nace wa Dr John lokaci-lokaci take zuwa ganin likita. DR JOHN SPECIAL HOSPITAL shi ne sunan asibitin da Mama Hasiya take zuwa ganin likita, asibitin a bayan gidan su Mommyn Raihan yake. Duk ranar da Mama Hasiya za ta zo ganin likita a gidan Daddy take kwana saboda asibitin sai goman dare Dr John yake fara ganin patient, wannan dalilin ya sa idan ta ga likita take dawowa gidan ɗan'uwanta ya kwana, yawaici tare suke zuwa da Mommy saboda mai gidanta yana tafiye-tafiye, kuma yawo babu inda ba su je ba don neman haihuwa. Cikin Dare. Wata irin guguwa mai ɗauke da amsa kuwwa marar daɗin sauraro ta fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dodon kunnuwanta, a hankali iskar ta fara kaɗa labulayen ɗakinta. A hankali ta fara ratso bangawayen da gidan tana raɓewa ta jikin ƙananan shukokin da ke harabar gidan, ta jikin bangon ɗakinta ta ratso jikinta ɗauke da jajayen kaya masu ratsin baƙi haɗe da ɗishi-ɗishin busasshen jini a jikinta. Tana shiga ɗakin Raihan ta tsaya cak a bangon gudu, ta fara huro mata iska nan take Raihan ta miƙe zaune hannuwanta toshe a kunnuwanta ta dubi Intisar. Cikin wata irin girgiza ta ƙaraso wurin Raihan ta kama hannuwanta tana shirin yin magana Raihan ta ce, "Intisar me kika zo yi yanzu gidanmu?" Intisar bata bi ta kanta ba ta hura mata iska a fuska nan take ta fara layi tana shirin faɗuwa, da sauri Intisar ta tarota tana dafe kafaɗarta ta ce, "Za ki bi ni?" Babu musu Raihan ta gyaɗa mata kai, Intisar bata bi ta kanta ba ta riƙe hannunta nan take suka ɓace daga ɗakin. Gudu suke zabgawa cikin sararin samaniya a can wani ƙasurgumin dajin wani makeken gida suka sauka, Raihan ban da ido babu abin da take bin ƙawarta Intisar da shi. A wani katafarn kogon dutse suka dira mai ɗauke da wasu irin mutane masu mummunar hallita, ɗauke suke da jajayan sitiru sai zanen jini a jikkunansu. Wata mummunar hallita ce a tsugunne mai ɗauke da kan barewa da manyan ƙahunhuna ga wani irin jini da yake ɗiga daga bakinta a cikin wani ƙaton faifai. Zuwansu ke da wuya wani tiƙeƙe da ya kasance babbansu ya dubi Intisar ya ce, "Hatsabibiya Bungulu na maraba da baƙuwa mai daraja." Intisar da dubi Raihan ta ce, "Ki yi gaisuwa ga Habibiya Bungulu ta saka miki albarka." Kamar bawa da uban gidansa haka Raihan ta dubi wannan hallitar ta duƙa kamar yadda ta ga suna yi ta miƙa gaisuwa. Da wani ƙaton sirinji wani ɗan tsamurmuri ya zuƙi jinin da wannan hallitar take ɗigarwa daga bakinta, a shammace ya samu damtsen hannun Raihan ya kafa mata har sai da ya juye jinin jikin sirinjin a jikinta, sannan ya zuƙo nata ya fesa a jikin hallitar. Lokaci ɗaya ta fara rawar ɗari kamar mai jin sanyi, tun tana daga tsaye har ta duƙushe a wurin tana karkarwa. Tana jima tana abu ɗaya sannan ta tsagaita da rawar ɗarin, a zabure ta miƙe tsaye cikin wani irin ƙarfi ta zurawa mummunar hallitar tana jiran umarninta. Buɗe bakinsa ya yi nan take wasu baƙaƙen macizai suka fara fitowa daga bakinsa, suna faɗowa suke fasa kai suna zagaye Raihan. Cikin wani irin yanayi hallitar ta miƙe tsaye tana girgiza sannan ta fara magana da wani irin yare har sai da ta yi yare ya fi kala goma, sannan ta yi magana da harshen hausa. "Tabbas mun yi babban kamun da muka jima muna jiran wannan rana. Domin ƙara tabbatar da abin da muke zargi goɗiya za ta kawo mana jini mafi muhimmanci wanda zan shayar da mai gidana domin samun lafiyarsa." Tun bai rufe baki ba Raihan ta russuna tana faɗin, "An gama Hatsabibiya Bungulu." Mummunar hallitar ta nunawa Raihan wata ƙatuwar ƙwarya mai cike da tafasasshen jini ta ce, "Babu buƙatar haka domin da alama ke shugaba ce, muna buƙatar jinin wannan matar yanzun nan..." Raihan ta amsa mata tun bata ƙarasa maganar ba da cewar, "Jininta ya halarta a gare ki, duk duniya babu jinin da za ki buƙata ya gagara a wurina." Tana rufe baki Hatsabibuya Bungulu ta miƙa mata wani busasshen ƙashi da alama ƙashin jikin bil'adam ne. Raihan na karɓa ta wuce cikin sararin samaniyar iskar sihiri bata tsaya ko'ina ba sai a katafaran cikin gidan Mahaifinta, sai da ta zaga ɗakunan gidan sannan ta dira a ƙofar ɗakin mahaifiyarta. 🤭🤭🤭 WASAN YANZU YA FARA, MAZA HANZARTA KI BIYA NA KI DON JIN WACECE AINIHIN ZAUJATU JINNUL-ASHIQ ƊIN, SHIN A CIKIN SU WACECE ƳAR GABAN GOSHIN ALJANIN SOYAYYAR? SHIN WACECE WANNAN INTISAR ƊIN KUMA WACECE HATSABIBIYA BUNGULU? 😁 AMSOSHIN NA GABA DON JIN ƘULALLEN ƊAURIN DA KE CIKIN LABARIN. Share Fisabillah🌚 *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* FREE PAGE 4 Raihan na fita Intisar ta ƙarasa gaban Hatsabibiya Bungulu rai a matuƙar ɓace ta ce, "Hatsabibiya uwar hatsabibai, sai kai mai siffar dabba a bayan fage ki koma bil'adama. Babu hallitar da ta gagare ki rikiɗa duk girmanta duk ƙanƙantarta, yaya ina tunanin lokacin share mini hawayena ya zo amma na ga wankin hula yana shirin kaini dare. Na kawo Raihan domin a salwantar mini da rayuwarta amma da alama tana shirin samun fada a wurin nan, yake Hatsabibiya tun farko kin san ba haka muka yi da ke ba." Hatsabibiya Bungulu ta yi girgiza lokaci ɗaya ta rikiɗa zuwa wata kyakkyawar budurwar, zaune take tsirara sai wasu sassan gaɓɓoɓin jikinta da ke rufe. Wani malalacin murmushi ta saki sannan ta dubi Intisar ta ce, "Da mun san kina da wannan yarinyar da tuni mun jima da umartarki ki kawo mana ita, sai dai kash! Silar saninta na daga gare domin biyan buƙatarki. Kin kawota domin mu kashe ta sai dai ba za ta mutu ba." Da hannuwa biyu Intisar ta sa ta toshe dodon kunnenta saboda yadda ta ji kalmar a kunnenta, a duniya idan da wacce ta tsana to Raihan ce. Lokaci ɗaya ta murtuke fuska tana shirin yin magana Hatsabibiya ta ci gaba da magana. "Na tabbata baki san wacece Raihan ba, da kin san amfanin da za ta yi mana a cikin ƙungiya da bakinki bai furta kalmar kisa a tattare da ita ba. Shin ko kinsan Muraza?" Da sauri Intisar ta ɗago da kai tana kallon Hatsabibiya tana girgiza kai bakinta na rawa ta ce, "Ina zan santa ya ke Hatsabibiya mu da muke nemanta ido rufe." Matashiyar budurwar da ake kira da Hatsabibiya ta yi girgiza nan take ta rikiɗe zuwa surar wani ƙaton tsuntsu, sai da ya yi tsalle-tsallensa sannan ya koma kan kujerarsa ya zauna ya ci gaba da magana cikin siffar tsuntsu. "Tabbas Raihan ita ce Muraza, tun shigowarta kogon dutsen nan alaminta da babban matsafi ya sanar da mu suka bayyana. Ƙofar nasarorinmu ta buɗe ƙarfin iko, tsafi da sihiri da ƙarfin ƙungiyar asirinmu za ta sake dawowa da ƙarfin ikonta, domin haske ya bayyana inuwarta ɗauke take tartsakin wuta mai halakar da magautanmu, za mu riƙe hannu bibbiyu domin saminta tamkar samun lu'ulu ne a ƙarƙashin teku, idan muka yi sake ta kubce mana tabbas mun tafka babbar asara." Intisar ta faɗaɗa murmushinta sai da ta yi taku biyu sannan ta waiwayo ta ce, "Haƙiƙa zan jinkirta buƙatata har tsawon wani lokaci bayan mun cimma matsayarmu, amma tabbas ko ba yanzu ba akwai ranar da Ya za ta ɗakin ƙanwa, lokaci na tafe zan aiwatar da abin da yake ci mini tuwo a ƙwarya. Ni ma lokaci ya dawo mini da zan karɓo sihirtacciyar sandar mahaifiyata Bokanya Shirzan, a lokacin ne duk wani cikar ikona zai dawo." Tana rufe baki suka fara ƙyaƙyata wata irin dariya mara daɗin sauraron mai ɗauke da amsa kuwwar kukan jakuna, suna tsaka da kuka sai ga wani matashin saurayi ya diro cikin ɗakin hannunsa ɗauke wani jariri sabuwar haihuwa. Jaririn sai mutsu-mutsu yake ko jikinsa ba a gyara ba balle a yanke cibiyarsa, a kan tafin hannun wani gunkin tsoho da ke tsaye ya wara hannuwansa. Yana ɗora jaririn a kai nan take wannan Hatsabibiya da ke ɗauke da siffar tsuntsu ta taso ta dira a kan cikin jaririn. Wata ƙara ya ƙwalla saboda wata irin azaba da ke ratsa sassan jikinsa, da ƙafafuwansa tsuntsun ya huda ƙirjin jaririn ya kafa kai yana tsotsar jinin jaririn. Kafin wani lokaci tuni idanun jaririn sun ƙafe jikinsa ya saki numfashinsa ya ɗauke, tana ganin haka ta tashi daga kanta sai Intisar ta ƙarasa ta banƙare ƙirjinsa ta ciro zuciyarsa ta wurga bakinta ta cinye. Ɗaukan gawar jaririn ta yi ta miƙawa sauran mutanen wurin, da sauri suka caɓe shi suka buɗe wani ƙaramin ɗaki mai ja da baƙin labule suka wurga ciki. Raihan na zuwa gida a hankali ta fara zaga bangon da ke cikin ɗakunansu, ga mamakinta tana bi ta cikin ɗakinta ta hangi mai siffarta kwance a kan makwancinta a gefe ɗaya ga Mama Uwani tana zaune tana gadinta. Amma ga mamakinta sai gani ta yi ta gifta ta gabanta ba tare da ta lura da ita ba. Hasalima ratsawa take yi ta ko'ina ba tare da gini ko ƙofa sun yi mata shamaki ba, a hankali ta ci gaba da tafiya kamar mai tafiya a sararin samaniya har ta dira a ɗakin Mahaifiyarta sai da ta ƙare mata kallo sannan ta wuce ɗakin da Mama Hasiya take kwance tana bacci. Kamar yadda Hatsabibiya ta umarceta haka ta tsaya a saitin kanta, ƙashin hannunta ta kai saitin fuskar Mama Hasiya lokaci ɗaya ta buɗe idonta firgigit ta sauke su a kan Raihan, sai dai a cikin idanunta gani ta yi Raihan ta siffanta da wata mummunar hallita, cikin rashin tausayi Raihan ta ƙarasa gabanta ta damƙo maƙogaronta, nan take Mama Hasiya ta fara kakari idanunta suka firfito waje. Da murya mai wahalarwa Mama Hasiya ta fara karanta kalmar shahada, tana yi tana ambaton sunan Maigidanta da duk sunan wanda ya zo bakinta. Ana cikin haka wasu tafka-tafkan kunamu suka fara ratsowa ta jikin bango girman kowacce ɗaya ya fi girman kan jariri, da gudu suka fara rarrafowa suka haye gadon sun kai kusan goma suka maƙale a jikin Mama Hatsiya kowacce ta kafa bakinta suka fara zuƙar jini. Cikin tsananin azaba Mama Hasiya ta fara wani irin ƙaraji da gurnani, tun tana cikin hayyacinta har ta fara fita daga haka idanunta suka kafe rai ya yi halinsa. Raihan na ganin haka ta saki wuyan gawar Mama Hasiya ta faɗa kan gado yaraf ta ja mayafi ta rufeta sannan ta miƙawa kunamin nan hannu lokaci ɗaya suka maƙaleta, ta ɗago da su saitin fuskarta. Haƙoranta ne suka fara girma ga wata fiƙa irin ta karnuka da ta fito mata, bakinta ya fara zubda wani baƙin jini mai yauƙi. Ƙwayar idanunta zazzago suna wani irin juyi, a hankali ta fara takawa ta fice daga ɗakin ta koma ta sashen ɗakin Mahaifiyarta, ta jima a bakin window sai da ta yi ƙwafa sannan ta ratsa ta jikin bango ta fice daga gidan. Bayan sun wurga Jaririn cikin wannan ɗakin wata irin tsawa aka yi mai haɗe da walƙiya, a hankali hatsabibiya ta shiga ɗakin tuni wata mummunar hallita mai ɗauke da kawuna har guda goma a jikinta, a kowanne baki akwai aikin da yake aiwatarwa. A ɗaya daga cikin kan mummunar hallitar ta cafke jaririn tana laƙumewa, wani kan kuma ya fara amayo da kuɗaɗe kala-kala har da na ƙasashen waje, ya yin da wani kan ya fara tatsar da wani ruwa mai yauƙi yana zuba watsu ƙananan ƙwari suna zuwa suna tsotsa. Suna nan tsaya Raihan ta diro cikin gidan, hannuwanta biyu saƙale da kunamu tana tafe cikin takun ƙasaita dauke mummunar hallita. Tana zuwa Hatsabibiya ta fito fuskarta ɗauke da murmushi, shigar Raihan wurin ya sa jikin wannan dattijon ya fara ɓamɓarowa daskararran jikinsa ya fara rozayewa a hankali har ya rozaye gabaɗaya. Wata irin girgiza ya yi nan take ya fara kallon mutanen wurin ɗaya bayan ɗaya, Hatsabibiya ta tako a hankali fuskarta ɗauke da annuri ta ce, "Barka da dawowa cikin rayuwarka ta ainihini Ya masoyina." Hannuwanta ya riƙo yana bin ta da kallo lokaci ɗaya ya rungume ta yana shafa bayanta sannan ya ce, "Ina godiya da sadaukarwarki, amma ya aka yi kika samu tsarkakken jini alhalin an ce sai ta silar Muraza shin kun samota ne?" Hannunsa ta ja bakin wata tsohuwar rijiya da ke cikin ɗakin tana faɗin, "Mu je turaka zan baka labari." Tana rufe baki suka faɗa cikin rijiyar shigewarsu keda wuya wurin ya shafe tamkar ba a taɓa hallitar wani abu a wurin ba. Wani tutturnan mutum da suke kira da Mataimaki shi ya ƙarasa wurin Raihan ya karɓi kunamin hannunta, ya zuba su a cikin wani ƙoƙon kai sannan ya dubi Raihan ya ce, "An gaishe ki Jaruma, Shugaba mai cikakken iko sai ke gagabadau. Za ki iya tafiya sai ranar taro na gaba amma a ranar muna buƙatar tukwicin sabuwar gawar mace mai ƙarancin shekaru kar su yi ƙasa da talati kar kuma ta haura shekara arba'in." Raihan ban da jinjina kai babu abin da take yi, tana gama sauraronsa ta dubi Intisar alamar su tafi. Intisar ta nuna mata wata ƙoriyar ƙwarya mai cike da wani ruwa mai ɗauke da launin jini kamar anwanke nama, sannan ta ce: "Ki kuskure bakinki da ruwan tsarki domin samun albarka." Ba musu Raihan ta ƙarasa ta ɗauki ƙwaryar ta kafa kanta, tana kafa kai ta ji kanta ya sake yin nauyi dumm! A hankali ta iya kai ƙwaryar bakinta ta kuskure wata irin kasala ta mamaye jikinta, ga wani irin addababban bacci da ya lulluɓe idanunta. Tana ajiye ƙwaryar ta tafi luuuu za ta faɗi da sauri Intisar ta taro ta jikinta, sannan ta saɓa ta a kafaɗa ta fice daga cikin kogon dutsen kai tsaye ta wuce gidan su Raihan. Intisar bata tsaya a ko'ina ba sai a tsakiyar ɗakin Raihan, tana kallon Mama Uwani ta saki wani malalacin murmushi. Kwantar da Raihan ta yi sannan ta fara zagaye ɗakin ba tare da idanun Mama Uwani sun gane mata Intisar ba, lokaci ɗaya ta saki wata mahaukaciyar dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta durƙushe a wurin sannan ta ratse ta ƙarƙashin ƙasa ta fice daga ɗakin. WASHEGARI Da Asuba bayan su Inno sun gabatar da sallah suna zaune kowacce a sallayarta suna jan carbi, Goggo ta dubi Inno ta ce: "Wai ni kuwa yarinyar ta tashi sallah kuwa don ko motsinta ban ji ba, saboda Allah neman haihuwa ya fi bautar Ubaniji. Jiya na ga saboda neman haihuwa raba dare suka yi a wurin wancen Kafiriin, gaskiya a tambayi Malamai an ya; ya hallata neman haihuwa wurin kafiri." Inno takaici ya fara rufeta, ta dubi Goggo ta ce, "Zinaru ki yi ta kanki idan kika kafirta min yarinya a yau ba sai gobe wallahi sai Audullahi ya mayar da ke Albasu. Kafira ce da har yanzu za ta zauna babu sallah babu salati?" Goggo cikin nuna rashin damuwa ta wara hannuwa tana faɗin, "Allah shi ne masanin daidai, ba zan amsa ba ki sa na yi wa ƴar mutane ƙazafi akan abin da ban ji ba ban gani ba, ni dai na san da Hasiya ta tashi za ta leƙo wurinmu. Bari ki ga na je na tashe ta ko na samu lada mai tsoka, bar zancen Albasu tun da ko jini baki taɓa zubarwa a cen balle a binne mabiyyarki." Goggo na ƙarasa maganar ta fice daga ɗakin, tana tafe tana mita har ta ƙarasa bakin ƙofa tana ƙoƙarin buɗe ƙofar sai ga Inno ta rufo mata baya ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Saboda Allah Zinaru in haifi abartawa a ciki amma ki nemi ki yi mana farraƙu da ita, Allah ya sani idan Hasiya ta ga ban tashe ba na ɓalɓalce don ɗauka za ta yi baƙin cikin shiga aljanna nake yi mata." Goggo bata bi ta kan Inno ba ta tura ƙofar tana rangaɗa sallama, kamar haɗin baki suka shiga ambatar sunan Hasiya amma shiru suka ji kamar an shuka dusa. Inno ce ta yaye zanin rufar jikinta nan take suka yi tozali da gawarta, kusan suman tsaye suka yi aka rasa mai furta koda kalma ɗaya ne. Nan take Inno ta yanke jiki ta faɗi, Goggo jiki na tsuma ta juye hanyar waje tana ƙwalawa Mommy kira. Can sashenta ta wuce saboda fargaba tini ta zubar da carbi don lokaci ɗaya ya tsinke ya tarwatse, da kusan rarrafe Goggo ta hau sama tun bata ƙarasa ba suka ci karo da Mommy shi kansa Daddy kiran Goggo ne ya sa shi fitowa daga ɗakinsa a lokacin yana zaune yana cike-ciken takardu.Hankali a tashe suka shiga jera mata tambayoyi ban da nuna musu ƙofa babu abin da take yi, sai da ƙyar suka samu ta iya furta, "Hasiya babu ta riga mu gidan gaskiya." Cikin rashin fahimta suka ce, "Wace Hasiya?" Saboda ko a kaɗan basu kawo Hasiya a ransu ba. Goggo cike da jin haushi ta ce, "Hasiya dai ƙanwarka Audullahi ko kana da wata Hasiyan ne." Kusan tare suka nufi hanyar sauka don zuwa su ganowa idanunsu. Kamar masu rige-rige haka suka shiga ɗakin da Hasiya ke yashe a kan gado, Daddy ne ya fara zuwa kan Inno Mommy ta ƙarasa wurin gawar Hasiya ta fara tattaɓata tana ambatar sunanta amma shiru tafiya ta miƙa. Da hanzari Mommy ta wuce firji ta ɗebo ruwa ta fara yayyafawa Inno sannan ta yayyafawa Hasiya, nan take Inno ta fara motsawa saidai da alama bata cikin hayyacinta amma Hasiya ko alamar motsi bata yi. Daddy ne ya rungumo Inno ya fita a guje yana ƙalawa maigadi waya, kusan gware suka yi a hanya Daddy ya nufi wurin motoci yana faɗin, "Maza-maza buɗe min gate." Tun bai rufe baki ba Driver ya fara kiciniyar buɗe ƙofa nan take bawa motarsa wuta ya fice daga gidan, Mommy jiki a sanyaye ta bi bayan motar da kallo fuska ɗauke da hawaye. Ɗakin ta koma ta janyo hannun Goggo ta rufe ɗakin, kan kujera ta zauna ta rafka tagumi ban da hawaye babu abin da take yi, saboda ba ƙaramin shaƙuwa suka yi da Hasiya ba. Goggo ban da sintiri babu abin da take yi tana nan tsaye suka ga Mama Uwani ta fita, cikin rashin sani ta fara tambaya, Goggo da sai a lokacin kuka ya kubce mata cikin shassheka ta ce, "Bari Uwani yau mun wayi gari da tashin hankali Hasiya babu, yarinyar nan jiya-jiya muka gama hira da ita amma yau sai labari." A tsorace Mama Uwani ta nufi ɗakin don ganewa idonta, tana shiga ta samu gawar a kan gado cikin hanzari ta buɗe ta tana ƙarewa gawar kallo. Ido ta zurawa gawar tana jinjina kai a hankali ya furta, "Tabbas akwai lauje ciki naɗi amma akwai ɓoyayyan al'amari a dangane da gawar nan." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin zuwa falo, ba a ɗauki lokaci ba sai ga Daddy ya dawo. Dawowarsa babu wuya mommy ta tashi Raihan ta sanar da ita halin da ake ciki, murtsuke ido ta yi tana yamutsa fuska ta ce, "Mommy waye ya mutu?" Mommy ta sake maimaita mata, "Mamanki Hasiya yanzu haka gawarta na ɗaki mutane sun fara taruwa." Lokaci ɗaya ta ji kanta ya yi mata nauyi dum! Har sai da ta runtse idonta ta buɗe ta dafa kanta da hannu biyu ta ce, "Mommy me ya sameta ta mutu?" Da sauri Mommy ta rufe mata baki tana faɗin, "Raihan wa yace miki sai an yi ciwo ake yin mutuwa?" Jikin Raihan ba ƙaramin mutuwa ya yi ba, a hanakali ta tashi tana haɗa hanya jikinta sanye da rigar bacci shara-shara babu abin da ta ɓoye na surarta. Ɗakin da Mama Hasiya take ta tunkara Mama Uwani na hangota da sauri ta nufi wurinta ta rungomata tsam a jikinta tana faɗin, "Uwar ɗakina sai haƙuri." Wani iri Raihan ta ji a jikinta yarr a lokaci ɗaya kanta ya yi mata yaaaam! Tsigar jikinta ce ta ci gaba da tashi, a hankali ta saki hannunta tana bin Raihan da wani mayatattacen kallo. Kafin wani lokaci tuni gidan ya cika da mutane ban da koke-koke babu abin da ake yi, Raihan can gefe ta raɓe ta fashe da wani irin matsanancin kuka. Mai gidanta da aka gaya masa da farko ƙaryatawa ya yi sai da ya zo ya ganta, zama ya yi kamar mace ya yi ta kuka sai da ƙyar ya yi shiru. Kimanin ƙarfe goma aka gama wanke gawarta aka shiryata, ana gabda za a fita da ita sai ga Intisar ta turo ƙofa ta shiga gidan tana kallon mutanen gidan ɗaiɗai tana shigowa ana ɗaukan gawar, tana kalle-kalle Mama Uwani ta fisgi hannun Intisar ta ja ta ɗakin baya wanda baƙi suke sauka a ciki. Rai a matuƙar ɓace ta dubi Intisar ta ce, "Me ya kawo ki gidan nan?" Intisar dariya ta yi ta fara takawa a hankali sai da ta yi taku uku sannan ta juya ta kalli Mama Uwani ta ce, "Abin da ka ke yi cikin suffar tsofaffi shi ne ya kawo ni a wannan suffar." [7/1, 6:00 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI* ©AMEERA ADAM FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV FREE PAGE 1 Babban gida ne mai ɗauke da ɓangare daban-daban har kusan sashen mutum goma sha biyu. A taƙaice za mu iya cewa gidan gandu ne da ya haɗa Kakanni, 'ya'yaye da jikoki. Garin Ɗangwauro yana ɗaya daga cikin ƙanana ƙauyukan da ke cikin ƙwaryar Kano, Allah ya azurta su da noma, kiwo da kasuwansu. Gidan Malam Muhammadu mai dogon Carbi sanannan gida ne a kaf cikin garin Ɗangwauro. Tun daga titi idan ka tambaya za a kai ka har cikin gidan, sakamakon gida ne gidan yawa don wani lokaci mutane na yi masa laƙabi da gidan 'Ya'ya da yawa. Gidan Mai dogon Carbi cike yake da mutane sakamakom wayar gari da suka yi da rasuwar rashin wannan Dattijo mai yawan shekaru, ba iya gidan ba hatta garin Ɗangwauro ya girgiza da rashin wannan Dattijon mai dogon zamani. Yaya Babba da Inna Furai sune matan wannan Dattijo da ya rasu mutuwar ba ƙarmin taɓa su ta yi ba. Bisa ga al'adar Malam bahaushe a ranar da aka yi mutuwa mutane sun fi nuna damuwarsu ta hanyar koke-koke, kukan ma yana taƙaita yawancin bayan ankai mammaci. Hakan ce ta faru a gidan Mai dogon carbi domin an fita da gawarsa a yi mata sallah yara da Manya sai kuka suke yi. A gefe ɗaya Hali dubu na hango rakuɓe sai muzurai take lokaci-lokaci tana share hawaye, sai dai cikin zuciyarta haushin mutanen gidan take ji saboda ta lura babu wanda yake bi ta kanta don ya rarrasheta, duk kuwa da irin gursheƙen kukan da take yi. Kallonsu ta fara yi tana ayyana irin abin da za ta yi domin ta janyo hankulansu kanta. Tun da ai ita gani take kamar ta fi su jin mutuwar koda suna yawan faɗa da Mai dogon carbi amma kafin ya rasu, ai ita ma Kakanta ne. Sumi sumi sumi ta tashi da yaƙunannan hijabinta ta bi hanyar soron gidan tana waiwaye, sai da ta je soron ƙarshe daga shi sai fita Hali dubu ta ɗora hannuwa biyu akanta ta dawo cikin gidan da gudu tana cewa, "Wayyo Allah! Wayyo ni na shiga uku na lalace." Lokaci ɗaya hankulan mutanen gidan ya dawo kanta, da sauri aka yi carko-carko a kanta masu jero tambaya na yi. Zuciyarta ƙal don ko ba komai ita ma za a rarrasheta kamar yanda aka saka su Yaya Babba ana basu haƙuri. A fakaice take satar kallonsu tana sake sharce hawaye amma ta yi biris babu wanda ta tankawa duk irin tambayoyin da mutane suke yi mata. Baba Munkaila ne ya shigo ya hango cincirindon mutane a tsaitsaye da sauri ya ƙarasa wurin, ganin Hali dubu a zaune ya sa ya ja guntun tsaki sannan ya buga mata tsawa, "Ke lafiya kike yi wa mutane ihu?" Kamar sabuwar Marainiya haka ta ɗago shanyayyin idanuwanta ta kalle shi sai kuma ta waiga ta saci kallon ƙofa ta kuma duƙunƙune kanta cikin alamun tsoro da firgici. Kamar haɗin baki dukansu suka kalli bakin ƙofar suna neman ƙarin bayani, babu abin da ta furta musu sai ma kuka da take yi tana nuna musu ƙofar da ɗan yatsanta. Baba Munkaila tsawa ya sake buga mata ya ce, "Me ye a cen ɗin?" Hali dubu ta kuma kallon ƙofar ta rushe da kuka tana cewa, "Baffa ne!" Cikin haɗin baki duka suka ce, "Baffa kuma? Wane Baffan?" Bata bi ta kansu ba sai kawai ta baje a wurin ta fara wata irin birgima tana cewa, "Wayyo Baffa ne ya tafi ya barni!" Takaici ne ya rufe Baba Munkaila domin ya san za a rina don ya tabbata ganin Dubulliya tana wannan kukan ba banza ba. Cikin faɗa-faɗa ya fara yi mata magana amma ko gezau ba ta motsa ba. Can gefe ya hango wata igiyar dabbobi ai kuwa bai yi wata-wata ba ya fara tafka mata, tana jin shigar bulala ta tashi ta yi cikin gida ta gudu. Can ɗakin Yaya Babba ta shiga ta haye ƙarshen gado tana kuka, ga haushin Baba Munkaila ya tsinkata a cikin mutane. Tambayar duniya Yaya Babba ta yi amma Dubuliyya kanzil! Bata ce da ita ba. Sai ma ta yi zamanta a nan domin duk duniya babu abin da tafi tsana kamar taron jama'a a gidansu. Domin ba ƙaramin takura take yi ba, dalilinta na haka kuwa ta yanda za ta ji mutane na bata ji ko kuma ta cika rashin ji kamar ƴar aljanu. Tana daga kwance dabara ta faɗo mata ta yanda za ta kore jama'ar gidan ta ruwan sanyi domin ta san yanda danginsu suke sai a kusa arba'in da mutuwar da sauran baƙi tsiraru. Saboda haka Baffa mai dogon Carbi ya saba musu tun yana raye, idan suka zo taro baya barin ƴan uwansa su koma a kwana kusa. Wannan dabara tata ba ƙaramin daɗinta ta ji ba don har sai da ta murmusa saboda farin ciki. Kamar wacce aka tsirawa allura haka ta zabura da sauri ta fice daga ɗakin Yaya Babba, ita kanta Yaya Babba ba ƙaramin daɗi ta ji ba kasancewar duk duniya babu Jikarta da take so kamar ita sakamakon Marainiya ce gaba da baya. Dubu tana fita ta yi garau da ita kamar ba ita ta sharɓi kuka ba, nan fa mutane suka fara yi mata tsiya, har da masu cewa dama ita zuma ce sai da wuta. Wasu kuma su ce gara da ya yi mata haka ga shi ta ware ta fara harkokinta. Shiru ta yi babu wacce ta tankawa sai dai duk wacce ta yi magana tana auna maganar tata a mizani domin ta san irin hukuncin da za ta yi mata. Tun da Magriba ta doso Dubulliya ta fara haɗa kayan aikinta a fakaice cikin hikima da basira, ba tare da wani ya fahimci halin da take ciki ba. Sakamakon babban gida ne kowa da wurin da yake nema ya kwanta saboda ko ina a wadace yake hakan ne ya sa Yaya Babba bata damu ba da Hali dubu ta ce za ta sashen Baba Munkaila ta kwana a cen. DA DADDARE Da daddare gidan ya yi tsit ban da kukan tsintsaye da ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, sai munsharin bacci da yake tashi daga ɗakunan daban-daban. Dubuliyya tana daga sashen Baba Rufa'i cikin ɗaya daga cikin ɗakunan ƴaƴan gidan. Sai da ta ci baccinta ta more sannan ta farka cikin talatainin dare ta ji gidan tsit kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki ta zaro kayan marigayi Baffa ta saka rigarsa da babbar riga har da hula ta naɗa rawaninsa ta ɗauki zabgegen carbinsa ta maƙala ta fito, hasken farin wata ne ya haska mata hanyar da za ta rinƙa bi har fice daga sashen gabaɗaya. Can wurin da ya zamewa Marigayi Baffa mai carbi wurin alwala can ta je ta tsugunna, daga nesa idan ka hango Dubu a tsugunne sai ka rantse da Allah Baffa ne, sai da ta waiga hagu da dama sannan ta taƙarƙare ta fara zabgo kaki irin yanda Baffa yake yi, Baba Sule da ke kwance cikin baccinsa ya fara jin alamar kaki tamkar yanda mahaifinsu yake yi duk asuba. Fakare ya yi yana zare idanu, yana cikin wannan yanayin ya sake jin an yi kaki har da irin tarin tsofaffin nan da Baffa yake yi. Janyo wayarsa ya yi yana dubawa ya ga ƙarfe biyun dare, nan take ya hau murza idanu yana sake kasa kunne. Dubu kamar ta san ana sauraronta ta kausashe murya sai ka rantse da Allah Baffa ne yake magana ta fara cewa, "Tabbas rayuwar barzahu daɗi gare ta." Baba Sule ya waro idanu wace cikinsa na karta masa, don ya tabbata hatta dabbobin gidan da suna magana za su ce sun shaida maganar Baffa ce cikin daren nan. Dubu na tsugunne ta ji alamun tahowa wata zuciyar ta ce mata ta tashi ta ɓuya, wata kuma ta ce ta zauna ta ci gaba da abin da take yi. Tarin Inna Furai ta ji ta saci kallonta ta hangota da ƴar buta a riƙe za ta je banɗaki. Dubu wani kakin ta sake yi tana daga tsugunne, hasken farin wata ne ya hasko mata mutum durƙushe da fararen kaya da rawani tamkar marigayin mijinsu. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa ta fara motsa baki cikin addu'a don a zatonta mugun gamo ta yi. Ɗauke kai ta yi don ma kar ta ci gaba da kallon wurin da Dubu take ta ci gaba da tsoratata, sai da ta kusa da wurin da Dubu take ta ji muryar marigayin mijinsu raɗau a kunnenta yana cewa, "Wato ita dai rayuwar barzahu daɗi gare ta. Babban daɗin idan ka kawo ziyara tsohuwar rayuwarka sai kuma ka tafi da matarka." Inna Furai na jin haka ta dafe ƙirji tana ja da baya jikinta har tsuma yake ta ce, "Yau na haɗu da zazzagar rayuwa ni Furaira. Allah na roƙeka karka jarrabe ni ta wannan fannin." Dubu na jin haka ta miƙe tsaye tana gyara zaman babbar rigar jikinta ta sake kausashe murya ta ce, "Wuni ɗaya har na yi abokai miliyan ɗaya da ɗari biyar a cikin Fatalen har da masu tashi sama. Ƴan sama jannati ku zo ga wani naman mun samu, kuma daga yau mun fara ɗauka kenan a gidan nan. Duk wanda ya wayi gari ya ga likkafani a jikin kayansa shi za mu yi wa ɗaukan amarya." Inna Furai tuni fitsarin da take riƙewa ya samu sukunin tsiyayowa, sakin butar hannunta ta yi jikinta na tsuma donma bongon da ke bayanta ya tokareta. Dariya ce ta so ƙwacewa Dubu amma ta maze ta ce, "Ƴan uwana ƴan sama Jannati! Ku zo na fara samo muku ƴar uwa." Inna Furai ta saki salati tana cewa, "Yau na haɗu da zazzagar rayuwa shi kenan tawa ta zo ƙarshe." Dubu sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta fara takowa gaban Inna Fuarai ta ce, "Idan kina son fansar kanki sai kin sake shayar da ƴaƴanki tamkar yanda kika shayar da su suna jarirai, tun daga kan Larai (Ita ce babbar Ƴar Inna Furai) har zuwa kan Sabi'u (Shi ne autanta) idan kika kuskurewa haka tabbaci haƙiƙa sai mun zo ido biyu mun tafi da ke babu wanda ya isa ya hana." Baba Sule tuni cikinsa ya ɗuri ruwa yana son fita domin ceton Matar Mahaifinsa tsoro ya cika masa ciki, bai gama tsinkewa da lamarin ba da ya ji an fara kiran yan sama jannati. Dubu don ta ƙara razana Inna Furai ta sake dakushe murya ta ce, "Ki isarwa da mutanen gidan nan saƙona muddin suka ci gaba da kwanaki sai na yi musu ɗauki ɗaiɗai. Shi kuma na ɗaki da yake laɓe yana sauraronmu, shi kuma ɗauke shi za mu yi gabaɗaya." Dubu na cikin magana sai gani ta yi Inna Furai ta zube ƙasa. Gabanta ne ya faɗi ta ji fargabar kar tsohuwar mutane ta mutu a hannunta. Da sauri dubu ta waiga sai kuma ta kurma ihu tana maƙe murya ta zunduma ihu, sannan ta zuba a guje ta yi cikin gida. Ta nufi ma'ajiyar kayan Baffa ta lallaɓa ta shige ta kwanta. Ihun da Dubu ta yi ba ƙaramin razana Baba Sule ya yi ba da jim kalaman da da aka ce za a ɗauke shi matuƙar ya saki hannun matarsa. Yana daga gefen gado da sauri ya matsa ya kama hannuwan matarsa ya riƙe ƙam, don kar a neme shi a rasa. Cikin bacci Sahura ta fara masifa da yake Allah ya yi ta masifaffiyar macece. Tana jin ya riƙo mata hannu ta ce, "Don Allah sakarni Uban ƴan naniƙa." Da yake bacci ya hau kanta bata kuma tanka masa komai ba. Daga ɗaki mai kallon gabas Baba Auwalu ne ya ɗaga labule yana haskowa da fitila zaraf matarsa Yahanasu ta miƙe tana tambayarsa da yake su sabbabun amare ne. Daga can nesa suka hango Inna a yashe tana ko numfashi bata yi. Gabansa ne ya faɗi yace, "Wa nake gani kamar Inna a ƙasa." Sahura ta dafa kafaɗarsa ta ce, "Auwaluna ni ban yarda ita bace kawai magauta ne suka yi maka ture." Duk duniya babu abin da Auwalu ya tsana sama da a ɓata ran Yahanasu amma tabbas wannan karon ba zai iya haƙura ya bar Mahaifiyarsa a wannan yanayin ba. Kasancewar dare ne amma bai hana sakar mata murmushi ba ya ce, "Allah shi zai kare ni amma bana tunanin wani zai yi mini ture cikin dare." Kafin ta yi magana tuni Auwalu ya yi gaba, ganin haka ya sa ta ja tinga ta tsaya don har ga Allah a tsorace take musamman da ya kasance ranar ne aka yi rasuwa. Hankali a tashe ya fara yayyafawa Inna ruwa ganin ta fara motsi ya sa ya kamata yana bubbuga ƙofar Baba Sule, Baba Sule na ji ya yi fakare kamar mai bacci don gabaɗaya ya gama rikicewa. Sama-sama Sahura ta fara jin bugun ƙofa firgigit ta miƙe sai ji ta yi Sule ya riƙe hannunta gam, tana shirin yin magana Baba Sule ya janyota cikin raɗa ya fara cewa, "Kada ki yi magana za su yi sama da ke" Waigawa Sahura ta yi tana kallon ƙofa don ita a tunaninta masu buga ƙofar ne za su yi sama da ita. Suka ƙarajin bugun ƙofa Auwalu yana cewa, "Yaya Sule fito ka taimaka mini jikin Inna ya yi tsanani ina jin makewayi za ta ta faɗi." Sahura ta ja guntun tsaki ta ce, "To! Sai ka tashi tun da ta ka ji muryar Auwalu." Baba sule ya sake ƙasa da murya yanda daga shi sai Sahura ne za su ji abin da yake faɗa ya ce, "Ki koma ki kwanta kawai ina ji a jikina waɗannan ƴan sama jannati ne suka rikiɗa. Takaici ya kama Sahura yanda ta ga Maigidanta yana rawar ɗari ga shi ba lokacin zafi ba, ta miƙe tana fusgar hannu ta ce, "Sakarni ko ƴan ƙasa jannati ne babu abin da zai hanani fita."Tana jan hannu Baba sule yana ja don a tunaninsa muddin ta saki hannunsa shi kenan za su yi sama da shi. Sororo Sahura ta yi tana kallon ikon Allah, don ita a iya saninta da Sule ba su taɓa irin wannan wasan da shi, don haka ta sake ɓata fusaka ta ce, "Sule wai wani abu ne yake damunka ko gamo ka yi cikin dare n sani ba?" Baba Sule ya yi wura-wura yana kallon hagu da dama ya sake ƙanƙance murya ya ce, "Sahura a kowanne lokaci za a iya yin sama da ni." Wani takaicin ne ya sake rufe ta, ta miƙe tana ƙoƙarin fisge hanunta amma abin ya ci tura don ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya. Auwalu da ke jin ƙusur-ƙusur a ɗaki sai ya sungumi Inna don a ganinsa bai kamata ya sake buga ƙofar ɗakin ma'aurata cikin dare ba. Can sashen su Inna Furai ya nufa Yahanasu ta ƙwalla masa kira tana cewa, "Auwaluna ina za ka ni dai tsoro nake ji." Auwalu ya waigo ya ce, "Shiga ɗaki Inna zan kai na dawo." Dubu na daga ɗaki tana jin duk abin da yake faruwa, tana jin Baba Auwalu ya tafi ta yi zaraf ta fito cikin sanɗa sai da ta zo daga bakin ƙofar Yahanasu ta yi gyaran murya ta sake kausashe murya irin ta Marigayi mai carbi ta ce, "Wato ita rayuwar barzahu daɗi gare ta ni Mamman. Yanzu tun da na zagayo rayuwata ta baya dole na ɗauki mai ɗakin nan." Cikin Yahanasu ne ya kaɗa nan take jikinta ya hau karkarawa kamar mazari. Dubu ta yi irin tarin tsofaffin ta sake cewa, "Amma ita Yahanasu za mu ɗaga mata ƙafa sai dole ta bi sharaɗinmu ko ba haka ba ƴan sama jannati?" Dubu ta sake sauya murya ta ce, "Ai dole ma ta bi umarninmu ko yanzu mu faɗa ɗakin." Yahanasu bata san lokacin da ta yi farat ta ce, "Wallahi ku faɗa ko meye zan bi." Dubu ta maƙale murya ta ce, "Dole ki zama makauniyar ƙarfi da ya ji muddin kika buɗe idonki sai dai ki wayi gari a ƙiyama." Tun Dubu bata rufe baki ba Yahanasu ta runtse ido biyu ta ce, "Wallahi na rufe har abada ba zan sake buɗe su ba amma don Allah karku cutar da ni." Dubu har da ƴar tsawarta ta ce, "Kin tabbata kin rufe ko na aiko da Ƴan sama jannati su shigo?" Yahanasu ta sake runtse idonta tana cewa, "Na rufe wallahi na rufe." Dubu ta saki murmushin mugunta a ƙasan zuciyarta tana cewa, "Yau zan ga ƙaryar soyayya kullin a ishe mu da Auwaluna." A fili Dubu ta ce mata, "Maza tashi tsaye ki rungume bango." Da sauri Yahanasu ta fara lalaube-lalube har ta taɓo bango. A hankali Dubu ta zura kai ta leƙa ta hango Yahanasu na rungumar bango, zuruf ta faɗa ɗakin cikin sanɗa. Sai da ta je daidai wurin Yahanasu sannan ta ɗaga zabgegen Carbin Marigayi ta zabgawa Yahanasu a ƙeya, sai ta fara wani gunji tana cewa, "Gargaɗin yan sama jannati kenan." Tana faɗar haka har ta fice daga cikin ɗakin. Yahanasu tun da ta gantsare take hawaye a tsaye sai dai ta kasa buɗe idonta saboda tsoron abin da kaje ya zo. Duk abin da yake faruwa a kunnen Sahura da Baba Sule, cikin Baba sule ne ya sake ɗurar ruwa. Sahura ita kanta jikinta ya fara sanyi musamman da ta jiyo Ihun Yahanasu, shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta duk masifar da take yi ta daina. Domin da alama zancen Sule ya tabbata. Lokacin da Auwalu ya ƙarasa ɗakin Inna Furai, har lokacin bata dawo hayyacinta ba. Yana shiga ya kwantar da ita akan ƙaramin gado, sannan ya fara tashin ƙanwar Mahaifinsu Lantan da ta zo daga garin Zariya. Ganin halin da Inna Furai take ciki ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen ɗakin ya yi ba. Auwalu ya juya zai fita Inna Furai ta riƙo hannunsa ta ce, "Auwalu! Yau na haɗu da zazzagar rayuwa. Don haka ka haɗo mini kawunan ƴan uwanka mazan su da matan su a yanzun nan. Idan ba haka ba wallahi sai na zazzagar da albarkasu kowa ya lalace." Auwalu da sauran mutanen ɗakin sun yi tsammanin zafin ciwo ne ya sa Inna Furai take sumbatu. Lantan ta ƙara matsawa kusa da Inna Furai ta ce, "Furaira sanu kin ji Allah sa dai ba akan makarai kika faɗi ba." Wannan magana ba ƙaramin fusata Inna Furai ta yi ba, a zafafe ta ɗago ta ce, "A kan bulikiya na faɗi! Lantan bana son zazzagar wulaƙanci. Kai Auwalu ka tara mini ƴan uwanka a daren wallahi tun ban zazzage albarkar da ke kanka ba." Kamar sabon munafiki haka Auwalu ya fice sum sum sum daga ɗakin. Haka ya rinƙa bi ɗaya bayan ɗaya yana taso su. Wannan tashin da Auwalu yake yi wa ƴan uwansa ne ya sa kusan rabin mutanen gidan suka tashi daɗin daɗawa idan kowa ya ji ance Inna Furai ta faɗi a hanyar banɗaki sai ya wartsake masu tafiya ɗakinta na yi masu jaje suma suna yi. Kafin wani lokaci tuni ɗakin Inna Furai ya cika da ƴaƴanta su rai takwas maza biyar mata uku. Sai da ta kalle su ɗaya bayan ɗaya sai kawai suka ga ta ɗaga riga ta ce, "Larai bisimillah" Larai zuciyar ta ɗaya ta ɗauka Inna Furai so take a ƙarasa cire mata riga, nan take ta fara cikiniyar tuɓe mata riga. Cikin ƙaraji Inna Furai ta fisge tana cewa, "Larai yanzu bijirewa umarnina za ki yi? Ni za ki zazzagewa albarka a ka" Sai ji suka yi Inna Furai ta fashe da matsanancin kuka. Lokaci ɗaya suka kalli juna domin ba su ga abin da zai sa Inna Furai kuka ba. Auwalu ya sunkuyo ya ce, "Inna ki yi hakuri me kike so?" Inna Furai ta ɗago mamanta ɗaya ta ce, "Mahaifinku ya zazzage mini albarka ɗazu nan domin daga zuwansa lahira har ya haɗa kai da ƴan sama jannati. Ba zan zazzage maka bayani gabaɗaya ba amma Auwalu ungo sha ka ji." [7/1, 6:02 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI* ©AMEERA ADAM FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV FREE PAGE 2 Auwalu sam bai fahimci inda maganar Inna Furai ta dosa ba, don tun da ya ji ta ambaci Mahaifinsu ya tabbatar da zafin ciwo ne yake damunta da kiɗimewar rashin da aka yi musu. Saboda gudun faɗanta ya sa ya wayance da cewa, "Inna ban fahimci abin da kike faɗa ba. Amma kuma duk wanda ya mutu kin san sai dai mu bishi da addu'a ita ce mafita." Inna ta yi ƙuri tana kallonsa sai zuwan can kawai ta fashe da kuka. Lantan da ke gefe takaici da baƙin ciki gabaɗaya suka turniƙe ta, don gani take kamar har da biyu Inna Furai take lanjarewa. Kasa haƙuri ta yi ta ce: "Furaira don Allah ki shafa mana lafiya ki bar mu, mu ji da abin da yake damunmu. Haka kawai ki tayar mana da balli a tsakiyar dare akanki aka fara mutuwar miji? Ko kuma ke kaɗai kika san zafin miji muna zaune ki ishe mu da zancen fatalwa. Ki barni na kwanta na yi baccin da ban samu na yi shi jiya ba." Inna Furai ta fyace majina da gefen zaninta ta waiga ta ce, "Wallahi babu ƙatuwar Matar da za ta zo mini ɗaki ta nemi kawo mini zazzagar albarka ido biyu. Idan ba za ki iya ba ki tashi ki fice dama ni bana gayyar tsintsinya da bulugari, bare kuma mafici abin banza." Lantan jin maganar Inna Furai ta yi kamar ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta zaburo a hasaale ta ce, "Ban da ƙaddara da rashin ɗan'uwana da na yi, me zai kawo ni ɗakinki kaico Allah ya jiƙanka Yaya Mamman. Wai yau jininka ake wulaƙantawa saboda ƙasa ta rufe mata ido, kai jama'a ɗan'adam butulu. Wanne irin karamci ne Ɗan'uwana bai yi miki ba?" Inna Furai ta jingina da ƙarfen gado sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, tana yi tana fatar majina. Abin duniya goma da ashirin ne damu su Auwalu, don haka kowa ya yi jim! Babu wanda ya iya tofa magana ɗaya sai gani suka yi Inna Furai ta fara haɗa ƴan kayayyakinta na sawa da ke kan gado. Sabi'u ya ce: "Inna lafiya kuwa wai me yake faruwa ne kike haɗa kaya?" Inna Furai ta juyo a fusace ta ce, "Zaman ku a nan bai amfane ni da komai ba. Kuna gani ta gama zazzage mini rashin mutumci a ka babu wanda ya tanka mata. Wallahi ko ku bi mini haƙƙin zazzagar albarkar da ta yi mini a ka ko kuma yanzu na fice na baku wuri ku yi yanda kuke so. Gara ni tawagar Malam da ƴan sama jannati ta zo ta ɗauke ni ko kowa ya huta, dama na kiraku ne domin mu kashe mu binne amma da alama ku dai ba ƴan goyo ba ne, don na lura za ku iya zazzage mini sauran albarka da ta rage mini a kaina. Gabaɗaya shiru suka yi suna nazarin abin da yake damun Mahaifiyarsu, don rikici sun san Mahaifiyarsu mace ce mai matuƙar rikici amma wannan karon gani suke har da mutuwar mahaifinsu da ta taɓa ta. Lantan na gama sauraron Inna Furai ta miƙe tsaye tana shartar ƙwalla, ɗan ƙullin kayanta da ke ƙarƙarashin gado ta janyo ta fara kiciniyar ɗorawa a ka tana matsalar hawaye. Da sauri Auwalu ya miƙe ya riƙe kayan yana cewa, "Inna Lantana don Allah ina za ki a tsohon daren nan?" Lantan ta kunto mayafinta ta yafa a kanta ta ce, "Auwalu don Allah karka kawo mini maganar da za ta tunzurani har ta kai ga na nemi shaƙe wannan tsohuwar har lahira. Duk irin cin mutumcin da ta yi mini a gabanku baku gani ba za ka taso tsalo-tsalo kana tambayata ka bar ni yau ko ƙasa da sama za ta haɗe ba zan kwana a gidan nan ba." Nan fa hayaniya ta fara ta shi a cikin gidan, Inna Furai na gama saurarar maganar Lantan ta sa hannu bibbiyu ta dafe ƙirji a razane tana zare idanu kamar wacce ta yi tozali da kumurcin maciji. Bata tanka musu komai ba sai gani suka yi ta sauko ƙasa daidai wurin da Lantan take tsaye ta fashe da kuka haɗe ta rungumo ƙafafuwan Lantan tsam a jikinta. Tana cikin kuka ta ɗaga kai ta dubi Lantan tana cewa, "Wallahi ba za ki bar ɗaƙin nan ba sai kin zazzage ragowar numfashin da nake shaƙa, Lantan yau ni kike muradin kashewa a gaban ƴaƴana. Ai kuwa ko ba yanzu na mutu ba na rataya a wuyanki Kai Auwalu ku shaida haka." Inna Furai ta juya ga su Auwalu tana musu mugun kallo ta ce, "Allah na tuba wacce uwar na haɗa da su bayan alaƙar haihuwa? Da su Auwalu da Sabi'u kuma ni kam gara ma a ce ban da kowa tun da babu mai tare mini faɗa a gidan nan. Har ana niyyar halakani da sauran rayuwa kai jama'a Lantan an ya kina tsoron Allah kuwa? Duk wanda ya kashe wani dai wuta za shi." Lantan ta yi tsalle can gefe abin ka da da marar jiki, can gefen babban gado ta matsa tana cewa, "Laƙadi ja'akum... Tuf! Aniyarki ta faɗa kanki karki ja mini masifa ki maƙala mini sharrin kisan kai ina zaune ƙalau." A wannan karon Inna Furai bata tanka mata ba sai gani suka yi zaraf ta fice daga ɗakin, da sauri iyalanta suka bi bayanta suna roƙon ta dawo ɗaki saboda dare. Tana fita ita ma Lantan ta sa ƙafa ta fito ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin su Auwalu ya yi ba, musamman shi da yana tsaye a nan ne amma zuciyarsa na wurin Yahanasu yana tunanin halin da take ciki. Inna Furai na ganin Lantan ta fito ta bita jiki a sanyaye kamar kazar da ake jefa da gishiri ta ruƙo hannunta sannan ta fashe da kuka. Ita ma Lantan zuciyarta ce ta karye sai kawai ta fashe da kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan Inna Furai ta ce, "Yanzu Lantan da na barki tafiya za ki yi a daren nan?" Lantan ta fyace majina a haɓar zaninta ta ce, "Ina zan iya tafiya na barki Furai kina cikin jimamin rashin miji, Furaira rashin miji tashin hankali ne har kin tuno mini da rasuwar Mahaifinsu Ɗan'iya kai rayuwa babu tabbas Allah ya jiƙanka Malam Mudassiru." Lantan ta rushe da matsanancin kuka. Rabe ya matso da niyyar rarrashinsu Inna Furai ta doke hannunsa tana cewa, "Allah wadaran naka ya lalace. Wallahi kaf gidan nan banga wanda zai hanani zazzage muku albarka ba. Wai kamar yanda Lantan take a wurina ta tashi za ta tafi cikin dare amma babu mutum ɗaya da zai hanata tafiya kaico! Wallahi kun ji jiki ƴan bakinciki bantaɓa sanin bakwa ƙaunar aminiyata ba kuma ƙanwar Mahaifinku ba sai yau."Inna Furai na gama maganar ta ja hannun Lantan suka bar su Auwalu a tsaye sake da baki. Ba su da zaɓi haka suma suka bi su Inna Furai ciki, cikin ƙaguwa Auwalu ya ce, "Inna za mu iya tafiya yanzu?" Inna Furai ta saki salati ta na kallon Auwalu da wani yanayi har sai da ya tsargu ya ɗan fara sosa ƙeya sannan Inna Furai ta ce, "Wallahi kai dai Auwalu na riga da na san matsayina a wurinka. Tun mahaifinka na raye har ya mutu ban taɓa musa wa maganarsa ba, sai yau don ƙasa ta rufe masa ido?" Ta fashe da kuka tana ci-gaba da cewa, "Ban shirya mutuwa da shiga jahanna ba. Sharaɗi fatalwar mahaifinku ta bani sai na shayar da ku mama kamar yanda na shayar da ku kuna yara, kuma ban ga wanda zai hanani bin umarninsa ba." Lokaci ɗaya suka ɗauki salati gabaɗaya saboda ta'ajibin jin maganar Mahaifiyarsu, Larai cikin matsananciyar damuwa ta ce, "Inna kin san me kike faɗa kuwa? Yanzu kina nufin Baba ne ya yi miki fatalwa? Inna don Allah kar wani abu ya ruɗe ki ko ya tsorata ki saboda wanda ya mutu ya mutu kenan ba zai ƙara dawowa ba. Sai dai idan shaiɗan ne yake son razanar..." A hassale Inna Furai ta katse Larai da cewar, "A'uzubillahi minasshaɗanirrajim. Ba zan ga shaiɗan da idona ba Larai kafirta ni kike son yi da za ki haɗa ni da Shaiɗan la'anannan Allah?" Larai rasa hanyar da za ta ɓullowa Mahaifiyarta ta yi don gabaɗaya sun rasa gane kanta. Lantan da ke gefe ta kalli Larai ta ce, "Wallahi ki tubar wa Allah idan ba haka ba, azabar Allah tuni za ta yi fata-fata da ke. Kuma ni gani nake maganar Furaira tana kan hanya don ni kaina lokacin da Malam Mudassiru ya rasu har gizo ya riƙa yi mini a tsakar ɗaki. Don haka ku yi biyayya idan ba haka ba duk cikinku babu mai kaucewa azabar Ubangiji, musamman kai Rabe da ka fi tsoka wallahi tuni wuta za ta tsotse namanka ka lalace a jahannama." Ganin wannan lamarin yana ƙoƙarin zama babba ya sa Auwalu ya zame jikinsa ya je Shagon Soro ya taso Yayan mahaifinsu ya sanar da shi halin da ake ciki. Har ɗakin Inna Furai ya shiga yana shiga ya same ta, ta yashe riga a sama tana kumfar bakin Larai ta tsugunna ta fara karɓa tun da sauran mazan taurin kai za su nuna mata. Da sauri ya ɗauke kansa gefe don bai yi tsammanin abin da suka faɗa da gaske ba ne. Nan take ya shiga yi mata nasiha amma duk da haka Inna Furai ta shafawa idonta toka ganin haka ya sa ya fara lallashin ta bari zuwa safiya sai a san abin yi. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu shawo kan Inna Furai ta haƙura zuwa safiya sannan kowa ya kama gabansa. Bayan tafiyarsu Lantan ta zabga uban tagumi sannan ta ce, "Yanzu Furaira da idanunki biyu kika yi tozali da Yaya Mamman ni fa ɗazu ƙarya na kirfo da na ce ina ganin Fatalwar Mudassiru, saboda yaran nan sai su raina mu ni kuma a duniya babu abin da na ƙi jini irin raini." Inna Furai ta miƙawa Lantan hannu ta ce, "Lantan taɓa ni na ji." Da sauri Lantan ta kai hannu tana shafa hannunta. Inna Furai ta mirtsika ido ta ce, "Billahilazi idan har wannan taɓawar da kika yi mini mafarki ce to a mafarki na ga Malam. Wallahi da idanuna na ganshi a wurin zaman alwalarsa amma tun da baku yadda ba nan gaba na kuma ganinsa nasa ya fitowa kowa a zahiri." Kamar wacce aka tsamo daga ruwan sanyi haka jikin Lantan ya yi sanyi ta rasa abin faɗa don hantar cikinta ta fara kaɗawa musamman da ta san Inna Furai ba ta yin rantsuwa sai da ƙwaƙƙwaran dalili. Kwanciya suka yi sai dai kowa da abin da yake wassafawa a cikin zuciyarsa. Duk cikin ƴaƴan Inna Furai babu wanda ya fi farinciki da tafiyarsu irin Auwalu saboda zuciyarsa gabaɗaya hankalinsa yana wurin Yahanasu don ya san a wannan lokacin tuni ta yi fushi sai ya yi aikin rarrashi. Yana tafe yana haska fitila har ya ƙarasa ɗakin, sai dai turus ya yi a ɗan tsorace yana karewa ɗakin da Yahanasu kallo. Fitsarin da ya ƙarasa gangarawa ƙafarsa ne ya dawo da shi daga duniyar tunani, matsawa ya yi gefe yana leƙa fuskar Yahanasu da ke manne da bango ya ce, "Yahanasu lafiya kuwa?" Yahanasu na jin muryar Auwalu ta rushe da kuka tana cewa, "Auwalu fatalwar Baba na gani wallahi shi ne har cewa ya yi za su tafi da ni." Cikinsa ne ya bada wani sautin ƙulululu! Da sauri ya ja baya yana dafe ƙirji ya ce, "Kina nufin da gaske kema kin ga fatalwar Baba?" Yahanasu ta nuna masa gadon bayanta ta ce, "Duba ka ga shatin carbinsa a bayana har dukana ya yi da shi kuma ya ce daga yau kar sake buɗe idona." Tsoro ne ya mamaye zuciyar Auwalu musamman da idanunsa suka yi tozali da shatin carbin Mahaifinsu ruɗu-ruɗu a jikinta. Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da ya hango wani guntun likkani a gefen ƙafar Yahanasu. Da sauri ya fisgota suka faɗa gado jikinsa na rawa ya ce, "Yahanasu wallahi maganarki haka take kin ga Likkafani can a ƙasa." Yahansu na jin haka ta ƙara rintse ido tana kuka kamar hawayenta za su ƙare. Auwalu ne ya yi ta maza ta miƙe cikin sanɗa ya banko musu ƙofa da ƙarfi ya sa sakata. Duk abin da yake faruwa a kunnen Baba Sule da Sahura har zancen Likkafani, wannan maganar ba ƙaramin ɗaga musu hankali ta sake yi ba. Don da har bacci ya fara yunƙurin awon gaba da su kukan da Yahanasu ta rushe da shi ne ya wartsakar da su tare da sa su yin carko-carko kamar masu shirin ko ta kwana. Dubu tun da ta koma ta yi luf sakamakon motsinta ya so tashin Hasiya Matar Rabe, don haka ta yi kasaƙe daga haka ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita don hatta sallar Asuba sai da aka yi da gaske sannan Dubulliya ta samu gabatar da ita. Washegari. Jama'ar gidan gabaɗaya kowa ya tashi an ci gaba da harkoki kamar ba taron mutuwa ba. Sai dai gabaɗaya labari ya watsu a ko'ina Inna Furai ta yi ido huɗu da fatalwar Maigaidansu, labarin da wasu suka riƙa ganin kamar tsufa da rikici ne yayin da wasu suke ganin tsabar dukan da mutuwar ta yi mata ne. Sai dai babban abin da ya ja hankulan mutane ganin ɗakin Baba Sule da Auwalu ya rufe. Ko motsinsu babu wanda ya ji bare a sa ran za a ga fitowarsu. Ɗakin Baba Sule aka fara zuwa ana bugawa, Sahura ta zabura za ta miƙe saboda ta ji muryar mutane don ta yanda ta ayyanawa zuciyarta muddin ta samu ta fice daga ɗakin to ba za ta ƙara kwana a gidan ba sai gidan Mahaifinta. Sai dai tana miƙewa caraf Baba Sule ya damƙi hanunta yana cewa, "Ina za ki tafi ki bar ni?" Sahura ta ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce, "Ai mutanen gida sun tashi ka ga muma sai mu fita zaman ɗaki ba zai kai mu ba." Baba Sule ya yi fakare yana nazari sannan ya ce mata, "Sahura yau ko bayan gida za ki shiga wallahi sai dai mu tafi tare, don ba zan bari matattu su tafi da ni da kwana na a gaba ba." Bugun ƙofar ne ya tsananta don haka suka taso riƙe da hannun juna suka zare sakata, sai dai suna buɗe ƙofa kyallen likafanin da Dubu ta soka musu ya faɗo. Daga waɗanda suke tsaye a ƙofar ɗakin har su na cikin ɗakin bazama suka yi a guje, suka yi cikin gida. A cen ɗakin Yaya Babba suka yada zango sai dai har lokacin Baba Sule yana riƙe da hannun Sahura. Yaya babba sakin baki ta yi tana kallon Baba Sule da ya yi tsamo-tsamo a cikin mata ta ce, "Sule me kake yi a kan cinyar Uwani?" (Uwani ƙanwar Mahaifiyar Sahura ce.) Baba Sule gabaɗaya zuciyarsa a dagule take saboda gani yake rayuwarsa ta zo ƙarshe. Ba baka sai kunne. Baba sule ban da hawaye babu abin da yake yi. Wannan shirun da Baba Sule ya yi ba ƙaramin ɓata ran Yaya Babba ya yi ba, don haka ta dube shi ta ce, "Bana son iya shege kai Sule idan ba za ka yi magana ba, ka fice mini daga ɗaki ko na kwashe maka albarkar da ta yi saura a kanka." Baba Sule ya sake matsar ƙwalla ya ce, "Inna wallahi Fatalwar Baba ce za ta tafi da ni matukar na saki hannun Sahuwa ƴan sama jannati ne za su tafi da ni." Ku san mutuwar zaune Yaya Babba ta yi saboda labari ya risketa daga wurin kishiyarta ga shi Ɗan cikinta ma ya sanar da ita. Nan fa gida ya hautsine hantar cikin kowa ta kaɗa saboda fargaba, Sai da Yaya babba ta yi da gaske sannan Baba Sule ya saki hannun sahura. Ai kuwa yana sakin hannunta ta ranta ana kare. Baba Sule na ganin haka ya rufa mata baya. Sai da ƙyar aka samu aka tsayar da su a soron gidan tare da tura Baba sule cikin ɗaki don Yayan Mahaifinsu gani yake kamar gamo ne suka yi. Dubu ban da dariyar mugunta ƙasa-ƙasa babu abin da take yi. Sai daga baya aka farga da su Auwalu da suke ɗaki don haka da sauri Yayan Mahaifinsu ya je ya sa suka buɗe ƙofar da ƙyar, Auwalu yana maƙale da Yahanasu don gani yake idan ya sake ta kamar Fatalwar Mahaifinsa za ta yi awon gaba da ita. Malam Idi shi ne yayan Mai Carbi, tara mutane gidan ya yi gabaɗaya yana yi musu nasiha da nusar da su illar yarda da amincewa abin da suka yi tozali da shi. Sai da ya gama wa'azin sannan ya bawa Inna Furai damar ta yi magana. Inna Fuarai ta karkace ta ce, "Yaya Idi yadda na ga Fatalwar Malam na ga Annabi. Ganin idona na ganshi kuma har umarnin shayar da su Auwalu ya yi." Sai da suka gama jin jawabinta tsaf sannan aka ce Yahanasu ta yi faɗi abin da ta sani, Yahanasu da ta buɗe ido da kyar tana sunne kai ƙasa don duk yanda hankalinta ya ɗan kwanta har Yaya Idi ya sa ta buɗe ido bata gama sakewa ba. Ta fara yi musu bayani dalla-dalla sanna ta ɗora da cewa, "Kuma da bakinsa ya sanar da ni duk wanda ya wayi gari da likkafani a ɗakinsa to gaba shi za su ɗauka. Shi ya sa na ce tawa ta ƙare." Auwalu ya rumgumota yana cewa, "Ba za ki mutu ba Yahanasuna" Yaya Idi ya yi jim sannan ya ce, "Idan na fahimta wani ne kawai yake son razanar da mutanen gidan amma babu damuwa ku bar mini komai a hannuna zan san yanda zan ɓullowa lamarin. Dubu tana gefe tana jin duk wainar da ake toyawa don haka ta saci jiki babu wanda ya lura da ita, kuma babu wanda ya taɓa kawo ita za ta aikata wannan abin. Dubu na tafiya ta wuce ɗakin Marigayi ta zaro wasu kayansa da yake zuwa sallar juma'a da su. A wanke suke a goge fari ƙal da su, sai da ta bubbuɗa su ta je bakin katangar banɗaki wacce mutum zai iya haurawa ta wurin ta ajiye, hularsa ta saƙale a jikin wata itaciyar tunfafiya sai kuwa ta kwaso a guje ta shiga wurin taron da suke gabda kammalawa. Ihu take kwarawa kamar wacce ake ɗanawa wuta tana cewa, "Wayyo Allah na ga Fatalwar Baffa na gani zai tafi da ni. Kafin ka ce wani abu tuni wurin ya watse sai takalma da ɗankwalaye da aka barsu suna cin karen su babu babbaka. Yaya Idi sai da ya yi kusan adungure biyu sannan ya samu ya shige ɗakin Inna Furaira. Hularsa kuwa ta yi tsalle ya fi sau biyar kafin ta samu sukuni faɗuwa can bakin ƙofa. *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* FREE PAGE 5 Fuskar Mama Uwani ce ta rune saboda ɓacin rai nan take ta fara fesar da numfashi mai ɗauke da turirin hayaƙi mai zafi, sannu a hankali Hannuwanta suka fara fidda wasu irin baƙaƙen farata masu matuƙar kaifin gaske, harshenta ne ya fara zazzagowa haɗe da fidda waɗansu irin jeluna masu tsawo da santsi tamkar ƴaƴan maciji, fatar jikinta ce ta fara sauya launi zuwa kalar ja haɗe da wani gashi da ya fara tsattsafo mata. Cikin wata irin murya mara daɗin sauraro ta fara magana. "Wace ce ke?" Intisar ta saki malalacin murmushi ta fara zagaye ɗakin tana ƙarewa Mama Uwani da ke ɗauke da mummunar siffa ta ce, "Menene damuwarka har kake son sanin ni wacece? Dama ka yi abin da yake gabanka don sanin wacece ni ba zai amfane ka da komai ba." A haukace Mama Uwani ta buga uban tsalle da waɗansu manyan fuka-fukai da suka fito daga ƙasan hammarta, ta dira a gaban Intisar haɗe da karta mata faratanta bisa tsautsayi farcen ɗan yatsanta ɗaya ya karci gefen fuskarta. A zafafe ta matsa baya cikin huci, nan take fatar jikinta ta fara darewa tsokar namanta ta fara bayyana a fili, kanta ya fara rabewa gida biyu wani dogon ƙaho ta fara tsorowa daga tsakiyar kanta. Tana shirin mayar da martani daga can bakin ƙofa suka ji maganar Mommy na ƙwalawaqÁa Mama Uwani kira, kamar ƙiftawar ido tuni suka koma hallitarsu ta ainihi. Mama Uwani ta zubawa Intisar wani mugun kallo cike da takaici ta furta, "Idan kere na yawo zabo na yawo watarana za a haɗu." Intisar ta ɗaga kafaɗa cikin rashin nuna damuwa ta ce, "Kamar yadda Ungozoma ke jiran mai naƙuda haka koyaushe nake dakon haɗuwarmu domin nasan ba a dauwama da kashi a ciki." Dire zancen Intisar ya yi daidai da shigowar Mommy cikin ɗakin wasu baƙin mata na biye da ita, kallon Mama Uwani ta yi a ɗan faɗace ta fara faɗin, "Mama Uwani kina ji ina ta magana lafiyarki kuwa?" Kamar yadda ta saba ladabi a gaban su Mommy haka Mama Uwani ta dausashe murya ta ce, "Hajiya a yi haƙuri yanzu na zo wuce wa na hangi wannan baƙuwar ta shigo ɗakin nan shi ne na shigo don na sanar mata cikin gida ake zaman makokin, wallahi na sha'afa ban ji ki ba." Mommy ta faɗaɗa murmushi tana kallon Intisar ta ce, "Ƴanmata sannu da zuwa." A kunyace Intisar ta sunne kai haɗe da tsugunnawa har ƙasa tana faɗin, "Mommy ina kwana?" Mommy ta dafa kafaɗarta tana ɗago ta, ta c: "Lafita ƙalau 'yata tashi tsaye." Intisar ta amsa da, "Mommy ina Raihan?" A firgice Mama Uwani ta ɗago cikin suɓutar baki ta furta, "Me Raihan za ta yi miki?" Da sauri Mommy ta kalli Mama Uwani fuska babu walwala ta ce, "Mama Uwani ya haka ne?" Mama Uwani ranta ya sake ɓaci, ta russunar da kai tana faɗin, "Ayi haƙuri Hajiya." Mommy bata tanka mata ba, ta juya wurin baƙin da take tafe da su ta ce, "Ga baƙi nan ki wuce da su sashenku." Ta juya wurin Intisar ta ce, "Ni kamar Intisar nake gani." Intisar ta sosa kai a kunyace ta ce, "Ni ce Mommy, dama na ji abin da ya faru ne na zo in yi mata gaisuwa." Mommy ta sake goge hawayen fuskarta da yake zuba, don mutuwar Mama Hasiya ba ƙaramin dukanta ta yi ba, ta riƙo hannun Intisar don dama tun da ta ganta take yi mata kallon sani, abin da ya hanata gane ta sau ɗaya ta taɓa ganin wani zuwa da suka yi da Raihan. Intisar ta sake lafewa a jikin Mommy suka nufi hanyar fita, Mommy tana faɗin, "Allah sarki Intisar, ya su mommynku." Intisar ta ce, "Duk lafiya ƙalau ta ce a yi muku gaisuwa kafin ta shigo." Mama Uwani jiki a saluɓe ta ja baƙin suka nufi sashensu, Intisar tana tafe tana sakin wani shu'umin murmushi haɗe da bankawa Mommy harara a fakaice. Wuce mutane suka rinƙa yi duk in da ta keta sai gaisuwa ake yi mata, mommy har lokacin hawaye ne ɗauke a fuskarta. Suna zuwa ta wuce da ita sashen Raihan, Raihan na zaune da su Batula ƴaƴan ƙanne da yayyan mommy, suma ƴan mata ne kuma ta su ta zo ɗaya da Raihan. Intisar na shiga Raihan ta faɗaɗa fara'arta tana miƙa mata hannu daga zaune, da sauri Intisar ta rungumeta tana faɗin; "Besti ya ƙarin haƙuri." Idanun Raihan ya ciko da ƙwallah, sai da ta sa hannu ta goge hawaye cikin shassheƙar kuka ta ce, "Besti wai Mama Hasiya ce ta mutu, idan kin tuna hirarmu da ke last ba nace miki ni na ɗauki alƙawarin Baby shower ba idan ta samu Ciki?" Intisar ta matso hawaye cikin sigar tausayi ta furta, "Kayya Besti ya za a yi na manta da hirar Mama Hasiya." Raihan ta ci gaba da kuka tana faɗin, "Intisar Mama Hasiya na sona kamar ita ta haife ni, wai ita ce ta mutu shi kenan mun rasata." Kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka fashe da kuka mai ban tausayi, sai da ƙyar aka lallashe su musamman Raihan. Bayan wani lokaci suna zaune tuni an sallaci Mama Hasiya an kaita makancinta, Mama Uwani ce ta turo ƙofar ta shiga saboda gabaɗaya zuciyarta ba ta aminta da Intisar ba, don tun ranar da ta fara ɗora ido a kanta ta fahimci ita ba alheri bace a rayuwar Raihan. Sai dai duk yadda ta so bin diddigin gano wacece ita abin ya faskara, don haka ko da ta shiga ɗakin sai ta hau goge-goge don ganin abin da yake faruwa. Intisar na ganin haka ta saki murmushi a fakaice don ta san tsiyar da za ta shukawa Mama Uwani, yamutsa fuska Intisar ta yi ta ce, "Besti pls ki ce Mama Uwani ba ni ruwa and takalmana suna waje ta kwasominsu." A hargitse Mama Uwani ta wurgawa Intisar mugun kallo saboda ɓacin rai har sai da ta so bayyana fushinta a fili, kai tsaye Raihan ta dubi Mama Uwani ta ce, "Mama Uwani ki ɗaukowa Intisar ruwa a falo na firij ɗina ya ƙare." Ganin rainin hankalin Intisar ya yi wa Mama Uwani yawa ya sa bata tanka wa Raihan ba ta kalli Intisar, ta fara wani huci idanunta suka fara sauya lauyi ba tare da Raihan da sauran mutanen ɗakin sun lura ba. Kofar toilet ɗin Raihan ta kalla lokaci ɗaya kofar ta buɗe da ƙarfi, wani tafkeken maciji ne ya fara silalowa bakinsa na fidda baƙin hayaƙi. Wata uwar ƙara suka ƙwalla a firgice kowa ya fara neman hanyar fita, kafin wani lokaci tuni duk sun fice daga ɗakin har Intisar don ko kaɗan bata yinƙurin yin wani abu a gaban Raihan da zai bayyana ita ainihin wacece. Mama Uwani nan take ta ɓace a wurin, macijin ra rabu gida biyu ɗaya ya rikiɗa zuwa siffar Raihan ɗaya kuma yana nan a siffarsa ta farko, ita kuma Mama Uwani ta ɓace tare da Raihan ɗin ainihi. Kamar ƙiftawar ido haka Mama Uwani ta ɗira a wani tsibiri mai ɗauke da dogayen bishiyu masu duhun gaske, sai wasu korayen tsuntsaye masu yawan da wasu hallitu masu siffar ƙadangaru sai dai jelunar su gashi gare ta kamar jelar tunkiya. Raihan da take sume ta shimfiɗar, Mama Uwani ta zauna ta zura mata ido, nan take ta rikiɗa zuwa surarta ta ainihi wato HUZAIFA. Miƙewa ya yi da surar wata ƙatuwar hallita mai matuƙar tsawo, fatar jikinsa kamar bayan kada ga wata zabgegiyar jela a bayansa mai ɗauke da kawunan macizai masu fidda aman wuta. Hannuwansa ɗauke suke da manyan farata sai harshensa da suke dalalar da wani baƙin ruwa mai yauƙi. Kamar wancen karan da ya kaita daularsa ta ƙarƙashin ƙasa, a yanzu ma zuwa ya yi daidai wurin da take kwance ya zuba mata ido wata matsananciyar sha'awar Raihan na sake fisgarsa. A hankali Raihan ta sauke ajiyar zuciya sanyin shukokin wurin ya fara dukan gangar jikinta, motsi ta fara yi alamar za ta farfaɗo. Ruwan bakinsa ya ɗiga mata a saitin goshinta, a cen gefe ya je ya ɗauko wannan ƙaramar hallitar mai siffar kunkuru ya ɗagata da hannuwa biyu yana kallo yana jin daɗi, domin babu abin da ya fi saurin faranta ransa sama da ya ga ya haɗa Raihan da abin da ta haifa masa. Mayar da jaririn hallitar ya yi sannan ya dawo kan Raihan da ke kwance, a hankali ya fara mu'amala da ita yana sarrafa sassan jikinta ga wata irin kewarta da ya yi don ya jima bai kusance ta ba, tun ranar da ta haifi wannan mumummunar hallitar tun da ba ya iya ɗaukan kwana biyu cir ba tare da ya kusance ta har ya yi mu'amala da sassan jikinta ba. Yana tsaka da mu'amala da ita ya ji wata iska ta fara, kaɗawa mai tafe da sarewa. A hankali ya ɗago kansa yana kallon abin da yake faruwa don ko ba a faɗa ba, ya san Mugaza ce za ta dira a wurinsu. Tun bai gama tunaninta ba ya ji kecewar dariyarta a tsakar kansa, miƙewa ya yi daga kan Raihan a lokacin ya bayan ya samu nutsuwa da ita, ya taka wurin Mugaza fuska a haɗe cikin wata irin murya ya furta, "Me ya kawo ki Turakata bayan kinsan hutawa nake yi?" Haushi ne ya sake rufe Mugaza da ke ɗauke da surar wani ƙaton tsuntsu mai kan angulu. Sai da ta yi tsalle-tsallenta sannan ta dira a gabansa rai a ɓace ta mayar masa da martani, "Akwai wani hutu da ya dace ka yi bayan bana kusa da kai?" Huzaifa ya ƙare mata kallo yana shirin magana ta ci gaba da cewa, "Sau nawa zan gaya maka ka fita daga rayuwar yarinyar nan, idan ba haka ba wallahi sai na halakata ta hanyar kisa mai muni." Wani uban tsalle ya buga haɗe da girgiza sannan ya rikiɗa zuwa surar matashin saurayin bil'adam, ya kalli matarsa Mugaza tare da sakin wani shu'umin murmushi ya ce, "Wannan yarinyar da kike gani na fansar da raina a gareta idan kin ga ban tsayawa rayuwarta ba sai dai bana numfashi, ita ɗin ta zama jinin jikina ko iyayen da suka haifeta idan suka nemi raba ni da ita sai na tarwatsa rayuwarsu." Jinjina kai Mugaza ta yi haɗe da sakin wata irin shu'umar dariya sannan ta ce, "Wannan shi ne gargaɗi na ƙarshe da na yi maka a kanta, tun da baka ji ba za ka ga ni a gaba kuma idan kwaɓarka ta yi ruwa karka yi kuka da ni. Sai dai zan ci gaba da baka kulawa a matsayina na matarka mai ƙaunarka, amma a kan wannan yarinyar babu wata kalma da za ta sake shiga tsakaninmu. Sai na ladaftar da ruhinta ta yadda za ta yi danasani, sai na azabtar da gangar jikinta domin sai na shayar da ita azaba mai raɗadi" Tana gama maganar ta tashi daga cikin tsibirin ta fice, ko a jikin Huzaifa ya ƙarasa wurin da Raihan take kwance ya sake rikiɗa zuwa siffar marigayya Mama Hasiya haɗe da sauya fasalin wurin, a hankali ya sa hannu ya fara tashinta tare da faɗin sunanta. Ahankali ta buɗe idonta tana kallon wurin da take da Mama Hasiya da take kanta a tsaye. Bayan fitowar su Intisar a kan idonta Mama Uwani ta sauya Raihan da wata Raihan ɗin, murmushi ta yi don ta fahimci manufarta na yin haka kuma ita ma ta shiga nazartar yadda za ta ɓullo mata. Nan take gida ya ruɗe da maganar macijin da aka gani a ɗakin Raihan, hankulan mutane ba ƙaramin tashi ya yi ba. Lokacin da Mommy ta samu wannan labarin da sauri ta aika aka kira Kabiru (Matashin bafulatani Maigadin gidansu Raihan.) Saboda Kabir bai da tsoro sam, bai fi sati biyu da fara aiki a gidansu Raihan ba. Tsayayyen namiji ne mara tsoro don akwai ranar da aka samun kulɓa a kitchen ɗin Mommy, Kabiru na zuwa ya fitar da shi. Kafin Kabiru ya zo Sulaiman ɗan ƙawar Mommy ya miƙe yana faɗin, "Daga wurin ina yake yanzu na fice da shi, ba wani shege kura ma mun kara da ita mun kaita ƙasa." Babu wanda ya hana shi don jikinsa na rawa ya nufi cikin gidan, saboda yana mutuwar ƙaunar Raihan don haka yake son ya yi wani abin bajinta ko ya samu ya ƙara samun masauki a zuciyar Raihan. Yana zuwa duk matan da ke zagaye da ɗakin suka dare, ya tura ɗakin da ƙarfinsa. Yana shiga ya samu macijin a tsakiyar ɗakin ya naɗe wuri ɗaya kamar gammo ya fasa kai, bakinsa yana fitar da feshin wuta, a hankali ya waiga yana faɗin: "Wani ya miƙo min katako." Har rige-rigen tafiya mutane suke yi babu jimawa aka ɗauko masa wani ƙaton katako, kansa tsaye ya tunkari macijin cikin dakiya ya ɗaga ya buga masa a tsakiyar ka. Tsalle macijin ya yi, Sulaiman ya gantsare duniyar na juya masa. Sannu a hankali macijin ya rarrafo ya fara nannaɗe shi har sai da ya naɗe masa jiki, nan take Sulaiman ya hau kakari ƙwayar idonsa duka biyun ta faɗo ƙasa, jini ya fara zuba ta hancinsa da bakinsa. Tun Sulaiman yana iya kakari har ƙarfinsa ya ƙare, tsokar jikinsa ta fara burtsowa daga jikin fatarsa nan take hallitar Sulaiman ta sauya tamkar ba bil'adam ba. Mutane na ganin haka suka fita da gudu cikin kururuwar neman taimako. ************ Raihan ta shi ta yi zaune jikinta ba ƙaramin tsami ya yi mata ba, ta dubi Huzaifa da ke cikin siffar Mama Hasiya ta ce, "Mama Hasiya kece? Dama baki mutu ba?" Huzaifa ya gyaɗa wa Raihan kai yana furta, "Ban mutu ba amma na dawo nan wurin da zama za ki zauna da ni?" Raihan ta yi shiru tana nazartar maganarsa jiki a sanyaye ta ɗago tana cewa, "Gaskiya ban yarda ba ina su Mommy?" Huzaifa ya riƙo hannunta lokaci ɗaya ta ji wani yaarrr a cikin jikinta, tana kiciniyar ƙwacewa sai gani ta yi ta fisgo da ƴan yatsu biyu na jikin hannun Huzaifa, a tsorace ta wurgar da su ta fara ja da baya jikinta na karkarwa. Cikin rawar murya ta ce, "Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni." Ganin haka ya sa Huzaifa ya fara ƙyaƙyacewa da wata irin dariya har sai da ta sa hannuwa biyu ta toshe kunnuwanta, kakin yawu ya yi ya tofar nan take ƙasar wurin ta fara rozayewa ya sa ɗan yatsa ya nuna mata wurin yana faɗin, "Ki bar wahalar da kanki domin ba za ki taɓa guje min ba, ki zo ki shiga wurin nan idan ba haka ba za ki dauwama a wurin nan." ********* Al'ummar da ke zaman makoki kusan rabi da kwata kowa ya cika wandonsa da isa, don ceton rayuwarsa. Hatta Inno da Goggo cikin ayarin ƴan ceton rai suke ba tare da su mommy sun farga ba. Hankalin Daddy ba ƙaramin tashi ya yi ba da ganin abin da ya faru, a hankali Kabiru ya fara takawa cikin gidan dukda yana ta cin karo da mutane masu guduwa hakan bai hana shi sake kutsawa cikin falon gidan da zai sadaka da ɗakin Raihan ba, a bakin wata ƙofa ya ci karo da Intisar da ke tsaye ƙyam babu alamar tsoro a tattare da ita. Suna haɗa ido ya ji kansa ya sara juwa ta fara ɗibansa, sama-sama ya fara jin wata irin hayaniya har sai da ya dafa kansa da hannuwansa, a hankali ya fara karanto addu'o'in tsari yana karantawa duk wacce ta zo bakinsa. Lokaci ɗaya ya ji komai ya ɗauke masa, ya dawo cikin hankalinsa sai dai tuni jikinsa ya jiƙe da gumi sharkaf. Idanu ya kafe Intisar da su har ya gagara sarrafa kansa, ya fara takawa zuwa gabanta cikin hausar da bata gama zama a bakinsa ba ya ce, "Washeshe kai?" Intisar ta saki murmushi ta ƙarasa gaban Kabiru ta ce, "Kai bafulatanin ƙauye, karka shiga abin da babu ruwanka." Yana shirin sake magana Daddy ya ƙaraso wurin hankali a tashe yana faɗin, "Kabiru mu je ka ga abin da yake faruwa meye abin yi?" Kabiru ya yi gaba yana waiwayen Intisar haɗe da ɗora mata zarge-zarge a kanta. Da ƙarfin gaske Kabiru ya tura ƙofar ɗakin cikin zuciyarsa yana ci gaba da karanta ayoyin tsari dana kariya, Jabun Raihan ce ta ƙaraso ƙofar ɗakin. Abin da ya ji da farko a lokacin da yake tare da Intisar haka ya ƙara ji a wannan karon a haukace ya juya, ya shaƙi wuyan Raihan cikin wani irin ƙaraji ya furta. "Washeshe kai? Me kake yi a wurin nan?" DA ALAMA KABIRU YA YANKI TIKITIN BARIN AIKIN GADIN DA YAKE YI A GIDANSU RAIHAN😂 TO WAI SHI MA KO YANA DA ALAƘA DA SU NE😂 SHIN DADDY ZAI ZURA IDO YA GA AN MAƘURE GUDAN JININSA? SHIN SU DADDY ZA SU FARGA DA MAMA UWANI BA MUTUM BACE SHI NE AINIHIN ALJANIN DA KE RAYUWA DA ƳAR'SU? KO KUMA HUZAIFA ZAI ƘYALE KABIRU HAR YA TONA MUSU ASIRI🤭🤭🤭 TAFIYAR FA HAR YANZU BA A FARA BA DOMIN LABARIN TAFE YAKE DA SARƘAƘIYA🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ KARKU MANTA HAR YANZU RAIHAN BATA SAN MAMA UWANI CE TA KAWO WANNAN TSIBIRIN BA, ITA DAI TA BUƊI IDO DA MARIGAYYA MAMA HASIYA. WAI INA LABARIN INNO DA GOGGO NE INA SUKA BAZAMA WAYE ZAI TARO SU? 😂😂 Share Fisabillah🌚 *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* FREE PAGE 6 Raihan kallon ramin ta yi da yake ci gaba da rozayewa ƙasar wurin na ruftawa, ya yin da ramin yake ci gaba da ƙara girma yana tunkaro wurin da take. A hankali ta riƙa ja da baya cikin rawar jiki, firgici da tashin hankali. Tuni hawaye ya wanke fuskarta ta ci gaba da yin baya ba tare da ta fahimci wurin da take jefa ƙafarta ba, bata yi aune ba ta ji wani dutse ya tokareta ƙasar da ke zaftarewa ta ƙaraso har wurinta har sai da ya rage bai fi taku ɗaya ba ta dakata bisa bin umarnin Huzaifa da ke cikin surar Mama Hasiya. Cikin kuka Raihan ta dubi shi tana faɗin, "Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni, ban san abin da na yi miki ba kika kawo ni wurin nan alhalin mommy ta ce mini kin mutu." Huzaifa ya ƙyaƙyace da wata mahaukaciyar dariya ya fara takowa wurinta yana tafe yana zare sauran ƴan yatsun hannunsa yana zubarwa, kafin ya ƙarasa wurinta tuni ya tsinke yatsun hannunsa sai iya dungulmin kaɗai ya rage, daga guraben ƴan yatsun wasu baƙaƙen farata ne suka fara tsirowa a hankali har sai da suka fito zaƙwa-zaƙwa da su, ta cikin ramin ya shiga kamar ƙiftawar ido ya dira a gabanta cikin wata irin murya mai amsa kuwwa ya sake ce mata. "Ki biyo ni cikin ramin nan idan ba haka ba za ki dauwama a nan." Raihan ta sake girgiza masa kai tana cewa, "Don Allah ki mayar da ni wurin su Mommy." Baki ya buɗe zai fara dariya wasu dogayen fiƙoƙi suka fara fitowa, da sauri Raihan ta runtse ido tana ƙwallah wata razananniyar ƙara. Wata iska ta ji mai sanyi na ratsa jikinta a hankali ta buɗe idonta, ga mamakinta sai na yi ta yi wurin ya sauya mata ta ganta wani kogon dutse mai ɗauke da ƙananan bishiyu, a hankali ta fara takawa har zuwa bakin kogon dutsen don ta hango hasken rana daga bakin dutsen. Tana fita daga cikin dutsen ta fara gudu da iya ƙarfinta don ganin ta ceci rayuwarta. Daga nesa-nesa ta fara jiyo kukan jarirai haɗe da haniniyar doki, a hankali ta fara rage gudunta don yadda ta lura hanyar da take tunkara a nan take jin sautin kukan jaririn na sake karaɗe kunnuwanta. Tana tafe tana waiwaye ta bata yi aune ba ta ji ta yi karo da wata murgujejejiyar hallita, hallitar riƙe take da wasu ƙananan jarirai masu surarta, tsayin hallitarta ya ninka ta sau biyu, tana da ƙiba sosai don kaurin cinyar hallitar ya yi kaurin Raihan sau huɗu. Tana ɗauke ƙafa da hannuwa irin na birrai sai ƙaton kai irin na dorinar ruwa. Bakinta tsayi gare shi idanunta kwala-kwala masu ɗauke da launin ja, Raihan na shirin ja da baya Hallitar ta ƙurawa Raihan Ido tana miƙa mata hannu alamar ta zo gare ta. Da gudu Raihan ta juya don ta koma cikin kogon dutsen, karaf ta ji ta yi karo da Hazaifa da ke ɗauke da surar Mama Hasiya sai dai kammanina sun sake munana. Ajiyar zuciya ta sauke don ko ba komai ta ji daɗin ganinsa, hankalinta ya fi kawanciya da shi a kan na wannan mummunar hallitar. Hallitar na ganin Huzaifa ya ɗauke Raihan sun koma zuwa kogon dutsen ta juya ta koma daga wurin da ta fita, Huzaifa ya saki malalacin murmushi bayan sun koma ciki ya zaunar da Raihan akan wani faffaɗan dutse, ya zauna a gabanta yana kallonta. Tana shirin yin magana ya katseta da cewar, "Kina son komawa gida?" Da sauri Raihan ta gyaɗa masa kai. Jinjina kai ya yi sannan ya ce, "Zan mayar da ke gida amma da sharaɗin..." Da sauri ta katse shi da cewar, "Na amince da kowanne sharaɗinki indai za ki mayar da ni gida." Wannan jaririn hallitar ya ɗauko mata mai shige da siffar kunkuru ya ce, "Ya zama wajibi ki shayar da wannan domin shi ɗin jininki ne." Idanunta ne suka firfito waje ta ƙarewa hallitar kallo tana yamutsa fuska, bai saurari abin da za ta faɗa ba ya ci gaba da cewa. "Ya zama wajibi ki yanke alaƙarki da wannan yarinyar Intisar." A hargitse Raihan ta sake ɗagowa ta yi tana kallonsa don a duniya bata da aminiya sama da Intisar, bata da wacce tasu ta zo ɗaya sama da ita amma lokaci ɗaya ya ce dole ta rabu da ita. ********* A haukace Daddy ya yi kan Kabiru ya rufe shi da wani mahaukacin duka, sai da ya gaji don kansa sannan ya janye Jabun Raihan ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya. A cen gafe Kabiru ya faɗi yana sauke ajiyar zuciya yana sauke numfashi cikin wahala, ɗagowa ya yi suka haɗa ido da Jabun Raihan a fakaice ta sakar masa wani malalacin murmushi ta fara motsa baki tana magana ba tare da ta wani ya ji abin da take faɗa ba. Duk maganganun da Jabun Raihan take yi a kannen Kabiru, ransa ne ya sake ɓaci ya dubi Daddy da yake jifansa da mugun kallo, cikin bagwariyar hausarsa ya ce, "Alhagi shi wannan yaron ba mutumin kirki ba ne, azzalumi ne so yake ya shushe ki." Daddy ya sake dunƙule hannu ya kaiwa Kabiru naushi a baki ya ce, "Don uwarka a gabana kake ce min ƴata ba mutuniyar kirki ba ce, ina maka kallon mai hankalin ashe kaima ɗan iska ne, wallahi a yau ba sai gobe ba sai an rufe min kai na ga gatanka mahaukacin banza mahaukacin wofi." Raihan da ke maƙale da Daddy ta sake langwaɓewa tana ɗangale ƙafa. Alhaji Mustafa Indabawa ne ya dubi Daddy yana faɗin, "Abokina don Allah ka yi haƙuri, yanzu mu ƙarasa wurin da gawar yaron nan take." Kabiru ya yunƙura da kyar bakinsa na ɗigar da jini. Daddy na leƙa cikin ɗakin ya yi tozali da gawar Sulaiman, da sauri Daddy ya ja da baya jikinsa na tsuma don ba ƙaramin tsorata ya yi ba. Alhaji Mustafa shi ma yana leƙawa a zabure ya ja da baya har suna gware da Daddy. Lokaci ɗaya Daddy ya yi zuru-zuru hankali a tashe ya furta, "Wannan tashin hankalin ne ya faru a ɗakin Raihan?" Intisar da ƙarasowarta kenan ta amshe maganar da cewar, "Daddy tun da nake ban taɓa ganin maciji mai muni irin wannan ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyaya ya fara jinjina kai, suna nan tsaye macijin nan ya fara warware kansa daga jikin Sulaima. Ganin haka ya sa mutanen wurin suka fara darewa, Kabiru ne ya dafa ƙofar a hankali ya zura ƙafarsa ɗaya cikin ɗakin. Kallon-kallo aka fara yi tsakanin kumurcin macijin nan da Kabiru, a hankali Kabiru ya fara karanta duk wata addu'ar tsari da ta zo bakinsa. A zabure macijin ya fara ja da baya Kabiru na sake tunkararsa, wani kofi Kabiru ya hango da ruwa a jarka da sauri ya ɗauka ya zuba ruwa a kofi ya fara karanta ayoyin tsari yana tofawa. Daddy ban da leƙe babu abin da yake yi. Kasancewar Jabun Raihan ta san irin soyayyar da Mahaifin Raihan yake yi mata ya sa ta kwaɓe baki a lokacin da ta ga Kabiru ya tasamman halaka Macijin da ubangidanta ya turo, ta ƙwalla wata ƙara tana faɗin, "Daddy wuyana." Kabiru ya waiwayo yana kallonta, Daddy ya kai hannu kan wuyanta yana faɗin, "Mu je asibiti a duba ki, wallahi duk abin da ya samu ƴata ka kuka da kanka." Daddy ya ƙarasa maganar yana watsawa Kabiru mugun kallo. Raihan ta sake langwaɓewa ta ce, "Daddy don Allah a bar korar macijin nan kar wani ya ƙara mutuwa kawai ka kira fire service." Daddy ya kalli wurin da Kabiru yake ya ce, "Kai maza fito daga ɗakin nan kar kaima ka yi mana mushe." Intisar ta kalli jabun Raihan ta watsa mata harara, sannan ta mayar da kallonta wurin Daddy ta ce, "Daddy amma naga kamar macijin ya fara ja da baya mai zai hana a bari a ga ƙoƙarinsa..." Alhaji Mustafa ya katse ta da cewar, "Tabbas ni ma haka na gama ayyanawa don yaron nan kamar akwai wani taimako da zai yi mana." Kabiru bai bi ta kansu ba ya sake tunkarar wurin macijin, lokaci ɗaya ya watsa masa ruwan tofin hannunsa bakinsa na ci gaba da ambaton Allah. Nan take macijin ya faɗi gefe yana wani iri gurnani, zaburowa ya sake yi da niyyar kai wa Kabiru sara da sauri Kabiru ya watsa masa sauran ruwan da ke hannunsa. Wata dariyar farinciki Intisar ta saki don ko ba komai ta san an yi wa Mama Uwani illa, jikinsu Daddy ba ƙaramin sanyi ya yi ba da ganin gwagwarmayar da suka yi tsakanin Kabiru da macijin. Jabun Raihan ta sake kallon Intisar ta saki ƙwafa a takaice, ta so ace Huzaifa ya bata umarni da tuni ta nunawa Intisar iyakarta. A wahalce Kabiru ya sa hannu ya hanyo macijin, ya fito daga ɗakin fuskarsa ɗauke da gumi lokaci ɗaya Daddy ya ji Kabiru ya birge shi saboda jarumtar da ya nuna, wannan ne karo na farko da ya ji ba zai iya ɗaukan mataki a kan wanda ya taɓa gudan jininsa ba, saboda yana matuƙar son mutum mai dakakkiyar zuciya. Sai dai har lokacin yana jin haushin Kabiru saboda abin da ya yi wa Raihan a idonsa. Kusan tare suka tarkata suka fito daga sashen, kowa da abin da yake faɗa. Kabiru fita ya yi da macijin can bayan gidan Daddy ya kai ya wurgar da shi, Daddy da kansa ya sa aka rufe sashen Raihan tare da cewar sai ya kira ma'aikata sun yi wa ɗakin feshin magani, a ɓangare ɗaya yana tunanin barinsu daga gidan gabaɗaya. ************* Raihan bata da zaɓi don haka ta gyaɗa masa kai tare da faɗin, "Duk abin da kika faɗa na amince don Allah ki mayar da ni." Huzaifa ya yi murmushi jindaɗi don shi kansa ya lura da yadda Raihan ta gama tsorata da shi. Lokaci ɗaya ya ji ta bashi tausayi, ya sa hannu ya zaro fiƙoƙin bakinsa waɗanda suka tsiro ya wara hannuwansa da niyyar Raihan ta rungume shi amma fir ta ƙi. Ya kalli fuskarta ya ce, "Kina ƙaunata." Raihan bata da zaɓi duk abin da ya faɗa sai dai ta amsa masa da amincewarsa. Tana tsaka da tunani ta ji ya ce, "Rufe idonki." Kallon hagu da dama ta fara yi a hankali ta furta, "Don Allah kar ki yi min komai." Huzaifa ya yi murmushi ya ce, "Kina rufe ido za ki ganki a gida." Tun bai rufe baki ba Raihan ta rufe idonta da ƙarfi, bata jima da rufewa ba ta ji tashin hayaniya na tashi sama-sama. Tana buɗe ido ta ganta zaune a falon Daddynsu, a hankali ta fara bin wurin da kallo, ta hango Intisar da sauran ƴanmatan da suke tare da su a ɗakinta. Suna haɗa ido da Intisar ta ji gabanta ya faɗi rass musamman da ta tuna irin gargaɗin da Mai siffar Mama Hasiya ta yi mata, a hankali ta miƙe ba tare da furta komai ba. Tana fita ta nufi sashen Mommy a kan step ɗin bene ta ci karo da Mama Uwani, tana ganinta ta washe baki ta ce, "Barka da hutawa uwar ɗakina." Sama-sama Raihan ta amsa, "Yauwa Mama Uwani ina Mommy take?" Mama Uwani ta nuna ɗakin mommy ta ce, "Tana ciki yanzu na kaiwa baƙi abinci ko na yi miki jagora." Raihan ta dakatar da ita da cewar, "A'a Mama Uwani ki je kawai." Mama Uwani ta yi murmushi tana faɗin, "Hutawarki lafiya uwar ɗakina." Raihan bata amsa ba ta wuce cikin ɗakin. Kafin Mama Uwani ta sauka daga kan bene Intisar ta doshi wurin, kallon-kallo suka fara yi wa junansu don ma mutane na zaune a falon, Mama Uwani ta saki wani malalacin murmushi ta wuce ba tare da ta tanka wa Intisar ba. Intisar na shiga ta yiwa Mommy sallama don a cewarta za ta tafi gida, amma koda ta yi wa Raihan magana ko ƙurarta bata kalla ba balle ta tanka mata. Tun da ta ga haka ta sha jinin jikinta, don haka tana fita daga gidan ta ɓace daga ƙofar bata tsaya a ko'ina ba sai a tsibirin ƙungiyar asirinsu. Raihan na zuwa jiki a sanyaye ta zauna, tana son sanarwa da mahaifiyarta cewar Mama Hasiya bata mutu ba amma tana tsoron abin da zai sake faruwa da ita. Tana nan zaune Daddy ya kira wayar Mommy ta waya yake sanar da ita, ɓacewar su Inno da Goggo sannan ta ce ta haɗa duk wani kayan sakawarsu don ya sa a ɗauke su daga gidan da suke zuwa gidansa da ke Unguwar sharaɗa. A cewarsa gidan cike yake da miyagun dabbobi, ba za su ci gaba da zama a ciki ba. (Abin da bai sani ba duk in da zai je indai yana tare da Raihan tana tare da ZAUJATU JINNUL-ASHIQ😂 Idan kuma yana tare da Mama Uwani yana tare da JINNUL-ASHIQ😂 Mu je zuwa.😎) Duk yadda Daddy ya so hukunta Kabiru ya ji zuciyarsa ta gagara ɗaukan mataki akansa, sai dai abu ɗaya ya riƙe duk abin da ya samu Raihan sai ya ɗauki mummunan mataki a kansa. A wunin ranar suka tare a sabon gidan Daddy da ke sharaɗa, da sauran ƴan gaisuwa suka tare. Ɗakin da ke jikin gate aka bawa Kabiru, yana shiga ɗakin ya ga akwai komai na buƙata sai dai lokaci guda ɗakin ya rikiɗe masa zuwa tafka-tafkan maciji masu fasalin irin wanda ya kashe a ɗakin Raihan. Yana shirin ja da baya ya ji wani ya faɗ masa a gadon baya lafin ya yi wani yunƙuri, ya fara nannaɗe masa jikinsa. Intisar na zuwa ta kwashi gaisuwa wurin Hatsabibiya bungulu, bayan ta yi gaisuwa Hatsabibiya ta dubi Intisar ta ce, "Me yake tafe da ke da tsakar rana?" Fuska ba walwala ta ce, "Hatsabibiya akwai tarin matsaloli domin Huzaifa ya saka ni a gaba, bayan Huzaifa akwai wani bafulatanin maigadinsu da alama zai kawo mana matsala. Amma wanda ya fi kawo mana matsala Huzaifa ne, don haka na ce ba zan yi ƙasa a gwiwa ba sai mun san abin yi don yanzu haka..." Tun Intisar bata rufe baki ba Hatsabibiya Bungulu ta katseta da cewar, "Duk na ga abin da ya faru har ɗaukan Raihan da ya yi zuwa tsibirinsa." Intisar ta jinjina kai cikin huci tana cewa, "Da alama ya tsoratar da ita kuma a kowanne lokaci tana gabda bijirewa umarninmu." "Sai mu kashe Huzaifa idan zai kawo mana matsala." Hatsabibiya ta faɗa kanta tsaye ba tare da ji shakku ko shayi ba." A firgice Intisar ta ɗago cikin tashin hankali ta zubawa Hatsabibiya ido, bakinta na rawa ta furta. "Kin manta wanene Huzaifa a wurina? Mijina ne fa." Hatsabibiya ta wara hannuwa cikin halin ko'inkula ta ce, "Ci gabanki ya fi zamantakewarki da shi don haka bana ganin zai amfane ki da komai." Intisar ta turɓune fuska ta ci gaba da cewa, "Ba zan lamince a kashe mijina kuma uban ƴaƴana ba, amma tabbas dole a nemi wata hanyar da za a samu mafita." 🤭 NA SAN DA YAWA ZA KU YI MAMAKIN JIN INTISAR MATAR HUZAIFA CE, KO KUN TUNO MUGAZA😂 ITA CE INTISAR. AMMA MAI YA SA HUZAIFA BAI GANE TA BA HAR SUKE TAKUN-SAƘA, SHIN WACCE RIBA MUGAZA ZA TA CI DA TA JEFA RAIHAN A ƘUNGIYAR ASIRI? IDAN SU MOMMY SUKA KOMA SHARAƊA SUN TSIRA KO DA SAURAN TAFIYA? Share pls🌚 *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* FREE PAGE 7 Daddy yana tafe Raihan na riƙe a hannunsa har suka shiga cikin gidan ayyane-ayyane yake yi, yana mamakin wane irin macijine da nan take zai naɗe mutum ya kashe shi, kuma a ce ya fito daga ɗakin Raihan ɗin sa. Kwafa ya yi yana tunanin irin matakan tsaron da zai ƙara akan na da, har suka shiga ciki. Mommy jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba don tun lokacin da abin ya faru ta fahimci macijin ɗakin Raihan ba ainihin dabba ba ne. Sai dai a wannan karon ta ci alwashin faɗawa Daddy gaskiya duk irin ɓacin ran da zai yi, don haka suna zuwa ta nemi ganawa da shi a sabon ɗakinsa dama gidan ya gina shi ne da sunan bayan wasu watanni su tare, amma kasancewar ba a gama masa ƙaƙale-ƙaƙale ba ya sa suka dakata da komawar, amma dole ta sa suka tashi a rana tsaka suka koma. A gaggauce Daddy ya dubi mommy ya ce, "Faɗi ina jin ki, kin san yanzu aka yi mini waya wai ankai su Inno da Goggo Hisba dole sai na zo, wani tashin hankali wai an tsinci su Inno a cikin masallacin Malam Isa na ƙarshen layi." Sai a lokacin Mommy ta zaro ido don bata san abin da yake faruwa ba, ganin ta shiga tashin hankali ya sa ya dube ta fuska ba walwala ya ce, "Ba fa wani abu ne na ɗaga hankali ba, komai ya zo da sauƙi yanzu dai ina zuwa." Yana gama maganar ko jiran cewarta bai yi ba ya fice daga ɗakin, jigum Mommy ta yi abu goma da ashirin ya haɗe mata. Wani irin zafi Kabiru ya fara ji a jikinsa kamar wanda yake gaban wuta, hajijiya ya ji ta fara ɗaukansa ga wata irin matsa da macijin yake yi masa, tun yana daga tsaye har ya durƙushe a wurin yana son furta ayar Allah, amma macijin ya matse masa maƙogaronsa. Kakari ya fara yi kamar wanda ransa zai fita, a zuciyarsa yana son biya ko da ayatulkursiyyu ce amma wani abu mai nauyi ya ji ya tokare masa ƙirji kamar dutse. Yana cikin wannan halin ya ga ɗaya daga cikin macizan ya miƙe tsaye cak ya fasa kai, a hankali fatar jikin macijin ta fara saɓewa tana fita daga jikinsa sai kuma ya fara rikiɗa daga siffar maciji zuwa siffar bil'adam. A hankali wata matashiyar mace ta bayyana ilahirin jikinta gashi ne tun daga kanta har zuwa ƙugunta, ya yin da ƙugunta yake a nannaɗe cikin surar maciji. Harshe ta fara zaro masa nan take wani jaririn maciji ya faɗo, ta damƙe shi a hannunta ta kalli Kabiru da yake cikin mummunan hali ta fara magana, "Kai matashin bafulatani, wa yace maka takun saƙa da ni sauƙi gare shi? Ka san wa ka illata kuwa? Ka san wa ka kashe min kuwa? Ko kana tsammanin ka ci bulus ne?" Kabiru ya ɗago yana sauke numfashi da ƙyar idanunsa jawur ga gumi na ci gaba da tsiyaya daga jikinsa. Baki yake son buɗewa amma ya kasa, ganin haka ya sa ta sake bushewa da wata mahaukaciyar dariya sai da ta yi mai isarta sannan ta fashe da matsanancin kuka, ta jima tana yi sai ta tsagaita da kuka ta sake kallonsa ta ce, "Ba kai kana taƙama da addu'a ba ka yi ta mu gani, har za ka kashe min miji kana tunanin za ka zauna lafiya?" Macijiyar na gama maganar ta fara rarrafowa zuwa gaban Kabiru, ganin ta nufoshi gadan-gadan ya sa Kabiru ya ƙara yunƙura yana ja da baya, ya fara bude baki yana ƙoƙarin karanta addu'a haɗe da motsa baki sai dai ko kaɗan muryarsa bata fitowa, tana tunkararsa hushin numfashinsa ya doki gangar jikinta ba shiri ta ja da baya saboda wani irin zafi da ta ji yana fita daga bakinsa. Kallon-kallon suka fara yi a tsakaninsu, bata daddara ba ta sake yunƙurowa a kashi na biyu da niyyar hallakashi. Duk yadda Kabiru ya kai ga buɗe muryarsa ya yi addu'a abin ya gagara. Dabara ce ta faɗo masa ya fara biya ayatulkursiyyu a zuciyarsa, tana tunkaro shi ya fara tofa masa. Ganin tana niyyar hallaka ya sa ta sake yin baya, nan take macizan da ke gewaye da shi suka ɓace. Ƙaton da ya naɗe shi tuni jikinsa ya saki da ƙyar ya rarrafa ya bi ta jikin bangon ɗakin ya ɓace. Ɗakin Kabiru ya rage daga Macijiyar sai Kabiru, ya yin da ta sake kafe shi da ido tana ƙare masa kallo don ta fahimci makasar da za ta samu a jikinsa ta yi masa illa. A wahalce Kabiru ya faɗi can gefe yana mayar da numfashi, jikinsa gabaɗaya ya yi ja saboda irin tsananin matsar da macijin ya yi masa. A hankali jikinsa ya fara raɗaɗi, yana kai idanunsa kan fatarsa ya lura da yadda ta fara sauya launi zuwa fatar maciji. Macijiyar kallon Kabiru ta yi ta fara ƙyaƙyacewa da wata irin shu'umar dariyar ƙeta, hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya yi da ganin abin da yake faruwa da fatar jikinsa ba. Yana tsaka da tunani ya riski muryar macijiyar tana faɗin, "Ka kashe min mijina ba tare da wani dalili ba, Huzaifa ya nemi tallafin mijina akan ya zo taimakonsa ka kashe shi, zafin mutuwarsa ta sa na ji tamkar na kashe ka amma ba zan kashe ka yanzu ba sai na gama wahalar da ruhina da gangar jikinka sannan na hallaka da hannuna. Ka je ko da wannan hallitar fatar macijin na barka ƙuncin rayuwar duniya ya ishe ka." Tana gama maganar ta sake naɗewa ta koma murtukekiyar macijiya, juyi ta fara yi daga wurin da take nan take ta baje a ƙasa ta fara nutsawa cikin ƙasa har ta ɓace ɓat. Ilahirin jikin Kabiru ban da rawa babu abin da yake yi, babban tashin hankalinsa yadda ya ga fatar jikinsa ta koma ta maciji illa iya fuskarsa, hannu da ƙafarsa ne kaɗai basu rikiɗa ba da yake macijin bai taɓa masa nan ba. A fusace Hatsabibiya ta ɗago da ta sake kallon Intisar ta ce, "Idan ba mu kashe shi ba kina da hanyar da za mu ɓullo masa? Ko kuma kina da shawara akan yadda za mu kawar da tunaninsa akan Raihan?" Intisar ta yi shiru tana nazari don ita kanta ta san wanene Huzaifa da tsananin bincike irin nasa, ta san tun da ya kafa mata ƙahon zuƙa dole zai bi diddigin wacece ita da asalinta. Ta san muddin ya gano ta ba ƙaramar ƙura ce za ta tashi a tsakaninsu ba, a baƙar zuciya irin tashi yana iya hallakata. Don ma tana amfani da sirrin tsafi da sihiri ko a yanzu yadda ya ɗora ransa akan Raihan da tuni ya gama da ita. Tana cikin tunani ta sake riskar muryar Hataabibiya ta ci gaba da cewa, "Idan har baki da wata dabarar ga tawa shawarar." Intisar ta dubi Hatsabibiya tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ina jin ki Uwargidana maganin kukana, da ke da Abar bauta ku kaɗai na dogara da ku duniya da lahira (Wa'iyazubillah) ke kika saba ɗauke min duk wata damuwata a yanzu ma ina biye da ke don jin mafitar da za ki kawo mana kafin abar bauta ta bayyana." Hatsabibiya kanta ya sake girma, ta miƙe daga wurin da take ta ɗauki wani dogon ƙaho mai faɗi da tsawo ta kafa shi a bakinta sannan ta durƙushe a gurin. Ta kafa tsinin ƙahon a doron ƙasa sannan ta busa shi da ƙarfinta, lokaci ɗaya tsibirin ya ɗauka tsananin ƙararsa kamar zai tsaga dajin gida biyu. Tun bata rufe baki ba aljanu masu ɗauke da munanan hallitu suka fara fitowa wasu daga ƙarƙashin ƙasa wasu daga cikin duwatsu ya yin da wasu suka fara fitowa daga ɗakin tsafi. Kafin wani lokaci tuni sun taru suna masu sujjada a gabanta, tare da yi mata kirari kamar yadda suka saba sannan suka ƙame wuri ɗaya suna jiran umarninta. Wani irin kuka haɗe da dariya ne ya fara tashi, lokaci ɗaya tsibirin ya fara girgiza suna nan tsaye wannan mummunar hallitar mai ɗauke da kawuna (Abar bauta.) Ta ziro kawunanta zuwa harabar wurin da take. Suna yin tozali da ita suka kwanta a wurin har hatsabibiya suna masu yi mata sujjada, haɗe da kirari. Kafin ƙiftawar ido Wani baƙin aljani ya dira a gabanta cikin girmamawa yana tambayarta. "Ya ke uwargijiyata shin jariri kike buƙata, uwar jariri tsoho ko tsohuwa kike buƙata." Ɗago da kawunanta ta yi, sai ta saki kuka kamar na bujimin sa. Jin kukan San ya sa aljanin sake rissunawa yana faɗin, "Kin samu kin gama." Yana gama maganar ya ɓace daga wurin. Kallonsu ta yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta fara magana da murya mara daɗin sauraro, "Duk abin da kuka tattauna mun saurara don haka babu amfanin maimaitawa sai zartar da hukunci." Jikin Intisar tuni ya fara tsuma nan take gumi ya rufe ta, don bata san irin hukuncin da Abar bauta za ta yanke a kan Huzaifa ba. Tana tsaka da nazari ta riski muryarta tana ci gaba da cewa, "Ba za mu kashe Huzaifa ba sai dai dole a sauyawa taku salo, sanin kanku ne a da ɗanyan kifi yana haukatata. Sakamakon ɗan da ta haifawa Huzaifa yana da haɗin jinsi da hallitar kifi. A yanzu za mu sake haukatata fiye da lokacin baya, a cikinku waye zai iya aiwatar da abin da muke buƙata?" Wata aljana da ta miƙe tsaye tana faɗin, "Abar bauta zan riƙa haukatata da surar mahaifiyarta..." Tun bata rife baki ba Abar bauta ta katse ta cikin tsawa tana cewa, "Kina tunanin wannan mafita ce? Idan kika yi haka dole za su nema mata lafiya, mu kuma duk wanda zai nuna hanyar lafiyarta sai mun tsotse jininsa." Haka aljanun da ke wurin kowa ya riƙa ɗaga hannu yana faɗin abin da zai aiwatarwa Raihan. Duk acikinsu shawarar guda biyu aka ɗauka, ɗaya daga ciki ya ce zai riƙa shiga jikin maguna yana haukatata, sai wacce ta ce za ta riƙa shiga jikin ƙadangaru sai dai kowanne da abin da zai aiwatar. Abar bautarsu ta ji daɗin abin da suka yi, don haka ta yi na'am da wannan shawarar. Suna nan zaune aljanin da ya tafi ɗauko mata jinin da za ta sha ya dawo hannunsa ɗauke da wani Dattijon tsoho, suna shigowa tun ba su ƙarasa gaban abar bauta ba, ta miƙa hannunta guda ɗaya ya warto Dattijan haɗe da ƙwaƙule masa ido tun bai ƙarasa gabanta ba ya yi fata-fata da shi, sauran kawunan da ke jikinta suka kafa kawunansu nan take suka gama da Tsohon. Aljanin ya sake russunawa yana faɗin, "Abar bauta ya isa ko a ƙaro wani." Gyatsa ta yi, tana lashe jinin bakinta, sai da ta tsotse ƙashin ƙoƙon kan tsohon sannan ta ɗago ta ce, "A ina ka samu wannan hallitar mai daɗi?" Aljanin ya washe bakinsa yana murmushi bakinsa ya yi girman rijiya saboda wannan ne karona na farko da abar bauta ta yabi naman ɗan'adam. Ya russuna yana faɗin, "Fansar iyayena na mallaka miki abar bauta, ki fanshi wanda kike so. Ke kika hallakawa kike tseratarwa kike kashewa kike rayawa, na samu hallitar bil'adam a cen bakin wata ƙatuwar bola fitowarsa kenan daga wurin Boka Harisu, yana shirin saka laƙanin asirin da aka bashi a ƙarƙashin shara na ɗauko maka shi." Hatsabibiya ta sake kallon wurin da ƙoƙon kan Dattijon yake tana hura masa iska nan take ƙoƙon kan ya fara mirginawa, har sai da ya yi sau uku sannan hallitar tsohon ta sake dawowa kamar yadda take har da kayan jikinsa. Abar bauta ta kalli Aljanin da ya kawo Dattijon ta ce, "A ɗauke shi a mayar da shi wurin da yake rana ita yau a sake dawo min da shi jinin jikinsa bai ishe ni ba." A firgice tsohon ya kalle su nan take jikinsa ya hau tsuma, ya tsugunna yana roƙo da magiyarsu, yana cikin haka ya ga anɓace da shi daga wurin. Abar bauta ta dube su ɗaya bayan ta ce, "Na wakilta guda ɗaya daga cikinku da ƙadangare da mage, kuma ya zama wajibi a yau ba sai gobe Raihan ta kawo mana ziyara, shi kuma Huzaifa ku bar min lamarinsa a hannuna amma ba zan cutar da shi ba ko halaka shi alfarmar Mugaza da take kawowa ƙungiya ci gaba." Wata gwauruwar ajiyar zuciya Intisar/Mugaza ta saki tana lumshe ido, ɗaya bayan ɗaya suka fara darewa daga wurin, Hatsabibiya ta yi wa abar bauta rakiya zuwa turakarta sannan ita ma ta ɓace daga wurin. Daddy shi da abokinsa Alhaji Mustafa suka ƙarasa ofishin Hisbar da su Inno suke, yana zuwa ya samu su Inno a zaune duk sun yi zuru-zuru kamar waɗanda suka wuni suka kwana basu ci ba, musamman Inno da take tsaka da jin mutuwar Hasiya. Suna ganinsa Inno ta fashe da kuka ta kalli ɗan hisbar da ke gefe tana faɗin, "Amma dai kai ƙaramin ɗan sanda Allah ya watsa maka albarka, wallahi ku bar ni a ofishinku amma ni da gidan Audullah sai a lahira ma sadu da juna." Daddy yana shirin yin magana Goggo ta tsugunna a gaban ɗan hisban ta ce, "Yaro ka dubi Allah ka dubi Ma'aiki ko tasha ne ka kaini na wuce albasu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Inno me yake faruwa zuwa na yi mu tafi fa." Inno sunne kai ƙasa ta yi kamar ba ta ji me yake faɗa ba, ta kalli Goggo ta ce, "Don Allah ki duba min hallitar jikin Audullahi ta cika ko akwai nasaka, ada na ƙaryata ki amma Allah ya sani gidan Audullahi Makarai ne suke cin karensu babu babbaka a ciki." Daddy zai yi magana ɗan hisbar ya dakatar da shi, don labarin abin da ya faru tuni ya karaɗe ko'ina musamman da ƴan jarida suka samu zancen yaɗawa, Likitoci suka shiga binciken gawar Sulaiman a ya yin da suke neman Kabiru babu inda ba a duba ba amma basu ganshi ba. Ɗan hisban da kanshi ya yi wa su Inno nasiha, ya sake faɗarkar da su da cewar duk wani abu yana faruwa ne da izinin Ubangiji kuma addu'a takobin mumini ce. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu su Inno suka bi Daddy gidan har sai da ya tabbatar musu da cewar ya sauya musu wurin zama. Lokacin da su Inno suka koma gida tuni gidan ya yi shara-shara babu mutane sosai, don tun a tsohon gidansu ganin abin da ya faru ya sa mutane da dama kowa ya yi ta kansa. Su Goggo a ɗaɗɗare suka shiga sabon gidan, suna tafe bakinsu na motsi da alama addu'a suke yi don ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Mommy da kanta ta kaisu ɗakinsu, kowacce ta zauna shiru don ƙawayensu da suka zo gaisuwa tuni kowacce ta cika wandonta da iska. BAYAN MAGRIBA. Raihan na kwance a ɗakin mommy lamo kamar mara lafiya, don gabaɗaya wani sukuku take jin ta kamar ba ita ba tun da ta dawo daga duniyar aljanu. Tana daga zaune ta ga wurgawar abu, da sauri ta tashi zaune tsigar jikinta na tashi. Wani ƙadangare ta gani yana buɗe mata baki alamar dariya, sai kuma ya fara ƙada mata jela yana yi yana tunkarota. Ƙura masa ido ta yi lokaci ɗaya ta miƙe tsaye, ta fisge ɗankwalin kanta nan take gashin kanta ya hargitse, ƙananan kifaye ne suka fara fita daga bakin ƙadangare. Lokaci ɗaya ta yi kukan kura ta fisgoshi haɗe da ƙwalla uwar ƙara, tana ɗaukansa ta tura kansa cikin bakinta nan take ta fisge masa kai ta wurgar a wurin gangar jikin ƙadangaren yana hannunta. Mommy da wata ƙanwarta har rige-rigen shiga ɗakin suke saboda duk wanda yake gidan babu wanda bai ji ihunta ba. Suna tura ƙofar suka ganta a tsaye tana riƙe da gawar jangwalagwada jini yana ɗiga, ga kansa can gefe sai zare ido take tana faɗin, "Duk wanda ya ce zai hallaka mini Ɗana wallahi sai na fidda masa kai. 🤭🤭🤭🤭 WUYAR AIKI BA'A FARA BA, HAR YANZU FA ASHAFI NA BAKWAI AKE😎😎 KUN GA KUWA AKWAI SAURAN TAFIYA, AKWAI ƘURA A GABA.🤸🏻‍♀️💃🏼 Share Hilis🌚 *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* FREE PAGE 8 Ilahirin jikin mommy rawa ya ɗauka Aunty lubna ta zaro ido hankali a tashe don ko a mafarki bata taɓa cin karo da wannan mummunan abin da Raihan ta aikata ba. Mommy tana son tunkarar Raihan amma tana gudun hukuncin da za ta zartar a kanta, murya na rawa ta dubi Raihan ta ce, "Raihan lafiya me kike yi haka? Ƙadangare ne fa a hannunki." Raihan da har lokacin idonta jawur suke ta sake kai kallonta kan ƙadangaren hannunta, ta sake saka wurin jelarsa a baki ta cisgeta da ƙarfin tsiya ta kalli saitin da su Mommy suke ta tofar a wurin. Wani irin huci ta fara yi idanunta na sake firfitowa ta ce, "Ɗana yake shirin cinye min don haka dole na hallaka shi." Mommy ta tunkari wurin tana son Raihan ta wurgar da ƙadagaren hannunta amma tsoron abin da kaje ya zo ya hanata. Don a lokacin da take da shekara goma ntana da makamancin ciwon ta ya tashi ta taɓa cirewa wani almajiri ɗan yatsa, a lokacin shi ma zuwa ya yi zai ƙwaci agwagwar malaminsu da ta fito kiwo Raihan da Mommy sun fito daga mota, a lokacin da suka kai ziyara Albasu. Tuno da haka ya sa mommy take son tunkararta amma tana jin tsoro. Daga nesa da ita Mommy ta leƙa fuskarta tana faɗin, "Raihan ki yarda abin hannunki." Cikin wani irin ƙaraji ta nufo wurinsu gadan-gadan da ihu tini ba shiri su Mommy suka fice a guje kowa yana gudun ceton ransa. Hankali a tashe mommy ta nufi sashen Daddy tana ƙwala masa kira. A bakin ƙofa ta ci karo da shi tana ganinsa ta fara nuna masa hanya tana faɗin, "Alhaji Raihan ce..." Maganarta ta maƙale saboda yadda take sauke ajiyar zuciya. A zabure Daddy ya kama kafaɗarta yana jijjigawa yana faɗin, "Me ya samu Raihan ɗin ki faɗa min tana ina?" Hanya ta riƙa nuna masa tana faɗin, "Tana can ta tsintsinka ƙadangare da haƙoranta." Da gudu ya nufi hanyar ɗakin Raihan hankali a tashe. Nan take ragowar mutanen da ke cikin gidan suka yi tsilli-tsilli, kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci tana cikin matsanancin tashin hankali. Daddy kai tsaye ɗakin da Raihan take ciki ya tunkara yana shiga ya same ta a cen gefe ta faɗi da alama bata numfashi. Kallon ɗakin ya fara yi saboda yadda jinin ƙadangaren ya ɓata saman carpet ɗin ɗakin, daga gefen hannunta ya hangi gangar jikin ƙadangaren hannunta ya jiƙe sharkaf da jini. A hankali ya ƙarasa wurin ya mirgino da ita yana ambatar sunanta muryarsa a raunace, shiru ne ya ratso a ɗakin babu abin da yake tashi sai karar AC da saukar numfashin Daddy. Tsugunnawa ya yi a gabanta ya tallafo da kanta zuwa kan cinyarsa, murya na rawa ya furta: "Me yake samunki ne Raiha? Me ya sa waɗannan abubuwan suke faruwa da ke?" Kuka ne ya ci ƙarfinsa ya kafa kansa a jikinta yana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Daga bakin ƙofa Mommy ce ta shiga jiki a sanyaye, ita kanta lamarin Raihan ya fara bata tsoro. Kusan shekara goma sha biyar kenan suna fama da abu ɗaya, babban tashin hankalin da ciwon kullin gaba yake yi baya raguwa. A sanyaye ta zauna a gefen Daddy ta ce, "Daddyn Raihan." Ɗagowa ya yi ya dube ta idonsa na ci gaba da zubda ƙwallah, ita ma hawaye ne ya fara zuba a fuskarta ta sa hannu ta share sannan ta ci gaba da cewa, "Ka daina kuka don yanzu babu buƙatarsa a gurbin halin da muke ciki..." Tun bata rufe baki ba Daddy ya katseta da cewar, "Ido yana zubda hawaye ne ba don gangar jiki da ruhi suna buƙata ba, sai don samun sauƙi ga raɗaɗin ƙunan zuciya. A da na ɗauka rashin haihuwa babban masifa ne a gare ni sai ga shi a yau na wayi gari Allah ya bani gudan jinina ga kuma masifar da tafi min rashin haihuwar..." Da sauri Mommy ta rufe masa baki tana girgiza kai ta ce, "Bai kamata ka riƙa furta irin kalmomin nan ba, domin duk abin da ya samu bawa yana daga Ubangiji shi ya fi mu sanin dalilinsa na yin haka." Mommy ta numfasa sannan ta ci gaba da cewa, "Ya zama wajibi ciwon yarinyar nan a koma yin da Islamic don wannan yana da alaƙa da shafar aljanu..." A razane ya katse ta yana faɗin, "Kina hauka ne? Na gargaɗe ki da ki daina danganta jinina da jinsin aljanu." Wanna karon mommy ita ma hassala ta yi ta ci gaba da cewa, "Kar ka sake furta kalma ta ƙasƙanci a kaina, don duk taƙamar da kake yi ba kai kaɗai ka haifeta. Raihan ƴata ce idan kai ba za ka nema mata maganin Islamic ba dole ni zan nema mata." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin, Daddy ko a jikinsa tana fita ya ɗauki waya ya kira likitan da ke duba Raihan, zayyana masa komai ya yi sannan suka yi sallama ya ci gaba da zubawa Raihan ido yana tunane-tunane a zuciyarsa. Lokacin da Macijiyar ta ɓace daga ɗakin Kabiru, daga gefen hagunsa ya fara jin wani irin gurnani irin na riƙaƙƙun kumurcin maciji, a hargitse ya sake miƙewa yana kalle-kalle bakinsa na furta Amanarrasulu don a tunaninsa macijin ne zai sake bayyanar masa. Ya jima yana jin wannan gurnanin daga baya ya ji shiru komai ya ɗauke daga dodon kunnensa, daga jikin hannun rigarsa wata fata ya ga ta kwakkwaɓo irin saɓar fatar maciji wacce yake yi. Da sauri ya ɗago ta cikin tashin hankali don lamari ya fi ƙarfin tunaninsa, ido ya zurawa gwiwar hannunsa ta wurin da fatar ta faɗo ya ga wurin ya sake yin sheƙi tamkar bayan maciji. Kwalla ce ya ji ta zubo masa saboda duk wanda ya lura da halin da yake ciki ba zai taɓa zama a kusa da shi ba, kallo ɗaya za ka yi wa jikinsa ya firgita ka don bambamcinsa da maciji kai, hannu da ƙafafuwa. A hankali ya ƙarasa wurin buhun kayansa, nan take ya fara zazzagewa yana birkito kayan da zai saka don ya rufe jikinsa. Sanin kansa ne ko masu aikin gidan suka fahimci halin da yake ciki zamansa a cikin gidan ya ƙare balle kuma a ce Alhaji ya lura da yadda surar jikinsa ta koma. Sai da ya tura ƙofarsa ya rufeta ruf don kar wani ya turo, sannan ya tuɓe rigar jikinsa da yake mai gajeren hannu ce. A jikin mudubin ya tsaya yana ƙarewa jikinsa kallo fatar jikinsa ta koma sak irin ta maciji, wani hawayen ne ya sake gangaro masa ya sa hannu ya share sannan ya ɗauko wata tsohuwar rigar shadda mai dogon hannu, ya ɗauko wani tsohon mayafinsa da wanda ya gada a wurin mahaifiyarsa ya naɗe wuyansa da shi. A jikin bango ya jingina a fili ya fara magana cikin karyewar zuciya, "Allah sarki Baffajo ba don rashin lafiyarka ba, da babu abin da zai hanani barin wannan gidan, don da alama wannan ba wurin zama ba ne." Kabiru ya ɗaga hannu sama ya ci gaba da cewa, "Allah ka bawa Baffajo lafiya, da yardar Allah sai na bar gidan nan don na nemawa kaina lafiya." Daga gefensa ya ji an bushe da dariya, yana juyawa ya hangi matashiyar budurwa tana tsaye tsirara babu kaya a jikinta. Hannuwa biyu ta wara masa tana faɗin, "Ina da hanyar da zan kawo maka mafita matuƙar za ka bani dama." Kabiru ya kauda kansa gefe yana faɗin, "Wa'iyazubillah." Ɓangaren da ya juya fuskarsa ta sake komawa tana faɗin, "Indai akan matsalar abin da ya faru da jikinka ne zan warkar maka da shi matsawar za ka bani haɗin kai." Kabiru ya ɗago da kansa yana shirin yi mata magana, karaf idonsu suka haɗu wuri ɗaya nan take ya ji tsigar jikinsa na tashi. Da ƙyar ya iya saita kansa sannan ya furta, "Ki taimaka min ki raba ni da wannan fatar macijin, ki gaya min me kike buƙata daga wurina yanzu na aiwatar miki?" Duk wani shige da fice da su Mommy suke yi akan idon Mama Uwani, lokacin da ta ji labarin abin da ya faru ta shiga tashin hankali don ta san wannan abin da Raihan ta aikata baya daga cikin abubuwan da take saka Raihan tana aikatawa. Fitowa ta yi ta fara kaiwa da kawowa nan take wata dabara ta faɗo mata, sai da ta shige ɗakinta da yake babu kowa a ciki sannan ta ɓace daga ɗakin. A lokacin da ta ɓace Dr Hamza yana gidansa ya gama shiri don zuwa gidansu Raihan, Huzaifa na zuwa da ya ga haka don kar ya kawi masa matsala ya bige shi a kan gado nan take bacci ya yi gaba da Dr Hamza. Cikin siffar Dr Hamza ya kira lambar Daddy bugu ɗaya kawai ya yi ya ɗauka, a gaggauce Daddy ya furta, "Dr ka ƙaraso ne?" Huzaifa da ke ɗauke da surar Dr Hamza ya amsa masa, nan take Daddy ya bashi umarni da ya shiga. Daddy da Huzaifa a harabar gidan suka haɗu, Huzaifa sai murmushi yake ƙasa-ƙasa don ko ba komai ya samu damar da zai aiwatar da abin da yake ransa. Suna shiga Raihan tana nan kwance kamar gawa bata numfashi ko hannunta baya motsawa, ido ya zura mata yana son sanin musababbin abin da ya sa ta tsinka ƙadangare gida biyu don ko kaɗan babu sa hannunsa a ciki. Yana tsaka da nazari ya riski muryar Daddy yana faɗin, "Dr don Allah ayi wani abu ciwon nan sai ƙara gaba yake yi." Huzaifa ya miƙe tsaye yana zare gilashin idonsa, ya yi jim kamar wanda yake damuwa sannan ya fara magana, "Gaskiya yanayin ciwonta ya fara bani tsoro Alhaji, amma abin da ya fi akwai wani abokina a India ina tunanin sai an fita da ita, amma a yanzu zan yi bakin ƙoƙarina na ga ta dawo daidai kafin wani lokaci. Amma idan ba shawo kan matsalar aka yi ba lamarin zai rinƙa yin gaba, tun da sannin kanmu ne a da ciwonta bai yi tsanani haka ba." Daddy kamar jira yake ya ce, "Hakan ma ya yi min daidai, abin da ya sa ma ban sake tunanin fita ba saboda ka san ba irin yawon da ba mu yi ba tun Raihan tana ƙarama." Hamza yana shirin yin magana Inno ta turo ƙofa tana tafe Goggo na biye da ita, Inno cike da faɗa tana faɗi: "Saboda Allah haka kawai ace duk wani tashin hankali bai faru ba sai a ranar da Ƴata Hasiya ta kwanta dama, ina dalili yarinya sai rikiɗa take kamar wahainiya. To Allah ya sani idan ban watsa mata albarka ba Mamman mai ƙawa'idi bai haife ni ba, ku bar ni yau ko ni ko Rihanu a gidan nan." Daddy ya waiga wurin Inno da niyyar zai yi magana, suna gano halin da Raihan take ciki da sauri su goggo suka yi baya cike da tashin hankali. Goggo ta dafe ƙirji jikinta sai tsuma yake yi kaɗan ya rage fitsari bai zubo mata ba, ta nuna wurin da Raihan take ta fara faɗin, "Laƙadi ja'akum yau na shiga uku. Allah ya sani duk garin Albasu babu mayya ko guda ya aka yi aka samu maita a zuri'ata, a'a wannan lamarin dole akwai ayar tambaya wallahi idan Raihanu bata shiga ƙungiyar asiri ba Na koma Albasu a ƙafa." Huzaifa ya waigo wurinsu yana faɗin, "Iya don Allah ku yi shiru ina kan Patient bana buƙatar hayaniya." Inno ta riƙe haɓa saboda takaici don gani take abin nasa kamar har da cin fuska, ƴarta ta mutu ba a yi zaman makoki yadda ya kamata ba kuma a kawo mata maganar Patient. A zuciye ta ƙarasa gaban Huzaifa sai da saita daidai fuskarsa ta wara hannunta a kai tana faɗin, "Ƙaniyarka ka ji, fitsararre kana fama da fuska kamar teba." Huzaifa ya kalli Inno a zuciyarsa yana ayyana idan da ya ga dama wurgi ɗaya zai yi da ita ta baje a ƙasa. Bai dawo daga tunani ba ya ji ta sake nuna shi da yatsa tana ci gaba da cewa, "Kai baƙin munafuki ka gaya min idan da ƴarka ce ta musu waɗannan masifun suke faruwa me za ka yi?" Daddy ya zagayo ta wurinta yana cewa, "Inno don Allah ki yi haƙuri shi fa wannan babu ruwansa a ciki." Goggo ta leƙa fuskar Huzaifa tana kwaɓe baki ta ce, "Akan wannan baƙin munafukin kake shiga gaban mahaifiyarka?" Ta waiga wurin Huzaifa ta ci gaba da cewa, "Wallahi ka fito ka gaya masa gaskiya ko na watsa maka albarka, ka san dai ciwon Yarinyar nan bana mai jan kunne ba ne." Huzaifa ya dubi Daddy kamar abin bai dame shi ba ya ce, "Alhaji a kawo min ruwa." Daddy na jin haka da sauri ya fita daga ɗakin, yana fita Huzaifa ya warto su Inno a hannu ya matse su wuri ɗaya. Kamar waɗanda aka naɗe su da igiya aka ɗaura haka su Goggo suka ji, suna shirin yin ihu bakinsu ya yi musu nauyi. Sai da ya yi hajijiya da su sannan ya watsa su can gefe kamar kayan wanki, zannuwa da ɗankwalen su Inno tuni suka maƙale a saman fanka. Lokacin da Raihan ta faɗi a lokacin ne Abar bauta ta bada umarnin ga Raihan da ta kawo mata ziyara, nan take ruhinta ya fita daga jikinta zuwa tsibirin da ƙungiyar asirinsu take. Tana zuwa ta russuna ta yi gaisuwa ga Hatsabibiya, a take ta turɓune fuska ta dubi Raihan tana faɗin, "Mun aika kiran gaggawa ne don Abar bauta na buƙatar ku sha jinin mai naƙuda tare da ke, kuma yau ita ce ranar da za a yi miki wankan tsarki dole ke ce za ki kawo mana jinin da za mu sha daga jikinki, Muna buƙatar jinin mahaifiyarki daga yau zuwa gobe idan ba haka ba Abar bauta za ta iya yi wa danginki ɓarna." Ruhin Raihan wata irin zabura ya yi da jin wacce aka ce ya kawo daga cikin danginta, sai dai hakan bai hanata amincewa da buƙatarsu ba. Cikin girmamawa Raihan ta russuna tana faɗin, "Fansar Mahaifana yana gare ku na baku wuƙa da nama, mai naƙuda a ko'ina take zan kawo mana ita yanzun nan." Tana gama maganar ta bi ta iska ta fice daga tsibirin. Ruhin Raihan na fita bai tsaya a ko'ina ba sai cikin wani babban asibiti, kai tsaye daƙunan majinyata ta fara shiga har za ta fice ta hango wata tsohuwa da alama tana jin jiki, a kan ruwan cikinta ta dira har ta kafa bakinta za ta tsotsi jini majinyaciyarta ta ƙaraso gabanta tana karanta mata ayatulkursiyyu tana tofa mata saboda tuni sun samu bacci ya ɗauketa, ta karanta mata addu'a saboda ita ma bacci take son yi. Da sauri Raihan ta tashi daga kanta ta matsa gefe tana sauke numfashi, daga can gadon ƙarshe ta hango wata mara lafiya bata jinkirta ba ta hau kanta tuni ta kafa bakinta a kanta ta fara zuƙar jini. Nan take jikin matar ya rikice ganin haka ya sa majinyaciyarta kiran nurses, sun kai mutum huɗu a kanta duk yadda suka kai ga bakin ƙoƙarinsu abin ya ci tura, nan take rai ya yi halinsa. Raihan na ganin haka miƙe ta fice daga ɗakin kai tsaye ta wuce can ɗakin haihuwa. Raihan na shiga ta hangi mata kusan uku masu naƙuda, a kan idonta ɗaya ta haihu ta cikin mutum biyun ta dira a gadon ta tsakiya. Tana niyyar kafa kanta a ƙirjinta daga bayanta ta ji an ce, "Jinin Matata ya fi ƙarfinki." A zabure ruhin Raihan ya waiga don ganin wanda ya dakatar da ita ga abin da take shirin aiwatarwa. A MIN SHARE FISABILILLAH🌚 *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* FREE PAGE 9 Rangaji ta fara yi tamkar bishiyar dalbejiyar da take kaɗawa da iskar damuna, a hankali Kabiru ya ɗan fara ja baya don ko kaɗan hankalinsa bai kwanta da ita ba. Cikin wata irin murya mai jan hankali ta fara magana, "Ka amince min da buƙatata ƙwaya ɗaya ce tal na yi maka alƙawarin yaye maka wannan matsalar da take jikinka." Kabiru da yake jin wani abu yana yawo a zuciyarsa game da ita ya runtse idonsa sannan ya fara magana cikin wata irin kasalalliyar murya, "Ba na buƙatar ganinki cikin wannan yanayin." Tun bai rufe baki ba ta ƙarasa wurinsa ta sa hannu tana ƙoƙarin taɓa shi ta furta, "Laƙani aka bani domin cikar burina a kan Daularmu ta Daulatul jinnul-Turabiy. Idan har ka amince min za ka kusance ni kuma zan warkar da kai, idan ka yi min haka zan mallaki Daularmu da abin da yake cikinta, na zo a sirrance ne ta sanadi ƴar uwata wacce ta yi maka haka..." Tana tsaka da magana ya katse ta da furta, "A'uzubillahi minnasshaiɗanirrajim." Da sauri ta ja da baya tana hakki saboda yadda ta ji wani irin hucin zafi daga jikinsa. A hankali ya tattaro jarumta ya ci gaba da karanta ayoyin kariya da duk wata addu'a da ya san ya taba biyata. Nan take ta ɓace daga gabansa don yadda take ji tamkar zai halakar da rayuwarta, ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa saboda yadda hankalinsa ya sake tashi fiye dana da. A wannan lokacin ya yanke ƙauna don ji ya yi zama a gidan ya fice masa daga rai, gani yake zai iya haƙura da zaman gidan idan ya so duk wata sana'a da ya sani zai fita ya nema don ganin ya ci gaba da nemawa mahaifinsa lafiya. Yana gama nazarin ya miƙe ya ɗauki buhun kayansa, sai da ya leƙa ta window ganin hankulan mutane baya wurinsa ya sa ya yi zaraf ya fice daga ɗakin sannan ya zare sakatar gate ɗin ya fice daga gidan. Gudu-gudu sauri-sauri haka Kabiru ya fara tafiya, kasancewar unguwar shiru babu mutane ya sa bai haɗu da kowa a hanya ba, ta bayan wata doguwar katanga ya raɓa yana tafiya ba tare da ya san inda yake saka ƙafarsa. Yana tsaka da tafiya ya ji ya ci karo da mutum a gabansa, a hankali ya fara ja baya yana ƙoƙarin sake hanya ya ji mutumin da suka yi karo da juna yana faɗin, "Assalamu alaikum." Kabiru da ya fara tsorata a ɗan ja da baya sannan ya amsa masa sallamar, don gabaɗaya a rikice yake. Mutumin da har lokacin Kabiru bai tantance ko shi waye ba ya ci gaba da cewa, "Bawan Allah da wa ka dogara?" Kabiru ya fara sakin jikinsa don ya fahimci ɓoyayyan baƙonsa ne, murya can ƙasa ya ce, "Da Allah na dogara." Mutumin ya ƙara taku biyu zuwa gaban Kabiru ya ce, "Ka dogara da shi a ko'ina kake shi zai isar maka." Kabiru ya jinjina kai yana shirin yin magana, mutumin ya ci gaba da cewa: "Ina ƙaunarka fisabillahi don haka zan baka shawara karka ji tsoron kowa idan ba Allah ba." Kabiru na jin haka ya zaburo da sauri da niyyar kama hannun mutumin yana faɗin, "Don Allah wanene kai da kake yawan zuwa kana gaya min maganganu masu daɗi, da shawara akan al'amuran rayuwata?" Tun bai ƙarasa wurinsa ba mutumin ya ɓace, da sauri Kabiru ya hau waiwaye don neman wurin da zai ƙara ganin ɓullowarsa. Daga can bayansa ya ƙara jin muryarsa yana faɗin, "Karka damu da sanin wanene ni domin mai ƙaunarka na tare da kai a koyaushe, ni masoyinka ne ina mai ƙara tunasar da kai muhimmanci dogaro ga Allah." Yana gama maganar ya sake ɓace wa daga wurin. Jiki a sanyaye Kabiru ya jingina a jikin katangar, ban da kukan kwaɗi da ƙananan ƙwari babu abin da yake tashi a wurin. Lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa ta aminta da nasihar da bawan Allahn nan ya yi masa, nasihar da Mahaifinsa yake yi masa ta sake dawo masa, a fili ya fara furta Astagfirullah sannan ya koma ya nufi hanyar gidansu Raihan. Inno kusan suma suka yi ban da juwa babu abin da suke ji, Huzaifa ya ƙarasa gabansu ya ya zaro musu ido. Suna haɗa ido suka ga ƙwayar idonsa na ci da wuta, kakin yawu ya yi ya tofar a kan tafin hannunsa nan take wuta ta tashi. Goggo tuni ta saki fitsarin da take matsewa ta sunne kai ƙasa cikin tashin hankali, Huzaifa ya buga musu tsawa yana faɗin, "Duk wacce ta sake gangancin shiga lamarin Raihan sai na banka mata wuta ta ƙone ƙurmus, kuma duk wacce ta sake ta furta wata magana a kaina da abin da ya faru sai na hallata shi cikin dare." Huzaifa ya ɗago ya damƙi wuyansu sannan ya ci gaba da cewa, "Kuma duk wacce ta ce za ta bar gidan nan tana fita zan ɗaye fatar jikinta." Inno da idonta yake runtse ta ce, "Babana mun gode, ko a ɗakin nan ka ce mu dauwama har ranar mutuwarmu mun bar sauka ƙasa." Huzaifa bai bi ta kansu ba ya ɗebe su ya watsa a saman fanka, sai ga su Inno a maƙale jikin fanka sai ciccila ƙafafuwa suke yi. Sai da suka jigata sannan ya miƙa hannunsa ya ɗauko su yana nuna musu zannuwansu dake can gefe ya ce, "Maza ku ɗaura zaninku ku fice daga ɗakin nan." Tun bai rufe baki ba Su Inno suka fara wawurar zannuwansu suna yi suna layi kamar waɗanda suka maku saboda juwar da take ɗibansu. Suna zuwa bakin ƙofa Daddy ya turo ya shigo mommy tana biye da shi Inno ta kusa tafiya luuuu za ta faɗi da sauri Daddy ya ruƙota yana faɗin, "Inno lafiya?" Inno ta fisge jikinta tana faɗin, "Sake ni ka ji Audullahi, jeka kan Raihanu Allah dai ya watsawa Likitanan albarka." Daddy ya yi murmushin jin daɗi don ya ga sauyi a wurin Tsofaffin saɓanin kafin fitarsa da ya tafi suna kwashe wa Likita albarka. Su Inno na fita suka zube a bakin ƙofa suna mayar da numfashi, Goggo ce ta fara rarrafawa tana sauka daga ƙafar bene, Inno ta leƙa tana faɗin: "Kai jama'a yanzu a daren nan za ki rarrafa Zinaru sai makarai sun makeki a hanya." Goggo da ta gama zuwa wuya a zuciye ta juyo ta ce, "Yooo shi wanda kika kuɓuto daga hannunsa Mutum ne? Ki yi ta kanki daga nan ni kam Albasu zan wuce don na tabbata ko ba aljani bane yana cikin ƙungiyar asiri, don wallahi mutum ba zai aikata abin da ya yi ba idan ba haka ba Malam mai allo bai haife ni ba." Nan take cikin Inno ya sake kaɗawa da sauri ta fara rarrafawa ta bi bayan Goggo suka sauka, suka wuce ɗakinsu. Su Inno na fita Huzaifa ya koma kan Raihan tare da gayyato Jabin Raihan don ta maye masa gurbin Raihan ko ya samu ya sake dulmiyar da su Daddy ga zuwa ƙasar Indiya, saboda matuƙar suka je Indiya hakan zai taimaka masa wurin gano takamaimai abin da yake faruwa da ita. Kafin ƙiftawa ido sai ga Jabin Raihan ta fara motsawa tana sauke ajiyar zuciya, Sai dai babban abin da ya fi ɗaga masa hanakali da ya so ɗaukar gangar jikin Raihan zuwa Tsauninsa abin ya gagara, wannan ya sake tabbatar masa da akwai ɓoyayyan al'amari a dangane da ciwon Raihan, tashin farko Mugaza ce ta faɗo masa don ya san akan baƙin kishinta tana iya aikata komai don biyan buƙatarta. Daddy ne ya tsinke masa tunanin da yake yi yana faɗin, "My Raihan barka farkowa." Mommy da ke gefe ta ce, "Sannu Raihan." Da ido take bin su da kallo tana gyaɗa musu kai tamkar ƙadangaruwa. Mommy ce ta koma daga ɓangaren Raihan ta tsugunna ta fara karanta ayatulkursiyyu tana tofa mata, da sauri Huzaifa ya zabura ya matsa gefe cikin huci a gaggauce yana faɗin, "Shi kenan yanzu zan wuce Alhaji duk abin da ake ciki za ku ji ni saboda akwai wani patient da yake jirana." Daddy ya miƙa masa hannu suka gaisa cikin jin daɗi ya ce, "Ba damuwa na gode sosai Dr." Da sauri Huzaifa ya yi gaba har ya je bakin ƙofa Daddy ya ce, "Dr babu wani magani da za a ƙara mata akan na da ka san fa wancen ya ƙare." Huzaifa ya fara sosa kai sannan ya ce, "Babu damuwa zan turo maka text ta waya." Tun bai jira cewar Daddy ba ya fice daga ɗakin. A hankali Mommy ta ɗago Jabun Raiha tana yi mata sannu, Daddy ya zauna a ɗaya ɓangaren sannan ya riƙo hannunta ya ce, "Allah ya baki lafiya My Raihan." Jabun Raihan ta ɗago tana gyaɗa kai. Mommy ta miƙe tana faɗin, "Mu je na raka ki, ki yi sallah kin ga Magriba ta wuce ga Isha'i ita ma tuni an yi ta." Ras gaban Jabun Raihan ya faɗi don ko kaɗan bata ƙaunar sallah ba abin da ta ƙi jini irin ta ji an ambace ta. Idan aka ce ta yi ma bata san ta inda za ta fara ba tun da ba addininta bane, tana cikin nazari ta riski muryar Daddy yana faɗin, "Haba Zainab yaushe yarinyar nan ta farfaɗo, don Allah ki bari ta huta ta ci abinci ta sha magani tukunna." Mommy ta ɓata fuska tana faɗin, "Daddy babu wani uzuri game da mara lafiya a kan sallah, hatta majiyacin da yake kwance baya iya tashi matuƙar yana cikin hayyacinsa dole a yi masa alwala ko yana daga kwance ya gabatar da sallah..." Daddy ya katse Mommy cikin ɓacin rai yana faɗin, "So kike ki kafirta mu ni da Ƴata kenan? Ce miki na yi ba za ta yi sallah ba? Ki fita idona Zainabu akan katsalandan ɗin nan da kike min yana neman wuce gona da iri." Mommy ta miƙe cikin fushi ta fice daga ɗakin don ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. A hargitse Raihan ta waiga don ganin wanda yake shirin dakatar da ita ga cika umarnin Abar bauta, tana waigawa ta hangi Alhaji Ƙarami abokin mahaifinta. A hankali ya fara takowa gabanta cikin izza yana faɗin, "Matata ce irin dana dasa don ya ci gaba da yaɗo domin samun farinciki da rayuwa mai morewa." Raihan cike da ƙarfin gwiwa ta juya wurinsa tana cewa, "Wa'adin yabanyarka ya zo ƙarshe don a yanzu ba sai gobe ba zan sallamawa abar bauta jininta, ko mahaifana basu isa su dakatar da ni ga aiwatar da wannan kudurin ba." A zabure Alhaji Ƙarami ya fisgo Raihan da niyyar illata ruhinta, da sauri ta kauce ya kaiwa ƙasa duka. Duk abin da yake faruwa babu wanda ya lura daga masu naƙudar dake cikin halin naƙuda har zuwa Nurses ɗin da suke taimaka musu. Raiha ta kalle shi a fusace ta nuna shi da yatsa tana faɗin, "Ka fita a ido tun ban hallaka ruhinka kai da matarka ba, ka barni na yi abin da ya kawo ni tun ban fusata na yi ɓarnar da za ta girgiza ruhinka ba." Ko ba a faɗa ba Alhaji Ƙarami ya san wacece Raihan a cikin Daular ƙungiyar asiri, dukda ba ƙungiyarsu ɗaya ba ya samu labarinta da jimawa a wurin Babban Dodo, tun da jimawa ya so ya ringajayi ruhinta zuwa ta su ƙungiyar amma Huzaifa ya yi kaka gida ya hana shi aiwatar da abin da ya yi niyya. Amma dukda ya san wannan ƙarfin iko nata ba zai hana shi tsayawa tsayin daka don ganin ya ƙwato rayuwar Matarsa ba don ita ce komai na shi a rayuwa. Ya kalleta cikin dakiya da ƙarfin zuciya ya ce, "Na salwantar da rayuwar Mahaifana don cimma burina, na sadaukar da ƙwayoyin haihuwar jikin matata don samun farincikina, duk wani ɗigon numfashi da matata take yi ƙarin arzikina ne, matsawar babu ita duk wahalar da na yi ta tsawon shekaru ta kau don haka dole na dakatar da ke." Raihan na cikin sauraronsa ta ji kuka jariri a gefenta tana dubawa ta ga ta biyun ce ta haihu sai Matar abokin mahaifinta da suke taƙaddama akanta ita kaɗai ta rage, Raihan ta bushe da wata mahaukaciyar dariya haɗe da dukan ƙasa wurin, nan take wasu manyan kunamu suka fara fitowa suna tunkarar wurin da Alhaji ƙarami yake, da sauri suka fara rarrafawa har suka mammaƙale a jikinsa suka fara kai masa sara ta ko'ina. Da sauri ta koma kan matarsa da take cikin wani hali tana nishi da alama ita ma kan jariri ya fara hararamar fitowa, juyawa ta yi wurin da Kunamun nan suke fitowa ta sa hannu ta ɗauko guda ɗaya ta leƙa ƙarƙashin matar ta tura mata kunamar ta cikin gabanta. Lokaci ɗaya matar ta ƙwalla wata irin gigitacciyar ƙara, Raihan ta saki wani shu'umin murmushi ta waiga wurin da Alhaji Ƙarami da yake ta ƙoƙarin ganin ya ƙwaci kansa ta hanyar amfani da tsafi da sihiri, amma tuni kunamun suka kaishi ƙasa. Takawa ta yi har gabansa ta tsugunna a saitin furkarsa ta furta, "Da ka barni na yi abin da yake gabana da ka ceci rayuwarka, ba na son shisshigi a lamurana don haka bana jira ga duk wanda zai kawo min matsala." Tana gama maganar ta miƙe zuwa gaban Matar Alhaji ƙarami da Nurses suka rufu a kanta don ganin sun kawo mata ɗauki, tana nan tsaye Likita ya ƙaraso kanta don har ya fara tunanin a yi mata CS Raihan ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo sannan ta ɗauki ruhin Matar Alhaji Ƙarami ta wuce da ita zuwa kogon tsafinsu. A gaban abar bauta ta ɗire ta a lokacin tuni ta fara fita daga hayyacinta saboda irin saran da kunamar take yi mata, Abar bauta ce ta miƙa hannunta ɗaya daga cikin hannuwa sama da Ashirin cikin ƙasan matar, da ƙarfi ta fisgo kunamar da aka saka mata. Wata uwar ƙarar ta sake ƙwallawa kamar ranta zai fita, Abar bauta ta sake tura hannunta a karo na biyu ta fisgo jaririn cikinta da tuni ƙungiyar asirin Mijinta suka zuƙe masa jini. Abar bauta wurgi ta yi da jariri zuwa ɗaya daga cikin kawunan jikinta nan take suka yayyage shi da haƙwaranta suka fatattaka namansa. Abar bauta ta dubi Raihan da ke tsaya ta fara magana da muryarta mara daɗi, "Aiki ya rage naki yau mun baki wuƙa da nama." Raihan na zuwa ta kafa kanta a ƙirjin matar za ta zuƙu jini da sauri abar bauta ta dakatar da ita da cewar, "Ba iya jininta kaɗai muke buƙata ba, muna buƙatar ki ɗebo mana kayan cikinta kafin mu sha jini, a cirowa Autan kai zuciyarta ya cinye." Raihan na gama sauraronta ta tsugunna tana kallon hannunta nan take wasu irin manyan farata suka fara tsiro mata a hannu masu kaifi da tsini kamar mashi, waɗansu manyan fiƙoƙi masu kama da fiƙoƙin zaki suka fara tsiro wa a cikin bakinta. Hannuwanta ta tura cikin gaban matar faratanta na ratsa cikin jikinta har ta samu nasarar kwaso kayan cikinta, wata irin gigitacciyar ƙara take kwararawa iya ƙarfinta tun tana cikin hayyacinta har ta fita daga hayyacinta. Kamar yadda harshen kare yake lallagi hara Raihan ta zaro harshenta ta fara lasar jinin jikin kayan cikin. Tana gama siɗewa ta wurgawa Abar bauta ta karɓe ta haɗiyesu. Hannuwanta ta ƙara sawa a daidai ƙirjinta a lokacin tuni rai ya fita daga jikin matar, da zaƙwa-zaƙwan faratanta da farke kirjin matar ta zaro zuciyarta ta miƙawa Autan kan da ke jikin Abar bauta, ta saka kanta a saitin wurin da ta ciro zuciyar ta fara zuƙar jinin jikinta. Raihan sai da ta sha jini ta yi ƙat sannan ta ɗago, tana sauke ajiyar zuciya. Hatsabibiya na zuwa ta ja gawar matar zuwa ɗakin arziƙi ta wurgata ciki. Wata irin guɗa ce ta tashi a wurin mai haɗe da walƙiya nan take ƙofar ɗakin ta shafe kamar ba'a taɓa ƙera ƙofa a wurin ba. Abar bauta ta dubi Raihan cikin farinciki ta ce, "Kin haure mataki na farko a cikin ƙungiya yanzu za ki wuce zuwa mataki na gaba, muna buƙatar jinin Mahaifiyarki. Za mu sassauta miki don ba za mu bari ki hallakar da ita da kanki ba, ungo wannan." Abar bauta ta miƙawa Raihan wani kaifaffan ƙashin bil'adama, sai dai kafinsa tamakar kaifaffiyar wuƙa haka yake. Ba musu Raihan ta ƙarasa ta amsa da hannu bibbiyu tana jiran umarninta. Abar bauta ta miƙe tsaye tana faɗin, "Wannan da kike gani ƙashin bayan mahaifiyata ne, ki je da shi ki yanki ɗan ƙaramin yatsan mahaifiyarki ki kawo mana sauran aikin yana gare mu idan kika yi haka kin haure mata ki na biyu idan kika tafi mataki na ƙarshe tayuwu matsayinki ya zarce namu domin ke ɗin ta musamman ce, kina da bambamci da mu ƙungiya tana alfahari da ke." Raihan ta russuna cikin girmamawa sannan ta fice daga kogon dutsen. A lokacin da ta koma gida, gidan ya yi tsit babu kowa da alama duk sun yi bacci. A can gefe ta hangi Mama Uwani da wata mai siffarta a cikin ɗakinta. Ko kaɗan bata damu ba don a baya ma ta ga irin haka, sai ta yi tsammanin duk yana daga cikin aikin abar bauta ne. Kai tsaye ɗakin Mahaifinta ta wuce don tasan a cen mahaifiyarta take kwana, Daddy ta hanga a kan kujera yana danne-danne a laptop ɗinsa a gefe ɗaya ga cool misic yana tashi don idan yana aikin dare ya fi jin daɗin aiki yana jin sanyayyar waƙa musamman ta turawa. Bata bi ta kansa ba ta ƙarasa gefen gadon da Mahaifiyarta take kwance. 😰RASHIN TAUSAYIN RAIHAN YA FARA YIN YAWA, INA TSORON TA ZAMA SHUGABA A WURIN. WAI INA LABARIN KABIRU KUMA WANENE MAI YAWAN BASHI SHAWARAR NAN? SHIN ABOKIN DADDY YANA MUTUWA KO ZAI ƊAUKI FANSA AKAN MUTUWAR MATARSA? WANNE DALILI NE YA SA HUZAIFA ZAI SA A KAI RAIHAN INDIA? IDAN YA KAITA INDIA TA FITA DAGA ƘUNGIYA NE KO YAYA?🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ CHAKWAKIYAR ƘARA GABA TAKE YI😂 MAZA HANZARTA KI BIYA NAKI KAR A YI BABU KE DON WANNAN SHI NE SHAFI NA BIYUN ƘARSHE💃🏼 Share Fisabilillah🌚 *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* © *AMEERA ADAM* Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN. *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* LAST FREE PAGES 10 Ilahirin jikin Mommy ban da karkarwa babu abin da yake yi saboda tsananin tsoro, firgici da tashin hankali. A takure take a ƙuryar gado ta sunkuyar da kanta ƙasa saboda tozali da ta yi wata shirgigegiyar mummunar hallita, girman hallitar ta zarce goggon biri ga wasu irin ƙwala-ƙwalan idanu da suka zazzago kamar za su faɗo ƙasa. Bakinta ban da fiƙoƙi babu komai a ciki sai ƙaton hancinta mai ƙofofi takwas, tare da manyan ƙahunhuna guda biyu. Sautin takun Hallitar kan iya nakasta dodon kunne don haka Mommy ta sa hannuwa biyu ta toshe kunnenta da take jin sa kamar zai tarwatse, Hannuwan hallitar kama suke da ƙafafuwan doki don haka a duƙushe take tafiya rafkeken kanta shi ne a gaba. Jin shirun takunta ya sa Mommy ta ɗago da kanta a zatonta ko hallitar ta ɓace daga wurinta, sai dai tana ɗagowa suka haɗa ido da hallitar nan take ta hango Raihan maƙale a hannun hallitar tana kuka tana miƙawa Mahaifiyarta hannu, jikin mommy har rawa yake yi ta yunƙura don zuwa wurin hallitar tana faɗin, "Don Allah ki bani ƴata ita kaɗai na mallaka karki hallakata, Hallitar ce ta fara ja da baya tare da Raihan ta fara yunƙurin kai kan Raihan zuwa bakinta don ta laƙumeta, da sauri Mommy ta yunƙura cikin tashin hankali ta furta, "Raaaaihaaaaan." (Allah sarki Uwa kenan😰 Duk tsanani Mahaifiya ba za ta so ganin abin da zai cutar da Ƴarta/Ɗanta ba.) Firgigita Mommy ta farka daga mummunan mafarkin da take yi, har lokacin da ta farka jikinta ban da rawa babu abin da yake yi. Da allon gado ta jingina a hankali bakinta na furta Ayatulkursiyyu don ba ƙaramin tsorata ta yi da mafarkin ba. Raihan na gabda da yankar ɗan yatsan mahaifiyarta ta ji wani irn turiri ya yo kanta da sauri ta ja da baya don kaɗan ya rage bata ƙone ba. Farkawar da Mommy ta yi ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba don ta yi bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta aiwatar da abin da yake tafe da ita. Daddy ne ya ajiye takardar hannunsa ya ɗago yana kallon wurin da Mommy take ya ce, "Lafiya dai Mommyn Raihan na ji kina ambatar sunan Raihan cikin dare." Mommy ta yunƙura da ƙyar jikinta gabaɗaya a sanyaye yake ta zauna a kujera mai kallon ta Daddy ta ce, "Daddyn Raihan wani mummunan mafarki na yi akan Raihan, ina jin tsoro matuƙa kar wani abu ya faru da ita. Maganar gaskiya ina tunanin babu shaiɗanu a lamarinta kuwa, kana gani ƙa'ida bana iya kwanciya ba tare da alwala ba kuma addu'a bakin gwargwado ina yi amma idan mummunan mafarki na tashi yi sai na da yarinyar nan a ciki..." Daddy ya yi murmushi sannan ya katseta da cewar, "Zainabu kenan, duk fa abin da kafi sawa zuciyarka yana tare da kai. Ba tun yau ba na sha gaya miki ki bar danganta ciwon yarinyar nan da wasu shaiɗanu, ki gaya min Raihan ina take zuwa da za ta kwashi shaiɗanu? Ƴarmu a killace take ban da makaranta tana zuwa wani wurin? Karki manta silar ciwon yarinyar nan tun bata fi shekara biyar a duniya ba muka wayi gari da shi, ta yaya za a ce wai wasu shaiɗanu suna bibiyarta kamar wacce take bin kwararo tana jari bola a kan sharar kasuwa." Mommy ta yi guntun tsaki tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Na rasa ya akayi idonka ya rufe haka, kana tunanin shaiɗanu sai a waje ake samun su Daddyn Raihan? Ganin su muke yi da za mu shaida kamanninsu? Idan a baya ta wayi ido da ciwo shin muna da lasisin da za mu tabbatar da cewar babu haɗin jinnu a jikinta..." Daddy ya ɗaga mata hannu da cewar, "Zainabu ni da ke muka haifi yarinyar nan, don haka ki nema mata maganin Aljanu tun da so kike ki jawo mana wata masifar muna fama da wannan, shi kenan ki sakar min mara na yi fitsari." Daddy ya ƙarasa maganar a fusace yana tattara kayan gabansa, ya miƙe ya wuce kan gado, jiki a sanyaye Mommy ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala sannan ta saka hijabinta ta nufi ɗakin Raihan don zuciyarta ta gara amincewa ta bari har gari ya waye, a hankali ta fara sauka daga bene sai dai duk taku ɗaya idan ta yi sai ta ji kamar ana bin ta a baya don sai ta ji takun tafiya, sai da ta kusa sauka daga bene ta yi ƙarfin halin juyawa amma wayam babu wanda ta gani. Idanunta ne suka sauka a kan agogon bangon da ke jikin bango wanda ya yi nuni da ƙarfe biyu da rabi na dare, wucewa ta yi hanyar da za ta sadata da ɓangaren su Raihan don gabaɗaya sashensu ɗaya idan aka cire sashen Daddy da yake ɓangarensa daban, a hankali wata sanyayyar iska ta fara kaɗawa mai haɗe da walƙiya tun iskar na kaɗawa kaɗan-kaɗan har ta fara ɗaga labulaye, ƙofofin ɗaki da na window suka fara rufewa da buɗewa a ƙarfi, da sauri Mommy ta fara waigawa don har lokacin bata daina jin alamun takun tafiyar da ake bin ta a baya ba. Tana cikin tafiya ta ga ƙwan fitilar ya fara ɗaukewa yana kawowa, ba shiri ta fara lalube har ta samu ta taɓa jikin bango ta ci gaba da tafiya a jikin bango. Daga bayanta ta ji ƙarar fashewar kwalba tuuuush, a firgice ta fara lalube tana ƙwalawa Daddy kira don iya tsoro ta gama tsorata uwa uba ga shi har lokacin bata daina jin takun tafiya a bayanta ba. Ƙwan fitilar ne ya tsaya cak ya daina ɗaukewa, mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da tafiya a gaggauce cikin sauri. Tana zuwa ta wurin windon da ya fita ta harabar gidan ta hango wata matashiyar budurwa a zaune ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta, da mamaki Mommy ta tsaya tana kallonta sai jikinta ya fara bata kamar Raihan ɗinta don kusan yanayin jikinsu ɗaya, hatta doguwar rigar baccin irinta Raihan ce. Gashin kan yarinyar a barbaje yake ya rufe fuskarta ta yadda ba kya iya ganin ainihin fuskarta. Duk abin da yake faruwa tsakanin Raihan da Mommy Abar bauta tana kallo a cikin Kogon dutsen ƙungiya, ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi da ganin Mommy na son bata matsala ba. Abar bauta na ganin Mommy ta fito don zuwa ɗakin Raihan ta yi wa Raihan magana da cewa, "Ki hanzarta domin samun nasararki, a yanzu a wanni ne kaɗai suka rage miki don samun ci gabanki. Mahaifiyarki za ta fita ki yi ƙoƙari jan hankalinta zuwa harabar gidanku, sauran aikin ki bar min komai a hannuna ki dawo min da ƙashin bayan mahaifiyata don sauran aikin yana gare ni." Raihan da ke biye da a bayan Mahaifiyarta ta furta, "Biyayya gare ki ta zama wajibi fansar iyayena na gareki ya abar bauta." Raihan na rufe baki ta ci gaba da bin bayan Mommy, tana zuwa ta zauna a harabar gidan kamar yadda abar bauta ta tsara mata. Alhaji ƙarami ba ƙaramar azaba ya ci a hannun kunamun nan ba, sai da suka ga ya daina motsi sannan suka dakata da azabtar da shi, sakamakon umarnin da uwar ɗakinsu ta basu. Daga wurin da yake Dodon tsafinsu ya ƙarasa cikin takaici don ba ƙaramin haushi ya ji ba ganin ƴan wata ƙungiyar sun azabtar da ta su ɗan ƙungiya ba. A fusace ya kafawa Alhaji Ƙarami haƙora tun yana masa magiya har rai ya yi halinsa, sai da ya tabbatar da baya numfashi ya ɗaga shi yana faɗin, "Da ka mutu ta sanadin wasunmu gara mu ƙarasaka da hannunmu." Kusan lokaci ɗaya Alhaji Ƙarami da matarsa suka Mutu, Likitoci na kan matarsa ta jima tana wani irin fisge-fisge daga ƙarshe ta ce ga garinku nan. Kabiru yana tafe cikin zuciyarsa yana saƙa da warwara har ya ƙarasa cikin gidan, a lokacin da ya je ƙofar gidan a buɗe ya samu gate ɗin don haka yana turawa da ya shiga ya wuce ɗakinsa da yake a bakin ƙofa yake idan baka lura ba ma ba za ka san ya fita ba. Yana shiga ya ajiye buhun kayansa ya fito ya ɗaura alwala ya gabatar da sallar Isha'i ya yi shafa'i da wuturi . Ya jima yana addu'a da kaiwa Allah kukansa akan mummunar ƙaddarar da ta same shi daga ƙarshe bayan ya idar ya zauna ya fara tilawar alƙur'ani. Ya kusa awa guda yana karatu sai da ya gama sannan ya fito harabar gidan da babu mutane kowa ya kama gabansa, sai da ya kira Daddy a waya ya tambaye shi ko zai ƙara fita ya tabbatar masa da ya rufe gidan babu inda za shi kuma baƙi duk masu tafiya sun tafi. Sama-sama Mommy ta fara jin kamar ana ambatar sunanta, har ta yi kamar ta wuce ta ji ba za ta iya giftawa ta bar yarinyar da take ji kamar Raihan ɗin ta ba, don tuni zuciyarta ta fara ayyana mata ko ciwon Raihan ne ya tashi ta buɗe ƙofa ta fita harabar gidan ta zauna. Kai tsaye ta nufi hanyar da za ta sada ta da ƙofar fita, sauri-sauri ta fara yi har ta samu nasarar zuwa barandar harabar waje. Kamar wacce ake fisga haka Mommy ta fara jin zuciya da gangar jikinta na azalzalarta zuwa wurin da wannan matashiyar budurwar take bakin ta na furta, "Hasbunallahu..." Ta fara tunkarar wurin gabanta na ci gaba da tsananta faɗuwa, lokaci ɗaya ta ji wani irin tsoro ya mamaye ta sakamakon jin kukan wasu irin tsuntsaye na tashi a saman kanta. Ta maza ta yi ta ci gaba da takawa har ta ƙarasa wurin da Raihan take zaune, Mommy ta fara ƙoƙarin kai hannu za ta taɓa gadon bayanta tana kiranta, "Raihan!" Shiru ne ya biyo baya ba tare da ta amsa ba, Mommy ta sake sunkunyawa ta ce, "Raihan." A haukace Raihan ta ɗago tana bin Mommy da kallo, da sauru Mommy ta yi baya sakamakon tozali da ta yi da mummunar hallita. A madadin da ga fuskar irin ta bil'adam kamar yadda gangar jikinta ya nuna sai gani ta yi ta yage mata baki mai kamar na kura, cike suke da manyan haƙora da fiƙoƙi ga hancinta tamkar na kare haɗe da idanu jawur kamar garwashi. Mommy da ta faɗi can gefe ta fara ja da baya jikinta na rawa, Gadan-gadan Raihan ta fara takawa gabanta don ta bawa Abar bauta damar aiwatar da abin da yake gabanta. Cikin gigita Mommy ta fara karanta duk wata addu'a da ta zo bakinta, tana yi tana kiran sunan Daddy don ya kawo mata ɗauki. Tana cikin wannan halin sai gani ta yi wannan hallitar da ɓace daga gabanta, da ƙarfin gaske ta ji ana fisgarta kamar za a yagi naman jikinta. Kamar wanda aka tasa daga bacci haka fitsari ya farkar da shi, kasancewar ƙafa ta ɗauke ya sa Kabiru ya fito bakinsa ɗauke da addu'a don ya kewaya banɗaki. Bayan ya fito daga can bayan ɗakinsa ya fara jin motsi, har cikin zuciyarsa ya ji kamar ya leƙa ya ga abin da yake motsi amma sai ya yi tunanin dare ne ta yuwu ɓeraye ne suke dabdalarsu. Mommy na jin motsin Kabiru ta riƙa ƙwalla masa kira amma a banza ko kaɗan bai san ana yi ba, sai dai har lokacin bakinta yana ci gaba da karanta ayoyin Ubangiji, da abar bauta ta zo kawo mata cafka sai ta ga mommy ta zille mata kamar tarwaɗa. Kabiru na shiga ɗaki ya koma ya kwanta sai dai fir idanunsa sun bushe bacci ya ƙaurace masa, tashi ya ƙara yi ya fito a ƙofar ɗakinsa ya ɗaura alwala yana shirin shiga ɗaki ya ji ƙusur-ƙusur ɗin ya yi yawa. A hankali ya fara takawa yana haske-haske da ƙaramar fitilarsa, daga can bayan ɗakinsa ya hango Mommy a kwance sai shure-shure take yi tana motsa baki da alama magana take yi. Tsoro ne ya kama shi don ko a mafarki bai taɓa ɗauka mommy bace a wurin, a tsorace ya fara faɗin, "Hajiya lahiya kuwa?" Mommy hannu ta fara miƙa masa tana kiran sunansa, ganin haka ya sa Kabiru ya fara ƙoƙarin miƙa hannu don ya taimaka mata amma tunowa da abubuwan da suka faru da shi ya sa ya ja da baya yana karanto aytulkursiyyu ya fara tofa mata tare da falaƙi da nasi. Kamar wanda aka yi wa wankin kunne raɗau ya ji maganar Mommy a kunnensa saɓanin da; da baya jin abin da take faɗa, tsugunnawa ya yi a wurin yana faɗin, "Hajiya me ya fito da dake a tsakar daren nan?" Mommy da ta ji jikinta ya fara sarara mata ta ce, "Kabiru taimaka min ka kaini ciki kar su halaka ni." Kabiru ya zaro ido yana dube-dube yana shirin magana mommy ta dafo hannunsa da sauri ya yi baya yana kurma ihu don ya gama tsorata gabaɗaya. Abar bauta da take laɓe ta fara Allah-Allah akan Kabiru ya basu wuri don ta dawo ta ci gaba da abin da take niyyar aiwatarwa, donma ita kanta Mommy ba ƙaramar wahala suka sha akanta ba amma so take ko ta wanne hali ta samu ta lakuci jinin jikinta idan ya so ko da sihiri ne in sun kaiwa ɗakin arziƙi jininta magana ta ƙare. Kabiru har zai shige ɗaki da gudu sai wata zuciyar ta ayyana masa ta yuwu ita ma shaiɗanu sun yi mata abin da suka yi masa ne har suka tsorata ta fito. Bakinsa ɗauke da addu'a ya sake tunkararta Mommy ta dafa kafaɗarsa ta miƙe tsaye tana layi, da ƙyar ta iya tsayawa a kan ƙafarta ta fara takawa da ƙyar kanta na ci gaba da sara mata. Kabiru na raka ta bakin ƙofa zai juya fir mommy ta ƙi yarda don har sa da ta saka Kabiru ya rakata har ƙofar ɗakin Daddy sannan ya koma ɗakinsa, tana shiga ta zube a bakin ƙofa tana ci gana da karanta duk ayar da ta zo bakinta. A lokacin da ta koma ɗakin tuni Daddy ya yi bacci, da rarrafe ta fara rarrafawa zuwa bakin gadon tana kiran sunansa. Sai dai babban abin da ya sake firgitata yadda ta ji yana sauke wani irin munshari mai ban tsoro, ga ƙwan ɗakin da fara ɗaukewa yana kawowa. Raihan da abar bauta kusan tare suka koma kogon dutsen ƙungiya kowannensu fuska babu walwala, abar bauta ta dubi Raihan rai a ɓace ta ce: "Mahaifiyarki za ta bamu matsala domin tana da riƙo da addini. Sannan wannan Bafulatanin yana ƙoƙarin wargaza shirinmu tabbas za mu ɗau mummunan mataki a kansa, amma fa duk da haka Mahaifiyarki bata sha ba domin za mu ɓullo mata ta sigar da ba za ta taɓa tsammani ba. A yau saura kwana biyar ta fara al'ada don haka zan yi amfani da wannan lokacin, domin alƙawarinta na yi ga ɗakin arziƙi." Raihan ta jinjina kai cikin girmamawa, abar bauta ta nuna wata ƙaramar ƙorama ta ce,: "Ki ɗebi ruwan wanke zunubi ki yi wanka domin kin karya ƙa'idoji da dokar ƙungiya." Raihan na yin wanka kamar yadda Abar bauta ta umarceta ta fice daga kogon dutsen. Intisar ce ta ɓullo daga ƙarƙashin ƙasa ta yi gaisuwa ga abar bauta, kusan cikin haɗin baki suka furta, "Huzaifa zai aika da Raihan ƙasar India don bincike na musamman akan Raihan." Abar bauta ta yi murmushin takaici ta ce, "Na san da haka shi ya sa na nemo ki yanzu. Zai kaita India ne wurin Kakansa Jibbul-Ƙasi don ya yi mata bincike a kanta, ya ɗora zarge-zarge akanta ciki kuwa har da ke." Intisar ta jinjina kai sannan ta ce, "Tabbas na san za a yi haka domin na san wanenen Huzaifa da bin didiginsa." Abar bauta ta miƙe tsaye sai da ta yi zagaye wurin sau uku sannan ta ce, "Ba zai yi nasara a kanmu ba, domin za mu mallakawa Raihan duk wani ƙarfin iko, idan a da bata san wacece ita ba ya zama dole mu sanar da ita ta hanyar sakata a ɗakin arziƙi." Hankali a tashe Mugaza ta ɗago tana faɗin, "Kina nufin tun yanzu za ta mallaki shuɗaɗɗan ruhi ba sai nan gaba ba ya Abar bauta." Abar bauta ta ci gaba da tafiya tana jinjina kawunan jikinta ta ce, "Alƙawarin ƙungiya baya tashi, matsawar Huzaifa ya kaita wurin kakansa tabbas sai ya gane shirinmu kuma sai Kakansa ya wargatsa ƙungiyar nan. Idan kuwa muka saka mata shuɗaɗɗan ruhi dole zai zama garkuwa a gare ta, za ta gagari Jabbul-Ƙasi da dukkan wani shirinsa. WASAN YA FARA ƊAUKAN ZAFI🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ RAIHAN TA KUSA ZAMA SHUGABA LIKAFA TA CI GABA😂😂 MENENE ALAƘAR SHUƊAƊƊAN RUHI DA RAIHAN, SHIN DAMA RAIHAN NA DA WANI A ƘUNGIYAR ASIRI NE DA HAR RUHINSA ZAI MAYE GURBINTA KO YAYA? WACCE ALAƘA CE TSAKANIN SHUƊAƊƊAN RUHI DA KAKAN HUZAIFA JUBBUL-ƘASI? CAKWAKIYAR ƘARA GABA TAKE🥵 MAZA HANZARTA KI BIYA DON JIN YADDA ZA TA KASANCE GARA KI BIYA 300 KI KARANTA AMMA IDAN NA KAMMALASHI SAI KIN SAKA 500 ZA KI SAME SHI🥱🥱🥱 WANNAN SHI NE SHAFIN ƘARSHE WATO SHAFIN ƘAUTA😎 MU JE ZUWA ƳAN GROUP ƊIN *ZAUJATU PAID* A CI GABA DA GASH SUYA SAI RANAR BIKIN NAƊIN 👸🏻 RAIHAN A ƘOGON DUTSEN ƘUNGIYA🤸🏻‍♀️💃🏼 SHARE HILIS🌚 11 "Amma ya kamata ku kwana da sanin Jabbul-ƙasi hatsabibin aljani ne hatta cikin jinsin Aljanu suna matuƙar shakkar shiga gonarsa, ya wuce tunanin mai tunani ya wuce duk inda muke tsammani. Ina tsoron a samu matsala don na tabbata muddin aka samu matsala gabaɗayanmu ba za mu kuɓuta daga hannunsa ba." Hatsabibiya ta yi maganar tana ƙarasowa wurin hannunta sarƙe da na mijinta. Abar bauta ce ta kalleta tana jinjina kai sannan ta ce, "Na san wanene Jibbul-ƙasi don haka ba zan bar wani giɓi da zai sa kwaɓarmu ta yi ruwa ba, amma dole sai mun yi iya bakin ƙoƙarinmu don kar a samu matsala. Mugaza da har lokacin take cikin matsanancin tashin hankali, ta ƙarasa gaban Abar bauta tana cewa: "Abar bauta na shafe sama da shekara ɗari uku a cikin ƙungiyar nan, na yi muku biyayya tun bansan daɗin zaman ƙungiya ba. Ban taɓa bijirewa umarninku domin ku ɗin masu biyan buƙata ne." Abar bauta ta jinjina kai tana murmushin jin daɗi da irin kambabawar da Intisar ta yi mata, Mugaza ta sake marairace murya sannan ta ci gaba da cewa, "Haƙiƙa duk duniya babu wacce na fi tsana sama da Raihan, na kawo ta ƙungiya ne domin a hallakar da ita bisa karan tsaye da ta yi a zuciyar mijina. Amma sai ga shi a lokaci ƙanƙani tana shirin yi min fintinkau cikin ƙungiyar nan, Shin abar bauta kina tunanin idan ta maye gurbin shuɗaɗɗan ruhi alaƙata da ita za ta ci gaba da rufuwa kamar a baya. Karku manta a baya na je mata a zuwan Intisar wato aminiyarta da suke karatu a University ɗaya, babu wanda bai san abotarmu da Raihan ba kuma duk na yi ne don biyan buƙatar kaina. Ina tsoron kar ta samu nasarar maye gurbin shuɗaɗɗan ruhi asirina ya tonu a wurinta domin har abada ba zan yafe mata irin baƙincikin da ta jefa ni a ciki ba koda zan rasa raina. Ta gadar mini da ɓacin ran da har yau na gagar wanke shi, ta farraƙa tsakanina da miji tare da ƴaƴana gabaɗaya. Alƙwari na ɗaukarwa kaina duk daren daɗewa sai na hallakata da kisa mai tsanani ko dan na samu damar fanshe abin da ta yi min. Amma dole zan jinkirta har sai wa'adin zamanta a ɗakin arziƙi ya zo domin zamanta a ƙungiya ni kaina babbar nasara ce." Abar bauta ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya mai nakasa kunnuwan mai sauraro sakamakon kasancewar duk kawunan da ke jikin abar bauta ne suke ɓaɓɓaka dariya. Abar bauta na yin shiru Gawunge da ke gefe mijin Hatsabibiya ya sa hannuwa biyu ya fisge kansa da ke haɗe da gangar jikinsa sannan ya ƙurawa Intisar idanu lokaci ɗaya ya fashe da kuka mai haɗe da dariya. Sai da ya yi mai isarsa sannan bakinsa ya fara magana da yake jikin dungulmin kan da cewar, "Aikin abar bauta baya ɓaci domin ita shakundum ce, bata aiki kara-zube don komai nata a lissafe yake. Shekarata Ɗari da ashirin ina cikin daskararriyar rayuwa, tun kafin kasancewar haka Abar bauta ta min alƙwarin dawowa cikin rayuwata ta baya, don haka ki daina wasu-wasi akan duk abin da abar bauta za ta faɗa." Mugaza har lokacin fuskarta babu walwala sai dai ta ɗan samu ƙwarin gwiwa, Abar bauta ta fara wani irin zagaye lokaci ɗaya ta yi gammo tamkar wawakekiyar rijiya nan take ƙura ta garwaye wajen, daga cikin ƙurar wani ƙasurgumin maciji ya bayyana. Da ace mutum zai yi tozali da wannan macijin zai yi tsammanin wata shirgegegiyar bishiya ce don jikin macijin tauri gare shi tamkar jikin katuwar bishiyar kuka, tsayin macijin bashi da iyaka illlah ƙaton kanta da yake nannaɗe a tsakiyarta. Da ace Macijin zai kwanta zai iya rufe ƙaton gida da abin da yake cikinsa. Baki macijiyar ta buɗe sai ga amon wuta na fitowa daga ciki, ganin haka ya sa Intisar ta yi sujjada cikin neman afuwa tana faɗin, "Tuba nake abar bauta, a gafarce ni na aikata zunubi amma wannan shi ne na farko na ƙarshe." Wasu ƙananan hallitu masu kama da jaririn jakuna suka ƙaraso wurim Mugaza suna tayata nema mata afuwa. Wani ruwa ne ya fara fita daga bakin macijiyar nan take wutar ta mutu sannan ta fara magana cikin wani irin gurnani mai firgitarwa, tana jima tana gurnanin sannan ta fara magana cikin wani irin yare mai rikitarwa. 🥵 Bari mu ɗana yarensu🥱 ( Waskibatin kintasur minbaskila, haisartan kalbiskutu lakastu baksitu warkidasu baigalliasu fatafursu kininar.... Mu bar shi haka😂) "Mun yi miki rangwame domin aikata zunubi ba aikinki bane, amma ki sani ni abar bauta na gagari kowa a duniya saboda ina iya sarrafa komai yadda nake so. Asirinki ba zai taɓa tomuwa a wurin Raihan ba, za ki ci gaba da yaudararta kuma Huzaifa dole mu katange ki da shi domin ya saka miki ido yana bin diddigin ke wacece, duk da mun sakaya ruhinki a wurinsa. Sanin kanki ne ɗakin arziki kamar gadon mulki ne duk wanda ya hau shi sai ya sauka, za mu ɗora Raihan karaga mulkine don cimma burrin ranmu, da zarar aikinta ya kammala a wurinmu za mu shafe babinta. Amma ki sani ya zama miki wajibi ki kula da kwalbar sihiri domin muddin ta sha iska tamkar ruhin Raihan ne ya ke shaƙar isar ƴanci. Duk wannan abin da take yi tana yin sa ne ba a cikin hayyacinta ba, karku manta mun yi galaba a kanta a ranar da take Chartting a banɗaki lokacin da ta zagaya bayan gida tana tsugunno tana chartting ta nan muka yi amfani da wannan damar don ganin mun gayyaci ruhinta, ba zan ja ki da nisa ba amma zan jaddada miki adana kwalbar sihiri har lokacin da buƙatarmu za ta biya. A hankali mommy ta fara ja da baya bakinta na ci gaba da furta addu'o'in kariya, sai dai har lokacin a tsorace take. Ido ta sake zurawa Daddy lokaci ɗaya ta daina jin wannan gurnanin da yake yi mai abin tsoro, tana shirin yi masa magana daga can wajen ƙofa ta fara jin wata irin ƙara mai haɗe da kuka, ihun Raihan take ji sosai har da shassheƙa lokaci ɗaya zuciyarta ta sake tsinkewa sai dai wannan karon bata jin za ta iya zuwa, duba da irin firgicin da ta shiga. Daga kan Mudubi ta hango wayarta da sauri ta rarrafa ta janyota, cikin hanzari ta fara lalubar ɓangaren da Audio yake tana shiga ta ci karo da suratul baƙara, hannunta har rawa yake yi ta danna nan take karatun ya karaɗe cikin ɗakin. Kamar an yi ruwa an ɗauke haka ta ji komai ya ɗauke mata, wata nutsuwa ta sake saukar mata. Ta yunƙura ta ƙyar ta haye gado kusa da Daddy ta kwanta a jikinsa tana sauke wata irin ajiyar zuwa, ta jima a kwance tana saƙa da warwara dangane da abin da ya faru da ita sai daga baya bacci ya yi gaba da ita. WASHEGARI. Kasancewar bacci bai ɗauki mommy da wuri ba sai wurin asuba ya sa ta makara, ba ita ta farka ba sa wajen ƙarfe bakwai saura, da sauri ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala tana fitowa ta fara bubbuga filon da Daddy yake kai tana faɗin, "Daddyn Raihan ka tashi mun makara." Cikin magagin bacci Daddy ya yi miƙa yana faɗin, "Asuba ta yi ne?" Haushi ne ya kama Mommy don tana burin ta ga mijinta na da tsayayyir ibada amma hatta sallar asuba sai ta tashe shi, idan kuwa ita ta makara to sai dai su yi sallah da safiyar Allah. Kan dadduma ta hau tana saka hijabinta ta ce, "Don Allah ka tashi bakwai saura fa dubi rana har ta fito." Daddy ya yi juyi yana mutsuka idanu, Mommy tana gama magana ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta jima a kan sallaya tana addu'o' sannan ta shafa ta koma kan Daddy ta sake tashinsa. Bayan ya shiga toilet hijabinta ta ajiye ta nufi hanyar fita don ta tashi Raihan saboda ta tabbatar bata tashi daga bacci ba. Tana tafe gabanta na faɗuwa don abin da ya faru a daren ranar ne yake sake faɗo mata, cikin dakiya ta ci gaba da takawa tana tafe tana karanta Amanarrasulu. Lokacin da ta zo bakin windon da ta ga Raihan na zaune ta jima a wurin tana kallo sannan ta wuce sashen Raihan ta tura ƙofa, tana shiga ta same ta daga ita sai wata yaloluwar riga iya cibiya tare da gajeren wando da kaɗan ya fi pants. Bubbuga fulonta Mommy ta fara yi tana kiran sunanta, Raihan har ta ɗago ta kafe Mommy da ido sai kuma ta sake tafiya luuuu bacci ya sake yin gaba da ita. Mommy ta sake ɗago da Raihan tana faɗin, "Ke Raihan me yake damunki ne tashi ki yi sallah." A hankali Raihan ta buɗe idonta sannan ta yunƙura ta tashi zaune cikin magagin bacci ta ce, "Mommy lokaci ya yi ne?" Mommy ta watsa mata harara tana faɗin, "A'a ke ake jira, yarinya kullin sai antashe ki sallah amma kullin abin ki ƙara gaba yake." Raihan ta tashi tana tura baki gaba ta ce, "Ai ke dama kullin mommy a cikin masifa kike shi ya sa nafi son Daddy wallahi." Kanta ba ɗan kwali ta nufi banɗaki da sauri Mommy ta buga mata tsawa tana miƙa mata hularta da ke kan katifa. Ba don ta so ba ta amsa ta faɗa ba tare da ta furta kalma ɗaya ta addu'a ba. Mommy na tsaye Raihan ta fito ta fara duba drower kayanta tana lalubar hijabinta. Ganin haka ya sa Mommy ta fice ta bata wuri, kai tsaye ta wuce sashensu Inno. Tura ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama tana faɗin, "Inno barkanku da safiya." Bacci ta same su suna yi ganin haka ya sa ta fice daga ɗakin, ɗakin baƙi ta leƙa ta samu Safara'u wasu ƴan uwan Inno da suka rage basu fi mutum biyar ba, sai da suka gaisa sannan ta fito. Tana shirin hawa sama ta riski muryar Mama Uwani na gaisheta sai dai yanda ta lura kamar Mama Uwani na cikin damuwa. Bayan sun gaisa har mommy za ta haye sama da juyo ta ce, "Uwani lafiya kuwa?" Idanun Mama uwani suka ciko da ƙwalla ta ce, "Hajiya ina cikin damuwa, yanzu haka yau da farar safiya aka yi min waya ciwon Mahafiyata ya tashi." Fuska ɗauke da damuwa Mommy ta ce, "Ciwon Inna ne ya sake tashi." Mama Uwani ta gyaɗa kai tana sharce hawaye, Mommy ta yi ƙasa da muryar cikin tausayawa ta ce, "Allah ya bata lafiya amma gaskiya ya kamata ki je ki dubo ta yau don Mahaifi ba wasa ba." Mama uwani ta goge ƙwallar idonta tana faɗin, "Allah ya saka da alheri Hajiya." Mommy ta ɗan bata fuska ta ce, "Na ce ki daina yawan yi min wannan godiyar mama uwani mun riga mun zama ɗaya. Ki shirya yanzu idan kin gama ki yi min magana, kafin ki tafi ki shiga store ki tafi musu da kayan abinci." Mama Uwani ta tsugunna har ƙasa tana godiya bisa tsautsayi kofaton ƙafar Mama uwani ya bigi ƙafar mommy har sai da mommy ta ɗan yatsuna fuska saboda zafin da ta ji, amma sai bata kawo komai ba ta ɗago Mama Uwani tana faɗin, "Haba Uwani tashi don Allah. Mama Uwani ta tashi sannan mommy ta wuce wurin Daddy. Raihan na ɗago hijabi ta ji wani irin jiri na ɗaukanta, da ƙyar ta iya dafa bango ta ƙarasa bakin gadonta, ƙarasawarta keda wuya ta yanke jiki ta faɗi. Abar bauta na ganin ruhin Raihan ya fita daga jikinta ta yi murmushin samun nasara, Raihan ce tsaye a bakin ɗakin arziƙi wani irin farin hayaƙi mai ɗauke da surar wata irin hallita ya fara zagaye Raihan, sannu a hankali Abar bauta ta zagaya gaban Raihan ta ce, "Kasancewarki a nan yana nufin zamtowarki Shugaba, buɗe bakinki domin mallakar shuɗaɗɗan ruhi." Ba musu Raihan ta hangame bakinta nan take wannan farin hayaƙin ya fara shiga ta cikin bakinta, ya jima yana tafiya sannan ta haɗiye shi gabaɗaya. Tana gama Haɗiyarsa wani irin tari ya turniƙeta idanunta suka yi jawur, kanta ya fara sara mata ga wani irin gumi da yake tsattsafo mata. Ana cikin haka jikinta ya fara wata irin karkarwa kamar mai jin sanyi, tun tana daga tsaye har ta fara ƙoƙarin durƙushewa, cikin bada ƙarfin gwiwa Abar bauta ta fara magana da ƙarfi, "Kin kasance jaruma karki bari wani ruhin ya rinjaye ki, kin kasance mai nasara kuma har abada za ki kasance mai nasara." Ruhin Raihan ya sake yunƙura da ƙyar yana layi sannan ta samu ta miƙe tsaye daram, tashinta tsaye ya sa kogon wurin ya fara girgiza haɗe da hasken walƙiya. Lokaci ɗaya Hatsabibiya da abar bauta suka ƙyaƙyace da wata irin mahaukaciyar dariya cikin haɗin baki suka furta, "Barka da shiga sabuwar rayuwa yake shugaba." Raihan bata kulasu ba ta wuce ɗakin Kujera ta haye kan wata karagar kujera mai ɗauke da ƙoƙon kawunan bil'adam a saƙale a jiki. Sai da ƙare musu kallo cikin izza, isa da nuna tsantsar mulki ta ce, "Barka dai, a wannan lokacin bana buƙatar hayaniya hutu ya wajaba a gare ni." Tun bata rufe baki ba suka dare daga gabanta kowanne ya kama gabansa. Kafin wani lokaci Tuni Mama Uwani ta shirya tsaf cikin atamfa, sai da ta yi sallama da su Inno har ta zo bakin ƙofa Inno ta ce, "Saboda Allah Uwani idan muka bari kika tafi dubiyar nan ke kaɗai ba mu yi rashin kara ba?" Mama Uwani ta yi musu murmushi ta ce, "Babu komai Inno ni ma ai gobe zan dawo." Goggo ta yi karaf ta ce, "Ita fa ziyarar mara lafiya lada gare ta, ina ni ina barin lada a wurin Allah? Uwani bari na ɗauko mayafina mu tafi saboda Allah mahafiyarki ai kamar tamu ce gabaɗaya." (Har na gano idon Goggo a duniyar aljanu) Mama Uwani ta sake murmushi ta ce, "Ai na ga kuna amsar baƙi ƴan gaisuwa shi ya sa da kin yi zamanki Goggo." Goggo ta yi jim sannan ta ce, "Ke Uwani yi tafiyarki kin ji, ina ni ina zuwa ƙauyenku bansan kalarsu ba haka kawai su lashe min kurwa. A'a raba ni da wannan tafiyar daga nan gidan sai albasu, Albasu babu mai kambun baka balle maita je ki sai kin dawo ki duba mai jiki." Huzaifa ya yi dariya don har zuciyarsa Diramar su Inno bashi dariya take, sannan ya fice daga ɗakin. Kuɗi masu yawa Mommy ta ɗiba ta bawa Mama Uwani tare da kayan abinci sannan suka yi sallama. Huzaifa na fita daga gidan nan take ya ɓace ya fara lulawa cikin iskar sararin samaniya, bai tsaya a ko'ina ba sai Dajin Bolgal-Kissam a cikin ƙarƙashin ƙasa cikin wara tsohuwar ƙorama. Yana zuwa wasu dakarun aljanu suka dakatar da shi, waɗanda suke zagaye da wani tsohon aljani tukuf. A fusace Huzaifa ya fara fisgewa yana shirin yin magana Dattijon aljanin da ke zaune a tsakiyarsu ya furta, "Tabbas lamarinka ya munana Huzaifa, a kullin ina gaya maka kowa ya bar gida; gida ya bar shi." TO ME KUKE HARSASHE SHIN HUZAIFA ZAI SAMU BIYA BUƘATARSA KO ƘAƘA😂 INA LABARIN SHUGABA RAIHAN? 😂 INA MUKU FATAN ALHERI🥰 Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min magana ta wannan number 0706 206 2624 12 Huzaifa ya furzar da iska mai zafi cikin ƙunan rai ya dubi sauran sakarun aljanun da suka riƙe su, yana shirin fusgewa ya ruski muryar Dattijon na ci gaba da cewa, "Da ace wannan alƙaryar tana magana tabbas da ita da kaina za ta shaide ni akanka, idan baka manta ba shekaru ɗari huɗu da suka wuce ka yi bankwana da ni da alƙaryata. Kamar yadda nake zaune a wurin nan ranar da za ka tafi sai da na tabbatar maka ko ba daɗe ko ba jima za ka dawo gare ni, kuma sai da na jaddada maka za ka dawo gare ni kana mai neman buƙata a wurin shin akwai abin da na ƙaga na faɗa sabanin abubuwan da suka gabata?" Huzaifa ya murtuke fuska rai a ɓace ya dubi kakansa yana faɗin, "Ka zartar da umarni a sake ni domin wannan ƙasƙanci ne a wurina a ce ina jininka hadima su dakatar da ni."Jabbul-ƙasi ya yi murmushi mai ɗauke da ma'anoni sannan ya ce, "Kowa ya ƙona rumbunsa ya san a inda toka take kuɗi, Huzaifa ka ɓarar da damarka a lokacin da kake tsaka da iko da ita, karka ji haushin kowa ko ka ƙullaci kowa domin duk abin da ya fi kaine sanadi." Jabbul-ƙasi ya tsahirta da zancensa yana kallon Dakarun da ke riƙe da huzaifa ya ce, "Ku sake shi ya ku masu biyayya." Tun bai rufe baki ba suka saki Huzaifa, Huzaifa ya kalle su cikin jin haushi sannan ya fara takawa zuwa mazaunin kakansa. Tsugunne ya yi a gaban Jabbul-ƙasi sannan ya fara da cewa, "Na zo ne domin wata buƙata amma sai ka sallami waɗancan." Huzaifa ya yi maganar cikin isa da ƙasaita. Jabbul-ƙasi ya bushe da wata irin dariya, nan take jaririn aljanu suka firgice domin basu taɓa jin irin wannan dariyar ta sa ba, ƙananan dabbobin da ke kusa da tsibirin suka faɗi matattu wasu daga cikinsu suka bazama, hatta dakarun da ke tsaron tsibirin sai da wani irin matsanancin tsoro ya kama su. Huzaifa yana zaune ƙyam ko motsi bai yi ba, saboda ƙarfin zuciya irin tashi. Jabbul-ƙasi ya jinjina kai yana kallon Huzaifa ya ce, "Idan za mu ninka shekarun da muka yi a baya sau ɗari tabbas halinka ba zai taɓa sauyawa ba Huzaifa, ko ɓata ka yi a cikin dubbanin jinnu wannan ƙarfin izzar taka ita za ta sa na gane kai ɗin jinina ne. Ka aikata min babban laifi sama da shekara ɗari biyu ban sa ka a idona ba, amma yau ka zo da buƙatarka wurina sai dai maganganunka suna nuna min tamkar umarni kake bani." Huzaifa ya ɗago yana yi masa wani irin kallo ba tare da ya furta komai ba, Jabbul-ƙasi ya zurawa Jikan nasa ido yana jiran cewarsa. Sun jima a haka ba tare da Huzaifa ya ce uffan ba sannan Jabbul-ƙasi ya fahimci abin da ya sa Huzaifa ba yi magana ba, ɗaga ido ya yi ya kalli dakarun dake wurin tun bai yi magana ba suka ɓace daga wurin kamar yadda Huzaifa ya buƙata. Jabbul-ƙasi ya dube shi don jin abin da Huzaifa zai faɗa ba don ba shi da masaniya dangane da abin da yake tafe da shi ba. Huzaifa ya sake ɗaure fuska tamau ya ce, "Matata ce take cikin wani yanayi, duk bincikena na rasa gane inda ta dosa." Jabbul-ƙasi ya yi murmushin dattijantaka sannan ya ce, "Zaujinka wacce kana nufin Mugaza? Domin idan ita ko wata biyar da suka gabata ta kawo mana ziyara ba mu ga wani saɓanin lamari a tattare da ita ba." Huzaifa ya kauda kansa gefe cikin takaici sannan ya ce, "Matata Raihan nake nufi, na aureta tsawon shekarun baya. A da babu abin da yake mini shamaki da ita, ina kusantarta a duk lokacin da na yi niyya. Ta haifa mini ƴaƴa takwas amma duka Mugaza ta salwantar mini da su sai na ƙarshen nan ne ya tsaya. Yanzu haka ita nake zargi akan rikicewar al'amuranta don haka nake son ka yi mini wani abun a kai." Jabbul-ƙasi ya sauke ajiyar zuciya bayan ya gama sauraron Huzaifa ya ce, "Ka riga da ka yi sake ɗan zaki ya girma." Huzaifa ya dube shi cikin rashin fahimta ya yana shirin tambayarsa Jabbul-ƙasi ya ci gaba da cewa, "Raihan matarka ce amma kana tafe da gingimemen ƙalubale a gabanka, ta yi maka nisa mai tazarar gaske don yanzu baka da ikon da za ka sarrafata a ƙarƙashin ikonka." A firgice Huzaifa ya ɗago a firgice don jin abin da Jabbul-ƙasi ya faɗa, hankali a tashe ya furta, "Ka yi mini bayanin da zai gamsar da gangar jiki da ruhina."Jabbul-ƙasi ya kishingiɗa daga wurin da yake ya ci gaba da cewa, "Raihan har gobe matarka ce matuƙar za ka jajirce tsayin daka akan soyayyar da kake mata. Amma batun ka sarrafa ko ka kaita duk wurin da kake buƙa bai taso ba, baka da ikon sarrafata domin tana tare da ruhin Gurzuzu jinnu-nariy. A firgice Huzaifa ya miƙe tsaye jikinsa na karkarwa ya furta, "Ya aka yi ruhin Gurzuzu ya kai ga Raihan? Waye ya haɗa ta da shi wanene ya tari aradu da ka?" Jabbul-ƙasi ya tashi zaune ya ƙurawa Huzaifa ido yana kallo, kamar ba zai tanka masa ba sai daga baya ya ce, "Ni kaina bansan waɗannan amsoshin ba domin Gurzuzu ya wuce tunanin mai tunani balle ruhinsa. Matsawar tana tare da ruhin Gurzuzu duk wani bincike da zan yi aikin banza ne, a dul faɗin duniya babu wanda zai iya karya alƙadarin ruhin Gurzuzu mutum ɗaya ce tal, kuma a halin da ke ciki ba ni da yaƙinin har yanzu tana doro ƙasa domin tun ina ina goyon mahaifiyarka rabona da ita..." Cikin sauri Huzaifa ya katse Jabbul-ƙasi da cewar, "Wacece ita? A ina take? Wacce alaƙa gare ta da Gurzuzu da har za ta iya karya alƙadarinsa? Ya za a yi na ganta?" Jabbul-ƙasi ya yi murmushi mai sauti yana shirin magana wasu baƙaƙen aljanu suka shiga wurinsa suna sauke ajiyar zuciya, na farkonsu ya fara cewa: "Boka Iliyasu ya sadaukar maka da baƙaƙen raguna biyu tare da zakaru jajaye uku sakamakon aikin matar nan da aka kashe uwar mijinta wacce ka tallafa masa." Jabbul-ƙasi ya jinjina yana murmushi, na biyu ya ce: "Boka Harisu na saman tsauni ya baka kyauta mushen jaki da maguna biyar akan aikin mijin matar nan da ka taimaka masa wacce ta rufe bakin mijinta a kan dukiyarsa." A wannan karonma Jabbul-ƙasi ya sake yin murmushi, suna shirin tashi daga wurin ya dakatar da su da cewa: Yanzu aiki huɗu ne a gabanmu. Na ɗaya akan ɗan Kasuwan nan da za a haukatar da shi kai Bilgilu kaine zaka zartar da wannan aikin. Aiki na biyu akan ma'aikacin kwanstom ne wanda za mu cire masa ƙaunar aiki domin mataimakinsa ya samu nasarar ɗarewa kujerara, kai Billu kai ne da wannan aiki. Sai sauran ayyukan biyun da suka rage na macen nan da zamu sakawa warin jaɓa ne da saurayin nan da zamu kashe shi a kan budurwar nan. Cikin girnamawa suka jinjina kai, Jabbul-ƙasi ya ci gaba da cewa: "Za mu fara aiki daga gobe." Suna amsa masa suka ɓace daga wurin. Huzaifa da yake cike da ƙaguwa da jin amsar tambayoyinsa ya kalli kakansa yana cewa, "Ina ƙaugauce da jin amsar tambayata." Jabbul-ƙasi ya kalli Huzaifa yana faɗin, "Duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu, Huzaifa daɗina da kai gaggawa shi ya sa saurari lamuranka suke chaɓewa. Burtultika ita ce macen da za ta iya sarrafa ruhin Gurzuzu, a ƙalla ta bani shekari dubu ɗaya da ɗari biyu. Tana rayuwa ne a dajin KALULLUƁU da ke ƙarƙashin Tsauni Zukkin. Daga wannan tsaunin nawa tafiya ce ta shekara ɗaya da rabi, idan har ka same ta da rai za ka yi zaman watannin biyar a fadarta kafin ka samu ganawa da ita. Idan ka sadu da ita tamkar buƙatarka ta biya, ita ɗin tsohuwar budurwar Gurzuzu ce. Labari ya same ni cewar Gurzuzu ya mutu ne saboda tsananin kishinta, ko uwarsa baya jin maganarta kamar yadda yake jin maganar Burtiltika." Jabbul-ƙasi ya kalli Huzaifa cikin rashin damuwa ya ce, "Dabara ta ragewa mai shiga rijiya zaɓi ya rage naka, idan za ka juri wannan tafiyar zan iya taimaka maka da dakarun aljanu masu yi maka rakiya. Idan kuma ba za ka iya ba shi kenan ka ƙyale yarinyar mutane ta ci gaba da rayuwa, kaima ka ci gaba da rayuwarka da Mugaza. "Koda nisan tafiyar ta yi nisan zai ƙare numfashina zan hallici wurin domin zan iya sadaukar fa komai don ganin jindaɗi, walwalar Raihan sun dawo. Taimako ɗaya na ce ka yi min domin neman hanyar mafita, amma ba na buƙatar agajin dakarunka. Raihan tawa ce ni kaɗai don haka wannan yaƙim nawa ba na neman sa hannun kowa, zan koma gida domin na ɗaura ɗamarar zuwa ga dajin KALULLUƁU." Zumbur Huzaifa ya miƙe yana shirin tafiya Jabbul-ƙasi ya katse shi da cewar, "Ina alfahari da samun nagartacen jika tamkar ka, amma ka sani akwai ƙura a tatattare da yarinyar nan bincike na yana nuna wata baƙar ƙura na bibiye da inuwa yarinyar. Zan yi maka fatan nasara domin duk lalacewa kai ɗim jinina ne, dukda kai mai bijirewa umarnina ne zan fi son ka yi nasara ko ba komai za ka shiga kundun tarihi na wanda suka ziyarci Burtultika." Huzaifa har ya je bakin ƙofa ua waiga ya ce, "Ka riƙe fatan nasararka domin ni dama can ɓai nasara ne." Yana gama maganar ya fice daga tsaunin, Jabbul-ƙasi ya yi murmushi mai ɗauke da ma'anoni a fili ya furta, "Yaro kenan man kaza." Lokacin da Mommy koma ɗakin Daddy tuni ya yi sallah ya koma ya kwanta, a gefensa ta zaune murya a sanyaye ta fara yi wa Daddy magana. "Daddyn Raihan!" Janye blanket ɗin fuskarsa ya yi bai amsa mata ba ya zuba mata ido tare da sakar mata murmushi, ganin yanayinta kaɗai ya tabbatar masa da tana cikin matsananciyar damuwa. Nan take ya ji ta bashi tausayi don shi kansa ya san macece mai juriya da ƙarfin hali, tana shirin yin magana ya rigata da cewar: "Zainab!" A hankali ta ɗago idanunta tana kallonsa ya ci gaba da cewa, "Me yake damunki." A madadin ta bashi amsa sai kawai ta faɗa jikinsa ta fashe da wani irin matsanancin kuka, hannu Daddy ya sa a bayanta yana bubbugawa a hankali yana faɗin, "Shiiiii ba kuka na ce ki yi min ba." Mommy sai ta yi mai isarta sannan ta ɗago tana faɗin, "Daddyn Raihan gidan nan sam bashi da kyau, don Allah ka sauya mana domin jiya tsorata ni aka yi Allah ne kaɗai ya sa ina da yawancin kwana." Ido ya zura mata yana kallo sai kawai ya ji ta bashi tausayi, ya samu kansa da cewa: "Ina kike son mu koma? Kar ki manta kwananmu ɗaya yau da tarewa." Mommy ta yi jim sannan ta ce, "Haka ne amma gaskiya ina jin tsoro." Duk abin da ya faru da ita sai da Mommy ta sanar masa shi kansa Daddy jikinsa ya yi sanyi don haka ya amsa mata da cewar: "Kin ga muna shirye-shiryen tafiya India mai zai hana mu fara nemawa Raihan lafiya idan za mu dawo sai mu sauya gida, ina ga kamar haka zai fi." Mommy har ta fara aminta da maganar Daddy ta ce, "To idan mu za mu tafi India ya za mu yi da su Inno? Ina jin tsoron kar a tsorata su kasan ga jikin girma." Cikin gamsuwa Daddy ya gyaɗa kai yana cewa, "Tabbas kin yi tunani mai kyau a yau insha Allah zan san abin yi ina jin na sa a gyara gidana na Rijiyar zaki." Ba ƙaramin daɗi mommy ta ji sannan ta ce, "Ya kamata a yi saukar Alƙur'ani kafin a shiga gidan saboda shaiɗanu." Daddy ya yi dariya yana faɗin, "Oh Zainabu ko da mai rauhanai zan sa miki? Kullin baki da magana sai ta shaiɗanu, to ai shi kenan yadda kika ce haka za a yi uwargida sarautar mata tun da kin maidani mijin hajiya." Mommy ta kashe masa ido ɗaya tana faɗin, "To ai dama ba a canzawa tuwo suna." Daddy ya birkitota jikinsa yana cewa, "Wai yaushe za ki nemar mini ƴar budurwa na aura ne, ko a ƙawayen Raihan ki duba min mai hankali man." Mommy ta yi masa harar wasa tana faɗin, "Na ga ka fini manyan idanu ka duba wacce ta fi maka, ba don ina kishi ba da sai na ce ka auri Intisar don ta fi sauran nutsuwa." Daddy ya sa dariya ya ce, "Wai Allah don Allah daina faɗa gemai-gemai da ni ai sai girma ya faɗi, kedai kawai kin binne min kan angulu don kar na ƙanƙaro amarya." Gabaɗaya suka saka dariya. A ranar Daddy ya bada umarnin a gyara gidansa da ke Rijiyar zaki, mommy ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Bayan tafiyar Mama Uwani ta ƙara saka karatun kur'ani ta sake kwanciya don bata sami wadataccen bacci ba. Daddy na hanyar komawarsa gida ya kira lambar Dr sai da suka gaisa Daddy ya ce, "Dr ya ake ciki da maganar tafiyarmu, bizarmu fa ta fito duk abin da ake buƙata ya kammala na ji baka sake yi min maganar ba, ga shi har yau ba mu sake yin waya ba." Dr ya yi jam sannan ya ce, "Wacce irin tafiya Alhaji? Wallahi jiya na so na kira na baka haƙuri a kan rashin zuwan da na yi, sakamakon wani yanayi da na ji amma sai na ga dare ya yi..." Daddy ya katse Dr da cewar, "Ban gane abin da kake nufi ba." Dr ya yi gyaran murya ya ce, "Alhaji jiya ba ka kira ni akan rashin lafiyar Raihan ba?" Daddy cikin sauri ya amsa da, "Eh haka ne." Dr ya ci gaba da cewa, "Na taso zan zo dubata kaina ya sara ban kuma sanin wurin da nake ba sai goma saura, to na so na kira ka kuma dare ya yi." Daddy jikinsa ba ƙaramin sanyi ya yi ba, a hanzarce ya ce, "Dr ni fa kaina ya kulle jiya ba kai ka zo ka dubata har ka yi min maganar zuwa India ba?" Dr cikin mamaki ya ce, "Kai an ya kuwa Alhaji ko dai baka gidan ne Alhaji." A gaggauce Daddy ya ce, "Kana ina yanzu zan zo na same ka."Kai tsaye Dr ya kwatanta masa wurin da yake, Daddy ya bawa motarsa wuta yana gabda ƙarasawa ya ci karo da mata matashiyar budurwa tsugunne a kan titi ta kifa kanta cikin cinyoyinta da alama kuka take yi. Yau kunsha kura-kurai ban yi Editing ba a yi sorry🥱 LIttafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min magana ta wannan lambar. 0706 206 2624 13 Da mamaki Daddy yake bin wurin da kallo don hanyar babu hatsaniya kasancewar magriba ta fara kawo kai, horn ya fara yi a hankali a tunaninsa ko wata lalurar ce tasa yarinyar za ma a kan titi. Sai dai ko gezau bata ɗago ba duk da yana tafe yana ci gaba da danna horn ɗin motarsa har ya kusa ƙarasawa wurinta. A hankali ya gangara da niyyar yin parking wayarsa da take ringing ta katse shi, number Dr ya gani ya sake kiransa da sauri ya ɗauka ya kanga a kunne yana faɗin, "Hello Dr ga ni na taho wurinka." Daga can ɓangare aka amsa da cewar, "Alhaji ka yi haƙuri ɗazu arashi aka samu wani ƙanina ne ya ɗauki wayar ya maganar tafiya Indian?" A fili Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido ya ce, "Ni dama na yi mamaki da jin irin maganganun da aka yi ɗazu, yanzu kana ina?" Daga can ɓanagaren aka amsa da cewar, "Yanzu ka jira ni a gida zan zo na same ka." Daga haka suka sallame wayar, Daddy na ajiya wayar ya ɗago da niyyar ci gaba da Driven ya hangi saman titin fayau babu yarinyar babu alamarta. Da mamaki ya fara kallon wuraren don ko kaɗan bai lura da lokacin da ta tashi daga wurin ba, cikin rashin damuwa ya ci gaba da tafiya yana saƙa yadda tafiyarsu za ta kasance. Yana komawa gida har ɗaki ya je ya samu su Inno bayan sun gaisa ya ɗan sosa kai ya ce, "Inno dama zuwa na yi da wata magana." Goggo ta miƙe tsaye tana gyara zaman hijabinta ta ce, "Audullah don Allah ba ka cewa na baku wuri za ku yi sirri? Allah ya sani ba zan zauna na ji sirrin ɗa da uwa ba." Daddy ya yi murmushi yana faɗin, "Goggo ba fa wata magana bace, dama gobe idan Allah ya kaimu za mu wuce ƙasar India wurin duba lafiyar Raihan, sai kuma maganar sake gida da za mu yi." Inno ta yi kasaƙe tana kallonsa sannan ta ce, "Ita dai Raihanu ba zan hana ka nema mata lafiya ba, amma saboda Allah Audullahi me ye aibun gidan nan?" Goggo ta wara hannuwa tana faɗin, "Ta ya ni gani kuma wallahi ko a Albasu babu ƙerarran gida kamar wannan." Daddy ya zauna sosai yana cewa, "Zainabu ce ta buƙaci haka tana ganin kamar nan ya muku girma idan muka tafi, dukda zan sa a kawo wacce za ta ci gaba da taya ku zama." Goggo ta ɓata fuska ta ce, "To yanzu fusabillahi ƴan zaman makoki haka za mu riƙa gantalin gaya musu mun sauya gida daga wannan zuwa wannan, Allah ya sani ƙawayena na Albasu rankatakaf sun ce za su zo sadakar uku haka za su riƙa bilayin nemanmu?" Inno ta taɓe baki ta ce, "Bar shi Zinaru, Audullahi so yake ya nuna mana yawan arzƙinsa to Allah ya sani daga gidan idan ka matsa min sai na koma wani wurin zan bi zinaru mu koma Albasu." Daddy ya yi shiru don yadda ya ga sun rikice masa da wuya idan zai shawo kan tsofaffin, ganin ya yi shiru Inno ta leƙa fuskarsa ta ce, "Amma dai ba haushina kake ji a zuciyarka ba ko Audullahi?" Daddy ya yi murmushi ya ce, "Haba Inno kawai ina tunanin wacce zan ɗauko ta taya ku zama ina ga a samu budurwa da Dattijuwa ko?" Inno da Goggo suka washe baki suna faɗin, "Eh haka ya yi Allah ya yi albarka." Daddy ya amsa da Amin sannan ya fice daga ɗakin. Yana zuwa ya sanar wa da Mommy yadda suka yi da su Inno, Mommy ta so a sauya musu gida amma babu yadda ta iya haka za ta haƙura. Sai dai ta bawa Daddy shawara a kan ya kirawo malamai su zo su yi saukar karatun alƙur'ani. Kuma a ranar dangin Mahaifin Daddy na nesa suka zo, ita ma mommy ta yi wa wata ƙanwarta Hajiya Hafsa magana akan ta zo gidanta ta zauna kafin ta dawo daga tafiya. Su Abar bauta na tafiya Raihan ta miƙe tafara zaga lungu da saƙon da ke cikin tsibirin ƙungiya, daga can bayan wani dutse matatar jini ce a daskare. Hannuwan Raihan ne suka fara fidda wasu manyan farata, tana ƙarasawa wurin ta kafa hannuwanta a kan daskararran jinin da ya daske tamkar ƙanƙara, da hannunta ta fara kankararsu tana sakawa a baki tana shanyewa. Sai da ta sha ta yi ƙat sannan ta miƙe daga wurin tana yin gaba ta faɗi a wurin bacci ya yi awon gaba da ita. Raina ba ita ta farka ba sai yamma liƙis tashi ta yi zaune tana mittsika idanu, kai tsaye banɗaki ta faɗa ta fesa wanka sannan ta fito ta zauna a gaban mudubi tana shafa mai. A hankali ta wayarta ta fara ringing, daga ita sai ɗan ƙaramin towel ta ƙarasa ta ɗauki wayar, ganin baƙuwar lamba ya sa ta yi guntun tsaki ba tare da ta ɗauka ba. Ɗauko wayar ta yi ta ajiye a kan mudubi tana ci gaba da gyaran gashi da yake ta wanke kanta, tana tsaka da taje kai ta sake jin wayar ta sake ringing a hankali ta kai hannu ta ɗauka sai da ta yi kamar ba za ta ɗauka wata zuciyar ta bata umarni akan ta ɗauka. Cikin sanyayyar murya ta ɗauka tana furta, "Hello!" Sai da aka ɗauki ƴan sakanni sannan aka amsa da faɗin, "Assalamu alaiki." Taɓe baki ta yi bata amsa ba ta furta, "Da wa nake magana?" Daga can ɓangaren aka bata amsa da cewar, "Yin sallama ko amsata samun lada ne ga duk wani musulmi." Raihan ta yi tsaki a fili tana faɗin, "Idan baka da abin yi ni ina da shi." Bata jira cewarsa ba ta katse wayar." Duk da tana cikin ɓacin rai hakan bai hana ta sakin wani malalacin murmushi ba, a fili ta furta: "Wai ni zai nunawa muhimmancin sallama hmmm." Miƙewa ta yi ta ɗauko doguwar rigar atamfa mara nauyi ta saka don ta jima bata saka atamfa ba, haka kawai ta ji tana sha'awar saka su. Kan katifa ta koma ta kwanta ta buɗe Data ta shiga kafofin yanar gizo. Tana nan zaune Mommy ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, murmushi Raihan ta yi mata ba tare da ta amsa sallamarta. Mommy na tsaye daga bakin ƙofa ta ce, "Raihan yau duk wuni guda ban ji motsinki ba, an ya yau ko abinci kin ci kuwa." Raihan ta shafa cikinta tana cewa, "Mommy wannan cikin nawa ai har zuwa gobe ba lallai na buƙaci abinci ba." Hararar wasa ta yi mata ta ce, "Saboda kin cinye abincin gidan?" Raihan ta yi dariya ta ce, "Allah mommy na ƙoshi abincina na musamman ne." Mommy ta jinjina kai tana faɗin, "Allah ya shirya min ke wannan rashin cin abincin nan naki sai na nemar miki magani." Wayar Raihan ce ta sake ringing ta ja guntun tsaki za ta ajiye Mommy ta ce, "Ba kiranki ake yi ba." Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Wallahi mommy wani sakarai ne zai dame ni a waya." Mommy ta yi girgiza kai tana faɗin, "Kika sani ko classmate ɗinki ne ta yuwu ma gaisuwa za su yi miki tun da na san Intisar za ta sanar da su." Ba don son ranta ba Raihan ta ɗauki wayar tana faɗin, "Ya aka yi?" Daga can ɓangaren aka bata amsa da cewa, "Ina neman Saleem ya aka yi na ji number sa mace ta ɗauka?" Raihan cire wayar ta yi daga kunnenta ta ƙurawa lambar ido takaici ya rufeta, tana tsaka da nazarin irin baƙar maganar da za ta caɓa masa ta ji ya ci gaba da cewa, "Na rasa rawar kai irin na wasu yaran idan baya kusa in ya zo ki ce masa Salman ya kira, amma don Allah ki ce ya koya miki darasin sallama da amsata." Yana ƙarasa maganar ya katse wayar, cikin masifa Raihan ta dura wani uban ashar. Da sauri Mommy ta kai mata duka tana faɗin, "Wai me yake damunki ne Raihan?" A zafafe Raihan ta sanarwa da Mommy abin da ya gaya mata, Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce: "Hala sakarcin da kika saba kika yi masa." Raihan ta zumɓuri baki gaba ta juya ta yi kwanciyarta, Mommy ta zagayo ta gabanta tana faɗin, "Raihan ki haɗa kayanki idan Allah ya kaimu gobe za mu wuce india akwai wani Dr da za a haɗa mu da shi." Raihan tana daga kwance ta ce, "Tuni na riga da na san da tafiyar, abin da ya rage mu ƙarasa." Mommy bata kawo komai ba ta fice daga ɗakin. Duk wani shirye-shiryen tafiya da ake yi Huzaifa yana sane da tafiyarsu Raihan, don lokacin da Dr ya yi waya da Daddy waya suna gamawa Huzaifa ya sake shafarsa, a nan take wurin ya faɗi bacci ya yi awon gaba da shi. A daren ranar ya dawo gidan su Raihan cikin surara Mama Uwani, Mommy ta yi mamakin ganin Mama Uwani don sun gama magana akan kwana za ta yi amma da ta ce musu mai jiki da sauki duk babu wanda ya kawo komai a ransa. WASHEGARI. Tun da safe su Mommy suka kammala shirinsu tsaf, Raihan ma ta shirya cikin riga da wando. Hannunta saƙale da baƙar jaka ba ƙaramin kyau ta yi ba, wayarta ce ta fara ringing tana ɗaukota ta ga number Intisar. Murmushi ta yi ta ɗauka da sallama tana faɗin, "Intisco baby." Daga can ɓangaren Intisar ta amsa mata da cewar, "Besty ya kun tashi ko yaya? Kin san yau muka yi da ƴan Department ɗinmu za su zo miki gaisuwa." Raihan ta yamutsa fuska ta ce, "Yanzu za mu ƙarasa airport ayya ke gaya musu dalilin tafiyata amma ai ina jin bai fi mu yi two weeks ba." Sun ɗan jima suna hira sannan suka yi sallama. ƘASAR INDIA Tun daga Nigeria Daddy ya sanarwa da wani abokinsa da ke aiki a cen maganar zuwanci, da farko sun so sauka a hotel amma Alhaji Yusuf ya nuna sam sai dai su sauka a gidansa. A ranar da suka sauka Daddy na sanarwa da Alhaji Yusuf asibitin za su ziyarta ya yi jim don ko a gidan talabijin bai taɓa cin karo da sunan asibitin ba, da mamaki ya dubi abokin nasa ya ce, "Abokina wai har yanzu wannan matsalar dai ita ce?" Daddy jiki a sanyaye ya ce, "Abu ɗaya muke fama shekara da shekaru." Alhaji Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Shi kenan babu abin da yafi ƙarfin Ubangiji. Zan kira wani abokina don shi ne mai kula da asibitocin kuɗi masu zaman kansu na ƙasarnan, duk yadda muka yi zuwa safiya za ka ji ni amma lamarin ciwon nan nata akwai ɗaure kai." Duk tattaunawar da ake yi Huzaifa na laɓe a ɓoye yana jinsu, babban kuskuren da ya so aikata wa shi ne na rashin kautar da tunanin Abokin Daddy, lokaci ɗaya dabara ta faɗo masa a daren ranar ya sace abokin Daddy zuwa tsibirinsa tare da buɗe masa ido da sabuwar India a wurin hatta iyalansa duk na bogi ya saka masa. Abin da Huzaifa bai sani ba tun ranar da su Raihan suka zo ƙasar India aka ajiye masa jabun Raihan, Raihan ta koma cikin ɗakin arziƙi da zama. Duk wannan shirin na abar bauta ne, don ta ci alwashin aiwatar da komai cikin shiri ba tare da Huzaifa ya fahimci wani abu ba. A yanda Huzaifa ya so, ya so ace ya jinkirtar da rahin Raihan dukda Jabbul-ƙasi ya sanar da shi babu wata dabara ko hikima da ta rage masa game da Raihan matuƙar bai kai ziyara ga Burtultika ba, amma kafiya da taurin kai irin nasa ya sa ya jarraba kawo ta ƙasar India domin a nan babbar da'irarsa take. Sai dai duk wannan abin da ake ciki daga Daddy har mommy babu wanda ya fahimci shirin Huzaifa, saboda ya kaisu babban asibitin kuɗi da asibitin da likitocin duk na buɗewar ido ne da Huzaifa ya yi musu, gabaɗaya ba mutane ba ne har suka gama zaryar asibitinsu kuma a ganinsu buƙata ta biya don tun da suka zo babu wani abu da Raihan ta sake yi na tsoratarwa. Kwanansu goma sha biyar suka tarkato suka dawo ƙasar Najeriya zuciyar Mommy da Daddy fes, musamman Daddy da yake jin kamar an yi masa bushara da gidan aljanna. Kwanansu biyu da dawowa Kabiru ya ƙarasa cikin Falon ya miƙawa Daddy wata farar takarda, a cewar Kabiru Dr Muhsin ne ya kawo masa don ya kira wayar Daddy ta daina shiga. Daddy na karɓa Kabiru ya juya ya fice, don har lokacin jikinsa a naɗe yake saboda baya son ko kaɗan wani ya fahimci halin da yake ciki. Buɗe takardar ya yi cikin mamaki yana faɗin, "Ni fa kaina ya fara kullewa ya za a yi ace min Dr Muhsin ya riƙa zuwa nemana bayan ya san da tafiyarmu." Daddy ya ƙarasa maganar yana buɗe letter hannunsa, a fili ya fara karantawa Mommy na sauroronsa don ita kanta komai ya fara kwnace mata. Takardar ta ƙunshi ban haƙuri da Dr ya ke yi ga Daddy akan ya nemarwa Raihan wani likitan saboda rashin ƙwarin jiki da baya samu, daga ƙarshe ya ƙare maganar da cewar ya yi ta kiran wayarsa baya samunsa. Mommy ce ta riga Daddy maganar da cewar, "Tabbas akwai wani ɓoyayyan al'amari domin lamarin akwia rikitarwa." Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ni kaina al'amuran sun fara sha min kai." Sun jima a wurin suna tattaunawa daga ƙarshe Daddy ya yanke shawarar zuwa ya samu Dr Muhsin har Office ɗin sa. Bayan Wasu Kwanaki. Raihan ce shirye tsaf cikin doguwar riga kayan ba ƙaramin kyau suka yi mata, hannunta ɗauke da jakar makarantarta don tun dawowarsu daga India suka shiga first semester level 300 sai dai ba ta samu ta halarci makarantar ba. Da kanta ta ƙarasa wuri parking space ta ɗauki motarta, sai da ta je bakin gate ta fara zabga Horn. Da sauri Kabiru ya ƙarasa jiki na rawa ya buɗe mata ƙofa, da gudun gaske ta fice daga gidan ta ware sauti na tashi a cikin motar fuskarta ɗauke da ƙaton glass baƙi. A kan titin shigarta gate ɗin makarantarsu bisa tsautsayi motarta suka yi taho mu gama da wani matashin saurayi da ke kan babur ɗin lifan, sai dai Allah ya rufa asiri ba wata buguwa suka yi mai ƙarfi ba. A zafafe Raihan ta fito daga mota cikin masifa tana faɗin, "Kai wanne irin mutum ne da baka lura da gabanka..." Muryarta ce ta maƙale sakamakon tozali da ta yi da kyakkyawar fuskarsa, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wacce ta dawo da saurayin daga tunanin da ya faɗa na firgicin abin da ya faru. Bai tanka mata ba ya fara ƙoƙarin saukowa domin ɗauko wayarsa da ta faɗi can gefe, da sauri Raihan ta tsugunna ta ɗauko masa tare da sa gefen mayafinta ta goge masa. Tana shirin miƙa masa ta riski muryarsa yana faɗin, "Na gode." Ya yi maganar yana karɓar wayarsa, har zai tada mashin ɗinsa ta furta, "Ka yi haƙuri." Raihan ta samu kanta da furta waɗannan kalaman, murmushi ya sakar mata sannan ya ce, "Ba damuwa." Raihan ta gyara tsayuwarta tana lumshe ido sakamakon jin yadda muryarsa take rikitata, tun da take bata taɓa tsintar kanta a cikin wannan yanayin ba. Mutane da dama sun nuna suna soyayyarsu a gare ta amma babu wanda ya taɓa yi mata balle ta ji wani abu daga gare shi. Tana tsaka da tunani ta tsinkaye shi ya kunna mashin ya yi gaba abin sa, firgigita ta ɗora idonta a kan katafaren gate ɗin makarantarsu. Tana nan tsaye har ta ga shigewarsa cikin, hannunta ta sa ta dafe gefen ƙirjinta ya yin da ta ji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, tana nan tsaye cikin duniyar tunani ƙarar horn ɗin motar da ke bayanta ta dawo da ita daga duniyar tunani. ALLAH YA SA HUZAIFA YA BARI SOYAYYAR TA ƊORE😂 Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 14 Kamar wacce aka zare wa laka a jiki haka Raihan ta fara takawa a hankali ta buɗe motarta, tana shiga ta bata wuta da ƙarfin gaske. Duk yadda ta so cimma matashin sai dai kamar an yi ruwa an ɗauke haka ta neme shi ta rasa sama da ƙasa, daga gefen hall ɗin da suke da lecture ta yi parking ɗin motarta. A kasalce ta ziro ƙafarta ta fara takawa kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, ɗaga kanta ta yi tana ɗan waige-waige don har lokacin bata cire rai da tsammanin ganinsa ba, a haka har ta ƙarasa bakin hall ɗin tana tafe tana saƙa da warwara. Zuwanta ke da wuya ƴan Department ɗin su suka fara yi mata ta'aziyya sakamakon mafi yawa daga ciki basu halarci gidansu ba, Raihan yaƙe ta riƙa yi musu amma sam hankalinta baya wurinsu. Tana nan tsaye Intisar ta ƙaraso sanye da coffee ɗin hijabi, kalarsa ba ƙaramin karɓarta ya yi ba. Ta baya ta rungumo Raihan tana faɗin, "Oyoyo Besty." Hararar wasa Raihan ta yi mata tana faɗin, "To ƙarasani ki huta kin ji." Hannuwa biyu Intisar ta sa a daidai kunnuwanta tana cewa, "Tuba nake na ƙaryaki ina na kama." Gabaɗaya suka saka dariya tare da rankayawa cikin block ɗin sakamakon zuwan malamin da zai yi musu lectures, Mr Samuel shi ne lectural da yake ɗaukansu Oral Engilsh ɗalibai na ƙaunarsa sosai sakancewar ya iya koyarwa, yana shiga ajin ya yi tsit saboda a dokarsa matuƙar kuna surutu nan take zai yi test a kan topic ɗin zai koyar a ranar, kuma matuƙar ya ɗauka yana amfani da shi. Tun shigowarsa Raihan ta kafe shi da ido lokaci ɗaya ta ji ta kawaɗaita da shi, sunkuyar da kanta ta yi ƙasa tana son aiwatar da manufarta a kansa runtse idonta ke da wuya fuskar matashin saurayin nan ta faɗo mata a ƙwayar idonta. Ganin halin da take ciki ya sa Intisar murmusawa don ta fahimci abin da Raihan take buƙata game da Mr Samuel, a hankali ta ɗan zungurota tana cewa: "Wai yau lafiya Samuel yana lecture na ganki some how?" Muryar Raihan a raunace ta ce, "Ya tafi da zuciyata." Wata irin faɗuwar gaba Mugaza ta ji sakamakon jin magana Raihan, cikin ƙarfin hali ta wurga mata tambaya. "Wa kenan." Raihan ta manta shaf malami na ajin ta kwantar da kanta a kan desk muryarta na ci gaba da rawa kamar za ta yi kuka ta ce, "Kallo ɗaya ya yi min amma ya tafi da rayuwata, jin sa nake a ƙarƙashin zuciyata ta yadda duk bugun nufashi fuskarsa na walƙiya a fuskata. Sai dai kash..." Da sauri Intisar ta katse ta da faɗin, "Wanene shi? Ɗan gidan uban waye?" Ta yi wannan tambayar don so take ta ji daga bakin Raihan dukda zafin zuciyar da take ji a kanta, alwashi ta ci muddin Raihan ta furta waɗannan kalaman akan babban masoyinta Huzaifa za ta nuna mata iyakarta, don ta gwammaci ta halakata idan ya so ita ma su abar bauta su halakata kowa ya rasa. Raihan ta katsewa Intisar tunani da cewar, "Wani matashin saurayi ne, da alama shi ba kowa ba ne..." Nan take Raihan ta zayyanewa Intisar abin da ya faru tsakaninta wannan saurayin. Yanda Intisar take murna sai ka rantse da Allah ita ce mai saurayin, Raihan na shirin yin magana Dr Samuel ya hango su suna surutu. Da hannu ya nuno su yana kiransu, Raihan ko gezau haka ta miƙe ta nufi wurinsa Intisar ce take tafe jiki a sanyaye kamar mutuniyar kirki. Raihan tun bata ƙarasa wurinsa ba ya ce mata su fita, madadin ta yi takaici sai kawai ta bushe da dariya har sai ta bawa sauran ɗaliban mamaki. Tana fita Intisar ta bi bayanta suka zauna a dandamalin jikin block ɗin, Raihan na zaune ta runtse idonta nan take fuskar saurayin ta ci gaba da dawo mata. A fusace ta furzar da iska mai zafi, lokaci ɗaya faratan hannunta suka fara sauya launi, daga farare zuwa jajawur. Daga cikin lectura hall ɗin Dr Samuel ne ya fara jin wata irin juwa na neman ɗaukansa, cikinsa ya fara murɗa masa haka kawia ya ji kamar ana fusgar hanjin cikinsa. Tun yana iya daurewa har ya zage ya ƙwallah wata irin ƙara cikin fitar hayyaci, Raihan na daga waje ta bushe da wata irin dariya nan take hannuwanta suka fara dawowa daidai. Intisar ta dube ta cikin tsoron ƙarya ta ce, "Me yake faruwa Raihan?" Raihan bata kulata ba ta sauke idonta a kan wani narkeken jangwalagwada kamar tsuntsuwa tana tsaye ta cafe shi a haukace ta kaiwa kansa cizo, a daidai lokacin ɗaliban cikin block ɗin su suka fito da gudu sakamakon aman jinin da Dr Samuel yake yi, maza daga cikin ƴan Department ɗin su suka kama shi wasu suka wuce wurin hukumar makaranta don sanar da abin da yake faruwa. Carko-carko sauran ɗaliban suka yi dukda sun san Raihan na da aljanu amma ba su taɓa tsammanin za su ga tana gididdiba ƙadangare gida biyu ba, Wani irin huci ta fara yi mai ban tsoro haɗe da gurnani, tana yi tana tunkararsu ganin haka ya sa ɗaliban kowa ya fara yin ta kansu masu ciro waya suna yi mata suna yi daga nesa, Intisar ma wurin ɗaliban ta koma tana nuna tsoronta don duk wani abu da za a zarge tana ƙoƙarin kiyaye shi. Kafin wani lokaci tuni Malaman makarantar suka zo da motar makaranta aka ɗauki Dr Samuel sai dai tun kafin su je asibiti rai ya yi halinsa, amma ba su yi ƙasa a gwiwa ba sai da suka kaishi asibiti don tabbatar da haka daga bakin likitoci. Raihan na tunkararsu ta fara fige ɗankwalin kanta, hannu biyu ta sa ya ɓark doguwar rigar jikinta don ma Allah ya sa akwai T-shirt a jikinta. Kasancewar rigar na da santsi nan take ta zuge ta faɗi ƙasa, Raihan daga ita sai ƙaramar riga da gajeren wando da ko cinyarta bai ƙarasa ba. Wasu daga cikin securities ɗin makarantar ne suka tunkari wurinta da niyyar kamata don su killace ta saboda suna gudun ta yi wa kanta tsirara a cikin jama'a. Ɗaya wanda ya kasance a kan gaba ya fi ɗayan kwari don na bayan yana da ƴan shekaru zai iya haihuwar Raihan, suna gabda ƙarasawa wurinta ta buga tsalle haɗe da wani kukan kura ta cafko kansa ta kafa masa haƙora a kunnesa. Kamar yadda kura take yagar nama haka Raihan ta yake masa kunne guda ɗaya, tana ɗagowa ta wurgar da fatar kunnen a ƙasa ta dubi saitin idonsa tana shirin kai haƙoranta Dattijon security ya kai mata ƙafa a ƙirji cikin shammata, a cen gefe ta faɗi kafin ta miƙe ya sungumi matashin securityn da yake cikin wani yanayi ya zuba da gudu, don tana yage kunnensa nan take ya sume. Raihan kallon mutanen wurin ta riƙa yi a haukace tana shin-shine kamar sabuwar mayyar da ta yi tozali da jariri, duk girman makarantar an rasa wanda zai shawo kanta balle a samu a kaita gida. Gabaɗaya ɗalibai taruwa suka kowa da abin da yake furtawa, wasu ma tuni suka ɗora ayar tambaya akanta dangane da mutuwar Dr Samuel. Tafiya yake da ƙafafuwansa cikin nutsuwa, daga nesa ya hango cincirindon mutane wata zuciyar har ta raya masa ya je ya ga abin da yake faruwa don tun da ya ga wannan yawan jama'ar ya san ba na lafiya ba ne. Sai dai ɗayar zuciyar ta gargaɗe shi a kan ya yi tafiyarsa saboda yana da wurin zuwa, har ya ɗauko mashin ɗinsa daga wurin masu gadi kasancewar dama wurin wani malamai ya zo kuma bai same shi ba. Yana gabda wucewa ta hanyar ya ji wani matashi yana faɗin, "Kasan Allah surar yarinyar ba ƙaramin tafiya ta yi da ni ba, ban da ina tsoron wannan ciwon nata ba ai soyayya zan ƙulla da ita ko dan na ɗebi ganima." Na gefen hagunsa ya yi guntun tsaki ya ce, "A haka za ka ƙare kullin mata ne a gabanka, ni wallahi tausayi take bani. Dubi yadda aka zagayeta ana kallo kai gaskiya ciwon iskokai bai yi ba, yanzu da tana cikin hayyacinta yaushe za a ƙare mata kallo haka. Ni wallahi duk ji nake babu daɗi yanzu da ƙanwata ce fa haka za ta yi, gaskiya lamarin akwai tausayawa tun da take aljanu bata taɓa irin wannan ba." Al'amin yana niyyar wucewa ya ji sam ba zai iya ba, don maganar saurayin nan na ƙarshe ta taɓa zuciyarsa. A gefensu ya kafe mashin ɗinsa mai maganar yana ganinsa ya jinjina hannu cikin girmamawa yana faɗin, "Allah ya taimaki babban ƙwaro." Murmushi ya yi musu ya ce, "Hamza wai dama kune a nan." Tun bai ƙarasa maganar ba suka zayyane masa duk abin da yake faruwa, kafe mashin ɗinsa ya yi ya miƙawa Hamza mukullin, a hankali ya fara kutsawa don ganin halin da yarinyar take ciki. Da mamaki ya riƙa bin ta da kallo don gani yake kamar ya san inda ya taɓa ganin fuskarta amma ya manta sakamakon fuskarta ta yi kace-kace da jini, jikinsa ba ƙaramin sanyi ya yi ganin yadda ta yaga rigar jikinta kadan ya rage ta yage gida biyu. Bakinsa ya fara motsawa yana karanto ayoyin tsari yana ci gaba da tunkarar wurinta, cikin tashin hankali ɗalibai suka fara ihu waɗanda suka sanshi suka fara ƙwala masa kira. Kai tsaye ya tunkari Raihan ko waiwaye bai yi ba, tana kallonsa ta fara ja da baya hakan ba ƙaramin mamaki ya bawa kowa a wurin ba. Ƙirjinta ba ƙaramin bugawa yake yi ba duk yadda ta so zartar da wani abu akanta ta kasa. Yana ƙarasawa wurinta ya cafki kanta da hannuwansa biyu ya fara biya suratul baƙara da ƙarfi yana tofa mata, tun tana daga tsaye ta fara layi har ƙafafuwanta suka gagara ɗaukanta. Luuu ta faɗo kansa jikinta a sake cikin fitar hayyaci, kamar haɗin baki haka mutanen wurin suka ɗauki sowa fa tafi. A hankali ya kwantar da ita cikin ciyayin da ke ƙasa wurin sai da ya dubi hagu da dama sannan ya ciro mayafin da ya naɗe wuyansa ya rufa mata a jikinta. Ganin haka ya sa tsirarin ƴan department ɗin su suka fara ƙarasowa, kallonsu ya yi duk da bai san suwaya suke karatu da ita ba ya ce, "Su waye suka san gidansu yarinyar nan?" Cikin haɗin baki wasu samari suka ce, "Intisar."Sai dai duk yadda aka duba harabar wurin babu Intisar babu alamarta." Tun zuwan Al'amin wurin a firgice Intisar ta ja da baya, yana fara karatu ta ɓace daga wurin don wani irin tiriri ya tasamma halakata. Cikin gajiyawa da kallon da mutanen wurin suke yi masa ya ce, "Ita kaɗai ta san gidansu?" Wani lectura da ƙarasowarsa kenan ya ce, "Mahaifinta ba ɓoyayyaye ba ne, ƴar gidan Alhaji Abdullahi..." Yana tsaka da magana wata budurwa ta ce, "A unguwar sharaɗa suke mun je gaisuwar ƙanwar mahaifinta." Al'amin ya ƙarasa wurin Malamin ya ce, "Ya kamata akaita gida Malam zamanta a wurin nan bai kamata ba." A tsorace Malamin ya riƙo kafaɗar Al'amin ya ce, "Ai ya kamata ka ƙarasa ladanka kawai." Ganin a tsorace Malamin ya ke ya sa Al'amin yin jim yana nazari, ɗagowa ya yi ya kalli yarinyar da ta faɗi unguwarsu Raihan ya ce, "Ina jakarta take." Da hannu ta nuna masa wurin da jakar take, yana ƙarasawa ya ɗauko wayarta ya cire layinta ya saka a wayarsa. Number iyayenta ya duba amma duk searching ɗin da ya yi bai gani ba, yana cikin dubawa ya ga ansa My Heart. Guntun tsaki ya yi a zuciyarsa ya ɗauka ko lambar saurayinta ce, yana kira ya ji muryar Daddy ya ɗauka yana faɗin, "My baby ya school?" Al'amin bai amsa ba masa ba ya zayyane masa abin da yake faruwa da Raihan tare da shaida masa wurin da take, yana gama maganar ko jiran ta bakin Daddy bai yi ba ya cire layin ya mayar mata cikin wayarta. Jakarta ya miƙawa matashiyar budurwar sannan ya raɓa ta gefe ya wuce don shi kansa sauri yake saboda uzurin da yake gabansa, uwa-uba kuma ga jikinsa da ya ɓaci da jini kace-kace. A ƙasa da minti goma sha biyar Daddy ya ƙarasa cikin makarantar, ikon Allah ne kawai ya kaishi don yadda yake jin sa kamar zai tashi sama. Yana zuwa ya fara kutsawa cikin mutane, da hannuwa biyu ya ɗauke ta ya saka a mota ya figi motar da gudun gaske. Kai tsaye asibiti ya wuce da ita yana zuwa likitoci suka karɓeta sai dai dole sai da buƙaci ganin statement ɗin police, Daddy yana tsaye a wurin ya yi wa DPO ɗin unguwa uku waya ya sanar masa da halin da yake ciki, kasancewar abokinsa ne ya sa ba a samu jinkiri ba nan take ya turo da police officers guda biyu. Ƙarin ruwa da allurai aka yi mata sai allurar bacci, ta jima tana bacci sannan ta farka a lokacin Mommy na zaune a gefenta. Kallon wurin da take ta yi ta kalli Mommy da mamaki ta ce, "Mommy me ya kawo ni nan me ya faru da ni na ga jini a jikina?" Mommy ta dafa kafaɗarta ta ce, "Ba na son tambayoyin nan haka Raihan, na taimaka miki ki shiga toilet ne." Kai kawai Raihan ta gyaɗa mata, mommy ta riƙe ta sai a lokacin ta lura da abin da aka rufa mata jiki da shi. Shiru ta yi tana kallon mayafin ajiyar zuciya ta sauke ta sa hannu ta janyo mayafin tana ƙare masa kallo, lokaci ɗaya zuciyarta ta buga ƙamshin turarensa ya dokin hancinta. Kamar zautacciya ta dubi Mommy tana cewa, "Wallahi wannan ƙamshinsa ne don Allah yana ina Mommy." Intisar tsaye ta yi a gaban abar bauta bayan ta gama zayyane mata jawabin abin da yake tafe da ita, Abar bauta cike da farinciki ta ce: "Tabbas Huzaifa ya bata baya kamar yadda Jabbul-ƙasi ya shawartar da shi, amma ke kinsan wanene mijinki bai bar Raihan gabaɗaya ba sai don cimma burinsa. Tabbas ta faɗa tarkon ƙaunar wannan saurayin sai dai ina jiya masa uƙubar Huzaifa." Mugaza ta ɓata fuska tana faɗin, "Ina murna baƙo ya tafi ashe yana bayan gari, kenan a kowanne lokaci Huzaifa zai iya waiwayar Raihan?" Abar bauta ta jinjina kawunanta ta ce, "Faɗi ki ƙara domin tafiya ya yi domin ya dawo da shirinsa." Mugaza ta jinjina kai cike da takaici ta ce, "Menene abin yi a gare ni?" Abar bauta ta yi jim sannan ta ce, "Idan kin ga Huzaif ya rabu da Raihan sai an nema mata magani kuma sai dai ta auri namiji mai tsananin riƙo da ibada, ita kanta sai ta dage da riƙo da addini. Amma kina ganin muma za mu sha?" Mugaza ta girgiza kai cikin rashin fahimta ta ce, "Ban gane ba me ye haɗinmu da ita?" Abar bauta ta yi mata wani kallo sannan ta ce, "Kina nufin da ke da ni da sauran ƴan ƙungiya za mu tsira ne, muddin ta samu waɗannan abubuwan da na lissafa sai sun tarwatsa shirinmu da ni da ke da ƙungiya za mu halaka komai zai wargaje mana." Mugaza ta jinjina kai don lamarin ya sakata a tsakiya wannan shi ake cewa ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn ta wannan number 0706 206 2624 15 Jikin Magaza ba ƙaramin sanyi ya yi ba amma gani take tana iya haƙura da komai ba Huzaifanta ba, a wurin da take tsaye ta durƙushe ta zauna tana shirin yin magana Abar bauta ta katse ta da cewar, "Yanzu dabara ta rage tamu, domin shi kansa Huzaifa matuƙar ya dawo da nasara ba zai bar mu ba. Ban san mai yasa abubuwan suke neman rikice mana lokaci ɗaya ba, a kodayaushe nasara nake gani a gabana amma wannan karan tana neman kubce min." Zumbur Mugaza ta miƙe tsaye ta ce, "Ki bar min komai a hannuna ni na san yadda zan ɓullowa lamarin." Da yake kan abar bauta ya kulle nan take ta amince da buƙatar Intisar, ga Hatsabibiya da ƴan tawaga sun tafi nemowa dakin arziƙi jinin da zai sha ya ƙoshi. Kabiru tun fatar jikinsa na damunsa har abin ya fara zame masa jiki, watarana yana zaune a ɗakinsa bayan ya gama tulawar alƙur'ani, ya samu kofi ya karanta Ayatul kursiyyu bakwai falaƙi da nasi bakwai-bakwai sai ayatulkursiyyu da Amanarrasulu uku-uku kamar yadda ya saba kullin bayan ya gama tilawar alƙur'ani. Yana gama tofawa ya sha ya shafe jikinsa babu jimawa bacci ya ɗauke shi, ya jima yana bacci sai bayan wani lokaci ya farka kai tsaye ya ɗauki buta ya wuce banɗaki don lokacin har an fara kiraye-kirayen sallar Azahar, ba ƙaramin mamaki ya yi ba na bacin da yai mai tsawo, bayan ya idar da sallah kamar wanda aka cewa ya kalli mudubi sai gani ya yi jikinsa fayau babu wannan fatar macijin, farincikinsa ne ya ƙi rufuwa sai shafa jikinsa yake yana sake duddubawa. Nan take ya faɗi ya yi wa Allah godiya bisa ni'imar da ya yi masa ta yaye masa wannan lalurar da ya yi, kamar wanda aka yi wa bushara da gidan aljanna haka Kabiru ya riƙa shige da fice cikin farinciki. Washegari har mai ƙosai ya kaiwa kuɗi ta yi wa yara sadaka don nuna godiyarsa ga Allah S.W.A. Da mamaki Mommy ta dubi Rain don ta yi tsammanin har lokacin Raihan na cikin ciwonta, tana nan tsaye Daddy ya turo ƙofa yana ganin Raihan a zaune ya washe baki cikin jin daɗi ya ce, "My baby." Raihan ta yi wa Daddy murmushi sanna ta ce, "Daddy ina me wannan abin?" Ta ƙarasa maganar tana nuna mayafin jikinta, hannuwa ya wara mata yana faɗin, "Ban san na waye na, ina jin na wata classmate ɗin taki ce..." Turo ƙofar da Intisar ta yi ya katse maganar Daddy, Raihan ta girgiza kanta ta ce, "Wannan ba na kowa ba ne sai na mijin da zan aura wallahi Daddy ina son shi." Lokaci ɗaya Mommy da Daddy suka zaro ido don wannan baƙuwar kalma ce da basu taɓa jin ta a bakin Raihan ba, ko a baya da samari suke nuna soyayyarsu gare ta ba su taɓa ji ko ganin ta nuna alamun soyayya ga wani ba. Daddy ya yi saurin cewa, "Wane ɗan baiwa mai rabon ne wannan?" Intisar da ke gefe ta furta, "Daddy wani mai rabo ne, don nima yau sai da ta yi min maganarsa." Mommy ta mayar da kallonta ga Intisar ta ce, "Au wai da gaske ne lamarin?" Raihan ta tura baki gaba tana faɗin, "Mommy da baki yarda da abin da na gaya miki ba?" Mommy ta sa hannu a baki ta kare ta ce, "Ina na isa na ce uwar maigari ta yi ƙarya." Gabaɗaya suka saka dariya, tiryan-tiryan Raihan ta yi masa bayanin yadda aka yi suka haɗu da Al'amin, sai da suka gama sauraronta Mommy ta ce, "To Yanzu Raihan daga haka ta haɗa ku da mutum bai ce yana sonki ba sai kawai ki fara son shi, shin ma ke kin tabbatar da wannan mayafin na shi..." "Haba don Allah Zainabu yanzu ke ba murna za ki yi ba, kina gani duk saurayin da ya fitowa yarinyar nan ƙinsa take yi yanzu ba sai mu tayata so da neman yaron nan ba." Daddy ya katse Mommy cikin faɗa. Mommy ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta furta, "Daddy ka fahimci abin da nake nufi, shin shi yaron yana sonta ne? kawai daga haɗuwa bata san halinsa ba sai ta faɗa soyayya da shi?" Daddy ya ɓata fuska ya ce, "Ki bar batun soyayya idan kuɗi na magani zan nemar mata soyayyarsa a wurinsa, zan shi ga makarantar tasu na nemi wurin da yaron yake, ke kin tabbatar ɗan makarantar ku ne Raihan?" Raihan ta gyaɗa fuskarta ɗauke da murmushi don har ayyanawa take sun tsunduma cikin soyayya. Kwanan Raihan ɗaya aka sallameta saboda babu wani abu da yake damunta, a ranar ne Daddy ya fara binciken Al'amin sai dai ko mai kama da shi babu wanda ya ce ya sani. Wannan maganar ba ƙaramin ɗaga hankalin Raihan ta yi ba, hatta abinci sai mommy ta yi da gaske take samu ta ci. Ga binciken duniya da likitoci suka yi sun ce bata da wani ciwo sai matsalar damuwa (Depression) ce ta yi mata yawa, don haka za ta riƙa abubuwa kamar mara hankali ko shafar iska. Daddy na jin wannan bayanin ya hau kai ya ɗare har yana yi wa mommy ƙarin bayani dangane da ciwon, ita dai Mommy ta ji shi ne amma har zuciyarta bata aminta da maganar ba, daɗin da ta ji da likitan ya ce zai ɗorata a kan allurai wanda za a riƙa bata a kai akai, wanda za su taimka mata wurin rage halin da take shiga. Daddy na fitowa daga asibitin suka haɗu da Dr Muhsin sai dai duk lokacin da Daddy ya ɗago masa da zancen ciwon Raihan zuwa tafiyarsu India sai ya ji ya manta komai, sai dai ya yi ta yi wa Daddy kame-kame. Ganin haka ya sa Daddy ya haƙura ya daina yi masa maganar har ya yi tunanin sake mata wani likitan. Suna haɗuwa suka gaisa faram-faram Dr Muhsin ya tambayi jikin Raihan daga haka suka yi sallama, Daddy na shiga mota saƙo ya same shi daga hukumar makarantar su Raihan, daga harabar asibitin kai tsaye makarantar su Raihan ya wuce. Takarda suka aka bawa Daddy na dakatar da Raihan da aka yi daga makatantar har sai ta samu lafiya, wannan labarin ba ƙaramin ɗaga hankalin Daddy ya yi ba. Lokacin da ya shiga mota har sai da ƙwalla ta zubo masa, zuciyarsa a dagule ya wuce gida yana zuwa ya sanarwa da Mommy abin da yake faruwa. Ita kanta bata ji daɗi ba amma sai ta fauwalawa Allaha lamuranta, tare da addu'ar Allah ya bayyana ainihin ciwon da ke daminta da hanyar warakarsa. A wannan lokacin Mommy ta dage sosai da sallar dare kuma tun abin da ya faru da ita a baya bai sake faruwa da ita ba, wani lokacin idan tana sallar dare har kuka take tana gayawa Allah buƙatunta don komai ya dagule mata, ga mitar da su Inno suke yi mata a kan yarinya ta girma babu tsayayyan miji, abu goma da ashirin ne ya haɗe mata. Tun bayan dawowar Mama Uwani daga dubiyar mahaifiyarta duk ta sauya musu, hatta fara'a walawala da sauran abubuwan da take yi duk ya ragu, idan ba aiki za ta yi ko wani abin ba kodayaushe tana cikin ɗakinta. Da farko su Inno sun ɗauka jimamin rashin lafiyar mahaifiyarta amma daga baya sai suka lura da mu'amarce ta cikin jama'a bata so don haka suma suka ja baya da ita don tun suna tambayarta ko wani abu yana daminta ta ce a'a har suka zuba mata ido. Har bayan dawowar su Mommy ita kanta ta lura da haka amma sai ta yi mata uzuri kasancewar ɗan'adam ajizi ne yau da daɗi gobe babu. Amma abin na Mama Uwani ƙara gaba yake don yanzu ko aikin gida bata yi, wani lokacin Mommy ta yi ta ƙwalla mata kira amma fir ta ƙi zuwa. Wannan sabon yanayin da aka samu ya sa mommy ta fara tunanin ko gajiya Mama Uwani ta yi da aikin gidan, wata ranar laraba yamma liƙis Mommy ta ƙwallawa Mama Uwani kira tana zaune a falo yana kallo, sai bayan wani lokaci sannan Mama Uwani ta fito fuska babu walawa. Dama kuma Mommy ta kirata ne don ta tambayeta ko ta gaji da aikin a yi mata ihisani a sallameta a ɗauko wata. Ganin surar da Mama Uwani take ciki ba ƙaramin ɗaga hankalin Mommy ya yi ba, tun fitowara daga ɗaki ta fara ƙarewa ƙafarta kallo ƙirjinta na ci gaba da matsanancin bugu. Ilahirin jikinta rawa yake tun Mama Uwani bata lura da halin da Mommy take ciki ba har ta fara shan jinin jikinta, kallon idon mommy ta yi ta lura da wurin da take kallo nan take ta sauke kanta ƙasa tana kallon ƙafafuwanta, ganin Mommy ta gama ganin manyan kofatan dawakai ya sa Mama Uwani ta bushe da wata mahaukaciyar dariya, Mommy na daga kan kujera ta fara ja da baya don bata taɓa tunanin haka daga wurin Mama Uwani ba. Ɗago kofatonta ɗaya ta yi tana nunawa Mommy ta ce, "Gane-ganenki ya kaiki ganin abin da zai hana ki bacci. Tun da kin gano da idonki zan fayyace miki komai, ni ba mutum bace kamar yadda kuka yi tsammani tsawon shekaru. Hasalima ni zaman maye gurin nake yi domin ba ni ce ainihin Uwanin da kuka sani ba, ni sunana Mar'usa ƙanwace a wurin Huzaifa wato mijin ƴarki Raihan. Ya ajiye ni ne don na maye gurbinsa saboda wata doguwar tafiya da ya yi, idan ku ba daƙiƙai ba ne baku lura ɗabi'armu da tashi ta sha bamabam ba? Shi ya zauna da ku shekara da shekaru yana yi muku bauta saboda matarsa a gidan nan take, ni kuwa da babu uwar da zan ƙaru da ita kina ganin zan zage na yi muku bauta. Shi ma aikin da kika ga yana yi ya fansar da aikin wahalar ne a matsayin sadakinta, tun da yanzu kin san komai ni zan yi tafiyata sai ki jirayi dawowarsa don ba zai barki haka ba." Tana rufe baki Inno na ƙaraso wa wurin tana shirin yin magana turus ta tsaya baki a sake murya na rawa ta ce, "Na shiga aljanna na kasa fitowa, Uwani kofato nake gani a ƙafarki ko idona ne?" Mar'usu ta turawa Inno kofaton tana faɗin, "Ni ba Uwani bace ita kanta uwanin da kuke tsammani ba mutum ba ce." Tana rufe baki ta ratsa ta jikin bango ta wuce, Mommy na zaune bata yi aune ba sai ji ta yi kijiffff Inno ta faɗi ƙasa tana faɗin, "Lahamakasabat Wa'alaina makasabat, hasbunallahu La'ilaha'illahu. Wa'innahumin Sulaimanu..." Da sauri Mommy ta yi kanta tana tarota Daddy da shigowarsa kenan ya ƙarasa wurin yana salati, hankalina tashe ya ce, "Lafiya kuwa Inno garin yaya." Inno da ta fita hayyaccinta ta ce, "Idan mafarki nake yi Allah ka farkar da ni, Ina Zinaru take ta riƙe ni mu shiga ƙofar aljanna, Kalidina fiha'abadan cikin aminci." Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 16 Hankalin Daddy ba ƙaramin tashi ya sake yi ba ganin irin yadda Inno ta fara fita hayyacinta, a hargitse ya dubi mommy yana faɗin, "Zainabu me yake faruwa da Inno ne ko faɗuwa ta yi?" Mommy da ita ma ta fara fita hayyacinta ta nuna hanyar da Mar'usa ta bi tana faɗin, "Wallahi ba mutum bace." A daidai lokacin Goggo ta taho ta hanyar tana tafe tana faɗin, "Haka kawai kai ba arne ba kai ba baka haɗa iri da mai jan kunne ba ace gida kullin abu ɗaya, ina dalili ace koyaushe sai dai mu kalli ƙasashen turawa. Wallahi da sake, wannan tsohuwar ta bar ganin ita ta haifi Audullahi ni ma ina da iko da gidan tun da ai Ƴata yake aure, haka kawai wa ya sani ko zaginmu suke da yarensu ba mu sani ba. A'a raba ni da wannan lamarin ko a riƙa kunna min sangaya ko kuma na ɗauki ƙullin kayana na wuce Albasu, yoooo me gare su da babu a Albasu? Allah na tuba waccen tukunyar sanyin ce kaɗai ba ni da ita, tun kafin marigayi ya rasu ya ajiye mini talabijin na kalli sangaya na kalli Jan kunne. Ita ma tukunyar sanyaya ɗaki zan shiga adashin So dangi na haɗa da ƴan samiruna na bawa Zainbu ta cika ta saya min, zaman gidan siriki ko tashin hankali. Allah ya sani daga nan babu in da zan tsaya sai Albasu, abu ɗaya zan tsaya jira Audullahi ya haɗa min tsaraba na kaiwa su Rahila idan ba haka ba kullin suna liƙe da ni, su cika min ɗaki da tsamin kai da na hammata..." Bata kai ƙarshen maganarta ba ta ga Mommy na nuno wurin da take tana faɗin, "Da gaske ba mutum bace yaudararmu take yi aljana." Daddy na ɗaga kai ya yi tozali da Goggo, karaf maganganun mommy suka sauka a kunnen Goggo. Baki a sake ta ƙarasa wurin tana tafa hannuwa, Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Ni kam Zainabu kanki bai fara taɓuwa ba kuwa? Taimaka min mu kai Inno asibiti." Inno da take jin maganganun Daddy sama-sama nan take ta tuno irin jijjigawar da Huzaifa ya yi musu cikin siffar Likita nan take ta sake ruɗewa ta ce, "Ina Alhaji Babba?" Da mamaki Daddy ya ce, "Alhaji Babba kuma Inno." Alhaji Babba Mahaifin Daddy ne ya rasu kusan sama da shekara talatin baya. Inno bata san ma Daddy yana yi ba balle ta fahimci tambayarsa, ta sake wawuro hannun Mommy tana cewa, "Alhaji Babba ka riƙe hannuna ka shafa min ƙofar aljannah. Idan mun shiga karka bi da ni ta hanyar masu kofato a ƙafa." Daddy ya sake duban Mommy ya ce, "Wai me yake faruwa?" Mommy na shirin yin magana Goggo ta yi caraf ta karɓe maganar da cewa, "Yooo ka nemi ba'asi Audullah bayan matarka ta gama kwayewa uwarta baya, yanzu Zainabu ni kika maida sheɗaniya wacce ta fito daga jinsin aljanu?" Goggo na faɗin haka ta rushe da matsanancin kuka, ta sa gefen rigarta ta share hawaye sannan ta ɗora da cewa, "Don Allah Audullahi idan Allah ya tsine min za ta bi ni ko ba za ta bini ba?" Daddy da kansa ya ɗaure ya dafa kansa da hannuwa biyu ya ce, "Goggo me ya yi zafi haka?" Goggo ta nuna Mommy ta ce, "Ba ka ji irin tozarcin da matarka ta yi min ba? Na rantse da Allah idan wani ya taɓa maida ni jinsin Aljanu Allah ya watsa min albarka, amma tun da haka ne zan bar muku gidanku na ƙare rayuwata a Albasu ko mutuwa na yi idan ba a kai gawata can ba ban yafe ba." Mommy ta zauna zaman dirshan ta ce, "Goggo ni fa ba manufa ta kenan ba, wallahi uwani ba mutum bace aljana ce yanzu haka abin da muka gani kenan muka firgita ni da Inno..." Gabaɗaya Mommy ta zayyana musu abin da yake faruwa, daga wurin da Goggo take ta yi tsalle ta dira a gadon bayan Daddy cikin kiɗima ƙwaƙumeshi tana faɗin, "Wattaba'u matattulisshayaɗina Alamulki Sulaiman, don Allah Audullahi ka dubi girman Allah ka mayar da ni Albasu ko mayu bamu da su balle Aljanu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Zainabu!" Ɗagowa ta yi tana kallonsa, bai bi ta kanta ba ya ci gaba da cewa: "Yanzu saboda Allah haka kawai za ki riƙa razana kanki, ki dubi tsofaffin nan suma kin razana su." Mommy takaicin duniya da ashirin ya kamata, babban baƙin cikinta da komai ta faɗa Daddy baya amincewa da ita sai dai yace ta cika tsoro. A zafafe ta dube shi don wannan karon zuciyarta ta bushe ta ce, "Na ga ji da yadda idanunka suke rufe wa akan abubuwa da dama, ba tun yau ba nake zargin jinnu sun samu gurbin zama a jikin Raihan amma kullin cikin ƙaryata ni kake yi, me kake ɗauke ne? Kana tunanin duk duniya akwai wanda zai zo Raihan kamar irin soyayyar.da nake mata. Karka manta cikinta na ɗauka wata tara tun tana ƙwayar hallita har zama cikakkiyar mutum, ka san yadda laulayi yake kuwa? Ka san yadda nake son cin wannan ba na son wanna? Idan na ci na yi amai da ƙyar zan samu wani ya zauna. Lokacin da cikina ya tsufa ka san irin nauyin da Ɗa yake da shi a cikin mahaifa? Tun da cikina ya fara girma na daina kwanciyar rigingine sai gefe da gefe kasan irin wahalar da nake sha idan na zauna zan tashi. Tun lokacin da na fara naƙuda ka san irin raɗaɗi da zafin ciwon naƙuda kuwa? Ban raina abubuwan da kake yi min ba na kulawa duk macen da ta samu kamarka ta yi dace amma duk kulawar da kake ba ni; ni kaɗai na san irin abin da nake ji a jikina, shin ka san yadda ratsowar kan ɗa yake daga jikin Mahaifiya kuwa? Na shafe tsawon wata tara ina rainon cikinta, duk wani yanayi da nake ciki tana fuskata na farinciki ko baƙinciki, hatta sautin muryata ta tantance kalarta shin tana samun waɗannan abubuwan daga gare ka? Ka gaya min akwai shaƙuwar da za ta wuce tsakanin ta Ɗa da mahaifiya? Ka ga ya min akwai wanda zai nuna mata soyayya fiye da wacce zan nuna mata? Kana tunanih za ka fini ƙaunarta?" Mommy ta ƙarasa yi wa Daddy tambaya tana tsare shi da ido babu alamar tsoro a tattare da ita. Shiru ya yi yana nazarin maganganunta, Mommy bata damu da haka ba ta ci gaba da cewa, "Duk wannan gatan da kake nuna mata sam ba soyayya ba ce, kuma ba zan taɓa alaƙanta Raihan da ciwon jinnu ba kawai don son raina ba. Uwani da muka shafe tsawon shekaru da ita ba mutum ba ce ƙaton aljani ne da ya shiga jikin Ƴarka Raihan, ɗazun nan muka fahimci haka ni da Inno idan kuma kana musu wataƙila idan ta gaya maka za ka ɗauki abin da muhimmanci, idan kana tantama ka duba cikin gidan nan kaf idan za ka sake ganinta." A wannan karon hankalin Daddy ya fi na koyaushe tashi, jikinsa har rawa yake ya dubi Inno da hargagin Mommy ya dawo da ita cikin nutsuwarta yana shirin yin magana Inno ta ce, "Audullahi!" Daddy ya amsa mata murya a sanyaye Inno ta ci gaba da cewa, "Idan baka haɗa ni da Zinaru ta kaini albasu ba Alhaji Babba ya dawo duniya. Ganin idona na ga Uwani da Kofato har tana gaya mana ita ba mutum ba ce yau mai hanani tafiya Albasu sai Allah." Goggo na maƙale a bayan Daddy ba tare da ta fahimci a wurin wa take ba, tana miƙa hannu ta shafo gemun Daddy a zabure ta leƙa fuskarsa tana faɗin, "Yau na shiga aljanna na kasa fitowa yau ni ce maƙale a bayan Audullahi, astagafirullah Allah ka yafe min me ya kaini bayan siriki ana zaune ƙalau?" Goggo ta ƙarasa maganar tana zazzage ɗankwali sai da ta ɗaura shi akanta ta ce, "Me zan zauna na ci gaba da yi a gidan nan ban da abin kunya, wannan Idan ƴan Albasu suka ji kashina ya bushe gara na tafi sawuna a likafa tun Audullahi bai yanke hukunci ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyi ya ce, "Zainabu meye mafita?" Mommy kamar dama jira take ta ce, "Mafita dole ka nemo malaman Islamic chemist ɗin da baka son a kira su zo su yi mata ruƙiyya." Inno ta hangame baki tana tafa hannuwa ta ce, "Kai ni dai wallahi Ƙasimu ya nakasa min rayuwa da ya ɗoraka a turbar rayuwar masu jajayen kunne. Kai dai Audullahi da kasan taimakon da malamai suka yi maka kana ƙarami da baka guje su ba, wallahi ko labarin ƙarzuwarka na baka ya isheka ishara, a bar batun fitsarin kwance da sannu Allah sannu Ma'aiki da yaya muka samu ka daina, ka san irin tashin hankalin da na shiga lokacin da na ji za ka yi aure, na ce na ga ta kaina yaro ya zo yana fitsarin kwance mace ta raina shi. A'a wannan lamarin ba na aikin likitoci ba ne, ko rashin haihuwar matarka Allah ya sani ina zargin sheɗanu sun murƙushe maka ƙwayoyin hallita, don kar na yi shisshigi shi ya sa na saka muku ido amma da tuni na kira Ɗan wanzam har gidan nan zai zo shi da Kawunsa Malam mai farin allo sun baku magani." Daddy tuni ya gama ƙosawa da maganar Inno, tun bai ƙarasa jin abin da take faɗa ba ya miƙe yana faɗin, "Yanzu bari na kira Alhaji Munniru na ji a ina zan samu wurin da za a karɓo mata magani..." "Ba sai ka kira kowa ba, ga mu ga Waraka Islamic chemist a titin sharaɗa, kai tsaye ɗaukan yarinyar nan za mu yi mu wuce da ita, da zafi-zafi kan daki ƙarfe." Mommy ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Inno ta yi fiƙi-fiƙi da ido cike da firgice ta ce, "Billahillazi idan kun ga ba mu biku wurin nan ba Allah ya watsa mana albarka, haka kawai ku fice ku bar mu aljanu su dawo su casa hatsi a kanmu?" Mommy da yake neman mafita take bata jira cewarsu ba ta ce, "Shi kenan duk yadda kuka ce haka za a yi." Daddy da kansa ya tunkari ƙofar ɗakin Raihan sai dai lokaci ɗaya ya ji wani irin tsoro ya ɗarsu a zuciyarsa, yana daga tsaye ya fara jin wani irin gurnani kamar gurnanin zaki. Da sauri ya yi baya yana kallonsu Mommy a tsorace, Mommy na shirin yin magana ya ce, "Wallahi ji nake kamar ciwonta ya tashi gurnanin wani abin nake ji." Inno tuni cikinta ya kaɗa, ta maƙale a bayan Goggo tana leƙe. Mommy ita kanta hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, a hankali ta yi ta maza bakinta ɗauke da addu'a ta kalli Daddy ta ce, "Babu abin da ya gagari ubangiji, mu yi addua mu shiga ɗakin." Da sauri Daddy ya fara motsa baki yana biya ayatulkursiyyu yana tura ƙofar Raihan ta yi kuka kura ta faɗo kansu cikin wani irin gurnani mai tafe haushi kamar haushin kare. Idanunta a kakkafe suke kanta ya hargitse ga faratanta tuni suka fara sauya launi. Kafin su farga tuni ta fisgi hannun Daddy ta shige da shi ɗaki, ganin haka ya sa Daddy razana ya manta da addu'ar da yake yi ya fara ihu yana neman taimako. Yagarsa ta fara yi ta ko'ina da faratanta tana ƙoƙarin kai bakinta jikinsa Allah ya bashi sa'a ya hamɓareta ya doka ƙofar banɗaki ya shige ciki yana sauke ajiyar zuciya. Sai dai gabaɗaya ya gama tsinkewa lamarin don yadda ya ji tana bugun ƙofar tamkar za ta ɓalleta, a haukace ta juyo wurin ƙofa don mommy na wurin tana ihun kiran Daddy tana ganin Raihan ta yo kanta da gudu ta yi gaba cikin tashin hankali, Su Inno da goggo da rarrafe suka fice daga falon ban da ɗankwalaye da zannuwansu babu abin da suka bari a wuri. Da ƙyar Mommy ta samu ta fice daga falon tana fita harabar gidan ta ja ƙofar ta rufe da ƙarfi amma dukda haka sai da Raihan ta yage bayan Mommy da faratanta. Kabiru na kwance a ɗakinsa ya ji shigowarsu Inno ganin yanayin da suke ciki ya sa ya duburburci yana faɗin, "Hai Inno lafiya kuwa?" Goggo ta yi karaf ta ce, "Kai Kabiru buɗe mana ƙofa maza Albasu za ni." Kabiru ya dubi su Inno daga su sai ɗan fatarinsun zai yi magana ya ji ihun Mommy da sauri ya fito yana tambayarta, hankali a tashe mommy ta shiga nuna masa gidan tana faɗin, "Wallahi ciwon Raihan ne ya tashi Daddy na ciki ina tsoron kar ta yi masa illah." Cikin Kabiru ne ya kaɗa a tsorace ya ce, "Hajiya ya za mu yi ga Goggo ta ce Albasu za ta tafi." Mommy da hawaye ya gama jiƙe mata fuska ta ce, "Don Allah bar batun Albasun nan, wuce ka je Waraka a nan titin sharaɗa islamic chemist ɗin yake don Allah ka kira mana malamin." Kabiru ya yi jim ganin kamar ba gane abin da yake nufi ba, Mommy na hango hijabinta a kan igiya da aka yi wanki ta fisgo shi da sauri ta saka tana faɗin, "Kabiru ka kula da su Inno karka bari su fita." Tana gama maganar ta fice da gudu, Inno na shirin bin ta Kabiru ya sha gabanta ya datse ƙofar da ɗan mukulli ya cire ya koma ɗaki. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 16 Hankalin Daddy ba ƙaramin tashi ya sake yi ba ganin irin yadda Inno ta fara fita hayyacinta, a hargitse ya dubi mommy yana faɗin, "Zainabu me yake faruwa da Inno ne ko faɗuwa ta yi?" Mommy da ita ma ta fara fita hayyacinta ta nuna hanyar da Mar'usa ta bi tana faɗin, "Wallahi ba mutum bace." A daidai lokacin Goggo ta taho ta hanyar tana tafe tana faɗin, "Haka kawai kai ba arne ba kai ba baka haɗa iri da mai jan kunne ba ace gida kullin abu ɗaya, ina dalili ace koyaushe sai dai mu kalli ƙasashen turawa. Wallahi da sake, wannan tsohuwar ta bar ganin ita ta haifi Audullahi ni ma ina da iko da gidan tun da ai Ƴata yake aure, haka kawai wa ya sani ko zaginmu suke da yarensu ba mu sani ba. A'a raba ni da wannan lamarin ko a riƙa kunna min sangaya ko kuma na ɗauki ƙullin kayana na wuce Albasu, yoooo me gare su da babu a Albasu? Allah na tuba waccen tukunyar sanyin ce kaɗai ba ni da ita, tun kafin marigayi ya rasu ya ajiye mini talabijin na kalli sangaya na kalli Jan kunne. Ita ma tukunyar sanyaya ɗaki zan shiga adashin So dangi na haɗa da ƴan samiruna na bawa Zainbu ta cika ta saya min, zaman gidan siriki ko tashin hankali. Allah ya sani daga nan babu in da zan tsaya sai Albasu, abu ɗaya zan tsaya jira Audullahi ya haɗa min tsaraba na kaiwa su Rahila idan ba haka ba kullin suna liƙe da ni, su cika min ɗaki da tsamin kai da na hammata..." Bata kai ƙarshen maganarta ba ta ga Mommy na nuno wurin da take tana faɗin, "Da gaske ba mutum bace yaudararmu take yi aljana." Daddy na ɗaga kai ya yi tozali da Goggo, karaf maganganun mommy suka sauka a kunnen Goggo. Baki a sake ta ƙarasa wurin tana tafa hannuwa, Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Ni kam Zainabu kanki bai fara taɓuwa ba kuwa? Taimaka min mu kai Inno asibiti." Inno da take jin maganganun Daddy sama-sama nan take ta tuno irin jijjigawar da Huzaifa ya yi musu cikin siffar Likita nan take ta sake ruɗewa ta ce, "Ina Alhaji Babba?" Da mamaki Daddy ya ce, "Alhaji Babba kuma Inno." Alhaji Babba Mahaifin Daddy ne ya rasu kusan sama da shekara talatin baya. Inno bata san ma Daddy yana yi ba balle ta fahimci tambayarsa, ta sake wawuro hannun Mommy tana cewa, "Alhaji Babba ka riƙe hannuna ka shafa min ƙofar aljannah. Idan mun shiga karka bi da ni ta hanyar masu kofato a ƙafa." Daddy ya sake duban Mommy ya ce, "Wai me yake faruwa?" Mommy na shirin yin magana Goggo ta yi caraf ta karɓe maganar da cewa, "Yooo ka nemi ba'asi Audullah bayan matarka ta gama kwayewa uwarta baya, yanzu Zainabu ni kika maida sheɗaniya wacce ta fito daga jinsin aljanu?" Goggo na faɗin haka ta rushe da matsanancin kuka, ta sa gefen rigarta ta share hawaye sannan ta ɗora da cewa, "Don Allah Audullahi idan Allah ya tsine min za ta bi ni ko ba za ta bini ba?" Daddy da kansa ya ɗaure ya dafa kansa da hannuwa biyu ya ce, "Goggo me ya yi zafi haka?" Goggo ta nuna Mommy ta ce, "Ba ka ji irin tozarcin da matarka ta yi min ba? Na rantse da Allah idan wani ya taɓa maida ni jinsin Aljanu Allah ya watsa min albarka, amma tun da haka ne zan bar muku gidanku na ƙare rayuwata a Albasu ko mutuwa na yi idan ba a kai gawata can ba ban yafe ba." Mommy ta zauna zaman dirshan ta ce, "Goggo ni fa ba manufa ta kenan ba, wallahi uwani ba mutum bace aljana ce yanzu haka abin da muka gani kenan muka firgita ni da Inno..." Gabaɗaya Mommy ta zayyana musu abin da yake faruwa, daga wurin da Goggo take ta yi tsalle ta dira a gadon bayan Daddy cikin kiɗima ƙwaƙumeshi tana faɗin, "Wattaba'u matattulisshayaɗina Alamulki Sulaiman, don Allah Audullahi ka dubi girman Allah ka mayar da ni Albasu ko mayu bamu da su balle Aljanu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Zainabu!" Ɗagowa ta yi tana kallonsa, bai bi ta kanta ba ya ci gaba da cewa: "Yanzu saboda Allah haka kawai za ki riƙa razana kanki, ki dubi tsofaffin nan suma kin razana su." Mommy takaicin duniya da ashirin ya kamata, babban baƙin cikinta da komai ta faɗa Daddy baya amincewa da ita sai dai yace ta cika tsoro. A zafafe ta dube shi don wannan karon zuciyarta ta bushe ta ce, "Na ga ji da yadda idanunka suke rufe wa akan abubuwa da dama, ba tun yau ba nake zargin jinnu sun samu gurbin zama a jikin Raihan amma kullin cikin ƙaryata ni kake yi, me kake ɗauke ne? Kana tunanin duk duniya akwai wanda zai zo Raihan kamar irin soyayyar.da nake mata. Karka manta cikinta na ɗauka wata tara tun tana ƙwayar hallita har zama cikakkiyar mutum, ka san yadda laulayi yake kuwa? Ka san yadda nake son cin wannan ba na son wanna? Idan na ci na yi amai da ƙyar zan samu wani ya zauna. Lokacin da cikina ya tsufa ka san irin nauyin da Ɗa yake da shi a cikin mahaifa? Tun da cikina ya fara girma na daina kwanciyar rigingine sai gefe da gefe kasan irin wahalar da nake sha idan na zauna zan tashi. Tun lokacin da na fara naƙuda ka san irin raɗaɗi da zafin ciwon naƙuda kuwa? Ban raina abubuwan da kake yi min ba na kulawa duk macen da ta samu kamarka ta yi dace amma duk kulawar da kake ba ni; ni kaɗai na san irin abin da nake ji a jikina, shin ka san yadda ratsowar kan ɗa yake daga jikin Mahaifiya kuwa? Na shafe tsawon wata tara ina rainon cikinta, duk wani yanayi da nake ciki tana fuskata na farinciki ko baƙinciki, hatta sautin muryata ta tantance kalarta shin tana samun waɗannan abubuwan daga gare ka? Ka gaya min akwai shaƙuwar da za ta wuce tsakanin ta Ɗa da mahaifiya? Ka ga ya min akwai wanda zai nuna mata soyayya fiye da wacce zan nuna mata? Kana tunanih za ka fini ƙaunarta?" Mommy ta ƙarasa yi wa Daddy tambaya tana tsare shi da ido babu alamar tsoro a tattare da ita. Shiru ya yi yana nazarin maganganunta, Mommy bata damu da haka ba ta ci gaba da cewa, "Duk wannan gatan da kake nuna mata sam ba soyayya ba ce, kuma ba zan taɓa alaƙanta Raihan da ciwon jinnu ba kawai don son raina ba. Uwani da muka shafe tsawon shekaru da ita ba mutum ba ce ƙaton aljani ne da ya shiga jikin Ƴarka Raihan, ɗazun nan muka fahimci haka ni da Inno idan kuma kana musu wataƙila idan ta gaya maka za ka ɗauki abin da muhimmanci, idan kana tantama ka duba cikin gidan nan kaf idan za ka sake ganinta." A wannan karon hankalin Daddy ya fi na koyaushe tashi, jikinsa har rawa yake ya dubi Inno da hargagin Mommy ya dawo da ita cikin nutsuwarta yana shirin yin magana Inno ta ce, "Audullahi!" Daddy ya amsa mata murya a sanyaye Inno ta ci gaba da cewa, "Idan baka haɗa ni da Zinaru ta kaini albasu ba Alhaji Babba ya dawo duniya. Ganin idona na ga Uwani da Kofato har tana gaya mana ita ba mutum ba ce yau mai hanani tafiya Albasu sai Allah." Goggo na maƙale a bayan Daddy ba tare da ta fahimci a wurin wa take ba, tana miƙa hannu ta shafo gemun Daddy a zabure ta leƙa fuskarsa tana faɗin, "Yau na shiga aljanna na kasa fitowa yau ni ce maƙale a bayan Audullahi, astagafirullah Allah ka yafe min me ya kaini bayan siriki ana zaune ƙalau?" Goggo ta ƙarasa maganar tana zazzage ɗankwali sai da ta ɗaura shi akanta ta ce, "Me zan zauna na ci gaba da yi a gidan nan ban da abin kunya, wannan Idan ƴan Albasu suka ji kashina ya bushe gara na tafi sawuna a likafa tun Audullahi bai yanke hukunci ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyi ya ce, "Zainabu meye mafita?" Mommy kamar dama jira take ta ce, "Mafita dole ka nemo malaman Islamic chemist ɗin da baka son a kira su zo su yi mata ruƙiyya." Inno ta hangame baki tana tafa hannuwa ta ce, "Kai ni dai wallahi Ƙasimu ya nakasa min rayuwa da ya ɗoraka a turbar rayuwar masu jajayen kunne. Kai dai Audullahi da kasan taimakon da malamai suka yi maka kana ƙarami da baka guje su ba, wallahi ko labarin ƙarzuwarka na baka ya isheka ishara, a bar batun fitsarin kwance da sannu Allah sannu Ma'aiki da yaya muka samu ka daina, ka san irin tashin hankalin da na shiga lokacin da na ji za ka yi aure, na ce na ga ta kaina yaro ya zo yana fitsarin kwance mace ta raina shi. A'a wannan lamarin ba na aikin likitoci ba ne, ko rashin haihuwar matarka Allah ya sani ina zargin sheɗanu sun murƙushe maka ƙwayoyin hallita, don kar na yi shisshigi shi ya sa na saka muku ido amma da tuni na kira Ɗan wanzam har gidan nan zai zo shi da Kawunsa Malam mai farin allo sun baku magani." Daddy tuni ya gama ƙosawa da maganar Inno, tun bai ƙarasa jin abin da take faɗa ba ya miƙe yana faɗin, "Yanzu bari na kira Alhaji Munniru na ji a ina zan samu wurin da za a karɓo mata magani..." "Ba sai ka kira kowa ba, ga mu ga Waraka Islamic chemist a titin sharaɗa, kai tsaye ɗaukan yarinyar nan za mu yi mu wuce da ita, da zafi-zafi kan daki ƙarfe." Mommy ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Inno ta yi fiƙi-fiƙi da ido cike da firgice ta ce, "Billahillazi idan kun ga ba mu biku wurin nan ba Allah ya watsa mana albarka, haka kawai ku fice ku bar mu aljanu su dawo su casa hatsi a kanmu?" Mommy da yake neman mafita take bata jira cewarsu ba ta ce, "Shi kenan duk yadda kuka ce haka za a yi." Daddy da kansa ya tunkari ƙofar ɗakin Raihan sai dai lokaci ɗaya ya ji wani irin tsoro ya ɗarsu a zuciyarsa, yana daga tsaye ya fara jin wani irin gurnani kamar gurnanin zaki. Da sauri ya yi baya yana kallonsu Mommy a tsorace, Mommy na shirin yin magana ya ce, "Wallahi ji nake kamar ciwonta ya tashi gurnanin wani abin nake ji." Inno tuni cikinta ya kaɗa, ta maƙale a bayan Goggo tana leƙe. Mommy ita kanta hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, a hankali ta yi ta maza bakinta ɗauke da addu'a ta kalli Daddy ta ce, "Babu abin da ya gagari ubangiji, mu yi addua mu shiga ɗakin." Da sauri Daddy ya fara motsa baki yana biya ayatulkursiyyu yana tura ƙofar Raihan ta yi kuka kura ta faɗo kansu cikin wani irin gurnani mai tafe haushi kamar haushin kare. Idanunta a kakkafe suke kanta ya hargitse ga faratanta tuni suka fara sauya launi. Kafin su farga tuni ta fisgi hannun Daddy ta shige da shi ɗaki, ganin haka ya sa Daddy razana ya manta da addu'ar da yake yi ya fara ihu yana neman taimako. Yagarsa ta fara yi ta ko'ina da faratanta tana ƙoƙarin kai bakinta jikinsa Allah ya bashi sa'a ya hamɓareta ya doka ƙofar banɗaki ya shige ciki yana sauke ajiyar zuciya. Sai dai gabaɗaya ya gama tsinkewa lamarin don yadda ya ji tana bugun ƙofar tamkar za ta ɓalleta, a haukace ta juyo wurin ƙofa don mommy na wurin tana ihun kiran Daddy tana ganin Raihan ta yo kanta da gudu ta yi gaba cikin tashin hankali, Su Inno da goggo da rarrafe suka fice daga falon ban da ɗankwalaye da zannuwansu babu abin da suka bari a wuri. Da ƙyar Mommy ta samu ta fice daga falon tana fita harabar gidan ta ja ƙofar ta rufe da ƙarfi amma dukda haka sai da Raihan ta yage bayan Mommy da faratanta. Kabiru na kwance a ɗakinsa ya ji shigowarsu Inno ganin yanayin da suke ciki ya sa ya duburburci yana faɗin, "Hai Inno lafiya kuwa?" Goggo ta yi karaf ta ce, "Kai Kabiru buɗe mana ƙofa maza Albasu za ni." Kabiru ya dubi su Inno daga su sai ɗan fatarinsun zai yi magana ya ji ihun Mommy da sauri ya fito yana tambayarta, hankali a tashe mommy ta shiga nuna masa gidan tana faɗin, "Wallahi ciwon Raihan ne ya tashi Daddy na ciki ina tsoron kar ta yi masa illah." Cikin Kabiru ne ya kaɗa a tsorace ya ce, "Hajiya ya za mu yi ga Goggo ta ce Albasu za ta tafi." Mommy da hawaye ya gama jiƙe mata fuska ta ce, "Don Allah bar batun Albasun nan, wuce ka je Waraka a nan titin sharaɗa islamic chemist ɗin yake don Allah ka kira mana malamin." Kabiru ya yi jim ganin kamar ba gane abin da yake nufi ba, Mommy na hango hijabinta a kan igiya da aka yi wanki ta fisgo shi da sauri ta saka tana faɗin, "Kabiru ka kula da su Inno karka bari su fita." Tana gama maganar ta fice da gudu, Inno na shirin bin ta Kabiru ya sha gabanta ya datse ƙofar da ɗan mukulli ya cire ya koma ɗaki. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 17 Inno sai da ta kalli hagu da dama ta ga babu kowa a harabar gidan daga ita sai Goggo sai kawai ta faɗa ɗakin Kabiru tana faɗin, "Kai yaro idan kana neman albarka ka buɗe mana gida mu fice." Kabiru ya kauda kansa gefe ya ce, "Inno ko ba a ce karna barku ku fita ba ai bana barku ku fita a haka ba, ku dubi kayan jikinku fa. Gaskiya bari na miƙo muku zannuwan Hajiya ku ɗaura, don zamanku haka bai kamata ba." Goggo ta ja dogon tsaki ta ce, "Kai muna maganar zuwa Albasu kai kana cewa a ba mu zani, shi aljani ina ruwansa da ɗaura zani." Inno da ta gama zuwa wuya ta ce, "Kai Kabiru kake ko wa? Yau da idanunan nawa na ga aljana ko tsirara ka gammu ba za ka yi mamaki ba." Da sauri Kabiru ya ƙunshe baki yana faɗin, "A'uzubillahi gara dai da kuke cikin sitira." Yana gama maganar ya miƙe ya fice ya ɗaukowa su Inno zannuwa suka ɗaura, suka yi jugun-jugun sai dai kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin tashin hankali. Mommy ban da sauri babu abin da take yi kamar za ta tashi sama, duk wanda ya ga irin saurin da take yi sai tabbatar da tana cikin halin damuwa. Tana zuwa bakin titi ta fara taron adaidaita sahu don ko kaɗan bata yi tunanin ɗaukan mota ta fito da ita ba, sai da ta tsaida Adaidaita sahu sun fi uku babu wanda yake tsayawa saboda ganin irin yadda take yi musu magana a hargitse. Da ƙyar ta samu wani ya ɗauke ta tiryan-tiryan har Sharaɗa kwanar kasuwa a bakin Waraka Islamic chemist ya sauketa, ko waige mommy bata yi ba da ta sauka sai da ya ƙwalla mata kira tukunna ta waiga, da hannu ta nuna masa alamar ya jirata gata nan zuwa. Mommy tana shiga bakinta ɗauke da sallama ta dubi mutanen wurin tana tambayarsu, "Don Allah ina Malam yake?" Wata mata sanye da hijabi har ƙasa ta ce, "Hajiya lafiya?" Mommy ta ce Malam nake nema yarinyata ce babu lafiya." Matar mai hijabin ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin ce don masu kalar hijabinta kusan su biyar ne a wurin da alama shi ne uniform ɗin su. Kan kujera matar ta nunawa Mommy ta ce, "Ki zauna yanzu Dr ya shigo bari a yi masa magana." Matar na gama magana ta wuce ciki. Bata jima ba ta dawo tama faɗin, "Za ki iya shiga." Tun matar bata rufe baki ba Mommy ta shiga office ɗin, tana shiga ta samu kan kujera ta zauna. A gaggauce mommy ta gaida Malam Usman, yana ganin yanayinta ya tabbatar da tana cikin damuwa. Duk abin da yake faruwa da Raihan da Mama Uwani sai da ta zayyane masa, ko kaɗan bai yi mamaki ba don wannan ba sabon abu bane a wurinsu kasancewar suna samun cases makamantan irin waɗannan har ma da waɗanda suka fi haka." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Tabbas ɗaukota a wannan halin da take ciki akwai babban hatsari sakamakon halin da take ciki. Amma zan haɗa ki da ɗaya daga cikin ma'aikatanmu..." Da sauri mommy ta haɗa hannuwa biyu tana faɗin, "Don Allah Malam ka taho mu tafi tare." Murmushi Malam Usman ya yi ya ce, "Hajiya don Allah ki kwantar da hankalinki wannan fa ba wani babban lamari ba ne a wurinmu, ina nufin zan haɗa ki da Malama Nafisa ku tafi zan shiga motata sai na riƙa bin ku a baya." Cikin gamsuwa da maganar Malam Usma Mommy ta miƙe tsaye tana faɗin, "To Malam Allah saka da alheri." Mommy na fitowa Malam Usman na biye da ita nan take ya sanarwa da Malama Nafisa abin da yake tafe da Mommy, Adaidaita sahun da Mommy ta zo a shi suka tafi da ita, motar Malam na biye da su tiryan-tiryan har suka ƙarasa ƙofar gidan Daddy. A kunyace Mommy kalli mai adaidaita sahun ta ce, "Don Allah bari na shiga na ɗauko ma kuɗin." Ganin abin da yake faruwa ya sa Mai ɗan sahun bai damu ba, don ya san lalura bata wuce kan kowa ba. Da ƙarfi mommya ta riƙa bugun ƙofar babu jimawa Kabiru ya buɗe mata, a gaggauce ta karɓi rancen dubu biyu a wurinsa tana miƙawa mai ɗan sahun ta juya suka shiga da Malam, Nafisa da Mommy. Su Goggo na harabar gidan sun yi carko-carko Goggo na ganin Malam Usman kamar ta sanshi ta rangaɗa kabbara tana ci gaba da cewa, "Ka ga Ulama'u magada Annabawa." Inno ta ƙarasa gabansa ido ɗauke da ƙwalla ta ce, "Yaro ko wata biyu ba a yi da mutuwa Ƴata Hasiya ba yanzu ga Audullahi yana can ina jin tuni Aljanu sun riga da sun jajjage namansa." Malam Usman ya kalli Inno lokaci ɗaya ya ji ta bashi tausayi, cikin tattausan lafazi ya ce: "Insha Allah babu abin da zai faru da shi sai alkairi, bari na shiga ciki." Malam Usman ya yi gaba Nafisa da Mommy na biye da shi, daga Inno har Goggo babu wacce ta motsa ƙafarta don ta shiga cikin gidan. Malam har ya je bakin ƙofar ya dubi Mommy ya ce, "Babu Famfo a kusa ina son na yi alwala." Da hannu Mommy ta nuna masa can gefe famfam da Kabiru yake amfani da shi. Sai da ya yi alwala sannan ya tunkari ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da addu'a, mommy na biye da shi amma ilahirin jikinta rawa yake tana tsoron abin da Raihan za ta aika da halin da Daddy yake ciki. Tsit cikin falon ya yi kamar babu kowa a ciki, Malam Usman ya kalli Mommy ya ce, "A ina yarinyar take?" Mommy ta fara waige-waige ta ce, "Ga dai ɗakinta can, amma lokacin da ta biyo mu a falon nan na barta." Jinjina kai Malam ya yi yana faɗin, "Za ki iya duba mana cikin sauran ɗakunan don mu san a wanne take?" Da sauri Mommy ta ce, "A'a Malam don Allah ka duba da kanka." Lokacin da Raihan ta koma cikin ɗakinta wurin da Daddy yake ta tunkara a haukace tana faɗin, "Duk wanda ya nemi raba ni da matata sai na hallaka shi, Raihan matata ce mallakina ce babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da ita." Ilahirin jikin Daddy ban da rawa babu abin da yake yi, ga jinin da yake zuba daga jikinsa na ciwon da ta ji masa ga gumi tuni ya haɗu ya yi sharkaf, ya gama saddaƙar da rayuwarsa don gani yake tashi ta ƙare a kowanne lokaci Raihan za ta iya cimmasa, tun yana kukan zuci har ya fito fili ya fara kuka da hawaye shaɓe-shaɓe. Yana daga cikin banɗaki ya ji muryar mommy da Malam Usman suna magana, da ƙarfi ya ware murya yana faɗin, "Zainabu ku kawo mun ɗauki ina cikin banɗaki." Jin haka ya sa Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Malam ga Mahaifinta can yana ɗakinta." Da sauri Malam Usman ya nufi hanyar ɗakin sauna zuwa kai tsaye banɗaki suka ƙarasa Mommy ta ce, "Daddyn Raihan buɗe mu ne." Daddy da sauri ya amsa, "Zainabu kin tabbata ku ne kar na buɗe ta hallaka ni." Dariya ce ta so ƙwacewa Malama Nafisa, mommy ta ce, "Mu ne Daddyn Raihan tare muke da Malam." Daddy ya buɗe ƙofar yana zuro kai a hankali, sai da ya tabbatar da su Mommy ne sannan ya buɗe ƙofa. Yana fitowa Raihan ta shiga ɗakin a bakin ƙofa ta tsaya ta riƙe ƙugu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, da sauri Daddy ya juya zai sake faɗawa banɗaki Malam Usman ya fara takawa gaban Raihan, ko motsi Raihan bata yi ba cikib wata irin fusatacciyar murya ta fara magana. "Malam babu ruwanka da ni, karka shiga hurumin da ba naka na, wallahi ba zan rabu da ita ba saboda matata ce na aureta halak-malak na biya sadakinta me ya yi saura." Malam Usman ya matsa gaban Raihan yana faɗin, "A ina ka taɓa jin aljani ya auri bil'adam? Nan ba wurin zamanka ba ne tun wuri ka kama gabanka." Raihan ta fara takowa cikin isa da ƙasaita ta ce, "Malam Ina ganin mutumcinka tun wuri ka kama gabanka don ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zan fita daga jikinta ba. Ni Huzafa na auri Raihan sama da shekara goma sha ta haifa min ƴaƴa, na santa farin sani na yi mu'amala da ita har ta fi matata ta jinsina gamsar da ni. Na shafe tsahon shekaru ina rainon abata, yanzu haka ina hanyata ta zuwa neman warakarta Mar'usa ta sanar da ni halin da ake ciki, kana ganin duk wannan wahalar da na yi za ta tashi a banza ne? Mahaifinta shi ya damƙamin ita shi da kansa ya bani aurenta akan me rana tsaka za ka zo ka nemi raba ni da matata." Lokaci ɗaya jikin Daddy ya hau tsuma baki na rawa ya furta, "Ni...Kuma? Yaushe na sanka da har na baka auren Raihan?" A zabure Raihan ta nuno Daddy tana cewa, "Ƙarya kake munafuki ni za ka ƙaryata a gaban jama'a? Na fi ƙarfin ka ƙaryata ni kuma ina ɗaga maka ƙafa ne saboda kana nunawa matata kulawa, baka cika saka mata ido ba kamar mahaifiyarta. Kun ga wannan." Raihan ta nuna Mommy sannan ta ci gaba da cewa, "Ta yi bala'in saka min ido kuma ba tun yau na so halakata ba don dai tana da yawan ibada, ta matsawa Matata Raihan kuma ga shi ita ce sanadiyyar bankaɗo sirrina." Malam Usman ya jinjina kai ya kallai Raihan ya ce, "Ba na son ƙarya don na san akwai maƙaryata da yawa a cikinku, ya aka yi Mahaifinta ya baka aurenta kana tunanin akwai uban da zai damƙa auren ƴarsa a hannun aljani ne?" Tuno idanun Mommy suka kawo ruwa ta kalli Daddy cikin kuka ta ce, "Dama ashe soyayyar da kake yi wa Raihan bata kai zuci ba, wanne abu kake aikawata a ɓoye da har za ka damƙawa aljani auren ƴata?" Daddy zai yi magana Malam Usman ya dakatar da shi da cewar, "Huzaifa kake ko wa? Na ji sunanka da alama kai musulmi ne to da farko zan haɗa ka da girman Allah ka fice daga jikin yarinyar nan ko za ka samu salama a wurina, matuƙar ka nuna min taurin kai sai na ƙoneka ƙurmus." Raihan ta koma jikin bango ta zauna sannan ta ce, "Malam ka bar haɗa ni da musulunci don ni ba Musulmi ba ne, ba don kar in watsawa Mahaifiyata ƙasa a ido ba da sai na ce hanyar da musulunci take ban biyota ba. Mahaifiyata da danginta Musulmai ne, mahaifina da danginsa duka kafirai ne. Zan yi maka magana ta ƙarshe, ba zan taɓa fita daga jikin Raihan ba, duk abin da za ka min sai dai ka yi amma zama a jikinta yanzu na fara domin yanzu ta zama cikakkiyar budurwa, na raineta tun bata zama wani abu ba sai da na fara ɗanɗana zumarta za ka ce na fita? Ɗan da muka haifa waye zai ci gaba da shayar da shi?" Malam Usman ya jinjina kai a fili ya ce, "Tabbas za mu kai ruwa rana da shi domin wannan yana cikin masu taurin kai." Nan take Malam Usman ya yi A'uziyya ya fara karanta surartul Baƙara, Malam Ya jima yana karatu amma Huzaifa ya yi shiru sai da ya ji azaba ta ishe shi ya ƙwalla wata irin razananniyar ƙara. Inno na daga ƙofar ɗakin Kabiru ya saki dariyar farinciki ta ce, "Allah mai mutane da yawa, kai jama'a Allah na dawo Zinaru kin ji yadda Malam yake fata-fata da aljanin nan da ayar Allah?" Goggo ta sake baza kunne sannan ta ce, "Wuya mai sa Waziri shiga wandon Sarki ki ce da na tafi Albasu da na bar kallo." Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624 18 Kabiru yana daga ɗaki yana jin su Inno da har ya yi niyyar ya yi musu shiru sai ya ziro da kai yana faɗin, "Inno kar dai ku manta da ambaton Allah, don idan kuka yi sake ana cirewa daga jikinta za su iya faɗowa kanku." Inno tuni ta yi wuri-wuri ta ɗebi salati tana watsa wa Kabiru daƙuwa haɗe da cewa, "Gidanku ka ji ɗan nan, yoo ni me aljani zai yi da ni fata ta saki gijibgi duk ya sauko, kwarankwatsa ko da ina budurwa sai dai ya ganni ya ƙyale?" Goggo ta kalli Inno ta ce, "A'a bar faɗin haka wallahi tsaf za ki yi kyau da su ke dai mu roƙi Allah ya raba mu da su amma Aljanu suka haye mu na san Audullahi tarkata mu zai yi ya wuce Albasu da mu." Inno kamar mai nazari haka ta yi jigum cikin tsiro don har lokacin bata daina hango kammanin kofaton Mama Uwani a ƙafarta ba. Malam Usman karatu ya ci gaba da yi babu ƙyaƙƙyautawa don ya san dama sai ya ɓullo masa ta haka za a samu mafita, sai da ya lura da Huzaifa ya yi lugub sannan ya sarara da karatun yana tambayarsa, "Za ka fita daga jikinta ko ba za ka fita ba?" A wahalce Raihan ta ɗago da kai dana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Malam ka dakata mu yi magana da kai ta fahimta don Allah ka daina ƙonani." Malam Usman ya zauna a kan kujerar ɗakin Raihan ya ce, "Babu wata magana ta masala da za mu yi da kai da ta wuce ka amince da abin da na umarceka." Raihan ta gyara zamanta sannan ta ƙurawa Malam Usman ido cikin rashin tsoro ta ce, "Malam ka faɗi wata buƙatar taka amma ba wannan ba, don ba zan taɓa rabuwa da ita ba saboda ita ɗin mallakina ce ban taɓa ƙaunar wata hallita kamar yadda nake ƙaunarta ba. Zan iya fansar da dangina tas akan ta, amma ka daina furta kalmar rabuwa a tsakaninmu." Malam Usman kalli Malama Nafisa ya ce, "Ba ni ruwan Addu'ar nan da garin maganin nan mai haɗe da habbatais sauda." Nan take Malama Nafisa ta ciro abubuwan da Malam ya buƙata a cikin wata jaka mai ɗauke da tambarin Waraka Islamic Chemist. Malam Usman yana karɓa ya ƙarasa gaban Raihan ya yi bismillah ya fara yayyafa mata, ya miƙawa Malama Nafisa garin maganin ya ce, "Ki tabbatar da ta shaƙi wannan garin maganin." Malama Nafisa ta tunkari Raihan tana tafe tana addua, ganin ta tunkarota ya sa Raihan ta yo kanta suka fara kokawa da ƙyar ta samu ta shaƙa mata maganin. Raihan na shaƙa ta fara sakin atishawa cikin fitar hayyaci, Malam Usman ya ƙarasa kanta ya fara yayyafa mata ruwa yana ci gaba da karatu, azaba goma da ashirin ce ta sa Huzaifa a gaba. Ban da ihunsa babu abin da yake tashi a cikin ɗakin, Daddy da Mommy suna gefe suna kallon ikon Allah. Lokaci-lokaci Mommy take wurgawa Daddy mugun kallo don har lokacin maganar Huzaifa ta tsaye mata a rai da yace Daddy ne ya bashi auren Raihan. Daddy duk jikinsa ya yi sanyi duk ya yi zuru-zuru kamar wanda yake bakin bindiga, suna cikin wannan halin suka riski muryar Huzaifa yana cewa, "Dakata! Dataka Malam zan fita." Malam Usman ya tsagaita da karatun ya ce, "Za ka fita ta ina?" Huzaifa ya sauke numfashi ya ce, "Zan fita amma sai ta gama shayar min da jaririn ɗana." Ran Malam Usman ya yi mummunan ɓaci ba ɓata lokaci ya ci gaba da karatu duk yadda Huzaifa ya kaiga roƙon Malam bai saurara masa. Yana cikin karatun ya ji wata murya ta canji ta Huzaifa da yin sallama, "Assalamu alaikum." Malam Usman ya koma ya zauna sannan ya amsa, "Wa'alaikas salam da wa nake magana." Cikin nutsuwa dattijuwar ta ci gaba da cewa, "Kana magana da Malama Fatima, ni ce mahaifiyar Huzaifa." Malam Usman ya ce, "Malama Fatima me ya sa za ki katse min aikina ina shirrin hallaka ɗanki Huzaifa." Kafin mu ji amsar Mahaifiyar Huzaif mu koma waiwaye don jin Tarihin su waye Mommy da Daddy🥱 WAIWAYE... Alhaji Abdullahi Muhammad Zango shi ne ainihin cikakken sunan Daddy, Mahaifinsa Marigayi Muhammad Zango asalinsu mutanen Daura ne cikin unguwar Zangon Daura. Su uku ne rak a wurin Mahaifinsu da mahaifiyarsu Alhajia Al'ƙasim shi ne babba, Marigayi Alhaji Haruna mai binsa sai Alhaji Muhammad Zango ɗan autansu wato Mahaifin Daddy. Ana kiransa da Alhaji babba sakamakon cin sunan kakansa na wurin Mahaifiya da ya yi, Mahaifinsu Marigayi Alhaji Babba riƙaƙƙen ɗan boko ne ya karanci fannin Law. Don haka Mahaifinsu Daddy gabaɗaya sun yi karatun boko mai zurfi, kuma dukkansu suna da rufin asiri. Alhaji Babba sun taso cikin gata da rufin asiri kasancewar Mahaifinsu yana haɗawa da harkar kasuwanci yana da rufin asiri sosai, Alhaji Ƙasim shi ya fara yin aure yana koyarwa a babbar jami'ar Sokoto sai da ya shekara bakwai da aure ƴaƴansa biyu sannan mai binsa Haruna ya yi aure, shi kuma yana aiki a ƙarƙashin hukumar kare hatsarirrika da ababen hawa (Road safety.) Bayan ya yi aure da wata biyar Mahaifin Daddy ya kammala bautar ƙasa shekara na zagayowa ya samu aiki a babban asibitin Katsina da yake fannin likitanci ya karanta. Rayuwarsu sun taso gwanin birgewa tare da haɗin kai a tsakaninsu, suna matuƙar mutumta junansu don haka akwai kyakkyawar alaƙa da soyayyar ƴan uwantaka a tsakaninsu. Mahaifin Daddy shekararsa uku da fara aiki ya haɗu da Inno, a lokacin ankwantar da Mahaifiyarta a asibitin da yake aiki bayan sallamar Mahaifiyarta Alhaji Babba har garinsu Inno ya je, Inno Bafulatanar ƙauyen Madaka ce bata yi karatun boko ba, sai dai ta yi makarantar allo da makarantar dare. Ita kaɗai iyayenta suka haifa gaba da baya, da sassafe suke fita kiwon shanu sai yamma ta doso sannan suke dawowa su huta su ci abinci wurin ƙarfe huɗu su tafi makarantar allo. Idan dare ya yi bayan magariba su tafi makarantar dare, da farko ƴan uwan Alhaji babba ba su so auren Inno da shi ba don a ganinsu me zai yi da ƴar ƙauyen da ko cikakkiyar hausa bata ji. Amma da suka ga yana so a kan dole suka yi masa addu'a da fatan alheri, kuma cikin lokaci ƙanƙani maganar aurensu ta kankama aka tsaida lokaci aka sha biki. Bayan biki Alhaji babba ya ɗauki matarsa ya tafi da ita cikin garin katsina ya yin da yake ziyartar ƴan uwansa lokaci-lokaci, dama kuma tun kafin aurensa da Inno ma haka yake yi. An yi auren Inno da Alhaji babba da wata biyar Allah ya yi wa mahaifiyar su Alhaji babba rasuwa, wannan rashi ba ƙaramin taɓa su ya yi ba. Ana nan har Allah ya bawa Inno ciki sai dai cikin ikon Allah ta riƙa haihuwa suna mutuwa har sai da suka fidda rai da samun rayayyan ɗa. Kusan shekara goma da aurensu sannan Allah ya bawa Inno cikin Daddy a lokacinma ba su taɓa tsammanin zai rayuwa ba, amma cikin ikon Allah ya ɗore. Bayan haihuwarsa da shekara biyu Inno ta sake samun cikin Mama Hasiya bayan wata tara ta haifeta sai dai daga kansu bata sake samun haihuwa ba. A haka rayuwa ta ci gaba da gangara musu suka ci gaba da rainon ƴaƴansu cikin birgewa, kwatsam watarana aka wayi gari da rasuwar Mahaifiyar Inno ko kwana arba'in ba a yi ba shi ma mahaifinsu Alhaji Babba ya ce ga garinku nan. Wannan mutuwa ba ƙaramin girgiza su ta yi ba don kusan duka mamatan mutuwar faraɗ ɗaya suka yi. Mahaifinsu Alhaji babba ya rasu babu jimawa Alhaji Ƙasimu ya samu ci gaba ya yin da ya samu koyarwa a wata babbar jami'a da ke ƙasar Ingila. Ƴan uwansa ba ƙaramin daɗin samun wannan ci gaban nasa suka yi ba, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya da daɗi babu daɗi har Daddy ya shekara goma sha biyu a duniya, ya yin da Hasiya take da shekara tara. Kwatsam wata rana Alhaji babba ya tafi Zangon daura yi wa Yayansa Alhaji Alƙasim barka da zuwa da yake ya zo hutu daga Ingila, a hanyarsa ta dawowa ya yi hatsari nan take ya rasu ko shurawa bai yi ba. Wannan mutuwa ta girgiza Inno saboda zaman lafiya suke yi ita da mijinta ba ƙaramin kulawa suke samu ita da ƴaƴanta a wurinsa ba, gawar Alhaji Babba zangon daura aka mayar da ita. Alhaji Ƙasim ya aika aka ɗauko Inno da yaranta, kowa ya ga halin da take ciki sai ya tausaya mata matuƙa. Lokaci ɗaya ta zabge ta rame ta lalace har wani irin baƙi ta yi ko ruwan kirki bata iya sha, wasu daga cikin mutane har sun fara tunanin Inno na da ƙaramin ciki a lokacin, sai daga baya kowa ya fahimci tsantsar damuwa ce. Bayan sadakar Bakwai aka tara su Inno a ɗaki tashin farko da Alhaji Ƙasim ya sanarwa da Inno zai ɗauke ƴaƴan ɗan uwansa, Daddy da Mama Hasiya zuwa ƙasar Ingila. Inno na jin haka ta rushe da kuka nan take mutuwar mai gidanta ta sake dawowa mata sabuwa, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce sam bata ƴarda ba. Sai da aka kai ruwa rana sannan Alhaji Ƙasim ya amince zai barwa Inno Hasiya, don acewarsa babu yadda za a yi ta tafi da ƴaƴan ƙaninsa ƙauye. Ita kuma a lokacin Mahaifinta ya ce sam ba za ta zauna ita kaɗai daga ita sai yara a wani gari ba, ba tare da aure ba dole ta koma gidansa. Wannan lamari ya sake dagula rayuwar Inno tana ji tana gani aka tafi da Daddy, ranar da suka tafi kwana ta yi tana kuka daga ƙarshe ta fauwala wa Allah lamuranta ta rungumi ƴarta Hasiya ta ci gaba da bata tarbiyya. Rayuwar gidan Alhaji Ƙasim kusan rayuwar turawa suke yi, suna karatun boko sosai sai dai karatun addini ne basu bashi ƙarfi sosai ba. Ƴaƴan Alhaji Ƙasim suma a haka suka taso zuwan Daddy gidan ya sa shi ma ya ɗora daga in da suka tsaya, saboda da farkon zuwansa idan ya yi wani abin har dariya suke yi masa suna yi masa kallon ɗan ƙauye, sannu a hankali ya riƙa ɗaukan ɗabi'unsu har shi ma ya koma kamar yadda suke. Daddy sai da ya shekara biyar a Ingila (England) sannan suka zo ganin gida, Inno ba ƙaramin mamakin girman Daddy ta yi ba. Kamarsa da ta mahaifinsa ta sake fitowa sak, a lokacin Hasiya tana aji uku ƙaramar sakandire ta fara zama budurwa manema har sun fara fitowa, sai dai fir Hasiya ta ƙi basu fuska a cewarta ita ma so take ta zama babbar likita kamar yadda Mahaifinta ya zama. Da farko Inno ta ɗauka shafar aljanu ne ya hana Hasiya kula samari, don har ta fara yi mata ƴan jiƙe-jiƙe, amma da ta ji manufarta sai ta mara mata baya don duk wani abu da za a ce don a yi koyi da Alhaji babba ne, yana matuƙar faranta mata don tana alfahari da haka. Baffajo duk yadda ya so ya ga Inno ta yi aure haka ta ƙeƙashe ƙasa taƙi yarda don ta san muddin ta ce za ta yi aure ƴan uwan Mahaifin Hasiya ba za su bari ta yi agolanci a wani gidan ba. Ƴan uwan Mahaifin Daddy daidai gwargwado na zumunci suna taimakawa Inno da Hasiya don duk wata suke yi mata aike da kuɗi masu tsoka, wannan dalilin ya sa suka fita zakka ita da Hasiya a garin hatta mahaifinta ya huta babu yawon gonar da yake zuwa musamman da shekaru suka ƙara turawa. Lokacin da su Daddy suka zo sun kawo musu tsaraba kala-kala sai dai abu ɗaya ne bata ji daɗi ba ganin yadda yanayin tarbiyya da ɗabi'un Daddy suka sauya, hakan ya ɗaga mata hankali sai dai duk lokacin da ta yi sallah sai ta saka shi cikin addu'arta. Watansu ɗaya da zuwa suka koma a wannan karon Inno ta sawa zuciyarta dauriya, don ko hawaye bata yi amma ta fi sati tana jin kewar ɗanta a zuciyarta. A haka rayuwa ta ci gaba da shuɗawa har Daddy ya kammala karatunsa ya karanci Business Administration, Yaran Alhajin Ƙasim mazan tuni suka dawo Nigeria duka sun yi aure, Daddy na kammala karatunsa suka tarkato suka dawo gida Nigeria sakamakon yin ritaya da Alhaji Ƙasim ya yi, a lokacin tuni Hasiya ta yi aure ta auri wani lectural su da yake ta ci gaba da karatu zuwa matakin NCE a FCE Bichi amma ma zaunin garin kano ne. Alhaji Ƙasim ya ƙanƙare gidansa na gani na faɗa a cikin garin Katsina. Ya yin da Daddy ya koma wurin ɗayan ƙanin Mahifin nasa Alhaji Haruna da ke zaune a garin Kano, sakamakon wani babban kamfanin takalma da Alhaji Aƙasim ya buɗe masa. Sannu a hankali Daddy ya fara cin gashin kansa wannan dalilin ya sa ya sayi ƙaramin gidan a unguwar Sallari, Ya dawo da Mahaifiyarsa a cewarsa bai ga amfanin zamanta a ƙauyen ba tun da shi ma mahaifin nata ya rasu sai ƴan uwa da abokan arziƙi. Inno ba ƙaramin farinciki ta yi ba saboda ko ba komai ta dawo kusa da ƴaƴanta, tun da dama kullin hankalinta yana kansu. Shekararsa biyu da fara aiki ya haɗu da mommy a cikin garin albasu, lokacin ya je shi da Alhaji Haruna ganin wata ƙatuwar gona da za su siya a sake gida kamfanin shinkafa. Da haɗuwarsu ko shekara ba a rufa ba manya suka shiga magana, aka tsayar da ranar aure lokaci na cika aka ɗaura musu aure. Mu Dawo Labari, amma fa ba shi kenan ba za mu sake tafiya a gaba don jin asalin Goggon ƴar garin Albasu. Littafin Kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn ta wannan lambar 0706 206 2624 19 Ɗan jim Mahaifiyar Huzaifa ta yi ganin haka ya sa Malam Usman ya ce, "Idan baki da abin faɗa ki bani wuri na kammala abin da nake kai." Mahaifiyar Huzaifa ta numfasa sannan ta ce, "Malam ban jinkirta don gaza abin faɗa ba sai dai na rasa da bakin da zan yi maka magana, Ɗa ne ka haife shi baka haifi halinsa ba. Huzaifa tun yana ƙaraminsa baya ji ko kaɗan, ni mahaifiyarsa amma duk abin da zan gaya masa baya amfani da shi hasalima tuni ya yi hannun riga da mahallina, Malam ya gujewa addinina ya kama addinin kafirci wanda a kullin idan na tuna makomar kafiri na tuna addinin da Huzaifa yake bi zuciyata takanyi ƙuna, mahaifinsa ya cutar da ni ya ha'ince ni, domin shi ne silar duk abin da Huzaifa yake shukawa. Tabbas Huzaifa ya cutar musu da yarinya tun da jin kunnena na ji yana ambatar sama da shekara goma sha a jikinta, don Allah Malam ka yi masa afuwa saboda darajata, kada ka hallaka shi wallahi duk cikin ƴaƴana babu wanda Allah ya jarabce ni da tsananin ƙaunarsa sama da shi..." Tun bata rufe baki ba Malam ya katseta da cewar, "Akan soyayyar ɗanki sai na ƙyale shi ya dakusar da rayuwar yarinyar ƙarama, kina ganin adalci kenan." Murya na rawa Mahaifiyar Huzaifa ta ce, "Allah ya gafarta Malam ba manufata kenan ba, ina nufin ka jinkirta min zuwa wani lokaci zan tattauna da shi zan nemi ya fita daga jikinta amma don girman Allah karka ƙone shi." Shiru ne ya biyo baya Malam na shirin yin magana ya riski muryar Huzaifa yana faɗin, "Ba sai kin nemi wata alfarma a wurinsa ba, har kike zuwa kike kwaye min baya a gaban mutane. Sai me don kin gaya musu ni arne ne meye a ciki? Ni arne ne kuma mahaifina ma haka sannan ina alfari da kasancewata haka, amma ba ke ba kowa za a tara ba zan taɓa fita daga jikinta ba." A zafafe Malam Usman ya ce, "Kin ji abin da yake faɗa Malama Fatima ki ba ni wuri na babbake shi da ayar Allah." Mahaifiyar Huzaifa ta fashe da kuka sannan ta ce, "Ka dubi girman Allah Malam ka yi mini wannan alfarmar karka dubi baƙaƙen maganganun da yake faɗa, dukda dai na san Huzaifa ba lallai ya ji maganata ba domin nima rashin bibiya ga iyaye ne ya ɗora ni a wannan turbar. Tun Muna saurayi da budurwa ni da Mahaifinsa iyayena suka nuna basason alaƙata da Mahaifinsa Ibrahim, sakamakon sun ga take-taken tarbiyyarsa bata masu kirki bace duk da yana ƙoƙarin kwatantawa a zahiri amma a baɗini ba haka yake ba, amma zaƙin soyayya ya rufe min ido haka na watsawa iyayena ƙasa a ido har sai da aka aura min shi amma ba tare da yarjewar mahaifana ba. Ban taɓa sanin ƙasurgumin arne ba ne sai da zamanmu ya yi nisa da shi, mafi yawa daga cikin ɗabi'u da halaye bashi da su masu kyau. Ban taɓa sani ba ashe bakinsu ɗaya da wani hatsabibin aljani MARWAN, Wannan aljanin ko a cikin jinsinmu suna shakku da shayinsa saboda hatsabibancinsa. Sannu a hankali muka fara haihuwa sai muka samu yara uku Huzaifa ne babba, Hafsa ta biyu sai ƴar autata Nabila. Huzaifa tun yana ƙarami shi ne mai ɗauke da siffar mahaifinsu har halayya wannan dalilin ya sa tun yana ƙarami mahaifinsa ya tabbatar mini da tabbas Huzaifa tun da namiji ne addininsa zai bi. A lokacin hankalina ba ƙaramin tashi ya yi amma ganin bani da kowa sai Allah sai shi ya sa dole na amince da buƙatarsa, saboda iyayena suna aura min shi suka zame hannuwansu daga kaina. Haka na ci gaba da mummunar rayuwa a tare da shi, ban taɓa shiga tashin hankali ba sai lokacin da san waye mahaifin mijina wato kakan Huzaifa. A ranar da muka kai masa ziyara ina ɗauke da ciki amma yana tozali da ni nan take ya ce zai yi sihiri da abin ciki sakamakon jinin da wani bokan bil'adam ya zubar masa a kan wani babban aiki da zai yi wa ɗan siyasa. Amma babban abin da ya fi ɗaga min hankali gani yadda Ibrahim ya bashi goyon baya ɗari bisa ɗari, tun basu gama magana ba nan take na ji naƙuda ta kamani amma daga lokacin ban sake sanin wurin da kaina yake ba, sai farfaɗowa na yi na ganni a makwancina. Sannu a hankali na shafa cikina sai dai wayam na ji babu komai amma tsoro, firgici da tashin hankali suka hana ni furta ko da kalma ɗaya ne akan ɗan cikina. Tun daga lokacin duk cikin da zan samu baya zuwa ko'ina sai ya lalace, haka na ci gaba da rayuwar ƙunci har Ibrahim ya fara bijiro min akan dole na yanke alaƙa da addinin musulunci, a nan ne ni kuma na bijire masa muna tsaka da wannan turka-turkar Mahaifana suka rasu. Wannan lamarin ya sake ɗugunzuma mini hankali domin a wannan lokacin ne nake da niyyar zuwa neman yafiyar Mahaifana, amma kash sai rai ya yi halinsa. Haka muka ci gaba da cuɗawa da shi daga ƙarshe har muka rabu domin alwashi na ci akan ba zan taɓa barin addinina ba, da farko ya so ɗauke mini yara gabaɗaya amma na jajirce akan na bar masa Huzaifa domin tun yana ƙaramin ba ya jin maganata sai ta mahaifinsa, ƴan uwansa mata sun fi ƙaunata da tausaya min. Haka na rungumi ƴaƴana na ci gaba da basu tarbiyya, mahaifinsu shi da Huzaifa suka watsar da lamurammu ko waiwaiyarmu basa yi. Sai ni ce nake kaiwa Huzaifa ziyara idan kewa da begensa sun dame ni. Na san duk abin da ya faru da ni ta silar rashin biyayyar iyaye ne kuma na yi nadama har gobe ban daina neman gafara wurin ubangiji akan laifin da na yi wa iyayena ba. Amma duk wasu miyagun ɗabi'u da Huzaifa yake aikawa da sa hannun Mahaifinsa, shi ya gurɓata shi da miyagun ɗabi'unsa. Amma don Allah Malam ka ba ni dama domin na na yi tattaunarwar sirri da shi ko zai fahimci abin da nake nufi ya haƙura da yarinyar nan." Ilahirin jikin mutanen ɗakin ba ƙaramin sanyi ya yi, Mommy tuni ƙwalla ta ciko idonta Daddy jikinsa ya yi sanyi tausayin Mahaifiyar Huzaifa ya kama shi. Hatta shi kansa Malam Usman sai da ya ji wani iri a jikinsa amma hakan bai sa zai sararawa Huzufa ba. Ya kalli Raihan da ke zaune cikin yanayin tausayi sakamakon Mahaifiyar Huzaifa da ke kanta ya ce: "Yaron da tun yana ƙarami bai ji maganarki ba bana jin yanzu zai tasirantu da abin da za ki faɗa masa, ki sani Huzaifa yana da kunnen ƙashi ba baki na yi miki amma babu yadda za a yi ya ji maganarki tun da bai ɗauke ki da muhimmanci ba, ya kamata ki cire ranki da kika ƙwallafa akansa domin ba shi kaɗai gare ki ba. Ki nunawa masu nuna miki kulawa domin sune za ki amfana ba wannan ba, Huzaifa yana ɗaya daga cikin JINNUL-ASHIQ kuma ba a wanyewa lafiya da su. Maganar iyayenki kuma kin matuƙar tafka kuskure sai dai kamar yadda kika faɗa ko ci gaba da yin addu'a komai ya yi tsanani maganinsa Allah, amma ki bar ɗauka ɗanki zai fita daga jikin yarinyar nan ta daɗin rai." Mahaifiyar Huzaifa na jin haka ta rushe da kuka, mommy ta sauke ajiyar zuciya don duk wata uwa sai ta fahimci abin da Mahaifiyar Huzaifa take ji. Tana tsaka da kuka ta kalli Malam Usman ta ce, "Na fahimci abin da kake nufi malama, shi kenan na gode matuƙa da shwararka a gare ni. Haka Huzaifa ya ga ya fiye masa don haka duk abin da ya faru da shi don kansa, ina mata fatan samun lafiya mai amfani na barku lafiya." Malam Usman na yin sallama ya yi bismillah ya ci gaba da yi wa Raihan Ruƙiyya, Huzaifa shiru ya yi don ya gama zuciya da abin da Mahaifiyarsa ta gama zayyanewa Malam Usman, sai da ya ji wuya ta yi wuya sannan ya gudu daga jikinta. Yaraf can gefe Raihan ta faɗi jiki a mace kamar mara numfashi, ban da ajiyar zuciya babu abin da take yi. A galabaice ta ɗago tana kallon mutanen ɗakin da yanayin mamaki, Malam Usman ya ƙarasa wurin Daddy ya ce, "Zo mu je falo ina son magana da kai." Daddy na jin haka ya bi bayan Malam, suna zuwa falo Malam Usman ya ci gaba da cewa: "Huzaifa ya gudu daga jikinta amma fa ba tafiya ya yi gabaɗaya ba, mafi yawanci dama haka suke yi idan azaba ta ishe su. Ya kuke gani maganar gaskiya wannan aljanin yana da matuƙar hatsari domin a kowanne lokaci zai iya dawowa kuma a fusace yake komai zai iya faruwa." Da sauri Daddy ya zaro ido yana faɗin, "Malam babu wata mafita?" Yadda Daddy yake magana ne zai tabbatar maka da ya ji jiki iya jiki. Malam Usman ya yi murmushi ya ce, "Akwai mafita, mafitar kuwa ita ce muna da gadaje a ɗakuna da muke kwantar da masu wannan larura idan kuka ganin za a bata gado babu damuwa idan kuma a barta a nan ana zuwa dubata shi kenan..." Tun Malam bai gama magana ba Daddy ya yi karaf ya ce, "A tafi da ita salamun ƙaulan Malam don matuƙar Aljanin nan yana jikim yarinyar nan, wallahi za a wayi gari ta yi daga-daga da namanmu ta cinye." A wannan karan Malam Usman murmushi ya yi mai sauti ya ce, "Alhaji kuma kuna tsoronsu ne?" Daddy ya dubi hagu da dama sannan ya ce, "Allah ya gafarta malam wane mutum baka ga jikina ba." Nan Malam Usman ya ci gaba da gayawa Daddy irin abubuwan da za su yi wa Raihan idan aka kaita wurinsu. Mommy na son ƙarasawa wurin Raihan amma tana shakkun abin da zai je ya zo, a hankali Raihan ta ɗago cikin galabaitarwa ta ce, "Mommy kaina." Hawaye ne ya ciko idon mommy a hankali ta taka gaban Raihan, tana zama Raihan ta faɗa jikinta Mommy idonta na zubda ƙwallah. Jikin Raihan zafi ya ɗauka zau ta janyo hannun mommy ta ɗora a kanta tana faɗin, "Mommy kaina ciwo." A hankali Mommy ta kama Raihan Malama Nafisa ta taimaka mata, mommy ta shiga banɗaki bakinta ɗauke da addu'a ta wankewa Raihan jiki. A kan katifa ta zaunar da ita tana kallon Malama Nafisa da kallon tuhuma, Malam Nafisa na shirin fita Malam Usman da Daddy suka shigo ɗakin, hankali a tashe Raihan da dubi Daddy ta ce, "Daddy me wannan? Wa ye ya ji maka ciwo a jikinka?" Daddy ya yi tsilli-tsilli da ido don bai san amsar da zai bawa Raihan ba. Malam Usman ya ƙarasa gaban gadon ya ce, "Malama Raihan ki kwanta ki huta kafin zuwa an jima." Raihan ƙurawa Malam Usman ido ta yi tana son gano inda ta san kammaninsa amma ta rasa takamaimai wurin da za ta shaida ta san shi, haka kawai ta ji mutumin ya kwanta mata ba za ta iya yi masa musu ba. Ba ta san ya aka yi ba amma kawai sai ta tsinci kanta cikin faɗuwar gaba, Malam Usman na niyyar fita ta ce, "Amma Abba don Allah me ya faru da Daddyna?" Daddy ya yi murmushin ƙarfin hali ya ce, "Ɗan accident na samu amma babu wani ciwo da na ji." Malama Nafisa ta dubi Mommy ta ce, "Hajiya ki sauya mata kaya ki haɗa kayan buƙatarku sabida tare za mu wuce." Daddy tare da Malam Usman suka fita harabar gidan, su Inno na jin motsinsu da sauri suka fito, Goggo ta raɓe a bayan Inno kamar mai shirin fita da gudu. Inno ganin Daddy da yanayin da yake ciki ta rafka salati tana faɗin, "Audullai yanzu haka wannan hatsabibin ya yi maka, kai wallahi ba don zai iya ji na ba tuni na faki ido na kwashe masa albarka." Daddy ya fara takowa wurin yana faɗin, "Inno ai komai ya zo da sauki." Goggo ta matsa can gefe tana nuna Daddy da ɗan yatsa tana cewa, "Audullahi ka bar matso mu, don Allah ka tsaya Malam ya wanke aljanun da suka shafe ka. Allah ya sani idan ka ƙara tunkaro mu, taku ɗaya ba zan yi ba sai a Albasu, ina dalili Aljani ya shafi fatarka ka matso wurinmu." Inno ta fututtuke cikin ɓacin rai ta waiga wurin Goggo tana faɗin, "Wallahi a yau ba sai gobe ba Zinaru sai kin tafi Albasu, haka kawai ɗana da gidansa ki riƙa saka masa ido haka kawai gidan wani ko nasa? A gidan nan babu abin da Zainabu ta mallaka idan ba Raihanu ba, yoo kayan ɗakin da kika yo mata naga dududu da Tsahare dillahi ta siya ko dubu hamsin ba su yi ba." Goggo ta gama zuwa wuya sai kawai ta nufi saitin windon Raihan ta fashe da kuka tana ƙwalawa Mommy kira, a hargitse mommy ta fita tana tambayar ba'asi. Goggo ta kalli Daddy ta ce, "Wallahi ka sakar min ƴata a yanzunan don yau duk dare a Albasu za mu kwana." Malam Usman da farko ya ɗauka wasa suke yi wa juna da sauri ya kalli Goggo yana faɗin, "Don Allah Mama ku yi haƙuri wannan ba girmanku ba ne." A zafafe Goggo ta dakatar da Malam Usman tana nuna shi da hannu tana cewa, "Dakata Malam wannan ba abin da ya shafi aljanu ba ne, ka bari idan muka zo fagen sai a neme ka, ka yi ruƙiyya yau zan nunawa wannan matar almatsutsan kaina sun fi nata. Zainabu dai nina haifi abata don haka yau ko a ƙafa sai mun tafi Albasu idan ya so duk abin da zai faru sa dai ya faru." Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 idan kina buƙata ki min magana 0706 206 2624 20 Ilahirin jikin Daddy ba ƙaramin sanyi ya yi ba, ya ƙarasa gaban Inno ya ce, "Don Allah Inno me kuke yi haka wannan abin da kuke yi ko Raihan ba za ta yi shi ba, ba fa mu kaɗai ba ne a gidan nan don Allah ko ma meye ku bari komai ya daidaita." Inno ta saki baki da hanci tana kallon Daddy sai da ya gama magana ta dubi Malam Usman ta ce, "Malam don Allah saboda wa nake haƙiƙance wa?" Malam Usman ya yi shiru don bai fahimci abin da Inno take nufi ba, Inno ganin haka ya sa ta dubi Daddy tana faɗin, "Audullahi saboda ina kare ka za ka ci zarafina?" Kafin Daddy ya yi magana Goggo ta dubi mommy ta ce, "Wai Zainabu duk maganar da nake yi ba ki ji abin da na faɗa ba ne? Na ga ko gezau baki yi ba." Mommy baƙinciki goma da ashirin ya cikata ta dubi Goggo tana faɗin, "Don Allah Goggo yanzu me kike so mu ce, kina gani yanzu haka kaya nake haɗawa za mu tafi nema wa Raihan lafiya, da wanne zan ji?" Goggo ta riƙe haɓa tana cewa, "Wai kina nufin yaron nan bai yi fata-fata da aljanin jikin Raihanu ba." Mommy ta jinjina kai fuska babu walwala ta ce, "Kin san ciwo shi yake shiga farat ɗaya sauƙi sai a hankali, balle irin wannan larurar ta Raihan sai an bi a sannu." Inno ta kalli Daddy rai a ɓace tana faɗin, "Amma dai Audullahi kun shammace ko in ce kun yaudare mu, yanzu a madadin ka gaya mana mu kame bakinmu sai ka bari mu yi ta sakin zance, Allah ya sani idan wani abu ya shafe mu kai da matarka kuna da kamasho a ciki don haƙƙinmu ba zai bar ku ba."Inno ta waiga wurin da Kabiru yake tsaye ta nuna shi da yatsa ta ci gaba da cewa, "Allah dai ya watsa maka albarka ka ji Kabiru, yaron nan bai bari mun furta ko tuf ba bayan ayar Allah, ban da hailala da istigifari babu abin da muke yi don kariya daga kaidin wancen hatsabibin." Malam Usman ya yi murmushi don rikicin tsofaffin ya fara bashi dariya, ya ƙarasa gabansu ya furta, "Mama babu abin da zai faru da ku in sha Allah. Ita ma Raihan za ta samu lafiya da yardar Allah." Cike da gamsuwa Goggo ta matsa gabansa sai da ta kalli hagu da dana cikin raɗa ta ce, "Ka dubi girman Allah malam ka yi min wani abu ɗaya kafin ka ƙone yaron nan." Lokaci ɗaya suka juyo wurinta, Goggo kuwa ko a jikinta ta sake kallon gabas da yamma tana faɗin, "Amma dai ba zai iya jinmu ba ko?" Inno ta ƙarasa wurin ta ce, "Shi wa?" Goggo ta yi mata alamu da hannu a kan ta yi maganar ƙasa-ƙasa sannan ta ce, "Wannan hatsabibin da ya yi rayuwa da a siffar uwani." Inno ta yi kasaƙe ba tare da furta komai ba don ita tsoron magana take akan Huzaifa, tana tsoron kar ya farmaketa a kowanne lokaci. Malam Usman ya gyaɗa kai yana cewa, "Eh ina jin ki Mama." Goggo ta zura hannu cikin kajarta (Siket ɗan ciki na tsofaffi mai aljihu a jiki.) Ƙullin goro ta ciro ta miƙa wa Inno ta ce, "Don Allah ci ki ji daushe ne ko namijin goro." Inno ta karɓa ta wurga a baki ji kake garas, Inno ta miƙa wa Malam Usman guntun wanda ta gutsira ta ce, "Ɗana ci ka ji kamar Daushe." Daddy ya kalli Malam Usman a kunyace ya ce, "Don Allah Malam ka yi haƙuri ka san lamari tsofaffi sai..." Malam Usman ya katse shi da cewar, "Babu komai Alhaji muma muna nan da su." Ya karɓa ya sa a baki yana fara tauna Goggo ta ce, "Don Allah ka taɓa jin goro mai daɗin wannan?" Malam Usman yana ci gaba da tauna yana girgiza kai, ganin haka ya sa Goggo ta washe baki tana faɗin: "Duk faɗin garin nan ban taɓa siyan goro a nan ba sai na niƙi gari na tafi Albasu duk ƙanƙantar wanda zan siya, amma hatsabibin can da ya yaudare mu da siffar Uwani kusan tare muke cinye wa da shi. Kai wallahi ina zargin har satar min yake ban sani ba, don idan na siyo na dubu biyar baya rufa wata biyu don Allah cin wannan goron ai daga ji ba na lafiya ba ne." Inno ta gyaɗa kai ta yi ƙasa da murya ta ce, "Ni nadamar da na yi da muka sakankance shegen nan yake ƙare wa tsirancinmu kallo. Allah ya sani da Alhaji babba zai dawo mai raba Huzaifa da shi sai Allah, don Allah Zinaru baki taɓa sauya kaya a gabansa ba? Ni tsorona Allah da Ma'aiki kar ya sake dawo mana, kuma wallahi da Alhaji babba zai dawo sai ya bi mini haƙƙina saboda Allah ya sani ban yafe ba." Goggo ta yi jim tana nazari sannan ta ci gaba da cewa, "Ki bari a fara sauraron shari'armu da shi tukunna." Malam Usman ya yi dariya mai sauti ya ce, "Mama wannan ai ba abin da damuwa ba ne tun da za a ƙone shi kin ga hukuncin ai ya yi har na cinye goron da ya yi miki." Goggo ta wara hannuwa tana washe baki ta ce, "Shi kenan ma! Amma don Allah ka ƙone shi da manyan ayoyi masu saurin babbake aljanu." Malam Usman ya amsawa Goggo; Inno na shirin magana ya ce, "Alhaji lokaci na tafiya ya kamata ya kintsa sai mu wuce ko?" Inno ta kalli Goggo murya a sanyaye ta ce, "Zinaru ni kam na roƙe ko gafara man." Goggo ta sunkuyar da kai ta ce, "Allah ya yi mana aikin gafara, amma ni kam baki taɓa yi min komai ba wanda ya faru ma sharrin shaiɗan ne." Inno ta karɓe zancen da cewa, "Allah na tuba Audullahi da Zainabu ko a lahira na ji za su raba gari ai sai in da ƙarfina ya ƙare, yoo ana zaune ƙalau mu ɗaukar wa kanmu zunubi. Kin san hukuncin wanda ya datse igiyar sunnar Annabi kuwa." Goggo ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, "Ai ko yau sai na kwana hailala da istigifari don tun a Albasu ban sake aikata irin wannan zunubin ba, ina ni ina raba auren Zainabu haka kawai na faɗa Sa'ira ko kuma Hawuya, a'a raba ni da wannan lamarin ai ko a Aljanna ma muna sahun masu shiga Firdausi." Mommy da Daddy suka yi murmushi saboda da farko hankalinsa ya tashi don tsofaffin ba ƙaramin rikici gare su ba. Cikin gida Mommy ta koma ta ci gaba da taimaka wa Raihan ta shirya, sai da ta bata ruwan Tea ta sha sannan ta haɗa musu kayansu a jaka. Daddy ya jima a toilet yana gasa jikinsa sannan ya samu ya ɗan ji daɗin jikinsa dukda raunin da ta yi masa dole sai ya dangana da asibiti. Kafin wani lokaci tuni sun gama shiri tsaf. Inno da Goggo har lokacin ba su fahimci Mommy da Raihan za su koma Waraka da sunan sai Raihan ta samu lafiya za su dawo ba, sai da suka ga Mommy da kaya niƙi-niƙi sannan Inno ta wurga mata tambaya, "Zainabu ni kam wai baki huce ba ne Allah Albasun za ki tafi na ganki da kaya?" Mommy ta manta shaf da maganar tafiya Albasu don haka ta ce, "Inno Waraka za mu je fa, kin san suma Islamic chemist ɗin an ci gaba yanzu har gado ake bawa mara lafiya." A zabure Goggo ta ce, "Mu kuma mu zauna a ina?" Inno ta cafe da cewar, "Taya ni ji kin ji." Ajiyar zuciya Mommy ta sauke don ita hankalinta ya yi gaba ta manta cewar abin da ya faru ko me za a yi wa su Inno ba za su taɓa kwana a gidan ba. Cikin gida ta koma suka tattauna da Daddy sannan suka fita, yana fitowa ya ce ya kira waya za a kai su Albasu idan ya so bayan Raihan ta dawo sai a dawo da su. Wannan magana ba ƙaramin daɗi ta yi wa su Inno ba, basu ɗauki lokaci ba Direban Daddy ya kwashe su da kayansu, don kayan sawarsu ma sai Mommy ce ta kwaso musu sun ce ba za su taɓa shiga gidan ba. Daddy ya ɗebo kuɗi masu yawa ya basu haɗe da kayan abinci ya zuba musu a boot sannan suka wuce Albasu. Mommy lokacin da ta ce wa Raihan ta fito su tafi da farko ƙi ta yi sai da Malam Usman ya shiga gidan da kansa ta fito, tana tafe tana harare-harare. Ganin haka ya sa Daddy ya fara yin baya-baya da ita saboda dukan da ta yi masa bai gama wartsakewa ba. Kabiru ba karamin tausayin Raihan ya yi ba don lokaci ɗaya gabaɗaya ta fita hayyancinta duk ta yi wani iri ga wata rama da ta yi ta lokaci ɗaya. Ilahirin waɗanda suke wurin daga jinsin mutane har zuwa jinsin aljanu sun yi jigun-jigun don da alama yanayin da suke ciki ba mai daɗi ba ne. Abar bauta ce ta miƙe cikin tsananin fusata ta fara zagaye su ɗaya bayan ɗaya tana jinjina kawunan jikinta, tana zuwa wurin wani dutse ta fara buga kanta da dutsen cikin ɓacin rai har sai da ta fara illata kanta. Hatsabibiya ta miƙe ta ƙarasa wurinta tana son taɓa ta don ta dakatar da ita amma tsoron abin da kaje ya zo ya sa ta tsaya daga baya tana faɗin, "Yake Abar bauta wannan ba ita ce mafita ba." A zabure Abar bauta ta juyo wannan karon bakinta har fidda amon wuta ya ce, cikin wata irin fusatacciyar murya ta ce, "Yana neman ruguza alƙaliman tsafinmu, cikin ƙasa da wuni guda ya yi mana mummunar asara. Na shafe dubannin shekaru ina burin cimma burina amma ya wargaza farincikina ya wargaza tasirina, me kuka ganin za mu yi me ye mafita a halin yanzu domin a halin da muke ciki Huzaifa ne ya kawai yake ba mu kariya, yana ba mu kariya ne saboda yana jikinta amma idan ba mu yi da gaske ba matuƙar ya fita daga jikinta ta mu ta ƙare gabaɗaya hallakar da mu za a yi. Don na lura wannan malamin da yake yaƙarmu da gaske yake ba da wasa ba, kuma yana da matsananciyar kariya da tuni mun dunfare shi mun gama da shi, sai dai na san ko karen hauka ya cije mu ba za mu yi gangancij yin haka ba don lokaci ɗaya zai gano mu kuma ya hallaka mu, tun da yanzu babu wanda ya san tana tare da mu hatta shi kansa Huzaifa." Mugaza da ke gefe ta yi shiru tana nazari don idan Huzaifa ya fita daga jikin Raihan tafi kowa farinciki, sai dai ita ma a halin da take ciki matuƙar ta ce ita kaɗai za ta gudanar da nata ɗaukan fansar za ta iya halaka, don yadda aka halakar da tsaunin abar bauta ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba. Ta ci alwashin ko ba komai sai ta shayar da Raihan azaba ta hanata kwanciyar hankali kamar yadda ita ma ta hanata nutsuwa. Daga wurin da take ta miƙe tsaye ta fara magana, "Matuƙar ina raye Huzaifa ba zai taɓa barin jikin Raihan ba." Lokaci ɗaya suka juyo wurinta cikin mamaki, ganin ta ja hankalinsu ya sa ta ci gaba da cewa, "Ƙwarai abin da na faɗa haka ne, Huzaifa ba zai bar jikin Raihan ba matuƙar ina raye domin daga nan zan je na sake tunzura shi akanta. Babu abin da ya tsana sama da na ce dole zai bar jikinta ko na furta kalma mara daɗi a kanta." Cikin jin daɗi Abar bauta ta matso ta rungumi Mugaza, abin da bata taɓa yi wa wani a cikin tsibirin ba. Mugaza ta yi shu'umim murmushi don ita kaɗai ta san manufarta ta gaya musu haka, a ganinta idan ta yi haka za ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Na farko za ta ƙara jefa soyayyarta da samun shiga a wurin abar bauta da ƙungiyar tsafinsu. Darajarta za ta ƙaru matsayinta zai ɗaukaka za ta zama ƴar gaban goshin abar bauta. Na biyu za ta ci gaba da hillatar Raihan har sai ta kai mizanin da take son aiwatar da mugun ƙudurinta a kanta. Nan take suka ci gaba da tattaunawa Intisar na ci gaba da yaudararsu da zantuka kala-kala don ta ga maganganunta ba ƙaramim shigar su ta yi ba. "Duk wanda ya ce zai haɗiyi gatari sai a sakar masa ƙota, dama na gaya maka idan wani ya yi rawa an biya shi wani idan ya yi duka zai ci. Amma ba zan fasa gaya maka Raihan ta fi ƙarfinka, ka fita daga rayuwarta. Wai me za ta nuna min da kake neman salwantar da rayuwarka a kanta, idan ka mutu sun kashe banza sun kashe wofi fa. Ka ga an cuce ni da ƴaƴana akan wata sakarai." Mugaza ta yi maganar cikin zolaya da son harzuƙa zuciyar Huzaifa. Kallonta ya yi yana huci don ta kara wa Barno dawaki domin dama ransa a matuƙar ɓace yake kuma ta ƙara masa da wani. Gyambon jikinsa ya sa wani ruwan magani yana wankewa ta sake bushe wa da dariya a lokacin da idonta ya sauka a kan wata lafceciyar kuna a gefen kafaɗarsa, tana shirin magana ta riski muryarsa yana faɗin. "Ki bar murna karenki ya kama kura, domin koda kura ta rame ta fi ƙarfin ƙosassun karnuka. Ba zan taɓa bari a raba ni da Raihan ba wannan alƙwari ne da na ɗaukar wa kaina, domin ita rabin jikina ce. Na yi sakankancewar da babu mahalukin da zai raba ni da ita, idan kuwa aka nemi halaka ni zan kashe ta kowa ya rasa don ko da na mutu gawata ba za ta iya jurar jin Raihan ta tare da wani namijin ba ni ba. Na yi rantsuwa da girma tsafi da hatsabibancin kakana idan na fito daga tsatson jinin hatsabibin kakana sai dai Raihan ta mutu babu aure, yanzu haka shiri zan sake yi na tunkari Malamin don sai ya fahimci a cikin jinsinmu ma rukuni-rukuni ne, domin wasu jinnun rako wasu suka yi duniyar ni da kike gani bil'adam bai isa ya ga bayana ba. " Daɗi ya ratsa zuciyar Mugaza don ko ta wannan fannin ta san ta yi galaba akansu, kafin ita ma ta fara dasa nata ɗaukar fansar. Kafin fitarsu sai da Daddy ya jadaddawa Kabiru cewar duk wanda ya zo basa nan kar ya buɗe masa gida kuma ya ce masa kawai sun fita unguwa ne, Kabiru shi kansa ta maza yake yi don tun da ya ga an ɗaɗe an bar shi, shi kaɗai yake saƙa da warwara. Ganin tunanin banza na neman yi masa yawa ya sa ya ɗauro alwala fara tilawar Alƙur'ani. Su Mommy suna zuwa bakin ƙofar Waraka Islamic chemist Raihan ta coge, juyin duniya aka yi da ita ta fito ta ƙi. Kifa kanta ta yi a jikin kujerar mota ko ɗago wa ta kalle su bata yi ba balle su saka ran za ta kula su. Malam Usman bai yi mamaki ba don kusan masu irin matsalarta suna yin fiye da abin da ta aikata. Da kansa ya ƙarasa wurin motar ya tsaya, Raihan bata ɗago ba ta ci gaba da zama kamar yadda take. Malam Usman ya dafa jikin murfin motar yana faɗin, "Ka taso ka fito mu shiga ciki ta daɗi tun ban shigar da kai ta yanda ka ɓullo ba." Raihan ta ɗago da kanta ta kalli Malam da idanunta da suka rine kamar sabon barkono. Kamar ba za ta tanka masa ba sai kawai ta kalli wurin da Malam Usman yake tsaye ta tofar da yawu nan take wuta ta tashi a wurin. Baya Malam Usman ya yi yana jinjina kai don ya lura abin Huzaifa ƙara gaba yake ba baya ba. Ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin Mommy ya yi ba, tana daga gefe ban da hawaye babu abin da take yi. Malam Usman kira ya ƙwalawa ɗaya daga cikin yaransa ya basu umarni akan su kawo masa ruwan addu'a, suna kawo masa ya watswa wutar tare da Raihan ɗin gabaɗaya. A fusace Raihan ta kalli Malam tana cewa, "Malam karka bari na kai bango akan hukuncin da kake son yankewa a kaina. Meye haɗinka da yarinyar nan da kake son raba ni da ita ƙarfi da yaji? Na gaya mata matata ce ba zan fita ba ana dole ko so kake sai na illataka, tun da ban ji maganar Mahaifiyata ba kana tunanin kai da na haɗu da kai sama ta ka zan bi umarninka ne?" Malam Usman bai bashi ba amsa ba ya ci gaba da zuba masa ruwan addu'a yana nan tsaye ɗaya daga cikin yaransa suka kawo kasko da wuta aciki ya fara yi masa turare da habbatussauda.Cikin ƙaraji Huzaifa ya dubi Malam Ya ce, "Ya isa haka Malam mu je zan shiga." Matsa wa Malam ya yi sannan Raihan ta fito jiki ba ƙwari don Malam ya gama sagar da duk wani kuzarinsa. Kallon titi Raihan ta yi ta hango wata babbar motar da alama cike take da fetir, kukan kura Huzaifa ya yi ya faɗa kan tsakiyar titin. Don yanda ya ayyana wa ransa da ya bar jikin Raihan gara ya yi sanadin da za ta mutu, idan ya so kowa ya rasa. Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn ta wannan lambar.0706 206 2624 21 Malam Usman da Daddy kusan a tare suka yi dirar mikiya a gaban Raihan, da sauri Daddy ya riƙe ta a gigice yana faɗin: "Raihan titi ne fa." Da wata irin murya mai ban tsoro Raihan ta dube shi idanunta suka ƙara firfitowa ta ce, "Ni ba ƴarka Raihan ba ce." Malam Usman ya kama hannun Raihan a fusace ya fisgota gefe, duk yadda Raihan ta so fisge wa ya gagara don haka Malam Usman ya ja hannunta har cikin ɗakin da suke kwantar da marasa lafiya. Kowanne ɗaki mutum biyu ne sai dai akwai ɗakin mutum ɗaya idan kana da buƙata, sai dai kowanne da tsarin yadda kuɗinsa yake. A ɗakin mutum ɗaya aka kwantar da Raihan, Malam Usman ne ya buƙaci a kulle ta a ɗakin ba tare da kowa ya shiga ba saboda gabatowar sallar magriba. Mommy gabaɗaya kuzarinta ya ƙare saboda lamarin ciwon Raihan kullin gaba yake yi, don haka ta jima tana addu'a bayan ta idar da sallar Magriba. Malam Usman bai buɗe ɗakin da Raiha take ciki sai da ya haɗa kayan magungunansa wuri ɗaya tare da ruwan addu'ar da yake ƙone jinnu. Shi da ma'aikatan wurin mata suka shiga wurinta tana zauna a ƙasa ta ɗaga kanta sama Tana ganin Malam Usman ta miƙe tsaye tana wurga masa mugun kallo, Malam Usman turare ya fara yi mata sannan ya ɗauko turaren miski tare da wani garin magani ya sake shaƙa mata sannan ya yi bismillah ya fara yi mata ruƙiyya. Wannan karan Huzaifa ya daɗe bai yi magana ba har sai da Malama Zainab ta ce, "Malam ina ga kamar baya jikinta fa." Malam Usman ya yi murmushi ya ce, "Malama Zainab kenan ya yi lamfa ne don ya shammaci hankulanmu, amma har yanzu yana jikinta. Kin san waye Jinnul-ashiq kuwa? Kin san me ake nufi da Zaijatu Jinnul-ashiq? Kina tunanin matar aljani daidai take da sauran mata? Sam ki sake hankalta domin matuƙar namijin aljanin soyayya ya auri macen bil'adama akwai aiki ja kafin a samu a rabata da shi. Duk wannan abin da yake yi iya taku ne, kuma ba zai yaudare ni ba don na kara da waɗanda suka fi shi saboda haka mu ci gaba da abin da yake gabanmu." Nan take suka ci gaba yi wa Raihan ruƙƙiya sai da suka kusa shafe awa ɗaya da rabi sannan Huzaifa ya fara magana cikin tsananin azaba. "Ya isa haka Malam zan fita daga jikinta wannan karon ba da wasa nake yi maka ba." Malam Usman ya ce, "Huzaifa ka yi mana wasa ka gani ai ga fili ga mai doki, yanzu tun wuri ka fice daga jikinta kafin na ƙarasa babbake ruhinka." Huzaifa ya sauke ajiyar zuciya a wahale ya ce, "Amma matuƙar ka raba ni da ita wallahi ba a yi mini adalci ba domin ba ƙaramar bauta na yi mata ba, yanzu kana nufin ta tashi a banza kenan." Malam Usman ya bashi amsa, "Dama garin banza ai a farau-faraun wofi yake ƙare wa, me ya sa baka zauna ka yi wa matarka wahalar ba? Raihan jinsinka ce da za ka bauta mata da aikin wahala?" Wannan magana ta Malam ba ƙaramin tunzura Huzaifa ta yi ba, a hassale ya dubu malam yana cewa: "Duk duniya babu macen da nake tsananin kishi kamar Raihan don haka ba zan taɓa bari wani ya raɓe ta ba, mahaifinta ma kulawar da yake bata wani lokacin ɓata min rai take don dai kawai na san babu aure a tsakaninsu ya sa ban taka masa burki ba." Daddy da yake ta waje ya ji abin da Huzaifa ya faɗa nan take ya hau raba idanu don ba ƙaramin tsorata ya yi da lamarinsa ba. Ganin yana ɓata wa Malam lokaci ya sa ya ci gaba da ƙone shi da ayara Allah, faɗuwa Raihan ta yi a can gefe tana sauke ajiyar zuciya. Malam ya ji sautin wani tsoho ya fara magana, "Saboda me za ka riƙa azabtar min da jika babu gaira babu dalili? Da farko na yi kawaici don na san Huzaifa baya jin magana amma azabtarwar ta yi yawa ai. Kana ta iƙirari Huzaifa ya auri bil'adam ko me ya faru ba ku kuke ja ba? Idan matanku sun killace kansu za mu gansu mu yi sha'awa ne? Ko kuwa haka kawai sai mu auri macen da bata burge mu ba? Idan haka ne ai da gabaɗaya mun aure matan bil'adam. Ni na san waye Huzaifa farin sani, kuma ni na haifi mahaifinsa. Ni hatsabibin Aljanine har bil'adam ina basu kariya, amma tun da na ga Huzaifa ya dage akwai dalilinsa na shiga jikinta." Malam Usman ya mayar masa da martani, "Kenan kana ɗaure masa kar ya fita daga jikinta ko?" Kakan Huzaifa ya amsa da cewa, "Ban ɗaure masa komai ba amma ka yi nazari ka duba irin abubuwan da ƴaƴanku na bil'adam suke yi, kai ko a cikinku na san da babu hukunci maza da yawa sai sun riƙa afkawa mata a titina. Ba zan ɓata lokacina a nan ba domin ina da aikin yi yau zan kashe wani babban mutum a duniyarku, amma ka sani matuƙar aka kashe mini jika akwai mummunan mataki da zan ɗauka." Malam Usman na shirin yin magana Kakan Huzaifa ya matsa daga wurin. Malam bai saurara masa ba ya ci gaba da ƙone Huzaifa, cikin galabaita Huzaifa ya furta: "Dakata Malam na yi maka alƙawari matuƙar ka bar ni zan fita daga jikinta amma don Allah ka barni na sanar da kai abin da ya kaini jikinta." Malam Usman banza ya yi da Huzaifa sai da ya ga ya galabaita sannan ya rabu da shi ya ce, "Ina jin ka, a ina ka haɗu da ita?" Huzaifa ya sauke ajiyar zuciya a galabaice sannan ya ce, "Wata rana..." TARIHIN SU MOMMY. Malam Bala Shu'aibu shi ne ainihin cikakken sunan Mahaifin Mommy amma mutane da dama sun fi saninsa da Malam Bala Magini. Asalinsa ɗan garin Albasu ɗaya daga cikin ƙananan ƙauyukan da suke cikin garin Kano, ya taso su bakwai a gidansu amma shi kaɗai ne namiji a cikin ƴan uwansa duk mata ne. Mahaifinsu Malam Shu'aibu malamin makarantar tsangaya ne yana da almajira da yake koyar da su, wannan dalilin ya sa Mahaifin Mommy ya taso cikin da ilimin addini mai zurfi. Sai dai abu ɗaya mahaifinsu ya gindaya musu karatun boko, don ko kaɗan bai amince da karatun boko ba shi ya sa ƴaƴansa mata suna fara zama ƴan mata yake aurar da su. Malam Bala ya so karatun boko a lokacin da Mai garin Albasu ya kawo musu wannan ci gaban sakamakon gwamnatin jaha da ta gina musu ƙananan makarantun boko a cikin gari, mutane da dama ba su karɓi abin ba amma da Mai gari ya wayar musu da kai sai wasu daga ciki suka amince wasu kuma suka juya wa abin baya aciki har da Mahaifinsu Malam Bala Magini. Dole ƙanwar na ƙi ta sa ya haƙura da karatun ya kama na addini hannu bibbiyu, da ya fara zama saurayi sai ƙanin Mahaifiyarsa yake tafiya da shi wurin aikin leburanci. Tun bai iya ba har ya ƙware ya iya gine-gine kala-kala, a lokacin iya cikin garin Albasu kawai suke yin aiki amma daga baya sai Allah ya sa masa nasibi yake samun aiki har cikin garin kano. Zinaru Sama'ila Mai kaba shi ne ainihin sunan Goggo ita ma ƴar garin Albasu ce, ita kaɗai ta taso a wurin Mahaifiyarta. Amma a wurin Mahaifinsu su goma ne da yake matan aurensa Uku, Mahaifiyar Goggo ita ce amarya ta yiyyi ɓari kafin cikin Goggo ya zauna sai daga baya Allah ya zaunar mata da cikin Goggo aka haifeta. Mahaifin su Goggo sana'ar Kaba yake a garin Albasu duk garin babu wanda bai san shi ba, ko daga tasha ka tambayi gidansu kai tsaye za a kaika cen. Ta yi karatun addini daidai gwarwado macece mai barkwanci, amma bata da san raini. Mahaifin Mommy ya haɗu da Goggo ne a makarantar mahaifinsa, sakamakon nan ne makarantar allon da Goggo take zuwa ita da sauran ƴan uwanta. Tun suna soyayyarsu a ɓoye har manya suka shiga magana daga ƙarshe aka tsayar da rana aka sha shagalin aurensu. Malam Bala Magini yana matuƙar nuna kulawarsa ga Goggo, haka suka ci gaba da zamansu cikin kwanciyar hankali, Goggo sai da ta shekara biyu sannan ta samu ciki tana cikin ta uku Allah ya sauke ta lafiya ta haifo Ɗanta namiji. Ba ƙaramin farinciki suka yi ba ranar suna aka saka masa suna Abubakar, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Abubakar na da shekara huɗu Goggo ta haifi ƴarta mai suna Hafsa, sai dai kafin suna Allah ya yi mata rasuwa. Rasuwa Hafsa babu wuya Goggo ta sake samun wani cikin bayan wata tara ta sake haifo ƴa mace aka saka mata suna Zainabu (Mommy) Daga kanta sai da Mommy ta shekara biyar sannan Goggo ta sake haihuwar ƴa mace aka mayar mata da suna Hafsa. Daga kan wannan hafsar Goggo bata sake haihuwa ba, haka suka ci gaba da kula da ƴaƴansu cikin rufin asiri duk da su ba masu kuɗi ba ne. Bayan Wasu Shekaru. Abubuwa da dama sun faru ciki har da mutuwar iyayen waɗannan bayin Allah, wato Goggo da Malam Bala Magini. Abubakar ya fara bin wani yayan Goggo suna tafiya Lagas suna sayar da kayan gwari, a lokacin Mommy ta zama budurwa tana da shekara goma sha shida a duniya. A wannan lokacin tana aji biyu na babbar sakandire sakamakon Mahaifinta bai bi sunnar Mahaifinsa ba, don ya ci burin yadda bai yi karatun boko ba ƴaƴansa ba za su taso haka ba. Dukda ya tsaya musu tsayin daka akan karatun addini, Abubakar sai da ya yi diploma sannan ya fara tafiya neman kuɗi. Ita kuwa mommy a lokacin da take aji biyu na sakandire ne wata rana ta fita ɗiban ruwa ta haɗu da Daddy sun shigo garin Albasu don siyan wata gona su mayar da ita kamfani, Haɗuwar Mommy da Daddy babu jimawa Allah ya yi wa Malam Bala Magini rasuwa, bayan wani lokaci da rasuwarsa Daddy ya tura ƴan uwan Mahaifinsa don a nema masa aure. Da farko Goggo ta so dakatar da maganar a cewarta bai kamata a katse wa Mommy karatu ba alhalin ta kusa candy, amma da Daddy ya nuna ba zai hanata karatu ba ya sa Goggo ta amince. Sai dai a ɗaɗɗare take da su Daddy musamman ta da ga irin galla-gallan motocin da suke shigo wa da su cikin garin albasu. Bayan auren Daddy da mommy ko shekara biyu ba su yi ba ya ɗauko Goggo ya dawo da ita gidan da ya sayawa Inno, saboda tun bayan bikin Mommy zaman garin ya gaza yi mata daɗi. Ga Abubakar yana nesa ga ba miji ita ma Mommy da suke kashewa su binne an yi mata aure, ga ƴan uwan Goggo da suke Uba ɗaya sun saka ta a gaba wai ta ga kuɗi ta sayar da ƴarta saboda zalama. Ɗaukan da Daddy ya yi wa Goggo ba ƙaramin daɗi ya yi wa mommy ba a lokacin Hafsa ita ma ta fara zama budurwa, daga ci da sha har karatun Hafsa Daddy ne yake ɗaukar nauyi. Daga baya da ya kammala gidansa wanda ya fi wanda suke ciki girma, sai ya kwashe su gabaɗaya ya mayar da su kusa da shi. Mommy da Daddy sai da suka shafe shekara sama da goma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, sun yi wayon asibitoci gari-gari ƙasa-ƙasa amma duk wurin da suka je sai dai ace lafiyarsu ƙalau. Da yake Daddy sam bai yarda da maganin gargajiya ba shi ya sa ko na hausa bai yarda sun nema ba, tun suna damuwa har suka fauwalawa Allah lamuransu. Inno ta so Daddy ya ƙara aure amma da yake ta lura bashi da ra'ayi sai ta kawo ido ta saka masa, kuma da yake Mommy na matuƙar basu kulawa tana haƙuri da su ya sa take jin daɗin zama da ita. Don shi kansa Daddy wani lokacin idan suna rikici abin ɓata masa rai yake, sai a sannu da Mommy take nusar da shi wani abin da suke yi har da yanayin tsufa sai Daddy yake zura musu ido. Bayan sun fitar da rai da samun haihuwa kwatsam wata rana mommy ta wayi gari da matsanancin zazzaɓi da ciwon ƙirji, da yake tana da olsa ko da ta je asibiti abin da ta cewa likita kenan. Suna bata tasa-tasai ciki ya bayyana, nan fa suka shiga murna da farinciki su Inno baki ya ƙi rufuwa. Daddy da kansa ya shige musu gaba suka fita ƙasashen waje don siyayyyar kayan jarirai. Bayan wata tara mommy ta haifo kyakkyawar ƴarta mace, tun a ranar Daddy ya saka mata suna Raihan. Haka ya ƙwallafa rai a kanta ko ƙuda baya son taɓa ta, soyayyar duniya ya ɗora mata duk abin da zai saka ta kuka baya so don wani lokacin har faɗa suke yi da Mommy akanta. Haka suka ci gaba da rayuwa da har Raihan ta fara girma kyau da wayonta ya sake fito. Lokacin da Raihan tana da shekara biyar a duniya, kwatsam watarana sun fita shan Ice-cream suna hanyar dawowa ta hango wata agwagwa a bakin wani kanti da Daddy ya yi parking zai sayi kayan provision, murfin ƙofar ta buɗe da sauri tana fita ta tunkari agwagwar ta ruƙota da hannu biyu, a daidai lokacin Daddy ya fito daga shagon. Murmushi ya yi don ya yi tsammanin agwagwar birge Raihan ta yi, daga wurin da yake ya furta: "My love kina son na saya miki ne..." Tun bai rufe baki ba Raihan ta ɗago agwagwar ta damƙe fuka-fukanya ta da hannu sosai sannan ta talata da ƙarfi lokaci ɗaya fuka-fukan agwagwar suka fita daga jikinta, suka tsintsinke gabaɗaya. A haukace ta juyo wurin Daddy cikin ƙaraji tana faɗin, "Ita ta cin ye min Ɗana shi ya sa nima ba kasheta." Ilahirin mutanen da ke wurin sakin baki suka yi a tsorace suna kallon ikon Allah, don wannan abin da Raihan ta yi ba su taɓa ganin irinsa ba. Nan take wasu suka dasa mata ayar tambaya suna ganin kamar mayyace maitarta ce ta fito fili. Littafin kuɗi ne Idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624 22 Daddy kusan suman tsaye ya yi jikinsa har rawa yake yi, ya ƙarasa wurin Raihan yana fisgo hannunta ya ce, "Ke Raihan me kike yi haka?" Idanunta jajawur ta ɗago tana kallonsa cikin wata irin ta ce, "Duk wanda ya hallaka min ɗana sai na yi masa abin da ya fi haka." Da sauri Daddy ya waiga yana kallon mutanen da ke zagaye da su, ya yi ƙasa da murya a daidai kan Raihan ya ce, "To zo mu je gida duk abin da kike so ta zauna." Yana rufe bakinsa ya kai hannu zai riƙota ta fisge, ba tare da ta kula shi ba ta wuce ta buɗe murfin mota ta shiga. Cike da kunya Daddy ya kalli mai kanti yana faɗin, "Don Allah wa kuka sani mai agwagwar nan?" Mai kanta ya yi jim sannan ya ce, "Gaskiya Alhaji ba na ce ga mai ita ba tun da muma a inda ka ganta mu ma a nan muke ganinta." Daddy ya zaro kuɗi masu yawa ya miƙa musu ya ce, "Gashi nan sadakar kuɗin agwagwar ne." A ɗaɗɗare mutanen wurin suka karɓa don ganin abin da Raihan ta yi ya dasa musu shakku a zuciya. Lokacin da Daddy ya shiga mota Raihan na zaune ta kifa kanta a tsakankanin cinyoyinta, kai tsaye daga nan wurin asibiti ya wuce da ita. Bayan ya gama yi wa Likita bayani allurar bacci suka samu suka yi mata da ƙyar don fisge-fisge da bige-bige take yi har sai da ta kai wa Daddy cizo a hannu fatar wurin ta kwaile. Mommy na gida lokacin Daddy ya sanar da ita abin da yake faruwa, hankali a tashe ta tafi asibitin ba tare da ta sanar wa su Inno takamaiman abin da ya faru ba. Bayan ta farka daga bacci garau ta yi kamar ba ita ba, ba a ɗauki lokaci ba likita ya sallame su. Haka suka ci gaba da rayuwa tun Raihan na yin abin sama-sama har ya fara bin jikinta, tun da ta haɗu da wannan larurar babu damar Daddy ya siyo kifi cikin gidan ko wuce wa suka je ta wurin da ake suyar kifi take haukace musu ta yi ta neme-neme tana cewa wani ya sace mata ɗanta zai hallaka shi. Idan kuwa ɗanyan kifi ta ci karo da shi babu wanda ya isa ya ƙwace daga hannunta. Rungume shi take yi ta ƙwaƙume shi tana sunbatarsa haɗe da yi mata wasa kamar yadda babar mace take yi wa ɗanta ko ƴarta. Duk wanda ya tunkareta a lokacin da take riƙe da wannan kifin cikin biyu za a yi ɗaya, inma ta illata shi da yaƙushi ko kuma ta kafa masa haƙora har sai an kwace shi da kyar. Wannan lamari ba ƙaramin saka su Mommy ya yi a uku ba, duk farincikin da suke ciki ya dakushe kullin cikin fargabar wannan ciwon nata suke yi, kuma idan ciwon nata bai tashi ba sai ta yi ta sabgoginta kamar yadda sauran yara suke yi.Wannan dalilin ya su Inno suka fara ɗari-ɗari da ita, akwai ranar da ciwon ta ya tashi ranar mommy ta je shopping wani store a lokacin daga Goggo sai Inno a gidan, Inno na tafe ta hango Raihan a tsaye ta ƙurawa kusurwar bango ido tana murmushi Inno ta ja guntun tsaki ta ce, "Ƙarfi da yaji Audullahi ya koma bayahude, yanzu saboda Allah yarinyar nan ko makaho ya shafata ai ya san ba ita kaɗai ba ce." Goggo da ƙarasowarta kenan wurin ta karɓe zancen da cewar, "Wallahi don kar na faɗa Abu ta ji haushi na shi ya sa na yi shiru, ki dubi yarinyar kamar jikar ifiritu yau da lafiya gobe ta hau cije-cije ni tun da na yi rayuwa a Albasu ko mai kwantankwacin wannan ciwon ban gani ba." Mama Uwani ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da mopper ta ce, "Gafaranku dai." Cikin haɗin baki suka amsa mata, jin yadda suke yi wa Raihan ya sa ta ce, "Yanzu dai Inno tun da ba wani abu kuka ga ta yi ba don Allah ku sararawa Uwar ɗakina haka." Rufe bakin Mama Uwani ya sa Raihan ɗagowa ta kalle su da jajayen idonta, Inno na ganin haka fara salati tana ƙoƙarin jan ƙafarta zuwa ɗaki. Kamar tsuntauwa haka Raihan ta dira a gaban Mama Uwani ta fisgi mofar hannunta ta fara bin su Inno tama raɗa musu sandar mofar a baya. Ganin Raihan ta tasamma nakasa su ya sa ba shiri suka neman tsira da rarrafe suka fita gate, a lokacin Marigayi Ado mai gadi yana nan, yana zaune yana jin rediyo ya hango su Inno sun tunkaro shi da rarrafe. Da sauri ya nufi wurin yana son kora Raihan gida ta yo kansa gadan-gadan, tana faɗawa Ado su Inno suka samu nasarar bankawa ɗakinsa. Sufa Raihan ta yi ta fisgo ƙafar Goggo ɗaya ta Inno ɗaya ta fara saka baki tana gantsara musu cizo, Mama Uwani ce ta zo ta janye Raiham daga wurin su Inno ban da kuka babu abin da suke yi, Goggo kuwa saboda ruɗewa ta yi fitsari ya kai uku a wurin. Kafin Mommy ta dawo tuni Raihan ta dawo hayyacinta, sai Mama Uwani ce take sanarwa da Mommy abin da ya faru. Ba ƙaramin tausayi su Inno suka bata ba, tun daga ranar idan za ta fita unguwa ta daina barinta da su a cikin gida dukda dai akwai Mama Uwani. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yau ciwon Rihan ya tashi anjima ya lafa, har ta fara girma ta fara nisa a makaranta. Tana gama firamare sai kuma ciwonta ya fara yin sanyi wani lokacin sai ta shafe wata shida wani abu bai faru da ita ba, sai kuma ya zamana idan ciwon nata zai zo ma sai dai ta yanke jiki ta faɗi kamar mai farfaɗiya sai ta kusa wuni guda bata farko ba. Ita ba mai bacci ba ita ba ido biyu ba. Tun da mommy ta duba yanayin ciwon Raihan babu yadda bata yi a nemar mata magani ba amma abin ya ci tura, daga ƙarshe ma ɗaukanta ya yi da Mommy suka sakamakon harkar ƙaro da ya fara yin safararsa daga nan gida najeriya. Ba ƙaramin samu yake yi ba don haka ya ce zamansu a can yafi don a can ne za a newa wa Raihan lafiya yadda ya kamata. Ko kaɗan Mommy bata so ba amma babu yadda ta iya haka suka tafi suka bar su Inno da Mama Uwani a gidan, lokaci bayan lokaci Daddy na turowa ɗaya daga cikin yaran kawunsa kuɗi yana yi wa su Inno duk siyayyar da ta dace. Daddy da iyalansa ba su suka dawo Nigeria ba sai da Raihan ta gama secondry school a lokacin tana da shekara goma sha shida, sai dai an samu sauki sosai don ciwon nata yana jimawa har fin shekara bai tashi ba, musamman da su Mommy suke kiyaye abubuwan da yake tayar mata da ciwon, amma sukan zo gida lokaci zuwa lokaci a lokacin ƙanwar Mommy wurin haihuwarta biyar. Duk wannan tsahon shekarun da aka ɗauka Mama Uwani tana tare da su Inno suna zaune gwanin birgewa, dawowarsu Nijeriya samari da dama ƴaƴan abokan Daddy sun nuna soyayayrsu ga Raihan, sai dai gabaɗaya babu wanda ta taɓa aminta da shi. Hasalima daga ranar da ka ce kana sonta shi kenan ta yanke duk wata alaƙa da kai, ko kaɗan abin bai damu Daddy ba da yake dama bai yi niyyar aurar da ita a lokacin ba. Ya ci burin sai ta yi karatu mai zurfi ta karanci harkar lafiya, amma ita Raihan sam karatun likitanci ba shi ne a gabanta ba tafi sha'awar lecturing. Mommy tun tana ɗaukan abin wasa da shirmen ƙuruciya har abin ya fara damunta a zuciya, don har Raihan ta kai shekara goma sha takwas babu wanda ya taɓa fitowa ya ce yana sonta ta amshi tayinsa. Hasalima daga ƙarshe samarin ma daina zuwa suka yi, idan mommy ta yi wa Daddy magana sai dai ya rufe ta da faɗa ya ce Raihan nawa take da don bata yi saurayi ba har za a damu. Daga ƙarshe Mommy daina bin ta kansa ta yi, ita ma Raihan ɗin idan mommy ta yi mata magana sai dai ta ce mata ita fa tana da mijin aure. Kusan kullin sai Mommy ta yi nafilar dare ta kaiwa Allah kukanta akan ya bayyana musu abin da yake daminta dan kuma jinkirin aure ne ya sa jinkirin ya zama alƙairi. MU DAWO LABARI. Jin Huzaifa ya datse maganar da ya fara yi ya sa Malam Usman ya ce, "Idan baka da abin faɗa Huzaifa kar ka ɓata min lokaci." Huzaifa ya sake numfasawa sannan ya ce, "Wata rana ina shawagi a sararin samaniya ranar ina cikin farinciki, kawai ta raya min na bi gidajen Bil'adam ko na kashe ƙwarƙwatar idona, a wani gida na ci karo da Raihan a lokacin bata fi shekara huɗu a duniya ba. Cikin dare ne don dare ya tsala sosai, tana kwance a ɗakinta wanda ya ƙayatu fa ƴar tsanoni kala-kala, daga gefen gadonta Mahaifinta ne a zaune yana ɗan danne-danne a laptop. Sai wayarsa da take fitar da sautin sasaanyar waƙa turawa, har na yi hiyyar giftawa na hangi surara yarinyar gwanin birgewa kanta ba ɗankwali gashi tana rungume da wani teddy. Shafata na yi nan take naji wani sabon yanayi da ban taɓa ji a jikina ba, dukda na yi mu'amala da matan bil'adam babu adadi amma yanayin da na ji game da ita na musamman ne. Ina cikin wannan yanayin Mahaifiyarta ta shigo ɗakin tana yi wa mahaifinta magana, "Haba Daddyn Raihan. Dare fa mahutar bawa ne ka rinƙa hutawa ranka mana, ga shi ka kunna waƙa biyu saura fa. Ni ma daga yin shafa'i da wuturi shikenan bacci ya yi gaba da ni, yarinyar nan ban san lokacin da ka kwnatar da ita ba." Ina kallo mahaifinta ya miƙe yace, "Ai na gama mu wuce kawai." Mahaifiyarta ce ta ƙaraso wurin da nake rungume da Raihan ta fara yi mata addu'a ba shiri na tashi daga wurin daga ƙarshe ma karatun kur'ani ta kunna mata a waya akan dole na haƙura da gidan gabaɗaya." Wash🤭 yau na sha typin. Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgna 0706 206 2624 23 Na yi tsammanin barina daga gidan zai sa na manta da duniyar Raihan, amma sai dai wani abin mamaki har zuwa wayewar gari haka na yi ta fama da dakon tunaninta. A ranar matata har sai da ta fahimci sauyin da na tsinci kaina a ciki, don sai da ta tambaye ni na ce mata babu komai. A ƴan kwanakin nan haka na yi ta ƙoƙarin ganin na sake shiga gidan amma da na zura kaina zan ji wani tururi, sakamakon a ƴan kwanakin na yi tsammanin mahaifiyarta na yawaita saka karatun alƙur'ani. Duk yanda na yi na sake samun damar ganin Raihan sai abin ya ta'azzara, a gefe ɗaya ni kuma ina ta fama da dakon soyayyarta. Ana cikin haka kwatsam wata rana sun fita unguwa idan ban mata ba gidan wasan yara aka kaita, kawai sai na ga wannan wata dama ce a gare ni domin ranar har Mahaifiyarta sun manta ba su yi addu'ar fita daga gida ba. Dama ba a zancen mahaifinta don shi waɗannan abubuwan ba su dame shi ba, dabbara ce ta faɗo min akan na tunkari wurin da suke cikin siffar ƙadangare don na san mafi yawan mata sun fi tsoronsa. Na yi haka ne don na samu damar da zan kori mahaifiyarta, don yanda na lura ita ce za ta fi bani matsala. Ina zuwa kuwa kamar yadda na yi tsammani haka ce ta faru, ba ita kaɗai ba hatta tsirarin matan da suke wurin duka dare wa suka yi. A madadin na wuce sai na tsaya a wurin na fara tsintar abubuwan da suka ci suka zubar a wurin ina ci, Raihan na ganin haka ta fara watsa min ruwan lemon da ke hannunta. Amma a madadim na ji haushin abin da ta min sai ma ƙara kwanciya na yi a wurin, Mahaifiyarta na daga nesa ta zabura tana kwaɓarta akan ta daina amma nan take Mahaifinta ya rufeta da faɗa wai wata ƙila burgeta na yi. Daga wurin da Mommy take na fahimci irin kallon da take yi min na zargi, don haka ta ƙaraso wurina tana karanta addu'o'i da sauri na matsa daga wurin suka ci gaba da harkokinsu. Tun a wurin na fara tunanin yanda zan shagaltal da Mahaifiyarta don ta rage saka karatu a cikin gida, saboda na samu damar kawo wa Raihan ziyara. Ana cikin haka sai suka shiga shagalin wani bikin ƴan uwansu, tun ranar da mommy ta dawo a gajiye ta kwanta ko addu'ar kwanciya bata yi ba na fara saka mata nauyin bacci haɗe da kasala. A ranar kwana na yi a jikin Raihan tun ina ƙare wa hallitarta kallo har sha'awarta ta fara fisgata na fara kai hannuwa a sassan jikinta. Ranar kwana na yi a jikinta na yi bacci mai daɗin da ban taɓa irinsa ba, daga haka kusan kullin na samu wurin kwana tun Mugaza bata fara zargin wani abu ba har ta fara bibiyar sahuna. A nan ta gano wurin wacce nake yada zango don haka ta kafa mata ƙahon zuƙa, saboda na juya mata baya komai nata baya birgeni, sai da na yi da gaske sannan Raihan ta tsira daga kaidin Mugaza. Tafiya da ta miƙa daga ƙarshe sai na yanke shawarar fara neman aiki a cikin gidansu Raihan, ni da kaina nine na kashe Laraba mai wanke-wanke." Jin wannan furuci na Huzaifa ya sa Mommy da Daddy da ke kan kujeru a zaune suka ɗauki salati cike da mamaki, don ba ƙaramin sabo suka yi ba Laraba ba mace ce mai kirki a lokacin da tana raye. Sun shafe sama da shekara goma tare da ita, kwatsam suka yi wayi gari ta fara wata irin rashin lafiya. Tun tana yi a gidan su Mommy har lamarin ya yi tsamari suka mayar da ita garinsu, suka bata kuɗi masu yawa. Lokaci-lokaci suke zuwa duba ta bayan doguwar jinyarta sai waya aka yi musu Allah ya yi mata rasuwa. Su mommy na tsaka da tunani suka riski Huzaifa ya ci gaba da cewa, "Na kashe ta ne don na san matuƙar na zo neman aiki ba za su ɗauke ni ba tun da Laraba babu abin da ta gaza musu, tun bata bar gidan ba lokacin tana jinya wata rana da safe na zo a siffar tsohuwa na roƙe su akan su ɗauke ni wanke-wanke da aikin gida. Ban samu matsala ba suka amince min na fara rayuwa a cikin gidan, tun zama na a gidan na fahimci sam Mommy bata saki jiki da ni ba, don ba na manta akwai ranar da na ji tana gaya wa Daddy wai duk lokacin da ta zo kusa da ni gabanta yana faɗuwa, tsigar jikinta na tashi. A ranar Daddy ya so aminta da zancenta, ina jin haka a washegari na fara yin duk wani abu da na san zan shiga zuciyar Raihan. Na zama bawa duk don na zamu gurbin zama a gidan, kuma buƙata ta biya domin Daddy na ganin irin kulawar da nake bawa Raihan na kawar da zancen tafiyata. Ita kanta mommy aka ce mai Ɗa wawa tana ganin irin kulawar da nake bawa Raiha ta bar abin a ranta ba tare da ta sake furta wata kalma a kaina ba. Wannan shaƙuwa tamu ba ƙaramin daɗi ta yi min ba, kuma dama duk dare a wurin Raihan nake kwana. Na fara kusantar Raihan tun tana shekara biyar a duniya, kafin na fara kusantarta har sai da na biya sadaki ba haka kawai na fara haike mata ba. Wata rana Daddy ya ɗauke ta sun fita suna hanyar dawowa motarsa ta ɗan samu matsala, Yana tsaye a gefen titi ita ma Raihan ta fito tana jingine da shi a lokacin Daddy na jiran bakanikensa. Ina ganinsu na ɓullo ta hanyar cikin siffar Tsoho kuma almajiri, Ina ƙaraso wa wurinsu na yi masa bara nan take ya ciro dubu biyu ya miƙa wa Raihan ya ce ta kawo min. Da murmushi na karɓa na ce, "Amaryata ya makaranta." Nan take Raihan ta yi dariya ta ce, "Lafiya ƙalau." Ganin muna wasa da Raihan ya faranta ran Daddy ya ce, "Baba Wannan amaryar taka za ta cika ka da surutu." Na ji daɗin maganar Daddy ƙwarai don haka na ce, "Alhaji ban yi wa amaryar tawa tsufa ba kuwa." Daddy ya ɗauka maganar a wasa ce don haka kai tsaye ya kalli Raihan ya ce, "My Love wai baba ya miki tsufa?" Abinka da yaro Raihan bata san me ake nufi ba don haka ta girgiza kai, Daddy ya yi dariya ya ce, "Ka ji ko ai tun da Raihan na sonka na baka ita." Nan take na ciro dubu ɗaya a cikin kuɗin da aka bani na miƙa mata na ce, "Ga sadaki Amaryata." Kallona ta tsaya tana yi Daddy ya karɓa ya miƙa mata sannan ya sake ƙara min kuɗi, a daidai lokacin bakanikensa ya ƙaraso ganin haka ya sa na yi musu sallama na bar wurin. Tun daga ranar na fara kusantar Raihan, kuma sai na ji matata ta fice min a ka don haka ta fara kawo wa Raihan farmaki. Ana cikin haka ta haifa min yaro namiji, Mugaza na ganin haka ta ɗauke shi ta kashe shi, a lokacin da Raihan za ta haihu na ɗauketa zuwa duniyarmu kuma ta ga abin da ta haifa mai siffar kifi da ƙarninsa, ita kuma Mugaza tana zuwar mata da siffar wasu dabbobin a duk lokacin da za ta ɗauke mata Ɗa. Raihan sai da ta haifar min ƴaƴa masu yawa amma Mugaza tana kashe su sai wannan na ƙarshen ne ba ta samu wannan damar ba, na sha ɗaukan Raihan na kaita duniyarmu na ajiye musu jabinta amma babu wanda ya taɓa lura da haka. Kuma tun zamana a gidan nan basu taɓa fahimtar ni ba jinsunsu bace sakamkon takatsantsan da nake yi. Bala mai gadi ne ya taɓa ankara shi ma a ranar da ya tabbatar da ni wacece a ranar na kashe shi." Wannan karon ma Mommy da Daddy jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, don sun gama tsorata da lamarin Huzaifa. Suka riski muryarsa yana ci gana da cewa. "Na kashe masu gadi kusan uku sai wannan yaron Kabiru ne ya gagare ni kasancewar ba haka kawai yake zaune ba, yana da riƙo da addini kuma jikina yana bani akwai wani ɓoyayyan al'amari a tattare da shi. Na kashe samari kusan Biyu a kan Raihan saboda na lura suna yunƙurin bani matsala, kuma har gobe ba zan taɓa bari Raihan ta ƙaunaci wani namiji bayan ni ba. Lokacin da na tafi nemar mana mafita gabannin bayyanar hallitata ta ainihi, na ji labarin ta faɗa soyayyar wani yaro tabbas sai na hallaka shi. Kuma abin farimcikin ma kisa zan yi masa mai matuƙar wahalarwa." Huzaifa na gama maganar Malam Usman ya ce, "Idan har na barka a raye ko?" Malam bai saurari abin da Huzaifa zai faɗa ba ya buɗe masa wuta da ayar Allah, duk irin roƙo da magiyar da Huzaifa ya yi Malam bai saurara masa ba sai da ya yi lugub da ƙyar yake iya magana ya ce, "Malam wallahi zan fita." Malam Usman ya ce, "Ta ina za ka fita?" Huzaifa a galabaice ya ce, "Ta ido zan fita." Da sauri Malam ya ce, "Ba za ka fita ta ido ba ka sauya wuri." Huzaifa ya ce, "Zan fita ta hannu ko ƙafa." Wannan karon Malam ya ce, "Ka fita ta hanci kuma umarni ne nake baka." Huzaifa ya yi shiru bai sake magana ba, ganin haka ya sa Malam ya ci gaba da karatu. Sai da Huzaifa ya ji Malam ya tasamma halaka shi ya ce, "Wallahi zan fita ta hancin." Malam Usman ya ce, "Maza ka fice kuma babu kai babu ita har abada ka ji mai nace?" Huzaifa ya amsawa Malam. Yana gama magana Raihan ta fara jero atishawa ba adadi. Ajiyar zuciya Malam Usman ya yi yana furta, "Alhamdullah." Kayan aikinsa Yaransa mata suka shigo suka fara kwashe wa jin hamdalar da Malam ya yi ya sa su Mommy suka fahimci an yi nasara. Fitowa ya yi ya ce Malama Rahama da Mommy su shiga su taimaka mata don jikinta gabaɗaya babu ƙwari, a hankali Raihan ta fara kallon wurin tana ganin Mommy ta miƙa mata hannu. Mommy ɓoye ƙwallar idonta ta yi don kar Raihan ta fahimci abin da yake faruwa, ɗakin da Raihan take har da toilet a ciki don haka mommy ta taimaka wa Raihan suka shiga ta sauya kaya, kafin su fito Malama Rahama ta kunna garin habbatussauda. Da mamaki Raihan ta dubi Mommy ta ce, "Mommy ina ne nan?" Mommy ya ce, "Raihan baki ji daɗi ba ne muka kawo ki nan amma insha Allah kina ƙarasa warware wa za mu koma gida." Jinjina kai ta yi sannan ta ce, "Ina Daddy fa?" Mommy ta yi murmushi ta ce, "Oh Raihan wannan rai naki yana son Daddy ƙila da ni ce ba za ki tambayi inda nake ba ko?" Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Kai Mommy wallahi a'a." Abinci aka kawowa Raihan ta ci tana cikin ci Daddy ya shigo, ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin ta samu lafiya. Ya jima a zaune sannan ya tafi office ɗin Malam don ya ce yana son ganinsa. Da sallama Daddy ya shiga bayan sun gaisa Malam ya fara yi wa Daddy bayani, "Alhamdulillah mun samu nasara ya fita daga jikinta, amma za ta ci gaba da zama a nan tana karɓar magani na tsawon sati guda. Sai dai ya zama dole a kiyaye wasu abubuwa kuma koda komawa gida kuka yi dole ne a riƙa kunna karatun alƙur'ani akai-akai, a hanata jin kiɗe-kiɗe da yawaita bayyana tsiraci. Ta riƙa zama da alwala kuma so samu a farko-farkon nan kar a riƙa bari tana kwana ita kaɗai a ɗaki don shi shaiɗani binbini gare shi fiye da yadda kake tsammani. Sauran bayanin zan yi muku ranar da za a sallame ta, don a kiyaye Allah ya bata lafiya." Daddy cikin jin daɗi ya ce, "Amin Malam mun gode ƙwarai Allah ya ƙara ilimi." Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624 24 A wannan lokacin ganin halin da Huzaifa yake ciki ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, da farko ta so share shi saboda kishin Raihan da yake cinta a zuciya amma da ta tuna mijinta ne kuma uban ƴaƴanta akan dole ta yakice komai ta ƙarasa wurinsa da yake kwance kamar gawa. A hankali ta ɗago shi ba shiri ya saki ƙara sakamakon wani irin raɗaɗi da yake ratsa cikin jikinsa, ganin halin da yake ciki ya karya zuciyarta lokaci ɗaya ta rungumo shi a jikinta ta fashe da matsanancin kuka. Sai da ta yi mai isarta ta ɗago shi cikin kuka tana faɗin, "Ina amfanin irin wannan rayuwar Huzaifa, me ya sa ba za ka tsaya a iya matsayinka ba? Dubi irin azabtarwar da aka yi maka duk akan yarinyar nan meye take da shi wanda ba ni da shi. Haka kawai za su kashe min kai su illata ka su cuci ƴaƴana, gaskiya ya kamata ka sauya rayuwa Huzaifa wannan ba hanyar ce mai ɓulle wa ba." Huzaifa bai tanka wa Mugaza ba kasancewar yana cikin wani yanayi mai wuyar fasaltuwa, taimaka masa ta yi ta gyara masa jikinsa sannan ta shiga jinyarsa. Abar bauta hankalinta ya kai matuƙar tashi don ganin irin illar da aka yi musu lokaci ɗaya kuma aka fatattaki wanda suke ganin shi ne bango madafarsu. Taron gaggawa ta sake haɗa musu don sanin makamar abin da za su gudanar dangane da Raihan. Ilahirin ƴan tawagar ƙungiyar asirin sun hallara a wurin Intisar ce kawai bata samu halarta ba sakamakon jinyar Huzaifa da take yi, wannan uzurin da ta kawo bai sa ta samu wata matsala ba saboda abar bauta ta san abin da yake faruwa. Sai da ta ƙare musu kallo sannan ta fara magana, "Ya zame mana wajibi mu tashi tsaye don mu yi yaƙi da hannuwanmu, tabbas an cutar da mu kuma ba za mu bari wannan cutarwar ta tashi a banza ba. Malam Usman ya fatattaki Huzaifa idan muka zura kanmu a yanzu muma za a iya fatattakarmu, me kuke ganin shi ne mafita a gare mu?" Abar bauta ta wurga musu tambaya, aljani batoyi ya miƙe tsaye ya ce, "Ni a ganina mu afka musu lokaci ɗaya don sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi." Abar bauta ta jinjina kai ta kalli sauran haka suka riƙa tashi suna faɗar ra'ayinsu sai daga ƙarshe Hatsabibiya ta miƙe ta ce, "A ganina mu sararawa Raihan na tsawon lokaci matuƙar ba ma son kwaɓarmu ta yi ruwa, jinkirtawar da za mu yi ba shi zai nuna gazawarmu ba sai dai don mu samu damar da za mu farfaɗo da ƙungiya idan muka ce gaggawa za mu yi tabbas za mu iya tsintar talatarmu a laraba. Mu ci gaba da gina ƙungiya idan ya so daga baya sai mu yi zaman shawarar da za mu sake jawo Raihan cikinmu, kin ga kafin lokacin ƙarfinmu ya dawo muna da jajircewar da za mu iya tunkarar Raihan ba tare da wata matsala ba." Abar bauta na gama jin haka ta fara ɓaɓɓaka dariya saboda shawarar ba ƙaramin daɗi ta yi mata ba, don haka a lokacin ta bada umarnin a fito don a samo mata jarirai biyar sababun haihuwa, sai jinin tsofaffai uku da na matasan samari biyu. Kafin wani lokacin tuni an aiwatar da abin da ta buƙata, nan take suka farke musu kayan ciki suka sha jini suka ci gaba da harkokinsu da tunanin yadda za su gyara ƙungiya su sake ƙafata ta tsaya akan ƙafarta. Jikin Raihan na ci gaba da samun sauƙi saboda yadda take samun kulawa daga cibiyar Waraka islamic chemist, tana cin abinci sosai babu wani abin da yake damunta. Akwai magugungunan da ake bata safe da yamma da turarrikan da ake yi mata haɗe da wasu mayuka da ake shafa mata masu haɗe da magani a jiki. Ita kanta Raihan sai da ta ji daɗin jikinta sakamakon jinta wasai da take yi, duk wasu miyagun mafarkai ta daina yi. Ta daina mafarkin an biyota da gudu ko wani namiji yana saduwa da ita, hatta ɓacin rai da take yawan jin haka kawai ranta na ɓaci ta daina. Wannan sauyi da ta samu ba ƙaramin faranta zuciyar su Mommy ya yi ba, Daddy ne kaɗai yake komawa gida ya kwana shi ma a ranar farko da ya koma tsoro ne ya fara kama shi, sai da ya ɗauko laptop ɗin Mommy ya kunna karatun Alƙur'ani sannan ya samu bacci mai daɗi ya ɗauke shi. Haka ya ci gaba da zarya daga gida zuwa wurinsu Raihan duk wasu harkokinsa ya dakatar da su, don ko fita ya yi hankalinsa na wurinsu. Su Inno da suke garin Albasu ta waya suke kiran mommy ko ta kira su, don su ji sauƙin jikinta. Yadda suka ji jikinta ya yi sauƙi ba ƙaramin daɗi ya yi musu ba. Satin Raihan guda Malam Usman ya basu sallama, a ranar da za su tafi Malam ya jima yana yi musu nasiha da cewar: "Masha Allah, dama an ce komai ya yi farko zai yi ƙarshe amma don Allah ina so ku bani aron kunnuwanku. Duk abin nan da ya faru da Yarinyar nan dama can rubutacce ne a wurin Ubangiji, amma kun san komai yana da sanadi." Lokaci ɗaya Daddy da Mommy suka gyaɗa kai sannan Malam Usman ya ci gana da cewa, "Kun yi sakaci matuƙa dangane da tarbiyar yarinyar nan musamman kai Mahaifinta, a mafi yawan maganar da Aljanin ya yi duka idan ka tattara maganganunsa yana nuna cewar kai Mahaifinta kai ne ka fi bashi goyon baya wurun samun zama a jikinta, ya nuna gazawar addu'a ƙarara don haka yanzu dole ku zage dantse. Duk Ɗan da ka gani yana da iyaye kuma duk iyayen da ka gani suna ƙaunar ƴaƴansu, amma muddin muka bari soyayyarsu ta rufe mana ido dole watarana kwaɓarmu za ta yi ruwa, kuma dama an ce ka so naka duniya ta ƙi shi ka ƙi naka duniya ta so shi. Idan har muna son ƴaƴanmu su taso da tarbiyyar koyarwar gidan Manzo dole mu tsaya kai da fata akan tarbiyya irin wacce addini ya bamu, daga ƙarshe ina mai ƙara jaddada muku da sa ido sosai akan yarinyar nan don kar wannan la'anannan ya sake bijirowa a jikinsa. Ina roƙon Allah ya bata lafiya ya tsare dukkan ƴaƴan musulmi kuma ya fito mata da miji nagari." Mommy da Daddy cikin haɗin baki suka amsa da Amin, suna sake yi masa godiya sannan suka yi sallama suka tafi. Ana sauran kwana biyu za a sallami Raihan Daddy da kansa ya kira malamai suka yi saukar alƙur'an, a ranar da suka koma haka aka turare gidan da Habbatussauda Mommy ta kai kayan Raihan ɗakinta don ta gama tsara Raihan a wurinta za ta koma da kwana. Kwanan su Mommy biyu da dawowa aka ɗebo su Inno aka dawo da su, da ido suka riƙa bin Raihan da kallo. Har sai da Raihan ta tsargu ta ce, "Inno Lafiya wannan kallon fa." Inno ta yi tsumu kamar kazar da aka tsamo daga ruwa ra ce, "Haba Raihanu me kika gani?" Raihan ta taɓe baki ta ce, "Wallahi duk na ga kwana biyu kun zama wasu salihan bayi tsofaffin nan an ya ba wani abin kuke ƙullawa ba?" Mommy da ta kawo kai cikin ɗakin ta watsa wa Raihan daƙuwa ta ce, "Gidanku Raihan Iyayen nawa ne za su ƙulla miki wani abin?" Raihan ta yi dariya mai sauti tana nuna Goggo da ta rufe ido a zuwan bacci take yi, amma kana kallon yadda take motsa ƙwayar idonta za ka fahimci ba bacci take ba. Raihan ta ce, "Allah da gaske ki ga fa yadda Goggo take mintsina idanu kai da gani kasan baccin ƙarya take." Mommy ta kai mata dukan wasa ta ce, "Raihan wai yaushe kika raina su Goggo haka?" Goggo ta ɗago da kai ta ce, "Duk wanda ya raina uwar wani ta shi ya raina." Daddy ya shigo ɗakin ya zauna suka ci gaba da hira, ita dai Inno sai ɗari-ɗari take yi tana tsoron abin da kaje ya zo. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a gidansu Raihan gwanin birgewa don a wannan lokacin sam ba su da wata damuwa, duk wasu hanyoyi da suke katange ɗan adam daga kaidin aljan su Mommy suna ƙoƙarin ganin sun bi. Hatta al'amuran yau da gobe Mommy ta fara nusar da Rainan, har aikin gida da girki babu wanda bata nuna mata saɓanin lokacin baya da sai dai a girka a bata ta ci. Daddy yana ganin duk abin da yake faruwa sai dai uffan bai ce ba don nasihar Malam Usman ba ƙaramin ratsa shi ta yi ba, kuma lokaci bayan lokaci suna ci gaba da karɓo mata magunguna da turarika. Babban abin da ya tsayewa Raihan a rai tun da ta kwanta jinya ko a waya Intisar bata kira ta ba balle ta je duba ta, bata kawo ƴan Department ɗin su za su je ba saboda da dama wasu ba mu'amala suke da ita ba. Mazan ajinsu uku ne suka taɓa zuwa gidansu Raihan, Kabiru ya kwatanta musu Waraka Islamic Chemist, lokacin da suka je duba Raihan Daddy da Mommy ba ƙaramin daɗi suka ji ba. Raihan na zaune ta dubi Mommy ta ce, "Ni kam na yi tsammanin ko kowa zai guje ni Intisar ba za ta guje ni ba, tun fa a Asibiti rabona da ita ko da muka dawo gida bata zo ba, babu waya ko text message yau fa sama da wata biyu da yin ciwona." Mommy ta dafa kafaɗarta ta ce, "Ki yi mata uzuri mana Raihan kin san ɗan adam jiki da jini kika san abin da ya hanata zuwa? Me ya sa baki kirata kin ji uzurinta ba? Ni fa ina ga haka kawai ba za ta ƙi zuwa dubiyarki ba kema kin sani." Cike da gamsuwa Raihan ta ce, "Haka ne Mommy amma duka layikanta a kashe idan na kira, kuma kin san tun kwanaki iyayenta suka koma Kaduna a hostel take da zama kin ga da sai na je gidansu na ji ko lafiya. Amma zan kira Farida hostel ɗin au ɗaya." Mommy ta jinjina kai ta ce, "Allah ya sa mu ji alheri." Raihan ta amsa da Amin. Raihan ta warware garau har Daddy ya yi yunƙurin mayar da ita makaranta suka nuna ya yi wuri a mayar da ita, saboda da yin ciwonta da komawarta makaranta ko wata shida ba a yi ba. Ganin za a bata lokaci ya sa Daddy ya yi mata transfer zuwa wata Al-muwadda Privite University, babu ɓangaran da ba sa koyarwa. A tashin farko suna bawa ɗalibi zaɓi idan kai tsaye zai rinƙa ɗaukan darasi ko kuma ta online, saboda larurar Raihan ya sa Daddy ya cike mata karatu ta online. Duk wani abu da ya dace daddy ya yi mata, kuma ta ci gaba da karatunta daga in da ta tsaya. Wannan lamarin ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba ita da Mommy su Inno kuwa sai mita suke, wai ita dai a boko za ta ƙare kullin tana abu ɗaya gara ta fitar da miji ta yi aure. A kullin bayan la'asar Khalid zai fito harabar gidan ya yi ta karatuttuka daga na Alƙur'ani har zuwa sauran littafan addini, ganin yana da ilimi mai zurfi ya sa Mommy ta yi masa magana akan zai riƙa ƙara wa Raihan karatu idan ya so sai a ƙara masa albashi. Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yi wa Kabiru ba kasancewar kuɗin da yake samu duk wata a wurin jinyar Mahaifinsa take ƙarewa, kuma a hakanma ba isar Mahaifiyarsa suke yi ba. Kuma ko da ganganci bai taɓa sanarwa da Daddy akan ya taimaka masa ba. Raihan sam bata da girman kai don haka duk yammaci take tafiya wurin Kabiru yana yi mata ƙarin karatu, don a lokacin ko izu talatin bata haɗa ba. Tun Kabiru yana ɗari-ɗari da Raihan ya fara sakin jikinsa da ita, don ta mayar da shi kamar kakanta kasancewarsa hausarsa ba ta daidaita ba yana magana za ka gane cikakken bafulatani ne. Da wannan take zolayarsa har take kiransa da suna Fillo, daga ƙarshe ma cewa ta yi bayan karatun addini har fillanci zai riƙa koyar da ita. Kwana Raihan biyu da fara ɗaukan Darasi suna zaune za su fara karatu sai ga Inno ta taho sanye da hijabi hannunta ɗauke da kur'ani. Raihan ta dube ta don ta fahimci sarai abin da Inno take nufi, tana shirin yi wa Inno magana ta ji Goggo ta ce. "La'ilah'illahu Muhammada Rasulillahi Sallallahu AlaihiWasallam. Yanzu haka za ki min saboda Allah daga na ce miki zan fara ɗaukan darasi wurin Kabiru sai ki rigani?" Inno ta ja farar kujera ta zauna ta ce, "Shi dai karatu ba a yi masa masifa, ki bi a sannu Zinaru wallahi kika sa masifa ƙwaƙwalwarki ta ƙi ɗauka. Ina dalili don za a biya min karatu ki hau kaina da faɗa, Izifina goma sha biyar ke kuma kin ce goma Allah na tuba ko sauka sai na kusa shekara da yi kafin ki sauke." Goggo na daga wurin da take ta sauri ta ce, "Tuf tuf tuf bakinki ya sari ƙaton kashi, wallahi ko a albasu na haure izifi ashirin, sauka kuma kamar na yi na gama." Raihan ta kalli Inno ta ɓata fuska tana cewa, "To wai Inno wa ya ce ku zo a biya muku karatun?" Inno ta dubi Kabiru ta nuna shi da yatsa, Kabiru ya zaro ido don shi bai san lokacin da aka yi haka ba da shi ba, yana tsaka da tunani ya ji Inno ta ce, "Yanzu Kabiru samun ladan tsofaffi har sai an ce maka ka yi?" Kabiru yana murmushi ya ce, "Shi kenan Inno amma ku bari na gama biya mata sai na dawo kanku." Da wannan shawara ya samu ya shawo kan su har ya fara biyawa Raihan karatu, Goggo na ƙarasowa a ƙufule ta ce, "Wallahi idan ban yi wa mutum adda'u ƙwaƙwalwarsa ta toshe ba." Inno ta watsa wa Goggo harara ta ce, "Mutum yana surutu ana karatu idan ya zama daddawa babu abin da zai hana ni kai shi kasuwa na sayar, na sayi lamurje na sha na fitsarar da abin banza." Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 25 Goggo na jin haka ta zabura za ta yi magana Kabiru ya katse karatun da yake yi ya ce, "Don Allah ku yi haƙuri Goggo idan ana karatun alƙur'ani ba a surutu saboda muhimmancinsa." Inno ta sa hannu a saitin bakinta ta ce, "In dai ni ce kabiru an bar maganar har abada." Murmushi ya yi mata ita ma Goggo ta ja bakinta ta yi shiru, sai da ya gama biya wa Raihan karatu sannan ya biya wa su Inno kowacce ya yi mata ƙari daga in da ta tsaya. Suna cikin karatu Daddy ya shigo abin ba ƙaramin birge shi ya yi ba, karo na farko kenan da ya ji Kabiru ya matuƙar birge shi. Sai da ya yi musu sannu da hutawa sannan ya wuce gida. Yana shiga Mommy ta tare rungumo shi tana faɗin, "Daddy barka da zuwa." Zagayo da ita jikinsa ya yi haɗe da ɗora kansa a jikin wuyansa ya ce, "Zainabuna bakya girma." Mommy ta juyo wa ta yi ta kashe masa ido ɗaya ta ce, "Addu'a nake Allah ya kawo wa Raihan mijin aure ta tafi gidanta ta ba ni wuri ta yadda zan ci duniyata da tsinke." Daddy ya yi dariya yana faɗin, "A gaban su Inno?" Mommy ta ɗaga masa kafaɗa cikin nuna rashin damuwa ta ce, "Su Inno tuni ai sun zama Kakannina don budurin da suke yi, yadda ka san a gidan Raihan haka suke yi." Daddy ya yi dariya har da ƙyaƙyatawa ya ce, "Ai ko baki faɗa ba na sani don diramar su Inno sai mai haƙuri ne zai iya jurawa." Ɓangaren Daddy suka wuce ta taimaka masa ya shiga wanka bayan ya fito suka ci abinci. Akwana a tashi babu wuya a wurin Allah haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa, wata rana Raihan ta fita shopping ɗin kayan shafe-shafenta da turarruka a WAHIDAH SHOPPING COMPLEX. Kayan shafa ta siyo har ta kusa zuwa wurin Accountant don ta biya kuɗi ta manta ba ta ɗebo da turarruka ba, da sauri ta juya don ta lura yamma ta ƙarato sosai ga shi Mommy ta ce karta sake ta kai magriba a waje, juyawar da za ta ci suka yi gware nan take kayan da ke hannuwanta suka tarwatse a wurin, wayarta ta faɗi daidai ƙafarsa. Kusan tare suka miƙa hannu don ɗaukar wayar da sauri ta ɗago tana kallonsa, karaf suka haɗa ido da shi. Wani shu'umtaccen ƙamshi ne ya doki hannunsa ga wani irin kwarjini da ya yi mata. A hankali ta janye idonta sakamakon kasa jure kallon da yake yi mata, cikin inda-inda ta furta. "Am...Kawo...Bari na kwashe." Ta ƙarasa maganar tana miƙa hannunta za ta ƙarɓi wayar, janye hannunsa ya yi yana ci gaba da kallonta cikin wata sasaanyar murya ya furta, "Ni ne mai laifi don haka a bar ni na goge laifina." Ajiyar zuciya ta sauke don muryarsa ba ƙaramin kuwwa ta yi mata a dodon kunnen ba, a hankali ta ja gefe ya tsugunna ya fara tattare kayan sannan ya ce, "Kin gama ne?" Girgiza masa kai ta yi cikin kasalalliyar murya ta ce, "Zan je wurin turare." Gaba ya yi yana riƙe da kayan ta ƙarasa ta fara ɗaukan irin waɗanda take amfani da su, sai da ta gama ta miƙa hannu za ta karɓa tana faɗin, "Na gama bari na wuce gida." Hannu ya sa ya sake ɗebo mata waɗanda ya fa ta ɗiba da farko, Raihan ta fara bin sa da ido kamar za ta yi masa magana sai kuma ta ja bakinta ta rufe don ta ga iya gudun ruwansa. Yana gama ɗiba ya wuce wurin biyan kuɗi kafin Raihan ta zo har ya ciro ATM ɗin sa ya bayar. A hankali Raihan ta kalle shi ta ce, "Ka bari da kuɗi a wurina." Yamutsa fuska ya yi yana girgiza kai ya ce, "Gaskiya na wurinki sun yi kaɗan, na san ko 50k ba su kai ba." Waro ido Raihan ta yi da mamaki ta ce, "Kai ta ya ka sani." Dariya ce ta suɓuce masa ganin lokaci ɗaya ya yi mata dabara. Raihan na ganin haka ta gane wautar da yi lokaci ɗaya ta tura baki gaba ta ce, "Ai ATM ɗin biyu na taho da su idan wannan bai kai ba sai na ciro ɗayan." Murmushi ya yi mata ya miƙa hannu ya karɓi reciept sannan suka fito ya raka har wurin mota, hannu ta miƙa masa za ta karɓi kayan ya girgiza mata kai yana cewa, "Ba zan baki ba sai kin biya tukwici." Cikin rashin fahimta Raihan ta ce, "Tukwici kuma? Dama ai ba ni nace ka biya ba, ba na ce zan biya ba ka ce za ka biya?" Gyaɗa mata kai ya yi sannan ya buɗe murfin motarta saka kayan a ciki ya ce, "Eh! Lambarki za ki bani." Kunyace ta kama Raihan don ita bata taɓa kawo abin da zai karɓa ba kenan." Tana cikin tunani ya miƙa mata waya a hankali Raihan ta karɓa ta saka masa lambarta, nan take ya yi kira lambarta. Daga nan suka yi sallama sannan Raihan ta shiga mota ta tafi, sai da ya ga tafiyarta sannan shi ma ya koma cikin Store ɗin don ya manta da tashi siyayyar. Raihan na zuwa gida ta zube a falo nan ta hau bawa Mommy labarin abin da ya faru tsakaninta da matashin saurayin, su Inno ban da murmushin farinciki babu abin da suke yi. Duk da bata ce musu saurayinta ba ne amma kana ganin yanayin yadfa Raihan take hirarsa za ka fahimci ya kwanta mata. Tana tsaka da basu labari sai ji ta yi wayarta ta yi ƙara, kallon Mommy ta yi ta ce, "Mommy wallahi shi ne ya kira." Ta ƙarasa maganar ta miƙewa za ta nufi ɗakinta, Mommy ta yi dariya tana cewa: "Don Allah Raihan ki san yadda za a ki yi masa magana kar ki je ki yi ta sakarci a waya." Kafin Raihan ta yi magana Inno ta ce, "Ummhumm yoo ban da abin Raihanu bata fara ba ni wayar, shi saurayin nata ya gaishe ni. Ni fa na haifi ubanta Zainabu ko bata gaya masa tana da kakanni ba?" Mommy ta gimtse dariya da ke cinta ta ce, "Inno ina zan sani yanzu fa ta gama ba mu labari a gabanku." Goggo ta taɓe baki tana faɗin, "Mutum dai ya gama zagaye-zagayensa mu muka haifi uwa da ubansa idan muka gama mu ce saurayin bai yi mana ba dole a fasa auren." Inno ta yi karaf ta karɓe zancen da cewar, "Wallahi faɗi da ƙarfi Zinaru, wai yarinyar nan rana ɗaya za ta watsa mana katsa a ido. Saboda Allah idan bata ba mu ya bai gaida mu ba ta ya zai ga darajarta ya san ƴar babban gida?" Goggo ta taɓe baki ta ce, "Ga ne min hanya dai." Raiha na jin su ta shige ɗaki sai da ta zauna ta ɗauka da sallam, amsa mata ya yi sannan ya ce: "Rowa kika yi min ni kuma na gagara haƙura." Kamar tana gabansa ta zaro ido ta ce, "Ni kuma?" Ya bata amsa da, "Eh baki gaya min sunanki ba." Raihan ta yi masa murmushi sannan ta gaya masa sunanta, ta riski muryarsa na cewa: "Sunana Salim Muktar." Bata san lokaci da ta furta, "Wow Nice name." Murmushi ya yi sannan ya ce, "Ya kai sunan saurayinki?" Raihan kanta tsaye ta ce, "Ni fa ba ni da saurayi." Daɗi ne ya ratsa zuciyar Salim don yadda yake ji akanta idan aka ce tana da saurayi bai san ya zai yi ba. Saboda lokaci ɗaya ya ji ta kwanta masa a rai, bai ɓata lokaci ba wurin zayyana wa Raihan abin da yake cikin ransa, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba sai dai lokaci ɗaya ta ji wata irin matsananciyar kunyarsa ta kama ta, bata iya bashi amsa ba sai katse wayar da ta yi. Duk kiran da Salim ya yi mata bata ɗauka ba sai text message da ta tura masa na amincewart, bakin Raihan ya ƙi rufuwa saboda farinciki. Haka kawai ta riski kanta cikin nishaɗi a ranar Daddy na dawowa sai da ta bashi labarin abin da ya faru, shi kansa ya ji daɗi sosai musamman da ya ga Raihan ta aminta da Salim. Kafin wani lokaci tuni shaƙuwa da soyayya ta shiga tsakanin Raihan da Salim, Ranar da ya ce zai zo hira farinciki fal zuciyar Raihan. Kabiru na zaune ya ga shiru Raihan bata fito karatu ba har ya gama biya wa su Inno karatu suka koma, sai da Raihan ta fito Kabiru ya ce, "Fillo yau ba ɗaukan darasi." Da yake shi ma Kabiru Fillo yake kiran Raihan kamar yadda take gaya masa. Takawa ta yi har gabansa tana murmushi sannan ta ce, "Fillo yau a haƙura da karatun nan amma don Allah kar ka gaya wa Daddy." Hararar wasa Kabiru ya ce, "Hai kin san ba a aikin banza yanzu, ki ba ni cin hanci sai na yi shiru amma idan ba haka ba Daddy na zuwa an yi an gama." Da sauri Rainan ya buɗe baki tana ɗan ɓata fuska ta ce, "Wallahi Fillo ka lalace da son kuɗi, yanzu dai nawa zan baka?" Kabiru ya yi jim sannan ya ce, "Sai kin faɗi uzurinki don kowanne uzuri da yawan kuɗinsa." Raihan ta riƙe ƙugu tana yi masa fari da ido ta ce, "Saurayina ne zai zo kuma yanzu haka girki nake yi, don Allah ka rufa min asiri Fillo mu kashe mu binne." Kabiru ya sa dariya don ya gano lagonta ya ɗauke kai gefw ya ce, "A yanzu ma va zan karɓi kuɗinki ba sai Saurayin ya zo na ga kamun ludayinsa idan bai min ba, sai na zuga Daddy son raina." Raihan ta watsa masa harara tana juyawa cikin gida ta ce, "Kanka ake ji wallahi Saurayina ya fi nesa ba kusa ba." Tana gama maganar ta shige cikin gida. Bayan sallar magriba Raihan ta gama shiryawa tsaf cikin doguwar rigar jar atamfa da mayafinta ja, ba ƙaramin kyau ta yi ba dukda ba wata kwallita ta yi ba. A ƙaramin falon su ta sauke shi sannan ta shiga kawo masa kayan ciye-ciye da shaye-shaye, Tun bai sha komai ba ya ce zai fara zuwa ya gaida su Mommy. A babban falo ya samu Mommy bayan ya same ta sun gaisa shi da Raihan suka koma ainihin falon da ta sauke shi, zuciyar Raihan fes da bata ci karo da su Inno ba don ta san da ta haɗu da su sai sun tsinkata a gaban Salima. Tana tsaka da tunani ta riski muryar Inno da Goggo sun tunkaro falon Inno ce a kan gaba tana faɗin, "Saboda Allah Zinaru ai kya bari na fara shiga tun da yarinyar nan dai ni ce na haifi Ubanta, duk yanda aka yi Raihan bata gaya wa yaron nan tana da kakanni ba da bai shigo ya ƙi zuwa gaida mu ba." A YI HKR DA ERRORS BAN YI EDITING BA. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 26 Goggo ta karɓe zancen da cewar, "Ni dai sai na ga kamun ludayin yaron nan tukunna, saboda Allah ya sani ba zan bari Raihanu ta auro ɗan da bai fito daga gidan tarbiyya ba." Inno na bankaɗa labule ta rafka sallama har tsakiyar kan Salim, Raihan na ganin haka ta ɓata rai don ta san abin da zai hana su Inno su tsinkata a gaban Salim sai Allah. Inno na haɗa ido da Salim ta washe baki tana faɗin, "Wannan ne saurayin namu ashe?" Salim na ganin su Inno ya sauko ƙasa cikin girmamawa ya ce, "Baba Ina wuni?" Goggo da Inno suka amsa cikin haɗin baki, "Lafiya ƙalau samari ya tsofaffin?" A kunyace Salim ya amsa, "Duk suna lafiya suna agaishe ku." Inno na jin haka ta sake washe baki haɗe da zama akan kujera ta ce, "Allah sarki ashe har sun san da zamanmu? Kai wannan abu ya yi daɗi to ni dai da ka ganni ni ce na haifi Uban Raihanu, wannan kuma ita ce ta haifi uwarta Zainabu. Ka gansa nan Audullahi shi kaɗai ya rage min kamar tsoka ɗaya a miya, ita kuwa Zinaru tana da wata ƴar bayan Zainabu." Inno ta yi maganar tana nuna Goggo da tun shigowarta take ta sakin murmushi, Salim shi ma murmushi ya yi. Goggo ta kalli Salim ta ce, "Ashe shi ya sa Raihanu ta kasa tsaya wa a biya mata ayar Allah tana ta zumuɗin ganinka." Kunyar duniya ta kama Raihan da ido take yi wa su Inno sigina amma ko kallon wurin da take basu yi ba, Salim daɗi ya kama shi ya riski Inno tana faɗin: "Salmanu kake da suna ko Ɗan nan?" Raihan ta tura baki gaba kamar za ta yi kuka ta ce, "Inno sunansa Salim fa." Inno ta dubi Salim har tana leƙa fuskarsa ta ce, "Salim tashi ka hau kujera nan fa gidanku ne, ai na ɗauka Salmanu sunanka in ce sunan wani ɓarawon kaji kenan a Madaka." A kunyace Salim ya tashi ya hau kujera Goggo ta miƙe tsaye ta ce, "Yaro bari mu wuce don yanzu sai mu yi laifi a wurin Raihanu bayan tafiyarka ta zo ta riƙa yi mana faɗa ta ce mun tsinkata a gabanka." Inno ma ta miƙe tsaye suka yi wa Salim sallama har sun je bakin ƙofa Goggo ta ciro ledar goronta ta juya wurin Salim ta ce, "Yaro na ce tsofaffin suna cin goro ne? Ungo ka tafi musu da shi." Salim ya yi dariya don tsofaffin ba ƙaramin birge shi suka yi ba, lokaci ɗaya suka tuno masa da tsohuwar kakarsa da ta rasu ba da jimawa ba, fara'a ɗauke a fuskarsa ya ce. "Wallahi ba sa ci amma ni ina ci Goggo." Goggo daɗi ya kamata ta miƙa masa ta ce, "Allah ya yi maka albarka, ai kuwa duk ranar da na je albasu sai na taho maka da shi." Raihan ta yi zuru tana kallon su Goggo don tun da take da su ba su taɓa yi mata abin da ya ƙona mata rai ba irin na wannan ranar. Suna fita Salim ya kalleta da murmushi ya ce, "Baby zama da tsofaffi da daɗi amma sai ka yi haƙuri." Raihan ta ɗauke kai gefe ta ce, "To amma kawai kana zuwa sai su shigo ai sa bari ka ɗan zo da yawa." Salima ya yi dariya yana gutsurar goro ya ce, "Yanzu kenan kunya kika ji." Raihan ta ɗan zaro ido ganin ya zage yana cin goro ta ce, "Wai da gaske kana ci dama?" Kafaɗa ya ɗaga mata ya ce, "Wallahi a gurin Jadda na koya kin san ni fa goyon kaka ne." Dariya Raihan ta yi ta ce, "Ashe kaima da wuri za ka tsufa." Salim ya kwaikwayi muryarta yana faɗin, "Daɗin abin ma tare za mu tsufa kin ga tsoho mijin tsohuwa kenan." Raihan ta yi dariya don barkwancin Salim ba ƙaramim birgeta yake ba, kayan snack ɗin gabansa ya ɗauka ya fara ci haɗe da lumshe ido ya ce, "Haka kika iya girki Dear?" Kunya ta kama Raihan ta rufe ido tana dariya. Salim ya kalle ta ya sake cewa, "Wai da gaske yau saboda ni kika ƙi zuwa Islamiyya." Raihan ta rufe ido ta yi murmushi tana faɗin, "Ba fa islamiyya ba ce, Fillo ne yake koyawa min karatu a gida ni kuma yau ina aiki na ce ya bari sai gobe." Salim ya yi murmushi sannan ya ce, "To ashe ni ma za ki fara yi min ƙari kenan." Raihan ta saka dariya. Sun jima suna hira sosai sannan Salim ya tashi ya yi wa Raihan sallama, sai da suka je harabar gidan ta gabatar masa da Kabiru har sai da suka gaisa. Salim na murmushi ya miƙa wa Kabiru hannu ya ce, "Malaminmu ina wuni?" Kabiru ya yi dariya ya ce, "Hai Samrayin Ɗaliba har ka fito." Kabiru ba karamin dariya ya basu ba, yana yi wa Kabiru sallama ta raka shi ƙofar gida a lokacin ya buɗe motarsa leda ce guda cike da alawoyi da chocolate ya miƙa mata. Da farko ƙin karɓa ta yi sai ta ga ya ɓata rai sannan ta karɓa ta yi masa godiya, tana shigowa ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Kabiru yana fito wa ta ɗaga ledar hannunta ta ce, "Ka ga irin abin kirkin da ake yi wa budurwa, ka koya don wataran idan za ka fara neman aure, na san ku fulani akwai maƙon tsiya." Kabiru ya girgiza kai ya ce, "Aradun Allah ina iya gaya wa Alhaji baki zauna karatu yau ba." Raihan ta taɓe baki ta ce, "Oho dai ko ka faɗa ai yanzo ya tafi." Ta ƙarasa maganar tana wuce wa cikin gida. Raihan na shiga sashensu su Inno suka fara washe baki, Raihan tana shirin yin magana Goggo ta ce: "Zainabu yaron nan na yaba da hankalinsa, ni sai yake min kama da wani yaro a albasu." Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Mommy wai yau kin ga irin abin da Tsofaffin nan suka min? Allah saura kaɗan na sa kuka saboda takaici." Mommy ta yi dariya saboda dama ta san za a rina tun lokacin da ta ji muryar su Inno a falon da ta kai Salim, cikin yanayin zolaya ta ce: "To meye don kakanni sun gaisa da saurayin jikarsu?" Raihan ta kwanta akan cinyar mommy tana faɗin, "Wallahi ni dai daga yau kar su ƙara zuwa idan ya dawo." Raihan na rufe baki Inno ta ɗago ledar ta ce, "Wallahi da ganin yaron nan zai iya riƙe gida, dubi ku ga abin kirkin da kawo mata." Nan su Inno suka fito da alawoyi suna dubawa. Zumbur Raihan ta miƙe ta kwashi wasu daga cikin alawar ta kaiwa Kabiru sannan ta dawo cikin gida. Soyayya sosai suke yi tsakanin Raihan da Salim babban abin da yake ƙara birgeta da Salim riƙo da addininsa don duk bayan sallar isha'i zai kirata a waya su yi bitar karatu. Kuma duk karatun da Kabiru ya biya mata sai ta sake biya wa Salim, wannan dalilin ya sa suka samu kyakkyawar fahimta a tsakaninsu. Hatta su Mommy sun yaba hankali da sanin yakamatan Salim saboda nutsuwarsa da girmama na gaba. Salim asalinsa ɗan garin Kano ne Mahaifinsa Alhaji Muniru babban likita ne a asibitin Malam Aminu kano. Mahaifiyarsa asalinta ƴar unguwar Gwale ce, suna zaune a unguwar Gyaɗi-gyaɗi. Salim shi ne babba a gidansu sai ƙannensa biyu duka mata Farida da Fatima, dukansu ƴan mata ne suna karatunsu a jami'ar Maitama Sule. Salim Yana da ilimin addini sosai da na boko, ya fi sha'awar kasuwanci don haka bayan ya gama karatu Mahaifinsa ya buɗe masa manyan shaguna a kasuwar kwari, shi yake safarar kaya daga ƙasashen waje yana kawowa cikin gida Nigeria. Yana da nutsuwa da tarbiyya sakamakon mahaifin bai da wasa a fannin addini, Salim ya taɓa budurwa ƴar aminiyar mahaifiyarsu, amma da ya fahimci ba me kamun kai ba ce tuni suka yi hannun riga. Magana Raihan da Salim ta yi ƙarfi har manya sun shiga tsakani, bayan dogon bincike da Daddy ya yi akan Salim da Iyayensa Mahaifan Salim suka kawo kuɗin na gani ina so. Aka tsayar da ranar aure shekara ɗaya bayan Raihan ta kamallah karatunta, farinciki ba ƙaramin kama su Daddy ya yi ba haka suka shiga shirye-shiryen bikin Raihan. Raihan ta mayar da hankalinta sosai wurin karatu da ginin tubalin soyayyarta. Mahaifiyar Salim da ƙannensa ba ƙaramin ƙaunarta suke yi ba, takanas Salim ya ɗebo ƙannensa watarana suka kawo wa Raihan ziyara. Lokacin da za su tafi haka Raihan ta haɗa masu sha tara ta arziƙi ta basu suka tafi, sun ji daɗin ganin yadda Raihan ta karɓe su hannu bibbiyu. Lokacin da za su tafi Fatima ta dubi Raihan ta ce, "Matar Yaya don Allah zan dawo a koyana min Meatpie ɗin nan." Raihan za ta yi magana Salim ya karɓe zancen da cewar, "Princess ɗina ba kukunku ba ce, idan snacks za ku koya ku je Catering school." Fatima ta ɓata fuska tana kallon Raihan ta ce, "Kin ji fa matar Yaya." Raihan ta yi murmushi sanna ta yi wa Fatima raɗa a kunne, lokaci ɗaya Fatima ta ƙwalla ƙara ta buga tsalle ta maƙale Raihan tana cewa, "Allah ya kaimu asha biki yasin gidanku zan dawo." Raihan ta yi dariya tana kallon Salima, Salim ya naɗe hannuwa a ƙirji ya ce, "Wato wariyar launin fata za a nuna min?" Yanda ya yi magana ba ƙaramin dariya ya basu ba, lokaci ɗaya suka saka dariya. Suna zuwa harabar gidan Kabiru ya fito ya ce, "Samrayin ɗaliba har ka hito?" Salim ya miƙa masa hannu suka gaisa ya ce, "Fillo mun fito za mu wuce sai jango." Farida ta zuba wa Kabiru ido lokaci ɗaya ta ji ya matuƙar birgeta, Kabiru na shiga ɗaki da sauri Farida ta matsa kusa da Raihan cikin raɗa ta ce, "Matar Yaya don Allah wannan waye? Ma sha Allah he looks so..." Raihan ta zaro ido waje ta ce, "So..." Fatima ta katse Raihan da cewar, "Bar ƴar rainin sence Farida fa bata da saiti." Dariya suka yi Raihan ta yi musu sallama amma har suka je gida Farida na tunanin Kabiru don ba ƙaramin burgeta ya yi ba. BAYAN WANI LOKACI. Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya abubuwa da dama suka shuɗe kwanaki na ƙarewa. A haka har lokacin bikin Salim da Raihan ya ƙarato, sai dai har lokacin idan Raihan ta tuna babu aminyarta Intisar za a yi aurenta tana jin babu daɗi a ranta. Daga ɓangaren su Mommy shirye-shirye sun yi nisa su Inno sai jiƙe-jiƙe suke yi wa Raihan a cewarsu sune ya kamata su yi Raihan gyaran da duk yakata a yi wa Amarya. Saura sati biyu biki aka kawo lefen aure daga gidansu Salim, lefe ne ɗan ubansu na kece raini dukda akwatuna shida Salim ya yi mata amma an zuba mata kaya masu tsada tare da ƙunshin kuɗi masu yawa. A ranar da aka kawo kayan lefen saboda farinciki Mommy kasa bacci ta yi, lokaci-lokaci take tuna wai Raihan ɗinta ce za ta yi aure. Ita kanta Raihan ba ƙaramin farinciki ta yi ba saboda murna har da ƙwallarta, daga ƙarshe ta tashi cikin dare ta yi sallar nafila tare da gode wa Allah bisa wannan ni'ima da ya yi mata. "Ya ke abar bauta wannan shirin da muka yi gani nake kamar ya yi yawa, kina ganin Raihan gadan-gadan aure ta yi yanzu haka za mu saka ido nasarorin ƙungiya suna dakushe wa." Hatsabibiya ta yi maganar hankali a matuƙar ɓace. Abar bauta ta saki wata shu'umar dariyar sannan ta ce, "Auren Raihan ba zai hana mu gudanar da abin da muka yi niyya ba, ba na ganin auren Raihan zai kawo mana cikas domin yin aurenta shi zai ba mu damar aiwatar da duk abin da muke so, saboda idan ta yi aure duk wanu zarge-zarge da ake yi mata na jinnu zai kau za mu biyar da ita yadda muke so." Hatsabibiya ta lalubo hannun Mijinta ta saƙale shi sai da suka je bakin wata baƙar rijiya sannan ta ce, "Tabbas abar bauta ke ya cancanci ki amsa sunan Hatsabibiya saboda kin wuce tunanin mai tunani. Wai Abar bauta Mugaza har yanzu babu amo baby labari ne?" Abar bauta ta wage ɗaya daga cikin bakunan jikinta ta hau ɓaɓɓaka dariya sannan ta ce, "Mugaza tana can tana jinyar Huzaifa saboda kaɗan ya rage bai mutu ba, kin ga ta yuwu lokaci da za mu mallaki gangar jiki da ruhin Raihan har lokacin Huzaifa bai maro daga jinyar da yake ciki ba." Hatsabibiya ta sake bushewa da dariya sannan ta suka faɗa cikin taohuwar rijayar nan take ta shafe daga kamar ba a taɓa ƙirƙirar rami a wurin ba. Wata ƙawar Mommy Hajiya Safiya ita take zuwa har gida tana yi wa Raihan gyaran jiki, sana'arta ce har wasu garuruwan take zuwa gyaran amare. Hajiya Safiya gyara take yi wa Raihan ciki da waje don har magungunan gyaren jiki take haɗawa, Daddy ban da shige da ficen shirin biki babu abin da yake yi. Bikin Raihan saura sati guda tuni Daddy ya gama tanadar komai na hidimar biki, an sanarwa da ƴan uwa da abokan arziƙi tuni shirye-shirye ya yi nisa daga gidansu Raihan zuwa gidansu Salim lokacin biki kawai suk jira. Ƙawayen Raihan ba ƙaramin mamakin jin bikin Raihan suka yi ba, haka suka yi ta tsegungumi kowa yana son sanin waye mijin da ya yi shahada zai auri Raihan, saboda Daddy bai ɓoyewa Salim da iyayensa komai ba game da ciwon Raihan, duk da ƙawayenta sun san warkewarta amma mafi yawan ƙawayenta ba su yarda ba. MUN KUSA SHAN AMARCI🤸🏻‍♀️ ALLAH YA SA DAI KAR SALIM YA HAƊU DA AMAYAR KAZA😂 Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn ta wannan number 0706 206 2624 27 Raihan ba ƙaramin kyau ta yi ba fatar jikinta ban da sheƙi babu abin da take yi, ta yi wani irin fresh kallo ɗaya za ka yi mata ka ji kamar ka sace ta. Tun ranar Laraba aka fara bikin Raihan, a ranar ne ta yi bridal shower da ita da wasu tsirarin ƙawayenta. Doguwar riga baƙa ta saka mai ratsin fararen duwatsu, kasancewarta mai hasken fata ba ƙaramin kyau kayan suka yi mata ba. Ƙawayenta su Shida suka yi ankon Ash ɗin material, a cikin gidansu Raihan aka yi komai. Suka kira masu decorations suka tsara musu komai gwanin birgewa. Ranar alhamis aka yi kamun amarya da ango, a ranar Raihan ta saka blue ɗin atamfa shi kuma Salim ya saka blue ɗin shadda. Ba ƙaramin burge mutane suka yi ba, kasancewar Salim mai matuƙar barkwanci ya sa ban da fara'a babu abin da yake yi. Abokansa ba ƙaramin ƙoƙari suka yi ba don sun yi masa kara matuƙa, da su aka yi komai aka watse daga taro. Ranar juma'a aka ɗaura aure da kimanin ƙarfe biyu na rana lokacin an sauko daga sallar juma'a, an ɗaura auren Salim da Raihan a masallacin Marigayi Sheik Jafar da ke unguwar ɗorayi. Ƙarfe goman dare aka fara dinner su Raihan a Lailan Event center, wani rantsattsen leshi Raihan ta saka wanda Daddy ya siyo mata daga Dubai. Su Inno an kame a kan kujeru sai kallon mutane suke ɗaiɗai bakin nan ya ƙi rufuwa. A yadda aka tsara Dinner babu mutane da yawa amma su Inno suka kafe kai da fata akan duk mutanen da suka zo daga Albasu da waɗanda suka zo daga Daura sai an shiga da su. Sai da Mommy ta yi musu dabara sannan ta samu suka bar maganar. Farar Shadda Salim ya sa daga shi har Raihan sai dai mutum ya ce sam barka, sai mai hassada shi zai kushe irin kwalliyar da suka yi. Anci an sha taro ba ƙaramin kyau ya yi ba mommy sai hada-hada take yi da mutane, ita kanta ba ƙaramin kyau ta yi ba. Kimanin ƙarfe sha biyun dare aka tashi daga dinner, Salim da Raihan a motar abokinsa Muhsin suka zo. Da za su koma gida ma motarsa suka shiga, Salim riƙo hannun Raihan ya yi lokaci ɗaya gabanta ya faɗi sakamakon haka bata taɓa kasancewa tsakaninta da shi ba. Ɗagowa ta yi suna haɗa ido ta sunkuyar da kai ƙasa saboda wata irin kunyarsa da ta ji. Janyota ya yi jikinsa a lokacin Muhsin ya buɗe ƙofar zai shiga, yana ganin haka ya koma da baya. Raihan ta zaro ido waje ta ce, "Habibi Muhsin fa ya ganmu." Salim ya sumbaci gefen wuyanta cikin kasalalliyar murya ya ce, "Shi ma yana komawa gida wurin matarsa za shi, laifi ne don na zo wurin tawa matar?" Kunya ta kama Raihan ta yi shiru tana murza ƴan yatsunta, Salim ya sake kwantar da murya ya ce, "Ni dai gaskiya ki cewa su Daddy a kai ki yau Allah gobe fa ta yi nisa." Raihan ta buɗe baki tana zaro ido ta ce, "A'a wallahi rufa min asiri inmutu maza su kaini." Muhsin ne ya kira shi a waya yana ɗauka Salim ya fita daga motar zai yi magana Muhsin ya ce, "Kai fa ɗan iska ne ai ka bari idan Allah ya kaimu gobe ka fara ɗana amarcin." Salim ya yi dariya ce, "Ɗan sa ido me ye naka a ciki." Dariya suka yi gabaɗaya sannan suka shiga motar suka wuce gida. Washegari. Bayan sallar Magriba aka shirya Raihan cikin wata tsadaddiyar alkyabba, ba ƙaramin kyau ta yi ba sai dai tun da gari ya waye ban da kuka babu abin da Rainan take yi. Lokacin da za a tafi kaita su Inno ne suka yi mata nasiha sosai da sauran tsofaffin da suke wurin, ana cewa Raihan ta fito ta rungume Mommy ta sa kuka. Ita kanta Mommy tun tana dakewa har ta gagara ta fashe da kuka, da ƙyar aka cireta daga jikin Mommy kai tsaye ta falon Daddy aka wuce da ita tana ganin Daddy ta rungume shi ta fashe da wani irin kuka. Murmushi Daddy ya yi don jin kukanta yake har cikin ransa. Nasiha ya yi mata mai ratsa jiki daga nan aka wuce da ita ɗaya daga cikin motar da Salim ya aiko don ɗaukan amarya. Tsayawa tsara gidan Raihan ɓata lokaci ne saboda Daddy ba ƙaramin kuɗi ya kashe mata ba, kai tsaye gidansu Salim aka fara kai Raihan Mahaifiyarsa ta yi mata nasiha sannan ta ɗauko turarrika da kuɗi ta bawa Hafsa ƙanwar mommy da take riƙe da ita daga nan suka wuce da ita katafaran gidanta da ke Tudun yola. Katafaran gida ne mai ɗauke da ɗakuna kala-kala an ƙayace shi da kayan alatu na more rayuwa, ƴan uwa da abokan arziki ban da santin gidan babu abin da suke yi, lokacin da su Inno suka shiga gidan sakin baki da hanci suka yi ban da kalle-kalle babu abin da suke yi. Suna shiga kitchen Goggo ta dubi Inno hannu riƙe a haɓa ta ce, "Ni kam Audullahi ya san zafin dukiya kuwa?" Inno ta wara hannuwa ta ce, "Taya ni duba wa Zinaru wai nan fa madafa ce. Ki duba ki ga yadda wasu gilasai suke sheƙi sai kace shagon ɗan kasuwa." Inno na ƙarasa maganar ta miƙa hannu kan wasu fulasai tana shafawa, gabaɗaya ɗakunan babu inda ba su shiga ba. Da sun keɓe za su fara mitar Daddy ya narkar da dukiya, don gidan Raihan sai mahassadi shi zai kushe shi. Kafin wani lokaci tuni kowa ya watse an bar Raihan daga ita sai su Safna ƴaƴan Mama Hafsa ƙanwar Mommy. Raihan na zaune Salim ya kirata a waya, a hankali ta zame mayafinta ta ɗauke muryarta har ta dashe saboda kuka. Haka kawai ta ji gabanta ya faɗi har sai da ta sauke ajiyar zuciya, tattaro jarumta ta yi a hankali ta furta, "Hello!" Daga can ɓangaren Salim ya amsa mata cikin fara'a tare da faɗin, "Habibity ina ta tunaninki." Murmushi Raihan ta yi ta ce, "Amma zan yi missing ɗin su mommy da rigimammun tsofaffin nan." Salim ya kwaikwayi muryarta yana faɗin, "Ni ma missing ɗin ki nake tun ɗazu da safe, kuma ni hanyar nisa take min na ƙagu na ƙaraso wurin Cutie." Kunya ce ta kama Raihan har sai da ta saci kallon su Safna ta ga suna ta danne-dannen waya ta bashi amsa, "I really miss you My Zauji." Dariya sosai Salim yake don shi mutum ne mai barkwanci da fara'a, Raihan ta yi murmushi tana shirin magana ya ce, "Kin san me nake tunani?" Raihan ta ce, "A'a sai ka faɗa." Salim ya yi jim sannan ya ce, "Gaskiya na musamman ne idan na ƙaraso sai na fi jin daɗin sanar miki." Raihan gabanta ya sake faɗuwa don haka kawai take jin faɗuwar gaba tun da aka taho da ita hanyar gidanta. Ta yi ƙarfin halin cewar, "Allah ya kawo min kai lafiya." Salim ya yi ƙasa da murya kamar mai raɗa sannan ya ce, "I so much love you Cutie." Raihan ta yi ƙasa da murya don kar su Safna su ji ta ce, "I Love you too Zauji." Daga haka suka yi sallama sannan suka ci gaba da hira. Kimanin ƙarfe goma na dare Safna ta kalli Raihan ta ce, "Raihan ni fa na gaji wallahi bacci nake ji, ki kira mijinki su yi su ƙaraso don kar bacci ya ɗauke ni." Raihan ita kanta ta ji shirun ya yi yawa sai dai tana kunyar kar ta kira shi ta ce shiru bai ƙaraso ba, tana cikin nazari suka ji ƙarar tsayawar mota a ƙofar gidan. Tsayuwar motar ya yi daidai da faɗuwar gaban Raihan, ta dubi Safna ta ce: "To ga shi nan ma sun zo da har kina niyyar yi min tijara." Safna ta miƙe tsaye tana gyara ɗankwalinta ta ce, "Babu wata tijara wannan Angon ai ya fiye jinkiri har kusan goma bai ƙaraso ba." Tana rufe baki suka fara jin bugun gida, Safna ce ta fita ta buɗe ƙofar. Da mamaki take bin ta da kallo tare da faɗin, "Mami lafiya ke ce da daren nan?" Mama Hafsa bata kula Safna ba ta ƙarasa ɗakin wurin Raihan a daidai lokacin saƙo ya faɗo wayarta, da sauri ta duba don a tunaninta Salim ne sai dai baƙuwar lamba ta gani, tana shiga saƙon ta riske shi kamar haka: " _Amarya! Amarya!! Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida, ina taya ki murnar amarcewa tare da yi miki jimamin babban rashin da kika yi. Daga mai ƙaunarki ba dare ba rana_." Tun bata ƙarasa karantawa ba jikinta ya fara rawa gabanta na ci gaba da tsananta faɗuwa, muryar Mama Hafsa ce ta risketa tana faɗin, "Raihan ta so mu wuce gida." Bugun zuciyarta ne ya tsananta ta riƙo hannun Mama Hafsat ta ce, "Mama Hafsa gida kuma? Me yake faruwa? Ina Salim yake?" Mama Hafsat ta fakaici idon Raihan ta ce, "Salim yana can gida wurin Daddy wani uzuri ya kawo shi ya sa Daddy zai haɗa ku ya yi muku magana." Raihan za ta yi magana ta ji wayarta ta fara ringing ganin wannan baƙuwar lambar ya sa ta saurin ɗauka jikinta na ci gaba da karkarwa. Murya na rawa ta furta, "Waye?" Tun bata rufe bakinta ba ta ji an ce, "Mijinki ne, ku hanzarta ɗauke wancen mushen da ke cikin mota shi da abokansa kafin su ƙone su zama toka, na faɗa musu ni kaɗai ne mijinki ni kaɗai zan mallake ki har abada. Duk wanda ya sake yin gangancin aurenki sai na yi masa abin da ya fi wannan muni." A haukace Raihan ta furta, "Waye kai? Ina Salim yake?" Ƙit ta ji an kashe wayar. A furgice ta dubi Mama Hafsa ta ce, "Wani abu ya faru da Salim wallahi ni na sani, tun ɗazu Salim ya ce min ya kusa ƙarasowa amma har yanzu shiru don Allah karki ɓoye min Mami me ya faru da Salim." Raihan ta ƙarasa maganar kuka na cin ƙarfinta. Mama Hafsa hawaye ne ya fara zuba a fuskarta ta dafa kafaɗar Raihan ta ce, "Mu je gida Raihan." Mama Hafsa na rufe baki Wani kiran ya sake shigowa wayar Raihan, number Farida ta gani. Jikinta har rawa yake ta ɗauka sai dai kukan da ta ji Farida na yi ne ya sake karya mata zuciya, tana shirin yin magana Farida ta ce. "Matar.Yaya yanzu shi kenan Yaya Salim ya rasu ɗazun nan fa muka rabu ina tsokarta wai shi ne ya..." Raihan bata ƙarasa jin abin da Farida take faɗa ba wayar ta zame daga hannunta luuuu ta faɗi sumammiya. Hankali a tashe Mama Hafsa ta kama Raihan, Safna na ganin haka ta ɗauko ruwa aka fara yayyafawa Raihan amma ko motsi bata yi ba. Hankali a tashe Mama Hafsa da yaranta suka kama Raihan suka fitar da ita kai tsaye suka saka ta a mota, ban da ruwan hawaye babu abin da Mama Hafsa take yi. Kulle gidan suka sannan suka wuce gidan su Mommy hankali a tashe, saboda irin gudun da take sharawa ya sa ba su jima ba suka ƙarasa gidan. Tun kafin su ƙarasa hankalin Mommy a tashe yake don babban tashin hankalinta bata san halin da Raihan za ta shiga ba matuƙar ta ji rasuwar Salim, Daddy ban da zarya a falo babu abin da yake yi gabaɗaya mutane kowa ya yi carko-carko. Inno na daga kan kujera ban da sharɓar hawaye babu abin da take yi, Goggo ta dubi Inno ta ce, "Kaico mutuwa duniya zancen banza.Ɗazu yaron nan ya gama zolayata wai yanzu shi ne ya yi hatsari motarsu ta ƙone ƙurmus, Allah ka jiƙan Salmanu ka gafarta masa." Inno ta sharce hawaye da gefen zaninta ita ma ta ce, "Ki duba irin budurin da aka yi ni babban tunanina halin da Raihanu za ta shiga, Allah ya sani Salmanu yaron arziƙi ne halinsa na gari ya bishi." Suna cikin wannan halin Mama Hafsa ta shiga ta sanar musu halin da Raihan take ciki, da sauri Daddy ya fita hankali a matuƙar tashe. Ganin halin da Raihan take ciki ya sa Daddy bai yi wata-wata ba ya wuce da Raihan asibiti, da matsanancin gudu ya bar cikin unguwar wanda ya yi daidai da fitowar Mommy cikin kiɗima don ganin halin da Raihan take ciki. Zuciyarta ba ƙaramin karyewa ta yi ba nan take da fara hawaye sai ƙanwarta Hafsat ce ta kama ta suka wuce gida. Daddy na zuwa asibiti da sauri likitoci suka shiga bawa Raihan taimakon gaggawa, sun jima a kanta sannan suka samu numfashinta ya daidaita, suka yi mata allurar bacci don ta samu hutu. Daddy ban da zarya babu abin da yake yi hankalinsa gabaɗaya baya jikinsa, wayarsa ce ta fara ƙara don tun yana tuƙi wayar tashi take ringing bai samu sukunin ɗauka ba. Jiki a matuƙar sanyaye ya ɗauki wayar ya kara a kunne ba tare da ya furta komai ba, Mommy na jin an ɗauka ta fara magana cikin kuka. "Daddyn Raihan kuna wane asibitin don Allah me yake faruwa da ita? Ina Raihan..." Tattaro jarumta ya yi irin ta Namiji ya daidaita muryarsa tare da katse ta da cewar, "Zainab!" Ya kirata da wata irin murya, Mommy na jin haka kuka ya sake kwace mata jikinta har rawa yake ta ce, "Don Allah Daddyn Raihan..." Sake katse ta ya yi da cewar, "Zainab ki ba ni hankali ba na son shiririta." Shiru mommy ta yi hawaye na zarya a kan dakalin fuskarta. "Raihan ta samu bacci a halin yanzu, ba na son ki sawa kanki damuwa saboda duk abin da kika ga ya faru da bawa rubutacce ne a wurin Ubangiji. Idan Allah ya rubuta Raihan ɗin za mu rasa muna da ikon hanawa ne?" Daddy ya yi maganar zuciya a dake. Kamar Mommy tana gabansa ta girgiza masa kai sannan ta ɗora da cewa, "Ina fargabar halin da Raihan za ta shiga, ban san ya abin zai zo mata ba. Yanzu kuna wane asibitin zan ƙaraso." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke sannan ya ce, "Idan har kuka za ki zo kina yi tun wuri ki haƙura da zuwa, yaron nan Salim ya samu kyakkyawar shaida tun daga wurin mutanen gari. Shin ita Raihan ba musulma bace da ba za ta karɓi jarrabawar da Allah ya yi mata ba, idan kina faɗan irin haka ta yaya za ki bata ƙwarin gwiwa har ta cire komai a ranta?" Jiki a sanyaye Mommy ta ce, "Haka ne na fahimce ka, gaya min sunan asibitin yanzu na ƙaraso. Allah ya gafarta masa halinsa na gari ya bishi." Kwatanta mata asibitin ya yi sannan suka yi sallama. Mommy ita da Mama Hafsa ne suka tafi suna zuwa Daddy ya wuce gidansu Salim. Su Mommy suna zaune jigum-jigum Raihan ta buɗe idonta, kallonsu ta fara yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta runtse idonta ta sake buɗewa. Da sauri ta zabura za ta tashi zaune Mommy ta riƙe za ta yi magana Raihan ta riƙo hannunta tana hawaye ta ce, "Mommy da gaske Salim ya mutu, Mommy ɗazu fa muka yi waya yace zai gaya min wata magana don Allah ki gaya min gaskiya ko wasa ake yi min?" Mommy ta fakaici idon Raihan ta goge hawayen idonta ta ce, "Raihan!" Raihan ta sake fashewa da kuka ta ci gaba da cewa, "Mommy don Allah kar ki ce min Salim ya mutu!" Mommy ta sauke ajiyar ta ce, "Raihan muna da ikon dakatar da mutuwa ne? Ke fa musulma ce me ya sa ba za ki rungumi ƙaddararki hannu bibbiyu ba? Allah shi ya halicci Salim kuma ya karɓe shi babbar soyayyar da za ki nuna masa ki yi masa addu'a." Raihan ban da hawaye babu abin da yake zarya a fuskarta. Kamar wacce ake yi wa raɗa haka ta ji maganganunsa na dawo mata a lokacin da suke waya, a zabure ta miƙe tsaye jikinta har rawa yake ta ce, "Ina wayata don Allah ba ni wayata na kira lambarsa na ji." Mommy na ganin haka hawaye ya ci gaba da zubo mata don ta san duk abin da Raihan take yi tana yin sa ne cikin ruɗewa da tashin hankali. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn0706 206 2624 28 Lokacin da Daddu ya ƙarasa ƙofar gidansu Salim cike yake da mutane sun yi jigum-jugum, yana tsaye motar asibiti ta ƙaraso ƙofar gidan tana zabga jiniya. Mahaifin Salim ne ya fito daga motsarsa babu jimawa aka fara kiciniyar fito da gawar Salim daga Amblance, matsawa mutane suka fara yi don a bayar da hanya su shigar da gawar. Lokaci-lokaci Mahaifin Salim yake share ƙwallah da take zuba daga idonsa, ana shiga da gawar Salim Mahaifiyarsa da ƙannensa suka fashe da matsanancin kuka. Mahaifin Salim na ƙofar gida mutane suka fara yi masa gaisuwa, jiki asanyaye Daddy ya ƙarasa wurinsa ya ce, "Alhaji ya muka ji da haƙuri?" Mahaifin Salim ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, "Alhamdulillah da godiya duk abin da Allah ya yi mai kyau ne." Daddy ya jinjina kai ya ce, "Haka Allah ya jiƙansa halinsa na gari ya bishi." Mahaifin Salim ya ce, "Amin ya rabbi, amma ya ya matarsa ina fatan babu wani abu da yake same ta?" Daddy ya ɗan yi jim sannan ya ce, "Ka san sha'anin ƙuruciya yanzu haka dai tana asibiti ta farfaɗo amma jikinta da sauki." Mahaifin Salim ya furta, "Allah ya bata lafiya." Gabaɗay suka amsa da amin, sun ɗan jima suna tattauna yadda jana'izar Salim za ta kasance sannan suka yi sallam. Jikin Daddy duk ya yi sanyi ko da bai ga gawar Salim ba amma yadda ya ji ana maganar irin ƙonewar da suka yi abin ya ɗaga hankalinsa. A lokacin da Salim ya gama waya da Raihan kallon Nadabo abokinsa ya yi ya ce, "Mutumin ni fa na yi muku nisa sai kun biyo sawu." Nadabo da yake driving ya yi murmushi ya ce, "Allah na tuba da me kwaɗo ya fi gaya, amma duk cika bakinka ai yanzu dai ɗaya muke da kai tun da yanzu muke kan hanyar zuwa kaika. Ni Allah sa ya sa ma karka ba mu kunya duk kurin nan ka kasa cika aiki." Salim ya saka dariya yana saka wayarsa a aljihu ya ce, "Allah ya kiyaye kai fa shegen kaya ne, an gaya maka abin da zan je yi kenan." Nadabo ya yi masa hararar wasa ya ce, "Ɗan iska irinku ne idan kuka rufe ƙofa tun safe sai bayan isha'i." Lokaci ɗaya suka saka dariya don Salim mutum ne mai shiga rai, mu'amala ta rana ɗaya za ku yi ya shiga ranka. A daidai Zayyan suya spot suka yi parking, Salim da Nado suka fito kowanne sanye da babbar riga. Sauran motocin abokan Salim ne suka yi parking kasancewar suna bayan motar su Salim. Kaji huɗu Nadabo ya sa mai Naman ya saka a leda, mai naman da murmushi ya dubi Nadabo yana murmushi ya ce, "Abokina da alama kai ne angon don na lura ban da ƙyalli babu abin da goshinka yake yi." Nadabo ya sake buɗa babbar riga yana dariya ƙasa-ƙasa ya ce, "Ga angon nan amma yadda kasan ni aka ɗaurawa don ko sheƙin angoncin baya yi." Salim ya yi dariya ya dubi mai nama ya ce, "Wallahi za ka ja na bar maka kazarka don sai mu koma wani wurin haka kawai Allah ya ba ni girma ka sauke min." Mai naman ya yi dariya yana miƙa musu manyan ledoji, Nadabo ya karbi ledar yana taɓe baki ya ce, "To ya na iya dole na biya kuɗin kaza kuma na yi dakonta, idah da rai da lafiya nima baɗi war haka ja rako ni ɗakin matata." Nadabo ya yu maganar yana miƙawa mai nama kuɗinsa. Mota suka buɗe suka shiga juyawar da Nadabo ya yi zai sa ledar kazar a mazaunin baya ya ci karo da wani baƙin kare mai jan ido, ƙirjinsa ne ya buga ya runtse ido ya buɗe amma sai bai ga komai ba. Jiki a sanyaye ya waiga ya ce, "Salim don Allah baka ga komai a bayan motar ba." Salim ya waiga babu komai a wurin ya ce masa, "Kamar ya fa? Ba abin da na gani." Shiru Nadabo ya yi ya kunna motar suka fara tafiya. Ba su yi nisa ba sai jin wani irin haushin kare wanda ya ratsa har tsakiyar kansu, a firgice duk suka juya don ganin abin da yake faruwa. Kafin su kaiga ganin kammanin kare ya yi kukan kura ya faɗa kan Salim tare da kai bakinsa kan daidai maƙogaronsa, Nadabo ba ƙaramin razana ya yi ba nan take motarsu ta fara tangal-tangal akan titi ƙarshe ta faɗa cikin wata babbar kwalbati, motar abokansa da ke biye da su ita ma ta i bayansu sai ta ukun ce Allah ya kare. Nan take wuta ta tashi a wurin mutanen da ke bakin titin suka fara kawo ɗauki ta hanyar zuba ƙasa da ruwan kwata, amma wutar tamkar ƙwara mata fetur suke, sai da ta ci don kanta sannan ta lafa a daidai lokacin ƴan kwana-kwana suka ƙaraso wurin tare da motar asibiti. Sai da suka ƙarasa kashe wutar sannan aka ɗebi gawargwarin su Salim aka wuce asibiti da su. Kafaɗar Raihan mommy ta dafa ciki dakakkiyar murya ta furta, "Raihan!" Raihan bata amsa ba sai hawaye da yake zarya a fuskarta, ta kafe mommy ta ido amma ilahirin jikinta rawa yake. Zuciyar mommy babu daɗi amma duk da haka ta kauda kanta gefe ta ci gaba da cewa, "Ke muslma ce! Don haka ki rungumi abin da Allah ya jarabce ki da shi. Salim ya mutu kuma lokacinsa ne ya yi idan ke ni ko ke Ubangiji ya so ɗauke wa ye yake da ikon hanawa?" Raihan ta kasa furta komai ban da hawayen da ke zuba a fuskarta. Mama Hafsa ita kanta hawaye take don duk wanda ya ga halin da Raihan take ciki sai ya matuƙar tausaya mata. Mommy ta riƙo hannun Raihan ta ce, "Ta so mu je ki ɗauro alwala ki yi sallah raka'a biyu ki yi wa mijinki Addu'a." Raihan na miƙe wa daga kan gado ta faɗa jikin Mommy ta fashe da matsanancin kuka. Bayanta ta fara bubbugawa sai dai ta kasa bata haƙuri, a hankali ta ɗago Raihan daga jikinta ta raka ta banɗaki ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah raka'a biyu tana yi tana zubda ƙwallah. Lokacin da Daddy ya ƙarasa asibitin dare ya tsala sosai, don lokacin kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Yan zuwa asibitim ya samu su Mommy a zaune jigun-jigun, Raihan na zaune a kan dadduma ta kifa kanta da cikin ƙafafuwanta. Daddy na zuwa Raihan ta ɗago tana kallonsa sai kawai ta fashe da kuka ta ce, "Daddy kaima ka ji Salim ya mutu? Wallahi ɗazu muka gama waya da shi Daddy don Allah me ya sa..." Daddy ya ƙarasa gaban Raihan ya sa hannunsa ya rufe mata shi yana cewar, "Raihan ba na san ki riƙa surutu haka." Yana daga tsugunne ya kalli mommy ya ce, "Yi wa nurses ɗin nan magana su yi mata allura ko za ta samu relief." Mommy ta jingina kanta da bango ta ce, "Tun ɗazu suka zo wallahi fir taƙi yarda." Daddy ya jima yana yi wa Raihan nasiha ta yi shiru tana sauraronsa tana hawaye. A haka suka ƙarasa ganin daren ba tare da kowa ya iya runtsawa ba. Mahaifin Salim sai da ya tsawatar wa Mahaifiyar Salim da ƴan uwansa sannan suka yi shiru amma kana kallon Mahaifiyarsa za ka fahimci irin tashin hankalin da take ciki. A daren aka suturta Saim sai dai ko wanka ba a yi masa ba sakamakon mummunar ƙunan da jikinsa ya yi. Su Salim su Biyar ne suka rasu sai dai gabaɗaya a cikinsu da ƙyar mahaifansu suka gane su saboda sun ƙone ƙurmus sun yi baƙiƙƙirin musamman Salim da gawarsa ta fi ta kowa munana saboda irin kisan gillar da mummunan karen nan ya yi masa. Wannan mummunan labarin na rasuwar su Salim lokaci ɗaya ya yaɗa ko'ina musamman da ƴan jarida suka taimaka da masu manyan wayoyi suka riƙa watsa labarin, duk wanda aka cewa Ango ya rasu da abokan a hanyar zuwa raka ango gidansa ba ƙaramin jimantawa suke ba, musamman da hotunan bikin su Raihan ya ratsa kafofin sada zumunta sai kuma katsam aka samu wannan labarin. Mutane waɗanda suka sansu da waɗanda basu san su ba haka suka riƙa ɗora hotunan Salim da Raihan na ranar Dinner da Kamu suka saka alamar kuka tare da yi masa addu'ar Allah ya kyauta makwanci. Wani irin baƙin hayaƙi ne yake fitowa daga ko'ina na sassa jikinta, ya yin da bakinta yake fitar da harshen wuta ƙasanta na fesar da wani irin tafasasshen ruwan mai yauƙi. Ɗaukan bil'adam ta riƙa yi ɗaya bayan ɗaya tana wurgawa cikin bakinta dukda kasancewarsu halattatun ƴan ƙungiya, ganin haka ya sa suka fara nema ceton ransu suna tserewa da ƙafafuwansu. Ƙanananun aljanun da suke wurin a tunaninsu sun tsira sai dai ba su yi aune ba suka riski Abar bauta ta faɗa ɗaukan wasu daga cikinsu tana haɗiyewa. Lokaci ɗaya wurin ya kacame da iface-iface da kururuwa don abin da ba su taɓa gani ba ne, Hatsabibiya gefe ta zauna ta zurawa Abar bauta ido sai da ta gama duk abin da take yi sannan ta furta, "Ko ba komai kin rage mana ƴan ƙungiya sai dai hakan ba yana nuna ƙungiyarmu ta ci baya ba, amma kina ganin wannan ɓacin ran naki zai kai mu ga cin abin da muke buƙata? Aikin gama ya gama tun da Huzaifa ya riga da gama ɓata mana shiri tun da ya kashe mata miji, na ci burin ɗora duk wani shirinmu akan ta bayan aurenta domin shi zai kaimu ga cimma burinmu." Wani irin huci Abar bauta ta yi sannan ta ce, "Laifin Mugaza ne kuma dole za mu ɗauki mummunan mataki a kanta. Ita idanunmu ce kuma kunnuwanmu ce mun sakakankance akan za ta ba mu jawabin halin da ake ciki amma wannan karon tana neman ba mu kunya, na fara zargin tana sane da komai akan a duk hukuncin da Huzaifa ya ɗauka." Hatsabibiya na shirin yin magana suka ji an furta, "Babu sa hannu ko kaɗan akan abin da Huzaifa ya aikata hakazalika ni kaina yaudarata ya yi domin bai taɓa nuna min ya samu lafiya ba. Kullin cikin kwanciya yake amma jiya kawai na neme shi na rasa, ina ganin Huzaifa buɗe mana hanya ya yi don mu ƙara miƙe wa tsaye don mu san ta yadda za mu shawo kan matsalar. Huzaifa ya fargar da mu baccin da muka fara domin na lura da sabon shiri ya dawo na tabbata ko ni ce na kawo masa wargi akan Raihan zai iya kawar da ni." Mugaza ta yi dogon sharhin tana ƙarasawa cikin tsibirin. Asubar fari bayan sun idar da sallah Daddy yake sanarwa da Mommy cewar ƙarfi takwas na safe za a yi jana'izar Salim a ƙofar gidansu, hakan ne ya sa suka nemi sallama a lokacin don tun farkowar Raihan taƙi yarda su yi mata wata allurar baccin. Kai tsaye daga asibitin gida suka wuce suka kintsa sannan suka yi mota uku suka wuce gidansu Salim, tun da aka doshi hanyar gaban Raihah yake tsananta faɗuwa nan take jikinta ya fara karkarwa. Suna zuwa mommy ta riƙe hannunta suka shiga cikin gidan, su Farida na hango Raihan suka tafi da sauri suka rungume ta suna kuka. Da ido mutane suka riƙa bin su da kallo gwanin ban tausayi, sainda Mahaifiyar Salim ta ƙarasa ta riƙota tare da mommu suka wuce ɗakinta. Mahaifiyar Raihan sosai ta yi wa Rainan nasiha sannan ta ja zuwa ɗakin da aka shirya gawar Salim don ta yi masa addu'a kafin a tafi da shi. Tana tafe gabanta na faɗuwa haka suka ƙarasa ƙofar ɗakin, tana shiga ya same shi a kwance an gama haɗa shi. Jikin Raihan nan take ya fara karkarwa a hankali ta zube a wurin tana fara yi wa Salim addu'a, lokaci ɗaya kuka ya kwace mata ta jingina kanta a jikin Kan Salim ta ci gaba da rera kuka mai tsuma zuciya. A hankali Mommy ta riƙo hannunta tana shirin fito da ita sai gani ta yi numfashinta yana sama, kafin Mommy ta yi wani yunƙuri Raihan ta faɗi a wurin. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min magana 0706 206 2624 29 Hankali a tashe Mommy ta yi kanta da sauri Mahaifiyar Salim ta ɗauko ruwa aka fara yayyafa wa Raihan, a hankali take sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe idanunta tana kallon su Mommy. A daidai lokaci Mahaifinsu Salim da sauran ƴan uwansa suka shigo ɗakin suna faɗin, "Za mu ɗauke shi mu yi masa sallah mutane sun gama taruwa." Hawaye ne ya ciko idon Mahaifiyar Salim, Raihan na jin haka ta fara bin su da kallo a zuciyarta take ayyana shi kenan ita da Salim sun yi bankwana. Tana raɓe a gefe suka ɗauke shi suka fice da shi lokacin ƙafafuwanta suka fara karkarwa. Tsugunnawa ta yi a wurin don yadda take ji ƙafafuwanta ba za su iya ɗaukanta ba. Zoben hannunta ta zurawa ido tana tuna ranar Dinner su da Salim ya saka mata shi a hannu, murza ɗan yatsanta ta fara yi a hankali kamar almara sai jin irin muryar Salim ta yi an ce, "Ki ba ni zobena na tafi da shi." Zaburar da ta yi ne ya fargar da Mommy da sauri ta riƙe ta tana faɗin, "Ke Raihan ina za ki?" Raihan ta nuna bakin ƙofar fita ta ce, "Wallahi Salim magana yake min, don Allah ku duba bai mutu ba." Ganin yadda Raihan ta firgice musu lokaci ɗaya ya sa Mahaifiyar Salim ta dubi Mommy ta ce, "Hajiya mai zai hana ku wuce da Raihan gida ina ganin kamar zai fi." Mommy ta yi jim sannan ta ce, "Shi kenan Hajiya Allah ya gafarta masa, za mu wuce insha Allah zuwa anjima zan dawo." Maman Salim ta yi murmushin ƙarfin hali ta furta, "Karki damu Hajiya ki kula da ita don tana cikin wani irin hali ko baki dawo ba anjima babu komai, Salim addu'a kawai yake buƙata amma yana da kyau ita ma a ji da ita." Daga haka Mommy ta riƙe hannun Raihan gam suka fito duk in da suka gifta mutane kallonsu ake yi. Lokacin da su Mommy suka fito a lokacin aka gama sallarta Salim har an saka gawarsa a mota za a wuce da shi, wasu daga cikin masu rakiyarsa na cikin mota wasu na kan mashina wasu ma da ƙafa suke takawa. Ganin haka ya sa Mommy ta ja hannun Raihan suka koma da baya, sai da suka jima a tsaye mommy ta fahimci masu rakiyar gawar sun yi nisa sannan suka fito suka shiga mota suka wuce gida. Suna zuwa gida Raihan ta wuce ɗakinta ta turo ƙofa, kan gado ta faɗa lokaci ɗaya ta saki wani irin marayan kuka. Sai da ta yi mai isarta ta tashi zaune ta takure wuri ta fara ayyana irin rayuwar da suka yi da Salim, ta jima ita kaɗai a zaune gabaɗaya rayuwarta ta yi mata zafi. Lokaci-lokaci take share hawayenta tana yi wa Salim addu'a. Tana nan zaune ƴan jarida suka yi wa gidan Iyayenta ƙawanya, duk yadda mommy ta so hana su naɗar rahoton Raihan abin ya ci tura sai da suka yi mata hikima har ta amince musu. A falo Raihan ta same su a zaune suna ganinta kowanne ya fara gyara abin naɗe sautinsa tare da faɗin, "Sannu Hajiya ya ƙarin haƙuri." Da ido Raihan ta bisu hawaye na zuba, nan take suka fara jero mata tambayoyin abin da yake tafe da su. Sai da ta share hawayen idonta sannan ta ce, "Tabbas na yi babban rashi saboda Salim yana ɗaya daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawa da shi ba, na yi rashin masoyi na rasa Salim a lokacin da nake tsananin ƙaunarsa. Ni na san irin abin da nake ji a zuciya har yanzu gani nake kamar tatsuniya ake gaya min akan mutuwar Salim, kunnuwa na jiyo min sautinsa amma mutane gaya min suke Salim ya mutu, gabaɗaya na rasa wanda zai ce min Salim yana raye ko na ji daɗi har kuma kuna ganin Salim ya rasu ko..." Raihan bata ƙarasa magana ba kuka ya ci ƙarfinta da sauri ta faɗa ɗakinta. Kalaman Raihan ba ƙaramin sanyaya musu jiki ya yi ba, daga haka suka yi wa su Mommy gaisuwa sannan suka kama gabansu. Haka taron gidajen bikin ya koma gidajan zaman makoki. Kullin sai Mommy da ƴan uwanta sun je gidan su Salim dukda bata jimawa saboda ba ta son barin Raihan ita kaɗai a gida. Sannu a hankali kwanaki suka riƙa shuɗewa har aka yi sadakar bakwai ɗin Salim, Sai dai har a lokacin Raihan bata daina zubar hawaye akan mutuwar Salim ba. Ta rame sosai idan ka ganta sai ka rantse kwanciya ta yi matsananciyar jinya, hatta abinci sai da Mommy ta yi mata da gaske sannan Raihan take ɗaukan ruwan tea ta sha. Bata da aiki sai zaman ɗaki don kodayaushe tana ɗaki a kwance, sai dai idan mommy ta ji shirun ya yi yawa sai ta shiga ɗakin ta riƙa janta da hira don kore mata damuwa. Kamar kullin tana zaune a ɗaki ta idar da sallar Azahar tana zaune tana jan lazumi wayarta ta fara ringing. Kallon lambar take don bata san da ita ba, amma sai ta yi tunanin ko masu yi mata gaisuwa ne. Murya ba kuzari ta furta, "Salamu alaikum." Sautin muryar da ta ji an amsa mata ne ya sa ta sakin carbin hannunta, zumbur ta miƙe tsaye baki na rawa ta ce, "Don Allah kaine? Salim muryarka nake ji." Daga can ɓangare aka yi dariya kamar yadda salim yake ma'abocin fara'a sannan ya ce, "Kina mamaki ne Cutie ni ne man ko baki yarda ba." Jiki na rawa ta ciro wayar daga jikin kunnenta tana kallon lambar sannan ta fita da gudu tana ƙwala wa Mommy kira. A lokacin Mommy na kan dianning tana cin abinci jin kiran Raihan ya sa ta miƙe wa tana faɗin, "Lafiya Raihan?" Da sauri Raihan ta miƙa wa Mommy wayar ta ce, "Salim ne ya kira ni wallahi Mommy muryarsa na ji." Rass gaban Mommy ya faɗi, don ta san duk wanda ya mutu ya mutu har abada ba zai sake dawo wa ba, ganin har lokacin wayar na harbawa ba a katse ba ya sa mommy ta karɓi wayar jiki a sanyaye ta kanga a kunnenta. Kai wayar kunnenta ya yi daidai da ta ji muryarsa ta ce, "Cutie ba na jin ki sosai bari na sake kira." Gabanta ne ya sake tsinkewa ya faɗi sakamakon jin muryar Salim raɗau a dodon kunnenta, hannun Raihan har rawa yake ta fisgi wayar a hannun Mommy ta sake kira ta kara a kunne amma fir wayar ta ƙi shiga. Da sauri ta kalli mommy ta ce, "Don Allah mommy muryar wa kika ji idan ba Salim?" Hawaye ne ya fara zubo mata ta ci gaba da cewa, "Wallahi dama na faɗa muku Salim bai mutu ba Allah muryarsa ce." Lokaci ɗaya Raihan ta rikice wa Mommy ban da kuka babu abin da take yi, Mommy daskare wa ta yi a wurin saboda ita kanta abin ya girmewa tunaninta. A jiyar zuciya ta sauke ta ja hannun Raihan zuwa Falo ta zaunar da ita, sai ta da kalli Raihan sannan ta ce: "Raihan ki kwantar da hankalinki. Na fahimce ki amma ki bari Daddynki ya dawo za mu yi magana da shi, tabbas ni ma muryar Salim na ji." Da sauri Raihan ta fara gyaɗa kai tana faɗin, "Mommy kin dai yadda da magana ta ko?" Mommy ta bi Raihan da kallon tausayi don ta kwantar da hankalinta ya sa Mommy ta gyaɗa mata kai haɗe da cewar, "Na yadda Raihan shi ya sa na ce ki kwantar da hankalinki." Inno da take gefe ta kalli Mommy ta riƙe haɓa ta ce, "Alkazzibu ƙarya dai haramun ne." Lokaci ɗaya Mommy da Raihan suka waigo wurin Inno, Inno ko a jikinta ta watsa musu harara ta ce, "Gaskiya Zainabu kin ba ni kunya. Yanzu saboda Allah ki zauna ki jirkice wa yarinya ƙarya, ta ina matacce yake iya dawowa? Ni kam ko lokacin da Alhaji Babba ya rasu na kusa shekara kullin sai na yi mafarkinsa amma ko kaɗan ban taɓa tunanin zai dawo ba." Raihan wani ƙululun baƙin ciki ya kamata ta dubi Inno a ƙufule ta ce, "Don Allah Inno ki fita a harkata, yanzu dai ban sa da ke ba." Inno ta wara hannuwa sannan ta ce, "Ko ki sa da ni ko karki sa da ni ke kika sani, amma ni da kika ganni babu abin da zai hana ni nema miki magani don na lura mutuwar yaron nan so take ta zautar da ke. Saboda Allah mutuwar miji bata da daɗi amma keda ma baku shaƙu ba, ko zaman dare fa baku yi ba ni da nake miki fatan nan da wasu ƴan watanni Allah ya kawo miki wani mijin ki yi aurenki." Raihan na jin haka ta fashe da kuka cikin ɓacin rai ta ce, "Wallahi ba zan sake aure ba kuma wallahi kika kawo min wani maganin sai na matse ki kin shanye shi tass." Mommy ta rufe mata baki cikin raɗa ta ce, "Don Allah ki daina biye maganganun tsofaffin nan kamar ba ki san halinsu ba?" Raihan ta share hawayenta tana shirin yin magana suka riski muryar Goggo tana faɗin, "A yau ba sai gobe ba dama na yi niyyar zuwa Albasu don na karɓo wa Yarinyar nan taimako, tsorona Allah tsorona kar yarinyar nan ta fara gane-gane na shiga uku." Shiru ne ya biyo baya mommy ta faɗa nazari don ita kanta ta fara zargin akwai lauje cikin naɗi, don babu tantama mutuwar Salim na son jefa Raihan cikin wani yanayi. Miƙe wa ta yi ita da Raihan suka wuce suka bar su Inno suna ta zancen su akan nema wa Raihan magani. Da daddare bayan Daddy ya dawo yana tsaka da cin abinci ya dubi Mommy ya ce, "Mommyn Raihan na fahimci akwai abin da yake damunki tunanin me kike yi haka?" Mommy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Daddyn Raihan ka gama cin abinci magana nake son mu yi." Ajiye spoon ɗin hannunsa ya yi ya zuba mata ido a nan ya sake karantar irin damuwar da take ciki, ganin irin kallon da yake yi mata ya sa ta saki murmushin yaƙe don ta san matuƙar ta sanar da shi abin da yake faruwa ya bar cin abincin kenan. Tana tsaka da tunani ta riski muryarsa na cewa, "Me yake faruwa Zainab?" Murmushi ta sake yi a karo na biyu ta ce, "Alƙwari na ɗauka sai ka kammala komai zan sanar da kai, kuma karka ɗaga hankalinka don ba wani abin damuwa ba ne." Daddy har lokacin kallon Mommy yake don kar ya yi mata musu sai kawai ya ci gaba da cin abincin ba don yana jin daɗinsa ba saboda yanayin da ya gani a tattare da ita. Bayan ya kammala cin abinci Mommy ta dube shi ta ce, "Daddyn Raihan! Don Allah Salim yana da ɗan uwa ne?" Da mamaki Daddy ya dube ta ya ce, "Kamar yaya ɗan uwa?" Mommy ta gyaɗa masa kai tana kallonsa. Girgiza mata kai ya yi sannan ya ce, "A iya sanina Salim shi kaɗai ne namiji a wurin Mahaifinsa amma me ya sa kika yi wannan tambayar." Wayar Raihan da ke gefe ta ɗauko ta fara dubo lamabar da aka kira Raihan da ita ta miƙa masa ta ɗora da cewa, "Ɗazu wani ya kira Raihan a wayarta mai irin muryar Salim kai hatta irin kalaman da Salim yake mata sai da ya furta." Murmushi Daddy ya yi ya ajiye wayar Raihan ba tare da ya kalli lambar ya ce, "Haba Zainab na ɗauka ke za ki riƙa kwantar wa yarinyar nan hankalinta amma sai kike ƙara ɓullo hanyar da za ki tayar mata da hankali." "Ba da wasa nake ba Daddyn Raihan saboda tun ina ƙarama na san mutuwa na san zafinta, duk wanda ya mutu ya tafi kenan har abada ba dawowa. Da kunne na ji abin da nake gaya maka ba Raihan ce ta sanar da ni ba, da ita ce kasan ba zan taɓa yadda ba." Da sauri Daddy ya ɗauki wayar Raihan ya ƙurawa lambar ido yana kallo, lokaci ɗaya ya danna kira amma fir taƙi shiga. Miƙe wa ya yi tsaye ya fara kaiwa da kawowa a dakin, Mommy ta ƙarasa wurinsa ta riƙo hannunsa sannan ta ce, "Ni ina ganin mai zai hana ka yi report wa ƴan sanda idan ya so sai su bibiyi layin don ganin wanda yake aikata haka." Lokaci ɗaya ya aminta da maganar Mommy har ya ciro waya zai kira D.P.O. abokinsa, sai kuma Malam Usman ya faɗo masa, don tun ranar da za a sallami Raihan ya ke sanar da su duk wani abu da za su gani na almara ko ɗaure kai su sanar da shi. Lambar Malam Usman ya kira ba a jima ba aka ɗauka, sai da Malam ya sake yi masa gaisuwar rashin Salim sannan Daddy ya zayyane masa duk abin da yake faruwa. Malam Usman jim ya yi sannan ya ce, "Tun bayan rasuwar yaron shin tana yin wasu abubuwa ko tana ganin wasu abubuwa na ban al'ajabi." Daddy ya yi shiru yana nazari sannan ya ce, "Eh to, tana yawan ce mana tana jin muryar Salim ya yi mata magana amma bayan haka babu wani abu da take gani ko ji sai yau da wannan kiran ya shigo cikin wayarta." Malam Usman ya ce, "Babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji, insha Allah akwai magungunan da zan sake haɗa mata, amma duk da haka sai ta sake dage wa da Addu'a kuma a daina barinta a cikin kaɗaici ko ta riƙa keɓewa wuri ɗaya. Idan da hali a riƙa yawan zama da ita kuma tana yawaita sauraron karatun alƙur'ani." Daddy da Malam Usman sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama akan zuwa wayewar gari Daddy zai je ya amsowa Raihan maganunguna. Sannu a hankali duk wasu abubuwa da Raihan take ji sai suka fara ja baya, Mommy na bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta kawar wa da Raihan damuwa. Inno da Goggo kowaccensu sai da ta karɓo wa Raihan turare da maganin sha da wanka. Sai da Mommy ta yi da gaske sannan Raihan ta karɓa don ba ƙaramin haushin su Inno take ji ba, musamman idan ta tuna zancen sake wani auren da suke yi mata. Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da gangarawa kwanaki suka riƙa wucewa watanni suka shuɗe, Raihan ta rage damuwar da take ciki sosai tana walwalarta kamar kowa sai dai lokaci-lokaci Salim yana faɗo mata a rai. A duk lokacin da ta tuna shi tana jin ba daɗi sai dai ta yi masa addu'a, amma har lokacin gani take babu wani namiji da zai iya maye gurbin Salim don haka ko maganar yin aure bata son ji. Zumunci mai ƙarfi ne ya sake shiga tsakanin gidansu Raihan da gidansu Salim, ƙannensa na matuƙar ganin girmanta suna ganin mutumcinta. Lokaci-lokaci sukan kai mata ziyara musamman Farida da ta ƙwallafa ranta a kan Kabiru mai gadi. Bayan shekara biyu. Abubuwa da dama sun faru ciki har da auren Fatima ƙanwar Salim, Raihan ta haɗa mata sha tara ta arziƙi don su Fatima ba su yarda ita ba. Ranar da suka je Dinner bikin su Fatima ita kaɗai ta riƙa kallonsu tana tuna lokacin ta su dinner, hawaye ta ji ya zubo mata a fakaici ta goge idonta jiki babu ƙwari ta miƙe ta je ta yi wa su Fatima liƙi sannan ta wuce gida. A ƴan kwanankin haka ta yi ta fama da tunanin Salim sai daga baya ta watsar da komai ta fauwala wa Allah lamuranta. Azumi saura sati ɗaya Daddy ya biya musu zuwa Dubai daga nan za su wuce umara ƙasa mai tsarki, don Raihan da kanta ta yi wa Daddy magana akan za ta fara sarin kaya daga Dubai zuwa Nigeria, bai hanata ba don ta nuna masa zamanta haka ba daɗi kuma aikin gwamnatin da ta ci buri a baya duk ya fice mata a ka. Tare da su Inno suka tafi gidan sai Kabiru kadai suka bari, kwanansu biyu a ƙasar Dubai da daddare Raihan da Mommy sun fita zuwa wani store don yin siyayyar abin da ba a rasa ba, kwatsam suna gabda fitowa kamar almara Raihan ta ganta hannunta ɗauke da wasu ƙananan yara biyu mace da namiji. Cikin tsananin mamaki ta furta, "Intisar!" Ke nake gani ko idona ne?" Intisar cike da mamaki ita ma ta dubi Raihan ta ce, "Raihan ke ce?" Rungume juna suka yi Mommy ta ja hannun yaran wanda da alama ƴan biyu ne mace ba za su wuce shekara ɗaya da rabi-rabi ba. Raihan ce ta fara ɗagowa ta dubi Intisar ta ce, "Yanzu Intisar kina duniyar kika guje ni an ya amintaka ta ce haka?" Intisar ta yi murmushi ta ce, "Raihan ba za ki gane ba, abubuwa da dama sun faru bayan rabuwarmu labari ba zai yuwu a nan ba sai mun zauna." Raihan ta juya wurin yaran Intisar ta rungumo su tana jin wata irin ƙaunarsu, ido ta ƙura musu tana son sanin inda ta san fuskarsu amma ta kasa. Ɗaukan macen ta yi ta ce, "Amma twins ne ko Intisar?" Intisar ta yi murmushi ta ce, "Su uku ne Salma na hannun Daddynta." Kafin Raihan ta yi magana wani sihirtacen ƙamshinsa ya doki hancinta, waigawa ta yi don ganin mai wannan ƙamshin da ko a mafarki ta ji shi ba za ta manta ba. Karaf idonta ya sauka akansa wanda ya yi daidai da faɗuwar gabanta har ya sa jikinta ya ɗauki tsuma kamar mazari. Bakinta na rawa ta furta, "Salim! Don Allah kai ne?" A lokacin Mommy ta kai idon wurin cikin tsananin mamaki take bin sa da kallo don ko makaho ya shafa zai tabbatar da wannan Salim ne ko tantama babu. Salma da ke hannunsa ya miƙawa Intisar ba tare da dubi wurin da Raihan take ba ya ce, "Cutie kin san Salma ta fi kowa rigima kika haɗa ni da ita." Intisar karɓar Salma ta yi tana murmushi ta ce, "Hubby ga aminiyata Raihan da nake gaya maka, yau Allah ya yi mun sake haɗuwa." Da murmushi ya dubi Raihan wacce ta kafe shi da ido ya ce, "Hey Aminiyarmu ina kika shiga kullin Cutie sai ta min hirarki." Hawaye ne ya fara zarya a fuskar Raihan ta furta, "Salim baka gane ni ba ne?" Da mamaki ya dube ta Intisar ma ta kalle ta sannan ta ce, "Salim kuma? Waye kuma Salim? Daddynsu Salma ne fa Raihan ko kin san shi ne." Kuka ne ya kwace wa Raihan ta ce, "Wallahi mijina, don Allah Salim ka gaya mata." Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 30 Mijin Intisar da ke tsaye cikin mamaki ya ce, "Mijinki kuma? Cutie kin ji me take faɗa kuwa?" Da sauri Mommy ta riƙo hannun Raihan ta ce, "Raihan ki nutsu me yake damunki kina hauka ne?" Raihan ta dubi Mommy ta ce, "Don Allah mommy kin gani ko maganaina ne suke yi mini gozo? Kina ganin abin da nake gani ke ma kin ga Salim ko?" Intisar fuska ɗauke da damuwa ta ce, "Mommy don Allah me yake faruwa waye kuma Salim." Ganin mutane sun fara kallonsu saboda hayaniyar da Raihan ta fara yi ya sa mommy ta ce, "Mu fita waje don kar idon mutane ya yi mana yawa." Ba musu Intisar ta riƙe hannun yaranta Maigidanta ya riƙo mata ɗaya Raihan kuma tana riƙe a hannun mommy. A wurin motarsu Intisar suka tsaya har lokacin Raihan bata daina kallon Mijin Intisar ba, Mommy ta ciro wayarta ta nunawa Intisar hotunan auren Raihan ta ce, "Salim da kika ji Raihan tana faɗa yana tsananin kama da mijinki amma suna da bambamci saboda Salim yana da siririn tsagu a goshinsa. Haka Allah yake lamarinsa ya yi mutane masu kamanni iri ɗaya kuma mazauna wuri mabambamta." Tun daga farko har ƙarshe sai da Mommy ta bawa Intisar labarin abin da ya faru a auren Raihan, Intisar na gama jin labarin ta fara ruwan hawaye. Intisar ta dubi Raihan fuska ɗauke da hawaye ta ce, "Bestie a ranar da abin nan ya faru da ke a ranar na samu waya daga gida cewar Mahaifina ba shi da lafiya. Ban yi ƙasa a gwiwa ba na wuce garinmu don yananyin ciwonsa ance yana jin jiki. A ranar sa na je a ranar Allah ya yi masa rasuwa nan muka shiga tashin hankali, Mahaifinmu shi ne komai namu kuma ya rasu dama duk abin da yake yi mana ƙarfin hali ne. A kan dole muka shiga gwagwarmayar rayuwa don dangin mahaifinmu ba sa taimaka mana da komai. Kwatsam bayan wasu watanni aka yi wa Mahaifiyata shawarar tafiya saudiya yin aikatau, don haka muka shirya mahaifiyarmu ta sayar da duk wani abu da ta mallaka muka tafi ni da ita. Zuwanmu ƙasar babu wuya sai Allah ya haɗa ni sa Salman, shi ma asalinsa ɗan Najeriya ne amma shi da iyayensa duk mazauna saudiya ne. A ganina ya yi min nisa saboda shi ɗan masu kuɗi ne amma ya nuna ni yake so don haka zai iya rayuwa da ni, yanzu haka shekararmu biyu da rabi da aure kuma yaranmu uku ga su, Salma, Salim Suhaima. Haihuwar fari na haife su ƴan uku yanzu haka jiya muka zo ƙasar nan jibi za mu wuce Spain." Intisar ta ƙarasa bayaninta tana kallon Raihan. Salman cikin yanayin tausayi ya dubi Mommy ya ce, "Dama haka rayuwa take Allah ya gafartawa Salim, na so ace yana raye da na ga wannan mai tsananin kama da ni." Raihan ta goge hawayen idonta har lokacin tana karanta hailala acikin zuciyarta, wata irin nutsuwa ce ta zo mata. Ta dubi Salman tana murmushin ƙarfin hali ta ce, "Don Allah ka yi haƙuri Salman da abin da ya faru, wallahi a duk lokacin da wani abu na Salim ya zo gare ni ina kasa riƙe kaina tabbas mutuwa gaskiya babu wanda zai mutu ya taɓa dawowa." Intisar ta karɓi lambar Raihan tana tambayar mommy address ɗin hotel ɗin da suka sauka. Sunan hotel ɗin mommy ta gaya mata Intisar ta ce su shiga mota su sauke su idan ya so sa je su ga hotel ɗin. Babu musu su Raihan suka shiga motar sai dai wani irin ɗaci Raihan take ji a zuciyarta. A hankali ta lumshe idonta tana jin wani iri a zuciyarta. A daidai bakin hotel ɗin Salman ya sauke su Raihan, mommy ta yi musu godiya sannan suka yi sallama Raihan ta sumbaci yaran Intisar tana jin kamar kar ta rabu da su. Su Intisar sai da suka ga shigewar su Mommy sannan suka ja mota suka yi gaba, Salman ne ya waiga wurin Intisar ya ce: "A cikin hatsabiban aljanu ma ke ta daban ce, a gidan uwar wa muka haɗu a saudiyya?" Intisar ta bushe da dariyar ƙeta sannan ta ce, "A da'irar abar bauta. ke kin ga yadda ta susuce lokaci ɗaya mahaukaciyar banza, ni na ɗauka ciwon haukan nata zai tashi ma." Hatsabibiya da ke ɗauke da siffar Salim ta ce, "Ai na gaya miki ta warke garau wannan karan dama dole mu sauya salo idan ba haka ba waɗannan ƴan iskan iyayen nata su gama da mu." Intisar ta waiga wurin su Suhaima ta ce, "To garda'u har yanzu kana kan sunanka na Suhaiman ne?" Kusan lokaci ɗaya su Salma suka sake bushewa da dariya suka ce, "Wa ya ga Suhaima." Salma ta rikiɗe zuwa wani mummunan tsuntsu ta ce, "Ni fa ban so ta sauke ni daga jikinta ba don wallahi jikinta wani irin taushi na ji an ya ba zan maye gurbin Huzaifa ba." Mugaza ta saka wata irin dariya mai ɗauke da ma'anar ka kusa kai kanka halaka ta ce, "In dai Huzaifa ne ga fili ga mai doki." Daga haka suka ɓace daga titin Ba su yada zango a ko'ina ba sai a cikin tsibirin ƙungiyarsu. Abar bauta na ganinsu ta bushe da dariya saboda duk abin da yake faruwa tana ganin komai, kallon Intisar ta yi tana yage manyan bakunanta ta ce, "Kin burge ni da wannan shawarar da kika kawo matuƙa, yanzu haka na san tana nan cikin wasu-wasi kuma haka za mu ci gaba da jefa mata wasu-wasi kala-kala har sai mun mayar da ita ruwa mun cimma burinmu a kanta. Wannan karon ba za mu dogara da Huzaifa ba domin shi ma kansa yaje yi wa yaƙi, da mu da shi kowa ya yaƙi abin da yake niyyar cimma buri idan ya so kowa tashi ta fisshe shi." Lokaci ɗaya suka ɗauki soya da wani irin ihu mara daɗin sauraro saboda farincikin samun mafita. Su Mommy na shiga ɗakin su Inno suka same su duk sun yi jigum-jigum da alamun suna cikin damuwa, mommy ta yi musu barka da hutawa kamar dai ba za ta tanka musu game da yanayinsu ba sai kuma ta ce, "Inno lafiya na ganku duk wani iri?" Inno kamar me jira ta ɗago hijabinta ta ce, "Don Allah me ye wannan Zainabu?" Mommy ta ce, "Hijabi ne Inno." Inno ta ce, "Wallahi yanzu nake shirin fita na bi jikata. Ina dalili ce mana kuka yi kanti za ku je siyayya, ya ilahi kanti da yake cikin unguwa. Tsorona Allah kar yarinyar nan Raihane ta ɓace miki a hanya na shiga uku." Raihan na daga gefe ta ja guntun tsaki ta ce, "Da yake kuma kowa irinku ne ko Inno?" Mommy ta yi mata daƙuwa, Raihan ta turo baki gaba. Goggo da ke gefe ta ce, "Ni abu ɗaya ne ya hana ni fita, ina tsoron kar na shiga cikin larabawa na ɓace don Allah Zainabu ko hasken fitilun ƙasar nan ba su isa kashe min ƙawayar ido ba?" Mommy ta yi murmushi tana cewa, "Ai shi ya sa muka ce ba za ku fita ba sai ranar da za mu tafi saboda kar a wahalar da ku." Inno ta kalli window ta ce, "Zo ki ga Zainabu ni kam waɗannan dogayen gine-ginen an ya ace laburorine suke ginawa? Kai gaskiya akwai ayar tambaya don mutanen nan da alama hatsabibai ne." Goggo ta karɓe zancen da cewar, "Zainabu ba don kar nace idona gizo yake min ba Allah da sai na ce Sha'aban mai aski mijin Safare na hango a wancan wurin a tsaye." Mommy ta riƙe baki ta ce, "Sha'aban Goggo kuma? Me kika ga yana yi?" Goggo ta washe baki ta ce, "A tsaye dai na hango shi." Raihan ta girgiza kai cike da ɗoki ta ce, "Inno yau dai na ga Intisar har da ƴaƴanta sai kuma..." Raihan ta katse maganarta da cewar, "Wallahi baki ga yaran ba gwanin sha'awa. Su Inno suka yamutsa fuska Goggo ta ce, "Wace kuma mai wannan sunan?" Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Ƙawar nan tawa fa." Ganin ba su gane ta ba ya sa Raihan ta tuno musu da Intisar nan take suka gane ta. Nan Raihan ta ci gaba da ba su labarin yadda ta ga Intisar da ƴaƴanta. Sai dai ko kaɗan bata gaya musu ta ga mai kama da Salim ba, don tun a lokacin da ta bawa Kamal haƙuri ta ci burin ba za ta sake yin zancen Salim ba saboda ta lura tana aikata abubuwa da dama cikin rashin nutsuwa. Mommy ta ji daɗi sosai ganin hankalin Raihan bai ta shi ba sai dai yanayinta kaɗai zai nuna maka tana ɗan cikin damuwa. Ko da Mommy ta ƙarasa ɗakin da suke ita da Daddy tas ta bashi labarin abin da ya faru, shi kansa ya yi mamaki matuƙa mommy ta nuna masa ba abin mamaki ba ne a cikin lamarin ubangiji tun da haka na iya kasancewa baka san mutum ba bai sanka ba ka ga yana yi maka kama da wani ko kuma kai kanka. Daga haka suka ci gaba da hirar yadda kasuwanci Raihan zai kasance da irin kayan da zai saya mata, da bayan sun koma Nigeria har zuwa yadda za ta ci gaba da sarrafa dukiyar da kanta. Raihan a ranar kusan kwana ta yi tana tunani daga ƙarshe da ta ga abin ya yi mata yawa sai kawai ta miƙe ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar nafila raka'a biyu ta kai wa Allah kukanta akan ya yaye mata damuwar da take ciki. Satin su Raihan ɗaya suka ɗunguma zuwa ƙasa mai tsarki, kafin tafiyarsu Daddy sai da ya gama yi wa Raihan komai ya yi mata awon kayanta sannan suka wuce ƙasar Saudiya. Su Inno baki ya ƙi rufuwa dukda wannan zuwan nasu ba shi ne na farko ba amma farincikin kasancewarsu a ƙasar ya sa murna ta cika su. Mommy sosai ta duƙufa wurin yi wa Raihan addu'ar Allah ya cire mata damuwar da take ciki, ya kuma mantar da ita Salim daga zuciyarta. Ta yi mata addu'a sosai akan Allah ya fito mata da miji nagari. Ita kanta Raihan ta yi wa kanta addu'a sosai a harami, ta kuma yi wa Salim addu'a mai yawan da neman Allah ya zaɓa mata abin da ya fi alheri a rayuwarta. Ana gobe za su dawo Nigeria da daddare sun dawo daga sallar Tarawi za su tsallaka don zuwa hotel ɗin da suka sauka. Kamar a mafarki ta hango mutum a bakin titi zai tsallaka, wani ni'imtaccen murmushi ne ya suɓucewa Raihan ta dubi Mommy ta ce, "Mommy kin ga mutumin nan da nake baki labari." Gaban mommy ne ya faɗi don tana tsoron kar Raihan ta sake gano mata mai kama da Salim, kallon wurin ta yi ta hango wani matashin saurayi da yake tsaye da baƙar jallabiya a jikinta. Da ganin yanayinsa shi ma baƙar fata ne don haka cikin rashin fahimta Mommy ta ce, "Waye wancen ɗin?" Raihan ta ce, "Wanda na taɓa baki labari na bige shi yana mashin ina cikin mota. Don Allah mommy na je na yi masa magana." Haɗe fuska Mommy ta yi ta ce, "Ba na son sakarci me kike yi haka? Raihan ko kin manta ke mace ce ne? Idan kin yi masa magana ki ce masa me?" Raihan gabanta na ci gaba da faɗuwa ta ce, "Wallahi ba wani abu zan yi ba Mommy haƙuri kawai zan bashi." Tsaki Mommy ta yi ta ce, "Da can baki bashi haƙuri ba sai yanzu." Idon Raihan ya ciko da ƙwallah ta ce, "Don Allah mommy." Mommy ta sake ɗaure fuska ta ce, "Maza ki je yanzu ki dawo ina jiranki." Daɗi ne ya kama Raihan har a fili sai da ta murmusa. A hankali ta fara takawa tana gabda ƙarasawa wurinsa ya fara haramar tsallakawa, da sauri ta furta: "Bawan Allah ɗan tsaya!" A hankali Al'amin ya tsaya juyo jin muryar bahaushiya na yi masa magana, takawa ya fara yi wurinta sannan ya nuna ƙirjinsa ya ce, "Da ni kike?" Raihan kai ta gyaɗa masa ta ce, "Am dama haƙuri na zo in baka." Da mamaki ya ɗan zaro ido ya ce, "Haƙuri kuma me kika yi min?" Raihan ta ɗan sosa kai a kunyace ta ce, "A nigeria ne dama na taɓa yi maka laifi." Wannan karonma zaro ido ya sake yi don rabonsa da Nigeria ya haure shekara biyu. Raihan tana cikin nazari ta riski muryarsa ya ce, "Duk irin laifin da kika min na yafe miki." Murmushi ta yi masa tana son sake yi masa magana ta ji ya ce, "Idan babu damuwa zan tsallaka wani Bro ɗina yana jirana." Raihan na son karɓar lambar wayarsa amma sai ta rasa me za ta ce masa kunya ta kama shi, don haka ta yi masa godiya suka yi sallama Al'amin ya tsalla ita kuma ta koma wurin Mommy sannan ita ma suka tsallaka suka yi ɓangaren wurin da Hotel ɗin su yake. Wani irin farinciki Raihan take ji har sai da mommy ta fahimci halin da take ciki, mommy murmushi ta yi don ta fahimci Raihan na matuƙar ƙaunar bawan Allahn tun kafin wannan ranar. Abin da ya sa bata ba ta goyon baya bata san ya halin yaron yake ba tun da a wannan lokacin da ake ciki namiji ya nuna shi yake sonka ma ya gari ya waya balle a ce mace ita ta kai kanta. Abin da Mommy ta ƙudurtawa kanta komai rubutacce ne a wurin Ubangiji Idan Allah ya yi mijinta ne babu makawa sai ta aure shi, idan kuma ba mijinta ba ne duk yadda ta ƙaunace shi ba za ta taɓa aurensa ba. Don haka take ci gaba da yi wa Raihan addu'a da fatan alheri akan dukkan lamuranta. Su Raihan sai da suka shafe sati biyu a ƙasa mai tsarki sannan suka dawo gida Nigeria, tun daga ranar da Raihan ta ga Al'amin kullin suka fita ta rinƙa baza idanu ko za ta ƙara ganinsa amma ko mai kama da shi ba ta gani ba, ta ciza yatsa sosai don ta yi dana-sanin rashin amsar lambarsa hasalima ko sunansa bata sani ba balle ta san wani abu game da shi. Har addu'a ta riƙa yi Allah ya sa ta gan shi ko a hanya ne kamar wancen karon amma ko walƙiyarsa bata gani ba, ranar da za su tafi ƙuncin duniya ya rufe ta don ko kaɗan ba haka ta so ba. Tun tana fushinta a ɓoye har ya fito fili, a nan Daddy yake tambayarta abin da yake damunta don ya san Raihan ba ma'abociyar fushi bace. Bata ɓoye masa komai ba tun daga lokacin da ta ga Al'amin har lokacin tafiyarsu, shi kansa ya ji babu daɗi amma sai ya ƙarfafeta ta hanyar yi mata nasiha akan abin da ya dace da wanda bai kamata ba. Tare da nusar da ita illar abin da take shirin aikatawa dukda ba haramin ba ne a musulunci mace ta furta soyayya ga namiji, har ya nuna mata da ace ya san yaron yana iya yi masa tayin auren Raihan ba wai don ta gaza ko bata da masoyi ba. Ko ba komai Raihan ta ji daɗi don haka ta ci gaba da harkokinta. Suna Airport gabda za su shiga jirgi suna zaune su Inno sai kalle-kalle suke yi, idan suka hango wani abin da bai yi musu ba sai dai Mommy ta ji suna ƙusƙus abin su. Idan kuma wani abin ne ya ba su dariya sai dai su ji su Inno sun tuntsire da dariya, Raihan ce ta shiga yi musu hotuna da Videos ba tare da sun sani ba sai da ta gama yi musu sannan kuma suka ɗaɗɗauki hotuna gabaɗayansu. Daddy na daga zaune ya hango Malam Usman da wata mace a tare da shi, kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da iyalinsa ce. Fara ce matar mai ɗan jiki yanayinta zai tabbatar maka da babarbariya ce duba da yanayin shigarta da tsagun fuskarta, Malam Usman bai ga Daddy ba sai Daddy ne ya yi masa magana haɗe da ƙarasawa wurinsa. Cikin mutumci suka gaisa Daddy ya ce, "Malam Usman kar dai jirginku ne ya sauka." Matar Malam Usman suka gaisa da Daddy a daidai lokacin Mommy ta ƙaraso, Malam Usman na hango su Inno ya ƙarasa ya tsugunna har ƙasa ya gaishe su sanna ya dubi Daddy ya ce, "Wallahi zuwanmu kenan hala duk jirgi ɗaya muka hau?" Daddy ya yi murmushi ya ce, "A'a mu ai yau za my wuce." Raihan ce ta gaida Malam Usman ya amsa har yana tambayarta sauƙin jikinta ta amsa masa. Adaidai lokacin jirgin su Daddy ya fara shela, Malam Usman ya ce, "To Alhaji sai mun taho. Ni ma na jima a nan ɗan wurina nake jira Al'amin tun ɗazu bai ƙaraso ba." Daddy da suke haramar wuce wa ya ce, "Kasan yaran nan da shiririta ta yuwu wani abu ne ya tsayar da shi." Daga haka suka yi sallama suka wuce ɓangaren da za su shiga ya sada su da jirgin da za su hau. Barin wurinsu ke da wuya Al'amin ya ƙaraso cike da zolaya ya ce wa Mahaifinsa, "Ahlan wasahlam ya Abiey." Malam Usman ya ce, "Balaraben Sudan ka shanya mu da yawa, tun ba wannan tsohuwar taka ba yau ina jin sai ta yi wa ƙafafuwanta ruwan zafi." Murmushi ya yi sannan ya yi musu barka da zuwa babu jimawa suka wuce masaukinsa. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 31 Raihan har suka dawo gida Nigeria bata da tunani sama da na Al'amin, ita kaɗai take sakin murmushi lokaci-lokaci idan ta tuna lokacin da suke tattauna wa ita da shi. Saboda yanayin daɗewar da suka yi basa gida ya sa kafin komawarsa Mommy ta yi wa Mama Hafsa magana ta turo wasu maƙonta da byake ba su da ƙarfi kuma ana ɗan basu wankau da sirfau, sai ta haɗo su da su Safna suka zo suka gyara gidansu Raihan. Don tun daga kan Mama Uwani su Mommy suka ce sun yaye ɗaukan kowacce mai aiki, ana gobe su Raihan za su dawo tuni an gyaran gidan komai ya yi tsaf don haka suna dawo wa suka samu komai tsaf gwanin sha'awa. A gajiye Raihan ta faɗa ɗakinta sai da ta ajiye jakar hannunta sannan ta ta fara rage kayan jikinta, a gajiya ta shiga banɗaki ta watsa ruwa. Kan katifarta ta kwanta ta lumshe ido tana hakaito fuskar Al'amin a lokacin da yake yi mata murmushi. A hankali ta tashi zaune ta furta, "Sau biyu kaɗai na taɓa ganinsa amma soyayyarsa na neman malale birnin zuciyata. Allah ka bayyana min shi a matsayin masoyi idan da alheri a tarrayata da shi" Hannunta ta kai saitin ƙirjinta a daidai lokacin bugun zuciyarta ya ƙaru, ta janyo fulo ta rungume haɗe da ɗora kanta a kan fulon ta furta, "Bayan Salim ban taɓa jin mutumin da ya ƙawata birnin zuciyata ba sai wannan gwarzon mazajen." Tana zaune tana zancen zuci har ta ji bacci na neman lulluɓe idonta ta, a hankali ta ja blanket ta kwanta, babu jima wa bacci ya yi awon gaba da ita. Kwance take daga ita sai ƴar ƙaramar riga iya cikinta, ɗan gajeren wandonta ko gwiwa bai ƙarasa ba. Mama Uwani ce ta shigo ɗakin ta zauna a gefenta haɗe ta tallafo ta jikinta tana shafata ta ce, "Uwar ɗakina hutawa kike yi." Raihan ta ɗago ta ce, "Huta wa nake Mama Uwani ya aiki?" Mama Uwani ta kai hannu ta ci gaba shafa saman cinyoyin Raihan haɗe da bayanta ta ce, "Uwar ɗakina kin guje ni yanzu ke bakya kewata?" Raihan ta janye jikinta haɗe da tashi zaune ta ce, "Mama Uwani na gaya miki ba na buƙatar ki riƙa taɓa min jiki." Mama Uwani ta miƙe a fusace ta ce, "Ai dama na daɗe da sanin an yi mana farraƙu a tsakani kuma da ni kike zancen." A fusace Raihan ta miƙe ta ce, "Mama Uwani ni kike gaya wa haka? Tsaki Mama Uwani ta yi ta fice daga ɗakin, da sauri Raihan ta bita amma ga mamakinta sai ta ganta a wani ƙaton fili. Waige-waige ta fara yi don kanta ba ƙaramin juyewa ya yi ba, ganin bata da mafita ya sa ta fara tafiya har ta isa bakin wani ƙaton kogi. Wani ƙaton baƙin sa ta hango yana tunkarota yana tafe yana jijjiga kansa, ganin girma da munin san ba ƙaramin razana Raihan ya yi ba. Hankali tashe ta fara gudu don ta lura kanta yake san ya yi gadan-gadan, tana tafe yana biye da ita har ta yi masa nisa sai dai tana shan wata kwana ta ci karo da shi. Da sauri ta ja da baya ƙirjinta yana bugawa da ƙarfin gaske bata yi aune ba ta ji ya fisgi hannunta ya yi gaba da ita, cikin matsanancin tashin hankali ta ƙwalla wata gigitacciyar ƙara haɗe ta zabura wanda ya farkar da ita daga nannauyan baccin da ya yi awon gaba da ita. Ajiyar zuciya ta riƙa sauke wa jikinta na rawa a daidai lokacin Mommy ta turo ƙofar ɗakin tana faɗin, "Raihan lafiyarki kuwa kike yi mana ihu a gida?" Ganin yanayin da Raihan take ciki ya sa Mommy ƙarasawa bakin gadon ta ce, "Raihan! Me yake damunki?" Raihan ta ruƙo hannun Mommy har lokacin jikinta na rawa ta ce, "Wallahi wani mafarki na yi mommy daga kwanciya bacci." Mommy ta kalle ta sosai ta sake maimaitawa, "Mafarki? Mafarki wane iri?" Nan take Raihan ta zayyane wa Mommy duk abin da yake faruwa sannan ta ɗora da cewa, "Wallahi na yi kewar Mama Uwani ko tana wace duniyar yanzu oho?" Hankalin Mommy ba ƙaramin tashi ya yi ba, da sauri ta riƙo hamnunta ya ce, "Mu je ɗakina ki huta a can." Ba musu Raihan ta bi bayan Mommy suna zuwa Mommy ta kunna karatun Alƙur'ani, Raihan ta kwanta akan gadon Mommy ita kuma ta zauna a gefenta tana shafa kanta. Tunani kala-kala ne ya riƙa zarya a birnin zuciyarta tana Allah-Allah Daddy ya dawo don ta sanar masa abin da yake faruwa, don ko da wasa ba ta fatan Raihan ta riƙa ire-iren mafarkin nan saboda ba alheri ba ne. Baccin da Raihan bata koma ba kenan, ita kanta ta jima tana maimaita yanayin mafarkin da ta yi a zuciyarta, amma tunaninta ɗaya Mama Uwani ko tana wace duniyar don ba ƙaramin sabo suka yi da ita ba, dukda ta ji Mommy ta ce wani dalili ya dakatar da ita da yi musu aiki gabaɗaya. Mommy na jin shigowar Daddy ta miƙe ta fice daga ɗakin, a falo ta same shi ya kunna television yana kallon labarai. Murmushi ya yi mata yana miƙa mata hannu, martanin murmushi ta sakar masa cikin yaƙe ta zauna a gefensa ya tallafota da hannu ya ce, "Ni kam matar nan ban gane wa yanayinki ba. Tun a Dubai nake zarginki don wallahi duk kin sauya kamar ba ke ba." Kallonsa ta yi don bata fahimci in da maganar Daddy ta dosa ba ta ce, "Daddyn Raihan ni fa ban gane zagaye-zagayen nan naka ba, me kake nufi kana nufin ƙasar wasu tafi karɓa ta kenan?" Daddy ya yi dariya sannan ya ce, "Zainab ga ki dai shekarun sun fara yawa amma wani abin idan kika faɗa kamar Raihan." Hannunsa ya kai kan cikinta ya ce, "Jikina yana ba ni akwai ajiyata a nan." Mommy zaro ido waje ta yi ta kalli Daddy ta ce, "Don Allah ka daina faɗin wannan maganar Daddyn Raihan, tsofai-tsofai da ni wace irin haihuwa kuma? Yanzu da Raihan na tare da Salim ɗan/'yarta da sun doshi shekara har da wani abu." Daddy ya jinjina kai ya ce, "Nawa kike Zainab kawai don Raihan ta yi tsawon ƙafa ni kin rufa talatin kuwa?" Hararar wasa Mommy ta yi masa ta ce, "A'a ka manta ashirin zan yi." Ta sauya murya cikin shagwaɓa ta ce, "Wai don Allah Daddyn Raihan me ka mayar da ni?" Daddy ya yi dariya ya ce, "Yarinya mana." Mommy ta jingina da kujera ta ce, "To ka sauke don wallahi ni ma girma ya zo." Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Serious Habibty ina zargin ciki gare ki don tun kafin mu tafi Dubai na fara zargin haka." Mommy ta yi sak jiki a sanyaye ta ce, "Ni wallahi ba ciku gare ni ba, don Allah yanzu na samu ciki na cewa mutane me? Kawai sai Raihan da su Inno su wayi gari ina tura ciki gaba?" Daddy ya yi dariya har da riƙe ciki ya ce, "Su Inno da Raihan ba sun san kina da mijina, yanzu dai yaushe rabonki da baƙon wata?" Mommy shiru ta yi ta faɗa duniyar tunani nan take gabanta ya yanke ya faɗi. Tunawa ta yi sam bai zo mata ba saboda tun kafin tafiyarsu Dubai take sa ran ganinsa amma har suka tafi bai zo ba, zuwan su Dubai sai ta manta da komai sai yanzu da Daddy ya tuna mata. Idonta ne ya ciko da ƙwalla ta ce, "Wallahi tun kafin mu tafi Dubai nake sa ran ganinsa bai zo ba." Daddy ya wara hanninsa haɗe da cewa, "Shi kenan kin ga na ci gari." Mommy ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba amma don kar ga nuna wa Daddy ya sa ta kawar da zancen da cewar, "Daddyn Raihan da matsala fa." Ya kalleta cikin nutsuwa ya ce, "Matsala kuma? Wacce iri?" Nan take mommy ta zayyane masa irin mafarkin da Raihan ta yi, kai kawo Daddy ya fara yi cikin damuwa ya furta, "Huzaifa-Huzaifa. Huzaifa ba zai bar min yarinya ta sarara ba ne wannan waccen irin rayuwa ce. Ni ina zargin ba shi ya cire wa yarinyar nam son kula samari ba kuwa? Kina ga kowa ya nuna yana son Raihan za ta fara maganar tsohon mijinta, yanzu haka rayuwar yarinyar nan za ta ƙare?" Mommya ta ƙarasa wurim Daddy ta riƙo hannunsa sai da suka zauna ta ɗauki sauran ruwan da ya sha ta miƙa masa, ajiyar zuciya ya yi sannan ya karɓa sha. Mommy ta dube shi cikin ƙarfafa gwiwa ta ce, "Idan aka san ciwon abin da yake damun mutum kamar an ci rabin magani ne, sannin Raihan na tare da wannan shaiɗanin ba ƙaramar rahama ba ne a wurinmu. Mafita kawai mu ci gaba da yi mata addu'a muna nema mata magani dukkan tsanani yana tare da sauƙi, kuma wannan abin yana daga cikin shafin ƙaddararta. Fatanmu akanta Allah ya bata lafiya ya tsare dukkan musulmi bakiɗaya." Daddy ya amsa da amin sannan ya fara tunanin zuwa don karɓo wa Raihan magani. Sun jima suna tattauna wa akan matsalolin da suke damun Raihan sannan mommy ta ƙarasa ɗakin su Inno don tun dawowarsu da suka shige ɗaki bata ƙara jin motsinsu ba. Mommy na shiga ɗakin ta same su sun baje kaya ɗaiɗai da yake dama jakunkunansu daban mommy ta yi musu, Mommy na shiga Inno ta ɗago wani leshi da Daddy ya sawa musu ita da Goggo ta ce, "Zinaru wannan leshin a ƙasan akwati zan saka shi, idan Allah ya kaimu Allah ya sauki Zainabu lafiya ranar suna zan rangaɗa kayana." Goggo ta ware wasu kaya kala uku a gefe ta ce, "Ai ba zan ɗinka kala ɗaya ba, saboda ko a Albasu ba na fitar suna da kala ɗaya. Kai amma yarinyar nan ta shammace mu, a lokacin da muke saka rai da ciki babu sai yanzu da Allah ya nufa." Inno ta yi wani murmushin jin daɗi ta ce, "Ni kam na ɗauka Audullahi ya yi bankwana da haihuwa ashe Allah ya ɓoye ajiyarsa mu muke abin mu." Mommy ta ɗan yi gyaran murya haɗe da sallama don ta ji duk hirar da suke yi, gabanta ne ya faɗi take ayyana ashe suma kallon ciki suke yi mata ita take abinta. Su Inno suna ganin Mommy suka washe baki Inno ta ce, "Zainabu an shigo?" Mommy ta zauna a gefen gadon Goggo ta ce, "Inno yanzu tun baku huta ba kun hau kwance kaya, don Allah ku kwanta ku huta man." Goggo ta sake janyo wani ƙunshin kaya da wuƙa a gefe tana kiciniyar yankawa ta ce, "Zainabu kenan a bari ya huce shi yake kawo da rabon wani, kin taɓa ganin na bar kaya sun kwana ko Albasu na je?" Mommy ta girgiza kai haɗe da miƙe wa ta ce, "To bari na baku wuri don na gaji bacci nake ji." Inno ta ce, "Ai dama gara ki huta don gaskiya kina buƙatar hutu." Mommy ta juya ta fita tana daga bakin ƙofa Goggo ta yi ƙasa da murya ta ce, "An ya yarinyar bata ji hirar mu ba?" Inno ta waiga ta kalli ƙofa ta ce, "Da ta ji za ta yi mana magana, idan ta ji ai na ga ta kaina ina uwar miji guda ai sai ta ce na saka mata ido. Don ma Zainabu dai yarinyar kirki ce ni uwa ta ɗauke ni ba sirika ba, amma wallahi matsalata ɗaya da ita da bata son yi mana tuwo saboda Allah ina laifi a ce duk dare mu ci tuwo a gidan nan." Goggo ta wara hannuwa ta ce gane min hanya amma wallahi Audullahi ya fi ta laifi don Allah shi ba zai tsawatar mata akan abin da muke so ba?" Inno ta yi guntun tsaki ta ce, "Bar batun Audullahi baƙin Bayahude ne har gara Zainabu tana yi mana tuwo sau uku a sati amma kin taɓa jin Audullahi ya ce ta yi tuwo?" Goggo ta girgiza kai. Inno ta ci gaba da fito da kaya ta ce, "Ki bar su ƙarƙari idan muka gaji mu kama gabanmu ina dalili gida kullin ka ci shinkafa, ko kunu sai na yi sati biyu ban sha ba." Goggo ta ce, "Ba don ina jiran haihuwar Zainabu ba ai wallahi daga Iyafot (Airport) Albasu zan wuce." Mommy ban da dariya babu abin da take yi don tsofaffin ba ƙaramin dariya suka bata ba. Daga nan kai tsaye ɗakinta ta wuce don ba ƙaramin zafi idonta suke yi mata ba, tana kwanciya babu jima wa bacci ya yi awon gaba da su. A ranar da Mommy ta sanar da shi mafarkin Raihan a ranar ya je Waraka Islamic chemist, da yake duk yaran Malam Usman sun san Daddy da irin magungunan da ake haɗa wa Raihan ya sa suka haɗa masa magunguna tare da yi masa bayanin yadda za ta yi amfani da su. Kuma tun daga ranar Raihan bata sake irin mafarkin nan ba, su Mommy sun dage sosai wurin nema mata magani kuma babu wani abu da ya sake faruwa da ita. Raihan suna yawan gaisawa da Intisar wani lokacin har video call suke yi, musamman yaran Intisar da Raihan take jin su har cikin ranta. Daddy tsaraba ta musammam ya yi wa Kabiru kasancewar ya shiga ransa sosai saboda Kabiru yana da hankali da nutsuwa. Mommy tun tana ganim kamar duk zancen ne maganar da Daddy ya yi mata na ciki har ta fara zargin kanta sakamakon irin sauye-sauyen da take samu, daga ƙarshe watarana ta shirya ta je asibiti a ranar likita ya tabbatar mata da ciki, sakamakon gwaje-gwajen da aka yi mata. Raihan kasuwancin da take yi ba ƙaramin karɓarta ya yi ba, ganin haka ya sa Daddy ya yi tunanin buɗe mata Boutiqe. Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yi wa Raihan ba, haka ta ci gaba da rayuwarta haɗe da kasuwancinta gwanin birgewa. Sai dai a fagen samari duk yadda suka kai ga ganin sun saye zuciyar Raihan abin ya ci tura. Tun bata kula su daga ƙarshe ma suka daina zuwa gabaɗaya, da farko abin ko kaɗan bai damu Raihan ba saboda a ganinta ba za ta ƙara samun masoyi kamar Salim ba, shi kuma wanda take bege har tsawon wannan lokacin bata sake cin karo da shi ba. Don haka rashin zuwan samarin da basa yi ya fara damun Raihan har take ganin kamar rashin saurar da ba ta yi musu ne ya sa suka ja da baya. Abin da Raihan bata sani ba tuni wasu daga cikin mutane suka yanka mata ayar tambaya don tuni mutane suka ɗora zargin mutuwar Salim akan rashin lafiyar Raihan ta baya, saboda zancen duniya ko kaɗan baya ɓuya. A haka suka ci gaba da gudanar da rayuwa har cikin Mommy ya kai wata takwasa da sati biyu, a wannan lokacin aka yi wa Mommy Cs don tun a lokacin awon cikinta Likita ya ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda shekarunta sun ɗan ja, idan aka ce a bari ta haihu da kanta za ta sha wahala. An yi aiki lafiya aka ciro mata jaririnta Namiji lafiyayye gwanin birge wa, murna wurin Raihan abin ba a magana. A gaggace take tafiya don ganin ta ƙarasa wurin da ta yi parking ɗin motarta, za ta koma gida don karɓo wa Mommy ruwan shayin da su Inno suka dafa. A jikin motarsa ta same shi a tsaye da waya a hannu yana dannawa, a gaggauce ta buɗe murfin motar ta kalle shi tana faɗin, "Don Allah Malam zan ɗauki mota sauri nake yi." Bai ɗago ya kalle ta ba kuma ko kaɗan bai motsa ba balle ta saka ran zai tanka mata, haushi ne ya fara kama Raihan don a yanayin mutumin da ta gani bai yi kama da wata ɗan ƙabilar ba balle ace baya jin hausa. Haushi ya kama ta a ɗan zafafe ta ce, "Wai Malam baka jin abin da nake faɗa ne?" Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta sai dai bai tanka mata ba ya ci gaba da latsa wayarsa. Ƙugu Raihan ta riƙe ta dawo ta gabansa tana nuna shi da yatsa ta ce, "Malam ba na son wulaƙanci ka matsa min daga jikin mota." Raihan na rufe baki ya ɗago sai da ya kalleta na ƴan daƙiƙu ya ce, "Ki fara koyo sallama kafin ki furta wa ɗan'adam koda kalma ɗaya ce." Littafin Kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624. 32 Shiru Raihan ta yi saboda ba ƙaramin kunya ta ji ba, amma don kar ta nuna masa yanayinta sai ta ɗauke kai gefe ta ce, "Tun da kai ka iya ya wadatar ba sai na koyo ba don Allah ka matsa ka ba ni wuri." Kafin ya bata amsa daga bayanta ta ji an furta, "Barista Huzaifa! A sanyaye ya ɗago ya kalli mai kiran nasa don suna haɗa ido ya faɗaɗa fara'arsa da cewar, "Likita bokan turai." Mamaki ne ya kama Raihan don yanayin fuskar wanda aka kira da Barista Huzaifa bata taɓa nuna mata alamar ya taɓa dariya ba. Dr Hussain ne ya ƙarasa ya bashi hannu suka gaisa sannan ya kalli Raihan ya ce, "Raihan kar dai kuna da relation Barista?" Ya yi tambayar cikin fara'a don duk wanda ya ga irin tsayuwar da su Raihan suka yi zai ɗauka suna da wata alaƙa. Dr Hussain na gama magana Raihan ta taɓe baki ta ce, "Dr wallahi bansan shi ba, don Allah ka ce ya matsa min zan je gida na kawowa mommy ruwan zafi." Jikin Barista Huzaifa ne ya yi sanyi don yadda Raihan ta yi maganar ya nuna masa a ƙagauce take, don alamu sun nuna Mahaifiyarta ce babu lafiya. Dr Hussain ya yi murmushi ya ce, "Barista abokina ne." Ya juya ya kalli Barista Huzaifa ya ce, "Barista kun yi shiru kamar bakwa duniyar, saboda kun danne manya kaya sai ku yi wa talaka nisa." Barista Huzaifa ya matsa daga jikin motar Raihan ya ce, "Wallahi ba haka ba ne, ka san yanayin aikinmu sai a slow. Yanzu haka na shigo gari wani abokina ne aka kwantar da shi da babu lafiya." Dr Hussain ya ce, "Subhanallah ya sunan patient ɗin?" Barista ya waiga yana kallon motar Raihan da ta fice daga harabar asibitin, sannan ya juyo ya ce, " Sunansa Barista Sani ƙofar nasarawa. Amma mun fi kirsansa da ƙofar nasarawa." Da yanayin mamaki Dr Hussain ya ce, "Kar dai shi ne mai matsalar ciwon siga?" Barista Huzaifa ya jinjina kai yana faɗin, "Exertly, and yana jin jiki sai dai mu yi fatan Allah ya bashi lafiya." Gabaɗaya suka amsa da amin. A hankali suka fara takawa Dr Hussain ya ce, "Yanzu za ka wuce ne Barista?" Barista Huzaifa ya kalli agogon hannunsa ya ce, "Gaskiya wuce wa zan yi dama akwai wani abokina da nake jira but ina da uzuri a waje saboda akwai case ɗin wata yarinya da aka yi rapping ɗinta da nake bincike akai." Dr Hussain cikin jimami ya ce, "Ai dama kuna ganin cases kala-kala Allah ya sa mu dace." Suka amsa da amin har sun je wurin motar Barista za su yi sallama Barista Huzaifa ya ce, "Dr wannan yarinyar da ta wuce fa?" Dr Hussain irin mutannan masu surutu yana jin haka ya washe baki ya ce, "Wai Raihan?" Barista Huzaifa ya gyaɗa masa kai. Nan take Dr Hussain ya zayyane masa komai akan Raihan na haihuwar Mommy, da yake shi ne likitan da ya yi mata Cs. Cikin gamsuwa Barista ya jinjina kai ya ce, "Tsiwarta ta birge ni." Dr Hussain ya yi dariya ya ce, "Mutumina ka rufta dai kawai. Yanzu sai wacce shekarar za mu sake haɗuwa?" Barista ya yi murmushi mai sauti haɗe da faɗin, "Zan ɗan kwana biyu a Kano insha Allah saboda mun samu hutu, zan iya kai kwana huɗu kafin na wuce Kaduna." Sun jima suna tattaunawa daga ƙarshe suka yi sallam Barista ya shiga motarsa ya wuce, Dr Hussain ya koma cikin asibitin. Raihan tun da ta shiga motarta lokaci-lokaci take zabga tsaki don mutumin ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba, tana zuwa gida ta shiga zabga horn kamar mai shirin tashi sama. A hargitse Kabiru ya leƙa don ganin mai wannan horn ɗin don a iya saninsa mutanen gidan ba sa irin haka. Ganin Raihan ce ya sa shi faɗaɗa fara'arsa, tsayuwarsa a wurin ya dulmiya shi cikin kogin tunani don zuciyarsa ta jima tana yaudararsa akanta. Shi kansa ya san ko a cikin mafarki Raihan ta yi masa nisa kwatankwacin yadda sararin samaniya ta yi hannun riga da ƙasa. Bai yi aune ba ya sake jin ta danna wani horn ɗin da ƙarfi, jiki babu kuzari ya fara jan gate ɗin a hankali ya buɗe yana tsaye wuri ɗaya yana bin ta da wani irin sassanyan kallo. Tana shigo wa tun bata ƙarasa wurin parking ba ta faka motarta a wurin ta sauko, wurin Kabiru ta sake koma wa ta riƙe ƙugu tana kallonsa. Ganin har lokacin bai san tana yi ba ya sa ta ƙarasa wa wurinsa tana tafa hannuwa ta ce, "Filloooo!" A firgice ya ɗago yana sauke ajiyar zuciya suna haɗe ido ya sakar mata wani ni'imtaccen murmushi. Ba ƙaramin kyau ta yi masa ba kasancewar tana sanke da doguwar rigar leshi kafaɗarta maƙale da ƙaramin mayafi. Da ido ta kafe shi tana karantar yanayinsa tamkar wata uwarsa ta haɗe fuska tana faɗin, "Kwana biyu na ga kana cikin damuwa me yake damun ka?" Ba ƙaramin dariya ta bashi ba don yadda ta yi maganar kamar wata uwarsa ko yayarsa, dariya ya yi mai sauti sannan ya ce, "Hai kai yanzu sai na gaya maka abin da yake damuna?" Raihan ta sake haɗe fuska ta ce, "Ban isa ba ne wai me ya sa fillo ka raina ni da yawa?" Kabiru ya jingine sandar hannunsa ya ce, "Don Allah shekara nawa na baki? A ƙalla na baki kusan shekara bakwai." Raihan ta taɓe baki ta ce, "Wallahi na ɗauka ka fi haka don wannan manyancen naka sai kace ka haife ni." Dariya Kabiru ya yi Raihan ta ce, "Da gaske kana cikin damuwa me yake damunka ko jikin Baba?" Raihan ta faɗa a sanyaye da yake daga baya da zama ya yi zama Kabiru ya sanarwa da Raihan rashin lafiyar da Mahaifinsa yake yi, kuma Daddy ba ƙaramin taimaka masa yake yi ba. Wannan kalma ta Raihan na ɗaya daga cikin abin da ya sa ta sace zuciyarsa saboda tana matuƙar ambatar iyayensa da nuna muhimmancinta akansu. Jin ya yi shiru ya sa ta ce, "Idan jikin nasa ne ya yi tsanani ya kamata ka sanarwa da Daddy a yi wani abu, idan kuma zuwa kake son yi sai ka saka rana ka tafi." Murmushi ya sakar mata ya ce, "Duk ba wannan ba ne wata yarinya nake so amma na san zuciyata yaudarata take yi, don na san ko a mafarki ta min nisa." Tsaki Raihan ta yi haɗe da yin wata irin dariya ta ce, "Don Allah da akan tunanin wata yarinyar har ka shanya ni a ƙofar gida?" Kabiru ya marairaice murya ya ce, "Kin san tasirin soyayya kuwa? Kin sa yadda zuciyata take lugude a kanta? Don Allah kar ki ce haka don na yi nisa a soyayyarta." Jikin Raihan ba ƙaramin sanyi ya yi ba musamman da ta tuna tata tsohuwar soyayyar, don haka ta ɗago ta ce masa. "Lallai su fillo a faɗa ruwa tsamo-tsamo, kasan dai ni ce babar aminiyarka yanzu dai ka bari na je na dawo sai mu yi magana ko ƴar gidan waye zan je nema maka soyayyarta." Kabiru ya yi murmushi don ba ƙaramin jin daɗin bayanin Raihan ya yi ba. Cikin gida ta wuce tana kwaɗa sallama, a hakimce ta samu su Inno sun zabga kwalliya kowacce ta saka sabuwar atamfa hannu ɗauke da hijabi, Raihan na ganinsu tun daga bakin ƙofa ta ce, "Inno ina za ku ne haka?" Inno ta kalli ƙofar da Raihan ta shigo ta ce, "Ke ina Audullahi?" Raihan ta ƙarasa tana ajiye mayafinta ta ce, "Yana wurin matarsa." Goggo ta ce, "Mu fa shirya wa muka yi ya kai mu." Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Ya kai ku ina? Don Allah ina ruwan zafin da zan tafi da shi don sauri nake ina koma wa Daddy zai tafi uzurin gabansa." Ta yi maganar a gaggauce don ta fahimci su Inno asibiti za su ce za su je. Inno ta miƙe tsaye ta ce, "Ai sai dai mu tafi tare amma Allah ya sani yau sai na je na gano jikana duk baƙincikin ki." Raihan ta wara hannu alamun rashin damuwa ta ce, "Na hana ku tafiya ne? Amma gaskiya babu wacce za ta shigar min mota ta riƙa yi min ihu. Na ga jiya ma kun je asibitin nan ya ilahi wurin nan fa ba biki ake yi ba, ina jin ma da yamma Dr zai iya sallamarta." Goggo ta miƙe tsaye a fusace ta ce, "Ki gode wa Allah ba a Albasu nake da zama ba wallahi da kullin sai an yo mota guda daga can an zo duba ta, a farke cikin mai rai sannan ace ba za ka je ka yi masa sannu ba. Ƴar nan kina cikin hayyacinki kuwa." Raihan ta nufi hanyar kitchen tana faɗin, "Ku faɗi duk abin da za ku faɗa amma babu wacce za ta shigar min mota." Flask ɗin shayi ta ɗauko har ta nufi hanyar fita wani tunani ya faɗo mata don ta san sarai idan ta fita su Inno suna iya cewa za su fita su tafi da kansu, juyo wa ta yi ta: "Ku taso mu tafi. Amma wallahi kuka nemi tara min mutane Allah a titi zan zube ku." Ba musu su Inno suka taso suka biyo bayan Raihan suna zuwa Raihan ta buɗe musu suka shiga baya. Kabiru na ganin fitowarsu ya ce, "Su Hajiya Inno yau ma fita za a yi?" Inno ta ce, "Bari Kabiru za mu koma dubo jikin Zainabu kaima ba don tsaron gida ba ai da mun je tare." Kabiru ya ce, "Sai kun dawo a yi mata sannu." Ya ƙarasa maganar yana buɗe musu ƙofa sannan suka fice. Su Inno suna tafe sai kalle-kalle suke babu damar a zo wurin danja sai su hau mitar an tsayar da su, a haka suka ƙarasa asibitin har lokacin Daddy yana zaune. Shigar su Inno ya sa Daddy ya miƙe har zai fita Inno ta ce, "Audullahi dawo magana nake son yi da kai." Daddy ya koma ya zauna Inno ta ci gaba da cewa, "Audullahi saboda Allah me muka tsare wa ƴarka ta ɗauki karan tsana ta ɗora mana, ko don muna zaune a gidan iyayenta." Inno na gama magana Mommy ta waiga ta kalli Raihan saboda dama tun da ta gansu tare ta san za a rina. Daddy ya dubi Raihan rai a ɓace ya ce, "Raihan me kika yi wa su Inno?" Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Saboda Allah Daddy me zan yi musu kasan dai halin tsofaffin nan fa." Goggo ta yamutsa fuska ta ce, "To idan saboda zaman mu ai sai mu kama gabanmu ina dalili, daga mun ce za mu zo asibiti yarinya ta saka mu a gaba da jaraba." Daddy ya kalli Raihan ya ce, "Bata kyauta ba amma Inno ku yi haƙuri, ke kuma..." Daddy ya katse zance shi yana nunata da yatsa sannan ya ci gaba da cewa, "Idan kika sake kika ƙara sai ranki ya ɓaci." Inno ta gyaɗa kai sannan ta ɗora da cewa, "Audullahi duk ba wannan ba gaskiya mota za ka saya mana kowa ɗaiɗai, mu riƙa tuƙa abar mu muna zuwa inda ranmu yake so. Haka kawai kullin za ka fita a riƙa ja maka rai, shi kuma direban yaron can ba shi da saiti. Kullin ya zo a ɗame wando kamar zai tsage sai kace jikan Elinzabet, a'a raba ni da wannan lamarin don wallahi sumar kansa tsoro take ba ni ga wari kamar an buɗe shadda."Daddy sai da ya gama jin jawabin Inno ya ce, "Inno mota fa? Duk motocin cikin gidan ba su yi muku ba? Idan Abbati ne bai yi muku ba ai sai na sauya wani." Goggo ta ɓata fusta tana cewa, "A'a ka bar Abbati kar mu zama silar barin cin abincinsa, amma dai mota za ka saya mana ka koya mana. Don idan ka saka Raihanu ta koya mana alƙur'an wataran murje mu za ta yi kamar ƴaƴan boris." Gabaɗaya mutanen ɗakin sai da suka saka dariya har Daddy don yadda Goggo ta yi maganar ne zai baka dariya, Daddy ya dubi Goggo ya ce, "Goggo yanzu dai don Allah ku ɗan tsahirta da siyan motar nan a bari Zainab ta samu lafiya jikinta ya yi ƙwari kun ga duk abin da zai zo daga baya mai sauƙi ne." Su Inno suka jinjina kai cike da gamsuwa sannan Daddy ya tashi ya fice. A ranar da yammma aka sallami Mommy saboda dama a ƙa'idarsu kwanan mace huɗu da yin Cs suke sallamarta idan har ita da Babynta suna lafiya. Komawar Mommy gida ƴan dubiya da barka suka riƙa zarya, suna zuwa sake ganin Mommy sai dai bata yi taron suna ba don ta ce ta wuce wannan lokacin, taron suna sai Raihan ta haihu. Mommy ta yi shar da ita gwanin birgewa ita da jaririnta suna cikin ƙoshin lafiya, Daddy ya so saka sunan Mahaifinsa amma gudun rigima tsakanin Inno da Goggo ya sa ya saka masa suna Muhammad. Kusan rainon Muhammad a wurin su Inno da Raihan ake yi don Mommy aikinta bayar da mama kawai. Wata ranar talata suna zaune da yamma suna hira; Muhammad a lokacin kwanansa arba'in cif, Raihan na rungume da shi sai kawai ta ji ina ma ita ma ace Muhammad Ɗanta ne. Ta ɗago ta dubi mommy ta ce, "Wallahi mommy Allah ya taimake ki ina gida da ban san ya za ki yi da rainon Muhammad ba, yanda yaron nan yake da rigima ba ƙaramin wuya za ki sha ba." Mommy ta kalli su Inno ta ce, "Yanzun ma ai bake kike min ba ga iyayena su suke min raino, dan gidanku da za ki ce haka da wa ya yi min naki rainon?" Raihan ta miƙe tsaye ta miƙa wa Goggo Muhammad ta ce, "Ai kuwa shi kenan daga yau kuwa na daina taya su." Tana gama maganar ta wuce bakin gate, sanye take da doguwar rigar abaya kanta yane da mayafi. Kujera ta janyo tana ƙawala wa Kabiru kira, yana fitowa ya hangota sannan ya janyo kujera yana fuskantarta ya ce." Don Allah fillo ki daina min kiran mafarauta." Raihan ta yi dariya sannan ta ce, "Ango! Ango!!" Tsaki Kabiru ya yi ya ɗauke kai gefe zai yi magana Raihan ta ce, "Wai ya shgalin bikin zai kasance? Sai wani basarwa kake ka zo mu yi shawara ko garinku ba a komai lokacin biki?" Cikin yanayin damuwa Kabiru ya ce, "Tun farko na gaya miki ba na son auren nan saboda akwai wacce na mallaka wa zuciyata. Amma me ya sa za ki riƙa tambayata akan shirin biki bayan kin san ba son auren nan nake yi ba, biyayya ce kawai zan wa su Baffajo." Ba ƙaramin tausayi ya bawa Raihan ba don haka ta ce, "Ba tun yau ba na tambaye ka, wacece ita a ina take? Idan ka na ganin ni na yi yarinta sai na sa mommy a maganar amma wannan kamar ka daɓa wa kanka ne." Kabiru na shirin yin magana ya ji an fara horn a bakin gate, da sauri ya miƙe ya buɗe ganin motar Daddy ce, sai wata motar da take biye da shi. A jere suka shigo har wurin parking space, Daddy ne ya fara fito wa sai Dr Hussain da ya fita daga tashi motar. Daga ɓangaren mai zaman banza Barista Huzaifa ne ya buɗe ya fito cikin farar dakakkiyar shadda, sai baƙar hula, baƙin takalmi da baƙin agogo ɗaure a hannunsa. Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cikakken bafulatani ne, kayan jikinsa ba ƙaramin amsarsa suka yi ba don shi dama ma'abocin son ado da kwalliya ne. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 33 Da ido Raihan ta bi su don ba ƙaramin mamaki ne ya kamata ba, musamman ganin Barista da ta yi don sarai ta gane fuskarsa. Miƙe wa ta yi ta nufi wurin Daddy ta karɓi jakar hannunsa ta furta, "Daddy barka da zuwa." Tana amsar jakar Daddy ta kalli Dr Hussain ta furta, "Dr yau kai ne a gari?" Dr Hussain ya yi murmushi ya ce, "Ba zuwana ba ne ni ma taso ni aka yi." Ya yi maganar yana kallon Barista haɗe da yin dariya. Raihan ta taɓe baki ba tare da ta kalle shi ba, tana niyyar wuce wa cikin gida Daddy ya ce, "Raihan ki kawo wa su Dr abin sha muna falon baƙi." Ɓata fuska Raihan ta yi don ko kaɗan ba ta so ba, murya can ciki ta amsa sannan ta wuce cikin gida. Daddy ne ya yi musu jagora suka wuce falon da Daddy yake saukar baƙi, bayan sun shiga Dr da Barista suka zube ƙasa cikin ladabi suka gaida Daddy. Daddy ya yi mamakin wannan gaisuwa ta Dr Hussain don sun daɗe da shi kuma bai taɓa yi masa irin haka ba, kujera ya nuna musu ya ce, "Ga kujera ku zauna man kwa zauna a ƙasa." Dr ne ya fara miƙe wa sannan Barista ya miƙe suka hau kan kujera. Da sallama Raihan ta shiga ta dire tiren hannunta wanda yake ɗauke da ruwa da kayan lemuka, bayan ta ajiye ta sake fita ta shigo da wani farantin mai ɗauke da kayan marmari ta ajiye, sannan ta fice daga ɗakin. Daddy ya zuzzuba ya miƙa musu sannan ya ɗora da cewa, "Ai lokacin da ka kira ni Dr na fito daga office babu jima wa don haka ba ce kawai mu haɗu a gida, sai ga shi mun zo kusan lokaci ɗaya." Dr Hussain ya yi murmushi sannan ya ce, "Alhaji dama wata magana ce tafe da mu don haka na ce ya dace mu fara samun ka da maganar hakan ya fi dace wa, wannan dai abokina ne tare muka taso tun muna ƙanana shi ma ɗan Kano ne daga baya da kowa ya samu aikin sai kowa ya kama gabansa. Sunansa Barista Huzaifa kuma haifaffan unguwar Kurawa ne, lauya ne a babbar kotun shari'ar musulunci da ke jihar Kaduna." Daddy ya sake kallon Barista Huzaifa yana jinjina kai sannan Dr ya ɗora da cewa, "Tun kwanaki lokacin da aka yi wa Hajiya aiki ya ga Raihan ya ji yana sonta da aure, don haka da ya same ni da maganar ya ce ya fi son ya fara samun mahaifinta ya sanar da shi kamar yadda ya fi cancanta. Cikakken sunansa Huzaifa Rufa'i Mustafa, amma ana kiransa da Barista Huzaifa." A firgice Daddy ya ɗago yana kallon Barista tare da furta, "Huzaifa!" Da mamaki duka suka kalle shi jin yanda ya ambaci sunan. Dr ya ɗan sosa kai sannan ya ce, "Alhaji shi ne muka ce bari mu zo ba mu sani ba ko an yi mata miji." Daddy ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta, "Raihan ba a yi mata miji ba amma gaskiya ina buƙatar yin nazari sannan kuma sai na ji daga bakin yarinya." Barista Huzaifa ya jinjina kai sannan ya ce, "Babu damuwa Daddy Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alheri." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Lemo kawai suka sha don sauyin da suka gani a tattare da Daddy ba ƙaramin sanyaya gwiwarsu ya yi ba, ba su jima ba suka yi wa Daddy sallama suka wuce don shi Barista tun a lokacin ya fidda rai da samun Raihan saboda yanayin Daddy kaɗai shi zai tabbatar maka da yana cikin ɓacin rai. Suna fita Daddy ya yi cikin gida a lokacin har an fara kiran sallar Magriba, sai da ya yi alwala ya yi sallah ɗsannan ya samu Mommy da maganar. Duk abin da Dr ya gaya masa game da Barista haka ya ba wa Mommy labari sannan ya ɗora da cewa, "Maganar gaskiya ba zan bawa yaron nan Raihan ba, ba don komai ba sai don yana ɗauke da sunan wanda na fi tsana a duniya. Kin san komai game da Huzaifa yanzu kina ga wani zai zo mu bashi aurenta ne?" Mommy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Don yana ɗauke da suna Huzaifa ba zai zama aibu ba Daddyn Raihan matuƙar mutumin kirki ne, yanzu don Huzaifa aljani ya cutar da Raihan sai mu ce duka masu Suna Huzaifa ba su da Hali kenan? Ka yi tunani sosai Daddyn Raihan kuma ka yi bincike tun da gidan iyayen Dr Hussain ba ɓoyayyun ba ne ka ga kuwa shi ma gidansu Barista Huzaifa ba zai yi wuyar sani ba. Amma batun ka hana shi auren Raihan bai ta so ba, tun da shekarun yarinyar nan ƙara gaba suke yi yanzu a ƙalla Raihan fa ta tafi shekara ashirin da huɗu." Daddy ba ƙaramin gamsuwa ya yi da maganar Mommy ba don haka ya numfasa ya ce, "Shi kenan Allah ya zaɓa mana abin da ya fi zama alheri." Mommy ta amsa masa, "Amin ya rabbi. Addu'a ita ce mafita." Daddy ya karɓi Muhammad yana yi masa wasa sannan ya ce, " Zan sanar da Raihan idan ta amince sai na bincika wanene yaron, asalinsa da tarbiyyarsa." Mommy ta faɗaɗa murmushi sannan ta ce, "Allah ya sa mu ji alheri." Daddy ya amsa da amin. A daren ranar Daddy ya sanar wa da Raihan abin da yake tafe da Barista, Raihan mamaki abin ya bata. Don haka ta cewa Daddy sai ta yi shawara tukunna, su Inno na jin wannan zance suka riƙa murna da farinciki Goggo har da guɗa yadda kasan an ce mata ɗaura auren Raihan aka yi. Washegari da yamma tana zaune a wurin Kabiru suna hira, don Kabiru shi ya zame wa Raihan babbar ƙawa duk wasu shawarwari a wurinsa take nema kuma yana bata shawarwari masu kyau. Tun da su Barista suka zo gaban Kabiru yake faɗuwa ya rasa dalili, fargabarsa ɗaya kar ace masa manema aurenta ne, amma da ya ga sun fito da wuri sai ya ɗauka kawai baƙi ne wani uzuri ya kawo su. Suna zaune Raihan ta dube shi ta ce, "Fillo shawara na zo nema!" Ras! Ya ji gabansa ya faɗi sai ya yi ƙarfin hali ya ce, "Ina jin ki fillo me yake faruwa?" Raihan ta ajiye lemon hannunta ta ɗora da cewa, "Ina mutanen da suka zo jiya? Ba ka lura da wani mai baƙar hula ba?" Da sauri Kabiru ya gyaɗa kai gabansa na ci gaba da faɗuwa, Raihan ta taɓe baki ta ce, "Wai sona yake da aure shi ne ya zo ya samu Daddy da maganar kasan abokin Dr da ya yi wa Mommy Cs ne." Nan take Kabiru ya sauya fuska cikin yanayin damuwa, gudun kar Raihan ta harbo jirkinsa ya ce, "Ah kai masha Allah, Allah sanya alheri." Raihan ta ɓata rai ta ce, "Shawara da na zo ka bani ko ka ga ya yi ne." Hararar wasa ya yi mata sannan ya ce, "Malama ki ce kin faɗa sonsa kawai, to da za ki tambaye ni, ni zan zauna miki da shi?" Raihan ta yi murmushi cikin zolaya ta ce, "Ina za ka zauna min da shi na zauna da abina dai, kaima wataƙila kana can da amaryarka." Wannan maganar ba ƙaramin dagula wa Kabiru rai ta yi ba, cikin damuwa ya miƙe yana faɗin, "Fillo kin yi na lokacinki sai gobe." Raihan ta miƙe tana dariya don ita bata kawo komai ba ta ce, "Au yaji za ka min, shi kenan wallahi idan ni ce ina zaune za ka zo nemana." Tana gama maganar ta wuce cikin gida. Kabiru na shiga ɗakinsa ya fara kaiwa da kawo wa don zuciyarsa ba ƙaramin zafi take yi ba, shi kansa ya san Raihan ta yi masa nisa amma babu yanda zai yi don zuciyarsa har kullin azalzalarsa take ƙaunarta na ci gaba da ruruwa a ruhinsa. A cikin ƙasa da sati guda Daddy ya sa aka binciko masa wanene Barista Huzaifa asalinsa, sana'arsa, mu'amalarsa da waɗanda yake hulɗa da su. Huzaifa ɗan asalin unguwar Kurawa ne wata unguwa da ke cikin garin Kano, su biyar ne a wurin iyayensa yana da yaya Ibrahim shi ne na biyu sai ƙannensa mata guda uku biyu suna ɗakin aure ɗaya budurwa ce tana karatu a FCE Kano. Tare suka taso da Dr Hussain gidajen iyayensu na maƙotaka da juna, daga baya sai iyayen Barista suka tashi daga unguwar kurawa zuwa Fagge, sakamakon gina musu gida da yayan Mustafa ya yi. Barista Huzaifa yana da ilimin addini da na zamani daidai gwargwado, ya karanci ɓangaren shari'a a jami'ar Bayero. Ya samu aiki bai fi da shekara guda ba Mahaifiyar Dr Hussain Allah ya yi mata rasuwa. Fara aikinsa da shekara biyar ya samu canjin aiki zuwa garin Kaduna. Barista Huzaifa yana da kyawawan halaye sai dai abu ɗaya gare shi mummuna wato bin mata, wannan ya samo asali ne tun lokacin da ya fara soyayya da wata yarinaya Sakina, ya so sakina matuƙa daga ƙarshen iyayenta suka ce wani ɗan uwanta za su aura mata. A wannan lokacin ya shiga matsanciyar damuwa, ganin halin da yake ciki ya sa wani abokinsa yi masa tayin fara zuwa Club. Duk da bai taɓa zuwa ba amma ko kaɗan bai musa wa abokinsa Abubakar ba, saboda a lokacin neman duk wani abu da zai ɗebe masa kewa yake yi. Tun a ranar farko ya haɗu da Sima wata riƙaƙƙiyar karuwa, kuma dama tun da ta lura da Barista Huzaifa yawunta ya tsinke a kansa. Babban farincikinta da Abubakar ya sanar da ita sabon yankan rake ne bai saba harkar ba, haka suka jone da Sima suka ci gaba da rayuwa kamar mata da miji. Sannu a hankali Abubakar ya nuna masa ai zama wuri ɗaya tsautsayi ne don haka ya riƙa yi yana cancanza mazauni, wato ya riƙa neman mata kala-kala sun fi ɗebe kewa. A da Barista Huzaifa ya ɗauka ba zai taɓa jin daɗin mace bayan Sima ba, sai da ya tsunduma a harkar sannan ya ji ashe ita ma shafar mai ce. A haka ya ci gaba da rayuwa lokaci-lokaci yana kawo wa iyayensa ziyara, sai dai kullin cikin yi masa faɗan ya fito da mata suke yi, sai dai ya ce musu aure lokaci ne idan lokacin ya zo zai yi. Daga ƙarshe ma sai ya ke ce musu akwai yarinyar da suka daidaita karatu take yi sai ta gama za a yi maganar aure. Bayan Daddy ya gama bincike da kansa ya samu Raihan da maganar Barista Huzaifa, bata da zaɓi don ita kanta tana sha'awar ace yau ita ce ta yi aure take zaune a gidan mijinta. Musamman da take ganin mafi yawan ƙawayensu duk sun yi aure, don haka ta dubi Daddy ta ce, "Daddy na amince Allah ya tabbatar mana da alheri." Daddy ya yi murmushi ya amsa da Amin. A ranar Daddy ya kira Dr Hussain ya ce masa ya amince ita ma daga ɓangaren Raihan ta amince, Dr Hussain godiya ya yi sannan ya ce zai sanar da Barista Huzaifa duk abin da yake faruwa da yake tuni ya koma wurin aiki. Lambar Raihan Dr Hussain ya roƙa a wurin Daddy a cewarsa zai tura wa Barista kafin ya zo, idan ya so sai su fara gaisawa. Daddy bai musa ba ya turawa Dr Hussain number Raihan, shi ma Daddy na tura masa bayan ya kira Barista ya gama sanar da shi yadda suka yi da Daddy sannan ya tura masa lambar Raihan. Da daddare bayan sallar Isha'i Raihan na zaune da Laptop a gabanta tana binciko wasu kaya da take son yin order su, wayarta ta fara ringing. Ganin baƙuwar lamba ya sa bata ɗauka ba har sai da aka kira sau biyu. A gajarce ta ɗauki wayar ta furta, "Assalamu alaikum." Sai da ya amsa mata sannan ya ce, "Ashe dai ƴanmatan ta ɗauki nasiha ta, ta koyo sallama." Guntun tsaki Raihan ta yi don a yanayin maganar sa ta fahimci wanene shi. Bata tanka masa ba ta riski muryarsa yana cewa, "Barkanki da dare ina fatan ban takura miki ba." Raihan ta furta, "Kusan haka ne." Siririyar dariya ya yi wacce ya saba saye zuciyar ƴanmata da ita sannan ya fara yi wa Raihan bayanin abin da yake tafe da shi, amsa ta riƙa bashi daki-daki daga ƙarshe ta shaida masa ta taɓa aure da yadda yanayin auren nata ya kasance. Sun ɗan jima suna hira sannan suka yi sallama. Sannu a hankali soyayya ta fara ƙulluwa tsakanin Raihan da Barista Huzaifa, tun Raihan bata sakin jiki da shi har ta fara saki. Sai dai abin da ta lura da shi Barista Huzaifa yana da matuƙar son zolaya, gashi da barkwanci don idan suna hira yana dariya kamar ba shi ba. A haka har manya suka shiga maganar aka tsayar da ranar aure wata biyar, a lokacin kuwa saura wata biyu auren Kabiru da ƴar yayan Mahaifinsa wacce aka yi alƙawarin aurensu tun suna ƙanana. Kasancewar Barista Huzaifa a nesa yake ya sa bai cika zuwa akai-akai ba, don zuwansa biyu aka tsayar musu da ranar aure sai dai waya da chart da suke yawan yi. Su mommy ba ƙaramin farinciki suka yi ba, haka daga ɓangaren ƴan uwan Salim da suka samu labari har gida Farida ta zo ta yi wa Raihan murna. A ranar ne kuma Raihan take gaya mata maganar auren Kabiru, don a lokacin auren Kabiru saura bai fi sati biyu ba. Wannan maganar ba ƙaramin muni ta yi wa Farida ba, don haka ta wuce gida zuciyarta babu daɗi. Lokacin da za ta tafi Raihan ta haɗa mata sha tara ta azziki, har atamfa ta ɗauka daga cikin atamfofin da ta sayawa Kabiru sabida so take ta yi masa bazata ko akwati biyu ta haɗa masa, duk da ta lura ko kaɗan auren baya gabansa. Ita kanta tana damuwa da rashin walwalar Kabiru saboda a baya mutum ne mai matuƙara barkwanci, da son hira. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 34 Raihan ba ƙaramin kaya ta haɗa wa Kabiru ba kusan akwati uku don akwati biyu ta cika taf, wasu kayan masu yawa suka ragu don haka ta ɗora masa da kit. Ba ƙaramin daɗi ya ji ba duk da ko kaɗan baya maraba da auren, daga ɓangaren Daddy kuɗi ya ba wa Kabiru masu tsoka a cewarsa ya sayi duk abin da yake da buƙata wajen hidimar biki. Mommy kayan abinci ta saya masu ɗan dama a lokacin da Kabiru zai tafi ta bashi don a yi hidimar biki kafin su je. Kabiru ba ƙaramin daɗi ya ji ba don dama ya san za su yi masa saboda mutane ne masu karamci da kyauta, ko kaɗan abin hannunsu bai rufe musu ido ba. Saura sati guda biki Kabiru ya tafi garinsu don Mahaifiyarsa kusan kullin sai ta kira shi a waya game da aure. Kabiru ɗan asalin garin Shanono ne cikin wani ƙauye mai suna Rigar Arɗo, daga dangin mahaifi da Mahaifiya gabaɗayansu haifaffin garin shanono ne. Mahaifinsa sunansa Musa Balarabe amma an fi saninsa da Baffajo, sai mahaifinyarsa mai suna Karime ana kiranta Inna wuro sakamakon ta ci sunan kakarta ta wurin Mahaifi. Kabiru su biyar ne a wurin iyayensa, shi ne babba sai ƙanwarsa mai bin sa Rahane wacce ake kira Rahe. Tana da aure da ƴaƴa shida, sai mai bin ta Fatsim ita ma tana da aure da ƴaƴa uku, daga ita sai Shatu wacce take da ƴaƴa biyu sai ɗan autansu mai suna Bala wanda yake da shekara goma sha biyu. Baffajo manomi ne kuma makiyayi ne ya riƙi sana'ar noma da kiwo tubalin da yake gina iyalinsa ta hanyar ci da sha, ilimi da tufatarwa. Yana da rufin asiri sosai kasancewar Ubangiji ya yalwata su da arziƙin dabbobi musamman shanu da awaki. Baffajo yana tsayawa ƴaƴansa kai da fata wurin ganin sun samu ilimin addini sai dai basa karatun boko kasancewar basu ɗauke shi da muhimmanci ba. Kabiru tun yana da kimanin shekara goma Mahaifinsa Baffajo ya ɗauke ya kashi almajiranci can garin gombe, sai dai bai bar shi kara zube ba yana shirya wa lokaci-lokaci yana kai masa ziyara haɗe da kai masa kayan abinciki ya damƙa wa Malaminsu Malma Iro. Kasancewar Malam Iro mutane da dama sun shede shi akan kula wa da almajiransa, Mutum ne mai amana da kula wa da haƙƙin da aka ba shi don haka ya sa su Kabiru suke matuƙar ƙaunarsa. A makarantar Malam Iro Kabiru ya haɗu da wani almajiri mai suna Babbale, Babbale nutsattse ne ba shi da hayaniya kamar dai Kabiru don haka ta su ta zo ɗaya suka ci gaba da rayuwa da daɗi babu daɗi har Allah ya kai su lokacin da suka yi saukar alƙur'ani kowa ya kama gabansa. Kabiru ya koma garinsu ko shekara bai yi ba watarana shi da Baffajo sun shiga gona wasu ɓata gari da ake zargin ɓarayi ne suka shiga gonaki suka riƙa illata manoman da makiyaya sannan suka kaɗe duka shanun garin suka yi awon gaba da su. A cikin waɗanda suka jikkata har da Mahaifin Kabiru wanda suka harbe shi har a wuri biyu. Harbin farko a gwiwar ƙafarsa harsashi ya ratsa sai tsakiyar bayansa da nan ma suka sakar masa harbi. Kabiru kuma karaya ɗaya ya yi a ƙafa sakamakon saran da suka riƙa kai masa har suka ci galaba akansa. A wannan lokacin mutanen wannan ƙauyen sun shiga firgici da tashin hankali sakamakon ba su taɓa cin karo da irin wannan ta'addancin a cikin garinsu ba. A haka suka ci ga ba rayuwa waɗanda suka rasu aka yi musu sitira waɗanda suka jikkata aka shiga nema musu magani. Mahaifin Kabiru yana ɗaya daga cikin mutanen da aka yi wa mummunan rauni, saboda da farko maganin hausa ake yi masa sai da suka ga ƙafarsa ta tasamma lalace wa sannan aka fara kai shi cikin gari babban asibiti. Tashin farko likitoci suka tabbatar da yanke ƙafar Baffajo za a yi saboda ta riga da ta lalace ba zai sake morarta ba, a wannan lokacin su Inna wuro ba ƙaramin tashin hanakali suka shiga ba. Amma da yake suna da ragowar ƴan kadarorinsu sai suka ganganɗa suka sayar da aka biya kuɗi aka yanke wa Baffajo ƙafa tun daga wurin gwiwarsa har zuwa idon sawunsa. Sai da likitoci suka sake yin gwaje-gwaje da hotuna aka sake gano babbar matsalar da take tattare da Baffajo domin ƙashin bayansa ya samu matsala, don haka sai an yi masa aiki. Tashin farko kuɗin hoton ƙashin bayansa kusan dubu ɗari biyu da hamsin aka caje su sannan da aka gano ciwon aka tabbatar da za a yi masa aiki amma sai sun zube maƙudan kuɗi naira miliyan ashirin da biyar. Wannan magana ta likitoci ba ƙaramin ɗaga hankulansu ta yi ba, Kabiru da kansa ya riƙa bi cikin rugarsu yana neman taimako koda karo-karo ne amma ko dubu ɗari a cikin ƙauyensu bai samu ba. Ganin ba su da damar waɗannan kuɗaɗen suka tattaro suka dawo gida da Baffajo ya ci gaba da jinyar jikinsa ana yi masa maganin hausa. Sai dai tun da ya kwanta wannan jinyar komai sai an yi masa, sai an ɗaga sa an kwantar hatta fitsari sai dai ya yi a wurin idan kuwa aka zo gyara shi ya rinƙa ihu saboda tsananin azabar da yake ji a jikinsa. Ana cikin haka har duk abin da suke da shi ya ƙare har ya kai Inna Wuro ta fara sayar da sitirar da suke saka wa. Ganin haka ya sa Kabiru ya yi tattaki zuwa gidan kansilan garinsu don ya yi masa hanyar zuwa wurin sanatan yankinsu ko zai samu ya taimaka masa. Amma fir Kansilan ya ƙi daga ƙarshe wani abokinsa Na Sa'ade ya kira bayan ya zauna ya nuna Kabiru sannan ya yi masa bayanin halin da Baffajo yake ciki, Na Sa'ade mazaunin garin ne amma yana zuwa kasuwanci cikin garin Kano don haka ya fi su wayewar kai don haka Kansila yake ji da shi a garin. Na Sa'ade yana gama jin bayanin Kansila cikin yanayin tausayi ya ce, "Taimako ɗaya zan yi maka na haɗa ka da wani mutumi a birni amma shi aikinsa zai nema maka gida ka riƙa gadi amma a ƙa'idarsa albashinka na wata ukun farko shi zai karɓa. Amma fa zai kai ka gidajen masu yatsu da yawa, don ba za ka yi zaɓen tumin dare ba. Ina taƙaice maka wataƙila duk wata ka riƙa samun dubu hamsin." Jin wannan maganar ya sa Kabiru ya ce zai je ya yi shawara da Mahaifiyarsa idan ta amince, saboda suna fuakantar matsanancin talauci. Lokacin da Kabiru ya sanar wa da Inna wuro ƙin amincewa ta yi saboda tana tsoron kar a tafi da Kabiru birni a sayar da shi, amma da Kabiru ya nuna mata mutumin na hannun daman Kansila ne sai ta amince amma da sharaɗin sai sun je gaban Mai gari an yi maganar a gabansa. Lokacin da Na'sade ya ji wannan maganar ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba har ya nuna ya fasa tafiya da Kabiru, amma da Kabiru ya lallaɓa shi kuma ya nuna masa yanayin rikicin tsofaffi ne sai ya amince. A gaban Mai gari aka yi komai bayan wannan zaman da kwana biyu Kabiru da Na Sa'ade suka taho garin kano. A washegarin ranar da suka sauka Na Sa'ade ya kai Kabiru gidan Malam Haru sannan ya gabatar da Kabiru, cikin mutumci ya tarbe shi sai da suka zauna sannan ya sanar wa da Kabiru sharuɗɗansa nan take ya amsa tun da dama Na Sa'ade ya sanar da shi kafin su zo. Satin Kabiru ɗaya a gidan Malam Haru aka zo masa da maganar samun aiki a gidan Daddy, ba ƙaramin daɗi ya ji ba don haka ya fara aikinsa cikin mutumci da mayar da hankali. Haka Kabiru ya ci gaba da aikin gaidinsa sai dai tun zuwansa yake waɗansu irin miyagun mafarkai masu ban tsoro, a ranar da ya fara cin karo da Mama Uwani ranar kwana ya yi kansa na tsananin yi masa ciwo da mafarkin manyan baƙaƙen shanu suna biye da shi za su halaka shi. Haka kawai ya ji ta su bata zo ɗaya ba don haka ko shiga sabgarta baya yi tun da dama ba fito wa harabar wurinsa take yi ba. Ana gobe ɗaurin auren Kabiru da amaryarsa Dije su Raihan suka dira a garin su Kabiru da kwatance ta waya, duk sai kunya ta kama Kabiru da ya tuna irin katafaren gidan da su Mommy suke rayuwa a ciki ya duba nasu gidan, ya ga ko kwatan na Daddy bai kai ba. Haka su Inna wuro suka riƙa nannan da su Mommy don ɗaki guda suka basu gabaɗaya ita da su Inno. Shi kuma Daddy aka sauke shi a gidan Mahaifin Amarya wato yayan Baffajo. Raihan gabaɗaya ji ta yi kamar tana kewar Kabiru don kusan kullin tun tafiyarsa sai sun yi waya da shi wani lokacin idan Barista Huzaifa ya ji tana yawan ambatar sunan Fillon har haushi yake ji. A daren ranar da suka sauka bayan sun huta Kabiru da Raihan suka fito suna tafiya a cikin garin, don Raihan ta tilasta masa sai ya kaita gidansu amarya ta ganta. Amma a ɓangare ɗaya haka kawai ta riƙa jin ranta yana matuƙar ɓaci, ganin yanayinta ya sa Kabiru ya furta, "Lafiyarki kuwa fillo?" Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Ba komai Fillo, wai don Allah baka yi missing ɗina ba saboda Allah ace amini guda wai ko dai ka samu sabbin abokai ne Fillo?" Kabiru ya yi dariya zuciyarsa wasai don ko ba komai ta nuna ta damu da shi sannan ya ce, "Da gaske ne abin da kike faɗa fillo kin yi kewata?" Kabiru ya tambaye ta kasancewar ya gane me kalmar missing take nufi. Raihan ta taɓe baki cikin zolaya ta ce, "Wai fa har ka ji daɗi ko? To ni ma zolayarka nake yi." Ƙarasa maganarta ya yi daidai da zuwansu wani ƙofar gida da yara suke ta atisaye da ƙasa. Kabiru yana shirin aika yaro don ayi sallama da Dije Raihan ta dakatar da shi tare faɗin ita za ta shiga ta fito da amarya da kanta. Da sallama ta shiga cikin gidan, lokaci ɗaya suka tsaya suna kallonta saboda daga shiga da sautin muryar Raihan duk ta bambamta da ta su. Bayan sun amsa mata Raihan ta ce, "Ina Amarya Dije." Dije na jin haka ta mayafi ta rufe fuskarta, saboda tsananin kunyarta. Ras Raihan ta ji gabanta ya faɗi wani irin abu ya turniƙe zuciyarta. A hankali ta ƙarasa wurin ta ce, "Tare muke da angonki yana ƙofar gida mu je yana jiranki." Dije ƙin buɗe fuska ta yi sai ƙyar Raihan ta samu suka fito suna zuwa ƙofar gida hasken farinwata ya haske fuskar Dije. Wani abu ne ya sake taso wa Raihan amma sai ta kawar da kanta ta ci gaban da zolayar amarya da ango. Don ita kanta bata san dalilin da ya sa take jin haushin Dije ba, duk da wannan ne haɗuwarsu ta farko. Sun jima suna hira sannan Su Raihan suka yi mata sallama suka koma gida. A washegarin wayewar garin Juma'a aka ɗaura auren Kabiru da Dije akan sadaki Dubu hamsin, Daddy ne ya bayar da kuɗin bayan an gama abin da za a yi suka ɗauko hanya suka nufo garin Kano. Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da gangarawa, har Kabiru ya gama rayuwar amarcinsa da amaryarsa ya koma bakin aikinsa na gadi, a lokacin bikin Raihan saura bai fi sati biyu. Daga ɓangarorin nan biyu duka kowanne shirye-shiryen biki suke yi, Daddy shi kansa ya dage sai sayayya yake haka daga ɓangaren mommy abin ba a cewa komai. A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har aka shiga satin bikin Raihan. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 35 Tun da bikin Raihan ya ƙarato kullin cikin ɓacin rai Kabiru yake, har sai da Raihan ta gagara haƙuri ta same shi a harabar gidansu. Wannan karon ma ɗaure fuska ta yi tamau kamar wata uwarsa ta nuna wata farar kujera da hannunta ta ce, "Zo ka zauna." Ba musu Kabiru ya ƙarasa ya zauna jiki babu ƙwari. Hannuwa biyu ta haɗa ta zabga tagumi tana zura masa ido sannan ta ce, "Fillo!" Yadda ta ambaci sunansa har tsakiyar kansa kallonta yi ba tare da ya furta mata koda kalma ɗaya ba sannan ta ci gaba da cewa, "Fillo me yake damunka?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Tabbas ina cikin damuwa, zuciyata na azalzalata domin furen da nake ƙoƙarin bawa ruwa ya bushe. Na jima ina ƙoƙarin ganin na mallaki ɗan itaciyar amma tuni bakin alƙalami ya bushe domin sama ta yi wa yaro nisa sai kallo sai hange daga nesa. Ki taya ni roƙon Allah da ya cire min sonta a cikin zuciyata domin babban goro sai magogin ƙarfe." Ran Raihan ba ƙaramin ɓaci ya yi ba a fusace ta dube shi ta furta, "Yanzu akan wata kake ɓata ranka a banza, ba na gaya maka ka cire ta a ranka ba tun da kullin cikin cewa ka rasa ta kake yi." Muryar Raihan ce ta fara rawa idanunta suka ciko da ƙwallah cikin rawar murya ta ci gaba da cewa, "Wacece wannan da ba za ka iya rabuwa da ita ba? A ina take? Me ya sa za ka takura rayuwarka a kanta, ka cire ta daga zuciyarka ko dole ne sai ka so ta?" Kuka ne ya ci ƙarfin Raihan wanda ita kanta bata san dalilin zubarsa ba, jiki a sanyaya Kabiru ya kai hannunsa saitin zuciyarsa da take buga masa da sauri-sauri sannan ya furta, "Da ina da halin cire ta a raina da tuni na cire na huta da azabtacciyar soyayyarta, kamar yadda na gaya miki ki taya ni da addu'a shi ne mafita." Raihan ta miƙe a sanyaye sannan ta ce, "Shi kenan Allah ya kyauta." Taku biyu ta yi Kabiru ya ce, "Wai Fillo dama haka kike ji da ni? Gaskiya zan yi kewarki idan kika tafi." Raihan ta juyo ta taɓe baki sannan ta ce, "Kar ka min sharri haka nace maka?" Raihan na ƙarasa maganar ta wuce cikin gida. A ranar haka Raihan ta wuni duk jikinta ba daɗi, zuciyarta a dagule daga baya da ta rasa dalilin fushinta akan Kabiru sai da watsar da lamuransa ta ci gaba da harkokin gabanta. Washegari kamar kullin Kabiru yana zaune a harabar gidan gefe ɗaya ga rediyo tana ta aiki ita kaɗai, a yadda ya nutsu za ka rantse da Allah sauraron ma'aikatan gidan redio yake amma a baɗini sam ba haka ba ne, hankalinsa da tunaninsa sun tafi duniyar tunani daban. Raihan ce tsaye a kansa ta kira shi ya kai sau uku sannann ya yi firgigit ya ɗago haɗe da sakar mata wani yalwataccen murmushi. Guntun tsaki ta yi ta ƙarasa ƙofar ɗakinsa ta janyo kujera ta zauna suna fuskantar juna, yana shirin yin magana Raihan ta ɗaga masa hannu fuska babu walwala ta ce, "Don Allah idan zancen wannan budurwar taka za ka min na yafe, tun da baka da aiki sai na begenta. Kuma wallahi idan ka cika ni zan kira ƙanwata Dije na gaya mata halin da ake ciki, don ba zai yuwu ka aje min ita a can Shanono ba ka zo kana begen wata." Da ido Kabiru ya bi Raihan yana kallon yadda take sauke kowacce kalma ɗaya da bakinta, ganin irin kallon da yake yi mata ya sa ta juya masa ido haɗe da tura ɗankwali gaba tana faɗin, "Fillo don Allah ba wannan ba, zuwa na yi kaban shawara game da bikin nan ka ga saura kwana huɗu, kuma Barrista ya ce yana son a yi dinner da wacce uwa ni kuma yanzu duk waɗannan abubuwna ba sa gabana." Raihan ta jim sai kuma muryarta ta fara rawa idonta ya ciko da ƙwalla ta ci gaba da cewa, "Ban sani ba ko za mu yi doguwar rayuwa da Barista don gabana faɗuwa yake ina jin tsoron kar wani abu ya faru da shi kamar yadda ya faru da Salim, Fillo soyayyar Salim a jinina take har yau na saka cire shi a zuciyata. Ranar ɗaurin aurena da take tunkaro ni a kullin na tuna sai gabana ya faɗi ina fargabar kar wani abu ya sake faruwa tun da shi ma na riga da na saki jiki da shi." Ba ƙaramin tausayi Raihan ta bashi ba, sai dai duk da yana jin zuciyarsa na ɗaci a game da aurenta bai hana shi ya lallasheta ba saboda yana matuƙar san ganin farincikin Raihan. Har cikin zuciyarsa ya ji baya ƙaunar aurenta da Barista Huzaifa amma ba shi da wata hujja ko wani dalili da zai sa ya furta wannan maganar, ta wani fanin kuma yana ganin kamar ya so kansa da yawa idan ya ce baya son Raihan ta yi aure domin rayuwar mace taƙaitacciya ce, kuma shi bai furta mata kalmar soyayya ba ai baya rugeje mata tata soyayyar ba. Kamar yadda ta saba masa a duk lokacin da ta fahimci yana cikin damuwa haka ya yi mata, miƙe wa ya yi tsam ya shiga ɗakinsa ya buɗe ɗan ƙaramin firjinsa ya ɗebo mata ruwa mai sanyi, har lokacin da ya koma bata motsa daga yadda ya bar ta ba. Sai da ya tsiyaya mata ruwa a kofi ya miƙa mata sannan ya zauna a kan kujera ya furta, "Fillo!" Ɗago wa ta yi ta kalle shi bata san dalili ba sai ji ta yi hawaye na zuba. Kawar da kansa gefe ya yi yana jin kukanta har cikin zuciyarsa miƙe wa tsaye ya yi ya bata baya sannan ya ce, "Idan kina son mu yi magana don Allah ki daina barin hawaye na zuba daga idonki." A hankali ta sa hannu ta goge ƙwallar idonta, juyo wa ya yi mata hararar wasa ya ce, "Ga wata nan a gefe." Ya faɗa yana nuna gefen fuskarta. Ita ma harar wasa ta sakar masa ta ce, "Ai dole ka ga makwancina Fillo tun da ina hawaye a gabanka." Kabiru yana shirin yin magana suka ji ana buga gida. Da sauri Kabiru ya ƙarasa wurin ya leƙa don ganin mai buga wa nan take ransa ya yi mummuna ɓaci, sai da furzar da iska mai zafi sannan ya dubi Raihan murya a daƙile ya ce, "Kin yi baƙo!" Da mamaki ta dubi Kabiru ta ce, "Baƙo kuma? Waye haka?" Ta yi maganar cikin mamaki don ko kaɗan ba su yi hirar zuwan Barista Kano ba. A hankali Kabiru ya zare sakatar ƙofar Barista Huzaifa ya shiga yana watsa wa Kabiru kallo, haka shi ma daga ɓangaren Kabiru wani ƙasƙantaccen kallo ya watsa wa Barista sannan ya shige ɗakinsa ba tare da ya tanka masa komai. Raihan na ganin Barista ta faɗaɗa fara'arta haɗe da faɗin, "Amini kai ne a gari? Gaskiya ka iya suprise me ya sa baka gaya min ba?" Fuska babu walwala Barista Huzaifa ya ce, "Dole ki ce haka tun da kina wurin mai gadi kuna hira, na kira ki ya fi sau shurin masaƙi baki ɗauka ba." Raihan ko kaɗan bata ji daɗin kalmar da ya gayawa Kabiru ba don haka ta nuna masa kujerar da Kabiru ya tashi, yamutsa fuska ya yi ya ce: "Wannan ba mahallina ba ne ki bari wanda ya fi cancanta da ya zauna idan na baku wuri sai ya zauna, ku ci gaba da hirarku. Amma fa ki yi haƙuri na katse muku jin daɗi don na san ba haka kuka so ba..." Tun bai rufe baki ba Raihan ta katse shi da cewar, "Haba Barista me kake faɗa haka ne, wai baka san waye Kabiru ba?" Tana rufe baki Barista ya rufe ta da faɗa Raihan tun tana kare kanta har ta ja bakinta ta yi shiru, duk da ta san Barista na nuna kishinsa akan Kabiru bata taɓa tsammanin abin nasa ya kai haka ba. Kabiru na daga ɗaki ya ji ba zai kasa daure ba don haka ya fito a zafafe ya kalli Barista ya nuna masa ƙofa haɗe faɗin, "Malam zo ka fice idan ka gama." Da mamaki Barista ya kalli Kabiru sai ya saki dariyar takaici ya ce, "Lallai mai gadi ya samu wuri..." Raihan ta ƙarasa gaban Kabiru ta furta, "Me kake yi haka Fillo ka na cikinn hayyacinka kuwa? Mijin da zan aura ne fa me ye naka a ciki?" A hargitse ya ɗago ya kalli Raina don maganganunta ba ƙaramin ƙara masa ɗaci a zuciya suka yi ba, Barista ta naɗe hannunsa sannan ya ce: "Da baki ba shi damar ya min haka babu yadda za a mai gadi ya raina mijin da za ki aura." Raihan ta dubi Kabiru ta ce, "Fillo ka bashi haƙuri." Wannan karonma kallonta ya yi ba tare da ya furta komai ba, sai da ta sake maimaita abin da ta faɗa yana shirin yin magana ta katse shi da cewar, "Ba na buƙatar jin komai ka bashi haƙuri na ce." Kabiru ya ƙarasa gaban Barista suka yi ido biyu sannan ya waiga ya kalli Raihan ya ce, "Komai zan yi saboda ke ne don kina ɗaya daga cikin mutane masu muhimmanci a gare ni." Babu musu ya bashi haƙuri sannan ya koma ɗakinsa. Barista ya jima Raihan tana bashi haƙuri sai daga baya ya sauko sannan suka ci gaba da tattauna akan lamuran da ya shafi bikinsu. Duk yadda Raihan ta so kauce wa yin wata bidi'a a bikin sai da Barista Huzaifa ya shawo kanta ta aminci, za su yi Dinner da Kamu amma daga haka sai ɗaurin aure. Duk abin da yake faruwa Kabiru yana daga ɗaki yana jin su, sai dai gabaɗaya zuciyarsa a dagule take. Sun jima suna hira sannan Barista ya yi mata sallama ya wuce gida, Raihan duk da yadda zuciyarta ta kai ga azalzalarta yi wa Kabiru magana haka ta danne don ta san kowaye aka yi masa abin da Kabiru ya yi ba zai ji daɗi ba, don haka tana raka Barista ta wuce gida. Sannu a hankali haka suka ci gana da rayuwa Kabiru na fushi da Raihan ita ma tana yi don ko fita wurinsa ta daina yi, Raihan tuni aka shiga yi mata gyaran jiki kala-kala ban da ƙamshi babu abin da take yi. Hatta kaya idan ta cire ƙamshi suke yi saboda yadda turare ya ratsa jikinta. Ranar laraba aka yi kamun amarya a cikin gidansu Raihan, wani ɗinki aka yi mata da atamfa ba ƙaramin kyau ta yi ba. Kowa ya ganta sai dai ya ce masha Allah saboda yadda aka zane hannunta da ƙafarta da jan lalle, ga kwalliyar da aka yi mata daidai misali ta yi mata kyau. Washegari Alhamis aka yi dinner ɗin Raihan da Barista a Nihal Event center, wurin ba ƙaramin ƙayatuwa ya yi ba. Haka aka yi dinner aka tashi wannan karon su Inno ba su je ba, a cewarsu wurin zuwan yara ne ba na su ba. A haka aka tashi daga taro gwanin birge wa, don sun yi taro lafiya sun tashi lafiya kowa yana santin yanayin bikinsu. Ranar Juma'a kamar yadda sanarwa ta gabata aka ɗaura auren Raihan da Barista Huzaifa akan sadaki dubu Ɗari, saboda tun kafin lokacin bikin Daddy ya nuna baya buƙatar kuɗin sadaki masu matsanancin yawa, ya fi buƙatar albarkar abin musamman da ya ga irin manyan akwatunan da Barista ya dire wa Raihan har saiti biyu. Wannan karon su Goggo har mai kiɗan ƙwarya suka ɗauko, haka mata suka cashe su kaɗai Raihan kuwa tana ɗaki tana tunanin lokacin bikinta Salim da irin shagulgulan da aka sha. Zuciyarta ce ta karye, a hankali ta miƙe jiki ba ƙwari ta nufi sashen Mommy kai tsaye ɗakinta ta nufa ta ci sa'a babu mutane da yawa tana shiga ta faɗa jikin mommy ta saka kuka. Mommy bata hana ta ba don ta lura tun da bikin Raihan ya matso take cikin damuwa, sai da ta yi mai isarta sannan ta: "Mommy tsoro nake ji kar wani abu ya faru an jima ba na son na rasa Barista ina ji..." Da sauri Mommy ta rufe mata baki haɗe da cewar, "Ki sawa zuciyarki kin yi aure ne na tsakani da Allah, don Salim ya rasu a daren aurenki bashi yake nuna Barista zai tafi ba." Mommy ta jima tana yi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin. Kimanin ƙarfe takwas saura motocin ɗaukan amarya suka kafa da'ira a ƙofar gidansu Raihan. Sai da aka yi mata nasiha mai ratsa jiki sannan aka damƙata a hannun Goggo da Inno suka shiga mota da ita, kamar wancen karon sai da aka fara kai Raihan gidan Iyayen Barista sannan aka wuce da ita katafaren gidanta da ke unguwar Maidile, kasancewar Barista ya ɗauki hutun wata biyu don haka za su zauna Kano bayan sun cinye hutun su wuce garin Kaduna. Dr Hussain shi ne babban abokin ango duk wani shige da fice da shi ake yi, don haka baya zaune baya tsaye. Bayan an kai Raihan gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi, jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba don ta gama saddaƙarwa jira take ta ji wani labarin daban. Tana nan zaune ita da su Safna ta ji muryar su Barista da abokansa suna yi masa tsiya irin ta abokan angwaye. Bayan sun shigo sai da aka yi siyan baki sannan su Dr Hussain suka ɗauki su Safna za su mayar da su gida. Barista Huzaifa har bakin gate ya raka su sai da ya ga fitarsu sannan ya tura ƙofar haɗe da bushewa da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci ɗaya ya murtuke fuska sannan ya furta, "Alƙawari na ɗaukar wa kaina Raihan tawa ce ni kaɗai, ni ne mallakinta daga ni babu wani Namiji da zan lamunce ya mallaketa bayan ni. Ni Huzaifa duk wata hanya da zan bi na faɗa sai na bi ta don ganin na Mallaki matata." Huzaifa yana gama maganar ya wuce cikin gida wurin Raihan. Su Dr Hussain har sun fara tafiya Safna ta ce, "Kai! Dr wallahi na yi babbar mantuwa." Da mamaki ya tambaye ta nan take ta gaya masa wayarta ta manta a kan gadon Raihan. Dr Hussain magana ya yi wa sauran Abokan tafiyarsa da farko har sun ce ya je ya rakata su ɗauko, kasancewar dare ya fara yi ya ce su bari ya kira wayar Barista amma ɗif ya ji ta a kashe. Juya motar ya yi zuwa hanyar gidan Raihan amma duk yadda suka kai ga dube-duben su sun nemi gidan Raihan sama ko ƙasa sun rasa. 🤣 Ina masu cewa suna Allah-Allah Barista ya mutu🤣🤣🤣 To dai yanzu how market?🤣 Mu je zuwa Huzaifa kana wuta ina bin ka da fetir💃🏼 Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624 36 Ganin zagayen da suke yi ya yi ya wa ya sa Safna ta dubi Dr Hussain ta furta, "Dr ni fa kaina ya kulle, wai da za mu taho ba ta wancan layin muka biyo amma na ga mun yi zagaye ya kai sau huɗu ban ga gidan ba." Dr Hussain tuni shi ma kansa ya ɗaure a cikin zuciyarsa ya furta abin da Safna ta faɗa a don shi ma ba ƙaramin mamaki ya yi ba, yana jin ta yi magana cikin sauri ya ce: "Wallahi kin rigani a fili na riga ki a zuci." Munira da ke kujerar baya ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, "Ya kamata mu wuce gida idan ya so gobe in Allah ya kaimu ba sai mu dawo ba, tun da yanzu fa dare ya fara yi kar a ga mun daɗe..." Maganarta ce ta maƙale sakamakon wayarta da ta fara ringing ganin lambar Mama Hafsa ya sa ta ɗago fuskar wayarta tana faɗin, "Kun ga abin da nake gudu ko? Safna ga Mommynku tana kira." Miƙa wa Safna wayar ta yi jiki a sanyaye Safna ta ɗaga tana faɗin, "Mommy muna hanya wallahi wayata na manta..." Daga can ɓangaren Mama Hafsa ta katse Safna da cewar, "Ba na son sakarcin banza kin san ƙarfe nawa yanzu? Maza ku dawo gidan idan har ba ranki kika manta a gidan ba ai kya bari da safe ki koma ki ɗauko." Mama Hafsa na gama maganar ta katse wayar, jin irin faɗan da aka yi wa Safna ya sa Dr Hussain ya ja akalar motarsa ya juya hanyar gidan mommy. Ba su jima ba suka ƙarasa gidan, tare da yi wa Dr godiya sannan suka buga gida Kabiru ya buɗe musu. A lokacin da Huzaifa ya tafi raka su Dr sauke ajiyar zuciya Raihan ta yi tana jin wani irin farinciki yana ratsata, ƙaunar Huzaifa ta ji na ratsa cikin zuciyarta ita kaɗai ta saki wani malalacin murmushi. Tana jin alamar shigowarsa ta ƙara jan mayafinta ta rufe fuskarta, lokaci ɗaya ta ji gabanta na tsananin faɗuwa ga wata irin matsananciyar kunyarsa da take ji. Wannan yanayi da ta tsinci kanta a ciki ya sa ta faɗawa duniyar tunani don ta tabbata rashin saboda tun da hakan bai taɓa kasancewa da ita ba ne, ya sa take jin gabanta na faɗuwa. Tana nan zauna ta ji shigowarsa ras! Ta sake ji gabanta ya sake faɗuwa har sai da ta sauke ajiyar zuwa. Babbar rigarsa ya cire haɗe da ajiye wa akan gado sannan ya ƙarasa bakin gadon yana faɗin, "My happiness bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida." Murmushi ta yi ba tare da ta furta komai ba, a hankali ya zame mata mayafin kanra haɗe da rungumota jikinsa. Shiru Raihan ta yi tsigar jikinta na tashi sakamakon jin sabon lamarin da take fuskanta daga wurinsa. Ledojin da ya ajiye ya ɗauko ya buɗe a ƙasa sannan ya kalli Raihan ya ce, "Sauko my baby." A kunyace Raihan ta ce, "Na ƙoshi." Murmushi Huzaifa ya yi ya furta, "Ashe kuwa zan ɗauko ki cak daga wurin nan." Da sauri Raihan ta sauka ƙasa ai kuwa me zai yi mata ba dariya ba, ya lukuce kumatunta tare da faɗin, "Baby kin fiye tsoro why?" Shiru Raihan ta yi tana murmushi, a hankali Huzaifa ya riƙa yagar naman kazar yana saka mata a baki. Raihan tun tana jin kunya har ta fara sakin jikinta tana karɓa suna ci Huzaifa na sake janta da hirar soyayya. Huzaifa ya iya sace zuciyar mace da kalamai don haka suka ƙara tasiri a zuciyarta Raihan ta ƙara jin wata matsananciyar ƙaunarsa ta malale birnin zuciyarta. Sai da suka ci suka yi ƙat sannan Huzaifa ya kwashe kayan wurin ya kai su cikin kitchen, Raihan na rakuɓe a gefe fargaba fal cikin zuciyarta Huzaifa ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi ya riƙo hannunta. A sanyaye ta bishi ya zauna akan gado ya tallafota jikinsa haɗe da fara shafa jikinta yana faɗin, "I really miss you wifee." Murmushin yaƙe Raihan ta yi don har lokacin gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi, tun tana ɓoye tsoronta har ya bayyana a fili don saƙwanni Huzaifa yake aikawa Raihan zafafa. Ganin duk ta firgice ya sa Huzaifa ya ja ta har tsakiyar gado, tana biye da shi tamkar raƙumi da akala. Sauka ya yi ya kashe ƙwan fitilar da ke cikin ɗakin sannan ya kunnawa musu night lamp, kallon Raihan ya yi ya fara ƙoƙarin cire rigarsa. Raihan na ganin haka ta runtse idonta jikinta na karkarwa, tana cikin wannan yanayin bata yi aune ba ta ji Huzaifa a gefenta yana yunƙurin rabata da kayan jikinta. Muryarta na rawa ta dube shi ta ce, "Hubby ba mu yi sallar nafila ba." Cikin wata irin kasalalliyar murya ya furta, "Wacce irin sallah kuma?" Huzaifa bai san ya yi wannan maganar ba domin tuni ya fara fita daga hayyacinsa. Raihan ta fara ƙoƙarin kare jikinta ta ce, "Sallar Nafila." Huzaifa ya saka hannunsa cikin jikinta haɗe yawo da su cikin sassan jikinta. Yarrr ta ji tisgar jikinta na tashi, shi kuwa Huzaifa tuni ya yi nisa gabaɗaya ya fita a hayyacinsa saboda ƙamshinta da yake sake rikita tunaninsa. Kai hannunsa kan ƙirjinta ya sake ruɗar masa da lissafi haɗe da sauke ajiyar zuciya akai-akai. Jikin Raihan sai rawa yake don haka ta kai hannunta da niyyar dakatar da shi cikin yanayin fitar hayyaci ya furta, "Kar ki dakatar da ni don Allah, domin ke mallakina ce." Hawaye Raihan ta fara yi a hankali ta furta, "Don Allah ka bari sai gobe."Sannu a hankali Huzaifa ya fara neman kusantar Raiha nan take ta ji wani irin abu yana sukarta, tun bata tanka ba har ta ji ba za ta iya shiru ba domin abin na ƙoƙarin illatar da ita. Cikin tsananin azaba Raihan ta fara ja da baya a firgice tana faɗin, "Hubby don Allah ka bari wallahi ciwo nake ji me ye a jikinsa yake sukata." Huzaifa bai bi ta kanta ta sake fisgota da ƙarfi don babban burinsa ya ga ya cimma manufarsa. Wata irin azaba ce ta riƙa ratsa cikin jikinta da sauri ta ƙwalla wata irin gigitacciyar ƙara, ta tattare ƙarfinta wuri ɗaya ta hankaɗe shi tana ja da baya haɗe da takurewa wuri ɗaya. Ta dishi-dishin hasken da bai gama garwaye ɗakin ba ta hango wasu irin gajerun gashi masu kaifi kamar ƙayoyi na tsirowa daga jikinsa. Ƙirjinta ne ya buga tsoro ya fara kamata, tana cikin wannan halin ta riski muryarsa yana faɗin: "Me ya sa kike son hana ni halalina?" Raihan na daga gefe a zaune ta ce, "Wallahi wani abu ne yake fitowa a jikinka sukata yake yi." Hannunsa ya kai ya kunna ƙwan lantarkin ɗakin, nan take haske ya garwaye ko ina. Ganin haka ya sa Raihan ta fisgo mayafinta ta rufe jikinta a kunya ce. Kawar da kanta ta yi daga kallonsa don kunyarsa take ji. Tana zaune bata yi aune ba sai jin ta, ta yi tana yawo a sama mayafin jikinta ya faɗo ƙasa. Dariya Huzaifa ya saka ba shiri Raihan ta dubi wurinsa tana faɗin, "Hubby mai yake faruwa wayyo Allah na." Suna haɗa ido gabanta ya faɗi ganin waɗansu irin baƙaƙen gashi masu tsini suna tsirowa daga jikinsa, tana shirin yin magana ta ji ya sake cewa, "Ke matata ce don haka a yadda kike haka nake son ganinki." Yana rufe bakinsa waɗansu irin Manyan ƙaho ƙwaya biyu suka fara hudowa ta tsakiyar kansa, runtse ido Raihan ta yi a firgice tana cewa, "Waye kai Dama kai matsafi ne ka aure ni ban sani ba." Tana rufe baki ta bayanta ta ji an fara shinshinarta, a hargitse ta juya baya nan take ta ci karo da shi. Wata irin gigitacciyar ƙara ta ƙwalla jikinta na rawa ta fashe da wani irin matsanancin Kuka, dafe kansa ya yi da hannu biyu sannan ya furta: "Ba na son ki riƙa dagula lissafin rayuwarki, don ko kaɗan ba zan cutar da ke ba. Ni mai ƙaunarki ne har abada don haka ki kwantar da hankalinki mu yi rayuwar farinciki." Cikin kuka Raihan ta ce, "Ni wallahi na fasa aurenka don Allah ka mayar da ni wurinsu Daddy." Huzaifa ya bushe da wata irin dariya mai haɗe da kuka, sai da ya jima yana yi sannan ya ɗaure fuska kamar bai taɓa dariya ba ya ce, "Idan kina wannan mafarkin tun wuri ki daina domin ni da ke mutu ka raba, babu wurin da ya fi miki cancanta da zama kamar nan don haka ki daina tunanin akwai ranar da za ki koma wurinsu." Wannan magana ta sake ɗugunzuma hankalin Raihan a firgice ta sake fashe wa da kuka, luuuuu ta ji ta faɗa kan katifa tana kwanciya babu jima wa ta ga Huzaifa ya faɗo gefenta cikin wannan mummunar surar. Hannuwa biyu Raihan ta sa ta kare fuskarta tana ci gaba da kuka jikinta sai karkarwa yake kamar mai jin sanyi, Huzaifa bai damu da ganin halin da take ciki ba ya ci gaba da kai hannunsa masu ƙayoyi yana shafar fatar jikinta. Duk shafa ɗaya idan ya yi mata sai dai ta ji kamar yana zane jikinta da ƙananan allurai, ganin bata da Mafita ya sa Raihan ta sadaƙar rayuwarta ta gama zuwa ƙarshe, tana jin hannunsa ya sauka a gabanta jikinta ya ci gaba da ɓari zuciyarta ta sake tsinkewa. Huzaifa wannan karon har ya fi karon baya rikicewa don haka ya tasamman kusantarta ta kowanne hali, Raihan na ganin haka ta runtse idonta hawaye na zuba ta fara karanto duk wata addu'a da ta zo bakinta don ubangiji ya kawo mata ɗauki. Jin shiru kamar an yi ruwa an ɗauke ya sa ta buɗe idonta da mamaki take kallon ɗakin, ganin Huzaifa baya ciki zumbur ta miƙe cikin sauri ta fara laluben kayanta. A can gefen gado ta hango su hannunta har rawa yake ta yi sauri ta saka su tana waige-waige amma ko motsinsa bata ji ba, ɗaukwali kawai ta iya ɗaurawa ko mayafi bata bi ta kansa ba ta yi maza ta buɗe ƙofar ɗakin ta fara zabga gudu don fice wa daga gidan, don a yanda ta ayyana ko a ƙafa ne za ta ƙarasa gida matuƙar ta samu ta fice daga gidan. Tana zuwa bakin ƙofar da za ta sada da gate ta ci karo da tashin hankalin da ya fi na baya, tana buɗe ƙofar da niyyar zuwa gate ta ga wani ƙaton kogi tsayuwarta keda wuya wasu tafka-tafkan kadoji suka ɗago haɗe da buɗe mata baki tamkar za su haɗiye ta. Da sauri Raihan ta yi baya ta rufe ƙofar ƙirjinta na bugawa, babban abin da ya fi bata mamaki yadda aka yi cikin gidanta ya shafe da ruwa wanda a daren ranar da aka kawota ba haka ba ne. Su Daddy ne suka faɗo mata a rai, da gudu ta faɗa cikin ɗakin ta fara laluben jakarta. Daga can jikin bango ta fara jin numfashinsa sama-sama wannan ya sake ɗaga hankalinta hannu na rawa ta ɗago waya ta nemo lambar mommy, amma wayar duniya da ta yi bata shiga. Haka ta riƙa bin lambobin wayar mutane tana kira amma babu wacce ta shiga balle ta saka ran za ta ji an ɗauka. Huzaifa da yake daga jikin bango ya dubi Raihan a ƙufule yana faɗin, "Akan wane dalili za ki yi addu'a ko kina son na haike miki ta dole." Raihan bata kalli wurinsa ba tana daga zaune ta cusa kanta cikin cinyoyinta nan take fashe da wani irin matsanancin kuka. Tana cikin kuka nasihar Mommy ce ta faɗo mata da take yawan gaya mata a duk lokacin da ta ganta cikin damuwa ta yi sallah ta yi addu'a ta kaiwa Allah kukanta, a hankali ta ɗago ta share hawayenta lokaci ɗaya ta ji tsoron komai ya fita daga ranta. Miƙe wa ta yi ta taka ta kan gado don ko kallon Huzaifa bata son yi balle ta bi ta ɓangarensa, banɗaki ta shiga bakinta ɗauke da addu'a ta ɗauro alwata. Tana fitowa Huzaifa ya fara nunata da hannu yana faɗin, "Kar ki yi abin da kike shirin yi, na gaya miki kar ki yi." Da farko tsoro ne kama Raihan har take ganin kamar Huzaifa zai iya yi mata wani abin, saboda ko kaɗan bata kawo Huzaifa ba mutum ba ne. A tunaninta yana daga cikin ƴan ƙungiyar tsafe-tsafe ya aureta ne don ya tsaface ta. A ɓangare ɗaya kuma wata zuciyar na azalzalarta akan ta je ta gabatar da nafila ta roƙi Allah ya kawo mata mafita a rayuwarta, tun da ta lura addu'a ta yi tasiri akan Huzaifa. Daga gefe ta raɓa ta fara sallah, tana sallah tana kuka a sujjada tana kaiwa ubagiji kukanta. Raihan ta yi salla ta fi a irga bayan ta idar ta zauna tana addu'a, daga gefenta ta ji Huzaifa ya zabga ƙara daga nan ba ta sake ganinsa ba. Bata saurara ba ta ci gaba da addu'a sannu a hankali ɓarawon da ya fi kowa iya sata ya yi awon gaba da ita. Washegari. Tun da sassafe wasu daga cikin baƙin da suka hallaci bikin Raihan suka fara haɗa kayansu, don yawanci a ranar suka ce za su tafi. Mommy zuciyarta fari ƙal da ta wayi gari da tunanin Raihan ɗin ta tana gidan mijinta, har tana ayyana a wannan lokacin tuni ta riga da ta zama cikakkiyar mace. Shi kansa Daddy zuciyarsa fes ya wayi gari da ganin an yi komai lafiya an gama lafiya ba tare da wani abu mara daɗi ya faru ba. Ko babu komai zuwa wannan lokacin hankalinsa ya kwanta tun da ya aurar da Raihan, don haka yake jin sa wasai kamar ba shi ba. Su Inno da Goggo sai hidima ake da baƙi suna yi suna masifa don ko abu kaɗan mutane suka yi ba daidai ba sun rinƙa faɗa kenan. Wani lokacin Mommy har kunya take ji har sai ta ja su ɗaki ta yi musu magana, amma suna fitowa duk irin faɗan da Mommy ta yi musu za su zayyane shi a waje. Kimanin ƙarfe goma wasu daga cikin tsirarin da ba su je gidan Raihan ba suka shirya tare da Mama Hafsa da wasu sauran waɗanda aka je da su da dare, Mommy ce ta ɗauko waya ta nemo lambar Raihan don ta kirata ta gaya mata ga baƙi nan za su ƙaraso gidanta. Sai dai a kiran farko aka tabbatar mata da wayar a kashe. Bata kawo komai ba don haka su Mama Hafsa kai tsaye suka shiga mota suka wuce unguwar Medile, Su Mama Hafsa sun zagaye unguwar da suka kai Raihan ya fi sau biyar amma ko mai fasalin kama da gidanta ba su gani ba, ganin haka ya sa suka fara jajantawa a junansu daga ƙarshe suka yanke shawarar tambayar wani Mai shagon aski, da yake sun gane shi shagonsa a farkon layin gidan Raihan yake. Sai da Mama Hafsa ta yi masa sallama sannnan ta jefa masa tambaya, "Ƙanina don Allah gidan wata amarya da aka kawo jiya muke tambaya." Ɗan jim ya yi sannan ya ce, "Amarya kuma a nan layin? Kai gaskiya ƙila ba a kwatanta muku daidai ba, amma nan kusan wata guda kenan ba a kawo sabuwar amarya ba." Mama Hafsa jin maganarsa ta ji kamar har da rainin wayo a ciki, don haka ta yi masa sallama suka ƙara gaba. A can gefen wata ƙatuwar bola ta yi parking ɗin motarta, ta dubi Hajiya Lawisa ƙawar Mommy ta ce: "A daidai wurin bolarce wallahi nake ganin kamar jiya nan nan ne daidai wurin da gidan Raihan yake." Hajiya Lawisa da ta cika da mamaki ta ce, "Ba kama ba ce, wancen shagon telan shi yake kallon gidanta kuma ga shi nan a yadda yake yanzu ma haka yake, tun da jiya har magana na yi da shi kafin mu tafi na ce zan kawo masa ɗinkin wani les. Tabbas jikina yana ba ni akwai matsala." Mama Hafsa ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Matsala babba ma kuwa, amma mu fara zuwa Fagge gidan Iyayen Huzaifa kafin mu koma gida." Tana rufe baki ta tayar da motarta kai tsaye suka wuce unguwar Fagge sauran motoci biyun da suka taho tare suka rufa mata baya. Littafin Kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 37 Mama Hafsat tana tafe zuciyarta fal fargaba da tashin hankali, zuciyarta ce ta shiga wassafa mata tunane-tunane ban da saƙa da warwara babu abin da take yi, lokaci ɗaya zuciyarta ta karye tsora ya dirar mata tana fatan kada Allah ya tabbatar da abin da take zargi. Shiru motar ta ɗauka babu mai iya furta komai, don lamarin ba ƙaramin ɗaure kai gare shi ba. Suna tsaka da tafiya wayar mommy ta shigo wayar Mama Hafsa, gabanta ne ya faɗi ta rasa ya za ta yi don ta san idan ta ɗauka baya wuce ta ce a bata Raihan su yi magana, tun da dama kafin su taho ta gaya mata idan ta je gidan ta haɗa su za su yi magana. Ajiyar zuciya ta sauke ta ajiye wayar ba tare da ta ɗauka ba, idonta ta mayar kan titi haɗe da furta, "Hasbunallahu Wani'imal Wakeel." A ƙofar gidansu Huzaifa suka yi parking ɗin motocinsu, jiki a sanyaye Mama Hafsa ta kashe motar tare da fita tana gaba suna biye da ita, suna shiga suka ci Karo da Mahaifiyar Huzaifa ta rako baƙin da za su tafi tana yi musu su gaida gida. Ganin su Mama Hafsa ya sa ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin, "Hajiya barka da zuwa, ku shiga ciki kafin na shigo." Mama Hafsa yaƙe ta yi ta amsa sannan suka shiga ciki aka yi musu masauki a falo. Jigum-jigum suka yi suna nan zaune aka kawo musu ruwa amma babu wanda ya iya ɗauka ya sha. Mahaifiyar Huzaifa ce ta shiga ɗakin fuska ɗauke da fara'a tana faɗin, "Hajiya sannunku ya gajiyar hidima da jama'a?" Mama Hafsa ta yi murmushin da bai kai zuci ba ta ce, "Alhamdullah." Sai da ta gyara zamanta tana kallon Mahaifiyar Huzaifa ta ci gaba da cewa, "Hajiya dama wata magana ce tafe da mu." Mahaifiyar Huzaifa ta tattara hankalinta wurin Mama Hafsa ta furta, "Ina jin ku Hajiya." Mama Hafsa ta kashe wayarta ta jefa jaka sannan ta ce, "Yanzu haka daga unguwar su Raihan muke, mun tafi domin raka bayin Allahn da ba su samu damar zuwa jiya sun ga ɗaki ba." Mahaifiyar Huzaifa ta saka dariya haɗe da cewa, "Allah sarki ya ƴarta tawa da fatan sun tashi lafiya?" Mama Hafsa ta kalleta ta ce, "Gaskiya ba ƙalau ba." Gaban Mama ya yanke ya faɗi tana shirin yin magana Mama Hafsa ta ci gaba da cewa, "Mun shafe sama da awa guda a unguwarsu Raihan amma gidanta ya ɓace mana sama da ƙasa babu shi babu alamarsa, hasalima duk wanda muka tambaya gidan da aka kawo amarya sai dai su ce ba nan unguwar ba ne." Mama Hafsa ta tsahirta cikin damuwa ta dubi Mama ta ci gaba da cewa, "Na san kin san ni ƙanwar Mahaifiyarta ce cikinmu ɗaya, hasalima tun kafin bikin nan muke zarya ni da Mahaifiyarta muna kai kayan jere. Gidan Raihan ba ɓoyayyen wuri ba ne ko a jiya da dare na je gidan mun kai yarinya amma a yau da nake yi miki magana babu gidan Raihan babu alamarsa. Hatta yarinyata a jiya da dare ta manta wayarta a gidan amma da suka koma tun a daren suka nemi gidan suka rasa, da take gaya min ban kawo komai ba na yi zaton dare ne ya sa ba su gane ba kuma abokin Huzaifa shi ya mayar da su. Shi ya sa muka ce bari mu zo mu ji yadda aka haihu a ragaya." A rikice Mama ta ce, "Ban gane ba a ga gidan Raihan ba kamar wani gidan tsuntsuwa, Hajiya wai me kike faɗa ne haka?" Mama Hafsa ta furta, "Abin da dai kika ji na faɗa Hajiya haka ne, mu kan mu muna cikin tsananin mamakin wannan lamarin." Mama ta fara ƙwalawa ƙanwarta Maryama kira, tana zuwa ta nuna mata wurin zama haɗe da faɗin: "Zauna Maryama ba zancan tsaye ba ne. Jiya ba ku kuka ɗauko amaryar Huzaifa ba?" Maryama da gyaɗa kai. Mama ta wara hannu tana faɗin, "To kin ji wai gidan Huzaifa ya shafe babu shi an neme shi an rasa." Nan take Maryama ta saka dariya don ita gani take kamar ma zolaya ce, ganin haka ya sa ran Mama Hafsa ya ɓaci nan take suka ɗauki abin da muhimmmanci don cewa ta yi dole su zo a je a ƙara duba gidan tun da sun ɗauki abin a zuwan wasan yara. Ba shiri Mama ta kira Mahaifin Huzaifa ta sanar masa halin da ake ciki tare da yayansa. Kusan mota huɗu suka yi har da ta su Mama Hafsa suka nufi unguwar su Raihan, Yayan Huzaifa ne ya kira Dr Hussain ya sanar masa halin da ake ciki, nan take shi ma ya zayyane musu abin da ya faru da su da dare na komawa da suka yi karɓo waya amma ba su ga gidan ba. Wannan magana ba ƙaramin sake ɗaga hankulansu ta yi ba, haka suka je unguwar su Raihan suka gama bulayi amma ko gida mai yanayi da na Raihan ba su gani ba. Mama Hafsa da tuni zuciyarta ta karye nan take fa fara kuka tana faɗin akan dole sai su Mama sun faɗi wurin da Huzaifa ya ɓoye musu Raihan, a ɓangare ɗaya kuma tana tsoron kada Allah ya sa ba Huzaifa aljani ne ya ɓatar da su ba ita da mijinta ba. Carko-carko suka yi a wurin da suke tsammanin nan ne daidai gidan Raihan, wani babban fili ne mai ɗauke da kangwaye sai wata ƙatuwar bola wacce da alama duka ƴan unguwar a cikinta suke zuba shararsu. Yara da manya na bakin layin ne suka fara kallonsu kowanne da alama mamakin ganinsu suka yi a tsaitsaye a wurin. Mahaifin Huzaifa ne ya ciro waya ya kira kambar Huzaif don duk cikinsu babu wanda ya yi wannan tunanin, da yake ya ware sifikar (Speaker) wayar nan take suka ji wayar tana shiga. Sai dai har ta katse ba a ɗauka ba yana shirin sake kira wayar Huzaifa da shigo, hannun Baba har rawa yake sannan ya ɗauka yana faɗin, "Huzaifa kana ji na..." Ƙit Baba ya ji an katse wayar gabaɗaya. A hanzarce Baba ya sake kiran wayar amma ɗif ya ji ta a kashe. Hankalin mutanen wurin har ya fi na koyaushe tashi, sunan tsaye saƙo ya shigo cikin wayar Baba da sauri ya shiga dubawa kamar haka haɗe da karantawa a fili. " _Ku daina wahalar da kan ku akan sai kun nemo wurin da Raihan take domin tana tare da ni, kuma yanzu haka da ni da ita muna kallon duk abin da kuke yi, Ina kallonku a tsaitsaye wurin ƙofar gidana don haka ya kamata kowa ya kama gabansa kafin na ɓatar da ku kamar yadda na ɓatar da gidan tare da Amaryata Raihan. Ni kaɗai ni ne mamallakin Raihan ni ne mijinta na har abada HUZAIFA._" Ɗago wa suka yi daga kallon wayar ilahirin jikinsu ban da rawa babu abin da yake yi. A ruɗe Baba ya ce, "Wai yaron nan yana da hankali kuwa an ya bai shiga ƙungiyar asiri ba? Kuna jin abin da yake faɗa kuwa?" Mama Hafsa ta sauke ajiyar zuciyar tana faɗin, "Tabbas akwai wata a ƙasa, yanzu dai kun tabbatar da abin da muke faɗa ko? Shi kenan ku dakace mu." Tana gama magana ta yi wa sauran mutanen da suka zo tare magana suka shiga motar suka wuce gida. Sai da suka kusa ƙarasa wa Mama Hafsa ta yi parking a gefen titi sannan ta ciro waya ta kira lambar Daddy, sai da ta kusa katse wa sannan ya ɗauka yana faɗin, "Maman Safna!" Mama Hafsa a sanyaye ta amsa, "Daddyn Raihan kana ina akwai maganar da nake son yi da kai." Da matuƙar mamaki Daddy ya furta, "Ni kuma? Me yake faruwa ba dai wani abu ne ya faru a gidan Raihan ɗin ba ko?" Mama Hafsa ta ce, "Ina son magana da kai da fatan baka kusa da Aunty Zainab." A gaggauce Daddy ya ce, "Kina ina yanzu ni fito wa zan yi yanzu dama." Mama Hafsa ta ce, "Muna kan titinku za ka ga motoci biyu a har tawa." Daddy bai jira cewarta ba ya katse wayar. Ko minti uku Daddy bai ƙara ba ya fito daga gidan saboda tashin hankali da fargabar abin da za a gaya masa ko mota bai fito da ita ba, Mama Hafsa ce ta fito daga motar tun bai ƙarasa wurinta ba ya ce, "Hafsa me yake faruwa da Raihan? Me ya samu mijinta ko shi ma mutuwa ya yi?" Mama Hafsa idanunta suka ciko da ƙwalla tana faɗin, "Daddyn Raihan mun rasa gidan Raihan hasali ma daga ƙarshe har wani saƙo Huzaifa ya turo wa Mahaifinsa a waya..." Duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe sai da Mama Hafsa ta sanar wa da Daddy, a hargitse ya furta: "Huzaifaaaaa! Dama na faɗa sai da jikina ya ba ni wannan Huzaifan ba alheri ba ne." Idanunsa ne suka kaɗa jawur rai a matuƙar ɓace ta dubi Mama Hafsa ya ce, "Ba ni key." A sanyaye ta miƙa masa ya karɓa ya shiga motar ganin haka ya sa sauran matan suka fito daga cikin motar suka yi carko-carko, cikin matsanancin gudu Daddy ya fita da gudun gaske. Mama Hafsa ce ta dubi su Hajiya Lawisa ta ce, "Tsaiwa a wurin nan ba za ta kaimu ba, mu ƙarasa gida mu sanar da Aunty Zainab don wannan ba maganar da za a yi shiru ba ce." Cike da gamsu wa da bayanin Mama Hafsa suka fara takawa da ƙafa don ƙarasawa, su Hajiya Shafa da suke cikin ɗayar motar suma suka rufa musu baya. Suna shiga cikin gidan mommy ta tare su fuskarta ɗauke da fara'a tana faɗin, "Wallahi ke dai Hafsa wayarki bata da amfani sam. Na kiraki ya fina a irga amma baki ɗauka ba." Mama Hafsa bata amsa mata ba a ƙoƙarinta na danne hawayen da yake son ziraro mata, ganin yanayinsu babu walawala ya sa Mommy ta ruƙo hannun Mama Hafsa tana faɗin, "Lafiya Hafsa me yake faruwa? Me ya faru da Raihan don Allah ki gaya min." Jin haka ya karya zuciyar Mama Hafsa ta faɗa jikin mommy tana fashe wa da kuka, a madadin Mommy ta sake tambayar abin da ya faru jikinta rawa ya fara yi nan take hawaye ya fara zubo mata, ta faɗa kan kujera daɓass ta zauna sannan ta iya furta, "Idan wani abu ne ya faru don Allah ku sanar da ni." Inno da shigowarta ɗakin kenan ta dafe ƙirji da hannuwa biyu ta ce, "Kuka wane iri nake ji da kunnuwana? Me ye kuma ake kuka kamar gidan mutuwa? Huzaifan shi ma mutuwa ya yi ne?" Shiru suka yi ba tare da wani ya iya furta komai ba, Mama Hafsa ta yi ƙarfin halin zama kusa da mommy sannan ta zayyane musu duk abin da yake faruwa. Salati mutanen ɗakin suka ɗauka Inno da Goggo kuwa tuni suka fashe da kuka, Mommy na zaune a wurin da take kasa motsa wa ta yi lokaci ɗaya ta ji kanta ya sara, wata irin juya na ɗaukanta ƙirjinta na wani irin buga wa da ƙarfi, ba su yi aune ba sai gani suka yi luuuuuu ta faɗa jikin Mama Hafsa a sume. Hankali a tashe Goggo ta faɗa kan Mommy tana kuka da sauri mutane suka janye ta aka shiga yayyafa wa Mommy ruwa amma ko kaɗan bata motsa ba, da sauri Mama Hafsa da sauran mutanen wurin suka taimaka aka fita da Mommy aka saka ta a mota, ganin wannan lamarin ya ƙara tsinka zuciyar Kabiru, duk da bai san abin da ya faru ba amma jikinsa yana ba shi wani abu ne ya faru da Raihan don ko a daren da aka kaita kwana ya yi bai yi bacci ba sai gabannin asuba, kuma ko da bacci ya ɗauke shi wani irin mummunan mafarki ya yi da ita. Jikinsa har rawa yake ya ƙarasa bakin falon bayan fitar da mommy daga gidan, jin kukan su Inno ya ƙara dagula lissafinsa har ya manta da matsayinsa na mai gadi ya faɗa cikin falon hankali a tashe yana tambaya. Inno sai da ta sharce majina ta ce, "Kabiru yanzu dama yaron nan Huzaifa azzalumi ne ba mu sani ba? Wai an nemi gidan Raihane an rasa ya ɓace da ƴar mutane ɓat kamar masu layar ɓata." Ƙirjinsa ne ya buga jikinsa ya fara karkarawa a firgice ya kuma tambayar halin da ake ciki, su Inno suka yi masa bayani dalla-dalla kamar yadda Mama Hafsa ta yi musu. Kamar wanda aka zare wa laka a jiki haka ya fice daga falon ya koma ɗakinsa ya zauna, shiru ya yi ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba nan take kansa ya fara juyawa lokaci-lokaci ya fara furzar da iska mai zafi. Daddy ko da ya je ya shafe minti talatin a tsaye wayarsa ya ciro ya kira lambar Dr Hussain ko sallama bai yi masa ba ya ce, "Wallahi duk wurin da abokinka ya kai min ƴata sai ya fito min da ita, na rantse da Allah sai ya fito min da ƴata tun wuri ka gaya." Daddy bai jira cewar Dr ba ya katse wayar sannan ya kira D.P.O abokinsa ya sanar masa halin da ake ciki. Suna gama waya wayar Daddy ta fara ƙara Mama Hafsa ce a nan take sanar da shi halin da Mommy take ciki, da asibitin da suke ake bawa Mommy agajin gaggawa don har lokacin bata farfaɗo ba. Daddy bai gama jin abin da Mama Hafsa take faɗa ba ya katse wayar tare da shiga mota ya fita a guje, kafin Daddy ya ƙarasa asibitin saboda irin gudun da yake yi har sai da ya bige wani ɗan makaranta don ma Allah ya taƙaita yaron bai ji ciwo sosai ba. Yana shiga asibitin likitoci suna shiga yi masa bayanin zuciyar Mommy na gabda buga wa saboda matsananciyar damuwar da ta faɗa lokaci guda. Raihan ba ita ta farka ba sai bayan da gari ya fara yin haske, kukan waɗansu tsuntsaye ne ya fara tashinta. A hargitse ta miƙe lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ta fara hakaito mata da abin da ya faru, da sauri da fara dube-dube tana neman ta wurin da Huzaifa zai ɓullo mata sai dai babu shi babu alamarsa. Banɗakin ɗakin ta fara nema amma abin da ya bata mamaki ƙofarsa ta shafe tamkar ba a taɓa yin sa a wurin ba. Zarya ta fara yi a ɗakin tana neman ruwan da za ta yi alwala da shi, sai dai hatta ruwan jarkokin da Huzaifa ya kawo mata a daren ranar babu su ta neme su ta rasa. A hankali ta buɗe ƙofar ta fita zuwa falo, cikin sanɗanta ta fara dube-dube a cikin gidan amma sama da ƙasa da ta duba babu ruwa, kogin da ta gani a daren ranar ne ya faɗo mata da sauri ta ƙarasa wurin tana son buɗe ƙofar tsoro fal zuciyarta, ta jikin ƙofar ta leƙa amma sai gani ta yi kogin ya koma wawaken ƙaton rami. Dawowa cikin gida Raihan ta yi ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ganin kuka ba zai kaita ba ya sa sake miƙe wa ta fita wurin ramin nan, da niyyar zura hannunta ta fara yin taimam. A ɗarare ta zura hannunta ta fara taimama tana shirin gamawa ta ji wani abu ya riƙe hannunta gam, a gefe ɗaya ga wani irin gurnani da yake tashi. Ƙara Raihan ta ƙwalla haɗe ta fisgar hannunta da ƙarfi, jini ne ya fara zuba sakamakon gefen ɗan yatsanta da wannan ƙanƙanuwar hallita ta kaiwa cizo. Jiki na rawa Raihan ta rufe ƙofa ta koma ciki, ganin jinin na zuba ya sa ta yaga ɗankwalinta ta ɗaure wurin. Zuciyarta na rawa ta gabatar da sallar asuba a lokacin tuni gari ya waye, wani abin mamaki har ta fara jin hayaniyar mutanen unguwar da yaransu. Tana nan zaune tunanin su Mommy ya faɗo mata da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga kira amma fir ta ƙi shiga, hawaye ne yake bin kuncinta ɗaya bayan ɗaya, ga wata irin addababbiyar yunwa da take cinta kasancewar ranar ɗaurin aurenta ban da ruwan tea babu abin da ta iya sha saboda fargaba. Tana nan zaune ta ji turowar ƙofa da sauri ta matsa ta takure wuri ɗaya, Huzaifa ta ga ya shigo cikin ƙananan kaya ba ƙaramin kyau ya yi mata ba duk da tsoronsa ya riga da ya cika zuciyarta, amma da ta ƙare masa kallo sai take ganin kamar ba shi ne Huzaifan da yake son hallaka a daren jiya ba. Ƙirjinta ne ya buga da ya fara tunkarota, hannu ta ɗaga masa tana faɗin, "Don Allah ka mayar da ni gida." Murmushi ya sakar mata sannan ya tsugunna a ɗan nesa da ita ya ce, "Raihan!" Ɗagowa ta yi tana kallonsa ba tare da furta komai ba. "Kin san irin ƙaunar da nake yi miki kuwa? Ina yi miki soyayyar da ko iyayenki ba sa yi miki ita. Ni Huzaifa na rabu da kowa nawa akanki me ya sa ba za ki haƙura da su mu yi rayuwa mai ɗore wa cikin farinciki ba?" Huzaifa yana rufe baki Raihan ta fara jin alamar tsayawar motoci, waigawa Huzaifa ya yi ya saki wani shu'umin murmushi, karaf Raihan ta ji muryar su Mama Hafsa. A zabure ta miƙe ta fice falo haɗe da bankaɗe labulen window ta tura ƙofar windon da ƙarfi tana ƙwala mata kira. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 38 Ganin babu wanda ya waigo balle ya nuna alamun ya ji kiranta ya sa ta cire takalminta ta jefa a saitin wurin da Mama Hafsat take tsaye haɗe ta ƙwala mata kira, amma ko alamin juyo wa Mama Hafsa bata yi ba. Huzaifa yana daga wurin da yake tsugunne ya saki murmushi haɗe da cewa, "Da ma kin bar wahalar da kan ki domin babu wanda zai ji ki balle ya waiwayo gare ki, saboda wurin nan da kike yana da kamceceniya da dajin ƙare kukanka." A wurin Raihan ta durƙushe tana zubda hawaye mai zafi, Huzaifa yana son ƙarasawa wurinta amma wani irin turiri yake ji a duk lokacin da ya kusanceta. Takawa ya yi ya tsaya daga bakin ƙofar ya ce, "Kina da buƙatar abinci ne?" Cikin kuka Raihan ta girgiza masa kai haɗe da cewa, "Ka dubi girman Allah ka mayar da ni wurin iyayena." Guntun tsaki Huzaifa ya yi ya juya a fusace yana faɗin, "Idan na mayar da ke tabbas na san ta kowanne hali sai sun raba ni da ke ko kuma su hallaka ni, wallahi da na mayar da ke gara na hallaka ki kowa ma ya huta." Yana gama maganar ya fice daga wurin, jin maganar Huzaifa ta ƙara hargitsa tunaninsa cikin tashin hankali ta furta, "Innalillahi wa'inna'ilahirraji'un." Jin tashin motar su Mama Hafsa ya sa Raihan ta sake leƙa wa ta windo sai kawai ta kifa kanta ta wurin tana zubda ƙwallah. Raihan haka ta ci gaba da zama a wurin tana zuba wa sarautar Allah ido, don duk abin da yake faruwa a harabar wurin tana kallo har waɗansu yara ta gani masu buhu a hannu suna tsince-tsince a wurin gidan nata amma kiran duniya ta yi musu babu wanda ya amsa mata. Ta jima a wannan yanayin kamar almara bayan wani lokaci ta ji muryar Daddy, wannan karon a haukace ta ƙwallah ƙara haɗe da bubbuga ƙauren windon amma ko kaɗan Daddy bai ji ba. Tana ji tana gani Daddy ya ja motarsa ya bar wurin, wannan karon zama ta yi a wurin daɓas don tuni hawaye ya ƙauracewa idonta ta ji gara ma mutuwarta da rayuwarta. Damuwa goma da ashirin ce ta mamaye zuciyar Daddy, ban da zarya a cikin asibitin babu abin da yake yi. sauƙin da ya ji da likitoci suka samu damar ceto rayuwar Mommy, amma sun sake jadadda masa zuciyarta tana barazanar bugawa. A ranar tawagar D.P.O suka ƙarasa unguwar su Huzaifa suka kwashe iyayensa domin zargi ƙururu ake yi akan Huzaifa na ɓatan Raihan. Duk ciwon da Raihan take da shi sai da Daddy ya zayyana wa D.P.O tas sannan ya bashi labarin yadda aka yi Dr Hussain ya rako Huzaifa har cikin gidansa, nan take zancen ɓatan Raihan da Huzaifa ya watsu a cikin garin Kano da sauran garuruwa daga ƙasar Nigeria. A wannan karon duk yadda ƴan jarida suka so jin ta bakin su Daddy abin ya ci tura, don haka suka dangana ga wurin ƴan sanda a nan suka samu bayanin da ba a rasa ba. Wannan tashin hankali da aka wayi gari ya sa ƴan bikin da suka ziyarci gidajen bukukuwan tuni kowanne ya kama gabansa zuciya a dagule, maganar ɓatan su Raihan ita ta kai har kunnen ƙungiyoyin lauyoyi ta ƙasa. Babu shiri suka tuntuɓi hukumar ƴan sanda haɗe da neman a haɗa su da iyayen Raihan don jin duk yadda abin ya kasance. Kamar yadda abin ya faru haka Daddy ya sanar da su iya abin da ya sani, daga ƙarshe ɓangarorin biyun suka ci alwashin binciko duk wurin da Raihan da Huzaifa suke. Tuni Hotunan su Raihan ya karaɗe kafofin sada zumunta lamarin da ya sake hautsina labarin kowa da abin da yake faɗa, wasu su ce aljanun Raihan kashe mazanta suke yi, wasu su ce su suka sace Raihan har ma su zargin tuni an gama da Huzaifa sai jiran bayyanar Raihan. Lokacin da Dr Hussain ya tabbatar da ɓatan Raihan ya shiga banɗaki ya fi a irga don ko a radio ya ji maganarta sai cikinsa ya karta ya faɗa banɗaki, daga ƙarshe Daddy ya bayar da umarnin a tafi da Dr Hussain shi ma. Har kawo wannan lokacin Iyayen Huzaifa na kulle ba a sake su ba, sai da aka kai ruwa rana sannan Daddy ya lamunce aka saki iyayen Huzaifa da sharaɗin a kowanne lokaci za a iya buƙatarsu don bayar da bayani. BAYAN KWANA BIYAR. Duk waɗannan kwanakin mutanen gidansu Huzaifa da Daddy sun yi su cikin rashin nutsuwa, fargaba da tashin hankali. Su Inno ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, ko abincin kirki ba sa iya ci. Kabiru tuni ya fige ya rame ya lalace don ko abinci bai fi ya yi cokali biyu ya ajiye shi ba, ba shi da aiki sai addu'a da sallar dare yana fatan Allah ya kuɓuto da Raihan cikin ƙoshin lafiya. Daddy tuni ya sanarwa da Malam halin fa ake ciki, ya bi makarantun islamiyyu da ta allo ya riƙa rarraba kuɗi yana neman a yi wa Raihan addu'a akan Allah ya bayyanata cikin alheri ko a mace ko a raye. Jikin Mommy yana sauki amma sai dai a kira shi da samun sauƙin mai haƙan rijiya, don kullin tana kwance ana bata kulawar da ta dace amma kullin ta farfaɗo maganarta ɗaya, "Ina Raihan?" Da ta kalli Daddy sai dai ta riƙa zubda ƙwalla. Ana cikin wannan yanayin Inna wuro ta kira Kabiru hankalina tashe tare da sanar da shi ciwon Baffajo ya tashi, wani sabon tashin hankalin ne ya dirarwa Kabiru don haka a ranar da Raihan ta kwana shida da ɓata, ya shirya da safe zuwa asibitin da Mommy take ya sanarwa da Daddy duk abin da yake faruwa, tare da faɗin zai je ya gano halin da yake ciki. Duk da Daddy na cikin damuwa bai hana ya gano tsananin damuwar da Kabiri yake ciki ba, kuɗi ya tura masa masu yawa ta Account ɗinsa. Kuka Kabiru ya gashe da shi har ƙasa ya tsugunna yana yi wa Daddy godiya. Daga asibitin gida Kabiru ya koma ya yi wa su Inno Sallama ya ɗauki ƙaramar jakarsa ya fita. Lokacin da ya fice daga gidan zuciyarsa ce ta karye game da lamarin Raihan, zuciyarsa ta fara tunane-tunane akanta don haka idanunsa suka ciko da ƙwalla ya sake waigawa ya kalli gidan sannan ya goge ƙwallar idonsa ya fara tafiya. "Tabbas na sake lamincewa Huzaifa ya dawo da ƙarfinsa fiye da na baya, ina da yaƙinin ya samu taimako ne daga Kakansa Jabbul-ƙasi. Idan ba haka ba babu yadda za a yi ace Huzaifa shi kaɗai ya dagakatar da dukkan tsafi da sihirinmu. Ya auri Raihan ba tare da mun iya dakatar da shi ba, jikina ya gama ba ni ya fara fahimtar wani abu daga gare mu domin babu yadda za a yi Mugaza tana ji tana gani ta bari Huzaifa ya auri Raihan ba tare da wani abu ya gifta a tsakani ba. Ku shaida ne yau kusan watannin Mugaza huɗu kenan ba tare da ta halarci ƙungiya ba, kuma duk iya bincikenmu mun yi don ganin mun gano halin da take abin ya ci tura, shin me kuke tunani meye abin yi a wurinmu?" Abar bauta ta yi maganar a sanyaye saboda ta gama tsinke wa da lamarin Huzaifa. Hatsabibiya ta rungumo mijinta tamkar wani zai ƙwace shi tana shirin magana, ya miƙe zumbur ya fara sauya launi sai da ya rikiɗa zuwa kaloli kusan biyar sannan ya tsaya cikin kalar yello da baƙi. Kallon abar bauta ya yi ya numfasa sannan ya ce, "Yau kusan shekarata bakwai ban tofa muku komai a game da lamarin ƙungiya ba, ina buƙatar a bani damar na furta wani ba." Da yake Abar bauta mafita take nema don haka cikin sauri ta amsa masa, "Faɗi koma meye a bakinka." Mijin Hatsabibiya can gefenta ya koma ya maƙale matarsa sannan ya ce, "A wannan halin da ake ciki Huzaifa ya gawurta, tasirin tsafi da sihiri ba za taɓa aiki a kansa ba. Laƙanin Jabbul-ƙasi yana da matuƙar ƙarfi. A shawarce duk yadda ake ciki kar mu sake mu tunkari Huzaifa gaba da gaba. Kar ma mu jefa rayuwarmu cikin tashi domin matuƙar ya fahimci muna mu'amala da Raihan a cikin ƙungiya ta mu ta zo ƙarshe, don haka sai mun yi takatsantsan koda za mu cimma burinmu akansa. Sannan dole mu tabbatar da mun ceto Mugaza a kowanne yanayi take ciki idan ba haka a kowanne lokaci asirinmu zai iya tonuwa." Abar bauta ta jinjina kai cike da gamsuwa don bayaninsa ba ƙaramin ankarar da ita ya yi ba. Miƙe wa ta yi tana kai wa da kowo wa sannan ta dube shi ta ce, "Yanzu ta ina za mu fara?" Kai tsaye ta ji ya furta, "Dole mu ziyarci tsibirin Jabbul-ƙasi mu nemi agajinsa." A haukace duka suka kalle shi cikin hargitsattsiyar tsawa Abar bauta ta ce, "Kana hauka ne za ka ce mu ziyarci Kakan Huzaifa don mu nemo sa'a?" Murmushi ya yi sannan ya ce, "Na san waye Jabbul-ƙasi ba ruwansa da duba nasaba ko dangantaka. A yadda muka je da buƙata to buƙatar kawai zai kalla babu ruwansa da wanda za a aikatawa." Daɓass! Abar bauta ta zauna jiki a sanyaye zuciyarta na yi mata wasu-wasi akan ta amince da maganarsa ko ta yi watsi da ita. Tashi ta sake yi za ta shige raminta sannan ta waigo ta ce, "Ku dakace ni don na yi nazarin abin da ya kamata mu yi don gaskiya zuciyata na rawa akan wannan shawarar taka." Tana gama maganar ta shige ciki. A cikin ƙasa da kwanaki bakwai Raihan duk ta lalace ta fita hayyacinta ta rame, idan ka ganta a yanayin da take ciki za ka yi tsammin ta yi wata doguwar jinyar. Ta koma tamkar mahaukaciya da yake gashin kanta ba a kitse yake ba ya sa duk ya hargitse, fuskarta duk ta jeme ga koyaushe cikin kwanan fargaba take babu wadataccen bacci idan ba ɗaukanta ya yi bata sani ba. Kullin cikin kuka take da addu'ar Allah ya kawo mata ɗauki take yi, sallah kuwa tun ranar da ta yi da dare kullin sai dai ta yi taimama ta yi, daga ƙarshe ma da ta tsorata sai wani ƙaramin dutse ta samu ta riƙa yin taimamar da shi. A kullin ta wayi gari sai Huzaifa ya ziyarce ta har yana nuna mata buƙatarsa a fili amma ƙarfin addu'a da Ayatulkursiyyun da Raihan take yi ya gagare shi ƙarasawa koda kusa da ita ne, sai dai ya tsaya daga nesa da ita. Hasalima sai ya riƙa tsoratata da waɗansu ƙananan halittu masu yanayin mutane amma ba sa kama da bil'adam ga su gajeru ko tsayin gwiwar Raihan ba sa kaiwa. Waɗannan Halittu su suka sake haukata Raihan don wani lokacin har ji take kamar suna yawo a jikinta, bata da aiki sai ihu da kiran sunan su Mommy. Abinci kuwa duk yadda Raihan ta kai ga tsoron cin abincin da take kawo mata dole ta zubar da makamanta ta fara karɓa tana ci, duk da ba kullin yake bata ba a cewarsa sai ta bashi haɗin ya yi mu'amala da ita. A ranar da Raihan ta cika kwana bakwai a wannan yanayin ta yanke shawarar bashi kanta don ta gaji da irin wahalalliyar rayuwar da take ciki, gara ta bashi kanta ko mutuwa za ta yi ta huta don ta lura a wannan wurin da take babu alamar fitarta, idan ta mutu ta sa mu sauƙin rayuwarta kowa ya huta. Tana nan zaune ta ji shigowarsa a wannan karon sanye yake waɗansu irin kayan saƙi tare da wuri sai waɗansu baƙaƙe da jajayan duwatsu, a wurin da ya saba tsaya wa ya tsaya yana kallonta ya ce, "Raihan na nuna miki ƙauna da kulawa amma ko kaɗan baki gani ba, a duk lokacin da na zo wurinki idan na koma sai na yi jinyar jikina saboda a kullin sai kin ƙona min ni, Raihah da ba na sonki ba zan juri haka ba." Durƙushe wa ya yi a wurin cikin rawar murya, nan take hawaye ya fara bin dakalin fuskarsa. Kuka yake sosai kamar ƙaramin yaro wannan ya sake raunana zuciyar Raihan, wata irin soyayyar Huzaifa da tausayinsa ta ji na ratsata. Kuka take sosai tana jin babu daɗi a zuciyarta, tana cikin haka ta riski muryarsa. "Duk duniya ba na ƙaunar wani abu kamar yadda nake ƙaunarki ba, na tabbata wannan yana daga cikin tsarin ƙaddarata. Raihan na haukace a kanki na yi nisa ba na jin kira ta yadda kunnuwa suka doɗe ban da harshenki babu abin da nake iya ji. Ni ba Mutum ba ne kamar yadda kike tsammani ni aljani ne, ina mata da ƴaƴana amma saboda ke duk na haƙura da su na haƙura da kowa nawa don Allah ki ƙaunace ni koda na rana ɗaya ne." Kuka ne ya ci ƙarfin Raihan don ko tsoron ma ya fita daga zuciyarta, cikin kuka ta dube shi ta ce: "Idan na ce ba na ƙaunarka na yaudari kaina ina sonka kamar yadda kake sona Huzaifa, amma zaman mu a inuwa ɗaya ba zai taɓa yuwa ba, saboda kai ba jinsina ba ne. Me ya sa ka hura wutar soyayyarka a zuciyata bayan kasan ba za ka iya kashe ta ba, ina ƙaunarka Huzaifa ina jin soyayyarka amma ka dubi girman Allah kar ka cutar da iyalinka a kaina, ka ci gaba da bawa iyalinka kulawa kamar yadda kake ba su a baya." Raihan ta goge hawayen idonta sannan ta haɗa hannuwanta wuri ɗaya alamun roƙo ta ce, "Ka dubi girman Allah ka mayar da ni wurin iyayena don na tabbata yanzu haka suna cikin wani hali." Cike da farinciki Huzaifa ya dubi Raihan ya furta, "Tabbas zan aiwatar kamar yadda kika buƙata zan ci gaba da bawa Iyalina kulawa, amma don Allah ki daina zancen na mayar da ke gida. Tun da har kin amince kina ƙaunata don Allah ki watsar da komai mu ci gaba da rayuwa, ni Huzaifa na yi miki alƙwari ba za ki taɓa hawaye ba. Zan baki kulawar da ba babu wani ɗan'adam da zai baki ita, wallahi ko kallon banza babu wani mahaluki mai numfashi da ya isa ya yi miki shi. Matuƙar baki amince min ba wallahi ba za ki taɓa fita daga wurin nan ba, balle wani namijin ya samu damar raɓarki har ya kai ga aurenki." Raihan na jin haka ta rushe da kuka don zuciyarta ta fara yi mata wasu-wasi akan ta amince da buƙatar Huzaifa. Fuska ɗauke da damuwa Daddy ya dubi Malam ya ce, "Shi kenan Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alheri amma a wannan lokacin da muke ciki na fara sare wa da samun Raihan, shi kenan ya yi nasara a kanmu." Malam Usman ya girgiza kai haɗe da cewar, "Da ƙarfin addu'a da ikon Allah Huzaifa ba zai taɓa nasara akan mu ba. In sha Allah nan ba da jima wa ba Raihan za ta bayyana, mu ci gaba da addu'a kuma na gaya maka tuni akwai aljanun da na tura don su nemo min su a ko ina suke." Jikin dadi ya gama sanyi don haka murya na rawa ya amsa, "Shi kenan na gode Malam." Yana shirin fita Al'amin ya shiga har ƙasa ya russuna ya gaishe da Daddy tare da sake jajanta masa akan ɓatan Raihan, Daddy ya yi musu sallama ya koma asibiti. Mama Hafsa ita take jinyar Mommy akan dole aka bar wa su Inno Muhammad suke kula da shi, da yake ya saba da su ko rigima baya yi. Jikin Mommy yana sake samun sauƙi jininta ya sauke har tana iya miƙe wa ita kaɗai ta yi wasu abubuwan da kanta, nasihar da su Daddy suke yi mata ne ya sake ƙarfafa gwiwarta ta faula wa Allah lamuranta. Lokacin da Kabiru ya ƙarasa gida ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba sakamakon ganin yadda jikin Baffajo ya rikice, ƴan uwa sun zagaye shi sai koke-koke ake yi. A daren ranar da ya koma ya sa aka ɗauki Baffajo aka wuce da shi babban asibitin garin Shanono, duk wanda ya ga yadda Baffajo yake jin jiki sai ya tausaya masa. Suna zaune a asibitin Kabiru ya dubi Inna wuro ya ce, "Inna ya kamata ki koma gida ni zan kulla da Baffa, kin ga an bar gida ba kowa ki wuce kawai." Gabanta ne ya faɗi a ɗan firgice ta ce, "Shi kenan wataƙila ya shiga gari." Da mamaki ya dube ta ya ce, "Waye Inna." Miƙe wa ta yi tana yafa mayafinta ta ce, "Ɗan tsintuwa ne Kabiru Allah sa dai bai shiga gari ba." Kabiru sam bai fahimci maganar Inna wuro ba don haka ya sake tambayarta. Inna wuro ta ƙarasa bakin gadon Baffajo sannan ta ce, "Wani yaro ne ƙaninka ya tsinto shi a kogin Iro mai garke, to da yake makarai sun taɓa shi ya rinƙa nema guje-guje kenan don haka muke kulle shi a ɗaki, amma duk da haka yara suna zuwa suna tura shi." Kabiru ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, "Allah ya bashi lafiya." Inna wuro ta amsa sannan ta yi musu sallama ta wuce gida. Hasken rana da hayaniyar yara ne suka sata farkawa jiki a tsamame, wani mummunan wari ne ya doki hancinta da ƙarar ƙudaje da ta karaɗe kunnenta. A zabure ta miƙe tsaye tana dube-dube sakamakon tsintar kanta da ta yi a tsakiyar bola, tana shirin karkaɗe jikinta ta riski muryar yara suna faɗin: "Mahaukaciya ƴar macu kul..." Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 39 Da matuƙar mamaki Raihan ta dube su a hankali ta riƙa takawa kai ba ɗankwali, ganin suna ci gaba da tsokanarta wasu har da masu jifanta da dutse ya sa Raihan ta fara tunkararsu tana faɗin, "Don Allah kuna ji na kuma kuna ganina." Dariya suka fara yi wasu daga cikin yaran suna jan rigarta ta baya suna faɗin, "Mahaukaciya ƴar macukule." Tafiya Raihan ta fara yi ba tare da ta san wurin da take jefa ƙafarta ba, sai da ta ji zafin wani ƙaton dutse da wani yaro ta jefeta a kanta, sanann ta tabbatar da ba mafarki take yi ba tabbas ita ce Allah ya kuɓuto da ita. Waiga wa ta yi tana ƙare wa mummunar bolar mai ɗauke da caɓalin kayan ƙazanta iri-iri, wani tunani ne ya dirar mata a zuciya. Ta ayyana kada Huzaifa ya sake sace ta, ƙafa ba takalmi kai ba ɗankwali Raihan ta zuba a guje don ta ci alwashin ko a ƙafa ne sai ta koma gidansu. Tana tafe tana gudu yara na biye da ita har ta ƙarasa bakin titi, duk Ɗan adaidaita sahun da ya zo da Raihan ta tsayar da shi idan ya dubi yanayinta da yaran da suke biye da ita sai ya ja mashin ɗin sa ya ƙara gaba. Yaran da suke biye da ita ne suka fara damunta don haka ta fara yi musu magana, daga ƙarshe da abin ya damu Raihan sai kawai ta fashe da kuka. Wani mutum ne da ya je wuce wa ya yi wa yaran tsawa amma suna ganin ya wuce suka ɗora daga in da suka tsaya. Ganin haka ya sa Raihan ta ci gaba da tafiya a ƙasa, nan take yaran suka fara ɗiban ƙasa suna watsa mata sai dai wannan karon bata kula su ba. Ganin abin nasu ya sake yawa suna ta jifanta da manyan duwatsu ya sa Raihan ta ɗiba da gudu za ta tsallaka titi bisa tsautsayi wani mai mota ya zo wuce wa ya make ta. Da sauri yaran suka yi carko-carko, Raihan ta faɗi a can gefe kanta ya fashe yana fara zubda jini. Ban da juyi cikin azaba babu abin da take yi, a rikice Al'amin ya fito daga motar yana sallallami, da taimakon wasu matasa aka saka Raihan a cikin mota wani ɗan sanda na daga gefe ya ƙaraso ya shiga gaban motar suka fara zuwa Police station aka rubuta report sannan suka wuce asibiti. Wani private hospital Al'amin ya kai Raihan da ke unguwar sharaɗa, nan take likitoci suka shiga bata kulawar da ta dace. Al'amin zaune ya yi ya haɗa kai da gwiwa a hankali ya fara ƙare wa Raihan kallo yana son sanin wurin da ya san fuskarta amma ya kasa tunawa, kasancewar yawancin hotunan Raihan da aka watsa duk na bikinta ne kuma da kwalliya a fuskarta shi ya sa farat ɗaya ba za ga ce ita ba ce. Wayar Malam Usman ce ta shiga da sauri Al'amin ya ɗauka bayan ya yi sallama Mahaifinsa ya ce, "Ka ƙarasa ne?" Jiki a sanyaye Al'amin ya gaya wa mahaifinsa abin da yake faruwa a rikice Malam Usman ya furta, "Hasbunallahu Wani'imalwakeel. Yanzu kuna wane asibitin?" Al'amin ya ce, "Health Care Clinic na kan titin mu." Malam Usman bai gama jin abin da Al'amin yake faɗa ba ya katse wayar, ba a ɗauki lokaci ba Malam ya ƙarasa asibitin. Daga harabar asibitin ya kira Al'amin yana tambayar ɓangaren da suke, Malam na shiga ya sauke idonsa akan Raihan yana faɗin, "Garin yaya hatsarin ya faru..." Sauran maganarsa ce ta maƙale jiki na rawa ya ƙarasa bakin gadon yana faɗin, "Raihan!" Police ɗin da Al'amin suka juya da sauri suna kallonsa, cikin tsananin mamaki Al'amin ya ce, "Daddy ka santa ne?" Malam ya sake matsa wa gaban gadon da Raihan take bacci saboda allurara baccin da aka yi mata ya yi, ya juyo wurin yana kallon Al'amin ya ce, "Raihan ita ce yarinyar da ta ɓace ranar daren aurenta." Da sauri Al'amin ya ƙarasa gaban gadon yana ƙare mata kallo, sai a lokacin ya tabbatar da kammaninta. Police ɗin da ke gefe ya ƙarasa yana faɗin, "Wallahi Alhaji tun gani na da ita nake wasu-wasi idanuna suke gane min kamar ita ce amma sai na yi tunanin wannan ko masu rangwamen hankali ce." Malam na gama jin sa ya sauke ajiyar zuciya haɗe da zaro waya ya furta, "Ai ta kwana gidan sauƙi. Kai Alhamdulillah Allah shi ne abin godiya." Wayar Daddy ya kira bata daɗe tana shiga ba ya ji an ɗauka, ko ƙwaƙƙwarar gaisuwa ba su yi ba Malam ya ce, "Alhaji don Allah ka ƙaraso yanzu ina Health Care Clinic na kan titin sharaɗa." Cikin sauri Daddy ya ce, "Malam Allah ya sa an dace ko an ganta ne." Malam ya yi murmushi mara sauti ya ce, "A'a ba haka ba ne amma ka dai ƙaraso yanzu." Katse wayar Daddy ya yi cikin sauri ya shiga mota kamar Yadda Malam ya gaya masa sunan asibitin sai ga shi bai ɗauki lokaci ba ya ƙaraso, kiran Malam ya yi ya sanar da shi yana harabar asibiti nan take Malam ya tura Al'amin ya taho da shi, sai da Al'amin ya gaishe da Daddy cikin girmamawa sannan ya yi gaba Daddy na biye da shi zuciyarsa sai buga wa take yi. Shigarsa ɗakin ya kusa daskarar da numfashinsa, murza idonsa ya yi ya sake ware su akan Raihan da ke kwance a kan gadon cikin wani irin yanayi, duk wanda ya ganta a wannan lokacin ba zai taɓa tsammanin mai cikakkkiyar lafiya ba ce, kana ganinta za ka yi tunanin ko mahaukaciya ce sabon kamu. Da sauri Daddy matsa gaban gadon sai kawai ya rungumeta haɗe da ruƙo hannunta tsam kamar wani zai ƙwace ta, Malam ne ya riƙo hannunsa ya ɗago Daddy ya nuna masa kujera sannan ya ce, "Godiya za mu yi wa Allah da ya bayyana mana ita, komai ka ga ya faru da bawa yana daga cikin jarrabawarsa don haka sai mutum ya sa hannu bibbiyu ya rugumeta a yadda ta zo masa, kuma ya gode wa Allah." Jinjina kai Daddy ya yi ya ce, "Wannan haka yake sai dai mu ce Alhamdulillah." Nan take Malam ya zayyana wa Daddy duk abin da ya faru, jim Daddy ya yi ya furta: "Shi Huzaifa ba a gan shi ba kenan? Ya Rabbi! Ubangiji ka bayyana wannan yaron cikin ƙoshin lafiya." Gabaɗaya suka amsa da amin. Daddy ne ya ciro waya ya kira Mommy ya sanar mata halin da ake ciki, a take ta miƙe ta ce ta warke don duk yadda Likitoci suka so dakatar da ita ƙi ta yi. Ita da Mama Hafsa suka ƙarasa asibitin Mommy na shiga ta saka kuka haɗe da faɗa wa jikin Raihan, a hankali Raihan ta buɗe idonta tana ƙare wa mutanen da ke ɗakin kallo. Karaf idanunta suka sauka akan Al'amin da yake danna waya yana sakin murmushi. Yunƙura wa ta yi za ta tashi zaune Mama Hafsa ta taimaka mata, kallon su Daddy ta fara sai kawai ta saka musu kuka. Duk yadda Daddy ya kai da yin dauriya sai da hawaye ya zubo masa. Ganin haka ya sa Malam ya miƙe yana shirin yi wa Al'amin magana Raihan ta nuna Al'amin ta ce, "Mommy kin gan shi, don Allah kema kina ganinsa." Sai a lokacin Mommy ta kai idonta wurin Al'amin da ya ɗago suka haɗa ido. Ita kanta mommy ta yi mamakin ganinsa tana shirin yin magana Malam ya ce, "Raihan wa kike gani Al'amin ko wani ne daban?" Ya yi mata wannan tambayar ne don ya tabbatar da ba buɗe mata ido suka yi ba. Raihan ta sake nuna Al'amin ta ce, "Abba wannan fa mai baƙaƙen kayan nan wallahi a Harami na taɓa ganinsa." Malam ya yi murmushi ya ce, "Yayanki ne, ai yarona ne sunansa Al'amin." Mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Raihan da jin Al'amin ɗan gidan Malam ne amma ta shafe shakaru tana dakon soyayyarsa, ba su yi aune ba sai gani suka yi murmushi ya kuɓuce mata. Ta koma ta kwanta haɗe da lumshe ido, Malam da Al'amin sallama suka yi wa Daddy suka tafi tare da cewar zai turo wa Raihan waɗansu magunguna a riƙa bata da na turarawa. Inna wuro na yin sallama da Kabiru ta wuce gida shi kuma Kabiru ya ci gana da kula da Baffajo duk da ciwon nasa sai dai a ce da sauƙin musulunci. Washegarin ranar da Kabiru ya je garin a ranar ne Allah ya yi wa Baffajo rasuwa, mutane da dama sun ji mutuwarsa musamman da jinyar Baffajo ta zama sananniya ce a cikin garinsu Kabiru, kafin wani lokaci tuni aka karaɗe cikin rugar da sanarwar mutuwar tare da cewar za a yi jana'izarsa bayan sallar Azahar. Duk da kasancewar Kabiru namiji ne amma hakan bai hana shi zubar da ƙwallah ba, kafin a yi jana'izar Baffajo ya kira Daddy ya sanar da shi a nan kuma shi ma yake jin daddaɗan labari na dawowar Raihan, Daddy ya ce masa za su shiryo washegari su zo gaisuwa. Farinciki ya yi sosai ya yi wa Allah godiya sannan suka yi sallam, kamar yadda aka shelanta ana idar da sallar Azahar aka yi wa Baffajo sallah sannan aka kai shi gidansa na gaskiya. Da yammacin ranar Kabiru ya shiga cikin gari ya siyo kayan abinci masu yawan gaske, saboda masu zaman makoki, a rumbun hatsi ya ce a riƙa shiga da kayan abincin ana buɗe wa suka ga ya yi tsalle ya fito tsidik sai ga shi a gaban Kabiru. Ras ƙirjin Kabiru ya buga ya kalli hagu da dama yana shirin yin wani yunƙuri ya ji Talatuwa na cewa, "Hai ga mari babban kifi ya fito." Da hannu ya riƙa kai wa yaran duka yama zaro harshe waje. Ganin bai kalli ƙurar Kabiru ba duk da sun haɗa ido ya harzuƙa shi, don gani yake rainin wayon Huzaifa har ya yi yawa. Afusace ya sha gaban Huzaifa ya tattakura ya ɗauke shi da mari, kafin ya an kara Kabiru ya sake ɗauke shi da wani marin jikinsa na rawa ya shaƙi wuyan Huzaifa yana faɗin, "Me ya sa ka wahalar da ƴar mutane bayan ka san ba ƙaunarta kake ba? Ka fito ka gaya mana wanene kai?" Huzaifa ya dafe kunci yana kallon Kabiru a tsorace sai kawai ya fashe da kuka. Da sauri Jume da fasa ihu tana kiran maza su zo su taimaka Kabiru yana dukan ɗan tsintuwa, kafin wani lokaci tuni wurin ya ɗinke da mutane kowa yana bawa idonsa abinci. Da ƙyar su Baffa Giɗaɗo suka kwaci Huzaifa suka rufe Kabiru da faɗa, duk yadda Kabiru ya so fahimtar da su wani abu game da Huzaifa fir suka ƙi sauraronsa. Kaiwa da kawowa ya fara yi a cikin gidan jikinsa na rawa, da sauri ya fice daga gidan ya wuce can bayan gari. Sai da ya yi nesa da jama'a sannan ya kira lambar Daddy ya sanar masa da abin da yake faruwa, wannan labari ba ƙaramin faranta ran su Daddy ya yi ba, nan take ya kira iyayen Huzaifa da jami'an tsaro ya sanar musu da abin da yake faruwa. Tun a ranar Jami'an tsaron da ke kula da shiyyar jahar Kano suka kira wasu daga cikin jami'an tsaron da ke garin Shanono, suka sanar musu duk abin da yake faruwa. Duk wani shirye-shirye game da zuwan su Daddy da iyayen Huzaifa garinsu Kabiri a ranar suka yi shi. Saboda Kabiru ya sanar musu da babu yanda bai yi don su saurare shi amma sun ƙi. A washegarin Ranar Daddy da Mahaifin Huzaifa sai yayansa suka shirya zuwa garinsu Kabiru, da yake Daddy ya san garin ba su sha wahalar kwatance ba. A headquarter hukumar ƴan sanda suka fara sauka kasancewar tare da su za su ƙarasa garin, da yake dama an san da zuwan su Daddy ba su ɓata lokaci ba suka wuce cikin rugarsu Kabiru. Tun da suka shiga yara suke bin su da kallo, tsararu daga cikinsu suna biye a bayan motar suna kurma ihu don abin mamaki da tsoro ne a wurinsu, sakamakon sun jima ba tare da sun ga motar ƴan sanda a cikin rugar ba. Kabiru na jin dirar motocin ya fito ya yi wa su Daddy barka da zuwa, sai da Daddy ya yi masa gaisu sannan suka ƙarasa ya nemi ƴan uwan Baffajo ya yi musu gaisuwa. Har cikin gida ya shiga ya gaida Inna wuro ita ma ya yi mata gaisuwa sannan ya sa Kabiru ya buɗe booth ɗin mota ya riƙa shiga da kayan abinci. Bayan sun gama gaisuwa Baffa Sama'ila ya dubi Daddy ya ce, "Hai Alhaji da mun san wannan lamarin har da hukuma a ciki da tuni mun sallama wa Kabiru ya kawo maka yaron nan har gida." Daddy ya yi murmushi ganin yadda duk suka firgice lokaci ɗaya, ya juya ya nuna Baba sannan ya ce, "Ga mahaifin yaron nan, kuma Alhaji Sama'ila don hukuma ta shiga cikin maganar ai ba wani abu ba ne." Baffa Sama'ila ya nuna ɗakin da Huzaifa ya ke ciki a ɗaure ya ce, "Kai Kabiru shi ga ka fito da shi, su tafi da shi ko hankalinmu ya kwanta." Da sauri Kabiru ya buɗe ya fito da Huzaifa sai dai wannan lokacin bai da kuzari sai kallon mutane yake a tsorace. Baba na ganin Huzaifa ya rungume shi ya fara kuka shi kuwa ban da yaƙe baki babu abin da yake yi. Cike da mamaki Daddy ya ce, "To wai yaushe Huzaifa ya zo garin nan Kabiru?" Inna wuro na daga gefen dokin ƙofa ta ce: "Yaron nan Huzaifa yau kusan watansa biyu cir a garin nan yara sun tafi kiwo suka dawo da shi sun tsinto shi a kogi suka ɗoro shi akan jaki ya sha ruwa ya ƙoshi don ma Allah ya sa da kwanansa a gaba, tun da ya farko yake a wannan halin don ga dukkan alamu makarai sun shafa masa kai." Inna Wuro na rufe baki Huzaifa ya zubara ya fusgo wani dokin kara da yake hannun wata yarinya, ya ɗare kai yana faɗin, "Mu je ka kaini gaban Mai shari'a." Da sauri Baba da sauran mutane suka yi kan Huzaifa suka rirriƙe shi. Ganin yananyin Huzaifa ya sa aka ɗaɗɗaure shi sannan suka ci gaba da tattaunawa. Daga ƙarshe aka damƙa Huzaifa a hannu su Daddy suka saka shi a mota, sannan suka yi sallama da su Baffa Sama'ila suka wuce tare da yarjewar jami'an tsaro. Har su Daddy suka tafi Kabiru gani yake kamar Basaja Huzaifa yake yi don shi bai yarda da ciwon haukan da yake yi ba, ya so ace an bar su da shi ya lillisa shi ko ba komai zai yi magana idan ya ji wahala. Sai da su Daddy suka ɗauki hanya sai kuma tsoro ya dira a zuciyar Daddy, zuciya ta raya masa kar suna cikin tafiya suma ya ɓace da su kamar yadda ya faru da Raihan, duk da har lokacin yana wasu-wasi game da lamarin Huzaifa da Huzaifa. Ba shiri ya kunna karatu a cikin motarsa sannan suka ci gaba da tafiya, suna shiga garin Kano kai tsaye Daddy ya bayar da shawara akan su wuce da Huzaifa Waraka Islamic Chemist, idan aka gwada aka ga ba na islamic chemist ba ne sai a yi ci gaba da na asibiti. Malam ya yi murna sosai da bayyanar Huzaifa sai da bai ji daɗin ganin halin da yake ciki ba. Tun daga jin jawabin da suka yi masa ya saki murmushi don ya fahimci wannan Huzaifa shi ne na ainihi wancen nunke su kawai ya yi ya samu ya tafi da Raihan. Sannu a hankali raunikan da ke jikin Raiha suka riƙa warke wa tana samun sauƙi, kwananta biyu a asibitin aka sallame ta sakamakon ba wasu munanan raunuka ta samu masu yawa ba, lokacin da su Inno suka samu labarin dawowar Raihan, har da kukansu don a ranar sai da Daddy ya kai su asibitin suka ganta sannan hankalinsu ya kwanta. Tun a asibiti Raihan ta riƙa ba su labarin rayuwar da ta yi tare da Huzaifa, har zuwan su Mama Hafsa da Daddy duk sai ta gaya musu, saboda tausayi haka suka riƙa yi mata hawaye daga baya kuma wani abin ya ba su dariya. Malam Usman dama abin da ya yi tsammani shi ne ya tabbata, lokacin da ya fara yi wa Huzaifa ruƙiyya nan take Huzaifa aljani ya fara magana cikin izza, taƙama da girman kai. "Malam Usman ka na yawon son shiga gonata da yawa, a kodayaushe ina jaddada maka wahainiyarka ta kiyayi ramata. Wai ma me ya sa ka addabi rayuwata? Me na tsare maka da za ka riƙa bibiyar sahuna?" Malam Usman ya bashi amsa, "Abin da ya kai ka jikin bayin Allah shi ne silar dalilin bibiyarka. Idan har ita Raihan birgeka ta yi har ka aure ta shi kuma wannan bawan Allahn me ya yi maka da za ka nemi salwantar da rayuwarsa." Huzaifa ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya sannan ya ce, "Ba sai an yi wa Huzaifa wani abu ba yake shiga rayuwar bil'adam ba. Hasalima wannan Huzaifan babu abin da ya yi min kwangilar aikinsa kawai aka bawa Kakana Jabbul-ƙasi a yayin da nake durƙushe a wurin neman tawa buƙatar, babban abokinsa kuma amininsa na wurin aikinsu wato Abubakar shi ne ya kai wa Boka Naziru aikinsa, akan yana son a ɓatar da shi ta kowanne hali domin ya jima baya ƙaunar ganinsa a bakin aikinsu, sakamakon yana yawan samun ci gaba tun da ƙwararre kuma gogagge ne abakin aiki. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 40 Da farko na yi niyyar kashe shi faraɗ ɗaya amma sai na fasa don na san idan na kashe shi lokaci ɗaya mutuwarsa za ta zo masa da sauƙi, ni kuma wanda ya bayar da kwangilar cewa ya yi a kashe shi da kisa mai muni. Kakana ya so hana ni ɗaukan wannan aikin a tunaninsa na shiga halwar soyayya ba zan iya taɓuka komai ba, amma sai na nuna masa sam ba haka ba ne hasalima na yi amfani da surarsa don cimma tawa buƙatar, ranar da na fara zuwa gidansu Raihan har a raina na tsorota don na yi tsammanim Mahaifinta zai zargi wani abu har ya hana ni aurenta, amma sai da na ci galaba akansu suka amince min suka ba ni aurenta. Ba zan daina faɗa ba babu maccen da nake so a duk duniya kamar Raihan, don haka da na aureta na ajiyeta a ƙasaitaccen gidana da na fi ji da shi sai dai ko kaɗa ban samu nasarar kusantarta ba, daga ƙarshe a ranar da na so yin galaba akanta na wayi gari da matsanciyar gobara hatta ni kaina ban tsira daga kaidin wannan gobarar ba, kuma na tabbata ba komai ya haddasa min haka ba face kaidin addu'o'in da kuke yi tare da wanda ita kanta Raihan take yi ba dare ba rana. Shi kuma wannan Huzaifan lokacin da na tashi yaudararsa a siffa budurwa na je masa saboda na san ya ƙware wurin neman mata, a ranar na je wurinsa ban sha wata wahala ba don ina yi masa tayin kaina muka jone, muna shiga ɗakin da suka saba aikata baɗalarsu na ɓace da shi ban sauke shi a ko ina ba sai a tsakiyar kogin wani ƙauye, na danna shi can ƙasan ruwa na yi tafiya saboda na tabbata ko awa guda ba zai ƙara ba zai baƙunci lahira, tun a wannan kogin Aljana 'yar Dugwal take ita kuma bata da aiki sai zuƙe jinin bil'adama idan ta gama da shi ta turo gawarsa sama. Hasalima duk wani kogi da kuka sani mai cin mutane zuri'ar 'yar Dugwal ne a ciki domin ita tana daga cikin jinsin jinnu masu zuƙe jinanen mutane. Dalilin da ya sa kuka ga su Daddy sun ɗauko Huzaifa lafiya, sun kawo shi ba tare da wani abu ya faru da su ba saboda ina matuƙar daraja soyayya. Daddy ya nuna min ƙauna matuƙa kafin daga baya ya fara ƙyamatarka, ni kuma ina daraja shi ne saboda soyayya ita ce abu na farko da ya fara nuna min ba ƙiyayya ba domih sai da ya san wanene ni yake ƙi na. Shi kuma wannan yaron zan isar da saƙo ku gaya masa hawainiyarsa ta kiyayi ramata domin na lura yana son tsalla gonar da ba tashi ba, to ahir kabewar kan kabari tafi ƙarfin taushe idan kuma taurin kansa ya kai shi zan nuna masa shayi ba ruwa ba ne don sai na nuna masa ba a ja da ni a soyayya. Yaron da nake nufi ba kowa ba ne face Kabiru idan kuma ya yi gaddama zan bambamce masa tsakanin tsaba da tsakuwa. " Malam Usman ya ja kujera ya zauna sannan ya ce, "Tabbas Huzaifa ya cika gawurtaccen hatsabibi." Huzaifa na jin haka ya bushe da dariya yana faɗin, "A cikin hatsabibancina ba na jin na tsakuro maka cikin cokoli, ni kaina na san ba ni da kyau hatta ni kaina tsoron kaina nake yi." Malam Usman ya kafe Huzaifa da ido ya furta, "Don na faɗi haka ba ina nufin ka gagare ni ba, Huzaifa ba za ka taɓa gagarata ba balle ka gagari ayar Allah. A wannan karon ba zan saurara maka ko na baki dama ba domin na lura kai zuma ne sai da wuta, zan ƙoneka idan ya so kowa sai ya huta." Huzaifa ya fara takawa a hankali sai kuma ya huyo ya sake kecewa da dariya sannan ya ce, "A wannan karon ba zan baka haƙuri ba ka yi duk abin da za ka yi Malam, amma na tabbata ba za ka taɓa hallaka ni ba. Na yi gawurtar da sai na futune ka kai da iyalinka, a da ban yi niyyar taɓa wani naka ba amma a yanzu ni da kai ɗan Halak ka fasa. Zan ganye daga jikin Huzaifa domin wanda ya kawo mana aikin bai cika mana alƙwarinmu ba, zai binne jariri sabuwar haihuwa da ransa ya aiwatar amma bai yanka mana farar jaka ba. Zan bar jikin takwarana amma ka sani ba wai na bar jikinsa kenan ba lokaci-lokaci zan riƙa kawo masa ziyara. Ita kuwa Raihan har abada ina tare da ita, ba za ta taɓe gujewa halwata ba domin ni ne mijinta na har abada." Huzaifa na gama maganar sai Malam Usman gani ya yi ya yanke jiki faɗi yana wani irin numfarfashi, da sauri Malam ya kira sauran yaransa da suke kula da marasa lafiya. Zuwan su keda wuya suka riski Huzaifa yana ta zabga atishawa, turaren habbatussauda aka yi masa sannan Malam ya shafa masa wasu magunguna. Sun jima a kan Huzaifa sannan ya dawo hayyacinsa, a hankali ya riƙa bin mutanen wurin da kallo, miƙe wa ya yi yana tangaɗi sannan da mamaki ya furta, "Su waye ku? Don Allah ku yi haƙuri kar ku cutar da ni wallahi na daina bin kowacce mace, kema da muka haɗu da ke tsautsayi ne." Malam ne ya ƙarasa wurin Huzaifanya ruƙo hannunsa sai da ya kai shi kan gado ya zaunar da shi sannan ya ce, "Huzaifa!" Malam ya kira shi da dakakkiyar murya, kallonsa Huzaifa ya yi yana waige-waige sai kuma ya sa hannu bibbiyyu ya dafe kansa haɗe fa faɗin, "Wash kaina." Da sauri Malam ya sa aka ɗauko wani turare aka turara masa sannan aka shaƙa masa wani a hanci tare da shafe masa jikinta da wani ruwan tofi. Lokaci ɗaya jikinsa ya saki ya faɗi yaraf can gefe yana sauke ajiyae zuciya da sauri, Malam ne ya sa aka kunna masa fanja saboda gumin da Huzaifa yake sharɓawa. Huzaifa ya jima a haka sannan ya ɗago yana sake ƙare wa mutanen wurin kallo, a hankali ya buɗe baki yana faɗin, "Su waye ku? Don Allah nan a ina nake?" Malam ya ƙarasa gabansa ya ce, "Huzaifa!" Da kallo Huzaifa ya dubi Malam yana shirin yin magana ya riski muryara Malam ya ci gaba da cewa, "Ko za ka iya fahimtar a ina kake yanzu." Kallon wurin Huzaifa ya sake yi ya ce, "Don Allah ka yi min rai kar ka halaka ni, wallahi duniya da lahira ba zan sake neman mata ba har abada wannan ma sharrin Shaiɗan ne." Kafaɗarsa Malam ya dafa ya ce, "Dube ni da kyau Huzaifa ka nutsu ka ji." Shiru Huzaifa ya yi yana bin Malam da kallo, kai tsaye ƙofa ya buɗewa su Baba suka shigo Huzaifa na ganinsu da gudu ya maƙale shi yana faɗin, "Don Allah ku zo mu gudu wallahi a taiku za ta jefa ni." Nan take Huzaifa ya sake rikice musu sai da Malam ya yi da gaske sannan ya samu ya koma kan fado ya zauna. Jan Mahaifin Huzaifa ya yi suka fita waje sannan ya dube shi yana faɗin, "Alhamdulillah na san duk abin da yake faruwa kuna ji sheɗanin nan ya fita daga jikinsa, amma duk da haka yana buƙatar kulawarmu domin bai gama dawo wa daidai ba. Za a bar shi ya zauna a nan na tsawon mako guda mu ga yanayin yadda jikin za yi, shi kuma wannan karon ba zai taɓa tsallake wa ba domin na lura taƙadari ne don haka duk in da ya shiga zan saka a kamo shi kuma duk inda ya shiga zai an nemo shi na ƙone shi ƙurnus." Baba gyaɗa kai ya yi cikin farinciki don tuni ya sanarwa da Mahaifiyarsa halin da ake ciki suma sai murna suke yi, Daddy ne ya ƙaraso wurin a kunyace ya dubi Baba ya furta, "Don Allah ka yi haƙuri ku gafarce ni akan abin da ya faru. Wallahi na shiga ɗimuwa akan wannan lamarin don haka nake ganin kamar Huzaifa ne ya tafi mini da ƴa ashe ba haka ba ne." Baba ya dubi Daddy ya ce, "Ka yi abin da kowanne uba zai iya aiwatarwa don haka ja daina ba mu haƙuri, Allah ya kiyaye gaba ya katange mu daga kaidi da hatsabibancin shaiɗanun nan." Lokaci ɗaya suka amsa da Amin. Kafin wani lokaci tuni labarin dawowar Huzaifa ta watsu a cikin danginsu, ƴan uwa da abokan arziƙi sai zuwa duba shi suke yi suna yin Allah sanya alheri. Abin ba iya nan ya tsaya ba har zuwa kafafen watsa labarai haka ka yi ta maganar cikin ta'ajibi don har sai da ƴan jarida suka ji ta bakin Daddy da Baba suka watsa wa duniya. Daga ƙarshe wasu mutanen har ganu suke kamar ƙarne wannan sharhin abin da ta faru, har sai da Ƴan jaridu sula sake hira da Malam Junaid Malunfashi ƙwararran masani ne kan abin da ya shafi harkar aljanu, bayani ya yi sosai na kusan minti ashirin dangane abin da ya shafi jinnu da al'amuransu. Daga ƙarshe ya shawarci al'ummma da su riƙe azkar na safe da yamma, su yi riƙo da addu'a domin takobin muminu ce. Haka Huzaifa ya ci gana da samun kulawar da ta kamata har ya shafe tsawon waɗannan kwanakin, kuma cikin ikon Allah jikinsa ya warware hatta surutan da yake yi ya daina. A ranar da Huzaifa ya ƙarasa warware a ranar ne abokinsa Abubakar ya wayi gari da hausa tuburan don shi har yagar nama jikinsa yake yi yana cewa zai ci, tun abokansa na bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sun taimaka masa har suka gaji daga ƙarshe suka tattara shi suka kai shi garinsu, da yake iyayensa tsofaffine kuma ba su da ƙarfi ya sa suka gagara kula da shi ƙarshe ya ɓige da yawo akan bola. Ranar da Huzaifa ya cika kwana takwasa a wurin Malam ne aka sallame shi sakamakon ya warke garau babu wani abu da yake damunsa. Raihan ta warware raunukan jikinta duk sun warke, kuma tun da Kabiru ya samu labarin dawowar Raihan kusan kullin sai ya kira wayar mommy ya ce a bawa Raihan zai dubata. Mommy har mamakin wannan kulawar da Kabiru yake bawa Raihan yake yi amma da ta tuna irim ɗawainiyar da Daddy yake yi masa sai take ganin kamar saka alheri da alheri ne Kabiru yake yi kuma hakan ba ƙaramin faranta ransu yake yi ba. Su Baba faɗa suka yi wa Huzafa sosai game da abubuwam da yake aikawata, ya yi nadama sosai don haka ya ji aikinma gabaɗaya ya fice masa da kai. Sai da Abokan aikinsa suka ƙarfafi gwiwarsa sannan ya koma bakin aiki, kuma kafin tafiyarsa sai da aka ɗaura masa aure wara cousine sister ɗinsa da sakamakon dama ya jima yana son ya yi mata magana tun a lokacin gaya, amma sai a wannan lokacin Allah ya yi don haka ba a ɗauki lokaci ba dudu wata uku aka tsayar lokaci na cika aka ɗaura musu aure ya tafi da matarsa. A wannan lokacin tuni Kabiru ya dawo garin Kano sai dai a lokacin da zai baro garinsu Matarsa na ɗauke da cikin wata biyar don har ya fara fitowa, a da baya jin komai game da Maryama amma ɗan zaman da ya yi lokacin rasuwar Mahaifinsa ya ƙara musu shaƙuwa tsakaninsa da ita, sosai ya riƙa jin kewar matarsa lokacin da zai taho sannan ga wani irin ƙaunarta da yake ji ita da abin da yake cikinta. Tun bayan da komawar Raihan gida Daddy ya samu Malamai game da auren Raihan da aka ɗaura, nan take suka nusar da shi auren Raihan babu shi domin an yi shi ne a cikin rashin sani hasalima ba shi ne ainihin mai wannan siffar ba kuma ba jinsinta ba ne. Don haka babu wurin da aka halatta aure tsakanin jinsin mutum da aljani, da farko iyayen Huzaifa sun so a tambayi Raihan ko za ta amince ta auri wannan Huzaifan idan ya so sai a ɗaura musu aure. Daddy ne ya dakatar da maganar a take don cewa ya yi ko Raihan ɗin ba zai gaya mata ba, saboda ba za ta iya rayuwa da Huzaifa saboda a kodayaushe ta gan shi zai riƙa tuna mata da wancen. Tun da ko daga baya ita kaɗai idan ta dubi hotunan bikinsu sai ta riƙa ganin suna yi mata gizo, har ta kai ga hotunan kamar sun fara tsorata. Ba shiri ta ware rana ɗaya ta ƙone su gabaɗaya, waɗanda suke cikin wayarta da na Mommy suma duka aka gone. Rahan haka ta ci gana da kasuwancinta gwanin birgewa saboda da farko ne ta saka wa ranta damuwa amma daga baya duk ta watsar ta fauwala wa Allah lamuranta. Sai dai babbaj abin da ya fi nuƙurƙusar zuciyarta bai wuce tunanin Al'amin da take kwana take tashi da shi ba, tun tana iya danne wa har ta samu Mommy da maganar don a lokacin ba ta da aiki sai na mafarkinsa da tunanin suna gudanar da rayuwa cikin farinciki da annushuwa. Wannan tunane-tunane ne ya sake rura wutar da ke cikin zuciyar Raihan, ba a ɗauki lokaci ba ta zabge ta rame ita kaɗai ta rasa abin da yake damunta. Ga shi tana fargabar tarar Mommy ta gaya mata don bata san yadda za ta ɗauki maganar ba, watarana tana zaune da tunanin Al'amin ya addabi rayuwarta miƙe wa ta yi ta ɗauki key ɗin motarta. Tun bayan bikinta da Huzaifa ba ta sake fita ira kaɗai ba sai ranar, Inno na ganinta da mukullin mota ta ƙanƙance ido tana sannan ta ce, "Raihanu ni kam wannan makullin gidan abinci ne?" Raihan ta ɗago shi ta nuna wa Inno sannan ta ce, "Mukullin motata ce fita zan yi." Da sauri Inno ta zaro ido waje ta furta, "Fita ina ban gane ba." Tura baki gaba Raihan ta yi, ta yi ƙasa da murya ta ce, "Idan na je na dawo kya gane." Da sauri Inno ta ta shi ta tare bakin ƙofar tana kiran Mommy, nan take ta ƙaraso tana tambayar ko wani abu ne ya faru. Inno ta nuna Raihan ta ce, "Gata nan wai fita za ta yi, wallahi ki shaida Zainabu idan waccen hatsabibin ya sake ɗauke ta ko ƙyallin hawaye ba za ki gani a idona ba." Mommy na shirin yin magana Goggo ta ce, "Wallahi balle bikin ƴar gidan Safare gare ni ko ƙarƙashin kukar Bulukiya ya kai ki babu abin da zai hana ni tafiya Albasu biki." Mommy ta dubi Raihan ta ce, "Ina za ki je?" Idanun Raihan suka ciko da ƙwallah kafin mommy ta yi aune sai ga hawaye na zuba." Baki suka riƙe gabaɗaya suna kallonta, Goggo ta tafa hannuwa cike da takaici ta ce, "Raihane kin ji kunya gwandamemiya kamar ke kina wannan sakarcin daga tambaya." Raihan kukan da take yi fargabarta kar ta hana ta fita don haka ta tattaro jarumanta ta goge hawayen ta ce, "Mommy shop zani fa komai na maka up ɗina ya ƙare." Mommy jim ta yi sannan ta ce, "Ba na son ki riƙa fita ke ɗaya Raihan gaskiya ki kira Daddy idan ya ce ki fita shi kenan." A nan take Raihan ta kira Daddy ta sanar da shi da farko bai amince ba sai daga baya. Raiham kamar za ta yi tsalle ta tashi sama saboda sauri, don lokacin da ta fita mommy har kallonta ta yi tana mamakin saurin da take yi. Amma da yake ba fita take ba, sai ta yi tunanin ko ɗokin fita ne take yi. Sai da ta fara zuwa store ta siyo kaya shafe-shafe sannan ta ɗauko hanyar Waraka Islamic store, tana parking ƙirjinta ya buga sakamakon hango shi da ta yi a barandar asibitin. Ajiyar ta sauke a hankali ta furta, "Allah ka cika mij burina wanda yake alkairi a gare ni." Cikin shauƙin so ta nufi wurin da yake zaune a kan kujera, tana ƙarasawa ta ɗan yi gyaran murya sannan ta yi sallama sakamakon ta same shi yana yin waya. Sai da ya ɗago ya kalleta sannan ya gyaɗa mata kai ya furta, "Ok Ur hightness i wll call you later..." Daga can ɓangaren aka katse shi da cewar, "Baby ba dai wata beb ɗin ka yi ba?" Lumshe ido ya yi sannan ya furta, "No wara patient ce da Daddy bawa magani." Amsa ta bashi sannan ya furta, "Na yi kewarki dear yaushe za ku kawo ne, gaskiya zan biyo ki garin Dutsen nan." Afwan ban tace shi i ba. Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 0706 206 2624 41 Tamkar wacce aka watsa wa ruwan zafi haka Raihan ta ji kalaman Al'amin a cikin zuciyarta, ƙwallah ce ta ciko idonta zuciyarta na tururi. Tana cikin wannan yanayin riski muryar Al'amin yana faɗin, "Take care Hayaty" Sai da ya saka wayar a aljihunsa sannan ya kalli Raihan ya furta, "Wa'alaikis salam." Murmushin yaƙe Raihan ta yi ta ce, "Abba fa?" Ɗan jim ya yi sannan ya ce, "Daddy bai shigo ba sai an jima." Raihan duk ji ta yi zuciyarta babu daɗi saboda yadda Al'amin ya tarbe ta tamkar bai taɓa saninta ba, duk da sun jima ba su haɗu ba amma a ganinta ba zai ce bai gane ta. Tana nan tsaye Jamila ɗaya daga cikin ma'aikanta Malam ta ƙaraso ganin Raihan ya sa ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin, "Raihan yau ke ce da kanki." Raihan ta sakar mata murmushi sannan ta ce, "Wallahi na zo karɓar turare wurin Abba ashe baya nan." Kasancewar ma'aikanta wurin duka sun san Raihan ya sa Jamila ta furta, "Ai kuwa bai ƙaraso ba sai zuwa anjima bari na baki kujera ko za ki shigo ciki?" Murmushi Raihan ta yi ta ce, "A'a Aunty Jamila nan ma ya isa." Kujera Jamila ta kawo wa Raihan ta zauna, sai da suka shafe wasu mintuna a zaune ta riski muryar Al'amin yana faɗin, "Ya jiki?" Sai da ta kalli hagu da dama ta juya bayanta don neman da wanda yake maganar amma bata ga kowa, saboda a ƙalla sun shafe kusan minti goma sha biyar ba tare da ya furta mata komai ba, kuma a yananyin yadda ya yi maganar sai ka rantse ba da ita yake ba. Murya a sanyaye Raihan ta furta, "Da sauƙi na gode." Bai tanka mata ba kuma bai sake ɗago wa ya kalleta ba, sai dai tun zaman Raihan gabanta yake faɗuwa har ta gagara saita kanta ban da kallonsa babu abin da take yi tana jin zuciyarta na yi mata zillo a kansa. Babban abin da ya fi ɓata mata rai jin yadda yake gaya wa wata macen kalamai masu daɗi, saɓanin ita da kallon arziƙi bata samu a wurinsa ba. Tana cikin wannan nazarin ta riski motar Daddy ta ƙaraso harabar wurin, miƙe wa ta ga Al'amin ya yi ya ƙarasa wurin Motar Malam sannan ya karɓo jakar hannunsa, tun daga wurin motarsa ya hango Raihan a zaune tana ganin sun nufo wurinta ta miƙe tana yi wa Malam murmushi, yana ƙaraso wa ya faɗaɗa fara'arsa yana faɗin, "Ƴar gidan Abba ba dai tun ɗazu kike nan a zaune ba." Sai da ta russuna har ƙasa ta gaida Malam sannan ta amsa masa, "Eh to zan kai minti Arba'in zuwa hamsin Abba." Kallon Al'amin ya yi ya ce , "Amma dai ka fiye sakarci Aminu a madadin ka tambayeta maganin da ta zo karɓa amma sai kawai ka barta a zaune, da ban ƙaraso da wuri ba fa?" Al'amin ya sosa kai sannan ya ce, "Daddy ai bata ce min magani ta zo karɓa ba na ji dai tana gayawa Jamila." Takaici ne ya kama Malam don haka ya yi tsaki yana faɗin, "Allah ya kyauta Raihan mu je ciki kin ji." Ba musu Raihan ta bi bayan Malam suka shiga ciki, wayar Malam ta fara ringing sai da ta zauna sannan ya ɗauka bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa aka yi; Raihan ta ji Malam ya ci gaba da cewa, "Insha Allah a gobe ne Yaya da kimanin ƙarfe biyun rana, a'a gidansu yarinyar a unguwar Karkasara yake. Ai idan mun je bai fi a tsayar da ranar auren nasu wata huɗu zuwa biyar ba, sai dai gobe insha Allah ma ƙarasa maganar." Gaban Raihan ne ya ci gaba da lugude jikinta har rawa yake don ita kanta ba ta san abin da yake damunta ba. Ji take kamar ta tambayi Malam auren wa za a saka amma ko kaɗan ba za ta iya ba, yawun bakinta ne ya yi mata ɗaci ga wani irin sarawa da kanta yake yi. Ba ta yi aune ba ta riski muryar Malam na yi mata magana, "Ƴar gidan Abba me kika zo karɓa maganin sha ne ko turare, sai da ta mayar da ƙwallar idonta kai a ƙasa ta furta, "Abba turare da garin habbatussaauda ne babu." A jikin wani ƙaramin kati ya rubuta mata da yake Raihan ba baƙuwa ba ce a wurinsa ya sa ya rubuta suna da shekarunta ba tare da ya tambayeta ba, miƙa mata ya yi ta yi masa godiya har ta miƙe ya kira sunanta. Cak ta tsaya wuri ɗaya jiki ba ƙwari ta juya tare da amsawa, kujera ya nuna masa ya ce: "Zauna!" Ba musu Raihan ta zauna tana sake sauke kanta ƙasa don bata son ya fahimci halin da take ciki, sunanta ya sake kira sannan ya ci gaba da cewa, "Me yake damunki? Ko akwai wata matsalar ne Raihan?" Kamar mai jira sai kawai Raihan ta fashe da kuka, shiru ya yi sai da ta yi mai isarta sannan Malam ya miƙa mata wani hankici ta karɓa ta goge hawayenta. Ido ya zuba mata yana sake karantar yanayinta ya ce, "Me yake damunki?" Raihan ta sake goge hawayen da ya zubo mata sannan ta furta, "Babu abin da yake damuna Abba, haka kawai nake jin ɓacin rai sai na yi kuka nake jin daɗi." Jinjina kai Malam ya yi ya ce, "Yaushe kika fara jin haka?" Shiru Raihan ta yi kamar mai nazari ta ce, "Na ɗan kwana biyu." Karɓar katin hannun Raihan ya yi da kansa ya wuce ya haɗo wa Raihan magunguna masu yawa ya dawo ciki ya bata, kowanne sai da ya yi mata bayaninsa dalla-dalla. Godiya Raihan ta yi har ta sake miƙe wa ta zauna ta ce, "Daddy babu teller..." Katse ta ya yi da cewar, "Gidanku kin ji Raihan, fice ki bani wuri kar na karye ƙafarki." Dariya Raihan ta yi sosai ta fice daga office ɗin don babu yadda za a yi ka haɗu da Malam baka yi dariya ba saboda shi mutum ne mai barkwanci. Tana fito wa ta ji shi ma ya fito yana ƙwala wa Al'amin kira, ƙarasowa ya yi wurinsu Raihan. Malam ya dubi Raihan ya ce, "Za ka raka ta gida duk da a motarta ta zo, amma ban lamunce ta tafi ita kaɗai va saboda bata jin daɗi. Idan za ka dawo sai ka hau Napep." Haɗe fuska ya yi ya ce, "Daddy da wuce wa gida zan yi fa." Malam ya wuce ƙofar Office ɗin sa sannan ya ce, "Ni dai na ce ka raka ta gida. Dududu minti nawa ne ka kaita gida ka dawo." Al'amin wuce wa ya yi wurin motar ba tare da ya furta komai ba, a sanyaye Raihan ta ƙarasa wurinsa. Hannu ya miƙa mata sai kawai ta tsaya tana kallonsa don bata fahimci abin da yake nufi ba. Ganin ta yi shiru ya sake harzuƙa shi ya dube ta ya ce, "Ko ba da key kika tuƙo motar ba?" A duburburce Raihan ta fara duba jakarta hannu na rawa ta miƙa masa key, da sauri ya buɗe motar ya shiga. Jikin Raihan na rawa ta buɗe motar ita ma ta shiga, da gudun gaske ya figi motar suka fice daga harabar wurin. Gaban Raihan ban da faɗu wa babu abin da yake yi, sai dai duk abin da Al'amin yake yi ko kaɗan bata ji haushinsa ba hasalima sai ta riƙa jin haushin kanta don gani take kamar ita ta yi abin da ya harzuƙa shi. Suna hawa kan titi ta ji ya furta, "Ta ina za mu bi?" A rikice Raihan ta riƙa kwatanta masa saboda muryarsa ba ƙaramin rikita masa lissafi ba, suna zuwa ƙofar gidansu Raihan ya faka motar ya fito ba tare da ya furta mota komai ba. A tunanin Raihan ko fita yin wani abu zai yi, jin shirun ya yi yawa ya sa Raihan fitowa daga motar sai dai tana fito wa ta hango Al'amin a can ƙarshen layinsu har ya kusa zuwa titi. Wani irin gwauron kuka ne ya zo mata ta kafa kanta a jikin motarta tana rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Kabiru na daga cikin ɗakinsa da farko ya ji tsayiwar mota a tunaninsa Raihan ce ko Daddy, amma jin shirun ya yi ya wa ya sa ya yi tsammanin ko wuce wa aka zo yi. Jin kuka sama-sama ya sa ya tako a hankali ya zare sakatar gidan, turus ya yi yana kallon Raihan sannan ya fito yana waige-waige jiki na rawa ya furta, "Waye ya taɓa ki?" Sai a lokacin Raihah ta ɗago fuskarta har ta yi jawur saboda kuka, ganin yanayin da Raihan take ciki ya sake ɗaga hankalin Kabiru. Jin irin tambayar da ya yi mata ya sa ta sake rushe wa da kuka, takawa Kabiru ya fara yi yana dube-dube amma unguwar shiru take ko tsuntsaye babu. Dawo wa ya yi gabanta a fusace ya buga mata tsawa yana faɗin, "Na ce miki waye? Wanene ya taɓa ki." Zaro ido Raihan ta yi don tun da take da Kabiru abin da bai taɓa yi ba kenan, ko magana mai ƙarfi baya yi mata balle ya buga mata tsawa. Tsoro ne ya kamata don haka lokaci ɗaya ta haɗiye kukanta, ajiyar zuciya Kabiru ya sauke don ya lura da halin da take ciki. Tausasa murya ya yi ya buɗe mata murfin motar ya ce, "Shiga!" Ba musu Raihan ta shiga ya rufe motar, ya ƙarasa ya buɗe mata gate ɗin gidan ta shige da motarta. Yana ganin ta shiga ya rufe ƙofar ya ƙarasa bakin motarta, Raihan na fito wa daga motar da sauri za ta wuce Kabiru ya sha gabanta fuska a haɗe ya sake tambayarta, "Waye ya saka ki kuka?" Wani hawayen ne ya ziraro mata sai dai bata jin za ta iya gaya wa Kabiru saboda ta lura ko hirar mijinta na baya son ta riƙa yi masa. Cikin muryar kuka ta ce, "Babu komai kaina ne yake ciwo." Haɗe fuska ya yi ya ce, "Ƙarya ba halinki ba ne tabbas akwai wani abu da yake damunki daga ina kike?" Harara ta watsa masa ita ma ta haɗe fuska ta ce, "Fillo wai me ya sa ka raina ni ne?" Bai tanka mata komai ba ya kafe ta da ido, ganin haka ya sa Raihan ta shammace shi ta yi cikin gida a guje. Ba ƙaramin dariya ta bashi ba don har sai da ya murmusa sannan ya wuce ɗakinsa, amma kukanta ya tsaya masa a rai saboda ya tabbata ruwa baya tsami banza. Mommy da su Inno suna zaune a falo Raihan ta shiga da gudu tana dariya, don haka kawai idan tana tare da Kabiru ko a cikin fushi take sai zuciyarta ta yi wasai. A tsakiyar falon ta tsaya tana mayar da ajiyar zuciya haɗe da riƙe ƙugu, Goggo ta riƙe baki tana cewa, "Kai gaskiya wannan yarinya baki da ɗabi'ar aziƙi saboda Allah baki da aiki sai na gudu kamar kin yi wa sarki ƙarya ya sa a kamo ki?" Mommy ta dubi Raihan ta ce, "Raihan kedai bakya girma, so kike Muhammad ya taso ki koya masa wannan guje-gujen naki?" Zama Raihan ta yi a kujera sannan ta ce, "Wallahi Mommy Fullo ya raini." Mommy ta yi salati haɗe da kai wa Raihan duka a baya ta furta, "Yanzu saboda Rashin kunya Kabirun za ki ce ya rainaki." Inno ta yi guntun tsaki haɗe da banka wa Raihan harara ta ce, "Wannan sakarcin da kike yi ba Kabiru ba nan gaba Muhammadu sai ya rainaki." Raihan ta miƙe tsaye tana murguda musu baki ta wuce ɗakinta haɗe da cewa, "Allah ya kiyaye wallahi duk ranar da ya min fitsara sai na yi masa Walmukalifatu." Mommy ta yi dariya ta ce, "Ji sakarcin banza yanzu MD kike gaya wa haka kamar wani sa'anki." Raihan na shiga ɗakinta ta faɗa gadon haɗe da lumshe ido nan ta tuno fuskar Kabiru ta yi lokacin da ya tsare gida yake tambayarta, murmushi ta yi haɗe da furta: "Fullo! Fullo ka ga makwancina da yawa wallahi " Al'amin shi ne abu na biyu da ya faɗo mata, nan take ranta ya sake ɓaci musamman da ta tuna irin ɗiban karan mahaukaciyar da ya yi mata haɗe da kalaman da ta riske shi yana faɗa a waya. Uwa-uba kuma wayar Malam da ya yi ita ta sake tsinke igiyar da ta yi shanyar kwanciyar hankalinta akai, lumshe ido ta yi tana furzar da iska mai zafi nan take hawaye ya fara bin idonta. Filo ta janyo ta rungume a hankali ta furta, "Ba ni na ɗora wa kaina ba soyayyarka ta dira a zuciyata tamkar dirar mikiya. A duk bugun numfashi wutar ƙaunarka ƙara ruruwa take a cikin raina sai dai ga dukkan alamu babu ni a zuciyarka, don Allah ka so ni ka ƙauna ce ni idan ba haka ba zuciyata za ta iya buga wa a kowanne lokaci." Haka Raihan ta ci gaba da surutai ita kaɗai ganin damuwa ta yi mata yawa ya sa ta ɗauko wayarta ta shiga dandalin sada zumunta. Washegari da daddare su mommy suna zaune suna hira Daddy ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, Mommy na ganinsa ta miƙe ta tarbe shi tana cewa, "Daddyn yara yau ka daɗe tun magriba nake saka ido." A gajiye ya zauna Raihan ta yi masa barka da zuwa, su Inno ya fara gaisarwa sannan ya ce, "Wallahi a gajiye nake. Ni ba na manta Malam ya ce za mu kai gaisuwar Al'amin gidansu yarinyar da yake nema ba, wallahi sai ɗazu ya kirani to mun yi niyar zuwa da rana sai kawai muka yanke shawarar zuwa da dare. Mun je an saka ranar yaron wata uku, ashe wai ya jima yana jiran yarinyar sai da ta kammala karatu." Tun da Daddy ya fara maganar Mommy take kallon Raihan ƙasa-ƙada gabanta na faɗuwa, don tun Raihan na ɓoye soyayyar Al'amin har sai da watarana ta sanar wa Mommy, sai dai tun a lokacin mommy ta yi mata nasiha akan ta cire soyayyar Al'amin daga zuciyarta. Mommy na shirin yin magana sai ji suka yi Raihan ta fashe da kuka, ta tashi da gudu ta wuce ɗakinta. Mamaki ne ya kama Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Lafiyar Yarinyar nan ko ciwonta ne ya dawo?" Mommy jiki a sanyaye cike da tausayin Raihan ta ce, "Babu ko ɗaya Daddyn Raihan, wallahi ba tun yanzu ba yarinyar nan ta ƙwallafa ranta akan wannan Al'amin ɗin, ko kwanaki dai da ta yi min maganarsa na ce mata ta fita daga harkarsa amma ta ƙi. An taɓa soyayya dole ne tun da shi bai taɓa nuna yana sonta ba..." Katse ta Daddy ya yi ta hanyar ɗaga hannunsa sama ya ce, "Dakata Zainab! Yaushe aka yi haka ban sani ba? Me ya sa baki gaya min ba tuntuni na yi wa Malam magana?" Ganin Daddy na son rufeta da faɗan da bata da laifi a ciki ya sa ta ce, "Idan ka gaya wa Malam, shi zai aureta ya zauna da ita? Daddyn Raihan kai fa namiji ne ka san yadda halin maza yake mace tana son su ma ya aka cika balle ita ta tsaga billenta ta nuna tana son shi. "Shiru Daddy ya yi ba tare da ya furta komai ba, ya miƙe ya nufi ɗakin Raihan da yake jiyo shasshekar kukanta tun daga waje. Yana shiga ya tsaya daga jikin gadon Raihan ya furta, "Raihan!" Shiru ta yi ta ɗago tana goge ƙwallar idonta, sake ambatar sunanta ya yi sannan ya ci gaba da cewa, "Tun yaushe kike ƙaunar yaron nan baki gaya min ba." Hawaye na zuba Raihan ta ce, "An daɗe amma mommy ce ta hana ni." Daddy ya jinjina kai sannan ya ce, "Kin Makara Raihan saboda Mahaifin yaron nan ya ɗauke tamkar ɗan uwansa yanzu me kike so naje na gaya masa, tun farko da kin gaya min zan iya gaya wa Malam idan ya so sai a gaya wa yaron inkun daidaita shi kenan. Amma gaskiya a yanzu ina jiye miki wulaƙancin namiji saboda yana da wacce yake so, hasalima ya shafe shekara huɗu yana jiranta yanzu kina ganin za ki shiga zuciyarsa kamar waccen ne? Ki yi ta addu'a Raihan har Allah ya canza miki da wanda ya fi shi, a kullin zaɓin Allah shi ne zaɓi." Daddy ya jima yana yi wa Raihan nasiha sannan ya fito daga ɗakin, ai kuwa yana fita ta sake rushe wa da matsanancin kuka don har ji take zuciyarta na wani irin raɗaɗi kamar za ta hudo ƙirjinta. Tun bayan faruwar wannan al'amarin Raihan ta yankar wa kanta tikitin zaman ɗaki bata da aiki sai na kuka da tunani, tun Mommy na fushi da ita har ta watsar ta fara rarrashinta amma duk a banza don ko abincin kirki Raihan bata ci. Lokaci ɗaya ta zabge ta rame ta yi baƙi idan ka ganta sai ka rantse ta jima tana jinya, Kabiru tun yana saka idon ganinta har ya daina. Kuma a wannan lokacin bikin Al'amin bai fi saura wata ɗaya ba, har lokacih Daddy ya gagara sanar wa Malam halin da ake ciki, dom gani yake kamar ya so kansa da yawa. Wannan lamarin ba ƙaramin damunsa ya yi ba har sai da ya gagara wataran ya tambayi Daddy ita, Daddy shi kansa abin na Raihan ya fara ɗaga masa hankali don ko kaɗan baya ƙaunar wani abu da zai iya salwantar masa da rayuwarta. Sai dai Daddy yana jin daɗin irin kulawar da Kabiru yake bawa Raihan don haka ya ƙara shiga ransa, bayan ya bawa Kabiru amsa yana shirin tafiya Daddy ya kira shi da wata irin mura sannan Kabiru ya dawo. Cikin girmamawa ya russana Daddy ya ce, "Kabiru wani hukunci na yanke amma ban sani ba ko zai yi maka daɗi, amma na ce sai na fara jin ta bakinka duk da harkar ƙaruwa ce... Eheeeem 🌚 na ce ba! To wai meye harsashenku? Barkanmu da juma'a bayin Allah🌚 Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 42 Cike da ladabi Kabiru ya jinjina kai yana cewa, "Babu komai Daddy na amince duk da ban san akan abin da ka yanke shawara ba, amma ina fatan ya zame min alheri domin na san ba za ka yi min zaɓen tumun dare ba." Murmushi Daddy ya yi saboda nutsuwa da ɗabi'un Kabiru na matuƙar birge shi, dafa kafaɗar Kabiru ya yi sannan ya ce, "Allah ya yi maka albarka na gode da wannan karramawa da ka yi min. Da ma ba wani abu ba ne na yake shawarar canza maka wurin aikine, ina son na kai ka kamfanina ku riƙa aiki da sauran yarana saboda na yaba da ƙwazo, hankali da riƙon amanarka. Tun da nake babu mai gadin da ya jima yana yi min aiki kamar kai, Kabiru jin ka nake tamkar ɗan cikina saboda irin girmamawar da kake yi mini da girman da kake ba ni. Idan baka manta ba na sha gwada ka na zubar da kuɗi a harabar wurin nan don na ga yadda za ka yi da su, amma sai ka yi sallama da ni ka dawo min da abina. Allah ya yi maka albarka Kabiru ya jiƙan mahaifa." Kabiru ba ƙaramin daɗi ya ji ba har ƙasa ya tsugunna ya fara yi wa Daddy godiya, ɗago shi Daddy ya yi ya ce, "Na hana idan na yi maka wani abu ka fara yi min godiya. Sannan wani hanzari ba gudu ba, na ce mai zai hana ka dawo da ƙaninka autanku ya maye gurbin aikinka idan ya so su Inno wuro sai a gyara musu ɓangaren da yake kallon na su Inno su zauna." Kabiru na jin haka ya fashe da kuka tare da ruƙo hannun Daddy yana cewa, "Ba ni da bakin gode maka Daddy domin ka yi min komai,har na rasa mai zan ce maka Allah ya saka da alheri ya ja ran tsohuwa ya jiƙan mahaifi, Ubangiji ya biya maka buƙatunka na alheri duniya da lahira." Daddy ya yi murmushi ya amsa da "Amin." Motarsa ya buɗe ya shiga Kabiru ya buɗe gate sannan Daddy ya fice daga gidan, Kabiru cike da murna ya faɗa ɗakinsa ya ciro wayarsa ya kira Inna wuro ya sanar mata. Ita kanta ba ƙaramin farinciki ta yi ba, Kabiru saboda farinciki haka ya fara kai kawo a ɗaki. Raihan ita ta faɗo masa a rai yake jin ina ma tana cikin ƙoshin lafiya, da bayan Inna wuro ita ce mace ta farko da zai fara sanarwa. Sai kuma ya sauya fuska cikin damuwa domin ya san ba ƙaramin ciwo ne zai sa Raihan ta daina fitowa wurinsa ba, hasalima ya kira wayarta ya fi a irga amma koyaushe zai jita a kashe. Maryama ya kira ya sanar mata hukuncin da Daddy yanke da kuma ci gaban da suka samu, ita ma ba ƙaramin daɗi ta ji amma amma a yadda ya ayyana su Inna wuro ba za su dawo ba har sai Allah ya sauki Maryama lafiya saboda cikinta ya kai kusan wata bakwai. Yana son ya yi sallama da Mommy don ya duba jikin Raihan kuma ya yi mata godiya game da abin da Daddy ya yi masa, amma ya rasa yadda zai yi don haka ya yi ta maza ya yi sallama a ƙofar falon lokacin shiru falon da alama ba bu kowa a wurin, a daidai lokacin Raihan ta ɗauko Apple akan Dianning saboda bata iya cin komai, shi ma sha'awarsa ta yi shi ne ta ɗauko za ta wuce ta ji sallamar Kabiru. Tana tafe tana dafa bango saboda jirin da yake ɗibanta ta ƙarasa muryarta can ƙasa ta amsa masa, da ido ya kafe Raihan saboda tsananin mamakin irin lalacewar da Raihan ta yi lokaci ɗaya. A sanyaye Kabiru ya ƙarasa wurinta ya furta, "Me yake damunki haka Raihan? Kin ga yadda kika koma kuwa?" Kamar ya tunzurata ta ji zuciyarta ta sake rauni hawaye ya ciko idonta, a hankali ta jingina da bango jikinta har rawa yake saboda yadda yunwa ta ci ƙarfinta, ga rashin ƙwarin jiki da tsananin ciwon ƙirji da take fama. Lumshe idanu ta yi ta furta, "Ka ta ya ni addu'a Fillo saboda rayuwata na cikin wani yanayi." Hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya sake yi ba, har ji yake ina ma yana da ikon taɓa wani ɓangare na jikinta da ko ba komai ya ruƙo hannunta ya lallasheta domin ya ji ainihin abin da yake damunta. Takawa ya yi zuwa gabanta ya ce, "Gaya min abin da yake da mun ki ko ina da ikon taimaka miki." Girgiza masa kai ta yi hawaye na zuba ta ce, "Za ka iya taimaka min da addu'a fillo domin ita kaɗai ce abin da za ka iya tallafa min da ita." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Zan yi ƙoƙari matuƙa na yi miki addu'a daidai bakin gwargwadona amma a dukkan lamuranki ki riƙa neman zaɓin ubangiji, domin shi ne zai yi miki zaɓin alkairi. " Kuka ne ya ci ƙarfin Raihan ta gyaɗa masa kai ba tare da ta iya furta masa komai ba, da ido ya raka ta yana jin zuciyarsa babu daɗi. Kamar kazar da aka tsamo daga ruwa haka Kabiru ya wuce ɗakinsa ya zaune haɗe da faɗawa duniyar tunani. Daddy yana tafiya hanyar office wayar Malam ta shigo masa, sai da suka gaisa sannan Malam ya ce idan ya samu lokaci yana son ganinsa. Jin haka ya sa Daddy ya fasa zuwa office ɗin ya wuce wurin Malam don jin maganar da yake son yi masa, bayan ya ƙarasa cikin girmama juna suka gaisa sannan Malam ya ce, "Alhaji dama na kira ka ne game da maganar hatsabibin Aljanin nan." Daddy ya tattara hankalinsa wurin Malam yana jinjina kai. Malam ya ci gaba da cewa, "Wannan Aljanin na jima ban haɗu da hatsabibin junnu kamar shi ba, ka san ya ci alwashin gujewa kusanci da mu don buƙatar kansa. To na tura wasu aljanu su kawo min shi amma ya yi musu ƙafar rago ya rufta su ciki, intaƙaice maka dai waɗannan aljanun ya yi garkuwa da su. Domin sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, saboda Huzaifa ya samu ɗaurin matsayi a wurin Kakansa Jabbul-ƙasi don haka sai na tashi sosai na yi shiri kafin na sake tunkararsu. Na san waye Jabbul-ƙasi ina da tarihinsa sama da shekara talatin baya." Zaro ido Daddy ya yi ya ce, "Dama suna garkuwa da junansu?" Malam ya yi murmushi sannan ya ce, "Ai Alhaji duk yadda kasan muna mu'amala suma haka suke gudanar da mu'amala a tsakaninsu, na kira ka ne don na sanar da kai ba don ka tada hankalinka ba sai don a ƙara tsayawa tsayin daka dangane da yarinyar nan Raihan. Saboda suna da matuƙar wayo fiye da tunanin mai tunani, sun san hanyar da za su bi su yaudari mutum." Daddy ya jinjina kai cike da gamsuwa sannan ya ce, "Allah ya ƙara tsare mu bakiɗaya." Magunguna kala-kala Malam ya sake haɗa wa Raihan don wannan karon ya ci alwashin sai ya ga bayan Huzaifa ta kowanne hali. Bayaninsu ya yi wa Daddy da yadda za ta yi amfani da shi, godiya Daddy ya yi wa Malam sannan ya tura masa kuɗi masu yawa suka yi sallama ya koma gida. Yana zuwa gida ya yi wa Mommy bayanin abin da yake faruwa tare da yi mata bayanin yadda Raihan za ta gudanar da magungunan. Cikin damuwa Mommy ta sake yi masa zancen halin da Raihan take ciki, shi kansa yana lura da yanayin yarinya, ji ya yi babu daɗi amma babu wani abu da yake ganin zai iya yi saboda da kunya ya tunkari Malam da wannan maganar. Ɗakin Raihan ya shiga a lokacin tana zaune ta tasa laptop a gabanta tana hawaye, sakamakon kallon hoton Al'amin da ta yi a shafinsa na fuskar littafi, (Facebook). Tana ganin shigowar Daddy da sauri ta rufe laptop ɗin tana goge hawaye. Daddy zama ya yi akan kujera ya kalle ta duk sai ya ji ba daɗi saboda lokaci ɗaya ta rame ta lalace, da wata irin murya ya kira sunanta jiki a sanyaye ta amsa sannan Daddy ya ce, "Raihan yanzu wannan rayuwar kika ɗaukarwa kanki, dubi yadda kika rame kika lalace. Raihan me ya sa kike son saka rayuwarki a cikin wani hali, me ya sa ba za ki miƙa wa Allah lamuranki ba ki cire yaron nan daga zuciyarki? Ki yi addu'a Allah ya kawo miki mafi alheri ina ganin haka ya fi da ki saka wa ranki damuwa har wani ciwo ya kama ki." Raihan ta faɗa jikin Daddy tana fashe wa da kuka, sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta ɗago ta ce, "Daddy wallahi na kasa cire shi a rana amma kullin ƙaunarsa nake ji a zuciyata, don Allah ka yi wani abu Daddy." Raihan ta ƙarasa magana tana haɗe hannuwanta wuri ɗaya alamun roƙo, hawaye bibbiyu yana zuba. Jikinta ya ji zafi zaau da zazzafi tausayinta ba ƙaramin kama shi ya yi ba, hannuwanta biyu ya kama ya ce, "Ki yi Addu'a Raihan domin babu abin da ya fi ƙarfin addu'a, kuma insha Allah zan san yadda za a yi Allah ya shiga lamuranmu." Cikin kuka Raihan ta amsa da Amin. Sai da Daddy ya jima a wurin yana lallashinta sannan ya fice daga ɗakin, yana fita ya sa Mommy ya haɗa mata ruwan tea ta shiga ɗakin da ƙyar ta matsa mata ta iya sha sannan ta sha maganin ta kwanta. Wannan ciwo na Raihan ba ƙaramin damun su Mommy ya yi ba, ba su kaɗai ba hatta su Inno lamarin Raihan damunsu yake don mommy bata sanar da su takamaimai abin da yake damunta ba, don tana gudun mitar su Inno kuma duk wanda suka haɗu da shi ta san sarai sai sun sanar masa da abin da ake ciki ita kuma tana gudun surutun mutane. "Na tara ku ne domin na sanar da ku game da hukuncin da na yanke, sanin kanku ne mun ɗauki dogon hutu mai tsayi saboda halin da ƙungiya take ciki. A bisa shawarar da aka ba mu wancen karon za mu kai wa Jabbul-ƙasi ziyara akan buƙatarmu domin matuƙar mu ka ce za mu ɗore a haka tabbas kwaɓarmu za ta yi ruwa kuma ba za mu kai labari ba. Ni da Hatsabibiya da mijinta, sai zaratan Aljanu goma daga jinsin Bil'adam goma za mu shirya mu tafi, dole mu shirya da shirinmu domin tafiya wurin Jabbul-ƙasi ba wasan yara ba ne. Za mu haɗu da ƙalubale a hanyar tafiya domin duk wannan tsawon lokacin na yi bincike negame da yanayin hanyar tsibirin Jabbul-ƙasi. Kuma na tura Aljani Ɓurƙum domin ya karɓo mana izinin zuwa wurinsa, saboda idan ka cire zuri'arsa wato waɗanda suka fito daga tsatsonsa haramun ne ka kai ziyara wurinsa ba tare da ka nemi izini ba. Wannan magana da nake yi muku ba za mu kai labari duka ba, domin ya faɗa wa Aljani Ɓarƙum cewa gabaɗayanmu mu rai goma ne zai tsira domin sauran duka za su halaka. Abin da bai sanar da mu ba su waye za su mutu su waye za su rayu, amma ni na yanke wani hukunci duk wanda aka kashe za mu ɗora zuri'arsa a gurbinsa." Abar bauta ta ƙarasa maganar cike da ƙarfafa musu ƙwarin gwiwa. Da farko jikkunansu ya yi sanyi da jin bayanin Abar bauta amma da suka ji yadda ta ƙarfafa gwiwarsu sai suka saki jikinsu, amsa mata suka yi cike da ladabi sannan ta ɗora da cewa, "Za mu zaɓi waɗanda za mu yi tafiyar da su sannan za mu bar waɗanda za su yi gadin ƙungiya saboda ba zai yuwu mu bar wurin haka sasakai babu kowa ba, sannan abin da zan ja hankulanku da shi wannan sunan na Abar bauta da kuke kirana da shi dole ku daina daga yanzu domin ya bi bakinku, kuma ya zama wajibi ku daina bauta min domin babban zunubin da zai iya kaimu ga hallaka shi ne a yi min bauta a hanyar mu ta zuwa tsibirin Jabbul-ƙasi. Ba wai sai kaɗai hanya ba Jabbul-ƙasi bai amince da wata bautar ba don haka ko da kuskure kar ku sake ku bauta min idan ba haka ba gabaɗaya mun zama halakakku." Cike da gamsuwa suka amsa sannnan Abar bauta ta ci gaba da yi musu bayanin yadda tafiyar su za ta kasance, ta tabbatar musu da cewar za su yi tafiyar cikin kwana Talatin masu zuwa. Lokacin da Mommy ta ji bayanin Daddy game da Kabiru da ƴan uwansa ta yi farinciki sosai, saboda ita kanta Kabiru na matuƙar birge ta saboda kyawawan ɗabi'unsa. Bayan kwana biyu da faruwar haka Kabiru ya samu Daddy da magana akan yana son sai mai ɗakinsa ta sauka idan ya so sai su dawo gabaɗaya, Daddy ya ji daɗin haka domin shi yake nuna ya san mutumcin mace kuma yana tausayawa matarsa tun da ya yi tunanin haka. Amma sai ya nunawa Daddy ƙaninsa zai zo a cikin satin domin ya kama na shi aikin idan ya so shi kuma ya fara aiki a kamfanin da Daddy ya ce, Daddy da kansa ya bawa Kabiru kuɗi don ya turawa ɗan'uwansa na mota ya taho, cikin jindaɗi Kabiru ya karɓa yana yi wa Daddy godiya. Wata ranar laraba da dare Daddy ya samu Kabiru ya yi masa magana akan ya shirya saboda a washegari zai fara aiki kamar yadda ya gaya masa, ranar Kabiru kusan kwana ya yi bai yi baccin kirki ba saboda murna, gari na waye wa ya shirya yana jiran Daddy bayan wani lokaci ya fito suka tafi. Duk wainar da ake toyawa Raihan bata sani ba sai lokacin da Kabiru ya kusa sati biyu da fara aiki a kamfanin Daddy tukunna, tana daga ɗaki ta ji Daddy na yabon ƙwazo da aikin Kabiru. Raihan ba ƙaramin haushi ta ji ba don gani take a yadda ta ɗauki Kabiru bai kamata ya ɓoye mata wannan ci gaban da ya samu ba, da ta so zuwa ta same shi a ta yi masa tas amma sai wata zuciyar ta hana ta ita ma ta ce ba za ta kula shi da maganar ba. Sannu-sannu ciwo ya fara saka Raihan a gaba tun tana jinyar kanta ita kaɗai har Mommy ta fara fuskantar ciwon Raihan ya fara tsanani. A ranar wata Litinin ne suka wayi gari da tashin hankali sakamakon tashi da suka yi Raihan na wani irin amai mai haɗe da sirkin jini a jiki, kafin suyi wani yunƙuri tuni numfashinta ya ɗauke ta suma a wurin. Hankali a tashe Mommy ta kira Daddy take sanar da shi, da ƙyar ta iya kama Raihan ta saka ta a mota ta wuce da ita asibiti. Tana zuwa asibiti likitoci suka rufu a kanta sai dai har lokacin da Daddy ya ƙarasa ba su shawo kan matsalar ba, sai da suka shafe kusan awa guda da mintuna sannan suka samu damar daidaita numfashinta. Amma lokaci-lokaci wani irin jini na fita daga bakinta, wannan lamarin ba ƙaramin ɗaga hankulansu ya yi ba. Mommy ban da kuka babu abin da take yi, Kaburi yana harabar Asibitin ya haɗa kai da gwiwa ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Bayan Likitoci sun samu komai ya lafa suka samu Daddy Dr Muhammad ya fara yi masa bayani, "Alhaji gaskiya yarinyar nan tana cikin matsananciyar damuwa, wanann damuwar ita ce take barazanar tarwatsa rayuwarta. Kuna ina haka ya faru why? Yarinya ƙarama ta samu irin wannan condition ɗin? Yanzu haka zuciyarta na barazanar fashe wa sai dai wani ikon Allah amma gaskiya akwai gaggarumar matsala." Jiki a sanyaye Daddy ya ce, "Wallahi likita babu abin da yarinyar nan ta nema ta rasa, jarabar soyayyar wani yaro ta ƙwallafawa ranta alhalin shi yaronma bai san tana yi ba." Dr Muhammad ya mayar da glass ɗin idonsa sannan ya ce, "To gaskiya ku tsaya ku duba lamarin nan domin komai zai iya faruwa Allah ya kiyaye." Damuwa goma da ashirin ce ta yi wa su Daddy yawa. Don sai da Raihan ta kwana uku a asibiti ba tare da ta san wanda yake kanta ba, a rana ta huɗu ta fara gane mommy amma bayan ita babu wanda take gane wa kowa sai dai ta bi shi da ido. Ranar da su Inno suka zo duk iya zaman da suka yi bata tanka musu ba, sun yi kuka sosai saboda duk wanda ya ga halin da Raihan take ciki sai ya tausaya mata. A wannan lokacin Daddy ne ya yanke hukuncin sanar wa Malam ainihin abin da yake faruwa don ko kaɗan baya son ya rasa Raihan, lokacin da Malam ya ji wannan batu ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba saboda gani yake ba komai ba ne don Daddy ya yi magana an haɗa Raihan da Al'amin, kuma a wannan lokacin ya tabbatarwa da Daddy Al'amin zai auri Raihan bayan aurensa da sati guda. Wannan magana ba ƙaramim daɗi ta yi wa Daddy ba, sai dai har lokacin ba a sanarwa Al'amin takamaiman abin da yake faruwa ba. Ranar da Raihan ta cika kwana biyar a asibiti Malam ne ya je dubata bayan magariba kamar yadda ya saba. Kabiru na zaune akan kujera ya haɗa mata tea ya bata tana sha, Daddy da Malam ne suka shiga ya dubata. A kunyace Raihan ta amsa sannan Malam ya ce, "Ƴata duk na ji abin da yake faruwa don haka na zo da kaina na yi miki albishir don Allah ki kwantar da hankalinki indai Al'amin ne nan da sati biyu za a ɗaura miki aure da shi. Ni da na san haka ne ai da tuntuni an yi an gama, amma yanzun ma bata ɓaci ba tun da dai saura sati ɗaya bikinsa bayan auransa da sati guda sai a ɗaura naki." Wani irin farinciki ne ya kama ta don duk yanda ta so ɓoye wa sai da ta murmusa, Kabiru miƙe wa ya yi hankali a tashe jiki na rawa saboda ɓacin rai ko gabansa baya gani ya fice daga ɗakin. Daga Daddy har Malam babu wanda ya kawo komai dangane da fitar Kabiru, Daddy ya miƙa wa Malam Hannu suka sake gaisawa yana yi masa godiya. Daga bayan gatangar asibitin Huzaifa da ke laɓe ya furzar da iska mai zafi rai a matuƙar ɓace ya furta, "Tabbas na so ki kuma na ƙaunace ki amma dole zan haƙura da ke, zan yi miki abin da ban taɓa yi ba domin ba zan juri ganin wani ya same ki bayan ni na rasa ki ba." Rufe bakinsa ke da wuya Raihan da ke shan shayi ta ƙware nan take ta fara tari tun suna ganin kamar ƙwarewa ce har ta fara kyalawa wani irin aman jini ta baki da hanci. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 43 Hankali a tashe Daddy ya fita yana ƙwala wa Likitoci kira, Kabiru har ya suka fita ya ji muryar Daddy yana juyawa ya ga Likitoci sun nufi ɗakin Raihan. A guje ya juyawa jiki na rawa don ya ji lokacin da Daddy yake gayawa Dr Bashir halin da Raihan take ciki, yana niyyar shiga ɗakin Dr Muhammad ya dakatar da su shi da Daddy suna nan tsaye Malam ya fito cikin tashin hankali, don tun da yake bai taɓa ganin matsanancin abin da ya faɗar masa da gaba kamar wannan ba. Mommy ce ta ƙaraso fuskarta ɗauke da fara'a da yake a lokacin ta fita raka wata ƙawarta da ta zo dubiya, ganin yanayin da suke ciki ya sa ta sha jinin jikinta don haka jiki a sanyaye ta dubi Daddy ta furta, "Daddyn Raihan lafiya kuwa?" Jinjina kai ya yi ya ce jikin Raihan ne ya tashi." Tun bai rufe baki ba Mommy ta nufi ƙofar za ta shiga Daddy ya sha gabanta da sauri yana cewa, "Ina za ki shiga Zainab? Baki gan mu a waje ba Likitoci ne suke aikinsu don Allah ki bari su gama." Hawaye ne ya taru a idon Mommy ta ce, "Daddyn Raihan ina son ganin halin da take ciki ne." Girgiza mata kai ya yi don ya tabbata da tana nan Raihan ta fara aman jini babu ko tantama ita ma sai an tallafi tata rayuwar, cikin dakiya ya ce mata: "Na ce ba za ki shiga ba, idan ki shiga kina da abin da za ki yi mata ne?" Gefe mommy ta matsa tana hawaye don a wannan lokacin jikinta ya gama sanyi da lamarim ciwon Raihan, sun jima a nan wurin Dr Bashir ya fito fuska babu walwala jiki a sanyaye ya furta, "Alhaji gaskiya yuwar canja wa yarinyar nan asbiti domin lamarin ciwonta yana neman gagararmu, mun yi mata allurar tsayar da aman nan abin ya ci tura babban tashin hankalinmu yanda jini ya ɓalle daga gabanta. Yanzu haka bata cikin hayyacinta so za mu taimaka da Amblance aka kaita babban asibiti, da gudu Daddy ya faɗa ɗakin ba tare da ya tsaya jin ƙarashen zancen Dr ba. Yana zuwa kusan mutuwan tsaye ya yi ganin yadda Raihan take kace-kace cikin jini, jiri ne ya ji ya fara ɗaukansa a hankali ya dafa bango sannan ya riƙo gefen rigar Dr Bashir ya ce, "Dr don Allah kar ku yaudare ni, idan har kun san yarinyar nan ta rasu kada ku ɓoye min domin dukkan mai rai mammaci ne." Dr Bashir ya kalli Daddy ganin yana hawaye ya sake sanyaya gwiwarsa domin shi kansa baida tabbacin Raihan za ta tashi ko ba za ta tashi ba, don kar ya sake karya gwiwar Daddy ya girgiza kai ya ce, "Alhaji idan mutuwa ta yi ba za mu ɓoye muku ba domin ba ma ɓoye wa mutane mutuwar patient ɗin su. Raihan tana da rai sai dai tana cikin wani irin yanayi da take buƙatar agajin gaggawa. Mun yi bakin ƙoƙarinmu amma mun kasa sai dai aka kaita babban asibiti domin suna da manyan injinan da ba mu da su." A gaggauce aka ɗauki Raihan aka saka ta a mota ba tare da ta san waye a kanta ba. A wannan karon Mommy kasa kukan ta yi saboda yadda zuciyarta ta bushe, Malam da Kabiru a mota ɗaya suka tafi Daddy da Mommy a motar asibitin da aka saka raihan. Kai tsaye daga nan asibitin AKTH aka wuce da ita ɓangaren Emergancy, da sauri suka karɓe ta suka shiga bata agajin gaggawa. Allurai suka yi mata suka shiga ƙoƙarin neman jijiya domin saka mata ledar jini saboda na jikinta sai zuba yake, amma suka nemi jijiya sama da ƙasa suka rasa. Likitoci kusan bakwai ne akanta amma tana sharɓe tamkar gawa ko motsi bata yi. Daga mommy har Daddy babu wanda bai fidda rai da Raihan ba, saboda duk wanda ya ganta ba zai ce tana numfashi ba. Malam da Kabiru suna zaune duk sun yi jigum-jigum, kuɗi ya zaro ya miƙa wa Kabiru ya furta, "Siyo min ruwan gora guda biyu." Kabiru ya miƙa masa ya ce, "Yanzu miƙewar da ka ga na yi shi zan siyo ina son na yi wa Raihan tofi, riƙe kuɗinka Malam zan taho maka da shi." Malam ya ce, "Ah haba ina ba za a yi haka ba ni ma tofin nake son yi mata saboda wannan yanayin nata ya ba ni tsoro." Kabiru ya ɗora masa kuɗin akan cinyarsa ya fice, bai jima da fita ba ya dawo da ruwan gora guda huɗu tare da man zaitun ya ɗauki biyu ya miƙa wa Malam biyu. Bakinta ya buɗe ya ɗan kurɓi kaɗan sannan ya fara karanto ayoyon alƙur'ani yana tofawa. Daga ɓangaren Malam ma tofin ya fara yi mata don tun da ya ji an ce jini har ta gabanta yake zuba daga jikinta, Huzaifa ya faɗo masa duk da ya san ciwon zuciya babu abin da baya saka wa amma zuciyarsa ta ƙi aminta da ciwon zuciya ne ya haifarta mata zubar jini ta gabanta. Saboda ya san sheɗanu na iya shiga jikin mara lafiya musamman idan sun shafe shi su ƙara tunzura ciwonsa, idan har abin yanzo da ƙarar kwana sai a rasa. Idan kuma da yuwuwar a tashi sai a sha matuƙar wahala. Duk yadda Likitoci suka kai ga ƙoƙarinsu abin ya ci tura, suna nan kan Raihan Mommy da Daddy na daga gefe suna yi mata tofi cikin ikon Allah aka samu jijiya aka saka mata jini, haka aman da yake fita ta hancinta shi ma ya tsagaita. Malam da kansa ya ƙarasa bakin gadon ya yi bismillah ya fara karanta addu'o'i yana tofa mata, sai da ya jima akanta sannan ya miƙa wa Mommy jarkar hannunsa ya ce ta yi bismillah ta shafa mata a jiki kuma ta samu ko yaya ne ta ɗiga mata a bakinta. Kabiru yana daga gefe bayan ya kammala tofin ya ciro wata ƙaramar kwalbar man zaitun da habbatussauda ya tsiyaya a ciki sannan ya ƙarasa bakin gadon Raihan, ganin haka ya sa likitocin suka fara faɗa don a cewarsu ana ɓata musu aiki tun da sun fara kamo bakin zaren. Kabiru bai bi ta kansu ba sai da ya gama yi mata addu'a sannan shi ma ya miƙa wa Mommy ya ce ta shafa mata a hafin ƙafarta da tafin hannunta sai fuskarta, a zuba ɗan kaɗan a tsiyaya a kunnenta da tsakiyar kanta. Da ƙyar likitoci suka bari Mommy ta shafawa Raihan waɗannan tofin, tana gama shafa mata jikinta ya fara fitar da gumi sai kuma ta fara rawar ɗari kamar mai jin sanyi. A hankali ta buɗe idanunta da suka shanye tana bin mutanen wurin da kallon, A fili su Mommy suka furta Alhamdulillah Kabiru ya ɗaga hannu sama yana gode wa Allah. Da taimakon Allah da taimakon litocin suka samu Raihan ta dawo hayyacinta, nan take suka yi mata allurar bacci Nurses ɗin da suke da duty a lokacin suka zo suka fara gyara wurin. Tun daga ranar wani abu bai sake faruwa da Raihan ba saboda kullin akwai tofin da Malam yake yi mata ana bata, haka shi ma Kabiru duk dare sai ya biyo daga Kamfani ya yi mata tofi da addu'o'i sannan ya wuce gida. Malam da Al'amin kusan kullin sai sun je asibiti duba Raihan saboda har lokacin Malam bai sanar masa da komai ba, haka Mai ɗakin Malam ita ma zuwanta uku daga haka suka yi sabo da Mommy sosai saboda Mahaifiyar Al'amin macece mai kirkin gaske, idan za ta zo har girki take yi wa su Mommy wannan karamcin ya ƙara wa Malam da iyalansa matsayi a wurin su Mommy. Raihan ta warke sosai tana cin abincinta kuma duk wani abu da yake damunta ya yi sauƙi, don haka likitoci suka sallame su. A ranar da aka sallami su Raihan da dare Kabiru bayan ya gabatar da sallar Isha'i yana shirin kwanciya ya ji kamar ana bubbuga ƙofar ɗakinsa, mamaki ne ya kama shi don bai taɓa samun haka daga masu gidan ba saboda ko abu Daddy zai saka shi sai asuba yake yi masa maganar idan ya fito sallar asuba. A hankali ya ƙarasa ya buɗe ƙofar amma babu kowa a wurin, komawa ya yi ya kwanta har bacci ya fara ɗaukansa. Ta jikin windonsa ya ji haushin kare ya ƙi ci ya ƙi cinye wa. Haska fitila ya yi a hankali yana kallon windon daga kwance, guntun tsaki ya yi ya koma ya kwanta yana nan kwance yana saƙa da warwara bacci ya yi awon gaba da shi. Cikin baccinsa yake jiyo kukan mage kamar a saitin kansa, firgigit ya motsa saboda ko kaɗan baya ƙaunar mage. A guje ya ga ta ɗare kan windon ɗakinsa tana zaro masa idanu, baƙa ce wuluk sai hasken idanunta da yake gani. Rigarsa da ya cire ya ɗauka yana korarsa don ya lura Muzuru ne amma ko gezau, kamar almara ya ji ya furta: "Saƙo na kawo maka kafin na cika aiki." Wata farar takarda ce ta faɗo, sai kuma ya nemi magen ya rasa. Wata zuciyar har ta hana shi ɗauka sai kuma ya yi bismillah ya ɗauka ya fara karanta rubutun da aka yi da ajami kamar haka: "Ina ƙara jan kunnenka akan ka fita hanyar Raihan ka ƙi, ka tsaya matsayinka amma sai cusa kanka kake wallahi sai na nuna maka iyakarka, idan har Raihan kake so sai na damalmala rayuwarka ta yadda ko wata macen ka gani ba za ka yi sha'awar kallonta ba balle ka ji ɗigon santa a zuciyarka. Ba dai matarka ciki gare ta ba, wallahi ka saurari saƙona yana tafe nan ba da jimawa ba. Mai HUZAIFA mijin Raihan har abada." Kabiru na gama karanta wa ya fahimci wanda ya aiko da saƙon, ƙirjinsa ne ya buga musamman da ya ji ya ambato Maryama da ke ɗauke da tsohon ciki don yana tsoron kar ya cutar masa da ita, hannunsa har rawa yake ya lalubo wayarsa ya kira lambarta amma yana kira ya ji a kashe take. A hankali ya miƙe ya faɗa banɗaki ya ɗauro alwala ya shiga gabatar da sallah yana kai wa Allah kukansa akan ya shiga tsakaninsu da sharrin Huzaifa da dukkan wani abin ƙi, baccin da bai koma kenan ba a ɓangare ɗaya kuma ya shiga tunanin wanda Raihan take yi wa tsananin soyayyar da har ciwon zuciya yake barzanar kamata. Tausayin kansa ne ya kama shi don ya san zuciyarsa bata yi masa hallaci ba da ta faɗa ƙaunar Raihan, don ya san dama ba tsararsa ba ce domin ya kwana da sanin hanyar jirgi daban da ta mota. Ba shi ya koma bacci ba sai gabanin asuba har so ya yi ya makara, don ma ranar babu aiki kasancewar juma'a ce. Kuma tun daga juma'a Daddy yake bada hutun ƙarshen mako har zuwa ranar Lahadi. A razane Al'amin ya ɗago ya dubi Mahaifinsa baki na rawa ya ce, "Daddy ban fahimci abin da kake nufi ba fa." Malam ya sake ɗaure fuska ya ce, "Abin da ka ji na faɗa da farko shi za ka sake tarayo wa ka saurara, yarinyar nan saboda kai har tana neman salwantar da rayuwarta. Yanzu Aminu aibu ne don an ɗaura maka aure da mata biyu a rana ɗaya, na ga kowacce da halinta za ta zauna kuma kowaccensu tana ƙaunarka. A da na ce sai bayan aurenka da sati guda amma ina ganin babu fa'idar ɗagawa gara a ɗaura rana ɗaya, idan ya so ko bayan sati ɗaya da bikin ne sai ita Raihan ta tare tun nasan ba lalle sun gama shiri ba." Al'amin ya ɓata fuska kamar zai yi kuka murya na rawa ya ce, "Kuma yanzu yaro da ji a riƙa cewa matana biyu, wannan wanne irin abu ne Daddy." Mama na daga gefe ta karɓe zancen da cewar, "Al'amin wanda ya ce ya sonka ya fi wanda baya sonka, menene aibun yarinyar nan ba sai ka gaya wa Sumayya halin da ake ciki ba ka yi mata bayani." Al'amin ya miƙe murya a ciki ya ce, "Shi kenan ba komai." Daɗi ne ya kama su Malam suka shiga saka masa albarka, saboda dama sun san Al'amin ba zai ƙi Aurenta ya bujire musu ba. Yana shiga ɗaki ya fara zarya don bai san ta inda zai fara gaya wa Sumayya ba saboda ya san kishinta, yana cikin wannan tunanin ya ji muryar Daddy yana waya da Mahaifinta. Kamar wanda ruwa ya cinye haka Al'amin ya yi sak jikinsa tamkar an zare masa lasa, kasa motsa wa ya yi yana jin abin kamar a mafarki, a hankali ya ja ƙafarsa ya hau kan katifarsa daga haka bai sake fahimtar abin da Daddy yake faɗa ba ya zurfafa cikin tunani. Mahaifin Sumayya bai ji komai ba hasalima shi da kansa ya ce zai sanar wa da Summaya halin da ake ciki don ta yi wa Al'amin kyakkyawar fahimta. Malam ya ji daɗi ƙwarai da fahimtarsa da Mahaifin Sumayya ya yi, hira suka taɓa dangane da harkar bikin sannan suka yi sallama. Lokacin da Mahaifiyar Sumayya ta samu labarin tsalle ta yi ta dire ta ce sam bata lamun ce ba, sai da Mahaifin Sumayya ya yi mata ba daɗi sannan ta sauko. Ita kuwa Sumayya yana gaya mata ta fashe da kuka haɗe da shiga ɗaki da gudu, tana zuwa wayarta ta ɗauka ta kira lambar Al'amin sai da ta katse tana shirin kira ta ga ya kirata. Cikin kuka ta furta, "Hubby da gaske ne abin da Daddy ya gaya min wai mu biyu za ka aura? Shi kenan ka daina sona ko?" Al'amin shuru ya yi yana jin kukanta har cikin zuciyarsa, tattaro jarumta ya yi ya ce, "Don Allah ki fahimce ni Dear kin san ina ƙaunarki kuma na tabbata za ki yi min adalci, idan kika ce na daina son ki kamar ba ki yi min adalci ba. Ina son ki ina ƙaunar ki kuma ba zan taɓa haɗa ƙaunarki da kowa ba, don Allah ki kwantar da hankalinki kin san komai muƙƙaddari ne daga Ubangiji." Hawaye ta goge sannan ta furta, "Amma me ya sa ba za ta nemi mijinta ba sai mijina, Hubby har yanzu zuciyata rawa take yi akan yarinyar nan gani nake kamar kana ƙaunarta, idan ba haka ba ya za a yi maganar aure lokaci ɗaya ta kankama kai da ita." Al'amin dafe kansa ya yi don duk yadda ya so nusar da Sumayya sam taƙi fahimtarsa idonta ya riga ya rufe, daga ƙarshe ma katse wayar ta yi tana kuka ya yi kiran duniya ta ƙi ɗauka. Sai dai ko kaɗan bai ji haushinta ba saboda ya san zafin kishi irin na Sumayya kuma kowacce macce aka yi wa haka abin da za ta yi kenan, lokaci ɗaya ya ji haushin Raihan ya kama shi don ita yake ganin ta zame masa linzamin da ta ja dokin rayuwarsu faɗa wa cikin matsala tsamo-tsamo. Tarihinsu Al'amin. Usman Ahmad Kafin Hausa shi ne aihinin cikakkan sunan Malam, asalinsa ɗan garin Jigawa ne a wani gari Kafin Hausa. Su biyu ne a wurin iyayensu daga shi sai Yayansa Alhaji Mu'azzam amma akwai tazara mai yawa tsakaninsu ta kusan shekara goma, Mahaifinsa manomi ne don kafin rasuwarsa har sai da aka bashi sarautar sarkin noman yankinsu. Mahaifiyarsu ta rasu tun suna ƙanana daga nan Mahaifinsu ya auri wata mata mai suna Hajjo amma ba yarinya bace, don ko da ya aureta bata haihu da shi ba. Lokacin da Malam ya fara tasowa yaro ne mai ƙwazo da son ilimi ganin haka ya sa Mahifinsu ya yanke shawarar kai shi almajiranci, da yake yayan matarsa a garin Maiduguri yake yana da tsangaya sai Mahaifinsu Malam ya ɗauke shi tare da ɗan'uwansa ya kai su can neman ilimin Muhammadiyya. Yayansa ba a son ransa ya je ba sai don babu yadda zai yi, saɓanin Malam da yake farinciki don kullin burinsa bai wuce ya zama malami kamar limamin garinsu ba. Shi kuma yayansa burinsa ya gaji mahaifinsa ya zama babban manomi, don haka koda aka kaisu Malma ya fi mayar da hankali wurin karatu fiye da ɗan'uwansa. Daga ƙarshe ma sai Yayansa ya riƙa bin kasuwanni yana ƴar buga-bugarsa da haka ya samu ya tsinci abin da ya tsinta saɓanin Malam da ya mayar da hankalinsa kacokan kan harkar neman ilimi. Ba ƙaramar kulawa suke samu ba kasancewar Mahaifinsu na yawan kai musu ziyara akai-akai, kuma duk lokacin da za shi sai ya tafi musu da kayan abinci niƙi-niƙi. A haka suka yi saukar Alƙur'ani suka dawo gida, suna dawo wa yayansa ya faɗa harkar kasuwanci da Noma kamar yadda yake buri. Shi kuma Malam ya sake komawa garin Maiduguri a nan Malaminsu ya saka shi makarantar boko tare da ƴaƴansa sannan ya fara ɗora su akan harkar kasuwancinsa saboda ya fahimci Malam mutum ne Mai amana. Ana cikin haka Malam suka daidaita da Amina Mahaifiyar Al'amin wacce ta kasance cikakkiyar babarbariya. Amina Umar Babagana shi ne ainihin cikakken sunan Mahaifiyar Al'amin, asalinta babarbariya ce ɓangaren uwa da uba duk haifaffin ƴan Maiduguri ne. Ƴar aminin Malamin su Malam ce kusan komai a gidan su Malam take yi, tun suna soyayayarsu a ɓoye har aka fara fahimtarsu. Alokacin da ta kammala firamare (Primary) Malamin Malam ya yi wa iyayensa maganar halin da ake ciki, ba a ɗauki lokaci ba aka saka musu rana lokaci na yi aka ɗaura aure a lokacin tuni Malam ya gama sakandire. Kasuwancin da suke yi Allah ya saka masa albarka don har garuruwa sun fara zuwa suna sarin kaya suna kawo wa Maiduri, kwatsam aka wayi gari da mummunan labarin hatsarin da ya ritsa da Malaminsu. Wannan mutuwa ta ratsa shi bayan kwana arba'in aka yi wa iyalansa rabon gado, akan dole Malam ya koma Kafin hausa tare da iyalinsa da zama. Daga haka ya fara buga-buga yana haɗa wa da aikin noma har ya fara tunanin buɗe ƙaramar tiredar sayar da mayukan habbatussauda da sauran magungunan musulunci, kasancewar yana da ilimi a wannan fannin domin Malaminsa ya koya masa iliminsu tun zamansa a Maiduguri da yake yana da babban shagonsa da yake taimakawa marasa lafiya da masu matsalar aljanu. Da wannan shawarar ya amicewa zuciyarsa har ya yi tunanin buɗe tiredar a jikin shagon Yayansa da ke cikin garin kano, da ƙaramar tireda ya fara sannu a hankali har Allah ya sa masa albarka ya dawo da iyalinsa sakamakon yana zaune a gidan Yayansa. Dawowarsa keda wuya Mahaifinsa Allah ya yi masa rasuwa, wannan rashi ya taɓa su sosai bayan wani lokaci kowanensu ci gaba da neman kuɗinsa, sai dai Malam ya ci gaba da neman kuɗinsa haɗe da neman ilimi sannu a hankali Allah ya riƙa buɗa musu. Al'amin su biyar ne a wurin iyayensu shi ne ɗan su na uku domin sun haifi yara biyu mace da namiji duk sun rasu, daga Al'amin sai ƙannensa mata huɗu, Aisha, Shamsiyya, Hauwa sai Zarah. An yi wa mata aure Aisha da Hauwa aure ya yin da Zarah da Shamsiyya suke karatunsu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Al'amin ya yi karatunsa tun daga na boko har na islama a cikin garin kamo, ya karanci ɓanagaren Islamic a jami'ar Bayero yana da matuƙar ƙoƙari da hazaƙa don haka wasu suke kiransa da Babban ƙwaro. Bayan ya kammala Degree ɗin sa Malam ya tura shi jami'ar Madina ƙaro karatu, bayan ya kammala karatunsa suka riƙe shi saboda yaba wa da ƙwazonsa da ƙoƙarinsa da suka yi. Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yi wa Malam ba amma sam Al'amin bai so haka ba saboda ya fi son zama kusa da iyayensa, sai da ya shafe sama da shekara biyu sannan ya zo ya ga iyayensa Amma kafin zuwansa lokaci-lokaci suna kai masa ziyara. Ya shafe kusan shekara biyar yana koyarwa sannan ya nemi dawowa ƙasarsa don ya ci gaba da tallafawa ƙasarsa, yana dawo wa Jami'ar Bayero suka bashi gurbin zama domin dama ba baƙo ba ne a wurinsu, a lokacin da Raihan ta haɗu da shi bai dawo ƙasa Najeriya da zama ba ya dawo ganin gida ne ya shiga saboda akwai wata takarda za a yi masa signing a jiki. Mu dawo Labari. Shirye-shirye ya kankama daga gidaje uku na ƙaratowar bikin, daga ɓangaren Amarya Sumayya babu wani shiri da take yi hasalima bikin duk ya fice mata daga rai. Fushi ta ɗauka sosai da Al'amin sai da kyar ya lallasheta ta sauko, sanann suka shiga tsara yadda bikin zai kasance. Duk wata lalura ta Raihan sai da Malam ya sanar wa Al'amin don gudun samun matsala, kuma ya tilasta masa zuwa wurin Raihan don ya tambayeta abin da take buƙata game da biki kuma su fahimci juna kafin auren. Wannan karon ta gan shi ba yabo babu fallasa sai dai babu wata doguwar hira da suka yi, bai jima ba ya yi mata sallama ya tafi saboda ya tambayeta abin da take buƙata na biki ta ce masa bata buƙatar komai don babu wani abu da za ta yi. Idanun Kabiri akan Al'amin har ya zo ya tafi, haka kawai ya ji baya ƙaunar Raihan da Al'amin don ya lura babu soyayyarta a tare shi. Haka ya ci gaba da lallashin zuciyarsa amma kullin ji yake kamar sake rura watar ƙaunarta ake a ransa. Ana saura kwana biyar biki Malam ya kammala haɗa lefen Raihan a daren Ranar shi da wasu abokansa da Yayansa suka kai gidansu Raihan. Ranar juma'ar da ta zagayo cikin satin aka ɗaura auren Raihan, Sumayya da Al'amin. Babu wani shiri da Raihan ta yi don ko event ɗaya babu wanda aka kama aka yi biki a ciki, ƴan uwa ne kawai suka taru aka yi yinin biki. Su Inno sai murna suke don har cewa suka yi irin wannan auren zazzafan rabo ne yake sa a yi shi cikin gaggawa, Kabiru yana ji yana gani aka sake ɗaura wa Raihan aure babu yadda ya iya. Da daddare bayan an yi wa Raihan Nasiha Malam da kansa ya zo ya ɗauki Raihan ya wuce ya ɗauki Summaya dama Al'amin tare suka taho, tun a mota Summaya ta zame mayafinta tana watsawa Raihan wulaƙantaccen kallo. Sai da Malam ya biya ya yi musu siyayya irin wacce ake yi wa amare a daren amarcinsu sannan ya kai su gidansu da ke Kuntau. Kowacce ɓangarenta daban don haka kowacce sai da ya kai ta ɓarinta, kafin tafiyarsa sai da ya haɗa su ya yi musu nasiha mai ratsa zuciya sannan ya yi musu sallama ya fita daga gidan. Littafin kuɗi ne 300 idan kina mgn ki min mgn 0706 206 2624 44 Raihan na zaune shiru akan gado a hankali ta zame mayafin kanta tana ƙare wa ɗakin kallo, lokaci ɗaya gidan Huzaifa ya faɗo mata da lokacin da take zaune ya dawo wurinta. Gabanta ne ya faɗi a hankali ta matsa ta jingina da fuskar gado, wayarta ta zaro ta kunna karatun Alƙur'ani kamar yadda Malam ya gaya mata, lumshe ido ta yi tana jin wata nutsuwa na shigarta. Hannuwa biyu ta haɗa ta yi tagumi tana tunanin sabuwar rayuwar da za ta fara, a hankali ta ji an turo ƙofa ƙamshin turarensa ya dokin hancinta. Numfashinta ne ya kusa ɗaukewa gabanta na ci gaba da faɗuwa, ɗago kanta ta yi karaf suka haɗa ido. Ɗauke kanta ta yi ta sunkuyar da kai gefe tare da amsa masa sallamar da ya yi, a gefen gadonta ya ajiye ledojin hannunta sannan ya harɗe hannuwansa a ƙirji ya ce, "Ki fito Falo ina jiranki." Jiki a sanyaye ta amsa masa daga haka ya fice daga ɗakin, yana fita ta miƙe ta gyara tsayuwar mayafinta sannan ta bi bayansa. A falo ta same shi zaune shi da Sumayya akan kujera, kujerar da take kallon tasu ta zaune kanta a ƙasa. Tun da ta shigo Sumayya take bin ta da harara, ganin ta zauna ya sa Sumayya ta sake kwantar da kanta a jikin Al'amin, ta gefen ido take kallon duk abin da yake faruwa don haka ta ji wani abu ya caki gefen zuciyarta. Cikin zuciyarta ta fara ambatar sunan Allah don jin sanyi a zuciyarta, tana cikin wannan yanayin ta riski muryarsa yana faɗin, "Dukkan godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, Alhamdullah muna sake nuna godiyar mu da Allah ya nuna mana wannan rana mai albarka. Dalilin da ya sa na tara ku a nan domin na sanar da ku dukkanku matana ne, babu wacce take zaman wata duk zamana kuke yi, kuma kowacce ɓarinta daban don haka bana buƙatar tashin hankali ko rashin girmama juna, ku haɗa kanku ku zauna lafiya saboda Allah ne ya haɗa mu don haka sai mu haɗu mu gina rayuwarmu bisa tubar addinin musulunci." Yana gama maganar Sumayya ta ɗago ta dubi Raihan sannan ta ja dogon tsaki ta ce, "Ya kamata ka ce dukkanmu matanka ne amma kowacce da matsayinta a zuciyarka, don ka sakan akwai bambamci mai tazara tsakakin matar na gani ina so da matar shige, tun da ko hausawa sun ce matar shige bata dara..." Kallon da Al'amin ya wurga wa Sumayya ne ya katse ragowar maganar bakinta, ganin haka ya sake ƙona mata rai ƙwalla ta ciko idonta cikin kuka ta ce, "Wallahi dama na san kana sonta kawai ka yi haka ne don ka tarwatsa farincikina, tun da haka ne ka je gata nan na bar mata kai." Tana gama maganar ta miƙe cikin kuka ta wuce ɗakinta. Dafe kai Al'amin ya yi rai a ɓace don ko kaɗan ba haka ya so daren amarcinsa da Sumayya ya kasance ba, ajiyar zuciya ya sauke ya dubi Raihan cikin jin haushi ya furta, "Shi kenan hankalinki ya kwanta!" Ɗago wa Raihan ta yi ta kalle shi nan take idonta ya ciko da ƙwalla, Al'amin ya ƙarasa gaban Raihan da ƙarfi ya fisgi hannunta ya wuce ɗakinta yana shiga ya zaunar da ita akan gado fuska a haɗe ya furta, "Ba dai ni kike so ba? To ga ni." Hawayen da Raihan take dannewa ne ya suɓuce mata, ta fara ƙwalla haɗe da shassheƙar kuka. Kaiwa da kawo wa ya fara yi cikin takaici ya kalleta sannan ya ce, "Me kike buƙata yanzu." Shiru Raihan ta yi ba tare da ta furta komai ba sai kuka da take rairawa gwanin ban tausayi, a ɗan tsawace ya furta: "Ba magana nake yi miki ba?" A zabure Raihan ta ce, "Ba na buƙatar komai." Da sauri Al'amin ya nufi ƙofa yana faɗin, "Ban da shiga haƙƙi haka kawai a haɗa ni da mata biyu ina ji ina gani ƙanƙanin yaro da ni." Waɗannan kalamai ba ƙaramin taɓa zuciyar Raihan suka yi ba, wani irin ɗaci ta ji a zuciyarta musamman da ta tuna wurin wata zai tafi, kifa kanta ta yi akan gado ta ci gaba da raira kuka mai ban tausayi. Al'amin na shiga ɗakin Sumayya ya same ta kwance akan fado tana gursheƙen kuka, ta baya ya ɗagota ya zauna akan gadon yana jinginata da jikinsa. Ajiyar zuciya take sauke wa sai kuma ta fara mutsu-mutsu tana son ƙwace jikinta, riƙe ta ya yi gam a jikinsa ya kwantar da kansa jikin wuyanta yana cewa, "Kina son Allah ya ƙona ni ne Sumayya?" Shiru ta yi bata tanka masa ba ya ci gaba da cewa, "Ke da ita duka matana ne don haka babu wacce zan fifita saboda sai Allah ya hukunta ni da yin haka..." Wani abu ne ya soke ta a zuciya ya fisge hannunta ta furta, "Dama na jima zuciyata na gaya min kana ƙaunar yarinyar nan idan ba haka ba babu yadda za a yi ka fara wulaƙanta ni a gabanta." Janyota jikinsa ya sake yi yana murmushi don ya fahimci zallar kishi ne ya lulluɓe idon Sumayya, wannan karon bata yi yunƙurin ƙwace wa ba. A daidai kunnenta ya fara lallashinta da cewar, "My Summee kin san dai ina ƙaunarki don Allah kar kishi ya hana ki yi min adalci, na gaya miki ke kaɗai ce a birnin zuciyata ta yaya wata za ta zo ta samu gurbi a wurinki? Ko kina shakku akan soyayyar da nake yi miki?Yarinyar nan na gaya miki Daddy ne ya tilasta ni aurenta amma babu ko ɗishin ƙaunarta a zuciyata." Al'amin ya jima yana lallashin Sumayya sai da ƙyar ta sauko sannan suka gabatar da sallar nafila, da kansa ya riƙa ciyar da Sumayya sai da suka ci suka ƙat sannan ya riƙe hannunta suka fita ya riƙa nuna mata sauran ɗakunan, tsarin gidan ba ƙaramin birgeta ya yi ba takaicinta ɗaya da ta tuna ba ita kaɗai ba ce a wurin Al'amin. Amma da ta tuna irin kalaman da yake yi mata sai ta ji komai ya ɓace daga ranta, ta ci alwashin sai Raihan ta bar gidan da ƙafarta don ko da wuta take yawo sai ta bar mata Al'amin ɗin ta. Raihan na ɗaki sai da ta ci kukanta ta godewa Allah sannan ta miƙe ta ɗauro alwala ta fara gabatar da sallah tana kai wa Allah kukanta, ta jima akan dadduma don har sai da bacci ya fara awon gaba da ita sannan ta miƙe ta sauya kayan bacci ta hau kan gado. Sai dai a madadin baccin ya ɗauke ta sai tunani ya hana ta, babban abin da ya tsaya mata a rai da take ayyana irin soyayyar da Al'amin yake yi wa Sumayya, bata yi aune ba sai ji ta yi hawaye na zuba. Gefen hannunta ta sa ta goge ta janyo blanket ta rufa sakamakon zazzaɓin da ta fara ji a jikinta, ledar da Al'amin ya ajiye mata ta ƙurawa ido tana ayyana wai yau daren amarcinta ne amma take kwance haka miji yana wurin wata. Mutuwar Salim ce ta dawo mata sabuwa take tuna irin kulawar da yake bata da alƙawarurrukan da ya yi mata har zuwa ranar Dinner su, da irin abubuwan da ya shiga tsakaninta da shi a ranar. Kuka take sosai kamar ranta zai fita, sai da dare ya tsala sannan bacci ya yi awon gaba da ita. Washegari Al'amin shi ya taimakawa Sumayya ta gyara kanta ban da raki babu abin da take yi, duk ta cika ɗakin da ihu don ma Al'amin yana nuna mata ta yi shiru kar maƙota su ji abin da yake faruwa, ita kuwa Sumayya da biyu take ihun don Raihan ta ji ta tabbatar da wani abu ya faru a tsakaninsu. Ya rakata toilet suka gyara jikinsu sannan ya ɗauro alwala yana fito wa ya zura jallabiyarsa ya ɗauko dadduba ya fita, ɗakin Raihan ya wuce ya tura ƙofa har a lokacin bacci take yi. Amma kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci baccin da take yi ba na daɗi ba ne, a takure ya ganta wuri ɗaya ya sa hannu ya fara buga ƙafarta. Buɗe ido ta yi yana ganin haka ya furta, "Ki tashi ki yi sallah." Jiki ba ƙwari Raihan ta miƙe ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah. Tana zaune tana lazumi bacci ya yi awon gaba da ita ba tare da ta sani ba, don bacci ne sosai akanta tun da bata samu yin bacci da wuri ba. Cikin baccinta ta ji ana kiran sunanta, tashi ta yi tana murtsika ido sai a lokacin ta fahimci a wurin da take kwance. Ganinsa ta yi cikin ƙananan kaya ba ƙaramin kyau ya yi mata ba har bata san lokacin da ta shagala da kallonsa ba, iska ta ji ya hura mata a fuska sannan ya ce, "Ki zo ki taimakawa Sumayya ta gyara jikinta daga nan sai ki girka mana breakfast, saboda gari ya waye almost nine thirty yanzu." Raihan ji ta yi kamar an kwaɗa mata guduma akanta don ta fahimci abin da Al'amin yake nufi, haɗiyar yawu mai ɗaci ta yi ta miƙe jiki ba ƙwari ta furta: "Ok bari na yi wanka na zo." Guntun tsaki Al'amin ya yi ya ce, "Na saka ki abu yanzu jira zan yi sa kin yi wanka, jiranki za ta yi tana fama da kanta har sai kin shirya." Ajiye daddumar hannunta ta yi ta wuce sum sum sum ba tare da ta iya furta masa komai ba saboda yadda zuciyarta take zafi. Tana tafe gabanta na faɗuwa har ta tura ƙofar ɗakin sumayya ta shiga, daga falo ta riƙa sallama sai da ta yi kusan sau uku sannan ta ji Sumayya ta amsa ta kuma ce mata ta shiga. Raihan na shiga ƙirjinta ya buga ganin yadda Sumayya ta yi ɗaiɗai daga ita sai ɗaurin ƙirji, ga kayanan kayanta na ciki duk a warwatse a ƙasa. Daga bakin ƙofa Raihan ta tsaya ta ce, "Ina kwana?" Sumayya ta taɓe baki da kamar ba za ta amsa ba sai kuma ta amsa sannan ta ɗora da cewa, "Na tura Hayati don ya kira ki, ki zo ki taya ni gyara jikina saboda da asuba shi ya gyara ni so kuma na ga ya gaji da yawa. Amma na ga ke bazawara ce kin san komai wannan ba baƙonki ba ne, sai kuma na ga kin yi min ƙerere aka." Zuciyar Raihan ce ta fara tafasa wani irin abu ya tokare maƙoshinta, bata furta mata komai ba ta ƙarasa bakin gadon ta ce, "Ai da asubar ma da kin turo shi sai na zo na gyara ki, ai duk yi wa kaine." Sumayya ta fahimci baƙar magana Raihan ta caka mata don haka ta yi murmushi tana faɗin, "Na so tura shi amma yadda ya liƙe min ya sa dole na haƙura saboda kin san irin wannan daren sai ana yi wa Angwaye uzuri." Maganar Sumayya ba ƙaramin ɓata ran Raihan ta yi ba, takaici da baƙin ciki suka lulluɓe zuciyarta. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla da ƙyar ta samu damar mayar da su ba tare da Sumayya ta gani ba. Amma yanayinta kaɗai zai nuna alamar bata ji daɗin maganar ba, miƙa mata hannu Sumayya ta yi ta ce: "Riƙe ni mu shiga toilet ki sirka min ruwa." Babu yanda ta iya don ta ji takun Al'amin ya nufo ɗakin, Raihan na ruƙo sumayya ta zuba wata uwar ƙara tana yarfe hannu. Da sauri Al'amin ya ƙaraso yana cewa, "Baby lafiya? Jikin ne?" Girgiza kai ta fara yi tana cije baki, tsaye ya yi a gabanta ya dubi Raihan yana faɗin: "Kamata ya yi ki yi mata a hankali bata da lafiya fa, bakya ganin yanayinta.." Da ido Raihan ta bishi don ranta ba ƙaramun ɓaci ya yi ba, bayan cin kashi da cin fuskar da aka yi mata amma ya zo ƙoƙarin rufeta da faɗa yake akan abin da bata da hurumi da shi. Sumayya ce ta riƙo hannunsa tana cewa, "Hubby ka ɗaga ni ba zan iya tashi ba." Jiki na rawa Al'amin ya ƙarasa bakin gadon yana shirin ɗaukan Sumayya da gayya ta saki zanin jikinta tana faɗin, "Hubby ba haka ba wallahi ciwo nake ji kamar yadda ka ɗauke ni da Asuba." Jin zuciyar Raihan na neman tarwatse wa ya sa ta fice daga ɗakin idonta na zubda hawaye, tana shiga ɗakinta ta faɗa kan gado haɗe da fashewa da matsanancin kuka. A baya ta ɗauka idan ta samu Al'amin ta gama maraicin soyayyarsa, tana yi masa soyayyar da take jin ba za ta iya sharing ɗinsa da wata ba amma sai ga shi akan idonta yana rungume da wata, ta ɗauka zama da shi a inuwa ɗaya shi ne gushewar baƙincikinta amma alamu sun nuna sabon babi ta buɗe na ƙunci da matsin rayuwa. Kuka take sosai kamar ranta zai fita, sai da ta yi mai isarta ta faɗa toilet ta yi wanka bayan ta shirya ta fita kitchen don girka musu abinci kamar yadda Al'amin ya ce. Tana shiga kitchen ɗinta babu abin da babu don haka kai tsaye ruwan tea ta fara dafa musu ta zuba a flask, sannan ta fere dankali ta soya musu sai kuma ta soya ƙwai daban don ta so soya kayan miya ko miyar jajjage ta yi musu, bayan ta haɗa komai tunani ta fara yi a wurin da za ta ajiye musu abinci. Nata ta haɗa daban sannan ta haɗa musu na su a tire ta saka komai ta ɗauka ta nufi ɗakin Sumayya. Da sallama ta shiga a lokacin tuni Sumayya ta shirya cikin ƙananan kaya riga da wando, kanta a ƙasa ta shiga da shi ta jiye musu sannan ta koma ta ɗauki nata ta wuce Main falonsu ta zauna tana karyawa. Ƙarar turo ƙafa ta ji tana kai idonta ta ga Al'amin ɗauke da tiren ya fito da shi ya kawo falon da take zaune, da ido ta bishi har ya koma ya riƙo hannun Sumayya suka dawo cikin falon. Tana zaune ta ci gaba da cin abincinta kamar ma bata gansu ba haka ta ɗauke kanta sai dai gabaɗaya ta daina jin daɗin abincin, turawa kawai take yi don kar su fahimci halin da take ciki. Akan idonta suka riƙa ciyar da juna cikin shauƙin so da ƙauna, suna gamawa Al'amin ya kwashe kayan ya kai su kitchen. Dawo wa ya yi ya zauna Sumayya ta kwantar da kanta a jikinsa cikin shagwaɓa ta furta, "Darling don Allah ka roƙi alfarmar Aunty Raihan ta taimaka t gyara mana ɗaki wallahi zan ji kunya idan baƙin gidanmu suka zo, ka ga a gabanka Mami ta kira ni wai baƙi za su zo ganin ɗaki." Jim Al'amin ya yi yana ganin kamar saka Raihan gyran ɗakin baccinsu bai dace ba, kamar ta san abin da yake nazari ta tashi zaune tana marairaice murya ta ce, "Wallahi ko yatsana da ƙyar nake iya ɗagawa, ka ga ita ma lokacin da za ka koma ɗakinta duk abin da ya dace na gida ai ni zan yi. Amma ka yi haƙuri idan baka so haka ba." Ta ƙarasa maganar tana kwanciya a jikin kujera. Miƙe wa ya yi cike da jin daɗi don gani yake kamar Sumayya ta sauko don su haɗa kansu da Raihan ne ya nufi ɗakin Raihan yana faɗin, "Menene amfanin zaman tare My baby? Bari na yi mata magana." Tura ƙofar ɗakin ya yi a lokacij Raihan na waya da Inno don ta yi kewarsu, tsaye ya yi yana kallonta babu laifi tana da kyau daidai gwargwado gata da gashi irin na fulani har baya. Yana son mace mai tsayin gashi duk da Raihan ba fara ba ce kuma bata da wani jiki amma bata da muni a fuska, tana gama waya ta juyo tana kallonsa. Ɗauke kai ya yi kamar bai ganta ba sannan ya ce, "Am dama cewa na yi ki ɗan gyarawa Sumayya ɗaki ba za ta iya ba." Ɓata fuska ta yi har bata san lokacin da ra furta, "Gyaran ɗaki?" Gyaɗa mata kai ya yi ya ce, "Eh saboda baƙi za su zo ita kuma kin ga yadda jikin nata yake." Raihan bata tanka masa ba zuciyarta na suya ta wuce ta nufi ɗakin Sumayya don ta manta ko ɗankwalinta bata saka balle hijabi. Daga iya sai doguwar rigar leshi, kayan ba ƙaramin kyau suka yi mata ba. Sumayya na ganin Raihan sai da gabanta ya faɗi, saboda koda ta san Raihan bata fita kyau ba amma babu wanda zai kalli Raihan bai ce ta yi masa kyau ba. Kai tsaye ɗakin ta shiga ta fara kaɗe gadon cikin takaici, kayan Raihan duk a warwatse har da ƙananan kayanta na ciki. Sai da ta kwashe su da cusa mata a drower sannan ta gyara gadon ta mayar da komai yadda yake ta wuce ɗakinta. Hankalin Sumayya bai kwanta ba sai da ta ga Raihan ta shiga ɗaki, amma abin da ya ɓata ranta yadda ta lura da irin satar kallon da Al'amin yake yi wa kan Raihan. Idan ka kalli Sumayya tashin farko za ka fahimci ta fi Raihan kyau sai dai Raihan ta nuna mata dirin jiki da tsayin gashi domin Sumayya fara ce kyakkyawa, ita ma doguwa ce amma tafi faɗi daga sama. Shigar Raihan ɗaki babu wuya suka ji bugun gida, ta window Raihan take kallon hanya Al'amin na buɗe wa ta hango su Mama Hafsa da sauran baƙin da ba su gano ɗaki ba. Mamaki ne ya kama ta ganin yadda Al'amin yake gaida su cikin mutumci fa girmamawa yana sunne kai ƙasa, suna shigo wa da sauri ta ɗane Mama Hafsa tana murna. Ita ma rungumeta ta yi cikin farinciki don ta ji daɗin ganin Ƴar ƴar'uwarta cikin ƙoshin lafiya, sai a lokacin ta baje musu kajin da Al'amin ya kawo mata, kaɗan suka yi suka saka mata sauran a firji. Babu ƙofa ɗaya da Raihan ta buɗe musu da take nuna tana cikin damuwa don haka sai santin ɗakinta suke yi, sai da suka leƙa sashen Sumayya suka gaisa ta amsa musu cikin mutumci sai yabon sauƙin kanta suke Raihan ban da murmushi babu abin da take yi, daga ƙarshe suka koma ɗakin Raihan suka yi mata nasiha mai ratsa jiki, akan ladabi da biyayya sai juriya da haƙuri. Sun yi mata nasiha sosai akan yadda za ta kula da mijinta ta ɓangaren kissa da tarairaya Mama Hafsa na gaya mata har kunya take ji, ba su wani daɗe a gidan ba suka yi mata sallama suka tafi. Lokacin da za su tafi har da ƙwallarta ta raka su bakin gate tana ɗaga musu hannu, ɗakinta ta koma ta ɗauki waya ta kira wayar mommy. Sun jima suna hira da mommy duk a game da baƙi ne da sauran ƴan biki, bayan sun gama ta kira Daddy cikin farinciki ya amsa mata bayan sun gaisa suka taɓa hira sannan suka yi sallama. Sannu a hankali haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Raihan na zaman haƙuri da kai zuciya nesa, kusan kullin sai sun yi waya da Mommy amma bata taɓa gaya mata halin da take ciki ba saboda ta fahimci abin da mommy take guje mata, kuma gani take da kunya ta faɗi irin zaman da take yi. Tsakaninta da Al'amin daga gaisuwa sai saka aiki bayan wannan babu wata hira da take shiga tsakaninsu, tana ji tana gani suke shan soyayya tsakaninsa da Sumayya har sai da ta ji ina ma ita ce yake riritawa haka. Idan ta ga abin zai ɓata mata rai sai dai ta koma ɗakinta ta ɗauki waya ta shiga Whatsappa, mostly ta fi sha'awar karanta littafan Ameera Adam don ba ƙaramin birgeta suke yi ba musamman na barkwanci don ko ranta a ɓace yake sai zuciyarta ta yi wasai, wani lokacin idan tana karantawa tana dariya har falo Sumayya take jiyo dariyarta, wannan lamarin ba ƙaramin tunzura zuciyarta yake yi ba. Hakan ne ya sa wataran ta tura ƙofar ɗakin Raihan ta gaggasa mata magana, uffan Raihan bata gaya mata ba sai ma ta ci gaba da dariyarta don ta zo wurin da Ɗan tsoho mai buhu ya zuba ihu haɗe da wurgar da buhun hanunsa ya nausa daji, a daidai lokacin da ya ji passingers ɗin motarsu za su kamo shi da ƙarfi su mayar da shi motar da ta gama yin hayaƙi. (LITTAFIN YAWON SALLAR HAJIYA IYA.) Haushi ne ya kama Sumayya ta fice daga ɗakin, Al'amin kuwa na dawowa ta shirya masa ƙarya da gaskiya ta gaya masa nan take ya rufe Raihan da faɗa ba tare da ya bi ba'asi ba. A hana ya ƙare kwanakinsa bakwai cif na ɗakin Sumayya a ranar da zai koma ɗakin Raihan Sumayya har da kukanta, har sai da ta saka shi a gaba ya yi mata alƙawari akan babu wani abu da zai shiga tsakaninsa da Raihan. Alƙawari ya ɗaukar mata don shi kansa gani yake babu wani abu da zai nema a wurin Raihan bayan wanda ya samu a wurin Sumayyansa. Tun bayan magriba Raihan take zuba idon ganin Al'amin amma har bayan tara na dare ba ta ji motsinsa ba, akan dole ta haƙura ta yi kwanciyarta. Cikin bacci ta ji shigowarsa amma sai ta yi kamar bata ji shi ba, a gefenta ta ji ya kwanta ya juya bayansa nan take ƙirjinta ya buga ta sake naɗe wa wuri ɗaya. Da shigarsa ko minti goma bai yi ba suka ji bugun ƙofar Sumayya tana bugu tana kuka wai tsoro take ji ta ga gilmawar wani abu ba za ta iya kwana ita kaɗai ba, a zabure Al'amin ya miƙe ya nufi ɗakin nata. Ya duba ko'ina amma babu wani abu da ya gani, don haka ya zauna yana gadin sumyya da niyyar idan ta yi bacci sai ya koma ɗakin Raihan don ya fita haƙƙinta saboda ko da baya santa ya san tana da haƙƙi akansa, ada bai yi niyyar haɗa komai da ita amma da ya tuna Ubangiji da haƙƙoƙinta sai yake ƙoƙarin saukewa. Haka Summaya ta riƙa yi yau ta tsiro wannan gobe ta tsiro wannan har kwana ta taɓa yi a ɗakin Raihan don kar ta bari wani abu ya shiga tsakaninsu. Saboda a yanda ta san Al'amin zai yi wuya ya shafe kwanaki bakwai ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, saboda mutum ne mai taƙatsantsan da rashin son shiga haƙƙin na ƙasa da shi. A haka har su Raihan suka shafe wata guda ba tare da ya wani abu ya shiga tsakaninsu ba, ana cikin haka Sumayya ta fara wani irin laulayi mai saka bacci don a daddafe take iya yin sallar Isha'i. A ranar wata juma'a Al'amin ya yi niyyar sauke nauyin Raihan da ke kansa, siyayya ya yi musu kamar yadda ya saba duk dare kowacce ya miƙa mata. Ganin yanayinsa ba ƙaramin faranta mata rai ya yi ba, alwala ya sata ta ɗauro bayan sun gama cin abinci don yanzu idan yana ɗakinta har yana yadda ta zuba masa abinci ya ci a ɗakin, bayan sun gabatar da sallar Nafila Al'amin ya jima yana yi musu addu'o'i sannan ya shafa. Jikin Raihan ba ƙaramin sanyi ya yi ba gabanta na faɗuwa, hannunta ya kama suka wuce kan gado sannu a hankali ya fara sarrafata cikin ƙarfin hali don ko kaɗan babu ɗigon soyayyar Raihan a zuciyarsa. Sai dai yanayin surarta ba ƙaramin hargitsa tunaninsa ta yi ba har ya gagara bambamce Sumayya da Raihan wacce ta fi wata. Hannunsa ya saka yana yawo da shi cikin jikinta, jikin Raihan ban da rawa babu abin da yake yi ana cikin haka ta ji Al'amin na ƙoƙarin... Allah ya sani ina taya Kabiru kishi ba zan ƙarasawa ba sai Allah ya kaimu😰 Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn +234 706 206 2624. 45 Gabanta ne ya ci gaba da faɗuwa jin Al'amin na ƙoƙarin shigarta, ƙwace kanta ta shiga ƙoƙarin yi don yadda fargaba ta mamaye zuciyarta gani take kamar yadda Huzaifa ya yaudareta da siffar bil'adam haka Al'amin zai yi mata, cikin fitar hayyaci ya sake janyota jikinta a hankali ya furta, "Shiiiii." Shiru Raihan ta yi ta saka hannu tana shafa fuskarsa sannan ta ce, "Don Allah Al'amin kai ne dai?" Idonsa a lumshe ya gyaɗa mata kai Raihan na shirin sake magana suka ji an fara buga ƙofa da ƙarfi, muryar Sumayya ce take ihu haɗe ta ƙwala masa kira tana cewa, "Habibi ka taho maciji da kunama za su kashe ni." Hankali a tashi Al'amin ya miƙe ya janyo jallabiyyarsa ya saka. Raihan na daga kwance ta ɗauko zaninta ta ɗaura sannan ta saka hijabinta. Al'amin na buɗe ƙofa Sumayya ta maƙale shi jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi, ƙofar ɗakinta take nuna masa bakinta na rawa ta ce. "Wallahi suna ciki." Janyeta bayansa ya yi ya mayar da ita wurin ƙofar ɗakin Raihan, a hankali ya fara takawa har ya ƙarasa ƙofar ɗakin yana maimaita addu'a a bakinsa. Yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin ya shiga ga mamakinsa wata irin tafkekiyar kunama ya gani kwance a tsakiyar gadon Sumayya, tun da ya zo duniya ko a labari bai taɓa ji labarin makamanciyar wannan kunamar ba. Haka kawai ya ji tsigar jikinsa ta tashi yaarrr! Idanu ya lumshe ya buɗe yana sake ƙurawa kunamar ido, motsi ya ji daga gefen madubi yana kai idonsa ya hango wani baƙin maciji jikinsa baƙi siɗik har sheƙi yake. Tsalle macijin ya yi ya haye kusa da kunawar yana zagayeta tuni ta maƙale jikinsa tana wani irin zagaye a doron bayansa, tsoro ne ya fara kama Al'amin don haka ya ci gaba da karanto ayayon kariya yana tunkarar macijin, yana kusantarsu suka fara nufar hanyar windon Sumayya da yake a buɗe. Da sauri suka ɗare suka fice daga ɗakin, Al'amin sai da ya lalleƙe ko ina sannan ya zuge windon ya rufe shi ruf. Ƙofar ya rufe ya zagaya ta bayan gidan don ganin wurin da macijin ya yi amma babu shi babu alamarsa, duk iya dube-dubensa babu abin da ya gani don haka ya janyo ƙofar ya rufeta ruf sannan ya dawo wurin su Raihan, a daidai lokacin Sumayya ta dafe mara tana ihu haɗe da faɗin, "Wash marata Al'amin." Da sauri ya kamata yana faɗin, "Lafiya Sumayya?" Bai rufe baki ba ya ga jini na bin ƙafarta, ƙirjinsa ne ya buga hankali a tashe ya furta, "Me ye wannan sumayya?" Ganin jini ya sake hartsiga Sumayya ta sake ruɗewa, Raihan ya kalla yana faɗin, "Ɗauko mata hijabi mu tafi asibiti." Jiki na rawa Raihan ta koma ɗakinta ta sako doguwar rigar bacci ta saka hijabi ta ɗauko wa Sumayya hijabinta ta fita, a gaggauce Al'amin ya saka mata ya ɗauke ta cak saboda yadda ciwon mara ya murɗeta suka wuce asibiti, asibitin ba shi da nisa da gidansu don haka ba su jima ba suka ƙarasa. Cikin gaggauwa likitoci suka karɓeta suka shiga bata agajin gaggawa, duk yadda suka so ceto abin cikin sumayya sai da ta yi ɓarinsa. Ta sha wahala sosai don kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci ta ji jiki, Raihan ta yi jigum don ita kanta hankalinta ba a kwance yake ba. Kimanin ƙarfe ɗaya na dare aka samu jikin Sumayya ya yi sauki saboda fitar cikin jikinta, allurar bacci suka yi mata sannan Al'amin ta ɗauki Raihan suka wuce gida don ɗauko duk abin da ya kamata su buƙata. Daga Raihan har Al'amin babu wanda ya tankawa ɗan'uwansa sai dai kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci kowannensu yana cikin tashin hankali. A gaggauce suka ɗauki abin da za su ɗauka suka koma asibitin sai dai har lokacin bacci Sumayya take yi, daga Al'amin har Raiban a zaune suka kwana kowane na yin gyangyaɗi. Tun asuba Sumayya ta farka Raihan ce ta taimaka mata ta gyara jikinta, duk kayan jinin da ya ɓaci Raihan ce ta wanke su tas ta gyara wurin sannan ta haɗa wa Sumayya ruwan tea, tun da sumayya ta farka take aika mata da harara tun Raihan bata lura da irin kallon da Sumayya take yi mata ba har ta ankara ta sha jinin jikinta.Tun da suka tashi Raihan take yi mata sannu amma ko sau ɗaya bata amsa mata, ban da yauƙi da shagwaɓa babu abin da take yi wa Al'amin. Kimanin ƙarfe takwas na safe Mahaifiyar Sumayya da ƙannenta suka shiga cikin asibitin, Mami na shiga Sumayya ta fashe da kuka tamkar a lokacin ne ta yi ɓarin cikin.A wulaƙance suka riƙa kallon Raihan suna yamutsa fuska, Al'amin na gaida su ya fice daga wurin. Cikin girmamawa Raihan ta gaida ita tana yunƙurin tashi Mami ta ce, "Yo dama tun da na ji an ce wai kin ga maciji a ɗakinki ai nasan ture ne aka yi miki, ana baƙinciki kin samu ciki ba gara a ɓarar da shi ba. Ai duk makircin mutum ya ƙare akansa don ba a taɓa canjawa tuwo suna kece dai Uwargida wacce kike zaune ɗaram a zuciyar Al'amin amma su shigege sai dai a yi ta cusa kai babu kwarjini to laƙadija'akum tsakaninta da ke, dama ba ance aljani ya aureta har ya taɓa tserewa da ita ba, ni babban tashin hankalina ma kar haukan jikinta ya tashi watarana ta shaƙe min ke a gida ta kashe ki, ta cuce ni tun da ba a shari'a da mahaukaci." Ƙwalla Raihan ta ji na niyyar zubo mata a hankali ta nufi ƙofa ta fice don idan ta ci gaba da jin kalamanta za ta iya gaya mata mara daɗi. Tana fita ta kira Mommy ta sanar da ita abin da ya faru da Sumayya daga ƙarshe Mommy ta ce tana nan tafe da yamma, suna gama waya Ammi da ƙannen Al'amin suka ƙaraso cikin asibitin. Da gimamawa Raihan ta gaida Mami suma ƙannen Al'amin suka gaishe ta ba yabo babu fallasa, sannan suka wuce cikin ɗakin da Raihan take, da yake Malam baya gari sai a waya ya duba Sumayya. Bayan fitar Raihan daga ɗakin Mami ce ta yi ƙasa da murya ta ce, "Wallahi sai mun yi da gaske akan yarinyar nan idan ba haka ba na lura haramta miki zaman cikin gidan za ta yi, a yau ba sai gobe ba zan tafi na amso miki alƙwarin da muka yi da ke. Da zazzaɓi nake fama da shi amma ko ma meye dole na shirya na je don wallahi yarinyar nan dole ta bar miki gidan nan." Daɗi ne ya kama Sumayya ta sake rungume Mami tana faɗin, "Shi ya sa nake ji da ke Mommcy." Shigar su Ammi ya daidaita nutsuwar Sumayya ta sake narkewa tamkar wani azababben ciwo na damunta. Ammi na zama bayan sun gaisa ta fara tambayar Sumayya yadda lamarin ya kasance, Sumayya ta sauya fuska cikin damuwa tana cewa, "Wallahi mommy ina cikin bacci na ji kamar an kira sunana, ina tashi na ga babu kowa sai na koma na kwanta. Ban yi aune ba sai ji na yi abu mai ƙayoyi yana bin jikinta, ina buɗe ido na ga wata irin murtukekiyar kunawa ga maciji a gefen cikina a kwance shi ne na tafi ina ƙwalawa Al'amin kira. Daga haka kawai jini ya ɓalle min, wallahi ni dai Ammi na san lafiyata ƙalau ko ciwon kai ba na yi sai da abin nan ya faru gashi yanzu Likitoci sun ce cikin ya zube." Sumayya ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, lallashinta mutanen ɗakin suka riƙa yi sai daga ƙarshe ta yi shiru, su Ammi sun jima a asibitin sannan suka yi wa su Mami sallama suka tafi. Da yammacin Ranar Mommy ta zo hannunta ɗauke da kayan dubiya niƙi-niƙi, da murna Raihan ta tare ta don wannan ne gani na biyu da ta yi wa Mommy bayan aurenta. A lokacin da Mommy ta zo su Mami sun tafi daga Sumayya sai Raihan da Al'amin, sai da ya gaida Mommy sannan ta ce masa Daddy yana bakin gate, a hanzarce Al'amin ya je ya shiga da shi. Daddy bai zauna ba atsaitsaye ya duba Sumayya ya dire mata kuɗi masu yawa sannan ya tafi, Mommy ta lura da irin ramar da Raihan ta yi, ta rame sosai sai dai ta yi haske, amma sai Mommy bata kawo komai ba don a zatonta ita ma ko Raihan ɗin cikine da ita. Ganin yadda zamansu yake ita da kishiyarta sai ta ji daɗi sosai, don ko kaɗan babu wani abu da Sumayya take nunawa Raihan a idon mutane, har a gaban Al'amin ta rage nunawa Raihan komai sai dai ta yi ta kissa da kisisina tana jan hankalinsa ta yadda sai ya yi mata abin da zai baƙanta ran Raihan. Mommy ba ita ta tafi ba sai da dare ya fara yi sannan Daddy ya kirata yana bakin gate don shi ma wata unguwar ya je ya dawo zai ɗauke ta su tafi. Raihan da Al'amin har bakin mota suka rakata suna yi mata ta gaida gida, duk wanda ya ga su Raihan ba zai ɗauka babu wata rashin jituwa a tare da su ba. Kafin su koma ɗaki tuni Sumayya ta kwashe kuɗin da Daddy da Mommy suka ajiye mata ta ɓoye su don a tunaninta Raihan za ta gaya wa Al'amin wanda sam Raihan bata damu da abin da aka bata ba. Sannu a hankali Sumayya ta warware jikinta ya yi sauƙi kafin a sallameta sai da ta samu Likitar ta zana mata irin dokokin da ya kamata ta gayawa mijinta dangane da lalurarta, lokacin da Dr Halima ta ji bayanin Sumayya bata kawo komai ba ta ɗauka tana son a gayawa Al'amin ne don ta samu kulawar da bata samu, don ko kaɗan bata kawo Raihan kishiyarta ba ce saboda irin kulawar da Raihan take yi da ita. Sai da suka gama komai Dr Halima ta kira Al'amin office ɗinta sannan ta ce, "Malam Aminu yau dai mun sallami Sumayya saboda jiki ya yi kyau, amma fa ba yana nufin shi kenan ta ci gaba da aikin gida ba. Ya kamata ta haƙura da mai gida na tsawon wata guda nan gaba, sannan idan da hali a bari sai bayan wata shida ta sake samun wani cikin saboda mahaifarta ta yi ƙwari. Sannan ta daina aikin wahala da duk wani abu da aka san zai jigatata..." Dr Halima ta jima ta gayawa Al'amin hanyoyin da ya kamata su bi don kaucewa sake samuwar wannan matsalar saboda su a ɓangaren asibiti ba su yadda da asiri ko turen iska. Tun da aka sallami Sumayya Al'amin ya koma ɗakinta da kwana, Raihan ce take komai a gidan ta girka musu abinci ta kai musu wani lokacin ma sai su kusan azahar bata ji motsinsu ba. Ga cin fuska kala-kala da take gani idan ta je kai musu abinci, wannan lamari ba ƙaramin sakata a damuwa ya yi ba ita da Al'amin sai kallo daga nesa, don haka ta ci alwashin samunsa su yi magana don ta gaji da irin zaman gadin da take yi, a ɓangare ɗaya ga wata irin kyara da ta lura yana yi mata abu kaɗan idan ta yi sai faɗa. A ranar wata Juma'a da safe yana shirin fita tana zaune a falo tana jiransa ta ji ƙamshin turarensa ya doki hancinta, muryar Sumayya ta ji cikin shagwaɓa tana faɗin, "Allah sai ka goya ni ka kaini gate haka kawai ka gama gajiyar da ni kuma ban fanshe gajiyata ba."Ji ta yi an buɗe ƙofar tana kallon wurin ta hango Al'amin rungume da Sumayya, ajiyar zuciya ta sauke ta kawar da idonta haɗe da miƙe wa tsaye. Sai da ta gaishe shi ya amsa sama-sama sannan ta ce, "Dama magana nake son yi da kai." Haɗe fuska ya yi ya ce, "Sai da kika ga na shirya za ki ɓata min lokaci." Sumayya ta sake maƙale shi tana zira ƙafafuwanta don ta sauka ta ce, "Haba Hubby ka saurareta mana." Al'amin ya dubi Raihan ya ce, "Ina jin ki." Jiki a sanyaye Raihan ta ce, "Mu je ɗaki." Dariyar ƙeta ce ta ƙwace wa Sumayya sai ta maze ta ce, "Hubby bari na shiga ciki don gyaran ɗaki zan yi." Tsaki Al'amin ya yi ya wuce ɗakin Raihan, Sumayya na ganin haka ta faɗa ɗaki tana tsallen murna da sauri ta ɗauki waya ta kira Mami, tana jin ta ɗauka ta yi ƙasa da murya ta ce: "Mami buƙata ta biya lamari na ta ɗaukan zafi fa." Amsa mata Mami ta yi cikin farinciki sannan Sumayya ta ci gaba da yi mata bayanin irin zama da Raihan take yi da Al'amin, cikin jindaɗi Mami ta sake ɗora Sumayya akan miyagun shawarwarinta. Al'amin na shiga ya dubi Raihan cikin kallon tsana ya furta, "Sauri nake ina jin ki." Ƙwalla ce ta ciko idon Raihan murya na rawa ta ce, "Yau kimanin kusan wata biyu da wani abu kenan da aurenmu amma..." Da sauri Al'amin ya katse ta da cewar, "Dakata don Allah, wai ni da bakina na je gidanku na ce ina sonki ne? Na san maganar da kike shirin yi wato can mazajen da kika aure sun koya miki jaraba da rashin haƙuri har ta kai saboda ina bawa matata kulawa kina baƙinciki ko? Don Allah matsa karki ɓata min lokaci." Fuuuu Al'amin ya saka kai ya fice ya bar Raihan sake da baki, don bata yi tsamanin lamarin Al'amin haka yake ba. Durƙushewa ta yi a wurin tana wani irin kuka mai ban tausayi, ta jima tana abinta sannan ta koma kan gado ta yi kwanciyarta don zuciyarta wani irin turiri take yi mata. Tana cikin wannan yanayin ta ji wayarta na ringing lambar Mama Hafsa ta gani, sai da ta goge hawayenta ta ɗauka amma kalma ɗaya za ta furta ka fahimci yanayin da take ciki ba mai daɗi bane. Sai da suka gama gaisawa Mama hafsa ta tambayeta abin da yake damunta don ta fahimci muryarta, Raihan dama zuciyarta cunkushe take da baƙinciki don haka tana jin tambayar Mama Hafsa ta fashe da kuka, lallashinta Mama Hafsa ta yi sannan Raihan ta sanar da ita gutsire daga cikin irin zaman da suke yi, duk da Raihan bata sanar da ita babu wani abu da ya taɓa shiga tsakaminta da Al'amin ba ta fahimci duk maganganun Raihan, don haka ta ce mata za ta ƙaraso gidan. Raihan ta ji daɗi sosai ko ba komai ta san Mama Hafsa za ta zo ta tausheta ko zuciyarta za ta yi sanyi. Kamar yadda Mama Hafsa ta faɗa ko awa ɗaya da rabi bata yi ba ta ƙaraso gidan, a lokacin Sumayya na zaune a falo. Cikin mutumci suka gaisa da ita sannan ta wuce ɓangaren Raihan. Haka kawai Sumayya ta ji zuciyarta bata yarda da zuwan Mama Hafsa ba don ta yi zargin Raihan ce ta yi mata waya ta gaya mata wata maganar. Tana shiga ta samu Raihan zaune akan gado ta zabga uban tagumi, murmush Raihan ta yi mata sannan ta ɗebo kayan marmari da ruwan sha ta ajiye mata, ruwa kawai Mama Hafsa ta sha sannan ta dubi Raihan ya furta, "Kin ba ni mamaki Raihan." Gaban Raihan ne ya faɗi don haka ta fara ayyana wataƙila wani faɗan za ta yi mata haka ne ya sa koda wasa bata taɓa gayawa kowa halin da take ciki ba, tana cikin nazari ta riski muryar Mama Hafsa na ci gaba da cewa, "Yanzu kamar ba wayayya wacce take da ilimi ba za ki zauna kina shaƙar takaici da baƙinciki? yaron nan fa mijinki ne kamar yadda take a wurinsa kema haka. Ki riƙe tsafta kwalliya da dressing kala-kala, kuma ki daina cusa kanki wurinsa don wani lokacin namiji da gayya yake wulaƙanta mace musamman idan ya ga ta mutu akansa, duk abin da ya saki ki yi masa biyayya matuƙar ba saɓon Allah ba ne, komai ya yi zafi maganinsa Allah ki riƙe sallar dare kina kaiwa Allah kukanki, sannan ki dage da Azkar babu wanda zai ga kukanki da ikon Allah, kuma karki mayar da kanki sakarai kishiyarki ta rainaki ki ja ajinki da matsayinki." Jinjina kai Raihan ta yi a hankali ta furta, "Na gode Aunty insha Allah zan rinƙa yi." Mama Hafsa ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta ta ce, "Dole ki cire kunya ki ƙwaci kanki don kunyar mara kunya asara ce, ni yanzu zan wuce don wallahi ban yi niyyar zuwa gidanki yanzu ba, kar na zama uwar banza niyyata sai baɗi idan Allah ya sauke ki lafiya." Kunya ce ta kama Raihan har da rufe fuska sannan suka fito ta raka Mama Hafsa, a lokacin da suka fita Sumayya bata falon don haka Mama Hafsa ta wuce. Tun bayan auren Raihan sai gidan ya yi wa Kabiru wani iri, duk da gabannin bikinta ba wani yawan hira suke ba amma kaɗaicinta bai dame shi kamar bata gidan ba. Ranar da aka kaita gidan mijinta kusan kwana ya yi yana juyi don tuni zuciyarsa ta riƙa yi masa tunane-tunane kala-kala, so da ƙaunar Raihan suka ci gaba da nuƙurƙusarsa a haka har gari ya waye. Haka ya ci gaba da danne soyayyarta kullin sai ya yi addu'ar Allah ya yaye masa sonta don ya gama tabbatar da cewar ya rasa Raihan har abada, tun da ga shi ta shafe wasu kwanaki a gidan mijinta lami lafiya. Lokaci-lokaci tana kiransa su yi waya har ta tambayi jikin Maryama don ta san tana ɗauke da juna biyu, ko a waya idan ta kira shi ta rinƙa yi masa tsiyar tun da ta yi aure bai zo gidanta ba. Kabiru sai dai ya yi murmushi ya ce mata zai zo amma gani yake ba zai taɓa iya zuwa gidanta ba, har ya ganta da wani namijin a matsayin mijinta, saboda shi kaɗai ya san irin kishin Raihan da yake ɗawainiya da shi a birnin zuciyarsa. Watanta biyu da aure wata ranar Asabar su Inno wuro suka kira Kabiru hankali a tashe Maryama na naƙuda amma ta shafe wuni guda idan haihuwa ta zo gadan-gadan sai ta koma, hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya yi ba don haka nan take ya turawa Baffansa kuɗi ya ce su tafi babban asibitin garinsu kafin ya ƙaraso. A lokacin ya kira Daddy ya sanar masa da halin da ake ciki, kasancewar wata ya yi nisa ba a yi albashi ba Daddy ya ɗebi kuɗi masu yawa ya bashi, ya ja kunnensa akan su tabbata sun kai Maryama asibiti. Bayan wasu mintuna Inno wuro ta kira shi take sanar masa sun je asibiti amma an tabbbatar musu da CS za a yi mata saboda ta gama galabaita ba za ta iya yunƙurin haihuwa da kanta ba. Tun Inna wuro bata gama maganar bata Kabiru ya amsa mata, don ya fi son Maryama ta rabu da cikin jikinta lafiya saboda a ƴan kwananin nan kullin sai ya yi mummunan mafarkinta. Lokacin da Kabiri ya isa garin an yi wa Maryama aiki lafiya, Inno wuro ta dubi Kabiru a lokacin likitoco sun tafi da Jaririn Maryama don duba lafiyarsa ta ce, "Kabiri hai sai dai mu yi haƙuri da abin da Allah ya ba mu..." Zaro ido Kabiru ya yi ya ce, "Inno ba dai Jaririn ya mutu ba?" Jiki a sanyaye Inno wuro ta ce, "Yana da Rai sai dai ba daidai yake ba." Kabiru na shirin magana wata Nurse ta shigo da Jaririn naɗe cikin showel, Inno ta miƙa wa sannan ta fice daga ɗakin. Kabiru ne ya miƙa hannu ya karɓi jaririn sai dai nauyisa tamkar ƴaƴa biyu aka haɗa a wuri ɗaya, yana ido biyu da jaririn zumbur! Ya miƙe sakamakon tozali da ya yi da jaririn mai ɗauke da wata irin hallita. Kan jaririn ya kusa na jarirai huɗu ga idanunsa a warƙale, hannuwansa da ƙafafuwansa duk a juye. Jikinsa ne ya fara wata irin karkarwa, kansa ya sara masa wata irin juwa za ta ɗebe shi. Nan take fasalin Kabiru ya sauya muryarsa ta canja daga fasalin harshen fulani zuwa ta tsurar bahaushe. Dangwarar da jaririn ya yi akan gado cikin wata irin murya ya furta, "Tabbas Abokantaka ita ma Ƴan uwantaka ce, wannan ba jaririn Aminina ba ne an taɓa masa shi. Haƙiƙa Jikan Jabbul-ƙasi ka taɓo wa kanka tsuliyar dodo domin a wannan karon na rantse da zatin Ubangiji ba za ka sha daga hannuna ba. A baya ma saboda ba hurumin abokina ka shiga ba da na nuna maka iyakarka, kuma na yi nisan zango sai daga baya na samu labari amma a wannan karon zan nuna maka ina girmama aminantaka." Hankalin Inno Wuro ba ƙaramin tashi ya yi ba muryarta na rawa ta furta, "Ibrahim ka dubi girman Allah ka yi haƙuri wannan Ɗa da kake gani haka Allah yake son ganinsa." Kallon Inno Wuro ya yi sannan ya kai hannu ya cakumi wuyan jaririn ya furta, "Wannan ba jinin Abokina Kabiru ba ne wannan wani bawan Aljanin Jabbul-ƙasi ne kuma a yau ba sai gobe zai tabbatar da ni ba kanwar lasa bane." Eheeem 🤭 Nace ba. Kun tuna wanda ya taɓa tare Kabiru lokacin da aka tsorata shi zai bar aikin gidansu Raihan, idan baku manta ba a take ya yi masa nasiha kuma ya ɓace.🌚 Wanene Ibrahim ya aka yi Inno wuro ta san da zamansa? Shin ya za ta kaya tsakanin Ibrahim da Huzaifa? Ina labarin gidansu Raihan za ta ƙwato mijinta ko yaya?🫣 Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 46 Tun bayan tafiyar Mama Hafsa Raihan take saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa lamarin dangane da shawarwarin da ta bata, gani take kamar ba za ta iya wasu abubuwan ba don sai ta ga kamar kunyar Al'amin za ta ji. Amma da wata zuciyar ta sake tuno mata da irin shawarwarin da Mama Hafsa ta bata sai ta ayyana za ta fara gwada wasu ko babu komai ta fahimci yanayin yadda zai karɓi abin. Sai da yamma ta ƙarato ta fesa wanka ta ɗauko wani ƙananan kaya riga da wando, farar riga ce kar da jan wando sai kuma wata jar hula da ta saka mai baƙaƙen duwatsu. Har ta saka ta sai kuma ta cire ta dubo wani ƙaramin jan mayafinta saboda tunowa ta yi da yadda gashinta yake ɗauke masa hankali. Ɗaura shi ta yi ta bazo gashin ta baya sannan ta fara gwada irin tafiyar da za ta yi idan Al'amin ya dawo. Tuwon shinkafa miyar agushi ta dafa musu sai lemon abarba da ta yi mai daɗi ta saka shi a firji, tun da ta shirya bata fita waje ba don ta ci alwashin Al'amin ne zai fara ganin wankan da ta yi ba Sumayya ba, saboda ta fahimci wani abun tana kwakwaiyarta. Tana zaune a ɗaki ta ji muryar Al'amin da alama dawowarsa kenan, don haka ta tura ƙofar a hankali wani irin ƙamshinta ya doki hancinsa, a hankali ya ɗago yana kallon wurinta ta yi kamar bata gan shi ba saɓanin lokacin baya da idan ta gan shi jikinta na rawa take zuwa tana yi masa sannu da zuwa. Kai tsaye firji ta wuce ta ɗauko lemon da ta yi sai da ta zo gabansa ta tsiyaya ta miƙa masa sannan ta furta, "Barka da dawowa." Tun da ta shiga falon yake bin ta kallo don haka bai san lokacin da ta yi masa barka da zuwa ba sai da ta sake maimaitawa, a kunyace Al'amin ya sosa kai haɗe da faɗin, "Yauwa barka." Kan kujera Raihan ta koma ta zauna ta ɗauki wayarta tana dannawa ɗaiɗai kamar ba ta san yana falon ba. Cikin takun isa Sumayya ta turo ƙofa tana tafe ƙamshi na biye da ita, doguwar rigar shadda ta saka ta ɗaura ɗankwalinta ita ma ba ƙaramin kyau ta yi ba. Tana ganin Raihan ta haɗe girar sama da ƙada, da gayya ta ƙarasa wurin Al'amin ta zaune haɗe da cewar, "Barka da zuwa Husbee." Murmushi ya yi ya amsa mata da cewar, "Barka dai Wifey ya gida." Wani ɗaci Raihan ta ji a ranta amma sai ta ci gaba da taunar cingam ɗinta tana karkaɗa ƙafa tana danna waya, harara Sumayya ta wurga mata sannan ta furta, "Hubby an kawo maka ruwan wankin hannu da abinci kuwa?" Sumayya ta faɗi haka ne don ta san Al'amin zai sake aiken Raihan kuma ta san ba zai yi mata daɗi ba. Tana tsaka da tunanin ta riski muryar Al'amin yana faɗin, "Ke! Tashi ki miƙo min abinci." Shiru Raihan ta yi tana kallon waya, yana rufe baki ta kishingiɗa ta ci gaba da abin da take yi. Kallonta ya sake ya furta, "Ke Raihan ba magana nake yi miki ba." Murmushi Raihan ta sakar masa sannan ta furta, "Ban yi tsammanin da ni kake ba na ji kana kiran matarka da ke Daz why ban kawo da ni kake ba." Daga Al'amin har Sumayya ido suka bi Raihan da shi don tun da ta zo gidan wannan ce doguwar maganar da ta yi. Cikin wani irin taku ta miƙe ta nufi kitchen ta ɗebo ruwa ta dawo ta ajiye ta sake komawa ta ɗaukon abincinsa sannan ta koma kwanta, sannu a hankali Sumayya ta lura da irin satar kallon da Al'amin yake yi wa Raihan. Cike da ɓacin rai ta dubi Al'amin tana cewa, "Hubby mu wuce ɗaki mu ci a can." Sam ba shi da sha'awar tafiya don ko babu komai Raihan ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, musamman gashinta da yake ta sheƙi da ya zubo har baya. Abincin hannunsa ya cinye sannan ya furta, "Am comportable a nan, bayan na gama cin abinci ma ina da aikin da zan yi." Ganin babu wasa a fuskar Al'amin ya sa Sumayya ta yi shiru sai dai gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi saboda babban tashin hankalinta kar Al'amin ya faɗa ƙaunar Raihan don kallon da yake yi mata mai ɗauke da ma'anoni ne. Wurgawa Raihan mugun kallo ta fara yi cike da jin haushi ta tashi fuuuu ta shige ɗaki. Zuciyar Raihan fes don har sai da ta murmusa ta ci gaba da danna wayarta, a lokacin Al'amin ya samu damar more wa Raihan kallo haka kawai ya ji tana birge shi uwa-uba ga girkin da ta dafa ba ƙarmin daɗi ya yi masa ba, kasancewar ba zai tantance girkin Sumayya ba don tun da suka yi aure bai fi sau uku ta yi girki ba, yau ta ce nan na ciwo gobe ta ce can. Don haka Raihan ta karɓi ragamar gyaran gidan gabaɗaya, sai dai koyaushe idan ta tuna bata da wata fada a wurin mijinsu abin yana yi mata ciwo. Bayan Al'amin ya gama cin abinci Raihan ce ta kwashe kayan gabaɗaya tana yin aikin idon Al'amin na kanta, tana sane da shi don haka ta riƙa taku ɗaiɗai har ta gama kwashewa gabaɗaya. Tana gamawa ta wuce ɗakinta bakinta ɗauke da dariya don ta lura da yadda yake shan magani a duk lokacin da ta ɗago suka haɗa ido da shi, kwanciya ta yi tana murmushin farinciki don ko babu komai ta san yau rana ɗaya ya yi mata kallon ƴa mace saɓanin lokacin baya da baya ɗaukanta a komai. Bai gaji da kallonta ba don haka kai tsaye ya nufi ɗakin Raihan sai da ya je bakin ƙofa sai kuma ya ja guntun tsaki don bai san abin da zai ce ya zo yi ɗakin ba. Ɗakin Sumayya ya shiga don ya lura sarai haushinsa ta ji din haka ta wuce ɗakinta a fusace, yana zuwa ya same ta tana ƙwallah nan ya shiga rarrashinta daga ƙarshe ta sauko suka dawo falo. Zaman Raihan da Al'amin haka ya fara ɗaukan sabon salo, don yanzu ta rage rawar jiki akansa sosai dukda a koyaushe tana jin soyayyarsa da kewarsa a zuciyarta. Girki kuwa tuni Sumayya ta karɓi abinta don tuni Mahaifiyarta ta yi mata faɗa akan wannan wautar da ta yi, don haka suke girkin kwana bibbiyyu amma duk ranar Raihan bata da kwana sakamakon duk ranar girkinta tun magriba take kwanciya wani irin bacci mai nauyi ba ita za ta farka ba sai bayan sallar asuba, lamarin wannan bacci nata ba ƙaramin damunta ya yi ba akwai ranar da ta zauna a falo tana jiran dawowar Al'amin ana yin sallar Isha'i bacci ya yi awon gaba da ita ba ita ta farka ba sai da ana kiran sallar asuba. Tun abin bai ɗaga hankalin Raihan ba har ya fara damunta don haka ta dage da nafilfili tana kaiwa Allah kukanta. Sai da ta shafe sati biyu cikin wannan yanayin sannan Allah ya yaye mata, ana cikin haka har ranar girkinta ta zagayo tun ana gobe za ta karɓi girki ta sa Al'amin ya yi mata cefanen dambu, tun bayan azahar ta shiga kitchen ta fara haɗa kayan dambu wurin bayan sallar la'asar ta gama dambun shinkafarta ban da ƙamshi babu abin da yake yi. Tun lokacin da Dambun ya turaro Sumayya ta kasa zaune ta kasa tsaye, yawunta ba ƙaramin tsinkewa ya yi ba amma faɗin rai ya hanata zuwa ɓangaren Raihan. Ganin ta kasa daurewa ya sa ta taka har ɓangarenta fuska ɗauke da murmushi ta ce, "Aunty Raihan na zo cin dambu wallahi Ɗan baba nake ji kamar zai fito." Ras gaban Raihan ya faɗi don saboda a ƴan kwanakin nan ta lura da sauye-sauyen da take gani a tattare da Sumayya, murmushin ta yi mata sannan ta ce, "Dama yanzu nake shirin kai miki don gaskiya karki haifo min Ɗa da rowa, na zo na ji kunya ace uwa ta yi wa Ɗanta rowa ai ba kanta." Sumayya ba haka ta so ba don ta so maganar da ta faɗa ta ɓata wa Raihan rai amma sam bata lura da haka ba." A wani food flask Raihan ta zuba wa Sumayya ta miƙa mata sannan ta fice, jin ƙamshin na bugarta ya sa tun a hanya ta ɓuɗe ta damƙi loma ɗaya ta ci tana lumshe ido. Tun bayan fitar Sumayya jikin Raihan sanyi ya yi, ƙwallah ta ciko mata ido don a yanzu ta yadda da zarginta Sumayya wani cikin gare ta, hawaye ne ya zubo mata da ta kalli yadda ta shirga kwanukan Al'amin ta ƙarewa kanta kallo sannan ta tuno yau kusan watansu huɗu da aure amma babu wani abu da ya taɓa shiga tsakaninta da shi. Jiki a sanyaye ta ƙarasa aikinta ta koma Falo ta zauna tana ɗan danne-danne a wayarta. Har aka yi sallar magriba Al'amin bai dawo ba sai gabannin isha'i ta ji alamun shigowarsa, tana nan zaune ya shigo ƙamshin turarenta ya doki hancinsa har sai da lumshe ido, kallonta ya yi tana sanye da riga da sike na leshi ba ƙaramin kyau suka yi mata ba. Murmushi ta yi masa ta ƙarasa ta karɓi jakarsa, wannan karon ta yi mamaki da har ya mayar mata da martanin murmushi. Al'amin ji yake kamar ta rungume ta saboda yadda ya ga ta yi masa kyau, ita kanta Raihan ta lura da irin kallon da yake yi mata don haka take cikin farinciki haɗe da fatan ta samu babban matsayi a zuciyarsa. Sai da ya yi wanka a ɓangare Sumayya ya sako ƙananan kaya ya fita sallar isha'i ya dawo sannan ya ci abinci, yana cin dambu yana lumshe ido don ba ƙaramin daɗi ya yi ba, ita kuwa Sumayya a daddafe ta yi sallar Isha'i kasancewar wannan laulayin nata shi ma ba ƙaramin bacci yake saka ta ba. Lura da yanayinta da Al'amin ya yi kama ya sa idan ya dawo ko ranar girkinta ne idan ya ga tana bacci baya tashinta, don haka a wannan lokacin ma Al'amin ya ke ta kallon Raihan yana jin wani baƙon yanayi a tattare da ita. A zuciyarsa ya ƙudurce a ranar sai ya sauke mata nauyinta da yake kansa don ba ƙaramin nadama ya yi ba saboda tuna hukuncin da Ubangiji ya hukunta akansa, tausayi ta bashi da ya tuna tsawon watannin da suka ɗauka ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, har zuciyarsa ta fara ayyana masa da a ce ba mai tsoron Allah ba ce tuni ta nemar wa kanta mafita. Bayan ya gama cin abinci Laptop ɗin sa ya ɗauko saboda wasu aikace-aikace da yake da su, Raihan na gajiya da zama ta wuce ɗakinta ta cire kayan jikinta ta saka wata doguwar riga mai shara-shara. Fitilar ɗakin ta kashe ta yi addu'a ta haye gado ta yi kwanciyarta, sai kusan goman dare Al'amin ya gama aikin da yake yi don haka ya miƙe ya fita daga gidan don ya tuna kayan tea ɗin su ya ƙare gashi washegari da wurwuri zai fita. Fitarsa ke da wuya Sumayya ta fito daga ɗakinta don wata irin azababbiyar yunwa ce ta tashe ta. Tana zuwa falo ta ga wani matashin saurayi ya fito daga sashen Raihan a furgice yana gyara tazugensa, tsoro ne ya kama Sumayya don a tunaninta Al'amin ne ya ji motsinta ya fito don haka a firgice ta furta, "Hubby me nake gani haka dama amanata kake ci ban sani ba?" Sai da ya gama ɗaure tazugensa sosai ya juyo ya kalli Sumayya ya ce, "Na miki kama da mijinki? Ni ma wurin masoyiyata na zo kuma na gama biyan buƙatata." Zaro ido Sumayya ta yi kafin ta yi magana ya fice daga ɗakin, a hargitse Sumayya ta riƙa ƙwalawa Al'amin kira jin shirun ya yi yawa ya sa ta faɗa ɗakinta ta rufe don tsoro ne ya kamata. Wayarta ta ɗauka jiki na rawa ta lalubo lambarsa ta fara kira, katse wa ta ga an yi babu jimawa ta ji kiransa ya shigo. Hannu na rawa ta ɗauka tana faɗin, "Kana ina Hubby?" Jin yadda take magana ya faɗar masa da gaba don haka ya furta, "Na ɗan fita amma ina hanyar dawowa." Sumayya ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "To wallahi yanzu na ga kwarto ya fito daga sashen Raihan ni dai ka yi sauri wallahi tsoro nake ji." Ras! Gaban Al'amin ya faɗi, har sai da ya yi parking ɗin motarsa a gefe jiki a sanyaye ya ce, "Gani nan ki rufe ƙofarki In sha Allah babu abin da zai faru." Bai jira cewarta ba ya katse wayar. A gaggauce ya lalubo lambar da aka kira shi babu jimawa, sake karanta sakon ya yi yana jin kansa na wani irin sara masa. "Ka na tare da Raihan ne ba don kamai ba amma ni saurayinta muna jone ni da ita, Raihan tsohuwar budurwata ce kuma ta gaya min duk irin zaman da kuke yi hasalima babu abin da ya shiga tsakaninku. Wannan dalilin ya sa take gayyatata a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, a yanzu haka ina can gidanka ina ɓarje shagalina don tun bayan fitarka ta kira ni a waya, idan kana musu ka buɗe Whatsapp ɗinka za ka tabbatar da abin da nake gaya maka. Na gaya maka ne domin ka sakar min abar ƙaunata idan ba haka ba kuwa mu ci gaba da shan shagalinmu a cikin gidanka ko kuma ta riƙa biyoni har mahallina kamar yadda ta saba zuwa da farko." Jikin Al'amin na rawa ya sake buɗe Whatsapp ɗin sa ya kuma duba waɗansu irin munanan hotunan Raihan maƙale da wani saurayi da lambar ta turo masa sai dai kiran duniya ya yi wa lambar ta ƙi shiga. Da wani irin gudu ya take motarsa ya nufi gida zuciyarsa na wata irin suya da raɗaɗi, a hargitse ya yi parking ya nufi cikin gidan kai tsaye ya wuce ɗakin Raihan. Tana kwace ta yi ɗaiɗai da alama ta ji daɗin baccin da take yi, cikin bacci ta ji an yi mata wata irin daƙuma. A firgice ta wartse idanunta suka sauka akan Al'amin, ganin yanayinsa ba ƙaramin tsoratata ya yi ba. Tana shirin yin magana ta riski muryarsa yana faɗin, "Ke munafuka ce annamimiya maci amana ashe duk wannan ladabi da biyayyar da kike yi min a munafurci ne?" Hawaye ne ya fara wanke fuskar Raihan don irin zagin da yake yi mata tun da ta zo duniya ba a taɓa yi mata irinsa ba, kasa buɗe baki ta yi balle ta yi masa magana sai ji ta yi ya wurgar da ita kan gado. Wayarta ya hango a gefen fulonta don haka ya ɗauka ya fice daga ɗakin, kan kujerar falo ya koma ya zauna ya haɗa kai da gwiwa maganansa suna sake tarayo masa munanan hotunan da aka tura masa. Ɗakin Sumayya ya ƙwanƙwasa sai da ji muryarsa sannan ta buɗe masa ƙofar, yana shiga ta faɗa jikinsa tana fashewa da kukan kissa ta ce, "Na rantse da Allah ban yi wa Raihan ƙarya ba da idona na ga kwarto ya fito daga sashenta." Jinjina kai ya yi cikin ɓacin rai ya furta, "Na ga komai kuma dole na ɗauki mataki akai." Daɗi ne ya kama Sumayya don ta san shi kenan ƙarshen zaman Raihan ya zo a cikin gidan, musamman da ta san halin Al'amin mutum zmai tsananin kishi. A daren ranar kusan kwana Al'amin ya yi yana jin wani irin kishinta don haka ya ji zuciyarsa na ɗaci duk da ba zai ce yana ƙaunar Raihan ba amma kishinta ya gama mamaye zuciyarsa. Yadda Al'amin ya riƙa juyi haka Raihan da bata san hawa ba balle sauka aka hau ta da faɗa ta riƙa juyi tana hawaye, ta maimaita maganganun Al'amin ya fi a irga. Daga ƙarshe ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah tana miƙa wa Allah lamuranta. Tafiya suke cikin tsananin zafin rana a galabaita don kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da suna cikin wani irin mawuyacin hali, Hatsabibiya ce ta yanke jiki ta faɗi tana sauke numfashi da ƙyar. Ta ɗago jemammun idanunta tana kallon Abar bauta ta ce, "Wannan tafiyar da muke yi tana yi min kamanceceniya da dajin ƙare kukanka saboda ɗaya bayan ɗaya muna ta rasa rayuwarmu." Kuka ne ya ci ƙarfinta ya yin da ta tuna baƙar kurar da ta laƙume gawar mijinta, ta share ƙwallarta tana ci gaba da cewa, "Na yi babban rashi na maigidana wanda har abada ba zan taɓa manta mummunar mutuwar da ya yi ba, mun rasa Barira matar Alhaji Bala. Mun rasa Aljani Burdudu wakilin zuƙe jini shin kina ga za mu samu wanda zai maye gurbinsa? Mun rasa Alhaji Gali kasuwar kwari shi ma yana taimakawa Ƙungiya ta fannin shayar da ita jini, anya kina ga sannu a hankali ba za mu ƙare ba kafin mu ƙarasa tsibirin Jabbul-ƙasi?" Abar bauta da ita ma ta gama galabaita ta numfasa da ƙyar ta furta, "Ba za mu mutu mu duka ba kamar yadda Jabbul-ƙasi ya furta amma ni kaina ina jin tsoron wannan baƙar rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki. Ni kaina na fara sarewa duk da sarewa ba halina ba ne, amma ina yi mana fatan zuwanmu lafiya tun da tafiyar da ke gabanmu ko ta sa'a uku bata kai ba." Babu wanda ya sake tankawa ɗan uwansa suka ci gaba da tafiya a galabaice tafiyar da suke cin karo da munanan halittu masu firgitarwa, sai da suka shafe awa biyu da rabi suna tafiya sannan suka fara hango wani dogon tsauni wanda kallonsa kaɗai zai iya rikitar da idanu, daɗi suka ji har cikin zuciyarsu a lokacin saura su goma sha uku waɗanda suke rayayyu. Da sauri suka ci gaba da tafiya suna gabda shi ga tsibirin wata irin guguwa ta taso ta turbuɗe su haɗe da fara wurgi su tana maka su da ƙasa, sai da ta jima sannan ta fara sararawa, a hankali suka fara dawowa hayyacinsu lura suka yi da sun gabda ƙofar shiga tsibirin don haka suka miƙe a hankali, daga can nesa da su suka hango ragowar gawarwakin abokan tafiyar ta su, ba su damu ba don sun tabbatar da sun kawo tudun tsira tun da har ga su a ƙofar tsibirin Jabbul-ƙasi. Waɗansu gajerun baƙaƙen aljanu ne suka zo suka yi musu rakiya ta wata siririyar hanyar, suna tafe suna ƙare wa hanyar kallo, tafiya suka yi ta kusan minti goma sannan suka ɓulla a wani ƙaton fili mai ɗauke da wani irin haske tamkar hasken rana. Sai dai wurin a rufe yake ruf babu wata ƙofa da hasken rana za ta shigo, aljanun da suka yi musu wannan rakiyar ne suka dube su sannan suka furta, "A nan za mu dakata akwai wakilai na gaba." Suna rufe baki suka nutse ta ƙarƙashin ƙasa. Suna nan tsaye a daga bangon arewa suka hango wata mace ɗaure da wata saƙar baƙin ƙarfe, jin alamunsa ya sa ta ɗago a galabaice ta cikin ɗimuwa ta furta, "Ku yi min rai ku kawo min agaji wahala za ta kashe ni." Idan ba gizo idon Hatsabibiya yake yi ba gani take tamkar Mugaza, da hannu ta yafito Abar bauta ta yi mata maganar a hankali. Ware idanu ta yi karaf suka sauka akann Mugaza da ta jeme ta bushe ta lalace, jikinsu ne ya yi sanyi wata irin nadama ta shige su don haka suke ganin babbar wautar da suka tafka. Suna cikin wannan yanayin wasu dogayen Aljanu suka zo suka wuce da su zuwa ƙofa ta gaba, haka aka riƙa shiga da su ƙofofi har ƙofa saba'in da bakwai sannan suka ƙarasa wani babban fili, kallon wurin kaɗai ya isa kaɗa hantar cikin bil'adam idan bai aro jarumta ba ya haɗiyi zuciya ya mutu. Jinsin jinnu kuwa suna iya razana su shiga firgici don haka zuwansu Hatsabibiya ya saka su firgicewa har suna niyyar zubawa a guje suka ji wata irin razanannitar tsawa. Lokaci ɗaya suka tsaya ƙyam wuri ɗaya jikinsu na karkarwa daga bangon kudu suka hangi wata irin kujerar farin dutse na hudowa daga cikin ƙarƙashin ƙasa, mamalallakinta Jabbul-ƙasi na zaune akai hannunsa ɗauke da wani zabgegen takobin farin dutse. Wani irin yawu suka haɗiya wanda saura kaɗan su tafi da maƙogaronsu, suna shirin yin magana suka hango Huzaifa ya hudo ta bangon Kudu yana ƙyaƙyacewa da wata shu'umar dariya. Jin hayaniya ta fara yawa ya sa Nurses suka taho wurin da sauri, suna ganin abubuwan da Kabiru yake yi da sauri suka kira security don ya fita da shi, amma bugu ɗaya Kabiru ya yi masa har sai da ya bugu da bango sannan ya faɗi ƙasa yana ƙwalla ƙara. Nan take suka fita da gudu suna kuruwa don lamarin ba ƙaramin tsoro ya ba su ba, Maryama ce ta farka daga bacci tana ƙarewa wurin kallo ganin Kabiru a tsaye ya sa ta saki murmushi ko da tana jin nauyin Inna wuro amma ta ji daɗin ganinsa don ta yi kewar mijinta. Inna wuro ce ta ƙarasa wurin Kabiru cikin kuka ta furta, "Ka dubi girman Allah Ibrahim ka yi haƙuri." Shiru Kabiru ya yi adaidai lokacin su Baffa suka ƙaraso cikin asibitin, tun ba su ƙarasa cikin ɗakin ba Inna wuro ta nufe su cikin tashin hankali cikin kuka tana faɗin, "Baffa ku zo ku gane min halin da yaron nan yake ciki, yana ganin jaririn Maryama shi kenan Ibrahima ya ziyarce shi." Da hanzari su Baffa suka ƙarasa gaban Kabiru Baffa ya dubi Kabiru sannan ya furta, "Ibrahim ka dubi girman Allah ka kama gabanka indai har yadda ka faɗa gaskiya ne Kabiru aboki kuma ɗan uwanka ne." Baffa ya dubi Inno wuro da ke sharɓar kuka sannan ya ci gaba da cewa, "Ka na ganin yadda mahaifiyar Kabiru take zubda ƙwallah shin jin daɗinka ne ko kuwa za ka so abin da zai musgana ran mahaifiyar amininka? Don Allah ka tashi mu wuce can gida amma a nan za ka tara mana jama'a ne." Kamar raƙumi da akala haka Kabiru ya bi bayan su Baffa suka wuce gida. Tun da suka tafi uffan Kabiru bai sake tankawa ba don haka babu wanda zai kalli Kabiru ya yi tsammanin baya cikin hayyacinsa. A haka har Maryama ta shafe kwana uku tana karɓar kulawa daga wurin likitoci, a kwanansu na huɗu aka sallame ta ita da jaririnta. Sai dai tun ranar da Kabiru ya tafi gida har ranar da aka sallami Maryama uffan bai sake tanka musu ba, wannan lamarin ba ƙaramin sake ɗaga hankalin su Inna wuro ya yi ba don komai ka cewa Kabiru sai dai ya bika da ido. Sai dai ya ci abinci ya yi sallah ya shiga banɗaki amma babu wani abu da yake yi bayan wannan, don haka koda lokacin suna ya zagayo babu wani taro da aka yi kasancewar shi kansa jaririn ba lafiyayye bane ga kuma shi ma Kabiru halin da yake ciki Kullin cikin yi masa turare da jiƙe-jiƙen magunguna suke. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 47 Ibrahim Alƙasim Bn Muhammad Mustafa shi ne ainihin sunan aljanin da ke jikin Kabiru, asalin haɗuwarsu sun haɗu ne a tsangaya tun suna ƙanana. A lokacin da aka kai Kabiru karatu ne suka ƙulla abota da Ibrahim da ke ɗauke da siffar mutane don ko kaɗan babu wanda ya san Ibrahim ba mutum ba ne sai Malaminsu, dalilin da ya sa ta su ta zo ɗaya kasancewar kusan shekarunsu ɗaya, kuma lokacin da aka kai Kabiru almajiranci ya daɗe idan ya tuno su Inno wuro yana kuka. Idan yana kuka shi ma sai Ibrahim ya zo kusa da shi ya zauna ya fara kuka sakamakon tuno na shi mahaifan da ya yi. Haka za su zauna su ci gaba da koke-koke idan suka gama su share hawayensu su tafi yawon bara. Kamar yadda Baffajo yake ziyartar Kabiru shi ma haka Mahaifinsa yake kai masa ziyara bayan wani lokaci, a haka suka taso cikin soyayya da shaƙuwar junansu saboda duk inda aka ga Ibrahim za a ga Kabiru, a wannan rayuwar suka girma har suka yi saukar Alƙur'ani. A lokacin Kabiru na shekara ashirin daidai haka shi ma Ibrahim, tun da lokacin saukarsu ta ƙarato idan suka tuna lokacin rabuwa ya zo kowannensu yana jin babu daɗi hasali wani lokacin har ƙwalla Kabiru yake yi. Saura sati guda su Kabiru su tafi wata rana suna zaune suna hira Ibrahim ya dubi Kabiru ya ce, "Kabiru ga shi lokacin rabuwarmu ta zo amma daga ni har kai babu wanda ya san garin kowa." Cikin damuwa Kabiru ya ce, "Wallahi kuwa Ibrahim amma mai zai hana na fara zuwa garinku idan ya so in Baffa zai zo tafiya da ni ba sai ka bi mu ni ma ka gano ƙauyenmu ba." Ibrahim bai damu ba ya ce, "Shi kenan babu damuwa amma ba za ka ji tsoron mutanen garinmu ba kuwa?" Cikin halin ko'inkula Kabiru ya ce, "Sai ka ce wasu dodanni zan ji tsoronsu. Allah ya kaimu kawai mu tsayar da lokaci." Nan take suka tsayar da ranar tafiya sai dai tun da aka tsayar da lokacin tafiya Ibrahim yake cikin damuwa, fargabarsa ɗaya kada ya bayannawa Kabiru kansa ya zo ya guje shi a ɓangare ɗaya kuma yana tsoron kada ya kai shi duniyarsu wani abu ya faru Kabiru ya razana abotarsu ta zo ƙarshe duk da ya san babu wani abin cutarwa da ahalinsa za su yi masa. A haka har suka samu Malaminsu da maganar, da farko ya so ya hana su tafiyar amma a wani dare sai Ibrahim ya samu Malam ya roƙ shi akan ya bar shi su tafi. Ba don ya so ba ya amince musu Kabiru ya ɗebi kayansa kala biyu suka ɗauki hanya, sai da suka ɗan yi tafiya ta ƙasa mai nisa har sun fara shiga cikin daji Kabiru ya dubi Ibrahim ya ce, "Kai Abokina wannan wacce irin tafiya ce haka har yanzu ba mu zo tashar da za mu shigar motar garinku ba?" Ibrahim ya yi murmushi ya ce, "Kai ragon maza rufe idonka." Babu musu Kabiru ya rufe ido yana faɗin, "Ni da kai a samu ragon don ko makaho ya shafa ƙwanjinmu ya san da bambamci." Jin hayaniya ya sa Kabiru buɗe ido da sauri ya fara bin wurin da kallo tare da mutanen da ke wurin, Ibrahim ne ya riƙo hannun Kabiru ya ce, "Mun ƙaraso waɗannan mutanen garinmu ne ka ga ƙofar gidanmu can." Ya nuna masa wani katafaren gida mai siffa da na sarauta, daga bayansa ya ji wasu magidanta suna faɗin, "Abokin Ibrahim muna yi maka barka da zuwa." Kabiru ka sa amsawa ya yi ya dubi Ibrahim ya ce, "Ibrahim yaushe ka fara aiki da aljanu ban sani ba, wato duk gargaɗin da Malam yake yi mana akan laƙanin rufa ido baka ji ba kenan?" Dariya ce ta kama Ibrahim sai da ya yi mai isarsa sannan ya ce, "Kai don Allah wuce mu je." Kamar wanda aka zare wa laka a jiki haka Kabiru ya bi bayan Ibrahim har suka shiga cikin gidan, cike da girmamawa Mahaifiyar Ibrahim ta sauke su da abinci kala-kala. Har lokacin jikin Kabiru a ɗarare yake don haka Ibrahim da ya lura da yanayinsa ya riƙa jan sa da hira amma gabaɗaya ji yake wani iri. Yayar Ibrahim ce ta shiga gidan hannunta ɗauke da ƙaramin jariri, tana ganin Kabiru ta washe baki tana faɗin, "Ikon Allah, wannan fa shi ne karo na farko da bil'adam ya zo cikinmu gaskiya Ibrahim abotarka da Bil'adam ɗin nan ya matuƙar burge ni." A fusace Mahaifiyarsu Ibrahim ta dubi Yahanasu ta ce, "Wai me ya sa wani lokacin baki da tunani Yahanasu kamar ba ki ji kashedin da Malam ya gama yi ba jiya ko?" Daga bakin ƙofa Kabiru ya hango yadda yara da manya suke leƙensa don haka ya sake shan jinin jikinsa, ya dubi Ibrahim a tsorace ya ce: "Don Allah kar ka cutar da ni Ibrahim domin a zamantakewata da kai ban taɓa zalintarka ba, idan ma na yi sai dai wataƙila lokacin da muna cikin ƙuruciya." Dafe kai Ibrahim ya yi jiki a sanyaye don ya fahimci Kabiru ya gano shi ya ce, "Ba zan taɓa cutar da kai ba Kabiru domin jin ka nake har cikin zuciyata saboda Baffajo bai taɓa bambamta mu ba duk abin da zai kawo maka sai ya kawo min, kuma zaman da muka yi na amana ne babu zalinci a tsakaninmu." Ganin hankalin Kabiru ya tashi ya sa Ibrahim ya saka shi sake runtse ido, muryar malaminsu ce ta farkar da shi yana buɗe ido ya gan shi zaune a shagon Malam. Malam ya kalli Kabiru ya yi murmushi ya ce, "Dama abin da na yi gudu kenan amma gudun kar ku yi min mummunar fahimta ya sa na amince da tafiyarku. Ibrahim ba mutum ba ne kamar yadda ka yi tsammani, tun kafin zuwanka Mahaifinsa ya kawo shi karatu wurina saboda Mahaifinsa abokina ne mun haɗu da shi ne a wani aikin Hajji da na je. Ka kwantar da hankalinka Ibrahim da zuri'arsa ba za su taɓa cutar da kai ba domin su cikakkun musulmai masu kyawawan ɗabi'a ne, sai dai ka yi haƙuri don na tabbata ba lallai ka sake ganin Ibrahim a nan tsagayata ba sai dai wataƙila idan ka koma rugarku." Kabiru cikin damuwa ya furta, "Amma har yanzu tsoro nake ji, zuciyata ta gaza aminta da Ibrahim na jinsina ba ne Malam." Malam ya yi murmushi sannan ya ce, "Ka ji tsoron Allah Kabiru domin shi zai isar maka, babu abin da mutum ko wani jinsi zai yi maka wanda Allah bai ƙaddara ba, ka yarda da maganata Ibrahim da zuri'arsa ba za su cutar da kai ba." Jinjina kai Kabiru ya yi ya miƙe ya ci gaba da harkokinsa sai dai gabaɗaya ji yake babu daɗi kamar ya rasa wani ɓangare na jikinsa, don a daren ranar da ya je kwanciya ya kalli wurin kwanciyar Ibrahim sai kawai ya fashe da kuka, haka ya ci gaba da rayuwa cikin kaɗaici da damuwa har ranar da Baffajo ya zo ɗaukansa a nan Malam yake sanar masa da komai game da Ibrahim, bai gama amincewa da maganarsa ba sai da Malam ya kira Mahaifin Ibrahim da Ibrahim suka bayyana a wurin suka gaisa cikin mutumtawa sannan suka sake ɓace wa. Shi kansa Baffajo ya yi mamaki da wannan lamarin, daga haka ya yi wa Malam alheri da godiya mai yawa sannan ya ɗauki Kabiru suka tafi daga Malam har Kabiru kowannensu yana zubda ƙwallah. Wannan dalilin ne ya saka lokaci zuwa lokaci a duk lokacin da Kabiru ya shiga wani yanayi yake kawo masa ziyara ba tare da ya fahimci shi ba ne, don ko kaɗan baya son ya razana abokinsa don haka a duk lokacin da ya ziyarce shi baya taɓa bari ya ga fuskarsa. Lokacin da lamarim gidansu Raihan ya same shi a lokacin Mahaifiyarsa ce babu lafiya a gaggauce ta tafi birnin ƙudus don ɗebo mata wata ciyawa wacce take tsakiyar tekun Milabi, don yi mata magani. Shi ya sa bai nemi karawa da Huzaifa ba, a ɓangare ɗaya kuma yana ganin duk abin da yake faruwa akan lamuran Raihan sai ya yi kamar ya shiga sai wani uzurin ya faɗo masa. Shafin Rayuwar ƙunci ne ya buɗe wa Raihan a gidan Al'amin ban da tsangwama kyara da habaici babu abin da take fuskanta, fushin da Al'amin ya ɗauka da ita ya fi komai ɗaga mata hankali don ko gaishe shi ta yi baya kallon ƙurarta balle ta saka ran zai amsa mata. Ita kuwa Sumayya ta samu abin da take so don haka bata da aiki sai yi wa Raihan habaici da baƙaƙen maganganu, saboda ko kofi Raihan ta taɓa sai Sumayya ta saka omo ta wanke a cewarta karta shafa musu dattin zina a jiki. Waɗannan maganganu na su ya sake jefa Raihan cikin ruɗu don ita bata san duk abin da yake faruwa ba, wata rana da safe tana zaune a falo Al'amin ya fito da sauri ta ƙarasa gabansa ta ce, "Don Allah ka taimaka ka gaya min laifin da na yi maka ko na samu sassauci a zuciyata." Wani irin kallo ya bita da shi sai kawai ya saki tsaki ya wuce." Sumayya na fitowa ta bita da kallon ƙyanƙyami tana yarfe hannu ta gegareta ta gefe ta wuce. A wurin Raihan ta durƙushe tana wani irin kuka mai cin zuciya, tana ji tana gani Sumayya ta raka Al'amin ta dawo ta zazzage mata baƙaƙen maganganu ta wuce ɗakinta. A hankali Raihan ta ja ƙafa ta koma ɗaki tana ci gaba da kuka mai tsuma zuciya, tunani goma da ashirin ne ya mamaye zuciyata. Wanda ya zame mata jigo shi ne halin da take ciki tsakaninta da Al'amin, na biyu kuma rashin lafiyar Kabiru da Mommy kira sabon layin da Al'amin ya sauya mata take sanar mata Daddy ya kira waya don ya ji dalilin da ya saka Kabiru ya shafe kwana da kwanaki ba tare da ya dawo bakin aiki ba ake sanar masa. Waɗannan abubuwan ne suka sake dagula lissafin rayuwarta ya sa ko abinci bata iya ci daga ruwa sa ruwan tea. Wata ranar Asabar Mommy ta ce mata za su je duba Kabiru don haka Al'amin na dawowa da dare ta same shi da maganar duk da baya amsa maganarta. Bayan ya gama sauraro ta kallon tsaf ya yi mata ya ce, "Wato jaraba na cinki kin ga babu yadda za ki yi shi ne za ki ɓullo min ta haka, fasiƙar banza fasiƙar wofi tashi ki bani wuri ba Kabiru ba ko waye babu inda za ki." Jin haka ya sa Raihan ta fashe da wani irin matsananci kuka tana shiga ɗaki ta kira Mommy ta gaya mata ba za ta samu damar zuwa ba. Mommy na son fahimtar Raihan game da lamarin zaman aurenta amma babu wata shaida da zata kafa hujja da ita, amma akwai abubuwa da dama da take lura da yanayinta don dai kar ta yi magana ne ta ga kamar ta saka mata ido. Daddy da Mommy ne suka shirya suka tafi gano jikin Kabiru, Mommy har da kayan barkarta rigib masu yawa wanda ta kaiwa Mai jego da jaririn da aka haifa. Sai dai har suka je suka ƙaraci zamansu uffan Kabiru bai tanka masa ba hasalima bai nuna ya san su balle su saka ran zai tanka musu. Jiki a sanyaye su Daddy suka dawo gida lamarin ciwon Kabiru ya matuƙar ba su tsoro, kusan kwana su Mommy suka yi suna jajantawa a junansu daga ƙarshe Daddy ya ci alwashin taimaka wa su Inna wuro da duk abin da Kabiru yake yi musu, har yake ayyana ko ya yi wa Malam maganar ciwon Kabiru don dai kuma yana ganin kamar kar su ga ya yi musu shisshigi a lamarin Ɗansu. Sumayya ce take fama da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai don haka wayewar garin wata talata Al'amin ya ce ta shirya don ya kaita asibiti. Lokacin da suka fita Raihan na ɗaki a kwance don haka bata yi tsammanin da Sumayya suka fita ba, Al'amin da Sumayya suna zuwa asibiti aka yi mata gwaje-gwaje daga ƙarshe aka tabbatar da tana ɗauke da ciki har na tsawon sati bakwai. Murna wurin Al'amin da Sumayya abin ya baya musaltuwa, tun a mota Al'amin ya fara kafawa Sumayya dokokin abubuwan da za ta riƙa yi don ya ce wannan cikin baya fatan wani abu ya same shi. Al'amin na shawo kwanar layinsu ya hango Raihan ta fito daga wata baƙar mota, da sauri ya taka burkin motarsa Sumayya bakinta har rawa yake ta ce, "Hubby waccen ba Raihan aka sauke ba?" Da hannu ya yi mata nuni da ta yi shiru yana ƙare musu kallo, akan idon sa ya ga ta zagaya mazaunin direba ta sumbaci mutumin da ke cikin mota. Abu ya ji ya tsikari kahon zuciyar shi yana gani ta ƙarasa bakin gate ta saka key ta buɗe ta shige hannunta ɗauke da wata farar leda. Yana ganin mutumin ya fara tafiya ya kunna tashi motar ya fige ta da gudu amma yana shan kwanar ya nemi motar sama da ƙasa ya rasa, da gudun gaske ya juyo har sai da suka kusa yin gware da wani maƙocinsa ya ƙarasa bakin gate. Yana kashe motar Sumayya na fitowa ya saka wa motar key, buɗe ƙofar gidan ya yi da ƙarfi jikinsa har rawa yake, da kayan da ya ga ta fita da su ya same ta ta zubo abinci daga kitchen tana zaune a falon. Yana zuwa ya fisgota da ƙarfi ya damƙi gashin kanta cikin wani irin ƙaraji ya furta, "Uban waye ya sauke ki a mota? Gidan uban wa kika je da izinin wa?" Tsoro ne ya kamata bakinta na rawa ta ce, "Wallahi babu in da na je yanzun nan na fito daga wanka na fito cin abinci." Da ƙarfin gaske ya sake fisgota gabansa ya ce, "Ƙarya na yi miki kenan ko? Ki bi ni a sannu wallahi darajar Mahaifina kike ci amma ba don haka ba da tuni na aika ki gidanku don har abada ba zan taɓa hanya da fasiƙi ba." Ya wurgata ƙasa ta faɗa kan abincin da zubo ruwan shayin da ke gefe ya kwaro mata a hannu, a fusace ya nuna ta da ɗan yatsa ya furta. "Wallahi kin ci sa'a ba na daga sahun maza masu duka da yau dai na baki mamaki." Yana gama maganar ya shige ɗaki, Sumayya ta watsa mata harara sannan ta ce, "An dai ji jiki wallahi karuwancin ma ai yana cin darajar aure da sai ki bari idan ya sauwaƙe miki sai ki ci gaba daga inda kika tsaya." Tana gama maganarta wuce ɗakinta ta ci gaba da zuga Al'amin san ranta. Idanunun Raihan bushewa suka yi saboda ɓacin rai, nan take ƙirjinta ya ƙulle wani abu ya turnuƙeta ta fara wani irin kakari jini na fita ta bakinta. A hankali ta rarrafa ta shiga ɗakinta ta wuce banɗaki da rarrafe ta saka ruwa ta wanke sannan ta koma kan carpet ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Wuni ranar haka Al'amin da Raihan suka yi kowa zuciyarsa babu daɗi musamman Raihan da duk abin da yake faruwa bata da masaniya akai. Sumayya babu yadda bata yi da Al'amin akan ya saki Raihan ba amma yaƙi sai magana ɗaya da yake nanata mata na cewar darajar Mahafinsa ta sa ba zai sake ta amma zaman da za ta yi ta gwammace dama sakinta ya yi. Duk da ba haka ta so ba amma abin ya yi mata daɗi don ko babu komai ta san ko kaɗan Raihan bata gabansa, shi ya sa ta ci gaba da shuka tsiyarta san ranta. Sati biyun da aka ɗebawar Sumayya sun cika don haka Talata da ta zagayowa Al'amin ya shirya zai kai Sumayya asibiti amma da yake yana da uzuri sai ya ce ta bari ya kaita da yamma, kamar yadda ya faɗa mata bayan la'asar ya ƙaraso cikin gidan. Yana gabda wuce sashen Raihan ya ji muryarta da namiji suna faɗin, "Tabbas kai kaɗai kake faranta min zuciya, ko kwanaki haka mahaukacin can ya zo yana ta haukan banza wai sai na faɗi wanda ya zo ya ɗauke ni." Muryar namijin ya ji ya bata amsa da cewar, "Ni dai yanzu duk ba wannan ba, kin san dai yau sau biyu kawai kika faranta min. Yanzu yaushe za mu kuma haɗuwa?" Dariyar Raihan ya ji sannan ta ce, "Ka bari na ji sakaran nan yana gayawa matarsa zai yi tafiya idan ya tafi ba sai mu sha shagalinmu ba. Amma kafin nan bari na ɗauko maka rigarka ka saka..." Da ƙarfi Al'amin ya doka ƙofar Raihan a daidai lokacin Sumayya ta fito wurinsa tana faɗin, "Dear ashe ka shigo tuntuni kana wurin Raihan..." Magarta ce ta maƙale sakamakon wata bangaza da ta ji an yi mata sai da ta ji ta har tsakiyar kanta, cikin zafin nama Al'amin ya rufa masa baya don wannan karon ya ci alwashin sai ya kama koma wane ne yake cin amanarsa da matarsa, tun da lambar da yake zargi duk iya binciken ƴan sanda sun gagara gano mai amfani da ita. Duk yadda Al'amin ya kai ga son ganin ya kama mutumin da yake gudu daga shi sai gajeren wando abin ya ci tura, ihu ya ji Sumayya ta ƙwalla tana faɗin cikinta, wannan ya sa Al'amin ya rabu da shi don dama tuni mutumin ya je bakin gate ya fice. Yana komawa Raihan ta fito a hargitse daga ita sai ɗaurin ƙirji da alama daga wanka ta fito, dafa Sumayya ta yi ta ce: "Lafiya Sumayya me yake faruwa." Azababben marin da Al'amin ya zabga mata ne ya sa ta gani wasu taurari don har sai da kanta ya yi dum! Na wucin gadi ta riski muryarsa yana faɗin, "Ni za ki mayar ɗan tasha saboda kin raina min hankali har gidana za ki riƙa kawo kwaratanki?" Raihan riƙe gunci ta yi tana bin sa da kallo don ta rasa abin da za ta ce masa. Daga Abar bauta har Hatsabibiya rasa mai bakin magana aka yi, mamaki, tsoro haɗe da tashin hankali ya mamaye zuƙatansu. Huzaifa ya fara takawa a hankali cikin takun isa da ƙasaita har sai da ya zo wurinsu ya fara zagaye su ɗaya bayan ɗaya yana ƙyaƙyata dariya. Sai da ya zagaye su kusan sau uku sannan ya ce, "Waɗanda suka mutu kafin ku ƙaraso ina yi musu murna da farinciki domin duk waɗanda kuka ga irin wulaƙantacciyar mutuwar da suka yi rahama ce akan taku. Ni Huzaifa na tumbatsa ban ga wani Mahaluki da zai ga bayana matuƙar ina numfashi a duniya, ban da toshewar tunani da basira irin taku ta yaya za ku zo neman sa'a a kaina kuma wurin Kakana? Kun san kaf jikokin Jabbul-ƙasi babu wanda ya fi ƙauna sama da ni ta yaya zai taimaka muku ku hallaka ni? Na san kafin ku ƙaraso kun ga mace a ɗaure ban sani ba ko kun gane ta, to idan ma ba ku gane ta ba Mugaza ce. Na gano duk kaidinta da cin amanata da na yi domin dama na jima ina ɗora zargi akanta. Yau kimanin sama da watanni biyar kenan tana ɗaure babu ci babu sha kuma a duk rana ina kawo wasu kifayen aljanu suna tsotsar jininta. Ina raga mata azaba ne saboda ita ɗin uwar ƴaƴana ce ko babu komai mun haɗa zuri'a ɗaya da ita. Amma ba zan yafe irin cutarwar da ta yi matata Raihan ba, ta mayar min da ita matsafiyar ƙarfi da ya ji ta saka ta aikata kisa ba tare da tana cikin hayyacinta ba. Ta saka ta shan jini alhalin ba ɗabi'arta bace ya za a yi na yafe mata waɗannan laifuffukan?" Ilahirin jikin su Hatsabibiya ban da rawa babu abin da yake yi, baki na rawa Abar bauta ta ce, "Wallahi babu laifinmu a ciki ita ta gayyato mana ita cikin mu amma bata gaya mana..." Abar bauta ba ta gama magana ta ji an raɗa mata wani abu a tsakiyar kanta nan take ta faɗi sumammiya. Jabbul-ƙasi na zaune akan kujerar farin dutse ya kalli Huzaifa cikin jin daɗi ya furta, "Dalilai biyu ne suka sa na fi jin ƙaunarka a cikin zuciyata, dalili na farko duk cikin jikoki da ƴaƴana babu wanda ya ɗauko halaye da ɗabi'u irin nawa sai kai. Dalili na biyu ina ƙaunarka saboda taurin zuciya, taurin kai da rashin tsoronka. Tabbas kai namiji ne kuma ka cancanci ka gaji kujerata koda ba na raye, amma ka sani tsugunne bata ƙare maka ba domin zuri'ar gidan Alƙasim Bn Muhammad Mustafa na gabda tunkararka akan jinin ɗan abokinsa da ka ɗauke. A kullin ina yi maka fatan nasara sai dai wanann karon zuciyata rawa take domin Muhammad Mustafa kakan Ibrahim Alƙasim hatsababin Aljani ne fiye da tunanin mai tunani. A shekaru ɗari uku da suka wuce ya taɓa zuwa tsibirin nan har ya ci ni da yaƙi don haka nake jin ɗar a zuciyata domin sun dogara da Alƙur'ani. Na sani kaima ka sani Alƙur'ani zancen gaskiya amma saboda..." A hanzarce Huzaifa ya furta, "Dakata Jabbu. Ba na buƙatar jin yabo da ambaton kowanne addini bayan wanda na buɗi ido nake gani kuma nake wanzarwa." Jabbul-ƙasi bai damu ba don haka ya murza hannun kujerar da yake kai nan take ya koma cikin ƙarƙashin ƙasa. Inkiya Huzaifa ya yi nan take wasu tsuntsayen Aljanu suka ƙaraso suka kwasu su Hatsabibiya kai tsaye aka fara wucewa ɗakin horo da su, ana watsa su ciki kofar wurin ta shafe gabaɗaya. A fusace Al'amin ya nunawa Raihan ƙofa ya ce, "Fice min daga gida." Idanunta ne suka ciko da ƙwallah tana shirin yin magana ya buga mata tsawa da cewar, "Fice min daga gida na ce." A tsorace Raihan ta juya za ta koma ɗaki ta ji ya fisgota yana faɗin, "Kina hauka ne baki ji me na ce ba?" Jikin Raihan na rawa ta ce, "Kaya zan saka..." Da ƙarfi ya wurga ta jikin ƙofa yana faɗin, "Baƙar munafuka kina kunyar za ki riƙa mu'amala da maza? Ki fice min daga gida na sake ki saki ɗaya, na sake ki saki biyu na sake ki saki uku babu ni babu ke ko a lahira ba na fatan haɗuwa da ke." Wani irin abu Raiha ta ji yaaaam! A tsakar kanta kalaman Al'amin suka fara yi mata amsa-amo adodon kunnenta. Bata ankara ba ta ji ya fisgi hannunta da ƙarfi bai kaita ko'ina ba sai ƙofar gida ya wurgar, da sauri ya dawo kan Sumayya da je kwance cikin jini don tun buguwar da mutumin ɗakin Raihan ya yi mata jini ya fara zuba. Da sauri ya ɗauketa ya saka a cikin mota ya fice daga gidan, Raihan na gefe a zauna ya fito a mota ya saka wa gidan key ya tayar da motar ya bar wurin. Daga ita sai ɗaurin ƙirji haka ta kunce ɗankwalin kanta ta rufe kanta da kafaɗarta ta fara takawa, tafiya take ba tare da tasan inda take jefa ƙafarta ba. Gani take tamkar a mafarki don har a lokacin da take tafiya bata gama gasgata abin da yake faruwa a duniyarta ba. Tana tafe a gefen titi mutane sai kallonta suke, wasu ma kallon mahaukaciya suke mata ya yinda wasu suke yi mata kallon mabaraciya. A bakin titi ta tsaya duk Ɗan sahun da ta tsaida sai dai ya wuce, tana nan tsaye wata mota ruwan toka ta faka a gabanta. Daga mazaunin mai zaman banza aka buɗe tana fitowa ta furta, "Matar Yaya." Kallon wurin Raihan ta yi tana ganin Fatima ta furta, "Na yi rashin masoyi Fatima, na rasa Salim na rasa masoyi na har abada. Na san Salima da yana raye ba zai min haka ba kuma ba za taɓa bari a yi min haka ba." Kallon yanayinta Fatima ta yi ta furta, "Matar yaya daga ina kike haka." Idanun Raihan suka ciko da ƙwalla ta ce, "Daga gidana nake don Allah ki kaini gida." Ba ta musa ba ta buɗe mata baya sannan ta ce, "Tare muke da Abban Salim (Mijinta) bari mu sauke ki." Raihan bata amsa mata ba ta shiga motar sai kawai ta kifa kai a cikin cinyoyi ta ta fashe da matsanancin kuka. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 48 Kukan da Raihan take yi har cikin zuciyar Fatima don haka ita ma ta ji duk babu daɗi ga shi bata son ta tambayeta don ta fahimci tana cikin wani irin yanayi. Nuna wa mijinta hanya ta riƙa yi har ya nufi unguwarsu Raihan, a daidai ƙofar gidansu Raihan ya yi parking ɗin motar jin haka ya tabbatarwa mata da an ƙaraso gidansu. Ɗagowa ta yi fuskarta jawur ta furta, "Na gode Fatima." Daga haka bata sake furta komai ba ta fice daga motar, kai tsaye gate ɗin gidansu ta fara bugawa tana nan tsaye ta ji motar su Fatima ta bar wurin. Daga cikin gidan ta ji ana faɗin, "Waye?" Murya na rawa Raihan ta furta, "Ni ce." Daga cikin gidan ta ji an sake cewa, "Alhaji bai daɗe da shigowa ba, ku yi haƙuri zuwa safiya." A tunaninsa irin matan da suke zuwa maula ne, saboda duhun magriba ya fara yi. Da ƙarfi Raihan ta sake buga ƙofar tana faɗin, "Ni ce Raihan ka buɗe min." Da sauri ya zare sakatar ƙofar ta tura ta shiga ba tare da ta bi ta kansa ba. Da idanu Auwalu ya bita don ba ƙaramin mamakin ganinta ya yi a wannan ɗokacin ba, tafe take ƙafa babu takalmi zani a tsangale babu kykkyawan mayafi a jiki, tana cikin tafiya hango Daddy akan baranda da alamu waya yake don ta riske shi yana faɗin, "To shi ke nan Malam haka za a yi, don lamarin yaron akwai rikitarwa. Zan kira su a waya na sa su kawo shi don a san abin yi..." Maganarsa ce ta maƙale sakamakon hango Raihan na tunkaro shi ƙafa ko takalmi babu. A hanzarce ya furta, "Zan kiraka Malam." Katse wayar ya yi da sauri ya ƙarasa wurin Raihan yana faɗin, "Raihan! Ke ce a daren nan? Daga ina kike?" A madadin ta bashi amsa sai kawai ta faɗa jikinsa ta rushe da matsanancin kuka. Jikin Daddy har rawa yake ya fara hangen bakin gate sai ya ɗago ta yana faɗin, "Wai me ya faru ina Al'amin ɗin?" Cikin matsanancin kuka Raihan ta furta, "Ya sake ni Daddy. Al'amin ya sake ni ban san me na yi masa ba." Sak Daddy ya yi yana jin maganar Raihan na zaga ƙwaƙwalwarsa, rungumota jikinsa ya yi ya ja ta cikin gida. Lokacin da suka shiga Inno da Goggo na falo a zaune suna cin Abinci Inno ta furta, "Saboda Allah me ake da sirika irin Zainabu, yarinyar nan na riƙe ta tsakani da Allah kamar yadda na ɗauki Audullahi amma kulli ta riƙa dafa mana shinkafa kayan basir, yanzu don Allah Zinaru idan ciwon suga ya samu matsuguni a jikinmu wa gari ya waya?" Goggo ta taɓe baki tana tura kwanon gabanta gefe ta ce, "Wallahi ko mutuwa na yi a gidan nan kina da kamasho saboda kullin sai na yi niyyar komawa Albasu ki ba ni haƙuri, ina dalili Audullahi yana da kuɗi daidai misali yau ko gonar masara ba zai iya siya don ya kawo a riƙa dafa mana ba? Ita kuma Abu son namiji ya rufe mata ido sai abin da yake so za ta girki mu ko oho." Inno ta wara hannuwa sannan ta ce, "Bar ta Namiji ƙarin kunama ne balle Audullahi da ya yi rayuwar turawa ina jin tsoron kar wataran ya auro mata Elizabet..." Maganar Inno ce ta maƙale ganin Daddy rungume da Raihan tana kuka, kusan tare suka tashi Goggo na salallami. Inno ta gyara ɗaurin ɗankwalinta tana cewa, "Audullahi wa nake gani da tsohon daren nan?" Zaunar da Raihan ya yi a kujera ya furta, "Raihan ce." A tsorace suka dubi Daddy, Goggo ta dafe ƙirji ta ce, "Raihan kuma a daren nan meye haka na ganta kamar korarriya. Ni wallahi ko a Albasu ban taɓa ganin ziyara irin wannan ba." Mommy ce ta ƙarasa cikin falon hannunta ɗauke da Muhammad ta cewa, "MD wallahi ka fiye rigima ka zauna a wurin su Inno amma fir ka..." Maganarta ce ta maƙake ganin su Inno carko-carko suna tsaye akan Raihan da take sharɓar kuka. Jikinta har rawa yake ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Daddyn Raihan lafiya me yake faruwa?" Daddy ya kalleta fuska babu walwala ya ce, "Je ki da ita cikin ɗaki ki taimaka mata ta yi wanka da saka kaya." Cike da damuwa Mommy ta dubi Raihan tun daga ƙasa har sama ta ce, "A ina ka tsinto ta Daddyn Raihan ko a hanyar Office ɗinka? Ya na ganta kamar ko takalmi babu kamar wata korarriya..." Daddy ya katse ta da cewar, "Ki wuce da ita ciki na ce." Hannun Raihan Mommy ta kamo suka wuce ɗaki suna shiga Mommy ta zaunar da Raihan akan gado tana tattaɓa jikinta ta furta, "Daga ina kike haka Raihan ko kaya babu a jikinki?" Raihan ta kwantar da kanta a jikin mommy tana ƙwalla ta furta, "Mommy ya sake ni." Zaro ido Mommy ta yi tana ja da baya ta furta, "Wa kenan waye ya sake ki me kika yi masa?" Kuka ne ya sake ƙwacewa Raihan ta ce, "Ban sani ba Mommy, ban san me na yi masa ba." Ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan ta ce, "Shi kenan shiga ki watsa ruwa ki same ni a falo." A hankali Raihan ta shiga toilet sannan mommy ta dawo falo ta samu su Inno ban da faɗa babu abin da suke yi, Daddy ne ya dubi su Inno ya ce, "Inno ba a yanke hukunci ta bakin mutum ɗaya, ya kamata mu tsaya mu ji ta bakin yaron nan kafin mu yanke masa hukunci ta yiwu akwai abin da ya haɗa su wanda ba mu sani ba." Mommy da ranta ya kai ƙololuwar ɓaci ta karɓe zancen da cewar, "Amma ko me ta yi masa bai kamata ya koro mana yarinya a wannan lokacin ba, ka lura da jikinta ko riga babu daga ita sai ɗaurin ƙirjin wannan wanne irin wulaƙanci ne?" Duk da zuciyar Daddy na raɗaɗi bisa abin da ya faru sai ya danne ɓacin ransa ya furta, "Duk ba wannan za mu duba, kamata ya yi mu duba mu ji ta bakin Raihan idan muka ji ta bakinta sai na nemi Malam na ji abin da yake faruwa, saboda da alama bai san abin da yake faruwa ba tun da muna tsaka da waya da shi ta shigo." Mommy bata tanka ba sai jinjina kai da take yi, su Inno kuwa ba su yi shiru ba ban da ɗebewa Al'amin albarka babu abin da suke yi ba. Al'amin na zuwa asibiti aka karɓi Sumayya aka shiga bata kukawar da ta dace, ban da zarya babu abin da yake yi lokaci-lokaci yake kaiwa iska naushi. Lambar Mahaifiyar Sumayya ya kira nan take yake sanar musu halin da ake ciki, yana gama waya da ita babu jimawa ya kira lambar Ammi ita ma ya sanar mata. Mahaifinsa ne ya faɗo masa a rai don haka ya ji gabansa ya yi wani mummunar faɗuwa. A ɗarare ya kira Malam tana fara shiga ya ji an ɗauka, sai dai yanayin yadda ya ji muryar mahaifinsa ya tabbatar masa da bai san abin da yake faruwa ba. Har lokacin jikinsa a sanyaye yake ya sanar masa abin da yake faruwa da Sumayya da asibitin da suke, a gaggauce suka yi sallama Malam ya ce zai ƙaraso. Abin duniya goma da ashirin ne ya dagula lissafin Al'amin, wani irin fargaba da tashin hankali ya riski kansa a ciki, amma da ya tuna irin cin kashin da Raihan take yi masa sai ya ji ƙwarin gwiwa ta lulluɓe shi. Ammi ce ta fara shiryawa ta tafi asibitin tana sauka daga Adaidaita sahu mahaifiyar Sumayya da ƙannenta suka ƙaraso, fuskokinsu ɗauke da damuwa suka gaisa haɗe da jajantawa juna abin da ya faru. A harabar asibitin suka samu Al'amin da ke kai-kawo, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali. Ganin Ammi ya sake tsinka hanjin cikinsa, suna ƙarasowa wurinsa ya tattaro jarumta ya gaishe su. Mahaifiyar Sumayya ta dube shi sheƙeƙe tana faɗin, "Al'amin garin yaya haka ta faru ko wannan karon ma kunamar aka sake turo mata?" Sosa kai Al'amin ya yi ya ce, "Amm dama dai...dama..." Ammi ta yi masa kallon tsaf cikin tausayawa don ba ƙaramar damuwa ta gani kwance a fuskarsa ba. Waigawa ta yi ta ce, "Ina Raihan ne ko bata ƙaraso ba?" Da sauri Al'amin ya furta, "Na'am Raihan...Ehto...Dama..." Wata Nurse ta katse Al'amin da cewar, "Ina mijin Sumayya ko ƴan uwanta suke?" Da sauri Al'amin ya isa gabanta ya ce, "Gani." Juyawa ta yi ta ce, "Dr yana son ganinka yanzu." Tun bata rufe baki ba ya bi bayanta suka ƙarasa Office ɗin Dr Mu'azzam. Su Ammi na tsaye jigum-jigum da ka dubi fuskokinsu za ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa. Bayan Raihan ta fito daga wanka doguwar rigar Mommy ta zaman gida ta saka, har lokacin fuskarta a kumbure take ta ƙarasa falon. A inda ta bar su a nan ta koma ta same su, tana zuwa Daddy ya nuna mata kujera yana faɗin, "Zauna nan." Ta lura da Fuskar Daddy babu alamun wasa don haka jikinta ya yi sanyi, a takure ta zauna Daddy ya dube ta yana cewa, "Laifin me kika yi Al'amin ya sake ki don na san haka kawai ba zai sake ki ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba." Hawaye ne ya zubo mata ta kalli Daddy za ta yi magana kuka ya ci ƙarfinta. Murtuke fuska ya yi cikin tsawa ya ce, "Ba kuka na ce ki raira min ba amsa za ki ba ni idan ba haka ba, ranki ya yi mummunan ɓaci." Tun da take da Mahaifnta wannan ne karo na farko da ta gan shi a wannan yanayin ba, bakinta na rawa hawaye na zuba ta ce, "Wallahi ban san me na yi masa ba ina fitowa daga wanka na ji ihun Sumayya, zuwana wurinta ke da wuya sai kawai ya wanke ni da mari daga ƙarshe ya ce ya sake ni." Kafe ta da Ido Daddy ya yi tana rufe baki ya furta, "Kin tabbata abin da kike faɗa haka ne?" Raihan ta gyaɗa masa kai. Inno ta yi kicin-kicin ta haɗe fuska Daddy na miƙe wa ta ciro wayarta daga cikin ɗan tofinta ta miƙe masa tana faɗin, "Audullahi ungo kira min Faruku." Da mamaki Daddy ya ce, "Inno wane Faruku kuma." Inno ta sake ɗaure fuska ta ce, "Faruku barista ɗan uwana za ka kira min wallahi mai hana ni ɗaure wannan fitsararren yaron Aminu sai Allah, saboda Allah baiwa aka kai masa zai rufe ta da duka ya korota kamar mara gata?" Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "To kawo akira shi." Daddy karɓa ya danna lamabar Inno ya kira don ya san idan ba haka ya yi mata ba, tun da ta hau sama ba za ta yadda da duk lallashin da zai yi mata ba. A kunnenta ta ji ƴar baturiya na magana, don haka ta ja dogon tsaki ta miƙa hannu ta karɓi wayar tana cewa, "Allah wadaran naka ya lalace shi dai Faruku a haka zai ƙare kullin waya a kashe." Daddy fita ya yi ya bar su Inno suna ta sababi. Ita kuwa Mommy baƙinciki goma da ashirin ne ya mamaye zuciyarta, don haka uffan bata tanka musu ba tana ayyana abubuwa da yawa a cikin zuciyarta. Da farko Daddy ya yi niyyar ya taka har gidan Malam ya same shi amma sai ya yanke shawarar kiransa a waya, ɗakin da yake saukar baƙi ya shiga ya zauna ya danna wayar Malam bugu biyu Malam ya ɗauka da sallama sannan ya ce, "Alhaji ɗazu muna magana ba mu ƙarasa ba." Muryar Daddy babu walwala ya furta, "Malam akwai ƴar matsala." Da sauri Malam ya furta, "Ta me fa?" Nan take Daddy ya zayyane masa duk abin da yake faruwa, salati Malam ya ɗauka ransa a matuƙar ɓace ya furta, "Yanzu haka Al'amin zai watsa min ƙasa a ido ban sani ba, ni Al'amin zai wulaƙanta ya nuna ban isa ba kenan?" Daddy ya ce, "A'a Malam abi lamarin a sannu kasan sha'anin yaran nan ka fara jin ta bakinsa ka ga sai a ji komai." Malam cikin huci ya furta, "Ina zuwa Alhaji." Malam ya kira wayar Al'amin ya fi a irga amma ba a ɗauka ba da yake ya saka ta a silient. A fusace ya shi ga motarsa kai tsaye ya nufi asibitin, saboda tsabar sauri gani yake hanyar na ƙara yi masa tsayi. Wurin da aka tanada saboda ajiye motoci (Parking space.) Ya ƙarasa ya ajiye motarsa, a gaggauce ya fito ya ƙarasa cikin asibitin tun daga nesa ya hango Al'amin a bakin wani ɗaki a tsaye. Al'amin na hango Malam hantar cikinsa ta kaɗa gabansa ya yi mummunar faɗuwa, Malam na ƙarasawa Ammi ta furta, "Malam har ka ƙaraso?" Bai tanka mata ba ya ƙarasa wurin Al'amin ya ɗauke shi da wani azababban mari, yana ɗago wa ya sake ɗauke shi da wani marin. Takaici, baƙinciki haɗe da baƙin rai suka sake mamaye zuciyar Malam. Ya dubi Al'amin a fusace yana faɗin, "Na gode Al'amin, na gode ka ji. Yanzu ka nuna min na haife ka ne amma ban isa da kai ba. Wallahi ka ji na rantse idan har ni na haife ka, ka je maza ka ɗauki ƴar mutane ka wuce gidanka da ita." Ammi da bata fahimci komai ba ta shiga tskiyar su Malam tana faɗin, "Me yake faruwa Malam?" Da hannu ya nuna mata Al'amin sannan ya furta, "Ki tambayi ɗanki zai gaya miki irin rashin mutumcin da ya aikata." Malam ya juya a fusace zai bar wurin har ya fara takawa ya juya ya ce, "Idan ka ga dama ka same ni a gida." Daga haka bai sake furta komai ba ya wuce ya shiga motarsa ya fice daga asibitin. Da tsananin mamaki Ammi ta dubi Al'amin ta ce, "Me yake faruwa Al'amin." Al'amin da hankalinsa ya fi na koyaushe tashi ya ce, "Ammi laifi ne don na saki Raihan alhalin cin amanata take yi, Ammi har fa maza take kawo min cikin gida amma kina jin abin da Daddy ya faɗa." Idanu ta zaro waje ta ce, "Innalillahi'wa'inna'ilahirraji'un. Yanzu dai kar ka ɓata lokaci ka ga a yadda mahaifinka ya fita maza ka je kiran da ya yi maka." Amsa mata ya yi jiki babu ƙwari ya wuce wurin da motarsa take, Mahaifiyar Sumayya ce ta cika fam don ba ƙaramin haushi ta ji ba ganin irin abin da Malam ya yi wa Al'amin akan Raihan amma ko ta kan tata ƴar da take kwance bai bi ba. Lokaci-lokaci take kallon wurin Ammi tana wurga mata harara, suna nan zaune wata Nurse ta ƙarasa wurinsu ta ce za su iya shiga wurin Sumayya amma bata buƙatar hayaniya. Al'amin na zuwa gida a ɗarare ya shiga falon Mahaifinsa, ƙafa ɗaya ya saka Malam ya dakatar da shi da cewar, "Koma mu je gidansu Yarinyar nan za mu." Al'amin na son yin magana amma yana fargaba don yanayin Mahaifinsa ba ƙaramin tsorata shi ya yi ba. Al'amin ya yi tsammanin motarsa Malam zai shiga, amma ga mamakinsa sai gani ya yi ya buɗe ta shi motar ya shiga. Motarsa ya koma ya zauna sannan ya kunnata suka wuce gidansu Raihan, sai da suka je bakin gate sannan Malam ya ciro waya ya kira Daddy da yake ta zarya shi kaɗai a falon baƙi. Yana ɗauka Malam ya gaya masa suna ƙofar gida don haka da kansa ya je ya buɗe musu, Al'amin sai sunne kai ƙasa yake kamar sabuwar amarya. Falon baƙi ya kai su bayan sun sake gaisawa suka sake jajantawa juna abin da ya faru, sannan Malam ya ce sun zo ne su ba shi haƙuri don Raihan ta koma gidan Mijinta. Daddy da kansa ya je ya kira Raihan tana tafe gabanta na faɗuwa har ta shiga ɗakin, a can gefen ta rakuɓe ta gaida Malam ya amsa mata cikin tausayawa don kallo ɗaya za ka yi wa Raihan ka fahimci tana cikin matsananciyar damuwa. Raihan na daga tsugunne ta ji suna maganar komenta a hankali ta ɗago ta ce, "Daddy saki uku fa ya yi min." Daga Daddy har Malam buɗe baki suke yi haɗe ta yin salati, Malam ne ya fara faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Daddy ne ya dakatar da Malam yana faɗin, "Malam ba haka ake ba, yaron nan yau tsawon watansu nawa ko ƙara ɗayansu babu wanda ya taɓa kawowa, ya kamata aji ta bakinsa ba a rufe shi da faɗa lokaci ɗaya ba." Daddy ya ƙarasa maganar yana tambayar Al'amin. Sunkuyar da kai ƙasa ya yi ya sanar musu iya abin da ya sani game da duk abin da yake faruwa a tsakaninsa da Raihan, sannan ya ciro waya ya nuna musu duk abubuwam da aka taɓa tura masa na Raihan da wani matashin saurayi. A razane Daddy ya miƙe tsaye ya furta, "Kabiru? Wannan cin amanar Kabiru zai yi min?" Raihan da a lokacin ta kai idanunta wurin ta zaro ido ganin Hotonta da Kabiru a maƙale da juna a yanayin da suke kamar ma'aurata, ko ma'aurata bai kamata su ajiye irin wannan hoton a wayarsu ba. Jikinta na karkarwa ta miƙe tsaye tana faɗin, "Wallahi-wallahi Daddy ban san komai ba Allah ba ni ba ce sharri aka yi min..." Raihan ba ta ƙarasa magana ba Daddy ya katse ta, ta hanyar zabga mata mari. A fusace ya shaƙo wuyanta yana faɗin, "A gidan uban wa yake yi miki ƙarya? Allah ya sani mun baki tarbiyya daidai gwagwado don haka..." Daddy bai ƙarasa magana ba, Malam ya riƙo hannunsa ya zaunar da shi da ƙyar ya ƙwace Raihan daga hannunsa. A gefen ƙafarsa ya zaunar da ita ya nemi Raihan da ta sanar musu da duk abin da yake faruwa. Nan take Raihan ta zayyane musu duk abin da yake faruwa tun daga farkon aurensu har lokacin da Al'amin ya saketa. Ba ƙaramin mamaki suka yi ba Al'amin tun da ya sunkuyar da kai bai ɗago ba saboda kunya, Daddy ya kalli wayar Al'amin da ke hannunsa ya kalli Daddy ya ce, "Waye Kabirun?" Cikin huci Daddy ya furta, "Shi ne yaron da na gaya maka rashin lafiyarsa." Murmushin takaici ne ya suɓucewa Malam, Daddy ya bishi da wani irin kallo yana shirin magana Malam ya ce, "Alhaji ka nutsu ka ba ni hankalinka a nan?" Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana wurgawa Raihan harara, sai dai a lokacin ya rage jin zafinta. Malam ya ci gaba da cewa, "Yau kwanan Kabiru nawa yana jinya?" Daddy ya yi jim sannan ya ce, "Zai yi wata ko fi ma ina jin." Malam ya jinjina kai ya kalli Al'amin ya ce, "Na ji ka ce wannan na jikin hoton shi ne wanda ya fito daga ɗakin Raihan ɗazu ko?" Cike da gamsuwa Al'amin ya gyaɗa kai ya ɗora da cewa, "Kuma wallahi ko Sumayya aka tambaya za ta faɗa don ba wannan ne zuwansa na farko gidan ba." Malam ya kalli Daddy ya ce, "Ban yi mamaki ba." Daddy ya dube shi da alamun tuhuma yana faɗin, "Kamar yaya Malam?" Malam ajiye wayar Al'amin sannan ya ɗora da cewa, "Huzaifa!" Ɗauuu! Haka Daddy ya ji maganar Malam har tsakar kansa, yana cikin nazari ya riski muryarsa yana ci gaba da cewa, "Tabbas Huzaifa ya ci kasuwarsa ya watse kuma buƙatarsa ta biya domin ba na raba ɗaya biyun wannan yana daga cikin kaidinsa. Alhaji ba sai na yi maka dalla-dalla ba tun da, da idanunka ka je ka gano Kabiru a garinsu ko magana baya yi sannan kuma ace har yana zuwa wurin Raihan. Shin tun da kake kiran lambar ka taɓa samun ta shiga? Ko kuma ka taɓa zama ka tambayi Raihan don ka ji ta bakinta?" Al'amin sai girgiza kai yake, Malam ya kalle shi sannan ya ci gaba da faɗin, "Ka ba ni mamaki Aminu da baka da dogon nazari da lissafi domin tun kafin ka auri yarinyar nan ban zayyana maka matsalar da take fama da ita ba? Ban ce maka duk wani abu da ka gani ba daidai ba ka sanar da ni? Kai fa mai ilimi ne ina tarin ilimin naka da ba za ka yi aiki da shi ba? Tun wuri ka dawo hankalinka domin muddin ka ɗore a haka soyayyar matarka za ta kai ka jahannama." Malam ya dubi Raihan ya ce, "Je ki ciki ƴar gidan Abba." Raihan ta miƙe kanta na sara mata ta wuce cikin gida, a tsawace ya dubi Al'amin ya ce, "Sakaran banza sakaran wofi, ka buɗe kunne ka ji ni da kyau. Dama matuƙar matarka ta warke ka cewa iyayenta su wuce gidansu da ita. Yadda na faɗa maka haka za ka shaida musu." A firgice Al'amin ya dubi Mahaifinsa. Malam ya nuna masa ƙofa ya ce, "Fice ka ba ni wuri." Kamar sabon munafuki haka Al'amin ya fice sum sum sum daga ɗakin gwiwarsa a sanyaye. Malam ya kalli Daddy ya ce, "Khalid Saleh wani amintaccen Aljani ne da mun ɗauki tsawon shekaru tare, a daren jiya ya sanar da ni ya gano wurin da Huzaifa ya samu mafaka, ban so gaya maka ba na so ace sai sun kamo min shi zan kira ka, amma tun da lamarin har ya kai ga haka a gobe ina da buƙatar ganin wannan Kabirun mara lafiya." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya furta, "Shi kenan Alhaji zan kira Mahaifiyarsa mu yi magana."Malam ya miƙe yana daɗa bawa Daddy haƙurin abin da ya faru, har ƙofar gida Daddy ya raka shi sannan ya nemi Malam da ya janye hukuncin da ya yanke akan Al'amin amma fir ya ƙi amincewa. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 49 Jiki a sanyaye Daddy ya dawo gida wurin su Mommy, Inno na ganin Daddy ta ce, "Audullahi yanzu nake shirin zuwa wurinku ni fa ban gane ba." Daddy ya zauna akan kujera yana faɗin, "Da me fa Inno?" Da yatsa ta nuna Raihan sannan ta ce, "Yarinya nan ko baiwa ka siyo daga garinku sai haka, saboda Allah haka yaron nan zai zo ya tafi shi da Mahaifinsa salin-alin babu wani cin mutumci da ka yi musu balle ka sa hukuma ta kama su?" Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya ce, "Inno duk wannan abin da yake faruwa Huzaifa..." Da sauri Inno da Goggo suka katse shi cikin haɗin baki suna cewa, "A'uzubillahi minasshaiɗanir rajim." Goggo ta girgiza kai sannan ta ce, "Ka dubi girman Allah Audullahi ka bar ambatar sunan nan a gidan nan ko ma samu kurwarmu ta zauna lafiya." Daddy ya miƙe tsaye yana cewa, "Shi kenan Goggo." Har ya yi gaba ya juyo ya kira Mommy sannan ya shige cikin ɗaki. Nan take Mommy ta miƙe ta bi bayansa don ita ma bakinta cike yake da tambayoyin da take son yi masa. Mommy na wuce wa ɓangaren Daddy, Goggo ta dubi Inno ta ce, "Wai Audullahi ko haushinmu ya ji?" Inno ta taɓe baki ta furta, "Ni ma abin da zan faɗa kika riga ni, amma saboda Allah ina ce Huzaifa dai ba ƙanin Alhaji Babba ba ne?" Goggo ta kalli hanyar sashen Daddy tana cewa, "Baki ga ya kira matarsa ba, ko shawarar me za su yi oho." Raihan na jin maganganun su Inno sun fara damunta ta tashi ta wuce ɗakin Mommy, tana shiga ta haye gado ta kwanta ta shiga tunanin matsalolin rayuwarta. Hawaye ne ya zubo mata saboda tausayin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki, tuno abubuwan da suke faruwa da ita ta fara yi tun tana ƙarama. Tun bata san kanta ba take wata irin wahalalliyar rayuwa gashi har ta girma bata samu sassauci a cikin ta ba. Mommy na shiga ɗakin Daddy ya nuna mata gefen gado, ganin haka ya sa ta zauna jiki a saluɓe tana shirin yin magana ta riski muryarsa yana cewa, "Tsugunne bata ƙare ba." Mommy ta kalle shi ta furta, "Da aka yi yaya?" Wayarsa ya ciro ya fara lalubar lambar Baffan Kabiru sannan ya dubi Mommy ya furta, "Huzaifa ya taka muhimmiyar rawa akan mutuwar auren yarinyar nan domin yanzu haka saki uku Al'amin ya yi mata." A hargitse mommy ta furta, "Saki uku fa?" Daddy ya gyaɗa kansa sannan ya kanga waya jikin kunnensa nan take ta fara shiga, ba a jima ba ya ji Baffan Kabiru ya ɗauka suka gaisa cikin mutumci sannan Daddy ya sanar masa da dalilin kiransa akan kawo Kabiru wurin Malam. Sanin halin Fula ni da mutanen karkara ya sa Daddy ya tabbatar masa da kafin ɗaukan Kabiru zai yi magana da jami'an tsaron garinsu, Baffa ya fahimci abin da Daddy yake nufi don haka ya yi dariya ya furta, "Alhaji yanzu ai babu wannan a tsakaninmu domin mun san ba za ka taɓa cutar da mu ba, Kabiru ai ɗanka ne Allah ya nuna mana gobe da rai da lafiya." Daddy ya ji daɗi don haka ya amsawa Baffa sannan ya tambayi jikin Kabiru, Baffa ya tabbatar masa da yadda yake kullin haka yake har wannan lokacin baya ummm baya umm-umm. Suna gama waya Daddy ya dubi Mommy ya sanar mata da duk abin da ya faru tun daga zuwan su Malam har tafiyarsu. Lamarin ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba, tausayin Raihan ya mamaye zuciyarta ta dubi Daddy ta ce, "Daddyn Raihan an ya Raihan na da rabon aure kamar kowacce cikakiyyar mace kuwa? Ta yiwu haka tata ƙaddara take ƙila mu muke ta abin mu..." Daddy ya katse Mommy da cewar, "Haba Zainab ke fa kike ƙarfafa min gwiwa ta yaya za ki furta irin waɗannan kalaman, Raihan Allah ne ya ba mu ita kum shi zai yaye mata duk wasu matsaloli da ke tattare da ita, duk wanda kika ga bata zauna da shi ba dama can Allah ya rubuta adadin zaman da za su yi da lokacin rabuwarsu, ina kika bar yaron nan Salim wa ya taɓa tsammanin ba za su yi zaman aure da Raihan ba? Wannan abin da ya faru da Raihan da ma can Allah ya ƙaddara mata sai dai mu yi fatan Allah sa haka ne ya fi zama alheri, ta yuwu mijinta yana gaba ta yuwu kuma akasin haka amma duk abin da Allah ya yi mai kyau ne." Jinjina kai Mommy ta yi ta ce, "Tabbas haka ne shi ya sa tun lokacin da yarinyar nan ta ƙwallafa ranta akan yaron nan nake yi mata faɗan ta nemi zaɓin alheri ba son zuciyarta ba, domin ba kowanne abu ne idan muka so shi muka a lokacin yake zame mana alheri ba. Kuma ba komai muke nema a rayuwa mu samu ba don haka a komai ake so ɗan'adam ya riƙe neman zaɓin Allah domin shi ne zaɓin da ba a yin kaico ko nadama a ciki." Daddy ya ajiye wayarsa sannan ya furta, "Wannan gaskiya Allah ya zaɓa mana abin ya fi alheri ." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Tun a cikin daren Daddy ya kira Direbansa ya sanar masa da tafiyarsu zuwa Shanono, gari na wayewa suka ɗauki hanya sai dai kafin tafiyarsu tun asuba Malam ya kira Daddy ya bashi wasu addu'o'in tsari daga shaiɗanu, sannan suka yi sallama. Tun da suka fara tafiya Daddy ya sa aka ware sautin Alƙur'ani mai girma a cikin motar, don haka zuciyarsa wasai yake jinta babu tsoro ko fargaba a zuciyarsa a haka suka shafe doguwar tafiya har Allah ya kai su rugar su Kabiru lafiya. Cikin mutumci da karramawa su Inno wuro suka tarbi Daddy, duk yadda ya ƙi yarda ya ci abinci sai da Inna wuro ta dama masa fura ya sha. Yana gamawa ta yi masa iso wurin Kabiru da yake zaune a ɗakinsa shi kaɗai. Daddy yana shiga ya kalle shi a hankali ya furta, "Allah sarki, Allah ya baka lafiya ka ji Kabiru." Kabiru bai ɗago ba kuma bai tanka masa ba sai Inna wuro ce ta je ta kamo hannunsa, kamar raƙumi da akala haka Kabiru ya bi bayanta har suka ƙarasa wurin Daddy ta damƙa shi a hannunsa. Ba don Baffa ya so ba Daddy ya tilasta masa akan sai sun tafi tare an yi komai akan idonsa, da farko Baffa cewa ya yi shi Daddy ya wadatar a yi komai amma Daddy ya nuna sam ba zai yiwu ba. Kabiru da ƙafarsa ya ƙarasa ya shiga motar sannan su Daddy suka shiga Musa Driver ya fara tuƙi suka ɗauki hanya. Ba su suka shigo cikin garin Kano ba sai bayan sallar Magriba, kai tsaye Daddy ya sa aka wuce da Kabiru wurin Malam. A ɗaki mai lamba biyar aka bawa Kabiru gado, sai da suka saka shi ya gabatar da Alwala ya yi sallah sannan Malam ya sa aka kai masa abinci . Daddy da Baffa suka wuce gida a cewar Malam sai wayewar gari da safe zai fara yi wa Kabiru magana tun da ya lura jinnun jikinsa musulmi ne baya hana shi yin ibada. Baffa na zuwa ya saki baki yana kallon irin dukiyar da aka narka a gidan Daddy, ɗakin da aka kai shi na saukar baƙi kaɗai ya isa abin kallo, ɗakin da Auwalu ya nuna masa da sunan na shi ne gani ya yi har ya kece na Gunduman garinsu. Mamakin irin sauƙin kan Daddy yake don idan kana mu'amala da shi kamar ba shi ne mai tarin dukiya haka ba, abinciccikan da aka ajiye masa kuwa kasa cinye su ya yi sai da gari ya waye aka kwashe wasu. Lokacin da Al'amin ya fita daga gidan yana shiga mota ya kifa kansa akan sitiyarin mota, haka kawai ya tsinci kansa a cikin nadama bai san dalili ba. Tausayin Raihan ya ji don ya san a zamantakewar da suka yi ba ƙaramin cutar da ita ya yi ba, ji ya yi yana dana-sanin rashin neman yafiyarta don ya san akwai tarin haƙoƙinta akansa da bai sauke ba. A haka ya kunna motarsa ya nufi asibiti yana cikin tafiya ya ga wayarsa na haske, sai a lokacin ya tuna da ya saka ta a slient tun tuni. Misscall ya gani rututu na mahaifiyarsa da Mahaifiyar Sumayya sai kuma na Sumayya da baƙuwar lambar da ake tura masa hotunan tsirancin Raihan, alamar gajeren saƙo ya gani don haka da sauri ya gangara gefen titi ya shiga yana dubawa. Wannan lambar ce da aka saba yi masa magana yana shiga ya ga saƙon kamar haka: _Ina taya ka murnar rabuwa da Matata da ka yi domin wannan shi ne samun kwanciyar hankalinka, Raihan tawa ce ni kaɗai har abada babu wani lusari da ya isa ya zauna da ita a inuwar auratayya. Ka gode Allah duk irin cin kashin da kake yi mata ban ɗauki fansa mai tsanani akanka da iyalinka ba, daraja ɗaya ka ci shi ne Azkar ɗin da kuke yawan yi, shi ne ya katange ni da ku amma ban ƙyale ka haka ba indai ina numfashi kai da haihuwa sai dai ka ga wasu suna yi, don dama cike nake da mahaifinka saboda abaya ya so halaka ni akan iyalina Raihan. Tun da har Mahaifinka ya gano lagona zan sake tabbatar maka da komai, domin ni Huzaifa ba na tsoro komai ka ga ya faru Raihan ba ta da masaniyar akai, kuma mahaifinka ya yi ƙarya ya sa a kamo ni matuƙar ina numfashi._" Takaici, baƙinciki da ɓacin rai ne ya mamaye zuciyar Al'amin a fusace ya daki sitiyarin motarsa sannan ya fisgi motar da gudun gaske cikin ɗacin zuciya. Yana zuwa Ammi ta riƙa jero masa tambaya sai dai babu wacce ya ya amsa mata don cewa ya yi ta wuce gida zai zo da safe ya same ta. Mahaifiyar Sumayya kuwa saboda ɓacin rai ko ƙurarsa bata kallah ba, yana shiga Sumayya ta kalle shi haɗe da yin guntun tsaki ta ɗauke kanta gefe. Mahaifiyarta ce ta miƙe ta fita sannan Al'amin ya samu damar janyo kujera gaban gadon Sumayya, yana shirin magana Sumayya ta furta, "Tafi ka koma gidansu. Don Allah ka rabu da ni tun da ta fini muhimmanci a wurinta." Al'amin ya haɗiye yawu mai ɗaci don har lokaci ransa a ɓace yake sannan ya ce, "Ya jikinki?" A daƙile ta furta, "Ciki ne ya riga ya fita me ya yi saura, ai dama na san matsiyaciyar matar nan ba za ta bar ni haka ba. Kwartonta ya sa na yi amma ka saka ƙafa ka tafi gidansu, na san ko limamin garin nan za ka kawo aure ne kai da ita ya ƙare tun da saki uku ka yi, kuma duk mai son aurenta da kai sai dai ya yi haƙuri. Cikin fa ya zube Hubby yanzu wannan ma mun yi asararsa?" Sumayya ta fashe da kuka. Tausayinta ne ya kama shi ya kwantar da murya ya fara lallashinta, kuka Sumayya ta saka sai da ƙyar ta yi shiru. Mahaifiyarta na dawowa ya ce su tafi shi zai kwana da ita a asibitin, yadda ya ga rana haka Al'amin ya ga dare don tunanin Raihan ne ya riƙa yi masa kai-kawo a zuciya, tuno waccen rashin lafiyar ta Sumayya ya yi da irin ɗawainiyar da Raihan ta riƙa yi, haka ya riƙa saƙa da warwara har gari ya waye. Washegari da safe bayan su Daddy sun shirya kai tsaye Waraka Islamic Chemist suka tafi, suna yin parking ɗin motarsu ta Malam na shigowa. Sai da ya yi parking ɗin motarsa sannan ya fito suka gaisa suka wuce ciki, ma'aikatan wurin ne suka riƙa gaishe su cikin girmamawa su Daddy suna amsawa cikin sakin fuska. Duk wani abin buƙata da gari ya waye an yi wa Kabiru, Malam ne kan gaba ya tura ƙofar ɗakin ya shiga baƙinsa ɗauke da sallana. Ga mamaki sai ji suka yi ya amsawa Malam, Baffa ya saki baki cike da mamaki sannan ya yi masa daƙuwa yana cewa, "Hai amma dai Kabiru ka cika shakiyyin bawa, saboda Allah tuni Ibrahim ya wuce ka ke wahalar da mu?" Malam ya yi murmushi yana kallon Kabiru ya ce, "Kabiru yana nan sai dai za ku ɗan ba mu wuri ina son tattaunawa da shi." Babu musu su Daddy suka ja da baya suka koma kan kujerun da ke reception amma duk abin da Malam yake faɗa suna jin sa. Zaman su babu daɗe wa Al'amin ya ƙarasa sai dai ganin Daddy ba ƙaramin nauyi ya yi masa ba, har ƙasa ya gaishe da su a kunyace sannan ya wuce ɗakin da Kabiru yake don zuwansa gida kenan Ammi ta ce Malam ya bar sallahu ya same shi a office. Yana shiga Malam ya nuna masa kujera a gefen gadon Kabiru, Al'amin ya zauna sai dai yana son tambayar Malam dalilin kiransa ganin babu wasa a fuskarsa ya sa ya ja bakinsa ya tsuke, sai kallon Kabiru yake yi yana jinjina hatsabibanci irin na jinnu, don babu abin da ya bambamta Kabiru da mutumin da ya ga ya fito daga ɗakin Raihan. Malam ne ya kalli Kabiru ya ce, "Assalamu alaikum. Bawan Allah da wa nake magana?" Kabiru ya amsa masa sallama sannan ya ce, "Kana magana da Ibrahim Alƙasim Bn Muhammad Mustafa." Malam ya jinjina kai yana faɗin, "Malam Ibrahim me ya sa ka shiga tsakanin bawan Allahn nan da iyalansa har na tsawon wasu kwanaki kuma ba tare da ka furta koda kalma ɗaya ba." Kai tsaye Ibrahim ya furta, "Saboda ba na son buɗe baki a gaban Mahaifiyarsa don na san matuƙar na yi magana za ta roƙe ni akan na bar abin da na furta zan aikata, ni kuma ina ganin girmanta ba zan iya yi mata musu ba." Malam ya ce, "Amma ba ka gani kamar akwai shiga haƙƙi?" Ibrahim ya furta, "Ba wani shiga haƙƙi domin abin da aka yi masa ne ban ji daɗi ba kuma alƙwari na ɗauka ba zai tashi a banza ba." Nan take Ibrahim ya zayyanewa Malam dangantakarsa da dalilin da ya sa ya ce sai ya hukunta Huzaifa, sai da ya gama jawabinsa sannan Malam ya yi murmushi ya ce, "Masha Allah, Ibrahim ba Kakanka ba ne Mustafa shi ne ya riƙe Limanci a yankinku tsawon shekarun baya da suka wuce." Da mamaki Ibrahim ya gyaɗa kai ya ce, "Tabbas haka ne don tun ba a haife ni ba haka Mahaifina ya ba ni labari." Malam yana shirin yin magana Ibrahim ya ci gaba da cewa, "Don Allah Malam karka dakatar da ni domin abin da Huzaifa ya aikata rashin imani ne, na yi maka alƙwari ba zan sake hana shi magana ko jinkiri a jikinsa ba kuma kana nan sai na kawo maka Huzaifa da yardar Allah." Malam ya ce, "Amma wani hanzari ba gudu ba, akwai wasu da suka tafi nemo min shi..." Malam bai ƙarasa magana ba Ibrahim ya katse shi da cewar, "Babu damuwa sai na taimaka musu saboda Huzaifa hatsabibin gaske ne, kuma dama akwai tsohuwar rigima tsakanin Kakana da Kakana ka ga kenan akwai ƴar tsama." Malam ya yi jim sannan ya ce, "To shi kenan Allah ya sa mu ji alheri." Ibrahim ya amsa da Amin. Malam na yin sallama da Ibrahim sai Kabiru ya faɗi gefe jikinsa na karkwarwa kamar mai jin sanyi, a hankali ya yunƙura ya tashi zaune yana ƙarewa wurin kallo. Malam ne ya ƙwallawa su Daddy kira suka shiga, Kabiru na ganin Daddy ya ce, "Alhaji yaushe na zo nan Ina su Inno wuro." Baffa na shirin yi masa magana don kar ya fahinci lalurar da ta same shi, Malam ya yi masa bayanin duk abin da yake faruwa da abin da Ibrahim ya faɗa dangane da neman Huzaifa. Jikin Kabiru ne ya yi sanyi haka kawai ya ji yana kewar abokinsa kuma ɗan'uwansa Ibrahim, ga wani irin farinciki da ya ji musamman da aka ce ga rawar da zai taka dangane da Huzaifa wanda yake son za me musu ciwon ido. Al'amin yana zaune yana kallon ikon Allah, Malam ya dube shi cikin takaici ya ce, "Tashi ka ba ni wuri dama abin da na kirawoka kenan kuma an yi an gama." Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka Al'amin ya fice daga ɗakin, haka kawai ya ji yana jin haushin kansa da kansa. Kwanan Kabiru ɗaya Malam ya sallame shi suka wuce gida, shi kuma Baffa a washegarin ranar da aka sallami Kabiru ya wuce garin Shanono. Jikin Sumayya ya yi sauƙi sosai har an bata sallama don haka cikin dabara Al'amin ya ce mata zai yi tafiya don haka tun da gidan ita kaɗai ce ta wuce gida kafin ya dawo, ba don ta so ba haka Sumayya ta bi su Mami suka wuce can gidansu. Kamar yadda Malam ya bashi umarni haka Al'amin ya koma kwana a gida shi kaɗai Sumayya na gidansu, tunanin duniya ya fara cika masa ƙwalƙwala kuliin sai dai su yi waya shi da ita. Raihan ta miƙawa Allah lamuranta don ba ƙaramar nasiha Mommy ta yi mata ba, haka ya sa ta fara ƙoƙarin fitar da duk wata damuwa daga zuciyarta, don ta fahimci duk irin nasihohin da take yi mata kuma sai a lokacin ta gane ba ƙaramar wauwata ta yi ba, domin a tunaninta idan ta auri Al'amin shi zai wanke mata duk wata damuwa da take ciki. Ɗakin saukar baƙi aka gyarawa Kabiru yake zaune a ciki saboda Malam ya ce a bari ya kwana biyu a nan tukunna. Wannan Dalilin ya sa Daddy ya turawa su Inno wuro da kuɗin mota kamar yadda ya yi alƙwari a baya zai dawo da su ya sa suka taho garin Kano. Tun kafin su ƙaraso Daddy ya sa aka gyara musu sauran ɗakunan saukar baƙin da suke kusa da na Kabiru, lokacin da su Inno wuri suka ga wurin da Daddy ya ba su har da kukanta saboda Farinciki. Shi kansa Kabiru har da ƙwallarsa yana yi wa Daddy godiya, don ma Daddy ya tsawatar masa akan baya son yawan godiyar da yake yi masa. Tun dawowarsa gidan yake ganin Raihan sai dai ya lura tana cikin matsananciyar damuwa, ya yi mamakin yawan kwanakin da ta ɗauka a gidan yana son sanin dalili amma yana tsoro, don tun da ta yi aure yake yin baya-baya da duk wata alaƙa da za ta shiga tsakaninsu. Su Mommy hannu bibbiyu suka rungumi su Inno wuro sai Maryama da jaririnta, lokacin da Raihan ta ga jaririn hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba. Tana son ta samu Kabiru da maganar tana ganin kuma kamar bai dace ba, don haka ta bar abin a cikin zuciyarta. Satin su Inno biyu da dawowa gidan Daddy Malam ya kira Daddy ya haɗa shi da wani yayan maƙocinsa Sarkin ruwa na garin wudul, Daddy ne ya sake yi masa bayanin yanayin Jaririn Maryama nan take ya buƙaci da su je gidan ya gan shi. Lokacin da suka je a harabar gidan suka tsaya Maryama ta fito da Sadiq a hannunta, Sarkin ruwa na ganinsa ya jinjina kai ya furta, "Yarinya wannan ba ɗanki ba ne." Hawaye ne ya ciko idonta don ita kanta ta san kowaye ya ga yanayinsa ya san ba jininsu ba ne. Gudun kar a saka mata wasu-wasi ya sa Sarkin ruwa ya ce ta kira har Mahaifiyar Kabiru don zai je bakin ruwa za su ga abin da zai yi masa. Babu musu ta fito suka shiga motar Malam za su ɗauki hanya tun ba su fita daga layin su Daddy ba jaririn ya riƙa mimmiƙewa sai gani suka yi yana kakari jikinsa ya yi laƙwas numfashinsa ya ɗauke. Sarkin ruwa na ganin haka ya yi murmushi ya ce, " Ina ruwan Lurzu, Ya san ba zai ji da daɗi ba kun ga ya karaya har ya fice daga jikinsa, yanzu abin da za a yi ku binne shi ke kuma yarinya Allah ya baki wani mai albarka." Maryama ta saka kuka saboda ko ba komai sun ɗan shaƙu da shi, Malam da Sarkin ruwa ne suka wuce su kuma Daddy ya yi gida da su. Kamar yadda Sarkin ruwa ya faɗa Kabiru da kansa ya je ya binne shi sai yake jin sa sakayau kamar an cire masa ƙaya. Sumayya tun tana yi wa Al'amin kawaice har ta same shi da maganar komawarta, don ta gaji da zaman gidansu. Shi kuma tun yana yi mata hanya-hanya har ta fahumci akwai abin da yake ɓoye mata don haka wata ranar Alhamis da suna hira ya fito ya gaya mata irin hukuncin da Malam ya yanke, don shi kansa lamarin ba ƙaramin damunsa yake ba tun da har sun doshi wata basa tare ga wata irin kewarta da yake ji. A ɓangare ɗaya kuma har lokacin ya kasa cire tunanin Raihan a zuciyarsa har lokacin ji yake kamar ya zalinci rayuwarta. Shi kuma Malam har lokacin ya ƙi bada fuska don ko gaishe shi ya yi daga ita ba sa doguwar hira balle ya saka ran zai sakar masa fuska, ranar da Ammi ta yi masa maganar fata-fata ya yi mata don sai da ita ma ranta ya ɓaci. Lokacin da Sumayya ta gama jin Al'amin surutai ta riƙa yi kala-kala har tana cewa gara ya saketa ko ta huta da yawo da aurensa akanta. Wannan lamarin ya sake dagula lissafin Al'amin don ko abincin kirki baya ci, duk ya fige ya lalace ya rame. Watan Kabiru guda da dawowa gidan Daddy Ibrahim ya dawo jikinsa, yanayinsa da maganganunsa ya sa Maryama ta fahimci haka don haka ta sanarwa da Inna wuro, ita kuma Inna wuro ta sanar da Mommy. Nan take Mommy ta kira Daddy ta gaya masa don tuni ya fita aiki, da yake har lokacin Kabiru bai koma bakin aiki ba. Daddy na kiran Malam ya sa motar office ɗin su ta zo har gida, wasu daga cikin ma'aikatansa suka tafi da shi har office ɗin Malam. Kusan tare suka ƙarasa da Motar Daddy don yana gama waya da Malam shi ma ya ɗauko hanya, a galabaice Ibrahim ya fara magana."Alhamdulillah Malam mun yi nasara, sai dai ba mu samu damar kama Huzaifa ba don tun kafin zuwanmu Kakansa ya sa shi ya tsere. Amma mun kamo Kakansa kuma mun baje tsibirinsa mun hukunta na hukuntawa mun kashe na kashewa, sai tsiraru da suka karɓi kalmar shahada." Cike da farinciki Malam ya furta, "Alhamdulillah." Ibrahim ya ci gaba da cewa, "Yanzu haka muna tare da Kakansa da wata mace wacce ta roƙi alfarmar mu kawota za ta roƙi gafarar Raihan."Malam ya ce, "Ikon Allah muna ji." Murya na rawa Mugaza ta ce, "Ni dai sunana Mugaza amma Raihan da iyayenta sun fi sanina da Intisar..." Nan take Mugaza ta zayyane musu duk wata alaƙarta da Raihan da yaudararta da yi har zuwa lokacin da Huzaifa ya gano sannan ta ɗora da cewa, "Na kai Raihan Ƙungiyar tsafinmu ne don na bayar da jininta saboda mijina na mutuwar sonta ni kuma kishi ya rufe min ido, saboda matan bil'adam sun fi mu kyau da kyawun siffa nesa ba kusa ba. Da na kaita ashe sa'a ce tare da ita kuma da yake da sauran kwananta a gaba sai su Abar bauta suka gano tana da muhimmanci a cikin ƙungiya. Yanzu haka Huzaifa ya kashe mini ƴaƴana duka saboda na gano maɓoyar ɗan da Raihan ta haifa masa na kashe shi, kuma ya kashe su abar bauta ni ma yana ƙoƙarin kashe ni muka ji alamun zuwan baƙin nan, to da yake dama Jabbul-ƙasi ya san da labarin zuwansa kuma ya ba shi ɓoyayyayun sirrika sai ya ɓace daga wurin mu." Gaɓoɓin jikin Daddy ba ƙaramin sanyi suka yi ba, kusan mutuwar zaune ya yi yana mamakin maganganun da Intisar ta faɗa. Jabbul-Ƙasi ne ya fara magana shi ma cikin gadara duk da a wahale yake ya furta, "Jikana ba zai taɓa kamuwa ba a wurinku don haka na bada kaina koma meye ku yi min domin kuwa dama tsufa ya cimmi ni mutuwata ta kusa." Takaici ya saka Malam ya sa aka yi turare Habbatussauda sannan ya fara yi musu ruƙiyya, ganin sun galabaita ya sa Malam ya tambayi ta ko za ta musulunta amma dukkansu suka ƙeƙashe ƙasa suka nuna matuƙar suka karɓi addinin musulunci sun zubda ƙimarsu. Ita kuma Mugaza ta ɗora da faɗin gara ma Malam ya ƙoneta don ta tsani musulunci kuma gara kisan da Malam zai yi mata akan na Huzaifa. Malam bai saurara musu ba ya ci gaba da karatu duk yadda suka kai ga taurin kai sai da suka galabaita suka fara roƙon Malam cikin ɗimuwa. Bai saurara musu ba ya ci gaba da yi har sai da ya ƙone su ƙurmus. Cike da farinciki Malam ya furta, "Alhamdulillahi." Sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin. Su Daddy ba ƙaramin farinciki suka yi da jin an ƙone su Mugaza don haka suka ci gaba fatan shi ma Huzaifa Allah ya ba su sa'ar kamo shi a ƙone shi kowa ya huta. Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 50 Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya Kabiru ya warke garau ya koma bakin aikinsa, a hankali ya fahimci duk abin da yake faruwa don a wannan lokacin ya gano auren Raihan ne ya mutu har ta dawo gida da zama. Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗe wa Al'amin don ji ya yi duniyar ta yi masa zafi ga takurar da Sumayya take masa don daga ƙarshe ma Mahaifinta ne ya kira Al'amin ya ce masa matuƙar yana son ci gaba da zama da Sumayya ya bashi sati guda ya je ya tafi da ita, idan ba haka ba sai dai ya sakar masa saboda ba za ta ci gaba da zama ba tare da ta san matsayinta ba. Tashin hankalin da ya sake zugar da shi har yake tunanin hanyar da zai samu Mahaifinsa da maganar, a ɓangare ɗaya kuma ga tunanin Raihan ya damalmala zuciyarsa har ji yake zuciyarsa na ingiza shi akan ya je ya nemi yafiyarta wataƙila idan ta ce ta yafe masa zai daina jin damuwar da ya yi da ita a zuciyarsa. Da wata safiyar Juma'a ya je gidansu ya samu Mahaifiyarsa ya sanar mata duk abin da yake faruwa dangane da maganar mahaifin Sumayya, Ammi ba ƙaramin tausayinsa ta ji ba sai dai ita kanta tana fargabar samun Malam ta yi masa magana don wancen karon bata ji da daɗi. Kallonsa ta yi ta furta, "Shi kenan ka je Al'amin zan samu Mahaifinka da maganar." Miƙe wa Al'amin ya yi har ya fara tafiya ya juyo ya ce, "Amm dama Ammi na ce..." Kallonsa ta yi ta ce, "Akwai wani abu ne?" Sunne kai ƙasa ya yi ya ce, "Wallahi Ammi na zalinci Raihan, gani nake kamar na je neman yafiyarta..." Da sauri Ammi ta katse shi da cewar, "Kai da bakinka kake faɗin ka zalinci Raihan Al'amin? Tabbas Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Shi ya sa ba a wulaƙanta ɗan'adam a rayuwa duk ƙasƙancinsa domin baka san baiwa da martabar da Allah ya yi masa ba. Yarinyar nan ta nuna maka soyayya a duniyar nan amma ka yi amfani da wannan damar ka riƙa cusguna mata, ai shi kenan sai ka je idan ka samu ta saurareka to, idan baka samu wannan damar ba shi kenan. Ka ga wannan sai ya zama izina a gare ka domin ɗan'adam duk yadda yake yana da daraja." A hankali Al'amin ya fara tafiya yana zuwa bakin ƙofa suka haɗu da Malam, gaisawa kawai suka yi Malam ya fahimci yana cikin matsananciyar damuwa. Yana shiga cikin dabara Ammi ta sanar masa abin da yake faruwa da Al'amin, murmushi ya yi ya furta, "Yaro man kaza. Shi kenan Allah ya kaimu ranar Litinin sai ya je ya tafi da ita. Ita kuwa Raihan yanzu ai baida iko da ita ruwanta ne ta saurare shi ko akasin haka. Wallahi ni na san dama haƙƙin yarinyar nan ba zai bar shi ba, Allah ya sa dai ta saurare shi." Ammi ta jinjina kai don ta fahimci kamar Al'amin ya faɗa tarkon son Raihan sai dai bata gaya wa Malam ba don ta san ba ƙaramin faɗa zai yi ba. Da daddare Al'amin ya fi minti talatin a ƙofar gidansu Raihan sai ya yi kamar ya ƙwanƙwasa ƙofa sai ya wata zuciyar ta hana shi daga ƙarshe ya yi ta maza ya ƙwanƙwasa. Yana bugawa Auwalu ya leƙa yana tambayarsa, Al'amin ya aro jarumta ya furta, "Am na ce don Allah Raihan za ka kira min." Da mamaki Auwalu ya ce, "Malam Raihan fa?" Al'amin ya ce, "Eh." Amsa masa ya yi sannan ya wuce cikin gida, a lokacin Raihan ita kaɗai ce a zaune a falo tana shan ruwan tea Auwalu na leƙawa ya ce, "Hajiya yanzu wani ya ce a yi sallama da ke." Da mamaki Raihan ta ce, "Ni kuma?" Aulwalu ya amsa sannan ta ce, "Ka je ka ce bata nan." Kamar yadda ta faɗa haka Auwalu ya koma ya faɗa sam Al'amin bai ji daɗi ba, don haka ya buɗe motarsa ya cito Memo ya yi rubutu ya miƙawa Auwalu ya ce ya bata. Ba musu Auwalu ya karɓa sannan Al'amin ya wuce gidan su Sumayya, yana zuwa kamar yadda ƙannenta suka saba tarbarsa a falonsu haka suka yi masa. Yana nan zaune ya ga wata baƙuwar lamba ta shigo masa har sai da ya ji gabansa ya faɗi, don ya ɗauka Raihan ce ta kira saboda a rubutun da ya yi har da lambar wayarsa a jiki. Da sauri ya fita ya zagaya ta bayan ɗakin su Sumayya ya ɗauka, yana ɗaga wa ya ji an yi sallama da muryar namiji. Guntun tsaki ya yi cikin girmamawa aka gaishe shi bayan sun kasa ya ji an ce, "Malam wallahi dama maganar Assignment ɗin da ka karɓa ranar ban zo ba shi ne..." Cikin takaici Al'amin ya furta, "Ban gaya muku a cikin rules and regulations ɗina ban da kira a min complain ba? Ba na son sakarcin banza da wofi." Bai jira cewarsa ba ya katse wayar. Yana zagayowa ta daidai windon ɗakin Mahaifiyar Sunayya ya ji muryar Mahaifiyar Sumayya na faɗin, "Ki tabbata kin ya sha lemon nan domin maganin da na karɓo a wurin Malam ya tabbatar min matuƙar ya sha lemon nan wallahi ba Raihan ba ko bebyn roba ba zai kalleta da sunan so ba." Sumayya ta shagwaɓe murya ta ce, "Mommy ina gidansa ma fa haka kika ce, wallahi hatta layar da kika ba ni na saka a cikin filonsa da wacce na binne duk babu wanda ya yi aiki. Ita kanta Raihan duk asirin da muke yi mata da banga yana wani tasiri a jikinta ba, har gwara lokacin da aka haɗa mata da jinin Kasa shi ne ta riƙa baccin nan. Ni kuma so nake yanzu na gama da Al'amin ko tsohon nan da yake shiga lamuranmu kar ya ce masa ya bi gabas ya bi." Jikin Al'amin ba ƙaramin sanyi ya yi ba, yana nan tsaye har ya gama jin duk irin hirar da suke yi. Yana jin alamun tahowar Sumayya da sauri ya wuce cikin falon, tana ganinsa ta yi farrr da ido tana faɗin, "Hubby ina ta jiranka ina ka je ko ka je yin waya da Raihan?" Murmushin ƙarfin hali ya ƙirƙiro ya ce, "Haba dai wani ɗalibina ne ya kira ni." Lemo ta tsiyayo masa tana fari ta miƙa masa sai da ya karɓa har ya kai bakinsa sannan ya cire ya ɗago yana kallonta ya ce, "Sumayya ada na ɗauke kina daga cikin sahun mata masu tunani ashe sam ba haka ba ne." Ras gabanta ya faɗi abinka da mara gaskiya a rikice ta furta, "Ni kuma me na yi?" Haɗe fuska ya yi sannan ya ce, "Yau da safe na tsinci layu a ɗakinki, ɗaya a cikin fulo ɗaya kuma a cikin kayana har da wacce aka binne a ɗakin Raihan. Sannan har wani wuri na ga an haƙa rami an binne abu a ɗakinki..." Shiru ya yi sai kuma ya kalli kofin hannunsa ya ce, "Sai kuma wannan lemon da na ji ana ce miki na mallaka ne, ashe dama soyayyar da kike min bata tsakani da Allah ba ce?" Hawaye ne ya fara zuba daga idonta ta furta, "Ka dubi girman Allah ka rufa min asiri Al'amin wallahi ba halina ba ne soyayyarka ce ta sa na kasa haƙuri har nake ganin ba zan iya haɗa ka da wata..." A fusace Al'amin ya furta, "Kin ci amanata kin cuci kanki, na so ki tsakani da Allah amma kike neman shan gaba tsakanina da iyayena, tir da halinki kin ba ni mamaki." Al'amin na gama maganr ya dire mata kofin ya fice a zafafe, don akwai ciwo wanda ka yarda da shi ka aminta da shi kake yi masa so na tsakani da Allah ya nemi cin amanarka har ta kai ga yana son ganin ya raba ka da mahaifanka. Hankali a tashe Sumayya ta bazama cikin ɗakin Mami tana ihu, kamar wacce ake kwarawa ruwan dalma. Auwalu na kaiwa Raihan takardar hannunsa mamaki ne ya kamata, a sanyaye ta karɓa don bata yi tsammanin ga daga wurin wanda takardar ta fito ba. Tana karɓa ta fara karantawa kamar haka: "Amincin Allah ya tabbata a gare ki, na zo ne domin na baki haƙuri a bisa zamantakewarmu domin har yanzu zuciyata ta gagara nutsuwa akan abin da na aikata miki. Na zo neman yafiyarki don Allah ki yafe min duk abin da na yi miki a zamantakewarmu ta baya. Saƙo daga Al'amin." Tana gama karantawa daga ƙasa ta hangi lambar wayarsa, hawaye ne ya ciko idonta tana jin wata irin kewa da ƙaunarsa ta mamaye mata zuciya. Rungume takardar ta yi a hankali ta furta, "Na yafe maka duniya da lahira Al'amin saboda kai na musamman ne a birnih zuciyata, na yafe maka saboda Allah, Allah ya yafe mana gabaɗaya." Ƙwallar idonta ta goge ta tashi ta shiga ɗakinta ta ajiye takardar acikin takardunta masu muhimmanci. A ranar kusan kwana ta yi tana tunane-tunane don soyayyar Al'amin sabuwar fil ta dawo mata a zuciya. Al'amin na fita daga gidansu Sumayya kai tsaye gidansa ya nufa, a hargitse ya fara birkice ɗakin Sumayya yana zazzage filonta sai ga layu sun faɗo, ɗaya bayan ɗaya ya riƙa bi yana buɗe su yana karantawa shi abin ma zame masa ya yi tamkar a mafarki. Nan take wata nadama da kewar Raihan ta kama shi yana jin sam bai kyauta ba, don tun da yake a duniya zai iya cewa wannan shi ne abu mafi muni da ya taɓa aikatawa wato cin zarafi da wulaƙanta Raihan. Ranar Lahadi da dare Daddy ya kira shi bayan ya zauna Daddy ya fara yi masa magana, "Aminullah na kira ka ne domin na sanar da kai Kaza na taka ƴaƴanta ne ba don bata son su ba sai don ta koya musu zaman duniya ne, na yi maka hukuncin baya ne don na nusar da kai laifin da ka aikata sam baka kyauta ba, abin da ya faru tsakaninka da yarinyar nan Raihan ban ji daɗinsa ba sai dai ba ni da yadda za mu yi Allah ya rubuta ba za ku yi zama mai tsayi ba, a kullin a kodayaushe ka zama adali ko ba akan Raihan ba kai namiji ne ta yuwu za ka iya ƙara aure nan gaba don haka idan ka ce za ka fifita soyayyar matarka za ka kai kanka halaka. Ka shirya gobe idan Allah ya kaimu ka ɗauki matarka ku wuce gida don..." Da hanzari Al'amin ya furta, "Haka ne Daddy amma wani hanzari ba gudu ba gaskiya ba zan iya mayar da Sumayya gidana yanzu ba. Ita kuma Raihan wallahi na yi nadama Daddy Allah da dama sai na mayar da ita..." Dariyar Daddy ta katse shi sannan ya ce, "Dama ta riga ta wuce maka Aminu. Ita kuma matarka meye dalilin ƙin mayar da ita?" Al'amin ya furta, "Ba komai amma a ɗan bari sai bayan kwana biyu." Jim Daddy ya yi yana nazartarsa sannan ya ce, "Ban lamunce ba, maza umarni na baka gobe ka ɗauki yarinyar mutane ka mayar da ita tun da dama ni na bada umarnin ta wuce gidansu." Fitar Al'amin ke da wuya Daddy ya yi jim yana nazartar lamarin su Al'amin don ya san ruwa baya tsami banza. Kamar yadda Malam ya gaya masa washegari Al'amin ya je ya ɗauki Sumayya ita kanta ba ƙaramin mamaki ta yi ba, don ta fara fidda rai da sake komawa gidansa saboda tsananin fushin da ya ɗauka da ita, sai dai kallo ɗaya ta yi masa wani irin tsoronsa ya ɗarsu a zuciyarta don fuskarsa a tamke take babu alamar wasa. Suna zuwa gida ta shiga ɗakinta a sanyaye shi kuma ya faɗa ɗakin Raihan don tuni ya saka ƙaramar katifa a ɗakin yake kwana a ciki. Zaman Al'amin da Sumayya sai ya koma tamkar zaman doya da manja, saboda daga gaisuwa babu wani abu da yake shiga tsakaninsu. Ko girki ta yi sai ya ga dama yake ci, idan abincin bai yi masa ba ya fita ya siyo takeaway tana kallo ya cinye. BAYAN WANI LOKACI. Abubuwa da dama sun faru Raihan ta cire komai a zuciyarta don haka ta kama kasuwancinta hannu bibbiyu, wannan ya sa ta mayar da jikinta ta yi kyau don babu wani abu da yake damunta domin ta fahimci idan so cuta ne haƙuri magani ne. Kabiru gagara haƙuri ya yi da soyayyar Raihan yana son ya tunkareta da maganar yana shakkun abin da kaje ya zo, domin a kullin yana duba matsayinsa da matsayinta don haka watarana ya samu Inno wuro don jin shawararta game da gabatar da soyayyarsa ga Raihan, sai da ta gama saurarsa cikin tashin hankali, tsoro da firgici ta furta, "Hai lallai Kabiru na yarda baka da hankali, yanzu saboda ka samu wuri har bawan Allahn nan ya taimake mu ya jawo mu jikinsa har za ka ce za ka auri ɗiyarsa? Kana cikin hayyacinka kuwa an ya Kabiru baka haukashe ba? Ka dubi ƴar mai arziƙi kamar wannan ka ce ita za ka aura? Aradun Allah ka na aikata wanna ɗanyen aikin ka san shan ruwanmu a gidan nan ya zo ƙarshe, a kull ka rufa mana asiri mu ci arziƙi mu bar arziƙi a mazauninsa." Cikin Damuwa Kabiru ya furta, "Inno wuro wallahi ba tun yau nake son yarinyar nan ba..." A harzuƙe Inno wuro ta katse Kabiru haɗe da yi masa daƙuwa tana faɗin, "Soyayyar gidanku Kabiru, wai yaushe mutanen birni suka lalataka har kake fitsara a gabana. Kwarankwatsa dubu idan Alhaji ya ji maganar nan sai ya kaika wurin Gunduman garin nan, idan baka yi sa'a ba ya sa a ɗaureka har igiya ta yi saura." Zuciyar Kabiru a dagule ya dubi Inno wuro jiki a sanyaye ya ce, "Yanzu shi kenan Inno haka zan haƙura da Raihan?" Inno Wuro ta wara hannuwa tana faɗin, "Eh ka haƙura da ita tun da dai aurenta ba farillah ba ne, muna hannun Allah muna hannun Alhaji shi yake yi mana komai a rayuwa. Idan kuma bijirewa maganata za ka yi ga ka ga hanya nan je ka Kabiru." A sanyaye Kabiru ya amsawa Inno wuro sannan ya fice daga ɗakin, can ɗakinsu ya wuce ganin yanayinsa ya sa Maryama ta fara tambayarsa amma fir ya ƙi sanar mata abin da yake damunsa, sai dai ta lura ransa a matuƙar ɓace yake. Jim Daddy ya yi bayan gama jin jawabin Alhaji Shatima, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, "Alhaji ka san dai matsalar yarinyar ba sai na gaya maka ba, amma Alhamdulillah jikinta yanzu ya yi sauƙi babu wani abin da yake faruwa da ita. Kuma ban san daga ɓangaren ita Raihan ba ko yaya za ta amshi wannan maganar." Farinciki ya mamaye zuciyar Alhaji Shatima, ya dubi Daddy ya ce. "A yi mata a hankali ka san yara wani lokacin ba a tikasta su, kuma ba da faɗa ake yi musu magaba ba, maganar lalurarta wannan ai mai sauƙi ne Alhaji tun da ansan ciwon neman magani ai ba zai gagara ba." Daddy ya yi murmushi sannan ya ce, "Shi kenan Allah ya tabbatar mana da alheri." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Daddy ne ya raka Alhaji Shatima bakin mota suka yi sallama, yana komawa gida ya samu Mommy tana zaune a dianning da alama jiransa take. Bayan ya zauna ta fara zuba musu abinci tana cewa, "Daddyn Raihan tun ɗazu cikina yake kiran ciroma, har na yanke shawarar zuba abinci na ci don na san hirarku da su Alhaji Shatima bata ƙarewa." Daddy ya yi murmushi ya ce, "Neman auren ƴarki ne ya kawo shi." Mommy ta yi murmushi don ta ɗauka zolayarta yake ta ce, "Alhaji Shatima da ba ƴaƴa maza ba wa zai nemarwa aure, ai gara ku nemi wata dattijuwar ku ba shi tun yau kusan shekarar Hajiya Asabe uku da rasuwa." Daddy ya ɗauki cokali ya fara cin abin ci sannan ya ce, "Allah da gaske Raihan yake so da aure." A hargitse Mommy ta ce, "Raihan kuma?" Daddy ya gyaɗa mata kai. Mommy ta ajiye cokalin hannunta cikin sanyin jiki tana ci gaba da cewa, "Amma kana ganin Raihan za ta amince da shi, duk da bai kaika a shekaru ba amma fa ya bawa Arba'in baya sai na ga kamar ya yi mata tsufa." Daddy ya saka dariya cikin zolaya ya furta, "Ni ma na yi tsammanin haka amma idan ta ga ya yi mata ai shi kenan, ba Alhaji Shatima ba ko yanzu ai zan iya ɗaukan budurwa don hango wata fillo a rugar su Kabiru." Mommy ta wurga masa hararar wasa sannan ta ce, "To zan yi mata magana na ji Allah ya tabbatar da alheri. Ai ba wani abu ba ne Daddyn Raihan ni da kaina zan haɗa maka laife ka ga MD ya samu mai raino." Dariya Daddy yake sosai don ya san halin Mommy macece mai kishi amma duk zafin kishinta ba za ta bari ka gane lagonta ba. Washegari da safe Mommy ta samu Raihan da maganar Alhaji Shatima, Wani iri Raihan ta ji maganar sai dai a wannan lokacin duniya ta koya mata ladabi ba komai take zafafawa ba, domin ta lura ko ka zafafa matuƙar abun ba mai alkhairi a wurinka ba ne sai dai ya wahalar da kai a banza. Jiki a sanyaye Raihan ta furta, "Mommy tsoron aure nake ji don gani nake kamar ba ni da rabo a ɓangarensa. A yanzu ba ni da zaɓi sai neman zaɓin Ubangiji domin a baya na ɗauka son raina shi ne alheri ashe ba haka ba ne, don haka matuƙar kun amince da ɗabi'unsa na amince zan aure shi." Ba ƙaramin tausayi Raihan ta bawa Mommy ba, ta riƙo hannunta cikin kulawa ta ce, "Allah ya yi miki albarka Raihan, insha Allah zan sanar da Daddynki duk yadda ake ciki za ki ji." Raihan ta sakar wa Mommy murmushi don ta lura mahaifiyarta na cikin damuwa da halin da take tsintar kanta a ciki. Daddy na dawowa Mommy ta sanar masa duk yadda suka yi da Raihan, sai da ya sake tambayar Raihan ya ji daga gare ta sannan ya ce zai sanar da Alhaji Shatima domin ba baƙo ba ne a wurinsa tun da abokin kasuwancinsa ne. Alhaji Shatima na shiga motarsa ya daki sitiyarin motarsa haɗe da sakin wata ƙaramar ƙara a hankali ya furta, "Burina ya kusa cika domin na tabbata matuƙar na auri Raihan sai na san yadda na yi na mallaki Kamfanin maganin sauronsa da ke unguwar Tudun murtala, ba zan yi ƙasa a gwiwa ba sai na mallako har katafaren kamfanin takalmansa na unguwar sharaɗa. Domin babu yadda za a yi na nuna masa yadda ake kamun kifi sannan ya fini iya kamawa. Idan na mallaketa sannu a hankali zan nemi hanyar da zan bi domin na halaka shi, daga nan Raihan za ta samu kaso mafi tsoka don haka idan ta samu kamar na samu ne." Alhaji Shatima ya yi ajiyar zuciya ya ci gaba da cewa, "Ina baƙin cikin na ga na buɗi ido na ga bawan Allahn nan domin arziƙinsa kullin gaba yake baya yin baya. Alhalin wasu shawarwarin dangane da kasuwanci ma ni na ke bashi, amma ni kullin ji-iyau ba na yin gaba." Yana gama surutansa ya figi motarsa da gudu ya fice daga layin. Sati ɗaya da zuwan Alhaji Shatima Daddy ya kira shi tare da sanar masa Raihan ta amince da batun aurensa, murnarsa har sai da ta ƙi rufuwa a gaban Daddy. Shi kuma Daddy a tsamminsa tsananin soyayyar Raihan ce ta saka shi yin haka don haka ya sake jin wata irin ƙaunar Alhaji Shatima a cikin ransa. Nan take ya yi masa kyautar wata gonarsa da ke garin Kura, farinciki ya sake lulluɓe Alhaji Shatima ya riƙa zuba masa godiya da fatan alheri don wannan ne ya tabbatar masa da Raihan ita ce daidai macen da yake so mai ƙashin arziƙi tun da ga ƙofofin arziƙi nan sun fara buɗe masa. A ranar sai da suka gaisa da Raihan yanayinta babu yabo babu fallasa, ya gabatar mata da kansa da adadin yaransa da wasu al'amuransa na yau da kullin. A cikin ƙasa da wata guda Alhaji Shatima suka daidaita da Raihan don har kuɗin gaisuwa ya kawo an tsayar musu da ranar aure wata biyu, su Inno baki har kunne don kusan duk zuwan da Alhaji Shatima zai yi ƙullin ledar su na musamman ne, don wata rana da ya ciko musu ƙatuwar leda da kaza suna ci faɗa ya kacame a tsakaninsu har sun fara lissafin idan Raihan ta haihu su za su je zaman daɓaro. Sai da Mommy ta shiga faɗan ta sasanta su da cewar wuyarta dai a yi auren a samu cikin tana haihuwa duka za su je gidan su zauna har sai ta yi kwana arba'in. Raihan ba wata soyayyarsa take ji a zuciya ba don dai kawai ta faranta ran mahaifanta ne ya sa ta lamunce za ta aure shi, don haka bata wani zafafa ba saboda wannan karonma ta ce babu abin da za ta yi, tun da aure ba na ɗaya ba ba na biyu ba. Hasalima wasu ƴan uwan na nesa ma ba a gaya musu ba don gudun surutu. Ranar ɗaurin auren Raihan da gayya Malam ya kira Al'amin bayan ya gaida shi ya ce, "Al'amin ina son ka zo ka kaini wurin ɗaurin aure don yau da ƙafar hagun nan na tashi tana yi min ciwo." Al'amin ya kalli ƙafar Malam ya ce, "Subhanalla Daddy ka haƙura da zuwa tun da baka jin daɗi." Malam ya jinjina kai sannan ya ce, "Da ace da yuwar haka da na haƙura amma Raihan kamar ƴa take a wurina hasalima Mahaifinta ya mallaka min komai na aurenta." A hargitse Al'amin ya furta, "Aure kuma? Tun yanzu za ta yi aure?" Mamaki da dariya suka kama Malam ya ce, "Me ye naka a ciki? Ga abin da na ce maka ƙafa tana yi min ciwo ka zo ka kaini ɗaurin aure." A fusace Al'amin ya yi gaba Malam ya kalle shi yana ƙunshe dariyarsa don dama da biyu ya yi haka don ya harzuƙa masa zuciya, saboda har lokacin idan Malam ya tuna abin da Al'amin ya yi wa Raihan ransa sai ya ɓaci. Wani irin gudu Al'amin yake yi fuska a murtuke babu walwala don haka Malam ya dube shi ya ce, "Aminu ni ko wani abu yana damunka?" Al'amin ya furzar da iska mai zafi sannan ya ce, "Lafiya ƙalau Daddy me ka gani?" Malam ya furta, "To ka ja ni a hankali don na ga gudu kake kamar za ka tashi sama, kuma yanayinka duk sai a hankali." Da to kawai Al'amin ya amsa baƙinciki ya mamaye zuciyarsa har suka ƙarasa ƙofar gidansu Raihan da ke cike damƙam da mutane, suna zuwa Malam ya ce masa, "Sauko mu je don babu jimawa kai za ka mayar da ni." Kamar Al'amin zai yi kuka ya ce, "Gaskiya ni ba zan je ba Daddy ba na son hayaniyar mutane." Malam ya yi murmushi sannan ya fice daga motar, Malam na fita Al'amin ya juya akalamar motarsa ya bawa gidansu Raihan baya sai dai jin zuciyarsa yake kamar za ta hudo ƙirjinsa, don da ace Malam ba Mahaifinsa ba ne babu yadda za a yi ya iya jiransa a ɗaurawa Raihan aure yana tsaye a wurin. Yana nan zaune ya ji an ɗaura auren Raihan tare da Alhaji Shatima akan sadaki dubu ɗari, maimatawar da maroƙa suke yi shi ya sake dagula lissafinsa har ya gagara haƙuri ya kira wayar Daddy don ya ce masa ya fito su tafi amma har ta katse ba a ɗauka ba. Malam bai fito ba sai da suka gama gaisawa da mutane sanaan ya yi wa Daddy Allah sanya alheri ya shiga mota, a lokacin Al'amin ya haɗa kai da sitiyarin mota yana jin ɗaci a zuciyarsa. Yana tayar da mota ya hango wani babban mutun da wata dakakkiyyar shadda yana tafe maroƙa na biye da shi da alama shi ne Alhaji Shatima, karaf ya ji Malam ya furta, "Al'amin ka ga Angon Raihan nan idan ma baka son hayaniya nan babu mutane ya kamata ka yi masa Allah sanya alheri tun da ga Mahaifinta can shi ma ka ƙarasa ku gaisa." Al'amin bai gama jin maganar Malam ba ya figi motarsa ya kamar zai bi ta kan Alhaji Shatima. Daga cikin gida mata ne suke gudanar da yini sai dai babu wasu mutane da yawa, yawancinsu ƴan uwa ne da abokan arzƙi. Raihan ta yi kyau sosai an yi mata ɗinkuna gwanin birgewa sai shiga take tana fita, su Inno suma sun fito shar Daddy ya yi musu ɗinkuna kusan duk iri ɗaya ne. Bayan sallar magriba Daddy da kansa ya ɗauki Raihan ya kaita gidanta da ke unguwar Gaida, yana dire Raihan motocin su Mama Hafsa suka yi parking. Bayan shiga gidan Raihan nasiha suka yi mata sosai kowa maganarsa ɗaya ta riƙe mijinta hannu bibbiyu kamar yadda yake ƙaunarta, ba su ɗauki lokaci ba suka yi mata sallama suka tafi. Fitar su ke da wuya Alhaji Shatima ya shigo tare da abokansa biyu, Raihan tana jin su suna zolayarsa wata maganar idan suka yi har kunya take ji. Su ma ba su daɗe ba Alhaji Shatima ya yi musu rakiya sannan ya dawo wurin Raihan, cike da shauƙin so da ƙauna ya zame mata mayafi yana sakar mata murmushi. Ita ma murmushi ta mayar masa sannan sunne kanta ƙasa, sauka ya yi ya baje musu lodojin da ya shigo da su ya fara ƙoƙarin jan Raihan da hira don ya lura kunyarsa take ji ya ɗora da cewa, "Amarya bakya laifi." Murmushi Raihan ta yi ya ruƙo hannunta suka ba je a ƙasa ya fara bata kayan ciye-ciye a baki tana karɓa a kunyace. Don ba ƙaramin mamaki ta yi ganin yadda Alhaji Shatima ya iya soyayya kamar matashin saurayi ba. Bayan sun ci sun ƙoshi Alhaji ya miƙe don ya ɗauro alwala su gabatar da sallah, wayarsa ta fara ringing yana ɗauka wata baƙuwar lamba ya ga ta shigo kamar kar ya ɗauka sai kuma wata zuciyar ta ce ya ɗauka don ya ji wanda yake kiransa a wannan lokacin da yake shirin amarcewa da amaryarsa. Wayar ya kara a kunne tun bai yi magana ba ya ji an ce, "Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa, don haka ka yi hanzarin zuwa gidan gonarka da ke By pass ta yuwu kafin ka je ka sa mu matattun awaki da shanunka idan kuma ka yi jinkira sai dai ka samu tokarsu." Na ce ba🥵 Auren suger Daddy's fa duniya ne🤭🌚 Na so kammala book ɗin nan a wannan shafin amma sai a na gaba insha Allah, don sai Alhaji Shatima ya hallake mata wancan gayen Huzzy kenan☹️ Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 51 A hargitse Alhaji Shatima ya furta, "Kai yaro saurare ni da kyau ka san da wanda kake magana kuwa." Dariya mai sauti ya ji an yi sannan aka ce, "Azarɓaɓin me kake yi haka Dattijo, indai ni ne da sannu za ka fahimci ko wanene ni." Daga haka ya ji ƙit an kashe wayar." Shiru ya yi yana kallon lambar, Raihan da ke gefe ta ɗago ta ce, "Lafiya kuwa Alhaji." Alhaji Shatima ya ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali don tuni hantar cikinsa ta kaɗa ya ce, "Wani sakarai ne ya kira ni yana yi min surutan iska da wofi, amma share kawai irin ƴan iskan gari ne." Sai da ya ajiye wayarsa ya fara naɗe hannun babbar riga ya ce, "Mutane ba su da hankali wallahi, sai kana cikin farinciki su nemi su dagula maka lissafi." Har ya kai bakin toilet wayarsa ta sake yin ƙara ya saki guntun tsaki ya furta, "Ƙyale ƴan wahala sa yi su gama." Banɗaki ya shiga ya ɗauro alwala ya dubi Raihan ya ce, "My baby shiga ki ɗauro alwala." Ajiye mayafinta ta yi har ta gifta ta gefensa ya rungumo ya haɗe ta da jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, sunkuyar da kanta ƙasa ta yi jikinta ya fara rawa. Alhaji Shatima ya sakar mata kiss a kumatu sannan ta shiga banɗaki don ta ɗauro alwala. Yana zaune ya ga lambar Alhaji Tasi'u ta shigo wayarsa, da mamaki ya dubi lambar ya kai hannu ya ɗauka cikin shaƙiyanci ya ce, "Haba mutumina wannan lamarin akwai shiga haƙƙi fa, ka sa ni ko ina nan ina takara da miraja'a za ka kira ni yanzu..." Bai ƙarasa maganar ba Alhaji Tasi'u ya katse shi da cewar, "Wai baka san abin da yake faruwa ba ne Alhaji Shatima?" Gaban Alhaji Shatima ya yanke ya faɗi cikin hanzari ya furta, "Ban gane ba wani abu ne ya faru?" Alhaji Tasi'u ya ce, "Ga ƴan kwana-kwana can a gidan gonarka tana ta ci da wuta nima yanzu Hafuz ya shigo yake gaya min ya wuce ta hanyar ya ga abin da yake faruwa." Wani irin gumi ne ya riƙa tsattsafowa Alhaji Shatima, jiki da karkarwa ya ce, "Don Allah abin da kake faɗa haka ne?" Haushi ya fara kama Alhaji Tasi'u a daƙile ya ce, "Wai ina yi maka irin wannan wasan ne? Ai ko zan yi maka ƙarya ba zan yi maka akan wannan abin mara daɗin faɗa ba." Alhaji Shatima tun bai katse kiran ba ya wurgar da wayar ya fice a guje wurin harabar motarsa, yana shiga motarsa ya riƙa sakin horn har sai da Maigadi ya fito da sauri ya buɗe masa gate ya fice a guje. Yana fita Raihan ta fito da gudu don ta ji fitarsa ta samu mai gadi a tsaye da alama shi ma jimamin yanayin yadda Alhaji Shatima ya fita yake yi. Da sauri ta tambayi Maigadi wurin da Alhaji ya tafi, hannuwa biyu ya rungume sannan ya ce, "Wallahi Hajiya idan na ce ga wurin da Alhaji ya tafi na yi ƙarya, ina cikin ɗaki na ji yana zabga horn sai na fito na buɗe masa ya fice a guje." Jiki a sanyaye Raihan ta amsa sannan ta koma ɗaki ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido, dabara ce ta faɗo mata ta ɗauko wayarta ta kira lambarsa sai jin ringing ɗin wayar ta yi a bayanta. Tagumi ta zuba hannu bibbiyu tana jiran ta ji shigowar mijinta amma har ta fara gyangyaɗi bata ji motsinsa ba. Miƙewa ta yi ta rage kayan jikinta, ta gabatar da shafa'i da wuturi sannan ta koma gado ta zauna tana nan zaune bacci ya yi awon gaba da ita. Sama-sama cikin baccinta ta ji motsin shigowarsa, da sauri ta zabura tana mutssika idanu ta kalle shi ta ce, "Alhaji ina ka je haka? Tun ɗa zu nake jiranka." Kamar wanda aka zare wa laka a jiki haka ya zauna ya haɗa hannuwa biyu ya rafka uban tagumi, tana shirin sake yi masa magana sai gani ta yi hawaye na zuba bibbiyu a fuskarsa. A rikice Raihan ta dube shi ta ce, "Me yake faruwa ne Alhaji?" Zuciyarsa na zafi ya furta, "Gidan gonata gabaɗaya ya babbake da wuta, hatta dabbobi da tsuntsayen da suke ciki babu wanda ya tsira. Wannan wacce irin masifa ce a ce a daren Angwancina wannan bala'in ya faru da ni." Jikin Raihan ne ya yi sanyi a hankali ta furta, "Innalillahi'wainna ilahirraji'un. Addu'a za ka yi Allah ya sa haka ne ya fi alheri..." Tun bata rufe baki ba a zafafe Alhaji Shatima ya furta, "Alheri a gidan uban wa? Asara kamar wannan ta same ni ki ce Allah sa shi ne mafi alheri? Ko shanu kaɗai kin san guda nawa ne a ciki? Ko shanun da suka ƙone sun haure guda tamanin kar a zo ga raguna da ƙananan dabbobi." Shiru Raihan ta yi don ta lura kamar akanta yake shirin sauke zafin da ya ɗauko, a hankali ta bi gefen gado ta zauna tana nan zaune har bacci ya sake yin awon gaba da ita. Kiran asubar farko ne ya tashe ta, tana tashi ta hangi Alhaji Shatima ya ɓingire a jikin gado da alama shi ma a zaune baccin ya yi awon gaba da shi. Sai da ta ɗauro alwala ta yi raka'atanal fijir sannan ta fara tashinsa, a hargitse ya farka yana faɗin, "Ku yi sauri ku kashe shanu da awakin ciki za su ƙone." Murza ido ya yi da ya ji muryar Raihan tana faɗin, "Na ji masallaci sun kusa shiga ka tashi ka yi sallah." Guntun tsaki ya yi ya miƙe don wani irin haushinta yake ji uwa-uba ga ɓacin ran da yake damunsa. Yana dawowa daga masallaci wayoyin mutane suka fara shigo masa, mafi yawa daga cikinsu masu yi masa jajae ne. Daga cikin masu kira har da Daddy don tun cikin dare ya samu labarin faruwa lamarin, sai da ya yi masa jaje sannan ya ce zai tura masa da tallafin wasu ƴan kuɗaɗe don ya rage asara. Ba ƙaramin daɗi Alhaji Shatima ya ji ba haka abokanansa suka riƙa kiransa kowa da irin gudummawar da yake bashi. Wannan ne ya rage masa raɗaɗin zafin abin da ya faru don wunin ranar haka ya yi ta amsa wayar mutane, Nura da Abubakar ƴaƴansa ne biyu rak a duniya. Suna karatu a Sudan suma sun samu labarin abin da ya faru don haka suka kira mahaifinsu suka jajanta masa akan abin da ya faru. Washegarin ranar haka ƴan uwa da abokan arziki daga ɓangaren Raihan zuwa na Alhaji Shatima suka riƙa zuwa suna yi musu jajaen abin da ya faru, gidan su bai sarara da mutane ba sai bayan la'asar sannan Raihan ta samu ta sake fesa wanka ta shirya cikin doguwar rigar shadda. Ranar da Raihan ta tare Al'amin ji ya yi kamar zai yi hauka saboda tashin hankali, hatta Sumayya ta fahimci abin da yake faruwa da shi don haka ta riƙa baya-baya da shi don ta tabbata idan bata yi da gaske ba sai ya sauke faɗan akanta. Haka daga ɓangaren Kabiru wani abu ya ji ya tsaye masa a rai don har ji ya yi kamar ya fice daga gidan saboda yadda duniyar ta yi masa zafi. Tallafin da Alhaji Shatima ya samu ne ya bashi damar samun ƙwarin gwiwa har ya rage jin zafin Raihan, saboda ya samu kuɗaɗe masu yawan gaske. Don haka magriba na yi ya fita ya sake yi musu siyayyar kamar yadda Angwaye suke yi idan za su shiga ɗakin amarensu, lokacin da ya dawo Raihan na kwance tana danna wayarta ta yunƙura ta yi masa barka da zuwa sannan ta karɓi ledar hannunsa. Plate ta ɗauko a kitchen ta fara saka musu Alhaji Shatima na tayata, da kansa ya ɗauko musu ƙananan kofuna ya zuba musu lemo suka fara ci yana yi mata hira a hankali. Wannan karon Raihan da kanta take ci sai dai Alhaji Shatima na jikinta tsam kamar wai zai kwaceta. A haka har suka gama ci suka taɓa hira sannan suka ya da zango akan gado, ƙirjin Raihan sai bugawa yake jikinta na rawa don haka Alhaji Shatima ya raɗa mata a kunne, "Karki tsoro haba kamar ba jarumar mata ba." Ajiyar zuciya Raihan ta sauke yana ci gaba da aika mata sakwanni masu zafi, tun tana ɗari-ɗari da shi har ta saki jikinta. Jin yana ƙoƙarin shigarta ya sa ta dube shi duk da tana jin nauyinsa, ta kamo hannunsa ta ɗora akanta sannan ta furta. "Don Allah karka manta da addu'ar da Annabin Rahama ya koyar da mu a wurin kusantar iyali." Saboda ita kaɗai ta san irin abin da ta fara ji a jikinta game da shi, ta tabbata akwai abin da yake shirin faruwa don ko kaɗan bata ji Alhaji Shatima ya ambaci sunan Ubangiji don neman tsari. A kunyace Alhaji Shatima ya furta, "Tabbas ko rannan na ji wani Malami ya karantata amma sam ban iya ba." Raihan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce, "Duk abin da na faɗa ka maimaita, saboda mutane da dama na manta wa da wannan addu'ar kuma tana da muhimmanci domin idan Allah ya ƙaddara za a samu rabo shaiɗan ba zai yi tasiri a rayuwar wannan yaron ba, duk wani sharri da kaidin shaɗan da tawagarsa Ubangiji zai kare ku daga sharrinsu." Gyaɗa mata kai ya yi sannan ta fara karanta masa kamar haka: "Allahumma Jannibnasshaɗan,Wajannibnasshaiɗana Marazaktana." Sannan ya ci gaba da aikata mata da kalaman soyayya har ya cimma burinsa. A hankali Alhaji Shatima yake sauke ajiyar zuciya, ya yunƙura ya faɗa banɗaki don tsarkake jikinsa sannan ya dawo ya taimakawa Raihan ita ma ta gyara jikinta sannan suka yi addu'a suka koma bacci. Asubar Fari Raihan ce ta fara tashi yana jin motsinta shi ma ya tashi, tare suka shiga toilet suka ɗauro alwala Alhaji Shatima sai nannan yake yi da ita, Raihan har mamaki take yi zuciyarta fes don ko babu komai Alhaji Shatima ya nuna mata kulawa da tsantsar soyayya. Doguwar riga ya zura ya wuce masallaci Raihan ta tayar da sallah bayan ta idar ta ɗaga hannu ta godewa Allah da ya bata miji mai ƙaunarta yake bata kulawa.Tana nan zaune ta ji shigowarsa, shigarsa ta yi daidai da kiran wayarsa. Kallon Raihan ya yi ya sakar mata murmushi sannan ya ɗauki wayarsa, ganin baƙuwar lamba ya sa ya yi zaton ko masu yi masa jaje ne don tun da abin ya faru mutane kala-kala suke kiransa. Yana ɗauka ya ji an ƙyaƙyace da wata irin mahaukaciyar dariya, ransa ne ya fara ɓaci a harzuƙe ya ce, "Wa ye haka kamar mara aikin yi?" Daga can ɓangaren aka amsa masa da cewar, "Ni ne kuwa mai aikin yi tun da na fara yi maka ɓarna a daren jiya, bar ganin ka shiga gonar da ba taka ba na rantse da hatsabibancin da kakana ya bar min ba za ka keta haddin Raihan a banza ba, Raihan tawa ce kamar yadda na faɗa ina ƙara nanatawa Idan kuma kana tantama ka buɗe Whatsapp ɗin ka zan turo maka hotunan da muka ɗauka a daren jiya bayan fitarka wurin gidan gonarka da ya babbake. Sai da muka ɓarje amarcinmu sannan kuma muka yi hotuna..." A fusace Alhaji Shatima ya katse shi da cewar, "Kai wai me kake faɗa ne? Wacece matar taka?" Dariya aka sake yi sannan aka ci gaba da cewa, "Saurin me kake yi za ka ga gane ko wanene ai, amma kafin nan ina yi maka albishir da na cinnawa kamfanin shinkafarka da na robobinka wuta sai ka ɗauki duk wani mataki da ka ga damar ɗauka. Amma ka duba Whatsapp ɗin ka za ka gani idan ƙarya na yi maka, kuma wallahi da ni kake zance." Ƙit! Alhaji Shatima ya ji an katse wayar, a rikice hannunsa na rawa ya kunna data saƙonni na fara shigowa ya ga wata lamba an turo masa hotuna rututu, yana shiga ya ga hotunan tsiraici ne na Raihan da wani matashi. Raihan na daga gefe jikinta ban da rawa babu abin da yake yi, hawaye ne ya taru a idonta don duk hirar da suka yi ta ji ta a kunnenta. Fuskarsa ce ta haɗe murtuk ya kalli Raihan suna haɗa ido ta fara matsawa da baya tana faɗin, "Na rantse da Allah ban san komai ba. Wallahi duk sharri ne ya yi min ni ban san akan me yake magana ba." Miƙe wa ya yi yana huci ya ƙarasa kan Raihan ya daƙumota, yana shirin kai mata mari wayarsa ta sake ringing. Ganin lambar ɗazu ya sa shi ɗauka da sauri yana karawa a kunne aka ce, "Idan ka sake ka taɓa min mata wallahi sai na yi maka kisan da kare ma ba zai ci ba, don yadda na ƙone gidan gonarka da kamfaninka haka zan ƙoneka ƙurmus." Kashe wayar ke da wuya Alhaji Shatima ya wurgar da Raihan a gefe, lambar mai gadin Kamfanin shinkafarsa ce ta shigo yana ɗauka ya furta, "Haladu lafiya kake kirana da asubar fari?" A hargitse ya ji yana faɗin, "Alhaji wuta ta kama a kamfani yanzu haka da fara mamaye ko ina." Alhaji Shatima bai gama jin maganar Haladu ba ya fita da sauri, kai tsaye motarsa ya ɗauka ya fita da gudun gaske da niyyar ya nufi kamfaninsa. Yana tafe a hanya ya kira lambar Fire service yana ji an ɗauka ya kwatanta musu kamfaninsa da abin da yake faruwa. Gudu yake shararawa kamar zai tashi sama bisa tsautsayi kan motarsa ta ƙwace ta yi wani gidan mai da ke gefen titi, nan take wuta ta tashi gabaɗaya har motar Alhaji Shatima. Duk yadda ya yi ƙoƙarin fitowa ya kasa, kasancewar da sassafe ne ya sa babu mutane a hanyar mutane ba su lura ba sai da wutar ta ruru sosai sannan aka riƙa ɗiban ruwan kwata da ƙasa ana zubawa, daga ƙarshe sai da aka kira ƴan kwana-kwana sannan Allah ya taimaka wutar ta mutu bayan ta ƙone komai ƙurmus, don har ta fara taɓo ƙananan kantunan da ke maƙotaka da gidan man. Rayuka uku aka rasa a wurin daga Alhaji Shatima sai wasu ma'aikatan gidan man mace da namiji, sun ƙone ƙurmus haka aka riƙa ɗaukan hutunansu ana yaɗa wa a shafikan sada zumunta, daga ƙarshe aka samu da ƙyar aka ciro gawar Alhaji Shatima a mota aka haɗa da ta guda biyun aka wuce da su mutuware. Tun bayan fitarsa Raihan ta kasa zaune ta kasa tsaye don bata san fitarsa me zai yi ba, tana nan zaune har gari ya waye sai dai ko ruwan tea ta kasa sha saboda tashin hankali da fargaba. Ta kira wayarsa ya fi a irga amma shiru ta ƙi shiga, tana nan zaune wajen ƙarfe tara na safe ta ji Mai gadi na ƙwanƙwasa mata ƙofa. Sai da ta yafa mayafi ta buɗe ta ji ya ce, "Ranki ya daɗe wani bawan Allah yana bakin gate ya ce Mahaifinki ne." Da mamaki Raihan ta ce, "Mahaifina kuma." Ya gyaɗa mata kai. Dakatar da shi ta yi ta je ta duba wayarta don ta kira wayar Daddy ta ji, sai a lokacin ta ga misscall ɗin Daddy da yawa, tana shirin kiransa ta ga wani kiran ya shigo wayarta, cikin girmamawa ta ɗauka tana faɗin, "Daddy ina kwana." Bai amsa mata ba ya furta, "Ina ƙofar gidanki ki fito yanzu za mu wuce gida." Rass! Raihan ta ji gabanta ya faɗi, tana shirin yin magana ta ji ya katse idonta ne ya ciko da ƙwallah. A hankali ta furta, "Na shiga uku me Alhaji ya ce wa Daddy ko shi ma sakina ya yi?" Hawaye na zuba ta zura takalminta ta fice, a bakin gate ta samu motar Daddy tana buɗe motar bayan ta dubi Daddy ta ce, "Daddy wallahi ban san komai ba sharri ne aka yi min." Kallonta ya yi ganin tana kuka ya sa ya yi tsammanin ko ta san abin da ya faru, amma daga yanayin maganrta ya fahimci ba abin da yake tsammanin ba ne. Cikin tausayawa Daddy ya ce, "Da aka yi me Raiha? Ki gaya min tsakaninki da Allah Raihan." Raihan bata ɓoye wa Daddy komai ba daga ƙarshe ta fashe masa da kuka tana faɗin, "Don Allah Daddy ka gaya masa ba na son ya sake ni ban san me mutane za su ce ba. Idan ya sake ni mutane za su ci gaba da surutu akaina kamar yadda suke yi a baya." Tausayin Raihan ne ya kama Daddy ya girgiza mata kai sannan ya ce, "Mu wuce gida tukunna." Daga haka Daddy ya tayar da motarsa suka wuce gida. A hargitse Raihan ta ɗago tana jin maganar Daddy har sai da ta ji wani irin dum! A kunnenta kamar an buga mata guduma, hawaye ne bibbiyu yake bin fusakar Raihan ta ce, "Daddy ɗazun nan fa ya fita ka ce min ya mutu an ya kuwa ba wani mai kama da shi ba ne." Daddy cikin lallashin ya ce, "Raihan mutuwa ɗaya ce Alhaji Shatima ya tafi sai dai mu yi masa addu'ar Allah ya gafarta masa." Kuka Raihan take sosai zuciyarta na ƙuna jikinta har rawa yake, Mommy ce ta riƙa lallashinta tare da yi mata nasiha har ta daina kukan fili ya zamana sai hawaye da ke bin idanunta. A ranar Daddy da sauran Abokan Alhaji Shatima suka tsaya kai da fata aka bada gawarsa, bayan an sanarwa ƴaƴansa da ƴan uwansa aka yi masa sallah aka kai shi makwancinsa. Mutuwar Alhaji Shatima ba ƙaramin taɓa su Daddy ta yi ba, Raihan har bayan sadakar bakwai gani take kamar Alhaji Shatima zai dawo don har lokacin gani take kamar wani ne ya mutu ba shi ba, saboda a ƴan kwanakin da ta yi da shi ya nuna mata kulawa babu wata magana da za ta faɗa ta ɓatanci akansa, irin kulawar da ta samu ta ƴan awanni ko a gidan Al'amin ba ta same ta ba. Daga haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, Raihan ta ci gaba da zawarci a gidansu tana takaba. Wannan mutuwar ta Alhaji Shatima ita ta sake sarewa Raihan rai ta fidda maganar aure da soyayyarsa a zuciyarta, ta saka wa zuciyarta daga kansa ba za ta sake yin aure ba balle wani abu ya ƙara faruwa da ita ba. Malam da Al'amin da su aka gama zaman makokin Alhaji Shatima, sai dai Malam bai kawo komai ba dangane da zaman makokin da Al'amin yake zuwa a yi da shi sai a ranar da Raihan ta fita daga takaba sannan ya je ya samu Malam a gida. Bayan ya gama sauraronsa Malam ya furta, "A wannan karon ba zan jagoranci neman aurenka a wurin yarinyar nan ba domin a baya ka watsa min ƙasa a ido a wurin mutumin da nake ganin mutumcinsa yake ganin nawa. Ka je ka nemi soyayyar yarinya idan ta ga za ta saurareka shi kenan, idan bata yi da kai kuma Allah ya fito mata da wanda ya fika." Al'amin kamar zai yi kuka ya dubi Daddy ya ce, "Wallahi Daddy kunyarta nake ji." Malam ya riƙe baki sannan ya ce, "Amma dai baka da kunya Al'amin, wato ni ne ba na jin kunya da zan shige maka neman aurenta a kato na biyu ko? Fice ka ba ni wuri kafin ranka ya ɓaci." A sanyaye Al'amin ya miƙe ya fita, ya fi minti talatin a mota yana saƙa da warwara daga ƙarshe ya wuce gida. Tun da Sumayya ta ji rasuwar mijin Raihan hankalinta ya yi matsanancin tashi, don tana tsoron Al'amin ya ce zai dawo da ita ga shi har lokacin ba zaman daɗi suke yo ba balle ta nuna bata amince ba don a wannan lokacin ta san bata da wannan power.Tana zaune ya shiga tana yi masa sannu da zuwa da yauwa kawai ya amsa mata sannan ya wuce ɗaki, jiki a saluɓe Sumayya ta bishi don ya fito ya ci abinci amma ya ce mata baya ci. Duk yadda ta kai ga lallashinsa ya ƙi ƙarshe ma sai cewa ya yi ta fita ta bashi wuri baya son hayaniya, haka Sumayya ta fito fuska ɗauke da hawaye don ta lura yanzu ko kaɗan Al'amin baya gudun gaya mata magana ko ya ɓata mata rai. Tsananin soyayyar Raihan ce ta hana shi sukuni har ya yanke shawarar zuwa gidansu don ya nemi soyayyarta, sai dai cike da ƙwarin gwiwa ya tafi saboda ya san a baya Raihan na mutuwar son sa. Lokacin da ya ce a yi sallama da ita fir ta ƙi fita don tuni ta daɗe da shafe shafin aure daga ranta. Al'amin babu yadda bai yi ba amma ta ƙi fitowa daga ƙarshe ma cewa Auwalu ta yi idan ya kuma zuwa wurinta sai ransa ya ɓaci, Al'amin haka ya juya ya tafi ba tare da ya samu abin da yake so ba. Lokaci ɗaya ya kaɗe ya lalace kamar ba shi ba, Malam na lura da yanyinsa duk da yana jin tausayin halin da yake ciki amma ya ji daɗin rashin haɗin kan da Raihan bata bashi ba, Ammi kuwa da har ta ce za ta je gidan su Raihan domin ta nemi alfarmarta akan a mayar da aurensu, Malam ya ce mata matuƙar ta fita ita ma sai ranta ya yi mummunan ɓaci. Wannan lamarin shi ya sake ɗaga hankalin Al'amin ga shi bai san wurin da zai sami lambarta ba, tun da ya yi zuwa ya fi biyar amma duk lokacin da ya je sai dai ace masa bata nan. Watarana Kabiru yana gidan da ya ji abin da Auwalu ya faɗa kishi ya turniƙe zuciyarsa, a fusace ya fito ya samu Al'amin ya gaya masa magananganu marasa daɗi. Al'amin ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ya dubi Kabiru ya ce, "Akan matata kake gaya min magana saboda baka da mutumci ko?" Kabiru ya yi dariyar rainin hankali sannan ya ce, "Amma dai kai baka da hankali, idan matarka ce me ya sa baka shiga ka ɗauki abarka ka tafi da ita ba. Indai Raihan ce ka rasata kenan har abada lusari mai ƙaramin tunani." A zafafe Al'amin ya yi kan Kabiru a daidai lokacin Daddy ya dawo daga masallaci, da sauri ya shiga tsakaninsu yana ƙoƙarin jin ba asi." Al'amin cikin ɓacin rai ya ce, "Daddy wai akan Raihan wannan banzan yake gaya min magana saboda na aika ayi sallama da ita." Kabiru ya karɓe maganar da cewa, "Daddy ana dole ne Raihan ta ce ba za ta fito ba, wai don na ce ya haƙura zai ce min matarsa ce a ina ta zama matarsa?" Daddy ya tura Kabiru cikin gida ya ce, "Wuce ciki bana son maganar." Sannan ya juya wurin Al'amin ya furta, "Don Allah ka yi haƙuri Al'amin." A kunyace Al'amin ya furta, "Ba komai Daddy ammm... Dama..." Sai kuma kunya ta kama shi ya kasa magana ya furta, "Shi kenan sai da safe Daddy." Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624 52 🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Al'amin na tafe a mota lokaci-lokaci yake sakin tsaki don ya fahimci wani abu a tattare da Kabiru, ya hango kishi ƙarara a ƙwayar idonsa. Babban tashin hankalinsa da ya rasa ta yaya zai samu lambar Raihan balle ya sake bata haƙuri ya nemi soyayyarta. Gashi ya yi juyin duniya akan Malam ya yi wa Daddy magana fir ya ƙi yadda, ya kawo ido ya zura masa don ya ce sai dai ya nemi soyayyarta. Daddy na shiga cikin gida ya samu Raihan a falo tana lissafin wasu kaya da ta yi order su. Zama ya yi a kujera ta kalle shi da murmushi ta ce, "Daddy barka da shigowa." Daddy ya amsa cikin sakin fuska sannan ya ce, "Raihan ashe Al'amin ya zo." Nan take ta haɗe fuska ta ce, "Ya zo Daddy amma ban fita saboda a yanzu ba na son abin da zai sake dagula lissafin rayuwata." Daddy ya yi murmushin irin nasu na manya ya ce, "Amma da kin saurare shi ki ji abin da yake tafe da shi." Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Ai duk abin da yake tafe da shi na yafe masa ya riƙe kayansa Daddy." Dariya Daddy ya yi ya ce, "Shi kenan Raihan ɗin Daddy ba zan yi miki dole ba duk abin da kike so haka za a yi, amma fa kar ki manta aure sunnar Annabi ne." Raihan ta yi murmushi tana cewa, "Daddy ni fa ba komai nace ba amma gaskiya ni da aure kam sai nan da wasu shekaru." Daddy ya nufi hanyar part ɗin sa yana faɗin, "Shi kenan Allah ya nuna mana lokaci." Raihan ta amsa da Amin sannan ta ci gaba da abin da take yi. Duk wata hanya da Al'amin zai bi ya samu Raihan ya kasa don haka wata dabara ta faɗo masa, searching ɗin sunanta ya yi ta shafin sada zumunta, nan take sunan da take kasuwanci da shi ya bayyana wato R-Raihan's Investiment. Farinciki ne ya mamaye zuciyarsa tamkar Raihan ɗin ya samu gabaɗaya, lambar da ya gani a jiki ya ɗauka don haka ya yi saving a wata sabuwar lambar wayarsa don ya tabbata idan ya yi mata magana da layinsa ta yuwu ta gano shi, don a sanin da ya yi mata na baya ta haddace lambarsa. Nan take ya yi mata magana ta Whatsapp. A lokacin bata online sai dai yana danna profile ɗin ta ya ga irin kayan da take oder da branches ɗinta, magana ya yi mata a zuwan zai sayi kaya. Ya yi mata maganar da minti goma ya ga ta duba ta yi masa replay wani irin farinciki ne ya kama shi, nan take ya buƙaci Acc number ta akan zai yi siyayya ta dubu ɗari biyar. Raihan ta ji daɗi sosai har sai da ta yi masa discount na 20k amma da ya tashi a madadin ya tura mata iya kuɗin da suka yi ciniki sai ya tura mata kusan ninkin haka. Ganin haka ya sa Raihan ta tambaye shi ko zai ƙara kaya ne amma ya ce a'a. Mai motar da yake kai mata kaya ta kira tare da bashi address ɗin wurin da za kai. A iya bakin titin Sharada Al'amin ya tsaya ya karɓi kayan ya tafi, da haka Al'amin ya samu mazauni a wurin Raihan domin tana girmama duk wani wanda ya sayi abu a wurinta. Don haka suke yawan gaisawa akai-akai da yake ya ci gaba da siyan kaya a wurinta. Ana cikin haka watarana Al'amin ya bijiro mata da maganar aure, ba ƙaramin dariya ya bata ba don a lokacin ta bashi amsa da cewar, "Yanzu kai ba mu taɓa haɗuwa ko waya ba mu taɓa yi ba sai ka ce kana so na." Al'amin ya yi mata replay, "Ai ba wani abu ba ne indai kin amince za ki aure ni a yanzu zan zo na same ki." Alamar dariya ta tura masa ta rubuta, "Ka yi haƙuri domin na riga da na rufe shafin aure a rayuwata." Duk yadda Al'amin ya so shawon kan Rainan fir ta ƙi amince masa daga ƙarshe ma sai ta daina yi masa replay koda ta ga abin da ya rubuto mata. Ganin wannan dabara bata kai shi ba ya sa ya yanke shawarar zuwa ya samu Daddy duk da yana tsanannin jin kunyarsa akan abin da ya yi wa Raihan. Ranar da ya je Office ɗin Daddy bai yi mamaki ba don tuni Malam ya gaya masa komai game da halin da Al'amin yake ciki, sai da Daddy ya gama sauraronsa sannan ya ce, "Insha Allah zan yi wa Raihan magana idan ta amince shi kenan saboda ka ga Raihan ba budurwa ba ce balle mu yi mata zaɓen miji da kanmu. Amma insha Allah za ta amince da buƙatarka, kar ka samu damuwa Allah ya shige mana gaba." Gwiwa a sanyaye Al'amin ya fita yana fita Daddy ya kira Malam bayan sun gaisa ya ce, "Gaskiya wannan abin da ake yi wa yarona ya yi yawa, a zo a mayar da auren nan ko ya samu kwanciyar hankali amma ka zuge yarinyar nan sai ja masa aji take. Wallahi kar na zuciya na nema masa wata tsaleliyar budurwar ya aura masa." Malam ya yi dariya sannan ya ce, "Ai ko ka nema masa ba zai so ta kamar Ƴata ba ka ga kuwa an yi aikin baban giwa." Daddy ya kwantar da murya ya ce, "Don Allah ya isa haka Malam zan je na samu yarinyar nan na yi mata magana." Malam ya ce, "Ai da ka bari an kwana biyu don ban so ya samu Raihan yanzu ba, na so ace sonta ya galabaitar da shi tukunna." Sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Daddy na zuwa gida ya samu Raihan da maganar Al'amin a zaton Raihan Daddy bai san yadda suka yi da Malam ba, sai da ya gaya mata ta yi ta mamaki sannan ya ce, "Ba tilasta ki na zo yi ba Raihan ki zaɓi zaɓin ranki, kin ga yau Alhaji Shatima kusan shekararsa guda da rasuwa. Kina da ƙuruciyarki don haka lokacin aure bai wuce miki ba. A baya Al'amin ya yi kuskure kuma ya gane kuskurensa don haka mai zai hana ba za ki yafe masa ki amshi tayinsa ba? Na san kin fuskanci ƙalubale da dama a rayuwarki ta fannin auratayya amma haka ba shi zai sa ki ce ba za ki sake yin aure a rayuwarki ba. Ban yi miki dole ba amma ke kanki kin san yadda Al'amin ya haukace a soyayyarki, na sani kin sani ke ma kina ƙaunarsa kin ga tun da ya gane kurensa ki ba shi dama ya gyara, mahaifinsa mutumin kirki ne ya yi mana komai a rayuwa ko don darajarsa ya isa ya sa ki amince masa tun da kina ga da kansa ya baki shawarar irin shan ƙamshin da za ki yi masa. Atoh ni dai babu ruwana don na gayawa Baban naki idan ajin na naku ya tsinke babu ruwana, babu abin da zai hana aura masa tsaleliyar budurwa kina kallo mu sha biki ya tare da abarsa." Murmushi Raihan ta yi a kunyace tana rufe fuska ta ce, "Shi kenan Daddy Allah ya tabbatar mana da alheri." Daddy ya furta Amin sannan ya wuce part ɗin Mommy, a ranar ya sanar da ita da su Inno, da farko su Inno faɗa suka fara yi sai da Daddy ya nusar da su karamcin Mahaifin Al'amin da abin da ya yi musu dangane da ciwon Rainan sannan suka sauko suka saka wa komen auren albarka. Daddy da kansa ya kira Al'amin ya gaya masa a kowanne lokaci yana iya zuwa hira wurin Raihan sannan ya tura masa da lambar wayarta, saboda farinciki har sai da Daddy ya fahimci halin da Al'amin yake ciki. Yana kira ya ji tana shiga amma ba a ɗauka ba, sai da ya kira a na biyu sannan ya ji ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta, "Wa'alaikis salam." Shiru ne ya biyo baya sannan ya ce, "Raihan don Allah ka yafe min duka abubuwan da suka faru a baya." Lumshe ido Raihan ta yi tana mamaki wai yau ita ce Al'amin yake bawa haƙuri haka. Murmushi ta yi ta ce, "Allah ya yafe mana bakiɗaya." Kame-kame Al'amin ya fara yin ganin haka ya sa Raihan ta ce masa tana da uzurin da za ta yi duk da ta faɗa masa haka ne kawai ba don tana da wani uzuri ba, kashe wayar ya yi yana jin farinciki a ransa. Ita kanta Raihan ta jima a wurin zuciyarta wasai soyayyar Al'amin na sake dawo mata sabuwa fil a ranta. Amma ta yi wa kanta alƙwarin za ta kiyaye wurin nuna soyayyarsa ba tare da ya fahimci har lokacin tana matuƙar sonsa ba. Sannu a hankali Al'amin ya kuma zaunar da soyayyarsa ɗaram a zuciyar Raihan, tun tana sha masa ƙamshi har ta fara sakin jikinta saboda yadda ta ga yana nuna mata kula da tsantsar soyayya. Duk wannan abin da yake faruwa Sumayya bata sani ba sai dai ta fahimci a ƴan kwnanakin yana cikin farinciki tun da har ita ma yana ɗan sakar mata fuska. Lokacin da Kabiru ya fahimci Al'amin ya koma wurin Raihan ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba amma ya san babu yadda zai yi don haka ya ci gaba da addu'a akan Allah ya cire masa soyayyarta, don ya san da ƙyar idan Raihan rabonsa tun da ga maganar da mahaifiyarsa ta gaya masa. Kuma ya saka wa zuciyarsa a duniya mutum baya taɓa auren matar da ba tashi ba, haka mace ba za ta taɓa auren mijin da Allah bai ƙaddara mijinta ba ne. Maganar mayar da auren Raihan gabaɗaya sati uku aka saka domin Al'amin ya ce a shirye yake babu abin da ya rage masa, Raihan ta so a ɗaga amma Daddy ya ce su a junansu Manya sun gama magana don haka babu buƙatar sake ɗagawa. Sai a lokacin Al'amin ya sanar da Sumayya maganar mayar da aurensa da Raihan, a lokacin ji ta yi kamar ta yi hauka saboda tashin hankali. Amma har ta gaba surutanta Al'amin bai tanka mata ba, ga shi ya matse mata komai hatta fita sai ta shafe wata guda bata fita ko ina ba. Daga ƙarshe ma tuni ta watsar da huɗubar asire-asire da Mahaifiyarta take ɗora ta akai, wanda ta yi a baya ma ta riƙa neman yafiyar Ubangiji domin Al'amin ba ƙaramar nasiha ya yi mata akan haka ba. Shirye-shirye sun yi nisa daga ɓangarori guda biyun, Mommy da Mama Hafsa suka dage sosai wurin gyaran Raihan. Al'amin har tambayar Raihan ya yi ko akwai wani abu da take buƙata ta ce masa babu, saboda wannan ma ta ce babu abin da za ta yi don har aka ɗaura aure gani take zamanta kamar ba me daɗe wa a gidansa ba ne, tun da a baya ma haka duka aurenta ya kasance. A wannan karonma Daddy da kansa ya ɗauki Raihan ya kaita ɗakin mijinta don dama ba wani taron mutane da yawa suka yi ba, sai ƴan uwa na jiki da abokan arziƙi. Sai dai mutane da dama na tofa albarkacin bakinsu akan auren nata ba wani ƙarko zai yi ba saboda abubuwan da suka faru da ita a baya. Ɓangaren da aka fara kaita da farko nan Al'amin ya gyara mata, sai wurin Sumayya da aka yi wa kwskwarima shi ma ba ƙaramin kyau ya yi ba. Ya canza mata abubuwa da dama sai dai wannan sam bai birgeta ba, haka ta riƙa cika tana batsewa amma Al'amin ko a jikinsa. Raihan tana zaune a ɗaki Al'amin ya yi sallama, hannunsa ɗauke da ledoji ya ajiye su ya ƙarasa gefen da Raihan take zaune. Ajiyar zuciya ta sauke mai sauti, ya sa hannu ya zame mayafinta da sauri ta sunkuyar fa kai ƙasa. Murmushi ya yi ya furta, "Wai kunyata kike ji?" Raihan murmushi ta yi ba tare da ta ɗago ba. Al'amin ya ruƙo hannunta ya furta, "Ta so mu je Sumayya na falo." Miƙewa ta yi a hankali yana gaba tana biye da shi har suka ƙarasa falo, Idanun Sumayya sun yi jawur fuskarta ta kumbura. Sumayya na ganinsu tare baƙinciki ya mamaye zuciyarta, ƙwalla ta ji na neman gangaro mata don haka ta gogeta a fakaice. Nasiha ya yi musu sosai sannan ya miƙe shi da Raihan suka wuce ɗaki. Ledar da ya bata ta kalla a wulaƙance ta yi jifa da ita, wani kuka ne ya zo mata ta shige ɗaki ta faɗa kan gado tana fashewa da matsanancin kuka. Bayan sun shiga ɗaki babbar rigarsa ya cire ya fara fito da kayan da ke cikin ledar, ƙarasawa ya yi wurin da Raihan take zaune ya matseta tsam a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya. Kissis ɗin wuyanta ya fara yi a hankali ya dangana da kunnenta sannan ya furta, "Na yi matuƙar kewarki Hayaty." A kunyace Raihan ta ce, "Allah sa ba zolayata kake ba." Da sauri Al'amin ya ce, "Au haka kika ce? Za ki yi min bayani." Miƙe wa ya yi ya ɗauro alwala sannan Raihan ta ɗauro alwala suka fara gabatar da sallar Nafila, suna gama wa Al'amin ya janyo Raihan jikinsa ya fara ciyar da ita cikin so da ƙauna tun tana kunyar karɓa har ta fara sakin jikinta. Shagwaɓe fuska ya yi ya ce shi ma sai ta bashi, babu yadda ta iya ta riƙa ba shi a baki suna ci Al'amin na aika mata da saƙwannin soyayya. Ba ƙaramin kunya Al'amin ya bawa Raihan ba don ita gani take kamar ba Al'amin ɗin baya ba, duk yadda ta kai ga noƙewa sai da Al'amin ya sa ta suka watsa ruwa tare, da farko ƙi ta yi sai da ta ga zai ɗauketa ta yarda ta bi bayansa. Bayan ta saka rigar bacci suka yada zango a makwancinsu. Raihan na maƙale a jikinsa ya tura kansa cikin wuyanta yana ya fara yawo da hannuwansa cikin sassan jikinta yana faɗin, "Ina fatan dai matacccan tsohon nan bai wuce gona da iri ba." Raihan ta yi masa harara wasa ta ce, "Idan ma ya wuce ai kai ka bashi dama ka nuna baka yi shi kuma ya ce idan baka yi ba ni wuri." Da ƙarfi Al'amin ya matse ta har sai da ta saki ƴar ƙara, haɗe bakinsu ya yi wuri ɗaya yana ci gaba da aika mata saƙwannin soyayya. Sannu a hankali hirarsu ta fara canza salo, Raihan tun tana kunyar mayar masa da martani har huɗubar su Mama Hafsa ta dawo mata wacce suka yi mata kafin a kawo ta, ta zage sosai ta nuna wa mijinta kulawa da soyayya sai da ya yi musu addu'a sosai sannan ya fara ƙoƙarin shigarta. A zaton Raihan tun da Alhaji Shatima ya santa ba za ta ji zafi ba sai gashi a wannan karon tun tana daurewa har sai da ta fara hawaye, duk roƙo da magiyar da take yi masa bai san tana yi ba har sai da ya dawo hayyacinsa. Da fatan dai ban saki layi ba ko🥵🤭🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ Raihan ba ƙaramin laushi ta yi ba, Al'amin ya sake ƙanƙameta a jikinsa a daidai kunnenta ya furta, "Allah ya miki albarka Hayaty." A hankali Raihan ta amsa sai kuma hawaye ya zubo mata ta furta, "Ina ƙaunarka Al'amin tun kafin na san menene so don Allah kar ka bari na rasa ka. Babu namijin da zuciyata ta so kamar kai don Allah kar ka bari na yi maraicinka a baya na jure raɗaɗin rashin, don Allah karka bari na sake rashinka ban san ya zan yi ba idan haka ta kasance." Wani abu ya ji yana yi masa yawo game da ita lokaci ɗaya ya furta, "Shiiii." Sai kuma ya sake haɗe bakinsu wuri ɗaya, salon da Al'amin yake sake nuna mata ne ya ƙara tsoratata, ta kai masa duka a ƙirji tana faɗin, "Don Allah ka bari wallahi da zafi, kuma wallahi ban saba ba kafin kai sau ɗaya kawai aka taɓa yi..." Ya katse ta yana kwaikwaiyar muryarta tare da faɗin, "Ni kuma gaskiya ban gaji ba ki bari na tafi second round." Kuka ta saka masa don ta gama tsorata da lamarin ganin haka ya sa ya riƙa yi mata dariya, da kansa ya kamata ya wuce toilet ya taimaka mata ta gyara jikinta sannan suka koma bacci Al'amin na rungume da ita kamar wani zai ƙwace ta. Asubar fari jikin Kabiru ya rikice a dadddafe gari ya waye Daddy ya da su Inno wuro suka wuce da Kabiru wurin Malam, don tuni dama Daddy ya kira Malam ya sanar masa abin da yake faruwa. Suna zuwa bayan da Malam ya shigo Kabiru ya ce, "Assalamu alalikum." Malam ya amsa masa sannan ya ce, "Malam Ibrahim lafiya ka tayar da bayin Allahn nan ido biyu?" Kabiru ya amsa da cewar, "Lafiya ba lau ba. Domin tare muke da Huzaifa, mun yi gwagwarmaya mun yi artabu da shi har Allah ya ba ni nasara akansa na kamo shi." Malam ya faɗaɗa fara'arsa ya faɗin, "Kai Alhamdulillah. Huzaifa sai ga ka an kamoka ina cin alwashin naka?" Huzaifa ya yi dariya sannan ya ce, "Ba zan taɓa karaya ba wallahi, Ɗanka Aminu ya kusanci matata ya shiga gonar da bata tashi ba wallahi sai na kashe shi kamar yadda na Kashe Alhaji Shatima, salati Malam ya ɗauka ya ce. "Dama kai ne ka kashe Alhaji Shatima?" Huzaifa ya amsa. "Tabbas ni ne, aurenta da Al'amin ni na kashe shi saboda na bi duk hanyar da zan bi don na cutar da shi amma hakan ya ci tura don haka na ɓullo ta hanyar makirci, kuma na yi amfani da zafin zuciya da ƙiyayayyar da yake yi mata, don haka a duk lokacin da Raihan za ta yi wani kuskure zuciyarsa za ta hauhawa har ta ka ga na yi duk abin da na ga ya fiye min har ya sake ta. Da farko ban yi niyyar kashe Alhaji Shatima ba saboda bai aureta saboda yana son zama mai ɗorewa da ita ba, ya aureta ne don cin dukiyar mahaifinta. Ni kuma sai na ci alwashin talauta shi na fara saka masa gobara a gidan gonarsa, so na yi na mayar da shi matsiyancin ƙarfi da yaji. Kwatsam sai ya samu nararsa kusantarta don tun a daren da ya yi niyyar kusantarta na so halaka shi ƙarfin addu'a da tasirinta ne ya hana ni, na so na wahalar da shi kafin na kashe shi don haka na ga ɓatawa kaina lokaci ne saboda haka na jefa motarsa gidan mai suka ƙone ƙurmus." Huzaifa na rufe baki Ibrahim ya ce, "Shi kuma Aminina me ya yi maka da ka ɗauke masa ɗansa?" Kai tsaye Huzaifa ya amsa, "Kulawa ce ta sa, saboda yana ƙaunarta kuma yana matuƙar bata kulawa ni kuma ya sa na ji ina kishin haka, kuma duk hanyar da zan bi don na cutar da shi na kasa saboda mutum ne shi mai riƙo da addini shi ya sa na fakaici matarsa watarana ta fito fitsarin dare ba tare da addu'a ba na sauya mata shi na ɗauke wancen na binne shi da ransa. Wallahi kamar yadda na faɗa da farko hatta mahaifinta ba don na san babu aure a tsakaninsu ba irin kulawar da yake bata da tuni na gama da shi." Ran Malam ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ya ce, "Waɗannan abubuwan da ka yi zalinci ne ka hana yarinya zaman aure kana zalintar mutane kai wanne irin mara imani ne? A yau ba sai gobe ba zan ƙoneka domin kai ba irin sheɗanun da za a bawa zaɓin tuba ba ne, kai azzalumi ne ba za taɓa tuba na fahimci ba ka da rabo." Huzaifa ya bushe da dariya tare da furta, "Ba zan tuba ba matuƙar addinin musulunci kake so na karɓa domin babu addinin da na fi tsana sama da shi, kuma tun a daren jiya na ci alwashin zan kashe kaina na kashe Raihan domin babu amfanin zamanmu a duniyar, don ba zan iya rayuwa a doron ƙasa na ganta tana rayuwa da wani Ɗa namiji a matsayin miji ba ni ba, Raihan tawa ce ba zan taɓa barin rayuwarta ba matuƙar ina duniya tana duniyar. Da ace za ku mallaka min ita zan amshi musulunci saboda soyayyar da nake yi mata, amma matuƙar ina raye Raihan ba za ta taɓa zaman aure lafiya ba in dai ba ni za ta zauna ba." A fusace Malam ya ce, "Ai kuwa ka yi karya a mallaka maka Raihan domin ita ba jinsinka ba ce, don babu wata soyayya tsakanin mutum da aljan don haka har abada ba za ka same ta ba." Huzaifa ya ce, "Eh ba jinsina ba ce kuma yanzu haka ba ita kaɗai ce matata ajinsin bil'adam ba amma na fi jin soyayyarta don ita a wurina ta musamman ce. Matana goma na jinsinku. Ta ɗaya na aure ta saboda rashin addu'ar kwanciyar bacci na shiga jikinta don a duk lokacin da na rasa Raihan a wurinta nake yada zango na biya buƙatata, ta biyu saboda idan tana al'ada daina duk wani azkar take yi hatta ta shiga banɗaki irinmu kuma dama haka muke so. Ta uku na shiga jikinta saboda yin charting ɗin tsakiyar dare domin kullin idan ta yi charting ta gama wayar ma hannunta take ko data bata kashewa bacci yaka awon gaba da ita. Ta huɗun kuwa matar aure ce bata da aiki sai yawo da ɗaurin ƙirji a cikin gida kai ba ɗankwali ni kuma surarta ta burge ni kawai na shige jikinta don yanzu haka rabonta da mu'amala da mijinta kusan wata huɗu kenan, shi mijin na rage masa sha'awarta ita kuwa dama na cire mata sha'awar komai a ranta. Ta shida budurwa ce amma har ta fara manyanta domin na saka mata baƙin jini babu wani namiji da take birgewa har ya ji yana ƙaunarta, ita kuma na aureta ne saboda shigar tsiraici da ƙarin gashin da take yawan yi burinta maza su kalli tsiraicinta. Duk da ina matuƙar son komai na Raihan amma kwalliyar Rukayya mai fidda surar jikinta ta fi jan hankalina saboda har waƙa take kunnawa ta yi bacci ni kuma na yi ta shan shagalina da ita. Ta bakwai ma matar aure ce kuma amarya ce na aureta ana gabda bikinta lokacin da Mahaifiyarta ta kaita wurin Malam Murtala akan a yi mata aiki akan mijin da za ta aura, ita dama na ci alwashin ba zan bari ta haihu ba, don yanzu haka watanta biyar da aure ɓarinta uku. Ta takwas kuma ƙanƙanuwar yarinya ce don bata fi shekara uku ba, mahaifiyarta bata ciki saka mata wando ba don sau tari na je wucewa zan ganta da yara suna wasa wani lokacin a gida wani lokacin a waje daga haka har al'aurarta ta birgeni tun ina wasa da wurin har na yanke shawarar aurarta yadda zan samu yadda nake buƙata. Ta goman kuwa yau kwanana goma da aurenta ciff wata ƴar matashiyar budurwa ce bata fi shakara sha biyar ba, saboda tsinanniyar ƙasanzatarta na aureta saboda Mahaifiyarta irin iyayen nan ne marasa kula. Tuni yarinyar ta fara Al'ada amma har ta yi ta gama uwar bata san ta yi ba, hasalima har yau uwar bata son ta fara al'adar ba. Kuma hatta ɓangarori na jikinta bata gyarawa kuma Mahaifiyarta bata sakata ta gyara, ga shi ko wankan tsarki bata iya ba. Wannan ƙarni da wari-warin jikinta ya sa nake baƙuntarta saboda mu ba ya damun mu tun da dama wurin najasa nan ne makwancinmu. To ka ga duk cikin matan nan nawa wallahi babu wadda nake jin ba zan iya rayuwa babu ita ba sai Raihan, Raihan jinina da tsokata ce ban taɓa son wani abu a duniya kamarta ba don Allah karka raba ni da ita. Don Allah Malam tun ina ganin mutumcinka karka shiga tsakanina da Raihan, Na so Raihan na ƙaunaceta ka barni da ita har ƙarshen rayuwata." Malam ya sauke ajiyar zuciya yana cewa, "Dole kuwa na rabaka da su ba Raihan kaɗai ba domin kana zalintar bayin Allahn da ba su ji ba ba su gani ba." Malam na gama magana ya yi bismillah ya ɗauki haramara ƙone Huzaifa. Taurin kai da taurin zuciya irin na Huzaifa bai sa ya saduda ko ya karaya ba duk irin azabar da yake ji a cikin jikinsa, abu ɗaya kawai yake nanatawa sunan Raihan. Da farko wata zuciyar har ta cewa Malam ya ɗaga masa ƙafa ko zai haƙura da rayuwar Raihan amma sai kuma ya tuna irin ɓarnar da taurin kan da Huzaifa yake da shi da zalincin da ya aikata nan take Malam ya ci gaba da buɗe masa wuta da ayar Allah, tun Huzaifa yana iya magana yana kiran sunan Raihan har ta kai ga ya yi laushi Malam ya ƙone shi ƙurmus. Goge gumin fuskarsa Malam ya yi ya furta, "Alhamdulillahi dukkan yabo sun tabbata ga subhanahu wata'ala. Wannan shi ne ƙarshenka domin matuƙar kana doron ƙasa ba za ka daina aikata ɓarna ba." Ibrahim ya ce, "Malam ni zan wuce don ni ma sai na yi jinyar jikina saboda irin raunin da Huzaifa ya ji min." Malam ya yi wa Ibrahim godiya sannan ya matsa daga jikinsa. Wunin Ranar a a wurin Malam Kabiru ya ƙarasa sai da magriba sannan Malam ya sallame shi, bayan da Malam ya bawa Daddy magugunan ya ɗora da cewa, "Yarinyar nan Raihan ya kamata ta sake dagewa da addu'a tun da akan kunnenka kana jin rabe-raben matan da Huzaifa ya aura kuma kowacce ya kawo dalilinsa. Yawancin mata suna da saka ci don haka jinnu suka fi raɓar jikinsu, Allah ya sake kare mu ya tsare mu daga kaidinsu bakiɗaya. Daddy ya amsa da Amin. Al'amin da Raihan buɗe shafin soyayya sabuwa dal suka yi suna gurzar amarci, Al'amin idan ya shiga ɓangaren Raihan sai sallah ce take fito da shi, Sumayya na daga ɗaki take jiyo hayaniyar wasanninsu da iface-ifacen wasannin soyayya, sai dai idan abin ya yi mata ciwo ta yi kuka ta share hawayenta. Ga shi har lokacin Al'amim ya ƙi sakin jiki da ita ya yarda da ita, komai ta bashi gani yake kamar ta saka asiri a ciki don wani lokacin ma sai ya sakata ta ɗanɗana yake cin abincin ko abin sha. A hankali har Raihan ta fara fahimtar yanayin zaman nasu don haka ta samu Al'amin da maganar da farko ya ƙi sauraronta, sai daga baya ya fahimceta sannan ya ci gaba da bawa kowacce kwana bibbiyunta a lokacin da kwananta na amarci ya ƙare. Sumayya ta sauko sosai ta kama Raihan hannu bibbiyu suna zamansu cikin kwanciyar hankali. Raihan watanta uku laulayin ya takura mata, wata rana da safe Al'amin na shiryawa bayan ya fesa turare da gudu Raihan ta tafi banɗaki tana kwara amai, sai da ta fito a galabaice Al'amin zai ruƙota ta sa hannu ta toshe hanci tana faɗin, "Love don Allah mu je asibiti aman nan ya takura min ga warin turarenka babu daɗi." Ƙarasawa ya yi wurinta ya shafa saman cikinta ya ce, "Ajiya ce na yi anan ki bar damun kanki amma dole dama za mu je asibiti sai na dawo daga wurin aiki ko mu bari sai gobe." Gyaɗa masa kai kawai ta yi don yadda take jin ta tana buɗe baki za ta iya yin wani aman saboda yadda warin turaren yake yamutsa hanjin cikinta. Kabiru ya warware garau, Maryama ta yi wani irin haske da yake laulayin ciki ya karɓeta. A cikin wannan ƴan kwanakin Kabiru ya sayi fili a unguwar Maidile ya fara ginawa, Daddy ne ya wuce masa kan gaba aka yi cinikin filin sannan ya mayar da hankalinsa wurin ginin gidan. Laulayi ya saka Raihan a gaba sosai ta rame ta yi wani irin haske, wata ranar Litinin bayan Al'amin ya kaita asibiti ya sauketa a gida idan ya dawo da daddare zai ɗauketa su wuce gida. Raihan ba haka ta so ba ta so ace ya barta a gida ta kwana biyu saboda ta sake warwarewa don ko abincin kirki bata ci. Bata da abinci ban da kwaɗon rama da zogale, don haka kusan kullin sai Al'amin ya saya ya kai mata. Shi ma tana cin na kwana biyu ya fita daga kanta, tana zaune Mommy ta ƙaraso cikin falon. Da gudu Raihan ta maƙale Mommy tana faɗin, "Mommy wai Ina MD ban ji motsinsa ba?" Mommy ta zauna tana faɗin, "Daddynku ya fita da shi, kin san Allah Raihan kar ki karya ni ina zaune ƙalau ki cuci mijina ki gudu gidanki ki bar ni." Inno da ke gefe ta saki murmushi tana faɗin, "Raihane ni kam wai gidanku akwai safayar ɗaki ko?" Raihan kanta tsaye ta ce, "Eh akwai me za a yi Inno." Inno ta ɗaga hannuwa sama ta ce, "Alhamdulillahi. Allah ya sani haɗa kayana zan yi na koma gidanki da zama, ina dalili ciki ya saka ki a gaba wai Aminu yana baki abinci kina ƙoshi kuwa?" Raihan ta tura baki ta ce, "Wai ke Inno ce miki na yi ciki gare ni?" Goggo ta yi dariya tana ɓallo mata goro ta ce, "Shakiyyar yarinya ga idanunki da hannuwanki nan sun nuna, amshi goro ko kyaji daɗin bakinki kin ji. Ai zuwa Albasu ya kama ni don na ci alwashin babu wanda ba zai zo ba idan kin sauka, Daddawa ma zan sa a yi mini ta kwano guda." Kunyar duniya ta kama Raihan don su Inno babu ruwansu ban da sako zance babu abin da suke yi. Suna nan zaune suna hira Daddy ya dawo, bayan sun gaisa Daddy ya kira Mommy ɗaki. Cikin damuwa ya dube ta yana faɗin, "Zainabu an ya yarinyar nan tana jin daɗin zaman gidan yaron nan kuwa?" Mommy ta yi murmushi ta ce, "To me ƴa me kuma ka gani?" Daddy ya sauya fuska cikin damuwa ya ce, "Na ga fa ta rame ta lalace gaskiya..." Dariyar Mommy ce ta katse shi sannan ta ce, "To ramar Raihan dai ba komai ba ce Jika za ka samu don yanzu haka daga asibiti suka dawo mijinta ya sauketa, kuma na tabbata ciki gare ni don su Inno tuni sun harbo jikinta." Farinciki ne ya mamaye fuskar Daddy, kamar almara haka yake ganin abin wai shi ne zai ga ɗan da Raihan za ta haifa. Bayan sallar Isha'i Al'amin ya zo har gida ya tafi da ita, sun jima suna hira da Kabiru a ƙofar gida. Lokacin da Al'amin ya zo Raihan na sashen su Inno wuro suna hira, lokacin da za ta tafi har ƙulle-ƙulle Inno wuro ta yi mata dangin su Daddawa da kuka. Raihan ta ɗauki Inno wuro kamar kakarta haka Maryama ta ɗauki Raihan tamkar yayarta don ita take koya mata abubuwan kula da miji da haɗin magungunan da zata gyara kanta. Don haka ta sake zama dass a zuciyar Kabiru, har idan ta yi wani abun ba ƙaramin mamaki take bashi ba. Su Raihan suna komawa gida suka samu Sumayya a falo, tana ganinsu ta ɗauke kai gefe tana tura baki da alamun fushin wasa. Raihan tun daga bakin ƙofa ta nuna Al'amin tana wara hannu haɗe da faɗin, "Wallahi ban da laifi ko ɗaya mijinki ne." Hannuwa biyu Al'amin ya sa ya riƙe kunne ya ce, "Kaina bisa wuya ranki ya daɗe." Sumayya ta miƙe sai da ta je gabansu sannan ta ce, "Wallahi kin ci daraja babyna ke ba zan baki punishment ba amma kai dai Hubby sai ka ɗana tsallan kwaɗo." Raihan ta dubi Al'amin tana yi masa gwalo ta fara tafiya ɗaiɗai sannan ta ce, "Dama ai na ce maka ka zo ka ɗauke ni da wuri kar mu barta ita kaɗai a gida ka ƙi." Al'amin ya marairaice murya yana ƙoƙarin tsugunnawa ya furta, "Ni ma fa aiki ne ya yi min yawa amma ya na iya guda nawa zan yi?" Sumayya da Raihan suka saka dariya don yadda Al'amin ya yi maganar sai ka rantse da Allah kuka zai yi. A falo suka zube Sumayya ta kawo musu abinci, kaɗan Raihan ta fara ci ta ji ya fita daga ranta sai furar da Al'amin ya siyo musu ta iya sha sannan suka ci gaba da hira. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya zaman Raihan da Sumayya lafiya ƙalau babu wata matsala, a haka har cikinta ya tsufa ya shiga watan haihuwarta. Gabanin za ta haihu Sumayya ta samu ciki don ma ita bata cika laulayi mai wahala ba sai dai yawan baccin da take yi. Ranar wata juma'a da asuba Raihan ta tashi da naƙuda ba shiri suka tafi asibiti anan ma wuni ta yi cir tana naƙuda sai ƙarfe ɗayan dare Allah ya sauketa lafiya ta haifo Jaririyarta mace gwanin sha'awa. Kamarta ɗaya sak da Al'amin sai hasken fatar Raihan da ta ɗauko, Sumayya ita ta kula da ita a asibiti har a washegari aka sallameta suka wuce gida. Farinciki wurin Al'amin da su Mommy abin baya musaltuwa, Al'amin ya so a wuce da Raihan gidansa amma su Mommy suka buƙaci da a kaita gida. Kusan kullin sai sumayya ta je har sai da aka yi suna, ranar suna Jaririya ta ci sunan Zainab ake kiranta da Nihla. A lokacin da Raihan ta haihu tuni Kabiru ya kammala gidansa sun koma can har su Inno wuro da zama, Maryama ta sake haihuwar Jaririnta namiji kyakkyawa mai kama da ita, sha tara ta arziƙi su Kabiru suka haɗowa Raihan Daddy ba ƙaramin daɗi ya ji ba. A haka har Raihan ta shafe kwana Arba'in da haihuwa, ranar da ta yi kwana Arba'in da ɗaya Al'amin ne ya je gidansu yana fitowa daga mota Kabiru na parker Lifan ɗinsa Maryama ta sauko, sai da suka gaisa ta wuce ciki ta bar Kabiru da Al'amin suna gaisawa Kabiru na zolayarsa sannan suka shiga cikin gidan. A falon baƙinsu Raihan take saukar Al'amin yana zaune ta shigo sanye da doguwar rigar Abaya, sai baza ƙamshi take ga wata ƙiba da ta yi jego ya karɓeta. Nihlanta ta ƙara girma tana shiga ya rungumo su ya haɗe goshinsu wuri ɗaya, a ɗan kunyace Raihan ta fara ƙoƙarin ƙwacewa tana faɗin, "Kalbee kar fa wani ya shigo." Al'amin ya sake matseta yana faɗin, "Wai don Allah yaushe za a mayar min da matata, i always miss you, yau fa kina Fourty one days." Cikin zolaya Raihan ta ce, "Ka san mu sai an yi Arba'in uku ake mayar da mace gidanta idan ta haihu..." Tun bata ƙarasa ba Al'amin ya katseta da cewar, "What? Ashe kuwa su Mommy za su neme ki su rasa don wallahi guduwa zan da matata." Raihan ta saka dariya ta ce, "Amma wallahi da an yi mara kunyar siriki, amma ina ƙanwata ya jikinta." Al'amin ya karɓi Nihla sannan ya ce, "Wallahi tana nan jikinta da sauƙi kullin sai ta yi min maganar yaushe za ki dawo." Daga bakin ƙofa suka ji muryar Kabiru yana faɗin, "Za mu iya shigowa ko mu koma?" Cikin Shakiyanci Al'amin ya ce, "Gaskiya ka koma don ina tare da iyalina kar ka shigo a samu matsala." Kabiru ya ɗaga labulen ɗakin cikin dariya ya ce, "Wallahi sai dai ka yi wa Gwauro wannan gorin daɗin abin na riga shiga daga ciki, nima kuma tare da matata nake." Al'amin ya yi dariya sannan ya furta, "Oho dai amma baka ji me haushe ya ce ba Mai mace ɗaya aminin gwauro." Kabiru ya rungumo Maryama ya ce, "In dai haka ne ni da kai ai ɗaya muke yanzu, tun da sai dai ka zo ka rage zafi ka yi gaba yanzu ma zan shiga na ce su Mommy su bari sai ta ƙara Arba'in huɗu nan gaba." Raihan ta dubi Kabiru tana faɗin, "Fillo ban san lokacin da ka ƙuna ba wallahi yanzu baka kunyar faɗar magana sam." Har ya juya za su tafi ya juyo ya ce, "Gashi nan ki hukunta mijinki shi ya lalata ni da surutu don wallahi idonsa a soye yake." Gabaɗaya suka saka dariya lokaci ɗaya. TAMMATA BIHAMDULILLAH🥰 Anan littafin nan ya zo ƙarshe ta yiwu akwai kura-kurai da wasu abubuwa da kuka karanta da bai yi muku daɗi ba, ni ƴar Adam ce tara nake ban cika goma ba kuskuren da na yi a labarin Allah ya yafe mana gabaɗaya. Faɗarkawar da na yi Ubangiji ya ba mu ikon ɗauka ya tsare mu daga sharrin dukkan wani shaiɗani. Na gode sosai da yadda kuka juri karanta labarin nan ba dare ba rana yau na yi posting gobe ban yi ba, na ji daɗi ƙwarai da yadda kuka saka kuɗinku kuka sayi abin da na rubuta wannan ma ƙauna ce kuma ina alfahari da haka. Allah ya bar zumunci ya saka da alheri ya bar zaman tare.🌚 Mu haɗe nan gaba cikin wani littafin, shima salonsa daban yake lbrn na musamman ne, za ku ji tsantsar zalinci😰 ban tausayi da Al'ajabi. Don Allah a taya ninda addu'ar samun nasara Monday zan fara exams👏🏼 Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki yi min mgn 0706 206 2624