♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ _MARUBUCIYAR_ *ZAINABU ABU* *ZAZZAFAR KISHI* *LADIDIN KAUYE* *NANCY YAR KARYA* _AND NOW_ 👇 *♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️*. Whattpad Momislam2021 Zainabhabibu713@gmail.com _INA MIKA GODIYATA GA ALLAH DAYA BANI IKON SAKE RUBUTO MUKU WANAN TAK'AITACCEN LABARIN ALLAH KAYAFE MANA ZUNUBAN MU AMEN_ WANAN LABARIN K'IRK'IRA NE BANYISHI DAN CIN ZARAFIN KOWA BA ,INYAZO DAI _DAI DA LABARINKI KO LABARINKA TO HASASHE NE KAWAI 👌. *GARGA'DI* _BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI BA WLHI DUK WANDA NAKAMA BADA IZININA BA TO ZAN'DAU MATAKI MAI TSAURI_ *JINJINA* _INA MIK'A GODIYATA GA MASOYANA ABIN ALFAHARI NA ALLAH YABAR ZUMUNCI._ ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* EPISODE 1 & 2 📖______Zazzau ne suke shida mahaifinshi da mahaifiyar shi , suna hira cikin jin dad'i momyn Haruna ta mik'e ,domin d'auko plet a kitchen, fitarta keda wuya ,su dady suka jiyo k'arar alamun ana harbi , da gudu momy ta dawo ,dady yace ”barin lek'a momy na kiranshi amma ina yatafi ,yana zuwa aka harbeshi a k'irjinsa , daganan ya kwanta ciwo tundaga ranar yazamo bashida lafiya." Gidane babba kai dakaga gidan zakasan nera ta zaune , 6angare biyu ne a cikin gidan kuma duka komai nasu kala d'aya ne, wa da k'ani ne a cikin gidan ,wato da Alhaji Haruna da Alhaji Bashir ,suntaso cikin kulawa da tarbiya mai kyau , Alhaji Haruna shine babba yaro ne ga Alhaji muntari shikuma Alhaji Bashir d'ane ga Alhaji Yusif , Alhaji Muntari yayane ga Alhaji Yusif , y'a y'an nasu suntaso cikin wadata da k'aunar junansu a fili kenan ,komai 'iyayen zasuyi tare suke yimusu haka iyayensu mata ma basa ban banta komai nasu a tare suke yimusu , wata rana Alhaji Yusif ya kwanta rashin lafiya ashe cutar ajali ce , Allah ya k'ar6i abinsa , yabar Haruna ,a hanun Alhaji Muntari , kulawa Alhaji Muntari kebawa y'ay'an duka biyu , sai dai 'iyayen mahaifiyar Haruna sun ,buk'aci da koma gida tunda ta tafi bata sake wai wayar gidan ba ,dukansu suna zaune a Kano unguwa uku , Alhaji Muntari yanada budurwar y'a fara kya_kyawa da wuya ta wuce bataja hankalin jama'a ba y'ar gata kenan kome ta fad'a shiza'ayi babu tangard'a , mahaifin Haruna yafi na Bashir kud'i dan haka ,maman Haruna da rasuwar mahaifinshi ta dank'awa Mahaifin Bashir komai hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba saboda yana facaka da dukiyar d'an uwan 'nasa." Tun da mahaifin Haruna ya rasu rayuwa tayi masa k'unci bashida walwala a cikin gidan bare yasake suyi wasa da Bashir , tsangwama harara kyara babu wanda bai saba dashi ba , shine yake yiwa wanan budurwa mai suna Fauziyya wanki ko pants da bra ta cire shine meyi mata wanki tun yana kuka haryazo ya saba , lokacin da yacika shekara goma yafara bijirewa umar ninsu, a lokacinne daga uwar har y'ar suka tsiro da wata azaba ta musamman da suke gallaza masa." Yanzu kam banbanci ya wanzu tsakaninsa da d'an uwansa yasan ba d'aya suke ba , yafara sanin hankalin kansa ,shiyasa yafara ja baya da komai na gidan baya zuwa inda ba'a kirashi ba ,hakan da yakeyi yasa suka fara kiransa magulmaci a cewarsu yayi gadon munafurci , bashida bakin magana sai dai yabisu da ido ,hatta makarnta an ban bantasu boko da islamiya kowa da tashi ." Alokacin da Haruna ya cika shekara goma sha takwas ,baya barin bashi ,amma ya maida hankalinsa ga karatunsa , baya wasa ko kad'an gashi Allah ya hore masa ilimin islama dana boko ,bashida mugunta ko k'an amma yanzu yafara koya kasancewar ya taso cikin rashin jin dad'in rayuwa..✍️. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Follow me on wattpad Momislam2020 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mun gode *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 3 & 4 _____Kwance yake a k'ayataccen gadon sa ga sanyin AC dake k'adawa Bash kenan baban yaro baya harka da y'ay'an talakawa ,wayarsa ce tafara ring ,d'agawa yayi murya mai kamada na mai bacci yace ”yane ? kinwani dameni nacemiki 'inna fito zanmiki transfer ko? daga d'ayan 6angaren budurwar tace ”ai kagama 'aikinka dole kadinga k'osawa da bani hakki na , dariyar mugunta Bash yayi yace ”ke y'ar tasha niba talaka bane kuma bamuyi gadon talauci ba, so kizo guest hause d'ina kizo ina jiranki , Bash ne yayi wata razana niyar dariya lokacin da yaji ta kashe wayar , k'wayoyi ya 6allo har guda uku ,ya sanyasu cikin fanta ta roba , dan yasan tana zuwa ,saitasha fanta ,kasan cewar tabashi labarin dad'in da fanta take yimata , bayan ya zuba ,wanan magani ya gir giza ya maida fridge , yakoma bedroom d'insa ya kwanta ,jin alamun an danna door bell yasashi mik'ewa sbda gidan babu masu gadi , da Sauri ya fice yana killer smile ya bud'e mata gate d'in , ganinta yayi tayi shiga gunin ban sha'awa 'amma a zuciyar babu tsoron Allah , hijab ne a jikinta har k'asa ga nik'af data sanyawa fuskarta , saikuma hand bag d'inta data rataya kamar mai shirin zuwa islamiya ." Asma'u kenan y'a ga malam haliru iyayenta na zaune a nan kano gidan k'an k'ara , ta taso cikin tarbiya mai kyau, kowa yasan babanta babban malami ne yana koyarwa kuma yana bawa mutane temako , Asma'u ita kad'ai Allah yabasu , ta taso cikin gata suna da rufin asiri dai _ dai gwar gwado , inka shigo gidansu ka ganta bazakace ba mutuniyar kirki bace ,wanan shi ake kira da zul waja haini ,wato masu fuskoki biyu , mahaifinta ya sanyata 'a makarantar boko ta dai dai halinsa , yanzu tana matakin sakandiri aji biyar ,mahaifiyarta tayi bakin k'ok'arinta gurin bata tarbiya , kaf anguwar su Asma'u batada 'abokin fad'a gashi kowa tagani bata yimasa kallon raini , tana bawa babba girmansa kuma duk cikin k'awayenta babu wacce tasan metake aikatawa sai wata k'awarta guda d'aya ." Rik'o mata hannu Bash yayi cikin salonsa na yaudara ,babu musu ta mik'a masa suna tafiya yana k'ok'arin cire mata hijab , dakatawa tayi cikin tuhuma tace ”nazofa kar6ar kud'inne , kashe mata ido Bash yayi yace ”to muje ciki man ko drinks kisha kinsan fa d'azu nasa aka cika fridge da fanta , wow Asma'u tace ”ta shige ciki da gudu , shikuwa Bash kafin ya shiga saida ya taka rawa , da shigarta ta yada zango a kan lallausan kujerun da suka k'awata madai daicin d'akin , fridge ta bud'e ta hango d'aya ce a gidan k'an k'ara ,d'auko wa tayi tana k'walawa Bash kira , shigowa yayi yana dariya to kisha man sai in d'auko miki kud'in d'azu na ciro a Bank farr da ido tayi masa yin hakan ya k'ara rikir kita bash burinsa kawai yaga Asma'u tasha fanta yafara aiwatar da nufinsa Harun 'ne zaune zauren karatu rik'e da wani littafi , wasu y'an mata ne su biyu sukayi masa sallama ,amsawa yayi ya maida hankalin sa kan karatun sa kasancewar yanzu ya dawo cikin makaranta da zama kuma sunada lecture anjima , budurwar mai suna Sadiya ta ta6o d'ayar k'war tata cikin muryar 'rad'a ,tace ”wanan gayen fa ya had'u amma yanada girman kai , ta juyo ta fuskanci Harun tace ”to malam ai kayi bak'i ka tsaya da karatun kaji ko dame sukazo ko ?" Harun 'nne ya d'ago kya wawan idanunsa masu sanya y'ammata fad'awa batare da sun ankare ba ya k'are musu kallo ya bud'e jajayen lip d'insa yace ”afuwan a tunanina duk wanda kuka ganshi a nan kunsan ba gurin hira bane gurin karatu ne ? tsayawa kallon sa sukayi harya kai ga tashi Sadiya batasan ya mik'e ba saboda dimple d'in kuma tunsa da suka tafi da komai nata, k'awarta ce ta ta6o ta tareda janyo mata hannu tace ”dallah banza 'akan wanan yamu tsatsen gayenne zaki wani tsaya bada mata , cikin jin haushi Sadiya tace ”kul walhi duk mutuncin da mukeyi dake zamu 6ata , wanan gayen da kike gani ni kaf cikin makarantar nan banga mai kyansa ba ko ke ,sedai in bazaki fad'i gaskiya ba , gashida haske ga sumar kai kamar na India ga sajensa gunuin ban sha'awa ga hannayensa a murd'e wow nifa yayimin lips d'insa kuwa suma abin kallo ne bare inya lumshe fararen idanunsa wayo k'wata ki temaka min , juyawa Sadiya tayi taga k'awar tata ta tafi , oh ashe ni kad'ai naketa haukata ,cewar Sadiya...✍️. 🤏 Kunsan fa salon labarina daban yake🤷‍♀️ kudai muje zuwa . Amma please masu cewa na kara yawansa suyimin afuwa yau ciwonkai wlh nake fama dashi , yakamata afara sharhi 🥰. Comments ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 5 & 6 ____ Bud'e murfin gorar tayi seda ta shanye tass sanan ta yarda gorar , jin wani yanayi a tare da ita yasata fara lumshe ido tana kiran sunan Bash cikin could voice d'inta ,da sauri ya k'araso ya rik'o mata hannu tare da cewa baby ,meyafaru , idanun Asma'u a rufe ta maida kanta bisa kujera bata yimasa , magana ba hakan yabashi damar cici6arta ya kaita bedroom d'insa a uzubillahi ya Allah ka tsare mana zuciyoyin mu , k'ok'arin cire mata riga yake amma ina jin wani nauyi da tayi yasashi mamaki , juyi tayi da jajayen idanunta ta waresu ,hakan ko ba k'aramin tsorata Bash yayi ba , yana cikin kallon tane yaji wani azababen mari a kumatunsa , a zuciye ya mik'e yana nuna Asma'u da yatsanshi yace ”dan ubanki ko ubanki bai....yakuma jin wani gigitaccen marin belt d'inshi ya cire yana shirin dukanta ta fizge tashiga zula masa , cikin jigata Bash yace ”wlh saikinyi nadamar dukana , wata irin dariya yaji kamar bata mutane ba , jada baya yakeyi tana nufoshi har sai da suka k'ure bango ... Kwance Harun yake a madai dai ciyar katifar sa wayace a hannunsa yana chart a whtsapp , jin kira ya shigo wayarsa yasa shi duba sunan mai kiran babu suna , saida aka kuma kira sanan ya d'aga cikin sanyayyar muryar sa yace ”Aslamu Alaikum , wow budurwar tace ”amincin Allah yatabata a gareka Harun , amen yace ”tare da cewa dawa nake magana ?"daya can 6angaren tace ”Basmah ce d'iya ga Alhaji Hamisu mai nera , smile Harun yayi yace ”to ina tunanin kinyi wrong number ne , no Basma tace ”nasani kai nakeson muyi mgna , ohk inajinki a gur guje dan inada abin yi , maganar ta daki Basma 'amma itace mai so dole ta daure , am Harun gaskiya ina sonka , what!! soyayya ?Harun ya mai _maita ,oh am sorry ko baka soyayya ne , eh Harun ya bata 'amsa dakin adana kalamanki wata k'ila suyi miki amfani kuma kiyi hak'uri ni ba soyayya nazoyi makaranta ba , runtse ido Basma tayi idanunta sunyi ja tace ”amma bai kamata kadinga gayamin magana ba koda yake nice na zubar da class d'ina da har nake neman ka amshi soyayyata ta kashe wayar , rik'e kai Harun yayi yanajin zuciyarsa babu dad'i to shi y'amma tan da suke bibiyarsa ya gaya musu soyayya yazoyi , shikad'ai yake surutun sa , ya mik'e yashiga madai _daicin toilet d'insa ya watso ruwa ya dawo , ganin kayan abincin sa sun k'are kuma bashida isasun kud'i a hannunsa yasashi niyar zuwa gida yau , motarshi ya shiga driving yakeyi amma tunani ya 'addabi zuciyar sa ,to yanzu mezan cewa dady gashi komai nawa ya k'are banida isashen kud'i a account d'ina , ganin yashigo anguwar tasu yasashi kawar da tunanin yayi horn megadi ya bud'e masa , parking yayi a parking spice yafito ya nufi cikin gidan ." Direct part d'in Dady 'ya nufa a hankali yake tafiya kamar wanda k'wai ya fashewa a ciki ,jiyo wata muguwar dariyar da dady keyi ne yasashi.k'arasawa da sauri , la6ewa yayi a k'ofar d'akin yana jiyo maganar da dady 'yakeyi , a razane ya dire guwai woyinsa a k'asa cikin tashin hankali ya fara nuna k'ofar d'akin , can kuma ya mik'e yana layi ya nufi part d'inshi , gado ya fad'a tare da sakin wani mahaukacin kuka yana buga bango ,jiyayi duniyar tayimasa k'unci to shi yazaiyi da rayuwarsa ina zesa kansa wayo ya ilahi , tashi yayi ya d'auko ruwa mai sanyi yasha bacci mai nauyi yayi nasarar d'aukarshi makarkai yakeyi iri_iri , tun karfe biyu na rana bashi ya tashi ba sai k'arfe hud'u ,mamakin tashin hankalin da yaji ne yake kuma mamakin baccin da yayi hoton mahaifiyar sa ya kalla wanda yake a jikin bangon d'akin ,mik'ewa yayi yana murmishi ya shafo gefen fuskarta ya mik'e yaje yayi alwalah yazo ya gabatar da sallah , yana idarwa ya sauya kaya zuwa shadda mai ruwan toka ,ba k'aramin kyau tayi masa ba dama shid'in kya_kyawa ne , agogonshi ya d'aura ya sanya turarukansa ya fice ,kasancewar d'akinshi yanacan nesa da sashin mutanen gidan shiyasa wani lokacin basa sanin shigowarshi bare fitarshi , wayarshi yasa a aljihu ya d'auki key d'in motarshi ya nufi gurinda ya ajiyeta da bismillah ya shiga mai gadi na d'aga masa hannu , ya fice daga gidan ." titi ya hau yafara sharara gudu ,wata anguwa naga ya iso da batada yawaitar mutane my lovely mom ya dannawa kira ko 3mins ba'ayi ba naga mom d'insa ta fito , mai gadin gidanne ya bud'e masa gat d'in ya shiga da motarshi , mom na dariya tace ”manya ashe ana ganinku ?"cikin fara'a yace ”mom karatu ne yasamu gaba kinsan munzo k'arshe , fatan alkairi mom tayi masa ta mik'e domin kawo masa abin ta6awa , Hajiya ce tashigo wato mahaifiyar mom , rik'e da plet a rufe sai kashi ke tashi , da sauri Harun ya isa gurinta ,yace ”toke wayace miki yunwa na kwaso , yana shirin kar6a yana tsokanar ta , Hajiya ce tace ”wato karramakan danayi da dambun naman shine kake gwaleni ko ? a'a Hajiya ba haka bane niyau hira ma nazo ko kinyi ajiyar manshanu ki zubomin dan inasn shi wanda kika bani ya k'are , mirgud'a masa baki Hajiya tayi hakan ko ba k'aramin dariya yabawa Harun ba to menene haka kina abu kamar wata k'waila , cewar Harun ,wabce plet d'in Hajiya tayi ta shige ciki tana cewa kajira uwarka ta kawo maka nidai kabar cin nawa." Mom ce tafito d'auke da k'ato tire da aka cikashi da kayan ciye² ta saukeshi a dining , to shugaba ga abinci najiku kuna rigima da hajiyata ko ?"dariya Harun yasa ya mik'e ya nufi dining , saida ya cika cikinsa sanan ya sauko ya zauna suka fara hira ,mom ce tace ”kasamu aiki fa , fara'a ce ta baiyyana a fuskar Harun yace ”da gaske mom ?"Allah kuwa , a company ne na kayan sawa kakusa zama alhaji , wow godiya nakeyi baisan sanda ya rungume momy ba , cikin jin kunyar Hajiya ,tace ”sakeni man , Hajiya ce ta ta6e baki tace ”bokon naku ya motsa ko ?jibeka jibgege d'an shekara ishirin da biyar amma kana wani rungumeta , Harun ne ya sake momy yafara rawa yana wak'a , Hajiya ko shigewa tayi tana cewa yahudu sun gama daku mom na dariya jin kiran sallahr magrib yasashi mik'ewa yace ”to sai gobe natafi ina dady yo mom ce ta dake fuska tace ”mahaifin nawa ne dady yo ko yayi kyau ,yana dariya ya fice ." Bash daya sha azaba yace ”yau hukuma ce zata rabani dake shegiya ,wani marin yakuma ji an kwasa masa akace ba Asma'u bace , nine nan uban y'an taurin kai kozaka jada nine mara kunya , shiru Bash yayi yace ”bangane ba , wani gurnani da yaji yabashi damar sakin futsari a wando , ka danne mata Hak'inta to dagayau babukai babu zaman lafiya , jin haka yasa Bash bud'e wani akwati yaciro kud'in da baisan adadin su ba ya durk'usa ya mik'a cikin wata firgi tacciyar dariya akace katsira , kwai Bash yaga Asma'u tayi atishawa , zaro ido yayi yaga kuma ga kud'i a hannunta , yana tsoron magana a wanka masa mari ta sanya hijab d'inta ta rataya jakarta ta tura kud'in acikin jaka tace ”B S ko kiss babu ne yau ? wata uwar harara ya watsa mata yace ”kificemin dan Allah kokin ganni a hanya bana bukatar kinuna kinsanni please, cikin tuhuma tace ”to menayi maka? bakomai Bash yace ”yana nuna mata hanyar fita , ficewa tayi 'itadai a iya saninta tasan tasha fanta tayi bacci kuma yabata kud'inta bayan nan batasan komai ba ." Sadiya na zaune a gida tana gurin flawoyin da suke sanyata nishad'i kafa fuwanta na cikin ruwa tana wasa dasu , number Harun ta dannawa kira , lokacin yana kwance yana bacci dan tun baccin asbh daya koma bai tashi ba gashi yanzu k'arfe shabiyu , ring wayarsa ne ya tadashi baisan number ba yasan dai baya wuce y'anmata tunda yanzu kunyarsu ragaggiya ce lol....✍️. *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 7 & 8 ____Zaune suke a baban palorn su da Momy da Fauziyya da Bash , Fauziyya na kwance a cinyar Momy tana yimata shagwa6a , yarinyar da a k'alla zatakai shekara goma sha takwas 18yrs , cikin shagwa6a Fauziyya tace ”Momy nifa banga Harun ba , tsaki Bash yayi yace ”to menene damuwarki dashi ? tunda ba san mutane yakeyi ba , murmishi Momy tayi tace ”ai yakoma makaranta da zama rabona da ganinsa nima na dad'e , Fauziyya ce ta tace Momy bani number sa , mik'a mata wayar Momy tayi ta d'auki number Harun ta mik'e tayi bedroom d'inta , fad'awa gado tayi tafara k'ok'arin kiran sa , Harun dake kwance yana kallo a TV kasancewar yau baije ko ina ba , janyo wayarsa dake ring yayi , wata murya yaji amma yana tunanin kamar yasan mai muryar ,kawar da tunanin shi yayi yana saurarar mai kiran , cewa tayi d'an saurayi yakk kasan jiya nayi missing d'inka ? zaro ido Harun yayi yace ”ina tunanin kinyi wrong number ne , k'ara mak'ale murya tayi tace ”katsaya ka saurareni , anjima dai ina zuwa , Harun ne yace ”karki kuskura kikara ran wanan number ni ba kalar y'an iskan nan bane , dariya Fauziyya tasa ta katse wayar , tafara rawa tana cewa wlh sai na jefaka cikin masifa shege mai farin jini kawai ." Asma'u ce zaune a gida tana tsincewa umman ta shinkafa wani amai ne ya taho mata da gudu ta mik'e taje ma kwarari tayi tasami ruwa ta d'auraye bakinta ta dawo ta zauna , umma dake yanka latas ta kalle ta irin kallon tuhuma , sunkuyar da kai Asma'u tayi , umma ce tace ”dama bakida lafiya ne ?"gaban Asma'une ya fad'i tafara in ina tana cewa um am ...dakatar da ita umma tayi , tasa aka siyo mata abin gwajin ciki saboda , ganin haske dakuma nononta dasuka ciciko ga k'iba datayi tashi daya , umarni umma tabata akan taje tayo fitsari a wata k'aramar kwalba , seda umma tasata yin fitsarinne tafara dana sanin zargin y'arta datakeyi da abinda ko a mafarki bazata aikata ba , sun san sunbata tarbiyar mai inganci , kawar da tunanin Umma tayi ganin Asma'u tadawo da fitsarin , gwadawa umma tayi ganin result din yasata.... Yau Harun yafara zuwa aiki ba laifi gurin yayi sosai kuma akwai albashi mai tsoka wanda dan danan mutum zai tara arzik'i na ban mamaki , kullum yana busy bashida lokaci , yana gurin aiki kasancewar shi mutum ne mai maida hankali a abinda yasa , a gaba wata k'ya k'yawar yarinya ce ta shigo sanye da hijab mai hannu ba k'aramin kyau tayi ba , k'are mata kallo Harun yayi zatakai shekara sha bak'wai , karo na farko daya tsaya ya k'urawa budurwa ido kenan mamakin kansa yakeyi , can kuma yaji k'irjinsa na bugu , dawowa wanan budurwa tayi , tacewa ”Harun barka ,dady na ya gayamin munsami sabon ma aikaci , washe fararen hak'waran sa yayi yace ”barka sister , dariya tayimasa tana yimasa wani irin kallo mai wuyar fassara , Harun baisan wanan budurwar ta tafi ba saboda ya fad'a kogin tunanin ta lol , kodai kodai🧏‍♀️.. *WASHE GARI* Da safe yayi wanka sashen su momy ya nufa da sallama ya shige samunsu yayi a dining suna breakfast , momy ce ta washe baki tace ” a 'a my son zoman kaima ka karya , durk'usawa yayi ya gaida dady ciki ciki dady ya 'amsa kana ya juya ga momy , cikin fara'a ya amsa ,jiyayi ance brother barka da safiy, ywwa kintashi lpy sis cikin shagwa6a tace ”lafiya lau , a d'a rare ya zauna a dining chair d'in yayi karin kumallo ,tunda ya zauna fara'ar fuskar dady ta gushe , shigowar Bash ce yasanya Harun juyawa , sanye yake da gajeren wando iya guwai warsa sai singlet fara a , k'arasowa yayi yace ”good morning dad ,good morning mom, amsawa sukayi cike da kulawa suna yimasa ya aiki ,dady ko janyo Bash yayi kusa dashi yazuba masa farfesun kaza , Fauziya ce tace ”ya Bash inason muyi wata magana saboda is very important to me and yau lol , kashe mata ido yayi yace ”oky yanzu dai kibari na gama sai muje muyi ko , suna had'a ido da momy ta galla mata harara , Harun ne ya dubi gefen da Bash yake zaune yace ”brother babu magana ne , cikin zafin rai Bash yace ”bana magana da y'an iska irinku , yana magana yana nuna Harun , hankalin su momy ne yakoma gurinsu , yacigaba da cewa wlh dady ciki yayiwa wata yarinya yanzu gashinan iyayenta suna nemanshi ido rufe yama samu na rufa masa asiri , a razane ido yai ja Harun ya d'ago yana kallon Bash yace k'iyayyar mu harta kai ga kayimin sharin zina ?"nine fa d'an uwanka , dariyar mugunta Bash yayi yace ”a da kake d'an uwana amma yanzu an sauya bani babu abota da mazinaci !! kalmarnan ba k'aramin dukan Harun tayi ba ,har lokacin idon Momy da dady da Fauziya na kanshi ,wasu hawaye ne masu zafi suka kwaranyo daga idonsa ya had'a hannuwansa biyu yace ”na rantse da Allah dady da momy ku yarda dani ko kula y'ammata banayi walhi , wani mari dady ya wanka masa yana cewa d'an iska dama shiyasa kake shigo mana gida ?"to kull kar in sake ganinka a ginanan kaje can 6angaren ka amma nayi maka iyaka da iyali na so get out ko bakaji ba , Harun na kuka yana cewa dan Allah ku amince da magana ta, haka ya fice zuciyarsa babu dad'i ." Dady ne ya kalli momy yace ”kinga abinda yaronnan ze janyo mana ko ? sunkuyar da kai momy tayi hawaye na zuba a fuskarta ta d'ago ta dubi Bash tace ”Bashir kaji tsoron Allah kuma kasan zaka mutu kaje ka tarar da Allah shin gaskiya ne ko k'arya ? Bash ne yatashi yana mita , ni dama ai ba'a yarda da maganata ya fice , a hanya ya had'u da Harun ya tsuguna ya dafe kansa , dariya Bash yasa yace ”d'an samari kana lokaci , bai sami damar maidawa Bash martani ba ya mik'e jiki na rawa yanufi part d'inshi , gado ya fad'a tare da sakin kuka mai ban tausayi . Rurin dayaji wayarsa na yine yasashi cirota a cikin aljihu bai mai number ba 'amma tunda yafara zuwa sabon gurin aiki bari dai ya d'aga ,yana d'agawa yaji ance Malam Harun nine ma manjan ma aikatar ku , kasancewar baisan ko waye manaja ba yasashi gaisheshi cikin ladabi , mutumin da yakira sunanshi a matsayin manaja , yace ”inason mu had'u a gidan Zoo sabo wanda kasani ,hak'ika Harun ya firgita amma tunda umarnin manaja ne dole yabi , haka ya share hawayen fuskarshi ya mik'e yashiga toilet yayi wanka yana fitowa ya shafa mayukansa masu k'amshi ga turaruka ,yasanya ya d'auki k'ananun kayansa ya sa ya d'aura agogo , ya dauki wayarsa da key d'in motarshi ya fice , yana shirin shiga motar yaji wani kiran yasake shigowa , d'agawa Harun yayi cikin rawar jiki yace ”manaja ga ninan zuwa , cikin sauri ya shige motar yatada ta yanufi titi tafiya yakeyi amma gabanshi na fad'uwa ...✍️. Vote me on wattpad ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 9 & 10 ____Bash ne shida Fauziya a bedroom d'insa kwance take yana wasa da gashin kanta ,kanta ta d'aga tayi masa rad'a a kunne , mik'ewa naga sunyi ta zura hijab suka fice , Allah ka karemu da rayuwar dabbobi🤦‍♀️,zama yayi a cikin mota yana jiran fitowar Fauziya ,bedroom d'in momy taje ta sameta a zaune tana goge mirror , gefen gadon tasamu ta zauna ta rik'o hanun momy ta shagwa6e fuskar ,momy ce tace ”to shagwa6u ,meyafaru ?" cikin shagwa6a tace ”momy zanbi ya Bash shopping , momy ce ta dubeta tace ”mezakije siyowa , turaruka cewar Fauziya , to Allah ya tsare ki kula da kanki please ,oky momy natafi , tashige mota suka wuce , suna tafiya suna hirarsu wacce ni kaina banajin abinda suke fad'a ." Umma na fito da abin gwajin cikin taga ya zana mata layi biyu , waro ido tayi cikin tuhuma tace ”Asma'u tsiyar da zaki janyo mana kenan?"shikenan na shiga uku cewar umma ,Asma'u dake zaune ta sunkuyar da kanta k'asa ,idanunta na kan shinkafar da take tsincewa tace ”Umma dan Allah kiyi hak'uri dan girman Allah , wani wawan mari umma tabata yayi dai dai da shigowar Malam , cikin alamun tambaya ya zauna yana ”cewa meyafaru kike dukan budurwa kamar wanan gaskiya bai kamata ba , hawayen da Umma take k'ok'arin 6oyewa ne sukayi nasarar zubo mata , Malam daya kasa gane me yafaru ya dakawa Umma tsawa yace ”bana san sha shanci ina tambayar ku meya faru amma duk cikinku babu mai bani amsa ? juyawa malm baya umma tayi tare dacewa ”to cikin shege Asma'u tayo , mik'ewar da Umma zatayi ta yanke jiki ta fad'i , Asma'u dake cikin tashin hankali ta nufi d'akin umma a d'an madai_daicin fridge d'insu wanda yad'an ji jiki ta d'auko ruwa a gora ta yayafawa Umma , ajiyar zuciya umma ta sauke tare da cewa wlh kinyi asara a rayuwarki duk tarbiyar da muka baki bin mazan waje yafi yemiki komai ko? Malam da zuciyarshi ta hassalo ya mik'e yashiga d'akinsa da yake ajiyar bulalai ya d'auko mai baki biyu yakuma d'auko mai baki d'aya ya had'asu yashiga , zabgawa Asma'u , saida yayi dukan ya gaji dan kansa yaga idanuwanta ne masu k'iftawa alamar taji jiki , zama yayi ta gefenta ya yarfe gumin goshin sa yace ”Asma'u yanzu irin tarbiyar da na baki kenan ?"sakaiyyar da zakiyimin kenan wlh bakiyi mana adlci ba kin cucemu kin 6atawa gidannan suna , saita bulalar yakumayi yana shirin zabga mata yace ”ubanwa yayi miki ciki ?" rufe bakinta tayi tana shirin yin amai , takasa mik'ewa dole ta kwararo amai a gurin , Malm ne yace ”tambayarki nakeyi kokuma kinason ink'ara miki bulalar ne , shiru tayi tak'i magana , Malam ko kamar jira yakeyi tak'iyin mgna ya zuga mata bulalar yana shirin k'ara kaimata na biyu ne tace ”malm kayi hak'uri zan fad'a maka , to ina saurarar ki cewar Malam ,Asma'u ce tayi jimm can kuma tace ”Harun ne , gyara zama Malam yayi yace waye Harun??? ,d'ane ga Alhaji Muntari yayan Alhaji Yusuf mahaifin Bashir ,Malam ne yace ”kina nufin kintsatsen yaronnan dashi kukayi watsewar ?"sunkuyar da kai k'asa tayi Malam ko saida yakuma yimata lilis sanan yafice domin yin sallah la'asr." Da isar Harun gidan Zoo d'in ya hango wani bak'in mutumi ya rufe fuskarshi , yana shirin ciro waya yakira wanda yace ”yazo aka shak'e masa wuya aka sanyashi a mota sukabar gurin ." Washe gari malm ta saka Asma'u a gaba wai saita kaishi gidan wanda yayi mata abin kunya , saida suka hau a dai daita sahu ta kaisu har zuwa anguwar , Malam ne yatsa a nesa da get d'in gidan yacewa Asma'u , taje ta k'wan k'wasa , tafiya take cikin sanyin jiki ta nufi get d'in , k'wan k'wasawa tashiga yi , megadi ne yace waye ?"Asma'u dake waje tace ”nice munzo gurin masu gidanne , to bari a sanar musu cewar mai gadi , dawowa yayi yace ”alhajin yana ciki wai kushiga , Malam ne yataso da sanyin jiki , shigewa sukayi tundaga k'ofar dazata sadaka da cikin gidan Malam jikinshi yayi sanyi dubada ganin yanayi dakuma tulin nerar da aka kashewa gidan yasashi tafiya kamar mai k'irga k'asa , suna isa k'ofar da zata sadaka da baban palorn gidan sukaja suka tsaya , jin alamun bud'e k'ofa ne yasa su Malam razana Fauziya ce ta fito cikin riga k'arama mai siririn hannu sai wando gajere fari tass , da ganinsu tasan ko suwaye , cewa tayi gurin dady kukazo ne ?"Malam na rawar jiki yace ”eh jagora tayi musu suka shiga k'ayataccen parlorn da yakuma tsinkawa Malam zuciya dan yana ganin idan yace ”Harun ne yayiwa ,Asma'u ciki tabbas bazasu yarda ba , da shigarsu suka tarar da momy zaune ta pillow a ciyanyarta zama sukayi a k'asa suka gaida momy , amsawa tayi cikin sakin fuska tace ”daga ina kuke ”ban ganeku ba , malm ne yace ”dama nazone akan maganar Harun ,Harun momy ta mai maita cikin fad'uwar gaba , me Harun d'in yayi ,kalon Asma'u Malam yayi yace ”wanan tarinyar ita k'adai Allah yabani a duniya , munbata tarbiyar dai dai gwargwado kuma tayi karatun islama tayi na boko tana sakandire , to ni inacan gurin neman abinda zamusa a bakin salati nadawo nasamu mahaifiyarta tana yimata fad'a yanzuma munbaro ta a gida tayanke jiki ta fad'i , dady dakejin komai yana daga saman step yace ”malm ban gane ba?" Malam ne yace "Harun ne yayiwa y'ar wajena ciki !!momy da taji gabanta yayi mumunan fad'uwa ta nuna Malam da yatsa tace ”kull Harun ba d'an iska bane walhi , Malam ne yace ”to gatanan dai insharri nayimasa Allah yasaka masa ,itace tagayamin , dady ne ya k'arasa saukowa yace is okay , kome akace Harun yayi bazanyi musu ba , amma kuyi hak'uri insha Allah dole ya aureta what!!! momy tace ”hankali a tashe wanan bazai yuwu ba wlh , haka kawai bawan Allah beyi Abu ba ace yayi ?" haka su Malam suka mike ,dady ne yaciro dubu ishirin 20k yabasu suka fice daga gidan." Mom ce taketa gwada number Harun amma switch of yau kwana biyu kenan , Hajiya ce tace ”ki kwantar da hankalinki tunda yasami aikinnan baicika zuwa a kan kari ba , badan mom tayi na'am da maganar hajiya ba ta sai saita yanayin fuskarta , amma tanajin gabanta na yawan fad'uwa , alwalh tayi tazo ta tayar da sallah , addu'oi tadin kuwararo wa Harun na bud'i dakuma na kariya ta dad'e akan sallahya daga nan ta mik'e tanufi bed ta kwanta da tunani kala kala a cikin ranta." Basma ce kwance tarasa meke kimata dad'i rabonta da ganin Harun a makaranta harta manta ko muryarshi bataji , momynta ce tazo ta zauna kusa da ita tana rarrashinta akan taci abinci koda ad'anne ,haka dai Momynta ta tilasta mata tutura abincin...✍️. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 *_SALON ALK'ALA MINTA DA BANNE✍️_* 💃 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 11 & 12 ____Wani d'aki aka shiga dashi mai duhu , magunguna kala² mutanen suka d'irka masa dan zasukai su hud'u , kwanciya Harun yayi bacci mai nauyi ya kwashe shi , bayan 30mins ,ya mik'e alamar jikinnasa yana yimasa wani iri sha'awa ce ko kuma buk'atar mace a kusa dashi ne yakasa ganewa , mutanen ne suka shigo jikinshi babu k'wari dan bazai iya magana ba bare har ya ta6uka wani abu , wanka suka masa suka ciro masa wani sabon kaya wando ne iya guwai wa sai riga irinta nigogi , haka harun ya koma kamar d'an arna , wani jan abu suka shafa masa a kansa tare da mik'o masa cup da Vijumilk a ciki da wani abu da suka sanya, jiki na rawa Harun ya kar6a yasha mik'ewa yayi yana layi yana cewa beb kizo gareni man , wata budurwa da alamu ba musulma bace "wani gaye da gefen , Harun yayi mata alamu da ido , tafiya tayi da wasu shegun kayan jikinta da kana ganinsu kasan shed'an yasami mazauni , kwanciya tayi a cinyar Harun tana shafashi had'i da sakar masa zazzafan kiss , daganan lamarin nasu ya k'azanta harta kai ga Harun ya cire kayan jikinshi sun yi zina shida wanan budurwa , nishi yake saukarwa kamar wanda yayi gudu , itako shu'umar cigaba tayi da kwanciya a jikinsa , a lokacin Harun bai dawo hayyacin sa ba , yana kwance a gurin tsirara ,haka suka d'aukeshi suka kaishi toilet suka yimasa wanka , kayansa wanda yazo dasu suka sanya masa ,mik'ar dashi sukayi suka sanyashi a mota , direct gidan su suka nufa dashi ,ganin babu kowa a tsakar gida suka turashi cikin d'akinshi suka kullo k'ofa ." Zaune Asma'u take tana da ddna wayar da Bash ya siya mata , tuno hud'ubar da bash yayi mata tayi akan cewar ko me za'ayi mata karta sake tace shine yayi mata ciki tace ” Harunne , tausayin Harunne ya kamata , dukda bata sanshi ba amma yanada kya kyawan hali lokaci guda hankalin ta ya tashi tana tunanin anya tayiwa Harun adalci kuwa , amma kuma ai bata isa tace ” ba Harun d'in bane tunda maganar farko da ita ake amfani ,wani hawaye ne yazubo mata mai tattare da nadama ." Bacci yakeyi ko motsi bayayi , sallamar da akayi ne tasa shi k'ok'arin farkawa , jin idanunsa sunyi masa nauyi yayi dak'yar ya bud'e idon ya d'orasu a kan wacce ta shigo , mom ce fuskarta sha6e sha6e da hawaye , tace ”Harun ina kashiga ?"Harun babu magana sai dai yana binta da ido , kiran drivern daya kawota tayi. yana shigowa tace ”ya temaka mata tasa Harun a mota , babu musu ya kama Harun mom ma ta rik'eshi suka nufi mota , direct hospital suka wuce da azama aka kar6e su sbda nan asibitin su momy ke zuwa kulawa aka fara bashi ta gaggawa , mom banda kuka babu abinda takeyi , wani doctor ne yafito hancinsa sanye da abin rufe hanci yace ”hajiya wanan yaron akwai matsala 'a tattare dashi , yasha abin da zai gusar masa da tunani , bayannan ba a bisa k'a ida yasha ba sbda abubuwan dayasha na maye dakuma na tada sha'awa suna neman salwantar da rayuwarsa, rik'e baki momy tayi tana kallon likitan harya gama jawabinsa ya fice .* Dady ne yake yiwa Bash shirya shiryen tafiya India karatu komai ya kammala ,gobe insha Allah jirgin zai d'aga , momy ce take cewa dady ,nidai bana son tafiyar shi k'asar waje gaskiya , wlhi tarbiyar y'a y'a watsewa takeyi , dakatar da ita dady yayi tare da cewa inhar bazakiyi masa fatan alkairi ba to kija bakinki kiyi shiru , karki manta shine magaji na kuma inada buk'atar yayi karatu sosai , mik'ewa momy tayi ta wuce bedroom d'inta tafad'a gado tana kuka , Fauziya ce tafito sanye da dogon hijab ta gaida dady washe baki yayi yace ”malama Fauziya ke a wace k'asar kikeson yin karatu ¿ shagwa6e fuska tayi tace ”dad nikam abarni a gurin momyna , dariya dady yasa yace ”to brother'nki gobe zai wuce , fatan alkairi tayi masa tana tayashi murnar cikar burinsa ,dan Bash ba karatu zashi ba , sun shirya shida wata budurwar sa zasuje honeymoon lol ." 🤭an rainawa dady hankali 🤏😎. Harun kusan awan shi d'aya a hospital ,baiyi mgna ba sai dai bin mutane dayakeyi da idanunsa , doctor ne yace ” Indai yaron nan yakuma kaiwa 1hour bai farka ba idanunsa ne a bud'e to dole zamuyi muku transfer wlh , mom da tunda suka kawo Harun take kuka yanzun ma kukan tasaki tana jijiga shi amma babu magana sai ido ." Washe gari plane d'in su Bash ya d'aga zuwa India babu wanda yasa budurwar tana cikin jirgin kasancewar bai nuna alamun tare da wata sukazo ba , momy da dady da Fauziya sai d'aga masa hannu sukeyi daganan suka d'aga , dady ne yawuce dasu momy supermarket , kaya suka jido masu tsadar gaske daganan suka wuce gurin shan ice cream , suka dawo gida ." Kwance yake shi kad'ai a d'akin mom taje gida ta dawo doctor kuma yana office , tuno abubuwan da suka dinga faruwa dashi yayi a club inalilahi yadinga mai _maitawa wayo Allah na garinya gariya wayo mom!!! lokacin mom da hajiya sun taho suka dingajin hayaniyar sa da sauri suka k'arasa , yaci gaba da cewa wlhi sai Allah ya sakamin Allah baya azzalu mai Allah kayimin sakaiyya da gaggawa , hawayen da mom ke k'ok'arin 6oyewa ne suka zubo a fuskar da bata gushewa da zubarda hawaye , kujeru suka samu suka zauna suka fara kwararo masa adu'a, yunk'urin mik'ewa yakeyi yakasa , hajiya ce ta rik'o shi ya mike yana salati , bud'e idanunsa yayi ya saukesu a kan na momy da sukayi ja jawu kamar gauta , tausayin mahaifiyar tashi ne ya kamashi yanajin sonta na dad'uwa a cikin zuciyar shi , doctor ne yashigo d'auke da wata takarda a hanunsa da alamu ta sallama ce "cewa yayi dama tashinsa muke buk'ata to yanzu kubiyoni office saboda ka'idojin shan maganinsa , hajiya ce ta nemi guri ta zauna momy kuma tabi doctor , doctor ne yace ”kullum zai dinga shan maltina da madara sau uku a rana , mom ce tace ”wanan ba matsalar su , okay doctor yace tare da ciro magungunan daya sanyasu a leda , kinga wanan yana shansa zaiyi amai please kukiyaye dokokin insha Allah zai sami sauk'i godiya mom tayiwa doctor suka fice sbda komai mahaifin mom ne zai biya , tattarawa sukayi suka koma gida ." Da isar Bash shida wata tantiriyar yarinya mai suna Bahijja ,Bahijja yarinya ce y'ar shekara ashirin da biyu ,ta taso cikin gata da nera batasan babu ba a rayuwarta , kasancewar iyayenta y'an boko ne yasa sukace bazatayi aure yanzu ba harsai ta kammala komai , hakan yasata fad'awa harkar karuwanci , kuma a mazan ma ba da kowa take hurd'a ba setaga mutum ya iya d'aukar wanka kuma wayayye ajin k'ar she bugu da k'ari mai bud'a d'en ido wanda kunya bata gabansa ...✍️. Muje zuwa 🥰karku manta da salon alk'alamin✍️marubuciyar taku kudai kubiyoni karkuce ina jamuku rai a kowanne page 😉hakan shizai sa kudingajin sha'awai bibiyar page d'in gaba ,dafatan kungane ko🤙. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 *_Masu sharhi naga sharhin ku 🤙kuma ina godiya da soyayyar da kuke nunamin👏kuyi hak'uri jiya babu wanda na kula am sorry 🙏wlh kuna raina kuyimin uziri please 🥰. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 13 & 14 __Wata k'awar Asma'u wace suke watse warsu tare ta shigo gidan su da sauri , Asma'u dake gyara d'aurin zaninta tace lafiya Rumaisa ?infa lafiya cewar Rumaisa , kujera yar tsugunno , Asma'u tabawa Rumaisa , ganin umma batanan yasa Asma'u cewa to wace gulmar kika guntso ?" cikin rad'a Rumaisa tace ”wlh Allah Bash yatafi k'asar waje , eeeh cewar Asma'u data dafe k'irji , k'asar waje fa kikace ?"wato ni yabarni nan ga shegiya ko , kuka ne ya ku6ce mata itako , Rumaisa ficewa tayi tunda tayi abinda ya kawota , zama Asma'u tayi tafara sak'a da war wara ." Kwance Harun yake da wayarshi a hannunshi , watsapp ya hau yana kunna data sak'onni ne suka fara shigowa , wani video ne yaja hankalin sa ganin number babu suna , bud'e videon yayi , ganin shi aka fara nunowa sai kuma wata budurwa tsirara , haka shima tsirara , gyra zamansa yayi yafara tuno abubuwan da suka faru dashi dakuma fuskar wanda ya daukoshi sai dai ba lallai ya ganeshi ba kasancewar , fuskarsa a rufe take idanunsa da bakinsa ne a bude , a razane ya tsayar da vidion yana tunanin to da yaushe har ya aikata zina!!!?" innalilahi wayo Allah na ,dayake bashida wuyar kuka aikuwa yafara kamar k'aramin yaro , sak'one yakuma shigowa ta number me vidieon dubawa yayi ,yafara karantawa ... _Barka dai maijin tsoron fad'awa halaka to gashinan yanzu saika nunawa danginka kazamo mazinaci , dan wanan yarinyar tace ”a kawo mata kai yanzu , kuma bazamu sa6awa umarninta ba , zaro ido harun yayi tacigaba da karantawa , waanan video da kake gani kana bijire mana saimun watsashi a social media , blocking number Harun yayi yana tunanin yin hakan shine hanyar datafi dacewa ,yakuma goge sak'onin duka , gaban shi na dukan uku _uku_ Bash ne kwance a gurin shak'atawa na k'asar waje ,k'afafuwan sa sanye suke cikin ruwa swimming pl.. yayin da Bahijja take gefensa ,tana sanye da pant da bra ,kasanceawar babu ruwan kowa da kowa ,kuma kowa kagani shek'e ayarsa kawai yakeyi babu mai kallon shi , kallonta yakeyi tana yimasa wasu abubuwa 'amma bai kulata ba , tasowa tayi ta zauna a kan cinyarsa tana hura masa iska a kunne , kawar da kanta yayi gefe , tunani yakeyi karfa Asma'u ta tona masa asiri sbda batasan ya taho ba , Bahijja ce ta dubeshi itama fuskarta da alamun damuwa tace ”da alama kana cikin damuwa amma inba komai ka fad'amin kozan iya temaka maka , Bash ne yayi dariyar gefen baki , kana yace ”wanan ba matsalar da ta shafeki bane just ki k'yaleni but yanzu bansan mgna okay Bahijja tace ”tare da tashi tabar gurin , tana cikin tafiya tana kar kad'a k'ugu ta bugi wani k'aton mutum , rungumeta yayi , yana murmishi itako Bahijja turarensa ne yasata k'ara ruk'oshi , d'agota yayi yana yimata dariya , ware idanunta tayi tace am sorry... hannu ya d'aga mata yace , zomuje room d'ina , kasa yimasa musu tayi yana rungume da ita suka wuce wani tsararen gida suka shiga , da shigarsu yace ”zo kiyimin wani aiki , tasowa tayi cikin yanga , ganin wani jan zane tare da kan mutum a d'aurin d'an kwali a k'irjinsa yasata mutuwar tsaye ,nunfashinta ne ke barazanar d'aukewa sbda inbazata manta ba..... Mik'ewa Harun yayi ya shiga wanka bayan ya shirya ne ya nufi part d'in mom , samunta yayi kan sallahya tana adu'a zama yayi nesa , shima ya d'aga hanunsa , a tare suka shafa adu'ar , juyowa tayi tace ”son barka ykk sunkuyar da kai yayi yana gaida mom cikin kulawa ta amsa tare da cewa inason zamuyi wata magna dakai dumm!!! yaji gabansa ya fad'i , cikin zuciyarsa yace ”kardai mom tasan abinda yafaru na shiga uku, k'are masa kallo mom tayi cikin hikima da tausayawa tace ”Harun ? na'am mom ,inason sanin me kasha haryayi sanadiyar rashin maganarka , ka koma kamar me maye ?" karfa ka manta ko kayimin k'arya zan gane , Harun ne ya nutsu yace ”mom wlh Allah ina zaune wani mutum ya kirani yace ”wai yanason ganina shi manajan company d'inmu ne to shine ya yimin kwatancen , gunda zamu had'u , shine naje tun daga lokacin bansan meya faru ba , tausayin shine ya kama momy tasani sarai Harun bayason mai yin k'arya bare har shima yayi k'ok'arin yi , kuma tasan yanada mak'iya gaba da baya , hakan yasa tadage da yimasa adu'a , bayanin WhatsApp da ya hau aka turo masa video yayi wa mom , gumi ne ya wanke mata fuska tace wanan wane irin mutum ne ?"amma babu komai mu had'ashi da Allah kawai, kuka Harun ya fara yana cewa dama ba'a haliceni ba , shiii momy tace ”akan wanan zakayiwa Allah butulci to karna k'ara ji , am sorry mom Harun yace ”yana share hawayen fuskar shi , mik'ewa yai yaje part d'in Hajiya ya gaisheta ,ya dawo d'akinsa dan a halin yanzu baya sha'awar fita waje , kwanciya yayi ya fara tunani iri _iri kirane ya shigo wayarsa dubawa yayi , yana ganin number yagane mai kiran Basma ce , kuka takeyi babu k'a k'autawa , Harun ne yace ”ina tunanin kinyi wrong number ne Basma na tsoron karya kashe wayar tace ”Harun wulak'anci bashida dad'i wlh , dan nace ina sanka dan Allah ka kar6i soyayya ta na rok'eka ko kanaso in rasa rayuwata ne ?shiru Harun yayi baice komai ba , magana ta k'arayi da muryar kuka tace ”kodan kana tunanin Kyan da Allah yayi maka shine zakayi amfani dashi ka cutar dani , Harun da bama Basma yake saurara ba ya kashe wayar duka." Jefar da wayar Basma tayi tafara kuka tana ihu , momynta dake shirin fita wani taro da zasuyi ta shigo da sauri , tace ” my daughter what happen ?" juyawa momyn nata baya tayi tacigaba da rera kukanta , janyota tayi kamar yarinya ta rungume ta tace ” please kifad'amin meke faruwa?"momy wlh ina ganin kun kusa rasani , zaro ido momy tayi tace ”bana san kina irin wanan maganar meyafaru ?"momy Harun na neman tarwatsa ratuwata , momy ce ta dafe goshinta tace ”wai shi wanan yaron a ina yake , tsnanta kuka Basma tayi tace ”nima bansan gidansu ba wlh momy ce tace ”bari ina dawo zamuyi maganar nida dadynki , rungume momynta tayi tana murna , momy ta fice ." Number Asma'u Bash ta lalubo ,danna kira yayi Ring d'aya ta d'auka cikin masifa tace ”wato ka maidani jaka abincin ka ko ka d'uramin ciki katafi ka barni ko ?kuka kasa nida mahaifina munje munyiwa iyayenka k'arya akan Harun ne yayimin ciki hmmm , yanzu dawowarka nake jira , Bash ne yace ”kome zaki fad'a ki fad'a ,danayi miki cikin ta k'arfi nayi miki ? shegen son kud'inki ne ya janyo miki kuma koda wasa nak'arajin maganar wai nine nayi miki ciki to wlh sekinyi dana sani banza yar malm mtsw, kuka Asma'u ta saki mai ban tausayi shiko Bash kashe wayarsa yayi , lokacin cikin asma'u yana wata hud'u dan yanzu bata fita ko nan da can saboda cikin ya fito...✍️. Comments and sharhi👏 ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 _Masoya bazan gaji da mik'a sak'on gaisuwata a gareku ba sbda soyayyar da kuke nunamin nida kowane littafi nawa nagode🥰👏_ ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 15 & 16 ____Mutumin d'azu ne yakuma kiransa , k'in d'agawa yayi yana tsoron abinda zai biyo baya , wata zuciyar tace ”ka d'aga man , amsa kiran yayi yana salati a cikin zuciyarsa, he he he Harun yaji daga can 6angaren ,yaro yaro ne ,wato kana nufin mu bamuda wayo ko ,ha ha ha kayi blocking d'inmu a watsapp bakasan gidan da kake muna bibiyarsa ba hhhh , innalilahi wa inna ilahairraji'un na shiga uku ,cewar Harun , jiyayi kansa na juyawa ya fad'i a gun sumamme , k'arar buguwar abu momy taji ,hakan yasa ta nufi d'akin , Harun da sauri , samunsa tayi kwance a sume ko nunfashi bayayi , abinka da mai ara har hawaye , momy tafara kuka ta nufo d'akin Hajiya da gudu tana cewa ”son _son Hajiya tace ”meyayi ?"kuka yaci k'arfin momy takasa magana , Hajiya ce ta mik'e ta biyo momy suka nufi d'akin Harun , samunshi sukayi kwance ya mirgina gefe can kuma y'an yatsun k'afarsa jini ne ke fita a kowane farce na k'afarsa , ganin haka yasa momy k'ara kid'imewa ta rusa ihu ta fad'i sumammiya , Hajiya tarasa wazata kama wa kuma zata bari kawai tazauna ta zuba uban tagumi tana kuka , tana cewa "Allah ka duba lamuran mu Allah ka sauk'ak'a mana wanan matsala , wasu hawaye masu zafi suka zubo mata , jiki babu k'wari tayi bakin get kasancewar mijinta yatafi Dubai , driver da mai gadi takira da gudu sukazo suka tsuguna , Hajiya dake share hawaye tace ”temako zakuyi min ,cikin rawar jiki sukace " to Hajiya , kubiyoni ciki ,tana gaba suna binta a baya haka suka shigo d'akin , da shigarsu sukaji mom nata wasu surutai ,sosai Hajiya takuma tsorata dan mom bata ta6a yimata haka ba ,mai gadi da driver ne sukayo kan mom k'o k'arin dagota sukeyi amma sun kasa ,Hajiya ce ta taho tace ”kuzo mu kamata ina ko k'afafuwanta babu wanda ya iya d'auka , rud'ani tashin hankali firgici duk Hajiya ta shiga ." Waya ta d'auka takira wasu y'an uwanta ,basu d'au dogon lokaci ba sai gasu sun iso su uku ne samari ,d'akin da mom da Harun suke ciki Hajiya tayi musu bayani , shigowa sukayi suka fara aikin temako , da mai gadi da driver da Hajiya da y'an uwanta guda uku mutum shida ,dak'yar suka d'aga momy , suna nishi adu'oi Hajiya tadinga kwararowa mom tare da yayyafa mata ruwan adu'a atishawa mom tayi tana farkawa tace ”ina son , dagudu ta fice ,zuwa gurin Harun dake kwance kamar gawa jijigashi takeyi iya k'arfinta amma shiru ga jini yana fita ta farcen k'afarsa kad'an k'adan.... Cikin Asma'u yashiga wata takwas ,Bash ya turo mata kud'i masu yawa , tayiwa jinjiri siyayya , wanan lokacin Asma'u na cikin farinciki da nishad'i kasancewar sai abinda ranta keso takeci , bata nunawa umma iya adadin kud'in ba dan a k'alla kud'in zasuyi dubu d'ari , dubu hamsin taba umma , abinci sai wanda ranta keso ,rubutu ko da adu'oi duk malam nayi mata a cewarsa hanunka baze ri6e ba ka yanke ka yar, tana cewa Bash batada kud'i yake turo mata baya yimata musu ,kasancewar tace ”zata tona masa asiri ,dakuma gidansa da babu wanda yasani , sunyi siyayya sosai itama tayi d'inkuna dan burin Asma'u taganta tana shiga wancan tana fita wanan ." Sumaiya ce tabada cigiyar Harun da a cewarta indai ba Harun ta aura ba to bazatayi aure ba har abada , wata rana suna zaune a dining itada momman ta da Abbi wato (babanta)suna breakfast , ya dubeta yace ”daughter na'am tace ” tana karkad'a cokalin hanunta , inason zamuyi wata magana , to Abbi ,momma dai na jinsu batace k'ala ba , yau zakiyi bak'o , cewar Abbi zaro ido Sumaiya tayi tace ”Abbi bak'o kuma?" eh yace mata ina fatan dai bazaki bani kunya ba ko?"uhm insha Allah , fuskarta babu wal wala , bayan sun gama abinda zasuyi ta shige bedroom d'inta ta shiga gallery gurin pics d'in Harun wanda tayi masa besani ba tadinga kissing d'insu tanaji kamar tana tare da Harun ne , kira ne yashigo wayarta , rashin gane ko waye yasata danna busy ,sai da akayi sau uku sanan ta d'aga , batayi magana ba , tayi shiru , mai kiranne yace ”barka da wanan lokaci sarauniyar kyawawa , ya jindad'i wata uwar harara ta zabga kamar yana kallon ta tace ”kai malam bansan ko kai waye ba kuma bansan daga ina kake ba zakazo kana yimin wata magana kamar ta y'an koyo." Daurewa yayi yace ”wato bakisan ko waye ba ?to nine yaron wanda mahaifinki ke aiki a company d'inshi , da alamu bakisan koni waye ba ,karkiga na tsaya ina yimiki magana kiyi tunanin ina barar soyayyarki ne no , kema in tursasaki akayi to ki gayawa mahaifin naki bakya sona so nima na fad'awa dad d'ina bana sanki kinga munsamo wa kanmu mafita , hak'ik'a wanan maganar ta 6atawa Sumaiya rai sosai zuciyarta kamar zata fashe ta wurga wayar kan gado tana huci ." Yau kwanan Bahijja biyar a gidan wanan k'aton mai suna Emanuel , soyayya yake nuna mata sosai yanzu ma bata fita bare ta kula kowa ,shiko Bash bai damu da rashin Bahija ba tunda dama ance barki ... wata rana suna zaune itada Emanuel take gaya masa maganin planing d'inta ya k'are , janyota yayi ya d'orata a kan cinyar sa yana wasa da gashin dokin , datasa a kanta , yace ”beb karki damu da hausarshi da bata game bakinshi ba , a zabure Bahija ta mik'e tace ”ban gane ba shiii yace ”mata alamar tayi shiru don't worry just ki manta kawai , cikin fushi ta mik'e zata fice ,ya janyota yafara yimata nasa salon mancewa tayi da maganar magani suka fad'a duniyarsu ta shed'anu." Shiko Bash ya had'u da wata yarinya wace ake yayi y'ar India samari ke rubibi a kanta , kasancewar ta lula a soyayyar Bash yasata dena kula kowa sai shi gida ya kama musu mai kyau amma madai daici , sunkoma kamar mata da miji sosai suke k'aunar junan su ." Yau watan bash uku yana cikin na hud'u ,a India , zaune suke shida baturiyar sa suna holewa a wani katafaren gurin wasa , daga shi sai gajeren wando iya cinyarsa babu riga , lol baturiya kuwa skirt ne dashi da babu duk d'aya sai wata riga mai shara_shara , Bash ne ya janyo hanunta tare da cewa "zomuje mu huta , bai gama rufe baki ba , abinda ya hango ne yasashi mutsike idanunsa .... Asma'u tashiga watan aihuwa umma ce da malm a asbitin, dan babu wanda ya rako su , mutane sai tsegumi sukeyi , umma dai bata kula kowa ba ta me aihuwa takeyi , tun karfe takwas na safe Asma'au ke nak'uda gashi yanzu k'arfe hud'u na yamma shiru wuya kam Asma'u tasha , doctors ne suka cewa su umma inhar Asma'u ta wuce biyar na yamma to tiyata zasuyi mata , cikin tashin hankali malm yace ” wa umma to yanzu a ina zamu samo kud'in tiyatar nan , umma dake share hawaye tace ”wanan yarinya ta janyo mana abinda yafi k'arfinmu wlh...✍️. Wow my pans mom Islam tana yinku kamar inda kuke yinta wlh kuna matuk'ar ji dani to nagode 🥰Allah yabar love muje zuwa 🤙. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 17 & 18 ____Bahijja Bash ya hango ita da Emanuel ga k'aton ciki a gaba , rik'e suke da hannun juna suna tafiya suna dariya , daka gansu zakasan suna cikin farinciki , kasa kawar da fuska Bash yayi yana dad's k'arewa Bahijja kallo ,shin ta yarda ta d'auki ciki da wanan k'aton arnen tabb Bash yace ”yayinda ya mik'e ya nufi gurinsu , da zuwanshi yace ”Bahijja ?"ko kallon sa Bahijja batayi ba ta maida kai gefe tana rik'e da hanun Emanuel , Emanuel da hankalinshi yayi gaba ya sunkuceta suka bar gurin , Bash kuwa yashiga tashin hankali , sosai ,a ranshi yana cewa tare mukazo ta gujeni taje ta d'auki ciki da k'aton arne , budurwar shi ce ta matso kusa dashi tana shafa masa kai tace ”meya faru ne my man , idanunsa da sukayi Ja jawur yace ”bb komai zomutafi , after dree budurawar tasa suka wuce gidan nasu , da shigarsu bashi ya bud'e kwalbar beer sha yakeyi kamar an aikosa , sanda ya cika cikinsa tabb da giya sanan ya kwanta yafara surutai marasa kan gado ,budurwar sa ce ta rungumo shi tana tambayarshi meyasa zesha over ?"ina Bash yayi nisa bayajin kira ,wata gyatsa yake fitarwa mai wari sosai , da haka ta gyara masa gurin kwanciya ta barshi a gurin ." Ana shirin shiga da Asma'u d'akin tiyata ,tafara yunk'urin aihuwa , malm da umma ko sai adu'oi suke jero mata suna daga waje dan ba'a barsu sun shiga ba , cikin ikon Allah ta haihu nurses ne suka gyra jaririn tare da yimasa wanka , jin kukan jin jiri yasa umma nufo d'akin ,lokacinma angama gyara komai saura mai jego tayi wanka ." Malam ne zaune a masallaci yana adu'ar Allah yabasu kud'in biyan asibiti , ya shafa adu'ar gami da mik'ewa , ya nufi cikin asibitin , samun Asma'u yayi tana kwance ,lokacin tayi wanka ." Harun ne kwance a hospital likitoci sun rasa gane kan ciwon sa anyi gwajin anyi amma duk shiru babu sakamako , kuma har yanzu jini zuba yakeyi kuma ana k'ara masa jini , mom tayi kukan harta gaji , hajiya ko kullum adu'a take kwara rowa Harun na Allah yabashi lafiya , suna zaune a kan tabarma sukaji sallamar momyn Bash cikin fara'a Hajiya da mom suka tareta ,ledace k'atuwa a hanunta cike da kayan mar mari , gakuma food flaks na abinci na farfesun kifi , gaisawa sukayi momy ta tambayi jikin Harun suka cemata da sauk'i , kasancewar doctors sunrufe k'afarsa babu wanda zai gane sai an gaya masa , momy ta d'an dad'e a hospital d'in daganan tayi musu sallama tare da ajiye musu ledoji ." Kwance take tana bacci ,wani gun guni da taji ne yasata yin azamar mik'ewa da tsohon cikinta , agogo ta duba k'arfe 3pm na dare ,duba gefenta tayi babu Emanuel , a tsorace ta mik'e saboda jin wani gurnani dake tashi a gidan , wata k'ofa da tunda tazo gidan bata ta6a shigarta ba anan tajiyo gurnanin , tafiya yakeyi sad'af sad'af har ta iso k'ofar ,ta jikin wani huji na k'ofar ta lek'a , hango Emanuel da jajayen kaya tayi da wani k'o k'o a hanunsa bakinsa duk jini , jin kanta tayi yana juyawa saboda tsabar firgici , da sauri ta dawo ta kwanta cike da firgici ." *GIDAN BASH* Ya watsake sosai ,wanka yayi yasa kayansa masu kyau ya fito parlor ganin baiga budurwar tashi bane yasashi k'wala mata kira , ko ina ya duba babu ita babu alamar ta , wayarshi ce tafara ring ganin number Asma'u yasashi jan tsaki yace ”to kuma menene ?"cikin shagwa6a tace ”na haihu ina asibiti kuma gobe za'a sallamemu babu kud'i , Bash da yanzu haushinta yakeji , yashi cewa nawane kud'in ,dubu d'ari biyu cewar ,Asma'u , kan uba ubanwa kika mayar mai gonar kud'i bakida hankali ne baki da tunani ne , kokuma wani naki ya ta6a ciyar dani ? Asma'u da muryarta bata fita sosai tace ” Bash ,wlh kayi yunk'urin wula k'antani wlhi zan tona asiri , cikin zafin rai yace ”ki tona mana , y'ar talakawa kawai , wanan furucin ba k'aramin k'onawa Asma'u rai yayi ba , cikin hassala tace "wulak'ancin ya isa haka whattt, ki san dawa kike magana ,inace dai kud'i ne to zan turo turomin account , hmm (halinka da babu zuciya) tace ”toh ." *NIGERIA* Zaune suke su biyar kowa da bak'in kaya a jikinshi , wanan budurwar da sukayi sex da ita , duban wani mutumi tayi tace ”oga yakamata a kawo min wanan saurayin , wata muguwar dariya sukasa cike da jin dad'i oga yace ”lokaci muke jira karki damu nan bada jimawa ba ,wani mutum ne yashigo da jar hula yana tafiya yana dariya yace ”nifa na matsu nima yaron make jira , suka kuma shek'ewa da dariya tare da nuna video d'in da sukayi masa lokacin da suke sex ,fuskar Harun tafi fitowa sosai , oga ne yace ”duk da wanan videon da mukeda shi zamu k'ara had'awa da namu ." Sumaiya ce zaune a parlor tana kallo a TV , Abbi ne yafito daga d'akin momy yace ”daughter ya kukayi da Mubin ?"sunkuyar da kai tayi k'asa tace ”Abbi yace ”baya sona, ehe shida bakinsa ya gaya miki hakan ?"eh Sumaiya tace ”tana girgiza kai alamun tabbatarwa , Ammi ce ta fito sanye da wani dakakken less mai adon duwatsu , zama tayi gefen Abbi tace ”ni a ganina yakamata mu bata za6i ko ?"Abbi ne yace ”tunda wancan yaron ya watsa mana k'asa a ido ai ba naman kai mukeyi da ita ba , ita dai Sumaiya na zaune bata k'ara magana ba , Abbi ne yace ”daughter ya kamata acikin mane manki ki fitoda mijin aure , Sumaiya ce ta shagwa6e fuska tace ”Abbi wlh sekuma ta mik'e ta ruga da gudu tana dariya , suma su Abbin dariya sukeyi ." Momy ce zaune ita da dadyn Bash suna hira , kwanciya tayi a kan cinyarsa tace ”dan Allah kaje ka gaida Harun a hospital bashida lafiya , wata uwar harara ya daka mata tare da cewa shid'in kun had'a dangi ne dashi , kokuma ,yaron d'an uwanki ne ?"momy da ranta ya 6aci tace ”koba yaron d'an uwana bane ai mahaifinsa amana yabar maka , cikin fusata dady yace ”to bazan jeba ya mutu ,wayasani ma ko a yawon zinace zinace ya kwaso cutar , momy da hawaye ke ambaliya a fuskarta tace ”yakamata kasani Allah ne yayi mutuwar Muntari kuma kai.....wani mahaukacin mari dady ya wankawa momy tare da k'ara mata wani , da gudu ta shige bedroom d'inta tasa key ,takifa kai a gado tana kuka ,mai tsuma zuciyar mai sauraro ." Harun dai na nanan inda yake sauk'i sai na Allah , dare babu bacci sai da rana amma daga Hajiya har momy babu mai bacci da daddare , adu'oi kan ana yinsu sai dai har yanzu Allah bai nufa yasami lafiya ba amma akace mai rai baya fidda rabo da samun rahamar ubangiji." Alert ne ya shigo wayarta na dubu d'ari , tana dubawa ta buga tsaki umma dake gefe tace ”keda waye ?"Asma'u tace ”nida wancan shegen ne , Bash , umma ce tasa dariya da alamu dariyar takaici ce tace ”ai tare kuke kuma wlh Allah ki kiyayi had'uwarki da ubangiji ,nidai nayimiki tarbiyar iya iyawata amma dare d'aya kin watsar da komai , umma ta fashe da kuka , Asma'u ko ta6e baki tayi ta kawar da kanta gefe ....✍️. Vote me on wattpad Please share👏 ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 My whtsapp group https://chat.whatsapp.com/J7cmS5wP5fBHAnF0ut8905 Bakandamiya Mom Islam Habib Facebook Mom Islam *✨GODIYA TA MUSAMAN GA YAR MALAM NAGODE DA NUNA SOYAYYAR HAK'IK'A INA YINKI OVER WANAN SHAFIN NAKINE NABAKI SHI KYAUTA ✨* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 19 & 20 ____Emanuel ne zaune da jayen kaya yana kur6ar abu wani jan abu , ya dubi shugaban su yace ”nidai ayimin rai kar a kashe ni ,zanyi k'ok'ari inga na kashe jaririn da Bahijja zata haifa ,shugaba ne ya shek'e da dariya yace ”kasan yanzu saura mutum uku ka gama koh ?" cikin rawar jiki Emanuel yace ”haba kuyimin rai a ina zan sami mutane kuma na jikina guda biyu yanzu , banida uwa banida uba duk nabawa dodo jinin su yanzu kuma kuce sai na k'ara muku ina , wata tsawa da shugaba ya daka masa ne yasashi tsorata , shugaba yace ”kasani kafin ka shiga k'ungiyar mu sai da kayi mana alk'awarin bada jinin mutum biyar yanzu kana so kace ,zaka yiwa dodo k'arya ko kuwa , a tsorace , Emanuel ya ce ”a 'a zan baku nayi alk'awari ." Fans jinin wa Emanuel zai bada bayan jinjirin Bahija da yace ”zai bada muje zuwa. Anbiya kud'in hospital dubi goma , su Asma'u sun dawo gida cikin k'oshin lafiya itada jaririn ta , ranar suna malm ya rasa wane suna zai sanya masa kwai ya Sanya masa Muhammad ,ranar suna mai jego ta tara k'awayenta , umma ko rasa wazata gayyata tayi sbda bata gaiyaci kowa ba kuma babu wanda ya lek'o gidan haka akayi sunan babu wani kaya da Asma'u tasamu dama umma tace ”mata duk mai cikin shege bazai ga dai_dai ba ." Hutun Bash ya k'are yau jirginsu ya d'aga zuwa Nigeria , babu wanda ya gayawa gashinan zuwa kawar surprise ya shirya yiwa su dady , da saukar su ya trolley d'insa ya ya fita daga airport d'in ya nufi titi , motar haya ya hau ya nufi gidan su , mai gadi najin k'arar mota ya wangale get ya d'auka ko anyi bak'i ne , hango Bash yayi ya fito daga mota yana mik'awa mai mota kud'i , gyara zaman jakar dake rataye a bayansa yayi ya nufi cikin gidan , mai gadi ne yaketa jera masa sannu amma ko kallonsa bai yi ba ya shige ciki , da shigarsa ya bud'e k'ofar d'akinsa da take waje nesa da ta momy , samun d'akin yayi fess dashi babu datti kasancewar momy ba mace mai son k'azanta bace , kayan jikinsa ya fara cirewa yana gamawa ya shige toilet bayan yayi brush ya kunna ruwan d'umi yayi wanka , ya fito d'aure da tawul a jikinsa , yafara rawa , mayukansa masu k'amshi ya sa sanan ya fesa turarukansa had'i da ciro kayansa a drowa , riga da wando tsadaddu masu kyau , taje gashin kansa yayi ya sa takalmi ya fito zuwa part d'in momy ." Samunta yayi zaune ita k'ad'ai a parlor tana kallo ta zuba tagumi , k'arasawa yayi babu salama yace ”my momy oyoyo ya rungumeta , momy ce ta share hawayen da suka kwaranyo mata , Bash sam bai lura da halin da momy ke ciki ba , bubuga bayansa momy tayi tace ”my son babu sanarwa ?"dariya yayi yace ”momy surprise nayi muku , murmishi momy tayi tace ”kazo lafiya ya karatu , alhmdulilh my momy nasha karatu bakiga na rame ba ? kallonsa momy tayi tace ”naga dai kayi k'iba kuma ka k'ara fresh sosai , dariya yasa yace ”momy yunwa nakeji sosai , mik'ewa momy tayi ta je kitchen tasami y'ar aikinta na soya doya ,tace ”please had'awa son shayi karkisa madara , kasancewar bayaso , to Hajiya ,cewar y'ar aikin , dafa shayin tayi da citta da kaninfari da na'ana da lemon grass ,da lemon tsami kad'an ta d'auki jug da tirai da small spoon ta nufi parlor , samun Bash tayi a zaune kansa na kwance a jikin momy tayi sallama ta ajiye a dining , mik'ewa yayi ya nufi dining d'in yasa zuma yafara sha ." Yau jikin Harun da sauk'i sbda adu'oi da mom da Hajiya ke kar6o masa daga gurin wani malami ,amma har yanzu jinin nanan yana zuba kad'an , yanzu kam yana cin abinci sosai kuma suna hira da mutane , sallama aka kuma rubuta musu suka koma gida , wani doctor yana zuwa yana wanke masa ciwon , yanzu ba laifi mom ta rage tunani sbda ganin jikin Harun yayi sauk'i , momyn Bash kuwa bata sake zuwa ba ." ********************* Mom da Hajiya ne zaune a kusa dashi suna hira ,Harun ne yace ”barin tashi yau in zaga ,Hajiya ce tace ”mutumin da bashida k'afa ina shi ina yawo , kwai gani sukayi Harun ya mik'e k'afar tadena zubar da jini , farinciki da nishad'i a zuciyarsu mom da Hajiya ba'a magana , kowane na cikinsu sai masha Allah yakeyi , Harun kuwa dariya ya kama yi yace ”yaukan naji sauk'i zuwa gobe zani ma aikata ko makaranta , mom ce tace " no kabari zuwa next week in ka kuma jin sauk'i saika tafi ,baya San yiwa mom musu haka ta hak'ura , jinya ta k'are ." Anya warkewar Harun babu lauje cikin nad'i🧏‍♀️. Dady ne yayi sallama , momy dake zaune ta amsa da wa/alaikumusalam sanu da zuwa , ywwa dady yace ”a tak'ai ce , har yanzu fushi kikeyi dani ?" cewar dady , hawayen da momy ke 6oyewa ne suka zubo ta kawar da kanta gefe , rungumota dady yayi tare da rik'o hanunta ya mik'ar da ita suka haura sama 😉base na bisu ba." Fauziya ce ta dawo daga hutu driver ya d'aukota sbda a boarding school take , tana hango Bash yayi shirin fita ta fito daga mata ta rungume shi , suka shige ciki , dady da momy da suka sauko yanzu suka fara dariya suna cewa oyoyo daughter , shiko dady cewa yayi shikuma Bash yaushe ya dawo?" momy ce tace ”jiya nima ko gayamin baiyi ba , dady dake dariya yace ”to muje dining muci abinci , Bash dake rik'e da mukullin mota yace dady nidai zani anguwa yanzu zan dawo , okay to sai ka dawo , momy ma Allah ya tsare tace ”masa , anguwarsu Asma'u ya nufa , da isarsa anguwar ya tsaya can nesa da gidan kiranta yayi a waya , cikin mamaki da sauri ta d'aga , tace ”Bash yaushe a gari number Nigeria nagani , cikin rashin fara'a yace ”in kinada lokaci kizo yanzu gani a waje , to tace ”batare da ya k'ara magana ba ya kashe wayar ." Yamma ce kuma umma na zaune a tsakar gida , fitowa tayi da abin kwashe shara a hannunta , tana tafiya kamar mara gaskiya , umma ce tace ”bance kidena fitowa ba?" cikin in ina tace ”zan zani zan zubar da shara ne ,ko kallonta umma batayi ba Asma'u ta fice ,da hijab a mara ,tana fitowa ta saka hijab d'in , duk lek'en da takeyi Bash na kallon ta har lokacin da tasa hijab , cikin zuciyarsa kuma ranshi na k'una sosai wanan kucakar yake kulawa jibeta talauci yayi mata yawa kash , gyara zamanshi yayi yana shafa sumar kanshi , ganin bai fito a motar ba yasata bud'e murfin ta shige ,da fara'arta tace ”sanu da dawowa ka dawo lafiya?"lafiya Bash yace "tare da cewa ”nazo gurinki ne akan maganar da mukayi dake dakuma wace dadyna ya gayawa mahaifinki , so yanzu sonakeyi asan inda za'ayi , ki auri Harun , Asma'u ce ta dafe k'irji tace ”Harun!!! eh Bash yace ”alamun babu wasa a tattare dashi , gaskiya bazan iya ba haba ,Bash kamar ba musulmi ba ?" har Bash ya d'aga hannu zai kaimata mari sai kuma ya fasa ya dunk'ule hanunsa , Asma'u ki fahimceni karkiyimin mumunan fahimta indai kud'i ne karki damu ko nawa ne zan baki , Asma'u da jikinta yayi sanyi ta ce zanyi tunani , ta bud'e murfin motar zuciyarta babu dad'i ta fice ...✍️. Kufayi hakuri da salon alk'alamin nawa sbda duk mai karanta book dina yasan salon sa 🥰 so da sababbi dakuma masu bibiyarsa kuyi hak'uri Ku biyoni insha Allah zanyi kokarin dena Ja muku rai 🤙. comments and sharhi👌 ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 21 & 22 ____Bismillah Harun yayi ya bud'e gat , mai gadi dake zaune a benci ya d'aga masa hannu yana cewa "Allah ya tsare mai gida , cikin fara'a Harun yaciro d'ari biyar ya bashi , Allah ya tsare mai gadi yakuma yimasa ,daganan ya fice batare da yahau mota ba , direct bakin titi ya wuya ya tari napep zuwa gidan su momy , kasancewar gidan babu nisa yasa basu dad'e ba aka iso , a k'ofar gidan mai napep yai parking , ya sauka tareda mik'o masa kud'in sa , bubuga get d'in yayi , mai gadi ne ya bude , yana ganin Harun ya washe baki yana yimasa sannu da zuwa , gaisawa sukayi ya shige ciki , da shigarshi yaci karo da dady da momy da ,fauziya da Bash yana zaune yana danna ,waya sallama Harun yayi cikin nutsuwa , momy ce ta fad'ad'a fara'arta tace ”oyoyo yaron kirki da sauri Harun ya k'araso gurin momy , tana mik'o hannu alamar yazo kusa da ita , yana zuwa zai kwanta a cinyarta ,dady ya daka masa tsawa , tare da cewa " kai d'an iskan ina ne ?"god'ai god'ai dakai kake shirin kwanciya a cinyar matata , to wlh kull kema kika kuma hukuma ce zata rabamu daku , tunda ke bakida hankali kema , momy ko kallon dady batayi ba a zuciyarta tace ”Bash yake hawa cinyata bana hanashi amma shi Harun ne za'a nunawa ban banci , bata bari maganar ta fito fili ba ta ja baki tayi shiru , Harun ne yaje gaban dady ya durk'usa yace ”ina wuni dady , wata uwar harara dady ya galla masa sanan yace ”lafiya , suna had'a ido da Bash ya sakar masa wani killer smile , tare da kashe masa ido d'aya , Harun ya kasa fasara wanan kalo mai cike da abubuwa na rashin kyautawa ." Emanuel ne yafito sanye da gajeren wando , ganin Bahija na bacci yasashi murmishi ya shige toilet yayi wanka , yana fitowa ya shafa wasu matuka masu tsada da turare , ya sanya farar riga marar nauyi , ya kwanta , matsowa yayi kusada Bahija ya rungumeta yana kissing d'inta , lol duk abinda Emanuel ya keyi tana kallonsa , amma bata bud'e idanunta duka ba , matsota yayi sosai ya d'aga ,y'ar k'aramar rigarta ya fara shafo cikinta , yana jin soyayyar babyn har cikin ransa , yanzu kam tunanishi anya zai iya bawa k'ungiya ,jaririn da Bahija zata haifa ?"ya k'ara rungumo ta yana wasa da gashin kanta , daganan bacci ya d'aukesu , dama ba sallah sukeyi ba dukansu , washe gari Bahija ta tashi da san cin pizza , Emanuel kuwa yau hutu yakeyi kasancewar yau Sunday , haka suka shirya suka nufi wani katafaren shagon kayan k'walama , komai Bahija tace ”tanaso baya yimata musu , ya kashe mata kud'i sosai , bayan sungama da nan ne suka nufi kasuwa , shagon kayan jarirai , sosai ya jido kaya masu kyau ,amma cikin zuciyarsa sam babu dad'i." Kwance Asma'u take tana bawa jaririnta nono , kira ne ya shigo wayarta , cikin sanyin jiki ta d'aga Umma dake zaune kusa da ita ta kasa kunne dan kwana biyunnan bata gane mata , Umma ce taji Asma'u na cewa ganinan zuwa , ajiye yaron tayi a cinyar Umma tana shirin sa hijab Umma tace ”Asma'u ina zaki?"gabanta ne ya fad'i tace ”zani gurin Bash ne wai ya siyowa yaro madara , hmm Umma tace ”cike da takaici , kafin Umma ta gama tunani , Asma'u ta fice , da fitar ta , ta hango motar Bash sauya tafiya tayi tana yanga , Bash daga cikin mota yaja tsaki yace ”banza marar amfani , tana isowa ta bud'e murfin motar ta zauna a gaba , shagwa6e fuska , Asma'u tayi tare da cewa haba Bash tun lokacin da ka gane inada ciki shikenan ka dena sakarmin fuska ko ?"sake fuskarsa yayi, yace ”no ba haka bane aiyuka ne zukayimin yawa kuma dai yanzu kinsan abinda ya kawoni , Asma'u ce ta d'aga hijab d'inta tare da cewa kaga breast d'ina wlh zafi yake yimin , wata uwar harara Bash ya doka mata tare da cewa wato kin d'auka yanzu zan iya had'a jiki dake ko , to bari kiji ,ko tsautsayi na fishi samako , dan haka karki kuma k'okarin yimin haka , ranta a 6ace tace ”bazan auri Harun d'in ba kai zan aura !!!." Da fitar Harun daga gidansu momy ya fice ya tari napep zuwa makarantar su ,yana sauka a bakin get yaga makarantar a rufe , ji yayi an rufe masa ido tare da sunkucesa aka turashi cikin mota , tafiya sukeyi cikin wani jeji da bakajin k'arar komai sai na tsuntsaye , wani guri da aka had'ashi da buhu suka ajiyeshi tare da turashi cikin d'akin , suka rufo d'akin da wata sanda da tazamo a jikin buhun Harun ne ya farka daga mutuwar tsayen da yayi sabda tsabar tsoro ya bud'e idanunsa , ya Gandhi cikin wanan d'aki , ya Allah ka dubeni , wani gurnani yaji na namomin daji , cikin tsoro ya had'e hanuwansa duka biyu yana adu'a , neman hanyar fitowa yakeyi amma babu ko alamar gurin fitowa , shin nan ina ne ?". Juyi yakeyi ko Allah zai bashi ikon ganin hanyar fita amma ina babu hali , Harun tunanin rayuwarsa ya fara tun farkon tashinsa har kawo yanzu bai ji dad'in rayuwa ba , banda wuya babu abinda yake sha , Allah kenan , tuno mom da Hajiya yayi ya fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai karatu , daga jin sauk'i nafito ziyara nakuma cin karo da wani iftila'in , laluba aljihunsa yayi yaga babu wayarsa babu komai a tare dashi , y'an kud'in da ya rik'o dubu goma suma babu su , tsananta kukansa yayi yarasa ihu zai yi ko me wama zai jishi ? ya mimik'e k'afafunsa yana salati ." *_BAYAN KWANA BIYAR DA 'BATAN HARUN_*. Mom ce zaune ido ya jeme tsabar kuka ,ga wani bak'i datayi , yau ne Alhaji zai dawo daga saudiya wato mahaifin mom , hidima sukeyi itada Hajiya amma jikinsu duk a sanyaye , komai cikin rashin walwala sukeyi , kira yayi a waya jirginsu ya sauka , Hajiya ce tace ”mom taje ta taho dashi itada driver , gyale mom ta d'auka ta shige mota suka nufi airport, datijon kirki kenan wato Alhaji Ahmad , sakowa yakeyi cikin takun k'asaita ko kwarjininsa ya ishi mitum dai daita nutsuwarsa ,yana gama saukowa ya iso inda momy take tsaye , harya yi mata magana bata sani ba , Aslamu Alaiki Fad'imatu , a razane mom ta ware idanunta tare da kallon fuskar mahaifin nata tace ”barka da zuwa Alhaji dafatan ka iso lafiya , janyo hannunta Alhaji yayi kasancewar ya gane motar gidansu ce yasashi shiga gaba mom kuma ta shiga baya, sunyi tafiya mai nisa sanan suka iso gidan , driver na parking ,mai gadi ya taso da gudu ya bud'ewa Alhaji muffin mota , rik'o hanun mom da itama aka bud'e mata yayi suka shige ciki ." Sanu da zuwa Hajiya tayi masa ywwa Alhaji yace ”lokacin da ya ga mom ta zauna batare da tace uffan ba. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 Facebook mom Islam Bakandamiya mom Islam Habib *🌹🌷Wanan page nakine shugaba tagari hak'ik'a samun kamarki sai an tona ina alfahari dake a kowane rubutu nawa*💃 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 23 & 24 _____Alhaji ne ya dubi mom cikin tausayawa dan tausayi take bashi tunda ta rasa mijinta tak'i aure , Zainab a firgice mom ta d'ago tare da kallon Alhaji tace ” na'am na fuskanci , kina cikin matsala ?"sunkuyar da kai mom tayi tace ”Alhaji kaci abinci gashican hajiya ta gama , murmishin su na manya Alhaji yayi yace ”tambayarki fa nakeyi , hawayen da take 6oyewa ne sukayi nasarar zubo mata , Alhaji bayason ganin 6acin ran mom , Yakuma magana cikin sanyin murya meyafaru?" son ,kawai mom ta iya cewa saboda matsanancin kuka , son ? Alhaji yace ”meya faru dashi ?"sun saceshi cewar mom , innalinali Alhaji ne ya kira Hajiya , cikin sauri ta taho tana cewa ai wanan yaron sai dai mutayashi da adu'a ,dan wlh suna son ganin bayanshi , bayan jinya dana gaya maka yayi ,to yanzu rabonmu da ganinshi kwana biyar kenan , Alhaji da ya nutsu yana jin zancen yace ”Allah ya baiyano dashi ,amma yau zan bada cigiya kowace kafa ta sadarwa insha Allah." Emanuel ne zaune suna breakfast shida , Bahija , kallonta yakeyi cikin so da k'auna , kashe masa ido tayi tace ” haba wanan kallo haka , murmishi kawai yayi dan shikad'ai yasan abin ke cikin zuciyar sa , tasowa tayi ta zauna a kan cinyarsa tare da shafo fuskarshi tace ”my man two days naga komai naka ya canza ne , kodai akwai matsala ne ?" waya gaya miki babu wata matsala burina inga kin aihu lafiya ,my happiness, dariya tasa tana tace ”gobe zan koma hospital zaro ido Emmanuel yayi yace ” gaskiya abar maganar hospital d'innan , sbda kindena fita , cikin mamaki , Bahija ta dubeshi tana cewa "saboda me ?bai kulata ba ya shige bedroom d'inshi , rayuwa Emanuel yakeyi cike da fargaba sosai bayasan abinda zai ta6a lafiyar , Bahija musaman ma babyn dake cikinta dan Allah ya zuba masa san y'a ya'a ." Bsh ne a mota yana tafiya yana jin kid'a ya k'ure volume sosai , wata budurwa ya gani a hanya , fara kya_kyawa , tana sanye cikin riga doguwa bak'a ,itama budurwar bak'a ce , hannunta sanye suke da tsadadun zobuna masu tsadar gaske , parking d'in motar yayi a gefe ,ya bud'e murfin motar ya fito ,isowa gurin wanan budurwar yayi , tare da cewa aslamu alaikum lol wa/alaikassalm , tace ”tana mumishin da yakuma baiyana kyawun ta , Bash ne yace ”inba komai y'an mata muje na rage miki hanya man , a'a kabarshi tace ”tana gyara zaman d'ankwalin rigarta datayi rolling dashi a kanta , Bash ne ya rik'o mata hannu , yasata back side shikuma yashiga gaba , suna tafiya yana kallonta ta mirror , cikin zuciyarsa cewa "yakeyi zan kwashi rabona dan naga kamar sabuwar budurwa ce , a ina zan saukeki , fashewa da kuka tayi tace ”iyayena sun mutu sakamakon gobara data tashi a gidanmu yanzu ban san ina zansa kaina ba , wani farinciki ne ya mamaye zuciyar Bash , yace ”barin saukeki a gidana matata tayi tafiya ,to nagode cewar budurwar ,menene sunanki , cewa tayi Rahama ,Bash ne yace ”suna mai dad'i nikam sunanan Bash ,ya shiga da motar ya bud'e suka wuce ciki , kallon gidan tafara wasu abubuwa da bata sani ba tafara gani , sbda batasan fridge ba da wasu kayayyakin , ruwan sanyi ya bud'e fridge ya d'auko mata ,kallon Bash kawai takeyi , batasha ruwan ba ta ajiyeshi gefe ,shikuma bayan yagama ciri kayan jikinshi a gabanta daga shi sai gajeren wando ya wuce toilet, wanka yayi da sabulu mai k'amshi yayi brush ,ya fito d'aure da tawul , parlor ya nufo , ganin baiga bak'uwarsa ba yasashi le lek'a gidan hangota yayi a can gurin hutawa a bishiyar lemu ,waro ido yayi , yace ”to ita kuma menene had'inta da bishiyar lemu ?" bashida mai bashi amsa ya wuce gurin da take ." Tun a kwana na biyu yasamu ya 6alle k'ofar ya fito , jeji ne da babu gidajen mutane a cikinsa , yanzu ko me za'ayi masa baisan hanyar komawa gida ba ,yana tafe yana d'ingishi , hango bishiyar da tazame masa abinci ya yi wato.bishiyar ayaba irin manyan nan ,kullum itace abincin sa , tafiya yakeyi yana dad'a kutsawa cikin jejin ,har yanzu Allah bai had'ashi da mutum ko d'aya ba gashi bashida komai a gurinshi , yana cikin tafiya yaji an k'wala masa kira , juyowa yai yana nazarin mai muryar jiyakeyi kamar ya santa , dawowa ya dingayi saboda tsakanin gurinda yabari da nisa ." Wa innan mutanen ne zaune da k'ok'on tsafinsu , babban cikinsu ne yace ” a halin yanzu yaronnan baya gidan su , to ina yayi ?"kuzo mushiga gurin dodo , shiga sukayi da baya suna yiwa dodon nasu kirari zan sha jini ,zan sha jini shine abinda dodon ke cewa "kowanne daga cikinsu ya zaro ido ." Muryar Basma Harun yaji , cikin mamaki , yace ”wai ke dama... yana nunata da yatsa , murmishi tayi ta ciro wata had'a d'iyar kujera daga mota , wareta tayi ta ajiywa , Harun ko kallon kujerar baiyi ba ya fara jero mata tambayoyi , shin menayi miki ?meyasa kika za6i wahalar dani nida iyayena ? dama kece sanadiyar 6atana na farko ?Allah ya isa tsakanina dake , taku takeyi cike da isa da gadara ,ta iso gabanshi tana juya jikinta dayake matsatsun kaya tasa kuma ko ina na jikinta girgiza yakeyi , Harun ne ya kawar da kansa gefe , yana fad'in astagfirullah cikin zuciyarsa ." "Harun ka tsaya kaji , wlh banida niyar saceka abinda yasa nayima haka ,inasan ganawa dakai ne ,mahaifina ya matsa min akan nafito da mijin aure to nace masa ,kai nakeso ,shida momyna to shine na rasa mafita amma banida burin cutar dakai " turr Harun yace ”cike da tsana ya dubi Basma yace ”karya kikeyi bakya sona wlh meysa baki bani amsar 6atana na farko ba , Basma ce tace ”na rantse da wanda raina yake hanunsa na rantse da Allah banida sa hannu gurin 6atanka na farko wlh , Harun ya yarda dan yaga hakan a k'wayar idanta ,to ki maidani gida inba hakaba wlh zanja miki d'aurin rai da rai , dariya Basma tayi cikin takaici tace ”ko kajamin inhar a kan soyayyarka ne babu damuwa tunda iyayena sunki daukar mataki , bud'e Jakarta tayi ta d'auko masa wayoyinsa da kud'insa ,kar6a yayi yace ”to maidani gida , motar ta bud'e masa suka d'auki hanya , sunyi tafiya mai nisa sanan suka iso cikin gari." Yau alk'awarin Bash da Asma'u zai kammalu , fitowa tayi da k'aton hijab ,shigewa motar tayi tafara tambayarsa ya maganar auran namu ,gimtse hararar da yake shirin watsa mata saboda yasan wanan shine last na zancensu ,ciro bandir bandir d'in y'an dubu dubu yayi guda biyar , yace ”wanan dubu d'ari biyar ne , inhar kika yarda da auran Harun to wanan kud'in sunzamo mallakinki , kuma bayan hakan kar iyayenki suyi komai na d'aki nizanyi miki ya cire wata rantsatsiyar waya ya mik'a mata tare da sabon layi yace ”duk nakine , Asma'u ce tafara hango wasu taurari masu haske ,shikenan tayi kud'i wow tazo duniya a sa'a , murmishi Bash yayi yace ”kuma duk wata zandiga yimiki transfer na 20k juya kud'in takeyi tana k'ara jujuyasu , sunyi yawa ne ?"cewar Bash zaro ido Asma'u tayi tana yimasa wani irin kallo...✍️. Vote me on wattpad ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 *🌹🤙MASU FARAN TA MIN WANAN PAGE D'IN NAKUNE NABAKU SHI HALAK KUYI YADDA KUKESO SHARHINKU YANA SANI JIN SOYAYYARKU 😘* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 25 & 26 _____Asma'u ce ta kar6i kud'in tare da shek'ewa da dariya tace ” Bash d'an duniya , bai kalleta ba yace ”Asma'u abokiyar aiki , sukasa dariya , tsayar da dariyar Bash yayi kana ya cewa Asma'u yanzu zakizamo matar Harun kenan ko hhh ai babu matsala ,tanayi tana fifita da kud'in hanunta , ficewa tayi a motar shima ya wuce , tunda ta shiga gida Umma taga yanayin fuskarta cikin farinciki Umma tace ”meyafaru , Asma'u ce tace ”wai Abban Harun zai zo juwa jibi akan maganar , auranmu , tsaki Umma taja tace ”kun gama iskancewar ku keda Harun d'in to uban mezakuyi a gidan auran ?"6ata rai tayi tana sosa kai , mik'owa Umma dubu d'ari tayi ragowar harta je ta turasu cikin kaya , kar6a Umma tayi fuskarta babu wal wala ta fice , tsalle Asma'u ta doka tana wak'a ,juyowa tayi taga jin jirinta na kuka , hawaye ne ya zubo mata tace ”yanzu da wanan yaron zani gidan Harun d'in ?gashi ba nashi bane , share hawayen tayi tafara bashi nono." Bash ne zaune a gefen dadynsa , dady ne yace ”my son kamar kanada abin cewa , sunkuyar da kansa yayi kamar mutumin kirki yace ”dady dama yarinyar da Harun yayiwa ciki ne ,iyayenta sukeson sa ranar auransu , dady ne ya gyara zama yace ”to su basusanni bane da saikai zasu fad'awa , a'a ba haka bane dady malm d'inne yace ”wai in gaya maka cewar Bash , to babu komai naji ance kakansa yadawo ma, yanzu zani gidan in bashi labarin abinda jikinshi ya aikata , Bash bai ce komai ba yasandai yanzu asirinsa bazai tonu ba , ficewa yayi daga d'akin dady ya koma d'akinshi ya kwanta cikinshi fal farinciki ranshi fess ." Dady ne yai wanka a toilet d'in d'akinsa ya shafa mai ya sanya kaya ya nufi bedroom d'in momy , samunta yayi tana tsefe kanta , zama yayi kusada ita , ya kamo hanunta tare da cewa , zan fita yanzu zan dawo , momy ce ta kwanta a cinyar dady ta marai raice fauska kamar yarinya , tace ”uhm ina zaka , dady na bala'in san shago6a dan haka yake k'ara son momy , amma in bala'inshi ya tashi baya da mutunci har ita ma bai k'yaleba." A dai _ dai saitin makaranta ta ajiyeshi , k'in fitowa Harun yayi yace ”wallahi sai kin kaini har gidan iyaye na , dama abinda Basma take sonji kenan ta juya mota ya fad'a mata anguwar suka d'auki hanya , da isarsu tayi Horn mai gadi ya bud'e suka Shiga, Harun ya rigata fitowa itama ta bud'e ta fito , mai gadi ne da drivern su suketa gaida Harun ,amsawa yayi da fara'arsa , yana gaba Basma na baya , da shigarsu parlor sukaji muryar Alhaji na cewa tunda ya zamo d'an iska ai shikenan tunda ta haihu ai babu abinda ya rage gara ya aureta kawai zai gane kuransa , Harun ne yaja ya tsaya dan ya fuskanci dady yazo gidan , tunowa yayi da sharin dasu ,Bash sukayi masa akan yayiwa wata ciki , hawaye masu zafi suka kwaranyo masa daga idanunsa , durk'usawa yayi ya d'aga hanunsa sama cikin murya mai alamun kuka , Basma na gefensa tana tsaye bata gane menene yake faruwa ba , sai dai a yanayin da taga Harun tasan ko maganar tanada alak'a dashi ne oho ." Harun ne ya d'aga murya sama yana kuka yace ”Allah ka jarabceni da jarabawa iri iri Allah yanzu kuma ka jabceni da wata nadawo daga wata , Allah kaduba maraya Allah ya ceto rayuwata Allah kayi gagfawar baiyana gaskiya Allah narok'eka Allah kasa wanan shine k'arshe wahala ta , ya shafa adu'ar yana kuka mai cin rai , Basma itama kukan takeyi tanata share hawaye , mom da tun d'azu taga shigowar Harun tasa hanunta ta d'agoshi tana kuka tace ”nasan bakai kayi ba ,ba'a shedar d'an yau amma ni wlhi zan shedeka ,nasani ba tun yauba dadynku ba sonka yakeyiba burinshi yaga rayuwarka ta salwanta tunda yasamu ya salwantar da rayuwar mahaifinka , to wlhi wanan karon bazan lamunta ba sam." Dady da yajiyo surutun mom ya fito yace ”wato kina nufin ni zanyiwa Haruna k'arya kenan ko ? har da yaushe kika haifi d'an da nanunawa tsana kiji tsoron Allah , momy tana kuka tace ”walhi tsakanina daku kaida yaronka da matarka Allah ya.....wani kid'ima mmen mari aka wanketa dashi , jiri na d'ibarta tana shirin fad'uwa Basma ta d'agota tare da shiga da ita ciki , batasan d'akin da zatasa mom ba yasa ta kaita wani parlor da babu komai cikinsa sai lallausan kafet ." Wasu surutai mom tashiga yi hankalin Basma ya tashi sosai , kasancewar , tasan adu'oi da yawa kuma saukar alqur'anin ta biyu ,tafara yiwa mom adu'oi tana tofa mata tana yimata kabbara a kunnenta , atishwa mom tayi tare da rik'o Hanun Basma tana kuka , jijigata Basma tayi itama hawaye na zuba a fuskarta , Harun ne ya shigo fuskarsa jik'e sharab da hawaye ya durk'usa a gaban mom yana k'ara yimata wasu adu'ion ." Alhaji da dady suka dawo parlor suka zauna , zuciyar Alhaji sam babu dad'i yana huci yana bawa dady hak'uri, cikin salon yaudara dady yace ”ka haifi d'an ne baka haifi halinsa ba , ,daganan sukayi sallama akan duk inda gidan su Asma'u sukayi dady ya gayawa Alhaji maganar auran kasancewar Hajiya batanan , Alhaji ya zartar da komai ." Mom ce ta mik'e dan lokacin taji k'arfin jikinta dake inhar ranta ya 6aci to sai aljanunta sun motsa ,godiya Harun yayiwa Asma'u da irin temakon mom d'inshi da tayi. mom ma godiya tayi mata , ta mik' tace ”zata tafi , mik'ewa mom tayi suka fito waje dukkansu mom na cewa Harun ina yashiga ? yau kwana shida ranbonshi da gida , Harun ne ya nuna Basma , kuka Basma tasa tace ”mom ki gafarceni wlh banayi haka bane dan in cutar dashi , mom sanshi nakeyi tun tana zuwa makaranta amma yak'i saurarata cewa yakeyi shi baya soyayya , nikuma wlh shi nakeso , iyayena basu d'auki abin da muhimmanci ba shi 'isa nayi hakan ." Murmishi mom tayi tace ”banda abinka Harun ai wanan yarinyar ta can canci ka aureta , rakata gida ka dawo inyaso mayi magana kaji , to kawai Harun yace ”ya shiga gurin driver ita kuma ta shige gaba , yacewa drivern gidansu ya biyoshi da motar Basma suka shiga tashi , Allah ya tsare mom tayi musu ta koma d'akinta dan bata sami Alhaji a parlor ba." *INDIA*🌹 Nak'uda Bahija takeyi tun jiya amma har yau shiru , Emmanuel ne ya sanyata a mota da kayan baby suka nufi hospital , da isarsu labor room aka wuce da ita , likitoci ne suketa bata temako amma ina sunfara tunanin abin yaf'i k'arfinsu , Emmanuel kuwa har kuka saida yayi , kifa kanshi yayi yana kiran Jesus , can saiga wata nurse ta fito tace ”masa matarka ta aihu amma munsami baby ta gugutsure a cikinta dole wankin ciki za'ayi mata , Emanuel ne yace ”ya mutune ?!!eh nurse d'in tace ”wani uban ihu ya zuba yana bubuga k'afa yana surutu....✍️. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 27 & 28 _____Hajiya ce tadawo daga tafiya , dama garinsu taje , suna za,zzaune a parlor tana kunce tsaraba ta dubi mom , data zuba uban tagumi , Hajiya ce tace ”wai ke bazaki cirewa kanki damuwa ba , banaji kince Harun yadawo ba to yanzu menene na damuwa ?"Alhaji dake gefe ko kallon mom beyi ba ya kawar da kanshi , sabda shima yafara k'aryata zancen dady to kuma yanzu ai bakin alk'alami ya bushe ,tunda ya yarda amma baze sake shed'an yayi tasiri a zuciyarshi ba ,na yarda da cewar ba Harun ne yayiwa wanan yarinyar ciki ba , dole ba'a shedar d'an yau ." Mik'ewa mom tayi ta shige bedroom d'inta ta fad'a gado tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu , Hajiya ce ta shigo ta d'ago mom tace ”wai meke faruwa ne?" mom ce tace ”Hajiya dadyn Bashir ne ya lak'abawa son sharri , sharrin me ?"Hajiya ta tambaya "cewa yayi wai son yayiwa wata yarinya ciki , Hajiya ce ta firgita cikin tsoro tace ”yanzu me Alhaji yace ”dan beyimin maganar ba , share hawayenta mom tayi tace ”Alhaji ya yarda wlh , eh cewar Hajiya ta mik'e tayi parlor tana gyara d'aurin zaninta , cikin masifa tace ”ina Zakarin wlh bakayi wa jikinka adlci ba , Alhaji daya fito da redio a hannu yace ”to yaukuma babu girma mawa ?" harara Hajiya ta galla masa tace ”wlh Zakari garama ka k'aryata wanan sharrin da kayiwa jikanka shine kad'ai Allah yabaka , amma har za'ayi masa sharri kabasu goyon baya , mamakin masifar Hajiya Alhaji yayi dan ita ba mesan tashin hankali bace ." Bash na isa gurin bishiyar lemon yaci karo da budurwar da yake kira da beauty , k'walo masa lemu tayi a kansa , tana daga sama tana dariya , Bash ne yace ”beauty wanan wacce irin mugunta ce kuka tasa tace ”Allah bansani ba , saukowa tayi daga bishiyar , ganin yarinyar yayi ta koma masa kamar y'ar shekara goma sha uku , zaro ido yakumayi yana dad'a k'are mata kallo wai shin itace kuwa ?"to dai itance tunda babu wanda yake shigo masa gida ,ko dama kallon tsoro yayi mata ?"bashida mai bashi amsa yasashi rik'o mata hannu sukayi parlor." Da shigarsu ya d'auko mata Maltina , juya gwan gwanin tayi murya irin ta yara tace ”kana shan giya ne dama?"keee , Bash yace ”cikin tsawa , had'a ido sukayi yaga bazai iya yimata masifa ba , tunani yafara anya mutum ce kuwa ?"kawar da tunanin yayi ya k'aita wani bedroom da komai akwai a cikinsa harda kayan mata , kwanciya tayi tana ware ido , gani nayi ta zamo babbar budurwa tana dariya , dajin k'arar bud'e k'ofa harta koma inda take , Bash ne yashigo dagashi sai gajeren wando jikinsa babu riga , beauty ce ta k'wala ihu , da sauri ya fice , yazo fita ya sulle a k'ofar d'akin , ihu yakeyi amma baiwar Allah bata fito ba tanacan tana dariya , yayi k'ok'arin ya tashi ya kasa cikin sa sanyar murya yace ”beauty zoki temaka min , fitowa tayi tana dariya ,tana cewa am banja gala daka fati , wani uban ihu yasa yace ”wayoo Allah kardai aljana na d'auko , na d'auko ta babba d'azu ta koma k'arama ,yanzu kuma ta koma yarinya y'ar shekara goma , nashiga uku." Da isar su Harun Basma tace ”sai yaje ya gaida iyayenta , baiyi musu ba suka shiga , momynta tasamu a parlor tana rubuce_ rubuce , durk'usawa tayi tace ”momy please afuwan ,nabiya gidansu Harun ne mom d'inshi batada lpy , momy cikin fara'a tace ”ah barka son zoka zauna ga guri , durk'usawa yayi har k'asa ya gaida momy ta sanya masa albarka , mik'ewa momy tayi ta tattara takaddunta ta shige ciki , abinci mai rai da lafiya dakuma kayan k'walama da lamu Basma ta kawowa Harun , y'ar aikin gidanne ta shigo da tirai a hanunta tare da gaishe da Harun farfesu ne a ciki sai apple da kankana da sauransu ... Harun ya d'anci babu lefi ya yi godiya , satar kallon sa Basma takeyi ,dasun had'a ido ta sakar masa murmishi mai alamar love🤣 mik'ewa yayi yace ”to nagode nizan tafi , Basma kamar zatayi kuka tace ”sai yaushe zaka dawo ?"murmishi yayi wanda ya baiyana kyawunsa dakuma dimple d'in kumatunsa , yace "sai lokacin da Allah ya nufa , Basma ko kallon pink lips d'insa takeyi inda yake motsasu kamar bashike magana ba , rakiya tayi masa tare da k'ara jadada masa ya gaida mom." Bash ne kejin dariyaku sunkai na mutum biyar gashi babu damar tashi kwankwaso na ciwo ,kamo jikin bango yayi ya d'ingisa ya mik'e ,yafara tafiya kamar mai aihuwa , aikuwa beautyin tasa ta shek'e da dariya , da shigarsa d'aki ya kwanta juyin da zaiyi yaji ya soke da alura ,yakuma juyawa ta d'ayan 6angaren yakumajin ya k'ara sokewa , jiki duk ciwo ya mik'e yace ”wlh gobe sai India bazan zauna a Nigeria ba , wanan yarinyar kuma ta nemi iyayenta dan temakonta nayi amma takoma min kamar aljana ." *INDIA🤏😎* Bahija ce a d'akin hutu anyimata duk wani temako taji sauk'i gobe za'a sallame su , iya kulawa Emmanuel yana bata musamman ma dayaga ta mugun ramewa , washe gari an basu takaddar sallama suka tattara kayan babyn da suka jido yasasu a motarshi sukayi gida , da isa rsu lokacin anyi magrib suna gama cin abincin nasu da baya wuce kayan mar mari , ta kwanta dan jiya cikinta nayi mata ciwo bata sami damar bacci sosai ba yau kuma da rana abokanansa sun zo da yawa kuma ko wanne saiya bata kud'i mai tsoka , duk ta adanasu a kayanta , bacci ne ya sureta , shiko Emmanuel yana zaune da wata takadda a hanunsa , misalin k'arfe biyu na dare baccin Bahija yayi nisa , Emmanuel yashiga d'akinsa na tsafi , mutanene zaune a ciki da yawa , kasancewar tsafin nasu duk wani mai yi to yanada d'akin sirri a gidansa kuma duk dare yashiga zai samu ana meeting , yauma kamar kullum ya shige amma saida ya duba Bahija ." Bahija ba bacci takeyi ba saboda dama burinta tafito daga hospital ta gudu dan tasan dodo ne ya cinye mata jariri kasancewar ta ma bamai tsoro ba , jakar hannu kawai mai kud'ad'en ta ta d'auka sai hijab zumbulele da tasa tabud'e k'ofar a hankali ta fice da gudu , nidai bansan ina ta nufa ba cikin wanan dare, gudu takeyi Allah ma yasa ko ina da haske kamar rana mutane sai kallonta sukeyi , sai da tayi nisa da gidan sosai ta zauna tanata haki , tana hutawa ta d'ora da inda ta tsaya ." Sumaiyya wato inbaku manta ba budurwar Harun ,wacce Abbin ta yakawo mata saurayi tayi masa wulak'anci . Zaune suke a dining suna dinner rabonta da zaman hira da iyayenta harta manta , kullum cikin silent take daga d'aki sai wanka ko cin abinci , Ammi tun tana damuwa harta dena kulla ramuranta , gashi yau har wata d'aya komai bai sauya ba, Abbi ne yadu beta da farin gilashi a idansa yace ”daughter wato mu bamu isa dakeba kenan ko , damuwarki kinfi k'arfin sanar damu ...✍️. Please share Vote me on wattpad ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 29 & 30 _____Washe gari ya shirya kayansa , ya nufi parlorn momy , samunsu yayi itada dady suna kallo , gaishesu yayi yace ” yau zan wuce , dady cikin tuhuma yace ”ina zakaje ?"Bash ne ya mik'e tare da duba agogon hanunsa yace ”india zan tafi ancemin za'ayi wata gasa , momy ce tace ”kabari a koma hutu , yana shirin kuka yace ”ni wlh an takuramin , banida ikon yin komai , dady ne ya mik'e ya zo gurinshi yana bashi hak'uri yace ”to ya maganar plane d'in ?" Bash ne yace ”dady komai ya kammalu ,ya yiwa momy sallama zuciyarta babu dad'i , bataso tafiyar Bash ba amma dole tayi masa adu'a kuma tadena fushi dashi tunda hanyar mota zai bi , dady ne ya ce " masa ya shiga mota ya rakashi ." Tunda gari ya waye ya fito da beauty da jakar tafiyarsa , ya turota waje , dariya beauty da kamayi tana nuna Bash , zagunta yashiga yi yana cewa ko dai aljana kokuma wata halittar da ban dan banyarda dake ba , dahaka yabarta a gurin ." Tunda ya shiga jirgi gabansa ke fad'uwa , tuno beauty yayi cikin zuciyarsa yace ”ko tana ina oho , jiyayi mutum ya d'anne kan cinyar sa , zaro ido yayi yace ”dan ubanki waya kawoki cikin jirgi , lokacin jirginsu ya tashi , Bash kukane kawai be zo masa ba gashi ,be isa ya hanata abu ba , to wai shin mutum ce ko aljan?"babu amsa kuma babu mai bada amsa ." Dady ne yakira Alhaji a waya , akan maganar zuwa gidansu , Asma'u ,cikin sanyin jiki alhaji yace ”gashinan zuwa , Alhaji ne yafito ba tare da ya gayawa su Hajiya ga inda zai je ba , had'uwa sukayi a bakin titi a motar dady ,suka nufi anguwarsu Asma'u ,da zuwansu suka aika yaro yayi sallama da malam ,cikin sa'a suka sameshi yace ”su shigo , tabarma malam ya shimfid'a musu a d'akinsa kasancewar Umma da Asma'u basanan malam ne yace ”musu ina zuwa , fita yayi waje ya aiki wani yaro ya siyo musu ruwa da lemu ,ya dawo ciki suka gaisa , bayan sun gaisa ne ,Alhaji yace ”munzo akan maganar auran Asma'u ne da d'an wajen mu , malm ne yace ”ai basanan ma ni da naso abari yaron yayi wayo sosai , zuwa nand a wata uku ko hud'u se ayi bikin , yaro ne ya shigo rik'e da kayanda malam ya aikeshi , ajiyewa yayi a gabansu Alhaji , ruwa suka d'auka sukayiwa malm godiya suka fice ". Da saukar Bash ya rik'o hanun Beauty yace ”k'ila ubanki ya ta6a zuwa k'asar waje ko ?" beauty na kallon shi batayi magana ba , janyo hanunta yayi ta k'arfi ya sa6a jakar bayansa suka shiga mota , a anguwar da yake da zama suka sauka , gidan yashige da beauty , suna shiga yaga beauty tazama k'atuwar budurwa , mamaki da tsoro ne suka dira a zuciyar Bash ya finciko gashinta had'e da hijab d'in jikinta yafara kifa mata mari , saida yayi mata mai isarshi sanan ya turata , duk wanan marin da gabjenen hanunsa ,batayi kuka ba sai dariya da takeyi da muryoyi da dama." Mom ce tabawa Hajiya labarin Basma , dukda bata ganta ba tasan duk abinda mom ta yaba to lallai mai kyau ne , Alhaji na shigowa Hajiya ta labarta masa , yayi na'am amma da sharad'in Harun zai auri Asma'u , babu inda suka iya kuma babu mai war ware komai sai Allah , haka Alhaji ya sanarwa da dady a waya kasancewar , shima yanada hak'i a kansa , dady dayaji wanan zance baiyi farinciki ba , amma yasan koba komai kuma koshi yayiwa yarinyar ciki ko bashi bane duniya zata dinga yimasa kallon mazinaci ." Yau Harun yayi shirin zuwa gurin aikinsu , an sami nasarori da dama kuma ansami sauyi a gurin , zaune suke shida wani abokinsa wanda jininsu ya had'i , tambayarshi Harun yayi yace ”ina wanan yarinyar , dariya abokin nasa yayi yace ”ai tayi aure sati uku da suka wuce , shafa sajensa Harun yayi yace ”ashe tayi aure , dariya abokin yakuma sawa yace ”yadai aboki ?"wani ya rigaka ko ?"Harun ne yakama murmishi yana basarwa ,daganan ya wuce gidan su momy ." Da isarshi gidan ,ya sami momy ita kad'ai ce , sallama yayi ya durk'usa ya gaida momy , amsawa tayi cike da kulawa tace ”Harun ka gujemu ko ?" dariya Harun yayi yace ”momy ba haka bane , kitchen momy ta shiga ta d'ibo masa abinci da dambun nama , ta kai masa dining , tace ”masa yaje yaci ,Harun beyi musu ba ya wuce yaci ahinci ya cika cikinsa , saukowa daga dining d'in yadawo sunata hira da momy , duk rabi hirar tasu akan karatunsa ne." *INDIA*🤟. Da fitowar Emmanuel , daga d'akin tsafi ya nufi toilet , wanka yayi yasanya kaya da turare mai k'amshi , fitowa yayi ya nufi , d'akin Bahijja , bai lura da batanan ba ya kwanta tare da laluba hannunta , jin bai ji mutum ba ,yasashi mik'ewa zaune ,Bahijja ,yafara k'wala mata kira , babu ita babu alamrta , ko ina na gidan ya lek'a amma shiru , tunani yafara to ina yarinyar nan taje oho ,tashin hankali sosai Emmanuel yashiga zama yayi yafara kuka ,k'ara ficewa waje yayi ya zagaye ko ina na gurin bai ganta ba , nunfar fashi yake saukewa kamar mai shirin shid'ewa , ga uban k'aton ciki a gaba ,komawa gidansa yayi yana layi , rana zafi inuwa k'una wayoo , haka yayi kwanan zaune yayi ." Bahija ta rasa inda zata dosa ga ciwon jiki ga wani zafi da cikinta ke yimata , tarasa da wanne zataji , zama tayi tana kuka gashi gobe takeson komawa Nigeria , wayo Allah na , haka gari ya waye tana zaune tana kuka ko runtsawa batayi ba gari nayi haske ta ,hau motar haya ta nufi airport domin shirin tafiyarta , ta kammala komai dan jirgin safe zatabi , tasami ragowar kud'i masu yawa , hotel ta kama na masu k'aramin kud'i , tasi abinci , washe gari wanka tayi ko kaya bata canza ba ta nufi airport , k'arfe goma na safe jirginsu ya tashi zuwa Nigeria garin Kano." Yau Bash yakeda niyar fita wani wasa da za'ayi akan wata fitacciyar yarinya baturiya duk wanda yaci gasar to shi zai aureta , tun ana gasar saura sati Bash yaketa shiri yanata zumud'i, dan haryayi mafarki yaci gasar , wanka yayi yayi brush ya fito ya sami beauty zaune tana kallo a TV tsaki yaja yace ”kewai bakida iyaye ne ?"guntse dariya tayi inda akwai abinda yake bawa Bash dariya bai wuce dariya ba , mari ya wanka mata ,takuma tuntsurewa da dariya , d'akinsa ya wuce ya shirya koni danaga Bash sai da abin rubutu na yakusa fad'uwa , yayi kyau sosai kuma babu budurwar da zata ganshi ta kawar da kai , yana fitowa da kum na taje kai ya wurgawa beauty yace ”kaimin d'aki , dariya sata ta shige da kum d'in , ,k'arar wayarshi ce ta dakatar dashi daga bud'e k'ofar dazeyi , d'auka yayi yace ”abokina ganinan zuwa fa anfara ne ?"to ganinan , bude k'ofar yayi, yaji a rufe what ke dan ubanki zoki bud'e min k'ofa ,sama yaji anayi dashi kamar yaro kuma baiga kowa ba ,gashi yana lilo ....✍️. Sharhi and comments👌 Please share👏 Vote me on wattpad ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 31 & 32 _____Bash ne keta ihu yana salati tabb niko nace yau wace rana , fitowa beauty tayi ,wanan karon a y'ar yarinya tafito , aikuwa Bash yakuma tsorata sosai , gashi yanzu baya iya kallon fuskarta ,wasu abubuwa yake gani wanda bazaiso k'ara kallo ba , ruwa beauty ta d'ibo a jug tadinga watsa masa , gashi bakinsa bai mutu ba , sai aika mata da zagi yakeyi , itako tana dariya , bedroom d'inshi tashiga ta bud'e bed site d'insa kud'i tagani masu yawa , fitowa tayi tana nuna masa , Bash daya zaro ido cikin masifa yace ”wlh kika fitarmin da kud'i sai naci ubanki , dariya beauty tasa ta fice da kud'in , kasancewar , garin duk ,yare ne ba kowa kejin hausa ba , yasa beauty cewa , kowa yazo tana nuni da hannu sbda ba iya turancin tayi ba , watsa musu kud'in tadingayi , mutane basu fahimceta ba , amma tana watso kud'i suka dinga d'iba , komawa gidan tayi tasamu Bash ya jigata , hannu ta d'aga sai gashi ya fad'o ." Babu labarin zuwa gurin gasa dan haka duk wanda ya kirashi a waya baya d'agawa , washe gari da safe , Bash ya shirya muguntar da zeyiwa mutuniyar tashi , shiga d'akin da take kwanciya yayi ya hangota tana bacci fuskarta d'auke da murmishi , dariyar mugunta yayi yace ”shegiya maiyya zakisani yau , yana shirin d'aga rigarta kawai yaga batada ,k'afafu , ja da baya yayi yace ”nashiga uku wanan yarinyar dama haka take ?"kokuma yaune ta koma haka ?to babu mai bada amsa ,yasashi yin shiru ya ruga da gudu ." Maganar Basma da Harun tayi k'arfi dan yanzu ya saki jiki da ita sosai yana zuwa hira , amma ba'a kai kud'in aure ba ." Asma'u na shagalinta ita da kanta take tiwa kanta gyara maganin mata kuwa ta kashe kud'i sosai dakuma gyaran jiki , Umma dai ta zuba mata ido ne kawai dan rawar kan yayi yawa ." Mota ta tara zuwa gidan su , gidane babba kai da ganin gidan kasan wanda ya mallaki gidan mai nera ne , wato mahaifin Bahija Alhaji Saminu , hamshak'in mai kud'i ne ,sai dai wata matsala itace bashida lokacin iyalin sa koda wane lokaci yana k'asar waje gurin harkar kasuwancin sa amma kud'i kam ba'a magana , kuma kaff cikin matansa babu wacce bata mallaki kadarori ba ,kasancewar yana turo musu da mak'udan kud'i tun wata na 23 , matansa biyu , Hajiya Aisha dakuma Hajiya Salma basa fad'a ko kad'an kuma ko kaga y'ay'ansu bazaka ban bance ba , kasancewar suna zaune cikin rik'on amana." Hajiya Aisha itace babba kuma itace ”mai yara biyu Bahija da momy , duk cikinsu aure sukeso amma babu wanda ya isa ya tari mahaifinsa da zancen , a cewarsa wai sunyi yara , itakuma Hajiya Salma yarinyarta d'aya Saudat itace k'aramar cikinsu tanada shekara goma sha takwas , kowane yaro na gidan shek'e ayarsa yakeyi ,iyayen mata suna iya bakin k'ok'arinsu amma ina tsiyar d'an yau tafi gaban wasa." Bubuga get d'in Bahija tayi , cikin sauri mai gadi ya bud'e mata tana yimata sannu da zuwa cikin mamaki , ko kulashi batayi ba ta shige ciki direct d'akin Hajiya Salma tayi , bata wuce d'akin mamanta ba , Hajiya Salma da suke kira da Anty tana kwance a d'akinta taji sallama kuma murya irinta Bahija , a zabure ta mik'e tace ”Bahija , Bahija ce ta k'araso da sauri tana kuka ta fad'a kan Anty ,itama anty kuka takeyi , babu mai rarrashin kowa sai da sukayi mai isarsu sanan Anty tafara zazzago mata fad'a kamar zata daketa ,jibeki Bahija kinyi bak'i kin rame kamar mai ciwon k'anjamau , daga ina kike ?"Bahija babu abinda ta 6oyewa Anty , wani sabon kukan anty ta kumayi tace ”to ai yanzu da kika gudo wlh baki tsiraba tashi muje , suka nufi d'akin mahaifiyar Bahijan da suke kira da mama , Bahija ce ta durk'usa tana kuka , kallon mamaki mama keyiwa Bahija sekuma ta fashe da kuka tace ”kome kukayi bazanga lefinku ba wlh lefin mahaifinku ne ,kaf cikin gidannan babu yarinyar da bata kawo wanda takeso ba amma fur yace ”sai karatu wallhi mu ya cuta." Anty ce ta rufe mata baki suka fashe da kuka , dan duka y'a y'an idanunsu a bud'e yake. " *INDIA🤙* Kwanansa biyu rabansa da ganin Bahija amma ji yakeyi kamar yayi wata biyu ne , gashi yau yanada shiga gurin dodo , komai yayi masa zafi , haka ya mik'e daga kwanciyar da yayi ,ya koma bedroom d'insa yasa jajayen , kayansa ya shiga d'akin tsafi , dama shi ake jira , da shigarsa fuska babu wal wala yace ”yaza'ayi ku kashemin yaro babu sanina ?"dodo ne yayi wata mahaukaciyar dariya yace ”kana nufin kaci banza ne ?"dukiyarmu da kakeci fa ?"Emanuel zai kuma magana yaji wata firgitacciyar tsawa , akace ”yanzu ma jinin uwar yaron mukeso zamu hak'ura daga ita mungama da faninka , cikin razana ,Emmanuel ya d'ago da jajayen idansa yace ”kuyi hakuri ni ku sha jinina amma karku ta6a Bahija , yana kuka yana rok'onsu." Babu wanda ya sake magana sai ganin kowa na watsewa yayi , fitowa yai daga d'akin tana kuka sosai , shidai damuwarsa Bahija karsu ta6a ta , yana mai maitawa ahaka bacci 6arawo ya k kwashesa,da tashinsa ya tuna basa bacci da wanan kaya cikin tsoro yahau cire kayan amma me abinda yagani ne yayi matuk'ar firgitashi yanada , bin doka amma dan rana d'aya ya mance sai ayi masa haka, su sam basa uzuri ,ya fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai karatu ." *NIGERIA* Alhaji ne ke shirin komawa saudiya yau amma zai dawo bikin Harun , su mom da Hajiya sunyi masa soye soye dakuma abubuwan da ba'a rasa ba , cikin farinciki suka rakashi airport , tare da yimasa kyakyawar adu'a , sai da sukaga tafiyarsa sanan driver ya maidasu gida." Basma ce ta shirya cikin doguwar riga bak'a mai adon duwatsu da d'an k'aramin hijab fari mai kyau , jakarta ta d'auka dama tun jiya ta gayawa momynta zataje gidan su mom d'in Harun , turaruka masu k'amshi ta bata dakuma turaren wuta , kasancewar su y'an Meduguri , bata d'auki driver ba , ita da kanta take driving , super market ta nufa , siyayya tayiwa mom da Hajiya dakuma uwa uba Harun , ta sa a booth , tana cikin tafiya ne ta hango agogon hannu a wani shop , parking tayi ta shiga shagon , za6o masa wani mekyau tayi tare da zobe mai tsada da turaruka masu k'amshi , da isarta tayi horn mai gadi ya bud'e mata , get , kasancewar ya ganeta , parking tayi a parking spice na gidan , ta fito ciro kayan tayi a bayan mota , da gudu mai gadi yazo ya kar6i kayan ya shige dasu , itama shiga tayi , a parlor ta tararda mutanen gidan amma Harun bayanan ,mai gadi na shirin tafiya ta mik'a masa dubu d'aya , har k'asa ya durk'usa yana yimata godiya , hakan da Basma tayi takuma samun gurbi a zuciyar mom ... Hajiya cikin murna tace ”wanan itace kishiyar tawa , sukasa dariya , har k'asa ta durk'usa ta gaida mom da Hajiya , Hajiya nata tsokanar ta , samun gurin zama tayi tare da , ciro wayarta ta aikawa da Harun sak'o ....✍️. 👏masu sharhi ina godiya da soyayyarku a gareni kuyimin afuwa kunsan jiki da jini kuma dai yauma banajin dad'i wlh , karkuyita jirana ne yasa nayi muku 🤙. Comments &sharhi Vote me on wattpad ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 *MASU SHARHI KUYI HAKURI NA JINA SHIRU INA GODIYA NAGODE DA NUNAMIN SOYAYYA NATASHI LPY NAKUMA JI SAUKI ALLAH YABAR ZUMUNCI HAKIKA KO NAYI FUSHI KUNA SANI FARINCIKI 🥰* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 33 & 34 ____ Soyayya dai tayi gaba , dan tsakanin Harun da Basma babu mai bacci ba tare da yaji muryar d'an uwansa ba, soyayya sukeyi mai tsafta dakuma amana , yanzu ma Harun ya zamo d'an gida a gidan su Basma , momymta kuwa kullum yabawa takeyi da hankalinsa , gashi biki nata matsowa , komai cikin nutsuwa sukeyi , Basma kuwa tun tanzu tafara shan gyara , tayi kyau tayi haske gwanin sha'awa ." Muhammad d'in Asma'u yayi wayo sosai dan yana koyon zama , yanzu , Umma ce ta shigo d'akin da take zaune a ciki , Asma'u ce ta canza fuska tace ” Umma gyaran kayana nakeyi , jikin Umma a sanyaye tace ”Asma'u ,waye yabaki kud'in danaga kike wadak'a dashi ?"d'an hararar Umma tayi tace ”nikuma ?"wane kud'i ?"sarai Umma ta gane so takeyi ta kawar da zancen , Umma ta dubeta tace ”wlh kibi duniya a sannu ina tausaya miki Asma'u , kullum sai naga takardar tsire da gwan gwanin madara , waye yake baki ?"nasan dai tunda kikaje kikayi abin kunya babu d'an arzik'in da yake zuwa gurinki , kuka Asma'u ta fashe dashi mai cike da munafurci , tace ”yanzu umma ni kike zargi ?"mik'ewa Umma tayi tabar d'akin , tana fad'awa d'akinta ta fashe da kuka , tana cewa "ka haifi d'a baka haifi halinsa ba yanzu rayuwar da yarinyar nan ta jefa kanta tana ganin yayi kenan ." Zaune suke cikin wasu bak'ak'en kaya , da tsogon dare , lokacin ma k'arfe biyu dai dai , wata mahaukaciyar dariya ce ta ke tashi a fad'in gurin , ogan su dake zaune da jan kaya da bak'i yace ”kai munyi jiranka har mun fara gajiya , wai yaron yafi k'arfinku ne ?"cikin rawar jiki wanda aka yiwa magana yace ”ba haka bane ,yaron yanzu ko d'akinshi dodo baya iya zuwa , wani ihu ne ke tashi kuma duk dodon ne mai hakan , shugaban su yace ”wanan fa kawowar da zakayi bawai iya dodo ne zai amfana da abin ba kaima yazamo arzik'i a gurinka ." Cikin sanyin jiki yace ”to zanyi k'ok'ari inga na kawo , daganan kowa ya watse . Bahija ce zaune ita d'aya a d'akin ta , wayarta ta ciro , ta kunna dan tuda tazo bata wai wayi wayar ba , gurin sak'onni ta fara dubawa , cin karo tayi da sak'on Emmanuel bud'ewa tayi tana karantawa , _my Bahija meyasa kika gujeni kinsan ina sonki bazan iya rayuwa babu ke ba, kidawo gareni please mukuma gina sabuwar rayuwa tare da samo baby please_ Sak'on ma haushi yaba Bahija ta wuce gurin , kirane ta shigo wayar , number Emmanuel tagani , cikin tsoro tace ”kodai na fasa wanan wayar , karfa azo ina zaune mutumin nan ya gama shanye min jini , da haka wayar da gama ring ta gaji yayi kira yayi goma amma tak'i d'agawa ." Momy ce zaune itada Fauziya , suna hira , gani tayi Fauziya ta mik'e tana layi , a tsorace momy ta taso ta rik'e ta , bedroom d'inta ta kaita amma kan kace me ,rai yayi halinsa ,momy ce ta rungume gawar Fauziya tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu , batasan lokacin datace , mutuwa babu ciwo ba , takuma fashewa da kuka , ta mance da Allah babu ruwansa , number dady ta gwada tace ”masa yazo maza maza , Fauziya batada lafiya , cikin kid'ima dady ya shigo mota ya dawo gida , bai sami momy a parlor ba , kai tsaye d'akinta ya wuce ,acan ya sameta rungume da gawar Fauziya tana kuka , dady ko tsayawa yai kallonta cikin tuhuma , yace ”saboda batada lafiyan ne kika sata gaba kina kuka ." Momy ta kasa magana ta d'ago Hanun Fauziya , haka ya koma yarab alamun babu rai , innalilahi anan ya tsaya yana kuma mai maita hakan , durk'usawa dady yayi a gurin yana kuka , momy ce ta tsayar da nata kukan tana bashi hak'uri , lokacin k'arfe biyu na rana , dady ya sanarwa Alhaji da abokansa na arziki , momy kuwa tanata kiran y'an uwanta da su Hajiya da mom da Harun , kowa ya jinjina mutuwar nan musamman Bash da momy takira shi yanzu take gaya masa har kuka sai da yayi." Kan kace me gida har yacika da mutane sosai , masu zuwa gaisuwa dakuma masu shirin kaita makwancin ta , wata dattijuwa ce tayi mata wanka tare da yimata sutura aka sata a makara , maza suka nufi mak'abarta , momy kukan ma ya dena zuwa , su hajiya sunzo itada momy sunyiwa momy gaisuwar rasuwa , kirane ya shigo wayar momy , Bash ne yace ”momy gobe ina hanya , fatan alkairi tayi masa daganan suka kashe wayar ." Washe gari kwanan Fauziya d'aya da rasuwa mutane kuwa shigowa sukeyi sosai kasancewar momy tanada mutane , wasu mata dady ya d'auko suka girka abincin sadaka haka gidan ya koma babu wata wal wala a cikinsa kullum cikin kar6ar gaisuwa suke. *INDIA*🌹 Bash ya gama had'a kayansa guri d'aya , gashi bashida kud'i , Beauty ta sace kud'in duka , tagumi ya zuba ga jaka a gabansa , wayar dady ce ta shigo , cikin rawar jiki ya d'auka yayiwa dady gaisuwa , dady ne yace ”kanada kud'ine a gurinka ?"da sauri Bash yace ”ko sisi dady banidashi , dady ne ya turo masa kud'i mai yawa , sukayi sallama ." Tunanin Bash ina beauty ta je gashi gobe zai tafi , d'aga kafad'a sama yayi yace ”dama ba dake na zo ba dan haka bazan koma dake ba , yacigaba da loda takalmansa a jikin jaka... Washe gari jirgin wuri zai biyu yagama komai tun jiya , ya kulle gidan ya nufi airport , cikin ikon Allah jirgin su ya tashi zuwa Nigeria." Sumaiya ce zaune gaban Abbi yana yimata nasiha akan rayuwa , sunkuyar da kai katsa tayi tace ”Abbi yanzu dai banida kowa amma in kana dashi ka za6omin , cikin farinciki Abbi ya sanya mata albarka , Ammi ma taji dad'in hakan , dan sun riga da sunyi mata miji , suna tsoron sanar da ita , yau gashi Allah ya amsa adu'arta , Abbi ne yace ”to y'ar albarka tashi kije ki kwanta , da komawarta d'akinta ta fashe da kuka tana tunanin anya shawarar data yanke, ta yiwu kuwa ta fashe da kuka babu inda zatayi dole ta kar6i za6in iyayenta da hanu bibiyu ." *AIRPORT* Zane Bash yake a cikin jirgi , ranshi fess wanan munafukar bata biyo sa ba , wani farinciki yakeshi , in ya tuno da rashin k'anwarsa da yayi sai yaji babu dad'i , yana cikin tunani ne ,yaji mutum ya fad'o cinyarsa , a zabure ya mik'e yana ihu , hankalin mutanen dake zazzaune ya dawo kansa , kowa sai kallonsu yakeyi , Beauty ce ta fito a zabgegiyar budurwa ,amma kamaninta basu 6ace ba , Bash besai ya zaiyi da rayuwarsa ba ,yasa hannu a ka kamar zaiyi kuka , beauty ko na cinyarsa gata k'atuwa ." Cikin masifa ya yaye zanin daya luly6e zaninta , kofato ya hango wani ihun yakuma sawa yana cewa ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba , kiyi hak'uri ni dama nasani ina tare da Aljana ne ,babu Wandaya kuma bi takansa shi kad'ai yake shirmensa , hawaye sha6e _ sha6e a idansa yaci kuka gashi koyaya idanshi yakai kan k'afar Beauty a tsorace yake , tunanin ya fara to tayaya ta shigo jirgi batare da tagama komai ba ......✍️. Vote me on wattpad Please share ♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 35 & 36 ____ Da haka dai jirginsu ya sauka a Nigeria , driver ne yazo d'aukarsa , juyawa yayi yaga baiga Beauty ba , babu wani farinciki da zaiyi tunda yasan yana shiga motar zai ganta a ciki , driver ne ya d'auki jakar kayansa yasa a Booth , ya rufe , yana tada mota sukaji alamun kamar mutum ya fad'o Beauty ce keta dariya , Bash yarasa inda zeyi kawai yafara kuka , ga wani tsoro daya ziyarci zuciyarsa , driver ganin wanan yarinyar yasashi taka burki ya fice da gudu , Bash ne yace ”Idi kazo ka tuk'amu mu wuce ,ina Idi ya bazama ko tsayawa baiyi ba ." Bash ne yaji mota na tafiya , zaro ido yayi yana salati , kafin ya tsalako , gurin zaman driver Beauty ta zauna ,tafara driving , Bash dai yariga ya suma babu nunfashi , driving takeyi tana dariya har ta iso gidansu Bash , tana horn taji shiru , ba'a bud'e get d'inba , sauka tayi tafara bubugawa kamar ba hanun mutum ba , kowa na cikin gidan ya tsorata , haka mai gadi ya fito ya bud'e get d'in , suna had'a ido da Beauty ta sakar masa murmishi , a zabure ya juya kansa dan , gani yakeyi idanunta suna yimasa kamar na mage , parking tayi a parking spice na gidan ta fito , gyara zaman d'an karamin hijab d'inta ta nufo cikin gidan." Kowa sai kallonta yakeyi ita ko babu wanda ta kula ta shige parlorn momyn Bash , da ganinta momy tace ah y'ata barka , da fara'arta Beauty ta zauna momy ce takawo mana ruwa da lemu , abin mamaki babu abinda Beauty tasha , ta dubi momy dake kallonta tace ”Bash na cikin mota , daga haka Beauty ta 6ace , ihu momy tasa tana salati , wanan mutum ce kuwa ?" to in mutum ce ya za'ayi ta 6ace ?"babu mai bata amsa yasata fitowa waje cikin tsoro , bataga Beauty ba , haka taje ta bud'e k'ofar motar , ganin Bash a kujerar baya jiki a sandare yasata k'wala ihu , tana kuka , hankalin su dady ne yayo gurinta mutane suka taso kowa yazo ya lek'a cikin motar , dady ne yace ”shikuma mai yasameshi , momy takasa bada labarin wacce ta shigo mata hartace Bash na mota sai dai kuka kawai , dady ne yace ” wa momy ta Shiga motar su wuce hospital , a tsorace ta shige ko mayafi babu ,dady ya tuk'a motar , da isarsu aka wuce dashi d'akin gaggawa wato emergency , aka fara bashi temako , basu sha wiya ba gurin samun dai _ dai tuwar nunfashin sa." Yau bikin Harun saura sati uku , shiri kam anayi ta 6angaren su , Basma sosai momy ta ke gyarata kasancewar taga angon nata tsaf tsaf , magugun guna na mata itatuwa ne su kankana apple ayaba da aya da dabino da sauransu momy na bawa Basma , musamman ma dataji za'a had'a Bash da wata bayan y'arta , Basma ta k'ara k'iba tayi kyau fuskarnan sai k'yali takeyi ga wani k'amshi da inka zauna kusa da ita kokuma ta zauna kusa da kai baza kaso tashinta ba ." Asma'u kam ita ke gyaran jikinta da kanta bata jira Umma ta temaka mata ba , sai rawar kai , gashi bata ta6a ganin angon ba lol , ko number shi batadashi bare sanin ko inane gidan su , itadai tana gyara kanta ." Mom ce ta dawo daga kasuwa , kaya masu gadi da drivers suke shigowa dashi , akwatuna ne set goma sha biyar , palorn Hajiya sukayi dashi , oyoyo Hajiya ke yiwa mom , cikin fara'a mom ta ce ”Hajiya na gaji wlh , kayan Hajiya tafara fitowa dasu masha Allah , gaskiya koni da nake rubuto muku duk abinda nagani ,hmm zan iya mancewa da wasu , akwatunan atamfofi daban akwatin gyaluluka daban haka ma na skirt shima daban na bra daban na ves daban na turaruka daban , kai barin barku haka ,dan kayanfa sunyi babu makusa , tundaga akwatinma zakasan kayan na manya ne." Bayan 1 hour da zuwansu ,komai ya zama normal , aka sallamesu suka dawo gida ,Bash kam yariga ya tsorata , shi besan wanan wace masifa bace , tunda ya had'u da Beauty bashida zaman lafiya kodai dama tazo ganin bayansa ne ?"oho yadinga tunaninsa barkatai ." *INDIA*🌹 Yau alk'awarin Emmanuel da dodo zai cika , gashi wanan ne na k'arshe ,yarasa jinin wa zai bada , gashi ya bada na mamanshi da na babanshi da jinin k'anwarsa dakuma na jaririn da mamansa ta haifa duk ya badasu , ga jaririnsa na gurin Bahija , yanzu kuma bashida wanda zai bada , misalin k'arfe 2 pm na dare kowa ya hallarci d'akin tsafi , shikam yazuba uban tagumi ta kansa dodo yafara , yau mukayi dakai zaka cika mana alk'awari , Emanuel ne yace ”nace muku Ku kasheni ko nace kusha nawa , cikin masifa yake maganar , tsawa aka daka masa ,shiru yayi yana maida nunfashi , dodo ne ya d'ago ,wani k'aton k'ok'on tsafi , fuskar Bahija ce ta baiyyana , daga inda mutanen suke zaune suna hango komai na cikin k'ok'on , cikin masifa Emanuel yace ”inko kukayimin haka bakuyimin adlci ba , zan fita a wanan k'ungiyar kuma koda yin hakan zai janyo mutuwata ." Hango Bahija a cikin k'ok'on tsafi yayi ,tanata jujuya kanta tana cije baki , kuka Emmanuel yafara tare da cewa tur da wanan k'ungiya kuma sai kunyi nadamar yin hakan , babu wanda ya kulashi ,kuma duk maganarshi bazata sa su tsaida k'udirinsu ba , haka aka tashi taro ran Emmanuel babu dad'i komai ya birkice masa , direct offishin matakan tsaro ya nufa wato sojoji , yana kuka yana bada bayanin abinda ke faruwa , wani farin mutumi bature yace ”masa a inane zamu samesu , Emmanuel ne yayi musu kwatancen inda zasu had'u , sashi a motar sukayi suma suka shiga , abin mamaki da zuwansu sukaga gurin ya koma jeji." Kallan kallo suka fara , sumadai sunsan akwai gidaje bila adadin a gurin amma gashi babu alamun anyi gini yanzu , Emmanuel ne tsoro ya kamashi yana tunanin hukuncin da zasu yanke masa." Bikin Sumaiya da yaron k'anwar momyn ta ya matso ,yau saura kwana biyar , kyau kam amarya tasha dan kobatayi kwaliya ba tanayin kyau to inaga ranar bikin , yanzu kam ta hak'ura ta mik'awa Allah komai ta amshi za6in iyayenta , sosai suke zuba soyayya da saurayin nata mai suna Khalid , kamar masoyan da suka shekara." Wani abin mamaki ashe beauty na d'akin Bash tana bacci tun lokacin da momy ta nemeta ta rasa , suna shirin shiga da Bash d'akinsa , suka hango Beauty na kwance tana bacci cikin nishad'i , tsabar tsoro momy sake Bash tayi a k'asa ta ruga da gudu tabarshi shi da dady , Bash ne yafara cewa "nidai nashiga uku bansan yazanyi ba ko wane lokaci aljanar nan na tare dani." Ashe zancen zuci ya fito fili ,dady yaji duk abinda yace ”aljana ?"dady ya mai maita ,eh wlh dady , tsoro ne ya fara kama dady yace ”ai ance ljanu basuda k'afafuwa bud'e nata mugani , a tsorace Bash ya kalli dady dady ya kalli bash , dakewa Bash yayi yaje gurin bak'ar jallabiyar Beauty ya bud'e k'afarta , kofaton suka hango cikin tsoro dady zai zura da gudu k'ofa ta rufe , gashi ga Bash kuma ga Beauty aljana lol." Bash ma neman gurin guduwa ya keyi amma babu hali k'ofa a kulle take , Beauty kuma na bacci , Bash yana tsoron yacewa "dadynsa wanan aikin ma Beauty ne ta farka tabashi horo , yaja bakinsa yayi shiru ...✍️. Vote me on wattpad ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 *JININ ABBANA FANS GROUP* *JININ ABBANA PANS (2)* *WANAN PAGE 'DIN NAKUNE 🤙* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 37 & 38 ____ Mutane suka gani cike a d'akin , kuma duk sa'anin Beauty ne , da bak'ak'en kaya , tsalle suketa yi suna dariya , dady da tsoro ya gama kamashi ,ya ce ” kai Bash tashi waccan mai baccin , ido Bash ya zare yace ”dady wlh itace babbar su , dady na kallon Beauty ,yace ”ke tashi , beauty ce ta mik'e tana dariya , wanan dariya ba k'aramin firgita dady tayi ba , yaran da suka zagaye dady da Bash suka fara magana wata iri , suna cewa "baku kun iya mugunta ba ?daga kai harshi bakuda tausayi ,to yau zaku gane kuranku , kowa yazo ya fad'i abinda yayi ,inhar kunaso mu bud'eku ." Jin shiru har dare yasa momy bubuga k'ofa amma shiru , ko motsin mutane bataji , number Bash da number dady bata shiga , hankalin momy ya tashi sosai ,tarasa ina suka shiga ,gashi d'akin Bash yak'i bud'uwa , tunani tafara kodai wanan aljanar tana d'akin ne ?"toshi Bash a ina ya samota , tattara zancen zucin tayi gefe ta nufi waje , driver ta hango zaune a takure kamar mai rawar sanyi." Cikin tashin hankali momy ta k'arasa gurinshi tace ”Idi zoka nemo min malamin ruk'iya , cikin tsoro Idi ya kalli momy yace , Hajiya karfa inje garin nemo wa a kwashe ni , tsawa momy ta daka masa , hakan yasashi ficewa da gudu , tunda ya fita yaketa gudu har ya wuce anguwarsu ,amma baisan ya zoba , mutane sai kallonsa sukeyi ." Pans kuzo muje mu taro Idi fa🤣. Komawa momy tayi ta zauna a parlor tana jiran dawowar Idi , agogo ta duba har k'arfe shida na yamma shiru , tagumi ta zuba tace ”to shi wanan ina ya tsaya , lol niko ina gefe ina dariya Idi ya falle da gudu , mik'ewa tayi ta d'auko wayarta a bedroom , number wani malami da yake zuwa yimusu sauka farkon tare warsu a gidan , gwada number tayi , cikin rashin sa'a akace mata number bata tafiya , tashin hankali momy ta shigeshi , babu miji babu d'a , ga Idi ma shiru , rasa wazata kira tayi kawai ta zauna tadinga cin kuka gashi babu mai rarrashi ." Bahija ce zaune itada anty da mama ,suna hira , yanzu kam jikinta yayi kyau ,washe gari da safe ta tashi da matsanancin ciwon kai tun ana ganin abin kamar ,wasa har takai ga tafara surutai da basuda kan gado , mahaifinta suka kira , "cewa yayi su kaita ,hospital , cikin gaggawa suka , kaita hospital , temakon gaggawa doctor suka fara bata , ciwo dai kamar wasa abin ya gir mama." Bahija batacin abinci sai ruwa shima ruwan dak'yar yake tafiya mahai fiyarta ko tana ganin kamar mutuwa zatayi , ganin wata uwar rama da tayi. " Yau kwanansu biyu a hospital d'in ,jiki babu sauk'i sai abinda ya dad'u , Allah sarki rayuwa , mutane sai zuwa gaisheta sukeyi , y'an uwa da abokan arzik'i ,duk wanda yasan Bahija to da k'yar zai ganeta , saboda tsananin ramar da tayi ." Tun su dady da Bash na kuka , har bacci ya d'aukesu , sai sunfara bacci sai suji dariyaku , haka dai gari ya waye da asbha momy ta fice daga gidan tayi wani gida a mak'otansu , tunda take bata ta6a shiga gidan ba yaukan dole ta janyo hakan , shiga tayi da sallama , gidane madai daici sunada rufin asirinsu dai dai gwsrgwardo , da shigarta mata gidan ta shimfid'a mata tabarma ,bayan sun gaisa ne momy take tambayar matar ko tasan gidan wani malami nan kusa , akwai matsala a gidanta, matar ce tace ”barin yiwa malam magana ,momy na zaune matar ta shige d'aki ta fito tana cewa "bari malam ya shigo kiyi masa bayani , to momy tace ”tana jin jina lamarin gidan ta , bayan 5minutes wani mutumi ya fito da malun malun , ya nemi guri a can nesa da momy ,a tabarmar da aka shimfid'a masa , momy ce tafara gaishe shi danan yace ”tafad'i abinda ke faruwa , labarin abinda yafaru tabashi , malm ya jin jina wanan lamari amma baiyi magana ba ,dan haka ya d'auki Alq'uranin sa yace ”muje , momy na gaba malm na baya , gashi garin beyi haske sosai ba, haka malm ya kunna touch light , momy kam tama mance da batun fitila , haka ta bud'e get d'in suka shige , kai tsaye parlorn suka shiga , nuni momy tayi masa da hannu kaga d'akinnan , murmishi malm yayi yace ”to , momy komawa kan kujera tayi ta zauna tana maida nunfashi ." Da shigar malam d'akin Bash yaga mutum uku a kwance , d'aya mace akan gado biyu kuma a kafet , zama yayi a kujerar da take gefe da gadon ya bud'e Alqu'ani yafara karanta suratul bak'ara , daga dady har Bash babu wanda ya motsa sai macen da tafara motsi da jikinta cikin tuhuma malam yace ”koma waye ya fito yanzu dan zan k'onashi , shiru babu mai magana , malam ne yaciga ba da karatun yana yarfa wani ruwa na adu'ar , Beauty ce ta mik'e da bak'ar riga tana dariya , tana cewa bazamu barsu ba bazamu barsu ba." Malamin ne ya tsaya da karatun ya dubi Beauty yace ”ke wacece? cikin dariyarta da batada dad'in sauraro tace ”nima kamarku nake , ta tuntsire da dariya , malm dayake yasan ba mutum bace "ya cigaba da adu'arsa ,hak'uri tafara bashi akan yayi hak'uri , malm ko saurararta beyi ba yacigaba , zaki fad'amin gaskiya ko bazaki fad'a ba ?" Beauty ce tace ” kabarni zan yima bayani , malm bai gamsu zata fad'a ba ya watsa mata wani ruwa ,ihu tafara tana ya k'yaleta , tambayarta ya kumayi a karo na biyu ,me bayin Allahn nan sukayi miki kike cutar dasu ?". Yau ta kama daurin auran Sumaiya , manyan mutane da dama sun halarci bikin , kowa kagani fuskarsa cike take da farinciki , Abbi ma farincinne shimfid'e a fuskar sa , haka Ammi sai albarka suke sanya mata ,gidan ango duk da dai tuwona miyata ne ,sunyi rawar gani sosai akwatuna set goma sha biyu , kuma shak'e da kaya , masha Allah amarya tayi goshi, hango Sumaiya nayi tasha bak'in lalle fuskar nan tasha make-up ga wani tsararen kitso da aka yimata , gaskiya ta had'u abinka da farare abin ba'a cewa komai , wayarta ce tafara ring ,sunan my sweetheart ne ke yawo a screen d'in wayar ,cikin sassanyar murya ta d'aga , kunsan marubuciyar taku da son jin k'wa k'waf hhh , ango ne yace ”my honey dafatan dai baki wahalar min da kanki ba , kukan shagwa6a tayi kamar yana ganinta tace ” sweetheart , bana jin cin komai yanzu ,oh my honey kinason wahalar min da kanki , wata irin dariya tayi da nima na dara hhh my fans dariyar fa ta masoya ce." Ki fito please muje kici abinci , uhm uhm nikam bazan iya ciba ,okay to bari in aiko Shamsu ya kawo miki ,cewar Khalid salama sukayi kowa ya ajiye waya, k'awayen ta ne keta yimata tsiya wai tafiya shagwa6a Khalid zaiyi , fama ,lol niko nace ai mace babu shagwa6a to ai babu kanta 🙈 kuka tasa tana shure shure , tin tsirewa da dariya suka tafa."...✍️. 👏👏👏👏👏👏👏👏 *GASKIYA MASOYANA* ina alfahari daku da kuma soyayyar da kuke nunamin wlh ina gani kuyi hakuri yanzu aiyuka ne sukayimin yawa , ina neman Adu'arku please kuyimin adu'a Allah ya rabani da abinda nake tare dashi lpy , kuna rai na, nagode da nuna soyayyar. Please share👏 Vote me on wattpad ♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 39 & 40 ____ Mama da Anty na hango a hospital , suna fitowa daga d'akin da aka kwantar da Bahija , kuka Anty takeyi sosai , juya kai mama tayi tana adu'a a hankali doctors ne suka shigo cikin rashin walwala suka rufe gawar Bahija , kulli nafsin za'ikatul maut Allah ka kar6i tubanmu , Allah yayiwa Bahija rasuwa , da dawowarta daga India , ba k'aramin aikin alkhairi tadinga yiba , itace sadaka dakuma ibada , Allah kaji k'an musulmai Allah ka gafartawa wanda suka rigamu gidan gaskiya ." Babbar k'awarta ce wacce sukayi primary tare , idanunta a bud'e suke dan haka kowa ke tsoron ta ra6i yaronsa, Umma tayi iya yinta amma abin ya fi k'arfinta , kasancewar yanzu Asma'u tanason fin k'arfin Umma , kusan kullum Umma sai tayi kuka gashi malam ya kwanta ciwo na bak'in cikin Asma'u , Umma takoma abin tausayi ." K'awar tata mai suna Zubby , duban Asma'u tayi tace ”my sis mai yasa kika bari kika d'auki ciki ,gaskiya bakida wayo sekace bakiyi karatun boko ba , shiru Asma'u tayi tace ”ke nifa ban ma san na sami ciki ba , kawai gani nayi ina amai, Asma'u ce tabawa zubby labarin , abinda ya faru tsakaninta da Bash har lamarin auransu da Harun da za'ayi nanda kwana biyar , Zubby ce ta bugi cinyar , Asma'u tace ”kee!!, kud'in banza , kud'in hofi , ke baki iya bariki bane ?"yanzu fa ragamar komai a hannunki take , dan haka ki janye maganar aure kizo mu fasa bariki , ita kuma , Basma da kikace , Harun zai aura , to inada mafita wlh ,mu watsa musu bala'i kuma mubari sai sunyi auran sanan , zaki godemin k'awata , Asma'u ce ta dubi jaririn hanunta tace ”to wanan yaron ya zanyi dashi , Zubby ce ta karkace ,d'aurin d'an kwali tace ”tambaya ma kikeyi ?"to tsaya tambaya wlh garama ki bud'e idonki , ita wanan tsohuwar aikin me rakeyi ki jefa mata shi kizo muyi tafiyarmu , Asma'u kallon Zubby takeyi , a can k'asan zuciyarta tana tunanin , inhar ta tafi to mahaifinta fa gashi babu lpy baima san waye a kanshi ba ." Maganar Zubby ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da take , maiyasa zaki tsaya watsar da damar da Allah ya baki , just ki share tausayi da wani abu , kizo mu fasa , zan baki kud'in siyan atamfofi da lass da duk wani kaya na yayi , kingafa harkar nan , wlh bazaki dingayi da k'ananan mutane ba , zaki waye kiyi fresh hmm ,sai kin shigo zaki gane manufata beb , hud'ubar Zubby tasami gurin zama a zuciyar Asma'u , sun shirya nanda kwana biyu zata bar gida , Zubby ko tanata k'ara jaddada mata abubuwa na more rayuwa dakuma wanda zata k'ara fasowa gari. " Sallama sukayi , Zubby tazo fita sukayi kaci6us da Umma , Allah yasa yanzu ta dawo daga anguwa , har k'asa Zubby ta durk'usa ta gaida Umma , cikin sakin fuska Umma ta amsa ,ta fice , Umma ce ta shige d'akin Asma'u , tafara zuba mata masifa , tace ”wlh Allah ki kiyayeni ke bakida hankali ne , wanan shed'aniyar yarinyar kika k'ulla k'awance da ita , to kifita harkar ta kokuwa ranki ya 6aci dan wlh zakisha mamaki tunda bakida hankali , kukan k'arya da munafurci Asma'u tafara , tace ”umma ba k'awata bace fad'a ma mukayi da ita yanzu , Umma ki yarda dani insha Allah nakoma Asma'un da kika sani a da wlh na tuba Umma." . Allah sarki rayuwa , Umma ta rungume Asma'u tana kuka , tace ”nayi farincikin shiryuwarki , Allah yakuma shirya mana ku , amen Asma'u tace tare da nufar d'akin Umma tafara gyra gado ta gyara ko ina ta share ,ta koma kitchen ta share ta dawo tsakar gidan shima ta share tazo kan bayangida shima ta wanke ta share , Umma zuciyarta fal farinciki sosai takejin son y'ar tata ." Ruwan sanwar abinci Asma'u ta d'ora ta kar6i kayan cefanen hanun Umma ta fara gyarawa tuwon shinkafa za'ayi miyar taushe , cewa Umma tayi ta juye ruwa tayi wanka ita zatayi sauran , cikin farinciki Umma ta juye ruwan wanka ita kuma Asma'u na wanke tumatur zata kai markad'e ." Yau Alhaji ya dawo daga saudiya murna gurinsu Mom da Hajiya ba'a magana , bayan an d'aukoshi daga airport , yaci abinci yayi wanka yake gaya musu cewar , ya siyawa , Harun gida a rijiyar zaki , mom da Hajiya babu zama suka d'unguma zuwa tsararen gidan , tunda suka hango get d'in gidan sukasan ba k'aramin kud'i ,Alhaji ya kashe ba , bud'e gidan sukayi da key ,suka shige cikin gidan , mom da Hajiya da driver kowa sai santin yanayin tsarin gidan yakeyi , da shigarsu , sukaci karo da shuke shuke na flawoyi masu kyau , daga 6angaren dama kuma bishiyoyi ne na kayan itatuwa , irin na turawa , shigewa cikin gidan sukayi , komai akwai a ciki , kama daga kafet na parlor , dakuma labule , da labulen window ga abin kama labule mai flawoyi , hango kujerun da suke zagaye a k'aton parlorn nayi , gaskiya fad'ar kyawunsu bazai fad'uba , ga kafet mai kwaliya daya malale tsakiyar parlorn , daga yamma kuma , TV ne plasma k'ato a manne jikin bango k'asanshi resrver ce da CD ga remote a kansu , mai karatu ,in natsaya lisafo kayan parlor zamu cinye lokacin anan , daga tsakiyar parlorn bene ne shimafa ya tsaru , gida ya tsaru ,mom seda tayi kukan farinciki." Hajiya ma tayi farinciki sosai , shiga kowane part sukayi na parlorn , k'asa d'akuna hud'u ne ,da bedroom biyu da kitchen da store dakuma d'akin bak'i , hakama sama shima hud'unne , gida ya birge sosai ,an kashe nera ." Gidansu Basma shiri sukeyi babu kama hanun yaro , mutane cike a gidan kamar ,ranar ne d'aurin aure , daga masuyin cin cin sai masu suyar nama da masuyi donut da sauransu kuma kowanne ba kad'an akeyi ba , amarya tabar gidansu takoma gidan yayar mahaifiyarta da zama , yau kwananta hud'u a can ." Harun ne zaune shida abokanan sa kowa sai tsokanarsa yakeyi , da kamar ba shine y'ammata suke rubibi ba, yanzu gashi , Basma ta cafke gasar dariya yasa yace ”nifa banida ra'ayi a soyayya , hasali ma bansan abinda masoya suke jiba ,wlh sai yanzu dana had'u da sarauniyar mata uwar y'a y'a na , abokinshi dake gefenshi a zaune yace ”eyee kace ka waye sosai , wanan small mouth d'inne ke furta wanan kalmomi nice , na jinjina maka shugaban masoya , sukasa dariya , hirarsu sukeyi ,mai cike da barkwanci dakuma nishad'i." Gidansu Bahija yau akayi sadakar uku , dole dadynsu ya dawo gida dan mutuwar ta girgiza mutane da dama haka shima , saida ya zubar da k'wallah yaji rasuwar Bahija , sauran k'annenta da yayunta da basuyi aure ba ,jikinsu yayi zanyi musaman da sukaga anzo tafiya da Bahija makwancinta , Allah sarki rayuwa mudinga kwatanta aikin alkairi 👏...✍️. Masu sharhi ina ganinku karku gaji da sambad'omin sharhi nikuma bazan gaji da nishad'antar daku ba I love you my fans ana tare 🤙. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 41 & 42 _____Washe gari Asma'u ta tashi da asbha , bayan tayi sallah taje d'akin Umma ta gaisheta , sanya mata albarka Umma tayi tare da yimata fatan gamawa da duniya lafiya , mik'ewa Asma'u tayi taje d'akin mahaifinta ta gaishe shi , Alhmdulilh jikin nashi da sauk'i , dan yanzu ma yana magana ." Washe gari , wayar Asma'u ce take ring misalin sha biyu na rana , Zuby ce , ke wai ya akayi ne najiki shiru ,ko kin canja shawara ne ?"cikin k'asa da murya Asma'u tace ”no yanzu dai mubar maganar zuwa , gobe , ta ajiye wayar , tunani tafara iri iri amma babu wacce ta gamsu da shawararta irin Zuby." Bayan su mom da Hajiya sun dawo gida ,ta zauna a parlor , tana santin gidan Harun amma taji dad'i sosai , shigowar Alhaji ne yasata tsugunawa ta gaishe shi , zama yayi a kujera two sitter kana ya dubi mom yace ”ya kukaga gidan ?"fad'ad'a fara'arta mom tayi tace ”wlh Alhaji gidan kamar a turai , dariya Alhaji yasa yace ”masha Allah komai dai yayi ko?"eh yayi Allah ya k'ara bud'i , amen y Allah Alhaji yace ”kinga bikin yau saura 2 days ,mom ce ta sunkuyar da kai tace ” Allah yasa munada rai da lafiya ." Misalin k'arfe biyar na yamma angon Sumaiya ya rangad'o mata kira , d'agawa tayi cikin sanyin murya tace ”barka da yamma , ywwa yace ”kungama shiryawa ne ?"eh Sumaiya tace ”ku suke jira , waro ido yayi yace ”suwa kenan ?"k'awaye na man , to kekuma fa ?"Sumaiya ce tace ”ni bazan zo ba , a zabure yace ”bar maganar wasa ,Sumaiya ce tace ”da gaske , juyawa tayi taga kowa na shiri , itako kwanciya tayi tare da jan mayafi ." Sunyi tashin harsun gaji bacci mai nauyi ne yayi awon gaba da ita , k'awayen suka shige mota suka barta , ana cikin gabatar da mutane , kowa yaga gurin zaman amarya da ango wayam babu kowa , mc ne ya tsaya da magana yafara tambayar abokanan sa ko menene dalilin rashin zuwansu ?"suma basu sani ba dan lokacin da zasu taho angon yace ”musu zashi d'auko amaryarsa , mc ne ya d'aga abin magana yace ”to kowa yayi hak'uri iyayen gayya basu iso ba kuyimana afuwa mu jirasu ." A gidan su , Sumaiya ango Imran ne ya shigo a sukwane dan bayason kowa ya ganshi ,direct d'akin Sumaiyan ya nufa da babu kowa a cikinsa , samunta yayi tana bacci , hankalin ta kwance ,rasa inda zai ya tasheta yayi , gashi yanayi yana duba lokaci , zama yayi gefen gadon yafara hura mata iskar bakinsa a fuskarta , wani juyi tayi ,da alamu baccin ma yanzu yafara dad'i , Imran ne , ya d'agata tare da ruk'o mata hannu , kaya yagani a kan gadon da alamu natane, kunyace ta kama sumaiya tak'i had'a ido dashi sai shigewa toilet tayi , a gurguje ta watsa ruwa ta sanya kayan a toilet , duk yana zaune yana jiran fitowarta , shagwa6e fuska tayi tace ”to ina sukayi , suntafi man , cewar Imran , rau rau tayi da idanu kamar zatayi kuka ,tunaninta shine yaya zatayi kwaliya banda mai da powder da man baki babu abinda ta iya sawa , gani tayi Imran ya rik'o mata hannu ya zaunar da ita a stool d'in dake gaban dressing mirror ." Itadai batace komai ba kallonsa kawai takeyi , mai ya shafa mata , a k'afa da hannnu dakuma fuska , kasancewar sauri yakeyi , powder ,ya shafa mata tare da yimata jagira da janya mata purple d'in janbaki ya zagaye gefen bakin da kalar maroon , wow nimafa naga wankan kyau hatta d'ankwalin shiya d'aura mata ya d'auketa suka fita ta k'ofar baya hand bag d'inta da gylenta da d'ankune da sark'a dakuma warwaro da sauransu duk a mota aka saka , ango dai ya iya kwaliya lol amafa an 6atawa y'an taro lokaci ." Ba' a d'auki lokaci mai tsayi ba suka iso katafaren hall d'in da yacika da masoya , da shigowar su aka fara tafi masu video nayi masu camera nayi masu wayoyi nayi , samun guri sukayi hanunsu sak'ale a na juna, adu'oi akayi tare da sake zazzafan kid'a mai gigita masoya , kowafa ya tashi ya taka ango da amarya ma ansha rawa , umartar su akayi da yanka cake , hanunta tafara sawa shima ya d'ora nashi suka yanka jikakeyi raf raf anata tafi , suna gamawa aka sanya musu wak'ar bikinsu , an zubar da nera kurin manni kuma kowa yayi farinciki , sai misalin k'arfe bakwai aka tashi, kutt. sai anje gida ayita ramakon sallah ,nidai ina gefe yasin ." Kai tsaye gidanta aka wuce da ita , wani katafaren gidane mai cike da kayan more rayuwa , tsayawa misata kyawunsa ma babban aiki ne , saboda gidan ya tsaru iya tsaruwa , amma ba gidan sama bane , bedroom d'inta aka wuce da ita , color d'in sa kuwa wait and purple ne , komai ya tsaru , angawaye kam tuna suka kawo amarya suka fice , bayan iyaye da k'awaye da amarya sunyi saloli ne aka fara yiwa , Sumaiya nasiha tare da koyar da ita laduban zaman aure , kuka tafara , kowa na gurin yana kallonta k'awaye na shirin dariya iyaye na tausaya mata , wata k'anwar mahaifiyarta ce ta rik'o mata hannu suka fice., d'akin dake jikin na amaryar suka shiga , shimadai kala d'aya ne komai akwai a cikinsa , zaunar da Sumaiya tayi ,tace ”daughter , yakama kisani nasanma an fad'a miki amma zan kuma jaddada miki, aure ya wuce tunaninki kuma ya wuce zatonki , aure ba abin wasa bane ,shi miji da kika ganshi to yanzu karatunki zai d'auka haka kema karatunshi zaki d'auka." Kizamo mai yiwa mijinki biyayya, karkice zaki diga yimasa rowar hak'k'insa , saboda Allah yace kibi mijinki ,karkiso 6acin ransa kiyi masa biyayya banda yimasa gardama , kiso abinda yakeso , kuma babban abinda yake , taka muhimiyar rawa shine k'amshi , ki kasance mai son k'mshi mai sanyi , ki guji k'azanta , 6angaren gyran jiki shima nazo miki da kayan gyaran jiki ba kizauna bakya gyara jikinki ba kuma yana k'arewa kiyimin magana , inaso kisani maganin wayo kunyar fad'e nakeyi riders kun bazo ido da kunne to yasin ku gane nikam inada kunya wayo 🤏😎... Karkiyi wasa da cin aya da dabino da rake da kankana da gwanda da cucumber da karas , da farfesu musaman ma na kifi ko farfesun kaza wlh babu ruwanki da cacar kud'i gurin siyan kayan k'arin ni'ima ,lol nimafa nad'au darasi yasin 💃 , jikin Asma'u ne yayi sanyi , kuma karki dinga bari kayanki suna datti yakamata , ki kula da ado da kwaliya saboda namiji d'an ado ne, batun shagwa6a kuma karkizamo kina yimasa murya kamar ta maza ,kidinga tausasa kalamanki kafin ki fad'esu , janyo hanunta anty tayi suka koma bedroom d'inta, anty ce ta shiga toilet ta had'a mata ruwan wanka wanda yaji turaruka masu k'amshi kuma masu zama a jiki , cire kaya Asma'u tayi tashige toilet tafara wanka , ga wani ruwan shima mai k'amshi an tarashi a bahon wanka , tana gama wankan tashige tayi luf a ciki , kamar mai shirin yin bacci ..✍️. Please share👏 Vote me on wattpad ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 43 & 44 ____ Malm yasha artabu da beauty ,tun asbha ake abu d'aya har azhar , beauty tace ”zata fasa k'wai , anyi nasarar samun dady da Bash sun dawo normal , saidai beauty tace kota tafi bazata k'yale Bash da dady ba , sundai yi farinciki , da haka ta fice daga gidan ,domin ayar Allah bata fad'i k'asa banza , ammafa hankalin dady a tashe yake ,da magan ganun da beauty take cewa ,Bash ya rame sosai kamar wanda yayi sati yana ciwo." Su Anty ne suka mik'e dan lokacin k'arfe tara ne na dare , bayan sun gama yiwa asma'u kwaliya da wata nasihar , suka yimata fatan zaman lafiya , haka tadinga kuka kamar wace za'a zare ranta." Ana gobe biki , da misalin k'arfe hud'u na asbha , asma'u na hango da akwati a hannu tasa dogon hijab , ficewa tayi cikin hikima da dabara , da fitarta ta shige wata mota da tatsaya a k'ofar gidansu , tana shiga motar tayi gaba ,Zuby ce a cikin motar ,tasha bak'in glass ,wanda ya rufe har saman kumatunta , duban Asma'u tayi cikin farinciki tace ”barka da fara shigowa sabuwar rayuwa , hak'ik'a na tayaki murna yanzu kinzamo mai y'ancin kanki bakida matsala please ki saki jikinki man , Asma'u batace komai ba sai tunanin da ya addabi zuciyarta , shin tayi adlci kuwa ?"tayiwa mahaifiyarta da mahaifinta adlci ?"ga jinjirin yaro data bari yana bacci , to inya taso wace irin rayuwa zaiyi , can kuma wata zuciyar tace ”ke ga daula zaki shiga ,yanzu kinzamo free babu mai takura miki karki bari tausayinki ya rinjayi dukiyar da zaki samu so ki manta da iyayenki... Murmishi tayi cikin samun k'warin guwaiwa ,ta goge guntun hawayenta , sunyi tafiya mai nisa , nisa sosai dan harsun fita a garin kano sun nufi Kaduna , suna tafiya suna hira , abinci mai rai da lafiya Zuby ta mik'o mata tare da abin sha ." Wayar Zuby ce ta fara ruri , d'agawa tayi tare da cewa my man ya akayi ne nakusa zuwa fa ,kasan a kano na kwana ,ta kashe wayar , Asma'u dai na gefe bata magana ." *GIDAN SU AMARYA BASMA* Yau akeyin walima y'an uwa da abokan arzik'i sun taru anata fad'akarwa , an raraba kyautu tuka sosai , kuma anyi taro lafiya , daganan aka kowa ya watse , washe gari ,aka saka amarya a lalle , kowa sai sambarka , washe gari Assabar d'aurin aure ,gidan su mom da Hajiya da Alhaji wanan rana suna cikin farinciki , Alhaji da dady da abokan Alhaji suka cika gurin masha Allah , an d'aura auran Basma da Harun akan sadaki mafi albarka , dubu d'ari , d'aurin auran yasami halartar manyan bak'i ta 6angarori da dama ,anci kuma ansha an godewa Allah ,ango na hango yana sanye cikin wata shadda gezna mai azabar kyau ga gashinan yasha gyara bakinan kamar ansa masa janbaki , ni a ganina ma sai naga kamar yayi haske , zaune yake a gidansu Mom d'inshi sunata yimasa nasiha dakuma sanin hakkin aure a musulunci , Alhaji ne ya kirashi lokacin yana shirin tafiya gidansu Asma'u , kasancewar ya kira ance masa an fasa suzo su kar6i kud'in su , Harun ne yashiga da sallama , samun Alhaji yayi a zaune yana waya, yana gamawa yace ”Harun ya fito da mota zasuje wani guri , cikin bin umarni ya fito da mota suka shige shida Alhaji sukabar gidan , wani katafaren company na Alhaji suka nufa , wanda ake sauke kayan sa na saudiya , turaruka da jallabiya da sauransu , katafaren shago ne mai girma ga tsari ,da shigarsu kowa yahau durk'usawa yana gaida Alhaji da Harun , Alhaji ne ya amsa tare da cewa ga sabon shugaba na kawo shine zai dinga kula da komai na shigar kud'i , kai kuma Bala kazo muje sabon company na zaka koma can da aiki." Cikin zumud'i da godiya , Bala yabi su Harun ,shimadai sabon company d'in ya tsaru sosai , bayan sun koma gida ne Alhaji ya cewa Harun yanzu kabar aiki a waccan ma'ikatar zaka dawo tawa , kuma maganar auranka da ,wanan yarinyar iyayenta sunce basusan inda ta nufa ba , shikuma yaro nanda wata biyu inya kuma wayau Allah zai baiyana kamanninsa da ubansa , cikin farinciki Harun ya kalli Alhaji yana godiya , lokacin k'arfe biyar na yamma dayake ranar Asabar akayi d'aurin auran , Wayarshi ce tafara ruri , ganin number abokinsa yasashi fitowa , jinayi yace ”ganinan zuwa yanzu , ya kashe wayar , parking spice ya d'auki motarshi ya fice daga gidan , gurin abokan nashi ya nufa , hak'ik'a ,sunyi rawar gani kud'ad'e masu yawa suka had'awa Harun , shima yayi farinciki kuma yak'ara sonsu a zuciyarshi." Kukan jariri ne ya karad'e gidan , Umma na idar da sallah ta nufo d'akin Asma'u , ganin babu kowa sai yaro da wata k'atuwar takarda yasata dogon tunani , kodai Asma'u ta shiga band'aki ne ?"to ina ma zataje da sanyin safiyar nnan?" tunani iri iri Umma tafara , goya yaron tayi ta lek'a bayi babu Asma'u ko ina ta lek'e batanan , d'aukar takardar mai cike da rubutu tayi , bata iya karatun boko ba ko hausa yasata nannad'e takardar ta kaita d'akinta ta 6oye , tunaninta shine ina Asma'u tayi ?"batada mai bata amsa yasa ta fito ta koma d'akin Asma'u , ganin kud'i turus a zube yasa Umma tsorata tafara ja baya cikin tsoro." Cikin sanyin jiki ta nufi d'akin malm da yake karatun Alqu'ani , ta durk'usa ta gaishe shi , gyaran murya yayi mata , hakan yasata ficewa da tunani iri iri a zuciyarta , misalin k'arfe bakwai na safe gari yayi haske , Umma ta lek'o waje ko zata sami yaro mai d'an wayo , cikin sa'a ta hango yaron ,mak'otansu ta kirashi , yana zuwa tace ”yazo dan Allah , shiga gidan sukayi , Umma tace ”ya shigo , yana shigowa ta mik'o masa takadda , tace ”dan Allah ka temaka ka karantamin , wanan , kar6a yayi yafara karantawa .... _Aslamu Alaikum Umma nasan baza kiji dad'in tafiya ta ba gaskiya bazan iya zama da yaro a gabana ba da k'uruciyata , naza6i nabi k'awar arzik'i ki kwantar da hankalinki insha Allah munkusa fita daga talauci ga Muhammad nan ki kula dashi kuma nabar kud'i zasukai dubu d'ari, maganar aure kuma dama ba sonakeyi ba ,narasa mai bani shawar ne yanzukam nasamu fatan alkairi_ Zufa ce ke karyowa Umma duk sanyin da akeyi bai hana ta sharce gumi ba innalilahi wa inailaihirraji'un Allah gani gareka , Umma tasa kuka , shima yaron sai da yashare hawaye ya mik'e ya fice , bak'in ciki tashin hankali duk sun dira a zuciyar Umma kuka umma takeyi tana rok'on Allah sassauci , sako yaron tayi daga bayansa ta fashe da kuka , tana kallonsa ." Misalin k'arfe takwas na dare ankai Amarya gidanta kowa sai yaba kyan gidan yakeyi , basu wani jima ba suka mik'e suka fice bayan iyaye sunk'ara yimata nasiha akan ladabi dakuma biyayya da hak'uri da soyayya , kuka Basma takeyi tana ruk'o mayafin k'awarta ,da haka suka watse suka barta ....✍️. Ina kuma baku hakuri masu sharhi ko awane group akayi inhar ina ciki ina gani kuyi hakuri na rashin maida muku da martani kuyi hakuri 👏aiyuka ne sukayimin ywa amma ina ganin sharhinku nagode 🤙. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 45 & 46 ____ horn Zuby tayi a wani makeken gida kuma tsararre , tsayawa misalta tsarinsa ma 6ata lokaci ne dan zumu dad'e , mai gadi ne ya wangale get d'in tare da d'agawa Zuby hannu , rik'o hanun Asma'u tayi yayinda suka sauka , drivern gidanne ya d'auke motar a gurin ya maidata gurin ajiyar motoci , k'arasawa cikin gidan sukayi , babu kowa a gidan , hakan yasa ,Asma'u cire hijab d'inta ta lalubo wayarta data kashe ta duba lokaci , sbda bata lura da agogon parlorn ba , Zuby ce ta kalli Asma'u tace ”kifa saki jikinki wanan gidana ne kuma mallaki na , kinada right d'in yin komai a cikinsa , yanzudai kitashi ki shiga wanka ki wanke kan ki da sabulun wanke kai , akwai new brush kiyi using dashi , zan fido miki sabon kaya kisa kiyi sauri zanyi bak'i ne , lol tom Asma'u ta amsa ta shige toilet , tsaruwar toilet d'in ma abin kallo ne bare kuma gidan mai gaba d'aya , wata y'ar aiki ce mai suna Happiness ta kawo musu kayan abinci mai rai da lafiya ta jere a dining." Zuby na waya jinayi tace ”yaufa ansami kaya kuma walh kud'inta daban ne , ni zaka dingaba kud'in ina bata , mutumin dake zaune a kujera a office ya juya yace ”bakida dama angama , ki kilace min ita zuwa yamma zan zo , okay Zuby tace ”tare da yin dariyarsu ta y'an duniya , ta kashe wayar , Asma'u na fitowa Zuby ta nuna mata wani had'ad'en bedroom ,acan tayi kwaliyarta , kaya tagani akan gado da alama shine wanda zata sa zaro ido tayi ,ta d'aga kayan , riga ce mai k'aramin hannu iya cibiya ,sai wando 3 quarter ma tsatse sai hula fara mai adon stone a jiki , sa kayan Asma'u tayi takasa fitowa , ta zauna tana tunanin yazatayi tayi rayuwa da wanan kayan cab , Zuby ce taji Asma'u shiru bata fito ba , hakan yasata mik'ewa ta nuf'i d'akin , murmishi tayi tace ”zomuje karki damu babu kowafa a gidan , kifito muci abinci gashi can a dining , mik'ewa Asma'u tayi jiki a sanyaye ta rufawa Zuby baya ." Farfesu ne wanda yaji kayan k'amshi ,abin nema ya samu Asma'u zai tsotsar k'ashi takeyi tana k'arawa , Zuby duk ta karanci halayen Asma'u hakan yasa tak'ara samun k'warin guwaiwar kasuwanci da ita ." Suna gamawa , Zuby ta ciro wata k'waya a aljihun wandonta ,mik'awa Asma'u tayi tace ”kinga wanan tana maganin gajiya , kuma kince jiya bakiyi bacci ba to yau zakiyi sosai , kar6a Asma'u tayi cike da gamsuwa ta d'auki ruwa tasha d'aya , ta mik'awa Zuby sauran , dariyar gefen baki Zuby tayi tace ”kozaki kwanta ne ?"a 'a Asma'u tace ”tana juya kanta da tafarajin mood d'inta yafara sauyawa , sai da Zuby taga magani yafara aiki ta rik'ewa Asma'u hannu ta kaita bedroom d'inta ta kwantar da ita , jiyo k'arar wayarta tayi tana ring a parlor , da sauri ta tafi gurin wayar , lokacin k'arfe shida na yamma , mutumin ne wanda sukayi waya d'azu , ganinan fa nashigo , okay Zuby tace ”tare da komawa d'akin Asma'u ,ta kuma shafeta da humra mai k'amshi ta bata wani magani na gari a cup ." Fita tayi ta shigo dashi suna dariya , d'auko masa tiren abinci tayi da kanta ta mik'a masa , bayan yaci dankalin turawa soyayye yace ”hajiya ina ajiyata kinsan fa dan ita nazo tinda kika turamin pics d'inta wlh namatsu in ganta ." Dariya , Zuby tayi tace ”tana cikin d'akina ta kwanta itama labarinka takeyi , zaro bandir d'in kud'i yayi yace ”nan dubu d'ari uku ne , amma somin ta6i ne ,inhar ta sanyani farinciki to fiye da hakama zan bata , wata munafukar dariya Zuby tasa tare da fifita da kud'in ,tace ”to kashiga ,ai kagane d'akin ko ?"eh yace ”tare da washe hak'ora , da shigarshi ya hango Asma'u kwance idanunta a bud'e sunyi jawur , yana matsowa kusa da ita ta cakumoshi , tana shirin mik'ewa , daganan nace barin lek'a gidan amarya Basma ." Wasu dank'wala dank'awalan kaji na hango a plet , da Asma'u da Harun ne zaune ,fuskarsu cike da farinciki , fara bata yayi a baki itama ta bashi da haka suka ciyar da junansu , lemu ya tsiyayo musu a cup sukasha ya sunkuci , Basma yace ”tayi alwala , batayi musu ba , kasancewar tasha wa'azi kuma ta karanta ta gani , bayan tayi alwalar ne ta dawo bedroom ta zauna , shima alwalar yayi ya ciro mata hijab a drowa , ya sanya mata , raka'a biyu sukayi , suka zauna adu'a ,sund'au lokaci mai tsayi suna yiwa junansu adu'a suna gamawa ya mata tambayoyi akan wanka dakuma tsarki da sauransu , daganan yace ”to darefa 🙈 yayi muje mu kwanta, cikin fad'uwar gaba tabi gadon ta kwanta , Harun ne ya lulu6e su da blanket kasancewar lokacin ana sanyi , Basma ce ta juya bayanta , inalilahi ,Harun yace ”tare da juyo da ita ,kin mance zunubin da mace take kwasa inhar ta juyawa mijinta a yayinda suke tare ?" kunyace ta kama Basma ta juyo tare da mannewa a jikinsa , mik'ewa yayi ya kashe wutar d'akin yayi , tare da rungumo ta yafara kissing d'inta ta ko ina ." Ganin lamarin zai fara fin k'arfinta yasata cewa ,please bacci nakeji ,ina Harun yayi nisa ,nima Miyoshi nayi yana adu'ar da manzon Allah yace ayi .. *BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNISH _SHAI'DANA WA JANNIBISH _SHAI'DANA MA RAZAKTANA."* Wani uban salati najiyo Basma ta rafka , lokacin nikuma na koma parlor na kwanta dan nagaji da d'auko rahoto eheee su masu baza ida nuwa🤣.. Misalin k'arfe hud'u na asbha , Harun ne yafara farkawa , ya zare jikinsa a na Basma ya kunna glob haske ya baiyana , ya shige toilet yayi tsarki sanan yayi wankan tsarki tare da alwala , nafila yafara jerowa ,tare da adu'ar farinciki daya samu a gurin Basma , yasameta a matsayin budurwa , bayan ya idar da sallah ne yaje ya kwanta gefen da ta kwanta yafara kwararo mata adu'a yana tofa mata, hango fuskarta yayi da ruwan hawaye ya bushe , murmishi yayi tareda manna mata kiss a goshi, yafara yimata tafiyar tsutsa a k'afarta , bud'e ido tayi tasa dariya , rik'o mata hannu Harun yayi tare da , d'aukarta kamar baby ,ya kaita toilet ." Ruwa mai d'an zafi ya tara mata a bahon wanka kana ya zuba delot a ciki ya sanyata , k'ara tasa ta rik'o masa riga, hak'uri yadinga bata , ruwan zafin ya ratsa jikinta hakan yasata yin shiru , d'agata yayi Yauma tara wani ruwan saida ya salamce ,ya tara mata wani na wanka bayan ya bud'e wancan ya tafi ya tara sabo , wanka tayi cikin jin kunya shiko angon yana tsaye yana kallonta , da niyar wanka da tayi duk yana hankalta , tabbas yayi sa'ar mata, fitowa sukayi tana cogala k'afafu , suka nufi gado , hijab da kayan da zatasa Harun ya ciro mata , bayan tasa ne ya koma d'akinsa ya sauya kaya yatafi masallaci , ita kuma ta shafa mai da turaruka ta sa hijab tafara sallah...✍️. 😫wayo hanuna🤏. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* __wattpad ________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 47 & 48 ____Tun Asma'u na dauriya tana biyewa duk wani salo nasa , yanzu kam takasa da alamu maganin yafara sakinta , shigo mutumin ko gajiya baiyi ba Alhaji Khalifa kenan ,ze iya yin sa'an k'anin baban Asma'u amma kasancewar sa mai nera , yasashi babu inda bazai je budurwa ta kusheshi ba kowace zumud'i takeyi sbda kud'insa suke so , gashi ya iya sarafa mace kamar k'aramin yaro ,baya gajiya gurin sxx da mace , yanada manyan y'a y'a harda masu aure da maza samari hakan baisa ya dena abinda yakeyi ba, sai da jikinta yai lilis sanan ya d'agata , batasan halin da take ciki ba hakan yasata bacin da bata shirya ba , shiga toilet d'in dake gefe da d'akin yayi ya watsa ruwa ya fito ya sanya kayansa , wayoyinsa ya d'auka ya fice , samun Zuby yayi a parlor tana danna waya , mik'ewa tayi fuska cike da fara'a tace ”ya akayi washe hak'ora Alhaji Khalifa yayi yace ”gobe zan dawo fa ga 50k tasi kayan shayi , dariya tasa tana rangwad'a ta kar6e kud'in ." Ware dubu d'ari biyu tayi a gefe da nufin shi zata bawa , Asma'u mik'ewa tayi ta nufi d'akin da Asma'u take kwance , tsamunta tayi kwance tayi sharf kamar mara nunfashi , cikin sauri ta k'araso ta dafata jitayi jikinta yayi zafi , a tsorace ,ta d'aga waya ta kira likitanta , kazo please da matsala dan Allah , doctor ne yace ”oky ganinan zuwa yanzu , ba'adau wani lokaci mai tsayi ba sai ga doctor ya iso , k'arar motarsa ce yasa ,Zuby ficewa da gudu ta isa gurin da yayi parking d'in motarsa , yana fitowa tace ”dan Allah ka hanzarta da sauri suka nufi d'akin da Asma'u take kwance , jikinta ya ta6a yaji zafi y'an gwaje gwaje yai mata ,yace ”zazz6i ne amma insha Allah zataji sauk'i , magunguna ya had'a mata Zuby ta bashi kudin da ya buk'ata ya fice tare da yiwa Asma'u fatan samun sauk'i ,dawowa d'akin Zuby tayi kasancewar tun kafin doctor ya zo ta gyara mata jikinta ." Zuwa yamma Asma'u taji dad'in jikinta amma ta rame sosai , fitowa parlor tayi bayan tayi wanka ta kunna TV , Zuby ce tafito sanye da doguwar riga iya guwaiwa , ta zauna a parlor , kujerar dake kallon Asma'u ,tace ”ya jikin ?"da sauk'i Asma'u tace ”zuby ce ta mik'a mata kud'i , zaro ido Asma'u tayi tace ”wanan fa ?"karki damu dubu d'ari biyu ne karki damu yanzu kika fara kama dollars , murmishi Asma'u tayi , tace ”nagode sosai samun k'awa irinki wlh sai an tona suka tafa." To yanzu ya maganar auran da kikace saurayinki zaiyi , yaushe zamuje gurin boka , Asma'u ce ta kalli kud'in hanunta tace ”banason ta6a wanan kud'in , dariya Zuby tasa tace ”karki damu ga 50k sai muje gobe , daganan suka sauya hirar tasu ga duniyarsu ." Kwana uku kenan da bikin Bash ,soyayya kamar zasu cinye junansu , Basma tayi kyau a tsakanin kwanakin gashi tasami mazauni a zuciyar Bash , bata bari ranshi ya 6aci haka shima bayason 6acin ranta , da sallama ya shigo tanajin shigowarsa ta ruga da gudu ta rungumeshi juyi yafara yi da ita bai direta ko inaba sai tsararen gadonta , ya fara yimata wak'a tana dariya , zomuje muyi kallo , mik'ewa sukayi rik'e da hanun juna , Harun ya kunna TV ya rungume Basma 🙈lamarin n masoya ne lol , misalin k'arfe goma sha biyu , suka shiga kitchen sukayi girki , kowa ya shigo gidan su Harun baya fita bai d'auki wani darasi na soyayya ba." Washe gari suka shirya zuwa gidan su Harun , siyayya sosai suka yimusu , tafiya sukeyi cikin nishad'i Bash na tuk'i hanunsa na kan na Basma idanunsa ma na kanta , a haka suka isa gidan , yana parking d'in motarsa suka fice , sukayi cikin gidan ,da shigarsu sukaci karo da mom , cikin fara'a ta tari Basma ta rungumeta , Hajiya na fitowa ta fara rawa tana cewa "ga ango ga kishiyata yau nice da ango sukasa dariya , zama sukayi aka fara gaisawa , kowa fuskarsa cike da fara'a ." Girki na musaman aka yiwa amare ga farfesu na kifi dana kaza ga lemu da mom suka had'a itada Basma , mom taji dad'in samun suruka irin Basma batada duhun kai komai nata cikin nutsuwa takeyi , gida dai yacika da farinciki sosai ." Da dady akayi bikin Harun sai dai bai cika shiga mutane ba sbda wani gargad'i da beauty tayi musu shida Bash , rabonshi da fita gurin aiki yayi sati biyu , kuma ya hana momy zuwa gurin bikin taci kukanta har tagaji, wanan d'akin da Harun yata6a jin dady na waya harya tsorata ,acan yake kwana yanzu baya wuni a cikin gidan gashi yanzu momy tarasa gane kan dady itadai tana ganinsa yana hidimarsa batasan me yake aikatawa ba ." Malam ya tashi da amai da gudawa , tun ana k'irga ledar ruwa har Umma ta zubawa sarautar Allah ido , gashi duk kud'in da Asma'u ta bar mata sun k'are gurin jigilar magani , Umma tarasa wane guri zataje nemo kud'i , ga malam kwance ya kwanta a asibiti , sunfito babu kud'in magani ga yaron Asma'u na kashin hak'ori ,ya rame sosai damuwa ta taru tayuwa Umma yawa ,wani lokacin ta zauna a d'aki tayita kuka wani lokacin tai alwalah takai kukanta ga Allah." Yau da bikin Sumaiya sati biyu kenan tayi fari tayi k'iba sosai , Khalid ne yashigo da 3 quarter yana rawa yace ”my princess tauraruwa zomuyi rawa ,d'agata yayi yana juyi yana rawa da ita ,suka hau dariya , albishirinki, sumaiya ce tace ”goro , nabiya mana makka , a zabure Zumaiya ta mik'e tace ”dan Allah fa ,suka sake kid'a suka fara rawa , hhh kowa na nuna iyawarsa , saida suka gaji sosai sanan suka baje a kan capet suna hutawa , da gudu sumaiya ta mik'e tayi bedroom d'inta , toilet ta shige rik'e da bakinta , wani amai ne ya taho mata ,Khalid ne yabiyo bayanta da sauri ya rik'eta ,meke faruwa ne ?"a wahalce tace ” amai saida tayi aman mai yawa zata zauna a toilet d'in Khalid ya wanke mata baki ya fito da ita ya kwantar da ita a gado lulu6eta yayi da blanket , ya zauna kusa da ita ya zuba tagumi kamar ba d'azu suka gama kwasar rawa ba ." Wani jeji suka shigo mai cike da bishiyoyi iri iri bakajin k'arar komai sai na tsuntsaye , Zuby da Asma'u ne tafe sai nunfar fashi zukeyi , Asma'u da tagaji tace ”zuby nagaji mukoma zare ido Zuby tayi tace ”wlh babu inda zamu koma muzo har nan d'in kice mukoma tabb , wata tafiyar mai nisa suka kumayi ,jiyo wani irin gurnani ne zai tabbatar maka da anzo gurin hatsabibi , ya Allah ka tsare mana zuciyoyinmu, wata mahaukaciyar dariya Asma'u ta jiyo dan Zuby komai na gurin ba bak'onta bane tasaba , Asma'u ce ta k'ank'ame Zuby a haka suka k'arasa gurin , da zuwansu boka yafara yare ,Asma'u ko tana ganin kamaninsa sai da ta tsorata , kanshi gashi ne a murd'e ga wasu uban wuri daya rataya a wuyansa k'afarshi kuwa ganyene a d'aure ga layoyi , zama sukayi a gabansa Zuby tafara yimasa kirari ,washe bak'ak'en hak'waransa yayi yace ”inajinku meke tafe daku ?"dukda aljani firsus ya bani labari zanso ji daga gareku ...✍️. Please share👏 Vote me on wattpad ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 49 & 50 ___ Asma'u ce tace ”so nakeyi a hanasu zaman lafiya kuma , matarshi ta zamo kamar dodo inya kalleta , wata shu'umar dariya boka yayi yace ”karki damu komai zaiyi dai dai , kud'i Zuby ta mik'a masa ya mik'o mata wata laya bak'a , yace ”wanan ki hak'a rami ki sata a ciki , ki d'ibi tafasashen ruwa ki kwara a gurin , ya shek'e da dariya ,kana yace ”kowa bazaiga kamaninta ba sai mijinta , kutashi ku ficemin ." Da baya suka fita har suka wuce gurin bokan suka kuma tafiya mai nisa ,sanan sukazo gurin motarsu , farinciki fal zuciyar Asma'u ,amma a k'asan zuciyarta tana tunanin , shirinta na gaba akan Bash ne , suna tafiya cike da nishad'i , suka tsaya a wani katafaren gurin abinci , I scream suka buk'ata tare da sauya salon yangarsu , wasu mazane suka taho da alama suma y'an yine , zama sukayi a nesa ta kujerunsu , suna aika musu da murmishi , Zuby ce ta kashe musu ido d'aya tare da cewa hi d'ayanne ya taso yana washe hak'ora ya kamo hanun Zuby ,shikuma d'ayan ya rungumo Asma'u , wata galleliyar mota ce tai parking a gefen titi ." Wasu mata na hango guda biyu , sun fito daga motar ko wace da glass no respect a idanta , direct gurin su , Asma'u suka nufi gasu jibga jibga , wani wawan mari ta wankawa Zuby d'ayan ta cakume wuyan Asma'u , nanfa kokawa ta 6arke aka had'a harda mazan ana kaimusu naushi , da 'alamu dai matansu ne shiyasa sukayi muk'uss." Zuby taja hanun Asma'u suka shige mota da uban gudu sukahau titi , sunyi tafiya mai nisa suka iso gidan , mai gadi najin k'arar motar ya mik'e da gudu ya bud'e get , a guje ta shige ciki , goshin Asma'u na tsiyayar jini , cikin tashin hankali Zuby ta kama hanunta suka shige ciki , doctor ta kirawo yace ”gashinan zuwa , bai jimaba ya iso kasancewar baya 6atawa Zuby lokaci a gunta yana samun kud'i sosai dan ha r ciki yana zubarwa hakan yasa Zuby batada wani doctor sai shi doctor Sameer kenan babanshi babban likita ne Allah ya yimusu arziki sai dai yanada auri saki , kuma duk matar da ya aura bata aihuwa , haryanxu Allah bai bashi ba , shiyasa ya d'au alwashin zubarwa da mata ciki subhanallh 😥." Yana zuwa ya wankewa Asma'u ciwon yabata magani ,Zuby ta biyashi yai gaba , gani nayi Zuby ta mik'e a razane tana duduba jakarta , zuge zip d'in tayi naga tana zaro ido cikin firgici , kardai na yarda layar nan a gurin fad'a , nashiga uku , in Asma'u ta sani nasan bazata koma ba , tayi dube duben harta gaji bataga laya ba , hankalinta ya matuk'ar tashi ." Malam ne ya shigo da tabarma a hanunshi Alhmdulilh yaji sauk'i sosai , yaron ma ya warware , Allah cikin ikonsa ya yalwata masa acikin almajiran da yake koyarwa wani ya bud'e masa shago a k'ofar gidansa , yana saida su shinkafa wake madara sugar da sauransu , cikin sati biyu Allah yakuma buk'asa shagon yanzu kam Umma hankalinta yafara kwanciya ba kamar da ba tayi k'iba sosai ta murmure , shima jaririn yana samun madara akan kari." Tunda Emanuel yakai report , gurin jami'an tsaro suka kamashi suke gana masa azaba , sunyi neman abokan harkar tasu sun rasa , kasancewar suna had'awa da tsafi , shiko gashi a hanunsu bashida sukuni har sai ya fad'o musu gaskiyar inda abokansa suke , yayi kukan yayi rok'on ya rantse amma duk a banza ." Zaune dady yake a d'akinsa na sirri ,ya rufe ko ina babu haske wani jan abu nake hangowa dishi dishi ko meye oho ... Sumaiya da Khalid ne suka nufi hospital , test akayi mata da saurnsu , likita ne ya mik'awa , Khalid hannu yace ” kyakyawan albishir kakusa zama baba , matarka na d'auke da cikin 2 weeks , tsalle Khae ya doka dama shida matar tashi ba baya ba gurin rawa yana yiwa doctor godiya , d'akin da ake k'ara mata ruwa ya nufa , saura kad'an ya k'are , bud'e idanta tayi tace ” Prince K nagaji da kwanciya ,ta kashe masa ido , oh pans kuzo mud'au darasi kullum canzawa kansu suna sukeyi 🤔shafo cikinta yayi yace ”baby ka huta sosai karka wahalar da momy , Sumaiya bata gane me yake nufi ba tace ”baby kuma ¿"eh a cikinki ba ,dariya tasa ta 6oye fuskarta cikin tafin hanunta , Khalid ne ya dubeta yace ”kunya ko , zaki sani ,yanzu mekikeso kici ?" cikin shagwa6a tace ”wainar fulawa ,tuntsirewa da dariya yayi yace ”to menene hakan ?". Misalin k'arfe biyar na yamma suka bar hospital , aka dawo gida ,abu kad'an Khalid yayi Sumaiya zata shagwa6e fuska , yanzu dai tunda Sumaiya tafara laulayi , shi kad'ai ke rawarsa tana dariya , yau befita ba kasancewar lahadi ne yana kitchen gimbiya na kan doguwar kujera tana ganin girkin , awara sukayi ko ina yayi biji biji , Khalid kuwa yakoma abin tausayi dan hanunshi zuwa fuskarsa duk k'ulin awara , gashi Asma'u tak'i sa hannu sai dai tadinga cewa haka zakayi , harda aiken mai gadi aro musu abin tata ,haka dai sukayi awarar da tsami gaye hhh , a fagen suya , Khalid ya yarfe hannu yana shirin fita ,Asma'u tasa kuka tace ”wlh inbaka soya minba zanta tsalle inta tsalle kumadai kasan doctor yace ”banda aikin wahala harsai cikin ya girma ko ?"da sauri ya k'araso ya rik'eta yana am sorry my princess zanyi jeki zauna , an sa a tirai an yayyanka , aka sa mangyad'a a wuta aka zuba ruwa a roba da gishiri da maggi , ya fara d'iba yana zubawa , wani tsalle da man yayi sai a k'afar Sumaiya da gudu ta mik'e tafara kuka tana tsalle." Hankalinshi na gurin suya yace ”dan Allah kidena tsalle kiyi hak'uri , zama tayi tana fifita k'afar ,da Khalid yazo yaga k'afar gurin ma kad'an ne babu dai halin yin dariya ne , tasa masa kuka , yana kwashe kaskon farko ta kwashe a plet , tasa yaji , Khalid ne yace ”wlh Sumaiya bakida.... bai k'arasaba Sumaiya tafara bubuga k'afa tana cewa toni ba mai ciki bace ? dole fa kadinga lalla6a ni wlh ko indinga tsalle , shidai Khalid ya gaji sosai yana kwashe kasko na biyu ya kashe gas d'in ya kwashe a plet ya fice , tana zaune , takusa cinyeta tana jiran ya kwashe yakuma zubo mata ,da sauri ta bishi ,ina harya kulle k'ofar da key , dole ta koma kitchen tacigaba da suya." Tanayi tana dangwala da yaji , shiko Khalid wanka yayi ya canza kaya , ya shafa mai ya sanya hula da turarensa mai d'aukar hankali ,ya fito kamar bashine mai aikinnan ba , kitchen ya nufa ,samun Sumaiya ta kuk'e tana suya ,k'unshe dariya yayi yace ”mom twins ya aiki tare da sunkuyawa ya shafo cikin ,lumshe ido tayi tace ”to inakuma zakaje ?"maida mata maganar yayi kamar inda tyi masa a shagwa6e , uhm zani gurin Ammi ne da Abbi ,in gaishe su....✍️. Please share 👏 Vote me and follow me on wattpad [26/02, 6:13 am] Mom Islam ce💃: ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 51 & 52 ____Yau satinsu Harun biyar , Basma tayi kyau ta k'ara haske ga kumato lol , tafe suke a mota itada Harun zasuje gidansu momy , da isarsu ,yayi horn mai gadi ya bud'e musu , washe baki idi yayi yace ”kaga angon dariya Harun yasa lokacin da ,yake fitowa a mota , Basma ma tafito , tana sanye cikin shadda maroon color da wani tsararen aiki wanda rabi shine a jikin rigar , gyalen a k'afad'a ta yafa , hakama Harun shima kalar shaddar ce a jikinshi , kai tsaye part d'in momy suka nufa , tana zaune a parlor tana kallo , ganin su yasata fad'a d'a murmishinta , tace ”amare barka da zuwa , tana mik'owa Basma hannu alamar tazo , zuwa kusa da ita tayi ta zauna ,cikin girmamawa suka gaisheta , harunne yace ”dady nanan kuwa ?"eh momy tace ”lokacin da take mik'ewa , yana part d'inshi , okay Harun yace ”barin lek'ashi , please Basma ki jirani in sanarwa dady na , hanyar sashen dady ya nufa ,da isarshi d'akin , yajiyo wata mahaukaciyar dariya had'e da maganganu wanda k'wa k'walwarshi bazata d'auka ba , cikin zafin rai Harun ya fara bugun k'ofar dady yana gurnani na 6acin rai ,k'ofa dai tak'i bud'ewa dady yana surutansa da alamu waya yakeyi." Momy ce ta fito a guje ta rik'e Harun tare da cewa meke faruwa ne my son naganka haka ,babu magana Harun ya ture momy gefe idanunsa sunyi jawur alamun 6acin rai , wani duka da yakaiwa k'ofar ne yasa bud'ewa , momy na gefe ta mik'e ta share hawayenta ,ta wuce parlor taja hanun Basma suka wuce bedroom d'inta , tinkarar cikin d'akin da baka ganin komai sai duhu , babu haske a parlor , haka yadinga shiga yana gurnani kamar zaki , d'akin da yakuma jiyo magana a karo na biyu ya tinkara , hango dady yayi da bak'in kaya a jikinshi da jan k'ok'o ga wani mutum ,k'waran gwal da alamu ba yaro bane ." Harun ne ya cakumo wuyan dady , tare da buga kansa a bago yace "wlh ko ka kasheni ko in kasheka na rantse da mahalicci na sainaga bayanka ina mahaifina yake ?" Dady ya shek'e da dariya yace ”oho kabani ajiyarsa ne ?"wanka masa mari Harun yayi tare da cewa wlh yau zan kasheka kokuma na kasara ka dan bakada amfani bkada tausayi bakada imani , meyasa zaka kashemin ubana , kabarni maraya , uwata kuma ka rabata da mijinta mezakaje ka cewa Allah, yana kuka yana jijiga dady , shiko dady tsabar ya jigata layi ya fara yana cewa tsaya zan gaya maka , yayi dai _ dai da shigowar momy d'akin idanunta sun ciko da hawaye , batace komai ba itadai tana kallonsu , Harun ne yaja dady ,yace ”kai ka turo aka kashemin mahaifina ko , wani matsanancin kuka Harun yakeyi mai cike da tausayi , dady ne yace ” YUSUF!!!!....wani mahaukacin kud'i ne ke zubowa daga bakin wanan k'waran gwal d'in , zaro ido momy da Harun sukayi tare da rufe baki da hannu ." Innalilahi wa ina ilaihirraji'un yanzu dady rashin tausayi da imaninka harya kai ka maida mahaifina dukiya , dady ko a jikinshi , kukan kura Harun yayi yafara jibgar dady yana kuka yana kalon abinda aka kira kud'i ya zubo, da sauri momy ta fito parlor ta d'auki wayarda data ajiye akan kujera tafara lalubar number mom , cikin sa'a number tashiga , as.... wani mari taji an wanketa dashi cikin kid'ima ta juya dady tagani , d'aure da hannaye ,fitowar Harun ne yasata komawa bayansa , momy ce takuma kiran wayar mom , cikin sauri tace ”wlh kuyi sauri kuzo kuga abin mamaki ,kuyi sauri ta k'arashe zancen da kuka mai cin rai , Bash ne yashigo sanye da doguwar riga jallabiya , gurin mahaifinsa ya k'arasa daya ganshi a k'ulle, wani wawan mari Harun ya kaiwa Bash , daganan fad'a ya sauya gashi dady babu halin temako duk Harun ya d'aureshi , kuka sukaji na wata murya wacce bata gidan ba , Basma ce raku6e a gefe tanata kuka ." Momy bataso fitowar Basma ba amma aikin gama ya gama tunda taji komai kuma taga komai , shigowar mom da Hajiya da Alhaji yasa kowa maida hankalinsa gurinsu , amma banda Harun da yaketa kaiwa Bash duka ba ji babu gani ,Alhaji ne ya k'araso a fusace ya wanke Harun da mari mom ma ta k'ara masa , kukan kura Harun yakumayi a karo na biyu ya cakumo dady idanun Harun sunyi ja kamar gaushi ya turashi , d'akinsa yana cewa , ka nuna musu wulak'ancin da kayiwa mahaifina , yana kuka yake maganar , dady da zuciyarshi a halin yanzu ta bushe babu tsoro a cikinta yace ”bazan fad'a ba , Harun na marin dady Alhaji na marin Harun cikin fushi momy ta k'araso tace ”Alhaji bakasan dalilin kiranka ba ,dazakazo kana dukansa wlh MUNTARI shine abin duka." Hanun mom momy ta kamo suka shiga d'akin dady , itadai mom na biye da momy wani d'aki suka shiga mai komai na cikinsa ja , hango k'waran gwal mom tayi ,momy ce tayi mata nuni da hannu , momy tace ” YUSUF!!! mom taga kud'i yana zubowa daga bakin abin , cikin firgici mom ta fice da gudu , Alhaji ne yayi nasarar kamota saboda yasan ,halinda zata shiga bata iya kallon 6acin rai , cikin surutanta , tace ”wlh shine ya kashemin miji kuma bazan barshi ba , gida ya kacame da tashin hankali , ga Basma na kwance zazza6i mai zafi ya rufeta , Bash tunda ya fita da gudu bai dawo ba ,ga mom tanata surutai momy kuma na kuka ,Harun na shirin kaiwa dady naushi Alhaji na tareshi ." Hango Bash sukayi a hanun wata budurwa , dady na ganinsu ya sunkuya da niyar guduwa yaji an cafkeshi , budurwar tace ”dama nace ”saina tona asirinku ka fad'a da bakinka waye ya kashe mahaifin wanan yaron ,Bash da yasami Halin guduwa gurin momynshi yace ”BEAUTY!!! karki k'ara danganta mahaifina da wanan bak'in lamarin , yana rufe baki yaji an shak'oshi , baiga kowa ba yasashi , zaro ido tare da rik'e wuyan yasan wanan aikin na beauty ne." Dady dai yak'i amsa lefinsa , dan haka Alhaji ya kira police , suka wuce dashi mom da Harun da Hajiya da tunda tazo batace komai ba sai kuka da takeyi ,suka nufi mota Basma dake bacci tsabar zazza6i ta fito tana rawa sanyi ta shiga mota ,duk cikinsu fuskar su babu wal wala." Sumaiya na kwance tana bacci, Khalid ne ya shigo da cokali da plet a hanunshi , had'awa yayi yafara ganga , dan dole Sumaiya ta tashi tana mita , Khalid na dariya yace ”oh ashedai babu dad'i ,jiya nadawo na gaji sosai inason hutawa kika isheni da kuka kikace sai na ciyo miki cin cin ko kin manta ?"uhm uhm nikam kabarni nayi bacci please my Honey, Khalid ne yasa dariya yace ”yawwa zoki bani hak'ina dan walh nayi hak'uri , kuka Sumaiya tafara tana shure shure ,dole ya fice ya k'yaleta , yana fita ta tuntsure da dariya , yana fita kitchen ya nufa abubuwan da ta ajiye zataci duk ya kwashe yakai d'akinsa✍️. [26/02, 10:58 am] Mom Islam ce💃: ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 53 & 54 ____ Tana tashi daga bacci ta je toilet ta wanke baki ta nufi kitchen , dube dube tashiga yi amma bataga abinda take nema ba , Khalid na d'akinsa yana kwance a bed yana chart da abokansa , shigowa tayi tana bubuga k'afa , d'ago kai yayi yakai idanunsa kan cikin nata daya fara fitowa , ya kashe mata ido d'aya , my gimbiya ya akayi ne ?"ni ni wlh kazo ka dubomin kayana ,tafad'a cikin shagwa6a , oh mom twins wai yaushe zaki dena rigima ne , kin girma kuma kinkusa bamu yara ,toshe masa bakin tayi da hanunta ta kwanta saman k'irjinsa tace ”please ka tashi , ta kwantar da kanta a kan cinyarsa , kasala ce ta saukar masa da har yasashi ....zanfa wuce nan kasancewar Khalid nayimin nuni da inbasu guri ." Mik'ewa tayi cikin mutuwar jiki tana kuka tace ”daban zoba ma wlh , ko tausayi na bakaji ko , Khalid ne ya janyota kana yace ”nine abin tausayi bakya gudun in fad'a wani halin ,please kidinga dauriya , ganin yana mata wasa da gashin kanta yasata mik'ewa da gudu shiko yana dariya." Umma ce zaune itada Malm , indomie takeci da k'wai , ga shayi da yaji madara , malm ne yakai loma bakinsa yace ”wai ni bazamu bada cigiyar wanan yarinya Asma'u ba ?6ata rai Umma tayi tace ”tunda bata damu da damuwarmu ba mai zaisa mu bada cigiyarta ?"kaga malam dan Allah wanan zancen ya wuce ”jibi zamu d'auki yaronnan mu kaishi gidansu saboda muga dawa yayi kama tunda yanzu kamaninsa sun fito sosai , eh gaskiya kam tun wuri gara a nemi ubanshi ." Tunda su mom suka dawo gida kan kowa yad'au zafi kowa ta kansa yakeyi , mom na d'akinta a kwance sunyi sa'a bacci ya d'auketa , Basma kuma na d'akin hajiya itama baccin takeyi Alhaji da Harun suna falo kowanne fuskarshi cike take da bak'in ciki , Alhaji ne ya dubi Harun yace ”zomu koma gidan wancan azzalumin , karya gudu ." Harun na driving , Alhaji na gefe , da isarsu babu mai gadi a gidan ya gudu yana gudun shima kar a had'a dashi , kutsa kan motar Harun yayi suka wuce ciki , yana parking Alhaji ya fito shima Harun d'in ya fito , tun daga nesa suka farajin hayaniya , da sauri suka k'arasa cikin gidan , hango dady a cukuwai kuye sukayi kamar wanda aka d'aure , gashi kuma babu igiya a jikinsa , Beauty dake zaune a kujera tace ”yawwa sun iso , Alhaji ya kali Harun shima ya kalle Alhaji , beauty ce tace ”kai zoka tambayeshi duk abin da yayi maka na cutarwa kai da mahaifinka , wani mugun kallo Harun yai mata , kana yace ”ke wacece ?"dariya beauty ta shek'e da ita mai sauti kuma marar dad'in saurara tace ”ku bil adama kun fiya raini , ina tausayinka dana nuna maka koni wacece "Alhaji ne yashiga bada hak'uri sbda ya lura da kofaton k'afar beauty , doguwar riga bak'ace a jikinta har k'asa , cikin kid'ima Alhaji yace ”ayi masa afuwa kai Harun bata hak'uri." Bash dake raku6e a gefe guda ya gallawa Harun harara tare da dariya marar sauti dan yasan beauty bazata barshi ba tunda yayi mata gardama batada hak'uri ko kad'an ?"jiyo muryar Beauty sukayi tana cewa ,kai ta nuna Alhaji da yatsanta tace ”waye ya fara shan jinin wanan yaron ta nuna Harun , cikin wahala dak'yar yake magana yace ” videon da aka yiwa Harun yana tsirara nine sila kuma jininsa muke d'iba lokacin da , jini yake fita ta k'afarsa da yatsun hanunsa , kuma duk ciwon da yakeyi mune nabadashi a k'ungiyarmu , sunce yafi k'arfinsu , inaji ina gani suka d'auke Fauziya , momy dake gefe zazza6i ya rufeta tace ”mugu azzalumi Allah bazai barka ba , bayanan mekuma yafaru , dady na fitarda nunfashi kamar mai shirin shid'ewa yace ”muntari yazamo kud'i a gurina dan ya zamo arziki dalilin sa nasami aiyuka a k'asar waje kuma bana talauci , dodo yasha jininsa , nikuma anbani gangar jikinsa ." Na rufewa kowa baki da maganar Yusuf , babu mai tambayar menene ya kasheshi sai yau da wanan shed'aniyar kuma hatsabibiya ta takurawa rayuwata , menayi miki ya tofawa beauty yawu , mari yaji daga inda baiga hanun marin ba ,Harun da yake ganin lamarin kamar almara yafara ,tuno abubuwan dasuke faruwa wanda ada bazai iya mai maita tunaninsu ba , tabbas shine ,Harun ya shiga nuna shi da yatsa , ana cikin haka , saiga malam da Umma tana goye da Muhammad ." Hankalin kowa yayi gaba babu wanda yaji salamar su momy ce kawai hankalinta yakai gurinsu , zama sukayi a kan ragowar d'ayar kujerar da babu kowa a kanta mai zaman mutum uku , Umma ta kunto ,Muhammad tare da gaisheda mutanen gurin amsawa sukayi kowa hankalinsa ya koma gurinsu Umma Beauty ta 6ace ,Dady na gefe haryanzu babu halin tashi ,hakama Bash babu damar mik'ewa , Umma ce tace ”munkawo muku yaronku ne a tan tance kamaninsa ,na wanda Asma'u zata aura ne kokuma na wani ne yakamata yabar hanunmu , malm yace ”gaskiya kam, zama Alhaji yayi harun kuma ya zauna ,a k'asa gefen Alhaji ." Kar6ar yaron Alhaji yayi ,suka had'a ido da Bash , yana hararar yaron , murmishi Alhaji yayi yace ”hospital zamu nufa yanzu , momy dai babu bakin magana , tamik'e dukansu da sunayen Allah aka samu Bash ya tashi suka shige mota banda dady da anyi anyi ankasa d'agashi a gurin haka suka kulle gidan suka barshi shi kad'ai a gurin ,yana zaro ido." *BAYAN WASU WATANN* Asma'u , ta goge ta kuma k'warewa a harkar bariki yanzu kam tamafi Zuby manyan samari , kowa kaji yana cewa Asmy kowa Asmy , yanzu fad'a sukeyi da Zuby kasancewar ita tazamo tsohuwar yayi kuma har yau bata rasa masu 6arin kud'i ba ,sai dai Asma'u tafita kud'i yanzu , tama siya ginannen gida mai kayan more rayuwa komai tsadar abu inhar tanaso bata shayin siyansa." Wata rana yaron gwamna yazo neman Asma'u saboda yaji labarinta akwai iya sarrafa ...😫 dayake yanzu ba gidansu d'aya ba , tunda sukayi fad'a kowa ya kama harkar gabansa , uhm damafa haka barikin take , Zuby tunda taji labarin tayi bak'o tak'ara komawa bedroom d'inta ta k'ara janbaki da turare da powder ,ta fito da wasu matsatsun kaya sai k'ar kad'a jikinta takeyi." Ta isa gurinshi yana kusada get ko sauka beyi daga motar ba , tunda ta taho yakejin anya zai iya da wanan kuwa?" inhar itace Asmy to ya hak'ura , bud'e motar tayi zata shiga gaba yace ”toh babu sallama? kuma kinsan dai ban baki izini ba ko ?"nasan kinsan koni waye dakuma tushena , zaki iya shiga back side , cikin dauriya Zuby ta shige sbda kalamansa basuyi mata dad'i ba , tana zama k'ofar ta rufe da kanta , murmishi yayi irinna gefen baki yace ” you're well come Asmy , wata fargaba ce ta dirar mata tare da fad'uwar gaba tace ”ni Zuby ce ”wani irin kallo✍️." *💦🌹MASOYA MASU KARANTA LITTAFINA INA YIMUKU ALBISHIR DA SABON LITRAFINA MAI ZUWA MAI SUNA🌹💦* *💦🌹LAMARIN K'ADDARAR AURE NA*🌹💦 Zai fito a 10...3....2021 Da abaki labari gara kibayar , a lokacin ne zangane masoyana💃💃 Please share👏 Vote me on wattpad ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 55 & 56 ____ kina nufin bakece Asmy ba ?"eh Zuby tabasa amsa , to bani number ta ,kwarjinin da yayi mata ne yasata bada number Asmy batare da ta shirya ba, godiya yayi mata , kana ya ciro bandir d'in y'an d'ari biyar , ya bata godiya tayi masa ta fice ,zuciyarta babu dad'i , ficewa yayi da motarshi dan ko address d'in gidan bai kar6a ba , number ta yafara gwadawa ,cikin sa'a tashiga , muryarsa ce ta bugi dodon kunnen Asma'u , sunana Haidar , ni yaron shugabar k'asar kd ne dafatan zan sami kar6uwa so yanzu dai kiyimin kwatancen gidanki , cikin rawa jiki Asma'u tabashi adireshin gidanta jikinta na rawa , juya motar yayi ya d'auki titi , kasancewar anguwar da nisa , wayarsa ce tafara ruri cikin nutsuwa yace ”nasa sojoji su zagaye gidan ... Da isarsu hospital , aka fara d'aukar jinin su Bash, banda zaro ido babu abinda bash keyi , jinin Harun aka d'auka aka d'auki na yaron daga baya aka d'auki jinin Bash , zuka koma suka zauna kowa na jiran sakamako , cikin lokaci k'alilan ,sai ga doctor nan ya fito ta result , mai d'auke da sunansu , mik'awa Alhaji yayi yayinda d'ayan momy ta rik'eshi , mik'ewa Alhaji yayi yafara duba , takardar ,Alhaji ne ya dubi Bash ya kuma duban jinjirin dake hannun Umma yace ”tabbas biri yayi kama da mutum , Bash da fuskarsa ta nuna rashin gaskiyarsa , Mom kuwa hamdala tayi tace ”k'ai k'ayi koma kan mashek'iya , Allah mungode maka , dama mutum yadinga kwatanta adalci shine dai dai , Daga hospital suka koma gida kowa na alhinin abinda yafaru." Haidar na isa anguwar ya fara k'arewa anguwar kallo , anguwace ta masu kud'i batada hayaniya , kiranta yayi ,babu 6ata lokacin sai gata nan ta lek'o , tace ”k'araso ciki , cikin sigar jan hankali , murmishi yayi ya shiga da motar kana yayi parking , fitowa yayi ,yana k'arewa Asma'u ,da gidan kallo , tsararen gida ne mai kyau komai na cikinsa abin burgewa ne ga wasu flawoyi masu kyau , hmm Haidar yace ”tare da bin bayan gimbiyar suka shige ciki , mazauni ya yiwa kansa batare da izini ba , kitchen ta wuce da zumbulelen hijab d'inda tasa gurin taryar Haidar." Fitowa tayi da wata fitinaniyar riga wace komai na jikinta ana kallo hatta pant d'in jikinta bobs d'inta da cibiyarta duk a waje , kawar da kansa gefe yayi , cikin zuciyarsa yace ”ba abinda ya kawoni ba kenan , abincin ta jera masa a dining tare da lemu iri iri ga dambun nama , izini tayi masa , shikuma yanason ita da kanta ta kai kanta gurin hukuma , jin ring d'in wayarsa yasashi kallonta ,bashi take kallo ba danne danne takeyi a wayarta hakan yasashi ficewa , jinayi yace ” okay ya Hajj karmu kaisu office ?okay zamuzo amma nafison tazo cikin rwan sanyi , ya kashe wayar , komawa ciki yayi yasami ,Asma'u ta kuma baza turare mai saukarda kasala , wanan shu'umin turaren inhar Allah yasa mutum ya fad'o hanun Asma'u to sai wani ikon Allah shine zai iya ku6utar da mutum amma yanada matukar tada hankali ,musaman ga maza masu yawan Sha'awa." K'in komawa dining yayi ya zauna a kujera yana kallon shirin da akeyi a TV , mik'ewa tayi ganin baizo ya zauna cin abincin ba yasata , zuwa gabansa ta kai hanunta zata kamo nashi ya dakatar da ita kana yace ”zomuje kasuwa , muyi siyayya so kinga daganan sai muje mu d'auki photo , cikin murana ta koma d'akinta ta canza shigar da tayi zuwa wandon jeans da t sheet fara , tasa k'aramin gyale tayi rolling kanta dashi ." Tana shirin rik'e masa hannu ya kauce , tunani tafara anya wanan bashida nufin cutar da ita kokuma da aure yake sonta gaskiya bata gane ba , motarshi suka nufa ,jin ya sanya karatun Alqur'ani mai girma suratul bak'ara yasa jikinta yin sanyi sosai ,wai shin meke damuta ne , shiko Haidar yana kallon duk wani sauyinta , bacci ne yai awon gaba da ita dan haka ya cigaba da tafiya zuciyarsa fal farinciki zai cikawa Alhaji alk'awari ." Horn yayi aka wangale masa get d'in , ya shige da motarshi dake Alhaji yayi masa kwatancen gidan da zai kawota , zuwansu yayi dai dai da shigowar wata mota wace aka d'auko Zuby a ciki tana ihu , Haidar yarasa yazaiyi ya d'auki , Asma'u kwai ya wuce ciki , samunsu dady da su Bash da Harun da Malm da momy yai a palorn gaishesu yayi kana yace ”gatacan a mota , da gudu Umma ta mik'e fuskarta d'auke da fara'a ta nufi motar , tashin Asma'u tafarayi ,kamar a mafarki Asma'u tajiyo wata murya mai kamada ta umman ta , a zabure ta mik'e idanunta sunfara fitar da hawaye , sosai take kuka kamar ranta zai fita duk wanda ya kalli fuskarta zaiga alamar nadama ta gaskiya ." Umma baki na rawa tace ”Asma'u ashe zamuga juna ¿"ashe. zamu gana ?"fitowa Asma'u tayi ta rik'e Umma tana kuka ,Zuby ma fitowa tayi ta rungumi Umma da Asma'u sukaci gaba da kuka , kaf y'an parlorn sun fito babu wanda bai zubarda hawaye ba sai malam da , ko gezau bai yi ba ,hatta Alhaji saida ya share hawaye." Malm ne yaje gabansu ,Asma'u ya janyota yafara dukanta da k'afa yana cewa "gara in kasheta walh gara mutuwarta da rayuwarta , janyeshi Alhaji yayi yace ”wanan wane irin sa6o ne , Allah ya shiryeta ta tuba kuma shine kakeson ka dawo da hanun agogo baya , haba Allah ma muna yimasa laifi ya yafe mana bare d'an Adam , kukan Umma ne ya tsananta ,Harun ya durk'usa yana share mata hawaye shima kukan yakeyi , Asma'u da rayi tozali da Bash ta watsa masa harara tace ”mugu macuci ma yaudari ma ha'inci insha Allah k'arshenka bazaiyi kyau ba wlh sai kayi nadama cikin k'an k'anin lokaci , ta d'aga hanunta sama tace ”. Ya Allah ka kar6i tubana Allah ka yafemin Allah natuba asragfirullah Allah kasa mucika da imani Allah ka shirya masu shirin shiga harkar da muka fito , Allah wanda suke ciki kuma Allah ka ku6uto dasu hanya ma dai dai ciya ,kowa ya shafa adu'ar ,Zuby da kuka yak'i tsaya mata tazo gabansu , Umma tace ”umma na tuba Ku yafemin nice silar watsewar Asma'ua karo na biyu ,na farko bani bace , amma dan Allah Ku yafemin , Umma cikin kuka ta d'ago , Zuby tace ”ta yafe mata , kowa ya waiga baiga momy ba ko ina tayi oho." Da haka sukayi adu'oi masu yawa kan Bash na k'asa ya kasa had'a ido da kowa , Alhaji shida Malm suka shige parlorn da zai sadaka da d'akin dady , ganinshi sukayi kwance a gurin kamar wanda baya nunfashi komai nasa ya sauya bakinshi na fitarda jini sosai hanunshi sunyi ja , malm ne ya girgiza kai suka nufi d'akin da mahaifin Harun yake , sutura sukayiwa abin kana aka yi masa sallah suka nufi mak'abarta....✍️. ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️. _Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_ *Story and writing* *By* *ZAINAB HABIB* _(Mom Islam)_ Zainabhabibu713 @gmail.com Wattpad momislam2020 Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk Telegram https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2 *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* EPISODE 57 & 58 ____ Suna dawowa daga kai Dadyn Harun ,suka sami dady rai yayi halinsa babu wanda yayi ko d'arr sai dai dole rasa rai za'aji babu dad'i , Bash tunda dadynsa ya rasu yasan gatansa ya k'are ,gaban momy yaje ya nemi gafara da gaban su Alhaji da malam , kowa ya kar6i tubansa , amma Asma'u tace ”sai dai a warware alk'awarin aurensu da Harun dan ba Harun ne yayi mata ciki ba , shidai Bash baice komai ba , Haidar ne yazo yace ”ni zan auri Asma'u saboda Allah , kana ya tuntsire da dariya ya kalli ,Zuby yace ”nifa ba yaron gwamna bane ,ni jami'in tsaro ne , ware ido , Zuby tayi dan a yanayinsa kai kace ”yaron gwamna ne , sukasa dariya komai yanzu yayi normal a familyn , Haidar yace ”zai rik'e yaron Bash , da yardar Allah Bash ya zamo mutumin arziki , ya durk'usa gaban Harun yace ” dan Allah ka yafemin d'an uwana kayimin gafara dan Allah ,kamo hanunsa Harun yayi yace ”d'an uwana ni ban rik'eka da komai ba na yafe maka Allah ya yafe mana , momy data shigo yanzu tasamu fuskar kowa da walwala." Haka aka yiwa dady sutura aka kaishi , momy bata nuna halin damuwa ba amma jikinta babu k'wari sosai , haka suka koma parlor kowa na farinciki ." Bayan watanni , cikin Basma yanada wata hud'i ,ya fito kowane a cikinsu yana iya k'ok'arinsa waje farantawa d'an uwansa , shirin fita sukeyi zasuje , gidansu ,Bash Harun ne ya kira Bash a waya yake gaya masa gasunan zuwa , Harun ne ya d'auko sark'a da d'an kunne ya sanyawa , Basma , ya ciro mata jaka ,ta k'arasa sa shauran suka fito parlor , material ne a jikinta milk color mai adon black stone , ba k'aramin kyau tayi ba , shikuma boyel ne a jikinsa bak'i sai shek'i yakeyi ,da milk d'in hula , turarensu kala d'aya ne basa sa daban , bak'ar jaka da takalmi da gyale ta ciro , rik'e da hanun juna suka fito ,Harun ya kullo musu k'ofa suka fice , da isarsu gurin ajiye motoci ,Harun ya ciro fara , kasancewar aikin da Alhaji ya nema masa akwai Alkairi sosai , da shigarsu mai gadi ya bud'e get tare da ficewa da motar , suka d'auki hanya , sai da suka tsaya sukayi siyayya mai yawa sanan suka nufi gidan su momy , yana horn mai gadi ya bud'e get tare da washe hak'ora , 1kk Harun ya ciro ya bashi , yai parking d'in motar ,suka k'arasa ciki ,da shigarsu momy ta rik'o hanun Basma cikin murna ta zaunar da ita a kujera , Bash ne yace ”my bro kayi sa'a da yanzu nakeson tafiya hira , dariya sukasa momy tace ”ko kunyata ma ba'aji ?", gaisawa sukayi cikin mutunci aka cika musu gaban su da kayan motsa baki ." Sai da Basma ta taya momy wanke plets da gyra gidan ,misalin k'arfe hud'u bayan sunyi sallah suka yiwa momy sallama , turaruka ta ciro masu k'amshi da turaren wuta ta bawa Basma , godiya tayi mata suka tafi ,suna fita daga gidan suka d'auki hanya , suna hawa titi ,Hatun ya hango Sumaiya rik'e da hanun wani ,ga k'aton ciki a gaba , tafiya ya farayi a hsnkali yana rage tsayin glass d'in , hakan yasa Sumaiya hangoshi , dariya tasa tace ”Harun ashe rai kanga rai , ko cigiya babu , murmishi Harun yayi ya sauka suka gaisa da Khalid cikin fara'a ,basu tsawaita hirar tasu ba suka tafi , bayan Basma tabawa Sumaiya adreshin gidansu ,da number ta... Harun ne yafara bawa Basma labarin Sumaiya , tad'anji kishi amma tunda ba shi ta aura ba ai shikenan , da isarsu gida aka bud'e musu get d'in , Basma ta gaji da zama a mota hakan yasata saukowa da k'yar , dariya Harun yake mata yana tsokanar ta , suna shiga parlor suka yada zango , Harun yashiga yimata tausa tana k'ara narkewa ." ********************* Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah . Abubuwa sun faru da dama na rayuwa , ciki harda aihuwar Sumaiya , dakuma auran Bash yau satinsa d'aya , da auran Asma'u da Haidar , abin guwanin birgewa , kowane gida na cikin k'oshin lpy ." Sumaiya ta haifi yaro namiji gatan da ake nunawa yaron ba'a magana , Allah sarki rayuwa kowa ya rasa iyaye yayi kuka , Khalid baiso Ammi ta d'auki , Sumaiya ba , itako Ammi ganin rawar kan tayi yawa yasata d'auke Sumaiya ." Cikin Basma watanshi tara da kwana goma , tun lokacin da tayi zazza6i Hajiya ta d'aukota ta dawo gabansu , sam Harun baiji dad'in hakan ba , ko gurinta zashi , suna ganinshi , zasu fara tuhumarshi shiko ya tsani wanan lamarin shida matarsa amma ana yimasa haka." Kulum cikin sa rai da aihuwa suke amma cikin ikon Allah shiru babu labari , ranar cikin yana wata tara da kwana goma sha d'aya , su Hajiya sukaje gidan wata rasuwa da akayi musu , akabar Basma dame aiki , Harun ne ya shigo sad'af sad'af ya wuce bedroom d'in kusada na Hajiya , kasancewar anan d'akin Basma take , tura k'ofar yayi a hankali , idanta biyu suka had'a ido dashi dariya tasa tace ”sai na fad'awa Hajiya , kafin ta gama magana ya had'e bakinsu guri d'aya , itama ta biye masa sukaci gaba , dawowa parlor nayi dan in huta kafin anjima na koma lol , bayan 30mints Basma ta fita haiyacinta ,Harun kamar wani zaki idanunsa sun rufe babu batun tausayi , saida yaji ta k'wala k'ara ya d'auketa da sauri ya kaita toilet , babu abinda zata iyayi , sbda hanunta na kan mararta tana kuka , wanka yayi mata tare da goge mata jiki ya sanya mata kayan da tacire yanzu , gudun kar azo a ga canji kuma a zargi ya shiga d'akin , shima wankan yayi ya dawo kusa da ita , abu kamar wasa ya zamo gaske , Basma ta koma abin tausayi a ciwon mara da baya daya sata gaba, Sallamar su Hajiya ce tasa gaban Harun fad'uwa , Hajiya na shigowa gidan kai tsaye d'akin Basma ta nufa , ganinta kwance ,Harun nayi mata sannu yanayinshi duk sun sauya , bansan meta gani har ta gane , Harun ne silar ciwon ba , masifa tashiga yi tana cewa kai bakada tausayi ne ?"kasheta kakeso kayi ?"gashinan kaje ka tsonano mata nak'uda , sai ka fitoda mota muje adibiti , cikin rawa jiki Harun ya fito da mota aka rik'o Basma aka sata a ciki tare da kayan aihuwa Hajiya ta shiga mom dama bata dawoba suka nufi hospital, da isarsu aka wuce da ita labour room , su Hajiya nata adu'a , temakon gaggawa suka shiga bata kasancewarsu musulmai harda adu'oi suma sukayi , Hajiya dake zaune a bakin k'ofar d'akin , ta jiyo kukan jinjiri , da sauri ta fad'a d'akin , ana gyara d'aya akaga Basma na sabuwar nakuda , haka Allah cikin ikonsa takuma sam6alo mace ”mai kamada babanta , duk yaran kamar Harun suka d'auko ana gama gyrasu aka nad'esu , zuwa anjima kad'an aka yimusu wanka itama aka d'aurayeta , kai masha Allah , tunda garau take babu rashin lpy yasa doctors sallamar ta, Gida ya cika da farinciki sosai , An sanarwa kowa na dangi , Bash kuwa kamar jira suke sai gashi da matarshi , mom bakinan yak'i rufuwa , haka momy ma cikin farinciki tazo , Sumaiya ma tazo kai aihuwa dai masha Allah yara sunfito cikin dangi mai kyau ." Beauty bata k'ara dawowa ba , dan haka farinciki da zumunci dakuma had'in kai da kwanciyar hankali ya wsnzu a tsakaninsu . ALHAMDULILH👏. Allah nagode maka daka bani ikon kammala wanan littafi hak'ik'a masoya kunyi rawar gani gurin nunamin k'auna Allah yabar zumunci Allah kasa abubuwan dake ciki zasu amfani al Umma amen. Ga masu buk'atar sabon littafina mai fitowa a 10.....3.....2021 zaku iya tun tu6ar wanan number 👇 08141799224 Please inba maganar book zakiyi ba karki yimin mgna 👏 FATAN ALKAIRI.