*Dr HANEEFAH* 👩🏼1 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Bismillahir-rahmanir-rahim Darasi ake musu amma hankalinta baya kan abinda ake koyarwa musu, zubawa malamin idanu tayi kamar mai fahimtar abinda ake. Qararrawa aka kada domin canza malami fitarsa ke da wuya itama ta tashi domin bin bayansa nan take hadiza da ta lura da yanayin da tashiga tabita a baya. Nesa da ajinnasu tayi sannan ta samu wani lungu ta tsaya, hawayene kebin kuncinta sai taji an dafata kafadarta. Ganin hadiza yasa ta fashe da kuka sosai tare da sulalewa ta zauna kan wani dutse, kuka take sosai hadiza bata ce da ita komai ba, ganin ta saida kuka da kanta hadiza tace haba haneefah duk abinda ya faru hakuri zakiyi tare da cigaba da addu'a yariga ya wuce kuka da damuwa bazai zamto solution ba, murmushin takaici haneefah tayi taga aminiyar tata tace hadiza ba lamarin nazir ke damuna ba nasan ina sonshi ya yaudareni yayi aure lamarin abbanane har yanzu bansan me zan mishi na birgeshi ba, sun hadani da abbana kullum cikin ganin laifina yake bansan mezanyi in wanke kaina ba, cike da tausayi hadiza tace kada ki damu Allah na tare take duk daren dadewa gaskiya zata bayyana, abinda nake so dake ki kwantar da hankalinki, ki dage da karatu insha Allah wata tana sai labari da irin wannan kalamai hadiza ta rika kwantar mata da hankali suka koma aji. Alhaji hamisu shine mahaifin haneefah sannan umma salamatu itace mahaifiyar haneefah. Haifaffun garin kano ne,Yana da mata biyu hajiya hafsa(inna) da salamatu (umma). Inna yaranta takwas biyar mata uku maza salim shine danta na farko, bilkisu, zainab, jibril, zuwaira, Ibrahim, shukra da sadiya sannan yaran umma Nana khadija itace babbar yarta sai ahmad, haneefah da kannenta biyu amal da bintu. Alhaji hamisu adaline tsakanin matansa da yaransa yanada rufin asiri daidai gwargodo domin ma'aikacin gwamnatine, bayi da buri kamar yaga yayanshi sunyi karatu badon su zama wani abuba, domin duniyar yanzu karatu nada muhimmanci arayuwar dan adam. Inna ta daurewa yaranta gindi wajen yin abinda suka ga dama shiyasa sam basu aje hankalinsu wajen yin karatu ba kullum cikin bin yan mata suke matan ko dakyar suka qarasa karatunsu na sakandari aka aurar dasu sai kannensu qanana shukra da sadiya haka yan maxan karatu yaga garesu suka nuna aure suke so aka aurar dasu banda ibrahim. Akullum alhaji hamisu yana takaicin halin yaransa domin shi mutum ne mai son karatu domin yasan muhimmancin sa amma babu yadda zayyi tunda haka suka ga yafi musu. Itako umma ma'aikaciyace, macen kirki marason magana sannan takasance ta tashi tsaye kan tarbiyyar yaranta da ilminsu hakan yasa take gaban goshi wajen maigidanta, hakan yasa inna kishiyarta ta dauki alwashin sai ta tarwasa su, Allah cikin ikonsa lokacin Alhaji yayi retired, rayuwa yayi halinsa, yau akwai gobe babu hakan yasa yacanza makarantun yayanshi izuwa na gomnati. Umma su biyune gun mahaifan su, yayarta hajiya lubna. Tun suna qanana Allah yayiwa haifinsu rasuwa mahaifiyarsu ta dauki dawainiyar karatunsu har lubna ta kammala ta samu miji tayi aure, yanema mata aiki a ma'aikatar ilmi hakan yasa ta samu kwarin gwiwar dauko kanwarta taci gaba da karatu ta kammala har tasamu miji tayi aure. Lubna yaranta bakwai hudu maza auwal, sadiq, musa, khalifa uku mata muhibbat, humaira da amina. Auwal, muhibbat da humaira suna da aure da yaransu. Duk dukiyar da Allah ya azurtasu hakan baisa sun sangarceba, duk sun kasance yara masu tarbiyya. Sannan burin umma da mama suga kan zuri'arsu a hade. Cikin ikon Allah sun girma suna kaunar junansu. Haneefah yar shekaru 17 aduniya yarinyace mai biyayya da hankali, sannan takasance yarinya mai barkwanci, bata son raini sannan bata kaunar ta rainamutane, saurin fushi gareta ga saurin hucewa sannan yarinyace mai tsananin bincike kan abinda tasa gaba, ga ilmi. Yarince mai son kwalliya tare da yin duk wani gyara na diya mace, tana matukar son abubuwa daya shafi mata, sannan ita ba kyakykyawa bace ba mummuna bace JININ KYAU GARETA domin ta iya kwalliya. Haneefah itace yar gaban goshi gun mahaifiyarta da yan uwanta suna matukar ji da ita, hakan yasa bata da tamkarsu kullum burinta son faranta musu da wuya kaga sun samu sabani tsakaninta da su domin burinta kullum su hade kai. Yarinyace mai saurin shiga rai duk inda ta zauna tana dibar jama'a saboda yawan fara'arta, hakan da inna ta fahimta shine ta dada karkatar da hankalinta ga haneefah domin lalata mata rayuwa. Kishi sosai inna da yaranta suke nunawa umma, duk da haka umma bata bi takanta ba saida taga sun fara shiga rayuwar yaranta ta soma taka musu birki, duk da haka saida tayi nasarar bata sunan haneefah gun abbanta. Haneefah komai tayi baya birge abbanta hakan yana damunta ga yan uba sai wahalar da ita suke, duk da wani lokaci ba raga musu take ba shakkanta suke. A haka ta soma soyayya da wani matashin yaro mai suna nazir, tana sonshi sosai domin ya hadu iya haduwa. Tana matukar sonshi domin irin mutananne da basu iya so ba, akarshe ya auri wata duk da abin nadamunta kawai ta watsar dashi tare alkawarin bazata qara yarda da wani namijin ba... Amma burinta gyara tsakaninta da abbanta *Dr HANEEFAH* 👩🏼2 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Gidane babba amma an rabawa kowa mashiganshi tun daga bakin gate. An taso daga makaranata ta hade kan kannenta suna tahowa tare dashike tsakaninsu da makaranta babu nisa, dai dai sunzo shiga gida taga yaya jabir da abokinsa suna tsaye idanu sunyi jajaye, daganinsu kwayoyi suke sha ta girgiza kai cikin takaici tare da cewa Allah shiryeku tayi nasu gidan su shukra ma suka shige. Bayan shiganta sahabi yadubi abokinsa jabir yace aboki ya maganar haneefah saifa shareni kake da zarar na kawo maganarta cike da maye jabir yace ai dama so nake ta kammala makarantarta tunda yanzu tana ss3 amma tunda ka matsa ku daidaita tsakaninku inyaso agudanar da biki inta kammala cike da zumudi sahabi yace to shikenan nagode. Zai juya ya tafi jabir yace anjima ka dawo daga zarar an idar da sallan magriba, yace zan dawo daukeda murmushin mugunta jabir ya shige nasu gidan. Agajiye tashigo gida bayan sun taso daga islamiyya ta tarar da yayarta a kitchen tana girki tace sannu Dr da aiki yau baki dawo gida da wuri ba, tace bari kawai yau muka fara fita asibiti shine kumayi yamma inaga kullum haka zan kasance, haneefah tace tab yanzu a asibitin zaki iya wuni wlh nikam bazan iyaba, cike da zolaya tace toh accounter haneefah, ta hada girar sama da kasa tace bayan kunce sai dai na zamo Dr, to wai dukka zamu hadu a fanni daya ayyakamata mu karanta abu daban-daban cike da murmushi nana tace zamu karanta health line amma fannin kowa daban kinga..... Tun kafin ta karasa takatseta tace nidai bazanyi ba yadda nake burin accounter zanyi ko banyi ba.... ta gyada kai tashige ciki nana namata dariya. Bayan ta idar da sallah tana lazimi amal tashigo tace ana sallama dake a wace, tayi mata nuni data tsaya ta kusa kammalawa, bayan minti biyu tayi fatiya cike da tsoro tace waye? Abokin yaya jabir cike da mamaki. Sallama tayi ya amsa cike da murna yace nasan zakiyi mamakin ganina amma ba abin mamaki bane, inasonki kuma da niyyar aure nazo bude baki zatayi magana taji an bude gate, kallon da taga abbanta nayi mata ne yasa hankalinta ya dada tashi bai ce da ita komai ba yayi wucewarsa cike da bakin ciki tace wlh kaci sa'a, ko kunya bakaji ba wai kana sona? Toh wlh nakuma ganin kafarka cikin gidannan ta kyada kai ta wuce. Zama tayi bakin gado ta rasa mezatayi, tunani kala-kala yanzu kuma wani hukunci za'a yanke mata? Cikin wannan hali nana tazo ta tarar da ita tace haneefah yau meya faru? Me kika gani? Yanzu nakaiwa abba abinci yake surutu yaushe zaki gyaru, imma auren kikeso kituro amma shiya fita hakkin ki wajen ganar dake, har dan shaye shaye kika kawo masa gida ransa ya baci sosai, nasan bazaki aikata haka ba sai dai turosa akai, nan take haneefah ta dago kai idanunta cike da hawaye, murmushi tayi tace ba komai Allah na tare dani, cike da tausayi yar'uwar tata tace kada ki damu zaizo yagane gaskiya cike da bacin rai haneefah tace yaushe? Tun na taso yataba saurarona? Komi aka fada mishi daukawa yake, yazama dole in masa biyayya da zan entar da kaina damuwar da nake ciki. Tunda ta fara magana ta kafa mata idanu, tabbas tananuwa haneefah so amma tana tare da kyakykyawar tarbiyya data bata bazata iya aikata irin wadannan abubuwan ba. Taqaraso ciki ta zauna kusa da haneefah tace in fada miki mafita? Tace eh umma zanyi, umma tace toh yazamto mai biyayya gareshi tare da kusanto farin cikin shi ko da ke zai baqanta miki rai, kinsan farin cikin sa yaga kuna karatu sosai, inaso ki kwantar da hankalinki kiyi karatu sosai domin fita da saka mako maikyau sannan ki hada kanki da yan uwanki duk da su ba hakan take agun suba, sannan ki dage da addu'a sosai kan Allah yaraba ki dashi lfy last one shine ki daina damun kanki, ki kawar da kanki kinji? Ta rungume ummanta insha Allah zanyi ta shafa kanta that's my haneefah. Tun daga wannan rana haneefah ta kudurci aniyar yin karatu, ta tattare hankalinta gurin kararu tare da dagewa da addu'a. Ta fita harkansu inna duk da dama ita ba shiga tsabgarsu take ba. *** *** *** *** Kwanci tashi ba wuya cikin nasara haneefah ta zana jarabawarta na SSCE kuma ta fito da saka mako mai kyau cike da farin ciki ta nunawa mahaifinta shima ya yaba mata sannan ta ce tana da ra'ayin tafiya nursing ganin yadda ta dage yasa shi farin ciki tare da yi mata alkawarin zai nema mata. Ranar haneefah tayi farin ciki ganin mahaifinta na farin ciki haka yan uwanta suma sun taya ta. Alhamdulillah ta fara ganin sassauci gun mahaifinta kuma cikin ikon Allah ta samu admission a nursing, tare da kawarta hadiza. Farin ciki ba'a magana gun haneefah, kowa ja mata kunne yake akan tayi karatu cike dajin dadi tace da yan uwanta duk abinda kukeso ina so bazan baku kunya ba. Hakan ko akayi, hadiza da haneefah an dage basu dauki sabbin kawaye ba domin sun aminta da juna sosai dukkaninsu ma'abota son karatune duk da anason kawance dasu amma basu bawa kowa dama ba. Sun tashi daga aminai sun zama yan uwa. Hadiza kyakykyawace sosai domin tafi haneefah da kyau tun suna ss1 hadiza ta aminta da haneefah dakyar ta shawo kanta suka zama aminai, domin haneefah ita kowa natane. Cikin nasara suka cinye shekara daya da rabi saura daya da rabi sannan a asibiti zasu karasa. Babu matsalar da haneefah ke fuskanta kamar rashin iya turanci sosai, ta iya amma bazata dade tabayin shiba wato kadan-kadan takeji, tana iya karatu sannan ta fahimta amma mayarwane bata iyawa, wannan matsalar na damunta. *Dr HANEEFAH*👩🏼 3 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Zaune take tana nazarin wasu littattaifa nana tashigo tace sannu da kokari tace yauwa atakaice tace me kike dubawa ne? Tadanja tsaki tace gobe zamu fita asibiti kuma inaga ranar ante-natal (awon cikine) kinsanni da surutu Amma kada abani topic da ban kware akaiba, nana tace inaga za'a baku kuyi takaitaccen jawabi kan awon cikine, mata diyewa in sun fara zuwa awon ciki kalilanne suke kammalawa harsu haihu, hakan ko bashi da kyau sannan da dama basa son shan magani kamar yadda aka kayyade musu hakan na kawo matsala musamman in mace tazo taihuwa, kamata yayi in mace ta lura tana da juna biyu ta rinka ziyarar asibiti ba fashi harta sauka lfy, in munajin kanmu babu matsala bamusan yaushe matsalan zata auku ba bari in takaita miki yadda zaki jawabi Bayan kinyi sallama tare da tambayarsu kowa lfy saiki soma bayani kamar haka; Zamuyi bayanine akan awon ciki ga wadda bata taba haihuwa ba kuma tana jinta kalau, ya dace tayi gwaje-gwajen da akeyi a awon ciki sannan sume akeyi a awon ciki? Yana da kyau sosai ko da kalau kike jinki ki je a gwada lafiyarki yayin da kike da juna biyu, musamman ma idan na fari ne. Wannan shi ake kira awo. Bari a yi miki bayani mai dan gamsarwa game da awon. Awo wata hanya ce ta amfani da gwaje-gwaje, domin tabbatar da lafiyar uwa da jaririnta da kuma gano matsaloli da ke tattare da yanayin juna biyun, don magance su da wuri tun kafin su zama alakakai. Wato dai hanya ce ta kariya daga galabaita a yayinda ciki ke girma ba kuma lallai bane a auna kowanne a ziyararki ta farko, a’a yau a duba wannan, wani zuwan a duba wancan. A wasu matan da aka ga juna biyunsu ba shi da hadari sosai, ba lallai ne a auna komai ba. Ga abubuwan da aka fi aunawa a zayyane: Na farko ana auna tsayin mai ciki domin duk matar da tsayinta ya gaza mita 1.5 tana cikin hadarin yin doguwar nakuda. Don haka sai a sa alama a katinta cewa wannan matar idan ta zo haihuwa a shirya sosai, ko da doguwar nakuda za ta kamata. Sai kuma nauyi, wanda idan ya wuce misali shi ma ana kyautata zaton ko dai mai juna biyu ta iya samun hawan jinni, ko ciwon suga a wannan lokaci na ciki. Domin wasu matan a lokacin ciki suka fi samun wadannan ciwuka ko da ba su gada ba, kuma yawan nauyin mace kan sa a fara tunanin hakan. Kamata ya yi mace mai ciki ta rika kara rabin kilo na nauyi a mako guda da zarar ciki ya fara tsufa. Amma idan aka samu nauyin da ya wuce wannan, an san akwai matsala. Sai kuma awon cikin shi kansa. Duk sati ciki ya kamata a ce yana kara kwatankwacin santimita guda, don haka ana aunawa ne a gani ko jariri na girma yadda ya kamata ko kuma a’a. Idan awon ciki bai kai daidai watannin cikin ba, to yaro ba ya girma sosai, kuma akan dauki mataki, idan kuma awon ya wuce yadda ake so to shi ma yana nuna wani abu daban, wato ko dai cikin tagwaye ne, ko jariri na girma fiye da yadda ake so (kamar yaran mata masu ciwon suga), wanda hakan kan jawo doguwar nakuda. Za ta iya kasancewa kuma ruwan da yaron ke ciki ya yi yawa sosai, wanda shi ma alama ce ta illa a jariri. A wannan lokaci akan hada da hoton scanning da zai nuna halin da jariri da mahaifa suke ciki. Na hudu sai a auna bugun jini don a tabbatar ba hawan jini a tare da mai ciki. Idan akwai a ba da magani da sauran shawarwari. Sai kuma a tura mace auna yawan jini. Saboda bukatar da jariri ke da ita na wani kaso na jini, kowace mai ciki sai an duba yawan jininta a gani ko isasshe ne. Akan ba da magungunan karin jinni, ko ma shi kansa jinin daidai da bukatar matar. Akan ba su shawara su rika yawan cin nama da koren ganye, saboda suna daga cikin abinci masu kara jini sosai (suna dauke da sinadarin iron). Sai kuma a auna yawan suga. Shi ma don a tabbatar matar ba ta da ciwon suga, idan kuma akwai a fara ba da magunguna. A lura cewa da hawan jinin da ciwon sugan da aka samu a lokacin ciki za su iya warkewa bayan an haife cikin, ko kuma su ki warkewa. Sai kuma a ce mai juna biyu ta ce ta yi fitsari a kwalba, don a gwada sinadaran da ke cikin fitsari. To a nan ma ana iya gano ko akwai matsalar ciwon jijjiga ko na suga a jikin matar. Wadannan su ne muhimman abubuwan da ake aunawa. Ban da tsayi, kusan duk abubuwan da aka zayyana a sama ba sau kadai ake aunawa ba, wato kusan duk zuwa sai an sake aunawa saboda lokacin da ciki ke kara tsufa, lokacin hadarinsa ke kara yawa. Allah baku ikon zuwa ya saukeku lfy *Dr HANEEFAH*👩🏼 4 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Saiki shirya da amsar tambayoyi domin baza'a rasaba, haneefah dake kallon nana tace yanzu haka mutum zai tayi? Wlh ni bazan iya cigaba da health ba ,innayi gaba canza abuna zanyi. Nana tace kici gaba yar uwa, al'umma na bukatar irinku, ke yarince mai tausayi sannan zaki aje uzurinki domin wasu na tabbata zakiyi taimako, haneefah tace wannan shine dalilin naki? Ayyuka da dama al'umma na bukatar taimaka amma ai lfy yafi koma cewar nana. Haneefah tace yauwa sis yaushe zamusha bikine Allah duk na kagu kinga kin gama makaranta. Nana tace da saura, abba so yake muyi karatu sosai haneefah tace haba nana ai karatun da kikai is ok, aiki yarage miki fa! Haneefah ina matukar so naga nacikawa mishi buri, in kikai la'akari da yanayin gidannan cikin yaran inna babu wadda karatunsu yayi zurfi, duk da yakasance bayida arziki irin na baya amma yana mana kokari sosai, inason nayi aure kuma umma tanaso amma zan bari ba yanzu ba sai nayi MBBS zaro ido haneefah tayi tace kina da kokari, shine ko kula samari bakyayi? Eh bazan kula kowa ba sai naga komai ya dai-daita. Ajiyar zuciya haneefah tayi tace haba nana, kin dan samu karatu ai saiki godewa Allah, bakyaga irin yadda kasarmu take ciki? Wace yar talaka kikaji tana MBBS duk yayan masu kudine sannan aure ai baya hana karatu, ina mamkin wasu iyaye da suke dagewa yaransu akan sai sunyi karatu koda sun nuna aure suke so, dayawa yara suke shan wahala wajen danne kudurinsu su faranta ran iyayensu, wai shin karatun boko meyake so ya zamane? Yadda mutane suka dauka muhimmanci suka bashi, zakiga yaron da ya iya turanci yana kokari anfi tarairayarsa amma ba'a kula da na addini ba, yaro daya dace ya taso addininsa yasani amma yafi sanin kan boko, zakiga wasu yara masu shekara 7 basusan banbancin tsakanin wuta da aljannah ba amma an hada suda tv babu abinda basu sani ba. Muyiwa kanmu fada kamata yayi yara su taso da Qur'an a bakinsu ba sanin story books ba Allah sa mugane ameen, nana tace kina da gaskiya na dogara ga Allah kuma insha Allah inna samu admission ko apart 1 me zanyi aure haneefah tace karma kiyi mana. Suna taba karatu ahmad ya leko yace kuzo umma nakiranku. Zaune suka taddata haneefah tace sannu da hutawa ta amsa mata tace yauwa, ta kalli haneefah cike da murmushi tace dama lokaci yayi dama batun zaki bude account ne, lokaci yayi da kema zaki fara adani kamar yan uwanki nana da ahmad, ajiyannan da zakiyi zai amfanar dake damu watarana, dubu goma ne a ko wacce wata, nasan yanzu ba wani sutura kika damu dashi ba tunda kullum cikin uniform kike, gabama in zaki saya kisiya daidai karfin ki sannan ki rage tambayar abbanki kudin makaranta sai wadda ya dace ki tambaya ina fata kuna jina? A sanyaye tace eh sannan ko lokacin auran ku yazo bazamu sha wahala sosai ba ammafa sai kuna tattali, Allah ya muku albarka tashi ku tafi. Haneefah tana matukar son mahaifiyarsu, duk kudin da take samuwa akansu yake karewa tasan tanayin hakanne domin su kauda idanunsu akan abin hannun jama'a, duk da basu da kodayi amma ummansu tana wadatar dasu da komai. Gaskiya iyaye abin tausayawa ne musamman uwa, zata salwantar da dukkanin farin cikin ta domin ta faranta ran yaranta, babu abinda ya'ya yadace suyiwa iyayensu kamar su faranta musu sannan su bisu da addu'a. Washe gari ta tashi da tsananin tsinkar zuciya, ta idarda sallah tayi dukkanin abinda ya dace kuma ta saba na ibada amma stil zuciyar bata daina ba. Kokarin shirin fita take amma takasa shiryawa cike da mamaki tace yau kuma mezai faru. Dauko Qur'ani tayi ta zauna karatu, a hankali taji zuciyar ta lafa, ta dauko carbi ta soma addu'a. Takai kimanin minti ishirin sai ta tashi ta shirya taje yiwa umma sallama, umma ta bata kudin da zata bude account tayi musu sallama ta fita. Zaune take a ward (pediatric) dinsu amma takasa tabuka komai sai addu'a take a zuciyarta, zaman ya gagareta ta tashi ta nufi gun aminiyarta dake labour ward. Kasa shiga tayi domin jirine ke daukanta intaga jini. Tana cikin tsaye sai ga hadiza ta fito tace ah yar'uwa kece kika tsaya anan, haneefah tace so kike abani gado kenan domin nikam fadiwa zanyi, dariya hadiza ta soma yi domin sarai zata iya tace meya fito dake lokacin lunch bayyi ba? Haneefah tace wlh yau nakasa gane kaina tun dazu wani iri nakeji. Hadiza cike da damuwa tace kodai wani abu yafaru ne? Aa babu komai tace kiranka anbato _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musi bati wakhlifni khairan minna_, haneefah tace inshaa Allah zanyi nagode, zan tafi bank yanzu innatashi zan wuce gida tace toh Allah kiyaye hanya ki gaida gida. Saukowa tayi cikin adaidaita sahun da ya kawota ta sallameshi ta shiga bank zuciyarta na dada tsananta wajen bugu. Zaune take tana jiran a sallami wadda suke gabanta tana karewa cikin kallo tana kara sha'awar zama accounter. Daidai wani bakin ko fa da yayi lungu ta tsugunna take cika forms da aka bata, zata mike takai takardun tana kara dubawa batare da ganin gaban taba. Gaisawa yayi da abokinsa zai wuce office din manager hanakalinsa nakan abokin nasa, tafiya yake baya duba gabansa ya juya yana yiwa abokin sallama cikin sauri. Dab zai karyo kwanan yaji yayi karo da wani abu, tarwatsewar takardune ya tabbata mishi mutum ne. Cike da tsiwa ta dago zata fara magana hada idanun da sukai me yasa fasa abinda take shirinyi. *Dr HANEEFAH* 👩🏼5 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Kallo cikin ido suke, a take taji wani irin nishadi ya lullubi zuciyarta, kimanin dakika goma suka dauka, tayi saurin kawar da kanta ta sunkuya ta fara daukan form da suka tarwatse. Baice da ita komai ba saida ta kammala ta dago yace am sorry, najuya ina maganane batare da kula da abinda yake gama naba. jin muryar tasa take tamkar kada ya daina magana tsaban dadi, bata tabajin murya irin tashi ba. Batare cewa komai ba zata wuce yace kinji? Ta daga ido cikin wani salo da itama batasan tayi ba ta murmusa tayi gaba abinta batare da tace dashi komai ba. Ta kammala komai ta nufi gida. Misalin karfe goma da rabi ta kammala shirin baccinta ta kwanta, idanunta a lumshe ta soma karanto suratul mulk (yana tsare dan adam da azabar kabari) sannan ta soma neman gafarar mahaliccinta tana ambaton _ASTAGFIRULLAH WA'ATUBU ILAIK_(yana dakyau mu koyawa kanmu wannan dabi'ar, yin istigfari har bacci ya daukemu. Allah sa mudace) bayan ta kammala tanemi bacci ta rasa, kalaman wannan mutumin suke mata yawo a kunne, ta tsinci kanta da son sake jin maganarsa koda sau dayane.... tunani takeyi sosai taga ba mafita bane ta dauro alwala ta fara jera nafiloli saida bacci ya dameta sosai ta kwanta kan sallayar bacci ya dauketa. *** **** **** **** Dr Hassan ke zageye da daliban da suke zangon karshe, duk cikin su an angagara wadda zai dauki jinin yaro, duk yabi ya tada musu hankali shi baza'a dauki jininsa ba, mum kice su tafi allura a hannunsu kuka yake yana maganar..... tazo wucewa Dr Hassan ya daka mata tsawa tare da kiranta, cikin hade rai yace inason ki debamin jinin yaronnan cikin harshen turanci, zuciyarta ke bugu domin tsoron kada ya dameta da yaren da bazata iya tsawaita magana ba. Ta dauki allura ta nufi gefen gadon ganin yana kuka yasa ta ajiye alluran, bayan sun gaisa da mamar tasa da dubi yaron tace sannu ya amsa da yauwa. Tashiga share mishi hawaye tace ya sunanka? Habib masha Allah suna mai dadi saitaga yayi murmushi, tace ina fata jiki da sauki yace eh, tace kana son zaman asibitinne? Yace aa inason tafiya gida. Dr dake tseye yana kallonta yace shine aikin da nasaki? Bata kulasaba taci gaba da cewa habib in kanaso ka tafi gida toh ya zamto..... tsawan da aka daka matane yasata mikewa cikin bacin rai, tafara magana cikin harshen hausa kai ka sani amma ai ina kanyi ne ko haka zanzo gun yaro in riko hannun shi yana fizgewa allaura ta karye ace ban iya aiki ba? In bazaka zubamin ido ba ga alluran wadda kasasu agaba su dauka. Ta mika masa allura, cikin fusata zayyi magana Dr Mubarak dake bayanshi yariko shi ya kalli haneefah yace kici gaba. Ta juyo kan habib tace tunda kanason komawa gida in anzo yi maka allura kada kayi kuka, kuma nasan kana da dauri ko ? Yace eh I'm strong like ninja, tace yauwa kuma zan sayo maka choculate muddin kamin alkawarin bazaka sake kuka ba cike da jin dadi yace toh, tace ka rufe idonka saika mikomin hannun ka bazaka ji zafi ba... haka ko yayi ta rinka lallashinsa baisan sanda aka dauka jinin ba, ji yayi tace bude idonka, yana budewa yace aunty babu zafi gobe kizo ki kara daukawa. Tayi masa murmushi tace toh. Dukkansu suka zuba mata ido, ta mikawa Dr ta juya gun mum din habib ta mika mata dari biyar tace kisiya masa choculate. Zata wuce Dr Hassan yace kina wani level? 200 cike da mamaki ke kallon sauran daliban nan ya soma surutu kan su aje hankali suyi karatu. Dr Mubarak yace kisame ni a office tace toh. Tun wuce warta ya zuba mata ido tabbas itace wacce jiya suka hadu a bank, yadda tashawa kan yaron cikin kankanin lokaci yafi birgeshi atake zuciyarsa ke raya masa wani abu da bazai iya fassarawa ba. Haka kawai yaji yana son yi mata magana. Sallama yayi gun mara lfiyr da yazo dubawa amma kash ya dubata ko ina bai ganta ba gashi gobe yake son komawa gurin aikinsa. Zaune kan kujerar shi ta same shi, ta gaishe shi ya amsa cikin fara'a tare da bata izinin zama. Yafara magana cike da damuwa zakiyi mamakin kirana sbd nasan baki taba ganina ba tace hakane, yace taimako zakimin a sannan ta dago ido tana kallonshi Allah sa zan iya ta amsa mishi, wato inada mata da yara biyu mace da namiji, ina matukar son matata domin auren soyayya mukai. Ina matukar son yara dayawa amma ta kafe biyu sun ishemu nayi nayi amma taki karshe tace cire mahaifa zatayi, inaso in rufa mana asirine bana son maganan yaje kunnen manya domin za'a iyace in qara aure ni kuma bana tsammanin zanso wata daban kamar yadda nakesonta yakarashe maganar kamar zayyi kuka. Cike da tausayi haneefah ke kallonsa, tace yanzu me kake so ayi? Gobe misalin karfe 9:30 kizo da ciwon ciki zamu karasa sauran insha Allah. *Dr HANEEFAH*👩🏼 6 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tare suke shigowa asibiti da hadiza daga restaurant karaf idanunta suka sauka kanshi, jingine yake jikin wata CRV 2015. Yayi bala'in kyau cikin manyan kaya, sannan ta kare mishi kallo, fari ne amma ba sosai ba, shiba dogo ba, ba gajere ba ba amma yadan fita tsayo. Idanunta suka dada hango kwantacciyar gashin kanshi kamar balarabe sannan sajenshi da ya matukar karbeshi. Kallo daya zaka mishi ka fahimci nutsuwa da kamala tattare dashi. Kallo shi take sai dai ta fahimci kamar wani yake nema domin idanun sa nakan mai fita da shigowa. Karaf suka hada ido ya sakar mata murmushi daya kara mishi kyau, gani tayi ya nufo inda suke ta kawar da idanunta akanshi. Sallama ya musu suka amsa, ya gaishe su hadiza kadai ta amsa. Kallonsa ya koma gun haneefah dake kallon wani guri daban yace sister nazo na dada baki hakuri domin naga baki amsa min ba. A hankali ta juyo suka hada ido tace ba komai, taja hannun hadiza suka soma tafiya yace in bazaki damu ba inason magana dake! Budar bakinta tace matar aure ce. Hadiza cike da mamaki ke kallonta harsuka wuce ward dinsu. Binsu yayi da kallo tare da tsananin mamaki. Ba matar aure bace take yabawa kansa amsa, amma me dalilinta nasarar dani? Bincike ya soma tunanin farawa sai dai jirgin yamma zai yau ya wuce gurin aikin sa. Murmushi yayi daya tuno inda zai samu information akanta, ya juya ya nufi motarsa. Dakatar da tafiyan hadiza tayi tare da jan hannunta suka koma kan wani benci suka zauna. Haneefah mesa kikace kina da aure? Banason dogon surutune yasa na katse zancen, aina kuka san juna? Nan ta labatar mata da abinda ya faru. Hadiza tayi murmushi tace in yazo da batun so fa? Haneefah cike da mamaki tace har tunanin haka kika? Hadiza tace babu yadda Allah baya hada bayinsa, mesa zai tako yazo domin amsa hakurinsa? Haneefah tayi murmushi tace da aminiyarta haba yar uwa, kallo daya zaki masa kinsan dan masu kudine, sannan yafini kyau nesa ba kusa ba kuma tabbas mazan yanzu sai wadda tafisu kyau taya tayaya kike tsammanin zai soni? Cike da mamaki hadiza tace ban taba tunanin kemai irin wannan tunanin bace, kinsan so saboda Allah baya duban ilmin mutum ko kudi ko kyawu? Abinda yake bukata shine kikasance mai gaskiya da rikon amana babu cuta babu cutarwa! Haneefah tace tabbas ina sane da hakan amma cike da murmushi, amma ina jiyewa kaina randa za, fada tarkon so sbd ban iya shiba. Hadiza tace in tambayeki mana? Ina mai sauraronki, shin wani irin miji kike burin aura? Lumshe idanunta tayi tare da soma magana ina son namiji wadda yasan darajar dan adam, wadda ya wadatu da ilmin addini wato mai tsananin tsoron Allah, wadda duniya bata gabansa wadda zai soni tsakani da Allah ya nunamin tsantsar kauna da kulawa, wadda annabinmu Muhammad (S.A.W) ya kwadaitar damu mu aura, wadda..... hadiza tayi saurin dakatar da ita tace ai kin gama komai insha Allah kin samu, kijira lokaci amma kada ki manta duk mabukaci baya bacci ki dage da tsayuwar dare, ta murmusa tace insha Allah. **** **** **** **** Washe gari misalin karfe 9:30 yasameta a kofar Dr Mubarak, idonta cike da hawaye ta turo kofar yashiga. Zaune suke suna fuskantar juna, hade rai yayi ya dago fuska yace waya baki izinin shiga? A sannan haneefah ta fashe da kuka tana cewa cikina cikin tsawa yace fita? A hankali kyakykyawar matarshi wadda fuskarta alamar tausayi tace haba Dr, ka dubata mana shine zata shigo babu excuse? Ganin bata ce komai ba kuma kar planning nasu ya rushe yace ga guri zauna, wani irin ciwon ciki? Tace nidai tun da dare nake fama amma yanzu ya tsananta, yace in period naki zaizo wani irin alama kike? Yana ciwo amma ba ko wanni lokaci ba, ok. Yace yaushe ne next zuwan shi? Ina kanyi... a matsayinki na student of health bazaki iya banbanta menstrual pain ba? Haneefah ta sunkuyar da kai, ki tashi kibani wuri. Ta dago tace, Dr ina banbantawa, babban burina shine inyi aure in hayayyafa, shine nake tsoron duk wata ciwon ciki domin kada ya tabamin mahaifa. Cike da mamaki matar Dr ke kallon haneefah, Dr yace shekarunki nawa? 19 tabashi amsa ya juya gun matarsa yace kindai ji abinda take cewa, yarinya karama tun kafin tayi aure take tunanin future ta, amma ke kokarin cire mahaifa kike. Zuro ido tayi ta fuskanci inda take kallo tare da cewa aunt gun Dr kika zo domin a cire miki? Mesa? Tana so tayi magana haneefah ta katseta ta hanyar cewa baki da wata hujja nayin hakan. Ko kinsan cewa babu wadda ya isa yayiwa wani kyautar da ko ya inba mahaliccin muba? Kina da tabbacin za'a maida miki mahaifane? Duk yawan yaranki kinsan zasu dauwama tare dakene? Yau Allah ya baki daman da mutane da dama suka rasa amma zaki nemi rasashi da sanin ki da wayonki? Akwai mata da dama da suke tunanin yawan haihuwa na tsufar da mutum da wuri, abin ba haka bane. Kiyiwa mijinki kwalliya in yaran kikarasa su kiyi meh? Kina takamar mijinki na sonki? Hmm kallesu da ido kawai, yaranki sune rayuwarki, Kisani cewa duk sonda mijinki ke miki muddin kika rasa yara zai iya rage sonki ya auro wadda zata hayayyafa mishi kuma ta mamaye masa zuciya a barki da kunar zuciya, sannan yan uwanshi su gujeki. Wasuma tsabar rashin tausayi jarirai suke hadawa da fida saboda basaso nonuwansu su zube, namijin banza, kinsan sinadarai da suke dauke da nono kuwa? Abincin yaro kuma lafiyar yaro. Nidai shawarata kada ki soma domin dana sani na gab da zuwa miki, mahaifarki itace abin alfaharinki a gidan miji, kada kibiyewa kawaye domin wasun tsantsar muguntane a zukatansu. Ki zauna da mijinki lfy kada aji kanku inma bai sani ba kada ki fada mishi, in kika fita bakisan gidan wa zakiba, kimin afuwa in maganganuna sun bata miki rai. Dago kanta tayi hawaye na tsiyaya a kuncinta tace, ya sunanki, haneefah. Ta kama hannunta gam ta rike tace hakika nayi nakusa fadawa rami mai zurfi wadda babu wadda ya isa fiddoni, sai gaki bansanki ako inaba kinzo kin haskamin gabana nagane ramine. Dayawa muna cutar da kanmu, yarana biyu, na manta akwai rashi. Sai yanzu kika tunomin, bansan da wani irin baki zan gode miki ba. Murmushi haneefah tayi tace ba komai Allah shige mana gaba a al'amuranmu. Dr Mubarak bai tabajin cewa akwai yara masu baiwa masu ilmin addini da kaifin hankali irin haneefah ba. Ya kalli matarsa yace kin janye? Tace eh najanye sannan ina neman afuwanka, kai hakuri ka yafemin. Haneefah tace zan wuce a sanyaye. Matar Dr tace pls inaso in kulla zumunci dake, murmushi haneefah tayi tace toh. Matar tace sunana Barrister Ramlat ga lambata. Haneefah ta karba ta fice ta barsu. *Dr HANEEFAH*👩🏼 7 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Ward nasu ta wuce ta duba abinda zata duba ta wuce ward dinsu hadiza. Agajiye ta shigo gida domin tasha aiki a labour ward, ta tarar da nana a sakar gida zata shiga falon abbansu. Nana ta nufota tace wadda suka taba aiki da abba yakawo ziyara kije ki canza kayanki ku gaisa. Cikin ladabi suka gaidashi ya amsa yace masha Allah ya karatu? Haneefah tace Alhamdulillah nana tagama nice da saura haryanzu. Cike da murmushi abokin abban nasu yace toh Allah bada sa'a, tare suka ce amin gaba da mikewa suka shiga ciki. Alhaji mudassir ya dubi abokinsa Alhaji hamisu bayan fitarsu yace masha Allah, nana tagama makaranta aiki take ko takusa aure? Abba yace babu ko daya jiran admission take amma har yanzu shiru. Cike da mamaki Alhaji mudassir ya dube shi yace irin matsayina a garinnan amma yaranka su nema admission har so biyu? Abba yace ai komai da lokacinsa, bazayyu in rika daurawa wasu nawi ba. Wannan shine zumunci? Nasan abinda kake gudu amma kasani bana daya daga cikin mutanennan. Metake so ta karanta? MBBS. In bazaka damuba ka kawo requirment dinta saura dalibai biyar yarage na wannan fannin wadda zasu kasan Egypt (scholarship)sai insa hannu su tafi. Abba yace har Egypt? Abokin nasa yace tunda tayi niyya kada kahanata tunda ta samu wannan damar, sannan binta zakai da kyakykyawar addu'a. Abba ya numfasa yace to shikenan, nayarda da tarbiyyarta ,nagode kwarai da gaske. Magana yaje kunnen su haneefah sai murna ake. Umma ko ranta bai so ba, tafison yaran suyi aure amma dai batai shishshigi lamarin ubangiji ba, addu'a tayi maata na samun nasara. **** **** **** **** Zaune yake ya kurawa files din gabanshi ido, ya kasa aiwata komai sai tunanin wannan yarinyar yake. Runtsa idanunsa yayi a hankali ya bude. Kwanan sa biyar kenan yana abu daya wadda ya kasa tantance meye. A hankali ya dauko wayarsa da ke kan table dinsa ya fara dialing no. accounter, ajiyar zuciya yayi jin layin a kunne ana dagawa yace haba accountr tun yaushe nake kiran layinka? Daga daya bangaren aka amsa, am sorry, wlh wayanne ya fadi naje nayo welcome back, toh bai fara aiki ba sai yau kuma ban gane mai magana na. yace ba komai, engineer yusuf ne. Allah sarki ina fata kana lfy? Alhamdulillah amma wata alfarma nake so kamin, accountr yace ina jinka. Kwanaki nazo bank naku, sai na hadu da wata yarinya taje bude account domin naga form a hannunta, abinda nake so shine informations nake so akanta like her phone number & address. Accounter yayi dariya yace toh yanzu inba kaiba, ai customominmu suna dayawa, yusuf yace abinda nake nufi shine zaka turomin hotunan duka customomin ta WhatsApp saina zani wadda nake neman pls yanzu aboki, yace badamuwa ya bukaci date, sallama kan zai masa text. Cikin qanqanin lokaci yaga sako dauke da abinda ya bukata. A hankali har idanunsa suka sauka a kanta. Babu bata lokaci ya qara turawa accountr wadda yake nema. Take ya kuma aiko mishi da abinda yake bukata. Da daddare misalin karfe 9 suna zaune da nana ana hiran yadda tafiyan zai kasance taji wayanta na qara. Ganin babu suna ta katse ya kuma kira ta dauka tare da yin shiru jin mai maganan. Amincin Allah ya tabbata gareki taji ance, cike da mamaki ta amsa wadda ke magana amma bata nuna ba, yace kin gane wadda ke magana? Aa tabashi amsa. Yace wadda kika hadu dashi a bank last wk, tace ok lfy? Kuma aina ka samo lambata? Murmushi yayi kamar tana gabansa yace hakuri zan dada baki da....... tun kafin ya qarasa ta katseshi tace nagode. Kiransane ya qara shigowa tadaga yace pls kada ki katse aiko yana fada ta qara kasewa. Dafe kansa yayi, ya zanyi? Kodai matar aure ce da gaske? Aa yabawa kansa amsa. Jawo wayarsa yayi ya shiga WhatsApp. Farin ciki yayi ganin tanayi, bai dauki lokaci ba yayi mata sallama tare da rokanta kada tayi blocking nashi. Kamar jira take sai gata online taga sako. Murmushi tayi tace bazanyi ba, amma narokeka karabu dani. Yace ba cutar dake zanyi ba, Allah nasane. Toh me kake so aguna? Nace na hakura! Yace in bazaki damu ba inaso muzama frnds. Tace duk abokanen ka maza basu ishekaba saika hada dani? Kuma ai babu tsari yaza'ai ina matsayin mace zakai abota dani? In matarka ta sanifa, nidai baruwana bazanyi abinda nima banaso amin ba. Banida aure kuma yabata amsa, Allah kawo tagari da zuri'a nagari cike da jin dadin addu'a yace ameen. Nan takashe wayan gaba daya don ji take wani irin abu daban tada kasa fassarashi tunda suka soma magana. Washe gari ko kunna wayan batayi ba haka ta fita zuwa asibiti. Ward dinsu aminiyarta ta nufa ta jawota gefe hadiza tace yau kuma wani lbr muka samu mai dadi. Nan haneefah ta labartar mata da komai. Hadiza tace nina sanki nasan halinki tunda muka taso bamu taba abota ko da class mate ba, abinda nake so ki fahimta shine bakisan Allah ya turoshi ya zamto silar wani abu bane. Ki karbeshi da zuciya daya, kada kiyi tunanin mugun nufi sannan ki tuna hadisi na ashirin da takwas An ruwaito daga Abdullahi bn Umar -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Muminin da ke shiga cikin mutane, ya ke kuma hakuri kan cutarwarsu ya fi girman lada akan muminin da baya hulda da mutane, kuma baya hakuri da cutarwarsu*. *Dr HANEEFAH* 👩🏼8 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Haneefah ta numfasa tace maganarki hakane, amma inya wuce gona da iri wlh zanyi maganin shi. Murmushi hadiza tayi tace ji nake ajikina alkhairi ne agareki, ta qara da cewa nextwk usman manyansa zasu zo asa ranar aure. Haneefah dake kokarin kunnan wayarta ta daka tsalle ta rungumeta tare da tsananin farin ciki tace nayata ki murna Allah sanya alkhairi yasa gidan kine har abada tace ameen kema Allah kawo nan bada jimawa ba kafin ta bata amsa wayanta ya soma ringing Ganin lambar jiya yasa ta dauka tare da sallama amsawa yayi ya gaisheta. Murmushi tayi tace ai kaine babba nice da gaisuwa, farin cikine ya lullubeshi jin yasamu karbuwa. Bayan sun gaisa take tambayarsa yadda yasamu lambarta, bai boye mata komai ba ya sanar da ita. Ita kanta tayi tunanin haka. Tace tana asibiti sukai sallama Bayan ta koma gida da dare sukai waya tare da sanin junan su atakaice. Ba laifi ta sake jiki dashi domin ta dauki shawarar kawar tata. Cikin sati biyu suka gama fahimtar junansu baki daya, domin ya tashi daga aboki zuwa yayanta. Sannu a hankali shakuwa ke dada shiga tsakaninsu. Shidai yusuf ya tabbatar son haneefah yake domin irin matar da yake so ne. Yasha alwashin saiya koyawa haneefah soyayyar shi. A sannan haneefah ta gane wanene yusuf, mutum ne mai hankali wadda yasan darajar dan adam, wadda yake da ilmin addini sosai sannan mai aiki dashi. Zuciyartane ya fara saka mata abubuwa da dama kanshi amma tafi fassarashi da shakuwace. ***** ***** ***** ****** Gab suke da zana jarabawar tsallakewa shekarar gamawa. Ansa ranar bikin hadiza wata biyu masu zuwa. Tun a sannan haneefah ta fara shiri domin tana matukar ji da kawar tata. Shirye shiryen tafiya haneefah take yiwa yayar tata. Sunje dangi da abokan arziki sunyi musu sallama, kowa na yiwa nana fatan alkhairi domin yarince mai nutsuwa kowa na alfahari da umma da yaranta, domin kyakykyawar zuciyarta da hakurinta. Zauna suke su biyar ranar alhamis daidai yake da washe garin juma'ar zasu wuce abuja domin can jirginsu nana zai tashi sannan haneefah kadai zata rakata. Nana ta kalli kannenta sosai tace nidai zan tafi kamar yadda na sanku ku dada hada kanku, kunga yadda su inna sukai baqin cikin tafiyana amma Allah ya kaddara saina tafi harda ta kaiga suna yadawa a anguwa abba yaki aurar damu sai boko. Abinda nake so da ku shine ku toshe kunnuwanku akan dukkanin abinda zaije ya dawo. Nasanke haneefah kina da karancin hakuri, kidaina biye musu wata rana sai lbr. Sannan ku maida hankalinku sosai gun karatu domin cimma burin mahaifan mu. Ahmad ka kara hakuri insha Allah zaka samu admission duk da abba yana da hanyar samuwa mutanen duniyar nan sai a hankali, domin shi yana da gaskiya Idan kana so gaskiya ta yi saukin fadi a harshenka, kuma mutane su kiyaye ka, to ka nisanci kwadayi kuma kar ka ji tsoron kowa sai Allah, in lokaci yayi zaka samu. Sannan ke haneefah kema ki dage da karatu kinyi nisa a health babu zancen accounting sannan ki dada hakuri akan hadaki da abba da suke a hankali zai gama sanin komai kudai ku zuba musu ido, babu maida martani. Nasiha sosai yayarsu ta musu sannan ta bukaci shiga suyiwa su inna sallama. Abban su dake bakin koma yazo shiga yayi saurin barin gurin. Bangarenshi ya nufa yayi alwala tare da godewa Allah daya bashi zuri'a masu albarka. Suna shiga suka tarar da zuwaira bakin kofar suka gaisheta suka wuce. Gaida inna sukai sannan suka samu guri suka zauna. Nana ce ta fara magana tace dama nazo in muku sallama ne. Inna ta dubesu a wulakance tace naji gobe zaki tafi, Allah kiyaye hanye, haneefah gudun kada wani magana ta taso taja hannun nana zasu fice taji ance sai kiyi abinda ya kaiki domin kada a zo mana da jikan da zamu nema uba mu rasa cewar zuwaira, inna ta karba tace gaskiya kam sbd muna furci suka mallake shi suka kwashe kudin zasu qasan waje su cinye. Jabir da ya salim daya shigo yace munafukai wlh sai Allah ya saka mana ku da matsiyaciyar uwarku. Saukan mari yaji ras a fuskar sa, cike da mamaki ya bude baki yake kallon ta, suma duk suka taso cike da mamaki ganin wadda yayi mari *Dr HANEEFAH*👩🏼10 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Kawar da kanda zatayi tagan shi ya nufosu. Yayi matukar kyau cikin kananan kaya. Kallon shi take harya iso cike da murmushi zatayi magana yace waye wannan? Kanin auntynane. Shine kika tsaya akan layi da mutum. Shigo ganin anzo an tsare ta da tambaya yace mallam lafiya? Yusuf ya juyo cike da bacin rai yace kada ka sake furta mata wata kalma, ya juyo kanta biyoni. Itako cike da mamakin abinda yayi take bin bayansa har suka iso inda motarsa take. Yadan jingine tare da dubata yace yaushe kika shigo shine ko waya bazaki mun ba? Dariya tayi tace yau nazo kuma gobe zan koma, na rako nana ne zata fita karatu, shine bazaki fadamin ba sai dai inji kinzo kin tafi. Tadanyi murmushi ta juya zata koma gun yan uwanta taga suna nufota. Duk da ya girmesu yadan risina ya gaishesu suka amsa. Yace in bazaku damu ba zan kaiku inda kuke muradi? Aunty tace aa gida zamu koma babu nisa. Duk da haka saida yace zai kaisu. Yayi parking suka sauka yace aunty anjima zan iya zuwa. Tace Allah kaimu. Haneefah zata fita yace minti daya, ta juyo suka hada ido taji wani irin shock take ta sunkuyar da kanta. Yace na katse miki hira da saurayinki shine kike fishi? Allah baki hakuri. Ta juyo tace ba komai ta fice ta barshi. Karfe takwas ya same shi a gidan yayi sallama ya shiga. Zaune ya tadda auwal a parlour, suka gaisa. Ya mishi bayanin gurin haneefah yazo. Ya shiga yakirata. Sanye take da himar har kasa ta zauna mesa dashi ta gaishe shi kanta a sunkuye domin tsoron hada ido take dashi yadda nan take takejin wani iri. Nazarinta yayi sosai sannan yace haneefah in tambayeki? Ina mai sauraronka. Shin kin yadda dani? Kai tsaye tace eh. Mesa ya qara jefo mata tambaya? Sbd ka kasance mutum nagari. Shiru yayi yakasa ce komai. Inaso in sanar dake ko ni wanene. Tace ina sauraron ka; Kamar yadda na sanar dake sunana yusuf. Haifaffen garin kano ne ni, anan nayi dukkanin karatuna nakaranta computer engineering. Bayan na kammala nayi masters dina sannan nasamu aiki a garin kano. Daga baya ne akamin transfer zuwa nan. Mahaifina Alhaji ismail da da mahaifiyata Hajiya hauwa wadda muke kira momy. Mahaifina dan kasuwa ne babban sannan mahaifiyata lecturer ce a university. Hausa fulani ni ne, mahaifina mutumin kano, mahaifiyata daga adamawa suke. Nine first born gidanmu, sai kanne na salma, aisha da autanmu alkali. Salma tana da aure da yaronta daya sannan ma'aikaciyace a PHC agency dake kano. Ita ko aisha na university 200lvl autanmu kuma yana jss3. Cike muke da kaunar junanmu, iyayenmu sun wadatamu da kyakykyawar tarbiyya. Amma nafison aisha cikinsu. Ya mika mishi wayarsa dauke da family picture. Haneefah takurawa hoton ido, suna da matukar kyau. Dukkaninsu fararene sannan kyakykawan jikansu na kwance jikin kakanshi. Idonta ya fada kan aisha taji tana sonta. Batasan sanda ta soma addu'an Allah ya bata ikon shiga cikin suba. Tace masha Allah, Allah dada kawunanku, ya albarkaci zuri'arku. Cike dajin dadi yace ameen. Ya saci kallonta yace sannan abu daya. Mahaifiyata naji da kanwarta umma nusaiba. Ita umma nusaiba yarta daya ne. Wadda mahaifiyata ke shirin hadani da ita aure. A sannan haneefah ta dago ido suka hada ido, taji wani irin faduwar gaba da bazata iya fassarashi da menene ba. Ganin yana kallonta ta sakar mishi murmushi ta hadiye hawayen da ke shirin zubomata tace Allah sanya alkhairi yaba ku zaman lfy. A sanyaye yace ameen. Amma haneefah bana son aure, kusan shekara biyar amma sai dauko min da maganar ake. Cike da mamaki take kallon sa tare da cewa zabin mahaifiyar taka? Nayi nayi in saba da sonta amma nakasa, nayi musu bayani amma sun kasa ganeni aisha ce kadai ke tausayamin, amma tace dani zan auri zabina amma itama in auri zabinta. Kabsha!!! Da yana ganin zuciyar haneefah ko zancen bai dauko mata ba. Hamman karya ta kirkiro tare da mitstsike ido alamar bacci. Tace in zaka dauki shawarata ka aureta saboda babu wadda takai mahaifiya. Ce mata zayyi ina sonki amma ya gagareshi. Sallama sukai akan gobe zaizo su koma kano tare. Tadai amince amma tayi hakanne domin ya tafi. Ban daki ta wuce ta ta zauna bakin bafon wanka, hawaye taji yana tsiyaya a kumatun ta. Ji take kamar ta kurma ihu. Toshe bakinta tayi ta soma kuka mai tsuma zuciya. Shin kishi take? Hakan na nufin tanason yusuf? Innalillahi tashiga furtawa a zuciyrta. Abinda nake gudu kenan yanzu ya zanyi? Addu'a ta bawa kanta amsa. Take ta dauro alwala ta fito domin kai kukanta ga mahaliccinta tun kafin abin yayi tsanani. Bayan ta idar da raka'o inta ta zauna yin addu'a. Bayan ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye. Meyasa baya iya furta mata yana son ta? Yanzu in wani ya rigaka fa? Iya saninta da yayi basu tana hiran wani ba. Dauko wayansa yayi yashiga kiranta. Zaune take tana addu'a taji kiran wayarsa busy ta danna masa. A naga bangaren kuma kodai tana wani abinne? Jiran kiranta yake amma ya ji shiru. Itako ta kasa rintsawa sai faman tunani take tare tsare kanta da tambayoyi yaushe ta fara sonsa?? Mesa take bata lokacinta? Kusan idanunsu biyu. Ta gama yanke shawarar rabuwa dashi tunda ba sonta yake ba. Shima ya dauki alkawarin zuwa gobe zai sanar da ita zabinsa. *Dr HANEEFAH* 👩🏼9 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Haneefah idonta dake cike da hawayen bacin rai ta nuna shi da dan yatsa tace duk zagin da zaka mana zan lamunta amma kada ka kuskura ka sa mahaifiyata ciki, kai har kana da bakin da zaka ce da munata TSIYA? Gaku matsiyata, duk girman da muka baku bakwa gani? Meza mu muku mu burgeku? Muda kake gani ka cire idanu a kanmu domin Allah na tare damu. Gwamma ka fuskanci rayuwa na kwarai kaji dadin duniya da lahira, Idan kana so ka zauna lafiya: Ka bar kallon rayuwar wasu, ka kalli taka kawai ka bar duba mai wane yake da shi, ka kalli abun da kai kake da shi ka wadata da shi, ka bar kokarin sai ka zama abun da wane ya zama, in ba ka tsaya a in da Allah ya ajiye ka ba to ka hadu da wahala ta har mutuwa sannan duk abun da kake nema, ka nema a wajen Allah, ka bar tunanin Mutum zai maka, ko da a ce ya shigo rayuwarka a matsayin sila, wata rana zai iya goranta maka. Kai namijine ka tsaya ka nemawa yaranka ilmi sannan ka datar da rayuwarka da tsoron Allah. Tana kaiwa nan zata juya ta fita ya fizgota zai wanka mata mari yaji an sake marin nasa. Abba suka gani tsaye cikin bacin rai, ya kalli inna da yaranta yace nagode miki ya juya yafice tare da su haneefah. Zaune take zuciyarta na mata kuna, jawo wayanta tayi ta kira yusuf. Sallama yayi ta amsa suka gaisa suka somo hira ko zata dan mance bacin rai, yace meke damunki cike da mamaki tace me kagani? Ji nayi a muryarki. Murmushi tayi tace babu komai. Yace bazan matsa miki ki fada min ba amma ki sani in kakasance cikin bacin rai ko farin ciki dole akwai wadda zaka ware ka fada mishi duniyarnan, nayi zaton tuni na tashi matsayin aboki na koma yayanki, amma bansan ko kina shakkata bane. Haneefah tace ko daya kawai dai banajin dadine, zazzabi ke damunki? Aa yace toh tashi masha ki dauro alwala ki fara karatun Qur'ani har bacci ya daukeki. Cike da murmushi ta amsa ta katse wayan. Yusuf na matukar birgeta musamman in suna hira sayya sako mata batun addini, tana matukar jin dadin hakan. Washe gari misalin karfe goma suka dau hanya kan zasu sauka gidan auwal (yaron mama) domin ya koma can da zama. Nana na ta kuka har suka iso birnin tarayya. Sun sami kyakykyawan tarba. Da misalin karfe 5 na yamma haneefah tace da matar auwal tana son sudan fito su zaga anguwa. Sanye take da dogiwar riga abaya, tadan shafe bakinta da jan baki, sannan tayi rolling dankwalin abaya da dan takamin ta mai tudu. Tayi matukar kyau sosai. Tafe suke suna hiran manyan gidajen abuja kamar ba Nigeria ba. Cike da mamaki yake kallonta har suka zo suka wuce. Suko basu lurama da ana kallonsu ba. Tafiya suke sai matar auwal taga kanin kawarta yayi parking ya fito suna gaisawa. Ya dubi haneefah dake kallon wani gida yace kannen kine? Tace aa cousins nashi ne. Yace Allah sarki aunty banyi hanzari ba zaki aramin wannan minti biyu ya nuna haneefah tayi dariya tace bismillah. Suka danyi nesa dasu. Kafin ya soma magana tace haba mallam ya zaka ce abaka aroma sai kace kaya tana magana tana hade girar sama da kasa. Dariya sosai ta basa yana dariya. Yusuf dake cikin mota yaji wani irin abu ya tokare masa wuya. Me tace dashi har yake mata irin wannan dariya? Cike da bacin rai ya bude motan ya fito ya nufufi gunsu. *Dr HANEEFAH* 👩🏼11 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Washe gari misalin karfe takwas da rabi yasamesu a airport sbd karfe tara dai dai zirginsu nana zai tashi. Nana kuka take na barin gida, ita ko haneefah kukan rabuwa da yar uwarta take da soyayyar da yayi mata ba zata. Sanda akai kiransu kamar sun rabu kenan take kuka. Suna ji suna gani suka rabu. Tunda tazo gida takasacin komai inbanda shayi. Auwal yayi fadan harya gaji. Zaune take duk tabi ta dami kanta tsakanin jiya da yau. Ta kammala shirinta ta tuno da maganar yusuf inda yake cewa; Duk lokacin da kake so ka zama cikin mutanen da suka rabauta, to ka kiyaye abubuwa kamar haka: *_Kar ka takurawa kanka akan wani abu da bai iso gare ka ba_* *_Kar ka damu da me zai faru gobe?, domin idan ka inganta yau dinka, to gobenka ma za ta yi kyau_* *_Ka tsarkake zuciyarka daga hassada, mugunta da kyeta_*. Goge kwallar da suka zubo mata tayi. Mesa zan dami kaina? Nan take ta fara addu'a Allah bata ikon fin karfin zuciyarta. Tagama shirinta tsaf ta fito. Ta ganshi zaune a parlour shida auwal. Bude baki zatayi magana auwal yace gata ta fito, yanzu nake shirin shiga in kiraki, kin gama zaku wuce ko? Rasa abin fada tayi. Shiko ganin idonta a kumbure alamun tayi kuka sosai sai hankalinsa yadan tashi. Cikin sauri ya tashi ya mikawa auwal hannu yace kada mu makara zamu wuce. Sukai sallama. Tuki yake amma hankalinsa baki daya na kanta. Ita ko tunda ta shiga ko kallon inda yake batayi ba. Ina kwana yace da ita tace lfy atakaice. Tabbas akwai wani abu domin tunda yake da ita bata taba amsar gaisuwan shiba sai dai ta kara gaishe shi. A sanyaye yace jiya nakira amma baki samu daga waba. Tace eh wani abin nake. Tambayanki nakeson yi. Kina da ra'ayin auren mai mata? Lumshe ido tayi sannan tadan kishin gidu tace meye aibunsa in har yana tattare da abubuwan da annabi ya kwadaitar mu auren irinsu? Wasu matan suna wahalar da kawunansu wajen zaban miji, suna ganin aure shine jin dadin rayuwa. Duk macen da fassara aure haka ko shakka babu cikin wahala zata kasance... mika al'amura ga Allah yafi komai. Murmushin jin dadi yayi yace zaki aure ni? Dariya tambayar ta bata tace auren irinku sai mata masu ilmi da class kyawawa irinku ta karashe maganan da zolaya. Yace bakisan irinku kunfi tsada ba? Ga namiji wadda yasan me yakeyi baya bukatar komai gun mace sai kyawun tarbiyyarta. Murmushi tayi ta rufe idanunta sannan tace aikai ka samu. Mu kabari a baya. Dadin hira take ji dashi, haka shima. Cikin yar tafiyannan sun dada fahimtar juna, kusan ra'ayinsu daya. Sun shigo garin kano tace ya sauketa ta karasa gida yace kiyi hkr in kaiki. Ba yadda ta iya haka ta hakura tafada mishi anguwan nasu. Dab zasu shigo layinsu tace saukeni anan. Ya dubeta inane gidan? Tace nidai bazan qarasa dakai kofar gida ba. Parking ya gyara sannan ya dubeta yace haneefah kalleni. Dagowanta suka hada ido yace ina sonki haneefah, so na hakika. Batace komai ba sai hawayen da ta soma zubarta. Motan ta bude ta fito ta dauki kayanta sannan tayi wucewarta. Kwala mata kira yayi amma kamar bada ita yake ba. Jan motarsa yayi yadau hanyar gidansu. *Dr HANEEFAH* 👩🏼12 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 A hankali ya bude motar ya fito. Ganin motar abban nasa yasa ya nufi bangaren shi. Zaune suke suna tattaunawa ganin dansu yasa suka dakata tare dayin murmushi. Sallama yayi suka amsa. Cike da nutsuwa yake gaida iyayen nasa. Abban nasa yace ko sanarwa babu. Murmushi yayi ya sunkuyiyar da kansa sbd. Momy tace tashi kaje ka huta zansa aisha ta kawo maka abinci, yace toh ya mike ya fice. Sallama tayi ta tura kofar, kwance ta taddashi sanye da jallabiya. A hankali ya bude idanunsa yace sannu aisha. A ajiye tiren hannun nata ta fara zuba masa abinci ta soma gaidashi, cike da kulawa yake amsawa. Ta mika masa ya fara ci suna hira irinta wa da qanwa. Bayan ya kammala ta kalleshi sosai ta fara magana, yaya yanzu bazakai wani abu game da auren ka da Rahma ba? Wlh bata dace da kaiba. Yarinya an sangartata bata da nutsuwa ba tarbiyyar kirki ba? Murmushin takaici yayi yana kallon kanwarsa dake matukar tausaya masa yaace toh ya zanyi? Babban sirrin zaman rayuwa da jin dadin gobe kiyama ya tabbata ga mutumin da shine wadda yake yiwa mahaifiyarsa biyayya, nabi ko wace irin hanya domin in kawar da zancen auren amma maganar har yanzu tananan. Allah na mikawa lamurana ya dubamin yabani ikon rabuwa da ita lfy. Na danne zuciyata zan auri zabinta tunda itama zata barni in auri zabina. Cike da tausayawa aisha tace Allah tabbatar da abinda yafi alkhairi agaremu yace ameen. Bayan fitar ta ya kawo waya domin kiran haneefah domin muryarta kadai yake sonji amma yaji wayar a kashe take. Tafe take tana sharar hawaye. A hanya suka hadu da ahmad tayi saurin goge hawaye yace kukanne har yanzu baki daina ba? Girma yazo miki gomma kin hakura. Murmushi tayi domin ita kadai tasan abinda ke damunta. Tarar da umma da kannenta tayi suna kallo, suka mata sannu da zuwa. Tadan taba hira sannan ta wuce dakinsu. Kwance take tana tunanin kalmar yusuf. Ya cancanci a soshi amma yaushe ne auren sa da zabin mahaifiyarsa? Mafita dayane matakin da na dauka yayi. Hira suke amma hankalinta nakan yusuf. Shi take gani tunaninsa ya hanata sakat. Mikewa tayi ta musu saida safe ta nufi dakinsu. Tagama shirinta tsaf ta hau kan gado a sannan taji kewar yayarta sosai tace Allah sarki nana da kinanan hiran kafin mu kwantama daban. A hankali ta bude wayarta. Babu wani tunani takirashi. A hankali yake magana cike da ladabi momy baqin maganarki nake ba. Kimin uzuri ayyukane suka shigemin gaba. Tace yusuf hakurin mu yakare shekaru biyar ba wasa bane, yarinya kowa ya fito tace kai take jira to wannan karan ya zamo maka dole ka aureta ko in hanaka auren zabin taka tunda yan matanne ke naka wasa da hankali. Cikin sauri ya dago kai yace aa momy baza ai haka ba, na miki alkawari zuwana nagaba sai afara shirin bikin. Badan taso ba tace Allah kaimu. Yana shiga dakinsa yaji wayansa na ringing, daga wanda zayyi yaga sunanta cikin sauri ya daga tare da yin sallama. Amsa sallamar tayi daganan bata karace komai ba, katse wayar yayi ya sake kiranta. Tace ya gajiya, Alhamdulillah ya amsa. Shiru kamar dakiku biyar tafara magana yusuf nagode da kasancewar cikin rayuwata sannan nagode kwarai da gudunmawarka kan cigaban addinina amma kasani bazan iyaci gaba da zama dakai ba... shakuwar inta yawaita zan kasance cikin tsananin damuwa, kai kuma aure zakayi kaga ko gonda na hakura kaje ka auri zabin mahaifiyarka. Ajiyar ziciya yayi yace haneefah pls kece zabina, kada kisa wannan ya zamo hujjar rabuwarmu, ina sonki so na hakika, ina kwadaitar wa zuri'ata samunki a matsayin uwa, sannan suruka wajen iyayena. Nasanki na yarda da tarbiyyarki. Jin yayi shiru tace hakane amma ina gudun bacin raine, iyayena da yan uwana suna sona nima ina sonsu, bakin cikinsu nawane musamman mahaifiyata, ina tsoron kada wani abu yaje ya dawo. Murmushi yayi yace haba haneefah? Duk wanda ya ji tsoro zai samu damuwa a zuciyarsa, amma ban da wanda ya ji tsoron Allah. Shi kam wanda ya ji tsoron Allah zai samu aminci da kwanciyar hankali a zuciyarsa... addu'a makamin mumini ce ... Don haka muyi riqo da addu'a kuma mu dogara da Allah ko yaushe komai zaizo mana da sauki, nidai pls amincewar ki nake bukata. Gaba ki daya ya gama daureta. Itadai tana son shi amma kamar tana hango akwai matsala.... sannan yayi gaskiya duk zuciyar da tayi riko da Allah to tabbas babu wani sauran damuwa da zai dameshi. Jin tayi shiru yace momy ta bani daman auran wadda nake so, ko bakya tunanin zanyi adalci tsakanin? Murmushi tayi tace kai mutum ne da zaka zaunar da wasu ka musu nasiha kan suyi adalci tsakaninsu, ina da tabbacin kai adaline. Murmushin jin dadi yayi yace godiya nake. Taci gaba da cewa zan kasance tare dakai, sannan na baka amanar rayuwata baki daya, yadda ka tarbiyyantar da ni matsayin masoyiyarka haka zan kasance. Cike dajin dadi yace kin amince kina so na kuma zaki aure ni?? Tace eh na amince Allah tabbatar mana abinda yafi alkhairi kuma in hakan ta faru pls I banason zama gida daya tare da ita in zayyu. Cike dajin dadi yace ameen, nayi alkawarin rikeki amana sannan zanyi haka da yardan Allah. Nan suka soma hira tamkar sun jima suna tare. ***** ****** ****** ****** Cike da takaici tayi wulli da wayar dai-dai inda mum tata tashigo. Cike da damuwa ta qaraso ganin yartata kamar wani abu na damunta. Baby rahma waya tabamin ki cikin kuka tace mum tun dazu nake nemanshi amma number busy ko da wa yake waya, wlh mum kiyi wani abu hakurina ya kare kibarni kawai in auri wani. Haba rahma saida aski yazo gaban goshi? Mum baya so na, masu kudi da dama sun nuna suna so na do ki bari ince wani ya fito ni wlh nadai na sonshi, cikin cigar lallashi tacewa yar tata aurenma ai kowanne ba iri daya bane, dan uwan naki na da kudi kuma harkanshi bunqasa yake.. zaki fi jin dadi zamanki acan, in kukai aure kika haifo na miji saiki fito ki auri wadda kike so in kinyi hakan kin gama min komai. Cike da kauna ta riko hannun mahaifiyar tata tace mum na miki alkawari aikata abinda zai saki farin ciki, amma ki gaggauta aikata hakan. Mum tace to shikenan in watannan ya kare da kaina zanje kano sai ansa ranar aurenku zan dawo. *Dr HANEEFAH* 👩🏼13 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Zaune suke ita da hadiza cikin makaranta kasancewar zasu fara zana zarabawar sati mai zuwa, sunzo duba time table. Hadiza tayi murna jin maganar kawartata sosai tayi mata fatan alkhairi. Suna cikin magana taji wayarta na ringing, cike da murmushi ta daga tare da yin sallama, shima murmushi ya saki suka gaisa yace ina cikin asibiti. Haneefah tace mun koma makaranta yace ok ina zuwa. Kawarsu suka hango ta inda suke zaune mai suna sadiya. Tayi sallama ta zauna ta ciro powder ta fara. Haneefah data kasa hakuri tace sadiya ina zaki haka da safe kina kwalliya? Wlh wani saurayinane zaizo shine nake dan shafe shafe domin nayi haske a idonsa, kinsan mazan yanzu in baka kwalliya ko na soyayya bazaka samu ba bale na aure. Sama har kasa haneefah ta ke kallonta hadiza dake mintsininta alamar tayi shiru haneefah tace wlh saina fada, sadiya mesa matan yanzu kuke wahalar da kanku? Dubeki kina da kyau kina da haske amma saida kika kara da bleaching, kinsan hakan zai taba lafiyarki ko? Wato baza'ai so Dan dan Allah ba. Na kasa gane meke yawo a kawunan mu, kowa ya damu daya kasance yana da saurayi ko aure wannan abinfa nufi ne na Allah, misali matan yanzu sun damu da sai sunyi aure dan sunga kawayensu duk sunyi, sun manta cewa kowa da yadda Allah ya tsara masa tasa rayuwar, tun kafin muzo duniya Allah yarubuta mana duk abinda zamuyi kuma da lokacinsa. Muyi la'akari da auran yanzu kowa zaman hakuri yake, babu wadda yake zaman kwanciyar hankali 100% sai kinyi shi domin Allah zakiji dadin hakan.... lokaci bai kure mana ba mu dage da addu'a Allah kawosu lokaci mafi alkhairi kuma wadda zamu kasance domin Allah. Hadiza ta nunfasa tace tabbas maganarki gaskiyane, gaggawa aikin shaidan musamman a lamari irinta aure. Matan yanzu sun fison a musu karya, wani namijin dan yana sonki zakiga ya fada wannan harka. Abin takaici akwai matanda basa biye kodayinsu, wani namijin zaita kashe miki kudi da zarar ya aureki shikenan, wani bazai kashe ba sai kinshi go gidanshi, shiyasa ake cewa mu dage da addu'a sannan mubarwa Allah sabinmu. Allah bamu mazaje nagari dukkaninsu suka amsa da ameen. A sanyaye sadiya ta tashi tabar gurin, suka ci gaba da tattaunawa kan matsaloli irin ta rayuwa. Suna zaune taji wayarta na ringing tana dagawa ta masa kwatancen inda zai sameta. Sanye yake da fararen kaya fari tas, komansa fari da glass da ya matukar karbeshi. Sai daya kusa hadiza ta lura da irin kallon da haneefah take mishi hadiza tace malama aja aji irin wannan kallon, harara ta daka mata. Ya karaso tare da sallama suka amsa, hadiza ta basa guri ya zauna tace Alhamdulillah kawata ta sanar min komai, naji dadi kwarai, sannan ina tayaka farin cikin samun haneefah, badan ita kawata ba, haneefah ta kasance diya tagari wadda kowani irin namiji zayyi alfahari kasancewa da ita matsayin mata. Allah ya tabbatar mana abinda yafi alkhairi. Dukkansu suka amsa da ameen banda haneefah data amsa azuciya domin tun isowarshi kanta sunkuye, kunyarshi sosai takeji. Hadiza ta musu sallama ta tafi. Kallon ta yake yanajin wani irin jin dadin. Yafara magana a hankali bazaki dago ki kalleni ba? Shiru tayi. Murmushi yayi yace nagode wa Allah daya nunamin wannan rana gani gake a matsayin masoya. Allah bamu ikon cimma burin mu. A hankali tace ameen. Yace yaushe zaki gama makaranta? Shekara mai zuwa insha Allah warhaka mun gama, yace Allah nuna mana ameen ta amsa. Ya qara jefo mata tambaya kina da ra'ayin muyi aurene ko sai kin kammala? Bani da raayi nafiso inna kammala sai ayi bikin amma anan zamu zauna ko? Yace aikin nawa fa cike da zolaya tace saika ajeni anan, inda nake aiki zamu zauna nima zanso ki kammala amma kafin inaso inje gida su abba susan da ni. Tace ba komai yaushe zaka je? Ko yanzuma a shirye nake domin nayi sallama da mutanen gida inna tashi zan wuce. Tace yanzu dai babu kowa gida sai dai in kazo wani lokacin. Toh shikenan duk yadda kikace. Suka dan taba hira sannan ta damesa da ya tashi ya tafi kada ya makara. Taku suke a tare har suka iso inda yayi parking. Tace next month insha Allah auren hadiza zaka zo? Yace mezai hana in aka gayyo to ni, Allah kaimu. Yace inga wayar da kike amfani ta nuna masa gionie p4 yace shikenan. Allah baku sa'a a exams naku, nasan kina maida hankali sosai a karatu, ni mutum ne mai son karatu sosai dan haka ki dage kinji ? Ta amsa tare da murmushi. Sallama sukai kamar kada ya rabu da ita. Nana takirata take sanar da ita sun iso lfy har sun gaisa da umma da abba. Cike da farin ciki haneefah ta sanar da ita batun yusuf, fatan alkhairi tayi mata sukai sallama. Bayan sun kammala abinda zasuyi haneefah ta wuce gidan auntin ta muhibbat. Taci sa'ar samun humaira, anan take sanar dasu batun yusuf sannan take sonjin ra'ayinsu game da lamarin. Humaira tace yanzu wazai fara aura? Ke ko ita? Kuma har kinsawa ranki zama da kishiya, dukkanin mu bamu da kishiyoyi haka muke fatan kuma ku soma shiga as first wife, sbd ko yaushe mune kan gaba, don me kike gaggawa? Haneefah tayi murmushi tace tabbas naji mata da dama suna fadin haka, amma nawa ganin ba dukkanin mata suke rike matsayin first wife, sbd duk sanin da kikai masa danya qaro aure in kika daina, wadda yazo tazo ta fiki kwazo ta karbeshi kenan. Mata mudaina gadara da hakan... lokacine da zamu ninka kyautatawarmu ga mazajenmu. Kinga wlh banajin tsoron tazo ta sameni ko in sameta abin bukata shine ki tsaftace zuciyarki sannan ki dage da dukkan abinda zai dauke masa hankali.... muhibbat ta buge kafadunta tace shisa muke ji dake haneefah, Allah tabbatar muku da alkhari dukka suka amsa da ameen. *Dr HANEEFAH*👩🏼 14 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Soyayya ake na gaskiya, tsaftatacciya wadda babu yaudara ciki. Suna mutunta juna tare da kokarin kawar da duk wata hanya da zasu samu sabani tsakaninsu. Hakan yasa dukkaninsu sunyi dace sosai. Bangaren haneefah ko banda kulawa da soyayya da take samu, ta samu qaruwa sosai game da addininta domin abubuwa da dama tasani da qarin haske akai, hakan yasa ta dada rikeshi. Kwanci tashi ba wuya gurin Allah. Yau su haneefah suka gama jarabawarsu tare da hutun sati biyu. A daren ne take sanar da yusuf ta kammala exams. Yayi mata fatan alkhari tare da tambayarta inta gama wani course takesonyin specializing akai? Tace nidai har yanzu ban yanke shawaraba, hasalima ba so nake yiba. Cike da mamaki yace mesa? Accoutr nake son zama tukun aka turoni nan, Allah akwai wuya. Yace haba dearie nasan zaki iya, a matsayinki na mace bai kamata ki karanta wannan fannin ba, kinsan aikin dan jama'a zakiyi, Allah kadai yasan irin ladan da zaki samu. In zaki bi shawarata inason ki zamo gynecology. Zaro idanu tayi jin abinda ya ambata tace ina ni ina waccan gurin! Nida yaren kuma ban gama koya ba. Cikin rashin fahimta yace wani yare? Turanci mana ta bashi amsa. Duk da dakewar da yayi saida abin yasashi dariya sosai. Jin yadda yake dariyar hakan yasa taji dadi, da sauri ta danna record. Yace amma kin sani dariyar da na dade banyi ba. Aishi karatu fahimta yake bukata, in wannan matsalarne zaki koya da yardan Allah. Haka suka kasance kullum cikin kyautatawa juna. Sun matukar kara shakuwa. ***** ***** Auren hadiza sai matsowa yake yi domin saura wata daya. Haneefah sai faman shiri ake. Ana saura sati uku suka fara rabon anko. Ga karatu sai kara zafi yake. Sunje gidan wata qawarsu da sukai makaranta tare tsokanar haneefah saura ke. Nima insha Allah bazan jima ba cewar haneefah. Kawar tasu tace inada matsala, tun dana sami cikinnan na tsani mijina banson ganinshi. Ko zaki bani shawara. Haneefah ta fara bayi; Idan mace ta Sami ciki me ya kamata tayi game da muamalar ta da mijinta??? A: gudunsa zatayi su fara wasan buya da hantara?? Ko B: Naniqeshi zatayi tare yin wasu abubuwa na yarinta da shagwaba?? Lokuta da dama idan mace ta Sami ciki babu abinda ke fara zuwar Mata Sai tsanar mijin ta...bawai ko wace mace ke Hakan ba...Amman 80% haka muke. To anan abinda ya kamata mace tayi a irin wannan period din shine. Dolene ta daure bawai Sai tana soba..A'ah saidan rikewa kanta wata dama da take da ita domin Har idan ta bari ta kubce Mata to dawowarta Sai a slow. Ki kasance ko yaushe kina tare da megidanki Kamar yarda kika saba koma fiye da hakan...tunda a wannan lokacin shi namiji yake jinki fiye da ko yaushe a baya...saiki dage wajen jikawa....surfawa...dakawa...da Kuma tukawa...hakan zai Kara Miki martaba sosai domin kin bashi damar yaso abinda yake da bukata darajar Ki zata Kara karuwa can kololuwa Amman rashin samun hakan zai iya jawo Miki matsaloli Kamar haka zai fara Zaman waje...maana majalisa a tunaninshi daya dawo gida yaga ba daidai ba maana baki jika mashi kayan wankin shiba...bare yasa ran Zaki wanke mashi wata kilama harda guga...gara ya zauna a waje idan kinyi bacci saiya lallavo ya kwanta. Wata matsalar idan ya hadu da mugun aboki daganan za a saka mijinki cikin mugun hali...idan akai rashin saA shikenan ya kama wata tashar Kenan inda zai rinkq samun signal...tunda ke kin zama baki da network. Saimu kiyaye ALLAH yayi mana jagora ya kare mana mazan mu a duk inda suke. Duk suka amsa da ameen. Biki ya matso, saura kwana uku haneefah taje gidansu hadiza domin qarasa shirye shirye. Shiko yusuf yana son zuwa ya halicci daurin auren sannan yana matukar son kallon abar kaunarsa. Zuwa gidan nasu ne baiso, kada momy ta dago masa maganar aure, duk da ba auren bane baya so, yafison auren haneefah kafin waccan. Babu irin hakurin da bai bada ba amma anqi hakura. Yanke hukuncin zuwa garin kano yayi amma gidan abokinsa zai sauka bazai wuce gidan su ba. Bangaren momy kuwa jiran dan nata take yazo domin a tsaida ranar aure. A sannan yar uwar tata tazo. Ta dubi momy tace inata jira naji shiru shine nace bari inzo inji me ake ciki domin yarinyar nan tayi kokari, tana son dan uwanta biye da shekara biyar take jiransa, in wani abinne sai a sanar in san meya kamata, domin anawa ganin inaso in hada kawunan yarannan. Momy ta dubi tilon kanwarta tace magana nanan, aini namiki alkawari. Jiran dawowarsa nake domin asa ranar aure. Cike da jin dadi umma nusaiba tace Allah dawo dashi lfy sannan a zuba mishi kinsan yaran zamani, wata qila wata ce ke masa wasa da hankali, yan mata basu kai ko inaba amma sunsan hanyar gidan Malawi da boka ye, su mallake maka da baka jiba baka gani ba. Momy tace bazan bar haka ta faru ba, domin nasa ido akanshi sosai. Rahma ta ishe shi har abada. Murmushi umma nusaiba tayi suka canza hira. An daura auren hadiza da usman. Ganin fuskar haneefah kadai ya isheka tabbacin ita qawace ta hakika domin cike take da farin ciki. Duk wata zirga zirga da ita ake. Yusuf ma yasamu halartar auren. Kamar yadda ya yanke shawara gidan abokinsa ya sauka. An kawo amarya gidanta angwaye sunzo siyan baki. An kammala komai bisa al'ada kowa ta fice domin komawa gida. Haneefah ta fito ta nufi motar da ta kawo ta, taga wata mota na mata flashing, bata qula ba sai da yaleko yace ni ne. *Dr HANEEFAH*👩🏼15 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Juya warda zatayi ta ga yusuf. Mamakin ganinsa tayi ta karaso ya bude mata gaban mota. Ta shiga da sallamarta ya amsa ya kura mata, ganin haka yasa ta sunkuriyar da kanta ta gaishe shi. Ya amsa tare da cewa dearie kinyi kyau sosai pls bari in dauke ki a pic. Tace aa gele ne a jikini fa, bai jira cewarta ba ya dauke ta duk da ba kallonsa ta ke ba. Ya tada motar suka wuce gida. Wannan karon har kofar gida ya kawo ta yace insha Allah gobe zanzo in gaida umma da abba. Allah kaimu ta amsa masa. Zata fita ya locking door ta juya zata kalleshi karaf ya dauke ta da hoto. Ta turo baki nidai... nanma yadauketa.. dakyar sukai sallama kan gobe zaizo ya gabatar da kanshi gurin abba. **** **** **** Washe gari misalin karfe goma ya dauki hanyar gidan su haneefah. Ya samu kyakykyawar tarba gurin abba kasancewar haneefah ta sanar da umma. Abba ya fahimci yusuf mutumin kirki ne, duk da haka abba sai da ya masa wasu yan tambayoyi da son zurfafa bincike kamar yadda yazo a tsarin addini. Shima yusuf yaji dadi domin yagama gane gidan manya ne. Abba ya amince nasa da haneefah sai fatan alkhairi da yayi musu. Haka abin yakasance gun umma, ta matukar jin dadin zuwan yusuf. Ita ko haneefah tayiwa umma sallah kan zata je gidan aunty muhibbat. Murmushi tayi domin ta dago ta, Allah kiyaye hanya kice ina gaisheta. Labewa tayi inda ta tabbata hanyar zaibi ya wuce. Ba'a dade ba ta hango motarsa ta fito. Yana ganinta ya tsaya ta zaga ta shiga. Amaryata! Ta dago ido suka hada ya sakar mata murmushi har an daura auren ta bashi amsa. Yace insha Allah ai mun kusa tunda makarantarki nake jira, haneefah tace nidai gidan aunty muhibbat dani, yace fadi gaskiya kin fito ganina dai. Yanata tsokanarta tana sashi dariya. Driving take cikin nutsuwa cikin moyarta kirar matris. Traffic ya tsada su kamar ance ta juya idonta ya sauka kan yusuf. Dariya yake cike da nishadi. Mamakine ya kamata yaushe yazo? Kuma wacece take gefensa yana mata irin wannan dariyar? Iya saninta tasan dan nata nada kamun kai baya kula yan mata bale ya sakar musu fuska. Ta dauki waya ta kira shi tana kallonsa. Jin wayarsa na ringing ya tsaida dariyar zaisa hannu ya dauka aka basu hannu. Yaci gaba da tukin. Momy taso binsu amma bangarensu ba'a basu hannu ba. Aunty tayi matukar jin dadin ganinsu tare, itama fatan alkhairi ta musu. Ya mata sallama kan zai wuce abuja kada ya makara. Shigarsa mota ya tarar wayarsa na ringing, da sauri ya daga ganin sunan momy cike da lada bi ya gaidata ta amsa. Ina ka shiga inata kiranka cewar momy? Am sorry momy ayyuka ne sukamin yawa. Naji, kana ina ne? Ina gun aiki amma nakusa komawa gida. Ta rasa me zata ce ma dan nata tsabar mamaki kawai ta katse kiran. Shiko waji wani iri domin yau yayi abin da bai taba yiba. A hankali ya furta am sorry momy, ina kano amma nakasa kara sowa gida... Inason ganin farin cikin nayi alkawarin auren zabinki domin samun farin cikin ki, da fe kansa yayi ya kifa kansa kan sitiyarin mota... a hankali ya soma furta innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun. Saida ya samu nutsuwa tukun ya tada mota ya nufi hanyar abuja. Kai komo take a dakinta... wai yau dan cikinta yake mata karya? Bayan tagansa da idanunta! Tabbas akwai abu. Tuna fuskar yarinyar tayi yana mata gizo. Tace saina sanki sannan inji alaqarki da dana. Bayan haneefah ta koma gida umma ke mata gargadinta kan ta aje hankali kan maza, duk da yusuf yazo amma har yanzu bata aureshi ba. Sannan ta aje hankali kan karatun ta sosai tunda tazo shekarar gamawa. Suna cikin tattaunawa nana takirata, ta labatar mata zuwan yusuf. Ta nuna farin cikinta sosai amma daga baya taji babu dadi data tuno batanan za'ai bikin. Bayan sunyi sallama kiran barrister ramlat ya shigo. Bayan sun gaisa tace nakira domin inji lafiyarkine tunda ke bakya neman mutane kullum sai annemeki. Dariya is haneefah tayi tace wlh ba haka bane inason kira Allah bai bani iko bane. Tace Allah sarki ba komai ga Dr ku gaisa. Suka gaisa da Dr Mubarak yake ce mata kiyi karatu sosai fa kune kuke shirin zama graduate. Tace insha Allah sukai sallama. Umma ke tambayarta waye? Nan ta bata labarin abinda yashiga tsakaninsu. Umma tace ina alfahari dake *_Dr HANEEFAH_*. **** **** **** Momy ta dubi mijinta tace auren yarannan nakeso ayishi nan da wata daya. Mijin nata ya maida dubansa gareta yace wani yara kenan? Yusuf da rahma ta bashi amsa. Kallonta sosai yake yana nazarinta. Can ya numfasa yafara magana, na fahimci kimason ta kurawa yaronnan, tuntuni ya nuna bayason auren nan yakamata ki jenye, yaran zamaninnan ba'a musu haka! Ya aka kare ga wadda suke kaunar juna ma bale basa so? Nidai kada ki takura mishi ki barshi ya kawo zabinshi. Momy tace haba alhaji, ina son dada karfafa zumuncin mune da kanwata sannan ai ita rahma tana sonshi... wannan shine hujjar ki? Nidai bada yawuna ba. Ban yarda da auren da yusuf bazaiyi farin ciki dashi ba. Yana kaiwa nan ya juya yayi shigewarsa ciki. Dauko wayarta tayi ta kira yusuf taji number busy... kusan sau goma take amma amsar daya ce. Cike da mamaki take dubar wayan nata. Ta tura masa message in ya gama yakirata. Shiko yusuf waya suke da abar kaunarsa. Haneefah tace ai tunda karatune burinku zan cika muku shi kada ku damu, ku tayani addu'a. Insha Allah muna kai kuma munsan bazaki bamu kunya ba. Murmushi tayi tamkar yana gabanta tace pls kada ka rabu dani, ina sonka sosai... bana kwadayin rayuwa a inuwar kowa matsayin matar aure inba kaiba... ka sanar dani momy tana da nata zabin, ko su ukune indai zan kasance dakai na yarda na zama ta hudu. Jawo pillow dake gefensa yayi ya runguma yace dearie bazan rabu dake ba, ke kadai ce kike gabana. Insha Allah zamu kasance duniya da lahira matsayin ma'aurata, muci gaba da addu'a domin neman zabin Allah. Kinsan wani abin muna ganinshi alkhairine amma sharrine, wadda muke ganin sharrine alkhairi ne agaremu. Addua itace mafita. Haka sukasance masu kwantar da hankalin junansu har suka sallama. Ganin message din momy yayi, lokacin kuma dare yayi domin kusan karfe shadaya da rabine. Yayanke shawaran sai gobe zai kira. Yana aje wayar yaji kira na shigowa, da sauri ya dauka ganin mum. Ko sallama bata yiba tace dawa kake waya? Nan ya soma kame-kame tsaf ta dago shi. Inason ganin ka gobe duk aikinka, ka aje shi dif ta katse wayar. Zuciyarsa ne ke bugawa uku-uku ganin ba mafita ya tashi domin gayawa mahaliccinsa ya zamto wannan kiran alkhairine. *Dr HANEEFAH*👩🏼 16 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Karfe goma yayi p arking cikin gidansu. Bai nufi ko inaba sai sashin momy, kannen sa ya tarar a parlour suna kallo. Cike da kulawa ya amsa gaisuwarsu ya tambayi momy, tana ciki aisha ta amsa. Zai wuce tace pls yaya ina son kabani aron wayarka, ya mika mata ya wuce. Zaune ya taddata tana amsa waya. Bayan ta gama yake gaisheta. Ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar. Ta dubeshi dakyau tace badon komai nakira kaba, so nake kaje ka sanar da mahaifinka ka amince da maganar auren rahma, nan da wata daya masu zuwa a daura aure ina nufin kace dashi cikin satinnan a kai kudin sadaki da komai nanda wata daya asa ranar aure..... Cike da rashin nin dadin maganan yace, umma ban ki zabin kiba, kince nima in auri zabina.... sai nace kada ka auri rahma? Yusuf kwana kinnan nakasa gane kanka, toh wlh in bakai yadda nace ba sai na hana ka aurenta ko wacece ita. Cikin sauri yace momy na amince ko yauwa a daura, zanje in sanar da abba yanzu. Murmushi tayi tace yauwa ko kaifa. Yaje ya sanar da mahaifinsa. Mahaifinnasa yace yusuf kada kaje kayi abinda zai dame ka. Yace ba komai insha Allah. Allah tabbatar muku abinda yafi alkhairi ya amsa da ameen ya fice a folansa ya nufi nashi bangaren. Bayan ta kammala dukkanin ayyukanta ta nufi dakinsu ta kwanta, duk da gajiyan dake tattare da ita tana son kiran yusuf domin yau tun safe basuji muryar junansu ba. Tunanin ko ayyukane suka dan masa yawa. Sanda kiran ya shigo wayar na hannun aisha, mamakine ya bayya a fuskarta ganin *Dearie* arubuce. Aiko da sauri ta daga wayar taji ance amincin Allah su tabbata gareka abin alfahari.... ni shikenan ma tun dazu jiran kiranka nake amma shiru ka manta dani yau kana ta aiki. Jin anyi shiru ta qara cewa hello! Aisha tace wayar bata tare dashi. Ras taji gabanta ya fadi, kamar zata katse wayar taji ance aishace kanwar shi amma yanzu zan kai mishi. Ajiyar zuciya haneefah tayi tace ba komai nagode. Kishin gide ta sameshi kan gadonshi. Tashiga da sallama tana dariya yace yau kuma me ya fadu irin wannan nishadi aisha? Yaya kiranka akai nadaga cikin sauri yace bani wayata, ya karba yana duba mai kiran nasa. Ganin haneefah yayi murmushi yace meye na dariya? Yaya shine ko kasanar dani munyi sabuwar aunty? Wlh a muryarta naji nutsuwarta. Yusuf yace kardai kin cika ta da surutu irin naki. Aa yaya, dan Allah meye sunanta? Haneefah ya bata amsa. Very cute!!! Yaya dan Allah muga hoton ta? Inta tura zan tura miki... Suna cikin magana haneefah ta kara kira, suga gaisa cikin shaukin so. Tana shagobe masa tace tazu nakira aisha ta dauka baka ji yadda gabana yafadi ba.. ayya sorry dear. Ban dade da shiga kano ba. Cike da mamaki haneefah tace lfy? Lafiya lau. Ajiyar zuciya ta saki tare da cewa Allah qara mana lafiya mai albarka. Yace ameen. Yana son sanar da ita amma yakasa. Haneefah tace inada tambaya, Allah sa nasani ya amsa. *IDAN MUTUM YA SAMU RAKA'A DAYA A SALLAR DA AKE RAKA'A HUDU YAZAI KAWO SAURAN UKUN?* Wato ina nufin inaso akarayimani bayani akan sallah tare da liman idan mutum yasami raka'a daya wurinda ake raka'a hudu yaza ya kawo sauran ukun, sbd a makaranta hakan na yawan faruwa ga dalibai mata. Idan mutum yasamu raka'a daya a cikin sallah me raka'a hudu. Idan ya tashi ramuko zeyi raka'a daya da karatun surah, sannan ya zauna tahiya ya kawo biyu a sirran ce. Idan har sallan isha ne, idan la,asar ne ko azahar shima haka zeyi babban cin da zai nuna a gurin shie, rashin bayya nawa. Amma idan mutum ya rasa raka'a daya a sallan magriba, to ze kowa raka'a daya da karatun sura a bayyane, sanna yayi tahiya, ya sake kawo daya a sirran ce batare bayyanawa ba. Domin manzon ALLAH sallahu alaihi wasallam yanuna cewa ''ka ciko abinda ya kubuce ma" Shiya sa idan Kazo kabi liman sallah, da wannan raka'ar da ka samu kai a wajen ka itace na daya, Daga ya idar se ka cika tazama ma, cikon da kayi shine na Qarshe. kamar yadda ka saba a sauran salloli cikakku, sannan idan ka rasa raka'a daya daga cikin raka'o'in da ake raka'a biyu. Shine zaka kawo ta a sirran ce, batare da karatun sura ba. Allah sa mudace ameen. Haneefah tace nagode sosai. Yace anjima zanzo kamar bayan sallah isha'i. Allah karaso dakai lfy. Bayan sallar isha'i kamar yadda ya sanar da ita tsaf ya shirya. Yana tafiya can ya hango kanti saida waya nan ya tuno yanason siyawa haneefah. Ya tsaya ya cire kudi a ATM sannan ya nufi wani babban shago. Ya rasa wani irin waya zai siya mata gashi yanason suprising natane. Daga karshe yasiya mata Samsung note3. Ya fito ya tsaya wani shopping mall yasiya mata dogayen riguna masu kyau kala biyu da chocolates ya fito ya kama hanya. A kofar gida yayi parking ya shigo. Ya turo kafar kenan ya hadu da Ahmad suka gaisa. Yace ka shigo da motarka mana aikazama dan gida, yace barshi kawai ko a wajen. Dole Ahmad yasashi shiga da motar shi. Yace yayi mishi sallama da haneefah. Sanda yayi mishi jagora har zuwa falon abba, kasancewar yau ba girkin umma bane tukun ya fito ya je kiran haneefah. Light make up tayi, tasa dogon hijabinta. Tasame shi zaune yana aikin danna waya. Sanye yake da manyan kaya. Dago kansa yayi tare da amsa sallamarta. Bayan tasami guri nesa dashi kadan ta zauna dukkaninsu sukai shiru tsawon minti biyar. Yusuf ya fara magana ya kuma kikai shiru kamar ba mai surutu a waya ba. Ita dai qara shiru tayi domin kunyarsa take ji. Murmushi yayi ganin ta qara shiru. Yace umma ce takirani shiyasa kika jini yau gani a kano amma gobe da safe zan koma. Ya dago ido ya kalleta yace ina fata zaki bani goyon baya wajen yiwa mahaifiyata biyayya. Gabanta taji ya fadi amma ta dake bata nuna ba tace insha Allah. Yaci gaba nanda wata daya aure na da rahma shine dalilin kiran. Numfashinta ta nema ta rasa jin aure daya ambata. Dakyarta daidaita numfashin tace Allah sanya alkhairi, ina tayaka murna *Dr HANEEFAH* 👩🏼17 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Ji take kamar ta cire zuciyar tayar ta huta saban wani irin kunar dake mata. Ji tayi wani irin abu ya tokare mata makoshi. Duk halin da tashiga kanta sunkuye yake, Allah-Allah take yayi mata sallama yatafi kada yaga hawayen dake makale idonta. Yagama nazarinta tsaf yace bayan anyi bikin zan dauko da maganarki tunda makarantan yakusa, kina gamawa sai ayi biki. Ganin shirun nata yayi yawa yace ni zan wuce inna koma zamuyi waya. Batace dashi komai ba suka fito, har gurin motarsa suka iso a sannan ta dago kai tace Allah kiyaye hanya. Zata juya yace haba dear hankalina bazai kwanta ba in mukai irin wannan sallamar. Karfin hali tayi ta murmusa masa tace yi hakuri, inaso kaje ka kwanta ne domin ka tashi da wuri bana so ka makarane. Yace ba komai kafin ki wuce ga wannan ya bude mota ya dauko leda ya mika mata. Qin karba tayi zata wuce ya dakatar da ita yace kiyi hakuri na canza miki mood naki, amma wannan itace first gift na pls ki karba ba danni ba dan Allah. Ta karba tace nagode cikin sarkewar muryar kuka. Tuni ya hango hawayenta cikin dacin rai ya shiga motarsa ya fice zuciyarsa na masa kuna. Ya tsani ganin bacin ranta ko kadanne. Itako haneefah tana zuwa bakin kofar falonsu ta share hawayenta. Tana shiga ta tarar da kannenta da umma suna kallo. Ta mikawa umma ledan tace shine yakawo, kannen nata sukayi gurin ledan suka soma ihun murna tare da cire kwalin wayar suka nunawa umma. Itama mamakin irin wannan kyautar tayi. Itako ko kallon inda abin yake batayi domin jira take tashiga ciki. Umma ta katse tunaninta da cewa zoki gani haneefah. Tana gani tana yabawa kawai dan karsu gane halin da take ciki. Umma ne tace sai abari in abba yazo yagani saiki fara amfani dashi amma ga chocolates din. Haneefah ta dauki biyu ta musu saida safe. Shigarta dakin ta kulle da key ta nufi bandaki. Tsayawa tayi ta rasa ne zatayi, ta qara fitowa ta zauna bakin gado. Tabbas kishi nake amma mesa zan damu kaina? Tunda zai aure ni ai shikenan. Yanzu in mahaifiyarsa tace bazayyi mata kishiya bafa? Nan hawaye ya fara zubo mata tace aa hakanma bazai faru ba. Nan ta rushe da kuka tana tausaya kanta Kwance yake kan 3seater falon shi, yanayin da yabarota shike sosa masa rai, ya dauki waya ya shiga kiranta. Kusan 5missed call bata daga ba, ya kyaleta yasan ba lallaine tayi magana a irin wannan yanayi. Bayan awanni ya qara kira karshe yaji wayar a kashe. Haneefah tana kwance tana kuka har kusan karfe sha biyu, tsabar kuka har kanta sarawa yake. Daga karshe ta dauko wayarta ta kunna domin muryar shi kadai zataji ta iya tsagaita kuka. Zaune yake kan sallaya yana karatun Qur'ani mai girma yaji sautin wayar sa, yayi saurin dakatar da karatun da fatiha ya dauko wayarsa. Dadine ya lullubeshi ganin itane ya dauka tare da sallama. Shiru tayi bata ce komai ba. Yace pls kiyi magana tun dazu nake tabinki arai, Allah sadai ba kuka kikai ba. Kiyi hakuri in har ban fada miki ba yazama wani abu daban shiyasa na sanar dake amma Allah baki hakuri, kinji? Katse wayar tayi sannanta tashi daga kwanciyar da nufi bandaki tayo alwala ta fito ta fara jero nafiloli sannan ta fara neman gafaran mahaliccinta kan ya yafe mata, ya bata ikon kadaitashi a zuciyarta da tsoronsa da soyayyar ma'aiki annabi Muhammad (S.A.W). Sannan tayi addu'a Allah tabbatar mata abinda yafi alkhairi tsakaninta da yusuf. Ta soma karatun qur'ani har bacci ya dauketa inda take. Har an fara sallah a masallaci tukun ta farka, kasancewar batayi bacci ba. Da sauri ta nufi banda ki tayo alwala tazo tayi sallah. Bayan ta kammala ta jawo wayarta ta kunna ta shiga kira yusuf. Dawo warshi daga masallaci kenan yaji kiranta. Yana dagawa ta gaishe shi ya amsa cike dajin dadi, yace pls dearie.... ka tseshi tayi tace ya wuce muddin ina sonka dole in tayaka yiwa momy biyayya, ko da tace bazaka aure niba na yarda. Farin cikinta shine hanyar shiga aljannar ka, niko ina alfahari tayaka ko wace irin biyayya domin inason ka gama da duniya lafiya. Dole nayi kishi saboda ina sonka! Son da banyi tsammanin yiwa wani ba, ban taba ko da mafarkin kasancewa irin wannan yana yin ba, sannan dabi'atane in raina ya sosu muddin banyi kuka ba banajin abin zai gushe amma da zarar na zubda hawaye, everything is over. Am sorry. Murmushi yayi yace am proud to have u, banida abinda zance. Dariya tayi tace abubuwa da dama, naga tsarabarka nagode sosai sannan nayi matukar farin ciki, amma ai sunyi yawa? Babu wani yawa kin wuce haka haneefah, Allah bani ke matsayin mata. Tace ameen, ka kwantar da hankalin ka, kayi tuki cikin nutsuwa inka iso sai muyi waya ko? Toh shikenan ranki shi dade, saina kira. Wani sanyi yaji aransa, haneefah yarinya karama amma rayuwarta so simple. Hannu ya daga yana addu'ar Allah mallaka mashi haneefah. Itako bin wayar tayi da kallo, a hankali ta daura wayar a kirjinta tana cewa ina sonka yusuf. Sannan taci gaba da laziminta har rana ta fito. Abba ya shigo da safe umma ke nuna masa kyautar yusuf. Yabawa yayi yace a sufar lafiya. Haneefah tana sake kallon kyautar tana murmushi. Tana son manyan wayoyi sai gashi Allah ya mallaka mata, a sannu Allah zai mallaka maka ni yusuf ta fada a hankali. Tasa wayar a chargy ta kama ayyu kan gida. Bayan ta kammala ayyu kan gida tayi kwalliya, tayi kyau sosai. tasa daya daga cikin dogayen rigunan da yusuf ya kawo mata ta cire wayar a chargy ta kira bintu ta fara daukanta a hotuna. Tayi kala kusan goma ta qara canza riga da siket na atamfa Shi ma tayi hotunan dasu. Ta zabi guda biyar masu kyau ta tura masa ta WhatsApp. Bayan ya koma yakira haneefah yake sanar da isowarsa tace na tura maka sako ka bude ka gani. Idonsane suka sauka kan hotunan, sun matukar yin kyau, ya tsaya wani kan rika da siket da bata da gele.. zubawa surar jikinta ido yayi ko giftawa baya yi. Lallai haneefah shiyasa kullum kike cikin hijabi. Farin ciki da godiyarsa ya nuna gareta, sannan addu'a Allah mallaka musu juna. Dariya tayi tace ai nazama taka, fatiya da shaidu muke jira. Shima dariyar yayi yace Allah nuna mana *Dr HANEEFAH* 👩🏼18 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tun daga wannan lokaci alaqarsu ta dada nunkuwa, kullum kowa so yake ya faranta ran junan su. Anje har adamawa ansa ranar aure rahma nan da wata daya. Murna gurin umma nusaiba ba'a magana, sai dada hura kunnen yar tata take da hudubar banza, ita ko rahma burin magaifiyarta zai kaita gidan ba zaman har abada ba. Su haneefah an koma makaranta amarya hadiza ma ta fito. Haneefah ke tsokanarta har tagaji. Hadiza tace nidai bazaki ji komai abakina ba zaki gani da idonki in lokacin ki yazo. Haneefah ta kawar da kanta ta danne zuciyarta kan auren yusuf, domin ta fahimci damuwar ta itace tashi, ita ko batason bacin ransa. Ita yanzu karatu tasa agaba, domin cike burin mahaifanta da mosoyinta. Bangaren nana ma bata samun wata matsala abangaren karatun ta. Sai dai muce Allah basu ikon cimma burinsu. Biki yazo momy sai shirye-shirye, shiko yusuf baisanma suna yiba. Kayan lefema momy ce ta hada, sannan rahma ta da meshi kan occation, shidai yace babu ruwansa haka ta hakura. An daura aure amma ko ango bai halarci wannan aure ba. Momy tace ya aiko kudin jirgi a wuce da amarya rashin son gardama yace a kawo ta kano side nashi inyaso inya gama gyaran gidanshi sai suzo abuja. Haka ko akai, aka kawo amarya kano. Haneefah har wata daya yayi yusuf baice an daura auren ba, hakan yasa taja bakinta rayi shiru. ***** ***** ***** Bayan wata biyu amarya na jiran ango bata sashi a ido ba amma yakan kiranta su gaisa. Momy ma in sukai waya yace zaizo, so yake in yazo ya koma da ita, hakan yasa ta saurara mishi. Haneefah ko saura wata shida ta kammala makaranta, a sannan ta bukaci tafiya gidan aunty muhibbat domin cikinta ya tsufa. Yau lahadi suna gida. Haneefah ta gama shara tana mopping sai yaron aunty muhibbat yazo da gudu tsantsi ya dauke shi kadan ya rage ya fadi yace auucchhh! Aunty haneefah badan kin rike niba da na fadi... tseye tayi tana kallonshi, bismillah zaka ce in kazo fadiwa ko wani abu daban? Mu haka muka saba fada! Muhibbat dake jinsu tace bari haneefah babu yadda da su ba amma sunki dainawa. Haneefah tace waya ce tun farko ki koya musu? Zakiga yaro shekaranshi shida amma baisan banbancin wuta da aljanna ba! Don ki tsoratarshi in kikace wuta bai sani ba sai spider man, wlh gomma ku farka, ya zamto yara su tashi da dabi'a ta addinin musulunci ba dabi'an wasu ba. Aunty muhibbat tace toh malama sakita cika ni da surutu. Gaskiyace saina fada.... jin sautin wayarta ta jefarda mop ta wuce amsar kiran masoyinta domin sautin shima daban ne Sallama tayi suka gaisa, yace zaki iya fitowa da safennan ina kofar gida. Mamakine ya cika ta tace yaushe kazo? Jirgi na biyo. Ok ina gidan aunty muhibbat, saika karaso ta katse wayar. Bandaki tashiga ta watsa ruwa ta fito. Tsaf ta gama shiri yakirata tace ya shigo . Zaune tasame shi a falo, taga ya canza mata yadan rame. Ta zauna nesa dashi, suka kara gaisawa yace inason ganin kine shiyasa na biyo jirgin safe nanda awa daya zan koma. Murmushi tayi tace nagode da ziyara nima kamar kasan kewar ka nake, ka wuce gida? Aa, mesa? Banason zuwa. Shiru tayi tana ganinsa bata ce komai ba. Kasa hakura tayi tace meke damun ka? Me kika gani? Ka rame sosai. Ya kalleta yace aure suka min, ina bin yadda zan sauke hakkin wannan aure, banasonta, na jure amma ko ganinta banason yi. Narasa me zanyi, tun 6years back nace bana so amma sai da akamin, gashi yana son halakani. Duk zafin kishinta amma ta tausaya mishi. Tasowa tayi yazo kujeran da ke fuskantar shi tace haba yusuf bansan ka da haka ba. Da ilmin ka kada ka soma daukan halayen jahilai. Saboda soyayya bazaka sauke nawin da ya rataya a wuyar kaba? Haba ka dadayin hakuri insha Allah wata rana sai labari, yaushe akayi auren ? Kuna tare? Aa ya bata amsa, tana gidanmu, anyi auren watanni biyu da suka wuce. Zaro ido tayi sosai tace ai zaka bata lamarin mu. Cikin rashin fahimta yace wani lamari? Taya kake tunanin momy zata amince da auren mu in kana yiwa diyarta haka? Rufamin asiri ban shirya rabuwa da kaiba. Dariya ya soma jin yadda take maganan. Murmushi tayi tace inaso ka kasance fiye da daa, ka kwantar da hankalin ka. Allah sa hakan shine mafi alkhairi agare ka. Maza kaje gida ka gaishesu pls, ran momy da amarya zai baci, shiru yayi. Kaji ango ya bata rai. Ta soma dariya tana cewa jama'a kuzo kutayi shari'a amarya batayi fishin kishi ba ango yana fishi. Dariya ya soma. Nan haneefah ta fara zolayarshi yanata dariya har ya manta bacin rai dake tattare dashi. A hankali take kallonsa yadda yake dariya cikin nutsuwa tace zanso ka kasance cikin farin ciki har karshen rayuwarka koda bana tare dakai. Shiru shima yana kallonta yace kece farin cikina... zatai magana taga agogon dake manne jikin bango tace ai lokacin tashin naka yayi, ya mike itama ta mike domin yi masa rakiya. A hankali take binsu a baya har suka iso bakin titi, haneefah ta tsayar da mai adaidaita sahu yusuf ya shiga sannan ta koma. Ganin haka yasa momy tabi bayan a dai daita sahun daya shiga har taga inda ya tsaya wato airport. Juyawa tayi ranta abace tana kissima hukuncin da zata yankewa yusuf da wadda tagansu karo na biyu dashi *Dr HANEEFAH* 👩🏼19 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tafiya take amma tunanin yusuf take da auran shi har ta iso gida. Aunty muhibbat ta iske a falo take tambayarta har ya tafi? Haneefah ta amsa da eh. Shiru tayi ta samu guri ta zauna tana tunani, aunty muhibbat ta kura mata ido tace meya faru? Haneefah ta dago ido cike da hawaye tace yayi aure! Ta bata labarin yadda abin yake da yadda suka rabu, ta qara da cewa wallahi ni yanzu shi nafi tausayawa baki ga yadda ya canza ba duk yabi ya dami kanshi. Aunty muhibbat tace Allah sa haka shine mafi alkhairi agare ku, sannan yanzu lokacine da zaki dada janshi a jiki kibasa kulawa ta musamman, duk da kuna son juna wasu mazan in suka dandani zumar amaryansu zasu manta da wata a waje, ki kwantar da hankalin ki sannan lokacine da zaki dage da addu'a kan wannan lamari. Haneefah da tuni ta fara hawaye tace wlh yusuf bazai iya rabuwa dani ba, ni matar shi ce, shi mijinane, we belong to each other..... cike da dariya aunty muhibbat ta katseta da cewa mai da wukar hajiya, an daura muku aure shaidu muke jira. Haneefah tace kullum haka yake cewa, makaranta muke jira na kammala. Ta tashi ta qarasa ayyukanta na cikin gida, tayi girki ta koma daki ta dauko qur'ani tana karantawa har aka kira sallah azahar. Bayan ta idar aunty muhibbat tace yaushe kikai alwala da har zaki tashi kiyi sallah? Aini da alwala nake zama. Aunty muhibbat tace duk surutun da kikai dazu alwalan ki bai karye ba? Haneefah tace wayace surutu yana karya alwala? Abubuwan da suke karya alwala shine; yin iska, yin bayi, fisari, suma, nauyayyan bacci, kiss da sauran su... amma banji yadda surutu ke karya alwala ba, sai dai in mutum baya iya rike najasar da zata fito masa daga jiki misali in mutum baya iya rike iska, sannan in yana hira baisan sanda zayyi ba to wannan rike alwala bazayyu masa ba saboda lalurarsa. *SAKAMAKO (LADAN) ZAMA DA ALWALA* Daga Abdullahi Ibn Buraidah daga Babansa Allah shi kara masu yarda yace: Watarana da safe Manzon Allah SAW ya kira Bilal RA da me ka rigayeni a Aljannah, na shiga Aljannah sai naji karar takalminka a gaba na, sai Bilal yace Ya Manzon Allah SAW da dai ban sanni da wani abu ba sama da yin Sallah rakao'i biyu kuma dazarar alwala ta warware nike sabuntawa, sai Manzon Allah SAW yace itace. [ Ibn Khuzaima ] Ko shakka babu zama da alwala na kare bawa daga sihiri in sha Allah. Ya Allah ka azurtamu da kasancewa cikin alwala a tsawon rayuwarmu ameen. Suna cikin tattaunawa yusuf yakirata ya sanar mata sun sauka lafiya amma ta dadana nuna mishi rashin jin dadin baije gida ba. Ko sauraron ta bayyi ba ya katse wayar. **** Kwance take tana fuskantar kofar shigowa daki, gidan da wadda suke ciki baki daya sun fice mata arai. Tunanin barin gidan take. Tasan a baya tana son yusuf amma yanzu gaba ki daya ya fice mata arai tun kafin auren su, inba dan mum ba ai wannan wulakanci ne. Ace yau watanta kusan uku bata sashi a ido ba... zan bar gidannan amma nayi alkawari bazaka auri zabin ka ba ko wacece ita. Wayarta taji yana ringing ta daga hello mum ina kwana. Daga daya bangaren tace ya kike baby? Lafiya lau mum, mum nagaji da gidannan wlh nifa banyi tsammanin burin ki zai cika ba. Mum tace wai har yanzu ba ciki ne ko kinje scan suka ce macece? Takaicine ya kama rahma tace mum tun da nazo gidannan ban sashi a ido ba bale maganar ciki ni gaskiya nagaji. Cikin rarrashi tace kada ki damu namiki alkawarin zuwa gobe zai dawo, yanzu zan kira yaya in sanar da ita. Bata kira amsar taba ta katse wayar. Momy na office tana ayyuka kiran yar uwarta ya shiga. Bayan sun gaisa mum tace haba yaya, ni nayi tunanin rahma zata fi samun kwanciyar hankali yasa na baku ita amma gashi har yau wata uku bata sa mijinta a ido ba? Nidai nayi mamaki, tunda abin yazama haka gobe zanzo in tafi da ita. Tana kaiwa nan ta katse wayar. Momy ta rasa mezatayi, wato rahma har ta sanar da mamarta. Kiran umma nusaiba tayi tace haba nusaiba, kinsan ni maison kwanciyar hankalin zuri'ar ki ne. Ki zauna kada ki dawo, nasan yadda zan bullowa al'amarin. Bayan sunyi sallama takira yusuf tace lallai yabiyo jirgin yamma yazo kada ya kuskura ya kwana a abuja. Ya amsa mata da insha Allah zaizo. Cike da faduwar gaba ya iso ya sameta zaune a falo. Ko gaisuwarsa bata amsa ba zata fara magana yayi saurin cewa momy dan Allah kiyi hakuri, nasan na bata miki rai amma na miki alkawarin hakan bazai kuma faruwa ba. Shiru tayi tana kallonsa bata ce komai ba tace shikenan tashi ka tafi. Duk da yasan ba cira yayi ba amma yana addu'an Allah sa ta sassauta masa. Rahma tana kwance a falo tana kallo ya shigo da sallama. Ko kallonsa bata yi ba bale ta amsa. Jin shiru bai fito ba yasa ta bishi. Waya yake da haneefah idanunsa a lumshe da alama yana jin dadin wayar. Kare masa kallo tayi tsaf sannan taja dogon saki ta fice. Haneefah tace next month fa zamu shiga last semester. Tsaban dadin jin maganarta baisan sanda ya mike ba yace Allah dear? Wayyo mun kusa kasancewa tare. Murmushi tayi tace Allah kaimu rai da lfy. Nan suka soma hiran yadda zasu tsara auren. Bayan sun kammala wayar yake tunanin yadda zai bullowa momy da maganar. *** *** *** Tun daga wannan lokaci kowani weekend yusuf zaizo kano amma babu abinda ya taba shiga tsakaninsa da rahma. Ita ko kallonsa bata kaunar yi bale ta kaiga su tsaya suyi hira. Haka shima baya shiga tsabgarta har tsawon wata biyu. Daga nan hankalinsa ya karkata kan auren sa da haneefah, yadda zai dauko da maganar. Yau lahadi dukkanin su suna gida. Ya shiga bangaren mahaifinsa domin gaishe shi ya tarar da momy. Bayan sun gaisa mahaifin nasa ya fahimci kamar da magana a bakin dan nasa yace yusuf kamar kana da abin cewa. Yace eh abba dama wadda muke tare ne tana shirin gama makaranta nan da watanni biyar shine nake son aje neman mun auren ta... Momy ce ta daka masa tsawan da yasashi yin shiru. Har kana da bakin cewa zaka kara aure? Yaushe kayi auren wlh yusuf ka kiyayeni kada kaga ina daga maka kafa. Abba yace tunda ke zaki daura masa auren saiki hana in gani. Tun da farko yana da wadda yake so amma kika dage sai ya aureta, saiki bari shima ya auri wadda yake so yusuf Allah tabbatar mana da abinda yafi alkhairi, anjima zan sami abokaina da sauran yan uwa insha Allah gobe zamu je nema maka aure, saika sanar da ita zasuyi baki. Cike da farin ciki ya amsa da toh ya tashi ya fice. Momy ma ficewa tayi ranta a bace ta nufi sashenta. Zama tayi bakin gado tana tunanin maganan mijinta. Alhaji sai dai kai hakuri amma wlh ko bayan raina yusuf bazayyi zaman aure da kowa ba sai rahma *Dr HANEEFAH* 👩🏼20 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Yusuf yana fita ya nufi sashin sa cikin sauri ya kira haneefah yana sanar da ita yadda sukai da abba, itama ta nuna farin cikinta. Da yamma ya dauki hanyar gurin aikinsa. Yasan momy na fishi dashi amma yasan yadda zai shawo kanta. Haneefah ta sanar da umma, umma ma taje ta sanar da abba. Kwarai sunyi farin ciki, a sannan abba ya sanar da dangi su biyu da makocinsa akan zuwan bakinsa. **** **** *** Su aunty muhibbat da humaira sune kan gaba wajen shirye shiryen taran baki. Inna ko lekowa bata yiba ita a yaranta sai tura jabir tayi ya kalle musu wani irin mutane zasu zo. Haneefah ko tana gidan aminiyarta hadiza anata ta hiran yadda auren zai kasance. Zaune momy take tana tunanin yadda zata bullowa lamarin. Rahma ta shigo ko sallama babu ido cike da hawayen munafurshi tace momy da gaskene yau yusuf za'akai kudin auren shi? Cike da tausayi momy tace zo diyata. Tazo ta zauna kusa da ita. Kada ma ki tada hankalinki namiki alkawarin ba'ai aurannan ba koda bana raye. Toh momy ki hana tafiyar mana! Murmushi momy tayi tace abbanku ya dage yanzu, zan kyale suje amma wallahi aure dai bazai aurota ba. Murmushin jin dadi rahma tayi ta tashi ta fice. Aisha dake sauraronsu tayi maza taja da baya ta koma inda ta fito. Sai data tabbatar rahma ta tafi itama ta fita ta nufi sashin su... a daki ta tarar tana waya kan ta gama rusa maganar auren yusuf. Ba shiri aisha ta koma daki ta zauna bakin gado. Wannan wani irin son kai momy take son aiwatar wa?? In aka rusa maganar auren yayanta shinya zai kasance? Tabbas tasan yadda yake son haneefah ! Tunani ta tsaya yi ta yadda zata nemi mafita. Inta sanar da yusuf hankalinsa zai dada tashi, bata isa ta tunkari momy ba domin yadda itama ta dau zafi, mafita shine Addua. Ta daga hannu sama tana rokon Allah ya duba musu wannan lamari. Yadda aka tarbesu sunji dadi sannan abba yabada haneefah ga yusuf, an bada sadaki ranar aure kuma wata biyar aka sa, dai-dai da gama maarantar ta da wata biyu kenan. Labari yaje kunnen masoya. Babu wadda yakai yusuf murna a wannan rana . Tun daga wannan rana ya fara irga ranar auren shi. Su inna bakin ciki sun rasa inda zasu shiga ganin yaron daga gidan masu hali yake. Abba da umma an fara shiri ba kamar umma ba, yadda take ji da haneefah. Haka sauran yan uwa dukkaninsu suna murna tare da Allah nuna musu wannan rana. ***** ****** ***** _BAYAN WATA BIYU_ Haneefah jinta take complete. Komai yazo mata dai-dai. Babban burinta takasance ta kammala karatu tana tare da abar kaunarta. Haka abin yake ga yusuf. Yana bawa rahma kulawa. Zaune take ta baje takardu tana hira. Taji wayarta na ringing taga matar Dr Mubarak na kiranta tace nashiga uku nidai bani da kirki. Ta daga cike da kunya tace dan Allah kiyi hakuri kullum inason kiranki Allah bai bani iko ba. Barrister ramlat tace ba komai haneefah kina lafiya? Lafiya lau, ya Dr da yara? Duk suna lafiya. Barrister tace dama nakira in sanar dake na haihu gobe suna amma dan Allah wannan karon kizo gidana. Haneefah tace Allah raya bisa tsarin addinin musulunci, zanyi kokori insha Allah inzo, yauwa haneefah nagode yanzu zan tura miki address din gidan nawa. Haneefah taje ta gayawa umma tace Allah kaimu goben sai kije . Washe gari haneefah ta tashi da matsanancin faduwar gaba, so biyu wannan abin ke faruwa mata. Na farko haduwarta da yusuf sai yanzu na biyu. Ko wanni abu zai faru Allahu a'alam. Suna waya da yusuf amma kwata-kwata jinta yake wani iri yace dearie lafiya? Haneefah ta bashi labarin abinda ke damunta. Shima yace abinda yake fama dashi. Cike da mamaki tace Allah sa da mu da alkhairi. Yanzu kina ina? Yusuf ya tambaya. Zanje anguwane. Ya dubi agogon hannun sa yace turomin address din gidan da zaki. Haneefah tace meza kai? Yace kedai turomin. Ta katse wayar ta tura masa. Yusuf dake aiki ya tattara kayan shi ya nufi gida. Bayan yagama shiri ya dauki mukullin mota ya dauki hanyar kano. Misalin karfe daya da rabi haneefah ta sauka bakin gate da ta tabbata shine gidan. Ta sallami mai a daidaita sahu ta tsaya tun daga bakin gate tana karewa gidan kallo tace mashaa Allah . Ta kira barrister tace ta iso. Duk da jama'an dake gidan hakan baisa ta fito ta dauki haneefah ba. A tare suka shigo ta zaunar da haneefah ta mika mata baby. Barister ta shigo da wata mata ta nuna mata haneefah. Suka karaso wannan mahaifiyata ce cewar barrister . Cike da ladabi haneefah ta gaisheta. Bayan sun gaisa tagabatar mata da sauran yan uwanta. Matuka haneefah taji dadin karrawa da sukai mata. Bayan awa biyu haneefah ta tashi tace zata tafi. Godiya suka mata har bakin gate suka rakata. Tana fita zata tari abin hawa taga motar yusuf. Cike da mamaki ta qarasa ta bude tashiga tace dama kana garine? Tun fitowarta ya kafa mata, tayi kyau sosai. Yace yanzu zuwana. Ya tada mota suka soma tafiya. Ganin ya dau hanyar gida tace zan biya gidan hadiza in amshi sako, ya nufi inda ta fada masa. Tuki yake ko magana bai mata ba har suka iso gidan yayi parking. Ta lura da fuskarsa a daure shiyasa ko magana batayi masa ba. Zata fita ya kulle motar. Ta juyo suka hada ido ganin idanunsa sun kada sunyi ja ga hawaye da ke kokarin taruwa a idonsa. Yace dearie bana jin dadin zuciya ta bansan meyake son faruwa dani ba. Kwarai ya bata tausayi yadda yake magana. Ta danne nata abinda take ji a zuciya tace babu abinda zai faru sai alkhairi, ka kwantar da hankalin ka. Babu abinda zai faru. Ciro wayarsa yayi yace kiyi hakuri abinda zan miki. Bata ce komai ba ya jawota kusa dashi kansu a hade ya dauke su a hoto kusan kala uku sannan ya dauketa ita daya. Karban wayan ta yayi ya tura mata hotunan da sukai da nashi shi daya. Abubuwan da yakene yasa ta fara zubar da hawaye. Ganin haka yasa yace pls dear kidaina haka kawai yau najini wani irine. Mika mata wayar yayi yace next year war haka kina dauke da babyn mu.... wayar ta amsa zata fita tace ni kabudemin kofa cikin shagwaba. Ya koikoyeta tasa dariya tace baka iya bama. Haka har suka mantar da junansu abinda suke ji yayi mata sallama kan anjima da dare zai dawo. Tana shiga gate din harta iso bakin falo zata shiga taji an bude ko fa. Wadda taganine yasa bugun zuciyarta ya tsananta wato mahaifiyar yusuf. *Dr HANEEFAH* 👩🏼21 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tsananin fargaba da tsoro ya hana haneefah ko da taku daya. Ganin ta tabbatar momy ce ta sunkuyar da kanta kasa. Har kasa haneefah ta durkusa gaida momy, da fara'a ta amsa tare da cewa inason magana dake. Nan da nan zuciyar haneefah ke bugawa da sauri. Ta musu jagora zuwa ciki. Babu kowa a falon kuma tayi mamakin ganin falo a bude. Guri momy ta samu ta zauna, sannan ta karewa haneefah kallo. Yarinya qarama amma tana son birkita rayuwar familinta. Momy ta fara magana da cewa nasan kin sanni, ko da a hoto ne yusuf zai nuna ma ki ni amma niko bansan ki ba saida kika so raba kan dana sannan na nemi sanin wanene ke. Yanzu zuwan shi amma ko matarsa baije ya gani ba yazo inda kike. Toh inaso ki bude kunnen ki kiji abinda zance miki. Ina so kimin alkawarin abubuwa biyu: na farko ki janye aurenki da yusuf, na biyu ki fita arayuwarsa ma'ana ki yi nesa dashi inko ba haka ba zan tsine mishi, kinga ko bazai amfane ni ba nima bazai amfane niba... amma in kikamin alkawarorinnan biyu to tabbas masoyinki zai kasance cikin albarkana har tsawon rayuwarshi. Hadiza dake bacci taji alamun mutane ta tashi ta nufi falo. Abinda kunnuwanta suka jiye mata ne yasa ta qaraso da sauri ta durkusa gaban momy tace Dan Allah mama kiyi hakuri, wlh suna son juna. Haneefah tana da kirki bazata cutar miki zuria ba. Kada kira ba soyayyar da Allah ya hada. Momy ta miki tace nidai nagama magana, muddin tana so masoyinta ya gama da duniya lafiya toh tayi abinda nace tana kaiwa nan tayi ficewarta. Haneefah tunanin tane ya tsaya, ta nemi koda yawu abakinta ta rasa. Ta rasa tunanin me zata yi. Murya a dashe ta cewa hadiza ki tasheni a mafarkin da nake. Hadiza dake kuka ta qaraso gurinta ta rungumeta tace haneefah dan Allah na rokeki da girman Allah kada ki tada hankalin ki, ki dauka a matsayin kaddara ne ... bata qarasa ba taji wayar haneefah na ringing. Haneefah ce ta daga wayar tana kallon mai kiran. Tace yusuf ne hadiza a sannan ta tuno da kalamun momy. A tayi rejecting kiran, ya qara kira. A sannan haneefah ta fashe da matsanancin kuka. Kuka take kamar ranta zai fita. Hadiza na tayata. Kimanin mintuna arba'in suka dauka haka. Nan take haneefah ta tuno da nasihar yusuf: A matsayinka na musulmi, a koda yaushe, ka shiryawa zuwan kaddara da zata iya samunka, mai kyau ko marar kyau, ta alkhairi ko ta sharri. Idan ta alkhairi ta same ka, sai kayi godiya ga Allah, idan kuma ta sharri ce ta same ka, to sai kayi hakuri. wannan shi ne mataki, kuma matsayi na zama cikakken mumini. Sannan godiyarka da hakurinka akan nau'ikan kaddarori biyu da suka same ka, suke nuna cewa dukkanin al'amuranka alkhairi ne. Babu wanda ke samun wannan matsayin a cikin Musulmai sai Mumini. Wannan shi ne ma'anar fadin Annabi s.a.w. "Abin mamaki, abin sha'awa ga al'amarin mumini, hakika dukkanin al'amarin sa alkhairi ne, babu wanda ke samun haka sai mumini; idan abin farin ciki (alkhairi) ya same shi, sai yayi godiya (ga Allah), sai hakan ya zama alkhairi a gare shi, idan kuma abin bakin ciki (sharri) ya same shi, sai yayi hakuri, sai hakan ya zama alkhairi a gare shi ". Imamu muslim ne ya rawaito. Ya Allah kasa mu sifantu da wadannan sifofi na mumini. Allah kasa mu zama muminai. Haneefah ta qara fashewa da kuka tana mai ambaton Allah. Momy ko tana isowa gida ta nufi sashin su yusuf. Kwance ta same shi a falo yana tunanin meye dalilin rashin daga wayarsa da haneefah tayi. Ganin momy yasa ya tashi ya zauna. Bata amsa gaisuwar shiba tace inaso kaban aron hankalin ka. Da farko inaso ka janye maganar auren ka. Ba shiri yusuf ya dago kai Momy taci gaba inaso ka fidda yarinyar nan a rayuwar ka da duk wata mace domin rahma har abada itace taka. Abu na karshe inaso ka samu mahaifin ka adarannan kace gobe ya sanar dasu ka fasa. Umarni na baka in ko kaki, Allah ya isa tsakanina dakai ka nemi wata uwar ba ni ba. Yusuf idon shi ya kada yayi ja. Kallo daya zaka mishi kaga tsananin tashin hankali a tare dashi. Maganar ummansa ya tuno. Inbai rabu da haneefah ba zata tsine mishi? Inta tayi hakan meye amfanina a duniya? babu ya bawa kanshi amsa. Tashi yayi ya shige daki ya kulle da makulli sannan ya kwanta kan gado. Tashi ya kuma yi ya dafe kansa dake mugun sarawa. Inna lillahi wa'inna ilaihi rajiuun ya soma furtawa a hankali ya soma hawaye. Yana bude baki yace Alhamdulillah! Tashi tsaye yafara kai koma. Ya sake zama bakin gado ya dauki wayarsa yashiga hotuna yafara kallonta. Take tun haduwarsu har zuwa rabuwansu abin yake zuwa mishi. Zuciyarsa yaji yana tafasa daganan zuciyarsa ta kare ya fashe da matsanancin kuka. Kuka yake yana ambato Allah har aka kira sallah la'asar. Tashi yayi yashiga yayi wanka sannan yayi alwala ya fito. A daki yayi sallah. Sujjadarsa yake sanar da mahaliccinsa halin da yake. Bayan ya idar ya dauki qur'ani yafara karantawa. Har aka kira sallah magriba. Sallah ne ya tada shi. Bayan ya idar ya sake ci gaba da karatunsa domin baisan abinda zayyi da yafi haka ba. Ita ko haneefah tunanin mahaifanta dayan uwanta take, muddin suka ganta cikin wannan hali hankalinsu zai tashi, ita ko batason hakan ta faru. Bayan ta idarda da sallah tana zaune tana sharar hawaye hadiza tazo kusa da ita tace haneefah kiyi hakuri, babu abinda zamuyi da yafi haka. Murmushin karfin hali tayi tace bani da mafita daya wuce haka. Amma inason kisan ina matukar bukatar addu'a. A hankali tace momy zanbi umarnin ki, nayi alkawarin barin rayuwar yaronki har abada. Ta mike ta tattara kayanta tayiwa hadiza sallama kan sai sun hadu gobe. *Dr HANEEFAH* 👩🏼23 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Ganin haka yasa matafiya suka tsaya ganin hatsarin da ya auku. Ganin yadda motar yusuf ya zamto babu kyan gani babu wadda yayi tsammanin akwai mai rai ciki. Dakyar suka samu suka ciro shi. Suna cireshi motar ta kama da wuta. Ganin jini kota ina zuba yake yasa wani bawan Allah yace ataimaka asashi motarshi zuwa asibiti domin tabbatar da yana da rai ko ya mace. Gari mafi kusa suka nufeshi wato kaduna. Emergency akashigar dashi. Bayan anyi bincike aka gano yana da rai amma yana bukatar jini sosai, ko neman wadda yakawo shi basuyi ba suka sa masa jini domin ceto ransa. Bayan likita ya fito ya nufi gun mutumin da ya kawo sa yace yabisa office. Likita ya kalleshi yace wadda ka kawo yana cikin hadari sosai domin mun kasa binciken meya same shi sai mun qara masa jini. Yanzu dai ga kudin jinin ka biya nanda awa daya zamu soma binciken inda yaji ciwo sosai. Mutumin ya numfasa yace Alhamdulillah yana da rai, amma likita accident ne, niba kowansa bane. Likita yace baku samu wayarsa ko wasu abubuwan da za'a samu cikekken bayani akan saba? Aa likita motar ma kamawa tayi da wuta, zan biya dukkanin abinda kuke bukata har Allah sa ya farfado ya sanar da mu daga inda yake. Likita ya numfasa yace zamuyi iya kokarin mu, kaima Allah biyaka abinda kayi. Sukayi sallama ya fice domin biyan kudin jini. **** Haneefah ta samu guri ta zauna can nesa da inda za'a ganta. Tana zama taji gabanta yayi mugun faduwa, nan take yusuf yafado mata arai. Tunani take ta fitar dashi aranta kwata-kwata ta daina tunaninsa, a hankali tace bazan iyaba. Nan da nan taji wani irin daci a zuciyarta, yanayine wadda bazata iya fassara yadda ta tsinci kanta ba. Ta dago ido tana kallon inda take, nan take taji garin kano ya fice mata arai. Tsintar kanta tayi tana cewa ya Allah kabani ikon barin garinna, nayi nesa da shi. Hawaye take sosai Hadiza ne ta tsaya nesa da ita tana kallon aminiyarta, kwarai ta matukar tausaya mata domin tasan yadda take son yusuf amma babu abinda zatai daya huce hakuri. Hawayen da ke zubo mata ta share tare da nufo inda haneefah take. A hankali ta dafe kafadarta tace inata nemanki ashe kinanan. Haneefah waigo a hankali suka hada ido da aminiyarta. Murmushi ta sakar mata tace inanan ina zaune, nasan zaki zo. Hadiza ta share hawayen haneefah tace nasan dole abin yadame ki amma haneefah ki kwantar da hankalin ki kiyi addu'a, addu'a ba ta faduwa kasa. Ko a baka yau, ko a baka gobe, ko kuma a baka abin da ya fi wanda ka roka, addu'a makamin mumini ce 'yar-uwa... Don haka muyi riqo da Addu'a kuma mu dogara da Allah ko yaushe. Haneefah tace insha Allahu zanyi amma ba lallaine in manta abin cikin sauki ba. Hadiza tace nasani, exam namu fa sati mai zuwa ki kwantar da hankalin ki kiyi karatu. Allah zai kawo miki wadda ya fishi. Haneefah ta tsaya kallon kawarta tace wadda ya fishi?? Zamanin yanzu kina tunanin zan samu kamar yusuf, mai hankali da nutsuwa, wadda zai so ni tsakani da Allah sannan ya kula dani? Wadda zai kasance kullum zai sakani farin ciki haba hadiza ya kike tunanin zan samu wadda zai maye gurbin yusuf, nidai nasan nayi rashi, bansan mesa momy bata so na ba, bansan mesa ta rabani da danta ba... bana jin zan ji sha'awar tarayya da wani matsayin miji. Hadiza dake yi mata kallo tausayi tace nasan radaine yasa kike fadin haka, amma duk da haka kada kibari yazamo wannan tunani ya dauwama cikin zuciyarki. Shin kinyi tunanin haduwa da yusuf ne? Ba shirin ki bane sannan ba shirin yusuf bane, momy ba itace ta rabaku ba Allah daya hadaku shi ya rabaku , hakan na nufin akwai boyeyyen sirri cikin lamarin, ki dage da addu'a insha Allah komai zaizo ya wuce. Kuma ai agun Allah kike tsammanin abu ba gurin dan adam ba. Haneefah tayi tana nazarin maganganun kawarta tace hakane, amma wlh inason barin gari. Hadiza tace ina zaki? Duk inda Allah ya kaini amma nidai banason ci gaba da zama anan. Hadiza tace to ko zakiyi applying scholarship? Haneefah ta kalleta tace agarinnan wa nasani dazai shigemin gaba duk yaran manya ne. Duk da haka haneefah ki jarraba in Allah yayi da rabonki sai ki ga an dace. Haneefah tayi shiru tana jin kawarta. Daga ido tayi taga hadiza tana hawaye haneefah tashiga share mata tace yi hakuri mana, kukan ya isa aini na hakura. Hadiza tace toh dan Allah ki kwantar da hankalin ki. Murmushi ta mata suka tashi suka nufi inda ake tutorial. Yinin wannan rana haneefah babu abinda take fahimta, bata ci komai ba haka ta koma gida. Abba kasa yiwa haneefah magana yayi lokacin da taje gaida shi. Domin yarinyar ta soma bashi tausayi. Umma ce ta sanar da ita zuwan abban yusuf, anan ta tabbatar cewa ta rabu da yusuf. Tunanin inda zata je ta fara domin batajin zata rayu a inda zata rika jin motsin yusuf, gashi babu wadda tasani a garuruwan Nigeria sai auwal dake abuja, bazata soma tafiya ba saboda inda yusuf ke zama ne. Nan ta tuno da shawarar hadiza kan tayi applying scholarship. Haneefah ta canza, ba kamar itama ba, ta rage yawan dariya, batacin abinci sosai, bata iya karatu kullum tana daki, ko asameta tana karatu kota lumshe ido tana addu'a. Duk wadda yaji labarin abinda ya faru saiya tausaya mata. Itadai jarabawa tayi amma batajin zata wuce. Cikin sati biyu ta rame, maganar tama ya canza. Ya zamto babu ruwanta da kowa da komai. Zaune take gaban abbanta tana sauraronshi. Yace haneefah meke damunki? Mesa bazaki sake ranki ba? Fadamin duk abinda kikeso muddin baifi karfina ba zan miki. Kanta sunkuye tace abba inason inyi applying scholarship ne, ina neman izininka, nayi maka alkawarin tsare mutuncina ka yarda dani abba. Cike da tausayi abba yace na yarda dake haneefah sai dai banyi tsammanin zaki samu ba amma duk da haka kije bazan hanaki ba. Allah sa hakan shi yafi alkhairi. Tace toh abba nagode. Taje ta sanar da umma yadda sukai da abba. Fatan alkhairi tayi mata sannan ta hada mata qualifications nata ta shirya ta tafi ministry of health. Inda ta tabbata nan ake karban takardun. *Dr HANEEFAH* 👩🏼22 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Haneefah tana shiga gida bata tsaya ko inaba sai gun ummanta. Zaune ta sameta kan sallaya tana lazimi. Ganin haneefah cikin irin yanayinnan yasata yin fatiha. Umma cike da kulawa tace meya faru haneefah? Haneefah tayi murmushi tace umma ki kwantar da hankalinki, kamar yadda nazo da karfin gwiwa ki saurareni. Sanin kankine cewa banason abinda zai tabamin ke harta kaiga yana damunki, nasan damuwata na daya daga cikin abinda zai saka ki cikin damuwa, amma da yaddar ubangiji bazan bar nawa damuwar ya gusar da farin cikin mu ba. Nan haneefah takwashe duk abinda sukai da momy ta sanar da ita. Haneefah taci gaba umma narasa tunanin mezanyi inji dadi, umma nasan rayuwata zata canza na lokaci kadan amma kuyi hakuri da hakan. Na tabbata wannan jarabawane Allah ya aikomin, ki tayi da addu'a Allah bani ikon riketa hannu biyu. Umma ina bukatar addu'a. .. Nan ta fashe da matsanancin kuka. Umma karfin hali tayi ta soma rarrashinta, tabbas sai yau nasan kina aiki da ilmin ki. Allah baki miji nagari. Kuka take kan cinyar mahaifiyarta har aka kira sallah magriba. Daganan haneefah tashiga daki ta kulle. Umma tace su amal kada kowa ya sameta su kyaleta. Bayan abba yadawo daga sallah umma taje ta sanar da shi abinda sukai da haneefah. Abba baice komai ba illa Allah sa hakan shi yafi alkhairi. Zaune take kan sallaya tana tuno yusuf, abin kamar a mafarki yau saura wata biyu aure aka fasa. Murmushi tayi tace Allah na nasan kana min shiri abinda yafi alkhairi agare nine. Insha Allah zan kasance mai addu'a domin wannan alkhairin ya iso gareni. Kallon wayarta tayi ta dauka tace nasan kaima momy taje tasameka, muyi hakuri wata qila hakan shi yafi alkhairi agaremu. Tadauki wayar ta kashe tasa a drawer sannan ta dauki qur'ani ta fara karantawa. ***** ***** Mahaifinsane yace yusuf kana da hankali kuwa? Wata biyu ya rage kace ka fasa aure? Yusuf yace abba ban taba neman wani alfarma ba, amma ina rokonka wannan karon kamin abba. Abba cikin bacin rai yace zanje in sanar dasu amma ka sani alhakin wannan yarinya bazai barka ba. Tashi ka bani wuri. Yana tashiwa ya nufi gun mahaifiyarsa ya sanar da ita yadda sukai da abba sannan yace momy ki yafemin, inban kasance da albarkan kiba babu amfanina a duniya, zanyi duk abinda kika sani amma banason jin wannan kalamai ya karasa maganar yana hawaye Cike da tausayin danta tace ba komai tunda kayi yadda nace. Allah yi maka albarka. Yace ameen, gobe zan fita da safe zuwa abuja, zuwana nagaba zan tafi da rahma. Ya tashi ya fita. Tunanine fal cikin zuciyar momy, shi namiji kenan ya macen zata kasance? Yana fita ya nufi dakin aisha. Kusa da ita ya zauna yace aisha kitayani addu'a. Tace yaya lafiya? Bai bari taga idanunsa ba yace ba komai ya fice. Lap top nasa ya jawo yayi uploading dukkanin hotunan haneefah. A hankali yace Allah ne ya hadamu kuma shizai rabamu. Umma zanyi miki biyayya amma nasan haneefah alkhairi ce agareni, zanci gaba da addu'a har Allah ya kawo min ranar da zan mallaketa. Murmushi yayi ya tashi yayo alwala ya shiga gayawa Allah halin da yake ciki. Haka haneefah takasance, tana karatun qur'ani tana kuka, daga baya ta tashi ta fara jero nafiloli. Yadda suka ga dare haka sukaga rana, babu alamun bacci cikin idanunsu. Basu biyewa tunaniba domin babu mafita, Allah suke gayawa lamuran su. Haneefah ko karatu takasa sai addu'a. Da asuba ta tashi ta idar da sallah sannan ta fara karatun qur'ani har gari yawaye. Misalin karfe bakwai ta shirya ta fito. Ta samu umma da sauran kannenta suna breakfast. Ta gaida umma sannan ta dauki kofin shayi ta hada tana sha. Shan shayi take amma bajin dadinsa take ba, kada umma ta damu kan bataci komai bane take sha. Amal ta dubeta tace yaya haneefah kada ki damu, kici gaba da addu'a Allah zai sauya miki abinda yafi alkhairi. Bintu ta amsa tace zamu taya ki addu'a babu komai insha Allah. Murmushi tayi tace ko saboda ku bazan damu ba, nagode da kulawar ku kannena. Umma dake kallon su ta hadiye hawayen da suka ciko mata tace Allah yi muku albarka, ya dada hade kanku. Dukkansu suka amsa da ameen. Haneefah ta musu sallama ta fito ta fita makaranta. Bata je gaida abba ba saboda ba gidan su ya kwana ba. Tana isowa bakin titi ta tare adaidaita sahu ta shiga. Tunda suka soma tafiya babu abinda take banda zubar da hawaye. Jin gine jikin karfe, sun tsaya traffic. Adai dai inda suke tsaye shima yazo ya shiga. Rungume sitiyarin motan sa yayi yana hira abasu hannu, ya juya inda take. Jajayen idanunsa suka sauka a kanta. Kallon ta yake tana zubar da hawaye shima ya soma taro su idanunsa. Kada ta jawa kanta kallo yasa ta dago domin goge hawaye suka hada ido. A sannan hawayen idanunsa suka sauko, ya goge hawayensa sannan ya mata nuni da tayi yadda yace. Ba musu tayi sannan ya girgiza mata kai yana murmushi, itama murmushin ta soma. Anan aka basu hannu sunaji suna gani ko magana sun kasa yiwa juna suka rabu. Haneefah ne tunaninta ya karkata ina zaije da safennan? Abuja ta bawa kanta amsa. Take tashiga yin addu'a Allah kaishi lfy Tunda yaganta ya kasa nutsuwa. Mesa momy zata mishi haka? Wani hali haneefah take? Wani matsayi haneefah zata dauke ni? Na yaudareta? Aa nasan bazata fassarani da hakan ba. Tausayinta yaji ya lullubeshi. Yayi nisa cikin tunani, tuki yake amma baya fahimtar abinda ke gabansa. Saida yazo dab yaga babbar motar da ke gaban sa, kokarin kaucewa mai motar yake wajen canza hanya shima mai motar ganin yusuf bai bashi hanyan ba yake kokarin bin gefensa domin kauce mishi. Guuuufffff!! Kake jin haduwan mota, ganin haka driver babbar motar ya rikice tukin ya kubce a hannunsa ya tura yusuf kan motar dake bayansa. Mummunan hatsarine ya auku domin manyan motoci biyu suka sa motar yusuf a tsakiya. Kallon motar zakayi ka tabbata wadda ke cikin baya raya. *Dr HANEEFAH* 👩🏼24 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Kusan mutum goma ta tambaya kafin aka nuna mata ofishin. Knocking tayi aka bata izinin shigowa. A sanyaye ta shiga ta zauna. Bayan ya gama rubuce rubucensa ya dago ya kalleta yace ko akwai taimakon da zai mata. Haneefah ta sanar dashi yace ai lokaci ya wuce sai dai shekara mai zuwa. Ta tashi tafita jiki ba kwari. Can nesa inda ake parking motoci ta jingina jikin wata bishi domin jirine ke debanta dalilin yunwarda ta addabeta. Jira take tadanji sauki saita qarasa gida. Dr waccan ba haneefah bace, Dr Mubarak ya juyo inda aka nuna masa. Itace ko amma ko me takeyi anan? Barrister tace muqarasa mugaisa da ita sai mu wuce. Haneefah tadan fara jin sassauci tashi tayi ta soma tafiya sai kuma ta kasa, ganin zata fadi yasa ta koma ta zauna. A hankali take zubar da hawaye tace sai shekara mai zuwa, bana kaunar qara koda wata dayane agarinnan .... bata qarasa ba taji ana mata sallama. Saurin goge hawayenta tayi ta juyo domin amsa sallama amma tuni sun gano. Murmushin karfin hali tayi ta gaishe su. Cikin damuwa barrister tace haneefah meya sameki? Me kikeyi anan? Haneefah ta qara murmushi tace wlh yanzu nake son komawa gida. Ganin tana kame kame yasa barrister tace dan Allah haneefah fadamin gaskiya meya sameki? Ganin zasu takurata ne yasa tace nazo summition ne na tarar anyi closing sai next year, shine na tsaya anan domin jirin da nake ji inya lafa zan kama tafi gida. Dr yace inga takardun naki? Ta mika masa ya kalla. Barrister tace kiyi hakuri, in wannan ne matsalan bari in shiga in kara confirming kinsan wasu lokutan basa sauraron mutane. Zo mushi ga. Barrister ta rikota suka shiga. Bayan sun gaisa da mutumin ya nuna cewa ya taimaka mata inda guri. Mutumin yace Dr sanin ka danai yasa bazan maka jayayya ba, wlh sai dai tajira next year. Barrister tace ka fadi ko nawa zan baka indai sunanta zai fita, nasan bakuyi placing sunayen su ba. Mutumin yace haba madam, Dr ya wuce haka agurina. Ranta ne ya baci ta juya ta kalli haneefah tace kijiramu a waje. Nan haneefah ta juya ta fice. Bayan fitarta tace Dr mezai hana ka biya mata tunda Allah muke roko ya nuna mana randa muma zamu faranta mata rai. Dr yace kin rigani fadane nima abinda nakeson. Ya dubi mutumin yace alfarma muke nema, ya za'ai mu samu visa nanda sati biyu, domin inason tafiya london nan da sati uku acan zan nema mata university. Mutumin yace wannan ba damuwa bane, indai student ne zamusan yadda za'ai domin suma wadda muka turasu sun fara lectures saiku hanzarta. Suka masa godiya. Haneefah dake zaune a bakin office tana jiransu ta tashi suka tafi. Tana musu kwatancen gida har suka iso. Dr yace saikimin magana da abba in yana ciki ta amsa da toh. Tare da barrister suka shiga cikin gida. Umma na kitchen tashi sallama haneefah, da sauri ta fito taganta tare da bakuwa. Da fara'arta ta musu sannu da zuwa tare da yiwa mata isowa zuwa falo, haneefah ta nufi kitchen dauko ruwa. Bayan anyi gaisuwa haneefah take sanar da ita matar Dr ce Barrister ramlat, tare muke da Dr in abba na nan yace zai shigo su gaisa. Umma tace Allah sarki mun gode da zumunci, haneefah kirawo shi ya shigo abban naku yananan. Haneefah ta fice sanar da Dr. Falon umma ta kaishi sannan taje ta sanar da abba yana da baki a falon umma. Bayan anyi gaisuwa Dr yafara magana wato dazune muka tarar da haneefah a minstry of health ta kai takardun ta neman karatu a kasar waje amma akai rashin sa'a sun rufe sai shekara mai zuwa, nazarin da nayi ba lallaine ko shekara mai zuwan yayi ta samu domin suna cike sunayen wadda suka sani ne, ma'ana suna da candidates nasu, shine ni da mata ta mukai shawaran biya mata karatun ta. Ba abba da umma ba, haneefa ce ta dago ido cike da mamaki tana kallon shi. Dr yaci gaba haneefah badan kin taimakamin ba zan miki, aa ina da niyyar Allah nuna min randa ni da matata zamu faranta miki domin kin cancanta fiye da haka, sannan nazarin da nayi wajen fitar dake kiyi karatu tamkar sadakace garemu. Domin nasan mutane da dama zasu amfana da abinda kika karanta. Dr ya dubi abba yace kada kayi mamakin jin haka, Ba haneefah ba. nan ya kwashe abinda ya faru tsananin su yafadawa abba, dan haka ku bani dama Allah yana gani bazamu cutar ta ba, zan kaita london domin nafi zuwa can ziyarar wasu asibitoci kuma bazan samu wahalar samarmata makaranta ba domin nayi zaman can nasan mutane da dama. Abba da duk mamaki ya cika shi yace Alhamdulillah, hakika nagode da shaidar da kukai mata sannan nagode da abinda kazo dashi, bani da abin cewa sai Allah ya saka da alkhairi sannan na amince da tafiyarta sai dai ku nemi amincewar ummanta. Umma ta numfasa tace babu komai Allah sanya alkhairi. Haneefah ta dago ido cike da hawaye tace nagode Dr Allah biya ka, Allah azurta ka da zuria nagari. Dukka suka amsa da ameen. Bayan tafiyar su haneefah tana kwance kan gado momy tayi shiru tana ambaton Allah kamar yadda ta saba, umma tashigo ta sameshi a haka. Zama tayi kusa da ita tace haneefah. Haneefah ta amsa tare da matsowa ta kwanta kan cinyarta umma. Umma tace nasan kin zabi barin garin nan akan rabuwa da yusuf, amma zanyi farin ciki da tafiyarki bisa sharadi daya. Haneefah tace umma zanyi shi, nayi miki alkawari ko menene. Umma tace inaso kimin alkawarin abinda ya kaiki zakiyi wato karatu. Haneefah tace indai wannan ne umma namiki alkawari. Sannan ta qara dubarta tace haneefah ki rage yawan tunani da damuwa, domin hakan zai dagamin hankalin sosai. Haneefah ta tashi zaune tace umma bazan miki karya ba, tunani kam sai a hankali zan rage, kadai ki tayani da addu'a. Tace insha Allah. *Dr HANEEFAH* 👩🏼25 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Wayar umma ne tab soma ringing, tana dagawa taga nana. Bayan umma tayi sallama ta daga sun gaisa nana tace haba umma, yau sati uku baku nemeni ba duk shirye-shirye bikin yarki ya hanaku tunoni ? Itama inata kiran layinta bana samu domin inyi congratulating nata ta gama makaranta... tunda ta fara magana umma tayi shiru tana kallon ta. A hankali ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da nana, nana kuka take sosai tace umma mesa bazaku sanar dani da wuri ba Umma tace karatunki yayi nisa, bama so mu daga miki hankali amma yanzun ma yazama dole tunda barin garin zatayi. Haneefah dake zaune tana jinsu tace da umma ta bata wayar. Jin muryar haneefah yasa ta qara fashewa da kuka. Haneefah tace haba nana, ni da kaina banyi irin kukan da kike ba ko so kike nagaza juriya nima nasoma kuka? Cikin sauri nana ta tsayar da kukanta tace aa shikenan dan Allah kada kiyi, kuma namatukar jin dadin jin haka. Allah zaba miki mafi alkhairi arayuwarki. Haneefah tace ameen. Ta goge hawayen da ke sauko mata tace cikin zolaya ainima nakusa keta hazo cikin turai, nana dan fadamin abinda ake cikin jirgi kar inyi kauyanci. Nana tayi dariya tace wannan kam dole sai kinyi gaki da shegen karambani da zumudi! Haneefah tayi dariya.... nan suke ta hira har ta tabbar ma nana ita komai ya wuce gun nata. Umma dake zaune tana jinsu ta goge kwallar data zubo mota, tana addu'ar Allah qara hade kawunan su. Shirye shirye haneefah take sosai domin Allah-Allah take su tafi, kullum babu abinda take sai taje cikin yan uwanta ana hira dole ta mantar dasu cewa ita ba damuwa take ba, wadda bata boye damuwar ta itace hadiza domin tana kwantar mata da hankali sosai. Sau tari sai aganta tayi shiru, wani lokaci tunani take wani lokaci addu'a take. In dare yayi saita kasance cikin addu'a tare da karatun qur'ani. HANEEFAH baiwar Allah. Visa ta yafito sai dai tafiyar ta matso sosai domin sallamar Dr suka ji, bayan an gaisa yace tafiyar gobene sannan zamu biya Egypt, an wakiltar dani inje inga karatun yaranda aka tura shekaru hudu da suka wuce, bayan kwana biyu sannan mu wuce london domin na kin samu admission ma. Cikin murna haneefah tace Dr akwai yayata da take Egypt bansan ko university su bane, ta sanar dashi. Yace can zamu, saiki shirya gobe da safe zanzo mu tafi domin jirgin safe zamu hau zuwa abuja daganan sai mu wuce. Hakikanin murna haneefah ta bayyana. Gidan dukka murna suke. Ahmad dai yace kuje kuyi karatu nima ku fitar dani. Cikin murmushi haneefah tace inda rabonka harsai ka gaji dashi. Da daddare Ahmad ya dauki motar abba suka je gidan mama, tayi mata nasiha sosai tare cewa komai kaddara ne amma ta sani wani kaddaran addu'a na canza shi, ki dage sosai da addu'a Allah maji rokon bayin sane. Nan suka wuce gidan aunty muhibbat da humaira. Suma nasihar suka mata dajan kunnen tayi karatu tace tana neman alfarma gurinsu su mata alkawari, tace duk sanda yusuf yajo nemana kuce nayi aure. Aunty humaira tace aidama basu sameki da arhaba bale azo ace a qara bada ke. A gidan hadiza ne tadan jima sannan ta wuce sannan ita ta bukaci tayi mata alkawarin sanar da yusuf tayi aure inya zo nemanta. Bayan sun koma gida, ta shiga gidan inna domin yin sallama babu yabo babu fallasa sunyi sallama. Kwance take kamar yadda ta saba dakin umman tare da kannenta da Ahmad sai umma. Haneefah tace inaso kumin alkawarin in yusuf ko daya daga cikin dangin yusuf yazo kuce nayi aure banaso susan banida aure. Dukka suka amsa da toh. A wannan daren haneefah ta saki ranta sunyi hira sosai da yan uwanta musamman umma sannan ta nuna musu tafiyarta na daga cikin kwanciyar hankalinta domin zata danyi nesa da garin ko zata manta abinda ya faru cikin sauki. Washe gari da safe ta nufi gun abba domin gaishe shi. Yace haneefah cikin turai zaki duk da bana shakkar komai amma kada ki zamto mai son mu'amala dasu, ki kawar da kanki akan komai kije ga abinda ya kaiki, yarda da sukai dake ne yasa suka biya miki wannan makaranta kada ki zuba musu kasa a ido, muma kin nuna can kike so yasa muka amince amma bamusan hukuncin Allah ba, Allah yayi miki albarka yasa kifara a sa'a ki gama a sa'a. Ta amsa da ameen. Taje ta dauko jakarta da wayarta amma ta kasa kunnawa. Karfe takwas da rabi Barrister da Dr suka zo. Dr yace na gode abba kuma na maka alkawarin sa ido kanta da karatunta. Har airport ramla takaisu sannan ta mikawa haneefah wani dan karamin jaka, ta karba tayi godiya. Tara jirginsu ya tashi zuwa abuja, da rabi suka daga zuwa kasar Egypt. Da dare suka sauka, motar makarantan yazo daukan su. Tunda suka shiga haneefah ta baje ido tana kallon duniya, bata san anzo makarantar ba sai da Dr yace bani number yar uwar taki. Dr yakira nana yasanar da ita inda zata zo ta sameshi. Cikin minti goma sha biyar saiga nana, da sauri suka tashi suka rungume junansu. Nana kuka take sosai na tausayin yar'uwarta ganin yadda ta rame. Dr yace jibi zamu wuce saita zauna gurinki nizan wuce masauki na. Nana ta dauki jakar haneefah suka wuce hostel nasu. Su biyune a dakin, ita da wata yar sudan. Tayiwa haneefah sannu da zuwa cikin harshen turanci ta amsa duk da ba wani gane yaren take sosai ba. A wannan daren yan uwa biyu basu runtsa ba. Washe gari bayan sun karya karfe bakwai da rabi suka fito aji harda haneefah. Mamakin yar uwarta take yadda tajita take yaruka daban daban ,in anzo gun haneefah shiru. Nana tace nasan zaki fini domin inda zaki je kunfimu da komai. Takaitattun guri nana ta zaga da ita. Ta dada kwantar ran haneefah tace komai zaizo ya wuce. Karewa nana tayi da kallo tace inba munafurci ba gurin da babu iyayenki da yan uwanki jibi yadda hankalin ki ya kwanta har kika qara kyau! Nana tayi dariya tace haneefah bansan sanda zaki canza ba. Haneefah cikin zuciyarta tace karfin haline nana. Dr ya gama abinda ya kawo shi dan haka ya tattara suka wuce london. Tunda suka sauka haneefah ke karewa garin kallo. Hotel suka wuce domin hutawa, kowa dakinsa daban daban. Saida suka huta sosai tukun suka fita, Dr yasiwa haneefah sim. Tasa wayarta ta kira umma taji shiru bata dagaba, Dr yace ai yanzu darene kamar anjima zaki same su. Cikin sa'a ya tarar da abokinsa yayi masa jagora suka karbi admission, radiography suka bata. Dr baiso hakan ba amma haneefah tace ita tafison shima sai dai qasar zuciyarta gynecology take so. An mata komai cikin sa'a , hostel ma sai da ya tabbata dakinsu daya da musulma tukun ya amince. Yadda haneefah taga Dr na mata zirga-zirga yasa ta dauki damarar karatu. _(Masu karatu bari mu zaga muga halin da yusuf ke ciki)_ *Dr HANEEFAH* 👩🏼27 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tsayawa yayi gaban yusuf yana kare masa kallo, yadda ya rame ya fita hayyacinsa. A hankali abba ya goge hawayen da suka zubo masa. Kiran momy ne ya shigo take tambayar halin da ake ciki, yace yanzu haka gashi gabana kwance amma zamuyi kokarin kawo shi ko zuwa gobe. Shigowar Dr yasa ya aje wayar. Doctor yace nina likitan dake kula da lafiyar sa, wanene mahaifinsa ciki? Abba yace nine. Likita yace biyoni office. Bayan sun gaisa ne yake bashi labarin yadda yusuf yazo hannun shi da irin raunin da yasamu, ya qara da cewa dama muna kokarin turashi teaching hospital dake zaria domin wadda yake daukan nawin treatment nashi ya bamu go ahead amma tunda kazo menene ra'ayinka? Zan tafi dashi kano inyaso sai ayi treatment din acan, sannan ka bani number wadda yaka wosa. Ya amshi number yafice. Abba bai runtsa ba har gari ya waye. Dr yazo aka fara shirye shiryen kawoshi kano. Ambulance aka bada, batare da bata lokaci ba suka dau hanya. A hanya abba yake sanar da kwararrun likitoci da ya sani kan suna hanya. Daki daban aka bashi, aka sake fara bincike akanshi. Momy sunajin labarin zuwanshi dukkaninsu suka dau hanyar asibiti. Kwance yake likitoshi ne kusan biyar a kansa. Bayan sungama dukkanin bincike suka fito daya daga ciki ya kira Abba. Doctor yace dan ka ya samu rauni sosai, amma yanzu munyi masa taimakon da ya kamata, sai dai kafafunsa sun samu karaya sosai ta yadda tafiyar sa zai dauki lokaci, amma zamuyi iya bakin kokarin mu muga ya dawo dai dai. Abba yayi wa likitan godiya ya fice. Tsaye yake kan dan nasa yaji turowar kofa, iyalansa ne baki daya suka shigo duk hankalin su a tashe. Babu wadda bai tausayawa Yusuf ba, musamman momy wadda take kuka sosai tasan yawan tunanine yasa shi har ya kaiga wannan hatsari, tana dana sanin abinda ta aikata. Kannen sa duk hawaye suke zubdawa na tausayin yayansu musamman aisha, rahma da kanta saida ta tausaya mishi ganin yadda ya rame kamar ba shiba. Ganin kukan ba na dainawa bane Abba ya soma fada, addu'a zakui mishi ba zaku tsaya kuyi kuka ba, ku dubi halin da yake ciki ai abin godiyane ga Allah daya sada mu dashi... Allah tashi kafadarshi dukkansu suka amsa da ameen. Da daddare Abba ya kira mutumin da ya taimakawa Yusuf, bayan sunyi sallama yake sanar dashi yadda akai yasami lambarsa tare da yi masa godiya, mutumin yace ba komai Allah bashi lafiya nima in na shigo kano zan nemeka. Sukai sallama. Wasa-wasa yau satin Yusuf uku amma bai bude idanunshi ba. Iyalan gidan babu wadda yake cikin nutsuwa, kullum suna asibiti tare da dan uwa, yan uwa da abokan arziki sai zuwa suke dubiya, duk wadda yaga Yusuf sai ya matukar basa tausayi domin kowa yana tuna alkhairi dake musu da son zumunci. ***** ****** Watan su daya da sati biyu cif yau a asibiti, amma Yusuf ko kifta ido bayayi. Misalin karfe goma na dare Abba ke zaune kusa dashi sai Momy dake dan nesa dashi, kannen sa ne aisha da Muhammad. Kallo daya zaka musu kasan basa cikin hayyacinsu, addu'a suke Allah bawa dan uwansu lafiya. Momy da Abba tunanin ko su fitar dashi kasan waje suke amma babu wadda ya furtawa junansa. A hankali Yusuf ya bude idanunsa, ganin wajen ya mishi haske sosai ya qara lunmshe idanunsa. Ya sake bude idanun a hankali harya waresu baki daya, Momy ce ta fara kallon sa, da sauri ta mike tana fadin Yusuf!!! Dukka ninsu suka nufoshi suna mishi sannu. Shidai baice komai ba, dakyar ya iya juya wuyarsa yana kallonsu, zai bude baki ya musu magana amma tsaban radadin da yake ji bakin shi ya mishi nauyi. Tuno da abinda ya same shi yayi nan take ya rufe ido. Innalillahi wa'innailaihi rajiuun ya soma yi cikin zuciyarsa domin kasa furta ko da kalma dayane ya gagara. Abba ne yace ku dakata mana, yanzu ya bude ido sai a abari likita yazo yayi bincike kafin a ce dashi komai. Nan Abba ya fita kiran doctor. Bayan likita ya gama bincikensa ya cire robar da aka sa masa a hanci ya dubi Abba yace za'a iya bashi black tea yasha amma kada a dameshi da hayaniya, yin hakan komai na iya faruwa. Abba ya amsa da za'a kiyaye insha Allah. Bayan fitar doctor aisha ta hada masa tea kamar yadda doctor yace, tazo gaban shi ta zauna. Yusuf yayi yunkurin tashiwa amma ya kasa, jinshi yake kamar ba shiba, baya iya motsa kafa da hannu. Aisha data lura da hakan a hankali tace kabari zan baka a kwance. Shiru yayi yana binta da kallo. Mika masa tea tayi da cokali amma yaki bude bakinsa. Aisha tace yaya likitane yace a baka bude bakin ka. Hawayene ya soma sauka idanun Yusuf, yanzu ko bude baki ya gagara? Alhamdulillah! Yace gami da lumshe ido. Abba da Momy suka nufoshi lallashinsa suka soma. Bude ido yayi ya soma girgiza kansa a hankali. Abba yace bazaka iya bude bakin ka ba? A hankali ya girgiza kansa alamar eh. Dukka ninsu suka soma furta innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun. Aisha ta kwanta kusa da kansa tana hawaye a hankali. Abba ganin halin da suka shiga yasa ya danne nasa hawayen yace haba, hakan zai daga masa hankali, muci gaba da addu'a, insha Allah komai zai daidaita, gobe in likita yazo saimu sanar dashi. Aisha ta tashi tashare hawayenta ta soma kallon yayanta, tausayinsa take ji sosai ta shiga share mishi hawaye. Bude idanu yayi yana kallonta tace yaya kada ka damu, Allah zai sauwa ke maka kayi kokarin cin wannan jarabawar. Murmushi taga yayi tare da lumshe ido ya bude. Tace har yanzu bazaka iya bude baki ba? A hankali ya daga mata kai. Ta shafa kansa tace do not warry dear, komai zai daidaita da izinin Allah. Nan HANEEFAH ta fado masa arai, tabbas yasan tana can tana wahala karshema kuka take tayi, tsoronsa kada ta sawa kanta wani ciwo.. addu'a yayi Allah ka sauka kawa baiwar ka da bata jiba bata gani ba, ka bamu ikon juriyar wannan lamari da muka tsinci kanmu. Nan ya baza ido neman rahma ko zai ganta. Bai ganta ba, duban shi ya koma kan momy, ya sakan mata murmushi. Isowa tayi gabansa tace kada ka damu muna nan muna tayaka addu'a, zaka samu sauki. Ya daga mata kai ya lumshe ido ya koma bacci. Sai da suka tabbatar bacci yake sannan Abba yace yakamata su koma gida dare yayi. Bayan sun koma gida aisha ta nufi gun rahma. Bude kofar falo tayi taga bata ciki, sauri take taje tace mata Yusuf ya bude ido, turus tayi jin wayar da take yi. *Dr HANEEFAH* 👩🏼26 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Bayan an masa qarin jini binciken su ya tabbatar musu ya zamu rauni sosai. Bayan an masa taimakon da ya dace Dr ya fito domin sanar da mutumin daya yusuf halin da yake ciki. Dr ya dubeshi sosai yace lallai yakamata mu samo yan uwansa, domin ya raunana sosai, munyi nasaran cire glasses da suka ke makale ajikinsa sannan ya zamu karaya a kafafunsa biyu da hannu daya, sannan kansa yayi mugun buguwa sosai ta yadda abinci ma bazai iya ci da kansa ba, sai dai mubasa ta hanci atakaice sai mun dauki hoton kwakwalwarsa mun tura asibitin psychiatric domin tabbatar da lafiyarsa. Mutumin ya numfasa yace yanzu abinda nake so dakai ga numberta duk abinda kuke bukata ku sanar dani, yanzu zanje gidan qanwata in sanar da ita domin ni abuja zan wuce, insha Allah zamusan yadda za'ai munemo yan uwansa. Dr yace ba komai. Yabi mutumin da kallo yana mamakin irin karamcin sa. Kamar yadda yafada haka akayi, ya hada kanwarta da likitan dake lura da yusuf, yace zata rika zuwa ta dubasa amma ya ware nurses da zasu zauna dashi. Yau kwanan yusuf goma baisan inda yake ba, ko bude ido bayyi ba, likitoci suna iya kokarinsu. Ganin haka yasa mutumin yada hoton yusuf domin neman yan uwansa. _Bari mu leka jama'an gida_ **** **** Abba na ganin fitar yusuf da safe yasan ba lafiya bane. Ko momy saida taji abinda tayi mishi bata kyauta ba amma tana addu'ar Allah kaishi lfy. Kwana biyar kenan hankalin su ya soma tashi, kullum wayar yusuf a kashe. Da daddaren ranan aisha taje dakin momy, zaune ta same ta bakin gado amma kallo daya za'ai mata asan hankalinta a tashe. Aisha tazo ta zauna kusa da ita cike da damuwa tace momy kwana kinnan meyake damunki? Momy tace babu komai, ina tunanin yayankune tunda yatafi bai kira ba sannan inna kira bana samun shi. Aisha ta tashi zaune tace momy nima inata kiransa amma bana samunshi, banyi tsammanin lafiya ba domin bai taba kashe wayoyinsa ba kuma..... abba ne ya shigo hannunsa rike da waya yace yusuf nake nema yau kwana uku amma ban same shiba, na aika yaron abokina gurin aikin nashi amma yace tun last wk baizo aiki ba, bana tunanin lfy. Momy ne gabanta ya fadi tace to yanzu ya za'ai? Abba yace gobe zan bishi inji lafiya domin bai taba ko da kwana daya bai kirani ba. Allah sa dai lafiya cewar aisha Washe gari misalin karfe goma sha daya jirgin su abba ya sauka, abokinsane ya aiko driver ya dauke shi, bai wuce dashi ko ina ba sai gidan dansa. A kulle suka tadda gidan, nan yacewa driver muje gurin aikin nasa. Sunjene aka tabbata mishi suma nemansa suke domin sunyi mamakin jin har yanzu bai komo aiki ba domin sanin da sukai masa shiba mai wasa da aikin sa bane. Innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun abba yake furtawa. Kiran abokin nasa yayi yace bazai samu karasowa ba zai wuce kano amma da driver nasa zai tafi. Yace babu damuwa Allah kaisu lfy. Wayarshi yasa a silent sabida kada a dameshi da kira. Ina yusuf yake? Wani hali yake ciki? Ya Allah ka tsaremin shi a duk inda yake. Tunani ne ya hana abba sakat. Jin gine yake yana kallon window har suka zo daidai inda yusuf yayi hatsari. Karaf idon shi yafada kan motar, zuciyarsa tayi mugun faduwa ganin mota duk da bai tabbata wace irin mota bane domin. Da sauri ya tsaida driver sannan yafito ya nufi gun motar. Ganin yadda motar take yasa ya tausayawa wadda yake ciki domin ba lallaine ya fita da raiba. Zai juya ya tafi idanunsa suka sauka kan ID card, da sauri ya iso yaga ashe rabine domin rabin wuta ta koni saura gurin hoto wato passport. Inna lillahi wa'inna ilaihi rajiuun ya furta da karfi, hankalinsa ne ya tashi sosai ganin hoton yusuf, ya dada juyawa gun motar ya kare masa kallo, sai yanzu ya tabbata motar yusuf ne. Kasa dauke idonsa yayi har yazo kusa da motar yace... yusuf motar kace wannan! Yananan tsaye yaga wani tsoho ya taho gunsa yace mallam lafiya kake tsaye gun motar? Abba yace motar da nane. Tsohon yace Allah sarki yau kwana biyar da hatsarin motar nan, tsohon ya kwashe labarin yadda akai aka cire mai motar da yadda wani bawan Allah yayi taimako aka nufeshi garin kaduna amma baisan da ranshi ko bayi da raiba. Abba ya dafe kanshi dake sarawa, yace da tsohon nagode baba.Bayan yashiga mota yace da driver su tafi. Sun fara tafiya sai kuma yace mu tsaya garin kaduna. Hotel abba yayi masauki. Sai da ya tsaya yayi sallah sannan ya shiga ya kama daki. Yana shiga ya daga wayarsa yaga missed calls yawanci na momy ne. Abokinsa yakira dake garin kaduna. Bashi lbr abinda ya faru tare da neman alfarman neman mota domin neman gawan dansa. Abokinsa yace ai baka tabbatar ba, dan kaga motar sa bai sa hakan ya rasu ba, yanzu da kaina zanzo mu zaga asibitoci nemansa. A sannan hankalin momy ya tashi, kuka take sosai ta kira yan uwansa ta gaya musu. Hankalin gidan a tashe Abba da abokinsa sun yini wajen neman yusuf amma babu labari, hakan yasa hankalinsa ya dada tashiwa. Zaune yake a falon a abokinsa yayi shiru ya zubawa tv idanu amma ba kallon tv yake ba, tunani yake ko dai yusuf ya rasu ne? Karaf aka hasko hoton yusuf, tsaye ya tashi yana nuna tv da hannu. Sauraron asibitin sukai sannan suka dauki mukullin mota suka fice. Basu sha wahalan neman bangaren da aka ajeshi ba domin yana emergency, cikin hanzari suka fara bin dakuna har suka zo dakin shi. Nurse macece zaune kusa dashi, shigowarsu ya ta tashi tare da tambayarsu kosu wayene. Abokin abba ne ya sanar da ita tafita kiran Doctor *Dr HANEEFAH* 28 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Durling na maka alkawari, bazan qara ko da shekara daya a gidannan ba, mum ce tasani auren sa nida shi ba son auren muke ba kaga ko babu maganan zama tare da shi, ok toh zanyi yadda kace...... Takaicine ya tokare wuyar Aisha, mayar aure tana waya da wani? Kuma tsaban rashin imani bata damu da rashin lafiyar dan uwanta ba? Komawa tayi a hankali ta maido mata kofar kofalon yadda ta samu. Aisha shiru ta zauna bakin gado tana nazarin wannan lamarin, ganin haka ba mafita bane yasa ta tashi ta dauro alwala domin samin mafita gun mahaliccinmu. Washe gari misalin karfe bakwai sun gama shiri tafiya asibiti, Momy tacewa Aisha taje ta kira Rahma su tafi, kamar bazata je ba ta nufi bangarensu. Sallah ta tarar tanayi, sanda tajira ta idar tace Momy tace ki fito mu tafi asibiti, bata jira amsar taba ta juya ta fice. Tsaki Rahma taja ta tashi tana gunguni ta fito. Gurin motar ta nufo ta gaida Momy a tsaye ko rissinawa batayi ba, Momy ta amsa da fara'a tace ai jiya ya bude ido shine nace bari mu tafi da safe, Allah sarki Allah bashi lfy cewar Rahma. Aisha ta kalli Muhammad tace shiga gaba mutafi. A hanya babu wadda yayiwa wani magana har suka iso asibiti. Tsaye suka sami Abba bakin kofar dakin, hakan yasa suka tabbar likita na ciki. Bayan sun gaishe shi ne yana kan amsawa likita ya fito yace Abba da Momy su biyoshi office. Likita ya dubesu yace hakika danku yayi mummunan hatsari, sbd glasses sun shige jikinsa sosai, amma da ikon Allah yana samun saukin raunukansa cikin sauki. Sai dai matsalan yanzu shine muscles din fuskarsa ma'ana wajen yadda zai sarrafa bakinsa ya samu shock, ta yadda bazai soma magana ko motsa su sosai ba sai nanda wasu lokuta in magungunan da muka basa sun masa aiki, inko muka samu sabanin haka sai dai a masa aiki. Abba ya numfasa yace muna godiya da kulawar ku garemu, Allah bashi lafiya. Suka ma likita godiya suka fice. Aisha ce ta fara shiga dauke da kular abinci. Ta iso gare shi ta zauna gabansa, hawayene ke tsiyaya a idanunta. A hankali Yusuf ya bude idanunsa yana kallonta, murmushi ya sakar mata tare da girgiza mata kai da sauri ta goge hawayenta. Yusuf yana son kama hannuwanta ya lallashe ta amma yakasa, yayi mata nuni da ido ta kama hannuwansa, ita ko ta dauka ce mata yake hannuwansa na masa radadi. A hankali ta dafe kansa tace kada ka damu zaka warke nan bada jimawa ba. Ya lumshe ido yana jin wani irin radadi a zuciyarsa, lallai duniya abar tsoroce, yanzu kana lafiya anjima zaka rasata. Tunani yake yau shine a kwance baya iya komai sai kallo! Ya Allah kabani ikon komawa gareka kana mai alfahari dani. Momy ce tashigo ta nufeshi tana murmushi tace Allah baka lafiya, kana cikin addu'a ta. So yake yace Momy amma ya kasa, dubansa ya koma kan rahma da ko sallama batayi ba. Ganin kallon da yake mata yasa ta zo kusa dashi tace masa sannu, amsa mata da murmushi. Abba ya shigo yace shizai wuce sai yazo. Da dare Abba yace yakamata yarannan su koma makaranta tunda anfara samun nasara kan lafiyarsa. Haka ko akai, aisha da Muhammad sun koma makaranta, Momy ma tana leqa office amma ba aiki ke kaita ba. Momy ce ke kula da Yusuf sai Abba da yake kwana agunsa. Rahma ko kamar ba mijinta kuma dan uwanta ba, sai ance taje dubasa zata je, ganin haka yasa Momy ta kyaleta tace tunda ita batasan yakamata ba saita zauna domin tin yanzu ta fara dana sanin aurensu. Duk wadda yazo duniyar Yusuf saiya tausaya mishi, ya rame sosai kamar ba shiba. Momy inta zauna tana kukan itace sanadiyyar shiga danta wannan hali domin tunanin fasa auren sane yaja masa hatsari. Amma ta dage da yiwa danta addu'a Allah bashi lafiya. Yusuf ma kullum yana addu'a Allah bashi lafiya domin yana jin azabar ciwukan dake jikinsa. Sau tari zai lumshe ido kamar mai bacci amma tunanin Haneefah yake, da ita yake kwanciya da ita yake tashi. Duk da halin da yake ciki baifasa yi musu addu'a Allah hadasu matsayin ma'aurataba, SO kenan! ***** Allah maji rokon bayinsa, yusuf yafara samun sauki domin har hannunsa yafara motsawa, maganar dai har yanzu bai soma ba. Aisha ce zaune tayi shiru tazubawa yayanta idanu. A hankali ya bude ido ya juyo inda take, Aisha tace sannu da barci yaya, yanzu abokananka suka zo kana barci. Murmushi yayi kamar yadda ya saba, duk da ba magana zai iyayi ba yace ina Momy? Ras maganan ta fito. Shi kansa yayi mamaki, yaya magana ka fara? Sake fada inji? A hankali yace ina Momy? Alhamdulillah ina iya magana! Dadine ya lullube Aisha nan ta fara hawaye! Zatayi magana Abba ya turo kofa. Da sauri ta nufeshi tana nuna Yusuf takasa magana, Abba cikin tsoro da tashin hankali yace menene? Aisha cikin murna tace yafara magana. Da sauri Abba ya iso gareshi yace Yusuf? Yusuf yace na'am. Alhamdulillah Abba ya soma furtawa. Nan suke cike da murna. Aisha tarasa mezatai dan farin ciki. Yayarta takira salma ta gaya maya. Nan da nan suka hade a asibiti, kowa ya zagayeshi yana tambayar ya jikinsa. Ganin yadda kowa ke farin ciki hakan yasa hawayen farin ciki zubowa a idanunsa. Sannan tunaninsa yaje gun ina ma zaiga Haneefah! Aisha da ta lura da hakan tasa hannuwa ta share masa hawaye tace yaya komai yazo karshe mudai mu dage da addu'a. Allah cikin ikonsa Yusuf na samun sauki, hannunsa ma yayi sauki sai dai karatun nasane sai a hankali. Yana samun kulawa gurin iyayensa da kannensa. Likitoci na aikinsu yadda ya dace. Rahma ko babu ruwanta da shiga tsabgarsa, jiran mum dinta take tazo ta yanke mata wannan zama da take. Aisha kadai ta lura da takunta, tana tausayawa yayanta domin tasan raba shi akai da Haneefah. Kullum tunaninta ta yaya zata shawo kan wannan al'amarin? Watan su uku aka sallame shi suka dawo gida, amma har yanzu yusuf bai samu kafa ba, da keke yake amfani. Ganin haka yasa Rahma hankalinta ya tashi kan bazata iya rainon gurguba. *Dr HANEEFAH* 👩🏼29 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Hankalin Rahma baki daya ya tashi domin ganin wahalar zatai mata yawa. Nan ta fara neman mum dinta a waya. Mum tace kada ki damu zanzo asan yadda za'ai. Abba da Momy sun yanke shawarar fitar da Yusuf kasan waje domin duba lafiyar kafafunsa. Cikin wata daya aka kammala shiri zuwa india, Abba da Yusuf kadai zasu. Hakan yayiwa rahma dadi sosai domin yanzu batason shiga al'amaransu. Suna sauka motar asibiti tazo ta dauke su. Bayan sun sami ganin likita suka masa bayanin komai. Dogon bincike sukai game da lafiyar Yusuf baki daya. Likita ya samu guri ya zauna ya fuskanci Yusuf da Abba. Likita yace kunzo mana da cewar kafafunsane suka samu rauni al'alin akwai babbar abu bayan wannan. Abba yace ka fahimtar damu likita. Likita yace ya samu shock sosai a hatsarin da yayi domin dakyar in zai sake haihuwa. Cikin rashin fahimta Abba yace kamar yaya likita? Wannan case din muna samunshi amma ba sosai ba, domin jijiyoyin da suke hanyar da maniyyinsa zai samu fita sun kumbura, in akace za'ai aiki hakan zai zamo hatsari domin zasu iya tsinkewa garin taba su, sai dai zamu bashi magunguna da zasu sa jijiyoyin su sabe, in ya taki sa'an maganin zai mishi aiki inko bai dace ba sai dai kuyi hakuri shi da haihuwa. Duk asibitin da zaije a duniyar nan abinda zaiji kenan. Abba ya share gumin da ya feso mishi yace toh yanzu likita maganin yaushe zai fara amfani? Likita yace zamu daurashi kai muddin kuka bamu hadin kai, sannan ko wani bayan wata hudu zaizo medical checkup, batun kafafunsa kuma ba abin tada hankali bane zamusan yadda zamuyi amma shima sai an masa aiki. Abba yace ba komai likita mun gode, a shirye muke da duk abinda kuka umarcemu. Abba ya juya kallonsa gun Yusuf daya jingina a jikin pillow yana jin dukkanin abinda suke tattaunawa. Abba yace Yusuf kai hakuri sannan ka jure wannan jarabawar da ta sauko maka, hakika inka jure zaka kasance mai kyakykyawar rabu duniya da lahira. Yusuf ya murmusa yace babu komai Abba , fatana a duniya nakasance mai tsoron Allah da tawakkali dashi a duk halin da na tsinci kaina. Wannan abin bazai tada min hankali ba sai kara nutsar dani da yayi, domin shekararun baya da kafafuna da hannaye na lafiyayya, yau dan nawayi gari nasamu canjin rayuwa bazan yi fishi ba, Alhamdulillah! Da ya bani ikon kasancewa cikin musulunci, fatana na koma garesa yana mai alfahari dani. Abba yace tabbas zaka kasance cikin bayin Allah salihai, Allah yayi maka albarka. Cikin sati daya akayiwa Yusuf aiki kuma ansamu nasara sai dai bai soma tafiya dai dai ba. Watan su daya suka dawo gida Nigeria. Abba ya sanar da Momy halin da danta yake ciki, kwarai tayi matukar tausaya masa. Tasan duk ita taja masa, amma tayi alkawarin bazata sake saka ido akan abinda yayanta suka so ba muddin bai kaucewa shari'a ba. Rahma ko jin haka yasa taji sanyi a ranta domin ta samu hujjar rabuwa dashi taje ta auri wadda taga dama. Takira mum ta samar da ita, ba karamin bakin ciki umma nusaiba tayi ba amma ta soma lallashin yarta kan zata zo kada ta kuskura ta dago wata magana. Rahma ko tace inanan ina jiranki amma kizo da wuri domin ko wacce kwana na daya a gidannan sai naji sun fice min arai. Da dare bayan ya huta ya nufi dakin Momy domin tunda yayi wannan jinyar bai samu ya sanar da ita abinda ke ransa ba. Zaune ya tadda ta kan sallaya ta idar da sallah tana shirin tashiwa. Yayi sallama ya shigo ya zauna kasan carfet yana qara gaishe ta, cike da fara'a take amsawa tare da yi masa ya jiki? Ya amsa da sauki. Ya dago ido cike da hawaye yace Momy sirrin cigaban zaman lafiyane ga dukkanin wani ďa da yake faranta ran iyayensa musamman mahaifiyarsa, ina alfahari dake samun ki uwa domin kin bani cikekken abinda duk wani dan Adam zai bukata ta bangaren uwa, hakika bani da abinda zan biyaki sai dai in miki addu'a tare da faranta ranki..... amma Momy yunkurin nuna bacin ranki gareni yasa na gamu da wannan hatsari, Momy zan miki komai amma ina mai rokon ki kada sake fishi dani.. na yarda da fushin Rayuwa ta dawo Yusuf sabuwa domin ko wani wayewar gari sai yaji tsananin son Haneefah, ya rasa ya zayyi kowa da rabuwa da kowa amma bazan hira fushin kina, in maganar Haneefah ne na rabu da ita wlh bazan kuma zuwa ko da kofar gidan sune ba nidai Momy dan Allah ki yafeni bazan qara ba... ya karashe maganar yana hawaye. Momy dauriya tayi ta hadiye hawayenta tace babu komai ya wuce, nidai ka rike Rahma amana domin ina da tabbacin ta isheka komai na matar da kake so, nasan zata rufamin asiri ta zauna dakai lafiya domin ýar uwar kace. Na yafe maka Allah albarkaci rayuwarka ya baka lafiya. Yusuf baiso jin wannan amsar ba ya amsa da ameen. Yace Momy kitayani addu'a Allah bani ikon daina son Haneefah. Momy tace zaka daina nan da wani lokaci. Ya tashi ya fita jiki a sanyaye. Bayan fitarsa umma nusaiba takira Momy take sanar da ita tana nan tafe gobe idan Allah ya kaimu. Yusuf yana fita ya nufi dakin Aisha. Tana zaune tana karatun qur'ani, jin shigowarsa yasa ta dakata ta fuskance shi. Ta gaishe shi sannan ta mishi ya jiki yace da sauki. Aisha tace yadai yaya kamar fuskar ka na cikin damuwa? Babu komai Aisha ina laptop na? Ta tashi ta dauko mishi tace yaya Allah ya rufawa laptop naka asiri da shima ya kone! Murmushi kawai yayi yace ina ga nan da sati daya zan koma abuja. Aisha tace haba yaya kabari ka dada samun kwarin jiki saika tafi. Yace inna zauna anan babu abinda nake gomma inje can zan rika mosa jiki da ayyu kan office. Aisha tace Allah qara lafiya. Kallon kanwarsa yake sosai yace inason sanar dake wani secret but kimin alkawarin bazaki fadawa kowa ba sannan dalilin sanar da ke so nake ki sani a addu'a na musamman domin nasan zaki yi. Aisha tace insha Allah zan tayaka ko menene *Dr HANEEFAH* 30 Dedicated to Batul Mamman (Mrs) 💖 Idonsa cike da hawaye yace sis, wallahi har yau ina har gobe inajin son Haneefah amma Momy takasa gane Haneefah wata bangarece na farin ciki a rayuwata, ina sonta tana da hankali she have all qualities da nake bukata agun mace, Momy ta rasa lokacin da zata rabamu sai saura wata biyu auren mu? Kuma ta sani nayi nesa da ita, tabbas nasan Haneefah zata jure amma nasan tana can tana fama da zuciyarta, nasan irin son da take min mun kwallafa rai zamu mallaki juna muyi zama na amana but it's over! Ina tunanin wani irin hali Haneefah take ciki na gamu da hatsarinnan, dubi yadda na koma. Murmushi yayi yace nagode wa Allah daya tasheni har ya bani ikon dada neman afuwar Momy, amma dan ta rabamu zuciyar mu a hade da Haneefah nasan addu'ar mu bazai fadi kasa ba, sannan agun Allah nake tsammanin mallakar Haneefah. Sis inaso ki tayani addu'a Allah bani ikon jure rashin ta na dan lokaci kadan domin nasan zata dawo gareni. Aisha as duk tausayin dan uwanta ya cika ta tace na maka alkawarin tayaka addu'a, kuma inada tabbacin Momy zata fahimce ka wata rana! Just keep praying. Aisha tazo kusa dashi tana ci gaba da kwantar masa da hankali. Murmushin jin dadi yayi ganin yadda kanwarsa take kokarin kwantar masa hankali. Yanuna farin cikin sa ya tashi ya nufi sashin sa. Kwance ya sameta kan doguwar kujera tana waya... jin abinda take cewa ne ya dakatar dashi! Sweetheart wallahi ba haka bane amma na maka alkawarin ka bani nan da 1wk kacal kasan ina sonka.... Yusuf dake tsaye yana jinta ya girgiza kai ya shiga cikin daki ya kulle kanshi da key. Zama yayi bakin gado ya kunnan laptop nashi. Gurin hotuna ya shiga yana kallon hotunan Haneefah har yazo inda suka dauka su biyu acikin motarsa! Hawayene ya soma sauka idanunsa yace a wannan rana muka rabu gashi yau kusan wata biyar bamu ji muryar juna ba. Nan ya tuno da maganarta lokacin da yayi kwana bai kirata ba tace _na maka uzuri kana aiki amma inaso ka kasance dani a tunanin ka, ni ko da bacci ya sace ni kana cikin mafarkina, kaine tunanin domin na damka maka duniyar soyayyata_ A hankali yace Haneefah duk inda kike pls don't give up on me, muci gaba da addu'a, nasan rabuwarmu nadan lokacine inada tabbacin sake rayuwa dake. Tuno Rahma yayi, nan take ransa ya baci wadda a dalilinta aka hana auran mosoyiyarsa gata da igiyar auren ta tana waya da wani. Tsaki ya ja ya share hawayen sa... zan zauna da ke dan Momy amma bazan lamunci wannan wulakancin ba. Ya tashi da nufin shiga ban daki ya koma da sauri ya zauna jin wani irin azaba da mahadin(joint) cinyoyinsa sukayi. Lumshe ido yayi yana ambaton Allah. Ya kai kusan minti goma kafin ya samu tashiwa a hankali yana dingishi ya shiga ban daki, bayan ya fito ya dauki qur'ani ya soma karatu. Washe gari misalin karfe takwas ya fito domin gaida iyayensa ya tarar Rahma na kwance inda ya barta tana bacci, da alama ko sallah bata yi ba. Tashin ta yayi yace gari yayi haske. Tsaki taja ta qara kwanciyarta. Bai kara cewa komai ba ya fice. A falo ya tarar da Abba yana shirin fita, da sauri ya gaishe shi. Abba ya amsa tare da yi masa ya jiki yace da sauki. Abba yace nizan fita saina dawo. Yusuf ya wuce bangaren Momy. A falo ya same su Aisha na shirin fita. Ya gaida Momy ta amsa ta masa ya jiki. Anan take sanar dashi zuwan umma nusaiba yau, yace Allah kawo ta. Suna cikin magana suka ji sallamar salma. Bayan sun gaisa tace nazo duba jikin yaya Yusuf ne kafin in wuce office. Yusuf yayi murmushi ganin yadda yan uwansa suke kula da shi hakan na mishi dadi. **** **** Dr Mubarak ya dubi Haneefah yace inaso ki maida hankalinki kiyi karatu, ni yanzu a matsayin qanwata na daukeki shiyasa na zabi kiyi karatu a wannan jami'ar domin nayi karatu cikin sa nasan mutane da dama cikin sa, kamar yadda nasanki da kwazo ina so ki ninka kwazonki kiyi karatu, ban lamunci kiyi soyayya ba sannan bazan hana ki hulda da jama'a ba amma kisan wadda zakiyi da su nidai fatana ki maida hankalinki akan abinda ya kawo ki. Haneefah tace nayi maka alkawarin bazan baka kunya ba, zan maida hankalina akan karatu. Dr Mubarak ya kalli wayar dake hannun ta yace naga wayarki babbace abinda zaki bukata shine laptop da iPad, zan dawo miki dasu anjima sannan ki bani account number ki, abu na karshe shine inaso kimin alkawarin duk abinda ya shafi abin bukata na makaranta ki nemeni kada ki fada a gida sannan duk wata zan tura miki kudi shi na al'amuran yau da kullum ne ina fata zaki kiyaye? Insha Allahu nagode sosai Allah qara arziki. Cikin kwanaki goma Dr Mubarak ya nuna mata ko ina game da department nasu, tare yake rakata suke attending lectures, kullum in sun fita da safe sai yamma suke zuwa sai dare yake samun tafiya gurin bukatunsa, ya nuna mata muhimman gurare da zata bukata misali kasuwa, gurin ciyan abinci da sauran su. Ta tabbatar wa kanta cewa Dr yayi mata abinda qanwarsa ma sai taje. A washe gari zai koma gida suka zauna ya dada sanar da ita komai kan makarantar nasu. Washe gari har airport ta rako shi sannan ta koma. Haneefah abinda ta fahimta game da wannan balarabiyar shine, farkawa take tana ganinta ido biyu akan sallaya tana addu'a bayan tagama zata idar da sallah asuba saita zauna karatun qurani amma a hankali take ta yadda bazata dami kowa da daga murya ba har rana ta fito, bayan karfe bakwai yayi zata shiga wanka ta fito tashirya saita fita, da dare zata bude takardun makarantar ta tayi karatu in dare saita dauki takardu manya na addini ta soma karantawa zuwa awa daya sannan ta kwanta. Wannan tsarin yayi matukar bala'in burge Haneefah, babu abinda yake hada su sai gaisuwa. Nan Haneefah tayi sha'awar yi mata magana sai kuma tayi shakka ta kyaleta. Hakarayuwar Haneefah takasance a birnin London, dabi'ar su ya zamo daya da wannan balarabiyar amma sai dai basu san koda sunan junansu bane da department nasu. Sai gaisuwa. **** **** **** Haneefah ta maida hankalinta sosai gun karatu, bata kula kowa daga ta gama abinda takeyi zata koma hostel, wani lokacin zata wuce library ko wani guri wadda aka warewa dalibai ta zauna shiru tana nazarin mutane da yadda suke rayuwa. Sau tari in taga guri shiru zata zauna tayi ta kukanta inta tuno da Yusuf, wani lokaci kuma ta zauna tayi shiru tana tunanin ko wani irin hali yake sannan ta godewa Allah daya bata ikon daukan al'amarin a saukake amma bata fasa addu'ar Allah daidaita tsakanin su ba. Tana waya da mutanen gida sannan tana tabbatar musu komai na tafiya mata yadda ya kamata. Haka ga barrister suna gaisawa bayan kwanaki kadan. *Dr HANEEFAH* 👩🏼31 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Zaune take tayi shiru tana kallon fararen fata yaruka daban-daban wadda suke aji daya. Kowa na harkan gabansa... tunanin tashiwa take ta fita taji an zauna kusa kusa da ita Juyowar da zata yi suka hada ido cikin harshen turanci tace kema kinanan ajinne? Haneefah ta daga mata kai alamar eh! Balarabiyar tace in bazaki damu ba inaso mudanyi wata magana. Haneefah tayi murmushi tace zan so sauraron ki amma bana tunanin zan tsawai ta ina magana cikin harshen da ba nawa ba saboda ban iya sosai ba. Balarabiyar tace kada ki damu zan fahimce ki. Suka tashi suka nufi bangaren da aka ware saboda hutawar dalibai. Haneefah tayi mamakin gurin domin bata taba zuwa ba kuma gurin ya bata sha'awa, babu hayaniya kowa a zaune yake wasu suna tattaunawa wasu suna karatu. Balarabiyar ta dubi Haneefah tace ni sunana Raihana Aaqil, haifaffiyar garin Saudi Arabia ce, nazo nan makaranta ne, ina da burin yin karatu sosai a rayuwata a kasashe daban-daban hakan yasa na zabi zuwa London. Tun da nasi admisson nake rokon Allah ya bani abokiyar karatu mai hankali da nutsuwa wadda tarbiyyarmu zata daidaita sai kuma cikin ikonsa ya hadani da ke, tunda na ganki naji kin kwanta min arai amma sai na kasa tunkaran ki domin bansan wani irin tarba zan samu agun ki ba. Ba karamin5 farin ciki nayi ba da na ganki kullum cikin ajinmu domin na tabba inba gurin karatun ki bane bazaki zo ba. Kina burgeni sosai yadda kike tafiyar da rayuwar ki babu ruwanki da kowa kuma inason mutum haka pls Allah ne ya hadamu mukasance masu kulla zumunci cikin yarda da amana. Haneefah tayi murmushi tana kallon Raihana, kyakyawace fara tas, kallo daya zaka mata kaga nutsuwa tattare da ita. Babu komai ina maraba dake Allah bamu ikon gudanar da zumunci domin shi. Cikin murna Raihana tace nagode yanzu tashi mu tafi aji kada lectures nagaba ya wuce mu amma baki sanar dani sunan ki ba? Haneefah ta bata amsa tana mikewa. Tare suka jera har suka tadda an soma lectures. Bayan sun koma hostel misalin karfe hudu sunci abinci sun huta Raihana tace yanzu time table zamuyi na karatu da sauran al'amuran amma in bai miki ba zaki iya canza wa. Haneefah tace yi in gani. Raihana ta dauko paper da biro ta soma zanawa, da safe misalin karfe bakwai zasu shiga wanka suyi shirin makaranta zuwa karfe bakwai da rabi, kafin takwas sun iso makaranta kuma zasu samu zaman gaba. Bayan sun gama lectures ko akwai interval kafin karfe biyar zasuje library library mu tattauna kan abinda mukayi a aji sannan in muka fahimta zamu wuce next course line mu rage karatu domin zamu fahimci abubuwa, sannan in muka koma gida zuwa magriba lokacin hutu ne in muka zamu it's fita zai mu fita mudan zaga gari, bayan mun dawo mukai sallah zamu kasance masu addu'a har akira sallah isha'i daganan sai mu rinka karatu zuwa goma ko sha daya saimu dauki littafin addininmu mu karanta daganan sai mu kwanta, zuwa asibahi saura awa daya zamu tashi muyi rako o'i muroki gafarar mahaliccin mu, in aka kira har lokacin asuba bayan mun idar sai mu dauki alqurani har zuwa karfe bakwai. In muna weekend zamu ware awa uku na karatu saimu fita zaga gari. Ina fata wannan tsarin yayi miki? Cike da mamaki haneefah ke kallonta tace yanzu na dada tabbatar da zanyi dacen kasancewa dake, tsarin yayi wallahi amma fa ban sauke alqurani ba. Raihana tace kada ki damu zan rinka gaya miki har ki haddace tare da tilawa in harma kina so da sauran littataifai da baki karanta ba. Cike dajin dadi Haneefah tace na amince. Tun daga wannan rana Haneefah ta fara sabon rayuwa da Raihana, rayuwace bisa tsarin addini, dan suna cikin turai basa barin lokacin sallah da mutane, kullum cikin lullubi suke ita Raihana kullum tana cikin habaya. Haneefah har mamakin sauran bakaken fata suke yadda suka watsar da komai kamar ba musulumai ba. Duk sanda suka samu lokaci suna fita suna yawo da haka suka fara gane gurare. Hankalinta Haneefah ya kwanta amma duk dare sai ta saka Yusuf addu'a, inda alkhairi tsakaninsu Allah basu ikon sake haduwa in ko babu alkhairi Allah albarkaci rayuwarshi ya basa ikon gamawa da iyayensa lafiya. Bata taba nunawa Raihana tana da damuwa, itama Raihana ta dangata ga wadda basason yawan surutu, Haneefah tana jin dadin yadda Raihana ta ke fahimtarta sai kuma ta tuno da aminiyarta hadiza. Kwance tashi ba wuya gurin Allah, yau su Haneefah suka gama jarabawarsu ta first semester tare da samun hutu na sati biyu. Zaune take tayi tagumi tana kallon Raihana dake hada kayanta zata tafi gida hutu, tabbas kwanakin da tayi da Raihana tana matukar debe mata kewa gashi suna komai tare. Har mamakin Raihana take in tana mata bayanin abinda ya shige mata duhu domin yarinyar tana da baiwar ilmin addini, zaman da tayi da ita ta qara samun nutsuwa domin addini ya dada shigarta, har sunyi nisa a qur'ani, yanzu inta ta tafi dawa zata rika karatu..... Firgigit Haneefah tayi daga tunanin da takeyi jin an tabata. Raihana ta sakar mata murmushi tace kamar yadda kike tunani haka nima nake tunani, nasaba dake domin kin cancanta domin ke mai riko da addinine, mun hadu domin Allah, zamu kasance domin Allah kuma mu rabu dominsa, in bazaki damu ba ki bini muje gidanmu. Haneefah tace nagode da shaidar da nasamu agunki kema hakanne yasa na kwadaitu in kasance dake, amma bani da halin binki bayanzu ba, insha Allah wata rana zamu tafi tare, zanyi kewar karatun da muke ne kuma zan kasance ni daya ce shiyasa kika ga na damu. Raihana ta tashi ta zauna kusa da ita, ta dubeta tace in wannan ne ba damuwa zamu rika yi tru video call nidai kada ki kula kowa bazan ma kai sati biyu ba just a day's. Haneefah tace toh naji. Ta tashi ta taimaka mata suka hada kayanta domin ba l dogon magana take ba, azuciyarta tace ni da biyamin kudin zuwa akayi aina zan samu kudi da zamu rika video call? Zan dai daure har kizo , sunata hira jefi-jefi domin yanzu Haneefah turanci ta fara zama a harshenta wani sa'in da larabci Raihana take mata magana dan haka har larabci ta soma ji amma kadan-kadan. Har airport ta mata rakiya Raihana ta bukaci lambarta, garin cirewa ta bata Haneefah ta yar da ID card nata. Saida jirginsu ya tashi sannan Haneefah ta kamo hanyar komawa makaranta. Sun kusa isowa motarsu ta baci, saita sauka tadan fara takawa. Dab ta iso makarantar taga wani hanya da kullum anabi amma basu taba bi ba... ganin mutane nabi itama ta dauki hanyar tana tunanin karambani irin nata. Saida tayi tafiya kimanin mintuna goma sha biyar taga tazo bakin ruwa. Duwatsune manya ga korayen ganye gwanin sha'awa.... ruwane blue wadda ba'a ganin karshen sa, gurin babu hayaniya shiru ga kallon gurin take cike da sha'awar gurin taji an katse mata tunani tare da kiran sunanta HANEEFAH! Ras taji gabanta ya fadi jin muryar namiji a irin wannan guri. *Dr HANEEFAH* 👩🏼32 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Farine sol kyakykyawa, kallo daya ta mishi tasan ba dan qasarsu bane wato Nigeria, cike da tsoro karara bayyane a fuskarta tafara ja dabaya ganin yana zuwa kusa da ita. Mirmishi taga yayi ya mika mata ID card nata tare da yi mata magana cikin harshen turanci yace na tsinta ID card naki ne a airport, kina fitowa na ganki shine nabiyo ki. A jiyar zuciya tayi tare da mika hannu ta karba tace nagode ta juya ta soma tafiya, shima yayi tafiyarsa. Hango wasu kujeru tayi, tana leke- leke harta iso ta zauna tana mai ambaton Allah. Kallon ruwan tayi cike da sha'awa, juye juye take taga wasu suna zaune fararen fata sun mannu da junansu tace da'alama soyayya suke. Kusan mintuna goma tana zaune ta kurawa ruwan ido, hakika gurin yayi mata dadi can ta hango wani qaramin gada wadda yana da iyaka ba sallake ruwan yayi ba. A hankali take tafiya harta iso ta soma tafiya akai, tana takawa taga wasu suna fitowa ta ciki ta basu hanya suna wuce taji macen na tambayar namijin mesa kake son nan dayawa? Ya bata amsa saboda inajin dadin kasancewa anan, inason irin wadannan gurare. Ras taji gabanta ya fadi da ta tuno da kalaman Yusuf, take ta ciro wayarta ta shiga gurin hotuna, WhatsApp images ta shiga har taje gun hotunan da take so, tsaye yake gaban ruwa ya dauki kanshi a hoto ya tura mata sannan ya dauki inda yake ya tura mata, gurine babu kowa babu komai sai ruwan da ke kwance da korayen ganye. _Haneefah tace Masha Allah gurin yayi kyau dear! Yusuf yace saboda inajin dadin kasancewa anan, inason irin wadannan gurare_. Ji tayi hawaye na neman zubo mata, duk yadda tayi domin kada su zubo amma sai da suka soma zubowa a hankali ta maida kallonta cikin ruwa sai taga ya canza kala alamar rana na dab da faduwa (sunset), ya hasko ruwan. Yusuf mesa bazan daina son ka ba? Mesa bazan iya hakuri dakai ba? Mesa nakejin bazan samu tamkar ka ba? Momy mesa kika rabani da danki? Kinsan yadda muke son juna? A lokaci daya Haneefah ke jerowa kanta wadannan tambayoyi. Sai ta fashe da tsananin kuka wadda har muryarta ya bayyana. A hankali ta tsaida kukan tana share hawaye tace bazan daina addu'ar Allah mallaka min shiba, agurin Allah nake tsammani ba ke ba Momy, sannan na miki alkawarin zama dashi amana. Sai kuma murmushi ya bayyana a fuskarta da ta tuno da kalaman Yusuf _Ana hakuri da kishin ruwa a nan duniya domin neman ruwa da inuwa a ranar alkiyama_. _Don haka, kasance mai yawan azumin nafila a nan gidan duniya domin neman dacewa da inuwa da ruwa mai sanyi a lokacin tsananin ranar alkiyama_ Nagode daka kasance a rayuwata, mai tunamin kyawawan rabo duk da bama tare, zan kasance mai juriyar kishin ruwan duniya insha Allah domin ko wacce jaraba ga dan Adam, tamkar ishine agareshi don haka zan tashi domin neman na lahira ta. Ta juya ta soma tafiya taji wayarta na ringing, tana dagawa taga Nana. Da sallama ta amsa suka gaisa tace ya karatu da sabon wuri? Ina fata bakya samun matsala? Haneefah tace babu komai wallahi sai alkhairi. Nana tace haka ake so, muma sai nextweek zamu gama exams, amma next year muke da shirin gamawa insha Allah. Allah taimaka Haneefah ta bata amsa. Suka dan taba hira Sukai sallama. Bayan ta iso hostel ta nufi banda ki tayi alwala ta fito ta zauna kan sallaya tana jiran lokacin sallah. Wayar ta taji yana ringing, ganin sunan hadiza yasa ta dauka da sauri tana mai cewa amin afuwa yar uwa wlh yau muka gama exams dama so nake na kiraki ko gobe. Hadiza tace ai kya bari mu gaisa tukun, bayan sun gaisa tace na tura miki hiton diyarki amma shiru baki hau online ba shine nace bari in kiraki. Wani irin farin cikine ya lullube Haneefah tace dan Allah yaushe kika haihu? Hadiza tace few hours ago. Murna gun Haneefah ba'a magana nan ta soma yi mata barka tace yanzu inna idar da sallah zan hau in duba sukai sallama. Bayan ta idar da sallah ta dauki wayarta domin kallon diyarsu. Kura mata ido tayi tare da tsananin kaunarta da yake shigarta. A hankali ta shafa hoton yarinyar tace Allah sa ki gaji mahaifanki wajen tarbiyya da ilmi. Zaune take ta kurawa yarinyar ido tace ko yaushe nima zan kasance da tawa? Murmushi tayi data tuno Yusuf yana cewa _mu ma next year da babyn mu_ tace ni nasan kaine uban yarana, zan kasance mai jiran lokaci nasan Allah na tare da masu hakuri. Tana cikin surutai Raihana ta kirata tace sun iso lfy amma zuwa anjima zata kirata suyi hira yanzu tana airport, sukai sallama. Ranar sunan hadiza yarinya taci sunan maryam mahaifyar usman suna kiranta da ummulkhairi. Haneefah sai da tayi hawaye batanan akai suna amma umma da kannenta duk sun tafi suna domin zumuncin Hadiza da Haneefah mai karfine wadda iyayensu ma kansu a hade yake. Kullum suna waya da Raihana, kamar yadda ta sanar mata ita take kiran Haneefah video call, Haneefah har mamakin Raihana take. *** *** Haka rayuwa takasancewa Haneefah a birnin London, kullum cikin karatu take ita da Raihana, babu ruwansu da kowa. Allah cikin ikonsa ta hada qur'anin ta baki daya, da sauran littataifai wadda Raihana ke biya musu, Raihana ta zamo kawa gun Haneefah sannan malamarta. Hakan yasa Haneefah take dada ganin girmanta. Tunanin Yusuf ya daina damunta sosai, sai randa abin ya taru ya mata yawa sai ta fita ta nemi guri shiru tana mai tunanin shi sannan bata gajiya da yi masa addu'a da dukkanin zuri'arsa. Karatu ya fara tsanani domin ko wani lecture sai sun fita asibiti. Nan suka yanke shawaran ko babu darasi su rika fita asibiti, in sunje zasu nuna ID card nasu. Kasancewa ba wani aiki bane sosai suke a radiography Haneefah takan wucewa gynecology department dake asibiti, nan ta fara sanin abubuwa da sama game da fannin. Raihana tana lura da yanayin da Haneefah take a sanda ta tuno Yusuf, kyaleta take ra fada mata komai da kanta bazata takura mata ba amma tana sakata addu'a Allah saukaka mata komai. Kullum waya suke da mutanen gida, tana kiran inna suna gaisawa sai dai inta kira yayun nata ne basa daga waya harta gaji ta daina kira. Yau asabar babu makaranta, Raihana tana waya da mamarta ita ko Haneefah tsaye gaban madubi take cikin bandaki tana karewa gashinta kallo, yadda yayi tsayi yayi baki tace lallai man gashinnan ya karbeta. Nan ta kurawa kanta ido, ta kara fari tayi kyau, kurajen fuskarta duk sun tafi ga yadda fatarta take sheki. Tace lallai wannan garin ya karbeni babu abinda nake shafawa amma dubi yadda nayi kyau? Menene sirrin? Yayan itatuwa tabawa kanta amsa, kullum cikin shansu take ga ruwa da take sha akai-akai wannan ma wani sirrine ne daya kamata mace ta rike. Ta fito tana shiri Raihana tace zuwa ina? Asibiti in zaki bini ta amsa atakaice. Itama tashiwan tayi suka fito a tare. Da kafa suke tafiya dan tsakaninsu babu nisa. Yana kallonta har suka zo suka wuce. Kevin dake kusa dashi yace guy gaskiyan ka yaran suna da kokari yakamata musa su cikin team namu koya kace? Nan ya juya kallon abokinsa yace bakar ta fi burgeni. *Dr HANEEFAH* 👩🏼34 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Dr Mubarak yace haba Haneefah bance kada ki nunawa wadannan mutane kwazonki ba? Shine ana meeting da manyan mutane kika sako baki toh gashi yanzu sun rikeki zama ya kama ki a wannan garin, amfani dake zasuyi tayi! Karshema su hanaki karatun Kash!! Mesa kikayi haka Haneefah?? Tunda taga ransa ya baci hawaye ya taru a idanunta, cike da muryar da na sani tace Dr dan Allah kayi hakuri, wlh banqi jin maganar kaba gani nayi ceton rai za'ai shiyasa. Nan Haneefah ta soma hawaye tana mai bashi hakuri. Ganin yadda take hawaye yasa yaji babu dadi ya soma lallashinta sai da ta tsada hawaye yace kimin alkawarin kada ki sake yin haka sannan kada ki qi karban aiki da dukkanin abinda zasu baki, babu plan nasu ya hau kanki muddin baki karba ba zasu san anason hanaki zama anan daganan zasu nemi mutanen da ke mu'amala dake susan gaskiya, kada kiji tsoro Allah na tare dake in munje anjima ki kula jin dadin ki da aiki kingi? Tace toh insha Allah bazan sake ba, zanyi yadda kace. Suna tattaunawa suka ga Kevin ,Rohan da Raihana sun nufo su. Bayan sun gaisa da Haneefah ta gabatar masa da kowannen su duk da yana jin labarin kowannen su. Ya nuna farin cikin sa yadda suke tare da qanwarsa, fatan samun nasara ya musu sannan suka nemi guri suka zauna. Duk motsin Haneefah akan idon Dr Mubarak, mamakine yarinyar take basa, bai taba zaton haka take sharp-brain ba, bangare daya kuma tausayinta yake ko son ta yake? Duba agogo yayi yaga awa dayan yayi, dan haka ya sanar da Haneefah su tafi office din Dr Michael. Dr Charlie ya dubi Dr Michael yace mesa kayi saurin yanke shawarar bata aiki kuma ita daliba ba yar kasar muba? Dr Michael yayi dariya yace nasan zakayi mamaki amma zan zo ka duba asibitin John akwai wadda ya kaishi tashe da yawan patient? Charlie yace a'a, Dr Michael yace tara baqaqen fata yayi cikin asibitin domin ana samun gifted cikinsu, mu turawa mun fisu bincike amma su sunfimu saurin fahimta, atakaice tsanarmu garesu yasa suka gane harya kaiga suna zuwa qasarmu domin su kwashe abinda muka bincika, ganin haka yasa John da zarar dalibi ya kammala makaranta zai dauke shi aiki da albashi mai tsoka, da taimakon wadannan ya gina asibitin shi. Nasan asibitina yayi suna amma wannan yarinyar zata tada min asibiti ya zamto duk duniya anaji da asibitina, bakai mamakin yadda cikin qanqanin lokaci ta bani amsa ba dazu a meeting? Kuma tana 200level in takai gaba ya zata kasance? Cike da fahimta Charlie yace hakane, yanzu sai a bata gida a cotest na qananan likitoci da mota da albashi mai tsoka. Dr Michael yace ashe ka fahimta, suka kwashe da dariya. Dai dai nan su Dr Mubarak sukai knocking, aka basu izinin shigowa. Suka sami guri suka zauna. Haneefah ce ta nuna farin cikinta game da aikin da suka bata. Dr Michael yace in bazaki damu ba har masters naki zamu so kici gaba anan kuma asibitine zai dauki nawinki. Haneefah ta kalli idon Dr Mubarak baice da ita komai ba tace ranka ya dade zanso na karasa karatun nawa kafin in dauko da wannan maganar sannan zan nemi shawaran iyayena duk da nasan ba zasu kiba farin cikin sune ace yarsu tana aiki a wannan asibiti. Sunji dadin furucin Haneefah nan suka mata albishirin da gida, mota da albashinta kimanin dubu dari da hamsin matsayinta na qaramar staff. Ba Haneefah har Dr Mubarak yayi mamaki. Charlie ne ya kaisu har gidan da kyakykyawar motar ta a fake a gaban gidan. Tsarerren gidane wadda ya kunshi komai na bukata a ciki, babban falo da dakuna uku. Komai na cikin yayi amma Charlie ya tambayeta ko akwai abinda take son canza wa ciki? Haneefah tace babu komai. Yace zata iya tarewa ko yanzu ma. Dr Mubarak yace abari ko zuwa gobe sukai sallama ya tafi. Bayan sun zauna Dr Mubarak ya dubi Haneefah yace kinga da irin wadannan ababe suke zolayar mutane, kuma na tabba ke bazayyi tasiri akanki ba. Haneefah ta dago ido suka hada da Dr tace yaushe kazo ne? Dab da zaku shiga meeting, shine na biyo ku, dalilin zuwana shine inason tafiya dake Egypt an wakilceni wajen yaye dalibai wato su Nana. Tsantsar farin ciki ya bayyanu fuskar Haneefah. Dr nagode Allah saka maka da alkhairi, nayi farin ciki kwarai. Yace babu komai saiki soma shiri jibin da safe zamu tashi sannan kada ki sanar da Nana ina son muyi suprising nata. Haneefah doki take harta iso hostel nan take sanar da Raihana tafiyarsu jibi sannan take shaida mata sabon gidanta. Da dare Haneefah taje ta muna musu domin da Raihana zasu koma gidan da zama, sun yaba da tsarin gidan, ta damka wa Raihana makulli tace kafin suzo tayi abinda ya kamata dan ba zasu wuce kwana biyu ba. **** **** An fara gudanar da taro tukun jirginsu ya sauka, da saurin gaske tukun suka iso amma dab ake da kammalawa. Basu wuce minti goma sha biyarba aka gama taron, kowa yana dauka hoto. Nana saye take tana murmushi farin ciki, bakin cikin ta kuma shine bata ga dan uwanta daya da zasu dauka hoto a wannan rana ba. Ji tayi an rungumeta ta baya, Haneefah ta daga wayarta tace say cheese! Ta dauke su a hoto, hotuna kusan goma sukai kafin Nana tace tsaya tukun ya akai kika zo? Nuna mata Dr Mubarak tayi tace ga wadda ya taho dani je ki mishi godiya. Godiya harda hawaye tayiwa Dr. Shiko ganin Haneefah cikin farin ciki yasa yaji duniyar ta masa dadi domin ya rinyar ta soma birge sa _toh fah_ Nana tayi murnar ganin yar uwarta, sannan tayi mamakin jin aikin da ta samu amma sai da ta gargadeta akan tabisu a hankali. Nana dai baki yaki rufuwa ganin Haneefah ta canza ko dai ta riga ta mance da Yusuf ne? Ta so tambayarta amma tsoron kada ta canza musu mood yasa ba tace komai ba. Washe garin ranar Dr da Nana suka bi jirgi zuwa Nigeria ita ko Haneefah take jiran jirgi zuwa London. Taxi ta tara har zuwa bakin makarantar su. Bayan ta sauka ta nufi hanyar hostel. Tana zuwa ta tarar a kulle. Waya ta ciro ta kira Raihana tace kina ina nazo fa? Tace ina asibiti amma yanzu zanzo sabon gidan mu, murmushi Haneefah tayi ta katse wayar. Tafiya take a kafa harta iso bakin Cotest, daidai zata knocking kofa taji horn. Motarta ta gani Raihana tana ciki. Cikin fara'a Raihana ta sauko tace amin afuwa nayi karanbani. Haneefah tayi dariya tace haba dai gidan ma an baki bale mota. Ta bude mata suka shiga, subhanallah! Haneefah ta fada ganin yadda falon yayi kyau ya tsaru, Raihana taja hannun ta zuwa kitchen nan ma ya hadu domin irin tsarin turawannane masu tsananin kyau, zagaye gidan tayi cikin tana mamaki harta iso sama inda aka yi domin shakatawa, glass ne ya rufe gaban sai gefen wardrop na takardu da kujeru biyu da table a tsakiya. Gidan ya tsaru sosai, Raihana tace saura bedroom amma ki rufe idanun ki kafin mushiga. Idanunta a rufe suka tura kofar suka shiga, a hankali ta bude idanun ta, neman numfashinta tayi ta rasa dalilin abinda idanuwanta suka hango mata. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼35 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Murmushi yake wadvda ya bayyana fararen hakoransa cikin fararen kaya, adon kayan da baki a jiki sai hularsa da agogon hannunsa baki, yayi matukar kyau sosai cikin hoton. Gefen hoton ta gani su biyune cikin mota yadan matso kusa da ita ya dauke su randa bazata taba mantawa ba, randa Momy ta nemi alfarman rabuwa dashi. A hankali ta soma tafiya tana goge hawayen da ke fita a idanunta harta karaso inda hotunan suke. Ta tsaya tana murmushi tace Yusuf ka sanar dani, muddin dan Adam yana son zama wani abu a doron kasa zai zamo sai dai niyyarsa kadanne, in suna yake nema zai zamo, ka sanar dani cewa koda mutumin da banza ne mutum zai zama amma ba so daya ko sau biyu da aikatawa zai samu suna ba, yau da gobe har zai kasance cikin matakin da yake nema, yau gashi ni Haneefah ban nakai matakin da na samu gidan kaina, mota da albashina amma banyi farin ciki dasu ba, cikin shekara biyu nasan abubuwa da dama! Tabbas komai sa kaine muddin mutum yace zayyi abu zayyi sai dai bayyi niyya ba, ban manta da kai ba kana cikin raina Yusuf! Yaushe zaka iso gareni? Ina zaman jiranka. Nan ta fashe da kuka mai tsanani ta sulale ta fadi a kasa tana ci gaba da kukan ta. Raihana da ta aikata hakan sai taji babu dadi. A hankali tazo ta durkusa gabanta tana share mata hawaye tace kiyi hakuri banyi tunanin abin zaikaiga haka ba, gani nayi a duk sanda kika dauki wayarki kina kallon shi kinajin nishadi wani sa'in inga kina hawaye shiyasa na tura hotunansa wayana nakai akai enlarging nasu amma kiyi hakuri zan shire su kidaina kuka. Haneefah ta tsaida kukan tace aa kada ki ciresu inason kayana kuma nagode da kikai haka, banyi niyar sanar dake ba amma ya zama dole in sanar dake wannan bawan Allah. Nan Haneefah ta sanar da ita komai game da Yusuf ta qara da cewa ina zaman jiranta duk sanda taga ya dace na auri danta zata zo ta nemi alfarman in aure shi. Raihana tace gaskiya abin akwai ban tausayi amma mesa zata tauyewa danta hakki? Babu kyau ga iyaye dan sunga dansu na musu biyayya su juya su yadda suke so... da sauri Haneefah ta katseta tace danta ne tana da ikon yin komai akansa. Raihana tace duk da haka zamanin yanzu dole kabi yaro da hankali, ita daji dadima ta samu mai mata biyayya! Allah shirye mana zuri'armu. Naga kuskuren ki daya Haneefah. Haneefah ta dago ido tana mata kallon tambaya? Tun farko kuna addu'an Allah tabbatar muku da alkhairi, toh kun rabu mesa bazaki dauki hakan cewa shine mafi alkhairi ba? Yakamata kici gaba da addu'a Allah kawo miki mafi alkhairi arayuwarki tunda kun rabu bawai zaki ci gaba da addu'a Allah kawo shi ba. In bai zoba ya zakiyi? Nan Haneefah ta shiga tunani, maganar Raihana gaskiyane toh amma ya zatai da sonshi da ke adda barta? Mafita shine ta kawar da wannan son, wani sashe na zuciyarta na mata gargadi da hakan. Cikin kankanin lokaci taji tunani ke son rikita mata kwakwalwa. Tashiwa tayi tabar gurin. Har dare Haneefah na abu daya, da gaske Yusuf sun rabu kenan? Ina! Nasani zaizo yana sona. Raihana data lura da ita tace nasan abune mai yuwa agareki kiyarda da abinda nace amma arayuwa anason bawa yakasance baya riko kan al'amarin duniya ki barwa Allah zuciyarki kawai. Tashi tayi ta fita a dakin. Zaune tayi cikin kujerun alfarman dake falo tana tunanin anya ko zata iya kasance da wani? Nan ta soma ambaton Allah ya duba mata wannan lamari. Tashi tayi ta dauki qur'ani ta soma karantawa, a hankali ta soma jin sassaucin kuncin da take. Murmushi ta soma yi tana kallon qur'ani. Rufewa tayi ta daura kirjinta tana cewa nagode maka Allah da ka yini musulma kuma makaranciya, rayuwata da zuciyata na hannun ka, ka zabanin abinda yafi alkhairi. Tana kaiwa nan ta kwanta ta soma barci. Cikin mafarki taga Yusuf yana mata murmushi, gani daya ta masa taga ya rame yace da ita Haneefah kada ki barni ina bukatar ki pls! Firgigit ta tashi tana waige- waige. Ganin agogo tayi karfe uku, tashiwa tayi ta dauro alwala tafara nafiloli. Bayan sun idar da sallah asuba taji wayarta na ringing, tana dagawa taga Abba. Da sallamar ta ta amsa suka gaisa tare da tambayar mutanen gida? Abba ya amsa da kowa lafiya ya qara da cewa dazu yar'uwarki tazo lafiya, kema muna miki fatan kizo lafiya duk da Mubarak ya sanar dani halin da kike ciki, ki kwantar da hankalin ki yadda kikaje lafiya haka zaki zo lafiya. Murmushi tayi tace Abba nagode, zan kasance mai farin ciki muddin ina biye da albarkan ku. Allah miki albarka Haneefah. A hankali tace ameen sukai sallama. **** **** **** Jiran driver yake yazo ya tafi da shi airport domin wucewa gurin aikin sa. Rahma ta fito cikin sauri ta nufo shi tace ina zaka? Airport zanje ya bata amsa, zaka iya kiran mum na ta iso domin driver yaje daukan ta a airport. Yusuf yace ok kafin bari inje in karbi sim na dana bada amin welcom back. Rahma tace kada ka dade domin akwai maganan da nake so nayi dakai in mum ta zo, bataji me yace ba ta nufi bangaren Momy. Ganinta yake cike da mamaki ko mesa bata son fitarsa yau. Ya dau hanyar gate sai kuma ya tuno sim park nashi dake wardrop, ya juya dakyar yake tafiya har ya isa sashen shi. Rahma najin qarar tsayiwar mota tayi sauri ta fito ta tare mum, janta tayi zuwa sashen su. Mum ta dubeta tace ai kya tsaya in gaida yayartawa ko? Rahma tace mum wllh sai kin saurareni kafin ki gaisa da kowa suka nufi sashen su. Momy jin kanwarta bata shigo ba yasa tace bari ta lekata ko dai lafiya? A falo ta samu Aisha zaune tana kallo tace taso muje mu dubo umman ku nusaiba naji shiru bata shigo ba. A tare suke tafiya har suka iso gurin motar sukaga wayam. Aisha tace Momy ina suke? Momy ta kira driver tace ina bakuwar daka kawo? Driver yace Hajiya Rahma tazo sun nufi sashin su tare. Momy mamakine ya kamata tace da Aisha su wuce sashen nasu. Abinda kunnuwan su suka fara jiye mu sune yasasu daka tawa da shiga falon. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼33 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Kevin ya dubeshi sosai yace duk wadda suke 100level su kadai suka damu zuwa asibiti, mu qara musu kwazo ta hanyar nuna musu hanya koya kace Rohan? Yace great idea tashi mu bisu dan nasan can zasu nufa. Su Haneefah basu tsaya ko ina ba sai bangarensu, suka tarar a kulle dan haka suka wuce laboratory nan suka tadda a bude. Bayan sun gaisa da wani ma'aikacin da suka tarar suka ce muna bukatar tayaka aiki amma mu dalibaine... Nan ya zage yafara gabatar musu abubuwa tare da amfanin kowannen su. Sun kusan awa daya suka nufi gynecology. Nan sundan san jama'a suka ci gaba da daukan lecture. Su kansu baturen yadda su Haneefah suke daraja su ne abin yake burgesu har su koya musu abubuwa da dama. Su Kevin sanin basa department nasu yasa suka nufi inda zasu same su. Zaune su Haneefah suke gaban wata staff tana musu bayani akan abinda suka gama treatment. Suna fahimtar bayaninta sosai. Jin anzo an zauna kusa da su ta dago ido tana kallon shi. Shima kallon nata yake yace me kukeyi anan bayan nan ba bangaren ku bane? Tsab ta ganeshi, wadda ya taimaka da ID card nata daya fadi a airport. Baturiyarce ta kallesu tana dariya tace kunbiyo colleagues naku ne? Toh sunzo karin ilmine wannan bangaren domin naku bangaren kulle yake. Kevin yace taso muje mu bude sai muyi karatu tare. Haneefah batayi niyan tashi ba Raihana ce taja hannun ta suka tafi. Sun bude department nasu suka kaisu gurin manyan na'urori nan su Haneefah suka bude baki sai kallo. Kevin ne ya soma magana yace ni sunana Kevin daga nan garin nake wato London, wannan kuma Rohan daga India yake. Department namu daya amma muna gaba da ku, muna kallon kwazon ku wajen zuwa asibiti duk da ba'a fara fitar daku ba, sau tari muna ganin ku a library atakaice duk cikin daliban wannan shekaran kune kusan na farko wadda suka san meya kawo su wannan makaranta, hakan yasa muke son shiga rayuwarku mubaku wani abu game da abinda muka sani amma sai da yardan ku. Haneefah ta kalli Raihana cikin harshen larabcin da bata kore ba tace nifa ki tashi mutafi tsoron su ma nake ji, ya za'ai mufara karatu da maza? Raihana tace su suka ce da yardan mu amma mesa bazamu basu dama ba tunda karatu kawai suka ambata. Rohan yayi murmushi cikin harshen larabci yace daama zaku bamu duk da mutanen yanzu ba'abin yarda bane amma in kun damka kanku Allah amanar kanku babu abin sharri dazai fuskance ku sai alkhairi. Haneefah taji wani bala'in kunya kamar kasa ta tsage ta shiga, dama yana jin larabci? Kevin ne ya katse mata tunani da cewa mun iya yaruka daban-daban cikin shekaru biyu, in bakwa shiga cikin mutane abubuwa zai barki, bawai zakiyi mu'amala dasu sosai ba kawai dan ki fahimci wani abu game da abu na rayuwa. Rohan yace mu musulmaine, Kevin ne mahaifinsa christer, tun yana karamin ya musulunta, mahaifinsa ya yarda da musuluntarshi amma yanemi alfarman ko da zai musulunta kada ya canza sunshi domin takwaran kakan shine. Ni kuma dukkan gidan mu musulmaine dan haka kada kuyi shakka mu yan uwanku ne. Raihana tace Alhamdulillah, ai yazo da sauki, mun amince Allah saka da alkhairi. Rohan ya dubi Haneefah yace bakice komai ba? Haneefah tace ba komai Allah shige mana gaba. Sannu a hankali Haneefah ta gama sanin bangaren karatun da wasu bangaren da ba nata ba musamman gynecology, sannan tana jin dadin tarayya da Rohan da Kevin domin duk abinda ya shige mata duhu tana samu bayani sosai gurinsu. Sannan sun fahimce Rohan da Kevin ana matukar ji dasu domin ba kananan dalibai bane domin suna matakin karatun masters ne, bangaren addini ma sun rike addini basa shaye shaye da sauran munanan dabi'u, hakan yasa kansu ya dada haduwa su hudu. Su Haneefah anyi nasaran shiga 200level. Sun gama exams nasu na 2nd semester sun shiga na 3rd a wannan lokaci dukkanin dalibai anturasu asibitoci. Zaune suke bayan sun gama ganin wasu patients, Haneefah tayi shiru tana tunanin yadda zata tafi Egypt wajen Nana domin nan da jibi za'a yayesu kuma tunda Dr Mubarak ya tafi bai sake zuwa ba. Raihance ta tabata tace an shiga meeting tashi mubi su. Gurine da cika da manyan likitoci da manyan dalibai bangaren radiography, wani daga cikin baturai manyan mazauna gurin ya tashi ya soma bayani yace ina mika gaisuwata da ko wannen ku, ba tare da bata lokaci ba zan gabatar da abinda yasa mukai taro na gaggawa, aka hasko wani hoto yace wannan sabon case ne wadda yazo mana a jiya, munyi yadda zamuyi domin gano abinda yake damun wannan amma abin yaci tura, mu kuma bama so mu mayar dashi batare da gano abinda ke damun shi, dan haka muna jiran duk wadda zai iya gano wani abin. Haneefah dariya yaso kubuce mata amma tayi shiru domin yadda gurin yayi tsit, azuciyarta tace yau na tabbata baturai mayu ne, basu ga komai ba amma sai sun tabba akwai abu. Zaune a inda take ta kurawa hoton ido domin ta soma hango matsalar. Kusan minti goma babu wadda yayi magana hakan yasa ta daga hannu alamar tana son magana, Raihana tayi saurin saukar da hannun ta amma tuni an bata damar tashiwa tayi bayani. Jama'ar gurin baki daya kallon su ya koma gunta, ita dai Haneefah a hankali take taku harta iso inda aka hasko hoton ta juya kallon jama'an. Cikin nutsuwa ta soma bayani yadda abin yake da yadda mafitar zata kasance muddin akai aiki yadda take ganin haka ne, sannan ta karasa bayani da cewa ayi hakuri innayi kuskure domin kasancewa ta daliba. Komawa zatayi ta zauna taji an soma tafi, juyawa tayi taga wani tsohon bature wadda take tsammanin shine mai asibitin, ganin haka yasa dukkanin gurin suka soma tafi. Baturen ya tashi yace wannan case na taba treating nashi shekaru goma da suka wuce kamar yadda wannan yarinyar ta fada, nayi mamaki da kike daliba har ilmin ki ya kaiga nan duk da haka kin samu karin girma a mtsayina na mai wannan asibitin zaki fara aiki. Murmushi Haneefah tayi tace nagode amma bazan iya aiki ba domin karatu ya kawoni. Ji tayi ance zaki iya. Da sauri ta juyo dan jin muryar Dr Mubarak, ya karaso yace ranka ya dade zata iya domin karatuma a karkashin ku take bale aiki. Baturen yayi murmushi yace kusameni a office anjima bayan awa daya. Nan meeting ya tashi mutane suna zuwa mata domin tayata murna da nuna kwazonta. Ita dai tsananin mamakin zuwan Dr Mubarak tayi. Bayan sun fito ne suka samu guri suka kebe. Kallonta yake sama har kasa, habayane jikinta Brown colour sai tayi rolling da black gele, ba wani makeup ne tayi ba amma tayi kyau sosai. Dr Mubarak kallonta yake kamar ya hadiyeta duk da yasan barrister ta fita kyau amma kyan Haneefah dabanne. Ganin yayi shiru yasa Haneefah tace Dr sannu da zuwa kawar da kai yayi sannan ya hada rai. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼36 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Rahma tace mum hakuri na ya kare, farin cikin ki nake so nayi aurennan don kina son samun jikan da zai gaji Yusuf, toh Yusuf yayi hatsari ya samu matsala bazai sake haihuwa ba, sai kisan yadda za'ai na fita nabar gidan naje na auri wadda..... Umma Nusaiba ta toshe mata baki da hannuwa tace so kike ki tonamin asiri , yar uwan tawa zan duba cikin ido ince abaki takarda saki sabida danta baya haihuwa? Yanzu bazaki rufawa dan uwanki asiri ku zauna ba? Cikin kuka rahma tace Mum wallahi bazan iya zaman gidannan ba, ba so na yake ba, kuma ai dama bada niyyar zama nazo ba cemin kikai inna haihu zanbar gidan, mum na hadu da wadda zai so ni kada kisa nafara bin maza da aure na wlh nagaji da zaman gidannan. Mum na kokarin buge mata baki taga Yusuf ya fito daga bedroom. Durkusawa har kasa yayi ya gaisheta, bai nuna mata ya ji dukkanin abinda suke tattaunawa ba. Ganin bata amsa ba ya tashi ya nufi hanyar fita, turus yayi ganin Momy da Aisha bakin kofa. Momy ce ta kamo hannun sa ta shiga dashi falo har gaban Rahma. Tace wannan kike kira juya? Kinyi babban kuskure, sannan bazanki ya sake kiba, bazan so ki kasance kina bin maza da auran ki ba. Ta juya ga Umma Nusaiba tace da kingayamin wannan shine manufarki akan da na ban biye miki ba, wannan shine sakayyar da zakimin matsayina na yar uwarki? Ciki daya muka fito fa? Dubi yadda ya kama sanadiyyar janye auren da na sashi yayi kawai saboda yarki takasance cikin farin ciki da samun soyayyar da na. Babu abinda zan iya ce miki, ta dubi Yusuf tace rubuta mata takardan saki... Zayyi magana tace ban lamunci kace min komai ba nina ce kayi. Nemo takarda tayi ta mika masa ya rubuta mata saki daya. Momy ta karba ta mikawa Rahma tace zaki iya tafiya ki auri duk wadda kike so, sannan kin horar da mahaifa irin mu masu son hada yara aure musamman maza, darasine agareni sannan ke kuma nusaiba nan gaba ko hijabine kada ki bata zabi kinci sa'a nakasance yar uwarki mai rufa miki asiri. Inkin huta zaku iya barin gidana. Tana kaiwa nan ta juya ta fita. Aisha ce ke biye da ita har bedroom, ta zauna kan gado ta dafa kanta tace Aisha ni wace irin uwace? Dubi abinda najawowa Yusuf, yanzu da wani ido zan dube shi? Nina jawo masa rashin auren zabinsa gashi zabin nawa sun zubamin kasa a ido har suka kiran da na juya! Aisha tazo kusa da ita tace Momy ki daina fadin haka, nagode da Allah daya bayya gaskiya dan nasan innice nazo na fada miki bazaki yarda ba amma tunda gaskiya ta fito shikenan, ke uwace abin alfahari agaremu, domin kin mana abinda bazamu iya biyan kiba, abinda nake so dake neman lafiyarshi zamu ci gaba da yi tare da yi masa addu'a. Da wadannan kalamai Aisha ta kwantarwa Momy hankali. *** *** *** Zaune yake aiki ya gagaresa ya kurawa hoton Haneefah ido yau shekara biyu kenan da rabuwarsu, yana son dakkowa Momy maganar Haneefah amma tsoro yake domin bayason wani abinda zai taba tsakaninsa da Momy. Wayarsa ce ta soma ringing ganin Aisha ce ya daga tare da sallama tace yaya albishirin ka yace goro. Salma ta haihu namiji mai kamar ka! Dariya yayi yace haba weekend dinnan zanzo ashe inga young engineer, sukai sallama ya ajiye wayar. Lumshe ido yayi yana rayawa a ranshi yaushe Haneefah zata fara haifa masa nasa yaran? Ya Allah dan girman zatinka ka bamu ikon kasancewa a inuwar ma'aurata. Haka yake ta kissimawa aranshi har lokacin tashi yayi yabar office ba tare da yayi komai ba. Bangaren Momy kuwa damuwa tashiga sosai, da kanta ta yanke shawarar tafiya gidansu Haneefah domin neman afuwarta sannan ta dawo mata da soyayyarsu. Batayi tunanin tafiya ko ina ba sai gidan Hadiza, domin acan ne tasan zata samu address din gidan su Haneefah. Parking tayi bakin gate din ta shigo a hankali. Knocking daya tayi akazo aka bude mata. Hadiza ba karamin mamakin ganinta tayi ba, bata hanya tayi ta wuce. Bayan ta zauna sun gaisa Hadiza ta tashi ta shiga kitchen domin kawo mata ruwa. Tsayawa tayi tana tunani meya kawo ta? Tuna ranar da ta durkusa gabanta tana bata hakuri tayi, share hawayenta tayi ta dauko ruwa da cup ta aje akan plate ta fito. Momy duk kunya ta cika ta dakyar ta bude baki tace dama address dinsu Haneefah nazo nema. Hadiza ta dago tace ko lafiya? Momy tace gaskiya gane kuskurena nayi nake son bata hakuri. Murmushin takaici hadiza tayi tace kuskure? Kin manta lokacin da na durkusa gabanki ina baki hakuri? Ko da Haneefah bata kasance matar aure ba bazaki sameta da sauki ba balle yanzu da aurenta haihuwa yau ko gobe. Momy cike da dana sani tace tayi aure? Hadiza tace eh lokacin da kika hana auren cikin manemanta suka fito a wata biyu aka daura auren yanzu haka tana kasar waje da aure batama Nigeria. Cikin sanyin jiki ta tashi tace nizan wuce. Har bakin gate hadiza tayiwa Momy rakiya tace ta gaida gida. Bayan tafiyarta Hadiza tace am sorry na miki karya amma Haneefah ce ta nemi wannan alfarma agurina, kuma bazan iya katse mata karatu a wannan lokaci ba Allah zaba musu abinda yafi alkhairi. ***** ***** ***** *BAYAN SHEKARA DAYA* Zaune take cikin office tana tunanin sabon salon Dr Mubarak, in ma sonta yake ya sani bazayyu ba domin bazata sakawa da barrister da haka ba. Bangare daya kuma ga Rohan daya fitineta da nashi salon, da tayi magana yace kawai missing nata zayyi inya koma India. Juyo da kujeranta tayi tana fuskantar hoton yusuf dake gaban table nata. Raihana ce ta shigo da sallamarta tace Haneefah a gyne ward kina da patient ana neman ki. Dago ido tayi tace Raihana zo nan, tazo kamar yadda tace ta nuna mata hoton Yusuf tace dubi shi kullum cikin tunaninsa nake bansan ko shi yana tunani na ba, nayi escaping daga Nigeria ko zan daina tunaninsa amma gashi sauramin shekara na koma ban dain..... Bata qarasa ba taji wani irin murdan mara daya hanata motsi, shirun da tayine yasa Raihana tace ina jinki. Amma sai ganin Haneefah tayi tana salati tare da rike mararta kafin tace meye ta fadi su mammiya. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼37 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Raihana ta matukara rudewa, ta rasa wani irin taimako zata fara bata, da sauri ta saki Haneefah ta fito domin kiran taimako ta ga Kevin da Rohan. Ganin rudewarda tayi yasa suke tambayarta, ganin ba bata amsa zasuyi ba yasa suka shigo office din. Dukka sukayo kanta suna jijjigata amma ko motsi batayi, Kevin ya bude fridge ya dauko ruwa aka yayyafa mata amma shiru. Ganin haka yasa Rohan daukarta suka fita. Emergency suka kaita, Kevin ne yayi kokarin kawo musu rigar shiga threater ganin haka yasa Raihana yasa fashewa da kuka tana cewa meya sameta ne zaku shiga da ita? Rohan a rude yace kisa mana! Dai dai nan Dr Michael yazo yake tambayar Raihana lafiya take kuka? Cikin kuka tace sir Haneefah ne unconscious, cike da mamaki yace Haneefah? Bai jira amsarta ba ya wuce inda aka shigarda ita. Likitoci kusan goma akanta. Sanda suka tsananta binciken awa biyu suka gano matsalar dake damunta. Raihana nesa da su tayi tana kallon irin binciken da sukeyiwa Haneefah, babu abinda take sai addu'a Allah bata lafiya. Hawaye take da ta tuno dazu tare suka ta ho asibiti amma gashi yanzu itace kwance bata san ma inda take ba. Duniya kenan babu abinda zamu nema muji dadi kamar mu kasance masu kyakykyawar zuciya. Sharar hawayenta tayi lokacin da ake kokarin daga Haneefah acireta a daki zuwa daki na musamman. Bayan an kwantar ta ne Dr Michael ya kalli Raihana yace nan da awa daya zata iya tashi, komai zai daidaita amma ki kirani ina office, ta amsa da toh. Dukkanin su zubawa Haneefah ido sukai ganin yadda ta koma cikin awa uku! Duk dauriyar Rohan saida ya zub da hawaye lallai dan Adam bamu da tabbas, rayuwa muke da buri amma bamusan yaushe zamu koma ga Allah ba, yanzu ne anjima aa Allah shiya barma kansa sani, ji yake kamar ya ciro cutar ya dasa a jikinsa. A hankali ya tako har ya iso dab da ita yace Haneefah ki bude ido dan Allah, kitashi kiga yadda muka damu da ganin kin bude idanunki, in wannan ne matsalar na miki alkawarin maganance miki ita zan kasance da ke har abada.... Raihana ta katseshi da cewa Rohan na rokeka da Allah kayi shiru ka kyaleta, irin wannan yanayin zaka danko mata maganar zaka rayu da ita inta tashi lokacin hayaniya sannan in ciwon bai ragu kuma fa? Ko kallon Raihana bayyi ba yaci gaba da surutan shi. A hankali ta bude ido tana kallon inda take, lumshe ido tayi jin abinda take ji ajikinta. Sake bude idonta tayi ta juya kenan suka hada ido da Rohan. Rohan yace sannu Haneefah, da sauri Raihana tazo kusa da ita tana cewa Haneefah meya sameki? Kina iya magana? A hankali Haneefah ta tashi ta zauna tace am fine but.... kuma sai kuma ta kasa karasawa. Raihana tace bari inje in kira Dr yace inkin tashi in kirashi. Dr Michael ya dubi Kevin da Rohan yace su basu guri. Ya dubi Raihana yace dalilin da yasa bance ki bamu guriba shine duk lokacin da irin wannan matsala ta taso mata zaki iya taking action domin na tabbata tare kuke. Dr yace Haneefah kina da aure? A sanyaye tace babu. Ya fara bayani yace abinda ya sameki ba abin tada hankali bane amma sai kinyi saurin daukan mataki wato aure, inba haka ba abin zai samo miki babbar matsala. Yaci gaba da bayani wato kina da tsananin sha'awa right? Ya jefo mata tambaya Nan Haneefah tayi shiru tare da sunkuyar da kanta katsa. Dr yace wato kwayayen haihuwan kine da basu samu mazauni suke son fitowa ta hanyar baki wahala amma mun gano kuma kina da tsananin sha'awa, ciwon marar da kikai yana nufin muddin baki samu haihuwa ba ko sau daya ne hakan zaici gaba da faruwa dake, kuma zai iya haifar miki da matsala a mahaifa, shawarar da zan baki shine kiyi gaggawar yin aure. Ke kuma Raihana nan gaba taimakon da zaki bata shine allurai zaki mata ki kwantar da ita, da zarar ta farfado zata koma daidai. Ya kalli Haneefah yace Allah baki lafiya yanzu zan aiko miki da alluran naki, zaku iya tafiya. Bayan fitar Dr Raihana ta taso tazo kusa da Haneefah, zatayi magana taga su Rohan sun shigo. Sannu sukai mata ta amsa, ta tashi a hankali ta lullube jikinta tace da Raihana zata je tattaro kayanta a office ita tajira akawo mata alluran sai su wuce gida. Rohan yayi saurin shan gabanta yace Haneefah baki da lafiya zanje in dauko miki duk abinda kike bukata ki kwanta ki huta tukun sai mu wuce. Wani kallo Haneefah ta watsa mishi, ba shiri ya bata hanya ta wuce. Tana shiga office ta maida kofar ta rufe da makulli. A hankali taje kan kujerarta ta zauna, hannu tasa ta dauki wayarta dake katsa ta kunna. Idanunta suka sauka kan hoton Yusuf. Kamar kullum ta shafa hoton a hankali tace har yaushe zan jira ka? Zuciyata da dukkanin gangar jikina takace yaushe zaka zo mukasance cikin farin ciki? Banajin zan iya kasancewa da wani da namiji inba kaiba Yusif. Runtse idanunta tayi da jin murdan marar har yanzu bai dakata ba. Ya Allah ina rokonka da kyawawan sunayenka, dan soyayyar da kamawa annabinmu fiyeyyen halitta, annabi Muhammad (S. A. W) Ka bani ikon tsare kaina da aikata zina, ka bani ikon killace budurcina har izuwa gidan mijina, ka bani ikon cire son bawanka Yusuf a zuciyata inba alkhairi bane shi gareni, inko shi mafi alkhairine gare ni kabani ikon hakuri da har izuwa randa zaizo gareni, ya Allah ni baiwar kace mai yawan zunubai ina neman tuba gare ka... Nan ta durkusa ta soma kuka kamar ranta zai fita. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼38 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Saida taji bugun kofar tamkar za'a balle kofar sannan ta tashi taje ta bude kofar. Rohan tagani biye da Raihana, basu hanya tayi suka wuce. Da taimakon Raihana suka tattara dukkanin abinda take bukata suka fita. Cikin mota babu wadda yayiwa wani magana. Raihana ke tuki gefenta haneefah, kevin da Rohan suna baya. Har suka iso gida babu wadda yayiwa wani magana. Haneefah ce ta fara shiga gidan, bata tsaya ko ina ba sai bedroom. Rage kayan jikinta tayi tashiga bandaki domin wanka. Da ruwan dumi tayi wanka ta fito daure da towel. Gaban mirro ta tsaya tana karewa kanta kallo ganin lokaci daya harta fada, ikon Allah tace cikin zuciyarta, yanzu nice cikin qanqanin lokaci na koma haka? Kuma nake buri da son haduwa da Yusuf, dan Adam kullum cikin buri muke yanzu in fadi na rasu a wannan lokaci babu abinda zan tsira dashi illa abinda nake sakawa a zuciyata, in sharri ne yaragemin. Allah sa mucika da imani. Ko shafamai bataiba tasa doguwar riga da himar ta tsaya sallah. Bayan ta idar ta kwanta ba'ajima ba bacci ya saceta. Jin shiru yasa Raihana lekowa taganta tana bacci, ta koma falo tace dasu tayi bacci. Sallama sukai mata akan anjima zasu zo su ganta. Gab da magriba ta bude ido. Raihana tagani gabanta tayi tagumi ta zuba mata ido. Janye mata tagumin tayi tace nasamu sauki fa, banajin... kallon agogon da tayine yasata tashi da sauri ta nufi banda ki yin alwala. Bayan ta idarne ta zauna lamizi domin mintina kalilan suka rage lokacin sallah. Zaune suke suna cin abinci kan dining table, duk motsin Haneefah idon Raihana na kai, data lura da hakan tace na samu sauki, abaya yanamin irin wannan ciwon amma na yaune ya tsananta kuma nasan insha Allah shima daga yau na daina. Raihana tace tausaya miki nake, lokaci daya yadda kika rame, kenan kowanni wata haka zaki kasance, pls Haneefah kiyi auren kada wani ciwon ya tashi. Haneefah tace in rashin lafiya ta sameka kafin ka tuna da likita, kafin ka tuna da komai ka tuna da Allah. Ko wanni bawa ya kamata ya kiyasta a zuciyarshi Allah shi ya kawo wannan cutar sannan Allah shi zai warkar dani, ban karyata abinda suka ce ba domin nima nakarance shi amma kada zawa ranmu cewa lallai hanyar da suka fada mana itace kadai mafita, addu'a ma maganine, sbd haka zanyi kokarin yin auren amma saina kammala karatuna tunda na kusa sannan bani da miji sai Yusuf. Raihana wani sa'in tana mamakin rayuwar HANEEFAH, tabbas komai na rayuwarta baki daya bisa tsarin Allah ne amma taki yadda zata manta da wannan saurayin nata, duk da batasan abinda ke zuciyarta ba domin wani sa'in zasu kai wata biyu bata ambaceshima amma lokaci daya wataran ta hoton shi gaba tayi ta kuka. Raihana tace Haneefah kina bani mamaki sosai, kina cewa kin mika lamuranki ga Allah amma haryanzu kin kasa rungumar kaddarar rabuwa da Yusuf, yakamata ace yanzu kin manta da shi. Haneefah tace mantuwa? Kenan ba kaunarsa nake ba, inkinga na manta da Yusuf bana numfashi, inna daina addu'a samunsa matsayin miji saina ganni cikin gidan wani aure, auren ma bana tunanin zanyi shi dan ina so, nan da shekara daya zan koma gaban iyayena kinga bazasu so ganina ina zaune gaban su ba dole inyi aure, a sannan zanyi yunkurin mace yin rayuwa da Yusuf. Haneefah ta share hawaye yanta tace family na suna so na, basa kaunar bakin cikina musamman ummata, ko aiki bazan soma a kasar muba sai da aure akaina. Raihana tace Allah zaba miki miji nagari, ya zakiyi da Rohan da dukkan alamu yana sonki. Tsaki taja tace rabu da shirmen shi, shida saura wata uku mu rabu, insha Allah zamu rabu lafiya. Haka suka ci gaba da tattaunawa har lokacin sallah isha'i. Bayan sun idar ta dauki waya domin kiran umma su gaisa, ba lallaine ta sameta ba a irin wannan lokaci ba takira Nana. Bayan sun gaisa take mata albishirin ansa ranar auren ta nan da wata daya. Ihun murna har yasa Nana katse wayar. Raihana dake kusa da ita duk hankalinta ya tashi tace lafiya? Bata saurareta ba ta kara kiran Nana. Nana tace so kike ki toshemin kunnuwa da wannan ihun? Haneefah tace sis yi hakuri duk cikin murna ne, amma nayi murna sosai wallahi ya sunan shi? Abdullahi Nana ta bata amsa, naje interview ne muka hadu dashi, saurayine bayyi da mata sannan na yarda da tarbiyyarsa da ilmin addininsa atakaice mun yarda da junan mu cikin kankanin lokaci shine yace da gaske yake kuma baya son a dauki lokaci, watan mu uku da haduwa. Haneefah tace wallahi nayi matukar murna amma ai wata daya yayi kadan wani irin shiri kuka tana da? Nana tace nima so nake na kiraki mu fara shirin kika rigani kira, yanzu abinda nake so da ke nan da sati uku zanzo amma kada ki fadawa kowa a gida nasan zasuce zasu hanani. Nana tace ai in babu ke auren ma bazai dauru ba. Dariya Haneefah tayi tace yanzu me yarage dan nasan kun gama siyayyar kayan kitchen? Sai kinzo kedai... cike da doki suke hirar yadda bikin zai kasance, sunyi sallama akan anjima zata kirata. Sanar da Raihana abinda ya faru tayi, ta tayasu murna itama tare da yi musu fatan samun zaman lafiya. Sauki ya samu gurin Haneefah domin tana fita aiki kuma tana samun yin karatun ta. Rohan yayi duk wata hanyar da zaibi ya samu hadin kan Haneefah abin ya gagara, ganin tana son watsar dashine yadan hakura da takura mata. Kamar kullum bayan ta samu nutsuwa da aikin ta ta nufi wani bangaren asibiti domin tayasu aiki. Daga nesa ta hango bakaken fata cikin asibiti, tazo dab dasu taji suna hausa. Farin ciki ne ya kamata, a hankali tayi musu sallama suka amsa... Daidai inda dayar take cewa umma kiga Yusuf da dansa, ta mikawa mamar wayar kenan idanun Haneefah suka sauka kan hoton Yusuf rike da jariri yana dariya. Kallon wayar take harta soma ganin duhu.... ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼40 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Zaune suke cikin jirgi tana kissima farin cikin da yan uwanta zasu kasance in sun ganta, zata ga Umma, Abba, Ahmad, Bintu da Amal? Bude ido tayi tana murmushi. Bayan an sanar dasu zuwa mintuna kadan zasu sauka cike da takaici tana kallon Raihana tace na manta sim card na a London, yanzu nayi loosing cantact na. Tsaki taja najin haushi. Raihana tace saiki sake sabo, ai ba wani abin bacin rai bane. Bayan sun sauka a airport suka ci sa'an samun zirgi zuwa kano. Basu sami wahala wajen samun ticket ba. Misalin karfe tara na dare suka sauka a airport. Ga kaya ta rasa yadda zatai, kiran Nana tayi ta sanar da ita isowarsu. A nanne Nana ta sanar da zuwan Haneefah a gida. Motar Abba Ahmad da Nana suka shiga zuwa airport. Zaune suke tana shakar iskan kano, marmari take wajen ganin iyayenta musamman Umma. Suna hira jefi-jefi da Raihana domin ta gaji, banda Haneefah da tsaban farin ciki taji babu gajiyarma tattare da ita. Tunanin Yusuf ya tsaya mata a kasan zuciya amma farin cikinta ya rinjeye tunanin wannan karon. Karaf idonta ya fada kan Nana, duk girmanta bai hanata tashiwa da gudu taje rungumar yar'uwarta ba. Murna sosai suke da ganin juna. Ahmad tsaye yayi yana kallon kanwar shi da dukka ta canza, farin cikine fal azuciyarshi na ganin ta canza hankalinta kwance duk ta canza. Sai a sannan ta iso gare shi ta kama hannun shi. Dariya ya soma yace keda zan ganki da jean ko mini skert saina ganki da katon hijabi. Dariya itama tayi tace ai tunda nazo sai kun gaji da gani. Raihana ta iso suka gaisa cikin harshen turanci, daganan suka soma tattara kayansu zuwa gida akan gobe zasu zo su karasa kwasan sauran kayan. Bintu ce ta bude gate suka shigo. Umma da Amal tsaye a haraba gida, murna bayyene a fuskokinsu na jiran Haneefah. Motar bai gama tsayawa ba Haneefah ta fito da gudu taje ta rungumi Umma tana hawayen farin ciki tace Umma nayi kewar ki. Umma ta dagota tace muma haka zomu shiga daga ciki sannun ku da zuwa. Bintu da Amal suka kamo hannuwanta cike da farin ciki suka shiga. Basu tsaya ko ina ba sai dakinsu. Haneefah ce ta fara shiga wanka sai Raihana. Bayan sun kammala komai gurin abinci Raihana ya gagareta ci. Saida Ahmad ya fita ya nemo mata gasassan kaji ya kawo ta samu ci, daganan ta musu sallama ta kwanta bacci domin gajiya take ji. Zaune take gaban Abba tana gaishe shi, dukkaninsu sun zagayeta tana musu karin bayani yadda take tafiyar da rayuwarta da yadda ta hadu da Raihana. Dukkanin su farin ciki suke ganin hankalinta a kwance, fatarta ta canza, ga kyau da ta kara. Sai karfe kusan sha biyu Abba yace toh kowa yaje ya kwanta abarta ta gaji. Su biyu aka barwa dakin. Haneefah tsananin farin ciki duk da ta kwanta dakyar baccin ya saceta. Washe gari da asuba dakyar Nana ta tashe su sukai sallah. Bayan sun idar suka koma bacci. Lafiyeyyen breakfast Nana ta hada musu. Umma ne ta shigo tana yiwa Nana sannu da aiki. Nana ta turo baki tace rabu da yarki, maimakon tazo daya da yan uwanta yan Nigeria saita dauko balarabiya Allah kadai yasan wahalan da zata bamu kafin ta koma. Umma tace bakon ka annabinka kada ki bata ladan ki, mukasance masu karrama baki a duk sanda suka zo mana, sannan ciyar da mutum ba karamin abu bane dan haka mu kwadaitawa kanmu ciyarwa komi kankantar sa. Nan da sati biyu kina gidan ki, in kikai baki kada kibarsu su tafi batare da sunsa abinci a bakin su ba, bayan kauna da kimar da zaki samu gun jama'a akwai kyakykyawar saka mako gurin Allah. Sannan batun dangin miji, ki toshe kunnuwan ki da dukkanin huduban da zakiji, ki zauna dasu tsakani da Allah, ki kauda da kai ga dukkanin abinda zaki ji game dasu. Ki kyautata musu, tabbas dan Adam ba'a iya musu amma duk musguna miki da zasuyi muddin zuciyarki daya ne wata rana zasu sauko su fara binki, wasu matan basa la'akari da suma dangin mijine sannan kada mu manta, duniyarmu ta yau duk abinda kayiwa mutum kaima za'a maka saboda komi qanqantar alhaki zai bika. Allah sa mudace Nana tayi murmushin jin dadi tace Ameen, insha Allah zanyi yadda kikace Umma, hakikanin gaskiya inka bude ido aduniyar nan ka fahimci kana tare da uwa tagari toh tabbas kayi dace domin duniyar kama dabanne. Murmushi Umma tayi ta fice a dakin. Karfe tara suka farka daga bacci. Sunje sun gaida Umma suka wuce gaida Abba. Raihana ta sake jiki suna ta hira da Abba, tana yaba yadda tarbiyyan Haneefah take da yadda suke zaman su lafiya. Karfe sha daya suka gama breakfast a sannan Nana ta soma kiran aunties na su. Kan kace meye kafin azahar gida ya cike. Mama da yaranta baki daya suka zo, bakin su yaki rufuwa tsaban farin cikin hasken family su, sunji dadin yadda ta kwantar da hankalinta tayi karatu harta canza. Bayan anyi sallah ne Ahmad yashigo da yaron Mama wadda suke sa'a dashi wato Khalifah, suna shiri sosai nan suka soma tsokanar juna yace zaki tashi ki kawo mana balarabiya dan kinsan bamu da kudin auranta ko? Dariya tayi tace ni da naji labari ka samu aiki shekaran ka daya aika tara kudi, nan suka soma hira tace akwai kayanta a airport in suka samu lokaci sune su dauko mata. Aunty Muhibbat ce zaune kusa da ita ta kama hannuwan ta suna hira suka ji sallamar Hadiza aiko tsalle Haneefah tayi suka rungumi juna suna murna. Bayan ta sake tane ta ganta da ciki tace shine baki gayamin ba inje in jefar dake? Ina ummulkhairi bata gama rufe baki ba ta ganta a hannun Sadiya. Da sauri ta karbeta tana dariya. Suka shiga ciki. Farin cikin Haneefah baya misaltuwa domin ji take daban take a yau. Raihana kam zuba mata idanu tayi tana Murmushi azuciyarta tana saka dama haka take? Haneefah ta gabatar da Raihana gun kowa, sunyi farin ciki kuma yadda suka karbeta abin yayiwa Raihana dadi sosai. Suna cikin hira suka ji sallamar Inna a falo ita da sauran yaranta. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼39 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Ganin zata fadi ne a hankali ta nemi guri ta zauna ta dafe kai. A wannan hali Dr Michael yazo ya sameta yace Haneefah? Da sauri ta dago kai tana kallon sa idanunta sunyi ja domin zubar da hawayen ma ta kasa. Ganin yana son saka hannu ya dagota ta tashi da sauri tana gaishe shi. Bai amsa ba yace meke damunki lafiya? Haneefah tace lafiya kaina kemin ciwo yanzu nake son komawa gida. Yace kije ki huta saikin samu sauki ki fito ki daina wasa da lafiyarki. Murmushi tayi zata wuce yace nima yanzu zanyi tafiya zuwa Canada sai bayan wata daya zanzo. Da sauri tace sir inaso in halarci daurin auren yar'uwarta, inason tafiya nan da sati biyu amin izini. Michael yace yaushe zaki zo? Wata daya zanyi ta bashi amsa. Yace ok ba komai, zan aika miki sako ta account, saiki soma shiri amma kada ki wuce lokacin da kika dauka. Tayi masa godiya zata wuce office ta juya kallon mutanen da tayi niyar musu magana amma bata gansu ba, wucewarta tayi office. Kuka ta zauna yi, ba komai take gani ba sai Yusuf rike da jariri yana dariya. Lallai ina da kishi! Toh ina ruwana da dansa? Dafe kai tayi tana hawaye. Yusuf yaushe zaka zo ka aureni? Ka manta da ni ne? Yusuf ina sonka? Momy bazan iya hakuri da danki ba ina son shi? Surutai take taji an turo kofa an shigo. Da sauri suka iso gareta suna tambayarta lafiya? Mesa kike kuka? Rohan da duk yafisu tashin hankali yace kiyi magana Haneefah meya faru? Cikin kuka tace nashiga uku, bansan wace irin rayuwa bane wannan, a lokaci da dama ina tuhumar kaina bana daya daga cikin bayin Allah wadda suka yarda da kaddara, yaushe zan daina son sa? Nayi tunanin barin kasarmu kozan manta dashi amma banyi ba, yau gashi shekara daya yarage na koma amma ko kadan ban daina ko jin daina son shi ba. Ta tashi ta kamo hannun Raihana tana cewa ki fadamin mezanyi na daina sonshi, wallahi ji nake kamar zan mutu yanzu dana ga shida dan sa, ku bincikeni saboda shi wata kila na kamu da hawan jini... na gaza cire shi a raina, ina tsoron Allah kada yayi fishi akan yarda da kaddaran da banyi ba.... Da sauri Raihana ta toshe mata baki tana girgiza mata kai cike da tausayi. Haneefah taje kusa da Rohan tace nasan kana so na, amma ba zayyu in taba son wani ba. Ta kuma matsowa gun Kevin tace ka fahimtar da abokin ka, banajin wani zai mori dadin zama dani matsayin mata sai dai in mishi biyayya yadda Allah ya umarceni amma bazan iya son shi ba, ya daina damuna kan soyayar shi wallahi bazan iya son Rohan ba Yusuf nake so, shekara hudu ina rainon soyayyar shi auren mu saura wata biyu aka janye amma ina da tabbacin zaizo gareni domin ina son shi.... Cike da tsananin tausayi Raihana taje ta rungumi Haneefah tana tausaya mata yadda take surutu akan so, tace yi shiru sis Yusuf zaizo gare ki, dan kinga yaronsa ba yana nufin ya manta dake bane, kamar yadda kema baki manta dashi ba, biyayya yake kamar yadda kema kike tayasa yi, kada ki manta kullum cewa kike faranta ran iya da yi musu biyayya na daga cikin sirrin zaman jin dadi a rayuwa. Sannan ki daina ambato da kanki cewa kina da karancin hakuri, yarda da cewa Allah yana jinki kuma yana ganin halin da kike ciki shine ya kaiki ga matakinnan, da baki da hakuri kullum sai kin rinka jituwa da Yusuf amma kin daure ko waya baki taba yi masa ba, dan haka ki kwantar da hankalin ki, kici gaba da addu'a Allah zai kawo mafi alkhairi a rayuwarki. Sannan Rohan ka daina damun Haneefah da soyayar ka, a irin halin da take ciki bai kamata ka dauko da maganar kaba, karatune ya hadamu toh muyishi, kabar maganan nan da wata uku mun rabu toh dan Allah muyi rabuwar arziki. Tana kaiwa nan taja hannun Haneefah suka fice daga office. Dakyar Raihana ta shawo kan Haneefah harta dawo normal. A zuciyarta tace ka hadu da mutanen da basason damuwar ka ma ka godewa Allah, musamman mutanen da ke zagaye dakai, Alhamdulillah tace. Da yamma suka koma gida. Bayan sun huta taga alert a wayarta kimanin miliyan daya, mamaki ne ya bayyana a fuskarta. Da gudu ta shiga daki nunawa Raihana. Tana karba ta gani tace sunan Michael nagani, Haneefah ta zaro ido tace nashiga uku me mutuminnan yake so ya mayar da ita? Nan ta kwashe komai ta sanarwa Raihana. Murmushi Raihana tayi tace take-takensa kada ki rabu da asibitinshi, kada ki manta turawa bazasu taba mu'amala da musulunci dan Allah ba suna so su kwadaitar dake kudin sune amma Allah ya fisu, kada ki kuskura cewa zaki bar asibitin da zarar kin gama amma kina gamawa ki gudu garin ku domin sunga kina da kwakwalwa zasu iya amfani dake. Haneefah tace Allah ya tsare. Raihana tace ina neman wata alfarma in zakimin? Ina jinki zan miki da yardan Allah. Raihana tace zan biki Nigeria amma kafin ina so mu tsaya Dubai kwana hudu zamuyi sai mu wuce. Haneefah tace na yarda domin ke kin wuce haka a gurina, sai dai zamu bar kasannan dawuri. Raihana tace muje makaranta muyi report sai mu soma shiri. Lokacin da tasan zata samu Nana takirata take sanar da ita tafiyarta amma kada ta sanar gida sannan tana da isheshen kudi kada su saya komai su jira zuwanta. Haka ko akai cikin satin sukai shiri tsaf da kwana biyar suka daga zuwa Dubai. A gidan kanwar maman Raihana suka sauka, sun samu kyakykyawar tarba. Raihana tace be komai nazo yiba siyayyan Habaya na zo saya, nasan baki taba zuwa Dubai ba zo mufita yawo. Tun adaren suka fito kallon gari, Haneefah taga Dubai sai santin shi take. Washe garima suka fita. Saida suka koma gida Haneefah take sanar da Raihana tana bukatar funitures da kayan kitchen. A daren suka je suka nemo masu kyau tare da foodflask masu kyau. Haneefah tayi tsaraba ga yan uwanta sannan ta kashe kudi wajen siyan kayan dakin yar uwarta. Itama tayiwa kanta siyayya. Taji dadin zamanta a Dubai sannan tayi sha'awar kara zuwa in Allah ya nufa. A kwana hudu suka dauki hanyar Nigeria. _Shin ko wace irin al'amari zai wakana a komawar HANEEFAH_? ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼41 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Da sallama suka shigo dakin, dukkanin su murmushi a fuskokinsu amma banda Inna da Zuwaira. Bulkisu, Zainab da ibrahim suka soma gaishe da Haneefah tare da yi musu ya gajiyar da karatu? Haneefah ta amsa da Alhamdulillah. Dakin yayi shiru, su Aunty Muhibbat anyi shiru ne saboda basason bakaken magana domin yawanci in suka hadu koda da mutunci suka gaisa sai zuwaira da maida musu bakar magana hakan yasa suma suka daina shiga tsabgarsu. Haneefah ta katse shirun da cewa Ibrahim ya makaranta? Kodai kaima kamar Ahmad zaka bautar kasa ne? Yace Eh amma inaga sai nanda wata biyu. Haneefah tace Allah taimaka. Hira ake jefi jefi harna tsawon mintuna goma sha biyar daganan suka sallama. Isarsu gida Zuwaira ta zauna bakin gado tana cije labe. Ibrahim daya lura da ita yace gwamma kin saukar da kanki kun zauna lafiya kamar yadda Zainab da Bilkisu, me kuke nema a duniya da zaku qarar da rayuwarku da hassada? Umma ita tayi hanyar nemamin makaranta kuma take son nayi karatu amma ko dan haka bazaki saukar da kaiba, yaranta daikam sun fiki nesa ba kusa ba, da ilmi da tarbiyya. Bilkisu ta amsa da cewa hakane maganarka Ibrahim, in bata gyara ba duniya zata gyara domin ko Inna da su yaya Salim sun sauko. Zuwaira ta numfasa tace tabbas naga asaran kishi domin ya rikidu ya koma hassada, wani kishin ma mugunta ne domin biyewa shaidan ake ya rinka bamu umarninsa da zai kaimu ga halaka, tunda muka taso bamu taba jiyarda kannen mu dadi ba wai mu muna *YAN UBA* da su amma banga laifin muba saina Inna. Inna dake zaune tana jinsu tace nidai? Zuwaira tace eh, domin da kina tsawatar mana da bamu taso da hakan ba, ku duba Nana itace babba amma duk muzgunawan da muke musu bata taba yunkurin ramawa ba sai Haneefah, itama Umma na dakatar da ita. Kinga ko da kina dakatar damu da duk haka bata faru ba. Cike da nadama Inna tace shikenan ayya wuce. Nan suka soma tattaunawa yadda zasu fara kyautatawa Umma. Amal da shukra da suke tsaye bakin koma sukai murmushin jin dadi tare da godewa Allah. Haneefah tace da Hadiza ummulkhairi bata qin jama'a, dubi yadda muke da ita amma batai yunkurin zuwa inda kike ba?Hadiza tace haka take babu ruwanta. Haneefah ta bukaci zata rika kawo ta in zata fita aiki. Hadiza tace shikenan zamu rika sayawa mu ajeta, inna tashi sai inzo in dauketa. Da yamma kaya ya iso. Sai da dare ta bude ta'ajewa kowa tsarabar sa. Ahamd da ibarahim tsadadden waya suka samu. Sanda Haneefah ta gabatar da kayan dakin Nana babu wadda bayyi mamaki ba. Umma tace aina kika samo kudinnan? Haneefah tace asibitin da nake aiki ne na sanar shine suka bani yin tsaya ba, da muka tsaya Dubai shine na sayo domin babu tsada acan. Salary da nake samuwa ne nayo tsaraba dashi. Nana ta shiga hawayen farin ciki da tsananin kaunar kanwarta, tashiwa tayi ta rungumeta tana cewa bani da bakin yi miki godiya sai dai ince Allah albarkaci zuri'armu ya hada kawunansu. Haneefah tayi murmushi tace duk abinda na samu naki ne da kannena saboda haka ki daina yimin godiya domin dukkanin abinda na mallaka naki ne. Umma farin ciki take sosai domin kullum addu'arta Allah hada kawunan yaranta. A hankali tace Haneefah naji dadin furucin ki, Allah yayi muku albarka. Suka amsa da ameen. Abba shima ya nuna farin cikin sa musamman yadda bata banbanta yaran Inna ba tayo musu tsaraba sannan ya kara da cewa ku dage da addu'an samun aiki mai albarka. Bayan sun koma daki Nana tace yanzu saura kujeru da sauran decorations na falo, ina da tabbacin komai zai isa da kudin sadaki da sauran kudin Abba domin kinsan yanzu ba aiki yake ba, in kuka huta ko cikin satinnan sai muje kizabamin sannan mu siyo anko. Washe gari kamar jiya yan uwa suka zo gaida Haneefah. Sun wuni suna hira sannan suka soma tsara yadda bikin zai kasance da ranankun da za'ai shirye shirye. Nana tace ba wani hayaniya za'ai ba. Ranar alhamis da dare dinner, juma'a bayan sallah za'ai walima, sai asabar daurin aure da dare akaita. A lahadi kuma yini. Da yamma misalin karfe biyar ita da Raihana suka shirya tafiya gidan Dr Mubarak. Ahmad ne yakaisu a motar Abba. Suna isowa bakin gate Haneefah ta tuna da Yusuf, haduwarsu na karshe randa yazo ya dauketa Momy tabiyota, a hankali hawaye suka taru a idonta. Mai gadi ya budi musu gate suka shiga. Knocking sukai kofan falo, Dr Mubarak ne ya bude. Tsayawa yayi yana kallon ta cike da mamaki. Ganin baice komai ba kuma sai kallonta yake tace Assalamu alikum. Amsa mata yayi ya bata guri ta wuce. Bayan sun gaisa Dr yace amma nayi mamaki saukan yaushe? Jiya da daddare Haneefah ta bashi amsa. Cike da kulawa yace amma shine baki sanar dani ba saiki shiko hanya ke kadai? Ganin yadda yayi maganar sai jikinta yayi sanyi domin Ahmad na zaune. Murmushi tayi tace ko gida ma basu sani ba, nazo auren Nana ne da zarar an daura aure zan tafi bayan sati daya, Dr kai kadaine a gidan? Ina Barrister? Ta tafi sunan yayarta acan zata kwana sai gobe zata dawo. Haneefah tace toh inta zo kagaisheta zan sake zuwa insha Allah. Haneefah ta tashi suma suka tashi sukai hanyar fita. Dr na cewa su zauna ko ruwane susha amma Haneefah kin tsayawa tayi domin tasan kawai ranta ne zai baci. Da dare tana zaune Ahmad ya shigo yace Dr Mubarak yazo yana jiranki a waje. Himar tasa ta fito domin batai mamakin ganin saba. Sallama tayi suka gaisa tace ya shigo ciki. Ba musu ya bita har falon Abba. Kallonta yake yadda ta kara kyau da fari kamar ba itaba. Dago ido tayi suka hada. Yace Haneefah kinsan cewa ina sonki, kuma koda barrister tasan cewa kece bazata hanani auren kiba domin ta yadda dake. Alfarma nazo kimin inaso a hada aure na dake ranar auren Nana. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼42 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Ko dagawa batayi ta kalleshi ba domin batai mamakin furucinsa ba sai dai tayi mamakin aure daya ambata. Tunani ta tsayayi, yanzu inta furta batason shi babu dadi domin yana qima a idanunta. Ta dago ido ta kalle shi shima kallonta yake tace zaka iya bani lokaci nayi tunani? Yace of course, amma bana fatan jin abinda zai dagamin hankali. Ya mike tabi bayansa da kallo tace wallahi ko zan mutu banyi aure ba bazan sakawa barrister da haka ba. Tana shigowa daki Ahmad yace ina fata ba soyayya yazo ba? Haneefah taja tsaki ta zauna. Nana da suka daurewa kai tace Dr Mubarak din? Haneefah ta kwashe abinda sukai ta fada musu tare da cewa bacen ce dashi komai ba dan kanshi zai gene ba sonshi nake ba ya kyaleni. Nana tace aurensa ba aibu amma in kikai haka baki kyautawa matarsa ba, domin ta daukeki tamkar kanwarta da kuka fito ciki daya, ita ta fara bada shawarar a fitar dake waje kiyi karatu kinga ko bazakiyi mata sakayyar da auren mijinta ba domin in akwai abinda mace bata so shine kishiya. Haneefah tace bazan soma ba, nan gaba in yazo kuce bananan balle ma ai zamu fara fita. Washe gari Hadiza ta kawo ummulkhairi ta ajeta, yarinyar bata kin mutane gata da saurin sabo. Haneefah gidan kowa takaiwa tsara ba, sunyi murna sosai. Ta fara ziyara amma duk inda ta gifta takan tuno Yusuf, kullum bakinta yana son tambayarsa amma tayi shiru ta kasa. Sun shaku da ummulkhairi sosai, Haneefah tamkar ta hadiyeta take ji. Aure yazo domin saura kwana daya. Yau ake shirin yin dinner party, Haneefah sunje karban kaya gurin tela sun dawo. Lace ne blue-black da cap silver colour. Zaune suke cikin daki ita da auties nata, yau kan saita tambaya domin ta kasa jurewa. Tace baku bani labari bayan tafiyata ko Yusuf yadawo ba? Kowa yayi mamakin wannan tambayar Aunty Muhibbat tace nikam yaushe zanji kin daina ambatan wannan yaro, nikam ya cuce mu, tace da Raihana cikin harshen turanci Haneefah tana ambato sunan wani Yusuf? Raihana tayi murmushi tace sosai domin bana tunanin Haneefah zata mance dashi, bansan wani irin so take mishi ba yanzu haka da naji ta ambace shi nasan tambayarsa tayi duk da banajin yaren naku amma Haneefah inaso ki sani; ZUCIYA an halicce ta ne saboda soyayyar Allah madaukaki. So, kada ka bata lokacinka wajen neman soyayya, amana da kamala a wajen wanin Allah. Baza ka taba samu ba. Inji Ibn Taimiyyah (Rahimllah) Sufyan Bin Uyainah (Rahmhullah) yana cewa: "Ranaku mafi tsanani da bawa yake tsintar kansa acikinsu 3 ne: 1- Ranar da aka haife shi ya fito gidan damuwa (duniya) 2- Daren da zai kwana tare da matattu (kabari) ya hadu da makwaftan da bai taba ganin irin su ba. 3- Ranar da za a tashe shi (qiyama) yaga taron da bai taba ganin irin saba!! Allah ya ce game da Annabi Yahya (A.S) akan wadannan ranaku 3: (Kuma aminci ya tabbata agare shi a ranar da aka haife shi da ranar mutuwarsa da ranar da za a tayar da shi da rai." Dan uwan Iman... Annabinmu (SAW) ya kasance me son ALBISHIR. Ya ce : Kuyi bushara, kada ku zama masu korewa, kuma ku sassauta kada ku tsananta" Dan haka, kada ka boye magana me dadi ko na alkhairi a ranka, ka gayama waninka shi ma yaji irin dadin daka ji ko ya karu, ka samu lada. Ka yaba in an yi abin yabo, ka gode, kama wanda kake so addu'a, kuma ka fadi alkhairi ma kowa. Magana me dadi, sadaka ne, ibada ne, shiriya ne. Allah ya ce" Kuma an shiryar dasu zuwa ga magana me kyau... Kuma ka sani, jin dadin duniya yana samuwa ne gwargwadon kyautata alaqarka da Allah. Idan kana son rayuwa me kyau to ka rayu yanda Allah yake so ba yanda kai kake so ba. Kayi HAKURI wajen yin da'a, kayi HAKURI wajen barin haramtattun abubuwa, kayi HAKURI da qaddara. Kayi HAKURI kayi HAKURI.... sabida gobe qiyama ka zamo cikin wadanda mala'iku za su ce ma. Nidai tunda nake arayuwata ban taba ganin irin Son Haneefah da takewa Yusuf..... Aunty Muhibbat ce amshe da cewa maganarki hakane amma ki sani, soyayyar da aka gina shi domin Allah haka take, sai dai ke Haneefah ki dada hakuri domin an miki iyaka da soyayyar shi kuma mahaifiyarsa ce, bai kamata har yanzu kina tambayar zuwanshi ba kuma baizo ba, tun bayan tafiyanki ko akan hanya ban taba haduwa dashi ba. Aunty Humaira tace Haneefah lokaci yayi dazaki mance shi, mun fahimci soyayyarku amma babu abinda zakiyi kamar kiyi hakuri, ki fito da wani mu aura miki shi. Haneefah tayi murmushi tace indai akan Yusuf ne na daina ambaton shi agaban ku. Tana kaiwa nan ta tashi ta fice. Nana tace maganarku bazai tasiri akan taba sai addu'a. Suna kan tattaunawa Hadiza tashigo da sallama, Nana tace wayyo yau Haneefah murna Hadiza tazo kwanan biki. Aiko tana jin muryar Hadiza ta fito ta dauki ummulkhairi suka fice. ***** ***** A hankali yayi parking ya fito. Kamar kullum ya nufo falon Abba. Da sallama ya shigo suka amsa, Momy tace yau da yamma ka dauko hanya? Abba yace ai auren yaron abokina ake, shi yaron tare sukai karatu sai dai likita ne. Yusuf yace yau suke da dinner party shine yace lallai sai nazo afara komai dani, kuma inason zuwa in duba lafiyar Aisha ma. Momy tace Allah bada zaman lafiya, Aisha tana lafiya. Suka dan taba hira ya tashi ya fice. Da dare misalin karfe takwas ya shiga yiwa Momy sallama, ya tarar suna hira da kaninsa. Muhammad yace yaya kayi kyau sosai, murmushi yayi yace nagode auta. Yayiwa Momy sallama ya fice. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼45 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Haneefah kallon Yusuf take tamkar bata taba ganinsa ba. Niyyar yi masa magana tayi saita tuno alkawarin da ta daukarwa Momy. Ta hade rai zata wuce yasha gabanta yace dan Allah ki saurareni kiji abinda zance dake dan Allah Haneefah. Jin ya ambaci Allah ta tsaya duk da zuciyarta bai amince da tsayuwar nan ba. Yusuf cike da wani irin yanayi yace Haneefah hakika na miki laifi duk da bani da niyyar aikata hakan amma yazama dole innemi afuwarki, nasan bazaki kullaceni da zalunyar kiba amma ya kama dole na nemi afuwarki domin manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce: _"Mutane uku (3) Allah Ta'ala Ya na karban addu'ansu ko shakka babu: Addu'ar wanda aka zalunce shi, Addu'ar matafiyi da Addu'ar Mahaifi ga abun da ya haifa"_. Tirmizi ya fitar da hadisin, Sheikh Muhammad Nasiriddeen Albani ya inganta shi. Ina nemar afuwan ki dan Allah Haneefah ki yafemin. Ganin hawayen idanunta na neman zubowa ta rabe ta gefensa ta shiga mota ta tayar tayi wucewarta. Ganin haka yasa shima ya koma motarsa ya juya domin barin gurin domin kwanciya yake bukata baya jin zaici gaba da tsayiwa. Tsayiwa tayi agefen hanyarsu ta rushe da kuka. Bakamin komai ba Yusuf na yafe maka duniya da lahira, wlh ina matukar sonka amma bansan ko kai har yanzu kana so na ba! Ganin anfara tafiya sallan juma'a yasa ta share hawayenta ta qarasa gida. Shiga dakinsu tayi ta tarar babu kowa sai Raihana, tana shiga tasa mukulli ta kulle dakin tazo bakin gado ta zauna tana share hawaye. Raihana ta taso da sauri tace meya faru Haneefah? Ke da waye? Haneefah tace nida Yusuf ne, mun hadu yanzun nan yace yana neman afuwa na. Raihana tace kinga irinta ko? Yanzu aida yana sonki binki zayyi! Ya isa haka Raihana, kina nufin baya so na? Ban damu da sonshi gareni ba abinda ya dame ni yaushe zanji na daina sonshi? Yaushe zuciyata zata daina tunani ta daina wahala akanshi? Raihana tace kamar yadda kika fara sonshi haka zaki daina, dan haka kidaina wahalar da kanki kawai kiyi aure amma duk wadda zaki aura ki tabbata yana sonki kuma wadda zayyi hakuri dake da soyayyar dake cikin zuciyarki. Maganarta gaskiyane. Jin an fara kwankwasa kofa yasa ta tashi taje ta bude kofa taga kannenta ne, komawa tayi ta kwanta jin kanta ya fara ciwo nan take bacci ya dauketa. Har aka fara gabatar da walima tana bacci domin bata sallah shiyasa ba'a damu antashe daga bacci ba. A hankali ta bude ido taji loudspeaker wadda ake gabatar da walima dake harabar gidansu tana cewa; Suna daga cikin siffofina ce saliha: *TANA TARAYYA DA MIJINTA* :A cikin domin taimaka masa wajen kafa gida mai tarbiyya da kuma iyali mai taimakon addini matukar dai ra'ayinsa bai sabama Allah ba. *TANA KARFAFA MIJINTA* :Domin cin nasara wajen abunda yasa gaba.Saboda mace tana da tasiri kan mijinta in ta karfafashi zayyi aiki,in ta karya masa gwuiwa ba zai ci nasaraba . *TANA TAIMAKONSA KAN BIN ALLAH* :Domin Manzo ( ) Yace *MUMINI BAI TABA SAMUN FA'IDA BA BAYAN TSORON ALLAH KAMAR MATA SALIHA MAI TAIMAKAWA MIJINTA AKAN ADDINI* (Sahih Muslim). *MAI DAI-DAITA 'YA'YANTA*: Mai tarbiyyantar dasu,mai karfafasu wajen ibada,mai tausayi, da Rahma, mai koyamusu ilimin dake dashi domin su amfana. *MAI NUNA KAUNA GARESU* :Da tausayi da basu hakkin da yakamata. *MAI NASIHA GA MIJINTA DA 'YA'YANSU*: Domin addini nasiha ne gaba d'ayansu,kamar kowa yasani domin gina gidan da mijinta,da 'ya'yanta da 'kasa da al'umma gaba d'aya. *MATA WATA HALITTACE*: Mai mahimmacin tane Allah yasa kowane mutum sai ya shiga ta hannunta zuwa wannan duniya da muke ciki ko malami,ko sarki,ko mai kud'i, ko gwamna,ko shugaban 'kasa kai koma waye sai yakoyi halin mace shiyasa insunyi kyawu to duniya zatayi kyau,misali inda matan duniya kowanne zata kame farjinta bazatayi zinaba to da zinan ma ta mutu a duniya don haka manzanci Manzo ya basu muhimmanci ya kuma girmamasu,matar da zata bada gudumawa ta zama mai ilimi mai hakuri ,mai hali nagari, mai tarbiyya, mai kamun kai kamar yadda muka gani abaya da kuma nan gaba. *TAZAMA MAI KYAKKYAWAR 'DABI'A*: Manzo ( ) Yace *Babu wani abu da zai kai mutum aljannah kamar kyakkyawan d'abi'a* Sannan kuma Yace *Babu wani abunda yafi kyakkyawan dabi'a nauyi akan mizani kamar kyakkyawar dabi'a* Ya kuma ce *Wanda Yafi kowa cikar imani shine mafi kyakkyawan dabi'a* (IMAM TIRMIDHI) *MAI GASKIYA*: Kamar yadda Allah Yace *YAKU MASU IMANI,KUJI TSORON ALLAH KU KASANCE TARE DA MASU GASKIYA*(Suratut-tauba) Manzo Yace *Gaskiya tana shiryarwa zuwaga bin Allah,bin Allah Yana shiryarwa zuwaga Aljannah* (Bukhari da Muslim) 54, *BATA SHAIDAR ZUR*: Wato bata ji bata ganiba kiran karya kawai saboda Manzo ( ) Yace *Shaidar Zur yana cikin manyan zunubai* (Bukhari da Muslim) *MAI NASIHA DA MUTANE*: Kan ayyukan alheri saboda Manzo Yace *Wanda ya shiryar zuwa ga aikin alheri,kamar wanda ya aikata*(Sahih Muslim).Haka kuma wanda ya kafa mummunar hanya ko kyakkyawa yana da lada ko zunubi batare da anrage na kowayeba. *Allah Yasa muna daga cikin wad'annan mata salihan*.(Amin) Jin yasa ta tashi zaune taci gaba da sauraron nasihohi: Ka gode ma Allah a duk yanayin da ka samu kanka. Wata rana wani mutum suna tare da abokin shi sai ya ga wasu gidaje masu kyau, sai ya ce ma abokin: _"Wai ina muke lokacin da aka raba wadannan dukiya haka? "_ Sai abokin ya kama hannun shi ya tafi da shi asibiti ya nuna masa marasa lafiya a kwance, sannan ya ce mishi: _"Su kuma wadannan muna ina aka raba musu wadannan ciwo dake damun su?"_. Don haka ka mu zama masu godiya ga Allah 'yan uwa. Raihana ce tashigo tace nazo duba kine ko kin tashi, amma yanzu kika tashi ko? Haneefah ta daga mata kai tace eh, kinzo da allurar da Dr Michael ya baki na ciwon marata? Cike da damuwa Raihana tace na manta ban dauko ba. Haneefah tace zama bai kama muba nanda kwana biyar zamu wuce london nafasa karasa sati biyun dan haka saimu fara shiri. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼43 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Momy tabi bayansa da kallo hawaye na taruwa a idanunta. Sau tari tana jin bakin cikin raba shida tayi da Haneefah domin bai manta da ita ba, tana kallon hoton ta a dakinshi. Batasan da wani ido zata ganshi tace Haneefah tayi aure ba, ban maka adalci ba Yusuf amma ina maka addu'a samun mace tagari. Jin motocin daukan amarya yazo yasa aka fita da Nana da tasha ado harta gaji da kyau. Haneefah zirga-zirga ya hanata zama guri daya domin fitan ta daga wanka kenan zama'a suka soma fita. Aunty Muhibbat ce ta bata mukullin motar ta tace su tafi inta gama. Tsaye take gaban madubi tana kwalliya, cikin nutsuwa take kwalliya harta gama, ta dauki lace nata gown ta saka. Ta nannade gashinta yadda bazai fito waje ba ta tusa cikin cap. Tsayawa tayi tana kallon kanta, dankunne da tsarka da abin hannu da agogo, cap da style na jikin kayanta duk silver, duk da wannan kwalliyar saida ta dauki gyale. Raihana ne ta dauki waya ta soma daukarta a hoto tace dama haka kike kullum bakya kwalliya. Haneefah tayi dariya tace ai karatu naje yi. Itama sanye take da habaya irin ankonsu tayi rolling. Suna fitowa suka hadu da Umma. Umma ta tsaya tace maasha Allah, ki zamto mai ambaton Allah irin wannan kyau haka. Cikin mota suke amma Raihana sai daukar Haneefah take a hoto. Duk saurin su sunje sun tarar ba'a gama shiga hall din ba. Tana sauka kallon jama'a suka koma kanta. A hankali take tafiya harta iso gurin rike da hannun Raihana. Aunty Muhibbat tace duk irin wannan kwalliyar saida kika dauki gyale? Hadiza tace ai gonda da kika dauka saboda yadda ake kallonta da gyale ma. Anan Haneefah idonta ya fara kallon jama'a saboda a tunanin ta kallon Raihana ake. Sai taji kunya duk ya lullubeta. Bayan sun shiga sun zauna aka bude taro da addu'a tare da kiran kanin anko ya gabatar da yayansa tare da fadin takaitattcen tarihi akanshi. Bata Ankara ba taji ankira sunanta. Kamar bazata tashi ba sai kuma ta tuna Nana ce fa, ta tashi rike da hannun ummulkhairi. Bayan ta gaisar da kowa tagabatar musu da takaitaccen tarihin Nana, sannan ta kara da cewa Allah basu zaman lafiya, babu wadda bata birge ba yadda ta tsara maganar tamkar tana kallo ne. Zamanta keda wuya aka kunna waqa, khalifa yazo ya zauna kusa da ita yace kin birge fa, bani wannan yartaki in rike ta. Ya karbi ummulkhairi yace tashi kice ki watsa musu naira kin wani zauna anan, ya matso kusa da kannenta yace muna so mu aurar dake tashi ko zakiyi kasuwa. Haneefah tace ai banyi kwantai ba haka ba, kuma ni banga..... shiru tayi ganin su Aunty na shiga filin rawa. Babu yadda ba'ayi da itaba amma taki shiga, a hankali ta tashi ta fara gaisawa da yan uwa, kowa yana mata fatan alkhairi a karatun ta. Tazo zata wuce gurin zamanta khalifa ya ja hannunta suka shiga, bata ankara ba taji an soma yi mata ruwan kudi, duk yadda taso fita sunki hanata haka ta hakura tana dan takawa. Yadda sukaga ana rubibi akan Haneefah yasa suka kyaleta ta fita taje ta zauna. Zaune take rungume da ummulkhairi suna kallon yadda party yake gudana. Haneefah tace lallai anayinta, kusan yan matan gurin kaf babu lullubi ajikinsu saika rasa banbanta wanene matan aure cikinsu. Tananan zaune har lokacin da Hadiza tace da ita za'a fara rabon abubuwa ta tashi su fara. Duk inda tayi ummulkhairi na makale da ita hakan yasa wadannan da basusanta ba suke zatan ko diyartane. Tazo kan wata kawar Nana na hannunta ya qare dan haka ta fita domin dauko wasu cikin mota. Tafiya take cikin rashin sani tsantsin tiles da ruwa yazube ya dauketa, da hanzari Ahmad yazo ya riketa yana mata sannu. Hannunta ya rike har suka zo inda aunty Muhibbat take. Aunty Muhibbat tace ai duk sa idon abokannan nakune yasa taso faduwa. Ahmad yayi dariya yasa hannu yana gyara mata cap nata daya kusa faduwa, garin gyara ya fadi gashinta suka kwance. Haneefah takaici yacika tace sakeni na gyara kayana. Yasa hannu ya karbi ummulkhairi ta soma gyara cap dinta. Tun saukarta cikin mota ya kura mata ido, shin itace ko mai kamarta? Saida ya shiga yaga Nana ce amarya ya tabbata Haneefah ce toh amma aina ta samu yarinya? Gabansa ne ya fadi daya tuno kardai aure tayi? Take ya nemi hankalinsa ya rasa. Dakyar yake iya gaisawa da abokanan sa, babu abinda yake sai kallonta. Yadda take magana cikin kwarewa da nutsuwa cikin harshen turanci ne abin ya dada basa mamaki, tuna kalamanta yayi inda take cewa_aini yaren naku ne ban iya ba. Yusuf yace wanne? Haneefah tace turanci_ tabbas yasan Haneefah bata kware ba amma aina ta koyo? Sanda ya ganta cikin filin rawa jama'a na mata kari sai yaji wani abu ya tokare masa makoshi. Sai yaji tamkar ya tashi ya fizgota ya fitar da ita cikin filin. Amma shi kam bai yarda da wannan yarinyar da ke makale da ita. Yana son yi mata magana amma yana tuno da Momy, amma wannan karon saiya mata magana kodaa gaisuwane. Ganin ta fita ne shima ya tashi ya bita a baya. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼44 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Aunty Muhibbat ce tagansa tsaye ya kura mata ido, neman abinda zai kawar da hankalinta Haneefah take, sai ko ga kawar Nana ta fito zata tafi ta nufo inda suke tace Haneefah dama kinyi aure harkin haihu baki gaya mana ba, aiko Nana bata gari a lokacin yakamata ki sanar damu? Haneefah tayi dariya zatai magana Aunty Muhibbat ta amshe da cewa kinsan auren yazo a kurarren lokacine kuma yanzu bata kasarnan da zama ba anan ta haihu. Haneefah ko sai murmushi take. Allah raya, Nana ma Allah basu zaman lafiya, dukkaninsu suka amsa da ameen. Neman tsayawa yake amma yagagara, a hankali ya soma tafiya har yaje ya zamu bakin fulawowi ya zauna duk da duhun gurin. Idanunsa sun kada sunyi ja zuciyarsa na masa kuna _Allahumma ajirni fii musibati wakhlifni khairan minna_ ya samo ambata, tunaninsa sun tsaya cak! Aunty Muhibbat ta samu abinda take so, tace da Haneefah ina zuwa. Tarar dashi tayi a zaune ya dafe kansa da hannuwansa, kwarai ta tausaya masa domin tasan tunanin yar uwarta yake amma inba haka tayi ba hankalin Haneefah zai tashi. Ko agaba ina gargadinka daka fita harkan Haneefah domin yanzu matar aurece hankalinta ya kwanta. Haneefah tayi maka afuwan dukkanin abinda ka aikata agareka amma kasani wannan karon yarda ka mata magana har mijinta yaganta, muddin ka bata mata aure toh wallahi bazamu yafe maka ba cewar aunty muhibbat, bata jira cewarsa ba tajuya ta fice. Gurin haneefah ta nufo, taja hannun Haneefah suka koma ciki. Suka tarar ana dauka hotuna, Haneefah ja da baya tayi ta zauna. Azuciyarta tace kana ina Yusuf? Rungume kake da danka niko gani inata tunanin ka. Hawaye take kokarin zubar wa amma ta maidasu. Raihana ce ta dafa kafadarta yace a duk sanda na ganki kina tunaninsa nakan gane ki, mesa bazaki bawa yayarki daman tayata farin ciki ba, wannan taron duk saboda ita akai amma saiki ware kanki kinzo kina tunanin wani? Kina tsammanin zata ji dadi? Batace da ita komai ba ta kamo hannun Raihana suka nufo inda amarya take suka soma dauka hoto. Raihana cikin zuciyarta tace ur so special Haneefah, kinajin magana koda bakiso shisa duk yayunki suke sonki. Tashiwa yayi yashiga mota. Ikon Allah kadai ya kaishi gida. Bangarensa ya wuce kai tsaye cikin kunar rai. Kan gado ya kwanta ya soma zuba da hawaye. Wannan karon ya kasa controlling kanshi, ya tashi zaune, ji yake kamar ya cire zuciyar ya jefar ya huta. Momy jin yadda Yusuf yashigo yasan babu lafiya, dan haka da sauri ta tashi ta nufi bangaren sa. Kuka tarar yake, cike da tashin hankali ta iso gare sa tana lafiya Yusuf? Meke faruwa? Tazo ta zauna kusa dashi Ganin Momy ya sake fashewa da kuka yana cewa Momy tayi aure harda yarta, nashiga uku Momy kullum sonta yana qaruwa cikin zuciyata bansan mezanyi na manta da ita ba. Ba bakin cikin auren ta nake ba hasalima ina taya mijinta murnan samun mace kamar ta amma bansan ya zanyi da sonta ba. Ya qara fashewa da kuka Momy dauriya tayi tace nasan da auranta domin nima naje sasanta sakaninku naji tayi aure, ban maka adalci arayuwarka dana rabaka da ita ba, ban kyauta ba. Nayi dama ka yafemin Yusuf, nakasance uwa maisa ido kan rayuwar yaransu bansan me kamin dazan saka maka da haka ba.... jin yayi shiru yasa ta kira sunan shi amma kafin ma ta taba shi ya fadi sumamme. Momy tace nashiga uku Yusuf!! Amma ko motsawa bayayi, cikin sauri Abba dake tsaye a kofar ya shigo yace Yusuf? Amma ko motsi bayayi Abba ya juya yana kallon Momy yace duk abinda yasamu dana saina dauki mataki. Kwantar dashi sukai kan gado Abba ya dauki ruwa a fridge ya yayyafa mishi. Ajiyar zuciya Yusuf yayi ya bude ido. Momy cikin kuka tace dan Allah ka daina damin kanka kada ka jawowa kanka ciwo kaga plss. Murmushi Yusuf yayi yace Momy komai ya wuce ki tayani da addu'a. Abba ya soma fada Yusuf yace Abba yariga ya wuce, nabarwa Allah komai, nasan yana jina kuma yana ganina, shi maijin qaine, mai tausaya wa inada tabbacin hakan alkhairi ne agareni. Momy kusan sha biyu tabar dakin nasa. Kukan zuciya ya zauna, ganin abin ba na dinawa bane ya tashi ya fara nafilfilu. Haka abin yakasance wa Haneefah, kowa yayi bacci amma banda ita, shikenan yanzu babu ita babu Yusuf! A wannan dare ta soma addu'ar Allah bata miji nagari ya azurta rayuwar Yusuf da farin ciki mai dorewa. Washe gari walima. Misalin karfe tara Amal ta shigo tace da Haneefah Dr Mubarak yazo yana falon Abba. Tsaki tayi tace ina zuwa. Zaune ta tadda shi, bayan sun gaisa bai bari yace komai ba tace dan Allah Dr kayi hakuri, kabari Inna qarasa karatuna sai mu dakko maganar domin kasan yanzu ina final year. Dr Mubarak ya gama nazarinta yace toh shikenan Allah kaimu, amma zaki rika surarata ko? Haneefah tace aa. Ganin zai takura mata tace ni Dr kawai kayi hakuri ta tashi ta fice. Dr yace bazanyi hakuri ba, sai nasan yadda zan bullo miki, ko ban aureki yanzu ba inada tabbacin nine mijinki ya tashi ya fice. Sanye take da habaya baki tana tuki zuwa gidan aunty humaira, zata je ta dauko snacks. Bayan ta sauka ta kulle motar ta fito taga wani mota gaban nata mai bala'in kyau, kallon motar take har tashiga gidan. Mai gadine ya taimaka ta fito da su ta bude boot suka aje. Aunty humaira tace sai anjima zamu zo saboda akwai sauran ayyuka daban kammalaba. Ta fito tana takawa a hankali har zuwa bakin mota. Har zata shiga motar ta ta juya zata qara kallon motar domin ta mata kyau, Dammm! Taji gabanta ya fadi ganin sa a tsaye waya makale a kunnensa. Shima abinda ya faru dashi kenan, yakasa ci gaba da wayar. Kallonta yake tamkar bazai daina ba. A hankali yazo gabanta yana kallonta yace HANEEFAH! ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼47 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Haneefah ta nunata yatsa tace wlh kika kuskura kika qara jefa ta da kalmar rashin kunya sai kinga abinda zan miki, in kina yiwa wasu suna kyaleki amma ni baki isa ba. Wani likitane ya fito yace meke faruwa? Nan likitar ta fashe da kuka tace marina tayi kuna banyi komai ba. Likitan ya zaro idanu yace mari? Ya matso kusa da Haneefah yace mesa kika mareta? Kinsan ita wacece? Haneefah ba wannan yakamata ka tambayeni ba, tambayata zakai menene dalilin marin. Na mareta ne saboda ta kiramin mahaifiya KE, yanzu kai in akaiwa mahaifiyarka haka meza kai? Shiru yayi yana kallon Haneefah. Haneefah tace bata san aikin ta ba, domin a tsarin kwantar da hankalinsu yakamata tayi ba rashin kunya ko isaba da gadara ba, gadaranki kinyi karatu kin zama likita amma ke ba komai bane tunda baki iya treating mutane ba... Jin muryar Dr Mubarak tayi yace meke faruwa anan? Likitar cikin kuka tace marina tayi. Dr Mubarak yace me kikai har aka mareki? Kada ku tara mana jama'a ku sameni a office. Da sauri Haneefah tace ina da patient zan iya shiga in dubata. Dr Mubarak yace zaki iya shiga. Da sauri ta shiga labour room, ta tarar Aisha na fama. Bazata manta fuskarta ba. Da sauri ta nufota ta kama hannuwan ta tana mata sannu. Su Momy ikon Allah suka tsaya gani, tabbas wannan Haneefah ne. Ita salma bata taba ganinta ba dan haka bata ganeta ba. Aisha ta kalli Haneefah tace mutuwa zanyi, dan Allah ki kiramin Momy. Haneefah tace bazaki mutu ba kirika ambaton Allah, zaki sauka lafiya. A hankali Haneefah ta fara duba matsalarta, nan ta gano kwanciyar yaronne ba daidai ba, a hankali ta gyara kwanciyar sannan ta kara ta, cikin taimakon Allah ta haihu kyakykyawar yarinya fara tas. Mikawa nurses din tayi suka amsa domin gyara ta. Ita ta gyara Aisha ta kaita bed rest sannan ta fice. Neman kaucewa su Momy take amma saida suka ganota. Salma ce ta tare ta tare da tambayarta ya ake ciki? Haneefah tace ta sauka lafiya, ta haihu mace duk suna lafiya yanzu zanje in karbo allura ne ina sauri. Ta saci kallon Momy ta lura duk kunya ta lullubeta, wucewa tayi abinda. Hadiza da take jiranta bakin kofa ta jawo hannunta tace Haneefah ina ke ina kaiga marin yar commissioner? Haka fa take da wulaqanci. Haneefah tace ni nunamin office din Dr Mubarak inje in qara mata marin. Hadiza ta zaro ido tace wato hanyarzu akwai sauran halayyarki da baki daina ba, kina da saurin hannu yakamata ki daina. Dai-dai suka shigo office din Dr. Zaune ta same su ,itama ta nemi guri ta zauna. Haneefah ne ta soma magana, labayar mishi abinda ya faru tayi sannan ta qara da cewa babu ta riga ta haihu. Cike da mamaki suke tambayarta ta haihu? Haneefah tace ai gaggawar kune yasa kuke ganin sai CS, yaron breach yake in kuka gyara kwanciyar kuka dan karata kasancewar primi ce zata haihu, sannan yadda kike tsawatar da relative na patient bai kamata ba, wannan ilmin da kika samu ko kinsan Allah ne ya zabe ki amma kike wulaqanta bayin sa, sam dan Adam bai kamaci wulakanci ba, koki dauka maganar da nagaya miki ko kada ki dauka wallahi kika kuma wulakanta wani har raina ya baci mari kam zaki sha. Murmushi Dr yayi ya kalli Haneefah yace am proud of u, Allah albarkaci karatun ki, ke kuma suwaiba ki daina ta kama da komai dan cikin qanqanin lokaci zaki rasa komai ki koma ba komai ba, dan haka wulaqanci babu kyau Allah kyauta. Jikinta yayi sanyi, a hankali ta dubi Haneefah ta bata hakuri. Murmushi tayi tace ba komai. Dukkansu suka mike dan zasu fita taji muryarsa yace ki tsaya inason magana dake. Kamar bazata juyo ba sai kuma ta koma ta zauna. Azuciyarta tace wannan karon ka daukomin maganan SO ko AURE saina baka mamaki... Katse mata tunani yayi da cewa yaushe zaki koma? Tace jibi zan koma ta bashi amsa kai tsaye. Shine bazakije gaida Ramlat ba? Yanzu nake son tafiya inna fita daga asibitinnan. Murmushi yayi ganin yadda take bashi amsa a takaice yace ina fata bakya kula kowa domin nariga kowa duk wadda kika saurarama bata lokacinsu suke domin nizan aure ki. Murmushi Haneefah tayi sannan tace yanzu kai aurene kake son yi? Baka tunanin rashin dacewar hakan? Duk abinda kukai min da matar ka sakayyar da zan mata kenan? Ka manta irin son da kakewa matar ka, kai da ba kinka kake cewa bazaka iya yi mata kishiya ba! Waiku mesa kuke haka ne, in kunsan bazaku iya rayuwa da mace daya na mesa kuke sawa matayen naku arai, ina so yazamo lokaci na karshe da zaka furtamin wannan kalmar aure domin saboda ni bazan lamunci bacin ran matar ka da ta daukeni tamkar yar'uwarta ba kaima na dauke ka tamkar yayanane... Bata qarasa ba taji ance kada ki hana aikata alkhairi dan farin cikin wani.. tashiwa tayi tsaye ganin Barrister Ramlat. A hankali ta shigo ta zauna kujerar da ke fuskantar Haneefah tace zauna ya kika tsaya? Jiki a sanye Haneefah ta zauna tare da sunkuyar da kai. Barrister tace tabbas nasan mijina yana so na, kuma munyi zama na amana dashi, bai taba nunamin qin abinda nakeso ba don haka dama ne tazomin tazan barsa yayi abinda yake so. Nasan dalilin da yasa yafara sonki har yake sha'awar aurenki, Haneefah ke yarinya ce mai saurin shiga rai, kinsan yadda zaki bi da mutum ku zauna lafiya kuma akwai abinda baki sani ba, kin zabi rayuwa bisa tsarin addini sannan kika samu karbuwa gurin mahaliccin ki Duk bawa daya kasance mai tsantsar biyayya ga mahaliccin sa babu shakka zai kasance cikin bayin Allah da yake alfahari dasu musamman bayin Allah masu tsananin hakuri da wadadanda rayuwar duniya bata gabansu, lokacin da Allah ya so bawansa zai kira mala'ika jibril yace ka shaida na so bawana WANE, sannan mala'ika jibril zai sauko zuwa sama ta farko yace da sauran mala'iku ku shaida Allah ya so bawan sa WANE haka zai rika sanar da sauran mala'iku har zuwa sama na bakwai, a sannan za'a sauko da soyayyar da wannan bawa zuwa doron kasa, sai kiji jama'a suna son bawan Allah. Ba komai ke jawo haka ba sai tsantsar ibada, sbd haka bazanyi mamaki son da mijina ke miki ba, amincewarsa amincewata ne. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼46 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Shiru Raihana tayi tana kallonta. Ganin kallon yayi yawane tace ciwon ya kusa tashiwa nafarajin alamu, alluran kadai zai iya controlling yanzu babu shi. Raihana tace inka zo nan da zama fa? Haneefah tace kafin ma zanyi aure. Bude baki Raihana tayi tana kallon Haneefah tace yau da kanki kike furta hakan? Haneefah ta daga mata gira alamar eh. Tashiga bayi ta wanke fuskarta ta dan shafa powder suka fito. An watse taro cike da dadin rai. Da dare Haneefah take sanar dasu kiran gaggawa ake musu a makaranta dan haka ko sati bazata kuma anan garin ba. Kowa baiji dadin hakan ba amma suna mata addu'a Allah sa nanda shekara ta dawo cikinsu lfy. Washe gari aka daura auran Dr Nana khadija da Dr Abdullah. Yan uwa da abokan arziki sun shaida auren sanna ana taya wadannan ma'aurata murna. Haneefah ba'a samu zama ba domin tana tare da Nana tana serving kawayenta. Barrister Ramla ma ta dawo, ta samu karbuwa hannu biyu a sannan Haneefah take bata hakuri amma ta mata alkawarin zata je mata kafin ta koma. Da dare akazo aka dauki amarya zuwa tsararren gidanta da duk wadda yagani koda makiyine bai isa ya kushe ba. Washe gari akai yini nan akabar amarya ita daya. Haneefah ta soma yiwa jama'a sallama. Hadiza tana wajen aiki Haneefah takirata a waya take ce mata tana hanyan zuwa gurinta domin zibi zata wuce London. A harabar asibiti tazo ta dauketa zuwa dakin hutawan nurses, nan ta hadu da wata colleague nasu suka gaisa tace Haneefah kema naji labarin auren ki bayyu ba, am sorry inshaa Allah zaki samu wadda yafishi, ke ai kina karatu ma kada ki damu zaki zamo wani abu da har sayyayi nadamar barin irin ki. Koni nan kin ganni bana kula kowa sai na zamo wani abu ta fanni likitanci. Haneefah tayi murmushi tace muna damuwa da yanda za ayi mukai Matsayin da za a kira mu da sunaye masu daraja a duniya... Professor, Engineer, lawyer, likita dss.. Amma me muke yi saboda mallakar sunayen matsayi a lahira? Me azumi, me tsayuwan dare, me taqwa? Wannan tambayan na bukatar tunani. Idan ya kasance kana rayuwa ba tare da yin sunno ni ba, ba wutiri ba sallar walha, ba karatun Qurani, ba azkar, ba azumin litinin bare na Alhamis, ba ka wani aiki da kake fatan ya amfane ka gobe Qiyama. To kada kayi mamaki idan ka rasa nitsuwa a nan duniya. Kuma kada kayi mamaki idan ka ta shi kaga ba kada komai gobe qiyama. Kana gani ana kiran mutane, wannan ya shiga aljannah ta kofar ma su azumi, wannan ta masallata, zumunci, jihad dss. Uwaisul Qarni (Rahimahullah) yana cewa : "Da ace mutun zai kama hanyan haduwa da abokan gaba... Sai rigar yakinsa ta masa nauyi ya cire ta a hanya, takwabinsa ta masa nauyi ya jefar, guzurinsa su masa nauyi ya tafi ya barsu. Kawai sai ya hadu da abokan gaba, ba komi a tare dashi. Yaya za ayi yayi nasara a kansu??? Kamar hakane wanda zikiri ya masa nauyi yabarta, sunnoni suka masa nauyi ya kyale su, yin farillai akan lokaci suka masa nauyi yake jinkirta su... Kuma wai a haka yana kukan halin kunci na rayuwa dayake ciki... Shai'dan ya zama shi ke hukunta zuciyarsa. Miskiynnn! Ya halaka kansa tun kan abokan gaba su halaka shi" Misalin wanda ba ya shirya ma lahira kenan. Abokin gabansa (wuta) na jiransa a lahira, ga kuma maganinta atare dashi anan duniya (ibadu da halin kirki) In suka masa nauyi anan ya watsar... ya san sauran. Dan uwan Iman... Ka yawaita tuna fadin Allah (Kaico na! Da na gabatarda aikin kwarai domin rayuwata) Ayar za take tuna maka cewa rayuwar duniya ba rayuwa bace. Rayuwan nan dai da kake mantawa dauwamammiya. Lahira ba... Abinda nake bance karatu babu kyau ba amma yadda muke fifita muzamo wani abu a duniyarne akwai takaici Allah yasa mu dace. A sanyaye suka amsa da ameen. Kawar tasu tace gashi shekaru sai qara yawa suke mazan ma ba wani son manya suke soba, da zarar kin wuce shekaru ishirin shikenan an dainayi dake. Haneefah tace inji wa? Saidai baki killace kanki ba, aure lokacine yan uwa mudaina sa irin wadannan tunani a zukatanmu, yanzu ke nawa muke da zamu damu kanmu shekara ishirin da uku zuwa hudu nefa! Ga yayata satin da ya wuce aka daura aurenta, abin yarda da Allah kawai, wasu basa aure da wuri saboda hakan yafi musu alkhairi, wani auren gomma babu tsabar wahala. Dan haka ki kwantar da hankalin ki komai lokacine. Nan suka ci gaba da hiran su. Haneefah ta kalli agogon hannunta tace zan wuce domin guraren zuwana dayawa yake. Hadiza bataji dadin hakan ba amma dolene yasa zasu rabu. Tafiya suke har suka zo daidai labour ward. Daidai sunzo wucewa idanun Haneefah suka sauka kan Momy, ganin wata mai labcourt ta fito tamikawa Momy tace gashi kusa hannu za'a mata CS domin ceto ran danta. Momy dake cike da damuwa tace yaushe muka kawo ta? Batai nakuda sosai bama muka kawota yanzu za'a mata CS? Likitar tace ke mata bazaki gaya mana aikin muba, in zaku sa hannu toh in bazaku saka hannu ba zaku iya daukarta ku koma. Salma tace a'a zamusa hannu kiyi hakuri mudai Allah sa ayi a sa'a. Haneefah tayi hanzarin karban takardan cike da bacin rai tana kallon likitan tace me kika ta? A wulakance likitar ke kallon Haneefah tace KE! nace da ita, Haneefah ta matso kusa da ita tace maimaita inji? Zata qara cewa K... bata qarasa ba Haneefah ta sauke mata kyakykyawar mari. Kallonta tayi cike da mamaki tace kika mare ni? Haneefah ta kuma yi mata marin ji kake Tasss!! ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼48 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Sannan na tabbata baki da son kai tunda har kina gudun bacin raina innaji zancen aure, namiji in ya soma maganar aure ba'a iya dakatar dashi, kuma ba yinsa bane yin Allah ne zanfi jin dadi inya auro ki domin nasan halin ki, pls Haneefah ina taya mijina neman auran ki. Ba Haneefah ba hatta Dr yayi mamakin matarsa. Dukkan su shiru sukai kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa. Tashiwa Haneefah tayi zata fita Ramlat ta kama hannunta tace bakice komai ba? Haneefah tace zanyi tunani. Hadiza ta samu a bakin kofa tana jiranta. Hadiza tace Haneefah zan kara missing naki, gashi wannan cikin zan kara haifa bakyanan nikam duk na kagu kizo tsorona daya kada ki hadu da mazaunin can kiyi aure. Haneefah maganar dariya ta bata tace shekara mai zuwa zanzo insha Allah. Hadiza ta rike hannuwanta tace sis ki manta da Yusuf, lokaci yayi da zaki mance shi, nasan abin da wuya domin haduwarku kunyi soyayya, yadda ra'ayinku da dabi'arku yazo daya ne kikejin kamar bazaki samu kamar saba amma kada ki manta, Allah daya hada ku shizai kara hadaki da wadda yafisa, kiyi la'akari da yadda kowa bayason damuwarki, fatansu ki kasance cikin kwanciyar hankali, da wannan nake rokon ki kicireshi azuciyarki ki daina damuwa kansa, insha Allah komai zai daidaita. Haneefah tayi murmushi tace sis bazanyi alkawarin daina sonshi ba domin Allah ne ya halicci wannan son azuciyata, zan miki alkawarin aure da zarar nagama duk wadda ya fitomin zai aureni zan amince amma saina dawo gida Nigeria, sannan bazan amince da auren Dr Mubarak ba. Hadiza ta zaro ido tace yana sonki ne? Haneefah tace eh. Hadiza tace bazamu miki dole ba duk wadda kike so shi zamu baki. Sukai sallama tamkar kada su rabu da juna. Haneefah tana tafiya tana tunani "_ Hakika inka hadu da yan uwa da abokai nagari ka godewa Allah domin kullum ganin ka cikin farin ciki shine burinsu, sannan zasu kasance masu maka nasihohi masu ratsa zuciya_" Me nake nema arayuwar duniya?? Yardar Allah, tsoron Allah da soyayyar annabi aduk inda nake, faranta ran iyaye da rabuwa dasu lafiya! Iyaye da dangi suna alfahari dani, tabbas babu abinda abinda yafi wannan dadi. Sai taimako ga mabukata tare da rayuwar gidan aure ya saura, tabbas zanyi biyayyan aure ko waye na aura bisa tsarin addini insha Allah. Da irin wadannan tunanen ta iso gida. Tana zuwa ta shiga gidan Inna bayan sun gaisa ta fito ta shiga gidansu. A sannan suka soma shirin tara kaya. **** **** Tunda suka zo gida kowa jikinsa yayi sanyi musamman Umma, mijin Aisha rike da sabon baby yana kallonta. Ganin dukkaninsu sunyi shiru yasa ya ajiyeta ya tashi ya fita. Salma tace aini da nasan itace bazan bari ta tafi ba, hakuri zan bata. Momy tace kibata hakuri akan tazo ta auri yayanki? Lokaci ya kure domin tana sa aure tuntuni. Aisha ta mike tace what? Nashiga uku ina yaya yake bansan yazai dauki al'amarin ba. Momy tace aiya sani, nan ta kwashe labarin daya auku daren da yake dinner party Dr Abdullahi ta kara da cewa ban san wace halin ya shiga ba kafin wannan abin ya faru. Salma da Aisha dukkanin su kika suke, Aisha tace yanzu meye amfanin rabasu? Wadda kikai dominta tanar gidan, irin halin da yaya Yusuf ya shiga Allah kadai yasani kullum nice abokiyar shawarar shi ina bashi hakuri akan ki sauko, gashi kin sauko amma tayi aure dole ya hakura. Salma tace yanzu in akaiwa Aisha ko ni tabbas bazakiji dadi ba, in zamu aikata abu murinka jin in mukaiwa kanuwan mu ya abin zai kasance, amma dubi ita harta manta domin yadda ta mare nusaiba dan ta miki rashin kunya. Aisha tace yanzu dai ya'isa sannan kada ku gayawa yaya abinda ya faru gudun kada murinka maida hannun agogo baya. Ta dubi yarinyar da take kwance tace zan roki mijina alfarman yasa takwaran HANEEFAH. Haka ko akai, ranar suna yarinya taci sunan HANEEFAH amma suka yanke shawarar a tambayi Yusuf ya zabi sunan abinda za'a kirata. Yusuf yayi farin ciki da mamakin wannan takwarar daya samu yace akirata da *RA'IMA* wato farin ciki. A take ya shiga WhatsApp ya sa hoton ta a dp sannan ya rubuta a status nashi _my little princess RA'IMA_ _Ko ninan ~BINTU RAMADAN~ ina mamakin irin wannan soyayyar ta YUSUF da HANEEFAH_ **** **** Agajiye suka dawo daga makaranta kasancewar yau ne aka yaye daliba gaba dasu wato su Rohan, su kuma nanda wata takwas za'a yaye su. Raihana tace gobe walima zakije? Haneefah tace ai dolena saboda kosu Rohan da Kevin dan haka anjima da dare inmun huta zamuje mu siyo kayanda zamu saka. Raihana tace da kin sanar dani tun wuri sabbin kaya zamu sa da naje Dubai nazo. Haneefah tace aiko kun koma Dubai da zama bai kamata ki dauki zuwansa tamkar a mota bane don siyayya koda yake kuna dashi takashe maganar a hankali. Raihana tace inason tambayarki, a cikin class namu akwai bakken fata mesa bakyason mu'amala dasu? Haneefah tace Kar ka yarda ka shiga cikin mutanen da suke da dogon buri har rayuwarsu ta kare basu aikata wani aiki na alheri mai yawa ba sannan su rinka cewa: ai muna kyautata ma Allah zato. Wannan karya ne, domin inda sun kyautata ma Allah zato, da sun kyautata biyayya gare shi. Mutanenmu da kike gani yawancinsu yaran masu kudi ne, niba yar kowa bace bazan cusa kaina inda rayuwata da nasu da banbanci ba. Inason kasancewata haka domin yar Adam nake kada in zamo mai dogon buri, kema ai bansan kin fito daga gidan masu kudi bane saboda ke rayuwarki daidai kike yinsa. Raihana tace hakane. Allah bamu ikon tsare kawunan mu ameen **** Kwance yake rigingime yana tunanin irin matsayin da ya taka yanzu, yana da kudi, motoci, da dukkanin abin bukatar rayuwa sai dai haryanzu bai cika ba domin bayi da mata kuma ba cikekken lafiyane dashi ba. Jawo wayarsa yayi kirar GALAXY S7 yana so yakira likitanshi amma ya fasa domin yagaji da tafiya India. Browsing yafara asibitoci amma idanunsa yakai kan wani asibiti dake London. Nan yashiga yaga yanayin asibitin zuciyarsa ta raya masa da ya tafi can. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼49 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Cikin sati biyu ya kammala shirin tafiya London. Yaje gida yi musu sallama suka masa addu'an samun nasara. Cikin sati na uku ya daga jirgi zuwa London. **** **** Zaune take ta zubawa hotunan gabanta ido tana nazarin gano wasu matsaloli... ajesu tayi agefe ta dauki takardanta na makaranta ta soma karantawa domin suna gama wannan semester wadda zasu shiga gaba shine zasu gama makaranta. Aje takardun tayi ta dafe kanta a hankali tace ya Allah gani gare ka, ka bani ikon rabuwa da wadannan bayinka lafiya. Nan ta fara tunanin da ta saba a duk sanda taji abubuwa sun fice mata akai, wayarta ta jawo ta kunna karatun qur'ani mai girma tana sauraro. Shafa cikin ta tayi da taji murdan da ke mata. A hankali tayi murmushi tace ko yaushe zan ganni da ciki? Tunani take yadda take sha'awar itama ta mallaki da ko ya. Tana cikin tunani taji anturo mata kofa an shigo. Tana ganinshi ta hada rai. Murmushi Rohan yayi yace murmushi dabi'ar kwarai, duk da rasuwar dukkanin 'ya'yanshi illa nana Fadima r.a Duk da rasuwar matar shi ta kwarai kuma mahaifiyar 'ya'yanshi Duk da kasancewarshi maraya gaba da baya tun daga yarintarshi Duk da rasuwar makusanta kuma masoya a gare shi Hamza r.a, Ja'afar r.a ga baffanshi Abu Dalib Duk da irin 'dumbin nauye-nauyen da suke kan shi na al'umma wajen ya'da kalmar Allah da kawo gyara a cikin al'umma da kuma fama da mushrikai da kaidinsu. Amma bai kasance ba illa mai yawan murmushi da fara'a!! Wannan shine Manzon rahma sallallahu alaihi wasallam. kayi murmushi domin koyi da abinda yake yi, sannan kuma ka dace da samun lada na sadaka, kamar yadda Manzon Allah s.a.w yace: (( murmushin ka ga fuskar 'dan uwanka sadaqa ne)). Kimin murmushi domin bakisan ko rabiwarmu dake bane domin sallama nazo miki anjima zan wuce India. Jikinta ne yayi sanyi dajin kalamunsa, a hankali tace kayi hakuri da dukkanin abinda nake maka ina maka nunene abinda kake kokarinyi bazayyu bane. Rohan yace bakiyi niyya ba shikenan na hakura, ina miki fatan alkhairi a rayuwarki Allah sa gaba inmun hadu kimin magana kada kice baki sanni ba. Da fara'arta tace na'isa! Kada ka damu indai wannan ne insha Allah ba rabuwarmu kenan ba zamu hadu nan bada jimawa ba. Hira sosai sukai da Rohan tace inya tashi yafiya ita zata kaishi airport. Saitaji babu dadi domin ta saba dasu, dan ma Kevin na kusa da sune. Da wuri ta tashi a asibiti taje gida tayi musu girki ta gayyaci Rohan da abokinsa suka zo. Ko Raihana da tazo tayi mamaki, sanda taji labarin tafiyar Rohan tayi dariya tace nasan da biyu kikai haka Haneefah. Hira sosai sukai tare da basu wasu sirrika da bazasu wahalaba in sunzo jarabawar gamawa. Har airport suka rakoshi saida sukaga tashinsu sannan suka koma cike da kewar shi **** Kwance yake cikin hotel da yayi masauki yana hutawa. Saida ya huta sosai sannan ya fito nemar waya. Kiran layin asibitin yayi sannan ya musu bayani atakaice. Cikin mintuna da bazasu wuce goma sha biyar ba aka zo aka dauke shi zuwa wannan asibiti. Yayi duk abinda ya dace akace gobe yazo ganin likota tunda yasamu ya bude file. Komawa yayi hotel din dai baisan inda kuma zaije ba. Can kuma ya tuno yakamata ace ya kira mutanen gida domin sanar dasu ya iso lafiya, ya yanke shawarar idan yayi sallar magriba zai fita yakirasu. Su Haneefah an dawo daga rakiyan Rohan. Dai-dai zasu shiga gida tace na manta iPad dina a office bari in biya in dauka. Kevin yace bani makullin office din in dauko miki in bazaki damu ba? Mika masa tayi domin ta gaji bacci take so tayi. Bayan ya dauko ne yayi mantuwa yana da abinyi. Yaje yayi bukatarsa kenan yabi hanyar makarantar su domin zaifi saukin sadashi da gidan Haneefah. Tafiya yake yaji yayi karo da mutum har iPad dake hannunsa ya fadi. Hakuri Kevin yafara bashi tare da sunkuyo ya dauki iPad nasu, tsayawa kallo yayi domin iri daya ne. Yusuf yayi murmushi ya karbi dayan yace babu komai yayi wucewarsa. Shima ya wuce. Ya kaiwa Haneefah ya musu sallama ya fice. Washe gari Haneefah taje makaranta suka tarar an fara test dan haka bata samu shigowa asibiti ba. Shiko Yusuf daya je asibiti akace dashi saiya jira wadda take duty domin ta tafi makaranta saita dawo. Ganin ba zuwa zatai ba ya kama hanya ya shiga gari. Bayan ya dawo ne yaja iPad nashi domin amfani dashi. Mamakine yakamashi daya kunna yaganta babu passward alhalin nashi akwai passward. Gabansa ne yayi mugun faduwa ganin Haneefah agaban screen din iPad. Mussuka idon shi yayi amma ya tabbatar itace. Shiga hotuna yayi yaga hotunan dukka na Haneefah ne . Ya fita yashiga e-mail nan yaga e-mail din ba nashi bane. Kallon iPad din yake nan ya tabba ba nashi bane, ya tuno da mutumin da sukai hasari jiya acan sukai musayya. Amma mamakinsa shine aina wannan baturen zai hadu da Haneefah? Shiga hotuna yayi yana kallon ta. Ganin tunaninsa na neman rikicewa yarufe iPad din ya kwanta. Washe gari misalin karfe goma ya tafi asibiti wannan karon office din Dr Michael aka nufa dashi, yayi masa bincike ya gano matsalar. Dr Michael yayi murmushi yace damar sake goda kwakwalwar Haneefah yazo, ya dubi nurse data kawo shi yace kikai shi office din Dr HANEEFAH . ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼50 Dedicated to Batul Mamman Mrs 💖 Gaban Yusuf ne yafadi jin an ambaci Haneefah. Tashiwa yayi zai fice yaga Kevin. Kevin ne ya mika masa hannu suka gaisa yace kaine wadda muka hadu jiya ko? Ajiyar zuciya Yusuf yayi sannan yace eh nine iPad din ba nawa bane inaga munyi musanya ne. Kevin yace kai hakuri na Haneefah ne amma yanzu tare muke inhar bata fita zuwa makaranta ba zamu iya samunta in mukai sauri. Nurse din tace dama office nata zan kaishi kace da ita Dr Michael ne yaturo shi. Kevin yace banyi tsammanin zata duba patient ba amma bari muje. Shiko Yusuf gabansa ne yake faduwa domin Haneefah da ake ambata. Da sallama Kevin ya shigo ganin kofar a bude take. Haneefah ta sunkuya tana neman littafinta daya makale kasan durowa jin muryar Kevin ne yasa bata dago ba taci gaba da abinda take. Kevin yace patient kika samu... tun kafin ya karasa tace ina da test a makaranta babu wadda zan iya dubawa yanzu. Kevin yace Dr Michael ne yace in kawoshi fa. Dagowa tayi tana duba takardan ta tace kaga abinda nake nema yanzu zan karanta kafin na tafi ma..... dago ido tayi domin ganin wadda ke tsaye, takardun hannuwan tane suka zube ganin Yusuf a tsaye gaban ta ya kura mata ido. Shiko tsaye yake ya zuba mata idanu tamkar baitaba ganinta ba. Lokaci guda hawaye ya taru idanunsu. Karfin hali tayi ta kauda idanunta tace bani da lokaci yanzu zan tafi makaranta. Zata fita taga Dr Michael yashigo yace Haneefah kin dubasa? Tace sir inada test nanda mintuna kalilan inason tafiya makaranta. Yace wannan ba abin damuwa bane zan kira lecturer da kuke da course nashi sai musan yadda za'a amma inaso ki dubamin wannan patient din domin complicated case ne kuma inaga akwai aiki da za'a masa. Saitaji hankalinta ya tashi dason jin abinda ke damunshi amma bata nuna ba tace toh shikenan zan same ku a dakin na'ura kafin zan dauki history. Bayan sun fita ta koma ta zauna a mazauninta har lokacin Yusuf ya kasa motsawa daga inda yake. Cikin sarkewar murya tace ga guri zauna. A hankali ya zauna amma ya kauda idanunsa a kanta. Haneefah ta kallesa tace meke damun ka? Batare da yakalleta ba yace shekaru uku da suka wuce ne nayi hatsari nan ya kwashe dukka nin abinda likitoci suka sanar dashi. Shiru tayi ta lumshe idanunta tana jinjina abinda ya faru dashi. Mikewa tayi tace ka biyoni. Sun tarar da Kevin ya kunna komai suna jirarsu. Kevin ya mika masa rika na marasa lafiya yanuna masa daki yace shiga ka canza. Bayan ya canza ya fito Haneefah ta masa nuni daya kwanta kan wani na'ura. Yana kwanciya ta danna wani madanni yashiga dashi. Tsayawa tayi gaban screen din tana ganin sassan cikinsa. Nazarin wuraren da ta gani take har na'urar ya kammala ya fito dashi. Hoton ya fito Haneefah tasa hannu ta karba ta wuce office. Tausayinsa ne yake ratsa illahirin jikinta, tabbas yasha wahala domin alamu sun nuna. Bangare daya kuma wani irin sabon soyayyar shine take ji. Wannan ba lokacin tunani bane ta bafa azuciyarta. Kurawa hoton ido tayi tana nunanin yadda za'ai, turo kofar da akayine ta dago ido tana kallon me shigowa, hada ido suka yi taji wani irin fadiwar gaba shima haka. Ya salam! Ya fada azuciuarsa, daidai inda Dr Michael yashigo ya nufo inda Haneefah take yace kin gano matsalar? Ba tare da bata lokaci ba tace eh, har yanzu akwai glass biyu dake jikinsa wadda suke dada nitsewa kowani wayewar gari cikin jikinsa Hannu tasa ta nuna masa tace kaga nan? Za'a gani jijiyoyine suka kumbura amma akwai glass daya sannan cikin cinyarsa akwai shima glass daya makale wadda wani sa'in in yana tafiya yana sashi dingishi. Anan ta masa karin bayani yadda za'abi ayi masa aikin cikin sauki. Dr Michael yace great! Bayaninki haka ne sannan treatment dinma haka ne. Ya juya gun Yusuf daya wangale baki da hanci yana kallon Haneefah. Yanzu dai mungano matsalarka, zamu maka aiki in har ka amince kaje ka biya sai gobe mu fara domin ba abin daga lokaci bane, kwayoyin maganin da kake sha babu abinda zai maka sai tarin illah... Sallamar Raihana suka yi, ganin Dr Michael yana ciki zata koma Haneefah tace shigo yanzu nima zan tafi. Ta kalli Dr Michael tace patient nane zaku iya cirewa a salary na. Dr Michael yace cike da mamaki aida kin fadamin tun farko, yanzu shikenan za'a iya masa gobe sai kizo ayi dake. Haneefah tace inada abinyi zaku iya masa sannan nurses su kula dashi. Raihana tunda ta shigo take kallon Yusuf da mamaki? Tambayar Haneefah takesonyi amma sai sun fita waje. Zata fita Dr yakirata tace pls sir banasonyin jayayya dakai tana kaiwa nan tasa kai ta fice. Shiko Yusuf mamaki ya hanasa cewa komai, saida da Dr Michael yace dashi zai iya tafiya gobe da dare za'a masa aiki misalin karfe bakwai yazo. Ya tashi jiki ba kwari ya fito yana tafiya ya tsaya ya siya Sim ya koma hotel. Kasa tafiya makaranta tayi suka wuce gida. Zama tayi kan kujera tana hawaye, Raihana dake kallonta tace hawayenki zayyi nasaba da kallon masoyin ki ko nace ki dakata bazaki daka ta ba amma zanso jin ya akai kuka hadu. Tana kuka ta labartar mata yadda suka hadu. Murmushi Raihana tayi tace Allah mayyin yadda yaso, kun rabu kunyi nesa da juna tsawon shekara uku amma yau kuka sake haduwa amma me dalilin biya masa kudin aiki? Haneefah tace taimako ne kawai nayi. Raihana ta fashe da dariya tace taimako manya, naji kinyi taimako amma kada ki manta alkawarin da kikaiwa mahaifiyarsa inko kina son gamawarsa da duniya lafiya kada ki yarda maganar SO tashiga tsakanin su infact ki nemi hutun sati biyu a asibiti sayya gama abinda yake saiki koma dan ba patient naki bane shawarar dazan baki kenan. Haneefah ta share hawayenta tace lallai ne nayi nesa dashi domin alkawarin da nayiwa mahaifiyarsa. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼52 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Yusuf ji yayi gabansa ya fadi, ina shi ina kallon Haneefah da wani? Yayi murmushi yace nagode aboki amma inani ina sauka a gidan matar aure. Dr Abdullahi yace kada ka damu bata da aure, karatu take aka dauketa a asibitin shine suka hada mata da gida. Kallon Abokin nasa yake tamkar baisan abinda yake furtawa ba. Yusuf yace ba Haneefah dake rike da yarinyarta ranar dinner party kuba? Naganta akace da ni matar aure ce. Dr Abdullahi yace ba yarta bane, bansan inda ta samo ba, matata tace ansa ranar aurenta saura wata biyu aka fasa, shine ta samu scholarship ta tafi karatu can London, yanzu haka saura watanni yarage ta gama amma naji suna cewa in tazo zatai aure, kada ka damu Yusuf na yarda dakai bazaka cutar da ita ba. Yusuf yakasa yadda zai fassara yanayin da ya tsinci kanshi domin kwata kwata tsaye yake amma ya kasa mosi. Dr Abdullahi ne yace kada ka damu engineer na yarda dakai, yanzu Inna je gida zan sanar da matata sai ta hada ni da ita inyaso taban address din sai in tura maka inyaso taje ta dauke ka a airport. Yusuf yace dagaske batai aure ba? Dr Abdullahi ya tsare sa da ido yanason gano wani abu. Ganin haka Yusuf yace nifa in tana da aure ka fadamin saboda bana sauka gidan ma'aurata. Dr yace wallahi bata da aure in har bazaka sauka gidan taba shikenan. Sukai sallama akan saiya jishi a waya Zaune yake cikin mota yana nazarin maganan abokinsa, da gaske Haneefah bata da aure? Toh ya aunty Muhibbat tace tana da aure? Abin ya daure masa kai sosai. Sai kuma ya tuno in dagaske ne bata da aure fa? Wani irin farin ciki ya lullubeshi. Da sauri ya tada mota ya dauki hanya zuwa gidan Aisha. Mai gadi na bude masa ko fa ya fito cikin hanzari ko rufe motar bayyi ba. Cikin sauri ya shiga gidan ya tarar tana zaune kan kujera tana yiwa Ra'ima wasa. Cike da tsananin farin ciki yayi sallama tare da karban Ra'ima yace my little princess takwaranki ta kusa zuwa gare ni. Aisha tashiwa tayi ta tsaya karewa yayan nata kallo ganin farin cikin da ke fuskarshi da abinda yake fada tace Yaya irin wannan farin ciki haka? Kuma kake cewa Haneefah ta kusa zuwa gareka? Yusuf yace zauna in baki labari, zama sukai ya sanar da ita abinda sukai da Dr Abdullahi. Shiru Aisha tayi tana kallonsa tace har Momy taje gidan akace da ita Haneefah tayi aure. Turus yayi yana kallon ta. Tunani yake wannan lamarin yana da daure kai... Aisha ce tace yanzu Yaya kasan mafita? Girgiza kai yayi alamar aa domin jikinsa ya gama yin sanyi kada muyi gaggawa a wannan lamarin, in kaje London ka sauka gidan nata saika tabbatar inma tana da aure ko bata dashi nima anan zansan yadda zan gano lamarin amma kada ka nunawa kowa abinda ke faruwa tatta ita da kanta amma kafin nan zan so ka sanar da abokin naka lamarin. Gyada kai yayi alamar ya fahimceta yayi mata sallama ya wuce gida. Tunda ya kwanta tunani barkatai suke masa yawo a kwakwalwa, wani bangare na zuciyarsa kuma tsananin farin ciki yake ji amma bai bada damar wannan farin cikin ya samu zama a zuciyar shiba. Tagumi yayi yana kallon kasan tiles. Momy ta turo kofa tashigo da sallama. Da sauri ta iso tace lafiya ? Meyasaka wannan ta gumin? Murmushi yayi yace Momy a kullum fatana rabuwa dake lafiya, bana son kusan toh abinda zai bata miki rai. Durkusawa yayi gabanta yace Momy yafiyarki nake nema dan Allah bana bukatar tsinuwar ki, albarkanki nake nema wadda jikokina zasu kasance cikin albarka. Momy da duk jikinta yayi sanyi ta zaunar dashi tace kada ka damu, zaka kasance cikin albarkata har karshen rayuwata, nayi kuskure abayi da na ambata maka wannan furuci yanzu da kaina nake nadama. Da inada damar aura maka Haneefah da na aura maka nasan tunanin ta ne yasa kake irin wadannan maganganu, amma ka sani kada son zuciyarka ta kaiga ga halaka, kabar tunaninta tayi maka nesa ka nemi wata ka aura. Yusuf yace wata qila nakusa aure Momy! Cike da murna Momy tace Allah nuna mana ya sanya alkhairi, aina take da zama? Yusuf yace in na zo daga London zamuyi magana. Dadi ya cika Momy dakyar sukai sallama sai hira suke. Daren ranar Yusuf bayyi barci ba. Washe gari misalin karfe sha daya ya musu sallama ya fita. Waya yayiwa abokinsa yaci sa'a yana wajen aiki. A office ya same shi suka gaisa. Batare da bata lokaci ba ya sanar da shi abinda ke tafe dashi, bai boye masa komai ba ya sanar dashi haduwar su da Haneefah da yadda rashin auren ya kasance, yadda sukai da aunty Muhibbat da yadda suka hadu da Haneefah a London ya qara da cewa tabbas akwai boyeyyen al'amari tsakanin mu, pls ka fahimce ni sannan ina bukatar taimakon ka, nasan kafin in sameta zan sha kuma family suna fishi da ni amma nasan in kayiwa Nana bayani zata fahimtar da su. Dr Abdullahi yace bansan haka abin yake ba aboki, amma insha Allah komai ya zo karshe tunda mum naka ta sauko, mafita daya ne muddin tana son ka har yanzu, kuma babu wadda ya nemi auren ta abin zaizo da sauki, yanzu zan baka address din in kaje kawai kaje gidan direct. Yusuf yace amma inason maganan ya zamo sirri, zanje mu daidaita kafin nan. Abdullahi yace babu matsala Allah tabbatar muku abinda yafi alkhairi. **** Dr Mubarak ya kasa aiki, juyi yake akan kujera yana tunanin yadda zai bullowa Haneefah, gashi ta kusa gama makaranta, shi tsoron shi kada ta zo gida manema su fito ta amsa musu tunda ya fahimci bata son auren nasa, domin hujjarta baikai taki auren sa ba. Tunanin tafiya London ya fara. Ya yanke shawarar tafiya neman soyayyarta, domin yanzu *_Dr HANEEFAH_* ce babban burin shi. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼51 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Kwance yake akan gado kansa yayi masa za fi tsabar tunani? Allah mai iko mai yadda yaso, wannan itace Haneefah? Itace ta zama DOCTOR? Ta zama consultant? Cikin shekaru kalilan? Tabbas in kayi niyyar abu zaka yishi sai dai kana da karancin niyya. Murmushi yayi daya tuno ko turancin kirki bata iya ba amma yanzu kwarewarta cikin harshen har mamaki take basa, yarinya karama amma halinta da nutsuwarta yananan. Tashiwa yayi ya jinginu jikin gado ya lumshe ido. Hango tsantsar soyayyarsa yake cikin idanun sa. Allah sarki dearie har yanzu kina so na? Goge hawayen daya zubo masa yayi yace but it's too late, ur already married. Babu abinda yakamace kamar HAKURI. Amma meya kawo ta London? Zaman aure yabawa kansa amsa. Mesa ta biya maka kudin aikin da za'a maka? KYAUTATAWA da nuna yafiyarta gareka. Murmushi ya kuma yi yace ya zama dole in fita rayuwar ki Haneefah, domin in ina kallon ki hankalina sake tashiwa yake nesanta kaina gare ki shine mafita. Tashiwa yayi zai shiga banda idonsa ya hango iPad din ta. Yasa hannu ya dauka yace kenan abokin karatun tane. Sha'awar budewa yaji yana yi, nan taje ya kunna babu inda yayi niyar shiga sai hotuna. Duk inda yaganta a waje lullube take da habaya ko dogon hijabi, kuma yawanci hotunan suna makaranta ko wani guri daya tabbata library ne. In yazo inda bata da lullubi da sauri yake wucewa dan ba tsayawa yake ya kare mata kallo ba. Baya ganinta da kowa sai wadda ya sukai musanyar iPad da wani dan India hakan ya tabbata mishi wata kila abokanan kara tunta ne. Ya dauki tsawon lokaci yana kallo domin ganin mijin nata amma bai gani ba, kuma baiga yarinyar daya ganta a auren Nana ba. Fita yayi yashiga gurin videos nanma ba abinda yake nema bane sai kawai ya kashe ya' aje iPad din. Murmushi yayi yace ina tayaki murna domin kula da mijinki daya ke yine yasa kika canza. Allah baku zaman lafiya. Da dare ya kira Abba yana sanar dashi abinda sukai da likitoci amma bai sanar dashi komai game da Haneefah ba, Abba yace kai kadai Yusuf. Yusuf yace babu abin damuwa Abba inaga abin yana da sauki kuma akwai wadda nasani cikin likitocin zasu kula da komai nidai addu'ar ku nake bukata. Abba yace Allah baka lafiya yasa ayi a sa'a. Ya amsa da ameen sannan sukai sallama ya katse wayar. Kwanciya yayi amma ya kasa bacci bayananta ne ke yawo cikin kunnensa. Ganin kada ya aikata haramci yasa ya tashi yayi alwala ya soma nafilfilun yana rokon Allah yabashi ikon fin karfin zuciyarsa. Itama abin haka yakasance agunnata, duk yadda taso daurewa abin yaci tura. Raihana data fuskanceta tace haryanzu lokaci bai kure miki ba, kina da rai da lafiya sannan kina da bukata ba juyi zakirika yi kan gado ba, duk mabukaci baya bacci, naga alama bazaki iya hakura dashi ba, shima haka, saiki tashi ki sanar sa da Allah halin da kike ciki, cikin ikonsa mahaifiyarsa da kanta zata zo neman aurenki wa Yusuf. Tsaki Haneefah tayi tace kina tunanin shine yake damuna ni jarabawarmu nake bi arai tana magana tana mikewa taje tayo alwala ta soma nafilfilu. Washe gari hankalin Haneefah ya kasa kwanciya, so take taje ayiwa Yusuf aiki amma tananan amma ta rasa abinda yasa bazata ba, ganin sai tunani take yasa ta yanke shawarar in an masa kafin ya farfado zata tafi. Cikin nasara akai aikin, Dr Michael da kanshi yayi aikin dan ganin kada a samu kuskure domin Haneefah. Daki na musamman aka kai Yusuf. A hankali ta turo kofar ta shiga. Har yanzu alluran bai sake shiba. Tafiya tayi gabansa tana kallonsa, bai canza ba domin yadda tasan shi abaya haka yake sai dai fari daya kara. Ji take tamkar ta maida shi ciki, ganin ya fara motsi ta tashi da sauri zata fita amma tuni ya ganta. Murmushi yayi ya sake rufe ido domin baya son dogon tunani game da ita. Tana fita ta tsaya gefen dakin tana hawaye, ganin kada azo a sameta ne ta wuce da sauri zuwa office din Dr Michael. Yana fita suka hadu. Ta gaishe shi ya amsa tare da cewa munyi nasarar aikin da mukai sannan aikin da mukai free ne ba sai an cire a salary ki ba sai dai zai rika zuwa checkup wata biyu sau biyu domin qara tabbatar da lafiyarsa. Tace sir ku sanar dashi domin yau bazan sake zuwa ba sai bayan sati biyu banajin dadin jikina. Yace babu komai duk sanda kika samu sauki zaki zo sannan muna son baki hutu a asibiti domin kije kiyi karatu tunda kun kusa. Tayi godiya ta wuce abinta. Tun daga wannan rana ta yanke zuwa asibiti. Ta aje hankalinta sosai tana karatu. Addu'a take Allah bata ikon hakuri da juriya inko haduwan sune alkhairi Allah janyo lamarin kusa. Kallon hotunansa kadai yana sa taji sanyi aranta dan haka damuwarta ta ragu domin tanaji ajikinta komai ya wuce. **** **** Yau kimanin watansa biyu da zuwa Nigeria. Bai gayawa kowa haduwansa da Haneefah ba. Alhamdulillah ya samu sauki, zafin da yake ji a kafafunsa duk yadaina ji komai ya koma normal. Lamarin Haneefah fa duk ya tattara ya aje a gefe domin ya hakura da ita tunda takasance tare da wani a matsayin ma'aurata. Yau juma'a ya dauki excuse gurin aiki domin tafiya London ranar lahadi, ba tare da bata lokaci ba ya dauki hanyar kano domin yiwa iyayensa sallama. Tun kafin ya isa gida ya ji yana sha'awar biya su gaisa da abokinsa domin tun ranar dinner sa suka rabu, don haka ba tare da bata lokaci ba ya nufi gurin aikinsa. Yayi parking kenan Dr Abdullahi ya fito da alama gida zai tafi. Ganin Yusuf yasa ya tsaya yana murmushi harya iso ya mika masa hannu suka gaisa. Dr Abdullahi yace kaikam shiru Abuja ya boye ka. Yusuf yayi dariya yace amin afuwa wlh abubuwanne sukai yawa yanzu ma nazo gida sallama ne shine nace bari in biyo mu gaisa. Dr yace ka kyauta ina zaka ne? Medical check up zanje London. Wani asibiti Dr ya tambaya? Yusuf ya sanar dashi. Dr yace ai asibitin da kanwar matata take aiki kenan Haneefah, in bazaka damu ba zan hada ku ka sauka gidanta saiku tafi tare ganin Dr ma zaizo maka da tsauki. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼53 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Kasancewar yau babu aiki da makaranta yasa tun safe ta tashi yin sharar dakin da bakon zai sauka, domin sunyi waya da Nana ta sanar mata da zuwan bako. Dakin farko wadda ke nesa da nasu kadan ta gyara. Tsaf ta gyara dakin tamkar kullum ana rayuwa ciki, tanakan wanke ban daki Raihana ta leko tana ganin gyara tace Haneefah kekam kin huta arayuwa, komai kin iya, girki, kwalliya, gyara, kula da mutum komai na rayuwa, ki godewa Allah sannan ina taya Dr Mubarak samun ki matsayin mata. Murmushi take amma jin an ambaci Dr Mubarak saita hada rai tace saiki auramin shi ai. Raihana tayi dariya dace zan so ganin wadda zaki aura, Allah saiya jure zama da ke domin kina da taurin kai ta fannin aure ace ke kin makalewa wadda baki da tabbas akansa? Haneefah tace yanzu ke kika nemi tsokanata, aure dai zanyi kuma bauta zai kaini gidan miji dole inyi biyayya. Dr Mubarak dai bazan aura ba sai dai wani daban, Yusuf kuma na mance da shi hotunan sa da kika makala bazan cire ba sai na tashi barin gidannan, yadda na cire zan koma Nigeria haka zan yakice shi in cireshi a zuciyata. Raihana tace Allah sa da gaskene, me sunan bakon da zamuyi? Haneefah tace wallahi ban sani ba, ban ma tsaya na tambaya ba amma tace zaizo ba sai munje dauko shi a airport ba. Duk hiran da suke cikin harshen larabci domin yanzu in dai da Raihana suke sai larabci. Bayan sun gama komai sukayi wanka. Hira suka zauna a daki Raihana tace ni yanzu bana son nagama makarantar nan, nasaba da garin sannan ina tare da amintacciya wadda ta gama sanin halayyata muna zaman lafiya. Haneefah tace kada kiyi tunanin zumuncin mu zata yanke, har abada muna tare. Hira suke sosai Haneefah ta fara canza fuska. Raihana tace lafiya Haneefah? Da sauri Haneefah tace cik.... kafin ta karasa ta fadi tana rike da mararta. Hankalin Raihana ya tashi sosai tana jijjiga Haneefah. Ganin ko motsi batayi ta soma kuka, tashiwa tayi ta nufi inda ta aje allurar tana ciwon mara. Bayan ta saka mata da minti biyu taji ajiyar zuciyar Haneefah. Raihana tayi hamdala ta gyara mata kwanciyarta ta rufeta da bargo. Zama tayi gabanta tana kallon ta tana tunanin kowa da irin cutarsa a duniyar na, shiyasa a duk halin da mutum yakasance ya godewa Allah. Tayi sallah la'asar tana kan sallaya taji motsin Haneefah. Da sauri ta iso gareta domin tafi awa biyar tana bacci. Gani tayi tana dan birgima ta rike cikinta, Raihana ta hayo kan gadon ta riketa tana mata sannu. Addu'a take tana tofa mata, suna cikin wannan yanayin taji bell na kofa yana ringing. A hankali ta aje kan Haneefah a pillow ta tashi domin ganin waye. Tana bude kofa ta ganshi tsaye da jakar kayan shi. Mamakine ya bayyana fuskar Raihana domin ta gane shi. Cike da mamaki ta bude baki cikin harshen turanci tace wa kake nema? Yusuf yace nine bakon da akace in zoni nan gidan. Babu musu ta bashi hanya ya wuce. Shigowa yayi da sallama yana ware idanu ina zai ganta. Gaisawa sukai sannan ta mishi jagora zuwa dakin shi. Mamaki fal a zuciyar Raihana ta fito ta nufi kitchen ta hada masa komai ta nufi dakin shi. Bayan ta aje zata fita ta nuna masa banda ki. Bayan fitarta ya tashi ya shiga ban daki yayo wanka sannan ya dauro alwala. Har dare yaji gidan shiru, ji yake babu gajiyar hanya tattare dashi, so yake ya kafa idonsa akan Haneefah. Wayar Haneefah ce ta soma ringing, ganin sunan Nana yasa ta dauka wayar suka gaisa da Nana ta sanar da Haneefah bata kusa da wayar. Nana tace bakon ya iso ko? Raihana tace eh amma.... jin motsin Haneefah yasa ta katse wayar kallon ta ya koma kan Haneefah. Birgima ta soma yi tana salati, kuka Haneefah take, wannan karon ta fita hayyacinta sai kuka, wasa wasa sun kusan raba dare a wannan yanayin, ganin haka yasa Raihana ta tashi ta nemo allurar bacci ta sawa Haneefah. Nan take bacci ya sace ta. Tsaye tayi tana kallonta, lokaci daya ta rame duk ta fita hayyacinta, ganin tunani ba mafita bane ta fito domin neman drip ta sawa Haneefah. Duk wucewarta yana kallon ta, gani yayi ta nufi wani guri tazo dauke da drip a hannunta. Ita ko Raihana sam bata lura da shiba domin cikin sauri take. Yanzu ya tabbata babu lafiya. Tashiwa yayi ya shige daki ya zauna tunani, ina Haneefah take? Ko dai bata da lafiya ne? Kusan karfe biyu tukun ya samu ya runtsa. Daidai karfe uku ta farka. Ta tashi a hankali ta zauna, ganin drip a hannunta yasa tasan ta dade. Ganin Raihana tayi kan sallaya tana sallah. A hankali tacire ta tashi dakyar ta nufi ban daki. Ruwan zafi ta hada sannan tayi wanka da alwala ta fito. Bayan ta rama dukkanin sallolinta tayi addu'a ta juya ta fuskanci Raihana. Ya jiki ta mata? Da sauki ta amsa. Kasa tashi tayi nafilfilu, karatun qur'ani ta zauna. Idonta biyu har aka kira sallar asubahi, bayan ta idar zata tashi ta kwanta domin allurar baccin har yanzu bai saketa ba tace da Raihana bakon yazo? Raihana tace eh, Nana ta gaya miki wanene bakon? Aa bata fada ba, ita dai tace abokin mijinta ne zaizo checkup asibitin mu, tana kaiwa nan ta kwanta bacci ya soma daukarta. Raihana kam shiru tayi. Ganin gari na qara haske ta tashi tashiga kitchen ta soya chips, ta dauki try yasa akai da ruwan zafi, bread da kayan shayi ta nufi dakin Yusuf. Sallama tayi ya amsa ya bude kofa, ta aje tire tare da gaida shi ya amsa tayi saurin ficewa. Shiri tayi ta fita siyo drip domin wadda ta sawa Haneefah ya kare. Fitowa yayi a hankali ya nufi falo. Kusan mintunansa goma baiji motsi ba, dan haka ya tashi zai koma daki yaga wani glass da alama wajene ya nufi gurin domin ya leka. Daidai yazo wucewa kamar ance ya juya ya hangota kwance lullube da bargo. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼54 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Baisan sanda yakaraso dakin ba, tsayawa yayi yana kallon ta. Lullube take ta rabu guri daya, hannunta dake makale da drip ne kadai ke waje. Da hijabi ajikinta purple, colour ya dada haskata. Ji yayi tausayinta da tsananin sonta na ratsa illahirin jikinsa. Ya dauki tsawan lokaci yana kallon ta tare da tambayar kansa me yake damunta? Ya kalle bedside drower da fuskanta ke kallo, dauko hoton yayi yana kallo. Rufe bakinsa yayi da tafukan hannunsa yana kallon hoton shi, a sannanne ya dago idanun shi zuwa dakin, hotunan sa yake kallo. Yanzu ya yabbata Haneefah bata mance dashi ba kamar yadda shi ma bai mance da ita ba, tana sonshi kamar yadda shima yana sonta, wani irin so sukewa juna? Sunkuyo yayi yana mai sharar hawaye a hankali yace tun kafin naji komai daga gare ki nasamu abinda nake bukata.... Ji yayi ance me kakeyi cikin harshen turanci? Tashiwa yayi yana kallon Raihana yace meke damun Haneefah? Haneefah ta soma birgima tana salati, Raihana tazo da sauri ta kama hannun ta dake makale da allura gudun kada ta jima kanta ciwo tana mata sannu... Raihana ta dago kai tana kallonsa duk yabi ya rude amma ya kasa cewa komai tace ka fita! Ganin kamar bazai fita ba ta daka masa tsawa ka fita!! Yana tafiya yana kallon su har yakai bakin kofa. Ganin ba matsawa zayyi bane yasa ta tashi ta rufe kofar da key. Haneefah wannan karon tasha wahala sosai, dakyar ta samu ta nutsu. Raihana kam sai kuka inta tuno hira suke amma cikin kankanin lokaci Haneefah ta nemi lafiya ta rasa. _Kamar haka ne duk wani bawa yana raye batare da ciwon komai ba lokaci daya zai fadi ya rasu babu ciwo, shi yasa ake cewa kullum mukasance da kyakykyawar niyya_. Kusan karfe 11:00am Haneefah ta farfado. Wasai ta tashi kamar ba ita tayi ciwo ba sai dai rashin karfin jiki. Kallon Raihana tayi taci kuka idanunta sunyi ja tace Yanzu meye na kuka? Kinsan ciwon nadan lokaci ne zan farfado kike kuka? Raihana tace baki ga yadda kika koma ba? Wallahi duk wadda yake tare da ke sayya tausaya miki. Haneefah tace na ki tausayin ya wuce misali, domin har ciwon kai zaki iya sawa kanki tana magana ta mike ta shiga banda ki. Tseye take gaban madubi bayan ta fito daga wanka tana kallon kanta yadda ta rame, juyowa. A hankali ta gama shirin ta cikin dogon kaya kamar yadda ta saba, ta dauko babbar himar tasa zata fita Raihana tace mata ina zaki? Haneefah tace ba office zan fita ba, bako zanje in gaisa da shi, tun jiya yazo fa. Raihana tace wai basu fada miki bakon bane? Abokin mijin Nana ne cewar Haneefah. Sannan ta fita Raihana ta bita da kallo cikin zuciyarta tana cewa wannan wani lamarine yake son wakana? Nana da kanta ta bari Yusuf yazo? Shiru tayi tana jiran shigowar Haneefah dan tasan bazata shigo lafiya ba. Ita ko Haneefah tana fita ta nufi dakin, sanda ta bude baki zatai sallama saida taji gabanta ya fadi. Baki na karkarwa tayi sallama, jin anyi shiru ta kuma yi, nanma shiru zata kwankwasa kofar kenan taji an bude kofa. Ganinsa a tsaye yasa gabanta yayi mugun faduwa. Ja da baya tayi tana kallonsa, shima kallon nata yake amma sun kasa furta ko da kalma dayane. Da sauri ta jiya ta nufi dakinsu. Tana shigowa ta rufe kofar da sauri tazo gurin Raihana cikin muryar kuka tace nashiga uku, bayan tunaninsa har kallonsa nayi yau cikin gidannan, dan Allah kije ki kara dubamin nasan bashi bane gizo ne. Raihana ta kamo hannun ta tace shine Haneefah, pls control urself kada ya gane hankalin ki a tashe yake. Haneefah ta dafe kanta tana salati. Mikewa tayi zata dauki wayarta ta kira Nana Raihana kamar tasan abinda zatai ta fizge wayar a hannunta tana cewa nasan kiranta zakiyi akan mesa ta bari Yusuf yazo amma inason k isan cewa itama tana da hankalin da bazata aikata miki haka ba. Haneefah bata tanka mata ba ta karbi wayarta ta shiga kiran Nana. Nana tana daukawa ko karasa sallamarta batai ba Haneefah tace kin kyauta, bakon da kuka turomin keda mijinki, harkin manta abinda ya shiga tsakanina da mahaifiyarsa shine kika barsa yazo? Nana tace wayene kike magana akanshi? Badai Yusuf ba? Haneefah tace shine yazo, inaso kice da mijinki yace da abokin sa ya tattara kayansa yabarmin gidana bana son ya qara ko da awa dayane tana kaiwa nan ta katse wayar. Kuka ta zauna yi. Raihana bata ce da ita komai ba zata fita domin hada lunch tace inkin fita kice dashi ya fita yabar gidannan... bata qarasa ba taji yace kibari in kikaji da me nazo sai nabar gidan. Haneefah tashiwa tayi tace babu abinda nake sonji infact bana bukatar ganinka ka fita! Babu yadda bayyi akan ta sauraresaba amma kememe taki. Yusuf yace in bakyason ganina me ya kawo hotunana? Pls Haneefah nasan har yanzu muna kaunar junan mu ki tsaya kiji me zance. Dago ido tayi tana kallon shi, gani yayi ta nufi inda hotunan suke ta soma cirowa, gaba daya ta zo ta zubar gabansa glass din baki daya suka fashe. Raihana dake kitchen ta taho da sauri jin fashewar glass tazo ta tarar da abinda Haneefah ke aikatawa. Haneefah ta nuna hotunan da ta zubar gabansa tace indai nine ga hotunan ka kwashe ka tafi dasu har abada bana son kara ganin ka! Yusuf ya dago manyan idanunsa da suka kada sukai ja yace nine bakison gani? Haneefah tace eh!! Nadaina sonka ina da wadda nake so. Damm!! Yaji gabansa ya fadi. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFA* 👩🏼55 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Dr Mubarak durkushe yake gaban Abba yana jiran amsar da zai fito daga bakinsa. Abba yace Alhamdulillah gaskiya naji dadi kwarai da gaske wannan maganar taka domin kai yarone mai tarbiyya, amma zan so naji ra'ayin ita Haneefah kafin ka turo magabatan naka domin bazan aurar da yarana ga wadda basu aminta ba. Dr yace dama izini nazo nema, in ka amince min zuwa gobe zan wuce can London mu daidai ta. Abba yace toh yayi kyau, Allah kiyaye hanya. Sukai sallama. Bayan fitarsa ya wuce gida ya sanar da barrister yadda sukai, ta nuna masa farin cikinta tare da masa fatan alkhairi amma kishin na nan, babbar dutse ta ajiye a zuciyarta daya danne mata shi wato _AMBATON ALLAH_. Shiri tsaf yayi yana jiran wayewar gari. * Umma da jin zancen tayi farin ciki amma ba can cikin zuciyarta ba amma bazatayi shishshigi lamarin ubangiji ba zata ci gaba da addu'a Allah tabbatar da alkhairi rayuwar auren su **** **** Da sauri Raihana tazo ta riketa tace haba Haneefah kin manta baki da lafiya ne? Fizge rikon da Raihana tayi mata tayi tace kice dashi ya fita banason ya qara ko da awa dayane, tana kaiwa nan ta dauki wayarta ta fice tabar musu gidan gaba daya. Raihana ta bita da kallo cike da mamaki, yau ita take tsawata Yusuf dinta haka? Ita da ko a hoto a nutse take masa magana. Fita tayi domin bin ta Yusuf yace dan Allah ki saurareni kada dan ita taki saurarata kema kice bazaki saurare ni ba. Raihana tace mu koma falo sai inji meke tafe dakai. Jikinsa a sanyaye yace dagaske Haneefah tana da wadda ta ke so? Raihana tayi murmushi tace iya zamana da ita yau kusan shekaru hudu babu wadda take so tamkar ka, bata da zancen kowa sai naka, dukkanin burin ta da farin cikin ta a tattare dakai take hangowa. Yusuf yace Alhamdulillah, tabbas nasan muna son juna tunda duk tsawon lokacinnan bamu daina dawai niyar soyayyar muba, amma bansan dalilinta naqin sairarona ba. Raihana tace akwai dalili, mahaifiyarka ta nemi alfarman inaga wannanne dalili. Yusuf yashiga mamaki, wato Momy har Haneefah bata bari ba? Cike da damuwa ya sanar da ita duk abinda ya faru dalilin rabuwansu da bayan rabuwarsu ya qara da cewa dan Allah ki sanar da ta saurareni na sake dawowa rayuwarta. Raihana kam taga abu, sun rabu kuma suka sake zuwa suka hadu lallai mahakurci mawadaci tace kada ka damu zan mata magana, insha Allah zaku daidaita nayi farin ciki sosai. *** Nana na katse wayar ta juya tana kallon mijinta tace wanene bakon da ya sauka gidan Haneefah? Kai tsaye ya bata amsa abokina Yusuf, nabaki labarin sa ai. Nana tace ko kana da hoton sa? Yace menene na bukatar son ganin hoton sa? Tace nidai inason ganin pls ka nunamin. Dauko wayarsa yayi ya lalumo hoton Yusuf ya nuna mata. Nan take ta hade rai tace ai dana san shine ban bari ka hada sa da ita ba. Yace dalili? Nana ta sanar dashi komai tace sun rabu, yanzu ta ganshi hankalinta ya tashi,nasan yanzu haka tana ta kuka domin har yanzu bata daina son sa ba, ni abinda nake gudu kada damuwar ya taba karatun ta. Abdullahi yace ki kwantar da hankalin ki, inshaa Allah bazai taba karatun ta ba yanzu ki kirata ki kwantar mata hankali. Nana ta samo kiran Haneefah yana ringing bata dagawa. Nan hankalinta ya tashi tace dan Allah ka kira abokin naka kace kada maganar komai ya hada su nasan yadda take sonshi ganin sa ma tada mata da hankali yake. Ganin yadda hankalinta ya tashi yace to zan kirashi, dakyar ya lallabata tayi bacci. ***** Zaune take tana kuka mai cikin sauti mai tsuma zuciya, gata bata da lafiya duk ta rame na lokaci gida abar tausayi. Babu abinda takeji kamar ta cire zuciyarta, tunani take duniya gidan wahala. Wannan wace irin so ne? Mahaifana suna so na amma duk nabi na tada hankalina?? Anya Haneefah abin naki bayyi yawa ba? Tu no da abinda taiwa Yusuf ne yasa ta kara fashewa da kuka tace ina sonka amma bani da mafita bayan wannan, mahaifiyar ka tamin iyaka da kai, zanbi ko wacce irin hanya domin ganin zamanka lafiya da mahaifanka. Ganin tunani da kuka ba shine mafita ba, shiru tayi tana kallon yadda kowa ke harkan gabansa babu ruwansu da kowa. Jin tsananin yunwa yasa ta tashi da nufin komawa gida amma ta kasa domin jiri ke dibarta, ganin lokacin sallah yayi ta tashi ta lallaba ta kamo hanyar gida. Dakyarta iso domin yunwa ya galabaitar da ita. Tana bude kofa ta ganshi abude, alamar babu wadda ya fita bayanta. Dakyar take tafiya har ta iso kitchen, neman ruwan zafi tayi ta zuba a kofi ta zauna tukun ta soma sha domin hada shayi ma tana ganin wahalane. Bayan ta sha ta kifa kanta tana fitar da numfashi a hankali. Takai kimanin mintuna takwas tukun ta tashi ta nufi hanyar daki. Sam bata kula da mutum a falo ba domin duk tagalabaitu. Shiko Yusuf shiru yayi ko motsi ya kasa ya zuba mata ido. Duk yabi ya damu, domin ganinta bata da lafiya amma tsoron mata magana yake mata... Tana shiga daki ta tarar da Raihana kan sallaya ta idar da sallah. Itama ban daki ta nufa domin dauro alwala tayi sallah. Dakyar tayo alwalan jin kasan mararta na mata wani iri. Bayan ta idar ta tashi ta nemi magani tasha ta kwanta kan gado. Raihana ta mata sannu tace ko zata kawo mata abinci? Aa ta amsa. Shiru sukai na dan lokaci sannan Raihana tace pls Haneefah ki sauko daga fushin da kike, Allah ya amshi addu'ar ki Momy ta amince dake, hakurin ki da juriyarki ne yakai ki cimma wannan nasara, hakika duk wadda yakasance yana tare da hakuri to nasara na biye dashi dan haka saiki tashi kije ki gana da angon naki ku daidaita. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼56 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Ganin Haneefah tayi shiru yasa ta kira sunanta, nan ma shiru. Tashiwa tayi taje domin ganin lafiya? Bacci ta tarar ya dauketa, murmushi Raihana tayi ta lullubeta da bargo. Raihana taji wayarta na ringing, tana daukawa taga course mate nasu yace lafiya yau baku shigo ba? Raihana tace Haneefah fa ce bata ji dadi ba amma yanzu da sauki. Yace dama yanzu akai kiran gaggawa na dalibai bangaren karatun mu, amma kada ki damu kizo innaji komai zan kiraki in sanar dake ta amsa da toh sukai sallama. Shiko Yusuf kallon kofa yake ko zaiga Haneefah ta fito amma shiru bata fito ba, jin tsananin yunwa yasa yaje ya soma cin abinci da aka tanadar masa. Dab da magriba Haneefah ta bude ido. Tashiwa tayi ta nufi bandaki ta wasa ruwa ajikinta sannan ta dauro alwala. Bayan ta idar da sallah ta zauna kan sallaya tana jiran magriba tareyin lazimi. Bayan sun idar da sallah Raihana taje ta kawo musu abinci, ta tarar Haneefah tana karatun qur'ani a sirrince har lokacin isha'i yayi domin babu nisa, tashiwa tayi ta idar ta soma cin abinci domin yunwa take ji sosai. Raihana kallon tausayawa take mata domin yadda takecin abincin sai maijin yunwa sosai. Haneeah tace ban hanaki cin abincin ba in zaki zo kici, Raihana tayi murmushi tace aa, ki gama ci saiki ragemin. Tana gama cin abinci wayar Dr Michael yashigo wayarta. Da sauri ta daga tare da gaishe shi tace yanzu nake kan hanya sir. Yace takardar hutun ki da nace zamu baki zaki zo ki karba domin daren yau zanyi tafiya. Haneefah tace toh sir ganinan zuwa. Tana gama wayar tayi tsallen murna tace Alhamdulillah, sis zanje karban takardan hutu na saina dawo. Raihana tace bari in kaiki baki da lafiya. Zan iya tafiya kafin nazo kice da wannan bakon ya tattara yabar gidannan, tana kaiwa nan ta sauki makullin mota ta juya ta fice. Zaune yake yayi shiru idanunsa nakan Tv amma hankalinsa baya kai tunani yake yadda zai bullowa wannan al'amarin. Yana tunani ya ganta ta fito cikin sauri. Har taje kofa zata fice ta juya suka hada ido. Dam!! taji gabanta ya fadi da sauri ta kawar da idanun nata ta bude kofa ta fice. Raihana ta fito taga harta fice Yusuf yace ina zata je bata da lafiya? Kiran gaggawa aka mata yanzu zata zo ba dadewa zatai ba, kafin tazo ka koma daki domin haryanzu bata sauko ba cewar Raihana. Yace meke damunta? Shiru tayi, ya sake tambayar tace ciwon kai ta juya ta shiga ciki Ji yake kamar ya bita, tashiwa yayi ya shiga daki jin kanshi na sarawa, kwanciya yayi amma ya kasa runsawa. Tabbas tana sonsa amma mesa take masa haka? Ko Raihana bata sanar mata komai bane? Ya Allah daga gareka muke kuma gareka zamu koma ya furta a hankali yana mai runtsa idanu jin tsananin sonta da yake fuzgarsa. Tuki take amma hankalinta yana tare dashi, wani irin so nake maka? Maimakon son naka ya ragu kullum ninkuwa yake shin yaushe zan daina sonka? Duk sanda na ganka ina rasa mekemin dadi musamman inna tuno ammin iyaka dakai, ya Allah ka dubamin lamarina tsakanina da wannan bawan naka. Daidai tayi parking ta share hawayenta ta sauko. Direct office din Dr Michael ta wuce. Turo kofar tayi tashiga, shi kadaine yake zaune waya makale a kunnen sa, zata juya ta fita ya mata nuni da hannu ta shigo sannan ya katse wayar yana mai cewa zai kira anjima. Bayan ta gaishe shi ya amsa cike da fara'a yace dama zanyi tafiyane shine nace bari in baki takardan domin rashin sanin ranar zuwana wata kila inzo kun fara exams. Ya mika mata farar takarda yana mai cewa in kuka gama exams da hutun wata biyu saiki koma bakin aikin ki, bayan kin komo kin zama senior staff sannan asibiti zata dauki nawin ki karatunki wato masters amma in kina da ra'ayin karatun a wannan shekarar in ko baki da ra'ayi sai zuwa next year. Karbar takardan tayi tana murmushi tace nagode sir. Zata tashi yace kamar baki da lafiya? Tace eh amma da sauki. Shiyasa baki samu fitowa aiki bako, meke damunki? Ciwon mara ta amsa a takaice. Yace Haneefah yakamata kiyi aure, kamar yadda na sanar miki watannin baya, kada kikai stage dinda allurar dana baki bazai rike ciwon ba, muddin kikakai wannan stage zaki samu matsala a mahaifarki. Kanta a sunkuye tace sir zanyi. A sanyaye ta mishi sallama zata fice yace ammm! Ina Yusuf ne? Yakamata ace yazo checkup saboda duba aikin da muka mishi. Kamar bazatai magana ba saita tuna lafiyar sane za'a duba gomma Dr Michael yananan ayi komai. Komawa tayi ta zauna tace ya dawo in bazaka damu ba in kirashi yanzu ka duba shi? Yace babu matsala kirashi. Karban wayansa tayi domin tabar nata a gida ta kira Raihana, tana dagawa tace kizo da bakon ki nanda mintuna kadan Dr Michael nason ganinshi dan zayyi tafiya tana kaiwa nan ta katse wayar. Cikin minti ashirin suka iso. Ko kallon su bata yiba Dr ya mike yace bari muje dakin na'ura. A takaice kusan ita ta duba lafiyarsa. Duk motsin junansu akan idanunsu, ita Haneefah satar kallon shi take shiko baya boye kulawarsa gareta. A haka suka bincike tas Dr yace yaranka nawa? Nan wani abu ya taso ya tokare wuyan Haneefah, amma da mamakin ta taji yace babu ko daya. Nan Dr Michael yace kada ka damu aikin mu yayi kyau. Daganan sukai sallama suka fice. Raihana ce ke tuki gefenta Haneefah, bayan kuwa Yusuf ne ke zaune yayi shiru. Duk sai taji babu dadi abubuwan da take mishi amma ya ta iya, jugum suka iso. Ta riga kowa shiga gida, gurin karatun su suka wuce shi kuma ya koma daki. Sun soma karatu kenan sukaji kira daga makaranta gobe su fito da shirin su karfe uku na rana zasu tafi Chicago sati daya zasuyi. A wannan dare dukkaninsu sun kasa bacci, kowa tunani yake ga su a ruf daya amma ko gaisawa sun gagara, Haneefah zuciyarta ta kasa daurewa. Ta raya wannan daren tana mai ambaton Allah dakai kukanta gare shi. Shima Yusuf ya mika lamarunsa ga mahaliccin sa yana mai nemar mafita agareshi. Raihana kam tana ganin ikon Allah amma tayi alkawarin zuwa gobe saita sanar da ita komai. Bayan asuba Haneefah ta kwanta bacci. Sai kusan karfe goma ta tashi. Yau kam tajita jikin da sauki, tana tashiwa ta nufi banda ki tayi wanka ta fito. Bayan ta shirya tsaf ta fito neman abinci. A falo ta tarar da Yusuf da Raihana suna hira, jin bell yasa ta nufi ko fa taga wayene. Tana budewa taga Dr Mubarak tsaye. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼59 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Take Dr ya gano cewa jininsa yayi mugun hawa, cikin kayansa ya dauki allaurar bacci yasa mishi domin ya samu hutu. Nan take Yusuf ya soma bacci. Dr Abdullahi ya dubi Abba yace yana bukatar hutu, ku biyoni falo in muku bayani komai. Suna fitowa falo Nana taga Aisha. Aisha ma taganta da sauri ta karaso tana kuka tace dan Allah aunty Nana kiyiwa Haneefah magana, kice ta amincewa Yaya Yusuf kingan shi wallahi yana cikin wani hali. Kallo daya Nana ta musu taga damuwa tattare dasu, ta qara dubar Aisha cike da lallashi tace calm down sister! irin wannan damuwar da kuka shiga shi zai yadda sashi cikin wani matsalan, babu abinda zai same shi. Dr Abdullahi yace ina so ku kwantar da hankalin ku, insha Allahu komai zai dawo mana da sauki game da abinda zan fada. Wato Yusuf jininsa yayi mugun hawa ta yadda zai samu illah amma kafin ma zamusan yadda zamuyi, nasan damuwarsa bazai wuce Haneefah bane yanzu hanyar nemo ta takasance dashi zamuyi domin muddin yaci gaba da damuwa a lokaci daya zuciyarsa zata iya bugawa domin tana tara damuwan ne. Abba kasa magana yayi ya tashi ya fita, Aisha da Muhammad kam sai kuka babu bakin magana. Momy ce tayi karfin hali tace Abdullahi tayi aure fa! Yanzu ya zanyi da raina in Yusuf wani abin yasame shi, yau sabo dani gashi yana neman rasa ransa. Nana tausayin wannan bayin Allah ya cika mata zuciya tace Haneefah batai aure ba, hasalima haryanzu tana son danki tamkar yadda yake sonta. Momy tace ni da kaina naje har gidan yar uwarta tace dani tayi aure, shima ya tabbata da auren da tayi. Nana tace ni yayarta ne uwa daya uba daya, yar'uwata batai aure ba, hasalima tana jiran izinin kine tsawon shekaru hudu. Cike da mamaki Momy ta taso daga inda take tazo kusa da Nana tace Nimai laifice, nasan ban kyauta ba, saura wata biyu aure na janye maganar nasan family ku suna jin haushin abinda na aikata amma ina neman afuwa *YAR ADAM*, bansan soyayyar nasu mai karfi bace sannan bansan da ku nake tare ba, ZURI'A wadda annabinmu ya kwadaitar mana mu hada wadda zamu gina ingantaccen ZURI'A, dan Allah ina mai baki hakuri, kada ku hukunta Yusuf ni yakamata ku hukunta. Nana ta dago idanunta da suka cika da hawaye tace idan kowa zai rama laifin da aka yi masa yaushe ne za a daina yin laifi? Laifi kowa ana yi ma shi. Amma masu rauni su ke daukar fansa. Masu karfi su suke yafewa. Masu wayo sukan manta ne da an yi masu. Bamu da irin wannan hali kuma bamu zamu koyo ba, ki kaddara Allah bai nufi auren su a wannan lokaci ba ko kuma in sukai akwai hadari cikinta, sannan shi aure lokaci ne, in Allah ya kaddara ko kina so ko bakya so dole ayi auren. Umman da Abba basa bamu he wadda bama so, dan haka babu abinda zai sami Yusuf zan kirata da kaina inji abinda ya faru da suka hadu a London. Dr Abdullahi dake zaune yana murmushin jin dadi samu Nana matsayin mata domin ji yake kaf duniya babu wadda yakaishi dace, a zuciyarshi yace abokina dole ka damu domin gidan su Nana akwai tarbiyya, mace mai tarbiyya kuma duk namijin da yasameta tabbas yayi dace Momy tace itama can take? Eh Abdullahi ya amsa, labatar musu abinda ya faru tsakaninsa da Yusuf yayi, Nana tasha mamaki haka ga Momy. Amma suna jiran farkawarsa domin suji abinda yafaru. A wannan rana gidan yazamo tamkar zaman makoki ake, salmace kadai take gidanta batasan wainar da ake toyawa ba, Abba ko yayi fishi bayayiwa kowa magana. Sai dab da sallah isha'i yafarka domin harsu Nana sun shiga mota zasu tafi suka ga Muhammad na tsayar dasu yana cewa ya bude ido. Dukkansu suka dunguma zuwa dakin shi. Tashiwa yayi ya dafe kansa da hannuwan sa yana tuno abinda ya faru dashi. Da sauri Abdullahi yazo ya rike shi yana mai cewa relax kada kuma ka tuno komai ya wuce. Dago dakai yayi yana kallon abokin nasa da mamaki yana tambayar kansa yaushe yazo? Kallon daya bayan daya yakewa jama'ar dake dakin karaf idanunsa yakai kan Nana. Ganin yadda yake kallon tane yaji hawaye na neman zubo masa yace Nana Haneefah taki saurarona ta amince da DOCTOR! Ya qarashi maganan cikin sarkewar murya. Da mamaki take kallonsa tace Dr Mubarak? Yace eh shi, ya share hawayensa yaci gaba da magana nasan nayi rashin Haneefah domin bazan aikata haramci ba wato neman aure kan neman aure, xan kasance mai hakuri tare da fidda rai akanta. Shiru kowa yayi tamkar ruwa ya cinyesu. Dr Abdullahi yace ba komai, yanzu dai rashin damuwarka muke bukata bacci sosai yakamata kayi kafin mu nemi mafita. Momy da Aisha sun kasa magana sai ido. Sai da suka tabbatar da hankalinsa yadan kwanta tukun sukai musu sallama akan gobe zasu zo. Bayan fitarsu ya tashi yayi sallah yana mai addu'ar Allah tabbatar masa da alkhairi rayuwarsa. Abba ma ya shigo yayi masa nasihan bai kamata ya rika sa abu a ranshi harya dame shi sosai ba. Nuna musu yayi insha Allahu zai rage. Kusan goma suka fice Momy tamkar kada ta barshi shi daya. Shiru yayi yana kallon sallaya dake zaune akai, tabbas saboda damuwarshi bai kamata ya daga musu hankaliba amma shi baisan sanda damuwarma take damunsa ba, amma yaci damarar mancewa da komai insha Allahu. Tsawon kwana uku ya dauka baya fita ko ina, Dr Abdullahi yana zuwa yana dubashi haka ga kannensa ma suna tare dashi. Momy ajiye aikinta tayi tace zata kula da danta. Kyakykyawar kulawar da yake samuwa ne yasa yadan warware. Abba ganin dan nasa ya warware yasa ya sauko daga fushin da yake hakan yayi wa yaran dadi domin tun tasowarsu basu taba ganin rashin jituwa tsakanin iyayen nasu ba. Bangaren Nana kuma mamakin abinda Haneefah ta aikata take. Kullum cikin kiranta take amma bata dagawa, tayi mata text amma shiru ba replay. Kamar kullum takira yau taci sa'a ta daga wayar ko sallama bata gama yiba Nana tace yayi miki kyau yau kwana uku tukun kika daga wayata. Haneefah tace lectures muke fa bana samu dama, lokaci da nake free kuma inna kira kina bacci shiyasa bana kira. Nana tace nayi mamakinki Haneefah dama duk cika baki kike? Da kanki kaka amincewa Mubarak? Suna cikin magana batery Haneefah ya mace, Nana ta dauka katse wayar tayi baki daya, a hankali tace zaki gamu dani. Da dare Abba da Yusuf suna zaune suna tattaunawa tare da kallon Yusuf mai gadi ya shigo yace ana sallama da Abba, Abba yace ya shigo Yusuf ya tashi zai fice a bakin kofar shigowa falo suka ci karo da Dr Mubarak. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼57 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Murmushi tashigayi ta bashi hanya ya wuce. Da sallama ya shigo Haneefah na biye da shi har falo. Ganin Yusuf yasa yadan tsaya ya waigo yana kallon Haneefah alamar tambaya. Batare da cewa komai ba ta wuce kitchen kawo masa ruwa. Bayan ta dawo ta tarar babu Raihana ta shiga ciki shida Yusuf suke gaisawa. Ta dire try dake hannunta ta zauna kan kujera tana gaishe da Dr Mubarak, ya amsa da fara'a. Haneefah tace saukan yaushe? Yace ban jima da sauka ba nace babu hutu zuwan naki ne bari na biyo tanan kafin na wuce masauki. Haneefah tace kayi sa'a domin zamuyi tafiya nan da awa biyu masu zuwa insha Allah. Dr yace zuwa ina? Sanar dashi inda zasu da kwanakin da zasuyi ta sanar masa. Yace babu damuwa nazo na tarar dake da bako. Tace eh, abokin mijin Nana ne yazo checkup asibitin mune yayi masauki anan. Dr Mubarak yace Allah kara lafiya. Ya kalli Haneefah sosai yace dama bazan wuce kwana uku ba sannan inason magana dake. Tun kafin suce dashi komai Yusuf ya mike ya basu guri. Dr yace nagaji sosai jin zakiyi tafiyane zan sanar dake, naje gun Abba yabani izinin auren ki amma yace sai na nemi izinin ki, pls Haneefah kin kusa gama makaranta ki bani dama in mallake ki pls! Wadda kike ganin baki kyauta mata ba tana farin cikin kasancewa da ke matsayin kishiya, bansan mesa kike kin aure na ba. Na miki alkawarin rikon ki da amana tsakani da Allah ki bani dama. Shiru tayi tana sauraronsa. Wanna karon dole ta amince masa, dago ido tayi tace na amince, Allah tabbatar mana abinda yafi akhairi amma bana bukatar zama gida daya da barrister. Cike da farin ciki Dr yace indai wannan ne bani da matsala, in akwai wani abinma ki fada inajinki. Tace bana so auren ya dauki lokacin da saina gama makaranta daz ol, inaso inje in fara tara kaya lokaci yana tafiya. Cike da farin ciki ya mike yace indai wannan ne babu matsala na gode sosai, sai munyi waya pls take care of ur self. Murmushi tayi har bakin kofa ta rakasa. Rufe kofa tayi tana share hawayen da ya makale mata. Tana cikin yanayin nan ta ganshi ya fito dauke da jakarshi idanunsa sun kada sunyi sha yace nagode da abinda kika min amma ki sani har yau har gobe ina kaunar ki, ina miki fatan samun zaman lafiya gidansa, zan bar miki gida... kasa cigaba yayi ganin hawaye na neman sauko masa ya bude kofa ya fice. Gudu tayi ta nufi daki ta kwanta kan gado tana kuka. Raihana dake hada musu kaya tace subhanallah! Meya faru? Haneefah tace baisan hukuncin dana yanke shine daidai ba, i love him wit ol my heart, nima bazan daina son ka ba sai dai lokaci yayi dazan hakura dakai ko naki ko na so. Raihana da kanta ya daure tace ban gane abinda kike nufi ba. Haneefah ta sanar mata komai tace inaga ya saurari duk abinda muke tattaunawa da Dr Mubarak ne. Raihana ta tashi tana mai ambaton innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun! Haneefah kinsan abinda kika aikata? Momy ta amince da auren ku yazo domin sanar dake zaki bawa wani damar auren ki? Cikin sauri Haneefah ta taso ta dawo kusa da Raihana tace kina nufin Momy ta amince da auren mu ta janye kudirinta?? Nashiga uku me na aikata haka Raihana? Naga rashi naga samu, jin jiri yana neman daukarta yasa ta zauna bakin gado tana rera kuka. Daukar waya tayi zata kira Nana taga wayarta ya shigo, da sauri ta daga tace Nana nashiga uku, ki tabbatar min maganannan in gaskiyane? Nana tace it's ok nasan bazai wuce akan Yusuf bane yanzu haka ina tare da Sister shi Aisha wadda ta sa miki takwara, Haneefah ki godewa Allah soyayyarku ta dawo. Katse wayar tayi ta fashe da kuka tana cewa nashiga uku MEKE FARUWA dani ne? Dashi nake kwana dashi nake tashi tsawan shekaru da dama ina addu'ar daidaitawa tsakanin mu amma gashi yau ka zo gareni rashin sauraron ka ya jamin, nashiga uku. Raihana ki taimakeni ji nake kamar zan mutu, bana kaunar zaman duniyar nan. Da sauri Raihana tace shiru Haneefah babu kyau irin wadannan kalamai, kada ki manta hakan kaddarar kine,imani da qaddara, yana cikin ruku nan Imani guda shida, wanda imanin bawa baya cika ya inganta har sai ya samu karbuwa a wajan Allah har sai ya yarda da Qaddara mai kyau ko marar kyau. Ibn Umar R.A yana cewa: "......Na rantse da Allah da dayansu zai ciyar da misalin dutsen Uhudu na Zinare Allah bazai karba ba har sai sunyi imani da qaddara mai kyau ko marar kyau...." @Muslim Imani da Qaddara yana nufin: "Yarda da amincewa lallai dukkan abubuwa da suke gudana tun daga farkon duniya har zuwa karshenta, Allah ya sani kuma shine ya tsara faruwarsu, sannan ya rubuta hakan acikin LAUHUL MAHFUZ, sannan suna faruwane da ganin damar Allah kuma yadda ya tsara, sannan shine wanda ya halicci dukkan aiyukan bayi mai kyau da marar kyau. Yarda da wadan nan abubuwa da sallamawa da gaskata su shine Imani da Qaddara. Imani da Qaddara ya kunshi Martabobi guda Hudu-(4):- i-Ilimi ii-Rubutawa iii-Mashi'ah iv-Halitta. 1-Martaba Ta farko "MARTABAR ILIMI" Shine mutum yayi imani Lallai tabbas Allah yasan dukkan komai, a dunkule da dayday kunsu, ya san abinda ya faru tun farkon duniya, kuma yasan abubuwa da zasu wakana nan gaba har zuwa ranar alqiyama dama abubuwa da zasu biyo bayanta,da abinda yake faruwa yanzu da abinda ma bazai faruba da zai faru Allah yasan yadda zai faru. Allah yana fada: "(Wanda Ya saukar da Alƙur'ani) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai. (Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma daga ƙasã kwatankwacinsu, umuruinSa yanã ta sauka a tsakaninsu dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõme, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõme da) (Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Sã'a bã zã ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra ba ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma ba ta nisanta a cikin ƙasa, kuma bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin masu imani)" Sannan duk mai son ya samu imani, to ya rinka la'akari tare da tunani game da ayoyin Allah da HalittunSa. Duk mai son ya rayuwa cikin nagarta da mutunci, to ya rinka fadin gaskiya da aiki da ita. Ke alkawari kika rike na mahaifiyarsa amma yana dakyau arika sauraron uzuri, sannan amincewa da auren Dr Mubarak nemawa kanki lafiyane domin lalurar da kike tattare dashi, kada mu biyewa so a komai na rayuwa mubarwa Allah zabi. Haneefah ta share hawayenta tace yanzu shikenan zanci gaba da danne zuciyata na tabbata barin kaina da zuciyata a hannun Allah babban sadaukarwa ne domin na tabbata saiya jarabce ni amma na tabbata alkhairi yake nufi gareni. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼60 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Yusuf ya tsaya da mamaki yana kallon sa. Dr Mubarak ya mika masa hannu suka gaisa yace mu shiga daga ciki. Jiki a sanyaye Yusuf yayi gaba Dr na biye dashi. Bayan sun gaisa da Abba yace nasan bazaka ganeni ba amma shi Yusuf ya ganeni, nine wadda nake neman auren Haneefah wadda shekarun baya aure tsakanin su bayyu ba. Abba yace Na'am ina sauraron ka. Dr yaci gaba yace lastweek na hadu da Yusuf a gidan Haneefah, wadda a wannan lokacin bansan shiba sai kwanaki dana zurfafa bincike a kanshi. Ya dubi Yusuf yace lokacin da na karashi maganata da Haneefah game da aure a London na fita, na komo da sake tattaunawa wani abin da ita na ganka ka fita a gidan ranka a bace da alamar kana hawaye, ni kuma bin yaban mamaki ban tsaya na tambaye kaba sannan baka kula da komai dake gaban ka. Bayan nashiga gidan na wuce dakinsu, maganar da naji ke fita abakinta yasa na dakata nake sauraron su. Tabbas halin da tashiga taban tausayi haka kaima. Anan na fahimci kuna tsananin son juna. Bayan na koma masaukina nake nazarin kalamun Haneefah game dakai. Bayan na dawo gida batare da bata lokaci ba na wuce gidansu, ina shiga layinsu na hango yayanta Ahmad nan na tsayar dashi nake tambayar tarihin rayuwar soyayyarta, nan ya sanar da ni komai ba tare da ya boyemin komai ba saboda nazamo family member su. Na tausaya Haneefah sosai sannan shi Yusuf na tausaya mishi domin suna son juna raba su akai. Haneefah tamin abinda bazan manta da itaba, kuma naji dadin zama da ita hakan yasa naji inason kasancewa da ita da kula da ita. Ta taimakeni lokacin da muke bukata, taimakon da duk dukiyata bazatai minba, wasu suna ganin kudi shine jin dadin rayuwa, wasu suna ganin rashin sa ke hanawa . Rashin kudi bai hana jin dadin rayuwa. Abinda ke hana jin dadinta shi ne rashin hakuri da rashin wayewa da rashin sanin ya kamata Allah yasa mu dace. Ya basu labarin yadda suka hadu da Haneefah, ni da matata muna sonta sosai, a kullum muna neman abinda zamu kyautata mata. Yusuf nasan inason Haneefah amma kafini sonta, ka fini bukatar ta sannan ina da tabbacin zaka kula da ita, na bar maka Haneefah ka aure ta. Tunda ya fara magana kan Yusuf sunkuye yake yana jinjina lamarin masoyiyarsa sai da yaji an bar masa Haneefah ya dago kai da sauri yana kallon doctor, ya dubi Abba yace dagaske ya barmin ita? Abba ya dubi dan nasa ya gyada kai sannan kallonsa ya koma kan doctor yace lallai wannan al'amarin akwai ban mamaki ciki, kaganshi akanta yake fama da rashin lafiya gaskiya nagode da wannan sadaukarwa Allah saka da alkhairi. Yusuf ya taso yazo gaban Dr ya tsuguna yana kallonsa, hawaye yaji yana kwaranya a idanunsa a hankali ya tashi ya rungumi doctor yana cewa mun gode doctor, hakika imanin ka cikekkene domin ka so min abinda ka sowa kanka, Allah shi kadai zai saka maka na gode. Doctor ya dago shi yace babu komai dan uwa, Allah baku zaman lafiya ku kasance tare anan duniya da can lahira. Yusuf ya rasa abinda zayyi don farin ciki kawai ya yashi ya fita ya nufi asashen sa. Yana shiga ya kwanta akan gado yana addu'ar Allah mallaka mishi abin kaunar sa, inya runtse ido ita yake kallo. Tashiwa yayi ya dauki sallaya yayi sujjada yana godewa mahaliccin sa. Bayan fitar Yusuf Abba ya dubi doctor yace yanzu bansan da wani ido zan dubi mahaifin yarinyar nan ba, irin wannan abin haka... Doctor yace kada ka damu, za su fahimce ka sannan bazasuyi jayayya da lamarin ubangiji ba, in har ka shirya gobe zan shiga muku gaba wajen neman auren Haneefah. Abba godiya sosai yayiwa doctor sukai sallama. Washe gari misalin karfe uku na rana Abba da abokinsa da yan uwa biyu sukaje neman auren Haneefah. Kamar yadda doctor ya fada dashi akaje neman aure. Abban Haneefah yana zaune yanajin labaru a radio yaji sallama, kasancewar babu kowa gidan sai su Amal da kanshi ya tashi ya fito yaga Dr Mubarak. Da fara'a yace ya shigo daga ciki. Dr ya mase bayani da ba ki yake, Abba yace ya shigo dasu. Abba na kimtsawa sukai sallama suka shigo. Bayan an gaggaisa Abba ya fito yace da Amal yayi baki ta kawo musu abin sha. Cike da kunya abban Yusuf yace ina fatan ka ganeni? Murmushi abban Haneefah yayi yace ai bazan mance ka ba, nagane ka. Cike da kunya yace yauma bara muka so ina fatan sa'a taimaka mana, mu mance da abinda ya faru domin haka Allah ya kaddara amma yanzu komai ya wuce. Dr Mubarak yace Abba kada kayi mamaki da ikon Allah, na barwa Haneefah Yusuf domin zuciyarsu a hade take tun fil azal, muddin sun kasa mantawa da juna tsawon shekaru bana tsammanin zasu mance da juna, in zamu musu adalci mu barsu su kasance da juna. Abba yayi murmushi yace hakika ban rike kai ko Yusuf ba domin na dauka cewa hakan shine mafi alkhairi agaremu amma mesa zaku nemi aure kan aure? Dr Mubarak yace ko daya babu laifinsu anan ni da kaina na yanke wannan hukunci. Abba yace toh shikenan amma indai neman aure kuka zo dagaske yanzu a daura domin bazan jinkirta ba wannan karon. Batare da bata lokaci ba suka amince, Abba ya kira yan uwansa da mijin mama da Ahmad. Bayan an fito daga sallar la'asar a masallaci aka daura aure abokin Abba ya biya sadaki. Sunyi godiya sosai sannan sun nuna farin ciki. Abba yana zuwa gida ya sanar da Umma, taji farin cikin wannan aure. Nan takira aunties nata take sanar da su, sunyi mamaki sosai musamman Nana cewa tayi hakurin su ne ya ja musu auren ba zata amma zamu so ta tare bayan tagama karatu. Da sallama ya shigo ya tarar da family shi sunsa Yusuf agaba suna ta faman hira, shiko ogan rike yake da Ra'ima yana mata wasa amma hankalinsa yafi karkata da zuwan abban nasa. Abba nashigowa da sauri Yusuf ya tashi yana mishi sannu da zuwa har dariya yabawa Abba, cike dajin kunya ya koma ya zauna. Bayan sun zauna Abba ya dubi Momy yace toh Alhamdulillah yanzu aka daura auren Yusuf da Haneefah. Ba Momy ba har Yusuf saida ya dago tsabar mamaki. Momy tace wanne Yusuf? Abba yace Yusuf wadda ke gaban ki da Haneefah da kika ki amincewa da auren su toh yau Allh yakawo lokaci naga kokarin mahaifinta domin ko jayya bayyi da mu ba nan ya kwashe abinda sukai ya sanar da su dan haka sai a soma shiri sannan bana bukatar jin wani magana daban. Kowa idanunsa nakan Yusuf, tsantsar hawayen farin ciki suka hango cikin idon nasa. Rarrafawa yayi ya taho kusa da Abba yace Abba an auramin Haneefah? Abba ya gyada mishi kai. Zama yayi ya rungume kafan Abba yana cewa nagode Abba, Allah saka da alkhairi Allah albarki zuri'armu ya sadamu gidan aljanna baki daya... Abba bansanme zance ba Abba.. Momy ta taho a hankali tace babu abinda ya cancanceka kamar ka godewa mahaliccin ka, kayi hakuri iya hakuri amma gashi hakurin ka ya amfane ka, ina tayaka farin ciki samun mata kamar Haneefah. Haka kowa daya bayan daya yake zuwa tayashi murna amma shi ko murnar ne ta mishi yawa ya kasa cewa komai? Haka Momy da yaranta suka kasance cike da farin ciki a wannan yammaci tare da shirye shiryen yadda amarya zata tare. **** **** Zaune take kan doguwar kujerar da ke falon su, dayar kujerar kuwa Raihana ke zaune tana duba littafi. Kwanakin da sukai a Chicago babu abinda ta tsinana duk tayi abinda ya kaita amma yadda jikinta yayi sanyi batabi abin yadda yake ba. Ko da yake babu ta korance a fannin karatun ta,domin in sun shiga meeting da sauran likitocin asibitin Dr Michael tana koyan abubuwan da dama har wadda suka dara level nata. Haka yakasance a Chicago yawancin abubuwan ta sansu. Ta rasa tunanin me zatai daya, mukewa tayi taje daukar littafinta domin ta soma karatu. Daidai zata zauna taji faduwar gaban da sai da ta sake takardun hannunta suka fadi taje mai ambaton innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun tana mai dafe zuciyarta da hannu. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼58 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Raihana tashiga rarrashinta tace ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru kinji? Allah yana tare dake kinga yanzu jarabawa mukasa agaba dan haka saiki kwantar da hankalin ki mu soma karatu. Haneefah babu abinda take sai hawaye, a haka suka fita zuwa makaranta dan lokaci yayi. **** Aisha cikin nasara ta soma bincike, gidan Nana ta fara zuwa. Bayan sun gaisa ne take cewa sister Yusuf ne. Babu yabo babu fallasa Aisha ta amsheta. Cikin nutsuwa Aisha ta shawo kan Nana sannan tana neman alfarman dawo da Yusuf da Haneefah tunda har yanzu suna son juna. Nana batai mamaki da lamarin ubangiji ba domin ko da zasuyi fishi dasu hakan zai zamo aibu domin abin yariga ya wuce sannan Haneefah bata daina son Yusuf ba. Fatan alkhairi ta musu sannan takira Haneefah. Aisha taji dadin yadda ta samu karbuwa ba tare da bata lokaci ba, nan ta sanar da ita ai diyarta takwaran Haneefah ce. Cike da farin ciki Nana ta karbi Ra'ima tana sa mata albarka. Ta nuna farin cikinta kwarai,sukai exchanging number, zasu tafine Nana tace ki sanar da Momy kada halin da ake ciki domin Haneefah fa ce ta nemi alfarman in yazo ace tayi aure amma ni da kaina zanje in same su ko zuwa gobe. Aisha taji dadin hakan, basu so suka bar gidan ma. Washe gari Nana da kanta taje ta sanar da Umma, Umma tace Alhamdulillah nasan har yanzu suna son tunda mahaifiyarsa ta amince ai shikenan akan ta auri wannan Dr Mubarak domin har wajen Abban ku yazo neman aure. Nana ta zaro ido waje tace lallai dagaske yake, sai dai yayi hakuri domin Haneefah ta samu wadda take so. * _2days later_ Momy zaune take tana tunanin halin da Yusuf yake domin basuyi waya ba, sallamar Aisha ce ya katse mata tunani ta tashi ta tarbesu da fara'a. Bayan ta gaisheta take tambayar Abba na nan tace ya fita amma yakusa zuwa. Shiru sukai sannan Aisha tace ko kinji labarin Yaya? Momy tace tunanin rashin samun sa a waya da nakeyi nake kika shigo, nayi kiran harna gaji, Allah sa lafiya...... Bata karasaba taga Muhammad rataye da jaka Yusuf na biye dashi. Kallo daya Aisha tayiwa fuskarshi ta fahimci babu nasara amma ta dake ta tashi tana mishi sannu da zuwa. Shiru yayi ya kasa magana, ganin haka yasa Momy tace ko dai gajiyane Yusuf? Muhammad yace Momy flight yabi fa, yana sauka a taxi muka taho amma bansan ko direct daga London yake ba? Momy cike da damuwa tace Yusuf ya kayi shiru? Me likitocin suka ce? A sannan ya dago idanunsa da suka kada sukai ja yace komai lafiya, mikewa yayi ya soma tafiya Aisha da taje dauko masa ruwa tace Yaya tsaya kasha ruwa. Bai saurare taba ya fice daga falon yana sharar hawaye. Yana fita yaga motar Abba yana shigowa, sauri yayi ya shige falonsa amma tuni an hango abinda yake boyewa. Momy ta tashi cike da damuwa tace Aisha wai meke damun yaronnan? Nashiga uku in wani matsalan aka kuma hangowa. Muhammad cike da damuwa kamar zayyi kuka yace Momy hawaye yake zubarwa fa? Aisha batasan sanda ta saki kofin hannunta ba ta nufi hanyar falo. Driver bai gama parking ba Abba ya bude motar ya fito yana kiran Yusuf shikuma tuni ya rufe kofar. Sai gasu Momy sun fito sun nufoshi, Abba ya juya yace meya same shi? Me kuka masa? Babu wadda ya bashi amsa suka fara dukar kofar falon Yusuf. Yusuf yana shiga ya rufe falon, sauri yake har ya iso baedroom nashi. Zama yayi kasan tiles yana hawaye, yarasa mezayyi yaji sassauci dukkanin tunaninsa sun tsaya, Haneefah taki sauraronsa, lokacin mallakanta yayi amma bayida wannan damar, wazai SO ta maye mashi gurbin ta? Jin numfashinsa sama- sama yasa yayi lamo ya kwanta yana fitar da numfashi a hankali domin jin nawin da kirjinsa yayi. Babu irin dukan kofar da basuyi ba amma shi ko ji bayayi. Abba ne yayi sauri yaje ya dauki key yazo ya bude, a wannan hali suka zo suka same shi. Muhammad ne da Abba suka taimaka shi suka kwantar dashi akan gado. Momy ne ta fashe da kuka tace nashiga uku Yusuf me nake gani dan Allah kada ka mutu ka tashi, Aisha da tuni kuka kubce mata ta dauki wayarsa ta kira Dr Abdullahi tace pls kazo, Yusuf babu lafiya it's urgent ka taimaka. Dr dake tuki yace babu damuwa gani nan zuwa ya katse wayar, ya juya ya kalli Nana yace abokina babu lafiya bari mu biya mugansa. Tace babu matsala. Yusuf ya kawar da kanshi domin baya son ganin halin da suka shiga, magana yake son yi amma yadda yaji zuciyarsa na masa kwata-kwata ya kasa. Hannun Aisha ya riko yana girgiza mata kai yace HANEEFAH Aisha tace Yaya dan Allah ka kwantar da hankalin ka, zaka aure ta, kada ka shigarda kanka cikin wani hali, hannu tasa tana goge masa hawaye. Momy tace nidai ban kyauta maka arayuwaba, na rabaka da wadda ta tace ta kasance matar auren ka wadda tasan darajar iyayen ka, ku nemomin ita na nemi afuwarta. Abba ya daka musu tsawa yace kun isheni da surutu, kin riga kin aikata abinda kike ganin shine daidai, dubi yadda yaronnan ya koma asanadinki! Ko yarinyar nan batai aure ba inna koma neman auren ta me iyayenta zasu dauke mu? Yaro kamar Yusuf ace yau shine ya fito da damuwarsa karara? Dan kawai yana miki biyayya? Duk sunyi jugum suna hawaye, ran Abba yayi matukar baci yana ta surutu saida wayar Yusuf ya soma ringing tukun yayi shiru. Aisha ta amsa wayar ganin Dr Abdullahi ne. Muhammad ne yashigo dasu, Nana ta zauna a falo tace zata jira shi anan shi kuma suka wuce bedroom inda Yusuf ke kwance wadda ya soma fita hayyacinsa. ~Bintu Ramadan~ *Dr Haneefah* 👩🏼61 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Da sauri Raihana ta taho tana mata sannu tare da tambayarta ko lafiya? Tace babu komai ta zauna. Kasa samun nutsuwa tayi ta soma ambaton LAHAULA WALAQUWWATA ILLA BILLAHIL AZEEN. Ganin hankalinta ya karkata gida yasa ta mika hannu ta dauki wayarta ta soma kiran Umma, kusan sau biyar takira no answer, nan ta shiga kiran Ahmad shima baya daga wayar. Haneefah ta tsure gani take akwai abinda ke faruwa. Tana kiran Abba bugu biyu ya dauka, ko amsa sallama batayi ba tace Abba lafiya inata kiran gida basa daga waya gashi sai faduwar gaba nake ji? Abba yace babu komai sai alkhairi Haneefah amma meya tadaki da tsakar darennan? Ajiyar zuciya tayi tace Alhamdulillah , Abba karatu nakeyi shiyasa na taso kasan mun kusa fara exams. Abba yace Allah bada sa'a ya rabaki da makarantar nan lafiya. Ta cike da jin dadi ta amsa sannan tace Abba ka gaidamin dasu Umma. Zataji amma inason sanar dake wani abu, ki daina fargaban komai ki kwantar da hankalinki domin yanzu ke matar aurece, dazu na daura auren ki, saboda haka saiki aje hankali kin zama matar aure. Murya na rawa tace Abba aure akamin? Yace eh, na aikata hakan ne badan komai ba sai saboda kowa ya huta sannan in tabbatar musu cewa bana rike mutum azuciya ma'ana kada su zaci abinda sukamin yananan arai na domin hakan bai kamacemu yan adam ba, duk kankantar laifi bai kamata murikeshi a ran muba domin Allah S.W.A shi mai yafiyane sannan yana bamu damar kubcewa daga aikata wani abin hani Saboda haka mu guji rike abu arai da son ramuwa ga abinda aka mana, shin duniyar ma nawa take? Yau mune wata rana bamu ba, mu rika saurin yafiya sannan kada inji in gani kince komai ga mahaifin yaronnan saboda itace sanadi, tunda lokacin yayi komai ya wuce kinji Haneefah. A sanyaye tace Abba naji, kuma inshaa Allah zan kasance mai kawar dakai ga dukkanin wani laifi da akamin. Abba yace Allah miki albarka sukai sallama ya katse wayar. Tana dauke wayar daga kunnenta kiran Umma ya shigo, tana dagawa ta fashe da kuka tana cewa Momy shikenan dan anje gaisuwa sai a dauramin aure... Umma tayi saurin katseta da cewa ai da amincewarki kika turo shi hakan na nufin ur ready to get marriage, komai ma menene anyi auren sai fatan samun zaman lafiya sannan ina miki jan kunne da kada ki kuskura inji kincewa mahaifiyarsa komai domin babu komai ya wuce. Cikin daurewar kai take tambayar Umma ni babu abinda mahaifiyarsa tamin hasalima ban taba ganinta ba, nidai munyi dashi kada lokacin ya tsawaita shine harda daurin aure Umma tace nasan kina son Yusuf shima yana son ki, inaga abinda mahaifinki ya aikata yayi daidai. Haneefah tace Yusuf kuma? Umma tace eh Dr Mubarak yayiwa mahaifan Yusuf jagora aka daura auren dazu, kada ki tada hankalinki kowa na farin ciki da wannan auren, ta wannan hanyar Allah ya kaddara daurin auren ki kada ki damu kinji? Haneefah dakyar ta bude baki tace kina nufin da Yusuf aka dauramin aure Umma? Tace eh. Katse wayar Haneefah tayi ta sulale ta zauna kasa tana kuka tana dariya. Raihana dake kallonta tace wai meke faruwa ne? Kallon Raihana tayi tace an dauramin aure da Yusuf dazu Raihana ta dago hannayenta sama tana Alhamdulillah, Allah mun gode maka Haneefah kinga ni ko? Yarda da kaddara, hakuri akan abinda aka rasa akan lokaci, yawaita addu'a tare da yarda da addu'a gashi yau kin wayi gari kin samu abinda kike so. Haneefah ta tashi ta shiga daki ta dauro alwala ta zauna kan sallaya tana murmushi tace Allah kaine abin godiya, duk wadda yaji tsoron ka ya so annabinmu ya rabauta daga kuncin duniya da lahira, kamin baiwar da dukkanin dan Adam ke bukata, sannan yau nawayi gari nakasance matar YUSUF, Allah na tuba ka yafemin. Fashewa tayi da kuka tana cewa ya Allah nagode maka, duk wani musulmi dake tattare da kuncin rayuwa ka azurtashi da zuciya mai tsananin hakuri.... Haka ta kasance tana zantuka har aka soma kirayen sallar asuba. Bayan ta idar ta dauki waya ta nemo layin Dr Mubarak domin tasan dare bayyi sosai ba a Nigeria. Bugu daya ya dauka suka gaisa, kasa cewa komai tayi kawai ta fashe da kuka. Murmushi Dr Mubarak yayi yace shikenan Haneefah menene abin kuka? Godewa Allah zakiyi kuma kada ki damu dani domin komai ya wuce agurina, yadda na fahimci kuna son juna inna shiga tsakanin ku ban kyauta muku ba. Cikin kuka tace amma ai dakai akafa.... katseta yayi yace babu komai Haneefah na fahimce ki, Yusuf yafi cancanta da ke kema kin cancanci kasancewa dashi, Allah baku zaman lafiya kedai pls ki karashi karatun ki kada ki damu. Katse wayar yayi batare da tace komai ba, jingina yayi jikin seat na motarsa ya lumshe ido, tabbas yana jin son kasancewa da Haneefah amma yana son ganinta cikin farin ciki. Ganin yadda ya faranta mata sai yaji sanyi a ranshi tamkar an mishi bushara da aljanna *_( a kula aduk lokacin da mutum ya aikata aikin alkhairi kuma saboda Allah tabbas sai yaji ni'imtaccen al'amari ya ziyarci zuciyarsa)_*. Haneefah ta lumshe ido tana matukar jin farin ciki a zuciyarta, ko bacci ta kasa komawa tsabar murna. **** Kwance yake kan gado ya kurawa hoton ta dake laptop nashi ido. Wai yau shine mijin Haneefah? Allah mai yadda ya so a laokacin da yaga same. Abin kamar mafarki yaji. Tuno da irin soyayyarsu da burin kasancewa tare da sukeyi aka rabasu amma gashi yau lokaci daya sun mallaki juna. Babu abinda yake bukata kamar yaji muryarta kuma yayi nesa da ita. Tambayar kanshi yake shin ya takeji domin yasan maganar yaje kunnuwarta. Lumshe ido yayi yana hangota tana aiki. Ganin an kusa kiran sallah ya tashi ya shiga bandaki ya watsa ruwa tare da yin alwala. Shigan alfarma yayi ya dauki makullin mota ya fice. Bayan ya idar da sallah ya nufi gidan abokinsa Dr Abdullahi. Parking yayi bakin gate ya ciro wayarsa yakira sa yace yana kofar gida, Dr Abdullahi yace kashigo daga ciki. A falo aka masa masauki. Nana ta fito rike da waya a kunne tana dariya. Ganin Yusuf yasa ta dada fara'a tace ashe kanin nawa yazo dama nayi tsammanin zuwan ka. Yusuf ya sunkuyar da kai yana murmushi suka gaisa. Nana tace yanzu ake sanar da ni kai amma naji dadi Allah baku zaman lafiya. Dr Abdullahi yace ban gane Allah basu zaman lafiya ba. Tace yanzu aka kirani a gida ake sanar da ni an daura auren Haneefah da Yusuf. Cike da mamaki yace Allah sarki amma nayi murna aboki Allah baku zaman lafiya ya amsa da ameen. Tun kafin yayi magana Nana tace nasan lambarta kazo nema gashi nan. Yusuf duk kunya ta rufeshi, shi dai a dole kunyar Nana yake. Abdullahi abin ma dariya ya bashi yace kiyi hakuri girma ya hau kanki ki shiga daga ciki nizan bashi lambarta. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼62 Dedicated to Batul Mamman Mrs 💖 Nana tana dariya ta mike tashiga ciki. Tana shiga Yusuf ya tashi da sauri yazo kusa da abokin nashi ya fizge wayar hannun as yana cewa da wani suna kayi saving lambarta? Abdullahi dake dariya sosai yace Sis Haneefah. Gudun kada yayi mistake ya tura ta WhatsApp yana cewa nagode nizan wuce. Dr Abdullahi ya tsagaita da dariyar da yakeyi yace aa tsaya mu tattauna kasan yanzu mun zama so close, yanzu dai kabarta ta karasa karatun da kafin ku tare Wani kallo ya watsawa Dr yace shekaru nawa muna jiran wannan rana? In ma taro ko occasions kuke son yi mun yafe, nasan dangi sun shaida aure ,saiku jira in muka haihu saikuyi komai. Dr Abdullahi ya kuma kwashewa da dariya yace kada kayi haka, itama bazata ji dadi ba kabari sai tadawo Nigeria saiku tare aganina hakan zayyi amma yanzu da wanne zata ji? Ya qarasa maganar da zolaya. Shidai Yusuf shiru yayi yana jiran isowar contact. Yana gani ya mike yana cewa nizan wuce mayyuwa bazamu hadu ba domin cikin satinnan zan wuce London. Abdullahi yana ta mishi tsiya akan kada ya soma amma ko kula abokin nashi bayyi ba. Bayan ya koma gida ya nufi falon Abba ya tarar Momy na can. Murmushin jin dadi tayi da taga dan nata cikin walwala. Bayan ya gaida su sai kuma yayi shiru yana sosa keya. Abba abu kadan ya fashe da dariya ya kawar da idanun nasa zuwa kallon tv. Momy da ta gano shi tsaf tace yakamata ka soma shirin tafiya can London ko zaka jirata tazo ne? Karaf ya sako baki yace dama inason fara shiri gobene, shine nace bari inzo in sanar da ku. Momy tace ai hakan yayi kyau sai zuwa gobe ka shirya zuwa Abuja. Yusuf ya kalli Abba dake kallon tv yace Abba gobe nake son wucewa. Abba yace Allah kiyaye hanya amma inason tarewarta yakasance inta kammala karatun ta, tunda kadan ya rage saika bari ta kammala amma zaka iya zuwa ku gaisa. Toh shikenan ba komai Abba. Zai tashi Abba yace a gidan da kake zaune yanzu zaku zauna ko akwai wani plan naka? Aa Abba a sabon gidana. Abba yace babu damuwa, zan karasa maka sauran ginin sauran shirin kuma mahaifiyarka da sauran yan uwanka yazu karasa cikin nutsuwa tunda har yanzu akwai sauran lokaci. Godiya Yusuf yayi ya tashi ya nufi sashin sa cikin sauri. Momy tabisa da kallon tana binsa da addu'a. Ya gama shirin kwanciyarsa tsaf ya hau kan gado ya kwanta rike da pillow ya kurawa lambar ido. Shiga WhatsApp yayi ya duba lambarta yaga tanayi. Dp ta ya kurawa ido, itada Raihana, Kevin sai Rohan. Sunyi matukar kyau musamman Haneefah domin gani yake tafi mishi kowa kyau. Wayarta na ringing harya katse bata daga ba domin bacci ya soma daukarta. Ganin an sake kira yasa ta dauki wayar da nufin ta sa a silent taga lambar Nigeria ne. Ganin batasan lambar ba yasa ta daga tare da yin shiru. Shima shiru yayi. A hankali ta furta wanene? Shiru yayi ya lumshe ido jin muryarta. Ta sake maimaita tambayar tare da cewa banaji fa.. shima a hankali ya furta DEARIE Idanuwanta ta bude baki daya jin muryar shi, ta nemi bacci ta rasa amma ta dake ta qara tambayar wanene? Murmushi yayi yace in hukunta ni zakiyi kada ki hukunta ni ta wannan fannin bazan iya jurewa ba. Wani irin farin ciki ke ratsa illahirin gabobin jikinta, kasa magana tayi ta lumshe ido tana sauraronsa. Jin yayi shiru yasa ta fashe da kuka Hankalinsa ya soma tashiwa yana tambayarta meya faru? Lallashin duniyar nan yayi amma taki shiru, ganin hakan yasa ya soma bata hakuri amma nan ma taki shiru, da kanta ta katse wayar ta kashe baki daya tana murmushin jin dadi. Shima hankalinsa a tashe tunaninsa baki daya ya karkata gari ya waye ya soma shirin tafiya amma wannan daren bai iya runtsawa ba farin ciki sosai yake tare da godewa Allah. Da safe dakyar ya kai karfe tara ya nufi gidan su Haneefah. A waje yayi parking yana kokarin fitowa yaga Ahmad da yaya jibril. Sallama ya fito yayi musu suka amsa. Bayan sun gaisa ne Ahmad ya mishi iso zuwa falon Abba shi ko jibril ya nufi gida sanar da Abba yayi bako domin gidansu ya kwana. Kasancewar su Amal sun fita yasa Ahmad da kanshi ya kawo masa ruwa tare da yiwa Umma magana dake shirin fita aiki. Har kasa ya sauko gaida Umma, Umma da fara'arta ta amsa tare da tambayar mutanen gida? Duk suna lafiya, ya qara da cewa Umma ina nemawa mahaifiyata afuwa.... bai karasa ba ta katseshi da cewa babu koma ya wuce, ai komai lokacine sai yanzu Allah ya nufa babu komai Allah hada zuciyarku ya baku zaman lafiya. Cike da murna ya amsa da ameen. Sukai sallama ta fita. Bai jima ba Abba ya shigo. Bayan sun gaisa ya dauko da maganar afuwa Abba ya masa nuni da komai ya wuce fatan zaman lafiya ya musu tare da yi masa nasihar akan rayuwa baki daya. Yusuf yaji dadin lafuzzan mahaifan Haneefah, hakan ya qara masa qimar Haneefah a idanunsa. Ya sanar da Abba yana son tafiya gurin Haneefah. Fatan tafiya lafiya da zuwa lafiya yayi mishi. Agurguje yaje gida ya tattara abin bukatarsa ya nufi Abuja daukan excuse gurin aikin shi. **** **** Zaune take tayi shiru ta zubawa takar dun gabanta ido, duk da irin karatun dake gabanta hakan bai hanata tunanin sa ba. Meya hanasa kiranta? Sau daya ta gwada kiransa amma bai daga wayarba. Raihana cikin tsokana tace an zama ma'aurata amma ana yawan tunani. Bata ce da ita komai ba ta dauki wayarta tayi dialing number shi amma bata samun sa. Ji tayi kamar ta jefar da wayar ta tarwa tse. Suna cikin haka wata balarabiya ta nufo su ta sanar dasu lectures suke dashi yanzu. Bayan ya sauka a airport batare da bata lokaci ba ya nema taxi domin yana da address dinta. Da murmushi ya nufo kofar ta ya danna qararrawa amma yaji shiru, ya dauki tsawon minti goma yana haka amma ya tabbatar babu kowa domin ba'a bude kofar ba. Nesa da gidan kadan yayi yanemi guri ya zauna yana kallon mutanen da suke zarya. Kusan karfe tara na dare babu alamarsu gashi gajiya da yunwa ta addabeshi, ruwa ya ciro cikin kayansa ya sha. Karfe tara da minti arba'in suka yi parking. Sunzo daidai zasu shiga Raihana ta ja ta tsaya ta hangosa yana bacci kasancewar gurin haskene tamkar rana. Haneefah ma ta tsaya tana kallon inda Raihana ke kallo, da sauri ta mika mata takardun hannunta ta nufo shi da sauri. A zaune yake ya lumshe ido tamkar mai bacci, tausayinsa taji ganin wahala tattare dashi a tunaninsa bacci ya soma. Tsugunowa tayi tana tunanin yadda zata tashi daga bacci, jin motsi yasa ya bude idanunsa a hankali yana kallonta. Da sauri ta mike zata juya shima ya mike da sauri ya fara binta amma yakasa cewa komai. Juyowa tayi tana kallonsa taga duk ya canza, hannayensa ta gano empty dan haka tace dashi ka shiga ina zuwa. Kasa motsawa yayi yana kallonta har tazo ta wuce ta nufi inda jakarsa take ta dauko ta nufi gida shima yana biye da ita. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼62 Dedicated to Batul Mamman Mrs 💖 Nana tana dariya ta mike tashiga ciki. Tana shiga Yusuf ya tashi da sauri yazo kusa da abokin nashi ya fizge wayar hannun as yana cewa da wani suna kayi saving lambarta? Abdullahi dake dariya sosai yace Sis Haneefah. Gudun kada yayi mistake ya tura ta WhatsApp yana cewa nagode nizan wuce. Dr Abdullahi ya tsagaita da dariyar da yakeyi yace aa tsaya mu tattauna kasan yanzu mun zama so close, yanzu dai kabarta ta karasa karatun da kafin ku tare Wani kallo ya watsawa Dr yace shekaru nawa muna jiran wannan rana? In ma taro ko occasions kuke son yi mun yafe, nasan dangi sun shaida aure ,saiku jira in muka haihu saikuyi komai. Dr Abdullahi ya kuma kwashewa da dariya yace kada kayi haka, itama bazata ji dadi ba kabari sai tadawo Nigeria saiku tare aganina hakan zayyi amma yanzu da wanne zata ji? Ya qarasa maganar da zolaya. Shidai Yusuf shiru yayi yana jiran isowar contact. Yana gani ya mike yana cewa nizan wuce mayyuwa bazamu hadu ba domin cikin satinnan zan wuce London. Abdullahi yana ta mishi tsiya akan kada ya soma amma ko kula abokin nashi bayyi ba. Bayan ya koma gida ya nufi falon Abba ya tarar Momy na can. Murmushin jin dadi tayi da taga dan nata cikin walwala. Bayan ya gaida su sai kuma yayi shiru yana sosa keya. Abba abu kadan ya fashe da dariya ya kawar da idanun nasa zuwa kallon tv. Momy da ta gano shi tsaf tace yakamata ka soma shirin tafiya can London ko zaka jirata tazo ne? Karaf ya sako baki yace dama inason fara shiri gobene, shine nace bari inzo in sanar da ku. Momy tace ai hakan yayi kyau sai zuwa gobe ka shirya zuwa Abuja. Yusuf ya kalli Abba dake kallon tv yace Abba gobe nake son wucewa. Abba yace Allah kiyaye hanya amma inason tarewarta yakasance inta kammala karatun ta, tunda kadan ya rage saika bari ta kammala amma zaka iya zuwa ku gaisa. Toh shikenan ba komai Abba. Zai tashi Abba yace a gidan da kake zaune yanzu zaku zauna ko akwai wani plan naka? Aa Abba a sabon gidana. Abba yace babu damuwa, zan karasa maka sauran ginin sauran shirin kuma mahaifiyarka da sauran yan uwanka yazu karasa cikin nutsuwa tunda har yanzu akwai sauran lokaci. Godiya Yusuf yayi ya tashi ya nufi sashin sa cikin sauri. Momy tabisa da kallon tana binsa da addu'a. Ya gama shirin kwanciyarsa tsaf ya hau kan gado ya kwanta rike da pillow ya kurawa lambar ido. Shiga WhatsApp yayi ya duba lambarta yaga tanayi. Dp ta ya kurawa ido, itada Raihana, Kevin sai Rohan. Sunyi matukar kyau musamman Haneefah domin gani yake tafi mishi kowa kyau. Wayarta na ringing harya katse bata daga ba domin bacci ya soma daukarta. Ganin an sake kira yasa ta dauki wayar da nufin ta sa a silent taga lambar Nigeria ne. Ganin batasan lambar ba yasa ta daga tare da yin shiru. Shima shiru yayi. A hankali ta furta wanene? Shiru yayi ya lumshe ido jin muryarta. Ta sake maimaita tambayar tare da cewa banaji fa.. shima a hankali ya furta DEARIE Idanuwanta ta bude baki daya jin muryar shi, ta nemi bacci ta rasa amma ta dake ta qara tambayar wanene? Murmushi yayi yace in hukunta ni zakiyi kada ki hukunta ni ta wannan fannin bazan iya jurewa ba. Wani irin farin ciki ke ratsa illahirin gabobin jikinta, kasa magana tayi ta lumshe ido tana sauraronsa. Jin yayi shiru yasa ta fashe da kuka Hankalinsa ya soma tashiwa yana tambayarta meya faru? Lallashin duniyar nan yayi amma taki shiru, ganin hakan yasa ya soma bata hakuri amma nan ma taki shiru, da kanta ta katse wayar ta kashe baki daya tana murmushin jin dadi. Shima hankalinsa a tashe tunaninsa baki daya ya karkata gari ya waye ya soma shirin tafiya amma wannan daren bai iya runtsawa ba farin ciki sosai yake tare da godewa Allah. Da safe dakyar ya kai karfe tara ya nufi gidan su Haneefah. A waje yayi parking yana kokarin fitowa yaga Ahmad da yaya jibril. Sallama ya fito yayi musu suka amsa. Bayan sun gaisa ne Ahmad ya mishi iso zuwa falon Abba shi ko jibril ya nufi gida sanar da Abba yayi bako domin gidansu ya kwana. Kasancewar su Amal sun fita yasa Ahmad da kanshi ya kawo masa ruwa tare da yiwa Umma magana dake shirin fita aiki. Har kasa ya sauko gaida Umma, Umma da fara'arta ta amsa tare da tambayar mutanen gida? Duk suna lafiya, ya qara da cewa Umma ina nemawa mahaifiyata afuwa.... bai karasa ba ta katseshi da cewa babu koma ya wuce, ai komai lokacine sai yanzu Allah ya nufa babu komai Allah hada zuciyarku ya baku zaman lafiya. Cike da murna ya amsa da ameen. Sukai sallama ta fita. Bai jima ba Abba ya shigo. Bayan sun gaisa ya dauko da maganar afuwa Abba ya masa nuni da komai ya wuce fatan zaman lafiya ya musu tare da yi masa nasihar akan rayuwa baki daya. Yusuf yaji dadin lafuzzan mahaifan Haneefah, hakan ya qara masa qimar Haneefah a idanunsa. Ya sanar da Abba yana son tafiya gurin Haneefah. Fatan tafiya lafiya da zuwa lafiya yayi mishi. Agurguje yaje gida ya tattara abin bukatarsa ya nufi Abuja daukan excuse gurin aikin shi. **** **** Zaune take tayi shiru ta zubawa takar dun gabanta ido, duk da irin karatun dake gabanta hakan bai hanata tunanin sa ba. Meya hanasa kiranta? Sau daya ta gwada kiransa amma bai daga wayarba. Raihana cikin tsokana tace an zama ma'aurata amma ana yawan tunani. Bata ce da ita komai ba ta dauki wayarta tayi dialing number shi amma bata samun sa. Ji tayi kamar ta jefar da wayar ta tarwa tse. Suna cikin haka wata balarabiya ta nufo su ta sanar dasu lectures suke dashi yanzu. Bayan ya sauka a airport batare da bata lokaci ba ya nema taxi domin yana da address dinta. Da murmushi ya nufo kofar ta ya danna qararrawa amma yaji shiru, ya dauki tsawon minti goma yana haka amma ya tabbatar babu kowa domin ba'a bude kofar ba. Nesa da gidan kadan yayi yanemi guri ya zauna yana kallon mutanen da suke zarya. Kusan karfe tara na dare babu alamarsu gashi gajiya da yunwa ta addabeshi, ruwa ya ciro cikin kayansa ya sha. Karfe tara da minti arba'in suka yi parking. Sunzo daidai zasu shiga Raihana ta ja ta tsaya ta hangosa yana bacci kasancewar gurin haskene tamkar rana. Haneefah ma ta tsaya tana kallon inda Raihana ke kallo, da sauri ta mika mata takardun hannunta ta nufo shi da sauri. A zaune yake ya lumshe ido tamkar mai bacci, tausayinsa taji ganin wahala tattare dashi a tunaninsa bacci ya soma. Tsugunowa tayi tana tunanin yadda zata tashi daga bacci, jin motsi yasa ya bude idanunsa a hankali yana kallonta. Da sauri ta mike zata juya shima ya mike da sauri ya fara binta amma yakasa cewa komai. Juyowa tayi tana kallonsa taga duk ya canza, hannayensa ta gano empty dan haka tace dashi ka shiga ina zuwa. Kasa motsawa yayi yana kallonta har tazo ta wuce ta nufi inda jakarsa take ta dauko ta nufi gida shima yana biye da ita. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼63 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Basu tarar da Raihana a falo ba dan haka ta ajiye jakarsa ta nufi dakin da zata sauke shi ta shiga gyarawa. Bayan dakin yayi fes ta nufo falo amma ta kasa karasawa. Ta rasa me zata fara ce masa dan haka ta tsaya nesa da mashigan falo. Kusan mintuna goma tana tsaye taga Raihana ta fito. Ajiyar zuciya tayi tace pls inkin je falo ki mishi iso zuwa dakin shi Tsaye Raihana tayi tana kallonta tace nifa na dauka kuna daki, nemo ruwa na fito ashe ko masauki baki kai shiba kuma kinsan nisan Nigeria a London akwai gajiya.. Haneefah ta wuce ta shiga daki batare da tace mata komai ba a zuciyarta tana cewa ni nasan gajiyar da ya dauko amma bansan me zance dashi bane. Raihana tashigo falon da fara'arta tana cewa irin wannan zuwan bazata haka? Shima murmushi yayi baice komai ba yana ware idanu ko zai ganta. Tsaf Raihana ta gano shi ta tashi tace yazo masauki. Yana shiga ya lumshe ido yace ina kike? Shiga toilet yayi. Tunda tashiga daki ta kasa zaune sai zarya take. Tana jin budewar kofar Raihana tazo da sauri tace kin kaishi? Raihana har dariya abin yabata sannan ta amsa da eh, yana jiranki, sai..... Tun kafin ta karasa ta fita da sauri ta nufi kitchen. Cikin mintina kalilan ta dafa masa abinda zaisa abaki, ta hado masa da fruits ta aje kan try ta nufi dakin da yake. Duk da gabanta ba karamin faduwa yake ba amma yazama dole ta je inda yake domin bazata barshi da yunwa ba. Sallama tayi taji shiru, ta dauki kusan minti biyar tana sallama amma ba'a amsa ba. A hankali ta bude kofar ta shigo da sallama amma bata ga kowa ba, da sauri ta ajiye abinda ke hannunta ta fice a dakin. Tunda yaji sallamarta yake sauri amma kafin ya fito babu ta fice a dakin. Da sauri ya nufi inda try yake ya bude su, murmushi yayi ganin abinda ta kawo masa yace delicious!! Tunani tare da farin ciki ke ratsashi wai yau shine zaici abincin Haneefah a matsayin matarsa? Murmushi ya kuma yi ya tashi yayi sallah sannan ya zauna cin abinci. Rabonshi da yaci abinci ya koshi har ya mance amma yau har kari yake nema. Bayan ya kammala komai ya zauna tare da zubawa ko fa ido ko zata shigo amma shiru. Tam yasan bazata zo ba dan haka ya tashi ya lallaba ya kwanta domin bacci da yake ji. Itama haka abin yakasance agun nata, farin sosai tayi da ganinsa amma bazata iya komawa gurinsa ba domin tambayar kanta take me zata ce dashi? Ga murmushin jin dadi da baya yankewa a fuskarta. Raihana tace ni kada ki dame ni da wannan murmushi in zaki tashi ki tafi to, in ko so kike in bar muku gidan ne zan iya komawa hostel Da sauri Haneefah tace na daina yi hakuri, muyi karatun mu. Cike da farin ciki na musamman tayi karatun ta. Washe gari da safe ta tashi tayi breakfast sannan ta shirya domin fitan safe zasuyi. Bayan sun shirya ta dauki karamar ta karda tayi rubutu ta ajiye daidai kofar Yusuf tana murmushi suka fice. Tunda yaji tashiwar mota yadan suna suka fice, bai kawo komai aransa ba yaci gaba da kwanciyarsa sai kusan karfe goma ya tashi. Bayan yayi wanka ya shirya ya bude kofa ya fito domin zuwa kitchen. Yana bude kofa yaga karamar takarda an ajiye biro akai kada iska ya dauke shi. Saka hannu yayi ya dauka domin bazai wuce sakon sa bane yaga an rubutu: _Ina fata ka tashi lafiya? Ya gajiyar hanya? Nasan kana tattare da gajiya shiyasa banyi yunkurin bude maka kofa ba domin nasan kana bacci. Na fita makaranta breakfast naka na falo, a huta gajiya_ Murmushi yayi tare da kissing paper yace Allah dawo dake lafiya. Ya nufi falo ya tarar da lafiyayyun breaskfast ya soma ci. Bayan ya kammala ya tattara kayan ya tashi ya nufi kitchen. Zaga gidan yafara yana nazarin yadda akai ginin, gidan ya mishi kyau gashi ba babbane sosai. Bayan ya gama yazo ya kunna tv ya soma kallon news. Zaune suke suna karatu dayan uwanta amma hankalinta ya soma tafiya gida, ganin karfe daya yakamata ace sunje ta dafa masa lunch. Tun kafin tayi magana Raihana tace mu zamu wuce gida sai zuwa gobe. Daya daga cikinsu tace haba Raihana da wuri haka? Raihana tace daliline yasa, sukai sallama suka tashi. Bayan sun iso gida sukai parking Raihana ce agaba, da sallama ta shiga falo. Ganin Yusuf zaune yasa ta nufi inda yake da fara'arta tana gaisheshi. Shima gaisheta yayi yana tambayarta ya karatu? Tace Alhamdulillah. Yace Allah taimaka ya amsa da ameen. Suna dan taba hira Haneefah ta shigo da sallama, ta kasa kallon inda suke zaune tace wani kalma tayi wucewarta. Raihana baki bude take kallonta harta shige Yusuf yace inkin shiga ciki ki turomin ita. Tunda ta shiga taji kunya ya lullubeta, mesa nayi haka? Tana cikin tunani Raihana tashigo cike da mamaki tace Haneefah lafiyarki kuwa? Nifa nakasa gane kanki, keda kanki kike wahalar da kanki? Mutum yazo tun daga garin ku mai nisannan amma kinkasa ce masa ya yadawo? Koma menene kije yana kiran ki. Jin yana kiranta yasa taji babu dadi, maimakon ita taje ba sai ya nemeta ba. Jiki babu kwari ta nufi banda ki ta watsa ruwa ta fito ta shirya cikin mintuna kalilan ta fice ta nufi falo. Wayam ta gani bayanan, hakan na nufin yana dakin shi. Kamar zatayi kuka ta nufi dakin shi. Knocking daya tayi taga an bude mata kofa, da sallama ta shiga amma taji shiru. A hankali ta shigo dakin tare da maimaita sallama. Daga bayanta taji an amsa tare da rufe kofa. Da sauri ta juya tana kallonsa. Shima kallonta yake cike da tsananin so. Dukkaninsu sun kasa cewa junansu komai, a hankali ya tako yazo dab da ita, ganin haka yasa ta soma ja da baya. Tsayawa yayi yana kallonta yakacewa komai. Sulalewa tayi ta zauna kasa tana furta ina yini Baice da ita komai ba, ganin yayi shiru a hankali ta dago idanunta suka hada ido. Abinda taganine yasa gabanta ya fadi tare da mikewa. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFA* 👩🏼64 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Hawayene cike a idanunsa wadda yake kokarin zubowa abinda bata taba gani ba. Bakinta na rawa tace meyafaru? Bani bace ko?? Da sauri ya matso kusa da ita tare da rike hannayenta yace na rokeki ki daina fushinnan, zan iya jure komai amma banda fishin ki, bani da laifi cikin al'amarin nan sannan in kika duba mahaifiyata ce bani da zabi da ya wuce inbi umarnin ta, amma badan raina ya so ba, ina sonki kina so na kada wannan abin yasa mu wahalar da kawunan mu bakisan yadda nake jiba lokacin da na rasaki amma yanzu Allah ya qara hadamu plss ki huce.... Kasa karasa maganan yayi ya lumshe ido sai ga hawayen dake makale ya zubo. Haneefah tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskarta. Itama fashewa da kuka tayi zata gudu ta fita ya rikota. Tsayawa tayi tana kokarin fizge hannunta domin kukan yaci karfinta amma yaki sakinta dan kanta ta tsaya hakan taci gaba da kuka. A hankali ya janyota jikinsa ya rungumeta yana cewa shikenan tunda nine bakison gani nizan koma inda na fito. Cikin kuka tace a'a Yusuf yace toh me abin kuka? A hankali tace farin cikine yamin yawa amma ni ina sonka, ban taba kawo araina ina da sauran rayuwa tare dakai ba, yau gashi lokaci daya mun kasance tares. Alhamdulillah ya furta a hankali, nima ina sonki sosai Haneefah mukasance masu godewa Allah... kokarin kwace kanta take ya saketa yana kallonta tace lunch zanje in girka maka. Murmushi yayi yace akoshe nake domin jinki atare da ni... da sauri zata fita ya rikota a tsoroce ta tsaya domin da gaskenta tsoro take ji. Zagayowa yayi zuwa gabanta, ganin yadda ta sauke kai ya saketa yace jeki... tana fita yabi bayanta da murmushin jin dadi yana kara godewa Allah cikin zuciyarsa da ya azurtasa da abin kaunar sa wato Haneefah a matsayin mata. Kamar jiya abinci mai kyau ta dafa masa amma tsoron kaiwa take, ta dauki ita da Raihana ta wuce dakin su. Bayan takai tazo ta dauki nashi ta nufi dakin shi tayi knocking ya amsa ta shigo a hankali. Zata juya ta fita yace ina zaki? Ganin ta tsaya bata ce komai ba ya ta so da kansa yazo yace bazaki zauna muci tare ba? Nan ma tayi shiru ganin yana kokarin riketa ne tace a'a naka ne ni naci nawa. Ganinta a tsoroce yace toh zauna ki tayani hira. Rashin son jayayya yasa ta koma inda ta ajiye abinci ta fara zuba masa. Duk wani motsin ta akan idonshi, ji yake tamkar ya maido ta ciki amma ya lura kamar a tsorace take. Bayan ta gama ta samu guri ta zauna ta sunkuyar dakai domin jikinta ya bata idanunsa na kanta. Ya soma cikin abinci, yace yaushe exams naku? Next month ta bashi amsa. Farin ciki ya bayyana a fuskar shi yace ashe kun kusa. Tace eh amma zamuyi sati uku that's mean sai upper month zan gama. Yace good. Ya zakiyi da aikin ki? Bazanci gaba da aiki dasu ba, zan san yadda zamuyi mu rabu lafiya. Dauko wayarsa yayi ya nuna mata hoton kyakykyawar yarinya yace wannan itace diyar Aisha sunanta Ra'ima. Haneefah ta karba tana murmushi tace Allah raya ta ya amsa da ameen. Garin mika masa wayar ya tsanta ya taba wayar nan ya canza zuwa hoton sa rike da jariri. Nan da nan hawaye ya ciko a idanunta tace ya sunan babyn ka? Kallon hoton yayi yace ba nawa bane na salma ne, ni bani da yara amma inshaaww Allahu mun kusa samuwa ni da ke. Shiru tayi tana kallon hoton tace yaran Rahma nawa? Murmushi yayi yace har muka rabu bamu haihu ba. Cike da mamaki ta dako kai tana cewa rabuwa? Wacce kenan? Yace already tayi aure, tun shekaru uku da suka wuce. Mamakine ya cika Haneefah amma bata kuma cewa komai ba. Ya gama cin abinci ta soma tattarawa zata fita yace inkin kai ina son ganin ki. Kamar yadda ya bukaci ganinta ta shigo ta same shi zaune kan gado da alama yana jiran isowarta. Nesa dashi ta zauna a kasa. Murmushi yayi yace ta so ki zauna nan ya nuna mata kan gado. A hankali tazo ta zauna dan nesa dashi ta sunkuyar da kai. Yace Alahmdulillah, aduk abinda dan adam zayyi kada ya gajiya da godewa mahaliccinsa, yau gashi ni da ke mun kasance tare matsayin ma'aurata, burina ya cika arayuwa, bayan mun fidda rai a mallakan juna sai gashi yau mune abu daya, gaskiya bazan so nesa da ke ba amma zan baki daman karasa karatun ki in yaso nizan koma in soma shirin tarewar mu amma zan rika kawo miki ziyara immediately kina gama mkaranta sai mu kasance tare. Babu shiri Haneefah ta soma hawaye. Ganin haka Yusuf ya rikice yace menene? Bakya son na koma? Zan zauna it's ok stop crying. Haneefah tace ni dan Allah ka fahimce ni nasaba karatu ni daya, zanzo na kammala ni daya kuma inna koma gida ina son hutu kamin na tare gidan ka. Tsaf ya gano ta yace hutu kamar zuwa yaushe. Haneefah tace inna koma gida kamar 5-6months. Mikewa Yusuf yayi ya taso yazo kusa da ita yace in kyaleki ki gama makarnta ke kadai kuma in barki a gida wata biyar kina matsayin matata? Fashewa tayi da kuka tana gyada kai alamar eh. Yusuf yace ya salam! Shikenan naji hkan kika fi so hankalin ki zaifi kwanciya tace eh. Yace shikenan tare da mikewa yaje ya zauna wani bankare daban. Ganin haka yasa ta tashi ta fice a dakin, binta yayi da kallo azuciyarshi yana mai cewa nidai ba iyawa zanyi ba. Bayan ta koma daki ta tarar Raihana na bacci. Tajo plate na abinci ta soma ci tana murmushi. A zuciyarta tace ya Allah nagode maka, amma bansan mesa nake kunyarsa da yawa ba? Kwata-kwata na kasa sakin jiki dashi. Murmushi tayi data hango rashin amincewa a fuskarshi. A haka ta kara shi cin abinci ta zauna zuwa minti goma sha biyar tukun muke ta maida plate kitchen itama ta zo ta kwanta ta soma bacci. Sai bayan la'asar suka tashi. Saida sukai wanka domin samun karfin jiki sannan sukai sallah. Bayan sun idar suka zauna shiru domin kowa gajiya tattare dashi. Raihana ta dubi Haneefah tace ke bazaki je gun mijinki bane? Ko kallonta batai ba bale ta bata amsa. Raihana ta kuma cewa innine fa zan bar muku gidan. Nan ma bata ce komai ba ganin haka yasa itama tayi shiru da bakinta. Sai kuma suka dauko hiran karatu. *8:30pm* Dauke take da try, knocking daya aka bata izinin shigowa. Zaune ta samesa kan sallaya yana waya. Tana ajewa zata fita ya mata nuni da ta tsaya. Nesa dashi ta zauna ta sunkuyar da kai. Bayan ya kammala cike da nutsuwa ta gaishe shi. Amsawa yayi yana murmushi, baice komai ba ya zuba mata ido kamar mai nazarin wani abu. Ganin yayi shiru ta dago idanunta karaf suka hada tayi saurin sunkuyar da kanta. Allah-Allah take tayi sallama dashi batare da yayi mata komai ba.... tana cikin tunani taga ya ta so a inda yake ya nufo ta... ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼65 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Ganin yazo dab da ita ta nannadu guri daya kamar taga wani abin, shi abin dariya ma ya bashi anan ya fahimci tsananin tsoro tattare da ita. A hankali yace Dr HANEEFAH! Duk da cike take da tsoro hakan bai hanata tsananin jin dadi yayin kiran sunanta ba, ji take tamkar shi kadai ya iya kira. A hankali ta dago kai amma ta kasa hada ido dashi. Yace shikenan ina tare da matata amma sai in tafi in barta, kimin adalci ki bari na ci gaba da zama dake hankalina zaifi kwanciya. A hankali tace ni fa banqi zaman ka ba, ayyu kan ka kuma ni karatuna.... ta karashe maganan cike da soma kukan shagwaba. Yace shikenan naji but nikam zan rika zuwa kuma tare zamu rika kwana da matata a daki daya.... tun kafin ya qarasa ta turo baki ta soma hawaye. Shiru yayi yana kallonta. Mikewa tayi ta soma zuba masa abinci, har gabansa ta kawo ta ajiye zata tashi ya jawota ta fada jikinsa. Riko sosai ya mata ya soma mata rada a kunne ina zakije? Nagaji da kwana ni daya yau da ke zan kwana. Lamo tayi jikinsa tace kamin afuwa mubar kasarnan kafin mukasance tare dakai daki daya, kada ka manta mu biyu ne a cikin gidannan, kuma karatuna yazo karshe kullum nake cikin karatu yanzu haka karatu Raihana take na barota, amma in kana son in kara maimaita shekara daya ne zanyi yadda kace amma bawai nima inason nesa dakai bane, inka sabarmin bazan iya ci gaba da karatu ba. Da gota yayi yana kallonta, tana dago idanunta yace mai wayo, na fahimce ki. Zan koma gida in soma mana shirin inda zamu zauna kema saiki karasa karatun ki amma kina gamawa a gidana zaki sauka... Zatayi magana ya rufe mata baki da nashi, dakyar ta kwaci kanta ta gudu tana cewa cikin zuciyarta saika kara ganina ai. Kamar yasan abinda take fadi ya fashe da dariya yace zanga yadda zakiyi in muka koma gida. Kwanan sa uku ya soma shirin tafiya domin gurin aikin sama na bukatar sa sosai sannan yana son yaje ya soma shirin inda zai saukar da amaryarsa, babu yadda zayyi domin Haneefah ta dage saiya koma gida. Har airport ta rako shi a motar ta, zata fita yayi saurin riko hannunta ta juyo suka hada ido, tayi saurin kawar da kanta domin duk sanda suka hada ido sai taji wani irin abu mara misaltuwa. A hankali yace ina sonki sosai Haneefah, pls take care of ur self. Murmushi tayi ganin yana matsowa tayi saurin fitowa ta zagaya ta zo ta bude mishi kofa. Qin fitowa yayi, ko kallon inda take bayyi ba. Zuwa tayi gabansa ta durkusa tare da kamo hannuwan sa tace nima inason ka sosai... da sauri yace naaqi ai ban karasa ba kika fito. Murmushi tayi tace kada kayi missing flight naka! Yace in baki komo mazaunin ki ba sai dai inta zama anan. Bata son musu domin zai aikata yasa ta tashi ta zagayo tashiga ta zauna tare da sunkuyo da kanta. A hankali yasa hannu ya dago fuskarta ya manna mata kiss a goshi sannan ya bude mota ya fito ya zagayo ya bude mata. Da murmushin jin dadi ta fito. A hankali suke taku har suka shiga sai taji kamar kada ya tafi, shima Yusuf daurewa yayi. Saida taga tashiwarsa sannan ta koma gida. Yinin ranar bataji dadi ba sai da taga kiransa ya koma gida lfy kafin ta runtsa ta samuyin bacci. Cikin taimakon Allah ya soma shirin sa, Abba ya dauki nawin duk wani irin gini yake bukata a birnin tarayya. Can gida kano ma aka fasa sashin Yusuf aka masa gyara sosai. Kowa na murna da bikin Engineer Yusuf da Dr Haneefah. **** **** A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, a yau ake yaye daliban kiwon lafiya dake jami'ar Oxford university London. Kowa cike yake da farin cikin wannan rana musamman dalibai. Raihana tare take da mahaifanta sai yayanta, hannunta na cikin Haneefah domin kada ta ji wani irin yanayi amma duk dauriyar Haneefah sai da taji tana sha'awar ganin mahaifanta a wannan rana. Makaranta ta soma nuna farin cikinta a game da dalibai da suka nuna kwazo da sukai karatu kan gaskiya... sannan ta bukaci dalibai guda uku da suka cancanta yabo agun illahirin malamai da maarantar baki daya.... Haneefah da Raihana aka kira abinda basu taba tsammani ba duk da sunsan ana ji dasu a bangaren su amma basu dauka dukkanin makaranta na Alfahari dasu ba. A hankali suka taso suna tafiya har suka iso gaban taro, sai wani bature mai suna Felix. Sun samu kyaututtuka da dama har Haneefah ta kasa hakura ta soma kuka. Raihana na lallashin ta, aka bukaci kowa yazo dan uwanshi. Nan Haneefah tayi shiru, Felix matar shi ce ta fito, Raihana kuma yayanta har akazo kan Haneefah. Sun kuyar da kai tayi kamar daga sama taji muryar Ahmad. Da sauri ta dago kai tana kallon sa da mamaki. Bayan ya gama yazo gurinta da sauri tana farin ciki ta kama hannuwan sa tace Ahmad kaine? Yana dariya yace eh nine. Zata kuma magana taga Dr Mubarak shi da Bar. Ramlat. Daga bayansa kuma Umma da Abba sai Yusuf dake biye dasu. Tana hawaye tana murna, da gudu taje ta rungumi Umma tana kuka. Dakyar Umma ta dagota tana ya'isa haka Ahmad dake gefen Umma yace in bakiyi shiru ba zamu koma inda muka fito, dagowa tayi da sauri tana share hawayenta tace ashe zaku zo? Abba yace Umma da Ahmad kika sani ko? Haneefah tayi murmushi tace Abba banyi tsammanin zuwan ku ba, nan ta soma gaishe su. Suna gaisawa kafin tazo gun Yusuf Raihana ta iso itada mahaifanta suna gaida su Umma, Haneefah ta gabatar da iyayen Raihana ga su Umma. Bayan sun sami guri sun zauna da mintuna kalilan aka yaye su Haneefah daga makaranta. Bayan an kammala aka soma dauka hoto anan Haneefah tazo gaban Dr Mubarak da Bar. Tana cewa nagode sosai da gudunmuwarku a rayuwata, bani da bakin gode muku sai dai in tayaku da addu'a, nagode sosai... Bar. Tace babu komai Haneefah, Allah qara mana zumunci. Shiko Dr Mubarak bai iya cewa komai ba sai murmushi domin farin ciki sosai yake da karatun Haneefah. Suna gama dauka hotuna saura Yusuf, tsaye yake daga gefe yana kallon ta. A kunyace take kallonsa har ta karaso inda yake. Shiru tayi yana kallonta ya cije lebe yace zaki gamu dani ai. Yayi gaba ta bisa a baya tana dariya kasa-kasa. Bayan sun gama komai suka kamo hanyar zuwa gidan Haneefah tare da Raihana da yan uwanta. Suna shiga suka ga Kevin da Rohan suna shirya abinci. Haneefah ta tsaya da mamaki tana kallon Rohan tace yaushe kazo? Yace tambayi Raihana. Raihana tana dariya tace nasan da zuwan dukkanin su kawai sunce nayi shiru kada na sanar dake ne. Wannan ranar yana daga cikin ranaku da Haneefah da bazata taba mancewa ba, musamman inta tuno da yau ta kammala karatun ta, ta kasance matar YUSUF abin ba qaramin dadi yake mata ba. Yusuf duk yadda ya so su hada ido da Haneefah hakan baya yiwuwa, harya gaji ya zuba mata ido. Sun zauna cin abinci Yusuf ganinsu Umma yasa yaji bazai iya ciba, Dr Mubarak ya fahimce shi dan haka ya kalli Haneefah yace nida Yusuf, Kevin da Rohan da yayan Raihana ku kai mana daki acan zamu ci. Abba baice komai ba dan yasan dalili. Kamar yadda akace dasu haka akai, mazan suka tashi suka shiga ciki inda aka shigar musu da abinci. Haneefah tana kokarin shiga falo taga anja hannunta zuwa dakin dake dab da shigowa................ ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼67 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tsaban rudewa ya kasa magana, babu abinda bai mata amma ko motsawa bata yi. Cike da tashin hankali ya bude motar yazo mazaunin driver yaja ya soma tafiya. Yana tafiya yana waigawa yana kallonta. Ikon Allah kadai ya kawo shi asibiti, ko gyara parking bayyi ba ya fito ya. Dr Mubarak dake kokarin fita a asibiti yaga babu hanyar wucewa, fitowa zayyi yayi magana a gyara parking yaga Yusuf na ciro Haneefah cikin mota ko motsawa bata yi. DA sauri shima ya fito ya nufo gunsu yana tambayar lafiya? A sannan Yusuf ya bude baki yace Mubarak Haneefah ce... sai kuma yakasa cewa komai. Cikin sauri Dr Mubarak ya bashi izinin biyoshi. Tsananta bincike yayi sosai akanta, kusan awa daya yayi kafin ya gano abinda ke damunta. Tsananin mamaki ne ya cika Dr Mubarak yana kallon Haneefah da bata san inda take ba. Yana kokarin fita Haneefah ta bude ido dakyar tace na rokeka da girman Allah ya zamto lalurata sirrine tsakanina dakai, sannan ta sanar masa allurar da take amfani dashi. Shiru yayi yana kallonta baice komai ba ya fice nemo allurar. Yusuf da tunani fal yacika masa zuciya ya rasa mezayyi, yana kai komo yaga Dr Mubarak ya fiti. Da sauri ya nufi gunshi... tun kafin yace komai yace ka kwantar da hankalin ka zata samu sauki yanzu zanje siyan allurane. A hankali ya turo kofar ya shigo, hangota yayi ta dafe kasan mararta tana hawaye. Da sauri ya nufota yana mata sannu, ta kasa bude ido taganshi tsabar azaban da take ji. Yusuf ji yake tamkar ya cire ciwon ya mayar jikinsa. A hankali ya zauna gefenta yana mata sannu. Ganin ta kankame hannunsa ta fashe da kuka yayi, rungumeta yayi yace shikenan yi hakuri pls.. Dr yashigo dauke da allura yana sauri, Yusuf yace an kawo allura bari asaka miki kinji zaki samu saunki. Haneefah ko jinsu bata yi domin wannan karon har wani irin abu take ji, kuka sosai take. Yusuf ya soma gyara ta domin asa mata allurar amma gani sukai ta sake faduwa sumammiya. Saida Dr Mubarak yayi kokarin cire Yusuf kafin ya soma bata taimako. Alhamdulillah ta samu bacci, dan haka ya fito domin sanar dashi halin da take ciki. Bayan ya sanar da Yusuf yace yana zuwa ya fice. Zaune yake ya zuba mata ido, tsoro ne kodai bata da lafiya? Yana cikin tunani kiran Dr Abdullahi ya shigo wayarsa. Ganin agogo yayi karfe goma sha daya da rabi, yana dagawa yace kumin afuwa wlh ina asibiti ne bata da lafiya. Daga daya bangaren kuma Dr Abdullahi yace rashin lafiya kuma? Kuna wani asibiti? Ya sanar dashi. Cikin mintuna kalilan ya iso, ya tarar da Haneefah sai birgima da ambaton Allah take. Yusuf ya gama rudewa yana ganin kamar shine silar komai. Dr Abdullahi bayason sa hannun akan patient da bashi ya fara dubawa ba dan haka yaja da baya ya tsaya. Dukkanin wani taimako Dr Mubarak ya bawa Haneefah. Samun bacci tayi sosai domin. Dukkanin su sunyi shiru, Dr Abdullahi ya duba agogo yace nizan wuce gida, sai zuwa gobe da safe zan shigo. Yusuf baima san me suke cewa ba sai da Dr Mubarak ya tabashi sannan ya dawo hayyacinsa. Dr Mubarak yace zan tafi office inta tashi saika kirani, suka karbi number juna sukai sallama. Dab da sallar asubahi ta bude ido, a hankali zata mike taji an rikota, da sauri ta juyo tana kallonsa. Ganin rikon da yamata ne yasa yayi saurin saketa a tunaninsa wata kila tsorone yake sata sumewa. A hankali ta mike ta zauna. Ciro waya yayi ya kira Dr Mubarak yace tafarka. Ko minti biyu basuyi ba yayi sallama yashigo. Tambayoyi yake mata... ganin yayi yawa yasa ta dago idanunta ta kalli Dr Mubarak tace babu abinda nake ji gida nake son komawa yanzu. Babu yadda basuyi da ita ba amma tace ita gida zata koma. Duk yadda Dr Mubarak yaso kebewa da ita taki amincewa illacewa ta warke batajin komai. A mota babu wadda ya iya cewa junan shi komai illa Yusuf daya lura tana cije labe. Bai iya cewa komai ba ya nufe gidan Nana da ita. Suna zuwa aka soma kirayen sallar asubahi. Nana idonta biyu da babynta taji shigowar mota, ta tashi mijinta yaje ya duba kosu Haneefah ne suka zo domin hankalinta na kanta duk da mijinta ne yazo ya dauke su? Da sauri ya bude mata kofa, ta fito. A hankali take tafiya harta iso dakinta. Dakyar ta zauna bakin gado tana rera kuka. Nana da' mijinta sai Yusuf dake biye dasu har cikin dakin suka tarar ta a wannan hali. Jin shigowarsu yasa ta share hawayenta tana kokarin mikewa amma sai taji bazata iya ba. Nana tazo ta dafata tana tambayarta dama baki da lafiya? Haneefah ta gyada mata kai alamar eh, sannu suka mata. Ta gyara kwanciyarta. Yusuf da Abdullahi suka fice sallah. Tunda ta kwanta bacci sai karfe goma ta tashi, shima dakyar. Kamar kullum yau ma rama tayi sai kukan da take duk dauriyar Haneefah wannan karon ciwon daban yake. Zaune take bakin gado ya shigo cikin kananan kaya. Kallo daya ta masa ta dauke kai tare da fadin _sarki ya tabbata ga wadda yayi wannan kyakykyawar halitta_. Zama yayi kusa da ita yana kallonta, tausayinta ne ke ratsa shi. A hankali yace ya jikin naki? Ta amsa da sauki. Yace meke damunki yanzu? Tace babu komai. Mamakin raman da tayi yake. A haka Dr Mubarak yazo, yana kokarin dubata ne tace ta samu sauki. Dr Mubarak yace kinsan abinda ke damunki kike cutar da kanki? Matsayinki na wadda ya dace ki lura lafiyar kanki, mesa kikai haka Haneefah? Ganin ba magana zatayi masa ba ya tashi ya fice ranshi a bace. Yana fita ya samu Yusuf zaune a falo yayi shiru. Dr Mubarak ya zauna kan kujeran da ke kallon Yusuf yace yaushe Haneefah zata tare? Yusuf na kallon shi yace a gaskiya zuwa yanzu bamu sa lokaci ba amma inta samu sauki zamuyi magana. Dr Mubarak yace samun saukin ta na la'aka da komawarta saboda zatafi samun kulawa a hannun ka, yanzu abinda nake so kaje ka soma shiri amma kada ya dauki sati daya ko kwana biyar. Yusuf yace zanfi so nayi magana da ita domin jin ra'ayinta..... bai karasa ba Dr Mubarak yace kada ka bi ta Haneefah, kayi abinda na ce muddin baka so ta kuka samun kanta a irin wannan yana yi Cikin rashin fahimta Yusuf yace ban fahimci abinda kake nufi ba. Dr Mubarak yace baka ga yadda ta rame ba? Babu abinda take bukata kamar kasancewa tare da ita u have to do something. Ya mike tare da yi masa sallama. Yusuf yayi shiru yana tunani, tashiwa yayi ya nufi gidansu Haneefah. Kamar kullum yauma da Ahmad suka hadu. Har falo ya kaishi sannan ya shiga ciki yayiwa Abba magana. Cike da fara'a suka gaisa yana masa ya gajiya? Ya amsa da alhamdulilah. Shirun da Yusuf yayi ya tabbata akwai magana abakinsa kuma bazai wuce na tarewar sa da Haneefah ba. Kamar daga sama yaji Abba yace Alhamdulillah Haneefah dai ta komo gida lafiya, kuma kimanin wata hudu da daurin auren ku, inason ka nan da sati daya ka zo ka tafi da ita, bazan hanaka komai ba amma bana son ta wuce sati daya. Farin ciki ne ya lullubi zuciyar Yusuf ya shiga godewa Abba. Yana fita ya nufi gidan Aisha ya sanar mata, farin ciki take tayasa tace yanzu bazamuyi shagalin biki ba? Yace zaku batamin lokaci domin nafi bukatar matata. Aisha tayi dariya tace in abban Ra'ima yazo zan tambayesa sai mu je gida mu soma shirin tarban amarya amma zan sanar da salma. Yana fita ya nufi gidan su yana murnar sanar dasu abinda ya faru. Yana shiga yaga motar salma, murmushi yayi yace kinzo a daidai yar'uwa. Da sauri ya shiga falo. Ganin rahma da Umma nusaiba yayi suna zaune. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼66 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Shi kadai tasan zai iya aikata mata hakn. Kulle kofan yayi ya tsaya bakin ko fa yana kallonta tare da harde hannayensa a kirji. Shiru tayi ta saukar da kai kasa domin kwarjini ya mata sosai ga bala'in kunyar sa da take ji. Baice da ita komai ba yana kallon ta. Ganin shirun yayi yawa ta dago ido suka hada, fuskarsa ko murmushi babu. Tace kayi hakuri ni fa.... yace me kikamin da zaki bani hakuri? Ni kallon ki kawai nakeson yi tunda ke baki bukatar kallon mijinki. Hawayene suka taru idanunta tana kokarin zubda su ya jawota tare da rungumarta ya soma lallashin ta yace shikenan me abin kuka godewa Allah zamuyi a wannan rana. Congratulations my dearie, proud to have u in my life. Lumshe ido tayi ta kwanta a jikinsa sosai tace am sorry dear sai yau kazo min inata jiranka, i really missed u.... yayi sauri dago ta yace da gaske? Zatai magana taji Raihana na kiranta. Da sauri ya saketa ya bata hanya ta wuce yana murmushi. Bayan sun gama cin abinci Kevin ya bukaci suyi masauki a gidansa domin gidan Haneefah bazai ishe su ba. Kafin su tafi Dr Mubarak yace yana son kallon Dr Michael. Raihana tace in akan maganan aikin Haneefah ne ina son biyo ku. Mota biyu suka ciko suka nufi asibiti amma basu same shi ba, Kevin ya musu jagora zuwa gidan sa. Babban gida ne wadda yake kunshe da dukkanin abin bukatan rayuwa, duk fadin gidan Dr Michael da dan sa ne kadai ke rayuwa ciki sai masu aiki. Suna shiga yana shirin fita. Yana ganin Haneefah ya fadada murmushin sa tare da tayata murnan gama karatu. Shiga ciki yayi dasu yana cewa yanzu nake shirin tafiya. Bayan an gaisa Dr Mubarak yace kamar yadda is sanni ni yayan Haneefah, mun gode da kulawar da kuka bata har ta kaiga wannan mataki amma yanzu muna so ka sallameta a aikin ta. Da sauri Dr Michael yace dalili? Dr Mubarak yace saboda inta koma aure zatai sai dai intayi auren mijin da ta aura yana da sha'awar zuwa nan saiku sake daukan ta aiki amma in har baku sallameta ba hakan zai jawo matsalar da bazata sake zuwa ba. Dr yace bana bukatar matsalar da zai hanata zuwa, Haneefah yarinya ce karama mai kwazo ina da tabbacin ko mijinta zai barta tazo. Haneefah tace sir ina bukatar sake zuwa amma in bakai yadda yayana yace ba hakan zai kawomin matsala domin al'aldunmu daban da naku. Dakyar baturennan ya amince ya sallami Haneefah. Murna kowa yake a haka suka je gida domin sanar da Abba. Bayan sunje sun sanar da su sunyi farin ciki sosai dan haka suka soma shirin tara kayansu domin koda yaushe zasu iya suce su tashi. Gidan Kevin babba ne sosai, wadda kowa is samu daki daidai. Haneefah na makale da Umma, tana sane da Yusuf amma tasan inta koma Nigeria bazatayi cikekken sati uku a gida ba za'ace ta tare gidansa dan haka take moran umman ta son ranta. Kullum suna cikin fita su zaga iyaye guraren tarihi da ban mamaki da, sanin da Raihana da Haneefah sukayiwa London ko Dr Mubarak sai da yayi mamaki. Iyayensu sunyi farin ciki da karatun su domin babu wani abin aibu da suka aikata sai dai ma yabon yaransu da ake. Ana gobe Raihana zasu wuce Dubai Haneefah duk taji babu dadi,dukkan su suka zauna jugum sunyi shiru. Basusan ma an kwankwasa kofa ba ganin Ummi da Umma sukai. Zama sukai suna lallashin yaran nasu suka ce ai dan an rabu yau har abada suna tare. Washe gari har airport suka raka su, dukkansu suna kuka har suka rabu. Yinin ranar Haneefah taji babu dadi domin sunyi zaman amana da mutunci da Raihana, bazata taba manta ta ba. Suma suka soma shirin zuwa Nigeria. Tun tafiyar Raihana, Haneefah ta zamto abin tausayi domin bata da hira sai na Raihana. Bata iya hira da kowa sai na Raihana. *_Zumunci domin Allah ba karamin abu bane_* **** **** Misalin karfe bakwai motar su tayi parking cikin gida. Kowa na tsaye yana jiran shigiwarsu. Suna sauka a mota akayo kan Haneefah ana mata oyoyo. Itama murnan ganin yan uwanta ta rungumesu tana farin ciki. Ko zama su Dr Mubarak ba suyiba suka ce zasu wuce gida, Yusuf ma yace su sauke shi a gida. Duk hankalin Haneefah na kan Yusuf har suka fice daga gidan. Kowa na murnan zuwan ta, so da kauna annuna matashi, inna da yaranta babu magana anata hidima. Hadiza ta zo ita da ummulkhairi da kaninta sadiq, Haneefah tayi murna sosai kullum tana cikin dangi ko wayarta bata kula ta nemi sim card ba amma masoyin nata na nan cikin zuciyarta tana son kiran shi. Bayan zuwan su da kwana uku Nana ta haifi danta namiji. Ranar suna danta yaci sunan surikinta wato baban Dr Abdullahi. *** Da yamma misalin karfe hudu. Zaune take tana nazari ciwon da takeji a karkashin maranta, tunani take abinda take boyewa ya kusa bayyana amma in har yasameta wani magani zata sha? Gashi tun da tazo bata samu zama ba bale Yusuf yazo su fara maganar tarewarta ko dai yayi fishi ne? Itama bata kira shiba. Mukewa tayi ta dauki wayarta ta nufi dakin Nana, ta tarar bata nan. Daukar wayar Nana tayi ta saka lambarda kwana ki yakirata dashi ta soma kira. Zaune yake ya kurawa hoton ta ido. Yau kusan sati biyu amma ko saya basu yiba. Tunani yake yadda zai tunkareta da maganar tarewarta gashi gurin aikinsu an damesa da kira, gini ya kare.... yana cikin tunani yaji ankirashi a waya kamar bazai daga ba amma ya yadaga tare da yin shiru. Jin sallamarta yasa ya lumshe ido tare dajin wani bakon abu na ziyartan zuciyarsa. Baice da ita komai ba ta kareshi gaishe shi. Sai taji bata kyauta mishi ba tace kayi hakuri ban samu zama bane amma.... bance komai ba amma kina bani hakuri, in har kina son na hakura zan so ganin ki zuwa anjima. Shiru tayi sannan tace ina gidan Nana amma zuwa gobe zan koma gida. Yace zanzo anjima misalin karfe takwas. Katse wayar tayi jin wani abu na sokinta a ciki amma tayi shiru tana nazari. 8:00pm Duk da ciwon da take ji amma ta daure ta shirya domin tana bukatar ganin masoyinta. Wayar Nana na hannunta taji an kira, tana dagawa yace ina kofar gida ina jiran ki ya katse wayar. Mikewa tayi zata sako hijabi Nana tace gun mijin naki saikin dauki wani hijabi? Karba tayi ta mika mata gele tace kitafi da wannan. Haneefah ta karbi gelen domin bata son dogon surutu, so take taje ko gaisawa ne saita komo domin abinda takeji ya soma yawaita. Hangota yayi ta fito sanye da gele, kasancewar gurin da haske ya kare mata kallo, light makeup tayi. Ganin zata koma yasa ya hasko mata huta tare da kashe wa a lokaci daya kasancewar inda yake da duhu. Haneefah ta nufo inda yake zata bude kofar gaba taga an bude kofar baya. A sanyaye ta shigo ta rufe motar. Shiru yayi yana kallonta Dakyar tace dashi ina fata ka yini lafiya? Lafiya ya amsa. Yadda ya amsa yasa ta dago ido tana kallon shi, wannan karon ba ita yake kallo ba alamun kamar yana fishi da ita. Kokarin bude motar ta fita ya kulle motar da remote dake hannunsa. Juyowa tayi tana kallonsa shima kallonta yake. Yace, ban samu ganinki ba tun da muka zo, baki kirani ba yanzu da kuka zo ko minti goma bakiyi ba zaki koma? Ta sunkuyar da kanta, kamo hannunta yayi yace yanzu kin zama matata, kin gama makaranta ya dace ace mun fara maganan tarewarmu..... kayi hakuri ba laifi bane tana magana tana kokarin kwace hannunta Shima yace in kina son na hakura bani minti biyar zan hakura.... kafin tace wani abu ya dora bakinsa kan nata, kuka ta saka marar sauti, saida taji ya saka hannayensa cikin riganta ta soma kuka. Kokarin zuge zif na rigarta yake cikin kuka tace dan Allah kayi hakuri zan koma gida.. baice da ita komai ba yarungumeta tareda mata rada a kunne yace saikin amince nan da kwana uku zamu tare inba haka ba bazan kyale kiba. A tsorace ta tureshi tace nidai kai hakuri... sake rufe mata baki yayi da nashi.... wasa sosai yake da ita bai ankara ba yaga ta fadi jikinsa sumammiya. Shima a tsorace ya dagota amma yaganta ta koma, yace shikenan na kyaleki tashi Haneefah... dagota yake amma sai yaga ko motsawa bata yi. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼69 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tana cikin wannan hali taji ana konkosa kofar falo. Shiru tayi domin Yusuf yace kada ta bude kofa sai ta tabbar wanene.Tsorone ya lullubeta ta zo daf da kofar tana tambayar wanene? Yusuf yace nine. Jin muryarsa yasa ta bude kofar da sauri, tana budewa ta rungumesa tare da fashewa da kuka tana cewa ina ka tsaya inata jiranka.Kamshin turarenta ya bugi hancinsa ya shaka tare da lumshe ido yace yi hakuri dearie motatane ta baci ko gyarawa ban samu ba. Rungumeta sosai yayi yace sorry nabarki ke daya ko, gani nazo bazan kuma ba. Rungume da ita yashigo ya rufe kofa. Har bedroom suka je a haka. Saida suka zauna bakin gado yake kallonta. Kura mata ido yayi tamkar zai maidata ciki ya nemi gajiyan da ya dauko ya rasa. Ita kuma ta tashi tashiga bandaki hada masa ruwan wanka. Duk motsinta yana kallonta har tazo ta soma taya shi rage kayan jikin shi. Kasa hakura yayi yajawota jikinsa yana shakar kamshin jikinta yace kullum kara kyau kike. Kwanciya tayi jikinsa cike da shagwaba tace aika fini kyau... bata karasa ba taji ya kwantar ta kan gado. Ganin abinda yake shirin yi tace pls ka tashi na hada maka ruwa Da sauri yace pls dear yau zaki tayani? Zaro ido tayi ya tashi yana yar dariya yace matsoraciya kada yauma ki sumemin. Yana shiga ta tashi ta ciro masa kayan da zaisa ta dauki nata ta nufi dakinta dashi. Bayan ta fito daga wanka ta shirya tsaf cikin nighty daya tsaya mata iya gwiwa. Ta kama kanta da ta fashe jikinta da turaruka ta fito. Zaune ta samesa ya shirya yana amfani da laptop. Tunda ta shigo ya kura mata ido, ya rasa ya zayyi ga abinda yake ji cikin zuciyrsa. A hankali ta'iso tace dare nayi yakamata kaci abinci. Babu musu ya taso suka nufi dinning table. Bayan sun gama cin abinci ta fara hamman bacci. Suka kashe komai suka nufi bedroom. Kwance take a girjinsa tana kokarin bacci, yana shafa bayanta a hanakali har ya sauko da kanshi daidai fuskarta yace pls dearie yau kada ki suma. Yadda yayi magana harta ji tausayinsa amma tace ka gaji sosai bacci kake ji ka kwanta kayi baccin ka. Ganin bazai samu hadin kai ba yasa ya lumshe ido amma ya qara budewa a hankali yace pls dear watan mu biyarfa nayi kokari ai. Tsananin tsorone yasa tajuyar da kanta bangare daya. Tanaji yana mata magana amma tayi shiru kamar mai bacci, shima shiru yayi yana cije lebe. Tabbas Yusuf yayi kokari amma tsoro take ji. Gabanta ne ya fadi data tuno tsinuwar mala'iku ga matar da taki amincewa da mijinta. A hanakali ta juyo da kanta ta kwanta a kirjinsa, rungumota yayi sosai a hankali tace tsoro nake ji. Shi kuma yace shikenan kiyi baccin ki, ke kadai nake bukata gashi nasameki. Cikin sanyin murya tace na amince. A hankali ya dagota suna fuskantar juna yace kin amincemin? Gyada kanta tayi alamar eh tana kokarin hawaye. Bai kara ko second daya ba ya soma mata salon da ta mance wani duniya take. ** Bayan ya fito daga wanka ya nufi gurinta tare da taimaka mata suka nufi banda ki, kin amincewa tayi ya mata wanka dolensa ya kyaleta ya fito. Mamaki ne ya cika shi abinda ya gani, da sauri ya canza bedsheet din ya gyara, tana fitowa ta nemi magani ya kawo mata tasha sannan ta kwanta. Bacci take hankalinta a kwance. Shiko ogan sakata agaba yayi yana kallonta, tsananin kaunarta ne ke fizgeshi musamman inya tuno a wanni da suka gabata. Tashiwa yayi ya soma nafilfilu tare da nuna farin ciki da godiya Allah daya mallaka masa wannan baiwar tasa. Dakyar ta tashi sallar asubah, domin ya zame mata jiki bata taba barin wannan lokaci ya wuceta sai rashin lafiya mai tsanani ko tasha magani mai karfi. Tana idarwa ta koma bacci, shima yana zuwa daga masallaci ya kwanta rungume da Haneefah. Kusan karfe tara da rabi ta tashi, ita kadai ta gani hakan na nufin yana falo. Daurewa tayi ta mike tashiga toilet. Ta sake hada ruwan zafi ta shiga ta zauna sannan ta tashi tayi wanka. Daure take da towel tana nazarin kayan da zata saka domin bazata irin na jiya ba duk shi yaja mata. Riga mai dogon hannu zuwa gwiwa da dogon wando ta nemo, duk cikin kayan shine mai dama dama, ta dauki hula ta saka. Ta feshe jikinta da turare tare da shafa powder da man baki. Gani tayi light makeup din ma ya canzata, tana shirin fita shi kuma yana shigowa. Da sauri zata koma yayi saurin jawota ta fada jikinsa. Daukarta yayi sai kan gado, tsoro ya dada lullubeta kada ayi gidan jiya. Kamar yasan me take tunani ya kwantarta a hankali yayi kissing nagoshinta, babu shiri tace pls kayi hakuri bani da lafiya. Cike da tsokana yace warkewa zakiyi da zarar' na mik.... mikewa tayi tana kokarin boye kanta cikin kirjinsa. Murmushi yayi yana shafa bayanta tare da cewa wasa nake miki, ina fata kin tashi lfy? Kunya ya lullubeta tace ina kwana? Ya amsa cike da farin ciki ya mata ya jiki? Shiru tayi tare da yin lamo a kirjinsa. Lumshe ido yayi, yana matukar jin dadi aduk lokacin da takasance a kirjinsa. A hankali yace nagode Haneefah, a kullum ke dabance, a kullum salon ki kara yawaita soyayyarki da kimarki yake aguri, all these years u keep ur self for me? Nayi sa'a a duniya tabbas dukkanin wani bawa daya fawwala komai nasa a hannun Allah alkhairi na biye da lamarinsa. Haneefah tace tabbas maganan ka haka yake, nasan zamu sake kasancewa domin inada yakinin Allah maji rokon bayin sane, ta dago a hankali tana kallon shi. Kama hannuwansa tayi tace ni nasan nayi dacen miji, mai so na, wadda yake gudun bacin raina, wadda ra'ayinmu yazo daya tabbas nina kasance mai sa'a Lallausan murmushi ya sakar mata yace me kike so a duniyar nan? Itama murmushi tayi tace kulawarka kadai nake bukata. Rungumeta yayi yace kin samu. Jinsu suke tamkar su hadiye juna tsabar SO. Zaune suke kan dinning table suna breakfast amma taji bata kaunar zaman ma. Daurewa tayi suka karasa. A tare sukai komai, zaune suke taji ya kira office ya dauki excuse bazai samu shigiwa ba madam nashi bata da lafiya. Haneefah taji dadin haka, a haka har bacci ya sace ta. Shiya kaita bedroom ya kwantar da ita. Yusuf kallon Haneefah baya isarsa. Haka yakasance cikin jinyarta. **** Rayuwa ya dawowa masoya biyu sabuwa fil, Haneefah ta kauda kunya tana nunawa mijinta kulawa haka shima, ya bata dukkanin lokacinsa da kulawa, komai nasa Haneefah. Zaman lafiya ke wakana tsakanin Umma da Inna haka yaranma kansu a hade. Babu wadda yakai Momy ji da Haneefah, haka ga family gaba daya kowa Haneefah. Burin Haneefah ya cika tsakaninsu lafiya da kowa hakan na mata dadi sosai sai dai haryanzu babu ciki, yanzu burinta bai wuce takai Umma, Abba da Inna saudia ba. _Bayan wata biyar_ Zaune take tana jin tashin zuciya, yau breakfast nasu tayi toasting bread da kwai, tunani take ko warin mai ne ke sata jin tashin zuciya? Shiga banda ki yayi yaga bata wanke ba bale ta hada masa ruwan wanka. Bayan ya gama shiri tsaf ya zo ya sameta a inda ya barta, zuwa yayi ya tsugunna gabanta. Dago idanu tayi cike da hawaye tana kallonsa, da sauri zata mike bata ankara ba ta koma ta fadi..... ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼68 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 A hankali ya karaso falo ya tsugunna har kasa ya gaishe ta. Ta amsa cike da jin kunya. Salma ce tace yaya yanzu Aisha ta kirani a waya take sanar dani labari mai dadi, amma Yaya sati daya ai yayi wuri Momy dake zaune tana murmushi tace ai kun gama shirin ku tun wuri salma saura daukar amarya. Ganin Yusuf ya tashi ya shiga yasa salma ta bishi a baya. Momy ta dubi yar uwarta tace, Yusuf da dukkanin yarana naki ne, abinda ya wuce yariga ya wuce sannan kin aikata hakan a kuskure sai dai a kiyaye na gaba. Babu yadda zanyi domin ba ni da wata yaruwa da ta wuce ki. Sannan bazan kyamace ki ba domin kin aikata hakan, fatana shine Allah yarabamu da duniya lafiya Umma nusaiba ta goge kwallar da ta zubo mata cike da nadama tace nagode, insha Allah bazan kuma aikata makamancin haka ba. Dukkaninsu suka kasance masu danne zukatan yan uwansu tare da addu'ar kore dukkanin wata sharri. Labari yaje kunnen yan uwa na kusa domin umma tace walaima kadai za'ayi. Haneefah ta komo gida. Kuka ta zauna yi tana cewa wani irin shiri zatai a sati daya? Aunty Muhibbat dake zaune tace aike kin gama shiri domin auren naku tun yaushe? Ko kina nufin tafiyan da yake gunki babu abinda yashiga tsakanin ku? Haneefah tace ni sau daya ya tafi kuma tunda nace yayi hakuri bai sake zuwa ba sai ranar graduation namu da suka tafi. Mamaki suka shiga yi. Haneefah ta share hawaye tace ni yanzu Dubai nake son tafiya shopping, amin gyaran jiki amma lokaci duk ya kure. Hadiza tace lokaci bai kure ba, indai gyaran jiki ne akwai wadda za'a miki kwana biyar kadai zaki haska, amma hakan ma ai kin canza Haneefah amma kuma yafi kyau a miki dilke, yanzu inna tashi daga nan zan wuce inje in dauko mai dilke, bayan kwana uku sai a miki kunshi tunda dilke muddin ana yinshi safe da yamma for you kam 3days ma is ok. Sannan yanzu ki kira Raihana tunda taga shopping da kukai na auran Aisha saiki aika mata kudi ta miki... Aunty humaira tace shopping a Dubai is not easy akwai kaya masu kyau anan garin sai muyi shopping ai. Haneefah ta yarda da hakan amma tace kada kowa ta dame kanta da tsumi saboda irin fruit da nasha ba kadan bane shi kadai ya gama min aiki. Dariya suka kwashe suna cewa lallai Haneefah kinyi baki, duk cikin mu fruits muka rike hannu biyu, sai Zuma. Tun daga ranar suka soma shiri, ita dai Haneefah har yanzu tana jin ciwon marar daurewa take aka soma shiri da ita. Cikin kwana uku suka kammala siyayya aka yiwa Yusuf magana domin tafiya da kayayyakin abuja. Aunty Muhibbat, zuwaira da Hadiza aka hada suka tafi jeren amarya. Ana gobe walima aka kawo kayan lefe, mamaki ya cika su, auren ma ya wuce amma sai sun hado lefe. _Ko ban fada ba masu karatu kunsan lefen Dr HANEEFAH bazai misaltuba_ . Haneefah zaune take gidan Inna tana jiran isowar mai kunshi taji ana sallama, kafin ta tashi ta shiga ciki taga Aisha rike da Ra'ima sun shigo. Da sauri suka rungume juna suna murna. Gaisuwa sosai suka da nuna farin cikin sake haduwa da juna. Aunty Haneefah Allah ya dubi zuciyarku yanzu gashi har kunyi aure. Murmushi Haneefah take. Mika mata Ra'ima tayi ta sanar da ita takwarar tace ana kiranta da Ra'ima. Haneefah ta karbeta cike da tsananin son yarinyar. Mamakin irin son da Yusuf da family shi suke mata takeyi. Rungumeta tayi tace nagode Aisha Allah bani ikon zama daku bisa amana da lafiya. Aisha tace ko shakka babu kemai amana ce, muna farin cikin zamanki matar Yusuf. Haka suka kasance masu yiwa junansu kyakykyawar zato. Washe gari akai walima gidan amarya da ango. Yan uwa sai fatan zaman lafiya suke musu. Da dare aka Abba da Umma suka sa Haneefah agaba sukai mata nasiha sosai kan zaman hakuri. Washe gari aka turo mota domin tafiya da sauran kaya. Duk shagalinnan banda Nana akai domin mai jego ce. Sannan aka sake turo mota inda wadda zai tafi amma amarya zirgin safe zata bi. Abba ya hana kowa tafiya yace dasu Amal insun sami hutun makaranta suje. Washe gari aka zo tafiya da Haneefah, kuka kama tayi shi na rabuwa da iyaye ba shiri. Gidansu Yusuf aka wuce da ita, Momy da Abba ma sukai musu nasiha sannan akai mata rakiya airport. Cikin jirgi babu aikin da take sai kuka, lallashin duniyar nan Yusuf yayi amma batayu shiru ba haka suka iso. *** Tsararren gida ne, wadda kaya da aka jerasu sun amshi gidan. Haneefah komai na cikin ya burgeta. Bayan kwana biyu su aunty Muhibbat suka koma gida. Haneefah abin babu yadda ta iya sai hakuri. Amma a duk sanda ta bude ido taganta cikin gidan Yusuf ba karamin jin dadi take jiba Da dare bayan ta idar da sallah tana zaune bakin gado yashigo yace tashi suyi sallah domin godewa mahaliccinsu daya kawo su wannan rana. Bayan sunyi dukkanin abinda aka koyar bisa sunnah yace zo muje dakina. Kamo hannunta yayi har suka iso. Tsarerren dakine babba. Gurin wardrobe ya nufeta ya bude side daya yace wannan dukkaninsu English wears ne. Daga yau su nake bukata ki rika sakamin. Ya bude daya side yace wannan kuma nighty ne. Daya bayan daya ya nuna mata ko ina, Haneefah gidan ya mata kyau. Sai dai cike take da tsoro domin yau zata kasance da Yusuf a makwanci daya. Tsaf ya ganota da tsoro dan haka ya kwantar mata da hankali yana cewa baki da lafiya yakamata ki kwanta da wuri ko... ganin haka yasa ta rage tsoron nata. _Bayan sati biyu_ Tsantsar so da kauna, kula da juna, kyautatawa da aminci ke dada yawaita tsakanin masoya biyu. A kullum yana godewa Allah daya hada sa da mata kamar Haneefah, domin ta gama hada komai wadda namiji ke bukata agun mace. Sau tari zai kura mata ido yana kallonta, shi kawai kullum cikin tsananin sonta yake ga tsananin sha'awarta da yake amma yana tsoron tabata domin gani yake kamar zata suma kamar yadda tayi kwanaki. Itama anata bangaren haka abin yake gunta, ta fahimci mijinta na bukatar ta saboda haka yau zata bashi mamaki domin ta gane nufinsa. Zaune take kamar kullum tana jiran isowarsa. Sanye take da wani English wear wadda yayi masifar mata kyau, ya fito da dukkanin surar jikinta tasha kwalliya. Jiransa take amma shiru baizo ba har karfe tara da rabi. Gabanta ne ya soma faduwa ganin har goma ta wuce bai zoba. Ta kasa zaune ta kasa tsaye ta soma zagaye falo. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼70 Dedicated to Batul Mamman Mrs💖 Da sauri Yusuf ya taro ta. Haneefah na kokarin tureshi amma ya rungumeta yana tambayar are u alright? Bai gama rufe bakinsa ba ta gama wanke shi da amai. Baibari ta tashi ba saida ya tabbatar ta gama sannan ya taimaka mata suka nufi toilet. Shiya gyara ta sannan ya gyara inda ta bata yana mata sannu. Yana kokarin canza kayansa tace pls kada fesa turare shi ya sani amai. Yana gama shiri yace tashi mu tafi asibiti. Juyarda kanta tayi tace ni zan samu sauki a gida. Zama yayi kusa da ita yana cewa meke damunki? Cikin kuka ta matso ta fada jikinsa tace babyn mu na wahalar dani. Cikin rashin fahimta yace baby? Gyada masa kai tayi tace eh ciki ne dani wata uku. Dagota yayi cikin tsananin farin ciki yace what! Ciki gare ki? Rungumeta yayi cike da murna yana cewa Alhamdulillah. Allah kaine abin godiya, yace tashi muje asibiti a dada dubaki Cikin shagwaba tace ni bana so su hada ni da magani. Yusuf ya shiga lallashin ta dakyar ta amince suka tafi aka dubata. Tun daga wannan lokaci tattalin ciki ake, Yusuf baida hira sai na baby. Har Haneefah ta samu sauki a wannan lokaci ne Yusuf yace dama yana son biya musu kujerar hajji amma su saita haihu zata tafi shima ya fasa tafiyar. Labari dayazo kunnen Haneefah tayi tsananin murna domin Yusuf ya biyawa iyayenta kujera... zamansu gonin ban sha'awa. **** Watanta takwas amma kamar yau zata haihu domin cikin yayi nawi kuma yayi babba. Wannan lokacine take so ta tafi kano amma Yusuf bai amince da tafiyar ba gashi ba aiki take ba sai zaman gida. Zaune take tana waya da Raihana, basu manta da juna ba, Haneefah a kullum bazata taba mancewa da barrister ramlat da Dr Mubarak ba, sai Kevin, Rohan da Raihana wadannan mutane sun taimaketa arayuwa bazata manta da su ba. Yusuf zaune kusa da ita yana kallonta, shi tausayi yake bata yadda take fama da cikinnan amma ya lura kamar fishi take dashi. Bayan ta kammala wayarta ya dubeta yace dearie nifa banki tafiyarmu kano ba, wasu abubuwa nake kokarin yi saina kammala nake so mu tafi. Haneefah tace babu komai Allah kaimu. Ganin har yanzu bata huce ba yace toh shikenan dama so nake na maido da aikina kano sannan na kammala ginin da zamu zauna ciki shine... da sauri Haneefah ta juyo tace da gaske dearie? Gyada mata kai yayi Kokarin tashiwa take amma Yusuf yayi sauri tashiwa yaje ya rungumeta yace basai kin tashiba. Tsananin murnanta ta nuna mishi tare da tambayar yaushe yake tsammani? Yace duk sanda ya kammala zai sanar da ita. Anyi haka da sati biyu suka tattara suka koma kano, Haneefah murna dangi murna. Komawarsu da wata daya ta haifi yan biyu mace da namiji. Ranar suna namiji ya samu suna Muhammad ba'a dangana ga kowa ba sai annabinmu Muhammad (al'ameen) tsira da amincin Allah su tabbata gareshi. Macen taci sunan Momy(ummi). Rayuwa ya koma so wonderful tsakanin family biyu, Haneefah ta soma aiki a TH dake garin kano. Watannin yaranta biyar Yusuf ya mata albishiri da sabon asibiti daya bude mata. Tsananin farin ciki Haneefah take, tabbas rayuwa duk wadda ya fuskanci matsala toh tabbas zaiji dadin juriyarsa. Fatanta a kullum ya barta da mijinta cikin tsananin farin ciki ya karesu da sharri. Zaune yake yana aiki da laptop ta shigo rike da ummi a kafada ta kwantar da ita. Zama tayi gefen mijinta ta rungumo shi tace aikinnan ya'isa ka huta. Kashe laptop yayi ya juyo gareta yana cewa dama ke nake jira, kizo in samar wasu al'ameen kani.. zaro ido tayi tace da wuri haka? Yace nidai yanzu nake so...... Tammat bihamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki daya bani ikon kammala wannan littafi mai suna Dr HANEEFAH. Dalilin rubuta wannan littafin nawa dalililaine da dama amma babban abin shine HAKURI. Muddin muka kasance masu hakuri tare da barwa lamuranmu a hannun mahaliccinmu to tabbas zamu ribance abin fiye da tsammanin mu, hakuri a lokacin da ka rasa abu, hakuri akan abinda aka maka sannan kana da halin ramawa, hakuri tare da kau dakai akan abinda ya wuce in muka rike haka tabbas zamu ji dadin zaman rayuwa. BIYAYYA GA IYAYE Musani duk abinda muke a duniyar nan muddin bamu biyayya ga iyaye, bama neman albarkan su to tabbas muna cikin hatsari. Babu wani bawa da al'amarin sa zai gudana yayi daidai face yakasance mai yiwa iyayensa biyayya, iyaye ba abin wasa bane ko da gangan fushinsu na bin yara saboda haka mu guji yankewa yaranmu hukunci saboda wani sa'in mu da kanmu muke jefasu ga hakala. Duk da Yusuf na yiwa tsananin yiwa mahaifiyarsa biyayya amma saida ta hukunta shi da abinda bai kamata ba, wani abin takaicin wasu iyaye har mallake yaransu maza suke, me yayi zafi? Keba gidan miji kike zaune ba? Waya takura miki? Abinda zaki hukunta matar yaronki bakisan Allah zai saka mata ba? Ko ke babu yara mata gabanki? In ma tsoron kada a mallake miki yaro ake mesa bazaki dage masa da addu'a ba? Ko kinsan addu'ar uwa ga danta karbebbene? Mu kula kada mu daurawa yaran mu abinda zai cutar dasu. YAN UBA Duk abinda kishiya zata miki kada ki kuskura ki koyawa yaranki kishi domin alhaki zaki dauka, kamata yayi ki nuna musu kaunar yan uwansu muddin suka girma suna kuntata musu zaki gani da kansu zasu ja jiki su daina kula su batare da YAN UBANCI BA. NIYYA. A duniyar nan duk abinda dan adam yayi niyya toh tabbas zayyi/zai zama sai dai yana da karancin NIYYA. In ilmi kake so ko daukaka ko menene mutum zayyi amma muzamto masu kyautata NIYYAR MU, misali ga Haneefah. Bata so karatun likitanci ba amma da tayi NIYYA lokaci daya ta zamo Dr HANEEFAH, ba bangaren daya bama bangarori da dama. Saboda haka mu koyarda yaranmu kyakykyawar NIYYA ba buri ba. Sannan ina rokon iyaye muzamto masu gyara tarbiyya yaran mu da dabi'unsu, yazamto kalmomin addini ya zauna abakinsu ba wadda suke gani a cartoon ba. YARDA DA ADDU'A. A kullum mu kasance masu ambaton Allah, mukasance Allah shine jin mu, ganin mu, tafiyarmu komanmu. In abu yasame mu kafin mu yanke hukunci mu rika ambaton Allah. Muddin muke rike haka to tabbas zamu kasance masu jin dadin zaman duniya domin duk wadda yace Allah ya gama komai. Yadda Haneefah ta tafiyar da rayuwarta yayin da ta rasa Yusuf, da yadda ta dage da addu'a da yadda ta yarda da addu'an ta shi ya kaita ga wannan matsayi, yarinya ce karama amma tasan yadda ta tafiyar lamuranta wato tabarwa Allah. Shi addu'a amsar shi ya kasu kashi uku; 1. Eh an amsa maka yanzu 2. Eh an amsa maka amma sai zuwa wani lokaci 3. Aa abinda ka roka ba shine mafi alkhairi agare kaba amma zamu baka abinda yafi alkhairi. Yan uwa me muke bukata daya wuce zabin Allah? Me zamu gani dahar zai rudemu a a wannan duniyar? Duniyar da zamu barta. Shin kina son jin dadin zaman aure? Kiyi niyya zakiyi aure badon jin dadin zama ba zakiyi aure saboda ita ibada ce. Mu koyawa yaranmu da kannen mu wannan dabi'a sannan muyi musu nuni ba'a gaggawa a al'amarin aure. Mu tuna lokacin da Momy tayi calling off aurensu, biyayya Yusuf ya mata, itama ma Haneefah hakuri tayi amma bayan shekaru suka zo suka sake haduwa shin ko kunsan tarayyarsu a wannan lokaci babu alkhairi? Lokaci da dama muna ganin abu tamkar alkhairi ne amma sharri ne, sharrin kuma zamu ga alkhairine. Idan ka zamanto Mutumin kirki,mai kyakkyawar manufa a rayuwa, sai Allah ya hadaka da mutanen kirki masu kyawawan manufofi irin naka, domin samun cikar burinka. Koda ka samu matsala da wani daga cikin Jama'arka, kar ka fidda tsammanin alkhairi daga gareshi. Watakil idan kayi masa uzuri ka kyautata zato gareshi, ka yafe masa, sai alkhairi ya biyo bayan hakan. Mutanen kirki anan duniya, sune ma'abotan alkhairi a lahira. Kuma mutum ba ya zama mutumin kirki har sai tunaninsa da ayyukansa duk sun zama na kirki. Kayi kokari ka chanza rayuwar wani bawan Allah daga mummuna zuwa kyakkyawa. Ko ta hanyar shawarwari, ko taimako, ko agaji, ko kuma ta dalilin afuwarka. Allah shi bamu dacewa aduniya da lahira. Ameen. Gaisuwa ta musamman gare ki BATUL, nagode da gudun mawarki, nagode kwarai Allah kara lafiya ya albarkaci zuria ameen. Gaisuwa gareku makaranta littafin Dr HANEEFAH. Ina ganin sakonni. Nagode da addu'ar ku sosai Allah sadamu da alkhairi. Sannan ina bukatar addu'ar ku aduk inda kuke. Dr HANEEFAH is my first novel and last. _Bintu Ramadan take muku fatan alkhairi_