2/2/24, 10:13 PM - Messages to yourself are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more. 2/7/24, 4:18 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: KOMAI NISAN JIFA free novel* *HAKAN BA KUSKURE BANE paid book # 300* Anda now馃憞馃徎馃憞馃徎 *RASHIN IYAYE* *(Babbar musiba) free novel* *馃實MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION馃摎馃枈* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.馃馃徎``` *_________________* Ina farawa da sunan ALLAH mai rahma mai jin 'kai, tsira da aminci suqara tabbata ga shugaba ANNABI abun za'bi da alayensa da sahabbansa da matansa da ''ya'yansa da duk wanda yake riko da sunnarsu har izuwa ranar sakamako, bayan haka ina mikawa ALLAH subhanahu wata ala godiya daya bani ikon fara wannan littafi *RASHIN IYAYE* ALLAH yasa yadda nafara lafiya ALLAH yasa nagama lafiya, ALLAH yabani ikon rubuta abunda zai amfanar da al'uma, inda nayi kuskure kuma ALLAH yagafartamin馃檹馃徎馃檹馃徎馃檹馃徎馃檹馃徎 Na fara rubutawa wannan littafi ranar lahadi hijirar maaiki nada 8/6/ 1444 wanda yayi daidai da 1/1/2023 *PAGE 0NE 1* " Yaudai wata yakusa qarewa ayi salary kibani kud'ina da kika ranta" cewar wata matashiyar mata wanda a'kalla zatayi 40 years, tana kallon matashiyar budurwar da take kusa da ita a zaune, nasani aunty, ki qaramin wani kud'in dan ALLAH cewar budurwar a kalla zatayi 18 years,jin zazzakar muryarta yasani dubanta, fatabarakallah ahsanil kaliqin haka na fad'a azuciyata ni Rabiatu, saboda ganin kyakkyawar halittar da tayi magana, ALLAH ya zuba halitta anan ga kyau ga fari kuma, masha ALLAH, to shikenan zan qara miki wasu amma ana baki kud'inki biyar bazan rage miki ba saikin bani, cewar matar da aka kira da aunty,to aunty bari na dauko miki littafin da kike rubuta kud'in dana karba(... Lallai wannan abun nayine..)to cewar matar, aikuwa sai gashi ta dauko littafin matar babu kunya ta rubuta sannan, ta zuge post d'inta, ta dauko 1k tabata sannan tasa hannu ta karba tana ficewa daga gidan, itakam aunty murna take da hakan..... Bayan fitar ta daga gidan provition taje, ta siyo milk. Sugar, lipton(... Burinta kenan anan kud'inta suke qarewa...) Bayan tadawo gida d'akinsu ta shiga, ta cire mayafinta, sannan ta zauna tafara tunanin duniya.... Wai itace yanzu kayan da zatayi break fast dashi saita siya, kuma wacce take ranta mata kud'in itace aunty, rayuwa kenan wata rana sai labari, banda halin rayuwa ina ita ina wani rance, tunanin da takeyi a ranta kenan, bata saniba saijin hawaye tayi yana zuba daga fuskarta, shigowar da khadija tayi yasa ta kuma goge hawayenta , domin batason tasan halin da take ciki, in ma tasani ita bazatasan me takewa kukanba, haka wannan budurwa take kasancewa a kullum indai tana tuna rayuwarta to saitayi kuka musamman idan ta tuna 'yar uwarta.............. ******* ****** "Kiyi sauri kizo nabaki wannan kud'in daya rage kije kisiyo garri saiki jiqa kusha keda *Hunaif* cewar wata dattijuwar mata a kala zatayi 60years, wacce akayiwa magana ta fito jiki babu kwari da hijab a hannunta tana sanyawa, ina duban fuskarta bansan lokacin da book d'ina da biro na danake rubutu dashi ba suka fadi a kasaba, saboda tsananin kyaun wannan halittar, fatabarakallahi ahsanul kaliqin haka nafad'a, inq yunkurawa 'kasa domin daukar book da biron dana yar a kasa, lokacin harta qaraso wajen matar" baabah kawo kud'in, masha ALLAH jin wannan murya tata mai taushi da dad'in sauraro, mika mata kud'in tayi, tasa hannu ta kar'ba jiki babu kwari sannan ta fice cikin tafiyarta a nutse, itakam baabah ganin ta kar'bi kud'in ta fitane yasa ta koma ta zauna a kan tabarmar datake shimfid'e a d'akin.......... Tunani takeyi a ranta na halin da suke ciki itada wad'annan yara guda 2,wanda kullum saita tausaya musu, a halin da suke ciki,wai sune suke cikin wannan hali,wanda ko a mafarki bata ta'ba tunanin zasu kasance a hakan ba,koda yake dama ita rayuwa haka take, ALLAH ne me yadda yaso da bawansa, itakam taga abun mamaki sosai, koda yake babu mamaki Acikin lamarin mutane.......... Tana wannan tunanin taji sallamarta har ta dawo daga aiken, "gashi baabah nasiyo bari najiqa mana, cewar budurwar tana cire hijabinta da "to" baabah ta amsa tana cire tagumim datayi na tunani, bayan ta jiqo garri d'in ne tace "baabah gashi, bari naje ta taso *Hunaif*"(... Barcin wuya yake, na yunwar dayasha tun safe...) Yaron ta d'auko wanda jikinsa babu kwari, zaunar dashi tayi a jikin baabah, tana fara bashi ya kar'ba yafara ci hannu baka hannu 'kwarya, itama zaunawa tayi tafaraci da cokali(... Wanda har sannan bata saba dashi ba, kawai tana cine maganin yunwa, wataram har amai takeyi____ lallai FAN'S munso muji shin su wane wannan iyalai?...) itama baabah fara ci tayi, haka wannan iyalai suke kasancewa a kullum ta ubangiji, idan sun samu suci idan basu samu ba kuma suyi haquri.............. Dagajin wannan salon daban yake da sauran kudai kubiyoni domin kuji sakon danakeson isarwa gareku akwai ban tausayi da marachi da zallar cin amana da zalunci Please COMMENT'S and SHARE in other group's 馃檹馃徎馃檹馃徎馃檹馃徎 Nice dai taku Rabiatu Aminu MUHAMMAD 'yar mutan kanawan dabo馃拑馃徎馃拑馃徎馃拑 2/7/24, 4:18 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: 鉁嶐煆籇aga Al 'kalamin *Rabiatu Aminu MUHAMMAD* 鉁嶐煆籑arubuciyar *KOMAI NISAN JIFA free novel* *HAKAN BA KUSKURE BANE paid book # 300* Anda now馃憞馃徎馃憞馃徎 *RASHIN IYAYE* *(Babbar musiba) free novel* *馃實MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION馃摎馃枈* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.馃馃徎``` *_________________* Ina farawa da sunan ALLAH mai rahma mai jin 'kai, tsira da aminci suqara tabbata ga shugaba ANNABI abun za'bi da alayensa da sahabbansa da matansa da ''ya'yansa da duk wanda yake riko da sunnarsu har izuwa ranar sakamako, bayan haka ina mikawa ALLAH subhanahu wata ala godiya daya bani ikon fara wannan littafi *RASHIN IYAYE* ALLAH yasa yadda nafara lafiya ALLAH yasa nagama lafiya, ALLAH yabani ikon rubuta abunda zai amfanar da al'uma, inda nayi kuskure kuma ALLAH yagafartamin馃檹馃徎馃檹馃徎馃檹馃徎馃檹馃徎 Na fara rubutawa wannan littafi ranar lahadi hijirar maaiki nada 8/6/ 1444 wanda yayi daidai da 1/1/2023 *PAGE TWO 2* Bayan tagama tunanin ta tashi ta fita, d'akn aunty ta shiga, sannan tace mata, Aunty me za'a girka ne yau naga yamma tayi, me za'a girka kuwa *HADIYYAH* kinsan dai yau babu abun girkawa, Alhaji baiyi aikeba, wayyo Aunty yunwa nakejifa, gashi Zahrah itama zata dawo daga school kuma, cewar *HADIYYAH* tana nuna alamun tausayawa ga rayuwarsu gaba d'aya, sallamar 'yan makaranta khadija, Farouk, Haydar zeenah, suna zuwa kowanne ya cire takalminsa Farouk yafara magana Aunty ina abincin mu? Hakan ne yasa aunty d'ago kanta ta zubawa wad'annan yara idanu, ba komai takeba sai tausayinsu , wai abinci shine yake musu wahala? Rayuwa kenan wata rana sai labari, yau babu abinci Farouk sai haquri abunda aunty ta fad'a masa kenan, sauran khadija Haidar da zeenah jikinsu sanyi yayi suka koma gefe d'aya suka zauna ko sucire unifoam, itama *HADIYYAH* yaran sun bata tausayi sosai, tashi tayi ta koma d'akinsu, tashiga tunani, itakam da ace kud'in data keyi na lession mai yawane aida ta ringa siyowa 'yan uwanta kayan abinci, to amma 5k nawa take me zata siyo musu da ita, wannan tunanin take azuciyarta, to amma kuma ai kud'in itama a provition yake qarewa , to in hakane meyasa Aunty in tana da kud'i bazata dinga musu girki ba saidai ta dinga ara mata ita? Wannan tunanin takeyi a kullum , Farouk ya leqo d'akin yaya *HADIYYAH* kizo inji aunty, ganinan zuwa to, fitowa tayi ta nufi d'akin da aunty take sannan tace "gani Aunty" ok dama aikenki wajen Maryam zanyi kice tabani sakon,to aunty, idan tabaki kije kisiyo shinkafa rabi sai kuma man kuli da barkono, da maggi,kizo adafa to Aunty cikin murna ta fad'a, suma yaran murna suka fara jin abunda Aunty tace, taje ta kar'bo Aiken ta siyo komai, ta dawo gida, sannan Aunty tabawa khadija kud'i tasiyo icce a makota(... Nifa mamaki ya kasheni sosai da tambayoyi, kuma nasan haka FAN'S, in gaya muku, wlh gidane me kyau gini iya gini, gashi gidan daga gani irin na masu kud'in nanne, amma kuma a haka gidan yafara lalacewa, ga abun hayaqi, ko ina kam gashinan sai a hankali...) Haka khadija takawo icce d'in khadija ta kunna wuta, lokacin kuma har angama tsintar shinkafar, aka d'ora abincin, khadija ta daka yaji, har aka gama kowa aka zuba masa babu yabo babu fallasa dan bata ishesu ba, kuma lokacin zahra(... Yayar HADIYYAH ce daka gani...) ta dawo itama daga school(naga kam university take zuwa, school of hygyne, to ya haka kuma FAN'S suda abinci yake musu wuya, aina take samun kud'in hidimar school d'in? Muje dai zuwa) d'in, taci abincinta itama, haka suke rayuwa kullum.............. ********* ******** Ki shiya kizo ku tafi makarantar nan *HIDAYAH* tun d'azu *hunaif* yake jiranki fa, dad'i na dake akwai nauyin shiri, cewar baabah tana gyatawa hunaif takalminsa, sunje islamiyyah sun dawo kam, *HIDAYAH* take cewa baabah yaushe zamuje KANO? Nikam nayi kewar 'yan uwana ALLAH, taqarasa maganar cikin shagwa'ba, itakam baabah kallon *HIDAYAH* takeyi tana mamakinta, sannan tayi magana, lallai yarinya abinci namana wuyar samuwa, balle kud'in motar zuwa KANO, kina kallon wata yayi nisa kawunki bai mana aikeba, kuma kud'in da ake kawo mana naku wata yayi nisa, kina kallo munci bashi, ana kawo kud'in zan biya bashi ragowar kuma mu siyi abun bu'kata, KANO a rabu da ita ba Yanzu ba , baabah taqarasa tana kallon idon *HIDAYAH* shikenan baabah, ALLAH yakawo mana kud'i mai yawa, mufita daga wannan halin, ta qarasa magana idonta nakawo ruwan hawaye,baabah tace kidaina kuka man kina tadamin da abunda ya sameni shekarun baya fa, ki dinga addua kinji ALLAH yana sane damu zai kawo mana mafita,to baabah ina addua kullum ai yawwa 'yar albarka....... Kullum maganar *HIDAYAH* kenan yaushe zamu kano baabah, naga 'yan uwana? Hakan yana sa baabah cikin kunqi da tunanin abunda ya sameta, amma kuma in sha ALLAH zasuje KANO, ko dan tagano 'yan uwa da 'ya'ya da jikokinta wadanda ta jima bata gansu ba......... Baayi kwana biyu ba aike yazowa baabah, ta kudi 10k da sabulu da man shafawa, haka ake kawo musu lokaci zuwa lokaci , amma wani lokacin ba'a kawo musu, wuri, ranar cikin walwala suka tashi, ta biya abunda ake binta, sannan tasiyo musu abun bu'kata, haka suke Rayuwar su.............. In sha ALLAH next page zamuji Tushen labarin ta yaya wad'annan iyalai, kubiyoni wannan salon daban yake akwai fadakarwa da waazantarwa da ban tausayi........ Please COMMENT'S and SHARE in other group's 2/7/24, 4:18 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: 鉁嶐煆籇aga Al 'kalamin *Rabiatu Aminu MUHAMMAD* 鉁嶐煆籑arubuciyar *KOMAI NISAN JIFA free novel* *HAKAN BA KUSKURE BANE paid book # 300* Anda now馃憞馃徎馃憞馃徎 *RASHIN IYAYE* *(Babbar musiba) free novel* *馃實MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION馃摎馃枈* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.馃馃徎``` *_________________* Ina farawa da sunan ALLAH mai rahma mai jin 'kai, tsira da aminci suqara tabbata ga shugaba ANNABI abun za'bi da alayensa da sahabbansa da matansa da ''ya'yansa da duk wanda yake riko da sunnarsu har izuwa ranar sakamako, bayan haka ina mikawa ALLAH subhanahu wata ala godiya daya bani ikon fara wannan littafi *RASHIN IYAYE* ALLAH yasa yadda nafara lafiya ALLAH yasa nagama lafiya, ALLAH yabani ikon rubuta abunda zai amfanar da al'uma, inda nayi kuskure kuma ALLAH yagafartamin馃檹馃徎馃檹馃徎馃檹馃徎馃檹馃徎 Na fara rubutawa wannan littafi ranar lahadi hijirar maaiki nada 8/6/ 1444 wanda yayi daidai da 1/1/2023 *PAGE THREE 3* Malam Yassir yanada rufin asirinsu sosai, saboda komai yanawa 'ya'yansa, matarsa guda d'ayace mai suna sakinah, sunada 'ya'ya biyar, bilkisu, zainab, isma'il Ammar, Asiya sulaiman... Ammar wanda ake kira da *BIN YASSIR* mutum ne mai haquri sosai haka tun tasowarsa, har yayi Aure, inda ya auri matarsa mai suna *Ummu Ruman* sun zauna cikin rufin asiri a gidan haya, har suka haifi ' yarsu ta farko mai suna Zakiyyah, lokacin kuma ALLAH ya fad'awa bin yassir kofofin arziqi, domin yakai mahaifiyarsa ta sauke farali, mahaifinsa kuma dama shekararsa d'aya kenan da rasuwa,lokacin Arqizi yayi yawa shima yaje ya sauke faralin, kuma ya canza musu gida mai tsarin kyau ankashe kud'i wajen ginin, haka Ummu Ruman takoma sabuwar unguwa itada yarinyarta zakiyyah, arziqi yanata yawa ga Bin yassir, sun kuma haifar yarinya mai suna zahra, lokacin kuma ALLAH yabawa Bin yassir Ikon qara aure, inda ya auri *Sa'adatu* tunda tazo gidan tasamo fada a wajen mai gida, saita farawa ummu Ruman makirci,ta had'ata da mijinta, tana ganin magrib tayi zata wanke kanta dama ta tsefeshi tafara ihu , alamun asiri wai, gashi tana ganin yadawo zata shige d'aki tadinga raku'bewa wai ummu Ruman ta takurata, a wannan hali ALLAH ya azurta ummu Ruman da haihuwar tagwaye duk mata, wad'anda ALLAH yazuba musu kyau, yarane tun suna jarirai farare ga hanci masha ALLAH, ko mamansu daqar take ganesu, gaskia ansha shagali iya shagali a haihuwar twins, wanda Bin yassir yayi bajinta sosai, Sa'adatu yabada kud'i yace taje tayowa twins siyyayah suda mamansu, haka kuwa taje tacinye kud'i tasiyo abunda takeso ta kawo, ALLAH sarki ummu Ruman babu abubda tace, tabarta da ALLAH, Ranar suna kuwa in kunga dangi FAN'S ba'a magana, Maman Bin yassir kwana tazo tayi a gidan washe gari tawagarta 'yan taro sukazo, haka akasha wannan budiri yara sukaci sunan HASSANA ana kiranta da (Hadiyyah) HUSSAINA kuma (Hidaya) ake kiranta, haka wad'annan twins masu kama d'aya suka taso suda 'yan uwansu Zakiyyah da zahrah, kunga kenan FAN'S Ummu Ruman batada d'a namiji ko d'aya, shekarar 'yan biyu 1 a duniya, lokacin sunyi wayo abunsu, kamarsu ta dad'a fitowa, ga gashi masha ALLAH, ta abu daya ake banbancesu ta Hadiyya akwai kulafuci bata yarda da kowa sai Ummynta, itakuwa Hidayah batada rigima haka ake zuwa d'aukarta raino takai yamma acan amma Hadiyyah kullum tana gida......... Lokacin kuma Sa'adatu itama ALLAH ya azurtata da haihuwar d'a namiji, mai suna Yassir ana kiransa da Alhaji wanda 'kiri_'kiri Bin yassir yasanyata a mota da d'anyen jiki suka tafi siyayyar haihuwa, wai itakam tace bataso Ummu Ruman taje ta siyo mata, haka Ummu Ruman tasa musu ido, sa'adatu irin mata masu kissa da kisisina be, domin wani fannin kissa tafi asiri...... Wata sabuwa kuma ai tun lokacin da sa'adatu ta haifi d'a namiji sai, hajiya sakina wato uwar miji da sauran 'yan uwa aka farawa ummu Ruman habaici, ai yanzu Ammar yasan ya haihu, amma kizo kicikawa mutane gida da 'ya'ya mata, itakam ummu Ruman idone nata, domin shagali da bidirin da akayi ko twins lokacin sunansu ba'ayi hakan ba, a haka dai Ummu Ruman tadinga ganin ikon ALLAH a sarari qiri qiri ake nunawa ya'yanta banbanci wai don suna mata...... Arziqi ya fad'ad'a ga Ammaru, lokacin yasiyi motar hawa, yanawa iyalinsa komai na rayuwa, ita dama zakiyyah tana wajen kakarta wato hajiya sakinah, kuma tana nuna mata kulawa, saidai an sangartata gatanande dai komai bata iyaba tun tana qarama Ummu Ruman bayan twins, ta haifi zeenah da, khadija.. Itama sa'adatu bayan Alhaji, dayake tare suke haihuwa ta haifi Farouk da haidar...... Kuma a wannan shekarun saida sa'adatu ta 'kulla makircin da Alhaji Ammar ya saki Ummu Ruman akan abunda bashida dalili........... Yanzu aka fara, wannan salon daban yake da sauran kuci gaba da biyoni 'yan amana Please COMMENT'S and SHARE in other group's 2/7/24, 4:19 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗🎗️🎗️🎗️🎗🎗️️🎗️🎗️ ✍🏻Daga Al 'kalamin *Rabiatu Aminu MUHAMMAD* ✍🏻Marubuciyar *KOMAI NISAN JIFA free novel* *HAKAN BA KUSKURE BANE paid book # 300* Anda now👇🏻👇🏻 *RASHIN IYAYE* *(Babbar musiba) free novel* *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` *_________________* Ina farawa da sunan ALLAH mai rahma mai jin 'kai, tsira da aminci suqara tabbata ga shugaba ANNABI abun za'bi da alayensa da sahabbansa da matansa da ''ya'yansa da duk wanda yake riko da sunnarsu har izuwa ranar sakamako, bayan haka ina mikawa ALLAH subhanahu wata ala godiya daya bani ikon fara wannan littafi *RASHIN IYAYE* ALLAH yasa yadda nafara lafiya ALLAH yasa nagama lafiya, ALLAH yabani ikon rubuta abunda zai amfanar da al'uma, inda nayi kuskure kuma ALLAH yagafartamin🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Na fara rubutawa wannan littafi ranar lahadi hijirar maaiki nada 8/6/ 1444 wanda yayi daidai da 1/1/2023 Note........ 'yan amana kuci gaba dasani acikin adduar ku akan ALLAH yabani lafiya, yanzu dai ga wannan babu yawa, da babu gwara babu dadi, idan naji sauki ssai zan dinga muki POST mai yawa wann ma karfin hali nayi wlh *PAGE FOUR 4* Yau da gobe taqi karfin wasa a wannan hali ummu Ruman taci gaba da zama acikin gidansu gaban iyayenta,kuma tana cigabata da addua akan ALLAH yadawo mata da hankalin mijinta akanta, domin tasan wannan tuggun Sa'adatu ne ba komai ba, Amma Babu abunda zatacewa Ammaru domin iya soyayyah da tattali ya nuna mata, wannan abun yasamo asali ne tun daga lokacin da ya auro sa'adatu shikenan, yafara sauya mata, ta taallaka hakan da makircin Sa'adatu(... Aikuwa kam ki kiyayi kanki sa'adatu akwai ranar kin dillanci ranar da ko kud'i aka baki bazakiyi hakan ba....), itakam zakiyyah lokacin dama tana gidan hajiya kaaka, kuma har lokacin batada saiti, goyon kaka ce , amma kuma tana zuwa wajen ummunta tunda dama unguwa d'aya suke, ita kuma zeenah ce kawai a hannunta, can gidansu kuma akwai zahra *Hadiyyah* & *hidayah* sai kuma khadija(.... Wad'annan yara ALLAH ya kiyayeku ya albarkaci rayuwarku dai........... ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ Bangaren su Zahra da 'yan biyu da khadija kuwa abun gashinan dai yau shuni gobe daud'a, domin qiri qiri sa'adatu take saka zahra wanke wanke, wanda kuma suna dame musu, amma kuma sai tacewa yarinyar da take musu aikin, qaleta wasila itama tafara koyon aikin saboda itama macece,(.....lokacin fa zahra tana 6years fa....) Kuma babu abunda mahaifinsu ya raga musu dashi, amma zalunci irin na sa'adatu, sai wani alfahari takeyi wai ai itace mai 'ya'ya maza ai kuwa sai iya shegw suke musamman Alhaji wanda yafara tasawa shima,,,,,,,,,,,,,,,, ALLAH sarki *hadiyyah* tagafa ummu taqi dawowa kuma kullum tana ranta, aikuwa ta sarki kuka kullum tana barci tana mafarkin ummu batada magana saita ummu, tadaina walwala, hakan yasata kuma cuta wacce saida takwanta a asibiti, kuma ummu din taje dubata aikuwa tana ganinta, tai wata ajiyar zuciya ta qanqameta, tana dariya, cikin maganarta wacce bata fita sosai, saboda ciwom dayake damunta, ummuna ina kika tafi kika barmu nida *Hidayah*? Sai nemanci mukeyi, kowa gurin saida ya tausaya wannan rayinya, lokacin kuma Ammaru yana wajen ga hajiya ma tazo dubiya, itakam ummu Ruman babu abunda takeyi sai tausayawa 'ya'yanta,musamman *hadiyyah* wacce take da qulafuci tun tana 'yar qaramarta, kiyi haquri kinji *kyautar ALLAH ne* (... Haka take ce musu itada hidayah mafi yawan lokuta...) zan dawo ne unguwa naje, bakyaso nasiyo miki kayan wasane, inaso ummu cewar hadiyyah " to kidaina kukan kinji yakiji sauki kuma zan dawo gareku kinji, a hakadai ranar Hadiyyah tunda taga ummansu saita ware harda su dariya da wasa a ranar kuwa aka sallameau daga asibiti, wanda kowa yayi murna da hakan, musamman 'yar uwarta Hidayah, domin sun shaqu sosai zuwanta asibitin ya janyo, rage walwalarta, duk da ita dama batada hayaniya kwata kwata, amma kuma tanason Hadiyyah d'in ta, 'yan biyu kenan masu abun mamaki (.... ALLAH kabamusu masu albarka👏....) Wanda kuma a ranar dayake sai dare aka salllamesu, hadiyyah bata san cewa ba ummu suka tawo gidaba, domin lokacin tayi barci, safiya nayi data duba daga babu ummu aikuwa saita saka kuka babu ji babu gani, nan danan zazzabi ya dawo yarinya tafara shidewa alamun zata suma kenan............... Lallai kam FAN'S anya kuwa hadiyyah meyake damunki kuma hakanan? Mujedai zuwa wannan salon daban yake da sauran..... Nice dai taku ✍🏻 Rabiatu Aminu MUHAMMAD 'yar mutan kanawan dabo💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 2/7/24, 4:19 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗🎗️🎗️🎗️🎗🎗️️🎗️🎗️ ✍🏻Daga Al 'kalamin *Rabiatu Aminu MUHAMMAD* ✍🏻Marubuciyar *KOMAI NISAN JIFA free novel* *HAKAN BA KUSKURE BANE paid book # 300* Anda now👇🏻👇🏻 *RASHIN IYAYE* *(Babbar musiba) free novel* *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` *_________________* Ina farawa da sunan ALLAH mai rahma mai jin 'kai, tsira da aminci suqara tabbata ga shugaba ANNABI abun za'bi da alayensa da sahabbansa da matansa da ''ya'yansa da duk wanda yake riko da sunnarsu har izuwa ranar sakamako, bayan haka ina mikawa ALLAH subhanahu wata ala godiya daya bani ikon fara wannan littafi *RASHIN IYAYE* ALLAH yasa yadda nafara lafiya ALLAH yasa nagama lafiya, ALLAH yabani ikon rubuta abunda zai amfanar da al'uma, inda nayi kuskure kuma ALLAH yagafartamin🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Na fara rubutawa wannan littafi ranar lahadi hijirar maaiki nada 8/6/ 1444 wanda yayi daidai da 1/1/2023 Note........ 'yan amana kuci gaba dasani acikin adduar ku akan ALLAH yabani lafiya, yanzu dai ga wannan babu yawa, da babu gwara babu dadi, idan naji sauki ssai zan dinga muki POST mai yawa wann ma karfin hali nayi wlh *PAGE FIVE 5* Hankalin Alhaji Ammaru a tashe, yafito da mota,lokacin Sa'adatu ta d'auko *hadiyyah* wacce lokacin a sume, lokacin dare yayi wajen 11:00pm ne duk yawancin yaran sunyi barci, amma idon *hidayah* biyu tana kusa da 'yar uwarta,wadda tayi kewarta kwana da kwanaki tunda ba tare suke kwana a asibiti ba,tana ganin halin da yar uwarta take ciki itama kukan tafara musu, a haka sa'adatu ta qaraso da *HADIYYAH* a hannunta itama *HIDAYAH* d'in biyosu tayi, babu 'bata lokaci Abby ya d'au hanya sai asibiti(... Da yake wani asibi ne na kud'i kuma 24hour ne...) Nan dana likitoci suka had'u akanta, kafin su samu numfashinta ya dawo........ Abby yacewa sa'adatu takoma gida saboda yara anbarsu su kad'ai, duk da akwai mai gadi,jikinta sai rawa yakeyi, wai ita a lallai taba tausayawa Hadiyyah d'in, wanda azuciyarta kuwa sai kwashe mata takeyi, saboda tasan wannan qarshe Alhaji yace zai mayar da Ummu Ruman, tunda rashin uwarta ne yasa mata wannan zazzabin da ciwon, hakanne yasa duk cikin 'ya'yan Hidayah, zahra da khadija, babu wacce ta tsana sama da Hadiyyah d'in, saqe_saqen datake a ranta kenan, Alhaji yace mata takoma gida, " to shikenan babu damuwa, amma kuma nabar hadiyyah kuma, ta fad'a cikin nuna tausayi, wanda shi kuma Ammaru hakan da sa'adatu takewa 'ya'yansa da nuna kulawa yakesa yake qara kaunarta a koda yaushe(... Lallai Ammar bakasan makircin sa'adatu bane...)........ A haka dai sa'adatu tadawo gida, cikin zuciyarta fal tsanar Hadiyyah, tana fatan ace ta rasu kowa yahuta......... Kafin safiya kowa yasan da cutar hadiyyah, abunka da Ammaru yanada kud'i, haka 'yan uwa kowa yadinga zuwa da abun arqikinsa, ana fadanci, hakama hajiya Sakinah tazo itada Zakiyyah(... Yayarsu Hadiyyah...) Lokacin da Ummu Ruman takuma zuwa hankalinta a tashe jin cewa washe gari ciwon hadiyyah yakuma tashi, tana barci lokacin da tazo, babu yabo babu fallasa haka suka gaisa da sa'adatu da sauran 'yan uwa........ Hadiyyah tana farkawa taga ummunsu, aikuwa nan ma dai kukan tafara, ikon ALLAH kuma 'yan uwa duk ana tare, shima Alhaji Ammaru yananan...... Ummu kidaina barina kina tafiya kullum sai nayi kuka, nida Hidayah, kuma kin tafi da zeenah bama wasa da ita, indai kika kuma tafiya ummu zantayin kuka, kuma kaina ciwo yakeyi, ta qarasa tana kukan, tare da rungume ummu d'in kowa a gurin ya tausaya musu, itakam ummu Ruman babu bakin magana, tadai rungumeta, amma cikin zuciyarta babu dad'i......... Nan dai Hajiya sakina tasan cewa cutar hadiyyah ya samo asali na rashin mahaifiyarsu a tare, anan kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa akan hakan, daga karshe dai Alhaji Ammaru yace zai mayar da Ummu Ruman d'akinta, Itakam ummu Ruman dama tana addua akan hakan kuma gashi ALLAH ya amsa mata rokonta, Ranar a asibitin ta kwana saboda jikin hadiyyah d'in, kuma ansamu cigaba sosai, kwanasu Uku aka basu sallama, kuma a washe gari aka mayar da AURENSU da Ummu Ruman, karkuso kuga murna wajen Hadiyyah........ Wata ba'ayi ba hadiyyah, takoma walwalarta ko yaushe tana maqale da Ummu, itakam hidayah dama gidan sauqi ce, su zahra da Khadija(... Ita datake kanwa ma bata kulafucin da Hadiyyah take...) Sa'adatu fa tahi hausin wannan kome da akayi na Ummu Ruman, amma kuma saita nuna kamar babu komai, ita kuma ummu Ruman tacigaba da addua tare da kulaa da 'ya'yanta, kunsan addua bata fad'uwa kansa a banza, idan sa'adatu tayi makaircinta karshe ya koma kanta, ko kuma yaqi tasiri......... Muje zuwa FAN'S yanzu wasan yafara wannan salon daban yake, RASHIN IYAYE labari ne na tsantar maraicin iyaye guda 2 akwai tausayi da dai sauransu muje ziwa zakuji duk anan gaba ✍🏻Nice dai taku Rabiatu Aminu MUHAMMAD 'yar mutan kanawan dabo💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) ✍️Daga Al 'kalamin *Rabiat Aminu Muhammad* Marubuciyar Komai nisan jifa📚 Hakan ba kuskure bane📚 And now *RASHIN IYAYE (babbar musiba🙆‍♀️)* Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu duk anan gaba zakuji 🌏MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu Nazari da Aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fada'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙 *__________________* *PAGE SIX 6* """Haka lokaci ya dinga tafiya,,, Ummu Ruman taci gaba da xama agidan mijinta Alhaji Ammar ta rungume "ya"yanta, tana Basu kulawa.... Tun daga sannan Hadiyyah ta samu lafiya, Babu wata cuta Kuma, Itama makira wato Sa'adatu tunda taga tadawo gidan Kuma, saita haqura da wannan makirce_makircen nata, suka zauna lafiya ta ciki na ciki ta baka na baka,kunsan dama xaman kishi..................... Lokaci yanata tafiya duk 'yan matan Ummu Ruman Zahra, Hadiyyah da Hidayah, Khadija da Kuma zeenah duk sun tasa musamman Zahra Hadiyyah da Hidayah... 'ya'yansa mata Zakiyyah(ita dama tana gidan kakarsu) da Zahrah duk ya siya musu gold abunsu, sun tasa sannan Zakiyyah tana da shekara 15 ita Kuma Zahra tanada 13...... Suma yara maxan Alhaji, farouk da Haidar kowanne Yana Masa Hidima(...'ya'yan Sa'adatu...) Zakiyyah 'yar gidan Kaka yarinyace,irin masu girman jikinnan baza kace 15years takeba, Amma duk Wanda yagani yasan akwai yarinta Kuma hutu ne yasa hakan,Domin kuwa Babu abunda takeyi gidan kaaka,daidai da girki,shara,wanke_wanke, duk bayi takeyi ba a gidan, gata yarinya mara wayo, ga'buwa, tana jss 3 .............. Ana haka mukhtar yaganta, saurayine zaikai 30years yace Yana sonta, aikuwa Hajiya kaaka ta ara ta yafa, saita Aurar da Zakiyyah a wannan lokacin, shikam Alhaji Ammar Dan bayanda zaiyi be,akwaishi da biyayyah, Amma Zakiyyah guda nawa take? Meta iya da za'a mata Aure yanzu, Bata iya komai na mata ba, Kuma ko candy batayiba..... ita dama Ummu Ruman Babu ruwanta da ita, tunda Hajiya kaaka ta dauketa, tabar mata ita, Amma Kuma rashin nutsuwar Zakiyyah Yana 'bata mata Rai, Kuma ko zuwa gidan batayi, balle ta dinga sat wasu aikace_aikace na gida, sannan ta dinga tsawatar mata, acikin tarbiyyarta to Amma Babu Hali...... Koda Alhaji Ammar yace mata wai Zakiyyah tanada masoyi itakam haka tace Allah ya kyauta, acikin zuciyarta cewa tayi Amma Zakiyyah tayi yarinta da aure, Nufin Mukhtar dama asan dashi, idan yaso idan tayi candy anyi auren Amma Ina....tunda yazo Hajiya kaaka taketa azalzala akan ayi_ayi ai auren(...kujifa fans sai kace wacce ake neman Kai da ita Allah yakyauta halin Hajiya kaaka...) Cikin qanqanin lokaci kuwa aka kawo kud'in Zakiyyah (yarinya sha_sha_sha) kowa yayi mamakin hakan, sai sannan Kuma Hajiya kaaka ta tasarwa Zakiyyah da koya mata abubuwa, Wanda batayi da to Allah yasadai Fan's ta koya d'in........ Anyi bikin Zakiyyah, Alhaji Ammar yayi mata Kaya nagani na fad'a, kowa yagani yasan 'yar gatace, saidai Allah yabada zaman lafiya......... Su Ummu Ruman ana daga gefe abunta, Domin itama a 'yar gayya taje bikin gidan Hajiya kaaka........ Shekara d'aya da Auren Zakiyyah ta haihu, Amma Babu Rai 'Dan,dayake da akwai kud'i, wajen babanta Alhaji Ammar ranar suna bakuga mutanen da sukaje sunanba, bakwace Babu 'Da ba, har sannan Zakiyyah anashan ga'bunta haka dai Mukhtar yake haquri da ita, shima yasan yarinya dama ya aura sai haquri...... ******** ******** Sai wannan Haihuwar Allah yabaiwa Ummu Ruman 'Da namiji, kar kuzo kuga shagalin da akayi, ranar sunan Hunaif, Anyi shagali da budiri, Alhaji Ammar yayi 'barin kud'i, ya wadata "ya"yansa maza da mata da suttura ta fitar suna, wannan Karan ma Sa'adatu Alhaji Ammar yabawa kud'i taje tasiyowa Ummu Ruman kayan Jaririn, itakam Bata damuba...... Alhaji Ammar kamar Bai ta'ba haifar namiji ba, Itama Hajiya sakinah tayi gayya sosai,(...ko kunya fans, ita datace Bata haifar namiji, sai mata...) Itama lokacin Sa'adatu tanada karamin ciki ajikinta..... Rayuwar gidan Alhaji Ammar Rayuwace ta Jin d'ad'i da walwala, Domin kuwa Babu abunda suka rasa na rayuwa, duk Wanda yagansu yasan suna cikin Gata.......basai sallah yakewa iyalansa d'inki ba, takalma da sauran abun amfani kuwa sai godiyar Allah komai a ajiye yake....... Suma matan nasa duk haihuwa saiya canza musu kayan d'akinsu, Alhaji Ammar akwai hidima ga iyalai...... Hakama 'yan uwansa, mahaifiyarsa ma kullum cikin kula da ita yake, danginsa ana sonsa saboda kyautarsa, indai. Yana dashi to zai baka, mutane nawa yakai hajji da umara.......... Zahra, Hadiyyah da Hidayah Khadija da zeenah, da Kuma Alhaji da farouk da Haidar suna cikin Gata Babu abunda suka rasa......... Allah yad'orqwa Alhaji Ammar son Zahra, komai tace tanaso xai Bata,hatta Keken d'inki yasai mata, lokacin ko iya Dunkin batayiba koyo takeyi, komai yace Zahra.... Twin's dinsa ma Yana nuna musu kuluwa Hadiyyah da Hidayah, yara masu kyau da shiga Rai komai nasu iri d'aya, saidai hali daya banbanta... Hidayah akwai haquri, magana Bata dameta ba, itakam Hadiyyah akwai tsiwa da iyayi, Bata ragawa Kowa inya tsokaneta ....... Su Alhaji an Fara Zama saurayi shima komai Alhaji Ammar Yana Masa, tare da sauran 'kannansa Farouk da Haidar......... A wannan lokacinne Alhaji Ammar yakamu da rashin lafiya, Hunaif Dan Ummu Ruman Yana da wata biyar a duniya, ita Kuma Sa'adatu tanada ciki wata takwas............. Muje zuwa Fan's yanzu aka Fara labarin RASHIN IYAYE babbar musiba labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu, akwai tausayi, cin amana, ha'inci dadai sauransu duk anan gaba Nice dai taku Rabiatul adawiyyerh 2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) ✍️Daga Al 'kalamin *Rabiat Aminu Muhammad* *08128131163* Marubuciyar Komai nisan jifa📚 Hakan ba kuskure bane📚 And RASHIN IYAYE (babbar musiba🙆‍♀️) Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu duk anan gaba zakuji *__________________* 🌏MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine fada'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙 *__________________* *PAGE SEVEN 7* " "Yan biyu Hadiyyah da Hidayah suna junior secondary, komai nasu iri d'aya ne, ba'a gane kamarsu, sai a halinsu,sunashan Gata sosai, Shima Alhaji school dinsu d'aya, ita kuma Zahra tana senior school, duk a makaranta d'aya suke pravet ce Mai tsada, su Farouk da Haidar,zeenah da Khadija Suma duk suna zuwa, duk dai wani Gata 'ya'yan bin yassir suna dashi Babu abunda suka rasa, saidai kunsan Rayuwa ba komai kake samu 💯 ba.... in kukaga inda 'yan uwan Alhaji Ammar suke nunawa 'ya'yansa da matansa kauna abun ba'a magana, yanada kud'i, Amma Kuma Suma suna Yi musu bajinta..... ********* ******* Cutar data samu Alhaji Ammar itace ruwane yake tarar Masa aciki, in kuka kalleshi kwa zata haihuwa zaiyi wata Tara, tun a sanan yabiya kud'i Domin yaje saudia ya roki ubangiji akan allah ya saukaka masa ciwon, Amma fafur Hajiya sakinah tace itace zataje umarar badai shiba, shida bashida lafiya,bazai yiwu yaje wata qasa ba, yace mata zai tafi da Ummu Ruman, saboda ita Sa'adatu tanada tsohon ciki lokacin, fafur Hajiya kaaka tace, vata amince ba, ita zataje umarar tayi Masa adduoin, ai bakin mahaifiya kamar yankan wuqa haka take, saboda biyayyah ta Alhaji Ammar haka ya haqura ya qale kaaka ta tafi umarar, Shi Kim yazauna a gida saidai Yana zuwa hospital,kuma likitansa duk sati Yana zuwa ya duba Shi, Ana haka kuma sai Kuma ciwon ciki Mai tsananin gaske ya kamashi, Wanda tun Yana yiwa kansa komai Saida yadaina komai Yi Masa akeyi,ana hakan aka ce Dole aiki za'ai Masa,a zuqe ruwan cikin nasa, shine yake saka Masa ciwon cikin, Allahu Akbar Alhaji Ammar ko magana baya iyawa baya sanin Wanda yake kansa...... A AKTH aka bashi kwanciya, idan kukaga yadda 'yan uwa da abokan arqizi suke tururuwar zuwa dubiya, saikuyi zaton biki akeyi, flaks da cooler abinci kala_kala,(... Wanda akeyi danshi Bai San anayi bama, mutane basayin Abu Dan Allah, da ace bashida kud'i ko mutum biyar Allah yasa suje dubashi balle ma har Sukai Masa abinci, mugyara 'Yan uwa Riya batada dad'i...) Allah sarki Ummu Ruman tunda Alhaji Ammar yafara rashin lafiya, itama tafara Rama, kana kallonta kasan Bata cikin kwanciyar hankali, sai kuka kawai aikinta, Yan uwanta suyita Bata haquri suna cewa cuta ba mutuwa bace, Amma itakam sai a hankali, ga Hunaif kunsan abunka da Bata ta'ba Haihuwar da namiji ba, yanada rigima sosai, yaita kuka baya yarda da kowa, kullum itace take zuwa asibitin, Sa'adatu ciki ya tsufa, ba kullum take zuwaba, lokacin itama jikinta yayi Sanyi duk wani iskanci ta ajiyeshi gefe,to Wanda ake danshi bashida lafiya,ga kuwa ciki haihuwa ko yau ko gobe..... Hajiya sakinah tanacan saudia tana ibadarta ta umara, tanawa danta Kuma adduar samun sauqi, tunda kullum suna waya taji yane jiki, harta dawo gida, dataga halin da Alhaji Ammar yake ciki tayi kuka,tayi Dana sanin hanashi zuwa saudia d'in, yanason zuwa Amma ta hanashi,gashi yanzu baisan Wanda yake kansa ba...... Yara kuwa duk suna samun kulawa sosai, wajen 'yan uwan babansu da abokansa, komai ana ajiye musu da abinci da sauran abun amfani, suna zuwa duba Abby,Kuma kullum sai sunyi kuka musamman Zahra sun shaqu dashi, Shi yasa ma aka hanasu zuwa asibitin, Amma Hajiya sakinah tace a qale yara suzo duba mahaifinsu dame zasuji ne..... Zakiyyah tana zuwa duba mahaifinta itama duk kwana d'aya,tana xaune da mijinta lafiya sai halinta na shashanci, Almubazzaranci,da Kuma ga'bunta da fita maqota,komai na gidanta maqota sune suke roqewa, gishiri Maggi, mai, tun abun baya damun Mukhtar har ya Fara damunsa, bacin ransa d'aya da ita shine rashin Zama a gida, ko ta tara Masa mata a gida, tun kafin Alhaji Ammar ya kwanta rashin lafiya aka Fara wannan sulhun tsakaninsu, Hajiya sakinah taje tai mata fad'a shima yaje, Amma da ankwana biyu zata Kuma komawa 'Yar gidan jiya,a haka yake haquri da ita darajar iyayanta(... Allah ya kyauta, musani cewa duk abubuwan da ake Mana kyautatawa yawansu darajar iyayanmu mukeci, da zarar qasa ta rufe musu Ido wlh Babu Mai kyautatawa garemu sai masu tsoron Allah kawai...) Matsalar Zakiyyah kenan........ Anyiwa Alhaji Ammar aiki lafiya, anata murna Domin ya samu sauqi, Yana iya gane mutane, Yana magana, ko sati ba'ayi da aikinba ruwan yadawo Wanda yafi nada, dama ta qirjinsa akayi aikin, aka saka roba ruwan yana biyowa, idan yaqarasa fita sai likitoshi su cire Masa, ruwan Yana qarasa fita aka cire Masa, ya samu lafiya, shine Kuma ba'ayi sati da aikin ba, wani ruwan take biyowa ta wajen da akayi aikin Yana fita da kansa, cuta tafi ta da Muni ya kunbura sosai, sai abunda Hali yayi dai Kam Alhaji Ammar......... Za'a fitar dashi waje ai Masa aiki, an saka ranar aikin, ana gobe, tafiya, wajen la'sar ummu Ruman tana sallah kusa da gadon da take kwance, tayi ruku'u, kenan taji hannun Alhaji Sharaf a gadon bayanta, ya Fad'o ........... Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Fan's meke faruwa da Alhaji Ammar ne? Muje next page Domin muji meke faruwa......... Akwai maraicin iyaye guda biyu a shekara d'aya,tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu ✍️Rabiat Aminu ( Oum Arqam 👩‍🍼) 2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) ✍️Daga Al 'kalamin *Rabiat Aminu Muhammad* *08128131163* Marubuciyar Komai nisan jifa📚 Hakan ba kuskure bane📚 And RASHIN IYAYE (babbar musiba🙆‍♀️) Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu duk anan gaba zakuji *__________________* 🌏MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine fada'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙 *__________________* *PAGE EIGHT 8* " Ummu Ruman Bata kawo komai a ranta ba, da fadowar hannun Alhaji Ammar,tayi tunanin barci yayi hannunsa ya langa'bo....... Bayan ta idar da sallah d'in, ta tashi Domin tagyara Masa hannun, Amma saime? Ganin idon Alhaji tayi abude Yana kallon sama, gigicewa tayi aguje ta fita zuwa Kiran likita, Yan uwa da suke waje ganin ta fito a gigice rudewa sukayi,a rude suka biyo bayan likitan dayake qoqarin shiga wajen Alhaji Ammar d'in, Koda likita,yashigo Yana dubashi yace saidai haquri, Alhaji lokaci yayi ya amsa Kiran mahaliccinsa, innalillahi wa Inna ilaihi rajiun...... Ummu Ruman tanajin abunda likita yafada,ta yanke jiki ta fad'i Babu numfashi, sauran Yan uwa kuwa da Hajiya sakinah dayake tana gurin tazo, sai koke_koke sukeyi...... Taimakon gaggawa likitoci ska farawa ummu Ruman, bayan an lullube gawar Alhaji Ammar (...Allah yajikan mazan jiya,Allah yasa yadda yan uwanka da abokanka suke kulaka da y"ay"anka ya Dore har bayan ranka, ba ganin Ido za'a yiba..) A motar asibiti aka saka gawar Alhaji Ammar zuwa gida Domin a kaishi makwancinsa, ita Kuma Ummu Ruman aka barta a asibitin Domin har sannan farfad'oba..... ********* ******** A can gida kuwa yau dama Sa'adatu batazo asibitin ba, saboda jiya tazo, ga ciki ya tsufa, daqar take Zama daqar take tashi,,, Yara sundawo daga makaranta,kowanne jikinsa a sanyaye, musamman Hadiyyah, wacce take da surutu, Da neman fad'a wajen Yar uwata Hidayah, Amma ranar shiru,fad'an da suke da Hidayah na saka Kaya,inta dauka tace natane,duk da irin kayan daya, ba'a banbancewa, Amma saboda rigimarta,,, Wayar Sa'adatu ce tayi qara, tana kusa da Alhaji, miqa Maya yayi, tana dubawa number ce Babu suna, Saida gabanta yafad'i, batasan kome yasaka hakan ba,tana d'agawa taji ance "Assalamu alaikum Sa'adatu, Isma'il ne(... 'Dan Autan su Alhaji Ammar ne,idan Baku manta ba...) Muryarsa Babu dad'i yake maganar, Sa'adatu tace Isma'il ya akayi? gabanta na fad'uwa tayi maganar, Isma'il yace Babu komai keda yara ku tawo gidan Hajiya, abunda yafada kenan ya kashe wayar.... Sa'adatu kallon wayar tayi gabanta Yana fad'uwa,jikinta yabata Babu lafiya, kodai wani abune ya samu Abby? (...Saikinje gidan kyagani Sa'adatu kyayi tambaya acan koba hakaba fans...) Jikinta Yana rawa tacewa yara kuzo muje gidan Hajiya kawunku yakira waya Wai muje can, Allah sarki yaran sai suka Fara kuka kodai Abby rasuwa yayi?suka Fara tambayar kansu,sunsan dai haka kurin baza'ace suje gidan Kaaka su duka ba, Hakan suka fita, suna kuka,Adaidaita sahu, suka samu, wasu sukayi goyo wasu suka hau sama, Alhaji Kuma ya zauna a gefe, (.. mota ta alhaji ce, Kuma tana ajiye bashida lafiya an rufeta da tampol dama, Babu Mai hawanta...) Kafin su qarasa har an d'auko gawar Alhaji Ammar, kofar gidan Hajiya sakinah cike take da mutane, suna qarasawa y"ay"an suka Fara kuka, Babu Wanda bai tausaya musu ba,maraici akwai ciwo.......... Ita kuwa Sa'adatu Allah ne yakaita cikin gidan lafiya Bata fad'i ba a qofar gidan, kuka take tayi kafin ta ta yanke jiki ta fad'i, Allah yakawo Wata makotansu Hajiya zasu shigo jana'iza, suka tallafeta,akayi d'aki da ita(... Inda ta fad'i akwai matsala fans faduwar Mai ciki, ga Kuma fargaba...) Gidan haka ya gauraye da koke_koke saboda shigowar iyalan mamacin, da kukan da sukeyi, akwai tausayi, ********* ******** Acan kuwa Asibiti daqar ummu Ruman ta farfad'o, da kuka ta farka, yanata sambatu, da kukan Rashin mijinta uban y"ay"anta, Kuma jigon rayuwarta, kwanciya suka Bata, saboda tasamu wutu zuciyarta akwai fargaba a tare da ita,magiya ta dinga yimusu, su qaleta take wajen mijinta, suyi sallamat kafin akaishi kushewarsa,dayake Mahaifiyarta ce da kanwarta ,Wanda suke uba d'aya, dama sune tare da ita, ganin halin datake, ciki baza abarta ita d'aya aciki Asibiti ba,Babu musu suka yarda suka tafi, zuwa gida,(...kiyi haquri ummu Ruman sai haquri mutuwa akwaita da d'aci...)...........😭😭😭😭😭😭 Domin sharhi ko shawara sai a tuntubeni a wannan number *08128131163* Saina jiku Yan amana Muje next page fans Abun akwai tausayi wlh , Kamar nayi kuka ✍️ Rabiat Aminu ( Oum Arqam 👩‍🍼) 2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cy82IooiC1LE5S0e2tkKcj RASHIN IYAYE (babbar musiba) *Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu* Na bude group dinnnan saboda comments ko sharhi na littafin RASHIN IYAYE (babbar musiba) please kubani hadin kai a kowanne lokacin danayi sabon post *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) *✍️Daga Al'kalamin ©️Rabiat Amin* (oum Arqam👩‍🍼) *08128131163* Marubiciyar Komai nisan jifa📚 Hakan ba kuskure bane 📚 And now RASHIN IYAYE (babbar musiba🙆‍♀️) Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu duk anan gaba zakuji....... *__________________* 🌏 MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️(M°W°A) *Kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine ta fada'akar da wa'azantar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙* *__________________* *PAGE NINE 9* "Lokacin da Ummu Ruman suka dawo gida, har an kammala had'a gawar Alhaji Ammar, Y'AY'ANSA da 'yan uwansa sai kuka suke abun tausayi, musamman da Ummu Ruman tashigo tana kuka, ga ranar datayi na lokaci d'aya..... Itakam Sa'adatu da aka shigar da ita d'aki, suma tayi aka dinga Zuma Mata ruwa, daqar ta ta farfad'o, tana kuka maicin Rai, Matar kawu Isma'il Hauwa ce akanta take lallashinta(... Irin Facalar da ake qawance sosaine, sunsan sirrin juna, tare suke komai, itakam dama Ummu Ruman tana gefe Babu abunda ya dameta dasu...) Tana farfad'owa tafara kuka, sai haquri ake Bata, ana cewa tayi haquri saboda cikin dake jikinta sai haquri....... Haka akakai Alhaji Ammar gidansa na gaskia, "Yan uwa da y'ay'a da Mata suka dinga kar'bar gaisuwa, abun tausayi, idan kaga Y'AY'AN kasan sunji mutuwar jajirtaccen uba a garesu, Wanda Basu rasa komai na rayuwa a wajensa ba....... Zakiyyah ma kamar ta susuce saboda rashin mahaifi, kullum cikin kuka take(... Sai haquri kinji, Allah yasa mutuwar tasa ki nutsu kidaina ga'bunta,da rashin sanin ciwon Kai...) Sai da Alhaji Ammar ya cika sati da rasuwa a gidan Hajiya sakinah duk akayi xaman ta'aziyyah, sannan iyalansa suka koma asalin gidansu...... Wanda komawar yaxamar musu wani tashin hankali, gashi suke kamar Abby zai dawo ne, Amma Ina yariga yatafi tafiyar da Babu dawowa,sai dai addua kawai zasu bishi da ita,daga iyayan har Y'AY'AN in suka zauna sai kuka sukeyi kawai, Babu Mai rarrashin wani, abokan Abby dasu kawu Isma'il sune suke ajiye musu kayan abinci, da kud'in cefane,Basu rasa komai ba, sai rashin mahaifi....... Sun koma makaranta yara, duk jikinsu yayi Sanyi, maraichi ba Wasa ba, Allah sarki Duk wannan neman fad'an da Hadiyyah takeyi a wajen Hidayah duk tadaina, ta Zama shiru_shiru, yanzu Babu surutu, Daman abunda ya banbantasu kenan, yanzu to sun xama iri daya, sai ankira sunansu wacce ta amsa sannan ake ganesu..... Haka masu takaba suke takabarsu, tsakanin Sa'adatu da Ummu Ruman, duk sun rame sun fita kamanninsu, musamman Ummu Ruman tun bayan rasuwar Abby taketa Rama yau da lafiya gobe Babu lafiya, kullum cikin tunani, a hakan har hawan jini ya kamata Mai tsanani.... Ita Kuma Sa'adatu kwanan Alhaji Ammar talatin da rasuwa, Allah ya sauketa lafiya, ta haifi yarta mace taci suna *Hafsat* Ranar da Sa'adatu ta haihu Rasuwar Abby ta zamo musu sabuwa, sunga daban da Abby yananan da tuni anfara dinke_dinke na suna, ga hidimar da zai Fara tun ranar Haihuwar har zuwa suna, hakan ma dai Babu laifi, (...Alhaji Ammar dama dayaga matansa cikinsu yakai wata bakwai,yake Ware kud'in da xai musu hidimar haihuwa dashi na kayan jarirai Dana Mai jego, yabawa Sa'adatu ta Fara siyayyah, kunsan dama itace Mai wannan hidimar daga nata har na Ummu Ruman itace Mai siyowa...) Ragon suna Kuma aka d'auka acikin kud'in Alhaji Ammar aka siya, hakan akayi wannan sunan, babu wani armashi..... Zancen Rabon gado dama Bari akayi aga abunda abunda Sa'adatu zata Haifa, sannan ayi...... Alhaji Ammar yana Gina wani gida a gaba da gidansa kad'an irin ginin dayake ciki Amma be kammala ba, ga sauran kadarorinsa, da kudadensa, ga motarsa...... Ita dama Sa'adatu ta kammala takabarta, tunda ta haihu, saura Ummu Ruman kad'ai... Haka sukaci gaba da zamansu, acikin gidansu, yau da dad'i gobe Babu dad'i, Ummu Ruman dai sai a hankali, ga Hunaif yaro Mai rigima yaita kuka kenan, baya yarda da kowa, bayan rasuwar Abby rigimar tasa ta qaru.... Zahra ta kammala secondary School d'inta, burin dama Alhaji Ammar Y'AY'ANSA suyi karatun boko, duk da Bai samu damar haka daga Zakiyyah ba akai Mata auren wuri. Anyi Mata registration na University,bayan tayi jamb dinta, ta samu gurbi a school of hygiene burinta kenan,tazama, jami'ar kiwon lafiya,gashi tasamu, duk da Tasha kuka, burin Abby kenan Allah yakaimu lokacin Inga zahrata ana zuwa jami'a , Ashe Allah bazaiyiba(.... Rayuwa kenan...) Suma su Hadiyyah, Hidayah,Alhaji sun shiga babbar secondry, Farouk Khadija,sun shiga qaramar secondary, Haydar da zeenah Kuma suna primary, Allah sarki yara sun Fara sabawa da rashin Abby tare dasu, shine kullum take kaisu makaranta, Amma yanzu ina, saidai suje su hau Adaidaita sahu, Rayuwar kenan........ Hunaif da Hafsat haka suka bud'i Ido Babu kulawar Abby a garesu, sun cika marayu sosai, gwanda ma Hunaif Abby yasanshi, ita Hafsat ma da cikinta ya rasu fa, Allah sarki Rayuwa...... An kammala musu rabon gadu lafiya, Kowane ambashi Hakkinsa, na Sa'adatu tanada, Alhaji,Farouk Haydar da Kuma Hafsat, kaso uku da rabi kenan sai tumunin takabarta Kuma, ita Kuma Ummu Ruman tanada, Zakiyyah,Zahra, Hadiyyah, Hidayah, khadija,zeenah da Kuma Hunaif tanada Kaso hudu kenan sai Kuma tumunin takabarta... Kungadai duk hassadar da Sa'adatu ta dinga yiwa Ummu Ruman lokacin batada d'a namiji, duk Dan gado ne tana ganin ai ita maxa ne da ita , ita Kuma Ummu Ruman Mata, Allah kenan gadai matan Nan da kuma Allah yakawomata Hunaif yasa tafi Sa'adatu d'in dai samun gadon, burin Sa'adatu kenan a kullum gado, ita kuwa Ummu Ruman baya gabanta, Allah sarki.......... Gidan da suke cikinsa a rabon Y'AY'AN Sa'adatu yazo, Shi Kuma Wanda Alhaji Ammar yafara ginawa yazo ana Ummu Ruman, Dan hakan an Ware kud'i za'a karasa gina mata, saita koma itada yaranta, ta barwa Sa'adatu nata.... Rayuwa kenan mutuwa Babu abunda Bata sawa,gashi yau Y'AY'AN Alhaji Ammar da matansa zasu rabu kowa yakoma gidansa..... Tun bayan Rabon gadon da akayiwa iyalan Alhaji Ammar saine Kuma? Sai Kuma duk wad'anda suke taimakawa iyalan NASA suka jabaya da taimakon(... Lallai fans kujifa, da dukiyarsu kenan za'a dinga ciyar dasu,kud'in makaranta,suttura, rashin lafiya da sauran abubuwan buqata,lallai fans akwai matsala kenan, Allah sarki Alhaji...) Kud'ad'en Alhaji Ammar Wanda take juyawa, su kawu Isma'il ya kar'ba, zaici gaba da juya musu, ribar ana musu amfani da ita, Shi Kuma har sannan dai Yana ajiye musu abinci, kud'in cefane Kuma cikin ribar kud'in dayake juya musu(... Lallai fans iyalan Alhaji Ammar suna cikin halin maraici fa, Babu idonsa komai yafara sauya musu...) Rayuwa fa tafara sauyawa iyalan Alhaji Ammar, ba yadda suke rayuwarsu kamar da ba, akwai qalubale akansu sosai,..... Kawu Isma'il shine yafanshi motar Alhaji Ammar yabada kud'in ta, dayake shima ba'a nesa yakeba, unguwar d'aya Amma da 'Dan tazara,duk kwana biyu Yana zuwa duba Y'AY'AN yayansa....... tun bayan da Sa'adatu ta haifi Hafsat, sai kuma kullum Isma'il yake zuwa gidan, Wai Ashe son Sa'adatu yake Wai zai Aureta, (... Kujifa fans d'an Autan su mijinta, mijin nata yafishi komai...) Farko 'boye_boye Sa'adatu ta Fara batasan Ummu Ruman tasani, itada ba yarinya ai tasan komai, a hakan har magana ta fasu, cewa Isma'il zai auri , Matar Wansa........ Masifa da bala'i kenan, cin amana Sa'adatu tayiwa Hauwa matar Isma'il kenan, qawartace qus da qus, tasan sirrinta itama tasan nata, gashi Kuma zata Aure Mata miji,ansha ruwan masifa da Hauwa tazo har gida tayiwa Sa'adatu cin mutunci na qarshe, "azzaluma Maci amana,kamar ni Hauwa Sa'adatu Zaki auri mijina, bayan kinsan sirrina, mijin ma qanin mijinki, Allah ya Isa tsakanina dake, tana kumfar Baki da fita,daga gidan, sunyi baran_baran da facalarta Kuma aminiyarta,wacce sukasan sirrin juna wanda Sa'adatu ko gezau abunta, Aure dai Babu fashi, saita Auri Isma'il.... Shima Kuma Isma'il d'in, saiya fake da cewa ai don yakula da yara ne yasa zaiyi hakan, Kuma Hajiya sakinah ta goya Masa baya, akab ya auri Sa'adatu d'in, Hauwa har Yan uwa da Hajiya sakinah takejin haushi bayan Sa'adatu,Domin Saida yardarsu ai Isma'il zai Aureta d'in....... Saura qiris a kammalawa Ummu Ruman gininta itada yaranta, Takoma gidanta, ta qale Sa'adatu a gidanta, kunga FANS sai tafi sakewa in tayi auren ma ko? Ummu Ruman tana tunanin Lallai Sa'adatu, harta mance da Abby zatayi aure, aurenma kaninsa, itakam itada Aure har abada, wazata Aura? Har yaushe Abby ya rasu da zatai wani auren, duk da ba wucewa tayiba, inda ita Isma'il ya taya Aida bazata aureshi ba, to Ina Shi ina ita, ba sa'ar aurensa bace, ita ta girmi Sa'adatu, tsakaninta dashi akwai mutunci da girmamawa.... Wannan tunanin yasa Ummu Ruman kwanciya a asibiti, hawan jininta ya tashi,zuciyarta ma tanaso ta kamu da ciwo, dama Kuma ta rame tayi baqi ta fita daga hayyacinta, gaba d'aya tun bayan rasuwar Abby, ga rigimar Hunaif baya yarda da kowa... Allah sarki Ummu Ruman kunji soyayyar gaskia, ita kuwa Sa'adatu aure ma zatayi ta shafe babun Abby, ta samu wani mijin mjinma qaninsa,tunda dai bayan rasuwar sa tad'an girgije alhinin rasuwar ya wuce .... Wata sabuwa, sai Kuma Sa'adatu take yawo da Ummu Ruman cewa ai ba'kin cikin Isma'il zai Aureta ne yasa, zuciyarta take so takamu da ciwo, bakin cikin abun tasa a ranta(... Kuji FANS Lallai Sa'adatu bazata saduda ba ta koma ga Allah, nazata rasuwar Abby zatasa kiyayya da sharrin da takewa Ummu Ruman zata daina,tunda Wanda akeyi danshi baya Raye...) Tunda akakai Ummu Ruman Asibiti batasan waye akanta ba, karkuso kuga y'ay'anta,wayyo Zakiyyah kullum tana zuwa asibitin, taita kuka, suma haka su Zahra, Hadiyyah, Hidayah, khadija, zeenah gani sukeyi itama Ummu rasata zasuyi kamar yadda suka rasa Abbynsu, kwanan Ummu Ruman biyar a asibitin, komai saidai ayi Mata Kashi da fitsari duk batasan tanayiba, duk Wanda yaganta sai ya tausaya Mata, ance ayi mata hoton 'kwa'kwalwa, Domin aga meyake damunta, 'yan wanta ne suka had'a kud'in, hoton, (... baza 'a dauka acikin duniyar da ake juya musu ba...) Anbiya kud'in hoton Ranar da za'ayi hoton Kuma Allah da ikonsa ................. Muje next page FANS, Wannan labari akwai tausayi bansan lokacin da nake share hawayeba,Ina tausayawa Ummu Ruman wlh da y'ay'anta da Kuma Y'AY'AN Sa'adatu d'in gaba d'aya Amma Banda ita Domin kuwa Bata tausayawa kanta ita d'in 😭😭😭😭😭😭 Karku manta dai har yanzu muna cikin tushen labarin wad'annan iyalan bamu dawo daga labarinba, tushen labarinne wannan .. karku manta kuci gaba da biyoni, har mukoma , cikin labarinmu da muka Fara daga farko Yan amana Yanzu muka Fara akwai tausayi cin amana ha'inci maraicin iyaye guda biyu a tsakankanin watannin da Basu da yawa ....... ✍️©️ Rabiat (Aminu Oum Arqam 👩‍🍼 ce) 2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cy82IooiC1LE5S0e2tkKcj Na bude group dinnan saboda comments ko sharhi akan wannan littafi, please idan kinyi joining ki bani hadin Kai, duk lokacin danayi sabon Page's ki daure kibani lokacinku kiyimin comments, rashin hakan Yana sawa nayi removed d'in ki ✍️ *Daga Al 'kalamin ©️ Rabiat Amin (Oum Arqam) 👩‍🍼* *08128131163* Marubuciyar KOMAI NISAN JIFA📚 HAKAN BA KUSKURE BANE📚 *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu *__________________* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION 📚🖊️(M°W°A)* Kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine ta fada'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙 *__________________* *PAGE TEN 10* "Allah da ikonsa ranar da za'a yiwa Ummu Ruman hoton 'kwa'kwalwar Kuma, Allah yai Mata Mata Rasuwa, tana jikin Mahaifiyarta kawai taga numfashi ta ya tsaya, dama tunda aka kaita asibitin ba motsi take ba, ta numfashi ake gane tana da Rai, idonta a rude yake dama, sai zubar hawaye dayakeyi, innalillahi wa Inna ilaihi rajiun! fad'ar tashin hankalin da Y'AY'AN Ummu Ruman suka shiga 'bata bakine! acikin wata shida ace ka rasa uwa da uba! wad'anda sune komai naka na rayuwa! mahaifi yafara rasuwa Wanda yakemusu komai! a haka suka haqura suka jure maraicin! saboda akwai uwa tare dasu, duk da dai Rayuwar tasu ba kamar da mahaifinsu ba, to yanzu gashi mahaifiyar ma, wacce take rage musu zafi, suke ganinta sukejin dad'i itama lokacin ta yayi, ta amsa Kiran ubangiji, Kar kuso kuga Zahra Hadiyyah da Hidayah, da Khadija, kamar zau haukace haka suka koma, itama zeenah duk da akwai kuruciya taji mutuwar "ummi" ga Kuma *Hunaif* d'an wata Goma a duniya, Allahu akbar , Rayuwa kenan sai haquri...... Zakiyyah tabada qaramin ciki lokacin, tana asibitin Ummyn tasu ta rasu, ai a take anan tayi 'bari saboda tashin hankali, sai kuka takeyi, to itama kenan FANS Wanda Basu shaku da Ummu Ruman ba, ba a hannunta ta tashiba, tana gidan kakarsu ta shiga wannan Hali inaga wad'anda suke tare.... Haka aka d'auko gawar Ummu Ruman zuwa gida, itama a gidansu akayi xaman makokin nata, Babu nisa da asibitin, kawai sai aka Kai gawar gidan anan aka dinga kar'bar ta'aziyyah, Allah yajiqan musulmi Baki d'aya.... Sa'adatu sai kukan munafurci akeyi, na mutuwar Ummu Ruman d'in, Sa'adatu kenan ga Ummu Ruman Nan tabar Miki duniyar, da kike cewa Wai bakin ciki take Miki Dan zakiyi Aure, Bata duniyar sai kiyi aurenki yanzu Babu Mai Miki ba'kin cikin, ita Tata ta qare ta tafi wajen masoyinta na gaskia mijinta Wanda soyayya tayi riba, zasu tashi ita dashi a lahira, kekam gakinan ga kawu Isma'il d'in nan..... Kanwar Ummu Ruman Wanda suke uba d'aya, Aisha itace ta d'auki Hunaif, dama tun lokacin da aka kai Ummu Ruman d'in asibitin, tanada yaro namiji kusan tare suka haihu, gidanta take tafiya dashi, Yaita rigima acan, Amma kukan da yayi ranar da Ummu Ruman zata mutu yafi na kullum, tun dare yake kuka, yaqiyin shiru, Saida Ummu Ruman ta rasu Kuma yayi shiru, Aisha yace ka gano mutuwa kenan (... Allah sarki yaro ya hango rasuwar mahaifiyarsa, Wai dama ance yara suna ganinta...) Kafin rasuwar Ummu Ruman ana katashi ajikinta yasa nono, to bayan Rasuwar Tata Kawai Aisha saita Fara bashi nononta, ta hadashi da d'an ta tana shayarwa...... Bayan anyi sadakar bakwai Babu Wanda ya tambayi inda Hunaif yake, to yanzu dama Ina kud'i dadai Ummu Ruman d'ince ta rasu, Alhaji Ammar yananan da anyi rububin daukar sa Amma, dayake shima qasa ta rufe Masa Ido, Yan uwanwa Babu Wanda ya nemeshi, Allah ya kyauta... Mahaifiyar Ummu Ruman Amina, shekara biyu da suka wuce ta koma Kaduna state da Zama, saboda jinyar Mahaifiyarta, ita kad'ai ta Haifa anan Kano, itama Yar Nan kanonce, mijinta ya rasu, shine tayi aure a kaduna state, to rashin lafiya takama ta, ita kuma lokacin mahaifinsu Ummu Ruman ya rasu, ita Kuma mahaifiyarta acan kaduna state duka maza ta Haifa, gashi tana fama da rashin lafiya 'barin jikinta ya shanye Babu Mai jinyarta, kawai sai Amina mahaifiyar Ummu Ruman Takoma Kaduba state d'in take jinyar Mahaifiyarta..... Yanzu ma rashin lafiya d'in Ummu Ruman d'in ce takawota Kano, gashi Kuma allahya kar'bi, Abarta.... Da aka share makoki ta tashi tafiya Kaduna state sai tace zata tafi da 'yan biyu *Hadiyyah da Hidayah*, Amma sai Hadiyyah tace ita bazata iya barin unguwar da aka haifeta ba, anan ummy da Abby suke San sun rasu, bazata bar unguwarba tananan itadai, cikin kuka take magana, kowa ya tausaya Mata, anan Ra'ayin tagwaye masu Kama d'aya ya banbanta, ita kuma Hidayah tace qafarta qafar Baaba wato kakarta, bazata iya zaman unguwar da take da iyaye guda biyu ba acikin shekara d'aya ta rasasu, kullum batajin dad'in unguwar, dama burinta tabarta, gashi Kuma Baaba tace zata tafi dasu...... Kowa akan Ra'ayinsa ya zauna tsakanin Hadiyyah da Hidayah, d'aya yaqi haqura yabi Ra'ayin d'aya, wannan shine ya raba tagwaye masu Kama d'aya, d'aya tana Kano state d'aya tana Kaduna state......... Ita dama Zahra a gidansu zata zauna, karatunta yafara nisa,dasu Khadija da zeenah ma suna gidansu,Allah sarki Allah yayi Ummu Ruman bazata zauna a gidan da ake Gina Mata ba, itada Y'AY'ANTA, Dan haka a gidan Sa'adatu zasu zauna gaba d'aya, ta had'a da Y'AY'ANTA ta riqe, Dama Kuma qanin mahaifinsu ne, ze Aureta, da kud'in ribar da ake samu na kasuwanci da kud'insu, ake musu wahala..... Saida aka had'a kayan Ummu Ruman data mutu tabarsu, kayan sawa da sauran kayan amfani aka warewa Y'AY'ANTA, gadonsu, haka sukace basaso abayarwa ummy sadaka Allah yakai hasken kabarinta itama Baaba aka bata wasu kayan..... Kayan d'akinta Haihuwar Hunaif Abby ya canza Mata, Yan Dubai ne masu tsada saboda haka sai, Zakiyyah aka batasu, ita Kuma ta siyar da kayan nata gud'a d'aya, tunda baduka Yan Dubai Abby yai Mata ba lokacin Aurenta, da Yan gida Nigeria,saita siyar dasu, ta fanshi na ummy d'in bataso a siyardasu, ta dinga tunawa da mahaifiyarta..... Har sannan da sauran kayan sawar Hunaif Wanda bai ta'ba sawa ba, da kayan barka da Ummu Ruman ta samu,Dan hakan aka. Tarkatawa marikiyarsa Tai Masa amfani dashi...... Saida aka kammala kasafta kayan Ummu Ruman sannan Baaba tayi Shirin tafiya Kaduna state itada Hidayah,ranar tafiya ansha kuka kamar ranar Ummu Ruman ta rasu, Hadiyyah tayi kuka kamar me saidai haka ta haqura tana kallo Hidayah tayi nesa da ita,Zahra Khadija da zeenah Suma sunsha kuka sai haquri yara, mutuwa Mai tonon silili kenan...... Haka su Hadiyyah da Zahra da Khadija da Kuma zeenah, sukaci gaba da Zama a gidan Sa'adatu,Babu uwa Babu uba, kullum sai Hadiyyah tayi kukan hakan,da Kuma rashin Yar uwarta ta haihuwa, Wanda komai sukeyi tare, a haka sukaci gaba da Zama anan suna zuwa makaranta, kawu Isma'il Yana ajiye musu abinci, yabasu kud'in cefane acikin ribar kud'in dayake zuya musu..... An d'aura Auren Sa'adatu da Isma'il, anan gidan yake zuwa duk ranar girkinta....... Tunda Aisha qanwar Ummu Ruman ta d'auki Hunaif Babu Wanda acikin dangin mahaifinsa dayake zuwa dubashi, duk da suna unguwa d'aya da Hajiya sakinah d'in, da wasu Yan uwan Alhaji Ammar d'in, ko biyar Kuma Shi ba'a Kai Masa ace ase Masa wani abun acikin ribar kud'in da ake juya musun, komai Aisha ke Masa, itada mijinta duk da ba wani kud'ine dashiba, Amma haka ya dauke nauyin Hunaif, har yoghurt yake siyo Masa, Yana tausaya Masa sosai, a hakan Hunaif yadinga rayuwa a gidan Aisha, itadai tana ganin ikon Allah, lallai kan Wai Alhaji Ammar d'an da akewa haka, Babu Mai kulashi, da ace Yana Raye Ummu Ruman ta rasu Aida rikon Hunaif Hunaif xazaizo hannunta ba, rubibi za'ayi a Yan uwansa, saboda duk Wanda yad'auka kud'i Alhaji Ammar zai dinga kashe masa, ga Kuma kayan abinci da na masarufi, Allah dai ya kyauta, saboda Babu idonsa Amma yanzu ko kar Babu Wanda take xai d'auki dansa riko.... Banda Amina mahaifiyar Ummu data d'auki Hidayah, sai Aisha data d'auki Hunaif, Amma sauran duk suna gidansu wajen Sa'adatu, itama ga nata, Y'AY'AN an barwa dai Isma'il riqonsu gaba d'aya, (....shima fans Allah yasa hakan ya d'ore, ba Dan zai Auri Sa'adatu take kula suba...) *******************" Acikin kud'in da ake juya musu ake turawa Hadiyyah can Kaduna state kud'in sabulu, da dai abunda zata buqata da kud'in, duk wata kamar yadda ake bawa Y'an uwanta... saboda dama itama Baaba acan Kaduna state d'in ba wani kud'i be da y'an uwanta ba kawai dai rufin asiri, ga Kuma jinya da take cinye kud'in, Yan uwanta maza din kowa yanada Y'AY'ANSA, saidai rufin asiri, ga halin rayuwa sai haquri ****************** Allah sarki Zakiyyah duk yazama shiru jikinta yayi Sanyi, Allah yasadai ta canza Hali, tayi hankali yanzu, zata daina Tarawa mijinta Mata agida, da Kuma fitar gaira Babu dalili, da rashin iya magana da ga'bunta Allah yasa ta daina, Shi Kuma Mukhtar Allah yasa dai yajure halin Zakiyyah d'in, Kar yaga Babu idon mahaifanta ya dinga Mata hulakanci Kuma, Dan kuwa darajarsu takeci a idonsa................ Yanzu aka Fara labarin, abubuwan suna gaba, akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu ✍️ ©️ Rabiat Amin (Oum Arqam 👩‍🍼 ce) 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cy82IooiC1LE5S0e2tkKcj *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) *✍️Daga Al 'kalamin ©️ Rabiat Amin Oum Arqam 👩‍🍼* *08128131163* ✍️Marubuciyar..... *Komai nisan jifa📚* *Hakan ba kuskure bane📚* *__________________* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ (°M°W°A)* Kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine ta fada'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙. *__________________* *PAGE ELEVEN 11* Zakiyyah tana xaman gidan mijinta, halin ta Kuma baamta fasa ba, na tara Mata da zuwa yawon makota, komai yasiyo Mata Mukhtar Nan danan zatace ya qare, tun Yana haquri da halinta harya Fara gajiya da halin nata, dama tanacin darajar iyayanta ne, idonsu yake gani ya qaleta yanzu Kuma Babu su, saura kakarta Hajiya sakinah wacce ta nuna Masa qauna lokacin aurensu...... "Yauma da zai fita kasuwarsu yace "Zakiyyah karki fita banason fitarki maqota, banson kina taramin kata a gidana, kiyi zamanki a gida, me Kika rasa,hakan dai yagama nata fad'a da nasiha, kamar taji, karku manta dai fan's Zakiyyah dai yarinya ce Kuma goyon Kaka, wacce Bata iya komai ba, sai ga'bunta da sangarta... Yana fita kasuwa tasa 'kafa tayi ficewarta itama,ta mance fad'an da yayi Mata na fita, Wanda dama ba ranar yafara fad'an tana sa qafa tana shurewa ba, mantuwa yayi a gidan wajen azahar ya shigo motarsa yadawo gida, Yana zuwa gidan yafara bugu Amma shiru kakeji, alamu sun nuna matar gidan yau Bata Tara mata ba, yau itace ta bisu gidansu, gajiya yayi da bugu,ya dauki wayarsa ya kirawota a zummar Kiran d'aya Saba mata ne, Mukhtar yace" fatan dai kina gida Zakiyyah yau Baki fitaba ko? Babu komai acikin ran Zakiyyah tace "eamn kaganni ma barci nakeyi wayarkace ta tasheni, Mukhtar yace "yawwa haka nakeso mamata kidaina fita yawo kina taran Mata, dama yanzu ma mantuwa nayi ne akan kujera, shine can dawo na d'auka ganinan zuwa gidan, sannan Mukhtar ya kashe wayarsa, Yana mamakin lallai halin Zakiyyah yafara yawa, hardasu karya Kuma, gashi a kofar gida bayanan,Amma tace yananan, shikam zaiga ikon Allah daga gidan zata fito ko Yaya? Ita kuwa Zakiyyah tana can wani layi, da taji yace gashinan dawowa saita maza ta fito zuwa gida,Kar Mukhtar yadawo yaga bataban, tana shawo kwana motar Mukhtar ta gani yayi parking, ya fito ya zauna akan dakalin barandar kofar gidansu, yayi tagumi, sai Kuma tayi turus, kunya duk ta kamata...... Ko magana Bai mataba kawai miqa mata hannu yayi, alamun ta bashi mukulli, a sanyaye tabashi, ya bud'e kofar gidan yashiga, ta biyo bayansa, "sannu da zuwa kadawo kaga dama fita nayi gidan Aunty na karbo kalanzir na zuba a risho zanyi girki, gas yaqare namance ban gaya makaba, shine kadawo baka sameni ba, Amma yau ba inda naje... Cikin fushi Mukhtar yace " Amma Zakiyyah ke wace irin yarinyace marar hankali, kalanzir ajiye Miki nakeyi, saboda irin hakan, gas yaqare bada saniba, saikiyi amfani daahi,to ya kikayi da kalanzir din cikin jarkarsa? "Aunty ce ta ara, gani nayi ba amfani zanyi dashi sannan ba, to tace za'a siyo Mata, nata na qare shine nataba, shine sainaje karba yanzu, Zakiyyah ta fad'a cikin ga'bunta da sangarta, Wanda hakan ya fusata Mukhtar sosai..... Kaca_kasa Mukhtar yaiwa Zakiyyah, yace "babu abunda na raga Miki na abun amfani, Amma kindinga 'barna kenan komai naki baya dad'ewa yake karewa, saboda kinfi kowa iya Aiko, to wlh kin Fara kaini bango kinacin darajar su Abby da ummy yanzu, kuwa Kinga basa Raye, tunda bakisan mutunci ba, wlh duk sanda Kika 'batamun sai Kinga abunda Zan Miki, banza ballagaxa sha_sha_sha kawai , yanzu kinci darajar Hajiya, Yana nufin kakarta..... Haka Mukhtar yayiwa Zakiyyah tatas ya qare mat tanadi, sannan yayi ficewarsa yakoma kasuwa.... Zakiyyah ranar tayi kuka sosai, tunda suke da Mukhtar vai ta'ba Mata irin cin mutuncin yau ba,lallai ta tabbata iyaye wata katangace ga y'ay'ansu, Ashe dama haka mukhtar yake? Idon Abby da ummy ne yasa take qaleta? Lallai ma, Wai a hakan ma yace saboda kaaka yai Mata wannan da sauran Ido akanta, lallai maraici masifane,(.... Fans Allah yasadai hakan ya gyarawa Zakiyyah halinta, tayi hankali tadawo hanya, tasan cewa yanzu fa komai nata ya canza Bata da gata saina Allah, Allah yasa ta riqe maraicinta...) Haka suka kasance tsakanin Zakiyyah da Mukhtar duk sanda tayi ya bud'e Baki ya wanketa tatas, saidai tayi kuka, Hmmm Zakiyyah kenan, ki daina halinki, karkikai Mukhtar bango fa ....... ******************** "Bangaren Aisha kanwar Ummu Ruman kuwa, haka da dad'i Babu dad'i, take ruqon Hunaif, Kuma har sannan Bai daina kukan dayakeyi ba, na rigima, yaita kuka kenan, ga itama yaronta Mai rigima ne, Allah ya taimaketa ma rainon Hunaif Yana dawowa wajenta, sai Shi Kuma Allah yasa Masa dangana yadaina daidai kawai Hunaif d'in yayi Shi kad'ai, ga rashin barci ga kashin kwance Dana wando, rikon maraya dama ai sai haquri, Haka Aisha taketa wahala da Hunaif, yau da dad'i gobe Babu dad'i, har Allah yasa suka Kai lokacin yaye, zata yayesu, ai kuwa har gidan Hajiya sakinah ta aika cewa Allah yayi lokacin yayensu Hunaif yazo zata yayeshi, Hajiya sakinah tace " oh kuce Mata Allah ya rayashi...... Kwanan Hunaif uku da yaye, Dan rigima kenan, ai rigima ta dad'u tafi tada, sai ga aike daga wajen Hajiya sakina ta Aiko Asiya 'kanwar Alhaji Ammar Wai abata Hunaif tunda an yayeshi a had'a Shi acikin 'yan uwansa, can gidansu wajen Sa'adatu.... Tashin hankali Wanda ba'a saka Masa Rana, haka Aisha tashiga cikin tashin hankali tana kuka mijinta yana kuka, suka bada Hunaif yaro Mai shiga Rai, tasa Rai tare da Abul khairi d'anta zasu taso kamar Yan biyu, suna tafiya tare duk da Shi Hunaif tafiyar batayi kwari ba, saboda maraici ya ta'ba Shi,tayi kuka Aisha sunyi saboda da Hunaif, duk da yanada rigima, Amma tana sonsa, sai haquri Aisha Allah yaso kema kinada naki............ ******************** Haka Hadiyyah da Zahra Khadija zeenah, suke zaune a gidan Sa'adatu suna zuwa makaranta, aikin gidanga komai Zahra keyinsa, itada Hadiyyah, Mai aiki Dama bayan mutuwar Mai gidan aka sallameta, Ranar girkin Sa'adatu dayake kawu Isma'il tasan zaizo yaga suna aiki Mai wahala ne kawai itama Sa'adatu takeyin aikin, Amma duk ranar girkin Hauwa a a gidan yakeba sune suke aikin komai,(...kun mance fan's lokacin da Ummu Ruman ta fita daga gidan suna qanana haka tadinga Basu aiki Kuma da me aiki sannan, balle yanzu taga sun girma Kuma Babu Mai aiki, lallai Sa'adatu halinki yananan.. ) Wankin su Zeenah, Hafsa, Hydar duk sune masuyi Hadiyyah da Zahra ita Kuma Khadija tayi nata, itada Farouk Dan wajen Sa'adatu, sun d'an girma su ai....... Shikam Alhaji d'an wajen Sa'adatu tun bayan rasuwar mahaifinsu, dama yafara fita yawo sai yayi fitarsa a mance dashi sannan zai dawo gida, yafara had'uwa da abokai marasa kirki da Kunya, sunason Fara koya Masa shaye_shaye, wataran sai an kulle gida dare yayi sannan yake kwankwasawa abud'e Masa, sai ranar da kawu Isma'il yaje gidan sannan yake dawowa da wuri, Sa'adatu fa abunda Alhaji yake Yana damunta Amma Kuma qaunar da tasa batai Masa fad'a..... A wannan halin Kuma Hajiya sakinah ta kawowa su Zahra Hunaif, wahalar aikin gida ma ta ishesu, ga Kuma qaramin yaro kamar Hunaif, aikinsan yadawo hannunsu shima Domin, kuwa Sa'adatu ko kallonsa batayi, balle ta tausaya ta daukeshi ta had'a da Hafsat ta rainesu, yamanta dasu kuka kawai yaketayi Babu dare Babu Rana, cikin dare yayi Kashi sau nawa, kunsan d'an yaye wasu suna Kashi, Wanda dama tun kafin yaye Shi yarone Mai kashin kawance, ya hanasu barcin dare da kuka da safe Kuma wankin Kashi, Allah sarki Zahra da Hadiyyah,idan Yana kukan Suma kukan sukeyi, Yara y'an Mata, 'kanana an had'asu da jego, mutuwa ta jawo muku, tunda Hunaif yadawo gidan, mutuwar Ummu tadawo sabuwa a garesu, idan Yana kukannan, sai sun tuna da ummy lokacin tana Raye baya yarda dasu kullum Yana gurinta .... Wannan wahalar ta Hunaif da aikin gida yasa yaran suka Fara ramewa makaranta sai ta Zama ba kullum suke zuwaba, to wa zasu bawa rainon Hunaif?, Ba kullum suke zuwa makaranta ba, ga Zahra Mai University Kuma karatun fannin lafiya, akwai son kwanciyar hankali da karatu akoda yaushe da wannan suka Fara samun matsala............. ******************** "Hadiyyah anacan Kaduna state tunda taje garin tafara samun canjin rayuwa, Rashin y'ar iwarta Hadiyyah komai tare sukeyi yanzu sai ita kad'ai a gidan kullum sai tayi kukan hakan, harta Fara Kuma sakewa Y'AY'AN kannen Baaba suna zuwa gidan itama Kuma tana zuwa can, Saida tayi sati biyu acan sannan akayi Mata cuku_cukun makaramtar boko, tare da islamiyyah, alhmdllh komai ya kammala tana zuwa makaranta, Amma kullum tana cikin damuwa, sai Baaba tana Mata nasihar tayi haquri kowa da tasa kaddarar su tasu kaddarar itace maraicin iyaye guda biyu a tsakankanin watanni shida, ga Kuma rabuwa da y'an uwa tayi haquri kawai , aikin Baaba ga Hidayah kenan kullum nasiha, Baaba tanada waya anan suke gaisawa da y'an uwanta, sa'i da lokaci in Allah yasa akwai kud'i a wayar.............. Muje next page FANS 😭😭😭😭😭 yanzu aka Fara labarin akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu....... Domin sharhi ko shawara ku tuntubeni a wannan number d'in *08128131163* ✍️ *©️Rabiat Amin Oum Arqam 👩‍🍼 ce dai* Bissalam👋 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M°W°A)* *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) *✍️daga Al'kalamin Rabiat Aminu (Oum Arqam 👩‍🍼)* Marubiciyar✍️ Komai nisan jifa📚 Hakan ba kuskure bane📚 *PAGE TWELVE 12* "Zama yayi Zama tsakanin Sa'adatu da kawu Isma'il, ana xaman dad'i, tsaninsu, gidan da take ciki yafi nasa girma Wanda matarsa Hauwa take ciki, Dan hakane ma kawu Isma'il yace ta fansar Masa da nata gidan kason Y'AY'ANTA Wanda sukaci gadonsa, ya had'esu itada Hauwa hankalinsa zaifi kwanciya,wajen kula da yara, haka yace mata, shikuma yabata nasa Wanda yake ciki sai yayi Mata cikon kud'i (...kujifa fan's Koda yake Babu ruwana tsakanin Mata da Miki be...), Sa'adatu ta Amince Masa kuwa da hakan,nana gaba Wai zai cika mata kud'in Nan gaba, tabashi natan kuwa shikuma yace xai cika mata kud'in, Hauwa matarsa da Y'AY'ANSA sun dawo gidan Sa'adatu da Zama , Shi Kuma gidansa Sa'adatu ta kar'ba zata saka haya cikinsa... Gidan Alhaji Ammar sama da qasa ne, su Hadiyyah da Hidayah d'akinsu d'aya, zahra ma d'akinta ita kad'ai, sauran yaran Khadija zeenah suma d'akinsu d'aya duk aqama suke, d'akin Alhaji Dan GIDAN Sa'adatu shima nasa aqama yake, sai d'akinsu Farouk da Hydar Suma su biyu a qasan, sai sama Kuma d'akin Alhaji Ammar turakarsa tana sama, d'akin Matansa ma a sama yake, babban falon gidan ma a qasa yake da dakunan Sa'adatu da Ummu Ruman ma a qasa, gidan Alhaji Ammar babban gidane sosai, ga farfajiyar gidan wajen ajiye mota,kafin kishiga gidanma akwai tafiya, wannan gidan Sa'adatu ta mallakawa kawu Isma'il Wai yabata nasa, zai Mata cikon kud'i.......... Bayan rasuwar Ummu Ruman sai su Hadiyyah da zahra Khadija da Kuma zeenah, suka koma kwana d'akin ummy d'in gaba d'aya,sama suka koma kenan, sun bar qasa........ Ita Kuma Sa'adatu ta dawo qasa da Zama d'akinta na qasan, saman Kuma tabarwa su Alhaji dasu farouk da Haidar, Suma anan suke kwana..... Bayan aurenta da kawu Isma'il Kuma, saita dawo da yaran gaba d'aya qasa, kawu Isma'il saita bar Masa saman turakar Alhaji Ammar lokacin Yana raye(... Lallai abun yayi yawa ta aureshi Kuma tabashi turakar mijinta, dad'in xama. D'akinta na saman nan ma tana zuwa........ Da Hauwa matar Isma'il ta dawo gidan kuma, sai suka koma kamar yadda suke zamansu da Alhaji Ammar da Ummu Ruman, d'akin Sa'adatu dana Hauwa sai turaka sune a saman, Yara kuma suna qasa, lallai fan's gidafa yazama na kawu Isma'il duk girmasa duk kyaunsa....... Tunda Hauwa tadawo gidan basa zaman lafiya da Sa'adatu, duk wannan mutuncin da qawancen anbarshi, Hauwa mugun haushin Sa'adatu takeyi, taci amanarta ta Aure Mata mijinta,har lokacin su Hadiyyah da kud'in ribarsu ake musu wata wahala, kud'in makaranta, sabulun wanka na wanki, takalma, rashin lafiya dadai sauransu, abokin Alhaji Ammar ko d'aya yadaina kawowa Y'AY'ANSA tallafi, kamar yadda ake Masa lokacin da bashi da lafiya kafin ya rasu..... Dawowar Hauwa gidan saita d'auki Hunaif, in zasu tafi makaranta a gurinta yake zama, sai sun dawo ydawo gurinsu, har sannan rigimar sa tananan, kashin wando Dana kwance yananan, tana tausayawa su Hadiyyah, tana jansu ajiki sa'banin Sa'adatu, sai Kuma Sa'adatu da taga hauwa tadawo saita daina azabtar dasu Zahra d'in, tana sasu dai aiki dai_dai gwargwado, wanke_wanke, shara, wanki Kuma nasu kawai sukeyi, Sa'adatu takoma yima yaranta yanzu, Su Hadiyyah sun Fara samun sauqi fa ganin idon Hauwa, lallai Sa'adatu Babu tsoron Allah (... Yakamata Mata musan cewa duk abunda kukayiwa d'an kishiyarku na alkhair Kona sharri za'ayi naku, ...) Alhaji d'an Sa'adatu fa shaye_shaye yafara nisa, tun Yana 'boyewa har Abu yafito filo, qiri_qiri yake zuwa da kwalaben maganin tari, wiwi acikin d'akinsa yakesha warin yaita fitowa daga d'akin, Kawu Isma'il yakama yai Masa warning had'e da duka, Amma me sai Alhaji ya miqe yanawa kawu Isma'il rashin kunya, har Yana karya Kuma dukansa zai Rama ne, ai ba ubansa bane, da Sa'adatu tasa Baki akan abunda yakewa kawu Isma'il gaba d'aya ya had'asu yai musu tatas, ya zagesu, ya gaya musu magana, Babu uban daya Isa ya hanashi abunda yaga dama(... Kunsan dai Yara maza masu tashen balaga, jinsu suke dai_dai da kowa musamman ga shaye_shaye yanayi, basa ganin kowa da gashi...) Duk su yaran suna kallon abunda Alhaji yayi, Zahar da Hadiyyah sunsha kuka, Wai yau Alhaji ne take shaye_shaye, saboda Rashin mahaifi, me Abbynsu ya ragesu, Alhaji yaro Mai hankali, da nutsuwa ko fita waje bayayi, Amma shine yanzu Abby Yana Masa duk abunda yakeso, Amma yazama hakan, lallai sunyi rashin Abby rashinsa yasa Alhaji yazama Mara kunya Kuma d'an shaye_shaye rayuwa kenan..... Zuciyar kawu Isma'il kamar zata fashe saboda ba'kin cikin abunda Alhaji yakeyi Kuma yai Masa,yanke hukunci yayi zai kaishi makarantar kangararrun Yara........ ******************** "Bangaren Hidayah mutanen Kaduna state Kuma , suna waya dasu Hadiyyah anan taji labarin cewa Hunaif Yana wajensu, Hidayah tanason Hunaif tun asali dama, Dan hakan tagayawa Baaba cewa idan sukaje Kano kawai su d'auko Hunaif yadawo wajenta da Zama, tunda can sunada yawa,ita Kuma ita kad'aice, Hadiyyah tana gayawa Hidayah duk irin wahalar da sukesha, wajen Sa'adatu, Hidayah har kuka take tana Basu haquri, tace idan sukazo Kano da Hunaif zasu dawo kaduna, itama Nan zamanta yanada amfani wajen Baaba Domin tana tayata jinyar Mahaifiyarta wajen y'an wanki wanke_wanke da sauransu, itama zaman nata yanada amfani da saita dawo gida kawai su zauna tare cewar Hidayah, Koda tagayawa Baaba yadda sukayi dasu Hadiyyah.... itakam Baaba batayi mamakin Sa'adatu ba Dan tanayiwa su Zahra mugunta, la'akari da yadda akasha fama da ita farkon Aurenta da Alhaji Ammar d'in, makirci kala_kala tadinga yiwa Ummu Ruman y'arta, badon Allah yayi Ummu Ruman zatayiwa Alhaji Ammar takaba ba Aida tuni Aurensu yaqare tuni, yadda aka Fara sakinta bayan auren Sa'adatu da Alhaji Ammar d'in, Amma dayake Allah yafi qarfinta Kuma makircinta baiyi tasiriva, haka dai sukaci gaba da Zama har mutuwa ta rabasu da juna, daga baya itama Ummu Ruman d'in tabishi... Baaba kullum tanawa su Hadiyyah da Zahra nasiha akan suyi haquri da Sa'adatu komai mai wucewa ne, sukayi haquri da *RASHIN IYAYE* biyu ma, balle wani muguntarta da makircinta suda suke Mata duk ranar da lokacin aurensu yayi suka tafi suka bar mata gidan shikenan, wannan nasihar da Baaba take musu tana kwantar musu da hankali a Koda yaushe...... ******************** "Zahra wani d'an saurayi Mai hankali da nutsuwa, ya nuna yanasonta, Kuma Yana tausaya Mata da halin maraicin da suke ciki, anan gaba da unguwarsu yake, d'an masu kud'ine sosai, sunansa IBRAHIM Yana zuwa xance wajenta, Shirin kawo kud'i akeyi ma, jira yake Zahra suyi exam tukunna.... IBRAHIM marayane shima mahaifinsa Alhaji bala ya rasu shekara d'aya da tawuce, sai mahaifiyar sa, Hajiya maimuna, yayyensa duk matane sunyi aure, Hajiya maimuna macece Mai tsaninin kishi, ga kishiyoyinta tun Alhaji baka Yana raye, Amma bayan Wannan batada wani mugun Hali, Koda IBRAHIM yace Mata yasamo wacce yakeso Bata nuna wani abuba tace Allah ya Sanya albarka yakaimu lokacin lfy......... ******************* Halin Zakiyyah yananan Babu abunda tacanxa, na yawonta, da Tara Mata a gidanta, sai Mukhtar yayi tunanin kodan batada yaro ne yasa take hakan? Har wajen Hajiya sakinah yaje yace yanson abashi zeenah qanwar Zakiyyah d'in xai riqeta, Hajiya tabashi kuwa zeenah , yakawowa Zakiyyah ita Wai ko kula da yarinya xaisa Zakiyyah tadaina fita yawo an samarwa xeenah makaranta pravet school Mai tsada, tun safe sai magrib, ake dawowa, Mukhtar Yana son yarinyar sosai, yasiyo Mata kayan Wasa, kayan ciye_ciye...... Zuwan Zeenah Bai canzawa Zakiyyah hali ba, Domin da safe idan ta shirya Zakiyyah Isma'il ne yake tafiya da ita yakaita makaranta, suna fita itama zata saka qafa tafice, yawan bin makota, d har lokacin tashin su Zeenah sannan take ta d'aukota su dawo gida, mukhtar Bai San da wannan ba, Shi zai bayan sallar isha'i yake dawowa, yayi tunanin Zakiyyah tadaina fita d'in, tunda inya dawo Yana damunta a gida..... IDan Zakiyyah taji zance yayi zance, a makota anata Hira wataran mancewa takeyi da zeenah tana makaranta fa, har atashi bataje ta d'auko taba, yarinya tagaji da jiran Aunty Zakiyyah, saidai takamo hanya tadawo gida, ta ra'be a bakin gate, Kota shiga wasu maqotan, sai Zakiyyah tadawo sannan ta nemota su koma gida, haka halin Zakiyyah yake, ko tausayawa qanwarta batayi, shikuma mukhtar Bai saniba...... Yau, Zakiyyah Hira tayi Hira, tanacan makota, har Zeenah tadawo daga makaranta Bata dawoba, gidan da zeenah ta shiga shine matar ta aiki zeenah d'in bakin titi ta siyo Mata abu a kanti, a wannan lokacinne Kuma Allah da ikonsa zeenah...... Muje next page kuji mexai faru da zeenah marainiyar Allah, Wanda Allah yahad'ata da sha_shashar Yaya Zakiyyah, gwanda ma abarta a gidansu cikin Yan uwanta masu hankali ba rikon kaaka ba Kuma ga'buwa marar hankali *✍️©️ Rabiat Amin Oum Arqam 👩‍🍼 ce* Domin sharhi ko shawara *08128131163* 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M°W°A)* *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) *✍️daga Al'kalamin Rabiat Aminu (Oum Arqam 👩‍🍼)* Marubiciyar✍️ Komai nisan jifa📚 Hakan ba kuskure bane📚 *PAGE THIRTEEN 13* "Hajiya sakinah takirawo kawu isma'il tace maza_maza yad'auki Hunaif ya kaishi kaduna, rana tsaka su baaba da Hidayah, sukaga ankawo musu shi, to dama dai baaba tayi niyya ko ba'a kawo Shiba zataje ta d'auko shi, koda aka kawoshi Babu tantama ta kar'beshi, su Hidayah anata murna Hunaif yadawo wajensu, ga Kuma wahala ta ragewa su Hadiyyah,,,,, Haka baaba yau da dad'i gobe Babu dad'i take riqon su, domin kuwa dai sai kawu isma'il yayi ra'ayi yake musu Aiken sabulu da man shafawa, da y'an kud'i, acikin ribar da ake samu nasu, Amma lissafin dayakeyi duk wata kowanne ake bashi hardasu Hunaif da Hidayah d'in... Amma banda Zeenah domin mukhtar mijin Zakiyyah yace abunda zaiwa y'ay'an daya Haifa in Allah yabashi itama xai matane.......... ************* "Bangaren Sa'adatu da Hauwa kishiyarta kuwa, abundai Babu yabo Babu fallasa, Hauwa ta takurawa Sa'adatu da habaici da cin mutunci kala_kala, Babu damar ta fito tsakar gida ta zauna, acikin d'akinta ma Bata tsira ba, ikon Allah kenan ai dama duk abunda kayi sai an maka kad'an tafara gani, Allah sarki Ummu Ruman kuduba irin xaman da sukayi da ita gallazawa iya gallazawa ga makirci iya makirci da kisisina Babu Wanda Sa'adatu batayiwa Marigayiya Ummu Ruman, a wajen marigayi Alhaji Ammar (bn yassir)to yanzu dai Kashi tasamu dai_dai da ita, shukam su Zahra da Hadiyyah Babu ruwansu abunsu, suna gefe suna ganin ikon Allah, suna tuna xaman Aunty(Kamar yadda suke Kiran Sa'adatu dashi) dama akwai Wanda Sa'adatu zataji tsoro? Akwai Wanda yafita dama rashin mutunci? Lallai kam hakkin ummyn sune, ta qarkashin qasa Hauwa ta fara bi tana yaqar Sa'adatu tasa yanzu kawu isma'il kwata_kwata baya wani kulata, ya mayar da ita Kamar banza a gidan, duk abunda Hauwa take na rashin mutunci agabansa takeyi baya magana, idone nasa, idan Kuma ta rama yayo kanta da masifa, yace batason xama lafiya,halin da Sa'adatu take ciki kenan tsakaninta da Kawu isma'il da matarsa Hauwa....... Hajiya sakinah kuwa, tun bayan rasuwar Abby ta samu kud'ad'e acikin kud'in daya bari, duniyarta takeci da tsinke, gidan datake ciki, an qawatashi da kayan qawa Kai bakace gidan tsohuwa kamarta bane, ko wata yarinyar mace d'in albarka, kowa sai mamakinta yakeyi ace d'an ka Wanda yakeji dakai, ya fad'e ya mutu Amma kamance, duk da lokacin mutuwarsa tajita Amma yanzu ta girgije, tana kallon y'ay'an daya mutu yabari an rasa me d'aukar nauyinsu, da dukiyar da ake juya musu ribar da ita ake musu wahalhalun yau da gobe, Kuma tasan kawu isma'il Yana almundahana da dukiyar Amma takasa magana....... Gidan da ake ginawa Ummu Ruman, zasu tare Allah be yiba, an kammala ginashi Masha Allah yayi kyau, wannan gida bai kamata da haya ba, saboda tsaruwarsa,Amma hakadai aka saka haya d'in, sama da qasa mutum biyune suka kamashi, wa da qanine xasuyi Aure, shine suka kama, Masha Allah Saida akayi jere aka tsara gidan yayi kyau, kud'in haya kawu isma'il ne Wai xai dinga kar'ba duk shekara, Wai xai bud'e banki ya dinga zuba kud'in idan Allah yakaimi Auren y'ay'an Ummu Ruman su Zahra Hadiyyah da Hidayah da Khadija sai ayi musu wahala dasu,to FANS Allah Yasa hakan...... ************* "Allah da ikonsa zeenah zata tsallaka titi saura qiris wata mota ta kad'eta tabi takanta, Allah ya kiyaye tad'an bigeta Amma,Kuma ta wad'i qasa, mutumin dayake tuki ya fito Yana sallallami, Abba ne (wato mukhtar) cewar zeenah, mukhtar Yana zuwa wajen zeenah ya d'auketa daga qasan da take tana kuka, mukhtar karkad'e mata jiki yayi, zuciyarsa kamar ta 'billo daga qirjinsa saboda masifar da take cinsa, cikin murya wadda take nuna 'bacin Rai tambayar zeenah yayi wane ya aikeki Zeenah? Cikin shashsheqar kuka Zeenah Babu wayo ta kashe komai ta gayawa Mukhtar cewa ai ita ta dawo daga makaranta Kuma tana gidan Maman Waleed yau bataga Yaya zakiyyah ba, shine ta aikota tasiyo mata Pampers, zuciyar mukhtar yau takai karshe, rike hannun Zeenah yayi yasata a mota, bayan ya duban yaga bataji ciwo ba, razana ce tasa ta fad'i a qasa, sai kujewa kad'an datayi a gwiwa,koda sukaje gida har sannan zakiyyah Bata dawoba, sauka yayi yaje ya bud'e gidan ya bud'e gate ya shiga da motarsa ciki, cirewa Zeenah Kaya yayi Yasa tayi alwala Shima yayi sannan sukayi sallah agida,sai Kai kawo yakeyi yaga ta Ina zakiyyah zata shigo......... Ita dama zakiyyah tasan Zeenah tana gidan Maman Waleed, takanas gidan taje tun daga bakin qofa ta qallowa Maman Waleed Kira tace Ina Zeenah ne? Ta tawo mutafi gida, shiru taji, sai sannan takula da qofar Maman Waleed a rufe take.turus zakiyyah tayi tana mamakin Ina Maman Waleed tayi haka? Kaqewa tunaninta yayi lokacin da Maman Waleed tace wa zakiyyah, Kinga Aiken Zeenah nayi bakin titi ta siyomun Pampers naga shiru_shiru Bata dawoba,nabita kantin batanan, jimamin Ina taje nake, sororo zakiyyah tayi, saboda ta qware a harkar qarya saita d'auko waya ta Kira mukhtar Wai zata Gaya masa cewa, Zeenah bayan tasowa daga makaranta Bata ganta ba, taje d'aukota, Mai gadin makarantar yace yaganta ta tafi gida, tana Kiran wayar mukhtar ya d'aga kamar Babu abunda ya faru, zakiyyah Saida tagama Yi masa qarya sannan ya qatseta, cikin fad'a to maqaryaciya gani da Zeenah acikin gida idan kingama barbad'a da yawon naki ki dawo gida banza ballagaza marar hankali, wacce batasan inda yake mata ciwo ba, Saida zakiyyah tagama jin cin mutincin da mukhtar yai mata sannan ta kashe wayar, sai Kuma tabasar tacewa Maman Waleed ai mukhtar ne yadawo ya had'u da ita ya tafi da ita gida, da safe na Aiko Miki da Pampers d'in,kuji FANS lallai Zakiyyah babu hankali, Bata gano rashin hankalin abunda tayiba,ta 'batawa mijinta hankaki Amma ko ajikinta,,,, Lokacin da Zakiyyah ta dawo cikin gidanta, sunyi bala'i itada mukhtar, ya gaggaya mata magana Mai ciwo, yace da ita "shashasha ballagaza Y'ar iska jaka mahaukaciya wacce batasan meyake damunta ba, sannan ya d'auketa da maruka lafiyayyu, itama cikin ga'bunta da rashin iya magana da rashin hankali Zakiyyah tace " Wai akan Zeenah kake gayamun wad'annan maganganun? To Ina ruwanka da Zeenah Y'ar uwarka ko Y'ar uwata, mene had'inka da ita? Uwartace Kai ko ubanta? Acikin banza aikin wofi,taja tsaqi tayi wucewarta cikin d'akinta,da makamantan wad'annan maganganu, Zakiyyah tagayawa mukhtar. Lallai fans Zakiyyah batada Hankali..... Aikuwa mukhtar cikin d'akin ya bita yace ki fitarmun daga gidana, bana buqatar ganinki a wajena, Zeenah tafiyemun ke sau dubu, ita yarinyace Amma tafiki Hankali, zo ki ficemun daga gidana,..... Zakiyyah kuwa Babu wani tsoro tace " saime Dan nabar gidanka, irin cin mutuncin da kakemun da zagin iyayena, da kakeyi ya isheni, ta d'auko Zeenah daga d'akinta har tafara barci "zo mu tafi gidan ubanmu Zeenah, aikuwa mukhtar ya riqe hannun Zeenah yace ai bakece kika bani itaba Dan haka baki Isa ki kar'beta daga hannuna ba, kedai kije ki gama haukanki acan....... Haka Zakiyyah ta fice daga gidan a wannan Daren, ta nufi gidan Hajiya sakinah, koda taje qarya da gaskia ta gayawa Hajiya sakinah, Hajiya sakinah tace " nasan halinki Zakiyyah bakida dama bakida hankali da tunani,sai mukhtar yazo naji ta bakinsa...... Mukhtar Kiran mahaifiyarsa yayi Hajiya Jamila yagaya mata, yadda sukayi da Zakiyyah d'in, Amma maman mukhtar rufe idonta tayi taciwa mukhtar mutunci, tace meyasa bakada Haquri Mukhtar kadinga haquri da Zakiyyah yarinyace Kuma gata marainiya, sai haquri wata rana sai labari, kadaina kulata akan abunda takeyi, zanzo nai mata magana akan halinta,in Sha Allah zata daina, wuyarta Allah yabaku Haihuwa wata macen haka take saita haihu take hankali, hakadai Mama tayiwa Mukhtar tatas, yace Kuma gobe kaje ka d'aukota ka dawo da ita gidan karshe ta kashe wayar...... Duk irin xaman da mukhtar yakeyi na haquri da Zakiyyah, da laifukan da take masa, muddin zai gayawa Mamansa Bata goyuwa da bayansa, Haka take goyuwa da bayan Zakiyyah, ita tausaya mata takeyi, saboda halin maraicin da take ciki.lallai FANS Anya xa'a samu irin Hajiya Jamila, batasan halin Zakiyyah bane Allah Yasa kar takaita qarshe.......... Muje zuwa next page yanzu aka fara wasan, har yanzu bamu shiga cikin labarin tagwaye masu kama d'aya ba wato Hadiyyah da Hidayah........ *✍️©️Rabiat Amin oum Arqam ce 🤱* Domin shawara ko sharhi *08128131163* 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M°W°A) *✍️Daga Al 'kalamin ©️Rabiat Amin (oum Arqam🤱)* *PAGE FOURTEEN 14* "Washe garin Ranar kuwa mukhtar yatashi da safe ya shirya Zeenah yakaita makaranta,yatafi kasuwa, sai yamma yaje gidan Hajiya sakinah,fuskarsa Babu walwala suka gaisa da Hajiya sakinah d'in, bayan sun Gama gaisawa Hajiya ta tambayeshi meya had'ashi da Zakiyyah? Tiryan_tiryan ya kwashe labarin duk halin da suke ciki da irin halin zakiyyah yagayawa Hajiya sakinah,duk da Daman dai ta sani, Zakiyyah tana cikin d'aki Hajiya ta qwala Mata Kira, bayan ta fito, Hajiya tace "duk kinaji abunda yafad'a kinayi, kije kici gaba dayi, bazan hanaki ba, Zakiyyah bansan halin wa kika d'auko ba, mahaifiyarki ba Haka takeba,nima Dana riqeki hakan, ke kikasan a inda kika kwaso, Zakiyyah tana ganin Hajiya sakinah tana Mata fad'a,(wannan ai ba fad'a bane FANS anawa ganin fa,mutuniyar da take wannan Rashin wannan xa'a yiwa irin wannan fad'an?) Kumbure_kumbure ta fara, to itama Hajiya sakinah itace dama ta 'batata da sai abunda takeso, sai tace kiyi haquri kinji Zakiyyah ta ki qara haquri nasan ke Yarinyace me hankali, shidai mukhtar yana zaune Yana kallon ikon Allah, duk da baiyi mamaki ba bayau yata'ba ganin wannan halin na Hajiya sakinah da Zakiyyah ba Amma abunda tai masa be kamata a wani lalla'bataba, ai shikenan muje zuwa ni daku,tunda Haqurin danake da ita bakya gani ko Hajiya? Mukhtar yafad'a a zuciyarsa, Saida Zakiyyah tagama iskancinta tagama Hulaqanci sannan ta tashi ta d'auko mayafi ta taiwa Hajiya sallama, suka tafi, ko a mota Zakiyyah Bata kula mukhtar ba,Shima Kuma bai kulata ba har sukaje gida....... Haka Xaman Zakiyyah da mukhtar yaci gaba, kunsan tsakanin Mata da miji sai Allah, a halinta Babu abunda ya sauya, in tayi yayi Mata fad'a, in yagayawa Hajiya Jamila Kuma ta goyi bayan Zakiyyah tace shine bashida Haquri, Zeenah tana zuwa makarantar ta yau da dad'i gobe Babu dad'i, harta Saba da halin Zakiyyah,yanzu dakanta take dawowa daga makaranta, inta sameta a gida ta shiga idan batanan ta zauna a qofar gida ta jirata, don yanxu Zakiyyah Bata kaiwa sallar magrib a maqota, Zakiyyah yanzu cikine da ita, ga cikin Mai sa laulayi da kasala, Bata aikata komai, fita maqota tadaina yinta,Inna tashi Bata iya ta'bukawa kanta komai, aikin gida mukhtar kafin yafita yakeyi Mata, kullum tana gida, samun cikin sai yayiwa mukhtar dad'i, gwanda yayi aikin gidan, ita Kuma ta zauna a gida dadai tayi aikin gidan kullum tana maqota, ko ta Tara masa Mata a gida, itama Zeenah taji dad'i kullum Aunty tana gida, har wata qiba tayi,yanzu Babu zaman bakin gate,tun daga laulayin Zakiyyah kuma saita rage fita har cikin ya tsufa........ Cikin ikon Allah Zakiyyah ta sauka lafiya Namiji ta Haifa, mukhtar yasaka masa suna *Ammar* Sunan babansu Zakiyyah suna kiransa da *ABIE* ko taron suna ba'ayiba, sai Wanda Allah yayi shine yazo yayiwa Zakiyyah barka, duk rashin hankali na Zakiyyah Ranar Saida tayi kukan Rashin iyayenta data tuna Haihuwarta ta fari Babu Rai tayita, lokacin Abby da ummy suna Raye Babu Wanda zaice Babu d'a irin yadda akayi cikowa zuwa Yi Mata barka da Kuma Allah ya jiqan Rai, Amma yanzu darai ta haifi yaro y'an uwansu ba kowane yazo ba, sai wa'yanda baza'a rasaba, sai Kuma maqotan da suke mutunci dasu..... Baaba da Hidayah da Hunaif sunzo Kano Sunan Zakiyyah, Masha Allah Hunaif yaro yayi girma Yana samun kulawa ke bakyace shine Wanda yasha cutar Kashi ba, ya murmure abunsa, Kuma sun xagaya dangi, sai mamakin d'an maraya akeyi ya gagije,ai suna zuwa Hidayah da Hadiyyah rungume juna sukayi sunata murna, sun fara zama y'an Mata abunsu,kamarsu taqara fitowa Babu banbanci kam,ansha hirar zumunci Hidayah tadinga bawa y'ar uwarta labarin kaduna, Ranar ansha hira ai Zahra da Khadeeja sunyi murnar zuwan Baaba......... Hadiyyah ce taje yiwa Zakiyyah zaman wanka, tunda lokacin anyi hutun makaranta, sai Hidayah ta bita can kafin su koma kaduna, Ranar Sunan da Zakiyyah take kuka Baaba tadinga Mata fad'a kuwa "ai inajin duk halin da kike ciki keda mijinki, duk abunda yake faruwa dake baxaisa kiyi hankali ba Zakiyyah, yaronan Mukhtar meya raga Miki? Yazake Miki mijin marainiya, komai baki rasaba ga Y'ar uwarki Zeenah Yana riqonta kamar shine ya haifeta, sauran y'an uwanki sunanan an rasa Mai kula dasu saboda Allah, kinadai kallo abinci sabulun wanka Dana wanki da sauran abubuwan buqata Babu Wanda yad'auke musu acikin kud'in da ake juya muku ribar da ita ake musu amfani,Amma hakan be zame Miki izina ba, yakamata kiyi hankali dai yanxu gakinan da d'anki a hannu, ki gyara Halinki karki Kai mukhtar bango ya sakeki, ko ya qara aure bakisan wacce iri zai auroba me halin kirki ko akasin hakan, inkinji mgana ta ke kika sani idan kin watsar kece aciki, y'an uwanki y'an Mata ma a gidanku xaman wahala da haquri sukeyi balle ke, nikuma danake Rikon Hidayah da Hunaif sai haquri ba sana'a nake ba sai rufin asirin Allah kawai da Rikon marayu kuma. Nan dai baaba taiwa Zakiyyah fad'a tayi shiru kamar taji, Hadiyyah Saida tasa baki, (kuji FANS yarinya ta fita hankai..) nima baaba abunda nake gayawa Aunty Zakiyyah kenan, muma cikin halin matsin rayuwa muke ta riqe Yaya mukhtar hannu bibbiyu Babu abunda ya raga Mata Amma,saita dinga cewa Wai Zan mata rashin kunya daga nafad'a Mata gaskia, shiyasa nadaina nikam, ai shikenan Hadiyyah qaleta in kunne yaji jiki ya tsira cewar baaba..... Kwananau baaba biyu a Kano suka juya kaduna, saboda babu me jiyyar Inna acan, sai Ranar da zasu tafi Hunaif yadawo daga gidan Aisha ummansa, tun Ranar da sukazo baaba takaishi can, Kuma tana Gaya masa dama cewa Aisha itace ta raineka ta shayar dakai bayan rasuwar mamanka, sannan kadawo Nan wajena aikuwa Hunaif ya riqe wannan suna zuwa Kano yace "baaba kaini wajen ummana naganta(.. kujifa FANS yaro bai manta da alkhair ba..). Haka suka dinga Wasa da Abul_khair abokin shayarwarsa, Aisha da mijinta sunyi mamakin girman Hunaif yakusa yafi Abul tsayi ma, tunda dama shi dogone, Haka suka tarkata suka koma kaduna, kamar Aisha bazata bada Hunaif ba, kwanci tashi Babu wuya har Zakiyyah tayi Arba'in Hadiyyah ta koma gida..... ************** Bari muleqa bangaren Hajiya sakinah man, ciwon qafa ne ya sakata a gaba, tun tana iya saukowa daga sama zuwa qasa harta daina duk abunda zatayi iya samane, idan qafarta ta tayar Mata da ciwo kamar bazata kwanaba, Kuma a wannan halin kawu isma'il sai yayi sati baizo ya duba data, sai Kuma taita kuka, tana tunanin Babansu Zakiyyah dashine da tuni hankalinsa ya tashi duk inda magani take zaije ya Nemo Mata, Amma isma'il ya zuba Mata ido, 'kafa ta fara kumbura ga qurji ne yafito a gwiwa ya zame Mata kamar wacce taqone gurin Babu kyan gani, anata jigilar asibiti, maganin hausa anayi Asiya da bilkisu da zainab y'ay'anta Mata sune suke wahala da ita sai Auta sulaiman,shikam isma'il Yana gefe abunsa sai yaga damar zuwa wajenta, Amma duk da Haka Bata gani tadinga masa addua kenan idan yazo sai kace shine yake mata komai,qafar Hajiya sakinah da tafara wari, abun Babu kyan gani, suna zuwa asibiti akace saidai a yanke, iya galabaita Hajiya ta galabaita Bata sanin abunda takeyi(... Lallai FANS duk abunda kakeyi dama ce kasamu yanzu ina iskancin Hajiya? Ina kud'in da take taqama dashi, Ina watsi da marayu da tayi yanzu keya amfana Mata?..) a halin haka aka yanke wa Hajiya sakinah qafarta ta dama, abun tausayi duk da farko banji tausayinta ba Amma rashin sassan jiki akwai tausayi...... Saida tayi wata d'aya a asibiti Ana Bata kulawa kafin a sallameta zuwa zuwa gida, liktoci sunce xa'a iya Mata qafar roba, kawu isma'il yace to zai duba yagani amma, kafin sannan kawai abata karfen da zata dinga dogarawa akansa,(... Hajiya tayi kuka da Ammar be da tun a Ranar zai bada kud'in ayi mata.. kad'an kika gani..) Anata zuwa dubata a gida su Zahra Hadiyyah da Khadija da sauran yaran gidansu y'ay'an Kawu isma'il da y'ay'an Sa'adatu sunje dubata sunyi kuka ganin yadda Hajiya Takoma duk wannan fad'an Babu, jikinnan duk ta xazzage komai Yi mata akeyi, Babu qafa, rayuwa kenan Allah yakyauta........ Gadai Hajiya sakinah tafara girbar abunda ta shukawa d'an da da y'ay'ansa Dan taga qasa ta rufe masa ido............ ************** Babu abunda ya sauya dangane da Halin Alhaji na shaye_shaye, rashin mutunci kuwa Babu abunda ya fasa, shida kawu isma'il Babu jituwa yadinga zaginsa kenan, maci amana kacinye Mana kud'inmu gidan da muke ciki ma ka mallakeshi yakoma naka, mahaifiyarki ma ka aureta saboda cin amana Dan kaga Abbynmu ya rasu Allah xai saka Mana ne, abunda Alhaji kullum yake gaggayawa kawu isma'il keban, idan Sa'adatu tayi magana itama ya qare Mata " ai kema maci amana ce kika d'auki gidanmu da kud'in da mahaifinmu ya rasu yabar Mana kika mallakawa wannan banzan sai ya nuna kawu isma'il,bayan Haka saboda cin amana kika aureshi kikaci amanar Maman meenal(Hauwa yake nufi) wane irin Aminci be bakuyiba,Amma kika Mata hakan karki Kuma samun bakinki in Ina maganata da wannan maci amanar (kawu isma'il yake nufi) ire_iren kalaman da Alhaji yakeyi a duk Ranar datayi shaye_shayensa kenan, anan kawu isma'il zai masa duka, Shima Yana qoqarin ramawa, ita Hauwa kam Y'ar kallo ce, Sa'adatu Kuma saidai tashige d'aki abun tana damunta a zuciya, Zahra da Hadiyyah kuwa sai kuka suna tausayawa Alhaji irin wannan rayuwar daya tsinci kansa acikinta...... Yadda zaku fuskanta FANS baqin cikine da 'bacin Rai ya jefa Alhaji shaye_shaye, ta yadda Kawu isma'il ya kwace musu gida, dukiyars Kuma Wai Yana juya musu, da ribar ita ake musu wahala, ga auren da yayi na mahaifiyarsa itama Sa'adatu yanajin haushinta,tunda Abby yamutu Alhaji ya fara shiga damuwa, Allah sarki d'an marayan Allah wannan wane irin hakkine akan kawu isma'il da mahaifiyarsa Sa'adatu,fita wajen d'aya farane abokan banza suka ce masa indai damuwa ce Yana fara korawa zai barta, shi kuma dayake yarone Babu hankali Kuma maganin damuwar yake nema Babu tunani yafara kora maganin tari tun daga Nan Kuma Abu yayi gaba yanzu har wiwi Yana Sha, Kuma dai damuwar Bata barshiba Allah sarki rayuwa, kunji abunda Yasa Alhaji rayuwarsa ta lalace sanadin maraicin da Kuma halin mahaifiyarsa marar Imani Sa'adatu da kawunsa isma'il Maci amana,....... Da Kawu isma'il yaga abun Alhaji Yana gaba shine fa ya jajirce akan cewa xai samo makarantar woro da tarbiyyah yakai Alhaji ya zauna acan, shikam abun nasa ya dameshi, kuji FANS kodai tonon sililin dayake masa ya dameshi nikam nasan badan ya samu tarbiyya bane......sai Dan ya bashi gurine..ya saka Ranar kaishi makarantar. Itakam Hauwa tana gefe abunta tana cigaba da quntatawa Sa'adatu da habaice_habaice da makirce_makirce musamman idan Alhaji yagama tijararsa, to itama zata d'ora natane, tace" mutum yanzu yafara gani, tunda cin amana ne aikin mutum gashi a Halinki kin jefa d'anki a wani halin, ga y'ay'an abokiyar xamanki baki riqesu amanaba, kinci amana dayawa Sa'adatu bakiga komai ba, ire_iren maganganun da Hauwa take ya'bawa Sa'adatu kenan, dayake tasan batada gaskia ko tace ta tafasa balle sauke... Keken d'inkin Zahra dama tun tuni ya lalace yanzu haka yaran Sa'adatu ne suke Wasa da qafar duk sun lallata sun karya, kafin ya lalace ma farouk da hydar ne suketa wanashi, Kuma Babu damar Zahra tayi magana, yanzu gashi ta iya d'inkin Amma Babu keken d'inki, ta tambayi kawu isma'il kud'in gyara zatakai keken yace Mata saiya samu, meyasa tabari Yara suka ka lallata Bata killaceshi ba, Shima sau nawa Yana gani anata wana keken batayi magana ba, sai yanzu to baxai bayarba, Haka Zahra ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido,itadai bazatace ai Aunty tana kallo suke wasan dashiba bata hanaba, ko tace Ai Aunty zatai fad'a idan nai musu magana, ita Kuma Sa'adatu ko giyar wake Tasha bazata tambayeta kud'in gyaraba..... A makotansu take zuwa tayi d'inkin, tafara kwarewa na Yara ake kawo Mata...... Da Hauwa ta fuskanci Keken d'inkin Zahra ya lalalcene, shiyasa take zuwa maqota ai kuwa kud'in gyara tabata aka kaishi aka gyara, sannan tasai Mata sabuwar qafar,domin wannan bazata gyaruba,kujifa FANS Hauwa tafi tausayawa su Zahra akan Kawu isma'il da Sa'adatu lallai rayuwa kenan, ai inda kayi alkhair a rayuwarka zaka samu Mai kula maka bayanka, koda wani bai kula suba,wani xai kula dasu, gashidai y'an uwan Alhaji Ammar hatta mahaifiyarsa da abokansa da Sa'adatu matarsa abokiyar xaman mahaifiyarsu Bata kula dasu yadda ya kamata sai Hauwa matar qaninsa Allah ka kula da bayanmu bayan qasa ta rufe Mana ido, Allah Yasa mu aikata alkhair a rayuwa kodan bayanmu a kula da ita tayi kyau Muje zuwa next page FANS domin Miki mene xai faru Nan gaba wannan labarin akwai tausayi maraici cin amana da dai sauransu muje zuwa yanzu aka fara wasan............ *©️Rabiat Amin (oum Arqam ce)* Domin shawara ko sharhi *08128131163* 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE FIVETEEN 15* Duk wani shirye_shirye kawu isma'il yayiwa Alhaji na kaishi makarantar horo da tarbiyyah ta matasa, Mai suna *TALLAFY CHARITY FOUNDATION(T°C°P)* Wanda dama an bud'e ta domin matasa irinsa masu shaye_shaye, acan Ana horar da matasa ilimi tun daga na addini Dana xamani aka koya musu sana'oi kala_kala Wanda idan angama Basu horo sun shiryu idan sun fito zasu dogara dakansu, lokaci kawai take jir karshen shekara yakusa, dayake haka tsarin makarantar yake duk shekara d'ai_ d'ai ake yaye matasa, Kuma cikin ikon Allah xakaga cajin wajen yaronka, duk abunda yake zai daina tun daga shaye_shaye, rashin kunya da sauransu Allah dai yataimaka Yasa akai Alhaji wannan makaranta a Sa'a Yasa shiryuwarsa ce zatazo........... *TALLAFY CHARITY FOUNDATION{T°C°F}* wata Makaranta ce ta bada tarbiyya Wanda wani shahararren Mai kud'i ya tamfatsa ta, makaranta ce babba Wanda aciki Babu abunda Babu dakuna ne aka ginasu irin dai yadda tsarin Hostel na makarantun kwana take,Amma banbanci su shine ita kowanne gado guda d'ayane, akusa dashi akwai kwaba , sannan akwai taxara tsakaninsa da wannan gado sosai, haka tsarin d'akunan su suke, kowanne d'aki gadaje biyar_biyarne ne sannan akwai 'Bandaki acikinsa, akwai labulaye ajikin tagogi da bakin kofa gurin kwanansu kenan, wannan makaranta tana d'auke da dakunan kwana guda hamshin yakama Ana daukar mutane d'ari biyu da hamsin duk shekara.... Gurin d'aukar karatunsu na addini Dana boko, shima tsarin yadda ajujuwan makarantar boko yakene, akwai bencina, akwai allon rubutu da sauran abubuwan buqata......... Sannan tsarin shiga makarantar kowanne yaro da iya karatunsa na addini Dana xamani inda ya tsaya xa'a had'ashi tare su d'auki karatu, kowanne ajin karatu mutum ashirin da biyar ne, makarantar tanada ajujuwa guda goma...... Farkon Kai yaronka wannan makaranta sai yayi tsawon sati hud'u shi kad'ai a d'aki d'aya saidai akawo masa abinci yayi wanka yayi sallah, kullum Kuma akwai Wanda zai shiga gurinsa Yana masa wa'azi da nuna Masa illar shaye_shaye da Kuma kwad'aita Masa zama yarona nagari iyayanka zasu saka maka albarka Kuma Allah zai maka albarkar, sai an tabbatar wannan nasiha yashiga jikinka, sannan xa'a fitar dakai daga wannan d'aki a kaika d'aki Wanda kuke ku biyar_ biyar Haka tsarin wannan makaranta take zakuji wasu abubuwan a gaba, duk wannan tsari na makarantar Babu ko sisi da iyayen Yara suke kashewa illah kawai xasu dinga kawowa yaransu kud'in abinci duk wata, da kud'in sabulun wanka Dana wanki sai Kuma matsalar rashin lafiya, Amma sauran duk Wanda ya assasa wannan makaranta ya d'auke nauyin akansa,sai kawowa d'an ziyara duk sati, saboda kwantar Masa da hankali ma hadda y'an uwansa ake zuwa suna jansa ajiki basa nuna Masa qyama kamar yadda suke suna Masa lokacin Yana kan shaye_shayensa a gida............... Sa'adatu taji dad'in wannan makaranta da xa'a Kai Alhaji, suma su Zahra da sauran y'an uwa duk sunji dad'i d'an uwansu Mai hankali xai shiryu ya nutsu yakoma kamar yadda yake da, lokacin Abby Yana raye yaro Mai hankali da nutsuwa, Allah yabiye bakunansu marayun Allah.......... ************** Bari muleqa Wajen Zakiyyah muji wacce wainar take toyawa...... Tun bayan Arba'in da Haihuwarta Babu abunda ta rage na halinta da yawo da Tara maqota,yau tana can gobe tana can, Allah yabata yaro Mai haquri bashida rigima ko kad'an,wata Rana ma har kulleshi a gida takeyi idan Yana barci taje yawonta ta dawo, wataran ta sameshi ya farka Yana kuka ko Kuma Yana baccinsa, har gida Hajiya Jamila (mahmah) tazo taiwa Zakiyyah fad'a akan yanzu fa tayi hankali ta girma d'ane da ita yakamata tayi xamanta acikin gidanta, metake nema a wajen, ta rungumi Y'ar qanwarta ta zauna tare da ita tana koya Mata ayyukan gida tunda macece, kamar dai Zakiyyah taji, Haka mahmah ta fito ta koma gidanta......... Zakiyyah tana da socket a kusa da jikin gadonta, saboda tsabar iskanci da rashin hankalin Zakiyyah saita dinga jona heater ajiki acikin karamin bukiti, ta d'ora akan gadon idan ruwan ya tafasa saita juye, tanada kettle a kitchen fa, Kuma tanada heater a bayi, Tafison tayi amfani da wannan heater d'in, tun bayan haihuwar *ABIE* mukhtar yace Mata yanzu dai saiki daina kunna heater akan gado, Kinga akwai yaro Kuma shi yanada juye_juye kar watarana ki d'ora ruwa ki mance kin kwantar dashi.kinacan wani aikin yazo ya qone, Kuma Yana girma Yana wayo, shima ABIE yanada gadonsa, Amma Zakiyyah a kowanne kwantar dashi takeyi, indai ba da daddare bane Bata kwantar dashi akan nasa gadin, da Rana tafi kwantar dashi akan gadon nata, aikuwa dai Zakiyyah Bata jiba,Bata fasa d'ora ruwan akan gadonba,Kuma Bata fasa kwantar da ABIE akaiba,banda ma rashin hankali saiki daina kwantar dashi akan gadon,tunda bazakiji maganar daina d'ora ruwan zafi akaiba sai muce Allah ya tsare......... Zeenah anata zuwa makaranta anqara girma yanzu zatakai 6years abunta gata itama akwai jikin girma, irin Mai riqonta , Allah dai ya rabata da halinta, tanason ABIE sosai taitai Masa Wasa Yana dariya, aikuwa Zakiyyah haka takeso idan ta Bata shi tai ficewarta Ranar da Babu nakaranta ta kullesu a gidan, Zeenah ansamu abunso aita Wasa dashi, ABIE yaro Mai haquri ya gado Mai sunansa........ Akwai makaranta yau Zeenah anacan, Zakiyyah bayan taiwa ABIE wanka, yakama barci,ta kwantarshi akan gadonta, itama saita jona ruwan wankanta a heater ta d'ora akan gado, tana Dora ruwan kuwa sai yawonta yaciyota, ta kulle gida tayi ficewarta FANS meke faruwa ........ ************ Kawu isma'il fa Hulaqanci sosai yakewa Sa'adatu (Aunty) Haka kawai Babu gaira Babu dalili, Kuma tanata Dana sanin aurensa(... Wanda Ashe dama ta qarkashin qasa tabiyo kawu isma'il akan ya aureta,asiri tayi Masa,ta qulle bakin mutane yadda Babu Wanda zaice wannan Auren Bata kyauta ba saidai ace Allah ya Sanya alkhair..) yanzu kika fara Dana sani Sa'adatu,itakam Hauwa tana gefe abunda duk Hulaqancin da Kawu isma'il yakewa Sa'adatu itama Babu abunda ta fasa na habaici da hulakancin da takewa Sa'adatu,saima gaba , Kuma har sannan Hauwa tana bawa su Zahra Hadiyyah da Khadija kulawa sosai kamar y"ay"an cikinta, Zahra karatu yayi nisa, itama Hadiyyah suna shirin fara jarrabawar shiga aji shida na babbar secondary,Anzama y'an Mata sosai,kyau sai qaruwa yakeyi iyayi ya qaru da gwalli, saidai maganarta ta ragu yanzu maqerin budurci yafara qera Mana ita anfara hankali........... Hajiya sakinah saidai muce alhmdllh tunda aka Mata Aiki aka yanke Mata qafa, shikenan lafiya tai Mata sauqi, yau da lafiya gobe Babu lafiya, gurin da aka yanke Mata wajen gwiwar ya kumbura suntum Yana zubar da ruwan mugunya, abun Babu kyan gani,kullum cikin kuka take duk Wanda yaje dubata saitayi kuka, duk ta sauke makaman yakinta, an tattaro Mata y'ay'an Alhaji Ammar Tai musu addua,ta nemi yafiyarsu akan,rashin kulasu datayi,sukam su Hadiyyah sunce Babu komai Babu abunda kikai Mana Kaaka Allah yabaki lafiya,cuta ba mutuwa bace,ita Kam Hidayah sai a waya sukayi da Hajiya sakinah Babu halin zuwa akwai makaranta, duk da hakan Hidayah tace idan akayi Hutu zatazo ta dubata, Hajiya sakinah dai sai shi musu albarka take,har Hunaif aka Bata suka gaisa, Hajiya sakinah taita kuka, data tuna abunda Tai Masa Yana hannun qanwar Mamansa ta daukeshi takaiwa su Zahra shi, ta tozartashi, Ashe dai yaro yanada sauran Rayuwa, Haka Hajiya sakinah take cikin ciwo, Kuma kawu isma'il yabada kud'in qafar roba xa'a Yi Mata,sai qafar tafara kumbura tana ruwa Babu damar ayi qafar,saidai jiran agani idan Allah Yasa ta warke, Ana kaita asibiti kullum a wanke qafar, asaka Mata magani, Kuma a gida anayin na hausa .. sai muce Allah yatakaitawa Hajiya sakinah wahala ya karbi tubanta ya yaye Mata......... ************** Bangaren Hidayah mutanen kaduna itama abun Haka yake kamanninsu da Y'ar uwata yaqara fitowa sosai nidai bansan wacce tafi wata gwalli da iyayi ba,hakam bangaren tsarin jiki qirarsu d'aya da Yar uwarta tagwaitakarta Hadiyyah, dama itacan shiru shiru ce Hidayah sai abun ya qaru mutane da yawa suna cewa ita Y'ar hulakanci ce Bata kula mutane, jinta take kamar Y'ar wata da wani, Allah yaso munsan asalinta da bama anan garin takeba,Kuma Wai ance iyayenta sun rasu marainiya ce Kuma twin's be Wai, Haka y'an makarantar su Hidayah suke idan sun xauna sun dinga xancenta kenan, Allah yakyauta basusan cewa Haka halinta yakeba, Amma qawayenta sunsan halinta ba Haka bane saika zauna da ita zakasan cewa Haka Allah ya halicceta,shima Hunaif yanata girma Masha Allah an sashi a makaranta tun daga boko har islamiyyah akwai qoqari.... Babba tana zaune lafiya da jikokinta idan kawu isma'il ya Aiko musu da sabulu da kud'i ta kar'ba idan Bai turo ba Kuma ta haqura ta dogara da Allah, kud'in makaranta Amma wannan yasan Dole ya bayar duk lokacin da aka nema, shugaban makarantar dama yanada number d'in kawu isma'il d'in da lokaci yayi yake tura musu ta account.......... Muje zuwa FANS in Sha Allah next page zamu kammala tarihin wad'annan ahalai na Alhaji Ammar bn Yassir, Wanda yanzu labarin yafara bamuyi komai ba, Allah yabani ikon rubuta abunsa zai amfanar da Al uma Baki d'aya kuskure Kuma ubangiji ya yafemun azijancine na Dan Adam... Nice dai taku Rabiat Amin (oum Arqam) Domin shawara ko sharhi ku tuntubi wannan number *081281331163* 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE SIXTEEN 16* Duk wani cuku_cuku na tafiya TALLAFY CHARITY FOUNDATION kawu isma'il yagamawa Alhaji dakansa yakaishi makarantar tare da rakiyar Hauwa da sauran y'an uwansa, Babu Sa'adatu acikin Wannan tafiyar Dan lokacin kawu isma'il tsanar dayayi Mata abun yayi gaba, ko magana basayi Mata,Kuma abun Yana damunta sosai har kuka tana shiga d'akinta tayi, sauran Yara kuwa Babu abunda ya raga musu na hidimar da yake musu....... Kamar yadda tsarin makarantar yake haka akayiwa Alhaji, Wanda kafin tafiyar Saida akasha fama dashi yanata zag_zage da rashin kunya ga kawu isma'il da Sa'adatu uwarsa...... Bayan tafiyar Alhaji TALLAFY CHARITY FOUNDATION ne Sa'adatu masifarta ta tashi ta inda take shiga batanan take fita ba, ta tasarwa kawu isma'il da tijara kala_kala take Masa akan ya dawo Mata da gidanta da sukayi musanye aidama ga gidansa Nan Daya Bata har yau Bai cika Mata kud'inta ba, to tafasa Haka kullum takewa kawu isma'il, to dama shi ya tsaneta bayason ganinta a tare dashi, zagi da cin mutuncin da take masa ya fara isarsa, maha'inci mayaudari Maci amana, ka kar'be min gadon y'ay'ana Kuma daga baya kazo kana hulakantani to Auren nagaji dashi ka sakeni Kuma kadawomin da gidana, ga gidanka can ,tun danaga take takenta dama hayar danasa acikin gidan daka bani shekara tayi da suka bani kud'in hayar na sallamesu Kuma bansa wani ba, maganar Sa'adatu kullum kenan ga kawu isma'il,,,,,, Wannan rigimar har Saida taje kunnen Hajiya sakinah, aikuwa tayiwa kawu isma'il tatas, acikin fad'an datayi Masa tace" isma'il da bakinka kacemun gidan y'ay'an Sa'adatu daka kar'ba kabata nata kayi Mata ciko, sana'a takeyi dasu Ashe duk qarya kakeyi,Dan haka ka mayar Mata da gidanta in kanason zaman lafiya da kwanciyar hankali, haka Hajiya sakinah taiwa kawu isma'il tatas ya dawo gida ransa a matuqar 'bace, Bai jima da dawowa ba Sa'adatu ta d'ora nata tijarar to dama zuciyarsa a kusa take, a take anan yaiwa Sa'adatu saki d'aya bayan ya gaggaya Mata maganganu, ko ajikin Sa'adatu dam burunta kenan ta gaji da xama da Kawu isma'il ga Hauwa ma ta dameta....... A gurin Hauwa kamar sallah Wannan rabuwa da akayi tsakanin Sa'adatu da Kawu isma'il, kawu isma'il Kam haka yace a gobe ba jibi ba xai tattara yanasa_yanasa yabarwa Sa'adatu gidanta yakoma nasa, Allah sarki su Zahra Hadiyyah da Khadija marayun Allah sun girgixa da wannan lamari daya faru, yanzu shikenan gatan da Hauwa ta Samar musu acikin gidanga ya qare wahalarsu xata dawo sabuwa, gashi yanzu Babu namiji kenan acikin gidan, kawu isma'il suke gani suji dad'i shi ya zamar musu kamar Abby, kukan da suke tayi kenan tun Daren da wannan husumar ta faru... Da safe y'ay'an Hauwa da y'an uwanta sukaje gidan kawu isma'il suka sameshi Babu wani datti sosai sai abunda baza'a rasaba suka gyara gidan, kafin azahar kawu isma'il ya kashe kayansu dake gidan Sa'adatu ko tsinke Bai bari ba,ko sallama Hauwa Bata yiwa Sa'adatu ba balle kawu isma'il su Zahra dai ansha kukn rabuwa, haka kawu isma'il da Hauwa suka har gidan Sa'adatu suka qaleta ita kad'ai sai Zahra Hadiyyah da Khadija da y'ay'anta farouk da hydar da kuma Hafsa wacce lokacin tuni ta yayeta ko nace ma ta zama budurwa,surutu salo_salo har aikenta akeyi maqota.... Tun daga Ranar rayuwar wad'annan marayun ta sauya kawu isma'il akan abunda Sa'adatu tayi Masa kwata_kwata yadaina kulasu sai yaga dama yake zuwa dubasu, abincin da yake ajiye musu sai ya qare Bai kawo wani ba Wai saboda bakin cikin Sa'adatu zataji............. ************** Bari mu dawo wajen Zakiyyah....daga zuwa maqota ta samu Hira saita mance da cewa ta d'ora ruwan zafi Kuma tabar ABIE akan gadon,, acan gida kuwa ABIE ya farka daga barci yanata wasansa, to saiya fara shure_shure har yazo wajen botikin ruwan zafin ai Yana shurar bokitin aikuwa ya tintsire akan gadon, ita Kuma heater tana jikin socket saita maqale ajikin gadon taci gaba daci abunda ruwan Daya zubo saiya wankewa ABIE qafafuwansa, a take dayaji ruwan zafi ya suma,saboda azaba, ita Kuma katifa ta dinga naso har Saida taso wajen cinyoyin ABIE har gurin gadon bayansa wayyo ABIE ya qone, Saida Zakiyyah tagama iskancin surutunta sannan ta dawo gida, lokacin heater Kuma takama fuskar kadon gurin yayi ba'kikkirin sauwa kad'an wuta takama a gadon gaba d'aya sai hayaqi gashi ita heater d'in tayi jajir abunta, salati ta fara sannan taje ta d'auko wani katako ta bige heater wacce saura kad'an tayi bindiga, sai sannan takai duba ga ABIE har sannan barci yake, a tunanin Zakiyyah fa, ai tanakai hannu kansa taga idonsa a bud'e ya qaqqafe a gigice tasa hannu xata d'aukeshi,Wanda garin hakan ta kwashe Masa qunar gadon bayansa sai ganin fad'owar fata tayi iwu iya karfinta tasa tana na shiga uku na lalace jama'a ku kawomin d'auki, kafin me maqociyarta Maman Waleed itace kawai taji aguje ta shigo gidan, domin taga me yake faruwa, Zakiyyah miqa Mata ABIE tayi tana cewa" duban ABIE Maman Waleed ya qone dayawa wayyo nashiga uku,yanzu mezan cewa mukhtar ya hanani jina heater akan gado Amma banji ba,gashi yanzu yaronsa ya qone,Kuma ya rasu, tunda baya motsi zancen da Zakiyyah takeyi kenan tana kuka, haquri dai Maman Waleed take bawa Zakiyyah sannan tace kawoshi mugani, ki d'auko hijab d'inki, muje mukaishi asibiti, Amma Bari a zuba Masa ruwa Naga suma yayi ai ba mutuwa ba, aikuwa Ana zubawa ABIE ruwan sanyi ya farfad'o Yana sheqa uban ihu, Wanda Bai samu damar yinsa ba sai yanzu, abun tausayi wlh,da sauri Zakiyyah suka tafi asibiti da ABIE Yana tsala iwu, da sukaje asibiti gaba d'aya kafafun ABIE sun sa'bule da bayansa haka likitoci suka sa'bule Kunar aka wanketa da hydrogen, Babu kyan gani, zasu dawo gida likitoci sukace kwanciya xa'a Basu sai ya warke tukunna, Maman Waleed ta Bari a wajen ABIE domin ta Bari wayarta a gida Kuma Bata gayawa Mukhtar halin da ABIE take ciki ba, tana zuwa gida ta tarar gadonta yakama da wuta sosai har zuwa saman d'akin duk Fentin ya qone, aguje ta fito tana neman taimako mutan unguwa aka had'u aka kashe Wannan wuta Allah yaso ita gadon sai bangon d'akinta Daya kone, sai kuka take tana danasanin barinta gidan Bata yarda da maganar mijinta ba gashi tafara gani, takira mukhtar tagaya Masa duk abunda ke faruwa, hankalin mukhtar yayi mugun tashi baro kasuwa yayi sai gida lokacin Zakiyyah tananan Bata koma asibiti ba, dayazo ya sameta yai Mata dukan tsiya ga gaggaya Mata magana Mai ciwo, karshe yace wlh indai wani Abu ya samu yarona ya rasu wlh saikinyi Dana sani a rayuwarki, kalli yadda saboda Baki da hankali da tunani hi yadda kika mayar da gidan, na hanaki jona heater kinqiji gashi sanadin hakan kin qona mun yarona da gidana, na hanaki fita maqota kinqiji,yau dai Zakiyyah Babu rashin kunya sai kuka daban haquri takewa isma'il, a Haka suka koma asibiti mukhtar Saida yayiwa ABIE kuka ganin yadda ya qone sosai, ya Kira Hajiya Jamila ya fad'a Mata abunda yake faruwa, Koda tazo taga abunda ya samu ABIE duk qaunar da takewa Zakiyyah yau Kam ta sire Mata tatas tayi Mata, ta inda take shiga batanan take fita ba,duk Wanda yazo yaga halin da ABIE yake ciki a y'an uwanta Dana mukhtar kowa sai yayi Mata fad'a, itadai Babu bakin magana sai kuka, Anan suke kwana a asibiti domin jinyar ABIE, Zeenah kuwa da akazo da ita daga halin da ABIE yake ciki taita kuka abun tausayi, a wajen Maman Waleed aka barta saboda makarantar ta, kawu isma'il dayaso yaga yadda ABIE yaqone Saida yayiwa Zakiyyah mugun duka a asibitin sannan yaita bawa mukhtar haquri, itama Hajiya sakinah Babu halin zuwa dubiya saboda kafarta Bata fita,ta kirata a waya tayi mata tatas, fad'an tsakanin da Allah a wannan karon tayi Mata,itadai Zakiyyah Babu bakin magana, baaba mutan kaduna itama dai takira Zakiyyah tayi Mata fad'a "wato duk abunda nake Gaya Miki Zakiyyah bakiji ba ko ai shikenan Allah ya kyauta inkin kashe aurenki Babu ruwana nikam, Hidayah da Hunaif suma sun Mata yamai jiki, sunce xasuzo Kano idan anyi wutu,,,,, dayake Allah ya taimaki ABIE Kuma yanashan nono baiyi wata d'aya a asibiti ba ya samu sauqi qunar ta warke sai dai abunda baza'a rasaba,suka dawo gida, Zakiyyah kamar tayi nadama nake gani FANS fa ..... ************* Ba'ayi wata d'aya da yiwa hajiya sakinah 'kafar roba ba itama d'aya kafar ta kamu da ciwo, ciwo kuwa sosai har wari takeyi, ana shirin yankewa Allah yayi ikonsa akan Hajiya sakinah ta amsa Kiran mahaliccinta, Allah sarki rayuwa gashidai itama ta Hajiya sakinah taqare duk wani qale_qalen duniya tabarshi inda Alhaji Ammar ya tafi gashi itama taje, Allah ya yafe was Hajiya sakinah kura_kuranta, Haka aka akayi zaman ta'aziyya aka kammala, shikenan su Hadiyyah Babu uwa da uba yanzu Kuma Babu kaka, wacce duk da hakan Ana raga musu wani Abu saboda idonta, shi kansa kawu isma'il saboda Hajiya sakinah yake musu wani abun badon Allah ba..... Mutan kaduna Hajiya baaba da Hidayah da Hunaif sunzo gaisuwa Amma kwana d'aya sukayi saboda school suka juya gida, y'ay'a da jikokin Hajiya sakinah da y'an uwa da abokan arqizi sunji mutuwarta to dama Haka rayuwa take kowa na hakane saidai fatan cikawa da Imani............ Muje zuwa FANS a next page zamu dawo dafa labarinmi in Sha Allah, Kuma yanzu wannan labari yafara, na wannan ahali .... ✍️oum Arqam ce 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE SEVENTEEN 17* "Rayuwa fa ta sauyawa marayun Allah fiye da yadda zakuyi tunani, tun barin kawu isma'il cikin gidansu ya banzatar da rayuwarsu ko waiwayarsu bayayi, Dama abincin dayake kawowa Auren Sa'adatu ne sukaci darajarsa tun da Auren ya rasu shikenan kuma, tun bayan ficewar kawu isma'il daga gidan Sa'adatu tasanya cigiyar y'an haya wad'anda zata saka acikin gidanta, saboda ta ragewa kanta wasu abubuwan na rayuwa, Dan kuwa itadai da bakinta bazata wani tambayi isma'il kud'i ba, taqaleshi da haqqinsu akansa, kunji FANS Saida yazo kanta sannan tasan cin hakkin marayu....... Abubuwa sai gaba sukeyi a Wannan halin Hadiyyah da Hidayah suka kammala secondry school d'insu, yau da dad'i gobe Babu dad'i, tun bayan kammala makarantar su Kawu isma'il Bai leqo gidanba, itakam Hadiyyah tanada burin cigaba da karatunta kamar yadda Zahra taci gaba, yanzu gashinan karatun ta yayi nisa gwanin sha'awa, kud'in mota ta samu har gidan kawu isma'il, Ranar da tasan xata sameshi ta Gaya masa cewar Hadiyyah "munyi candy nida Hidayah kawu, Kuma munason ci gaba kamar yadda Abby yakeson muyi karatu Allah Bai kaishi lokacin ba,kawu isma'il yace naji abunda kika fad'a Ina sane daku ai, Kinga yanzu kasuwancin sai a hankali Kuma karshen shekara yazo duk ban kar'bi bashiba Ina kar'ba zanmuku registration keda Y'ar uwarki, Kinga banjima da yiwa Alhaji hidimar makaranta ba,ga 'batamun Rai da Auntynku tayi(Sa'adatu) shiyasa nafita daga harkarku,Inna Baku Abu kamar har ita nabawa, Hadiyyah kiyi haquri da daina saurarar ku danayi, Sa'adatu ce ta janyo muku Hadiyyah tayi murna sosa da wannan magana ta Kawu isma'il na cigaban karatunsu, Kuma tayi baqin cikin Jin cewa abunda Aunty tayi masa me Yas yadaina kulasu, Banda abun Kawu isma'il su Ina ruwansu,hakadai tayini a gidan Hauwa tana Bata haquri akan kawun nasu dacewa tana masa itama nasiha akan daina kulasu datayi yamance abunda Sa'adatu tayi Masa, Koda yake ai laifinsane, Banda hakan wannan Abu da sukayi tun daga aurenta har musanyan gida ai Bai kamata ba,,, sai yamma tadawo gida abunta, Bata jima da Candy ba kuma tayi saukar Al qur Ani Mai girma, Masha Allah Hadiyyah akwai qoqari sosai ba iya qur Ani Mai girma ta sauke ba hadda wasu littattafan addini d'in ahlari,ishmawi,iziyyah, risala bangaren fiqhu kenan, bangaren hadisai kuwa irinsu bughyatul Muslim,umdatul ahkam, Bukughul maram, riyadus salihin, bangaren sirah ma ba'a bar Hadiyyah a baya ba ta kware a Wannan fannin, indai taji tarihin maaiki ko sahabbansa in Sha Allah ta haddace kenan, Dan d'aya daga cikin baiwar da Allah yaiwa y'an biyu Hadiyyah da Hidayah kenan riqe Abu ba kasafai suke mantuwa ba, tauhid ma ta karanta littattafai da dama, Masha Allah xamuce domin kwakwalwar Hadiyyah da babu Wasa tun daga na addini har na Boko, nasan xasuyi mamakin a Ina kamar Hadiyyah Mai qananun shekaru kamar hakan ta iya wad'annan littattafai saina ce muku, tsarin islamiyyah tasu akwai malami Wanda idan kana da sha'awar ka iya wani littafi Babu takura bayan Wanda ake muku acikin ajinku, xaka iya zuwa da Wanda kakeso malamin yadinga biya maka to anan Hadiyyah tayi wayo data kammala wannan littafi zata saka wani,anan tasan wad'annan littattafai d'in da wasuma wad'anda ban ambataba, sunyi karamar Al qur Ani Mai girma Babu wani shagali Dan ko walima batayi ba irin yadda sauran y'an qjinsu sukayi,lokacin kawu isma'il yayi fushi dasu, kannen ummy d'in su Wanda suke uba d'aya da namiji guda d'aya Wanda suke uwa d'aya uba d'ayan sai Kuma y'an uwa na dangi sune suka had'a Mata daga Mai kawo flour, take away, Leda da sauransu a Haka tayi Y'ar walima Tata Babu yabo Babu fallasa, Ranar sunyi kuka daga Hadiyyah d'in har Zahra yadda suka tuno da ace Abby Yana raye Wannan Rana tazo da anga yadda ake karyar kashe kud'i, akan su, da qaryar y'an uwa sai a d'auka Biki akeyi a gidan nasu ko suna, Amma yanzu Kam mafi yawa dangin ummy ne sukazo sai Zakiyyah mutuniyarku itama tayi hidima ga qanwarta, aidai Kunga anan tayi hankali ko?😅dangin Abby kalilan saboda yanxu qasa ta rufewa Hajiya sakinah ido ragowar kulawar da ake Basu bayan nutsuwar Abby ta qare itama,sun tuna lokacin da Zahra tayi sauka Abby Yana raye sunsha kuka irin hidimar da akayi,gidansu kamar ana Biki ko suna, qaton rago Abby ya yanka a saukar Zahra Amma wannan karon Kam ko kaza ba'a yankawa Hadiyyah ba Yarinya Mai kokari hakan ga littattafan data sauke bayan Al qur Ani Mai girma sukam sunga rayuwa, makarantar bokonsu tare take da islamiyyah a hade Kuma dama kana Candy kake saukar Al qur Ani Mai girma, ka kammala makarantar gaba d'aya kenan, yanzu saidai asanar Mata wata islamiyyah ta unguwa kenan,to Allah Yasa kawu isma'il yayi hakan kar yace bashida kud'i yanzu karshen shekara yazo ..... ************** Hidayah sai godiya Babu abunda xatace da Baaba domin kuwa kulawa daidai gwargwado tana Bata itada Hunaif, tunda sukayi candy bayan Hadiyyah taje gidan kawu isma'il tagaya Mata cewa ai kawu yace Yana sane dasu xai musu registration naciga da karatunsu bada jimawa ba, yanzu kam bashida kud'i, tun daga sannan taci gaba da zuwa ismaliyyah abunta, ba tsarin makarantar su d'aya ba Kano da Kaduna kowanne da irin tsarin pravet school dinsu, tasu Hidayah iya Boko ce, islamiyyah kuma saidai a saka wata daban, itama Kam badai kwakwalwar ba bansan Wanda yafi wani ba,sun rabu da Y'ar uwarta ne bawai rabuwa ta karatu ba duk abunda Hadiyyah take koya shi Hidayah take koya, da d'aya ta saka littafi xata gayawa d'aya itama Kam zata saka sai ayita rige_rigen gamawa, lokacin dama suna tare da juna tare ake musu qarin, bayan komawar Hidayah kaduna anan ma Bata fasa hakan ba, wani malami Mai qoqari ya sauke littafi da dama na addini shi Hidayah ta samu yake mata qari Masha Allah tana iyawa, Koda itama tayi saukar Kare daga dangin Abby Babu Wanda yaje Mata, iy_iyasu dangin ummy na kaduna da qawayenta nacan sune suka tayata murna, Hadiyyah Zahra Khadeeja hydar farouk kawu isma'il ne yakaisu a motarsa,ta Abbynsu Hidayah d'in Bata jima a hannunsa ba yasai wata jibgigeyi wacce tafi Wannan tsada da girma, ko kallon Sa'adatu baiyi ba, itama Hauwa da y'ay'anta biyar sunje Taya Hidayah saukar Al qur Ani Mai girma, Hajiya Zakiyyah a mukhtar yakaita itada Zeenah tsakanin saukar Hadiyyah data Hidayah watanni ne, dai_dai gwargwado itama Hidayah baaba da sauran y'an uwansu sun Mata wahalar saukar saidai ba kamar ace Abby Yana rayeba, maraici Kam y'ay'annan kun ganshi a duniya lallai wad'annan y'an biyu Abin asone, Haka akasha hidima kafin sudawo gida.............. ************** Tun bayan qonewar da ABIE yayi mukhtar ya canzawa Zakiyyah duk Wannan kulawar da uwa uba haqurinsa ya qare,duk Sandra zata Yi wani kuskure zai rufe idonsa yaci Mata mutunci, yace" tunda Kinga Ana rabuwa dake shine iskancinki da hulakancin ki yake yawa ko to kin kaini bango, kinata cin darajar ummy da Abby har suka rasu Baki daina halinki ba, Hajiya Kaaka ma(sakinah) kikecin darajarta itama ta rasu Baki daina halinki ba , to wallahi yanzu Babu darajar Wanda zakici idan kikayimin Yi miki zanyi, tunda Baki da mutunci,tun bayar warkewar ABIE Zakiyyah halinta ya dawo na fita maqota,Amma dai tadaina jona heater akan gadon, Zeenah anata zuwa makaranta abunta, gata itama da wayo da qoqari, Hajiya Jamila tacewa mukhtar gaskia Zakiyyah batada Hankali sosai hakan, sai a qunar ABIE nagani,nikam ko xaka qqra aure ne hakan nake ganin kamar zaisa tayi Hankali, kaga Naga Y'ar wajen kawunka bilkisu ta kammala karatunta na nursing, yarinyace Mai hankali baxaka samu sa'bani da itaba, inaga idan Zakiyyah taga ka Aurota zata dinga koyi da ita Kuma xata rage fita yawo maqota, saidai ta zauna a gida sudinga koqarin faranta maka Dan kowacce mace bataso taga kishiyarta tafi kulawa da mijinta,a zahirin gaskia bilkisu yarinyace Mai hankali da nutsuwa Y'ar wajen qanin Maman mukhtar ce, dama Kuma sun saba dashi akwai mutunci tsakani, tajima tana sonsa, mukhtar baiyi gaddama ba yacewa Hajiya Jamila Mamansa Allah Yasa sanadin Auren Yasa Zakiyyah ta gyara halayenta, Amma shikam halinta ya isheshi, bayan Gama Wannan tattaunawa mukhtar Yana dawowa gida yacewa Zakiyyah xan qara aure, Wanda Zan aura kinma Santa bilkisu ce, banson fitina tsakaninku da ita, Kinga ma ba xaman gidannan Koda yaushe zata dinga yiba tana zuwa hospital ,kiyi haquri Zakiyyah Wannan Auren bayana nuna cewa nadaina sonki bane, Haka mukhtar yadinga gayawa Zakiyyah kalamai na kwantar da hankali Amma bayan Gama maganar da bud'ar bakin Zakiyyah haka tace "Ina ruwana da qara aurenka inma guda uku xaka auro akaina zasu zauna, matsalar kace kaida wata bilkisu bansan taba, qarin aurenka ko d'aya bazai dameniba ka qara aurenka Mana(... Anya kuwa FANS Zakiyyah tanada Hankali, Amma mijinka abin sonka yace zai qara aure ka fad'i Wannan magana,Wai Ina ruwana ka qara aurenka, kodai sai munkai ta asibitin mahaukata?) Lallai Wannan magana da Zakiyyah tayi ta girgixa mukhtar ba kad'an ba, Rashin hankalinta da shasancinta uwa uba ga'buntar maganarta sun bashi haushi duk da bayau ya Saba Jin su ba , Amma nayau daban suke, Zakiyyah Bata sonsa ko kuwa shiyasa Bata nuna kishi akansa ba dayake xai qara aure?.... Mukhtar Yana tambayarku FANS kubashi amsa.............. Koda aka gayawa bilkisu cewa, mukhtar zata aura Babu wani damuwa ta amince, abunka da dangi d'aya Nan danan aka Kai kud'in aure harda saka Rana ma,sai zuwan Biki kawai,,,,, y'an uwan Zakiyyah duk Wanda yaji mukhtar xai qara aure tausaya Mata ake Amma itakam ko ajikinta sai tace Ina ruwana akaina zata zauna tazo ga gidannan ............... Muje next page In Sha Allah daga shi page din zamu dawo daga ainahin labarinmu, acikinsa zamuji yadda rayuwar Alhaji ta kasance a makaranta,shin yafara karatun ko kuwa? da sauran labarin da bamu kawo ka'barsa ba , kamar yadda yake a page one na farkon labarinmu,idan Baku mantaba Page d'in mu na farko Hadiyyah tana d'aukar albashi fa Wanda Sa'adatu take kar'beshi shin wane albashine wannan? sai next page zakuji. yanzu labarin yafara bamuyi komai ba...... ✍️ Oum Arqam ce 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cy82IooiC1LE5S0e2tkKcj *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE EIGHTEEN 18* Kawu isma'il fa dun zuwan da Hadiyyah tayi wajensa akan xancen cigaban karatunsu itada Y'ar uwarta, Bata Kuma ganin saba, Kuma bai Kuma xancen ba, xaman gida ya isheta ga rashin kud'i wataran sai su tashi basuda abunda zasuyi Karin kumallo balle abincin rana, a unguwar tasu wata islamiyyah ta baza komar neman malamai wad'anda dazu dinga yiwa Yara karatu, shugaban makarantar har gida yazo ya nemi alfarmar Sa'adatu akan tabar Hadiyyah tana zuwa koyarwa makarantar tunda tanada ilimi sosai aikuwa take Sa'adatu ta amince duk wata xa'a Bata 10k aikuwa Hadiyyah akaita murna, saboda itadai har sannan Bata Saba da shan koko ba idan sun samu da safe ba da cin garin rogo shima, Amma tunda Bata sana'a haka takesha idan yunwa ta dameta,Ranar da ciwon ciki take kwana,aikuwa Ana Bata albashin farko Babu inda ta zarce dashi sai provision store taje taiyo siyayyar kayan shayi da pad abarda zasu buqata itada Y'ar uwarta Zahra, Dan kuwa WANI fannin ma Saida tsinma suke amfani(Allah sarki rayuwa) Babu kud'i gashi Basu sababa, musamman Hadiyyah irin mutanen da suke da kyankyami ne, Amma saboda wahala tai wahala daina jin wannan kyankyami d'in tayi,tana dawowa gida da kaya sai y'an ragowar canji aikuwa Sa'adatu ta rufe ido tai maya tatas Wai ai ko xatayi siyayya tabari ai takawo gida tagani, itadai Hadiyyah Babu bakin magana tunda tasamu abunda takeso, ai kafin wata kayan data siyo sun qare, saidai ta dinga ranta wajen Sa'adatu itakam ko biyar Bata Basu a matsayinsu na mata dole zasu buqaci pad da sauran abun amfani, hakane Yasa take rance a wajen Sa'adatu d'in, aikuwa ko kunya harda saka littafin bashi biyar ta kar'ba sai anrubuta, ai kafin wata ta kar'bi kud'i wataran sama da albashin ma, itakam Sa'adatu Babu lamuni haka ake rubutawa Ana albashi zata kar'beshi duka sannan tace Ina binki ragowar.......... Ita Kuma Sa'adatu tun bayan da Kawu isma'il yadawo maya da gidanta,sitting room ta mayar dashi shaguna guda biyar ta zuba y'an haya Ana Saida kayan miya,Me refelling na gas yakama,Mai islamic chemist da Mai siyar da kayan d'inki, Mai cajin waya, dayake layinsu irin babban layinnan ne duk irin wad'annan Sana'ar ba'a Yi kowa Yana cikin gidansa saidai yayi tafiyayyiya idan yana buqatar wad'annan abubuwan ai kuwa Sa'adatu tana saka haya kafin kuce mene sai aka Fara kasuwanci a gurin masu shagunan Suna samun ciniki, da kud'in hayar tayi wadaqarta aciki take arawa Hadiyyah kud'i, aciki take musu koko da jiqa musu garin rogo d'in, (...to FANS zara Bata barin dami ai Sa'adatu kud'in xai qare ai, Kuma shekara ba kwana bace, kafin kud'in hayar su sake dawo miki kinji jiki...) ************* Can Kaduna state ma da Hidayah sukayi waya da Hadiyyah tagaya mata cewa kawu isma'il Bai Kuma xancen cigaban karatunsu ba saita haqura Amma zuciyarta babu dad'i domin na 'kwallafa ranta akan hakan, tun bayan da sukayi candy shikenan kawu isma'il saiya ga damar tura musu kud'in da yake tura musu balle man shafawa dasu sabulu d'in, suma Haka su suke kasancewa yau da dad'i gobe Babu dad'i, shi dai Hunaif dayake har sannan Yana zuwa makaranta ta account d'in shugaban makarantar yake tura kud'in term to wannan ne bai fasa ba ,Dan kuwa da term yayi koda kawu isma'il Bai turoba take headmaster d'in xai kirashi yai Masa tuni Kuma babu batun yaqi turawa, Hadiyyah taci gaba da zuwa islamiyyah Suna Y'ar Sana'a acikin gida da ita suke rufawa kansu asiri, in sun samu suci idan babu suyi haquri............ ************* Ansha bikin mukhtar da bilkisu Y'ar uwarsa, Kuma har sannan ko ajikin Zakiyyah harkar gabanta takeyi, ba gida d'aya ya had'asu ba, saboda bayason bilkisu taga irin rashin arziqin da Zakiyyah takeyi itama bilkisu tadinga Masa shi,(... Lallai mukhtar baison mataba ne, Amma mace Mai hankali ai burunta taga abunda kishiyarta ta gazawa mijinsu ita Kuma ta zage dantse tana masa, nikam dana bawa mukhtar shawara ai had'asu waje d'aya yayi, ta yanda ko idan bilkisu tana bashi kulawa sosai yada Zakiyyah tayi hankali itama su dinga rige_rige wajen faranta Masa, ko fita yawon maqota da shashancinta xai ragu ta koma xaman gida ya kilukace FANS😅...) Saidai Kuma unguwa d'aya suke da Zakiyyah d'in, Babu nisa, mukhtar yayi kwana bakwai a gidan amarya kamar yadda musulunci ya koyar da ayiwa budurwa ga mijin da yayi Aure idan yanada wata matar, zaman da yayi da bilkisu mukhtar yaga soyayyah da kulawa uwa uba ga tarairaya, to dama ita bilkisu tasan me Zakiyyah takewa mukhtar, tasan duk halayenta, koda ta shigo itakam ta qudurce a ranta duk WANI kulawa da tarairaya da farantawa zata dinga Masa kodan taxamo, matar so wajen mukhtar, taxamo Babu ya ita, tasa mukhtar yadaina rangwantawa Zakiyyah a duck sanda tai masa ha daidai ba yanuna Mara kuskurensa, shikam mukhtar sai yaji kamar karya koma wajen Zakiyyah, saboda babu abunda yake kwasa sai ba'kin ciki da 'bacin Rai (... Yakamata y'an uwa mudaure mugyara musani cewa,koda mazajenmu sunyi aure karsu manta da kulawar da suke samu a gurinmu, karmu yadda muxamo kamar Zakiyyah🙏 miji yadinga tunanin kamar karya koma wajen mu...) Koda yadawo gidan zakiyyah dai WANI kunbure_kunbure takeyi, shi ko takanta bai biba, harkar gabansa yakeyi, ya d'au ABIE Wanda yake tai masa dariya, nufin yaron ina kashiga Daddy Kwana biyu, itama Zeenah taita murna, duk da darana Yana leqosu ai kwanane bayayi kawaii a gidan,Kwana biyu dayayi a gidan zakiyyah Babu abunda ya kwasa sai ba'kin ciki,da baqaqen maganganu da tadinga gaggaya Masa,shima dama zuciyarsa tana kusa bai qale taba, ta gaggaya mata magana Kuma yace "daga yanxu duk abunda kikaimun wlh saina rama nadaina tausaya miki tunda Baki tausayawa kanki ba,Babu yanzu Wanda nake ganin mutuncinsa, ko idonsa naki Wanda zaisa na raga Miki, tunda Baki da mutunci baki da tarbiyyah, tun iyayenki da kakarki Suna raye ake sulhu tsakaninmu Amma ko bayan rasuwar su HAKAN baisa kin daina halinkiba,sai abunda yayi gaba to muzuba mugani, ni dake shege kafasa,to tun daga auren da mukhtar yayi tsakanin Zakiyyah da mukhtar kullum Suna ta fad'a sai kace karnuka, lallai FANS baxa kubawa Zakiyyah shawara ba........ ************* Alhaji mutanen TALLAFY CHARITY FOUNDATION anacan duk WANI 'ka'idojin da ake buqatar d'an makarantar yacike ya kammala yanzu haka Shirin fitar dashi ake daga ajin dayake zaune shi kad'ai, a had'ashi da sauran dalibai, saboda ana ganin nasara sosai a wajensa duk Wannan kunbure_kumbure dayake yadaina, Rashin kunya itama yadaina, shaye_shaye kuwa dama aina zai samu,Masha Allah Allah yad'orar a hakan Alhaji Allah ya shiga lamarinka marayan Allah........ Alhaji 'Dalhat Abdur_rahman *(TALLAFY)* wannan satin xai kawowa TALLAFY CHARITY FOUNDATION ziyara, domin yakwana biyu baya qawar, yaje ganin likitansa da Kuma ziyarar y'ay'ansa a *NEW DELHI* Wato india can suke karatunsu, to wannan satin xai dawo, sai muce Allah yadawo dashi lafiya.......... Salon daban yake Muje zuwa FANS ✍️Oum arqam ce ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE NINETEEN 19* Ina godiya ga seerat, mumy Waleed, Alhamdulillahi da irin kulawar da kuke bani Dan ganin ina typing akoda yaushe, nagode da adduarku gareni naji sauqi sosai, RASHIN IYAYE zai dinga zuwar Muku a koda yaushe sai uziri ya sameni 🥰🥰🥰 IDan kadubi cikin TALLAFY CHARITY FOUNDATION kai kace Biki akeyi ko wani babban taro, kowa sai hada_hada akeyi tun daga kan ma'aikata da d'aliban wannan cibiya,bakomai yajanyo hakaba sai ziyarar da Alhaji TALLAFY zai kawowa Wannan cibiya, yau Kimanin wata hud'u Kenan bai zoba, dama kaidarsa wata uku_uku shiyasa ma'aikata suke cikin Murna idan yazo Ranar rabon kud'i kawai yakeyi musu......... Alhaji dai yau dai yasamu y'ancinsa xa'a fito dashi daga d'aki na musamman da aka killaceshi, a wannan lokacin ne Kuma Alhaji TALLAFY yace Ranar yanason ya gana da wad'annan da xa'a fito dashi,(... Indai irin wannan lokacin yazo na fitar yaro daga cikin d'aki na musamman a Ranar Alhaji TALLAFY zaizo to kafin a fitar dashi daga d'akunan, Alhaji TALLAFY dakansa zaije wajensu yai musu nasiha ta musamman sannan Kuma ya saurari mene matsalarsu meyasa suka jefa kansu a wannan matsalar, duk Wanda yanar dazai fita daga d'aki na musamman Alhaji TALLAFY yazo to tabbas sun ciri tuta...) Duk abunda ya kamata Alhaji TALLAFY yayi a cibiyarsa, sannan yayi ganawa da d'aliban da suka Samu y'ancinsa, haka duk yagana dasu kowanne yai Masa nasiha da illolin shaye_shaye duk jikinsu yayi sanyi, ayoyi da hadisai yadinga janyo musu wad'anda Allah da manzon sa suke tsoratarwa Akan Mai shaye_shaye da Kuma illolin sa'bawa iyaye, domin kuwa iyayensu basason shaye_shayen da sukeyi, kowanne Saida jikinsa yayi sanyi,Kuma suka yiwa Alhaji TALLAFY alqawarin sun daina in Sha Allah, Alhaji yayi murna da Wannan, Kuma duk yaji mene ne musabbabin Fara shaye_shayen yaran mafi yawanci, sanadin abokai ne wad'anda suke had'uwa dasu a makaranta, suke Fara zuwa da maganin tari azuba a lemo wannan azo ga manyan su wiwi, taba uwa uba giya, yawanci dama duk y'ay'an masu hannu da shuni ne.......... Alhaji 'Dalhat Abdur_rahman (TALLAFY) dayazo kan Yassir Ammar Yassir (Alhaji) lokacin ma shi, yatafi duniyar tunani Halin daya tsinci kansa aciki, wai kamarsa shine aka kawo nan aka killace akan shaye_shaye da rashin Kunya, kullum tunaninsa Kenan, Yana tuno Aunty(Sa'adatu) da Kuma irin cin amanar da Kawu isma'il yai musu Dan yaga Abbynsu baya raye, uwa_uba da irin xaluncin da Aunty takewa su Zahra da Hadiyyah,shine yake sawa yake shiga cikin qunci, Wanda shine Kuma yake shan wiwi saboda yafita daga cikin tunanin, yanxu Daba wiwi d'in in Yana tunanin kawaii Saidai aga hawaye Yana zuba a fuskarsa musamman idan yatuna irin gatan da Abby ya nuna musu, da Kuma kulawar Ummy(Ummu Ruman mahaifiyar su Hadiyyah) ta nuna musu Bata banbantasu dasu Hadiyyah, Amma yanzu ita Aunty gashinan Bata yiwa su Hadiyyah hakaba sai wahalar dasu take, har Mai tsaron bayan Alhaji TALLAFY yazo kan Alhaji Yana Masa magana baisan Yana yiba,Saida Alhaji TALLAFY ya taso dakansa yazo ya tallafo fuskar Alhaji d'in (... Domin yaron tun farkon ganinsa dashi yake bashi tausayi, Yana Masa kama da Halin da y"ay"ansa guda uku suka shiga shekarun baya, suma Haka suke takurewa aguri guda suna hawaye🥹meyasa HAKAN FANS? Nagadai Alhaji TALLAFY yayansa me zasu rasa...)...... Saida yad'ago da fuskar Alhaji sannan yadawo hayyacinsa, ya duqa a kasa Yana gaisar da Alhaji TALLAFY d'in, sannan Yana goge fuskarsa,ruqo hannunsa Alhaji TALLAFY yayi suka qarasa gurin da aka ajiye Masa abun Zama, sannan Alhaji yasamu kasan wajen ya zauna, sai sannan Alhaji TALLAFY yaiwa Alhaji magana dayaga yanxu yasamu nutsuwarsa," yaro wannan tunani namene kakeyinsa kamarsa kana d'an yaronka? Shin meyasa kajefa kanka a wannan mawuyacin hali, inason karka boyemin komai kaji Ammar, yawarasa maganar a tausashe(... Tausayi yaron yake bashi, tun farkon ganinsa dashi,daga gani d'an gata ne, Amma wannan damuwar dayake gani a fuskarsa ta menene kodai irin abunda yasamu su AKILA ne.. FANS inada tambayoyi Akan iyalan Alhaji TALLAFY fa kufa.?..... ) Tiryan_tiryan Alhaji ya zayyanawa TALLAFY labarinsa da maraicin da suke ciki da labarin y'an uwansa su Zahra da Hadiyyah Khadeeja da Kuma zeeenah sai babbar banza Zakiyyah, da irin maraicin da suke ciki duk WANI gata da suka kasance acikinsa da yagayawa Alhaji TALLAFY masu takewa Alhaji TALLAFY baya duk Saida suka tausayawa Alhaji sosai,Amma Kuma ababan tausayi a yanzu y'an uwansa mata su Hadiyyah Wanda Suna y'an biyu Amma Saida aka rabasu d'aya tana kano d'aya tana Kaduna..... Alhaji TALLAFY ya jinjina kai bayan Gama jin labarin Alhaji, shima yai Masa nasihohi sosai Akan yacire komai a ransa, indai saboda y'an uwansa ne zai tallafa musu, Kuma idan kawu isma'il yazo zasuyi magana, Alhaji Kam yaji dad'i sosai, dajin abunda TALLAFY ya fad'a, dama burinsa shi dai yanzu kawu isma'il ya saki Aunty(baisan kawu isma'il ya saketa ba ) yadawo musu da gidansu daya kwace musu, da dukiyarsu da take hannunsa yake cinye musu, itama Aunty(Sa'adatu) yanzu haushinta yakeji ganin irin azabtar dasu Hadiyyah data keyi..... Akwai qura fa FANS........... ************* Zakiyyah anadai zaune itada mukhtar babu mutunci kwata_kwata rashin mutunci salo_salo take Masa, ABIE yayi wayo Dan kuwa an yayeshi Amma kafin yakai Wannan matsayin Yasa wuya qonewa kala_kala yayita da ruwan zafine da abinci, Zeenah kam tuni tabar gidan,tun WANI gurmi da akayi tsakanin Zakiyyah da mukhtar d'in, yai mata dukan tsiya aikuwa yasha zagi ta uwa ta uba, shikam yakorata gidansu yace ta tafi, baya buqatarta a tare dashi, ya d'auke ABIE da Zeenah zai kaiwa amaryarsa bilkisu Akan ta riqe Masa, aikuwa nan fa Zakiyyah tabud'e baki tadinga zagin mukhtar har dacewa ABIE idan ka kar'ba bazan hana kaba saboda d'an kane,badashi dama nazoba, Amma Zeenah kam ba ikon kabace ba uban ta bane kai, baka Isa ka kar'beta ba da ita zan tafi, Kuma in kai ba d'an halak bane ka kar'beta ka kaiwa Wannan jakar(bilkisu), duo da HAKAN baiyi gaggawar Bata Zeenah ba(... Tsakani da Allah yakeson Y'ar nan, Yana sonta kamar Y'ar cikinsa, Kuma karatunta yake tsoro Takoma baya, yanzu tana aji hud'u a primary ne, Kuma Yana tsoron Mata shiga cikin halin da y'an uwanta suke ciki Khadeeja dasu Zahra, domin kuwa tun kafin ya d'auko ta tadawo wajensa bayan rasuwar Ummu Ruman hydar 'Dan wajen Sa'adatu yafara dukanta batada sakat a gidan Wanda da Baya mata HAKAN Saida yaga Ummu Ruman ta rasu, saidai taita kuka, inya daketa sakontane ya girmeka da Wajen wata biyar, su Zahra Babu damar magana, suma Basu tsira ba, wayyo Zeenah FANS halin da Zakiyyah zata kaita ciki kenan, Allah dai Yasa karya badata...)....... Saboda kar mukhtar yayi gaban kansa sai da ya d'au wayarsa ya Kira Mana( mahaifiyarsa Hajiya Jamila) domin yaji shin yabawa Zakiyyah Zeenah ta tafi da ita, gidansu itama Zakiyyah d'in ya koreta............ Muje zuwa FANS shin Hajiya Jamila zata bar mukhtar ya kori Zakiyyah ko Kuma abunda ta Saba zatai Masa nacewa ya qaleta......... ✍️ oum ARQAM ce ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* Kuyi haquri da wannan nagama typing page Mai shegen tsayi Amma ya goge😭😭😭 gaskiya banji Dadi ba nasha wahala a banxa *PAGE TWENTY 20* Hajiya Jamila Mukhtar ya Kira bayan ta d'aga wayar sun gaisha zuciyarsa nai masa quna a muryarsa babarsa tasan cewa tabbas Yaronta yanada damuwa" meyake damunka mukhtar cewar Hajiya Jamila cikin kwantar da murya" duk yadda sukayi da Zakiyyah ya kwashe yagayawa mahaifiyarsa karshe yace" Mama abunda Zakiyyah takemun takaini bango cewa nayi ta tafi gidansu nasa hannu na d'auki Zeenah da ABIE shinefa taketa cimin mutunci wai ai iDan na d'au ABIE nine babansa ita Kuma Zeenah wai ai bamu da had'i da ita dole nabata ita su tafi....... Kwarai dagaske haka nace aiba Y'ar ka bace Zeenah mene had'inka da ita? Kace natafi gidanmu itama Zeenah yau sai kwanan gidan ubanmu, domin kuwa Banga me zaisa ta zauna a gidanka ba!! Abunda Zakiyyah take fad'a cikin d'aga murya kenan, Kuma Hajiya Jamila tana jiyowa ta wayar, cikin muryar damuwa mukhtar yace" Mama kinji irin abunda take gayan ko? Tunda na Auri Zakiyyah bana cikin kwanciyar hankali itace yawan ma'kota, Tara mata acikin gidana, itace banzatarmun da kayan abinci, komai nawa Baya jimawa tace ya qare, a haka mama kike goyuwa da bayanta kona kawo qararta wajenki saidai kibini da fad'a kice banida haquri ai Zakiyyah yarinyace, haka nake haquri da ita,karshe kikace ai iDan ta haihu xatayi hankali to YANZU wane hankali tayi, bayan Haihuwarta wane irin wahala ce d'an data Haifa baisha ba, 'konewa kala_kala,ciwuka wanne irine baiji ba a tsawon shekara uku da haihuwarsa! Mukhtar yake fad'a cikin muryar damuwa itakam Hajiya Jamila tanajin d'an ta Bata katse Shiba,saboda tasan mukhtar yanada haquri Amma idan aka kaishi bango bai iya fushi da fad'a ba, Saida yaja ajiyar zuciya sannan yaci gaba daga inda ya tsaya kince mama idan Zakiyyah ta ta haihu xatayi hankali to YANZU haka ina hankalin yake? Cewar mukhtar tana duban indai Zakiyyah take a tsaye tana girgiza jiki alamun babu mutunci...... Sai sannan Hajiya Jamila taja doguwar ajiyar zuciya alamun duo maganganun da d'an nata yafad'a sun shigeta zata Fara magana ne Zakiyyah ta d'ora da cewa" duk abunda zaka gayawa mama kagaya mata wallahi saika bani Zakiyyah Kuma daga yau d'in nan kwanan gidanka bazan yiba, ita Maman ba itace ta zugaka tasa ka aure Y'ar kanin taba, me xata gayan? Inma ta fad'a baji zanyi ba ehe! Inji Zakiyyah tana tattafa hannayenta.... Ikon Allah gaskia mukhtar yayi haquri da xama da wannan yarinyar dama haka take? Batada tsinkaya, lallai kam na takurawa yarona xaman haquri shida ita, Allah yai maka albarka haqurinki ya biya maka, ha kowanne najimi bane zai zauna da irin wannan matar Mai Rashin kunya ga miji abunda yafi duka ma saikayiwa mace abunda Hajiya Jamila take fad'a acikin zuciyarta kenan"" YANZU dai samu waje ka zauna zanyi magana dakai mukhtar cewarta, to Mama ya fad'a yana riqe da hannun Zeenah yana dosar d'akin barcinsa da ita, saboda karya saketa Zakiyyah ta d'auketa ta fice, aikuwa saiji yayi Zakiyyah ta wawuri Zeenah dake hannunsa tana cewa' wallahi baka isaba Ina zaka da ita? Wato xaka je ka shige da ita d'aki ka kulle? Wallahi saika bani Zeenah ai ba Y'ar ka bace Inka riqe ABIE Wannan kam ba iko(.... Anya FANS Zakiyyah tanada Hankali kuwa, duk irin d'awainiyar da mukhtar yayi da Zeenah take gaya Masa Haka?..) har sannan Hajiya Jamila najinta, Mukhtar sakar mata Zeenah d'in kaji, cewar Hajiya Jamila to inji mukhtar yana sakarta kuwa Zakiyyah ta d'auketa, Lallai Zakiyyah FANS da dasassafe ne fa, matsalar ta faru tsakaninsu yace tabar Masa gidansa, Kuma karta sake ta d'auki ko d'a d'aya ta tafi dashi, TSAKANIN Zeenah da ABIE duk barci suke a d'akinsu, shine yace tabar Masa gidansa, aikuwa tayi kukan kura ta fad'a d'akin ta d'auko Zeenah wacce take barci tace dashi" ABIE ne ikonka Zeenah kam babu iko dole mutafi tare,itakam Zeenah sai muka take taga abunda yake faruwa tsakaninsu, duk da bayau tasaba ganiba Amma nayau yafi na kullum....... Yana shiga d'akinsu bakin gado ya zauna zuciyarsa tana Mana quna da rad'ad'in abunda Zakiyyah tai masa, Amma Kuma yaji dad'i sosai datayi a kunnen Mama tanaji, yanxu babu yadda za'ayi ta barshi yaci gaba da xama da ita Anya kuwa FANS..? Ajiyar zuciya mukhtar yayi sanna yace kinji irin abunda take mun akoda yaushe ko Mama? Ni gaskia nagaji da halinta tsakani da Allah fa kawai zan aika mata da takardar sakinta ne cewar mukhtar yana magana a sassarke cikin 'bacin Rai...... Ajiyar zuciya Hajiya Jamila tayi sannan tafara magana" duk abun Zakiyyah tai maka naji mukhtar, kaduba halaccin iyayenta akanka, musamman Hajiya Sakinah yarinyarnan Bata Isa aure ba haka aka wanke aka baka ita, dai_dai gwargwado iyayenta tun Suna raye Suna mata fad'a sulhu wane irine ba'ayi tsakanin kuba mukhtar? Nima Kuma ina tausarka, kazo kacemun kanason aurar bilkisu nayi tunanin aurenta zaisa zakiyyah tayi hankali Amma ina! HAKAN babu abunda yakuma sakawa sai ta'bar'barewar al amari tsakaninku, Kayi tunani da hankali mukhtar saki baxai xama masalaha tsakanin kuba,ban amince ka saketa ba , saidai na amince kabarta taje gidansu ta d'ana zaman gidan uba bayan mace tayi aure, Kuma a gidan akwai kannenta y'an mata, babu uwa Babu uba zatayi hankali nina gaya maka, kabarta taje tawo hankali acan kaji mukhtar yaron kirki cewar Hajiya Jamila tana sassauta murya, mukhtar yace shikenan abunda mama kikace hakan zanyi Amma nikam dana haqura da ita, danasan Zaki ce karna saketa Mama sai bayan na aiwatar xan kiraki nagaya Miki kona zo har gida, Lallai mukhtar kasan hakan bamai yiwuwa bane ai koka saketa ai saika mayarta, a haka suka tattauna matsalar Zakiyyah d'in da mukhtar da mahaifiyarsa, inda aka tsayar da magana zai barta a gida har saitayi hankali, daga karshe tace yanxu dai ka d'auki ABIE da kayansa ka tafi gidan Bilkisu kafin Allah Yasa uwarsa tayi hankali, to shikenan Mama allah yasaka da alkhair har naji zuciyata tayi sanyi Amma da kamar takama da wuta nakeji, cewar mukhtar yana kashe wayar.......... Zakiyyah Kam mukhtar yana sakar mata Zeenah d'akinsu ta shiga da ita ta d'auko trolly ta zuba kayan Zeenah da nata aciki ta canza mata kaya kayan barcine a jikinta, ko wanka babu haka ta shige ta bar gidan ko kulle Masa 'kofa batayi ba(... Lallai Zakiyyah FANS bazaku Bata haquri ta zauna ba ko? Nikam Zeenah kawai nake tausayi...) Mukhtar yana fitowa yaga babu Zakiyyah Babu Zeenah alamu ya nuna ta jima da ficewarta, lallai yarinya bakida hankali zaman gidane yanzu Kika Fara saikinyi hankali kinyi laushi sannan xan dawo dake, biyar d'ita bazan aika miki da itaba, Allah sarki Zeenah Y'ar uwarki ta janyo miki Amma ina sonki a raina kamar ABIE, zan dinga aikawa da Mai adaidata sahu yana kawomi makaranta baxanso karatunki ya tsaya ba, da banbncin makaranta tsakanin y'an uwan Zeenah d'in da ita ita pravet ce mai shegen tsada yasanta mukhtar d'in, sukam tun bayan rasuwar mahaifinsu kawo isma'il yacanza musu makaranta itama dai Bata gomnati bace Amma batakai wacce mukhtar Yasa Zeenah ba(... Lallai fans allah Yasa Zakiyyah ta yarda a dinga kai Zeenah d'in makaranta..) Allah yajiqan iyayenki Alhaji Ammar bn Yassir da Hajiya Ummu Ruman sun Mana sulhu tsakaninmu saboda kar zamanmu ya lalace takaimu ga rana irinta yau Amma Saida hakan yafaru saboda Rashin hankali naki Zakiyyah, sannan kakarki mariqiyarki Hajiya Sakinah itama kafin rasuwarta taimana sulhu bazai qirguba Amma duk Kika Shure Saida HAKAN yafaru, Allah yagani banci amanar suba bayan ransu kome yafaru kece sila Abubuwan da mukhtar yake ta sa'kawa a ransa kenan...... d'akin su ABIE yafad'a har sannan yaro barcinsa yakeyi, baisan abunda take faruwa ba d'aukarsa yayi ya sa'ba a kafad'arsa ya d'ebi kayansa a wata trolly ya saka a mota shima yashiga ya fice daga cikin gidan bayan ya kulle gate d'in GIDAN,sai gidan Bilkisu (... Lallai FANS Zakiyyah ta saki damarta yanzu bilkisu ta samu mukhtar a hannunta...) Can bangaren Zakiyyah itama Haka ta qarasa bakin titi ta hau adaidaita sahu sai gidansu..... Tana zuwa lokacin gidan yayi tsit duk yarab suna makaranta Khadija, Farouk, hydar Hafsat autar Sa'adatu, itama Zahra tana school suka exam, Wanda Kuma Auranta kenan ya matso, in Baku mantaba saurayinta Ibrahim bala yayi maganar akace yabari sun kusa exam sai ayi maganar aure to gashi Allah yakawomu lokacin, Zahra Allah ya fito da sakamako Mai kyau, Allah sarki tagwaye su Hadiyyah da Hidayah sukam basu samu Wannan damar ba, koda yake itama Zahra d'in tun lokacin mahaifinsu Yana raye ta Fara school d'in, aidai da kunya kawu isma'il ya katse mata karatun Dan kuwa tafara nisa....... Y'an biyu Hadiyyah kuwa anacan makaranta ana koyarwa, Kuma Masha Allah Yara suka fuskantar karatun sosai, Dan kuwa saita bibbiya musu har sun iya, sannan kowa da kowa yabiya d'aya bayan d'aya, malam jibril yanajin dad'in samun Hadiyyah a makarantarsa domin kuwa sai samun albarkar dalibai yakeyi sanadin Hadiyyah.... Zakiyyah tayi sallama gidan nasu hanunta riqe da trolly d'aya hannun da Zeenah wacce taci kuka har tayi shiru, itama fuskar Zakiyyah d'in Babu walwala, Sa'adatu ce ta fito daga d'aki tana amsawa , turus ta tsaya ganin Zakiyyah ba cikin nutsuwa ba, daga ina Kuma Zakiyyah? Ina ABIE d'in? Zeenah itama ina makaranta naganku tare? Tambayoyin da Sa'adatu ta jerawa Zakiyyah lokaci d'aya Kenan, Zakiyyah batayi maganaba sai qarasawa d'akin Sa'adatu datayi itama Sa'adatu ta bita, bayan Zakiyyah ta ajiye trolly d'in hannunta ta samu waje ta zauna sannan tafara magana,,,,,,,,, Aunty nagaji da abunda mukhtar yakemun tunda yayi aurensa nadaina shiga harkarsa, banason ganin yazo gidana kwata_kwata shi,,,,, rufemin baki marar hankali kawai kekam Zakiyyah bansan lokacin da xakiyi hankali ba Sa'adatu ta katse Zakiyyah daga cigaba da maganar rashin hankalin datake,nikam babu abunda xance dake zaman gidannan kikeso gashinan, yau asamu aci gobe asha ruwa a haqura, halin da muke ciki kenan da y'an uwanki, kawunku Mara imani(kawu isma'il take nufi, lallai FANS sai yanzu tasan da HAKAN..😀)Rabon daya kawo Mana 'kwallon abinci har mun mance, balle sabulun wanka Dana wanki, wai Sunan dukiyar ku tana hannunsa,yana juyawa ana samun riba babu ruwansa da rashin lafiyar yarannan, su mutu babu ruwansa isma'il yaci amanar Ammar Kuma in Sha Allah baza aje ko inaba zaiga karshensa (..lallai FANS kema ai za'aga karshenki ne duk maciya amana ne dagake har shi...) Ga gurin xama nan Zakiyyah ki zauna dama su Zahra Suna makaranta banyi shara ba balle wanke_wanke saikixo kiyimin domin bazaki zauna ina kallonkiba, ruwankine ki Kira kawun naku kigaya Masa halin da kuke ciki keda mukhtar, ABIE Kuma kin barwa mukhtar kenan ko? Shi yace nabashi d'an da nikam nabashi ai badashi najeba, yaso kar'bar Zeenah nanuna Masa Wannan Kuma bai isaba ba ikon sa bace, cewar Zakiyyah tana kumfar baki, itama Sa'adatu ko a kwalar rigar ta da zuwan Zakiyyah gida Kota tausaya tace bari na mayarki gidan mijinki, naji meke faruwa? Burunta ma tai mata Aiki lallai FANS yakuke ganin xaman Zakiyyah a Wannan gidan? Yasu Zahra da Hadiyyah zasuji idan suka dawo sukaga Zakiyyah tayo yaji............... ************** "Yau kwana biyu kenan Abu *AQEEL* nake ganinka cikin damuwa, kodai WANI abune ya samesu dakaje dubasu a India?ko likitanka yace kana da wata cutane kake 'boyemin baka gayamun ba? " cewar Hajiya Aisha matar Alhaji TALLAFY tana kai duba zuwa gareshi tana Zama a kuwa dashi, a gefen tuntun daya kishingid'e a kansa,Ajiyar zuciya Alhaji TALLAFY yayi sannan yafara magana " ko d'aya Oum *AKEEL* duk tambayoyin da kikayimin Babu d'aya daga ciki, Alhaji TALLAFY yafad'a yana tashi daga kishingid'en dayake, dafa kafad'ar Hajiya Aisha yayi sannan yaci gaba, Oum *AKEEL* a cibiya ce na had'u da WANI maraya Wanda tunaninsa da y'an uwansa yake sani a damuwa sainaga labarinsu shigen nasu *AQEEL* duk da su kishiyar uwa ce takewa y'an uwansa Haka Kuma mahaifiyar yaron dayake cibiyar tawane, nan ya kwashe labarin da Alhaji yabashi tatas yagayawa Hajiya Aisha, lallai kam akwai tausayi a halin rayuwar yaran Abu *AQEEL* Kuma Wannan yaro Alhaji lallai yanson y'an uwansa Wanda akansu yashiga halin shaye_shaye, Kuma ba kowacce Mai azabtar dasu ba face mahaifiyarsa, sai Kuma ba'kin cikin cinye musu dukiya da kawunsu yayi, da Kuma aure masa uwa da yayi duk da ita uwar kome yafaru itace silar komai, yaron yabani tausayi sosai, Amma Kuma duk azabar da y'an uwansa suke ciki takai Wanda su *AQEEL* da *AKEEL* dakuma *AKEELA* suka shiga karka manta sufa kishiyar uwa ce tai musu hakan, Wanda haka ba sabon Abu bane, Dan kishiya ta azabtar da y'ay'an kishiyarta , sufa su *AQEEL* yayar mahaifiyarsu ce ta azabtar dasu, abunda Hajiya Aisha take tunawa Alhaji TALLAFY kenan tana kai duba zuwa gareshi da kalami Mai kwantar da zuciyar Mai sauraro, yakamata Abu *AQEEL* kacirewa kanka damuwa karka Kuma shiga halin daka shiga shekarun Baya da suka wuce kaji Abu *AQEEL* numfashi Alhaji TALLAFY yaja sannan yace karki damu oum *AKEEL* zan cirewa kaina damuwa in Sha Allah nai miki alqawarin haka, Amma inason zuwa naga halin da wad'annan marayun Allah d'in suke ciki, bazan manta wahalar da yarana suka shugaba shekarunta Baya, shiyasa nasawa raina a duk inda maraya yake ko WANI Mai neman taimako zan tallafa Masa indai nagani konaji cewar Alhaji TALLAFY........ A haka dai Hajiya Aisha ta kwantarwa da mijinta hankali har tayi Masa alqawarin da ita za'aje wajensu, aikuwa Alhaji TALLAFY damuwarsa kaso casa'in cikin d'ari ta goge, shiyasa yake alfahari da kasancewar Aisha matsayin matarsa duk WANI abun alkhair itace take goya Masa Baya........... Lallai fans alkhair Baya fad'uwa kasa abanza ga alkhair da Alhaji Ammar yayi yau gashi qasa ta rufe masa ido Allah yakawo Mai tallafawa zuriarsa Allah yakawo musu TALLAFY cikin rayuwarsu..... Muje zuwa FANS 🥰 yanxu aka Fara RASHIN IYAYE....... ✍️oum ARQAM ce ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE TWENTY ONE 21* "Lokacin da Zahra ta da wo da ga makaranta ta tarar da Zakiyyah da Zeenah ta yi tunanin Zuwa gidan kawai wuni ta yi, harda murnar ta, domin ba zuwa gidan take yi ba, sai sa'i da lokaci, Amma ta na shi ga cikin d'a kinsu sai tayi turus ganin trolly d'in Zakiyyah. "Ita Kuma lokacin Zakiyyah d'in tana flourn Aunty Sa'adatu tana kallo,ko ajikinta. A" san ya ye Zahra ta shi shi go flourn ta Sa mi Zakiyyah tam Baya ta Fara jefo mata, kamar Haka" Maman ABIE(.. haka suke ce mata tun bayan haihu warsa..) naga trolly d'in ku ke da Zeenah, Kuma Banga ABIE ba, ga shi magriba ta gaba to, baki ce Zaki tafi gida ba? Sannu uwa ta sannu uba na! Cewar Zakiyyah cikin d'aga muryar! Za kixo kina mun tamba yoyi ma su yawa Haka, wacce daga ciki kike so na Amsa miki Aunty Zahra? Domin na ga kece yayar tawa! Ta qa rasa kai aya tana wuwwura hanci da d'aga ba ki! "Nifa ba haka nake nufi ba kawai dai mamaki nayi ne, ban ta'ba ganin kin zo gida irin Haka ba,Kuma har da su trolly had'e da Zeenah Kuma, ita datake zuwa makaranta, shi kuma ABIE Banga kinzo dashi bane shi yasa Amma kiyi haquri!cewar Zahra domin ta ga Y'ar uwar Ta ta ta fusa ta da yawa. Sai sannan Sa'adatu tasan ya musu baki a maganar ta su, amma da tana zau ne, Hmm! Zahra Kenana Y'ar uwarki Kam ai abunda ta sa ba tayi Wannan karon mukhtar ya ga ji da halinta shi ne ya sallamota gidan! "Zaro idanu Zahra tayi sannan ta ce Lallai Zakiyyah kekam me yasa hakan? Babu abunda Abban ABIE Baya miki,Kuma in wannan matsalar ce ai tun su Abby suna raye ake sulhu tsakaninku, Amma sai da Kika janyo ya sakeki Zahra ta qarasa cikin kuka! "Ba sakinta yayi ba Zahra korota yayi, cewar Sa'adatu! "Sakin ma yana hanya ai cewar Zakiyyah (... FANS Zakiyyah ta nada hankali kuwa?..) Ai shikenan Zakiyyah Duk yadda xa kiyi nikam ko a jikina gidane ga kinan ga shi, cewar Sa'adatu tana ki shingid'a. "Dan Allah Zakiyyah ki Koma gidan mijinki ki tausaya wa ABIE, tunda ba sakinki yayi ba gobe zan raka ki,ki Koma kinji! "Lallai ma Y'ar nan saki raka ni ga ki uwata! yadda ya hula kantani ko zan ko ma gidan sai ya zo dakan sa ya bani Haquri! Ai shikenan Zakiyyah ga guri nan ki zau na, nikam babu ru Wana, abinci a gidannan ba kullum muke ko shi ba, sabulun wanka ba ma sa mu da omo muke wanka! Gidan ki kuwa B abu a bunda Kika rasa! Nan dai Zahra ta dinga nu sar da Zakiyyah ko zata sau ko daga do kin zuciyar Data hau Amma ina! Sai abun ya kaisu kamar zai xama fad'a! A haka Hadiyyah ta dawo da ga islamiyyah ta sa me su, itama bata ji da d'in fitowar Zakiyyah da ga gidan mijin ta ba, Amma yadda ta samu Suna gur mi da Zahra ba tayi gi gin saka mata baki ba, do min ta san baza ta tsinci ko mai wajen Zakiyyah ba , ha ka za tace ta dai na saka mata Ba ki acikin maganarta Sa'ar tace! Shi yasa tana jin abunda suke ta shige d'akinsu ta barsu nan(.. Hadiyyah akwai zuciya ba ta shi ga harkar da ba Ta ta ba, musamman Zakiyyah tun da a qone war ABIE da tayi magana race mata karta qara saka mata baki a sha'anin ta domin ita ba Sa'ar tq bace, aikuwa kam Hadiyyah ta haifu, Duk gurmin da ake ko yaro bata yi ba..) A haka sauran y'an makaranta su khadijatu da Farouk da hydar suka da wo, hydar ya na ganin Zeenah sai murna wai za suyi wasa, kuji fa hauka FANS, ka fin ya fara dukanta. Ranar ma Babu abincin da re a gidan sai dai ayi salati FANS ya kuke gane min Zakiyyah 🌚.......... ************** "Tun ba yan barin kawu isma'il da ga gidan Sa'adatu, Matarsa Hauwa da ta fuskanci bafa ya kula marayun Allah Wanda hakkin su yake kansa, tana nusar dashi cin dukiyar maraya, Amma Duk sanda tai masa magana sai yace " Hauwa ina ruwan ki da harka ta ne? Kina saka min ido fa, me kike nufi ne? Kina tunanin zanci amanar y'ay'an D'an uwanane? Ki shiga hankalin ki Hauwa kome nake ina yinsa da hankali da tunani na(... Wai haka FANS...) Tun daga Ranar Hauwa ta daina shiga hurumin mijinta isma'il Duk abunda zai yi yayi, Allah ya gani dai dai gwargwado tai Masa nasiha, Amma Kuma tunda shaid'an yana kansa ta rabu dashi. Tu ni ya canza motar Hawa,sai d'in Kuna yake zu bawa, yana wa daqa da kud'in marayun Allah,kawu isma'il ka kiyayi karshenka. Kwanan Zakiyyah biyu ta fa ra d'iban gashin yun wa Amma ba ta karaya ba, sai ta d'auki waya ta Kira number d'in kawu isma'il tai Masa bayanin cewa tana gida, Kuma babu abinci, ita tanaso ma ya Bata jari ne tafara Sana'a domin dogaro da kanta(... Lallai FANS xama kenan Zakiyyah tazo gida..) sannan tai Masa xancen saka Zakiyyah a makaranta, ho!ho!ho! Lallai kam Zakiyyah Tasha zagi ta uwa ta uba, a wajen kawu isma'il sannan yace ba shida kud'in ba ta, tun da xaman gida ta keso ga ta ga shinan, kud'in su ma dayake hannunsa ya qare a ne marwa Alhaji TALLAFY foundation, Haka yace musu kud'i dayawa ake kashewa idan xa'a Kai yaro, Amma ba suyi tunanin xaice hakan ba, sannan ya ce shi yanzu ba kud'i ne dashi ba, bare ya tallafa musu dana sa.... Kunsan dai FANS Zakiyyah ba bu kunya, tunda kud'in mu da yake hannunka kace ya qa re, inaso kaba ni a cikin kud'in da kake kar'ba na hayar gidanmu, ehe ko shima zakace ba bu ne? Lallai ne Zakiyyah ta tun zura kawu isma'il fa, fito na fito takeso tayi dashi fa fans, Anya kuwa hakan zai yiwu tsakaninsu? Ai dama gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta, Kuna gani fa FANS tunda Hadiyyah taje gidansa Akan yayi musu admission itada Y'ar uwarta har yau shiru, Kuma Bata Kuma cewa komai ba, to yanzu gashi Allah ya had'ashi da marar kunya marar hankali ga'buwa, shin Zakiyyah zata qara da Kawu isma'il kuwa...? ************** Kaduna state.... "Baaba tayi ba'kin ciki da Hadiyyah su kayi waya da Hidayah take ce wa ai Zakiyyah ta na gida yaya mukhtar ya koro ta, cikin 'ba cin Rai ta kar'bi wayar, ta ciwa Zakiyyah mutunci ta inda ta ke shi ga batanan take futa ba, karshe tace " Zakiyyah abun da nake Gaya Miki kenan, kiyi han kali kar Zakiyyah mukhtar ya sa ke ki, to gashi an Fara daga korowa nan gaba sai dai saki, kekam wannan yarinya anyi marar hankali,ki je duniya ce ta ishi Baga ruwa iya Jima ! Duk wannan fad'a da Baaba taiwa Zakiyyah baisa ta sauko ba, Duk sa ta Fara d'iban gashin yun wa, Hidayah itama bataji dad'i ba, Amma Babu bakin magana saboda su biyu tai wa tatas itada Hadiyyah lokacin haihuwar ABIE akan su daina saka mata baki Akan harkar da ta sha feta,ita ba Sa'ar su bace, tagwaye masu Hali iri d'aya itama Hidayah batai Mata magana Akan fitowar ta daga gidan mijinta ba,sun zuba Mata ido duniya ce ta fi Baga ruwa iya Jima.......... ************** 'Bangaren Alhaji TALLAFY kuwa sun xauna sun tattauna, shida Mai d'akin sa,Hajiya Aisha Akan yadda zasu 'bullowa sha'anin wad'annan marayun Allah da suka shigo rayuwarsu, Ita Hajiya Aisha tana tausaya y'an biyu Hadiyyah da Hidayah dataji ta yadda suka rabu da juna ba Ason ransu ba, yanzu Kuma sunason karatu Amma saboda zalunci irin na kawunsu ya hanasu, Wanda in yanada I Mana ko ubansu bai bar musu kud'i da kadarori ba tun da Allah ya hore Masa shi ya tsaya musu, suyi karatun Amma ina sai wa daqa yake da dukiyarsu, Shi Kuma Alhaji TALLAFY Alhaji yake tausayawa ganin halin da ya shiga Duk a dalilin halin da y'an uwansa suke ciki, lallai Wannan yaro yana da halin kirki da arziqi.. Sun tattauna yadda zasu bullowa al amarin komai a sannu xai bar shi, bazai je yanzu sama taka wajen kawu isma'il da zancen dukiyar marayun da take hannun suba, su asuwa? Shine a hakku daya riqe musu dukiyar su, musamman da suke Duk mata ne, yawancin y'ay'an, shi kuma Alhaji in ma xa'a bashi dukiyarsu shida y'an uwansa duk sai sun mallaki hankalin kansu sannan zai dawo musu da dukiyarsu, Hajiya Aisha. Ta bawa Alhaji TALLAFY shawarar a samu guda daga cikin body guard d'in sa guda, Akan yajewa kawu isma'il da harkar kasuwanci, sai bayan ya shiga jikinsa yagama jin sirrinsa sannan idan ya saka dukiyarsa acikin kasuwancin sai gaba d'aya a yaudareshi kada torino marayu da kud'ad'en su da sannu zasu dawo hannun body guard d'in, in yaso daga Baya Alhaji TALLAFY zai bayyanarwa kawu isma'il Akan ina dukiyar marayun Allah take, ya fito musu da ita,idan aka zauna ya Gama fayyace Duk indai dukiyar marayun Allah take kawai sai ayi one zero anan dukiyarsu zata dawo hannun su, shi kuma yadawo babu wan babu qanin, Shiyasa Abu *AKEEL* nakewa Allah godiya da ya bani kai matsayin mijin aure,Duk yadda zaka tallafawa Al mura da dukiyarka da wayonka kasan takai, Oum *AQEEL* ai kema inawa Allah godiya dayasa Kika shigo rayuwata lokacin danake tunanin, ya rana basu da WANI sauran jin dad'in duniya, kadaina wannan zancen Abu *AKEEL* d'a na kowa ne muta nene Basu gane HAKAN ba.. Da dukiya da y'ay'a ba'a muguntarsu baa'san nai amfanar su ba,Amma nikam *AQEEL* da *AKEEL* da *AKEELA* kamar y'ay'ana suke bana ta'ba kawowa ba y'ay'ana bane.... ALLAH yai miki albarka matar kwarai, abunda Yar mahaifiyarsu kenan taqi ganewa ta dinga gana musu axaba Wanda Bada sani na ba Saida karshen abun yazo sannan nasani, nan suka qarasa tattaunawa tsakanin wad'annan mata da mijin masu nunawa junansu tsantsar kulawa........ Inada tarin tambayi Akan Wannan ahali na Alhaji TALLAFY kufa FANS? Muje zuwa next page domin muji ya rayuwarsu take a baya kafin sukai wannan matsayi ✍️ Oum ARQAM ce ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE TWENTY TWO 22* " Tun daga lokacin da Zakiyyah ta Ki ra kawu Isma'il tai Masa wannan Rashin kun yar Ba ta Kuma jin d'u riyar sa ba kamar an shu ka dusa. " Zaman ci kin gidan su kuwa sai a hankali zan ce do min abubuwan fa sai a slow motion. "Yau ma ba yan fitar zahra ta tafi school, Hadiyyah i tama ta tafi koyarwarta(... Da yake Mai islamiyyar da ta ke ko yarwa ya nada wata pravet school, yadda yaga Hadiyyah tana koyar da Yara, sannan dama a CIKIN gidansu yanzu haka ana Zuwa ta nawa Yara lesson Aikuwa shima yace yana so ta dinga Zuwa school d'in sa da safe ta na koyarwa, Hadiyyah akwai kwa kwalwa yadda yaga tana koyarwa kai ABUN ya bashi sha'awa da Dad'i do min Hadiyyah akwai son Yara ta iya bi da yaro ta ko yar dashi CIKIN sauqi, yanzu salary d'in ta ya dad'u duk tearm malam Umar xai dinga Bata 45k, Amma ta gaya Masa uzirin ta na cewa tana so duk wata ya din ga had'a maya da na islamiyya, bai ce A'a ba, saboda yasan Maraicin da su Hadiyyah suke ciki Amma baisan suna CIKIN matsala ba,Duk wata Hadiyyah tana da kud'i a kalla 25k, Ma sha ALLAH, sha'anin ubangiji kenan babu ta yadda ALLAH Baya bu d'awa ba wansa musamman ma maraya..) " Zakiyyah fito ki yi wad'annan wanke_wanken! Cewar sa'adatu tana fitowa daga d'akinta "Wane irin wanke_wanke Kuma Aunty?! Cewar Zakiyyah ta na Mai da kai kan fillo! "E wanke_wanke nace ki Yi in kin gama ma ga shara nan tana jiranki, domin amfa ninki a gidan kenan, bazai yiwu ki zauna kiyi Shirim da ke ba,babu cas babu as, tun da kin'ki zaman gidan mijinki! Cewar sa'adatu tana tafa hannayenta" " Ke Aunty ki ke ko wa? Ni fa Ba Zahra da Hadiyyah bace, baxa kiyimin abunda kike so ba ehe! Zakiyyah ke fad'a tana yun'kurawa daga kwan cen da ta ke "Farkon zuwa na gidan nan na Fara wanke_wanke da shara ne saboda, ra'ayin kaina yan zu Kuma ra'ayin ba bu shi daga yau na daina wanke_wanke da shara, idan za kiyi kiyi idan baza kiyi ba ki barshi, aikin banza aikin wofi! Cewar Zakiyyah bayan ta ja dogon tsaki! Fans ku ji abunda Zakiyyah ta gaya wa sa'adatu ALLAH sarki Zahra da Hadiyyah Basu ta'ba fad'a sun fad'a ba, ga Alha kinsu tun ba'a je ko ina ba. "CIKIN masifa sa'adatu tace" wallahi yarinya kinyi 'karya ki zau na mun CIKIN gida, kice ba bu abun da Zaki dingayi, na ci uwarki a Rashin kunya, abun da kikewa mijinki wallahi karya kiyi min anan, mukhtar ya 'kaleki kin yi abunda ki ke so, hakama kaakarki wacce ta 'bata ki, Amma Nikam kinci karya! Sa'adatu ta 'karasa zancen ta na duban Zakiyyah wacce tayi tsallen al bar ka ta fito daga d'akin su" "Hmm Zakiyyah tayi ajiyar zuciya sannan tace "shege ka fa sa ni da ke! Zamu ga Mai gaskia ni dake, tana maganar tana wani Harare _harare kamar zata da ki sa'adatu sannan ta ko ma CIKIN d'akinsu abun ta. "Lallai ma yarinya ni Zaki nunawa yatsa ko? Daga Yau kin daina cin abinci a gidan nan, domin kuwa ba Wanda kawun naku yake kawowa bane, abinci dai nice mai ba yarwa a siyo a dafa idan i na da kud'i, to wallahi tallahi kin bar cin sa, omon wanki da wanka kin dai na amfani da shi, zan ga qaryar Rashin kunyar ki! cewar sa'adatu tana Zama domin tayi wanke_wanken ganin 'kudaje Suna bin malallautar. "An ya kuwa FANS Zakiyyah zata iya zaman GIDAN kunji dai abun da sa'adatu tace, kunsan wani Abu ma a HAKAN fa Zakiyyah ta Fara gala baita da yunwa, idan an ci abincin safe ba lallai aci da rana ba, idan anci da rana ba lallai aci da dare ba, ga jikinta ya Fara d'ad'ewa saboda wanka da klin (... Idan baku manta ba Zakiyyah cikin gata take har a sannan, domin halin maraicin da y'an uwanta suke ciki banda ita, a lokacin da iyayenta suka rasu tana gidan mijinta, haka zalika ma gidan mijinta Babu abunda ta rasa, wanki Bata yi, wanke_wanke ma al majiri yake mata, Duk wani Abu na aikin gida in Banda girki shine kawai takeyi, domin mukhtar bayason abincin Y'ar Aiki, uwa uba ma a HAKAN ta koyi girki, zamanin y'an matan cinta hajiya Sakinah ta sangartata Bata iya girki ba da duk wani abunda mace zata Yi na cewa itama macece..) Lallai Zakiyyah kin d'ebo ruwan dafa kanki Sa'adatu kam ba kwanwar la sa ba ce.... ************** Kaduna state... "Hidayah da Hunaif Suna zamansu cikin aminci a hannun kaakarsu, "Hidayah tun tana saka rai taji Hadiyyah ta kirata Akan zancen karatunsu da kawu Isma'il yace zai yi, shiru kakeji, Kiran Hadiyyah a waya tayi, Inda ta shaida mata cewa ai kawu Isma'il har yanzu bai magana Akan ci gaban karatun ba, ta ha'kura ta fawwalawa ALLAH lamarinta, ta Y'ar uwarta tayi itama lesson d'in takewa Yara, Kuma alhmdllh tana jin dad'in HAKAN. Hadiyyah take gaya mata cewa"Zeenah fa tunda suka dawo gidan bata zuwa makaranta, kawu Isma'il ya'ki zuwa ya saurari Aunty Zakiyyah, shin mukhtar xai Kira Takoma gidan mijinta, ko kuwa Zeenah za'a saka a wata school d'in, gashi abinci ya daina ajiye musu kwata'kwata, Hydar yaita dukan Zeenah Aunty, tana kallo Bata magana, sai dai idan Zakiyyah tana wajen ne Tak Masa magana ko ta rama mata, tunda yaga haka Kuma yadaina dukanta a gaban Zakiyyah d'in sai yaga Bata wajen. Duk wannan zancen da Hadiyyah ta gayawa Hidayah, Baaba taji domin wayar ta bud'e sifika ne, ranta ya 'baci, karshe ta barwa ranta cewa in ALLAH yakaita kano 'kafarta 'kafar Zeenah nan zata dawo da ita, ita Kuma Zakiyyah tun da zaman gida ta za'bar wa kanta, gata gashinan, Amma wallahi bazata yiwa mukhtar magana Akan zamanta a gida ba, taita zama har mahadi ya bayyana idan tayi hankali zayi zancen gidan mijin.... Kwarai dagaske Baaba kinyi magana Mai kyau.... ************** "Kawu Isma'il fa duniya ta Zama sabuwa, sai fantamawa akeyi da dukiyar marayun Allah, yanzu haka so yake Yasa hannun jari a WANI kamfani Wanda suke shigo da kayan electronic daga china ta girgin ruwa, ya zuba ma'kudan kud'i, ALLAH yasu bai had'a da na marayun Allah ba, wannan kam yaga hanyar da kud'insa zasu tumbatsa. "Tsiran sati biyu da body guard d'in Alhaji yajewa kawu Isma'il da zancen yanada kamfanin da suke sarrafa fata a kudu wato lagos, to shine sukeson zuba sababbin ma'aikata, Kuma mutum zai bada kud'i Kimanin miliyan hamshin, idan aka Fara harka in Sha ALLAH mutum zai nin ka kud'in sa, sau d'aya ko fiye da hakan,(...fans kunsan dai kawu isma'il da kud'i, mutumin da yaci dukiyar marayun Allah ai son kud'in sa yakai limit...) Da kamar kawu isma'il bazai kar'bi tayin Alhaji Abbas ba(body guard d'in Alhaji TALLAFY) saboda a hannun sa yanzu babu wad'annan kud'in da yake bu'kata, Amma sai yayi tunanin ga kud'in marayu ya bayar mana Ayi wannan harkar fata dasu man, in an samu shikenan idan ba'a samu ba ma, bata shafeshi ba, sai yace kud'in sun lalace ne yanzu ba'a samun riba,lallai kam kawu isma'il, Ha'kon Alhaji TALLAFY ya cimma ruwa FANS Kunga dama kud'in marayu yakeson su dawo hannunsa gashi kuwa zasu dawo, Abbas body guard d'in Alhaji TALLAFY ya kware wajen law kamar lauya haka yake, Duk Saida ya Fara karantar Kawu isma'il ,domin ta email d'insa ya tura Masa da Duk WANI yadda tsarin kamfaninsa yake, da yadda yake samun ci gaba, Kuma yasamu kawu isma'il ina ya fito kud'i I zashi kud'i, babu WANI tunani ko jayayya ya amince da batun shi, akwai kwanfani a jafan tabbas na sarrafa fata, Kuma Alhaji Abbas shahararren Mai kud'i ne, shima Yana da muqami babba a kamfanin dake japan, Wanda shine ma ya bud'e karamin kamfanin a Lagos d'in, saboda Yana da kishin 'kasarsa, Kuma Ma sha ALLAH ana samun albarka sosai, kawu isma'il yanajin yadda kamfanin ake samun kud'i, dama yajima da burin kasancewa ya xama maaikaci a kamfanin sai gashi har gida yasamu gara 'basa, Kawu isma'il yayi zaton budy guard d'in Alhaji TALLAFY shine Alhaji Abbas d'in gaskia, shiyasa ya amince, Kuma ALLAH yayi a dai_dai lokacin da wancan Alhaji Abbas d'in yake bu'katar maaikata ne shiyasa wad'uwa tazo dai_dai da Zama......... Ya kuke gani FANS haqon Alhaji TALLAFY zai cimma ruwa kuwa? Ya batun kud'in kawu isma'il daya sa a hannun jari? Ya rayuwar Zakiyyah a gidan Sa'adatu shin zatayi hankali kuwa? Da dai sauransu kubiyo oum ARQAM domin jin amsoshin ki da wasu wad'anda naki sani ba 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE TWENTY THREE 23* "Na Aiko yaro ya d'auki zeenah yakaita makaranta, kince baza ta jeba,me kike nufi ne? Abunda Mukhtar ya rubutawa zakiyyah a sa'kon kenan" "Ko da zakiyyah taga abun da Mukhtar ya rubuta mata na sa'ko, bata bi ta kansa ba , har karta ta ci gaba dayi. "Zuciyar Mukhtar ta dugun zuma ainun, sake tu ra mata sa'kon yayi. "Zakiyyah wai ke me yasa baki da Hankali, da tuna ni ne? Wallahi ranki zai 'baci idan ALLAH yakaimu go be, zan Aiko a d'au zeeenah Zuwa makaranta, wawiya kawai wacce batasan me take ba" Zakiyyah tana Gama karanta sa'kon da batayi niyyar Masa replay ba, Amma zuciyarta ta dugun zuma Bata san lokacin da ta Fara masa replay ba " kaga mukhtar wai menene had'in ka da zeenah ne? Ca nake Y'ar uwata ce ko? To in dai kai d'an halak ne ka 'kale Zeenah ka fitar da ita daga cikin shafunka, ABIE daya ke d'an kane ai na bar maka shi, shin ni daya ke d'ana ma ban ta'ba maka magana akan sa ba, balle kai Zeenah babu abunda ya had'a ku nice na had'a yanzu Kuma na raba, kai harkar rayuwar ka muyi tamu, aikin banza ai kin wofi!" "Mukhtar ya na ga ma karantawa zuciyar sa, tayimai za fi, maganganun da zakiyyah ta gaya Masa, tasa ta kuma sare Masa, ba bu abun da yazo zuciyarsa sai ya rubuta mata sakinta ta sa'ko, ka fin ya aika mata da takaddar sakin. "Sai dai Abu guda d'aya da mukhtar yakeyi a rayuwarsa shine Baya Duk wani Abu na rayuwarsa sai ya nemi shawarar mahaifiyar sa" "Ko da mukhtar ya Kira hajiyar sa, yagaya mata Duk yadda sukayi da zakiyyah, Bata ba shi goyon bayan sakin zakiyyah ba, tace ya 'kaleta dai har yanzu da lokacin da zata horu, Amma saki ita kam Bata amince ya saki zakiyyah ba, sannan Kuma zancen Zeenah da yace zai kaita makaranta, m ya ajiyeta a gefe ya qaleta, ya zuba mata idanu, kawunsu isma'il ya kai Zeenah makarantar da sauran y'an uwanta suke Zuwa kawai,saki Amma bai taso ba a tsakaninsu ko dan darajar iyayenta, ta yadda suka nuna Masa 'kauna, Y'ar su Y'ar 'karama aka aura Masa ita, yanzu dan 'kasa ta rufe musu idanu zai ce zai saketa, halin zakiyyah ai tun farkon AUREN su take a haka, meyasa bai sake ta tun iyayenta suna raye da kaakarta miri'kiyarta ba? Sai yanzu hakan bazai faru ba(... ALLAH sarki hajiya Jamila ALLAH ka had'a mu da sirika irin wannan, ALLAH yasa kuma halinta ya d'ore a HAKAN, kar halin zakiyyah yasa ta canza halinta, domin zakiyyah halinta sai ita wallahi nima tafara bani haushi, ta Fara zancan halina ni ma nadaina sonta😡..) "Amma Kuma zakiyyah ta bawa Hajiya Jamila mamaki ba KA'DAN ba, irin Wannan tijara haka?, Dan sa'kon daya tura wa Zakiyyah da sa'kon da itama ta dawo masa dashi,Duk ya tura mata Kuma ta karanta, "Taiwa mukhtar d'in fad'a Akan karya Kuma gayawa Zakiyyah wata magana Mara dad'i, wawiya da ballagaza Duk su fita daga bakinsa, wannan ba zancen mijin arqizi ga matarsa ta sunnah bane, wannan sai masu xaman daduro, ko karuwai Mukhtar yaji abunda mahaifiyarsa ta fad'a Kuma yayi mata al'kawari in Sha ALLAH shi ko sa'kon ma baxai Kuma mata ba, ita dai Hajiya Jamila tace ban rabaka da matar kaba domin har yanzu tana qar'kashin inuwar Auren ka. "Mukhtar haka ya ha'kura da zancen sakin zakiyyah, Amma ya 'kudirce a ransa, shi kam kafin ya waiwaya ga zakiyyah gaskia za'a dad'e, sai tazo da kanta ta ba shi ha'kuri, ko da zai dawo da ita CIKIN gidan sa.(... Lallai mukhtar Anya zakiyyah zatayi hakan kuwa Mije dai Zuwa fans...) "Tunda Wannan maganar da Zakiyyah ta gayawa mukhtar, yadawo gida cikin damuwa, da bilkisu ta fahimci HAKAN, ai kuwa Duk wata hanya da tasan zata samarwa mijinta walwala ya manta da damuwarsa tayi Masa, Amma ko da wasa bata tambayeshi me yake faruwa dashi ba, domin tasan may be Akan Maman ABIE ne, wannan kam ba wurimun ta bane,(... Mata kudinga fita abunda bahu ruwanku, idan mijinki yana damuwa kiyi qoqarin fitar dashi ta kowacce hanya da farantawa, bincike ba naki bane, idan yazo miki da zancen kiji idan shawara ce ki bashi idan Kuma addua ce ki tayashi, amma binciken abunda Bai shareki ba babu ke aciki, musamman idan kikasan matsala ce tsakaninsa da abokiyar xaman ki wato kishiya, kowa tasa ta fishsheshi, kedan kawai ki kyautatawa mijinki... Wannan shawara ce) Tun daga sannan bilkisu ta zage damtse wajen kyautatawa mukhtar da faranta masa da Duk hanyoyin da tasan zata sashi farin ciki, ga ABIE a gefe shima sai kuyi zaton d'an cikin ta ne. "Zakiyyah tana tu rawa mukhtar wannan sa'kon ta kashe wayar ta gaba d'aya, tuna jinta zai dawo mata da reply ne, tasan maganar da ta gaya Masa kowanne irin Mai ha'kuri ne dole ya tanka, Tun daga sannan, ta shiga harkar gabanta a gidansu, Bata kula kowa sai y'an uwanta Hadiyyah da Zahra, suma ba wata Hira suke ba,domin haushin ta suke ji, ganin tayi wauta da hauka, kud'in da ta tawo dashi daga gida su take dafa abunda takeso taci, tayi walwalar ta, babu abunda ya dameta, ko ABIE bata tunawa dashi, bata tunanin ko zai nemeta? Kuka yakeyi na Rashin ta ko wane Hali yake? Shin bilkisu ma tagari ce zata kula da ABIE ta bashi kulawa ko akasin HAKAN?(.. wannan wace irin uwace..?) Nika nace FANS za ra bata barin dami ai, kud'in zasu 'kare zamuga da wane kud'in zatayi fantama, taci ta sha d'in (..banza shashasha ballagaza Nima na d'ana abunda mukhtar yake mata🤪 ko zata rama ne Nima? Seerat Zaki ramawa 'kawarki Zakiyyah ne? domin naga kun jone ke da ita, Duk da har yanzu kinqi gayawa qawar taki gaskiya😱 tasan cewa xatayi kuskure matuqar Hajiya Jamila takai bango, Dan itace take tan'kwara mukhtar akan ya saurara wa Zakiyyah d'in, shikam yajima dakaiwa bango..) ************** "Ma sha ALLAH jibo, Komai ya na tafia dai_dai, ai nasan ba ni da shakka a kanka, kana da basira Duk ta yadda zaka yiwa mutum shigo_shigo ba zurfi, ka iya, musamman ka sa mu shi isma'il D'IN irin masu son kud'in nan ne, nan dai Alhaji tallafy su ka gama magana da body guard D'IN sa jibo(.. Wanda yakoma Alhaji Abbas🤣..) sannan su kayi sallama tsaka ninsu, jibo yana girmama Alhaji tallafy D'IN. "Oum AKEEL Lallai ka ga abubuwa Suna tafiya dai_dai, yadda Muke tuna bin abun zaizo da d'an matsala gashi ta shin farko bamu Sami matsalar ba, Lallai isma'il ya cika marar I Mani, Amma mukam sai muce Alhamdulillahi! Alhaji tallafy ya 'ka rasa zancen yana kai du bansa ga Hajiya Aisha, " Kwarai dagaske Abu AQEEL ka ga yanzu sai hankalin ka ya kwanta, Komai yazo da sauki, nan dai suka ci gaba da tattaunawa. 'kafin da ga 'karshe Hajiya Aisha (mommah) ta sako zancen su AKEEL da AQEEL, in da suke zancen CIKIN wannan watan za suzo wutun 'karshen shekara, duk da AQEEL shikam yace, Baya son Zuwa Nigeria ne, hakan Ya na tu na Masa da abubuwa da yawa, ba wannan karon ba duk lokacin da hutu yazo sai Alhaji tallafy yayi da gaske AQEEL yake zu wa hutu gida, shima AKEEL hakan, bayason Zuwa d'in, sai dai shi akwai sauqin zuciya, wani abun ma shine yake tausar d'an uwan idan ya botsare, Amma ba KAMAR AQEEL ba, domin shi akwai xuciya da kafewa akan Abu guda d'aya.... "Alhaji tallafy sai shirye_shirye da murnar tarbar y'ay'ansa yake, Wanda zasu ta so daga *NEW DELHI* Zuwa Nigeria kasa ta mu ta ga do, ALLAH yai Mana maganin abunda yake damunta ya gyara mana shuwagabanninmu baki d'aya tun daga na qasa har Zuwa na sama🙏 "IDan kaga Hajiya Aisha murnar da take zai kayi zaton y'ay'an CIKIN tane, zasu dawo, gurinta, ta tasarma y'an Aiki akan a guarawa triplets (fans kuji fa 🤔) d'in ta shashensu, musamman 'bangaren AQEEL akwai son tsafta, Komai Akayi ba'a iyaba,sai yace ba'a Yi shara ba ko ba'ayi mopping ba, al halin Kuma anyi,(.. nikam fans inason jin labarin wadannan ahali na Alhaji tallafy kufa...?) ************** Kaduna state " Hidayah sunyi waya da Hidayah Inda take gaya mata cewa sun kusa Zuwa kano, CIKIN wannan satin zasu zo, "Hajiya Hadiyyah sai Murna ake twin's sis d'inta za tazo, an jima ba'a had'uba, nan dai sukaita hirar su ta y'an uwa, "Hadiyyah tacewa Hidayah " idan ku kazo, kun ga ma har Baaba da Hunaif sai Muje wa Alhaji Visiting, tunda ba ku ta'ba Zuwa ba, mukwa dama CIKIN satinnan Aunty tace zamu kai Masa ziyara, sai mu ji ra zuwanku sai Muje ga ba d'aya" "Lallai kin kawo shawara sis zuwanmu Ashe yanada amfani, ALLAH sarki Alhaji sis Yana bani tausayi, ALLAH yasa dai ya daina abunda yakeyi, Muje muganshi fes_fes cewar Hidayah tana tattausa murya ala mun tana tausayawa d'an uwanta. " Allahumma Ameen sister cewar Hadiyyah itama. "Sister Aunty zakiyyah ta koma gidan tzuwanmut Hidayah ta tambayi Hadiyyah" Kekam Hidayah baki da zuciya, kamata ya yi ki daina zancen wata aunty zakiyyah in mu na waya dake,idan ba haka ba kuma zamu dai na waya dake, cewar Hadiyyah tana Jan ajiyar xuciya! Kafin taci gaba da magana" nifa bana shiga shirgin zakiyyah, bana tausaya mata sis, har tafara ramewa saboda, Rashin cima Mai kyau , ba kullum muke samun abinci sau uku a ra na ba, Aunty tace ma adaina ba ta abinci, ALLAH ya taimaka mata ta tawo da wasu kud'in daga gidanta yanzu dai dasu take amfani, in sun qare Kum maga da abunda zataci da kanta. Ita dai Hidayah tayi zukud'in tana saurarar Y'ar uwarta, tana kuma tunanin halin Y'ar uwarta kuma yayarta, Wanda batada hankali ko KA'DAN, nan dai suka tattauna abunda yake damunsu, kafin siyi sallama, lallai je ALLAH sarki twin's mutuwa ta rabaku, ALLAH yasa ma akwai waya kuna tattauna matsalar ku tanan. "Duk abunda suka tattauna Baaba tanaji ta wayar, 'kwafa kawai takeyi, domin halin zakiyyah yakaita bango, ko tausaya mata Bata yi, Kuma matakin da sa'adatu ta d'auka akanta bai mata ciwo ba, HAKAN tai mata daidai, idan taji wahala Takoma gidan mijin ko ba dan ALLAH ba, ita yanzu Zeenah take tausayawa Amma ai takusa dawo da ita gareta ita kuma zakiyyah taje ta qari tsiyarta can, albasa batayi halin ruwa ba, Ummu Ruman babu ruwanta da duniya, hakama Alhaji Ammar bn Yassir shima haka, ko kaakarta miri'kiyarta Hajiya Sakinah Marigayiya Duk da halinta bata da irin halin zakiyyah....... To fans a ina zakiyyah ta Samu irin wannan halin haka....... Kubani Amsa Muje Zuwa fans yanzu aka fara wasan............ ✍️Oum ARQAM ce ontop 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE TWENTY FOUR 24* "Ma sha ALLAH su AQEEL da AKEEL sun sauka a 'kasar mu ta ga do tun iyaye da kakanni wato Nigeria (ALLAH ya gyara Mana ke😰🙏) wannan dawo wa ta musamman ce dan kuwa Airport d'in malam Aminu kano ya Sa mu mutane ba bu 'karya tabbas ma su hada_hada sun san cewa Duk yadda aka yi Mani Mai mulkin ne ko me sarauta ko wani d'an gatan ne aka zo tarbar sa, ai kuwa kam hakane d'in domin wad'annan tagwaye ne babu mulki ko sarauta sai dai tsa bar ga tan kawaii, Wanda a da can Baya su ka rasashi sai yanzu. "A cikin wad'anda suka zo tarbar su harda mahaifinsu da kuma mahaifiyarsu(Hajiya Aisha domin kam wannan matsayin suke ba ta) a gefe ga body guard d'in mahaifinsu wane su Ashirin, ga y'an uwa da abokan arzi'kin shi Alhaji tallafy d'in. "Ko da suka fito daga cikin jirgin bayan yayi landing, fuskar mahaifin su Alhaji tallafy sai wani annurin murmushi ne yake fita, musamman lokacin da idanu wansa suka yi Masa tozali da sanyin idaniyar sa wato tagwayensa,shima AKEEL HAKAN take a fuskar sa, sa'banin d'an uwansa AQEEL wanda fuskar nan take kamar bai ta'ba dariya ba, ko Kuma bai san wad'anda suke a jere sun aika musu da murmushi na Jin dad'in dawowar su izuwa gare su ba, AKEEL ne a ga ba Wanda ya nufo gurin iyayen Basu Yana Mai murmushi da dariyar murna, AQEEL yana bayansa shima Wanda ya taho fuskar nan kam sai nace🤭 koda yake bari nayi shiru. " Da suka 'karaso gaba d'aya Alhaji tallafy ya rungume su Yana Mai farin ciki da murna, da fa kafad'ar AKEEL Alhaji tallafy yayi sannan yace "Keel naga kun sake girma kai da d'an uwanka, lallai ne Anya kuna karatun kuwa? Ni dai nasan karatu yanasa mutum ya rame Amma ku kam ma sha ALLAH! Ya 'karasa maganar yana shafa kan AKEEL d'in. Sai sannan Hajiya Aisha tayi magana cikin dariya " Abu AQEEL banda abun ka yaran naka ai girma zasu 'kara Duk da karatu suke acan wata uwa duniya, karka manta basu gama girma ba yaran naka har yanzu just 25years fa, ta qarasa itama tana shafa kan AQEEL, Wanda yake kamar gunki a tsaye, sa'banin d'an uwansa. Duk wannan Abun da yake faruwa FANS ban kai ido na ga fuskar y'ay'an Alhaji tallafy,nidai kawai ina d'auko muku rahoto ne,🤣, daka na dubi Alhaji tallafy saina dubi Hajiya Aisha sai kuma karewa airport d'in kallo da nake, kunsan abunda da Ba'a saba zuwa ba🤣, saboda kallo har Biro da littafina sun kusa fad'uwa 'kasa, sai sannan n dawo hayyacina, na tuna ban zayyano muku wad'annan y'ay'an masu abun mamaki ba🤣 kuyi min afwa RASHIN sabo ne😂 "Sai da Biro na ya kuma fad'uwa 'kasa, da'kar na lalu boshi, da na kai idona ga wad'annan y'ay'a. "Tsarki ya tabbata ga ALLAH kawaii na fad'a a saman la'b'bana, wasu halitta nagani kusa da Alhaji tallafy masu tsananin kama da juna, Wanda badon Suna tare ba sai nace ai Duk Abu d'ayane, sai Kum banbancin fuska da suka Sa mu, wannan yana murmushi, wannan kuma fuskar sa a had'e take sannan Kum akwai glass a fuskar Wanda ba na yaba d'ayan biyu medical glass ne( zan iya ganeshi FANS saboda Nima ina ta'ammali dashi😇) "Fuskarsu ma'abociyar saje da 'kasumba wacce ta 'kawata fuskar, sai 'kyalli take alamu sun nuna Suna shan gyara kenan 'kasumba da gemun,ido ne dara_dara ma sha ALLAH kamar Madara ma'abocin gashin ido gazar_gazar, haka ma gashin girarsu, sun had'e da juna saboda yawa, hanci ne siriri kamar boron da yake hannu na ko yafi shi tsayi ma,bana shakka Suna fito da harshen su zai iya ta'ba hancin saboda tsinin sa,bakin su dai_dai misali ne,gashi jajir dasu dai_dai hasken fatar fuskar,domin kuwa har WANI d'aukar ido fuskar take saboda HASKE, Yanayin tsarin jikinsu kuwa, irin giant d'in nanne, akwai tsayi daidai misali ga d'an jiki, Duk Wanda yaga wad'annan y'ay'a yasan akwai lafiyar jiki,domin akwai cikar mazantaka tare dasu, Hali da sauran mu'amala ku, haka suka d'un Guma zuwa gida, Ana ciki da farin ciki da murna, sa'banin mutumin ki AQEEL da fuskar nan kamar kududdufi🤣 biyo Oum Arqam domin jin su nan gaba kad'an, Amma y'ay'an Alhaji tallafy sun cika 10% fa, saidai bamusan a ina zasu tawaya ba domin ance d'an adam Tara yake bai cika goma ba.......... ************** "Kamar yadda Hidayah tacewa Hadiyyah wannan satin Suna hanya, aikuwa sun cika al 'kawari, sai ga mutanen Kaduna sun hallara a Kano, fad'ar irin murnar da wad'annan tagwaye Hadiyyah da Hidayah sukayi 'bata baki ne, kuyi hasashe, hakama sauran y'an uwa Zahra da khadija da kuma Zeenah anjima Ba'a had'uba, "Hunaif Zeenah ta so d'auka, saidai Kuma ta kasa, yaron akwai saurin girma ma sha ALLAH, saura kad'an ya kamo mata a tsayi, an samu d'an uwa fa sai Murna takeyi, tana kewar ABIE, ALLAH yaso ta samu yarinya Hafsat (Y'ar wajen Sa'adatu in baku manta ba wacce Alhaji Ammar ya mutu ya barta da cikinta, shi kuma Hunaif yana d'an wata goma) Haka dai wannan ahali suka kasance cikin farin ciki, ALLAH sarki rayuwa in Banda mutuwa Mai yanke buri Mai zai sa y'ay'an Alhaji Ammar bn Yassir, su watse haka, shi ko yaye irin Wanda ake kai Yara Baya barin akai masa y'ay'a, kullum Suna tare dashi,Amma yanzu gashi Hidayah da Hunaif ma basa kano gaba d'aya, itama Zeenah tana wajen Zakiyyah, ALLAH sarki rayuwa, uwa uba Kuma ga Alhaji ma yana can wata cibiya ta horar da Yara da ba su tarbiyyah, Wanda Alhaji ya lalace yana shaye_shaye ne rayuwa kenan ALLAH ya tallafo wad'annan yaran ya duba bayan su. "Bayan Duk gama Wannan murnar, ne akayi gaishe_gaishe tsakanin Sa'adatu da Baaba, da godiya wajen kula da tarbiyyar jikokinta da takeyi,(lallai FANS har WANI Kula dasu Zahra Sa'adatu takeyi?koda take ai tayi ko😂) 'Hajiya Baaba ko takan Zakiyyah Bata biba wacce take gaishe da ita,(da yake Suna y'ar wasa da Baaba na jika da kaka) "Tsowuwa kina ji ina magana kin min shiru, ko kishin ne Yasa haka? To ki kwantar da hankalin ki miji ne dai na bar miki kishi ya 'kare! Cewar Zakiyyah tana da fa kafad'ar Baaba Zakiyyah ta ta'bowa in da yake wa Baaba 'kaikayi, nan ta zage tana ci mata mutunci Akan baro gidan mijin ta da tayi, tazo ta na zaman kare a karofi babu rini babu ma tsa ita ba bazawara ba ita bame Aure ba, "Mene nawa aciki Zakiyyah? Zaman gida Kika za'ba gaki ga shinan babu Mai kuma miki magan,tunda baki da Hankali ko rashin zuwan 'kanin mahaifinki ya isheki ishara, yanzu in da Alhaji (mahaifinsu) Yana raye ai wannan abun bazai faru ba, isma'il yaci amanar zumunci, yashe rabon da ya nemi su Hidayah da Hunaif? Ko aiken da yake musu Duk wata yadaina, kuma nan Hadiyyah take cewa yadaina zuwa gidannan, Kuma yadaina baku kud'in cefane, da sabulun wanka Dana wanki,shinkafa ce sai yqga damar ajiye musu, shine dayake baki da Hankali Kikayo 'kundun bala Kika dawo cikin gidan, ai gaki ga shinan cewar Baaba tana ingije hannun Zakiyyah daga kafad'ar ta. "Duk maganar da ake Sa'adatu bata Sanya musu baki ba, tana cikin flourn tazo yiwa Baaba sannu da zuwa, Baaba yace "Sa'adatu kinaji inaiwa Y'ar ki fad'a Amma kinyi shiru? Kinason zaman nata tare dake. Kenan? "To Baaba mezance? Nan ta kwashe irin fad'an da sukayi ita da zakiyyah, yanzu haka ma bata Mara magana, Baaba ri'ke baki tayi sannan tace "lallai ne Zakiyyah abun naki azimun ne gaki ga duniyar ga zaman gidannan saboda gidan ubankine babu Mai hana ki, rayuwa ce ta isheki ishara, rasuwar mahaifanki data kaakarki mari'kiyarki bai zamar miki ishara ba, naga abunda zai zamar miki ishara shashashar banza Mara tunanin da lissafi, Ranar Baaba tai mata tatas babu 'karya, nayi tunanin ai zakiyyah ai zata ra ma, sai naga tayi shiru tana muzurai tana mammotsa baki, Mara kunyar banza😡 haka tun zuwan Baaba zakiyyah tazama sukuku, batada power ko kad'an sai zaman d'aki, babu Mai kulata ko d'aya, sai Y'ar rainon ta Zeenah 😂 Kwanan su 'Daya da zuwa, Hunaif ya damu sai an kaishi GIDAN miemie(Indo uwar goyonsa idan baku manta ba) yaro kam yari'ke al 'kawari har yau bai manta da ita ba, Indo tayi murna ita da mijinta da zuwan Hunaif, abokin shayarwarsa Abul_khair si murna yake, yaga Hunaif d'an uwansa, Duk da sa'i da lokaci Indo tana Kiran Baaba can kaduna state su gaisa ta had'a Hunaif da Abul_khair aita shirme. " Saida sukayi kwana uku da zuwa sannan, aka Fara shirye_shiryen zuwa visiting d'in Alhaji, Baaba ta tawo Masa da d'an kayan ma'kulashe ga abunda sa'adatu ta tana dar Masa itama gone in ALLA Yasa muna raye suke Shirin zuwa wajens, Tun kafin zuwansu dama Saida aka Kira Wanda yake kula da Alhaji yagaya Masa cewa' za'azo visiting d'in sa, haka tsarin tallafy foundation take idan zakazo wa d'an ka visiting saika sanar ta waya, Aikuwa Alhaji sai murna yakeyi da wannan ziyara, musamman dayaji ance su Hidayah sunzo rasu za'azo, saboda tun suna Yara tasu tafi zuwa d'aya da Hidayah, saboda ita shiru_shiru ce batada hayaniya, itakam Hadiyyah abokiyar fad'an sa ce, batada barin Takwana Akayi maya saita rama, yaji wannan labarin a bakin Hadiyyah,dan da aka Kira Mai jiran su Alhaji d'in Saida Hadiyyah tace abawa Alhaji zasuyi magana. Tun sannan Alhaji yake lissafin Ranar zuwansu gashi lissafinsa yabashi gobe ne zuwan y'an uwana a karo na farko yi Masa ziyara........... muje next page domin muji abunda zai faru a ziyarar da iyalan Alhaji Ammar bn yassir zasu kaiwa d'an uwansu a *TALLAFY CHARITY FOUNDATION* ✍️ Oum ARQAM ce ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE TWENTY FIVE 25* Seerat zakiyyah qawarki tana miqo gaisuwa tace kece kike qaunarta duk cikin Rashin iyaye fans group🤔😂 ". Nikam kwana biyu me gida naga sai sagada_sagada kakeyi, baka dawowa gida da huri, ince ko lafiya!? Cewar Hauwa matar kawu isma'il "Hauwa kulu kenan,wani bud'i ne yake daf da shigowa cikin rayuwar mu gaba d'aya" Inji kawu isma'il Wanda yake 'ko'karin cire hularsa yana kishingid'a" "Ban gane abunda kake fad'a ba me gida? Wane bud'i kuma gayan Wanda muke ciki? Hauwa ta 'karasa tana Mai ri'ke baki cikin jimami! Kafin taci gaba da magana" kayi min 'karin haske Mana me gida! Kabarni cikin duhu " Sannu uwa ta sannu ubana, idan ban miki bayani ba du kana Zaki yi? Cewar kawu isma'il cikin d'aga murya " Ha haka bane Mai gida!naga yanxu manya da ya ra, harkar Yahoo suke shiga, nan Danan sai kaga mutum yana da rufin asirinsa Amma saiya jefe kansa a wannan hanyar, kuma abokai ne masu yin shigo_shigo ba zurfi, sai sukai mutum su baroshi! "Hauwa ta 'karasa zancen tana duban fuskar mijinta, ko zata hango gaskia Akan maganar da ta fad'a, domin ta na da tabbacin zai aikata HAKAN, tunda shi dai kud'i komai nasa kud'i, in dai da kud'i babu magana. " Kawu isma'il katse mata tunaninta yayi da cewa' "Kwantar da hankalin ki Hauwa kulu, ba abunda kike tunani bane, kamfanin da yake sarrafa fata na lagos... Nan ya Bata Duk labarin yadda sukayi da Alhaji Abbas, karshe yace miliyan goma ale bu'kata ga Duk wani sabon ma'aikaci yabayar, in Sha ALLAH kafin shekara zai Sa mu riba Mai tarin yawa, ko kuma ya ninka kud'in sa fiye da hakama kawu isma'il ya 'karasa zancen yana Mai sakarwa Matarsa Hauwa murmushi. "Mai gida tabbas nasan da wannan kamfanin na sarrafa fa ta a Lagos, Kuma Ana samun alkhair, dan ina jin labarin sosai a gari, ko a social media ana xancen! Sai dai wani han zari ba gudu ba,aina Mai gida zaka samu wad'annan kud'in? Kai da kace ba ka da kud'i! Hauwa ta'karasa zancen CIKIN kallon tuhuma ga mijinta isma'il Yassir " Duk naji tamba yoyinki kuma sai wacce naga damar amsawa, zancen inada kud'i ko bani dashi Bai ta soba, kuma idan ina da kud'i saina Gaya Miki ko? To Babu ruwanki cikin hurimina idan baza ki min adduar alkhair ba ki saurara min kar raina ya 'baci! cewar kawu isma'il cikin 'karaji! Kafin ya d'ora zancen da uwata ba ma iya kamfanin sarrafa fata kud'ina ya tsaya ba bari jiki! " nasa hannun jari ma, a WANI kamfani da yake china, shi kuma cibiyarsa tana ogun state(abaekuta) Suna shigo da kayan electronic ta jirgin ruwa, to in Sha ALLAH komai yakusa tabbata, na tura kud'in nawa sai Shirin Ranar order kawai nakeyi, Kuma shima Ana samun alkhair fiye da wannan na fatar(kuji son Kai fans wai Wannan yafi Alkhair fiye da wancan da yabayar da kud'in marayun ALLAH🤔) "Hauwa dai sandarewa tayi daga zaune, jin ma'kudan kud'in da mijinta yace ya sanya su a harkar sana'o I har Kashi biyu! " Bazakiyi magana bane? Na ga kin kafe ni da idanu ne? "Mai gida kenan, ALLAH yakyauta zance, Amma nasan bakada wad'annan kud'in, daga lissafo, kaji tsoron ALLAH dai da kud'in marayu a hannun ka, kuma su ba'a Cinsu a zauna lafiya, nan dai Hauwa tafara wa Kawu isma'il wa 'azi Wanda abanza takeyi domin kuwa Wanda yayi miss ba yajin Kira! Karshe tace Amma kwanakin Baya can Hadiyyah ta zo maka da zancen ci gaban karatunsu kace baka da kud'i, yau Kimanin wata biyu kenan, da fitowar Zakiyyah daga gidan mijinta Amma baka nemeshi kaji meyake faruwa ba, bana jin GIDAN ma kana zuwa, kana du ba y'ay'an D'an uwanka Wanda aka ba ka amanar su! Kadai ji tsoron ALLAH Mai gida akwai Ranar 'kin dillanci! Na tabbata in da Kaine ka rasu Alhaji(Ammar) bazai wa y'ay'anka haka ba, ko baka bar komai ba shi Mai tsaya musu ne, balle ka bari, bana tantama kud'in ga don su biyar ba ta'ba musu zai ba a aljihun sa zai wayalta musu! Inji Hauwa kulu tana 'karasa zancen da jima'in rashin Alhaji Ammar bn Yassir " Gaskiya ne malama kin iya wa'azantar wa, Amma ki sani Duk abunda Zaki fad'a na fiki sani, wai ma ina ruwan ki da harkar y'ay'an Wana? Kin san dai bazan cuce su ba ko? Ko ki sarara min, Duk abunda ya dace zanyi musu zancen Zakiyyah banson ci gaban karatunsu ne shiyasa nace bani da kud'i, ita Kuma Zakiyyah Wannan shegiyar yarinya ce(kina ina seerat kinji abunda kawu isma'il yake cewa' kawarki😂) zaman gida takeso, gata ga shinan, shiyasa na daina kai musu kud'in ce fane, da sabulun wanka Dana wanki, nasan ai baza su rasa ba, dai kuma Zeenah inason Sanya ta a makaranta tun daa yanzu bata zuwa! Nan dai kawu isma'il ya zayyanawa Hauwa Duk WANI kud'irin da yake ransa . WANI tayi mamaki WANI kuma, tana addua ALLAH ya ganar sa mijinta Akan marayu domin kuwa sha'anin su akwai wahala, zata ci gaba da yi Masa wa'azi ko ALLAH zai dawo dashi hanya madaidaiciya domin ta ga yayi nisa kuma yanzu bazai ji kiraba Daga 'karshe yake ce mata su Hadiyyah zasuje visiting d'in Alhaji yana so itama su had'u suje, gaba d'aya har yaran, lallai ne Alhaji fa yayi goshi, ALLAH ya shirya kawu isma'il......... ************** "Bro ka'ki sakar jikinka, tun da mukazo nigeria, me yake damun kane? Nace ka cire Wannan abunda ya faru daga cikin zuciyar ka, ji nake mu uku harda AKEELA abun ya faru, ita ma ta saki ranta, Amma kai kullum jiya iyau, ko a NEW DELHI a haka muke dakai, Amma ja yanzu abun yafi 'kasanta! AKEEL naga ya dafa kafad'un d'an uwansa AQEEL Yana maganar! Amma ko gezau Banga yayi ba, sai ma sa'bule hannun d'an uwan da yayi daga jikin sa yana kwanciya Akan bed d'in da suke zaune a gefensa! "Nasan baza kayi magana ba Amma kana jina, sarai yakamata ko dan Abbu ka saurarawa kan ka hakan, muddin yana ganinka a wannan yanayin kana kallo damuwa yake shiga,kuma kana yana da matsala sosai Akan damuwa ko? Sai yaga kamar har yanzu akwai wata matsala tare dakai,(wacce iri FANS kodai bashi da Hankali ne Can baya?🤔) AQEEL dai Duk wannan zantukan da AKEEL yake masa baice 'kala ba, sai lumshe ido da yayi kamar Mai bacci ma, shi ma d'an uwan bathroom naga ya nufa, babu alamun yaji haushi ta yadda d'an uwansa bai nuna yaji abunda yake fad'a bama, sai ma murmushi da naga ni akan fuskar tasa shi AKEEL, yayin shigarsa bathroom d'in yana waiwayen d'an uwansa AQEEL. Haka y'an biyun Alhaji tallafy suka kasance tun dawowar su gida, AKEEL yana ta harkar gabansa dai'dai gwargwado, sa'banin d'an uwansa AQEEL da sai a hankali halinsa, y'an uwa da abokan arzi'ki sai zuwa sannu da zuwa ake musu(lallai FANS idan da kud'i babu abunda baza'a yi ba) ana ta tambayar AQEEL sai ace yana garden, ko study room ko Yana cikin d'akinsa,domin sune guraren zamansa, "Yau ma Alhaji tallafy Suna zaune a babban falon gidan gaba d'aya, AKEEL Hajiya Aisha, da kuma AKEELA, Amma babu ko 'kurar AQEEL, Alhaji tallafy yace "KEEL" ina d'an uwanka ne? Je room d'in sa ka Kira munshi, "To Abbu ALLAH yasa ya fito fa Dan, naga brother tun da muka dawo 9ja sai a hankali fa, kuma Abbu har acan ma haka yakeyi, na rasa sai yaushe brother zai koma mutum kamar kowa, ya dinga walwala,abun da ya faru da can ya faru, Amma ya'ki dai nawa, "ALLAH sarki d'an uwa Rabin jiki, AKEEL ai haka manta d'an uwanka ba tun asalinsa dama bayason hayaniya, haka ma magana Amma naga kai dashi kuna Hira "KEEL" cewar Alhaji tallafy yana shafa kan d'ansa AKEEL . Je ka kirawo mun shi kaji maza_maza Tashi yayi ya nifi room d'in twin's brother d'in sa. "Acan falon kuwa duba Alhaji tallafy yakai kan AKEELA wacce ita ma,tana zaune tayi shiru, babu um bare um_um kallon tv takeyi, Wanda zai kayi duban tsanaki zaka gane ba tvn take kallo ba WANI tunanin can daban takeyi. Nima duba nakai gareta, Lallai FANS badon AKEEL da AQEEL maza bane, da kuma cewa su sun fita girma, ita Kuma mace ce babu abunda bazai sa in ce su bane, kamar ta 'baci tsakaninsu, ko ince ma tafisu kyau, saboda ita mace ce su Kuma maza🤔 " Me ke faruwa AKEELA? Kema kin yi shiru ko? Wai yakukeso nayi. Da rayuwata? In kinzo gidan nan kiyi shiru, y'an uwanki suma suyi shiru, Amma gwanda AKEEL shi, "Babu Komai Abbu kawai dai karatu yayi nisa ne kasani ai, ai shikenan AKEELA In ji Alhaji tallafy yana Kai duba ga y'an tagwayen sa AKEEL da AQEEL Wanda yanzu suka 'karaso wajen, da 'kar AKEEL ya tattago AQEEL har yazo ya amsa Kiran mahaifinsu Ita kam Hajiya Aisha sai kallon mijinta da y'ay'ansu take, Wanda abun sha'awa ne, y'an uku rigis maza biyu mace guda d'aya Cikin ginshira AQEEL yace "Abbu barda da dare, Ummu barka da dare" (Inji AQEEL fa FANS) kinji muryar sa kuwa 🤔 Tare iyayen suka amsa Masa, kafin Ummu tace" ko kaifa yarona, Amma da kaje cikin 'kuryar d'aki kayi shiru, ka dinga sakin ranka kana walwala kaji d'an albarka! "In Sha ALLAH Ummu" Abun da AQEEL yace kenan, sai kuma yayi shiru. Haka dai iyayen nasu suka dinga jansu da Hira, cikin y'ay'an uku AKEEL ne kawaii yake d'an tankawa, Amma AQEEL da AKEELA babu umm bare um_um, Duk da sannan fuskokin nasu ba KAMAR d'azu ba ta d'an saki. Anan Alhaji tallafy yake cewa y'ay'an nasa in Sha ALLAH jibi, zamuje daku gaba d'aya cibiyata, kukai mata ziyara, KAMAR yadda Duk wutu kuke zuwa " ALLAH yakaimu Abbu da rai da lafiya" Cewar AKEEL" AKEELA da AQEEL kam jinjina kai sukayi, "Abbu yace banji kunyi magana ba, masu Hali d'aya? Ya 'karasa maganar da murmushi yana kai duba ga y'ay'an nasa AKEELA da AQEEL Duk da yasan ba maganar zasuyi ba.. Nan dai suka cigaba da tattaunawa tsakanin wannan iyalai me magana nayi masu jinjina kai nayi................. Kiyi Haquri da wannan FANS ✍️Oum Arqam ce ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE TWENTY SIX 26* tun da nafara book d'in nan banyi kyautar ko page guda ba🤣🤔 Anya Kuwa babu rowa a wannan tafiyar🤭😂 "Yau take kamar sallah a gurin su HADIYYAH, hakama ga Alhaji Wanda za'a jewa visiting d'in, murna suke sosai, kana kallonsu zakasan akwai magana. Hidayah ta 'kwallawa Zeenah Kira! Baza kizo ki saka kayan ki bane Zeenah? Kina kallon kowa Yana shiri, Su Hunaif, Hafsa, dasu Farouk da haydar Duk sun kammala shiri Amma banda ke! Hidayah ta 'karasa maganar tana le'ko kanta daga gefen labule, domin ta ga me Zeenah takeyi a tsakar gidan nasu da takejin surutun ta Arba tayi da Zeenah a zaune ita da Hunaif da Hafsa su da kayansu masu kyau a shirye tsaf, sa'banin ita Zeenah Suna ta qasa "Ta so Zeenah in sa miki kayan Mana Duk mun shirya fa, Yaya Hidayatullah(haka suke kiranta y'an gidansu, Amma mutane Suna ta'kaitawa ne da Hidayah ) mammah(Zakiyyah) ce ta shiga wanka, bata d'auko min ka yana ba, tace in bari ta fito ta d'auko min ni da ita iri d'aya zamuyi(Zeenah sarkin surutu fad'i ba a tambayeki ba🤣) "Tayi maganar dai_dai da fitowar Baaba daga d'aki a shirye tsaf, "Wa cece d'in zakuyi anko? Mamma take ko momo(lallai seerat Baaba fa ta takurawa qawarki yasin) babu Inda zata bimu da izinin wa? In ba ta da Hankali to mu muna dashi, sai ta Kira mijinta ta tambaye shi tukun" Ta 'karasa maganar da fincikar hannun Zeenah ta mi'kawa Hidayah ita" " Ri'ke hannunta kije ki Samar mata,kayan sawa ki bata ta saka, ki hanzarta, rana ta farayi" "Yadda Baaba ta gayawa Hidayah haka ta aikata. "Lokacin ita Kuma Hadiyyah tana 'karasa d'aurin d'an kwalin ta, "Jeki Wajen sis, ta zuge miki zip, ta d'aura miki d'an kwali na 'karasa zuba kayan can, "To yaya cewar Zeenah" "Yaya Hadiyyatur_rahman(lallai yau Zeenah fi'ili takeji dashi kowacce saita kirata da cikakken sunan ta, babu ragi, ai da sai ta hada da Hassana da Hussainar kawai 🤣) zugen zip ki d'auran d'an kwali... Haka dai Duk suka gama shirin su ma sha ALLAH sai ma kaga y'an biyu Hadiyyah da Hidayah abun Ba'a magana kamar ka sace su ka gudu(twin's malam ai duniya ne, musamman iri d'aya idan mata mataa, ko maza duka) "Duk maganar da Baaba ta fad'a wa Zeenah, Zakiyyah tana jin su. 'ko data fito daga wanka, fuskar ta a d'aure batayi magana ba, kaya ta d'auko zata saka, "baaba tace fatan kin Kira mijinki kafin kisa 'kafa ki fita ko? " Ni ban Kira shi ba,Akan me zan kirashi? Ya san da ni ne? " Ai ke dama baki da Hankali, to mu muna dashi Kuma babu Inda Zaki, matu'kar baki d'auki waya kin Kira mukhtar a gaba na kin tambayeshi, ba babu in da zamu dake, sai dai ki sha Zama a gida, sha_sha_sha! kawai wacce batasan me yake mata ciwo ba! " Baaba ta 'karasa maganar CIKIN 'karaji(kai Baaba ita ma masifaffiya ce dama, ko halin zakiyyah ya mayar ta HAKAN?🤔 Amma da babu ruwanta fa) "Ita dai Zakiyyah batayi magana ba,HAKAN ya nuna kenan bazata visiting d'in ba. " Baaba kenan kina tunanin ni zan Kira mukhtar a waya? Lallai ne kenan bani da Hankali kome? Shi Bai kirani ba saini ce zan kirashi ai ba ubana bane ALLAH ya raka Taki gona, sai kun dawo, Amma Kuma idan nayi niyyar zuwa WANI wajen wallahi bazan tambayeshi ba, " Maganganun da zakiyyah takeyi kenan. Ita dai Baaba bata kula taba, saboda taga,abun Zakiyyah sai an nata uziri, " A haka sukai wucewarsu, suka bar Zakiyyah a gidan zuwa *tallafy charity foundation* harda Sa'adatu za'aje 'A zuciyar Zakiyyah abun da take ayyanawa". Kai ni nayi Masa text a waya ma ina jiran takarda ta da, saboda bazai mayarni Y'ar iska ba, ni ba sakakkiya ba ni ba Mai aure ba, fita ma Ace babu gurin zuwa, idan babu Auren sa kuwa fa sai in fita in da naga dama!........ lallai FANS 'kawar seerat zakiyyah fa tafara kaini bango yasin😡kufa.......? ************** "Iya lan gidan Alhaji tallafy Suna dining area Suna breakfast ba kajin, 'karar komai sai na cokula, kowa sai bawa cikinsa yake bawa ha'k'kinsa, Alhaji tallafy, Hajiya Aisha, AKEEL, AKEELA, da kuma oga AQEEL. "Bayan sun kammala kowanne ya tashi ya goge bakin sa da tissue, " Yawwa y'an albarka kar lokaci ya 'kure Mana AKEEL da AQEEL kuje part d'in ku, ku shirya da wuri, ita ma AKEELA ta haura upstairs d'akin ta ta shirya,saboda ina da abunda zanyi acan foundation iDan mukaje" Cewar Alhaji tallafy yana duban y'an ukunsa cikin fuska d'auke da Annushuwa. "To Abbun mu, in Sha Allah ba bu matsala, yanzu kuwa zamuyi ready " cewar AKEEL, Sauran kuwa girgiza Kai sukayi, hannun AQEEL ya ri'ke suka fice zuwa shashen su, ita Kuma AKEELA tana haurawa sama. "Oum AKEEL bakya ganin zuwan mu da su, tallafy foundation bazai 'karasa cirewa AKEELA da AQEEL damuwar da tayi saura acikin rayuwar su ba, sabo da idan muka je, za'a duba file d'in Yara a za 'kulo ja wad'anda suka sha wahala a rayuwa fiye da wacce su kasha a baya, kin ga kamar yaron nan maraya Yassir(Alhaji) shikam zanso a koma bada tarihin rayuwarsu tun tasowar sa da sababbin shigar shi tallafy foundation d'in! " Nasan za suji tausayin rayuwar yaran gaba d'aya,duk da acikin su dasu AKEEL bansan labarin wane yafi muni ba, Amma suma kam labarin su akwai ta'ba zuciya! Alhaji tallafy ya kai aya a zancen sa a dai_dai lokacin da suke haurawa sama dakinsa, domin shi ma ya shirya d'in! "Hajiya Aisha yace. "ma sha Allah Abu AQEEL akwai ka da hangen nesa sosai gaskia, Wannan ma ai kaga WANI dabara ce, ta yadda zamu kawo 'karshen damuwar y'ay'an mu cikin sau'ki! " ALLAH ya tabbatar Mana da alkhair Abu AKEEL" "Allahumma ameen Oum AQEEL" ya qarasa maganar da dosar bathroom,itama Hajiya Aisha nata d'akin ta huce domin shiryarwa, bayan ta taimakawa mijinta da Abubuwan da zai bu'kata idan yafito daga wanka. Can bangaren su AKEEL ma sun shirya d'in, har ogan naku,(tun Ranar da Alhaji tallafy yai Masa magana ya d'an saki ransa KA'DAN🤣 a HAKAN FANS🤔) Masha ALLAH tagwayen Alhaji tallafy *iri d'aya sak!* suit Mai Arnan kyau tsa daddiya suka saka ba'ka, ku hangon farin mutum cikin ba'kin shiga! Takalmi white , kansu ba hula, shumar nan sai she'ki take alamun tana shan gyara Babu banbanci sai na Glass da AQEEL yake sanye dashi, da kuma sakakkiyar fuska wacce AKEEL shima yake d'auke da ita shine banbancin, sai 'kwamshin turare sukeyi() Itama AKEELA ma sha ALLAH tayi kyau abunta kamanninta da y'an uwanta ta fito sak! Tayi shirinta Tana fitowa iyayenta Suna fitowa harabar gidan suka fito gaba d'aya, a dai_dai lokacin suka su AKEEL suka fito" "Ma Sha ALLAH" Hajiya Aisha tace ganin yadda y'ay'anta sukayi kyau sosai, kamar ka sace ka gudu, Shi kam Alhaji tallafy sai murmushi yakeyi ganin y'ay'an sa. Body guard guda biyu ne suka taso daga wajen da aka tanadar musu, daya daka ciki ya bud'ewa Alhaji tallafy mota shi da Hajiya Aisha suka shiga, driver yazo ya ja motar bayan body guard d'in yashiga gaban motar shima. " D'aya body guard d'in shi ma dae wata mota again ya bud'ewa su AKEEL, AKEELA da AQEEL suka shige suma body guard shima ya shiga gaban motar , Mai gadi wa wangale musu gate a jere suka danna hancin motar su, Wanda a gaban motar su Alhaji mota ce body guard biyar aciki suke take musu gaba, bayan ta su AKEEL d'in ma body guard d'in ne a mota daban.... Sai nace allah yakaiku lfy Alhaji TALLAFY! Baya goya marayu! °°°°°°Can tallafy foundation kuwa, su Hadiyyah ai sun jima da Isa, Alhaji yayi murna sosai,da ganin y'an uwansa da mahaifiyarsa, DUK da dai a fuskarsa da alamun damuwa daya kai duba gareta,Basu dad'e da zuwa ba iyalan kawu isma'il suma suka hallara, nan fa akaita Hira, duk da TSAKANIN Hauwa kulu da sa'adatu ta ciki na ciki ta baka na baka, Wannan aminta ai ta kau tun bayan AUREN kawu isma'il da Sa'adatu tayi, DUK da an rabu. Mazauna tallafy foundation kam suna kallo lallai Alhaji dama d'an gata ne haka, rayuwa kenan (Nikam nace ina gatan anan FANS basusan su wanene y'ay'an Alhaji Ammar bn yassir bane) DUK abunda suka zo Masa fashi na masarufi, sun bashi,abin co ku wa anci an sha Alhmdllh, "Hira ta 'balle TSAKANIN Hidayah da Alhaji sai tsokanar ta yake wai ta girma ta sha ruwan Kaduna, ita dai sai murmushi kawai takeyi, Hadiyyah ce mai tare mata, da cewa Wai kai meyasa ka yaron nan ka raina mu ne? Alhaji yace lallai yarinyar nan, nine ma yaro ko? Da nawa kuke girmeni? Wata hud'un? DUK Wannan Hirar sunayi ne Inda aka killace shi domin visiting na d'aya daga cikin d'an foundation d'in in Allah yakawo lokacin, sai hirarsu u sukeyi.... A dai dai lokacin ne Kuma, hancin motar Alhaji tallafy da y'ay'ansa da body guard d'in sa ya danno harabar tallafy foundation..... FANS yakuke ganin Wannan ziyara? Shin me xai faru a lokacin? Da kuma nan gaba ✍️Ku biyo Oum ARQAM domin kuji wad'annan amsoshin da wacce baku furta ba ma take ranku Yanxu aka Fara wasan............. 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE TWENTY SEVEN 27* "Bayan iyalin Alhaji tallafy sun gama 'karbar gaisuwa daga ma'aikatan foundation d'in, AKEEL nedai Mai amsa gaisuwarsu fuska a sake, shikam gogan naku saidai jinjina kai, ko d'aga hannu sai kace WANI gomna ko sarki yazo gaban talakawansa, itama dai AKEELA HAKAN ne gareta, tunda ita macece ai babu laifi dan tayi hakan ga maxa Wanda ba Muharramanta bane, Ma'aikatan Tallafy foundation sai murna sukeyi Yau Alhaji yazo za'a Shana, sosai Dan kuwa Rabon kud'i yake musu, shiyasa sukeson ziyarar sa, balle wannan ziyarar ta bazata. Sai shigowa ma'aikatan suke Suna kwasar gaisuwa gurin Alhaji tallafy, tun bayan sannu da zuwan da sukai Masa, shida iyalansa suka tafi WANI gini can daga gefe, Wanda dama anan Alhaji tallafy yake yada zanzo DUK sanda yazo,bayan DUK angama hada_hadar da ake ta murnar zuwan Mai gayya Mai aiki abun cikin sha'awa kana ganin wannan kasan tabbas Alhaji tallafy yaci Sunansa yana tallafawa al umar da suke 'karkashinsa, yadda yake mu'amala da body guard da ma'aikan foundation d'insa babu wanda zaice shine sama da su sai kayi duba zuwa gareshi kayi duba zuwa garesu, Amma wasa da dariya abun Ba'a magana. An samu sabbin d'iba acikin TALLAFY CHARITY FOUNDATION, dan haka Alhaji tallafy Saida Duk ya gana da yaran kowanne yasan tarihin rayuwarsu da musabbabin shigowarsu, kowanne baya rasa nasaba da maraici ko kuma had'uwa da shaidanun abokai,su koyawa yaro shaye_shaye da sace_sace da kallon fina_finan banza ta yadda zasu dinga kallon iyayensu a banza da 'kokarin lalata Yara Mata 'kanana, Duk da yaran suma basa gaza 17_20 Duk haka suke, sai fatan ALLAH ya shirya. Duk wannan Abubuwan da suka faru a gaban AKEEL da AQEEL da kuma AKEELA ne, kuma da alamu suna sauraron matsalar kowanne yaro ne, musamman masu halin maraici ne sila, Basu da cin yau balle na gobe Wannan tasa suka Fara sata,da kuma masu mahaifiyarsu ce ta fita kishiyar uwarsu ce me gallaza musu, akwai kuma uwar tasu ba fita tayi ba, aikin asiri ne yake dawainiya da mahaifinsu bai san cin su Da shan su ba, su AQEEL fa sunji halayen Rayuwa kala_kala ga yaran Kuma sun tausaya musu, Amma fa har yanzu sukam Basu samu irin tasu rayuwar da sukayi tun daga lokacin kuruciya zuwa tasawar su ba, su fa yayar mahaifiyarsu ce tai musu Duk wani muzgunawa da zalunci, kuma ta hana mahaifinsu yasan halin da suke ciki, kullum cikin kyautatawa yake tunani take musu, ta yaya zaiyi zaton zata cuci y'ay'anta kanwarta, kowannen su irin tunanikan da sukeyi a ransu kenan. "Bayan Alhaji tallafy ya KAMMALA saurarar kowanne Bangare na sababbun zubi da akayi na foundation d'insa, yai wa Mai kula dasu magana Akan yanason azo Masa da Yassir Ammar bn Yassir (Alhaji) shikam yaronnan ya tsaya Masa a ransa, yanason yazo ya kuma bada tarihin rayuwarsa a gaban su AQEEL ne, yanason ganin y'an uwansa d'innan gaba d'aya.tun baisan lokacin su Hadiyyah sunzo visiting D'IN Alhaji ba. Kamar yadda Alhaji yaso hakan, akayi ma'aikaci yazo ya kirawo Alhaji Akan Yallabai yazo kuma yanason ganinsa, Alhaji kam yace to dan shima yanasan yakuma ganin Alhaji tallafy mutum Mai mutunci Mai karamci, 'lokacin da yake shigowa wajen, daga AKEEL da AQEEL da kuma AKEELA da uwa uba Hajiya Aisha sunyi mamaki sosai da akace musu. Wannan yaron Wanda babu alamun wahala a jikinsa,daga gani yaron d'an gata ne, Amma 'kaddara ta kawoshi Wannan cibiya, alamun shaye_shaye dai sun Fara bayyana a gareshi, ta yadda le'ben sa yad'anyi ba'ki da kuma idonsa yad'anyi ja, Duk da YANZU Duk yadaina Wannan al adar Amma komawa daidai sai a hankali kam. Sun tausaya Masa tun basuji ainahin cikakken labarinsa ba, daya qaraso gurinsu cikin girmamawa ya gaisar da Alhaji tallafy dasu AKEEL, sun yaba hankalinsa sosai, Nan Alhaji tallafy ya dinga jansa da Hira tun bai saki JIKI ba har yasaka, Saida Alhaji TALLAFY ya gabatar Masa dasu AKEEL sannan yace wad'annan yayyyenka ne, gasunan, suma irin abunda ya faru da y'an uwanka ne ya faru dasu, to yaro na kullum cikin damuwa suke sunqi walwala musamman Wannan da kake ganinsa, ya nuna Masa AQEEL wanda ya kafe Alhaji da idanu yana kallonsa shidai, Saida Alhaji tallafy ya nuna shi sannan ya sauke idonsa daga gareshi had'e da murmushi,shima Alhaji murmushi yayi, Yana tausaya musu najin suma a da sun shige irin halin dasu Hadiyyah suke shiga, har yaji yana 'kwadayin jin labarin su, ta yaya su da suke da kud'i da mahaifi su shiga Wannan halin? Yawwa Yassir kabawa y'an uwanka labarin ku tun mahaifinku Yana raye. "Tiryan_tiryan Alhaji yafara bada tarihin rayuwarsa gaba d'aya shida y'an uwansa, ai kafin yakai karshe idon AQEEL yayi jajawur alamun kam gaskia wannan ahali sun shiga cikin bala'i kan bala'i musamman y'an uwansa su Hidayatullah su kam sunga rayuwar maraici RASHIN IYAYE a cikin wata shida, fuskarsa tayi jajawur abunka da fari alamu sun nuna Lallai wannan labarin ya shigeshi alamun tausayi ya bayyana a fuskar sa, hakama AKEEL da AKEELA Duk sunyi zukud'in, ita kam AKEELA har da su Kuka, shima AKEEL Saida ya share wayayen tausayin wad'annan marayun Allah din, sannan Kuma sun tsinewa kawu isma'il yafi cikin carbi, Lallai kam wannan bashida i mani, y'ay'an d'an uwanka zakaci amana, ko da yake su ma fa anci amanarsu Amma ba irin hakaba,mahaifiyar Alhaji itama tayi nata sharafin sosai kuma ita ma batada imanin, Amma Kuma sunyi addua ALLAH yasa kawu isma'il ya cuceta ya kar'be mata komai na dukiyarta.....ai kusan hakan ya faru harda tago mashin saki ma , Amma Kuma dukiyar kam bai ci ba sai wacce aka bashi da amana Akan ya juya musu ita yake Shirin cinyewa, Duk bada'kalar da akayi tsakanin kawu isma'il da sa'adatu Alhaji bai sani ba idan baku mantaba ankawoshi tallafy foundation lokacin kawu isma'il da sa'adatu Suna jone kamar tip da taya.... 'Shima kansa Alhaji sai da yayi kukan tunowa da mahaifinsa da mahaifiyarsu Hadiyyah, Alhaji tallafy Saida ya rarrasheshi, sannan yajita ga oga AQEEL da, sannan sai ajiyar xuciya kawai yakeyi, kaji labarin wannan marayan ko da halin da y'an uwansa mata suke ciki ko? To inaso dan ALLAH kacirewa kanka damuwa Akan abunda ya faru shekarun Baya, kema AKEELA kinji dai ko? Yakai duba gareta ita kam Kuka take sosai Akan rayuwar da su Hadiyyatur_rahman suke ciki,.... Lallai kam AKEELA bakisan rayuwar da suke ciki bane bayan tawowar Alhaji, tallafy foundation bane ina ga da sai kinyi kukan jini, " Cikin Kuka tace "Abbu naji halin da suke ciki in Sha Allah zan cirewa kaina damuwar dake raina, Duk da har yanxu inajin ciwonnan Abbu" Ta 'karasa cikin Kuka Yawwa AKEELA da naji dad'i, wannan kuma ciwon da sannu zai warke kinji daughter cikin lallashi ya 'karasa zancen " In Sha ALLAH Abbu nai alqawari" Shikam AKEEL dama damuwar tasa da sauqi ba kamar y'an uwan sa ba, shima Abbu d'in sai da yai masa magana cikin share hawaye yace " in Sha Allah Abbu zaka samemu masu cirewa kanmu damuwa kaji abbuna cikin" Yawwa d'an albarka "Yakai duba ga AQEEL yace " AQEEL nawa kaima inason Dan ALLAH ka cirewa kanka damuwa Duk da abun daya faru dakai akwai ciwo, Amma ai yanzu komai ya wuce kaji, sakawa rai damuwar na iya sa ciwon ka ya tashi, kasan kuma abunda likitanka yace" Alhaji tallafy ya 'karasa maganar yana kai duban sa ga AQEEL d'in. Wanda har sannan ajiyar zuciya yakeyi, Kuma in Yana Wannan yanayin Baya iya magana saidai yayi shiru idonsa da fuskar sa suyi jajawur yai ta ajiyar zuciya, yafi shiga wannan yanayin in aka tuno masa da rayuwarsa ta Baya. Lallai Wannan ahali sun bani tausayi matu'ka gaya, inason jin tarihin rayuwarsu yadda Alhaji yakeson ji. "Ruwa Mai sanyi body guard ya tsiyayo a dispenser dake flourn Mai sanyi ya miqawa AQEEL da ke ta ajiyar zuciya, bai iya kar'ba ba sai AKEEL ne ya kar'ba ya kai Masa saitin bakinsa bashi sannan yasha, bayan ya gama sha ya lumshe ido, alamun yasamu relief, haka ake Masa In ya shiga irin wannan yanayin, Ajiyar zuciya Alhaji tallafy da Hajiya Aisha sukayi ganin AQEEL ya lumshe idanunsa alamun an samu nasara Kenan, shima AKEEL da AKEELA hankalinsu ya kwanta ganin abun baiyi nisa ba ga d'an uwansu,Duk da itama AKEELA d'in tana da cutar Amma batayi tsamari ba kamar ta AQEEL d'in. Alhaji ya tausaya Wannan ahali su da suke da uwa da uba a raye Kenan Suna da damuwa ina ga su Hadiyyah da shi kansa ma, da irin yadda kawu isma'il yasanya rayuwarsu cikin wani yanayi da uwa uba Aunty(saadatu) mahaifiyarsa ita ma ta bada kamasho dan idan bata auri kawu isma'il ba ai Duk wani abun bazaiyi tsamari ba. " To Yassir yaushe y'an uwanka zasu kawo maka ziyara ne, inason ganinsu baki d'aya, ALLAH yasa dai lokacin da Mutan kaduna za'a zo dan inason ganin wad'annan y'an biyun naku, Alhaji tallafy ya 'karasa maganar yana murmushi,alamu dai ya nuna yanason y'an y'an biyu, dai gashi su Hadiyyah har sun shiga ransa. "Yallabai ai yau suka zo Masa visiting d'in gaba d'ayansu abun gwanin sha'awa, har da wasu masu kama d'aya sak, kamar dai wad'annan y'an biyun naka ya nuna AQEEL da AKEEL, "Amma Tanko baka gaya mun ba,ai da dasu za'azo Ayi wannan zaman, lallai kam fad'uwa tazo dai_dai da zaka cewar Alhaji tallafy yana shafa gemun fuskarsa, jeka zo Mana da wannan a Hali masu albarka, "To Yallabai cewar Tanko yana yana fita cikin sauri domin tawo wa dasu Hadiyyah....... Wayyo hannuna y'an amana, wannan ma dai nayi muku ne Amma har yanxu ina cikin alhini ne. ALLAH ya gafartawa Zainab da y'ay'anta guda hud'u yakai haske kabarinsu ya kar'bi shahadarsu baki d'aya Yas aljannah makomarsu, ya bawa mijinta Ado haquri da sauran y'an uwanta, please FANS kusakata a cikin adduar ku, gobara suka samune cikin dare, daga ita har yaranta suka mutu ranar da akayi gobarar yarinyar data ke goyo ta rasu, washe gari gari kuma Yara biyu suka mutu, kwana biyu tsakani ita maman ta rasu itama kwana Daya tsakani itama guda dayab data rage ta bisu, munga masifa da bala'i y'an uwa mijinta ma abun tausayi 😭😭😭😭😭😭 ✍️Oum ARQAM ce 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE TWENTY EIGHT 28* ALLAH ya kai haske kabarinsu gaba d'aya iyalan Zainab da ita ma kanta,ya kar'bi Shahadarsu baki d'aya yabawa mijinta haquri da dangana da sauran y'an uwa baki d'aya "Lokacin da Tanko ya qaraso cikin Hall d'in dasu Hadiyyah suke ciki, sukam har sun 'kosa da Rashin dawowar Alhaji, Yara duk sai wasa sukeyi,manya kuma anata Hira, da murnar ganin Alhaji ya nutsu yadawo kamar yadda yake da , sai abunda ba'a rasaba, sai addu'a Alhaji tallafy yakesha daga bakunan wad'annan ahali masu albarka. "Ya isar musu da sa'kon Alhaji tallafy yana son ganawa dasu ne, ai sai aka shiga mamakin HAKAN, to Alhaji WANI ganawa zaiyi dasu su kam, koda yake yadda sukejin labarin sa ai Dan yace zai gana dasu ba abune na mamaki ba. "Tanko yace ina Zuwa Amma, Fita yayi yaje ya gayawa Alhaji tallafy cewa ai Basu kad'ai bane, mutane da yawa ne, Anan Alhaji yake cewa "ai dama ba y'an gidanmu bane kad'ai, harda matar kawu Isma'il da y'ay'an sa, "Ok to shikenan Tanko kirawo su gaba d'aya,ai ba WANI Abu bane,kawaii gaisawa zamuyi, sai Kuma muga y'an uwan nasa "To shikenan Yallabai bari nakirawo su, Tanko yafad'a yana ficewa "Gaba d'aya suka Antayo dan amsa Kiran Alhaji tallafy harda su Hajiya Baaba, dasu Hauwa matar kawu Isma'il,sai dai dana kai du bana Banga 'bur'bushin Sa'adatu ba ko ina tayi? "Tun bayan zuwan Hauwa matar kawu Isma'il fa sudai su Hadiyyah meya faru tsakaninsu da ita? sai alkhair da ta ke musu, lokacin zaman ta a gidansu baza su mance ba, yadda ta dinga kula musu da Hunaif in zasu makaranta da yadda ta dinga wankin kashin sa, ko bama haka ba, tun kafin tazo gidansu akwai girmamawa tsakaninsu da ita, saboda matar kawun suce, tun da tazo suketa murna aketa hirar yaushe rabo, hakama y'ay'anta, itama Baaba sun gaisa da ita da hirar bayan rabuwa, to wannan hirar da ake tsakanin su ita ta hassala Sa'adatu Akan dan me zasu Kula Hauwa tun da bata mata magana ai suma bai kamata suyi mata magana ba, shine taji haushi tayi tafiyarta gida,'karya tai musu wai zata dubiya asibiti ne, sun tawo sukam Suna takan Hira, da to suka bita babu WANI kulawa, shiyasa yanzu babu ita a tawagar zuwa wajen Alhaji tallafy d'in. "Su AKEEL kam Ashe Basu ga komai a kyau ba Saida suka ga twin's Hadiyyah da Hidayah sannan, da kuma Su Zahra da Zeenah ga Hunaif, dan kuwa su kyawun su daban yake da sauran y'ay'an Sa'adatu, DUK da suma d'in Basu da makusa, AKEEL ya ganesu Hadiyyah ne saboda Kamar da suke da JUNA, babu shakka sune twin's d'in su Alhajin, Wanda Halin maraci ya rabasu da JUNA, Amma shikam ai Baya ganin abunda xai rabashi da d'an uwansa AQEEL abune Mai sauqi. sai da suka shigo gaba d'aya sannan CIKIN girmamawa suka gaisa da Alhaji tallafy d'in, baaba sai godiya take Masa Akan tallafawa rayuwar marayu da marasa 'karfi da yake, da adduar ALLAH yasa yafi haka, Shi dai Alhaji tallafy sai "Ameen Ameen yake cewa, saboda matar ta kwanta masa a rai, Bayan an gama gaishe_gaishe ne, Alhaji tallafy yace" wad'annan sune twins d'in da Alhaji yabamu labarinsu, Lallai kam ALLAH yai muku albarka baki d'ayanku, Da Ameen suke amsawa Lallai sunga karamcin Alhaji tallafy yadda yake jansu da Hira, baza ka ta'ba yarda cewa shine Alhaji tallafy d'in ba, yadda ya tamfatsa Wannan foundation d'in da kadarorin daya mallaka, amma YANZU gashi CIKIN su sai Hira yake jansu da ita, DUK da dai ba wani ahi suke cewa ba daga "ea sai a'a" "Idon AKEEL ya'ki d'aukewa daga kan wad'annan twins d'in,dama akwai twins masu kama irin haka? Bayan su? Yana kallon motsin kowa tsakanin Hadiyyah da Hidayah, yaga dai d'aya tana wa d'aya surutu ita kuma d'ayar Bata magana sai dai kallon d'aya, shi kam shin burgeshi fa. "Ita ma AKEELA sun burgeta DUK da dai, ta girmesu, Amma Zahra zasu iya sa'a da ita, dan sun burgeta gaba d'aya y'an uwan Alhaji d'in. DUK Wannan Hirar da akeyi, babu AQEEL a wajen, tun bayan shan ruwansa barci ya kamashi, Dan uwansa ya kamashi ya shige dashi bedroom d'in da yake cikin flourn domin ya samu nutsuwa ko zai dawo dai_dai idan ya farka. "Tun bayan shigowar su Hadiyyah ya farka, duk surutun dasu keyi yana jin su, Amma kam bazai iya fitowa ba, shi yasa yaci gaba da kwanciyarsa. Bayan gaishe_gaishe da sauran abubuwan da akayi, su Hadiyyah sukayi haramar tafiya gida, nan Alhaji tallafy yake tambayar shin wacce school suke Zuwa ne? Sukace ai sunyi candy Amma Basu ci gaba ba, ya tausaya musu, dan kuwa yadda mahaifinsu yake da burin y'ay'ansa suyi karatu, bai kamata kawu isma'il ya dakatar dasu, ko da bai bar musu gado ba, tun da dai dai gwargwado yana da rufin asiri ai zai tsaya musu suyi karatun,nan dai aka tsayar da magana,cewa zaizo har gida ya duba lamarin karatun nasu zai tsaya musu, har kawo ALLAH ya kawo musu miji na gari, kar kuso kuga murna gurin su Hadiyyah,sai godiya sukewa Alhaji tallafy d'in, Nan Baaba take cewa ai cikin satin ga suke Shirin komawa Kaduna kuma har da Zeenah zata tafi,Alhaji tallafy yace idan babu damuwa ta d'an jira zuwan sa kafin su koma, zai san abunyi, ALLAH sarki Alhaji tallafy yadda kake tallafawa al uma kaima ALLAH ya tallafa maka. "Haka dai su Hadiyyah suka bar tallafy foundation cikin farin ciki da murna, shima Alhaji yakoma cikin y'an uwansa Hostel. "AKEEL ya shiga gurin d'an uwansa AQEEL yaga har ya farka ma, babu wata matsala tare dashi, damuwar ta ragu ba kamar da ba, dan kuwa idon sa ya washe da fuskarsa Jan ya ragu, haka ma Ajiyar zuciyar da yakeyi ta ragu, nan AKEEL ya dinga Jan sa da Hira, yana bashi labarin su Hadiyyah yaga twins masu kama d'aya kamar yadda suken nan, babu banbanci, sannan Abbu ya d'au nauyin karatunsu, zasu ci gaba da zuwa school,sun bashi tausayi sosai da ua gansu, da irin halin maraicin da suke dashi na babu uwa Babu uba a 'karancin shekarun su, shi dai AQEEL Duk yana saurarar dan uwansa har sannan bai yi magana ba, a haka Alhaji tallafy dasu Hajiya Aisha suka shigo suna Masa sannu yana d'aga kai, har lokacin da suka tattara yana su yana su suka bar tallafy foundation suka d'un Guma zuwa gida, maaikatan ta d'aga wa motar Alhaji tallafy hannu har suka fice, "Tun daga sannan, abokan karatun Alhaji suke ganin girman shi sun d'auka ko d'an uwan Alhaji tallafy d'in ne ganin sa y'an uwansa su kazo visiting har 'bangaren Alhaji suka shiga, ALLAH sarki basusan kauna ce kawai ALLAH ya had'a tsakanin zuri'ar Alhaji Ammar bn Yassir da Alhaji tallafy ba, da kuma alkhair d'in da Alhaji Ammar d'in yayi lokacin Yana raye ne yake bibiyar y'ay'ansa ba. ************** Sun koma gida lafiya su Hadiyyah, Zakiyyah Babu Wanda taiwa kallon arzi'ki a cikin su, Suma basu bi takanta ba. Sa'adatu gidan abokin marigayi Alhaji Ammar bn Yassir taje, uwar gidan sa aminiyar ce , Babu WANI uban nisa da tallafy foundation shi yasa ta wad'a gidan, ita kad'ai ta tawo su haidar da su Hafsat ta barsu wajen su Hidayah, Su nata hira da Hajiya ikilima sai ga Alhaji gambo ya dawo, nan aka gaisa da sa'adatu da tambayar ta Yara, tace DUK Suna lfy qlau, ya tambayeta ina Mai gidan Isma'il, nan take gaya masa "Yaushe rabona da Auren Isma'il ai da jimawa muka Rabu, duk ta bashi labarin komai yadda ya faru. Sai naga Alhaji gambo yana WANI kallon Sa'adatu ta kasaj ido ko HAKAN me yake nufi oho? Alhaji gambo dai abokin Alhaji Ammar bn Yassir ne tare suke Sana'ar su ta safarar shanu, Kuma shima ALLAH ya sa Masa albarka yanada kud'i, Amma saboda babu zumunci tun bayan rasuwar Alhaji Ammar d'in bai waiwayi iyalansa ba yaji me suke buqata me suka rasa. Matan sa uku Hajiya ikilima qawar Sa'adatu, sai Hajiya suwaiba da Amarya Hajiya sahura, kowanne daga cikin su asiri suke junan su naganin Alhaji gambo ita kad'ai ce y'ar gaban goshi a gareshi, shiyasa Alhaji gambo yake kamar Baya cikin nutsuwar sa,to anata yi maka asiri kala_kala ha dole ka Zama haka ba. "Bayan Sa'adatu ta gama hirarta ta 'kawarta Hajiya ikilima, sai da yamma tayi sannan tai mata sallama, tai tafiyarta gida, lokacin su Hadiyyah har sun manta da komawa gida suma,nan dai sukai mata yamai jiki tace da sauqi, kuji 'karya "Tun bayan zuwan Sa'adatu gidan abokin Alhaji Ammar bn Yassir Alhaji gambo fa da labarin da ta bashi nacewa ai isma'il ya saketa, sai kuma yafara tunanin ta da 'kwadayin aurenta, Saida yasan yadda yayi ya saci number d'in Sa'adatu a wayar matarsa Hajiya ikilima kuma aminiyar Sa'adatun a zummar zai kirata su kulla ala'ka, ta Aure ita ma Hauwa matar kawu Isma'il ta koma gida lafiya, kuma taiwa mijinta albishir d'in cewa aikuwa Alhaji tallafy d'in yace zai d'auki nauyin karatun su Hadiyyah zuwa university zai musu komai,da to take amsa mata kawai, dan hankalin sa yana kan system d'insa yana WANI Aiki Akan hannun jarinsa da ya zuba, kuma riba ma sha ALLAH an Fara samu fa, yafara jin alert ta account, Mai gida bakayi murna ba, cewar Hauwa To tashi zanyi ina rawa da wa'ka sannan zakiji cewa ina murna, please ki 'kyaleni Aiki nakeyi fa, Shikenan ai ALLAH ya kyauta maka, Nan kuma ta gaya Masa cewa Alhaji yayi 'kalau abun sa Duk WANI rashin Kunya da shaye_shaye ya daina, yazama yaron kirki, "Ai dama nasan za'ayi hakan tallafy foundation in dai yaro ya shige ta cikin ikon ALLAH yana shiryuwa ALLAH yasaka Masa da alkhair dai Allahumma Ameen cewar Hauwa tana barin gurin ganin hankalin mijinta yana kan system d'in sa alamu sun nuna WANI Abu mai muhimmanci yakeyi A dai dai lokacin kuma ya kammala aikin da yake a system d'in sa , yace Hauwa kulu ina Zaki kuma Mai naji kina cewa Akan su Hadiyyah ne? Banji sosai ba ,naji dai kince zancen karatunsu ko? Alhaji tallafy zai d'au nayi to shi kuma me ya.......... Muje zuwa next page muji abunda zai faru Me kawu isma'il zai fad'a Akan cigaban karatunsu Hadiyyah? Ya batun Sa'adatu da Alhaji gambo shin zata amince Masa idan ya miqa buqatarsa gareta???? Da sauran su Lallai Sa'adatu kin xama maci amana kenan mazajen aminanki ne ke Kuma suke son ki lallai, ALLAH yasa dai karta amince...... 😭😭😭😭😭😭ALLAH ya gafartawa Zainab da y'ay'anta Baki d'aya ya haskaka kabarinsu ya kar'bi shahadarsu Yasa aljannah makomarsu baki d'aya yabawa y'an uwa da mijinta Haqurin Wannan jarrabawa🙏🙏🙏 ✍️Oum ARQAM ce ontop 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE TWENTY NINE 29* An saka Ranar Auren Zahra da saurayinta Ibrahim bala wata biyu,Wanda da ma an jima da yin zancen Auren exam ta tsayar,lallai ne lokaci yazo zamuga kawu isma'il Wanda aka bashi gidan su na ga do aka saka y'an haya yace idan ALLAH yakaimu Auren su sai Ayi musu wahala da kud'in hayar. "Kamar yadda Alhaji tallafy yai al 'kawarin Zuwa wajen su Hidayah HAKAN akayi, kowa yasan Alhaji sananne ne a garin, dan haka bai d'au body guard ko d'aya ba, sannan motar d'aya daga cikin ma'aikatan foundation d'insa ya aya Mai sau'kin kud'i,bai samu wata matsala ba ta ganeshi har layin su Hadiyyah yaje yayi parking d'in motar dakansa, a bakin gate d'in gidan, wani yaro ya gani shi d'aya yace shiga kace Alhaji 'Dalhat ya na magan, ai Baaba naji tasan Alhaji tallafy ne, Ranar kuma Duk yaran gidan sunanan babu school ismaliyyah kuma sai azahar, shi kuma shigar wuri yai musu, wannan karon ma an samu sa'bani da sa'adatu batan, taje wajen saukar Y'ar 'kanwarta. "Haydar Baaba ta aika tace "kace ya shigo Alhajin, nan danan Kuwa Alhaji ya shigo a Flourn su Hadiyyah Baaba tai Masa iso, "Shikam Alhaji tallafy tun daga gate d'in gidan da tsarin ginin yasan tabbas Marigayiya Alhaji Ammar bn Yassir shima kam ya dama lokacin Yana raye, Amma ga yadda halin rayuwa ya Sanya iyalansa, d'aya d'an sa ma ya fad'a shaye_shaye, kuma yaga tsa rin gidan Duk ya lalace fentin gidan Duk yayi ba'ki da tiles din jikin bango Duk ya ciccire, 'kofofi Duk sun lalace, tarazo ne a tsakar gidan Duk ya faffashe,alamu ya nu na da ice suke amfani ga haya'ki nan Duk yayi shaida, fanfon dake wajen wanke_wanke shima kansa ya cire,Baya tunanin da ruwa ma a gidan yanzu, kai abubuwa da Yawa Duk sun lalace a cikin Wannan gida, Duk a lokaci guda Alhaji tallafy yayi nazarin wad'annan abubuwan, 'farko so yayi ya Aiko bodyguard D'IN sa yai Duk WANI Abu game da zancen school D'IN su Hadiyyah din, Amma Kuma sai yayi tunanin yazo da kansa kawai, Ashe ALLAH ne yaso yazo Dan yaga abubuwa da Yawa da suke bu'kata, Alkhair baya fad'uwa kasa a banza. Lokacin da Alhaji tallafy ya shiga flourn sun gaisa da baaba cikin mutunta juna tana bashi girma yana Bata,haka ma yaran gaba d'aya sun gaisar dashi ciki da tarbiyyah, shikam ya yaba yarannan, musamman twin's. Sun tattauna da Baaba Akan zancen school D'IN su Hadiyyah, sannan Baaba ta 'kwad'a musu Kira, dan bayan gaisar da shi da sukayi falon Sa'adatu suka koma su Basu guri su xanta, bakin Hadiyyah da Hidayah ya'ki rufuwa tun zuwan Alhaji tallafy domibln sun san zancen school ne. Murna ta 'karu lokacin da Baaba ta kirasu,sun tawo a tare cikin nutsuwa,shikam wad'annan Yara ALLAH ya Sanya Masa 'kaunar sa a cikin zuciyarsa tun lokacin da d'an uwansu Alhaji ya Basu labarin sa, Sun yi magana dashi Inda ya tambayesu wane course suke buqata a university d'in to ra'ayin su yazo d'aya Duk community health suke so, ya jinjina musu kuma ya Basu kwarin gwiwa, sannan yace anku sa Jamb da UTM in Sha ALLAH zai sai musu form, zai Aiko bodyguard D'IN sa sai su cike sunyi Murna sai Godiya suke Masa, yace babu Komai kamar y'ay'ana twin's nake kallon ku, su ma haka suke ra'ayin su d'aya su ma, "Sun yi magana da Baaba Akan zaman Hidayah a Kaduna state,sai dai ta dawo kano d'in su xauna ita da Y'ar uwarta suyi karatun tare,dan dama dole ce ta rabasu,yanzu Kuma sun dawo, Baaba tace ba bu Komai sai ta koma da Hunaif da Zeenah d'in, ta d'ebe mata kewar Hidayah d'in,kuma shi ma zai sa su a makaranta Mai kyau kuma zai dinga musu aike , Ita kam Baaba ba bu bakin magana sai Godiya take Masa yana ba bu Komai, Baaba kam tasan alkhair Alhaji Ammar bn Yassir ne yake bibiyar ahalin sa, Amma irin wannan tago mashin alkhair haka,kai ma sha ALLAH. A haka Alhaji tallafy ya gama Duk tataunawar da zaiyi da Baaba ya kammala, CIKIN salama sannan yai musu sallama. Alhaji tallafy yaga Zakiyyah yayi tunanin Zuwa ziyara gida tayi. 'Bayan tafiyar Alhaji tallafy daga gidan sai murna ta kacame tsakanin su, twin's kam baki yaqi rufuwa,yanzu sun dawo guri d'aya ga karatunsu ya kusa d'orawa burinsu kenan kuma burin mahaifinsu Akan su Ashe zai cika ALLAH yasakawa Alhaji tallafy da alkhair dai. 'ko da sa'adatu ta dawo Duk yadda sukayi da Alhaji tallafy Baaba ta gaya mata, Amma ko ta nuna wata murna sosai, zuciyarta, sai quna take mata, Akan me Alhaji tallafy zai d'auki nauyin karatunsu kuma, da ta sani bata ce aje wa Alhaji Visiting ba, ai da be gan su ba, lallaai Sa'adatu baki sani ba ai ko da basuje ba shi kam Alhaji tallafy yayi niyyar tallafawa marayun ALLAH kuma ta Allah bataki ba shi Mai haquri yana tare da ALLAH......... 'kwana biyu tsakani Baaba tai haramar tafiya gida Kaduna state ita da Hunaif da Kuma Zeenah, domin batayi gaddamar tafiya ba, saboda Hunaif itakam tana son sa, ALLAH yakaiku Lafiya, Alkhairin ALLAH ya kai miki Baaba, Baaba tace wa Hidayah in ALLAH yakaimu lokacin bikin Zahra sai na tawo miki da kayan ki da sauran abubuwan Amfaninki, sai da Baaba tayi kukan rabuwa da Hidayah itama tayi kukan, sabo kenan. Haka Hadiyyyah da Hidayah suka ci ga ba zama tare da juna, a gefe guda Suna ta shirye shiryen bikin Zahra. Zakiyyah Kam kud'in ta sun 'kare Wanda take ci, Wanda take Samu a gidan darajar idona Baaba ne, da kuma Zeenah, idan an bata nata taka wo mata taci. Rayuwa fa taiwa Zakiyyah zafi sai ta wuni ta yini bata ci ba, su zahra da Hadiyyah da Hidayah kam har kar gabansu sukeyi basa shiga wurimin ta shi yasa zaman gidan yai mata za fi, babu Mai kulata kuma Wannan hud'ubar Baaba ce, Khadija ce Mai kulata kawai ita ma idan ta na makaranta shikenan. Itama Hidayah ta samu koyarwar a islamiyyah d'in su Hadiyyah,su kam Yara sai mamaki suke su biyu irinsu d'aya haka, dan ma basa saka kaya iri d'aya nata Suna Kaduna state ai da abun sai yafi mamaki,sun fad'awa Mai makarantar cewa Amma fa sun kusa Fara zuwa school bai jii dad'i ba. ************** Tun bayan da wowar su AKEEL daga tallafy foundation, abubuwa da Yawa suka sauya na damuwar AKEELA da d'an sau'ki kam, tun ta ta ga abun da ta gani kuma ta ji abunda ta ji,sai tausayawa ma'abota foundation D'IN takeyi musamman su twin's d'innan. Shikam AKEEL dama damuwar ta sa da sau'ki Amma yana tausaya twin's din nan shima Kuma sun burgeshi, matuqa, shi kuma AQEEL dama bai gan su ba, yadai ji labarin su a Wajen AKEEL dan da sun zau na zai Fara ba shi labarin su, "bro ka ga wad'annan twins d'in y'an uwan wannan yaron na foundation d'in Abbu, ai suma kamar mu suke, kamar su d'aya, na so ka gansu, yadda Muke dakai d'aya Mai surutun tsiya, d'aya kuma bata da magana sosai, Amma dai ta fika magana dan ina kula dasu tana wa sister d'in ta magana in tai Mata Amma ba sosai ba, please bro kai ma kazama kamar ta, idan nai maka magana ka din ga mayar min, kadaina mun shiru ko ka dinga d'aga min kai kaji, rayuwar twins d'innan abun sha'awa, ina so mu zama irin su, kullum hirar da AKEEL yake wa AQEEL Kenan, tun Ba ya magana in Yana bashi labarin har yake magana,sannan Kuma yana son shi kam yaga wad'annan twin's din da brother d'in sa yake basa labarin su. 'ko da Abbu yaje gidansu Hadiyyah, sai da yadawo yake Gaya wa Ummuh Anan suke jin yaje,sai AQEEL yake tunanin ina ma Abbu yaje dasu gidan sun gan su d'in, ko dan ya huta da labarin da AKEEL yake ba shi na su, 'Da haka kuwa AQEEL ya d'an saki ransa KA'DAN, dan ana d'an Hira da shi yace "i ko a'a" Wanda da Ba'a samun haka sai dai d'aga kai ko kuma ya saka idon sa ana mutum alamun yana ji kenan, wannan canza war da AQEEL yayi tafi yiwa AKEEL sama da kowa a gidan dad'i, Amma da kuwa kamar ba shi da d'an uwa abo kin yin Hira,yanxu kam ma sha ALLAH Tun da dai asalin su da ma shi AQEEL ba Mai magana bane sosai, Amma sauyawar sa ta samo a sali ne tun daga lokacin da wannan mummunar 'kaddarar ta samesu musamman shi da AKEELA, HAKAN yafaru Duk sana din Rashin mahaifiya gare su, da cin amanar da Ammar su ta yi a garesu shine sanadin komai da ya sauwa rayuwar AQEEL da AKEELA, Duk da YANZU ka so 50% CIKIN100% ya ragu sai abun da Ba'a ra sa ba, Amma abubuwan sun yi yawa fa, a hakan ma an sha fa ma da AQEEL da AKEELA d'in kafin samun sau'kin rashin lafiyar da kowannen su ya had'u da ita, Duk da kowanne da kalar ta sa cutar Amma sanadin ta guda d'aya ne Yan amana Muje page 30 domin muji yadda zata kaya Amma YANZU aka Fara wasan..... Rashin IYAYE Akwai maraici, tausayi,cin amana da kuma xazzafar soyayyah Mai tsayawa a rai 😭😭😭😭😭ALLAH ya gafartamawa zainab da iyalanta gaba d'aya ALLAH ya haskaka kabarinsu ya kar'bi shahadarsu baki d'aya ya bawa mijinta da y'an uwanta ha'kurin jure rashin su 🙏🙏🙏🙏 ✍️Oum Arqam ce 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE THIRTY 30* "Alhaji Gambo ya Kira Sa'adatu a waya kamar yadda ya d'au al wa shin Kiranta, Sa'adatu tana zaune a Flourn ta, tana tufka da warwara Akan sha'anin Rayuwa yau da dad'i go be ba bu, wai sune suke cikin wannan Hali na Rayuwa, Anya Kuwa zata jure! Dama Sa'adatu ita da y'an uwanta basa Auren wan da ba shi da kud'i,in kuwa suka ga Mai kud'i ko a malamai sai sunyi asirin da zai so su, to hakane ma yafaru da Alhaji Ammar bn Yasir d'in shima ai ba son ALLAH bane, ta malamai ta bishi har ya Aureta, san nan Kuma tazo ta 'kalla bawa Ummu Ruman a CIKIN gidan ta, Wanda kuma tun kafin Alhaji Ammar bn Yasir yazama WANI suke tare, tun daga gidan haya Duk wahala Ummu Ruman ta sha a CIKIN gidan ta, Saida dad'i yazo sun Fara Tara Yara ALLAH ya had'a shi da Sa'adatu tazo CIKIN gidan ta dinga takura mata,makirci kala_kala ta shiga ta fita ta raba ta da mijin sai da ALLAH yakawo karshen abin sannan har saki biyu Sa'adatu ta sa Alhaji Ammar bn Yasir yaiwa Ummu Ruman ALLAH ne yayi zatayi Masa takaba ma, ai nasan baku manta da halin Sa'adatu ba.duk y'an uwanta babu wanda yake Auren talaka sai Mai kud'i, kuma ya na autar su idan yana da mata to matar zata koma bora in Basu koreta daga gidan ba ma gaba d'aya,kuma y'ay'an mijin su dinga gallaza musu, akwai ya yar Sa'adatu Wanda take zawarci akwai kanwarsu Mai kud'i take aure tazo haihuwa ta rasu,saboda abun kunya sai Wannan ya yar tasu babba ce fa ya yar Sa'adatu ce, ita Kuma 'kanwar tasu Sa'adatu ma ta girmr ta, Amma tana mutuwa suka din ga shiga su na fita har Saida mijin 'kanwar ya Auri babbar yayar ta su, saboda abun kunya ALLAH ya kyauta, suma su Sa'adatu Akan kud'i ba bu abun da baza su yi ba. "Ringing d'in wayarta ne ya dawo da ita daga tunanin da takeyi, ba 'kuwar number ta gani, da kamar baza ta d'au ka ba sai kuma ta d'auka "Assalamualaikum wake magana? " Fatan da Hajiya Sa'adatu nake magana? Cewar Alhajin gambo " Ea nice! Wake magana? "Ma sha ALLAH Alhajin gambo ne, fatan kinje gida Lafiya? Tun ranar da Kika zo nake son kiranki,Amma Kuma bani da number d'in ki,sai a wayar Hajiya na Samu! Sa'adatu kam mamaki ta shi ga, meya sa Alhajin gambo ya kirata? "Sa'adatu na ji kinyi shiru? Ko da WANI abun ne? " A'a Babu komai mamaki dai nake na Kiran da kai min, ai ba yau na Fara zuwa gidan ka ba, baka ta'ba Kira na kayimin ban gajiya ba! "Lallai Sa'adatu ban da abin ki lo kacin da kike zuwa gi da na, ai da aurenki kike zuwa, mezai sa na Kira ki a waya ki na Matar aboki na? Yanxu kuwa babu igiyar ko wa a kanki, kin san dai manufar da ta sa na kiraki ko' sabo da ke ba Yarinya bace Duk su ba dad'in da Alhaji gambo yake yi Sa'adatu tana saurarar sa "Auren ki zanyi Sa'adatu kuma nan ba da jima wa ba, ko dan na karewa Abokina iya linsa, tun da shi Isma'il bazai iya ba ni ALLAH ya kawo ni! "Alhaji Wannan zancen da kakeyi Duk na ji, WANI han zari ba gudu ba kar ka manta Alhaji Ikilima 'kawa ta ce fa 'kud da 'kud, bana son halin da mu ka shiga tsakanina da Hauwa Matar Isma'il yakuma faruwa da mu,Amincin mu ya ta'bar'bare fa Alhaji! Duk Wannan ba damuwa bace Sa'adatu, yanzu da Kuka rabo da Hauwa mene ya same ki? Kuma na ga Aure sunnar ma'aikin ALLAH ne, ba zaman da duro muka 'kulla ba, ba kuma mummunar Ala'ka ba, share komai zanzo gidan ma! Nan dai suka d'an ta'ba Hira tsakanin su, ba suyi sallama ba sai da suka tabbatar da tsayayyiyar magana, kuma Sa'adatu ta Amince da Alhaji Gambo. Dama zuciyar Sa'adatu ba 'kin Auren Alhaji gambo zatayi ba, ta yi hakan ne sabo da bariki, kar Alhaji gambo ya ce ta amince nan da nan. Sa'adatu ta yi murna sosai fa da Alhaji gambo yai mata zancen Aure, ita da ma burinta a koda yaushe Hakane, tun AUREN ta da Isma'il ta ke murna, sai da Isma'il d'in yq zamar mata mugu ne ta yi dana sanin Auren sa, Amma da kam murna takeyi ta haye ta bad Ummu Ruman a ta sha sai kuma ga shi Ummu Ruman d'in ta bar mata duniyar ga ba d'aya, shi kawu Isma'il d'in da take murna a kanshi ya so ya cu ceta ya 'kwa ce mata gidan y'ay'anta,ku ma dukiyar y'ay'anta yanzu ta na hannun sa yana so ya cinye. Su na gama wayar ta Kira Fa'izah yayarta ta gaya mata cewa ta yi kamun Alhaji gambo abokin Alhaji Ammar bn Yasir d'in, kuma mijin Hajiya ikilima aminiyarta ! Yaya fa'izah ta ce babu komai ki aureshi ina ruwan mu da wata hajiya ikilima Auren ta ya ke ke ma auren ki zaiyi,to shinenan Yaya cewar sa'adatu tana ka she waya. Tun DAGA sannan Alhaji Gambo suka jo ne da sa'adatu, kuma har gi dan yazo, ko kun ya tun da Alhaji Ammar bn Yasir ya ra su bayan gaisuwa bai Kuma zuwa gidan ba,dai sana din Sa'adatu, su yaran ba su ka wo komai ba, tun da sun san shi farin sani abokin Abby ne,sun yi tunanin ziyara ya kawo musu, yai abun da zaiyi yai tafiyar sa gida. Zakiyyah ta na d'aki, abun duniya ya ishe ta,babu Mai kula ta. Gidan, y'an uwanta za su kwana su ta shi, tare Amma ba bu Mai mata magana, Hadiyyah da Hidayah su na zuwa koyarwar su, su na samun kud'in su dai dai gwargwado, ku ma abun da su ke so su na saya,wa ni kud'in ku ma suna tarawa sabo da Bikin Zahra da yake 'karatowa, Amma babu Mai kulata, kuma Wannan Duk hud'ubar Baaba ne. tana fa ma da ciwon ciki CIKIN ta har za fi yake ma ta, yunwa ce Kuma ta sa HAKAN,ga ciwon kai tana ta shi jiri ya ke d'ibar ta, kamar za ta Fad'i, shi Yasa take wuni a kwance, Duk da hakan ba bu Mai kulata, a kwance ma gani ta ke garin yana juya mata, yau kwanan ta d'aya da wuni babu abinci, sai ru wa da ta ke sha, yanzu kuwa ruwan ma ta kasha Shan sa, kulle ma ta ciki yake yi,ga zafi da CIKIN ta yake mata. Sai tu nanin zaman gidan Hajiya Sakinah kaakarta miri'kiyarta take yi, irin jin dad'in take ciki, Wannan ai Duk da jimawa ne , zuciyarta ta ba ta amsa, ki tuno zaman mijinki me kika rasa? Mijin ki komai bai raga Miki ba, sai abun da Kika ga damar dafa wa, kiyi kwanciyar ki WANI ba yi kikeyi ba, sha ra da wanke_wanke ne ki keyi in kin so, Amma har ya ran ma'kota zuwa su ke su na Mata ta Basu abinci,irin Marasa 'karfin nan, ta ba su abinci da y'an kud'i,Amma wai yau ita ce akan Abinci ta Zama cu ta tana Shirin kama ta, ta yunwa, zantukan da Zakiyyah take ayyanawa a ranta kenan, ALLAH sarki *ABIE* na ko yana wane hali yanzu oho, ALLAH yasa dai Bilkisu ba zaluntar mun shi take ba, wad'annan zantukan dai Zakiyyah take tayi, zafin ciwo ne ko kuma nadama tayi ALLAH ne masani, sai nan gaba zamu ga yau Zakiyyah da zancen mukhtar da kuma ABIE ai da bata zancen su amma yau tayi maybe zafin yunwa ne, ta na samun abinci ta 'koshi zata da wo kan bakanta, tun da dai halin Zakiyyah sai ALLAH Anya kuwa zatayi nadama. Su Hadiyyah da Hidayah kamar yadda Alhaji tallafy yai musu Al 'kawari HAKAN ne kam yafaru, ana Fara registration ya Aiko musu da form da komai da komai suka cike, sai mur na kamar ba bu go be, ALLAH yakusa cika musu burin su,har ku kan murna sukayi da tuno Abby ai da yanzu Suna level two ma may be tun candyn su in da sannan suka d'ora. Hajiya Zahra amare sai 'kyallin Amarci akeyi ALLAH ya kusa yanke mata wahala xaman yunwa da talauci, uwa uba ga gallazawar Sa'adatu, a garesu,sai mur na takeyi ALLAH ya kawo lokaci,sai dai murnar ta na komawa ciki idan ta tuna da 'kannenta y'an biyu Hadiyyah da Hidayah da 'karamarsu Khadija, idan Allah yakawo Auren su za'a iyayi rana d'aya, ita kam khadijatu zata Zama sau ra ita d'aya ta na ba ta tausayi sosai, yarinya ba bu ruwanta shiru_shiru da I ta kamar babu ita a gidan,ita fa wat rana mancewa ta ke da ita,balle kuma oum Arqam wacce ba Y'ar uwar ta ba,shi yasa bana zancen ta sosai mance wa nake da ita, saboda babu hayaniya gareta. Bata saka Zakiyyah a sahun zan cen ta ba, d'an lokaci ne zata koma gidan mijinta, saboda ta Fara gano alamar nadama a tare da ita, Duk ta fice hayyacin ta, Babu walwala tare da ita,tana tausaya mata Amma Kuma ga ta ne Baaba take so tai mata zaman gida bai kama ce ta ba, idan ta ji wuya da 'kafarta zata koma gidan mijin ta, haka babba tace musu, shiyasa ma suka fita daga harkar ta tan,Amma d tafara Basu tausayi,zasu ci ga ba da kulata har su Hadiyyah da Hidayah d'in su dinga ba ta abinci sai su ka tu na,idan sukai mata ga tan hakan bazata koma zaman gidan mijinta ba, iskancinta zata ci ga ba dayi, Amma yanzu sun Fara ganin Amfanin nadamar Zakiyyah d'in, ALLAH sarki d'an uwa Mai dad'i ALLAH yasa Zakiyyah tayi nadamar kamar yadda y'an uwanta suke buri Nima inaso tai nadamar seerat na san kema kina son 'kawarki ta yi nadama ta koma gidan mijinta ko? ************** Alhaji tallafy ya 'kudiri niyyar gyara gidan su Hadiyyah da Kuma din ga kai musu abinci, Amma idan ya tuna da da wacece Sa'adatu sai yaji Baya son yin HAKAN,gwanda dai ya dinga bawa twin's kud'in zu wa makaranta da Yawa, yasan bazasu 'ki tallafawa 'kannensu ba, Amma shi kam Sa'adatu ya san idan ya ya gyara gidan, ya ajiye musu abinci buhu_buhu gallazawar da takewa marayun ba fasawa zataiba HAKAN kawai shine mafita, ALLAH yaba wa Alhaji tallafy hangen nesa da samu mafuta a irin hayayensa ma su kyau je ne ma da hangen nesan sa ya assasa tallafy Charity foundation, shi ne solution d'in sa na tallafawa al uma, da kuma bi gidajen marayu, da ma'kota da dangi Duk wad'anda ba su da rufin asiri yana tallafa musu da jikin sa da kud'in sa. Hajiya Aisha da Alhaji tallafy sun ga amfanin zuwan su tallafy foundation da su AKEELA da AQEEL, sabida an sa mu ci gaba ba KA'DAN ba, idan Suna tare musamman AQEEL da AKEEL Suna jiyo hirar su, har da Y'ar dariyar AQEEL d'in, Amma ba kamar AKEEL ba sai Alhamdulillahi da da Ba'a samu HAKAN ba kuma fa, Bangaren AKEELA ma HAKAN Suna had'uwa da y'an uwanta ita ma ayi hirar da ita, Hajiya Aisha d'in ma Suna Hira da ita, 'Nikam AKEELA Anya ba 'kawance kike so ku kulla da twins d'in nan ba? kiyi ta zancen su, in mun zauna! Cewar Hajiya Aisha fuska d'auke da murmushi, tana sha fa kan AKEELA da ke kan cinyar ta! "Habadai Ummu na gor me su fa, waje 'kawance?kawai dai burge ni suke, ai shinenan dan zan gani ne idan ba 'kawancen ake son 'kullawa ba, ai shi abo ta ba sai sa'an ka ba in ji Hajiya Aisha tana murmushi,ita dai AKEELA ba ta kuma magaba ba. Ita ma Hajiya Aisha shirun tayi tun da ta ga Mai zancen ta gaji kuma. AKEEL ma hakane zancen AKEEL su Hadiyyah da Hidayah, shi ya kewa AQEEL indai sun zauna, sai kuma zancen abun da ya sha fe su, sai kuma wata Ra na a tattauna matsalolin da aka fuskanta a Baya, Amma fa AQEEL ne me zancen, dan idan AKEEL ne ta taddi zancen Ranar kam babu lafiya dan ciwon sa sai ta kusa ta shi, Amma idan shine ya ta do zancen da sau'ki saidai idon sa yayi ja yana ajiyar zuciya...... 😭😭😭😭ALLAH ya gafartamawa zainab da iyalanta gaba d'aya Yasa aljannah makomarsu ALLAH ya kar'bi shahadarsu baki d'aya ya dad'a bawa mijinta haquri da juriya dan kuwa yayi Haqurin, da y'an uwanta baki daya🙏🙏🙏🙏🙏 In Sha ALLAH FANS next page 31 zamu kammala hidimar Auren zahra da kuma zancen Sa'adatu, Duk aciki da abun da Ba'a rasaba,page 32 ku wa in Sha ALLAH xamu ji ya rayuwar su AKEEL AKEELA da AQEEL takasance a Baya shin me yake damun su ne Duk da CIKIN kwanciyar hankalin da suke nasan wannan lokacin kuke ta jira to yazo Muje zuwa dai..... ✍️Oum ARQAM ce ontop I love you All FANS🥰🥰🥰🥰🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE THIRTY ONE 31* Abun na yine fa! an saci d'an barawo babu Zama, tsakanin Alhaji Gambo da Sa'adatu fa sai wani d'inkewa akeyi, Baya sa ti yake zuwa gidan, a kufi a kufi sai ya zo,tun ya ran ba su ga no ba kin zaren ba har suka ga no cewa lallai fa Akwai wata a 'kasa tsakanin Auntyn su da Alhaji Gambo Abokin Abbyn su. Abun ka da ba Yara ba an tsayar da Ranar d'aurin Aure dai_dai da Ranar d'aurin Auren Zahra, lallai ne Amarya Y'ar lallai Sa'adatu za'a amarce da angonta ra na d'aya da Y'ar ta lallai abun na yi ne uwa Amarya Y'a Amarya ALLAH yakaimu lokacin. Munafikin! Wato Alhaji gambo ko ma tan sa bai gayawa zancen ba zai 'kara Aure ba ma! sai da magana ta fasu a gari suke jin zancen, Tsakanin Hajiya suwaiba da Hajiya sahura sai habaici wa Hajiya ikilima suke mata da dariya, bawai basajin kishin bane wannan sun barwa zuciyarsu,Amma Amintar Hajiya ikilima D'IN da sa'adatu suke hange, Saboda tsabar Amince ko kulasu batayi in tazo gidan, an dinga dariya da shewa kenan, Duk da ba part d'insu d'aya ba sai tabi Duk hanyar da sa'adatu zata had'u da d'aya daga cikin su sai tayi ko ta aika Y'ar Aiki da habaici wa d'aya daga cikin su. Kowacce Y'ar masifa ce Hajiya sahura da Hajiya suwaiba sun yiwa Alhaji Gambo bala'i kala_kala Amma Duk da haka yace Auren Sa'adatu Babu fashi!babu gudu babu ja da baya! Sun bi malaman da suka saba Amma shiru kakeji Akan fasuwar Auren, Amma ina!sun ba shi ya ci! sun ba shi ya sha! sun zuwa Masa ya ta ka!Amma ina Auren Sa'adatu dai yananan, iDan Allah dan ya sakawa mutane daya wa ne yasa Sa'adatu shigowa cikin su ne oho😇 Bangaren uwar gayya kuwa Hajiya ikilima 'kawa kuma Aminiya ga Sa'adatu Duk abunda kishiyoyinta sukeyi ta na Jin su ta na ganinsu, ta sa Audiga ta to she kunnuwanta, Taji labarin Auren Sa'adatu ga mijinta Amma har yau batayi ma sa zancen ba yadda bai gaya mata ba I tama bata nuna ta sani ba, sun taci a HAKAN, Amma fa can 'kasan zuciyarta kam ALLAH ne yasan me take 'boyewa! Sai harkokinta takeyi ta toshe kunnanta ga maganganun sauran Aminansu da kishiyoyinta da suke mata na Auren Sa'adatu d'in. Hajiya ikilima fa Hmmm! Sanin halinta sai Allah Allah ne yasan meta kullata Akan Sa'adatu. Amarsu Sa'adatu ko ajikinta cin Amanar da tayiwa Hajiya ikilima, ta sha fe a cinya, harkokin gabanta ta keyi, sai shirye shirye takeyi hankalin kwance, koda yake mene aciki Duk amincinsu da Hauwa facalarta matar 'kanin mijinta haka ta Aure mata miji balle Aminiya matar abokin miji. 'Bangaren Gi dansu Ibrahim bala Mijin Zahra ma sai shirye shiryen biki ake, abun ka da d'an ga ta akwatuna dozen y'an uwansa suka had'a Masa abunka ga Auta! sai tausayawa Zahra suke na halin maraicin ta,Hajiya Maimuna surukarta kam ta na son Zahra, tun da d'an autanta ya nuna yana sonta ita ma take sonta, kishin da ta Fara da ita Duk ta sauke shi da Zahra d'in, farko ma ita Allah haka ya halicceta da kishin Amma yanzu kam ta daina Akanta, Lallai Zahra Allah ya taimakeki ya dubi maraicin ki allah yakaimu lokacin lafiya, Ibrahim bala ya kammala gidansa Mai kyau da tsari sama da 'kasa ne Mai shegen kyau sai Wanda ya gani, ku hango gidan d'an autan masu kud'i Wanda yayyansa Duk matane zaiyi aure Kum suma Duk ma su kud'in suke Aure, Zahra Allah ya lad'd'afa miki saura su Hadiyyah da Hidayah d'ina suma.. Ankawo lefen ma sha allah y'an uwa da abokan arzi'ki sai zuwa gani akeyi Duk da ba abun mamaki bane! Badanan allah ya d'auke musu uba Mai share kukan su ba ai da abun sai yafi haka, Su Hadiyyah da Hidayah da Khadeeja y'an ma ta sai shirye shiryen biki suke anata murna ankawo lefen yaya Zahra,Amarya Zahra sai gyaran jiki ake na Aure sai 'kamshi ake ana wal'kiya. Duk Wannan Hidimar da ake ba bu Zakiyyah aciki domin ta kanta takeyi, ta rame ta 'kwanjale abun gwanin ban tausayi,ga yunwa na cinta tana raraketa, Amma su y'an uwan sun ramewar yana da nasaba da Rashin kulata da sukeyi, da kuma ra shin ko shi da batayi, dan y'an uwan su na bata Abinci yanzu tun gatan cutar da tayi ta kwanakin baya, Wayyo olsa ta kama Zakiyyah iDan ta ci abincin ma baya mata magani, kamar ta sawa kan ta wuta ha ka takeji, shiyasa ma bata cin abincin in ambata, har y'an kud'i suke ba ta, sunyi tunanin da kud'in take cin Abinci tunda sun ga Tana Aiken Farouk. Zakiyyah fa sai a hankali babu lafiya, sai Kuka take tana tunanin Mukhtar Anya ba alhakin sa bane, da na ABIE ita kam ALLAH yakawo Mukhtar gidan nan za'a yita ta Kare. Ko da aka kawo lefe Sati uku aka saka, kawu isma'il yace ai babu damuwa Duk abinda ALLAH ya hore Masa Wanda akewa yarinya iDan za'ayi aurenta,zan mata Amma fa babu bidi'a, Lallai kam kuji fa sai kace kud'in sa Ya ra da kud'insu Amma zai fad'i WANI zance, Duk WANI Abu da ake bu'kata na kayan d'aki, kamar yadda Alhaji Ammar bn Yassir yaiwa Zakiyyah guda biyu d'aya y'an waje d'aya y'an Gida Nigeria haka kawu isma'il ya saiwa Zahra,da sauran kayan da uba yakewa Y'ar sa wannan acikin kud'in da ake juya musu yayi ma ta Hidima,su kujeru, labulaye zannuwan ga do, da dai kayan da uba yakewa Y'ar sa idan zai aurarta, Sai da akazo ba tun kayan kitchen kuka kawu isma'il yazo da wata maganar banza! Karku man ta fa gidan su Zahra Wanda suka ci ga do kawu isma'il Yasa musu haya a ciki,kuma yace ALLAH yakaimu Auren yaran sai Ayi musu wahalar da uwa takewa y'ay'anta dasu, ga Ranar ta zo! Acikin shekara biyar da rasuwar Ummuh Ruman,kuma tun sannan bayan kammala ginin gidan aka saka y'an haya, da akayi ma sa zancen, yabada kud'in zataje siyayyar kayan kitchen sai ya ce ai shi yanzu gaba d'aya kud'in hayar da yake hannunsa gaba d'aya dubu d'ari biyu ne, Lallai kam acikin shekara biyar fa gida kamar irin nasu Zahra d'in Wanda suke zama acikinsa fa ace a cikin shekara biyar dubu d'ari biyu aka Tara , sabon gida ginin ma su kud'i Ayi wannan zaluncin. Haka babu wanda yace Masa komai kowa ta ciki ja ciki ta baka na baka, aka rabu da kawu isma'il,yabada kud'in haka sai y'an uwan Sa mata da su Baaba da kud'in da su Hadiyyah da Hidayah su ke tarawa aka harhad'a akaje akayo kata tsince tsince, abun babu ya bo babu fallasa, su flasks da y'an abubuwan da Ba'a rasa ba aka siyo, ba'aje bangaren Television da su fridge da sauran kayan 'kale 'kale ba, ALLAH sarki Zahra tayi ku ka da tuna irin shagalin da akayi a bikin Zakiyyah da irin kud'in da Abbynsu ya kashe, sai Kuka sukeyi ba ita kad'ai ba, ALLAH ya saka muku dai y'an marayun ALLAH. Ranar Suna ta kukan ba bu dad'i Alhaji gambo yazo kuma yayi alqawarin saiwa Zahra tv da fridge, ALLAH yasa gaskene kar amarya Sa'adatu amaryarsa ta hana shi kunsan halinta. Haka dai wannan Biki yake ta qaratowa anata shirye shirye DUK da sai a hankali. Itama Sa'adatu tana nata Shirin, Mutanen Kaduna state su Hajiya Baaba da Hunaif da Zeenah anzo yarinya tayi 'bul'bul abunta babu takura babu hantara, kuma tana zuwa school. Da ragowar kayan sawar Hidayah suka tawo kamar yadda Baaba tai mata alqawari,da kuma y'an kayan kitchen Wanda Baaba ta tanada matsayinta na kaaka kuma mahaifiyar yaran bata raye,DUK bidirin da akayi da kawu Isma'il su Zahra sun gaya mata tace su barshi da Allah bubu komai Yau ina iyayensu. Biki budiri bire d'e!! Haka fa lokaci yazo na bikin Zahra da Angonta Ibrahim an sha shagali kamar baabu gobe ranar Dinner haka na hango y'an Rashin IYAYE fans group sunata cashewa irinsu Seerat qawar Zakiyyah da Haseena Habiebty ma naganta kowanne ya sha anko abunsa nikam ina waien su y'an biyu kunsan ni da su akwai amana Allah dai yabiya Hadiyyah da Hidayah kai kwace sune amaren sun yi kyau sosai wal'kiya sukeyi ha ka akace aka sha aka gwangwaje Abun Ba'a magana Y'an uwan ango Ibrahim sun yi 'barin kud'i Ba'a magana sai nan nan suke da Amarya kamar itace Y'ar su ba angonba, itama Hajiya Maimuna surukarta itama taje wajen Dinner din sai jawo Zahra jikinta takeyi Abun sha'awa sai Wanda yagani. Ranar d'aurin Auren ma ba'a magana dubban jama'a suka shaida d'aurin Auren Zahra Ammar bn Yasir da Angonta Ibrahim bala kan sadaki duba d'ari lakadan ba ajalan ba, kud'i yazo FANS sai su qara siyan abunda ba'a siya ba na kitchen d'in. Hakama aka d'aura auren Sa'adatu da Alhaji gambo Allah yabada zaman lafiya. Bayan d'aura aure sai maza ne suke shigowa ana gaisawa ana pics da angwaye, Allah sarki Zakiyyah DUK wanda yaganta ya san ba tada LAFIYA sai tambaya ake sai tace Ea,itama babu laifi tayi kwalliyarta, a masu shigowa idon Zakiyyah ya qallo mata mukhtar dayake gaisawa da mutane uw una da sa'adatu Yana Allah yasanta alkhair da kuma Baaba, Wanda hannunsa yake ri'ke da hannun ABIE Abun gwanin sha'awa yaro yayi 'bul'bul dashi shigarsa iri d'aya da ta babansa ya ro d'an shekara Hud'u Amma yayi girma kamar d'an shekara shida ko bakwai, lallai yayo jikin uwarsa Zakiyyah, da sauri Zakiyyah ta tumfaro mukhtar Wanda take ganin yagama gaisawa da mutane yana Shirin ficewa............. Muje zuwa FANS me kuke tunanin Zakiyyah xatayiwa mukhtar? A next page zakuji da biography d'in su Alhaji tallafy da iyalansa Yanzu aka Fara wasan da tafiyar CIKIN Wannan labarin Mai tausayi cin amana da sauransu ✍️Oum ARQAM ce ontop 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE THIRTY TWO 32* Shi dai mukhtar ya jiyo domin fita,sai ga Mace ta nufo Alamu sun nu na cewa wajensa zata zo,shi ya sa ya daka ta da fitar da ya ke shirin yi Amma kuma ya saki hannun ABIE, yana ma maki ita kuma wannan data ta wo gareshi wacece? A fusge ya ga kama da ƴan uwan su Hadiyyah ɗin,because duk in da ka ga ƴaƴan Alhaji Ammar BN Yasir dana ƴan uwan sa gaskia duk suna ka ma sai dai wani yafi wa ni kyau,musammam twin's du Hadiyyah da Hidayah su kyau na su da ban yake. Har ga Allah mukhtar bai ga ne Zakiyyah ba,kunsan dai ta yi ra ma yanzu ha ka ma ba tada lafiya,yaushe ra bon yaganta ma!tun ta na gidansa da jikinta da lafiyarta, ABIE ne yadawo da Mukhtar da ga Diniyar tunanin da ya lula,in da ya ji ihunsa yana "Abba ka ga Ummunah! Yana ƙarasawa ga Zakiyyah wacce itama ta ƙaraso kuma ta sa gwiwoyinta a ƙasa, ta na jiran ABIE ya ƙarasa ta rungume ɗanta ko ta ji sanyin Abinda ya ke damunta a cikin zuciyarta na ciwo da raɗaɗi, ko za ta samu sassauci a zuciyar! ABIE ya na ƙarasawa gareta yayi dai_dai da sanya gwiwarta a ƙasa, aikuwa cikin ƙirgin mahaifiyarsa ya shige yayi luf abinsa. Allah sarki ɗa da uwa kenan, duk daɗin da Bilkisu ta ke jiyar da shi baisa ya manta da mahaifiyarsa ba, duk tsananin ramar ta yagane uwa tasa tsaf! Yai luf dashi a ƙirjinta, yana wasu ƴan maganganu na nu na alamun ya yi kewarta duk da Hausar ta sa sai a Hankali. Mukhtar ya Sha mamakin jin cewa wannan Zakiyyah matarsa ce, tun da dai ABIE ga shi ya ganeta, ya shi ya ka sa ganeta ne? Nikam nace may be saboda wahalar dashi da tayi ne lokacin zamansu🤭 Kukan da Zakiyyah takeyi, da ABIE rungume a ƙirjinta, shine ya fi komai ba shi mamaki, sai kuma ra mar data yi, ABIE nai mata surutu ita ta na aikin share hawaye,Nikam nace Allah ya so ƴan ɗaurin Aure sun ƙarasa ficewa, da abun kunya ya ishi ƙawar seeerat,ace taga mijinta ta na kukan ya mayarta,har da Sharri ma an daɗa kunsan mutane dai a Hankali. ABIE ya fi to da ga ƙirjin Zakiyyah Zakiyyah zuwa wajen Abbansa, "Abbana ga Ummunah tajo cai mu fafi jijanmu da ita fo?(Abbana ga Ummunah tazo sai mu tafi gidanmu da ita ko?🤣 Haka ABIE yane faɗa) Ya ƙarasa ga Abban na sa ya riƙo hannun sa alamun, ya tawo su tafin. Kamar mukhtar jiran ABIE ya zo wajensa ya ke, Ya na ƙarasawa kuwa ya ɗauke Ɗansa ya saɓashi a kafaɗar, yai fice warsa daga gidan, ya bar Zakiyyah da ke durƙushe kan gwiwoyinta, tana Sha re ƙwalla idon ta a rufe. Ta na buɗewa kuwa ta ga Ba bu ABIE Babu ba bansa, kamar Allah bai haliccesu a wajen ba,Ba tayi mamaki ba , domin kuwa ta san wanene mukhtar akwaishi da haƙuri Amma kuma bai iya fu shi ba, ta san fiye da ha ka ma mukhtar zai mata, wani ku ka ne ya zo ma ta, ta yi jarumtar shanye shi,ta miƙe tsaye, jiri ya na kwasarta ta nufi in da ta fito, Allah ne yakaita ɗakin na su,Kuma Allah ya rufa ma ta asiri ba bu wanda ya Kula da ita, kwanciya ta yi , zuciyarta ta na ƙuna,Baaba ce a ɗakin kawai, ta ta ga ta kwanta ta yi tunanin, angama hotunan da akeyi da angwayene, tun da ta ga dai shigowarsu je ya sa Zakiyyah fita da ga ɗakin, lallai Baaba bakisan me ya fitar da Zakiyyah waje ba, ko kallon angwaye batayi ba, da suke wajen driving su na hotunan su, mukhtar ne ya fitar da ita sai kuma ga yadda su ka kwa she da shi mukhtar ɗin ko kallon ta baiyi ba, bai ma san da halittar ta q wajen ba. Baaba bata ku ma bi takanta ba,ta shiga sabgarta,dama gama gaisawa da su mukhtar ɗin ne yasa ta shigo ɗakin ɗaukar wani Abu,kuma ta ɗauka ta fice ta bar Zakiyyah da jiyyar zuciya da rai waɗanda suke mata ciwo, Allah sarki ƙawar seeerat da Haseena kuzo lallashi...... Ko da Mukhtar ya fi ta da ABIE da yake ku ka, lal la shinsa ya fara amma ya ƙiyin shiru, sai "Abbana Guyin Ummunah ja ni ta jo mu fafi jijanmu (Abbana gurin Ummunah zani, tazo mutafi gidanmu🤣) A haka suka ƙarasa driving ɗin gidan in da su Zahra Amarya ana ta Shan pics, wayyo sun yi kyau abunsu, musamman twin's ɗin mu, Abban ABIE kuka yakeyi? Inji Hadiyyah ta na kallon ABIE ɗin,fuska mukhtar ya saka sannan ya ce,Wai ku ka yake ya ga Mamansa, Hadiyyah tace "o kayi haƙuri ABIE unguwa za ku zai da wo da kai ka ji , ta ƙarasa maganar ta na Sha fa kan ABIE ɗin, Allah ya tai maka kuma ya yi shiru ɗin, saboda shi kam indai unguwa ne ina da ta fiya ne, Nan ta karɓeshi akaita pic's ɗin,shi ma mukhtar ɗin ya shi ga, ɗan Diniya kamar ba bu abunda ya faru a cikin gidan, kamar ra buwar mutunci su kayi da Zakiyyah ɗin yanzu. Allah sarki zeenah, ta ga Abbansu tai ta murna, shi ma mukhtar ya yi murna sosai,sai da zuciyar sa ta sosu, daya tu na da yadda Zakiyyah ta raba shi da ƴarsa zeenah, ya na sonta Amma ya ya iya da Zakiyyah masi fa, matsayin da yake ɗaukar zeenah kenan ƴar sa,baya ga ninta a ƙanwar ma tar sa, ta ɗauke ABIE ta na ma sa wa sa, shi ma ku ma bai man ta da ita ba sai yaya jeenah take Kira ya dariyar farin ciki(yaya zeenah). Nan aka Sha hotuna, ma su kyau, kafin mukhtar ya karɓi ABIE yai fice warsa da shi, kamar zeenah za tayi ku ka, Anan mukhtar ma ya san yanzu zeenah ba ta gidan ma ga ba ɗaya,ta na kaduna wajen Baaba, anyi musanye, Hidayah ta da wo kano ɗin, ita kuma zeenah ta koma. ABIE ya san ya a mota ya ɗau han ya sai gida, zuciyarsa a tunkushe. Haka aka ga ma shagalin wannan biki,aka kai Amarya ɗakin mijinta sai muce Allah yabada zaman lafiya, ya kawo Mana da ƴan biyun mu mu ma. Wani abun mamaki kuma shine kayan kitchen na ga ni na faɗa Hajiya Maimuna da kanta a kuɗinta ta fitar Ba bu wanda ya sani ba yan gama jeren da su Baaba sukayi, ƴan uwan ibrahim suka ga Babu tsila ba bu arziƙi a kitchen Amma kayan gado ma Sha Allah to shine fa akayo wa Zahra oder kayan kitchen ɗin masu tsada, Allah sarki Zahra Tasamu uwar mijin arziƙi Allah ya tabbatar da alkhair. Gi da ba yayi kyau sosai ga tsari, haka ƴan kai Amarya suka dinga santin gidan, an Sha kuka Zahra za'a rabu da ƴan uwa Hadiyyah da Hidayah da Khadija sai kuka yaya zahra an rabu sai fa tan zaman lafiya. Haka suka baro gidan, Zakiyyah bata kai Amarya ba tananan gida ta na jiyyar zuciya da rai da gangar jiki ga ba ɗaya, ana harkar jama'a Ba bu wan da ya bi takanta,kuma da ma ansan ba tada lafiya saboda ra mar da tayi sai sannu a ke ma ta,anganta a kwance, haka aka fece gidan Amarya aka bar ta ƙwallin ƙwal sai ɗaya amaryar wato Sa'adatu🤣 Ita tarewa ba yanzu ba, nan gidan Alhaji gambo zai dinga biyo ta duk ranar girkinta ,lallai ne Hajiya Sa'adatu so kike ki kwace wa Hajiya ikilima dasu Hajiya sahura da Hajiya suwaiba miji kenan ko? Muje zuwa ya zaman zai kasance..... ************** Ka tin gayyatar bikin Zahra har wajen Alhaji tallafy, Alhaji Bala mahaifin ibrahim Angon Zahra, abokin Alhaji tallafy ne lokacin ya na raye, dan haka ka ti har gidan su AKEEL, sai dai kash Alhaji tallafy lokacin ba ya ƙasar bai samu halattar ɗaurin Auren ba, Ya ki ra shi yai ma sa Allah ya sanya alkhair bayan ya dawo daga tafiyar, washe ga rin ɗaurin Auren ya dawo. Ibrahim Mijin Zahra Abokin su AKEEL da AQEEL ne tun ta shin su suke ta re, sai bayan ƙaddarar da ta faɗa musu ne su ka bar ƙasar zuwa india ne abotar ta su ta sa mu rauni, da kuma rasuwar mahaifin ibrahim ɗin wato Alhaji Bala. Yanzu ma abun da ya sa su AKEEL basusan da zancen Auren ibrahim bala ɗin ba,wayyo na so sun zo ɗaurin Auren, AKEEL ya ga twin's ɗin da suke birgeshi, shi ma AQEEL ya ga twin's ɗin da Brother ɗin sa ya dame shi da zancen su tun ba yan zuwa foundation na mahaifinsu da sukayi. AKEEL ne ma'abocin Social media, shi kam AQEEL hakan bai da me shi ba, AKEEL yanzu ma ha ka a instagram yake shawagi, ya tsintsi pic's ɗin Auren Ibrahim bala, Ma maki AKEEL ya yi sosai, sai yanzu ya tu na da Ibarhim, may be shi ma ya manta da su ne da zai gayyacesu ɗaurin Auren, Pic's ɗin da yawa yayi savings, lokacin, AQEEL ya na bar ci ne. Ya na ta shi kuwa ya shiga nu na ma sa pic's ɗin su Hadiyyah da Hidayah,wanda su ka Sha kyau kamar ba bu gobe,komai na su iri ɗaya, kwalliyarsu ma ba bu banbanci, banbanci guda ɗaya ne, ɗaya ta na dariya ne akayi pic's ɗin, saɓanin ɗayar da ɗan murmushi kawai tayi, da kuma na Amarya da Ango, AQEEL ya yi mamakin kamar waɗannan twin's ɗin da ba'a ganesu kamar shi da ɗan uwansa AKEEL "Yau dai Allah ya sa na ga waɗannan twin's ɗin da bro kullum yake mun zancen su,kuma na shaida cewa lallai suna kama da juna kuma su na da kyau sosai" AQEEL ya ƙarasa maganar cike da ƙosawa da zancen, dan kuwa ai yayi magana mai tsayi anan, AKEEL sai murna yake Allah yafara dawo ma sa da ɗan uwan sa cikin nutsuwarsa, tun da sukayi Hira mai tsayi a haka. Nan dai suka dinga tunawa da ƙuruciyar su tare da ibrahim bala,wan da ga shi Allah ya kawo shi ya yi aure ma,duk da zai iya ba su shekara 2, duk dai tare suka ta so, "Muma bro yakamata fa mu samu mata muyi Auren nan, musamman ma kai da kake da matsala da shi, Nikam da sauƙi dai ba kamar kai jarabuna ba" Ya ƙarasa zancen yana dariya haɗe, da du kan Ka faɗar ɗan uwan na sa alamun tsokana, dan in yana son yaga surutun ɗan uwan sa yace ma sa "jarabuna" to anan zai ga kare kai kai da zubu zance, "Ni yaro ya sin Babu ruwa na, da ka sani ban da yanzu, kaima shaida ne" Shi kuma AKEEL yace "Ba waninan ai duk yadda halinka yake na sani, kallon ka nakeyi kawai. Suna wannan chapter suna kwa sar dariya da musun da su keyi. acikin babban flourn gidan, Alhaji tallafy ya shigo, Murmushin da yakeyi bai ɓuya. Fuskar sa ba, Sannu da shigowa sukai Masa, bayan tsagaitawa da Musun da sukeyi, ya amsa yana Hawa upstairs ya na jin daɗi a zuciyarsa. Nan ya iske Hajiya Aisha, acikin ɗakinta, tana waya da Hajiya Maimuna ta na mata ban gajiyar bikin da ta zo mata, bayan ta katse Kiran,Hajiya Aisha sosai su ke mutunci da Hajiya Maimuna,ku ma ga ta Matar Abokin mijinta, ta san ibrahim ɗin sosai, ya na zuwa gidan ka fin barin su AKEEL daga ƙasar, ko da bikin ibrahim yazo ta gayyaceta kuma ta amsa Kira, karku manta bikin Zahra fa Alhaji tallafy yake yagaya mata cikin murna Su AKEEL da AQEEL ne suke Hira sosai kuma naji daɗin hakan, Musamman AQEEL na ga yafara sakewa sosai, "dana barsu a flourn ba su ta shi ba kenan! Na ji daɗin hakan gareshi, kwana biyu ai ya sake suna Hira da ɗan uwan, in Sha Allah komai yakusa zuwa ƙarshe" Allah yasa hakan Ummu AKEEL cewar Alhaji tallafy yana shingiɗa akan tumtum da ke gefen gadon na ta domin hutawa................. Wayyo hannuna wanna page yayi tsayi bari mu tsaya anan 🤣 Muje zuwa next page aimun afwa tarihin su AKEEL nanan ta fe💃💃💃💃💃 Maybe a 33 pages ko 34, so nake na kammala babutuwan da suke gabanin hakan kafin mu tsunduma cikin tarihin su AKEEL ɗin, akwai sauran zance kafin zuwan tarihin nasu Yanzu aka Fara wasan da tafiya sosai acikin wanna labarin kafin yazo ƙarshe labarine mai tausayi cin amana da sauransu ✍️ Oum ARQAM ce ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE THIRTY THREE 33* An kammala biki lafiya sai fa tan zaman lafiya! Su Hajiya Baaba da su zeenah Hunaif duk sun koma kaduna state cikin Aminci. Amarya zahra anacan gidan ibrahim angonta ana shartar ƙauna Allah ya ɗorar. Itama Amarya Sa'adatu fa anata shirin ƙarbar miji, ku kwace auren fari zata yi Tsarin yadda gidan yake tun lokacin asalin mai gidan, wa to Alhaji Ammar BN Yasir, da kuma aurenta da Kawu isma'il wannan karon ma hakan tayi. Lallai ne anya kuwa Sa'adatu ta na da Hankali namiji na biyu kenan zata shiga da shi turakar mijinta na fari wanda aka shafa musu lalle Allah ya shirya, kam yasa wannan shine na ƙarshen shiga turakar. Su Hadiyyah da Hidayah tu ni suka Fara zuwa school da ma tun bayan registration ɗin da Alhaji tallafy yai musu, da duk wani abun da yakamata ai musu kafin Fara halattar university, kuma sun yi jamb da sauran su duk sun tsallake wani haɗari cikin ikon Allah, da tarun addu'oin da sukeyi, Kowacce course ɗin da ta cike shi ta samu, na community health ɗin, cikin ikon Allah sun Fara zuwa skyline university nigeria, kuma su na ɗaukar karatu sosai, kunsan twin's ɗin na mu gifted ne, ba'a banbance wa ce Hadiyyah ko Hidayah? Lallai ne da ga zuwan su fa Samari ƴaƴan ma su hannu da shuni suka Fara musu caaaa! A ka gaskia duk ciki Ba bu wanda suke kulawa,Karatu y kawosu shi kuma sukeyi, ba harkar Samari ba, suna son cikawa Abby burinsa da kuma Suma burinsu na zaka cikakkun Nurse a fannin lafiya. Tun bayan bi kin Zahra, Abokin Ango Mus'ab zubair Ƙaraye, Allah ya haɗasu da Hadiyyah kuma ya ji cewa ya na sonta ya zayyana Masa ƙudirinsa a gareta, ita dai ta ce Masa zata yi shawara ne, Amma ya karɓi number ɗin ta to tun bata ɗaukar wayar sa har ta Fara ɗauka suna ɗan taɓa Hira dashi sosai, har soyayya ana Sha . Professor Zubair bashir Ƙaraye hamshakin mai kuɗine wanda yake harkar Noma a garinsu ƙaraya da ke jihar kano, Amma kuma cikakken ɗan boko ne, wanda yanzu yana matakin professor, kuma ɗan Aƙida ne na boko na bugawa a mujallah, to shine Mahaifin Mus'ab zubair Ƙaraye wanda ake masa laƙabi da MZ Ƙaraye. Itama Hidayah kusan hakane ta samu na ta , Amma kunsan kalar zaren ba kalar ya din bane,ma'ana ita dai Hidayah ba ta bawa ma za fuskar tun ka rarta da wata magana ta soyayya, dan ko kai mata magana, ba zata kula ka ba, ko iskar da ta kwaso ka ba ta kalla, kayi ta ɓaɓatun ka abanza in ma Allah ya sa ta tsaya kenan, a bikin Zahra maza kala_kala sun ma ta magana Amma ina ba ta saurari ko ɗaya ba, Sai ɗan naci Mahmud kabir MK Shi ma dai ba kulashi ta yi ba ibrahim yaiwa magana a kanta, cewar shi fa ya na ciki, ibrahim ya ce sai ka shiga ciki kam, ga ta ga kanan wannan yarinyar sai a Hankali halinsu ya banbanta da ƴar uwarta tanan, ita ba ta da magana Amma zan baka number ɗin na ta(Kowacce ta sayi waya daidai misali da kuɗin albashinsu)Allah ya sa a dace ya ce Allahumma Ameen. Duk yawancin abokan Ibrahim bala ƴaƴan ma su kuɗine da sukayi karatu ta re, shima Mahmud kabir MK haka ɗane ga ENG Kabir Umar wanda shima ya na daga cikin waɗanda gomnati take bawa gwangila ta harkar hutar lantarki kuma ma Sha Allah yana da kuɗin sosai shi ma. Aikuwa kam MK haka yake damun Hidayah ta text ja safe da rana da daddare daban kuma duk na kalaman soyayya ne da yadda yake ƙaunarta tun ba ta kulawa har ta Fara dubawa, kuma cikin ikon Allah tafara Masa reply, yai mata sako ta wattsApp Nan dai suka Saba abunsu anata ɗan soyayya Amma wani fannin MK sai haƙuri sha'anin Hidayah. madam Sa'adatu mata a gidan Alhaji gambo wacce kuma ita ce rufe ƙofar Alhaji ma'ana Mace ta huɗu, ta karɓi Alhaji a matsayin miji duk ra nar girkinta yana zu wa asha soyayya,su dai yara abunsu Ido Hadiyyah da Hidayah ba mazauna bane school tun safe sai wajen maghrib, su Khadija ne dai waɗanda suke Ss 2 yarinya an zama ƴan mata ita ma ba dai kyau ba Allah yai MATA shi, ga ta Babu ruwanta magana ba ta dame ta ba,sai kuma ƴaƴanta Farouk shi ma ya girma sa kon Khadija ne tsiransu wata huɗu, da Haydar tsaran zeenah, sai auta Hafsa tsaran Hunaif in baku mantaba. Ko da Hajiya ikilima ta ji ba tun ai Sa'adatu gidanta za ta janye Alhaji gambo bataji daɗi ba, tayi tunanin nan gidan zata zauna a shashe guda, "Amma kuma in kinsan wata bakisan wataba Sa'adatu! Mu zuba mu gani, ni dake, a tafin hannuna kike wallahi!muje zuwa yanzu aka Fara wasan! Cewar Hajiya ikilima Tana kai kawo acikin ɗakinta,bayan fitar Alhaji gambo na gaya mata cewa ai Sa'adatu a gidan zata zauna. Sauran ma Hajiya sahura da Hajiya suwaiba sunji maganar kamar saukar ma shi Amma kuma sunyi masifar sunyi bala'in ko a kwalar rigar mijin na su sai ma gori da yai musu da cewa suyi koyi da Hajiya babba (ikilima) wajen haƙuri,Nikam nace uhumm ta mai ciwon hakori......... ************** Ɓangaren Kawu isma'il kam sai san barka hannun jarin daya saka sai alhmdllh yake Kira dan ta shin farko ribar da ya samu ta ninka kuɗin da ya sa sai ɗaya da rabi, shiyasa wannan karon da ya tashi zuba kuɗin nasa sai ya saka da jarin da gundarin Ribar da ya samu, ya kuma narkawa ya tura musu, wannan karon babbar harka, ce ga Kawu isma'il har ya Fara lissafin filaye da gidajen da zai saya idan odar ta sauka, da irin motar da zai siya har yayi oder jiran riba kawai yake ya tura kuɗin ya karɓo motar, ƴaƴan sa ma tuni ya janza musu makaranta fiye da wacce suke zuwa a da, tun Hauwa ta na Masa nasiha yana ma ta faɗa har ta zuba ma sa Ido, akan wannan wadaƙa da ƙudin, kuɗin su wanene? Ko dai dukiyar marayuce? Ranar da tayi Masa wannan tambayar ne yace in dai takuma saka ma sa baki da magana akan abunda yakeyi a bakin aurenta, idan zakuma ta yi bismillah, ai kuwa tun daga sannan Hauwa sai Ido duk abunda mijinta zaiyi, Amma kuma tana Masa Addu'ar ɓacin ra na. Tun daga sannan cima da gayu da zauna a gidan Kawu isma'il ƴaƴansa dashi kansa sai wadaƙa suke su tsoma biyar su wanke goma, ya manta da ƴaƴan ɗan uwan sa marayun Allah, bikin Zahra kuna ga Fan's haka yace ha shi da kuɗi Amma yanzu ku diva? ya na saune zaman jiran oda, yana Hangoshi ya xama one in town, wannan motar da yayi oda ta na ran sa dan haka ma, ya je banki ya ciwo ba shin 30milions dan ya sayi motar da kuma ɗin ka sababbun suttura da sauran gyaran da zaiwa gidansa, da ma tuni ya siye gidan ku sa da shi da yake kango ne, zai faɗada gida na sa, duk maƙota su na kallonsa ga shi irin mutanen nan da Babu kyauta ko sadaƙa ne Kawu isma'il, maƙotan sa ba sa zaman arziƙi. 15milions yaje banki ya ciro ya ta wo da su gida, da ita sai cimma ginin gidan da sauya Masa fasali, ɗaya kuma 15milions ɗin ya turawa wanda yayi oder ta mota a gurinsa, a cikin babbar jaka, sai wani tunƙawo ya ke wai shi Jan wuya an zama Alhaji, ma'aikatan banki kuwa su ka loda ma sa kuɗi a butt sai gida. Duk wannan kuɗin da aka loda Masa a kan idon wani ɗan daba mai suna ROCI wanda da ma shi abunda yake ka wo shi banki kenan, ya saka Ido, akan masu haɗ_hada da shige da fice da kuɗaɗe ya na da uban gida SNAKE wato 🐍 hamshaƙin ɗan fa shi ne, duk abunda yake faruwa shi ROCI shine yake sanar wa da snake ɗin in dai akayi ca mama ana fitar ma sa da na sa kason,yau ya zo sai Allah ya ƙadddara Kawu isma'il yazo banking fitar da kuɗi, kuma yaga zunzurutun kuɗin daya fitar da su zuwa gidansa, dan haka ya hau machine ɗin sa shi ROCI ya biyo ba yan motar ka wu isma'il domin ya ga no gidansa, kuma ya sanarwa sa Snake uban gidansa.......... ************** Mu leƙa gidan Mukhtar fans, tun ba yan dawowar sa da ga ɗaurin Auren Zahra Bilkisu ta fahimci akwai abun da yake damunsa, kun san ita ku ma Bilkisu abun da ta tsana kenan,ganin mai gidanta a ha lin damuwa, ba ta tambayi me yake damun sa ba, ba wuriminta bane, huriminta shine ya fitar da shi da ga damuwar da ya kasance a ciki shine abu mafi mahimmanci a rayuwarta,sai kuma da ga baya idan ya gaya ma ta damuwar ta sa idan ta na da shawara ta bashi ko mafita ta gaya ma sa ta yadda zai fita da ga halin damuwar da yake ciki, wannan shine siffar Mace ta gari ƴan uwa a kullum muzamo masu kula da damuwar mazajenmu kamar Bilkisu, ya dai seeerat da Haseena Kunga dai Mace ta da ƙawar kuce me zatayi? Sai dai ta kuma ɓata ma sa rai, Da wannan da mar Bilkisu ta fitar da Mukhtar da ga damuwar da yake ciki, wanda mudai bamusan mene damuwar ba, Amma zamuso muji in zai gayawa mar atussaliha(sunan da Mukhtar yake kiran Bilkisu da shi kenan🤣aikuwa dai ta ci sunanta) Tun daga sannan ya Mance da wa ta Zakiyyah kamar da daya Mance da ita a ba bin rayuwarsa, sai silar zuwansa Auren Zahra yanzu kam yakuma mancewa🤣 ABIE dai ya na damun Mukhtar da Ummunah jani Abbana(Ummunah zani Abbana) sai kawai ya shareshi ya rabu da shi har ku ka yake akan hakan Amma mukhtar sai yace Masa Ea zan dawo maka da ita, to sai yayi shiru a haka yake rarrashinsa, bai taɓa ma sa zancen a gaban Bilkisu ba, ko da yake dai Matar so ce sai abunda tace ko da a gabanta ya faɗa, Yau ma dai mukhtar ya na dawowa daga Bilkisu har ABIE su ka tawo yi Masa Sannu da zuwa tun da ga bakin gate,ya fito da ga motarsa ABIE sai murna Abban sa ya dawo,kafin Husna, ƙanwar Bilkisu ce ta zo gidan Hajiya jamila shine fa ta biyo mukhtar ɗin da yaje su gaisa da Hajiya ɗin, budurwace ma Sha Allah tana da ɗan jiki dai dai misali, ta fito da ga motar ta juya baya zata rufe ƙofar motar, ABIE ya hangota, da sauri ya buɗe baki ya ce " Abbana Ummunah ce ta dawo ko? Ranar nan ai munje mun ganta,ku ma kace jaka dawo min da ita, yanzu cine ka aukota Abbana? Yana nuna bayan Husna mai rufe mota, a kunnen Bilkisu ABIE yai wannan maganar, Kafin Mukhtar yabawa ABIE amsa har Husan ta ƙaraso wajen, kuma ABIE sai ya kama ku ka ganin ba Ummunsa bace,Yaya Husna ya santa farin sani sosai ABIE dan tana zuwa gidan ku ma idan yaje gidan Hajiya jamila ya na ganinta, kuma itama Bilkisu tana zuwa da shi gidansu. Ba sai ABIE yakama burgima da kukan ba Ummunsa aka da wo ka sa da itaba, Mukhtar ya na aikin lallashin ABIE wanda yake aikin ku ka, da burgima a ƙasa. Bilkisu ta ja hannun Husna ƙanwarta suka shige cikin gida fuskarta Babu ya bo ba bu fallasa, jikinta a sanyaye, Inaga Bilkisu ta zata mukhtar ɗaukar ABIE ya ke suke zuwa bikon Zakiyyah,idan zasu makaranta ko zai ɗaukoshi, ko kuma in suka fita da yake ya na ƴar fita da ABIE ya sanyashi a gaban mota..... Lallai kam ya zata ƙarke da Kawu isma'il ga shi dai Rico ya bishi, ku sanya shi a Addu'a Allah ya tsare Masa dukiyarsa 🤣 Ga Bilkisu kuma ta ji abunda ABIE yake faɗa har ta yi fushi, ga ta kuma ƴar gaban goshi, ya kuke tunanin zata kasance, kunsan dai mar'atussaliha ce ga mukhtar bay son ɓata mata rai😇 Su Hadiyyah da Hidayah kuma buri ya cika ga shi kuma an tsunduma a kogin lobayya 🥰 Lallai akwai cakwakiya nan gaba,🤣😇 Labarine mai tausayi cin amana da tsantsar maraicida sauransu akwai.......... Kubiyo ✍️ Oum ARQAM a Hankali domin warware muku cwakwakiyar da komai ma......... 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *____________* *PAGE THIRTY FOUR 34* Tun bayan kammala bikin Zahra da akayi, Zakiyyah kam takama wani tari mai wuya, wanda idan ta Fara kamar numfashinta zai bar gangar jikinta,irin dai masu asma sauƙin tarin shine tayi amai, anan zata samu sala ma farkon tarin kenan, lokacin kuma ba bu mai bi takanta, su Hadiyyah da Hidayah suna school, sauran yaran ma hakan,dai Sa'adatu ita kuma da ma na harkar juna suke shiga ba,Shiyasa ƴan uwan Basu san halin da take ciki ba ko ƙadan. A haka a haka fa tari ya Fara ga ba wa Zakiyyah, idan ta Fara ta rin kuma sai ta ga ɗan tsallin jini a inda tai tarin bakinta yana gurin,Duk wannan yabiyo bayan damuwar da ta sawa kanta ne,akan mukhtar tun da yazo bikin Zahra, ta ga a fuskarsa baima gane ta ba, kuma kamar bazai yafe mata kuskuren ta a gareshi ba, sai kuma uwa uba yunwa da take damunta , ga baƙin cikin Ƴan uwanta gaba ɗaya sun daina kulata, hatta Baaba ko da tazo bikinnan iskar da ta ɗaukota bata kallaba kamar ita ƴar ga ta ai abunnan sun mata yawa sosai, yarinya kamar Zakiyyah ƴar gatan uwa da uba, ga kaakarta Hajiya Sakinah datake a wajenta ƴar lele, ai Abubuwan nan sun mata yawa zuciyar ta bazata iya ɗauka ba,ire_iren tunanin datake a koda yaushe kenan,shine yake ta azzara ma ta komai. Yau ma ire_iren tunanin da ta durfa fa kenan, Duk da ta na yakicewa saboda azabar da take Sha idan tayi, Amma abun ya gagara gareta. Ƴan biyu Hadiyyah da Hidayah shigowarsu kenan da ga school sun ga ji tun safe, ɗakin nasu suka shigo Kowacce ta cire uniform ɗin, maghrib ta gabato ɗauro Alwala Kowaccen su ta yi domin gabatar da sallah, Hadiyyah ta Riga idar da Sallah, dan haka ta ƙarasa cikin ɗakin na su, a dai_dai lokacin da Tarin da Zakiyyah takeyi ya Fara nisa sosai, sai yi take ba bu ƙaƙƙautawa ga idonta ya ƙafe numfashinta kam ya jima da sassarƙewa like asma, Ihu Hadiyyah ta kurma ta na zuwa kan Zakiyyah ɗin ta na jijjigata! jinin da take Fitarwa ya fi na kullum, dan yau gashinan a bakinta sosai kamar ta kwurɓu kunu, Hakan ne ya ƙara tunzura ihun Hadiyyah! Ba Hidayah da ta sallame Sallah da ga falour ba hatta Sa'adatu, wacce ta ke shirya girki dan yau I tace da miji, sai da ihun ya girgizata batasan lokacin da ta fito da ga kitchen a kuje ba ta na nufar ɗakin su Hadiyyah ɗin,ko da ta shi ga ɗakin Hidayah har ita ta ƙarasa wajen ƴar uwarta ita ma kuma ta aza na ta ihun! Halin da Sa'adatu ta ga Zakiyyah aciki ita kan ta Duk ra shin imanin ta saida ta razana,sauran yaran ma su Khadija da Haydar da Farouk da kuma Auta Hafsa Suma ihun ya sa sun shigo ɗakin ga ba ɗaya Suma sai ihun yaka gidan ya zama kamar gidan makoki! Daga uwar har ƴaƴan ba bu wanda ya kawo tafiya asibiti, sai aukin kukan da jijjiga Zakiyyah da Hadiyyah da Hidayah da suke, wanda lokacin ita ma ta dakata da Tarin numfashinta ya tsaya tsak! Alamun ba bu Rai ta re da ita,Ihu ya ci uwar na da,kenan Hadiyyah da Hidayah kam sannan da suka ga ba bu numfashi a jikinta sai suka ajiye ta suka kuma da sa Ihu, itama Sa'adatu da ta taɓa Zakiyyah ta ga komai na ta ya saki kukan ta Fara Amma ba kamar na sauran yaran! Duk da Yanayin unguwace wacce ba lallai ajiyo abunda ke faruwa a maƙota ba, to ihun ya yi yawa sai da maƙotan suka jiyo, aikuwa suka Fara shigowa ana Zakiyyah ce ta rasu sai sallallami akeyi. A wannan halin ne mai gida Alhaji gambo ya danni hancin motarsa layin,tun da ga nan yafara cin karo da ƴan tsirarun motane har ya ƙaraso ƙofar gidan anan yaji cewa wai Zakiyyah ce ta rasu, ai ko ciki bai kai motar ba ya ƙarasa da ƙafar sa cikin gidan, har ɗakin da su Hadiyyah suke ɗin, yasamu sai ku ka suke Babu wanda ya rufe Zakiyyah da ake ikirarin ta rasu ɗin, aikuwa nan yafara baɗa dayaga bakinta akwai jini, nan aka ɗaukota aka Sanya a motar Alhaji gambo ɗin jikinta gaba ɗaya ya sake, da Hadiyyah da Hidayah aka ta fi waɗanda suke ku ka kamar ba bu gobe, ɗan uwa kenan, wanda komai yafaru tsakaninku idan wani abu ya sameka saiya ji Babu daɗi, Allah yaqara Mana zumunci a tsakaninmu da ƴan uwan mu🙏 Anbar Sa'adatu a gidan Akan idan suka je asibiti komai yake faruwa sai akira a sanar da ita, a haka mutanen da suka taro a gidan suka warwatse suka adduar samun sauƙi ko Allah ya jikan rai idan sa'i yazo, sauran yaran Sa'adatu ta Fara rarrasa Haydar da Hafsa dan sune yara Amma Khadija da Farouk ai Babu wannan sunsan komai, Amma har sannan hankalinsu a tashe ya ke. Ko da motar Alhaji gambo ta ƙarasa asibitin da sauri likitoci suka karɓeta aka Fara bata taimakon gaggawa, tabbas da ranta,Amma fa ta Sha wuya sai sannan hankalin su ya ɗan kwanta domin kuwa robar ƙarin numfashi aka saka mata sannan numfashinta ya daidaita, abun gwanin tausayi kamar ba Zakiyyah ƙawar seeerat da Haseena ba😢. Sai sannan Alhaji gambo ya Kira Sa'adatu yake gaya MATA, cewar ta tawo da Abubuwan buƙata ya gaya MATA sannan ya kashe wayar. Likita ne ya Kira Alhaji gambo office ɗin sa, anan yake Masa bayani kamar haka, me ya faru da wannan yarinyar a ƙarancin shekarunta da ba su gaza Ashirin da biyu zuwa da biyar da zuciyarta ta Fara kamuwa da ciwo haka Alhaji? Cewar doctor yana kallon Alhaji gambo! Sai da ƙirjin Alhaji gambo ya bada sauti daram! Jin tambayar da likita yai Masa, Alhaji gambo ba shi da masaniyar komai kunsani Fan's, dan haka ya ɗan nawa likita labari a taƙaice na Zakiyyah wanda ya sani,har fitowar ta da ga gidan miji, abunka ga likita nan yasan cewa tabbas ta Sanya damuwar rabuwarta da mijinta ne ko kuma ɗan ta da aka rabata da shi, nan dai likita ya gargaɗi Alhaji gambo Akan ai wa Zakiyyah abunda takesu idan ta biɗa bayar farfaɗowarta kodan zuciyar ta ta ƙarasa kamuwa da ciwon, sai kuma yunwa nan ma da likita ya faɗawa Alhaji gambo ta na damun Zakiyyah ɗin wanda itace ta sa mata tarin, da amai a farko,kafin zuciyar itama ta kawo na ta gudunmawar, nan dai likita ya nawa Alhaji gambo shawarwari Akan Zakiyyah ɗin, shi Alhaji gambo yayi zaton damuwar da Zakiyyah ta ke cikine yasanya ta kasa cin abinci, nan kuwa bai san sharrin Sa'adatu bane da Kuma ita Zakiyyah ɗin Rashin kunyarta ta janyo mata Hakan,da kuma Rashin jin magana. An bata gado a nan, su ƴan biyu da Alhaji gambo yai musu bayanin abunda likita ya ce sun yi kuka, na yunwar da take damunta sunsan wannan su ma da kamshonsu a ciki, Amma matsalar damuwa da zuciya kuma wannan basusan ko mene sila ba, dan kuwa sunsan dai su Zakiyyah bata damu da Mukhtar ba balle ABIE harkar gabanta takeyi har bayan dawowarta gidan na su, kodai daina kulatan da sukayi ne sila? Wayasani ƴan biyu ku bari ta tashi saiku tambayeta😄 komai da Zakiyyah take buƙata na taimakon gaggawa an mata kuma ma sha Allah dan kuwa ancire Robar ƙara numfashi Amma ba ta farkaba, numfashinta ya daidaita , har Sa'adatu ma tazo, ta tausaya wa Zakiyyah ɗin sosai, suna zaman jungum_jungum Zakiyyah ta Fara motsawa, rige_rigen zuwa wajenta sukayi, Sa'adatu ce ta Fara zuwa gaban gadon wanda Zakiyyah taketa juye_juye kamar bata hayyacinta ta na ƙokarin cire ƙarin Ruwan da yake hannunta, Hadiyyah da ma tuni ta Garzaya kiran likita, ai kuwa tare suka shigo dashi, ya zo dan ya ƙarawa Zakiyyah allurar barci ko Allah zai sa ta samu nutsuwa ta farka daidai, anmata allurar, wanda kafin tafara aiki je ne bakin Zakiyyah ya ke furta "Ka yafemun mukhtar Duk abunda nai maka! ka yafemun mukhtar! Ire_iren zancen da Zakiyyah ta ke furta wa kenan har allura ta yi aikinta. Daga Sa'adatu har Hadiyyah da Hidayah Duk mamaki ne a fuskarsu mene haɗin Zakiyyah da Mukhtar kuma?ita da takewa Rashin mutunci, bata damu da shi ba kuma, tabar su kam cikin duhu, sun bar haka a Zafin ciwo kawai ne, Shi da ma tuni Alhaji gambo ya bar asibitin. Bayan Zakiyyah tayi barci, litika yace Duk yadda ake ciki wannan mukhtar ɗin da take akbata, cutar ta ta na alaƙa da Shi, dan haka a nemo shi ko ta halin ƙa_ƙane a nemoshi kafin farkawarta ta biyo, inji likita ya na ficewa da ga ɗakin, yabar su baki sake, yanzu ta yaya za su nemo mukhtar? Suce Masa mene? Shawarar da sukeyi kenan a yanzu.... ************** Ko da Mukhtar ya ƙarasa cikin gidan da ABIE a hannunsa, lokacin har Bilkisu ta kai Husna ɗakin da zata zauna kafin ta tafi gida,ita kuma ta dawo falour ta na zaune abunta, ku sa da ita ya zauna da ABIE a hannunsa wanda har sannan yake ku ka, miƙa hannu ta yi ta ƙarbeshi, ta na lallashinsa,Akan yayi shiru, "Ammienah Ummunah Abbana yace je damomin da ica gaci hal yanju bata dawo ba" cikin kukan ABIE yake faɗawa Bilkisu ɗin,ita dai batayi magana ba Akan wata ummansa,aikin lallashi takeyi na ya yi shiru Amma ina yaƙi shiru, kishin ƴan matan ya ta shi kenan, ko da yake Bilkisu ba ta shiga abunda bai shafeta ba,yanzu kuma abunda ya shafi uba da ɗansa da uwar ɗansa shiyasa maybe ba ta shiga ba,tun ya na bore ABIE Akan Ummunsa har barci ya kashe shi ya na ajiyar zuciya,bayan ta kwantar shi a ɗakinsa tai ma sa shirin barci tai Masa addua ta fito da ga ɗakin domin zuwa na ta ɗakin. Ta samu mukhtar ya na lissafin kuɗi dan haka ita ma ta yi shirin barcin Duk da lokacin bai wuce tara na dare ba, yau da wuri yadawo ne. Bayan ya kammala lissafin kuɗin da yakeyi,ne ya fuskanci mar atussaliha ya ji me yake damunta tun da ya dawo ya ga kamar ta na da damuwa! Mar atussaliha me yake damun ki? tun da na shigo farko naga ba haka na shigo na ganki ba! Da walwala na sameki Amma tun Daga lokacin da ABIE yai zancen mahaifiyarsa na ga kin canza mun!? mukhtar ya ƙarasa maganar ya na tallafo ta zuwa jikinsa, alamun rarrashi! "Zaujin saleh abar maganar nan kawai, abunda ya shafi Maman ABIE ba bu ruwana aciki,kadaina sakani ciki, wannan tsakanin kune , Babu Ruwan Bilkisu a ciki! Ta ƙarasa maganar ta na janye jikinta da ga na sa, Ƙara riƙeta yayi a jikinsa sannan yai magana "Ki kwantar da hankalin ki mar atussaliha, ba bu abunda ya ke tsakani na da ita ni a yanzu, Rabuwarsu ta gabato ma, zancen ABIE kikaishi gefe kawai ki ajiye, Zancen ɗaurin Auren Zahra yake miki da mukaje, mu ka ganta, ku ma zancen na ce zan dawo da ita, tun zuwana Ɗaurin Auren yakemun zancen uwar shiyasa nace zan dawo Masa da ita' Mukhtar ya ƙarasa zancen cikin kwantar da murya alamun rarrashi. Bilkisu Dai da take jikinsa bata kuma magana ba ta lafe a jikinsa, ta na ajiyar zuciya alamun ran ta da zuciyar sun samu salama, batada wata fargaba kenan, a dai dai lokacin ne kuma............. Muje next page ƴan Amana danjin meke faruwa Ga dai Zakiyyah a gadon asibiti Ga kuma madam Bilkisu itama ta na wasu zantuka da sauran wasu batu su na ga ba...... ✍️ OUM ARQAM ce ontop😍 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE THIRTY FIVE 35* Ƴan team ɗin Zakiyyah fa su 🤣🤣.... Seeerat Mummy Waleed Aisha sulaiman Haseena Maman eyshat MamaGee... Wayyo ALLAH nah ni uwar ARQAM🤔🙆‍♀️🥹 nasha caccaka fa a PAGE 34 fa nida Habiebtieh yasin Duk kun haɗe kun koma team ɗin Zakiyyah Ita Bilkisu bata da team kenan🥹🤔🙆‍♀️ daga ni uwar ARQAM sai habiebtieh kawai lallai kam Babu gudu ba bu ja da baya koma dai menene Zakiyyah ita ta janyo wa kanta eye muje zuwa PAGE 35 ALLAH yasa bayan caccaka karmusha tsatstsaga kuma a wannan Page ɗin🤣🤣🤣🤣 *---------------* OGA Ea Duk wank bayanai Akan wannan mutumin na samu!har unguwarsu na bishi har sai da ya shiga cikin gidan sa sannan na jiyo! ROCI kenan yake sanar da uban gidansa SNAKE" cewa ai ya bi Kawu isma'il yanzu yasan komai a kansa, yanzu kawai ranar operation suke jira,kamar yadda suke kiran fashin na su dashi, yawwa mutumin ai nasan Babu wa sa cikin aikinka cewar snake bayan ya gimtse wayar, domin yanzu shida yaransa shirin tunkarar gidan Kawu isma'il ne a gabansu,domin gaskia kuɗin da suka ga ya cire a banki sunsan ba shi kaɗai gareshi ba, za'a samu fiye da hakama, shiyasa suka Fara shiri, oh ALLAH sarki Kawu isma'il ko yaushe waɗannan muyagun zasu zo gareshi, Nikam zan sanyashi cikin addu'a ta. Koda Kawu isma'il yaje gida da waɗannan kuɗin ya ajiyesu bigire ma kyau,kafin Fara Masa aikin gidan sa . Yaiwa Hauwa gargaɗi Akan sake shiga sabgarsa,Amma yana shigowa da kuɗin sai da taji wani abu ya soki zuciyarta! Wai shin mijinta me yakeso ya zamane? Waɗannan kuɗin kuma da ga ina suke? Amma ba bu komai za ta saka mai Ido gaskia,zataga zuwan da dawowar,kullum addua take Masa ta shiriya,idan ba bu ita kuma ALLAH ya tona ma sa asiri muddin da dukiyar marayu yake wannan wadaƙar?! ALLAH sarki Hauwa mutuniyar kirki zakiga sakayyah kam ga mijinki, in kuma dukiyarsa ce ALLAH zai iya jarrabarsa sanadin zaluntar marayun ALLAH, ƴaƴan yayansa,wanda ko ba bu kuɗi shi nai jiɓantar al amarinsu ne, Amma ina kwata_kwata ya Mance da rayuwar su ta tasa da ƴaƴana yakeyi, to dan ALLAH ta ina zaiga dai_dai a komai nasa ne!? Tashin Hankali wanda ba'a saka ma sa rana kenan! Dan kuwa dai da ƴan damfara ALLAH ya haɗa Kawu isma'il waɗanda ya turawa 15millions ɗinnan, yayi odar mota Babu su ba bu labarinsu,da ma hake sukeyi, sai su buɗe account da emails na wucin ga di wanda suke damfarar mutane daban_daban da shi, ire_iren su Kawu isma'il, saboda ba kowanne mai hankaline sai iya Hakan ba, na tausayawa Kawu isma'il sosai fa, Amma kuma sai na ga shima bai da mu ba, saboda ya sawa ransa cewa dan wannan ƴan kuɗin! Ai ALLAH yakusa kawo ma sa riba mai girma da tsoka wacce zata ninka ma sa fiye da waɗannan kuɗaɗen, shiyasa ba bu wanda ya gayawa ko Hauwa bata sani ba sai shi kaɗai. Sai wani bala'in kuma again! wanda shima dai kawu isma'il ɗin bai gayawa kowa ba,shine ya wayi gari da nemar Asusun Alhaji Abbas mai mallakar kamfani a Japan, wanda ya zuba zunzurutun kuɗi har 50million na marayun ALLAH ga shi yau alamu sun nuna wannan account ɗin ba'a amfani da shi kwata_kwata an gogeshi, sai sannan ya shiga binciken sa ya ga alamun ba bu wa su mutane ma su bibiyarsa in ba shiba, wanda a farko beyi wanan tunani da lissafin na sanin bayanai Akan Alhaji Abbas ɗin ba sai yanzu in da a bincikensa da yakeyi ne, ya samu haƙiƙanin gaskiyar zance na account ɗin Alhaji Abbas na gaske, gaskiya Duk wanda ya ga Kawu isma'il yanda ya shiga firgici abun zai baka tausayi, Amma kuma yayi kurum bai gayawa kowa ba,saboda mugun abu, ko tsoron ALLAH bai ji ba yanzu kenan ƴan marayu ba su da tsuntsi ba su da tarko kenan, in banda gidajen da Suka mallaka shikenan Amma ko ƙadan Basu da kuɗi wanda zasuce wannan kuɗin gadon sune,shin waima yace ina yakai kuɗaɗen ne? Ko zaice da su yaiwa Zahra wahalar aure ne? Ko kuma zaice da kuɗin yaiwa su ƴan biyu wahalar makaranta ne? ALLAH yasa biyar d'insa ba bu aciki muje dai zuwa fans. Gani kawu isma'il yake abun kamar a shirin film ko a novels dan haka ma ya ɗau hanya har lagos inda, reshen kamfanin sarrafa fata na Japan mallakin Alhaji Abbas ɗin domin ya shigar da ƙorafinsa, Amma ina ba shi da wata hujja cewa ai ya tura waɗannan zunzurutan kuɗin, can dai ya haɗu da ƴan damfara ne sun yashehi, Amma kam, su ko mai kama da shi ba su sani ba, sai da Kawu isma'il ya fa ɗi aka yayyafa ma sa ruwa, kafin yadawo cikin hayyacinsa, ana ta ba shi baki Akan ya fawwalawa ALLAH komai, Amma karya kuma wannan gangancin da yayi, in zai saka hannun jari ko zaiyi odar abu a irin wannan yanayin yafara zuzzurfan bincike a account ɗin yasan tabbas ana bibiyarsa kuma shine aininhin wanda ake oda ko saka hannun jari, sannan sai sunyi a rubuce da komai da komai kafin ya tura kuɗin sa. shi dai kawu isma'il jinsu kawai yakeyi Amma ba ya fuskantar komai,yana can tunanin yadda zasu ƙarke da Sa'adatu ne yasan wallahi bazata ƙaleshi Akan dukiyar ƴaƴanta ba,sanadin abunda ya gifta tsakaninsu,in ya cuci su Hadiyyah ya zauna lafiya yasin yasan ƙarya ne ya cuci Sa'adatu,yasan yanzu ma wannan shirun datayi Masa yanada,ma'anoni sosai , Sa'adatu da kuɗi ai kamar Annabi da kafiri ne.yana warwarewa ya na kwancewa ne yaga Hakan bazai fussheshiba dan haka ya samu hotel ya kama, dan tafiya gida yau bai kama shi ba wannan ta shin Hankali ai kowa ya na ganinsa zai san ba lafiya ba,gwanda ya ɗan samu nutsuwa kafin yakoma gida kanon dabo. Zuciyarsa ta yi Sanyi lokacin da abokan kasuwancinsa suka kirashi cewar oda fa ALLAH ya kawo ta,dan haka an lodo kayan daga china nan da gobe ko jibi in Sha ALLAH kaya zasu shigo 9ja sai fatan samun riba mai girma kamar yadda suke fata,shiyasa Duk wannan fargabar ta Kawu isma'il ta kau washe gari ya hawo jirgi dan dawowa gida. ************* Mukhtar wayarsa ya ji ta na ringing daga gefen sa, Bilkisu ta fi kusa da wayar dan haka ta ɗauko zata miƙa Masa,shi kuma ya ce wa ke kirana da Daren nan kuma haka? Bilkisu dubawa tayi ta ga ansa *Hadiyyah* nu na Masa ta yi, na gani, sai zuciyarsa ta shiga wasi_wasin yanzu kuma Hadiyyah da wannan Daren wajen goma ta kirashi a waya meya faru kuma? Kardai Zakiyyah ce ta ɗau wayar Hadiyyah ta kirashi,dan tasan In ta kirashi a wayarta bazai ɗauka ba, lallai tanan Zakiyyah ki ka biyo aikuwa bazan taɓa ɗagawa ba ehe! Zata tsinke fa zaujin saleh! Ka karba man! Bilkisu ta katsewa mukhtar tunanin daya lula ƴan sakanni! "Ke Mar atussaliha ƙaleni ba bu wata Hadiyyah da take kirana,illah Zakiyyah domin tabbas nasan itace zata Kirani, tasan in ta Kirani da number ɗin ta ba ɗagawa zanyi ba, ta ma daina wahalar da kanta a kaina, domin Nikam ta ficemun a raina, Duk wani mutunci da alfarma da zan mata tun yaushe ta rushewa kanta a wajena, ni ko son ganinta banayi ma! Mukhtar ya ƙarasa maganar da ƙaraji! Bilkisu ta ga abun na mijinta yafi ƙarfinta,ga shi ya barta da waya a hannu,harta katse,dawowa ku sa dashi tayi kafin ta fa ra magana cikin tausasa murya! " Haba zaujin saleh kamar ba Kaine mai haƙurin nan ba mai yafiya mai karɓar uzirba! Kayi haƙuri Mana,kamance ne har yanzu Zakiyyah ta na matsayin matarka ne bari na tuna maka, kuma ma bakasan ita tai kiranka ba ko ba ita bace, bakada tabbas Akan Hakan, ko ma ita tai kiranta ka ɗauka Mana kasan da me tazo haba zaujin saleh! Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin kwantacciyar murya alamun nuna rarrashi, tun da da ma tasan lagon mijinta, A sannan kuma kiran ya sake shigowa, wanda har sannan wayar na hannun Bilkisu ne, saurin miƙa Masa wayar tayi da alamun, rarrashi a fuskarta alamun ya ƙarbi wayar,beyi musu ba kuwa ya karɓa yayi picking,to yan team ɗin Zakiyyah yau dai ga Bilkisu tai muku ra na ko? Ba don ita ba da bai amsa wayar ba ALLAH sarki Bilkisu baiwar ALLAH mar atussaliha kamar yadda mijinta yake kiranta dashi. Ta ɗaya ɓangaren kam kiran farko da Hadiyyah taiwa mukhtar ta ga bai ɗaga ba, Hankalinta ya tashi sosai,ganin kowanne lokaci Zakiyyah na iya farkawa kuma akwai matsala idan bai amsa wayar ba,ta yi tunanin ya yi barci ne, wayyo ALLAH ,har ta haƙura da kiran sai dai kuma ta kuma Kira karo na biyu ko ALLAH zaisa inma barci yake ringing ya ta sheshi, tunda dai bata da tabbas ɗin in dai barci ba ya saka wayarsa a silent,cikin yanke tsammani ta kuma Kira karo na biyu wanda cikin ikon ALLAH ta ga mukhtar ya yi picking,hamdala tayi ga ALLAH,zata fara Masa magana cikin ku ka Sa'adatu tai MATA alama da ta daidaita Hankalinta,karta tayar Masa da Hankali da Daren nan haka. Dan haka bayan mukhtar ya ɗaga yayi sallama ne, Hadiyyah ta Fara koro ma sa bayanin Rashin lafiyar da Zakiyyah da abunda likita ya faɗa musu na cewa lalläi ta farka da Mukhtar da take ambatarsa yazama shine abu na farko da ta Fara tozali da shi, Duk cikin kukan da Hadiyyah take ƙokarin shanyewa Amma ina Saida ya fito a Hakan tai Masa bayani, ta na mai roƙonsa Akan ya yi Akan ya taimaka musu ya ƙaraso asibitin kar Zakiyyah ta sake farkawa a karo na biyu,da to mukhtar ya kashe wayar. Wanda yabar su ƴan biyu da Sa'adatu da mamakin Hakan! Anya kuwa zaizo? Zuciyarsu ta tsinke sa lamarin fa, sun san da ma ba abune mai sauƙi ba da Mukhtar zai zai sakko cikin sauƙi,la akari da yadda Zakiyyah ta dinga Masa Rashin mutunci da halaye marasa arziƙi, kuma sun san ya na da haƙuri Amma kuma bai iya fushi ba, dan haka su ka tsaya cikin jimamin ALLAH ya kawo mukhtar dai a wannan gaɓar Nima OUM ARQAM nace Allahumma Ameen ba tayasu da addu'a🙏 Bayan ka she wayar da Mukhtar ya yi zuciyarsa kam ta sosu jin Abubuwan da suke damun Zakiyyah ɗin, ya yi mamaki ita da batada kunya ko ƙadan, bata ganin mutunci da ko ƙadan, ta nuna ma ba ta damu da shi ba shine yanzu kuma zata wani dinga sambatu ta na ambatar sunansa! Ko dai Zafin ciwone dan kuwa shikam ya san Zakiyyah, Akan taurin kai da Rashin jin magana, Amma ko alama bai ga alamun zata saduda ba, Amma da ya tuno da zuwansa Auren Zahra ya daiga tabbas ta rame,kuma dai batayi mai magana ba, Amma kuma dai tayi hawaye,ga gwiwarta a ƙasa,ya yi tunanin kuma ganin ABIE Duk yasata Hakan,Amma ita da bata damu da ABIE ɗin ba? Ita dai ta sani! "Zaujin saleh ka ji fa abunda yake faruwa da maman ABIE, kuma na ga ka zauna ba ka da alamun tashi ka saka kaya ka tafi asibitin fa? Cewar Bilkisu tana dafa kafaɗar mukhtar ɗin! "Mar atussaliha ƙale wannan Ba tu me Zakiyyah zata gayan kuma ni mukhtar?mutuniyar da ta mayar da ni ba abakin komai ba! Yafiya ce da ta ne ma na yafe ma ta ALLAH ya yafe Mana ba ki ɗaya, bari na Kira Hadiyyah na gaya mata in ta farka ace Mana ni mukhtar na yafe mata ba dai shikenan ba! Inji mukhtar ya na shirin kwanciya da juyawa Bilkisu ba ya da wayar a hannunsa ya na shirin dannawa Hadiyyah waya ya faɗa MATA sakon da zai isarwa da Zakiyyah ɗin, Amma shikam ba ya ganin da abinda zai sa yaje asibitin nan. Fisge wayar Bilkisu ta yi daga hannun sa cikin alamun tayi fushi! "Kafin tace gaskya zaujin saleh idan kayi Hakan haka kyautawa Zakiyyah ba,kai baka yafiya ne? kamata yayi kamayar da Abubuwan da ta faru tsakanin ku da ita ya Zaki akasi Man, dan kuwa kowanne namiji da kaganshi da matarsa bakasan me take ma sa ba kuma haka yake haƙuri da ita, kamayar da Abubuwan da Zakiyyah tai maka baya ka yafe MATA sannan ka taso ni zan rakaka asibitin, zaujin saleh ka tuna alkhair ɗin iyayen Zakiyyah a gareka, kamar yadda kullum kake faɗa,sun so ka sun girmamaka, musamman kaakarta Hajiya Sakinah kaji zaujin saleh! Ta ƙarasa cikin kwantar da murya! Tabbas Duk abunda Bilkisu ki ka faɗa gaskia ne na sani, kuma na ya fe ma ta Duk Abubuwan da tayimun, ALLAH ya yafe ma na baki ɗaya, Yawwa zaujin saleh indai dagaske ka yafe matan ka tashi yanzu ka saka yakanka muje asibitin nan wajen ta, ta farka dakai a idonta ko zata samu sauƙi a zuciyarta kaji, lallai Bilkisu ALLAH yasaka miki da alkhair kinji tawajena. Haka Bilkisu Duk da kishi ya na cin zuciyarta na mijinta haka ta danne ta ƙarfafa gwiwar mijinta har ta taimaka Masa dakanta ya shirya, ita ma ta shirya suka fito domin tafiya asibitin wajen Zakiyyah, Amma fa zuciyar mukhtar baiso Hakan ba,sai ɗan Bilkisu ɗin da ta san yadda take shawo kan mijinta ta sarrafashi ta sakashi aikata abunda takeso cikin hikima da iya karantar mijinta, lallai Bilkisu kinci sunanki na mar atussaliha. Haka suka fito shi mukhtar ya fita dan ga fitar da mota, ita kuma Bilkisu ta tafi ɗakin ABIE ta ɗauke shi ta shiga ɗakin da taiwa Husna masauki ta ce mata ga ABIE Husna zamuje mudawone, to Aunty cewar Husna tana karbar ABIE da gyara Masa kwanciya, Amma dai lafiya ko ? Lafiya lau Husna kawai dai siyayyah zamuje,in zamu siyayyah sai ya dawo Muke fita,shikenan Aunty ALLAH yakaiku lafiya. Haka Bilkisu ta fice lokacin har mukhtar ya fitar da motar waje ya kulle gate ɗin ma, dan haka waje ta fice bayan ta kulle kofofin gidan saboda tsaro, Haka suka dau hanya zuwa asibitin da Zakiyyah take kwance, wanda dama Hadiyyah ta gaya Masa sunansa a wayar da sukayi da ita .............. Up Up Up Up Gaskia wannan Page ɗin yaymin daɗi Allah ya ƙare mun ke ƙawata Bilkisu ALLAH sarki Kawu isma'il yafara bani tausayi sosai fa zah tayashi d addu'a kuma please kutayashi Muje zuwa dai yanzu aka Fara wasan akwai cakwakiya tausayi cin Amana maraici da kuma zazzafar soyayya a gaba muje dai zuwa yan amana Nice dai ✍️ OUM ARQAM ontop😍 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE THIRTY SIX 36* Ƴan team ɗin Zakiyyah hardai yanzu Bilkisu bata burgekuba 🤔 😳😒 Mukam ƴan team ɗin Bilkisu ta burgemu 100% ba kowacce mace bace zatayi abunda kikayi🥰🤝😄 "Gaskiya jibo ban taɓa tunanin wannan Aikin da muka ɗauko zai gamu a waɗannan ƴan kwanakin ba, lallai isma'il, na daɗa tabbatawar wa da Bashida imani ko ƙadan, kuɗaɗen marayu zunzurutun kuɗin har 50millinon,shu shiga hannun ƴan damfara Amma kabar maganar hakanan, ba bu wanda ya sani, shikenan kaci bulus kenan, ALLAH nai maka godiya da waɗannan kuɗaɗen suka dawo hannuna ,da ace ƴan damfarar gaske ne suka karɓe kuɗin ai da shikenan! Shi dai jibo Duk da a wayane Alhajin yake Masa magana Amma akwai alamun rissinawa kamar ya na gabansa,kuma bai motsi ba sai da Alhaji yakai aya da zancen na sa sannan shi ma ya yi ajiyar zuciya! Yace' Ranka ya daɗe ai ni dai abun nan ya bani mamaki matuƙa, saboda yadda ba bu wani jayayyah ya turomin da kuɗin, bayan nagama shiga jikinsa sosai, Duk wani sirrinsa na sani, hatta 50million ɗin da ya turan sai da ya tabbatar min da ta marayu ƴaƴan yayansa ce,wai so yake ba da jimawa ba kuɗin na su yayi yawa, ƴaƴan nan ya na tausaya musu sosai,yanzu haka biyar baya ɗauka a kuɗin da yake juya musu, da kuɗin sa yake musu Kowacce wahala, kwanannan akayi bikin ɗaya daga cikinsu ma(Zahra) ya kashe kuɗi da yawa biyar bai ɗauka a cikin kuɗinba, yanzu haka akwai ƴan biyu(Hadiyyah da Hidayah) acikin ƴaƴan university suke zuwa pravet ce, shine ya ke biyan kuɗin, akwai ɗan sa saurayi(Alhaji) shima yanzu haka baya ƙasar, Duk dai yadda jibo sukayi da Kawu isma'il haka ya kwashe ya gayawa Alhaji tallafy, Alhaji tallafy kam dai jinjina kai yakeyi, bayan zalunci kuma harda ƙarya isma'il ya keyi, Nan dai Alhaji tallafy yaiwa jibo godiya Akan namijin ƙokarin da yayi, da jajircewa wajen Cika ma sa aiki cikin lokaci ƙanƙani, a lokacin da baiyi tsammani ba, Wannan Aikin da jibo yayi ya farantawa Alhaji tallafy Rai sosai, yo da ma jibo ɗan saurayine Just 28_30ne dan haka wannan ƙwazo da yayi Alhaji tallafy ya ɗauki nauyin karatunsa, har zuwa abunda ALLAH yayi, fannin shari'ah tun da kam yaga anan jibo zaiyi taimako sosai, ya yi godiya sosai, kamar zai ari ba ki, shi kam Alhaji sai murna yakeyi. JIBO dama yana da burin karatu Rashin kuɗi a hannu ne yai ma sa cikas, sai kuma ya koma ƴan buga_buga kafin ALLAH yai Masa luɗufi Yasamu aiki a tallafy foundation,shi kuma Alhaji tallafy da ya ga yaron yana da Hankali da ƙokari sosai,In Alhaji ya kawo ziyara cibiyarsa yazo cikin girmamawa ya gaishe shi, shine fa ya ɗauke shi ya mayar da shi can gidan sa inda yake rayuwa, yake kula da shige da ficen gidan, anan Alhaji ya gane yaron yana da basira, Shirin da yayi Akan Kawu isma'il idan yasa jibo akai zai aikata abunda akeso, sai kuwa ga shi cikin ƙanƙanin lokaci komai ya yi daidai, nan sukayi sallama a waya da Alhajin (Alhaji tallafy ya na Abuja ne) Bayan gimtse wayar ne Alhaji tallafy ya shiga mama ki da al ajabi Akan halin Kawu isma'il "lalläi ma isma'il besan yasan halinsa ba, yasan wanene shi tun bai kai hakaba, tun Alhaji Ammar yana ra ye, kawai dai kallon sa yakeyi,da ma barinsa yayi ya ga iya gudun ruwansa ne,Tun asali bayan rasuwar Alhaji Ammar niyya ya yi ya karɓi dukiyar yaran yaci ga ba da kula musu da ita, Amma kuma sai ya ga ai bai kyautu ya karɓa ba, tun da ga ɗan uwansa na jini, kuma shima yana irin harkar da Alhaji Ammar ɗin yakeyi, kuma shine a haƙƙu da abawa, ƴaƴan Duk matane kuma ba wasu manya ba, Lallai kam fans Alhaji tallafy yasan Alhaji Ammar kenan?Har da Kawu isma'il ma,Duk yadda akayi Kawu isma'il bai gane Alhaji tallafy ba, ko da yake shi da bai ma ganshi ba, kawai dai sunan ya sani,ko lokacin cuki_cukun Zuwan Alhaji, tallafy foundation da yayi ai ba a hannun Alhaji tallafy yai Masa komai ba,maybe shiyasa bai gane kowa nene ba,ita kuma Sa'adatu kar ku manta Basu taɓa haɗuwa da Alhaji tallafy ba balle ko zata ga ne Shi... Lallai kam akwai lauje cikin naɗi🤔😳 Duk yadda sukayi da jibo Alhaji tallafy ha ka ya kwashe ya gayawa Hajiya Aisha(mommah) da nasarar da aka samu cikin sauƙi, ta yi murna sosai ta Taya mijinta murna Akan nasarar da ya yi ta amsarwa marayu haƙkinsu,Ranar Alhaji tallafy ya yi barci cikin murna da farin ciki, ita ma Mommah haka, Duk da dai batasani meyasa Hakan ba, Ba yau Alhaji ya taɓa wannan aiki na taimakon marayu ba, Amma kuma farin cikin wannan daban yake, kuma ba ya wani damuwa da Duk irin marayun da y haɗu da su, Amma waɗannan marayun ya shiga damuwa lokacin da suka haɗu hakama yanzu da aka ƙwatar musu haƙkinsu da kuma taimaka musu da yake yi yafi koyaushe murna da farin ciki. Lallai kam bake ba Mommah mu ma kanmu muna da ayar tambaya Akan Hakan ko ba hakaba fans Tun daga sannan wani tunani da Rashin barci da Alhaji tallafy yakeyi Duk ya daina, walwalar sa ta dawo, Duk Mommah ta shaida Hakan,su ma su AKEEL da AQEEL sun ga yanzu Abbu yadawo walwala kamar da kafin ya tawo da ga NEW DELHI(india) lokacin da yakai musu ziyara can, Tun bayan dawowar su suka san akwai abunda yake da mun Abbu ɗin,ko na ce AKEEL yasani, dan shikma AQEEL bai wani da mu da Hakan ba, mutumin da ba lura yake da Yanayin kowa ba, shi kullum ya na waje ɗaya ba bu uhum hare um'um ta ya zai gane wani ya na matsala ne, shima matsalar sa ta isheshi, Amma yanzu kam ma Sha ALLAH AQEEL da sauƙi shariya da shiru_shiru tun da AKEEL yake masa nasiha ɗinnan. ************** A haka dai mukhtar ya na driving fuskarsa ba bu walwala, Bilkisu dai ta na lura da yanayinsa, zaman kuramen ne ya isheta, "zaujin saleh Dan ALLAH ka yi haƙuri Akan Duk abunda ya faru, tsakanin ka da maman ABIE,komai ya wuce kamar yadda kace ka yafe MATA ɗin, Duk Abubuwan da suka fa ru,kadaina tunawa kamance da su kawai, ka tuna ALLAH ma munai ma sa laifi mu roƙeshi kuma ya yafe Mana, balle mu ƴan Adam, Haba Abban ABIE!kai da nasanka mai haƙuri da yafiya, me yakeson ya ruɗe kane? Kayi haƙuri yanzu ka saki fuskarsa kaji? Bilkisu ta ƙarasa maganar tana ƙasa_kasa da murya alamun rarrashi! Kaifa miji na gari ne abun Alfari, Hakanan Bilkisu ta dinga gayawa mukhtar maganganu cikin hikima da kwantar da murya,Har ALLAH yasa mukhtar ya saki ransa ɗin,kuma ya yi murmushi! Sannan yace"shiyasa nake ƙara ƙaunarki a koda yaushe Mar atussaliha! In dai Kika ganni cikin damuwa kema damuwar kikeyi,kuma ta kowanne Hali sai kinsan ta yadda kikayi Kika fitar dani,kin mayen gurbinsa da farin ciki ALLAH yau miki albarka! Ku ma in Sha ALLAH bazan kuma tu na abunda Zakiyyah tai nun ba balle raina ya ɓaci, suna a haka suka ƙaraso asibitin,fuskarsa a sake cike da annuri, mar atussaliha tayi aikinta. "Anya kuwa Aunty Yaya mukhtar zaizo kuwa? Hidayah ta faɗa ta na mai nuna alamun karaya zatayi kuka! Sa'adatu ta nisa ta ce "Nima ina tunanin hakan Hidayah, ko wayar Zaki ba ni nayi Masa magana dakaina, kar muje ta farka, dan Kinga ta na da ƙarfin jini allaurar da wuri ta ke sakinta! Hadiyyah ta ce "To Aunty ga wayar" muryar ta cike da karaya da lamarin. A dai dai lokacin kuma Bilkisu da Mukhtar suka ƙaraso bakin su cike da sallama wajen da suke a tsaye, sunyi cirko_cirko, hakan ne ya sa Sa'adatu fasa kiran da tayi niyya, ta miƙawa Hadiyyah wayar, Hadiyyah da Hidayah tare sukai ajiyar zuciya da amsa sallamar ta su, Sannu da zuwa Sa'adatu tai musu. Bilkisu gaisawa ta yi da Sa'adatu ta na mata ya mai jiki! Su ma su Hadiyyah suka gaisar da ita murya a sanyaye da alamun an Sha kuka, Mukhtar shima gaisawa da Sa'adatu yayi yanai mata ya mai jiki, Tun bayan da likita yace a nemo mukhtar wa Zakiyyah, ya ba su umarnin su fito da ga ɗakin, su ba ta iska, bata son hayaniya idan ba hakaba akwai matsala, shiyasa ma suka samu wajen da aka tanada na masu zaman jinya suka zauna, Amma kuma daga ƙarshe suka dawo bakin ƙofar Ɗakin da Zakiyyah ɗin ta ke su na jiran ikon ALLAH. Ganin zuwan mukhtar da sauri Hidayah Ta tafi office ɗin doctor domin ta sanar da shi ga Mukhtar fa yazo, ba ta jima da dawowa ba doctor ya zo ya not mukhtar zuwa office ɗin sa. Anan doctor yai ma sa bayanin Abubuwan da suke damun Zakiyyah ɗin, da kuma cewa tabbas cutar sa ta na da alaƙa da Shi, dan Haka yanzu dai zai zauna a nan ne har zuwa farfaɗowar Zakiyyah ɗin aga kuma mene mataki na gaba, nan dai doctor yai masa cikakken bayani, ta yadda komai zaizo da sauƙi. Fitowa da ga office ɗin suka yi mukhtar na biye da shi zuwa ɗakin da Zakiyyah ta ke kwance, su Hadiyyah sai su ma suka biyosu, doctor yace baya buƙatar su shi dai kawai yake so ya shigo ɗakin,a sanyaye suka juya zuwa wajen da Sa'adatu da Bilkisu suke zaune, su na ɗan tattaunawa. Sai da Mukhtar ya girgiza! Da ganin yadda Zakiyyah ta koma, ta ga za lokacin bikin zahra da ya ganta, nan wani tausayinta ya kamashi lokaci guda, da rayuwar da sukayi a baya, yadda ta ke mai jiki da ƙibarta irin Giant nan komai ta sa kyau ya ke mata, Amma ji yadda ta koma kamar ba wannan ƴar hutun ba, tayi baƙiƙirin ta rame, Duk wannan wasi wasin mukhtar yana yin sa je ne, a daidai kan Zakiyyah da yake tsaye,Ga ƙarin ruwa ajikinta, ga kuma Robar ƙara numfashi (Dan kuwa sai da aka mayar ma ta da ita komai yayi normal) Likita dai ya ga jikin mukhtar ya yi Sanyi,kuma ya hango nasara a tartare da shi, ko ma dai me wannan baiwar ALLAH tai Masa zai yafe matan,tun da dai ya shi yazo. Nuni yai Masa da kujera alamar ya zauna(dama kuma sun tattauna cewa zai zauna a wajen ne har ALLAH ya sa ta farfaɗowa aga me ALLAH zai yi,in ta farfaɗo kuma ya ƙarasa wajenta yai MATA magana yagani, sannan sai ya yi masa flashing a waya shi kuma zaizo)dan haka ya na Zama doctor ya fice abinsa. Doctor Yaje ya sanarwa da su Sa'adatu yadda abun zai kasance, yanzu haka mukhtar ya na can in Sha ALLAH kuma ta na farkawa zata dawo normal, da zarar ta ji muryar sa, in ya so in ma magana ce zasu yine. Hamdala su Hadiyyah sukayi, yayin da Bilkisu ta tuna alamun tausayi a fuskarta kuma tana adduar ALLAH yasa ta farfaɗo yadda suke tsammani, da Ameen suka sa, zuciyar su cike da begen halayen Bilkisu ma su kyau, ba kowacce ma ce zatayi haka ba,Kishiyarki ba bu lafiya, ki tawo tare dashi wajenta,kuma harki zauna jiran tsammani ga shi dare ya yi wajen 10:00pm, tsakanin Hadiyyah da Hidayah sai tattauna kirkin Bilkisu suke yi. ALLAH sarki Bilkisu bayanin da su Hadiyyah sukai mata Akan cutar Zakiyyah itace ta sa ta ƙara tausaya MATA matuƙa,lallai Bilkisu sai Kinga yadda Zakiyyah ta koma ma, danke rabonki da ita tun tana kan ganiyarta kafin aurenki da Mukhtar ɗin. Ganin Haka ne yasa Sa'adatu ta ce ba ri ta Kira Alhaji ta gaya Masa yadda akayi in yaso sai su tafi gida,tun da ga Bilkisu nan ga kuma mukhtar. lallai Sa'adatu ƴar daɗi miji, Zakiyyah ba bu lafiya Amma saikin koma gida ai shikenan da uwarta mahaifiya ce ai da bata tafi ba, Alhaji gambo yazo kuwa a motarsa suka tafi gida abunsu,da barin in ALLAH yakaimu da asba zasu dawo suji ya ake ciki, nan sukayi sallama sai gida suka bar Hadiyyah da Hidayah da kuma Bilkisu( ba kowacce mace zata iya hakaba) a asibitin Wajen 11:00 Zakiyyah ta motsa, bakinta ya na motsi alamun ta na son magana, mukhtar kama har sannan ya na zaune ya zubawa Zakiyyah idanu, ya na tunani, ai kuwa Mukhtar yana ganin haka, Kiran likita yayi kamar yadda suka tsara, minti 3 ba'ayi ba sai ga likita, ya cire MATA Robar ƙara numfashi, aikuwa magana ta Fara "mukhtar ka yafemun, Akan Abubuwan dana maka" bazan sake ba" sam batun da Zakiyyah keyi kenan, alamu likita yaiwa mukhtar da yayi MATA magana! "Zakiyyah na yafe miki Duk abunda Kika mun, buɗe idonki ki kalleni" mukhtar ya faɗa ya na kai hannu kan hannun Zakiyyah wanda ba ƙarin ruwa ajiki,alamun rarrashi! Kamar a mafarki Zakiyyah ta daina fusge_fusgen da take,Amma kuma ba ta buɗe idonta ba, sai numfar fashi takeyi, alamun numfashinta yanason daidai ta, "Ki buɗe idonki nace Zakiyyah! Ki kalleni nine mukhtar mijinki" wani ku ka ne ya kwancewa Zakiyyah da kuma tari mai ƙarfi wanda ya sa Jini fita da ga bakinta, yi ta ke ba bu ƙaƙƙautawa! Mukhtar ya girgiza da ganin halin da Zakiyyah take ciki, tausayinta ya tsirga Masa! Shikam likita ya san wannan kukan da Tarin da zubar jinin da Zakiyyah zatayi a daidai wannan lokacin shine sauƙin abunda takeji, a game da matsalar ta da Mukhtar ɗin,sai da tayi mai yawa kafin ya lafa mata, ta buɗe idonta da sauri mukhtar yaje ya ɗago da ita zaune a Hankali! Ya sa tissue ya na goge mata jinin bakinta, Sai mayar da numfashi dai Zakiyyah takeyi, ta kafe mukhtar da idanuwa, shikam sai kallon ta yake cike da tausayi a fuskarsa, Zakiyyah kam wani irin k........... Muje zuwa dai ƴan Amana akwai sauran tafiya Nasan akwai tarin tambayoyi a bakunan ku, to ku adana su amsoshinsu suna gaba ✍️ OUM ARQAM ce ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE THIRTY SEVEN 37* wannan karon kam Bilkisu Tasamu yabawa daga team ɗin Zakiyyah, yanzu kam kun faɗi gaskiyar lamari akan komai, da Amma soyayya ta rufe muku idanu😄 "Zakiyyah kam wani irin kallo na tausayawa gareta takewa mukhtar, shima fuskar ta sa kallon tausaya ne a tare da tasa fuskar wanda yake kallon Zakiyyah da ita, "Kayi haƙuri kaji Abban ABIE! Akan Abubuwan da na dinga mak...... Katseta mukhtar yayi da cewa "Na yafe miki Duk abinda kikamun Zakiyyah, yanzu ki kwantar da hankalin ki, kinga bakida lafiya, kinason zuciya da ƙwaƙwalwar ki ta samu salama,kar na kumajin zancen Abubuwan da kikamun ki tura komai baya, abunda yake yanzu shine a gabanmu! Mukhtar ya ƙarasa maganar da tausasa murya alamun rarrashi da tausayawa,yana kai hannu kan nata hannun! Ita kuma Zakiyyah tana mai sunkiyar da kanta da jin zuciyarta tai MATA wasai, ciwon.da ƙirjinta yake mata ta ji ya ɗan ragu, sannan ta ji kamar ta haɗiye wani abu wanda a ƴan kwanakin nan ya tokareta! "Abban ABIE inason ka mayarni ɗakina kaji! Zakiyyah kenan ai kece Kika ƙi ɗakin naki, Amma ba ni mukhtar na hanaki ba,dokin zuciya ki ka hau shiyasa na baki sarari, Amma tun da yanzu kinason komawa ai shikenan daga kinji sauƙi sai komawa gidanki! Ya ƙarasa zancen da murmushi da alamun tausayi gareta! Zata kuma magana yace ya Isa hakanan bakida lafiya. Tun Fara maganar su likita ya ba su waje, domin wannan zancen na su sirrin sune, ya na fita kuma ya je yake sanarwa da su Bilkisu ɗin Zakiyyah ta farka kuma Alhamdullillahi da sauƙi, dan har ta yi magana ma, Cike da zumuɗi suka ta shi da niyyar ɗunguma zuwa ɗakin, sai likita ya katse su da cewa ku bari ta ɗan samu nutsuwa,su ga ma zantawa sai kuje, jiki a sanyaye suka koma su ka zauna. Acan ɗaki kuwa bayan Zakiyyah ta yi shiru, a zuciyarta sai tunanin wa ya gayawa mukhtar batada lafiya ne? Shin waima wa ya kawota asibitin kodai shine? Da makamantan zantukan da take a zuciyarta sai dai kuma batada amsoshinsu. Bari na kirawo su Aunty da Hadiyyah ɗin ta re da Bilkisu nake ma, itadai Zakiyyah batayi magana ba mukhtar ya fice domin kiransu. Ko da yaje bai ga Aunty ba anan suke ce masa ai ta tafi gida tun ɗazu, shikam mukhtar yayi mamakin Hakan amma bai ce komai ba, Sun ɗunguma zuwa ɗakin gaba ɗaya Hadiyyah da Hidayah sai rige rige akeyi, ita kuma Bilkisu tare da Mukhtar suka jera. Anan take tambayar mukhtar ɗin jikin nata da sauƙi Amma ko? Da ea ya amsa MATA suka ƙarasawa ɗakin. Su Hadiyyah sai Sannu suke jerawa Zakiyyah ita kuma tana ɗaga kai alamun yawwa. Sai Bilkisu ta razana dataga Zakiyyah yadda ta koma, gaskia kam abar tausayice, wannan ra ma haka,Duk yadda akayi batajin daɗin zaman gidan nasu,zata yiwa zaujin saleh magana Akan yai MATA izinin komawa ɗakin ta ko Dan ABIE ma daya Fara kuka akan haka, saboda tana son yaron tanaso yai rayuwa da mahaifiyarsa,zancen zucin da Bilkisu takeyi kenan harta ƙarasa wajen Zakiyyah tai MATA ya jiki,ita kuma ta amsa a Hankali. Zakiyyah ta yi mamakin zuwan Bilkisu gurinta fa,kuma ta ji Duk wani haushi nata da takeji ta daina,saima burgeta da tayi, haka ai dama abun ALLAH yake Zakiyyah kam kinyi Hankali kinyi ta ƙawayenki. Haka dai suka zauna wajen Zakiyyah Babu mai alamun barci, mukhtar da Bilkisu su na kan kujera kusa da juna, su ma su Hadiyyah Hakan. Likita ya dawo yace zai kuma sakawa Zakiyyah ruwa da jinin da yayi saura dan taji ƙarfin jikinta kafin safe, acikin Ruwan yasa MATA allurar barci wanda zata kuma samun hutu sosai. ************* Bayan su Sa'adatu sun koma gida, anan maƙota sukejin labarin jikin Zakiyyah da sauƙi, ta farfaɗo ma kafin tawowarta,Amma ta kuma komawa, tana kiran mijinta, kuma yanzu haka yazo, su ma yaran su Khadija da Farouk da hydar sai sannan zuciyarsu tai Sanyi jin Yaya Zakiyyah bata mutu ba. An Sha ƙauna kam Sa'adatu da Alhaji gambo, sai asubar kamar yadda tace sannan ta komo asibitin,ita da shi Alhaji gambo ɗin, Hadiyyah tace ta tawowa da Zakiyyah kayan sawa, lokacin kuma Zakiyyah ta farka ma Sha ALLAH har tayi wanka ma da taimakon su Hadiyyah, da abun karyawa Sa'adatu ta tawo(Alhaji Gambo ya ajiye, albarka in Auren Sa'adatu da yayi) Sai sannan kuma Sa'adatu tacewa Mukhtar da Bilkisu suje gida, tun da ga ta tadawo,basuyi musu ba saboda sumbar Husna da ABIE a gida ba da zummar kwana ba,nan sukayi sallama suka fice sai gida. Nan Zakiyyah ta gayawa Sa'adatu cewa mukhtar yace idan taji sauƙi ta dawo ɗakinta, cikin murna tai maganar, Hadiyyah da Hidayah sunfi kowa murna da wannan zancen,Duk sun ƙarya, anata Hira jikin Zakiyyah kam ma Sha ALLAH,likita ya shigo ya bata magani, ya kuma jona MATA ruwa da jini danta samu ƙarfin jiki. Kafin safiya tuni zancen cutar Zakiyyah ta je kunnen Baaba Hadiyyah ta kirata, jin Abubuwan da Hadiyyah ta zayyana yana damun Zakiyyah ya tadawa Baaba Hankali,dan haka tace in anjima tananan zuwa day kaduna ɗin,kuma ta gaisa da Zakiyyah ɗin, har Baaba take MATA tsiya "in mijinki kike son komawa ai ba sai kins kanki a uku ba, sauƙi kirashi kubashi haƙuri, koda yake ai akwai kunya,sannan yunwa kuma bansan me ya sa ta sameki ba(Baaba batasan anawa Zakiyyah horon yunwa ba) Itadai Zakiyyah ba bu bakin magana sukayi sallama da Baaba. _____ Can gurin mukhtar ma haka da suka koma gida, sun samu har ABIE ya tashi yana rigima, Husna tai Masa wanka itama tayi, ta na mamakin daɗewar su, su da sukace MATA siyayyah zasuyi, barcin ma rabi_rabi tayishi, sai kuma sallamar su yanzu, a sanyaye ta amsa da tambayar su ina sukaje suka kwana?ta kwana cikin tsoro da fargaba, kwashe komai sukayi suka gaya MATA kuma ta tausayawa Zakiyyah ɗin tun da da ma tasanta. Saida sukayi wanka da karyawa, sannan Mukhtar ya Kira Hajiya jamila yake gaya mata,itama ta tausaya Zakiyyah ɗin dama kuma tana ƙaunarta tun asali,itace dai take haukanta a da,ku ma ta ji daɗi da yace MATA yace ta dawo ɗakinta in taji sauƙi, tai Masa addu'a. Mukhtar yacewa Bilkisu Zakiyyah zata dawo gidanta da taji sauƙi, Alhamdullillahi zaujin saleh da ma haka nake burin gaya maka kayi, ta bani tausayi sosai, ALLAH ya haɗe kanmu ya baka ikon yin adalci tsakaninmu Allahumma Ameen mar atussaliha cewar mukhtar yana tallafo hannun Bilkisu ɗin. Bilkisu ta yi girki na tafiya asibitin, mukhtar yace kinga dai bakiyi barci ba jiya, ga Kuma yanayinki,ki zuba abincin ni da Husna da ABIE sai mu koma ke kuma ki wuta, ta so wutawar dan haka tace to shikenan zaujin saleh ALLAH yakaimu gobe na je. Hakan akayi Husna da Bilkisu sun haɗa abinci mai rai da lafiya do akai asibiti wajen Zakiyyah, haka suka tawo asibitin da Husna da ABIE akabar Bilkisu a gida domin ta huta, da saƙon aiwa Zakiyyah ya mai jiki. Koda mukhtar ya koma asibitin acan ya tarar da Hajiya(kunsan dai Zakiyyah ƴar lelen Hajiya ce, badon taiwa kanta ba) itama har Baaba tazo, nan dai akaita shiwa mukhtar albarka Akan cewa Zakiyyah inta samu sauƙi ɗakinta zata koma. Zakiyyah kam ta na samun kulawa, tasha allurai da ruwa da jini da yawa,jikinta alhamdullillahi ta Fara samun sauƙi, kullum mukhtar sai ya zo gurinta,da kuma girkin da Bilkisu tayi akawo hakama Bilkisu tana zuwa sa'i da lokaci. Baaba tana asibitin gurin jinya, Amma su zeenah da Hunaif suna kaduna saboda makaranta acan ta barsu. Su Hajiya ikilima, da Hajiya suwaiba, da Hajiya sahura Alhaji gambo ya umarcesu da suke, Amma Kowacce daban ta zo, su Hajiya sahura da suwaiba ba su kula Sa'adatu ba dama kuma can basa shiri da ita, balle yanzu ta Zama kishiya kuma, ita dama ƙawar Hajiya ikilima ce shiyasa tun farko ba sa ga miciji, sun wa Zakiyyah ya jiki da abun alkhair ɗin su, sun gaisa da Baaba Amma Sa'adatu lala_lala. Koda Hajiya ikilima tazo Duk mutuncin nan da ake da Sa'adatu ko kallon ta ikilima batayiba, sai dai jinjina kai da ƙwafa da suke "Lalläi kam naga har wata ƙiba Kika Fara ko? Da Sannu Zaki tsiyaye kamar mai a fashashshiyar leda, abunda Hajiya ikilima take ayyanawa a zuciyarta kenan, lallai Sa'adatu na tausaya miki. Amarya Zahra kam ta zo duba ƴar uwarta, Ango ibrahim shine ya kawota da kansa, sunyi shar abunsu musamman Zahra harda wani fari da ƙiba da ta Fara, to tana cikin kwanciyar Hankali, kuma yanzu kuma haka aiki ake nemar mata,domin takardu sunyi kyau,ta ci exam ɗin ta,kunsan dai burin Zahra ta Zama Ma'aikaciyar jinya,kuma Ibrahim yace zai cika mata shi, ALLAH sarki Zahra kin fito daga ƙangin bauta,ga suruka da ƴan uwan miji kowa na sonta,kekam kin dace Nikam nace saura ƴan biyun mu Suma. Kawu isma'il a tsaitsaye yazo dubiyar ya fice, kunsan dai sai a Hankali yana cikin matsala, Hakama Hauwa da ƴaƴan ta sunzo taiwa Zakiyyah nasiha sosai, Akan ta gyara halinta,taga dai yadda ALLAH yayi da ita. Satin Zakiyyah biyu a asibiti ta samu sauƙi Alhamdullillahi, kuma a ranar aka ba su sallama,tare da nasihohi ga likita Akan adaina bata MATA rai, sannan kuma ta kiyaye shiga damuwa,ta dinga cin abinci da Shan magani kuma, in Sha ALLAH zuciyar data Fara samun matsala zata warke gaba ɗaya (Nikam nace ai cuta ta ƙare da ma mukhtar ne sai kuma Rashin abinci, yanzu kam Duk ansamu sai fatan warkewa) A haka suka dawo gida. A washe gari kuma su Hadiyyah da Hidayah sukaje suka mata ɗan gyare_gyaren da ba'a rasaba, da wanke_wanken Abubuwan da sukayi ƙura a gidanta da Baaba Sa'adatu Hadiyyah da Hidayah sune suka MATA rakiya zuwa gidan mukhtar ɗin mu,Bayan tasha nasihohi da faɗa Akan yanxu dai yaga yadda rayuwa tayi da ita, in kuma bata canza Hali ba shikenan, matsalar ta ce....Ƴan team ɗin Zakiyyah ku matso kuna inane su Seeerat da Haseena, MamaGee Aisha sulaiman,Maman eyshat,mummy Waleed da sauran ƴan team ɗin Zakiyyah ku fito kunce harda ya yi zakuyi Ranar da Zakiyyah ta komawa mukhtar,da kuma ɗimbin nasihohi a gareta,da kuma gyara sai su fito kam gata dai a gidan mukhtar...... Murna a gurin ABIE ba bu dama, da Abbansa yace Masa "ummunka dai na dawo maka da ita" Sai yace "Amma da Ummunah da Ammie nagancu ba a tale ba? Mukhtar yace "eamn Kowacce gidanta da ban, ABIE aina zaka zauna to? Mukhtar yana murmushi yake maganar haɗa da shafa kansa, inanan inacan Abbana cewar ABIE (dama kunsani Basu da nisa tsakanain gidan Bilkisu da Gidan Zakiyyah.kunji ɗan nema...... ************** "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun me kake cewa Alhaji buubah? Kawu isma'il ke wannan maganar cikin ta shin Hankali a zaune yake Amma ya Miƙe tsaye! "Kwarai dagaske kuwa isma'il kaya dai anyi odarsu ma Sha ALLAH,Amma cikin ikon ALLAH kuma daga jirgin har kayan gaba ɗaya sun nutse a teku gaba ɗaya,ta shin Hankali wanda ba'a sa Masa rana,Kawu isma'il ya shiga cikin bala'i yanzu dai ko biyar bashi da ita, a kuɗinsa wanda yake juyawa, kuɗin marayun Suma an damfaresu, yanzu haka akwai bashin 30millions akanshi na banki wanda yasan shi dai banki baya lamuni,tozartaka ne zaiyi, A gurin sa 15millions din da zaiyi gyaran gida ce ta rage masa a hannunsa kawai, yanzu ya zaiyi da ita ne? Ko dai ya mayarwa banki waɗannan In yaso da ga baya ya cika musu! To da wane kuɗin? Gidan su Hadiyyah dake hannun sa, ne ya Faɗo ma sa a rai Amma ta yaya zai siyar? Wata zuciyar ta bashi amsa, Tun bayan gama wayar da sukayi da Manager na mummunan labarin da ya bashi ya nutsewar jirgi da zunzurutan kuɗin sa gaba ɗaya na jari da kadarorin sa ya siyar a haɗa kuɗin, ALLAH yaso shi kaɗai ne a ɗakin Hauwa bata kusa,dan haka yaso ya danne damuwar sa,Amma kuma Hakan yaci tura(kuɗi fa ba wasa ba,kunsan dai Kawu isma'il da kuɗi musamman ace nasane waɗannan,mugu Amma nasu Hadiyyah da akayi yahoo ɗin su bai damu hakaba?) Hauwa ta so taga cewar mijinta ya na cikin damuwa amma da ta tambayeshi me yake damunsa? Cewa yayi zazzaɓine kawai dan Haka ta bashi magani,ya Sha ya kwanta,yaumshe idanu kamar yana barci Amma ina! Ba barci yake ba zuciyar sa ce take ƙuna da ɓacin ran rasa dukiyarsa baki ɗaya,ga bashin banki,sukuku Kawu isma'il yazauna a wannan yammacin ko fita bai ƙara ba. Har yara suka dawo daga makaranta sukaga Abba,yace musu bayajin daɗine,har zuwa dare suka gama abunda zasuyi,suka kulle kofofin gidan gaba ɗaya dan shirin barci. Wajen 12 na dare Hauwa ta na kwance ta Fara jin harbe_harbe a unguwar, dan haka tasan tabbas yau unguwar ba bu lafiya kenan, ƴan fashi sun shigo musu kenan,dana wannan tunanin ta ji harbi a cikin gidan, innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun Hauwa ta ambata kenan yau ƴan fashi gidansu suka kawowa Hari! Tashin Hankalin da Hauwa take ciki da jin komai shima Kawu isma'il yaji wanda shima ba barci yakeba,dama likimo yayi sai tunani yakeyi Hakan yasa ciwon gaske na kai ya rufe shi,shine fa yaji harbi,cikin tashin Hankali Hauwa ta taɓa Kawu isma'il tace "Abban meenal kaji ƴan fashi cikin gidanmu! Kamar me barci ya tashi firgigit yana sallallami, kafin a rude suka tashi suka tafi ɗakin yara, sun samesu suna barci dan haka suka kullo musu ƙofar da key adai_dai faloun da suka isa ne kuma.......... Wayyo ALLAH Kawu isma'il😢 Anya kuwa zai I shanye waɗannan tagwayej bala'oin😄 batare daya gayawa kowa ba,koda yake da alama su SNAKE ne suka kawo agaji😢 Kawu isma'il ALLAH ya kareka daga sharri🙏 Zakiyyah kuma ankoma gidan mukhtar💃 Sa'adatu kam bani da bakin magana🤐 Zaki ganine komene! Mike zuwa.... Yanzu aka Fara wasan yasin😄 ✍️OUM ARQAM ce ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE THIRTY EIGHT 38* Lallai kam team ɗin Zakiyyah naga anata murna da komenta anci ansha harda su anko, tariya kamar Auren fari, to ALLAH yasa dai ƙawar taku ta fitar daku kunya wajen Sanja halaye saɓanin na da 😒🤨 idan ba hakaba yasin Bilkisu Babu ruwanta wannan karon sai dai Zakiyyah tayi tafiyar da Babu dawowa🤣💃 "Gidan su Sa'adatu kam yanzu yazama shiru kakeji, ALLAH yaiwa Zakiyyah ɗagawa sai fatan zaman lafiya mai ɗorewa a gidan mijin nata. Sa'adatu ta Zama ita ɗaya abunta, Duk yara ana makaranta, sabo tirken wawa Duk da bawani abune yake haɗasu da Zakiyyah ba yanzu da ba bu ita a gidan sai taji ba bu daɗi ..lallai Sa'adatu gidan mijinta ai yafi ye mata nan gidan, kuma ma itada ba a gidan ta tasoba ko mugun nufi gareki😒 yau dau na tarewa Zakiyyah. hankalin Hadiyyah da Hidayah ya kwanta sosai yanzu Yaya Zakiyyah ankoma gidan miji, kullum suna ma ta addua akan ALLAH ya gyara mata halayenta, yasa karta koma irin halin baya Nikam oum ARQAM nace Allahumma Ameen tagwaye. Kuma har sannan su na zuwa school abunsu cikin NASARA, basa kula kowanne namiji, saboda mus'ab Saurayin Hadiyyah akwaishi da ɗan banzan kishi, bayason ya ga kowanne namiji ya kulatan, ita kuma da ma baisan Hakan takeba karatunta tasaka agaba, maza Basu isheta kallo na, har yanzu ma ƙawa mace batayi ba, ƙawarta ƴar uwarta Hidayah, tare suke Zama waje ɗaya abunsu, yan class ɗinsu suyita mamakin, wannan kama ta su hakanan, su fa basa ganesu komai iri ɗaya, sai in suna tattaunawa tsakaninsu ƴan ajin suna kallonsu anan suke ganin ɗaya tafi Jan ɗaya da Hira, ma'ana Ɗaya tafi ɗaya surutu, Mus'ab shi dama Hakan yakeso, kuma suna cigaba da soyayyarsu mai tsafta, Duk da dai Mus'ab ɗin kullum cikin busy yake baya bata wata kulawa sosai, ta fannin soyayya, Hadiyyah tana ganin yadda wasu ƴan matan suke soyayya wayar safe daban ta rana daban ta dare daban, Amma ita sai a slow basosai Mus'ab yake kiranta ba, wataran ma sai a online kawai zasu ɗan zanta idan bata hauba shikanan, bazai Kira yaji lafiya ba, Mus'ab kam wani bauɗaɗɗan namiji ne, wanda itadai Hadiyyah take sha'anin ta itama,karatu ne a gabanta shiyasa bata damuwa da halinsa. Hidayah kam kunsan halinta dama na miskilanci, in Mahmoud ya kirata a waya sai taga damar ɗauka ma, ko bai kiraba bata damuwa,shima suna ɗan tarayyah da Mus'ab wajen halaye akwai kishi shima bai amince ta saurari wani namijin bayan shiba, kuma dama bata kulawa, shi yasa ita kam Babu wata damuwa ta ɓangaren ta nacewa baya ba ta kulawa ko wasu ba haka suke soyayya ba, shima ba sosai yake kiranta a waya ba,sai sa'i da lokacin shima. Haka waɗannan tagwayen suke rayuwarsu ta ɓangaren karatu ma Sha ALLAH, ɓangaren soyayya ma dai hakanan, Basu da damuwa. Kuma Duk waya kulawa Alhaji tallafy yana musu tun daga kan kuɗin school Duk wata yake tura musu ta account Duk suna dashi, littattafai ma hakanan yana siya musu da sauran handouts, Basu da damuwa. Kuɗin school yana musu yawa(Alhaji tallafy yasan da haka saboda su dinga kashe wasu matsalolinsu ne) aikuwa sunayi Duk wani abun buƙata, Pad ɗan kayan sawa haka na yayi, takalmi jaka,tura ruka, sabulun wanke gashi, dan kuwa akwai gashin ma Sha ALLAH, ko wataran suje saloon(lallai ƴan biyu anfasi gari) da sauran abun buƙata da kuɗin school sukeyi kuma har su samu rarar wasu kuɗaɗen, Hakanan sukewa Khadija ma saboda ta Zama itama ƴan ma ta, yanzu fannin abinci sai godiyar ubangiji suna samu suci ko Babu yawa, sai su siyo wani abun da kudinsu su daɗa, Albarkacin kaza, ƙadangare ke samu yasha Ruwan kasko, Alhaji gambo ke ajiye abincin,sanadin Auren Sa'adatu dayayi, yanzu kam ma Sha ALLAH suna cikin rufin asirinsu dai dai gwargwado, kuma sani aiki da Sa'adatu take sakaso yanzu basanan, ina aikin ma yake ne, sai kuma sun dawo irin su wanke_wanke da shara sai wanki da suke ɗanyi, daga nasu saina Hafsat da Hydar, kiyi haƙuri ƴan biyu shima wannan ɗin lokacine. ************** Kawu isma'il suka zuwa falour suka tarar da ƴan gashin har sun duro cikin ga su a falour ma, su biyar ne ƴan fashin kowanne da bindiga a hannun sa, a tsaitsaye, suka ƙaraso wa kuma suka ɗau saiti da bindigar gurin saita kan Kawu isma'il da Hauwa da bindigar, sauran kuma suka Fara bincike a flourn suna ina kuɗi! Ko mu fasa kawunanku da harshashin wannan bindigar! Jikin Kawu isma'il dana Hauwa Ba bu abunda yake sai kakkarwa da tsima, Hauwa sai salati takeyi, shikam Kawu isma'il yakasa salatin ma, ya Zama kamar butun butumi a tsaye, Babban su wato Snake yana hakimce a ɗaya daga kujerun flour kai kace gidan ubansane mo gidansa,ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. "Ya Awale ku fa ra sassaɓa masa kamanni tun da ana maganar ina kuɗi yaƙi magana" cewar Snake ya ciccije baki Aikuwa Awale kamar Kira yake shida Funkaro da kuma duwalle (kaji wasu irin sunaye ALLAH ka shirya al Umar muslim baki ɗaya) nan suka saka bakin bindiga suka Fara dukan Kawu isma'il da shi! Makyarkyata ya kama da kuma sa ihun azaba! Ku ƙyaleshi hakanan yadawo hayyacinsa yanzu inji Snake! Duwalle ne yakuma ma sa tambaya ina kuɗi suke?! Bakin Kawu isma'il har rawa yakeyi wajen cewa suna can! Yana nuna musu ƙofar Ɗakin sa, saboda anan ya Adana jakar kuɗin, ko Hauwa batasan da itaba. Ba nuna Mana zakayiba ehe tashi zakayi ka ɗauko Mana!cewar Snake kamar irin kuɗinnan nasu Ai da sauri Kawu isma'il ya Miƙe yana ɗingisa ƙafa, dan ana suka bubbuga Masa bindigar,daƙar ya iya kaiwa ɗakin,cikin durowa ya buɗe ya ɗauko jakar ya muƙawa Funkaro, yakuma tiso ƙeyarsa zuwa falourn. Har sannan Hauwa tana durƙushe a gaban su an saita kanta da bindiga, sai salati takeyi kafin, snake yayi MATA tsawa da saurara Mana hakanan! Gum Hauwa tayi jikinta yana tsima, adai dai kuma nan ne su Duwalle suka taso ƙeyar Kawu isma'il da jakar kuɗin! Hauwa ta Sha mamakin aina Kawu isma'il ya samu waɗannan kuɗin, haka a gida, shi da yace ya sa jari waɗannan kuɗin fa, ko kuɗin marayun ALLAH ne kuma? Tana wannan tunanin ne Snake da duwalle ya miƙawa jakar kuɗin, ya buɗesu kuwa sai ga ƴan rafa_rafa na dubu_dubu sabbi farare, yanata fito da su, Har sannan Hauwa ta na cike da mamakin waɗannan kuɗin aina mai gida ya samesu hakanan, tasan yanzu yana tashan kuɗi Amma batayi tunanin akwai kuɗi a gidan ba, Kawu isma'il kam yana tsugunne shima a gefe,yana ganin ana fito Masa da kuɗaɗe waɗanda sune suka rage masa,kuma ma banasa bane, na bankine a hakanma sauran sa 15million, tunanin hakanne yasa zuciyar Kawu isma'il harbawa da sauri, dage kirjin yayi jin abinda Snake yake faɗi! Waɗannan kuɗin ba haka suke ba,ina kakai ragowar idan ba hakaba kuma... Ragowar kuɗin kenan ai nayi amfani da sauran! Kawu isma'il ya faɗa cike da raunin zuciya! Oh ka rage Mana kuɗinmu kenan saboda cuta(lallai ma kuji fa son zuciya a wajen Snake) meka yi dasu! cikin tsawa Snake ya faɗi Hakan Da raunin zuciya da na murya Kawu isma'il ya faɗawa Su snake cewa wannan ma kuɗin banki ne ya ranta, rabin kuɗin yayi odar mota kuma yanzu Hakan baisan inda mutanen suke a ma'ana an damfare kuɗin, waɗannan ragowar ne yatawo dasu gida zaiyi gyaran gidan, kai har odar da yayi da nutsewar jirgi Duk ya faɗa musu,Kawu isma'il fa yafara fita daga hayyacinsa sai zubar zance yakeyi,har hannun jarin da ya saka da kuɗin su Hadiyyah Saida ya fallasa(innalillahi🙆‍♀️) wannan batasa su Snake sunji tausayin sa ba saima ƙara Masa duka da sukayi, nacewa Duk waɗannan dukiyar ya salwantar ai da yabari sunzo ai rabon sune, ALLAH ya isa kawai cewar su Snake ɗin suna ficewa daga gidan bayan sun tafi da kuɗin jakar da sumar da Kawu isma'il ɗin, itadai Hauwa tun zubar zancen da Kawu isma'il yafara tasa Kuka Akan mai gida ka cuci kanka ka cuci marayun ALLAH sakayyah kaɗan kafara ganin, cikin Kuka taketa ire_iren waɗannan maganganun, Hakan kuma ya tunzura su Snake itama Saida suka sammata dukan da bindiga Amma duka ɗaya a hannu, ta ke ta sume,kuma suka tsallake suka bar su nan, suka shige motar da suka zo da ita. ALLAH sarki Hauwa Kawu isma'il ya janyo miki. Duk Abinda ke faruwa maƙota najin ƴan fashin,kuma hankulansu ya tashi, na cewa ko ba iya Gidan zasu shigi ba, Amma sunajin motar ƴan fashin ta tashi sukayi Hamdala, marasa shi na layin suka ALLAH shi ƙara, saboda Kawu isma'il kuɗinsa ba bu kyauta Babu sadaƙa, zakka wannan bayi yakeyi ba, daga shi sai ƴaƴansa,talakawa nawane a layin suke kawo kukansu gareshi Amma ya sa ƙafa ya Shure, har masu kuɗin layin sunsan Kawu isma'il bashida kirki ko ƙadan, shi yasa ba su damu ba da ƴan fashin suka shiga gidansa, aida baza'a rasa wanda zai Kira ƴan san da ba... (Wannan nasihace ƴan uwa daga oum ARQAM "kusani kyautatawa maƙota yanada tasiri sosai koda singa wani abu na cutarwa zasu iya ije maka ta kowanne Hali, koda ɓarayi ne suka zo maka bakanan sai indai ƙarfin su ya kare, ko gobara ta tashin maka bakanan zasu kare maka gidanka Amma idan bakada mutunci suna kallo za'a shiga ai maka sata suke gwanda wannan bashida mutunci ai masa ɗin, Hakama suna kallon wuta tanaci bazasu kashe maka ba,inda suna da kalanzir ko fetur ma zasu iya ƙarawa wutar saboda komai naka ya ƙare tunda baka tausaya marasa shi idan mutum ya kawo maka matsala baka warware Masa,irin dai halin Kawu isma'il, hakama a musulunci makoci yanada haƙƙi Akan maƙocinsa, wanda Manzon ALLAH saw yace jibril ya dingamin wasiyya akan maƙota har Saida nayi tunanin maƙoci zai gaji maƙocinsa, saboda irin girman hakkin maƙotaka, hakanan ko maƙocinka ba muslim bane akwai haƙƙi Akan ka dayawa nasa,Inaga kuma muslim yakamata ƴan uwa mugyara musan cewa maƙoci ɗan uwane, kuma kudinga saukewa juna haƙƙoƙi,wani fannin maƙoci yafi ɗan uwa saboda ina ɗan uwan naka yake abu zai sameka kafin ɗan uwanka yazo maƙocinka yai maka Rana,idan Babu zaman lafiya kuwa ai kafin ɗan uwan naka yazo koma mene ya faru ƴan uwa mu kiyaye) Duk wannan bala'oin da iyayen suke cike ƴaƴan Basu sani ba, suna barci kuma hakanan dama akwai nauyin barci, mai wayon meenal ce zatayi 12_13 years sai ƙasa da Hakan,Umma ke tashin su da asba, yau bata tashesu ba har gashi gari ya waye, dan Haka meenal ta fito taga lafiya meyasa yau umma bata tashesu ba, Saida kansu suka tashi!? Tunanin da takeyi kenan harta fito babban flourn gidan ai ganin umma da Babah tayi Duk a sheme Babu alamun numfashi!Babah kafafuwa a kumbure da hannu harda jini ma, itama umma hannun ya kumbura,uban Ihu Meenal ta saka! Wanda sauran kannen guda huɗu suka fito Suma suna ganin haka suka ka ma muka, suna ficewa waje. Dama maƙota tsammanin Hakan suke dan sunsan ƴan fashi kam sun jima a gidan bazasu ƙasa ɓarna ba, sai kuma ga ihun yara, Hakan yasa maƙota na kusa shiga gidan cikin tashin Hankali jin Meenal tana cewa wayyo umma da Babah sun mutu! Maƙota na sallallami suka antaya gidan zuciya da rai ba bugawa jin cewa Sun kashe Alhaji da Hajiya, saidai sukaje sukaga alamun suka sukasha a wajen ƴan fashin, dan haka suka tura komai baya na hulaƙancin Kawu isma'il suka sanyashi a mota shida Hauwa domin zuwa asibiti Hankali a tashe, aka bar su meenal a maƙota sunata Kuka abun tausayi..... Muje next page Na tausayawa Hauwa da ƴaƴan fa🥲 Wayyo Kawu isma'il ɗinmu😢 Yanzu aka Fara wasan Saura ƙiris mukawo tarihin Alhaji tallafy in Sha ALLAH nanne gaɓar daya dace kusan iyalan Alhaji tallafy ɗin dai sai kunfijin daɗi Akan tun baya, Zaku ruɗe wajen ganin bakin zaren yanzu kuwa kunsan wasu Abubuwan ai a Hakan, anyi sharar fage yanzu za'a kutsa cikin labarin kudai kubiyo ........ ✍️OUM ARQAM ontop🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE THIRTY NINE 39* "Ko da sukaje asibitin ba'a karɓe su kai tsaye ba sai da aka nemi ƴan sanda, saboda raunin da yake tare da Kawu isma'il sai jini yake Fitarwa,su kuma can maƙota ansamu wani munafikin ya kirawo ƴan jarida, Akan cewa ƴan fashi sun zo layinsu sun shiga gida ɗaya sunyi fashi har sun kai ga yiwa matar gidan da mai gidan dukan Kawo wuka,to kafin ƴan jarida harda na Gidan television ma duk suzo har anyi asibiti da Kawu isma'il,bayan sun gama jin ta bakin maƙota suka ɗunguma domin zuwa asibitin, lokacin ƴan sanda sun hallara dan haka suka ɗauki ɗan bayanan ƴan sanda kafin su ɗau hotunan su Kawu isma'il. Duk wani taimakon gaggawa anbawa Hauwa da Kawu isma'il, inda aka samu tsagewar ƙashi a hannun Hauwa,abun yazo MATA da sauƙi, shikam Kawu isma'il karaya a hannunsa saboda lokacin da duwalle ya kawo mai duka da bindigar a kansu hannu ya saka ya kare, ƙafar sa kuwa akwai targaɗe a ɗayar, ɗayar kuma buguwa ce sosai dan haka gaba ɗaya ƙafafuhan a kumbure suke, ga raunuka abun ba bu kyan gani duk anmasa dressing ɗinsu, dai jiran farfaɗowar sa, dan Duk Abubuwan da Akayi Masa bai san anyi Masa ba, baya hayyacinsa saboda yakuma samun hutu yasa aka Masa allurar barci. Ita kuwa Hauwa tun lokacin da aka Fara MATA gyaran hannunta ta farka,sai Kuka takeyi abun gwanin tausayi, dan haka likitocin suka MATA itama allaurar barcin dan ta samu nutsuwa, ba komai ne take sa Hauwa ku ka ba sai irin ha'incin da mijinta da muguntar da yayiwa marayun ALLAH ne, yanzu ya salwantar musu da kadarorin da Mahaifin su ya bar musu, Basu da tsuntsu Basu da tarko, lallai kaɗan ma yagani a rayuwarsa kam, kullum cikin nasiha da ban baki take Masa a kan sha'anin marayun ALLAH Amma bayaji har barazana yai MATA da duk sanda takuma saka Masa baki Akan harkarsa a bakin aurenta, shiyasa ta zuba Masa idanu, yanzu Baga shi ba kaɗan daga cikin Haƙƙin marayu ya fara bibiyarsa, kuɗin sa gaba ɗaya ya salwantar,ga bashin banki akansa, lallai kam Kawu isma'il kana ruwa fa waɗannan haƙƙoƙin ka kaisu ina ga na iyalinka. ______ zancen fashin da akayiwa Kawu isma'il yaje gidansu Hadiyyah,abunka da jini sun tausaya Masa sai Kuka suke da sukaji batun ance an Masa dukan Kawo wuka, yanzu haka ya na asibiti bai san a ina yakeba! Basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen tafiya asibitin, jikinsu a sanyaye, ita kam Sa'adatu kadaran kadaham dan kuwa bata tausayawa Masa ko ƙadan ba,kunsan dai ABunda ke tsakanin sa da ita , ga kuma matarsa itama basa shiri ko ƙadan,ita haka tace ma ALLAH yasa sun kasheshi Daga shi har Hauwa ɗin, kuma anzo gaɓar da za'ayi fito na fito da ita dan kuwa ba bu ruwanta da wani fashi da aka Masa dole abiyata Haƙƙin ƴaƴanta da ke kansa a yanzu ba sai wani lokaci ba, dama tanada wannan a ranta sai ga shi kuma wannan ta ɓullo Muje Zuwa isma'il yanzu aka Fara wasan! Shure Shure baya hana mutuwa! Yanzu zan fito maka a kalata! Cewar Sa'adatu tana tafa hannayenta alamun ashirye ta ke. _______ koda su Hadiyyah sukaje asibitin sannan Hauwa ta farka har Sannan sai aikin ku ka takeyi, tana ganin su Hadiyyah da Hidayah da kuma Khadija wani kukan ya ƙara kwace MATA, rayuwar waɗannan yaran itace abun tausayi ba bu uwa ba bu uba, gasu MATA sunason kulawa da ja ajiki, da tattali, Amma yanzu ƙanin mahaifinsu ya cucesu ya salwantar musu da dukiyar su,da ma yanzu komai dan kuɗi akeyi,koda ALLAH zaisa wani ya jiɓanci lamarunsu Amma ina sai addu'a kawai, sunga kukan da Hauwa take sai haƙuri suke bata "kiyi haƙuri maman meenal ƙaddara ce ta Riga fata,dukiya baƙuwa ce ALLAH zai sakawa kawunmu, kwana nawane zai mayar da dubunsu, ciwo kuma ALLAH zai yaye ma sa"cewar Hidayah ta na share ƙwallar idonta, Jinjina kai kawai Hauwa ta keyi alamun taji, zuciyarta kuwa fal take da tausayin yaran, su yanzu haka tausayawa isma'il suke suna fatan samun sauƙin sa da dawowar kuɗin daya rasa, lalläi basusan me ya aikata musu bane, maybe suyi Masa tofin ALLAH tsine. Daƙar Hauwa ta saurara da kukan da take hannu a kumbure, an gyara, ƴan jarida sun dawo sun ɗauki muryar Hauwa kuma ta Basu tabbacin abunda ya faru tun daga shigowar ƴan fashin. Hauwa tacewa Hadiyyah da Hidayah suje gidanta su gyara MATA Abubuwan da ƴan fashi suka watsa, kuma akwai su meenal a maƙota suci abinci suyi wanka da Abubuwan da ba'a rasaba dan haka suka wuce Gidan Kawu isma'il. Sun tsorata da yadda suka ga ƴan fashin suka yi da gidan, sun barbaza kayan ɗakin Kawu isma'il komai filla filla, haka suka shiga gyara. Lokacin asibitin ma Sha ALLAH su Bilkisu, Zainab da Asiya yayyan Kawu isma'il da kuma sulaiman ƙanin sa Duk suna asibitin abun tausayi sai tausaya ɗan uwan su sukeyi, Duk ƙannen Alhaji Ammar BN Yasir ne ai, Kowacce mace ta na Gidan mijinta da ƴaƴan su kuma, zumunci ne sai a Hankali tun bayan rasuwar Alhaji Ammar Kowacce ta janye jikinta sai a Hankali kawai, kafin ya rasu Amma kowa ƴaƴan Alhaji Ammar suje gidansa Amma yanzu shiru kakeji malam ya ci shirwa, shi kuma sulaiman shine Autan su Alhaji Ammar ne da ma yake Kula da sabgarsa tun bayan rasuwar sa kuma sai a Hankali Haka dai Hajiya Sakinah tadinga kula dashi,bayan rasuwarta kuma Babu mai kula shi ,kowa yaje gurinsa da buƙata sai yace halin rayuwa, haka dai Duk sukazo asibitin suna tausayawa ɗan uwan su isma'il wanda shi ba bu ruwansa dasu harkar gabansa yakeyi, dagashi sai ƴaƴansa,koda aka ba shi kuɗin marayun ALLAH sunsan za'a rina halinsa da kuɗi, to Amma mece ta su aciki? Ya kankane komai, kuma mutane suna tunanin zai Adana musu dukiyar su Amma ina! Kawu isma'il ya farfaɗo ras Babu abunda zuciyarsa ko gangar jikinsa ya samu, sai dai cikin zuciyarsa sai ƙuna take Masa,sai hawaye yake yi na azaba da na baƙin cikin da yake ciki, yanzu ya zaiyi da rayuwarsa, dukiyarsa ya fece wai!? Lalläi akwai ƙura fa ba bu tsuntsu Basu tarko!? Lallai kam anzo gaɓar da zaice gaba ɗaya kuɗin marayun ALLAH harshi ƴan fashi suka kwamushe musu, in yaso za'a tausaya Masa ai, in yace ya ciyo bashin banki ne, mutane zasu taimaka ma sa ai, tanan kuɗin sa zai dawo, da ma batun kuɗin marayu kam yanzu basa gurinsa ƴan fashi su amshe,ire iren waɗannan zantukan Kawu isma'il yake saƙawa a ransa,duk da halin dayake ciki Amma mugun nufinsa bai barshi ba, dan haka da yayi shirun nan ƴan uwa sai Sannu suke Masa, abokan sa sunata zuwa dubiya da ALLAH ya sauwaƙa,su Hadiyyah sun komo asibitin Suma sunyi murna ganin Kawun su ya farfaɗo sai aikin Sannu suke Masa, haka ma ƴaƴansa su Meenal sunata aikin "Sannu Babah! Suna ta murna kuma ganin jinjina Babah da sauƙi. Koda ƴan jarida suka dawo wajen Kawu isma'il, da jin ta bakinsa, ya Abubuwan suka wakana? Kuma wace irin ɓarna sukai Masa!? Ai Kawu isma'il saiya fashe da kukan makirci! Ya fayyace musu ƙaryarsa wacce da ma ya ƙware a cikinta, yanzu sun talauta ni sun cufeni, ba ma wannan ne abun ji ba, dukiyar marayun ALLAH da take wajensa, ya yi MATA ɓoye na ƙwarai har ita ƴan fashin suka sace shi kansa bai san adadinta ba, da a banki suke gaba ɗaya tsautsayi, ya sa ya karɓo ta ya Adana ta a gida, a she tsautsayi ne, yasa Hakan da fitar rabo, sai ya fashe da kuka! Lallai kam kowa ya tausaya wa Kawu isma'il hatta ƴan jarida,da sauran jama'ar da suka saurari labaran a radio da kuma ma su kallo a tv, anata tsinewa ƴan fashi da tausayawa Kawu isma'il (lallai kam basusan ko wane shiba, bulus zaici kenan? Yaci dukiyar marayun ALLAH yaci bulus kenan?) Su Hadiyyah da Hidayah ma sun tausayawa Kawunsu sunce ba bu komai dukiya ai baƙuwa ce ina Abby? Wanda ya bar musu dukiyar? To mema take amfana musu da dukiyar? Ya babbake ta ya cinye! Yanzu sai a wuta kuma, haka suka tattauna a tsakanin su da suka koma gida tsakanin Hadiyyah da Hidayah da Khadija, da kuma Farouk ɗan Sa'adatu. Ko da Sa'adatu taji batun tsalle tayi ta dire Akan wallahi zai fito daga asibitin ne a kotu zasu rabu da isma'il,dole ya biyata Haƙƙin ƴaƴanta biyar bazata yafe ba, ƴaƴan na ai sun yafewa Kawu isma'il ɗin, nan kuwa gaba ɗaya ta ɗuɗdura musu Ashariya harsu Hidayah ɗin akan jin cewa sun yafewa Kawu isma'il, ɗin tace kuma dole ya fito da dukiyar marayun. Hauwa Alhamdullillahi ta wartsake sai hannu dai, ambata sallama ita dan haka tai tafiyarta gida take jinya acan aka bar sulaiman yana jinyar Kawu isma'il, har Sannan Hauwa bata ce wa Kawu isma'il uffan ba! Haushin sa take ji ma, wannan ba bit ALLAH a ransa kwata kwata ji yadda ya sheƙawa ƴan jarida karyar cewa kuɗin marayu ƴan fashi ne suka ɗauke,a gabanta ya faɗi yadda yayi da kuɗin marayun ALLAH fa, Kuka kuɗin da ƴan fashi suka karɓa guda nawa suke! Kawu isma'il yana lura da ita, sai sannan yatuna fa ya buɗe cikinsa a gabanta fa! Wajen ƴan fashi, subhanallah Amma yasan ai yadda zai ɓullowa al amarin, nata mai sauƙi ne.ita ɗin banza, shi yake aurenta ko itace take aurentasa. Hakanma ƴan uwa su Goggo Aisya da Zainab sun saka ayar tambaya Akan abunda Kawu isma'il ya faɗawa ƴan jarida, Amma kuma ina ruwansa akwai ALLAH dai, ko gaskia ko akasinta isma'il ɗin ya faɗa. Acikin wannan satin da abun ya faru ko wace kafar yaɗa labarai zancen fashin da akawa Kawu isma'il ake faɗa, anata tausaya Masa , ana ALLAH wadai da ƴan fashi, nan kuma ƴan siyasa da masu kuɗi suke ta kai harin tallafawa Kawu isma'il Akan abunda ya sameshi, daka me zai bashi jari zai biya Masa bashin da banki yake binsa kowa dai da inda zai tallafa Masa,kuma Duk ya na dawowa kunnan sa ran sa fes,jin cewa Abubuwan sunzo masa da sauƙi,asiri a rufe, shikenan an rabu(lalläi fans Kawu isma'il kwata kwata bashida imani da tausayi,gani yake yaci bulus Akan Abubuwan da ya aikata Hmm muje zuwa dai) _______Ɓangaren su Zakiyyah kam Alhamdullillahi wajenta mukhtar ya kwana, shikam ABIE yana can wajen Bilkisu, tun daya gama murnar sa,Abban sa yace ma sa ai yanzu ya kwana a gidan ummansa ya kwana a wajen Ammin sa, ya ro kamar an gaya Masa, sai yace "Abbana jan dinga kwana da umma da Ammina ko ina! Ranar kuma da ya wuni wajen Zakiyyah da dare sai ya koma gidan Bilkisu, yabar Umman sa da Abban sa asa amarci kenan!🤣 Kwanan da sukayi Babu komai a cikinsa, sai Ban haƙuri da Zakiyyah ta dinga bawa mukhtar,Akan Abubuwan da suka faru, tana Kuka tana bashi haƙurin, kukan Zakiyyah da biyu na farin cikin dawuwar ta ga mukhtar da kuma yafe MATA da yayi,nan dai mukhtar ya dinga aikin lallashin Zakiyyah yana Kinga bakida lafiya.nace miki komai ya wuce fa! Idan ba haka ba kuma zan shiga fushi dake, so kike ciwon ki ya tashi, ne kinajin abunda likita ya faɗa Akan lalurar ki, "kayi haƙuri Abban ABIE farin cikine ya sani Hakan ba komai ba,ai kaga dole naiwa ALLAH godiya, na nu na Masa cewa nayi taubatun nasuwa! Zakiyyah ta ƙarasa maganar da goge hawayen fuskarta, nan mukhtar ya matso gareta yana lallashi, lallai ALLAH sarki mukhtar yaiwa Zakiyyah halacci ta ko ina,Duk wani abu da tai Masa ya turashi baya, ya bata kulawa ya tausaya MATA halin da ta shiga, ita kam sai aikin godiya takewa mukhtar ɗin, a haka yayi kwana biyu a gidan nata, kuma jikinta alhamdullillahi za'ace, dama cutarta damuwar Rashin mukhtar, da kuma yunwa, da Rashin kulawa gareta, yanzu kuma Duk ta samu, Kunga sauƙi ya samu kenan, harta Fara Haske da murmurewa a kwana biyun da tayi da komawa gidan mukhtar ɗin, a ranar ne yayi nufin komawa gidan Bilkisu, ita kuma mar atussaliha tace Masa "Zaujin saleh maman ABIE tana buƙatar kulawa, kaga batada lafiya dan haka ka koma gidanta harta kuma samun sauƙi sosai, kaga yanayin ciwonta bayason kaɗaita, dan haka ma yafe mata kwana na harta kuma samun sauƙi, girki ma zan dingayi sai na aika MATA dashi, ta yi hutawarta yanzu ita abar a tausayawa ce! Shi dai mukhtar sai kallon Bilkisu yake jin maganar da takeyi, shin wannan wace irin mace ce? ALLAH yabashi ne, mai Hankali da tunani, a kullum burinta ta ɗorashi a kan hanyar dai dai, yanzu dai ga shi Duk Abubuwan da ya faru tsakanin sa da Zakiyyah, da Rashin mutuncin da tayi MATA farkon Auren su da Mukhtar ɗin, Duk ta tura baya ta rungumi Zakiyyah hannu bibiyu! Matsawa yai kusa da ita da ma suna kan sofa ne! Rungume ta yayi tsam a kirjinsa Duk da haka da yayi da dabara ne, saboda halin da take ciki,hannun sa ya kai ya ɗago fuskar ta suna kallon juna! "ALLAH yai miki albarka mar atussaliha, ya sauke min ke lafiya, ya haɗe mun kanku keda Maman ABIE, ALLAH ya Kaɗe fitina tsakanin ku, ya canzawa Zakiyyah halayenta, yadda Kika ɗauketa itama ta ɗauke ki ko sama da haka ma,tasan cewa yanzu ɗaya kuke, Hakan shine zai faranta min raina!"ALLAHUMMA AMEEN zaujin saleh in Sha ALLAH zaka samemu fiye da yadda kake tsammani ma, saboda yanzu maman ABIE ya haƙura da komai, ta yadda yanzu gaba ɗaya tayi Sanyi! Bilkisu ta faɗa tana dafa hannayen mukhtar da suke kan kumatun ta daya tallafe MATA su, Hakane mar atussaliha ina fatan Hakan, Amma kuma zancen girki da kikace Zaki dinga yi, yanzu Kinga ke ma kina neman hutu fa!? Ki dai barta da dingayin nata kema kiyi naki ko!? "Nidai ka barshi zan dingayi ka ji Zaujin saleh! Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa da nuna alamun rarrashi! Mukhtar ya ce "shikenan Mar atussaliha ALLAH yai miki albarka, na yarda na Amince, dan innasan ban Amince ba zan sani ne, fushi ma ya isheni, ya faɗa yana lakace mata hanci da murmushi a kan fuskarsa! Yawwa nawan naji daɗi Bilkisu ta faɗa itama da murmushi a fuskar tata ta na kuma rungume mukhtar a Hankali. Kamar yadda Bilkisu ta faɗa haka akayi mukhtar yana kwana gidan Zakiyyah yana ba ta duk wata kulawa,jiki Alhamdullillahi, da safe da rana da kuma daddare Bilkisu ta na girki itada Husna, har sannan ta na Gidan, saboda da ma ta zo ta taimakawa Bilkisu a aikin gidane,saboda yanayin jikinta, sai da taimako(bazan faɗi ko mene ba kwa gwani kawai, ƙawayen Zakiyyah balle kuyiwa ƙawata wani abu😊) wataran in sunyi girkin ta aika Husna ta kaiwa Zakiyyah wataran kuma suje tare, tun Zakiyyah na ɗarɗar da Bilkisu harta watstsake suna ɗan taɓa Hira abunsu, gwanin sha'awa, da ma ita Husna ai tasan Zakiyyah, tun kafin mukhtar ya auri Bilkisu ɗin,A haka Zakiyyah ta murmure sai da Mukhtar ya daɗawa Zakiyyah sati biyu sannan ya raba musu kwana, kuma Alhamdullillahi Kowacce tayi girki ta na aikawa da ɗaya itama, ga ABIE ɗinsu ko ina yananan sai murna da farin ciki yakeyi. Ko da ƴan fashi suka shigarwa Kawu isma'il an hana a faɗawa Zakiyyah saboda halin ciwonta kar kuma wani abun ya kuma faruwa da ita, anfara samun kanta, shiyasa bata sani ba.sai da ga ƙarshe lokacin da Abubuwan sukayi tsamari zancen yayi yawane taji, koda taji bata wani tada Hankalin ta ba, ta kirasu Hadiyyah take musu zancen, sai sukace hakane saboda,katta ji wani fargaba yasa ba'a gaya mata ba, nan suka gaya nata abunda Aunty (Sa'adatu) tace zata kai Kawu isma'il ƙara, ALLAH ya sauwaƙa kawai tace, sannan tace ita fa da gaske ta yafe Masa, in ya cucesu kuma shida ALLAH, (fans da dane fa Zakiyyah zata ƙyale Kawu isma'il yanzu halin Zakiyyah na wani Rashin mutunci Duk babu tayi laushi, gaɓunta da Rashin mutunci da Rashin kunya Duk sun kwanta dama, lalläi Zakiyyah gidan Sa'adatu ya horaki🤣 ************** Alhaji tallafy ne yake zaune a ƙayataccen flourn gidan sa, yana kallon labarai a television, domin shi ma'abocin kallon labarai ne, anan yake cin karo da taimako ko wasu Abubuwan alkhair da zai tallafa da dukiyarsa ko jikinsa, dan haka baya rabo da Hakan, gefen sa Mommah ce, sai ɗaya sofa ɗin AKEEL da AQEEL suna zaune Suma abunsu, AKEEL ke Jan AQEEL da Hira wanda shi kuma Hakan ya takura shi ne, kunsan dai surutun AKEEL, dan ma yanzu ALLAH yaso AQEEL ɗin yana ɗan saurarar sa ba kamar da ba, "magana fa nake jarabuna! Cewar AKEEL yana daga kafaɗar AQEEL, tsonaka ce da ma tasa shi faɗar wannan sunan, dan AQEEL ɗin yayi magana ne, ai kuwa yayi ɗin cikin ɗaure fuska yana gyara zaman medical glass din da ke fuskarsa, wanda yake ƙara ƙawata Masa fuskar tasa! " Kasan ALLAH ko! Ka ƙara kirana da wannan sunan zan haɗaka da Abbu" nace maka banason wannan sunan yariga ya mutu, tun da jimawa! AQEEL ya ƙarasa maganar da alamun ƙosawa dan kuwa maganar tayi Masa tsayi ne "ALLAH ya wuce zuciyar brother ɗina bazan kuma ba, karka gayawa Abbu yaimun bulala" AKEEL ya faɗa yana dafa kafaɗar AQEEL ɗin, wanda yaci kunu, alamun ba bu raini, ai yana dafa kafaɗar AQEEL ɗin dai kuma murmushi ya ƙwashe Masa, jin abinda ɗan uwan yace cewa, sai fuskar tasa ta ƙara ƙawatuwa da kyau abun gwanin burgewa, Daga Abbu! har Mommah! Suna lura da ƴaƴan Basu na cewa lalläi suna cikin farin ciki, kuma Hakan shine burinsu musamman ma ga AQEEL da yake da matsala da Hakan. Suna tsaka da wannan nishadin ne kuma aka sako labarai, su ma suna saurarar labarai, kamar Abbu ɗin, shiyasa ma suka sauko falour dan su saurara tare d Abbu ɗin, dan nanne wajen saurarar labaransa. Adaidai lokacin kuma aka sako labarai aciki harda na fashin da akayiwa Kawu isma'il ɗin, gaba ɗaya sai falour yayi tsit jin irin ta'addancin da ƴan fashi sukayi na sace dukiyar marayun ALLAH data Kawunsu kuma wanda yake kular musu da ita, dakuma dukan da sukayi Masa shida mai ɗakin sa. Da daga bakin wanad akaiwa fashin sukaji maganar, bayan mai labaran ya faɗi kanun labaran. Sai bayan labarin ya ƙare ne Mommah tace "Abu AQEEL kaji zalunci fa, wannan mutumin ai abun a tausaya ne a tallafa Masa yakamata kaima ka tallafa, naga ma mutane daban_daban suna son su taimaka Masa" mommah ta ƙarasa maganar da fuskantar Abbu ɗin! Sai taga fuskar mijin nata fes Babu alamun tausayi wanda yasaba taɓa fuskarsa a Duk sanda akayi irin wannan ta'asar ko maiamancin Hakan, "Ya isa Ummu AKEEL wannan ba kowa bane illah isma'il, ƙanin mahaifin su Tagwayen nan, da Alhaji wanda yake cibiyata,Kinga ta inda ya ɓullo ko? Da nayi tunanin tunda dukiyar marayun ALLAH ta dawo wajena zan rabu da shi kawai, Amma yanzu tun da tanan ya ɓullo mu zuba mu gani ni da isma'il, na tsani zalunci a rayuwata shiyasa banayi kuma idan na samu mai yi bana bashi da ɗi, musamman ma isma'il, lokaci yayi da zan fito Masa a mutum, Duk wani ƙulli da makircinsa ya zo ƙarshe, Ba Mommah da Abbu yakewa bayani ba, hatta su AKEEL Saida su ka girgiza, dajin batun Kawun su ƴan biyunnan, sai mai da zance ake tsakanin Mommah da Abbu "kajifa Abu AQEEL wai har dukiyar marayun ALLAH ƴan fashin suka sace, yanzu da ba Kaine ƙasa Abbas ya ƙwato dukiyar nan ba shikenan, yaci bulus, Amma ina Dole ya girbi abinda ya shuka, Mommah ta ƙarasa maganar idanta yayi jajur alamun tausayi gasu Hidayah, da kuma ɓacin ga Kawu isma'il ɗin. Alhaji tallafy kam sai kwantarwa da Mommah Hankali yake Akan cewa a yau ba sai gobe ba tun kafin jama'a su Fara tallafawa azzalumi zan fallasa sirrin da ya kasance a ɓoye, isma'il ga Ɗalhat nan gareka, a lokacin da bakayi tsammani ba! Lokacin su AKEEL bayan sun ga ma jimama zancen Kawun su ƴan biyu, sun fice daga faloun zuwa ɓangaren su,su ma su mommah da Abbu dama suka haura, Abbu ya na ce matan in Sha ALLAH zuwa anjima da daddare dake da su AKEEL zan gaya muku wani abu da baku sani ba Akan alaƙa ta dashi, da kuma marigayi ɗan uwansa Alhaji Ammar BN Yasir baki ɗaya, buɗa baki mommah tayi zatayi magana Abbu ya ɗaga MATA hannu akan tayi shiru kawai, akwai anjima ta adana tambayoyinta zuwa jimawa .......... Meyake shirin faruwa da fallasa sirrin da Alhaji tallafy yace zewa Kawu isma'il? Wace alaƙa ce tsakanin Kawu isma'il da Alhaji tallafy da kuma Marigayi Alhaji Ammar BN Yasir? Lallai akwai badaƙala a gaba kenan? Kubiyo oum ARQAM domin ta warware muku cwakwakiyar ✍️OUM ARQAM ce ontop 🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY 40* "Kasan ALLAH Awale mutumin nan yai mana Sharri, abunda mukaje nema bamu samuba,dan ROCI sai da yagaya Mana cewa maƙudan kuɗaɗe wannan mutumin ya cira a bankin Ranar daya ganshi,Amma yanzu 15million muka samu,kuma ya gayawa mana yadda yayi da kuɗaɗen sa,da ma kuɗaɗen marayun daya gaya Mana, Amma shine yanzu yabimu da sharrin cewa wai mune mukayi Masa fashin da bai san adadin kuɗaɗen ba! Da alamar ɓacin rai Snake yake duban yaran nasa duwalle da Awale, Oga kenan ai sai mun ƙara Zuwa wajen wannan tsinannan mutumin,zuwan mu na biyu ba mai kyau bane,dole ya rasa wani abu nasa wanda ya mallaka!cewar Duwalle" Yawwa nawajena ai kai da ma bakada yafiya,kuma ba ai maka ka ƙyale,shiyasa nake Al fahari dakai cewar Snake yana dafa kafaɗar duwalle,mu sake shiri Muje zuwa karo na biyu sunan wannan tafiyar operation haddi,saboda sai mun Masa haddi Akan Sharri dayayi Mana! Dawadaiiiiii oga suka haɗa baki... _________kamar yadda Alhaji tallafy ya faɗawa Mommah bayan sun gama dinner,su AKEEL da AQEEL za su koma part ɗin su ne Abbu ya dakatar dasu da cewa inason zan ɗan tsakura muku alaƙa ta da Kawun su ƴan biyu, sannan kuma banson tambaya ko ɗaya da Zaku min, girgiza Masa kai kawai AQEEL yayi,yayin da AKEEL yace "to Abbu" Dan haka daga kan dining table ɗin cikin falourn suka dawo kowanne ya zauna a kan sofa yana saurarar abunda Abbu zaice, hakama Mommah. AKEELA ta na Gidan Aminatu, Amma Duk da Hakan zan gaya muku yadda abun yake Duk da Abun da ma bai shafi AKEELA yanxu ba tukunnah, daga AKEEL da AQEEL da kuma Mommah Duk sun bawa Abbu Hankalunsu suna jiran abunda zaice,,, " Alhaji Ammar BN Yasir abokina ne tun na ƙuruciya, abunda ba ku sani ba kenan,mun haɗu da shi a secondary school inda abotarmu tayi ƙarfi,muka Zama kamar ƴan uwa, shi kuma isma'il Duk tare mukai school ɗin Duk da dai mun fishi aji, makarantar tun daga primary har senior school a tare ne,bayan kammala secondary ɗin mu mu ka Fara zuwa uni kowanne da wanda yake zuwa har mukayi aure ma, na rigashi Aure gaskiya'har Sannan muna zumunci abunmu, to lokacin da aka haifeku da AKEELA kuma shima yana da Zakiyyah da Kuma Zahra, har kun ɗan tasa Kuma cikin ikon ALLAH sai shima ALLAH yabashi twins Amma duka MATA ni da shi muka ƙulla wani al ƙawari mai tsauri, ba da jimawa ba Zaku sanshi in Sha ALLAH. Sannan kuma ya ƙara aurar wata matar wato Sa'adatu, nasanta farin sani, saboda tare dashi Muke zuwa zance, wajenta, kuma nayi murna da ALLAH baisa mun haɗu ba, da Abubuwan da nake sa ran warware su da Hakan bazata yiwuba To bayan haihuwar ku, a haihuwar AKEELA kuma maman ku ta mutu, kunsan wannan,na Auri Hajiya jimmai, a lokacin kuma ALLAH ya yi rabuwar mu da Alhaji Ammar BN Yasir ɗin saboda haka kawai abotarmu ta lalace Babu mai neman wani tsakanin mu dashi, kuma har sannan akwai Wannan alƙawari da muka ƙulla, ƙarewa ma har mun cikashi. Duk wata yarjejeniya akai munyi shi, da Duk abunda yakamata acikin al ƙawarin kuma tare da isma'il akayi komai acikin shaidu har da shi, alaƙar mu da Alhaji Ammar BN Yasir ta kuma tsauri, Babu mai neman wani,har ALLAH ya azurtashi fiye da ƙima, sannan ya tara yara, nikuma ku ukune kawai,Ko ɗuriyarsa banaji shima bayajin tawa,daga cutarsa har rasuwarsa ban saniba, sai daga baya bayan rabuwarsu da Hajiya jimmai ne ashe itace tai Mana farraku dashi, wai kawai dan tun farkon Aurena da ita bai bada goyon bayaba, saboda ita mace ce Mara kamun kai ko ƙadan saɓanin mahaifiyar ku, to tun sannan saina so zuwa wajen Alhaji Ammar BN Yasir ɗin anan nakejin labarin ALLAH yai Masa rasuwa, kuma itama matarsa ta fari Ummu Ruwan ta rasu, nayi baƙin ciki da Hakan, kuma naje har wajen mahaifiyarsa nai MATA gaisuwa,ita ma sai sannan take mamakin ina na shige tsawon shekaru, ba'a jima sosai ba itama ALLAH yai MATA rasuwa, Duk wata badaƙala da isma'il yake sa dukiyar marayun ALLAH na sani, kawai dai na rabu da shi ne, na yi tunanin da Ya ga Alhaji Ammar BN Yasir ya rasu sai gayawa mahaifiyarsu alƙawarin da mukayi ni da Alhaji Ammar BN Yasir ɗin Amma koda naje wajen Hajiya Sakinah sai naji batayimun maganar ba, alamu sun nuna bai gaya mata ba,ni ma Kuka ban MATA zancen ba, sai kuma ba'a ɗau lokaci ba ALLAH itama yai ma ta rasuwa, naso fasa wannan ƙwai wajen Hajiya Sakinah Amma ina ALLAH baiyi ba, dan lokacin ku na New Delhi, Nima inacan na je dubaku kafin nadawo ta rasu, tun a gaisuwar Alhaji Ammar BN Yasir da muka haɗu da isma'il bai nuna mun wata alama ba,ta cewa wannan alƙawarin da mukayi da Yayansa ya tunamun ba ko na manta,Amma ina sai ya yi shiru abunsa,ni ma Kuma ban Masa magana ba, ku ma tun daga sannan ban kuma haɗuwa da shi ba har yau, zuwan Alhaji, tallafy foundation ma baisan tawa bace, saboda baisan ni da tallafy ba da Ɗalhat ya sanni, buɗe kungiyar Tallafy ma da wata manufata ta buɗewa, kuma sai murna takama ni lokacin da Shi isma'il ɗin da kansa ya kawo Alhajin cibiyar, da ma kuma ina bibiyar lamarunsu sosai, ina son kulasu Amma sanadin Sa'adatu da zalunci ta garesu na dakata bana taimaka musu, komai a kan idona,Shi ma isma'il na fice harkar sa, tun da har shine mai kasa cikawa ɗan uwansa alƙawarin da mukayi kuma shine shaida,tun da ni banyi maganar ba,kuma yasan akwai hatsari Akan ƙin cika Alƙwarin da fallasa komai ma" Alhaji tallafy ya kai iya nan wajen ya na mai ajiyar zuciya da nuna lalläi ya tuna Amininsa Alhaji Ammar BN Yasir da kuma Abubuwan da suke shuɗe tsawon shekaru. Tsakanin Mommah da AKEEL da AQEEL Duk sunyi shiru, suna son ci gaban labarin, da Abbu ya ke ba su sunason jin wane Alƙwarin Abbu da Alhaji Ammar BN Yasir sukayi? sannan kuma meyasa Kawu isma'il yaƙi bayyana wannan alƙawari ga mahaifiyarsu har ALLAH yai MATA rasuwa?mene kuma yasa da ya ga Abbu Bai tuna ma sa da alƙawari tsakanin yayansa da shi ba? Tambayoyin da suke zukatan waɗannan ahali kenan. Dan haka mommah zatayi magana Alhaji tallafy yace ma ta akwai lokaci Aisha, zakusan komai, kunji Alhaji tallafy ya faɗa ya na duban AQEEL da AKEEL waɗanda suka yi shiru, suka shiga tunani daban kuma may be wani abu daban su ke tunawa. Ku Adana tambaya da sauran Abubuwan da Zaku nemi sani akansu, yanzu dai kunsan alaƙa ta da Alhaji Ammar BN Yasir da kuma isma'il ɗan uwansa sauran Abubuwan kum sai nan gaba lokaci shi zai bayyana su, ku tashi ku tafi kuje ku kwanta in Sha ALLAH gobe da ni da ku da Mommah ɗin ku zamuje asibitin Da isma'il yake kwance domin warware sauran batutuwan acan, may ba saina faɗa muku ba shi dakansa zai gaya muku. Haka su AKEEL suka wuce zuwa barci zuciyarsu da Tarin tambayoyi da fatan kaiwa gobe lafiya, shima shi da Mommah sama su ka haura zuciyar kowa da abunda take saƙawa.... ************** Kawu isma'il jiki kam Alhamdullillahi da sauƙi, dan har hannun ya warke sai abunda ba'a rasa ba, itama Hauwa tuni ta warware kuma har sannan ba ta zuwa asibitin dan fushi take da mijin na ta, kuma ta na addu'a Akan ALLAH kar ya bawa masu ikon tallafa Masa suyi, saboda tasan mijinta azzalumi ne sosai, bulus zai ci Akan dukiyar marayun ALLAH, wanda take fatan in Sha ALLAH nan gaba abunda zai sameshi sai ya fi, haka kuma saita tona Masa asirinsa jira ta ke ya fito daga asibitin(ki kwantar da hankalin ki Hauwa ga Alhaji tallafy ga mijin ki nan) Cikin farin ciki Kawu isma'il yake saboda wani ɗan siyasa ya buƙaci Kawu isma'il ya kawo account ɗin da za'a saka Masa tallafin, dan haka ƴan jarida sukayi alƙawarin zasu je asibitin su amso account ɗin isma'il ɗin,dan haka yanzu yana tsammanin zuwan su ne,kamar haɗin baki yau Zakiyyah da su Hadiyyah da Hidayah kai harma Hauwa wanda take da alwashin a yau saita kartawa mijin nata Rashin mutunci da ƴaƴanta, da Sa'adatu(batajin daɗi ma, angamu) Wanda Alhaji gambo ya tursasata Akan ta je ta duba shin, ai komai zata tura baya,darajar Alhaji Ammar BN Yasir da kuma ƴaƴansa zataje, , dan bata taɓa zuwa dubashi ba, kuma yadda ta ga Alhaji gambo ya na lallaɓata shiyasa ta ce zata na asibiti dai ma Sha ALLAH sai shige da fice akeyi, shi kuna Kawu isma'il yana ta zuba idon ƴan jarida zuwa karɓar account number, har ya Fara lissafin Abubuwan da zaiyi da kuɗaɗen, ba bu tension akansa ko guda na wasu kuɗin ƴaƴan Ammar, ________ Sa'adatu ba ta jin daɗi jikinta, saboda rabo da ga ALLAH cikine da ita na Alhaji gambo, gashi ku ma da ma bai taɓa Haihuwa ba sai a kan Sa'adatu ɗin, dan haka yake ta murna kunsan dai ace mutum kamar Alhaji gambo ga MATA uku Amma ba bu Haihuwa sai a kan Sa'adatu ALLAH ya kawo, ku hango min kulawar da zata samu, da riritawa, Amma ku tunamun da Hajiya sahura da Hajiya ikilima da Hajiya suwaiba, aikuwa kam zuwa gidan su sai ya ga dama, ba shi da magana sai ta cikin jikin Sa'adatu zaiyi kaza_zaiyi kaza, har ya Fara tattara dukiya da Abubuwa ya na cewa na Sa'adatu ne da ɗan cikinta, ALLAH ya sa ta Haifa masa magaji, ba damar ya zauna yana magana da su sai ya sako Sa'adatu da ɗan cikinta, hakane ku ma ya sa suka zage damtse Akan aiwatar da sani ƙudiri na su Akan ita Sa'adatu Wanda daga Hajiya ikilima da Hajiya suwaiba da Hajiya sahura suka haɗe kawunan su waje ɗaya, tun da sunga masifar ga ba ɗaya ta tunkarosu, in Sa'adatu ta haihu, haihuwar ma namiji mene makomarsu a Gidan, sun Zama sorry, wannan yasa su ka Fara shige da fice Akan Sa'adatu da ɗan cikinta.... ************* Sai zumuɗi suke ba bu uwa ba bu ƴaƴan na ta dan Haka da suka farka da wuri su ka shirya, ƴan aiki sun share gidan sun gama komai, tafiyar da za'ayi Alhaji tallafy acikin guard ɗin sa har da JIBO,wanda tuni Alhaji tallafy yai Masa registration da Duk wani abu ya ke buƙata ba Fara zuwa school, saboda shine shaidar komai shine ya san lagon abun,da haka suka kama hanya zuwa asibitin da Kawu isma'il ya ke kwance. ___________ mota guda uku ya ɗauka, Alhaji tallafy ya ɗauka, mai tambarin Tallafy 1_30, Alhaji tallafy sananne ne sosai dan haka sai fatan alkhair ake bin motarsa da ita, mota ɗaya shida Mommah ne aciki, sai ɗaya AKEEL da AQEEL,sai kun ɗaya ta guard ɗin sa,ai mutane su na ganin motar Alhaji tallafy ta yi parking a Asibitin nan kowa yake cewa "ba bu shakka kaakar Isma'il ta yanke saƙa, tun da suka ga Tallafy yazo gareshi may be ma ya mayar ma sa da dukiyar sa ta fi ta da,ire_iren zancen da mutane tun daga bakin asibitin suke faɗa kenan, sai ma da Alhaji tallafy ya fito da ga motar shi da Mommah, su AKEEL da AQEEL Suma suka fito haka ma guard ɗinsa, mutane sun cika gurin suna ta wa Alhaji tallafy addu'oi na alkhair da fatan ALLAH ya raya zuri'a, haya niya har ɗakin da Kawu isma'il yake,kuma har zance ya iske su ai Alhaji tallafy ne ya zo wajensa, sai su Hadiyyah da Hidayah su ka Fara murna sunsan Kawunsu ya warke, dan Alhaji tallafy akwai kyauta,shi m Kawu isma'il ya san alkhairin Alhaji tallafy ga al uma, sai wata murna yakeyi ya na da ga kwance, har Alhaji tallafy yasamu Hanyar silalowa ya tawo zuwa ɗakin jinyar Kawu isma'il ɗin, saboda mutane daƙar ya samu hanya, ɗakin yana tumbatse da ƴan uwa da ƴaƴa da abokan arziƙi ,wanda Sa'adatu ba ta samu karɓuwa ba, tun da ta zo dubiyar, in banda su Hadiyyah da Hidayah da sauran ƴan uwa aka gaisa da ita, Amma itada mai jinya da kuma Hauwa matarsa ko kallon su batayi ba, ta na da ga bakin ƙofar Ɗakin, ta na Shan iska dan haka Alhaji tallafy Sa'adatu bata ga ne shiba, to ita da ta sanshi a Ɗalhat wannan kuma Alhaji tallafy ne, dasu AKEEL da AQEEL da guard ɗin sa ke biye da bayansa, har ya danganta ga cikin ɗakin, Kawu isma'il ɗin, ita kuma Sa'adatu ganin mutane sun yawaita a wajen ku ma batason hayaniya sai tayi tafiyarta gida ta hau Agaidata sahu abunta, a dai lokacin ne kuma ƴan jarida suka ƙaraso asibitin su ma domin karɓar account number a wajen Kawu isma'il ɗin......... Ya kuke ganin faɗa Kwan Alhaji tallafy zai kasance? Ga dai ƴan jarida sunzo? Wane sirrine tsakanin Alhaji tallafy da Alhaji Ammar BN Yasir? Wane dalili ne ya sa Kawu isma'il ɓoye Alƙwarin yaƙi sanarwa kowa bayan ya ga ƙasa ta rufe idon mai fallasa sirrin? Da Duk wasu tambayoyin da kuke da su Muje next page kawai........ ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY ONE 41* Ba'a jima ba Sa'adatu ta ƙarasa gida, ba bu kowa a gidan da ma,ya ra suna Asibiti abunsu, zuciyarta sai suya take MATA, dan kuwa tanaji a kafafen yaɗa labarai yadda Alhaji tallafy yake tallafawa marasa shi yabasu jari da marayu, ita ma Akan kanta ba gashinan su Hadiyyah da Hidayah sunacin gajiyar arzikin sa ba, yanzu karatu ya yi nisa, kuma a Hakan kuɗin makaranta da komai da komai shine yake musu, hakanan Alhajin ta shima ga shi yanacan foundation ɗin sa ya samu kulawa,yazama nutsatstsen yaro kamar da, Duk wasu Abubuwa ya daina, yai Hankali yanzu ha kama shirin saukar al ƙur'ani yakeyi da wasu littattafan ba bu ko sisi sai abunda ba'a rasaba,yaronta ya Zama Zakaran gwajin dafi, itakam ba bu abunda zata cewa Alhaji tallafy sai godiya, kenan ya zo fuska da fuska ya tallafawa Isma'il kenan kamar yadda ya Saba,ai kuwa da sake an baiwa mai kaza kai, in yasan wata bai san wata ba, zata ɓullo ma sa ta bayan fage, ai yasan wacece ita! I yunwar cikinsa, a tafin hannunta yake komai, zata ɓullo Masa a Sa'adatun daya santa can baya, "Amma kuma bakya ganin akwai ƙura in Kika ɓullowa isma'il tabayan gidan? Zuciyar Sa'adatu ta bata wannan sar! A daidai lokacin da tunanin ta yazo gaɓar nan! Ajiyar zuciya ta sauke ta na zuba ta gumi wan da ya zamar MATA kamar shine mafita yanzu a gareta. A wannan halin Alhaji gambo ya shigo gidan ya sameta, har yashigo da mota da hour ɗin da yayi Duk bataji ba! Tana tunani! "Haba irin albarka iri na gari"likita fa ya hanaki tunani barkatai, saboda Magajin Alhaji dake cikinki,ai in ALLAH ya yarda namiji ne Zaki Haifa, sai a saka Masa sunan Marigayi Alhaji Ammar BN Yasir ko? Ku ma bazamu ɓoye ma sa suna ba haka zamu dinga Kiransa dashi ko? Iri na gari! Yana ƙarasa Zama a kusa da ita Akan sofa! Yana kai hannu ya na riƙo hannunta, Ai da ma sunan ɗan nan inda amana ai Ammar, Sa'adatu ta faɗi ta na cire hannun ta daga na Alhaji gambo! Sannan ta ce Alhaji kar ya ra su dawo su ganmu a Hakan man, ka san banson Hakan ya na faruwa(kunji ƴar banza kuma) "to iri na gari an dai na, za'a kiyaye kodan saboda magajin Alhaji da ke cikinki, ni fa banson koda da minti ɗaya in miki abunda bakya so, ai ke alkhair ce a gareni, shekara ma wa na ɗauka, ALLAH bai ba ni ɗa ba sai a kanki, aikinga kuwa faranta miki da Duk abunda kikeso ya Zama dole,Yanzu ha ka me kikeso na baki ne? Ni da ma inason kabani kuɗi zanyi amfani da su, yah fa'iza zan ɗan ba wa jari kasan jarinta ya yi ƙasa! aikuwa ba bu musawa Alhaji gambo yaiwa Sa'adatu transfer na 200k ga wannan in da kuma wani Abu ki.... Wayarsa ce ta yi ƙara alamun an kirashi! Hakan ya hanashi ƙarasa maganar da yakeson yi "Hajiya Babba shine rubuce a screen ɗin wayar! Ɗagawa yayi, dagacan Hajiya Babba tai magana"Alhaji ya dai baka da wo gida da wuri ba,ince ko lafiya? Hajiya Babba kenan ban da abinki ai kinsan bana kaiwa iyanzu ban dawo gida ba, ka fin naƙara fita Kuma, ina gidan Sa'adatu ne,dole ku dinga haƙuri da Hakan,kunsan dai ba ita ɗaya ba, ku fa haka kuke zagargar mene abun damuwa? In dai Kunga ban dawo da wuri ba ina wajenta to! Cikin muryar faɗa ya ƙarasa maganar da kuma ka she wayar bai bari Hajiya Babba ta kuma wata maganar ba.! Wacece ku ma take kiranka ne Alhaji? Cewar Sa'adatu ta na wani yatsina ita ga matar so an tawo wajenta, alhalin yau ba a gidanta yake ba ya na can gidansa. Ikilima ce mai kiran Alhaji gambo ya faɗa, Lallai kam meyasa waini sukemun Hakan, sun Mance cikinka nake ɗauke da shi, ne dole abani kulawa, kodan su juyoyine ALLAH bai ba su ba shine,suke baƙin ciki! Sa'adatu ta faɗa tana kishin giɗa a kan sofa ɗin, alamun ko a jikinta, shi kam Alhaji gambo haka ya ce "rabu da su Iri na gari Duk ina kallon take_taken da suke tun samun cikinki, dan ALLAH bai Basu ba sai ke da kikazo Yanzu, zan takawa kowacce birki, dan Akan cikin nan zan iya sallamar su gaba ɗaya,to mene amfanin su gareni, aike kinfiye mun su, ƴan Iska sai dai aci ati kashi shekara da shekaru Alhaji gambo, Amma ba bu amfani! Ai kuwa da yafi sauƙi Alhaji dan Basu da amfani kwata_kwata gareka, riƙi_riƙi da su ko kunya, Kowacce Babu ƙwan haihuwa ai anyi ASARA! Ƙalesu Sa'adatu ina ciki da sune zanyi maganin Kowacce! Ki kwantar da hankalin ki kece Ta gaban goshin Gambo,uwar maganin sa! Alhaji gambo ya faɗa haɗe da shigewa turaka, ya bar Sa'adatu a kishin giɗe,ta na murmushin mugunta na ganin taiwa Hajiya ikilima zarra haɗe da sauran matansa.. lallai Sa'adatu anya bakiyi zalunci ba? ______ Hmm Hajiya kenan bana faɗa miki ba maybe ya na wajen waccen tsinanniyar! Hajiya Sahura ta faɗa ta na mai kallon Hajiya ikilima ba ki a sake! Da alamun mamaki dan Duk wayar da tayi da Alhaji gambo a handsfree ta saka ta! Lalai ne sahura naji zahiri, ai na shaida kuma, Amma wannan kam lokacin cin ubanta ya zo, ƴar Iska waccen a haka zata ƙare, cewar Hajiya ikilima ta na furzar da hucin baƙin ciki, Sai yanzu Hajiya suwaiba ta magana"aini Hajiya mamakin Sa'adatu nake ta iya aure miki miji, Duk irin amintarku da ita ba ta duba wannan ba, in mu rai Mana haka ai dama can ba ma shiri, Amma ke fa!? Ta na kallon fuskar Hajiya ikilima ɗin! Banda abinki suwaiba ni wacece? Kun manta da amintarsu da faccalarta, sunsan sirrin juna fa, kamar miji ɗaya suke aure, Amma daga ƙarshe ba aure MATA miji taiba, nan suke zuwa gidannan da Hauwa kamar ƴan uwa ƙarshe me tai MATA! Ai ta Saba cin amana, Alhaji Ammar BN Yasir ma ai Hakan tai Masa badan ALLAH ya aureta ba,kuma ta zo ta so ta tarwatsa zaman sa shida marigayiya Ummu Ruman har sakinta da yayi, ƙarshe da yake ALLAH yayi da sauran ƴaƴa tsakani da kuma xatai Masa takaba, kuma matarsa ce har a aljannah in Sha ALLAH ai gashi sun zauna! Hajiya ikilima ta ƙarasa musu zancen da sauke ajiyar zuciya ta ɓacin rai karo ba bu adadi. Suma ajiyar zuciya ɗin sukayi, suna saƙa wa da kwancewa. Dan kuwa yanzu tsakanin Hajiya ikilima da Hajiya suwaiba da Hajiya sahura sun ƙulle ga ba ɗayan su, wannan kishin na da sun zubar, mafita kawai suke nema Akan Sa'adatu, ganin zata rabasu da mijinsu, ga shi kuma shekara da shekaru suke tare ALLAH bai bashi Haihuwa ba sai akanta, kuma sunsan yadda Alhaji yake da son yara,komai zai iyayi akanta, da ma ga ta makira ƴar iska,Hakan suka cigaba da tattaunawa tsakaninsu ta yadda zasu wargaza Sa'adatu ta yadda ba bu wanda zai san shirin sune,yanzu aka Fara wasan Sa'adatu kintaro masifa da bala'i ƙarshen ki na cin amana ya zo ba bu wanda Zaki Kuma wa cin amana , Inji Hajiya Sahura tana kallon sauran ƴan uwanta. ************** Alhaji tallafy ya na ƙarasawa ɗakin su Hadiyyah da Hidayah suka Fara miƙa gaisuwa gareshi, ha kama sauran ƴan ɗakin,yau sune ga su ga wannan mutumin mai tausayi da imani!ita ma Hauwa ai ta sanshi lokacin zuwa visiting ɗin Alhaji, sai yau AQEEL ya ga ƴan biyu dai, wanda aketa zancen su kullum yaƙi ci yaƙi cinyewa shi da baki abun magana wato AKEEL,ai kuwa dai a zuciyarsa sai mamakin kamar su da juna yakeyi, ba bu banbanci har muryar kuma,Sai yaji wani abu ya ɗarsu a ransa game da wannan mai yawan maganar, surutu ya na damunsa Amma ita dai gashi bayan gaisuwar da akayi da ita sai surutu sukeyi ita da wata(Husna ƙanwar Bilkisu) sai kallon ta yakeyi ta kasan Ido,ba bu wanda zai kula, idonsa ya kai kan ɗayar a fakaice, sai yaga ta yi shiru abunta bata magana, sai kuma ya ji bata burge shiba(kuji fa ɗan rainin Hankali ba gwanda Hidayah da shi ba) musamman ma da yaji ashe Abbu yasan su sosai ƴaƴan abokinsa ne, ya so yasan babansu, badon Inno(Hajiya jimmai)aida tare ma zasu ta so a gidan su may be, tunanin da AQEEL yake kenan! Shima AKEEL haka yana kallon Hidayah data matsa tsan waje ɗaya, saɓanin ƴar uwarta,Hakan shi ma ya birgeshi, ya na son ya ga Mace mai shiru_shiru Amma aita magana ai Babu tsari ma(kunji fa shi kuma da yake surutun fa kamar lalataccen fanfo,har yake da mun AQEEL) iri iren zantukan da zuciyoyin su suke musu kenan. Tun shigowar Alhaji tallafy ɗakin Kawu isma'il ya sake lamo Akan katifa,alamun dai yaji jiki, Alhaji tallafy ya tallafa Masa,yaji tausayin sa musamman dayaji ana gaisawa da Alhaji tallafy ɗin hayaniya ne daga waje cikin ma anata gaisawa shiyasa bai ɗau murya ba,shekarun da yawa ƴan uwan Kawu isma'il ba su gane Ɗalhat ba, domin kuwa da da yanzu ba ɗaya ba, ga dukiya ga kwarjini, da sauran su, da ma kuma ha kowane yasan Alhaji Ammar BN Yasir da Alhaji Ɗalhat ba. Alhaji tallafy har gaban gadon Da Kawu isma'il yake kwance Yaje, guard ɗin sa da su AKEEL da AQEEL su kam sunan tsaye kamar zamani, su suna tunanin da suka Saba, "Isma'il ya jikin?ashe abunda ya faru kenan? Alhaji tallafy ya faɗa da muryar sa a nutse Tashin Hankali wanda ba'a saka ma sa Rana, ai ko za'ai shekara na wa Bazai Mance wannan muryar ba,Amma kuma ai Wannan sunan sa Alhaji tallafy, may be murya ce ta zo ɗaya, dan ya ka yai saurin buɗe idonsa dan ya gasgata abunda zuciyarsa ta gaya Masa, ai ya na buɗe idonsa! sai ya sauke Akan Alhaji tallafy! Bai san lokacin da ya Miƙe zaune ba, har ya na fa ma ciwon hannunsa, Tare da cewa "Ɗalhat da ma kana duniya? Nai ta nemanka ruwa jallo! Kawu isma'il ya faɗa ya na tsire Alhaji tallafy da idonsa wanda suka firfito waje alamun fa ya na cikin ta shin Hankali, Amma sai fuske a zummar mamaki ne? Hadiyyah ce ta ƙaraso wajen da su Meenal ƴaƴansa su na ma sa tambaya da ma Kawu kasanshi ne? Shi dai Alhaji tallafy ya na tsaye zuciya ta yunƙuro Masa, dan arayuwa ya tsani zalunci da ƙarya da cin amana, wai da ma ya na nemansa ai,Amma bari ya ga gudun ruwan sa, ya ji wace amsa zai ba wa ƴaƴan da sukai ma sa tambaya! Na sanshi man Hadiyyah ai Abokin Abban kune tun kafin a haife ku, ra na tsaka suka rabu aka nemeshi aka rasa,har ba yan rasuwar sa sai neman shi nake Amma ban same shiba, cewar Kawu isma'il ya na ƙarasa gawa su Hadiyyah Amsa! Lallai Kawu ai to shine Alhaji tallafy nan ai wanda ka kai Alhaji foundation ɗinsa ku ma muma shine ya ɗauki nauyin karatun mu, Amma kuma Rashin sani ai da tun sannan kasan shine! Hadiyyah ta karasa maganar da alamun mamakin wannan abu! "Ai Rashin sanine Hadiyyah yanzu ALLAH ba ga shi ya haɗamu ba, sanadin dukiyar ku da ƴan fashi su ka sace,ai dama Haƙƙin marayu ya na da hatsarin gaske, ai ƴan fa shi sun cuce ni kuɗin ku ma da suka sace yafimin ciwo, Kawu isma'il ya ƙarasa maganar da sa Kuka,wai na Duk Alhaji tallafy ya tausaya Masa,Aikuwa Alhaji tallafy zuciya tazo wuya na jin wannan miciyin amanar Shi ma da ace baisan wanene shi ba ai da yakuma damfarar sa, kuɗaɗe . Ita dai Hauwa ta na gefe ta na kallon drama da mijinta lallai ma, aikuwa bazata bari wannan Alhajin ya bashi ko sisi ba, sai ta fallasa sirrin cewa ba ko sisin marayu a wajen sa, ya cinye musu ne,Su kuma da sukaga za ma bana kare bane da kujeru a ɗakin dan Haka guard ɗin suka daukowa Alhaji tallafy ya zauna bai Musa ba ya zauna, dan kuwa ya ga abun isma'il na Zama ne, hakama su AKEEL da AQEEL saƙa musu kujerar akayi ba bu musu suka zauna dan sun Fara gajiya, ga kuma game ɗin da wannan Mara imanin yafara bugawa tsakanin sa da Abbu amma suna jiran su ga waze wining, da kuma fallasa sirrin da Abbu zaiyi. "To marar imani da tausayi! Duk halin da marayun ALLAH suke ciki ƴaƴan Aminina ina sane da shi, da Duk wani zalunci da ka musu, na sani, ba tun dukiyar marayu kuma da kace ƴan fa shi sun sace,su na wajena ni na saka guard ɗina yin hakan tun da bakada imani da tausayi, Duk da Hakan kuma shine baƙin nufinka bai ƙalesu ba,yanzu ma zaka ku ma zaluntar su na cewa ai harda kuɗin yan fashi suka kwamushe,anata haɗa maka kuɗi,to yai asirinka ya tonu! Alhaji tallafy ya ƙarasa maganar ya na du ban fuskar Kawu isma'il wanda shock ya baibaiye jikinsa, shin waya gayawa Alhaji tallafy wannan sirrin nasa, ko dai ƴan fashin da sukazo Alhajin ne ya kawo su? To Amma kuma ai yadda ya faɗa tun kan zuwansu,ya san da sirrin, kamar ruwa yaci Kawu isma'il haka yayi ya yin da Hauwa ta fashe da ku ka ta sa ba ki acikin maganar,Alhaji isma'il azzalumin mutum ne wanda kuɗi ba bu abunda kuɗi baza Susa ya aikata ba, ni ma yau nake da shirin fallasa asirinsa, dan kuwa agaba ya fayyacewa ƴan fashi cewa ai kuɗin marayu ya Sanya Hannun jari dasu kuma yanzu ba bu an damfareshi,da kuma kuɗin sa shima ya yo oda daga china jirgin ya nuste a cikin ruwa, ga bashin 30million da ya karɓo a banki, ya bada 15million zai sai mota nan ma an gudu da kuɗin, ragowar 15millions din shine ƴan fa shi suka zo suka saceta,Amma ya buɗi ba ki ya na ƙaryar har ita ƴan fashi suka sace, tsakanina da isma'il ALLAH ya isa bazan taɓa yafewa ba,Hauwa ta ƙarasa maganar cikin Kuka gwanin tausayi! Ai ɗakin sai aka ɗau salati dafa yara har manya,su kam su Hadiyyah da Hidayah da Khadija da kuma Amarya Zakiyyah sai Kuka suke ga ba ɗaya najin yadda Kawun su ya ƙware a zalunci! Ashe da ma kudinsu salwantar musu yayi, Amma yace ƴan fashi ne suka sace, Zainab da Asiya yayyan Kawu isma'il ɗin sai Kuka suke suna tsine Masa albarka! Gogan na ku ganin asirinsa ya to nu sai ya sunkuyar da kansa gwanin tausayi, su kam su AKEEL da AQEEL mutuwar zaune sukayi jin zalunci na wannan mutumin wanda a fuska kamar bazai aikata b. Guard ɗin Alhaji tallafy ne sukayi gyaran murya Akan a saurara Alhaji ya na magana!aikuwa tsit akayi anason jin ƙarshen zance. Jibo ne ya fita mota ya ɗauko wayar da sukayi kowanne alaƙa ta yadda Kawu isma'il ya amince Akan tura zunzurutun kuɗin nan,alhali bai san shi na, jita_jita ne bai tabbatar da shine Alhaji Abbas ba mai hannun jari na ƙasar japan,kawai ya amince dan ya ga ba kuɗin sa ban,Duk Saida JIBO ya karanta musu a bayyana yadda suka ƙulla alaƙa,da kuɗin da ya tura ɗin. Alhaji tallafy ya yi ajiyar zuciya yace kunji halin wannan marar inanan,dan marar imani zance masa, wane irin ga ta ne Alhaji Ammar BN Yasir bai Masa ba,ni shaida ne,Amma shine dan ya ga ƙasa ta rufe ma sa idanu shine ya ci amanar sa, Cewar Zainab yayarsa ALLAH wadaran ka isma'il,su dai su Zakiyyah sai Kuka kawai sukeyi su na tausaya rayuwarsu, da irin halin Kawunsu. Nadawo gareka azzalumi! Meya hanaka fallasa sirrin da mukayi tsakanina ni da Alhaji Ammar BN Yasir!?ba ka gayawa Hajiya ba tun ba yan rasuwar Alhaji Ammar ɗin? Ko Haramci kake so a aikata nan gaba? Alhaji tallafy ya faɗa cikin ƙaraji idonsa ya yi jajur( sai ya zamar mun kamar AQEEL fa)ya na duban Kawu isma'il da jikinsa ya yi Sanyi, ya sunkuyar da kansa ƙasa, alamun ruwa ya ƙarewa ɗan kada! Da ma nasan bazaka iya magana ba, ai da kunya ace Kaine ka aikatawa ɗan uwanka, wanda komai na gata yai maka shi, Amma ƙarshe kaci amanar sa da ƴaƴansa, wajen salwantar da dukiyar su. Duk zaluncin ka da Mugun halinka ai dai ka faɗi wannan sirrin, ko da kaga ban bayyana ba, ko wani abune ayi Amma ina ka ƙiyin Hakan, hatta Mahaifiyar ku ka ƙi faɗawa, ni yau zan fallasa sirrin shine waɗannan ƴaƴan Hadiyyah da Hidayah surukai na ne, ma'ana da Aure tsakanin su da ƴaƴana AKEEL da AQEEL Yanzu, haka a matsayin matansu suke su kuma mazajen su,Amma ya ƙi faɗawa kowa ku ma bansan wace manufa ce da shi Akan Hakan na............. Turashi fans. Ya haka kuma? Wata sabuwa lallali tsugunne bata ƙarewa ba ana wata ga wata kuma ya abun yakene ni Rãbiat🤔 ta yaya akayi Hakan kuma?ankuma kenan mace ta Haifi mace Muje zuwa dai......... ✍️ oum ARQAM ce ontop 🥰 2/7/24, 4:30 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY TWO 42* A lokacin da Alhaji tallafy yakewa Kawu isma'il wannan tereren ne kuma ƴan jarida sukayi wa ɗakin dirar mikiya,dan ALLAH Alhaji tallafy yaiwa guard ɗinsa JIBO nuni akan cewa su tsaya,daga waje ya na ganawa da marar lafiyar ne,Yan jarida dai sunsan Alhaji tallafy ba bu musu kuwa suka koma can gefe, suna jiran fitowar ne,su na ALLAH yasa su ma ya washesu da kuɗi kamar yadda zai washe majinyacin( A naku tunanin kenan, Amma shi kam Alhaji tallafy wankin babban bargo yakewa majinyaci). Meyasa baka gayawa ɗaya daga cikin ƴan uwanka, cewa ƴan biyu suna da Aure tsawon wannan lokacin!? Alhaji tallafy ya kuma jefawa Kawu isma'il tambaya ya na tsire shi da idanuwansa wanda sukayi jajawur alamun ɓacin rai! Shi dai kawu isma'il muzanta iya muzanta ya shata! Dan Haka ya kasa ɗago idanun sa ya dubi Alhaji tallafy ɗin! "Ka ɓude baki kai Musu bayanin komai, da ma saboda kai kasan wane ƙulli ne a zuciyarka da yasa ka ƙi fallasa sirrin! Sannan wannan cinye dukiyar marayun ALLAH dakayi bansan meyasa ba? Ko da yake zalunci ne ai yasa! Alhaji tallafy ya faɗa ya kallon Kawu isma'il ɗin a karo na barkatai! Su kam ƴan ɗakin har sannan Basu dawo daga suman wucin gadi da sukayi ba najin cewa Ƴan biyu suna da Aure! Balle kuma masu gayya masu aiki Hadiyyah da Hidayah ɗin, Kowacce idonta a zare yake gwajin tausayi! Balle ku ma su AKEEL da AQEEL su ma sock ɗin ne tare da su,to yaushe akayi Hakan amma ba su sani ba! Sai Alhaji tallafy yai wa Kawu isma'il ɗin ya fayyace musu wannan sirrin na Auren ne ya sa suka dawo hayyacin su domin suji yadda Abun ya faru... Cikin murya na rawa da alamun kunya Kawu isma'il yace "tabbas hakane kamar yadda Alhaji ya faɗa sirrin da ke tsakani Alhaji tallafy da yayana Ammar shine... isma'il tsakanina da Ɗalhat munyi alƙawari cewa zamu haɗa su Hassana da Hussaina ta da Hassan da Hussain na sa Aure, saboda mu ƙara danƙon zumunci da ke tsakaninmu, kuma kasan ina son twin's tun bayan da aka haifawa Ɗalhat ɗin, to ni ka ashe ALLAH yasa Nima zan samu nawa, kaga cikin ikon ALLAH sai gashi yabani ya bashi kuma kowane iri ɗaya, ka ga idan muka haɗasu Aure abu zanyi armashi zai to albarka in Sha ALLAH,Duk da dai yaran na mu ba wani girma sukayi ba, dududu Shekarar su Hassan din tara ne, sukuma su Hassana huɗu,haka yaya ya sameni yake gayan bayan sun gama magana dakai, Kawu isma'il ya faɗa yana kallon fuskar Alhaji tallafy ɗin kafin yaci gaba! Ni kuma nace "tabbas hakane yaya wannan abun ai ba wani abu bane, aure baya ƙanƙanta, musamman ma kune iyayansu su kune maɗaura aurensu, in yaso idan suka girma sai a faɗa musu, kawaii, Yaya yacemun" yawwa isma'il ka fuskanceni kenan inaso ka Zama shaida ne, saboda halin rayuwa,yau gareka gobe ga ɗan uwanka, in Sha ALLAH gobe zamu haɗu da kai da Ɗalhat ɗin sai mu ƙarasa maganar ka ji ɗan uwana,Haka muka ga ma wannan maganar dashi, ni nayi gidana shi ma ya tafi gida. Kamar yadda ya faɗa a washe gari muka haɗu dakai, a masallacin da kuke Sallah bayan an idar da Sallah, kuka yiwa Malam liman magana Akan kuna so a daura Aure da yaranku, Amma yarane sosai, shi kuma malam liman ya tambayeku Hakan bazai Zama an tauye Haƙƙin yaran ba, kar su girma kuma basason junansu, sai Kuka ce in Sha ALLAH Hakan bazai faruba, dan kuwa zakubi Duk hanyar da Zaku saka shaƙuwa tsakanin yaran na ku,har su Fara son junansu in yaso idan lokacin faɗar yayi cewa an Ɗaura musu aure baza'a samu matsala ba,malam liman yai adduar alkhair, dan haka Kuka ce ba sai mutane sun san da ɗaurin Auren ba, in ya so ALLAH yakaimu suka ƙara girma mutane sa sani,in aka tashi shagalin biki. kai da ɗan uwanka khalil, nikuma nida yaya aka Ɗaura Auren a wannan lokacin,kamar yadda addinin musulunci ya koyar, na dubi fuskar ka data Yaya ba bu abunda yake fita sai murmushi, kai kace Auren da aka Ɗaura na manya ne...Kawu isma'il ya ƙarasa fallasa sirrin muryar sa ta na rawa( bansan meyasa Hakan ba tunawa yayi da ɗan uwansa? Ko kuma nadama ce ALLAH masani) ALLAHU AKBAR! ALLAH yajiƙan Yaya Ammar Yasa aljannah makomarsa Cewar Zainab da Asiya yayyan Kawu isma'il ɗin, Amma ko meyasa bai faɗa Mana ba ar Hajiya oho! Sai ya faɗawa azzalumi irinka, kai ka baka faɗaba, ALLAH wadaranka isma'il, cewar Zainab ta na share hawaye, da ka bari kenan yaran nan su dinga kula Samari kasan da aurensu, sannan inta ka ma kuma a Ɗaura musu aure, kai wane irin azzalumi ne Wai isma'il, ai dai kasan Aure kan Aure haramun ne, sannan mace da Aurenta ta kula wani namijin, ai shima Haram ne ko? Asiya ta kuma faɗar Hakan Duk suna kallon Kawu isma'il wanda yayi abun tausayi kamar ruwa ya cinye shi, to rai wajen Ashirin kowa kallon sa yakeyi, ga uban abun kunya ace asirinsa yanzu ya tono, ai da kunya kuma a gadon asibiti, shi da take tunanin arziƙin sa ya zo,sai tonon silili ku ma ya sameshi, da jin kuna kaicona! Ni isma'il ya haka kuma! Sai ƙwalla nagani a idon su Hadiyyah da Hidayah bansan ko na menene ba! Na tuna Abbi ne ko kuma kukan Auren sa ke kan su ne oho! AKEEL da AQEEL ma fuskarsu ba bu ya bo ba bu fallasa, dan ko shi AKEEL ɗin mai sakin fuska gani nayi fuskar ta Zama iri ɗaya data AQEEL, shi ta AQEEL ku ma sai tafi da can kafin yafara sakewar nan ko mai Yasa Hakan oho? Kubiyo oum ARQAM a Sannu. ALLAH sarki Hauwa idanuwa sunyi ja jur alamun anata Shan Kuka, da kuma tunanin wane irin miji ALLAH ya haɗa ta dashi ne? Alhaji tallafy dai ya na zaune har sannan a kan kujera ko da Kawu isma'il yazo ƙarshe a zancen sa Banga canzawar da yayi ba, to mene bai sani ba fans? Amma meyasa to isma'il kasan da Duk wannan Amma baka faɗawa kowa wannan sirrin ba? Bayan mutuwar Alhaji Ammar BN Yasir ɗin? Tun da baka ga alamun ya faɗa wa Hajiya ba ma? Dan inda sun sani tun a zaman taaziyyar sa zakaji ana zancen, Hajiya ma Zaku iya zancen da ita Da sauran ƴan uwa? "Ka gafarceni Alhaji tun bayan ɗaurin Auren da akayi ba'a ɗau wani lokaci ba gaskia,yaya bai kuma mun zancen kaba, kuma ban kuma kin ɗuriyarka ba kaima, da naga haka Yaya yaci gaba da harkar sa, Nima kam mene nawa aciki? Yaka aka ɗauki shekaru har ALLAH yaiwa Yaya rasuwa, banji anyi zancen AUREN ba, ni ma Kuma ban yiba,har ALLAH yaiwa Hajiya itama rasuwa,Lokacin ma ai ƴan biyu sun Zama ƴan MATA,har sannan dai kuma Banga alamun ma suna kula wasu samari ba, harna auri Sa'adatu nai zaman gidan na su Banga alamun suka kula Samari ba,sai a ƴan kwanakin nan kuma, cikin bikin ƴar uwarsu, suka samu ƴaƴan manya, Anan tunanina Ya sauya tun da kai dai ba'a gan ka ba, kuma ba bu wanda yasan da wannan auren sai malam liman, kuma ALLAH yai Masa rasuwa tuni, kuma yaran ƴaƴan manya ne, tun haduwarsu da su Hidayah su ka faramun alkhair na kuɗi, shiyasa kawai nayi watsi da wannan auren nasa wannan agabana, saboda nasan na warke yaran marayu ne ba bu uwa ba bu uba, nine dai wanda za'ai wa alkhair sanadin su... Kawu isma'il ya ƙarasa maganar yana sunkuyar da kai alamun Rashin kyautatawa ga furucinsa! "ALLAH kuwa ya kyauta maka isma'il, kaikam bansan kuɗi wane irin so kake musu ba, Akan kuɗi kaketa saɓawa mahaliccinka zaka Ɗaura Auren kan Aure, ga cin amana dakayi nacin dukiyar marayu, da Haƙƙin zumunci, Duk dai Akan kuɗi ALLAH yasa dai wannan tonon sililin yazama izina gareka, ya sauya ma ka halaye, Amma ASARA kayita isma'il ta Rai bata kuɗi ba! Alhaji tallafy ya faɗa yana duban fuskar Kawu isma'il ɗin Sai sallallami ke tashi daga bakunan ƴan uwansa, Kuka gasu Hidayah da Hadiyyah, su ma ku ma su Zakiyyah da Khadija ba'a barsu a baya ba, hakama sauran abokan arziƙin da suke wajen.. "Haƙon ka bai cimma ruwa ba kam, dan Mus'ab zubair Ƙaraye da Mahmud kabir Duk ƴaƴan abokaina ne, kuma abokan su AKEEL ne shima kansa mijin Zahra Abokin su ne, Duk shirina ne, saboda ya ran ja fuskanta basa kula wasu samarin, shiyasa nasamu Mus'ab da Mahmud Akan su dinga kular mun da su, azummar su na sonsu, su sa musu sharaɗai,banda kula maza su nuna musu sunada kishi, da sauran su,nace musu ƴaƴan abokina ne, shine nakeson suyi muni wannan aiki, nan danan suka amince kuwa, dan yara ne masu nutsuwa da tarbiyyah,sai da suka Fara zuwa wajenka neman izinin zuwa zance, na zata sasuzo suce ka ce Musu ai yaran matan Aure ne Amma ina, sai kace gasunan ALLAH ya Tabbatar da alkhair, kuje wajensu nabaku izini, Hakan kuwa yai mun ciwo, jin ka wulaƙanta Auren yaran, saboda kuɗin da yaran sukazo maka dasu ko money mangal? Alhaji tallafy ya ƙarasa maganar da tambaya ga Kawu isma'il ɗin! Shi kam Kawu isma'il bai magana ba dan yasan cikin maganar Alhaji tallafy ba bu ƙarya! Anan dai Alhaji tallafy yaiwa kawu isma'il fallasa irin wanda bai taɓa tunanin za'a yi Masa a Duk irin abunda ya shuka da zalunci a tsawon rayuwar sa ba! Kar ya ta ƙare kenan bori ya Kar boka! Da zancen makarantar su Hadiyyah da Hidayah da kai Alhaji tallafy foundation da akayi Duk Alhaji tallafy yace Duk acikin Shirin sane, na kyautatawa iyalan Alhaji Ammar BN Yasir ne da kuma, tsare Auren yaransa dake kansu ne! A farkon haɗuwar su da irin gararin rayuwar da suka tsintsi kansu sanadin zaluncin isma'il da kuma na Sa'adatu ga su Hadiyyah da rabuwarsu da juna na tsawon shekara,Duk ya tausaya musu kuma yayi baƙin ciki da Hakan. Ƴan uwa suna ta godiya ga Alhaji tallafy ga irin jajircewa da yayi Akan iyalan abokinsa. Shi kam Alhaji tallafy sai murmushin ƙarfin Hali yakeyi, da nu na Babu komai ai shida marigayi akwai Amana ai. Kawu isma'il dai ba bu bakin magana idon sa ya yi jajur, abun gwanin tausayi, Hauwa kam ba bu musu race " a yau ba sai gobe ba dole ka sakeni bazan zauna dakai ba azzalumi, ba bu wanda yayi magana jin furucin Hauwa, ganin ta na tujara ne Kawu isma'il yace na sake ki Hauwa fa kikace?! bazaki tausaya min ba!? A halin danake ciki ba? Wallahi na yi nadama!? Kawu isma'il ya faɗa idonsa yana taruwa da ƙwalla! Kai kasan wannan nadamar ba ni ba komawa cikin gidanka,har abada! Ka ƙaraci tsiyarka! tun da kai azzalumi ne, zaluncinka ya yi yawa! Hauwa ta faɗa gwanin tausayi tana share hawaye, Meenal ce kawai a Asibitin dan haka ta riƙe hannunta ta fice daga ɗakin tana sharar hawaye! Suma su Hadiyyah da Hidayah kukan suke hakan Mommah, wanda tun da sukazo batayi magana ba kuma batayi motsi ba, jin irin waɗannan ƙulle ƙullen da Kawu isma'il ya aikata da zalunci, gurin su ta je ta na mai rarrashin su Akan su daina kukan, sai Shafa kansu takeyi, kamar ruwa ya cinye su shirun sukayi, tunda Mommah tai musu magana! AKEEL da AQEEL da suka Zama mutum mutumi basusan meke faruwa ba, saboda hankalin su sun tafi hutu, har sannan kuma na su dawo ba, Alhaji tallafy ya Miƙe alamun sai fice Hakan yasa guard ɗinsa su ma miƙewar haɗe daiwa su AKEEL magana cewa zasu wuce,har sannan ba bu nutsuwa tare da su haka suka fice daga ɗakin su ma,zuwa mota. Kafin shigar Alhaji tallafy mota sai da yasamu ƴan jaridar nan ya fayyace musu komai, na cewa Kawu isma'il ƙarya yake Duk abunda ya faɗa musu a baya, dukiya ba ƴan fashi bane suka sake ba, hannun jari yasaka ALLAH yaso shine, da tuni yai cuci marayu, kuma yaiwa ƴan fashi Sharri!, ƴan jarida an samu abun da akeso dan haka suka, suka naɗi muryar Alhaji tallafy, sannan suka ɗunguma ɗakin da Kawu isma'il yake dan su kuma samun tahoto,bayan sun yi sallama da Alhaji tallafy ya shige motarsa zuwa gida. Da ma kuma fitar Hauwa Saida ta samesu da ma tai magana dasu Akan ƙarya mijinta yake nacewa ƴan fashi sun sace dukiyar marayun ALLAH, da Duk wani tuggun da ya ƙulla,aikuwa suka naɗi muryar ta, ga kuma Alhaji tallafy shi ma ya kuma. Aikuwa ƴan jarida sun samu abunda sukeso, dan Aunty Zainab da Asiya sun bayyana musu komai su ma,su dai su Hadiyyah basuyi magana ba da sauran ƴan uwanus, dan kuwa koma dai menene ai Kawu isma'il ɗin Kawunsu ne dan uwan mahaifinsu baza sosu abunda zai tozarta ba Duk da shine ya janyowa kansa ɗin,Amma su kam ba bu bakin magana Zakiyyah ma batayi magana ba, Daga ƙarshe Kawu isma'il suka dangana gareshi, waƙa abakin me ita kenan, nan cikin Kuka kuwa da nadama tare da shi, ya warware gaskiyar zancen cewa ea hakanne Sharri yaiwa ƴan fashi, Amma yayi nadamar Duk abunda ya aikata. ƴan jarida na fita daga ɗakin kuwa kowa ya watse a ɗakin su Hadiyyah su aunty Zainab kowa ya kama gabansa, zuciyarsu ba bu daɗi kowa ya ci Kuka. An bar Kawu isma'il shi kaɗai a Asibitin, wanda sai ku ka yakeyi gwanin tausayi! Ai kafin kace mene yan jarida sun yaɗa zancen ko ina ya ɗauka cewa wannan wanda akaiwa fashin da yace sun sace dukiyar marayun ALLAH ƙarya yakeyi, sai tsinewa Kawu isma'il jama'a sukeyi, kafin dare ai sai zuwa ganinsa akeyi Ido da Ido ana ALLAH wadai gareshi, sai da likitoci duka ga abun zai wuce ƙima ne suka hana kowa zuwa wajensa. Wannan kukan da Tashin Da Kawu isma'il yake ciki ne ya sa jininsa Hawa, kafin kice me zazzaɓi ya kamashi, ba bu Shri likitoci suka ma sa allurar barci ko ALLAH yasa ya samu sauƙi..... ALLAH sarki Kawu isma'il yaban tausayi sosai yasin🤧 Meke faruwa ne AKEEL da AQEEL🥲 Kuma su Hadiyyah da Hidayah hakan🤔 ALLAH sarki Hauwa🤧 Muje zuwa ƴan Amana akwai sauran tafiya fa ✍️OUM ARQAM ce ontop 🥰 2/7/24, 4:30 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY THREE 43* "Mukhtar ne ya zo ɗaukar Zakiyyah da Husna, daga asibitin, saboda da ma haka suka shirya, shine zaizo ɗaukar su,dan ita Bilkisu batazo ba, anyi nauyi sosai Zama daƙar tashi daƙar sai fatan sauka lafiya. Ya na ganin halin da su Hadiyyah suke ciki,kawai sai yace bari ya sauke su gida,in ya so sai Suma su tafi gida, ba bu wanda baya ku ka acikinsu har Husna ma,wanda ita tausayin rayuwarsu ne yasa ta ku kan,suna ta fe a mota sai ku ka kawai suke, Musamman Zakiyyah itama fa ta iya ku ka,abu kaɗan ke sata kukan, shi dai mukhtar sai suyi haƙuri yake ce musu Amma ina! Kamar tunzura su yakeyi,ku ma ya tambayi ba'a si ba bu shi,dan haka yasa a ransa ko mene dai ya faru wannan abun yanada zafi gaskiya,in Yaje gida Zakiyyah ta wuce ya tambayeta yaji. Har suka je gidan su Hadiyyah har sannan suna kukan, dan haka kawai mukhtar bai bar Zakiyyah ta shiga gidan ba,yana parking suka buɗe murfin motar sukai cikin gida,shi ma yaja motarsa sai gidansa. Sannan ku ma har Alhaji gambo ya fita,dan haka Sa'adatu suka iske ita ɗaya a gidan,ana Hakimce a kan sofa, bayan angama ƙullawa su Hajiya ikilima makirci, shi dai Alhaji gambo hankalinsa ya gushe kwatakwata,kuma fans kunsan dai mutumin da bai samu Haihuwa da wuri ba,koma mene zai iya aikatawa ace matan da suke tare ba sune suka samu cikin ba Auren daya ƙara ne,ai Kunga sai anyi uziri, musamman ma ace irin Sa'adatu mai kissa da kisisina ce ALLAH ya haɗa shi da ita, ai fanfo zata kuma Masa, ta dulmiyar dashi,Akan zautuwar da yayi, to Sa'adatu ma tayi kissa haka kurum balle kuma ta samu abun kissar,yanzu ma tunanin da take kenan,wane makircin zata ƙulla ne da zaisa Alhaji gambo,ya sallami su Hajiya ikilima ne? Ta Zama ita kaɗai, musamman cikin nan dake jikinta,in ta Haifi namiji ai shikenan,kaakarta ta yanke saƙa, komai na dukiyar Alhaji ya zama nata, sai yadda ta ga da ma,in ya mutu kuma shikenan da ma ba bu mai sisin kwabo aciki,lallai wani hanin ga ALLAH BAIWA ne,in isma'il ya cinye mun gadon su Alhaji, wannan fa, shi ma dan ba yadda zanyi ne, Amma koya ne zan maganin sa! Zancen zucin da Sa'adatu takeyi kenan ta na daga zaune! Shi yasa batasan su Hadiyyah sun shigo ba, Da su Hadiyyah su ka shigo gidan ai sai suka ƙara ƙarfin kukan su,su na shigewa ƙuryar ɗaki gaba ɗayansu! Sai sannan Sa'adatu ta dawo hayyacinta, da ga zuzzurfan tunanin da takeyi,wanda likita ya hanata yi,saboda ya na shafar lafiyar cikin dake jikinta da ku ma damuwar da tasawa kanta a ƴan kwanakin nan wanda bamusan mene yake damunta ba? "Zuciyarta ce ta wani irin bugawa jin su Hadiyyah sun shigo su na Kuka,dan haka harda tuntuɓe da bakin ƙofa wajen shida ɗakin na su, dan ta ji meke faruwa?ko dai wani abunne ya faru?to ai ko da ta tawo lafiya ƙalau ta barosu,su na wasa suna dariya, tana wannan zancen zucin ya ƙarasa ɗakin! "Ku kuma lafiya kuke?Zaku shigowa mutane gida ku na Kuka? Sa'adatu ta faɗa zuciyarta cike da tararrabin abunda zasu faɗa MATA! Hadiyyah cikin ku ka tace" wai Aunty ashe wannan Alhaji tallafy ɗin, Abbi ya sanshi,Wai kuma ƴaƴansa tuntuni aka haɗamu Aure dasu tun kafin mu girma" Hadiyyah ta ƙarasa cikin Kuka! Ai Sa'adatu batasan lokacin da ta zauna ba bu shirba, dan cikinta yai wani irin juyawa wacce ta fice ƙima! Da rawar baki Sa'adatu tace"ban.ban..ban...gane me kike faɗa ba Hadiyyah? Abokin Abbi kuma?An Ɗaura muku Aure da ƴaƴansa? Lallai kam Ɗalhat ne ai! Sai sannan Hidayah tai magana "Aunty kinsan da ma komai Amma ki ka ƙi faɗawa kowa?! Ita dai Sa'adatu batasan me Hadiyyah tace ba, saboda su man wucin gadi ta tafi! da azabar da mamarta take MATA! Dan kuwa wannan ta shin Hankali ne wanda ba'a saka Masa rana ba!da tunanin ya Hakan ta faru kuma! Tunani ta lula na yadda abun ya faru..... Abbi ya shigo gida ranar Sa'adatu ce da girki ba yan ya kammala Abubuwan da ya sabayi, ya Kira Ummu Ruman da Sa'adatu ya haɗa su waje ɗaya a falourn sa, Anan yake faɗa musu cewa shi da Ɗalhat sun haɗa aurensu Hadiyyah fa yau ɗinnan, kuma da isma'il akayi komai, yana son a dinga kai su Hadiyyah gidan Suma su AKEEL adinga kawo su nan,tanan za'a samu shaƙuwa tsakaninsu wanda ko da sun girma za'a iya samun daidaito tsakanin su kawai sai a bayyana, to tun daga sannan kuma ba'a jima sosai ba, alaƙar dake tsakanin Abbi da Ɗalhat tai Sanyi, suka daina alaƙa, tun daga sannan kuma komai ya tsaya, bayan rasuwar Abby kuma ita bata faɗa ba, balle Ummu Ruman kuma da tun bayan rasuwar Abby ɗin itama ta haɗu da lalurar ajali, tana ta lafiyarta ba ta faɗawa kowa ba, kuma bataga alamun ansan da zancen Auren ba dan da cikin zaman jana 'izar Abby ɗin za'ayi zancen,har Hajiya Sakinah ita ma ta rasu bataga alamun kowa ya sani ba, ita ma ku ma bata faɗawa kowa ba, ko Auren ta da Kawu isma'il batai Masa zancen Auren ba, hakama ƴaƴan bata taɓa gaya musu ba, abunda yasa Hakan ga Sa'adatu shine, ita fa tasan wane Ɗalhat yana da kuɗi daidai misali, iyayensa ma suna da dukiya, shi yasa ma bata gayawa kowa ba, bata fatan su Hadiyyah su Auri mai kuɗi su huta,sai ku ma gashi ku ma Zahra ta Auri mai kuɗi ɗan gata,ta yi baƙin ciki sosai da Hakan, sai saidai ba yadda zata iya' sai kuma wata masifar da ta sameta shine samun su Mahmud da Mus'ab a matsayin Samari, tasan ƴaƴan ma su kuɗi ne,ta yi baƙin ciki sosai da Hakan, sai ta yi shiru da zancen cewa fa su Hadiyyah su na da Aure, su Mus'ab da Mahmud har wajenta suka zo suka gaisheta, ita ma kuma bata ce ai da Aure Akan waɗanda kuke ne ma ba..Anan Sa'adatu tunanin ta ya tsaya saboda murɗawar da marar ta tayi na lokaci barkatai. Ita Hidayah mai tambaya ta yi shiru tana kallon Auntyn da take jiran ta bata amsa Amma shiru,dan haka ta kuma je fa MATA tambaya? Aunty bakiyi magana ba dan ALLAH ki fitar da mu daga cikin duhu! Da ma kinsan Alhaji tallafy? Saboda shine ai Ɗalhat ɗin Abokin Abby! Kamar saukar aradu haka Sa'adatu taji wannan zancen! Alhaji tallafy shine da ma Ɗalhat dukiya ta fi ta da kenan! Ko shi yasa yake kulawa da su ne? Wayyo da ma ta tsaya Ranar da sukaje visiting ɗin Alhaji kaicona! Ƙara Sa'adatu tasaka jin mararta kamar zata ɓalle masu Kuka a hanzarce su ka ɗago jin Aunty ta saki ƙara mai rikitarwa da tsananin ƙara, ai tozali sukayi da Aunty ya she a ƙasa jini kam kamar an yanka karamar dabb a ya na biyo ƙafafaunta abun tsoro! Hidayah ce ta farga! Ta ƙwalawa Hydar Kira wanda yake tsakar gida, Yaje ya faɗawa maman Annour ta zo! Da gudu Hydar ya fice zuwa maƙotan inda suna mutunci da Sa'adatu ya kirawo maman Annour ɗin,domin ta ga halin da Aunty ta ke ciki! Hankalin su Hadiyyah fa yakuma ta shi, da ma ga damuwar da suke ciki, da kuma wannan ta shin Hankali na Aunty, sun san dai Aunty ciki ne da ita, gashi kuma ta na bleeding sun san Hakan matsala ce ga mai ciki. Suna ta aikin Sannu ga Sa'adatu, wacce takeshan wahala sosai, lokacin da Maman Annour ta zo gidan tuni Sa'adatu ta yi ɓarin cikin jikinta(ƙarshen tika tika tik fans) sai da maman Annour ta taimaka Sa'adatu ta gyara jikinta, su Hadiyyah suka wanke kayan,har lokacin cikin damuwa suke, Akan wannan al amari na cewa Aure ne da su kuma waɗannan, ƴaƴan Alhaji tallafy ɗin, marasa sanin darajar ɗan Adam musamman wannan ɗayan (AQEEL) ko ya nuna akwai mutane a wajen lokacin visiting ɗin Alhaji da sukaje, Kowacce cikinsu irin tunanin da takeyi kenan a zuciyarta! Ita dai Sa'adatu zuciyarta ba bu daɗi, na ɓarin cikin da tayi, shikenan yanzu tata ta ƙare, kenan duk wani makirci da take ƙullawa su Hajiya ikilima Akan cikinta ku ma ya ƙare, Amma ku ma ai ALLAH zai bani wani cikin ba da jimawa ba,dan haka ba bu damuwa ai! Sa'adatu ta faɗa a zuciyarta, tana daga kwance saboda gaskia ta Sha wahala fa, sai kuma tunanin Su Hadiyyah ya dawo MATA, ai nan da nan annurin fuskarta ya ɗauke, wata tsana mai zafi ta su ta shige MATA rai. A haka Alhaji gambo ya shigo gidan, Hankali a tashe, dan khadija ce ta ɗau wayar Auntyn ta kirawo shi ta ke faɗa ma sa,shiyasa hankalin sa a tashe ya dawo gidan, har Kuka Alhaji gambo yayi na asarar cikin nan, daya ƙwallafa rai akansa, gwanin tausayi (yanzu iskanci gasu Hajiya ikilima kuma Akan ciki ai ya ƙare ko? Inkuma zaka rabu da su a Hakan shikenan)Duk baƙin cikin da Sa'adatu ta ke ciki sai ta shanye bata ta dinga lallashin Alhaji gambo ɗin, da kalamai na kissa da kisisina Akan cewa " indai cikine ai kwana nawane ALLAH zai bata wani kar ya da mu! Shi kam Alhaji gambo kawai dai ya na jinta ne Amma hankalinsa a tashe yake, ga shi da hawan jini, kafin kace kwabo ya tashi sai da aka kirawo likita yai Masa taimakon gaggawa da allura sannan ya samu barci. Ita Hadiyyah Kiran mus'ab ta yi a waya Akan yaudarar ta da yayi, aikuwa kunsan ba ki abun magana sai da tai Masa tatas, shi kuma sai haƙuri ya ke ba ta Akan, Abbun su AKEEL ne ya aiko su daga shi har Mahmud wajensu,saboda su kula da su, kar su dinga kula wasu samarin, ya na son suyi karatu ƴaƴan Abokin san, sai yanzu kuma suke jin ai su ɗin matan su AKEEL ne, nan dai Mus'ab ya dinga bawa Hadiyyah haƙuri, daga ƙarshe yace MATA sai haƙuri, ai kema kina mun ƙorafi Akan mai Yasa bana ba ki kulawa kamar yadda kowanne masoyi yake bakwa masoyinsa kulawa, to hakanne ya sa ai saboda kar kusa rai da mu alhalin ba soyayyar gaskia Muke muku ba plan ne! Nan dai Hadiyyah ta kashe wayar zuciyarta kamar zata fito waje tsabar baƙin ciki! Itama. Hidayah haka sukayi da Mahmud gwanar ta ku bata iya magana ba,har ya ga ma zancen sa, kiyi haƙuri Hidayah abunda yasa da ma kenan Babu wata kulawa a soyayyar kenan, Muke kawai nu na kishin mu Akan kar ku kula Samari kenan, Abby ne ya wakiltamu Akan ku, saboda mu kula da ku Akan karatu kawai zakuyi Babu kula Samari, mu Duk ba mu kawo komai ba ashe ku ɗin matan su AQEEL ne! Cikin muryar dariya ya ƙarasa maganar, Hakan ya sa ba bu shiri Hidayah ta ka she wayar, ta na ci ga ba da kukan ta itama Hadiyyah Hakan,suka tattauna tsakaninsu. Hadiyyah "tace lallai su Mus'ab sun yaudare mu, ALLAH ya saka Mana" ita kuma Hidayah tace" Amma Nikam gaskiya waɗannan ƴaƴan Alhaji tallafy ɗin bana son su dukkan su ...... ************** Tun ranar da wannan zancen ya fallasa na cewa ƴan biyun Alhaji Ammar BN Yasir matan su ne shikenan fa, AQEEL ya koma ƴar gidan jiya,a halinsa yanzu yadaina walwala, shi ma AKEEL da sauƙi kam Duk wannan barkwancin ya rage. Duk Alhaji tallafy ya na sane da su, haka ma Mommah ta na lura da Hakan, dan haka suka tattauna Akan batun! Ya kake ganin Abu AQEEL tun da yarannan suka san cewa ƴan biyu matan sune shikenan su ke wani cika suke batsewa,anya ba akwai matsala ba kowa, baza su na mu matsala ba? Cewar Mommah ga Alhaji tallafy wanda suke zaune a kan sofa su na tattaunawa Akan zancen Kawu isma'il da kuma Auren su AKEEL ɗin, shi ne ta soko wannan tambayar gareshi? Bana jin hakan oum AKEEL in Sha ALLAH abun zaizo da sauƙi, kinsan ƴaƴan na ki sai a Hankali musamman wannan miskilin, kinsan a kwanannan aka samu kansa ai, Amma ni kam inada abun da zaisa kowanne ya so matarsa ai, kin manta ƴaƴan naki akwai tausayi da jin ƙai ga iyayen su,kar ki da mu kinji matar so, soyayyar yarinta ta na da tasiri sosai a zuciya, Hakan ne ma yasaka nida Aminina cika wannan soyayya ɗin da aura musu junan su, tun suna ƙananan,Kowacce wacce yake nunawa kulawa ita muka Aura Masa, ba don makircin Hajiya jimmai gareni ba, ai da tuni su AKEEL su na tare da matansu war haka tuni ai, ko dan lalurar shi AQEEL din ma,dan kuwa ba mune ma zamu faɗi cewa mun Aura musu juna ba, sune zasuce suna son juna, mu kuma muce da ama ai munmuku aure tun ku na yara, dan yadda tun a shekarun yarinta suke kulawa da juna da nunawa juna soyayya, abun gwanin dariya fa Oum AKEEL! Alhaji tallafy ya ƙarasa zancen da dariya, alamun ya tuna budurin da akasha dasu AKEEL ɗin itama murmushin ta yi, sannan yace MATA kamar ni nasan Hajiya jimmai zata rabamu ni da abokina, Duk kulawar da AKEEL da AQEEL suka nunawa su Hadiyyah muna ɗauka a waya mu Adana, da ga ƙarshe kuma muka kai aka fito Mana da a vedios ɗin flash, photon suma aka fitar,Duk muka ra ba ni dashi kamar shi ma yasan mutuwa zaiyi,ku ma isma'il zaici amanar sa ne, Amma shi dai bansan nasa photon da vedios ɗin waya bawa na saba? ALLAH ya gafartawa Ammar BN Yasir Allahumma Ameen inji mommah ta faɗa tana nuna alamun tausayi ga mijin nata da Abokin sa. Ni na wa suna nan a killace! Zan ɗauko na nuna miki su duka, shikenan Abu AQEEL ALLAH yakaimu lokacin lafiya. Nan suka ƙarasa tattaunawa tsakaninsu kafin su dangana ga ɗakin barcin su... Su kam su AKEEL da AQEEL suna can su ma kowanne da abunda ya ke saƙawa a zuciyar sa, dangane ga wannan auren da Abbu ya ce sun ƙulla shekarun da suka shuɗe! Shi AQEEL ya na tunanin ta yaya ma za'a ce wannan yaran ne wani matansu! Aina za'ayi Hakan? Lallai akwai sake Abbu! Haka yake faɗa a ransa. Shi kuma AKEEL mamakin Hakan yakeyi shima! Ta yaya Hakan ma zata faru wai wani su na da Aure,Auren ma waɗannan ƴan biyun!gaskia akwai sake an bai mai kaza Kai..... Lallai fans akwai cakwakiya fa😳 Ga dai cikin da Sa'adatu take taƙama dashi ta ƙwallafa rai akansa ya zube🙆‍♀️ Ya su Hajiya ikilima zasu riski wannan labarin🤧 Me su AKEEL da AQEEL suke nufi da Hakan😢 Su ma dai su Hadiyyah ta na alamun bara'a zasuyi Akan wannan auren🙆‍♀️ Ku biyo oum ARQAM dan jin Duk amsoshin ku da waɗansu ma Amma in Sha ALLAH next page zakuji aininhin tarihin Alhaji tallafy ɗin wanda da yawa nasan kun jima da matsuwa da ji irinsu Haseena kenan to Musha kurimin ku👌 page 44 na Alhaji tallafy ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 2/7/24, 4:31 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY FOUR 44* Ina miƙa ɗimbin godiya ga RASHIN IYAYE fans group da adduoinku gareni🙏 jikina da sauƙi sosai ga wannan Page ɗin na kune😍 Waiwaye......... Alhaji Abdul'rahman da Hajiya Binta sune mahaifan Ɗalhat (Tallafy) asalinsu ƴan jihar kano ne, tun iyaye da kakanni,sai dai zaman nasu bai daɗe ba, Tana haihuwar Ɗalhat ko ganinsa batayiba ALLAH yai MATA rasuwa,dan haka akwai ƙanwar Mamansa mai suna Rabia ita Aka mayar ɗakin yayarta, saboda ta kula da wannan jariri da yayarta ta Haifa, da yake lokacin ita Rabia batada saurayi kuma yarinya ce mai biyayya haka ta yadda ranar sadakar bakwai aka Ɗaura Aure da Abdul'rahman,wanda mutuwar Binta ta jigatashi sosai saboda wannan jaririn ne ma ya yadda zai auri Rabia ɗin, dan yana matuƙar tausayawa ɗan jariririnsa,yana kyautata Zaton Rabia zata kula dashi,kuma da ma suna kama sosai da Binta yanayin halin su ɗaya ma, akwai Sanyin Hali ga fari'a. Kamar yadda akayi tunani kuwa hakanne ta kasance dan Rabia ta riƙe Amanar da aka danƙa MATA, ta kyautata cikin rainon ɗan yayarta,ba bu wanda zaice ba ɗan ta bane,a haka shekaru suka ja, Rabia ta Haifa wa Ɗalhat ƙanne, kuma Abdul'rahman yana jin daɗin Zama da ita, fiye da yayarta ma, ko da yake zaman da sukayi da Binta guda nawane Akan wanda yanzu suke da Rabia. Sai da Ɗalhat ya girma sannan yasan ba Rabia ce ta haife shi ba, kunsan halin mutane,an dinga ga ɗan maraya nan da sauran waɗannan zantukan to anan yasan cewa ba itace mahaifiyarsa ba. Tuni ya kammala karatun sa na secondary ya ɗora da university kuma anan su ka haɗu da Ammar BN Yasir shima,sai dai karatun na Ammar BN Yasir baiyi nida ba ya koma kasuwanci, shi kuma Ɗalhat ya cigaba da karatun sa, ɗan kuwa shi mahaifin sa yana son Hakan, shi kuma Ammar BN Yasir shi ne ma ya tsayawa kansa da karatun, ƴan uwansa Duk kasuwanci sukeyi,. Har sannan kuma suna tare abunsu, Haka shekaru suka ja Ɗalhat yana karatunsa har ALLAH ya haɗashi da Ummul khair, Basu ji ma ba kuwa sukayi aure, Duk da yana karatunsa sannan,kuma ba wani girma yayi ba, lokacin shekarunsa basufi Ashirin da biyar zuwa da shida ba,irin mutanen nan ne ƙarfin sha'awa, to tun da yace yanason Auren mahafinsa bai tambayi ba'a si akai ba ko ai karatu kakeyi, yai Masa aurensa, kuma Auren bai tauye Masa karatun sa ba, abokansa kuwa sun Sha Masa tsiya shikam bai ji suba sai karatunsa yakeyi,shi ma Ammar BN Yasir sai da yayi mamakin Auren Ɗalhat ɗin, Duk da dai yasan yanayin Abokin nasa, Amma kuma ya ga karatu yakeyi, Ɗalhat yace "dan ina karatu kuma shine bazanyi aure ba, ai karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu, matuƙar akwai halin yi ɗin, Ammar yace "Hakane abokina, iyaye ne ai basa ganewa idan ɗan su yana karatu sai su hanashi Aure, ko shi da kansa ya hana kansa Auren, alhali yanason Auren, daga nan kuma sai ya bi wata hanya daban wacce zai dinga biyawa kansa buƙata ta hanyar saɓawa ALLAH Zina, ko kuma biyawa kai buƙata da hannu da sauran hanyoyi Marasa kyau" ALLAH yasa mudace ƴan uwa. Ummul khair yarinya ce mai Hankali da nustuwa, kuma itace ƙarama a wajen iyayenta sai yayye,Suma Duk sunyi aure, haka suke zaune itada Ɗalhat cikin soyayya da ƙaunar junansu, tana tsananin son mijinta shima kuma mijin yanason matarsa, Sun jima ALLAH bai ba su Haihuwa ba, dan haka mutane suke tunanin ko dan Ɗalhat yana karatu ne shiyasa ya ɗauki matakin hakan, nan kuwa ba haka bane, ALLAH ne dai bai kawo ba. Cikin ikon ALLAH kuma sai ga ciki ajikin Ummul khair kar kuso kuga murna a wajen Ɗalhat da sauran ƴan uwa anata addu'a ALLAH ya raba lafiya,cikin ikon ALLAH kuwa ALLAH ya bata ƴan biyu Duk maza,ranar suna suka ci Hassan AQEEL da Hussain AKEEL, zo kuga murna kamar ba gobe, Ammar BN Yasir yanason waɗannan ƴaƴa na abokinsa ƴan biyu, haka komai ya kawo yace na ƴan biyu ne,har lokacin ya na kasuwancinsa , shi ma ya haɗu da Ummu Ruman sannan, suna soyayya, itama ALLAH yayita da son ƴan biyu, to da ma kuma Ummul khair da Ummu Ruman tuni sun zama ƙawaye sanadiyyar Ɗalhat da Ammar ɗin,bine kaɗan ta Kira wayar Ummul khair ina ƴan biyu, nice zan raine su ai, bar Mana za'ayi idan mukayi Aure da Ammar wannan alƙawarine maganar kullum kenan. Ba'a jima sosai ba kuwa Ammar BN Yasir ya auri Ummu Ruman,zumunci ya daɗa ƙarfi tsakanin su, ƴan biyu basa rigima dan haka koda yaushe suna wajen Ummu Ruman tana rainon su,ko da aka yaye su sai rainon su ya koma gurinta gaba ɗaya, lokacin itama ALLAH ya bata Zakiyyah, ga rainon Zakiyyah gana ƴan biyu, dan ma su sunyi wayo sannan. Ita kuma Ummul khair ALLAH yabata wani cikin mai wahala tun farkon sa, itace ba bu lafiya yau ace ba bu jini yau ba bu ruwa, kullum suna yawon asibiti, bata sati biyu sai ta kwanta, ana tausayawa Ummul khair sosai, tuni An ya ye Zakiyyah kuma Hajiya Sakinah ta ɗauke ta, Ammar BN Yasir da Ummu Ruman ba su da mu da Hakan ba, tun da ga ƴan biyu a wajensu har sun ta sa ma, sannan ALLAH yabawa Ummul khair ɗin wani cikin mai wahalar da itan,kwanci tashi ba wuya a wajen ALLAH gashi har ALLAH yakawo lokacin haihuwar Ummul khair, ta Haifi yarinyarta mace sai dai ko ganin fuskarta batayi ba ALLAH ya karɓi abarta,tashin Hankali wanda ba'a saka ma sa rana kar kuzo kuga yadda Ɗalhat ya shige tashin Hankali,da Duk wasu ƴan uwa ma, sai ma an kalli jaririyar da Ummul khair ɗin ta Bari,haka aka dinga cewa Ɗalhat ɗin shima haka mahaifiyarsa ta rasu ta barshi, shima ga shi an bar Masa,Ummu Ruman tayi Kuka kamar ba bu gobe na rasuwar Ummul khair ƙawarta Aminiyarta, sai haƙuri, haka aka share makoki. Ummu Ruman ta na da ciki lokacin,har sannan kuma ƴan biyu suna wajen ta. Ɗalhat ya Zama shiru_shiru duniya tai Masa zafi ga jaririya an bar Masa kuma ya ce shi zai raini ƴar sa ba bu wanda zai bawa. Jimmai yayar Ummul khair mijinta ya mutu, ta na da ƴaƴa Biyu mace Shukra da namiji Usman, ya ɗan girmi su AKEEL da AQEEL, kuma Duk su na dangin ubansu, daga jimmai dai Ummul khair dan haka ba wata babba bace, ganin halin da Ɗalhat yake ciki ga jimmai a gida kawai sai iyayen su suka haɗa Auren tsakanin jimmai da Ɗalhat ɗin ko dan jaririyar nan(Ummul khair) wadda ake Kira da AKEELA, baiyi gaddama ba, aka Ɗaura musu aure,jimmai irin matan nan ne marasa tausayi da cikakkiyar tarbiyyah, Duk da iyayenta sun mata tarbiyyah ɗin, Amma tun da tayi aure ta watsar ta kama wani halin da tarbiyyah wacce ba iyayenta ne suka ɗora ta akai ba,mijinta ma haƙuri yakeyi da ita, asiri kala_kala take Masa Duk ta mallakeshi sai abunda tace Masa, iyayensa ba su iya komai a kai ba,sai a bunda ta ce,ana haka kuma ALLAH yai Masa rasuwa, aikuwa tana gama takaba a gidan ƴan uwan mijin suka amshe yaransu, ta dawo gidansu, shine fa yanzu kuma aka ƙallafawa Ɗalhat ita.. Ammar BN Yasir baiso wannan haɗin da akayiwa abokinsa ba, mijin jimmai yasanshi farin sani, Duk halin da Yake ciki game d it ya sani, shi yasa yaso ya nusashshe da Ɗalhat illar Auren ta zaiyi, amma ALLAH ya Riga ya ƙulla, jimmai ta na kallon take_taken Ammar BN Yasir na ƙin Auren ta da Ɗalhat da yaso ya rusa,shiyasa ta ƙudire wani abu a ranta game da shi ɗin wanda zata aiwatar. Haka jimmai da Ɗalhat suka tare, ita ke kula da AKEELA, ta goya ta sauke Amma bata shayarta ba,madara ake bata, sai kuma jimmai ta ƙalla Ido Akan su AKEEL da ke wajen Ummu Ruman ta ƙarkashin ƙasa tabi ta farraƙa su rana tsaka ƴan biyu, dama suna zuwa gidansu kodan ƴar ƙanwarsu akwaisu da son yara dan Haka suna zuwa,wani zuwa kuma sai suka ƙi dawowa wajen Ummu Ruman ɗin, jimmai ta ƙulle baƙin su shi Alhaji Ammar BN Yasir baice meyasa su ƴan biyu Basu dawo ba haka ma itama Ummu Ruman bata tambaya ba. Haka zaman yaci gaba da tafiya,ba bu irin muguntar da jimmai batawa ƴan biyu, bata ba su abinci ga duka a zagi,Amma ba a gaban idon Ɗalhat ba,dai taga bayanan tukunna, shi AQEEL da ma can bamai yawan surutu bane, idan ya zauna sai yayi shiru AKEEL ne ma me ƴar ƙuriniya da surutu ga ɓarna, aikuwa yana Shan duka wajen jimmai, Tuni lokacin Ummu Ruman ta na da zahra har tayi wayo ma abunta itama. Ƴan biyu ba bu kalar azabtarwar da jimmai bata musu,asiri kuwa tuni taiwa Ɗalhat yanzu a gabansa take musu bashida bakin magana,ya na kallo, lokacin ma Sha ALLAH Ɗalhat ya kammala karatunsa ya ka ma aikin gomnati, tuni ya sai mota kuɗaɗe sun zauna a hannu, tun farko da ma shi ALLAH ya yishi da son taimakawa na ƙasa dashi indai ya na da abu sai ya bayar, maƙotansa ma yana kyautata musu, balle ƴan uwansa kuma, sai son barka. Jimmai bata haihu ba har sannan AKEELA ta tasa, Ummu Ruman matar Ammar BN Yasir ita kuma ALLAH ya bata ƴan biyu Duk MATA,itama zo kuga murna wajenta, abun nema ya samu, ALLAH sarki Ummul khair , ALLAH baiyi zata ga ƴa biyun Ummu Ruman ba, dan intana nunawa su AQEEL da AKEEL ƙauna sai yace ALLAH kema yabaki ƴan biyun nan dai, in mata ne sai mu haɗasu Aure,idan maza ne kuma sai su Zama abokai kuma ƴan uwan juna! shima Ammar sai murna yake, shima hakanan Ɗalhat ya dinga hidima da su Hadiyyah da Hidayah, aikuwa su AKEEL da AQEEL a Karo na biyu, suka dawo gidan Ummu Ruman sanadin su Hadiyyah, dama kunsan akwaisu da son yara,abun ya musu daɗi sosai yara guda Biyu Iri ɗaya, kowannen su ya ɗauki ɗaya, yace itace ta sa, Hadiyyah akwai rigima ita AQEEL yake ɗauka bata minti biyar zata Fara Kuka, haka zai dawowa da Ummu Ruman ita ransa a ɓace, ganin shi AKEEL tasa Hidayah bata Kuka idan ya ɗauke ta har sai ya gaji ya dawo da ita dan kansa, idan kuma AQEEL yace wa AKEEL yabashi Hidayah sai yace Masa a'a ina taka kaje ka ɗauko Mana, a haka suke rainon su iyayen suna musu dariya ganin, yadda suke ta shirme Akan su Hadiyyah da Hidayah waɗanda Basu san sunayi ba, su ma su AKEEL da AQEEL ɗin yarinta nada munsu, dan haka idan ana wannan diramar Ummu Ruman ko Ammar sune masu musu vedio ko photo,har lokacin da su Hadiyyah suka Fara wayo, sai ku ma ta ɗan daina rigima idan AQEEL ya ɗauke ta yana Fara mata wasa zata kama dariya, shi kuma hakan yana birgeshi, yai MATA wasa ta yi dariya, saɓanin Hidayah ita kullum fuska cunkushe har sannan bata fara dariya ba, AKEEL yai tai Mata wasa ba bu dariya, shi kima AQEEL shi ma yasamu abun tsokana, suyita dariya shida ƙanwarsa Amma ƙanwar AKEEL ba bu dariya, Kunga kenan AQEEL ya rama shi ma kenan, aikuwa wannan abu na ƙonawa AKEEL rai sai ya kama Kuka yana shure_shure, a haka fa gidan Ammar BN Yasir yake kasancewa shima idan Ɗalhat yazo ana wannan rigimar aita kwasar dariya, shi kuma AKEEL na kuka, ana Masa vedio ko photo yanawa Hidayah wasa Amma fa fur taƙi dariyar.............. Muje next page muƙarasa acan akwai sauran badaƙala a gaba tsakanin Jimmai da Ɗalhat da kuma ƴaƴansa AKEEL da AQEEL..... ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 2/9/24, 1:57 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY FIVE 45* Dariyar da Hadiyyah takewa AQEEL ce ta sama Masa lafiya a wajen AKEEL ɗin,haka rayuwa ta dinga tafiya. Ita jimmai ta tsani Ɗalhat yayi mata zancen Ammar da Ummu Ruman kwata_kwata,shi kuma bai ganeba,indai zai zauna sai yayi zancen su,duk da tun farkon auren su yaso itama tazama kamar Ummul khair da Ummu Ruman amma abu yaci tura, fa fur taki yarda ta saki jikinta,in yayi magana sai tace ita dai ya kya leta ita bafa Ummul khair bace kowa da irin halinsa,kuma ma ita mijinta nabaya bayason irin wannan saboda me kulle ne to ta saba ko ma'kota bata shiga, hakan data fad'a sai 'Dalhat ya rabo da ita kawai,dan kuwa a halin yanzu shidai bai ta'ba samun matsala da ita ba, daidai gwargwado tana kamantawa y'ay'ansa tana kulawa dasu wanda shine burinsa da ma, ku ma bashida tantama akan hakan,saboda shi ganau ne ba jiyau ba,Umman sa Rabia ta kyautata rainon sa, itama jimmai hakanne ga y'ay'ansa ...lallai kam 'Dalhat besan wacece jimmai ga y'ay'ansa ba.... Rayuwa taiwa AKEEL da AQEEL wahala a gidan ubansu,duk lokacin da 'Dalhat zaije dasu gidan suna cin ba'kar wahala,basu da abinci a gidan ga d'an karan aiki da sukeyi,a matsayinsu na yara 'kanana,shiyasa basason zuwa gidannasu, saboda 'kanwar su Akeela suke zuwa gidan,suna son yarinyar,in sun cewa Abbu ya kawo musu ita gidan Ummu Ruman sai jimmai tace wa 'Dalhat d'in abun yai mata yawa ai,babu 'yan biyu sannan ita Akeela d'in ma d'auketa za'ayi, hakan ne ma yake sa 'Dalhat d'in lokaci zuwa lokaci kawo su gurin jimmai din. Su AKEEL da AQEEL Suna tasawa kulawar su ga Hadiyyah da Hidayah tana 'karuwa suma yaran duk kama da juna da AQEEL da AKEEL suke kowacce tasan me d'aukar ta muddin aka samu akasi AKEEL ya d'au Hadiyyah tanajin ba hannun data saba ji bane, Dariyar da take batayi, karshe sai kuka ya biyo bayan hakan, shi da ma AQEEL koda wasa baya d'aukar Hidayah saboda batai masa ba,shi bayason yaro mara fara'a, shiyasa yake cikin fara'a da Annushuwa in dai Hadiyyah tana hannunsa, dan kuwa shi dai ba ma'abocin Dariyar bane,Amma Hadiyyah ta canza shi,yanzu sai fara'a da murmushi,sa'banin AKEEL ɗin mai fara'a da murmushin yanzu yazama mai kuka,saboda tsokanar da AQEEL yake masa,na cewa 'kanwarsa bata dariya,kullum fuska a cunkushe shikam 'kanwarsa dariya harda kyakyatawa,ire iren tsokanar da AQEEL yakewa AKEEL kenan, karku manta fans shima yanzu AQEEL ramawa yakeyi, irin tsokanar da yake masa lokacin Hadiyyah tana rigima.. "Me zai hana Mu had'a yaranmu aure ne aboki! A yadda nake ganin wannan sha'kuwar hakan shine daidai, kuma ko bayan ranmu zuri'ar mu zata zamo gaba d'aya! Shine burinmu daman" 'Dalhat yake gayawa Ammar a wani tattaunawa da suke I junansu! Nima nayi tunanin hakan aboki, kaga babu wani abu aciki ai, rana kawai zamusa a d'aura Auren in yaso idan suka girma babu ruwanmu da wani daurin Aure,dan wannan sha'kuwar zata kai ga hakan!Ammar ya mayarwa da abokinsa da wannan amsar! Hakan akayi kuwa dan an d'aura Auren kamar yadda kawu isma'il ya bayyana muku. Har sannan kuma Amincin wannan abokai yana nan,su AKEEL da AQEEL suna gidansu suna gidan Ummu Ruman, wajen kula dasu Hadiyyah da Hidayah,wanda kowa matarsa yakewa Hidima bai sani ba😂,ga azabtarwar jimmai garesu kullum abu gaba yake, takai yanzu bata shayin cutarsu,ko a gaban 'Dalhat ne sai tace laifi sukai mata, ga asirin data masa,ga kuma yana kallon ta kamar Umman sa Rabia inda bata cuce shi ba, haka itama jimmai ai bazata cutar dasu AQEEL d'inba, farkon abun inta hanasu abinci ko aiki me wuya,suna gaya masa a take zai gwale su,yace shi bayason Hakan, ai jimmai mamansu ce karya kuma ji, shiyasa ma suka daina gaya masa,sai dai suyi kuka su godewa ALLAH.itama AKEELA duk da 'kan'kantarta haka jimmai take dukanta,bata tausaya mata,kunsan maraya sai a hankali,akwai 'barna da kiriniya,middin zatayi sai jimmai da doketa,ko da a gaban 'Dalhat ne sai tace ai tafiya 'barna haka take yini idan bakanan, kasan shi kuma yaro idan ba'a tsawatar masa tashi yake a sangarce babu saiti, ko mutane su zagen suce dan ba y'ata bace shiyasa na sangartata,ire-ren zantukan da jimmai ke gayawa 'Dalhat kenan, shi kuma ai yana ganin gaskia ne,shiyasa wahalar tai yawa gasu AQEEL da AQEEL har ma y'ar 'karamar su AKEELA. Lokacin tuni ALLAH ya had'a Ammar da Sa'adatu, Bayan Haihuwar Zahra harda 'Dalhat ake zuwa zance,wanda da farkon 'Dalhat d'in da 'kar ya amince da Sa'adatu d'in har fad'a sukaso suyi,akan me Ammar zaiwa Ummu Ruman kishiya,shikam badashi ba,har sai da Ummu Ruman ta fuskanci akwai wata a 'kasa tsakanin mijinta da Abokinsa,dan haka ta matsa masa,akan ya gaya mata mene? Amma ya'ki,sai da 'Dalhat ya kawo su AQEEL gidan bayan sun kwana biyu a gidan su,'Dalhat bai 'boyewa Ummu Ruman komai ba akan cewa Ammar ya samu budurwane, shi kuma yana ganin hakan bai dace ba, shine fa suka samu sa'bani, Ummu Ruman murmushi tayi a lokacin tace "Babu Komai ai shi aure lokacine Allah ya had'a kansu, shine fa tun daga sannan suka koma kamar da, Ammar yaci gaba da neman Auren Sa'adatu,babu matsala ga Ummu Ruman,Saadatu ta shiga ta fita sai da ta Auri Ammar dai, Ba'a jima sosai da Haihuwar Su Hadiyyah ba itama ta haifi 'Danta na fari Alhaji, har sannan dai su AQEEL suna wajen Ummu Ruman kuma suna kula Sa'adatu da d'an ta,zuwan Sa'adatu taso jan jimmai a jiji amma ta'ki bada had'in kai. To tun bayan Auren Ammar da Sa'adatu sai jimmai take tsoron kar itama fa 'Dalhat ya 'karo Aure, da kuma wata rana yazo gidan ya tarar Jimmai tana dukan Su AKEEL ,kuma a gaban 'Dalhat d'in bai magana ba,daya tambaya dai shi 'Dalhat d'in yace ai fitina sukayi,lokacin jimmai ta kawo kai ne taji Ammar yana fad'ar "Gaskiya 'Dalhat wannan dukan yai yawa,su da su AQEEL basu da hayaniya,wane laifi sukayi da za'a musu wannan dukan!gaskia kai mata magana,'Dalhat yace shikenan zan mata magana!dama jimmai akwai haushin Ammar da takeji, tun farko na son Hanashi aurenta, ga kuma yanzu zugashin da yakeyi akan wai 'Dalhat yai mata magana dukan da takewa su AQEEL yai yawa. Tun daga sannan kuwa indai Jimmai ta daki su AKEEL sai yai mata magana,ita kuma hakan yana damunta,kuma tana tsoron Shima karya 'kara aure, kamar Ammar d'in,kuji banza batasan Auren Ammar da Sa'adatu 'kaddara da nufin ALLAH bane.. Jimmai taci galabar raba abota tsakanin Ammar da 'Dalhat kuwa dan farra'ku tai musu rana tsaka suka rabu babu mai neman kowa,y'an uwansu ma babu mai cewa ya hakan, hakama su AQEEL kwata-kwata suka daina zancen zuwa gidan, da zancen wasu Hadiyyah. Haka dama Jimmai take so, sai ta bud'e shafin cuta da zalunci gasu AKEEL,da mallake 'Dalhat ta hana yaiwa kowa hidima daga ita sai y'ay'anta agololi,dan suna zuwa gidan,kota aika musu,iya azaba AKEEL da AQEEL da kuma AKEELA sunasha ta,babu mai ceto sai ALLAH. Inta kamasu da duka kamar ALLAH ya aikota,musamman AQEEL mai taurin kai idan tana dukan su baya bada ha'kuri, ko kuka sai ya cake,to tu yana neman taimako daa kuka da bada ha'kuri har ya sire,wata rana data kamasu da duka aikuwa ta kawo zata daki AKEEL da yake belt ta samu, to akwai 'karfe sai a idon AQEEL,saboda rashin tausayi kuma tana gamawa AKEEL d'in shima dama sannan batawa AQEEL nasa dukan ba,ta dawo kansa da dukan,shima garin dukan ta kuma samun sa a d'aya idon,kafin kice me sai ga jini a idon AQEEL, a sannan jimmai ta razana,amma kuma saita basar,ta d'au waya ta kira 'Dalhat tace AQEEL ya bige a idonsa, da ga sama 'karfe ya fad'o ya falle masa ido, aikuwa sai ga 'Dalhat akai asibiti da AQEEL wanda tuni ya suma saboda azaba, ta gama dasu AKEEL yadda tace 'karfe ya falle masa idanu a haka aka bar zancen, to dama akwai 'karfunan a saman gidan,wanda aka yi musu gyara dasu, kuma ALLAH baisa an d'auke ba,dan tuni akayi gyara-gyare a gidan an 'kawatashi kud'i sun 'kara zama a hannun 'Dalhat. Sana din wannan dukan ne hasa AQEEL baya gani sosai da idanun,farko ma anyi tunanin ya daina gani, sai da aka masa aiki yake gani dishi dishi, da taimakon medical glass,duk da haka,a hakan ma angode ALLAH, dan a 'kila a 'kala akayi aikin,zai dinga gani ko akasin hakan, abun gwanin tausayi,tun daga sannan AKEEL da AQEEL suka zama abun tausayi, lokacin sun dan tasa zasuyi irin 10-11years abun ya faru,duk da haka babu abunda jimmai ta rage na azabtarwa gasu AKEEL d'in sai ma gaba, shara,wanke-wanke,girki wanki, da duk aikin gida su AKEEL sunayi,duk da akwai masu aiki komai amma ina jimmai ta sallamesu,sai tacewa 'Dalhat aikin guda nawa yake,ita dasu AKEELA ai zasu iya,kuma 'karya takeyi,sune sukeyi. Haka shekaru suka da d'u, tuni AKEEL da AQEEL suna cikin wahala, anzama samari zasuyi 17years haka,AQEEL tun a sannan yake fa ma da ciwon ciki mai tsanani, idan yafara har fita yake a hayyacinsa,sai da aka kaishi asibiti,likitoci suka rufa akansa, da'kar numfashinsa ya daidaita, anan akai masa gwaje-gwaje da kuma hoto aka gano cewa yana daga cikin jinsin maza masu tsananin sha'awa, tun daga sannan AQEEL ya kame kansa, duk da 'karancin Shekarunsa Azumi ya mayar kamar me idan yau yaci abinci gobe xai tashi da azumi,ya kame kansa ga duk wani abu da ALLAH yai hani a aikata, tun daga sannan yazama so silent baya shiga harkar kowa, to girma ya kamashi da wuri haka,sa'i da lokaci ciwon cikinsa ya na tashi,kamar bazaiyirai ba, kuma sai ya sha suwa da allurai, kafin yadawo normal,Wannan abu yana samun 'Dalhat d'an sa guda nawa yake? Dama shekerun sa sunfi hakane sai ya masa aure, fans 'Dalhat fa ya manta da wasu su Hadiyyah fa balle auren sa aka 'kulla,amma guda nawa AQEEEL yake, 17 years ma basu cika ba, 'Dalhat yana mama kin wannan abun, koshi lokacin da yana saurayi yafi AQEEL,sha'awa ta dameshi....kunga badon Jimmai tayi farra'ku ba ai dama akwai aurensa ko fans? sa'banin AKEEL shi kam ba bu ruwansa da wannan, yara ne masu ilimi daga addini har na boko, tuni sunyi saukar Al 'kur ani, Boko kuma suna Ajin 'karshe a secondry bana zasuyi candy, AKEELA itama anzama budurwa ma sha ALLAH wajen 14-15years fa take,an tasa,irin masu jikin nan ne murjajje, jikinsu yafi shekarunsu. Tuni Usman d'an wajen Jimmai yadawo gidansu AKEEL da zama, irin 'yan iskan yaran nan ne masu tasowa, da tashen rashin mutunci, Bf kala-kala yake download a wayarsa haka zaita kunnawa yana kalla,yaso jan AQEEL ya koya musa kalla, musamman yai masa nuni da cewa idan yana kalla wannan ciwon cikin zai daina kuma zai samu nutsuwa da salama..kunji dan iska, karku manta ya d'an girmi su AQEEL d'in.. amma ina AQEEL ya'ki kulashi ko shiga harkar sa bayayi,balle AKEEL kuma shida wannan yanayin bai dameshi ba. Tunda Usman ya dawo gidan ya takurawa AKEELA, buni kad'an sai yace zai kai hannu jikinta, ita kuma bataso saitai masa RASHIN kunya akan bataso, kuma baya fasawa,Ranar da yakai hannu jikin AKEELA kuwa, wankeshi da mari tayi,aikuwa jimmai tai mata dukan tsiya akan dan rashin kunya zata daki Usman dan yana mata wasa, shine sai kuma raini, da'kar ta tashi bayan dukan data mata, da 'Dalhat yadawo ta shirya karya da gaskia ta fad'a masa cewa AKEELA tanawa Usman rashin kunya, harda mari, ba bu ba'asi an riga an mallake shi shima yaiwa AKEELA tatas akan ai yayanta ne,bayason RASHIN kunya, duk wannan abu dake faruwa su AQEEL basu sani ba, su na school exam suke................ Lallai akwai bada'kala nan gaba, had'e da cakwakiya''''' me kuke tunanin zai faru tsakanin Usman Da AKEELA Ya rayuwar AKEEL da AQEEL zata kasance, ga dai halin da AQEEL ya tsinci kansa aciki a 'karancin shekarunsa, sa'banin dan uwansa AKEEL me hakan zai janyo??????? Da sauran tambayoyin da suke bakunan ku muje next page ✍️oum ARQAM ce on top 😍 2/13/24, 12:45 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY SIX 46* Hakan ce taci gaba da faruwa da AKEELA a kullum burin Usman shine hannunsa yakai jikinta,kuma bata da bakin magana,Amma duk da Hakan tana gaggaya masa baƙaƙen maganganun,Amma a banza duk lokacin da yakai hannun ga jikinta, ita kuma saita kai Masa Mari ko bugu a ƙirjinsa, Amma gogan naku sai yayi murmushi kawaii, ya girgiza kai alamun ko a jikinsa,baiji zafin dukan ba. Su AKEEL da AQEEL zaman gida yai Musu wahala, balle ko Wataran idan sunga iskancin da Usman kewa ƙanwarsu su taka Masa birki, ko da Yake ina suke da wannan ikon,Suma takansu sukeyi, Amma kuma Kota halin yayane in kaga dan uwanka a halin cutuwa ko za'a cuceshi sai inda ƙarfin ka ya ƙare, saboda hausawa sukace bakin rai bakin fama..... Ɗalhat kam arziƙi yaci uban nada,kunsan dama abunda yake haɓɓaka dukiya shine, taimakawa ƴan uwa, zakkah, idan ALLAH ya kai dukiyarka matakin,sadaƙa taimakawa miskinai da marayu da Marasa shi, to Ɗalhat yanayi,tun dukiyarsa bata kai haka ba,balle yanzu kuma, ƴaƴansa duk wani jin daɗi suna samunsa,inka cire cutarwa da azabtarwar da Jimmai take musu, Basu da wata matsala,sai kuma AQEEL shima da matsalarsa, wanda yanashan magani sosai,kuma yana yawaita azumi, Alhamdullillahi Hakan kuma ya tsareshi daga duk wata fitina ta zamani da matasa kamarsa suke tsintar kansu aciki na samarwa kansu biyan buƙatarsu ta Zina ko kallace_kallacen banza,shikam baya ciki,ya miƙawa ALLAH kansa shi zai kawo Masa mafita, sannan Abbu kullum yana Masa nasiha da cewa ya riƙe kansa,idan kuma yaga Hakan ya gagara yai Masa magana,a halin yanzun zai masa Auren kuma yaci gaba da karatunsa,to Alhamdullillahi Babu matsala da Hakan,yama ƙudirce a ransa shikam karatu zaiyi Aure kuma ba yanzu ba, shida ɗan uwansa zasuyi Aure rana ɗaya ma, kuma ƴan biyu kamarsu, ko yaya da ƙanwa zasu Aura suna da wannan burin a ransu. Karatunsu ma Sha ALLAH,sun Zama samari komai nasu iri ɗaya yake tun daga kayan sawa,kamanni abunda ya banbantasu wannan glass da Jimmai tai masa sanadi,sai kuma halaye kowa da kalar nasa, AQEEL shi shiru-shiru ne dashi,hakanan baya magana da kowa idan ba ɗan uwansa ba,abokai sai dai ayi zaman kurame,ya zauna yayi shiru, saɓanin AKEEL akwai surutu ga faran faran da mutane, Abokai kam gasunan, kowa nasane. Usman ya samu jimmai "Mamah nidai inason AKEELA, dagaske kuma nakeyi a aura min ita" Jimmai zubawa Usman idanu tayi kawai tana kallonsa sai da yakai aya sannan tace "wannan abun Bazai yiwu ba,bazaka Aureta ba,Akan me!kar nakuma jin wannan zancen nan abakin ka, me zaka aura kayi da wannan yarinyar? So nake ka samu ƴar manyan mutane ka Aura,Amma in ƙudine ai gani ina Auren mahaifinta,anason samun ci gaba ai "Shikenan Mamah angama,bazan kuma zancen ba kinji" yawwa ɗan albarka,nasan ai bakason ɓacin rai na ..dama Usman bawai son gaskia yakewa AKEELA ba, Aurenta zaiyi daga zarar ya samu abunda yakeso a jikinta ya rabu da ita ya sake ta, sha'awar ta dama ce take damunsa,kuma yaga yarinyar bazata bada haɗin kai ba. "Lallai maama ai da kin amince da Aurenta gareni,dama ɗanɗanawa zanyi naji, yanzu kuwa kome ne zai faru sai dai yafaru, nida yarinyarnan mai hanani ɗanɗana ta sai ALLAH!Usman ke wannan tunanin a zuciyar sa, yana kuma juyi a gadon da yake kwance, yana ƙissima Abubuwa marasa kyau da Rashin daɗi ga AKEELA marainiyar ALLAH. Jimmai tana fice ficenta na yawan asirinta da mallaka to kusan kullum bata gida,shikam Usman dama ya samu gida,kamar Gidan ubansa, baya Zuwa ko ina yaci ya kwanta, sai kalle kallensa na banza, shine aikinsa a Kullum. Yau ma kamar kullum jimmai ta fice Usman ne kaɗai a cikin Gidan,Duk suna makaranta. Ya baje kolinsa sai kallen kallensa yake na Rashin mutunci, gaba ɗaya ya hau network ya fice a hayyacinsa, bashi da buri sama da yasamu Abar ɗebe kewa a daidai wannan lokaci! Kwatsam sai ga AKEELA ta dawo daga makaranta, tana shigowa falourn ta ga Usman yana kwance a kan sofa, ya kama pillow ya rungume sai wani juye juye yakeyi, ga vedios ɗin dayake kallo ya haɗa da bluetooth sai kauɗin Ƴan iskan ke tashin abun ba bu kyan gani, Usman dama yasan jimmai bazata dawo da wuri ba, AKEELA kuma bata kaiwa 4:00 take dawowa daga school,Abbu(Ɗalhat) kuma yayi tafiya yau kwanan sa uku,sai jibi zai dawo,su AKEEL kuma ana school, suna extra lesson, saboda exam ɗin da zasuyi, basa dawowa da wuri wataran sai magrib shiyasa a masallacin suke tsayawa su ɗau karatu a wajen liman ɗin, shiyasa Usman ya tamawa wannan ranar, Jimmai ta ga Abbu baya gari sai takai dare sosai, ga gida ba bu Ƴan aiki,sai mai gadi kawai shi kuma yanacan bakin aiki. Ai da wani mugun sauri ya tashi jin sallamar AKEELA ɗin, yatawo gadan gadan, tsuntsu daga sama gasasshe kenan, ai kuwa kano AKEELA yayi abunka da namiji, Duk shure_shuren sa take bai sauke ta ba, sai da ya dangana ga sofa ɗin a kan cinyarsa ya ɗorata, sannan ya ɗauko wayarsa vedios ɗin, daya kunna yaketa ƙokarin sai AKEELA ta kalla,ai kuwa taƙi kalla,Duk da yai mata kamun mage da ɓera,ko juye_juyen da takeyi ta kasa, ƙarfinta ya ƙare,ita dai AKEELA runtse idanu takeyi,alamun bazata kalla ba "ok shikenan yarinya tun da bazaki kalla ba shikenan, matsalar kice inda kin kalla sai rage miki wani Abun, dan kuwa yau me hannani Cika burina a kanki, ban ganshiba,dole na kashe ƙishirwa ta,na mayar da yahu na! AKEELA kam bata jinsa ma tashin hankalin da take ciki yayi yawa,yarinya 14_15 years mai ta sani, banda ALLAH yakawomu wannan zamanin, ihun kuka take na neman taimako Amma ina Babu maceci, Usman dai saiya cika burinsa a kanta tun a falourn yafara lallatsewa AKEELA jiki kafin ya dangana ga ɗakin su AQEEL da ita, tuni dama ya kashe vedios ɗin. Duk ihun da AKEELA take haka Usman yasa Rashin imani, ya keta mata mutuncinta, yai MATA fyaɗe, na Rashin mutunci wanda Duk wanda yagani sai yayi kuka,sai da ya kammala komai Babu imani da tausayi ya barta a wajen hakanan,sai kuma sannan tsoro ya kamashi na yanzu ya zaiyi? __________ Yau da ma tunda AQEEL ya tashi, yakejin yanayinsa yana sauyawa,da aziminsa da ma ya tashi, Amma sai a Hankali, har sukaje school wajen magrib sukayi sallah, AQEEL yasha ruwa ai sai abunda yake bujuro Masa yafi na da(irin masu sha'awa tabbas hakan yana faruwa dasu koda suna azimin yana rage sha'awa sosai,Amma kuma suna buɗa Baki sai sha'awar ta bujuro musu,Duk da Hakan dai da sauƙi yafi basuyi ba) Hakan yafaru da AQEEL, dan uwansa yashan yanayinsa, dan haka yace Masa" jarabuna kaje Gida kawai,yau ɗaukar karatu bazai yiwuba ba,ana yanayi, kaidai bro kashige su kamar ka sai jaraba, aje Gida asha magani kuma,kafin asamu relief! cikin shakiyanci AKEEL ya faɗi maganar, shi dai AQEEL bai kula shiba, takansa yakeyi,Amma sau tari yana kare kansa, su biyo sukayi niyyar tafiya gida kawai sai AQEEL yace "baza ayi hakaba bro, ka ɗau karatun in yaso sai ka ƙaramin, cikin dauriya yayi maganar! Kana ganin ba matsala zaka iya ƙarasawa gidan "ea Babu matsala cewar AQEEL,Amma gaskia baza kayi driving ba kabarmun machine ɗin kahau abun Hawa,saboda yanayinka! Cewar AKEEL "to shikenan sai ka tawo Inji AQEEL. Hakan kuwa akayi AQEEL ya hau abun Hawa zuwa gida, yabar AKEEL a masallaci ɗaukar karatu,liman yace ina ɗan uwan naka yau? AKEEL yace bai da lafiya yayi gida!liman yace ALLAH ya sauwaƙe. Lokacin da AQEEL ya ƙarasa Gida,yanayinsa yayi tsanani, shi kuma Usman tuni ya ida nufinsa Akan AKEELA yayi shiru yana tunanin mafita a gareshi, ya kawo kai kenan zai fito daga ɗakin sa,sai yaga AQEEL yana tangaɗi, ya shigo falourn, ai da sauri ya lafe a jikin labule, yana ganin AQEEL ya shiga ɗakin su ya biyo bayansa, abunka ga ɗan Iska yana ganin yanayin AQEEL yasan me yake damunsa, kuma dama sau tari yasan indai irin wannan yanayin ya samu AQEEL ɗin matuƙar bai Sha maganinsa Akan lokaci ba sumewa yakeyi, ya fice a hayyacinsa, sai anje ga likita,an Masa allurai da ƙarin ruwa kafin yadawo hayyacinsa, dan haka yana ganinsa yai hamdala ga ALLAH ga mafita, cikin Ruwan Sanyi!cewar Usman acikin zuciyarsa shi AQEEL ta kansa yakeyi burinsa Yaje ga maganinsa yasha, ko kula da AKEELA dake kan gadonsa, cikin mawuyacin Hali bai ba idonsa ya rufe, kafin Yaje durowar da maganin sa yake ciki domin ya ɓalla yasha abun yaci tura, tuni numfashinsa ya ɗauke, in irin haka ta faru AKEEL yana kusa dashi shine mai ɗauko Masa,maganin cikin gaggawa ya bashi, Duk da haka sai yasha baƙar wahala kafin yadawo normal, yanzu kuma yabarshi wajen ɗaukar karatu, Usman yana ganin haka da sassarfa ya ƙaraso ga AQEEL ya tallafo shi jikinsa, bai kai ƙasa ba, lokacin tuni har ya Suma, dan haka ba bu Ɓata lokaci Usman ya shiga cirewa AQEEL kayan jikinsa yaba ɗaya, sannan ya ɗauke shi ya ɗorashi Akan gadon kusa da AKEELA ta yadda Duk wanda yagani yasan tabbas shine tai mata wannan fyaden, jikin dake jikin AKEELA Duk yabi jikin AQEEL dasu inda yazama dole ya shafa, abundai ba bu kyan gani, Duk wanda ya ga wannan yanayin da AQEEL da AKEELA suke ciki, lallai zai tsinewa AQEEL ne musamman ace Abbu ko AKEEL yagani. Sai da Usman ya saita komai sannan yayi godiya ga ALLAH, cikin dariya yace" Shikenan mafita tazo min Babu wanda zaice ba AQEEL bane ya aikatawa ƙanwarsa wannan Aikin, Duk wanda yagani tabbas zai tsine Masa albarka, na kawar da ƙishirwata cikin salama Babu wanda yasani, ita kuma yarinyar nasan yadda zanyi da ita ta yadda bazata ce nine na aikata MATA wannan Aikin ba, kai gaskiya Nikam Usman inada Sa'a a duniya, gwanda ma maama da baki amince na aureta ba, ya ƙarasa maganar da kuma tunanin Ina AKEEL yake? meyasa AQEEL shi kaɗai ya dawo gida, kar dai tare suke, yana ganin abunda ya aikata, zuciyar sa kuma ta kawo Masa wannan tambayar, aikuwa juyowar da zaiyi yaga mutum a bayansa da Alamun Duk zantukan da yayi da abunda ya aikatawa AQEEL shi mutumin yaji, a razane ya ɗago idanuwan sa domin yaga wane yaga abunda ya aikata da jin zantukan da yayi, ai yana ɗagowa sukayi Ido huɗu da ............... Lallai akwai cakwakiya fa Shin fans wa Usman ya gani? Da alama dai asirinsa ya tonu fa Gaskiya Usman Babu imani fa, Ko da yake ta ina zai Imani, Jimmai ce fa mahaifiyarsa ALLAH sarki AKEELA tabani tausayi sosai Ya Rayuwar waɗannan Ahali zata kasance da wannan ƙaddara ta rayuwa da suka gamu da ita Muje zuwa fans Inada tambaya.... TSAKANIN SU HADIYYAH DA SU AQEEL SU WANE SUKA FI SHAN WAHALA? DA KUMA GANIN MARAICI? ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 2/18/24, 1:04 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY SEVEN 47* Jimmai ce a tsaye ta kafe ɗan nata da idanu, alamun tagama jin Duk abinda ya aikata, bai gane a wane yanayi Mahaifiyar tasa take ba, dan haka ya matso cikin firgici! dan ALLAH Maa... Dakata fito Daga cikin ɗakin ko sai wani yazo ya ganka asirinka ya tonu! Cewar jimmai! Aikuwa cikin azama Usman ya biyo maaman sa zuwa falourn, sai ta zarce ɗakinta Usman ma binta yayi, Sai da suka ƙule cikin ɗakin, sannan ta zauna a gefen gado shima Usman ya zauna ! Abunda ka aikata kenan ko? ALLAH ya shirya mun kai, Yanzu kuma shi AQEEL ɗin taya kai Masa Hakan, ko tsoron ALLAH ko kunya ya bawa uwarsa labarin yadda AQEEL ya shigo da komai da komai, Ajiyar zuciya jimmai ta sauke! Sannan tace yanx kuma inda AQEEL ɗin bai shigo ba fa? Ai maama Hankali na ya tashi lokacin na rasa yadda zanyi da ita, Yanzu dai shikenan ka ga cikin ruwan Sanyi ALLAH ya kuɓutar dakai, ubansu ba abinda zaiyi akai ai dai ɗan sane ya aikata bazaiso abun ya fito sarari ai abun a tsinewa yaron ne ka lalata ƴar uwarka cikin ummanka! "Aikuwa maama ALLAH ya rufan Asiri ai cewar Usman yana sauke ajiyar zuciya..... Lallai wannan Daga ɗan har uwar basuda imani, ko halin da AKEELA take ciki bai damesu ba,balle AQEEL wanda akama Sharri,wanda shima yana cikin mawuyacin Hali na taimakon. "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun! Usman an kashe maciji ba'a sare kansa ba, idan ita yarinyar ta farka ai zata faɗi ko wanene! Jimmai ta faɗa tana dafe kanta alamun wani abu ya sameka bakayi tsammani ba! A firgice Usman ya ɗago fuska cikin jimami ya Lallai Maman tasa! Ƙwarai kuwa maama mene mafita kenan, tana farkawa na shiga uku dam sai ta faɗa me kike tunanin zai faru dani har dake ma?jimmai dai ta kasa magana hannunta dai yana kanta har sannan tayi suman wucin gadi... Kuji fans anya jimmai tana da imani kuwa, ɗan ka yaiwa ƴar Ƙanwar ka fyaɗe irin Wannan na Rashin imani, sannan ɗan ki ya ƙallafawa ɗan uwanta Duk baki shiga tashin Hankali ba sai asirin ɗan ki da zai Tonu shine fargabar ki, Daga ita har ɗan basuda imani, ko ya ɗa yake ai bai uwa bama!dan dai suka zauna cikin jimami mafita a garesu, ƙarshe jimmai harda cewa dan nace bazaka Aureta ba shine kai MATA Hakan, ai da kasani shammata kayi ko kasa mata wani abu wanda nazata san Kaine kai MATA ba.. fans jimmai tanada imani kuwa? Ko da abunda ka shuka!? Haka dai suna saƙawa suna kwancewa akan mugun nufinsu ta yadda zasu samu mafita.... _____________ Tun da AQEEL ya tafi sai kuma Hankalin AKEEL ya tashi ta ganin a halin da ɗan uwansa ya tafi gida! Dan haka karatun kawai yajishi ne Amma bai ɗauka ba, hankalin sa ya rabu Biyu, ɗaya anan ɗaya acan, sai da yayi tunanin" infa AQEEL yakai wannan matakin daƙar yake kaiwa yasha maganin nasa ma, to inya ɗauko maganin wazai bashi ruwa yasha? Jimmai tana wajenta, ko tana nan ma ba kulashi zatayi ba, Usman ai basa shiga harkar sa gwanda ma shi AKEEL ɗin suna ɗan magana sallama da maiamancin Hakan,Amma shi AQEEL ko kallonsa bayayi, tun lokacin da yai Masa tayin kallon fina_finan banza,dan ragewa kansa damuwa... ALLAH sarki AQEEL kamar yasan Usman zai Masa wannan mummunan sharrin, da lalatawa ƴar uwarsu Rayuwa! Sai da yayi wannan tunanin ne kuma bai kammala karatun ba ya bawa liman uzirinsa Akan zaije gida yau, ya duba halin da ɗan uwansa yake ciki. A haka ya hawo machine ɗinsu yayo gida, yana tafe yana wasi wasi a zuciyarsa...Dan uwa kenan kamar yasan meke faruwa da ɗan uwansa AQEEL da kuma ƙanwarsa AKEELA abune marar daɗi,a haka har ya ƙaraso cikin gidansu mai gadi ya buɗe Masa gate, Sannu da dawowa yai Masa sannan malam sallau ya tambaya ina ɗan uwan naka? AKEEL yace ya rigani dawowa bayajin daɗi ne!oh lokacin na zaga kenan bansan yadawo ba,kai Masa Sannu, malam sallau a zuciyarsa yana tausayawa AQEEL dan kuwa yasan abunda Yake damunsa, sau tari a gabansa ake fita dashi in ciwon yatashi, ko likita yazo dubashi har gida, sau tari ma sai an dangana ga Asibitin ake samun lagon abun. Jimmai da Usman suna tufka da warwara sukaji alamun machine ɗin su AKEEL, sai sannan ma sukasan AQEEL shi kaɗai yadawo gidan, kenan ciwon ne yadawo shi gida, cewar jimmai tana kallon Usman, Ea gaskia maama saboda gaskia ko da yashigo alamu sun nuna baya hayyacinsa sosai ai! Yi Zamanka anan idan ya shigo sai ka sulale ka fice alamun baka gidan ma, Amma kuma idan ƴar nan ta farfaɗo ta faɗi wannan maganar akwai matsala! A Hakan AKEEL ya shigo falourn yai sallama Duk da yasan daqar zai samu wani a falourn dan Hakan ya nufi ƙofar da zai sadasu da ɗakin barcin su, yana shiga idansa ya hasko Masa AKEELA da AQEEL a Wannan halin da Usman ya sakasu, bakinsa yana rawa "B....ro m.e.z.a.n g.a.n.i h.a.k.a! yana dumfarar ƴan uwansa Hankali a tashe, ai ƙara kawai ya saki lokacin daya ƙarasa kusa dasu, ganin halin da AKEELA take ciki da shima AKEEL ɗin, zuciyarsa wani irin bugawa tai baisan lokacin daya saki wata ƙara mai rikitarwa ba yakai ƙasa a sume! Daga Usman har jimmai sun dan meyasa AKEEL wannan ƙarar, dan haka taiwa Usman nuni Akan yafita daga gidan,aikuwa da gaggawa yafice daga gidan ko tausayi ko ya duba halin da AKEEL ɗin yake ciki irin wannan ƙara da yayi ta firgitarwa wanda ba'a ɗayan biyu har mai gadi yajita,Duk da zurfin gidan! A gaggauce Jimmai ta shigo ɗakin nasu samu tayi shima AKEEL a sume yake alamu sun nuna wannan abun ya bugeshi kenan, ina kuma ga Ɗalhat inda shine yagani ko yaji labarin abunda AQEEL ɗin yayi! Cikin gaggawa ta ɗau waya ta Kira Abbu cikin Kuka tace Masa AQEEL da AKEEL Basu da lafiya, sannan itama AKEELA Hakan ai Ɗalhat gigicewa yayi jin ance iyalinsa Babu lafiya yaji jimmai tana Kuka dan haka zuciyarsa da ruhinsa suka tabbatar Masa abun babba ne, bai tsaya tambayar meya samesu ba kawai yace MATA gashinan, kunsan Ɗalhat da son ƴaƴa, dama ba wani nesa sosai yai ba, magana ce Akan foundation ɗin da yakeso ya kafa, shiyasa kwana biyu baya Zama, yau yana kano gobe yana wannan gari, so yake foundation ɗin sa ta kafu a gida Nigeria, bawai iya kano ba so yake ta ko ina ya taimakawa marasa shi da marayu, suna gama waya da Jimmai ya Kira likitan da yake zuwa dubasu idan basuda lafiya, Akan Yaje gida ya duba yara, basuda lafiya,shima gashinan dawowa. Abunka da kuɗi nan danan yasamu ticket jirgin da zai tashi daidai lokacin Babu Ɓata lokaci ya ɗauko hanya, to dama yana kaduna ne. Ɗalhat ya Kira Jimmai yace MATA ta kwantar da hankalin ta ga doctor nan ya turo ya dubasu, har sannan makirar Kuka takeyi, dan haka Hankalin sa yakuma tashi, ko da Ɗalhat yacewa jimmai ga Doctor nan batayi wani abuba Akan ta gyarawa AKEELA da AQEEL jikinsu, dan bai kyautu a gansu a haka ba, Amma ina sai tayi funfurus,a zuciyarta gwanda doctor yagani yazama shaida ai shima,ko da AKEELA ta tashi tace Usman ne ai doctor zai ce yazo yagani shima. Tanajin Horn da buɗewar gate tasan Doctor ne ya ƙaraso, dan haka sai ta zauna a falourn tana sharar hawaye! Doctor Najeeb yana shigowa ganin jimmai na Kuka yace MATA meyake faruwa! Cikin Kuka ta nuna ɗakin AQEEL tana magana " doctor shiga kaga ɗanyen aikin da AQEEL yai wa ƴar uwarsa! Abunnan yabani tsoro da mamaki, fita nayi shine fa ita shigowa na tsintsi wannan bala'in kai duniya ina Zaki damu! Ɗan uwa ya nemi ƴar uwarsa, ya lalata MATA rayuwa, yai MATA fyaɗe! yarinya kamar AKEELA guda nawa take, shi kansa AQEEL ɗin guda nawa yake, Nikam Jimmai naga Rashin imani Yau! Maganganun da Jimmai take kenan, kan doctor kullewa yayi jin wai AQEEL yaiwa AKEELA fyaɗe garin Yaya kenan, yana wannan tunanin ya shiga cikin ɗakin,ai da gaggawa ya fito, ƙirjinsa yana harbawa, lallai wannan yaro yacika marar kunya da tausayi ƴar uwarka zakaiwa haka, fitowa falourn yayi inda Jimmai take sharbar kuka, doctor cikin jimami yace "Hajiya gaskiya wannan abun bana gida bane sai munje ga Asibiti, Yanzu shiga ki sittirawa yarinyar jikinta shima Hakan,dan kuwa yana cikin wani Hali, cewar doctor yana ɗaukar waya dan yayi Kira! Cikin Kuka jimmai tace "ga kuma ɗan uwansa a ƙasa a sume, alamu sun nuna shigowa yayi yaga wannan ta'asar da ɗan uwansa yayi shine ya sume, ko ya Hakan ta faru oho? Dan kuwa tare suke dawowa! cikin Kuka take wannan maganar... lalläi fans Jimmai ko kwalaba batakai ta Sharri ba. Data shiga ɗakin sai da ta tausayawa AKEELA ganin yadda Usman yai MATA filla_filla yai MATA raga_raga,alamu sun nuna gaskiya ba wannan karon ya Fara mu'amula da mace ba, kenan Usman neman MATA yakeyi? Ta jefawa kanta wannan tambayar! Lallai ALLAH yasa kar likitoci su gane hakan,dan kuwa Babu yadda ja'ace ƙaramin yaro kamar AQEEL ya aikata wannan aika aikar, guda nawa ma yake banda ALLAH yayi halittarsa mai sha'awarce Amma kamarsa wasu ma Basu balagaba, ga ɗan uwansa ma! Tana waɗannan zantukan a zuci ta sakawa AKEELA kayan, wacce takenan kamar mara Rai ta jigata,shima AQEEL ɗin saka Masa kayan tayi,ko ganin halin dayake ciki baisa jimmai ta tausaya Masa, ta warware wannan Sharri da aka ƙwallafa Masa ba! Tana gama saka musu kayan cikin Kuka tai waje,alamun zuciyarta Babu daɗi Akan abunda AQEEL yayi. Tana fitowa falourn kuma ta samu doctor yana waya da Abbu inda shi doctor yazata jimmai ta faɗa Masa komai, dan haka yace " Alhaji gaskia abun Babu kyan gani yanzu dai sai munje Asibiti, dasu baki ɗaya, shima kansa baya. Hayyacinsa balle wacce yaiwa aika aikar, cikin ɗaurewar kai Ɗalhat yai wa doctor tambaya " ban gane abunda kake nufi ba, cikin girmamawa doctor Najeeb wanda hankalinsa bai kawo Ɗalhat baisan komai ba, "AQEEL yaiwa AKEELA gaikiya illa sosai, dan alamu sun nuna har dai da ta Suma kafin ya rabu da ita daga fyaɗen da yai MATA, tamkar saukar aradu ko fashi Ɗalhat yaji wannan zancen a kansa! kafin yadawo hayyacinsa kuma doctor yaci gaba da magana " dan haka zamu ɗaukesu zuwa Asibiti shi da ita, harma AKEEL dan shima mun sameshi a sume, ƙarshen zancen da doctor yayi ne ya dawo da Ɗalhat hayyacinsa, da ok kawai ya faɗa yana gimtse wayar, zuciyarsa da ƙirjinsa suna suwa wai AQEEL ne yaiwa AKEELA fyaɗe? To jimmai tana ina wannan abun yafaru? Meyake damun AQEEL ɗin? AKEELA zai wa Hakan?ta yaya ma? Inda ace Ɗalhat da tsautsayi ko ace yanada hawan jini da tuni yakai ƙasa zuciyarsa ta buga, Amma yanada ƙarfin zuciya, kuma sai addu'a yake a harshensa, najin wannan bala'i da ya tunkaro shi, wazai gayawa wannan magana ai abun kunya ne, sakayyar da AQEEL zai Masa kenan, Kullum nasihar dayake Masa kenan,ya kame kansa idan yaga bazai iya ba yafaɗa Masa shi zai Masa Aure bazai duba ƙanƙantar shekarunsa ba, Amma ina sai da AQEEL ya aikata Zina zinarma da ƴar uwarsa! innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun Allahumma ajurni fi musibati wa a ka lifni khairan minha! Adduar da Ɗalhat yake azuciyar sa kenan, da kuma tunanin AQEEL ɗin lallai ma. A haka har ya shige jirgi har zuwa tashin jirgin baisan a wane yanayi yakeba, gashinan ga kamarsa dai. Dan haka doctor Najeeb ya Kira wani doctor daban, haka aka cicciɓi su AQEEL aka Sanya a mota zuwa Asibiti. Koda sukaje asibitin abunka da kuɗi sai nan nan ale dasu, Amma kuma ganin halin da AKEELA take ciki yasa doctor da yawa zub da hawayen tausayi,dan doctor mace aka bawa ita, Usman yai aika aika,dan kamar ƙwarya haka aka ɗinke AKEELA, ALLAH ya kiyayeta da yoyon fitsari ko ƙwaƙwalwar ta ta samu matsala, cewar doctor Maryam tana duban abokiyar aikinta, dan sun san irin wannan matsalar tanasa Hakan, koda ake ɗinkin, sai da aka kusa gamawa sannan AKEELA tai wata mahaukaciyar ƙara tana fisge_fisge, sai da aka saka MATA Robar ƙara numfashi, kafin numfashin ya daidaita, sannan aka haɗa MATA da allurar barci, aka maƙala mata ƙarin ruwa,abun tausayi AKEELA dole ai ki galabaita! Yarinya ƙarama kamarki,ai miki fyaɗe fyaɗen ma na acire tausayi da imani a keta ki tun daga sama har ƙasa. Ɓangaren AQEEL ma taimakon da aka Saba Masa Duk sanda irin Wannan matsalar ta faru shi aka Masa, kafin ai Masa gwaje gwaje, anan kuma Doctor ɗin sukasha mamakin abunda gwajin ya tabbatar, dan doctor Najeeb bai ɓoye musu komai ba Akan abunda yafaru tsakanin AQEEL da AKEELA ɗin! Bayan doctor Najeeb ɗin yafito ne ya samu doctor Maryam, Akan ya kuma jikin AKEELA ɗin, sai sannan doctor Najeeb yai MATA bayanin abunda ya faru, fasta doctor tayi jin abunda doctor Najeeb ya faɗa MATA " wannan yaron ne ya aikata wannan aika aikar? Gaskiya da sake doctor daga ganin wannan Aikin babbane yayi shi, babban ma wanda yasan takan MATA, yasaba mu'amula dasu,Amma yaron nan ace farkon mu'amula da mace yai MATA haka, ina bazai iyaba, ai akwai Rashin sabo a harkar, da karancin shekarun sa ma ALLAH yasa in anbashi mace ya iya shigarta sosai, balle yai mata filla filla haka,ina da ja Akan wannan zancen, doctor Maryam cikin ƙaraji take zancen nan, doctor Najeeb yace "kwantar da hankalin ki doctor, gwajin dana fara Masa kenan, inda sakamakon ya fito, cewa tabbas yaron nan bai aikata komai ba,dan kuwa in da ya aikata kusantar bazai shiga halin dayake ciki yanzu ba, saboda azabar dayake ji ajikinsa, kusantar yarinyar zai rage masa wani abu, Duk da dai yakai limit, Amma kamar yadda in yasha magani daidai wannan matsalar ta sameshi Hakan zeyi, bazai Suma ba, Amma fa a sume muka ganshi, inda dai yakeyi in bai Sha magani ba,shima doctor Najeeb ya ƙarasawa doctor Maryam bayanin cikin jimami! Kafin yaci gaba dai MATA bayanin "lallai akwai lauje cikin naɗi kam, Amma abun da mamaki halin dana tsintsi yaran aciki, alamu sun nuna tabbas yaron shine yaiwa yarinyar fyaɗe,yanzu dai farfaɗowar yarinyar shine babban burinmu, Duk da muna da hujja muma! Doctor Maryam, ki kwantar da hankalin ki! in Sha ALLAH abun zaizo da sauƙi, mu jira Alhaji yanzu ya ƙaraso dan da muka gama waya dashi, yace mun yanzu zai tawo daga kaduna, sauke Ajiyar zuciya doctor Maryam tayi da doctor Najeeb ya ƙarasa MATA bayani, ai shikenan kawai tace shikam doctor Najeeb ficewa daga office ɗin yayi. Shima dai AKEEL an samu numfashinsa ya daidaita allurar barci aka Masa, shima. Jimmai dai sai kaiwa da kawowa takeyi alamun tana cikin tashin Hankali. Usman wanda ya fice daga gidan, hankalin sa Duk da haka bai kwanta ba, na halin daya leƙa yaga AKEEL shima ya shiga, Amma kuma zuciyar sa fesfes tun da dai ya fita daga tarkon zargi, sai kuma idan ya tuna AKEELA inta farka asirinsa dai zai iya tonuwa,dan haka yake ƙissima Abubuwa da yawa a zuciyar sa game da itan. Waya ya Kira uwar tasa dan yaji meke faruwa? Lokacin kuma jimmai tana kai kawo a Harabar asibitin ne ALLAH yaso ta ɗauko wayar tata, ko da Yake me zai hanata ɗaukowa, mutuniyar da Tashin Hankalin datake ciki na ƙarya ne, tana ɗaga kiran Usman yace MATA "ya dai maama meke faruwa? Ajiyar zuciya jimmai ta sauke sannan ta ce" gamu a asibi ma ai Alhaji nakira,nagaya Masa cewa ƴaƴansa Babu lafiya, shine ya turo doctor nan dai ta kwashe yadda akayi ta faɗawa Usman ɗin ajiyar zuciya kawai yayi ya kashe wayar! Miƙa yayi daga kwancen dayake, dan gidan wan ubansa ya tafi,inda ake riƙonsa shi da Shukra ƙanwarsa, wan ubansa bai taɓa Haihuwa ba shiyasa da Babansu Usman ya rasu shi ya ɗaukesu ya riƙe, tun suna yaran, Duk wata kyautatawa yana musu shida matarsa Basu rasa komai ba, ko da Usman yace zai koma gidan jimmai da Zama basuji daɗi ba,Amma haka suka haƙura.. Jimmai ta gaji da kaiwa da kawowa sai ta samu kujera ta zauna tai uban tagumi, a haka Ɗalhat ya iso asibitin, jikinsa a sanyaye gwanin tausayi,Duk wanda yaganshi yasan baya cikin Hankali da tunanin sa, Jimmai ta ganshi Amma sai ta nuna alamun ta zurme cikin tunanin abunda ya faru, sai da yazo kusa da ita ya dafa ta sannan tai firgigit, alamun ta dawo daga hayyacinta, ai Kuka ta rushe dashi " shikenan Ɗalhat AQEEL ya cucemu ya Ɓata Mana zuri'a, ya cuci AKEELA kamarsa ƙanwar sa zai lalata, wannan masifa dame tayi kama! Jimmai ta ƙarasa zancen cikin Kuka tana mai dafa kafaɗar Ɗalhat cikin tashin Hankalin data nemowa kanta na ƙarya, shi dai Abbu zuciyarsa shima ta tsinke ganin irin kukan da Jimmai takeyi! Lalläi AQEEL ya aikata abun ƙyama a rayuwarsa, wannan wane irin hali ne dashi, Amma fa ya cuce kansa kuma ya cuceni a matsayin mahaifinsa, kuma ya cuci ƙanwar sa, tur da halin ka AQEEL! Abunda Ɗalhat yake faɗa azuciyarsa kenan, lokacin tuni jimmai ta shige jikin Ɗalhat yana gursheƙen Kuka! Wanda Hakan yake daɗa tunzura zuciyar Ɗalhat ɗin da kuma ganin baƙin AQEEL ɗin................ Innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun kawai zance ni Oum ARQAM Amma Usman ya cuci AQEEL fa....... ALLAH sarki AKEELA😭😭😭😭 Gaskiya jimmai batada imani fa abun yakai ga haka Muje dai Zuwa next page yan Amana, Amma tsakanin wannan Page ɗin na 47 dana baya 46 bansan wanda yafi wani taɓa zuciya dasa Kuka ba Nikam wannan yafi ban tausayi🤧🤧 wancan ma yabani shima Amma wannan ya famamun mikin wancan🤧 ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 2/24/24, 5:29 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY EIGHT 48* Tun shigowar Ɗalhat Asibitin Doctor Najeeb ya san shigowar tasa,dan haka ko lokacin da jimmai take wannan kukan bai ƙaraso wajen ba,sai da ya ƙaraso kuma sannan yai tozali da jimmai tana ta gursheƙen Kuka, tun daga sannan Doctor Najeeb jimmai kukan da take ya Fara tsaya Masa a rai! Ga kuma sakamakon gwaje_gwajen da akayiwa AQEEL aina matsalar take? Yasan dai Hajiya jimmai Ba Mahaifiyar su AQEEL bace? Amma kuma shaƙiƙiyar Mahaifiyar su ce! Abunda Yake hasashe Anya kuwa ? To in ba AQEEL bane waya aikata wannan mummunan Aikin? Tunanin da Doctor yake a Ransa kenan har ya ƙaraso wajen nasu! Ɗalhat kuwa yana tsaye kamar dutse! Shi yasan abunda yake damunsa kawai!Amma wannan tashin Hankali haka! Aiwa ƴar ka fyaɗe! Abun Tashin Hankalin ma ace ɗan uwanta ne yai wannan Aikin! Ai ba kowane uba ne wannan abun zai sameshi zuciyarsa ta zauna lafiya ba! Shima kansa yanzu ya san inda za'a Auna jininsa za aga ya hau, dan lokacin da Doctor yake faɗa Masa abunda ke faruwa ba don ya Fara jero adduoi a Ransa ba,ai da tuni yaje ƙasa yanzu wani zancen ake ba wannan ba! "Yallabai ka ƙaraso kenan! Doctor ya faɗa Shi dai Ɗalhat Bai samu damar mayar da amsa ga doctor ba! Dan haka doctor yaci gaba da magana, yallaɓai inason Muje office Yanzu,ka Kwantar da Hankalin ka dan ALLAH,kar wani abu ya same ka, komai da ya faru muƙaddarine daga ALLAH abun da ya faru ya Riga ya faru! Kema Hajiya kiyi Haƙuri ki daina kukan doctor ya ƙarasa maganar yana kallon jimmai da ke share hawaye dan lokacin tabar jikin Ɗalhat ɗin, ganin bai tofa tasa ba, taso a Ranta ya dinga tsinewa AQEEL ɗin,Amma shiru ita kanta bai lallasheta ba sai yanzu da doctor yazo yai magana. Jiki sanyaye Ɗalhat yabi Doctor Najeeb office,kamar yadda ya buƙata, ruwa Doctor ya bawa Ɗalhat yasha, dan yaga alamu maƙogaronsa ya bushe da wannan tashin hankalin da ba'a saka Masa Rana! Ɗalhat Bai yi Musu ba karɓa yayi ya Sha ya sauke ajiyar zuciya! Doctor yai gyaran murya sannan ya Fara magana! Duk wani taimako da za'a yi wa yaran Duk anmusu, ita yarinyar tana CIKIN wahuyacin Hali, Amma an MATA Duk wani abunda take buƙata, yanzu haka an MATA ɗinki ciki da waje, ALLAH yasa ta farka Hankalin daidai kamar yadda Muke fata,Amma kam ƴar nan abun gwanin ban tausayi, Tunda doctor Najeeb yafara bayani Ɗalhat zuciyarsa take ƙuna, lallai ma yaronnan kamar sa shine zai wannan mummunan Aikin, lalläi yaro kana tare dashi ka haifeshi baka Haifi halinsa ba! sannan shi kuma ɗan uwansa ba wata matsala bace Babba firgici ne yasa shi Suma, Amma yana farfaɗowa in Sha ALLAH komai normal ne, shi kuma AQEEL ɗin shima Duk abun...... Tunanin da Ɗalhat yake sai da doctor najeeb ya Fara magana sannan yadawo hayyacinsa, sai kuma da yaji ya sako zancen AQEEL ne ya ɗago a fusace ya zubawa Doctor Najeeb idanuwansa wanda sukayi kamar garwashi,Hakan yasa Doctor ɗin ƴar in ina ........ Sai kuma yaji maganar sa kar kayimin zancensa Anan Duk abunda zai sameshi ma ya sameshi, ko Alhakin ƴar uwarsa da na ɗan uwansa ganin abunda yayi yasashi Suma, ga Alhakina ai bazai barshi ba Ɗalhat ya ƙarasa maganar yana sauke ajiyar zuciya wacce daga ji ta Tashin Hankali ce Tunda yafara magana doctor be katse shi ba, dan kuwa yayi dauriya shi kam dan ace danƙa yaiwa ƙanwar sa fyaɗe ai abunda yafi hakama zai faɗa,in wani mai raunin zuciya da tunani ne ai tsinewa ɗan zai Fara, da gaya Masa kalamai marasa daɗi, wannan ma ai kaɗan ne doctor Najeeb ya faɗa a Ransa! "Yallaɓai yadda dai yaronnan yake shiga mawuyacin Hali a Duk sanda lalurar sa ta tashi hakane! Babu wani sabon al amari a tare dashi wanda za'a ce ya samu nutsuwar da wata mace!shiyasa ma dan gudun tantama muka Masa gwaje gwajen da zai tabbatar da Hakan, tun kafin ma muyi Masa allurar da ale Masa,kuma munga alamun ba shine ya aikata fyaɗen ba,Hakan shine ni da doctor Maryam muka shiga cikin jima mi da tararbin ya Hakan ya faru? Yallaɓai kuma ta ni ganau ba jiyau bane ganin halin da AKEELA da AQEEL ɗin suke ciki Babu wanda zai ce bashi bane ya aikata! Doctor Najeeb ya ƙarasa yiwa Ɗalhat bayani cikin sanyin murya! Duk bayanin da doctor najeeb yakeyi Ɗalhat yana saurara har doctor yakai aya bai topa tasa ba! Amma kuma zuciyarsa ta shiga maimata maganganun da doctor yai Masa,to wanene ya aikata wannan mummunan Aikin kenan? Sai zuciyarsa ta shiga wasi wasi Akan Hakan! Doctor Najeeb ya cigaba da bayani " kuma yallaɓai ina Hajiya take wannan abun ya faru? Dan yarinyar zatayi ihun neman taimako kafin ƙarfinta ya ƙare, mun aunata munga Babu alamun an sheƙa MATA wani na juyar da Hankali kafin Hakan yafaru, kuma ma yadda doctor Maryam ta faɗamin,lokacin da yarinyar ta farka da Ihu ta farka da fusge fusge alamun lokacin da zata Suma ƙwatar kanta take Shirin yi, yallaɓai yanzu dai mujira farkawar yarinyar cikin Hankalinta, da shi AQEEL ɗin dan anan zamu daɗa tabbatarwa, da kuma AKEEL tun da shima maybe yaga wani Abu! Duk bayanin da doctor Najeeb yakewa Ɗalhat yanaji Amma kuma zuciyarsa da tunanin sa ta bashi tabbacin lallai ne ajira su farfaɗo,Amma kuma in na AQEEL bane wanene ya shigar masa har gida ya ketawa ƴar da mutunci, sannan aka fake da Lalurar AQEEL aka jefeshi da wannan baƙin ƙazafin?koma dai wanene yasan kan Gidan! Kamar yadda doctor Najeeb ya faɗa ina Jimmai ta tafi wannan mummunan Aikin ya faru? Duk wani bayani doctor Najeeb yaiwa Ɗalhat, hakama ya kira doctor Maryam ta ƙara Masa nata, daga ƙarshe suka dinga Kwantar Masa da Hankali Akan karya sa abun a rai in Sha ALLAH ko wanene yai wannan Aikin ALLAH zai tona Masa Asiri, daga haka ya fice daga office ɗin, in da yasamu Jimmai a Zaune a reception tana ta sharar hawaye, sai yaji zuciyarsa tana wasi wasi Akan jimmai sosai! Tana ganin Ɗalhat ya taho ta yunƙura tana mai kuma share hawaye na makirci,ta ƙarasa wajensa,shi dai har sannan bai mata magana ba, Meyake faruwa? Me sukace maka game da AKEELA da AKEEL ɗin? Dan ni bazan tambayi AQEEL ba kome ya faru shine sila,Yaro kamar bunsuru, ƙanwarka zaka Haikewa duk cikin Kuka jimmai take maganar kai kace gaske ne! Cikin baƙin ciki Ɗalhat yace koma mene ya faru kina ina? ɗuf kukan da Jimmai take ya ɗauke jin tambayar da Ɗalhat yai MATA! Sai tafara in da in dar kare Kai,fita kikayi kenan baki gayan ba? Ai shikenan Zanyi bincike Akan komai daya faru a Gidan, Ina da me gadi Zan tambaye shi komai, kuma Doctor sun mun bayanin cewa Ba AQEEL bane ya aikatawa ƙanwarsa fyaɗe ba, Kinga kenan akwai lauje cikin naɗi, wanda yasan sirrin gidan mune ya aikata Hakan, kuma kece Kika ba da ƙofa inda baki fita ba Babu ta yadda Hakan zai faru! Tashin Hankali wanda ba'a saka Masa Rana ga Jimmai! Duk bayanin da Ɗalhat yai MATA taji shinenan asirin Usman zai Tonu! Ita ma ta shiga uku kenan, sai ta Fara magana cikin karaya " kayi haƙuri daban fita ba Hakan bazai faru ba, Amma kuma nacewa ba AQEEL bane ina mamakin wane? Babu mai shigo Mana gida gida, kuma fa Yadda na ga halin da AKEELA da AQEEL suke ciki abun akwai mamaki fa, Amma tun da kace zakai binkice Shikenan! Jimmai ta ƙarasa maganar da alamun tausayi! shi dai Ɗalhat Bai kula zancen da Jimmai takeyi ba,Duk haushin ta yakeji,na yadda idan ba dan ta fita ba ai da ba ta yadda Azzalumin da yashigo ya cuci yarinya ƙarama zai samu da ma ba! Ɗalhat dai yana zaune a kujera yayi jugum yana jiran tsammani,yayin da Jimmai take kusa dashi taketa soke burutsun ta! Yana tsaka da tunani Usman ya Faɗo Masa a rai dan haka yaiwa jimmai tambayar da ta Lisa tsarwatsa MATA kwanya "Ina Usman yake wannan abun ya faru? Ban ganshi ba? Inji Ɗalhat ya na kafe Jimmai da Ido, Amma a Ransa baya tunanin Usman zai aikata Hakan,kawai dai tambayar yai MATA, ita kuma dayake Babu gaskia shine ta razana ta tsargu, kafeta da idon da yayi kuma na mamakin daga yace ina Usman shine ta tsargu! Ai tun washe garin da kayi tafiya shima ya tafi gidansu, wai babansa (wan baban su)bai ji Daɗi ba shine yaje gurinsa, Oh shikenan,Amma baki gayan ba ai shikenan. Suna wannan tattaunawar Zuciyar Ɗalhat Babu daɗi, yanzu AKEEL da AQEEL da AKEELA su farka shine burinsa! Zuciyar jimmai itama haka,Amma ita Rashin daɗin Zuciyarta na son zuciyarta ne da zalunci, ɗan ka yaiwa yarinya ƙarama fyaɗe har ka rufe abun,kuma ma wai sunan ƴar ƴar uwarki haba ai zaluncin yai yawa! A haka AQEEL ya farfaɗo,kamar yadda ya saba farfaɗo wa, dan haka nurse tazo tai kiran Ɗalhat Akan yazo AQEEL ya farfaɗo, Lokacin jimmai tace wa Ɗalhat bari taje gida ta tawo da abincin dare,bai hanata ba kuma bai bata amsa ba a haka ta fice da ga Asibitin, Ɗalhat ne ya nufi ɗakin da AQEEL yake, Alhamdullillahi kamar yadda yasaba tashi haka ya tashi, Babu wani razani ko jin kunya, na cewa tabbas shine ya aikata wannan mummunan Aikin! Dan haka Doctor Najeeb ya kuma Tabbatar wa ƙazafi ne aka ƙullawa AQEEL ɗin da cutarsa, da sassarfa Ɗalhat ya ƙarasa, ga AQEEL ɗin yana Masa Sannu, yana amsawa shi kuma daƙar saboda har sannan mararsa tana Masa ciwo kaɗan, kafin AQEEL ɗin yace "Abbu Yaushe kadawo? Nazata sai jibi zaka dawo?doctor Najeeb waje ya Basu, aikuwa Hakan yaiwa Ɗalhat daɗi, dan Haka yabawa AQEEL amsa da " eamn dawowa nayi kawai sai na sameka a halin da kake ciki! Meyasa bakyasha maganin ka ba? Kasan doctor yace kadaina sakaci da Shan magani! Cikin dauriya AQEEL ya kwashe Duk yadda ya kasance dashi tun da ya tashi da safe har sukaje school da zuwansu masallaci da tawowar sa gida Shan magani, inda yace Abbu nidai nasan na shiga cikin ɗakin mu daga nan sai Yanzu dana farka! AQEEL ya ƙarasa gayawa Abbu haɗe da cije bakinsa! Tunda AQEEL ya Fara yiwa Ɗalhat bayani zuciyarsa ta Fara cinkewa lallai akwai lauje cikin naɗi, Amma Babu komai yanzu saura AKEEL farfaɗowar sa da kuma me gayya me Aiki AKEELA! Ɗalhat ya ayyana a zuciyarsa Jinjina kai Ɗalhat kawai yayi yana shafa kan ɗan nasa,cike da tausayi yanzu da tuni shikenan ya tsine Masa, ko kuma ana kallonsa da aikata babban zunubi irin Hakan, shi AQEEL da baisan me yake damun mahaifin ba ma! sai ya tambaye shi ina AKEEL domin kuwa ya saba yana farkawa yake ganin sa tare dashi, Ɗalhat yace ai halin da AKEEL yaganka a cikine ya sashi shima sai da aka kawo shi asibitin ya Suma! Zuciyar AQEEL sai ta shiga wasi wasi ai ba yau yafara Suma ba Akan lalurar sa ba, kuma AKEEL bai taɓa Suma ba shi sai yau? Me Hakan yake nufi? Kuma ya ga alamun kamar Abbu yanada damuwa a Ransa, zantukan da yake mamaitawa a zuciyarsa kenan, suna wannan halin Nurse ta shigo tace shima AKEEL ya farfaɗo Amma sai Kuka yakeyi, doctor zai Masa allurar barci ya hana, daga Ɗalhat har AQEEL wanda komai ƙarfin Hali yake tare suka Mike tsaye jin abunda nurse ta faɗa, dan haka tare suka bi bayanta zuwa wajen AKEEL, AQEEL yana mamakin kukan da akace AKEEL yanayi, shikam Abbu bai mamakin Hakan ba, ALLAH yasa wani abu AKEEL ɗin ya gani zai warware musu komai inji Abbu a Ransa. Haka suka ƙarasa cikin ɗakin da AKEEL yake gurshe ƙen Kuka, baisan da AQEEL aka tawo ba ya zata Abbu ne kaɗai dan haka tun daga baƙin ƙofar da AKEEL ya hango Abbun ya Fara magana har sannan yana Kuka "Abbu ɗan uwana bazai aikata abunda naganshi a ciki ba, AKEELA nagansu tare alamun yai MATA fyaɗe kace Abbu mafarki nake ba gaskia bane, ɗan uwana ba yau yake cikin wannan halin ba,wanine yakeson cutar damu,shiyasa yai Masa Hakan,sai yau za'ace yayi Zina,zinar ma da ƙanwar mu wayyo ALLAH na Abbu cikin kukan yake zancen! Dayake cikin ƙaraji yake zancen, AQEEL da yake bayan Abbu saboda marar sa a Hankali yake tafiya,shi kuma Abbu yana zumuɗin ganin AKEEL da abinda zai faɗa,shiyasa bai wani kula da yadda AQEEL yake tafiya ba,balle ya riƙo shi,! Duk maganganun da AKEEL yake a kunnen AQEEL,zuciyarsa bugawa ta fara da sauri da sauri,jiri ne ya ɗebe shi, sai da ya dafe bango da ma ga jiki ba bu daɗi, ALLAH ne yabashi ikon ƙarasawa ciki,shi dai Abbu kallon AKEEL yake cikin tausayi,sai kuma AKEEL ɗin yaci gaba da magana ganin shigowar AQEEL ɗin " bro bakai ka aikatawa AKEELA wannan Aikin ba ko?kace sharri akai maka? Kan AQEEL ya kuma kullewa da wanga al amari! jijiyoyin jikinsa sun kuma tsinƙewa! jin abunda AKEEL yake faɗa Shi dai AKEEL cikin futar hayyaci yake magana, saboda ya tsorata da ganin halin da AKEELA tace ciki, jini kamar an yanka ƙaramar dabba, ga kuma ɗan uwansa kusa da ita,abun ba bu kyan gani! Abbu Yaje kusa dashi yana lallashin sa Akan "ba ɗan uwanka bane ya aikata MATA kaji AKEEL ɗina ka Kwantar da hankalinka ganin kamar baya hayyacinsa ne yasa Abbu yaiwa Doctor alamar yai Masa allurar barcin aikuwa yana Masa kafin kace me barci ya ɗauke shi, Doctor yacewa Abbu in Sha ALLAH zai farfaɗo cikin Hayyaci in Sha ALLAH. AQEEL kamar mutum_mutumi jin waɗannan kalamai da Ɗan uwansa yake faɗa, cikin tsinkewar zuciya ya Fara magana "Abbu ku futar da ni daga wannan duhun,wanene yaiwa AKEELA fyaɗe? Ni ne kuma? Ganin ya fita hayyacinsa ne Abbu yajo wajensa, yana Babu komai AQEEL da komai Abbu gashi AKEEL yana gayamun,wasu maganganu anya AKEELA fyaɗe sannan kuma ance nine innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun! Wayyo Abbu bani bane,shiyasa AKEEL yashiga wannan Hali, kaima shiyasa naga ka dawo alhalin tafiya kayi, wallahi Sharri akamun cikin ku ka gwanin tausayi AQEEL yake zancen!kafin daga bisani ya sulale ya faɗi ƙasa a sume................... Muje next page😭😭😭😭 hawaye ya cikan idanu ya hanayi ganin screen ɗin wayar balle naci gaba da typing ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 2/26/24, 10:16 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FOURTY NINE 49* Tun barin jimmai daga Asibitin dataje gida kasa Samar da abincin da tacewa Abbu zata ɗauko tayi! Sai saƙawa da kwancewa takeyi, da yadda zata ɓullowa wannan al amari da yake tunkaro ta itada Usman, dan indai asirin Usman ya tonu shine yaiwa Akeela fyaɗe itama ta shiga ciki. Sai kaiwa da kawowa takeyi a flourn ta, daga ƙarshe ta Kira number Usman dan tagaya Masa abunda ke faruwa, idan da wani shiri da zasuyi to! Lokacin Usman yana gidansu a kwance a ɗakin da ya kasance nasa tun kafin barinsa gidan,dan wan Babansu mai kuɗine sosai, Sana'ar daya saba yakeyi yanzu haka wato kallonsa na Vedios fin batsa, dan ya manta wata Akeela yanzu,ko tausayin halin daya barta Bai tuna ba, tsabar Rashin imani! Jimmai tana Kiransa sai sannan yadawo hayyacinsa saboda yatafi wata duniyar,kiran ne ya ɗan dawo dashi hankalinsa! Yana ɗagawa yaji muryar uwar tasa da alamun damuwa da Tashin Hankali! CIKIN muryar da ta daɗe ta tsumu a iskanci, dan kuwa Duk wanda yaji muryar yasan Babu nutsuwa sai wani shaƙewa take yana ajiyar zuciyar! Maama meke faruwa ne! Jimmai tanajin muryar sa tasan da abunda yake shukawa,Amma ko ta kula! Babu lafiya Asirinka yana daf da tonuwa!saboda Abbunsu yace zaiyi bincike Akan Hakan, wai kula likitoci sunce bashi bane yayi fyaɗen! Ko shine ma a matsayin sa na ƙaramin yaro Bazai iya fatattaka mace ba irin haka, dan kuwa akwai tausayi a Ransa da kuma Rashin sabo, ga wacce yaiwa yarinya ce ko kukan da takeyi kafin aikata fyaɗen zai sa yaji tsauyinta ya fasa aikata, Duk bayanin da Jimmai take wa Usman yanaji kuma sai Duk wannan yanayin daya shiga jin abunda uwarsa ta faɗa sai ya watstsake yaji tashin Hankali! Nashiga uku maama yanzu mene mafita? Kar asirina ta tonu!Nima shine Tashin hankalina Usman, meyasa ka aikata wannan Aikin ma wai? Yanzu gashinan kadani a fargaba kaima kasa kanka! Nan dai suka dinga tattauna ta yanda zasu ɓullo wa lamarin Duk ta yadda zasu ɓullo sai suga ba mafita,a haka dai ta kashe wayar jiki ba bu ƙwari ta waɗa kitchen domin Samar da abunda zata koma Asibitin da shi, Zuciyarta sai tsalle take kamar zata fita daga ƙirjinta,kar ma Ɗalhat yai tunanin wani abu da Rashin dawowar tata, dan haka abu mai sauƙi ta dafa,ta kama hanya ta koma Asibitin. _________ Ɓangaren Usman ɗin ma Hakane, dan kuwa kallon dayakeyi kashe shi yayi, komai na duniya tsaya Masa yayi,yanxu idan asirinsa ya tonu ina zaisa kansa? Dawane idanu zai ga Abbu? Abbu Babu abinda baya yi Masa tun daya dawo gidan kamar mahafinsa haka yake,Duk abunda yaiwa su AKEEL da AQEEL haka yake Masa, baya banbantawa,! Tunanin da yakeyi kenan, har Yanzu, daga ƙarshe yace koma dai menene ya kashe ishirwata ai, kuma ba kasheni za'ayi ba, ƙarƙari ya saki Maama,sai me matsalarta ce, a haka ya kau da Duk wani tashin hankali daga Ransa. ******************* Can Asibiti kuwa ALLAH yaso AQEEL bai kai ƙasa ba Abbu ya taro shi, dan haka sai da aka saka Masa Robar ƙara numfashi kafin numfashin ya daidaita, aka haɗa Masa da allurar barci. Idan Kuka dubi Ɗalhat saikun tausaya gareshi, ƴaƴa uku rigis Duk ba bu lafiya, ƙarshe ma aka ƙwallafa yaron sa cewa shine yaiwa ƙanwarsa fyaɗe,ai ba kowacce zuciya bace zata ɗauki wannan Abubuwan,shima adduar da yakeyi ne ta tausasa masa zuciyarsa,ai da shima halin da zai shiga sai ALLAH. Jimmai ta ɗauke hankalin sa daga kan ƴan uwansa, ba sosai yake kula suba, macewa yakeyi da su ma, haka na Suma ta juyar musu da hankalin basa nemansa, shiyasa bai Kira kowa ba yagaya Masa wannan tashin hankalin ba, gwanda ma haka dan kuwa wannan ai tonon asirine, gwanda ma idan gaskiya ta bayyana sa sani koya Kuka ce fans? Doctor Maryam yace a ƙyale Akeela ita kaɗai batason, hayaniya, saboda zuciya da ƙwaƙwalwar ta sun shiga wani yanayi, yanzu ma fatan farfaɗowar ta lafiya CIKIN Hankalinta shine fatan kowa, Amma Duk da haka Abbu yace yanason ganin Autarsa yaga halin da take ciki! Doctor Maryam batayi Musu ba tai Masa jagora har zuwa ɗakin da Akeela take! Tana kwance Akan gadon kamar gawa, ga Robar ƙara numfashi, ga ƙarin Jini, anai MATA ta zubar da jini fa, abun gwanin tsautsayi kamar me Haihuwa ko ɓari! A Wannan yanayin Abbu ya shigo ɗakin, ya tarar da ƴarsa kamar Gawa, Abbu baisan lokacin da Hawaye suka shiga zubo Masa a fuskar saba, doctor Maryam ,sai nuni take masa yayi haƙuri, saboda ba bu halin magana, shikam Abbu sai kallon Akeela yake kamar ba itaba, wannan itace AKEELA cikin lokacin ƙanƙani tai wani mugun rama, ga idanuwanta sun kumbura, abunka da Fara fuskarta tayi jajur hakama leben bakinta, kamar jini ya kwanta, dan ɗan iskan rufe MATA baki yayi da nasa, ganin taƙi daina Masa ihun neman taimako! Haka dai Abbu jiki Babu ƙwari ya fito daga ɗakin, zuciyar ciki da baƙin cikin halin da aka saka Masa ƴa,da Ɗaura ɗamarar fito na fito da Duk wanda yaiwa ahalinsa wannan mummunan Aikin,Babu tausayi Babu imani, yadda ya shayar dashi shida ƴaƴansa Ruwan guba, da azaba shima haka zai shayar dashi Ruman azaba na ɗaukar fansa, kowanene kuwa, yadda bai ji tausayin yarinya ƙarama ba ya keta MATA alfarma ba, sannan yaiwa ɗansa Sharri Akan shine ya aikata,shima bazai saurara Masa ba, shi ma AKEEL gashi yana cikin wani Hali daban, tsakaninsa da wannan mutumin shine ALLAH ya saka Masa yai gaggawar tona Masa Asiri, yana waɗannan tunanin yadawo ɗakin da aka tanadar Masa dan Zama, wani tunanin ya shiga, a haka Jimmai taxo ta sameshi,jikinta a sanyaye ko kulata bai ba,ko kula abincin bai ba ai cin Abinci na lafiya ne, cikin jimami kamar gaske Jimmai, ta tambayi Abbu shin wani ya farka a tsakaninsu? Anan yake ce Mara ea AKEEL da AQEEL sun farka, Amma AKEEL sai Kuka yakeyi,shi kuma AQEEL lafiya qlau ya farka,Amma kuma da akace AKEEL yana Kuka shine AQEEL ya biyoshi anan yaji zancen da AKEEL yake yanzu haka shima ya faɗi cikin wani yanayi sai da aka saka Masa Robar ƙara numfashi ma! Ƴar banza harda su nuna alamun tausayi, da Addu'ar ALLAH ya sauwaƙe, da cewa ALLAH ya tona asirin wanda ya aikata wannan aikin, Allahumma Ameen ko fans? zakuce nasan Kada na jima ko? Me gadi na tambaya waya shigo da bananan shine yace bai sani ba wai, ya zaga bandaki lokacin gaskiya, shi dai Abbu bai magana ba. Cikin ikon ALLAH AKEEL ya farka kuma cikin aminci Babu kukan ko ɗaya dan haka Abbu , Abbu cikin tausasawa ya Fara tambayar sa cikin lallashi, ya hakan ta faru meya gani da ya Suma, da kamar bazaiyi magana ba daga ƙarshe kuma ya warwarewa Abbu komai tun daga barowar da AQEEL yayi wajensa daga masallaci, har zuwa gida da yayi yana shiga ɗakinsu, yaga AKEELA da AQEEL a halin da ya gansu, sai a sannan kukan da take rikewa ya kufce Masa, Abbu ne ya Fara warwarewa AKEEL cewa ai ba AQEEL bane ya aikata wannan aikin, kamar yadda Doctor Najeeb yaiwa Abbu bayani haka taiwa AKEEL, kuma cikin ikon ALLAH ya fahimtu sosai,Duk da har sannan zuciyarsa Babu daɗi " Nima Abbu aban yabani mamaki sosai, brother bazai aikata wannan aiki ba,kuma AKEELA ma haba, to Abbu wane zai shigo gidanmu ya aikata wannan aikin ga AKEELA? Shin ina Maama? Abun yafaru Abbu? Dole ayi bincike sosai, cikin ƙaraji AKEEL ya ƙarasa zancen dan kuwa zuciyarsa tana ƙuna da halin da aka jefe ɗan uwansa da ƴar uwarsa? In sha ALLAH AKEEL zan yi wannan binciken!kaji ka Kwantar da hankalinka. Yanzu ina shi brother ɗin? Nan Abbu ya faɗawa AKEEL yadda ya faru da AQEEL ɗin, dan haka AKEEL yakuma Kuka, "yace ALLAH ya saka Mana kowanene yai Mana wannan mummunan Aikin cikin Kuka ya ƙarasa maganar, ka Kwantar da hankalinka kaji yaron kirki, yanzu Abbu inason ganin halin da Brother yake da kula sister? Ka kwanta ka huta kaji yarona barci sukeyi kamar yadda ka farka cikin aminci in Sha ALLAH su ma haka zasu farka kaji da lallashi dai aka samu AKEEL ya haƙura da zuwa wajen ƴan uwan nasa. A cikin Daren dai shima AQEEL ya farfaɗo sai dai jikin sai a Hankali, kuma da AKEEL da Abbu sukazo wajensa,sai aikin Kuka AQEEL yakeyi "Abbu saboda ALLAH ya jarrabeni da Yanayin halitta ta shine aka yimin Sharri, Akan nine naiwa ƙanwarsa fyaɗe!?shi wanene ma? Ya aikata wannan ga Auta(AKEELA) sai Kuka dai yakeyi daga baya ya Fara shaƙuwa sai Kuka idonsa ya Fara ƙaƙƙafewa! AKEEL da ke kusa dashi shima kukan yafara! doctor Najeeb yana gurin dan haka yai maza yai Masa allurar barci,da kuɗi da komai, anan Akayiwa AQEEL Duk wasu gwaje_gwaje anan kuma aka tabbatar da cewa zuciyarsa ta shiga firgici, lokaci Zuwa lokaci zai dinga shiga Irin wannan yanayi, na shaƙuwa da ƙafewar idanuwa,Amma da yayi barci ya farka shikenan, daga haka kuma zuciyarsa zata iya kamuwa da ciwo dan kuwa taji tashin hankalin da bata taɓa ɗauka ka, za'a samu sauye sauye daga gareshi, walwalar sa zata ragu sosai, da magana ma saboda zuciyarsa da ƙwaƙwalwar sa ta shiga ruɗani, ALLAH ne ya kiyaye bata bugaba tashi ɗaya,dan haka Yanzu sai a san abunyi,a kuji Ɓata Masa Rai. ALLAH sarki Abbu tashin hankali wanda ba'a saka Masa Rana, kunji bala in da ya samu Abbu kuma, ga AKEELA bata farka ba, Jimmai wannan haƙƙi ki kaishi ina? Duk fa wannan budurin da AQEEL yayi bayan farkowarsa da farkowar AKEEL Duk tana wajen sai aikin Kuka take kamar gaskiya, Alamun tausayi. Haka wannan Ahali dai suka kasance cikin tashin hankali, tsakanin Abbu da AKEEL wanda shi jikin Alhamdullillahi, yanzu AQEEL da AKEELA ne kawai saura, sai Jimmai mai tararrabin tonuwar asirinta dana ɗanta, shine kawai tashin hankalin ta. Kafin safiya CIKIN ikon ALLAH shima AQEEL ya farka, wanda doctor Najeeb yacewa Abbu CIKIN lallashi zai Masa bayanin ai ba shine akace ya aikata ba,shi AKEEL kawai dai yayi tunanin hakan ne dan kuwa shi da ita ya samu a gidan daya dawo daga masallaci ɗaukar karatu, shiyasa Amma bashi suke nufi yayi fyaɗen ba, doctor Najeeb shi ma sai da yaiwa AQEEL bayani dallah dallah Babu ƁOYE ƁOYE, Duk wannan CIKIN salon kwarewar aikine dan AQEEL ɗin ya kwantar da Hankalin sa,Amma yanayin daya samesu a ciki Duk sai da ya gayawa AQEEL ɗin, da gwajin da akai masa Akan ba shine ya aikata ba, Yanzu kawai bincike zasu Fara Akan wanene ya aikata wannan aikin shine yanzu burin mahaifinsa, dan haka AQEEL an ɗan samu salama a yanayinsa, dan tunda akai masa bayanin komai, ya ɗan ji sanyi, ba sosai ba yanzu wane mara imanine ya aikatawa ƙanwarsa wannan mummunan Aikin,har CIKIN gidansu, wannan ne yake cin zuciyarsa,Amma ya na daurewa ko dan ɗan uwansa daya damu da damuwarsa da kuma mahaifinsu wanda a tsaye dare ɗaya ya rame. Sai washe gari wajen asba ALLAH yabawa AKEELA ikon farkawa, Babu iface ifacen da takeyi,da fisge_fisge,kawai sai hawayen da takeyi ga idonta yana motsawa,tana buɗeshi kuma, dan Haka doctor Maryam ta na wajenta,tai ta mata magana Amma ina taƙi amsawa,Babu Alamun tana jinta ma, Nurse Biyu ta Kira suka taimaka mata aka ɗauki AKEELA aka kaita bayi, kafin sannan da ma an haɗa ruwa mai zafi da magunguna a ciki, wanda zai taimaka mata ɗin ƙin yai saurin warkewa,sai da tayi ƙara da aka motsata wajen ɗaukar ta, Zuwa bayi, abun tausayi wajen gashin da za'ai mata, sai Ihu takeyi, kuma har sannan da ɗan jini,dan Ruwan da aka saka ta ya ɗan canja, wajen ruwa huɗu Nurse ɗin sukai mata, sannan suka mata wanka,aka fito da ita, sun shiryata cikin uniform ɗin asibitin aka zaunar ta, Amma ina ta kasa sai jinginar da ita akayi a jikin fillo,sai sannan Doctor Maryam tacewa Nurse su faɗawa Doctor Najeeb cewa yarinyar ta farka,Amma yanzu ma sun gyara ta saboda hankalin iyayenta da ƴan uwanta ya kwanta. Doctor Najeeb kam ya faɗawa Abbu cewa AKEELA ta farka, kuma Alhamdullillahi, to da ma ba barci sukayi ba, tun jiyan zuciyoyi ba bu daɗi, Aikuwa kafin kice me sun ɗunguma Zuwa ɗakin da AKEELA take ciki, harda AQEEL wanda Alhamdullillahi shima Amma shi yasan meyake ji, Sun sameta yadda doctor Maryam ta gyara ta, Abun tausayi daga AQEEL har AKEEL rige rigen Zuwa wajenta sukayi, Fuskarsu cike da tausayi ga ƙanwar ganin daga jiya zuwa yau yadda ta koma abun gwanin tausayi, fuska da idanu a kumbure, ga rama, shigowarsu batayi motsi ba ko ɗaya, dan Babu wanda yayi magana, AKEEL da AQEEL sai da suka matsa kusa da ita sannan suka haɗa baki wajen cewa " Auta ya jikin naki? Ai jin muryar da tayi ne AKEELA yasa ta ɗago da sauri ta ɗora idanuwa akansu da sukayi maganar! kafin kace kwabo kuma ta Fara zabure_zabure da fusge_fusge, sai hankalin AKEEL da AQEEL ya tashi, shi ma Abbu dake gefe Haka, cikin kwantar da Hankali doctor Maryam tace, ku kwantar da Hankalin ku, Yanzu kuje waje, ALLAH yasa ba abunda Muke tunaninsa bane zai faru da ita, dan gaskia a ƙananun shekarunta, yadda Wanda yai mata fyaɗen Yaje MATA Babu tausayi ba bu imani, shine yasa mata tsoro da firgici a zuciyarta, da ta ji muryar maza ko ganin maza zata iya shiga wannan yanayin data shiga yanzu ko fiye da haka ma Yanzu, fatan da zamuyi shine ALLAH yasa Hakan bai shafi ƙwakwalwarta ba,Amma yanzu kafin ta farfaɗo zasuyi MATA gwajin a ƙwakwalwarta su gani, zuciya da ruhin wannan Ahali ba saina faɗe ta ba, kuma kanku fans ya kike ji? Duk wannan Tashin Hankalin da ake ciki Jimmai tana gurin tayi funfurus,har sannan ko ɗar Akan ƙudirinta na ɓoye wannan gaskia indai ba asirin bane ya tonu! Daga AQEEL har AKEEL sai a Hankali yanayinsu,saboda zuciyar AQEEL ta samu wutu kawai allurar barci aka Masa, AKEEL da Abbu kuma sa a slow hakam Jimmai . Abbu ya gargaɗi Jimmai karta baɗawa gidansu abunda ya faru, tabari Asiri ya tonu tukunnah,tayi niyyar faɗa Amma tunda taji likitoci sun ce ba AQEEL bane ya aikata wannan mummunan Aikin ba, da kuma cewa tabbas za'ayi bincike shikenan jikinta yayi Sanyi, dama ba'a gane cewa ba AQEEL bane ya aikata aida tuni tayi tonon silili kowa yaji, a tsinewa AQEEL ɗin, har kawayenta zata faɗawa cewa AQEEL yaiwa AKEELA fyaɗe, Amma yanzu kam itama a cikin Tashin Hankali take, sai kuma bayanin da doctor Maryam tayi, sai addu'a take Akan ALLAH yasa abun ya shafi ƙwakwalwar AKEELA ɗin, asirin ta dana Usman ya rufe, to sannan sai ta fallasa, yanzu haka harda riƙe carbi da addu'a, Akan ALLAH karya bawa AKEELA lafiyar da zatayi bayanin ga wanda yai MATA fyaɗe, dan kuwa bata tunanin wani yaga Usman, idan batayi bayani ba, za'ayi tunanin wani can da Ban ne yashigo gidan ya aikata wannan mummunan Aikin............... Muje next page😭😭😭 ALLAH sarki AQEEL lalura ta sameka AKEELA muna fatan abunda Jimmai take fata ALLAH yasa karya tabbata Jimmai ko Hmmmmm ✍️ Oum ARQAM ce ontop 🥰 2/27/24, 1:30 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FIVETY 50* ina godiya ga masu sharhi musamman Seerat da Oum nawwar, Aishatu Sulaiman, MamaGee,mmn Aslam,Maman eyshat,mummy Waleed, bintufatima,,,,,,,,,, Marasa comment na ina godiya sosai Amma kuma zan dawo kanku irinsu kuna dayawa dai bazan iya jero sunanku gaba daya ba....................... Tun da akawa Akeela da Aqeel allurar barci, lokacin dama gari ya waye Yanzu haka wajen 11 na safe, dan haka Abbu ya bar Jimmai a asibitin, yanason zuwa gida, zuciyarsa ba bu daɗi so yake yaje gidan ya Fara bincike Yanzu, ko da Akeela ta Tashin, ai shinenan dai, dan haka Akeel yace zaibi Abbu kuma bai Musa ba, Jimmai Zuciyarta kamar zatayi tsalle fa faso jin abunda Abbu yace "zanje wajen Malam sallau nai Masa tambayoyi shin wanene ya shigomin gida! Idan ba haka ba shi kansa sai na hukuntashi,dan kuwa shima yana cikin zargi, cikin in ina Jimmai tace "shikenan to Amma na tambayeshi wai ya zaga bayi! Ko saurarar me take cewa Abbu bai ba Akeel shi ma hakan, dan tashin hankalin ya daɗu,tasan muddin malam sallau yace Usman ya na Gidan shikenan shi za'a zarga ,Amma kuma Allah yasa malam sallau baya gurin shine kawai mafita. Abun Hawa suka hau zuwa gida, malam sallau yana gurin da ya saba Zama,zuciyarsa sai wasi wasi take!ina masu gidanne yasan dai Alhaji baya gari,Amma yadda aka fita da yaran gidan ba bu lafiya har Yanzu kuma Babu wani mosti, ga Hajiya dai jiya ta dawo zuciya da jiki ba bu daɗi a yanda ya ganta,Duk da dai dama ba wata mu'amala mai kyau take Masa ba,ya haifeta Amma ta dinga daka Masa tsawa kenan, Abinci sai taga damar bashi, Su Akeel ne kawai yakejin daɗin su, ko Mutuniyarsa(Akeela) itace mai zuwa wajensa suna Hira,hakanan in tai girki (Babu abunda bata iya girkawa ba, Jimmai tai mata horon aiki) tana kawo Masa, saƙawa da kwancewar da yakeyi kenan, yaga Alhaji da Akeel sun buɗe gate sun shigo, dan haka da sauri ya ya ƙaraso wajen su "Alhaji andawo kenan? Saukar yaushe? Shi dai Abbu da zuciya ba bu daɗi kawai ɗaga wa Sallau hannu yayi ba bu magana,hakan ne yakuma sawa Sallau shiga cikin ruɗu, Aikuwa dai Babu lafiya kam Tunda ga Akeel da Abbu ai dai ba tare sukai tafiya ba,kuma ma shima ranga_ranga aka fitar dashi,ai kuwa g rama nan yayi,komawa kan Akeel ɗin yayi "ya jikin mutumin? Ina ɗaya Abokin nawa yaji sauƙi Amma shi ma? Ina itama mutuniyar tawa jikin da sauƙi Amma itama? Duk tambayoyin nan ya jerowa Akeel! Da sauƙi baba Amma sunacan Asibitin suna barci Nima farkawa nayi shine na rako Abbu Akeel ya ƙarasa bawa Malam sallau amsa yana gaba zuwa bin Abbu cikin gidan. Ko da suka shiga gidan daƙar Abbu yai wanka ya canza wasu kayan, zuciya Babu daɗi, Hakama Akeel yayi wanka sannan ya ɗaukar wa Aqeel shima kayan da zai canza,da Duk abunda zasu buƙata, ya haɗasu a trolly guda, hakama Akeela Doctor Maryam ta Faɗi abunda zata buƙata a ɗauko mata, sai sannan Abbu ya zanyo trolly ɗin Akeel Babu ƙarfi,suna fitowa Harabar gidan Malam sallau yana hangowa da sauri yazo ya karɓa, Abbu ya bashi mukullin mota ya buɗe but ya saka ta, "Abbu yacewa Malam sallau Inason magana dakai yanzu! To Alhaji babu damuwa nan akwai rana, dan haka daga Akeel da Abbu da kuma malam sallau suka ƙarasa wajen da yake Zama Akan benci, wajen kuma inuwa ce,dan haka Malam sallau durƙusawa yayi a ƙasa bai hau bencin ba sai da Abbu yai Masa magana, kafin cikin girmamawa ya hau gefe ya fuskanci uban gidan nasa da ɗansa,dan yasan dai abun mai mahimmanci ne yasa hakan sannan kuma zuciyar ɗa da uban Babu daɗi daga ganin yanayinsu. ...Malam sallau nasan kasan abunda ke faruwa da yarana,da fitar dasu da akayi daga gidannan ba bu lafiya abunda yasa hakan shine.......turyan turyan Abbu ya zayyawana malam Sallau abunda ke faruwa bai ƁOYE Masa komai ba,tun kafin Abbu yagama bawa Malam sallau labari jikinsa yafara rawa, na tashin hankali jin abunda ya faru! Ka kwantar da hankalin ka malam ba bu wanda yasan wannan magana kaima abunda yasa nagaya maka saboda Inason ka gayan gaskiya Akan meka sani wanene yashigo mun gida?baka ga wata alama ba game da haka? Harda Kuka malam sallau yayi kafin ya ɗaga kansa domin tunani! Akeel dai yana gefe zuciya ba bu daɗi jin ankuma ɗago Masa da mikin dayake damunsa a zuciya da ganganr jiki! Abbu ma saurarar malam Sallau wanda ya Fara magana...... Tiryan tiryan ya Fara bawa Abbu labarin Ranar da abun yafaru, yace shidai Babu inda yake zuwa, a gabansa Akeel da Aqeel suka tafi makaranta da safe hakama Akeela, itama Hajiya ta fita bayan fitar yaran, har dawowar Akeela sai da malam Sallau ya faɗa,Anan kuma yace sai kuma Usman daya fito shi ma bai jima ba ya dawo kuma bai kuma fita ba gaskia har Akeela ta dawo ya na Gidan,tabbas yajiyo wata ƙara kamar daga Gidan kuma muryar Akeela ce, dayake yasan akwai Akeela da wasa ita kaɗai sai bai kawo komai a raina ba, Amma bai kawo komai ba, lokacin su Akeel Basu dawo ba haka ma Hajiya, sai dawowar Aqeel cikin ciwo da ko maganar da ya saba yimin bai ba, ina ganin yanayinsa nasan Babu lafiya, Hakama sai dawowar jimmai, bata jima da dawowa ba sosai, sai ga Akeel yadawo har nake tambayar sa yau ɗan uwanka ya rigaka dawowa, shine ma yake cemin ai bashida lafiya ne,nace Masa ALLAH ya sauwaƙe naga alamar sa kuwa dan ko magana bai mun ba a gaggauce ya shige gidan, Akeel yana shiga bai jima da shigowa ba sai ga Usman a gaggauce yazo ya fice, alamu sun nuna kamar baya cikin Hankalinsa, a tsorace yake,ni kuma lokacin ina wajen flowers dan haka bai ganni,Amma nayi mamakin ganinsa a Wannan yanayi, sai kuma zuwan likita da fitowa da yaran a halin rai da rayuwa da akayi dasu.....anan malam Sallau ya sauke ajiyar zuciya!alamun yagama magana! Abbu da Akeel kam kamar zuciya zata faso ƙirji alamu sun nuna kenan Usman ne ya aikata wannan mummunan Aikin ga Akeela? Tabbas Alhaji wannan yaron shine abun zargi yanzu,ganin a yadda ya futa a gidan, cewar malam sallau yana kallon fuskar Abbu! Hakane malam shine abun zargi, Mahaifiyarsa tace mun ai tun ranar da na bar gidan nan shima ya tafi gidansu, kaga alamu sun nuna kenan tasan da komai Amma take ɓoyemun, Jimmai ta cuceni ta cuci ƴaƴan ƴar uwarta, kuma tacemun jiya ta tambayeka idan da wanda ya shigo gidannan kace Babu kowa? Lallai kam Hajiya ta iya ƙarya Alhaji ni ko saurarata ma batayi ba, balle taimun magana, aini bata kula ni ko ƙadan malam sallau ya faɗa yana riƙe baki jin sharrin da Jimmai tai Masa. Shi kam Abbu ya kasa magana lallai jimmai kenan da saninta Ɗan ta ya lalata Akeela, in bai mantaba da ma Akeela ta taɓa gaya Masa cewa Usman yana taɓa MATA jiki, Amma kuma sai Jimmai ta gwale ta, shi ma kuma lokacin baisan me ya sa yakasa ɗaukar mataki ba,dana sani Abbu ya shiga, na bawa jimmai yarda da amana ita kuma ta cinye ta, sai sannan kuma yake ganin baƙin Jimmai da tuna Duk wata badaƙala da zalunci da taiwa ƴaƴansa ya shiga dawo Masa a kwanya Akeel yana zaune Duk tattaunawar da akeyi da Abbu bai magana ba, tsanar Usman ta shiga zuciyarsa yanzu da zai ganshi sai ya kasheshi kuwa, hakama maama Jimmai, dama su sun jima da tsanarta yadda take gana musu azaba! Kawai dai dan Abbu baya ganin laifinta ne, kuma agabansa ma tanai musu,Amma baya magana, in sun gaya Masa yace ai uwarsu ce bayason irin wannan halin! Shiyasa komai ya damalmale ai,yanzu Abbu ba ga shi ya gane gaskia ba. Nan dai Malam sallau ya kwantar wa Abbu hankali Akan kar ya nuna yasan Usman ne ya aikata wannan mummunan Aikin, yabari Akeela ta farka, aji ta bakinta kuma a gaban jimmai za'ayi komai ai taji,fallsara,in yaso anan Duk wani hukunci da Abbu zai MATA sai yai MATA, kuma Duk motsin jimmai ɗin yasa shi a idonsa, Abbu ya amince yaiwa Malam Sallau godiya sosai kafin jiki Babu ƙwari su shiga mota zasu koma Asibitin'kowanne zuciya Babu daɗi, Akeel ne ma yake dan faɗawa Abbu irin cin kashin da Jimmai tai musu, Abbu dai jinjina kai kawai yakeyi, Amma yakasa magana. ******************** Jimmai tana ganin Abbu ya fice daga asibitin ta kasa zaune ta kasa tsaye, yanzu idan Abbu yagano gaskia wajen Malam Sallau fa? Amma kuma ai Usman yace daya fita malam Sallau baya gurin,yanzu dai matsalar farkawar Akeela ce cikin Hankalinta tashin hankalin ta, dan haka takira Usman ta faɗa Masa, shi kuma yace gashinan zuwa zai san abunda zaiyi da Akeela ɗin,aikuwa cikin muntuna sai gashi yazo asibitin, uwar taje ta tawo dashi, bai tambayi jikin Aqeel ba balle Akeela wanda shine silar komai, doctor da take dubata yace yanason gani, nan kuwa aka nuna Masa office ɗin Doctor Maryam,yana zuwa kuɗaɗe masu maiƙo ya ajiye a gabanta, yace nine naiwa yarinyar nan fyaɗe, inason ki MATA allurar da zata manta komai, koda ta farka Shikenan bazata ce nine ba, wannan kuɗin Kafin al ƙalamine, indai ta farka a Hakan to madallah zan ƙara miki wasu kuɗin,Duk bayanin da Usman yakeyi doctor Maryam tana kinsa, kuma dama a kawai waya a hannunta yana Fara bayani ta shoga record, sai ta badar ta ajiye wayar, a zummar fuskantarsa takeyi,sai da yagama bayani sannan doctor Maryam tace bakada matsala indai akwai kuɗi a hannunka, Amma kai kam meyasa ka aikata wannan ga ƙaramar yarinya? Baka tsoron mahaifiyarka tai fushi dakai in taji Kaine ka aikata, baiwar ALLAH tananan cikin jimami, nan Usman ya kwashe da dariya kafin yace "Doctor ai plan ne tasan komai yanzu haka ma ita ta Kirani, sai da zuciyar Doctor Maryam tai motsi jin abunda ya faɗa, daga ƙarshe dai ya fice daga office, ɗin ran sa fesfes jin Doctor zatai Masa aikin daya sata shikenan komai yazo da sauƙi.ita kuma doctor Maryam ta Adana record ɗin ta,ta dannawa doctor Najeeb Kira kafin kace kwabo yazo office ɗin anan ta gaya Masa Duk ydda sukayi xa Usman, harda share hawaye tayi, shima Doctor ya girgiza jin ashe Duk abunda Jimmai takeyi pretending ne, to Amma waɗannan ƴaƴan me sukai MATA haka, har ɗan ki yayi wannan mummunan Aikin ki rufa Masa Asiri, haka ƴaƴan ƴar uwarki, kuma ƴaƴan mijinki, nan dai suka haka plan Akan kar a nunawa, Abbu yanzu sai ya gama bincikar gidan tukun, kuma ko Akeela ta farka a Hankalinta ta zauna tai mata bayanin komai, ta Zama kamar bata Hankalin na ta, ta yadda za'a kama Usman da Jimmai cikin ruwan Sanyi,daga ƙarshe suka rabu,kowanne jiki Babu ƙwari. Yaje gurin Jimmai ya faɗa mata yadda sukayi da doctor har dasu murmushi jimmai tayi makira!...... Kiyi komai kifi na ganinka mai jar koma asirinki dana ɗanki ya tonu, Abbu kar yake kallonki Kafin kice me ya fice da ga Asibitin domin zuwa gida a Fara sana'ar da aka Saba, babansa ba bu lafiya yana asibiti, acan aka kwantar sa, dan haka gidan kullum shine a ciki in dai bai je asibitin ba,sai ƙanwar sa Shukhra in tadawo daga school tazo ta shirya tai asibitin itama.da sauran ƴan aikin gidan. _____________ jimmai tana ganin Usman ya bar asibitin sai ta shige office ɗin doctor Maryam wai har Yanzu Akeela bata farka bane doctor, An cutarmun ƴa ALLAH ya saka MATA, sai sharar ƙwalla take, Doctor Maryam kam kallon ta kawai takeyi, lallai wannan Babu imani, kalli kamar gaske,nan tai MATA bayanin cewa" ai ki kwantar da Hankalin ki Maama pretending ya ƙare, yanzu Usman ya bar office ɗin nan, zan muku aiki Akeela kam ai ba ita ba farkowa a Hankalinta,sai ga Jimmai da murmushi, ai ban san yaga miki ni na sani bane shiyasa, Amma yanzu kam ai normal ne doctor, komai yazo cikin sauƙi, Nima zan ƙara miki wasu kuɗin,tun shigowar ta itama doctor Maryam ta danna record, tana gama zancen tayi save nasa, ita kuma jimmai ta fice daga office ɗin, ta koma ɗakin da suke zaman jinyar. Dan haka batasan dawowar su Abbu ba, anan doctor Najeeb yake cewa Abbu Aqeel ya farka kuma Alhamdullillahi yayi wanka ma,yanzu akai masa kayan sawa ya canza, tare suka shoga ɗakin da Akeel, Akeel ɗin ne ya taimakawa Aqeel yasa kaya, nan Akeel ya kwashe Duk yadda sukayi da Baba Sallau ya faɗawa Aqeel ɗin, nan idanun Aqeel sukayi ja ƙarshe yace tabbas Usman zai aikata fiye da Haka Abbu, ya faɗa yana kallon mahaifin nasa da yake zaune a gefensu yana tausaya musu, Shi ma Aqeel haka yagayawa Abbu cewa ko lokacin da lalurar sa ta tashi Usman yace Masa akwai hanyar warkar da matsalarta shine, ya dinga kallon finafinan batsa, zai samu nustuwa, kuma Abbu Babu kunya ko tsoro a gaban mu yake kunnawa yana kalla, sai dai mubar wajen musamman ni sai yaga ina zaune zai zo ya kunna, saboda yasan matsala ta, Nikam bana Zama, haka ma Akeela sai nawa tana cemin Usman yana kai hannu jikinta, ta mareshi Amma maama Jimmai ta zage ta tace zataiwa ɗan ta Sharri, kaima Abbu haka kace Akeela ɗin ƙarya take,sai Kuka ga Aqeel! Nan dai Abbu ya lallashin ƴaƴan nasa, da nuna musu kuekurensa,Akan cewa shi zuciya ɗaya ɗaya yake zaune da Jimmai, kuma ma yadda Inna Rabia ta riƙeshi ya zata itama jimmai haka take riƙonsu, shiyasa ma baya yarda da abunda zasu zo Masa da shi, kuma wani abun ma ƙasa magana yake suyi haƙuri, nan dai ya lallashe su Akan komai ai yazo ƙarshe,zuciyar Aqeel kamar zatayi tsalle ta faso ƙirjinsa, idonsa idon Usman sai ya hallakashi hakama, maama Jimmai itama saiya shata MATA layi, Abbu ya ce karsu nuna wata alama agaban Jimmai yadda zatasha jinin jikinta, dan haka sai suka ɗunguma ɗakin da take zaune har Abbu. Makira harda murna da cewa "ƴaƴana naji daɗin ganinku a haka, ta faɗa da ƙarasawa wajensu da tafa kafaɗar kowanne su, AQEEL kamar zai bankadeta haka yaji Amma kuma ya fuske,hakama Akeel , shikam Abbu zuciya ta yunƙuro Masa ganin jimmai Amma shima sai ya mallaki zuciyar, Ya kuwa Malam sallau yaga wanda ya shigo gidan? Inji jimmai tana kallon Abbu wanda ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin, "Abbu yace MATA yace Babu kowa, kamar dai yadda Kika faɗa min, yace ma ai kin tambayeshi! sai ga Jimmai da Ajiyar zuciya a bayyane wanda Akeel da Aqeel da kuma Abbu sai da suka kalleta, lalläi jimmai abun naki yakai limit.. A haka suka zauna a Asibitin, zuciya babu daɗi, Akeela ta farka sai dai ABunda aka guda shine ya faru, dan ƙwaƙwalwar ta kam ta shiga wani yanayin da su doctor Maryam Basu so ba, Babu damar tambayarta abunda ya faru da ita, Amma kuma in ita ALLAH yabata ikon faɗa zata faɗa Amma Hakan ma abune mai wuya, dan ƙwaƙwalwar tayi raunin tuna Abunda ya faru da ita, saboda birgicin da ta shiga cikin lokacin faruwar Abun,Amma ya zasuyi da ikon ALLAH, hakan ma sun godewa ALLAH, Sai kuma data ji muryar maza ko ganin su zata shiga yanayi na tsoro da firgici wanda zaisa ta fice hayyacinsa, Doctor Maryam tacewa Abbu ya Kwantar da hankalinsa wannan ya ɗan wani lokaci ne a Hankali komai zai Fara sauƙi, dan haka ma doctor tace wa Abbu ɗin da su Aqeel su dakata zuwa wajenta, ganinsu yana furgitata, Abbu bai ji daɗin Hakan ba,Amma ya ya iya, kullum ana gasa MATA jikinta da Ruwan zafi, ga magungunan da ale MATA amfani da su take Sha kuma har da Jimmai a jinyar, ALLAH ya taimaketa bata haɗu da yoyon fitsari ba, san kuwa tashin Hankalin da doctor Maryam take gudu kenan ko rudewar ƙwaƙwalwa , to yanzu dai rudewar ƙwaƙwalwa aka samu,Duk wata kulawa tana samunta, Abbu kuma yana gaf da fasa ƙwai da tozarta Jimmai,dan kuwa yanzu Hankalinta ya kwanta,jin Akeela ta farfaɗo da rudewar ƙwaƙwalwa,haka ma Usman doctor Maryam ta faɗa Masa cewa ai tai MATA allurar,sai murna yakeyi dan kuwa ya zata allaurar tai MATA daya sata,nan kuwa bai san ALLAH ne ya sa Akeela ɗin ta farka a Hakan ba.ya daɗawa doctor Maryam kuɗin da yai MATA alƙawari, hakama Jimmai ya ƙara MATA, dan haka doctor Maryam ta killace su ta ajiye, wannan ma hujja ce. Har anfara koyawa Akeela tafiya, dan kuwa sai da aka koya MATA, dan ta illatu fa da Kuka da karkarwar jiki ta Fara taka ƙafafuwanta taku ɗaya biyu sai a kyaleta. _________Usman Duniya saboda jin ta Kowacce hanya dai asirinsa ya tonu, har sannan babansa yana asibiti, kuma yana gidansu yai kallonsa na banza ya hau network ya gama malelekuwa ya haƙura,A wannan yanayin yake kansance idan kuma abun yafi karfinsa, ya fita ya samu wata Mara kamun kan ya rage zafi,sai kuma kusancin da shida Shukra ƙanwarsa sai ya ke ɗarsa wani abu a Ransa game da ita.............. Muje next page.... Turkashi fans Usman me yake nufi ne? Asirin jimmai kam yafara tonuwa konace ya tonu kawai fallasa ce Abbu bai MATA ba ALLAH sarki Akeela ke kam kinji jiki ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 3/1/24, 5:39 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FIVETY ONE 51* Alhamdullillahi zamuce dan jikin AKEELA sai ABunda ba'a rasaba, tun ta na ruɗewa idan taji muryar maza ko ta ga maza har abun ya Fara sauƙi, dan kullum sai doctor Maryam tai MATA nasiha Akan nuna MATA waɗannan fa ƴan uwanta ne, Wannan kuma mahaifinta ne, bawai manta su tai ba fa, wai dai tagaya MATA cewa abunda wancan marar imanin yai MATA su har abada bazasuyi MATA ba, Duk da har sannan bata buɗe baki ta ambaci sunan wanda yai MATA ba, Alhamdullillahi ba'a buƙatar wannan da ma dan kuwa ansan wanda yayi, fatan SAMUN lafiya kawai ake MATA, kuma tana Shan maganin da zai taimaka MATA a ɓangaren ƙwaƙwalwar shima ana samun ci gaba sosai,yanzu tana Zama waje ɗaya dasu AQEEL da AKEEL da kuma ABBU har a ɗan taɓa Hira da ita ma, kowanne yana burin faranta MATA, da mantar da ita abunda ya sameta, Amma Duk da haka akwai damuwa a tare da ita,magana da walwala tai MATA ƙaranci. Amma fa tun daga sannan AQEEL walwalar sa ta ragu gaba ɗaya,yanzu magana wahala take Masa, Hakama ba ta Amsa,kamar yadda doctor Najeeb ya faɗa zai sameshi ɗin,Amma kuma yace in Sha ALLAH komai zai wuce, wannan ba wata matsala bace,sai kuma abu na gaba a guji Ɓata Masa Rai, Saboda Duk sanda zai shiga ɓacin rai ko makamancin haka zai samu shaƙuwa da Ajiyar zuciya idanunsa zaiyi ja, da anbashi ruwa ya Sha, ya samu barci shikenan,zai farka normal, idan kuma aka ci gaba da tafiya a Hakan ana ɓata Masa Rai,ko ya shiga tashin hankali zuciyarsa zata samu matsala. AKEEL ne dai normal tun suman da yayi,bashida wata damuwa,Amma kuma ganin ƴan uwansa Basu da walwala shima sai ya rage tasa. ALLAH sarki ABBU shi kam ALLAH ya taimaka Masa,bayan hawan da jininsa yayi, tun lokacin da abun ya faru ABBU ya daina barci sai ɓarawo ya zauna yaita tunani kenan, Hakan ne yasa akai masa BP akaga jinin ya hau,aka bashi magunguna, doctors suna Bashi shawarwari to dan haka da sauƙi jikin, musamman yanzu da yaga jikin AKEELA yai sauƙi sosai,ta Fara mai da jikinta. Shi ma AQEEL Alhamdullillahi tun da ciwon ya sameshi har yanzu bai kuma ta shi ba. Jimami dai anyi damfanfan ya mai naƙuda ta samu katifa, dai fantama warta takeyi a Asibitin ganin, asirinta ya rufu da ɗanta, har sannan ABBU bai fallasa cewa yasan Usman bane ya illata Masa Rayuwar ƴar sa guda daya tilo mace, Hakanan ya tsarwatsa farin cikin Ɗan sa namiji ya goga Masa baƙin fenti,ba don ALLAH ya taƙaita wahala ba ai da yanzu wane zancen ake? Tsaf zai iya tsine Masa ya fitar dashi da ga sahun ƴaƴansa, fyade ai ko ƴar wani yaiwa baze ƙyale shi ba balle kuma ƴar cikinsa shi ma ɗan cikinsa. Ganin jikin AKEELA ya murmure ana Shirin Basu sallama, Hakama Jinin ABBU ya yi normal, tun da da ma shi mai miƙawa ALLAH zaɓi da addu'oi,hakane ya sa yasa bayan hawan Jinin bashi da komai, Amma in da wani ne ai maybe zuciyarsa ta buga, ko ya faɗi ɓarin jikinsa ya shanye, doctor Najeeb har office ya Kira ABBU shida doctor Maryam, suka nuna Masa kuɗin da Usman ya bada Akan a yiwa AKEELA allurar manta komai, da record ɗin tabbacin shine yaiwa AKEELA fyaɗe kuma da sanin mahaifiyarsa, itama Harda Bawa doctor Maryam kuɗi itama, har suka gama yiwa Abbu bayani bai ce komai ba, dan haka kawai ya miƙa wayarsa an tura Masa record ɗin komai, ya ƙarbi kuɗin, yaiwa Doctor Najeeb da doctor Maryam godiya Akan namijin ƙoƙarin da sukayi,yanzu badon akwai Amana ba Irin Wannan kuɗin da suka bayar, mai zai hana Doctor Maryam bataiwa Akeela Allurar ba,ku ma su rufe gaskiyar badon tun farko sun duba sun gani bashine ya aikata fyaden ba ma. Zuciyar ABBU ta tunzura kamar zata Faso ƙirjinsa ta fito sai addu'a yakeyi shine kuma sai zuciyarsa tai Sanyi take ƙasa,a Hakan ya fito daga office zuwa ɗakin da suke zaman jinyar, ai kuwa Jimmai na zaune, kamar mutuniyar kirki, ABBU yana ganinta sai yaji kamar Yaje ya shaƙeta,tun tana shure_shure har tadaina, Amma ya mallaki kansa! Abbun su Nikam ya maganar binciken wanda ya cuce mune? Jimmai har da sassauta murya wajen maganar! Ai wanda ya aikata zaluncin nasanshi!nasan ko wanene!ba tun yau ba! Cikin Zafin zuciya ABBU ya idasa zancen! "Alhamdullillahi naiwa ALLAH godiya Amma ta yaya? Cewar Jimmai har da ɗaga Hannu da safawa a fuska zuwa ƙurji, irin yiwa ALLAH godiya ɗin nan! Kinga kuɗin da har ila yau, yazo Asibiti ya bawa Doctor Maryam mai kula da AKEELA akan tai MATA allurar da zata Mance komai,SABODA zalunci har da mahaifiyarsa a bada gudunmawa, da yake ita doctor ɗin tana da zuciyar imani zuciyar tausayi ta karɓi kuɗin, alamun zatayi aikin da suka sata, hakana ALLAH mai iko sai ya Tashi yarinyar a halin da suke fata,wanda sunyi tunanin yadda zuciyarsu Babu imani, da tausayi, sheɗan ya rinjayi zuciyarsu ita haka ta ta take, aikuwa ina tata tsarkakakkiyar zuciya ce! ABBU ya ƙarasa zancen da watsawa Jimmai kuɗin a fuskar ta, Ita dai jimmai ba bu bakin magana! Tai suman wucin ga di! ABBU ya ci gaba da magana " Wannan Ɗa da uwa sunyi asara, ALLAH zai nuna Musu zaluncin su! ABBU ya ƙarasa zancen da kallon fuskar jimmai wanda gumi ya jiƙeta, A aljihu ABBU yasa Hannu ya ɗauko wayarsa ya kunna Duk record ɗin daga na Usman har nata ita Jimmai ɗin, yadda sukayi da doctor Maryam, ai kafin Usman ya gama magana, na Jimmai ya shiga! ABBU sai ihun Jimmai ya ji! Zata Fara Masa magiya! Cikin tsawa ABBU ya ɗaga murya " Baki da bakin magana anan, Duk abunda Zaki faɗa bani da lokacin saurarar su!ki sani Duk wani zalunci da makirci da Kika ƙulla tsakani da ƴaƴana yanzu ALLAH yabani ikon sani kuma nabarki da ALLAH hakama Suma sun barki da ALLAH,Duk da ni ma inada laifi in sunzo sun gaya mun abunda kike musu nake kwaɓarsu na nuna Musu cewa, ai ke mahaifiyarsu, da kuma la'akari da yadda Inna Rabia tai dawainiya da ni ba bu cuta ba bu cutarwa, ko ƴaƴan data hai fa acikinta bazasu nunan ga ta ba, ashe abun ba haka yake ba, ita Inna Rabia samunta sai an tona, Duk abunda Kikai kanki kikayiwa ga amanar zumunci da Kika ci ita kaɗai masiface a gareki! Sai Yanzu ABBU yai Ajiyar zuciya! Wanda ɗakin yayi tsit kukan da Jimmai take ma ta daina ta yi shiru ta na saurarar maganganun da ABBU yakeyi! Zuciyarta cike da mamaki da Al ajabi! ABBU yaci gaba da magana "Malam Sallau da Yake shima zuciyar imani gareshi, da na je na tambayeshi bai ɓoyen komai ba ya feɗemin biri har wutsiya,nayiwa ALLAH godiya daya sa daga ke sai ɗanki ne masu zuciyar fir'auna, dan haka Yanzu ba bu abunda zan miki kije ke da ALLAH zakiga sakamako tun a duniya, kinci darajar Ummul khair dan kuwa munyi zaman amana da soyayya ni da ita, wanda ke Baki duba Hakan ba waɗannan ƴaƴan ko baki Aure ni ba ai ƴaƴanki ne Zaki iya kula dasu, Amma ina kamar ɗanki shi Zaki haɗa baki da shi ya cuci ƴar ƙanwarki wanda shima ƙanwar sa ce! Zakiga sakayyah in Sha ALLAH badai kin yarje masa yaci mutuncin zumunci ba,ya cuci marainiyar ALLAH ba, zakuga sakayyah, nayi alwashin Duk wanda na samu da aikatawa yarinyarta wannan mummunan aikin, da yiwa yarona mummunan sharrin nan sai munyi shari'ah dashi, to Amma ina ALLAH ya rufa Asiri, mutuncin ƴata wajen shari'ah bazai zube ba, bayan ke sai ni sai doctors ɗin da suka san meke faruwa, da Baba Sallau, bana fatan maganar zata futa, yanzu ma haka zan bunne ta sakayyah ce Zaki gani da Sannu! ABBU ya ƙarasa maganar da rawar murya da ajiyar zuciya alamu sun nu na zancen da yake faɗa yana taɓa Masa zuciya dauriya yakeyi kawai! Jin ABBU yayi shiru sai yasa Jimmai cikin shashsheƙar kuka zata Fara magana "Dan ALLAH ka........... Ɗaga mata hannu ABBU yayi🖐️ wanda gama rubutunsa kenan, a wata farar ɗaukarda! Hullawa jimmai ya yi a fuska! Ga takarda nan hukuncin da zan iya yi miki kenan, dan haka banson ki ƙara ko minti 1a ɗakin nan,idan ba haka na komai na iya faruwa! Jimmai tasan halin ABBU akwai zuciya!kamar yadda yace komai na iya faruwa hakanne, dan haka tana buɗe takardar daya bata tai tozalai da saki Biyu a jiki, da ɗan short rubutu.. kar ki barmun ko tsinke acikin gidana wanda kikasan mallakiinkine, azzalamu macuciya mai zuciyar fir'auna. Kuka jimmai ta fashe da shi ba bu tsammani ABBU yaga jimmai a gabansa ta dafa ƙafafunsa, tana Kuka "dan ALLAH ka yafemun Ɗalhat ni mai laifi ce a gare..... Wani kukan kura da ABBU yayi ya watsawa Jimmai Mari ai sai da jinta da ganinta na wucin ga di ya ɗauke, kafin ta dawo hayyacinta kuma sai ƙwallo da ita ya harba ta Jikin bangon ɗakin, Hakan ne ya dawo da Jimmai hayyacinta ba bu shiri ta buɗe ƙofar ta fice ta na mai Kuka..kona mene oho? Baki ya fashe hakana ta na ɗingisa ƙafa! Sai sannan ABBU ya fashe da wani kuka abun gwanin tausayi, babban mutum kamar wannan, shigowar doctor Najeeb asibitin kenan, ya ga Jimmai ta fice ta na Kuka, ga fuska da jini ba ki ma haka, ko kallon ta bai ba yasan sauran may be Alhaji ne yai MATA Hakan,yasan jinin Alhaji ya hau kwanaki wannan ku ma abun zai iya sa jinin ya kuma Hawa, dan haka ɗakin da yasan Abbu yana ciki shi ya shiga,aikuwa ya sameshi ya na Kuka, dan haka yai tai Masa nasiha daga ƙarshe kuma tai MATA allurar barci dan ya samu relief. AKEEL da AQEEL ku ma suna Gida lokacin da abun ya faru, dan haka Basu sani ba,suna Shirin fitowa daga gidan ne Jimmai ta shigo gidan, tana Kuka AQEEL da AKEEL ko kallonta basuyi ba, raɓeta sukayi zasu wuce dan haka, kawai sai ta zube gwiwa ta na Kuka " ƴaƴannan ku yafe mun dan ALLAH ko roƙar mun mahaifinku, nan kuma kamar zararriya ta Fara basu labarin yadda sukayi da Abbu harda buɗe takardar sakin da nuna musu,sai sannan AKEEL yayi magana "kamar yadda Abbun mu ya faɗa miki muma haka zamu ce miki, ALLAH ya saka Mana, in Sha ALLAH zai Kinga sakayyah ke da Usman kamar yadda Kuka tarwatsa Mana farinciki, ku ka cutar Mana AKEELA, ga ɗan uwana ma kin sashi a wani yanayi, sai sannan yakai duba ga AQEEL wanda yafara shaƙuwa da ƙafewar idanuwa, da sauri AKEEL ya ja hannunsa ya bar Jimmai a tsaye ta na kuka cikin ikon ALLAH yakaishi cikin mota, a machine sukazo o Yanzu kuma ai bazai yiwu su koma a machine ba, sa'i da lokaci malam sallau ya iya driving ABBU yana aikensa da ita ɗauko wani abu da makamancinsu. Da Jimmai ta shigo sai da taiwa Baba Sallau magana wanda da batai Masa, shi kam ko kulata bai ba, dan kuwa da ma bata kulashi shima kam bai kulata ba, daga ƙarshe dai yace ALLAH ya shiryaki ya sakawa marayun ALLAH! Ganin halin da AKEEL yasa AQEEL a mota ne yasashi dawowa wajen inda har AKEEL ya ɗauko trolley ɗin da sukazo ɗauka da kuma mukullin mota da yasa AQEEL ɗin aciki! Itama jimmai ta ɗan kwaso kayan sawarta a trolly sannan ta wanke fuskarta ba bu jini, amma fuskar ta kumbura, hakama ƙafar ta kuma tsami daƙar take takawa, dan haka AKEEL da wata rana shi ma yanada zuciya, da sauri ya fusgo jimmai zuwa bakin gate ya wurgata, sannan ya miƙawa Baba Sallau mukullin mota alamu sun nuna ya jaso kenan, ABBU bai Basu damar driving ba a shekarunsu, shiyasa yasai musu machine, AKEEL ne ya buɗe gate baba Sallau kuma ya fitar da mota, sannan AKEEL yasa mukulli ya ƙulle gidan yazo ya shigo motar, Baba Sallau ya ja su zuwa asibitin, ko da suka fito har sannan Jimmai batayi nisa daga layin nasu ba dan kuwa akwai zurfi da ma sai mota ko mashine ne zai fitarka,abunka da unguwar masu Hannu da shuni. Lalläi ne Jimmai ta girbi abunda ta shuka ko nace bata girba bama, dan kuwa waɗanda taiwa Abun sunce sun barta da ALLAH,kunsan kuwa shi ALLAH yana kishin byinsa, hakana yana gaggawar amsa adduar wanda aka zalunta kuma aka kawo Masa ƙara akan ya saka ko yayi hukunci akai, sai mu jira muga ikon ALLAH akan jimmai da Usman. Yau dai Jimmai mai mulki mai izza mai zalunci yau itace ta fito a ƙafa ta na tafiya, hakana ABBU wanda da can baya taiwa asiri baya GANIN laifinta akan komai, yai shine yai MATA Hakan, Duk da ma dai yai MATA da sauƙi ko ba haka ba fans? "Ƙwarai kuwa muguwa! azzaluma! baƙar ashana ƙona gari! ____________ daƙar daƙar jimmai takai ga bakin titi ta samu mota har unguwarsu, ko da tace Gida mahaifiyarta(mahaifinsu ya rasu shekarun baya) ta ga halin da take ciki ta tambayeta Amma ina ba bu amsa sai kuka, daga ƙarshe kuma ta gaya mata cewa wai Ɗalhat ya saketa saki Biyu! Uwar tace akan me Amma ina ba bu amsa, haka uwar ta rabu da ita, lokacin fuska ta haye sai sa tai MATA Ruwan zafi dan kuwa ta maru,marin da ABBU yai MATA, ƙafa kam ta kumbura itama,haka tai mata Ruwan Zafin itama, shu'uma sai ta ɓingire da barcin wahala na dukan da ABBU yai MATA da na tafiyar ƙasa kuma ba'a saba ba......... ______________ malam sallau yai parking acikin Asibitin,dan haka AQEEL bai farka da ga barcin da ya ɗauke shiba, ALLAH yaso acikin motar akwai ruwa dan haka AKEEL yana shiga ya ɓalle murfin ya bawa AQEEL bai yi gaddama ba kuma ya Sha, lokacin shaƙuwa tai yawa haɗe da Ajiyar zuciya hakana idanunsa sunyi jajir abun tausayi, dan haka yana Shan Ruwan barci ya kamashi, gashi har sun zo bai farka ba,dan haka Malam sallau ya fita hakama AKEEL,saidai Acn motar da aka kunna,aka barshi aciki yasamu relief. "ABBU bashi da ƙarfin jini dan haka lokacin har ya farka,Ruwan da aka sakawa ABBU ya ƙare dan haka doctor Najeeb yazo cire Masa yagama zai fita suka haɗu da AKEEL mai shigowa, AKEEL da Baba Sallau suka shiga ɗakin,malam sallau yaiwa ABBU ya jiki da Addu'ar samun lafiya, hakana yai Masa nasiha a matsayin sa na Babba gareshi bawai wanda yake ƙasan sa ba, dan haka Abbu yaji nasiha yaiwa Baba Sallau godiya a haka Baba Sallau da ma mukullin gidan yana wajensa dan haka yakoma gida a napep. Hakanan ABBU ya gayawa AKEEL yadda sukayi da Jimmai, AKEEL shima ya kwashe yadda sukayi da Jimmai a gida ya faɗa Masa. Sa'i da lokaci AKEEL sai ya fita gano AQEEL ya farka,aikuwa komawarsa ta ƙarshe ya sameshi ya farka Amma bai tashiba, dan haka yana buɗe motar, ya gane idonsa biyu, sai da ya ɗau lokaci a Hakan kafin ya yunƙuro ya tashi daga kishingiɗen da yake, AKEEL ƙarasa bashi Ruwan dayasha yayi aikuwa bai musa ba ya karɓa, yai Ajiyar zuciya sannan ya riƙo hannunsa suka fito daga motar, zuwa wajen ABBU, nan dai ABBU yaiwa AQEEL nasiha Akan ya kwantar da hankalin sa yanzu kam ya rabu da Jimmai, Duk yadda sukayi ya kwashe ya faɗa Masa, shi dai AQEEL ba magana alamu sun nuna ya ji. Ranar dai ABBU da AKEEL da AQEEL sukuku suka wuni suka wayi gari, sai a Hankali,Sai da sukaje ɗakin da AKEELA take, shi ABBU ya Mance ma AKEELA batasan komai ba! Dan haka ya shafa kanta yace. "Auta ta kiyi haƙuri komai yanzu ya wuce, jimmai da Usman ALLAH zai saka muku abinda sukai muku, yanzu haka bana tare da ita, Usman kam abunda yai miki duniya ce ta isheshi Riga da wando, silar komai mahaifiyarsa, wacce haka kawai tacemun zai dawo Gidan nikuma, batare da ƙin nuna amincewa ba na Amince, ashe da abunda zai aikata miki, kiyi haƙuri kinji, tun d Abbu yafara magana AKEELA tai shiru ta kafeshi da idanuwa, ita kam itace tasan abunda takeji a kanta tun lokacin da Abbu ya Kira sunan Usman (azzalumi a gareta kuma mara imani ko tausayi) taji ƙwaƙwalwar kantata na tafarfasa, kamar ana kwara MATA Ruwan zafi, daga bisani kuma tayi wata mahaukaciyar ƙara da sume wa. Abbu da su AKEEL hankalin su ya tashi, dan haka da sauri AKEEL ya tafi office ɗin Doctor Maryam domin ya kirawota ganin abunda AKEELA takeyi na fisge_fisge da ƙara................ Muje next page......... Oum ARQAM ce ontop 🥰 3/8/24, 1:16 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FIVETY TWO 52* Ƴan amana ga wannan Page ɗin saboda ƙaratowar wata mai Al farma na Ramadhan da AJIYE Post zanyi Zuwa bayan Sallah,Amma ga wannan idan ALLAH Yasa kun samu wani bayansa to, ALLAH Yasa mushiga watan a Sa'a ALLAH Yasa muna da rai da lafiya, Yasa muyi ƙarɓaɓɓiyar ibada "Ko da AKEEL doctor Yaje office ɗin doctor Maryam domin kiranta hankalinsa a tashe,Kwantar Masa da Hankali tayi Kafin su tawo tare,har lokacin AKEELA ƙara takeyi da fisge fisge, Hankalin AQEEL da Abbu inka duba fuskarsu zaka gani a tashe take, Amma CIKIN ikon ALLAH Doctor Maryam ta dinga Kwantar musu da Hankali Daga ƙarshe tace musu, ai wannan ba wani abu bane alamu ne suka nuna cewa ruɗewar da ƙwaƙwalwar AKEELA tayi Yanzu idan aka MATA Allurar barci zata farka normal. Kamar yadda doctor Maryam ta faɗa CIKIN ikon ALLAH kuwa AKEELA ta farko normal, Amma kuma sai ku ka takeyi, ta rungume Abbu ta dinga zayyana Masa Irin cin zarafin da Usman yai MATA, Abbu sai rarra shinta yakeyi Duk da zuciyarsa ba bu daɗi,hakama ƴan uwanta su AKEEL, ALLAH ya taimaka AQEEL bai sume ba wannan karon Amma fa idanuwa sunyi ja jur kamar garwashi Hakanan sai shaƙuwa yakeyi CIKIN sauri aka Bashi ruwa yasha Kafin barci ya ɗauke shi, hankalinsa ya tashi ganin yadda AKEELA take ku ka,da yadda ta dinga faɗar gallazawar da Jimmai take MATA, da tsawon lokacin da Usman yakai ya na kai MATA Hari,har ALLAH yakawo lokacin da yai galaba akanta,Hakanan Abbu ya dinga bata Haƙuri Akan Irin da ƙiletan da yakeyi idan tazo MATA da xancen jimmai, inda ya nuna MATA cewa shi ya zata Duk ɗaya ne da Mahaifiyar su da Jimmai ɗin, nan Abbu yai MATA al bishir da cewa ya rabu da Jimmai yanzu. Kwana uku tsakani aka sallami su AKEELA daga Asibiti, su ka koma gida ta warke ragal, Baba Sallau ya na gidan kuma Duk wani kulawa ya na Bawa gidan, dan haka da suka dawo sai ABunda ba'a rasa ba, kusan kullum suna Zuwa gidan. AKEELA ta koma school wanda da ma Abbu ya faɗa ba ta da lafiya ne, yarinya mai surutu da ƙwazo da ƙokari Amma yanzu Duk tazama so silent,daga malamai har ɗalibai sun ɗauka RASHIN lafiyar da tayi ne,aka Kwana Biyu zata koma normal. Haka ma su AQEEL sun koma school Duk da haka dai kowa ya ga canji ga waɗannan twin's ɗin me walwala da marar walwala Duk sai a slow. Abbu yanzu tsoron MATA yakeyi, ganin Yadda jimmai taiwa gudan jininsa,ita ma gudan jinin ƴar uwarta, yanzu wa zai ɗauko wacce zata Kula da su musamman ma AKEELA da take mace, Kullum tunanin da Abbu yakeyi kenan,tun dawowarsu da ga Asibiti,Ya sa a Ransa zaiyi Aure ko dan su har a Kullum yanawa wacce zai aura fatan ta zamo kamar inna Rabia a halaye da ɗabiunta wajen Kula masa da ƴaƴa, kullum ya na addu'a. Mahaifiyar Jimmai kakarsu AKEEL ta Kira Abbu akan me jimmai tai Masa Hakanan zai MATA saki, Abbu ya danne zuciyarsa yacewa Inno "Inno ba bu abunda ya faru kawaii dai kinsan Aure rai ne da shi dan haka Aure tsakaninmu da Jimmai ya ƙare,Amma Inno jimmai ba bu abunda taimun, Inno tasan Abbu yarone mai biyayya tun lokacin Aurensa da Ummul khair, dan haka bataja aBun ba tai Masa addu'a da fatan alkhair, daga ƙarshe ta sako Masa zancen zamansa ba bu MATA ga Yara Harda mace ma kamar AKEELA, nan yace Inno ki tayani da addu'a, Nima ina tunanin hakan,lokacin Jimmai tana ɗakin ta na jin muryar Abbu har suka gama tattauna da Inno yai MATA sallama ya fice. Sai sannan ta fito "Inno na gaya miki haka kawaii Ɗalhat yace ya sakeni, Amma Babu abunda ya faru,Kika ƙi yarda Yanzu kinji ta bakinsa, da share ƙwalla Jimmai da ƙarasa zancen murya gwanin tausayi, ɗa da mahaifi nan Inno ta tausayawa jimmai, ta dinga Kwantar MATA da Hankali Akan idan da rabon komawa saita koma ga Ɗalhat tun da da sauran igiya ɗaya, tun da ga sannan Jimmai ta sake a gidansu haka ma CIKIN ƴan uwa, idan tace haka kawaii Ɗalhat ya saketa wasu suna yarda wasu ku ma suce da wata a ƙasa. ______________ Usman ko da Jimmai ta faɗa Masa yadda suka ƙarke da Abbu ko a kwalar rigarsa,sai cewa yayi Maama can ta matse Masa, ya barmu da ALLAH ,to ai dama dashi yaganmu kuma da shi zai kalemu, ita dai Jimmai Ajiyar zuciyar tayi suka gama hirar su ta kashe wayar. jikin ƙanin ba ban Usman sai a Hankali ya yi zafi har sannan suna Asibiti, dan haka yana Zuwa asibitin, Shukra in ta dawo daga school kuma tayo gida ta shirya Kafin ta bi Umma(mariƙiyar su) a Hankali shaiɗan ya dinga ƙawatawa Usman Shukra musamman idan ya yi mankas da kallon sa na banza ita kuma ta dawo daga school, da kunya dai ABunda zuciyarsa take shirya Masa ya yi, Amma kuma fa abunda yakeji game da Shukra ya fi ma abunda yakeji game da AKEELA na sha'awa, dan haka zuciyarsa ta yanke Masa shawara Akan ya zubawa Shukra, Maganin da zai bugar da ita kawaii ,ya yi amfani da ita bata sani ba,da ma kuma yana siyowa Shukra ƙanwarsa ice cream da sauran kayan makulashe ta nan kuwa ya zuba MATA, ta na dawowa daga school kamar yadda ya saba ya ɗauki ice cream da su juices ɗin ya bata aikuwa tai ta murna ta shige da su ɗakin ta , Shukra akwai son Zaƙi daƙar tayi wanka daga ita sai towel aikuwa ta ɗauko ice cream da juice ɗin da Usman ya bata ta hau Sha ta na lumshe idanu, gama Shanta ko minti 5 batai ba barci ya ɓingireta aikuwa nan Usman yazo ga Shukrah da yake wannan ya tsara abunsa cikin lallama yai Amfani da ida dan bazance fyade ba, Yasan Umma batanan ku ma bamai shigowa gidan war Haka ƴan aiki suna wajensu da ban,cikin kwanciyar Hankali yagama aikinsa ya gyara Shukra kamar yadda take yai shigewarsa ɗaki, bayan yai MATA allaurar kashe zugi wacce ya siyo a chemist. Ko da Shukra ta farka batayi tunanin komai ba, Amma tayi mamakin barcin da tayi wajen awa biyu, dan haka sai gaɓoɓin jikinta da taji sun mata tsami, da kuma Yanayin jikinta da taji sai a slow, cikin sauri da shiga bayi tayo Alwala tai Sallah Duk da taji ƙasanta ba kamar da ba, Amma bata kawo komai a Ranta ba, a gurguje tai haramar Zuwa asibitin,ko da taje Asibitin umma batayi wani tunanin zuwanta ba kamar yadda ta saba ba, tunda wataran ma bata Zuwa. Tun daga sannan Usman ya mayar da Shukrah kamar matarsa Duk lokacin da ya buƙaci kasancewa da ita hakanan yake Amfani da ita, lalläi Usman anya yanada Hankali kuwa ƙanwar ka uwa ɗaya uba ɗaya, ko da Yake abunda Jimmai ta shuka shi zata girba, lokacin da.yaiwa AKEELA fyade jimmai Harda cewa Usman mai Yasa bai bata wani abu ba kafin yai MATA fyaɗen, to Yanzu ga shi ya bawa Shukra ai kuma,Kunga kenan karatun Jimmai ya tuno dashi. Cikin ikon ALLAH jikin Baban su Usman ya yi sauƙi sosai har an sallamo su, sun dawo gida, kuma komai ya dawo normal,yaji sauƙi sosai, har Baban yake cewa "Usman kadawo gida ne? Ea baba na dawo ai shi ABBU ɗin ya saki Maama ne, kaga kuwa me zai kaini Zama a gidan na dawo gidanmu Usman d shagwaɓa yake ƙarasa maganar ga Baban nasa, Ai shikenan Usman ni da ma banso ka koma Gidan Jimmai da Zama ba, da ka nuna kanaso ne, Yanzu ai ga shi ka dawo ALLAH ya kyauta, inji Baba wanda yaji sauƙi sosai. _______________ Tun da Abbu ya saki Jimmai dai ƴan uwansa suka dawo Masa a kwanyar kansa, aikuwa cikin Tashin hankali Yaje gida, Inna Rabia tayi murna haka sauran ƴan uwa, su ma hakanan sukace Rana tsaka Ɗalhat mukaji tunanin ka da komai naka mun Mance, shi ma yace musu ai shima hakanan, baisan meyasa ya Mance su ba, akai ta jimamawa da koke koke, Saida suka keɓe da innar sa da Abba (tsoho mai ran ƙarfe) nan Abbu ya bayyana mahaifansa yadda Jimmai tai Masa, Amma ya roƙi karsu gayawa kowa, Inna Rabia da Baba Hankalunsu ya Tashi jin yadda Jimmai taiwa Ɗalhat da kuma ta'asar da ɗan ta Usman yaiwa AKEELA, nan dai Abbu ya kwantr musu da Hankali Akan cewa komai ya wuce ai, AKEELA ma ba bu wanda zaice wannan abun ya faru da ita idan ba faɗe akayi ba. Cikin satin kuwa Abbu dasu AQEEL ya kwashe su gidan inna Rabia da Baba,iyaye sai farin ciki da murna hakama su AQEEL. Nan akaita mamakin girman su AQEEL da kuma AKEELA, lokaci weekend ne dan haka suka kwana biyu a gidan. Aisha(mommah) da mahaifiyar Abbu da mahaifiyar ta ya da ƙanwa ne, karatu ta yi batafi 30_32 ba ƴar boko ce sosai, dan haka inna Rabia tace "Talle (haka take kiransa) ga Aisha nan tagama karatunta, Amma ALLAH bai kawo miji ba ka aureta kawaii, ina kyautata Zato a gareta, yarinya ce mai hankali da tunani da nustuwa, haka ma Baba yasa Baki, ba bu ja in ka Abbu ya amince da zaɓin iyayensa a Karo na Biyu Bayan Jimmai, ko da inna Rabia ta tunkari Aisha da maganar bata musa ba, ALLAH yagani da ma tana son Abbu a zuciyar ta, kuma tana tausayawa ƴaƴansa jin Irin wahalar da suka Sha Hannun jimmai,kuma ko ba bu Aure ai za'ta iya kulawa dasu. Dan haka ba bu jimawa aka nemarwa Abbu Auren Aisha dangin mahaifinta,ko da Abbu ya gayawa su AKEELA wacce zai aura basuyi baƙin ciki ba, dan kuwa sun santa Aunty Aisha tana da kirki, Amma su AQEEL kam kadaran kaga ham suka amshi Auren. CIKIN ƙanƙanin lokaci akayi Aure Aisha ta tare a gidan Abbu, ya sameta kamar yadda Yake fata dan kuwa tanada halayen kirki,a Hankali a Hankali ta dinga gogewa Abbu dasu AQEEL tabon da Jimmai taiwa MATA na kuɗin goron da sukai musu, har suka sake da ita AKEELA ce take ce Mata mommah sai kowa yakama Mommah har su AQEEL ɗin. CIKIN ƙanƙanin lokaci walwalar Abbu da AKEEL ta dawo Amma AQEEL da AKEELA sai a slow,Duk wani ga ta da kulawa Mommah ta na Bawa Abbu da ƴaƴansa. Baba da Inna Rabia sunyi murna da wannan Aure da aka hada, walwalar Abbu ta dawo da komai Amma asirin da Jimmai taiwa Abbu da Ammar BN Yasir kam har sannan bai warware ba, Bai tuna shi ba, haka ma sauran ƴan uwa Basu tuna ba. CIKIN ikon ALLAH foundation ɗin da Abbu yake ginawa ya kammala,wanda taci sunan *TALLAFY CHARITY FOUNDATION* sunan ya samo asali da sunan sa inna Rabia take kiran Abbu dashi wato *Talle* sai ya gyarashi da *TALLAFY* Duk wani abu da za'ayi an gama hakama gomnati tasan da zamansa,kuma Alhamdullillahi aBun ya karɓo, dan tashin farko yara da yawa aka kai, hakama Duk kangarar da RASHIN jins yaro ana kaishi CIKIN ikon ALLAH bazai fita ba, sai ansamu waraka Akan hakan. Wanda hakanne ya ƙarawa Abbu albarka a dukiyarsa, tuni gidan da suke ciki ya kuma siyen wasu filayen da gidajen kusa ya haɗe da nasa, su kuma ya sallame su da wani, yan uwa da abokan arkizin kam ana wutawa da Abbu, hakana zuwan Inna Rabia da Baba makkah nawa, Duk wani rufin asiri da arziƙi ALLAH yaiwa Abbu kuma hakan ya samo asaline Daga taimako da tallafawa marasa shi. Abbu ya mallaki kadarori da kamfanoni ba bu adadi,mai sunan *TALLAFY GROUF OF COMPANY*. Su AQEEL da AKEEL suna kammala secondary ya samar musu admission A *CANHWU UNIVERSITY* dake New Delhi, CIKIN ikon ALLAH kuwa suka tafi, sai fatan NASARA. Abbu bodyguard ɗin sa sunfi Ashirin waɗanda suke kula da lafiyar dayi Masa rakiya a kowanne lokaci, kuma suna jin daɗin mu'amula kai bakace a ƙarƙashin sa suke ba, hakana Ma'aikatan Tallafy foundation Suma. Zamansa da Mommah sai son barka, a yanzu kam sai kace AKEELA da AQEEL da AKEEL ƴaƴanta na cikinta ne, SABODA kulawar da take Basu, hakan yanawa Abbu daɗi,shiyasa a koda Yaushe yake ƙara ƙaunar ta a Ransa, tana kiranta da ABU AQEEL shikuma yake OUM AKEELA KO AKEEL,tuni Abbu ya manta da wata jimmai Tunda dama abunda tai Masa yace yabarta da ALLAH, Yasan tabbas ALLAH zai saka Masa yasakawa ƴaƴansa. ___________________ Tun da Babansu ya gama jiyya ya dawo daga asibiti kuma Usman tabbatacce ya ƙyale Shukra haka, to aina zai samu da ma. Cikin ƙanƙanin lokaci Shukra ta ƙara cika da fari, fiye da da, kuma ba bu wanda yakawo komai a Ransa game da hakan,tun da dai ita ba Rashin lafiya take ba,sai dai cikin dare Zuwa asba zazzabi yake kamata da zarar asba ta yi kuma zata dawo normal,sai kwaɗayi da takeyi kuma a school ne, irinsu agwaluma da su aya me gishiri haka zata dinga siya tana ci har tayo guzirinta, a gida ma haka taita kwaɗayi Akan abinci kenan yau tace wannan zata dafa gobe wannan, ko tace batason wannan, wannan take so, gidan kowa harkarsa yakeyi ƴan aiki suna wajensu,Hakanan Umma aikin gomnati takeyi ba zaman gidan take sosai ba lokacin da Shukra zatayi kwaɗayinta bata nan ko tananan ma ba mai kula bace........ Lalläi fans meyake damun Shukra ne Hakanan Wane irin Usman ne wannan wai kamar ƙuda yake baya gudun Haram ALLAH sarki Mommah lallai kin biyo halin inna Rabia goggonku gaba ɗaya keda Abbu ɗin Su AQEEL da AKEEL an cale India ALLAH yabada ilimi mai amfani Foundation ɗin Abbu ta kammala ALLAH ya taimaka ya ƙara arziƙi mai amfani da Budi ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 Muje next page ƴan amana idan ALLAH yayi Kafin ramadhan nakuma wani idan kuma sai Bayan Sallah ne to ALLAH ya ƙaddara ganawarmu yasa muyi ibada karɓaɓɓiya I love you All my fans🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 4/14/24, 12:03 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FIVETY THREE 53* Godiya ta tabbata ga ALLAH daya bamu kammala ibada ta RAMADHAN, ALLAH Yasa munyi karɓaɓɓiya ya biya Mana bukatun alkhair, Inawai yan uwa barka da sallah ALLAH ya maimaitamana *🕌EID MUBARAK All my fans*🥰🤗 A wannan halin shukhra ta kasance na kwaɗayi Babu wanda yasan meke damunta,tayi fresh da ita jiki sai sheqi yake indai mutum me Hankaline yana ganinta zaisan akwai labari, Saida aka kwashe wata huɗu a haka lokacin tafiya ta miƙa Sannan Umma ta fuskanci abunda ke faruwa da Shukrah, bata daɓa Haihuwa ba Amma kuma ko budurwa taga Shukra tasan akwai labari! Hankalin Umma ya tashi batayi Wani tantanma ba, ta tsare Shukra da Jan Ido Akan yaushe rabonki da ganin al al adarki? Shukra tai shiru kanta a ƙasa tunani ta lula ai zatayi wata biyar batayi ba, Umma 5month kenan dama inason gaya miki ko bani da lafiya ne! Akaini Asibiti! Umma dai idanuwa ta zaro waje Shukra waya miki ciki? Na shigesu! Ciki kuma Umma Babu kowa nida bana zuwa ko ina daga school sai gida cewar Shukra tana kallon idon Umma data zuba MATA shi! "Karki Raina min Hankali Shukrah ki gayan tun muna shedar juna! Innalillahi Umma ALLAH ya tsareni da abun kunya bana kula kowanne namiji ALLAH kema kinsani! Cikin kuka Shukra ta ƙarasa zancen" Suna wannan zancen Abba ya shigo yaga Shukra na kukan! Yace lafiya nan Umma ta gaya Masa meke faruwa! Salati ya Fara yana "Shukrah ki faɗa Mana GASKIA wane ɗan iska ne ya cuceki sai munyi shari'ah dashi ya qarasa faɗa da shafa kan Shukra alamun rarrashi,Duk irin lallashi da ban bakin da Umma da Abba sukewa Shukra Akan waya MATA ciki haka take cewa ita bata saniba, dan Haka Abba yakira lititansa domin ya tabbatar da hasashen su,Hasashen su yazama gaskia ciki ne da Shukra 5month harda sati biyu ma, Abba kam take hawan jininsa ya tashi umma sai Kuka takeyi abun babu daɗi, wannan Ahali abun tausayi Shukra dai batasan wanda yai MATA wannan ɗanyen aikin ba, an buga an Raya, haka sukayi kwanan baƙin ciki,balle Shukrah sai Kuka take Akan batasan ko wanene ba. USMAN kuwa daya dawo gidan yaga umma da Abba yanayi Babu daɗi, Shukra tana Kuka dai yai tunanin Wani abune daban! My sis meke faruwa ne wai? Usman yafaɗa lokacin da yake shiga ɗakin Shukra ɗin! Da sauri Shukra taje ta faɗa jikin Usman tana Kuka! Yaya wai cikine dani kuma ni Babu Namijin danake kulawa! Da ace Shukra tana cikin nustuwarta xata kula da halin da Usman ya shiga! Amma ina tashin hankalin da take ciki ya kore! Jikin Usman sharkaf yayi da gumi, cikin in ina yace ci...ci....ki k..u.m.a! Eamn Yaya nashiga uku na! Innalillahi wa Inna ilaihi rajiuun sis kidai tuna meke faruwa! Ciki da yadda akayi aka sameshi domin ba'a Sha a ruwa! ALLAH yaya ban saniba, haka dai Usman ya lallashi Shukhra ya fito daga ɗakin dan kuwa zamar Masa da tayi ajiki ya jefa shi cikin Wani yanayi!saboda kar asamu akasi yasa ya fice. Ɗakin Umma Yaje wacce taci Kuka, cikin alamun damuwa ya dinga kwantar MATA da Hankali,kafin yafice, ɗakin ABBA wanda yake barcin wahala da aka haɗa Masa da allura! Haka wannan Ahali suka kasance cikin baƙin ciki Abba da Umma da uwar gayya Shukrah Duk ta rame, har Asibiti ta kwanta likita yai MATA gargaɗi Akan ta kula da damuwa kar yashafi ɗan cikinta, kuma daga Umma da Abba Babu wanda yayi yunƙurin zubar da cikin sun zubawa sarautar ALLAH idanu. shi kuwa Usman tunda yaji cewa Shukrah tanada ciki yasan cewa tabbas nasane, ko wata fargaba baiji ba, cewa Shukrah ƙanwarsace uwa ɗaya uba ɗaya,ita yaiwa ciki kuma ba'asan ko wane ba! Yabar mutane cikin damuwa da azaba, musamman ita Shukra ɗin datake tunanin samuwar cikinta, kamar dai yadda yaiwa AKEELA fyaɗe haka ya sha shantar da zancen, shirin barin garin yake ma, da kudirce a Ransa Shukra nazata haihu yananan ba, ɗa ko ƴa kuma zai Bashi kulawa tunda dama ɗan ƙanwar sane ba wanda zai zargi Wani abu. Kwanciyar Shukra a asibiti sai sannan Umma take gayawa Jimmai meke faruwa! Sai ga Jimmai tana Kuka wiwi da tsinewa wanda yaiwa ƴarta haka,sai Ku ka take, tana lallaɓa Shukra Akan tagaya MATA wane Amma amsar daya ce! "Maama bansan wanda yaimun cikin nan ba" tun daga sannan Jimmai ta ƙasa lafiya, hawan jini ya kamata ga targaden da Abbu yaji MATA har sannan tanajin zafinsa sa'i da lokaci. Tuni Usman yabar gari a zummar Wata seminar ya samu, yana waya dasu Umma da Abba yana Kwantar musu da Hankali, haka ma Shukra, jimmai kuwa ko nemanta baiyi ba, sai itace ta nemeshi take Masa zancen cikin Shukhra! Babu kunya Babu komai yace ciki nawane, Duk yadda yayi da bawa Shukra maganin da yayi Saida yagayawa Jimmai wanda kafin tagama ji dama a tsaye take, sai uwarta ji tayi ta faɗi tiiiim! Cikin sauri tazo ta gareta Amma ina Babu numfashi, kururuwa inna tasa a waje da gaggawa maƙota suka cika gidan, kafin mene an taimaka ansa Jimmai a mota sai Asibiti,aka bata taimakon gaggawa,jininta yayi sama sosai hakan yasa paralyse ( cutar ɓarin jiki) ya sameta ga bakinta ya karkace Babu ikon magana sai yawu ne yake zuba Duk mai imani idan yaga halin da Jimmai take xai tausaya MATA! A haka har aka sallamota aka dawo Gida, Babu Wani cigaba, saidai a Kwantar a tayar tanason magana Amma Babu hali, sai kuma yawu na zuba, weekend yazo AKEELA tazo gaisar da kaakar ta anan taga halin da Jimmai take ciki, Duk da Hakan ta tausaya MATA, Amma ina Jimmai na tozali da AKEELA jiki ya Fara kakkarwa alamun tanason magana amma ba bu halin yi, AKEELA ganin halin da Jimmai take ciki sai da tayi Kuka. Inna ce ke kula da Jimmai dan haka sai a Hankali har tayi kashi da fitsari bata gyara ta ba,Duk jikinta ya ɗauke alamun kwanciya ga najasa kullum acikinta take. ALLAH kenan Jimmai tasan kowane yaiwa ƴarta ciki ba kowa bane illa ɗan ta na cikinta ,Amma Babu bakin magana, sai dai kukan kawai Watanni haka suka shuɗe cikin Shukhra ya isa Haihuwa, ta lalace ta jeme, shima Abba jikin sai a Hankali, gwanda Umma, bata da jini ko ƙadan ga kumburi gwanin tausayi, dan Haka aka ce C's za'a mata, anshiga da ita ɗakin kafin ayi ALLAH ya saiketa lafiya ta samu ɗan ta Namiji,mai kama da Usman sak! Babu wanda yakawo komai tunda dai ɗa kama da yayanta yakeyi kuma itama Suna kama, haka aka MATA kowanne irin taimako da kulawa suka dawo gida zuciyoyinsu babu daɗi,sai Da aka sallamo Shukra sannan aka gayawa waya a waya, ta mance da wata jimmai a gurin tana sallallamin ta " Shukra ta haihu, ALLAH gamu gareka ALLAH ya tonawa maci amana asiri,Amma kuma ta yaya ma wai Wani ɗan Iska yashigo gidannan yaiwa yarinyar nan ciki!ita kuma ba ko ina take Zuwa ba,ko a makaranta tana Zuwa Wani gurin ne,karfa yarinyarnan ta raina Mana Hankali fa ciki da ba'asha a ruwa dole akwai wanda yai mata,kuma ma ai amfani dakai bakaji alama ba kana budurwa, zanzo gidan ne dole yarinyar nan ta faɗa Mana gaskiya,nan dai suka tattauna da inna da Umman Shukrah. Jimmai Duk hirar da suke tanaji zuciyarta sai ƙuna take ba bu bakin magana,sai Kuka take haka inna ta lallasheta Amma taƙi shiru,nan danan zazzabi ya rufeta. Shukra Babu Aiki sai Kuka ko kula ɗan batayi, cikin ku ka take gayawa my bro aikuwa ya dinga kwantar mata da Hankali,Amma taƙi, picture ɗin yaron yace ta tura Masa, aikuwa cikin Kuka tace! "ni yaya Babu ruwana dashi! Naji dai ance yana kama dakai, komai da komai, ɗaukar min picture naga my son, sis kiyi haƙuri ki Kula da yaronnan kinji! Babu ruwansa! Nan dai Usman ya dinga lallashin Shukra Akan kula da babyn,Amma Babu Wani cigaba, dan bata shayar dashi sai madara kuma Babu wanda ya takurata,inna har gidan tazo ta inda tashiga batanan take fitana Akan Shukra ta gaya mata gaskia Akan wayai mata ciki Amma magana ɗaya ce batasan wanene ba! ALLAH sarki Abba haka ya dangana ya barwa ALLAH hakama Umma sai Jan Shukhra ajiki suke Amma ina! Baby yaci sunan Kabir sunan Babansu Shukra An Kiransa Daddy,yaro sak Usman kamar an tsaga kara,wane Zai kawo wani abu Akan hakan? Usman yadawo gidan daga tafiya haka yake kula da Daddy kullum yana wajensa, ALLAH yasanya Masa ƙaunarsa a zuciyarsa,yana kula da ɗansa yana fakewa da ɗan ƙanwarsa ne. Haka yaro yai ɓulɓul dashi, Shukra takoma school abunta,an faɗa batada LAFIYA ne abunka da makarantar kuɗi, AKEELA tai jimamin abunda ya faru da Shukra ta tausaya mata,Amma kuma tasan cewa Alhakin fyaden da Usman yai matane ya faɗawa Shukra ƙanwar sa, ABBU yasan da zancen abunda ya faru da Jimmai da ƴar ta Shukra ko ya nuna yaji yasan cewa kaɗan ya Fara gani,saura Usman shi ma zaiga sakayyah ne. ******************** *NEW DELHI* Farkon zuwansu AKEEL India Babu Wani karatu da AQEEL yakeyi sai damuwa da take Ransa,Hakan yana damun ɗan uwansa inya cika matsa Masa Akan karatu kuma cutarsa ta Tashi,dan haka yake tsoron Masa magana,yana kiran Abbu ya gaya Masa, halin da ake ciki Abbu inya kirashi sai dai yayi shiru in yana Masa faɗa, Ɓangaren lalurar sa ta desire (sha'awa) kuma dama ita sai da kwanciyar Hankali take samun mutum, dan haka kwata kwata yadaina ciwon cikin nan,balle ya fita hayyacinsa, sai ABunda ba'a rasaba tunda kuwa Namiji ne shi kuma me lafiya. Sai da suka ɗau watanni acan kafin ALLAH ya taimaka AQEEL yafara karatu,dayake akwaisu da ƙokari kuma Duk course ɗaya suke wato community health,har sannan Saida Glass AQEEL yake Amfani,shine kawai banbancinsa da ɗan uwansa,suna waya da AKEELA akai akai nan take gaya wa AKEEL abunda yafaru da Jimmai da Shukra, ALLAH ya sauwaƙe kawai yace, shi AQEEL dama ba Wani magana da sakewa yakeyi ba sai a slow ita kanta AKEELA ɗin ba Wani kulata kamar da yake ba,mutumin da da komai Auta AKEELA Amma yanzu sai a Hankali,to itama ma ai sai a slow ɗin dan Duk cikin damuwa suke, AKEEL ne me dama_dama. Ɓangaren su AKEELA ________Tun bayan barin AKEELA asibiti ALLAH ya ɗorawa doctor Najeeb ƙaunar AKEELA dan farko ma yazata tausayin ta dayake ji ne,Amma ina ƙauna ce Ashe, Babu Wani ɓata lokaci ya gayawa Abbu, shi kuma Abbu yace "Babu matsala Najeeb kaga dai ABunda ya faru da ita ko,banson asamu matsala daga Baya ne! Cikin karaya Abbu yaƙara sa xancen, kuma ka ga dududu yarinyar nan banda ƙaddara guda nawa take ko 14years batayi ba, "ea yallaɓai Babu matsala kuma zan jira ta ƙara girma ,magana dai nayi saboda kasan da maganar! Doctor Najeeb yaƙara magana cikin girmamawa. Aikuwa Abbu yayi murna da Hakan yagawa AKEELA yadda sukayi da doctor Najeeb ita kunya ma taji, kamarta ace anaso,su AKEEL sunyi murna da haka ALLAH ya rufawa ƙanwarsu asiri suna murna ALLAH ya sakawa doctor Najeeb da alkhair. Doctor Najeeb Baifi 25years ba ɗan masu kuɗi ne sosai, kunsan sha'anin kuɗi nan danan yana kammala karatu yasamu aiki,kuma yanada ƙokari sosai, dan Kano ne shine na uku a gidansu,akwaishi da Hankali da nutsuwa Bashi da wata matsala,koda yaiwa Mahaifin sa zancen AKEELA, Bappan sa yasan Alhaji Ɗalhat ma ai Babu damuwa ya amince,ya kirashi a waya sukayi magana Akan sai yarinya ta ƙarasa secondary school sannan,in yaso ta ci gaba a ɗakin mijinta da karatun. Mommah ta Zamarwa AKEELA kamar mamanta, komai yi MATA takeyi, hakana kullum cikin kiran su AKEEL take da kwantar musu fa Hankali Akan komai ya wuce tana Basu kulawa sosai. Dawowar su AKEEL wutun farko Abbu yabiya musu suka je gaba ɗaya suka sauke falali harsu inna Rabia da Baba Sallau, komai yana tafiya daidai, foundation kuwa yafi da haɓɓaka, daga garuruwa ake kawo Yara. Hakana Daddy tuni yayi wayo abunsa har sannan anrasa ubansa,ya saba da Usman sosai, har sannan Babu nafamar da Usman yayi sai ɓare barikinsa dayayi,gida guda ya ware inda yake kai MATA kala_kala yana watsewarsa dasu, ko kunya ko tsoron ALLAH to mutumin ma da yayiwa ƙanwarsa wazai ji kunya a duniyar nan,sai ɓarin naira yake musu. Jimmai dai har gida Umma tazo da daddy taganshi, sai da ta razana ganin kamminsu da Usman kamar lokacin tana goyonsa sai Kuka kawai takeyi, ana share MATA hawaye Babu halin magana,su dai Basu kawo komai a ransu ba,indai Usman yazo haka Take kukan nan hakana AKEELA, ko kuma haka kawai ma, Usman shi kuwa ko ajikinsa in yazo tana Kuka kallonta yakeyi Babu kunya ma a tare dashi, da tafiya ta miƙa ma daina zuwa gurinta yayi dan kuwa duniya ce shi yanzu a gabansa, Jimmai kam har sannan Babu Wani cigaba game da jikinta. Shukra kam magana Bata ɓuya sai gashi ana zunɗenta ai tayi cikin shege Babu damar taje makaranta ana matsawa daga jikinta, ashe ashe lokacin data haihu akwai wata ƙawarta itama ankawota zata haihu anan taga Shukrah da ciki, nan kuma anzo makaranta ance batada LAFIYA,sunzo dubata kuma anhanasu ganinta ance bata gida, aikuwa makaranta ta gagari Shukra Babu damar shigowa gidan tunda akwai masu gadi, Suna da groups na makaranta ga numbers ɗin ƙawayenta har anan habaici ake MATA Akan tayi cikin shege,Babu wanda bai san abunda ya samu Shukra ba yanzu Duk layinsu.... Lalläi ne Jimmai abunda ka shuka..... Su AKEEL dai ABunda tai niyya garesu gashi bai faruba.... AKEELA ta samu mijin Aure Babu wanda yasan meya sameta... Su AKEEL suna karatu.... Usman shikam sai duniya ta horarsa Inaga xaiyi nadama ALLAH sarki Shukra laifin uwarki da yayanki ya shafeki Wannan wace irin masiface ka Haifi ɗan shege kuma ace yayanta yai maka cikin kai jimmai kin cuci kanki, Alhakin marayun ALLAH ne Muje zuwa dai ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 4/18/24, 9:37 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)* *08128131163* ✍️ Marubuciyar... *Komai Nisan jifa* 📚 *Hakan ba kuskure bane*📚 *_____________* MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)* 'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙 *_____________* *PAGE FIVETY FOUR 54* Ko ina ka ji ana zancen Tallafy foundation saboda irin taimakon al Uma da cibiyar takeyi a koda Yaushe,tsakanin Abbu da al uma sai addua hakan ne yasa a koda Yaushe dukiyarsa take gaba,gashi yana ganin alkhair ta ko ina Babu indai a baɗin Nigeria zakace tallafy foundation a rasa wanda zaice bai sanshi ba, ga kuma Tallafy group of company, Babu abunda baya oda na kayan abinci da sauran kayan provision, da kuma Tallafy Holding company Duk wasu kayan karafuna da kayan wuta fanka generators,ion, fridge, da dauransu ga kuma injinan mota, har mota yake daga kashashen waje Kowacce irin mota akwai. Tun farkon Fara tasowar Abbu Alhaji Ammar BN Yasir yasan shi sosai Saidai kuma ina bai sanshi da Wani Tallafy ba, ai da yasani da tuni ya lalaubo Abokin amana,har Abubuwan da yake Amfani dasu yana siya a company ɗin, Rashin sani yafi dare duhu gashi kuma har ALLAH ya ɗau ran Alhaji Ammar Babu rabon ganawarsa da Aboki ko nace ɗan uwa nagari. ______AQEEL DA AKEEL______ yadda a koda Yaushe Addu'ar da akewa Abbu shi da zuri'ar sa itace take tasiri akansu dan kuwa ALLAH yana Basu Sa'a Akan sha'anin karatunsu sosai, Duk Wani shashanci da majority wanda suka tafi karatu ƙetare sukeyi irinsu shaye_shaye,neman MATA ALLAH ya tare su dashi, musamm AQEEL shi da dama baya shiga harkar kowa inba ɗan uwansa ba,balle kuma wata mace, miskilanci fa sai ABunda yayi gaba yana girma shima yana ƙara girma miskilancin, ɓangaren Cutarsa kuwa Duk yadda zata kaya ɗan uwansa baya sakashi a damuwa balle cutarsa ta Tashi, Amma kuma idan wataran yatuna irin wahalar da sukasha a Hannun jimmai sai dai ɗan uwan yaga idonsa yayi ja yana shaƙuwa, sai barci shikenan kuma, zamansu a New Delhi kam sai san barka, ABBU da Mommah da kuma AKEELA Suna zuwa dubasu idan Akeela anyi hutun school, Anan ma ABBU yake zuwa a duba lafiyarsa shida iyalansa shiyasa ma kamar su AKEEL suna kusa da iyayensune. AKEEL da AQEEL akwai kyau da tsafta sosai ba'a banbacesu saita halayya da kuma Glass a fuska. ***************** Usman fa duniya da tsinke akeci Lallai barikince a gaban sa, din da Hakan bappa da Umma basusan halin dayake ciki ba,daga gida kuma yaga gidan yai Masa kaɗan Rana Tsaka aka nemeshi aka rasa ya shiga duniya, Duk hankalin bappa da Umma ya tashi kwana biyu Basu ganshi ba idan ankira wayarsa ba'a samun sa,sai adduoi ake da nema Amma shiru, sai da aka ɗauki wajen wata guda sannan yakira su yake cewa shi fa ya koma kudu da Zama su tayashi da addu'a,kawai Amma gidan su abokinsa yakoma kuma zai samu adimission anan yaci gaba da karatun sa,saboda yatawo da takardunsa nan, Ko jiran maganar da bappa yake Masa baiyiba ya kashe wayar gaba ɗaya,wa afka masha'arsa shida sabuwar budurwarsa me suna Alxendara, ƴar Wani mai kuɗi ce yanzu haka shi da ita shirin barin ƙasar suke yi. Tun daga sannan kuma ina ba'a sake jin ko motsin Usman a waya ba iyayen sunyi Kuka Amma ina sai Haƙuri. Shukhra dai makaranta ta gagareta saboda tsamgwamar da ake MATA,Babu dama ta fito a unguwar,shikam Daddy yai wayo abunsa Babu abunda ya dameshi, ganin gidan Babu kowa daga ita sai shi ahaka shaƙuwa ta shiga tsakanin Daddy da Shukrah, tafara jansa a jiki,tun yana tsoronta harya daina, komai ita take Masa shaɓanin da Umma ko ƴan aiki, sanadin tafiyar Usman tasa Bappa yakamata cuta sosai jininsa yai sama sosai kwana biyu tsakani yace ga garinkunan, bappa yanason Usman sosai, darajar ɗan uwansa, umma tasha Kuka haka ta haƙura tafara takaba harta kammala Babu ɗa Babu jika. Su Shukra ansha kuka da daddy, wanda ya zata bappa ne mahaifinsa, har bappa ya cika yana ALLAH ya saka miki Shukra wanda yai miki wannan zaluncin Duk inda yake kar ALLAH yarufa Masa Asiri, ALLAH ya bayyana shi. _____JIMMAI____ Jimmai kam jiyya tayi jiyya yanzu tana Zama da kanta, bakinta ya daina zubar da yawu Amma fa babu magana,hakana tana ɗan motsa hannunta guda ɗaya,hakanan Babu tafiya sai Kuka, rana tsaka inna ta kwanta barci aka Tashi rai yayi halinsa, mai jiyyar Jimmai an mutu haka jimmai akasha Kuka, sai Shukra ce tadawo gidan take jiyyar Jimmai ita da Daddy suka dawo,indai jimmai yaga Daddy sai tayi Kuka, shi kuma kamar son kukan yake haka zaizo gefenta ya zauna ga ɗan banzan surutu,sak dai Usman lokacin yana yaro idan jimmai ta kalleshi, sha'anin jiyya sai Haƙuri musamman yarinya kamar Shukra dan haka sha'anin kula da Jimmai sai a Hankali,Babu wata cikakkiyar tsafta da dinga wari da zarni kenan, Duk abun bukata umma ke aiko musu dashi Umma kuma ƴaƴan ƙanwarta ta ɗauko suke tayata Zama, itakam batada matsala tunda ta shuka alkhair... ______AKEELA_____ Tana cigaba da karatunta yanzu haka ta shiga babbar secondary tana Aji biyu, ta xama cikakkiyar budurwa ma Sha ALLAH ga kyau da nutsuwa, Amma indai ta tuna Abunda yafaru da ita saita kasance cikin damuwa, kullum Mommah cikin Kwantar mata da hankali take, tsananin ta da doctor Najeeb kam soyayya suke mai tsafta,yace MATA ai munkusa zama abu ɗaya, burina akoda Yaushe in ganki a gidana,sai ta karaya tace wane abu ɗaya kuma Wane zumuɗi zakayi alhalin ni da ba cikakkiyar budurwa ba da ta faɗi haka Doctor Najeeb zaita gaya mata kalamai masu sanyaya zuciya Akan shi ma ruwansa da wannan burinsa a koda Yaushe ita wannan kuma ai ƙaddara ce to shiyasa wataran take samun salama a zuciyarta. Koma Alhamdullillahi yana tafiya daidai a Wannan ahali dai ABunda ba'a rasa ba, har zuwa lokacin dawowar Hankalin Abbu ya nemi Abokinsa, Ammar BN Yasir da baƙin cikin Samun rasuwarsa da yayi, da halin da ya fuskanci ƴaƴansa Suke ciki, na maraici da takura a wajen Sa'adatu, shine fa ya bibiyi ahalinsa ya taimaka musu sosai, yaiwa Kawu Isma'il talala, da fayyacewa su AKEEL cewa ai suna da Aure dasu Hadiyyah da Hidayah. Da kuma dawowar su AKEEL gida Nigeria wanda shine ma farkon Fara labarin Alhaji tallafy da iyalansa ɗin, fa sauran Abubuwan dasuka gabata garesu. Hakana har sannan Jimmai tana cikin jiyya, kuma ko da wasa AKEEL da AQEEL ko AKEELA basa zuwa dubata, balle kuma ABBU sun ɗau zafi da ita sosai, Hakan yana sata tayi Kuka sosai,Babu bakin magana, kuma har sannan Babu duriyar Usman, yanacan yanacin duniyarsa da tsinke, ya cilla london Ƴan matan turawa kala kala yake mu'amala dasu, ga shaye_shaye da yakeyi na garari. Shukrah kam dai a unguwarsu jimmai ta samu salama ba'a tsangwamarta dan har ta koma school, kuma tayi ƙawaye da yawa, su sun zata Daddy ƙaninta ne,ganin Suna kama, shi ma Daddy an sashi school ɗin yazama ɗan Saurayi kamanninsa da Usman ƙara fitowa sukeyi,yaro dai kam har sannan an rasa ubansa abu kamar al mara🤔 To ƴan amana anan na kammala tarihin iyalan Alhaji tallafy kuma in Sha ALLAHU page nagaba zamu ɗora daga indai muka tsaya..... Shin AKEEL DA AQEEL zasu karɓi su HADIYYAH DA HIDAYAH ko ya abun yake? Ya Rayuwar Usman zata kasance? Jimmai mece makomarta Duk Suna sauran pages na gaba OUM ARQAM ce ontop 🥰 Aci gaba da gashi ƴan amana 4/23/24, 11:44 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Mallakar Rabiat Amin {oum ARQAM} 08128131163 Marubuciyar..... Komai nisan jifa Hakan ba kuskure bane ____________________ *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)* Kungiya ɗaya tamkar da dubu masu nazari da aiki da ilimi burin kungiyar a koda Yaushe shine ta faɗakar ta kuma wa'azantar ta nishaɗantar da masoyanta 🤙 ____________________ *PAGE FIFTY FIVE 55* Up Up Up Up Burin seerat da Aisha Sulaiman da MamaGee mmn Aslam Maman eyshat mummy Waleed yacika mundawo daga tafiyar dogon zangon da mukayi na saurarar Rayuwar iyalan Alhaji tallafy da gwagwarmayar da sukasha Yanzu kuma mun dawo inda Muke a labarinmu ALLAH yabani ikon kammala wannan labari lafiya Yasa ya Amfani al uma, kuskuren dake ciki ina roƙon ALLAH ya yafe mun🙏 _____BANGAREN SU ZAKIYYAH_______ Zama tsakanin Zakiyyah da Bilkisu sai sam barka,Duk tunanin da mukhtar yake na ganin bazasu zauna LAFIYA ba, Amma ina ita dama Bilkisu baya tunanin za'a samu matsala da ita, Zakiyyah yake tunanin kuma gashi CIKIN ikon ALLAH Tunda ta dawo Babu wata matsala da ta taɓa faruwa tsakanin su kamar da can Baya,yanzu Zakiyyah tayi Hankali da tunani burinta kullum ta kyautatawa mijinta mukhtar bataso taga tafi ABunda Ransa zai sosu ko ƙadan,shi kuma Hakan da takeyi shine yake ƙara ƙaunar ta a Ransa, Duk wannan tsanar da yai MATA ta Baya yanzu a Hankali Take gogewa, ko da Yake dama Halin Zakiyyah mukhtar yake ƙi ba wai ita kanta ba yanzu kuma Alhamdullillahi komai ya gyaru sai dai zaman tare wata rana dole a ɓatawa juna idan kuma aka nemi ya fiya da gafafar juna shikenan. ABIE ɗan gatan mamman(Zakiyyah) sa da Amminsa(Bilkisu) Kowacce yana son zama da ita, ita Zakiyyah bata ɗaukar sangartar da Bilkisu takewa ABIE shiyasa ma yafi Zama a can gidanta ,nan Babu faɗa balle hantara Duk abunda zaiyi bata mai magana, bawai abu marar kyau ba, ya rone mai kazar_kazar yadinga wasa kenan Yaje nan da gudu yafito nan ga haɗa kaya to ita Zakiyyah bata ɗaukar haka, Bilkisu me ɗauka haka take cewa lafiya ce da ƙuruciya idan ya daɗa wayo bazaiyi ba to barin da Bilkisu takewa ABIE yayi Hakan shine fa yake Masa daɗi yake zaman gidanta can. Tun bayan daidaituwar komaj tsakaninsu mukhtar dama tuni ALLAH ya buɗa Masa ƙofofin samunsa ga kuma kwanciyar Hankali da Yake samu wajen iyalansa, Suma su Zakiyyah ɗin Suna roƙarsa Akan ya haɗe su guri guda sukam zasufi jin daɗi shima kuma hankalinsa zai,kwanta idan yana zaune waje ɗaya, Duk da dai unguwa ɗaya suke sai tazara wacce batada yawa sosai, tun daga sannan shima dama yana burin Hakan, gidan kusa da Bilkisu ya siya ya shigar dashi gidan abunka da kuɗi cikin ikon ALLAH aka Fara ginawa, Bilkisu takoma gidan Zakiyyah dama shima gidan Babu laifi yanada girmansa, gini yayi nisa jiran haihuwar Bilkisu sukeyi kawai da zarar ta haihu zasu tare a sabon gidansu wanda aka kawatashi yayi kyau sosai,part ukune sama da ƙasa Kowacce nata daban sai turakar mai Gida da ɗakin ABIE shida ƙannensa masu zuwa haka ma an tanadi na mata tun da yanzu ALLAH yafara ba su haihuwar, Bilkisu kam ana jiran tsammani ciki ya shiga wata na goma ma Amma har yanzu sai fatan sauka lafiya, Zakiyyah ce takeyin komai a gidan Duk da Bilkisu tana cewa ta barta tayi itama. ______BANGAREN ALHAJI GAMBO____ Tun da aka Masa Allurar barci bayan zubewar cikin Sa'adatu sai da ya ɗau lokaci kafin ya farfaɗo, jininsa ya hau sosai, ALLAH ne ya taimaka paralyse bai kamashi ba,sai da aka bashi gado saboda ya ƙwallafa rai Akan wannan ciki gashi kuma ya zube, kamar ƙaramin yaro Alhaji Gambo da ya tuna sai Kuka,abun gwanin haushi gwanin tausayi,sai kiran Hajiya ikilima, da Hajiya suwaiba da kuma Hajiya sahura a waya ake gaya musu cewa Alhaji fa ba bu lafiya yana asibiti Duk fushin da suke da Alhaji Akan wulaƙancin da yadinga musu Akan cikin Sa'adatu da sukaji Babu lafiya sai da hankinsu ya tashi Babu shiri sukayo asibitin gaba ɗayansu, Halin da suka samu Alhaji Gambo aciki sai da Kowacce ta tausaya Masa ganin yadda a lokacin kaɗan ya zabge yanata uban Kuka, sai Kowacce tsoron ALLAH ya shigeta da tausaya Masa, saboda Kowacce tasan Zafin Rashin Haihuwa dashi suke fama har yanzu Suma, Alhaji yanzu ALLAH yabashi kuma ya karɓa, ALLAH buwayi gagara misali kenan yabada lokacin da bakayi tsammani ba hakana lokacin da zai karɓa ma haka, Sai Sannu suke wa Alhaji Suna bashi haƙuri Akan yadaina Kuka ALLAH zai kawo Wani ne da yardar sa. Alhaji shima kanshi nadama yake da kunyar matansa ta yadda lokacin cikin ya juya musu Baya yake musu hulaƙanci, Amma gashi shi yanzu bashida lafiya Duk sun damu, ALLAH kenan shiyasa a koda Yaushe idan zakayi abu ka dinga tunani da hankalin gaba. Sa'adatu tun bayan ɓarin da tayi mugun ciwon ciki ya sata a gaba sai da aka MATA wankin ciki, ko lokacin da su Hajiya ikilima sukazo wajen Alhaji tana can ɗakin da take jiyya,bayan sun gama da Alhaji da lallashi ya samu barshi, suka rarrafa zuwa ɗakin da aka kwantar da Sa'adatu domin su dubada,dan kam ganin abunda ya faru da Alhaji Da ita kanta Sa'adatu ɗin sai imani ya shigesu suka sauke Duk makaman yakinsu Akan Sa'adatu yanzu shukam sunga ikon ALLAH, Duk abunka da isarka da tinƙa wonka akwai lokacin yi daga Alhaji har Sa'adatu ɗin su kam su Hajiya ikilima tausayinsu sukeji ma, idon Sa'adatu biyu da suka shiga ɗakin sai Khadija a Zaune ta gaisar dasu, Sa'adatu dai baƙin ciki goma da Ashirin ga na ɓarewar cikinta ga na zuwan su Hajiya ikilima asibitin uwa uba ga na su Hadiyyah na samun mazajen nunawa Sa'a uwa uba ga siriki kamar Alhaji tallafy, Suna MATA ya jiki Amma ko kulasu batayi ba idanunta ta rufe ma, su sunyi Zaton barci ma takeyi dan haka suka fice zuwa wajen mijinsu. Da suka koma Alhaji Gambo ya tashi daga barcin dama barcin Rabi da Rabi ne,Suna ta Masa Sannu da nasihohi anan yake kenan gafararsu, Hajiya ikilima tace "ai Babu komai Alhaji, yanzu ta lafiyarka mukeyi kuma ƴaƴane muna roƙon ALLAH yabaka ma ba ɗa guda ɗaya ba! Cikin muryar ciwo Alhaji Gambo yace " ALLAH yabiye bakinki suwaiba yabamu masu albarka Kowacce acikin ku ban fiddau tsammanin samun rabo daga gareta ba. Duk murmushi sukayi sukace ALLAH ya tabbatar da Hakan Alhaji. Cikin ikon ALLAH a Ranar aka sallamo Alhaji daga Asibiti sai gida ranar girkin Hajiya ikilima ne dan Haka daga Asibiti gidansu sukayi dashi. Itama Sa'adatu an sallameta tayo gidanta,zuciyarta ba bu daɗi, wato Alhaji ita zai juyawa Baya ganin cikin jikinta Babu da ita yake zance,su zuba dagashi har matan nasa shege ka fasa. Tun bayan Hakan data faru Alhaji Gambo ya Zama mutumin kirki tsakanin matansa Kowacce yana mutinta ta, Suma kuma Suna faranta Masa shaɓanin Sa'adatu yanzu sai Wani Shan ƙanshi da wulaƙanci take Masa! Amma shikam yana kau da kai ya na rabuwa da itane. ______ HADIYYAH DA HIDAYAH_____ Sukam gaba ɗaya Hankalunsu ya ƙi kwanciya Kowacce bata son Abokin Rayuwar da aka haɗata dashi, saboda sukam akwai waɗanda sukeso Mus'ab da Mahmoud ,Amma za'a musu haka, a yadda suke ganin waɗannan ƴaƴan na Alhaji tallafy basu da mutunci musamman ɗayan ma,wanda har sannan Kowacce batasan wanenen nata ba,tunda kuwa sun san dai ƴaƴan biyu ne kuma ba'a ce ke ga naki ba kema ga naki su dai sun san sunan ƴaƴan AKEEL da AQEEL kuma AQEEL ne na HADIYYAH, shi kuma AKEEL na HIDAYAH amma kuma basusan su a zahiri ba ne hulaƙancin ne na wacce oho, Hakan ne Yake sasu cikin tashin hankali, ga kuma mutuncin Alhaji tallafy a idanunsu ta yadda yadinga kulawa dasu da sauran ƴan uwansu, shi dai bashi da damuwa ƴaƴan nasane sai a Hankali Amma ya suka iya haka zasu haƙura su bawa zuciyarsu haƙurin Hakan, Amma a fuskar ƴaƴan tun a Asibiti Suna ganin tsantsar Rashin yarda a idanun ƴaƴan, Amma sukam zasuyi biyayyah ga Mahaifinsu na Auren da yayi musu tun suna ƙanana kuma yana yare yanzu da Babu Ransa bazasu iya bujirewa umarnin mahaifin nasu ba, ALLAH sarki Zakiyyah tun Bayan da abun yafaru kullum sai ta Kira ƴan uwanta a waya tana Kwantar musu da Hankali Akan su Kwantar da hankinsu in sha ALLAH su AQEEL zasu so su, kar su farawa Alhaji tallafy butulci na ƙin ƴaƴansa,zuciyar su Hadiyyah tana Sanyi ganin ƴar uwarsu yanzu tayi Hankali ta zame musu kamar uwa, itama Zahra Hakan takan kirasu tai musu NASIHA, tanacan tana zamanta da IBRAHIM ɗin ta cikin kwanciyar Hankali harda rabo ma tuni ansamu,g Khadija a gefen su itama Yarinya ce me Hankali da tunanin kullum tana nusar dasu itana Amfanin da Abbiy yagani ya haɗa wannan Auren suyi masa biyayyah zasu gani a gaba da kuma alkhair ɗin Alhaji tallafy garesu,Hakan shine sanyaya zuciyar ƴan biyu, sai dai idan sun tuno ogannin nasu AKEEL da AQEEL sai zuciyar kowanne ya tsinke, Sa'adatu kuwa bata daɓa ce musu komai Akan Auren ba, ta fake da batada LAFIYA ne. Daga Hadiyyah har Hidayah Basu da aiki sai tunani, Hajiya Baabah mutan kaduna itama ya Kira tai musu murna da suka kasance ƴaƴan Alhaji tallafy ne abokan rayuwarsu a matsayinya na kakarsu itama tai musu faɗa Akan su Kwantar da Hankalunsu komai me shigewa ne ALLAH ne yasan meya ɓoye Akan wannan abu. ____GIDAN ABBU___ Harkokinsu sukeyi kamar yadda suka saba, Babu wata matsala, saɓanin twin's Amma su Abbu Suna sane Suna kula da yanayinsu suka yi burus dasu, musamman uban gayya uban ƴan miskilanci, ita kuwa AKEELA tana gidan kuma sai murna takeyi da batum da taji na waɗannan tsala_tsalan twin's ɗin sune matan yayyenta,da ma tun farko taji sun kwanta a Ranta ashe_ashe sai murna da farin ciki takeyi. Hakana itama Mommah, Abbu shima murnar yakeyi ganin su Hadiyyah Basu watsa Masa ƙasa a idanunsa ba na bujirewa abunda suka ƙulla shekarun baya,sune da ma abinji Amma su AKEEL da AQEEL nasu mai sauƙi ne Duk abunsu basa tsallake umarninsa sai agama ƙuncin zasu saukone musamman AKEEL uban ƴan barkwanci,ya kudircewa Ransa muddin su Hadiyyah sukace basaso za'a fasane, Duk da dai wannan abu bamai sauƙi bane dan kuwa yana son cikawa abokinsa amininsa kuma ɗan uwansa Ammar BN Yasir burinsa,to abun yazo da sauƙi alamu sun nuna sun Amince Kenan kukan ne kawai akayi shi. Yaune bayan sun kammala cin Abinci gaba ɗayansu Abbu, Mommah, AQEEL, AQEEL da AKEELA Suna zaune a falourn ƙasa Abbu ya ɗauko waɗannan vedios ɗin nasu AQEEL dasu HIDAYAH Duk Suna ƙananun Yara zai kunna musu su gani,bai gaya musu ba kawai dai yace zai musu suprise na wani abune,dan haka fuskar AQEEL da AKEEL, gatanan dai ne sauran kuwa fuskarsu wasai a sannan ABBU ya kunna vedio na farko............ Muje next page ƴan amana domin muji yadda zata kasance Gadaisu AQEEL anzauna za'a kalli vedios na ƙuruciya da soyayya da suka nunawa su Hadiyyah ko Hakan zai sauko da zuciyar su? Su kuma su HADIYYAH ko ta Yaya zasu ga masu vedios ɗin? Ya Kawu Isma'il ne wai? Ku Muje zuwa in Sha ALLAH komai zai warware Nice dai tamu oum ARQAM 4/25/24, 2:54 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Mallakar Rabiat Ãmin {oum ARQAM} 08128131163 Marubuciyar.... Komai nisan jifa Hakan ba kuskure bane ____________________ *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A* ____________________ _______WAI INA HAUWA DA KAWU ISMA'IL NE?_______ "Hauwa tana riƙe hannun meenal,idonta yayi ja jur itama ƴar ku ka takeyi, "mama kiyi haƙuri Kinga Abbanmu bashi da lafiya ki kemo ki kula dashi, yanzu Abba abun a Kula ne, saboda halin da yake ci....dan ubanki rufemun baki, ke in kinada Hankali kyaso na zauna da mahaifin naku,Zama dashi ai ƙaddara ce! Hauwa ta tari numfashin meenal haɗe da fincikar hannunta suna ficewa daga asibitin suna tsaida abun Hawa,ita dai meenal bata kuma magana ba,ganin maman tasu ta ɗau zafi dayawa, kuma da ma maman tana da haƙuri Abba bango ya kaita ne. Mota bata sau ke su a ko ina ba sai a ƙofar gidan Kawu Isma'il sauran yaran ta kwasa da ɗibi kayan sawar su suka ɗunguma Zuwa gidansu Hauwa ɗin. Basu dau Wani lokaci ba suka je gidan, malam mahaifinta ya na ƙofar gidan nasu,ganin halin da ƴar tasa take ga ƴaƴa ga kawa,kuma ko kulashi batayiba yadda ta saba idan tazo Hakan yasa yabi bayanta zuwa Cikin gidan. Goggo mahaifiyarta ta samu a Zaune Akan tabarma ta na lazimi da casbaha, ganin irin shigowar da hauwa tayi ya sa goggo katse lazimin ta fuskanci Hauwa wacce ta saki Kukan baƙin ciki, A sannan malam ya ƙarasa shigowa cikin gidan, "Ke kuma meke faruwa Zaki kamawa mutane ku ka kamar wata ƙaramar yarinya? Furucin malam Kenan Goggo tace" Babu Sallama fa kawai sai Kuka naji a kaina, badai Isma'il ɗin bane wani abu ya sa meshi ba? Inji goggo Antaɓawa inda Hauwa yake MATA ƙaiƙayi cikin ku kan ta zayyanewa iyayen nata abunda ke faruwa! Tana kaiwa ƙarshe kuwa Malam yace" a kan wannan abun Zaki baro gidanki kun Riga kun tara yara, ai saidai kiyi haƙuri, tun da ALLAH ya kawo ƙarshen lamarin Isma'il ɗin ai yanxu kuma shiryuwa yayi ta,sai dai akiyayi gaba,yanzu Isma'il ai abun a tausayawa ne a jiɓanci lamarinsa a Wannan Halin, haba Hauwa sai kace ba ke ba ke fa me tausayi ce, yanzu inkin rabu dashi a I dai uban ƴaƴanki ne ina kikeson ya jefa rayuwarsa,ko kun rabu baku rabu bane,dan haka ki share hawayenki haƙurin da nasanki dashi kije kici gaba in Sha ALLAH zakiga amfaninsa, nan itama goggo ta sa baki " ki koma Gidan mijinki yanzu ba sai anjima ba, kuma abunda nakeso dake banson ki hulaƙanta Isma'il,muddin kikayi Hakan baza kiga daidai na,yanxu in kinada Hankali sai ki tantsi ƴaƴa ki tawo Mana dasu nan, mahaifin nasu kuma fa?kinsan tsarin malam gidansa ba'a yaji,nan dai Malam da goggo suka yiwa Hauwa NASIHA Akan zaman ta da kawu Isma'il shiyafi alkhair gareta Akan zaman gidan, da kuma yanzu ai shi abun tausayi ne, ba don son ran Hauwa na ta juya ta koma inda ta fito, zuciyar Hauwa Babu daɗi, Amma ina tanada haƙuri ga kuma biyayyar iyaye. Gidan Kawu Isma'il ta koma, bata koma a Asibitin a Ranar ba sai su Meenal ne Suma koma, zuciyarsu shar Mama ta dawo gidansu. ______Tun bayan watsewar kowa daga asibitin, da tafiyar Hauwa,bayan likitoci sun kori ƴan jarida da sauran jama'ar gari ƴan kallo, kawu Isma'il abun duniya ya isheshi zuciyarsa kamar zata fito waje,ga tozarci gashi Hauwa ta gujeshi, shikam ina zai saka Ransa, "Wannan wacce Irin Rayuwa ce ni Isma'il ta sameni? Na rasa Abubuwa da yawa kuɗin da nakewa yanzu Babu, kuma Babu mai tausaya mun tunda jama'ar gari sunsan ABunda na aikata! Allahu ka yafemun kasanya tausayina a zuƙatan al uma! Banking da Kawu Isma'il ya ciyu Bashi Lokacin da ya ɗiba zai biyasu kuɗin su yayi Harda kwanaki ma, ga jaridar da aka fitar ta Wannan satin maudu'inta akan kawu isma'il ne da duk abubuwan da ya aikata na zamba da munanan ɗabi'unsa duk an zayyana su ajiki, Aikuwa kunsan dai banking basa ASARA, takanas har gida suka kawo Masa sammaci Akan Suna buƙatar maƙudan kuɗinsu a yanzu ba sai gobe ba,sai suka tarar da Gidan nasa a kulle,suka tambaya kam akace musu ai mai gidan bashi da lafiya yana asibiti suka tambayi asibitin Babu ko tausayi ko imani, ko da Yake ina banking yaga imani shida ko mutum yana kwance an Masa suttura kafin akaishi makwanci sai an biyasu bashinsu kafin a binne mutum. Hannunka Baya ruɓewa ka yanke ka yar Zakiyyah da Zahra dasu Khadija duk suna zuwa wajen Kawu Isma'il su zauna dashi a Asibitin ko zaiji daɗi,Duk da karayar da yayi ta Fara warkewa Amma ba'a Fara koya Masa tafiya ba, muddin yaran zasu zo Kawu Isma'il ya dinga sunkuyar da kai Kenan alamun kunya.suna kula da halin da yake shiga a Duk lokacin da sukazo Duk da ko daɗewa ba'ayi da faruwar al amarin ba. Yau Babu wanda yazo daga su meenal sai Hauwa wacce bata shiga harkarsa biyayyar iyaye ce ta dawo da ita gidan Kawu Isma'il ɗin, shi hakan ma yayiwa Kawu Isma'il daɗi tun daa dai ta dawo ai shikenan, yau da gobe ai tafi karfin wasa zata sauko ne. Kawu Isma'il yayi shiru abun duniya ya isheshi,kawai yaji sallama ba sai an faɗa ba yasan Ma'aikatan banking ne, jikinsa ne ya Fara! rawa sai yanzu ya tuna da bashin baking dayaci, Basu kula da halin da yake ciki ba, suka miƙa Masa takarda ta neman kuɗin su nan da kwana uku idan ba hakaba za'ayi gwanjen gidan da Yake ciki, dan kuwa shi kadaine yanzu kadarar sa, kadarorin ya zuba oda ga yadda ta ka ma, sauran kuɗin kuma nasu Hadiyyah ne Kawu Isma'il ya karɓe dukiyar marayun ALLAH zai kula musu da ita ba bu gara ba bu zago. Wayyo Kawu Isma'il yabani tausayi matuƙa, ƴaƴansa sai Kuka suke, Hauwa kuwa ba'a san a wane halin take ba dan fuskarta Babu yabo Babu fallasa, numfashin Kawu Isma'il ɗaukewa yayi dan bala'in da bakin cikin da ya shiga, Babu shiri aka Masa taimakon gaggawa,har da su oxygen, sai da ƙar ya farfaɗo, ALLAH sarki Hauwa MATA da miji sai ALLAH, Hakan ce ta kasance da ita, kalamai masu sanyaya zuciya da kwantar da hankali ta dingawa Kawu Isma'il Akan yayi haƙuri, ALLAH ya soshi da rahma da yayi Masa haka tun a duniya, dan kuwa da anje lahira abun bazai kyan gani ba,dukiya da Haƙƙin maraya bala'ine babba, wannan yana sanyaya zuciyar Kawu Isma'il duk da dai Babu daɗi ace masifa kala kala daga Wannan sai wannan! Kwana uku tsakani kuwa banking yayi gwanjon gidan Kawu Isma'il, Amma ina kuɗin da Suke binsa yanzu, gidan bai biya ba, duk da haka jira Suke ya samu sauƙi ya Basu ragowar kuɗinsu ko kuma su kaishi prison, duk wanda yake jin haushin Kawu Isma'il Akan abunda yayi sai da ya tausaya Masa balle me ƙaunar sa, yanzu dai ina dukiyar dayake taƙama da ita? Ƙadan daga cikin masifar da take samun mai cin dukiyar maraya kenan, matuƙar bai nemi gafararsu ba, kuma ya dawo musu da dukiyarsu wacca yaci ba, abu goma da Ashirin f Ga kuma cin amanar zumunci da yayi. ALLAH ya tsare mu cin dukiyar maraya da cin amanar zumunci. _________ AKEEL DA AQEEL_________ "Tun da Abbu ya kunna Vedios ɗin Babu wanda yai motsi cikinsu kowanne da abunda Yake saƙawa a zuciyarsa, Amma idan sukace Vedios ɗin Baya burgesu ko kuma bai ba su nishadi ba ƙarya ne, su Abbu da AKEELA da Mommah Babu abunda suke kwasa sai dariya, ganin yadda su AKEEL da AQEEL lokacin Suna yara yadda kowanne Yake burin ace ƙanwarsa tafi ta kowa,da Duk Wani shirme da suka dinga yi akansu Hidayah ɗin,ga ƙaunar da aka zuba musu tun da ƙuruciya sai kace wasu manya,har lokacin da suka ɗan tasa Kowacce burinta ta Bawa yayanta abunda ta sai kace wasu manya abun gwanin dariya! Jin dariyar su ABBU taƙi karewane Yasa Babu shiri mai gayya mai aiki wato oga AQEEL ya tashi cikin sauri yabar falourn jin dauriyarsa ta ƙare,shima AKEEL kamar jira yake yabi bayansa suka bar su Abbu a flourn to dama Vedios ɗin ya ƙare,suka bar su Mommah baki a sake haɗe da kunshe dariyar da sukeyi. ABBU yace ƙyale ƴan wofi mu mukayi farin ciki da ganin wannan vedios ɗin balle su ma,zasu gama abunsu ne, haka Abbu ya haɗa kashe kayansa kowanne yashige wajensa suna kwasar dariya. AQEEL da AKEEL kuwa Basu tsaya a ko inaba sai daƙinsu AKEEL ne yafara dariya da kuma cewa " bro kalli wani abu sai kace a shirin film ko a Novel wai ni dakai ne Muke wannan show ɗin,lallai ne dole su Abbu suyi Vedios ɗin nan, yana dafa kafaɗar AQEEL yana ƙarashe maganar! Shi dai AQEEL bai magana ba sai dai murmushin da yakeyi a daidai lokacin, yana Zama a kujerar da ɗan uwansa ya zauna, "abun nan bro Nima yabani mamaki sosai,wai mune Muke Wannan abu KAMAR wasu manyan Samari kai ALLAH ya shiryamu fa, ai dole su ABBU su yanke Mana hukuncin Aure ya ƙarasa maganar ya na murmushin gefen baki, jin ABunda AQEEL yace ya daɗa sa AKEEL dariya, haɗe da cewa "musamm kai sai kace irin wannan ƙaton saurayin nan,kanayin abu Cikin gadara da taƙama kai dama,bro haka kake tun asalinka, Ashe abun naka gaba yayi ba bayaba! ALLAH ya shirya ka kai dama tun Asalinka kai mai izza ne da gadara, ga maganinka nan Abbu yayi Nima ka zanyo min Aure tun bansan mene shi ba, gwanda ma kai ai dama da sonsa ka ta......Duka AQEEL ya kaiwa AKEEL a Baki yana shigewa toilet yabar AKEEL yana kwasar dariya abunshi. Tun da yashiga toilet vedios ɗin nan yake dawo Masa na rayuwar ƙuruciyarsu suda waɗannan yaran,wani abune yaji yana shigarsa game da hakan a haka ya kammala abunda zaiyi ya fito daga toilet ɗin. Inda ya bar AKEEL anan ya sameshi a Zaune shima ya faɗa duniyar tunani "lallai wannan abu da mamaki yake ni dama yaran nan suna burgeni ashe dama da alaƙa TSAKANIN mu! Ikon ALLAH! Zama kusa dashi da AQEEL yayi shine ya dawo dashi daga tunanin daya lula" "Bro ganin vedios ɗin nan danayi ya Sanya nafara jin Wani abu game da yaran nan,Amma kuma bansan wacce daga ciki tawa ba? In dai wannan me surutun ce ai kuwa Kullum wannan bakin saina Masa hukunci kasan abunda banso kenan! AQEEL ya faɗa yana ɓata fuska! "Kayi ta tawa Kenan bro Nima dama suna burgeni kasancewar su twin's kamar mu,ga kuma halin da suka tsinci kansu, Amma Nima idan wannan me shiru shirun ce Nima ALLAH bazan ɗauka ba dole ta koma kamar ni,banson mutum ya zauna kamar dutse,nan dai sukai ta tattaunawa tsakaninsu abun gwanin sha'awa kowa yana faɗar albarkacin bakinsa. Tun daga sannan kuma sukeson ƙara ganin wannan vedios Amma ina! Ai da kunya su tunkari Abbu, mutanen da suka nuna basason Hakan, Kowacce hanya sunbi ko ALLAH zaisa su ga flash ɗin a inda Abbu ya ajiye Amma ina! _______GIDANSU HADIYYAH______ Ko ƙadan Basuji daɗin abinda ya faru da kawu Isma'il ba,kuma har jaje sukaje suka Masa,hakama su Zahra kai abun yaiwa Kawu Isma'il Zafi fa, yaran da yaso ya wulaƙanta su sune suke kulashi,har ita Zahra tagayawa Ibrahim hakana itama Zakiyyah ta faɗi ma mukhtar ALLAH ne yasan me zasu Masa. Alhaji fa andawo daga tallafy foundation anzama Saurayi sosai ga Hankali kai bakace shine ba a shekarun Baya ba, yadda rayuwarsa taso gurɓacewa,ya sauke al Ƙur'ani mai girma ga sauran littattafai abun gwanin sha'awa,ha Sana'a daya koya ta gyran kayan wuta,waya, computer,fanka,tv kai cikin ikon Duk Wani abu wanda yake amfani da wuta zai iya gyarashi, kuma Duk a tallafy foundation ya koya, kowacce Sana'a ana koyawa sai wacce kaga damar koya,saboda haka ma Alhaji tallafy ya ɗau nauyin karatun Alhaji wanda zai karanci electrical engineering a China in sha ALLAH. Gida ya kacame da murna da dawowar Yaya Alhaji, barinma abokan wasa Hadiyyah da Hidayah Duk da dai har sannan walwalar su sai a Hankali. Tun bayan tafiyar Alhaji foundation da Abubuwan da ya faru dabayanan sai da Alhaji yaji labarin, yayi murna da mutuwar Auren Aunty (Sa'adatu) da kawu) sannan kuma yayi murna da yaji labarin ai ƴaƴan Alhaji tallafy sune mazajen su Hadiyyah sai tsokanarsu yakeyi, dayaga basa so kuma sai ya koma nasiha,da nuna musu cewa fa ƴaƴan Alhaji tallafy Basu da matsala sun gaji halin Mahaifinsu bazasu wulaƙantasu ba in Sha ALLAH,saboda suna Zuwa foundation lokaci Zuwa lokaci kuma basa wulaƙanta mutane,har sannan dai Hankalin su Hadiyyah bawai ya kwanta da su AKEEL bane kamar yadda kowa Yake karfafa musu gwiwa,ganin Alhaji bazaiji daɗi ba idan Basu sake ba yasa suka sake kamar sunji nasihar ta sa,Hakana yaji Auren Aunty (Sa'adatu) da Alhaji Gambo, wannan kam sai da ya canza fuska, Amma bai magana ba ,haka yasa Hira kafin Yaje ya wuta. Sai da suka keɓe da Auntyn tasa sannan yai magana "haba Aunty har yanzu bazaki daina haka ba mijin Hajiya ikilima fa Kika aura alhalin ƙawarki ce,baki ga Auren ki fa Kawu yadda ya zame miki a ha...... Ya isheka ai ka dawo banson jin Kowacce magana daga bakinka idan ba hakaba zan saɓa maka wlh, cikin fushi Sa'adatu tai maganar" wanda dama cikin baƙin cikin Alhaji Gambo take tun bayan sallamarsa daga Asibiti, ga na su Hadiyyah kuma shine shi kuma yanzu zai zo ya ƙara MATA wani" "ALLAH ya wuci zuciyar ki Aunty cewar Alhaji yana barin ɗakin haɗe da yiwa mahaifiyarsa Addu'ar shiriya dan kuwa har yanzu da sauran ta , lallai Alhaji yayi Hankali da tunani in da da ne ai da tuni ya mayar MATA da magana, Tallafy foundation kenan ALLAH yasakawa Abbu da alkhair akan Samar da wannan cibiya, mai ba da tarbiyyah da taimakon al Umar musulmi musamman marayu. Yaushe Sa'adatu zatayi Hankaline da tunani, ai ko ganin ɗan ka ya Zama nutsatstsen yaro ga sana'ar sa a hannu ai ya isa kayi Hankali ka sauke kome ke kanka,dan kuwa ai da tuni ya zama ɗan daba. Alhaji bai zarce ko ina ba sai ɗakin su Hidayah,domin acigaba da hirar yaushe gamo, Duk da Ransa Babu daɗi Akan abunda Aunty tai masa,ganin ƴan uwansa yasa ya Mance Duk wata damuwa tasa, ACIKIN hirar sune ma ALHAJI yake cewa "sisters zan shigo ɗakin Abbiy, naji yana faɗawa Kawu, Duk da akwai ƙuruciya sosai gareni lokacin,sai na fasa shigowa na tsaya naji "Akwai wata jaka Isma'il acikin ɗakin nan waje kaza, lokacin yana Rashin lafiya,kafin akaishi asibiti yacewa Kawu dan ALLAH ya Adana Masa ita, yasan wannan cutar ba ta tashi bace, idan yaransa sun girma yanaso ya Basu ita, to tun daga sannan zancen jakarnan yake raina,har ALLAH yaiwa Abbiy Rasuwa, Ganin Aunty da kawu sun jone wai shine zai aureta, da irin zaman da suka Fara tsakaninsu Babu tausayawa gareku, Aikuwa naji Kawu Isma'il yana gayawa Aunty wai Abbiy yabashi wata jaka shi har yau bai duba ba Amma may be takardun wasu kadarorin ne aciki, ai kuwa sai Aunty tace yakamata kawai ka duba kagani idan yaso sai muyi kashi mu Raba ni dakai tun da Babu wanda yasani,sai da ƙirjina ya buga Lokacin! ALHAJI ya faɗa,banyi wasa ba,dama ɗakin Abbiy Kawu Isma'il yake ciki bai kulle ba yafito ɗakin Aunty cikin ikon ALLAH kuwa na haura sama inda Abbiy yagawa Kawu Isma'il nan kuwa nake ma duba sai ga jaka,na mayar da komai Yadda yake na fito, sai daƙina da ita,anan nai MATA kyakykyawan ɓoyewa yanzu haka inason muga ko mene aciki! ALHAJI yanakai nan a zancen ya ya saki murmushi,su dai su Hadiyyah jikinsu Duk yayi Sanyi jin wasu kuma Abubuwan da kawu ya shirya wanda asirin bai tonu ba sai da Alhaji ya dawo, Hadiyyah take "shikenan bro Amma ba yanzu ba sai ka kuma wutawa! Yadda kikace haka za'ayi ƴar kanwata,yasin ƙarya kakeyi na girmeka! Cewar Hadiyyah cikin tsiwarta dama ALHAJI tsokana tashi faɗar Hakan. ALHAJI yace tun lokacin dana fuskanci Kawu Isma'il baiga wannan jaka ba, matsala ta Fara faruwa tsakanin Aunty dashi,ita tana tunanin ya salwantar da dukiyarne, shikuma yace MATA ai bai ban gantaba,ni kuma dama ga baƙin cikin danake ciki ga wannan yasa ni a halin dana tsinci kaina Amma Yanzu kam ai sai labari in Sha ALLAH Bayan wuya sai daɗi sister's ɗina..... Tofa ƴan amana!!!! Muje dai zuwa next page dan muji yadda zata kasance, Amma fa nasha typing yau wayyo🤧 ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 5/7/24, 3:00 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM} 08128131163 Marubuciyar Komai nisan jifa Hakan ba kuskure bane ____________________ *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A* ____________________ *PAGE FIFTY SEVEN 57* _______WAI INA USMAN NE?_______ ___Usman Kowacce mace mu'amula yake da ita, Babu ruwansa da yarinya ko babba,indai ya taya aka siyar Shikenan,Ance zara bata barin dami kuɗin da yakewa MATA bushasha dasu sun tasamma ƙarewa, harka kenan zata dakata, farkon zuwansa UK da ma barikince ta kaishi ba Wani abu ba dan Hakan ƴan Homosexual (ƴan neman maza) suka kawo Masa tayi Amma farko yaƙi amincewa, kuma ba ƙaramar dukiya zai samu dasu ba, Yanzu ganin Babu kuɗi saboda shi harkar MATA yakeyi, Hakan kuwa akayi sai ga Usman tsundum a harkar neman maza, idan yasamu kuɗin kuma sai ya nemi MATA dasu, innalillahi wa Inna ilaihi rajiuun Abun Usman gaskia yayi yawa, bayan bin maza da MATA harda Shan giya, Haka Yake fantamawar shi, kwata kwata ya manta da rayuwar mahaifiyarsa da ƴar ƙanwarsa wacce ya cuta ya barta da miki acikin zuciya, balle wata Akeela kuma. Yajima da wannan harkar, matsalar da ya Fara fuskanta itace ta ciwon ciki mai tsanani kamar ze mutu daya ziyarci asibiti akace hantar sace ta Fara kamuwa da ciwo, hankalin Usman ya Tashi sosai, Amma doctor ɗin ya Kwantar Masa da Hankali akan in yanashan magani kuma yana kiyaye dokokin da aka gaya masa zai warke ragal,to amma Usman ya Riga yai mugun sabo da Shan giya ya kasa daina Sha,a haka fa yake rayuwarsa, sai abu na biyu riƙewar Baya da ciwon kai mai tsanini ma bari ɗaya, inda nan ma doctor yace Masa Homosexual da Yake ne yasa Masa Hakan,idan bai dai na ba nan gaba tashi ma zai daina,kuma sexual infection zai kama Shi,wanda al aurarsa zata samu rauni da matsalolin da zai fuskanta a ɓangaren mu'amular sa da MATA, bincike ya nuna yana yawan mu'amula da mata kuma mabanbanta ,kuma Baya kare kanka daga haka! Duk bayanin da doctor yakewa Usman yanaji hankalinsa ya tashi sosai,to amma kuma gaskia bazai iya rayuwa Babu mace ba,nan Doctor yabashi SHAWARA Akan kawai yayi Aure ya zauna da iya matarsa, ko kuma ya zaɓi mace ɗaya ya dinga mu'amula da ita,sannan homosexual yadaina yi saboda jijiyoyin al aurarsa sun Fara sanyi nan gaba akwai matsala . Usman Ya bi maganar doctor ta xama da mace ɗaya ,wata baturiya mai suna clara, ta maƙalewa Usman dan kuwa Usman irinta ne yana MATA abunda yakeso, takeso,kuna jarumine kamar yadda clara take faɗawa Usman, dama hakane yasa ta amince da Zama dashi, dan kuwa da kuɗi a hannunsa, ya mallaki Abubuwa da yawa ga dukiya, nan Usman yaci gaba da Zama da clara ita kaɗai, Shan giya ma da ya ga ciwon ciki yana so ya kashe shi sai ya daina sha yafara jin sauƙi, Homosexual ne dai bai fasa ba saboda anan yake samun kuɗi idan suka ƙare fa. Matsalar da Usman ya Fara fuskanta da clara itace ƙorafin ita gaskia bashi da lafiya Baya gamsar da ita, shi kansa Abun yafara damunsa Akan Rashin jimawa,ga Wani ciwo da Yake damunsa mai tsanani a gabansa, yai tunanin hakan ne yasa Baya jimawa, Yaje wajen doctor yai Masa Bayani, inda yace Masa Homosexual ɗin da yakeyi ne yasa Masa, hakan kuma idan bai Dena ba nan kaɗan wajen zai samu raunin da yafi na da ma, hankalin Usman ya Tashi haka yadawo gida da tulin magunguna. _____SU HADIYYAH DA HIDAYAH FA?___ Haka ALHAJI sai da yayi wajen sati biyu, sannan ya ɗauko wannan jakar, Sa'adatu batasan wainar da ake toyawa ba, dan yanzu ko kula yaran bayi takeyi ba har ALHAJI shima haushin sa takeji, dan Haka ma Duk budurin da akeyi bata sani ba. A ɗakin su Hadiyyah aka buɗe jaka, kunsan mene aciki🤔 ba komai bane illa wasu flash sai kuma wasu takardu wanda su Hadiyyah basusan ko ma mene ne ba! Dan haka takan takardun suka bi in da ALHAJI yace zai karanta a fili kowa yaji kamar haka zuwa ga Ƴaƴana ƴan biyu Hadiyyah da Hidayah...... Nan dai ALHAJI ya karanta musu Duk abunda takardar ta ƙunsa, ba komai bane illa yadda aka Ɗaura musu Aure dasu Akeel kamar yadda Alhaji tallafy ya faɗa musu, sai nasihar da yai musu, na Masa biyayyah Akan Auren, domin kuwa nasan wannan ciwon bazai barni ba nakai har lokacin da zan gaya muku komai ba basuyi mamakin Hakan ba,da ma ai sun yarda da abunda yafaɗa da kuma Kawu Isma'il shima, sai kukan kewar Abbiy da sukayi sai suka ga kamar a gabansu, Wannan flash ɗin ba kowa bane illah ku dasu Akeel da irin soyayyar da suka nuna muku tun ƙuruciya, nasan in Sha ALLAH zai faranta ranku, kusan cewa ba mu haɗa ku Aure ba sai dan mu karfafa Amincin da ke tsakanin,kuma kuma in sha ALLAH zakuyi alfahari da Hakan, ALLAH sarki su Hadiyyah sai suka ga kamar yanzu Abbiy yake maganar, kawai flash sukeson gani,gashi yanzu Basu da TV, nan ALHAJI yace bari ya fita wajen abokinsa Imran ya karɓo laptop ɗinsa,aikuwa yai Sa'a yananan dan haka Babu wata damuwa ya ara Masa dai gashi yadawo! "Vedio na farko da su Hadiyyah suka Fara kalla na dambarwar da akasha tsakanin Akeel da Aqeel ne na yadda kowanne Yake Bawa ƙanwarsa kulawa,sai ga su Hadiyyah suna dariya da shewa wacce sun manta rabon da suyi irinta,Hakan har ya damu Sa'adatu wacce take can ɗakin ta, ci gaba sukayi da kallon vedio bayan vedio, sun samu nishaɗi sosai Amma kuma Kowaccen su zuciyarta tana waswasi Akan abokin rayuwarta dan kuwa, sunga yadda su AQEEL suka canza da da da Yanzu ba ɗaya ba Amma sun barwa ALLAH komai shine Zai shiga lamarinsu akai! "Lallai su Hidayah Irin Wannan nuna soyayya haka nasan Yanzu soyayyar da Za'a Sha sai tafi ta da dan Yanzu anyi hankali!cikin tsokana ALHAJI yayi furucin yana kallon ƴan biyu, aikuwa ko wacce ta russunar da kai suna dariya ƙasa ƙasa, Hadiyyah ce tace" kai wai me yasa baka da kunya ne ALHAJI mu fa yayyenka ne kake faɗa Mana Hakan" cikin tsare gira Hadiyyah ke zancen! Nan ba dambarwa ta kaure tsakaninsu ALHAJI yana shine babba dan kuwa akwai shi da son girma, Alhalin yasan sun bashi watanni ƴan biyun! Ƙara hayamiyar ne yasa Sa'adatu fitowa daga ɗakinta zuwa wajensu rai a ɓace! "Wannan wane Irin iskanci da hulaƙancine Zaku mayarwa mutane gida kamar na mararsa Hankali! Duk sai suka shiga taitayinsu kuma, shi ALHAJI ya fice zuwa mayarwa da Imran laptop ɗin sa jikinsa a sanyaye,dan kuwa bayajin daɗin Hakan tun da yadawo yaga Aunty kamar batason dawowarsa ne ko me? Ta juya tanawa su Hadiyyah kallon banza! Tana kallon jakar dake gefensu, dan kuwa ta tunata, wacce take tunanin Kawu isma'il ya salwantar da ita, "wannan jakar fa nan sukayi mata bayan abunda jakar ta ƙunsa jikinsu a sanyaye, sai taji zuciyarta tayi Sanyi jin ashe isma'il dagaske Yake ɓata tayi, tayi alwashin cin uban ALHAJI idan ya dawo,wato ita zai wulaƙanta Akan jaka ya ɗauke ya ɓoye, to abunda Yake tunani ba shi bane ai ɗan banza marar mutunci, cewar Sa'adatu acikin zuciyarta,kafin ta fice abunta,ko ta tambayi ina takardun ta karanta,ko itama abata flash ɗin tagani. Hakan yabawa su Hadiyyah mamaki matuƙa! Akan wannan Hali na hulaƙanci da Shan ƙamshi da Aunty take musu, tunda tasan wannan zancen, fans Nikam nace musu hassada ce ai tasa ta Hakan🌝 ,abun suka yakice. Wani nishadi su Hadiyyah suke Ganin wannan vedios ɗin, da kuma mantar dasu baƙin cikin da su Mus'ab da Mahmoud suka sanya su,Duk da ɓangare guda akwai tausayawa kansu da sukeyi in suka tuna dasu Akeel da yanayin da suka shiga tun jin su matansu ne tun da jimawa. _______GIDAN MUKHTAR_____ cikin ikon ALLAH! ALLAH ya sauki Bilkisu lafiya inda ta Haifo baby gil, me kama da ABIE sak, wanda dama mukhtar suke kama dashi Kenan,daidai lokacin da an kammala ginin gidan da zasu koma ansaka komai na more rayuwa aciki, dan haka suka koma gidansu da sabuwar baby kamar yadda ABIE yake kiran babyn dashi. Babu wanda yakai Zakiyyah murna, tunda akayi haihuwar bata zauna ba tayi wannan tayi wancan, kai bakace Zakiyyah bace 🤔 Husna ƙanwar Bilkisu ita ce zatazo ta zaunawa Bilkisu saboda aiki Amma fa fur Zakiyyah taƙi tace Husna tayi zamanta ita me takeyi, Amma Duk da haka sai da baba kulu kakarsu mukhtar tazo ta zauna a wajen Bilkisu saboda wankanta da na Baby, kunsan dai Halin Zakiyyah bata iya wankan babyn ba ita ma 😅, wannan abu da Zakiyyah tayi ya ƙara MATA ƙima a idon mukhtar wanda dama tuni ƙimarta ta dawo, haka ma wajen maama(Hajiya jameela maman mukhtar) wacce da Zakiyya ta fice MATA a rai,Amma tun da yadawo da yadda tayi Hankali sai komai a Hankali ya dinga fita daga zuciyar Maama najin haushin Zakiyyah da takeyi,na ɗiban albarkar da tai MATA lokacin barowarta gidan mukhtar🤗 A Hakan gidan nasu Kullum da mutane masu zuwa ganin sabon gida da kuma barkar baby, ABIE yafi kowa murna da wannan, yaita jagula babyn, Bilkisu bata cewa komai Amma da zarar ya taɓa ta Zakiyyah tana wajen lallai nan zakiga yadda ake ƙuli_ƙuli da ABIE🤣, dan haka indai Zakiyyah tana wajen Baya kula babyn,saboda yasan Hali maganin kar ayi kar a Fara. Bilkisu tana jin daɗin Zama da Zakiyyah, wacce dama ita ma tun farko bada Wani abun ta shigo gidanba, halin Zakiyyah ne kawai ada Yanzu kam sai sam barka. Mukhtar yabawa Bilkisu zaɓin sunan da za'a sanyawa baby, ko ɗar Babu Bilkisu tace ita kam sunan babyn ta *ZAKIYYAH* mukhtar baiyi musu ba yai MATA kutuba da Hakan, kuma yaji daɗi sosai ganin matansa suna zaman amana Irin Hakan, Zakiyyah tafi kowa murna da wannan abu da Bilkisu tai MATA na kara, ta kuma sanin lallai Bilkisu Mutuniyar kirki ce, taji daɗi sosai! ABIE sai murna take yafara kiran babyn da little Mammah, kuji me wayi fa fur ya hana a canza MATA suna, sai sunan da Yake kiran mammahn tashi ta asali da shi, ya su Bilkisu suka iya haka suke kiranta dashi Suma ko suce Mammah ko little ɗin ki su haɗe kamar yadda ABIE yake faɗa🤩. Hajiya Jameela tana jin sunan baby tasan Lallai Zama yayi Dadi da Zakiyyah da Bilkisu wanda shine burinta ,ko dan kwanciyar Hankalin ɗan ta, wanda abaya bai samu ba. rainon mammah a wajen Zakiyyah yake indai ma mama zata Sha ba takaiwa Bilkisu ita, Hakan baiwa ABIE daɗi ba domin Baya sakewa ya taɓa Little in tana wajen Zakiyyah. Tuni aka saks ABIE a school dayake yaro ne mai wayo, nan danan da anyi karatu ya ɗauke. _______AKEEL da AQEEL____ Ƙaramar magana ta Zama Babba, Duk su biyun burinsu su mallaki wannan vedios ɗin, su sake kalla shine burinsu, shi AQEEL yana da dauriya dama kun sani, ba lallai a gane meke damunsa ba, Amma shi ma AKEEL Ba bu bai iya ɓoye ɓoye ba, yaga abun kullum gaba yakeyi dan haka, yace 'nidai bro kafini taurin zuciya da ɓoye damuwa, Nikam bazan iyaba yau zan wa Abbu maganar ya mallakamun flash ɗin nan inason ƙara gani, saboda ai dama namune mu yayi wa, kaga ya AJIYE a gurisa ai Babu amfani" tun da AKEEL yake magana AQEEL ya kafeshi da idanuwa, daga ƙarshe yace " tab Nikam bazan iyaba, Vedios ɗin me wannan shirmen ni fa har na manta da shi ma(kuji ƙarya fans,mutumin da kullum tunanin su yakeyi) ALLAH yabaka Sa'a sai kai ta karɓa, Nikam bazan iya ɓata lokaci na ba! Kamar gaske ya ƙarasa maganar yana haɗe Rai, " ai shikenan Nikam sai na kalli abuna mi kaɗai, kaishi zanyi ma Amayar mun dashi a turan ta waya ta kawai,cewar AKEEL ya zata da gaske AQEEL yake, nan kuwa baisan gwamma shi da shi ba ma Akan zaƙuwar samun vedios ɗin. Hakan ce tafaru da AKEEL bayan sun gama breakfast Duk Suna dining ɗin, Akeel yace"Abbu inason kabani flash ɗin nan nakai Amayar Mana dashi na waya inason ƙara kalla yana sani nishaɗi,Me AKEELA zatayi in ba dariya ba,haka ma Mommah jin abunda ɗan ta yafaɗa iya gaskiyar sa, dan dama shi Baya ɓoye ɓoye, gogan naku wato AQEEL ko motsi " kai yanzu Akeel sai kace kanason ƙara ganin wannan vedion,wanda naga baku kalla da muhimmanci ba, inji Abbu cikin muryar barkwanci yana kallon Akeel ɗin, Amma reaction ɗinsa yana ga AQEEL yaji ko shima zai ce yanaso amma sai yaji shiru". Ea gaskia Abbu inason ƙara gani sa yai mun kyau! To Shikenan ka kwantar da hankinka zan sa a mayar dashi Vedios na waya sai na sa atura maka,tun da kai kadaine me buƙata, shi Dan uwanka bayaso, " ea gaskiya Abbu mene abun ƙara kalla a Wannan vedios ɗin, shi ma AKEEL ne da bashi da aikin yi, AQEEL yai wannan maganar yana tashi yana barin dining ɗin, alamun ko ajikinsa, kuma bai damu da vedios ɗin ba, Amma cikin Ransa yafi kowa son ƙara gani😄,daga Abbu har Mommah bakinsu a sake take jin furucin AQEEL ɗin, haka na AKEELA me dariya sai ta ƙunshe kayarta, shi kam AKEEL sakato yayi yana bin bayan AQEEL da kallo! Shikenan AKEEL je ka zan baka kai kaɗai, ka rabu da ɗan uwanka mai bauɗaɗɗen Hali,shima yana so ne na Sani,kawai halinsa na miskilanci zai hanashi tambaya, haka suka watse a dining ɗin. AKEEL sai da yaiwa AQEEL magana Akan abun da ɗa zu yayi, aikuwa sai yace "bro ƙarya zanyi to bana buƙatar vedios ɗin ai! To Shikenan ai ni inason ganin abuna yana sani nishaɗi. Aikuwa a Ranar Abbu yacika alƙawari aka yiwa AKEEL editing nasa, yana zaune yana kalla yana kwasar dariya, Amma su AQEEL ya basar kamar besan me yake kalla ba,idan anzo wajen AQEEL da HIDAYAH sai yace "bro kallu show ya wuceka,Amma ina sai AQEEL yace 'kaine baka da aikin yi ai,Amma a zuciyarsa yana son gani, da zarar AKEEL ya ajiye wayar ko shigo bayi ko da daddare zai buɗe wayar AKEEL ɗin,yasan password nasa,me zasu ɓoyewa junansu, komai nasu tare sukeyi, ya kalli vedios ɗin yana nishaɗi, " nafika wayo ai dama bro tun muna Yara, yanzu gashi a Ruwan Sanyi ina kallan Vedios ɗin batare da na zubar da ajina ba😄,kai kuwa fa,haka kullum suke kasancewa, ALLAH ya tona maka asiri AQEEL, AKEEL ya kamaka kana kallon Vedios ɗin da kace baka damu dashi ba. ____HAUWA DA KAWU ISMA'IL___ Tun bata kulashi a Asibitin har tazo tana kulashi, Ganin tabbas yayi nadama ta gaskia,gana ɗaya kullum sai yayi Kuka, da neman gafafar ita kanta Hauwa ɗin, hakane ya sanyaya Maya zuciya take bashi kulawa, kuma ta na Kwantar Masa da Hankali, Ganin jininsa yayi sama sosai, saboda yasan yanzu dai yanajin sauƙi sai prison saboda shi banki Baya lamuni balle afuwa, karaya saura kaɗan dan har ya na takawa shi kaɗai, sallamar su za'ayi ma, Yanzu ina suka kama ne Babu gidan komawa, su Meenal sai gidansu Hauwa suka koma anan suke kwana, Kawu isma'il fa yau jikinsa da ɗan da ma, dan haka taje can gidansu domin gyara musu ɗakin da zasu zauna, malam babanta ya Basu, kafin Kawu isma'il ɗin ya samu mafita, jibi Za'a sallamesu, dan haka Shi kaɗaine a ɗakin jinyar ya na ta tunanin duniya! Yasan dai muddin aka sallameshi shikenan sai prison" wai shi isma'il ne a Wannan yanayin, mai juya nera kai ALLAH ya karemun da cin dukiyar maraya da cin amanar zumunci,dan kuwa shine ya janyo Masa komai, dan shima Kawu isma'il ɗin daidai gwargwado yana da rufin asirin sa tunda san zuciya kawai yakaishi taɓa dukiyar Amana,gashi yadda yanzu tazame Masa! Kawai sallama yaji akansa"ƙirjinsa yai mummunar bugawa! Dan kuwa bazai manta da muryar Ƴan fashin nan ba! Wato su snake da awale da roci........... Lalläi ne fans Muje zuwa ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 6/20/24, 10:19 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM} 08128131163 Marubuciyar Komai nisan jifa Hakan ba kuskure bane ____________________ *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A* ____________________ *PAGE FIFTY EIGHT 58* *My fans I'm back Again🥰 , Happy Eid Al Adha* Nadawo daga esolation na wajen 3month and above, idan kunci gaba da ƙarancin comment ko late comment zan kuma tafiya esolation ɗin ko na haƙura da typing ɗin kwayi imagination da kanku ku ku karasa🤣 ILove you All my Fans Seerat Haseena Mummy Waleed Aisha Sulaiman Zeetopha..........✍️kuna da yawa 🥹 Zakiyyah tana miƙo gaisuwa sosai🙏 _______USMAN_____ Daya Fara Shan maganin da Doctor ya bashi shikam baiji sani sauƙi ba,abu ma sai gaba Yakeyi, idan gabansa yafara Masa ciwo Kamar zai mutu,ga kumburi abun gwanin tausayi ga kwailewa da yakeyi, yana Ruwa,musamman wajen ball's ɗin sa kamar lalacewa yakeson yayi,tuni clara tabarshi,daga shi sai halinsa ta kwashe Masa ƴan kadarorin daya mallaka ta ƙara gaba,to dama abunda takeso a gareshi shine sex kuma yanzu Babu abunyi. Abokan shashancinsa ƴan Homosexual kuwa tunda suka ga yanzu Babu mammora gareshi suka kaleshi,ina Abun yake,ƙyanƙyamin sa sukeji ma,Duniya fa tajuyawa Usman Ɗan jimmai😀 Baya,ciwo idan yatashi kamar ya mutu,idan ya lafa kuna kamar bashi ba,akwai WANI Abokin Harkallarsa Bature me suna Alex yayi tafiya ya jima bai haɗu da Usman ba in zasuyi masha'arsu Baya WANI kiransa takanas yake Zuwa gidansa yau ma Hakan ce ta faru,yana Zuwa ya tarar da Usman a halin da yake ciki, kunsan turawa akwai tausayi,ya kwashi Usman sai Asibiti cikin gaggawa! Doctor ya dubashi, yace Ball's ɗin sa sun lalace sai dai a yanke,Amma shi da Haihuwa har abada,in Anyi Aikin andace ma Kenan,Amma yawanci ana mutuwa amma wasu kuna ana samun nasara! Cikin gaggawa Alex yabada maƙudan ƙudi aka shiga da Usman emergency surgery, Ba'ayi cikakken Awa biyar ba aka gurguro da Usman cikin gadon marasa lafiya gwanin tausayi! A Ranar ake farfaɗowa,Amma shikam sai da yayi Kwana da wuni ya farfaɗo,Anyi aiki a Sa'a sai dai shi da ƴaƴa sai dai yagansu a wajen wasu Amma shikam Babu,satinsa hudu a Asibiti yafara jin sauƙi,dan Kullum safe da yamma sai Anyi dressing ɗin wajen kuma sai ya fita daga hayyacinsa! Yanzu Alhamdulillahi. Alex yai tafiyarsa nan, Tun da Usman yaji sauƙi kuma sai tsoron ALLAH ya shigeshi Akan Abubuwan daya aikata a Rayuwarsa musamman cutar da yaiwa Shukrah yakuma tuna da Daddy Dole yakoma gida kam ya nemi gafarar ta ga Akeela ma da Mama wacce Yasan shine musabbabin cutarta datake fama da ita har yanzu,haka yafara shirin durowa 9ja......... ___KAWU ISMA'IL___ Kafin yadawo hayyacinsa har su snake da roci da awale har sun ƙaraso gaban gadonsa,sai ga kawu isma'il jikinsa na kakkarwa! Dan yasan zuwansu ba alkhair bane garesa, yatuna irin sharrin daya musu a Tv da Radio,yasan sunji Zuwa sukayi ɗaukar fansa! Isma'il Zuwa wajenka mukayi!dan kuwa munji irin sharrin da kai Mana a Media, lokacin munzo wuya mun ɗau Alwashin sai mun yanke maka ƙafa ɗaya shine fansar sharrin daka Mana nacewa mune Duk wata dukiya daka mallaka data marayun ALLAH mu muka ƙwace ta......Kawu Isma'il jin Abunda Awale yace ai iwu ya kurma kafin yafara magiya garesu Akan suyi haƙuri,ai ya janye furucinsa a inda yayi...... Dakatar dashi Roci yayi da cewa kai ka Mana shiru ai da ace bamu watsar da kudurin mu ba ai da tuni yanzu maganar nan da ake baka da ƙafa, ALLAH ya shirye ka ai kaga aya bayyana na yanzu,nasan ko kuɗi ka gani a ƙasa na marayu bazaka ci ba balle a baka ka Handame sai anjima cewar snake yana ficewa muƙarrabansa na bin bayansa!Kawu Isma'il kuwa wata ajiyar zuciya yayi haɗe da idanuwansa Suna ƙafewa gaba ɗaya alamun ruɗu yasa ya Suma! Su yaran snake wasu daban fashi sukaje Wani Gida to gidan soja ne me gadi aikuwa ya tumfarosu shine fa sukasa gudun wuce Sa'a a motar su! Aikuwa sukayi hadari Wani mummuna daga masu karaya sai masu mutuwa!Wani mai suna gwanki take kansa ya fashe sai ga ƙwakwalwa a ƙasa,shine fa aka kawo su Asibitin,dan shi sojan zuwaya gida yayi,bai bisu ba, dan kuwa yagansu da gangan makamai a hannunsa shikam ko Allura Babu yasan a banza zasu kasheshi,shine fa dama su Roci suna daga can gaba to daidai wajensu abun yafaru,sai sukayi dabarar kwashe makaman a motar su,A sa'annan suka Kira ƴan sanda , Kafin suzo fa suka bar gurin! Koda Ƴan sanda sukazo basusan Ƴan fashi bane! shine fa aka kawo jikkatattun Asibitin da kawu Ismail yake, Kuma tun Hatsarin da Ƴan uwansu sukayi jikinsu yayi Sanyi, tsoron ALLAH ya shigesu, Yanzu Haka Shirin miƙa kansu da Hukuma suke! sunzo shigewa zuwa dubiya kamar mutanen arziƙi shinefa suna hangi Kawu Isma'il ta window..... Doctor yazo yaga halin da Kawu Isma'il Yake nan ya ɗaura Masa ruwa, sai yamma Hauwa ta dawo sannan Kawu Isma'il ya farfaɗo yabata labarin yadda sukayi dasu roci, Addu'ar shiriya tai musu. Kwana biyu tsakani aka sallami Kawu Isma'il dan kuwa karaya ta warke, haka suka koma gidansu Hauwa da zama gwanin tausayi, Yanzu dai kawu Isma'il tsoron sammacin kotu yakeyi........... ___AKEEL DA AQEEL___ misalin 2:00am na dare. AKEEL ya Tashi ya shiga bayi,bargon da Yake jikinsa ya cire ya ajiye a gadonsa,sai yayi like yana kwance,to Dai Dai lokacin da AQEEL yasa alarm a wayarsa ,na Tashi kallon Vedios ɗin su HADIYYAH, yana tashi kuwa,Dama Glass ɗinsa yana wurin da Yaje ajiyewa saboda tashin dare,bayan yasa Glass ɗin ya dumfari wayar AKEEL kai tsaye ya shiga ya Fara kalla ya juya baya,yana kalla yanashan murmushi Abunsa,basaiwa junansu gate da wayarsu shiyasa bai turawa wayarsa ba,gwamma ya kalla a ta AKEEL ɗin, A daidai lokacin AKEEL ya kammala abunda zaiyi a bayi ya fito shi AQEEL ya tafi shauƙi beji ƙarar ruwa a bayi ba, da kuma ƙarar rufe ƙofa, mamaki yakama AKEEL Ganin bro yana kallo daidai wannan Lokacin,mutumin da bashi da lafiyar idanu da sassarfa ya tawo domin yaga ne yake kallo,Amma ina!!!! Har yazo gareshi yaga abunda yake kallo Amma ina AQEEL anyi nisa cikin nishaɗi baiji bro ba,sai da bro ya kwa che wayarsa sannan bro yadawo hayyacinsa sai kuma kunya! Ya haɗe Rai zai juya ya kwanta aikuwa bro yakewa bro " dakata Mana bro kwanciyar me zakayi aina kamaka,dole Abbu yaji wannan magana! Ya ƙarasa zancen da sheƙewa da dariyar shakiyanci! Shikam AQEEL ya shaƙa,kuna yaji kunyar kamashi da bro yayi,Amma kunsan gogan naku akwai shanye abu. Sai da Asba da suka Tashi,sai Wani kumbure kumbure AQEEL yakeyi,shikam AKEEL yana kallonsa ya basar, yasan koya kulashi bazai sauko ba,tabarmar kunya Kenan! A Masallaci bayan idar da Sallah sun shigo gida AQEEL yai wuf ya komo gida Babu jira,shi kuwa AKEEL yana wajen Abbu yana Bashi labarin yadda ya faru tsakaninsu aikuwa Abbu yasha dariya, yace wa AKEEL nasan hakan zata faru,ka ƙyale ɗan uwanka kasan halinsa ma ai Muje zuwa dai. A wajen breakfast ma haka AQEEL yake a kumbure, sai da Abbu yaga abun babu ƙarewa sannan yace ' mommahn AQEEL Ɗanki fa kumburin ankamashi dumu_dumu yana kallon Vedios ɗin ƴaƴana shine Yake wannan kumburin,Ai kinsan da kunya mutum yagama cika baki kuma akamashi!!!!!!!! Gaba ɗaya aka kwashe da dariya har AKEELA ma! Mommah tace "Abbu Dan ALLAH ku rabarmun da ɗa na Hakan ai shine daidai ba wai ya dinga zaƙewa ba, ai shine namijin! Bawaninan mommahn AQEEL kare Ɗanki kike kawai! Amma kowa yaji Hakan yasan....Abbun AKEEL ba fa haka bane....... To mene itama ta katseshi haka sukaita barkwanci a wajen breakfast ɗin nan like ahalin da suke cikin farin ciki kamar abaya Basu kasance cikin baƙin ciki ba! Daga ƙarshe AQEEL ya karɓi lefinsa da cewa "nifa kawai fa kallo nakeyi, shine fa ya ƙare Vedios ɗin ya shigo shine nifa nake kalla, kama faɗi gaskiya bro kallo talatainin dare sai aka kuma dariya......... ______HADIYYAH DA HIDAYAH_______ Tun daga kallon Vedios kuma sai Basu da Abun so su Gani Kamar AQEEL da AKEEL abu kamar tsafi fa kuma su biyun,sai suka Fara tunanin bro da bro ganinsu da sukayi a Asibiti da a Tallafy foundation ya dinga dawo musu,sarkin soyayya HADIYYAH sai taga tunanin AQEEL (wanda batasan wanene daga ciki ba me surutun ko miskilin) yana neman mantar da ita Mus'ab da yaudarar da take ganin yaimata Alhalin yai MATA bayanin komai fa. Mara soyayyar ma wato HIDAYAH wacce bata damu da Mahmoud bama sai gashi Yanzu tunanin AKEEL (itama batasan wanene daga ciki ba) ya zame MATA kamar me data zauna sai tunanin sa, su kam har mamaki Hakan yake Basu,sai suyita yiwa junansu tambaya Amma sis da sis sai suka ce kyautatawar da Abbunsu yai Musu ne,shiyasa suke tunanin ƴaƴansa kuji fa Fans wai hakane Fans? Yanzu dai burin HADIYYAH DA HIDAYAH suyi tozali da twins bro and bro na Alhaji tallafy........ _____SA'ADATU_____ Alhaji Gambo fa yakasa gane kanta, hulaƙancin yai daban na gobe daban! Shikam Baya ta tata,tsakani da ALLAH Yake Zaune da sauran matansa wato Hajiya ikilima da Hajiya suwaiba da kuma Hajiya sahura,Suma kuma yanzu sunyi Hankali tun Akan abunda Sa'adatu dashi Alhajin yai musu abaya ganin cikin da tasukewa iyayi zance ya ƙare. Sun haɗe kansu sun duƙufa da addu'a ALLAH yabawa mijinsu Haihuwa ko a wa cece kuwa!cikin ikon ALLAH kuwa sai ga Suwaiba Babu lafiya har dasu Amai,dan haka Sahura ta ɗau mota domin kai ta asibiti, Suna shiga asibiti itama taji warin asibiti itama tafara jin babu daɗi kanta yafara ciwo,Dan haka bayan duba Suwaiba akace ciki ne da ita ɗan Wata huɗu ma,sunyi murna sosai kamar Babu gobe sunwa ALLAH godiya, ciwon kan da Sahura take ne yasa itama aka MATA gwaje gwaje aka gano itama ashe cikin gareta wata Biyu ita kuma! Wannan wane irin farin ciki ne yasamu Alhaji Gambo Fans? Dan haka jikin Hajiya suwaiba babu ƙwari,na Sahura kuma kanta na sarawa harda jiri,dan haka takira Hajiya ikilima a waya suka mata albishir, aikuwa tai murna kan kace mene sai gata a Asibitin a da driver ya juya da motar ita kuma ta shiga wacce Hajiya Sahura suka shigo sai murna sukewa junansu kamar ba kishiyoyin da suka tafka masifa da bala'i a Baya ba. Tun daga sannan Hajiya ikilima take Basu kulawa ta musamman abun gwanin burgewa! Alhaji Gambo yayi murna da wannan kyauta ta ALLAH daya bashi Amma bai zaƙe kamar na Sa'adatu ba daga ne cikin har Mara cikin kulawa ɗaya yake Basu,sai Addu'ar ingantawa take wa matan sa fatan ALLAH yabawa ikilima itama da Sa'adatu wacce Yanzu yakasa gane kanta, har yau bai gaya mata cewa Sahura da suwaiba Suna da ciki ba.......topha ko me Sa'adatu zatayi intaji bayyanar cikin su Hajiya suwaiba da Hajiya Sahura ✍️Oum ARQAM 6/22/24, 9:47 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM} 08128131163 Marubuciyar Komai nisan jifa Hakan ba kuskure bane ____________________ *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A* ____________________ *PAGE FIFTY NINE 59* *My fans I'm back Again🥰 , in Sha ALLAH Har End,indai ba Halin Kuka kuma ba 🌝* _______USMAN_____ _Cikin ikon ALLAH da jikin ya kuma warwarewa dan Yanzu andaina dressing guri ya warke tatas, Doctor yayi mamakin Hakan saboda irin wannan aikin majority rasa rai akeyi. Ya sauka lafiya a 9ja ƙasarmu ta gado. Gidansu inda yabar Baba da Umma nan yanufa saidai yasamu labarin bakin cikin barinsa gida da kuma Abunda yasamu Shukrah yai ajalinsa Usman yaci Kuka,bai bai samu Umma a gidan ba saboda bata nan,Gidan ɗan yayanta daya ɗauketa nan yaiwa tsinke, aikuwa sai ga umma tana Kuka! Ganin yadda Usman Ɗan ƙwalisa ya koma yafita daga hayyacinsa,(Fans batasan bala'in daya sameshi ba, (Umma Usman ai shi Yanzu zan iya cewa dashi gwamma Babu yasin🤣dan kuwa Fanko ne) Suna hirar Yake gaya MATA cewa ai cuta yayi,bai faɗi ainahin abunda ya sameshi ba,nan dai Umma tai Masa tatas tace "Usman cuta tasa kadawo garemu ai dama duniya ba gida bane,haka naita gayawa Babanka,Amma yasa abun a Ransa ga ɓacin ran abinda ya samu Shukrah,sai ga Usman yana kuka da neman gafafar ta, sannan ya nemi Alfarmar yanason ta rakashi wajen Mama dan yasan Yanzu fushi take dashi, yagano Shukrah da Daddy batayi Musu ba ta shirya direban gidan ya haɗa daga ita har Usman sai gidan Jimmai ikon ALLAH. ______GIDAN JIMMAI______ Shukrah yau tana scholl exam suke za'a kammala Secondry,Daddy ma yana school, dan haka Saida tayi abunda tasan zatayi ta tanadarwa da Jimmai komai a kusa da ita,dan Yanzu hannunta yana motsi tana iya daukan abu dashi,tana Hawa fo tayi tsarki, saidai tabarshi wajen dan kuwa babu kafafun tafiya Babu bakin magana kuma,ta kammala Fitsari kenan umma tayi Sallama Duk da ba amsawa zatayi ba! Innah sai a slow Usman ne ya biyo bayanta,Hakan ne Yasa Jimmai shiga shock wanda yasa bakinta karkarwa kamar wasa sai ji sukayi tace"k..a..i.. k..a...i..k..a..i.n..e!cikin mamaki Umma tace "Jimmai kece yau kike magana Alhamdulillahi ea tabbas Usman ne ALLAH ya amsa du'a'in mu gashi yadawo Kuka ya ƙare (kowa yana tunanin kukan da Jimmai take na Rashin Usman ne,nan kuwa basusan.....) Umma Hannun Usman ta riƙe sannan ta jashi har in da Jimmai ke zaune tana sunkuyar dashi alamun ya nemi gafarar ta! Jimmai dai Kuka takeyi,shima Usman ɗin yafara kukansa yana kallon mahaifiyarsa wanda yasan kowanne Hali ta shiga shine sila,cikin kukan yake magana "Mama ki yafemun nasan Haƙƙinki kine ke bibiyata tunda na tafi........ Nan ya kwashe komai ya faɗa har cutar da yayi da cewa bazai Haihu a duniya ba! Saiga umma tana salati garin Yaya wannan wace Irin cuta ce Usman haka,cikin in ina ya fayyace musu ai an yanke Masa ball's ɗin sa ne,Amma bai faɗi meyasa ba,sai ga Umma tana Kuka, ita dai Jimmai idanu ta zubawa Usman kukanta ya tsaya, tabbas tasan Alhakin AKEELA marainiyar ALLAH ne,dan bazatace na Shukrah ba dan kuwa wannan SAKAYYAH ce ALLAH nuna MATA,nacin Amanar zumuncin da tayi... USMAN yaci gaba da magana Umma ki yafemun abunda zan faɗa ita Mama tasan abinda ya faru bakin magana ne bata dashi balle ta gaya muku... Ni..ne nai.wa.shukrah.faɗe ba ko.wa ba kuma Daddy ɗa na ne shi kaɗai ya ragemun a duniya ƙwaina in bayan shi Babu ni Babu Haihuwa,sai ga Umma tana salati "Amma Usman ka cuci kanka ni Hajara,kanwarka uwa ɗaya ina Hankalin ka da tunaninka sai tasa kuka! Yaci gaba da magana " kiyi haƙuri Umma abun da Yasa Hakan......nan ya gaya MATA lokacin zaman Asibitin Baba anan ya samu dama, ALLAH ya taimaki AKEELA bai faɗi nata ba,Kunga my Fans Asiri ya rufu ruf Umma sai Kuka take gwanin tausayi,data tuna tsinuwa da ALLAH wadai da sukaitawa wanda yaiwa Shukrah wannan aikin,sai da Usman ya fallasa sannan ma tunanin Umma yakai wajen to inba har gida akawa Shukra fyaɗe ba to Wanene? Ko a school aka MATA sai sharar hawaye da majina takeyi gwanin tausayi,daga sama Jimmai tafara magana Sosai " Usman ai dama nasan Duk inda kaje zaka dawo ne kuma ALLAH bazai baka ikon Zama lafiya ba,tunda ni dana gatataka ni kaiwa haka, ka tasa wacce zaka Lalata sai kanwarka uwa ɗaya uba ɗaya, ai abun ya ƙazanta kaɗan ma kafara Gani...... Sai tasa Kuka Umma ganin kukan Jimmai ya ƙara volume ne yasa ta Fara lallashin da cewa " haba Jimmai baki Masa baki bama yayi haka Inaga kinmasa wannan abu dai ya faru sai dai Haƙuri ALLAH ya kyauta gaba, Yanzu addu'a zamu Masa ta samuwar cikakkiyar lafiya gareshi fushi dashi ba namu bane,Ai yayi nadama sai dai Haƙuri mai faruwa ya faru yanzu yaron nan Abun tausayi wlh jimmai,, Umma tana zancen tana sharewa Jimmai idanu da baki wanda yahu yake zuba, Alamun anjima ba'ayi magana ba! Jimmai dai sai Kuka da maganganu marasa daɗi take ga Usman,shima sai Kuka yake yana Mama ki yafemun ki tausaya min..... Tun farkon Fara maganar Shukrah tashigo gidan da sallana Suna Cikin Hatsaniya shiyasa Basuji ba, dan haka jin kamar muryar Yah USMAN da Umma kuma Suna Kuka da maganganu n da Suke ne Yasa ta ɗan tsaya ai sai taji wata magana banbara kawai wai Yah USMAN ne yai MATA Cikin Daddy! Amma har dashi a masu neman wanda yai mata Lallai Yah USMAN ai MATA adalci ba, ya cuceta ya lalata MATA rayuwa ya zasuyi da wannan Abun kunyar! Daddy ɗan Yah USMAN ne kuma ɗan ya uwarsu ɗaya ubansu ɗaya! Wannan wace irin cakwakiya ce sai Kika ya ɓallewa Shukhra gwanin tausayi! Kafin daga bisani Numfashinta ya ɗauke gaba ɗaya, daga waje su Umma sukaji jiiiiiif! Alamun abu ya faɗi Usman ne ya leƙa sai yayi tozali da Shukhra ƙanwar sa, wacce ya zalunta a Rayuwarsa, Haƙƙinta dana AKEELA yake bibiyarsa da kuma saɓawa ALLAH wato neman maza da yadingayi da neman MATA Duk shi kaɗai ga Shan giya! Kai shifa Abubuwan sun Masa yawa! Salati yasa wanda Umma tayyo wajen itama aka bar jimmai na zubar da Hawayen nadama da baƙin Cikin! Sungumar Shukrah Usman yayi zai waje da ita Umma ta daka Masa tsawa "ina zak kaita ne ko so kake Ragowar asirin da yake rufe ya tone, shigo da ita ɗaki shock ɗin maganganun da nake tunanin tajine ne yasa ta Hakan,ana shafa MATA ruwa Shikenan! Jiki a sanyaye Usman ya juya da Shukrah ɗaki. Kamar yadda Umma ta faɗa Hakan ce ta faru ana shafawa Shukhra ruw takawo numfashi haɗe da ihun Kuka " mama nashiga uku na kice abunda nakeji ba gaskia bane! Yah USMAN bashine ya lalatan Rayuwa ba,ba kuma shine Mahaifin Daddy ba sai fisge fisge take gwanin tausayi! "Sai dai kiyi haƙuri Shukrah abunda kunnenki yaji miki hakane Babu batun ɓoye ɓoye! Wayyo nashiga uku nah ALLAH kaɗau raina da ganin wannan rana! Ganin halin da Shukhra take Ciki ne yasa jikin Usman kara Wani sanyin da share hawayen baƙin cikin biyewa Sharrin zuciya, ƴar ƙanwar sa wacce takewa son so ,shima yake MATA Hakan wai yai shine silar sata a Wannan yanayin shikam ina zaisa kansa A duniya! Da sassarfa Yaje gareta ya saka gwiwoyinsa a ƙasa ya Fara roƙar ta Akan ta yafe masa , sharrin SHAIƊAN da biyewa zuciya dan kuwa kallon BF ne Yasa shi a kowanne Hali (yakamata matasanmu samari da Ƴan MATA ku kiyaye kallon Blue film yana haifar da matsaloli da yawa a rayuwar duniya Harda irin halin da Usman ya shiga, ga matsalar idanu, awajen ALLAH kuma akwai babbn zunubi, ALLAH Yasa mufi ƙarfin zuciyarmu akoda yaushe,Kunga dai haƙurin da AQEEL yayi Akan irin tasa matsalar ya tsaya wajen Azumi da roƙon ALLAH samartakarsa tai Masa Amfani dan kuwa har yanzu gashinan nutsatstsene ALLAH Yasa mufi ƙarfin zuciyarmu akoda yaushe) Ita dai Shukrah Duk ban baki na Usman da magiyar da neman gafafar ta bata saurareshi ba sai sharar ƙwalla take, haka har yamma tayi Lokacin ɗauko Daddy daga school yayi, 3years yake Amma akwai wayo da surutun shiyasa aka kaishi school ɗin da wuri, idanun Shukhra kamar famke tsabar kumburi Amma haka tasa niƙaf ta fice domin ɗauko Daddy, bin bayanta Usman yayi ko kulashi batayiba, ta ɗauko shi ta riƙe hannunsa,Abun gwanin tausayi, shikam Usman yana zuwa ɗaukar Daddy yayi ya rungumeshi a ƙirjinsa yanajin nadamar Hanyar da yabi wajen Samar da yaron, gadai shi kaɗai ne ƙwansa a duniya Amma kuma Babu daɗin jin yadda aka Samar dashi, Daddy ya manta Usman Amma kuma tunda namiji ne sai gashi ya yarda dashi,ganin Usman ya ɗauki Daddy sai Shukhra tayi wuf tai gaba ta barsu Abaya. Koda suka koma gidan Jimmai da Umma sai zancen Bala'in da ya samesu sukeyi, kamar ba ita bace wacce ta shafe shekaru bata magana ba, tanajin sallamar Usman ta haɗe Rai tajuya fuska,sai Bayan magriba sannan Umma tabar gidan Shukhra itakam tace binta zatayi, Umma yace wazai kula da Jimmai ɗin? Dan haka ta haƙura da tafiyar Umma tai tafiyarta zuciyarta ba daɗi. Fin sati da dawowar Usman daga Jimmai har Shukhra basa kula shi, sai dai yaiwa Daddy wasa,haka Yake Zaune a cikin gidan zuciyarsa Babu daɗi,yana dan sanin abunda yayi, Yanzu ma so yake yake wajen Abbu dasu AQEEL da AKEELA na nemi gafararsu Akan Abubuwan da ya aikata musu...... ____KAWU ISMA'IL___ _kamar yadda likita ya faɗa a yau ya sallame shi sai gidan su Hauwa, su Minal anata murna Abba yadawoe, Kawu Isma'il sai sussunne kai yake yanajin kunyar su innar Hauwa,sai suka bagarar dashi kamar basusan ABunda yakeyi ba,shi tausayi ma yake Basu,mutumin daya saba riƙe kuɗi shine yau yake wannan Hali Duk da shine ya jawa kansa, Amma ai akwai Tausayi, ko sisin kwabo Bashi bashi dashi,sai a gidansu Hauwa and ci dashi da matarsa da ita kanta,idan ya zauna yaita tunani kenan, na tsoron haɗuwarsu da banki ,yasan Yanzu sunajin an sallameshi daga Asibiti zasu makashi kotu, ƙarshen sa ma gidan yari ne! Wannan abu yana ɗaga Masa Hankali shiyasa tunda aka sallameshi yake ɗar ɗar zuciyarsa Babu daɗi!haka innar Hauwa da Hauwa kanta tai tai Masa nasiha. Haka kwanaki sukaita tafiya shiru_shiru banki Basu nemi Kawu Isma'il ba kuma har sannan zuciyarsa bata kwanta ba,ga hawan jinin daya sameshi kusan kullum Babu lafiya yau shuni gobe Dauɗa, a haka harya Fara fita yana tattakawa Duk indai yabi sai kallo ake binsa dashi shikam wannan abu yana Bashi kunya Duk da yasan halinsa ne yajawo Masa, kullum sai yawo da carbi da istigfari da Hailala yakeyi akan ALLAH ya yafe masa zunubansa,Duk sanda zaiga su Hadiyyah da Hidayah da sauran ƴan uwansu sai yayi Kuka da neman gafararsu sukam Abun yana damunsu sukace "dan ALLAH Kawu komai ya wuce adaina sawa kansa tension kana kallon halin da kake ciki....... _____GIDAN MUKHTAR_____ _Zaman lafiya kamar a gidan aka same shi tsakanin Zakiyyah da Bilkisu zamansu sai san barka, kamar ba kishiyoyin juna ba,Kowacce burinta ta faranatawa mijinta rai, Hakan yana faranatawa mijinsu mukhtar Ransa yayi fresh sai wata ƙiba yakeyi ga kuɗi ya zauna da kwanciyar Hankali,Tuni ABIE an ƙara tasawa anyi Hankali sosai yanzu, waɗannan ƙiriniyar ya rage ta saura kaɗan, yana primary 3 yanzu,ka ƙoƙari sosai da Yake dashi ga wayo wanda yafi ƙarfin shekaraunsa,Har sannan a wajen Bilkisu yake komai nasa a bangarenta yake Babu wanda zai tunanin ba ɗan ta bane. Itama Zakiyyah haka ta riƙe takwararta kai kace itace ta haife ta, Little Mammah angirma sosai yanzu haka rarrafe take inta kama abu ma tana miƙewa gwanin sha'awa, tayo wayon ABIE dama Suna kama dashi Sosai kuma shi ABIE ɗin yana yanayi da mamansa shi yasa har wata kama ake Tsakanin Zakiyyah da little Mammah,tuni aka yayeta dan kuwa a wajen Zakiyyah take kwana kuma Babu abunda bataci, Zaman little Hannun Zakiyyah ko ƙarzane bai sameta ba ba kamar lokacin goyon ABIE ba lokacin Zakiyyah anakan hauka Yanzu kam anyi hankali. Naga itama ALLAH yakawo ciki ne da ita gashinan ya fito ba sosai ba, sai nace ALLAH ya Raba lafiya, su seerat da Aisha Sulaiman da MamaGee da oum Nawwar zeetopha,mummy Waleed a shirya zuwa Suna fa ƙawarku an kusa sauka , nasan za'asha shagali.... ______AQEEL DA AKEEL______ Tun daga lokacin da asirin AQEEL ya tonu kuma aka samu abun tsokana gareshi tun yana kumburi har ya daina,sai ya Fara murmushi ganin kumburin yana ƙara sawa ayi tsokanar, aikuwa sai ya fuske,Amma Duk xa Hakan fa shi AKEEL bai daina Masa ba, idan yaga Abun ya isheshi sai kawai yabarwa AKEEL ɗin wajen, shi kuma sai ya bishi ɗaki ya ɗauko waya like yadda AQEEL yai daya ɗauki wayarsa yana kallon Vedios ɗin su Hadiyyah,kawai sai ya daina kallon AKEEL ɗin in yana iskanci gareshi ko kuma ya cire glass ɗin idanunsa yadda bazai ganshi da kyau ba😀 ABBU burinsa Yaga Ƴan biyunsa kowanne ya danƙa Masa matarsa, ya cika wa Abokinsa masoyinsa burinsa,na haɗa ƴaƴansu Aure, Sai kuma Wata sabuwa, yanzu fa AQEEL kwanciyar Hankinsa yadawo kaso 70%cikin 100%,dan haka ciwonsa yai Masa Sallama, abu ma yaso yafi nada Yanzu ciwon Ciki da mararsa idan ya Yunƙuro kamar zai mutu,Jiya abun ya Fara dawowa,kuma yana dawowa sai da suka dangana ga Asibiti, aka rubuto wasu sababbin magungunan da suka fi nada ƙarfi, Doctor yaiwa ABBU gargaɗi Akan Hakan dan kuwa Maganin yanada nasa illar idan yayi yawa a jiki,mafita kawaii Amasa Aure in Sha ALLAH zai warke ne! nan ABBU yace wa doctor sh wannan yaron ɗan baiwa ne kamar munsan yanayinsa tun yana ƙarami muka Masa Aure, badan wasu Abubuwan da suka faru ba aida tuni yanzu Suna tare da iyalinsa, sai da yasha ruwa sannan suka dawo gida! Abun Tausayi AQEEL yini guda ya rame gashi baya miƙewa dakyau saboda ciwon marar,sai zuwa dubiya akeyi. ABBU yaso barin bikin nan da wata takwas masu zuwa a haɗa dana AKEELA wacce sannan tayi candy, To ga kuma yadda abu Yake tafiya, Dan haka Abbu ya yanke shawarar danƙawa kowanne number matarsa su Fara daidaitawa a waya in yaso dakansu zasu saka Ranar Zuwa wajen juna,sai matsalar AQEEL ta taso shiyasa Basu Kira ba Hankali bai kwanta ba,to Yanzu yafara jin sauƙi Alhamdulillahi sai shirin kiransu Hadiyyah...... ______ GIDANSU HADIYYAH_____ Shirye shiryen tafiyar ALHAJI china akeyi,kamar yadda Alhaji tallafy ya faɗa,Duk ABunda zai buƙata Saida Abbu yai Masa kwana biyu tsakani ya cilla china cike da kewar gidansu da Ƴan uwansa. Gida yakoma shiru dama zuwan Alhaji ne Yasa gidan aketa walwala da dariya, Kwana Biyu da tafiyar Alhaji sai ga Baabah mutanen Kaduna anwa gidan tsinke sai murna tadawo sabuwa!kar kuso kuga yadda Hunaif ɗan maraya ya girma ba,kamar ba shiba, sai da naduba naga Zeenah kai nayi mamaki fa Yarinya anzama budurwa kamar ba ƴar rainon Zakiyyah ba Lallai Kaduna ta karɓeta, kunsan dama irin jikin Zakiyyah gareta ga tsayi ga ƙiba ma Sha ALLAH,sai naga da kaɗan ma Khadija tafi ta. _Duk Abubuwan da suka faru su Hadiyyah sub zayyanawa Baabah,sai gashi tana kukan farin Cikin jin jikokinta kyautar da ALLAH yai musu na samun mazajen nunawa Sa'a kamar ƴaƴan Alhaji tallafy,da kuma samun siriki kamarsa aikuwa tayi murna sosai, Zahra tuni ta Haihu ƴan Biyu mace da namiji, Khadija ce taje ta zauna Mata,ƴaƴanta ma Sha ALLAH gwanin burgewa, ƙauna tsakaninta da mijinta sai Abunda yayi gaba hakana uwar mijinta Maimuna kowa son Zahra yakeyi, twin's sunci sunan Ammar da Ummu Rumana ana kiransu da Ummu da Abbiy,sun yi ɓul_ɓul kamar na kwacesu yakawowa seerat yasin🤗 Tunanin da Hadiyyah da Hidayah suke Akan su AQEEL sai Abunda yai gaba, Yasin Basu da tunani sai nasu, Yanzu burgesu sukeyi Basu da burin komai sai na Ganin su AQEEL,Kusha kuruminku su Hadiyyah saura ƙiris su AQEEL da AKEEL su Zama naku Yanzu zasuzo gareku.... _____TALLAFY'S ____ TALLAFY foundation.....Sai ABunda yayi gaba fa bayan yaye su Alhaji an kuma zuba Wasu daban, acikin su Alhaji ba shi kaɗai aka ɗauki nauyin karatunsa ba ,yara da yawa sun samu, Babu adadi yaran da suka shiryu sanadin TALLAFY foundation, Yanzu ba iya Kano ba wajen jahohi kaɗan ne Babu TALLAFY foundation, sai addu'oi yake samu ta ko ina,shiyasa Abbu Kullum yake ƙara gaba, lokacin cutar AQEEL Ƴan Dubiya kamar me da sassan nigeria daban daban,ga addu'oin alkhair da take samunsa. TALLAFY group of company yayi gaba ya kera Sa'a jahohin nigeria yanada rassa ba kaɗan ba, indai harkar idar kayan abinci ne ga sauƙi manyan shaguna dayawa a wajen suke sarin kayan masarufi Babu abinda Babu wanda ake sarrafawa aci Ayi amfani dashi, sai son barka. TALLAFY Holdings company ma Hakan take Duk WANI Abun amfani na zamani da wuta da karatuna akwai shi a Wannan waje shima akwai rassansa sosai a nigeria kayansa daga ƙasar japan Yaje oda Babu gara Babu zago, Abbu ya ya wuce yadda kuje sauraro kuma ba komai ne Yasa Hakan ba illah taimakon da yakewa marayu da Marasa ƙarfi........ ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 6/25/24, 12:05 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM} 08128131163 Marubuciyar Komai nisan jifa Hakan ba kuskure bane ____________________ *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A* ____________________ *PAGE SIXTY 60* *I LOVE YOU ALL MY FANS🥰* "Nifa bro bansan yadda za'ayi na Kira wannan Yarinyar ba fa Duk da bansan wacce acikiba! ALLAH yasa dai ba wannan dunkum ɗin bace dan bazan ɗau wannan Al amarin ba,Mutum ya zauna kamar Wani kurma! AQEEL ne ke wannan maganar a daidai lokacin da Suke tattaunawa Akan kiransu Hidayah a waya! Duk maganar da AQEEL yakeyi shi dai AKEEL shiru yayi kawai yana kallon bro ɗin sai da yakai Aya sannan shima ya tofa Tashi! "Banda abunka bro kaima ɗin menene?kaima da ita ai duk Babu banbanci,idan itace ai kaga ka huta sai kuyi zamanku Babu hayaniya!Babu takura Dan duk lokacin da zamu zauna tare dakai sai kace na fiye surutu na dameka!kaga kuwa idan wannan mai surutun aka haɗa ka da ita sai ta dameka ko? Ya ƙarasa maganar da duban bro ɗin sa! "Kai bro ya isa haka fa zaka tsaya wannan tsarin,kai ai surutunka yayi yawa ne, Yaushe zaka haɗa kanka da wannan yarinyar! Kawai dai ni na sare da wannan lamarin,idan dunkum ce ALLAH sai na daidai ta mata zamanta,bazai ɗauka ba, dole ta buɗe baki ta dinga mun Hira! Lalläi bro to wazai koya ma...... AQEEL Ɗagawa AKEEL hannu yayi alamun ya isheshi da surutu! Dan haka ya rufe bakinsa ya barshi yasan idan jarabarsa ta tashi ya dinga kumbure kumbure Kenan da ciccin maganin Babu gaira Babu Dalili dama gashi bashida lafiya cikakkiya. A haka yirar ta watse Haka bro da bro ɗinsa in ana Hira Rimi Rimi sai an gama ta baram_baram. Sai Bayan isha'i sannan AQEEL yasamu ikon Kiran waya,saboda mutanen da suke ta zuwa dubiya har yanzu Basu daina zuwa ba,guri guda ya keɓe saboda baison bro yasa Masa idanu,sai kuma gashi ma tun bayan isha'i ɗin bai ga bro ba,may be yana ɗaya ɗakin nasu dake wancan part ɗin ko yana ƙasa shi hakan ma yai Masa daɗi! "Ƙara shingiɗa yayi lokacin da yaji wayar tayi ringing! "Assalamu Alaikum wa rahmatullah" !Yaji muryarta cikin nutsuwa da Sanyi! Wanda sai da ya ƙara gyara kwanciyarsa haɗi da sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya! Kafin ya Amsa sallamar " Wa'alaiki salam wa rahmatullah"ya mayar mata kamar yadda tai Masa! Sai kuma yayi shiru,itama shirun tayi,sai da taga shirun yayi yawa! Sannan Hadiyyah (lallai ne ALLAH ya taimaki AQEEL wacce yai zata itace tasa,kutayashi murna) tace " bangane me magana ba! "Kina magana Da Hassan Ɗalhat ne" tunani Hadiyyah ta tafi wanene Kuma Hassan Ɗalhat? Ita dai a school ɗin su ba wanda take kulawa,hakanan bata Bawa wani mai wannan sunan number ɗin ta ba,ita da Babu inda take fita ma sai school,tunda maganar Aurensu ta ɓullo wai sai sun tambayi mazajensu!ta ina zasu tambayesu Alhalin Basu da number ɗin su kuma su bazuwa wajensu suke ba! "Ya dai naji kinyi shiru ko baki gane me magana ba har yanzu,tunaninki bai katse na! (Lalläi wai dama Fans AQEEL yana magana da yawa irin Haka,Amma in da bro ne yace ya dameshi) Bari nai miki gwari gwari "AQEEL ne! Ai Hadiyyah zare idanuwa tayi kafin ƙwarewar Babu gaira Babu Dalili ta biyo baya" Jin ta ƙware sai AQEEL yaji Babu daɗi,sai naji muryar sa yana "Sannu me kike ci ne?jin abunda yace sai tarin ya lafa ta Fara kame_kame kafin tace "Babu komai kawai ji Nayi tarin yazo ne" Gyara kwanciya ya ƙara a karo Babu adadi,dan muryarta tana Masa daɗi ne,fiye da tunanin mai tunani,har da ajiyar zuciya kuma🤔 Ita dai Hadiyyah zuciyarta fal da tsoro da tunanin yadda ALLAH yayi da ita ne, tasan halin AQEEL tasan sunansa, shine wannan mai tsare girar,kamar Baya magana, yai ta Wani yatsine yatsine ga Glass a idanunsa wanda yaƙara Masa kwarjini da kyau, ALLAH ga marainiyar ALLAH ka daidaita mata wannan Bawa da ka haɗasu inuwa ɗaya tun basusan kansu ba, ni ƴar nan wannan ne mijina na Babu! Tunanin da ya addabi zuciyar Hadiyyah kenan tun lokacin da tasan AQEEL shine mijinta. Tunanin ta ya Katse lokacin da AQEEL yace MATA " Inason nasan da wacce ALLAH ya zaɓa mun matsayin MATA ne, shin me shuru shurun ciki kamar kurma ce? Ko kuwa me surutun ciki kamar aku ce? Sai da dariya ta kwacewa Hadiyyah bata shirya ba! Jin abunda Yake faɗa gwanda in yace me surutu kamar aku,Amma idan yace me shuru shurun ciki kamar kurma ai shima Duk ɗaya ne,dan kuwa gwanda Hidayah dashi,dan ganinsu da tayi sau Biyu taga shi ko hirar da suke da Hidayah taga kam shi da ɗan uwansa shi kaɗai yake murmushin sa Amma shi baisan anayi ba! Ya naji kinyi dariya ne ko me shuru shurun ALLAH ya haɗa ni da ita ne? Aikuwa da sake dan sai kin koyo surutu a wajen sis ɗin ki kafin akawo min ke cikin gidana,bazan ɗauka ba ayi shuru kamar kurame labarai zanzo a dinga bani da Hira cikin walwala(lallai Haseena kinji wai AQEEL ne yace zantuka hakan) "Lalläi ma aikuwa nice Yanzu ya za'ayi kenan,banson hayaniya, surutu yana damuwana,sai dai kayi Haƙuri dani a Hakan! Hadiyyah da tsinci kanta da faɗawa AQEEL Hakan(kunsan dama ai ita aku ce baki abun magana kamar yadda AQEEL ya kirata dashi) "Hmmm Zaki zo mun cikin gida a Hakan zakiga yadda zanyi dake ne, wannan bakin saina gyara Shi ko ta tsiya da Arziƙi! Shima AQEEL ya tsinci kansa da faɗar Hakan ALLAH ya taimakeni ni Hadiyyah! da Hidayah ALLAH ya haɗa da wannan data bani Alhamdulillahi! To Amma kuma ya Hadiyyah zata ƙare da wannan mai surutun tsiyar! " Dan ALLAH kayi haƙuri karka tursasani saina iya surutu da magana,kawai kayi haƙuri dani kaji! "Za kigani kizomun gidana a Hakan" inason Inji sunan ki ne,Nasan dai Hadiyyah da Hidayah ne to wacce aciki? "HADIYYAH ce" Lalläi sunan ku akwai daɗi sosai,Amma nafijin daɗin Hadiyyah Duk ma'ana daya ne Amma wajen Furtawa akwai banbanci HADIYYATULLAH Da HIDAYATULLAH Duk ma'anar su guda ce wato KYAUTAR ALLAH kunci sunanku kam ƴan biyu KYAUTAR ALLAH! Ya ƙarasa zancen da murmushi wanda har kunnen Hadiyyah! Wanda itama murmushin tayi, Sannan itama tace Nima sunanku yanamun daɗi musamman naka AQEEL! Lalläi ne to kinsan ma'anar sunan ne? Ya jefa MATA tambayar nan! Yana lumshe idanu,alamun yau fa anjima ana magana,Babu sabo dole ya gaji, dan ma yanajin daɗin Hirar da Abar ƙaunarsa,gajiyar Duk ta kau "Ea Nasan ma'anar Sunan AQEEL (wanda hausawa Suke ɓatawa suce Haƙilu,fatan fans kungane) Sayyadina AQEEL BN Abiy ɗalib yayan Sayyadina Aliyu ƙanin Sayyadina Ja'afar bn Abiy ɗalib "Ma Sha ALLAH lallai ne kinsan ma'anar sunana, ƴar albarka! Saura Sunan bro ɗina!nidai bansan ma'anar sunan sa ba,ban ma taɓa ji ba sai a wajensa! Aikuwa sunansa yana da ma'ana mai kyau shima,zan gaya miki ne! Kinsan wane ya zaɓa Mana sunan? "A'a saika faɗa! Ummuh ce tasa Mana shi da Hassan da Hussain kawai ake Kiranmu! Kingane wacce ummuh ko? "A'a gaskiya to ummuh ku Mana ai Abbu yabani labarin Hakan! "ALLAH sarki Rayuwa kamar ba'a zauna ba, ALLAH yai Musu Rahma gaba ɗaya dai cewar Hadiyyah! Shi kuma AQEEL ya Amsa da Ameen ƴar albarka! _Abun mamaki sun shafe fin awa uku Suna waya! Sai kace sun jima tare Babu wanda zaice a Ranar suka Fara waya, mamaki na yafi ga AQEEL ma shida baison surutu ko ƙadan,gwanda ma Hadiyyah Baki Abun magana ce dama! Sun Sha hira sosai, To dama dai Hadiyyah tunanin AQEEL yai MATA yawa,shi kuma AQEEL ɗin shima wannan vedios ɗin yasa yafara jin Wani abu game da yaran tun sannan,sun rabo kowanne zuciyarsa ciki da nishaɗi da Annushuwa zuciyar AQEEL fal mamakin surutun Hadiyyah Mutuniyar da Bata magana a zahiri ,amma kuma sai mamakin yakau a Ransa shima ai baida magana Amma yanzu yayi maganar sosai ma! Yayi barci cikin nishaɗi da tunanin Hirar da suka yi shida matarsa! Har sannan bro bai shigo ba ko ina Yaje? AKEEL _Shi ma fita can yayi ɗaya dakinsu,dan yasan bro bazai barshi yayi wayar sa cikin kwanciyar Hankali ba,haka zaice ya dameshi da surutu,maganin kar ayi kar a Fara(lalläi AKEEL to shima yanacan yana soyewa daga tsaya,bazai ce ka dameshi na) Dan haka sai da shima ya kammala komai nasa sannan ya kishingiɗe a sofa! Ya rangaɗa Kiran wayar! Gidansu Hidayah yau Baabah itada da su Hunaif da Zeenah harda farouk da Haidar ma da Hafsat sunwa gidan Zahra tsinke can Zasu wuni,shiyasa Gidan yayi shiru, sai Hadiyyah da Hidayah kawaii sai kuma Sa'adatu a ɗakin ta tanacan abun duniya ya dameta, ta saƙa wancan ta kwance wancan,akan Alhaji Gambo dan har Yanzu bata kulashi ko yazo gidan ta ringa Masa hulaƙanci kenan,Amma Baya fasa zuwa Gidan a Ranar kwananta dan ya Bawa Kowacce haƙƙinta,Amma idan yazo Babu kwanciyar Hankali gareshi a wajen Sa'adatu! Ita Hadiyyah tana falourn su tana kallo abunta,lokacin da AQEEL ya kirata, shi yasa tasha wayarta itada mijinta Babu takura. Ita kuma Hidayah tana cikin ɗakin su a kwance Akan gadonsu,lokacin da AKEEL itama ya kirata tana ɗakin! Da AKEEL yaga wayar tana ringing ba'a ɗauka ba har ya fitar da rai za'a ɗauka,zuciyarsa tana bugawa Akan shin wacece daga ciki matarsa irinsa aku! ko kuwa irin bro kurma! Shi kam a zuciyarsa yana Addu'ar ALLAH ya saɓa halaye a waɗannan matan nasu, shi yasamu mai shurun kamar kurma, yakoya mata surutun, shi kuma bro ya samu mai surutun Kamar aku ta koya Masa surutun! ya Zama mutum kamar kowa ba Kullum baki a rufe ba kamar kurma..tunanin sa ya Katse lokacin da yaji an ɗaga wayar! Acan ɓangaren Hidayah kam tana kallon wayar tana ringing Amma miskilanci ya hana ta ɗauka,sai da taji ƙarar wayar ya dameta tana shirin kashe MATA dodon kunne(a cewar ta fa) sai ta ɗaga ba tare da tayi magana ba! Ganin an ɗaga Babu magana ne yasa AKEEL yace " "Assalamu Alaikum fatan ina magana da matana ce? AKEEL ya faɗa yana murmushin sa mai burgewa! Mutuniyar ku taji sarai abunda yace Amma tai burus! Ya dai ko baki ji nane matar! AKEEL ya kuma faɗa,zuciyarsa tana Addu'ar ALLAH yasa mai shuru shurun ce tasa,kuma kamar yaji alamun Hakan indai ba network bane yasa yaji Hakan ba! "Yadai matar ko abun ya tashi ne,ai na ganeki ni a Hakan ma ina maraba da wannan Rashin surutun indai surutu ne idan kinzo gidana na koya miki kinji! Sai a sannan Hidayah tai magana " To baki abun magana Hakan da kayi tabbas ya nunan cewa kaine AKEEL daga kirana a waya har kafara damuna da zancen ka, wanda Babu comma, balle full stop. Lalläi ne ni kike gayawa Hakan, AKEEL ya faɗa haɗe da sakin Ajiyar zuciya jin muryar ta mai Sanyi, "Ko ma dai menene yanzu nidai mijin kine,dole abini yadda nake,kuma surutun nan dai dole kema ki koya ki dinga yinsa,Zama tare dani ai zai sa ki koya,yanzu ma wazaice kece kin buɗa baki kinata surutu! "Kai haka ma zakace mun ina surutu to ai saina kashe wayar kawai! Cikin shagwaɓa Hidayah ta ƙarashe Zancen! "Aimun afwa ranki ya daɗe! Bazan kuma faɗar haka ba! Yanzu dai kinsan sunana ma kin faɗa, nasan sunanku Hadiyyah da Hidayah to waccece aciki Dan ALLAH? "To wannan HIDAYAH ce, ba aku mai bakin surutu bace Hadiyyah irinka ba, ni kam dama ita kasamu. Dana huta da surutun ka!ta ƙarasa maganar cikin ƙosawa "Nikam nayi murna da Hakan ai,dana sameki matsayin MATA ta! Indai surutu na ne karki damu bazai dameki ba,tunda zan mayar dake kalata bada jimawa ba! "Zamu gani kuwa bazaka koyamun surutun ka ba,saidai na koya maka Rashin magana ta Hidayah ta faɗa cikin murmushi jin wannan surutunsa yafi na wancan Ranar! To mu ƙulla alƙawarin Hakan Duk wanda ya rinjayi ɗaya daga cikinmu, idan Kika koma surutu na na ciki wasa,idan nakoma kurma kamar ke ko kincini wasa! Ya ƙarasa maganar sa dariya! "Shikenan na yarda da wannan Zancen, Amma shine kake cemin kurma ko? Cike da shagwaɓa (Lallai Hidayah masu shuru shurun nan sai a barsu sun iya soyayya kalli dai yadda AQEEL shima yayiwa Hadiyyah) Shikam AKEEL jin shagwaɓar da ake Masa ne,yasa wata ƙauna da soyayya tana shigarsa ta wannan tahalika, lallai AKEEL ma da bai damu da wannan ba barshi da surutunsa, soyayya Ruwan zuma. Sun jima Suna hirar su cike da soyayya,wanda rabin hirar Duk AKEEL ne Yake jan maganar ita kuma Hadiyyah sai ta mayar Masa da Amsa! Sun yi Hira mai tarin yawa, AKEEL sai bata labarin vedios ɗin daya Gani yakeyi yana kwasar dariya,itama tagaya Masa cewa ai sunga wannan Vedios ɗin itada Hadiyyah Amma fa sha'anin AQEEL da HADIYYAH yafi kowanne dariyar,sai kuma nasu ta yadda ita ɗin take bawa AKEEL ɗin Haushi na Rashin dariya in anmata wasa,Hakan shi kuma yanasa AQEEL nishaɗi,Duk da a farko shima AKEEL ɗin yaci dariyar shakiyanci a Lokacin da Hadiyyah ɗin take koke_koke bata yarda da AQEEL,shi kuma Hidayah tana yarda dashi! Ansha nishaɗi a ɓangaren wannan masoya Suma kamar sun jima tare, Nikam oum ARQAM sai na nemi shuru shurun Hidayah na rasa,Kodai abunda AKEEL yace na zai mayar da ita mai surutu idan sun zauna waje ɗaya zai tabbata? Tun da dai yanzu gashi a waya ma yafara canza ta! "AKEEL yace wai ke taka mai mai ma ya sunan ki ne na tagwaitaka? Cike da nishaɗi Hidayah tace "Hussaina Mana!Kaifa? AKEEL yace Hussain na Hussaina man,ai sunan mu ɗaya kai wannan abu yamun daɗi sosai matana! Kinga bro shima Hassan na Hassana kenan komai namu iri ɗaya,an Haifemu mu bibbiyu sannan mun Auri mata Suma su bibbiyu ga sunan mu iri ɗaya ma, dama muna da wannan burin nida bro ashe ma ALLAH ya tsara Mana Hakan! Ya ƙarasa Zancen Cikin Nishaɗi! Suma sun jima Suna Hirar har wajen 11:00 na dare, dan Basu Fara wayar ba sai wajen 9:00 sunyi Sallama cikin ƙaunar juna kamar bazasu rabu ba. Tana kammala wayar ta kashe kayan kallon tayi ɗaki Abinta zata kwanta, dan su Baabah Basu dawo ba ba har sannan maybe sai nan gaba Ibrahim mijin Zahra ya kawosu har gida. Ta tarar da Hadiyyah a kwance tayi barci,Dan ita wajen 8:00 suka Fara wayarsu wajen 10:00 suka kammala,itama Azkar tayi ta kwanta abunta. Bata jima da kwanciya ba mota tai horn alamun su Baabah sun dawo, Mai gadi ya buɗe musu gate(Alhaji Gambo ne yakawoshi saboda idan yana gidan inzai shigi Babu mai buɗe Masa) kowanne yana shigowa makwanci ya nema an raba dare a Hanya. AKEEL yana kammalawa waya da Abar ƙaunarsa kawai sai ya tashi daga sofa,ya shige cikin ɗakinsu na barci domin ya kwanta anan kawai. Lallai ne yau soyayya tayi daɗi abunda Basu taɓayi ba shida bro raba makwanci yau sunyi sanadin ƙauna. A Masallaci suka haɗe da bro sai hararar sa yakeyi,Akan shine yau ya Kwana a ɗaya part ɗin alhalin yasan basa Hakan,abunka da mai surutu nan ya gaya Masa cewa Hira da matarsa ce tasa shi Hakan ko kunya bai jiba! Ko da Yake basa ɓoye wa juna komai! Shima AQEEL ɗin ya gaya Masa yadda sukayi da tasa matar Amma baice sun jima Suna waya ba,kawaii dai yace sun gaisa,ko da Yake bro ai dai zai Gani tunda ɗaki ɗaya suke kwana. "A wajen breakfast Abbu yake tambayar AKEEL ya sun Kira yaran kuwa? Baki Abun magana wato AKEEL nan ya Bawa Abbu labarin yadda sukayi cikin nishaɗi,harda AQEELshima yadda sukayi. Abbu yana ganin yadda ɗan sa yadda Yake fara'a yasan tabbas yanason Yarinyar! Idon Abbu yanakan AQEEL yaga yadda shima fuskar sa sake take ,aikuwa yaga yana Wani makirin murmushi wanda bana komai bane illah na shima yanason Yarinyar ne,Amma kuma miskilanci da zurfin ciki ya hana ya nuna kamar yadda ɗan uwansa yake nunawa,cikin zuciyar ABBU murna da godiya ga ALLAH ne da ALLAH ya haɗa ƴaƴansa da abunda sakeso,da kuma cikar burin marigayi Amininsa Ammar ALLAH Kenan mai yadda yaso. Abbu ya nunawa Mommah AQEEL na murmushin da yakeyi, Mommah da Abbu suka haɗa ido Suna murmushi na jin daɗi, Mommah take "my son meke faruwa kake murmushi kai kaɗai ne tun ɗazu? AQEEL baisan ma tana magana na zuciyarsa tana can tunanin masoyoyar sa Hadiyyah ne, Abbu yace Mommah ta ina AQEEL zai jiki yanacan ya faɗa shauƙin soyayya! AKEEL ya taɓo AQEEL tun farkon maganar Mommah! maganar da Abbu yayi kuma a kunnen AQEEL dan haka yanajin Abunda Abbu yace sai ya Mike yana murmushi alamun kunya yabar dining ɗin,sai gaba ɗaya akasa dariya! cikin nishaɗi suka kammala breakfast ɗin kowa yakama gabansa. ABBU ya yanke shawarar zuwa wajen Kawu Isma'il Akan Zancen. ____GIDAN JIMMAI__ Usman kam zaman gidan baya masa daɗi kwata kwata, jimmai bata kulashi balle Shukhra,da Daddy kawaii yake Zama yai taiwa yaron wasa ko yai Masa home work, sai ya fita yake samun sukuni, abokansa kam sunga canji ga Usy yanzu bai kula MATA ko wucewa ƴan MATA sukazo yi sai ya kau da kai, ga ramar da yayi sunyi tunanin cutar da yayi ce tasa shi yana warwarewa zai koma ruwa(ALLAH sarki bakusan Usman yanzu ya shiryu na duniya ta bi dashi) Yana zuwa can gidan Umma itama Duk da na wai Wani kulashi takeyi ba, insun zauna ta dinga Masa nasiha ne Akan ya kiyayi duniya ga dai yadda tai Masa,yaci gaba da istigfari da neman gafarar jimmai da Shukhra ɗin, Usman cikin damuwa yace "umma kullum saina Basu haƙuri na nemi gafara Amma basa kulani,kaci gaba da Basu haƙurin kasan abunda Kayi Hukuncin da yafi hakama an maka, Amma kaci gaba da neman gafarar yau da gobe sai ALLAH,kuma akwai ƙaunar ɗa da mahaifi tsakaninku da Jimmai haka na itama Shukrah akwai ƙaunar ƴan uwantaka da shaƙuwa mai Zafi,sa Sannu komai zai wuce ne. Waɗannan zantukan da suka tattauna da Umma sai yaji zuciyar tayi Sanyi, ya ɗauri ɗamarar cigaba da neman gafafar su, ya ƙudircewa Ransa zaije har gidansu AKEELA da AKEEL da kuma AQEEL ya nemi gafararsu dan yasan Abubuwan bazai tafi daidai ba in bai nemi gafararsu ba. Tun daga Ranar Usman ya dage da istigfari da Hailala da salatin Manzon ALLAH, da tsaiwar dare da neman gafarar ALLAH Akan zunuban da ya aikata a Baya, kusan dama shi ALLAH gafurur raheem ne yana amsa Addu'ar bayinsa ne masu neman gafarar dan haka........ Yasin nagaji wai wannan typing me tsayi haka ku tara next page gaskia dan kuji ko mene zai far...... Yawan Comments ne next page kuma🥱 ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 6/30/24, 10:47 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM} 08128131163 Marubuciyar Komai nisan jifa Hakan ba kuskure bane ____________________ *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A* ____________________ *PAGE SIXTY ONE 61* Kwana biyu kunjini kurum🌝 yasin ina busy ne🥱baku ba Nima na ƙagu🥹 na kammala Cikin ikon ALLAH🙏, ai wannan Littafin yasha jinkiri ALLAH yasa ma Alkhair ne😩 tun 1/1/2023 fa na Fara shi😳 bansan Ranar gama shi ba kuma amma dai saura ƙiris👌 _______ABBU_______ " Kamar yadda ABBU ya ayyana a Ransa Hakan yayi,kwana biyu tsakani ya dangana ga gidansu Hauwa wato wajen kawu Isma'il. Sun tattauna zantuka da yawa,ciki harda yiwa kawu Isma'il Albishir da cewar ya biya Masa ragowar bashin da banki Suke binsa, shiyasa ma tun sallamarsa Daga Asibiti Basu kawo masa ziyara, Abbu yace Masa "saura kwana biyu a sallameka naje bankin nasa Hannun Akan zan biya maka cikon bashin,yanzu in ALLAH yakaimu Monday tunda yau Saturday zamuje banki na Basu ragowar kuɗinsu in yaso sai ayi rubutu,kasa hannu nasa" ALLAH ya kiyaye gaba" Sai ga kawu Isma'il yana Kuka wiwi! Gwanin tausayi yana tawa Abbu Addu'a ta Alkhair da Fatan ALLAH yayiwa zuri'a albarka!cikin kukan yake cewa " ALLAH kenan me yadda yaso da bayinsa ALLAH na tuba yaran dana dinga cuta na daƙilewa Rayuwa SABODA son zuciyata sune yanzu sanadinsu ALLAH yakawo mun Ɗauki, Nikam Isma'il naga rayuwa tabbas nasan cewa Ɗa na kowa ne,bakasan wanda zaka mora ba,wanda ka kyautatawa sai ALLAH yaso ya kyautata maka, ALLAH ya gafartawa Yah Ammar! Ka yafemun cin Amanar dana maka, ta tozarta ƴaƴanka, yanzu gashi ALLAH ya nunan iyakata tun ba'aje ko inaba, su ɗin ta sanadinsu da arzikinsu rayuwata zata ƙarasa na tuba" Ganin Irin kukan da kawu Isma'il yakeyi sai da Abbu ya tausaya Masa yasan cewa tabbas Isma'il ya dawo Hanya madaidaiciya! Gyaran murya Abbu yayi sannan yace " ya isa Hakan Isma'il kukan na menene kuma? Kasan halina da kake ciki ko? Baka da LAFIYA,dan haka ka saurara kanka,komai ai ya wuce ko? To ALLAH ya kiyaye gaba,ya karɓi tubanka! Cikin shashsheƙa kawu Isma'il yace "To shikenan Alhaji adaina Amma abunne yazo mun a bazata,dole Nayi kukan murna,kullum cikin tsammani da tashin Hankali nake,na jiran sammaci daga kotu ƙarshe kuma a miƙani GIDAN gyaran Hali! Kawu Isma'il ya ƙarasa da share hawayen nadama! " Komai ya wuce ai shiyasa ma nazo wajenka na gaya mata na biya maka,SABODA nasan hakan zai zame maka barazana ga lafiyarka! Duk irin tattaunawar da su kawu Isma'il da Abbu sukeyi a kunnen Hauwa wanda tabasu guri dan kuwa bai kamata ta zauna Suna magana ba,jin Abunda suka tattauna cikin murna take gayawa innarta jin Abunda Alhaji tallafy yai Musu, wannan ai ba baƙon abu bane,a garesu sunyi murna Suma da fatan gamawa LAFIYA! Yanzu haka tun zuwansa Unguwar Duk da basaja yayi bai ɗauko bodyguard ɗin sa ba ,hakana ba motarsa me number ya ɗauko ba,da Yake akwai mutane a ƙofar gidansu Hauwa ɗin sai da WANI Mutum yaganshi Aikuwa " sai gashi la Alhaji tallafy ne ai ALLAH yaƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, shine da ƙofar gidansu Hauwa yanzu haka ya cika da hayaniya da jiran fitowar ABBU, yanzu haka hayaniyar Har cikin gidan. Again Abbu Yaiwa kawu Isma'il Albishir da mallaka Masa ɗaya daga cikin gidajen da ya mallaka da suke Na'ibawa, kai ma Sha ALLAH gidan yayi kyau sosai Babu Abunda kawu Isma'il ko Hauwa zasu je dashi na Amfani in ba kayan sawa ba,ya kuma Bashi jarin da zai cigaba da kasuwancin da yafi wayo Akai wato shaida Dabbobi yana rabawa mahauta Suna yankawa su Bashi kuɗinsa! Waɗannan Abubuwan Alkhair da Abbu Yaiwa kawu Isma'il Albishir dasu faɗar farin ciki ko godiyar da kawu Isma'il Yaiwa Abbu Alƙalamina ni Oum ARQAM yasin bazai iya rubutawa ba domin sai ya karye,ku kimanta my Fans. Ganin irin ruɗewar da kawu Isma'il yayi tasa ABBU baiwa kawu Isma'il zancen Shirin Bikin Kece raini na su Hadiyyah ba yabari zuwa Monday ɗin Lokacin kawu Isma'il ya shiga nustsuwar sa,dan Abbu yanzu Yaga kawu Isma'il ya shigo shock da murna na kuɓutarsa daga tsaka mai wuya,Haka Abbu yabar gidan yanashan addu'a wajen iyayen Hauwa da Hauwa balle kawu Isma'il kuma, haka ya fita ƙofar gida daƙar yasamu ya bar unguwar SABODA cikowar mutane,kuma Saida yayiwa kowanne Alkhair, Alhaji tallafy kenan irin murnar da jama'a suke in sun ganshi abun ba'a magana ko sarki sai haka,bakomai yasa Masa Hakan b sai Alkhair da yakeyi, (ALLAH kabamu ikon aikata Alkhair a koda Yaushe kodan Ranar mutuwarmu ma samu shaidar Alkhair,yanzu kam nasan Abbu ko mutuwa yayi ai shaidar Alkhair ce zata isheshi kuma dama haka akeso🙏.......oum ARQAM✍️) ______Gidan Alhaji Gambo_____ "Cikin ikon ALLAH cikin Hajiya suwaiba yakai wata tara harda kwanaki ma,Abun gwanin tausayi Duk ta canza ta kukkumbura to ya ilayi Haihuwa ga wanda ya taɓa ma ya yacika balle baka taɓa ba ga jiki anfara ɗan Jan shekaru ALLAH yakawo dole aji jiki, Duk da abun ba'a nan yake ba. Cikin ikon ALLAH yau ta Tashi da naƙuda Amma Abun yaci tura,sai Suma take tana neman gafarar abokan zamanta,itama Hajiya Sahura ciki fa ya girma wata bakwai fa! Amma da sauƙi ita SABODA itace ƙarama acikinsu dama Hajiya ikilima ce uwar Gida. Alhaji Gambo dakansa ya ɗauki suwaiba zuwa asibiti tare da ikilima Anbar Sahura a gida. Tunda sukaje Asibitin ake Abu ɗaya Haihuwa shiru, likitoci suka ce saidai ai mata C's karfinta ya ƙare ɗan cikinta ma ya galabaita, an shiryata zasu shiga ɗakin tiyata ta farfaɗo! Alhaji Gambo sai Kuka yakeyi ya ƙara imani da tausayawa MATA, riƙe Hannun ikilima tayi cikin Kuka "ki riƙe Duk ABunda na Haifa ikilima na bar miki shi duniya da lahira,Nasan bazan Tashi ba,Alhaji ka yafemun ina neman alfarmar ku nemar mun gafara a wajen Sahura,hakanan Sa'adatu itama..... A haka dai aka gurgura gadon suwaiba zuwa ɗakin tiyata. Cikin nasara Anyi sa'ar ciro Ɗa namiji ma Sha ALLAH! An fito da Suwaiba daga ɗakin tiyata zuwa ɗakin wutu, Ƴan uwnta sai rige rigen karɓar jariri suke,anata cewa ashe da rabo Suwaiba zata Haihu, hakama Alhaji Gambo sai barka ake Masa! Amma ikilima da Alhaji Gambo jikinsu a sanyaye suke tun daga wasiyyar da Suwaiba take bayarwa, to amma ance tana lafiya,barci ta samu ne' shine ɗan hankinsu ya Kwanta, ba sosai ba Alhaji ya ɗauki ɗa yai Masa addu'a itama ikilima ta ɗauka sai da hawaye ya zubo MATA,tana tunani a Ranta ko itama tana da rabo? Alhaji Gambo Gidan Sa'adatu Yaiwa tsinke nan ya gaya MATA cewa suwaiba ta sauka an samu ɗa Namiji, Yanzu haka Abincin yakeso ta girka zaikai Asibiti, saboda ikilima ce a wajenta,ita ma Sahura batajin daɗi ne itama saura ƙiris,Karku manta Fans Sa'adatu batasan da samuwar waɗannan cikin na suwaiba da Sahura ba,lokacin tana kan bala'in ta bata Kula Alhaji Gambo suyi maganar arziƙi balle ya sanar da ita" Jin abunda Alhaji Gambo ya faɗa ai sai ga Sa'adatu ta miƙe tsaye da a Zaune take ko nuna da mutum a kusa da ita da maganar da Yake bata saurara ba da! "To maci Amana wanda bai san mutunci ba ba ɗan halak ba kaikam uwarka da ubanka sunyi asarar Haihuwa! Har kana da bakin da zakamun maganar cewa suwaiba ta Haihu,Gani mayyah zan cinye ta ita da ɗanko? baka gayan ba sai naji Haihuwa ko? To baza Ayi girkin ba butulu watsatstse kawai" Zuciyar Alhaji Gambo tayi baƙi jin munanan kalaman da Sa'adatu take jifan shi dasu,bakinsa a buɗe! Kafin yafara magana! Duk da yana cikin damuwa da firgicin farfaɗo war Suwaiba,saboda wasiyyar da ta dinga bayarwa,Amma Duk da haka sai da ya Kula ta "Ke Yanzu Duk maganganun da Kika jefeni dasu ai kece Kika dace da Hakan,karki manta fa Ikilima Ƙawar kice Kika Aure ni,hakanan yadda akayi akai Aurenki da Alhaji Ammar ai na Sani,ga kuma Wani abun kunyar Auren Isma'il da kikayi Hauwa fa babu wanda yake tsakaninku sai ALLAH amma kikaci Amanarta Kika Aure MATA miji, da Yake yin bana ALLAH bane ba'a je ko inaba gayyar ta watse! Nima cika yaudareni na ɗauko wa kaina kara da kiyashi, Ko Alhakin Ikilima bazai barni ba dole akwai SAKAYYAH,tunda na aureki ban huta ba,Babu kwanciyar Hankali tare dani, Ballagaza kawaii! Alhaji Gambo ya ƙarasa zancen da sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya wanda ko Babu komai yau dai ya nunawa Sa'adatu bafa tsoronta yakeji ba,yana ƙarasa maganar ya ɗau hanyar barin gidan! Aikuwa Sa'adatu jin kalaman da Alhaji Gambo ya yaɓa MATA! Tai kukan kura ta shaƙi wuyan rigarsa tamau ta murɗe kamar zata kaishi lahira! "Ai komai zaka faɗa min butulu kufan wuta!matsiyaci sake ni Yanzu dan kuwa Zama Tsakanin ni dai ayau ya ƙare! Idon Alhaji Gambo fa yayi jajur! Ina bakin magana ma se gumi Yakeyi? Daga can yai kukan kura ya warɓar da Sa'adatu gefe! Ya riƙe wuyansa ya kama tarin wuya!sai da yadawo Ɗan hayyacinsa tukunnah yace " ai basai kinmun haka da nasan cewa ke ƴar Akuya bace, kije na sakeki....na sakeki...na sakeki saki uku kenan! Banza ƴar wahala in Sha ALLAH sai Kinga SAKAYYAH Duk wanda Kika cuta sai ALLAH ya saka Mas...... Tun warɓar da Sa'adatu da Alhaji Gambo yayi taji zafi! Dan haka yana tarin dawowa hayyaci ta miƙe da ƙar da nufi kitchen ta ɗauko wuka taiyo kansa gadan gadan da ita! Bai ƙarasa maganar da zaiba ganin Sa'adatu da wuƙa a miliyan yabar gidan,Acan yabar motarsa..... Sa'adatu hawayen baƙin ciki take! Lalläi ma ita Gambo zai wa haka! Ashe suwaiba da Sahura ciki ne dasu,in Sha ALLAH sai ɗan suwaiba ya mutu,ita kuma Sahura idan tazo Haihuwa ta rasu! Addu'ar da Sa'adatu takeyi kenan! Alhaji Gambo Gidansa na Asali yakoma wajen Hajiya Sahura,koda Yaje ya sameta cikin zulumi da tunanin ko ya suwaiba an haihu? Dan Duk a kiɗime suka fice shi Alhaji da ikilima anan gida suka bar wayar su, 'Ya dai Alhaji fatan Suwaiba ta sauka? "Ƙwarai dagaske an samu ɗa Namiji,an MATA C's, Yanzu ma naga bakijin daɗi Abinci za'a musu akai can Asibitin, sai kuyi keda su dela da mero(ƴan aikin gidanne)ya ƙarasa zancen zuciyarsa a cunkushe da baƙin cikin da Sa'adatu ta yarfa masa, Alhaji fatan dai tana lafiya? Idan an kammala Abincin sai mu tafi baki ɗaya,naga idanunka yayi ja ne! Sahura ta ƙarashe maganar da duban fuskar Alhaji Gambo! Babu komai Sahura kawai dai Farko da tayi jinkirin Naƙuda ne nashiga damuwa Amma yanzu Alhamdulillahi ya ƙarasa zancen da kawar da damuwar da Sa'adatu ta jefa shi. Cikin ƙanƙanin lokaci aka kammala Abincin,Alhaji Gambo ya aika direbansa gidan Sa'adatu ya ɗauko motar da ya bari acan. Acan Asibiti kuwa Suwaiba ta farfaɗo cikin ikon ALLAH aka nuna MATA ɗanta tai Masa Addu'a, sai kuma wasiyyakafin daga bisani Numfashinta ya ɗauke gaba ɗaya,Rai yayi Halinsa innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun ALLAH ya karɓi shahadar ki, A daidai lokacin da ƴan uwanta da Hajiya ikilima Suke kukan rabuwa da Suwaiba sannan su motar Alhaji Gambo ta danno cikin Asibitin,ai ganin Suna Kuka ba sai angayawa Alhaji Gambo abunda ya faru ba, Tashin Hankali da ba'a saka Masa Rana. Faɗar Halin da Alhaji Gambo ya shiga da rasuwar Hajiya suwaiba ɓata baki ne,hakama Sahura ga ciki ajikinta ga Tashin Hankalin abunda yai ajalin suwaiba itama shine ajikinta,Ko itama Hakan ce zata faru da ita? Jininta yai mummunan Hawa, ga kumburi. A haka aka ɗau Hajiya suwaiba zuwa gida aka sallaceta aka miƙa ta zuwa gidanta na gaskiya (ubangiji ya kyauta ƙarshen mu....✍️oum ARQAM) Haka aka cigaba da karbar gaisuwar Hajiya suwaiba (haka dama rayuwa take ALLAH yayi suwaiba zata Haihu wanda take damuwa da Rashin haihuwarta to amma kuma gashi ALLAH yabata Haihuwar ashe ba itace zata raine shiba,saidai wata,Amma ai da Daɗi tunda za'a dinga tunawa da ita kuma tabar mai MATA addu'a) Haka gidan yazamo shiru yaro yaci sunan Abbas kuma yana wajen Hajiya ikilima kamar yadda uwarsa tabata shi, sai fatan ALLAH yatayata riƙo,aikuwa ta riƙeshi Hannu biyu kamar ita ta haifeshi, Farko madara aka Fara Bashi daga ƙarshe Hajiya ikilima ta nemo magani tayi wanka Ruwan nono yakawo aikuwa tafara shayar da Abbas cikin Aminci(ALLAH sarki Rayuwa ikilima bada Haihuwa ba Tasamu Yaro daga sama,dama abun haka Yake ALLAH yasa idan da rabo kema ki samu naki) Sa'adatu fa taji Haushi sosai ko gaisuwar Hajiya suwaiba batazo ba, kuma bataiwa Alhaji Gambo gaisuwa ba. Su Hadiyyah sunyi baƙin cikin Rabuwar Sa'adatu da Alhaji Gambo,Duk da bata faɗa Musu asalin mene ya haɗa ba, Ranar da akayi gurmi basa Gidan gaba ɗaya,sun kaiwa Zakiyyah ziyara ne, sai da suka faɗawa mazajensu kafin su fita,dan kuwa lokacin shaƙuwa da soyayya a waya ta ƙaru tsakaninsu Duk da har yanzu Basu zo garesu ba,Suna shirin kawo musu ziyara ne, Haka gidan yakoma yanzu Babu Namiji. Hajiya Baabah takoma Kaduna ita dasu Hunaif da Zeenah saboda school,ita data dawo sai ALLAH yakaimu bikin su Hadiyyah. _____GIDAN MUKHTAR_____ Gidan zaman lafiya kenan! Tunda cikin Zakiyyah ya isa Haihuwa Bilkisu ta ɗauke MATA komai na Aikin da takeyi, wanda ita Zakiyyah ɗin ba haka taso ba,to amma ya ta iya Dole ta haƙura,saboda wahalar da takesha da Cikin tunda yai wata bakwai, yai Wani Irin girma ga nauyi, gashi mukhtar yace baison scanning ALLAH yakaimu Haihuwa anga ko menene ma! Idan Zakiyyah ta zauna daƙar take Tashi ga wata ƙiba data ƙara ta mamaki! Yau Zakiyyah ta Tashi da naƙuda,karku manta dai Su Haseena da seerat da Aisha Sulaiman Bilkisu nurse ce ko? To dan Haka cikin nasara Ta taimawakawa Zakiyyah da taimakon ALLAH ya Haihu lafiya ta sulluɓo tagwayenta maza masu tsananin kama da juna kamar su ɗaya da mukhtar, faɗar murnar da wannan Ahali sukayi ɓata baki ne! Haka Zakiyyah da taimakon Bilkisu ta gyara jikinta! Haihuwar tazo MATA da sauƙi , hakama babies! bakin ABIE da yaƙi rufuwa Ganin an samo musu sabbin babies har guda Biyu,itama little sai murnar ganin yara takeyi dan kuwa akwaita da son Yara! Kafin Rana tayi sai zuwan barka akeyi,hakana Hajiya Jamila(maman mukhtar) sai murna takeyi da godiya ga ALLAH ta dauwamar farin cikin mukhtar da daidaituwar zaman lafiya na matansa,itama tazo wajen ganin jikokinta biyu kyautar ALLAH............ Kawarku dai seerat da Aisha Sulaiman da Haseena an sauka saiku shirya zuwa barka Wayyo Hannuna yasin nagaji hakanan Muje next page ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 6/30/24, 8:56 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (babbar musiba) Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM} 08128131163 Marubuciyar Komai nisan jifa Hakan ba kuskure bane ____________________ *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A* ____________________ *PAGE SIXTY TWO 61* Lalai ne su seerat da Haseena d Aisha Sulaiman an tafi kwari market da wambai market dake kano siyayyar kayan da zasu saka na sunan ƙawarsu Zakiyyah da gudunmawar da zasu baiwa ƙawarsu😊 ______USMAN______ "Addu'a bata faɗuwa ƙasa a banza,Yau da gobe tafi ƙarfin wasa neman gafarar da yaje wajen Jimmai da Shukrah yana Kuka! Tasa har suka daina ƙin kulashi idan yana kukan Jimmai tana cemai "hakan ya isa ka tashi kai tafiyar ka, ALLAH ya yafe maka ya shirya ka! Sai shi kuma Usman ɗin yace "Ameen Maama" zuciyarsa tana Masa Daɗi da Hakan da da bata kulashi kuma fa! Itama Shukrah idan yana MATA magana da neman yafiya sai tace Masa "Kadaina Kuka Yaya komai ya wuce ALLAH ya yafe maka" Nan ma sai yace "Ameen little sis" sunan da Yake kiranta dashi tun a da. Tun daga sannan kuma sai ya samu salama a zuciyarsa yakan shiga ɗakin Jimmai ya zauna duk da dai ba Wani Hira suke ba, Amma da da zaman gidan Yake Masa Zafi fa. Tuni Shukrah sun kammala exam sai shirin fitowar sakamako me kyau, Shi kuma daddy yana zuwa school Abunsa,sai murna yakeyi Abbansa ya dawo(Ai haka Daddy yake cewa, dama yana damuwa da Rashin Abba a gidansu,kowa Abokansa yana cewa Abbansa yai mai kaza yai mai kaza Amma shi Babu, Yanzu kuwa yasamu Daddy shi yasa yake ta murna...Nikam oum ARQAM nace Daddy aikuwa Abbanka na gaskiya ne Wannan ko ba haka ba Fans) Tunda Shukrah take zaman gida ba school sai Hakan yafara Bawa Jimmai tsoro,wai kar Usman yakuma aikatawa Shukhra abunda yai MATA baya(tsiyar aikata Zina kenan haka take ko mutum ya shiryu da zarar an ganshi da MATA ko ya keɓe dasu sai Ayi tunanin aikatawa yakeyi, ALLAH yarabamu da Aikata Zina) dan haka yau da ya shiga su Gaisa Jimmai take cemai "Nifa zaman gidannan dakai tsoro yake bani, dan haka ka samu wajen komawa,bazan iya zama dakai da acikin gidannan da Shukhra ba, tunda kai baka sa tausayi da Imani! Jin furucin da Jimmai tayi sai da Usman yasa Kuka " illar zinah kenan maamah, Amma ni yanzu ko wata mace aka bani me zan MATA Maama,Ai sai mace halal ɗina, wanda nake tsoron me Aure na a Yanzu dan babu macen da zata zauna dani tasan bana Haihuwa,sai ya ƙara ƙarfin Kukan nasa! Ɗa da mahaifi sai ALLAH sai da Jimmai taji Wani abu a Ranta da kukan Usman! Ko me yafaru kaine kajawowa kanka ai!DUK wanda yabi son zuciyarsa ƙarshen sa Nadama ai, ALLAH ya yafe maka dai,zancen matar Aure kuma tunda da kuɗin ka bazaka rasa ba,ai za'a samu wacce tai auren Farko bata Haihuwa saika aureta ku rufawa kanku asiri(lallai ne ALLAH yasa asamu Nikam, Usman fa yana da matsala ta wannan fannin,kyanta yasamu mai Rauni itama). Hakan ne Yasa Usman tun daga Ranar ya ƙauracewa zaman Gidan, sai Dare yake komawa gida,saboda Hankalin Jimmai ya kwanta! Jikin Jimmai Alhamdullillahi Yanzu tana miƙewa ta ɗan ɗingisa,tana tafiya ba sosai ba,kuma tana kula Usman duk da ba kamar da ba! Hakanan Shukhra itama tana kulashi sosai,bazadai su koma kamar da ba ai abun da kamar wuya! Yo to dama Dukiyar da Mahaifin Su Usman ya bar Musu tun bayan rasuwar Baba mariƙinsu, da ɓacewar Usman yasa Umma ta Bawa Junaid!ɗan yayarta da take wajensa yanzu,Yake juya musu dukiyar, tasu,Amma Yanzu tunda Usman ya dawo kuma ya nutsu,umma take shirye shiryen dawo wa da Usman dukiyarsa Hannunsa,ta Shukhra kuma aci gaba da juya MATA ana samun riba. Cikin Aminci Usman ya karɓi dukiyarsa, ya sai gida mai kyau yana laluban Matar Aure, Ya sai mota mai kyau ma. Ya Gina ƙatuwar plaza yasa haya, hakanan ya buɗe manyan shaguna ya zuba kaya yana siyar da wayoyi,caza,power bank, earpiece, da dai sauran abunda yashafi waya, ma Sha ALLAH Anata samun costumer, ya buɗe Branch Biyu yanzu haka. Takanas ya ɗauki Jimmai har Gidan Abbu neman yafiya! Fa fur aka hanasu shiga gidan, Saboda tuni Malam sallau Abbu yai Masa alkhair da yawa ya bashi jari ya yalwata Masa,inda shine ai zai san Su Jimmai ɗin. Securities ɗin bakin gate ɗin Gidan Abbu ,sun hanasu shiga,Saida Usman ya fito daga mota,A bakin gate ɗin Gidan, saboda horn daya damesu dashi ne yasa,suka leƙo daga cikin gidan, ko Alfarmar matsawa jikin gate ɗin ba'a bashi dama ba, yadingi musu magiya ko kallonsa basuyi ba daga ƙarshe ma suka koma cikin gidan. Zuciyar Jimmai fal nadama ganin Abbu ya kuma tsantsara gidansa ya ƙara girmansa da gidajen maƙotansa ya Basu wasu gidajen, duk matakin NASARA da Abbu da dukiyarsa Jimmai ta sani, nadama takeyi ,ita burinta ma Abbu ya yafe MATA, saboda tayi nadama Yanzu. Usman ni ba number Ɗalhat ba kaima Hakan,balle mu kirashi da Sauran ƴaƴansa ma,kawai mu juya gida,kaje can Foundation Ka samo Mana number ɗin sa in yaso muyi magana dashi,daga baya idan yasanar da securities ɗin bakin gate sai mu shiga! "A'a Maama mu jira ko ALLAH zaisa Wani yafito a gidan sai mu samu mafaka. Abbu yau Monday yana gida, fitowa yayi domin tafiya wajen Kawu Isma'il suje banki,kamar yadda suka tsara. Yana fitowa sai ya tarar securities ɗinsa a bakin gate kamar Wani abu na faruwa! Bodyguard ɗinsa suka taso zasu buɗe Masa mota, ya ɗaga musu hannu bada wanda zanje tafiyar sirri ce! Securities Suna ƙarasowa cikin gidan Yake tambayarsu meke faruwa a wajen da suka fita? Nan john ya zayyanewa Abbu yadda sukayi dasu Usman, ABBU sai ya shiga tunanin ko si wanene? Kawai ya yanke shawarar cewa a buɗe Musu su shigo? Sai ABBU yakoma cikin gidan ya fasa fitar! Sai ya gana da baƙin( Abbu yanada haka Baya hulaƙanta Duk wanda yazo nemansa) Security ɗaya Yaje yabawa Usman damar shigowa da motar sa,lokacin har Usman ya yanke tsammanin shawarar maama a barin wajen,dan haka cikin. Rawar jiki ya tashi motar ya cilla hancinta cikin gidan bayan security ya zuge musu gate? Sai da Usman yai parking inda ya kamata, sannan ya riƙo Jimmai ya taimaka MATA ta fito, ya riƙeta a hankali! Da taimakon ma'aikatan gidan suka shigar dasu falourn baƙi na Gidan,Mai aikin Mommah ta sanar da ita akwai baƙi, Babu Wani ɓata lokaci irin na wanda suka ci suka tada kai, Mommah ta fito, zuwa taga baƙin ta, cikin fuskar alamar bata gane ko su Wanene ba suka Gaisa, Jimmai ta yaba da Matar da Ɗalhat ya Aura! Dan haka Jimmai tace "Jimmai ce ƙanwar Mahaifiyar su AQEEL (kuji fa Haseena da seerat da Aisha Sulaiman,dama tasan da Hakan) " ALLAH sarki Sannu ya jikin kuma naga bakya jin daɗi ma,Cike da jin nauyi Jimmai ta amsa da yawwa! Usman ya gaisa da Mommah cikin girmamawa,itama ta Amsa (Mommah ta gane Usman tunda Jimmai tai bayanin wacece ita) Mommah waya ta Kira Abbu ta shaida Masa ko su Wanene suka zo, zuciyar Abbu kamar zata fashe tunu Abubuwan da Jimmai tai Masa Amma daya dingi addu'a sai yaji abun yafara sauka, Dan Haka yaƙaraso falourn cikin zati,ya samu kusa da Mommah ya zauna fuska Babu yabo Babu fallasa, Jimmai ta gaisa da Abbu kafin tafara Kuka tana neman gafararsa "ka yafemun Ɗalhat naga ishara a duniya Duk sanadin Alhakin ka dana ƴaƴanka.......nan ta kwashe komai daya sameta bayan barin gidansa da abunda yasamu Usman ɗin shima ta zayyanawa Abbu,mene baƙon Abbu abinda ya sameta da Usman ne kawai bai saniba dan haka Abbu yace "ALLAH ya yafe Mana gaba ɗaya, kinga illar cin amanar zumunci ai, ƙarshe Halin da kikaso jefa ni kinga ni akanki, Yanzu me gari yawaya ace ɗan ki yaiwa ƴar ki ciki ta haihu ai abun da kamar wuya! ALLAH dai ya kiyaye gaba kawai,"Kinga dai Yanzu Duk ƙula ƙullar da kikayi na rabani nida Amininsa Ammar komai ya warware, yanzu haka ƴan biyunsa ne ke Auren su AQEEL wanda tun a wancan lokacin aka Ɗaura, Yanzu shirin tarewa Akeyi, Da Duk wata nasarori daya samu saida ya zayyanawa Jimmai,itama AKEELA ALLAH yakawo mata mijin Aure, Doctor Najeeb dai ta sanshi ai, da tare za'a haɗa Auren danasu badon shi AQEEL ɗin da Yake da matsala ba! "ALLAH sarki ƴaƴana Suna Inane in nemi yafiyarsu, musamman AKEELA da AQEEL jimmai ta faɗi cikin kuka da nadama haɗe da face Majina! Shima Usman cikin kukan nadama ya zuba gwiwa a ƙasa yafara neman yafiyar Abbu! ABBU ya dafa kansa yace " ALLAH ya yafe Mana gaba ɗaya, Halin mahaifiyarsa nason zuciya yajefa ka a Wannan Halin tashi ka koma ka zauna a kujera! Mommah again kiran AKEELA tayi a waya tace tazo babban falour, minti Biyu AKEELA bata ƙaraba sai gata, Kusa da mommah ta zauna! Cikinta a sanyaye dan kuwa tagane Usman da maama Jimmai! Tana ƙarasa Zama Jimmai ta Fara Kuka da neman gafarar ta,shi ma Usman haka! Sai da AKEELA tai Kukan tuna irin uƙuba da azabar da Usman ya gana mata,Amma sai tayi tunanin ai komai ya wuce Yanzu,yada tada Usman da Jimmai tabbas sunyi nadama, ta tuna gudun tozarcin miji idan ya sameta ba a budurwa ba to ALLAH yai MATA liɗifi likitan da ya MATA aiki yasan komai, yasan iftila'in daya sameta Hakan data tuna ne yasa zuciyarta ta ɗan yi Sanyi! Tace " ALLAH ya yafe Mana gaba ɗaya AKEELA ta faɗa muryarta da alamun kuka tana ficewa daga faloun. Zuciyar Jimmai da Usman tayi Sanyi jin cewa AKEELA ya yafe Musu duk da bata kallesu da idan kulawa ba! AQEEL da AKEEL sun fita basa Gida Sannan,cikin ikon ALLAH Kafin tafiyar su Usman sun dawo, mommah ta kirasu a waya sukazo falour Suma nan dai Usman da Jimmai suka nemi gafarar AQEEL cikin kukan, domin kuwa shine babban wanda aka cuta, a maka ƙazafin zinah da ƴar uwarka uwa ɗaya uba ɗaya! Ai da ciwo! AQEEL yana gama jin abunda su Usman suka zo dashi bai ja Wani lokaci ba yace " AlLLAH ya yafe Mana gaba ɗaya idanunsa sunyi jajawur!Alamun ran ƴan maza ya ɓaci(Nikam Oum ARQAM nace ALLAH Yasa kar ciwonshi ya dashi) yana faɗa ya fice daga falourn,shima AKEEL Ganin Halin da ɗan uwansa yake ciki bin bayansa yayi yana tausayawa Jimmai da Usman ganin Halin da suka koma,dan ma baisan abunda Yake damun Usman bane shiyasa,da lalatar da yayiwa Shukhra. ALLAH Sarki Mommah Saida tasa akawa Jimmai da Usman girki duk da bakinsu Babu Daɗi an ɗago da ɓacin rai ,haka suka baro gidan! zuciyar su fal farin cikin yafiyar IYALAN ALHAJI TALLAFY.. ______KAWU ISMA'IL___ Tun bayan da Jimmai da Usman suka nemi yafiyarsa shikam yabaro gidan, saboda zuwansu banki shida Kawu Isma'il ɗin. Kawu Isma'il kam yana shirye Abbu yana aka gaggaisa, Sannan Abbu yasako zancen Bikinsu AQEEL! Kawu Isma'il kam cike da ƙasƙantar da kai yace ' aini Alhaji bani da tacewa Duk sanda aka tsayar da maganar Bikin ina maraba da Hakan! "Ai ba haka bane Isma'il haƙƙinka ALLAH ne baka, dole mubaka Haƙƙin" Abbu ya faɗa haɗe da murmushi yana duban Kawu Isma'il ɗin! To Shikenan nikuma na wakiltaka Akan ƴaƴan nan Duk abunda Kayi daidai ne, to Shikenan in Sha ALLAH nan da wata huɗu masu Zuwa za'a Sha BIKI,abunda Yasa ma nakai wannan lokacin su AQEEL zasu koma makaranta su ƙarasa exam ɗinsu banso su tafi tare ne,gwanda idan Anyi exam ɗin idan zasu koma nan gaba sai su koma gaba ɗaya ,akuma cigaba da Karatu,Suma su Hadiyyah da Hidayah ɗin sai a nema musu admission acan! "Ma Sha ALLAH Alhaji ubangiji yasaka da alkhair yasa afi haka ALLAH yiwa yaran albarka! "Ameen Ameen Abbu ya faɗi. Sannan ABBU yasako zancen dukiyar su Hidayah!sun tattauna akan Dukiyar su Hadiyyah dake Hannun Alhaji tallafy ɗin, da tsawon lokacin da tayi a wajensa juya musu akeyi, Yanzu haka ma ansamu riba mai tarin yawa, an buɗe musu Account ana zubawa. Daga ƙarshe Abbu yace shi fa zai dawowa da Kawu Isma'il ɗin Dukiyar dan shine a haƙƙu daya riƙe musu,tunda su mata ne yawanci, ALHAJI kuma bai mallaki hankalin kansa na,hakana sauran ƙannensa,aikuwa Kawu Isma'il harda rantsuwar sa Akan shi ya wakilta Alhaji tallafy Akan dukiyar ! Ba yadda Abbu ya iya haka ya karɓa, ya Kira direbansa dake waje a waya,ya shigo da fayal da rubutun komai na dukiyar, dan haka Abbu yasa Hannu shima Kawu isma'il yasa hannu ( Aikuwa Dukiyar su Hadiyyah Babu gyara Babu zago ALLAH yatayaka riƙo Abbu) Sai da aka kammala komai tukunnah suka ɗunguma zuwa banki,Nan ma Duk abunda za'ayi akayi Abbu Duk yabiya kuɗaɗen da ake bin Kawu Isma'il haɗe da saka Hannu, anan ma Saida Kawu Isma'il yakuma Kuka,wanda bana komai illah na farin ciki,Da Abbu yakuma cewa "in Sha ALLAH nan da kwana uku wadnesday zaka koma sabon gidanka! Sai farin ciki haka Abbu da kawu Isma'il suka rabu cike da farin ciki. Kwana uku tsakani kuwa kawu Isma'il shida ƴaƴansa da Hauwa da rakiyar ƴan uwanta suka koma gidan da Abbu ya mallakawa Kawu Isma'il ɗin, Wani ƙarin Armashin har dasu mota a gidan! Gida gari guda KOWA sai Santin gidan Yake, yafi wancan gidan nasa nada nesa ba kusa ba! Hadiyyah da Hidayah sun ƙara ƙaunar Mazajensu jin irin tagomashin da Abbu yaiwa kawunsu!wanda yazama abun tausayi a yanzu, Hakanan su Zahra,da Zakiyyah mai jego sun Kira Abbu sun Masa godiya,kai Alhamdulillahi Kawu Isma'il fa anfaso gari,acikin satin yakoma harkar sa ta cinikin Dabbobinsa, mutane sai mamakin Hakan suke, Abokan kasuwancinsa nada sun dawo Harda sabbi ma, dayawan jama'a Suna tunainin ta Ya ya Isma'il komai nasa yadawo,sai kuma su tuna da sirikin Alhaji tallafy ne fa,yaiwa Wasu ma balle sirikinsa. _____H+H= HASSAN(AQEEL) & HASSANA (HADIYYAH)______ Sun wata irin shaƙuwa da juna a waya,in aka ce muku AQEEL ne Yake zuba zance da surutu a waya saika ƙaryata,to amma ga zahiri ni Oum ARQAM ina gani,to dama ita Hadiyyah gwanace a fannin surutu dan haka ko ajikinta buɗe Baki take sunashan Hira,Anan kuwa AQEEL ya Tabbatar cewa Mrs parrot ɗin da yaso itace matarsa,ai sai murna a zuciyarsa, "Halawatiy"(Lallai Larabci ) nayi murna fa, Kinga abunda na zata shine! amma da yasin wannan bakin sai yasha Hukunci a wajena! Dole ya horu ya koyi surutu! Amma Yanzu tunda baki abun magana ne ai Shikenan ni Haka nakeso!idan kina mun magana ji nake kamar na janyo lokacin da ya rage Mana akawomin ke gidana,Gani gaki saboda murna nayi alƙawari Ranar bazan iya Barci ba saboda murna! Wannan uban zureren zancen AQEEL yake fitowa dashi daga bakinsa kamar ba Shiba! Murmushi me sauti Hadiyyah tayi wanda tasa AQEEL yajishi har cikin ɓargo da jijiyarsa sai da ya lumshe idanu, haɗe da cije leɓan kasa, shi kaɗai yasan Abunda yajeji a Wannan lokacin(kunsan dai AQEEL basaina faɗi muku ba) "Ajnabiy" kana bani mamaki fa idan kace inda bana magana sai kaiwa bakina hukunci to ta yaya? Hadiyyah ta ƙarasa zancen da sugar shagwaɓa! 'Hmm ALLAH ya taimakeki bake bace da Kinga yadda zan ladabtar dashi ɗin! Yanzu ma idan surutun ki yamun yawa nasan ta yadda zan ladabtar dashi! Ya ƙarasa zancen da magana ƙasa ƙasa yana makirin murmushi! Hakanan a Kullum suke ɓata lokaci a waya suna Shan soyayyar su,Wataran idan Abun yai yasa sai AQEEL yacewa Hadiyyah "Halawatiy kunna data muyi vedio call Please inason ganinki, ai kuwa Hakan zata kasance online ɗin Suna kallon juna Cike da so da ƙauna Suna hirarsu,idan yaga AQEEL ɗin yafara sauka daga layi ta kashe Data ɗin ta,tana mamakinsa, lallai ita Hadiyyah ALLAH ya haɗa ta da gamon ta da Ganin AQEEL Babu sauƙi fa, daga Ganin fuskar ta Alhalin jikinta Akwai kaya hakana kanta da kallabi saiya Fara, sakin layi! Haka sukeshan soyayyar su idan AQEEL yace zaizo,sai tace ita dai a'a tana tsoronsa ne ma,idan yazo daga ita sai shi sai ALLAH kuma yasan matarsa ce ai akwai matsala cewar Hadiyyah,to amma yace mata Dole zaizo ne, shi da AKEEL su rakasu ayiwa Yaya Zakiyyah barka,su gano takwarorinsu, "nima ALLAH yabamu twin's ɗin nan da shekara me zuwa ko wata tar... Tanajin abunda AQEEL yace Hadiyyah tai saurin kashe wayar cike d Alkunya tana mamakin Ajnabiy ɗin ta. _______H+H=HUSSAIN(AKEEL)& HUSSAINA(HIDAYAH)______ Suma ɓangaren su tun kan aje ga tarewa a gidansu da ƙudurin AKEEL na koyawa Hidayah surutu har tafara Koya ma a waya,idan Hidayah tana waya Abun zai baka mamaki, Duk da babu abunda zaka zaka tsinta a Hirar ta ta Amma tabbas zakasan waya takeyi, kuma surutu take zubawa Babu ƙarya! AKEEL fa ansamu aiki,shi surutu ba wahala yake Masa ba! dan Haka kullum cikin waya yake da Hidayah,yana kasheta da kalaman ƙauna, kunsan dai irinsu Hadiyyah masu shiru shirun nan idan suka samu soyayya sunfi uwar kowa baje kolinsu (gadai AQEEL) AKEEL yana kasheta da kalamai tana Masa shagwaɓar data saba! "Kinsan ALLAH "My Final choice" (Nan kuma turawane) inason Rashin maganar nan taki, hakanan nakeso ni nakoya miki surutun, Amma ace mace taita zance ai banso nidai! AKEEL ya faɗi haɗe da Dariya a ƙarshen zancen! "My only one Kenan"kai kuma da kake zancen kamar lalataccen fanfo kuma fa,ni nace me da kake damuna da surutun? Da shagwaɓa Hidayah ta faɗa "Ai so nake ki koyi surutun tun kafin akawoki gidana, idan yaso dakinzo cigaba zanyi wajen koya mikin! "Ai shikenan nidai nace bazan koya ba! "Lalläi ma yarinya yanzu me kike idan ba surutun ba? "Amsa dai nabaka Akan maganar da kamun,haka fa aketa dambarwa Tsakanin Hidayah da AKEEL Akan ita bazata koyi surutunsa ba, shi kuma yana Dole saiya koya mata. Sunata Hirar ta soyayya, Yake ce MATA za suzo shida AQEEL su rakasu ayiwa Yaya Zakiyyah barka kafin Suna, dan haka ma ta tanadar masa Abun daɗi, dan yanason yaci girkinta tun Yanzu yaji ya yake! Indai girkine "my only one" baka da matsala dashi har abunsha ma zan tanadar maka! Sai dai fatan kara cikani da surutun ka a Zahiri! "Karmu cika juna da surutu dai ai kema me surutun ce yanzu cewar AKEEL,cike da Farin ciki da Annushuwa suka rabu a wayar. Hadiyyah tacewa Hidayah "sis kinji wai zasuzo mu rakasu ayiwa Yaya Zakiyyah barka" Ea Nima haka Yake gayan Yanzu cewar Hidayah! Nikam ina tsoron zuwan AQEEL wajena fa sis! Hadiyyah ta ƙarasa zancen da zaro idanuwa tana kallon ƴar uwarta! "Wane irin tsoro kuma sis keda zakiyi murna? Baza ki gane abunda nake nufi bane sis,ni nasan ko wanene AQEEL sai a slow fa daga Gani baida Haƙuri cike da karaya ta ƙarasa zancen! "Lallai kin haɗu da gamonki Nika Babu ruwansa zancen girki yaimun ma, kuma bai taɓa nunan Hakan ba"cike da murna Hidayah ta ƙarasa zancen "Lalläi ma sis kinmanta wai da AQEEL da AKEEL Duk ɗaya ne, kowanne da Halin sa dai Shi AKEEL baida tone tone ne,shi kuma AQEEL Baya barin magana acikinsa,koma dai me Zaki ce Yasin AKEEL ba Ruwan sa! Ai shikenan sis zamu gani ALLAH yakaimu lokacin cewar Hadiyyah tana tagumin neman mafita tsakaninta da mijinta AQEEL,ita kuma Hidayah tai shigewarta ɗaki......... Wash Hannuna..............yasin nagaji hakanan Muje next page ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 8/10/24, 12:06 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE* (Babbar musiba) Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM} *08128231163* Marubuciyar Komai nisan jifa Hakan ba kuskure bane *___________________* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)* *__________________* *PAGE SIXTY THREE 63* Alhamdulillah my fans I'm back again🙋‍♀️,Ina godiya sosai da addu'oin ku gareni naji sauƙi sosai, ALLAH yabar zumunci🤝 muci gaba da gashi❤‍🔥 "Kamar yadda su AQEEL suka faɗi hakan ta faru,kafin Suna da kwana Biyu sukazo wajensu Hadiyyah dan zuwa yiwa Yaya Zakiyyah barka! Bayan su tawo da kayan jarirai da sauransu niki-niki kamar za'a buɗe kanti harda tagomashin gudunmawar Abbu. "Karkuso kuga rawar ƙafa wajen Twin's su AQEEL yau za'a gana da Ababan ƙaunarsu! Ɓangaren su Hadiyyah ma abun haka Yake kowa sai murna yakeyi,to dole ai wannan shine farkon Haɗuwar fuskokinsu a matsayin ma'aurata kuma masu son junansu! Ko da su Hadiyyah suka gayawa Auntynsu(Sa'adatu) zancen zuwan mazajen nasu cewa tayi "mecece tawa aciki? Matsalarku ce! Ni dama na matsu kuyi kuyi ku tafi can ku ƙari tsiyarku,nagaji da wannan iskancin na waya cikin dare Duk abunda kukeyi ina sane daku!(Fans ko Sa'adatu tamance Suna da Aure ne?) Kaji dashi kiji da abunda Yake damun ki ƴar wahala. "Kwalliya sosai su Hadiyyah suka Sha, kamar ka sace su ka gudu, Yasin babu ta yadda zaka ganesu abun gwanin burgewa! Sai kamshi sukeyi,Kowacce zuciyarta cike da tarrabanin wace tarba zata samu wajen angon nata, musamman Hadiyyah datasan halin nata mijin. AKEEL da AQEEL Suma An Sha gayu Suma kamar ka sace ka gudu, yau kwalliyar ta musamman ce garesu naga alama! Ga shinnan yasha gyara ga saje da gemu sai ƙyalli yakeyi gwanin burgewa,gargasar nan ta Hannu ta kwanta luf-luf sai ƙyalli, musamman AQEEL da wannan glass na fuskarsa ya ƙara Masa kyau shine banbancin dake tsakaninsa da ɗan uwansa Kenan! Mommah tace"ma Sha ALLAH Twin's ɗina kunyi kyau Sosai, ALLAH ya haɗa fuskokinku da alkhair! Shikam Abbu sai tsokanar AQEEL Yakeyi ganin sai wata firirita Yakeyi Akan wannan futar wai shi me MATA! mutumin da yake Wani shan kamshi Kwanakin baya! "Ikon ALLAH Mommahn AQEEL Kinga Ɗanki sai rawar ƙafa yakeyi zuwa wajen ƴata ko kunya ni Ɗalhatu! lalläi ɗan ki Bashi da kunya! Aikuwa an kunne AQEEL sai ya noƙe alamun yaji kunya ya kuma ɗaure fuska! Abbu da AKEEL dake gefe suka sa dariya! Mommah tace "haba Abbun AKEEL ai wannan maganar ta wuce da jimawa, please abarmun ɗana ya wataya!itama cike da dariyar ta ida maganar, cike da nishaɗi dai su AKEEL suka baro gidansu kowanne zuciyarsa kamar Auduga tsabar fari! Bayan Abbu ya yankawa AQEEL warning Akan Hadiyyah tunda yasan halinsa,kuma ya tunasar dashi batun likitansa! Sai naga jikin AQEEL ɗin yayi Sanyi da tunin da Abbu yamasa! Ƴan nema kowanne mota ya ɗauka guda,Abbu yace su hau ɗaya Ilu driver y kaisu Amma ina sukace dakansu zasuje Babu matsala,Sai da Abbu yai Musu Addu'ar Alkhair sannan kuma a irin motocin da Abbu yake fitar sirri a irinta suka ɗauka,idan ba haka ba daƙar su AQEEL zasusha da mutane dan kuwa Tallafy dai ba ɓoyayye bane balle number ta motarsa. Suna zuwa unguwarsu Hadiyyah sukayi parking a Layin, kafin AKEEL ya Kira Hidayah a waya cewar sun iso,sai da Hidayah ta leƙa ɗakin Sa'adatu Again ta sanar MATA sun iso bata daddara ba,aikuwa cikin tsawa tace "naji sai akayi Yaya kuma! Taja tsaki Hydar suka aika domin yai Musu iso cikin gidan, Ɗakin Sa'adatu sukaiwa tsinke kamar wata ɗan daren goma Sha ɗaya haka Suke gwanin burgewa, sai da taji Wani dum tsabar ganin kyaun Twin's Duk da tasansu lokacin ƙuruciya Amma yanzu ai ba wasa ba,tana Wani shan kamshi ta amsa musu, sannan suka ajiye mata salala, suka baro ɗakin zuwa hanyar waje,yar banza da Yake taga kuɗi sai tace "ya haka kuma AKEEL ku shiga Suna ciki ko gaisa Mana, sannan In yaso sai ku tafi gidan Zakiyyah ɗin ko ruwa ai kwa Sha! Cikin sinne kai suka amsa da to 'kafin suyiwa falourn su Hadiyyah tsinke. Duk maganganun da sukayi su Hadiyyah naji, jin cewar su shigo falourn Kowacce sai jikinta ya Fara karkarwa, Hadiyyah ɗaki ta gudu ita kuma Hidayah ta maƙure a faloun cike da kunya. AKEEL yana shigowa faloun ya wurga idanuwa yaga mutum ɗaya kunsan shi dai sai cewa yayi "ina ɗayar kuma? Mu da zamu ganku tare kamar mu haka gwanin burgewa! Shi kam AQEEL yana tsaye bai magana ba! Ni dai wannan bansan Kowacce ba,da nasan wannan Hadiyyah ce Babu shakka cikin ɗakin nan zanwa tsinke dan kuwa nasan Hidayata tana ciki! Cike da dariya da tsokana yayi maganar haɗe da nuna Hidayah dake gefe, wanda tunda taji yayi magana tagane kowanene Aku bakin magana ne wato AKEEL mijinta! Yanayin yadda Hidayah ta share su kanta a ƙasa ne tabbas yasa AQEEL ganeta dan indai Hadiyyansa ce dole ya shaida,bai ce komai ba ya dumfari cikin ɗakin dake gefen sa wanda yake da yaƙinin Hadiyyah tana ciki,ganin ɗayan kofarsa na kulle ga key nan ajiki. Hakan da AQEEL yayi ya tabbatarwa da AKEEL cewa yatafi wajen Matarsa ne Wannan itace tasa,ai Babu wata wata AKEEL cikin sassarfa ya tafi wajen Hidayah! Gaba ɗayanta ya ɗago ta daga zaunen da take Cikin muryar raɗa yace "wato ko aina sai kin nuna halin ko? Ai shikenan bro ya nunan cewa kece tawa dan haka sai yadda nayi dake! Ya ƙarasa maganar haɗe da kaiwa ba kinka sassanyan kiss,Sai da zuciyar Hidayah ta tsinke jin abunda AKEEL y MATA,sai ta tuno da ƴar uwarta Hadiyyah koya zasu kaya da nata, ita da yake nuna Masa maitarsa a fili,shikam AKEEL yai yanzu da yayi MATA a aikace! Ya jima bai saki bakin ba sai da ya tsotse lipstick ɗin data saka,kafin ya bari haka!murya cike da Sanyi yace karki kuma saka wannan in Zaki fita Kinga yadda bakinki yayi kuwa salon Wani ya kallemun shi ya cucan,Kinga yadda Nima kaina bakin yatafi da imanina kuwa" AKEEL ya faɗa haɗe da zaunar da Hidayah kan kujerar shima yana Zama kusa da ita yana ƙwaƙwume da ita kamar Wani zai ƙwace Masa ita! Ira dai Hidayah Babu bakin magana,tana ji tana kallo AKEEL sai taɓe taɓe yake yi a jikinta,mamaki ya kasheta sai kuma canta da surutunsa yakeyi amma ina taƙi kulashi(ba dole ba AKEEL wannan sabon al amarin da kazowa da Hidayah shiyasa ta hakan. Hadiyyah tana gefen gadonta a Zaune jin abunda AKEEL ke faɗe yasata murmushi jin bai san kowa cece ba,sai kuma jare idanu da tayi jin cewa AQEEL ya dumfaro cikin ɗakin nasu tana a Wannan halin AQEEL yaƙaraso ɗakin,fuskarsa cike da murmushi mai nuna alamun yana cike da farin ciki,Itama murmushin yaƙen tayi, yana zuwa gefen gadon ya zauna haɗe da cirewa Hadiyyah hannun ta na dana daga haɓarta wanda ta tallafe dashi tsabar tsoron daya kasheta, "wannan tagumin na menene mine? Nazata murna zakiyi da zuwana gareki! AQEEL cikin murya mai taushi da nuna kulawa yai zancen! "Ba haka bane kawai dai ina Mamakin shigowa ɗakin da zakayi ne? "ALLAH ko kina mamaki na kenan,wajen matata nazo fa kuma tana ɗaki dole nabiyota ai ko? Ya faɗi haɗe da tsure fuskarta da kallo 'ita kuma ta sunne kai ƙasa dan ganin Irin kallon ƙurillar da Yake mata tun daga fuskarta da ma ko ina inda idonsa ya kai! Wannan kallon fa! Inji Hadiyyah tana murmushi wannan kallon tanada ma'anoni da yawa, mamakin kamarku sa Hidayah nakeyi yasin baza'a shaida ku ba a yanzu dana shigo sai naga kamar ke nabaro a faloun ya wayance da bata wannan amsar! Amma a zahiri ba haka bane kallon tsantsar soyayya ce da buƙatuwa zuwa ga yarage Zafin abunda yakeji ne game da ita to amma ina, doctor yace Masa "matukar Yayi wani Abu na taddo da sha'awarsa al Halin bai kawar da ita ba akwai babbar matsala, wanda wannan Maganin da aka ɗorashi akai ne Yake zanyo hakan, sannan shima akwai daɗewar da yayi tana muradin abun shine sila. Dan haka ba bayan kama hannun Hadiyyah da yayi Babu abunda yai MATA,zuciyarta sai godiya ga ALLAH takeyi, nan kuwa batasan nata gwanin ba irin na wasu bane kawai lokacin da zai fanshe bashin Hakan,ya ɗan zata da hira an danan ta saki jiki dashi kafin daga bisani AQEEL yace "to Angon Hidayah zamu fito mufa kar muyi mummunan gani ya kimtsa cike da dariya ya ƙarasa zancen Saboda yasan ya rama tsokanar da AKEEL ɗin yake Masa, Aikuwa sai da aka dan Jima sannan AKEEL ya iya amsawa (wai dama haka Akeel ɗinnan yake shima), saboda sannan shikam yayi nisa wajen damun Hidayah ta taɓe taɓen sa na babu gaira babu dalili,Duk ya takurata, "Angayama kowa irinka ne,mukam hirarmu mukeyi sai dai idan kaine zaka shiga Wani halin dan kuwa nasan Hali shima AKEEL ɗin ya rama cike da kawar da abunda yakeyi ɗin. Da su Hadiyyah suka fito falourn a tsaye suka samu Su Hidayah ita dai sai sunne kai take zuciyarta fal mamaki,itama Hadiyyah hakan jin abunda AKEEL yace to amma ai dai yanzu gaisuwa sukayi dashi kawai bai MATA komai ba ko kawai dai tsokanar juna suke ne? Nikam oum ARQAM nace akwai Lokacin da Zaki tantance. Duk Halin da zuciyoyin su Hadiyyah suke bai hanasu kallon Twin's ɗin Abbu ba dan babu maraba garesu sai ta glass da ɗaya yake dashi Yanzu kuwa Hadiyyah da Hidayah sun san AQEEL ne mai glass. A haka suka fice daga gidan, Wanda Sa'adatu sai mamakin Twin's ɗin Abbu take lalläi waɗannan sai abarsu Basu da kunya gaskia daga shiga ku huta sai ku shantake waiku masu MATA ko kunya? Sai kiyi ke kaɗai sukam basusan kinayi ba ma, Har sukaje gidan Yaya Zakiyyah sai Hira suke kowanne a motar su gwanin burgewa motar a jere suke tayi fa,Duk da Hidayah bata sake da AKEEL ba ganin abunda yai MATA, a zuciyarta sai tunanin yadda Hadiyyah ta kwashe da AQEEL take,ganin yadda take bata labarinsa baida sauƙi. Sunje sunyi wa Yaya Zakiyyah barka an musu tarba ta mutunci,su AQEEL sun sha godiya wajen mukhtar da wannan karamci,haka suka baro gidan sai da su AQEEL suka mayar da Su Hidayah gidansu sannan sukayi gida. An sha sunan su Twin's ɗin Zakiyyah Hassan(na'eem) Hussain(na'eef) nan na hango su Haseena da seerat da Aisha Sulaiman da MamaGee da sauran ƴan RASHIN IYAYE Fans group anwa su Haseena da seerat kara anata hada hada aci wannan asha wannan,anko naga sunyi abunsu,gasu ga mai jego,Su AQEEL ma sun koma again suda su Hadiyyah nan naga anata gaggaisawa tsakanin su AQEEL da HADIYYAH dasu Haseena kai wannan abu yayi Armashi! sunan ƴaƴan ƙawarsu ne ai nan naji wai Sunan ƴaƴan ma saboda ƙauna Zakiyyah suta bari sukawa ƴaƴan Al kunya ,Amma fa Nima sunan yamun daɗi yasin na'eem da na'eef ALLAH ya rayasu. Saura bikin su Twin's kuma bansan wane irin shagali za'ayi ba kuma! _Kamar yadda Abbu yai alƙawari hakan akayi dan kuwa ba'ayi sati biyu ba,su AQEEL suka runtuma New Delhi chanwu university domin Exam da take gabansu dafa sun dawo kuma sai shagalin biki. ______USMAN______ Yanzu kam sai sam barka ALLAH yahadashi da wata bazawara wacce mijinta ya saketa Akan bata Haihuwa ƴan uwansa suka tilasta y saketa,saboda ya ƙara Aure matar ta Biyu ta Haihu, alamu sun nuna dai itace bata Haihuwa ɗin, Aikuwa nan danan Usman yayi wuf da ita,tunda shima Babu batun Haihuwar,ko wata Biyu ba'ayiba akayi bikin Usman da Amaryarsa zulaiha,sai fatan zaman lafiya, Usman yayi gidansa mai kyau nan ya tare sa matarsa,jimmai tayi murna da Hakan,hankalinta ya kuma kwanciya Yanzu,aikuwa dai Usman karɓe Daddy yayi sai abashi shi,shima daddyn yaso haka,baison Abban sa yayi nesa dashi. ______JIMMAI_____ jimmai cikin ikon ALLAH sauƙi sai samuwa Yakeyi saboda yanzu tension ɗinta ya ragu sosai ta kawar da Usman da ke zaune gidanta ga Shukrah Suna tare,Duk da tana zulumin mai Aurar Shukrah yanzu Alhalin batada budurci, Yanzu tana takawa babu mai riƙeta Amma dai kan ƙafa da hannu sun nakasa fa bamu sani ba ko in tanashan magani,mma tana sharar ƙafa hakama hannun yayi sanyi,a hakan tanawa kanta Abubuwa dayawa kuma tagodewa ALLAH, Shukrah kam bata sa batun aure a Ranta ita to Wanene zai aureta ne? Da wannan mummunan tabo da yayanta yai MATA aiko wanine yai MATA ta rasa miji balle yayanta,dan haka ta cire Aure a Ranta, Shukhra karki karaya ALLAH yana sane da kowa komai kuma akwai iyakarsa wannan ƙaddara ce da sakayyah Kika Gani akanki ko ba haka ba my fans! ____KAWU ISMA'IL__ komai Alhamdulillahi Yanzu zuciya ta tsarkaka yabi ALLAH Yanzu,Duk yayi Wani so silently dashi kamar ba shiba,shida Abbu yanzu sai girmamawa da mutunta juna gwanin burgewa, Hakan dama akeso ai. Su snake sun miƙa wuya ga kotu Akan sunyi saranda Akan Abubuwan da suke aikatawa mutane na fashi da makami, sannan kuma kotu ta nemi ko Duk waɗanda sukawa fashi zasu ganesu Amma sukace ina,idan sunyi fashin ashe a banki Suke adana kuɗaɗen sai dai su siyi abun bukata wajen fashin da sauransu dan haka mutanen da sukayiwa sata Baya Baya kawai suka tuna ciki harda Kawu Isma'il dan haka kotu ta kirashi ko da Yaje andawo masa da kuɗaɗen da suka sata shi kuma na danƙawa Abbu wai a ƙara a Tallafy foundation ,shikam Abbu yace bazai karɓa ba ai dukiyarsa ce yayi yadda yakeso da ita man,nan dai kawu Isma'il ya gina masallaci da borhole yace ladan wa Abbyn su Hidayah.lallai Kawu Isma'il anyi taubatun nasuha. Su snake Ragowar kuɗin da basusan inda zasu mayarwa da masu suba tunda wasu ba a gida suke musu ba a hanya ne ko a banki, dan haka kotu ta dinga Gina makarantu da masallatai da siyen kayan sawa dana Abinci ana kaiwa gidan marayu,anawa marashi dai hidima Akan ALLAH yakai ladan ga wanda suka cuta,wanda suka kashe kuma suda ALLAH, (wannan shine ƙa'ida a sari'ar musulunci yadda Akeyi da kuɗin hannun ƴan fashi idan sun musulunta) sannan aka yankewa su snake da yaransa hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan gyaran Hali. ALLAH yasa mufi ƙarfin zuciyarmu akoda yaushe. _____GIDAN ALHAJI GAMBO_______ Tuni Hajiya Sahura ta haifi ƴarta mace kuma an mayar da sunan Hajiya suwaiba ana kiranta da Asalamiyyah! Shikam Abbas tuni yayi wayo kai bakace maraya bane yayi ɓulɓul dashi,zaman lafiya sai ABunda yayi gaba tsakanin Ikilima da Sahura kamar ba kishiyoyin juna ba, musamman da mutuwar Sauwaiba ta dakesu sosai, Alhaji Gambo ma Hankalinsa ya Kwanta sosai ga kyautar ƴaƴa biyu lokacin da baiyi tsammani ba,ko Yanzu ya godewa ALLAH ai,yanawa Hajiya suwaiba addu'a a koda Yaushe. _____SA'ADATU____ Tuni ta gama iddarta ta shiga felelenta na Addu'ar samun miji mai kuɗi,wanda zata dinga ta tsar kuɗi, dan itafa tanason namiji mai kuɗi! ALLAH ya amshi roƙonta kuwa dan kuwa ta haɗu da Alhaji Hamza mai kuɗin gaske,matansa Uku da ita zaiyi ta huɗu,tun da yazo yake MATA ɓarin kuɗi dama haka takeso, sai murna takeyi,Amma tace Masa ya dakata Zatayi bikin ƴaƴan mijinta idan aka kammala sai Ayi maganar nata,kuma yace gidan mijinta ta saka ƴan haya, gidansa zata tare shi bazai iya zuwa Gidan Wani ba......... Topha Fans ya wannan Aure na Sa'adatu zai kasance shin wannan ma zataci bulus ne yadda ta Saba kubiyi Oum ARQAM Wayyo idona My Fans idonfa har yanzu da saura muddin najima da screen yadinga raɗaɗi kenan, ALLAH yakawomun sauƙi ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 8/19/24, 10:07 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: RASHIN IYAYE (Babbar musiba) *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)* *PAGE SIXTY FOUR 64* ______AKEEL & AQEEL______ "Cikin ikon ALLAH sun Fara exam wanda dama itace ta mayar dasu India,kuma har sannan Suna waya dasu Hadiyyah yadda ake soyayya kamar za'a cinye juna abun sai wanda yagani. Ɓangaren su Hadiyyah ma haka abun yake,karatu yayi nisa Suma kamar haɗin baki exam ɗin suke tunkara,tuni Baaba tazo daga Kaduna ita dasu Hunaif da Zeenah tunda anyi Hutun school,da guzurin maganin sanyi ta tawo mai yawa kuwa tabawa Twin's tace sufara amfani dashi tukunnah.bata Fara Basu ba Sa'adatu ta kaiwa tai MATA bayani,Amma sai taga Sa'adatu ɗin tana Wani ciccin magani,tayi watsi da ledar dan haka sai kawai Baabah tasa Hannu ta ɗauki kayanta,tanawa Sa'adatu Addu'ar shiriya a zuciyarta dan kuwa abun nata yayi yawa. Dan haka taiwa su Hadiyyah bayani yadda zasuyi dasu kuma su Fara abunsu,Zuciyar Hidayah akwai zulumin AKEEL tun ranar da sukaje barka wa Yaya Zakiyyah,ita kuwa Hadiyyah ko ajikinta saboda taga yadda suka kwashe da AQEEL lafiya lau!Amma fa kuma a waya ya dinga MATA sambatu da zantukan da Yake sawa tanajin kunya,a zuciyarta kuma tace iya baki ne,wai haka ne? ____GIDAN ABBU___ Mommah zata Aurar da Yaya har uku aikuwa tun sannan sai gyara gyaran gida akeyi Duk da ba Wani gyara yake so ba Amma dai kunsan idan da kuɗi Babu abunda baza'ayi ba,saboda haka ma sun bar gidan yanxu Suna Wani gidan Abbu shi wannan main house ɗin ana gyara shi ne kuma bazasu koma ba sai Bikinsu AQEE. Ɓangaren AKEELA kam cikin ikon ALLAH sun kammala neck/waec exam, soyayya kuwa ana Shanta ita da doctor Najeeb ɗin ta,Duk da a Kullum tanajin Wani ɗaci a Ranta na cewa ita fa ba budurwa bace Duk wannan zumuɗin da Doctor yakeyi a kanta,shi kuma yana Kwantar MATA da Hankali Akan cewa shi fa ba don wannan budurci zai aureta ba,so ne da tausayi tsakani da ALLAH,kuma ai ƙaddara ce ta sameta,daga ƙarshe kuma ya ƙarasa MATA tsokana "ai tana dai na ɗinke wajen cike da bai bazan ganeba,kin manta yanzu haka zaurawa sukeyi da ƴan MATA marasa kamun kai,ta yadda mijin daya Aurensu zai zata a leda suke sai yayi murmushi! Cikin shagwaɓa kuma AKEELA tace " ba waninan kuna ganewa man, kataɓa ganin anyi amfani da sabon abo yakoma kamar yadda yake,kuma kai ai kasan komai! "Ea naji ɗin a haka nakeson ki kuma har a raina budurwa nake ɗaukarki, kar kiji komai my soulmate! Ire iren maganganun da sukeyi da doctor Najeeb kenan Duk sanda mikin baƙin cikin AKEELA ya tashi na Cutarta da Usman yayi,Duk da ta yafe masa,kuma ta samu mijin da zai rufa MATA asiri wanda shine yai MATA aikin ma. Tsakanin AQEEL da AKEEL kam su da Usman ana gaisawa ta waya ko a haɗu online,komai ya wuce Yanzu Duk da dai Wani lokacin AQEEL yana jin raɗaɗi da ɗacin abunda Usman ɗin yai masa,to amma ai yanzu sai Mai da magana. Itama AKEELA kadaran kadahan da Usman tunda indai taganshi saita tuna azabar daya gana MATA, ita da Shukhra kam an koma an jone dama kamar twins suke dan kuwa sa'o'in juna ne,dan haka suna mutunci tana Zuwa wajenta itama AKEELA ɗin tana Zuwa Gidan Jimmai ɗin,Duk sanda jimmai zataga AKEELA sai tayi ƙwalla da neman yafiya,ita kuma AKEELA tace komai ya wuce ai,indai zata dinga MATA haka zata daina zuwa Gidan,to tahaka Jimmai ta ƙyale AKEELA. yanzu Usman Sa'i da lokaci yana zuwa gidan Abbu wajensa(A gurin Abbu yake odar kayan communication center ɗinsa,har wayoyi Abbu me auno Masa) haka ko Mommah su Gaisa idan sun haɗu Akan ɗanyi magana.dama shi Abbu mai yafiya ne, Usman yanzu ma Sha ALLAH Suna zaman lafiya shida zuhaiha matarsa, kuma Daddy yana wajenta bata kuma cutarsa,hakana Dukiya ta Usman sai daɗuwa takeyi plaza anata ƙara wasu,da shawarar Abbu inda har ba shin kayansa yake bashi,kuma Usman Baya masa wasa. Jimmai da Shukrah komai na rayuwa Usman yana tsaya musu akai, maganar jimmai ta ƙara washewa Amma fa hannu da ƙafa kam sai a slow har sannan Basu koma daidai yadda suke ba. Shukrah anyi candy (tare sukayi da AKEELA) kuma cikin ikon ALLAH ta haɗu da is'haq ɗan sa ɗaya wajen haihuwar ɗan matarsa ta rasu,baiyi Aure ba sai yanzu da ALLAH ya haɗashi da Shukhra ɗin, ALLAH maji roƙon bayinsa, kuma Duk abunda yafaru da Shukhra is'haq yace yaji yagani yana sonta ƙaddara ce bata wuce kan kowa ba,yanzu kuma ai komai ya wuce! Tun Shukrah bata kulashi har tafara kulashi da nasihar da AKEELA take MATA,da nusar da ita cewa tunda yasan Abunda yasameta shine rufun asirinta,Amma yanzu ta auri wanda bai sani ba akwai matsala,Duk da dai sunsan munafincin ɗan adam za'a tareshi a gaya masa,da haka Zuciyar Shukhra ta Amince da is'haq har suna waya da zuwa zance,kafin Ayi maganar Aure. _____KAWU ISMA'IL___ Alhamdulillah kuɗi fa sai hayaƙa sukeyi yanzu,hankalinsa ya kwanta haka na Hauwa itama tana godewa ALLAH da mijinta yadawo hankalinsa,ya zubar da makaman zalunci, yanzu hankalinsu ya kwanta,tana godewa ALLAH da godewa Alhaji tallafy tunda shine tushen farin cikinta da mijinta. Waya Aunty Hauwa taiwa su Hadiyyah tace sudawo gidanta da Zama har zuwa biki zata Fara Basu kayan gyara na amare ne,kafin afara gyaran jiki dan bazai yiwu ana gyaran jiki Suna fita rana ba,sai da suka gama magana da kawu Isma'il sannan tai musu wayar, nan suke gaya mata ma ai Baaba takawo musu na sanyi. Ko da suka gayawa Auntynsu Sa'adatu cewar zasu koma gidan Kawu Isma'il ko tari bata musu ba sai daga ƙarshe tace "Zaku koma gidan gayyar tsiya dai, ai Isma'il azzalumi ne(kuji fa) da wannan makirar Hauwa(ke kai makira) kuje sai kun dawo ALLAH ya tsare hanya. Zuciyar Sa'adatu ba komai bane illah baƙin ciki dan taji Duk sauyin da kawu Isma'il ya samu da kulawar da Alhaji tallafy yai Masa, Yanzu da Basu rabu ba Shikenan wannan arziƙin da ita za'a ci, ga baƙin cikin Alhaji tallafy komai sai dai yayiwa yaran nan(su Hadiyyah da ƴaƴanta) ita kam ko abun ƙwandala,sai dai arziƙin Abinci da kayan more rayuwar daya Sanya a gidan nasu wanda tasan arziƙin ƴaƴan Alhaji Ammar ne yasa itama ta dandala,kowanne yaro yanzu privet school suke zuwa ƴaƴanta Hydar, farouk,da Auta Hafsat, hakana Khadijatu(wanda tuni anzama ƴan MATA yarinya mai hankali, yanzu haka ta samu Saurayinta itama,Shikenan sai Sa'adatu tai abunda zatayi ita kaɗai ƴaƴan Ummu Rumana dai kam ALLAH ya sittura su duka,saura Zeenah kawai) wanda,da mutan Kaduna ma Zeenah da Hunaif ,Duk Wani jin daɗi suna samunsa daga Alhaji tallafy, Baabah kam gidanta kyace na Amarya ne! sai kuma tai ajiyar zuciya bayan tagama wannan tunanin, da kuma tuna Alhaji Hamza wanda ta samu yafi Isma'il komai ai har shekaru ma. Tun lokacin da Zancen biki ya Fara gabatowa Kawu Isma'il ya kafe kai da fata Akan cewa shine fa zaiwa Twin's kayan ɗaki komai da komai, Abbu yace ya barshi Amma yace shikam a'a,yabarshi yayi wannan haka Abbu ya Haƙura,ba ƙaramar dukiya Kawu Isma'il yai niyyar kashewa su Hadiyyah ba a Wannan biki,saboda magiya yaiwa Abbu Akan yabarshi dan ALLAH yayi Hakan kodan zumunci! Kawu Isma'il fa sai kyautatawa yakeyi yanzu dan Zakiyyah da Zahra ma bai barsu haka ba shine siyi wancan har kayan gado ya canza musu alhalin nasu baiyi komai ba sai yace abawa marayun da za'ayi Aurensu shi fa dole ya kyautata musu abunda bai musu a Baya ba, musamman Zahra wanda Lokacin Aurena Kawu Isma'il SHAIƊAN yana kansa lokacin,su Zakiyyah kam suna jin daɗin kawunsu yanzu sai sukaga kamar Abbiy ne yadawo da kyautatawar sa garesu lokacin yana raye! Takanas har china Yaje wajen ALHAJI(anzama Saurayi sosai) wanda Karatu yafara nisa,yanemi gafararsa,kuma shima sa'i da lokaci yana tura Masa kuɗin buƙata na kashewa dana harkar school nan ma sai da ya roƙi Abbu ya barshi sannan ya Amince,dan Hakan yanawa Abbu daɗi saboda Kawu Isma'il yana gyara kuskuren daya aikata ne,shi kuma Burin Abbu dama kenan. Gidansu Hadiyyah na gado wanda Kawu Isma'il ya riƙe,Ashe yananan,aikuwa kafin kace me Kawu Isma'il ya Tashi ƴan haya yafara gyaran Gida, so yakeyi daya kammala gyaran gidan yadawo da Baabah gidan ta zauna saboda su Hadiyyah suji daɗi,ace dai akwai Wani naka a kusa dakai, tunda Basu da uwa Baaba ce matsayin uwarsu, dan kuwa yasan Halin Sa'adatu ya yunwar cikinsa, su Zeenah da Hunaif su taso a mahaifarsu,(dama kuma jinya ce ta tsayar da Baaba a Kaduna na mahaifiyarta kuma shekara Biyu da Rasuwar ta kenan,sai ƴaƴanta kannen Ummu Rumana kawai acan yanxu kowanne kuma yayi Aure da iyalinsa) Ko da Abbu yaji wannan shawara ta Kawu Isma'il yayi murna,hakama su Hadiyyah ɗin,itama kanta Baaba batayi Musu ba,Amma sai biki yatawo zata dawo _____SAADATU____ Alhaji Hamza ya dameta Akan shi fa so yakeyi ayi Aurensu da ita,ita kuma tace yabari Zatayi Auren ƴaƴa biyu ne(Su Hidayah) badon yaso ba ya Amince. A daren Ranar kuma suna waya da yayarta zuwairah ta shaida MATA yadda sukayi da Alhaji Hamza ɗin,aikuwa nan zuwairah ta hau Sa'adatu Akan ina ruwanta da Wani Auren su Hadiyyah ƴaƴanta ne! Tayi Auren ta kawai,aikuwa Babu ɓata lokaci taiwa Alhaji Hamza maganar ta Amince Ayi Auren nasu kafin bikin ƴaƴanta ɗin. Da Alhaji tallafy yaji zancen Auren Sa'adatu ALLAH yasanya alkhair yace(yana Mamakin halinta) Kawu Isma'il shima haka, Alhaji Gambo ma dayaji zancen auren da ALLAH yasanya alkhair yabita,Hajiya ikilima da Hajiya Sahura kam zaman lafiya mai dorewa tuni Asalamiyyah da Abbas(ɗan wajen Hajiya suwaiba) sun tasa sosai kamar Twin's abunsu,Har sannan Hajiya ikilima ALLAH bai bata Haihuwa ba. Abbu ya karɓi gidan Sa'adatu za'ayi Masa gyara idan tayi Auren ta tare gidan Alhaji Hamza za'a zuba ƴan haya a dinga karɓarwa(farouk da Haidar da ALHAJI da kuma Auta Hafsat sai ita Sa'adatu ɗin) kuɗi a buɓe account ana tara kuɗin, Sa'adatu bata musa ba tasan kuɗin ta da gidanta Babu gyara Babu zago tunda Suna wajen Alhaji tallafy. ALHAJI yana daga China jin mahaifiyarsa(Sa'adatu) Zatayi Wani Auren daban sai da yayi kukan baƙin ciki Amma ya ya iya, bayan mutuwar Abbiy aurenta uku kenan! kawu Isma'il,Alhaji Gambo Yanzu ga wannan ai shikenan, ALLAH sarki Ummu(mahaifiyarsu Hadiyyah) yasan da tana raye sa itace bazata iya Aure ba bayan mutuwar Abbiy Amma itakam Aunty (Sa'adatu) gashi tayi uku Sa'adatu sai Wani rawar ƙafar Auren takeyi sai kace wata budurwa,har dasu magunguna takesha da gyaran jiki takeyi, wanda lokacin aurenta da kawu Isma'il da Alhaji Gambo Duk batayi ba, lalläi Alhaji Hamza na musamman ne kam (shu'uma Amma ga su Hadiyyah bata gyarasu ba),kuma sai walwali fa takeyi ko kunya,ha kuɗaɗen da Alhaji Hamza yake kashe MATA data ce kaza zai bata kuɗi ninkin abunda tace, sai murna takeyi,Alhaji Hamza ɗin shima sai murna yakeyi kamar bai taɓa aure ba ko kuma bai da mata har uku a gida, kamar yadda ya faɗa MATA,dan itafa Sa'adatu batayi bincike Akan sa ba batasan ɗan wane unguwa ko gari bane ta dai san shi kuma tanajin ana Zancen sa, saboda kuɗin sa. An Ɗaura Auren Sa'adatu da Alhaji Hamza kuma cikin satin zata tare,wanda Khadija tace itakam bazata bita ba gidan Kawu Isma'il wajensu Hadiyyah takoma,dan haka da Sa'adatu ta tashi tarewa gidan Alhaji Hamza da Auta Hafsat sai farouk da Haidar kawai ta tafi dasu,gida ma Sha ALLAH aljannah duniya kenan Sa'adatu da ƴan uwanta sai murna sukeyi ganin Irin aljannar duniyar da Sa'adatu ta tako,sai shewa akeyi haka gidan ƴan uwa kowa ya watse ɗaki guda aka bawa su farouk da komai nasu aciki ga ƴan aiki a gidan kamar buɗar ido komai sai anya Sa'adatu Auta Hafsat ma akwai mai kula da ita,tun Sa'adatu na jiran Ango Alhaji Hamza Amma ina taji shiru Babu shi Babu labarinsa,gashi har gari ya waye an kwana an hantse Zuciyar Sa'adatu sai wasi wasi takeyi shin mai ya hana Alhaji Hamza zuwa gareta a yau din a daren Aurensu? Nima dai oum ARQAM nayi mamakin Hakan! My Fans kubawa Sa'adatu amsa? Anya kuwa! Kodai Alhaji Hamza bashi da Lafiya ne? Amma mezai hanashi zuwa ga Sa'adatu Muje next page Muje meke faruwa kuma!!!!!! ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 8/22/24, 9:16 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: RASHIN IYAYE (babbar musiba) *PAGE SIXTY FIVE 65* ____GIDAN MUKHTAR____ Komai normal fa Yake tafiya tsakanin Zakiyyah da Bilkisu bazaka banbance ABIE da Twin's cewa ƴaƴan Zakiyyah bane,saboda komai nasu yana wajen Bilkisu abun gwanin sha'awa na'eem da na'eef sunyi kuɓul kuɓul abunsu sun ƙara kyau kamannin su da juna Suna ƙara fitowa har kasa banbancewa akeyi,Amma saboda shaƙuwa Bilkisu tana ganewa. Arziƙi mukhtar yaci uban nada bana zasuje su sauke farali Bilkisu Zakiyyah da shi kansa,ga ababan more rayuwa a gidan kamar me!Hajiya Jamila tafi kowa murna da wannan zaman lafiya na gidan mukhtar, yanzu haka Zakiyyah sai shirye shiryen bikin ƙannenta takeyi!magajiyar uwa kenan,su Hadiyyah sunajin daɗinta a Yanzu fiye da ƙima,a waya su Hadiyyah suke ce MATA Suna gidan Kawu Isma'il ai saboda ana gyaran jiki da magungunan Sanyi dana gyara Suna sha,tace ai shikenan dama itama zata musu ne Amma yanzu Abar Aunty Hauwa ɗin,idan yaso ta haɗa musu turaren jiki dana ɗaki dana kaya masu shegen kyau sai murna sukeyi inda dane ko kallo Basu isheta ba itama bata gyara kanta ba balle ta gyara wani. Zahran Ibrahim ma ma Sha ALLAH tana cikin kwanciyar Hankali da nutsuwa tuni ta yaye twins ɗinta kullum ƙauna karuwa takeyi tsakaninta da mijinta da uwar mijinta Hajiya Maimuna tuni ta ɗauke twins,saboda tana sonsu, Zahra tuni an ɗora Karatu daga inda aka tsaya yanzu haka Suna shirin graduation ne na kammala phc ɗinta ALLAH ya taimaka ______ABBU____ "Subhanallah! idan kunga gidan da Abbu yasa ake tamfatsawa su AQEEL yasin sai kun razana saboda haduwarsa tun daga waje balle aje ga ciki kuma, oh no oum ARQAM! lokacin danake ƙofar gidan bansan lokacin da nayi tuntuɓe ba sai jina nayi a ƙasa na zube bakina harya fashe azaba tasa na dawo hayyacina ALLAH yaso ban zubar da haƙoran gaba ba. Gaskiya Abbu ya kashewa ƴan lelensa maƙudan nerori,Asalin ginin acan new delhi suka ga irinsa yai Musu shine suka cewa Abbu sunaso,shi kuma takanas ya ɗauko magina daga can aka Fara aiki,dana shigo ciki yasin nazata a india nake,Amma seerat da Haseena da Aisha Sulaiman da MamaGee da mummy Waleed da sauran ƴan RASHIN IYAYE Fans idan BIKI yazo Kuka kai amarya Zaku kwashewa idanunku abunda nagani. Ba gida ɗaya bane kowanne dana sa amma manne da juna suke,kuma kalarsu ɗaya Babu banbanci, wannan gida gari guda kenan,daga parking lot ma kafin kaje harabar gidan sai ƙafarka tayi raɗaɗi in a ƙafa ne sai dai mota dama, dama kar asa security yasin ƴan Maula nisan wajen bazaisa su shigo ba😄 Nima yasin banda mota iyaka ta wajen gidan nida ba mota ba,in ALLAH yasa Ranar kai amarya naga yadda tsarin cikin gidan yake. Tuni Kawu Isma'il yayi oder kayan ɗaki dana kitchen daga germany ba ƙaramin kuɗi shima ya kashe ba, ankawo komai tuni an haɗa gida sai jiran lokaci. Amare an kammala exam lafiya sai fatan sakamako mai kyau,dan haka babu wasa Aunty Hauwa da Zafi zafinta tasa aka Fara musu gyaran jiki mai inganci mairo ƴar sudan ta ɗauko cikin kwana biyu da Fara gyaran jiki su Hadiyyah suka Fara Wani shining fatarsu tayi fresh sai annurin haske take fitarwa,dama can su masu kyau ne balle an ƙara da gyara!ga kuma maganin gyara na musamman wanda ba illah acikinsa kayan fruit ne aka sarrafa su kala kala,ga maganin sanyi ma Duk haɗa musu akeyi su kansu sunsan jikinsu ya canza daga ciki har waje! Khadijatu ƴan mata sai shiga da fita akeyi ga meenal ƴar Kawu Isma'il itama an tasa ansamu ƴar uwa a kusa sai Sha'aninsu sukeyi Suna tsara yadda bikin zai kasance. _____MOMMAH____ Za'a Aurar da ƴaƴa ai Babu Zama, Dubai tasa ƙawarta Hajiya indo tai MATA odar ta kayan lefe harda akwatuna abun sai wanda yagani akwatuna kamar buɗar idanuwa kayan ciki kuwa wai ku kiyasto su da kansu fans,dama Duk wasu Abu da Mommah takeso in batason zuwa ta siyo ita take sawa tai MATA tasan Babu gyara babu zago Hajiya indo ƴar Amana ce. Inda Mommah take rawar jiki da bikin nan yasin ko ƴaƴan cikinta ne albarka, AKEELA kam itama tuni anfara MATA gyaran jiki acan india da Mommah suka tafi idan suka tashi dawowa sai su dawo da angwaye gaba ɗaya,kunsan dai gyaran jikin indiyawa ko? To faɗar hadewar AKEELA ɓata lokaci da baki ne. ______AQEEL DA AKEEL_____ Anacan Karatun exam yayi nisa kai ya ɗau zafi final year ai dole a riƙe wuta,shiyasa ma suka saurara da yawan wayar da sukeyi dasu Hidayah sai sa'i da lokaci koda yake Suma lokacin Suna exam Suma. AQEEL fa da Alama ɗan love ne koda yake mukam munsan da wannan ai tun yana ƙwailan sa😄 inda Yake shiga super market na Birnin new delhi irinsu 'mahathtra' da 'srini krishna' yana lodar kayan kayan sawa irin nasu can na fitsararrun indiyawa abun ba'a magana wasu kayan Nikam bansan ta Yaya Hadiyyah zata sasu ba wasu dasu gwamma Babu kunsan dai irinsu, dama irin kayan Suna tafiya da imaninsa a Lokacin da sukazo farkon Fara karatunsu badon yana situation ɗin abinda Jimmai da Usman suka Masa ba da baisan abunda zai faru dashi ba, da kuma Addu'ar Abbu garesu itace tai Musu kariya! Dan haka yanzo baje hajarsa yakeyi anan,yana ɗaukar kaya yana hasaso Hadiyyah acikinsu sai kaga yawani lumshe idanuwa kamar me jin barci. AKEEL mutumin Hidayah ai dama shi kunsan halinsa babu ɓoye ɓoye a harkarsa,irin shigar sari dinsu da waɗannan ƴan kumnayen da awarwaro da sarkar kan goshi da wacce take haɗe da ta hanci shine hubby ɗinsa dan haka ya jidarwa hidayan sa wannan shigar yakeson tana Masa,Duk da shima ƙananun kayan ya ɗiba Amma ha kamar wannan ba. Lallai waɗannan angwaye ƴan Ayi ne, Suma fa za'a musu gyaran jikin da akewa angwaye na indiyawa haɗa baki sukayi gaba ɗayansu shiyasa ma bazasu tawo da wuri ba sai ankusa Fara shagali saboda kar gyaran yabi rariya cewar AKEEL. Mommah AKEEL yacewa " meyasa ba'a tawo dasu Hidayah ba Suma amusu gyaran jikin tare da AKEELA ne mommata? Babu ɓoye ɓoye tsakanin Mommah da ɗan ta AKEEL dama shi ba kunya gareshi ba! "Nayi tunanin haka AKEEL to amma da nayiwa Abbu magana cewa yayi Suna gidan kawunsu ana musu kuma ƴan sudan ne suke musu,Suma sudan badai gyaran jiki ba ga kamshi! AKEEL ya jinjina kai alamun ya gamsu da bayanin Mommah, ɗan gasken kuwa yana gefe baice komai ba Yasin, Alhalin shima yanason awa Hadiyyah Hakan. Cikin dare AQEEL ya farka zai shiga bayi,to dama bai cire cire Glass ɗin sa sai zai kwanta,yana buɗe idanuwa yaganshi tarwai kamar yasaka glass ɗin aikuwa da mamaki ya mike Yaje bayi yadawo batare dayasa Glass ba,sai murna yakeyi koda Asba AKEEL yaga bro babu Glass yace 'bro kanason kayi amarci da cirarren haƙori ko lemon goshi ko? Dan Nikam bazan mulmula maka ba,kuma kasan idan ba'a mulmula ba Baya komawa! AKEEL yaƙarasa da dariyar shakiyanci haɗe da bugun kafaɗar ɗan uwansa! "Bangaya maka ban...nan yakwashe yadda akayi jiya da daddare aikuwa AKEEL yayi murna jin AQEEL ganinsa yadawo normal sai ABunda ba'a rasa ba,aikuwa da suka Tashi sai da sukaje har sashen Mommah suka MATA albishir da Hakan kuma tayi murna(gida guda Abbu ya mallakawa su AQEEL a india suke ciki idan Suna da lecture suke school kawai,shima idan Yaje medical checkup anan gidan yake sauka, Yanzu ma Mommah da AKEELA a gidan suka sauka) Ko da sukaje Hospital an duba idanun AQEEL doctor yace Masa ƙarfin ganinsa ya daɗu sosai fiye da da,dan Haka Glass ɗin da Yake Amfani dasu yanzu sun Masa ƙarfi,Amma bazai dinga Zama haka ba saboda kwayar idanun tayi rauni ga ƙura da rana za'a Masa wanda zai dinga bashi kariya daga hakan da kuma kara ƙarfin ganin, Aikuwa nan danan aka Masa wasu masu kyau, Doctor yace yanzu indai ba fita mai nisa zaiba saboda Iska ko ƙura dan cikin gida zai iya yawonsa ba Glass sai murna yakeyi,haka suka dawo gida, ABBU yana germany lokacin dan Haka da suka kirashi a waya suka faɗa masa yayi murna sosai. ______ALHAJI HAMZA____ "Na barka kayi Auren nan ne saboda naduba naga akwai samu Sosai a jinin matar da zaka aura,Amma idan ba Haka ba kai kasan ƙarya ne, MATA nawa ka nema da Aure na hanaka saboda Auren nasu Babu samuwa sai ma koma Baya ita kuwa wannan ai za'aje da ita! Wata MATA nagani a zaune a Wani flour na Alfarma ta hakimce a kishingiɗe,Alhaji Hamza na Sa'adatu ya sunkuya a gabanta kamar mai neman gafarar ta! Cigaba da magana tayi "na Amince kaje gareta a yau na kammala Duk tsumakan da zanyi nayi,kana kusantarta Shikenan kakarmu ta yanke saka zamu samu ci gaba fiye da wannan muka samu nan gaba ta ƙarasa haɗe da nuna Masa Hanyar ƙofar fita,to "Shikenan ranki ya daɗe angama cewar Alhaji Hamza yana dosar ƙofar fita. Hajiya mansurah kenan Matar Alhaji Hamza wacce matsafiya ce ta ƙarshe,sun haɗu ne a wajen wata ƴar tuwo tuwo bayerabiya ce talauci yai Musu yawa bata,shine Tasamu takewa ƴar tuwo tuwo wanke wanke shi kuma yana zuwa cin abinci wajen,anan mansurah taganshi kuma taji tana sonsa, akwai wata ƙawarta seraph (bayerabiya ce Amma arniya)mamansu tsafi takeyi taso Saka mansurah Amma taƙi,dan seraph Babu abunda ta rasa na more rayuwa tana Bawa mansurah Amma tace itakam bataso,kayan tsafin gwanda tayi wanke wanke a tasha, asalin su ƴan imo State ne,Alhaji Hamza shi kuma anan yake harkar gwangwan to a tashar yake Zuwa cin abinci dan kuwa Hajiya maira uwar ɗakin mansurah ta iya girki da Ma'aika tanta,tun da mansurah taga Alhaji Hamza ta ɗimauce akansa ta daina walwala shi kuma ko kallo bata isheshi ba,to anan ne fa seraph taga ƙawarta a halin da take Ciki,ta tambayeta anan ita kuma mansurah tagaya MATA son Wani takeyi,dayake son Alhaji Hamza yaiwa mansurah kamun kazar Kuka koda seraph tacewa mansurah zona kaiki wajen mamana zata samo miki hanyar da wannan mutumin zai so ki,Babu Musu kuwa ta Amince. A Ranar maman seraph tasa mansurah a Hanyar tsafi,aka sata cikin ƙungiya mansurah Babu Wani ɗar ta Amince da Hakan,kuma acikin satin ta shawo kan Alhaji Hamza harya Fara kulata da magana. A gida kano state kuwa Alhaji Hamza yana da MATA 1 Faɗima da ƴaƴa biyu Salim da salima ga iyaye da ƴan uwa,Amma ina tun Haɗuwar sa da mansurah tafara sauya Masa Hali sai ABunda tace Masa,yafarawa faɗima hulaƙanci da ƴaƴansa, sannan yace Aure zaiyi anan imo State yaga matar Auren bayerabiya ce kuma,aikuwa inna da Baba sukace Basu Amince ba, ko da Alhaji Hamza ya faɗawa mansurah Babu ɓata Lokaci ta bada jinin su ba'ayi sati ba sukace ga garin kunan tsiran Kwana Biyu batare da ciwon komai ba. Kafin arba'in akayi Auren Hamza da mansurah Babu Wani bincike ko na komai,da zarar Wani ɗan uwansa yace Masa ya haka sai dai a wayi gari ya mutu. Haka yatawo da mansurah kanon sabo gidansa ya haɗa su da faɗima waje ɗaya,Amma fa faɗima ta Zama hoto a gidan,saboda kowanne aiki itace meyinsa Duk wannan ƙauna da soyayya da Hamza yakewa faɗima mansurah ta kawar da ita,balle kuma su Salim da salima kamar almajirai suka koma,Hamza yazama ɗan mansurah. Rana ɗaya mansurah tabada jinin Salim da salima aka wayi gari Babu su sun mutu,ko damuwa Hamza baiyi ba haka aka sittira su aka kaisu gidan gaskiya. Faɗima kuma taci gaba da Shan wahala a gidan Alhaji Hamza ƴan uwanta da ƴan uwan Hamza Babu mai magana, tuni tsafin mansurah ya ƙulle musu baki. Shi kuwa Alhaji Hamza tuni Mansurah yakoma a tafin hannunta sai ABunda tace Masa, kuɗaɗe kuwa ba'a magana Duk jinin da mansurah tabayar kuɗi ƙaruwa sukeyi a gareta,dan Haka Duk Wani abun more rayuwa dana ci ko Sha ko gidaje da kadadrori da Alhaji Hamza yake dasu a halin yanzu na tsafi ne wanda mansurah shima ta sashi aciki,bayan tai masa bayani, to dama sai ABunda tace Masa dan haka datai Masa tayi bai musu ba ya Amince,kuma har sannan sai abinda tace Masa. Tun Wani ciki da faɗima Matar Hamza ta samu take Shan wahala har zuwa Haihuwa Babu wata_wata mansurah tabada jininta harna jaririn gaba ɗaya aka aika dasu,wanda wannan bada jinin shine ya zamo Duk wata ɗaukaka ta Alhaji Hamza da Yake kai a yanzu inda mutane suka sanshi ga kadarori Babu adadi,har sannan sai ABunda Mansurah tace dashi. A Wannan lokacin ne kuma suka haɗu da Sa'adatu yana sonta har a ransa,Amma sai da Yaje yagayawa Mansurah data duba taga akwai samuwa da Auren nata jininta zai Amfani shine fa ta Amince Akan ya Aureta, kuma ya tawo da ƴaƴanta gaba ɗaya Gidan da zai ajiye ta. Ruwan tsafi ne mansura take tsuma Alhaji Hamza dashi shiyasa ta hanashi zuwa a daren Aurensa da Sa'adatu,wanda Wani sirri ne nasu na matsafa wanda ALLAH ne yasan meta shirya da hakan, yau kuma gashi tace ya tsumu zai iya zuwa wajen Sa'adatun. Sai rawar jiki Alhaji Hamza yakeyi acikinmota, direbansa yana tuka shi zuwa Gidan Sa'adatu sa'ar MATA ... Next page Akwai buduri Subhanallah meke faruwa ne? Sa'adatu Kinga abunda son kuɗin ki ya jawo miki ko? Wayyo ALLAH marayun ALLAH farouk da Haidar da Auta Hafsat Mezai faru gaba shin Mansurah zataci galaba Akan Sa'adatu kamar yadda taci akan faɗima Matar Hamza ta farko da ƴaƴanta? Gadai Sa'adatu har gidan mijinta,itama kuma Mansurah ba'a shiga shirginta da mijinta............ ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 8/31/24, 12:42 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SIXTY SIX 66* ✍️oum ARQAM ce "Lokacin da Alhaji Hamza ya ƙarasa gidansa wanda Sa'adatu take Ciki wajen maghriba ne,dan haka Kafin ya ƙarasa Anyi isha'i ma'aikatan gidan gaba ɗaya kowa ya kama wajen kwanansa,mai gadi ne kawai yake bakin aiki kamar Yasan yau mai gidan nasa zai Kwana a gida, dan haka driver yana horn aka buɗe gate ɗin ya cilla hancin motar cikin gidan,bayan driver Yayi parking Alhaji Hamza ya fito ya nufi Hanyar da zata sadashi da ainahin cikin gidan nasa,wajen Amarya tasha ƙamshi wato Sa'adatu sa'ar MATA. Ɓangaren Sa'adatu kam ta tsinke da Al amarin Alhaji Hamza ganin takwana na hantse Babu ango Babu labarinsa,takirashi a waya switch off Duk mamaki ya kasheta!da kunya ta tambayi ma'aikatan gidan Alhaji kam,haka wajen breakfast Abubuwa kala kala akayi sai wanda taci,Hakanan su Hydar ma sai kulawa ta musamman ake Basu shida Hafsat saboda sune ƙanana, shi kam farouk ya ɗan tasa yaro ne nitsatste mai Hankali like su Hadiyyah. Duk da Zuciyar Sa'adatu Babu daɗi haka ta daure taci abunda takeso tabar abunda bataso, har zuwa lokacin lunch shima Abinci wajen kala 10 akayi sai kace hauka,ita fa Sa'adatu tafara mamakin yawan ma'aikatan gidan aradu,Idan taga wannan bata kuma ganin Wata,sai da tafita wajen la'asar domin ta ɗan zazzaga gidan yaga ya yake,Anan mamaki ya kasheta gida iya gida,gajiya tayi da yawo ta dawo flour ta zauna tashiga tunnanin Rayuwa,wai ita Sa'adatu ce a Wannan aljannar duniya lalläi ne "Nikam naci sunana Sa'adatu sa'ar MATA domin nayi Sa'a ɗin,Haka ta ɓata lokaci har zuwa Sukayi dinner ƴaƴan suka tafi makwanci,itama kuma ta dangana ga aljannar duniyar Bedroom ɗin ta,tayi wanka zuciyarta Babu daɗin yau yini na biyu babu Ango,Lotion take shafawa taji An turo ƙofar ɗakin nata Babu excuse Tana ɗagowa kam Sukayi ido biyu da Alhajinta Hamza! Cike da sassarfa ya ƙarasa gareta itama Tawowa tayi gareshi ku kwace irin sabbin Auren nanne Saurayi da budurwa da suka mallaki juna lokacin da suka yanke tsammani. "Sai da Zuciyar Alhaji Hamza ta sosu tunowa da Yayi wannan zuƙeƙiyar Matar fa akwai wa'adi tsakaninsu,Amma da yayi tunanin irin ɗaukakar da zai samu da kuɗin da zai samu da ita sai ya basar! "Haba Alhajina ina matsayin Amarya jiya fa rana tace Amma shine ka gujeni,nakira wayarka switch off meke faruwa? Cike da muryar kissa Sa'adatu ta faɗa! "Aimun afwa Anam banji Daɗi bane jiyan, nikuma banson zuwarwa Amaryata Babu lafiya ne, yanzu bagashi nazo ba! Alhaji Hamza ya ƙarasa maganar haɗe da Tallafo fuskar Sa'adatu cike da ƙauna da so a zahiri a baɗini kuma tausayinta yakeji. "Shine ya tayata ta kammala kimtsawa tai Shirin Barci,bayan shima yayi wanka haɗe shiryawar! Sai kace wasu Ƙananan yara haka suka farantawa juna rai a Wannan daren. "Amma me tun bayan da Alhaji Hamza ya samu nutsuwa da Sa'adatu ta Fara jin Wani mugun raɗaɗi a jikinta na Azaba kamar ana zuba MATA Ruwan zafi musamman daga ƙugunta zuwa tafin ƙafafuwanta,tun tana daurewa har tafara gazawa dan sai hawaye takeyi! Lokacin kuma Ita kaɗai ce ɗakin dan Suna kammalawa Alhaji Hamza ya shiga bayi ya kimtsa jikinsa ya fito ta shiga bayin, futowar da zatayi bata ganshi a cikin ɗakin ba. Shi kam Alhaji Hamza ɗakin da Yake tsafinsa na cikin gidan yashiga,Bayan ya saka kayan tsafinsu,yai maganganun da zaiyi,sai ga wata mummunar Halitta ta bayyana,nan Alhaji Hamza ya zayyanewa wannan halittar cewa komai ya kammala Yanzu! "Cikin wata murya akace "munji daɗi da wannan abu siiisooo Amma Wani Hanzari ba gudu ba Sai dai muyi amfani da jininta a koda Yaushe sadaukar da rayuwarta gaba ɗaya sai nan gaba,saboda yaranta Marayu Sannan akwai Wani sirri ajikinsu wanda mahaifinsu ya dafa su dashi,ga Abubuwan Alkhair daya aikata a rayuwarsa shine Yake bibiyar rayuwarsu, sannan kuma Irin Haihuwa ce dan haka Duk cikin data samu zamu ɗaukeshi kafin wa'adin da muka ɗibar MATA yacika,na ka sadaukar da jininta ga Alhaji gohliiiiiiiiiiii Yana zuwa Anan ya ɓace ɓat Mummunar Halittar shi kuma Alhaji Hamza ya Adana komai yacire kayansa ya mayar da wanda yashigo dasu ɗakin. Haka Alhaji Hamza ya doso shashin Sa'adatu zuciyarsa da begen ƴaƴan da Aka Masa bushara dasu to amma Sadaukarwa ce ga aljani gohliiiiiiiiiiii,Shikam gohliiiiiiiiiiii Babu abunda nai Masa ba a duniya, ya iya bayar da Faɗima matarsa da Salim da salima ƴaƴansa uwa uba Inna da Baba ai kowa ƙarshene balle ɗan tayin da Yake Cikin mahaifa ( da Tuni Sa'adatu mushen gawarta xaije yagani,harda na yaranta to amma sanadin Hakan yasa abun yazo da ɗan sauƙi, Yanzu dai ga raɗaɗin da Sa'adatu takeji ajikinta kona menene oho?). A Wannan Halin Alhaji Hamza ya tarar da Sa'adatu aciki sai kakkarwa takeyi,yana zuwa yace MATA lafiya? Nan tagaya Masa abunda takeji, shi kuma yace mata " ko dai dan an kwana biyu ba'a haɗu bane? Haka dai suka kwana tana tashan azaba acikin jikinta! Cikin ikon ALLAH Kafin safiya Babu raɗaɗin sai dai tanajin wajen kamar banata ba. Komai na More rayuwa Sa'adatu tana samu gidan Alhaji Hamza yadda takeson rayuwarta. Haka take aiwatarwa,tuni su Hydar sun Fara zuwa school ko kunya aka musu transper daga wacce Abbu ya mayar Dasu. Sa'adatu Kullum jinta take gatanan to kullum ana Shan jininka! Alhaji Hamza kuwa tuni ya ƙara kuɗi fiye dana da ya ƙara samun matsayi. "Kulawar da Alhaji Hamza yake Bawa Sa'adatu ce ta damu mansurah bawai fa yadaina bin umarninta bane kawai dai tafiso taganta daga shi sai ita dan haka tai MATA mugun tsafi wanda dare ɗaya Sa'adatu ta Tashi bata motsi tana magana tana komai Amma ina Babu jikin motsawa! Ga wata uwar Rama da tayi ta ban tsoro sai kace tsowuwa haka takoma,gwanin tausayi,Alhaji Hamza sai da yayi tsafin da ya shafe Zuciyar Duk Wani ɗan uwan Sa'adatu wanda zai tuna da ita balle har yazo gareta! A Wannan Halin Sa'adatu tayi ɓarin cikin na farko Ga wahala ga cuta, Ma'aikatan gidan ke MATA komai tana daga kwance, farouk da Haidar da Auta Hafsat kuwa Suna can sha'anin gabansu suje school suyi abunda sukeso a gidan Amma ko tuna uwarsu basayi(sharrin tsafi)...... _____HAJIYA BAABA A KANO____ "Tuni An kammala kammala gyaran gidan su Hadiyyah har Baaba tadawo Gidan,gidan Yayi kyau sosai gwanin burgewa,oga Hunaif da Zeenah sai murna sukeyi anzama kanawan dabo. Zeenah kam ko sati batayiba ta gudu gidansu nada wato gidan Yaya Zakiyyah da Abbanta mukhtar tana ta Hidima da Twin's na'eem da na'eef har da Mammah ma, Yanzu anzama ƴan MATA ai ana secondary school ne js 2. Shima Hunaif ɗan alƙawari gidan Aunty indo(Ƙanwar Ummu Rumana wacce ta shayarshi) Nan ya tafi wajen Abokin sha yarwarsa Abul khair,Aunty indo da mijinta sunyi murna hannu bibbiyu suka karɓeshi, sun tabbatar da ɗan halak suka riƙa ba shege ba dan kuwa gashi bai manta dasu ba,Duk da sunsha baƙin cikin kwaceshi da Hajiya sakinah tayi wancan karon, Yanzu sai labari. "Anbar Baaba ita ɗaya a gida sai ƴar aikin da Abbu yakawota ta taya Baaba aiki,Aikuwa Khadija ta dawo gidan da Zama danta ɗebe MATA kewa meenal ƴar Kawu Isma'il biyo Khadija tayi Abinta,Ko kwana uku ba'ayi ba sai ga direban Alhaji Hamza dasu Hafsat da kayansu gaba ɗaya wai sun dawo gidan,idan akayi biki shikenan, Babu wanda yai Musu akace shikenan aikuwa sukaci gaba da Zama wajen Baaba sukabar Sa'adatu tana Shan azaba da gabza ita kaɗai Abinta.. _____MUTAN INDIA___ "Aradu bazaku shaida su AQEEL da AKEEL ba yadda suketa shining sunji gyaran angwanci na can ƙasar India,kyansu ya daɗa yawa ga gargasar nan ta jikinsu sai ƙalli takeyi,ni yasin ma sai naga kamar sun zama ƴan Indian ALLAH yasa su Hadiyyah su ganesu! To maza ma sukayi kyau sosai Inaga mace Wato AKEELA ma sha ALLAH nace lokacin dana ganta,kamar ka sace ka gudu, An gyarata ciki da waje sai glowing takeyi,Ta doctor Najeeb kenan Sha Alwashi Likitan zuciyarta kamar yadda take kiransa. Cike da kaya Niƙi niƙi suka antayo Nigeria kasarmu ta gado da shirin Bikin na kece raini, kowanne tsakanin AQEEL da AKEEL sai murna akeyi ana ta zumuɗin lokaci ya ƙarasa saura sati biyu kuma sati za'ayi anashan shagali. Dan kuwa bikin ƴaƴan gata ne ƴaƴa ga Alhaji Ɗalhat Abdurrahman(Alhaji tallafy) ko ina sai zancen bikin akeyi tun daga kano har maƙoftan jahohin mu ke harda kashashen waje ma waɗanda Suke hurda da Abbu zasuzo gangamin wannan bikin dan ma An ɗaura Aure da daɗewa!Amma Abbu yace sai an kuma maimaita Wani saboda gata. ______AMARE____ "Tabarakallah ahsanul ƙaaliƙiin" haka nace lokacin danaje gidan Kawu Isma'il nai Arba da Hadiyyah da Hidayah tsabar kyaun da sukayi ga Wani arnen ƙamshin da sukeyi lalläi ne Wani gyara sai sudan, naga alama Zaton da su AQEEL sukayi ya Tabbatar na gyara me kyau dasuke Addu'ar za'a wa matan nasu Addu'ar ta karɓu,su kansu sunsan sun canza tun daga cikin su har waje,dan sun jima sa Fara Shan magungunan kara ni'ima wanda da jallar ƴaƴan itattuwa aka samar dasu irinsu rake,mazarƙwaila da kanunfari dasu kankana ne da sauransu bayan sun gama Shan maganin sanyi,sun haɗu fa komai yayi normal, yanzu Haka Shirin dawowa gida sukeyi dan Akan za'a yi shagalin bikin. Ko da su AQEEL suka dawo sunso suzo gidan Kawu Isma'il wajensu Amma Aunty Hauwa fafur ta hanasu tace suyi haƙuri a kammala idan an kai musu su can su ƙarata,Dan gyaran da aka musu fatar jikinsu tayi santsi ga laushi kamar jikinsu kataɓa jini yayi tsartuwa! da ƙamshin da sukeyi komai ma iya faruwa idan suka keɓe dasu,shiyasa ta hana su zuwa,Duk da basuji daɗi ba haka suka haƙura da Umarnin Aunty Hauwa. "Amma fa anashan waya Babu dare Babu rana,muyi vedio call inji AQEEL Inga me ake ɓoyemun da ba'aso nagani sai zuwa an kawomin ke gidana! Ita kuma Hadiyyah suyi vedio call ɗin haka zaita Santi da sururai da koɗa ta Akan kyan datayi,Yana inama Suna tare sai dai kawai tayi murmushi. Shi ma AKEEL Hakan take gareshi anashan waya da vedio call ɗin, Hidayah tanashan Rashin kunya wajensa shi komai nasa Free yakeyinsa , ba kamar AQEEL da yake a baibai ba a wajen Hadiyyah take ganinsa kamar salihi nan kuwa yafi kowa Rashin kunya da komai ma........... Muje next pages sun kusa ƙarewa in Sha ALLAH ✍️ALLAH yakusa raba yari da ɓarawo RASHIN IYAYE yakusa gangarawa yaron da aka Haifa Fara typing ɗin Rashin iyaye ai Yanzu maybe ma ana aikensa😄😄 gashi har yanzu ban kammala littafin ba ALLAH yasa kafin na kammala kar yaron yafara Zuwa zance😅😅😅 Nikam oum ARQAM ALLAH yasa na kammala kwana kusa nahuta da fargabar typing kuma my Fans ku huta da zaman depon jiran update kuji shiru kunyi haƙuri dani fa sosai sai a slow fa🙏🙏 9/8/24, 8:08 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SIXTY SEVEN 67* "Duk Abunda aka saka Masa lokaci zaizo ne sai dai ba'a saka ba,zara bata barin dami ni Rãbiat Wannan satin aka Fara bikin ƴaƴan gata AQEEL da AKEEL da AKEELA a gefe guda ma akwai ƴaƴan gata na Kawu Isma'il wato Hadiyyah da Hidayah dan gaskiya fa ya ƙuƙe sosai to bansaniba ko zaikai Alhaji Ammar musu wahala inda yana raye! Dan gaskia Kawu Isma'il fa Dukiya tayi kuka kawai wadaƙa yakeyi da ita kamar baijin fitar kuɗin!kamar a fanfo yake kunnawa suke zuwa. Tuni Hadiyyah da Hidayah suka dawo gidansu na Ainahi suka zauna su da Hajiya Baaba,Babu laifi ƴan uwa sunyi kara Suna halartar bikin na kamar Lokacin bikin Zahra ba! Ko da Yake lokacin ai maraici yana kansu! Kuma dama ba'ayin abu dan ALLAH sai dai abun duniya ko ido(mahaifa guda Biyu ko Wani wanda ake girmamawa daya jibanceka) bansaniba ko dan ansan waɗanda su Hadiyyah suke Aurene? Ko kuwa dan idon Kawu Isma'il ne Yanzu?tunda wancan karon sheɗan yana kansa,yanzu kuwa ya sauka daga kansa. Da kamun Amare aka Fara! Wanda Mommah ce ta haɗa Hadiyyah da Hidayah da Auta AKEELA aka kamasu a katafaren gidan Abbu wanda yasha kuɗi Babu wanda zaice ba sabon gida bane saboda tsa rashin da akayi an canza Abubuwa dayawa a gidan,sai ƙamshin sabon guri Yakeyi. Wannan kamun Amare ya ƙayatar fiye da tunaninku Fans ku tambayi Rashin iyaye Fans group kusha labari irinsu Seerat da Haseena Aisha Sulaiman da MamaGee da mummy Waleed dan sune a gaba gaba harda Wani anko sukayi me kyau wai Duk saboda su kankaro ƙimarsu da mutuncinsu a wajen sai shiva da fita sukeyi anata hidima,wanda dama Yaya Zakiyyah ai Aminiyarsu ce dan bazance ƙawa ba,Duk Wani sha'anin bikin sa su akeyi aciki kai kace ƴan uwa ne😄 ni kam oum ARQAM ina gefe sai naga sun tafi nabisu a Baya,saboda ƙin Zakiyyah danayi abaya kar naje tana sane🏃‍♀️. Ƴan uwa na nesa dana kusa Duk sunzo daga ɓangaren gidansu Abbu sai hada hada akeyi gwanin sha'awa,Jimmai da Shukhra Suna daga cikinsu ,kamar ba'a taɓa samun Wani saɓani ba tsakani kuma dama ALLAH haka yakeso idan ansamu saɓani a yafewa juna idan an nema kuma akoma mu'amala kamar yadda ake da ko fiye da haka ma Amma idan ba'a koma kamar daba ana gaisawa Hakan ma ba laifi bane. Angwaye Ansha kyau sai wanda yagani a bikinnan dai AQEEL ya cire Glass ɗin sa dan haka babu wanda ya isa ya bayyana AQEEL ko AKEEL dan iri ɗaya sak suke komawa abunda Yake banbncesu ya ajiyeshi,sai Wani ƙalli suke gyaran Angwaye kam Yaji sai rawar ƙafa sukeyi Akan Haɗuwarsu da Matayen nasu a gidansu na Aure kowanne ƙiyasin da yakeyi kenan, musamman oga AQEEL dan sai a slow fa Ya kai geji shikam dama can haƙuri yakeyi Yanzu kuma yasan yanada dahir maganin matsalarsa, badon ma sharaɗin doctor ba ai da tuni yayi gaban kansa,to amma yanaso a kammala wannan biki yana cikin ƙoshin lafiya Abunsa,idan aka kawo Masa Hadiyyah in yaso acan komai sai ya faru yanzu kuma ai Babu batun Sharaɗin doctor da zaibi cin karensa Babu babbaka zaiyi. Katafaren gidan Amare Ya ɗau harama komai yaji ma Sha ALLAH a gidan kai kace a India ne iri ɗaya sak yasin,sai dai idan ka kalli sauran gidajen wajen ba irinsu ba Suma fa amma sunyi Kyau Amma ginin namu irin na 9ja ne tsantsararre,yan unguwa sunsan waɗannan Amare da angwayen ƴaƴan gata ne ta yadda aka dinga shiga da kayan Abinci kamar ana zubawa a hamsha ƙin store wannan Duk aikin Kawu Isma'il ne yace su Hadiyyah bazasu shiga ba sai da gararsu. Kayan lefen su Hadiyyah Nikam bazan iya magana akansu ba dan yasin sai nazata kasuwar kwari ta kano state ce yadda aka dinga shiga da akwatuna cikin gidan Baaba ba'a magana,Motocin da suka kawo kayan mallakin Amare ne inji Abbu,gwala gwalai acikin kayannan kamar Hajj Champ,iya su na hange saboda yadda suke ɗaukar idanuna sauran kayan kam tsoro sukaita bani,gashi su Seerat da Haseena Basu zo wajenba balle na raɓe ta jikinsu. Haka aka cigaba da shagali da ƙasaitaccen wannan biki,Amare sun gaji da haɗuwa sai kace ba ƴan 9ja ba saboda tsabar kyau! dama can su masu kyau ne basuyi kwalliya ba balle yanzu kuma sunyi kwalliya,balle Amarya Duk muninta kyau takeyi balle kuma abu me kyau yashiga lalle,kai wannan Amare da angwaye kyau ne da kyau ya haɗu sun dace da juna fiye da tunanin me tunani, musamman Lallen da shukasha Ƙafa da hannun na asalin Sudan me haɗe da turaruka da wasu sirruka nasu na Sudan. Ranar dinner wayyo ALLAH ni Oum ARQAM nera tayi Kuka na kaɗan ba abokan su AQEEL sun musu kara na gida 9ja dana India indai sukayi rayuwa,hakama su Hadiyyah ƙawayensu sun musu kara, Hajiya AKEELA ansha kyau sosai itada Angonta Doctor Najeeb,Suma iyaye da ƴan uwansa sunyi Masa kara,Ban gane ƴan Rashin iyaye Fans group ba gaba ɗaya saboda Suma sunyi ankon dinner ɗin,sai da na hangi seerat da ƴan kululluɓayan yara masu kama da juna guda Biyu tana tiri tiri dasu sannan na shaida ta Na'eem da na'eef ne sunyi masha ALLAH Amma Seerat sai yawo take dasu,ita Haseena Tana ta wajen Zakiyyah sai zuba abinci take tanaci ko koshi batayi MamaGee da mummy Waleed kuwa abun ba'a magana sai had hada sujeyi suyi nan suyi can da sunga Anbar juice ko ruwa zasu sakaye a jaka Aisha Sulaiman kuwa anacan ana tiƙa rawa kai taro yayi taro fa,Nima da bana rawa sai da Aisha Sulaiman ta rimbaceni bansan lokacin dana Fara takawa ba ina dansewa. Hajiya Mommah ikon ALLAH Ansha kyau sosai,Ga Alhaji Abbu namu shima ba'a maganar kyau dama wajensa Su AQEEL suka ɗosano kyaun dana Ummul khair. Har zuwa yau sati ana shagalin biki na kece raini Wanda yau ne biki ze kare,a yau ne Abbu yace za'a kuma ɗaurawa Ƴaƴansa Aure,aikuwa idan ka kalli ƙofar gidan Abbu da cikin gidan Duk girmansa da main faloun sa wanda yake yanawa da mutane a cike yake taf da mutane tun daga abokansa zuwa waɗanda ake zaman mutunci da al ummar gari waɗanda Abbu yakewa abun alkhair sun Nuna Masa zallar ƙauna da soyayyah,Duk wanda yaga waɗannan jama'ar tabbas yasan Abbu ɗan Arziƙi ne,Inaga komawa ga ALLAH yayi ai yadace dan Ma'aiki yace idan Mutane Arba'in suka sallaci gawar mamaci a kyautata Masa Zaton Rahmatullah. Dubbai ko nace miliyoyin jama'a ne suka sake shaida Ɗaurin Auren Hassana(Hadiyyah) Ammar yaseer da Hassan(AQEEL) Ɗalhat Abdurrahman sai kuma Hussaina(Hidayah) Ammar yaseer da Hussain(AKEEL) Ɗalhat Abdurrahman Akan zunzurutan kuɗaɗe da Motoci har da gidaje ga kowannen su(karku manta Fans wannan ihsani ne kawai Abbu yabasu dan kuwa sadakinsu na farko da aka Ɗaura aure shine sadaki) Wannan ɗaurin aure yayi Albarka sarakuna da gamnoni ga shugaban ƙasa da ministoci da kososhin gwamnati Duk sunzo bakajin komai sai tashin jiniya da algaita,Prime minister na kashashe daban daban sunzo kanon dabo saboda bikin ƴaƴan Alhaji tallafy. Haka aka cigaba da shagalin biki bayan Angwaye sunje gidan Hajiya Baaba Ansha hotuna na kece raini abun sai wanda yagani su Seerat da Haseena sai shiga picture suke su a dole sai sunyi picture da double twins. Har zuwa yamma lokacin da motocin Amare sukayiwa unguwar su Hadiyyah ƙawanya na jiran fito da Amare zuwa gidansu na neman tsira da taɓewa da neman neman aljannah da wuta(idan sunyi zaman ƙwarai su samu tsira da aljannah idan sunyi akasin haka su samu taɓewa da wuta ya ubangiji kabamu ikon yiwa mazajenmu biyayyah daidai gwargwado saboda mu samu tsira da aljannah ku barranta da taɓewa da shigar wuta🙏) Sai sannan Twin's idanuwa suka raina fata sai Kuka sukeyi abun gwanin tausayi Amma ina a haka aka taitayosu aka fito dasu sai a waje sukejin cewa Kowacce motarta daban zata shiga kuma da Angonta a gefenta kawai! Sauran motocin zasu ɗauki Yan matan Amare da Danginsu Saboda suyi musu rakiya zuwa Gidajen Aurensu. Jikin Kowacce Amarya ɓari yafara jin Wani sabon salon ɗaukar Amarya musamman Hidayah da tasan AKEEL ɗin ta baida kau da kai gareta indai sun haɗu saiya gwajilata,haka aka saka Kowacce a motarta bayan sunyi landing aciki divers suka ɗau hanya a nutse sauran motocin suka rufa musu Baya. _____SA'ADATU____ "Tsafi gaskiyar me shi dan kuwa ko ƙadan Babu wanda ya tuna da ita daga ƴan uwanta har zuwa wannan shagalin biki da akasha na ƴaƴan mijinta ko nace ƴaƴanta ,ko ace ina Aunty su kansu su Hadiyyah sun manta da ita kwata kwata,koda yake tunda su Auta Hafsat dasu farouk suka mance da ita ai kowa ɗazu ne,balle ALHAJI da yakecan wata uwa duniya. Ita kuwa Sa'adatu tana cikin masifa dan har sannan jikinta kamar banata ba,komai sai dai amata kuma ba ciwo takeyi ba,ga kuma Wani ɓarin tayi again wanda ba ƙaramar azaba tasha ba lokacin bata taɓa tunanin zata tashi ba. Mansurah tacewa Alhaji Hamza yadawo da Sa'adatu gidanta da Zama ,yafi ya dinga zuwa nan dana domin ita gaskia batason Hakan tafison kullum suna tare,dan haka Sa'adatu tadawo Gidan mansurah da Zama,kulawar da Alhaji Hamza yake bata yanzu ya daina ƴan aiki masu kula da ita tuni Mansurah ta hanasu, Sa'adatu tayi kashi da fitsari sai su kwana su wuni ajikinta Babu mai kulata, kafin kice mene jikinta yafara ɗaukewa saboda kwanciya, ga bakar yunwa da take addabarta ɗaki ne guda Mansurah tasa aka watsa Sa'adatu a ciki aka ƙulle sun Mance da shafin rayuwarta a ciki,gashi kullum anashan jininka ga yunwa ai akwai tausayi, Rashin kula Sa'adatu da Alhaji Hamza bayayine kwana biyu tunda tayi ɓari a wajen tsafi ya samu kashedi da babbar murya Akan dodo fa tayin cikin Sa'adatu yakeso akai akai tazarar wata uku ko huɗu kar yakai biyar,dan haka Yake sawa a gyara Sa'adatu lokacin da yake da buƙata da ita saboda kawai Tasamu ciki dodo ya ɗauke abunsa.................. Saura 👌 ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 9/15/24, 12:23 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SIXTY EIGHT 68* ______SA'ADATU____ "Sa'adatu Sa'ar Mata gwanin tausayi tazama fa, Yau kwananta Biyar da ɓarin datayi kuma tun ranar take zubar da jini gwanin tausayi Kamar an kwance fanfo zuba yakeyi,Babu me kulata shikam Alhaji Hamza Ko takanta baibi ba saboda yasan dalilin zubar jinin Yanzu haka makarin abun yake nema da zarar Ya samo ƙananan Yara guda uku Maza biyu mace ɗaya wanda basufi shekara Biyu zuwa uku ba DA zarar yabawa dodon tsafi Gohliiiiiiiiiiii Jininsu aka haɗa dana Sa'adatu na ɓarin nan datayi Shikenan Za'a bashi babban matsayi a kingiyarsu Yanzu haka shirye shiryen samun yaran yakeyi.... Sharaɗin aikinmu sisooo shine Karka bari mutum ɗaya yaganka lokacin da kake aiwatar day nufinka mun baka zaɓi cikin tsintsayen gida zaka iya mayar da yaran suffarsu lokacin da kake ƙokarin ɗaukarsu Amma da zarar an kamaka a Lokacin Alhaji gohliiiiiiiiiiii bashida iko akanka sisooo ka riƙe wannan Duk da bama fatar Hakan tafaru saboda kai tun farko Mai nasara ne sisoooo...... daga nan Dodon tsafin ya ɓace shikuma Alhaji Hamza ya cire kayan tsafinsa ya Adana ya fito domin Shirin tafiya samo Cikamakin aikinsa. "Shiryawa Alhaji Hamza yayi cikin Kaya marasa kyau sosai daidai talaka sannan ya fito yayi ɓad da bami,Mansurah sai fatan nasara take Masa,Dan itama matsayin dazai taka harda itane. 'Tsautsayi yarinya da ƙaninta mamanta Tabata shi tai MATA Reno a soron gidansu to yaron Yana ɗan takawa ya fito ƙofar gida Alhaji Hamza yana dafa yaron yazama 'zabo' yarinya tanacan tana wasa,haka yayi gaba abunsa saura yanzu mace da namiji. "Again dai a unguwar baiyi Nisa sosai ba yakuma samun Wani yaron namiji shima da alamu fitowa Yayi waje ALLAH ya haɗashi dashi take yamayar dashi shima zabo again, Yanzu saura yarinya mace yake buƙata Amma abun Kamar tsafi yakasa samu. Dan haka ya yanke shawarar Hawa motar haya hiece Ko ALLAH zai sa a dace aciki yasamu,fa zabinsa guda biyu ya hau motar kai kace mutumin ƙauye ne. Saura wajen Zaman mutum biyu gaba da Baya Alhaji Hamza yashiga Bayan,sai gashi ALLAH yakawo wata wace DA ƴarta mace a goye a bayanta batafi shekara 1 da rabi ba,Zata shigo to kunsan dai yanayin mota Hiece in zaka Shiga da goyo a bayanka gabje goyon kakeyi to gashi kuma yarinyar idonta biyu tana Kuka sai Zullo takeyi Dan haka Conductor yace "Hajiya sauketa ki Shiga tukunnna" Alhaji Hamza yasamu dama yana Daga Baya ya Miƙo Hannu ya karɓi yarinyar nan, karɓarta keda wuya kuwa ya mayar da ita zabuwa itama. Bayan matar nan ta shigo cikin Mota tayi landing conductor ya shigo mota tafara tafiya Mata ta juya wajen Alhaji Hamza domin ya bata ƴarta Amma sai me............ _____AMARE DA ANGWAYE____ Motar DA HADIYYAH da AQEEL suke ciki......... Tun Bayan Fara tafiyar day motar su tayi AQEEL yana inda Yake ko motsi baiba Amma ina!ganin Wani irin arnen ƙamshi day motar ta ɗauka ne yafara sawa AQEEL ya Fara Mance nutsuwarsa saboda dama fa shi a matse yake fa Wanga Al Amari,badon ALLAH ya taimaka Masa ba ai da tuni yakwanta ciwonsa wajen sau Babu adadi, A nutse ya matsa kusa fa Hadiyyah ya riko hannunta zuwa jikinsa, yana kasheta da murmushinsa me kyau,ita kuwa Hakan yazo Mata a baƙon Al mari ne Dan kuwa AQEEL bai taɓa kai Hannu gareta irin haka ba, lalläi ne Hadiyyah bakisan AQEEL yafison Hakan ba,lalurace tasa Shi kasa Nima miki kalarsa,mutumin daya Jima yana son kasancewa dake tun yana ƙaraminsa bai kai Hakan ba balle yanzu. Dan haka kukan day Hadiyyah takeyi ɗif ya ɗauke Jin yadda AQEEL Yake sunsunar wuyanta Kamar irin Magen nan tana shinshina Nama zataci! Yayi tunanin a iya wuyanta ƙamshin yake shiyasa yake Hakan! Amma dayaji ba anan yake ba sai yafara yawo fa hancinsa a Ko ina na jikinsa wanda Hakan yaƙara Masa Jin Wani irin yanayi ajikinsa,Dan haka Babu shiri ya haɗe bakinsa da nata yafara mata Wani irin Kiss mai tsayawa a zuciya da Rai! Tunda yasamu bakinka yaji abunda yakeji yafara lafawa dan Haka yayi ƙaimi wajen ƙara Sha Mata bakin Kamar yasamu Sweet Hadiyyah dai babu bakin magana Babu Hanyar tsira,sai mutsu mutsu takeyi Amma AQEEL Ko gezau Hakan ma Kara Masa Wani armashin yakeyi,Dan haka tazubawa sarautar ALLAH idanu a haka dai suke CI gaba da tafiya a motar driver bai San abunda suke ba,saboda motar akwai Wani frame yaya musu tsakani!haka AQEEL yaci gaba day Shan bakin Hadiyyah haɗe da shafa jikinta Duk inda hannunsa yakai kai lokacin harya Fara fita Daga Duniyarmu zuwa wata daban, lalläi ne fan's da doctor yaiwa AQEEL gargadi Akan Hakan Ashe dai day gaske ne🤔 wannan inda ba yau Amarya zata tare ba me kuke tunani ga AQEEL. Motarsu Oga AKEEL da Amaryarsa HIDAYAH...... "Iyayen rawar kai AKEEL kenan ita Dama Hidayah tasan ta haɗu da gamonta a yau ɗinnan me rabata dashi sai ubangiji, "Babu wata wata Bayan anshigo da Hidayah motar ana kullewa goganku ya matso gareta haɗe da yaye lulluɓin DA akawa fuskarta " inye Amaryata Duk wannan kwalliyar ni akawa lallai ne ni Hussain na Hussaina Yau ranata ce, An mallakamun Ke kimzama tawa nayi abunda naga dama take! Banda ALLAH wazai mana wannan ni'imar ta Aure mu biyawa kanmu buƙata ga dumbin Lada me yawa! Ya ƙarashe maganar haɗe da kallon cikin ikon Hidayah yana kashe MATA Ido ɗaya! Hidayah tafara sabawa day Rashin kunyar AKEEL fin haka ma tasan Zai iya faɗa mata! "Tun da bazakimin magana ba bakin naki yamiki nauyi bari na sauke miki kayan da suke bakin! AKEEL ya faɗa haɗe da Haɗe bakinsa Dana Hidayah yana lumshe idanuwa kamar me jin barci! Sai da yasha bakin son ransa duk irin mutsu mutsun ɗa take be barta ba sai Dan kansa,Bayan ya sanye zanbakin da aka shafa mata sannan yace " Yanzu na sauke miki kayan ina jira yi magana Ko kuma.... Ai Babu shiri Hadiyyah ta buɗe baki tace " Dan ALLAH ka Rabu dani muryarta cike da Alamun taci Kuka ta ƙoshi haɗe da ajiyar zuciya tayi maganar! Dariya AKEEL yayi haɗe day lalaubar jikin Hidayah ɗin yana cewa "lalläi ne ma Ke ɗinnan na rabu dake fa Kika ce? Me rabamu ai sai ALLAH tunda shine ya haɗa mu kuma haduwarmu alkhair ce rabuwarmu kuwa ai sharri ne Kinga kuwa ALLAH Baya nufin bayinsa da sharri! AKEEL ya Ida zancen haɗe da kafe Hidayah da idanunsa na Rashin kunya wanda sun sauya Kala,sai kace ba a mota suke ba sai budiri AKEEL yakeyi da Hidayah motarsu iri ɗaya da AQEEL sabuwa ce fil fil saboda Hakan Sukayi odar ta Daga Tallafy holdings kuma tukwicin Abbu ne yabasu. AQEEL fa an Fara nisa,Amma a haka ya daure ya saita kansa kafin azo gidan nasu, baison yaji kunya kunsan dai goganku wajen manyance ɗa miskilanci haɗe da shanye Abu. Shima AKEEL Hakan take ya kimtsa kafin motar ta ƙarasa gidan nasu..... A hakan motar Amare taci gaba da tafiya har zuwa katafaren gidan su na Alfarma wanda sai kace Rana zum a India ,Haka motocin suka dinga Shiga cikin gidajen Wanda akwai gate Wanda ya haɗe gidajen suka Zama ɗaya,to ranar budeshi akayi saboda mutanan Rabuwa sukayi wasu suka Shiga gidan Hadiyyah wasu ba Hidayah. To Nikam Rashin iyaye Fans narasa aina nake ganinsu irinsu Seerat da Haseena da Aisha Sulaiman da mummy Waleed day suransu suyi nan suyi nan sun kasa hankalunsu waje biyu,ga wani arnen Less da sukayi ankonsa na kawo Amare gwanin burgewa fa! Daga can na hango Seerat tare da Zakiyyah sunyi hanyar gidan AQEEL tana riƙe dasu na'eem da na'eef sunyi ɓangaren Gidansu Hadiyyah may be tsoron Rashin kunyar AKEEL suke,sun gwammace su kalli ta AQEEL, lalläi ne Yasin gwamma AKEEL day AQEEL shifa sai a slow.. Haseena da Aisha Sulaiman DA Bilkisu kam Suna ta wajen Hidayah sukam nasan kar suke zasu iya yiwa AKEEL Tatas musamman Haseena Bama kunyarsa zataji ba itama Aishan haka dama dama Bilkisun Mukhtar ma uwa ga ABIE. Har mutane suka kammala firfitowa Daga mota Babu ɗuriyar Amare fa angwaye sukam ƴan kai amarya saboda santin gida irinsu oum ARQAM ai ba'a kula da wasu Amare ba gaba nayi ina waiwaye . sai Daga can kuma Kamar haɗin baki suka buɗe Mota suka fito kowannen hannunsa cikin na Amaryarsa,dama driver Suna parking suka bar cikin motar,Ko me suke a motar oho😳 Zakiyyah da Seerat dasu Zahra fa Zaman jiran Amarya suke sukaji shiru ga dare nayi Dan haka suka fito Dan su musu magana sai gashi kuma sun Futo Daga motar a daidai lokacin da AQEEL ya sunkuwa ya ɗau ki Hadiyyah ya nufo ainahin gidansa da ita Kenan,aikuwa Daga seerat me riƙe dasu na'eem da na'eef day Zakiyyah kanta ai sai suka sake baki Suna kallon Rashin Kunya ta AQEEL a zuciyarsu Suna "shi ma dama haka yake!Nikam oum ARQAM nace oho muku ni nasan halinsa ai kuma ma seerat tasani bata faɗawa su Zakiyyah da Zahra halinsa bane kawai!Amma ai Seerat ai tasan halinsa farin sani sake da baki suka shige cikin ƙayataccen gidan nasu, Wanda akwai manya aciki Suna jiransu .... 'bazaina faɗa muku ba kunsan Sai halin AKEEL Babu shiri ya juya Baya haɗe day cewa ' matar Hau bayana kiji daɗinsa Yau ranar kice"batayi gaddama ba ta ɗane Bayan tasan idan bata Hau ba Zai mata abunda batayi zatoba. Suma Haseena da Aisha Sulaiman sun biyo sahun Amaryarsu ne har yanzu bata shigo ba sai sukaci Karo DA Amarya a goye a Baya Kamar jaririya,aikuwa Haseena Haka tace " yayi mutumina AKEEL kasan kuwa Amarya Sai da haka dama zuwa nayi nace maka karka bari taƙaraso day ƙafarta! haɗe da shewa Aisha Sulaiman tace " kwarai dagaske kuwa Haseena Amarya ai Kamar sarauniya take ranar tarewarta! Lalläi ne AKEEL yasamu abunda yakeso ai kuwa murmushi yaketa zubawa har suka dangana ga aljannar duniyar gidansu Su Haseena suka rufa musu Baya wanda sunbar tsofaffi acikin gidan ƴan kawo Amarya........ ______AKEELA_____ AKEELA Amaryar likita Itama fa Tasha Kuka lokacin rabata da Mommahn ta fa Abbunta sai da Mommah tashare ƙwalla itama ganin yadda AKEELA take Kuka gwanin tausayi,shikam Abbu yayi jarumta,a haka dubban ƴan kai Amarya daga dangin su Abbu Dana Mommah kai kace Yar tace ake aurarwa haɗe dasu Mama Jimmai sune a gaba gaba,Duk da jikin sai a slow Amma Usman Mota guda itama Shukhra da Daddy da matarsa ya ɗauka ya kaisu gidan AKEELA wanda yake Aljannar duniyar. Doctor Najeeb yayi gida iya gida ALLAH ya Kaɗe fitina za'ace,dangin Doctor Najeeb sun nunawa AKEELA ƙauna dam kuwa sunzo tarbar Amarya,sai ga MamaGee acikin ƴan kai AKEELA gidan miji,koda yake dama MamaGee tayi alƙawarin kai AKEELA ɗakin Mijinta. Sai da Usman ya tsaya ƴan rako ango,shikam doctor Najeeb Bai sabon salon ɗaukar Amarya na musamman ba irin nasu AQEEL da AKEEL ba shi bari yayi aka kawo Masa ita kamar yadda al'adar mu ta Hausa take sannan Yanzu kuma abokansa sukai Masa rakiya,Usman harda kukansa Akan sai Doctor Najeeb ya yafe masa cin Amanarsa da yayi ta hanyar kawarwa DA matarsa budurcinta ya Rigashi keta alfarmar ta,shikam doctor Najeeb baison taddoasa day Wannan maganar Dan ya Mance da itama , "komai ta wuce Usman a gurina na yafe masa ai komai ƙaddara ce,in banda haka aina zanga AKEELA harna aura! ALLAH yayi sai ta sandiyyar fyaden daka mata ne xan Santa,Nikam ita nakeso ba wai budurcinta ba ALLAH ya yafe Mana gaba ɗaya! Doctor Najeeb ya kammala maganar haɗe day dafa kafaɗar Usman day gogeasa hawayen fuskarsa. Haka abokai sukayi komai Kamar yadda Al Ada take kai kaga likitoci Kala Kala kuwa Duk sune ƴan siyen baki! Haka suka kammala aka bar AKEELA day doctor ɗinta Sai sharar hawaye takeyi............. Wayyo page yayi tsayi fa,kuyimin afwa sai da Rashin iyaye yazo ƙarewa nake ƙiwar typing,Amma lokacin danake typing ɗin komai nisan jifa Yaseen nan danan na kammala Shi har mararin typing nake kullum 2pages masu tsayi nake post haka ma Hakan ba kuskure bane badon ansamu matsala ba shima ina zuƙulƙulo Typing da posting Akan kari, to ARQAM ɗin kune rigimamme shine yake Hanani rawar Gaban hansti🥱🙄😀 Muje next page saura kiris in Sha ALLAH...... Muji ya Alhaji Hamza day yarinyar daya mayar zabuwa shin asirinsa Zai Tonu Ko kuwa? Sai ɓangaren Amare da angwaye Muji wace wainar zasu Toya ✍️oum ARQAM ce ontop 🥰 08128131163 9/18/24, 7:47 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SIXTY NINE 69 🤏* ✍️oum ARQAM........ _____ALHAJI HAMZA___ "Ganin ba ƴa a hannun Alhaji Hamza ne yasa matar tace 'Malam ina ƴa ta Daka karɓa ne? Cike da jarumta wanda Babu Alamun rashin gaskia A tare dashi 'yace bangane ƴar ki ba Yaushe Kika bani ƴa kuma? Ni danake Bayan kujerarki Ko Dan sharri! Harda ta da jijiyoyin wuya! Alhaji Hamza ya ƙarasa zancen. Ikon ALLAH Kenan sai Mota ta ɗau hayaniya ƴa wacce ba Allura ba anne meta an rasa sai CeCe kuce akeyi a mota kai kace gidan biki Ko suna ne! Mutane kowa sai faɗin Albarkacin bakinsa yakeyi! Anata Shan Mamakin ɓatan yarinya a mota,saboda kowa shaida me mata tabbas da goyon yarinya tazo motar nan,kuma Babu shakka ta miƙo ta cikin motar nan kafin tashigo,to Amma abun Mamakin Allura CE ita! da aka rasa wanda aka bawa. Mata dai ta kafe kai da fata cewa ƴarta fa Alhaji Hamza tabawa! kuma dole sai ya fito mata DA ƴarta,Mata fa Yar bala'i ce sai kumfar baki takeyi! Amma ina Alhaji Hamza dayake kunsan masu tsafi akwai taurin kai Dana zuciya,Ko gezau ganin yadda mata ta fita Daga hayyacinta Akan Yar ya baisa yaji tausayinta ba! Ko da yake mutumin dayake bada jinin mutane musamman ma matarsa da ƴaƴansa ga iyayensa Duk yabawa aljani gohliiiiiiiiiiii su balle wata ta tsitsiyar ƴar jaririrya! "Mota fa Abu yaƙi Ci yaƙi cinyewa fa!sai runtuma bala'i ake da Mata da Alhaji Hamza Akan ya fito mata da ƴa! Har sai da Takai driver ya tsayar da Mota fa, yace kowa ya firfito Daga motar! sai sannan hankalin conductor yakai kan hannun Alhaji Hamza sai yaga zabi guda uku 'Cike da Al'ajabi da mamaki conductor yace " Yallabai Anya kuwa Babu ƙamshin gaskia Akan matar nan nacewa kai tabawa Yar ta,saboda zabi guda Biyu na taro ka dasu lokacin da Zaka Hau motar nan har ina karɓar Maka wajen Shiga motar! Conductor ya ƙarasa zancen da tsare Alhaji Hamza day idanu kafin yaci gaba da magana "In kuma ba haka ba sai ka Mana bayanin ya Akayi zabi guda Biyu suka koma uku? Tunda conductor yafara magana jikin Alhaji Hamza yafara karkarwa da tsoron karfa asirinta ya tonu! Aikuwa daya Shiga ukunsa tunowa da maganar Dodon tsafin su """Amma fa zarar ankamaka a Lokacin da kake ƙoƙarin ɗaukar su to Aljani gohliiiiiiiiiiii bashida iko akanka sisooo ka riƙe wannan.............. Gumi ne yafara jiƙe fuskar Alhaji Hamza daya kammala tunano maganar! Su jama'a jin abunda conductor yafaɗa da kuma kakkarwar jikin Alhaji Hamza da gumin daya Fara jike Masa jiki yasa mutane sukayi caaaa kansa saboda alamun rashin gaskia ya bayyana gareshi! "Tabbas zabi guda Biyu yashigo dasu motar nan! Inji mutumin da yake kusa da Alhaji Hamza Bayan ya Lula duniyar tunani! Nan danan mazan cikin motar harda mutane ƴan wucewa suka kama Alhaji Hamza da Duka Akan dole sai ya Fadi yadda Yayi da wannan Yarinyar!Ko Dan yake magana ta fito zabuwa yamayar da yarinya,Dan haka ya dawo da ita sannan sauran zabbin ma dake hannunsa Babu shakka Wasu yaran ne! Nan fa aka rufarwa Alhaji Hamza da Duka tako Ina gwanin tausayi!Baki da hanci sai jini takeyi,har ya Fara fita Daga hayyacinsa ya Suma! sannan Wani dattijo yace "wannan ba mafuta bace fa kamata Yayi yafara dawo da Yar nan sannan komene ayi, yanzu idan Kuka kashe shi kuma fa ayi Yaya?sai sannan kuma kowa hankalinsa yadawo jikinsa! Dan haka aka samo ruwa aka sheƙawa Alhaji Hamza Daƙar yakawo numfashin azaba! Zaka dawo da Yar mutane Ko kuwa sai Mun rataya maka taya, Mun zazzaga fetur Mun ƙoneka! Cewar Wani zaƙa ƙuri aciki! Ita kuwa Mata ana cewa ai Yar ta Ammayar Mata da ita zabuwa takama Kuka harda Suma! gwanin tausayi Gani takeyi Yar ta ta tafi Kenan! Mata ne sukaje kanta ana yayyafa Mata ruwa ana rarrashinta! "Alhaji Hamza yaji zancen kisa Babu kunya Babu tsoron ALLAH yayi siddabarunsa yakira Aljani gohliiiiiiiiiiii 'aikuwa ya bayyana a idonsa "ni Yanzu Babu abunda zan maka sisoooo kaika Jawa kanka, kaɗan ma kagani akwai hukunci Mai tsakani gareka idan kagama Jin Wannan na mutanen! Sannan kuma ƴaƴan mutane zasu koma garesuuuuuuuu" Aljani gohliiiiiiiiiiii yafaɗa haɗe da ɓacewa ga idon Alhaji Hamza! yana ɓacewa kuwa Sai ga zabi guda uku sun Zama Yara guda uku! Abu sai kace Almara! Mutane salati suke suna ganin wannan bala'in badon ALLAH yasa wannan Matar a mota ya karɓi ƴarta ba, Shikenan ya cuci ƴaƴan mutane waɗanda ya sato, iyayensu maybe hawan jini Ko mutuwa ta samesu. Nan danan aka fara ɗaukar vedion Alhaji Hamza ana watsawa a duniya,kafin kace me ankira ƴan jarida Suna jin ta bakin mutane. Mutanen gurin sunyi niyyar kashe Alhaji Hamza Amma ina mutane masu hankali da ƴan Sanda day sukazo wajen Suka hana haɗe da tunasar dasu Akan dole aje dashi ya mayar da ƴaƴan inda ya satosu! Acikin motar ƴan Sanda aka saka Alhaji Hamza wanda yaji jiki a hannun mutane dan kuwa sun cire Masa haƙoran gaba,ga raunuka aka fa sauran sassan jiki,A haka har sukaje inda ya ɗauki ƴaƴan mutane! "wanda ya dauka a ƙofar gida kuwa koda akaje unguwar tuni uwar yaro ta fita a hayyacinta sai Kuka takeyi tayi nema harta gaji,ta tambayi yayar ɗan itama Dana wayo ba tace wasa yafito bata ganshi ba! Ta fitar da rai sai ga ƴan Sanda sun kawo mata yaronta,wanda yaci Kuka ya ƙoshi,Mata sai godiya takeyi haɗe da godewa ALLAH daya dawo Mata DA ɗanta lokacin data fitar da Rai, mutanen unguwa sai tsinewa Alhaji Hamza ɗan mafiya sukeyi. Haka suka ƙarasa inda ya ɗauki ɗaya yaron shima dama ba nisa, iyayen yaran ƙawayene ma,tare suka rufa nema,gashi ƴaƴansu sun dawo sai Hamdala, da ALLAH wadai da Alhaji Hamza akeyi. "Office ɗin ƴan Sanda aka koma da Alhaji Hamza ai Masa tambayoyi! Kafin kace me Gari da duniya baki ɗaya tasan Abunda Alhaji Hamza yayi,da wanda suka sanshi da wanda Basu sanshi ba,masu saninsa ma sunfi yawa sai ALLAH wadai ake Masa. "Mansurah kam a Facebook taga abunda yafaru da mijinta,dan Haka hankalinta yai matuƙar Tashi,data tuna da sharaɗin dodo Lokacin da zata saka Alhaji Hamza acikin ƙungiya, """mindiiiir Zaman sisoooo cikin ƙungiya zamanki cikinta! matuƙar yafita kema kin fitaaaaaa! Nan danan Wasu ƙuraje suka fitowa Mansurah acikin jikinta,manya manya take suke fasewa sai wari kuma,bakin Mansurah ya karkace yana zubar jini ga tsakiyar kanta kuma yayi ƙa toton rami tsutsotsi wane Miliyan sai Shan ƙwaƙwalwarta sukeyi! Duk Wannan azabar mansurah haɗe take jinsu cikin abunda baifi minti Biyar ba. "Alhaji Hamza sai raɗaɗi yakeji ajikinsa,ƙuraje sun fito Masa Duka cikinsa,sai ruwa me ɗoyi suke fitarwa! Ga shima again tsakiyar kansa tsutsotsi sun cika Masa,Wani abun mamaki ko guda ɗaya bata faɗuwa,sai wutsul wutsul Suke abun ƙyanƙyami! Sai da D.p.o yazo yabada Umarnin a ɗauki Alhaji Hamza zuwa gidansa domin Ayi screening ,tunda bashi da Imani baza'a Rasa wasu a gidan ba, gaba ɗaya Ma'aikan gidan ƴan kingiyarsu ne Dan haka akayi ram dasu Babu wanda aka bari. Aka Shiga cikin gidan kuma,shashen Mansurah suka Fara Shiga Nan sukaga abun tsoro da Al'ajabi ganin Irin halin da Alhaji Hamza yake ciki Itama Matara irinsa take Ciki Kenan,mugun abunsu ɗaya itama ram akayi da ita zasu fita daga gidan ne,Dan kwata kwata ba'a bi takan Sa'adatu ba wacce aka killace Wani ɗaki can taban. Alhaji Hamza ne yana kukan nadama da dana sani Akan shigarsa ƙungiya yanawa Mansurah ALLAH ya isa,yake faɗar Duk wasu mugun Abu dayayi day haduwarsa da Sa'adatu da abunda yai MATA. Babu Shiri aka je inda Suka killace Sa'adatu aka lalu bota,wacce tana Zaune kawai taji ta motsa kafafunta!DA hannayenta!tana yunƙurawa sai ta miƙe,abun Al Ajabi kuma shine jinin dake zuba ajikinta ya ɗauke, Amma fa sai Wari takeyi na jinin! Rashin ƙarfi da yunwa yasa takasa mikewa Daga wajen! Zuciyar Sa'adatu sai Mamakin wannan abu daya sameta tunda ta Auri Alhaji Hamza takeyi,da kuma hulaƙanta daya keyi!tana waɗannan tunanikan Ƴan Sanda suka shigo ɗakin! Dama da 6an Sanda mata suka tawo Suna toshe hanci suka ɗauko Sa'adatu suka Fito Da ita Daga ɗakin ! Sai ga ta razana ganin Halin da Alhaji Hamza yake ciki! Ga mansurah itama gaba ɗaya fatar jikinsu ta zagwanye Kamar waɗanda suka kone ga ƙuraje DA Ruwan dake zuba ga Wari! Alhaji Hamza yana Arba da Sa'adatu yafara kukan nadama! Yana neman yafiyarta da Duk irin abunda yai MATA,itama Mansurah Kuka tafara tana neman yafiyar Sa'adatu ɗin na Kwantar da ita datayi! Itadai Sa'adatu jiki Babu ƙwari sai Jin maganganun da Alhaji Hamza da mansurah takeyi sun razanata ba kaɗan ba, lalläi ma Ashe ALLAH ne ya ceceta, wai taga ƙarshen kwaɗayi ai sai Kuka takeyi. Ana tsaka da wannan ne sai gidan gaba ɗaya kuma yafara girgiza haɗe da wani ihu Mai razanarwa, ƴan Sanda musamman Matan ciki gudu suka Fara!take suka Kira ƴan jarida haɗe da kunna waya Suna ɗaukar vedio saboda wannan Abun abun Al Ajabi da jimami ne! Kafin kace me gidan Alhaji Hamza makota da sauran Jama'ar gari sunwa gidan tsinke,Bayan an ɗauki Sa'adatu zuwa Asibiti wanda ta jima da suma! Take D.p.o ya Kira Sheik ARQAM😘 (shahararren malamun Sunna ne wanda ya ƙware wajen Tafsir a radio da television, yana yana tsage gaskia da ƙarya,har shugabanni bai barsu ba,gaskia fadarta yakeyi) Nan d.p.o ya faɗawa Sheik ARQAM abunda Ke faruwa,wanda yasan yanzu ma yasani. Aikuwa Babu ɓata Lokaci Sheik ARQAM shida muƙarrabansa sukaiwa gidan Alhaji Hamza tsinke. Kuma Babu ɓata Lokaci suka Fara raira karatun Al kur ani Mai tsarki,saboda shine mafutar wannan girziga da ihun d ake a gidan Alhaji Hamza ɗin. Lokacin Alhaji Hamza da mansurah kam jikinsu fa yafara zagwanyewa Kamar yadda kyandir yakeyi idan yanacin wuta " Mindiir dama mun faɗa Miki ai kaɗan ma Kika Fara Gani! Wata katuwar murya ta faɗa wacce ba'asan Daga ina take ba, haɗe da cewa "Kaima sisoooo kasan sharɗinmu Dan haka Daga Yau Daga ku har mu Aljani gohliiiiiiiiiiii zaiga bayanmuuuuuu! Cike da ƙaraji wannan muryar take Faɗi! Shikam Sheik ARQAM da muƙarrabansa sai cigaba da karatun Al kur ani Mai tsarki sukeyi mutane sunata kabbara, Daga can wata wuta ta Tashi tanaci Kamar ana zuba fetur! Tanaci Bal bal Bal!sai gashi ta ɗigo Akan Alhaji Hamza aikuwa sai ya kama da wuta,itama Haka Mansurah wutar ta kama cinta gwanin tausayi!shikam Sheik ARQAM sai Karatu sukeyi ganin wuyar tana Kara ƙaimi ne yasa suka Mata Daga ɗakin Suna kallon sarautar ALLAH!sai da Alhaji Hamza da mansurah suka kone kurmus Ko gawayi Babu sai Toka! Sannan wanda ihun da girgizar Babu sannan Sheik ARQAM suka bar karatunnan, ƴan jarida ansamu abun so DA Mutane sai post akeyi,wasu Kuka da salati nayi masu ALLAH wadai ma ga Alhaji Hamza da mansurah nayi. Haka ƴan Sanda da tawagar Sheik ARQAM sukai tafiyarsu Bayan sun tabbatar da kowa yafice Daga gidan,aka haɗe tokar Alhaji Hamza da ta Mansurah aka Haƙa Rami aka bunne,mukulli aka sakawa gidan Alhaji Hamza (ALLAH ka karemu DA irin wannan Rayuwar, ALLAH kasa mugama da duniya lafiya,ka karemu DA saɓa maka DA kauce hanya Daga TAFARKIN sunnar manzon ka...oum ARQAM🙏 yanzu dai Alhaji Hamza da mansurah anzo duniya banza ankoma banza abunda Ake dansu Wato kuɗi an barsu an tafi Babu tsiya Babu arziƙi) _____GIDAN AMARE___ Ɓangaren Gidansu Hadiyyah....... Oga AQEEL dai kunsan a hannu yake Kamar lalle,Duk Yanda tsofaffi da su seerat suke jansa da surutu haɗe day tsokanar da akewa Angwaye! abun ya faskara sai Wani shan ƙamshi yakeyi! Yana daɗa ƙwakumar Hadiyyah wacce ya sauke ta Bayan ya shigo da ita a hannu ya sauke a hadaddiyar kujerar dake falourn,Suka karaci surutunsu da barwakcinsu yana ji yaƙi magana,ganin idanun AQEEL sunyi ka Kamar Gauta ne yasa seerat da raɗawa ƙawarta Zakiyyah a kunne cewar AQEEL fa bai DA nutsuwa yanzu,nan tagaya Masa irin lallurarsa aikuwa nan danan Zakiyyah ta dinga shelar cewa yakamata fa a tafi gida masu Motoci sunce zasu koma gida,kunsan fa ƴan kai Amarya da ance Mota zata tafi zakuga ana tsere kafin kice kwabo Babu kowa! Sai Daga ƙarshe Zakiyyah da Zahra sukaiwa Hadiyyah sallama itama Seerat da mummy Waleed sallamar sukai musu,zuciyarsu cike da tausayin Hadiyyah dan kuwa sun san Yau me raba Hadiyyah da AQEEL sai ALLAH! musamman Zakiyyah wacce yanzu tasan ya AQEEL ɗin yake. Ai Suna ficewa AQEEL yabiyo bayansu haɗe da kulle ƙofar falourn........... Gidansu Hidayah....... Su Haseena kam Basu Wani Jima sosai a gidanba,Bayan AKEEL ya Shiga gidan da Hidayah a goye a bayansa bai ajiyeta a falour ba, bedroom yayi da ita su Haseena da ƴan tsofaffin zasu biyo bayansu ya dakatar dasu! "Habadai mutanena ladan kuma ya isa hakanan,gatan yayi yawa, yanzu idan nace ki Shiga daƙina wanda zan Raya Sunna Nida matata sai ku biyo ni? Ku kallemun sirri to lala lala Lada ya isa! Nagode sosai da tayamu murnar aurenmu! AKEEL ya faɗi haɗe da shigewa bedroom ɗin da Hidayah goye a bayansa ƙofar ya kulle saboda kar su Haseena su shigo Masa ɗaki, Sukam su Bilkisu Da tsofaffin nan sun Sha mamakin AKEEL dawannan Rashin kunyar tasa,Amma Banda Haseena Dan kuwa tasan halin AKEEL. Shikam AKEEL ajiye Hidayah yayi a tsakiyar gadonsu na Alfarma Bayan ya sumbaci bakinta ya fito Daga ɗakin,yakuma kulle ƙofar ya cire key ɗin yasa a aljihun sa. Ya nufo su Haseena "Dan ALLAH Lada ya isa hakanan dare fa yanayi, Nikam inada abunyi fa,masu Mota sun mun waya Dana Shiga ciki Suna jira idan ba haka ba zasuyi tafiyarsu,sai kusan wajen zuwa Dan bazaku kwanamun a gidana ba, Alhalin ina sabon ango ku sanyamun idanu! AKEEL ya faɗi iya gaskiyarsa ko kunya. Tsofaffi dai da sauri suka dinga rige rigen fita Daga gidan!jin abunda AKEEL yace! Haseena shewa tasa haɗe da Tafawa da Aisha sulaiman Suna kallon AKEEL ɗin wanda yai dakon su fice ya kulle ƙofar sa,aikuwa dai da suka kuma tsokanarsa ya biye musu sannan suka fito Daga gidan shima ya ƙulle ƙofar falourn sa.. Tsofaffin gidan Hadiyyah da na Hidayah kam a parking lot suka haɗu Suna sallalamin Suna faɗawa juna Rashin kunyar AKEEL Suma na AQEEL Suna faɗar yanayinsa sai shewa sukeyi Suna Yaba Rashin kunyar Twins musamman ma AKEEL! Sukam su Haseena da seerat da Aisha Sulaiman da mummy Waleed sun haɗe sai kwasar dariya haɗe da Tabbatar da Rashin kunyar AKEEL a zahiri suke da dai oum ARQAM ce me gaya musu yanzu kuwa sunga Zahiri,haka ma kuma AQEEL sun Tabbatar da cewa shima fa babu sauƙi yanayinsa, a haka aka kwashe su gaba ɗaya a Motoci aka kai Kowacce gidajensu aka bar twins brother da twins sister a gidajensu domin barje amarci....... Dama ita MamaGee tuni doctor Najeeb yasa an mayarta gida..... Muje Next page 70 may be shine final Ko kuma 71 ✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰 08128131163 9/28/24, 2:19 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SEVENTY 70*🥳 ✍️oum ARQAM ce............. Burin kowanne masoya shine sukai ga Aure! musamman ma dai ace Suna matuƙar ƙaunar junansu!ai abun ba'a magana Hakan ce tafaru da AQEEL,Bayan ya kora su Seerat ya kulle ƙofar falourn,sai yaji kansa yaƙara Girma fiye da da! Wai Yau shine Yake da matar Aure,Abunda yajima yana kwaɗayin zuwan ranar tun shekaru da yawa,yake Fama da damuwa da lalura Akan Hakan,shikuwa me zaiwa ALLAH Idan ba godiya ba a daidai wannan lokaci, da yadda iyayensu suka musu Aure da wuri suka tsara musu rayuwa da ALLAH yayi nufin haka ai da tuni yajima da aure wannan lallurar dayake Fama d ita Aida tuni ta kau Daga gareshi,to dayake komai na ALLAH ne shine Yake tsarawa bayinsa Rayuwa sai yanzu lokaci yayi,kuma Duk da Hakan Alhamdullillahi! Shine abunda AQEEL ya Fadi lokacin yana tafiya zuwa falournsa. A yadda yabar Hadiyyah Akan kujera a lulluɓe a Hakan yasameta!kirjinta da zuciyarta sai Duka sukeyi,saboda batasan ya wannan lokacin Zai zamar Mata ba,Duk da zuciyarta cike take da zullumi da tunanin Yar uwar Haihuwar ta wato Hidayah!itama Ko a wanne yanayi take sai ALLAH,Dan tasan gwamma ita akanta,ita mijinta baida kunya Ko kaɗan! Tana tsaka d wannan tunanin taji ƙarasowar AQEEL falourn haɗe da faɗin 'Sweet Baby' Wannan lulluɓin na jiki fa! Na zata zanzo na tarar dake kin cireshi! AQEEL yai maganar haɗe da Zama kusa da Hadiyyah yana cirata sama, haɗe day warware lafayar da take jikinta, wacce ta amshi jikin nata sai Wani warwali takeyi, haɗe da fitar da Wani sihirtaccen ƙamshi! Amma ina yana warware lafayar sai yaji ƙamshin jikinta yafi na Lafayar sau nawa ma! 'Itadai Hadiyyah tun cirata sama day AQEEL yayi taji Wani tsoronsa ya kama ta!wai dama haka yake? Lalläi ne... Tana wannan tunanin taji AQEEL yana Mata wata irin sunsuna haɗe da yawo da hannayensa a Duk inda hannunsa yakai kai! Sai Wani sauke numfashi yake Akai Akai Kamar Zai shiɗe! Itakam Hadiyyah taga takanta Yasin. 'Daƙar ya saita kansa,ya mike tsaye da ita yana nufar ƙayataccen ɗakin sa,wanda yaji nera Kamar me!A makeken gadon sa yai mata masauki, haɗe dacewa 'Bari naje na dawo' kishiga Bayi kiyi wanka haɗe day alwala,akwai kayanki a ɗakinnan! Ki zaɓa kisaka,kinji sweet baby! AQEEL ya faɗa haɗe da sumbatar laɓɓanta! Itadai Hadiyyah batace komai ba. 'Yana fita Daga ɗakin aikuwa tayi saurin Shiga bayin, Aljannar duniya kenan, wannan bayi sai kace falourn shugaban ƙasa ko sarkin Zariya🤣,inda Yake walwali Duk abunda take buƙata akwai Dan haka tayi brush, haɗe da sauran abunda Zatayi,ga towel nan Kala Kala a hanger,sai dai Babu tsiya Babu arziƙi,ƙarƙarinsa inta Kaushi ƙirji yazo Mata cinya,in kuma ta Ɗaura a ƙugu shine zai kai mata ƙasa,Dan Haka Lafayar data shigo da ita bayin ita ta kuma mayarwa. Bata Jima DA fitowa ba AQEEL yadawo shima day Alama wankan yayi,yacanza Kaya zuwa wata rantsatstsiyar Jallabiyya sai kamshi yakeyi fatar jininsa ya shining haɗe da fitar da ƙamshi Mai daɗi. Kayan maƙulashen da aka tanadar musu a fridge ne ya ɗauko su,irinsu fresh milk, grapes, Apple, grilling meat wanda yaji haɗi na musamman! Ican Daga nesa DA ɗakin Wani ƙayataccen carpet ne kuma yadda akayi tsarin gurin dama nacin Abincin ma'abota ɗakin ne,Dan haka nan Yaje ya jera kayayyakin,ya dawo gareta! 'Kinyi wankan kuwa? Girgiza Masa kai tayi alamun Ea Amma Naga kin mayar sa kayan jikinki! Shiru Tayi Babu amsa! Shima baija zancen ba, wardrobe Yaje ya buɗe ya ɗauko Mata wasu sleeping dress haɗe da Hijab Mai Girma, Kayan ya ajiye a kan bed,hijab ɗin kuma ya miƙa Mata, Babu musu takarɓa tasanya, yashige gaba tabi bayansa, sallah yajasu,Bayan sun sallame ya juyo ya fuskanceta,ya dafa kanta ya karanta Addu'ar da Ma'aiki ya koyar damu Akan wanda yayi sabon Aure Ko ya sayi Bawa,sai ya dafa ta ya karanta wannan Addu'ar "Allahumma inniy asaluka khairaha,wa Khaira ma jabaltaha alaihi a auzubika min sharraha wa sharra ma jabaltaha alaihi" Bayan ya kammala yayi wasu addu'oi Akan ALLAH ya tabbatar da alkhair atare dasu,Lallai ne fan's dama haka AQEEL yake da ilimin Addini kai ma Sha ALLAH Abbu yayi ƙokari! Ya riƙo hannunta zuwa wajen daya Adana kayan ciye ciyennan,Babu musu tabishi,ya zaunar da ita ajikinsa,yana ɗiba yakai bakinta,ta kawar da kai, aikuwa kallonta yayi "Ki karɓa kici ta lallami Ko nayi miki ɗura! Ya Fadi haɗe da niyyar sauke ta Daga jikinsa day aiwatar da abunda yafaɗa Zai matan! DA sauri ta buɗe bakin,a haka yaciyar da ita wanda dole taci badon tanaso ba,sai da yaga tana Shirin Amai sannan ya ƙyale ta,shima yaci,Bayan sun kammala, bayi ya sungumeta ta kaita brush yasakeyi again,itama yamata sannan suka fito,Akan bed ya ajiyeta kafin yafara warware lafayar jikinta again,tana susunne kai Ko saura rarta baiyi ba,Dan Lokacin yafara fita a hayyacinsa! Daga Sanya Sleeping dress komai ya kankama! daƙar AQEEL ya karanta "Allahumma jannabnash SHAIƊAN wa jannabish SHAIƊAN ma razaƙtana" Daga sannan kuma komai ya kankama AQEEL fa yafice a hayyacinsa,komai cikin zafi zafi yakeyi!wanda Daga Gani Baya cikin hayyacinsa, ALLAH Sarki Hadiyyah tabani tausayi matuƙa gaya,Kuka take tana neman taimako,shima AQEEL ɗin kukan Yakeyi Shi bansan nasa na taimako bane kona mene oho! Iya wahala Hadiyyah tasha ta a hannun AQEEL,shima kuma yasha wahalar Sosai,saboda lalularsa,Yana samun nutsuwa tuni ya sume,itama Hadiyyah haka! Babu me taimakon juna Kenan,a haka Har Asba tayi Babu labari wajensu kowanne bai cikin hankalinsa.......... Mrs AKEEL (Hidayah) AKEEL Ɗakin daya ɓoye Hidayah ya nufa ya sameta inda yabarta,Aida gudunsa yaƙarasa gareta haɗe da sumbatar laɓɓanta da warware lafayar jikinta itama, ƙamshin dayaji a hancinsa ne yasa Shi saurin ƙarasa cire Mata ita gaba ɗaya! Hidayah zata hanashi yace mata "Kul ɗin ki ai Yau Babu ɓoye ɓoye tsakanina dake,Dan kuwa idan kikace Hakan zakiyi,la shakka bazan lamunta ba!Ke kinsan Halina komai nawa a bayyane yake! Cak Hidayah Kam ta tsaya da goce gocen datakeyi Jin abunda yafaɗa tasan Zai aikata! Sai da yacire Mata Lafayar sannan yaga inner's ne kawai ajikinta! Murmushi AKEEL yayi haɗe da faɗin "nazata ai bazakiji magana ta ba Dana faɗa Miki cewar,idan Zaki saka lafaya kawai ita nake buƙata,banson saka wasu kayan kafinta basaina Sha wahalar cirewa ba! AKEEL yaƙarasa maganar haɗe da shashshafa ilayirin jikinta, yana lumshe idanuwa kamar me jin barci! Har inners Saida AKEEL yacirewa Hidayah, wacce Kamar zata kurma ihu,ganin illar da AKEEL yai mata,Zama Babu Kaya gareta,kuma shine yai mata ai wannan Abun da kunya,Amma yata iya,tasan datayi gaddama,tasan shauran,Dan kuwa Babu abunda bai faɗa mata ba,wanda zai mata Daren Aurensu,Dan kuwa tasan sahibinta Baya magana biyu! sannan ya ajiyeta a gefe a Hakan,shima kayan jikinsa ya cire sannan ya ɗaukewa zuwa bayi,wanda Kamar Zuciyar Hidayah zata fito waje,tsabar tsoron daya shigeta na AKEEL! A haka ya sakar musu shower shine yamata wankan, sannan shima yayi,da towel ɗaya ya rufosu,tunda babba ne,dama yafaɗa Mata cewa "tare zasu dinga wanka,kuma a towel ɗaya zasu dinga tsane jikinsu! Koda suka fito Daga bayin tana maƙale ajikinsa,a haka ya ɗauko musu sleeping dress nasu yasanya Mata sannan shima yasanya,harda hijab ya ɗauko Mata, ya shimfiɗa sallaya ya zasu SALLAH,Bayan sun idar ya dafa kanta ya karanta Addu'ar da Ma'aiki ya koyar damu ga masu sabon Aure, haɗe da Mata tambayoyi Akan addininta,(wanda Hakan yanada kyau ga Duk Wani namiji wanda yai Aure,saboda yaji ya addinin matarsa yake,tun daga hukuncin jinin haila,nifasi,istihadha,DA kuma banbanci tsakanin maniy,maziy wadiy, kowanne mene hukuncinsa,da ita kanta janabar yadda take ta Yaya ma janaba take samun mutum da sauran su,ta yadda zakasan matarka shin da gyara a Al amuranta Ko komai normal,idan da gyara sai koyar DA ita,idan kuma Babu Shikenan,saika ɗora Mata, Hakanan shima idan mijin ne baida sani a Hakan Ke kin sani ki sanar dashi,ba Wani abu bane ai anzama ɗaya,saboda a gudu tare a tsira tare ALLAH yasa mudace,na rarraba bayanan ne daban daban Dana Su AQEEL kowanne cikin Daren nasu muƙaru da Abubuwa,Amma Duk Abu ɗaya suka aikatawa matan nasu, saboda Duk ƴan Ahlussunah ne) daidai gwargwado Hidayah tana da iliminta ba Addini. Sai sannan ma yatuna DA kayan ciye ciyensu,a gaggauce ya fita sai gashi ya shigo dasu, inda aka tanada Dan cinsu nan ya kai sannan yazo ya ɗauketa,a Bakinsa ya dinga zuba yoghurt ɗin sannan ya juye Mata a baki,haka take karɓa yata iya,Hakama Naman saiya tauna saiya Saka mata a baki sauran fruits ɗin ma Hakan, lallai AKEEL Naka salon daban yake. Tun Daga Cin Abinci Abubuwa suka Fara sausaya ga AKEEL daqar ya iya kaita sukayi brush,kafin su sake danganawa ga haɗaɗɗen bed ɗinsu,komai cikin nutsuwa AKEEL yake aiwatarwa kama Daga romance har zuwa Mai gaba ɗaya Bayan ka karanta Addu'ar da Ma'aiki ya koyar damu idan Mai iyali Zai mu'amalanci matarsa ,Bazance Hidayah bataji jiki ba a Wannan daren saboda nafarkonta ne,to dama Ta ina za'ace guri a rufe Babu alamar hanya sannan ace Wani abu Rana tsaka zaizo Yayi hanyar ai za'a Sha wuya,shima AKEEL farin shigane Yaji gajiya Sosai ta Rashin Sabo. A hakan Asba tayi a kunnen AKEEL Dan haka a daddafe ya Tashi ya Shiga bayi ya Tara Ruwan zafi,yazo wajen Hidayah wacce taci Kuka harta gaji idanu ya kumbure,abunka fa farar fata, fuskar nan Kamar Jan kosai,a Hakan ya sunkuceta zuwa bayin,Tasha Kuka wajen Gashin da AKEEL yamata na Ruwan zafi tun tana kuka harta daina, taji sauƙi sosai kuma sannan shima yayi wankan,yamata sukayi na tsarki sannan suka fito,a Hankali ya ajiyeta a gefen bed,ya shirya zuwa Masallaci,itama ya ɗauko Mata kayan sawa marasa nauyi,ya shimfiɗa Mata sallaya Amma ina bazata iyayi a tsaye ba, sai a Zaune Dan haka ya ajiyeta,da sauri ya fice,saboda sun shirya Hakan shida AQEEL zasu fita zuwa masallacin,Shi dama abunda Yasa yacewa AQEEL ɗin suje Masallacin shine, Doctor yacewa AKEEL ɗin Ranar da AQEEL yasamu biyan buƙatar sa in ba ALLAH ne ya taimaka ba zai samu Suman wucin gadi, sai an Masa wata Allura, wacce a Hankali a Hankali idan yana sex ɗin in Yana samun matsala har ya daina,saboda ƙarfin allurar da aka dinga Masa shekarun Baya. AKEEL Baya fatan Hakan ga ɗan uwansa,to Amma ina tunda yafito baiga alamun ƙofar AQEEL an buɗe taba,hankalinsa ya Tashi ganin Hakan,Dan haka yakoma cikin gidan sa,ya samu Hidayah harta idar da Sallah tana zaune,shima sallar yayi, sannan ya ɗauki Hidayah ya ɗora a kan bed,wacce har sannan bata daina matsar ƙwalla ba. "ALLAH yamiki albarka Hayateeenah, ALLAH yabamu zuri'a Mai albarka tagari, yadda Kika tsare mutuncinki har zuwa gareni ubangiji ya nesantaki Daga azabarsa, AKEEL ya faɗi haɗe da kallon idanun Hidayah yana Mata murmushinsa me kyau, ita dai sai Ameen take cewa,tanajin Daɗin wannan addu'a, sannan kuma tana tausayawa masu yawon tazubar Kenan Inda bata kawo mutuncinta ba ga mijinta na Sunnah Shikenan Duk wannan yabon da addu'oin bazata samuba,Saima fitina da zargi! "Hayateeenah Twins brother ɗina bai fito ba,alamu sun nuna........... Nan ya gayawa Hidayah komai game da AQEEL na ciwon sa,ta tausayawa AQEEL ɗin,Amma kuma fa Tana hango Azabar da Twins sister ɗinta zata Sha a hannunsa,Dan kuwa ita yanzu mijinta normal yake Tasha wannan wahalar Inaga wanda baida lafiya cikakkiya! Nan suka dinga tattauna yadda za'a ɓullowa Al amarin,game da halin da AQEEL yake ciki, sun yanke shawarar Kiran AQEEL ɗin a waya,ki ALLAH zaisa ita Hadiyyah ta ɗauka,Duk zuciyarsu fal tunanin Halin da itama zata kasance,Dan kuwa zataji jiki ainun a wajensa. Mrs AQEEL (Hadiyyah) Har sannan AQEEL bai farfaɗo ba,itama Hadiyyah ɗin a sumen take,ƙarar wayar AQEEL ce ta dawo da ita hayyacinta, ALLAH yaso tana kusa da ita,Dan haka motsawa tayi daqar,saboda azabar datake ji a ƙasanta,ga wani mugun ciwon jiki, haɗe Dana qirji daya sameta dare ɗaya,sai katsewa jiran yake daqar dai Takai hannu tadau Wayar sunan 'twins brother' ne Dan haka tasan cewa tabbas AKEEL ke Kira,juyawa Tayi ta dubi AQEEL dake gefe a sheme tayi tunanin barci yakeyi,Dan haka da dashashshiyar murya ta Kira sunansa Amma ina shiru kakeji,sai taga idanunsa ma a buɗe suke alamun Suma yayi,Dan Haka Daga ƙarshe ta ɗauki wayar cikin ƙarfin Hali 'Assalamu alaika' ta faɗa da murya ƙasa ƙasa 'yawwa Yaya (nufinsa yayar Hidayah abokiyar tagwaitakarta ,kuma shima matar yayansa Abokin tagwaitakarsa,🤣) Ga Hayateeenah , yafaɗa haɗe da karawa Hidayah wayar a kunne! Meke faruwa sister ina AQEEL ne? Fashewa da Kuka Hadiyyah Tayi tana faɗawa Hidayah halin datake ciki,dashima AQEEL ɗin cike da tausayawa Hidayah tadinga kwantarwa da Hadiyyah hankali haɗe da faɗa mata yadda zatayi tayiwa AQEEL ɗin sannan sukayi sallama. Yadda sukayi da Hadiyyah haka Hidayah ta faɗawa AKEEL,ya tausaya Mata, sannan ya tausayawa AQEEL shima. Itadai Hadiyyah da dabara ta yunƙura wanda sai da tayi dagaske, sannan ta Sauka Daga bed din,Bayan ta fashe da kukan azaba,Amma dole ta tallafi rayuwar abun ƙaunarta,Kamar yadda ƴar uwarta ta faɗa mata, Kaya tasa ajikinta daqar, sannan tasawa AQEEL ɗin nasa wanda yacire,Takoma takwanta tana kuka haɗe da Mai DA numfashi,sai da tahuta sannan Takuma yunƙurawa,ta tafi toilet ta haɗa Ruwan zafi tashiga ciki wanda Sai daqar ta iya Shiga ciki,Amma Hidayah tace Mata idan tayi zata samu sauƙi sosai,itama Yanzu haka Shi tayi, yanzu normal take jinta! Dan haka tadaure tadinga canza ruwa harta samu relief,tai wankan tsarki ta fito a hankali,Amma fa har sannan tanajin raɗaɗi a ƙasanta! Daqar tasamu Kaya marasa nauyi ta sauya Takoma bed ta kwanta,tana kallon AQEEL har sannan yana Kamar matacce. Can ɗaya ɓangaren kuma Doctor ne ya aiko da nurse da allurar da za'awa AQEEL yadawo hayyacinsa,Dan haka AKEEL aka bawa shikuma yakira Hadiyyah Akan tazo ta buɗe kofar room ɗin, ƙofar falourn Pin ne Wannan yabuɗe yasani,ciki kuma key ne daƙyar Hadiyyah ta fito ta karɓi Allurar,saboda ta iya Allura shima AKEEL ɗin ya iya to Amma ai wannan cikin ɗakin sirrinsune bai kamata ya shigar musu ba. Ko 10mins Hadiyyah Bata yi da Masa Allura ba yadawo hayyacinsa,sai sauke ajiyar zuciya yakeyi,yana jinsa Kamar Wani sabon mutum,mararsa data Masa nauyi haɗe da Tauri yanzu saura kaɗan, 'godiya yayiwa ALLAH a zuciyarsa na yadda ya Sanya Mata suttura ga maza Suma mazan suttura ga matansu, yanzu gashi yasamu nutsuwa wacce bai taɓa tunanin akwai irinta a Duniya ba, shikam yazata mararsa da cikinsa bazasu taɓa komawa daidai ba,tun bayan Hakan da sukayi, yanzu yaji alamun zasu koma normal saboda yadda yaji Daga yi ɗaya harya samu relief. Janyo Hidayah yayi jikinsa,yana Kuka haɗe da fadin ' ALLAH yayi miki albarka ya shafe kura kuranki,ya Amintar dake 'Halawateeynah' kinmun Abunda Duk duniya Babu wanda zai iya Mun Ko mahaifiyata inda tana raye balle mahaifina dayake Raye,saboda wannan wata baiwa ce DA sururi tsakanin ma'aurata da ALLAH ya Sanya Shi,nan dai AQEEL yaita yabon Hadiyyah dasa Mata albarka, yaci gaba da magana 'Kin kawomin Abunda Yake tsada a Wannan zamanin wato budurci, bakowacce budurwace take dacen kaishi gidan miji salin alin ba,saboda lallacewar Zamani,Yarinya budurwace Amma ina ta siyar da budurcinta,kekam Yar baiwa ce ALLAH yajiƙan Iyayenmu da Rahma yasa aljannah makoma. Bayan Hadiyyah tagama Shan yabo DA addu'oi,yadawo hayyacinsa sosai, ƙarfin jikin sa yadan dawo,Amma fa gajiya akwaita Dan yaji jiki, Abubuwan da suka faru bai yisu da sauƙi ba dan haka gaba ɗaya jikinsa ciwo yake Masa musamman,bayansa da ƙafafuwansa. Hadiyyah Tayi gaddamar binsa bayi tace Masa ita tayi wankan ta Amma dole ya tursasa ta Akan dole saita kuma yi,Babu yadda ta ita haka tabishi Saida yakuma gasata,shima ya gasa jikinsa yayi wankan tsarki suka fito, ganin Yadda take ciccije baki da tafiya a Hankali yasan tabbas Yayi ɓarna. Bayan sun gama kimtsawa yakira AKEEL,tunda Hadiyyah ta faɗa masa cewa yakirashi,Jin muryarsa a sarke yasa AKEEL bai tsonake ba kamar yadda Yayi niyya! Ka kirani lokacin ina bayi ne!cewar AQEEL yana lumshe idanu! 'To Zubair nasan komai fa, karka ɓoyen komai,Babu abunda bansaniba, ka fice hayyacinka ne saboda samun nutsuwa!Dan haka yanzu ya jikin Naka?Amma normal kake jinka ko?fuskewa AQEEL yayi sannan yace kakiramin Doctor yanzu Halawateeynah Babu lafiya fa!to dama ina zatayi lafiya ka cuci Yar mutane ka kasarata! AKEEL ya ƙarasa maganar haɗe da dariyar shakiyanci! Shikam AQEEL kashe Wayar yayi. Kamar yadda AQEEL yabuƙata,Doctor yazo haɗe da nurse,aka Masa alurai aka Bashi magunguna, Itama Hadiyyah anbata magunguna Saida aka Mata Ɗinki Amma kaɗan, Hidayah ma ambata magani, Shikam AKEEL Babu abunda aka bashi normal yake. Daga AQEEL har AKEEL haka suka dinga kulawa da matan nasu kamar kwai a cokali,haka Dama abun yake muddin Kika kai budurcinki ga mijin Aurenki,Zaki samu kulawa fiye da yadda kike tunani,Hakan take kasancewa ƴan mata mu riƙe mutuncin ku ku killatashi wa mazajenku,akasin Hakan najanyo kaskanci da wulakanci koda kuwa shine ya kawar miki da budurcin saboda zargi ne Zai Shiga tsakaninku. Lafiyayyen Abun Kari Mommah ta Aiko musu dashi,haka ma da rana,sai tarairaya sukesha wajen mazajen nasu, AQEEL ya Fara komawa normal, Su Seerat da Haseena da Aisha Sulaiman da mummy Waleed sunso komawa gidan Amare Amma ina angwaye sunbada umarnin kar Abar kowanenne yashigo musu gida Har zuwa sati ɗaya. Amarci akesha Babu algus a Wannan gidaje musamman gidan AKEEL,Shi AQEEL an kwafsa Masa saboda ɗinkin da akawa Hidayah,Amma kwana biyu ya sarara Mata, Daga bisani aka baje harkar Cin amarci babu kama hannun yaro. Tun Hadiyyah taqi harta ware abunta Takoma Kamar AQEEL kullum shikam yajishi a network. Saɓanin AKEEL daba kullum ba muddin za'ayi romance shikam anan yafi Kauri.to dama haka abun yake ai kowa d abinda ALLAH ya Sanya yazamo abun sonsa. Sunji abunda yasamu Auntynsu+ (Sa'adatu)sun Ji Babu daɗi sunwa Alhaji Hamza Tofin ALLAH ya tsine. Su Hydar farouk da Auta Hafsat dama Suna wajen Baaba,Dan haka Daga Asibiti Bayan sallama Gida Ƴan uwan Sa'adatu sukayi da ita,wacce tayi nadama ba kaɗan ba Akan halinta Nason abun duniya da cin Amana DA yaudara,sai istigfari takeyi,Ta warke Takoma normal Yanzu Kamar Babu abunda yasameta,so take ta samu lokaci tajewa waɗanda ta zalunta Akan su yafe Mata. Daga wannan page ɗin Rashin iyaye yayi ƙarewa🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 ✍️Oum ARQAM 08128131163 10/7/24, 10:55 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SEVENTY ONE 71 END* ✍️oum ARQAM ce....... Kamar yadda Sa'adatu ta kudirce a ranta Hakan tayi,Bayan ta warke ragal sumul tasa zuwairah yayarta wacce take Zaman gida Yanzu ta rakota gidan Baaba,lokacin duk Yara Suna school,Cikin Kuka tadinga zayyanawa Baaba irin mugunta da Cin zalin da tadingawa su Hadiyyah,tacewa Baaba ta nemar Mata afwa gunsu, Baaba tace Babu komai aidama rayuwa ita haka take,Nan Baba Tabata shawarar taje wajen mazajen data aura tanemi yafiyarsu haɗe da matansu kawayenta waɗanda taci musu Amana, Sa'adatu taiwa Baabah alƙawarin zata aikata Hakan,tajima a gidan Har Saida Yara suka dawo Daga school. Taga yadda su Hydar farouk da Auta Hafsat sukayi kyau abunsu Babu abunda yadamesu DA rashinta Ko abinda yasameta!tayi Hamdala ga ubangiji,ita ta cuci ƴaƴan wata ga nata ba'a cutar Mata ba(koda yake ai dama haka abun ALLAH yake ba Duk abunda kayi za'a maka ba,Wani sai kaje can lahira ALLAH zai biwa wanda Kawa hakkinsa,Ko kuma kai idan ba mutumin kirki bane,maybe mijinka Ko iyayenka Wani ɗan uwanka Nagari ne to sai Kaci wannan darajar tasa Ko ƴaƴanka su ci,haka kuma koda kai mutumin kirki ne maybe iyayenka Ko Wani ɗan uwanka bana gari bane wannan abunda yayin sai ya samefa, sakayyah tazo a kanka,Dan haka idan kana mutumin kirki Wani abu yasameka bana Dadi ba karkaji Babu daɗi Ko mutane sudinga cewa ai tunda kukaga Abu kaza yasamu wane maybe yana aikata irin abun a ɓoye,hakana idan mutumin banza ne shima abun alkhair yasameshi karka ce Wani abu Ko kace Shi wannan ba mutumin kirki ba Amma Babu abunda ya Sameshi ba haka ba ne akwai Lokaci,hakana Duk wanda yayi zina da ƴar Wani za'ayi da tasa,hakane Amma wlh Wani bashine ya aikata ba maybe mahaifinsa Ko kakansa na farko Ko acikin Jerin kakanninsa Wani yayi zinar Amma sakayyar batazoba sai a kansa, Kunga Ai shima sai Yar tasace Shi wanda ya aikata ɗin koda Baya duniya,ya UBANGIJI kaimana me kyau ka Tabbatar samu Akan tafarki madaidaici alfarmar masoyina shugabana Annabi muhammad Saw✍️) Kamar yadda Sa'adatu taiwa Baabah alƙawarin zata nemi yafiyar waɗanda ta zalunta ta aikata Hakan! Takanas har gidan Alhaji Gambo taje wajensu Hajiya ikilima da Hajiya Sahura ta nemi yafiyar su dayake yanxu sun Zama mutanen kirki Babu Wani jayayyya suka yafe Mata, musamman Hajiya ikilima wacce Sa'adatu tafi ciwa Amana sai sannan tai musu gaisuwar Hajiya suwaiba,taga Abbas ma Sha ALLAH ya Girma sosai hakana taga ƴar wajen Hajiya Sahura wato Asalamiyyah itama hakan ta zauna a gidan Har saida Alhaji Gambo yadawo ta nemi yafiyarsa d irin tozarcin data Masa yace ALLAH ya yafemu gaba ɗaya,haka tabaro gidan cike da murna. Taje gidan Kawu Isma'il shima tanemi yafiyar Aunty Hauwa tace Mata Babu komai ai dama haka rayuwa take. Shima Kawu Isma'il tanemi yafiyar sa yace ya yafe Mata ai dagashi har ita masu laifi ne sai dai sudage da istigfari. Takanas taje Har gidan Alhaji tallafy shima tana kuka, ALLAH yasa Ranar weekend ne yana gida nan tanemi yafiyar sa Bayan ta zayyane Masa makirci da tuggun dasuka dinga aikatawa itada jimmai sune silar rabuwar abotarsu ta har abada shida Amininsa ta yadda har yakoma ga ubangiji Basu gana ba,Abbu yace Babu komai ai komai yawuce. Zuciyar Sa'adatu Yanzu tayi wasai Amma idan tatuno da Ummu Rumana DA irin zaluntar ta datayi gashi Babu halin neman yafiya shike ɗaga Mata hankali,kullum cikin istigfari take. ______ƁANGAREN JIMMAI____ komai Alhamdulillahi za'ace Dan kuwa Yanzu ta saita kanta ta Dage da bin ALLAH itama tuni akasha bikin Shukrah da Angonta Is'haq kuma Alhamdullillahi Babu wata matsala a zamansu, Saida tayi satittika ya ɗauko dansa Shaheed yakawo mata tana ƙaunar ɗan nan, yayanta Usman ne yai mata komai kuma sosai yakashe Mata kuɗi wanda bazasu lissafu ba,saboda Yanzu Usman kuɗi sun zauna sai Sam barka. Jimmai tuni ta warke saidai fa akwai sharar ƙafa da harshenta ya ɗan karye idan tana Magana ba'a ganewa sosai,jimmai a Hakan ma tagodewa ALLAH. ___GIDANSU TWINS BROTHER (AKEEL DA AQEEL) DA TWINS SISTER (HADIYYAH DA HIDAYAH)____ AQEEL tuni ya warke tun Bayan kammala allurorin da doctor yace za'a Masa, yanzu sai Shan harka akeyi babu wata fargaba, Hadiyyah da AQEEL Suna zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu komai tare sukeyi,Bayan kammala biki da wata Biyu Abbu yai Musu maganar komawa India domin Dora karatunsu,Suma su Hadiyyah za'a Samar musu gurbin karatun acan,sai dai me ai tuni Hadiyyah tafara laulayi me zafi wanda shine ma ya dakatar da tafiyar tasu sai zuwa Wani lokacin kuma,karkuso kuga tarairayar da Hadiyyah takesha wajen sahibinta (lalläi ne Yanzu Hadiyyah wata Tara zakiyi a gidan miji ki haife lallai Haseena dama haka kikace maybe nan da wata Tara kuzo Suna ga hasashenki yazama gaskiya) Tsakanin Hadiyyah da AQEEL narasa wayafi wani nunawa ƙauna aradu,Nikam oum ARQAM nace ALLAH yaƙara danƙonta. AKEEL baban Rashin kunya na Hidayah Sha Alwashi wata irin ƙauna da soyayya Ake Sha,surutun nan da Rashin kunyar sa dai da yayi Alwashi sai da yakoyawa Hidayah Shi,takoya kuwa kunsan dai makoyi yafi wanda ya iya Abu in yatashi yin nasa! Yanzu Hidayah idan ta Tashi tana sambaɗa surutu Haseena seerat Aisha Sulaiman mummy Waleed Ko MamaGee Yasin baza ku ce ita bace sai dai kuce Hadiyyah tashi ɗaya Dan ita tajuye Yanzu,ita kuma Hadiyyah takoma ita,Amma ita Hadiyyah bamu sani ba Ko cikin jikinta bane tun Yanzu yasa tayi laushi! Zaman AKEEL da Hidayah akwai tausayi da fahimtar juna sosai,Babu batun ace Babu faɗa ai zo mu zauna zo mu saɓa ne,kuma Duk daɗin Zama bai kai harshe da haƙori ba Amma wataran haƙori taune harshe yakeyi,to Hakan Zaman nasu yake!sai sharɓar soyayyah akesha Kamar ba gobe! Lokacin da cikin Hadiyyah ya bayyanawa bakuga tsiyar da AKEEL yadinga wa AQEEL ba "kai ai dama nasan za'a Rina wannan jaraba taka kai kullum kajika a network ai dole ma wata Tara Ka haife,inda ana Haihuwa kwana ɗaya kai Kam Daka haife ai! Sai kuma ya sheƙe wa AQEEL da dariyar shakiyanci! (Kuji iskancin AKEEL fans dama namiji yana haihuwa?😂) AQEEL Baya kulasa sai yaga abun nasa yaje magaryar tukewa sannan "Ina ruwanka da ni ne wai ɗan sa Ido aidai naji,kai ina cikin ajikin matarka Ko sai Rashin kunyar aka iya! AKEEL yace " Mu ba Yanzu ba Yaushe mukaci amarcin da Har ciki Zai Mana sammako ,la,la,laaaa,la sai Mun wuta tukun,mu ba irinku bane kaida matar Daga kace gashi itama gayyar kwaɗayi ta amshe! Sai ya kuma fashewa da dariya! Nan danan AQEEL sai fusata "Kasan ALLAH bro in baka kyaleni ba xan maka Rashin kirki ALLAH! Muma a Hakan muma amarcin mu ai GA kuma sakamakon mu a gefe! AQEEL Zai ƙarasa zancen da murmushin daya Saba idan Abu yamasa daɗi! "Naga alama kam shiyasa naga kullum ana amaye_amaye da ciwe_ciwe Raina za'aci amarcin,kullum amsawa "Hayateeenah" da zafi kullum ta tare wajen matarka Yasin Zan hanata zuwa kaida kayi aika aikar ka zauna Kayi jinya mana,sai wacce bataji ba bata Gani ba!cewar AKEEL sai ya gudu shashin sa ganin AQEEL ya shaƙa ba ƙarya!!!!!! (Haka wannan tagwaye suke Rayuwarsu gwanin burgewa abun sha'awa wacce da za'a samu Maza ƴan biyu si aure Mata ƴan biyu ai da zumunci ya ɗore Sosai Har ƴaƴa da jikoko,Amma in Wani can ya Aure ɗaya Wani ma ya aura sai Kuga Duk shakuwarsu ta yarinya zuwa ƴan matanci ta Saraya kowacce ta zauna gidanta watama Wani Garin,may be ma ɗaya cikin rufun asiri ɗaya sai a slow! Duk da haka ALLAH Ke tsarawa bayinsa Rayuwa yadda yaga ta dace dasu ubangiji ya kyautata Rayuwar mu DA ta ƴan uwanmu baki ɗayanta alfarmar shugaba Saw) Kullum Hidayah tana wajen Hadiyyah tun kafin tayi ciki ma Suna Shan hirarsu komai tare suke gwanin burgewa,Yau wannan Na nan Yau wannan nanan,Amma yanzu Hadiyyah sai a slow Dan haka Hidayah ta tare acan! Sai Hadiyyah tana kwance Ko tayi Amai nan zakuga Hidayah ta zaro zance "Lalläi sis ni fa kinfara gajiyar Dani Yasin! Sai kace Nina miki cikin kiyita wahakarni,Amma DA mijinki yadawo Zaki maƙalemasa Kamar super glue! Ke ƴar daɗi miji ai GA ribar nan! Itama tana dariyar like mijinta! Hadiyyah Babu bakin magana ya mutu! Sai Daga can zatace "Kisha kuruminki indai cikine zaizo kanki ne yarinya naga nawa saura naki! Cewar Hadiyyah "Hohoho angaya miki koya irinkine sarkin raki! Zakiga nawa nema? Ai saidai kiga ciki ya Girma ya Zama ƙatoto saboda jarumta! Sai sannan Hadiyyah zata saka dariya tana kallon ƴar uwarta "e lallai da akace idan ka girmi mutum Ko da da 1mns ne ka girmeshi!Amma ALLAH yakaimu lokacin lafiya! Sai Hadiyyah ya ƙyale Hidayah! Wata Rashin kunya sai AKEEL yashigo zasu tafi shashinsu ma, Hayateeenah nagaji da zuwanki gidannan! Nima Hakan my huub ni Bada ciki ba ni da Zaman jinya ƙiri_ƙiri tana kallon AQEEL zata faɗi haka Ko kunya! Shi kuma AKEEL ɗin Zai ce "ba don hakinsu ba ai Nake barinki Albarkacin ɗan mu dake cikinta ne kawai!Amma da Sai wancan jarabatun ya kula da ita tana nuna AQEEL DA yatsa! Sai AQEEL ya yunƙuro Kamar Zai kawowa matar da mijinta Duka sannan sai su fice Suna dariya!!!!!!!! Sa'adatu har gidan su Hadiyyah tazo cike da sanyin jikinta na ganin Irin Aljannar duniyar da twins suke cike nan Takuma tsoron ubangiji, lalläi Duk abunda ALLAH ya tsarawa Bawa kawai dole ne Amma idan ba haka ba ai.... Tana wannan tunanin ta ƙarasa ciki,dama tuni takira su Hidayah tafaɗa musu shiyasa security Basu hanasu ba sunsan da zuwansu AQEEL ya faɗa musu! Ranar ba bu inda su AQEEL sukaje Suna gida suyi nan suyi nan saboda murnar zuwan Aunty, Aunty dai sai sussunne kai akeyi,alamun kunya,maybe tuna wulaƙanci data musu ne lokacin dazasu barkar Yaya Zakiyyah ne,batasan su sun Mance ba ma! Sun Mata jajen abunda yasameta da fatan ALLAH ya tsare gaba. Sai da lokacin Sallah yayi su AQEEL sun fita masallaci(masallacin jikin gidan yake) Sannan Sa'adatu tasa Kuka tana neman gafarar su Hadiyyah da Hidayah su Kam sukace tuni sun yafe Mata ALLAH ya karɓi tuba,tadinga warwarar cutar data musu tun fitar Ummu Rumana sukace ba komai,tace tagode cikin Kuka tace "ƴaƴan nan Ko haƙƙin Ummu Rumana Dana Ammar ya isheni a yanzu nakasa samun kwanciyar Hankali sai Kuka!gwanin tausayi! Kiyi haƙuri Aunty tasu ta ƙare ai kici gaba da neman Rahmar ubangiji kina sadaka DA kyauta a zummar ALLAH yakai ladan garesu! Daƙar ta lallasu kafin su AKEEL su dawo, DA Sha Tara ta arziƙi suka aikata driver yamayar DA ita Har gida. Sai da cikin Hadiyyah yakai wata huɗu sannan tayi lafiya abunta, sannan kuwa Duk wata hidima da za'a yi ta karatunsu a India dama Abbu yagama! Samun sauƙinta akeso kuma Alhamdullillahi. Ranar tafiyar sunje sallama gidan Baaba kowa ma Sha ALLAH yake cewa Twins yadda suka murmure sun ƙara Haske sun huni a gidan,sun samu Baaba Dan ƴan ma tanta Khadijatu day meenal ƴar Kawu Isma'il sai ƴan matanci akeci ma Sha ALLAH anyi candy ana shirye shiryen Shiga University , Zeenah na wajen uwarta Zakiyyah Dama itama anzama ƴan MATA anshiga JS one!Hunaif dama yana wajen Aunty indo wajen Abul khair Dan uwansa shima ya Girma ana primary 4. Har gidan Jimmai su AQEEL suka kai sallama,Taji daɗi da Hakan sosai,nan tamusu Addu'ar Alkhair. Sanadin AKEELA suka San Shukhra Har gidanta sukaje,itama AKEELA ranar doctor Najeeb yakawo ta ranar ansha budiri an raƙashe Babu ƙarya a gidan Shukhra Kowacce da tsarabar cikinta Amma Banda matar AKEEL😄.Ita Hakan wai murna takeyi amarci sukesha Har sannan wai, sannan kuma su ba zulamammu bane irinsu day mazajensu. Zaman AKEELA day Doctor Najeeb Sai ma Sha ALLAH zamane irin na so da ƙauna Kamar ɗaya ya haɗiye ɗaya,ba wani wulaƙanci na cewa ai ba shine ya sameta a budurwa ba no,zamane na Amana DA yardar juna,ai Doctor Najeeb yasan komai ƙaddara ce ta faɗa mata kuma shine na dakansa yamata aiki tana ƴar ƙaramarta. Tuni ya Samar Mata admission a wata tsadaddiyar pravet school law takeson karanta Ko Dan saboda irinsu Usman, tana tausayawa yaran day akawa fyade,shiyasa da kudirce a ranta zata karanci Shari'a ta yadda zata zamewa irin waɗannan yaran da iyayen su Katanga Abar jingina,sudaina Jin tsoron kar ƙara ana tauye musu haƙƙi. A ƙarshen ziyarar su Hidayah gidan Abbu sukaiwa tsinke karkuso Kuga murna wajen Mommah ta rasa ina zata saka su Ina zata ajiye! Ranar weakened ne Abbu yana gida nan yaita saka musu albarka! Yai musu nasiha Akan Zaman ƙasar da batasu ba musamman Matan Akan su riƙe mutuncinsu da darajar Aurensu Duk da yasan ba matsala Amma wannan yazama dole saboda halin Rayuwa,Anan yatuna DA Abokin sa kuma Amininsa Alhaji Ammar bn Yassir sai da Abbu ya share hawaye Suma su Hidayah haka AKEEL DA AQEEL ma sai da suka yi kukan,Bayan Tarin addu'oin nasara da fatan Fara karatu a Sa'a suka koma gidansu a washe gari suka ɗaga babban Birnin India wato New Delhi sai fatan nasara Rashin iyaye Fans kuzo kuje rakiya ƙasar India garinsu Shruti Haasan🥳. Anan gida 9ja kam sai sam barka harkokin Abbu sai budewa sukeyi!! Yanzu Tallafy foundation yakai inda bakuyi tunani ba sosai,miliyoyin yaran da silarsa suka shiryu ALLAH ne kaɗai yasansu,Da Yaro ya kammala Zai Dora karatun University anan gida 9ja Ko a abroad, idan kasuwanci yakeso Abbu Zai ɗauke Shi a company nasa,ga iyayen marayun da Yake ɗaukar nauyinsu wajen ci Da sha da suttura, Makarantu,Asibitoci,masallatai,rijiyoyin burtsatse da sauran abun buƙata Yanayi Bawa marasa ƙarfi jari,Aurar DA marayu Duk waɗannan Abubuwan Alkhair ɗin yanasa Hadiyyah ga iyayyensa DA Inno Alhaji Ammar bn Yassir da matarsa Ummul Khair, Addu'a ta alkhair shida zuri'arsa A kullim Alhaji Ɗalhat Abdurrahman A.k.a Alhaji tallafy A.k.a Abbu😇 yanasha ALLAH kai mana arziƙin da zamu dinga amfanawa kanmu dashi (abunda kaiwa Wani ai shine kaiwa kanka saboda shine a lahira Zai amfaneka) Anan 9ja yanzu ba Wani company sama da *TALLAFY GROUP OF COMPANY* wanda yake sarrafa kayan masarufi me kyau cikin sauƙi ƙananan companies ana sauke oder irinsu Usman,wanda yanzu anzama mutumin kirki sosai! harda ƴan tebura ma. Ɓangaren *TALLAFY HOLDING* Hohoho Duk wata irin Mota Ko machine sabon yayi Ko tallan sa aka Fara in Sha ALLAH a anan Zaki Fara ganinsa cikin Rahusa,ga sauran kayan karafa rankacakaf Babu abunda Babu fa Kaya masu Aminci da sauƙi,andinga Oder Kenan! Companies ɗin Abbu Suna da yawa my fans dayawa ya mallakawa su AQEEL su da jimawa,hardasu Hidayah acikin Rabo,kai ma Sha ALLAH ubangiji yaƙara arziƙi DA tsawon Rai Mai albarka. Albishirin ku Abbu ya samu jirgin Sama nasa wato *TALLAFY AIRLINE* wanda za'a dinga jigilar mahajjata da sauran tafiyoyi a Farashi mai Rahusa!!!! Dan haka Rashin iyaye Fans ku tawo akaimu Makkah da Madinah Daga nan muzarce wajensu Hadiyyah a batiiiiiiiiiiiiiii Tsakanin Abbu DA Kawu Isma'il zamansu sai Sam barka shima arziƙi ya faɗaɗa Amana kam yanzu Baya Cin ta kowa ma, Aunty Hauwa tana cikin kwanciyar Hankali da nutsuwa tare day mijinta, Yanzu haka ƴan uwansa Su Aunty Asiya Duk sun huta abunsu ALLAH ya ganar,balle ƴan gata su Zakiyyah, Zahra, Hadiyyah, Hidayah, khadijatu, Zeenah,Hunaif suda yasan Basu da uwa da uba,sai kaaka itama kanta tana wutawa dashi,gasu ALHAJI (wanda yazo wutun shekara gida kwanaki anzama aƙili ga addini,yaji abubuwan dasuka faru ga mahaifiyarsa yayi bakin ciki,Har Gidansu Hadiyyah Yaje lokacin sunanan,karatu ya miƙa ankusa Zama mechanical engineering) Farouk,Hydar da Auta Hafsat sunashan gata wajen kawunsu. Komai ya wuce tuni Abbu yaiwa Kawu Isma'il magana Akan ya mayar day Sa'adatu gidansa Ko Dan Haɗuwar kan zuciyarsu baki ɗaya,ko musawa Kawu Isma'il bai ba sati bai zagayo ba aka Ɗaura aure tsakanin Kawu Isma'il da Sa'adatu! Aunty Hauwa wannan karon bataji zafi Kamar wancan ba,Dan haka suka zauna Zaman Aminci itada da Sa'adatu Babu makirci Zaman Amana DA Aminci dama haka akeso ai, Yanzu kam Sa'adatu kuɗin Kawu Isma'il ma basa gabanta ita sai Sallah da istigfari take kullum carbi a hannu. Gidan mukhtar da matansa Zakiyyah da Bilkisu sai Sam barka Suna zaman lafiya day Aminci ga Yar su Zeenah anzama ƴan MATA Duk da Suna da me musu aiki Amma Zakiyyah ta Hana Zeenah Zama dole tayi aiki,saboda bata manta Bakar wuyar da Rashin iya aikin gida da sangarta ya zamar Mata ba a gidan mijinta a farkon Aurenta ba Dan haka ta tsaya tsayin Daka ta jajarce Akan Zeenah kuma Alhamdullillahi da Alama kwalliya tabiya kuɗin sabulu,Dan Zeenah Babu abunda bata iyaba,ga nutsuwa fa hankali. Su Bilkisu an kusa sauka ALLAH yarabata lfy. Zahra ma sai son barka zamansu da Ibrahim ga ƴaƴanta gwanin burgewa Yanzu ma naga Wani cikin jikinta, dangi miji ma Alhamdullillahi. ______NEW DELHI_____ Sai da Suka wuta sannan aka Fara Shiga school ɗaukar lecture ALLAH yabada Sa'a! Laulayi salamu alaikum Kenan ga Hidayah Suna zuwa India tafara Shi gwamma na Hadiyyah ma,Suma nan suka samu damar ramawa Iya yinsu,Suna kallo AQEEL da Hadiyyah in sunada lecture zasu fice Suna musu dariya Suma suji inda daɗi! DA yake sunfisu baki ina sai sun rama,ai gwamma su sun Sha amarci dai. A haka dai sai da suka daɗa wata Biyu Akan wutun dasukayi sannan suka Fara ɗaukar lecture cikin Aminci Kowacce Dama community health ta ɗauka sun Fara lecture tuni musamman Hadiyyah ma wajen wata Biyu! Su Twin's brother dama kunsan medicine suke ɓida karatu harya Tura musu,Ga kasuwanci da sukeyi na company wanda Abbu ya mallaka musu Alhamdullillahi komai yana tafiya normal ana samun RIBA Mai albarka. Duk Abubuwan dake faruwa a 9ja Suna Ji sunyi murna da mayar da Auren Kawu Isma'il da Sa'adatu. Sun samu Hutu Dan haka masu Abu da abunsu tuni sukayo 9ja kuma daidai cikin Hadiyyah 9mnth, koda sukazo tuni Shukhra ta Haifi Yar ta mace an sha Sunan Maryam(sunan matar is'haq data rasu) Suna kiranta nasrim Itama AKEELA an sauke namiji aka samu sunansa miƙdad ɗan ta tabarakallah ahsanul ƙaaliƙiin yanada kyau Sosai Gidan Baaba Hadiyyah ta Sauka Duk da AQEEL bai so ba Amma ya ya iya sai haƙuri. Ko sati ba'ayi ba ta Haifo Twins ɗin ta Duk Maza Bayan Tasha wuya, ƴaƴan ma Sha ALLAH Kamar ɗai ɗai,kai kace AQEEL DA AKEEL ne Suna jarirai! Faɗar murna fa shagalin da za'ayi ɓata baki ne ƴan Rashin iyaye Fans nake hange wajen sunan Suna haskawa musamman su Haseena da seerat da Aisha Sulaiman da mummy Waleed da MamaGee Yara sunci sunan Ammar da Ɗalhat ana kiransu Aimaan da Amaaan ALLAH ya Raya. An sha ALLAH shagali Hidayah da cikinta 5month itama Kar muzo Kuga ɓarin kuɗin da akayi a shagalin hohoho. Tsokanar da AKEEL yake Masa Har gidansa nacewa yazama gwauro yasa yakoma gidan Abbu DA Zama, haɗe da cewa Kaima akwai lokaci ai ɗan banza kawai! AQEEL sai zarya gidan Hajiya Baaba yake Amma ina Hajiya Baaba ta rantse sai Hadiyyah ta Arba'ie kuma haka akayi,Tasha gyara na musamman ciki da waje dan haka Ranar kar kuso Kuga zumuɗi wajen AQEEL. Aiman da Amaaan komai nasu na wajen Hidayah Dan ma cikin 7mnth na hanata Wani abu,hakama AKEEL komai ƴaƴana musamman dayaga Suna kama. Mus'ab da Mahmoud ALLAH yayi mijin su Khadijatu da Meenal ne fa sukazo sunan 'Twins ɗin Hadiyyah aka Jone abunka da manya Babu ɓata Lokaci aka tsaida magana Khadijatu ta Mus'ab ce Meenal kuma ta Mahmoud ALLAH yakaimu lokacin lafiya. An sha biki lafiya ankai Amare gidajensu,anashan ƙauna da soyayya abunka da ƴan Boko basu daɗe sosai ba suka Fara halartar University da suka nema kuma sun samu cikin ikon ALLAH. Hidayah ta Haihu itama Twins again Amma Duk Mata ,ma Sha ALLAH Kamar su Hadiyyah na jarirai Suma ma Sha ALLAH an sha shagali,ankuma maimaita shagali Rashin iyaye Fans Masa gajiya da Hidima! Yara sunci Suna Ummul Khair da Ummu Rumana ana kiransu Eaman da Amaanah Tuni su Aiman da Amaan anfara Zama kamannin su da iyayensu Maza ƙara fitowa take, Again sai da Hidayah ta Arba'ie a gidan Hajiya Baaba itama,sun rama tsiyar da AKEEL yadinga musu,sun dawo gida. Rainon Eaman da Amaanah yana wajen Hadiyyah gwanin burgewa! Haka Zaman waɗannan Twins yake day burgewa cikin Aminci da Yar dar juna,tuni Suna koma India Dan cigaban karatunsu.... A gida 9ja Komai yana tafiya normal Hamshaƙin Asibiti Abbu yake tsamfatsawa ƴaƴansa da iyalansu wato *DOUBLE TWINS H&H CLINIC* an kammala komai jiran dawowarsu Ake a ƙaddamar DA buɗe Shi,su shekara Biyu da kammala karatunsu ma,sun jira matansu su ƙarasa su dawo gaba ɗaya ne..... ________ Yau Ranar farin ciki ne saboda dawowar su AKEEL DA murnar kammala karatun da su Hadiyyah suka yi,da kwali Mai daraja kowannen su!ga murnar buɗe Asibitinsu da za'ayi A washe garin ranar . Faɗar shagali da bidirin DA akayi na yi murnar dawowarsu DA washe gari na buɗe Hospital ɗin su nayi pages 10 ban gama ba kuyi imagination ɗinsa. An sha mamaki DA Al'ajabin su Aiman da Amaan wanda sunyi Girma sosai,Indianci sai kace ƴaƴan Salman Khan😄, Su Eaman da Amaanah ma Haka Yara ɓul ɓul Kamar ƴaƴan Indian koda yake ƴan India ne man,dama an sasu a school acan,kamarsu DA AQEEL DA AQEEL su Aiman ƙara fitowa take,Suma su Eaman kamarsu dasu Hadiyyah da Hidayah fitowa take abun gwanin mamaki DA burgewa kowa sai ɗauka yakeyi Yara Babu ƙiwa! Anci an sha Anyi shagali kowa yayi murna A washe gari Hospital ɗin yafara aiki,Babu cutar da basa dubawa, Surgery, operation,Chemo ƙwararrun likitoci ga kayan aiki Daga Indian da Germany Abbu ya kawo Asibitin gasu AQEEL da AKEEL da Hadiyyah da Hidayah kuma Suma Suna Bada gudunmawa, Zahra ta Ibrahim ma tashigo tawagar, kai Wanga Asibiti ana yabawa da ƙoƙarinsa saboda Shi har masu kuɗi da masu Mulki rage fita waje sukayi neman lafiya Ko duba lafiya to me zasuje Suyi ga magani a gida 9ja, Abunda za'a musu acan Shi za'a musu anan fa asarar kuɗi(ALLAH yakawo mana wannan cigaban a zahiri a Nigeria alfarmar shugaba Saw🙏) _____________ Ba'a Rufa shekara ba *DOUBLE TWINS H+H CLINIC* yadinga samun awards+2 Kala+2 na yabo da samun nasarori,saboda jajurtattun kuma ƙwararrun likitocin da suke kulawa da Al uma,gashi harda marashi Abbu yake turawa Asibitin a dubasu kyauta(karkuyi Zaton iya masu kuɗi ne no masu kuɗi su bayar aduba su marashi amusu saboda zatin ALLAH matuƙar Sum samu Katin DA Ake rabawa na ganin likita, weekend Aka ware musu. kai ma Sha ALLAH. _____BAYAN WASU SHEKARU_______ Zama tsakanin AQEEL da Hadiyyah Alhamdullillahi komai normal akwai ƙauna da fahimtar juna ga ƴaƴansu twins Aimaan da Amaaan sai siddiƙa Mai sunan Mommah da akasa da kuma Rabiat (Adawiyyerh) karku manta marikiyar Abbu mana yan amana. Ɓangaren AKEEL da Hidayah ma haka Zaman yake akwaiyarda da juna tausayawa juna Suma ƴaƴansu Bayan Eaman da Amaanah sun ƙara Ahmad da Mahmoud sai Ma sunan Mommah Suma Suna kiranta saadiƙa. Rayuwar Ƴaƴan gwanin burgewa gwanin sha'awa ƙarya ne ka ware kace ga ƴaƴan Hadiyyah Ko Hidayah Ko ƴaƴan ma basa shaidawa in kuwa sun banbance to Yasin ba gaskia suka faɗi ba ƴaƴan Hadiyyah zasuce sune ƴaƴan Hidayah saboda yarda da Amana hakama wajen mazan tsakanin AQEEL da AKEEL banbanci a sunane kawai ɗaya Abiy Ɗaya Abbiy. Zuri'ar Alhaji Ammar bn Yassir day Ummu Rumana tana cikin kwanciyar Hankali da nutsuwa cikin ikon ALLAH Bayan Duk waɗannan ƙalubalen da sukasha Yanzu yazamo tarihi dama haka Rayuwa take komai yawuce Kamar ba'ayi ba,shiyasa a koda Yaushe ka shuka alkhair Ko Dan saboda zuri'arka ALLAH ya dubesu. ALHAJI an kammala karatu andawo 9ja fa nasara anzama samrayi Sosai ya Dage Aure zeyi Duk da su Hadiyyah Suna tsokanarsa bazasu Masa Aure yanzu ba yaro ne,aikuwa anashan danbarwa sai yace saboda bakida kunya ku Kalle ni da gemu na da hankali na sai ASA dariya gaba ɗaya! An sha bikin kece Raini shima yafara Tara kuɗaɗe. Su Farouk Hydar anshiga University Suma anfara karatu. Zeenah kam karatu ya nisa, Saura ƙiris Asha bikinta da Angonta Yusuf. Auta Hafsat angirma itada Hunaif. Su ABIE anzama samrayi fa su Haseena ku Nemo mata😄 ƙannen sa little Zakiyyah dasu Na'eem da na'eef Suma anfara tasawa ga iyayensu a gefe Zakiyyah da Bilkisu. Zahra ma anzama manyan Mata fa ƴaƴanta Bayan Twins Tayi wasu ma, Meenal da khadijatu ana Zaman lafiya a gidajen mazajensu Mahmoud da Mus'ab dama kunsan abokaine ƙud DA ƙud Dan haka ga gida ga gida,zumuncinsu ya ƙara ƙarfi! ga ƴa ƴa yansu bibbiyu Kowacce Maza Sa'adatu zamansu da Aunty Hauwa da Kawu Isma'il Alhamdullillahi komai normal kuma ta Haifa Masa Yara biyu, Ga iyalan Alhaji tallafy ma haka Abun yake Alkhair Baya faɗuwa kasa banza Duk abunda yakeyi shike bibiyarsu Duk wata nasara ALLAH yana Musu dashi kansa ma,Duk Wani ciwo na Zamani irinsu Suga,hawan jini, ALLAH ya tsallakar dashi kullum cikin ibada yake da godiya ga ubangiji,Duk Wani ƙablubale da suka fuskanta zamana tarihi Suma,kalli dai bala'in dasu AQEEL DA AKEELA da suka Shiga a hannun jimmai da Usman, Kamar bazai wuce ba sun Sha wahala da zalunci iri-iri. Mahakurci mawadaci Mommah ma ALLAH yakawo mata rabonta itada Abbu Dan haka ta Haifa Masa Ummul Khair (Ammy su AKEELA suka Saka mata) Abdulrahman (Abul bait wai baban gida kakansu) da rabiah (Ummul bait uwar gida ) lallai Hajiya AKEELA an iya saka suna. AKEELA itada doctor Najeeb Kullum ƙaunar junansu suke ga ƴaƴansu Bayan miƙdad akwai Ummul Khair (Nour) da Ɗalhat (Annour) da Safiyyah. Saudi Da Madinah a Wannan family saidai basuyi niyyar zuwa ba Ko ALLAH Bai Amince ba saboda Tallafy airline nasu ne,fa sauran kasashen fa suke son zuwa. Wannan family kullum Cikin Godiyar ALLAH day yawaita aikata Abubuwan Alkhair suke. Itama Shukhra tana cikin Aminci da mijinta ta sake hayayyafa itama. Daddy ɗan Shukra da Usman ya Girma Sosai ma Sha ALLAH,Amma Zancen duniya Baya ɓuya Saida yasan ta Yadda aka Sameshi yaci Kuka sosai,Har ya Haƙura saboda haka Usman ya Fitar dashi Daga ƙasar yayi Karatu acan Idan ya Girma sai ya dawo Lokacin Babu wanda ya isa ya nuna Masa yatsa. Mama Jimmai Kullu nafsin zaa iƙatul maut,ankwanta DA ita ba'a Tashi da itaba,mutuwar farat ɗaya su Usman day Shukrah ansha Kuka Yanzu ba uwa ba uba sai haƙuri,an sha Zaman ta'aziyyah su ABBU Duk sun halarta. ______MURFI______ Ɓangaren waɗannan ma'aurata wato Hadiyyah da mijinta AQEEL DA Hidayah da mijinta AKEEL sai Sam barka da yarda da juna sun zame musu mijin Marayu kullum suna alfahari kasancewarsu a matsayin mazajensu Kamar yadda Matan Suma wato Hadiyyah da Hidayah suke Alfahari da zamowar AQEEL da AKEEL matsayin mazaje garesu da Alfahari samun siriki irin Alhaji Ɗalhat Abdurrahman wato A.k.a Alhaji tallafy A.k.a Abbu wanda suke Mantar dasu cewa RASHIN IYAYE...Babbar musibace wacce ada sun ɗanɗanata kwarai dagaske Amma saboda samun waɗannan jajurtattun kuma ababen Alfaharin a Yanzu sun warke wannan tabon,wacce irin rayuwace Basu Gani ba a duniya! wai don Sun rasa uwa da uba acikin shekara ɗaya DA Kaaka a cikin shekarar da batafi biyu ba shine aka mayar dasu ababen tausayi,ba don Basu da kuɗi Ko kadororin da za'a Kula su bane AA,tsabar zalunci da kuma da rasin idanuwa nan guda uku akansu wato uwa ,uba Kakar wajen uban! Lalläi kuwa RASHIN IYAYE (Babbar musiba)(ALLAH ya gafartawa iyayen waɗanda suka rasu acikinmu waɗanda Nasu suke Raye ALLAH yaƙara lafiya da nisan kwana mai albarka ya rabasu lafiya dasu,masu kannen uba Irin Kawu Isma'il kuma ALLAH ya canza Zuciyar su Kamar Yadda ya canza ta Kawu Isma'il yanzu,masu kishiyoyin uwa Irin Sa'adatu Suma ALLAH ya shiryata yasa ta gane batare DA anmusu irin nata ba Ko irinta Kawu Isma'il ɗin cikin Ruwan sanyi shiriyar ta Alfarmar shugaba Saw🙏 ) Saboda shiryuwar Kawu Isma'il da Aunty Sa'adatu Duk sanadinsu ne me zasuyiwa ALLAH Inba godiya ba ALHAMDULLILLAHI ALA KULLU HALIN.................... WAÑNAN shine ƙarshen labarin Nima oum ARQAM Daga haka nace TAMMAT BI HAMDULILLAH Na Fara rubuta littafinan Ranar 1\1\2023 na kammala 7\10/2024 inawa ALLAH GODIYA sosai Duk typing yasha jinkiri Kala Kala na rashe rashe,Rashin lafiya fa sauran su Amma yanzu komai yawuce sai labari Ya ubangiji inda nayi daidai ubangiji kasanya Mun a mizani inda na kuskure ka yafemun ajizancine na ɗan adam ALLAH yasa wannan rubutun ya amafani Al Umar shugaba Saw Ƴar uwarku A musulunci ✍️ Rãbi'atou Aminou Muhammad {oum ARQAM} ce Yar mutan kanawan dabo Nake cewa Bissalam sai kun sake juna a sabon novel Dina Mai Suna RASHIN SANI hausawa sukace YAFI DARE DUHU wanda in Sha ALLAH zaifi wannan nishadantarwa DA fadakarwa DA wa'azantarwa da yardar ubangijin talikai........................... 10/7/24, 1:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: DOC-20241007-WA0023.zip (file attached) 10/7/24, 1:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: DOC-20241007-WA0024.zip (file attached)