*AURE DA KARATU* *RUMAISA SIDI* Page 1 (dandano) Kamar yanda na riga na al'adanta na gyara gidana tareda kicaniyar hadawa 'yan makaranta abin kari sauri-sauri nake komai saboda banson suyi latti har takai ga an dokesu a makaranta Duk abinda nasan zai saka yarana farinciki har su aje hankalinsu suyi karatu inayi kama daga kan cimarsu,suturunsu( uniform) har izuwa abubuwan da zasu taimaka musu suyi karatu duk term nake canja musu uniform saboda makarantar kudi sukeyi suna ganin yanda akewa sauran yara to nima ina bakin kokarina gurin yin abinda zan iya saboda kullum ina nuna musu ba zaka taba cimma wani ba kaima wani bazai cimma ba A kan wannan na dorasu suma akanshi suka ginu duk abinda suke so ina kokari in musu da dan abinda nake rufa ma kanmu asiri A halin yanzu ba abinda nakeso sama da yarana su kadai ke sakani farinciki su kadai suka ragemin idan har kaga dariyata to ina tsakiyar yarana suna min labarin makaranta da kuma burikansu da kullum suke kara yawa a kaina Yarana uku Safwan shine babba shekararsa 12 sai Aysha dake binshi ita kuma shekararta 9 sai auta Amra 'yar rigimata kenan itama shekararta 6 kuma farincikinmu gaba daya Karfa kuga na cikaku da zancen yarana ku kosa dani ko kuyi tunanin ina b'ata muku lokaci ko d'aya labarin bazai tafi yanda nakeso ba sai yarana sun shigo a farkon labarina Zakuce a ranku to duk wayannan yaran ina mahaifinsu????? Mahaifinsu Lawal muhammad yananan kuma muna tare da shi har yanzu saidai.......................Jin girkina na neman konewa ya ankaraddani bayan dogon zangon tunanin da naje da sauri na hada wa kowa nashi saboda nima makaranta zanshiga saboda inada lecture karfe 10 Kukan Amra da naji yasa nayi saurin fita ganin fitowa ta yasa tayi gurina tana kara doka kafarta kasa irinna rigimammun yara Mommy kinga Esha ta dakkomin socks ko? hannunta na rike ina karasawa cikin falon Ina Eshar? meyasa zaki dauka mata socks? Wallahi mommy bandauka mata socks ba kawai na duba na dau nawa shine wai tunda na taba mata abu saita rama a tawa Murmushi nayi araina nace "Rigimammiya" Daurewa fuskata nayi sannan na nuna Aysha "Karki kara tabawa shalelena kaya bakisan batason ana sama ta datti a kaya ba karki kara" Kama kunne Ayshar tayi tana kunshe dariya "Am so sorry mommy bazan kara ba" "To kowa ya zauna kuyi breakfast tun school bus bata iso ba" shayin na hada safwan ya zubawa kanshi ya zubawa Aysha ni kuma aka barni da 'yar lelena (dama aikinta sai ni) Tsittt naji gidan yayi bayan wucewarsu zama nayi nima nayi break sannan na hada kofunan da mukayi amfani da su na wanke sannan na wuce dakina don in shirya kar inyi latti Kallo guda nayiwa gadon da yake kwance na kawadda kaina inada tabbacin ko sallar asuba baiyi ba don yanda na fita na barshi haka na dawo yanzu ma na sameshi Har nayi wanka na shirya yananan kwance saida na kammala komai sannan naje gefen gadon daurewa nayi na taushe abinda nakeji idan tuna abinda yamin jiya bubbuga filon na shiga yi "Abban safwan" na shiga kiranshi a hankali kar yace na mishi ihu amma shiru Filon naci gaba da bugawa juyawa yayi yana yamutsa fuskar da har yau na kasa tantance abinda na gani gareshi da har na dage sai shi A kufule na buge filon wannan karon sai gashi zaune tsakiyar gadon yana aikomin sakon harara " Waike wace irin matace kashemin dodon kunne za kiyi? tun safe keda yaranki kun ishi mutane da surutun tsiya yanzu kuma ke kinzo min ihu a kai" Hadiye bacin raina nayi sanin ba abinda zai amfana min "Dama zan wuce makaranta ne kuma gidan ba kowa ba'a san mai shigowa ba" "Yanzu dama saboda banzar makarantarki za ki hanamin bacci nasha gayamiki ba abinda ya shafeni da wata makaranta taki idan kin cika in kinje karki dawo kuma wallahi idan har kika wulakanta min aure ke da Allah" Sauri-sauri na bar dakin ina mayadda kwallar da ke neman zubomin tare da tunatarda kaina alkawarin da na daukarwa kaina na bazan kara zubarda hawayena akan Lawal ba Tunda na shiga makaranta na watsar da tunanin damuwata na fuskanci abunda nazo yi lecture daya ce dama 12 na fito daga makaranta inata sauri in isa gida in hadawa yarana abinci kafin su iso Cikin sa'a kuwa muna fitowa na samu napep na shige ina yiwa abokan karatuna sallama ina jin lokacinda Nafisa ke cemin "Sai gobe uwar son 'ya'ya" haka suke cemin wani lokaci suna ganin kamar na cika son yara ina musu uzuri wani lokaci saboda basu san abinda yasa nakejin kamar nafi kowace uwa son 'ya'ya Kamar yanda na tsammananta yana zaune akan bencin mai shagon da ke haya kofar gidanmu suna gardamar siyasa "ai wannan fagen ka kware" na fada a raina kudin mai napep din na bashi ina kokarin juyawa yaro ya iso wurina yana bani mukullin gidan "gashi inji abbansu safwan" karba nayi tareda wucewa na bude gidan na shige Hmmmmmm salon na dabanne🥰💃 Ga sabon littafin mu mai taken AURE DA KARATU comment dinku shi zai bayyana karbuwar littafin ko akasin hakan AURE DA KARATU NA RUMAISA SIDI Page 2 Gyale na na kwabe tare da wucewa daki na watsa ruwa sannan na dauko doguwar rigata mara nauyi na dora hula akai na fito Kaitsaye kitchen na wuce na shiga hadamana abinci jallof din shinkafa na dafa da dan sauran kifin da muka ci jiya sauri-sauri nake komai kar su dawo bankare ba Karfe 1 dayan mintuna naji tsayuwar bus dinsu bayan na kammala hada komai Amra ce a gaba tana kwallamin kira "Mommy Mommy" tashi nayi tsaye kamar yanda muka saba kullum rungumeni su kayi su duka ukun kowa na fadin "Ni ne first, ni ce first" hadesu nayi duka ukun nima na rungumesu ina jin wata kaunarsu ta musamman tana ratsani tareda tausayinsu Dakinsu suka wuce suka cire uniform tareda aje kayansu Aysha ta canjawa Amra ni kuma na zubo mana abinci kafin su iso yasha iska suma basu ja lokaci ba suka fito Tsakiya na aza tiren abincin muka zagayeshi saida muka zauna na tuna da ruwa safwan na duba "Yaya dakkomana ruwa a fridge" tashi yayi ya dakkoma kowa sannan ya zauna muka fara cin abinci Amra ce tasaka rigimar ita zata fara bani abinci wannan ka'ida ce idan muna cin abinci to kowa zai bani a baki nima in basu wannan karon ma kowa saida ya bani nima na basu bayan mun kare safwan ya gyara wurin Aysha kuma ta kai kayan kitchen Jin an fara sallah safwan ya fita masallaci ni kuma na hadasu muka je muka yi sallah kasancewar yau alhamis ba islamiyya muka dawo falo saboda zafi gashi ba wuta system dina suka dakko suna game ni kuma na dau wayata ina duba costomers dina na whatsapp wayanda ke bukatar kaya ina tura musu suna zabawa Na shafa'a ga mutanen arzikina har na ware ina chat da kawayena a wani group dinmu na makaranta har safwan ya dawo shima ya jone dasu Aysha suna game sam banji shigowarshi ba ganinshi kawai nayi a kaina "Wannan wane irin iskanci ne ana miki magana kamar bakyaji to yama za'ayi kiji kina hira da samarinki duk abinda kika fita kikayo bai isheki ba sai kincimin mutuncin aure a cikin gidana to wallahi baki isaba " Kallon bangaren da yarana suke nayi suna nan zaune Safwan da Aysha sun sauke idonsu kasa amma sunbar game dinsu Amra ko kyam ta zubomana na mujiya "Safwan kuje dakinku kuyi game din" kamar mai jira suka mike Saida naga wucewarsu sannan na maida hankalina gareshi "Haba abban safwan sau nawa zan gayama bai kamata kake fadar kowace irin magana a gaban yarannan ba ina gujema hakan ya janyo ma raini" Kamar wanda ke jin haushina ya zaburomin "Raini na nawa kuma? bayan kingama nuna musu banida muhimmanci a garesu kina kallo nuna suke kaitsaye sun fi kaunarki a kaina kingama hore musu kunne wallahi nayi nadamar aurenki" wani bakinciki ne ya tunzuromin nima na mike tsaye ina kallonshi cikin ido ina kara jin tsanarshi fiye da yanda nakeji "Kaine da kanka ka kada girmanka a wurin yaranka lawal kuma wallahi nafika nadama da danasanin aurenka bansan bakinciki ba saida na aure ka bansan wata cuta hawan jini ba sai a gidanka kaine..........." shiru nayi jin kowane irin lokaci kuka na iya kwacemin wayata na dauka na wuce daki shima a sanyaye ya juya yabar gidan Da darema tare da Aysha na shiga kitchen na dafa mana abinci daidai cikinmu don alkawari na dauka bazan kara ciyadda shi ba zan nuna mishi wannan karon nima 'yar kodimo ce bazan kara daukar iskancinshi ba Bayan mun kammala cin abinci kowa ya dakko littafanshi sukayi home work ina duba musu da inda basu ganeba ganin dare yayi nace suje su kwanta Amra tasa rigimar ita tare dani zata kwanta nace zuje su kyaleta "Ku tabbatar kunyi addu'a yaya" Banjima ba nima na fara jin baccin tashi nayi nadauki Amra da ta dade dayin bacci dakinsu na kaita kayan wutar dakin na kashe tareda tofesu da addu'a Shirin baccin nayi nima zan kwanciya naji yana kokarin rufe gidan na gyara kwanciyata kamar nayi bacci ya dan jima da shigowa gidan sannan ya shigo daki kamar mai tunani yayi tsaye tsakar dakin yana kallona sai can ya karaso yana buga filon da nake kwance kamar mai baccin kwarai na shiga kifta ido tare da tashi zaune "Yadai" na fada tareda dage gira ina kallonshi kame-kame ya shiga yi "Am nace MY ZEE baku rage abinci bane wallahi yunwa nakeji kuma naje gida na taradda Salma ta haihu tana asibiti to abincin duk ankai can"(salma kanwarshi ce da tayi aure shekarar da ta gabata) Abin mamaki sai banji tausayinshi kamar lokacin bayaba da wancan lokacine da dasauri zan tashi koda abincin da zan cine to ni zan hanama cikina in bashi amma wannan karon kai tsaye na dubeshi "Wallahi babu shi duk mun cinye" daga haka na juya na gyara kwanciyata ina fatan bacci ya daukeni Sai asuba na farka baya dakin da alama ba ciki ya kwana ba fita nayi na wuce dakin yarana na tadasu saida naga sun tashi sunyo alwala sannan na fito hangoshi nayi kan doguwar kujerar da ke falon karasawa nayi wurinshi na shiga tadashi kamar yanda ya saba kullum idan na tadashi wannan karon ma harara ya bankomin "Lafiya kuma" murmushin tura haushi na mishi sannan nace "Lokacin sallah ne yayi abban safwan nace bari in tadaka karka rasa jam'i" Wani kallo yake bina dashi kamar ya shakeni"To ina ruwanki da sallah ta kabarinmu daya dake wai ni menamiki har haka zainab da kika bi kika addabi rayuwata ne ko so kike shima kwanan gidan in barmiki keda yaranki iye" ganin yanda yake daga murya kar ya janyo mana hankalin makwabta yasa na juya nashige daki kar in rasa jam'i wurin neman magana Har suka wuce makaranta yau ma yana daki ni kuma ina falo ina duba abokan business dina ina yin order kayan da mutane ke bukata nishadin da nakeji ne ya jani izuwa status din jama'a ina kallo wasu hotunansu suke posting wasu kuma sana'unsu can nakai ga status din Hannatu cousin sister dina wakokin soyayyane kala-kala tayi status tareda emojies na soyayya murmushi nayi "Su soyayya manya" na fada a raina ina tuna irin soyayyar da muka buga nida lawal kamar ba gobe idan naga masoya suna zuba soyayya saidai kawai nayi dariya tareda fatan suga mai kyau don nikam ba abinda ta tsinanamin sai tarin bakinciki Na tuna lokacin da lawal yake duke gabana yana kuka yana fadin "Ki taimakamin my zee kar na rasaki wallahi idan na rasaki to zan iya rasa raina na miki alkawarin rayuwa mai inganci nasan gidanku gani suke bazan iya rike ki ba saboda ina talaka wallahi zee indai kika aureni ko dako ne zanyi in ciyadda ke da abinda kika saba ci a gidanku" A wannan lokacin nima zubewa nayi a gabanshi ina kuka "Ka kwantarda hankalinka Nisful ba abinda zai rabamu ni kai nakeso da kai zan zauna banajin kona second daya zqn iya kula namijin da ba kaiba na tabbata inhar na dage kai nakeso abba zai auramin kai dawowarshi kawai nake jira" Hawaye naji suna zubomin "Allah sarki abba Allah ya gafarta ma gashi ka auramun abinda nace inaso na guji zabinka ni kuma ga abinda nake gani Allah na tuba ka yafemin" Hmmmmmm muje zuwa dai🤔 AURE DA KARATU NA RUMAISA SIDI Page 3 Kuka nayi marar misali saboda tuno abinda nake kokarin mantawa taurin kai duk shi ya kaini ga fadawa halinda nake ciki a yanzu bana zargin kowa da lalata rayuwata sai ni da kaina mahaifina mahaifiyata yayyena da duk wani masoyina ba wanda bai shawarce ni akan abinda suke hangomin ba amma na take saboda wata banzar soyayya tawa banci riba ba sam ba wani amfani da hakan yamun "Wannan wace irin mummunar dabi'ace me kuma aka miki yanzu da zaki zo kina min kuka a cikin gida ko sharrin naki ne ya tashi? to wallahi wannan karon a shirye nake da duk wani dan uwanki da zai nunamin yatsa ba wanda ya isa ya wulakanta ni " Da kallo na bishi har ya shige kitchen hawayena na goge banjin zan iya kula shi a wannan lokacin na gaji da biyemishi duk safiya muna raba hali gyara kwanciya ta nayi kan doguwar kujera tare da saka earpiece ina sauraren karatun qur'ani ina fatan samun nutsuwa da rahama a cikin zuciyata saboda abinda nakeji kowane lokaci rashin lafiyata zata iya tashi Dawowa yayi falon yana maganar da sam banaji saboda abinda ke cikin kunnena a hankali na sance kunne daya ina watsa mishi idanuwana da yake kira da oily eyes a lokacin da muke kan soyayyarmu yasha gayamin wani sanyi yakeji a ranshi idan ina kallonshi da su "Ina breakfast dina fita nakeso nayi" Cikin isa yake maganar kamar wanda yasiyo komai ya aje ya zo ya taradda babu "Hmmmm" na sauke ajiyar zuciya tareda kara kallonshi " Mun cinye" na fada kaitsaye tareda kokarin mayadda earpiece dina maganarshi ta dakataddani " bangane kun cinye ba kyaleki fa nayi ko jiya daga abincin rana har na dare ba wanda naci a gidannan yanzu ma don tsabar mugunta daga ke sai 'ya'yanki zaki cinye" "Anzo gurin" na fada a raina " Banyi tunanin kana bukatar abinci a gidanka ba saboda duk maigidan da ke bukatar hakan fita yakeyi ya nemo ya kawo a dafa aci amma kai banga hakan a tare da kaiba kuma wannan abin da kake kiran ba'a baka ba wanda kace kafi karfin wulakanci a wurinsu ne suka aje kaga ko bazaka ci ba" "Ai ba yau kika fara yimin gori ba Zainab ba yau kika fara nuna 'yan uwanki ke daukar nauyinki ba kuma ba wanda nace yayiwa 'ya'yana wata lalura abarsu su rayu kamar yanda nake rayuwa nima rashin sirrinki yasa kika gama zubarmin da mutunci a gurinsu shi aka nunamin tun farkon neman aurenki naki fahimta ana nunamin illolin auren 'ya'yan masu kudi amma kaddara ta riga fata don aurenki KADDARA CE" Daga zaunen naji jiri na dibata "Lawal, Lawal ne ke kiran aurena auren kaddara? lawal din? wayyo Allah na" dishi-dishi nake ganinshi saboda hawayen da ya cikamin ido amma yanda ya bakanta min nima zan bakanta mishi gorin da yadade yana fadar ina mishi yau daya zan mishi yasan abinda ake nufi da gori " Aurena ya wuce ka kirashi na kaddara lawal idan har ni ban kira aurenka da auren kaddara ba kai kayi kadan ka kirani da hakan wace riba naci a aurenka bayan 'ya'yan da ke tsakaninmu? bayanshi ba komai kai kuma silar aurena ka mallaki gidannan da muke ciki da motar hawa kai har suturar sakawa lawal" matsawa nayi kusa dashi ina kallonshi ido cikin ido "Har abincin ci kasamu sanadina lawal nafi karfin ka kirani da auren kaddara" na karasa ina dukan kirjina jinake kamar in shake lawal sai ya daina numfashi na tsaneshi fiyeda tunaninku masu karatu Shima cikin bacin rai idanunshi sunyi jajir ya shiga nuna ni hannunshi na rawa" Wallahi zainab ki iya bakinki kinsan dai igiya biyu ta rage tsakaninmu" tsaki na buga "to shine me? akwai wanda ke dannarka game da igiyoyin kayi yanda zuciyarka ke rayamaka akaina lawal" A fusace ya juya ya fita daga dakin yana banko kofar kamar zai ballata jagwabb na fada kan kujera tareda dafe kaina da nakejin yana saramin kamar ana dokamin guduma har cikin idanuna nakejin ciwon da lalube na tashi na wuce daki na dakko magani na tsakiyar falon na zube ina haki dafe da kaina sunan Allah na shiga kira "Ya Allah ka kawomin dauki Ya Allah ka yafemin Allah na tuba na tuba ubangiji Allah kayi abinda yake mafi alkhairi a kaina Yarana Allah ka kawomun dauki ko saboda rayuwar yarana Allah Allah ka......." kuka ne ya kwacemin na kife kaina kan kafet inayi kamar wata karamar yarinya Bansan loakci ya tafiba saida naji yarana a kaina ashe wai baccine ya daukeni a hankali na bude idanuwana da sukamin nauyi na sauke su akan Aysha da ke kallona kokarin tashi zaune nayi ina tattaro sauran karfina murmushi na musu "Kun dawo? baccine ya dauke ni ashe" hannuna Amra ta rike "mommy yau baki yi hugging dinmu ba" safwan ma matsowa yayi yana taba wuyana a razane ya zare idanunshi irin nawa (inji lawal) "Mommy bakida lafiya? jikinki zafi sosai mommy" sai hawaye " to miye na kuka kuma kamar ba namiji ba dubi kannenka suka kuka zasu yi common yarana ku kwantar da hankalinku naji sauki sosai" na fada tareda hadesu na rungume Indomie na dafa musu ganin lokaci ya tafi dayawa daurewa naci gaba dayi saboda yarana dako tari nayi zakaji suna hada baki wurin fadin "sannu mommy" Shareshi nayi nabawa banza ajiyarshi har dare ban kara kulashi ba shima shareni yayi dukanmu muna falo har shi nidai ina harkar business dina da wayata su kuma safwan na dubama su Aysha karatunsu shi kuma yana sana'arshi ta chat da kullum ko ya rasa na pure water bazai rasa na data ba Ganin dare yayi na kashe data ta tareda tashi na dauke yarana da bacci ya dauke anan falon kayan kallon da kunna su bayada amfani nazo na kashe ganin yana falon nabar hasken falon ban kashe ba na wuce daki shirin baccina nayi ina gaba mirrow ina kichaniyar daure gashin kaina ya shigo Tsaye yayi yana kallonta a ranshi yace "yarinyar nan fa bata tsufa wazai ganta yace ta haifi 'ya'ya har hudu a cikinta( bayanin ta hudun yana gaba) tun lokacin kuruciya zee kyakkyawace ajin farko yar kwalisa ba wanda ya taba tunanin zee zata aure shi kasancewar ta fito daga gidan manya kuma ba wanda baisan irin soyayyar da mahaifanta da 'yan uwanta ke nuna mata ba Karasowa yayi gaban mirrow yana kallonta ta ciki "Kinyi kyau zee" gira na dage mishi ina kallonshi ta cikin mirrow " dama can ni kyakkyawace kaima kasan wannan" daga haka ta zame tareda nufar gadon ta kwanta tareda lullubo bargon har kanta ta rufe ajiyar zuciya ya sauke "hmmmm bazata canjaba kenan" dakin ya bari ya koma falo ya kwanta Yau bacci nasha kasancewar weekend ce suma yaran daga sallah suka koma bacci sai wuraren 11 na tashi saboda kukan Amra "mai yara baya hutu" na fada ina saukowa daga kan gadon a gurguje na watsa ruwa na fito a jikin safwan na sameta tana shesshekar kuka mahaifinsu kuma na kwance kan kujera da remote a hannunshi yana canja channel "Me aka mata" na tambayi safwan "Wayar abba ta dauka shine garin kawomin ta fadi sai....." hannu na daga mishi saboda nasan kwanan zancen "ku je ku shirya fita zamu yi da munci abinci" ai dagudu suka ruga har amra dake kuka Kallo daya na mishi na wuce kitchen na hada mana abinci fitowa nayi jin yara na mishi addu'ar fita kamar yanda na koya musu "Amm nace abban safwan" na dakatar da shi ganin yana kokarin fita tsayawa yayi yana kallona karasowa nayi bakin kofar nace "Dama nace zamuje da yara muje muga babyn salma daga can in wuce gida" annurin fuskarshi ne ya bace da alama ba haka yayi tunani ba "Sai kun dawo" ya fada tareda ficewa daga gidan "can ta matse ma" na fada tareda juyawa nakoma inda na fito A kofar gidansu napep ta sauke mu na sallame shi tareda shiga gidan tareda yarana gidan cike yake da 'yan uwansu lawal duk yayunshi mata su uku da sukayi aure suna gidan gaisawa nayi da wayanda ke waje yarana ma suka shiga gaida su cikin ladabi don ba alfahari ba indai a fannin tarbiyyane banida sanya ga yarana Dakin mahaifiyarshi na wuce inda mai jegon take sallama nayi suna dakin har mama karasawa nayi gabanta na durkusa na gaidata kamar yanda na saba kullum har gobe ina ganin kimar matar "yawwa zainab ya gidan ya kuma yarannaku" sunkuyadda kaina nayi ina fadin "Duk lafiya lau muke mama ashe salma an sauka Allah ya raya akan sunna" "Amin Amin zainab" matsawa nayi wurin mai jegon nabar su Amra wurin mama suna zuba mata zance "Sannu salma barka da arziki" "yawwa" ta amsa a dage kamar wacca akama dole jinjirar na karba na kira su safwan suma na aza musu kowa ya dauka Amra ma ta sa rigimar sai an bata "to tara hannun na dora miki ita" da sauri ta miko hannu na doramata ba tareda na sakarmata 'yar ba "Kinason baby gashi uwarki ta rufe haihuwar" Anty mariya (yayar lawal wacca yake bi) ta fada kai tsaye tana kawadda kanta Sarai na jita amma sai nayi kamar banjiba hirarsu suka cigaba da yi ina jinsu amma bansaka musu baki ba babbar yayarsu ce ta shigo rike da hannun Aysha Anty A'i (wacca lawal yayiwa takwara da Aysha) "Anty ina wuni" itama kamar sauran a yatsine ta karba tana zama kan kujerar dakin "Shekaranjiya ai nazo bansameki ba nace abu ga gidan 'yan boko lawal kawai na samu nace Allah ya maka budi kaima ka fita Allah ya rabaka da tsaron gida" Caraf Anty mariya ta karbe "Ai anty ni ina mamakin matar da take hada AURE DA KARATU kuma tace duka zatayi wallahi ina tausayawa mijin da matarshi ke KARATU don ba wata kulawa da zai samu bare kuma lawal da yake cikin jarabawa saidai fatan Allah yasa ya cinyeta" Mikewa nayi tareda yi musu sallama na hada kan yarana mama na samu a falo don in mata sallama "zo nan zainab" umurtarsu safwan nayi da su jirani a waje matsawa nayi kusa da ita na durgusa " ya gidan naku ba wata matsala dai ko zainab" " A'a mama ba wata matsala" numfashi ta sauke "ki kara hakuri zainab nasan kinmana kokari zama da lawal ba sana'a amma insha Allah akwai shirin da nakeyi akan hakan da anyi sunannan komai zai daidaita ki kara hakuri kinji" Murmushi nayi "Insha Allah mama" ina ganin kimar matar sosai saboda dattijuwar arziki ce sam su lawal basuyi halinta ba "to ya karatunnaki" murmushi nayi "Karatu alhamdulillah mama wata 1 ya rage mu fara jarabawa insha Allah" "Masha Allah to Allah yasa a kare a sa'a" "Amin mama" Kudi na zaro a jakata dubu 20 kamar yanda na kebesu tun gida na aje a gefen da take "gashi mama a kara ayi hidimar biki" mikewa nayi tayi saurin rike hannuna "Dau kudinnan zainab tun ban bata ranki ba duk wannan halin da kuke ciki zaki dauko wayannan kudin ki kawo" "Wallahi ba komai mama don Allah ki karba" kudin ta dauko ta raba biyu " karbi nan na dau wannan dai mungode sosai Allah ya miki albarka" Daga nan kofar gidanmu aka sauke mu a bakin tangamemen get din gidanmu gaida maigadinmu nayi ya amsa shima yana gaidani cikin girmamawa yana yiwa su Amra wasa Motar da nahango a farfajiyar gidan ita ta tabbatarmin da YAYA na gidan babban yaya wanda ke taka matsayin uba a gidan tun bayan da kasa ta rufe idon mahaifinmu Muje zuwa daiiiiiii AURE DA KARATU NA RUMAISA SIDI Page 4 Bangaren mahaifiyata na wuce kamar kullum ko ina tsaf-tsaf kamar gidan sabuwar amarya to akwai masu kula da komai Tana hakimce akan hadaddiyar kujerar dake falon cike da kauna na karasa tareda rungumeta " nayi kewarki ummi" 'yar dariya tayi irin ta jin dadi " bansan sai yaushe zaki girmaba Abun abba ke bakisan kin girma ba wani lokacin ko yaranki basa sangartar da kike yi" gyara zamana nayi tareda shigewa jikinta "karkiga laifina ummi gurinki kawai nake samun hakan a yanzu" shafa kaina tayi "Allah ya miki albarka autata" "To ina kika baro uwayen rigimar kuma" waigawa nayi sai yanzu na lura da bama tare idanuwana sun rufe da kaunar mahaifiyata "Suna bangaren Yaya don munga motarshi a waje" "Eh yau bai fita ba kinsan weekend ce" "Haka ne fa" na fada ina sauke gyalena tareda ajeshi kan kujera "Asabe Asabe" ummi tashiga kwallawa mai aikinta kira da sauri ta fito "gani um....) maganarta ta katse tana karasowa cikin falon "Ahhh anty zee sannu da zuwa wallahi banma ji shigowarki ba ina su Amra" nima murmushin na mata "wallahi munshigo anty asabe su amra suna wurinsu Nihal" "Masha Allah" juyawa tayi wurin ummi "gani ummi" nuna ni tayi "je ki kawowa auta abinci ki zubomata farfesunnan da kika min suma yaran ki tanadar musu abinda za su ci kafin su tuna dani" "To ummi" ta fada tareda mikewa waigowa ummin tayi tana kallona " ko akwai abinda kike bukatar asama miki" girgiza kaina nayi inajin kwalla na neman cika min ido Allah sarki uwa duk lokacin da zanzo gidan to zakaji tana a girkamin kaza a girkamin kaza duk abinda take ganin zaimin wahalar samu a gidan mijina to kokari take ta samaminshi nida yarana Nan take aka cika gabana da kayan abinci kala-kala da fruit fadi take "ki bude ciki kici abinci tunda ba bakuwa kike ba" abincin na diba ina ci da kanta ta shiga kitchen ta hadomin fruit salad ta kawo gabana " kifa buda ciki kici" saida ta sani gaba naci abincin sannan ta kira asabe ta kwashe kayan "dubi yanda duk kika rame kindauki damuwa kinsawa ranki bansan randa kika koma haka ba zainab ada bakida kawa kamata amma daga lokacinda likita ya gayamana kinada hawan jini na aje wannan tunanin nasha gayamiki duk abinda kike so ki kirani ki sanarda ni ko ki kira yayanki ba abinda zaki nema a duniyannan indai akwai shi da bazamu nemo miki ba amma kullum abin inga kina cikowa kina kiba saidai kullum in ganki zuru-zuru da ido sai dogon hanci me kike tunani zainab? shin ke bazaki kwantar da hankalinki ba kodon yaranki" Murmushin yake nayi tareda riko hannuwanta duka biyu "ba abinda ke damuna ummi duk abinda nakeso ba abinda bakumin ba kawai dai may be yawon makaranta ne yasa kike ganin hakan" ido ta zubamin kamar mai nazari irin kallon da take mana a lokacin da idan tana zargin muna boye wani abu "Indai ko zirga-zirgar makaranta ce ta maidaki haka to zansa yayanki ya kaimiki mota daya cikin ta gidannan" Wannan karon kasa daurewa nayi saida na rungumeta tareda fashewa da kuka "don Allah ki yafemin ummi ku yafemin abinda kuka gudarmin kenan na kasa fahimta don Allah ku yafemin" bayana ta shiga shafawa " kingani ko? kingani ban gayamiki kar ki kara zuwa kimin kuka ba zainab kodai akwai abinda kike boyemin" kaina na shiga girgizawa tareda kara shigewa jikinta "bakomai ummi wallahi bakomai" "To karki kara kuka kinji karkisa mudinga ji aranmu kamar ba mu cika alkawarin mahaifinki ba Abbanki har ya rasu yana maimaita a kula dake a kyautatamiki ki gayamana zainab idan akwai abinda muka kasa miki don Allah" Ganin itama ina neman sakata damuwa yasa na ware na dinga zuba mata shagwaba ita kuma sai riritani takeyi daki ta shiga ta dakkomin abayas tace gani tayi ana talla suka burgeta tasanni da son abaya ta siyamin ai kwa nahau murna nashiga gwadawa ina tsalle kamar wata Aysha Bangaren Yaya Isma'il na shiga (shine babba a gidanmu) matarshi Anty nasma kawai na samu gaisawa muka yi cikin girmamawa na tambayeta su Safwan "Sun fita tareda abban nihal rigima suka sakamishi kan teddy shine ya kwashesu ke har yasir na hada nace duk a tafi" "Ai gwanda da kika mika su can ko bakinki ya huta" Sallama na mata na shiga bangaren yaya Abbas (shine kebin yaya babba) shikam yana nan gida gaidashi nayi cikin mutunci da kaunar juna itama matarshi na gaisawa mukayi ta kawomin dan abin motsa baki tareda wucewa dakinta ta barmu tare "Yadai ZEEN ABBA ba wata matsala dai ko" murmushi nayi "ba matsalar komai yaya" "Idan da wata matsalar kigayamin dubi yanda kika rame ko wani abun yake miki har yanzu" "Ba abinda yakemin yaya bakomai" "Idan har kikaga da wata matsala ki dawo gida don bazamu zuba ido ya kashe mana ke ba idan shi baya bukatarki mu muna bukatarki don haka bazamu zuba ido ya cigaba da wasa da rayuwarki ba kinji ko" "Insha Allah yaya" tun dama can yaya mutum ne mai zuciya kuma tsayayye kan ra'ayinshi shine mutum na farko da ya fara nuna tsanar aurena da lawal tun farkon soyayyarmu baya kaunar lawal bare kuma abubuwan da suka zo suna faruwa daga baya "Zan turo miki kudi ta account dinki ranar monday kije asibiti a duba dalilin wannan ramar" "To yaya" na amsa cikin girmamawa Sai la'asar nayi shirin barin gidan tareda sha tara ta arziki daga mahaifiyata da kuma 'yan uwana naji dadin fitar koba komai na kwanta jikin mahaifiyata ta kara kwantarmin da hankali Banyi girki ba saboda munzo da abinci tun daga gida wanda ummi tasa aka girka mana na musamman saida mukayi sallar magriba sannan na zuba mana abincin Muna tsaka da cin abincin ya shigo kallo daya yayiwa shinkafa kazar da muke ci ya kawadda kai tareda wucewa daki koda ya fito har mun kammala an kwashe kayan ina kokarin jona wayata caji ya dawo falon yana zama yaran suka dakatarda wasar da sukeyi kowannensu ya nutsu musamman amra da ta shige jikina Kallonsu yayi " meye kuma kuka daina wasan" hannu ya mikawa amra data shige jikina "zo amra na zo inji wa ya taba ki" kafada ta make cikin shagwaba take fadin "Um um ba kaine ka dakeni ba da safe" kunnuwanshi ya kama "yi hakuri shalelen mommy zo gurin abbanki kinji" Matsawa tayi ya dauketa ya dora akan cinyarshi wasa ya shiga yi mata tana kyalkyala dariya sakkowa yayi ya hada kan yaran duka yana musu wasa abinda na dade bangani ba sam baya cikin iyaye masu jan 'ya'yansu a jiki wani annurin farinciki nake hangowa a fuskokinsu Iyaye kowane akwai rawar da yake takawa a zukatan yaransu basu rasa komai ba daga gareni amma kuma yau sai na hango wani bangare na farinciki a tare da su saboda kasancewar Abbansu kusa dasu kamar a mafarki na tsinci maganarshi " mama tace kunje kinkai harda gudummawa an gode sosai" Kallo guda na mishi na kawadda kai " eh wallahi ba komai" hmmmm lawal kenan ai saidai in ba wani labarinka wallahi a wannan lokacin nasan abinda yake a zuciyar lawal na gama karantarshi tsaff kudin da mama ta rage yakeso in bashi "kaiii wallahi namiji bayada kunya" Washe gari saiga mota ankawomin daga gida godiya nakira na musu lawal na daki naje na sameshi ina murna " abban safwan ga mota can an aikomin daga gida in rika zuwa makaranta" "Allah ya kyauta" daga wannan bai kara magana ba jiki a sanyaye na juya na koma waje Da motar nayi amfani na sauke su safwan a makaranta nima na wuce tawa samuwar motar ya saukakamin sosai da ita nake kai yarana makaranta nima da ita nake zuwa Tunda muka fito lecture muke zaune muna fira da wayanda muke tare nafisa da kuma maman ayman sai zee lawal haka muke mu hudu saboda banason tarkacen kawayennan tun dama can Kallon Nafisa nakeyi da ta dage tana zuba kalaman soyayya a waya ko ba'a fada ba nasan Ahmad ne saurayinta ko kuma ince mijin da zata aura kallona tayi "yadai maman amra sai kallona kike ina zuba soyayya da hubby" murmushi nayi "ai dole na kalleki irin wannan love haka amma dai da zakiji shawarata da kindan rage " Ido ta zare "me zan rage maman amra? soyayyar? hmmm wallahi bazan iya ba don bakisan yanda nake kaunar hubby bane shima yake kaunata bazaki gane yanda nakeji ba hmmmm abin ba'a cewa komai" ta karasa fadi tana lumshe ido "hmmm da zakiji shawarata da kin rage wannan haukar don wallahi ba abinda zata tsinana miki sai wahala kinganni nan ko alama bakiyi irin soyayyar da nayi ba amma ba abinda ta tsinanamin" Matsowa zee lawal tayi " takwara bamu labari me yasa kike yawan nusarda mu akan soyayya" Hmmmmmm AURE DA KARATU NA RUMAISA SIDI Page 5 Murmushi nayi " nidai fatana ku hutadda zuciyarku da wannan zazzafar soyayyar da kuke dorawa kanku" " amma ya kamata ki gayamana dalilin da yasa kike cewa hakan ko zamufi ganewa ko ya kuka ce" Nafisa ta karasa maganar tana kallonsu Wannan karon maman ayman ce ta katse shirun da fadin " Mu bar maganar mana tunda kuka ga bata fada ba may be abinda ya shafi rayuwarta ne kuma dama ku daina tunanin samun irin wannan da kuke yi a waje a gidan aurenki" Nidai shiru nayi ina kallon zee lawal da ke fadin " don Allah ku daina sa muna tsoron aurennan tun kan mushiga" Wayata na duba tareda mikewa na dau jakata "Ni zan wuce gida banjin dadin jikina zan dan sha magani in gani" hada baki sukayi wurin yimin sannu maman ayman ta dubeni "kodai-kodai" saurin kallonta nayi ina kankance idona " kodai me" itama idon ta kankance kamar yanda nayi " ko ansamarwa amra kane?" Kai na girgiza "Allah ya shiryaki"dariya suka sa gaba daya dan sukayi takomin suka yi na shiga mota na dau hanyar gida a hanya naga mai kwa-kwa na tsaya na siya wa su Aysha da ke sonta Hamdala nayi bayan na kashe motar na fito kofar falon na taba najita a bude abinda ya tabbatar min yana gidan sallama nayi yana kwance a kan kujera da waya a hannunshi banga alamun amsa sallama akan labbansa ba Wuceshi nayi na wuce dakina jakata na aje tareda zare dankwalin kaina gefen gadon na samu na zauna ina sauke numfashi ina bukatar ganin likita kwanannan ciwon kannan ya matsamin mikewa nayi na wuce toilet in samu in watsa ruwa ko zanji sauki Bandau lokaci ba a toilet din nafito jikina na tsane da towel turare kawai na goga a jikina kallon kaina nayi a madubi inaso inga ramar da mutane ke fadar nayi bazan musaba domin ko bakincikin da nake kwankwada a gidan lawal ya isa ya ramadda ni riga na samu mara nauyi na zuba na dora hulata Har yanzu yana falon dama ina zaije kullum muna tare idan baya cikin gida to yana waje idan baya waje yana gidansu ko ni da nake mace bazan iya wannan zaman ba amma shi ko a kwalar rigarshi Kujera na samu na zauna ina sauke numfashi " kamin izini gobe inje asibiti banjin dadi" kallo daya yamin ya cigaba da latsar wayarshi ya dau lokaci sannan yace " Kinyi marmarin tonamin asirine shiyasa zaki koma asibitin ace kinada wata cutar 'yan uwanki su sakani gaba" kallonshi nakeyi kamar wata sabuwar halitta " wai lawal meyasa abin fada bayada kadan a gurinka fisabilillah yaushe maganar nan takai ka maidata haka maganar lafiyata nake maka fa kuma ko wata cutar akace ta sameni to ko wannan karon kaine silarta lawal" Kaina dake sarawa na dafe " wai me kakeson maidani lawal me kake nufi dani ne? na gaji wallahi nagaji" na fada hawaye na silalomin gabadaya abubuwannan sun isheni wani lokacin idan na zauna ina tunani sai na dinga jin inama ban hadu da lawal ba? inama bantaba saninshi ba? kai inama banyi aurennan ba (Astagfirullah) na shiga istigfari ganin damuwa na neman tabamin imani Har dare ina fama da ciwon kan ko abinci su safwanne suka girka sosai nakejin ciwon ina kwance ya shigo yarana na zaune tare da ni kusa dani ya matso "zainab ko zamuje asibitinne" harara naso ballamishi to amma idanun sunki bada hadin kai dakyar na bude idona na dubi yarana "kuje ku kwanta na samu sauki" ina kallo suka fita suna waiwayena tausayi suka bani to yanzu idan mutuwa ta dauke ni ya zasu yi? anya kuwa wannan shakuwar baza ta zamo cutarwa a garesu ba lokacinda kasa za ta rufe idanuna? saboda yanzu na fara gazawa zuciyata ta fara nauyi komai yana nema ya kawo karshe Cikin taushin murya ya sake fadin "ki daure muje asibitin ban dauka abin ya kai haka ba" ya fada yana kama hannuna ya shiga jeramin sannu da lallabani muje asibitin wata kila yana tsoron na mutu ace shi ya kasheni "Mu bari dasafe sai muje idan Allah yasa zan kai safen" Ban runtsaba saboda halinda nake ciki ga zuciyata da takemin zafi abin mamaki shima bai yi bacci ba duk lokacinda zan motsa to zanji yana jeramin sannu da safe ma shiya hadawa yara abin kari yace na shirya ya aje yara sai mu wuce asibitin saida ya sauke su muka wuce yana ta min iyayi nidai shiru nayi don ko magana nayi ba dadi Kaina na sunkuyar ganin irin kallon da anty hauwa wacca take matsayin yayata saboda 'yar gwaggona ce kuma itace likitar da ke dubani tun daga kallon da take min nasan akwai matsala "Ka jira ta a waje" ta fada batare da ta kalli lawal ba mikewa yayi tare da fita ta maida hankali gare ni mikewa tayi daga kan kujerar da take ta dawo wadda ke fuskantata (wadda mara lafiya ke zama) hannuwa na ta riko duka biyu tana kallona " Zainab dubi idona kiyi magana dani as your sister ki gayamin gaskiya zainab me kuma ke damunki yanzu da kike neman janyowa kanki wani ciwon? ki gayamin zainab wace damuwa ce wannan zainab? jininki ya hau sosai zainab sannan halinda kika jefa kanki ko wane lokaci za ki iya kamuwa da ciwon zuciya haba zainab akan namiji? namijinma lawal da ba wani abun kirki da za'a so shi saboda shi ki tuna yaranki zainab Ummi da mu 'yan uwanki wani hali za mu shiga idan wani abu ya sameki to gaskiya na gaji zanje in sami ummi kawai a raba wannan auren bazaiyu muna kallo rayuwarki ta salwanta saboda wani banzar lawal ba wannan karon dole ayita ta kare" Hannuwanta na jimke ina zubarda hawaye " don Allah kiyi hakuri anty hauwa na miki alkawarin cire kowace irin damuwa a raina bazanso aurena ya mutu ba anty idan lawal ya sakeni to yarana ya rayuwarsu za ta kasance? wazai rike su kinaji lokacin yanda yaya abbas yayi rantsuwar baza su zauna gidanmu ba itama maman lawal din tace duk ya sakeni bazata rika mishi su ba to ina zan barsu? don Allah karki gayawa kowa na miki alkawarin daina tunani da kowace irin damuwa" "Kinji abinda ke cutar da mata har su jefa kansu a wahala daga mace ta haihu da namiji to gani yake dole ta zauna da shi kodon wa'yannan yara akwai mata da yawa da ke fuskantar irin matsalarki a gidajen aurenki amma sun boye saboda tunanin makomar yaransu karki kashe kanki akan wannan zainab wannan karon ki yaki matsalar lawal daga zuciyarki" Na sha fama kan na shawo kan anty hauwa so tayi in kwana asibitin na lallabata nace ta bani magani kawai ta bani magunguna tare da shawarwari Kallonshi nayi "kaina na ciwo please" daga haka yayi shiru har muka isa gida bai kara magana ba Ayi hakuri da wannan mura🤧 AURE DA KARATU NA RUMAISA SIDI Page 6 Wani tattali na ke samu daga lawal kulawa yake bani ta musamman nida yarana nidai nawa idone kawai da kuma tsoron abinda zai biyo bayan kulawar hmmm Lawal ne fa lawal bazaimin haka a banza ba dole akwai wani abun Su kansu yaran sunga canji daga gareshi kai maganar gaskiya lawal ya iya kulawar da zata sa ka manta dukkan sharrin da ya maka Allah ya bashi baiwar tsara zance da wannan ya dinga amfani wancan lokacin yana kassarani Washe gari Alhamdulillah na samu sauki sosai ina jin lawal yana kiciniyar shirya yara "nanny lawal" na fada ina sauka kan gadon na shiga toilet wanka nayi nima don inason in daure in shiga makaranta Bakin gadon na sameshi zaune bayan na fito daga wanka kallona yayi yana murmushi "Lallai my zee jiki yayi kyau" nima murmushin na mishi "naji sauki sosai" mikewa yayi yana nufar mirrow ya dau key din mota " zan aje yara makaranta" sauri na kara wurin shafa man a jikina ina fadin "don Allah jirani in karasa shiri nima zan shiga makaranta" Kamar wanda na fadi mugun abu ya waigo da sauri " ba inda za kije sai kin kara jin sauki ko gobe ba zakije ba ko makarantar ai zaki karo ciwon kai ki bari sai kin kara samun sauki" daga haka ya juya ya bar gidan shiryawa nayi nafito falon nadau abin karin da suka ragamin a raina nace " lawal anga banza" har da su kwai aka soya Gidan naji yamin shiru ba dadi in shiga daki in fito in shiga kitchen na rasa aikin da zanyi gaskiya lawal na kokari na zaman gida ina kitchen ina goge plates dina naji sallama fitowa nayi ina amsawa da fara'a na karaso falon maman haidar ce makociyata ta amana " maman haidar ce a gidannamu" itama da fara'a take kallona "ai dole kice haka tunda ke kin gujeni yaushe rabon da ki lekamu nima shiyasa na daina shigowa sai jiya haidar ke gayamin sun hadu da safwan a masallaci ya gayamishi bakida lafiya" Zama nayi kusa da ita " wallahi banida lafiya maman haidar amma yanzu na samu sauki" gyalenta ta kwabe ta aje kan kujera kallonta nake ganin irin ramar da tayi "bakida lafiya ne kema" na tambaya ganin wata irin rama da tayi murmushin karfin hali tayi "A'a nikam lafiyata kalau me kika gani" "Kamar ya lafiyarki kalau wai kinga ramar da kikayi? sannan zaki cemin lafiyarki kalau" hawaye naga sun cika mata ido sannan ta dubeni " ina cikin damuwa zainab na rasa wanda zan gayawa naji sanyi ina cikin damuwa zainab" ta karasa tana barkewa da kuka kyaleta nayi tayi kukan ko zata sami saukin abinda takeji a raina nace " kenan bani kadai ce keda damuwa ba" saida naga tayi kukan sannan na lallasheta " kiyi hakuri bilkisu wallahi yanzu rayuwar nan sai a hankali damuwa yau akwai ta cikin zukatan kowa" hannuna ta rike " damuwata ta banbanta da ta kowa zainab banida wanda zan gayawa damuwa ta zainab banida kowa garinnan ki taimaka ki gayamin abinda zanyi" duk na rude bantaba ganinta cikin wannan yanayin ba kullum zakaganta cikin fara'a sabanin ni da kullum da sabuwar chapter da zamu buga da lawal Mijinta yana kaunarta wanda baya boye hakan a gaban kowa ko zaman minti 2 kayi dasu zaka shaida hakan "meke damunki bilkisu meya sameki" "Zainab ke kinsan banida kowa garinnan in ba abban haidar ba ni 'yar kano ce aurene ya kawoni sokoto ba yanda amma bai dubi wannan ba tun bayan haihuwar khairat na fuskanci Kasim ya canja ya daina dawo mana weekend sai ya kwashe wata 2 bai dawo ba kuma idan ya dawo ba alamun wata damuwa a tare da shi na yayi kewarmu ko wani abu ina shan wahala zainab saboda ya riga ya sabamin da kulawarshi nashiga damuwa sosai da wannan sauyin nashi sai a 'yan watannin nan na fahimci wani ya daina damuwa dani sai yayi wata 2-3 bai damuba idan ma ya dawo bayada lokacinmu ta wayarshi kawai yake baya bari in taba wayarshi idan ma ya dawo baya wuce kwana 3 ya koma wai ashe wata yake tareda ita acan din na fahimci hakanne ranar da yabar wayarshi ya shiga wanka zuciya ta dinga tunzurani na duba naga abinda yake boyewa a wayar nayi nadama nayi danasanin duba wayar saboda na shiga tashin hankali a wannan ranar munyi rigima sosai dashi tsorona kar abinda yakewa 'yar mutane nima wata rana ayiwa 'yata amma sai ya shawo kaina da min alkawarin ya daina na yarda ganin irin rantsuwar da yake min ashe karyace bai dainaba kwatsam shekaranjiya na fara rashin lafiya shiryawa nayi naje asibiti ana dubani akace ina fama da infection wato ciwon SANYI fadar damuwar da nashiga bata bakine zainab na tabbata shi ya kwasomana wannan abun ina shan magani zainab amma ba wani sauki har yanzu ga mahaifiyarshi da ta sawoni gaba ta hanani zaman lafiya gani take kamar na mallakeshi haka take fada kullum to nagaji da bakinshi ya gayamin bazai iya rabuwa da yarinyar ba aurenta ma zaiyi na yanke shawarar kawai ya sakeni bazan zauna da shi ya kassaramin rayuwa ba ya sakeni kawai inje in nemi magani" Dankari wato dai matsalar nan kowa da tashi "kiyi hakuri bilkisu ki daina kuka kasim bai kyauta ba kuma dole ki shiga damuwa insha Allah zamu samo maganin sanyi ba matsala bace zan gayamiki abubuwan da zakiyi amfani dasu amma ki dakatar da maganar saki yanzu har ki samu lafiya musan mafita mikewa nayi nashiga daki na dakko papper da biro na bata "Ki rubuta abubuwan da zan gayamiki yanzu shine maganin sanyi" Ku biyoni a page na gaba don amfana da abubuwan da ke maganin sanyi✍️✍️✍️✍️ AURE DA KARATU NA RUMAISA SIDI Page 7 INFECTION Da farko dai kisani yar uwa ciwon Sanyi ciwone da bawata ya mace face tana tattare dashi , ko tasani koma bata Sani ba Don haka ke mace kece ke janyo bayyanarsa a jikinki ko Kuma ki kwanta dashi yar uwa Mai daraja. ABUBUWANDA KE HABAKA CIWON SANYI 1- Yawan tunanin saduwa 2-yawan amfani da Pant kala Daya ko shearing dinsa da wata 3-yawan saka Dan yasa ga al'aura yayin tsarki ko wankan haila 4-fara wanke Kashi kamin tsarki 5- Yawan tsarki da ruwan Sanyi 6-saka unders da sanyinsu 7-yawan shan yaji 8-saduwa lokacin fushi 9-fitsari a ban dakinda kowa kan shiga 10-yin amfani da hannu domin biyawa Kai bukata KASHE - KASHEN CUTAR SANYI 1- Mai saka kai-kai ga al'aura 2-fitar wasu ruwa ga al'aura 3- Mai sanya warin al'aura 4- fitar wasu ruwa bayan kammala period 5- fitar wani gari ga al'aura 6- fitar kuraje ga al'aura MAFITA kisani cewa idan cutar tayimiki katutu to takan sa miji ya rinka tsanarki kila ma har yakai ga rabuwar aure (wa iyazu billah) MAGANI 1-kisamu bawan lemun Yami , yabushe ,amma bushewar daki bata Rana ba 2- kisamu garin Dan Sudan 3-kisamu garin Jan goro 4- kisamu ruwan tumfafiya 5-kisamu zuma maras hadi Duka kihade garin guri Daya kiyimasa Kashi biyu Kashi Daya ki damashi da ruwan tumfafiyar kishafa ga al'aura idan zaki shiga bacci Kashi Daya ki kwaba da zuma kina sha ( duk wadda take fama da wannan ciwon ta gwada yin amfani da wayannan don neman karin bayani DM👇 08104445106) Idan kikayi wannan yar uwa wallahi tallahi zakiije Dadi Kuma zaki zamo abar alfahari a wurin mijinki "Idan kika kiyaye dukkan abubuwan da na gayamiki to insha Allah zaki rabu da infection ki kwantar da hankalinki ba dadi amma ya zamuyi" Hawayenta ta share "wallahi maman Amna nagode sosai da na fita zan bayar asiyomin abubuwan da kika lissafa kuma zan kira Yaya Amina in gayamata wannan maganin itama tayi amfani dashi kai zainab wallahi har sha'awar rayuwarki nakeyi bakida damuwa kina zaune da babansu safwan lafiya bantaba jin ance an ganshi ya tare wata mace a waje ba hankalinki kwance wallahi Zainab tsorona Allah tsorona HIV kar ya kwaso mana mugun abu" murmushin karfin hali na mata " ba wacca batada damuwa a gidan aurenta bilkisu duk wata macen akwai kalubalen da take fuskanta a gidanta saboda haka ki kwantadda hankalinki Zaro ido tayi " duk yanda nake ganin zamannan naku yanzu kema kinada matsala zainab? naga baki rasa ci da sha ba sutura ma haka duk cikin zagayennan ba wanda zai nunamiki wani abu amma kice min kinada damuwa " wannan karonma murmushin na mata " bazaki ganeba bilkisu watakila damuwata tafi taki kuma duk ta gidan aurena ce bayan wa'yanda ke zagaye dani dangina ko nashi ba wanda yasan abinda ke wakana a tsakanina da Lawal ba amma ke zan baki labarina da kuma labarin zaman gidan lawal bawai zan gayamiki don inason fitar sirrina ba A'a zan gayamiki don kisan bake kadai ke fuskantar matsaloli ba" Tashi nayi na shiga kitchen sauran cin-cin din da mukayi na zubo a plate na dauko lemo gora biyu da cups na azo a babban tire na dawo falon da su na aza a center table lemun na zuba mata a cup na mika mata " mu jik makoshi ko" karba tayi nima na zuba nawa na samu guri na zauna Kamar yanda kika sani sunana Zainab Umar Gobirrr............. Allah ya kaimu gobe lafiya AURE DA KARATU NA RUMAISA SIDI Page 8 Kamar yanda kika sani sunana ZAINAB UMAR GOBIR mahaifina haifaffen garin sabon birni ne wani yanki a cikin jihar sokoto kuma sanannen dan boko domin yana taka matakin proff ne su biyu iyayensu suka haifa daga shi babana UMAR sai kanwarshi khadija mahaifiyata ma 'yar asalin jihar sokoto ce auren hadi aka musu da babana saboda iyayensu aminan juna ne Itama mahaifiyata 'yar bokoce domin a gidan mijinta ta hada digreen ta na biyu Mu biyar iyayenmu suka haifa kuma ni kadaice mace a cikinsu yaya isma'il shine babba kuma kwararren likita ne yanada mata daya anty nasma da kuma 'ya'ya biyu sai yaya Abbas shine mai zafin zuciya a gidanmu yanada fada sosai shi kuma lecturer ne a usmanu dan fodiyo university shima yanada mata anty yasmin da yara uku sai yaya mu'azzam shi ma yanada mata daya da yaro daya kuma yana aiki da gidan man NNPC sai yaya Mubarak shi kuma soja ne yana ibadan sai kuma ni shalelen abba da ummi Kasancewata nikadai mace yasa na taso cikin gata da kulawa ta iyaye da kuma yayye gata na musamman nake samu a gidanmu ba abinda na nema na rasa kai hatta gwaggona da take aure a kaduna to duk lokacinda za tazo ita da yaranta yaya bashir da kuma anty halima to suma burinsu su sakani farinciki zan iya cemiki nice farincikin gidanmu gaba daya bansan yanda zan misalta miki kaunar da nake samu daga gidanmu ba wallahi bansani ba Tun lokacin kuruciya nakeda burin yin karatun masscom inaso sosai sanin burina iyayena da 'yan uwana suke kara bani kwarin guiwa duk da ba haka suka so ba burin abbana nayi karatun likita hakama 'yan uwana lokacinda yaya abbas yaji karatun jarida nakeso nayi fada ya dingamin na bazan yishi ba na tsorata sosai kuma naji karatun yana neman fitarmun arai saboda ana nema a dakushemin burina saboda a lokacin nake rubuta jarabawar fita daga secondry saida babanmu ya taka mishi birki da gayamishi a barni nayi ra'ayina tunda shi nake kauna Banida kawa sama da mahaifiyata da ita nake shawara hakama yayyena komai tare mukeyi idan fita nayi saurayi ya biyoni ita zan fara gayawa ke zan iya cemiki a wurin mahaifiyata na koyi komai ta sakani a jikinta sosai ta yanda kaitsaye zata gane gaskiyata ko akasin haka RAYUWATA ta fara canzawa ne bayan haduwata da lawal dan wanka kuma dan kwalisa saurayi irinsu lawal ne akewa lakabi da (bakyau gareku ba shiga rai) mun hadu dashi ne bayan kammala secondry dina a bikin yayar kawata hafsa wankan lawal ne ya jani na kulashi a lokacinda ya fara min magana cikin yanga na tsaya na saurareshi bayan tsayuwarmu kuma labari ya sauya " banga laifinki ba don kinki kulani a karon farko domin kin cancanci hakan kyakkyawa saidai ina rokon don girman Allah ki aramin koda minti 3 ne cikin lokacinki" cikin wata sabuwar yangar da naji tana tasomin na fara magana "ina jinka minti 2 na baka saboda inaso in koma gida da wuri" tsayuwarshi ya gyara "nagode sosai Beauty tun lokacinda kika shigo idona ya sauka akanki ganin shigowarki na kara godewa Allah da ya sanya ina cikin wayanda aka gayyata a bikinnan" kallonshi nayi "saboda me?" "Saboda na hadu da beauty wanda bansa ran haka ba" kallon wayata nayi duk da yanda zuciyata ke ingizani da son sauraren yanda yake fitarda sautin kalamai kamar wani mawaki "zan wuce lokacinka ya cika" daga haka na fara tafiya har na isa wurin motata shi ya budemin na shiga " kiyi tuki a hankali beauty Allah ya tsaremin ke ya kaiki lafiya a gaida mommy ace sabon danta na gaishe ta" motata na rufe na shiga kokarin kunnata ba don wulakanci ba sai don yanda naji zuciyata na karbar sabon sako daga wannan mai zazzakan kalaman Ina tuki ina tunani to shi haka ake soyayyar? kofa number ta bai nema ba duk da bana raba number ta amma ina jin da ya tambaya shi zan bashi A bakin tangamemin get din gidanmu na shiga doka horn da sauri aka shiga wangalemin shi sauke glass nayi ina wa dattijon mai gadin namu murmush " barka da dawowa shalele kuma farincikin gidan gaba daya" "barka da aiki baba" shima da murmushin a fuskanshi yake fadin"Allah ya huce gajiya" amsawa nayi da "Amin tare da wucewa da motata na kaita ma'ajiyar motocin gidan kashe motar nayi tareda fitowa farinciki naji ya cikamin zuciya ganin motar yaya bashir a gidan sauri-sauri na karasa falon tareda kwalla mishi kira shima kamar kullum da murmushi a fuskarshi ya mike yana mini waka kuma yana tafi lokaci daya "ga shalelen abba ga shalelen ummi kai ga shalelen gwaggo kuma itace shalelen yaya"( ku rera wakar da kanku) Rausaya na shiga yi kamar kullum dariya suka shiga min saboda inda sabo sun saba indai yaya bashir yana sokoto to kullum muna tare ko wani gurin zaije to saidai mu tafi tare ko su yaya abbas bamuyi shakuwar da mukayi da shi ba bayan ummi da abbana shine mutum na uku da yasan sirrina kamar yanda zan nemi shawarar abba ko ummi haka zan kirashi in nemi shawararshi Tambayarshi su yaya halima nayi dasu gwaggo yace duk suna lafiya sunce a gaisheni "ga tsarabarki can da suka baki sai na huta zan baki" kafata na shiga dokawa kamar wata karamar yarinya "nidai wallahi aba ni abina yanzu tun ba'a min danwaken zagaye ba" na fada ina kallon ya mubarak (wanda nake bi) tsaki yayi " nasan tsarabarki bata wuce chocolate ko sweet tunda har yanzu kallon kanki kike a wata jaririya wallahi malaman university ne maganinki" baki na murguda " eh naji dai ai nasan haushi kakeji saboda ba kaine auta ba kuma da kake cewa hakan ai dai nima kwanannan zan fara jami'ar nan kuma zan baku mamaki" wata harara ya bankomin " wallahi har na matsu na ganki a jami'a" wannan karon ya bashir ne ya taremin fada "mubarak sai mun baka mamaki zakaga shalele a jami'a hankali kwance tana karatunta wata rana saidai mu ganta a gidan tv tana karanto news kamar baturiya" Tsallen murna na buga tareda riko hannunshi wata harara ummi ta bankomin abinda yasa nayi saurin sakin hannunshi tareda wucewa dakina don in rage kayan jikina inyi wanka Ina zaune gaban mirrow ta shigo dakin wurina ta nufo tana hararata kunnena ta kama ta murde "banhanaki taba mutum ba idan kina magana ban hanaki ba?" kara na saki saboda yanda naji zafin rikon "ummi bazan kara ba" kunnen nawa ta saki "nasha gayamiki ba kyau amma kinki daunawa kedai wuyarta fira tayi dadi yanzu zaki cumuimuye mutum ko su mabarak na hanaki yiwa haka bare kuma bashir da zai iya aurenki "aurena kuma ummi" na fada ina zare ido dakin ta bari tana gayamin in fito mu shiga kitchen Da dare kamar kullum bayan mun kammala cin abinci muka dawo falo har Abbana kusa dashi na zauna ina nuna mishi system din da nakeso ya siyamin " duk abinda kikeso zan siya miki Zainab indai zaki aje hankali kiyi karatu naso kiyi karatun likita sosai amma burina bai kai ya dakushe naki burinba shine kuskuren da iyaye ke tafkawa akan karatun yaransu yarinyarka tana sha'awar fanni kaza kai kuma kaza kakeso tofa ka sani idan har ka tursasata tabi naka ra'ayin to bazata taba maida hankali ba don ba shi takeso ba na barki kiyi ra'ayinki fatana ki maida hankali a karatunki banda kule-kulen samari ko tarkacen kawaye ki rike mutuncinki da kuma muruncin gidanku kece farincikinmu kema kinsan hakan to don Allah karki watsa mana kasa a ido" jikina naji yayi sanyi sosai bana cikin 'yan mata masu tara samari saboda a ganina hakan zai hanani cika burina abba yasha gayamin ko ina makaranta miji ya fito to za'a yi auren sai in hada biyu inyi AURE DA KARATU Ummi ma nasihar ta shiga min kamar ance gobe zan fara zuwa jami'ar nan tana gamawa shima yaya isma'il ya dora hakama su yaya bashir kuka na saka musu ina nuna ya mubarak" yaya shima ku mishi fada wallahi baya karatu kullum saidai yasa littafi gaba yana chat da ya jiku tafe ya aje waya" harara ta ya shiga yi " wa zaki yiwa sharri? kedai in kinsan bazaki iya karatunnan ba ki fada kar ayi hasarar na man mota" kuka nasa ina daddaga kafafuna kasa lallashina yaya bashir ya shiga yi yanawa ya muby fada abba na dariya Abin mamaki koda nazo kwanciya sai tunanin bawan Allah nan ya hanamin bacci ya iya tsara zance daga yanda yake fitarda kowace kalma cikin tattausan lafazi juyi na shiga yi da mamakin wannan sabon al'amarin da ya sameni tunanin wani namiji bai taba hanamin bacci ba saboda koda munyi magana da kai nan gurin zan barta bana sakawa raina barema abin ya dameni amma wannan mak'ale-matan ya hamin sukuni Jin wayata tayi kara alamar shigowar sako yasa na mika hannu akan bedside drower ta na janyo wayar zaune na tashi ganin sakon da ya shigo wayata "Barka da dare Beauty na fatan kin isa gida lafiya a yau zanyi bacci da wayata akan kirjina saboda number mai daraja da wayar ke dauke da ita mu kwana lafiya kiyi bacci cikin aminci" Sakon na shiga maimaita karantawa kamar wata hadda tabbas mutuminnan ne na dazu gurinshi kadai na taba jin kalamai irin wayannan wayar na rike ina kara kallon sakon daga nan wani bacci mai dadi ya daukeni sai asuba da naji ummi na tadani tareda yimin fadan kwanciya da waya ina kan dadduma ina azkar bayan kammala sallar asuba naji shigowar sako "MAYE" na fada a raina ganin yanzu ma number jiya ce "Barka da asuba Beauty fatan kin tashi lafiya Allah yasa haka Amin kar ki manta nima kimin addu'a sako daga MAYENKI" murmushine ya subuceminn "sai maye kam" na fada ina nade dardumata tareda komawa kan gado na gyra kwanciyata HMMMMM✍️✍️✍️✍️✍️ AURE DA KARATU NA RUMAISA SIDI Page 9 A bun sai ya zama kamar ibada kullum zai min text da safe da rana hakama da dare amma bai taba gwada kirana ba nima bantaba yunkurin yi mishi reply ba duk da abin ya riga ya zamemin jiki kullum na saba da karanta shi kuma kullum da kalar kalaman da zai turomin Yau haka na ke aiki ba k'wari saboda rashin ganin sakon MAYENA kamar yanda na radamishi suna na riga na saba da shi yau sai naji daban girkin kawai nakeyi amma hankalina sam ba ya wurin na damu sosai na rashin jinshi ashe haka na shaku da sakonshi "Lafiyarki kalau kuwa zainab" naji ummi ta daka min tsawar da ta sa na dawo hayyacina "dubi abinda kike yi" ta nunamin abinda nakeyi sanwar miya zanyi ashe na cika tukunya har ga baki Bakina na dafe ina kallonta "wallahi ban lura bane ummi" tsaki ta buga "ya za'ai ki lura? na dade da lura akwai abinda kike boyemin ki gayamin meke damunki" murmushin yake na mata "ummi dagaske ba abinda ke damuna" hanya ta nunamin "fice bani guri inyi girki na" hakuri na shiga bata sannan ta kyaleni muka dora sabuwar sanwa Har muka doshi kwana uku ba sakon MAYENA har wani daci-daci nakeji a bakina kamar wacca tayi zazzabi a daren ranar ne na kasa hankuri zuciyata nakeji kamar zata buga wayata na dauko na shiga laluben numbershi da nayi saving da sunan da na rada mishi Jinai kamar na samu baturiyar da ke gayamin wayarshi a kashe take na makure mata wuya tunani na shiga yi "to idan ya daga me zance mishi? ince na daina ganin text dinshi ko me? ko ince nayi kewarshi? kaii inaaaaa" wayar na aje tareda kokarin yaki da abinda zuciyata ke sakani Kawadda tunaninshi nayi kokarin yi daga raina naci gaba da harkokin gabana da kuma shirye-shiryen makaranta ta da nida yaya bashir muke komai kamar wata baby zata je boarding school haka mukayo siyayyar uwayen kayan biscuit sweet dasu chocolate ya gama kwanakinda zaiyi lokacin komawarshi yayi rigima na samishi " nidai wallahi ya bashir bangaji da ganinka ba don Allah ka dawo garinnan gaba daya ni banson komawarnan taka" ido ya zubamin yana kallona " dagaske kike shalele? dagaske bakyaso na koma? indai har hakan kikeso wallahi zan nemi transfer in dawo nan" washe baki nayi ina murna " wallahi inaso" hannuwanshi ya watsa "angama shalele" murna na dingayi Sai dare bayan munkare cin abinci ya sami abba da maganar fada ya dinga mishi wanda wani na fahimta wani ban fahimta ba "Wannan ai shashanci ne saboda tace kayi abu sai kace zakayi? ita yarinyarce zata gayama abinda za kayi to hakan za'ayi zaman ita ke bada umarni kenan ba haka nakeson ganinka a gidanka ba tsayayye nakeso na ganka shiriritarku ni ta isheni hakan nan kusa zanyi maganinku" wannan ne ya dakatarda ya bashir da dawowa sokoto Na fara karatuna cikin aminci a USMANU DAN FODIO UNIVERSITY da motata nake zuwa duk da yaya abbas yaso ya hanani tuki yace a hadani da driver amma na tubure na ce ni zan iya karatu nakeyi amma har yanzu wannan mutumin yananan makale a cikin zuciyata har yau na kasa goge sakonninshi dake cikin wayata kusan kullum sai na maimaita karantasu kamar wata hadda A hanyata ta komawa gida motata ta tsaya fitowa nayi gashi wurinda nake ba mutane ko ina tsit wayata na dauko na shiga kokarin kiran ummi cikin shagwaba na fara magana jin ta daga " ummi gani nan a hanya motata ta tsaya kuma ko ina tsit ba mutane" "Gashi ba kowa a gidan ko driver sun fita da su Antynki Nasma bari in kira bakaniken yazo inda kike ya duba motar ke kuma kisamu ko napep ki dawo gida zamanki a irin wurarennan hadarine" tsoro na rikaji nima ina kallon gabas da yamma ina nema inga napep Sai can ga bakaniken ya iso barmishi key din nayi idan ya kare ya kaimin gida na dawo dubin napep can na hangeta tafe taro na shiga yi cikin iyawar ubangiji ya tsaya "malam Arkilla za........."maganar ta makale a bakina ganin yanda shima yayi saurin dagowa yana kallona "Shine wallahi shine" na shiga nanatawa a raina dakewa nayi na karasa maganata " Arkilla zaka kaini" shima kawadda kai yayi " bismillah to" shiga nayi ya fara tuki a hankali mun danyi nisa naga ya tsaya kifa kanshi yayi akan keken sai can ya dago batare da ya kalleni ba ya fara magana " Na dauka zan iya na dauka zan saba ashe bazan iya ba na ga kamar ina takura ki tunda na hadu dake bankara bacci cikin kwanciyar hankali ba ranar da na ganki hankalina bai kwanta ba saida na koma wurin taron nabi duk hanyar da zanbi na samu number ki naci gaba da neman soyayyarki ina kaunar jin muryarki amma bana fatan hakan ya zama abinda zai bata ranki shiyasa na zabi na tura miki text da fatan watarana ki kulani kwatsam mahaifina ya rasu a wurin makokin aka dauke 'yar wayar ban san kuma inda zan kara samun number ki ba kullum fatana ina zan kara haduwa dake" juyowa yayi yana kallona " Ina sonki zainab wallahi ina sonki saidai naga kamar abinda nakeso bazai samu ba saboda ta kowane bangare kinfi karfina zainab" Abin mamaki sai nasamu kaina da cewa "dama mace tana fin karfin namiji" zama ya gyara "sosai ma kuwa" sai a sannan na fahimci bada kaina da nayi kallon wayata nayi " muje please ina bukatar isa gida da wuri" murmushi yamin wanda ya dakarmin zuciya "angama ranki ya dade" Sai kofar gidan yayi parking ina kokarin fita maganarshi ta dakatarda ni "Am Zee don Allah inaso idan ba damuwa mu samu lokaci muyi magana" hmmmmm abin takaici ban musaba " Kasameni a UDUS gobe karfe 12:00" "An gama ranki ya dade nagode sosai" kudi na zaro masu yawa bansan ko nawa bane na mika mishi girgiza kanshi yayi "Allah kiyaye ko karen gidanku na dakko bazan karbi kudinshi ba bare kuma ke" ganin zamu tsaya bata lokaci yasa na aje mishi kudin tare da shigewa gida bana son haka sam alakarmu daban sana'arshi daban kuma ni har yanzu ma ban gama tantance abinda ke tsakanina dashi ba Yinin ranar har dare ina cikin walwala ta musamman Washe gari da zanje makaranta sai na samu kaina da tsayawa zaben kayan da zansa inje makarantar daga karshe bakar abayata data sha adon stones na dauko saiko na fito fes dani ankare nake da agogo sai 12 muka gama lectures can na hangoshi zaune cikin napep kafafunshi da jikinshi suna waje Hafsat kwasare na kalla "ina zuwa hafsat nayi bako ne" baki ta dafe "Ahhh lallai wannan wane handsome ne mai wannan babbar sa'ar bantaba jin ko ganinki tare da wani ba" dube-dube ta shiga yi tareda riko hannuna "wai ina yake? ko tsoron amiki snatching kike" nuna mata shi nayi "kinganshi can kuma nifa bance miki saurayina bane kawai nace miki bako nane" fara'ar fuskarta ta bace "Aiko shi akayi kenan har na fara murna" dariya ma ta bani takawa na shigayi na isa wurinshi da isata ya mike tsaye yana kallona da murmushi a fuskarshi "barka da isowa gimbiyar mafa" murmushi na mishi nima "barka dai mu dan isa can ko" na nuna mishi wurin zama "Sunana Lawal muhammad kuma ni haifaffen garinnan ne maganar gaskiya tunda na ganki Allah ya dasamin kaunarki a raina sai kuma nake ganin kamar abin bazai yuba saboda ni dan talaka ne zainab a halin yanzu mahaifina ya rasu kuma ni kadaine namiji a gidanmu 'yan uwana duk matane kuma ni ke dauke da nauyinmu gashi banyi wani dogon karatu ba bare ince zan nemi aiki daga secondry na tsaya wannan keken ma ba tawa bace hayarta nakeyi shiyasa nake ganin kamar tarayyarmu bazata yuba saboda ke kam sam baki saba da wahala ba" Wani irin tausayinshi ne ya lullubeni "saboda kana talaka kake tunanin bazaka sameni ba ko kuma saboda bazaka iya yakin neman soyayyata ba?" murmushi yayi "zan iya gimbiya indai har kin bani dama wallahi zan iya" mikewa nayi ina gyara gyalen abayar da ke kaina "Allah yaba mai rabo sa'a" Aiko daga lokacin lawal ya dunga balbalemin zuciyata ya hanamin sukuni da zazzafan kalamanshi da suka sa nakejin zan iya komai a kanshi soyayyata da lawal ta canjamin rayuwa sosai ada duk abinda zanyi to zanyi shine da sanin Ummi amma a yanzu wani abun kafin ma ummi taji lawal yaji sannan ada can baya duk wanda zai hadu da ni to saidai mu hadu a gidanmu amma sabanin lawal da har yanzu bai taba shigowa gidanmu ba duk haduwar da za muyi saidai makaranta Babban kuskuren da na fara yi shine gwada siyawa lawal sutura domin shima ya rabuda wayannan kayan da yake sakawa kullum duk dan abinda nasan zai bukata ina siya in bashi batare da nayi duba da shi ya dace ya kyautatamin tunda nake dashi bantaba sanin wata kyauta ta hadani dashi ba kuma bantaba damuwa ba don ba shine gabana ba Kwatsam mai gidan lawal ya karbe napep dinshi bansan abinda ya hadasu ba amma lawal ya gayamin bazai koma wurinshi karbar napep din ba ya shiga damuwa sosai saboda da ita ya dogara da ita yake ciyadda 'yan uwanshi da mahaifiyarshi nima na shiga damuwa da tunanin hanyar da zanbi in taimaka mishi don bazan juri ganinshi a wannan halin ba Soyayya ruwan.............🤔 Comment & share pls🙏 AURE DA KARATU NA RUMAISA SIDI Page 10 Numfasawa nayi tareda duban maman haidar da ta kashe kunne tana saurarona "kinsan wani abu wai " kanta ta girgizamin alamun labarin ya fara tafiya da ita numfashi na kara ja " daya daga cikin sarkar gwal dina na dauka batare da kowa ya sani ba saboda a dakin ummi suke can take a jiyar su na lallaba na dauko saboda nasan idan na tunkari Abba ko su yaya da bukatar manyan kudi za su tuhume ni ne kawai ni kuma a yanzu ban shirya bayyanarda lawal gidanmu ba nafison sai ya dawo hayyacinshi yanda ba zai samu wata matsala ba Lokacin da na bashi sarkar fada ya dingamin tareda nuna min shi bazai karbi abina ya siyar ba nikuma kamar sakarya na shiga lallabashi harda kukana ina rokon ya karba indai har dagaske yana sona dakyar ya karba da sharadin bashi ne zaiyi kokari ya biya ni nace na yarda (hmmmm har yau ba'a biyani ba) Kaitsaye hafsat ta nuna rashin goyon bayanta akan soyayyarmu tareda min barazanar zata samu ummi ta gayamata ba karatu nakeyi ba soyayya nakeyi aiko ba karya ta fada ba don a yanzu ba yaren da nake ganewa idan ba yaren lawal ba " haba zee da ajinki da komai ki tsaya kina kula wannan ? me na sama yaci bare ya jefowa na kasa ko haka zaku zauna abinki ya kare akanshi kullum yazo ko kunya bayaji shi bai kawo miki komai ba amma idan kika siyo abu kika bashi yana iyayi zai karbe haba zee wallahi jira kawai nake yaya abbas ya dawo daga tafiyar nan da yayi ya dawo makarantar nan in gani shin zaki cigaba da abinda kikeyi wallahi baki dace da wannan kazamin ba" Wani irin zafi kalaman hafsat suka min domin zan jure ta zageni ta gayamin duk abinda zata gayamin amma bazan juri ta aibanta NISFUL-HAYAT a gabana ba "ya isheki malama cin fuskar ya isa haka" na fada cikin hargowa ina kara matsawa kusa da ita "Ke kin isa ki gayamin yanda zanyi rayuwata ko ke zaki gayamin wanda ya dace na kula? tun farkon tarayyata da bawan Allah nan baki taba furta alkhairi akansa ba kuma da kike kiranshi talaka a haka nakeson abina kuma a haka naji zan iya zama dashi kije kiyi rayuwarki yanda kike bukata nima nayi tawa period" na fada tare da zarar jakata nafice daga makarantar tareda jin haushin hafsat sosai duk da kawatace tun a secondary kuma duk abinda zanyi taga bai dace ba zata bani shawara na gyara amma yau sai na kasa duba abinda take kokarin nuna min Tsaye nake a gaban madubi ina kallon kaina so nake na hango kyawun da kullum lawal ke kiran inada shi nasan ni kyakkyawace duk da kasancewata wankan darza amma ni kyakkyawace kuma inajin hakan a gurin mutane musamman ya bashir to amma yanda lawal din ke fada ya banbanta da saura hirar mu na tuna ta dazun " wallahi my zee tunda nake kallon fina-finai daga bakar fata ke har turawa zuwa indiyawa bantaba ganin tsarin halitta irin taki ba wallahi ke kyakkyawace kuma ke ta musamman ce kyawunki na dabanne musamman idanunnan naki masha Allah gaskiya dole na kara kaimi kar late comer yazo yamin abinda ya saba nidai rokona ki rikemin alkawari kar ki jefa zuciyar marayan Allah a wani hali don Allah" lumshe idanuna nayi ina murmushi tare da tuna zazzakar muryarshi "Kanki daya kuwa zee" naji muryar anty halima da ta kwana biyu a a bayana juyowa nayi ina kallonta har yanzu da murmushi a fuskata " bakomai anty" itama murmushin tayi " ki gayawa wani ba komai amma bani ba kidaiyi a hankali karki zauce kuma wallahi ki wuce ki kwanta tun ummi bata shigo ta ganki gaban madubi a tsaye kina murmushi ba takai ga hasaso abinda na gane" isa nayi nima kan gadon na kwanta ina jan abin rufa tareda kokarin rufe jikina " wai baki yarda ba komai ba " " na yarda mana ai shiyasa naga dazu kin lake daki kina waya" ta fada batare da ta juyo ba shiru nayi da bakina gudun in ballowa kaina ruwa Soyayyar lawal ce ta kawo rashin jituwa tsakani na da hafsat domin kullum kokarin nunamin aibun lawal take ni kuma banaso ita kuma taki fahimta wannan yasa na fara ja baya da ita itama sai tayi fushi ta daina kulani ni kuma ban wani damuba saboda lawal ya zamemin madadinta domin ya siye babbar waya a 'yar sana'ar da ya fara da kudin da nabashi yace akwai haske sosai samuwar wayar sai muka kara dinkewa da rana muna tare a makaranta da dare muna makale a waya Abinda na kasa tsayawa in tantance shin wace sana'a ce yakeyi da kullum muna tare kuma bai taba gayamin abinda yake siyarwa ba nima bantaba yunkurin sake tambayarshi ba saboda a ranar da na tambayeshi fushi yayi tare da cewa saboda yana kudina nake tambaya shiyasa tun farko baiso karba ba Kwatsam yaya Abbas ya dawo daga tafiyar da sukayi washe gari ya shiga makaranta kuma a daren ranar maganar lawal ta dira kunnen iyayena da kuma yayyena Jin muryar ya abbas yana kwallamin kira cikin hargagi yasa hankalina ya tashi duk da yanada fada amma hakan bai taba faruwa tsakaninmu ba agogo na kalla karfe 9:07 irin wannan lokacin kowannensu yana bangarenshi to me kuma ya kawo su uzuri na bawa lawal da muke waya kan zanje in dawo a tsorace na fito Ya Abbas ne a tsaye jikinshi har tsuma yake sai abba dake zaune da ummi da kai duka ma mutanen gidan ke har anty halima isa nayi gabanshi na durkusa saboda yanda naji kafafuna sun fara rawa tun daga kan irin kallon da yakemin dakyar nasamu kwarin guiwar furta " gani yaya" " ka zauna abbas sannan kuyi magana" abba ya umurceshi sanin halinshi ko wane lokaci zai iya rufeni da duka ajiyar zuciya ya shiga saukewa sannan ya watsomin idanunshi masu firgita mai kunnen kashi irin nawa " me kika ce mana zakije kiyi a makaranta ?" ya watsomin tambaya tareda tsareni da idanunshi saina samu kaina da rashin gane inda zancenshi ya dosa saida ya dakamin tsawa " dake nake magana nace me kika ce zakije kiyi a makaranta " cikin rawar jiki na amsa ina kara matsawa baya " Karatu" " to da kikaje karatun kikayi" nanma shiru nayi "wallahi idan na sake maimaita miki magana saina sauyamiki fatar fuskarki da mari " karatun......na...yi" na fada a rarrabe " wayarshi ya janyo tareda budewa ya dagota yana nuna min " waye wannan" kaina na daga tsuwwwwwww cikina ya shiga wani kalar kida kamar an kunna disko " na shiga uku tawa ta kare" na fada a raina taya zan cewa yaya nasanshi ai kasheni kawai zaiyi " idan kika sake kikamin karya wallahi sai na karya miki hannu zainab" ya tare numfashi na daga karyar dana kammala shiyawa a raina Hannuwana na hade guri daya "don Allah kayi hakuri yaya wallahi bazan sake ba" " ka mata a hankali Abbas" yaya isma'il ya fada matsowa yayi yana kallona "meye alakarki da shi? ki fada karkimin karya" Kallon ummi nayi da ta zubamin ido tana kallona kallon mamaki da kuma tsoro " wai sona yake yaya" na fada cikin sakalci " sonki yake kuma bazai zo gidanku yayi magana da ke ba saidai makaranta zainab? wannan wane irin sone kenan ba karatun kike ba ko" kaina na girgiza hawaye na min zuba " Wallahi inayi yaya" Mikewa ummi tayi tabar falon abinda ya kara tayarmin da hankali hakama ya abbas sai yaya isma'il da ya tsaya yimin nasiha tareda nunamin kuskurena da kuma yimin jan kunne kan kar in kara in rabuda wannan mutumin saboda duk wanda bazai zo gidanku nemanka ba to ba kaunarka yake ba karin tashin hankalina abba ma baice komai ba Kuka na dingayiwa anty halima da muka koma daki tareda rokonta ta tayani neman gafarar su ummi itama nasiha ta shiga yimin tareda nunamin kuskurena muna cikin maganar lawal ya kirani wani haushinshi naji saboda yanda ta silarshi iyayena suka shiga damuwa kin dagawa nayi da naga ya isheni da kira na kashe wayar gabadaya RUMAISA SIDI✍️✍️✍️✍️✍️✍️ Shin an rabu kenan ko ana nan tare🤔 AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI Page 11 Washe gari anty halima ta jagoran ce ni wurin ummi na ba ta hakuri haka ma abbana dukansu nasiha su ka min tare da nuna min kuskuren abinda na aikata duk na ji na tsani kaina da wannan damuwar da na jefa su har na isa makaranta ba lakka a jikina kuma har lokacin ban kunna waya ta ba ban iya tuƙa kaina ba ranar saidai driver ne ya kaini Inda na hango hafsat can na nufa sallama na ma ta kallona ta yi sannan ta amsa "lafiya na ganku a waje na ɗauka ma an shiga lecture" na tambaye ta ganin lokacin lecture ɗin ya kama "kinsan halin malamin wataƙila ma bazai zo ba" gefenta na zauna "ai ko da bai kyauta mi ni ba wallahi ko lafiya banji a jikina amma haka na zo saboda sanin rashin mutuncinshi" sannu ta shiga min tare da tayin soyayyar farar da take ci "girgiza kaina na yi ina ya mutsa fuskata "ke kam hafsa Allah ya shiyaki da shegen kwaɗayi wallahi" lumshe idanuwa ta yi tare da buɗe ido ɗaya "bakisan daɗi bane malama fara ai ita ce kazar talaka" duk da yanda nake jin zuciyata amma hakan bai hana ni darawa ba kamar wadda ta tuna wani abu ta ɗan dubeni "na manta kinyi baƙo yace ki same shi inda ku ka saba haɗuwa" daga haka ta kulle bakinta gam tunani na shiga yi a raina naje ko kar naje daga ƙarshe na yanke shawarar zuwa domin na dakatar da shi da zuwa gurina don banason abinda zai haɗani da iyayena Tun daga nesa na hango shi ya na kaiwa da komowa a wurin da ya zama kamar mallakinmu a makarantar har na kusa isa wurinshi baisan na iso ba sallamar da na mishi da ƙarfi ya waigo tare da yi cikina kamar wanda zai riƙe ni ajiyar zuciya ya shiga saukewa kamar wanda yayi tsere "nagode Allah ba abinda ya same ki" wani tausayinshi ne ya shiga tsargamin a zuciya wurin zama na nuna mishi a sanyaye na ce "ka zauna muyi magana don Allah" zama yayi kamar yanda na ce nima na zauna na ɗau mintuna ina tunanin ta inda zan fara "me ya faru my zee? ko bakida lafiya?" kaina na girgiza mishi sannan na yi ƙundunbala na fara magana "kayi hakuri soyayyar mu ba za ta yuba" tsaye ya miƙe yana kallona kamar mai in-ina ya fara magana" Ba bangane me...ki ke cewa ba" Kallonshi na yi da idanuwa na da suka cika da ƙwalla hannuwana na haɗe guri ɗaya "don Allah kayi hakuri abinda zan iya cema kenan" daga haka na miƙe tare da ƙoƙarin barin makarantar ma gaba ɗaya maganar shi ta dakatar da ni "dama an gayamin hakan za ta faru a tsakaninmu amma na ƙi yarda kinsan ba za mu ci gaba da soyayya ba meyasa ki ka sabamin da soyayyarki meyasa za ki min hakan laifin mi zuciyata ta miki da ta cancanci wannan hukuncin daga gareki? saboda kawai na so ki? ko don ina talaka?" kuka na fashe da shi tare da durƙushewa a gurin na kasa bazan iya ba lawal rayuwata ne wallahi bazan iya ba shima hawaye ya ke gabana ya duƙa ya na kallona "kiyi hakuri zainab ki gayamin abinda ke faruwa" kamar sakarya na kwashe komai na gayamishi "ki kwantar da hankalinki insha Allah wannan bazai zamo sanadin rabuwar mu ba kinji ki kwantar da hankalinki" In taƙaice miki lawal bai bar makarantar ba saida ya tsaramin kalaman da suka saka naji bazan taɓa iya rabuwa da shi ba daga ranar kuma mu ka canja wurin haɗuwa saboda gudun ya abbas ya ganmu a makarantar ashe ba haka kawai ya abbas ya sakeni ba yana lura da kowane motsina ranar da ya damƙoni a wurin da muka haɗu da lawal ranar yamin dukan da bantaɓa tunaniba ba kukan dukan da yakemin nake ga a'a kukan rashin sanin halinda lawal ya ke ciki nake saboda tun a can ya damƙashi ga ƴan sanda ga kuma ummi da naga hawayenta na zuba nasan duk saboda ni ne Faruwar wannan abba ya dakatar da ni daga zuwa makaranta ya kuma karɓe wayata bansan yanda aka yi ba ranar sai ga lawal a gidanmu nidai na yi mamakin daga abba har ya isma'il ba wanda ya fita har wata rama na yi saboda tashin hankalin da nake ciki kowa ya janyemin a gurin anty halima kawai na ke samun sauƙi bansan wucewar lawal ba saida abba ya aiko a kirani Dukansu suna nan falon abba har ummi gabansu na je na duƙa tare da gaishe su kamar kullum ba wanda ya amsamin idanuwana da suka bushe kan kuka na lumshe abba ne ya fara magana "Allah ya sa ni tun tasowar ki da kuma shaƙuwar da ke tsakanin ku na kwaɗaitu na haɗaku aure ke da yayanki bashir to amma na fahimci hakan bazai sa mu ba saboda wasu sababbin halaye da kika tsiro da su a ƴan watannin nan bazan so haɗin aurenku ya zama silar taɓuwar zumuncin mu ni da 6ar uwa ta ba" Numfasawa yayi alamar abin bai mishi daɗi ba"Na kira wanda kike so munyi magana da shi ya je ya shiryo ko gobe ya tashi ya zo a ɗaura mu ku aure" Wata irin zabura na yi kuka na ƙwacemin "Aure kuma abba wallahi ni ba yanzu zanyi aure ba don Allah ka yi hakuri" ɓallina ya abbas yayi da ƙafarshi da ke kusa dani "za ki mana shiru ko sai na make ki ai duk hukuncin da aka miki ke kika ja" sannan ya dubi abba "Abba aura ma ta shi damuwa ce a rayuwarta na gayama nayi bincike kan yaronnan bayada wata sana'a sannan mahaifinshi ya rasu shi kaɗaine namiji a taƙaice ma har yanzu gidansu ake ciyadda shi saboda bayada hakuri duk inda yaje" hannu abba ya ɗaga mishi "haka ta ke son abinta abbas damuwa ba ta wuce na zuba musu ido suna zaɓar wurin da su ke son haɗuwa ba wata rana zanga abinda bama fata shi arziki na Allah ne indai tana son mijinta duk halinda ta tsinci kanta za ta jure" Ayi haƙuri da wannan AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI Page 12 Tun daga faruwar wannan karatuna ya tsaya na daina zuwa makaranta ke ba makaranta kaɗai ba duk wata fita abba ya dakatar da ni daga yinta a kuma lokacinne yaya bashir ya fito da ƙudirinshi a kaina a lokacin ya diro sokoto da ƙoƙon barar neman soyayyata kai tsaye na bayyana mishi ina da wanda nake so faɗar tashin hankalin da ya shiga ɓata bakine A wannan lokacinne kuma ummi ta magantu tun fara magana ta da lawal ɗakinta ta ja ni" kiji tsoron Allah zainab bashir bai cancanci hakan daga gare ki ba ko kina so kice tun baya bakisan ya na sonki ba?" nuna ni tayi sannan ta cigaba da magana "zainab zainab ki tsaida hankalinki wuri ɗaya kar soyayyar zamaninnan ta ruɗe ki zainab ki tsaya ki dubi wanda ya dace da ke kina ganin yanda kika ɗaga mana hankali ki dubi yayunki haba zainabu kiyiwa kanki faɗa ko don idon halima da kullum ke ƙoƙarin kare ki ya zataji kin fito fili kin nuna bakya ƙaunar ɗan uwanta ga gwaggonki da ke nuna miki ƙauna kina tunanin za ta ji daɗi kin nuna bakya ƙaunar ɗanta? shin wai ni da me wannan lawal ɗin ya fi bashir?" ban magantu ba don bansan me zance ba ƙwaƙwalwata ta toshe Kusan kowa a gidanmu saida ya zaunadda ni ya bani shawara amma zuciyata ta ka sa laraya daga ƙaunar lawal in taƙaice miki a ƙarshen watannan lawal ya gayamin zai turo magabatanshi saboda shima hankalinshi ya tashi sosai ya na tsoron ya rasa ni a ƙarshen watan ya turo kuma aka saka biki sati huɗu sanin halin da ya ke ciki ya sa na tura mishi kuɗi masu tsoka ta account ɗinshi ya ƙara ya kama gida Ana saura sati ɗaya biki abbana ya kira lawal bansan abinda su ka tattauna ba sai daga baya nakejin gida ya bashi da mota da kuma kayan fitar biki nima ya min faɗin murnar da na yi ɓata bakine ganin kamar abba ya fara saukowa a auren Daren da za'a miƙa ni gidan lawal abba yamin nasihar da ta sakani kuka sosai da sosai "Alhamdulillah Alhamdulillah ina ƙara godiya ga Allah da ya nuna min wannan ranar da zan miƙa ki gidan mijinki kuma zaɓinki ina fata idan kin shiga sai mutuwa ina bqki shawara da ki kasance mai biyayya ga mijinki duk abinda ya umurce ki matsawar bai ta ka shari'a ba to ki mishi ki nuna mishi mun baki tarbiyya domin rashin misi biyayya kamar tozarta mu ne ina mai gargaɗinki da ki kasance mai haƙuri don ina so ki sa ni bazan ɗauki shashanci ba ke kika kawo min shi kina so don haka zaɓinki na baki ban miki dole na baki zaɓina ba duk da ina da ikon hakan ina miki kyakkyawar fata a rayuwar aurenki Allah ya miki albarka ya baki zuri'a ɗayyiba Kallon maman haidar na yi da ta zubamin ido kamar ta samu tv sannan na dubi agogo zabura nayi "Wai kinga har ƙarfe ɗaya da mintuna nasan duk inda su ke suna hanya kuma ban girka mu su komai ba" ajiyar zuciya ta sauke "wallahi maman safwan na ƙagu inji irin halaccin da abban safwan zai saka miki da shi ji nake kamar mu kwana muna labarinnan don ko a littafi ban taɓa jin wadda tayiwa namiji irin halaccin da kika mishi ba" murmushi na ma ta "to sai kiyi haƙuri har wani lokaci" da sauri tace "gobe zan dawo" kallonta nayi a raina nace "matar nan taji gulma" a fili kuma na ce" gobe makaranta zan shiga saidai jibi" Na rakota tsakar gidan muna salllama sai ga motata ta shigo alamun yaran sun dawo buɗe motar sukayi kowa na rige-rigen isowa wurina " mommy ta warke" aysha ta faɗa tana ƙara ƙanƙameni a jikinta kanta na shafa "na warke da yardar Allah indo na ya makarantar ku shiga ciki gani nan shigowa" da gudu suka shige kallona na mayar kan oga lawal da ya dunƙule hannuwanshi yana jefomin wani kallo mai haɗe da murmushinnan nashi da na raɗawa na yaudara "naji daɗin yanda na dawo na same ki my zee ni sai naga ma kamar fitar nan da nayi har wani fari kika ƙara" Nuna mishi maman haidar nayi da ke tare da mu ganin kamar baignta ba zabura yayi kamar gaske yana sosa kanshi da key ɗin da ke hannunshi "Ahhh sannu maman haidar yau ziyara aka kawo mana anzo duba jikin madam"cikin mutunci su ka gaisa ta mini sallama tare da ƙara jaddadamin sai ta zo Ban yi girki ba ranar saboda abincin da lawal ya zo mana da shi mai rai da lafiya har da lemu ya siya mana aiko ranar mun raƙashe domin lawal ya canja sosai daga yanda muka sanshi nikam har yanzu ban aminta da wannan sauyin ba sam da dare ma da yaran suka yi bacci shi ya ɗauke su ya kaisu ɗakinsu To mu ma bari muje mu kwanta AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI Page 13 Sati ɗaya mukayi muna zaman mutunci da lawal hatta abinci yanzu a gidan ya ke ci duk da bashi ya siya ba a washe gari bayan yara sun wuce makaranta ni kuma ina gidan don banida lecture lawal ya sameni a ɗaki ina shirya kayana da aka kawomin daga wanki waigowa nayi na dubeshi ya tako har inda nake ya sami kujerar dake gaban mirrow na ya zauna yana fuskanta ta "Yadai abban safwan" na faɗa ganin kamar akwai magana a bakinshi ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kafamin idanunshi "magana nakeso mu yi dake zainab"aje aikin da nakeyi nayi na dubeshi ganin maganar mai muhimmanci ce "nasan kaso 70 na lalurorinki da na yara ke kike yi tare da taimakon ƴan uwanki kuma ina godiya sosai amma nima inaso in ɗauki nauyin ƴaƴana kamar yanda kowane uba ke yi shekaranjiya mama ta kirani ta bani kuɗi dubu ɗari biyu tace wai in samu ko ƙaramar sana'a inyi ita a shawararta ma in sari takalma a gurinki ko ba yawa in aza a shagon bilya ɗan yayarta tayi magana dashi" murmushine ya faɗaɗa a fuskata "Kai Alhamdulillah wallahi mama mungode sosai Allah ya sanya alkhairi yasa arzikinmu a sana'ar" Gyara zamanshi yayi "to maganar gaskiya ni bazan iya wani saida takalmi ina ma laifin ace gurina ake sarowa? ni wallahi farko da tace zata bani kuɗi inyi jari na ɗauka kuɗin sun kai miliyan ɗaya tunda filinta na gado ta saida to yanzu abinda nake nema gurinki ki rantamin dubu ɗari biyar sai ki haɗani da inda kike sarowa ina rabama mutane don ni bazan iya wannan zaman na kasa takalmi a kasuwa ba" galala na saki baki ina kallonshi kenan dai shi bazai canja ba kasa haƙuri nayi saida na magantu"wai abban safwan kai har yanzu zaman gidan bai isheka ba? meye laifin mama? kodon tana tausayama ai ba kai kaɗai ta haifa ba kuma kace bazaka yi sana'ar takalmi ba kafi ƙarfinta ne? wai me kake so ka maida kanka? yaushe za............" "Ya isheki malama" ya dakamin tsawa tare da miƙewa tsaye yana ci gaba da magana "karki so ki gayamin magana wallahi ranki zaiyi mugun ɓaci bazan ɗauki wannan ba duk da kike kallona a haka har yanzu banyi lalacewar da za ki gayamin magana in ƙyale ki ba kuɗi na ce ki aramin kuma shima ba dole" ji nai kamar in maƙure shi a hasale nima na miƙe "to banida kuɗin ranta ma kuma wallahi idan har kace haka za ka cigaba da rayuwarka wallahi akwai matsala ko ni da nake mace bazan iya zaman da kake ba sana'a ba yanzu kuma ka samu ta baka za ka wulaƙanta" tasssssssssss naji sautin mari tare da wata guduma a cikin kwanyar kaina tare da gilmawar wasu taurari Suman wucin gadi na tafi maganar shi ta dawo da ni a duniyar da nake "kinyi kaɗankiyi tsaye a gabana kina gayamin magana kuɗin ki na banza wallahi wahala za kiyi a wannan halayyar da kika tsiro da ita" bansan fitar shi ba saboda ina tunanin suma nayi a wannan lokacin na ɗau dogon lokaci kwance tsakar ɗakina Kamar wacca ta shekara a kwance haka nake komai jina nake kamar ba ni bace kamar an canja ni wai yau ni ce lawal ya mara marifa uban ƴaƴana sai a lokacinne na fashe da kuka tare da shafa fuskata da lawal ya gama wulaƙantawa kallon kaina nayi a madubi kamar wadda aka tsikara na isa ga hijab ɗina da ke aje na ɗauka tare da mukullin mota ta fita nayi na rufo ɗakina ban damu da yanda fuskata ta kumbura ba haka na shiga mota ta na ja Kai tsaye gidanmu na nufa kamar yanda na tsammananta ba kowa a falon ummi tana ɗakinta ɗakina na wuce wanda na zauna a lokacin da nake gida komai yana nan tsaf-tsaf saboda kullum sai an gyara shi kan gadon na faɗa tare da fashewa da kuka da sauri na rufe bakina jin kamar sautin kukana zai iya fita waje daga kukan bansan lokacin da bacci ya ɗauke ni ba Daga yanda naga rana ta fito ta window ɗina na tabbata na daɗe ina bacci tashi nayi na duba agogo ganin lokacin sallah yayi yasa na shiga toilet na ɗauro alwala na tada sallah saida na ƙare nayi addu'a sannan na buɗe kofar tare da fita falo Bayan ummi na hanga tana zaune a falon da hijabi ajikinta da kuma carbi a hannunta alamun sallah ta gama saida na kusa isa nayi sallama waigowa tayi da sauri tare da miƙewa tsaye da sauri ta ƙaraso wurina "Lafiya? yaushe kika zo? meya same ki a fuska haka? ina yaran? Ayi hakuri da wannan *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* Page 14 Haɗiye kukan da naji ya tasomin nayi sannan nayi gyaran murya ina ƙoƙarin saisaita muryata kar ta hango wani abin "Yau na tashi banjin daɗin jikina ne ummi shiyasa nace bari inzo nan" saki na tayi daga riƙon da ta min tana min wani kallo "kar ki raina min hankali zainab dubi fuskarki yanda ta kumbura alamun kin ɗau lokaci kina kuka sannan kin shigo baki neme ni ba wai kashe kanki za kiyi zainab?" ta ƙarasa muryarta na karyewa kamar za tayi kuka rungumeta nayi tare da fashewa da kuka hannuna ta riƙa ta zaunadda ni akan doyuwar kujera ita ma ta zauna tare da ɗora kaina a kan cinyarta tana shafa bayana alamun rarrashi "Kiyi haƙuri kowane bawa da kalar ta sa ƙaddarar zainab ba wanda aka saki haka kawai saidai ƙaddarar wani tafi ta wani nauyi ni bazance ki kashe aurenki ba don ba ni na haɗaku ba bale na rabaku an riga da an ƙaddara lawal mijinki ne kuma ba wanda ya isa ya tsinke igiyar aurenku sai in an rubuta wannan a ƙaddarar ku kiyi haƙuri nasan kina yi ki ƙara kuma ki rage saka damuwa a ranki kodon ceton lafiyarki Alƙur'ani da kike gani maganin damuwane zainab ki rage baccin dare ki tashi ki gayawa Allah kukan ki shi kaɗai zai miki maganin matsalarki duk wanda yace zai miki wallahi ƙarya yake" Ajiyar zuciya na shiga saukewa ita kuma tana shafamin kaina Asabe ta kira tace ta haɗamin abu mai ɗan ruwa-ruwa kamar yanda nace inaso ganin yanda ta sakani gaba na daure na ci abincin shawarwari ta shiga bani tare da addu'o'in da zan riƙa yi sai gani na ware ina zuba shagwaɓata a jikin ummina duk da tunanin yarana yana nan maƙale a raina Sallame sallar la'asar ɗina yayi daidai da fara ringing ɗin wayata ban miƙe na ɗauko ba na cigaba da salatina da addu'o'in da ake yi bayan ƙare sallah saida na kammala na janyo wayar tare da dubawa tsaki na ja ganin number lawal ce ina ƙoƙarin maidata na aje kira ya sake shigowa wannan karon ma shine ina kallo ta gama ringing har ta tsinke ban ɗaga ba ringing ɗin na ƙarewa wani yana shigowa ɗaga wayar nayi tare da karawa a kunne na ba tare da nayi magana ba" ina kika je na dawo ban same ki ba" wannan ita ce sallamar shi gyara zamana nayi sannan nace " inda aka san daraja ta inda kuma har gobe lafiyata tanada amfani a gurinsu ko so kayi ka dawo ka sameni ka ci gaba da jibga kamar yanda kake so" ajiyar zuciya ya sauke tare da yin shiru na sakanni " kiyi hakuri wallahi raina ne ya ɓaci amma na miki alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba" taɓe bakina nayi kamar yana gabana " bazan iya ci gaba da zama dakai a duk lokacin da ranka ya ɓaci ka dinga sauke fushinka a jikina ba wallahi bazai yu ba"tausasa yaudararriyar muryarshi yayi "nasan nayi kuskure amma kiyi hakuri" katseshi nayi"na gaji da haƙuri da kai ina cutuwa lawal na gaji ni shikenan banida damuwa sai kai? kullum kaine matsala ta? to na gaji wallahi"mamakine ya kamani jin bai ɗaga murya ko yayi fushi ba sai ma ƙara kwantarda murya da yayi "kiyi haƙuri zainab ko ba don ni ba ko don yarannan kinsan halin kayanki ga su can falo amna tunda suka dawo ta neme ki nace musu kina makaranta yanzu kuma sunga lokacin dawowar ki ya wuce sun samin rigimar in kiraki su yi magana da ke wallahi yanzu haka ko abinci ba su ci ba" Miƙewa na yi daga kishingiɗen da nayi ina saurarenshi da sauri na ce mishi"Ina yarana" ina jin alamun yana tafiya da alama shi yana ɗakine su kuma suna falo ina jin lokacin da yake ce musu ga mommynku ku ce ta dawo da wuri "mommmmmmy" naji muryar Amna tana kirana cikin muryar da ke nuna tasha kuka ta ƙoshi "na'am shalelena"na amsa mata nima "mommy ki dawo gidan ba daɗi idan bakya nan"wannan karon Aysha ce mai maganar "zan dawo Aysha amma sai kun min alƙawarin yanzu za ku ci abinci" alƙawarin su ka min sannan na kashe wayata text ɗinshi ne ya shigo wayata "bayan magrib za mu zo mu ɗaukoki ni da yara" aje wayar nayi Muna falo ni da ummi bayan ƙare sallar magrib muna firar yaya mubarak da muke saka ran dawowarshi a sati mai zuwa muka ji tsayuwar mota ba jimawa kuma sai gasu sun shigo a guje kowa yana kirana rungumeni su ka yi dukansu kowa yana gayamin yanda yaji da ya dawo ya tarar na fita sallamar shi naji a bakin ƙofar falon amsawa mu kayi sannan ya shigo ya duƙa gefen kujera kamar wani mutumen arziki yana gaida ummi cikin mutunta juna suka gaisa sannan ya fita Kiran sunana tayi lokacin da nake ƙoƙarin saka turarukan da ta bani a cikin ƴar ƙaramar jaka "ina mai ƙara jan hankalinki da ki kula kinsan dai wannan karon yayunki ba za su miki kowane kalar uzuri ba in har tarihi ya maimaita kansa" bana buƙatar ta faɗaɗa min bayani don na fahimci inda zancenta ya dosa Har muka isa gida duk yanda ya so sakani fira ban tanka shi ba Ina goge kaina da na wanke wurin wanka ya shigo "ga abincinki can idan kin tashi"ganin ya doshi ƙofa alamun barin ɗakin zaiyi yasa na ɗan ɗaga muryata na bashi amsa "baka taɓa ganin na je gidanmu na dawo gidanka da yunwa ba" ɗan tsayawa yayi na minti ɗaya sannan ya ɗaga ƙafarshi ya bar ɗakin Kwanakin da suka biyo baya wata rayuwa muke yi a gidan ni da shi ya daina shiga harkata saboda da ya shiga zanyi fata-fata dashi to sai ya kama kanshi ya canja gaba ɗaya an siyo sabuwar waya ƴar yayi ga sababbin shaddodin da yake bugu ga kayan daɗin da yake haɗiya ni dai ina daga gefe ina shan kallo don ko nasan kuɗin mama ne ake wulaƙantawa yanzu zai ɗau wanka ya fita kamar wani alhajin nera wani abin ma abin dariya idan naga yanda ya ke shan ƙamshi shi a dole yayi arziki ya wuce wulaƙanci na Yau ma ina kwance a kan doguwar kujerata safwan da aysha kuma suna riƙe da hannun amna suna koya mata hand writing ya shigo da uwar shadda har maiƙo ta ke ga hular da aka kafa kamar wani ango hannunshi ɗaya riƙe da haɗaɗɗiyar wayarshi ɗayan kuma yana riƙe da leda ta gefen ido nake gulma saboda banga fitarshi ba ina makaranta ɗaki ya wuce ya ɗanja lokaci a ɗakin har na fara shawarar tashi na bishi ɗakin kamar zan ɗau wani abu don inga abinda yake a ciki Har idona ya fara ciwo da leƙe ya fito wannan karon da sabuwar jallabiyya ya fito a raina nace "Malam lawal saboda bawa bacci haƙƙinshi shima an sabunta mishi" kitchen ya wuce yana wata taƙama ni idan dai ba idona ne ke gayamin ƙarya ba har wani ɗaga kafaɗa naga yana yi kwanannan bai jima a kitchen ɗin ba ya fito riƙe da plate saida ya ƙaraso tsakiyar falon naga ashe kifine irin manyannan ya gasu iya gasuwa komawa yayi kitchen ɗin sai gashi ya dawo da ƙaton kwalin lemu da kuma kofi ɗaya Janyo center table din falon yayi tare da kaishi gabanshi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya janyo waya ya kunna yana ɗibar kifin a hankali kamar mai cin ɗawisu fahimtar abinda ya ke nufi yasa na umurci su safwan da su je su kwanta ina kallon amna tana kallonshi kunsan halin yaro da kwaɗayi musamman abinda yasan bazai samu ba itama ina watsa mata harara ta bisu su ka tafi gyara zamana nayi tare da ɗora ƙafa ta ɗaya kan ɗaya kamar yanda yayi saida ya kammala sannan ya tashi yana gyatsa ya kwashe kayan ya wuce ɗakinshi da kallo na bishi ina kissima yanda zan rama abinda ya min saboda na sanshi tun dama ba dai kwaɗayi ba duk abinda yasan zaiyi ɗanɗano to yana ƙaunarshi "nasan maganinka" na faɗa a fili tare da tashi na wuce ɗaki Duk abinda nasan zai ƙarawa girkina ɗanɗano ko ƙamshi saida na zuba shi a dahuwar lafiyayyar kazata da nake wa farfesu harga Allah ban tashi cinta ba amma saboda lawal na ɓanɓarota daga freezer na shiga mata haɗin da nasan ba'a bawa marowaci daga yanda ya fito ya zauna falo nasan ƙamshinne ya fito da shi dama can hakan yake ko ya nake girki indai yana ɗaki sai ya fito yace bazai iya haƙurin jira a ɗaki ba kamewa yayi a kujera yana canja channel saida na ganshi sannan na shiga kitchen na zubo wa yara safwan na kira "ka ɗauka ku je ɗaki ku ci" ba don komai na tura su ciki ba sai don za su iya canko wani abu zubawa nayi a wani plate na ɗauka na nufo falon Da gayya na yi saitin lawal kamar wurinshi zanje saida naje dab dashi sosai sannan na duƙa na ɗauki remote ɗin da ke kan cinyar shi ƙiris ya rage dariya ta ƙwacemin ganin har yana ƙoƙarin ɗaga hannunshi kamar zai karɓa ganin na goce sai ya fara muzurai yana raba ido ba ƙaramin ƙoƙari nayi ba wurin taushe dariyata saboda nasan ƙiris ya rageyawunshi su zubo Tun dama Allah ya sa mishi son kaza ni kuma na fi son kifi ina da tabbacin shiyasa ya min abinda ya min jiya saboda har ga Allah kifin ya burgeni ga yanda aka gasa shi kuma nqce sai na rama don yanzu na daina yarda ina bar mishi bashi da ya min zan rama na daina ajiyar wutar damuwarshi zan riƙa fitarwa ta shafi kowa Har na kammala suɗe dabgena ban ragawa komai ba kai hatta ƙassa ban ragawa ba sai lumshe ido nake ina tanɗar baki a fili kuma ina faɗin "Allah ka ƙara mana lafiyar cin dajaja" tsaki ya buga tare da tashi ya shige ɗaki dariya na tuntsire da ita har ina dafe cikina saboda yaban dariya wallahi lawal ba dai kwaɗayi ba yaran nasa suka shirya na ce Amna taje ta ce idan abbansu zai fita ya biya da su wurin mama saboda sun ɗan jima basu je ba Ban ɗauka zai fita da su ba saida ya shiryo ya fito cikin dakakkiyar shaddarshi sai maiƙo ta ke ya ce su fito hannu su ka shiga ɗagamin nima na ɗaga mu su har ya kai ƙofa ya ɗan dakata batare da ya waigo ba yace "Nifa mashin zan hau ko napep"na fahimci abinda ya ke nufi ya ɗauka tunda na haɗashi da yarana in bashi key ɗin motata yayi yanda ya ke so da ita kawadda kaina nayi sannan na bashi amsa "ko a baro za ka tafi ai ba matsala bace yaranka ne kai ko a ƙafa ka jasu dai-dai ne" bai ƙara yin magana ba yayi fuuuuuuu ya fita Ina bedroom ɗina naji sallamar maman haidar sai yanzu ma na tuna da mun haɗu shekaranjiya tace za ta zo nace kar ta zo ta bari sai yau kai wannan matar badai son gulma ba fitowa nayi muka gaisa ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon lemu na kawo mata sannan na zauna gyara zamanta tayi tana fuskantata "tun lokacin da kika ban labarinki hankalina ya kasa kwanciya inaso inji yanda rayuwar aurenku za ta kasance duba da irin soyayya da kuma halaccin da kika nunawa abban safwan" dubanta nayi sannan na ɗan ya mutsa fuska "to ai ni nama manta inda na tsaya" da sauri ta katseni "yanda rayuwar aurenku ta kasance keda abban safwan" gyara zamana nayi sannan na ci gaba da bata labarin yanda rayuwar aurena ta kasance Da farko rayuwar auren mu da lawal.............. Hhhhhhhhhhh Allah sarki lawal😄 Shin kuma kun iya gulma kamar maman haidar😂 AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI Page 15 Da farko rayuwar aurena da lawal rayuwa ce irin ta soyayya kamar yanda muka daɗe muna tsarawa ina samun kulawa da kuma tattali daga gare shi zallar soyayya na ke gani a wurin angona Matsalar mu ta fara ne daga lokacin da garar da nazo da ita daga gidanmu ta ƙare buhu ashirin mahaifina ya baiwa lawal tare da naira dubu ɗari na cefane a matsayin kayan GARAR AURE na(littafina na farko) bayan an kai kayan gidansu buhu biyu ne kawai su ka shigo gidana bansan inda sauran su ka shiga ba Tunda naga kayan abincin sun yi ƙasa na gayamishi yace min zai siyo yau koda muka wayi gari bamuda ko ƙwarar shinkafa a gidan yana ɗaki yana shiri na same shi gefen gadon na zauna ina kallonshi "Nisful yau fa kayan abincin duk sun ƙare ko abin kari babu bale kuma shinkafar da za mu dafa anjima" "ohhhhhhhhh wallahi kina da matsala my zee ko jiya kin gayamin maganar nan nace miki zan siyo da inada kuɗi zan ƙi siyowa ne? kina kallon yanda nake fita kasuwar nan haka nake dawowa wallahi ni in banda mama bazan koma wurin mutumennan ba malam mutum don yana ganin kamar kana ƙarƙashin shi sai an tashi kasuwa ya ɗauko wata banzar dubu biyu ya baka kamar almajiri" Raina naji baimin daɗi ba yanda naga ranshi ya ɓaci akan maganar da na mishi"kayi haƙuri nisful ba wai don in ɓata maka rai yasa nayi maganar ba"miƙewa nayi na isa ga wadrobe ɗita ƴar ƙaramar jaka na ɗakko a ciki kuɗin da ke ciki na fiddo za su kai dubu hamsin ko ma su fi kusa da shi naje tare da miƙa mishi " ga wannan yaya mu'azzam ne ya bani su lokacinda za a kawo ni gidannan ka siya mana koda taliya ce kafin ka samu" Idanu ya ƙuramin sannan ya girgiza kanshi "bazan karɓi kuɗinki ba my zee saboda nauyin ciyarda ke akaina ya ke ba a kanki ba na fara tunanin ko in siyar da mota ta in siya mana kayan abinci saboda bazan juri ganinki a wani hali ba banaso kiyi nadama a aure na da kika yi" Wata ƙaunarshi ce naji ta ƙara cikamin ruhi "duk abinda na mallaka naka ne nisful ka daina tunanin sayar da motarka insha Allah komai zai dai-daita a shirye nake da naci duk abinda ka kawo a gidannan kuma idan har kana ƙaunata kamar yanda kake faɗa to ka karɓi kuɗinnan" Karɓa yayi ya shiga jujjuya kuɗin"ina ƙara gode ma Allah da ya bani ke a matsayin matata nagode sosai matar rufin asiri Allah ya nuna min nima na kyauta ta miki fiye da yanda kike min" wani daɗi ne ya lulleɓeni jin kyakkyar shaidar da nake samu daga mijina rakiya na yo mishi har tsakar gidan sannan na koma falo Ina ƙoƙarin zama na ji wayata da ke chaji ta na ringing sance wayar nayi tare da duba mai kiran murmushine ya faɗaɗa a fuskata ganin number ummina na yawo akan screen ɗin da sauri na ɗaga ina karawa a kunne "Umminaaaaaaaaaaa"naja sunan sosai ina jin kamar nayi tsuntsuwa na ganni gabanta saboda yanda nayi kewarta tun aurena banzo gida ba amsawa tayi na gaisheta a tsanake "magana nakeso na yi da ke" daga yanda naji tayi maganar nasan maganace mai muhimmanci gyaran murya tayi sannan ta ci gaba da magana "idan kina tare da mijinki ki keɓe magana za muyi kuma banaso kimin ƙarya" "ba kowa tare da ni ummi" na faɗa cikin sanyayyar murya "yawwa jiya da dare abbanki ya siyo mana sarƙa da ni da ke nace bari in haɗe inda nake ajiyar sarƙoƙinmu amma abin mamaki koda naje ba sarƙarki a ciki bayan kuma nasan duk suna tare kuma nasan ba ta hannunki sannan idan ɓarawo ne bazai ɗauki sarƙa ɗaya ya bar saura ba shine nakeso ki gayamin gaskiya zuciyata tana gayamin kinsan wani abu akan lamarinnan" Dakan lugude gabana keyi ni shaf na manta ma da na ɗau wata sarƙa" kar ki kuskura kimin ƙarya" ta katseni daga abinda nake shirin yi" ni naɗauka ummi" na gayamata gaskiya ganin ƙaryar ba abinda za ta tsinana min "me kika yi da ita" ta jefomin tambayar cikin taushin murya yanda bazan tsorata ba "Lawal na baiwa yayi jari kuma yace ranta yayi da zaran ya samu zai maidomin kuɗina sai in siyi sarƙar" shiru tayi na mintota na ɗaukama ta kashe sai can tace "kin kyautawa kanki kuma nagode sosai" daga haka ta katse wayar tsorone ya shige ni don ga dukkan alamu fushi ta yi kuma nasan illar fushinta akaina kiranta na shiga yi amma ta ƙi dagawa Kuka na shiga rerawa wata nadama na shigata number lawal na shiga nema saita muryata nayi jin ya ɗaga izini na nema inje gida ya tambaye ni lafiya na ce lafiya lau kawai naji ina kewar gidane yace in tafi amma kar in kai dare don ya yo mana siyayyar kayan abinci Gani nayi gidan yamin nisa ko da na isa ko baba mai gadi da ke tsokanata bayan mun gaisa ban tsaya kulawa ba saida naje tsakiyar falon sannan nayi sallama "keee lafiyar ki" ya mubarak ya faɗa ganin yanda na shigo a hargitse kallo ɗaya na mishi na ƙarasa gaban ummi na zube guiwowina ƙasa hannuwana na ɗora akan cinyoyinta "don Allah ummi kiyi haƙuri kar kiyi fushi da ni" ba ta min magana ba sai ma ya mubarak da ta kalla "kaje kawai" magana zaiyi ta dakatar da shi "kaje nace" "Don girman Allah ummi kiyi haƙuri wallahi fushinki akaina babbar matsala ce a rayuwata nasan nayi kuskure wallahi kuma bazan ƙaraba" janye hannuwana tayi daga jikinta sannan ta miƙe tana ƙoƙarin wucewa bedroom ɗinta ƙafafunta na riƙe ina kuka ina mata magiyar ta yafemin "Yanzu har aure ya miki daɗin da za ki ɗau dukiyarki ki bawa miji? namiji? namiji kike wa wannan rawar kan? ba baki nake miki ba zainab amma ina ji maki tsoron ranar da zai nuna miki butulcin ɗa namiji in za kisan ciwon kanki ki sa ni in kuma duk abinda kika mallaka za ki miƙawa lawal ɗauka ki bashi Allah ya bar ƙauna" Na sha kuka na sha magiya kafin ta sauko hankalina bai kwanta ba saida naga ta haƙura sannan na yi shirin komawa gida ɓangaren yaya isma'il na shiga nayiwa anty nasma sallama sannan na wuce na yaya abbas ita ma na mata sallama sannan na ja motata na lula titi Ko da na koma gida ya dawo da siyayyar da yace yayi katin ɗin taliya ne sai mai da kuma ƴan kayan magi sai da na gama dubawa sannan na dube shi ina so inyi magana kuma ina tsoron yayi fushi daurewa dai nayi nace "Nisful da ka sa ni shinkafa ka siyo ma na" Wani kallo ya mini sannan yayi fuuuuu ya wuce ciki kayan na kwashe na kai kitchen sannan na wuce na same shi ɗaki waigowa yayi ya dakata daga ƙoƙarin cire rigar da yake yi" bari in gayamiki bazan ɗau wannan ɗabi'ar ba idan ke san don ki sakamin doka za ki bani kuɗinki to nagode ki riƙe abin ki" Tun daga ranar taliyar ce ta zama abincinmu kuma bantaɓa yi mishi ƙorafi ba saboda ina tsoron yayi fushi bansan ya saida motarshi ba saida aka kwana biyu ban ganta ba na tambaye shi "Nisful lafiya kwana biyu banga motarka ba? ko lalacewa ta yi" Wani kallo ya min "saboda an bani motar daga gidanku shiyasa kike sakamin ido a kanta? to na siyar ne? ko akwai magana" kallon mamaki na ke mishi "meyasa za ka siyar da motarka nisful? wallahi banji daɗi ba" "Dole in siyarda mota in nemi kuɗi saboda na gaji da wulaƙancin mutumennan bazan ƙara komawa wurinshi ba" inaso inyi magana to amma ina tsoron abinda maganar za ta haifar Gyara zamana nayi sannan na sako mishi maganar da yaya abbas ya kirani ya min kan karatuna yana gayamin ƙyaleni ne abba yayi ya ga iya gudun ruwana nima kuma sai na ji ina sha'awar karatun yanzu "Nisful maganar KARATUNA ina so in koma makaranta" baya na ja ganin yanda ya wani zabura "makaranta kuma? ni sakarai ne da zan sakeki wasu mazan na kallonki? A'a wallahi ba da ni ba karatunnan dai ana yin shi ne don tara wani abun duniya to na miki alƙawarin nema har iyakar ƙarfina don na huce miki takaici " Haka ya ci gaba da tsara ni har na yadda naga ba amfanin wani KARATU da zanyi ya sa na kira ummi nace mata yace zan koma amma sai na haihu kamar yanda ya tsaramin su kuma jin maganar ciki sai suka jingine maganar karatu ashe ko mun sara bisa gaɓa domin lokacin ina ɗauke da cikin safwan da ko ni bansa ni ba Uhmmmmm AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI Page 16 Ba mu amfana da komai ba cikin kuɗin motar da ya siyar, don ɗaukar kuɗin yayi, ya baiwa abokinshi wai ya jujjuya mishi su raba riba.Lokacin da ya gayamin haka, na gayamishi sam wannan ba dubara bace, amma ya nuna min ai mai amana ne. Sai ga shi ya dawo ya na gayamin, kuɗi sun lalace na nuna mishi baiwa wani kuɗi da sunan ya ma sana'a ba mafita bace shi kuma ga yanda na lura sana'ar ce bazai iya ba ina mamakin yanda namiji ke ƙyamar sana'a to idan baiyi sana'a ba me zai yi? In taƙaice miki sai da duk abinda na mallaka ya ƙare wurin cefanenmu tun ina yi har nazo na ka sa domin ko banida komai wallahi akwai ranar da muka kwanta haka nan ba mu ci komai ba saboda ni banida komai haka ma shi ga ciki na rame duk na fita hayyaci na gida ma na daina zuwa don duk abinda zai sa aga laifin lawal banason shi Bikin anty halima da ya matso ya sa dole naje gida kusan firgicewa nayi yanda ummi da su yaya suka sakani gaba da tambayar meke damuna? bansan me zan ce musu ba kaitsaye yaya abbas ya turani mota sai asibiti gwaje-gwaje su kamin suka ce in rinƙa cin abinci mai gina jiki faɗa ya dingayi tun a mota yana gayamin ga abinda ake gudarmin Kayan abinci ya siyamin da kuma kayan fruit ma su yawa shi ya maidani gida yana tambayata me ya hanani zuwa da motata? nace mishi kawai bazan uya tuƙi ba saida ya kawoni nazo futa ya ɗakko kuɗi masu yawa ya bani yace in sa mai wataƙila ya fahimci rashin mai ne yasa ban fita da ita ba Lokacinda lawal ya ga kayan faɗa ya dingamin wai na je gidanmu nace ya barni da yunwa ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba nidai bance mishi komai ba don abin ya fara kaini maƙura abin haushi kuma kayan da yake faɗa a kansu da shi aka cinye Haka akayi bikin anty halima na shiga bikin duk a muzance yanda na lalace kamar ba ni ba cikin garinnan aka kai anty halima saboda mijinta ɗan sokoto ne kuma itama anan za ta ci gaba da aiki saboda har yaya isma'il ya samo mata aiki a inda yake aiki Tun da na doshi watan haihuwata na fara mishi maganar ya kamata a rage siyayyar wasu abubuwan to nima ina faɗane kawai don ko cikina ban cikaba bale kuma akai ga ajiyar wasu kaya A ranar da zan haifi safwan shi ya kaini asibiti da kayanshi aka rubuto kayan da ake buƙatar a siya abin baƙin ciki haka na kasance cikin wani hali har zuwa lokacinda ya kira gidanmu ya gayamusu ina asibiti Faɗa yaya Abbas ya dingayi ganin asibitin da ya kawo ni ganin halinda na ke ciki yasa ya biya komi cikin ikon Allah sai ga shi na haifo santalelen ɗana Tunda na haihu ba wani abu da ya fita daga aljihun lawal komai ƴan uwana ke yi ba abinda aka nema daga gareshi mahaifiyarshi sun zo da ƴan uwanshi Sai daren suna aka kawo kayan barka kala huɗu ya min dukansu ƙanana sai jaririn kala goma ban wani damuba saboda duk yayyena har yaya mubarak ba wanda bai min sha tara ta arziki ba cikinsu na fantama na kuma fita kunya Zamana gida sai gani na dawo hayyacina daga abbana har ummi wata kula suke ba ni sai gani na zama ƴar lukuta na yi wani kyau na musamman har banso inji ana maganar koma wa ta Haka na koma gidan lawal muka ci gaba da gurgura rayuwar a haka ba wata sana'ar arziki da ya ke yi taimakon da nake samu daga yayyena da iyayena da shi muke amfani Shekarar safwan uku na ƙara haihuwa na haifi Aysha (baiwar Allah) haihuwar aysha ko tsinke bai bamu ba daga ni har jaririyar daga ƙarshe ma samu na yayi da zancen zai ɗaga suna don bayada abin yankawa yarinya Nayi kuka a ranar marar adadi wane irin wulaƙanci ne ka haihu ko abinda za'a yankawa ƴarka ya gagara to bale kuma wata sutura da zaka saka ga shi banida komai duk ɗan abinda na mallaka ya ƙare ga lawal da kuma gidanshi Daga ƙarshe mahaifiyata na kira na gayamata halinda ake ciki daga gidanmu abin sunan Aysha ya fito da kayana da na jaririya ba abinda muka yi amfani da shi da ya fito daga lawal ko ƴan uwanshi Aysha na da shekara ɗaya da wata uku Abbana ya rasu ciwon ciki na kwana guda ne ya zamo ajalinshi ina riƙe da hannunshi lokacinda yake kan gadon asibiti har ya rasu yana jaddada mana ya yafe muna sannan yana roƙon ummi da su yaya su kula da ni kar su barni nayi kukan rashin shi Na shiga tashin hankali sosai saboda na shaƙu da abbana sosai fiye da tunaninki na daɗe ban dawo dai-dai ba saboda mutuwar ta taɓa ni Lokacinda aka raba mana gado ummi hana tayi a damƙaminsu tace a ci gaba da juyamin su gidan da aka bani kuma a ka zuba ƴan haya Haka na ci gaba da haƙuri da lawal yau ya bani gobe yace babu idan nayi magana kuma na yi laifi baƙin ciki ya min yawa na rasa ina zan saka kaina domin in ta ni ne abin mai sauƙine amma yaro sam baisan babu ba Magana na mishi kan makarantar safwan tunda ya isa aiko ya tasomin da faɗa" Ana maganar abinci ina naga kuɗin kaishi makaranta in baso kike in haɗiye zuciya in mutu kan baƙin ciki ba da me zanji? na ga ai kema kinada kuɗinnan kije gida ki gaya mu su a baki wani abu ki sa ɗanki makaranta nasan dai ba za su hanaki ba ai wallahi ni kin bani mamaki in wata ce wallahi gadon nan da aka raba muku za ki samu abinda kika bani inja jari tunda kinga halinda mu ke ciki" Da ido na bishi ina tambayar kaina "shin butulcin da ake faɗar maza na yi ne lawal ya fara nuna min" Wani zuwa da nayi gida yaya Mu'azzam ya dawo mu ka je gaida shi ya Isma'il ke tambayata an saka safwan makaranta nace mishi A'a ya ɗauke shi suka fita Kwana biyu sai ga uniform da komai ya kawo min yace an biya mishi komai ya fara zuwa ni ke kaishi na ɗakko shi saboda mahaifinshi yace baya da lokaci ba a wani daɗe sosai ba aka saka Aysha itama a sashen rainon yara Ban taɓa zama da kowa na gayamishi matsala ta ba domin har lokacin banson inji ana kushe lawal a gabana ashe abin yana nan yana taɓani daga tsaye na fara rama ga cikin Amna wanda Allah ne kaɗai ya ƙaddaro za ta shigo duniya saboda kai tsaye ya nuna min shifa baya buƙatar haihuwar nan dame zaiji (kamar wani abin arziki ya ke mana) Tun cikin bai isa haihuwa ba na fara kumburi duk na fita hayyaci na ga baƙin cikin da lawal ke ƙumsamin baya ganin tausayina ko kaɗan abincinma yanzu ya daina bani idan ina buƙatar abu saidai na kira ummi ita ma ganin kamar ina zubarwa lawal ƙima a wurinta na daina kiranta Ba wata magana mai daɗi a tsakaninmu ba hali yarana su je wurinshi zai kora su kamar ba ƴaƴanshi ba babbar asibiti ta kuɗi inda ya isma'il ke jagoranta nan ya turani ya haɗani da anty halima ganin halinda nake ciki kowane lokaci zan iya haihuwa ga wannan kumburin da na yi duk halittata ta canja Hannu suka nema asa cikin gaggawa a min cs a cire abinda ke cikina sai da aka gama komai aka ce kuma ba za'a taɓani ba saboda jini na ya hau sosai Duk wanda ke ƙaunata ya tausayamin a wannan lokacin saboda ina a wani hali ne na rayuwa da mutuwa kwanana biyu asibiti sannan aka min cs aka cire shalelena Amna Tunda aka sallame mu na wuce gidanmu acan nayi jegon amna ummi ke kula da ni da kuma anty halima wannan karon ma bayan abin suna ba abinda yayi shi ko kunya ba ya ji Daga ummi har su yaya tambayata su ka shiga yi meke damuna? me na saka ma raina da har ya janyomin hawan jini? saboda hankalinsu ya tashi sosai da jin wannan labarin ɓoye musu na yi nace cikinne kawai ya zo da hakan kula da ni suka ci gaba da yi tare da siyomin tsadaddun magunguna Da na tashi komawa suka haɗani da maƙuddan kuɗade suka ce inyi sana'a anty halima ta banu shawarar yin sana'ar laces da atamfofi da jakunkuna cikin iyawar ubangiji abin ya karɓeni sosai itama tana min talla a gurin abokanan aikinta nima gwargwado ina samu da wayar hannuna nake amfani na ke isar da sana'ata ga sauran mutane Hakan baisa na tsira ba sai ga lawal ya ɗanƙaramin saki kan abinda ko alama baya da haƙƙi ko ikon yi....................... Mu tara gobe AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI Page 17 Lamarin ya faru ne ranar wata juma'a bayan saukowa masallaci dama tun kafin ya tafi muka fara rigima da shi kan sai na daina sana'ar da nake yi ta waya don baisan da wa nake mu'amala ba abin ya ƙonamin rai sosai amma sai ban kulashi ba Sai bayan juma'ar ya dawo falo ya zauna ya na girgiza ƙafarshia alamun rigima ya ke nema naje na kawo mishi abinci zan fara zuba mishi ya dakatar da ni "wai mahaukaci kika maida ni ne da tun ɗazu ina miki magana kin ƙyale ni? shikenan ni kin maida ni namijin hotiho banida wani amfani kina fira da duk wanda kika ga dama da sunan sana'a to wallahi na gaji" Ajiyar zuciya na sauke ina kallonshi tare da zama ƙasan carpet ɗin falon "bansan me kake so ince ba nisf................." "Bangane baki san abinda za kice ba kenan haukar banza na ke yi kinga malama aje wani nisful gefe na gaji da ana kirana wani nisful ana yaudarata yawwa magana ɗaya ce zan gayamiki wannan banzar sana'a dole a barta don bazan yarda a wulaƙantamin aure ba" Nima cikin ɓacin ran da ya fara tasomin nake magana "wai da kake maganar darajar aurenka shin kamani kayi da cin amanarka kome? kuma meye laifin sana'ata? naga dai kafin in amfana da sana'ar nan sau uku kaida ƴaƴanka za ku amfana sau goma to miye kuma yanzu na kawo wani sabon al'amari? meyasa kai baka ƙaunar zaman lafiya? duk yanda na kai zuciyata nesa kan lamurranka kai bazaka fahimta ba to gaskiya ni ba wata sana'a da zan bari don da ita nake ci da kaina in cida ƴaƴana kai harda uban ƴaƴanma" na ƙarasa ina murguɗa ɗan bakina Miƙewa yayi yana nuna ni a harzuƙe "ke ki iya bakinki wallahi banida daɗi nan da kika ganni nima na iya rashin mutuncinnan" nima miƙewa nayi "to wai miye na duk wannan abun? saboda sana'a ne kodai akwai wani abu" na tambaye shi saboda abin ya fara ɓatamin rai nima Hannuwanshi ya shiga watsawa kamar sabon kamu" sana'arki ta banza ke kika ɗauketa sana'a ni wallahi duk abinda zan siyo da kuɗina in aje shi ina jiran wani yazo ya siya ban ɗauke shi sana'a ba" "Aiko shiyasa ka kasa kasuwancin saboda yanda ka ɗauke sana'ar da ban yanda ta ke daban" cikina yayo kamar zai dakeni yana nuna ni hannunshi har rawa ya ke dama lawal ba dai zuciya ba (ta banza tunda bazai iya ɗebewa kanshi takaici ba) "kin fara wuce iya karki kuma zan nuna miki har yau ina sama da ke" ya gyara tsayinshi sannan ya ci gaba da magana "dole cikin biyunnan ki zaɓi ɗaya SANA'ARKI ko kuma AURENKI" A razane nake kallonshi saboda ni ban ɗauka maganar ta kai can ba wannan lokacin ji nayi ba ni ke sarrafa zuciyata ba kamar sarrafata ake yi kai tsaye nace "Na zaɓi sana'ata" Idanunshi ya lumshe sannan ya juya baya " kije na SAKE KI saki ɗaya" Dummmmm kaina ya buga kamar an doka guduma jina da ganina suka ɗauke na wuccin gadi wani kalar tashin hankalinda ban taɓa tunani ba ya dira a kwanyata da ƙyar na iya ɗaga hannuna na nuna kaina "ka sake ni? ni ka saka lawal" Fuuuuuuu ya wuce ɗaki ba tare da yace komai ba kasa riƙeni ƙafafuna su ka yi na zube nan tsakar falon ina kokawa da numfashina ni nasan akwai matsala lalube na shiga yi saboda ɗif na daina gani cikin iyawar ubangiji naji wayar da nake nema farcena na ɗora abinda ya baiwa wayar damar fita security Sashen da nasan nan nake kira na shiga number da ke sama na danna batare da nasan ko ta waye ba "hello zee" naji muryar anty halima "kizo zan mutu kizo ki tafi da ni" na fitarda maganar a wahale Daga nan banƙara sanin abinda ya faru ba sai farkawa nayi na ganni a asibiti kwance ga ummina da kuma ya mubarak sai anty halima da ke kaina "Zainab" anty halima ta kirani ɗaga idanuwana da suka min nauyi nayi na dubeta a hankali kuma na maida su na rufe Hannun ummi da ke cikin nawa na ƙara damƙewa jin komai yana dawomin tar a cikin kwanyata kamar lokacinne abin ya faru kuka na fashe da shi kukane nakeyi mai ƙunshe da baƙin ciki da kuma dana sanin auren lawal Idanuwana da suka rine na ƙara buɗewa ina kallon ummi kamar wata taɓaɓɓa na fara jero zance "ya sakeni wai ummi sakina yayi anty halima ni lawal ya saka ban mishi komai ba ya mubarak ka tambayeshi kaji ban mishi komai ba to ko baisan abinda yace min ba?" na maidawa kaina tambaya Hawaye ummi da anty halima keyi "kiyi haƙuri zainab ki daure ki kira sunan Allah innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta shiga ambatawa A hankali nima na karɓa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ummi shikenan aurena ya mutu? na koma bazawara ko ummi? yarana ummi ina yarana" hawayenta ta share sannan ta dubeni" ki nutsu zainab kar ki bari wannan ya taɓa imaninki ki ci gaba da kiran sunan Allah" Inaaaaaaa mutuwar aure ba abu bane mai wuyar mantawa tabone da bazai taɓa gogewa ba a zuciyar ƴa mace sai da ya abbas yazo ya lallasheni ganin ban daina ba ya koma asalin kalar shi sai gani nayi muƙus Kwana na biyu asibiti na koma gida anty halima na tambaya "Anty wai ina su safwan tunda muka dawo nake zuba ido in gansu ban gansu ba na ɗauka suna ɓangaren su yaya sai gashi su nihal sun zo dubani kuma basu a cikinsu" Hannuna ta riƙe "ki kwantarda hankalinki suna wurin kakarsu tazo dubaki lokacin an miki allurar bacci amma suna wurinta don yaya abbas yace ba zasu zauna gidannan ba" Hawayene suka shiga min ɓulɓula "shikenan an rabani da yarana? shikenan suma za'a lalata musu future kamar yanda sauran yaran da iyayensu ba sa tare ke tsintar kansu? da ni kaɗai suka saba yini ɗaya idan mukayi bama tare kewata suke ya zasu yi bacci kenan? lawal ka cuceni" na ƙara rushewa da kuka A harzuƙe ta miƙe "shikenan zainab an ƙyaleki je ki kashe kanki akan lawal nace kije tunda mu bamuda wani girma da zamu ce ki bari ki bari an gayamiki halinda lafiyarki ta ke ciki amma kinƙi kwantar da hankalinki bari in gayamiki wallahi ko yau kika faɗi kika mutu lawal bayada asara mu da ƴaƴanki kawai zamu damu ki daure ki shanye kodon yaranki da kike mutuwar ƙauna don Allah ki cire damuwa ko don MU zainab" ta ƙarasa tana haɗe hannayenta alamar roƙo hawayen idonta ta share tare da barin ɗakin Washe gari sai ga gwaggo dije ta iso tare da yaya bashir itama ta jajanta tare da faɗan bar musu yara tace ya kamata a kawomin su ko saboda lafiya ta naji daɗi sosai ko ba komai ita ta fahimci halinda nake ciki Yaya bashir kuwa cewa yayi sai an sa ƙara ni dariyama ya bani "to acewa alƙali don ya sake ni ake ƙararshi hmmmm Allah ya kyauta kawai?" Da marece sai ga mama mahaifiyar lawal da kuma yaran gaba ɗaya sunzo dubani faɗar farincikin da muka shiga ni da su ɓata bakine rungume juna mukayi ni kuka su kuka saida ummi ta tsawatar haƙuri mama ta dinga bayarwa kamar ita tayi sakin "don Allah ayi haƙuri hajiya wallahi banji daɗin al'amarinnan ba sam lawal bai kyautawa rayuwarshi ba don Allah ayi haƙuri" Da zata tafi gwaggo dije ta mata maganar a barmin amna tunda ita ce ƙarama bata musa ba kuwa ta barmin ita tare gayamin gobe idan su mariya za su zo dubani zata basu kayanta ranar rungume da amna nayi bacci ina jin kamar za'a ƙwace min ita A haka tafiya tayi tafiya na shanye wata ɗaya da satittika a cikin kwanakin iddata za ki sha mamaki idan nace miki satina biyu a gida lawal ya fara zaryar inyi haƙuri in koma Ko alamabanji zan iya komawa gidanshi ba na fison in koma KARATUNA kuma gaba ɗaya gidanmu ba wanda ya bada goyon bayan na koma Ganin kwanci tashi ina neman in laƙume iddata sai hankalinshi ya tashi ya jingina da mahaifiyarshi bansan yanda ya ciyo kanta ba wata ƙila ta gaji da rainon yara sai gata a gidanmu tana roƙon su yaya su yi haƙuri gayamata su ka yi taje za su neme ni su ji ta bakina Lokacinda suka sameni kaitsaye na ce musu nidai bazan iya komawa ba nemanta suka yi suka gayamata sai gata ta dawo gidanmu har ƙasa tana roƙon nayi haƙuri na koma gigicewa na yi ina roƙon ta tashi naji zan koma Kiran lawal yaya isma'il yayi nima aka kirani tun bayan rabuwarmu da shi banƙara saka shi a ido ba sai yau sai satar kallona ya ke nima kallonshi na ke ta ƙasan ido ya rame sosai yayi baƙi ( to ba dole ba an bar samun na banza) maganar yaya isma'il ce ta dawo da ni hayyacina "Kamar yanda muka gayamaka tun a waje mun amince zainab za ta koma ɗakinta amma a bisa wasu SHARUƊƊA" kallon shi yayi yaya ya ɗaga mishi kai "yes sharuɗɗa na farko zainab za ta ci gaba da karatunta na biyu za ta ci gaba da sana'arta na uku ka kula da ita ina fatan ka gane" Kanshi ya ɗaga kamar wani munafuki gyara zama yaya abbas yayi " sannan ina mai gargaɗinka da ka kula da abinda zai taɓa lafiyarta wallahi idan har wani abu ya sameta zan iya ɗaureka har iyakar ranka" Da wannan na koma gidan lawal muka ci gaba da gurgura rayuwa duk da bai canja ba amma yayi sanyi sosai ga wasu abubuwan kodon yana tsoron wani abu ya same ni ace shine oho ko kuma halayyar da na dawo mishi da ita ce ke tsorata shi domin yanzu ko kaɗan bana raga mishi don naga baisan wannan ba Bayan Amna na ƙara haihuwa abun baizo da raiba daga nan kuma nace Allah ya raya abinda muka samu Har yau da kike gani bai canja ba nima kuma ban sauyaba abinci duk wata yayyena ke sauke min sutura banida matsalarta ina ɗinkawa kaina da yarana hakama ummi tana musu mama ma tana musu abbansu ne dai sai a hankali Alaƙa ta da ƴan uwanshi kuwa saidai Allah ya kyauta domin bama ga maciji su a nasu jahilcin kamar ni na sakashi talauci ni kuma nayi kuɗi ban damu da su ba domin ni yanzu ko lawal ɗin baya gabana bale kuma su Kinji labarina da kuma labarin ƙalubalen nawa auren don kima aje tunanin ke kaɗai ke cikin matsala Ina godiya sosai da kulawarku a gare ni🙏 comments ɗinku ya na saka ni nishaɗi ku ci gaba da watsomin ruwan conment ni kuma in ci gaba da raƙashe ku da typing Na gode ƙauna tari-tari🥰 HMMMMMMMM Saura na ji wani ya zagi lawal😹 AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI Page 18 Rakiya na yiwa maman haidar ina ƙara jaddada mata ta yi haƙuri hamdala nayi bayan na dawo daga rakiyarta "wai na rabu da sha labari" na faɗa ina zama kan kujerar falon ina jin wani takaicin kaina irin yanda na matowa lawal a baya kamar wata sakarya "Allah wadan na ka ya lalace" na gayawa kaina Ina nan kwance ya shigo kamar an jefoshi ko sallama bai yi ba nima kuma banma nuna nasan da shigowarshi ba fitowa ya ƙarayi har ya tafi ya dawo tsaye yayi akaina "mama za ta zo wai taji abinda nake saidawa nasan tsaf za ki ce baki sani ba" Ɗago kaina nayi na ɗage girata ɗaya" to na sani ne?" kallona ya ci gaba da yi kamar mai son gano wani abu kanshi ya jinjina alamar zuciyar tana kusa" shikenan idan ta zo kice ca-ca na ke" "to ai yanzu ka sanarda ni" na faɗa ina ɗauke ƙafafuwana na ɗauke na mayar kan kujera na kwanta sannan na bashi amsa yana gab da barin ɗakin dariya nayi a raina "ga tsoro ga ban tsoro"shine taken lawal Ashe yasan abinda ya ke wa ƙarfe 12 sai ga mama gidan takan jima ba ta zo ba saida ƙwaƙƙwaran dalili lemu na kawo mata da sauran abincin da na girkawa ƴan makaranta bayan na gaidata "kiramin mijinki kice na iso na gayamishi ganinan zuwa yace idan na zo a kirashi" "To mama" na shiga laluben number lawal da anty halima ta canjawa saving daga Nisful ta mayaddashi Abban safwan bugu biyu ya ɗaga "ga mama na jiran ka" daga haka na kashe ɗan katina Ba jimawa sai gashi (wata ƙila kasuwar ta su ba nisa😂) gaidata yayi ya na tambayarta gida tace komai lafiya zama yayi a kujerar da ke fuskanta ta "Na zaɓi na zo nanne muyi magana saboda tunda na baka kuɗinnan ban ƙara ganinka ba bayan kuma kace za ka zo da zainab kumin bayanin kalar sana'ar" Hankalinta ta mayar kaina "ke zainabu gayamin wace sana'a ce ku ke yi" kallon lawal nayi da ya zubamin ido ina ganin yanda ya ke ƙiftamin ido na yi banza da shi "bansan sana'ar da ya ke yi ba mama" na bata amsa kai tsaye "ban gane ba kai lawwali kace min tare ku ke sana'ar"ta faɗa tana tsare shi da ido nima kallonshi na ke yi sai raba ido ya ke murtuƙe fuska ya yi kamar wani zaki "da kai fa nake magana" ta daka mishi tsawa ganin ya na maisheta sakarya "Ni fa mama bazan iya wata sana'ar takalmi ba na bincika ba wata riba ake samu ba" "to ba ni kuɗina" ta faɗa tana miƙa mishi hannu "kai wane irin sakaran namiji ne da baisan kanshi ba? kamarka da iyali da komai ka naɗe hannu ka dawo gida ka kwanta don ma Allah ya ba ka mata ta gari mai rufin asiri ta na iyakar ƙoƙarinta akan ka duk wani nauyin yaranka ta ɗauke amma saboda zamanka sakarai ba wani alamun damuwa a tare da kai yanzu saboda kai na siyarda ɗan filina da na ke kallo a matsayin ƙadarar da na mallaka na baka kuɗin amma kake gayamin ba za ka iya sana'ar takalmi ba to ka bani kuɗina don ni ba sakarya bace irinka in rabawa ƴan uwanka su da za su iya sana'ar na baka nan da gobe ka kawomin kuɗina"miƙewa ta yi nima na miƙe ina bata haƙuri "ke za'a ba haƙuri zainabu ke da kike tare da sakaran miji wanda baisan inda ke mishi ciwo ba"rakata na yi sannan na dawo falon yana nan zaune kamar zane wayata na ɗauka ina ƙoƙarin barin falon "kinyi farinciki kin haɗani da mahaifiyata" waigowa nayi na kalleshi "saboda ni na cinye mata kuɗi" na mayar mishi da mai zafi don na kunna shi aiko ya kunnu don tashi yayi yana nuna ni "karki gayamin maganar banza naji ni na cinye kuɗi ai dai na mahaifiyata na ci ba na wani ba naga ai ke kinada kuɗin amma ba su da amfani tunda an makkale an hanaki ana yanda ake so da dukiyarki" "Dukiyata tana hannun waɗanda ya dace kuma waɗanda ba su damu da abin duniya ba da ma wanda ake tunanin zai cinye ake bibiya wanda aka san dama ya saba da su sai dai fatan alkhairi da kake faɗar an mallakemin dukiya kasan dai duk cikinsu ba wanda cefanen gidanshi ya fi ƙarfinshi" daga haka na cikawa sket ɗina iska ganin yanda ya harzuƙa kar ya cafkoni ya fara kirɓa Ina shiga na maida ƙofa na rufe da key ina sauke ajiyar zuciya don dama duk maganar da nake yi a tsorace na ke yinta ina maganar ina kallon motsin hannunshi ina tsoron saukar wannan gudumar a lallausan kumatu na Sai da naji hayaniyar yara sannan na fito ba ya falon da alama ya daɗe da fita Haka muka ci gaba da zaman bansan yanda ya ƙarasa da mama ba don ban ƙara kula shi ba ganin shima ya ɗau fushi da ni kamar ni na kama muka cinye kuɗin Karatuna na ci gaba da yi da kuma kula da tarbiyyar yarana ta ɓangaren kasuwancina Alhamdulillah ina samun ci gaba ina harkokina cikin iyawar uban giji Jarabawar da muka fara ita ta ƙara ɗaukemin hankali daga shiga harkar lawal sosai na duƙufa ina fatan cika burina da lawal ya ɗau aniyar tarwatsawa har muka kammala cikin nasara aka tafi hutu Yau tunda na wayi gari nake fama da faɗuwar gaba abin ba daɗi sunan Allah na shiga kira ina fatan ya bani ikon ɗaukar abinda ke tunkaro ni aiki nake yi amma sam ba ƙarfi a jikina Ina ƙoƙarin sauke abinci naji kukan amna abincin na sauke sannan na fita ina tambayar abinda ya faru "mommy Aysha ta zaga shine na buge mata baki" "Zagi? ina kika iya zagi? ai gwanda da ka doke mata baki" ƙara buɗe baki tayi tana min ihun kuka "za kimin shiru ko sai na ƙara miki" na daka mata tsawa wanda yayi daidai da shigowar lawal tashi ta yi da gudu taje ta riƙeshi tana shessheka "me ta miki da za ki doketa"ya tambayeni yana tsareni da ido kamar wanda ke son turkeni "zagin Aysha tayi kuma ba ma ni na daketa ba safwan ne ni yanzu zan mata nawa" "Saboda jakar ku ce?" ya tambaya cikin masifa kallon mamaki na bishi da shi "zagi fa aka ce maka ta yi ba wani abin kirki ba" "To ke bakya zaginne? ko shi da ya doketa baya zagin" wurin safwan ya isa kamar wani sa'anshi ya dinga dukanshi ido na zuba mishi tare da tunanin "anya saboda dukan da safwan ya yiwa Amna ne lawal ke mishi wannan dukan sam abin bai kai haka ba amma kuma ɗanshi ne banida halin dakatar da shi" juyawa nayi na koma ga girkina ina danne abinda ke tasomin Ɗaki na same shi bayan na bawa safwan magani saboda zazzaɓin da ya taso mishi .wataƙila harda kukan da yayi abinci na zuba musu sannan na wuce ɗaki yana rungume da ita sai wani narkewa ta ke idona na zuba mata ina nuna mata ƙofa "ki wuce ga abincinku can kafin ranki ya ɓaci" sauka tayi daga jikinshi ta bar ɗakin kallona na mayar wurinshi "ba haka ake hukunci tsakanin yara ba abban safwan ko ba komai shi babba ne a gurinta kuma hukunci ya mata kan abinda ta yi bai kamata ka dokeshi kan wannan ba dukansu ƴaƴanka ne" miƙewa yayi kamar yanda ya saba shi kullum ba za'ayi magana da shi a zaune ba "to sannu ƴar iya ai dama komai ban iya ba ke kika iya to bazanyi yanda kike so ba dama ba tun yau ba na fahimci duk cikinsu ba wanda kike so kamar shi ba ya laifi a gurinki to ni ba irinki ba ce son ƴaƴa bai rufemin idon da zan iya komai a kansu ba" galala na saki baki ina kallonshi wai kodai ya fara kurɓe-kurɓe? to nikam yaushe abin ya kai na ɗaga murya "Allah ya baka haƙuri"na faɗa tare da juyawa ɗakin na bar mishi na koma falo na kwanta ina kwance sai ga yaran sun fito wurina suka yo dukansu hannu na miƙawa safwan ya tako wurina gefena na zaunadda shi tare da kwantarda kanshi akan cinyata jin har lokacin jikinshi akwai zazzaɓi kallon amna da ke matsowa wurina tana kallona na yi harara na watsa mata "kar ki kuskura ki matso wurina tunda bakya jin magana" Kuka ta sa tana riƙe kunnenta kamar yanda suke yi idan sun min laifi "kiyi haƙuri mommy bazan ƙara zagi ba" tausayi ta bani na janyo hannunta "to ki ba yaya haƙuri kinga akanki abba ya dakeshi" matsawa tayi tana leƙen fuskar safwan "yaya kayi haƙuri bazan ƙara zagi ba" Faɗa na ƙara yi mata sannan su ka zauna muna hirarmu kamar wasu sa'anni na muna nan zaune ya fito ya murtuƙe fuska kamar wanda bai taɓa dariya ba kuɗi ya fitar daga aljihunshi 200 "kai karɓi amsomin sugar wurin idi" ya faɗa yana kallon safwan Dubanshi nayi "ka baiwa ko Aysha ta karɓoma zazzaɓine sosai a jikinshi wallahi" zabura yayi "zazzaɓinne zai hana mishi karɓo min sugar a waje? kai zaka tashi ko sai na ɓallaka munafuki kawai wallahi daidai na ke dakai yanzu" shiru na yi har safwan ya karɓi kuɗin ya fita miƙewa na yi na koma ɗaki ina ƙoƙarin shiga toilet maganarshi ta tsunduma kunne na "kar ki ƙara sakamin baki idan ina magana da yarana tarbiyya nake basu don bazan sake su haka kawai yanda ake so ba" HMMMMMMMM✍️✍️✍️ *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 19* Gajeriyar dariya na yi sannan a fili na ce"Su tarbiyya manya" na doshi toilet ɗina da shigowar shi ta dakatar da ni "Me kike nufi da su tarbiyya manya? ba nida tarbiyyar kike nufi ko me" "Wai don girman Allah Abban Safwan me ya sa kake son mai da masassara ciwo ne? na lura kwanan nan magana kaɗan ka ke jira in yi ka hayaƙo min, wai me ke faruwa don Allah" na tambaye shi ina so ya faɗa mini laifin da na mishi da ya ke jin haushi na.Wannan zaman ya ishe ni ta ya za a ce ke da mijinki amma ba wata magana mai daɗi da za ta shiga tsakanin ku? Shikenan mu ba mu da aiki sai gasawa juna magana kamar ba Auren soyayya mu ka yi ba? Magantuwa na ƙara yi ganin ya zuba min ido ya na kallona"Ka faɗa mi ni laifin da na maka sai in baka haƙuri,wannan abin ya ishe ni,da me kake so inji,da KARATUNA,ko da yarana,ko kuma da rigimarka? "Au wato ma rigima na ke yi ko?tunda ga ɗan ki ko? To bari ki ji,yadda ki ke ɗauka ta ba haka na ke ba,ni ba sakaran namiji ba ne da mace za ta riƙa juyawa yadda ranta ke so ba.Ki bar ganin kina da ƴan canji a hannunki hakan bazai canja matsayina na miji a gare ki ba,waƴannan yaran kuma ba za ki canja mu su wani uban ba ni ɗinne dai idan kuma za ki canja mu su to bismillah" Yadda ya ke fitar da maganar kaɗai ya isa ka fahimci haushina da ya ke ji,wanda ni har ga Allah ban san laifin da na mishi ba,wallahi ban sani ba ganin tsayuwar ta wa ba ta da wani amfani ya sa na shige toilet ɗina ina cewa "Allah ya kyauta" Abin mamaki har na kammala abinda zan yi na fito yana ɗakin kuma bakinshi bai huta da masifar da ya ƙirƙirowa kan shi ba. Ƙofa na dosa da niyar bar mishi ɗakin na ji an janyo bayan rigata da ƙarfi waigowar da zan yi na ga ya ɗaga gandamemin hannunshi alamar jikina zai yo na yi saurin kaucewa. A fusace nima na fara magana "Kar ka kuskura,wallahi kar ka kuskura hannun ka ya sauka jikina da sunan duka,wancan ma na baya na raga maka ne saboda igiyar aurenka da ke kaina,amma wallahi tallahi yanzu duk ka kuskura ka taɓa lafiya wallahi za ka yi nadama marar iya ka" Kallona ya ke sandare da hannun da ya ɗaga da niyyar shararamin mari jikinshi ne ya fara rawa idanunshi su ka rikiɗe "Ni kike faɗawa wannan maganar? Nufin ki idan na mare ki ramawa za ki yi? Ya na maganar ne bakinshi da kuma harshenshi na harɗewa alamar ya kai maƙura ga ɓacin rai.Nima kuma haka,don har ga Allah tsayin da na gyara na gyarane da shirin da ya mare ni zan rama don ni ba jakar shi ba ce. Zuwa da komowa ya fara yi a ɗakin,nima ina tsaye ina jiran duk abinda zai faru ya faru don ya na dukana wallahi ramawa zan yi.Dakatawa yayi tare da kallona "Na samo mafita,wannan ne kaɗai hanyar da za ki gane har yau ina gaba da ke...."shiru ya yi na ƴan sakanni sannan ya ci gaba da magana "Kije *NA SAKE KI SAKI BIYU*, ba sauran Aure tsakani na da ke,na katse igiyoyin da kike tunanin akwai sauran mutunci a tsakanin mu.Kuma kar ki kuskura ki ɗaukar min yara saboda ba da su kika zo ba,ki bar su gidan ubansu don ban faɗa miki na kasa ba" Kamar wadda ta hau lilo haka na ga ɗakin na juyawa da ni,kunnuwana kuma kamar an jona lasifika a ciki haka na ke jin shigar kowace kalma da ke fitowa daga bakin shi daƙyar na samu na fara kiran "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"na shiga maimaitawa jin gani na neman ɗaukewa. Zagaye ni yayi ya bar ɗakin,bakin ƙofar na kai zaune daɓass tare da dafe capet ɗin da ke malale a ɗakin nawa na sauke kaina ƙasa.Na rasa me zan yi?Shin kuka zan yi ko ihu? Me yasa ya min haka? Tabbas ya na da dalili,ko ya na tunanin ba zan iya rayuwa ba sai da shi? Ya sha faɗa min hakan "Zee irin wannan soyayyar da ki ke min wallahi da wahala ki iya rayuwa babu ni" To kenan haka ne? Me yasa kullum na ke bari Lawal ya na galaba a kaina? Duk abin da na sa mu ba ya wuce lawal, a kan shi na guji zaɓin iyayena.Tabbas sakamako na ke gani akan bijirewa shawarar iyayena.Na san da ace abin da na suke so na bi, da ban haɗu da wannan ƙalubalen ba.Idan kuma dama can an rubuto hakan zai faru da ni to Allah zai kawo min sauƙi ko don biyayyar da na yiwa iyayena. Amma ko yanzu ban makara ba,zan nuna wa lawala a da ne na mishi wannan mahaukacin son,amma a yanzu tsaf zan yi rayuwa ta ba tare da shi ba. Wani ƙwarin guiwa ne na ji ya na shiga ta miƙewa na yi na shiga haɗa tufafina da ƴan ƙananan kaya na da na ke amfani da su kullum a babban akwatina.Ɗakko hijabin sallah ta na yi da ya ke har ƙasa na zuba,agogo na kalla 8:47pm na san ba matsala zan iya tuƙi da yardar Allah. Falon na fito ina janye da akwatin kayana,shi ma ya na nan zaune rungume da Amna,Aysha kuma na kwance akan center capet da drawing book a hannunta.Tashi zaune ta yi tana kallona"Mommy fita za ki yi" idanuwana na zuba mata tare da jin wani irin tausayinta da ya lulluɓe ni,saboda duk cikin ƴaƴana ta fisu ƙulafucin uwa,ba ta ƙaunar ko nan da can na matsa na barta. Jin maganar da Aysha ta min ya sa Amna da mahaifinta waigowa kallon kallo muka shiga yi ni da shi,ni na fara janye idanuwana na mayar kan Amna da ta riƙe min ƙafafuwa "Mommy zan bi ki,kin san ranar da Aysha kika tafi,ki ka ce idan za ki ƙara fita za ki je da ni" hannuna na sa na janyeta sanin da na buɗa bakina kuka zai iya ƙwace min. Kanta na shafa tare da ɗaukar akwatina na tunkari ƙofar barin ɗakin,da ƙarfi na ji an rungumeni ta baya,zafin da naji ya fara ratsamin jiki ya sa na fahimci Safwan ne.Juyowa na yi ina kallonshi hannuwana ya riƙe idanuwanshi na zubar da hawaye "Mommy don Allah kar ki tafi ki barmu,kinga Aysha kuka ta ke yi,Amna ma kuka za ta yi,duba ki gani Mommy nima kuka zan yi,don Allah kar ki tafi" Rungume shi na yi da ƙarfi ina jin kamar in maida shi ciki saboda ƙaunar da na ke mishi.Da gaskiyar Lawal da yace duk cikin ƴaƴana na fi son Safwan bai faɗi ƙarya ba sai dai ban taɓa kuskuren nuna hakan a gare shi ba ballanta hakan ya raba min kan yara. "Ka kula da ƙannenka,Ku ci gaba da karatu,banda shiririta Allah ya muku albarka kai da ƙannenka" sakin shi na yi na ɗauki akwatina na bar ɗakin ina jin yadda sautin kukan yarana ke shiga kunnena ina gab da isa motata na ji sautin kukan Amna ta na kirana "Mommmmmmmmyyyy" har cikin kwanyata na ji sautin,Ina tuƙi ina kiran sunan Allah,da fatan ya kaini gida lafiya. Kamar ƴar maye haka na shiga falon na mu ina layi,Ummina da Yayyena suna zaune a falon da alama wani abu suke tattaunawa.Yaya Isma'il ne ya taro ni ganin ina neman faɗuwa ƙasa "Ke lafiyarki,Me ya same ki? Zaunar da ni ya yi a kujera kusa da Ummi,matsawa na yi jikinta tare da rungume ta ina goga kaina a jikinta kaina ta shiga shafawa a hankali,sai lokacin na samu na saki wani marayan kukan da na daɗe ina nema ko zan samu faɗawar ƙololon da ya tokare min maƙoshi da ƙyar na samu na fizgo maganar da na ke son fitarwa "*Ya SAKE NI*,Ummi Lawal ya sake ni,yau Aurena da lawal ya ƙare,komai ya ƙare ummi" Uhmmmmmm😢 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D84KccWmLGj6Iw3z7tTAh3 *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 20* "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"Ummi da Yaya Isma'il su ka shiga maimaitawa "Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi a rayuwarki Zainab,Allah ya baki juriya,ya kare mi ki yaranki a duk in da suke. Don Allah kar ki ɗaga hankalinki don kin rabu da Lawal ba shi ke nufin kin rabu da farin ciki ba,ki duba ga ni ga kuma ƴan uwanki masu son farin cikinki,don haka ki kwantar da hankalinki.Saki nawa ya miki?" Ɗagowa na yi daga jikinta ina kallonta hawaye na ƙara zubo min "Saki biyu ya min Ummi" "To ki kwantar da hankalinki ta shi muje ki samu ki kwanta kar ki jawowa kanki wani ciwon kuma" hannuna ta riƙe ta kai ni har ɗakin baccinta sai da na ce mata bacci na ke ji sannan ta fita.Amma inaaaa,ba na jin yau duk satar ɓarawon zai sa mu nasarar sace ni,mutuwar Aure fa ake magana,duk da ba abin da Auren Lawal ya tsinana min amma kasancewa ta inuwa ɗaya da yarana ya fi min daɗi fiye da rabuwa da su. Yanzu fa su na can hannun Lawal,ko sun yi bacci? shin ya mu su addu'a? Zaune na tashi tuna yadda na barosu su na kuka nasan in dai Amna ce sai ta raba dare ta na wannan kukan ba abin da ya dame ta,da ma can ni ce mai lallashin kayana to yanzu ga shi za mu kwana ba a tare ba,bansan a wane hali su ke ba. *FALO* "Wallahi Ummi sai ya yi nadamar wulaƙanta Zainab,zan nuna mi shi na fi shi ɗanyen kai"Yaya Abbas ke faɗa cikin matuƙar ɓacin rai miƙewa ya yi ya tunkari ƙofa "Abbassssss" Ummi ta kira shi da ƙarfi sanin abin da zai je yayi ba zai wa kowa daɗi ba"Dawo ka zauna"da ido Ya Isma'il ya bi shi har ya zauna "Haba Abbas da iliminka da komai,da ma Aure rai ne da shi to su nasu ya ƙare yau addu'a kawai za ku mata Allah ya zaɓa ma ta abin da ya fi alkhairi a rayuwar ta" Ya Isma'il ya tunatar da Ya Abbas Numfasawa Ummi ta yi sannan tace "Damuwa ta ɗaya yarannan da ke hannun shi,mutumin da ya kasa kula da kanshi ma ballantana wasu ƴaƴa.Idan har zai yu ina so a karɓo yarannan ko don kwanciyar hankalin mahaifiyar su,ni zan fitarwa da Abbas kono tun da ya yi rantsuwa amma ban lamunta da zamansu a can ba" A kan wannan su ka tsaya,kowa ya bada goyon bayan karɓo yaran ko don lafiyar Zainab. *LAWAL* A kan idanuwanshi ta ja jakarta ta bar gidan,ga ihun yaran da ya cika mishi kunne,bai san me ya sa ba shima ji ya ke kamar ya ɗora hannu a ka ya yi ta ihun.Yaran ya kalla tausayi su ka ba shi ganin yadda su ka makure gefen kujera Safwan na rungume da su,tausayi su ka ba shi ta shi ya yi ya isa in da su ke,hannu ya sa ya ɓanɓaro Amna da ihun ta ya fi na kowa Rarrashinta ya shiga yi ta na tuburewa "Wai za ku yi min shiru ne ko sai na haɗe ku na zane" ya da ka mu su tsawar da ta ƙara firgita Aysha,jikin Safwan ta ƙara shigewa ta na danne bakinta kar kukanta ya fita Ƙwacewa Amna ta yi daga jikinshi ta nufi ƙofa miƙewa Lawal ya yi tare da cafkota,zillewa ta shiga yi "Ni wallahi wurin Mommyna zan je,ni wallahi sai na je" gajiya ya yi da rarrashinta ya da ka mata tsawar da ta ya kamata ta sa tayi shiru amma sai ta faɗi tsakiyar ɗakin ta na shure-shure "Ni wallahi sai na je wurin Mommy,Ni wurin Mommy zan je,Abban tusa kawai" Kan shi ya dafe ya na jin kamar zai watse wannan bala'in da me ya yi kama,Zainab ta bar mi shi jaraba,Daga shi har yaran falo su ka kwana. *ZAINAB* Yadda na ga rana haka na ga dare,ba wai saboda mutuwar aurena na kasa bacci ba A'a saboda ƴaƴana ne da na san yadda na shaƙu da su. Ƙwarin guiwa na baiwa kaina na fita kitchen ina taya Anty Asabe aiki saboda ya ɗebe min kewa.Muna yi muna fira jefi-jefi har Ummi ta fito,daga yanayin fuskar ta na fahimci ta ji daɗin yadda na ke ƙoƙarin danne damuwata. Lokacin da na zo yin breakfast ɗina yarana na tuna shin sun ci abinci? To ko shi ba daƙyar ya ke samu ya ci ba ballantana ya ba su "Ya Allah ka zama gatan yarannan a duk in da su ke" *LAWAL* Bai ƙara raina kan shi ba sai da aka wayi gari ba ya da ko sisin da zai siyawa yara abin kari ga Amna ko yau ta tashi da rigimar ta wata dabara ce ta faɗo mishi ya tunkari kitchen sanin komai ana kawo ma ta daga gidansu. Ruwan Zafi ya ɗora har su ka tafasa ya juye,wurin da yasan tana ajiyar kayan shayin ya tafi sai dai ga sugar amma ba madara.Kayan ya kwaso ya fito da su,ɗakin yaran ya shiga dukansu su na kwance Safwan ta duba "Kai ina Mommynku ke aje madara? Ba tare da ya tashi ba ya bashi amsa "Madara ta ƙare ko jiya sai da ta bamu kuɗi mu ka siyo" ajiyar zuciya ya sauke tare da barin ɗakin Yaran ya ɗaga murya ya kira ya zuba musu ruwan zafin da ya zuba sugar a ciki "Abba haka za mu sha shayin ba madara kuma ba breadi" Amra ta faɗa tana ɓata fuska "Eh haka za ku sha idan kuma ba za ku sha abinda na baku ba to ku bari" "Ba kayanka ba ne,duk abinda ke kitchen ɗin na Mommy ne,kuma mu Mommy ba ta taɓa ba mu ruwa a matsayin breakfast ba" Safwan ne ke maganar,cikin wani sauti da ke bayyanar da tsanar mahaifinshi ƙarara. "Kai rashin kunyar ta ka har ta kai can? Ni za ka nuna wa ka girma? To wallahi ba zan siye madarar ba,duk wanda bai sha ya bari" Haka ya kwankwaɗi ruwan su kuma kowanen su ya kasa sha maganar makarantar su Safwan ya mi shi "Lokaci ya tafi ku bari sai gobe,yanzu ku tashi in kai ku wurin Mama don ni fita zan yi" A tsakar gidan su ka sami Mama ta na jawo ruwa a rijiyar da ke gidan,jawo gugar ta yi tare da zube ruwan da ta ɗebo a bokiti ta na kallon su cike da mamaki,saboda duk zuwan da su ke yi ba su taɓa sammako irin yau ba. "Wa'alaika salam,yau su mai gida ne tun da sassafe" durƙusawa ya yi a gabanta ya na gaida ta amsawa ta yi tare da wucewa ɗakinta Lawal da kuma yaran su na bayanta. "Lafiya na gan ka da yara tun da sassafe kuma na ga jakar kaya a hannunka? Kallon yaran ya yi "Ku je waje kafin in fito" sai da su ka fita sannan ya mayadda kallonshi ga Mama "Za su zauna ne na ɗan lokaci kafin in samo mafita" "Ban gane za su zauna ba ina mahaifiyar su? ta tambaya tare da fatan Allah ya sa ba gajiya Zainab ta yi da zaman ta yi yaji ba "Mun rabu da Zainab ne jiya Mama" Hannunta ta buga ga ƙirji "Kun rabu da Zainab? kana kuwa da hankali Lawwali?Zainabun ka saka? Matar da ta rufa ma asiri Allah ya rufa ma,ka na buƙatar ci gaba a rayuwar ka kai kam,innalillahi wa inna ilaihi raji'un" "Ita ce ta kai ni bango Mama,kullum nema ta ke ta mayadda ni sakaran namiji kuma................." "Dallah yi min shiru,to miye kai in ba sakaran namiji ba,hotiho wanda ba ya da aiki sai bacci,wallahi idan akwai abin da ya fi sakarai to kai ne.Kuma wallahi ba baki na maka ba sai ka yi nadamar wannan sakin da ka yiwa Zainab.Kuma wallahi ka yi gaggawar ɗaukar yaranka ku bar min gidana don bazan riƙa su ba sai ka san inda za ka kai su" daga haka ta tashi tare da shigewa ƙuryar ɗakinta ta mai da ƙofa ta rufe. A sanyaye ya kaɗa yaran su ka fita,tsaye ya yi bakin titi ya na tunanin yadda zai yi da yaran,Allah ya gani shi ya san bazai iya kula da su ba don ko abincin da zai ba su baya da shi ko na cikinshi wuya ya ke mishi ballantana na yara har uku. Gidan Anty A'i (yayarshi) ya nufa da su,tunda ta ganshi ta ɗaure fuska don ta ɗauka ya zo roƙonta ne kamar yadda ya saba.Sai da su ka gaisa ta sa aka zubowa yaran masa da miyar da ta ke siyarwa sannan taje ta samu Lawal da ke jiranta a falo. "A gaskiya Lawal idan na ce ma zan riƙe su Safwan na yi ma ƙarya,ka na kallo nima yadda na ke gurgura rayuwata da ƴan yarana duk da mijina ya na bani amma dole sai na ƙara saboda ba ya bamu abin da zai wadace mu,wallahi idan na ce zan riƙe su na tauye kaina.Ni da za ka ji shawarata da ka kaisu wurin mahaifiyar su kawai don ban tunanin za ka samu mai riƙe ma su a ɓangarenka.Ka na kallon halin da Mariya ta ke ciki,Allah ya haɗa ta da maƙetacin miji ba ya bata abinci sai dai ta nema ta ci,ni dai shawarar da zan baka ka miƙa su ga Zainab" Tafe ya ke yana tunani daga jiya zuwa yau ya tsinci kanshi a halin ƙaƙa ni ka yi ga shi sai yawo ya ke da yara kowa ya ƙi amsa a fili yace "Ke ki ka ja Zainab,da baki tunzura ni ba da yanzu kina nan tare da ƴaƴanki" *MAMA* Bayan wucewar Lawal hankalinta ka sa kwanciya yayi wallahi tayi baƙin cikin wannan asara da Lawal ya tabka.Wayarta ta jawo ta shiga neman layin Ummi mahaifiyar Zainab bugu uku ta ɗaga,gaisawa suka yi cikin mutunta juna "Hajiya ashe abin da ya faru kenan,wallahi ban sani ba yanzu ya zo da yara ya ke faɗa min.Don Allah ku yi haƙuri wallahi ban ji daɗin wannan al'amari ba sam" "Ba komai Hajiya ai dama aure rai ne da shi,zaman su ya riga ya ƙare sai dai dukansu mu yi mu su fatan alkhairi" Haƙuri Mama ta ci gaba da bawa Ummi kamar ita ta yi sakin sai da su ka yi sallama sannan Ummi tace "Am ni ko nace Hajiya idan ba damuwa don Allah ina neman wata alfarma a wurinki" "Wace alfarma Hajiya" "Don Allah ina so idan ba damuwa a bata yaran ta riƙe idan kuma ba zai yarda ba ko da ƙaramar ce ta dawo hannunta" *RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️ 08104445106 *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 21* Numfashi Mama ta sauke "Kar ki damu Hajiya In sha Allah ba matsala,zan yi magana da shi" daga haka suka yi sallama. *LAWAL* Kukan Amna ke ƙara ruɗashi tana kiran Mommynta.Tsawa ya buga mata a karo na barkatai amma ko gezau ba ta yi ba.Kanshi ya dafe ya na jin kamar shima yayi ta ihun ina zai saka kanshi? tunda suka dawo gidan ya ke tare da su. Ko abinci farar shinkafa kawai ya dafa musu saboda ita kaɗai ya iya itama kuma da ace babu shinkafa a kitchen ɗin da bai san yadda zai yi da yaran ba.Don bayada ko sisi dama da kuɗin Mama ya ke fantamawa to suma ƙalilan su ka rage kuma ta karɓe ba ya da wata madafa yanzu wani sashe na zuciyarshi yace "Yanzu da Zainab na nan da ita zata yi komai" Saurin kawadda tunanin yayi don sam ba ya son ya na tunawa da wata Zainab ballantana har yaji a ranshi ta na tare mishi wani abin. Wayarshi yaji ta na ƙara ɗagawa yayi tare da karawa a kunnenshi "Mama barka da dare" ya gaidata cikin girmamawa kamar yadda ya saba kullum "Ina su Safwan?Ka ba su abinci? Kallonsu yayi sannan yace "Ga su nan Mama kuma sun ci abinci" "Yayi kyau ina so gobe ka ɗau Amna ka kaita wurin mahaifiyar ta sauran kuma ka riƙe su" "Gaskiya Mama ni bazan iya baiwa Zainab ɗana ko ɗaya ba,zan iya riƙe abina" "Za ka iya riƙesu amma ka bar mata ragamar su? Banson shirme umarni na ke baka ka kaiwa Zainab yarinyar nan,idan kuma ba haka ba wallahi duk abin da na maka kai kaja" Daga haka ta katse wayarta goshinshi ya shiga murzawa.Sam ba haka ya so ba don bayason Zainab ta yi tunanin ko ya kasa da yaranne,dama haka ta ke gani kullum ,ranar ma bai yi wani baccin kirki ba. Tunda Asuba yaran suka hana mishi bacci saboda Zainab ta riga ta saba musu da tashin Asuba dole ba don yayi niyya ba shima ya tashi yayi sallah. Kamar jiya yau ma ruwan da suga ya dafa Safwan da Aysha kuma suka shirya Amna.Yau ma ƙin shan ruwan su ka yi dole ya fitar da ƴar ɗari biyun da ta rage mishi a aljihu ya baiwa Safwan yace ya karɓo madara ta naira 50 wani kallo Safwan ɗin ya mishi "Abba tun yaushe aka daina saida madarar naira 50? Sai dai ɗari,ita ma wallahi ko Amna ba za ta yiwa shayi ba" Zabura yayi "Bani kuɗina,in za ku sha haka kusha in ba zaku sha haka ba ku bari" Haka suka yi shayin da Madarar naira ɗari abu kamar ruwan banza haka suka sha shayin ba don daɗi ba.Gidan ya kulle sannan yace su jirashi ya tunkari wurin mai shagon da yake zama "Laminu don Allah ɗari biyar za ka ranta min in kai su Safwan makaranta" Wani kallo ya mishi "Da me za ka biya ni idan na ranta ma? Da shekarunka ko da ƙaton kanka? To bari kaji wallahi dama jiranka na ke inga kana da kunya ko ba ka da ita? to na gani don in banda rashin kunya banga dalilin da zai kawo ka wurina rancen kuɗi ba bayan ina binka kuɗi sun kai dubu biyar" Ran Lawal ya kai ƙololuwa wurin ɓaci "Kar ka faɗa mini magana malam,kuma yadda ka samu kuɗinnan nima zan samu da yardar Allah" "kana zaunen za ka samu? Ko kuɗin fiffike ne da su da zasu sauka kanka? To bari ka ji bazan bayar ba" Fuuuuuu Lawal ya bar wurin ya na ji kamar ya kashe kanshi ya huta don baƙin cikin wannan tozarcin da Laminu ya mishi "Haba Laminu bai dace ka mishi haka ba,ina laifin wanda ya zo neman wani taimako a wurinka da tunanin za ka taimaka mi shi amma sai ka mishi haka,bai dace ba sam kuma banji daɗi ba" wani da yazo siyayya a shagon ya faɗa Tsaki Laminu yayi "ƙyale shi kawai Aminu,haka ya ke kullum shi dai a ranta mishi,ko kaɗan bai san zafin neman kuɗi ba yana kwance matar shi ke nema ta ciyadda shi da ƴaƴanshi.Ba ya da aiki sai rance kuma bayada abin biya don ba wata sana'a ya ke ba duk sana'ar da ka nuna mishi zai nuna ta mishi ƙanƙanta" Kuɗi Aminu ya fitar daga aljihunshi "Nawa ka ke binshi? "Dubu biyar da ɗari huɗu" Kuɗin ya bashi sannan ya fita daga shagon.A bakin titi ya samu Lawal a tsaye riƙe da hannun Amna sauran yaran na gefenshi hannu ya bashi su ka gaisa sannan ya fitar da kuɗi dubu biyu daga aljihunshi "Gashi Malam Lawal a siyawa ƴan makaranta alawa,shima mai shagon ba sai ka bashi kuɗin ba na bashi.Kuma ina roƙonka don Allah ka tashi ka nema ko don future ɗin yarannan" Godiya ya mishi sannan ya samu adaidaita suka shiga ya sauke yaran makaranta sannan ya wuce gida wurin Mama Kuyi haƙuri da wannan Wallahi yau saboda farin cikin ku kawai na yi typing ɗinnan, Ina muku ƙauna lodi-lodi *RUMAISA SIDI* *08104445106* *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 22* *ZAINAB* Wani sanyi na ke ji a cikin raina matsalar rashin yarana ne kawai a gabana,duk wani ƙunci da nake ji akan mutuwar aure na ya kau saboda na mayadda hankalina ga addu'a abin da na yi sakaci tun farko. Idan ƙuncin Lawal ya sako ni gaba maimakon na na tashi na gayawa Allah matsalata, sai dai na shige ɗaki na dinga kuka.Amma yanzu In sha Allah wannan ya kau,zan yaƙi matsalata da ƙarfin addu'a da yardar Allah. Tsaf na shirya domin ina so yau in shiga makaranta a falo na sami ummi tare da yi mata sallama. Ina tuƙi naji wayata ta yi ƙara ban ɗauka ba saboda akwai ni da tsoro in dai har ina tuƙi to bana ɗaga waya sai in wayar daga Ummi ne ko su Yaya to shine zan yi parking sannan in ɗaga. Sai da na isa makarantar ban fita daga mota ba na duba ashe Hafsat ce ƙawata ta amana murmushi na yi tare da danna mata kira "Uwar gida a gidan Dr" "Kuma Amarya ba,Faɗi ki ƙara nice dai ba wata" dariya na yi "Allah ya shirya ki,na ga kiranki ina tuƙi" "Eh wallahi kwana biyu na jiki shiru,ya su Safwan" Numfashi na sauke "Su Safwan suna can tare da mahaifinsu" "Ban gane ba, to ke kina ina? "Ina makaranta Hafsat bari idan na koma gida zan kiraki mu yi magana" Sallama na yi da ita sannan na wuce in da muke ɗaukar darasi. Sai da na koma gida na kira Hafsat ina faɗa mata abin da ya faru "Amma wallahi mutuminnan ya ji daɗin shi,ki kwantar da hankalinki In sha Allah hakan shine mafi alkhairi a gare ki,Ki na kammala idda za ki samo mana wani handsome.Allah na tuba ban da ma ƙaddarar aure ai ke ba sa'ar shi ba ce" "Ni fa yanzu Hafsat na cire wani aure a raina,ki dubi ko Lawal yadda muka buga soyayya da shi,amma dubi yadda abin ya ƙare.Ni dai kawai karatuna na ke so na kammala" Tsaki Hafsat ta buga "To saboda Lawal za ki cire hope ɗin miji na gari? Ayi sha'ani kawai Hajiyata.In sha Allah kwanannan zamu shigo sokoto da na dawo za ki ganni" Wuraren ƙarfe 5:00 sai ga Amna ya kawo tare da kayanta.Bai shigo gidan ba Baba mai gadi ne ya shigo da ita,na yi farin ciki sosai da dawowar Amna wurina duk da dukansu na so,saboda bansan ya rayuwar su zata kasance ba. Da dare muna tare Amna na bani labarin ruwan da suka sha a matsayin breakfast na tausaya musu sosai shi ya sa da safe da zan kaita makaranta na dafa abinci har su Aysha. Ko da na isa makaranta su Safwan ba su je ba parking nayi ina jiran zuwan su.Sai 8:30 sannan ya shigo kamar wani almajiri ya na jaye da hannun Aysha Safwan na gefen shi.Har yaran suka shiga ina kallonsu sai bayan sun wuce nima na dawo. Kuyi haƙuri yau biki muke yi ku karanta wannan kafin gobe *Na gode sosai* *RUMAISA'U SIDI✍️✍️✍️* *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 23* Tsaftataccen zawarci na keyi saboda sam Ummi ba ta bari na yi wata shiga da bata kamata ba,duk abin da nasan bai kama ce ni ba ban yin shi. A kwana a tashi har na kammala iddata na ci gaba da sha'ani na,yarana suna zuwa duk lokacin da suka buƙaci hakan sai dai ba yanda nakeso na ke ganin su ba,daƙyar su ke komawa idan su ka zo. A kwanakinnan duk fitar da zanyi to sai wani ya biyo ni,tun ina damuwa har na ƙyalesu na shiga sabgata don ni yanzu lamarin rijalu tsoro ya ke bani.Musamman wani maƙale matan lecturer abokin ya Abbas da ya ke damuwata.Ni dai saidai in saurare shi kawai domin ni yanzu kalaman soyayya sun daina tasiri a zuciyata. Yajin aikin da aka tafi a makarantar mu yasa na yi shirin zuwa Kaduna wurin Gwaggo na.Wurin Ummi na bar Amna saboda su basu yi hutu ba.Na so inje da ita to amma su ma suna gab da fara exam. Driver aka haɗa ni da shi saboda Ya Abbas yace bai yarda na yi tuƙi har Kaduna ba. Cikin zumuɗi na shiga falon ina ƙwala kiran Gwaggona "Miƙewa ta yi daga zaunen da take da wannan murmushin ƙauna da ke kasancewa a fuskarta duk lokacin da muke tare hannuwanta ta buɗe min alamar nazo gareta. Da sauri na ƙarasa tare da shigewa jikinta ina jin wata ƙaunar ta ta musamman "Tun ɗazu nake dakon isowar ki,yayanki ma da wuri ya dawo office yana jiran isowar ki" Sakin ta nayi ina raba idona a falon "To ina Yayan,shine kuma bai jira ni ba? Hannuna ta ja ta kaini ga kujera "Yanzunnan ya shiga sashenshi,amma tunda ya san kina hanya yanzu zai dawo" Kitchen ta wuce bata jima ba sai ga ta tafito tare da mai aikin ta,kaya aka shiga jerawa a gabana kamar wata sarauniya. Shagwaɓe fuska na yi "Gwaggo hutawa zan fara yi sannan in ci abinci,wallahi bacci na ke ji" Hararata ta yi "Zaman awa nawa kika yi? kisha ko ruwane sannan ki je kiyi wanka kizo ki ci abinci" Lemun da ta zuba min na kurɓa tare da sanar da ita a kaiwa driver ahinci yana waje don juyawa zai yi. Ɗakin da zan sauka ta kaini,komai an gyare tsaf.Wanka na yi tare da ɗauro alwala kaya na saka mara nauyi.Gyara kwanciyata nayi kan daddumar da nayi sallah ina jin yadda ƙassan jikina ke amsawa na gaji sosai. Wayata na tuna da ita,tashi nayi tare da buɗa hand bag ɗita na ɗakko.Missed calls na samu na Ummi da su Yaya bansan me ya hanani jin ringing ɗin wayar ba. Number Ummi na danna "Kin kyauta Zainab,wato daga zuwa wurin dije har kin manta da ni ko? Zama na yi gefen gadon ina bata amsa "Haba dai Ummina,kema kin san ba yadda za'a yi in manta da ke koda na second ɗaya.Ba uwa irinki ake mantawa ba Ummin Zainab" Ina jin sautin murmushinta ta wayar "Allah ya shirya min ke Zainab,kun sauka lafiya ina dijen? "Lafiya lau muka sauka Ummi,gwaggo ma tana lafiya" na faɗa ina kallon Gwaggo da ta shigo ɗakin.Matsowa ta yi kusa dani suka gaisa da Ummi tana tsokanar ta na har ta fara kewata. Jin Ummi na neman kashe waya yasa na cire kunya na tambayeta Amna "To rasa kunya,ƴar ki na wurin su Nihal ki kwantar da hankalinki ko kewarki ma bata yi ba" Sallama muka yi tana jaddadamin na kira yayyena sun damu da rashin ji na" Sai da na kira su muka gaisa sannan na fita falon. A falon na sami Yaya Bashir da Gwaggo da kuma Sister Zubaida matar Yaya Bashir "Na yi fushi tunda sai yanzu za ka zo tarbata" Hararata yayi "Haka ma zaki ce,bayan kinsa na baro office tun ban tashi dawowa ba,hala dai tata drivern yayi? Dariya na yi sannan na dubi Matar tashi "Sannu Anty Zubaida,Na same ku lafiya,ina Takwara ta? Abin mamaki sai naga ta ɗauke kanta duk uwayen tambayoyinnan da na mata cemin kawai ta yi "Lafiya" daga haka ta rufe bakinta gam. Zama na yi kan kujera,miƙewa naga Ya Bashir yayi ya fara ƙoƙarin haɗamin abinci "Wai me zaka yi? Na tambaye shi ganin abinda ya ke shirin yi " Abin da annabi ya umarce mu da muyi,mu karrama baƙin mu.Shi ya sa zan zuba miki" Matar shi na kalla da ta kafa mana ido,plate ɗin na karɓe daga hannunshi "Ka bar shi zan zuba da kaina,ai ni na wuce ka kira ni baƙuwa Yallaɓai" Har na kammala cin abincin ina jin idanun matar shi na yawo a jikina,duk hirar da muke yi ko ɗaya bata saka bakinta ba,ban jima ba na musu sallama kan zanje in kwanta. "Ina gayyatar ki karin kumallo a gidana da safe" Waigowa na yi na dube shi "To sannu masu gida,gayyata bata karɓuba" na faɗa ina ƙoƙarin shigewa ɗaki,ban daɗe da shiga ba,bacci ya ɗauke ni. *WASHE GARI* Tunda na yi sallah na koma bacci saboda gajiyar da nake jin har lokacin bata fita jikina ba.Na daɗe ban yi irin tafiyar nan ba,auren Lawal ya hana mini zuwa ko ina iya kata kula da shi da ɗiyanshi. Sai ƙarfe 9 na tashi shima ba don na gaji ba,wanka na yi na zuba doguwar rigar abaya ta ban damu da shafa komai a fuskata ba saboda tun dama ni ban cika yin kwalliya ba. Ban samu Gwaggo a ɗakin ba shi yasa na wuce bedroom ɗinta a can na same ta gaida ta nayi ta amsa tana tambayar yadda na kwana "Tun ɗazu yayanki ke yawo nace baki tashi ba,kuma ba za a tada ki ba.Muje ki gaida Abbanku jiya ko da ya shigo kin yi bacci,sannan ki wuce ɓangarenshi tun bai dawo min neman ki ba" Sai da muka je na gaida Abba dattijon arziki,cikin nuna ƙauna muka gaisa da shi yana tambaya ta su Safwan. Na fito ɓangaren Abba na hangeshi tafe,murmushi na yi tare da tsayawa wurin da nake "Kin wahalda ni da yawa Zainu,tun ɗazu kin hana mu cin abinci ni da madam" Girata ɗaya na ɗage "Na hana ku cin abincin ne? Kuma ai bance muku nayi accepting wannan IV na cin abinci ba" Hararar wasa ya min "Wallahi ba ki isa ba,ko kina ci kina amai sai kin ci shi,baki isa ki hana matata cin abinci ba sannan kice ba za ki ci ba" Jerawa muka yi har ɓangaren nashi yana tambaya ta makaranta ina bashi labarin yadda abin ke tafiya. A ƙofar kitchen muka samu madam ɗin Ya Bashir da alama magana ta ke da mai aikinta,kallo ɗaya ta min ta kawadda kanta. Ina kwana na mata tare da isa ga Zainab da ke wasa a tsakar falon,ƴar Yaya Bashir wadda ya min takwara shekarar ta 2 yanzu,bayan haihuwar Amna yayi aure,shima saida suka shekara sannan aka samu cikinta.Dariya ta shiga ɓingilamin tana min gwaranci kallon Yaya Bashir da ya zuba min ido na yi. A bazata na ji maganar shi "Wallahi yau na ƙara ganin kamanninki da sweet heart da kullum Mama ke faɗa,kamar ke kika haifeta" "To da wa ya haifeta? Ni na haife ki ko Zainab" kamar ta san abin da nace ta shiga ɓingilamin dariya tanawa ubanta gwaranci. Dinning ɗin da aka shirya muka nufa ina ɗauke da Zainab abin mamaki matar gidan ma kamewa tayi a kujera tana ƙwalla kiran mai aiki ta zo tayi serving ɗinmu. Miƙewa nayi ina cewa ta barshi ni zanyi,ita na fara zubawa sannan na zuba mishi na zuba wa kaina.Zama na yi ina ci ina baiwa Zainab da ta maƙale min kamar ta saba da ni. Saida na kammala na tashi na koma falo tare da Zainab ina nan ya wuce sama yana cemin in jirashi ya fito. Ganin mutum kawai na yi a kaina tana girgiza jiki kamar wadda aka kunnawa disko "Bari kiji, wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara shigewa mijina ehe,ni dama tunda naji aurenki ya mutu na san ba za ki barni na samu kwanciyar hankali da mijina ba,kin kashe aurenki nima kina nema ki kassaramin nawa,to nikam mijina yafi ƙarfinki saidai na wata don................" "Keeeeeee......." ya daka mata tsawa yana saukowa daga matattakalar benen da zata sadaka da ɗakinshi.Nuna yi yayi "Kin san muhimmancin ta a wurina? Kin san alaƙa ta da ita da za ki zo kina faɗa mata maganganu akan wani banzar haukanki da kike kallo a matsayin kishi" Ƙara tubure wa ta yi kamar sabon kamu "Eh ai dama tare mata faɗa za ka yi,tun da ƙaunar ta kake yi,ƙaunar da bata ma amfanin komai ba tun da ta tsallake ta ɗauki wanin ka saida ya gama gurgunta rayuwarta za ta zo tana neman tarwatsamin farin ciki,wallahi ba zan yarda ba" Kallon mamaki nake ma ta kishina ta ke kenan ƴarta na dire mata a kan kujera sannan na tunkari ƙofa don wannan faɗan ba nawa ba ne. Ganin yadda Zubaida ta ke da zafin kishi akan mijinta sai na shiga ja baya da shi duk da shi sam ya ƙi fahimtar hakan,a wurina Zainab ke wuni mun saba sosai da ita duk da mahaifiyar ta bata ƙaunar hakan. Ina kitchen muna haɗa abincin dare ya shigo "Tunda na jiyo wannan ƙamshin na san kece a kitchen ɗin" Murmushi na yi "Kenan girkina har wani ƙamshi ne da shi na musamman" Shigowa ya ƙara yi kitchen ɗin tare da haye gefen cabinet ɗin "Ai tun kina ƴar ƙaramar ki nasan ƙamshin girkinki,kamar na Ummi haka ya ke,don haka yau bazan bar kitchen ɗinnan ba sai an kammala an zubawa ɗan almajiri" Aikina na ci gaba da yi muna ƴar hira shima ya na riƙe da wayarshi ya na latsawa. Kamar wadda aka jefo ta shigo kitchen ɗin raba idanuwanta ta shiga yi tsakanin Ni da Shi "Me kake yi a kitchen" ta tambaya kamar itace mijin shine matar "Laifine don kin same ni a kitchen ɗin mahaifiyata? "Ai da can baka shigowa sai yanzu da aka shigo da kai" ta ƙarasa tana bankawa bayana harara "To kenan kema shigo da ke aka yi" Tsaki ta yi wanda a ɗan zaman da muka yi na fahimci ɗabi'ar ta ce" Ka tashi mu je an kammala haɗa abinci" hannunta ya jawo "Yau girkin Zainab za mu ci,kiji kema ki huta da ganin laifina idan ina baki labarin yadda na ke santin girkinta" Ba tare da na waigo ba nace "Gara dai ka je ka ci wanda aka saka da kai don wannan babu rabonka a ciki" Hannunta ta ƙwace "Allah ya kiyaye ni,kaima kuma ba za ka ci shi ba" ta faɗa tana jawo shi kamar wata mai ƙarfi,ganin haukar ta ta fara yawa yasa ya daka mata tsawa "Wai ke a komai sai kin yi hauka? Nan ta ke idanuwanta su ka tara ƙwalla "Ai dole kace min mahaukaciya tunda ga ƴar so a gabanka,ni kuma matar cushe ce,wallahi tun mutuwar aurenta ban ƙara samun bacci mai daɗi ba saboda nasan abin da ke tunkaro ni" Girkina na sauke sannan na bar kitchen ɗin ita ma bayana ta biyo tana ƙara sautin kukanta kamar wata ƙaramar yarinya. "Lafiya Zubaida"Gwaggo da ke fitowa daga bedroom ɗinta ta tambaya.Nuna ni ta yi "Tun da wannan ta zo ya canja min Mama,komai za. a mishi sai dai yace ita za ta mishi,yanzu ma abinci na haɗa mishi wai ba zai ci nawa ba na ta zai ci" Kallon tuhuma ta mishi "Zo ku wuce,ba za ka ci min abinci ba kuje ku ci wanda kuka girka" Kaɗa su ta yi suka tafi sannan ta same ni a ɗaki ina zaune kamar mai tunani "Kar ki damu da Zubaida har yanzu akwai sauran ƙuruciya a cikinta,kuma ban cika son saka baki a lamarin aurensu ba tunda mahaifiyar ta bata ganin laifinta idan nayi magana kuma Alhaji zai ga dan ta na ƴar ƙanwar shi yasa na ke haka, amma shi kanshi ba daɗin zama ya ke ji da ita ba.Matar da bata san ta shiga kitchen ta girkawa miji abinci ba ai muna mata ce" Numfashi na sauke "Allah hay kyauta,bari in zubo miki abincin" Na faɗa tare da miƙewa nabar ɗakin. Duk kishin matar shi baisa ya fasa abin da ya ke min ba,ganin ina neman haɗa rigima ya sa na fara shirin barin garin. "Yanzu ke Zainab har kin gaji da zama kusa da ni,ko dai wani abu aka miki" Kai na na girgiza "A'a wallahi gwaggo ni ba abin da aka min sai alkhairi,kuma na ji daɗin zama tare da ku" "Kar ki yarda da ita Mama,kawai dai wani bazawarinta ne yayi kewar ta shi yasa ta ke son ta koma ya ganta" ya faɗa yana tsare ni da ido Murmushi ta yi "Dagaske Zainab surukina ne ya damu? Fuskata na rufe da tafin hannuna "A'a wallahi,ni ba wani bazawari da nake kulawa" "Ai ko gwanda ki kula,don ba za mu zuba miki ido a hakan ba.Miji za ki fitar musha biki don haka tun yanzu a cikin masu nemanki ki darje ki fiddo ɗaya.Ko Abbas kwanaki mun yi maganar da shi yace har da wani abokinshi ke son ki" Ajiyar zuciya na sauke "Ku ci gaba da taya mu da addu'a Gwaggo,In sha Allah zan fitar. Ina ɗaki ina shirya kayana domin gobe da sassafe na ke son tafiya naji ƙarar wayata,Ya Bashir ne ɗagawa na yi tare da sakata hands free na ci gaba da aikina "Wai dagaske tafiya za ki yi Zeen Abba" Wani abu na ji ya tsirga min jin sunan da ya kira ni da shi bayan tsawon lokaci,na tafi wata duniyar na ji maganar shi a kaina "Zainab" Ya kira ni kai tsaye "Na'am" na amsa cikin sanyin murya "Zainab yanzu ma bari za ki yi in rasa ki? Ya tambaya kamar zai yi kuka "Ban gane ba" na faɗa ina dakatawa daga ƙoƙarin rufe jakar da nake yi "Kin gane komai Zainab,ba abin da baki gane ba,sai dai ina son ki sani bana jin wannan karon zan haƙura ina kallo wani namiji ya ɗauke ki.Haba Zainab ki taimaka min mana,tsawon shekarun nan ina yin su ne a cikin wani kalar yanayi" Shiru na yi ina ƙara jin ya zama dole na yi gaggawar barin garin kafin Ya Bashir ya jawo min haukar matar shi. "Kayi haƙuri ni yanzu ba wani aure a gabana,karatuna na ke yi,bayan haka ma ni banajin zan iya auren mai mata" Na faɗa ba wai har cikin raina hakane ba sai don ya ƙyale ni amma bai ƙyale ni ba sai da yace "Zan zama yadda kike so,wannan ba matsala bace,za ki zauna ke kaɗai kamar yadda kike so" A tsorace nace "A'a wallahi ban ce ba,don Allah Ya Bashir ka daina wannan maganar,ka na zaune tare da matar ka cikin kwanciyar hankali me yasa za ka ɗakko wani aure yanzu" "Ai dama ban ce miki bama zaune da lafiya da matata ba,kuma ba don bana son ta na ke neman ki ba,kowa matsayin sa daban,sai dai ki sa ni wallahi wannan karon bazan yarda ba" daga haka ya kashe wayarshi ƙittttttt Kaina na dafe "Na shiga uku,Ya Bashir auren dole za ka yi dani???? *In ga ruwan comment kawai* *RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️ *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 24* Gudun haɗuwa ta da shi yasa nayi sammakon shiri,koda na fito kitchen na wuce a tsaitsaye na haɗa tea na sha,ɗakin na wuce na fito da kayana. Cikin sauri na ke komai don ban da buƙatar haɗuwar mu.Bedroom ɗin gwaggo na shiga ina faɗa mata na shirya "Wai dagaske tafiyar nan za ki yi Zainab? "Tafiya Zan yi Gwaggo,banson in rasa mota" Duk saurin da nake don kar mu haɗu ban samu riba ba a tsakar gidan muka haɗu shida ƴar lelenshi yana riƙe da hannun Zee. Kallo ɗaya na mishi na kawadda kaina ganin irin kallon da ya ke min maganar shi ce ta tilastamin kallonshi "Yanzu saboda ba ki da kirki sai ki bar gidannan ba ki min sallama ba? Matarshi na kalla da ta tsareni da ido sannan nace "Kaima kasan ba yadda za'a yi na bar gidannan ba ka sani ba,yanzu ma gwaggo ce tace na jira ta fito da sai dai na same ku" "Kin yi kyau Zeeeee" naji maganar shi cikin wani kalar sauti kuma a hankali matar shi na kalla a yanayin da na ganta na tabbata bata ji ba da yanzu ta haukace gurin. Tsaraba gwaggo ta haɗamin kamar wata GARAR AURE (Littafina na farko) Ya Bashir ne yace zai kaini tasha. Sallama na yiwa gwaggo tare da duƙawa na sumbaci goshin Zainab sannan na buɗe gaban motarshi ina ƙoƙarin shiga naji an mangaje ni ta shige gaban motar,Murmushi na yi tare da buɗe baya na shiga. A hasale yace "Wai kina lafiya kuwa? To yanzu ina za ki je? Cike da rashin kunya ta bashi amsa "Inda za ku je kai da ita,nima can zan je" tsaki yayi sannan ya buɗe in da nake zaune ya ɗora Zainab a cinyata ya koma mazaunin driver. Buɗe mishi get aka yi muka fita, ta mirrow ya ke kallona kamar ya samu TV,ido muka haɗa da shi naga ya kashe min ido yana marairaice fuska kamar wani ƙaramin yaro. Zaman kurame suka yi a motar don nikam nida Zainab sai hira muke tana min gwaranci har muka isa tashar. Cewa ya yi na zauna yaje ya dawo,shiru motar ta ƙara yi sai maganar ta ce ta katse shirun "Ina fatan wannan tafiyar ta zama kin tafi ne ba dawowa domin zan fi buƙatar ki zauna can duk lokacin da kika so zumunci ki kira a waya ku yi, amma don girman Allah ki zauna gidanku har lokacin da za ki samu miji kiyi aurenki.Na miki alƙawari zan taya ki da addu'a Allah ya baki miji in da zaki yi zama na har abada ko don kwanciyar hankalin mu dukan mu" Har ta kammala bata waigo ta dube ni ba,bayanta na ke kallo ina jin yadda take fitar da maganar har ƙasan zuciyarta.Ba zan iya bar mata bashin magana ba,Lawal ya riga ya koyadda ni da an mini in rama shi ya sa wannan karon ma ban bar mata bashi ba. "Ina so ki sa a ranki idan har Allah ya ƙaddaro aure tsakani na da Ya Bashir ke baki isa ki hana ba,sannan barazanar ki ba za ta hanani zuwa garinnan a duk lokacin da na yi ra'ayi ba.Ni mamaki ma kike bani yadda kike wani zaƙewa akan lamarin mu kamar bakisan in da aka fito ba,aro fa na baki baiwar Allah zaƙewarki za ta iya sa na waiwayo ajiya ta,zai fi miki kyau kiyi shirin tarbata don kowane lokaci za ki iya tsintar mijinki a hannuna" Daga haka na buɗe ƙofar na fita wanda yayi daidai da isowar shi yana faɗamin komai an kammala shi yayi mini jagora har na shiga mota ya na jaddadamin ƙarshen watannan zai zo. Haka muka ci gaba da rayuwa idan ka ganni yanzu kamar ba ni ba,na yi ɓulɓul nayi wani kyau na musamman. Yau ko da naje kai Amna makaranta har wuraren 8:30 ban ga shigowar su Safwan ba,sun saba latti amma ba su taɓa kai irin wannan lokacin ba. Ganin lokaci ya tafi yasa na ja motata jikina a sanyaye,ko da naje gida kasa haƙura na yi na kira Antynsu Amna ina roƙon ta bincika min idan sun shigo. Sai bayan 30minutes ta kira ni "Kiyi haƙuri Mommyn Amna,ko da ki ka kirani ina class amma da na fito na bincika aka ce ba su zo ba.Amma da ki kira kiji ko lafiya don gaskiya basu cika fashin zuwa ba sai dai su yi latti" Number Mama na kamo da niyyar kiranta sai kuma na ji nauyin kiran,bayan haka kuma ba wurinta su ke kwana ba,idan ya ɗakko sudaga Makaranta can ya ke kaisu,da dare ya ɗauke su,su koma gida. Ina ɗakina ina duba kayan da nayi order da suka iso,ina aza kowane a muhallinshi Ummi ta shigo,daga yanayin ta gabana ya faɗi ina tambayar ta lafiya? "Ɗakko hijabinki muje asibiti,ashe tun jiya A'isha na asibiti shine sai yanzu su ka kira suke faɗa min" Ƙirjina na dafe daga zaune "Asibiti kuma? Ummi ce ta ɗakko min hijabin muka fita driver ya jamu sai asibitin da suka gayawa Ummi. Da Mama muka fara cin karo,tun daga yanayinta bugun zuciyata ya canja,hankalina ya tashi daƙyar na iya ɗaga laɓɓana na gaishe ta,amsawa ta yi sannan suka gaisa da Ummi tana tambayar jikin Aysha. "Ai A'isha jiki da sauƙi sosai,yanzu ma likitan ya fita ya kira Lawwalin wata ƙil magungunan za a ƙara rubutawa" Cikin rawar murya na ce "Me ya same ta ne Mama? "Wallahi jiya lafiya lau ya kaisu makaranta,bayan sun dawo ta ke cemin cikinta ke ciwo da kuma bayan ta,sai na bata magani da tunanin ko zazzaɓine ke son kamata.Zuwa la'asar abin ya rikice shine na kira mahaifinta mu ka yo asibiti,jiya daga ni har shi ba wanda ya runtsa saboda halin da ta ke ciki amma yanzu kam Alhamdulillah sauƙi ya samu" Ɗakin da ta ke na tunkara na shiga,ɗakin yara ne kowa da kalar nasa ciwon idanuwana na shiga rabawa,can na hango Mariya a kusa da gadon da nake kyautata zaton Aysha ta ce a kwance. Matsawa na yi tare da yi mata sallama,ban jira naji ta amsa ko ba ta amsa ba na matsa kusa ga ƴata, hawaye ne suka shiga yimin sintiri akan dandamalin kumatuna ganin yadda Aysha ta ta koma,ciwon rana ɗaya,amma kamar ba ita ba. Hannunta da ke aje a gadon na riƙe ina jin wata ƙaunarta da kuma tausayinta suna shigata "Allah ya baki lafiya aysha" na faɗa a fili tare da barin ɗakin don nasan bazan samu amsar tambayar da nake so a wurin Mama ba. Kai tsaye office ɗin likitan na nufa,a ƙofar office ɗin na same shi a tsaye tare da wani,sai da na matso kusa na fahimci Lawal ne.Gaisawa mu ka fara yi. "Dr don Allah magana na ke so muyi akan rashin lafiyar ƴata,me ya same ta? Me ke damunta Dr? "Amma ai ba shi ya kamata ki sama da maganar ba tunda ba shine ke tare da ita ba,kuma ai...................." "Dan Allah Malam ba da kai nake magana ba,shi na tambaya kuma shi nake neman amsa a wurinshi,ina son in san abin da yasami ƴata,zai fi ma kyau kayi addu'a kar wani abu ya sami ƴata,domin wallahi banajin wannan karon zan zuba ido ka gurgunta rayuwar yara,kamar yadda ka so gurgunta tawa" Na faɗa ina nuna shi hawaye na wanke min fuska tare da wata kalar tsanar Lawal da na ke ji. *RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️ AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI FARAR ANIYA WRITERS Page 25 "Doctor,don girman Allah ka faɗa min halin da ƴata ta ke ciki" Na faɗa ina maida hankali na ga likitan.Office ɗin shi muka shiga na zauna ina jiran bayani daga gare shi. "A gaskiya yarinyar ki ta shiga wannan halin ne sanadiyyar cutar Thyphod da ta kama mata ƴan hanji,sakamakon cin abinci da kuma ruwa marasa tsafta.Wannan ya sa dole ta na buƙatar theater da gaggawa,shine ki ka samu ina faɗawa mahaifinta" Ashe a zaune ma ana jin jiri,ji nayi kamar ba ni. da sauran lakka,daƙyar na iya ɗaga laɓɓana nace "Doctor ka taimaka min ba na so in rasa ƴata,ko nawa ne zan biya a mata aiki" A sukwane na dawo inda su Ummi suke zaune na zube a tabarmar da suka shimfiɗa a gefen ɗakin da aka kwantar da Aysha. Hannuna Ummi ta riƙo "Ya dai Zainab,me suka ce na damunta? Na shiga na ga tana bacci" Idanuwana da suka tara ƙwalla na ɗaga na dubeta "Ummi aiki za a yiwa Aysha,Thyphod ce ta mata mugun kamu, a cikin satinnan za a mata aiki" "Innalillahi..........."Ummi ta shiga maimaitawa abinda ya ƙara karyar min da zuciya hawaye suka shiga ambaliya akan dandamalin fuskata. "In sha Allah za ta samu lafiya ki kwantar da hankalin ki Zainab,Lawwali na kan ƙoƙarin haɗa kuɗin aikin" Ji nayi kamar in ɗora hannu akai in fasa ihu "Idan har za a mata aikin ko yau,to zan bada kuɗin lafiyar ƴata na ke so" A ranar na shiga shirin yiwa Aysha aiki,kuma a gobe zasu mata. Sai bayan magrib Aysha ta farka,lokacin da ta farka ina gefen gadon riƙe da hannunta da aka cire wa drip,ina kallon yadda hannun ya fara kumbura.Motsin da naji ta fara yasa na dubi kyakkyawar fuskarta, a hankali ta fara buɗe idanuwanta tana kuma motsa hannunta da ke cikin nawa. A hankali kuma ta waigo fuskarta tana kallona a hankali ta furta "Mommy" ganin motsawar laɓɓanta yasa na fahimci abin da ta ke faɗi. "Na'am Indo na,ya jikin na ki? Hannuna ta cira tare da ɗorawa a cikinta "Mommy cikina,cikina na ciwo sosai Mommy" Miƙewa na yi "Bari in kiran likita sai ya duba ki"hannuna da na ji ta riƙe yasa na dubeta,a hankali tace "Mommy don Allah kar ki tafi ki bar ni,zan bi ki" ƙwalla ce ta cika min ido,duƙawa na yi na sumbaci goshinta sannan na fita don kiran likita. Wurin da su Ummi ke zaune na nufa don bawa likitocin damar yin aikinsu,ina isa Lawal ma na isowa tare da Safwan da aka baro gidan Anty A'i.Rungumeni yayi ya na hawaye. Gefe muka koma ni da Safwan ya na bani labari "Mommy kin ga Aysha ko? Tun bayan tafiyar ki ba a daɗe ba kullum sai ta yi ciwon ciki, na faɗawa Abba ya daina siya mana abincin gidan su Lami basu da tsafta an faɗa mana a makaranta zai iya samu ciwon ciki,sai yace ƙarya ce don kar mu ci ne,na hana Aysha ci ganin ya na cutar da ita.Da kuɗin da kike ba Amna ta bamu a makaranta na ke siya mata abinci ni in ci wanda ya bamu,don kar ya zane ni,yau muna a makaranta tace min cikinta ke ciwo,na karɓo mata magani amma koda aka tashi ya lafa,muna zuwa gida abin ya dawo" Hannuwan shi ya haɗe wuri guda alamar roƙo "Don Allah Mommy idan aka sallami Aysha ki tafi da ita,ko da ni ba za ki je da ni ba,wallahi kullum sai ta yi kukan rashin ki a tare da mu.Mommy don Allah" ya ƙarasa yana rungume ni da ƙarfi tare da fashewa da kuka nima kukan na ke amma sai na danne nawa na shiga lallashin shi. Sai dare Ummi tayi shirin komawa bayan su Yaya sunzo duba Aysha,tuburewa na yi kan ba inda zani,nan zan kwana tare da ƴata.Mama ce tace a ƙyale ni tun da ina so ba dan Ummi ta so ba suka tafi suka barni tare da alƙawarin shigowa kafin a shiga Theater da ita. A zaune na kwana riƙe da hannunta ina jin wannan karon dole in yi amfani da shawarar Safwan,amma duka ƴaƴana zan karɓe ba zan yarda sakacin Lawal ya gurgunta ni ba,Mama ma anan ta kwana tare da mu. Washe gari tun ƙarfe 8:00 su Ummi na asibitin,Kayan kari suka kawo na zubawa Mama don nikam banajin zan iya saka loma a cikina har sai naga an fito da Ayshata.Su Ummi basu jima da zuwa ba Lawal ya iso tare da Safwan. Ina kwana ya min kamar wani mutumin kirki na amsa mishi saboda idon Mama da kuma Safwan da ke wurin. Tambaya ta ya yi ina Amna? nace ni na faɗawa Ummi ta barta wurin su Nihal kawai. Lokacin da za a shiga da ita tana riƙe da hannuna ɗayan hannunta kuma tana riƙe da hannun Safwan a hankali tace "Mommy Ya Safwan yace da na warke wurinki zan koma wai? Kaina na gyaɗa mata "In sha Allah Indo na,tare da ke zan tafi"Murmushi ta yi wanda ya ƙara bayyanar da kyawunta sanna ta dubi Safwan "Yaya kaima da kai zamu tafi mu zauna tare da Amna" Haɗesu na yi na rungume ina jin wata ƙaunar su na shiga ta "Da ku zan tafi dukanku,Allah ya baki lafiya kawai" Hankalina bai ƙara tashi ba sai da na ga ana tura ta a gadon da zai shigar da ita zuwa ɗakin theater kuka na fashe da shi bayan ɓullewar su "Ya Ilahi ka rufamin asiri,Allah ya baki lafiya Aysha" na faɗa a fili tare da zubewa daɓas a wurin. Kaina da ke saramin na dafe,ina kiran sunan Allah a bakina.Mama ce ta shiga lallashina tare da kaini kan benci ta zaunar da ni. "Kiyi haƙuri Zainabu,ki kwantar da hankalinki,In sha Allah A'isha za ta samu lafiya.Ki mata addu'a ita take buƙata.Ki daure ko kaɗan ne ki saka wani abu a cikin ki,rabonki da abinci fa tun jiya" "Mama ba zan iya cin komai ba,zuciyata zafi ta ke min"Safwan da ya makure na duba "Je ka ɗakko min pure water a ciki in yi alwala" Ina alwalar ya same ni "Mommy nima zan yi in yiwa Aysha addu'a" tare muka shiga jera salloli tun ina ƙarda abin da nake faɗa har na kasa tantance abin da na ke yi. Carbin da ke hannuna na ke izawa batare da tantance abin da nake faɗa ba,na ji dawowar Safwan wurin ya zauna a kusa da ni. Sakanni suka shuɗe,mintuna ma suka zo suka wuce,har muka kwashe awanni a zaman jiran tsammani.Dukan mu munyi jugum,ba wanda ya iya kai lomar abinci a bakinshi,hatta Lawal har wata rama ya yi. Zabura mu ka yi dukanmu ganin fitowar likitan da muke dakon, jira,rige-rigen isa wurinshi mu ka yi tsakanin ni da Lawal. "Doctor yaya? An yi nasara dai ko?" Lawal ya tambaya cikin wata iriyar murya da ban taɓa sanin shi da ita ba,Ido na zubawa likitan ganin ya yi shiru yana kallon mu. Yaya Isma'il ne ya matso shima a sanyaye yace "Lafiya dai Doctor? Ina yarinyar?" "Sai dai kuyi haƙuri,uban gijin da ya fi mu sonta ya ƙarɓi abar shi" na ji wani kalar sauti mara daɗi na faɗa,yawun bakina suka kafe,bugun zuciyata ya rikiɗe,jiri naji ya fara ɗiba ta,lalube na dinga yi don in sami wanda zan jingina da shi. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" naji muryoyi mabanbanta suna shiga dodon kunnena. "Subhanallah ku tare ta, Zainab,Zainab Innalillahi" na ji ana faɗa bayan gilmawar wani baƙin ƙyalle a ido na,tare da kasa samun nasarar riƙe numfashina. Bansan ya na kasance ba tsawon lokaci,sai dai na farka ne a wani irin mugun yanayi.Zabura na yi bayan dawowar numfashina tare da motsawar gangar jikina. Waige-waige na shiga yi sannan na sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ina dafe ƙirjina da ya min nauyi Ummi da ƴan uwana da ke zagaye da ni na kalla. "Wai...Alhamdulillah,na gode Allah da ya kasance mafarki na ke yi" na faɗa ina jimƙe hannuwana wuri ɗaya sannan na dubi Ummi ina zare idona "Wai fa Ummi mafarki na yi wai Aysha ta rasu,Ayshata fa Ummi wai ita ta rasu" Na ƙarasa wasu hawaye na zubomin tare da Wani murmushi. Rungumeni Anty Halima tayi tana bubbuga bayana ina jin yadda hawayenta ke zubomin a kafaɗata.Ni sai yanzu ma na lura ba gida ba ne,hannuna na duba da ke ɗaure da drip,hannuna da ba a sawa drip ba na ɗaga tare da ture ta daga kafaɗata ina nuna mata hannuna "Me nene wannan Anty? Me kuma ya same ni da aka kawo ni asibiti? Ai yanzu na rabu da Lawal ko? Dama shine kullum ya ke zama silar zuwana asibiti,don Allah ku faɗa min me ke faruwa" Shiru kowa ya min sai hawayen da wasu ke zubarwa,cikin raunin muryar da ke gab da fashewa da kuka na ce "Kar ku cemin mafarkina ne ya tabbata,ina Aysha? ko dagaske ta rasu? Ganin wannan karon ma kowa yana sharar hawaye yasa na fizge allurar ruwan da ke jikina tare da ƙoƙarin sauka daga gadon.Riƙe ni Anty Halima tayi,cikin wani irin kuzari na shiga ƙoƙarin fizgewa daga jikinta,ganin kamar ba za ta iya ba yasa Anty Nasma matsowa suka riƙeni. "Ku sake ni,don girman Allah ku barni naje na dubo ƴata,batada lafiya,Aiki za a mata,kuma na mata alƙawarin tafiya da ita da zarar ta ji sauƙi.Ku daina riƙeni,kar ta mutu dagaske,don Allah" na ƙarasa tare da sauke kaina a kafaɗar Anty Halima. Banason sauraren zuciyata da ke son tunatar da ni Aysha ta mutu,dagaske kenan Aysha tafiya ta yi ta barni bayan tasha faɗa min tana ƙaunata,shikenan na rasa ƴata,ƴaƴana su ne farin cikina. A hankali na taka gaban Ummi da ke zaune kan kujera tana sharar hawaye da gefen hijabinta.Guiwowina na zube tare da ɗora kaina akan cinyar ta "Ke gani ko Ummi? Aysha tafiya ta yi ta barni,Ummi,kimin addu'a,zuciyata zafi ta ke min Ummi" Hannunta ta ɗora akan bayana "Kiyi haƙuri Zainab,kiyi haƙuri,ba ke kaɗai ki ka yi rashin A'isha ba,dukanmu mun yi rashi,amma ki daure ki bita da addu'a kawai kinji" Wani irin kuka na fashe da shi,ta tabbata na rasa Aysha kenan? Kalaman Ummi sun tabbatar min.Mutuwar Aysha ta girgiza ni ba kaɗan ba,lokaci ɗaya na zabge na fita hayyacina. Daƙyar na karɓi loma biyu a hannun Gwaggo na saka a cikina bayan lallashin da ta min kafin na ci.ƙoƙarin kwanciya na ke Ya Bashir ya shigo tare da matar shi,ashe tare suka zo,ɗazun shi kaɗai ya zo sai Gwaggo. Sannu ya min cikin matuƙar tausayawa tare da miƙawa Gwaggo ledar da ya shigo da ita "Ki bata ko fruit ɗinnan ta sha zama da yunwa ba daɗi"ya faɗa tare da kallon matar shi da ta kame a tsaye ta naɗe hannuwa. Kamar wadda aka yiwa dole tace "Sannu,Allah ya gafarta mata" "Amin" na amsa daƙyar saboda zuciyata da ke min zafi sosai,gyara kwanciyata na yi akan gadon ina jin kamar nayi tsuntsuwa na ganni a gida,na gaji da asibitin,gida nake buƙata. "Kaina na ɗago daga kwancen nace "Ummi ina Safwan? Matsowa tayi tare da kama hannuna "Safwan yana nan lafiya Zainab yana can tare da Mahaifnshi,shima Lawal ɗin ba lafiyar ce da shi ba,na so ya dawo wurin mu kafin a gama makoki amma ya roƙi alfarmar a bar mishi shi" Cikin raunin muryar da ke gab da fashewa da kuka nace "Ummi don Allah ki min izini in karɓo Safwan,wallahi Ummi kashe shi zai yi shima,don Allah Ummi ki taimaka ki bari in karɓo shi" na ƙarasa ina ɓarkewa da kuka. RUMAISA'U SIDI AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI Page 26 A bazata na ji ta fara magana "Ki daina kuka In sha Allah Safwan zai dawo hannunki,ko yanzu koma ba yanzu ba.Ina so ki cire tunanin Lawal ne silar mutuwar A'isha,ko da wannan ciwon ko ba da shi ba lokacin ta ya riga yayi,kuma yadda kike iƙirarin A'isha ƴarki ce,kar ki manta shima fa Lawal ƴarshi ce.Don haka ki cire tunanin wani abu zai sami Safwan itama A'isha lokacin ta ne yayi" Jagwab na maida kaina na kwantar,hawaye na bin gefen idona yana sauka kan filon da nake kwance.Shikenan ni ba zan yi farin ciki ba? Yanzu shima Safwan ina kallo zan rasa shi?Eh naji kamar yadda Ummi tace ba Lawal ne ya kashe Aysha ba,amma ai da gudummawar shi komai ya faru. Saida na ƙara kwana a ka sallameni,na koma gida domin in ci gaba da jinyar zuciyata.Bayan mutuwar mahaifina ko mutuwar aurena bai girgiza ni kamar mutuwar Aysha ba,da nasan haka zai faru da ban baro su ba,da nasan haka zai faru da ita zan karɓo,da nasan............... kuka na fashe da shi a fili nace "Da nasan haka zai faru da ban auri Lawal ba" haka na dinga gunjin kuka ina kallon fuskata da ta kumbura a jikin mirrow da ke toilet ɗin ɗakin. "Subhanallah,Zainab kuka kuma? Ki buɗe don Allah" daƙyar na isa na buɗe ƙofar tare da rungume Anty Halima.A bakin gado ta zaunar da ni tare da isa kan mirrow na ta yago tissue ta zo tana share min hawaye da ke min malala. "Ki daina kuka don Allah Zainab,haba kar ki bari imaninki ya taɓu don Allah" haka ta ci gaba da lallashina har na samu na taushe abin da ke tasomin. Kaina na ɗago ina dubanta "Don Allah Anty kimin wata alfarma" "Wace alfarma kenan?Ki faɗi duk alfarmar da kike so,in har bata fi ƙarfina ba zan miki" Hannuwanta na riƙe "So nake ki rakani wani gurin,ba zan iya tuƙi ba" cikin sauri na shirya tare da zuba hijab ɗina muka fito. Wurin Ummi na je cikin sanyayyar murya nace "Ummi fita za muyi tare da Anty Halima,ba jimawa za muyi ba" goshina ta taɓa "Har yanzu jikinki da zafi Zainab,ina za ki je bayan mutane na shigowa yi miki gaisuwa" Hannun nata na riƙe "Ummi dagaske ba jimawa zamu yi ba,yanzu nan zamu dawo" Hararar Anty Halima Ya Bashir yayi "Kina ganin bata da lafiya,za ki wani jata yawo ko? Bakinta ta dafe "Nifa Yaya rakiya kawai zanyi" Sai da muka lula a titin sannan ta dube ni "Ina muka nufa shalelen Ya Bashir? "Gidan Lawal zaki kaini" na faɗa cikin dakakkiyar muryar da ke bayyanar da ƙunar da ke cin zuciyata.Kallo ɗaya ta min ta juya ta ci gaba da tuƙinta. A ƙofar gidan muka yi parking ita ta fara fita sannan na buɗe gaban motar nima na fito.Ƙofar gidan Anty Halima ta nufa tare da tura get ɗin,waigowa tayi ta dube ni "Muje a buɗe ya ke" Bayanta na bi muka shiga,tsakar gidan tarr da hasken wutar lantarki.ƙofar falon muka isa,ita ta ƙwanƙwasa,amma shiru ba motsi sai da muka ƙara yi sannan naji alamar ana buɗe ƙofar. Kallon mamaki ya tsaya yana min bayan ya buɗe mana ƙofar,hanya ya bani ganin ina shirin bangaje shi in wuce.Sai da nazo tsakiyar falon sannan na fara magana ina kallonshi "Ina ɗana? Yau zuwa nayi ko ni ko kai Lawal,amma yau ba zan bar Safwan a hannunka shima ka kashe shi kamar yadda ka kashe Aysha ba.Dole ka bani ɗana" na ƙarasa da hargowa tare da yi cikin shi kamar wadda zata dake shi. Wani kallo ya ke bina da shi mai kamada na tsoro da kuma nadama "Kema kin yarda ni na kashe Aysha ko Zainab?Dagaske ni na kashe ta ko? Mama tace ni na kasheta,hakama Safwan yace baya sona saboda ni na kashe Aysha" ya ƙarasa yana nuna kanshi,ƙwalla na taruwa a idanunshi Zubewa yayi akan guiwowinshi tare da haɗe hannayenshi "Ina roƙonki ki yafemin Zainab,kuma ki roƙamin ƴaƴana su yafemin,na yarda,wallahi na yarda ni na kashe Aysha,sakacina ne ya jefa ƴarmu a halinda ta shiga.Tun bayan tafiyarki ban ƙara bacci mai daɗi ba,ban ƙara yin nadama ba sai da na rasa Aysha.Na rasa Aysha ne a bisa sakacina,da ace ina kula da ƴaƴana da hakan bata faru ba,nayi nadama,wallahi nayi nadama marar iyaka.Na rasa Aysha,shima Safwan ya faɗa min baya sona wurinki zai koma saboda kinfi kula da su,alfarma ɗaya zan roƙa a wurinki Zainab,don Allah kar ki rabani da Safwan,na ɗaun alƙawarin shiga kasuwa koda da dako ne in ciyadda shi da abinci mai gina jiki,zan yi haƙuri in jure wulaƙancin koma wanene saboda in kyautata rayuwar yarana.Laifina a gareki mai girma ne Zainab,na cutar da ke,na cutar da yaranmu ki yafemin don Allah" ya ƙarasa tare da fashewa da kuka. Zubewa na yi tsakiyar falon "Ka cuce ni Lawal,kaine silar komai,kai ka tarwatsa komai,bana jin zan iya yafema Lawal kuma bazan iya barma yarona ba" hannuna Anty Halima ta riƙo "Tashi mu tafi Zainab" Hannun na fizge "Ba inda zan je Anty sai ya bani ɗana,bazan taɓa yarda da ƙaryar Lawal ba,mutumin da ya kasa zaman kasuwa ya nema shine zai faɗa miki zai yi dako ki yarda?Wallahi na ƙare yarda da Lawal Anty" Gunjin kuka ya ke kamar wani ƙaramin yaro,abin da ban taɓa gani ba a iya tsawon zaman mu da shi "Na gane kuskurena,wallahi na gane"haka ya dinga maimaitawa har na yi nisa da ƙofar falon. Kuka nake har muka doshi isa gida,sannan Anty Halima tayi parking ɗin motar ta waigo ta dube ni "Ban taɓa tunanin akwai abinda zai zo naji tausayin Lawal ba,amma yau daga yadda ya koma ya isa ka fahimci nadamar da ya ke ciki.Zainab,ko kina so,ko bakya so Lawal uban ƴaƴanki ne,duk abin da ya same shi kamar ya same ki ne walau na farin ciki ko akasin hakan,a ganina tunda har ya nuna yayi nadama kuma ya gane kuskurenshi,to ki bashi lokaci ki gani.Ko ba komai shi mahaifin Safwan ne yana da ikon riƙonshi a hannunshi kuma yana da ikon hanaki har Amna da ke hannunki.Shawarar da zan baki,ki bar Safwan a hannunshi na ɗan lokaci ki gani,ki ba shi dama kamar yadda ya roƙa" Har dare yayi na kasa bacci ina tunanin shawarar da Anty Halima ta bani,da kuma halin da na sami Lawal a ciki.Anya kwa Lawal zai yi nadama? Ba dan na so ba na ƙyale Safwan a hannun Lawal,ina ci gaba da kula da Amna da kuma jinyar zuciyata akan rashin ƴata.Ga karatuna da muka zo gargara dole na mayadda hankalina. Rufe gambun motata na yi,ina kallon motar Ya Bashir da ke fake a wurin ajiye motoci.To duka yaushe ya koma? "Allah dai yasa lafiya" na faɗa ina nufar cikin gidan da kuma fargabar abin da zan tarar. Daga yadda na same su a falon suna fira na sauke ajiyar zuciya don nasan lafiya. Gaida shi na yi da tambayar su Gwaggo da takwarata. "Dukansu suna lafiya,sun ce a gaida ki" ya bani amsa yana bina da kallo.Ummi na gaida tare da nufar ɗakina,wanka na yi na sauya kaya,ina duba wayata Ummi ta shigo. "Kiyi ki kammala shirinki,wurinki ya zo" Ummi ta faɗa ba alamar wasa a fuskarta. "Wurina kuma Ummi?"na faɗa ina zare idona.Ƙara ɗaure fuska ta yi "Eh wurinki kuma wallahi in za kiyi hankali wannan karon kiyi,idan kuma ba za kiyi ba,kije kiyi duk yadda kike so.Ni dai iyakata da ke in faɗa miki gaskiya,a baya kinƙi Bashir ne saboda kina da Lawal,to yanzu ya rage na ki,ki zaɓi abin da ya cancanta a rayuwarki ko akasin hakan" daga haka ta juya ta bar ɗakin. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"na faɗa tare da dafe kaina,ya ake so na yi wai ina zan saka kaina???????? RUMAISA'U SIDI AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI FARAR ANIYA WRITERS Page 27 A gurguje na shirya cikin riga da sket ɗin atamfa da suka min cif tare da mayafin da ya dace da shi,kallon kaina na yi a madubi,wai ni ce zan fita,kuma a matsayin bazawarar da za ta fita zance. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi " Allah ka shiga lamarina" Bayan gida na fita ganin ba ya falon,tun daga nesa na hange shi yana zaune kan ɗaya daga cikin kujerun da ke gidan da wayarshi a hannunshi yana latsawa,ga kuma kayan motsa baki a gabanshi. Sallama na mishi sannan na ja kujerar nima na zauna,kallona ya dinga yi bayan ya amsa min sallamata "Ya ƙarin haƙuri? "Alhamdulillah"na bashi amsa a taƙaice.Zamanshi ya gyara sannan ya fuskance ni "Har na tafi hankalina ya kasa kwanciya,na ga ya dace dukanmu mu san inda muka nufa.Daga ni har ke ba ƙananan yara ba ne,mun wuce wannan Zainab,shi ya sa kawai na yanke in zo don in san matsayina,ki faɗa min Zainab,wannan karon za ki karɓe ni ko kuma yanzu ma ki na da wanda ki ke so? Shiru na yi ina wasa da gefen gyalena a hankali na ɗago na watsa mishi fararen idanuwana sannan na sauke kaina ƙasa "Ka daina tunanin bana ƙaunar ka Ya Bashir,kai ɗan uwana ne ina ƙaunarka kamar yadda na ke ƙaunar su Ya Abbas.Sai dai wannan karon ma ina roƙonka da ka yi haƙuri,ka janye maganar aure a tsakaninmu,saboda ni yanzu karatuna ne a gabana.Bayan wannan kuma ba na jin zan iya nisa da ƴaƴana.Shi yasa na ke roƙonka da ka janye wannan maganar a tsakaninmu" Jin yayi shiru baice komai ba yasa na ɗago kaina na dubeshi,ganin kallon da ya ke min yasa na yi saurin mayadda kaina ƙasa. "Yanzu na fahimta,ba auren ne bakya so ba,ni ɗin ne dai bakyaso Zainab.Kuma ba komai na gode sosai" daga haka ya ja kujerar baya tare da tashi ya bar wurin. Na kasa tashi daga in da nake zaune har ya shiga ba jimawa ya fito ya ja motar shi ya bar gidan,duk ina kallonshi. Kamar mai tsoron taka ƙasa haka na shiga falon,ina ƙoƙarin wucewa ɗaki na ji maganar Ummi ta ratsa dodon kunne na "Kin kyauta Zainab,kuma ki ci gaba da yin duk abin da kike so,ki bar ganin kin girma har da ƴaƴa,har yanzu ba ki wuce a miki faɗa ba.Ki shiga hankalinki da ni Zainab,wallahi wannan karon zan yi mugun saɓa miki" ta faɗa tana nuna ni da zallar ɓacin rai a cikin muryar ta. A sanyaye na ci gaba da kasancewa a kwanakin da suka biyo baya,duk da Ya Bashir bai daina kirana ba amma ya daina min maganar Aure,Ummi kuma ta ɗaure min sosai ta daina sakemin fuska,ga shirin Exam komai ya dagulemin.. Zaune muke ni da Amna da kuma Safwan da yazo wurina kasancewar weekend ce labari ya ke bani "Mommy har da sabbin littafai Abbana ya siya min,ga na Amna can ita ma ya bayar in kawo mata,har da sabbin uniform yace zai min.Yanzu a ƙofar gidanmu ya ke saida kayan miya,kuma wallahi ana siya sosai,yace kuma Islamiyya zai kaini,yanzu daɗin mu muke ci nida Abba" ya ƙarasa da zallar farinciki. Murmushi na mishi "To Allah ya kyauta,ya sanya alkhairi" har raina naji daɗin canjawar Lawal,ko ba komai yarona zai yi ingantacciyar rayuwa.Ko Amna da ke hannuna yana ƙoƙarin kyautatawa,wani lokacin har ni za a yiwa tsaraba idan Safwan zai zo. Yaya Isma'il ne ya sameni da maganar Aurena "Inaso ki fitar da miji a haɗe da na Mubarak da za'ayi nan da wata 2" Marairaice fuskata na yi "Ayyah Yaya don Allah ku min uzuri,kaga karatuna yazo ƙarshe mun kusa fara exam,na maka alƙawari da na kammala zan fitar da miji In sha Allah" kan shi ya girgiza "Wannan ba uzurine ba Zainab,kar ki manta lokacin aurenki na farko ma kin haɗa kika yi AURE DA KARATU,to yanzu ma haka za kiyi.Kamar yadda kika sani AURE ba ya hana KARATU,kamar yadda KARATU ba ya hana AURE.Za mu yi magana da mijin na ki" Hankalina ya tashi sosai,ga shi Ummi ta daina kulani,shiryawa na yi na nufi gidan Anty Halima. "Ki faɗa min abin da ya dace na yi Anty" na faɗa bayan na ƙare zayyane mata abin da ke faruwa. "Ni banga abin damuwa anan ba,ba wai don Ya Bashir yana ɗan uwana ba Zainab,amma wallahi da shi kika dace tun farko.Idan har shawara kike so a wurina zan baki shawara da ki baiwa Ya Bashir dama ina tabbatar miki da izinin Allah ba za kiyi nadama ba.Amma ko yanzu ki maida hankali ga Addu'a duk wanda kika ji yafi tsaya miki a rai to ki zaɓe shi" Ajiyar zuciya na sauke "Anty ba wai Ya Bashir ne ba na so ba,ina tsoron yadda zan tsallake garinnan na bar ƴaƴana,ga kuma Karatuna da ban kammala ba" "Haba Zainab,yanzu saboda su sai ki kasa samawa kan ki farin ciki? Ko kina tunanin yanzu kece ke tsare da su? Wallahi ko kina tare da su ke ba ki isa ki tare musu komai ba.Kuma kar ki manta Safwan yana wurin mahaifinshi kuma yanzu kema kinsan yana kula da shi,Amna kuma ta hannun Ummi,wurinda kema nan kika samu tarbiyya.To miye abin ɗaga hankali? Karatunki kuma ga yadda Ya Bashir ke sonki,ko bayan an ɗaurane zai jiraki ki kammala exam ɗinki.Kar ki bari wannan karon ma rayuwar Ummi ta ɓaci saboda ke" Maida hankalina na yi ga addu'a da neman zaɓin Allah.Text na turawa Ya Halima kan na zaɓi Ya Bashir,ko minti 2 banyi da tura saƙon ba sai ga kiranta "Ayyirrrrrrrrrrrrrr" ta rangaɗa mun guɗa a cikin kunne,janye wayar na yi a kan kunnena "Anty Halima ai sai ki kashe min dodon kunne" "Barni na yi Zainab,wallahi ina cikin farin ciki sosai,yau Account ɗina zai yi nauyi idan Ya Bashir yaji wannan albishir daga bakina,don Allah kar ki faɗa mishi bari in samu wannan goron" daga haka ta kashe wayar. Ɗakin Ummi na shiga,tana zaune a gefen gadon da waya a hannunta.Guiwowina na zube a gabanta idanuwana na cika da ƙwalla "Kiyi haƙuri Ummi da ɓata miki rai da na yi,ban yi don in ɓata miki rai ba" kaina na ƙara sunkuyarwa sannan a hankali na ce "Kuma..............."sai na kasa ƙarasawa "Kuma me?" ta tambaya da sauri "Na amince zan Auri Ya Bashir" na ƙarasa tare da barin ɗakin da ɗan guduna. Ɗakina na koma da sauri na zube kan gadon ina maida ajiyar zuciya,ƙarar wayata yasa na miƙa hannu tare da ɗaukota,batare da nasan mai kira ba na ɗaga "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah" naji muryar Ya Bashir na doka hamdala har sau uku. "Na gode sosai Zainab,na gode da damar da kika bani,kuma na miki alƙawari da yardar Allah ba zan baki kunya ba,kuma ki shirya tarbata a ƙarshen satinnan" "Ƙarshen satinnan kuma?Duka yaushe ka zo? "Ganinki na ke so na ƙara yi Zainab,wallahi ji nake kamar nayi tsutsuwa na ganni a sokoto don kisan irin farin cikin da nake ciki.Wallahi yau ina cikin farin ciki" "Hmmmmmm" kawai na ce na yi shiru,don jin abin nake wani iri.Wai yau ni ke maganar AURE da Ya Bashir,ko ya rayuwar za ta yi da ni yanzu kuma?????? Shirye-shirye kawai suke yi don nikam exam ɗina kawai na sa gaba,bansan in da Lawal ya ji zanyi AURE ba sai kirana yayi da wani sabon layin da bansan shi da shi ba "Zainab ashe AURE za ki yi" ya faɗa bayan mun gaisa "Eh in sha Allah a ƙarshen watannan" na bashi amsa kai tsaye "Allah ya kyauta ya sanya alkhairi,ya baku zaman lafiya,ina miki fatan samun kyakkyawar rayuwar da ta dace da ke.Allah ya baku zaman lafiya" ya faɗa da rauni sosai a muryar shi. "Amin nima na gode sosai" na amsa ina jin wani abu marar daɗi a cikin raina. BASHIR Dama ya san za'a rina,dama ya tsammananci wannan daga gareta idan ta ji maganar auren,amma bai ɗauka abin zai kai haka ba. Tun jiya take kan fashe-fashen kayan ɗakin shi,hatta suturar shi da ke cikin wardrobe duk ta zubo su ƙasa,haka suka kwana har saida ya kulleta a ɗakinta sannan ya samu ya shiga gyara abinda zai iya a ɗakin. Baiyi yunƙurin yi mata komai ba,saboda ya san abin ba daɗi,kuma ƙaunar da ta ke mishi ce duk ta janyo hakan.Shiyasa ya ɗauke Zainab ya kaita wurin Mama don ta kwana a can. Ɗakinta ya tunkara da mukullin ɗakin a hannunshi,tana makure ƙasan ɗakin,ta ɗora kanta akan gadon,ɗakin yayi kaca-kaca da fasasshin kwalabe. Duƙawa yayi gabanta yana kallon yadda fuskarta ta kumbura tayi jajir kasancewarta farar fata. Hannunta ya riƙo yana jin tausayinta na yadda ta ƙuntata rayuwarta a kan abinda bazai fasu ba sai wani ikon Allah "Kiyi haƙuri Baby,na faɗa miki ba don bana sonki zan auri Zainab ba kamar yadda kike tunani,ina ƙaunarki Zubaida,kar ki manta ke fa uwar ƴata ce ɗaya tilo da nake ƙauna.Wallahi banson wannan damuwar ta ki Zubaida" Kanta ta ɗago tana dubanshi da ƙananan idanuwanta da suka ƙara shigewa saboda kuka "To me yasa zaka aureta? Me yasa? Na haɗaka da girman Allah ka janye maganar aurennan,wallahi duk abin da kake so zan maka,har girki zan koya in maka,wallahi duk abin da kake so na maka alƙawari zan koya in maka" Kanshi ya girgiza " Ba saboda bakya min girki zan yi AURE ba Zubaida,ina so ki kwantarda hankalinki ki daina ƙuntata kan ki akan wannan maganar,an riga an rubuto zan AURE ki daga baya in AURI Zainab" "Ƙarya ka ke,tun farko haka ka tsara,mugu kawai,azzalumi mara adalci" ta faɗa da hargagi tana miƙewa tsaye,shima miƙewa yayi yana kallonta tare da nuna kanshi. "Ni ki ke kira da waƴannan munanan sunayen Zainab? "Na faɗa,kayi duk abin da za ka yi,wallahi ba zan taɓa yafe muku ba kai da duk wanda ke da hannu a ƙulla wannan Auren na zalinci" Juwaya yayi tare da barin ɗakin gudun yayi mata abin da bai kamata ba,saboda abin nata ya fara wuce gona da iri. Ɓangaren mahaifiyar shi ya nufa,a falon ya sameta suna magana da Anty Halima a waya.Da gudu Zainab da ke falon ta rungumeshi tare da haye ƙafafunshi. Sai da suka kammala ta dubeshi "Maganar kayan lehen Zainab muke yi,ya kamata ka tura mata kuɗi ta haɗa abinta,da har nace a haɗa nan shine Halima tace a tura mata zai fi" Kanshi ya shafa "Lehe kuma Mama? Harararshi ta yi " To da me kake tunani?Wallahi duk abin da ake sai ka mata don bazan yarda ba,garama ka shirya da kuɗi zaka fitar tunda kace ƴata kake so" Murmushi yayi "Shikenan zan kira Sadiyar inji yadda za mu yi" "Haka ya kamata,kuma ka ci gaba da lallaɓa matarka,karka biye mata.Abin ba daɗi dole ka mata uzuri,Allah ya haɗa kansu ya basu zaman lafiya,kai kuma ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu" RUMAISA'U SIDI AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI FARAR ANIYA WRITERS Page 28 Shirye-shirye ake ta kowane ɓangare,kowannen su ji suke kamar yanzu ne za su aurar da ƴaƴan nasu abubuwa ake shiryawa na kece raini. A ɓangarena kuwa exam ɗina da ke tunkaroni na fi mayadda hankalina akai,wani lokacin har mantawa nake da wani maganar AURE har sai na dawo gida naga yadda su Anty Nasma ke zaƙewa a wannan karon. "Ya Bashir ina so in roƙeka wata alfarma" na sako zancen a lokacin da muke tsaka da fira. "Ina jinki Habibty,kiyi sauri ki faɗa min me kike so? Ko menene zan nemo miki shi da yardar Allah" Ajiyar zuciya na sauke sannan na sanyaya muryata "Ka ga ina gab da fara exam ɗina" nayi shiru jin shima yayi shiru yana saurarena sannan na ci gaba "Ina roƙon ka barni in kammala tukunna" Shiru yayi na ɗan lokaci har na fara tunanin yadda zamu kwashe da shi don banajin zan yadda da wannan wulaƙancin in yi faɗi tashi kan KARATUNA sannan ya zo ya ruguza. "Shikenan,Allah ya bada sa'a"naji ya magantu bayan tsawon lokaci,naji.daɗi sosai don wannan ita ce alfarma ta ƙarshe da zai min. Ana saura sati ɗaya ɗaurin auren Ango Ya Mubarak ya iso,bayan kwana biyu Ya Mu'azzam ya iso tare da iyalinshi shima. Mamaki nake bayan wucewar su,na lura Safwan ya canja min sosai ko jiya da nazo kawo Amna da muka haɗu da su,gaidani kawai yayi yaja hannun Amna suka wuce,yau ma gaidani kawai yayi ya ja hannunta suka shige. Na shiga damuwa sosai,tsorona idan ba wani abu ke damunshi ba,tunanin hakanne yasa na fasa shiga motata na tunkari cikin makarantar. Office ɗin shugaban makarantar na nufa,gaisawa muka yi cikin mutunci kasancewar ta sanni ,roƙonta na yi kan inason magana da Safwan idan ba damuwa. Sanin yanzu ba ma tare da mahaifinsu yasa bata ja ba ta aika aka kiramin shi,tashi tayi tabar office ɗin tana faɗamin akwai zagayen da zatayi,na fahimci ta bamu gurine don in samu in gana da Safwan. Dubanshi nake yadda ya kame a ƙofar office ɗin ya naɗe hannaye idanuwanshi na kallon ƙasa "Meke damunka?" Na jefa mishi tambaya daga inda nake zaune,shiru ya min kamar bai ji ni ba,raina ne ya ɓaci yadda zaka haifi yaro amma kana mishi magana yana wulaƙantaka. Miƙewa nayi a fusace tare da isa inda yake zaune na fizgoshi da ƙarfi "Ba magana nake maka ba?" na daka mishi tsawa raina na ƙara baci. Kuka ya fashe da shi kamar wanda na yiwa mugun duka tare da durƙushewa a wurin,kallon mamaki na bishi da shi,ni dai nasan wannan abin bai kai yasanya shi wannan kukan ba. Komawa na yi inda na taso ina ci gaba da kallonshi har yaci kukan ya ƙoshi kamar wanda aka cewa Ni ko ubanshi Lawal ya mutu har ajiyar zuciya ya ke saukewa. "Me ke damunka?"na ƙara jefa mishi tambaya. Idanuwanshi ya ɗago da suka rine sannan a hankali ya ɗaga laɓɓanshi yace "Mommy dagaske AURE za kiyi?" Idanuwana na zaro "Shine kake wa wannan kukan" Rarrafowa yayi har inda nake zaune tare da riƙe hannuwana "Mommy don Allah kar ki yi AURE,Mommy banason kiyi nisa da mu,Mommy ki dawo gidanmu,wallahi yanzu Abba ya daina faɗa,har kayan daɗi yake siyo min in ci,kema idan kika dawo zai siyo miki.Mommy duk cikin friends ɗina nine kawai Mommynshi ta bar gidansu,don Allah Mommy kiyi haƙuri ki yafewa Abba kar ki AURI wani don Allah" ya ƙarasa tare da kife kanshi akan cinyoyina. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,shi nake gudu tun farko,wannan nake tsoro,yadda rayuwar ƴaƴana za ta kasance.Bayanshi na ke bubbugawa jin yadda yake sauke ajiyar zuciya "Kayi haƙuri Safwan ba zan iya dawowa gidanku ba,amma na maka alƙawarin ziyartarka akai-akai ka daina damuwa ka ji? Fizgewa yayi daga gareni tare da barin office ɗin kamar walƙiya,sunan Allah na shiga kira sannan na tashi jiki mace nabar office ɗin. Tuƙi nake amma gaba ɗaya hankalina baya jikina,banason damuwar ƴaƴana ko kaɗan,shi yasa tun farko naso in tubure kan maganar AURE N nan. Sai ga Safwan har da su zazzaɓi hankalina ya tashi sosai,tsoro ya shigeni,kar fa shima na rasa shi. "To miye don Safwan ba ya son AUREN? Ke kika haifi Safwan ko shine ya haife ki?Wai kina da hankali kuwa Zainab? kan yaron za ki ɗaga AUREN?Wallahi zai fi miki kyau ki kawadda shirmen Safwan a gabanki,mahaifinshi yake tayawa kishi,ki ƙyaleshi kawai kiyi harkar gabanki" Shiru nayi ina sauraren bayanin Anty Halima da ke jin kamar ta shaƙo wuyana,ƙoƙarin kawadda tunanin nayi a gefe kuma ina lallashin Safwan da kullum ƙara tubure min ya ke. Yau ma lallashinshi na ke amma sai wani tuburewa yake kamar shine gaba da ni "Ni gaskiya Mommy ba wani AURE da zaki yi,yanzu shikenan da kinyi AURE kin daina sonmu,wataƙila ma zaki manta da mu,ni wallahi idan har za kiyi wannan AUREN to ba ruwana da ke" Tsawa na buga mishi tare da tureshi daga lallashin da nake mishi "Je kayi duk abinda kake da niyya ina ruwana?AURE ne bazan fasa yi ba idan ma haɗiye zuciyarka za ka yi saidai ka yi,kar ka ƙara kulani ka ji ko?Na ce karka ƙara kulani,ka gani zan rayu ko bazan rayuba,ai ba kai kaɗai na haifa ba.Kaje kayi duk abinda kake so"daga haka na juya tare da barin makarantar. Shareshi nayi na ci gaba da harkokin gabana,ana gobe za'a yi ɗaurin AURE Gwaggo ta iso tare da Ango Ya Bashir.Ba yadda baiso mu haɗu ba ranar amma naƙi fita. Banyi mamakin rashin zuwan Matarshi ba,saboda dama nasan akwai kallo tsakanina da ita,don na lura ɗanyar haukace da ita,amma ba komai nima nayi training a hannun Dr Lawal zan bita yadda ya dace. Washe gari dubban mutane suka shaida ɗaurin AURE NA da Ya Bashir akan sadaki mafi daraja daga nan kuma aka wuce gidan Amaryar Ya Mubarak. Shigewa nayi ana hidimar bikin Ya Mubarak,ina ɗakin Ummi ina gauda baƙinta da ta naje na gaisar aka ce ana sallama da ni. Mayafin Lace ɗin da ke jikina na ɗora a kaina tare da tunkarar waje,daga inda ake aje motoci na hangeshi,wurin ne kawai yake da damar jama'a amma ko ina mutane ne wasu daga ɓangaren Ummi wasu kuma dangine na ƙauye. A tsaye yake cikin kamilalliyar shigar Yadi ya kafa hula a kanshi,murmushin ƙarfin hali ya aro ya watsawa fuskarshi bayan isata wurin. Sallama na mishi ya amsa muka gaisa cikin girmama juna "Zainab an ɗaura AURE,Allah ya kyauta ya sanya alkhairi" "Amin ya Allah" na amsa ina jin nauyin kallon idanuwanshi yadda naji muryarshi ta sanyaya sosai. "Bamu samu gaisawa da Angon ba,ya na ta hidima da baƙi,ina mishi Allah ya kyauta,ina kuma yi mishi barka da samun wannan kyautar ta ubangiji" Murmushi na yi tare da juyawa jin takun tafiya a bayana,Ya Bashir ne cikin wata dakakkiyar shadda,sai maiƙo take fara ƙal,ga hular da ya kafa kai daga ganin hular kasan ba ƙananan kuɗine suka ɗauko ta ba. Hannu Lawal ya bashi,sai da ya ɗan ja sakanni sannan ya bashi sukayi musabaha.Kallona yayi "Ki shiga ciki ko" Jiki a sanyaye na koma cikin gidan,ɗakina na wuce kai tsaye a can na sami Safwan zaune tare da Amna sai Labari take bashi shi kuma yana shareta. Kallo ɗaya na mishi na kawadda kaina,ɗakin nake ƙoƙarin bari ya riƙo hannuna da ƙarfi "Mommy don Allah kiyi haƙuri,ba zan ƙara ba" Hannunshi na cire daga nawa "Shikenan naji" na faɗa ina ɗago wayata dake ƙara,karawa nayi a kunnena bayan na ɗaga. "Ki same ni bayan gida"daga haka ya kashe wayar ƙittt. Ta ƙofar kitchen na bi kasancwwar wajen akwai mutane sosai,tun daga nesa na hangeshi a tsaye ya soke hannayenshi a aljihun wandonshi ya cire babbar riga saɓanin ɗazu da yake sanye da ita. Sallama na mishi bayan na isa inda yake,amsamin yayi sannan ya tambayeni baƙi nace Alhamdulillah. "Layinki na ke so ki bani"ya faɗa yana miƙo min hannunshi "Layina kuma?Da shi fa nake aiki,komai nawa da shi nake yi" Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa ya shiga zarya a wurin "Ba zan iya ba,ko da can da ban mallake ki ba,baki san irin ƙunar da nake ji idan na ganki da wani ba,bale yanzu da kike tawa ni kaɗai,Zuciyata ba zata ɗauka ba" "Lawal ne fa Yaya kuma..............." "Akwai banbanci tsakanin Lawal da sauran maza?Ba wani banbanci Zainab" Duƙewa wurin nayi na ɓarke da kukan da ni kaina bansan dalilin yinshi ba. Shima duƙawar yayi "Kuka kuma Zainab? Ni wallahi ban yi don in ɓata ranki ba,amma kiyi haƙuri don Allah ki daina wannan kukan banason kukanki kinji" Lallashina ya shiga yi kamar wata jaririya abin da na kasa samu a inda na fito,ni kuma sai ƙara narkewa nake ina shagwaɓewa. RUMAISA'U SIDI AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI FARAR ANIYA WRITERS Page 29 BASHIR A matuƙar gajiye ya isa garin Kaduna,cikin kasala ya fito daga motar tare da rufeta,sanin ya baro Mahaifiyarshi a can yasa kai tsaye ya tunkari ɓangaren Mahaifinshi da ya dawo tun jiya bayan gama ɗaurin Aure. Cikin matuƙar girmamawa ya gaidashi,ya amsa yana tambayarshi hanya da kuma mutanen Sokoto. Ya doshi ƙofar fita maganar Abba ta dakatar da shi "Idan ka huta kazo akwai maganar da na ke so muyi" duƙadda kanshi yayi sannan yace "To Abba" daga nan kuma ya fito tare da wucewa ɓangarenshi. Tunda ya isa ƙofar shiga ya fahimci ba kowa a gidan,gabanshi ne ya faɗi ganin yadda falon ya koma kamar inda aka yi yaƙi. Komai an canja mishi mazauni,hatta da kujerun falon sun tabbata anyi yaƙi a ciki,hotunansu da ke manne akan bangon falon suma duk an sauko da su,ga komai nan a harmutse. Raɓawa yayi ya shiga tare da tunkarar ɗakinshi don ya san wannan haukar ba iya nan ta tsaya ba "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"ya faɗa tare da dafe goshinshi ganin irin ta'asar da ta mishi a ɗaki. Kamar dai waccan rana,yau ma duk wata sutura tashi ta fitar da ita,takardunshi ma gasu a watse a tsakiyar ɗakin.Saurin matsawa yayi ganin ledar da sababbin kayanshi na angonci suke ciki,shekaran jiya ya karɓo su ya na sauri bai tsaya jerasu a wadrobe ba ya nufi Sokoto. Ɗaga wandon Shaddarshi mai tsada yayi yana kallon yadda Zubaida ta maida wandon three-quater kamar na ɗan yaro,rigar wani yadin ya ɗauko yana kallo ita kuma an rabata biyu an maida rigar kamar wata vest.(Kai Zubaida baki da kirki) Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya kalli scissors ɗin da ta yada a ƙasa bayan ta ƙare wannan aiki.Raɓawa yayi gefen gadon ya zauna tare a dafe kanshi da yake jin kamar zai cire. Me ke damun Zubaida?Yanzu haukar tata har ta kai ta wulaƙanta sutura? Ko kuma shima wannan kishi ne? Daƙyar ya samu yayi wanka bayan ya wanke toilet ɗin saboda yadda yake ƙazantar komai na ɗakin sakamakon wannan haukar da ke ciki.Kuma shi sam baya jin zai iya gyaran wannan gidan. Ko da ya fito bai damu da shiga ɗakinta ba,ɓangaren ya bari bayan ya kulleshi sannan ya tunkari masallaci jin an fara kiran sallar Magrib,sai da yayi Isha sannan ya wuce ya siyo abinci. Bayan ya dawo ɓangaren Mahaifinshi ya koma ya samu shima ya dawo.Wuri ya samu ƙasan carpet ɗin ɗakin ya zauna "Na san ka dawo ka samu matarka bata nan ai ko?" Ya tambaya yana tsare Bashir ɗin da ido"Eh Abba" ya amsa yana ɗaga kanshi. "Jiya bayan na dawo na samu Yayarta tazo sunyi ɓarna a gidan,raina ya ɓaci sosai kuma na musu faɗa daga ita har Amina" Ashe bayan na shigo,janta tayi suka bar gidan,banji daɗi ba sam,abin bai min daɗi ba,abin haushin kuma sai ga Hussaina ta kirani tana faɗa min abin da sam banji daɗin shi ba.Abin da kawai zan faɗa ma shine,gobe kaje ka dawo da matarka,kuma ka ci gaba da haƙuri,ka san halin mata musamman akan kishi,sannan kuma kaji tsoron Allah ka yi adalci a tsakaninsu,kar ka dubi Zainab zaɓin ka ce ita kuma Zubaida ni na tilastama aurenta ka yi amfani da hakan ka wulaƙantata,ba zan ɗau wannan shashancin ba idan kuma har kayi wannan gangancin ka sani bazan ƙyaleka ba" Kanshi ya ƙara sunkuyarwa "In sha Allah Abba,na gode sosai"Zaman shi ya gyara sannan yace "Abba don Allah key ɗin ɓangaren Mama na ke so ka bani,saboda ba zan iya zama a wancan ɓangaren ba,na kira masu gyara da safe za su zo su gyara" Tsakiyar falon yayi tsaye bayan ya kunna wutar falon,ba wani datti komai tsaf-tsaf ga wani ƙamshi na musamman da ke tashi.Ɗakin da yaga Zainab ta zauna lokacin da tazo ya nufa tare da tura ƙofar ɗakin. Idanunshi ya lumshe bayan ya shaƙi ƙamshin ɗakin,dagaske ƙamshin turaren Zainab ya ke ji,yana masifar son wannan ƙamshin,yana ɗaya daga cikin abin da ya ƙara janshi ga Zainab saboda tsaftar ta da kuma ƙamshinta. Wayarshi ya jawo tare da lalubo Number ta bayan ya kwanta akan gadon,bugu biyu ta ɗaga "Haka mace ta gari ke yiwa mijinta,bayan ya bar gari yana hanyar tafiya?" ya faɗa bayan ya amsa sallamar da ta mishi Shiru tayi sanin batada gaskiya "Kayi haƙuri,muna exam ne kuma koda na fito ban samu na kira ba,sannan da na dawo gida ma......." "Shikenan ya wuce,amma dai idan nayi tafiya a riƙa kulawa da ni" ya katseni daga jerin kumbun da na faro mara dalili "Ka isa lafiya?Ina takwarata?" "Lafiya lau na isa,takwarar ki ma tana lafiya,Ina su Amna? Ko Safwan ɗin ya koma? "A'a gasunan duk lafiya lau suke"na faɗa ina kallonsu Safwan da ke game a system ɗina. Fira muka ci gaba da yi daga ƙarshe yace in kaiwa Gwaggo wayar yana masallaci sun yi magana amma bayan ya fito ya kira yaji wayar kashe. A falo na samesu na vata wayar tare da shaida mata Ya Bashir ne,sannan na bar falon ina hararar Anty Halima da ke ƙifta min ido. LAWAL Ba ƙaramar jarumta yayi ba wurin hana kukan da ke taso mishi bayyana.Wai yau shine a tsaye a gaban Zainab yana taya ta murnar Aure da wani,yau a gabanshi wani ke nuna ikon shi a kanta,a gabanshi ta zaɓi bin umurnin wani. Daƙyar ya kai kanshi gidan Mama bayan mai mashin ya aje shi a bakin titi,kamar ɗan maye haka ya shiga gidan yana layi. "Subhanallahi Lawwali lafiya"? Mama ta faɗa tana miƙewa daga gawayin da take hurawa ganin yadda ya shigo gidan kamar wanda baya hayyacin shi. Cikin sauri ta shimfiɗa mishi tabarma tare da jawo hannunshi ta zaunar da shi,ruwa ta ɗebo masu sanyi ta bashi tace yasha.Ba yada zaɓin da yafi ya buɗe baki ya sha ruwan,shan ruwan ya ke da fatan zuciyar shi ta sanyaya daga zafin da take mishi. Wani irin yunƙuri yayi,da sauri ya sauka daga kan tabarmar ya shiga kelaya amai kamar zai amaye hanjinshi,ba komai a cikinshi bayan ruwan da ya sha yanzu,rabon shi da cin abincin kirki tun da yaji auren Zainab,yau ma ko ruwan shayin da ya ke sha bai sha ba,Safwan kawai ya haɗawa. "Innalillahi ba ka da lafiya?bari in ɗakko hijabi hijabi muje asibiti" ta faɗa tana zuba mishi ruwa yana kuskure bakinshi.Komawa yayi ya kwanta tare da lumshe idanuwanshi yana jin yadda bugun zuciyar shi ke canjawa. Fitowa Mama ta yi da hijabi a hannunta"Bari in kira Yayarka ta same mu a asibiti" ta faɗa tana lalubo Number Anty A'i" Idanuwanshi ya buɗe tare da ƙoƙarin tashi zaune "Kar ki kira ta Mama,maganin damuwata ba a asibiti yake ba Mama,Allah ne kaɗai zai yaye mini abin da ke damuna" Zama tayi gefenshi tana kallonshi "Subhanallahi,damuwa kuma Lawwali? Ko jarin kayan miyan ne ya karye?" ta faɗa tana tsareshi da ido. "Zuciyata ce ta karye ba jarina ba Mama,Mama yau aka ɗaurawa Zainab aure,yau a gabana wani ke nuna ikonshi akan Zainab Mama,shikenan na rasa Zainab Mama,wani ya ɗauke abin da ni na kasa sanin muhimmancin shi sai da yayi nesa da ni Mama,ya zan yi? Ki faɗa min ya zanyi Mama?" ya ƙarasa yana ɓarkewa da kuka tare da kife kanshi ƙasan tabarmar. Hannu tasa ta ɗauke hawayen da suka sakko mata na tausayin ɗan nata,ta daɗe tana gudar mishi irin wannan rana amma ya kasa fahimta,ta daɗe ta na nuna mishi muhimmancin Zainab amma yaƙi ganewa. Ba Lawal ba ita kanta lokacin da taje labarin auren ta taya Lawal jimamin rashin Zainab,saboda bata tunanin akwai sakaran namiji irin Lawal da zai same kamar Zainab yayi sakacin da za ta suɓuce mishi. Hannunshi ta riƙo cikin wani irin tausayi da ke tsakanin uwa da ɗanta cikin matuƙar raunin murya take faɗin "Kayi haƙuri Lawwali,dole ka yi kuka,kayi rashin mata ta gari,shi nake nuna ma tun farko amma ka kasa fahimta,ina roƙon kaima Allah ya baka mata ta gari kamar Zainab ɗin" "Babu ta,wallahi Mama babu kamar Zainab,ba wadda za ta soni kamar Zainab,ba wadda zata tausaya min kamar ita,kuɗi,kuɗifa take bani Mama,wallahi kuɗinta ta ke bani nayi jari,har zinarenta fa ta bani Mama.Wallahi ba macen da zata iya yi min abin da ta min" Ko da yaje kwanciya kasa bacci yayi,hatta abincin da Mama ta zubo mishi tace ya ƙara ci idan yazo, kasa ci yayi,wata irin nadama ya ke yi,na yadda rayuwar shi ta kasance a baya.Gashi baƙar zuciyar shi ta janyo mishi asara da yawa. Na farko ya kasa tsayawa ya nema da ƙarfinshi,yana ganin duk sana'ar da zai kasa a kasuwa azo a siya ɓata lokacine wanda ya wahaladda shi sosai. Sannan wannan yayi silar mutuwar aurenshi da Zainab,macen da ta taimaka mishi,ta kuma rufa mishi asiriasiri,a silar ta ya mallaki gidan da yake zaune a yanzu,a silar ta ya samu motar hawa,kai a silarta ya samu komai ma. Wannan halin da ya ke ciki na rashin sana'a yasa ya rasa ƴarsa,abar sonshi,wadda bai shaƙu da su ba,sai bayan tafiyar mahaifiyar su. Yau gashi ya rasa Zainab,yana kallo wani ya ɗauketa,ta mishi nisa. Nagode sosai da Addu'o'in ku kuma na samu sauƙi Alhamdulillah RUMAISA'U SIDI AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI FARAR ANIYA WRITERS Page 30 Washe gari sai bayan ya taso aiki sannan ya tunkari gidansu kamae yadda mahaifinshi ya jaddada mishi ko yau da zai fito. Ba ya jin zai ƙyaleta wannan karon taci bulus,dole ya nuna mata shima namijine ba wai tsoronta ya ke ba da yake ƙyaleta saboda ya lura haukarta sam batasan Allah ba. A bakin tangamemen get ɗin gidan ya shiga doka horn,da gudu mai gadin ya fito tare da shiga kiciniyar buɗe get ɗin. Cikin girmamawa ya duƙadda kanshi tare da gaidashi,amsawa yayi tare da ɗebo kuɗi ya damƙa a hannunshi. Amsa mai gadin yayi yana ta murna,Allah ya gani yana matuƙar ƙaunar zuwan bawan Allah nan saboda kyautatawar da ya ke mishi,lokuta da dama a zuciyarshi yana mamakin yadda Bashir ke zaune da Zubaida saboda sam batada kirki,halayensu sun banbanta. Sallama ya shiga dokawa a ƙofar falon amma shiru ba amsa,duk da daga inda yake yana hango yayar Zubaida wato Amina da kuma mahaifiyarsu. "Wai kai baƙone da sai an amsama sallama zaka shigo" Mahaifiyar zubaida da suke kira Anty ta faɗa cikin tsawa Shigowa falon yayi tare da duƙawa gabanta "Barka da yau Mama,na same ku lafiya" "Lafiya"ta faɗa tare da ɗauke kanta Shiru falon ya ɗauka kamar ba kowa sai shine ya gaji da zaman ya magantu "Mama na zo tafiya da Zubaida ne" Wani kallon wulaƙanci ta bishi da shi "Saboda Zubaidar ƴar roba ce ko? Ko an gaya ma na gaji da ita ne? To ban gaji ba,har yanzu ina ƙaunar ƴata kamar yadda uwarka Dije ke ƙaunarka.Wallahi Bashir Zubaida tafi ƙarfin wulaƙanci a wurinka,duk rashin mutuncin da kuke shiryawa kaida Uwarka ba wanda bansani ba,to wallahi ba zan ɗauka ba ehe,dole ka zaɓa ko Zubaida ko ƴar Dije don ƴata bazata yi kishi da zuri'ar Dije ba wallahi" Daga haka ta miƙe tare da nufar ɗakinta,dakatawa tayi tare da dafa ƙarfen matattakalar "Na baka yau zuwa jibi,kaje kayi tunanu kuma ka zaɓa tsakanin ƴar uwarka ko ƴar uwar Dije"daga haka ta haye sama. Miƙewa yayi tare da ƙoƙarin barin ɗakin,ranshi ya ɓaci matuƙa,ba yau ta fara zagin mahaifiyarshi a gabanshi ba duk lokacin da zasu haɗu sai tayi haka.Ya rasa me Mama ta tare mata da kullum bata faɗar alkhairi a kanta. Yana ƙoƙarin buɗe motarshi ya shiga motar gidan ta shigo tare da yin parking,da mamaki yake kallonta tana janye da hannun Zainab,itama kallonshi ta ke kamar taga baƙuwar halitta. Fasa buɗe motar yayi ya tsaya yana kallonta "Yanzu haukar taki har ta kai matakin da zaki fita bada izini na ba?" ya faɗa cikin matuƙar ɓacin rai tare da shafa kan Zainab da ta zo da sauri ta rungume shi. Ɗaure fuskarta tayi "To ai yaji nayi don haka ba ƙarƙashin ikon ka nake ba"ta faɗa cike da sakalci. Duƙawa yayi tare da ɗaukar Zainab "Zan je da ƴata,duk lokacin da kika yi ra'ayi kya iya biyo mu daga baya" Ƙoƙarin sauko da Zainab take daga jikinshi "Ni ba inda zanje,in har kana son in koma sai dai ka saki waccan bawarar don bazan iya zama da ita ba" Motar ya buɗe ya saka Zainab sannan ya dubi Zubaida "Ki zauna kina hauka,bazawarar da kike faɗi tazo ta kula miki da miji harma da ƴarki tunda kin maida kanki sakarya"daga haka ya shige motar yaja ya bar gidan. ZAINAB Saida gwaggo ta ƙara kwana biyu sannan ta wuce.A cikin gidan aka kawo.Amaryar Ya Mubarak tanada kirki sosai kamar su Anty Nasma. Anty Halima ko kusan kullum sai tazo gidan da sunan wai shirye-shiryen tarewata,nidai sai dai kawai nayi dariya don nasan yawonta ne kawai ke cizonta. Ita ta haɗani da wata mai gyaran jiki da kuma kayan ƙamshi wadda zan riƙa zuwa wurinta ana min,ba dan naso ba nake zuwa cikin kwana biyu sai gani na fara wani irin kyau na musamman ga ƙamshi duk inda na zauna sai na bar wannan ƙamshin. Yau ma daga makaranta can na wuce kasancewar yau muka yi exam ɗin ƙarshe,sai bayan da aka ƙare gyaran jikin na maida niƙab ɗin da na tsiri sakawa tunda aka fara gyarannan. Wayata na ɗauko na lalubo number Ya Bashir na doka mishi kira,kashewa yayi sannan ya kira kamar yadda yake min kullum. Saita muryata nayi cikin wata ƴar shagwaɓa da na fahimci na koya a yanzu "Ya barka da aiki" Daga cikin wayar ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Barka dai Amaryata,ya ex da kuma shirye-shirye zuwa gidana" Murmushi nayi ina jin kamar ana yawo da ni a sama "Komai lafiya lau,ya aikin"?na tambaya da tsantsar kulawa fahimtar hakan yana ɗaya daga cikin abin da ya ke so. "Aiki ga yanan muna yi Dear,sai dai kewarki da nake" ya faɗa kamar wanda zai yi kuka. Ƴar ƙaramar dariya nayi sannan nace "Ya don Allah ina son in shiga wurin Hafsat idan ba damuwa" na sako buƙatar da ta sa nayi kiran tun farko. "Allah ya tsare hanya,amma ki tabbata kin saka niƙab da safar da na gaya miki kinji ko?" "Zan saka Yaya,Na gode sosai" "Na faɗa miki banson wannan Yayan ko? ko haka kika ji Zubaida na kirana?" Ɗaure fuskata nayi "To ni miye damuwata da ita bale abin da take kiranka?" na faɗa ina jin wani ƙololo ya tokare min maƙoshi tare da kashe wayar jin dariya ma ya ke min Sallama na yiwa matar tare da fitowa daga gidan,napep na tara na shiga sai gidan Hafsat uwar rigima Rungumeni tayi cikin matuƙar farin ciki "Wallahi na ɗauka wasa kike da kika ce zaki shigo"harararta nayi ina cire niƙab ɗin fuskata tare da hijabin. Sakin baki tayi tana kallona har na zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon "Malama ya da wannan kallon?" na faɗa ina ɗage girata ɗaya ganin yadda ta zuba min idanuwa "Wai kinga yadda kika koma Zee? Irin wannan kyaun ga wannan mayen ƙamshin,wallahi har na fara tausayin Zubaida,Allah sarki Zubaida baiwar Allah" ta ƙarasa tare da tafa hannuwanta. Harararta na ƙarayi "Allah ya shirya ki wallahi,miye abin tausayi a Zubaida?Ita ma fa kyakkyawace ko kin manta?" Bakinta ta taɓe "Na dai yarda farar fata ce amma daina batun kyau hajiya,kuma wallahi ko da wannan sheƙin kaɗai zaki ƙwace mijin,gaskiya Zee bakida kirki irin wannan ƙamshin ai kin gama yi musu farraqu" Kitchen ta shiga tare da zubo min abinci da kuma kayan sanyi,zama tayi kan kujerar da ke kallon tawa,hannunta tasa ta tallabe kumatu tana kallona kamar ta samu TV. Shareta nayi kamar ban gani ba,har yanzu Hafsat bata canja ba,tana nan da wannan sheɗanar da kuma tsiwa. "Zee" ta kira sunana,ɗago kaina nayi na dube ta "Ya aka yi" Marairaice fuska ta yi "Don Allah ki bar wannan ƙamshin hakan kar ki shiga haƙƙin Zubaida" filon kujerar da ke gefena na wurga mata.Dariya ta rinƙayi sannan ta gyara kwanciyarta kan kujerar. Saida na kammala muka kwashi kayan kamar wasu yara muka kai kitchen,sai da muka dawo taja hannuna muka wuce bedroom ɗinta,turaruruka ta shiga kwasomin da kuma kayan gyaran jiki wai ni ta siyawa. "Na gode sosai Aminiyata,kema Allah ya kawo haske a rayuwarki" na faɗa ina ƙara damƙe hannuwanta da ke cikin nawa. Itama ƙwallarce ta cika mata ido "Amin Amin Aminiyata na gode sosai" "Ki kwantar da hankalinki in sha Allah kema matsalarki ta kusa zuwa ƙarshe" Hawayen da suka sauko mata ta ɗauke "Jiya nake ji ashe mahaifiyarshi na nan tana nema mishi auren ƴar wata aminiyarta har ma yaje ya ganta amma ni bai faɗa min ba" ta faɗa tana ƙara ɓarkewa da kuka. Rungumeta nayi "Kiyi haƙuri Hafsat kowa da inda aka jarabceshi ke taki jarabawar kenan,ki kwantar da hankalinki In sha Allah kema kin kusa ganin jininki ki rabu da su duk wadda zasu aura mishi su auro ɗin,ai kowa da halinta za ta zauna bana shakka akan ki Hafsat kar ki ɗaga hankalinki don Allah" Lallashinta na shiga yi da kalamai masu daɗi ina jin wani tausayinta na kamani.Dama daga anyi aure shekara ɗaya,biyu ba a haihuba sai ƙananun zance su fara tashi.Bale kuma Hafsat da aurensu keda shekara 5 amma ko ɓari bata taɓa yi ba. Har dangin mijin suka fara magana,duk da bata fuskanci wata matsala daga mijinta ba amma ƴan uwanshi sune matsalarta. RUMAISA'U SIDI AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI FARAR ANIYA WRITERS Page 31 Cikin iyawar ubangiji na kammala karatuna cikin ɗumbin nasara.Na samu taya murnar kammala karatuna tare da kyaututtuka na musawalir daga ƴan uwa da kuma abokan arzikina. Ana gobe zan tare na haɗa ƙwarya-ƙwaryar walima a gidanmu ƴan uwana ne da kuma ƙawayena,har da su Mariya ƴan uwan Lawal sun zo yimin kara.Nasha kyau a ranar cikin wani haɗaɗɗe kuma tsadadden lashin da na saka wanda yake ɗaya daga cikin kayan da na ɗinkawa kaina da maƙudan kuɗaɗen da Ya Bashir ya bani yace na haɗa lefe na. Washe gari muka ɗau hanyar kaduna tare da rakiyar Anty Halima,Anty Hafsat da kuma Hafsat da ta dage sai ta rakani gidan Ya Bashir,saɓanin aurena da Lawal da ta kafe bazata rakani ba. Shiru nayi a motar ina jina kamar ba ni ba,lumshe idanuwana nayi tuna ƴaƴana da na baro,lokacin da zamu tashi naga yadda Safwan yaja hannun Amra suna kuka.Mahaifinshi ne ya kawoshi don sumin sallama a cewarshi. Ya kuma yimin maganar dawowar Amna hannunshi tunda aure zanyi,Wataƙila ya ɗauka da ita zanje,nace mishi wurun Ummi zan barta. Tarba ta musamman muka samu a gidan kamar wasu baƙi,ɓangaren gwaggo muka sauka aka shiga hidima da mu,na kasa sakin jikina duk irin faɗan da gwaggo kemin na in saki jikina.Na kasa wannan zuwanfa yana da banbanci da sauran zuwan da na saba. Sai dare angon ya shigo sai watsar baki yake kana kallonshi zaka fahimci irin farin cikin da yake ciki ko kunyar mutanen falon baya yi ya kafamin ido. Tashi nayi na bar falon jin yadda duk na takura da wannan mayen kallon nashi,ina ɗakin kwance Anty Halima ta shigo "Taso muje kar mijinki ya ƙwaƙulemin ido"ta faɗa tana jan hannuna Fizgewa nayi ina kallonta "Haba dai yanzu sai in ratsa mutanen da ke falon inje wurinshi ni ga shugabar marasa kunya" Hannuwanta ta watsa "To shine me? Kinga wallahi ki tashi yana bayan gida yana jiranki,idan ba haka ba zan kirashi in faɗa mishi kince ba zaki je ba.Kuma wallahi kinsan halinshi tsaf zai shigo ɗakinnan" Mayafina na ɗora a kaina muka fito,ta ƙofar kitchen muka bi saboda ina kunyar in ratsa su gwaggo in fita,in don ta Hafsa da Anty Nasma mai sauƙice amma ina jin kunyar gwaggo sosai. Takowa yayi har inda muke yana hararar Anty Halima "Shine kika shanya ni ina zaman jiranki ko?" "Wallahi ba laifina ne ba,laifin Amaryarka ce gatanan"ta ƙarasa tana nuna ni Murmushi yayi tare da gyara tsayuwarshi yana fuskantata "Wa ya gaya miki Amarya na laifi Sadiya? Musamman ma irin tawa Amaryar" ya faɗa yana ƙoƙarin lallai sai mun haɗa ido dashi Tafi ta buga sannan kamar wadda ta tuna wani abu tayi saurin rufe bakinta da tafin hannunta.Hanya ya nuna mata "Bi nan,Kin ƙare aikinki na gode"Dariya tasa tana shigewa ta inda muka fito. Matsowa yayi yana ƙara ƙureni da kallo kasancewar wurin akwai wadatar haske kamar da rana,jikina naji kamar ya fara ɗaukar rawa,wannan kalon ya min nauyi "Nema kike ki kasheni da ƙaunarki Zainab,kullum kyau kike ƙarawa na musamman,kamar ba Zainab ɗin da na raina da hannuna ba,kamar ba kece uwar ƴaƴa uku ba" Kaina na ɗago karo na farko na dubeshi jin yadda yake jero zance,a bazata naji hannunshi cikin nawa "Ina ƙaunarki Zainab,ni kaina bansan iya adadin ƙaunar da nake miki ba,don Allah karki gujeni,ki zauna da ni,na miki alƙawari nima zan kula da ke kamar yadda uwa ke kula da jaririnta,zan shagwaɓa ki Zainab,zan nuna miki irin ƙaunar da nake miki,Ina fata zaki bani dama?" ya ƙarasa da sigar tambaya Daƙyar na iya ɗaga mishi kaina alamar "eh" idanuwana suka cika da ƙwalla wadda zan iya kiranta ta farin ciki,na tsammani daga samun irin wannan rayuwar ta farin ciki. A hankali nake ɗaga ƙafata tare da ɗorata gudun farkawar Anty Halima ko Hafsat,na kai tsakiyar ɗakin ina ƙoƙarin ɗaga ƙafar naji sun kwashe min da dariya. Idanuwana na runtse,ba haka naso ba,wallahi sam basuda kirki,shine suka min kamar bacci suke ashe na munafunci ne.Ƙin juyowa nayi na ci gaba da tafiyata na shige toilet ina jin yadda suke min dariya. Washe gari suka shiga shirin tafiya,shiryawa nayi cikin haɗaɗɗiyar atamfa ta na ɗora mayafina na fito a Amarya sak nayi kyau sosai ni kaina nasan wannan. Gwaggo ce ta riƙa hannuna har sashen da yake mallakina a yanzun,ba wancan da Zubaida ke ciki ba,wani ne na daban,addu'o'i ta min kamar yadda ta min lokacin da ta kaini gidan Lawal. Sallama suka min na rakosu har wurin motar da zasu shiga ta kaisu tasha,ji nayi kamar na ɓarke da kuka ganin motar ta bar gidan,sun tafi sun barni kamar yadda suka barni wancan karon. Hannun Zainab na riƙe muka koma tare,na shiga duba gidan komai ya min hatta fentin ɗakina saida Ya Bashir ya zaɓi kalar da nafi so,su Yaya ma sun cancaɗeni da kaya na kece raini kamar wata ƴar gwamna,ba abinda zance sai hamdala LAWAL "Wai Lawal me kake so ka maida kanka? Shikenan sai ka maida kanka sakarai akan wata mace, Saboda Zainab kake nema ka kashe kanka? Kamar itace autar mata?" Da kallo kawai yabi Anty A'i ganin yadda ta zaƙalƙale tana masifa.Mama ce ta dubeta "Zainab ta cancanci duk wani namiji da ya rasata ya shiga wannan halin,kema ƴar nan sai dai in kinƙi gaskiya,amma kema kinsan a yanzu ba macen da zata yiwa namiji abin da Zainab ta yiwa Lawwali.Nima na faɗa mishi ya kwantar da hankalinshi,yanzu dai gwargwado yana cikin rufin asiri,nayi magana da Asabe zai je yaga Nusaiba ƴarta ɗinnan da mijinta ya rasu,yarinyace don iyakarta kamar Zainab ɗin,amma zamanka haka ba zai yu ba" Ba don yaso ba sai don matsawar Mama yaje yaga Nusaiba,ba laifi tanada kyau,ƴaƴanta biyu ɗaya na hannunta ɗayan na hannun dagin mahaifin yaran. Ba wata ƙarya ko bidi'a aka ɗaura auren Lawal da Nusaiba cikin ɗan ƙaramin lokaci kuma Amarya ta tare. Da farko zaman gwanin sha'awa tana nunawa Safwan ƙauna duk da yadda yaron ke ja baya da ita,amma duk dai in Lawal na kusa to kamar ta hadiye shi. Daga baya sai ta tsiri muzguna mishi idan Lawal ya fita,to suma ƴaƴan zamaninnan yanzu sun iya yau ko ka haifi yaro ya ka ƙarasa dashi bale kuma ɗan miji. Tsaye tayi tana girgizar jiki"zaka tashi kaje kayi wanke-wanken nan ko sai ranka ya ɓaci?" ganin ya ƙyaleta yana ci gaba da rubutunshi a littafi yasa ta fizgo littafin tare da watsi da shi tana huci "Ni zaka mayar mahaukaciya?Ina magana kana ƙyaleni,idan uwarka ce zaka mata haka?" Idanuwanshi da suka rine kamar wani babba ya ɗago yana kallonta "Karki ƙara zagin Mommyna" ya faɗa yana huci kamar zaki "Idan na ƙara zagin nata dukana zaka yi"ta faɗa tana riƙe ƙugu tare da zare idonta "If you repeat again,you will regret it" ya faɗa jikinshi na ɗaukar rawa tsaki tayi tare da nufar ɗakinta tana faɗin "Kai dai ka sani,kuma idan har zagina kayi ka zagi uwarka" Bayan Isha'i yana kwance ɗakinsu,kewar Mommynshi yake ji,ita yake son gani,yayi kewarta,yayi kewar girkinta da komai ma nata.Idanuwanshi ya lumshe abin da ya baiwa hawayenshi damar zubowa. "Ka zo mahaifinka na kiranka"ya tsinkayi muryar matannan da ya tsana.Sai da ya shiga toilet ya wanke fuskarshi sannan ya fito. Wurinda mahaifinshi ke zaune ya isa tare da duƙawa yana gaida shi,amsawa yayi yana kallon yadda alamu ke nuna yayi kuka "Me ke damunka?"ya tambaya da kulawa Ɗago kanshi yayi ya dubi mahaifinshi jin ya nuna mishi kulawa kwatankwacin yadda Mommynshi ke mishi "Ba komai" Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Me ya haɗaka da Mamarka tace ka zageta hakane ko ba hakane ba?" Zabura tayi "Au wato ƙarya ma zan mishi kenan" hannu ya ɗaga mata "Ki barni inyi magana da shi don Allah,kai Safwan me ya faru" Leɓonshi na ƙasa ya ciza alamun abun ya mishi zafi "Mommyna ta zaga Abba,kuma ni ba zaginta nayi ba kawai na gaya mata idan ta ƙara zagar min Mommy za ta yi nadama" "Kinji ba,to me mahaifiyarshi ta miki da zaki zageta?"Shima ranshi ya ɓaci da jin maganar "Ba zan ɗauka ba,ki tsaya matsayinki karki ƙara zagar mishi uwa,aiki kuma idan zaki iya kiyi idan bazaki iya ba ki barshi,da me kike so ya ji? da karatu ko da aikinki" Lawal ya shiga surfawa Nusaiba bala'i kamar zai daketa,tsaki ta buga tare da shigewa ɗakinta. Shima tsaki yayi sannan ya saka hannunshi a aljihu ya ciro ƴar ƙaramar leda "Karɓi nan je ɗakinka kaci,tsirai ne na gani nace bari in kawo ma ka saka a bakinka" Hannu biyu yasa ya karɓa yana godiya tare da tashi ya shige ɗakinshi.Da kallo Lawal ya bishi yana jin wata iriyar ƙaunar yaron ta musamman,duk wata ƙaunar da yake yiwa Zainab a yanzu ya tattarata ya mayar kan ƴaƴanta saboda ya san wannan itace kyautatawa ta ƙarshe da zai mata. Kuyi haƙuri da wannan RUMAISA'U SIDI *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *page 32* Kwanakin da suka biyo baya kwanakine na farin cikin da suka shiga sahun manyan ranakun da bazan manta da su ba.Rayuwar Aure muka shimfiɗa a gidan irin ta soyayya da kuma girmama juna. Yana riritani da kuma shagwaɓa ni kamar wata jaririya,duk abin da nake so kai tsaye zai min,duk kuma abin da ya san zai sakani farin ciki to kullum ƙoƙari yake ya min shi. Ban fahimci Zubaida bata gidan ba sai da na kwana 3 a gidan,wanda a ƙa'ida ranar ne zata kama girki. Zaune nake gaban mirrow ina ƙoƙarin ɗaure gashin kaina ya iso tare da tsayawa bayana,duƙowa yayi muna kallon juna ta madubin "Wallahi ji nake kamar kar nayi fitannan"ya faɗa yana ɓata fuska.Murmushi na mishi "To ai ba wata doguwar tafiya ba ce" Ajiyar Zuciya ya sauke tare da komawa bakin gadon ya zauna "Yau me za a dafa muna Baby?wallahi na ƙagu naci daddaɗan girkinki" Dakatawa nayi daga abin da nake sannan nace "Honey ka manta ne yau zan aje girki?" Shiru ya min kamar baya ɗakin fahimtar baison maganar ne yasa nayi shiru nima har na kammala shirina ya riƙo hannuna muka je muka yi breakfast ɗin da gwaggo ke aiko muna kullum sannan na koma ɗaki na ɗauko mayafina don rakoshi. Ɓangaren Gwaggo muka nufa har yanzu hannunshi na cikin nawa,ganin har mun shiga falon baida alamar sakin hannun yasa na shiga kiciniyar ƙwacewa daƙyar na samu na fizgeshi tare da isa inda Gwaggo take zaune na durƙusa ina gaidata. Hannuna ta riƙo tare da zaunadda kusa da ita tana tambayata yadda na tashi "Allah ga bawanka,ba wanda ke tambayar yadda na tashi" Ya Bashir ya faɗa yana taɓe baki kamar yaro zai yi kuka Hararar shi tayi "To dama wa zai tambayeka kai,kinci abinci?" ta ƙarasa tana maida akalar tambayarta wurina "Eh munci gwaggo,mun gode sosai Allah ya ƙara girma,ina Zainab"na faɗa ina raba idanuwa ganin ban ganta a falon ba "Tana can ciki bacci take magani tasha jiya da zazzaɓi ta kwana" shiga muka yi tare a ɗakin,tana kwance sai baccinta take amma zazzaɓin ya sauka. Ƙofa ya tunkara yana yiwa gwaggo sallama,tsaye nayi a tsakiyar falon ina jin kunyar bin bayanshi,lura da hakan da gwaggo ta yi tace "Je ki raka mijinki mana" a hankali na ja ƙafafuwana na bi bayanshi. A bakin motar na same shi a tsaye,hararar wasa ya min "Ai na ɗauka ba za ki zo kimin sallama ba"shagwaɓe fuskata na yi kamar wata yarinya sannan nace "Kai ma kasan da kunya wallahi" Taɓe bakinshi yayi "Kunyar me to" gambun motar na buɗe mishi ya shiga sannan na duƙa ta tagar motar ina kallonshi kamar yadda ya ke kallona. Cikin wata murya da ni kaina bansanin ina da ita sai ina gabanshi nace "Ka kula min da kanka don Allah,ban lamunce ko ƙuda ya taɓa min kai ba har ka je ka dawo,kuma ban yarda ka dubi kowace mace ba" Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Na miki alƙawarin kula da kaina kamar yadda kike so,mata kuma ki daina kawo su a tunaninki daga kanki na daina banbancewa tsakanin mace da namiji" Murmushi nayi har raina naji daɗi saboda a halin yanzu a yadda nake jin ƙaunar Ya Bashir ko Zubaida idan na tuna da ita ji nake ina ma ni kaɗai ya aura. Wata irin rayuwar soyayya muke yi wadda ban taɓa tunanin za a sameta a irin ƙasashen mu na Hausawa ba,ba muda matsalar komai har na manta da shafin wata Zubaida rayuwar mu muke gwanin sha'awa. Satin mu 3 sai ga Zubaida ta dawo,ina zaune ina lissafin kayana ta waya ta shigo falon ta matse jiki da wata fitted gown da ɓingilen mayafi a hannunta. Kallo ɗaya na mata na ci gaba da abin da nake,tsaki ta buga sannan ta nuna ni "Na gargaɗe ki da shiga sha'anina da mijina baki ji ba saida kika shigo,to wallahi ina so ki sani sai kinyi nadama a lokacin da batada amfani,sai na nuna miki ba irin Zubaida ake shigar ma hanci ba,banza kawai mai ƙwacen miji" Har tabar falon ban ɗago kai ba bale kuma na dubeta,wayata kawai nake latsawa ina ƙoƙarin kawadda ɓacin ran da ke tasomin.Maganar gaskiya banji daɗin dawowar Zubaida yanzu ba sam ban kawo yau zata dawo ba,ni sam na ma manta da shiginta. Tsaki na buga tare da shigewa bedroom ɗina na kwanta,sallah kawai ke tadani.Ina jin lokacin da ya shigo falon yana kiran sunana.Runtse idanuwana nayi kamar mai bacci jin ya shigo ɗakin "Wai bacci kike Baby?" ya faɗa yana janye zanen da na rufa kaina. A hankali na buɗe idanuwana na dube shi,ruɗewa yayi ya shiga taɓa wuyana "Lafiya dai Baby,ko bakida lafiya?" Kaina na girgiza tare da sauka gadon na shige toilet na barshi nan zaune,koda na fito baya ɗakin komawa nayi na kwanta ina jin ko ɓangaren gwaggo ba zan iya shiga ba don banason ta tambaye ni meke damuna. Ina nan kwance naji ƙarar sabuwar wayar da ya canja min,shine ke kiran ɗagawa nayi tare da ɗorata saman kunnena tambayata jikina yayi na amsa mishi da sauƙi "Za ki iya zuwa ɓangarena ko mu zo nan mu same ki?" "A'a zan iya" na dakatar da shi,mayafi kawai. na ɗora akan doguwar rigar jikina,ɓangaren nashi yana nan tsakiyar namu ɓangaren. Tura ƙofar falon nayi tare da sallama,suna zaune a falon sai wani shigewa jikinshi ta ke,kallo ɗaya na musu na kawadda kaina tare da samun kujera na zauna. "Baby ya jikin da sauƙi dai ko" ya tambaya yana miƙomin wata leda da ke kusa da shi "Karɓi magani ne na karɓo miki ki samu kisha mu gani zuwa gobe da safe muje asibiti"karɓa nayi tare da yin godiya. Tsaki Zubaida ta buga tare da miƙewa cikin iyayi tace "Darling in zuba maka abincin? Yau dai nima zaka ci girkina" hannu ya ɗaga mata "Ki bari mu kammala maganar da tasa na tara ku anan" Nasiha ya muna tare da jan hankali in da daga ƙarshe ya kawo zancen rabon kwana inda ya tambayi meye ra'ayinmu,ni dai shiru nayi sai itace tayi magana "Yanzu dai Darling kaga sai an fara biyana kwanaki na da aka ci" "Wane kwanaki kuma?" ya faɗa yana tsareta da ido kamar yadda nima nayi.Cikin rashin kunya tace "Kwanakina da ka ƙarawa wannan azzalumar mana ai bance na yafe ba" Tsaki ya buga tare da kauda kanshi "Na rasa yaushe za kiyi hankali Zubaida,muna maganar kwanakin da zasu biyo bayane ba zancen ranka kwana ko wani waye,banson tashin hankali na riga na faɗa miki" Bakinta ta murguɗa tare da kauda kanta,guntun murmushi nayi a raina ina ƙara raina sakarcin Zubaida tambayata yayi me na yanke nace duk abin da aka yanke banida matsala.Daga ƙarshe ita tace a barshi kwana biyu,sallama na mishi tare da barin ɗakin. Kuka na ɓarke dashi bayan na zube kan gadona,birgima na shiga yi a kan gadon,ina jin gadon ya mun faɗi ji nake kamar zuciyata zata buga.Sunan Allah na shiga kira ina ƙoƙarin yaƙi da shaiɗaniyar zuciyata dake haskomin abin da bai kamata ba. Ina nan kwance naji ƙarar wayata,ɗaga wa bayi batare da nasan mai kiran ba,a hankali naji muryarshi "Baby idan akwai abinci wurinki ki zubo min ki kawo min ɓangarena" Har naji kamar nace babu amma sai naga rashin dacewar hakan shiyasa na amsa mishi da "To" tashi nayi na shirya mishi abincin da na dafa na kasa ci. Ɓangaren nashi na nufa dashi tare da yin tsaye a wajen na kira shi "Ka buɗe ka karɓa" na faɗa bayan ya ɗaga kiran "Ki shigo a buɗe ta ke" ya amsamin shima Ba don naso shigar ba na buɗe tare da shiga falon,yana zaune da remote a hannunshi sai kuma abincin da aka zuba wanda da alama ba'a ci cibi biyu a ciki ba gabanshi na dire kayan "Yawwa Baby Allah ya miki albarka" Amsawa nayi da "Amin" ina ƙoƙarin tashi "Ki zuba min mana" ya dakatar da ni. Zuba mishi nayi tare da janye wanda ke saman center table ɗin nakai gefe "Ki kaishi kitchen kawai"ya umarceni kaiwa nayi tare da wanke hannuna na fito wanda yayi daidai da fitowarta daga bedroom cikin shirin bacci. Ƙugunta ta riƙe tana kallonshi "Kam balastinnnnnn wato nawa abincin ne ba zaka ci ba kenan" *RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️ *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *page 33* Takowa tayi har gabanshi tana kallon abincin da na zuba mishi,maida kallonta tayi a kaina ƙwalla na taruwa a idanuwanta "Yanzu saboda tsabar wulaƙanci ranar girkina zaki kawo mishi abinci" Ji na nayi wani iri saboda nima sai yanzu nake jin ban kyauta ba domin kuwa idan nice ba zan ji daɗi ba duƙawa nayi da niyar tattara abincin "Kar ki taɓa komai,za ki iya tafiya" A sanyaye na bar ɗakin,koda na koma ɗakina daƙyar bacci ya ɗaukeni ina mai addu'ar Allah ya kareni daga shiga haƙƙin matar nan,saboda a duniya ba babbar asara kamar ka bari haƙƙin wani ya kaika wuta. Kuka ta fashe da shi bayan Zainab ta bar ɗakin "Wai Ya Bashir me na maka da ka tsaneni har haka? Ance ban iya girki ba na fara koya saboda kai amma yanzu na maka girkinnan kace bai yi daɗi ba,ai sai kace in dafa ma wani abun amma shine zaka kirata ta kawoma abinci saboda ka tozarta ni,ka nuna mata banida wani girma a idonka" Hannunta ya riƙo tare da zaunar da ita gefenshi,hawayenta ya shiga sharewa yana jin ba daɗi a ranshi "Shikenan kiyi shiru,tunda bakyaso baza a ƙara ba yanzu bari in dafa mana ko indomie ko?" kanta ta gyaɗa mishi. Shi ya dafa musu indomie ya zubo a plate suka ci tare,nan take sai ga Zubaida ta saki ranta suna zuba hira ita da mijinta. Washe gari a sukwane na tashi na gyara gidana tare da dafa ruwan shayi sai ƙwan da na soya,kamar dole haka nake shan tea ɗin saboda yadda nakejin bakina yana ɗaci,na rasa me yake min daɗi. Ina breakfast ɗin ya shigo yayi kyau sosai cikin coffe colour ɗin yadi,sallamar shi na amsa ina ƙara kurɓa ruwan tea ɗin da ke hannuna "Ina kwana" na gaida shi da ƙyar "Kin tashi lafiya,ya jikinki" ya tambaya da kulawa tare da ajiye briefcase ɗin dake hannunshi,zama yayi kan kujerar da ke fuskantata "Har yanzu jikinne" ya tambaya ganin yadda take cin magani. Kofin na ajiye tare da girgiza kaina "A'a naji sauƙi Alhamdulillah" tasowa yayi daga inda yake zaune ya dawo inda nake,hannuna ya riƙe "To meke damunki? Ki faɗa min don Allah" kuka na ɓarke da shi tare da ɗora kaina akan kafaɗarshi,lallashina ya shiga yi. Saida ya ga na ware sannan ya bar gidan,ɓangaren gwaggo na shiga acan ma nayi rabin yini,na warwarewa Zainab kanta na mata sabon kitso. Haka zaman namu ya ci gaba da kasancewa,Zubaida bata daina shigar min hanci ba,wani lokacin na ƙyaleta wani lokacin na kulata,kuma ina ƙoƙarin nusar da Ya Bashir akan kwatanta adalici a tsakaninmu. A ɗan zaman namu na fahimci Zubaida sam bata san wani kula da miji ba,ɗan girkin ma da ta fara yanzu ta daina,mai aikinta ke yi kamar yadda take yi tun farko,ba ruwanta da ƙamshi za dai tayi wankanta tsaf ta fito ƴar ƙwalisa ammafa ba ƙamshi,bata sarrafa harshenta lokacin da zata mishi magana,ko rigima suka yi bata ɓoye hakan ko a gaban waye zata nuna sun sami matsala,kuma ba ruwanta har gurin mahaifiyar shi za ta kai ƙararshi wanda wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya ƙara kada ƙimarta a idon Gwaggo. Ƴan uwanta ma idan suka zo indai zamu haɗu to sai an yada min habaici,ni wani zubin ma dariya suke bani don kusan har na haddace abin da suke gaya min duk lokacin da muka haɗu "Bazawara kawai mai ƙwacen miji" shine kawai abin da suke faɗa. Result ɗina ya fito Alhamdulillah kuma na samu nasara,a lokacinne nayi shirin zuwa sokoto don ganin ƴan uwana da kuma ƴaƴana,duk da kowannensu muna waya don ko Safwan idan ya sami dama yana kirana da wayar tsohuwar maƙociyata Maman Haidar. *LAWAL* Zaune yake a ƙofar gidan yana ƙoƙarin sallamar yaran da ke miƙo mishi kuɗi don ya sallame su.Dakatawa yayi daga ƙoƙarin saka tattasan da ya ɗebo da niyyar zubawa a leda ganin wani mai irin uniform ɗin makarantar secondary ɗin da ya kai Safwan bayan ya kammala primary ya sauko daga napep ɗin da ta faka.Sai ga Safwan ɗin shima ya fito,sakin ledar hannunshi yayi tare da miƙewa ganin yadda yaron ya riƙo Safwan alamar bayada lafiya. "Subhanallahi me ya same shi" ya faɗa yana kama Safwan ɗin ya shige dashi cikin gida,akan kujerar falon ya kwantadda shi tare da sheƙawa da gudu kamar wani yaro yayi kitchen,bai jima ba ya fito da ruwa a hannunshi tare da zama kan kujerar ya ɗaga Safwan yana ƙoƙarin saka mishi kofin ruwan a bakinshi amma ya ƙi karɓa "Wai me ya same shine"ya ƙara tambayar yaron kamar zaiyi kuka "Wallahi Abba ban sani ba,kawai an tashi daga makaranta mun fito har mun ɗanyi nisa naga ya faɗi nayi ta tada shi bai tashi ba,shine na tari mai adaidaita na kawoshi gida" Nusaiba ya shiga ƙwallawa kira yana girgiza Safwan ganin jikinshi ya fara saki saɓashi yayi a kafaɗarshi ya nufi ƙofar fita a harmutse.Wani abokinshi da ke zama wurinshi ya roƙa da ya kwashe mishi kayan asibiti zai je. Da sauri likitoci suka karɓe shi ganin halin da yake ciki,kaikawo ya shiga yi a ƙofar ɗakin da aka shiga da Safwan,ji yake kamar ya sa kuka,me ya samu yaronnan? Me zai cewa Zainab,kardai shima Safwan mutuwa zai yi kamar yadda Aysha ta mutu,kar dai dagaske bazai iya riƙon ƴaƴanshi ba"Allah ka kawo min ɗauki" ya faɗa yana goge zufar da ke wanke mishi fuska. Magunguna aka rubuto da allurai da ruwan da za a saka mishi da sauri ya haɗa ƴan kuɗaɗen da ke aljihunshi ya nufi wurin siyen maganin saida aka haɗa komai akayi lissafi kuɗin kayan sun kama 16k aljihunshi ya shiga lalabawa bayan ya lissafa dubu bakwai da ɗari biyar ɗin da ke hannunshi kallon mai saida maganin yayi "Don Allah ka taimaka min,na duba kuɗina basu kai ba,kamin alfarmar bani maganin na maka alƙawari yanzu zan je na kawoma kuɗinka" Girgiza kai mai maganin yayi"Kayi haƙuri wallahi nima kaga maganinnan ba nawa bane bazai yu in baka maganin mutane ba" ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa yana tunanin tafiyar da zai yi gida ya ɗauko kuɗi duk yaronshi na cikin wannan halin. "Kawo takardar"mai maganin ya faɗa cikin tausayawa "Kamin alƙawarin kawo min sauran kuɗinnan don Allah" "Na maka alƙawari yanzu zan je in kawo ma" Sai da Mama ta iso asibitin bayan Lawal ya kirata sannan ya koma gida don ɗauko kuɗi. Bayani ya kewa Mama bayan dawowar shi daga wurin likita"Kinji wai sun ce zafinnan da ake yi ne yanzu,sanƙarau ne yaso kamashi amma abin bai yi tsamari ba.Ina ganin zan canja mishi makaranta saboda yawan cinkosu tunda yace wajen su 100 suke a aji guda zan yi ƙoƙari in duba wata mai ɗan damar kuɗi in saka shi" Kallonshi kawai Mama ke yi a ranta tana ƙara godewa Allah da ya shirya mata Lawal,wai yau Lawal ne ke nema da kanshi batare da ya duba ƙarancin sana'arba,yau shine ke nuna kulawa kan ƴaƴanshi abin da bata taɓa gani ba,ko wani abune ya same su na rashin lafiya sai dai kaga tashin hankali a fuskar uwarsu amma shi "Tirmisisi tusar gaba ga miji"inji hausawa. Ƙarfe 3 na rana muka shigo garin sokoto tare da Ya Bashir da ya kawo ni,rungume Ummina nayi ina jin wata kewarta ta musamman.Amna ma riƙeni tayi tana gaya min bazan ƙara tafiya na barta ba. Mama ce ta kira Ummi ta faɗa mata Safwan na asibiti,don basu san na shigo garin ba. Ya Bashir ne yace na shirya muje don shi a gobe zai koma,shiryawa nayi jiki a sanyaye na fito yana motar na same shi ɗaure fuska yayi yana kallona "Kije ki saka hijabi ki aje wannan gyalen" duban jikina nayi gyalen nake sanye da shi amma babbane ya rufe jikina ko ina. Fita nayi kamar yadda yace na canjo hijabin,kallona ya dinga yi kamar shima hijabin bai yi mishi ba. Har muka isa asibitin bai ƙara magana ba,ina ƙoƙarin fita ya dakatar da ni"Wai meyasa kika daina saka liƙab ɗinnan naki?" ya tambaya yana wani ɗaure fuska Murmushi na mishi "Ka kwantar da hankalinka,Zainab taka ce,kuma mallakinka ce don haka ka daina damuwa da mutanen da bai kamata kana saka damuwa akansu ba kaji mijina"ta faɗa tana leƙen fuskarshi. Dariya yayi sannan suka fito suka tunkari inda aka kwantar da Safwan,sallama suka yi Safwan ɗin na zaune kan gadon Lawal na ɓare mishi ayaba,Mama kuma na zaune kan tabarmar da ke shimfiɗe tsakiyar ɗakin. *RUMAISA'U SIDI✍️✍️✍️* *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *page 34* Miƙewa Lawal yayi tare da jan kujerar da yake zaune baya,gaida Mama nayi tare da tambayarta mai jiki sannan shima Bashir ɗin ya gaidata. Hannu Lawal ya baiwa Ya Bashir suka gaisa yana tambayarshi mai jiki "Jiki Alhamdulillah ya samu sauƙi gashi nan sai sangarta yake wa Mama"ya ƙarasa yana ƙoƙarin ɗora murmushin dole a fuskarshi. Matsawa nayi kusa da gadon ina kallon Safwan da naga ya ƙaramin girma a ido,kamar ba shi ba "Mommy" ya kirani da murmushi a fuskarshi "Na'am Safwan,ya jikin naka?" na faɗa ina zama kan gadon saitin ƙafafunshi "Na samu sauƙi Mommy,yaushe kika zo?Ina Amna?" ya tambaya yana raba ido. "Yau ɗinnan na iso,Amna kuma tana gida tare zasu zo da Ummi" "Ya jikin My boy"Ya Bashir ya faɗa yana shafa kan Safwan,shima murmushi ya mishi "Naji sauƙi sosai uncle" Hira muka ɗan taɓa da Mama da kuma Mariya dake ɗakin,saboda Lawal tun shigowarmu ba jimawa ya bar ɗakin,yanzu ma Ya Bashir nake jira da yace in bari yazo. Hira Safwan ya shiga yi min,akan makarantar da mahaifinshi ya kaishi,da yadda yake gane karatunu. Muna nan zaune wata matashiyar mace ta shigo riƙe da ƴar ƙaramar kula a hannunta kallo ɗaya na mata na mayadda hankalina kan Safwan da ke roƙona wai in siya mishi waya. Ƴar ƙaramar dariya na mishi sannan nace "Wallahi Safwan ka gama raina ni"ƙara kallon matar da naji Mama ta kira da NUSAIBA nayi wadda nake kyautata zaton itace amaryar Lawal don kamar na taɓa jin sunan a bakin Safwan har na mishi faɗan kar in ƙarajin ya kira sunanta kai tsaye. "Ga Maman su Safwanu nan"Mama ta faɗa mata tana nuna ni.Wayata na ci gaba da dubawa ina jin idanuwanta a kaina sai can tace "Sannu" ɗago kaina nayi a hankali na dubeta "Sannu" na maida mata nima. Shigowar Ya Bashir ɗakin yasa na ɗago kaina,uwayen ledodi ya shigo dasu na kayan fruit da kuma ice cream daban,Safwan ɗin ya baiwa ai ko ya shiga murna yana godiya. Gaban Mama na isa tare da duƙawa ina mata sallama,kuɗi na dunƙule 20k na aje gefenta nace asiyi ko ruwa,godiya tayi tare da muna fatan zaman lafiya. Ɓata fuska Safwan yayi kamar bai so in tafi ba,har nakai ƙofa naji maganarshi "Mommy don Allah ki dawo kafin ki tafi"kaina na gyaɗa mishi tare da mishi addu'ar samun lafiya. Ziyara nasha har gidan Hafsat da ake ƙoƙarin kawo ma Amarya,kwana uku ya bani shima daƙyar. *ZUBAIDA* "Wallahi baki ji haushin da kike bani ba idan naji kina ƙorafi kan matar nan,tun yaushe nake gaya miki ki ɗauki mataki amma kika ƙi,kina tsammanin ita a banza tabar Bashir ɗin ne" Laila ƙawar Zubaida ta faɗa bayan Zubaidar ta gama yi mata ƙorafi akan Zainab Ajiyar zuciya Zubaidar ta sauke "Ba zaki gane ba Laila,ni fa duk harkar malaman nan ba ƙaunarta nake ba,duk da bamu yi Islamiyya ba amma naji ana faɗar duk wanda yaje wurin boka to kamar ya kafirta ne.Ni ko bazan yadda naje wuta a dalilin Zainab ba" Taɓe baki Laila tayi "To Allah ya yafe mana kawai za a ce,amma gaskiya banjin zan iya bari kishiya ta kawo min matsala,ke da kika ji zaki iya sai kiyi tayi,ke kuma kullum bazaki rabu da kayan takaici ba" Zaune take a falon bayan wucewar Laila a ranta take tunani "Wai me yasa Ya Bashir ke nuna wa Zainab ƙauna a gaban kowa? Me yasa su basa faɗa? Me yasa ko magana ake yi da zaran ta fara magana za a ce tayi kuskure amma idan Zainab tayi magana sai a dinga yaba mata? Me yasa ƴarta ta cikinta ma yanzu nuna take tafi ƙaunar Zainab?" Jifa tayi da filon dake gefenta tare da yin watsi da ɗan kwalin kanta "Why Zainab,me yasa komai Zainab?"ta ƙarasa tana yamutsa gashin kanta. Kuka take yi sosai,ita kaɗai tasan azabar da take sha a cikin zuciyarta,ita kaɗai ta san yadda take jin tsanar Zainab a cikin ranta.Ta rabata da mijinta,a da idan ta mishi abu yana mata uzuri amma yanzu baya mata uzuri ko kaɗan da tayi ɗan kuskure zai hauta da faɗa. Yau bata masan tare zasu yi tafiyar ba saida ya shigo yake faɗa mata Sokoto zaije "Amma ai ba adalci bane da zaka rakata ni kuma kayi tafiyarka ka barni"tayi maganar kanta tsaye. A fusace ya ke kallonta "Kema idan zakije to ki shirya sai mu tafi,Nasan dai damuwarki kwanaki ko? To karki manta gobe ma kwanan Zainab ne don haka daidai zan dawo bazan shiga cikin haƙƙinki ba" daga haka ya ajiye mata kuɗi tare da barin ɗakin. Har taji tashin motar tasu tana nan tsaye inda ya barta,wannan damuwarce ta hanata walwala,kuma har suka kwana bai kirata ba,ballantana yaji lafiyarta. Share hawayen da suka zubo mata tayi,tare da ɗauko wayarta,danna wurin kira tayi bayan ta samu ganin Number da take nema sallama tayi bayan wadda ta kira ɗin ta daga "Anty barka da yau"ta gaidata bayan sallamar da suka ƙare Da mamaki sosai a muryar Antyn lokacin da take amsawa "Barka dai Zubaida,ya gidan ina Zainab" "Tana nan lafiya Anty,am anty nace don Allah gobe zan same ki a gida? Ina so in shigo don Allah" Shiru Antyn tayi sai can tace "Lafiya dai Zubaida?" Murmushi tayi mai sauti "Lahhh lafiya lau Anty akwai maganar da nake so muyi ne" Anty matar mahaifin su Zubaida ce,wayayyace sosai mai son mutane.Sam basa ga maciji saboda irin tsanar da su Zubaidar suke nuna mata da sunan suna taya mahaifiyarsu kishi. Tun bayan aurenta da Bashir Anty ta taɓa zuwa gidan ta mata nasiha kan irin zaman da taga suna yi ita da mijin,a lokacin bata saurareta ba sai ma cin mutunci da ya biyo baya wanda har takai ga mahaifiyar Zubaidar wato Husaina ta shiga tace kar ta ƙara yi ma ƴaƴanta shisshigi a lamurran gidan aurensu. Wannan ne ya katange Anty da zuwa gidan,tun da abin ya faru bata ƙara yunƙurin zuwa wurin Zubaida ba,saboda duk abin da zai janyo mata matsala bata sonshi bale kuma har ya kawo ɓacin rai a zuciyar mijinta. Number Bashir ta danna da tun jiya da ya tafi bata ƙara jinshi ba,saida ta gama ringing sannan ya biyo bayan kiran gaida shi tayi ya amsa tare da tambayarta Zainab. "Kenan Ya Bashir da ban kiraka ba,ba za ka kiramu kaji lafiyar mu ba" ta sako ƙarafi kamar yadda ta saba "Ai nima naga ina buƙatar kulawar nan ko?Ko don kinfini baki,tun daga Kaduna har Sokoto ki kasa ɗaga waya ki kira mijinki ki tambayeshi ya hanya,sai ni zaki ga laifina kan naƙi kiranki,ke shikenan kullum ƙorafi dai ba randa za a miki daidai" daga haka ya buga tsaki tare da kashe wayar Da kallo tabi wayar bayan ta sauketa daga kunnenta,leɓonta na sama ta ciza tana ƙoƙarin haɗiye kukan da ke taso mata. Wai meye laifinta? Ina ta kuskure? Me ta rasa? Kyaun fuska ko kuma kyaun jiki? *RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️ AURE DA KARATU NA RUMAISA'U SIDI FARAR ANIYA WRITERS page 35 Number Ya Bashir ta ƙara dannawa kira bugu biyu ya ɗaga "Ya dai"ya tambaya kamar wanda aka yiwa dole.A sanyaye tace "Inaso ne inje gidan Anty Maryam idan ka bani dama" Jikinshi ne yayi sanyi jin yadda muryarta ta sauya "Allah ya tsare amma ki dawo da wuri saboda nima ina hanya" amsa mishi tayi da "To"tare da kashe wayar ba wata addu'a ko fatan dawowarshi lafiya. Shiryawa tayi tsaf sannan ta shiga ɓangaren Mama tare da gaidata,amsawa tayi ba yabo ba fallasa ta gaya mata fita zata yi,tace Allah ya tsare hanya. Driver tasa ya kaita saboda ita batada Mota,ba yadda batayi da shi kan ya siya mata Mota ba amma yaƙi sai yace ga driver nan duk inda zata je ya kaita,har ƙarar shi ta kai wurin mahaifiyarshi kan ai ga Zainab nan da mota,amma sai ya kafa hujja da ai bashi ya siyawa Zainab ɗin ba. A bakin get ɗin ta sauka tare da faɗawa driver lokacinda zai zo ya ɗauketa.Sallama tayi bayan ta isa tsakiyar falon,murmushin yaƙe ta saki bayan fitowar Antyn daga kitchen tana amsa sallamarta. "Ahh sannu da zuwa Zubaida,ki zauna mana"ta faɗa tana nuna mata kuhera,zama tayi kamar wata munafuka sai murmushi take dokawa kamar sabon kamu,saboda abu ne wanda bata taɓa kawo wa a ranta ba wai zata zo wurin wannan matar da tunanin neman taimako. "Yawwa Zubaida ɗan bani 5minutes please na kammala abin da nake yi"ta tsinkayi muryar Antyn tana faɗi tare da jera mata lemu da kuma cups. Tana nan zaune har Antyn ta fito ɗauke da manyan kuloli haɗaɗɗu,mayafi ta ɗora a kanta sannan ta fita da su,bata jima ba ta dawo,mayafin ta ajiye sannan ta koma kitchen nan ma ba jimawa ta dawo ɗauke da wani abincin da aka zuba a plate "Kiyi haƙuri na barki kina ta jira na,Kinga bismillah matso kici abinci,tun bai huce ba" ta faɗa tana tsiyaya ruwa ta sha Sha'awar da abincin ya bata da kuma ƙamshin da ke tashi yasa ta fara cin abincin da niyyar yin cokali 2 ko 3 sai gashi ta zarce,batasan ta cinye abincin ba saida taji Anty na faɗin "Bari in ƙaro miki"girgiza kanta tayi cikin kunya "A'a wallahi Anty na ƙoshi" Zama Antyn ta gyara tana fuskantar Zubaida"Ina jinki Zubaida,tun jiya da kika kirani hankalina ya kasa kwanciya,ina fatan dai lafiya" ajiyar zuciya Zubaida ta sauke idanuwanta na tara ƙwalla Hannunta Antyn ta kama tare da nufar sama inda inda ɗakinta yake,zaunar da ita tayi bakin gadon sannan ta jawo kujerar da ke gaban mirrow ɗinta ta zauna tana fuskantar ta "Meke faruwa ki gayamin" Numfashi taja tare da ɗauke ƙwallar da ta tarammata a ido "Ina cikin matsala Anty,na rasa da wa zanyi magana in samu mafita,duk wanda na tunkara da matsalata abinda nake ganin bazai yu ba yake kawo min a matsayin mafita,shi ya sa nazo gare ki da fatan in samu warwarewar matsalata a wurinki Anty"ta ƙarasa tana ɓarkewa da kuka. "Subhanallahi Zubaida me ya faru?Ki sanarda ni damuwar ki ni kuma na miki alƙawarin matuƙar inada dama zan samo miki mafita da yardar Allah" Idanuwanta ta zuba mata sannan sannu a hankali ta fara jero mata halinda take ciki "Da farko dai Anty zan alaƙanta duk wata matsala da nake ciki da shigowar Zainab cikin rayuwar mijina a karo na biyu,kamar yadda kika sani Ya Bashir ya so Zainab a lokacinda take budurwa,rashin samunta yasa Anty tayiwa Abba magana akan ai gani nan,ba don Ya Bashir naso ba aka yi aurenmu.Duk da ba shi ya zaɓeni ba,amma ya zauna dani zama na amana,yana ƙoƙarin faranta min a koda yaushe,duk shirmen da zan mishi baya fushi dani.Rashin girkina bai canja da yadda ya saba yi min ba,saidai ya shaida min nayi ƙoƙari na koya ni kuma na gaya mishi bazan iyaba gaskiya.Dama kuma ni gani nake idan na roƙeshi abu baya saurin bani wannan yasa idan inason abu saidai naje na faɗawa mahaifiyarshi ta mishi magana ya bani,yasha faɗa min na daina yi mishi haka idan ina son abu na dinga faɗa mishi da kaina,ni kuma ganin kamar idan ita tayi magana yafi saurin bani yasa naƙi dainawa.Ana haka na samu cikin Zee,nasha gata a wannan lokacin daga shi har mahaifiyarshi da Abba ba wanda baya kula dani.Ƙauna suka nunawa cikin kamar me,haka ma mahaifiyata da duk wani masoyinmu.Cikin kuma ya sako min fushi da saurin faɗa wanda kai tsaye zan fara cin mutunci ko da kuwa da shi ne,kuma a gaban kowa.Sosai muka yi rigima lokacin da na haihu na samu ƴa mace,tun a asibitin ya faɗa mini yayi wa yarinya huɗu ba da suna ZAINAB a gaban kowa na hau rigima nace ni ban yarda ba,saboda sanin muhimmancin Zainab ɗin a wurinshi.Duk haukar da nayi wannan bai canja komai daga sunan da ya sakawa ƴarshi ba.Rago Anty ta siya da nufin canjawa yarinyar suna amma Daddy ya hana.Bayan haihuwar ne Anty ta samo min yara ƴammata biyu,ɗaya mai shara da girki,ɗayar kuma wadda zata riƙa kula da Zee,saboda ni ko sakamata pampers ban iya ba,mahaifinta ke saka mata,to bayan zuwan mai aikin sai komai ya koma hannunta.Kullum Ya Bashir na faɗa min na rage yawan ƙorafi,bayan kuma duk abinda nayi magana to tabbas naga an tauye min hakkine,kinga ko bazan zuba ido a tauye min hakki ba.Bayan tasawar Zee ne na sallami ɗayar mai aikin,na bar wadda zata ci gaba da kula da gidan da kuma girki,mun fara samun matsala da shine bayan ya min gargaɗin kar in ƙara tura mai aiki ta gyara mishi ɗakinshi ya fi son in gyara da kaina,ni kuma a gaskiya bazan iya ba.Na shiga tashin hankali lokacin da naji mutuwar auren Zainab,saboda nasan abinda ke tunkaro ni,ban ƙara gigicewa ba saida tazo garinnan naga yadda yabi ya ruɗe akanta,har kashedi na mata amma baiwar Allah nan ta kasa barmin mijina"ta tsagaita tana share hawayen idonta sannan ta ci gaba. "Na roƙe shi kar yayi aurennan amma saida yayi,ina raye Ya Bashir ya auro Zainab ya kawota a cikin gidanshi,wanda a wannan lokacin ni ina gida bisa shawarar Anty Amina da tazo ta tafi da ni.Zamana gida ba abinda ya ƙaramin sai tashin hankali saboda biris da Ya Bashir yayi dani tun bayan komawata gida sau ɗaya yaje nace bazan koma ba daga nan bai ƙara dawowa ba.Ni da kaina na maida kaina ɗakina Anty bayan da naji Anty ta tubure akan sai Ya Bashir ya sakeni,ni kuma har ga Allah ina ƙaunar mijina.Ko da na dawo ɗin ma ba abinda na tsinta bayan takaici,saboda a fili Ya Bashir ke nuna kulawarshi ga Zainab,duk abinda tayi zai yaba,saɓanin ni da kullum banayin daidai,har video girki nayi downloading a wayata don in mishi nima in burgeshi amma da ya ci sai ya furzar ya kirata ta kawo mishi nata.Anty yanzu komai na yiwa Ya Bashir banyi daidai ba,komai nayi bana burgeshi,na rasa ya zanyi,har wata ƙawata tace nazo ta kaini wurin wani malami da yake bada taimako naƙi amincewa saboda ina tsoron faɗawa wata halakar.Abinda yasa nazo wurinki saboda kece mutum ta farko da ta fara ƙoƙarin nusar da ni akan gidana amma naƙi saurare,a yau nazo ina roƙon ki taimakamin Anty ki faɗa min yadda zan yi yaƙin ƙwato mijina a hannun Zainab" ta ƙarasa tana saukowa daga kan gadon ta zube gaban Anty tana rera kuka. Hannunta Antyn ta kama tare da zaunar da ita unda ta tashi,fita tayi daga ɗakin,ba jimawa ta dawo da gorar ruwa a hannunta,tsiyaya ruwan tayi a kofi sannan ta miƙawa Zubaida.Karɓa tayi tashi tana sauke ajiyar zuciya. Komawa Antyn tayi ta zauna tana kallon yadda Zubaida ke shan ruwan,tausayi ta bata har wata rama tayi alamun tana cikin damuwa sosai ga kishi da ke cinta. "Da farko ina so ki janye alhakin shigar ki wannan halin akan kowa,ke kika cuci kanki Zubaida,duk abinda ya same ki ke kika ja,maganar gaskiya ma Bashir yayi haƙurin zama da ke tsawon wannan lokacin.Haba Zubby sai kace ba ƴar zamani ba,ke shikenan ba abinda kika iya sai yin ɗinki ki matse jiki,bayan gyaran jikin ma baki iya ba.Ace mace da mijinta Zubaida amma ace bakya gyara?To ina mace anan,bari in faɗa miki ba wai ki shiga toilet ki bugo wanka ki saka sutura mai tsada ne kawai gyara ba a'a,ke gyara dai da zai janyo miki daraja da kuma girmamawa a idon mai gida,taya miji zai miki abinda kike so bayan ke baki mishi abin da zai ji daɗi? Ɗan turarennan ma mai ƙamshi bakya sakawa Zubaida,ba wai sai kina wari zaki saka turare ba,ke da kanki idan kika saka turare zaki jiki cikin nishaɗi,to bakya yi Zubaida,magana mai daɗi wannan bata fitowa daga bakinki a lokacinda kike magana da mijinki,namiji da kike gani tamkar jariri haka yake,duk yadda kike ganin idan ya fito yana muzurai to zaki samu ƙaramar yarinya ke juyashi a cikin gida,da zarar kin san kanki,kina gyara kanki ta ko ina,kin iya magana mai siye hankalin ɗa namiji,kina girmama iyayenshi da ƴan uwanshi,to wallahi da izinin Allah zaki same shi a tafin hannunki.Irin ku ne mazajenku ke faɗawa tarkon matan waje,saboda ku na cikin kun kasa yi musu abinda na wajen ke musu.Kinada kyau Zubaida,kinada ƙira da komai ma,to meyasa da ƙuruciyarki kike nema ki kashe kanki?Sannan da kike maganar Zainab ta ƙwace miki miji,yo ai dole ta ƙwace tunda ta samu sakarar kishiya,kinyi zaune kina kuka,kin barmata mijin,wallahi nan gaba kaɗan idan baki gyara ba har dukanki sai yayi.Saboda shi namiji zai iya yi miki uzuri a lokacin da yake tare dake ke kaɗai,amma da zarar kun zama ku biyu to bazai ƙara yi miki uzuri ba saboda zai yi tunanin dama rainashi kika yi tunda ga wata halitta irinki na mishi,daga nan ne wulaƙanci zai shiga,idan kika cika ƙorafi ya sallame ki saboda yana ganin ko kin tafi ba wata damuwa zai yi ba tunda ga wata yanada" tsagaitawa tayi sannan ta tsiyaya ruwa tasha tana kallon Zubaida da ta mayar da hankali tana saurarenta. "Abinda na fahimta manyan matsalolinki sune rashin gyaran jiki,rashin iya girki,rashin iya magana,da kuma rashin riƙe sirri,dukkan waƴannan abubuwane da rayuwar aure ke lalacewa matsawar aka samu ɗaya daga cikin waƴannan.Dole sai kin gyara,kin koyi girki,kinsan yadda zaki yi magana da mijinki,ba da kalar harshen da zakiyi magana da Amina za kiyi da mijinki ba,a'a muryar da kike amfani da ita idan kina tare da shi ta banbanta da wadda aka sanki da ita,kar ki kuskura muryarki tafi taki ɗagawa a lokacin da yake magana wannan haramunne,kar kiyi musu dashi,ko saɓani kuka samu kar kiyi ƙoƙarin fahimtar da shi a lokacinda yake cikin fushi,ki barshi sai ya huce tukunna sannan ki mishi bayani,kar ki ƙara kai ƙararshi wurin mahaifiyarshi ko taki mahaifiyar duka waƴannan biyun kuskurene babba.Ita dai mahaifiyarshi ƙimarki zata rage a idanuwanta,zata daina ganin girmanki za ta ga kamar kina tonawa ɗanta asirine a idon duniya.Mahaifiyarki kuma zata tsani mijinki zata ga kamar yana musguna miki,ke har ki manta ma da kunyi wani faɗa amma ita bazata manta ba zata ci gaba da kallonshi da wannan abun.Duk lokacinda ya kasance a rayuwar ma'aurata akwai third party to akwai matsala,kar ki kuskura ki bada wata kafa da third party zai shigo tsakaninku,duk wani saɓani da ya shiga tsakaninku ki rufe shi ki bari ku sasanta kanku,kar ki yarda wani ya fahimci akwai matsala a tsakaninku bale kuma har kishiya,wallahi dole ma Zainab ta rainaki"Anty ta ƙarasa tana buga tsaki tana jin kamar ta shaƙo wuyan Zubaida "To yanzu yasan kin fito ko haka kawai kika fito"ta tambaya ganin kamar harda hauka ke cin Zubaidar.Kanta ta gyaɗa "Ya sani saida na kirashi na fito" "Baya nan ne?"Anty ta tambaya kanta ta ƙara gyaɗawa "Eh ya rakata Sokoto,amma yace min yau yana hanya"hannu Anty ta buga a ƙirji tana salati "Yanzu mijinki na hanya ƴarnan amma kika biyo hanya kika zo? To idan ya dawo wurin wa zai sauka"ta faɗa tana riƙe haɓa.Shiru Zubaida tayi tana jin tausayin kanta "Idan miji na hanya ba'a fita Zubby,kuma ki kwantarda hankalinki zan kaiki wurin gyaran jiki da turarukka masu ƙamshi zan kuma koya miki abinda ya samu na girki,In sha Allah sai kin ƙwato Bashir ɗinki a hannun Zainab,sai kin karkato hankalinshi ya dawo kanki,ke sai ya koma ko zama zaiyi sai ya tambayeki"ta ƙarasa tana ƴar dariya Dariya Zubaida keyi itama tana share ƙwallar da ke mata zuba "Na gode sosai Anty,In sha Allah zan aje hankali in koya yadda ya kamata" RUMAISA'U SIDI *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 36* Ƙara gyara zama Anty tayi tana fuskantar Zubaida "Ki kwantar da hankalinka da yardar Allah zan kaiki inda za a share miki hawayen, ki daga yanzu kin daina zubar da hawayen ki akan kishiya,kuma zaki ciri taki tuta a idon Bashir" wayarta ta ɗauko dake ajiye akan mirrow sannan ta ƙasa dubin Zubaida "Zan haɗa ki da shahararriyar mai ingantattun magunguna da turarukannan wato MEERAH_B HERBS.A wurinta zaki samu duk abubuwan da ki ke buƙata,tsafta zata gyara ki da sahihai kuma ingantattun magungunan ta, har Amar'e take gyarawa ,ke uwar gidan ma ba'a barta a baya ba.Kin ganni nan lokacin da na haifi Marwan wurinta na siye kayan da naji daɗin su,nima wata ƙawata ce ta haɗani da ita,har yau ban daina sakawa wannan ƙawar tawa albarka ba kuma jima ban daina siyayya a wurinta ba.Kinga wannan tumbin da kika fara radawa sanadiyyar haihuwar Zauna,tsaf zai ɓata idan har kina amfani da magunguna ta.Maganin sanyi da na haihuwa duk tana yi.Don haka ki kwantar da hankalin ki" Ajiyar zuciya Zubaida ta sauke "Na gode sosai Anty wallahi har naji daɗi" murmushi Antyn tayi "Yanzu zan kira ta zata haɗa miki kaya masu kyau" wats number ta lalubo ta dannawa Kira bugu biyu aka ɗaga Cikin mutunta juna suka gaisa bayani ta mata akan kayan da take so a haɗa mata ta faɗa mata ba matsala. "Ki saka number ta idan kika tashi ki dinga kiranta" Wayar Zubaida ta ɗauka tana saka number da Anty ke karanto mata "08142800199.Wannan ita ce number MEERAH-B HERBS ki riƙa siyayya a wurinta za kiji daɗi" Kaya Anty ta duba mata masu kyau ta haɗa mata "Kiyi amfani da wannan kafin naki su iso,don Allah Zubaida ki maida hankali,ki cire wannan sakarcin,kisan ciwon kanki.Idan muka bi daki daki kema zaki ciri tuta a idon Bashir" Sauri-sauri ta dawo gidan,tana fatan wannan ya zamo silar warware war damuwarta. Kitchen ta shiga bayan tayi download ɗin video yadda ake kallon.Step step ta dinga bin abin har ta samu ta kammala daƙar. Toilet ta wuce ta feso wanka da wani sabulu da Anty ta haɗo mata a cikin kayan,turaren ta murza a jikinta tana jin wata mutuwa na shigar ta.Ƙamshin na daban ne,kayan ma na daban ne. Kallon kanta tayi a madubi bayan ta gama kafa ɗaurin ɗan kwalin atamfar ta.Ita kanta ta san tayi kyau. Turaren ta ƙara ɗaukowa ta fesa tana jujjuyawa gaban madubin.Wayarta ta ɗauka tare da fita falon, talabijin ta kunna sannan ta koma kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana danna wayarta. Bataji tsayuwar motar shi ba sai sallamar shi taji a bakin ƙofar,da sauri ta juya tare da tashi a hankali tana ƙawata fuskarsa da kyakkyawan murmushi. Sanarwar yayi a wurin yana kallon ta,saboda irin kyaun da ta yi a cikin atamfar.Kallonta ya ke Yadda take takowa a hankali kamar mai tausayin ƙasa. Ya shagala da kallon ta yaji tana mishi magana cikin wata sanyayyar Muryar da bai santa da ita ba"Sannu da zuwa Hubby"ta faɗa tana wani karairaya tare da zare jakar da ke hannunshi. "Bismillah muje ko"ta faɗa tana yin gaba ganin yadda ya zuba mata ido.Ɗakinshi suka nufa kallon ɗakin yake shima duk da ba wani gyara na musamman aka mishi ba amma sai ƙamshi ya ke. Toilet ta shige ba jimawa ta fito tare da samar da shi ga ruwan wanka can.Saitin zuciyarta ta dafe bayan ya shige,bata taɓa aza zata iya abinda Anty ta koyar da ita ba,amma ga dukkan alamu akwai nasara daga yadda taga ya fara canja wa yana bin ta da mayen kallo. Koda ta zuba mishi abincin ma kallon mamaki yake mata yadda take mishi fira mai daɗi kuma cikin natsuwa. Ba laifi tayi ƙoƙari wurin dafa abincin.Kallonta yayi bayan ta dawo daga kai kayan kitchen "Abincin yayi daɗi Babu,kin yi ƙoƙari sosai,haka ma wannan ƙamshin ya tafi dani sosai,wannan ma ya min kyau"ya faɗa tana shafa dogon gashinta da ta taje ta shafe da mayukka. Murmushi tayi tare da riƙo hannunshi ɗaya"Na gode da yabawar ka,idan har zaka ci gaba da min hakan ni kuma zan ƙara ƙaimi don in ga na farantama.Don Allah Ya Bashir kar ka daina so na,na maka alƙawari zan canja,duk abinda baka so zan daina,Ni dai fatana ka soni fiye da yadda kake son Zainab"ta ƙarasa ƙwalla na taruwa a idanuwanta. Hannunta ya ƙara damƙewa yana jin wani kalar tausayinta na ratsa shi,hannunshi yasa yana ɗauke ƙwallar da ta zubo mata "Bana son kina saka damuwa a ranki,ko kiyi tunanin bana sojoji,wallahi ina sonki Zubaida matsawar zaki ɗore a yadda na dawo na same ki yau,to zakiga zallar ƙauna" Wani daɗi ne ya ratsa ta,yaushe rabon da ta sami irin waƴannan kalaman daga mijinta.Tun zuwan Zainab komai ya canja,tana fatan wannan ya zama silar warwarewar matsalolinta. Wata kalar duniya take jinta a kwana ukun nan da tayi da mijinta ba Zainab tsakani. Zaune take tsakiyar gadon tana kallon yadda yake taje sumar shi "Gaskiya Ya Bashir kana ji da suman nan taka kamar wani gaye"ta ƙarasa tana sakin dariya Juyowa yayi ya dubeta tare da mata hararar wasa "Na san dai wata harda suman nan tawa ta jata ta ƙara soma,har take kuka idan bata aure ni ba zata mutu"ya ƙarasa yana mata gwalo. Ɓata fuska tayi tare da doddoka ƙafarta akan gadon"Ai kaima haka kace" Rakoshi tayi har bakin ƙofar,har ya saka ƙofarshi da niyyar fita sai kuma ya dakata tare da juyowa"Am nace Zubaida kar kiyi girki dani, kin san yau Zainab zata dawo" Shiru tayi tana binshi da ido,tana jin kamar ta saki ihu.Daƙyar ta iya jawo ƙafafuwan ta ta dawo falon,zubewa tayi kan kujerar falon tare da sa hannu biyu ta dafe kanta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"ta samu ta faɗa daƙyar.Ba ta so Zainab ta dawo yanzu ba,taso ace ta samu koda sati ɗaya da mijinta amma wannan makirar bazata bari ba. Number Anty ta dannawa Kira,gaidata tayi bayan ta ɗaga "Ya dai Zubaida,komai lafiya dai ko" "Lafiya lau Anty,ina murna farin ciki na ya dawo gare ni amma matar nan bazata bari ba Anty,yanzu yake faɗa min wai yau matar nan zata dawo" "To shine me?"Antyn ta tare numfashin ta "Ko baki san da ita ba?Dama ai kin san zata dawo,to miye abin damuwa?Ina magungunan da kika siya?" "Suna nan Anty ina amfani da su,kuma suna da kyau sosai" "Yawwa to ki ci gaba da harkokin gabanki kawai,matsawar zaki gyara to wallahi kin fi ƙarfin wata Zainab.Ke dai kawai ki ci gaba da gyara kuma ki dinga addu'a shine kawai" Bayan la'asar taji shigowar Zainab ɗin,tana zaune kan kujerar ta ko ɗaga kanta bata yi ba.Jin Muryar Bashir yasa ta miƙe tare da fita tsakar gidan tana kallon shi yadda ya tattalo jakar kayan Zainab ɗin. "Sannu Maman takwara mun same ku lafiya"Zainab ɗin ta faɗa tana duban Zubaida.Ƙyaleta tayi kamar bata ji ba tayi tsaye tare da riƙe ƙugu tana kallon Bashir "Bakiji tana gaida ki ba"Bashir ɗin ya faɗa ganin kamar bata ji ba. Tsaki ta buga sannan ta zubda yawu "Na jita,sannu ta min ko? To ni asibiti ce da zata min sannu?Ko kuma wata nakasa ta gani a jikina?"ta juya wurin Zainab ɗin tana nuna ta "Na gaya miki ki fita harkar,ba ruwana da ke,kiyi rayuwarki inyi tawa.Mijine dai kin aura ko? Kije ke da Allah,kuma wallahi duk wani hakki nawa da aka ci ban yafe ba"daga haka ta juya tare da komawa sashe ta. *RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️ *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 37* Guntun murmushi na saki bayan ɓullewarta,Allah ya gani na tsorata da irin kyaun da naga jikinta yayi,ga wani fitinannen ƙamshi da ke fita a jikinta. Amma daga lokacin da ta buɗe bakinta sai hankalina ya ɗan dawo.Shi ya jamin jakata har cikin gida,sannan ya fita bayan ya tambaya idan akwai abin da nake buƙata nace babu. Gyaran gidan na shiga yi,nan take na ƙalƙaleshi tsaf na watsa turaren da nazo dashi a cikin burner sai gashi gida ya game da ƙamshi. Kitchen na shige duk da na gaji,amma haka na daure na girka muna sauƙaƙƙen abinci.Wanka na ɗanɗasa bayan na ƙare sannan na jiƙe jikina da turare na fesa kwalliya ta. Dogon hijabi na ɗora akan kayan jikina sannan na ɗauki wata ƴar ƙaramar jaka na nufi ɓangaren gwaggo. Tsaraba ce da nayo na kaimata,tare da ta Zubaida "Ki kaimata da kanki mana,ai mun gode sosai wallahi kinyi ƙoƙari"ta faɗa tana miƙo min na Zubaida Ba zan iya musu da ita ba,wannan yasa na karɓar tare da yi mata sallama na fito. Ɓangaren na nufa,tsayawa nayi a bakin ƙofar falon ina doka sallama,daga ciki naji an amsa min saida na shigo na samu ƴar aikinta na wurin dinning tana zuba mata abinci,ita kuma tana hakince kan kujerar tana jira a kawo mata. Ƙara sawa nayi wurin da take zaune na ajiye mata ledar sannan nace "Maman Zainab ga wannan aci da haƙori"daga haka na juya ina ƙoƙarin barin falon Ƙiiiii naji an janyo hijabi na da ƙarfi,ban shirya wa hakan ba shi yasa kai tsaye nayi baya cikin iyawar Ubangiji na dafe kujerar da ke kusa da Ni. Miƙewa tayi a fusace ta watso min ledar da na kawo mata,nan take kayan miyar da na kawo mata suka zube ƙasa. Yatsunta ta buga suka bada sauti sannan tace "Wannan ya zama na ƙarshe da zaki je gida kuyo barbaɗe-barɗenku sannan ki dunƙulo ki kawo min.Su dai da kika shanye sun shanyu Amma wallahi ni nafi ƙarfi ki" Juyawa nayi da sauri don barin ɗakin don a yadda raina ya ɓaci komai zai iya faruwa.Amma me?Ina juyawa naji maganar ta ƙasa-ƙasa "Banza kawai Karuwa"cak na tsaya tare da juyowa da ƙarfi wanda ko ita saida ta zabura tare da yi baya kaɗan Wurinta na matsa "Maimaita abinda kika ce"na faɗa ina juya hannuna Cike da rashin kunya ta ƙara faɗi "To tsoron ki nake da bazan maimaita ba?Nace banza Karuwa mai ƙwacen.........." Tasssss na ɗauke ta da mari batare da jiran ta ƙarasa ba,dafe kunci tayi tana kallona "Ni kika mara"ta faɗa tana nuna kanta "Wannan ya zama na ƙarshe da ƙazamin bakinki zai ƙara faɗa min magana irin wannan,idan can gidanku ba a miki tarbiyya ba to ni nan zan miki.Kar kiga ina ƙyaleki,wallahi na fiki iya rashin mutunci.Amma idan kina musu ki ƙara magana ki gani" daga haka na bar falon zuciyata na tafasa sosai,na tsani wannan kalma. Ina zaune falona ina latsa wayata don ta ɗan ragemin abinda nake ji ya shigo kamar wanda aka koro. "Me Zubaida ta miki da zakije har gidanta ki mare ta"ya katse numfashi na daga gaida shi da nake ƙoƙarin yi "Ita da ta turo ka,bata faɗa ma abin da ya jawo hakan ba" na faɗa ina ɗauke kaina abin da ya ƙara tunzurashi "Ba zan ɗauka ba,wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara ɗora mata hannu da sunan duka,ko ni da nake mijinta ban taɓa dukanta ba.Don haka kema wannan ya zama na ƙarshe" Zuciyata ce ta kawo wuya nima na miƙe a fusace "Wallahi muddin ta ƙara shiga gonata sai nayi fata-fata da ita,idan har kana gudun wani abu ya taɓa ta to ka maida ta ciki ƙarewar ƙauna"daga haka na ɗauki wayata don in wuce ɗauki "Wato ina miki magana wuce wa ma zaki yi ko? Tafiyar kwana uku duk ta canja ki, ni bazan ɗauki wannan abin ba gwanda ki sani tun yanzu" Idanuwana ne suka cika da ƙwalla na dube shi "Tafiyar da nayi ai kasan inda naje,wata ƙila can aka koyo min baƙin halin"daga haka na shige ɗaki na. Nasha kuka sosai a wannan ranar,ko da dare yayi nayi shirin bacci tsaf na gyara kwanciyata sai gashi ya kirani in kawo mishi abincin shi. Haɗa kayan nayi na kai,koda naje tana kwance akan kujerar ɗakin,gabanshi naje sannan na aje tiren abincin "Yawwa ƴar albarka" Zuba mishi nayi sannan na miƙe tsaye,kujerar ya nuna min "Kinga ƴar uwarki zazzaɓi ke damunta saboda kukan da ta sha.Don Allah Zainab ku dinga haƙuri da juna" Ko gefen da take ban kalla ba nace "Ai tunda kana nan zaka kula da ita"daga haka na bar falon. Kwana biyun nan nawa haka suka tafi ba daɗi,duk da idan muna waje ba wanda zai fahimci abinda ke faruwa a tsakanin mu. Shima kuma shareni yayi suna zuba soyayyar su shi da sabuwar Zubaidar shi. A tsaye na fara rashin lafiya,bana cin abinci,ga jiri,nan take na rame.Gwaggo ce ta fara ankara da halin da nake ciki "Zainab ki faɗa min damuwarki,duk gidan nan baki da kamata.Ni kamar Mahaifiya nake a wurinki.Na daɗe da fahimtar akwai abin da ke faruwa a tsakanin ku da yaron nan,ki faɗa min kinji" Murmushi nayi mai ciwo sannan nace "Ba komai Gwaggo, kawai banjin daɗi ne kwana biyu, amma ba wata damuwa"ido ta zuba min alamun bata yarda ba Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Shi kenan,idan ma akwai abin da kike ɓoyemin Allah ya yaye miki damuwarki.Kuma gobe Kiyi ƙoƙari kije asibiti ba a zama da ciwo kinji" Kaina na gyaɗa "In Sha Allah zanyi ƙoƙari in je" Washe gari text na mishi nace ina so inje asibiti ko minti biyu banyi da tura saƙon ba sai gashi har cikin ɗakina. Wurina yayo da sauri ya shiga taɓa wuyana "Ba kida lafiya Zainab?Me ke damunki?Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Idanuwana na lumshe abinda ya baiwa hawaye na damar zubo wa,nayi kewar wannan kulawar tashi,ƙara ruɗewa yayi "Don girman Allah ki daina kuka Zainab" Kaina na girgiza hawaye na min zuba "Izini fa kawai na nema ka bani,naje na dubo lafiya,bance ka baro matarka ba" Rungume ni yayi da ƙarfi"Don Allah ki daina wannan maganar, wallahi ji nake na tsani kaina da faruwar wannan al'amari,ki yafe min Zainab"lallashina ya shiga yi da kalamai masu daɗi tare da neman yafiya a wurina Shi yasa na shirya tsaf muka fito, ɓangaren Gwaggo muka shiga muka faɗa mata zamuje asibiti.Alamu sun nuna taji daɗin yadda ta ganmu. Gambu ya buɗe min ina ƙoƙarin shiga muka ji Muryar ta tana magana "Ya Bashir kaifa nake jira"ta faɗa cikin shagwaɓa. Ko da muka dawo asibitin ƙin binshi ɓangaren gwaggo na yi na wuce nawa ɓangaren. Koda maganar samun cikina ta fita ba wanda bai yi murna ba.Kullum da kalar ƙwalamar da Gwaggo zata min,kuma ina jin daɗi sosai. Haka ma uban gayyar,wata kulawa yake bani ta musamman,kamar wanda za a yiwa haihuwar fari. A fili Zubaida ta nuna hassadar ta akan cikin,inda ta bi ta tada hankalin ta.Wannan yasa basa kwana biyu basu samu matsala da shi ba. Ni dai fatana Allah ya raba ni da shi lafiya. *LAWAL* Tunda aka sallamo Safwan daga asibiti,Lawal ya canja mishi makaranta.Ya maida shi mai sauƙin cunkoso. Kulawa yake baiwa yaron ta musamman,duk abinda yake so yana siya mishi.Haka ma Amna da ke gidansu Zainab duk wata yake siyayya yaje ya ganta. Nusaiba ma ganin bazata samu riba a Safwan ba yasa ta shafa mishi lafiya.Ta fita harkar shi,duk da mugun haushin yaron ta ke ji. Yau tun safe da Lawal ya tafi kasuwa bai dawo ba,har Safwan ya dawo makaranta ba a dafa abinci ba. Sai bayan la'asar ya dawo ya jigata sosai ya shigo gidan,da gudu Safwan ya rungume shi "Baba Ina ka tafi, nayi ta neman ka"kanshi ya shafa yana jin wata ƙaunar yaron na shigar shi. "Wallahi ina kasuwa Safwan,kayanne sai yanzu suka samu,idan nace na dawo ban siyo ba to ko gobe ba zan samu ba.Kaci abinci dai ko" Girgiza kanshi yayi "Aa banci ba Abba" Nusaiba da ke hakince ya duba "Yanzu Nusaiba shine kika kasa ranta min kuɗi ki dafa abinci ko don yaron nan" *RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️ *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 38* Wani kallo ta watsa mishi sannan ta ɗauke kanta "Ina naga kuɗin da zan ranta ma?Kuma kenan ta ɗan ka kawai kake ni kuma ko oho"ta ƙarasa tana girgiza jiki. Wani baƙin ciki ne ya turnuƙeshi a ƙufule yace"Yanzu saboda tsabar rashin tausayi kika bar yaron nan haka?Ina kuɗin da na baki jiya?Allah sarki Zainab,wallahi ta banbanta da matan zamanin nan" Tsaki ta buga cikin jin haushi "To amma duk wannan bai sa ta tsira a wurinka ba,kaga malam ba fa zaka zo ka saka ni gaba ka dinga min masifa ba ehe,na gaji wallahi"daga haka ta murguɗa baki tare da buga zane ta wuce ɗakinta. Idanuwanshi ne suka rine,jikinshi ya ɗauki rawa.Hannun Safwan ya kama ya fita dashi daga gidan. Abinci ya siyo mishi ya aje gabanshi "Kaci kaji Safwan,kayi haƙuri,na bar ka da yunwa"murmushi yaron yayi sannan ya riƙo hannun mahaifinshi ya zaunar da shi "Kar ka damu Abba, kaima ka zauna ka ci" Shafa kanshi yayi cikin tsantsan ƙauna yace "Allah yayi ma albarka Safwan" Sai da ya tabbatar yaron ya ƙoshi sannan shima ya samu ya siye abincin yaci,daga nan wurin mama suka wuce. *ZUBAIDA* Tunda taji samuwar cikin Zainab tabi ta addabi rayuwarta,ta hana kanta farin ciki,ta daina cin abinci kullum cikin fitina ta ke da Ya Bashir. Tsaye take gabanshi shi kuma yana zaune kan kujera ya ɗora laptop akan cinyarsa yana aiki. "Magana fa nake maka,amma ka ƙyaleni" Kallo ɗaya ya mata ya ci gaba da aikin da yake yi "To me kike so in Miki?" "Au wato baka ma san me zaka min ba ko? To wallahi dole ayi wacca za a yi"ta ƙarasa tana ɗaukar filon da ke gefenshi tayi jifa da shi. Haka ta dinga jifa da duk abin da takai hannunta.Miƙewa yayi ya riƙo ta da sauri kuma a fusace "Wai kina da hankali kuwa?" Kamar mai shafar aljanu ta juyo da ƙarfi tana watsa mishi idanuwanta da suka rine "Eh bani da hankali,ni mahaukaciya ce Bashir"ta ƙarasa tana dukan ƙirjinta. "Wallahi bazaka taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai ka haɗani da likitan da zai duba ni,nima na haihu kamar yadda zata haihu" Tureta yayi ta faɗa kan kujera ya nuna ta yana faɗin "Wallahi ba likitan da zan haɗa ki dashi, lokacin da kike yin allurar ki kin shawarce ni?Har nuna miki fushina nayi akan hakan amma kika yi biris, kika ce ke bazaki iya haihuwa kamar akuya ba.To yanzu na samu wadda zata haifo min ƴaƴa miye matsalata da ke" Zaburowa tayi da ƙarfi ta cakumo wuyan shi "Wallahi Bashir baka isa ba,kai kayi kaɗan ka tozarta ni.Mugu kawai maci amana Allah ya isar...................." Tasssss ya ɗauke ta da wani marin da saida ta tangaɗa,nuna ta yayi hannun shi na rawa "Na gaji da matsalolin ki,haukar ki ta isheni,wallahi idan kika kaini ƙul komai zai iya faruwa"daga haka ya ɗau kayanshi ya barta nan yashe tsakar falon. *ZAINAB* Na tsorata sosai da yanda ya shigo ɗakunan,tashi zaune nayi ina kallon shi cikin mamaki sannan na dubi agogon ɗakina ƙarfe 12:08. A hankali nayi magana ganin yadda jikinshi ke rawa "Lafiya dai Ya Bashir" Kanshi ya girgiza tare da dafe kanshi "Haɗa min ruwa toilet please idan zaki iya" A gurguje na haɗa mishi tsoro na ƙara shigata saboda ban taɓa ganin shi a irin wannan halin ba. Ina nan zaune har ya fito,cikin kayanshi da ke ɗakin ya ƙara shirin bacci ba tare da ya dube ni ba yace"Bani key ɗin ɗayan ɗakin" Idanuwana na zaro sannan nace "Lafiya dai,me ya sami ɓangaren ka" Tsaki ya buga tare da dafe kanshi "Don Allah ki bani" Washe gari ma anan ya shirya Amma yau koda ya fito ba wannan fushin na jiya,saima tsokana ta da ya shiga yi. A kwanakin da suka biyo baya na fahimci sun sami matsala da Zubaida ne,saboda kwana biyu da yin hakan mahaifiyar ta tazo gidan mun haɗu da ita tana ƙoƙarin fitowa daga ɓangaren gwaggo ni kuma ina ƙoƙarin shiga. Wani kallon banza ta min sannan ta buga tsaki ganin tana ƙoƙarin bangaje ni yasa na raɓe mata ta wuce. Daga yadda na samu Gwaggo na fahimci ba zuwan arziki matar nan tayi ba,duk da bata sanar da ni dalilin zuwan ta ba,amma ta gargaɗe ni da in tsare addu'a da neman tsarin jiki. Kwana biyu kuma sun dawo ɗinke kamar basu ba,dama ai mata da miji sai Allah. Rainon cikina na ci gaba da yi,ina samun kulawa sosai daga mijina har Gwaggo na. A Wannan lokacin ne na saka rigimar sai ya nemo min aiki,dariya kawai ya dinga yi min abinda ya ƙara tunzurani na saka mishi kuka. Tsagaitawa yayi da dariyar yana kallona"To naji aiki ko? Naji za kiyi"ya faɗa yana dafe bakinshi yana ƙoƙarin danne dariyar da ke taso mishi. Lallaɓani ya dinga yi tare da min alƙawarin barina nayi aiki idan na haihu,wannan ne ya rufe rigimar. A kwana a tashi har cikina ya fara tsufa,Ya Bashir da Gwaggo kullum cikin tariyar kayan haihuwa suke.Anty Halima ma ba a barta a baya ba,yadda take lissafin EDD ɗina ko ni bana lissafin shi haka. Kullum addu'a ta Allah ya rabani da wannan cikin lafiya,domin wannan cikin ya tanbanta da sauran,tun yanzu cikin ya mata wani irin girma. Zaune nake a kan carpet ɗin falon kasancewar yanzu bana son zaman kujera sam, na ɗora bowl da magarya a ciki akan cinyata ina sha. Kallon wayata da ke ƙara nayi,wannan kusan shine kira na 9 da ke shigowa wayar amma ba wanda na ɗaga. Tsaki na buga tare da jawo wayar da wani kiran ya ƙara shigowa, number Hafsa ce ɗagawa nayi tare da sakata hands free Ina ci gaba da shan magarya "Hello kina kina"naji Muryar Hafsat "Ina jinkiri"na faɗa ina ci gaba da abinda naie,dariyar mugunta ta saki "Takawarki lafiya uwar biyu,Amarya kuma shalelen Bashir ya hutawa"ta ƙarasa tana ƙara sakin dariya Ƙwafa nayi "Wallahi ki guji haɗuwarmu Hafsat,na rantse sai na kafta miki tsiya,ba uwar biyu ba,uwar tara"daga haka na katse kiran ina sakin guntun murmushi a karo na farko tun wayuwar garin yau. A kwanakin nan kowa haushi ya ke bani,hatta Ya Bashir ɗin haushin shi nake ji,lokuta da dama yasha kamani Ina harararshi sai dai yayi murmushi yace "Allah ya sauke ki lafiya Zainab" Hutun da su Amna suka samu a makaranta yasa Anty Halima tazo min da ita.Naji daɗi sosai,ko ba komai nayi kewar ƴaƴansu. A haka har na shiga watan haihuwa,har yazo ya ƙare shuru ba labarin haihuwa.Kamar wadda zata yi haihuwar fari haka na tusa Ya Bashir a gaba ina mishi kukan sai ya kaini asibiti an cire cikin. Lallashina ya dinga yi tare da kwantar min da hankali,haka ma Gwaggo ta dinga bani shawarwari. Duk lokacin da zamu haɗu da Zubaida to idanuwanta baya sauka ko ina sai akan cikina, fahimtar hakan da nayi duk lokacin da zamu haɗu naga tana min wannan kallon to zan dinga addu'a ina neman tsarin jikina. Amma yanzu da cikin ya tsufa bala'i nake ji da kowa, idan muka haɗu naga tana min wannan kallon a fili zan buɗa murya ina addu'a. Ko yau da muka haɗu na fito ina ɗan zagayawa,tana zaune akan wani ɗan dakali dake bayan gidan.Ban lura da ita ba saida na ƙaraso sosai,mun kwana biyu bamu haɗu ba sai naga kamar ta rame. Harara na banka mata tare da shafa cikina ina karanto addu'ar tsari tare da giftawa ta gabanta "Allah ya sauke ki lafiya Zainab"naji ta faɗa cikin sanyayyar murya. Da sauri na juyo ina duban ta cike da mamaki,kanta ta gyaɗa min tare da tashi ta matso inda nake.Ƙwallace ta cika mata ido a hankali kuma ta fara magana "Ina fatan Allah ya sauke ki lafiya Zainab,na tabbata matuƙar wani abu ya same ki to kamar ya same Ni ne,saboda ko yanzu Ya Bashir ta taki yake yi,baya bacci kullum cikin sallah yake yana roƙon Allah ya raba ki da cikin nan lafiya.Ba zan miki ƙarya ba Zainab,har yanzu bana jin ƙaunar ki a cikin raina,amma ina buƙatar zaman lafiya tare da ke.Ina roƙonki don Allah ki manta da abinda ya faru kizo muyi zaman aminci kamar yadda Ya Bashir ke so.Dama ni ce mai matsalar to wallahi na aje makamai na,zaman lafiya nake so,na gaji da wannan fitinar ba abinda ta tsinana min,sai tarin damuwa" Murmushin farin ciki nayi tare da riƙo hannun ta "Ina sha Allah komai ya wuce Zubaida,kuma naji daɗin wannan tunanin naki,nima kuma ina roƙon ki yafe min abubuwan da suka faru a baya" "Na yafe miki Zainab"ta faɗa tana goge hawayen idanuwanta. Shiru muka yi dukanmu saboda rashin sabo,ni ce ma na gaji da tsayuwar na mata sallama na koma sashe na. *RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️ *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 39* Wannan ne dalilin fara gaisuwar kirki tsakani na da Zubaida,duk da ban saki jiki da ita ba saboda ban gama yarda da tuban nata ba. Ita ma ba wani sakin jiki take sani ba,iya ka dai idan muka haɗu mu gaisa shi kenan. A daren wata juma'a ne na farka da na ƙuda,ni kaɗai ce a ɗakin kasancewar ba kwana na bane,ba yadda bai so ya dawo wurina gudun hakan amma nace a'a,tunda ba ita tace ta amince ba. Daƙyar na lalubo wayata na danna mishi kira,bugu biyu aka ɗaga "Hello"naji Muryar Zubaida ta ɗaga "Zubaida"na kira sunan ta daƙyar. "Innalillahi Ya Bashir,Ya Bashir tashi Zainab bata da lafiya"naji tana faɗa cikin ruɗewa da tashin hankali. A firgice suka shigo shi da ita,hannu na ya riƙa yana ƙoƙarin tayar dani daga tsugunnen da nake,shi ya nuna mata inda kayan da muka haɗa suke. A tsakar gidan muka haɗu da gwaggo,shi yayi driving ɗin mu har asibiti,mun samu likitoci a asibitin suka karɓeni tare da wucewa ɗakin haihuwa da ni. Aka bar su anan waje suna min addu'a da fatan sauka lafiya,Ya Bashir sai kai kawo yake yana jin kamar ya bini ɗakin yaga halin da nake ciki. *ZUBAIDA* Banbancin ta da Zainab dake naƙudar ƙalilan ne,za a iya cewa ma tafi Zainab ɗin ruɗewa. Zufa take sharcewa kallon Gwaggo tayi sannan ta dubi Ya Bashir fakar idanuwansu tayi ta matsa kaɗan. Number Ƙawarta Laila ta dannawa Kira jikinta na ɗaukar rawa,har ta katse bata ɗaga ba,sake danna kiran tayi shima har ta katse ba amsa. Bata yi sanya ba taci gaba da kira sai a kira na bakwai ta ɗaga cikin Muryar bacci ta fara magana "Haba Zubby,haba don Allah,ya kike nema ki ɗaga wa mutane hankali da kira a cikin wannan tsohon dare" Dafe kai Zubaida tayi ƙwalla na cika mata idanuwa"Ina cikin tashin hankali Lailai, Zainab na asibiti tana labour" "To shine me?baki yarda dani bane kome? Wallahi yau sai dai gawar Zainab ta bar asibitin nan ba dai ita ba" Kuka Zubaida ta ɓarke da shi jikinta na ƙara ɗaukar rawa "Don girman Allah ki taimaka a kwance abin nan, wallahi na fasa,ba zan yi ba, wallahi banida ƙarfin ɗaukar hakkin kashe mutum" Tsaki Laila ta buga "Wai duk saboda wannan ne ki ka bi kika ɗaga hankalinki?Mtssww,to akan ki aka fara wannan? Kuma ai bani na kira ki ba,ke kika kirani kika buƙaci a miki wannan aikin,to miye kuma na ɗaga min hankali cikin wannan tsohon daren" Zaman dirshan tayi a wurin bayan Laila ta buga tsaki ta kashe wayar.Jikinta sai rawa yake,tayi danasani,tayi nadamar biyewa zuciya. Ta jefa kanta a wannan rayuwar ne bayan da taji samuwar cikin Zainab, hankalin ta ya tashi ta rasa ina zata jefa kanta. Shaiɗaniyar zuciyace ta ƙawata mata kiran Laila,don neman shawarar ta ba ɓata lokaci ta bata gurguwar shawara kamar yadda ta saba. Ita ma kasancewar idanuwanta sun rufe yasa ta amince,ta tura ma Laila maƙudan kuɗaɗe, bayan kwana biyu tace mata anyi bincike aikin ba zai tafi yadda ake so ba,sai lokacin haihuwar Zainab ɗin yayi. Hankalin ta ya ɗan kwanta jin Zainab zata tafi ta bar mata mijinta,da farko ita so tayi kawai a fitar da Zainab ɗin,amma sai Laila ta nuna mata ai zata iya dawowa. Sai daga baya kuma abin yazo yana damunta,ta shiga ramewa a tsaye kullum tsoron ta yadda nauyin mutuwar mutum zai hau kanta.Bata ƙara ruɗewa ba sai da watan haihuwar ya kama,ta ma fi Zainab ɗin shiga tashin hankali. Wannan ne yasa ta nemi Laila tare da sanar da ita a kwance wannan aikin ita dai ta fasa,ita kuma ta sanar da ita bazai yu a kwance ba. Duk wani motsin Zainab ɗin tausayi take bata wannan ne yasa take bin ta da ido,tana jin ina ma zata iya da ta ɗauke cikin daga jikin Zainab ɗin ta mayar wa akan ta don ita ta mutu. Zabura tayi da sauri tare da matsawa kusa ganin likitan ta fito,ajiyar zuciya suka sauke a tare jin likitan na sanar da su an haihu an samu ɗa namiji. "To ya mai haihuwar"Zubaida ta faɗa da sauri,murmushi likitan ta yi "Ita ma tana lafiya komai normal In Sha Allah" Koda aka fito da Babyn tubarkallah kyakkyawa,tun da ya shiga hannun Zubaida ta kama ta rungume. Rungume Zainab Zubaida tayi bayan sun shiga ɗakin da take,hawaye na sauko mata,tana ƙara godewa Allah da wannan rufin asirin da yayi mata,dare da yawa ta kasa bacci saboda tunanin irin wannan rana. Kowa mamaki yake yadda Zubaida ta zage ake hidimar biƙi da ita,ta saki jikinta sosai kamar ba ita ba,ji take da Babyn kamar nata. Kaya masu kyau ta haɗawa jariri ta kawo mishi,ba wanda baiyi mamaki ba,Ya Bashir ma yaji daɗi sosai,wannan yasa ita ma ya yi mata kayan fitar suna masu kyau. Ranar suna yaro ya ci sunan ABUBAKAR SADIQ,an sha hidimar suna,an ci an sha an kuma riƙa a hannu. Su anty Halima tun kwana uku da haihuwa ta iso,da su aka yi hidimar suna,taso zuwa da Safwan amma Lawal yace ba inda zai je sai anyi hurumin dariya kawai tayi a ranta tace "kishi ne" Zaune nake ina kallon yadda Zubaida ta zage ita a dole sai ta sakawa Sadiq pampers,dariya nake mata ganin yadda take nuna ita a dole tayi ƙoƙari. "Wallahi nayi ƙoƙarin,dubi fa,ke dai bani kayanshi kawai"kayan na miƙa mata ina ci gaba da dariya. Tsaf ta shirya shi koda aka gama shirin har yayi bacci,miƙo min shi tayi tare da tashi tsaye "Goya min shi ki gani"ta faɗa tana juya bayanta. Ina ƙoƙarin tashi Ya Bashir ya shigo,harararta yayi sannan yace "Wallahi yanzu Zubaida na fahimci kin fi son Sadiq da ni,tun yaushe nace ki zo ki ɗauko min takardun da kika ajiye min amma kin ƙyaleni" Hannunta ta ɗora a bakinta"Shiiiiiiiii,don Allah kayi magana a hankali kar ya tashi"sakin baki yayi yana kallon ta sannan ya dube ni "Muje ki duba min Zee" Turani tayi "Yawwa je ki duba mishi don Allah" "Zubaida ta canja Honey,yanzu kamar ba ita ba"na faɗa lokacin da nake haɗa mishi takardun. Murmushi yayi tare da gyaɗa kanshi "Na sani Zee,nima na shaida hakan,kuma naji daɗin canja War tata,ko ba komai zaman lafiya zai samu a cikin gida na. Rayuwar da muke yi a gidan yanzu rayuwa ce ta zaman lafiya da kyautatawa juna. Na lura yanzu Zubaida ta canja takon kishinta,gyara take yi na musamman,ta canja har girki take yi yanzu.Wannan yasa na ƙara zage damtsen gyara nima saboda na lura yanzu ne zamu yi kishin. Sai da muka yi arba'in nayi shirin zuwa Sokoto,tsaraba na haɗa ta musamman ta ƴan uwana da kuma ƴaƴana. Wannan karon ni kaɗai zan tafi saboda Zubaida ta riƙe takunta,ta iya baiwa miji kula. Nima da shirin gyara na musamman na nufi Sokoto don bazan yarda na zama borar Zubaida ba. Mun samu tarba ta musamman Ni da Sadiq,a ranar da na sauka a ranar Safwan ya zo bayan ya dawo makaranta. Rungume Sadiq yayi kamar ya haɗiye shi, sumbatar gashin shi yayi sannan ya dube ni "Mommy Ina ta addu'a Allah yasa ki haifi mace a saka sunan Aysha" Murmushi nayi nima "To ai sai Maman ka ta haifo ma"ɗaure fuska yayi daga nan bai ƙara magana ba. Mun sha ziyara,sai da na gama yawon da zan yi sannan na fara zuwa wurin gyaran jiki,gyara ake min na musamman. Kuyi haƙuri da wannan muna fama da matsalar wuta wayata ba caji *RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️ *AURE DA KARATU* *NA* *RUMAISA'U SIDI* *FARAR ANIYA WRITERS* *Page 40 End* *Bayan shekara 6* A cikin shekarun nan abubuwa da yawa sun faru,na ƙara haihuwa bayan Sadiq na haifi mace Ya Bashir ya mayar min da sunan Aysha. Aysha ƴar gatan kowa ce a gidan,kowa ji yake da ita,hatta Safwan da ba ma gari ɗaya siyayya yake ya sako a mota yace nata ne. Kuma ni yanzu Aysha ce kawai a hannuna Sadiq yana wurin Zubaida,tun da na haife shi duk wani raino na shi ita tayi. Da za a yaye shi ma ita tayi,tun daga lokacin kuma bata mayar min da shi ba nima kuma ban mata magana ba,saboda tausayin da take bani na yadda ta ɗauki ƙauna ta ɗora mishi. Duk abin da ka gani a wurinta zaka ji tana faɗin "Wannan na Sadiq ɗina ne"duk da ni gaskiya bana cikin irin kishiyoyin da za su iya kyautar ɗa,ba zan iya ba gaskiya,amma nayi alƙawarin ƙyaleshi a hannunta ba zan taɓa yi mata maganar ya dawo wurina ba. Zubaida ma ta haihu amma abin bai zo da rai ba,daga nan kuma shiru sai yanzu da take ɗauke da ƙaramin ciki. A ɓangaren Ya Bashir ba abin da za a ce sai alhamdulillah,buɗi ya ƙaru,an ƙara zama Alhaji,ko da nayi mishi maganar aikina kai tsaye ya nuna min a'a duk abin da nake buƙata zai min amma ina aje maganar aiki ba yanzu va. Ya siya mana sabbin motoci,ya bamu kuɗi muyi jari,ko da ya bincike ta abin da zata yi sai tace irin sana'a ta take so,bai yi sanya ba kuma roƙe ni da na nuna wa mata yadda ake business ɗin. Ita ma bata saka girman kai ba,muka haɗa kanmu ina nuna mata.A ɗan zaman namu na fahimci bata da girman kai duk abin da bata gane ba zata tambaya. Ko girki ta samu ina yi da taji ƙamshin ya mata,zata same ni "Maman Aysha ya ake wannan,me kika saka yayi haka"haka zata maƙale min har sai na nuna mata,duk da wani lokacin kishi baya bari na nuna mata komai saboda ina gudun ta kwaɓe min tazo ta fini zaƙewa. Daga ni har ita kowa ƙoƙari yake ya ciri tuta a idanuwan mijin wanda na lura hakan yana matuƙar saka shi farin ciki.Ta dage sosai sai ta ƙwaci mijin Ni kuma na nuna mata har yanzu da sauran ta. A nawa ɓangaren ba abin da zance sai Alhamdulillah,komai yana tafiya cikin nasara,duk da ita rayuwar nan ba za a rasa ƙalubale ba,amma ina ƙara godewa Allah da Wannan canjin da ya min. Idan na kalli ƴaƴana sai dai na ƙara hamdala saboda na san ni'ima ce,ace duk waƴannan ƴaƴan nawa ne mallaki na ne. Ga Safwan ɗina ya zama saurayi har mamakin girman shi na keyi,tun da ya kammala secondary School mahaifinshi ya buɗe mishi shago ya saka mishi takalma na maza da na mata. Lokacin da ya faɗa min na yi farin ciki sosai,nima kuma na siya mishi shaddodi da atamfofi na bashi nace ya saka a ciki kuma ya kawo min riba idan an sayar. Mahaifinshi ma yaji daɗin hakan da nayi har cewa yaron ya faɗa min yana godiya. Cikin ikon Allah sai shago ya fara haɓaka sannu-sannu,yaron yana da nasibi sosai.Bincikar shi nayi maganar karatu yace mahaifinshi yace ya kula da kasuwanci ba ya da ƙarfin kula da karatun shi har jami'a. Jin haka yasa nace ya bincike shi in har ya amince ni zan saka shi,yace ba matsala,nan take ina daga can nayi magana da Ya Abbas aka shiga ƙoƙarin sama mishi gurbi a makaranta. Haka yake kula da komai,zai je makarantar shi idan ya dawo kuma ya buɗe shagon shi. *BASHIR* A nashi ɓangaren kullum ƙara godewa Allah yake da wannan ni'imar da ya mishi ya bashi mata kamar Zainab.Saboda zai iya cewa ta dalilin shigowarta rayuwarsu Zubaida ta canja,abin da ya ɗau tsawon shekaru yana ƙoƙarin fahimtar da ita,amma kai tsaye sai gashi ta canja. Ya sani soyayyar Zainab ta daban ce a cikin rashi,ƙaunar ta halittace da Allah ya dasa mishi wanda ba ranar gushewarta sai ranar da numfashin shi ya rabu da gangar jikinshi.Amma kuma a yanzu ita ma Zubaida tana da wani matsayi na daban a cikin zuciyarshi wanda baya fatan rasa ta ko na daƙiƙa.Yana ƙoƙarin sosai wajen kwatanta adalci a tsakaninsu,baya fatan tashi cikin masu shanyayyen ɓarin jiki kamar yadda Manzon mu Annabin rahama ya siffanta mazan da basa kwatanta adalci a tsakanin matansu. Buɗi yake samu ko ta ina,kuma ya san wannan baya rasa nasaba da kwanciyar hankalin da yake ciki.Ɗan gata ne a wurin iyalin shi, kowa ƙoƙarin kyautata mishi ta yake. Ga kuma ƴaƴanshi da yake jin kamar ya haɗiye su don ƙauna,yana ƙara godewa Allah duk lokacin da ya dubi yaran,ace wai waƴannan yaran nashi ne,jininshi ne sai dai yace Alhamdulillah. *ZUBAIDA* Duk da ba wai ta daina jin kishin Zainab ba,tana ji har yanzu amma tana ƙoƙarin danne wa da kuma addu'a kamar yadda anty Maryam ta bata shawara.Kuma har yanzu a wurin wannan matar da Anty ta haɗata da ita take siyayya. Saboda yanzu ta daina biyewa Anty Amina ko Laila,don ta lura ba inda shawarar su zata Kaita sai Wuta.Dama ita mahaifiyar ta matsalar ta ɗaya taji an taɓa ta yanzun nan zata zo ta fara cin mutunci.To da ta fahimci hakan sai ta daina faɗa mata komai,shima Ya Bashir ɗin sai ta daina kai ƙarar shi a wurin Gwaggo. Duk abin da take buƙata zata same shi ta roƙe shi,idan yana da hali zai yi mata ita ma Zainab ya bata,idan kuma baya da hali zai faɗa mata tayi haƙuri. Da tayi ƙorafin yana yiwa Zainab abu alhalin ai ita ta tambaya sai ya faɗa mata hakkine.Ita ma duk lokacin da taga ya bata wani abu to Zainab ɗin ta tambaya shi yasa ya haɗe ya musu. Allah ya ɗora mata ƙaunar Sadiq,tun da aka haifi yaron take jin ƙaunar shi ta daban.A wurinta yake wuni cin abincin shi kawai ke mai dashi wurin Zainab. Koda lokacin yayen shi ya yi ita ta yaye shi,daga nan ne kuma taƙi mayar da shi,kuma har yau Zainab bata taɓa nuna mata ko a fuska tana takura da rashin mayar mata da ɗan ta ba. Ko wani abun aka siyo to ita ake ba na Sadiq,ita kuma Zainab a bata na Zee da Aysha. Har ita ke fitar da kuɗi ta siyawa Sadiq Abu amma taƙi siyawa Zee,ita kuma Zainab ganin haka sai take yiwa Zee ɗin ita ma. Ga business ɗin da take yi,wanda Ya Bashir ya basu jari kuma da taimakon Zainab ta gane kan abin.Haka ma ta aje wani girman kai duk abin da bata gane ba zata tambayi Zainab saboda ta lura mutuniyar kirki ce,bata da mugunta duk abin da ta tambaye ta zata faɗa mata matsawar dai ta sani ba abinda zata ce yanzu sai alAlhamdulillah. *GWAGGO* Kwanciyar hankalin ɗan ta ya fiye mata komai,duk wanda ya gan shi a yanzu ya san ya samu kwanciyar hankali. Ita ma ta ji daɗin sauya war Zubaida ko ba komai hankalin ɗan ta ya kwanta,ya rabu da tashin hankali. Ga ƴarta ita ma tana gidan auren ta lafiya lau,ga jikokinta zagaye da ita.Ga kuma Zainab ɗin ta ita ma hankalin ta ta kwanta ba abin da zata ce sai Alhamdulillah. LAWAL To shima dai a nashi ɓangaren ci gaba yake samu ta kowa ne ɓangare.Ya ƙara faɗa ɗa shagon shi,ya mayar da shi ƙaramar plaza inda yake siyarda kayan miya da su arrish,kayan ɗanɗanon miya,taliya,shinkafa,masara da dai sauransu. Ga matar shi Nusaiba ta canja,tun bayan da ta daki Safwan ya tura ta gida tayo hutun sati biyu aka samu salama. Duk da dama can ba wani shiri suke da yaron ba,amma dawowar ta sai ta canja sosai.Ta kama kanta dama ita ce mai shiga harkar shi. Kuma Allah ya albarka ce shi da haihuwa ya sami ƴa mace,Safwan ne ya raɗawa yarinyar suna A'isha.Shima ya ji daɗin sunan da yaron ya saka don dama shi ya ke da burin sakawa Haihuwar A'isha ne yasa aka fara shiri tsakanin Nusaiba da Safwan,suka koma kamar ba su ba.Yanzu an mai da ƙofar ɗakinshi ta baya, kasancewar ya fara girma. A cikin waɗannan shekarun kuma Lawal ya rasa mahaifiyarshi, mutuwa ta fuju'a tashi kawai aka yi aka iske ta rasu.yayi kukan mutuwar mahaifiyar shi sosai,wanda har Zainab sai da ta zo musu gaisuwa. A yanzu yana cikin rufin asiri daidai gwargwado ba abin da ya nema ya rasa.Duk wata buƙatar iyalinshi yana ƙoƙarin tsare wa har Amna da bata hannunshi yana ƙoƙarin sauke hakkin ta da ke kanshi a yanzu ba abin da zai ce sai Alhamdulillah. *HAFSAT* A ɓangaren Hafsat ƙawar Zainab ma, komai na tafiya daidai mijinta yayi aure har matar ta haihu.Cikin iyawar Ubangiji ita ma ba jimawa da haihuwar matar ita ma ta samu ciki bayan wata tara ta haifo ƴan biyu mace da namiji. Ta yi murna sosai kuma ta gode Allah da wannan ni'imar da ya mata,gashi ta ci ribar haƙurin da tayi. Yaranta sun zama abin so ga kowa,mijinta na ƙaunar ta,bata da matsala da kishiya don ba ma gida ɗaya suke ba,ita kam ba abin da zata ce da wannan ni'imar sai Alhamdulillah. *UMMI* Kamar yadda muka sani burin kowa ce uwa kwanciyar hankalin ƴaƴanta,hakama farin cikin kowa ce uwa farin cikin ƴaƴanta. Tun bayan auren Zainab da Bashir hankalin Ummi ya kwanta zuciyarta ta samu salama.Addu'ar ta kullum Allah ya ƙara basu zaman lafiya da zuri'a ta gari. Ga ƴaƴanta maza kullum abubuwan su ƙara gaba suke saboda kyautatawar da suke mata. Zaman Amna a tare da ita ke ɗebe mata kaɗaici, yarinyar ta girma yanzu an zama ƴan matan Jss.Amna ta riga ta zama ƴar Ummi har bata son tayi nesa da ita, kullum tana maƙale da Ummi bata ma wani kewar mahaifiyar ta.Lokaci bayan lokaci kuma tana zuwa ta gaida mahaifinta. Ajiyar zuciya mai ƙarfi na sauke bayan na dawo daga dogon tunanin da na tafi hannuwana na ɗaga ina ƙara godewa Allah da wannan sauyin da ya min. Juyowa nayi da sauri jin ihu Aysha abin da ya tilasta min tashi na fito "Wa ya taɓa min autah?na tambaya ina ƙoƙarin ɗagota daga faɗuwar da tayi tana turmuza jikinta a ƙasa. "Mommy wallahi Sadiq ne ya ture ta"Zee na duba dake min bayani,raina ne ya ɓaci kusan kullum sai Sadiq ya saka Aysha kuka,rigimamme ne na ƙarshe. A fusace na tunkari ɓangaren mahaifiyarshi ina riƙe da hannun Aysha.Yana maƙale jikin uwar tashi ita kuma tana zaune da ƙaton ciki a gaba. Ɓoye shi tayi a bayanta alamun ta san bayada gaskiya.Nuna shi nayi cikin ƙunar rai "Wallahi idan ka ƙara dukar min ƴa sai na zane ka,na lura kai baka san ana ƙyale ka ba" Zuro kanshi yayi tare da yin gwalo ita kuma kamar sakarya ta sa dariya,raina ne ya ƙara ɓaci abinda ya kai ga nasa hannu na fizgo shi na shiga jibgarshi. Tureni tayi da ƙarfi sai da na kusa faɗuwa,idanuwanta suka cika da ƙwalla a fusace ta fara magana "Kin yi kaɗan ki zo har gabana ki dake shi,kuma wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara dukan min yaro idan ba haka ba duk abin da na miki ke kika ja"daga haka ta kwashi ɗan ta da ƙyar ta ɗora a kafaɗa taƙui-taƙui ta wuce ɗakinta. Ni na ma manta da anyi wata rigima kwatsam bayan dawowar Ya Bashir ya kirani yace in same shi ɓangaren shi. Ko da naje tana tsaye sai jijjiga take kamar wadda aka kunnawa disko kallo ɗaya na mata na kawadda kaina tare da isa wurin da Ya Bashir ke zaune da murmushi a fuskata na ce "Sannu da zuwa Honey"shima murmushin yayi yana nuna min Zubaida da idanuwanshi, murmushi nayi nima bayan na dube ta. Gyaran murya yayi sannan ya fara magana"An kawo min ƙarar ki Zainab"zaro idanuwana nayi "Ni kuma me nayi?" Duban ta yayi "Ki zauna mana"girgiza kanta tayi sannan ta fara magana "Ba wani zama da zan yi,kawai ka jawa matarka kunne kar ta ƙara dukan min yaro,idan kuma ba haka ba wallahi Zubaidar da aka sani a baya ce zata dawo.Don ba zan ɗauki aje har cikin gidana a dukanmin yaro a gabana ba,kuma ai ba shi kaɗai ke zaluntar ta ba ita ma tana zaluntar shi ko don ni bana magana.To wallahi ba zan ɗauka ba,idan ma kina son ki tunatar da ni ke kika haifi Sadiq to ki kwantar da hankalinki na sani kuma ban manta ba"daga haka ta bar ɗakin. Dariya muka sha ni da Ya Bashir bayan wucewarta,yadda Zubaida ke damuwa da sha'anin Sadiq ko kanta bata damuwa da shi haka. Koda na fita sai da na shiga na bata haƙuri ba kunya ta amshe tare da faɗa min ya wuce.Allah ya gani ina jin daɗin ƙaunar da Zubaida ir nunawa Sadiq,saboda duk wanda yace yana son abinka kamar kai yake so,kuma inda hankali na ke kwanciya bata nuna mishi saken da zai sa ya lalace,idan yayi ba daidai ba tsaf zata zane shi ko ta mishi faɗa amma idan mu muka dake shi to yanzu za a ji bakinta. Bayan kwana biyu Zubaida ta haihu ta haifi ƴarta mace kyakkyawa.Munsha bidirin sunan Khadijah takwarar Gwaggo. A hankali gidan mu ya cika da ƴaƴa,Gwaggo ta tara jikoki Ya Bashir ya tara zuri'a,Zee aka samu ƙanne,idan kaji gidan tayi shiru to tabbata sun tafi makaranta. Idan na gaji ɓangaren Zubaida nake turasu,da zarar an fara taɓa ɗan lelenta yanzu zata kaɗomun nawa ta riƙe nata. Idan na kalli ƴaƴana sai dai na ƙara hamdala saboda na san ni'ima ce,ace duk waƴannan ƴaƴan nawa ne mallaki na ne.A wannan gaɓar ba abin da zance sai dai nace *ALHAMDULILLAH.* Nima anan zan ce *ALHAMDULILLAH* Ina roƙon Allah yasa wannan littafin ya amfani jama'a da dama.Ina kuma bawa makaranta wannan littafin shawara da suyi ƙoƙarin yin amfani da kyawawan abubuwan da ke ciki,su kuma yi watsi da munana. Ina fata abinda na faɗa daidai Allah ya bani lada,ku ma masu karatu Allah ya baku. Inda na yi kuskure kuma Allah ya gafarta min ya kuma gafarta wa masu karatu. Allah ya gafartawa mahaifina da duk waƴanda suka riga mu gidan gaskiya. Allah ka ƙara wa mahaifiyata lafiya da nisan kwana. Allah ya ƙara muna zaman lafiya a jihohin mu da ƙasar mu baki ɗaya. Allah ka kawo muna ɗauki ga waƴannan musibun,ka magance muna abin da bamu da ƙarfi ko iko akan shi. Allah ka fi mu sanin abin da yake daidai, Allah ka gyara muna ƙasar mu. Allah ka yafe muna kurakuran mu,ka kuma ƙara hore muna abin da zamu yi lalurorin mu. Allah ka shirya muna zuri'ar mu,ka kare su da miyagun ƙaddarori.Ƴan mata da samari masu buƙatar aure,Allah ka aurar da su. Matan auren da ke cikin matsala a gidajen auren su, Allah ka yaye musu.Waɗan da ke cikin wadata da farin ciki Allah ka ƙara musu. Daga ƙarshe ina miƙa dubun godiyata ga makaranta wannan littafin da suka yi jimirin biyo ni tun daga farkon littafin har zuwa yau.Suka kuma ci gaba da bani goyon baya,ta hanyar nuna jin daɗin su da yin comment da sharing wannan littafin a mabanbantan groups,Ina godiya sosai da kuma fatan zaku biyo ni a littafina na gaba. *NAGODE*🙏🙏🙏 *RUMAISA'U SIDI✍️✍️✍️* *08104445106*