*BOROROJI* 🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Littafi na D'aya... Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris Mafarin labari... BABI NA ƊAYA Niger Republic. Tayi makotaka da wasu ƙasashen har guda bakwai. Chad Burkina faso Benin republic Libya Algeria Mali Nigeria. Kuma dukkan su ƙasashen a zagaye suke da kabilar Wodaadabe Bororo da wasu dangin Fulanin... 2000/ May/08 Nishi take a hankali, tare da cizon bakinta. Iska ta kuma ja alamar tana cikin tsananin zafin nakuda, juya kai tayi cikin tsannanin takaici da bakin ciki, ga wani abu da ya tsaya mata a makogaronta. Yau kimanin wata goma sha biyar kenan da take jin abin a ranta, har yanzun bata ji saukar shi ba. "Sannun Abuh ga ruwan addu'o'in sha Insha Allah zaki sauka akan gwiwar lafiya." D'ago kai tayi ta kalle shi cikin tsannanin k'iyayya da bakin ciki, sannan ta sunkuyar da kanta, tare da had'a kai da jikin itaccen da akayi gadon kara dashi. Ta kuma sauke wata ƙatuwar nishi a hankali jariri ya fado daga kasanta, cikin wani irin kakkarin kuka bayan ya zabga atishawa, Allah da idon shi ya diro da uwa baki daya. Murmushi tayi lokacin da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da wuccewar abinda ya tokare mata kirjinta. A hankali ta mike tare da ɗaukar wani mayafi da zani ta daura sannan ta dauki babban zanin da yake sayo mata, tayi kunzugu dashi. Kafin ta isa gaban shi tace mishi. "Kowacce rayuwa akwai samu akwai rashi, akwai nasara akwai faduwa. Kamar yadda ka zalince ni Ya Allah Ya ninka maka abinda kayi min. Kamar yadda ka saka ni kuka Ya Allah Ya sakaka kuka. Kamar yadda ka hanani farin ciki Ya Allah Ya hanaka, zan so Ubangiji ya jefa ka, kasar jahannama. Ya turaka ƙarƙashin fir'anuna da hamana, Ubangiji ya haɗaka da masifa da bala'i, Ya Allah Ya sanyaka bakin ciki sama da yadda ka saka ni." Takowa tayi gaban Jaririn ta juyar da shi, tana me kallon Mutumin da yake tsaye, ta sake murmushi me had'e da kuka, tace mishi. "Ba zan yi fatan kayi irin na wancan mujirimin ba, zan so kayi rayuwa cikin salama, wannan mutumin da ya samar da kai mugu ne, mugu mara alkibla, fasiki mara imani, kazami me dauke da datti da kazamta na bala'i da masifa da jahilci ya goga maka bakin fanti na har karshen rayuwar ka. Iya haka ma ya ishe ka, ka tsani wanda ya bada gudummawar jazaman ƙaddararka" Sannan ta tako gaban shi cikin bakin ciki mara iyaka, tace mishi. "Sama'ila kenan, gamu ga ka ga duniya ga Allah ya tsayawa me gaskiya." Ta juya ta nufi kofar dakin zata fita. Riko hannunta yayi tare da zuba gwiwar shi a kasa, cikin tashin hankali yace mata. "Don Allah ki rufa min asiri, ki dauki Yaronki, bai da gatar da yafi naki, Zainabu zan gyara kuskuren da nayi a shirye nake na isa gaban danginki don Allah ki rufa min asiri karki juya mana baya a daidai lokacin da muke bukatar ki" Cak ta tsaya tare da sake wata irin kuka da sai yanzun ta samu damar yi, tare da shasheka. "Aminci Allah Rahaman Allah, jin kan Allah Ubangiji ya hanaka su tun daga duniya har lahira" sannan ta saka ta bar dakin da rugar baki daya, tana tafiya tana kuka dukda sulisin dare ne, bai hanata tafiya ba, sai da tayi dogon tafiya kafin ta isa wata iyar karamar gari, tun daga nesa take hango kamar fili ne sahara babu kome sai rairayi. Kurawa gurin ido tayi alamar kamar ba nan take nima ba, dan haka ta cigaba da tafiya har alfijir ya keto sanyin Asuba ya kuma gabatowa zama tayi a kasar wata bishiya tare da kusa hannunta kasar cikin ta da yake murɗa mata jini na zuba a hankali. Barcin gajiya ce ya dauke ta. Kamar yadda Zainabu ta fita daga dakin da rugar baki daya, zama yayi yana kallon jaririn da yake ta kyankyara kuka kamar zai shiɗe, a hankali yake jin muryan jaririn zaaa a kunnen shi. Har ya kasa jure kukan jaririn, ya dauki wata zani ya lullube shi, tare da kallon fuskar shi, kamar ya shake shi. Amma ya fasa, can wata zuciya ta kuma bashi shawaran ta kashe shi ya huta da godon abin kunyan da ya aikata. Zama yayi tare da kurawa jaririn ido, babu abinda ya bar mishi. Domin kwayar idanun shi tarr akan na Ubanshi, kwallar da yake cikin idanun shi ce ta sauka akan na jaririn, ya kuma ware idanun shi tare lumshe nashi. Kwayar idanun yaron kamar an ja shi da kwali, cikin idanun zaiba ce kamar wanda aka zana da ruwan zinari. Sai dan digon bakin tsakiyar ya Kawata kwayar idanun Yaron goshinsa kuwa cike yake da gashi me shegen laushi da tsantsi. Gashin giran shi a haɗe yake da juna, karan hancin shi har bakin shi, bakin shi karami me kyau dai-dai ta jarirai, wanda Uban yake hangowa sakamakon hasken fitilar kwai da take ci. Hannun shi ya saka a bakin shi yana tsotsa cikin hakuri da juriya, wani irin kukan danasani ne ya shiga saukarwa Uban. Me yasa ya aikata abinda yake ganin dai-dai ne, me yasa bai hakura da Zainabu a ranar ba, me yasa ya rushe mata na ta farin ciki. Yana sane da iyayen ta, sun bar gurin su, ina zasu kuma haduwarl bayan yasan suma Bororoji ne, ba ma zauna bane kuma ba zasu tsaya ba. Zai yi wuya su tsaya tunda su din Fulanin tashi ne. Bai ga amfanin fitowar shi a cikin kabilar Wodaadabe Bororo ba, bai ga amfanin amsa sunan Bororo ba. Ya zai yi da rayuwar jaririn nan? Ya rabata da kowa nata, ya raba ta da farin cikin ta, ya kawo ta inda yayi ta gasata da bakin ciki da tashin hankalin, me yasa bayiwa rayuwar shi adalci ba? Me yasa bai tuna da wannan lokacin ba? Ya lalata rayuwar jinjirin shi, ya lalata kome nashi, me zai cewa duniya me zai gayawa mutanen da suka bugi kirji suka amsa karyar shi a a madadin gaskiyar shi? Wacce irin son zuciya ce ta kai shi da aikata wannan kuskuren! Lallai tafiyar shi rugar Alu yaja mishi bakin cikin da zai mutu yana danasanin kuntatta mata da yayi. Kukan jaririn da kiran sallar farko ya sa shi, fahimtar asuba yayi. A hankali ya mai da jinjinrin kamar ya kashe shi amma yana jin kamar haka ba zai yiwu ba. Tunda yasan makotan bukkar su. Wani irin tausayin jaririn ne ya kuma kama shi. Dan haka ya mike tare da d'aga labulen ya fita a hankali lokacin har anyi Sallah asuba. --- Bayan yayi alola ne ya dawo D'akin ya rasa yadda zai yi da jaririn, domin ya cikawa mishi kunne da ihu, har ta kai makotar shi sun fara zargin ko uwar yaron ta gudu ne yaki gaya musu, kuma har zuwa lokacin bai raba yaron da cibiyar shi ba, dan haka yayi ta zaman dakin yana kallon jinjirin. "Gafara dai Sama'ila, me nake ji a gari ana ta fadar cewa Abuh ta gudu ta bar maka jariri ba dai abinda su.?" Yadda ta kalle shi cikin tashin hankali, shima kuma ya sunkuyar da kai tare da mika mata jinjinrin yasata fashewa da kuka. Tare da cewa. "Kaico wannan wacce irin ƙaddara ce? Me yasa kayi haka? Gashi nan abinda kayi ya lalace ya Barka da kunya me yasa ka aikata haka? Me yasa ka rushe yarda da ke tsakanin mu? Meye muka gaza maka? Ni mijina Hamma Sama'ila ka cuci wanna abin ka zalince me zaka ce mishi idan ma abinda ake zargin ka dashi haka ne me yasa? Me yasa ka tozarta baiwar Allah, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun." Ta kuma fashe da mugun kuka tana kara rike dan jinjirin. Tana kuka kallon shi, sannan ta fita da jaririn tana wani irin kuka me ban tausayi, duk bukkar da ta shige sai taji sun ce mata "tir" har ta isa bukkar ta, mijinta me suna Sanda ya fito tare da kallonta da dan luɗi, yace mata. "Kabo lafiya?" "Sanda me zanyiwa Hamma Sama'ila ya fahimci abinda ya aikata? Me yasa yake da mugun son kanshi? Meye ya saka shi aikata abinda zai saka mu kuka har karshen rayuwar mu.". Shiru yayi sannan yayi kwafa. Kafin yace mata. "Shiga da jaririn ciki an fara cika mana" juyawa tayi ga wasu daga cikin mutanen da suke kewaye dasu har sun fara fito mishi, dan haka ya shiga cikin dakin, tare da sake labulen. Ta saka jaririn a gaba tana kuka.. Shi kuma ya nufi bukkar Sama'ila. Yana shiga ya same shi zaune ya cusa hannu a cikin gashin kanshi, yana nazarin makomar rayuwarsa da na abinda aka haifa. "Sama'ila meye ya faru? Ina Abuh?" "Ta tafi, kome ya lalace kuma nayi farin cikin faruwar haka. Domin ta haka ne zai saka na girbi abinda na aikata, kuskuren ne babba ka kalubalanci kaddarar wani, amma babban tashin hankalin yadda rayuwa zata juya maka idan har duniya ta san waye kai? Meye matsiyin shi a cikin al'umma? Meye zance mishi a cikin al'umma,? Me zan mishi idan ya min tambaya daya tak? Sai yaushe zamu daina aikata laifukan ci da karfi? Yaushe kuka zata daina wanzuwa a zukatar mutanen da suka fada irin abinda na aikata? Yan mata nawa ne zasu daina kuka? Yan mata nawa ne zasu daina gudun kabilar Wodaadabe? Me yasa muka yi kaurin suna ta hanyar lalata farin cikin wasu? Me yasa na san wani sirri har na saka Iyaye da yawa kuka? Sanda nayi tir da Allah wadaran halin irin nawa, a wancan ranar abinda take so ta zab'a amma na kasa Fahimtar haka,. Iyayen ta sun gudu sabida abin kunya, mijin da zata aura ya tare ni naashi dukar da sai dai wani ba shi ba. Tir tir tir da halina." Ya fada yana me fashewa da kuka. Can kuma ya shanye kukan yana kallon Sanda wanda yake kallon shi cikin tausayi. "Babu kome ya yaron yake ka duba min shi" Ta faɗa tare da juya mishi baya, yana kuka sosai, haka sanda ya fita daga dakin, shima idanun shi yana cika da kwalla, sau daya ake aikata kuskure amma sai ka kai sau dubu kana danasani mara amfani.Yau ga abinda ya nusar dashi ya faru karka zama mara adalci a rayuwarka domin goben ka zata maka rashin adalci. Koda ya koma gida ya samu tayiwa jinjirin wanka tass, sannan ta kuma yanke cibiyar da ba a yanke ba. Ta binne shi sannan ta nad'e shi cikin farin mayafi, kallon jinjirin take tana mamakin yadda bakin jinjirin ya bayyana tun bai sha iskar duniya ba, dan haka ta dauko kasko ta fara gasa mishi cibi yana ihu da kuka. Kafin ta gama ta kuma kwantar dashi dan ya sha ruwa ainun. --- Bude ido tayi tare da kallon dakin da take, kokarin tashi take taji alamar an saka mata abu a hannunta, kallon gurin tayi taga ƙarin ruwa ne. Da sauri ta bude bakinta zata yi magana. Wani farin dogon mutum ne ya shigo, cikin farin labcoat. Ya kalle ta yana murmushi. "Sannun ya jikinki?" "Da sauki" ta faɗa tare da juyar da kanta gefe Safar hannun ya saka tare da nufar kanta, zai duba ta tace mishi. "Karka tab'a" jan kujeran yayi yana kallonta, kafin ya nutsu ta fara kokarin dubata. "Kin haihu baki tsaya duba matsalarki ba, kika baro can din jini na zuba miki, me yasa kike haka?" "Me yasa ba zan yi haka ba? Me yasa kowa ya guje ni? Kai ma ai sabida ina kawo tallar nono nan yasa" "Zainab!" D'ago kai tayi tare da kallon shi. "Har yanzun babu abinda ya sauya! Kuma ban ga laifin su dan sun gudu ba, sai dai akwai matukar ciwo abinda ya faru dake, kuma ba dukkan iyaye bane zasu fahimci girman kaddarar da ta." "Me yasa ita ƙaddarar bata biyo ta kan kowa ba sai ni? Me yasa babu wanda ya gane akwai ƙaddara sai da ya faɗa min, idan har da gaske batu ne na kaddara jeka dawo da da ahalina da suka tserewa ƙaddara ta, idan kayi haka zan Fahimci girman abinda kake nufi da ƙaddara." "Kin jahilci ƙaddara amma zan barki nan da kwana uku idan kin ji sauki muje a dauko abinda kika haifa, ko ya mutu ne?" Cikin wani irin bakin cikin tace mishi. "Bai mutu ba,amma kuma ba zan dauke shi ba, ya zauna ya girbi kuskuren da uban shi yayi." "Me yasa baki da tausayi? Me yasa baki da hankali? Me yasa baki da imani, toh zamu je mu dauko shi." Cikin fushi ya fice daga dakin , ta fashe da kuka wanda take tun daga kasar zucuyarta. Tasan tunda ta ganta a cikin asibitin tabbas ta shigo garin Maradi ne, tunda dama a wani kauyen Maradi suke.... ** Yau kwana biyar da haihuwar Yaron, amma baki daya kauyen an tsangwame su, musamman Sama'ila wanda shi ya fi kowa fuskarta matsa kai ko masalaci, ya je ba a sallah dashi, wannan dalilin yasa aka daina ganin shi a masallacin baki ɗaya. Shiru da ta daina ganin dan uwanta shine tazo duba shi, dake ko aika ne an hana yara mata, tana tafe tana jijjiga yaron, wanda nonon akuya ake bashi yake sha. Abin tausayi, yana ta kyankyara kuka, tana isa bukkar ta d'aga labulen wayam ta gani, cikin tsoro ta kuma shiga dakin Babu Sama'ila babu dalilin shi, sai wata yar tsohuwar fatar rago da yayi rubutu da harshen ajami da shi ya rubuta mata. كي حقر مثني مك لف بذ أي ذم ا غرنني يثن بر غرا اني إكا قام الحر Kuka ne ya kuma kwace mata, tana gani da sauri ta fitar dashi wa mijinta domin bata san me ya rubuta ba, kuma duk abinda ya rubuta ba zai wuce bankwana ba. Dan haka ta fita tana gudu ana kauce mata a hanya, koda ta isa gidan tana shiga ta mika mishi. Yana dubawa yaga sakon. "Kash! Sama'ila me yasa baka da kirki? Me yasa baka da hankali kana tir" ya faɗa da karfi dan ya gama jin haushi kamar zai yi wani abu. "Ina fama da matsalar Ardo ya sallame mu a garin. Kuma haka shine mafi alkhairi domin idan muka cigaba da kallon wannan yanayin zamu iya shiga tashin hankalin da yafi wannan abin kunyar, kuma wannan abin zai fi mu shiga tashin hankalin da yafi ba mu. Dan haka zamu wuce Maradi kawai." "Wannan shine adalcin da zamu yi mishi." *_Toh gamu nan a wata tafiya! Me kuka gane_* [7/14, 1:05 PM] RamlatArManga: I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx '''Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida...🗣️🗣️Friday Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃🏻💃🏻''' 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Littafi na D'aya... Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris Akasin ƙaddara. BABI NA BIYU _Da alamu Jumma'a da zata yi kyau tun daga laraba ake gane ta, sai dai zaku yi hakuri sosai domin wannan tafiyar ba kamar sauran tafiyar bane bana ce yakai Kwarkwarah ba, amma ba mamaki zai iya kunnen doki da haka tafiya ce me matuƙar tsoho da bukatar hakuri Insha Allah zaku same Ni me cika alkawarin da na dauka naso na sayar da labarin amma kuma gashi nan dai mu karanta shi a kyauta! Idan Ubangiji yayi maka ni'ima ta wani gurin kai ma sai ka gwada taka azancin da fatan zaku amshi wannan lamari da girma is FREE BOOK_ Sab'a jaririn tayi a baya, tana me ce mishi da harshen fulatanci. "Kayi hakuri! Bawan Allah ƙaddarar kace tazo a tsakanin zukatar mugayen mutanen karshen karni, shi yasa ka fuskanci tozartawa, Ya Allah ga Al Mamoon, ka azurta rayuwar shi ta farkin da ban zata ba, ka mishi ni'ima da ilimi, ka daukaka darajar shi Ya Allah ka bashi juriya da hakurin ƙaddarar shi. Ya Allah ka rangwamta mishi tsangwama da hantara na Al'umma, Ubangiji ka sanyawa Al'umma soyayyar shi ta yadda ba zasu guje mishi ba, Ubangiji ka sa ya zama zakarar gwajin dafi Ya Allah ka raba shi da akasin ƙaddara." Ta faɗa tana kuka, sabida Allah bai bata haihuwa ba, sai take ganin kamar sun zo kan su ne da suka wofantar da Al Mamoon, dan haka ta gyara mishi goyon shi. Sannan suka fita da mijinta. "Yanzun kin ga na tambayi Babayo ya bani shanuna ya hanani, sai wata karsana ce ya bani. Mu dauka mushiga gari idan yaso sai na sayar na nima mana haya" ya faɗa cikin sanyin murya. "Toh babu kome nima tun d'azun na kama dabbobina, muje na sayar da su, dan nasan Hamma Sama'ila ya tafi da shanun mu" Haka suka hada kayan su baki daya. Suka bar rugar duk da zaman amanar da aka yi bai hana a musu koran wulakancin ba, dan har wajen rugar aka bisu, dakyar suka sami keken shanun suka hau, tare da lullube fuskar su. Suna fitowa wata mota kiran honda ta shiga garin garin, da gudu. Har sai da suka juya tare da kallon motar, jaririn da yake hannun Kabo ya fashe da kuka. Har da shashakewa, haka tayi ta jijjiga shi har suka bar yankin rugar Ardo bako. Suna shiga rugar Ardo bako, suka tsaya kallonta yayi tare cewa. "Kika ce mun iso sama a farkon gari suke." Lumshe idanunta tayi sakamakon rungume nonuwarta da tayi har suna wani irin cika da tsirta da ruwa. "Yaron yana bukatar ki sosai" Kallon shi tayi cikin kuka tace mishi. "Da fatan ba zaka tab'a juya mana baya ba, kar na dauko shi kuma kace ba haka ba, babu da Uwa bani da Uba, duk sun tafi sabida zanen ƙaddara ta, don Allah karka juya min baya, kai ne Ubana kai ne Uwata don Allah karka juya min baya." "Insha Allah ba zan juya miki baya ba." Ya fada tare da murmushi domin karfafa mata gwiwar ta, a tare suka fito daga motar domin yara sun yanyaye motar suna kallon kansu da ihu. "Laaa Abuh ce! Yaran suka fada tare da watsawa a gurin, a hankali take takawa, zuciyarta yana rawa, tsoro da tararradi ya zauna a fuskarta. Tana isa bukkar Sama'ila ta samu baya nan, juyawa tayi a kidime zata nufi gidan Kabo, wata dattijuwar mata tace mata. "Ayya ita ƙaddara sau daya takan fada maka, amma zafinta sai ta shekara dubu tana bibiyar ka, da lokacin da kika haihu kin dauki abinki bakin ki alekun babu wanda zai kuma ganin ki sai tsananin rabo. A yanzun kuwa abu biyu suka haɗu a guri daya. Tafiyar kaddara wacce baka iya tsayawa dole sai kayi, sai kuma akasin ƙaddara wacce idan ta same ka sai hakuri, ko minti talatin basu yi ba da barin garin nan sai wata rana." Dishi dishi, ta fara gani kafin ta ankara har ta zube a kasa, da gudu ya iso gare ta, bai tsaya ba wata dogon nazari ba ya dauke ta, suka bar garin baki daya. A mota yayi ta watsa mata ruwa bayan sun bar garin. "Wayyo Allah na, wayyo Allah na wayyo na shiga uku, meye nayi ne haka? Meye na aikata da Ubangiji ya sab'a haduwar mu, meye yasa ban hakura na dauke shi ba, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji na tuba Ubangiji, ina son jinjirina ina kaunar jinjirina, ya Allah na tuba ya Allah na tuba, na shiga uku me yasa nayi haka? Me yasa bani da zuciya na imani, Dr Khalid bani da tausayi na rasa Yarona na barshi a hannun mujirimi, ya rabani da Uwata ya Rabani da mijin aurena, ya rabani da Ubana ya kuma rabani da Yarona Wayyo Allah Ubangiji ka tsinewa Sama'ila, Ubangiji ka hana shi jin dadin rayuwar shi." Kuka yake tana buga kanta tare da dukar cinyarta, duk hakurin ka sai ka zubda kwalla haka har suka iso garin Maradi, gidan Mahaifiyarshi ya kaita dama a can ya kaita. Kallon su tayi cikin tausayi tace mata. "Kiyi hakuri Sama'ila yayi laifi amma laifin shi bai kai naki muni ba, da yayi miki sai kiyi hakuri da shi ki dauki d'anki ki dawo." Dauko wata jaka tayi tare da mika mata. "Wannan jakar Mero ta kawo ranar da abin ya faru, tace baffanki ya hana Sama'ila nisan zango dake ta hanyar da yayi amfani da ke, sai dai kabilar Bugaje basu cika zama ba suma, ba kamar Fulanin mu na yau da kullum ne ba, gashi dukiyar cikin shi sunce kiyi karatu kamar yadda kika so tunda har kinyi primary school da Secondry, since kiyi karatun da zaki amfani al'ummar Fulani, da wayar musu da kai. Domin sun tabbatar da zaki dawo, amma girman abin kunyar da ya faru dake ba zai iya sakawa su amshe ki ba, domin tunda suka ji labarin juna biyu gare ki, da shi Mijinki ya kai musu takardan sakin ki, shima yana cikin shi. Kiyi gudun abin kunya yasa suka tafi bawai basa kaunarki bane" Wani irin kuka ta kuma fashewa da shi, tana yi tana karawa, tare da k'amk'ame jikinta, meye yasa aka fidda al'adun da basu da tushe? Me yasa ita ƙaddara bata zab'i kowa ba sai ita? Ji take kamar an cinnawa zuciyarta wuta yake ciki. Kuka take tana kuma wa, har yamma lokacin da aka juye ruwan wankan ta nonuwarta sun kuma cika da zubda ruwa. Haka ayi ta watsa mata ruwan idanunta a lumshe bata buɗe ba balle kayi tsammani bata jin zafin ruwan ne kuma tana ji har cikin ruhinta da gangan jikin ta. *** Damagaram. Anan suka fara yada zango, kuma sun ji dadin yanayin garin domin sun sayar da saniyar su, yar kudin ce, Sanda ya kama musu haya. Gidan da ya kama musu akwai mutane dayawa, musamman kabilu mabanbantar harsuna dabam dabam, yan kudin hannun su, dashi suka saka ledar tsakar daki, da kuma taburma, sai yar tukunyar da zasu amfani dashi, dan basu iya daukar wani shirgi ba, sabida fitar bata nutsuwa bace kuma ma basu san inda zasu fada ba. Dan haka suka auno hatsi da zasu ci, dan ma sun shigo garin da yan dabbobin su. Ta watsa a tsakar gidan, bayan sun tambaya aka ce zasu iya saka kiwon su. Wani abinda ya Kum burge su da gidan akwai rijiya da wata tsohuwar turmi, dan haka ta nemi Izni gurin daya daga cikin matan gidan zata yi daka. Cikin kallon tsoro ta nuna mata inda turmin yake, ta wanke hatsin sannan ta zuba ta fara dakawa, ta surfe shi tass, sannan ta kuma wankewa har ya tsane ta koma ta dake shi sai da ya zama gari, lokacin Sanda ya shigo, da sauri ya amshi Jaririn bayanta. "Kabo bana son haka, taya zaki zo kina daka da goyon dan luɗi a bayanki, idan tabaryan ya fado daga hannunki fa?" "Kayi hakuri mai gida" ta faɗa cikin wani irin farin cikin, sabida yadda ya nuna kulawa kan Al Mamoon, yayi mata dad'i. Haka ta gama dakar tazo dakin ta same shi. "Ki dama mana kunu mana tunda na samo mana madarar Rakumi shi yafi yawa a garin nan" "toh me gida," Haka ta fito tana kallon yadda suke ta harkan gabansu. "Iya isuhu kunyi bakin Bororoji ne?" Matar da aka kira Iyar isuhu tace. "Eh wallahi, d'azun suka zo" "Toh kuyi a hankali" matar ta faɗa dake tana saman katanga ne, jikin kabo ne yayi sanyi, ta koma daki. "Maigida bari su gama nasu sabgar idan suka gama na fita nayi mana" dake shima yaji abinda aka fada, bai takura ba, haka suka zauna a dakin shiru, suna tarerayyar Almamoon. Sai da suka ji tsakar gidan shiru ya fito ya fara kokarin niman abinda zata hada wuta, sai da tafita ta sayi itaccen tazo ta haɗa musu wuta aka daura kunun nono. Bayan ya gama ta wanke jikin tukunyar ta itaccen. Komawa daki tayi, suka zauna tare da shan abin su. Tana jijjiga yaron su. Hakuri yayi ta bata taɓa gaya mata abinda suke so, rayuwar Yaron shine kan gaba, dan haka ba zai yi kasa a gwiwa ba, Insha ALLAH sai yaron su ya taka muhimmiyar rawa a duniya... ** Duk inda take tsammanin ganin Sama'ila da Aminatu bata same su ba,haka ta dauki kudin tai ta bin ƙauyuka da wanda suke iyakar Nijar da Najeriya, haka tayi ta b'atar da kudin ta, ta lalace sosai, bata da aiki sai na kuka, idan ta zauna kuka da kaunar danta take, yau ma tun sassafe take shirin fita Dr Khalid ya hana a barta ta fita. Yana sane da jininta yana yawan hawa. "Khalid me yasa ka hana Musa ya barni na fita?" Kallonta yayi sannan yace mata. "Sabida ina son na kilace ki daga fita ko ina, so nake na kuma sabunta rokon ki akan na baya. Ina son aurenki, kuma ba wasa nake miki ba, wancan ranar da kika tawo har kika kwanta a kasar bishiya, ba dan Allah ya nufa zan tafi niman ko zan ganki ba me kika san zai faru dake? Don Allah ki taimaka min aurenki zanyi ba wani abu ba, idan muka zauna a inuwa daya Insha Allah Ubangiji zai kuma baki wani Yaron ki duba lamirina." Hawaye na zuba mata ta kura mishi ido, tun lokacin da suke shigowa gari da nono yake Bin ta yana Sonta amma take gaya mishi ita tana da wanda zata aura, zama tayi dab'as tare da fashewa da kuka. Ta rarrafa gaban shi tare da rike kafarshi. "Don Allah karka manta ka tayani niman Yarona wallahi ina son shi" .d'ago ta yayi tare da cewa. "Insha Allah zan tayaki niman Yaronki Insha Allah." Da wannan shawaran ya sami mahaifiyar shi, dake itama dattijuwar arziki ce mai kaunar Ƴaƴan wasu da nata, tace mishi. "Allah ya tabbatar da alkhairi" Dan haka a cikin satin aka daura auren Zainab Hamza Bugaje, tare da Dr Khalid Agla, akan sadaki CF dubu arba'in da biyar. *** A hankali zaman garin Damagaram yake niman fin karfin su, kasancewar yadda mutane suke tsoron su. Yasa suke dan fuskar halin rayuwa. "Iyar Mamoon, naga kin iya surfe da daka ko zaki mana mu biya ki" "Kai Iyar isuhu zan yi mana," ta faɗa tare da amsar hatsin, kafin awa daya tayi musu daka cass, ta kuma daka musu. Ta tankad'e musu. Sannan ta basu, "Laaa. Iyar isuhu kiga yadda yayi laushi. Nima Iyar Mamoon zaki min" take mata suka shiga kawo mata surfe, matan maraya suna da banbanci da matan karkara, sabida matan karkara suna juran aiki, matan maraya kuwa basa iya juran ire iran wannan aikin. Shi yasa har makota kawo mata surfe suke, tare da bata aikin. Aminatu tana da mugun hakuri, ga dauke kai akan abubuwan da suke faruwa, idan yaron ta yana kuka zata goge shi. Du buga surfen su. *** Tunda aka daura auren kawai yasan da auren ne amma babu wani abu na auren sai yawan rikicin da take mishi dan haka ya shawarci mahaifiyar shi zasu bar kasar. Bata ki ba tayi musu addu'a, dan haka ya haɗa mata kaya suka nufi Faransa,. Zuciyar ta cike da kewar D'anta. Ranar da zasu bar garin Maradi, kuka tayi ta yi tana kallon yadda tayiwa kanta iyaka da D'anta ko iyayenta basu dame ta ba karma yadda tayiwa kanta iyaka da D'anta. Wannan shine sanadin Kenan da ta bar garin Nijar. *** 2011/August/04 Idan kace rayuwa tabbas Aminatu da Sanda sun ganshi,kuma suna kan ganin shi. Duk wani abin da zasu yi domin amfanin Almamoon suna yi, kuma Alhamdulillahi. Yaron ta taso babu tashin hankali, sai dai idan ka tsokane shine fa bai iya fada ba kamar kurma. Shi yasa yaran da suke gida daya dasu basa fada dashi sai dai idan an fi karfin su, shine zai shigar musu. A wannan yanayin har suka saka shi a makarantar boko, da arabiyya dan ma yana karatun Alqur'ani a gaban Baban shi Sanda yayi nisa. Almamoon Allah yayi mishi baiwar Ilimi, tun yana shekara biyar ya fara shiga musabaka, kuma yana lashewa, gashi da wani banzan hali shine karka nuna mishi ka damu dashi domin da wannan yanayin yake iya saka damuwa, idan kace kana son shi da abota, wayyo Allah..ka shiga uku domin zai ta baka wahala ne, yana share ka. Gashi da farin jini idan turawa yan yawon bude ido suka shiga makarantar su, har rige rigen daukar hoto ake dashi sabida bakin fatar shi, wanda idan ya shiga rana har wani kyali yake, idan ka cire kwayar idanun shi da hakoran shi sune fararre tass a jikin shi sai harshen shi ja, bayan nan babu wani abu da zaka ce fari ne a tare da shi.. Yanayin fatar shi ta janyo mishi soyayyar mutane, sai dai abu daya yake mugun bawa kowa haushi a tare shi a yanzun yana da shekara goma a duniya idan ya yab'a maka bakar magana sau ka rasa inda zaka saka kanka. A yanzun haka yana tare da wasu yan ajin sune. Amadu Bukar sai Salihu Muhmuda jarabawar suke ta gama primary. "Mamoon don Allah taimaka min da amsar nan mana?" Inji Amadu Bukar, Banza yayi dashi. Can Salihu Muhmuda ya taba shi. "Don Allah taimaka mana abokin mu" "Ai kusan ni na kawo ku makaranta shi yasa zan baku satar amsa," ya faɗa mu.... [7/14, 1:05 PM] RamlatArManga: I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx ```Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida...🗣️🗣️Friday Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃🏻💃🏻``` 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Littafi na D'aya... Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris _🙄 Daga farawa naga yadda kuke sakawa Dan baki namu ido fa😛🤭 Wallahi ko hmm_ BABI NA UKU. Wata tafiyar. Sake baki Salihu Muhmuda yayi tare da Amadu. "Amma zamu haɗu" suka fada mishi,.mik'ewa yayi cikin rashin tsoro yace musu. "Idan muka hadu abinda kuka bani ku hanani" ya faɗa yana fita daga kujeran, "Mara mutunci" "Lokacin da aka zo rabon shi bana nan" "Mugu" "Eh gadon shi nayi" "Dan iska kawai" "A'a sai dai guguwa" Ya fada tare da barin tabirin su, kamar zasu fasa jarabawar, karshe haka suka mike zasu kai, sai a lokacin Amadu ya kai idanun shi kasar tabirin su ya lura da rubutun da Almamoon yayi ya ajiye musu. Da sauri suka dauka. Murna kuwa baki yaki rufuwa. Koda suka gama, fitowa suka yi. Tare da samun shi a kasar bishiya ya zauna yana ta rubutu, idan ka ga hancin shi har baki, daga gefen fuskar shi kuwa saje ce ya kwanta gwanin ban sha'awa. "Kai mara mutunci" banza yayi musu. "Mun gode" " Da aka yi me?" "Da bamu amsar da kayi" Kallon su yayi sannan yace musu. "Ai ina mamakin yadda Uwayen ku suke kashewa jakuna kudin makaranta." Ya fada tare da mik'ewa. "Wawa kawai dan baki duna" "Eh toh ta yiwu ni bakin ne, amma kuma ina takaicin haduwa da katon jaki" ya faɗa tare da nufar hanyar ajin su. "Almamoon dan me gadi" Cak ya tsaya tare da juyawa ya sake murmushi, kafin tace mishi. "Eh toh dukda haka yafi cirani" da Yaron ya ji abinda ya gaya mishi fasa ihu yayi tare da burgima, an zage mishi uba an can dan cirani. Haka yayi ta kuka har Malamin su ya shigo tare da tambayar su meye ya haɗa su. "Zagina yayi na bashi hakuri" inji Almamoon, " Karya yake cewa yayi Ubana dan cirani" Tsaki malamin yayi sannan yayi musu fada. ... Bayan sun gama jarabawar suna nufi hanyar gida, yau ya shirya musu tsiya shi yasa bai kula su ba. "Yau idan muka je gida zan samu anyi mana abinci me dad'i?" Suna son yayi magana amma dake yayi shiru basu kuma takalo shi ba. Haduwa da wasu yan samarin unguwar su, suka tsaya tare da make su, amma ban da Almamoon, wuce su yayi. Sai da suka bar gurin. "Mamoon kai wani irin mugun mutum ne ka ga sun tsare mu ba tsaya ba." "Me ya faru daku?" Ya tambaye su, kamar bai ga abinda ya faru ba. "A'a babu" "Nima naga alama" ya ga musu tare da wuce su, matasan nan ba kome yasa suka make su Amadu Bukar da Salihu Muhmuda ba, sai dan tsokanar su da suka yi, kuma akan idanun shi suka tsokane su. Shi kuma baya tab'a bin bayan karya. Haka suka isa gida idan suka gaya mishi maganar banza ya gaya musu wacce tafi tasu muni. "Dan banza munafuki wanda baya yarda yayi wanka a gaban mutane." Wannan maganar tayi mishi zafi, da gaske ne baya tab'a wanka a gaban mutane, kuka kamar yadda babba zai shiga ban daki yayi wanka, haka shima yake. Rasa amsar basu yayi har suka isa cikin gidan, zasu nufi dakunan iyayen su yacewa Salihu.. "Ka tambayi Iyakar me yasa bata wanka a waje" Ya gaya mishi sannan ya shiga dakin su. Samun Innar shi yayi tana ta daman cura fura da aka kawo mata aikin shi take. "Sannun Innata" "Sannun D'an albarka, dauki abincin ka yau Allah ya taimaka malam ya samu dan albashi ya sayo maka shinkafa aka dafa, duba ka gani har da nama." Kallonta yayi sannan yace mata. "Innah hala ko cin namar baki yi ba daga ke har Baba." Ya fada idanun shi na cika da kwalla. "Mun ci mana" Ta faɗa tare da maida hankalinta kan aikinta, bude kwanon yayi ya ga Bama kusan ya lullube abincin, sai ganye da aka zuba a saman namar, ture abincin yayi tare da cewa. "Ba zan ci ba" "Yi hakuri Bawan Allah, sanyin idaniyar Innar, Dan da aka haifa tsiya na barci, Kasan yadda nake kokarin kyautata maka, toh maza ci sai ba baka labarin wani mafarkin da na jima ina yi akanka" "Wallahi ba zan ci ba sai dai muce tare" Shafa kanshi yayi tare da cire mishi hular kanshi, gashin kanshi irinta Bororoji yana nan daga tsakiyar kanshi anyi Mishi wata irin kitso me hawa biyu, doka sai wasu kanana da aka saka musu wuri wato braid, gashin nan baki suddin har gadon bayan shi, wuyar shi a daure yake da guru da azurfa, murmushi yayi sannan yace mata. "Gobe za a fara shadi a rugar Baima, zamu je don Allah Innah ki bar ni naje" kura mishi ido tayi cike da tsoro. "A'a ba zaka je ba" "Don Allah nace Innata..." "Iyar Mamoon! Wallahi nakawo miki dokaciya, kiyiwa Mamoon fada da irin maganar da yake zarowa nan." "Toh Allah yayi min baƙi bari nayi shiru kar kayi Magana" Rufe mishi baki Innar shi tayi. "Kiyi hakuri Iyar Salihu." "Ina dalili yaro sai kace mace gurin zaro magana, na kara jin yacewa Salihu me yasa bana wanka a gaban su." "Toh ai dalilin da nasa nima bana wanka a gaban jama'a kenan" ya faɗa tare da kallon Innar shi, kamar zai yi kuka. "Iyar Mamoon" "Toh kiyi hakuri" ya faɗa tare da kallon Iyar shi. "Kiyi hakuri iyar Salihu," ta juya tana cigaba da sababinta, dariya yayi sannan yace mata. "Zama da mutane sai ka koyi halin su" "Almamoon ka duba girman Allah ka daina harba mutane da magana marasa Dad'i,irin wannan halin shine ya faru shekaru goma sha daya, harbin wuni da bakin magana, karka jefa rayuwata cikin ukuba mana." "Shi kenan" ya faɗa tare da tura mata kwanon, haka bata so sai da taci yankar naman daya, sannan ya fara cin abincin. Abu biyu yaƙe dauke da Almamoon yanayin shi na Uwar shi ce da kamanin ta, bakin fatar shi na Hamma Sama'ila ne, domin har yafi Uban baki ma. Shekarun baya bata yarda cewa yaron zai kai haka ba, domin kuwa bayan ya shekara daya yayi fama da rashin lafiya, irin su bakon dauro, tamowa, da kuma laulayi irinta yara kananu, sai da ta kai ko abincin da zasu ci gagagrar su take, a lokacin gidan da suke suka sakota a gaba sabida rashin bawa Yaron nono da kuma bata mishi wanka a gaban jama'a. Suka yi ta gulmar su da kananun magana.. haka bai saka ya tab'a ko d'aga kai tayi magana ba. Dole Sanda ya fita niman aikin yi, domin ba zai iya rayuwa da iyalin shi babu abinda zasu taimakawa kansu ba, sabida yanayin da suke ci ko surfen an daina bata. Sun sha wahala da yaron, domin rashin nonon uwa yasa ya rasa lafiyar shi, sai da suka hada da na gargajiya, irin wanda suka sani da kansu. Suka hada mishi magani. Da yayi wayo kuwa idan basu samu wadataccen abinci ba, wanda suka samu suke hakura su bashi, su kuma su kwana haka. Allah cikin ikon shi Sanda ya samu gadin kasuwa, abinda ya rufa musu asiri kenan, duk da haka suke biyan kudin haya, tare da abin da zasu ci, tunda likita ya gaya musu, yana bukatar kayan gina jiki, suke wannan kokarin ki basu ci nama ba zasu saya mishi, a zuba mishi akan abinci. Madara kuwa, kullum idan zai dawo da safe zai sayo mishi ta gora ya kawo mishi. Wani irin kaunar yaron suke kamar su bada rayuwar su domin fansar nashi. --- "Innata na gama gaya min mafarkin da kika yi?" ya tambaye ta, " Wai na ganka ne tare da wasu manyan mutane, kuma ka zama babban mutum, sai farin ciki kake" "Daga karshe kuma kika tashi a barci ko?" Ya katse mata labarin. Girgiza kai tayi tana cewa. "Allah ya shirya min kai!" Tana murmushi, domin karfafa mishi haka take. Kiran sallah ne ya sashi mik'ewa yayi alola sannan ta dawo dakin yayi Sallah, kafin ya zauna yana kallon Innar shi. "Inna mun gama jarabawar mu yau, Allah yasa ki biya min kudin Makarantar sakandari" ya faɗa yana tararradi yadda zata dauki maganar. "Idan kayi min alƙawarin zaka yi karatu domin Allah da kuma tsayawa da kafarka me zai saka na ki biya maka" ta faɗa tana jan wani akwatin katako ta bude cikin shi. Kudine babu iyaka. Suka zauna aka yi lissafin su tsaf. "Innah har zai rage ma ai kuɗin." "So nake na cigaba da tarawa, dan ba zaka yi karatu a makarantar gwamanti da babu kulawa ba, kai ma makarantan kudi zaka tafi." Murmushi yayi sannan yace mata. "Insha Allah" *** Haka suka share wata biyu sannan sakamakon su ya fito, haka Aminatu ta fasa asusun aka biya mishi kusan makudan kudade na makaranta, ranar da zai fara zuwa. Suka zauna dashi aka mishi nasiha, tare da mishi gargadi. "Karka sake kayi wasa da karatunka, kayi hakuri da mutanen da zaku hadu makarantar yaran masu kudi ne dan haka karka bari a Kama ka da laifin da zai dame mu. Haka suka gama mishi fada, sannan zai fita Malam Sanda tace mishi. "Kin gaya mishi gaskiya akan" kallon shi tayi tare da cewa. "Wannan sirrin shi ne, karka manta wata rana zai fahimci dalilin haka, kai dai ka hana shi mu'amala da maza da mata," Kallon su yayi kafin yace musu. "Wani sirrin kuke boye min?" "Babu wani sirrin da a ke boye maka" "Toh shi kenan," ya faɗa tare da barin d'akin, shi da Baban shi. A iya yanzun haka kawai take jin kamar sun tauye mishi hakkin shi da kuma yancin shi, sai dai kamar yadda Mijinta ya faɗa haka ne, baya son tarihi ta maimaita kanta ne akan shi, shi yasa ya zab'i hakan a matsayin babban al'amari akan. Amma kuma tana ganin kamar haka ba hujja bane, kamar tauye hakkin shi ne, kai toh idan wani abu ya same shi fa? Gwara kawai a tafi a haka. Toh gaba kuma aka dawo aka samu akasi fa? Lallai bari malam ya dawo zasu yi magana domin ba zai tab'a yiwa ba, ka sayi kura da daddare da safe ka samu kare ne, haka ba zai tab'a yiwa ba..amma shi yaron ai bai san hujjar su na maida kome haka ba. ..... Bayan malam ya dawo ne ta kalle shi kafin tace mishi. "Malam anya bamu so kan mu ba? Taya zamu bari har zuwa lokacin da." "Ki bar kome a hannun, idan ta fara girma zamu fahimtar dashi kome, sannan zamu sauya mishi gari domin kar a samu matsala, karki yarda wani yasan wannan sirrin. Ya zauna a tsakanin mu." Had'iye yawun tayi sannan tace mishi. " Sai nake ganin kamar da cutarwa, a bar shi haka ba a gaya mishi dalilin da yasa yake raye a haka ba, sannan kuma. " "Karki karaya mana, tsoron abinda ya faru shekaru goma sha daya nake kara ada Yaron nan ba wai dan wata manufa bane, kawai ki tayani boye maganar shi nan bana son kamar yadda iyayen shi suka mishi, shima ace ya fuskanci haka. Duk da muna namu Allah yana shine gaskiya." "Ko a ina Sama'ila yake oho?" Ta faɗa cikin sanyin murya, me ban tausayi. A hankali yake kwalla suka zubo mata, tana kallon kasa. Ya tafi ya manta da gida, ya tafi bai kuma waiwayar baya ba, me yasa ya tafi shima? Me yasa ya gaza tsayuwa ya fuskanci rayuwar abinda ya bari, babu kome, Allah yana nan zata rike yaron ta kuma boye mishi waye shi. Domin samun goben shi. Amma Tabbas akwai sirri me girma ga rayuwar Almamoon. **** Asalin labarin. Fulanin Wodaadabe Bororo. Wato sune Fulanin da basu zama kuma basu da mazauni daya, idan suka shekara anan yau gobe zasu kara shekara a wani garin. Sannan Allah yayi musu baiwar ilimin addinin Muslunci, musamman Alkur'ani. Zunzurutun baiwar da Allah yayi musu kasancewar su bakakken Fulani masu jajjen shanu, yasa zaka sami yaro karami an daura shi a saman saniya yana tafe yana karatun Alqur'ani, kuma ya tafi da saniyar har wata tafiya. Yanayin shigar su ba kamar na sauran Fulanin bane, domin suna sanye da wata hafaffera, riga ce Armless, har gwiwar su rigar take, sai wandon yadi ce baka kowa wata kala, suna saka hular malafa akan su, matan su, suna tara gashi a gaban goshin su, me shegen yawa kuma suna saka bakakken kaya har kasa kamar riga da zabi ko doguwar riga. Suna shigowa gari da matan su, tallar maganin mata ko maganin gashi, suna bin gida gida suna tallar shi, zaku gan su dogaye ne matan. Kyakyawa bakakke... Duk da ana samun fararren su, amma bakakken sunfi yawa, suna da Albarka na dabbobi, sannan kuma suna da matukar kyakyamin abinda ya shigo musu, musamman abinda ya kasance sabon abu. BOROROJI suna da wata muguwar dabi'a wacce take salwantar da rayukan mata da yan mata, mace kome girman mata idan har tsautsayi ya faɗa akanki shikenan. Ismail Mohammed Wodaadabe. Shine cikakken sunan Sama'ila, yana da kanwa daya tal a duniya Aminatu. Dayawa abokan shi sun sha mishi barazana zasu dauke Kanwar shi, amma bai tab'a damuwa da haka ba, sabida yasan abinda ya shiryawa, wani mugun hali da yake dashi. Shine yawancin matasan bororo suna zuwa mishi yayi musu aiki, kuma idan yayi kamar yankar wuka taci. Umar sanda shine cikakken sunan abokin shi saurayin Kanwar shi Aminatu. Zaune suke a kasar bishiya. "Ila, shin da gaske zaka babu kanwarka dan naga baku da dangi ko daya a wannan rigar kace suna can mali" Mik'ewa yayi bayan ya kad'e jikin shi ya rufe Alqur'anin shi. Yana faɗin. "Duk cikin abokaina kai ne kawai kace min kana son auren Aminatu sauran kuwa cewa suke zasu yi *CIRENTA* shi yasa na amince ka nemi aurenta kai ma ai ba dangin ne da kai ba." "Toh meye na bakar magana? Daga tambaya sai bakar magana ta biyo baya." Kallon shi yayi da wutsiyar ido, yace mishi. "Ba bakar magana ba ce farar magana ce." "Ai kaji ka mutumin banza kawai" "Idan ni mutumin banza ne toh Sannun na Allah" ya faɗa yana kad'a kan shanun shi. "Ban da ina girmama Aminatu da ba zan tab'a yarda na bi ka ba" "Idan baka bini ba sai na fadi na mutu dan ka ki bina" "Wai kan Ila bakinka baya mutuwa ne?" "Sai ranar da kasa ta rufe min ido" ya faɗa abin shi haka bai dame shi ba, sai ma kara hada kan dabbobin shi yake suka bar gurin kiwon, ba tare da ya gayawa Sanda ba, ranar juma'a, Sanda ya shiga gari juma'a aka daura auren Aminatu, [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx ```Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida...🗣️🗣️Friday Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃🏻💃🏻``` 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Littafi na D'aya... Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris _🙄 Daga farawa naga yadda kuke sakawa Dan baki namu ido fa😛🤭 Wallahi ko hmm_ BABI NA UKU. Wata tafiyar. Sake baki Salihu Muhmuda yayi tare da Amadu. "Amma zamu haɗu" suka fada mishi,.mik'ewa yayi cikin rashin tsoro yace musu. "Idan muka hadu abinda kuka bani ku hanani" ya faɗa yana fita daga kujeran, "Mara mutunci" "Lokacin da aka zo rabon shi bana nan" "Mugu" "Eh gadon shi nayi" "Dan iska kawai" "A'a sai dai guguwa" Ya fada tare da barin tabirin su, kamar zasu fasa jarabawar, karshe haka suka mike zasu kai, sai a lokacin Amadu ya kai idanun shi kasar tabirin su ya lura da rubutun da Almamoon yayi ya ajiye musu. Da sauri suka dauka. Murna kuwa baki yaki rufuwa. Koda suka gama, fitowa suka yi. Tare da samun shi a kasar bishiya ya zauna yana ta rubutu, idan ka ga hancin shi har baki, daga gefen fuskar shi kuwa saje ce ya kwanta gwanin ban sha'awa. "Kai mara mutunci" banza yayi musu. "Mun gode" " Da aka yi me?" "Da bamu amsar da kayi" Kallon su yayi sannan yace musu. "Ai ina mamakin yadda Uwayen ku suke kashewa jakuna kudin makaranta." Ya fada tare da mik'ewa. "Wawa kawai dan baki duna" "Eh toh ta yiwu ni bakin ne, amma kuma ina takaicin haduwa da katon jaki" ya faɗa tare da nufar hanyar ajin su. "Almamoon dan me gadi" Cak ya tsaya tare da juyawa ya sake murmushi, kafin tace mishi. "Eh toh dukda haka yafi cirani" da Yaron ya ji abinda ya gaya mishi fasa ihu yayi tare da burgima, an zage mishi uba an can dan cirani. Haka yayi ta kuka har Malamin su ya shigo tare da tambayar su meye ya haɗa su. "Zagina yayi na bashi hakuri" inji Almamoon, " Karya yake cewa yayi Ubana dan cirani" Tsaki malamin yayi sannan yayi musu fada. ... Bayan sun gama jarabawar suna nufi hanyar gida, yau ya shirya musu tsiya shi yasa bai kula su ba. "Yau idan muka je gida zan samu anyi mana abinci me dad'i?" Suna son yayi magana amma dake yayi shiru basu kuma takalo shi ba. Haduwa da wasu yan samarin unguwar su, suka tsaya tare da make su, amma ban da Almamoon, wuce su yayi. Sai da suka bar gurin. "Mamoon kai wani irin mugun mutum ne ka ga sun tsare mu ba tsaya ba." "Me ya faru daku?" Ya tambaye su, kamar bai ga abinda ya faru ba. "A'a babu" "Nima naga alama" ya ga musu tare da wuce su, matasan nan ba kome yasa suka make su Amadu Bukar da Salihu Muhmuda ba, sai dan tsokanar su da suka yi, kuma akan idanun shi suka tsokane su. Shi kuma baya tab'a bin bayan karya. Haka suka isa gida idan suka gaya mishi maganar banza ya gaya musu wacce tafi tasu muni. "Dan banza munafuki wanda baya yarda yayi wanka a gaban mutane." Wannan maganar tayi mishi zafi, da gaske ne baya tab'a wanka a gaban mutane, kuka kamar yadda babba zai shiga ban daki yayi wanka, haka shima yake. Rasa amsar basu yayi har suka isa cikin gidan, zasu nufi dakunan iyayen su yacewa Salihu.. "Ka tambayi Iyakar me yasa bata wanka a waje" Ya gaya mishi sannan ya shiga dakin su. Samun Innar shi yayi tana ta daman cura fura da aka kawo mata aikin shi take. "Sannun Innata" "Sannun D'an albarka, dauki abincin ka yau Allah ya taimaka malam ya samu dan albashi ya sayo maka shinkafa aka dafa, duba ka gani har da nama." Kallonta yayi sannan yace mata. "Innah hala ko cin namar baki yi ba daga ke har Baba." Ya fada idanun shi na cika da kwalla. "Mun ci mana" Ta faɗa tare da maida hankalinta kan aikinta, bude kwanon yayi ya ga Bama kusan ya lullube abincin, sai ganye da aka zuba a saman namar, ture abincin yayi tare da cewa. "Ba zan ci ba" "Yi hakuri Bawan Allah, sanyin idaniyar Innar, Dan da aka haifa tsiya na barci, Kasan yadda nake kokarin kyautata maka, toh maza ci sai ba baka labarin wani mafarkin da na jima ina yi akanka" "Wallahi ba zan ci ba sai dai muce tare" Shafa kanshi yayi tare da cire mishi hular kanshi, gashin kanshi irinta Bororoji yana nan daga tsakiyar kanshi anyi Mishi wata irin kitso me hawa biyu, doka sai wasu kanana da aka saka musu wuri wato braid, gashin nan baki suddin har gadon bayan shi, wuyar shi a daure yake da guru da azurfa, murmushi yayi sannan yace mata. "Gobe za a fara shadi a rugar Baima, zamu je don Allah Innah ki bar ni naje" kura mishi ido tayi cike da tsoro. "A'a ba zaka je ba" "Don Allah nace Innata..." "Iyar Mamoon! Wallahi nakawo miki dokaciya, kiyiwa Mamoon fada da irin maganar da yake zarowa nan." "Toh Allah yayi min baƙi bari nayi shiru kar kayi Magana" Rufe mishi baki Innar shi tayi. "Kiyi hakuri Iyar Salihu." "Ina dalili yaro sai kace mace gurin zaro magana, na kara jin yacewa Salihu me yasa bana wanka a gaban su." "Toh ai dalilin da nasa nima bana wanka a gaban jama'a kenan" ya faɗa tare da kallon Innar shi, kamar zai yi kuka. "Iyar Mamoon" "Toh kiyi hakuri" ya faɗa tare da kallon Iyar shi. "Kiyi hakuri iyar Salihu," ta juya tana cigaba da sababinta, dariya yayi sannan yace mata. "Zama da mutane sai ka koyi halin su" "Almamoon ka duba girman Allah ka daina harba mutane da magana marasa Dad'i,irin wannan halin shine ya faru shekaru goma sha daya, harbin wuni da bakin magana, karka jefa rayuwata cikin ukuba mana." "Shi kenan" ya faɗa tare da tura mata kwanon, haka bata so sai da taci yankar naman daya, sannan ya fara cin abincin. Abu biyu yaƙe dauke da Almamoon yanayin shi na Uwar shi ce da kamanin ta, bakin fatar shi na Hamma Sama'ila ne, domin har yafi Uban baki ma. Shekarun baya bata yarda cewa yaron zai kai haka ba, domin kuwa bayan ya shekara daya yayi fama da rashin lafiya, irin su bakon dauro, tamowa, da kuma laulayi irinta yara kananu, sai da ta kai ko abincin da zasu ci gagagrar su take, a lokacin gidan da suke suka sakota a gaba sabida rashin bawa Yaron nono da kuma bata mishi wanka a gaban jama'a. Suka yi ta gulmar su da kananun magana.. haka bai saka ya tab'a ko d'aga kai tayi magana ba. Dole Sanda ya fita niman aikin yi, domin ba zai iya rayuwa da iyalin shi babu abinda zasu taimakawa kansu ba, sabida yanayin da suke ci ko surfen an daina bata. Sun sha wahala da yaron, domin rashin nonon uwa yasa ya rasa lafiyar shi, sai da suka hada da na gargajiya, irin wanda suka sani da kansu. Suka hada mishi magani. Da yayi wayo kuwa idan basu samu wadataccen abinci ba, wanda suka samu suke hakura su bashi, su kuma su kwana haka. Allah cikin ikon shi Sanda ya samu gadin kasuwa, abinda ya rufa musu asiri kenan, duk da haka suke biyan kudin haya, tare da abin da zasu ci, tunda likita ya gaya musu, yana bukatar kayan gina jiki, suke wannan kokarin ki basu ci nama ba zasu saya mishi, a zuba mishi akan abinci. Madara kuwa, kullum idan zai dawo da safe zai sayo mishi ta gora ya kawo mishi. Wani irin kaunar yaron suke kamar su bada rayuwar su domin fansar nashi. --- "Innata na gama gaya min mafarkin da kika yi?" ya tambaye ta, " Wai na ganka ne tare da wasu manyan mutane, kuma ka zama babban mutum, sai farin ciki kake" "Daga karshe kuma kika tashi a barci ko?" Ya katse mata labarin. Girgiza kai tayi tana cewa. "Allah ya shirya min kai!" Tana murmushi, domin karfafa mishi haka take. Kiran sallah ne ya sashi mik'ewa yayi alola sannan ta dawo dakin yayi Sallah, kafin ya zauna yana kallon Innar shi. "Inna mun gama jarabawar mu yau, Allah yasa ki biya min kudin Makarantar sakandari" ya faɗa yana tararradi yadda zata dauki maganar. "Idan kayi min alƙawarin zaka yi karatu domin Allah da kuma tsayawa da kafarka me zai saka na ki biya maka" ta faɗa tana jan wani akwatin katako ta bude cikin shi. Kudine babu iyaka. Suka zauna aka yi lissafin su tsaf. "Innah har zai rage ma ai kuɗin." "So nake na cigaba da tarawa, dan ba zaka yi karatu a makarantar gwamanti da babu kulawa ba, kai ma makarantan kudi zaka tafi." Murmushi yayi sannan yace mata. "Insha Allah" *** Haka suka share wata biyu sannan sakamakon su ya fito, haka Aminatu ta fasa asusun aka biya mishi kusan makudan kudade na makaranta, ranar da zai fara zuwa. Suka zauna dashi aka mishi nasiha, tare da mishi gargadi. "Karka sake kayi wasa da karatunka, kayi hakuri da mutanen da zaku hadu makarantar yaran masu kudi ne dan haka karka bari a Kama ka da laifin da zai dame mu. Haka suka gama mishi fada, sannan zai fita Malam Sanda tace mishi. "Kin gaya mishi gaskiya akan" kallon shi tayi tare da cewa. "Wannan sirrin shi ne, karka manta wata rana zai fahimci dalilin haka, kai dai ka hana shi mu'amala da maza da mata," Kallon su yayi kafin yace musu. "Wani sirrin kuke boye min?" "Babu wani sirrin da a ke boye maka" "Toh shi kenan," ya faɗa tare da barin d'akin, shi da Baban shi. A iya yanzun haka kawai take jin kamar sun tauye mishi hakkin shi da kuma yancin shi, sai dai kamar yadda Mijinta ya faɗa haka ne, baya son tarihi ta maimaita kanta ne akan shi, shi yasa ya zab'i hakan a matsayin babban al'amari akan. Amma kuma tana ganin kamar haka ba hujja bane, kamar tauye hakkin shi ne, kai toh idan wani abu ya same shi fa? Gwara kawai a tafi a haka. Toh gaba kuma aka dawo aka samu akasi fa? Lallai bari malam ya dawo zasu yi magana domin ba zai tab'a yiwa ba, ka sayi kura da daddare da safe ka samu kare ne, haka ba zai tab'a yiwa ba..amma shi yaron ai bai san hujjar su na maida kome haka ba. ..... Bayan malam ya dawo ne ta kalle shi kafin tace mishi. "Malam anya bamu so kan mu ba? Taya zamu bari har zuwa lokacin da." "Ki bar kome a hannun, idan ta fara girma zamu fahimtar dashi kome, sannan zamu sauya mishi gari domin kar a samu matsala, karki yarda wani yasan wannan sirrin. Ya zauna a tsakanin mu." Had'iye yawun tayi sannan tace mishi. " Sai nake ganin kamar da cutarwa, a bar shi haka ba a gaya mishi dalilin da yasa yake raye a haka ba, sannan kuma. " "Karki karaya mana, tsoron abinda ya faru shekaru goma sha daya nake kara ada Yaron nan ba wai dan wata manufa bane, kawai ki tayani boye maganar shi nan bana son kamar yadda iyayen shi suka mishi, shima ace ya fuskanci haka. Duk da muna namu Allah yana shine gaskiya." "Ko a ina Sama'ila yake oho?" Ta faɗa cikin sanyin murya, me ban tausayi. A hankali yake kwalla suka zubo mata, tana kallon kasa. Ya tafi ya manta da gida, ya tafi bai kuma waiwayar baya ba, me yasa ya tafi shima? Me yasa ya gaza tsayuwa ya fuskanci rayuwar abinda ya bari, babu kome, Allah yana nan zata rike yaron ta kuma boye mishi waye shi. Domin samun goben shi. Amma Tabbas akwai sirri me girma ga rayuwar Almamoon. **** Asalin labarin. Fulanin Wodaadabe Bororo. Wato sune Fulanin da basu zama kuma basu da mazauni daya, idan suka shekara anan yau gobe zasu kara shekara a wani garin. Sannan Allah yayi musu baiwar ilimin addinin Muslunci, musamman Alkur'ani. Zunzurutun baiwar da Allah yayi musu kasancewar su bakakken Fulani masu jajjen shanu, yasa zaka sami yaro karami an daura shi a saman saniya yana tafe yana karatun Alqur'ani, kuma ya tafi da saniyar har wata tafiya. Yanayin shigar su ba kamar na sauran Fulanin bane, domin suna sanye da wata hafaffera, riga ce Armless, har gwiwar su rigar take, sai wandon yadi ce baka kowa wata kala, suna saka hular malafa akan su, matan su, suna tara gashi a gaban goshin su, me shegen yawa kuma suna saka bakakken kaya har kasa kamar riga da zabi ko doguwar riga. Suna shigowa gari da matan su, tallar maganin mata ko maganin gashi, suna bin gida gida suna tallar shi, zaku gan su dogaye ne matan. Kyakyawa bakakke... Duk da ana samun fararren su, amma bakakken sunfi yawa, suna da Albarka na dabbobi, sannan kuma suna da matukar kyakyamin abinda ya shigo musu, musamman abinda ya kasance sabon abu. BOROROJI suna da wata muguwar dabi'a wacce take salwantar da rayukan mata da yan mata, mace kome girman mata idan har tsautsayi ya faɗa akanki shikenan. Ismail Mohammed Wodaadabe. Shine cikakken sunan Sama'ila, yana da kanwa daya tal a duniya Aminatu. Dayawa abokan shi sun sha mishi barazana zasu dauke Kanwar shi, amma bai tab'a damuwa da haka ba, sabida yasan abinda ya shiryawa, wani mugun hali da yake dashi. Shine yawancin matasan bororo suna zuwa mishi yayi musu aiki, kuma idan yayi kamar yankar wuka taci. Umar sanda shine cikakken sunan abokin shi saurayin Kanwar shi Aminatu. Zaune suke a kasar bishiya. "Ila, shin da gaske zaka babu kanwarka dan naga baku da dangi ko daya a wannan rigar kace suna can mali" Mik'ewa yayi bayan ya kad'e jikin shi ya rufe Alqur'anin shi. Yana faɗin. "Duk cikin abokaina kai ne kawai kace min kana son auren Aminatu sauran kuwa cewa suke zasu yi *CIRENTA* shi yasa na amince ka nemi aurenta kai ma ai ba dangin ne da kai ba." "Toh meye na bakar magana? Daga tambaya sai bakar magana ta biyo baya." Kallon shi yayi da wutsiyar ido, yace mishi. "Ba bakar magana ba ce farar magana ce." "Ai kaji ka mutumin banza kawai" "Idan ni mutumin banza ne toh Sannun na Allah" ya faɗa yana kad'a kan shanun shi. "Ban da ina girmama Aminatu da ba zan tab'a yarda na bi ka ba" "Idan baka bini ba sai na fadi na mutu dan ka ki bina" "Wai kan Ila bakinka baya mutuwa ne?" "Sai ranar da kasa ta rufe min ido" ya faɗa abin shi haka bai dame shi ba, sai ma kara hada kan dabbobin shi yake suka bar gurin kiwon, ba tare da ya gayawa Sanda ba, ranar juma'a, Sanda ya shiga gari juma'a aka daura auren Aminatu, [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Littafi na D'aya... Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx ```Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida...🗣️🗣️Friday Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃🏻💃🏻``` Zuciyar Mutum..! BABI NA HUDU Koda Sanda ya dawo aka bashi labari, mamaki ya bashi yadda aka daura. "Nagode sosai Abokina" duk ya rasa yadda zai mishi godiya, sai ga kuka. "Ji sakarai." Ya fada yana murmushi, "Nagode" "Abinda nake so ka rike min ita da Amana, shine abinda zaka min tsakani na da kai" "Insha Allah zan rike ta, da amana Insha Allah ba zaka tab'a samu na da laifi ba." Ba iya shi ba hatta sauran abokan su, sunyi matukar mamaki da abinda Ila yayi, sai ma dai kawai matsalar da aka samu wani abokin su da ya tab'a niman Aminatu har suka sami matsala da Sama'ila, shine kawai yayi barazanar dauke ta. Dan haka shima Sama'ila da ta shi, bai tsaya ba dan ya san halin su na Fulani da aikata abinda suka fada, sai yayi maza ya kad'a hankalin mutumin yayi gaba, haka ya saka suka zauna lafiya. Bayan shekara daya da auren su, Ado wani abokin Sama'ila ya gayyaci Sama'ila bikin shad'i na wani abokin shi a rugar Alu, suka tafi tare, dan sun tafiya da Sanda yace ba zai sami zuwa ba. ** Malam Hamza Ja'e Bugaje, babban malami ne a cikin rugar kowa yasan shi da mutunci da kamala, dattijon arziki. Haka yasa ake daraja shi. Kuma abin burgewa Ardo Mustapha babban Aminin shine dan har sunyi baikon yaran su, Zainab Abuh da Kabiru Almustapha, sai dai Zainab tana karatun ta na sankadire, kasancewar Malam Ja'e yayi cuɗanya da mutane, yasa ya saka yar shi karama a makarantar boko, duk da ana ganin kamar yazo da bidi'a amma haka bai saka ya fasa abinda yayi niyya ba. Tsakanin Kabiru da Zainab akwai soyayya mai karfi sosai, wanda ya saka kowa yake ganin kamar bai zama dole su mallaki juna ba, amma sun dauki haka a matsayin kaunar suce. Zainab tana kai kindirmo cikin gari, kuma a duk lokacin da ta tafi makarantar boko take tafiya da nonon, idan ta ajiye a Office din shugaban makarantar, sai ta wuce aji ana tashi zata dauki kayan ta ta nufi Asibitin Aminci da yake cikin garin Maradi. Ana take sayar da nonon. Dr Khalid. Matashi ne dan kabilar Buzaye, kyakyawa ne, ajin farko dogo me cikar halittar jiki. Idan ka ganshi zaka Fahimci namiji ne, mutum ne mai yawan fara'a da barkwace, haka haduwar shi da Zainab, da zolaya ya fara cewa yau yaga Yar Fulani da unifoam. Kamar da wasa aka fara. Wata uku yana dakon sonta, bai gaya mata ba, sai ana gobe zata daina kawo nono sun gama makaranta, tana da shekara goma sha bakwai. "Dr daga yau na daina kawo nono, sabida zanyi aure kuma." "Kamar Ya? Wallahi ina sonki na kasa gaya miki ne, toh Allah ya sanya Alkhairi, amma Allah ya gani ina kaunarki da aure." Murmushi tayi sannan tace mishi. "Kayi hakuri koda baka gaya min ba, ina da mijin da zan aura shi yasa na gaya maka ma yanzun Nagode da kaunar da kayi min." Haka suka rabu ita kam bata ji kome ba, sabida zuciyar ta yana ga mijin da zata aura.... *** Tunda aka fara shirin bikin nan kowa yake murna, dan haka zasu fita bikin shad'i idan aka yi kuma, zasu saka abu a fuskar su, tafi ta ta nuna musu mijinta a cikin su. Dan haka aka gayyace matasan fulani daga rugagge masu yawa. Kafin a fara wasan sun fita da yan mata, bakin wata rijiya suka zauna, suna hira shiru tayi tana kallon su. "Abuh meke damunki tun jiya" Murmushi tayi sannan tace musu. "Babu kome kawai ina kewar kune" murmushi suka yi. Matasa ne samari suka nufi gindin rigiyar zasu sha ruwa, watsewa yan matan suka yi, ya rage sai ita. Su dake suna zaman gida sun san su waye matasan, shi yasa suka gudu Ita kuwa bata ma tab'a jin ko labarin su ba, tana dai kallon su, suka gama shan ruwa, sau daya ta d'ago kai ta kalli Sama'ila, bata kuma kara kallon shi ba, har ya juya zai tafi yace mata. "Baki ga yan uwanki sun gudu bane ke gaki yar taurin kai?" Sauke numfashi tayi sannan tace mishi. "Toh meye zan guduwa? Ko mutuwa ai ba a gudunta, dan haka kuyi tafiyar ku, anan kuka same ni." Tab'e baki yayi tare da bin abokan shi suka tafi, dayawa abokan shi,sun san yana taimaka musu gurin samun mata, amma basu tab'a jin yace yana son wata mace ba, duk da kuwa yan mata dayawa suna kawo mishi kansu ya aura Amma yake ki. Dan ce musu yake matar da zai zauna da ita yana son wacce take tankawa ne ba wacce take tsoron shi ba. Haka yasa yake nan shirgegen tuzuru, shi baya ma niman yan matan, sau dari idan zai hadu da su dauke kanshi yaƙe, sabida baya son damuwa. Yana ganin yadda abokan shi suke kawo karan matayen su. "Ila yarinyar tayi maka ne?" "Ta cika kyau da farin fata".kuma haka ne, duk cikin rugar Alu babu ta biyun Zainabu kyakyawa ce fara kuma me kyau, doguwar ma'abociyar gashi da cikar kamala, kamar mahaifinta. Mahaifiyar ta tabiyo dan bafulatanar Libya ce ko nace balarabiyar Libya, haka take fara kal da ita. Shi yasa duk cikin rugar aka musu lakabi da, Fulanijo. Sabida basu yi kama da Fulanin asali ba. Dan haka yana tafiya gizo take mishi, itace mace ta farko da ya fara gani kuma tayi mishi, dan haka yana tafiya be amma bawai yana cikin nutsuwar shi bane. Bai kuma shiga dimuwa ba, sai da aka fara wasan ya ganta itace zata zab'i Kabiru kai tsaye bai iya boye abu a ranshi ba yace mata. "Bai dace dake ba, zan shiga shaɗin ni na dace dake" "Allah yayi min tsari, koda mazan rugar Alu sun kare wallahi na fi karfin zuwa a matsayin matar ka, balle ka duba da kyau ka ganshi, mijin aurena ne a can" "Lallai ina sonki da aure ki hakura dashi a daura auren da ni" "Ba zan tab'a koda ana mutuwa a dawo." Ta faɗa tare da juyawa ta zab'i mijinta a gurin, tana zaban shi ta gaya mishi abinda Sama'ila yake gaya mata, ai kuwa fada ya rikice a tsakanin su, dakyar aka tashi taron dan sabida faɗar da aka yi, --- Tunda ya koma gida, yake sintiri a dakin shi, yana huci sabida tsirta mishi yawu da tayi a fuskar shi. Takaici ne ya kama shi ya ciro kayan shi ya fara aikin shi da sunanta. Sai yaga haske me ƙarfi ya lalata nashi aikin. Karshe haka ya fita ya yanka tunkiyar shi ya fara aikin da ita, bai kai ga idarwa ba, yaga nashi aikin ya rufe na hasken. Har goshin asuba, kafin ya kammala. Yana idar da sallah bai tsaya ba sai rugar Alu, yana isa ana daura auren Zainab Hamza Bugaje da Kabiru Almustapha Bugaje. Yana zuwa bai kai ga musu magana ba ya shiga cikin gidan Malam Hamza Ja'e ya dauko amarya a gaba yayi tafiyar shi da ita, sai da ya bar gurin aka samu damar ihu ko kafin abi bayan shi sun b'ata babu shi babu ita. Koda ya dauko ta daure musu hanya yayi yadda bazasu sake su nime shi ba, ya nufi Mali da ita. Tunda ya tafi da ita suka yi tafiyar kwanaki kusan goma, sannan suka isa inda garin su yake, cikin wani ƙauye can, anan ya ajiye ta. Bawan Allah nan bai d'aga mata kafa ba, sai da ya rabata da kimarta, sannan ya cigaba da azabarta da ita, duk da tana kallon shi amma bata tab'a tunanin meye ya haɗa da shi ba, tana zaune dashi ne har tsawon wata biyar, sannan ya daukota ya dawo da ita, rugar Bako. Bayan tafiyar shi iyayen ta, sun tafi har rugar. Suka samu bayanan bai ma zo garin ba ita ba, abinda ya ya saka mahaifinta komawa kenan, duk bayan sati daya sai yazo, jin labarin ko sun dawo mishi da iya. Babu su babu labarin su. Har kusan wata biyar sannan ta dawo da ita. Ranar da ya dawo da ita, aka yi ta rigima da shi a rugar Bako. Ya kafe akan matar shi ce har itama yasa ta cewa mijinta ne, koda iyayenta suka zo yarinyar nan taki yarda akan iyayen tane, haka suka tafi suna kuka. Kuma abinka da jini sai sun tafi tayi ta kuka tana da nasani. A wannan yanayin ta samu ciki, haka tayi ta wahala, gashi mutanen garin sun tsangwame ta, shima yayi mata wulakancin. Mahaifinta duk da abin ya dame shi bai fasa niyyar shi ba, dan sai da yayi kokarin lalata abinda yayi mata, yana b'oyewa ne amma tun ranar da abin ya faru, mahaifin Kabiru ya kawo mishi takardan sakin, abinda tun daga lokacin ya fara kokarin ganin ya bar garin sabida abin kunyar da ya faru da diyar shi. Bai kuma gigita ba sai da Mahaifiyar Zainab ta je yaga halin da take ciki na laulayi, wannan dalilin yasa ka suka tattara suka tafi abun su, Kabiru ne yayi taurin kai yazo ya samu Sama'ila akan lallai ya sake mata matar shi. Shi kuma ya dake shi a kanshi karshe a anan aka sami gawar shi kuma babu wanda ya isa yayiwa Sama'ila magana, suma iyayen Kabiru sun bar garin da suke, rugar ta watsa babu kowa. Lokacin da Zainab ta ji labarin tayi bakin ciki amma bata iya magana ba, domin tana buɗe bakinta zata ji wani abu ya tsaya mata a wuya. Gashi duk abinda yayi da izza yake gaya mata, dan so yana matukar kaunar ta, amma matsalar idan ya tuna yadda ta wulakantashi a gaban jama'a, abin zafi yake mishi, shi yasa koda abokan shi suka zuga shi bai hakura ba sai da ya dauke ta ranar aurenta, da mijin. Wannan kawai ya saka shi ya Huce takaicin shi. Amma kuma lokacin da yaga cikin shi na d'agawa daga maranta ya daura musu kaunar duniyar nan ita da abin cikin domin har ya daina hulda da ita burin shi idan ta haihu a warware wancan auran a daura dashi. Sau dayawa yana ganin k'iyayyar shi a kwayar idanun ta, bai tab'a zaton zata girma haka ba. Tsawon Wata goma sha biyar ana wannan yanayin, har ranar da ta haifi abin cikin ta, wanda ko fuskar shi bata kalla ba, tayi tafiyar ta, wannan abin yayi masifar mishi ciwo, yasan muguwar al'adun sun na cire mace daga gidan mijinta a tafi da ita shi ya lalata mishi kome na shi. Tunda ta tafi ya kasa koda fahimtar kanshi da zuciyar shi, yasan ita yake so, amma bai san yadda aka yi ya iya cutar da ita da soyayyar shi ba. Yayi kuka yayi danasanin, ya ji a ranshi ya zalince ta, musamman abinda ya haifa, wannan abin ya saka shi jin tsanar kanshi da kanshi, meye matsayin Yaron? Meye zai gayawa Yaron? A yanzun ina uwar Yaron take, ya cuci kanshi da duniyar shi ya kore farin cikin shi da kanshi, har yayi nadaman zuwa bikin ranar. Kafin ya gudu yakan zaga yaje bayan bukkar Aminatu ya zauna yana jin shashekar kukan Yaron, zama yake yaji duniyar tayi mishi zafi da kunci shi yasa matukar zai cigaba da ganin halin da jaririn yake ciki zai iya sanya shi zuciyar shi ta buga yasa shi tafiya ya bar Aminatu da D'an shi ba wai ya gudu dan ya tsani Yaron ba, ya gudu sabida abin kunyar da ya janyo wa yaron, ya gudu domin barwa Kanwan shi da abokin shi yaron tunda Allah bai basu ba haihuwa ba, yasa shi ya bar musu shi. Kuma yayi alƙawarin ba zai tab'a dawowa ba, ya hakura da su, har da Aminatu da jinjirin. Yayi tafiya inda shima bai san zai tsaya ba shi yasa yace karta nime shi. *** Dawo labari.... -- A hankali ta goge kwallar da ya zubo mata, tare da cewa. "Iya wannan kawai ya isa ya tarwatsa mishi farin cikin shi.... [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀* ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx _Tambaya suna yawa! Wasu ina iya amsa su, wasu kuma ina kallon su na wuce su basu da Amsar a lokacin.... Kuyi hakuri labarin nan dauke yake da Zanen kaddara wanda alkalamin ƙaddara ta rubutashi ba labarin soyayya bace da za a ci soyayya akwai a soyayya labari ne wanda zaka samu yana tafiya da asalin rayuwa ban ce labarin ya faru da gaske ba, sai dai labarin iya iya tafiya kamar yadda yake faruwa a wani kaulin, zaku yi hakuri dani nima kuma zanyi hakuri da ku, idan uzurina ya shigo zan jingine nayi sabgar gabana, idan kuma na sami sarari zan baku sama da yadda kuke tsammani! Banyi alƙawarin kyautatawa ba, amma nayi alƙawarin farantawa ban yi alkawarin zai yi dadi ba, amma nayiwa kai na alƙawarin zai badda yadda zai tafi, idan kuka duba taken labarin Journey of Destiny! Wato Tafiyar ƙaddara... Dan haka idan nayi kuskuren ku min Uzuri sabida nima Yar Adam ce! Idan nayi dai-dai ku tuna da kalaman ku da tunatarwa! Kuyi hakuri dan labarin Yanzun muke Littafi ba Ɗaya fatan Alkhairi 👏_ Harshen ka... BABI NA BIYAR. Goge kwallar tayi tare da kurawa hatsin da aka kawo mata surfe, yau kimanin shekaru goma sha daya zuwa sha biyu, babu wanda ya tab'a ganin ta tayi fada da mutane, Allah ya zuba mata baiwar hakuri da juriya, ta kuma jure halin dan rikon su. Shi yasa yaron ya tashi da mugun kaunar su. B'ata tab'a daga hannu da sunan dukan shi dan yayi mata laifi ba, sai Addu'a, da fatan shirya shi yasa mutanen gidan da suke, wasu ke jin haushinta, ga Mamoon da mugun sakalci, bai san yayiwa kanshi wani abu ba sai an mishi. shi yasa ya tashi a sakalce, duk abinda akewa yara masu gata shi ake mishi, kai ko takalmi Mamoon baya saka me cinyayyen kasa. Kai rigar shi ce ta yage ba zai kuma sakawa ba sai wata. Gashi dai iyayen rikon shi talakawa ne futtik, amma bai taso da yanayin talauci ba, sai gata kamar jinin gwamna. Haka ta mike tare da shiga cikin gidan ta dauko langa ta dibo ruwa ta wanke mishi tufaffen shi, wanda duk bayan wata biyu sai an dinka mishi riga da wando, kala biyu koda su basu saka ba shi zai saka. Wani irin kauna suke mishi wanda shima Yaron yasan da haka shi yasa ya taso babu ruwan shi da kowa. Kai zunzurutun bakin hali inji mutanen gidan dan sukan ce bai gaji halin Aminatu da Malam Sanda ba, ya dauko mugun hali a wani gurin can, ko dakin mutane baya shi, yana bakin kofar shi, gashi da farin jini yara cika suke a dakin su. Idan ya kwanta ya mike kafa yace kar ayi magana babu me tari a dakin. Idan kuwa yace a fita dan Uban Yaro ko kaho ne akan Ubanka sai ka fita wannan yasa Yara dayawa suke tsoron shi. Bai da fada amma iya maganar fatan baki ya isheka bakin cikin wani guda.... <<>> Tunda aka nuna mishi ajin shi baban shi yayi mishi fada kafin ya ciro kudin tara ya bashi. "Bana kudin nan yayi yawa" ya faɗa yana juya kuɗin. "Yaron arziki kenan, bai yi yawa ba. Ka rike shi kaji karka yi faɗa kaji na san ka baka da abokin fada kayi karatu kaji yaron baba." Cogewa yayi yana kifi kifi da ido. "Almamoon meke damunka?" Duk ya rud'e. "Baba kazo ka ɗauke ni, a keken ka" murmushi yayi sannan yace mishi. "Insha Allah zan zo da kaina, na dauke ka yayi maka?" Ya tambaye shi gyada kai yayi, sannan ya kuma raka shi bakin aji, yayiwa malamin sallama, sannan ya ce. "Maza shiga dan Baba." Haka ta shiga bai kalli inda malamin yake ba, ya juya yana kallon Baban shi. "Baba idan kaje gida kaci abinci kaji" "Insha Allah dan Baba" Sake baki suka yi suna kallon ikon Allah, wannan irin soyayyar fa, ko makarantar Firamare da ya gama basu yi wannan dirama ba, gyara jakar shi yayi yana kallon ajin kafin ya hango wani kujera babu kowa. Ya zauna. "Meye sunanka?" Malam min ya tambaye shi. "Almamoon Isma'il Wodaadabe" ya faɗa a sanyayye, "Zauna" Ya zauna yana kallon allon, duk da makarantar kudi ne, haka bai hana shi fahimtar yadda ake koyarwa ba, kasancewar wanda ya gama ma, na kudin ne. Ana tashi tara ya ya dauki jakar shi ya fita. Dariya yan ajin suka mishi. Murmushi yayi musu tare da kallon su. Haka ya fita yayi break da aka dawo aji aka cigaba da karatu. Karshe daya Baban shi ya zo da keken shi ya dauke shi a gaba, a hanyar komawar su gida ne suka bi kasuwa, baban ya saya musu kayan abincin da za ayi na dare. Sannan ya dauke shi suka tafi. Har zasu tafi wani abokin aikin Malam na rana shima buzu ne yace mishi. "Malam Umaru, idan ka dawo ina son magana da kai" dan haka ya kawo Mamoon gida ya koma, zama yayi kusa da Mutumin yace mishi. "Malam Nasiru gani" "Kayi hakuri idanuna idan suka ga abu bakina baya shiru, musamman kai da muke tare da kai." Shiru yayi yana kallon ƙasa kafin yace mishi. "Idan ka tafi ka bashi wannan zoben ya saka a hannun shi duk da kana boye mishi abu akan shi. Kayi hakuri gaskiya rayuwar shi ce akwai daukaka akwai faduwa, bayan nan ban san meye Allah ya ƙaddara ba, amma gaskiya na tausaya mishi domin wata irin ƙaddara da zata sanya shi bayyana kanshi itace ƙaddarar da zata sanya shi kuka. Bana duba ko buga kasa, amma tabbas na hango abubuwa dayawa da yasa ba zan yaga maka ba, lokaci zai bayyana kanshi" murmushi yayi sannan yace. "Kuyi ta mishi addu'a Ubangiji ya shiga lamarin shi. Indai har zai jarabce shi ya jarrabce shi da abin da zuciyar shi zata iya daukar shi.". Jikin Malam yayi mugun sanyi sosai. "Karka cigaba da boye shi, domin zai fidda kan shi, wani lokacin muna son farin ciki amma sai kaga akasin ƙaddara ko tafiyar ƙaddara ta shigo mana, haka zamu yi hakuri da abinda Allah ya bamu, ba tare da mun katse wanda muke ba, idan ka duba ƙaddaran wasu sai ka zata laifi suka yiwa Allah ne yake jarabtar su. Wani lokaci kuma kaga kamar Allah ya fison wasu shine ya basu duniya da abinda yake cikinta, Ya Allah ka jarabce mu da abinda zamu iya, karka jarabce musu da abinda na zamu iya ba. Kayi hakuri na saka ka damuwa karka yarda maganata ta sanya ka damuwa, kayi hakuri don Allah." "Nagode sosai malam Nasiru." Malam Nasiru irin mutnen nan ne da Allah yayi musu baiwar ilimin addinin musulunci, musamman litattafan addinin musulunci, matsalar da aka samu yana da tab'in ƙwaƙwalwa ne, domin sabida ilimin shi aka jife shi, shi yasa yake abu kamar mahaukaci, amma kuma a haka Allah yayi mishi ido, idan ya fadi abu da ya gani tabbas Allah yana tabbatar da alkhairin, sai dai idan haukar ta motsa toh kome zai fada a surdudu zai fada. Dan haka Malam yana tashi ya koma shagon malam Bukar. A kasuwar nake yana sayar da shayi, shi ya nimawa Malam Umaru gadin kasuwa, nan ya kalli Malam Umaru yace mishi. "Naga Nasiru hoge ya kiraka, toh karka yarda da abinda zai fada dan kai ma kasan ba lafiyar kwakwala gare shi ba, dan haka ka watsar da batun da ya gaya maka shiririta ne kawai da haukar shi da ta MOTSA." Ajiyar zuciya malam ya sauke, duk da yasha ganin idan ya fadi abu yana tabbata, haka ya saka shi watsar da batun. *** Yana ajiye shi a kofar gida da cefene, ya juya yana faɗin. "Maza shiga gida Dan Baba" haka ya shiga, tare da sallama kamar wani babban mutum, matan da suke tsakar gidan basu amsa mishi ba sai Innar shi ta fito tana amsawa. "Barka da dawowa Dan Inna" wani irin murmushi yayi tare da kallonta yana faɗin. "Yawwa Innata" ya sa kai zai shiga Dakin kai Salihu yace mishi. "Almamoon wai da gaske ka fara zuwa boko?" Kallon kayan jikin shi yayi, sannan yace. "A'a ban fara ba ina jiran ranar da Iyarka zata biya min kudin ne" " Ba dai iyata ba sai dai Iyarka" "Eh gata nan jikin garka ta gode" ya nuna uwar Yaron da take bakin kofa zaune, ya shige da sauri dakin su. Matar me suna Murjanatu ta mike tsaye tare da cewa. "Wallahi sai na ci Ubanka dan banza me kama da yan daudu. Me mugun hali kawai" zuba mishi ido Innar shi tayi. "Me yasa ka cika rigima ne?" "Kiyi hakuri" ya faɗa tare da gyara zaman rigar shi, yana kallon jerin gwanon kwanonin da aka shirya na abincin shi da na Baban shi. Zama yayi tare da fara cin abincin shi. "Ya karatun kana Fahimta?" Gyada kai yayi ya a kwasar tuwon gero miyar kuka. "Ina fahimta, sai dai yaran ajin mu ne zan koya musu Yaren da zasu Fahimta." "Bana son damuwa, kayi hakuri mutane baka sauya musu halin su. Haka zaka gansu ka Barsu?" "Innah?" Kallon shi tayi, sai kuma ya share maganar. Lokacin islamiyyan na yi yaran gidan suka shirya baki daya, suka nufi islamiyyan. *** Zaune yake yana kallon matar shi, bayan ya gama cikin abincin rana, ya labarta mata abinda suka yi yau a kasuwa, kallon shi tayi na wasu dakikai. Kafin ta sauke ajiyar zuciya. "Me yasa ka tsaya kana sauraron shi ? Irin wadannan mutane basu da aiki sai na haddasa rikici a tsakanin zukatar al'umma insha Allah babu abinda zai sami Almamoon dina aniyar moɗa tabi Randa sannan ka mai da mishi zoben shi ba zai saka ba." Ta faɗa tana jin kamar ta rufe mutumin da duka, ina ma da zata ganshi da ta zabga mishi mari, kwafa take a kai akai. "Ayya Kabo kiyi hakuri mana." "Assalamun Alaikum, Barka da gida" sallamar Almamoon ya katse musu, abinda suke fada. "Waalaikumun Salam, shigo Babban mutum" inji Baban shi. Yana shigowa ya ajiye allon shi yana tab'e baki. "Yau na gaji, kai ka rantse da Allah nayi abin arziki" ya faɗa yana kwanciya a jikin Innar shi. "Ai karatun ai abin arziki ne, sannun kaji tashi kasha dawwo" da sauri ya tashi ta mika mishi kofin silver, yana sha yana murmushi. Sabida yadda yaji sugar kamar zai tsinke mishi kunne. "Innah hala baku sha ba?" Ya tambaya, mikawa Baban yayi yana faɗin. "Nasha itama tasha kai ne muka ragewa" "Allah ya kara muku budi, ya kuma raya ni, nayi muku abinda kuka min na zama me tausayi a gare ku iyaye na" Kallon juna suka yi kafin suka ce. "Amin Ya ALLAH" "Toh ni dai zan tafi Almamoon ban da rigima ko;" "Ubangiji ya kiyayye ya dawo da kai lafiya." Haka suka mishi addu'o'in, sannan ya fita, bayan fitar shi ne suka shiga hira har ta fita tayi musu abincin dare, Alhamdulillahi suna ci sau uku a rana haka ba karamin arziki bane. Kullum idan zai tafi makaranta Baban shi ke kai shi makarantar, haka ya mugun kawo renin hankalin a tsakanin yan ajin su, har ana mishi kallon abubuwan da yawa, akwai wani yaro me suna Abdul Hadi, kato ne ashe gurin zaman shi Almamoon ya zauna sunyi tafiya, ranar da ya dawo washi gari ya dawo makarantar, shine yazo ya ga Almamoon a kujeran shi, dama an kai mishi gulma. Yana zuwa ya daki kujeran, zunzurutun karfin kai bai saka Almamoon d'ago kai ya kalle shi ba. "Kai tashi min a gurin zama" "Daga gidanku kazo dashi?" Ya tambaye shi, "A'a daga gidan me kawo ka a keke" "Gaskiya kan shi yasa na ganka haka ashe abinda ake fada akan ka gaskiya ne" ya faɗa tare da mai da hankalinsa kan Littafin gaban shi. "Kai meye kake nufi?" "Yo ina zan gaya maka tunda baka gane bakwai da sha bakwai, wuce kawai tukekke" ya faɗa tare da bashi guri ya zauna. "Kai ba zaka zauna ba. Domin zaka shafa min bakin ka ne" "Ni kuma zan zauna domin zaka da irinka arziki ne, zan gaya maka abin da ake fada a kan a cikin ajin" Take yaron ya zaro idanu, kafin ya matsawa Almamoon, ya zauna . Yayi ta Bin shi ya gaya mishi me suke fada akan shi, fir yaki kashe idan ya dame shi da tambaya ya caka mishi bakar magana, haka yasa shi jan bakin shi yayi shiru, dan ya fahimci Almamoon ruwan sanyi ne dafa moda. Haka suka ci-gaba da zama a tare da juna, har zuwa lokacin da suka saba da juna. Dukda bai shiga harkan yan aji da mutanen makaranta, amma kuma, ilimin shi da kyawun dabi'ar shi ta janyo mishi soyayyar malamai, ta kai ko gasa aka saka shi yakewa makarantar su na daya, haka yasa malamai da dalibai ji dashi. A hankali ya zamewa makarantar su, tauraro duk inda aka shiga makarantar ne ke gaba, har sai da shugaban makarantar ya bincika suwaye iyayen shi, daga karshe ganin yadda suke iya daukar nauyin shi dukda faffutikar rayuwa suke, yasa shi dauke musu nauyin biyan kudin Makarantar, haka ba karamin dad'i yayi musu ba, domin kuwa basu zata zai zame musu Alkhairi ba, lokaci guda ya sauya musu ƙaddarar su. ** Lokacin da suka shiga aji uku, a lokacin ne suka tashi a gidan da suke, sakamakon sayar da gidan duk suka watse, suma suka koma wata unguwa kusa da makarantar su. A lokacin Almamoon yana da shekara goma sha biyar. Ya zama matashin saurayi, me tashe da kanshi. A lokacin kan shi yana masifar ja ga kuma Yan mata da suke mugun rigima akan shi idan yazo har hidima suke mishi, wasa wasa yaran masu kudi suka shiga mishi barin kudi, hidima suke mishi. Idan aka yi break haka zasu mishi sayayya kayan abinci har fada ake akan shi, bai tab'a d'ago kai ya kalle su ba. A lokacin daga Aminatu da Sanda, hankalin su yana kan shi kome yake suna kallon shi, ga Addu'a, da ake bashi na rubutu da na kariya saboda kambun baka da kambun ido, sai da ta kai baki daya basu da nutsuwa domin duk wata saiwa da itacce haka ake sassaka mishi ana bashi yana sha. Ba sai ga Almamoon ya fara gane gane ba, ranar da ta fara ganin abu, kwana suka yi akan shi. Domin kuwa hana su runtsawa yayi. Haka suka kwana akan shi, sai goshin asuba ya samu barci. A ranar bai je makaranta ba, sai da aka kwana biyu, sannan ya koma makaranta, sai da takai zoben da yake gurin Malam Umaru shi ya saka mishi a hannu, shine ya sami saukin abinda yake gani, sai suka kai ta kokarin rufe mishi ido, tunda garin niman gira an rasa ido baki daya. Karshe dai da yaga suna damuwa da halin da yake ciki sai ya daina gaya musu, amma yana tsorata sosai, dan ma yana da taurin zuciya ne. Haka suka yi jarabawar su ba gama aji uku. Suka shiga aji huɗu. Abu daya yake damun shi yadda abokan shi suke mishi tsaya da me muryan mata. Haka ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba, yazo gida yana gayawa Iyayen shi. Rarrashin sa suka yi tare da gaya mishi kar ya sake ya biye musu, dan ba abokan kwarai bane. Ya fita hanyar su. Sai ya ji maganar ya fita hanyar su, har ya fara maida hankali a abinda yake gaban shi, aka dawo da wata Daliba makarantar, me suna Salimah Dawood, kamar da wasa yarinyar ya makale mishi. Kullum sai anyi dambe da ita da wata tsuhuwar budurwan shi,(😛🙄 Maryam Mimi ayi a hankali dan baki yayi kasuwa dambe ake akan shi) Haka zai zauna yana murmushi cikin jin dadi, ana dambe akan shi idan kaga yadda ake abin zaka fahimci yarinta ke damun su baki daya. Idan shugaban makaranta ya kira shi shaida murmushi yake sannan yace mishi. "Yallabai ban me yasa suke dambe a kaina ba, sai dai kawai naji ana kiran suna na, Ni uwayena karatu suka turo ni ba soyayya ba, dan haka duk wacce take ganin zata iya tayi abinta, dama ta samu " Abin yayi matukar bawa kowa mamaki, domin tunda ake dashi bai tab'a magana kan ana dambe akan shi ba, sai yau. Haka suka fito bayan anyiwa yaran fada. Tare shi Salimah Dawood tayi tana kallon shi. "Ka kyauta abinda kayi?" "Meye ya faru!" Ya tambaye ta, "Toh kenan baka san meye kayi ba?" "Ina zan sani, tunda ba ofishin yan kai kara bane ni" ya faɗa zai wuce. "Wai meye ka taka ne?" Murmushi yayi tare da ce mata. "Abinda kike bi, abinda kika gaza gani a kan sauran mazan makarantar." Ya taka gabanta tare da kallon cikin idanunta, "Suna kike bi, abin da nake ji dashi kike bi, shi yasa baku gaba na karatu nazo yi" "Dan matsiyata kawai dan an damu da kai" Murmushi yayi sannan yace mata. "Sabida kudin Ubanki kika gaza mai da hankali akan karatun ki, kina bin malamai Office suna kara miki maki, shi yasa aka cire ki a can aka kawo ki nan, toh ki duba nan baki daya sansani na ne, kika sake na kuma kamaki kina dambe da Daya daga cikin yan matan makarantar nan sai na zane ki a gaban jama'a mata, Ni matsiya ci ne, amma kuma me tsaye akan kafarshi me bin maganar iyayen shi, bake da baki jin batun iyayen ki ba." Haka ya yab'a mata bakar magana sannan ya barta a tsaye a gurin, tana kuka. "Ai dama bata san waye shi bane, shi Sarkin mu ne, gashi talaka da babban zuciya, shi ba irin sakarkarun makarantar nan bane." Suka tafi suna mata dariyar renin hankali, tuni ta fara kuka me ƙarfi. Almamoon ba yawa ba dad'i, idan yayi yawa ma sai kayi kuka da kanka [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀* ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx _Real integrity is doing the right thing, knowing that nobody’s going to know whether you did it or not._ Tafiyar ƙaddara.. BABI NA SHIDA Rayuwar da aka gina shi domin Allah tafiya yake cike da Yardan Allah, duk wata nasara tana tafe da wanda Allah ya baka, wannan shine adadin farin cikin da Almamoon wanda yayi saukar Alqur'ani wanda yayi daidai da kammala makaranta shi na Sakandiri, kuma Allah cikin ikon shi ya samu tallafin karatun jami'ar Maryam Abatcha dake garin Maradi... Duk wani ƙaddara ta fara ne daga wannan yankin, duk wani tafiya daga nan ta fara, sai gashi cikin Ikon Allah tafiyar ta kuma canzawa izuwa Maradin. Bayan kwashe watanni suna jiran sakamakon, yana fitowa shi da iyayen shi suka kuma dawowa Maradi domin su abinda zasu iya mishi, Allah cikin ikon shi ya kuma basu tallafin wasu mutane, suka taimaka musu har aka kammala cuku-cukun makarantar, sannan suka dawo dashi gida, aka shiga fadi tashi yadda zasu sami damar nima mishi dakin makaranta domin nauyin karatun shi aka dauka su kuma zasu biya kudin daki da na littafai, abin tausayi wannan karon ma akwatin asusun ta kuma fasawa aka samu kudi me yawa, sannan ta bawa Malam suka dawo Maradi da Almamoon aka kuma biyan kudin makaranta. Sannan suka koma. Cikin kewar shi suke kallon shi. "Kasan waye kai? Ka kuma san dalilin ka na zama a gurin nan, akwai al'amarin da zamu gaya maka amma a yanzun shekarunka basu kai nauyin ɗaukar abinda zamu gaya maka ba. Jami'a ba kamar Sakandiri bane, a can gidan Yanci ne. Ba gidan da zaka zauna kayi laifi wani ya fito yayi maka fada bane, guri ne na kowa kanshi ya sani, dan Allah ka dubi girman Allah karka samu kuka, kamar yadda kace zaka sanya mu, farin ciki ka cika mana burin mu, mun san ba iyawar mu bane yasa kake kare kanka Allah ne yake kare ka, zaka shiga inda babu kunya ko tsoron Allah, don Allah karka watsa mana kasa a idanu, ka taimaka kayi abinda muka turaka Allah ya tsare maka imanin ka." Kallon su yayi yaga yadda suke share kwalla, sai yaji a ranshi akwai abubuwan da ya dace ya tambaye su. Amma kuma, "Babana me yasa kuke son na rayu a haka? Bayan akwai matsala idan wata rana." Rufe baki Innar shi tayi tana kuka tace. "Ban da karatun nan bamu muna biya ba, wallahi da ka fasa, tsoron goben ka muke ji, shi yasa muka lullube farin cikin ka, kayi hakuri kayi wannan tafiyar shima kamar tafiyar ƙaddara ce, babu wanda yasan me zaka taras a gaba, don Allah karka yarda wani ya yaudare ka, kaga kai ɗaya muka mallaka, don Allah ka rufa min asiri." Kallonsu yayi yana son tambayar su, amma a yadda yake hango firgici da tsoro ya saka shi had'iye tambayar, ya haɗa kayan shi da wanda yake daya sakamakon dan kudin da iyayen shi suke bashi dukda ba wani samu suke ba, dan Tun lokacin da yace musu yana son fara aiki a kasuwa suka daina barin shi yana niman abubuwan bukata, wani lokacin har kuka yake me yasa ba zai tafi kasuwa ba. Haka suke kokarin faranta mishi amma sabida sun hana shi sake yasa shi hakura. Yadda ake kaf-kaf dashi wallahi ko mace sai haka, akwai ranar da ya faɗa ai yana da yan mata, a makarantar boko, ranar sai da Innar shi tayi zazzaɓi, idan ta kalle shi sai ya fashe da kuka, tun yana daukar abin wasa har ya shiga tashin hankali, shi yasa ya daina subul da baka, domin yana tsoron abinda zai sami iyayen shi. Ranar Lahadi suka saka shi a mota har da kayan abincin shi, bayan an mishi fada. Kamar kullum. Basu bar tashar ba sai da motar ta bar gaban su, suka bar tashan. Haka suka koma gida cike da kewar dan su, me cike da al'ajabi. Karfe hudu tayi musu a garin Maradi. Daga nan makaranta ya wuce inda ya nufi can dakin kwanan dalibai, ya nufi dakin su. Ya samu dakin akwai matasa biyu shine na uku, bai musu magana ba, ya dauki kayan shi ya shiga cikin dakin, ya shirya tsaf, sannan ya bude yar robar da yazo da shi na Abinci yaci sannan ya koshi. Sannan ya wanke shi, ya fita bayan ya gyara kayan shi ya rufe ruf ya nufi kasuwa, ya sayo abubuwan da zai bukata, sannan ya dawo dakin su. Babu ruwan shi da kowa haka suma babu ruwan su dashi, washi gari ya riga su tashi dan haka har yayi wanka bayan yayi idar da sallah, ya zauna ya dama garin kunu yasha da yar kulin da Innar shi tasa wata makociyata tayi mishi. Yana ci yana kewar Innar tashi, bayan ya gama zuwa karfe bakwai. Ya fita abin shi har ya kai bakin kofar daya daga cikin yan dakin yace Mishi. "Malam Almamoon! Yana da kyau idan ka shigo guri kayiwa mutanen da ka samu magana koda ba zasu kula ka ba, suna na Mubarak Habib, wannan kuma Rabilu Adam, ga dan mukulin dakin guda uku ne ni daya kai ɗaya shi daya, idan muka kasance bamu na daya nan idan kuma tsautsayi yasa ya fadi toh sai ka rike wannan, haka dai dukkan mu zamu kasance, dan haka ina maka fatan Alkhairi, Allah ya bada sa'a." Duk sai kunya ta kama shi, ya fita tare da cewa. "Nagode" ...... Haka suka kasance, duk da babu wata mu'amalar arziki a tsakaninsu amma kuma dukda haka suna gaisawa da tambayar karatu. Bayan wata hudu lokacin da aka yi jarabawar zangon farko na karatun su dan lauya ya zab'a, sai da ya kasance dalibi mafi yawan maki a tsangayyar su, domin sunan shi ne na farko da A1 da maki 4.8, sai gashi ana niman shi ido rufe, wanda bai san shi ba so yake ya ganshi. (Abinda yasa na ke kokarin d'aga Darajar Almamoon ba kome bane dayawa yaran da suka kasance irin wannan a cikin al'umma zaka samu Allah yayi musu baiwar ilimin da daukaka na rayuwa, gasu nan dai basu da wata wata kyakyawan nasana, amma sai ka samu irin su Allah yana taimakawa rayuwar, idan kaga irin su sun lalace toh daga marikan sune, ko iyayen su. Ko uwa ko Uba, sun kashe musu sa ransu a gaban idanun su, irin wadannan Yaran idan ka tsaya musu da addu'a, ka basu ilimin addinin, ka nuna musu muhimmancin rayuwa da girman ƙaddara, sannan ka nuna musu ai suma mutane ne masu yanci wallahi sai su maka abinda dan Sunnah bai maka ba, su din kamar kowa ne, idan da zaka bincika su, zasu gaya maka suna jin kunyar amsa sunan suna na masu yanci, karka sarewa irin su gwiwa, show dem suma suna da Yancin irin na me Uba... Zasu rayu cikin farin ciki, amma idan society's suka fara kyamar su. Dayawa sai su fada halin banza da aikata abinda iyayen su suka aikata koda yake wannan hukuncin malam bahaushe ne, idan namiji ne za boye mishi asalin shi musamman idan yana da kudi idan kuma mace ce har karshen rayuwar ta, tana girban laifin da ba nata ba, don Allah al'ummar Hausawa mu sauya tsarin rayuwar mu, wallahi dayawa wasu nason fadan halin da suke ciki mune bamu basu kwarin gwiwa da fahimtar su. Abin tausayi...) Haka aka yi ta niman shi, shi kuma yana can wajen makarantar yana zaune, yana kallon yadda dalibai ke shiga ke fita, musamman idan suka leka sakamakon su, bai yi kyau ba. Abinda ya hana shi zuwa gurin kenan duk da akwai cunkoso mutane. "Kai ba kai bane Almamoon?" D'ago kai yayi ya zubawa mutumin da yake tsaye ido, malamin sune, mik'ewa yayi sa sannan yace mishi. "Eh nine" "Toh ka shiga makarantar ina taya ka murnan ka cinye jarabawar ka baki daya." Rufe bakin shi yayi yana murmushi, sannan tacewa malamin. "Nagode sosai" kura mishi ido malamin yayi, tunda yake bai tab'a ganin abinda ya burge shi sama da wannan dalibi nashi ba, murmushi yayi tare da cewa. "Toh a kara himma" "Nagode Insha Allah" haka ta shiga makarantar, malamin ba bin shi da ido, wani irin bugu zuciyar shi yaƙe, har sai da ya dafe kirjin shi, yana bin Almamoon da idanun. D'aga motar din shi yayi yabi bayan shi har inda ake kallon sakamakon, sannan ya juya. Bayan sunyi hutu. Sai da yayi ta damuwa da yaron ya dawo. Domin kawai yana jin yayi ta kallon yaron burge shi yake. Malam Ansar Yusuf Alhgabit, shine cikakken sunan shi, fari ne daidai ba me yawa ba, yana da matsanancin jiki me kyau, kyakyawa ne, kamar yadda ya kasance shi din Bazabarmen ne, daga garin Zinder. Dan kimanin shekaru talatin da shida, bai tab'a aure ba. Yana da kane da Mahaifiyar su, tana can, duk karshen wata yana zuwa gida, ya yi kwana biyu. Wannan hutun ba karamin gajiya yayi ba da gida, dan Allah ya jarabce shi da son ganin Almamoon. Hutun sati Uku suka yi, amma Almamoon bai dawo a satin farko ba, sai a na biyu. Ya dawo ya bar Baban shi babu lafiya, kamar na zai dawo ba. Haka suka sashi a gaba ya dawo. Bai da walwala duk da malam Ansar Yusuf yayi ta tambayar shi bai gaya mishi abinda yake damun shi ba. Ranar juma'a aka tafiya masallatai Jumma'a, ya nufi tasha sai Damagaram, Alhamdulillahi ya dawo ya sami jikin baban da sauki sosai. Rike kunnen shi suka yi tare da cewa. "Shi mutum mara jin magana Allah ya shirya mana shi, sai mun fara zane ka da girmanka" Cikin shagwaɓa yace musu. "Wallahi satin nan ban san meye na karanta ba, tab mahaifina bai da lafiya ina Ni ina karatu, wallahi gudowa nayi naga halin da Ubana yake ciki laifine?" Wannan kulawar da yake nuna musu yana masifar musu dad'i, dan haka suka ce mishi. "Babu laifi tunda kana shan nono ai shikenan." Dariya yayi ta musu Kawai. Ranar Asabar suka saka shi a mota ya dawo Makarantar. ** Ranar Lahadi ya fito zai tafi kasuwa ya hadu da Malam ANSAR. "Ina zaka Almamoon?" "Kasuwa zani!" Ya bashi amsa, "Shigo na kai ka" "Laa Nagode" ya faɗa tare da wuce motar, kura mishi ido Ansar Yusuf yayi ya kuma bin shi da mota. "Shigo nace" yadda yayi maganar a dake yasa shi shiga motar cikin jin babu dad'i, ya zauna suka nufi kasauwa duk da babu wanda yayiwa wani magana amma kuma haka yayi matukar sanya Malam Ansar farin ciki, koda suka isa yayi sayayya karshe Malam Ansar ya biya kuɗin. Lokaci guda abin ya daurewa Almamoon kai. "Malam wannan abun kamar bai dace ba, kuma idan ba zaka damu ba don Allah kayi hakuri karka kuma wallahi iyayena zasu min faɗa." Ya fada kamar zai yi kuka.yadda yake maganar yayi matuƙar burge malam Ansar, "Kai dube ka sai kace mace, amma yayunka mata ne ko?" Bai san ya tura baki ba, sai da yace mishi. "Kaga abinda nake fada ba, amma kai ne auta a gidanku ko? Da alamu kai mata na biyo" Sake fuska yayi tare da nuna mishi ya gode amma don Allah kar ya kuma wallahi karatu yazo yi ba kananun magana na,, haka suka dawo makarantar. -- a hankali kome yake tafiya. Farin jinin shi da nutsuwar shi yasa an kuma zaɓen shi mataimakin shugaban dalibai na makaranta, duk da ko shekara bai yi ba a makarantar, a bangaren addinin sun zo bashi wani matsayi aka hada musamman masu jin haushinsa suka ce ai dan daudu ne, hatta maganar shi ta mata ce, sannan akwai wata alaƙa tsakaninsu da malam Ansar, abin da yayi mugun b'ata mishi rai kenan, ya fita hanyar malam Ansar. A haka har suka gama aji daya suka shiga na biyu, a lokacin ma makin shi ya dara na kowa, lokacin da suka tafi hutu suka dawo, shakuwar shi da Malam Ansar tayi yawa, duk da akwai malaman da suma suke tare da Almamoon, musamman a ta bangaren addini, har tsoron shi ake idan yana karatun Alqur'an ko idan aka tambaye shi akan hukunce hukuncen addini, idan yana bayani sai ka zata babban shehin malami ne. Nan kuwa dan shekara goma sha takwas ne da ƙwaƙwalwar gigaby. A hankali malam Ansar ya wani gari ya mutu a kaunar Almamoon, dan sau dari idan ya saka shi a gaba, da idanun shi yake sauya mishi fasali daga Namiji zuwa mace, har gani yake idan Mamoon yasha kwalliya a matsayin mace ya maza zasu yi. Dan yana girma bakin fatar shi tana kara wani irin yanayi har wani Golden Golden yake idan ya shiga rana. Haka kawai abokan Wani dalibi da yaso a bashi mataimakin shugaban dalibai, suka nufi dakin su Almamoon suka mishi mugun duka, tare da watsa mishi kayan shi a waje, haka ya sa. Aka sami wani dalibi ya kira Malam Ansar yazo, ya dauke shi da kayan shi bayan sun rubuta Report da kome akan ɗaliban. Sannan suka nufi gidajen malamai. "Sannun ga dakin nan ka zauna kayi wanka an jima na kai ka asibiti a duba maka jiki ko kayi rauni." "A'a ba sai mun je ba, da sauki sosai." Tunda ya shiga dakin ya rufe kofar zama yayi yaci kuka sosai. Idan kaga yadda yake kuka sai ka tausaya mishi, bayan yayi wanka ya kwanta dan jikin shi ciwo yake. Dake ya gaji yana kwanciya barci yayi gaba dashi. Bai farka ba sai da asuba, yayi Sallah sannan ya kwanta, karfe bakwai ya tashi domin yana jin ana shara a falon, yana fitowa ya samu wata dattijuwar bafulatana ce. Kallon juna suka yi sannan tace mishi. "Akwai abinci a cikin dakin girki inji malam idan ka tashi kaci ga magani na baka," murmushi yayi mata sannan yace Mata. "Nagode" kara kallon shi tayi a karo na biyu, yaron ya shiga ranta" "Meye sunaka?" Murmushi yayi mata sannan yace mata. "Mamoon" ya zauna yana cin abinci shi a nutse, kallon shi tayi sannan ta nufi kitchen ta dibo mishi ruwan zafin da maganin ta ajiye mishi, shigowar malam Ansar ya sashi mik'ewa yana faɗin.. "Ina kwana malam?" "Lafiya ya jikin naka?" "Da sauki sosai" "Idan ka gama kazo ka wuce makarantar ana niman ka" "Toh" ya faɗa bayan ya sha maganin ya nufi dakin ya saka kayan shi. Sannan ya fito. Suka nufi Makaranta,. Duk wanda yaga yadda Malam Ansar ya damu da Mamoon sai da suka yi magana domin kuwa wata mahaukaciyar soyayya yakewa dalibin shi, har ta kai sai da aka yi maganar a gurin ai kuwa nan Almamoon ya gaya musu cewa babu wannan tunanin a ranshi, yasan malamin shine, bai taɓa mishi wannan abu na rashin ɗa'a ba, dan haka sune suke tunanin haka. Kuma batu na gaskiya Almamoon bai tab'a jin wani abu na burgewa.... [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀* ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx _Alhamdulillahi books dina baki daya wanda nayi su na kuɗi suna Okada akwai masu cewa suna bukata basu da Whatsp toh ga dama ta samu ku garzaya Okada na akwai su baki daya a can da sunan RamlatArManga_ _🙄🙆🏾‍♂️ Yanzun batun mata maza ya kare an koma Malam Ansar daga Taimako 😭 sai ya zama Shayyi 🙄😏_ *Assalamun Alaikum Jama'a, Ina iyayen da suke nimawa Yaransu malaman Lesson a cikin garin Kano! Dayawa basu da lokacin da zasu zauna sunyiwa yaran su extra lesson a gida toh shakurumin ku! Akwai dalibai mata shin ke Uwa ce? Indai har haka ne toh kin tab'a tunanin akan yaranki ko? Toh indai haka ne Mommy akwai Yan matan da suka kware a fanin computer, Islamic Studies! English da sauran darusa. Karki manta Yan matan nan dalibai ne, dan haka suke niman hanyar tsayawa da kafar su. Idan kika basu karki yi tunanin kome kisaka Allah a cikin lamarin zai tsaya mana Save our ladies please ku Basu damar koyar da Yaranku insha Allah zaki ji dadin haka, hausawa sunce a rashin tayi akan bar araha! Za a samu wannan damar ce idan kana garin kano a tuntube wannan Number 08147787720 mun gode only Kano sai an gwada akan san na kwarai,* Sirrin Zuciya... BABI NA BAKWAI. Sai da Almamoon yayi musu bayani da irin taimakon da Malam Ansar yayi mishi, sannan ya daura da cewa. "Bana tunanin kome akan malamina, sannan idan ma za ayi magana ne sai dai ace shi din Kamar Yaya yaƙe min, don Allah ku daina Yaɗa labarin karya akan mu. Wallahi Billahi azim, malam bai tab'a min kome ba, asalima Alkhairi ne a tsakanin mu, idan nace zan fadi Alkhairin shi yawa ne dashi, dan haka kuyi hakuri. Shima Malam Ansar yayi hakuri. Da bai shiga lamarina ba, haka ba zai faru ba, su kuma masu jin ba dad'i a kaina suyi hakuri." Ya fada tare da sunkuyar da kanshi. Hannun shi ya had'a a fuskar shi yana kallon yaron, idan ya nutsu yana magana a yangance wallahi sai ka dauka irin yan matan nan ne, Yayi imani da Allah da zai samu hutu fatarshi sai tafi haka kyau da haduwa. Balle kuma ya haɗa sabulai da mayukan shafawa. Kawai hango Almamoon yake cikin riga doguwa, kamar wanda aka buge kanshi ya girgiza kai yana kallon yaron da kyau. Malamai da sauran mutanen cikin dakin taron suka bashi hakuri, da kuma tambayar shi idan bai yafe ba a dauki mataki. "A'a ni kam na yafe" Ya fada tare da niman izinin zai fita, babu wanda ya hana shi, anan malam Ansar yayi magana me kama hankali, tare da nuna musu muhimmancin Almamoon a cikin makarantar idan har suka sake wani abu ya same shi tabbas za ayi ta. A kasar bishiyar lim ya same shi yayi nisa cikin tunani, dafa kafad'ar shi yayi da sauri ta cire hannun, yana karamin murmushi. "Yallabai" "Kaine Yallabai, me yasa ka yafe musu?" Murmushi yayi sannan yace mishi. "Suna jin babu dadi ne sabida ni ba kowa bane, kuma ina zuwa aka bani Matsayin da suka jima suna so, ko ni aka yiwa haka zan ji babu dad'i balle kuma su da suke tsofin dalibai na makaranta." "Na zata kayi hakuri ne dan kawai an baka" dariya ce ya subuce mishi a dan karamin bakin shi. Yace, "Wai ni din banza? Ni din wofi akwai mutane dai da su din wasu ne, na hakura ne dan bana son tashin hankali, kome ya wuce A bar zancen" ya faɗa bayan ya mike daga kujeran, yace. "Na gode da taimako, zan koma dakin kwanan mu" "A'a ban yi niyyar ka koma dakin ku ba, idan kuma kana zargina da abinda aka fada ne toh shi kenan ka bar gidan." Duk sai yaji babu dad'i, tare kawai baya son takura kanshi kuma baya son takura wani, dan haka kai a kasa yace. "Nagode" "Toh ka jirani na kai ka gida tunda nima na gama" ya faɗa tare da tsare shi da idanu, diriricewa yayi ya rasa inda zai saka kanshi tunda yake babu namijin da ya tab'a mishi haka, sai ya saka Mishi jin nauyin Malam Ansar sosai. "A'a yallabai zan biya ta dakin karatu na." "Bana son gardama" kasa yayi da ido, baki daya ya rasa me ke Mishi dad'i. "Toh shi kenan" ya faɗa tare da komawa gefe ya zauna, kanshi a sunkuye. Juyawa Malam Ansar yayi zuwa cikin ofishin su na malamai yaji gulmar shi da ake yi. "Ni nafi zargin yana bin yaron nan kawai sabida ilmin shi ba wai yadda ake tsammani ba, bayan haka bana da wata manufa akan alakar su." "Tab! A yadda duniya ta lalace nan ne zaka yi tsammanin haka? Shima munafikin yaro yasan abinda suke kulluwa, ban da haka meye zai dauki yaron jiya ya maida shi gidan shi da babu kowa sai su? Idan mai magana wawa ne majiyin shi ba wawa bane" inji wani malami, "Zato zunubi! Kuma tunda kuka fara wannan maganar ban saka muku baki ba, amma yana da kyau duk inda kuka ga musulmai ku kyautatta musu zato, domin babu wanda yasan daidai sai Allah, tayi mu da muke fada akan abinda bamu da tabbas mune akan b'ata basu ba, wallahi mu daina kashe wutar gaban mu muna hura na wasu sam Ansar bai da mugun nufi akan Yaron, da yana da shi da tuni ya gwada akan yaran makarantar, kuma duk idan hazikin dalibi yake kowa zai so mu'amala da shi, musamman wannan yaron da muke mishi kallon dan baiwa, don Allah mu wanke zuciyar mu kafin mu fadi Sharrin wasu mu." "Allahu Akbar, yanzun dama ka iya wannan nasihar kake zaune anan? Baka tafi masalaci ko kasuwa ba? Toh bari na gaya maka ba zan daina yiwa Ansar kallon mutumin banza ba, akan me zai dauke hankalin yaro karami yana jan shi a jiki, yaron nan ko magana kake mishi bai tab'a baka hankalin shi sai idan Ansar yayi mishi magana zaka ga jikin shi na rawa, dan haka akwai abinda suke kullawa wanda babu wanda ya sani sai Allah." Shigowar Malam Ansar yasa duk suka yi tsuru tsuru, murmushi yayi sannan ya nufi inda ya ajiye kayansa ya dauka, sannan ya juya abinci. "Ansar Yusuf" "La karka damu ban ji kome ba" ya faɗa yana lashe bakin shi, sannan ya saka kai ya fita daga ofishin, abin yayi masa zafi, kirjin sa sai zafi take kamar an cinna mata wuta,haka ya nufi gurin Almamoon. Tare da mishi alama ya taso su tafi, kura mishi ido yayi yaga yadda yake tafiya a hankali tare da dafe gefen cikin shi, lura yayi da yadda fuskar shi yake hade kamar baya jin dadi ne. A dame yace mishi.. "Meke damunka?" Murmushi yayi sannan yace mishi. "Kasan jiya sun dake ni a cikina, idan na zauna sosai yana mugun min ciwo, nafi son kwanciya" Ya fada bayan ya bude bayan motar ya kwanta. Malam Ansar ya rufe motar. "Toh mu wuce asibiti mana" "Da wa?" Ya tambaye shi a birkice yana zare fararren idanun shi nan, "Akwai wani bayan kai ne? Ko akwai wani a nan ne ban sani ba?" Ya tambaye shi yana tsuke fuska, "a'a wallahi bani zuwa su min allura, kawai ka kaini gida idan na kwanta rub da ciki zai dai na min ciwo" "Bana son shashancin,. asibiti zamu tafi" "Toh wallahi" yadda ya zuba mishi ido ne yasa shi kasa da kai, kamar wani yaro karami ya fashe da kuka, yana mita. "Ni nace ba zanje ba ka matsa min lallai naje uwar me zasu min? Ni wallahi ma barin gidanka zanyi na dawo makaranta." "Toh Allah ya baka hakuri, sai kayi ta zama da ciwo tunda baka son kulawar da za a baka." Shiru yayi yana jin shi amma yaki magana, har suka isa gida. Babu wanda ya kuma magana da d'an uwan shi, yana shiga dakin shi ya saka key tare da kwanciya a saman katifar shi da ya dawo dashi gidan, yayi rub da ciki, kwance. Har dare babu wanda ya kuma jin duriyar dan uwanshi. Sai washi gari. Ya fito tare da kallon Malam Ansar da yake zaune ya gama shiryawa yace mishi. "Ina kwana? Ina da test dan haka zan fita yanzun sai an jima" ya faɗa da sauri yana barin gidan. "Wannan yaron ko aljanu ne suke damun shi, baki daya ya kasa nutsuwa, kana mishi magana zai fita da sauri." Murmushi Baba Mari tayi sannan tace mishi. "Yaron kuwa bai da matsala idan ka cire rashin maganar shi, amma babu wani abu na aibu a tare dashi,yanayin shi da maganar shi yana min ɗibi da na wata wacce na sani wallahi." "Ayya! Yawwa Baba Mari kika ce min wata kika zo nima a cikin Maradi, shin kin gane inda take?". Shiru tayi sannan tace mishi. "Har yau ban same ta ba, sai dai na kasa cire rai da ita, domin ina Ni a jikina zamu hadu, kawai abinda na sani naje inda nake tsammanin tana nan sunce min basu nan, kimanin shekaru goma sha kenan da rasuwar matar, yaron matar ma baya nan shi da matar shi. Ina cikin halin kewa da Kaɗaitaka, amma ganin wannan yaron ya sani jin kamar ina Da sauran dangi a duniya." Cikin jimami da tausayawa yace mata. "Kiyi hakuri, Insha Allah zasu bayyana. Na tausaya miki wallahi. Kuma Yar uwanki ce ko?" Share kwalla tayi tare da kallon kasa. "A'a Ƴata ce karamar Ƴata ce, kamar wannan Yaron, har da tsayin da yanayin su, kawai shi bakin fata ne ya rabasu kamar yadda kagannin haka take jajjur da ita..wancan tsinannen dabi'ar tasu yasa na rasa ta har abada, nayi kokarin komawa inda suke amma shima aka ce basu nan, na yarda da Allah kuma na yarda da ƙaddara shi yasa na amshi abin hannu bibbiyu, ina kuma mata fatan Alkhairi Allah ya bayyana min ita, dangina kan sunyi min nisa sai dai nasan akwai wasu a iyakar kasar nan." Ta faɗa tare da zubda kwalla, kamar ba yanzun take murmushi ba. "Insha Allah, Ubangiji zai kawo miki mafita, shin wacce irin dabi'a ce haka?" Kallon shi tayi kafin ta zauna tayi mishi bayani, jinjina kai yayi tare da hango tsagoron rashin imani domin ban da rashin imani akan me zaka aikata haka. Hakuri ya bata sannan yayi mata sallama. Tare da barin gidan. Yana isa makaranta, ya hango mutumin nashi dalibai sun zagaye shi, yana musu bayani. Zama yayi a cikin motar, yana kallon yadda dan karamin bakin yake motsi hannun yana bayani da ita, fuskar me dauke da dan karamin gashin baki yayi mishi cass, wani irin farin ciki ne ya kama shi, ya kara zuba mishi ido, lokacin da daliban suka shiga mishi tafi, yana murmushi. "Ya Allah! Kai ka sanya min kaunar Yaron nan Ubangiji ka sauya min da wata ban da wannan namijin dan haukacewa zanyi." Ya fada a zauce. Kai ina ba zai iya boye sirrin zuciyar shi ba , zai gaya mishi koma yayya ne. Daga nesa yayi mishi horn. D'ago darara daran idanun shi yayi ya zuba a kan malam Ansar, a hankali ya mikawa wata abokiyar karatun shi littafan shi. Ya nufi motar, yana zuwa ya isa inda Malam Ansar yake zaune ya kalle shi. "Baka da aji ne Malam?" Murmushi yayi sannan yace mishi. "Ina da shi mana, kawai ina son nayi maka magana ne, sai kuma nake ganin kamar na haukace." "Ka haukace? Kamar ya? Bayan gaka a zaune anan din? Toh meke damun ka?" "Shigo sai na gaya maka" Shiga yayi yana kallon malam Ansar. "Ka tab'a ganin mahaukaci ido da ido?" "Eh mana, na sha ganin su," "Toh amma baka tab'a ganin wanda ya kai ni hauka ba?" Kallon mamaki yayi mishi sannan yace. "Subhanallahi, me yasa kake jifan kanka da miyagun kalamai?" "Sabida na zare?" "Kamar Ya?" "Sirrin Zuciya tace, zan ajiye shi har karshen rayuwata, Don Allah kar ka manta da kayi ta saka zararren malamin ka a cikin addu'ar ka, ba mamaki ko nasani saukin haukar da nake shirin farawa." "Toh amma ai naga lafiyar ka lau, sannan kuma babu abinda yake damunka" inji Almamoon, "Eh mana akan idanun ka nake lafiyayye, amma a zahirin gaskiya zararre nake, idan kana jin ana zararre ni ne lamba daya. Don Allah ka sanya ni cikin addu'a ba mamaki nayi katarin samun lafiya amma na haukace sosai." Dariya Abin ya bawa Almamoon, yayi dariya yayi dariya, shima shagala yayi da kallon yadda yake kyalkyalewa da dariya bai san lokacin da da ya tsinci kanshi da dariya ba, suka tabbata mahaukatan a cikin motar, domin daga Almamoon har Malam Ansar an rasa wanda zai dakatar da wani..... _#girmamawa.... Zaku yi min hakuri da Uzuri na kwanaki biyar Insha Allah, zan kammala Aliyu Asadullah ne Insha Allah don Allah ku gafarce ni, na san zan saka ku jiran amma Insha Allah idan na kammala, zan baku dogon page ina muku fatan Alkhairi 👏 And wallahi naga comments din Wattpad da vote yayi kasa, Insha Allah idan na dawo toh wallahi zan muku irin na zanen ƙaddara ta ne Yanxun haka yana Okada 700₦ zaka saya da shi da sauran books dina na kuɗi zaku iya samun shi a Okada, so ku motsa idan ba haka ba nima next zan bada a WhatsApp, kuma idan kika biyo ni daga Wattpad wallahi saya zaki yi shi yasa nake baku a free, idan ya koma WhatsApp toh wallahi ina gama book 1 Insha ALLAH zan kai Okada 2 ma haka. So ku karanta kafin na kai inda zan jin karan kuɗi 🤣🤸😛😜🤣😂_ [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀* ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx _Alhamdulillahi books dina baki daya wanda nayi su na kuɗi suna Okada akwai masu cewa suna bukata basu da Whatsp toh ga dama ta samu ku garzaya Okada na akwai su baki daya a can da sunan RamlatArManga_ Sauyin Yanayi... BABI NA TAKWAS. Tsagaita dariyar yayi yana kallon Mamoon. "Me yasa ka dariya?" Had'iye dariyar yayi sannan yace mishi. "Cewa kayi ka zare, shi yasa nake dariya ban kuma ga ta yadda ka zare ba shi yasa" B'ata rai malam Ansar yayi cikin damuwa yace mishi. "Da gaske na zare da, wallahi ka bar batun wasa, ina cikin damuwa kuma naji a raina na gaya maka ko zaka taimaka min" ajiye shiririta yayi a gefe guda, sannan ya fuskance shi. "Ina cikin soyayya mara iyaka, kuma na kasa fahimtar kuskuren da nake shirin aikatawa, shi zaka iya fahimtar dani?" Murmushi Mamoon yayi sannan yace mishi. "Ina ga kayi ƙoƙarin fitar da abinda yake ranka ga ita abar kaunar taka, zai fi ka rike abu a ranka kana yawo dashi." "Kana ganin idan nayi haka babu laifi?" Shiru Almamoon yayi yana kallon shi, kafin yace mishi. "Babu laifi matukar haka ba zai haifar da matsalolin a tsakanin ku ba" Kallon shi yayi sannan yace mishi. "Almamoon, ba irin soyayyar da kake tsammanin bane, SOYAYYA ce wacce duniya zata iya kirana da mahaukaci, Almamoon ina cikin jarabawar so, idan na fitar kyamata za ayi." Ya fada kamar zai yi kuka, "Idan kace sai duniya ta baka lambar yabo ne akan abinda kake Muradin zaka mutu baka sami abinda kake so ba, rayuwar duniya cike yake da dimauta dan haka ka rufe idanunka, ka gayawa zuciyarka muradinka zaka bi ba muradun wasu ba" "Almamoon! Ba yadda kake tsammani bane, ina jin tsoron fitarwa ne" ya faɗa a sanyayye, Bude mota Almamoon yayi tare da cewa. "Toh ka kashe soyayyar bata da anfani matukar ba zata amfani wanda ake dominta ba, Malam bari na gaya maka tunda nake ban tab'a son wani abu a raina ba, idan kaga ina son abu toh tabbas abin me daraja ne, malam ko da ake surutu akan mu wallahi wai muna mummunan alaƙa, malam da ace mace ce Ni ba zan tab'a baka matsayin masoyi ba, matsayin Yaya ne kake min. Ban tab'a jin ko fadawa yanayin ina sonka ba, kayi hakuri gaskiya na gaya maka, amma ina mutumtaka sama da yadda kake tuna, kai Ubane min, shi yasa tunda naga kana kokarin tsayawa rayuwata ya sani maka kallon Babban Yayana." Kamar wanda aka watsa mishi ruwan sanyi kalau, abin tausayi jikin shi yaji mugun mugun sanyi. Duk haukar da yake ashe da gaske da sikago yake raye, murmushin karfin hali yayi sannan yace mishi. "Balle kuma waye zai yi soyayyar jinsin ai haramun ce" yana dariya me mugun ciwo, haka ya fita daga motar suna kallon yadda dalibai suka watse, kowa ya kama gaban shi. "Almamoon" aka kira sunan shi. Wasu yan mata da samari ne na departmen din su. "Wai shin kai mace ce ko namiji? Ko dai mata maza ne bamu sani ba? Ai toh ko dai dan daudu ne musu mu duba dan kamfen ka" Suka fada tare da kwashewa da dariya. Murmushi yayi sannan yace musu. Kallon su yayi na wani lokaci, kafin ya tab'e bakin shi, yace musu. "Yo ku nan mata ne? Na zata kartin maza ne da sufar mata" ya fadi haka tare da barin gurin, yana. Zunzurutun maganar tayi musu zafi kallon kansu suke kawai cikin tashin hankali. "Ta ina muka yi kama da maza?" Suka juya suna niman wanda zai ganar musu da cewa basu kama da maza. Dariya samarin suka yi tare da cewa. "Amma Mamoon dan iska ne, duk duniya ban tab'a ganin mutumin da maganar shi take daidai da amsar mutane kamar Almamoon ba." Cikin fushi wata yarinya me suna Bara'atu ta kwasa da gudu, ta nufi inda Almamoon yake tsaye zai shiga aji ta janyo rigar shi dai da ya kusan faduwar. "Kai wai namiji ne?" "A'a kece a tsaye" ya bata amsa zai shiga cikin aji, "Dan daudu kawai" ta gaya mishi haka, wata shegiyar dariya yayi sannan yace mata. "Don Allah waye mai madubi a cikin ajin nan?" Ai kuwa aka samu wata ta mika mishi ya karba a yangance yace mata. "Ina ga kamar baki tab'a kallon kanki a madubi bane, amma babu wacce ta kai ki sufar maza duk cikin makarantar nan. Mai fuskar maza kawai" "Banza jaki dan luwadi kawai?" Cak ya tsaya yana kallon ta, kafin ya sake murmushi me ciwo, sannan yace mata. "Toh nagode, jakar aji" ya fadi haka yana me barin gurin ta, da gaske kalmar ta dake shi, ihu ta saka tana me sake kokarin shigowa ajin dalibai yan ajin suka hanata. "Kin zage shi ya rama, kin gaya mishi magana ya rama, yanzun ma kin gaya mishi ya kuma Ramawa me kike so ki mishi? Ba zaki hakura ba kenan?" Wani takaici ne ya kamata, ta shiga ihu tana faɗin. "Dan luwadi kawai mata maza, mara amfani kai har ka mutu haka zaka kare, kai ba mace ba kai ba namiji ba, dan iska karuwan namiji kawali kawai." Kifa kai yayi a kan kujerar shi, yana shashekar kuka, sabida kalmomin sun mishi nauyi, karewa Malam Ansar aka kira, shi yazo ya fatattaki yarinyar, ya shigo ajin. Dukar kujeran yayi yana kallon shi. "Ina jiranka a Office" ya faɗa tare da juyawa ya fita, ya kai minti goma kafin ya mike a sanyayye, su kansu yan ajin yau daya sai da suka ji babu dad'i, a hankali ya nufi ofishin Malam Ansar. Yana shiga ya nuna mishi kujera bayan ya mike tare da dauko mishi ruwa ya bashi, amsa yayi. Har lokacin kuka yaƙe. Bai hana shi ba. "Meye dan ta faɗa maka abinda ba halin ka ba? Meye dan kawai ta fadi abinda bai zama dole a yarda ba? Kayi shiru ka daina kukan nan haka" "Zan tafi Damagaram." "Me yasa zaka tafi kuna tsakiyar karatu, idan itace kayi hakuri zan saka a dauki mataki akan ta kaji" mik'ewa yayi zai fita ya riko hannun shi, juyawa Almamoon yayi tare da kwace hannun shi. "Don Allah karka min mummunar fahimta, kayi Hakuri" da sauri ya bude kofar ya fita. Ya kasa a guje yana kuka,aji ya shiga tare da ɗaukar jakan shi ya bar makarantar, bai tsaya ba, sai a can wajen makarantar ya tsaya tare da share kwalla. Abinda bai tab'a yi ba shi yayi yau. Tafiya yawo a cikin gari tafiya sosai bai koma gida ba dai karshe biyu na rana, ya isa gida a gajiye, wanka yayi sannan ya kulle kanshi a dakin dan tun shigowa gidan bai ga motar malam Ansar ba, ya tabbatar bai dawo ba..a sadadde ya shiga cikin gidan. Tare da nufar dakin shi, cikin dakakkiyar murya yace mishi. "Ka gama yawon?" A razane jikin shi na rawa, ya juya yana me fuskarta malam Ansar, wanda ya tako har gaban shi. Sai da suka kure bango. Kauda kanshi yayi tare da cewa. "Don Allah ka matsa a kusa dani, wallahi bana jin dadin yadda kake min, idan kana min haka zan na gani kamar ba taimako na zaka yi ba, wata Muradin ce da kai." Ya fada muryan shi tana rawa kamar zai fasa kuka, "Ni ban fasa kuka ba sai kai?" Makwat ya had'iye wata irin yawu da ta tsaya mishi a wuya, dakyar wanda yayi imani da Allah, yafi gayan tuwo wahalar wucewa ta wuyar shi. "Meye kace? Kana min kallon ne kamar yadda suke min? Na zata ko zasu min kallon haka kai ba zaka min ba ashe hasashe na ne haka? Almamoon naji mamaki da abinda kake fassara Ni dashi." Daga haka ya matsa a gaban shi ya wuce dakin shi, abin shi yana jin kamar zuciyar shi zata buga, zama yayi tare da fashewa da kuka. Ganin kukan ba zai kare shi da kome ba ya nufi dakin shi.. rufe kofar yayi tare da nufar ban daki. Bayan ya fito ne, ya kwanta a kasa, yana jin kewar gida da iyayenshi. Haka har gari ya waye, ya kuma fita ko karyawa bai yi ba, yayi tafiyar shi bai dawo ba sai can la'asar sakaliya, yana shiga ya samu Baba Mari ta fito gidan, cikin kulawa ta kalle shi. "Angona Barka da yamma" kunya ce ta kama shi yace mata. "Kiyi hakuri Baba ina wuni? Ya aiki da zafi" "Alhamdulillahi! Ka dawo makarantar ne?" "Eh wallahi" ya faɗa tare da gotawa ta gefenta, wani irin jan iska tayi da hancin ta, sannan ta bi bayan shi da ido. Haka kawai take jin wani irin abu a ranta dangane da yaron, sai kuma ta share tare da nufar inda gidanta yake, har ta zauna tana tunanin yaron. Haka suka ci-gaba da zama duk da babu wani kyakyawan mu'amalar da zata nuna maka ana shiri kamar baya tsakanin Ansar da Mamoon, haka bai hana shi ajiye mishi duk abinda yake bukata ba kusan har aka gama zangon karatun suka yi jarabawar da hutu, babu wata kyakyawan fahimta. A daren yau hada kayan shi yayi tare da tattara duk wani abu, haka kawai yake jin faduwar gaba, dan haka koda ya gama ji yaƙe kamar yayi ta kuka, dan bai san meke faruwa dashi ba. Haka ya gama had'a kayan shi, sai gashi an dan kira su sakamakon wasu dalilai ba zasu tafi hutu ba, sai watan gaba. Dan dole ya hakura amma a ranshi kewar gida yake, idan ya tafi makarantar dakyar yake fahimtar abinda ake duk da sati biyu ya rage ayi musu hutun, haka dai suka yi ta maida hankali da abinda ya rike su a makaranta. Yawan mafarkai da tashin hankali na faduwar gaba yasa shi kasa sukuni, abin da ya haifar mishi da zazzaɓin da ya kwantar dashi, Almamoon yana da makon iyaye, ya saka iyayen shi a ranshi. Har gida aka saka mishi ruwa dan yaki zuwa asibitin. "Likita ka duba shi da kyau, yana yawan kukan ciwon ciki?" Zaro idanu yayi yana kallon likitan. "Toh dan bamu guri" Haka ya fita ya basu guri sun jima suna tattaunawa, kafin likitan ya saka mishi ruwa da allurai. Bayan tafiyar likitan Malam Ansar ya shigo ya mika mishi magani. "Sannun Insha Allah zan tambaya maka damar tafiya gida ko" gyada kai yayi sannan yace mishi. "Nagode" Ya fada a hankali, yau kan yadda yake kwance ba lafiya muryan tafi kowa yaushe kamancecceniya da ta mata. "Yau kam kamar mace ka fito kayi laushi! And anya kai ba mata m.." Wani kallon banza ya watsa mishi. "A'a mazan mata ne ba mata maza, ba dalla fita ka bani guri" ya faɗa yana b'ata rai, dan dole ya fita daga d'akin. ---- Washi gari bayan likitan yazo ya cire mishi ruwan tare da kara mishi allurai, sannan ya tafi. Can da yamma Ya fito diban ruwa a kicin suka yi kicibis da Baba itama ta gama abincin zata leka shi ta koma gidanta. "Ya jikinka Mamoon?" "Da sauki Baba mari" ya faɗa a sanyayye, sake zuba mishi ido tayi zuciyarta tana wani irin bugawa kamar zata tsage, ta rasa me zata iya fahimta. Shiga kitchen ɗin tayi tana mishi wani irin kallo. "Waye kai?" Ta tambaye shi, "Ban gane ba, Baba Ni ne Almamoon fa" "Ba sunan nakeson ji ba, kai mace ce ko Namiji?" Gabansa ya fad'i, ya kalli kofar shiga abinka da kuruciya, sai ya rud'e tare da jin kamar an watsa mishi ruwan sanyi. "Baba don Allah" "Bani zaka roka ba bayanka zaka Duba, kai mata maza ne?" Kuka ne ya kwace mishi yana girgiza kai. "Toh amma ai jini ne a bayan wandon ka" ta faɗa mishi. Da gudu ya juya zai fita suka yi kicibis da Malam Ansar, durkushewa yayi cikin matsanancin kunya da kuka. "Don Allah karku gayawa kowa, ban san na b'ata jikina bane" ya faɗa yana kuka, mutuwar tsaye malam Ansar yayi tare da sake kayan da yake hannun shi yana kallon shi. Cike da mamaki da mugun al'ajabi. "Toh meye haka yake nufi? Shin kai mace ce ko namiji, ko mata maza ne?" "A'a ni m.." ya kasa fitar da koda kalama daya ce, sai kuka da yake,.yana ganin kamar yaci amanar iyayen shi. "Tashi muje asibiti ya faɗa a haukace" inji malam Ansar, Cikin wani irin kuka me matuƙar ban tausayi, yace. "Nace bana so! Abinda kuke son sani shine ni." Ya kasa furta kome sakamakon tuno yadda Iyayen shi suka yi ta rokon shi, ta shi yayi ya shiga daki tare da rufe kofar, ya jingina da kofar yana wani irin kuka. Da sauri ya shiga ban daki ta cire kayan shi, ya wanke wandon ya durkusa ya ci kuka kamar idanun shi zasu fita, "me yasa aka halicce ni haka? Me yasa na kasance haka? Me yasa ba a damu da nawa nau'in ba? Haka zan gama rayuwata? Ko haka ne zai saka na." Kuka ya sake me mugun karfi tare da zama ya kusa kanshi a tsakanin cinyoyin shi, kunzugun shi ya dauka ya gyara tare da ɗaukar wata gajeren wando ya saka tare da boye kanshi, ya ki fita ma a ban dakin balle ya koma dakin shi. .... Kallon juna suka yi daga Baba Mari zuwa Malam Ansar. "Toh amma ina ganin kamar jinsi biyu ne dashi,. Kuma baya son ta faɗa" Kamar ruwa ya cinye malam Ansar ya kalli Baba Mari, kafin tace mata. "Baba bana tunanin haka sai dai ina ganin kamar mace ce" ya faɗa a sanyayye, sama da koda yaushe, haka wunin ranar suka yi shi. Jacader Tun daga titin da zai kai ka cikin Unguwar zaka Fahimci unguwa ce ta masu hannun da shuni, wato attajirai masu kuɗi, yan siyasa da yan kasuwa, manyan mutane na cikin garin Maradi. Hukumar yan sanda ne zaka fara cin karo dasu, wanda sun kai kimanin dubu daya, a barbaje cikin unifoam, idan kayi tafiya gaba zaka taradda hukumar jami'an tsaron ko takwana wanda suke sanye da wasu kayan yaki, su kimanin dubu daya. Gaban su kadan idan ka wuce shigen wato (checkpoint) hukumar kunce bom ne koda za a ratsa tsakanin su a kawo harin bazata, suma kimanin dari biyar da kayan aikin su. Sai gaba hukumar fasakorin shige da fice wato (custom,) suma a nasu checkpoint, su kimanin dari bakwai, idan ka wuce su nan zaka samu get da zai kai ka first get, inda aka saka hukumar immigration, wanda sun kai dari uku a gurin, idan ka wuce get din zaka nufi get me dauke da Ash color wanda aka saka katin Stamp na Niger republic Army. Sojojin ne birji daga sojojin ƙasa, zuwa sojojin sama. Sai daura drum suke ana binciken sirri. A gaban kadan wasu manyan mutane ne zaune duk wanda zai shiga cikin gidan bayan ya tsallake wadancan checkpoint, sai ya isa gurin su, anan za a saka abu a duba ka har cikin jikinka sai an duba ka, Idan mata ne akwai jami'an tsaron mata, suke kome na bangaren mata, wani katon legendary house wanda za a iya kiran shi da Mansion, a tsakiyar katon fili, anyi ginin gidan kamar yadda akayi gina shi kamar bujr arab, wato wani hikima irinta fasihai kwararrun maganin duniya aka tara suka gina gidan, idan daga nesa ka hango zaka dauka kamar daukar gidan aka yi aka daura a saman koramar ruwa. Domin kuwa cikin tsari da baiwa irinta ma'abota hankali suka gina gidan a saman ruwa, kamar an dauki gidan ne aka daura a saman ruwa. Daga nisa kana hango cikin ruwan. Gidan da aka gina kamar gidan sama me hawa biyu, amma kuma Normal mansion ce, sannan anyi tubalin gina zaman a jikin gidan yadda kana kallon shi zaka Fahimci wannan ginin ya kai makura a haduwa, haka roof din gidan yadda kasan kwalba aka saka a saman gidan, gidan kewaye yake da manyan dogayen bishiyar dabino, ta gefen gidan kuwa wani kyakyawan lambu ce me dauke da manyan Swam wato agwagwan ruwa na kasar Austaraliya, lambun dankare yake da kayan ciye ciye, sannan akwai wasu kyawawan dawisu, fararre, daga can ƙasar China aka zo dasu. Ta gaban gidan kuwa parking lot ne, me dauke da manyan motoci guda biyar, BMW, Phantom, Mercedes Benz, sai Range, da Toyota Tacoma. Sai watan katuwar bike na kamfanin Nissan wacce aka mata ƙatuwar Stamp na sojojin. Gefe can hilux ce 40×40, army color. A jikin kusan da motar wani katon daki ne me dauke da Police Dog, lion dog, wadannan karanunakan ba a cika samun su a ko ina ba sai a China da Japan. Domin kowani guda daya ya kai girma giant Ram, wato katon rago irin me murdaddiyan kaho. Ko ina ma gidan dauke yake da Cctv. Duk inda ka gifta kuwa. Can bayan gidan sosai, akwai BQ, inda gabaki daya ma'aikatan gidan suke. Cikin gidan me dauke da dakuna biyar uku a sama biyu a kasa. Dakuna ukun saman dakin mamallakin gidan ne, biyu dakin kwana ne, daya kuma dakin al'amuran shi ne, gefen dakin wani study room ne, sai backyard me dauke da yar karamar gurin hutawa me kyau. An Kawata shi da wasu irin kujeru na musamman guda uku, duk yadda aka yi an tsara gidan ne daga mace daya da yaran su, sai abinda ba za a rasa ba. Daga step din da zai kai ka kasa an shimfid'a India capter. Red and Golden,. Sannan paint na gidan dauke yake da grey color sai minti colour. Dakin farko na sama, wanda aka zuba wasu mahaukatan furnitures daga Korea aka yi oda dinsu, kome na dakin Royal blue ne, sai furnictures din da paint dakin ya kasance cream colour. Daya dakin kuma dauke yake da simple design furnitures, whiter and Black, haka ma labulayen dakin. Fari ne me digon baki. Sai tiles da aka saka a kasan dakin yayi mugun yiwa dakin kyau. Haka ma wancan dakin shima tiles din shi me kyau ne. ... Dakin kasa kuwa daya dakin dauke yake da kome cream And Golden, yayi masifar kyau haka ma Furnictures din shi. Daya dakin kuwa dauke yake da blue and pink paint, kome na dakin Blue And pink ne, idan ka nutsu zaka ga har kayan wasa an ware. .... Falon me dauke da ƙatuwar cimma tv, baya kome a kashe yake. Sai falon da yake kawace da manyan sofa, har guda ashirin da hudu,, sabida girman falon. Kuma ba wai a guri daya ba, a'a kowani kusurwa a jiye yake da sofar shi. Wato kujeru. A can gaba da fakon wata luxury kitchen ne, wanda idan da zaka kira shi da modern kowani suna duk daya ne. Ma'aikata kusan shida ne. Kitchen ɗin suna aikin girki kawai, idan kaga yadda suke aiki zaka Fahimci sun gama gajiya da aikin kawai dan albashin su, sukewa wannan hidimar. A falon akwai wani hoton family, me dauke da hoton Wani kyakyawan Matashin Soja, dan kimanin shekaru arba'in a duniya, murmushi yake ana saka makon lambar karin matsayi. Kasar hoton an saka Firaministan Mamman Nasir Aghali. Da Major General Mohan Mamman Nasir Aghali. Jarumin sojan kasar Nijar. Fari kyakyawa ajin farko, dogo murdaddiyan jiki, ma'abocin manyan idanunawa da zunzurutun kwarjini. A watan Fabrairu waki'a ta faɗa mishi mara dadin ji, ana gab da fara bikin shi wanda ya rage sati Daya a fara, babban da ga Firaministan kasar Nijar, kuma shine kashin bayan mulkin mahaifin shi, sai dai kuma abin tausayin da ya faɗa mishi a filin yaki. Mamman Nasir Aghali. Shine firaministan Nijar, kuma shugaba me adalci, da son talakawan shi, mutumin da bai dauki duniya da zafi ba. Dan kimanin shekara saba'in da tara, duk da ya girma amma shugaba na gari ne, kuma adalin shugaba. Da ake matukar kaunar shi a kasar Nijar baki daya, kuma shugaban kungiyar kasashen Afrika baki daya,yana da mata biyu. Yara goma maza uku mata bakwai. Hajiya Latifah itace matar shi na saurayi da budurwa, kuma buzuwar Agadaz ce wacce al'ummar kasar ke mata lakabi da farar mace alkyabar mata. Duk inda kake niman Jarumar mace idan kayi katarin haduwa da ita ka samu. mahaifinta shahararren dan kasuwa ne mazaunin garin Tripoli na kasar Libya. Kasancewar ta taso daga wata kasar ta sami ilimin boko sosai me zurfi, haka ta sami na Addinin fiyye da yadda kake tuna, sai dai mace ce da take da d'agawa da son mulki, mace ce da take son Nasaba da kusancin mai kyau, shi yasa bata mu'amala da kananun masu hannu da shuni kuma uwa uba tana da nasaba da Gidaj Sarautan Agadaz tana da yara shida. Mohan kuma babban Sojar ƙasar shine babban ɗan ta, shi yasa taci alwashin dan ta macen da zata aure shi sai ta haɗa Kyakyawan tarihi da nasaba. Sai Hadder shine yake bin Mohan, yana kasar Faransa yana koyarwa, sai Salman yana kasar Nigeriya, yana aiki a ofishin jakadancin Nijar a Nijeriya,sai Khausar Likitan mata ne na babban Asibitin Nijar da yake Niamey, sai Radiyah, tana karatun ta a jami'a, sai Karamar su Nairah tana matakin sakandiri. Amaryan Mamman Nasir Aghali Safiya. Tana da yara huɗu duk mata, Mansura, Mahnoor, Hinduh, sai yar karamar su, Tawakaltu. A zahiran ce zaman lafiya a gidan sai a slow, domin Hajiya Latifah mulki take da Kowa hatta shi kanshi Firaminista sai yadda tayi dashi, sam Safiya bata gabanshi, idan ka ganshi a dakin Safiya ko tazo dakin shi dauki haka a matsayin babban al'amari ne na rabo ya dauko ta, haka yayi mugun fusatatta, domin itama yar babban gida ce, amma aka maida ta kamar baiwa. Dan haka bata tab'a wani yunkurin dan kwatar kanta ba, amma kuma a hankali ta lalata gidan, a zahiran ce sai da ta watsar da Yaran Hajiya Latifah, ta hana su shiga jikin Uwar su, ta kama su duk.ta rike su, kuma bawai dan Allah bane no cutar dasu take na fitan hankali. Mutum daya ne yafi karfin ta, Mohan Mamman Nasir Aghali, mutum ne mai matukar ilimin addini da na siyasa, duk yadda ka zo Mishi yasan take taken ka. Takai Mohan ba iya ita ba hatta mutanen da suke jikin Mahaifin shi shakkar shi suke, domin ya zamewa Mahaifin shi garkuwa, duk wanda yayi yunkurin cutar da Mahaifin shi tabbas sai dai kayi a wani gurin amma da'iran da yake karyan ka. Sabida dalilin haka, aka tsane shi babu irin sukan da ba akayi wa mahaifin shi ba, amma zai kira shi yayi ta Mishi fada, daga baya idan suka keb'e yakance Mishi. "Babana Ka kara himma akan na da, mutanen da suke kewaye dani basu san Allah ba, babu Allah a zuciyar su." "Insha Allah Abbih zan yi iya kokari na, na baku kariyan da ta dace." Tun lokacin ma bai samu matsayin Firaministan ba ma ake gwagwarmaya da munafukai, lokacin da ya samu Mohan ya kai matakin babba A soja, sai aka yi ta gayawa Uban ai zai Mishi juyin mulki. Ko dar uban bai tab'a ji ba akan Dan shi dan yasan abinda ya haifa. Duk cikin yara shida na Hajiya Latifah Mohan ne kawai bai juya mata baya ba, domin Hajiya Safiya tayi amfani da abinda Hajiya Latifah take na mulki ta nunawa Yaran ta ai ita babu alamar akwai adalci, a tsakanin su. Kawai tana zaune ne dan su, sabida basu samu kulawar Hajiya Latifah ba. Abinka da dan kulawar da ake badan Allah ba, sai gashi yaran sun juyawa mahaifiyar su baya, tare da nuna mata bata adalcin a cikin rayuwar gidan, bata da lokacin yaranta balle mijinta, abubuwa dai dayawa yaran suka lissafa mata, koda suka gama magana ce musu tayi. "Kuna da damar da zaku yi kome sabida ku ba zan fasa abinda nayi niyya ba." Hajiya Latifah bata da lokacin da zata cutar da kai,.ita dai kawai kimarta da mulkin ta take mugun so, daga haka yaran suka juya mata baya. Har rana me kaman tayau. Al'amarin Mohan Mamman Nasir Aghali, kuwa ranar da aka bashi matsayin Major a ranar wata muguwar ƙaddara ta faɗa mishi na cutar..... _Hi ya kuke? Kwana biyu zaku yi hakuri gaskiya ina fama da ciwon baya da hannuna. Dan haka gaskiya ba zan iya update daily ba amma Insha Allah idan nayi Posting yau sai laraba kenan, zamuna hutun kwana ɗaya da fatan zaku Fahimce ni...._[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀* ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE https://www.instagram.com/batool_spices Fatima Batool enterprise Yaji Ginger and garlic Onion powder Pepper soup Curry Biryani spices Mixed spices Indian spices Arab spices Chai masala Baharat blend Tandoori blend Thai masala Garam masala Provence Tea spice Zobo powder Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋 Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris Wani Al'amari... BABI NA TARA. Muhammad Mamman Muhammad Nasir Aghali. Shine asalin cikakken sunan shi, kasancewar sunan shi sunan babans shi da Kakan shi na Uba, yasa aka mishi lakani da Mohan. Duk inda kake niman mutum me tsaye akan ra'ayin shi Mohan ya kai gurin, yana da dadin mu'amala. Ga son mutane da yawan Alkhairi, sai dai mutum ne da bai da fara'a sosai , wani hali da mohan yake dashi wanda ba kowa yake iya zama dashi ba wato murɗaɗɗan hali, duk wanda zai zauna da shi sai tayi mugun hakuri dashi, kafin wannan lamari babu me iya gane abinda yake so sai Abokin shi daya tal a duniya wato. Captain Khalil Ibrahim Dan Ba'are, kaf duniya bai da Amini sama da dan Ba'are, bai da abokin arziki irin Dan Ba'are shi yasan Meye Mohan yake so, shi yasan Meye baya so, gashi Allah yayi mishi farin jinin Yan mata, shi kuma baya da lokacin su. Sau dayawa Yan mata har kawo kansu suke gurin shi, amma haka bai tab'a burge shi ba, gashi da mugun miskilanci kamar wani Balarabe, ga wani baiwa da Allah yayi mishi na kwarjini, duk lokacin da zai tsaya a gaban ka baka iya koda motsi. Sannan duk da haka baya cin abincin kowa sai na Dadda kakar shi na gurin Uba. Itace kawai yake cin abincin ta. Sai na Chef Hurayyah, wata yar Kasar Libya da ya dauko ta domin cika mishi cikin shi da abincinta. Domin ta iya girki sosai, balle shi da mahaifiyar shi ta girma cikin Larabawa. Babban matsalar Mohan yana da damuwa amma baya iya gayawa kowa sai Dan Ba'are, TOH shima basu cika zama guri daya na, dan haka yakan zauna yayi ta rubutun shi. Kafin faruwan Al'amarin da ya same shi, akan ganshi yana yawan zama shi daya ko kuma yayi ta yawo a gonar shi da yake cikin gidan shi, baya cika magana dama kuma halin shine. Wani lokaci kuma zai fito afujajjan ko wanka yake zai fito yana zare idanun shi, mutum me yawan ibada da tsare hakkin Allah sai gashi an wayi gari baya Kaunar jin kiran Sallah, karshe sai dai ya koma daki ya kwanta, ko kuma a sayo mishi wani abun da zai saka shi barci. Ranar da ya zama mafi muni a gare shi.... Biki ake tsakanin fadar shugaban kasa zuwa inda ake bikin, ko ina ka leka an cika makil, haka aka gama wannan bikin me cike da farin ciki. Kallon shi dan Ba'are yayi sannan yace mishi. "Muje na kai ka gida" shiru yayi kamar me tunani. Can ya kalli Khalil Ibrahim Dan Ba'are. "Kace me?" Ya fada cikin rashin kuzari, "Muje na kai ka gida" kurawa Dan Ba'are ido yayi, na wani lokaci kafin ya jinjina kanshi. "Muje" ya kuma nuna mishi hanya, haka ya shiga cikin motar, a sanyayye. Koda ya shiga motar kallon waje yake,.kamar akwai abin da ya manta. Haka kawai ya fara jin kamar ana harbe harbe,. Duk da ya san karan bindiga haka bai hana shi firgita ba, har yana faɗin. "Taka motar zasu harbe Ni" Ya fada da karfi, abin mamaki shi dai Khalil bai ga kowa ba, haka ya tadda motar babu shiri suka bar gurin sai rike kanshi da kunnen shi yake, har suka isa gida. Aikuwa a lokacin ne yayi karamin hauka, yayi ta fasa duk abinda ya kai hannun shi, haukacewa yayi sosai, koda aka kira likita, daukar shi aka yi zuwa asibiti, da farko yana gane kome yana magana, har yana faɗin zasu nan da bindiga ku bani bindiga na, na harbe su. Haka za ayi ta danneshi ana mishi allura. Tun daga lokacin ya daina himm balle humm, baya magana kuma baya fahimtar me kake fada, duk abinda zaka yi sai kayi babu wanda zai ce maka ga abinda yake so. A hankali iyayen shi suka manta dashi, domin yana cika sati biyu zuwa uku, suka ajiye batun shi. Suka saka duniya a gaban su. Hatta yan uwan shi babu wanda ya iya tunawa da shi. Sai dan Ba'are, shima dole ya barshi sabida aikin da yake fama dashi. Dan haka baya nan kawai sai jin labarin yayi a gurin Hajiya Safiya ta gaya mishi ai an maida Mohan Maradi, shima dalilin da ya sani sabida ya shiga cikin gidan nan ya nufi shashin Mohan, aka ce mai baya nan,. Koda ya nufi gurin Firaminista yace ya fita baya son jin sunan Mohan, itama haka Hajiya Latifah, dole ya nufi Hajiya Safiya ita ta gaya mishi ai Mohan an maida shi can, dan haka akan lokaci ya iso Maradi. Yaga kofar gidan babu masu kula da lafiyar shi, babu kowa sai yan sanda biyu da sojoji biyu, yana zuwa ya ga yadda gidan yake dama Mohan ya sha bashi labarin irin dukiyar da aka zuba a gidan bai tab'a zuwa ba, dan haka yana ganin yadda gidan yake kawai ya shigar da wani bayanai sai ga shi an rundunar sojojin sama da na kasa, da sauran jami'an tsaron,.masu kula da lafiyar shi. Haka ba ƙaramin samawa Dan Ba'are nutsuwa yayi ba, dan haka Yasaka aka dauko Hurayyah, da wasu ma'aikata da zasu kula da lafiyar Mohan. Wannan kenan.... A hankali yake tafiya ya jika jikinshi Jagwaf, a hankali yake rab'e rab'e, duk inda ya wuce sara mishi suke, haka ya shigo cikin falon tare da sake murmushin jin dadi, duk ma'aikatan gidan suka fito suna kallon shi, sunkuyar da kai yayi tare da haurawa sama da gudu kamar zai tashi sama, cikin tsannanin takaici da bakin ciki Hurayyah ta fashe da kuka, kasancewar tunda ta fara mishi aiki basu tab'a samun sab'ani ba, idan suka mishi laifi baya kula takan su, asalima sai ya daina shiga harkan su, kuma basu isa su daina girki ko kula da shsshin sa ba, abu daya yake musu idan suka mishi laifi, shine kara musu kwanaki a saman wanda suke misali idan yana biyan su duk bayan sati hudu ne, zai mai dashi sati biyar, kafin ya basu albashin su, daga baya ya bari sakamakon wani me mishi wanki da ya rasa Kanwar shi sabida bai biya shi akan lokaci ba, dan yayi mishi laifi. Tun daga ranar idan suka mishi laifi sai ya zuba musu na mujiya. Zama tayi ya ci kuka sosai kafin ta kira Bilal, suka haura zama. Sai da suka dauki hodar da Hajiya Safiya ta bada ana saka mishi, sabida idan ya tirje, idan zasu saka mishi kaya dambe ake dashi kamar za a tashi sama, amma idan ya kama mutum sai ya sumar da kai yake kyale ka, haka ba karamin tashin hankali bane. Shi yasa suna shiga suke hura mishi iskar hodan. Haka ce ta faru, suna shiga dakyar sha a hannun su, bayan ya musu dukar kawo wuka,sannan suka watsa mishi hodar ya fara barci, ita ta fita Bilal ya saka mishi kaya, sannan ya gyara mishi kwanciyar shi. Suna fitowa dan Ba'are yana shigowa gidan. "Barka da zuwa Yallabai" "Yawwa ina Friend yake?" Ya tambaye su, "Yana sama, barci yake." Kallon agogon falon yayi sannan yace musu. "Akan me zaku saka shi barci a irin wannan lokacin? Ko kunsan cewa bayi da lafiya kara mishi wani cutar zaku yi?" "Kayi hakuri" "Akan me zanyi hakuri? Jiya ma haka nazo ban ganshi ba, yau ma haka nazo har na tafi ban samu ganin shi ido biyu ba, me yasa kike saka shi barci?" "Sir" D'aga musu hannun yayi sannan ya wuce abinshi,ranshi yana barci dakin shi ya shiga tare da zama a kusa dashi, yana kallon kamilalliyar fuskar shi me dauke da kwarjini, rike hannun shi yayi. "Friend!" Ya kira sunan a hankali. "Kana cikin wani irin yanayi, ga Abbinka ce makiya sun sako mishi fitina a gaba" kamar wanda aka tashe shi ya bude idanun shi, kafin ya mai dashi ya rufe. "Friend ka tashi haka, Mahaifinka yana bukatar ka, duk da bai san kome akanka ba amma yana bukatar ka a kusa dashi" ya faɗa kamar ya zubda kwalla, Shafa kanshi yayi yaga yadda ya tara gashi yasan shi ba mutum ne da yake son zama babu gashi ba, dan haka ya shiga cikin ban dakin shi ya fara. Diban shaving cream, yazo ya shafa mishi sannan ya koma gefe ya duba jikin shi zuwa maran shi yasan da hankalin Mohan baka isa ganin dan kamfen shi ba, balle kuma jikin shi da yake riritawa. Haka ya aske a shi tass, sannan ya gyara mishi kwanciyar shi. Kana yayi shi sai da safe. Koda ya sauko damuwa ya shiga saura kwanaki ƙalilan ya koma gurin aikin shi, dan ma sanadin rashin lafiyar yasa an dakatar da Mohan har ranar da zai sami lafiya. Shafa kanshi yayi yana nazarin abinda ya dace yayi akan Mohan yana son niman Mutum me gaskiya da Amana ya bashi kula da Harkokin lafiyar shi amma gani yake kamar babu wanda ya dace da kula da Mohan sai shi. Toh a ina ya dace a fara nima mishi wanda ya dace. Dan haka a cikin kwanakin da suka rage zai maida hankali sosai gurin niman wanda zai kula da lafiyar shi. Da wannan tunanin ya bar gidan. *** Washi gari. Da sassafe Almamoon ya bar gidan, ko karyawa bai yi ba. Abinda ya d'aga mishi hankali, mahaifan shi da yake mafarki dasu, haka ya mugun d'aga mishi hankali, shi yasa yaji gwara ya tafi yasan halin da suke ciki. Tun a hanya yake kuka haka kawai yana jin wani irin yanayi mara daɗi. Har suka isa garin Damagaram. Daga tasha ya sami abin hawa zuwa gida. Haka kawai jikin shi ke kara sakewa, har ya shiga cikin gidan. Ya hango Innar shi tana sura hatsi. "Assalamu alaikum" Sake tabaryan tayi tana me dafe kirjinta. "Almamoon?" Ya tambaye shi tare da kura mishi ido. A hankali ya taka jikin shi yana wani irin rawa. "Innah!" Ya kira sunan a hankali, "Na'am Almamoon" Ya isa gaban ta tare da fashewa da kuka. "Ya aka yi?" Cikin kuka ta fara magana, "Ina Abba? Me yasa ya haife ni tunda yana son duniya tasan Ni? Na gaji sai zagi na ake ana aibanta ni?" Daga bayan shi yaji gyaran muryan Baba daga daki. "Baba na" ta juya tana me zare idanu, sakamakon kallon yadda wuta yayi mishi illar, amsa sallamar da yayi ya dakyar, zaman yan bori Almamoon yayi tare da sake wani irin kuka. "Innalillahi wa'inna ilahirajoun,.dama abinda ya faru da kai kenan, wayyo Allah babana" ya rarrafa da sauri kamar zai kifa akan shi. Sai kuma ya zauna, tare da hade hannun shi,.mik'ewa yayi tare da bude jakar ya shiga zazzage kayan ciki..ya ciro kudin da yake samu a gurin malam Ansar ya juya zai fita. "Zo nan" dawowa yayi da baya, ya zauna tare da kallon shi. "Meye zaka yi?" "Baba magani zan sayo maka" "Barshi ka bawa Innarka kudin a kara mana a cikin abincin da zamu ci ko?" Gyada kai yayi tare da sake wani irin kuka, d'aga labulen dakin yayi sannan yace mishi. "Baba kana son wani abu ne?" Ya tambaya hawaye na zuba mishi, sake kallon baban nashi yayi sannan yace mishi. "Ko kana jin zafi ne?" Murmushi yayi sannan yace mishi. "Almamoon! Bana jin zafin kome sama da hawayen ka, ka daina kuka bana son ganin kukan ka" Gyada kai yayi tare da rike rigar shi. Ya wani ja hancin shi, tare Sake shashekar kuka, muryan shi a raunane yace. "Baba zan fita niman aikin yi ne" Yadda yake maganar zai d'ago maka da sallar yarinta shi, yana yi yana wani murɗa yatsun hannun shi. Lips din shi sai wani irin rawa yaƙe. Yana kallon Abban shi. Murmushi yayi sannan yace mishi. "Karka damu, Allah yana sane damu." "A'a ko Allah yace a fita a nima don Allah ka barni na fita Insha Allah." "Kana hauka ne? A kananun shekarunka zaka fita wahala, ai rayuwar mu dan kayi farin ciki muke, bawai dan kayi wahala ba, babu inda zaka" Kallon su yayi tare da sake baki. "Toh ni me yasa baku barina nayi rayuwa irin na kowa ne? Me yasa kuka tsani nace zan fita ne?" Ya fada yana ihu, sabida takaici. Baki daya suka taru mishi, tare da rike hannun shi. "A'a Almamoon! Karka mana haka, tsoro muke ji kai yaro ne, tsoro muke ji kar wani ya cutar da kai? Ka" "A'a wannan ba hujja bane, kawai ku bari na koma aikin baba Insha Allah babu abinda zai faru" ya faɗa yana share kwalla, "Don Allah" ya kuma fada a karo na biyu, haka ya cigaba da rokon su yana kuka,rike hannun shi suka yi tare da cewa. "Zaka koma makaranta dan shine" "Insha Allah zan kama kai na, amma don Allah ku barni na tafi aikin kun ji" "Shi kenan" suka fada tare da kallon shi, basu so amma saboda kaunar da suke mishi yasa suka amince, rike hannun shi suka yi sannan suka ce mishi. "Don Allah karka bari wani rudin duniya ya rufe maka ido, ka tuna da mu,.muna raye ne sabida kai. Don Allah ka yi abinda ya kai ka" Gyada kai yayi sannan malam Ya gaya mishi inda zai tafi, a dace. Cikin farin ciki ya tafi kasuwa da wata ƙatuwar rigar shi irinta Bugaje, sai uban rawanin da ya buga. Da takalmin roban shi, yayi mugun kyau, yana zuwa inda baban shi yake zama yayi musu bayanin waye shi. Kai shi ruwan chairman aka yi, yayi mishi bayani. Murmushi chairman din yayi sannan ta saka aka mai da shi kan aikin baban shi, Haka wunin ranar yaki zama a bakin kofar kasuwa, dako ya shiga fafa, duk da bai saba ba amma duk inda ka ganshi yana mugun gajiya, dakyar yake ɗaukar kayan, bai bar kasuwa ba sai dab Magarib ya dawo gida ya basu duk kudin da ya samo, yaci abinci yayi wanka ya sauya kayan jikin shi da tsumar jikin shi, sannan ya kuma komawa kasuwar bayan yayi musu sai da safe. Kirga kudin suka yi CF dubu biyu, kamar su zuba ruwa a kasa. "Dakon yayi mishi nauyi halittar shi ba irinta maza bane idan ya cigaba da irin wannan abun." Kura mishi ido tayi sannan tace mishi. "Wani abu zai faru dashi ko? Ban taba jin haka a raina ba, kamar yadda yake rayuwa cikin maza" ta fada tana share kwalla, "Addu'a zamu mishi Allah ya kare shi." ... A kasuwa kuwa cikin dare aka kawo kaya, haka ta tashi yayiwa abokin aikin baban shi bayanin zai tafi aiki, bai hana shi ba. Haka ya nufi kasuwar ya........ Kuyi maneji, wallahi na saka shiririta ne a gabana wallahi 😜🤣 Yawwa masu tambaye account ɗina zasu sayi Aliyu Asadullah gashi nan, 0472282105 Ramlat Abdul Rahman Manga GTBNK... #Comments!Share!Vote... #Mai_Dambu, *🐂🐂BOROROJI🫀🫀* ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE https://www.instagram.com/batool_spices Fatima Batool enterprise Yaji Ginger and garlic Onion powder Pepper soup Curry Biryani spices Mixed spices Indian spices Arab spices Chai masala Baharat blend Tandoori blend Thai masala Garam masala Provence Tea spice Zobo powder Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋 Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris Wani Al'amari... BABI NA TARA. Muhammad Mamman Muhammad Nasir Aghali. Shine asalin cikakken sunan shi, kasancewar sunan shi sunan babans shi da Kakan shi na Uba, yasa aka mishi lakani da Mohan. Duk inda kake niman mutum me tsaye akan ra'ayin shi Mohan ya kai gurin, yana da dadin mu'amala. Ga son mutane da yawan Alkhairi, sai dai mutum ne da bai da fara'a sosai , wani hali da mohan yake dashi wanda ba kowa yake iya zama dashi ba wato murɗaɗɗan hali, duk wanda zai zauna da shi sai tayi mugun hakuri dashi, kafin wannan lamari babu me iya gane abinda yake so sai Abokin shi daya tal a duniya wato. Captain Khalil Ibrahim Dan Ba'are, kaf duniya bai da Amini sama da dan Ba'are, bai da abokin arziki irin Dan Ba'are shi yasan Meye Mohan yake so, shi yasan Meye baya so, gashi Allah yayi mishi farin jinin Yan mata, shi kuma baya da lokacin su. Sau dayawa Yan mata har kawo kansu suke gurin shi, amma haka bai tab'a burge shi ba, gashi da mugun miskilanci kamar wani Balarabe, ga wani baiwa da Allah yayi mishi na kwarjini, duk lokacin da zai tsaya a gaban ka baka iya koda motsi. Sannan duk da haka baya cin abincin kowa sai na Dadda kakar shi na gurin Uba. Itace kawai yake cin abincin ta. Sai na Chef Hurayyah, wata yar Kasar Libya da ya dauko ta domin cika mishi cikin shi da abincinta. Domin ta iya girki sosai, balle shi da mahaifiyar shi ta girma cikin Larabawa. Babban matsalar Mohan yana da damuwa amma baya iya gayawa kowa sai Dan Ba'are, TOH shima basu cika zama guri daya na, dan haka yakan zauna yayi ta rubutun shi. Kafin faruwan Al'amarin da ya same shi, akan ganshi yana yawan zama shi daya ko kuma yayi ta yawo a gonar shi da yake cikin gidan shi, baya cika magana dama kuma halin shine. Wani lokaci kuma zai fito afujajjan ko wanka yake zai fito yana zare idanun shi, mutum me yawan ibada da tsare hakkin Allah sai gashi an wayi gari baya Kaunar jin kiran Sallah, karshe sai dai ya koma daki ya kwanta, ko kuma a sayo mishi wani abun da zai saka shi barci. Ranar da ya zama mafi muni a gare shi.... Biki ake tsakanin fadar shugaban kasa zuwa inda ake bikin, ko ina ka leka an cika makil, haka aka gama wannan bikin me cike da farin ciki. Kallon shi dan Ba'are yayi sannan yace mishi. "Muje na kai ka gida" shiru yayi kamar me tunani. Can ya kalli Khalil Ibrahim Dan Ba'are. "Kace me?" Ya fada cikin rashin kuzari, "Muje na kai ka gida" kurawa Dan Ba'are ido yayi, na wani lokaci kafin ya jinjina kanshi. "Muje" ya kuma nuna mishi hanya, haka ya shiga cikin motar, a sanyayye. Koda ya shiga motar kallon waje yake,.kamar akwai abin da ya manta. Haka kawai ya fara jin kamar ana harbe harbe,. Duk da ya san karan bindiga haka bai hana shi firgita ba, har yana faɗin. "Taka motar zasu harbe Ni" Ya fada da karfi, abin mamaki shi dai Khalil bai ga kowa ba, haka ya tadda motar babu shiri suka bar gurin sai rike kanshi da kunnen shi yake, har suka isa gida. Aikuwa a lokacin ne yayi karamin hauka, yayi ta fasa duk abinda ya kai hannun shi, haukacewa yayi sosai, koda aka kira likita, daukar shi aka yi zuwa asibiti, da farko yana gane kome yana magana, har yana faɗin zasu nan da bindiga ku bani bindiga na, na harbe su. Haka za ayi ta danneshi ana mishi allura. Tun daga lokacin ya daina himm balle humm, baya magana kuma baya fahimtar me kake fada, duk abinda zaka yi sai kayi babu wanda zai ce maka ga abinda yake so. A hankali iyayen shi suka manta dashi, domin yana cika sati biyu zuwa uku, suka ajiye batun shi. Suka saka duniya a gaban su. Hatta yan uwan shi babu wanda ya iya tunawa da shi. Sai dan Ba'are, shima dole ya barshi sabida aikin da yake fama dashi. Dan haka baya nan kawai sai jin labarin yayi a gurin Hajiya Safiya ta gaya mishi ai an maida Mohan Maradi, shima dalilin da ya sani sabida ya shiga cikin gidan nan ya nufi shashin Mohan, aka ce mai baya nan,. Koda ya nufi gurin Firaminista yace ya fita baya son jin sunan Mohan, itama haka Hajiya Latifah, dole ya nufi Hajiya Safiya ita ta gaya mishi ai Mohan an maida shi can, dan haka akan lokaci ya iso Maradi. Yaga kofar gidan babu masu kula da lafiyar shi, babu kowa sai yan sanda biyu da sojoji biyu, yana zuwa ya ga yadda gidan yake dama Mohan ya sha bashi labarin irin dukiyar da aka zuba a gidan bai tab'a zuwa ba, dan haka yana ganin yadda gidan yake kawai ya shigar da wani bayanai sai ga shi an rundunar sojojin sama da na kasa, da sauran jami'an tsaron,.masu kula da lafiyar shi. Haka ba ƙaramin samawa Dan Ba'are nutsuwa yayi ba, dan haka Yasaka aka dauko Hurayyah, da wasu ma'aikata da zasu kula da lafiyar Mohan. Wannan kenan.... A hankali yake tafiya ya jika jikinshi Jagwaf, a hankali yake rab'e rab'e, duk inda ya wuce sara mishi suke, haka ya shigo cikin falon tare da sake murmushin jin dadi, duk ma'aikatan gidan suka fito suna kallon shi, sunkuyar da kai yayi tare da haurawa sama da gudu kamar zai tashi sama, cikin tsannanin takaici da bakin ciki Hurayyah ta fashe da kuka, kasancewar tunda ta fara mishi aiki basu tab'a samun sab'ani ba, idan suka mishi laifi baya kula takan su, asalima sai ya daina shiga harkan su, kuma basu isa su daina girki ko kula da shsshin sa ba, abu daya yake musu idan suka mishi laifi, shine kara musu kwanaki a saman wanda suke misali idan yana biyan su duk bayan sati hudu ne, zai mai dashi sati biyar, kafin ya basu albashin su, daga baya ya bari sakamakon wani me mishi wanki da ya rasa Kanwar shi sabida bai biya shi akan lokaci ba, dan yayi mishi laifi. Tun daga ranar idan suka mishi laifi sai ya zuba musu na mujiya. Zama tayi ya ci kuka sosai kafin ta kira Bilal, suka haura zama. Sai da suka dauki hodar da Hajiya Safiya ta bada ana saka mishi, sabida idan ya tirje, idan zasu saka mishi kaya dambe ake dashi kamar za a tashi sama, amma idan ya kama mutum sai ya sumar da kai yake kyale ka, haka ba karamin tashin hankali bane. Shi yasa suna shiga suke hura mishi iskar hodan. Haka ce ta faru, suna shiga dakyar sha a hannun su, bayan ya musu dukar kawo wuka,sannan suka watsa mishi hodar ya fara barci, ita ta fita Bilal ya saka mishi kaya, sannan ya gyara mishi kwanciyar shi. Suna fitowa dan Ba'are yana shigowa gidan. "Barka da zuwa Yallabai" "Yawwa ina Friend yake?" Ya tambaye su, "Yana sama, barci yake." Kallon agogon falon yayi sannan yace musu. "Akan me zaku saka shi barci a irin wannan lokacin? Ko kunsan cewa bayi da lafiya kara mishi wani cutar zaku yi?" "Kayi hakuri" "Akan me zanyi hakuri? Jiya ma haka nazo ban ganshi ba, yau ma haka nazo har na tafi ban samu ganin shi ido biyu ba, me yasa kike saka shi barci?" "Sir" D'aga musu hannun yayi sannan ya wuce abinshi,ranshi yana barci dakin shi ya shiga tare da zama a kusa dashi, yana kallon kamilalliyar fuskar shi me dauke da kwarjini, rike hannun shi yayi. "Friend!" Ya kira sunan a hankali. "Kana cikin wani irin yanayi, ga Abbinka ce makiya sun sako mishi fitina a gaba" kamar wanda aka tashe shi ya bude idanun shi, kafin ya mai dashi ya rufe. "Friend ka tashi haka, Mahaifinka yana bukatar ka, duk da bai san kome akanka ba amma yana bukatar ka a kusa dashi" ya faɗa kamar ya zubda kwalla, Shafa kanshi yayi yaga yadda ya tara gashi yasan shi ba mutum ne da yake son zama babu gashi ba, dan haka ya shiga cikin ban dakin shi ya fara. Diban shaving cream, yazo ya shafa mishi sannan ya koma gefe ya duba jikin shi zuwa maran shi yasan da hankalin Mohan baka isa ganin dan kamfen shi ba, balle kuma jikin shi da yake riritawa. Haka ya aske a shi tass, sannan ya gyara mishi kwanciyar shi. Kana yayi shi sai da safe. Koda ya sauko damuwa ya shiga saura kwanaki ƙalilan ya koma gurin aikin shi, dan ma sanadin rashin lafiyar yasa an dakatar da Mohan har ranar da zai sami lafiya. Shafa kanshi yayi yana nazarin abinda ya dace yayi akan Mohan yana son niman Mutum me gaskiya da Amana ya bashi kula da Harkokin lafiyar shi amma gani yake kamar babu wanda ya dace da kula da Mohan sai shi. Toh a ina ya dace a fara nima mishi wanda ya dace. Dan haka a cikin kwanakin da suka rage zai maida hankali sosai gurin niman wanda zai kula da lafiyar shi. Da wannan tunanin ya bar gidan. *** Washi gari. Da sassafe Almamoon ya bar gidan, ko karyawa bai yi ba. Abinda ya d'aga mishi hankali, mahaifan shi da yake mafarki dasu, haka ya mugun d'aga mishi hankali, shi yasa yaji gwara ya tafi yasan halin da suke ciki. Tun a hanya yake kuka haka kawai yana jin wani irin yanayi mara daɗi. Har suka isa garin Damagaram. Daga tasha ya sami abin hawa zuwa gida. Haka kawai jikin shi ke kara sakewa, har ya shiga cikin gidan. Ya hango Innar shi tana sura hatsi. "Assalamu alaikum" Sake tabaryan tayi tana me dafe kirjinta. "Almamoon?" Ya tambaye shi tare da kura mishi ido. A hankali ya taka jikin shi yana wani irin rawa. "Innah!" Ya kira sunan a hankali, "Na'am Almamoon" Ya isa gaban ta tare da fashewa da kuka. "Ya aka yi?" Cikin kuka ta fara magana, "Ina Abba? Me yasa ya haife ni tunda yana son duniya tasan Ni? Na gaji sai zagi na ake ana aibanta ni?" Daga bayan shi yaji gyaran muryan Baba daga daki. "Baba na" ta juya tana me zare idanu, sakamakon kallon yadda wuta yayi mishi illar, amsa sallamar da yayi ya dakyar, zaman yan bori Almamoon yayi tare da sake wani irin kuka. "Innalillahi wa'inna ilahirajoun,.dama abinda ya faru da kai kenan, wayyo Allah babana" ya rarrafa da sauri kamar zai kifa akan shi. Sai kuma ya zauna, tare da hade hannun shi,.mik'ewa yayi tare da bude jakar ya shiga zazzage kayan ciki..ya ciro kudin da yake samu a gurin malam Ansar ya juya zai fita. "Zo nan" dawowa yayi da baya, ya zauna tare da kallon shi. "Meye zaka yi?" "Baba magani zan sayo maka" "Barshi ka bawa Innarka kudin a kara mana a cikin abincin da zamu ci ko?" Gyada kai yayi tare da sake wani irin kuka, d'aga labulen dakin yayi sannan yace mishi. "Baba kana son wani abu ne?" Ya tambaya hawaye na zuba mishi, sake kallon baban nashi yayi sannan yace mishi. "Ko kana jin zafi ne?" Murmushi yayi sannan yace mishi. "Almamoon! Bana jin zafin kome sama da hawayen ka, ka daina kuka bana son ganin kukan ka" Gyada kai yayi tare da rike rigar shi. Ya wani ja hancin shi, tare Sake shashekar kuka, muryan shi a raunane yace. "Baba zan fita niman aikin yi ne" Yadda yake maganar zai d'ago maka da sallar yarinta shi, yana yi yana wani murɗa yatsun hannun shi. Lips din shi sai wani irin rawa yaƙe. Yana kallon Abban shi. Murmushi yayi sannan yace mishi. "Karka damu, Allah yana sane damu." "A'a ko Allah yace a fita a nima don Allah ka barni na fita Insha Allah." "Kana hauka ne? A kananun shekarunka zaka fita wahala, ai rayuwar mu dan kayi farin ciki muke, bawai dan kayi wahala ba, babu inda zaka" Kallon su yayi tare da sake baki. "Toh ni me yasa baku barina nayi rayuwa irin na kowa ne? Me yasa kuka tsani nace zan fita ne?" Ya fada yana ihu, sabida takaici. Baki daya suka taru mishi, tare da rike hannun shi. "A'a Almamoon! Karka mana haka, tsoro muke ji kai yaro ne, tsoro muke ji kar wani ya cutar da kai? Ka" "A'a wannan ba hujja bane, kawai ku bari na koma aikin baba Insha Allah babu abinda zai faru" ya faɗa yana share kwalla, "Don Allah" ya kuma fada a karo na biyu, haka ya cigaba da rokon su yana kuka,rike hannun shi suka yi tare da cewa. "Zaka koma makaranta dan shine" "Insha Allah zan kama kai na, amma don Allah ku barni na tafi aikin kun ji" "Shi kenan" suka fada tare da kallon shi, basu so amma saboda kaunar da suke mishi yasa suka amince, rike hannun shi suka yi sannan suka ce mishi. "Don Allah karka bari wani rudin duniya ya rufe maka ido, ka tuna da mu,.muna raye ne sabida kai. Don Allah ka yi abinda ya kai ka" Gyada kai yayi sannan malam Ya gaya mishi inda zai tafi, a dace. Cikin farin ciki ya tafi kasuwa da wata ƙatuwar rigar shi irinta Bugaje, sai uban rawanin da ya buga. Da takalmin roban shi, yayi mugun kyau, yana zuwa inda baban shi yake zama yayi musu bayanin waye shi. Kai shi ruwan chairman aka yi, yayi mishi bayani. Murmushi chairman din yayi sannan ta saka aka mai da shi kan aikin baban shi, Haka wunin ranar yaki zama a bakin kofar kasuwa, dako ya shiga fafa, duk da bai saba ba amma duk inda ka ganshi yana mugun gajiya, dakyar yake ɗaukar kayan, bai bar kasuwa ba sai dab Magarib ya dawo gida ya basu duk kudin da ya samo, yaci abinci yayi wanka ya sauya kayan jikin shi da tsumar jikin shi, sannan ya kuma komawa kasuwar bayan yayi musu sai da safe. Kirga kudin suka yi CF dubu biyu, kamar su zuba ruwa a kasa. "Dakon yayi mishi nauyi halittar shi ba irinta maza bane idan ya cigaba da irin wannan abun." Kura mishi ido tayi sannan tace mishi. "Wani abu zai faru dashi ko? Ban taba jin haka a raina ba, kamar yadda yake rayuwa cikin maza" ta fada tana share kwalla, "Addu'a zamu mishi Allah ya kare shi." ... A kasuwa kuwa cikin dare aka kawo kaya, haka ta tashi yayiwa abokin aikin baban shi bayanin zai tafi aiki, bai hana shi ba. Haka ya nufi kasuwar ya........ Kuyi maneji, wallahi na saka shiririta ne a gabana wallahi 😜🤣 Yawwa masu tambaye account ɗina zasu sayi Aliyu Asadullah gashi nan, 0472282105 Ramlat Abdul Rahman Manga GTBNK... #Comments!Share!Vote... #Mai_Dambu, [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀* ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE https://www.instagram.com/batool_spices Fatima Batool enterprise Yaji Ginger and garlic Onion powder Pepper soup Curry Biryani spices Mixed spices Indian spices Arab spices Chai masala Baharat blend Tandoori blend Thai masala Garam masala Provence Tea spice Zobo powder Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋 Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris _Gaisuwa gare ku Masoyan MLM ANSAR! Da Masoyan Mata Maza, Koda yake naga mutum daya tana yin Wancan me tambotsan 😜🤸_ Zafin Nima... BABI NA GOMA Fita yayi ya nufi gurin su, tare da gaya niman shugaban yan dakon. "Don Allah kasan mahaifina ya kone, ko zaka taimaka min na shiga cikin mutanen ka, don Allah don Allah" ya shiga rokon shi tare da jin kamar kwalla zai zuba Mishi. "Yanzun kai saurayi! Toh shi kenan, Haliru ga dan gidan Malam Sanda nan a yi aikin dashi" " Toh shugaba, kai saurayi zo nan" Da sauri ya nufi gurin su, ya tsaya aka ciro buhun alkama suna tambayar shi. "Zaka iya kuwa?" "Insha Allah" Daukar bugun suka yi tare da daura mishi a kafad'ar shi, sai da yaji kamar zai fadi, amma da ya tuna dusa yaga Innar shi take sakawa da sauri ya cira, cikin mugun yanayi da rashin sabo, ya nufi hanyar inda zai ajiye, abinka da kuruciya, sam baya tuna kowa sai Iyayen shi, haka suka yi ta kwasar kayan, har asuba tayi, dake bai da tsarki, tattarawa yayi ya nufi gida, bayan an bashi kudin shi da suka ga yadda yayi aikin ma kara mishi kudi suka yi tare da mishi fatan sauki na Babansa. Yana isa gida ya zube a gaban Baban shi yana sauke ajiyar zuciya. "Almamoon! Meye ya faru?" Suka tambaye shi a tsora ce. Cikin sansanyar murya yace. "Dako" sannan ya ciro kudin ya mika musu. "Inna Kafadana da wuyana ciwo" ya fada a sanyayye. "Maza daura ruwan zafi akan wuta, a gasa mishi jiki" inji Baban shi. "A'a Inna zauna kawai" ya kuma mikawa dakyar ya nufi wajen, ya haɗa wuta, sannan ya daura ruwan zafi, yana zaune sai gyangyadi yaƙe. Har Innar shi ta juye mishi ruwan ta dawo tace mishi. "Tashi dan arziki irin albarka dan da aka haifa tsiya tana barci ba ta farka ba balle ta rab'e shi" "Inna muje ki gasa min jiki don Allah" ya faɗa tare da marairece fuska. "Toh muje" Mikewa yayi ya shiga dakin shi ta cire kayan shi, ya dauki jallabiyar shi ya saka, sannan ya nufi ban dakin, ya cire rigar shi tare da zama ya juya bayan shi. "Innah ki shigo" ya faɗa a gajiye, tana shiga ta kalle shi, cikin tausayawa. Hannunta ta kai kanshi ta shafa gamon da ya tufke gashin kanshi a keyar shi, ita kanta gashin sai da Innar ta warware shi. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin halittar farko da karshe, Allahu Akbar. Shi kansa gashin baki ne wuluk, har kasa domin idan ka ce zaka kimanta zai yi wuya. "Innah don Allah ki saka almakashi ki yanke gashin nan damuna yake," "Kul na kuma jin haka daga bakin ka" shiru yayi yana kallon yadda take wanke gashin kafin ga dauki tsuma ta shiga gasa mishi kafad'ar shi, sai lumshe idanu yake. " Innah" "Idan ana ban daki ba a magana" shiru yayi, har ta gama gasa mishi jiki, shima yayi wankan tsarki, sannan ya dauki zanin sa ta kawo mishi ya nad'e gashin. Kafin ya wanke tsumar jinin shi. Ya fito tare da kaiwa dakin shi ya shanya. Sannan ya gabatar da sallah asuba da ya tsare mishi, kafin ya kwanta a gurin, sai barci. Wunin ranar a gajiye yayi shi, shi yasa bai farka na sai uku saura ya tashi yayi alola a gurguje yayi Sallah azhar, yana addu'o'in ya fita gurin iyayen shi ya zauna. "Sannun ku." Ya fada me jan kwanon abincin, ya fara ci a hankali. Yana gamawa ya tattara kayan kaf ya fita ya wanke su, sannan ya koma dakin shi yayi Sallah la'asar, kwanciya yayi dan har yanzun bai warware ba. Dakyar ya ke takawa, sabida ciwon jikin shi. Karfe biyar ya fara shirin zuwa kasuwa, kowa yaje bai zauna ba, haka ya shiga niman aikin yi dakyar ya samu wani kwashe kwata,. Lokacin da ya isa bakin kwatar, kallon gurin yayi kawai ya fara jin amai, babu shiri ya matsa tare da nufar gefe ya zubda yawu, sannan ya nutsu yana tuna hiran da yaji su Innah suna yi. "Malam maganin ya kare kuma babu kudin saya, wannan kudin na makarantar shi da." "Adana mishi, karki tab'a Allah zai kawo yadda zamu yi" Kwalla ne ya zubo mishi, sannan ya shiga ramin bayan ya saka takalmin aiki, ya fara kwashe kwatar, cikin juriya yake aikin har ya gama, sannan ya fita ya wanke jikin shi suka dauki CD dubu biyar suka miki mishi. Saboda sun nime mutane dayawa sai su yanka musu kudi shi kuma cewa yayi aba shi duk abinda ya samu. Kamar ya kwanta a.kasa dan murna dauki kudin ya saka a can cikin wandon shi sannan ya koma inda suke zaune, kasancewar a bakin kofar kasuwa ne a nan yayi Sallah bai bi masalaci ba, yana idarwa yace me shayin da yake Baban Salihu Bukar. "Baba Ina son na je na sayo maganin Babana, don Allah idan malam yazo ka gaya mishi." "Toh babu kome" ya faɗa bayan ya amshi bayanin shi. A gurguje ya nufi gida, ya shiga da sauri yace. "Innah bani kwalin Maganin Baba" "A ina" "Inna babu lokaci bani don Allah" ya faɗa mata a wujilance, dole ta bashi tare da kallon shi, ya fita bayan kamar minti goma sha biyar ya dawo, sannan ya dauki abincin shi na dare ya tafi, duba Maganin yayi sannan yace mata. "Yaron nan da iyayen shi sun tallafi al'amuran shi tabbas sai sun fi kowa moran shi, ina tsoron ranar da zai fahimci ainihin waye shi? Ina jin shakkar tambayar da zai mana, ban san amsar da zan bashi ba" "Allah ya rufa asiri" inji Innah. *** Maradi. Kurawa wasikar idanu yayi sannan yace mata. "Baba Almamoon mata maza ce" "Bana tunanin haka, idan har mace ce abubuwa dayawa zasu bayyana mata, kama da cikar halittar jikin ta, sauyawar ta na girma ko na wani iri. Eh kuma na fahimci wani abu mata maza ce shi yasa jikinta bai nuna alamar mace ce ba sai dai jinin da take." Kallonta yayi na wani lokaci kafin dafe goshinsa, idan yace baya kewar Almamoon yayi karya, bai san lokacin da son Yaron ya kama shi ba, amma tabbas zai iya kome dan samun damar rayuwar shi, Mik'ewa yayi tare da fita daga gidan yana faɗin. "Baba zan fita" Ya ce mata, "Allah ya dawo da kai lafiya" Koda ya fita makarantar ya nufa, gidan kwanan dalibai ya nufa tare da niman wani abokin karatun. Kallon shi yayi bayan ya fito yace.. "Malam gani" shiru yayi kamar mai tunani, kafin ya juya ya kalli Yaron. "Tambayar ka zanyi" ya faɗa haka yana kallon yaron, kamar yayi shiru. Sai kuma is very important, yasan halin da Yaron yake ciki kowa sunan garin su ne. "Daga wani gari Yaron nan yaƙe?" Ya tambaye shi yana kallon shi. "Eh toh gaskiya yace mana daga Damagaram yake, yayi makarantar Annur," ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce mishi. "Bai gaya maka sunan unguwar shi ba?" Shiru yayi sannan ya kuma kallon malam Ansar, kafin yace mishi. "Kamar yace gidansu na kusa da makarantar ne." "Nagode" ya faɗa har ya juya zai tafi yace mishi. "Karka fassara da wata manufa, naga ya tafi ne babu sallama" ya faɗa tare da muzurai. "A'a wallahi." Ya fada ina murmushi, dan shi bai tab'a shiga wannan shiga cikin shirmen da ake yi a cikin makarantar ba, asalima shi tausayin Almamoon yake, dan haka yayi tafiyar shi. *** Watsar da kayan wardrob din shi yake, watsarwa yake yana wasu irin surutai wanda baka gane abinda yake fada, ga bayan shi kuwa wasu mutane ne cikin bakakken kaya, juyawa yayi tare da niman inda zai cusa kanshi, sake juyawa yayi yaga tabbas matsowa kusa da shi suke. A mugun tsora ce, ya fara kokarin shiga wardrob din. Yana daidai sun tawo zasu caka mishi wukar har ya rutsa idanun shi, kawai yaji kamar an tare shi.... Karar da yaji tare da zuɓewa a jikin shi yasa shi bude idanun shi da sauri, ya had'a zufa sosai zama yayi yana kallon cikin kasuwar, sanan ya mike tare da ɗaukar karamar buta ya zaga bayan gidan yayi alola bayan ya kama ruwa, sanan ta dawo ya fara sallah nafilla, yana idarwa ya fito, sakamakon motsin da yaji. A hankali ya zuba ido akan Baba Nasiru. "Zauna Mamoon" zama yayi yana kallon dattijon. "Wato kaga rayuwar mun nan! Cike yake da al'ajabi, wasu na farin ciki, wasu na dariya da ban mamaki, wasu kuma masu saka kuka. Karka yarda Allah ya jarabce ka da laluran da bata da magani, karka yarda Allah ya daure maka kaddara da bata da iyaka, duniya cike take da mugaye, kowa da ka gani son kanshi yake, kowa da ka gani son abin duniya yake, kasan dai rijiya mai gaɓɓa dubu, idan ka fada kafin a ciro ka ai kasan ka sheka lahira, toh haka tafiyar ƙaddara take, na farko ba a tanada mata guri, sannan baka shirya mishi lokacin dawowa, sannan tafiya ce da motar da baka da matuki, tafiya ce da ko kana hanya ko baka hanya idan motar ta lalace tafiyar kafa zaka koma. Kasan yadda tafiyar yake a cikin tsannanin zafin sahara? Toh lallai wannan shine zanen ƙaddara, tafiya a cikin sahara ha zafi, ga babu guzuri, shi babu takalmi da zai rage mak ga zafi sahara, yunwa da ƙishirwa. Sai ya rage maka taki kad'an domin cimma manufar ka da burarrakinka na rayuwa, sai kuma kayi katari da alkalamin ƙaddara, wacce take rubuta fari da baƙi. A lokacin zaka ji duniya tayi maka zafi, kowa ya koma ya zuba maka ido. Allah Sarki sai ka ga lokacin duk inda zaka nufa cike yake da azzalumai. Duk inda zaka dafa mugaye cike suke da gurin, kowa kokari zai yi domin a sami dama daya tal! Kowa yunkuri yake yaga ya shiga cikin lamarin mutum, amma sai ka tadda zuciya ta kangare sakamakon jin bakon lamari, ƙwaƙwalwar mutum ta gigita. Fansa da rashin adalci ya girmama zukatar mutanen. Miyagun mutane suna karawa juna ilimi suƙa, masoyan asali sun koma a abokan gaba, taurin zuciya da ɗaukar zafin rai, zai zama linzamin farko na jagorancin zuciya, kafiya da rashin makusantan kwarai zai zama janabi na tunkarar mutanen da suke fadi tashi domin kaucewa kusakuran su. Yaro karka sake lokacin yayi kana me jin haka tabbas zai faru, karka yarda duniya ta baka damar amsar wasikar jaki, Rayuwar da aka gina bayan an saka Allah a cikin shi, bata lalacewa. Duk mutumin da ya dogara ga Allah baya tab'a tab'ewa, idan kaga Abu ya same shi, Ubangiji yayi haka ne domin ta tura mishi wani irin yanayi domin gyara alamarinshi. Allah ya kawo mu lokaci ne da mutane suka rufe idanun shi da yagar namar wasu, suna taunawa. Allah ya turo mu karnin da bamu da abinda zamu yi domin kaucewa tafarkin mugaye sai Addu'a, ina ma da zaka rike wannan tatsuniyar tawa, da ka kaucewa kuskure mara iyaka. Yaro mutanen da basu san darajar damuwa ba, a duk lokacin da damuwa ta faɗa musu, sun kan dimauta su gigita, Yaro kaga duniyar nan tsoro yake bani, gani dai a cikin ta amma ina shakkar mulkin da duniya take. Wasu mutanen basu da kirki, kana son aikata abin alkhairi, amma sabida sharrin zuciyar su, haka ,zasu yanyayemak da mugun nufin su, irin su basu barin mutanen kirki zama a kusa da mutum sabida sharrin su ya fi ta bakin maciji, fitinar su ta fi ta fitinar karni, bala'in su tafi ta annoba, kai yaro nasan ba fahimtatta kake ba..... _Don Allah kuyi hakuri 👏👏👏 wallahi na fita ne kuma fitar gaggawa ce ya kama ni! Kuyi hakuri ban cika muku alkawari ba amma muyi Abu daya mu sauya tsarin Posting ku fada min lokacin da ya dace na muku Posting naga kamar zai fi dad'i ayi da daddare sabida kowa ya gama busy na rana, kunga sai ina baku page me yawa ya kuka ce? Ina jiran ra'ayin ku idan kuma zan cigaba da rana ne shi kenan amma idan na shiga busy ba zan iya Posting ba ina jiran ku nagode sosai_ Hmmmm Wattpad ANYA?🙄🙄 Gaskiya toh wallahi zamu sake lalle domin zan bar Posting iya Whatsp.....🚶🏾‍♀️ Maneji.... [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀* ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE https://www.instagram.com/batool_spices Fatima Batool enterprise Yaji Ginger and garlic Onion powder Pepper soup Curry Biryani spices Mixed spices Indian spices Arab spices Chai masala Baharat blend Tandoori blend Thai masala Garam masala Provence Tea spice Zobo powder Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋 Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Idris *Hmm! Kalma ce da take kunshe da ma'anoni bila'adadin! Koda yake bana ce ba! Ba kuma zan fadi ba Amma idan har zan fadi gaskiya ku din masoyan gaskiya ne ba masoyan bogi ba. 🤣😜 Wato masoyan Mata maza, #Team Majnunu! Mukan Yan tawaye ne❤️🙄 Team Malam ANSAR* Wata Rayuwar.. BABI NA SHA DAYA.. Dariya ce ta so subuce mishi, ya kalli Baba Nasiru, sannan ya ce. "Ina fahimtar ka, kawai maganar ce tayi min nauyi sosai. Na gaza gane me kake son ka fahimtar dani" Tashi yayi dakyar ya nufi ban daki yayi alola sannan ya fito yana faɗin. "Wata rana zaka tuna da haka" Ya fada tare da nufar masallacin. Shima sallah yayi a cikin dakin, sannan ya zauna yana nazarin, mafarkin shi da. Can ya tuna da halin da yake ciki, iskar bakin shi ya ja, yana kallon hasken da rana da yake hudowa ta gabar. Ranar yayi wani irin kyau ta bada Wani irin yanayi, a hankali ya fito waje yana kallon yadda garin yake washewa. Shaƙar iska yayi me dad'i da ni'imar safiya. Ya lumshe idanun shi, yana kara tabbatar da kanshi, yana cikin nutsuwa. "Kasan wata ƙaddaran tamkar hudowar rana ce, idan ta shigo bata tab'a barin ka har sai tabbata akan ka." Kallon inda hasken ranan yake murmushi yayi sannan tacewa Baba Nasiru. "Zan koma gida" ya dauki kayan abincin shi ya juya tare da fita a kasuwan, yana isa gidan wanka yayi, Almamoon akwai tsafta ga son kwalliya, dan haka ya gama kome yana kallon Innah, sannan ya shige dakin ya kwanta. Barci me nauyi ya dauke shi. ..... Haka rayuwar su, take tafiya cikin ikon Allah da kuma matsin rayuwa, ga jikin Baban shi sai ruruwa yake, Nana cikin wannan yanayin aka yi sata a kasuwa, ai kuwa aka kama Almamoon. Aka rufe halin kunciin ya kuma rub'anyan sama da haka, rayuwar ta kuma ta'zara. A wannan gaɓɓar halin da Innar shi take ciki kawai ya isa ya karya maka zuciya, domin wallahi ba karamin matsanancin rashin hali take ciki ba. Ga ciwon Baban ya matsa mishi, wasa wasa sai da Almamoon ya cika sati biyu, sannan aka sake shi ya dawo ya daku, yayi laushi ko magana baya iya yi. Kwana shi uku yayi bai san inda kanshi yake ba, sai da ta haɗa mishi ganyen Tsamiya da wasu sassake ta dafa mishi yayi wanka, yana sha kafin Allah ya bashi lafiya. Sai dai kuma halin da yake ciki na rashin abinyi ga rashin abinci sai Innar shi ta tafi Bara suke samun abinda zasu ci. A hankali kwanaki suke tafiya, watanin suna kara nisa, abin mamaki Almamoon ya cinye zangon karatun shi a gida. ---- Burin shi nason zuwa ya duba Almamoon bai samu ba, sakamakon tura shi wani yanki da kayi na aikin zaɓe,yana dawowa kuma yayi ta faman zirga zirgan asibiti da Umman shi, baki daya yaron ya tsaya mishi a ranshi, ya rasa gane wani irin kauna yakewa Dalibin shi, a iya sanin shi. Dai kaunar da yake mishi bai kai yadda yake ji ba a baya, amma rashin dawowar shi makaranta Yasaka shi jin kamar zuciyar shi ce a Damagaram. * Yau ta kama lahadi. Gyara mishi gashin kanshi dan Ba'are yake, cikin kulawa da nutsuwa. Duk da yaki tsayawa amma kuma haka bai hana shi gyara mishi sumar da yake kanshi buyayya haka nan ba. Wayar tafi da gidanka na shine yayi kara. Dauka yayi sannan yace. "Kaga Bama bukatar mace? Namiji muke bukata don Allah kar ya wuce nan da kwana uku, matukar ya wuce haka da akwai matsala bana son tafiya na bar mara lafiyar ne" Kome aka gaya mishi sannan tace. "Alhamdulillahi, ku taimaka min daga fadar shugaban ne kuma albashin akwai kyau Insha Allah babu matsala, Nagode sosai" Sannan ya katse kiran, yana jin kamar ya janyo kwana ukun zuwa yau, dan an addabi rayuwar shi da kira, ya dawo bakin aikinshi. Bayan ya gama mishi gyaran gashin kanshi ne ya kuma dawowa kan fuskar shi, a nutse yake gyara mishi fuskar. Shi dai yana zaune sai yadda aka yi dashi, yana gamawa ya kama mishi gyaran farcen shi, har ya gama sannan ya mike ya haɗa mishi ruwan zafin wanka. *** Ofishin shugaban jami'ar, shiru yayi sannan yace mishi. "Yallabai yaron nan haziki ne, idan aka kore shi ba a mishi adalci ba, don Allah karka yanke hukunci Ni zan tafi garin su na duba bashi, don Allah yallabai ka du..." Daukar wayar gaban shi yayi ya fara waya, ya jima yana magana kafin ya ajiye. Har ya manta abinda Malam Ansar yake rokon shi nan ya shiga rabtabo bayanin. "Wai ana niman wanda zai yi jinyar wani na hannun damar shugaban kasa ne, kuma namiji matashi, sun hadani da aiki ina zan samu me wannan yanayin kuma wai basa son mace, don Allah ka taimaka min ka tayani cigiyar." "Toh yallabai ya batun Almamoon?" Ya fada a marairece, "Zan duba ka fara duba min yaron idan ma ta kama ma waye ka kawo min zaka nima akan aikin shi kenan, albashin sa na farko nawa ne, sauran kuma zamu yi ta kashe mu raba" "Hmm! Toh zan duba maka. Mun gode da alfarman da kayi mana daura dari biyu a fara jarabawa, dan haka Insha Allah zan tafi har Damagaram ɗin." Ya fada tare da gyada kanshi. Mikewa yayi tare da ɗaukar kayan shi ya fita, yana me cewa. "Insha Allah ba zan koma gida ba dai na nimo inda kake" ya faɗa cikin motar shi, ya bata wuta. Gidan mai ya fara tsayawa ta cika tanki, sannan ya dauki hanya. --- Karfe shida na yamma yana zaune a kofar gidan su, dake basu da nisa da Makarantar da yayi, yana hango motar kamar ya santa, Amma haka ya kura mata ido, har ta iso gare shi. Mik'ewa daga kan dakalin ya tunkari malam Ansar. "Barka da zuwa Malam" zuba mishi ido yayi ya kara lalacewa bakin shi ya karu ainun. Fitowa yayi yana kallon shi, sunkuyar da kai yayi yana wasa da hannun shi. "Baka iya tarba'n baki bane?" Da sauri yace mishi, "Kayi hakuri mu shiga daga cikin gidan." Almamoon yana gaba Malam Ansar yana baya, har cikin gidan. Inda yayi mishi shimfid'a a kusa da inda Malam Sanda yake zaune, yana fama da sauran mikin wutar da ta kona shi. "Barka da zuwa malam" inji Innar Almamoon tana kawo mishi ruwa, "Yawwa nagode Inna" Gaishe gaishe suka yi, kafin dai ya kawo dalilin zuwan shi. Mik'ewa Almamoon yayi Tare da cewa. "Ni dai bani komawa ko ina, zan zauna da iyayena babu wanda yafi dacewa da kulawa da lafiyar su sama da ni, sannan babu me taimaka sama dani, idan na tafi waye zai kula da lafiyar su? Idan na tafi waye zai nima musu abinda zasu ci? Ba kowani lokaci ake samun abinda ake so ba. Koda zaka samu dole sai ka dandani azabar da kowa ke sha, Na gode sosai malam" ya faɗa cikin sanyin murya, duk sai son shi da kaunar shi ya cika mishi zuciya, ya kuma jin yaron ta cancanci yayi rayuwa me kyau da tsada, toh amma shima ga halin da yake ciki, mahaifiyar da duk wata take cinye sama da rabin albashin sa, ga bikin kanen shi biyu da aka saka. Duk sai yaji babu dad'i Meye ma ya kawo shi? Kurawa Baban Almamoon yayi ido, kafin yace musu. "Ku saka baki ya koma makaranta Insha Allah zan nima mishi aikin da zai rike kan shi da kuma baki ɗaya" dukkan su a lokaci guda suka zuba mishi ido, sabida rashin yarda da ya shiga zukatar su. Ganin irin kallon da ake mishi yasa shi gyara zaman shi sannan ya fara da basu labarin yadda suka yi a ofishin shugaban jami'ar. "Idan har daga jikin firaminista ake niman shi toh ba makawa ba iya kune kuka huta ba, hatta wasu zasu huta a jikin ku, bawai dan na rena muku bane sai dai ina son yayi rayuwar da zata saka shi farin ciki ne, kar ku damu ni ma kamar dan ku nake, don Allah ku fahimce ni". Shiru suka yi kafin ya cigaba da cewa. "Wani sana'a kike anan?" Sunkuyar da kanshi yayi tare da labarta mishi ko sati biyu bai yi da fitowa ba daga ofishin yan sanda, sakamakon abinda ya faru. Idanun shi sunyi jajjur, "Dako fa?" Ya kuma tambayar shi. A hankali ya saka hannun shi a cikin aljuhun wando shi ya ciro kudi masu kauri, ya ajiye musu. "Ku dubi girman Allah ku taimaka gobe ya dawo makaranta, ba nazo dan na tilasta ku bane, a'a nazo ne dan na tsayawa dan uwana kanina zan tafi Nagode ga wanna Ku sayi magani" Duk da suna cikin damuwa da matsin rayuwa, bai hana su ce Mishi. "A'a , bawan Allah mun gode Insha Allah zamu turo shi amma ka dauki kudin nan kai Almamoon dauka ka bishi da abinshi mun gode" Cikin sanyin jiki ya zuba musu ido kafin yace musu. "Baku yarda dani ba kenan?" Yadda yayi maganar yasa Malam Umaru yace mishi. "Allah ya kara budi mun gode sosai, Allah ya tsare hanya Ubangiji ya jibanci alamarunka" Cikin wani irin jin dadi yace mishi. "Amin Ya Allah Nagode sosai baba Allah ya baka lafiya, Toh sai an jimanku Almamoon sai na ganka kenan" mik'ewa yayi suka fita. Mika mishi hannu yayi, amma fir ya coge, sai ma yayi kamar bai da lafiya. Shiru suka yi dukkan su. ... Bayan fitar su, a kidime Innar Almamoon ta kalli Malam, "Malam!" Ta kira sunan shi a sanyayye, "Kabo, bana son damuwa akan Almamoon. Ba wai dan ina cikin tsannanin rayuwa bane, sai dai ba zan ji dadin yaron ya kare rayuwar shi anan ba, kamata yayi ya tafi koda babu aikin da zai yi a jikin masu kuɗin." "Malam ba haka bane, na hango tashin hankali a kwayar idanun malamin, na hango kaunar Almamoon a cikin idanun shi." "A'a ki kyautata zaton ba wai ki munanan zato ba, ban ji dadin abinda kike tunanin ba." Tana son yin magana amma sabida yadda malam yaki amsar uzurin ta, yasa tayi shiru. .... "Almamoon!" Kasa d'ago kai yayi dan yasan yana nan yana kare mishi kallo, "Almamoon dama irin wannan rayuwar ne ya hanaka zakewa a ko ina? Me yasa baka gaya min ba tun farkon zuwanka makaranta a nima maka aikin yi yadda zaka rike kanka da iyayen ka? Me yasa baka tab'a gaya min ba?" Ya tambaye shi cikin wani irin yanayi. Tar ya kalle shi kafin yace mishi. "Bana niman taimako a gurin kowa sai Allah, bana son wanin da ba Allah ba ya goranta min, sannan idan daga haduwar mu nace maka ina son ka nima min aiki ya zaka ji? Dan haka ya yankewa kaina damuwar Kowa sai na iyayena, yanzun ma zan yi shawarwari dasu idan suka amince na dawo shi kenan, idan basu amince ba kayi hakuri. Na iya talaucina" ya faɗa kai tsaye ba zaka tab'a tsammanin zai iya fadar haka ba, domin babu shakka ko wani abu a ranshi sai ma tsantsar gaskiya wanda daga kin shi sai b'ata. Shafa kan shi yayi tare da hura iskar bakin shi yace mishi. "Ba zan yi kasa a gwiwa ba, idan har baka zo ba gobe jibi Insha Allah zan zo" daga haka ya juya tare da shiga motar shi. Har ya bar Unguwar, kallon motar Almamoon yake. "Hm" ta faɗa tare da shiga cikin gidan. Yana shiga ya lura da Innar shi fushi take dashi. "Inna" ya kira sunanta, "Wato baka jin maganar mu ko? Me yasa ba zaka gane yanayin ka da na sauran mutane bane? Sai da muka baka shawara kan babu ruwanka da mutane amma kayi kunnen uwar shegu damu, Allah ya baka sa'a tunda ka jajjubo shi." Kamar wanda aka dasa, haka yake tsaye bai tab'a ganin irin haka ko ji ba, sai gashi lokaci guda kome ya sauya. "Kai Almamoon zoka dauki kudin nan kasayo sabulu ka wanke kayanka gobe ka koma makaranta ko baka yi aiki ba, ai bamu ke daukar dawainiyar ka ba, tallafi ka samu, ina me rokonka da ka kame kanka. Insha Allah babu abinda zai faru sai Alkhairi babu ruwanka da kowa, don Allah ka rufa mana asiri. Ka ji" "Baba ni ba zan koma ba" ya faɗa kan shi a sunkuye, shiru ne ya ratsa tsakanin su, kafin Malam Umaru ya sake wata magana kamar saukar aradu. "Aminatu kenan, ba sai kin gwada min karfin ikon ki akan Jinin Sama'ila ba" ya fadi haka tare da mik'ewa, ba ita ba hatta Almamoon sai da ya mike tsaye. "Malam!!!" Ta kira suna shi jikinta na rawa. "Ayya Ayya Ayya Malam, Ayya Malam me yasa? Malam alƙawari bai ce haka ba, Malam me yasa zaka nemi kifar min da miyar da na jima ina wahalar had'a shi? Malam me yasa zaka kunce min zani lokacin da ban shirya kuncewa ba, Ayya Malam Ayya Ka yi min adalci kuwa? Malam me yasa baka Cigaba da YAKANA ba? Malam karka tulamin kasa a idanu mana, karka sare min gwiwa ta mana, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji." Shi kanshi bai zata maganar zata iya fitowa a bakin shi ba, kallon su Almamoon yaƙe, kafin yace. "Waye Sama'ila da nake amfani dashi a makaranta?" "Sunan Baba nane" inji Malam, sabida ya dauke hankalin Almamoon daga batun, ita kuwa Innar had'iye kukan tayi lokaci guda, haka kawai Almamoon yaji a ranshi, akwai abinda suke boye mishi, amma koma meye wata rana zai fito. Daukar kudin tayi tare da yafa mayafinta ta fita, sayo sabulu, kafin ta karasa ta tsaya a wani lungu. Ta fashe da kuka, sai da ta durkusa a kasa tana wani irin kuka. Me yasa malam yayi mata haka? Me yasa ya zab'i cilla rayuwar Almamoon wata duniya, me yasa ya aikata haka? Komawa tayi tare da zama. Tayi kuka kamar ranta zai fita, kafin ta goge idanunta, sannan ta nufi shagon, ta sayi abinda zata saya. Sannan ta juya tare da komawa gida. Ita da kanta ta ware kayan Almamoon ta wanke mishi aka kiran magarib tana shanya kayan, sannan ta zauna bayan ta ga Almamoon yana alola. "Gama ka bani butar na taimakawa malam" "Toh ina" Haka ya gama ya mika mata bayan ya cika ruwa a cikin butar, ya shiga dakin sallah. "Malam gashi" ta faɗa tare da dauke kanta daga gare shi. Riko hannunta yayi cikin nashi yana faɗin. "Nasan nayi laifi, amma haka ba yana nufin b'ata miki rai bane, idan har sabida kin yi fushi yace ba shi komawa makaranta waye zai gaya mishi yaji? Rayuwar shi zaki duba? Waye shi ba shi bane me muhimmanci ba, rayuwar shi na gobe shine mai muhimmanci. Idan da ace sabida ke ce wallahi ba zan saka baki ba, amma dake saboda yaron ne dole na saka baki, yana miki wata irin kauna ce ba iya ke ba hatta ni, kaunata yaƙe, sabida mu ya sadaukar da karatun shi ashe ba zamu tsayawa rayuwar shi dan wata dama ta same shi ba? Kinsan mutanen da suke niman dama irin da ya samu yau? Wallahi ba kwadayin abin duniya ya sani amsar wannan batun ba, sai dan rayuwar shi, ai ko babu kome zaki duba ki ga waye shi? Ina zai shiga? Meye Allah ya ƙaddara mishi, shin zai iya jure ƙaddaran shi? Shin meye mizanin ƙaddaran shi? Wannan shine abinda nake son ki Fahimta, amma idan kin fahimta idan baki fahimta ba, ki barshi yayi ya zama. Allah yayi mishi baiwa amma zai kare ta a matsayin dan dako, nasan waye na ke zaune dashi. Tunda nake da yaron nan bai tab'a ɗaukar abin wani ba, amma lokaci guda an daura mishi laifin da bana shi. Idan muka ce kullum gudun ƙaddarar shi zamu yi wata rana ba zamu iya gudu ba, kyale shi ya fita yayi rayuwar shi kamar kowa, ya fahimci muhimmancin rayuwa, ya san yadda Goben shi zai kaya, idan muka cigaba da boye shi wata rana zai iya tambayar mu me yasa? Ina jin kunyar na gaya Mishi waye shi. Don Allah Karki Cigaba da abinda kike aikatawa, don Allah na hadaki da shi karki kuma abinda ya sani magana." Share kwalla tayi tare da SUNKUYAR da kanta. "Malam don Allah karka kuma haka" "Insha Allah ba zan kuma ba, leka karki kuma ki barni nayi iko da shi." Ya faɗa, "Inna yau ba zaki mana abinci bane?" Ya fada tare da tura baki, Tashi tayi tare da cewa. "Ga tsakin can dambu ne" zama yayi tare da kallonta, "Innah dambun kuma?" "Ina da zogale da busheshen lawashi" "Inna da magarib zaki mana dambun?" Ya fada kamar zai fashe da kuka, haka ya mike. "Toh zoka sayo maka makaroni." Da sauri ya mike, tayi mishi lissafin, bayan ya mike ya dauki kudin ya nufi shagon unguwar. Tun daga nesa ya hango yan daban, sunan shi Shege. Cikin shi ne ya cika da ruwa, haka ya isa shagon ya gama sayayyan shi, sannan ya juya zai tafi, yaji an matse mazaunin shi. Maganar gaskiya Almamoon yana da halittar mazaunai, duwawun suna nan masu dan tudu, ba laifi abinda yake jan hankalin matasan yan daban suke bibiyar shi. Shege dan iska, yana bin mata da maza. Tun shekara daya da ya wuce yaga Almamoon yake Masifar son ya kusanci bayan shi. Amma haka bai samu ba, sai da magarib nan yake ganin kamar zai iya shigar shi da karfin tsiya. Kwace jikin shi yayi tare da kallon shi. "Malam Meye haka?" Wani nishi ya sauke tare da takowa gabansa. "Kamshin mace naji a jikinka" "Malam bana son damuwa" ya faɗa da sauri yana ja da baya, ganin Almamoon zai subuce mishi ya kara kai mishi cafka Allah ya bashi sa'a, ya arta a guje. Shi da yaran sa, suka mara mishi baya Allah bai basu Sa'a ba, har ya shiga cikin gidan, tare da rufe kofar gidan yana haki, kamar Mahaukaci haka ya shiga gidan yana haki. "Lafiya?" Nan ya basu labarin biyo shi da shege yayi, shiru Malam sanda yayi sannan yace mishi. "Insha Allah gobe zaka bar garin nan" Innah da cikinta ya duri ruwa kamar zata fashe da kuka. "Eh gwara ka tafi, zaman ka a nan masifa ce gwara can" Shima munafikin da yaji haka, ai amincewa yayi babu shiri a daren suka tafasa taliyar suka ci, wajen asuba. Ya shirya kayan shi. Sannan suka mishi addu'a, kafin suka sanya shi yayi Sallah tare da niman dacewa. Karfe bakwai na safe ya bar gidan, cike da zulumin rayuwa, Haka ya nufi tasha, yana zaune har motar su, ta tashi. Anan ya sauke ajiyar zuciya. ** Karfe hudu na yamma ya same shi a quarts din malaman jami'ar, a hankali ya shiga buga kofar get din, dake yasan Almamoon zai zo shi yasa ya bude da kwarin gwiwar shi, yana buɗewa, ya shigo. Bai san lokacin da ya fisgo shi tare da rungume shi ba, yana wani irin jin dadi da nutsuwa yana saukar mishi. (Labarin zai koma bakin Mata maza🙄🤣 Salon da na saba 🙆🏾‍♂️😜) Cikin wani irin takaici na kalli Malam Ansar. "Toh meye haka? Idan Baba Mari ta ganmu ta zarge mu da wani abu ko?" Kamar zai sake min kuka yace min. "Kayi hakuri nasan babu dad'i amma kuma nayi kewar ka ne sosai." Ƙaramin tsaki kayi a raina sanan nace mishi. "Toh Ni gaskiya bana son haka." Na ture shi tare da juyawa zan fita. "Don Allah kayi hakuri" Banza nayi dashi. Kamar dani yake ba, "Toh shi kenan, ba zan kuma ba." Ya fada a sanyayye, shiga cikin gidan nayi ina wani hura hanci irin ganin nan an min laifi. "A'a ba nan ba, BQ" na wuce da jakata ina shiga na kalli Baba Mari. Cikin wani irin murna ta taso tare da amsar kayana. "Dan mutum kai ne a gari" Kaunar tsohuwar ya taso min tun daga cikin raina har jinin jikina, ba zan iya cewa ga yadda nake ji akan ta ba, kwalla ne ya cika min idanuna. "Wallahi matar gani nan". Na zauna ina kallonta, kura min ido tayi, sannan tace min. "Idan na kalle ka sai na tuna da Abuh, yanayinku, kayi hakuri na tsare ka da surutu.." Tashi tayi ta fara hada min abinci, tare da duk wani abun da take dashi a dakin. Cikin kauna da gata, take min. "Maza zauna kaci" haka ta hada min na fara ciki ina janta da hira, har ma gama na kwashe kwanikan na wanke, na dawo dakin nayi sallah,haka na tattara kome na koma dakin da aka bani, na gyara shi tsaf. Sannan na dawo dakin ta muka shiga hira, har malam Ansar ya kuma zuwa, wani shegen kallon yake min, dan haka na dauke kai na tare da b'ata rai. Haka muka sha hiran mu tare da basu labarin halin rayuwar da muka sha, wanda ma na bar su. "Yanzun ma ai bawai na dawo bane saboda kaje, wani gantalallen mutum ne ya dame ni shine Inna da Baba suka yarda na zo." Ya fada tare da tsume fuska, dan bakin nan ya cuno shi gaba, alamar wannan Almamoon da mace ce (🙄😜🤣) tabbas zata yi tsiwar bala'i, ina dalili dauke idanun shi yayi daga kanshi, domin kowani seconds na bugawar agogo jin bugun zuciyar shi yake yana fita kamar da sunan Almamoon, tsabar kaunar da yake mishi (Dalla can mata mazan🙄😠😏) kasa sakewa yayi dan gani yake kamar Baba tasan abinda yake yi akan Almamoon, ya tashi ya bar gurin tare da cewa. "Baba bari na fita na dawo" "Allah ya tsare" Ta faɗa mishi. *** Abinka da mara lafiya, ganin yadda agwagwan ke wanka haka shima ya tawo da mugun gudu ta dirka a cikin ruwan ji kake famjammm, ya fashe da wata irin dariya yana gurnani kamar Mahaukacin kare, bakin shi yana zubda yawu, sai buge fuskar shi yaƙe alamar kuda na binshi. "Hrmrmrmnnnnnrrr" masu kula da lafiyar shi, ne suka taru a gurin da hodar da suke shaka mishi. "Ku nutsu a hankali" Inji Hurayyah, sadaddewa suka yi tare da shaka mishi hodar ta bayan shi, anan suka yi a rangama daukar shi, kai ciwo makiyin mutum. "Amma Hurayyah idan Dan Ba'are yazo da?" "Toh kai da mu bari ya dake mu ai gwara mu shaka mishi tunda naga ai ba laifi bane, kuma idan ba haka muka mishi ba kana ganin zamu sha lafiya ne, gwara mu shaka mishi." Haka suka dauke shi zuwa dakin shi, aka kwantar dashi, suna kokarin cire mishi kayan Dan Ba'are ya shigo. Ganin halin da suke ciki ya shi musu wani irin banzan kallo, babu shiri suka bar d'akin, tare da nufar waje, suka shi ya kintsa shi sannan ya zauna yana kallon shi. "Mohammed Insha Allah zaka samu lafiya ina jin haka a jikina, sai dai ta inda lafiyar zata samu ne ban sani ba" ya faɗa tare da rungume hannunsu guri guda. Tausayin shi yake, yasan idan ya samu lafiya bai zama dole ya koma bakin aikin shi ba, tunda ga halin da yake ciki. Koda ya ji sauki sai dai ya nemi wani aikin kawai. Kiran wayar shugaban jami'ar yayi suka yi magana, shafa kan shi yayi yana murmushin jin dadi. "Nagode" Ya fada cikin wani irin abu yaji ya tsaya mishi a raina, Dan haka ya mike tare da nufar waje, ya kalle su dakyau. "Insha Allah jibi za a kawo wanda zai na kula da lafiyar shi, ku sai ku tsaya akan aikinku,." "Toh" suka fada lokaci guda, sannan ya juya tare da barin gurin su. Ko minti biyar ba ayi ba aka kira shi, daukar wayar yayi tare da mannawa a kunnen shi. "Akan me zaka ce su tsaya akan aiki su? Karka yarda ka kawo min wani mutum da zai kula da lafiyar Mohan domin kome na shi yana hannuna." Murmushi yayi sannan yace mata. "Ko Ammi bata da ikon hana ni abinda ya dace akan Mohan balle ke, dan haka ki fita idona na rufe idan na rufe dake mmm" ya kashe wayar yana tsaki, fitowa yayi tare da tara su, "Wallahi sai na kore ku kuma na kwana lafiya, kunyi na farko kunyi na karshe kar na kuma kama wani dan iska da min tsurku, idan kuma na sami haka" Nad'e hannun rigar shi yayi tare da kallon su, yana lashe lashe bakin shi, cikin zunzurutun masifa da bala'i. Ya tsani renin hankali. Shi yasa ake ganin kamar baya son mu'amala da mutane kananun magana ne ce ya tsaya, yan iska kawai sai ya hana Hajiya Safiya shigowa gidan da shi take zancen fita yayi tare da danna wani kararrawa, kafin kace kwabo. Kafatan jami'an tsaron sun halara a filin gidan, haurawa saman wani dakalin yayi yana kallon su. Kafin yace musu. "Jibi Insha Allah zan bar garin nan zan koma gurin aikina, kuma jibin zan kawo me Kula da lafiyar Mohan, idan yazo ina bukatar a kula da lafiyar shi! A kula da duk wani abun da zai zo dashi sannan ina kyautatta zaton zai zauna anan ne zai na tafiya makaranta a bashi driven da zai kai shi ya dawo dashi. Ina son kuma a saka ido akan masu zuwa daga Fadar firaminista da sunan duba lafiyar Mohan, kowaye matukar Ba Hajiya Latifah bace ko Daya daga cikin Yaranta ko Mai Girma Shugaban kasa ban yarda a bude kofar gidan ba, idan kuka ga mutum ya matsa zai shigo ku bude mishi wuta. Sannan ku kara saka ido akan masu aikin kicin da sauran bangarorin akwai munafukai. Da fatan zaku bawa Major General Mohan Mamman Nasir Aghali Kariya da Yardan Allah" Duk suka hada baki da cewa sun amince, zasu yi aiki tsakanin su da Allah tare da bawa shugaban su kariya da yardan Ubangiji. Sanan ya gaya musu duk wanda ya karya dokan shi tabbas shima zai karya kafaffun shi. Dan haka su bi doka da oda. Suka kuma yarda tare da amincewa. Kafin ya sallame su, ya shiga cikin gidan, yana shiga ya kira su baki ɗaya. Kallon shi suka yi dan sun fara razana da al'amarin shi. Duk da sun zai bai da dad'i amma kuma basa tsammanin har ya kai yadda suke tsammanin. " Idan mai aikin yazo zan tambaye shi matukar ya iya girki ba zaku kuma dafa mishi abinci ba" a rude suka d'ago kai suna kallon shi, a ransu kuwa ba karamin kwashe mishi albarka suke ba, ayi mutum da zunzurutun masifar tsiya, kome sai ya sauya musu tsarin su yake, Ashari'a kuwa yasha babu iyaka da Tsinuwar su akan ya sauya musu alkibla.... Please if you read hope me sharing to family and friends😭😭😭 karku manta da komens da bote, ko muje hutun kwana uku 😛😁😜🙄😩 #Mai_Dambu... [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀* ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE https://www.instagram.com/batool_spices Fatima Batool enterprise Yaji Ginger and garlic Onion powder Pepper soup Curry Biryani spices Mixed spices Indian spices Arab spices Chai masala Baharat blend Tandoori blend Thai masala Garam masala Provence Tea spice Zobo powder Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Batool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋 Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azi_zat *Gaisuwar ce wannan shafin Aunty Safiya Jos, Ummi Ilham Gombe, Mom Sayeed Kano, Mrs Faruq matar kakana Nagode sosai* Sai da rai.... BABI NA SHA BIYU. Da'go kai yayi tare da kallon su, cikin nutsuwa da yanayin shi na cin Uban kowa ya kwana lafiya, yace musu. "Matukar wanda zai kula da ya iya kome dukkan ku barin gidan nan zaku yi domin ban yarda da fuskar ku ba. Ku b'ace min da gani marasa mutunci" Rabil da Hurayyah suka wuce kitchen, Bilal da Moussa suka wuce gurin wanki, Sarah da Nouhu suka wuce bayan dakin da ake ajuye kayan aikin cikin gidan. Hurayyah da Rabil girki suke, Bilal da Moussa, wankin da guga suke. Sarah da Nouhu sharan gidan suke da goge goge. Kusan idan ya cire Hurayyah itace Mohan ya kawo ta da kanshi sauran kuwa. Daga can fadar gwamnati aka kawo su. Kuma yana kyautatta zaton Hajiya Safiya ce. Ya tsani matar nan kamar me. *** Niamey. Shige take da fice, tana hango yadda Hajiya Latifah ta harde ana mika mata wasu takardu, zata saka hannu. Murmushi tayi sannan tace. "Da Sannun zan ruguza ki, tunda nai babban nasara kawar da wanda ya tsaya muku" Fitowa tayi cikin shigar Alfarmar ta nufi gurin da Hajiya Latifah take. "Barka da hutawa ranki shi dade" Sai da ta b'ata lokaci kamar ba zata amsa ba kafin tace mata. "Hmm" Ta cigaba da aikin ta, kamar bata san da tsayuwarta a gurin ba. "Hmm, dama ranki shi dade akan batun matsalar Mohan" Ta faɗa tana kallon yanayin da Hajiya Latifah ta shiga, ganin yadda Jikinta yake rawa yasata sake murmushin mugunta, sannan ta cigaba da cewa. "Dama naga" "Kije bana son jin sunan shi tashi ki bar min nan" Ta daka mata wani irin tsawa, wanda yasata mikewar dole, domin babu karya ta razana. Bayan tabar gurin kan Hajiya Latifah ya shiga sara mata kamar zai rabe biyu. Tsaki tayi tare da mik'ewa, ta nufi cikin gidan, koda ta shiga har ta manta kome akan shi. Itama Hajiya Safiyar dadi ya sata bata kuma bin wani abu akan Mohan din, sai dai tana da kudirin jibi Insha Allah zata dira a Maradi ta cirewa dan Ba'are rashin mutuncin da yake kan shi. Kuma wallahi ta isa sai ta ganawa Mohan azaba, dan duk cikin Yaran Hajiya Latifah ta tsani Mohan sama da kowannen su,, shi yasa bata yi kasa a gwiwar gurin tsayawa sai da kome ya faru dashi kafin hankalinta ya kwanta. Shima dan Ba'are sabida ba haka kawai yake ba da ta jijjiga shi da karfin ta. Ta kuma nuna mishi Allah daya ne. *** Washi gari Kamar ba zan shirya ba, amma sabida irin yadda Malam Ansar yake bina da idanun yasa ni hada kayana, na raba biyu. Na saka rabi a cikin wata jaka, rabi kuma na barshi a dakin Baba Mari, sanan na tsaya tare da cewa. "Baba idan aikin da sauki zan na zuwa duba ki, Insha Allah." "Allah yayi miki albarka, ya kuma kare ki daga sharrin shaidanun mutane da shaidanun Aljanu, karka yi wasa da ambaton Allah a duk inda kike, gurin da zaka shiga haka kawai nake ji a jikina akwai babban Al'amari a gurin. Dan haka a rike Allah babu wasa sallah nafilla, walaha da duk wani sallah bayan sallah farillah, ba ayi da La'asar da magarib, amma ana yin shafa'i da wutiri, karka manta Alhamis da Litinin kayi azumi ka nemi dacewar Ubangiji.." Rike hannu na tayi tana kallon fuskana tace min. "Wallahi nayi mafarkin inda zaka cike yake da ƙaya masu matukar hatsari, shi yasa na mike da nima maka kariya, Insha Allah zaka yi nasara amma karka manta gaskiya tafi kome tasiri kar manta da karatun Alqur'ani domin itama haske ce s duk inda mutum yaƙe." Wato matar nan jinta nake kamar ita ta haifi Innata, zunzurutun kulawa. Sannan ta bani addu'o'in. "Baba zamu tafi makara muke" "Allah yayi muku albarka" ta faɗa tare da juya mana baya, mu kuma muka fita, ina lura da take taken shi magana yake son min, amma na wani b'ata rai, sai da muka fita daga gidan ya rufe Kofar gidan sannan ya tako har zuwa inda nake, ya bude motar ya shiga. Shiru ne ya gifta tsakanin mu. Kamar ba zai yi magana ba. "Ina rokonka don Allah don sonka da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ka kame kanka, tunda kasan yanayinka ba irin tamu bace, yanayi biyu ne a tare da kai don Allah karka yarda wani ya fahimci halin da kake cikin har yayi kokarin cutar da kai, Wallahi idan wani abu ya same ka, kashe kaina zanyi da bakin ciki," "Ai makabarta bata cika ba, dan haka Allah ya jikan musulmai wanda ya kashe kanshi kuma Ubangiji ya san yadda zai yi dashi" (hali a jikin rai yaƙe Bakar magana) kallon shi Malam Ansar yayi tare da cewa. "Wai meye nayi maka ne ka bi ka tsane ni haka?" Ya tambaye shi kamar zai yi kuka, Wani banzan kallo na mishi, kafin nace mishi. "Kawai naji a raina na yi ta kafta maka rashin arziki ne" ya bashi amsa. "Indai akan dan rungumo ka da nayi jiya ne Allah ya baka hakuri." Dauke kai nayi kamar ba dani yake ba, gidan shugaban makaranta muka nufa, daga nan shima ya koro min jawabin shi da abinda zamu yi kallon shi nayi kafin nace mishi. ""Toh" sanan muka bar gidan, ina ji kamar na rufe su da dukka, kiran dan Ba'are yayi ya gaya mishi gamu nan mun iso amma akwai jami'an tsaro sosai. Bayan kamar minti goma sai gashi ya zo da kanshi, suka yi magana kafin ya leko cikin motar ya kalle ni. "Kai fito" ya faɗa babu wasa a fuskar shi. Ganin shi dirkeke, ga fuskar nan babu sassauci ya sani fitowa ina kamkame jakata.kallon na yayi sannan yace min. "Koma cikin motar" Komawa nayi, sai lokacin na lura da fuskar malam Ansar, ya b'ata rai ainun. Fuskarshi har wani ja yayi. "Malam Ya naga yaron kamar mace?" "Almamoon namiji ne, haka kowa yake gani kamar mace amma namiji ne" "Toh ince bai da matsala, irin dauke dauke da sauran su?" A wannan gaɓar kamar malam Ansar ya daka mishi mari, amma ya rarrashi kanshi yana kallon shugaban jami'ar. "Yaron bai da matsala, kuma ban tab'a jin malam Ansar ya fadi wani abu akan shi ba, ko abokan karatun shi basu tab'a koraafin yayi musu ta'adi ba." "Toh Shikenan, kuje dashi Insha Allah gobe idan ya taso makarantar yazo Insha Allah kafin lokacin an gama mishi kome nashi na gidan domin babu me tsallake wancan shingen babu alamar kai ɗaya ne daga cikin gidan." "Mun gode" d'aga musu hannu yayi tare da juyawa ya bar gurin su. "Gaskiya ban da dole da Almamoon ya hakura da wannan aikin kawai raina bai kwanta da wannan gida me cike da murɗa murɗan maza ba" Inji malam Ansar, jin haka shugaban Jami'ar ya lullube shi da faɗa, har suka isa makarantar. Kamar zai ajiye Almamoon sai ya dawo dashi gidan. Sannan ya nufi makaranta domin fushi yake sosai kuma ba kome ke damun shi ba sai kishin bala'i da ya daurawa kanshi akan Yaron. Dan shi har kwanan gobe kallon da Yakewa Almamoon ba na wasa bane. .... Bayan tafiyar su, ya koma cikin gidan. Zama yayi yana hasashen fuskar Almamoon, haka kawai yaji yaron yayi mishi kuma ya kwanta mishi, bai da nutsuwa da wata shirme irin n yaran yanzun, Kallon Mohan yayi tare da cewa. "Bana son barin ragamar rayuwarka a hannun mutane da suke kewaye da kai ne" shiru yayi sannan ya cigaba da shafa kanshi yana jin tsannanin tausayin halin da Aminin shi yake ciki. A hankali ya mike bayan ya nufi inda ya ajiye kome ya fara shirin shi da yasaka a ranshi, yayi ta aiki yana connect din na'ura a cikin gidan. Bayan nan ya fito. Akwai wani yardadden Yaron Mohan mai Suna Malik, har yau bai tab'a jin Malik yace mishi ga wani abu na Mohan ba, dan haka lokacin da Mohan ya fara jinya da zai zuba jami'an tsaron Malik ya bawa rikon su. Dan haka ya fita tare da kiran shi suka nufi lambu. Zama Dan Ba'are yayi yana me kallon Malik da ya sara mishi. "Gobe Insha Allah yaron da zai kula da Mohan zai zo, kasan me ina son ka zuba ido akan Yaron! Daga yau zan mai da kula da gidan a hannun Fahad, kai kuma ka zauna a cikin gidan kana taimaka mishi da wasu abubuwan. Akwai abinda nake zargi a cikin gidan amma ban tabbatar ba, don haka zaka ajiye unifoam. Nasan kai ɗaya ne kasan kome akan Mohan har da abinda ya shafi dukiyar shi, naji dad'i da ka zama mutum mai Amana da gaskiya, Insha Allah zaka ga sakayya a gurin Ubangiji. Gashi nan wannan key motar da zai na kai shi makaranta ne, wannan kuma duk wata zana cire CF dubu dari bakwai kana bashi katin bankin shi na kamfanin shi da yake doso ce, babu abinda zai yi da izinin Ubangiji. Don Allah ka zama me amana da na san ka dashi, bayan ku duk mutumin da ya nemi shigowa gidan nan" Jan hannun shi yayi kamar wanda ya ke jan bindiga ya dauke kamar yayi harbi, "ku gama dashi, idan ka fahimci Yaron yana da dauke dauke ka kira Ni ka gaya min zan zo na mai dashi, sannan duk bayan sati biyu kana ciwo mishi dubu hamsin kana bashi, sabida kashe wasu kannan bukatar shi. Idan kaga wani sauyi kai min magana, idan na samu lokaci Insha Allah zan zo na kai shi sokoto gurin kana na" Gyada kai yayi sannan yace. "Insha Allah" Daga nan ya bar gurin dan ya sallame shi, zuwa yayi inda motar da zai na kai Almamoon makaranta, yake ya duba yaga BMW ne, jinjina kai yayi sannan ya nufi sansanin su, ya saka sunan wani daga cikin su aka kira shi. Ko minti biyar ba ayi ba. Ya shigo tare da sara mishi. "Gashi daga yau aikin ka shine kai yaron da zai na kula da lafiyar Yallabai Mohan makaranta da duk inda yake buƙata." "Insha Allah" ya sara mishi, tare da juyawa ya fita..daga nan shima Malik ya haɗa kayan shi yayiwa Fahad magana, gyada kai yayi tare da rungume shi yana faɗin. "Allah ya baka sa'a" "Amin Abokina Nagode" suka tafa sannan suka bar gurin. *** Sake shirya kayana nayi, sannan na kalli Malam Ansar da yayi ciki ciki da fuska. "Wallahi karka sake abin duniya ya rinjaye ka" "Toh ai kai ma da abin duniyar ka janyo ni" na fada tare da gimtse fuskana, "Baba wannan Yaron ya rena ni, duk abinda nayi dan na kare shi nake amma ban da kwashe min albarka babu abin da yake." Ya gayawa Baba, "Almamoon bana son rashin kunya mana, me yasa ka rena malamin ka? Dan ya taimaka maka sai yayi laifi? Toh kul bana son haka, idan ka sake na kuma jin haka sai na sab'a maka" "Kiyi hakuri, kayi hakuri ba zan kuma ba" ya faɗa kamar zai fasa ihu, wuni ranar har dare suna manne a dakin baba. Washi gari da ya tafi makarantar, ya samu zasu fara jarabawa yayi rashin test da wasu abubuwan, dole zai maimaita wannan zangon da haka dake karatun a ranshi yake nan ya amince tare da yarda yayi duk abin da zai yi, yana tashi daga makaranta, ya nufi gida. Malam Ansar da kanshi yazo ya dauke shi suka nufi can gidan. Karfe biyu da rabi yayi mana. Kofar get din farko, dan haka ya kira mutumin , ko minti goma ba ayi ba sai gashi sun fito tare, da wani mutum, suna zuwa shi mutumin jiya yana sanye da kayan sojoji, sai jar hular da yake kanshi, yana zuwa ya mikawa malam Ansar hannu suka gaisa, sannan ya leka Ni. "Ban rike sunan shi ba" "Almamoon Isma'il Wodaadabe" "Ai kace Bororo ne?" "Eh haka nake tsammanin" inji malam Ansar, Bude min kofar suka yi na fito a hankali, ina kallon su. "Don Allah ku saka ido akan shi yaro ne, dan har yanzun bai cika sha tara ba, don Allah kar wani abu mara dadi ya same shi. Sannan Insha Allah zan ina zuwa duba shi" "Malik bashi Number ka, idan kazo ka kira shi, Insha Allah har cikin zai kai ka, Mamoon kai kuma mu wuce." .kasa tafiya nayi na tsaya a gaban shi, kwalla na cika daga idanuna. Riko hannuna yayi tare da kallon yadda nake kuka. "Baka son rabuwa da ni ne?" Gyada mishi kai nayi. "Me yasa?" "Babu" na fada ina jan dogon hancina. "Maza wuce Allah ya bada sa'a" ya faɗa min, kuka ne ya zo min na toshe bakina, haka suka sani a tsakiyar su, muka nufi inda wata mota take, wanda aka kira Malik ya bude min baya, juyawa nayi ina kallon Malam Ansar har. Na shiga motar, leken shi nake ta bayan motar, kwalla na zuba min. Kawai sabon da nayi dashi ne yasa haka, a hankali muka bar gurin ina kallon jami'an tsaron da aka girka a kofar gidan kafin ka shiga gidan ma tukun, Ashe ba karamin tafiya bace idan da kafa ne, kallon gidan nake me dauke da aljannar duniya duk inda muka wuce sake baki nake har muka isa cikin gidan sosai. Tun ban shiga gidan ba gabana yake faduwa, har muka shiga cikin gidan, a hankali suka shiga gaba. Ina bin su a baya har muka fada wata babban falo. Hoton wani soja ne yayi mana mara ba da zuwa gidan, ina d'aga ido na kalli hoton. Kamar wanda aka daki kahon zuciyata, wani irin bugu yake duk wani dakika jin shi nake kamar zai fasa kirjina, dafe kirjin nayi tare da saurin dauke idanuna akan hoton ba mamaki kodan kwarjinin da hoton yayi min me yasa na ji wannan yanayin a raina. Har muka fara haurawa sama, sake juyowa nayi na kalli hoton naga ya kura min ido, da sauri na bi bayan su da gudu, har suna juyowa. "Lafiya Mamoon?" Dakyar numfashina ya dai-dai ta, na girgiza musu kai. "Toh muje" haka suka kai Ni falon sama, sannan suka ce na tsaya. Suna shiga can sai gasu tare da mutumin hoton nan ne, Zuba mishi ido nayi, abu biyu naji a lokaci guda, wani mugun tsoron shi da kwarjin da yaji min, sai wani abu da na hango a tattare dashi, yadda ya kafe ni da ido ya sani sunkuyar da kai na kasa, jikin yana kerma sakamakon hango shi da nayi cikin fararren kayan barci. Zama yayi sannan ya kalle su, bai ma san me ke faruwa ba. "Yawwa Almamoon ga shi nan mara lafiyar mu, shi yake bukatar kulawa, wannan shine Malik zai taimaka maka a duk lokacin haka." Gyada musu kai nayi, domin ban san me zanyi musu bayan haka ba. "Kayi hakuri nasan kai dalibi ne ka iya abinci, sabida zan amshi kula da abincin shi a hannun masu yi na dawo dashi hannun ka ne?" "Na iya"na fada ina kallon kasa, "Shi kenan, and ka kula da lafiyar shi don Allah duk sauran bayanin yana gurin Malik. Shi zai taimaka maka" Haka ya mike tare da mika min hannu, kasa karb'a nayi sau da ya kuma min alama na mika mishi a karon farko a rayuwata da nayi haka dan ko da nake makarantar ban tab'a yarda ba, amma yau nayi. Sai naji kunya ya addabi ni, har ya fita sannan Malik yayi mishi rakiya. "Ka ciro kudi ka kai shi ya zab'i kayan da ya dace da shi, wancan kayan da ya saka sai kace wani Bugaje,. Ka nima mishi kananun kaya masu kyau da tsada, sauran kuma a hada mishi da takalmi da duk wani abun da zai fito dashi gari. Zaka iya tambayar shi dai ka sayo mishi. Haka suka tafi suna tattaunawar... Baya bata da kaɗan. Wato suna barin gurin, kaina a sunkuye, ba zan iya fahimtar yadda abin ya faru ba, amma tabbas sai dai nake kamar ba a duniyar mutane nake ba, domin wata irin shaƙa da Mutumin yayi min, ya sani fara ganin wata duniya na daban. Gashi ya danne ni akan kujeran, kamar zai kashe ni. Wutsul wutsul nake, kafin Allah ya bani nasarar buga mushi kararrawan sadarwan shi, zuɓewa yayi a kaina tare da dauke wuta. A lokaci guda muke kallon idanun juna, lumshe idanun shi yayi tare sake jikin shi alamar ya suma a jikina, wallahi gashi kaman gumgumemmen dutse, kasa motsi nayi.. a hankali na kuma kallon fuskar shi, naga yana lumshe sai kwalla da take bin fuskar a hankali yana diga a daidai saitin zuciyata. Kasa jan numfashi nayi, tare da jin wani abu ya cika min wuyana. A hankali na shiga janye jikina, amma kamar bana kome, gaskiya mutumin nan kato ne, dakyar na iya d'aga hannun shi da kanshi, shigowar Malik yaga yadda nake kiciniya sai da ya tintsire dariya, har yana nuna ni. "Sannun Kaji, da fatan bai maka kome ba?" "Da yanzun sai dai wani ba ni ba domin shake ni yayi zai kashe ni." Na fada kwalla na zubo min, "Kayi hakuri" Yazo ya had'a karfin shi guri guda ya dauke shi tare da sab'a shi a kafada,"biyo Ni" da sauri na ji bayan shi. Muka shiga cikin ɗakin.. haka kawai naji kaina ya sara, ina jin wani irin kauri kamar an gasa wani abu, kallon dakin kake naga yana fidda wani irin hayaki, me dauke da bakin duhuwa, lumshe idanuna nayi ina kallon yadda dakin yake fidda wannan yanayin. Hatta shi ma hakan ce,.da sauri na fita ina dafe kai na. "Mamoon" zuɓewa nayi akan kujera kamar danyen nama, ina sauke wata irin ajiyar zuciya, kafin wani lokaci zazzaɓi ya sauko min, "Mamoon" ya kuma kwala min kira. "Na'am" sai ga amai, sosai nayi ta kwarawa a falon, kafin na iya rarrafawa zuwa d'akin. "Ina ka tsaya? Baka da lafiya ne?" "Eh.." sai ga Amai, wani irin wari da dauyi yasani kwara amai. Kafin kace kwabo, zazzaɓi da wani irin firgita ya kamani, haka nayi ya dungure a dakin shi kam Malik komawa yayi gefe yana kallon ikon Allah. Sai da na kai minti talatin kafin na bude idanuna. "Ciwon shi nan ba daga Allah bane, ciwo ne na mutane." Na fada muryana yana rawa, Kura mishi ido muka yi, a hankali ya tako inda nake yace min. "Kamar Ya? Ban gane ba?" "Nima abinda ban gama fahimta ba kenan, amma don Allah karka bari a sani, Allah ya bashi lafiya" Ni kaina ban san me ya kai ni irin wannan katob'arar ba, sai dai na tsinci kaina da yarda da Malik din ne zuciya daya, shi yasa na gaya mishi. A hankali na gyara saman tsaf sannan na share ko ina, na saka wasu turaren zamani na gwangwani.. Sannan na kalli Malik nace mishi. "Kar mu kuma barin shi babu alola, ya zama jikin shi kullum da alola" "Amma kasan me? Wallahi nima tun farkon ciwon na fara zargin ciwon kamar ba ta Allah bace" Nan muka yi ta hira akan matsala duk da kasancewar shi ba me yawan magana ba. Bayan mun gama mishi alola, kallon shi nayi, ina kallon fuskarshi naji kamar an dake ni, sai da na kusan faduwa, sabida kwarjininsa, ga wani uban kyan da yake cika min idanuna. Fuskar shi nan kamar madubi, har hango shi nayi yana kyalkyali, da sauri na fice a d'akin. Ina hararan shi, ko yaushe na fara jin wannan shirin oho, haushi ma ya bani Dan ta cika kyau dayawa, na tsani namiji kyawawa. Tab'e baki nayi ina me jin haushin kaina, daga yanzun ba zan kuma yarda zuciyata ta buga akan wannan katon basamuden ba, mutum sai kace wani katon bishiyar kuka. *** Malam Ansar. Ya kai minti talatin a cikin motar shi bai tadda ita ba, dan ji yaƙe kamar zai tafi ya bar zuciyar shi a gurin, ya zaune ya kifa kanshi da sitiyerin motar, yana ji kamar ya shiga ya dauko Almamoon, yace ya fasa aikin. Ji yaƙe kamar ya kira Shugaban jami'ar yace sun fasa, amma baki daya bashi da confidence din yin haka. Bai san waye din shugaban kasa ba. Amma daga nan ya fahimci wanda yake cikin gidan ba karamin mutum bane. Ya kwana da sanin cewa sojoji basu da mutunci, yanzun kana musu wata shirme zasu sake maka wuta, shi yasa ba zai iya daukar kasadar komawa gidan ba, balle su bude mishi wuta, har Dan Ba'are ya wuce yana nan a gurin. Murmushi yayi a karo na farko da ya tuna yadda Almamoon yake tura mishi bakin shi alamar dai yaji haushin abinda yayi mishi. "Ina son Yarona".ya faɗa yana tadda motar. Ya bar kofar gidan cike da kewar Mutumin nashi.... Kusan weekend sai a hankali... Ayi maneji [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu BOOK ONE... Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza BABI NA SHA HUƊU. Kura mishi ido nayi ina mamakin zafaffawar shi a gare ni, ai ko babu kome ban cancanci ya jagorancin zuciyar shi a kaina ba, amma baki daya ya kasa fahimtar kome akai na. "Wai tsaya ni d'anka ne da zaka na sani abinda ban yi niyya ba? Ko kuma ajiyata aka baka ban sani ba? Inda kuma babu kome a tsakanin haka toh ka tsaya a malamina, bana son" Shanye da toka na harare shi,.domin ya fara wuce gona da iri. "Meye kake nufi? Wato ban isa nayi magana akan ka ba? Dan ka shigo inda baka saba gani ba? Kwaɗayi y kawo ka mata maza? Ai kowa yasan kai mata maza ne" "Idan rai ya b'aci bai dace hankali ya b'ata ba, Almamoon tashi ka bar gurin" inji Malik, Juyawa yayi ya kalle, Mikewa nayi ina kallon Malam Ansar, idanuna cike da kwalla. Sannan na wuce ban ce mishi cikanka ba, har zan haura step yace min. "Almamoon karka manta waye kai?" "Na sani! Na sani!! Ni din ruwa biyu ne shi kenan? Na san waye ni ba sai ka gayawa duniya waye ni ba, nasan matsayina da Matsala ta, don Allah ka daina cutar dani akan matsalar da kasan ba ni na halicci kaina da shi ba." Tura Ni Malik yayi na wafce kafadana, tare da kallon Malam Ansar Idanuna yana cika da kwalla, kamar wanda aka rike min baki. "Nagode sosai" na fada tare da barin gurin ina me jin wani irin kuka, amma haka na hadiye, ina shiga dakin da Hamma Mohan yake na nime b'acin rai din na rasa, yana tsaye a jikin window. Ya zuba hannun shi dukka biyu cikin aljuhun wando shi, yana kallon movement na tsuntsaye, sanye yake da riga da wando masu bala'in kyau grey color, sai hadaddiyar gashin kanshi da ya sauka a dokin wuyar shi,he look gorgeous, gashi yayi wata irin tsayuwar da ba zaka tab'a dauka bayi da lafiya ba. Motsin da yaji ne ya sashi juyawa, kafin ya koma kan abinda yaƙe. Daukar ruwan addu'o'in da yake sha nayi na mika mishi. Sau daya ya kalle ni sannan ya kuma dauke kanshi yana kallon yadda tsuntsaye suke shawagi. "Karb'a Hamma Mohan" Dake babu lafiyan bai ko motsa ba, haka ya cigaba da tsayuwa har zuwa lokacin da na isa gabansa, sai na ganni kamar irin a saka dan tsako a gaban giwa, duk sai na kasa tabuka kome, ina me mika mishi magani, ina kuma fatan ya sha, amsar maganin yayi sannan ya kalle ni, irin kallon nan na marasa lafiya. Kai hannuna nayi tare da tura mishi maganin bakin shi, gumtsa yayi sannan ya furza min a fuskana, sannan ya kwashe da kakkarfa dariya, yana kallona. Kamar na fashe da kuka, haka nake kallon shi. "Zaka gani ba zan kuma wasa da kai ba" na fada mishi ina jin kwalla na taruwa a idanuna, Hankad'a ni yayi na fadi can sai da bayana ya amsa,kallonshi nake kamar zanyi kuka. Wato shi ko a jikin shi sai dariya yaƙe kamar zai shiɗe, haka na bar mishi gurin na fita na koma dakina, sauya kayana nayi tare da kallon kayan da ya zuba min maganin. Duk abinda zai min bai tab'a min ciwo ba, duk abinda zai min baya min zafi, asalima Uzuri na zab'i na mishi a rayuwar shi, domin kuwa ai bai da lafiya. Murmushi nayi tare da kallon kofar. --- A fusace ya bar gidan, zuciyar shi tana zafi, a bakin kofar fita Malik yayi mishi magana. "Tsaya malam" cak ya tsaya, "Meye matsalar ka da Yaron nan ne?" "Tambaya kake nima sani?" Cikin isa da sanin waye shi yace mishi. "Gidan nan cike yake da sojoji, tabbas akwai matsala idan ka kuskura kayi wani shirme mara fa'ida, tambaya na da kai na karshe meye matsalar ka da yaron ?" Cikin karfin hali ya kalli idanun Malik yace mishi. "Ka je ka tambaye shi" ya juya tare da barin gidan, sam Malik bai wani damu can ba, amma kuma kalmar Almamoon ya tsaya mishi a rai. _Na sani na sani na sani, Ni ruwa biyu ne?_ shafa kanshi yayi yana jan iska a bakin shi tabbas akwai abinda yake faruwa a tsakanin su. *** Aiki yake bayan ya cire hular shi, duk da ya maida hankali akan abinda yake haka bai hana shi kara hango gizon Mamoon ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon abin da yake a Laptop din shi, amma ba fahimta yake ba tura na'urar yayi tare da dafe kanshi. Idan ya fahimci yanayin da yake ciki, lumshe idanun shi yayi na wasu few seconds, kafin ya bude akan na'urar wanda yake ganin kamar hoton Almamoon ne shimfid'e a kai. Murmushin sa yanayin Yaron kamar ba namiji ba, dafe kanshi yayi tare da mik'ewa yana me bude firjin din kusa dashi ya dauki goran ruwa, ya bude bakin ya kafa kan shi sai da ya sha rabin goran, kafin ya d'ago kai yana me bude window Office din shi da yake inda ake koyawa sabin sojoji training. Ltn Khalil Ibrahim Dan Ba'are, yana kallon yadda wani matashi yake ta ƙoƙarin, sai ya tuna mishi ranar da suka bar Almamoon a asibitin. Abinda ya tsaya a ranshi yadda yaron yake zubda kwalla, tare da nuna cewa yana son zama da Mohan. Shafa kanshi yayi tare da kurawa hoton Mohan idanun. Yasan Mohan sanin gaske koda ua dawo hankalin shi bai zama dole ya kula da Almamoon ba. D'aga wayar shi yayi tare da kiran Malik bayan Malik ya dauka sai da ya Lumshe idanun dhi kafin ya sauke ajiyar zuciya. "Ya Mohan da jikin?" "Yallabai da sauki sosai" "What about Mamoon?" "Gashi can" "Ok bashi" "Toh" Yana jin lokacin da Malik yake kiran shi, "Hamma Malik waye ne?" Ya tambaye shi yana me daura wayar a kunnen shi. "Mamoon!" Ya kira sunan shi sound tone. Kamar ba zai iya kiran shi ba. "Hamma Na? Ya aiki? Baka zo mana ba" Cikin wani irin farin ciki, Dan Ba'are ya shafa kanshi yana faɗin. "Cuter Brother zan dawo, Insha Allah ya jikin Mohan?" "Jikin Hamma Mohan da sauki sosai, kuma dai ya daina firgita. Sai dai toh Allah ya kyauta" "Gaya min meye?" Ya tambaye shi yana murmushin jin dadi, shima Almamoon murmushin yayi sai da Dan Ba'are ya cire wayar a kunnen shi, yana jan ajiyar zuciya, sannan ya saka wayar a record, ya maida kunnen shi. "Almamoon! Gaya min meye yake faruwa?" Ya tambaye shi a daukence, "Hamma ai babu kome," Ware idanun yayi kamar yana gaban Almamoon. "A'a gaya min dai" Ya fada da wata irin murya yana murmushi, "A'a fa Hamma na, kawai Hamma Mohan bai jin magana, idan ka zo sai yayi tsallen kwado sau goma, kuma dama d'azun na rike mishi kunne, sai na mishi bulala da tsintsiyar kwakwa." Zaro idanu yayi tare da cewa. "Mohan Mamman Nasir Aghali din zaka zane?" Ya tambaye shi yana dariya, kamar wanda yake gaban dan Ba'are ya shiga kunkuni. "Toh ka san meye yake min?" "Gaya min ina jinka?" "Yawwa wancan ranar zuba min magani yayi a jikina, jiya kuma ture keyata yayi na faɗi, yau kuma ina tsaye kawai sai naji ya dauke ni sama, gaskiya yaci na mishi duka." Wani irin abu yaji yana dukar kirjin shi. "Amma bai maka kome ba ko?" Ya tambaye shi kirjin shi yana bugawa very faster. Shi Almamoon bai fahimci ma'anar tambayar ba dan haka ya kwashe da dariya yana faɗin. "Ai yayi min kome, shi yasa nake son kazo muyi mishi bulala domin ya daina min haka" Kasa magana yayi jikin shi har wani rawa yake. "Hammah na kayi shiru baka ce kome ba?" Yadda yayi mishi tambayar yayi mugun kashe mishi jiki, kuma dama ga muryan Almamoon ba irinta maza bace. "Hmm" yace mishi, shima Almamoon ya sake murmushi yana faɗin. "Hammah na zan tafi na kula da abincin" ganin zai kashe wayar yayi saurin mishi magana. "Almamoon! Don Allah ka kula da kanka." Shafa kanshi yayi sannan kuma cigaba da cewa. "Karka yarda wani kazamin wasa ya shiga tsakanin ku, ka tsaya a mai kula da lafiyar shi, please" "Toh shi kenan" ya fada a sanyayye, "A'a ban ce karka kula da shi ba fa kawai ka kula da yadda kuke mu'amala ce, bawai ban yarda da kai bane na yarda da kai, dan haka ka kula da kanka" "Toh babu damuwa" suka yi sallama, Malik yana amsar wayar ya shiga masifance shi. "Tsabar shashancin taya zaka bar yaro nan shi daya yana kula da lafiyar Mohan? Baka san nauyin zai mishi yawa ba? Karka kuma bana son haka, ka saka ido akan su, Allah ya bashi lafiya" "Am sorry Yallabai" ya faɗa kamar yana gaban shi, "Ya Wuce" sannan ya kashe wayar shi, yana kuma hasashen yadda Mohan yake kokuwa da Almamoon, dukar tabirin gaban shi yayi yana me jin babu wani dad'i. "Toh me yasa nake jin babu dad'i? Me yasa nake jin kamar ana cutar da yaron?" Dafe kirjin shi yayi da yake bugawa kamar me, Kafin ya dauki sauran ruwan shi ya sha, yana jin kamar zuciyar shi zata kama da wuta. Shafa kanshi yayi ta yi, yana kuma sauke ajiyar zuciya. Wannan wacce irin jarabbtace haka? Zama yayi tare da kallon sama, yana nazarin meye yake shirin Faruwa da shi, a iya sanin shi dai Almamoon namiji ne irin shi? Kuma bayan haka babu wani abin da zai alakanta shi da mace, dafe goshin sa yayi da yatsu biyu na hannun shi. "Ina ruwan mahaukaci, kowa yaji labarin nan sai an nemi saka ni a turu, dariya ne kuma ya kama shi yana yi yana shafa kanshi, Tabbas ya cika babban mahaukaci, duk me hankali yaji abinda yayi sai yayi dariya balle kuma kuma mahaukata yan uwan shi. *** Wasu manyan mutane ne su uku, suka shiga wani sunkurun daji, bayan sun yi tafiya me nisa, kafin suka fara nufar wata tsohuwar hanya. Sai da suka yi tafiya me nisa, suna jin kukan wasu irin dabbobi masu matukar ban tsoro, wata siririyar hanya ce da zata kai su wani gada, haurawa suka yi, kowa yana nad'e babban rigar shi. Suna isa bakin kofar wanda yake sakale da Kwarangwal din mutum, suka shiga cire kayan su, tare da kwab'e kome na jikin su. Haka suka shiga cikin gidan, inda wasu yan mata suka taso musu da kwarya a hannun su, suka yi ta zuba musu wani irin ruwa, a saman kansu, kafin suka zuba gwiwar su a kasa, aka kuma basu wani irin ruwa suka shanye tass, rike hannun su yan matan suka yi har zuwa kofar dakin da bokon yaƙe. "Ina la'annnu suke? Ina marasa rabon suke? Ina tsinannun la'annnu suke? Ina marasa rahama suke, Ku zo ga la'anannen arnen nan a gaban ku." Dariya suka saka tare da shi, sannan suka shiga d'akin, tare da zuɓewa a gaban shi kamar masu sujada, kallon shi suka yi ganin wata budurwa kyakyawa akan cinyar shi, yana having sex da ita, duk da ya tsufa bai hana shi jin kanshi kamar wani matashi ba. Kallon juna suka yi, kafin yan matan dazun suka shigo dama suna sanye da wata fatar bauna na ya rufe musu gaban su, sai ganye da suka rufe kirjin su dashi. Suna shigowa suka wuce gaban su, tare da kallon su. Kowacce ta zauna akan cinyar mutanen a hankali sukayi ta kazamar mu'amalar su a gurin, kafin suka fara kokarin zubda ruwan kazamtar su, dan shi ya riga su gamawa, yana tashi ruwan shi da na yarinyar zubawa yayi a wata tasa,.mai fadi na zinariya, suma haka suka juye nasu a tasar, kafin Yan matan suka dauki wani irin abu kamar ludayi suka saka a gaban su, ruwan ya fito, suka juye a tasar, kana suka fita a d'akin. Tura tasar yayi can lungu, suna kallon gurin wani katon guza ya fito a hankali ya saka kanshi yana lasar kazamin maniyyin su. Yana gyada kanshi. Irin dadin da yake ji. Kara watsa wani abu yayi akan guzar,ya cigaba da lasar maniyyin su, har ya shanye tass. Ya koma lungun da yake, kallon su yayi. Tare da gyada kanshi. Jinjina kai yake yana kara jin wani irin gamsuwa, kafin ya kalli manyan mutanen. "Har ni za a lalatawa darajojina?" Watsa izgar yayi tare da kura mishi ido. Wata uban kara ya kwala tare da mik'ewa jikin shi yana rawa. "Waye haka?" Hoton Mohan da Almamoon, suka kokuwar zai bashi magani, bayan ya sha, ya fadi aka cilla Almamoon gefe, dakin ya dauki duhu, can sai ga Mamoon ya saka karatun Alkur'ani a wani radio, ihu da aljanun da suke tare da Mohan suke tare da yagar kamar jikin su, suna watsarwa. A tare bokan ya kuma tura wasu aljanu, basu kai da shiga cikin gidan ba, suka dawo a guje. Karshe da ya nace sai ya tura wannan guzar ce ta kuma fitowa tare da sake wata irin kara kamar karan Aradu. Cikin fusata da b'acin rai ya shiga aikin babu kama hannun yaro, yanayi yana watsa wata irin mai me kama da jini, yana karanta ɗalasuman tsafi..watsa manyan yaƙe, Zunzurutun taurin kai da bala'in zafin rai yake aikin domin gani yake idan ya kasa tankar ya gaza ne, taya za a cigaba da zuwa gare shi? Taya zai iya fuskantar mutane da cewa anyi galaba akan shi. Ina karya ne! Watsa man yayi wata irin koriyar wuta tayi sama sai da yaja da baya, take ya kuma dawowa cikin ƙwayar tsafin ya zauna. Yana yi yana juyawa. "Karya ne! Ba haife su ba, basu isa ba, da Ni zasu ja? Har sun kai matsayin da zasu buga dani?" Ya nuna kanshi s fusace yana aikin,.yaki ya saduda dan haka wutar tayi kanshi da karfi, dole ya juya tare da matsawa da baya. Cikin mugun tsoro sannan wutar ya kuma komawa cikin ƙwaryan. Ranshi ne ya b'aci, ya shiga aikatawa su Almamoon da wasu abubuwa da ban tsoro, yana kuma diban ruwan jini a wata kwarya ya bude wata kwarya ya saka hannun shi, kwari da tsutsa ya kwaso, ya zuba a cikin jinin nan yana karanta wasu mugayen ɗalasuman tsafi, munana ya d'aga ƙwaryan sama. Wadanan kalaman har da wasu kalmomin Arabia, tare da sunan Allah, kafin ya sake ƙwaryan a tsakanin sama da kasa, yana ambaton sunan Allah.(Look da gaske akwai kitabul sihir, na niman mallakar manyan ifiritai. Dan haka a sani akwai kalmomin sihiri wanda yake basu damar mallakar djinn) Su kansu masu nima a gurin shi hankalin su ya tashi, balle shi da yake aikin ba karamin bala'in wahala yake ci ba, kuma yaki ya nuna yana cikin damuwa, sai da ya sauke wannan shaidanin aljanin me kai kamar na maciji ta tura shi, sannan ya mishi magana akan lallai ya tafi ya shiga jikin Mohan, ajiyar zuciya ya sauke bayan aljanin ya shiga cikin ƙwaryan, ya cigaba da had'a wanda zai hana yana kallon ƙwaryan. Bayan kamar mintinan ƙalilan, sai ga dakin da suke yana girgiza, kamar za a fasa dakin, duhu ne ya mamaye d'akin, kafin wani abu ya fado dakin kamar wani katon dutse dif.... Ya dira a gaban su. Huuuhuuuuhuuuuu!!!!" Ya fashe da kuka, yana ihu yake yana burgima. "Karkuzu ka aike ni gurin da aka lalata min jikina wayyo ni, wayyo ni rayuwata." Burgima yake. "Tashi munkiri tashi mara kunya, har akwai mutanen da zasu ja dani?" Da sauri ya b'ace rashin a b'ace. Ya kalli Mutanen cike da bakin cikin yana me jin wani matsanancin kunya da faduwar darajar shi. Ya nuna musu hanya tare da dauke kai yace. "Ku dauki ƙwaryan jinin da zaku gani a waje ku had'a tare da jaririn mage da kuma jinjirin jaki ku binne su da ransu." Haka suka mike tare da mishi sujada, sannan suka fita da bayan sun. Suna fita yan matan suka wanke su da ruwan bayan sun basu wasu kananun kwarya me dauke da jini. Kafa kansu, suka yi sai da suka shanye tass, sannan suka yi gatsa. suka fadi bukatar su tare da yarda akan shi zai iya musu, tare da barin gurin, suna isowa suka kwashi kayan su, suka bar gurin. *** Yau kam yafi ko yaushe bani wahala, domin kuwa ban tab'a jin ko ganin tashin hankali ba tunda na bashi maganin, nake tsaye a bakin kofar. Cak naga ya mike kafin kuma ya fara amai, yana yi yana jijjiga, shigowar Malik ya sashi kura mishi ido shima, yana mamakin wannan al'amarin. Can ya fasa ihu, wanda ya sa dakin ya amsa. Kwanciya yayi yana burgima. Kafin ya fara karkarwa can kuwa sai ga dakin ya kama jijjiga, karatun Alqur'ani muka kunna, haka muka yi tashan wahala kafin can ya lafa, bayan ya gama gwara kan shi a bango. "Alhamdulillahi" inji Hammah Malik, ajiyar zuciya na sauke ina kallon shi, kafin nace mishi. "Da saura fa, dan har yanzun bai dawo hayacin shi ba. Ina jin sai mun had'a da limamin masallacin Makarantar mu ne Insha Allah" "Eh toh Allah yasa a dace." "Amin Ya Allah," muka bar dakin bayan mun gama gyara mishi kwanciyar hankali. * Wannan karon kudina ma gida na kai, sabida ban tafi hutu ba ne zauna a jikin Hammah Mohan, koda naje gidan Innah ta kasa ta tsare. Sai dai itama kamar Malam Ansar ce domin kuwa ce min tayi. "Karka ganka cikin gidan kudi kayi tsammanin Allah baya ganin ka ne, kasan waye kai ka kuma san yadda halittar ka yaƙe, karka sake naji wani abu ya fito, ka kame kanka domin masu kudin nan ba kirki ce ta wadacce su ba. Domin na lura da kwaɗayi na damun ka, nan Malam Ansar ya kawo min korafin rashin mutuncin da kake mishi Almamoon!" Ta kira sunana. Cike da tsoronta nace mata. "Inna shima me yasa baya jan girman shi. Sai ya" Kai mun duka tayi abinda bata tab'a yi ba, sabida Malam Ansar tayi min. "Kai min shiru butulu kawai, kasan kanka ai, kuma da yake kwadayi ya rufe maka idanun." Idan na fahimta malam Ansar yazo ya had'ani dasu Innah ne, lallai ka bar mutum a inda yake, ban yarda nayi wani abinda zai saka tayi fushi ba, na kwantar da kaina nayi ta bata hakuri, har ta sauko. Muna cikin ji Baba ya kawo min maganin da zan cigaba da bashi. "Assalamu alaikum! Sannun ku, Mamoon kana ta jirana ko?" "A'a kawai dai zan isa da wuri yasa na kagu." "Toh Toh,,, gasu nan dai sai dai ban sani ba ko zai amince ya ci, wannan garin maganin Insha Allah idan ka karanta suratul Yasin, zaka tofa ko ka rubuta mishi, sai wannan zaka had'a zuba a wani mazubi me kyau kayi ta bashi yana sha, wancan me suratul Yasin, duk wanda yayo mishi sharri zai koma kanshi kaikayi kenan, wannan kuma suratul Rahama zaki karanta mishi, duk inda aka nufi shi da sharri zai kasance yana kaucewa ba tare da ya sani ba. Wannan kuma Insha Allah zai kasance mishi kamar a saka wani abu ne s jikin shi, babu karfe ko itaccen da zai yi tasiri a jikin shi. Wannan kuma Insha Allah zai taimaka mishi gurin, gano duk me shirin cutar dashi, Allah yasa mu dace" Haka bayan mun gama na ce mishi. "Baba dama maganar gidan fa?" "Eh Almamoon mun gama kome sai dai muje ka gani, ko kuma." "A'a muje dai" na fada mishi, haka muka tafi gidan, muka duba yayi kyau kuwa, ba laifi daga nan muka sami me gidan muka zanta dashi tare da cewa. "Kayi hakuri Insha Allah nan da kwana ashirin zan kawo maka kudin ka, Nagode" "Karka damu, Allah ya kai mu lokacin." Haka ya faɗa tare da rufe gidan, Ni da Baba muka nufi tasha. Bayan na sami motar Maradi muka yi sallama da Baba na Danka mishi kudin hannuna dukka, sannan na shiga dama kamar ni ake jira. ** Isar dare nayi dan haka ban yi gangancin nufar gidan Hammah Mohan ba, na nufi gidan Malam Ansar domin zan kafta mishi rashin mutinci. Ina shiga na samu Baba tana sallah isha, zama nayi bayan nace mata. "Wash tsohuwa bayana" Tana idar da sallah ta mike tana murmushi. "Sannun Angona, yau kai ne a gidan mu?" "Tsohuwa gani nan dai" Ban daki ta shiga ta hada min ruwan zafi,sannan ta fito. Na shiga nayi, ina fitowa ta ajiye min abincin da man shafawa me gurguwa. A hankali na shafa sannan na zauna muka shiga hira muna gaisawa. "Daga ina kake?" Tsam nayi da hannuna kafin nace mata. "Naje ganin gida ne." Kura min ido tayi kafin tace min. "Wani gari?" "Damagaram" "Almamoon kana dauke min kewar Y'ata, maganar ku tafiyar ku, murmushin ku.. Almamoon idan. A ganka sai naji ina ma kai jininta ne, duniyar nan cike yake da azzalumai marasa imani, ya shigo ya lalata min rayuwar Y'a yasa kowa ya guje ta. Kimanin shekaru goma sha tara kenan rabon da naji muryanta. Ina kewarta saboda ita na kasa komawa ko ina, na kasa bin mijina da Yarana na kasa komawa Libya gurin dangina. Ina kewar Zainabu." Rike hannunta nayi domin ta bani tausayi, nace mata. "Me yasa mi Addah Zainabu?" Kwalla naji ya cika min idanuna, "Wasu daga cikin kabilar Fulani suna da wata muguwar al'ada wacce matukar ta faɗa kanka shikenan. Rayuwar mutum ya lalace" "Baba Mari wata al'ada ce haka? A'a Almamoon kai ne yau a gidan mu" Juyawa nayi na watsa mishi kallon banza, kafin na mai da kaina gurin Baba Mari. Da take kuka. Nima tsintar kai na nayi da kuka domin duk yadda aka yi labarin ba me dadin ji bane. Hakuri muka yi ta bata, har tayi shiru. Sannan ta gaya mana muguwar Al'adar fulanin, kallon ta nayi cikin rawan jiki nace mata. "Baba kina nufin da auren wani akanta ya dauke ta yayi zina da ita?" Na tambaye ta kuka na kwace min. Domin am very shock, tana matar wani zaka kwanta da ita? Taya zaka iya zama da matar aure bayan kasan igiyar wani na kanta, ban san me yasa na tsinci kaina da kuka kamar Ni aka yi wa laifin. Dan ma taki ta gaya min sauran abinda ya faru. Shima Malam Ansar haka ne, jikin shi yayi mugun sanyi. "Almamoon zo na baka sakon ka" kamar ba zan taso ba, na mike domin ina cike da shi kuma na sami yadda zan kafta mishi rashin mutinci, muna fita ya tsaya a gabana. "Ya isa haka kukan nan, meye ya kawo ka nan?" "Kai me yasa baka gane bayani da Yaren da muke yi? Me yasa ka je ka sami Iyayena da maganar da tsakanina da kai ne? Kai baka da lissafi ne? Kome aka ce nake gayawa Iyayena? Nasan ciwon su da darajar su, karka kara zuwa gaban iyayena da maganar banza domin idan ka kuma zan baka mamaki dole ne sai nayi alaka da Ni? Wallahi ka kuma duk abinda na maka kai kasayawa kanka, duk abinda kayi min ban tanka maka ba, sabida bana son damuwa amma akan iyayena wallahi za a jimu da kai domin na nasan darajar iyayena, shine abinda ya kawo ni gidan ka, kuma zan kwana gobe na wuce don't think that ko ban san me nake yi bane ina sane dashi ka fita idanuna" Na fada zan juya riko hannuna yayi tare da matse ni a jikin motar shi. "Ban ji kome ba, ban ji haushin ka ba, sai ma burge ni da kayi. Amma kasan me? Zo na nuna maka wani abu." Jan hannuna yayi har cikin gidan shi, ya kunna Laptop ɗin. Yana me nuna min wasu abubuwan. Kafin yace min. "Ina ta tura musu sako ne, sabida matsalar ka, kayi Hakuri nayi laifi zan k'iyayye gaba, amma is very important ayi maka aikin na. Domin kafi karfi ta jinsin mata." Cikin tsannanin takaici nake kallon shi kamar zan fasa ihu. "Toh impossible" na gaya mishi tare da barin falon shan gaban yayi tare da had'a hannun shi guri guda. "Please and Please listen to me, idan na kawo maka zancen shirme kayi tafiyar ka, amma abinda zanyi yana da matukar muhimmanci a rayuwarka." "Look ba zan yi ba, kuma idan ka nace sai na maka abinda ba ka zata ba, dalla bani hanya na wuce ban tab'a ganin mutum me mugun shiga abinda babu ruwan shi ba sai kai. Ina ruwan ka da lifestyle dina? Meye matsalar ka sa rayuwata? Ina ruwanka dani ne? Yes Ni mata maza ne, doesn't mean you have right to enter my personal life. Kayi rayuwarka nayi nayi nawa dole ne sai ka shiga rayuwata? Don Allah don Allah don sanka da Allah ka rabu dani" "Dan ban da arziki? Kodan ban da kome?" Ya tambaye ni a sanyayye, takaici ya sani rike k'uguna da hannu bibbiyu, ina kallon shi. "You see, ji abinda ka fada? Ji abinda ya fito daga bakinka? Kalli kalaman ka marasa dad'i da kyau. Yayi maka idan ka dagama kayi tunanin kome a kaina tunda baka san yadda ake gudanar da rayuwa ba, kana tare dani but kana drag din rayuwata." Na juya a fusace zan fita. Jin shi nayi ya wani k'amk'ame ni, kamar wani zai kwace mishi ni, "Don Allah don Allah karka tafi Almamoon, nasan za ayi nasara akan aikin da za a maka." Kasa motsi nayi ina matukar tausayin shi, amma bawai ina jin shi bane a raina. Zare hannun shi nayi tare da juyawa nayi ficewa ta, daga falon. Idan na cigaba da zama zan iya kafta mishi rashin mutinci. Dan haka ina fita na nufi dakin Baba Mari, na kwanta. *** Tun da Almamoon ya bar gidan, yake zaune a bakin kofar shiga gidan, ya zuba tagumi hannu bibbiyu, yana kallon ta inda zai fito. Duk sun zagaye shi, domin sun san Almamoon kawai yake jira. Har dare bai tashi ba, yana gurin Malik kuma baya nan, dan haka babu wanda yayi tunanin sashi yayi alola ko sallah kamar yadda yake kullum, tunda ya zauna yake kallon kofar harabar. Har dare ya raba, yana zaune a gurin. Yana ta gyangyadi, wasu irin kukan abu yaji ya bude idanun shi, bai ga kome ba, dan haka kamar yaro karami da ya rasa uwayen shi haka ya mike tare da shiga falon gidan, ya zauna a saman center table dake na Kwalba ce me ƙarfi. Haka ya zauna kamar maye har kusan asuba, kafin barci ya dauke shi a saman gurin. Washi gari masu aikin gidan ne suka ganshi a gurin. Tsoro ya kama su, dan dole suka hakura da aikin domin sun san idan Malik ko Almamoon. Yazo zasu sha wahala musamman Almamoon ma baki daya yake shuka musu tijara. *** Ina sallah Asuba na tashi, tare da shirya kayana. "Sai yaushe?" "Insha Allah zan na zuwa Asabar da lahadi." "Toh Allah ya nuna mana" haka na tattara na bar gidan, domin bana son na hadu da Malam Ansar, zai iya karya min zuciya, jiya kwana nayi da tunanin shi, sabida yadda yake damuwa da ni. Sam Ni ban damu dashi ba. Amma shi ya daurawa ranshi damuwa a kaina. * Na isa gidan lafiya. "Assalamun Alaikum" Zubur ya mike tare da zuba min ido, tashi yayi ya juya tare da nufar sama da gudu, irin ta me cikakken kuzari, yake tsallake step by step, har ya haura dakin shi, bin bayan shi nayi da kayana na ajiye su a d'akina. Sannan na nufi dakin shi yana gani na ya dauke kanshi. Takawa nayi har gaban shi. Juyawa min baya yayi, durkusawa nayi a gaban shi tare da riko hannun shi. "Kayi hakuri na dawo da dare ne sai ban karaso nan ba, muje na baka abincin kaji" Daura kanshi yayi akan cikina, tare da k'amk'ame ni, wani irin abu naji ya mike a jikina yarrrr, da sauri na ture kanshi, ina me kallon kofar. Daidaita tsawo na nayi ina kallon shi. A karon farko da kwayar idanuna ya faɗa cikin nashi. Wani irin abu naji yana shiga cikin nawa, lumshe idanuna nayi tare da jin wata irin faduwar gaba. Lashe bakin shi yayi yana me kumshe idanun shi, janye idanuna nayi akan shi, tare da mik'ewa, kawai naji ya riko hannuna. Kallon shi nayi bakina a sake, na kasa magana sai sunkuyar da kai da nayi. Zuciyata tana wani irin bugawa da sauri da sauri. Kwace hannun nayi ya kuma fisgo ni, tare da yi min dabaibayi da hannun shi. Ina son nayi magana amma baki daya kome na bakina ya kare, ga wani iskar da yake cika min bakina, kwalla ne suka cika idanuna. Dakyar Allah ya bani sa'a na kira sunan shi da cewa. "Hammah" Lumshe idanun shi yayi yana me kara rike ni gam a jikin shi. A hankali ya birkitani daga gaban shi zuwa saman gadon. Wani abu naji ya daki kirjina. Ina ƙoƙarin mik'ewa ya kuma danne ni. Sai na tuna wani hira da naji a gidan Radio BBC Hausa da Baba Yake sauraro. inda me tambaya yake cewa a hada shi da likita yayi mishi bayani shin mahaukata suma suna da sha'awa akan mata ko maza. Nan likitan ya yi bayani tare da cewa. "Halitta ce sha'awa, kuma tana jinin kowani irin jinsi mutum ko dabba, dan haka suma mahaukata suna da ita." Wayyo Allah na, na faɗa a raina da sauri na fara ƙoƙarin kwace kaina. Amma ina haka ya danne ni, tare da niman kwayar idanuna. "Hammah don Allah tashi kaji, ya hakuri ka tashi bani da karfi irin naka." Kamar wanda yaji abinda na faɗa mishi sai gani nayi ya tashi a hankali, tare da janyewa daga jikina, da sauri na dira a gadon ina niman hanyar fita waje, ai kuwa ya biyo Ni. Allah ya hada ni da bindi, domin duk inda nasaka kafa yana biye dani, har niman faduwa yaƙe idan yana bin bayana, haka na dafa mishi abincin duk da babu dad'i domin har yanzun ban iya girki ba, kuma dai sai a hankali baki daya rayuwana ban tab'a shiga cikin al'amarin girkin Inna sosai ba, ina yi amma ba wai ina nufin na iya bane. A'a Kawai ina yi ne sabida kar na mutu da yunwa. Ina juye mishi na zuba nawa na fara ci, kamar yadda nake ci. Rike hannun shi nayi sabida nashi cin a haukace ake yinta, ina ci ina nuna mishi. Haka shima yake ci a hankali yana kallona. Har na gama ci na sha ruwa sai cin nashi yaƙe, kuma abin da j fahimta shine bai san koshi ba, yayi ta durawa kamar yaro karami,dauke filet din nayi, wani irin narke min yayi da fuska sai da tsigar jikina ya mike min, ina ganin kwayar idanun shi cike da wani irin maiko, yana tara kwalla. Murmushin jin dadi nayi tare da cewa. "Kaga idan kaci kadan sai kasha ruwa, sai ka bar inda iska zai shiga, fadar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, a raba ciki kashi uku daya abinci daya ruwa daya kuma iskar da zaka shaka, idan kuma ka nace sai ka cika cikin ka ina zaka samu inda zaka sha ruwa?" Kura min ido yayi yana me lashe bakin shi pink dashi, kurawa bakin idanu nayi gasu da wani irin fadi dai dai misali. Ga gashin bakin da ya zaga bakin, sai karan hancin shi, dara daran idanun shi masu matukar kyau da haske. Mik'ewa nayi zan tafi ya riko hannuna, juyawa nayi ina kallon shi. "Kana son wani abu ne?" Shiru yayi yana kallona, a hankali na janye hannuna daga nashi. Ina barin kitchen yana biyo ni. Da sauri na fice kamar dama haka yake jira, sai ji nayi ya fad'i a bayana nima na fadi, ina jin wani irin yanayi a jikina, juyawa nayi na ina kallon shi, sai zare ido yaƙe. "Tashi a kaina babu kyau kaji" kamar wanda ya san ma'anar haka ya mike da sauri, yana me d'agani. Kafin na Fahimci nufin shi ya dauke ni cak. Ya wuce dani sama, yana zuwa bakin kofar ya kwala Ni da kasa ji kake timmmm. Yayi wucewar shi cikin dakin abinshi. "Dalla dube shi basamude a gurin zaka karya min k'uguna." Na fada ina jin kwalla a cikin idanuna. Ganin ban taso ba ya kuma juyowa zai sintume ni da sauri na tashi ina zare idanu. "Yanzun ka makani da kasa kace zaka kuma daukata ai ko daga birnin mahaukata irinka nake na zan yarda ba balle daga birnin masu hankali na fito." Na fada ina mishi mugun kallo, tsayawa yayi. "Kuma ka bar kallona katon kawai" Da sauri ya sunkuyar da kanshi, karasawa nayi gaban shi, tare da tsagalgale shi da masifa, ina yi da baƙi, hannun nayi, wato d'ago kai yayi tare da kallon bakina. Sannan ya fashe da kuka. Zaro idanu nayi ina kallon shi. "Toh kayi hakuri" na fada mishi ina mi d'age kafana ina share mishi kwallar da yaƙe, murmushi yayi tare da kai hannun shi kan hanci na, yaja da karfi zunzurutun mugunta. "Auchewww! Kaga mugunta sake min hancina..... *_🤣🤣🤣🤣🤣 Mahaukaci kenan, sorry wallahi mun fasa Chakwakiyyar rashin wutar lantarki 🤣🤣🤣 Wallahi sai a hankali domin kuwa ban san iya adadin lokacin da zamu dauka kafin mu samu wutar ba, so please zaku ji Ni shiru idan kunga update toh wallahi mun sami wuta ne idan baku gani ba sorry nagode sosai da ta'aziyar da kuka min Allah Yasaka da Alkhairi nagode sosai_* [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu https://www.wattpad.com/1099088650?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=4lwvUq4CDNgGO6G8hSqWOpKF0xTz1GVp6y7Sxeme%2Fg5OCwGdT5AJbfyarf93zolA7FBbhl2FOh%2FpFU0pdrB84Lq2xdZkHArH%2Bvs7uiWokSFzxRJ27Z5Ikm4Ezg7evEig Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SHA BIYAR. "Sake min hancina!" Na maza na kwace kaina a hannun shi ina lailaya hancin nawa, kamar zanyi kuka. Harara shi nayi tare da cewa. "Maza zauna a nan na shiga ban daki na yi wanka." Na nuna mishi inda zai zauna na shiga ban dakin. Sai da na shirya sannan na fito, na same shi yana zaune kwayam. "Kayi hakuri kaji na Barka kai ɗaya a daki." Bai kula Ni ba, kamar yadda ban saka rai zai amsa ba, haka na cigaba da uzurin gabana, ban kuma bin takai shi ba, domin abubuwa da zanyi na maganin shi yana dayawa, dan haka na shiga haɗawa ina kaiwa ban daki nasaka shi ya cire kayan shima da kokuwa, haka na samu ta cire na fito na kira Hammah Malik yazo yayi mishi wanka Tunda suka fara yaƙe rawan sanyi. Har suka gama ya fito, na shafa mishi addu'o'in, sannan ya kwanta, ban yi tsammanin zai yi barci haka ba, sai gashi yayi dan haka ma na fita na barshi a dakin nayi sallah, ina idarwa na kuma leko shi, ina dawowa na samu bai farka na, dama Baba ya gaya min zai ta yawan barci. *** Kasa zama yayi ya kasa tsayuwa. Kallon Mutallab yayi sannan yace mishi. "Kasan me? Ba zan iya boye maka abinda yake raina ba, amma wallahi ina masifar kaunar Almamoon" ya faɗa a sanyayye, yana kallon yadda Mutallab ya sake baki, mik'ewa yayi zai fita Ansar ya riko hannun shi. "Don Allah saurarre ni mana" fauce hannun shi yayi yana zare mishi ido. "Shika min hannuna, da alamu ka haukace? Ba banza aka yi ta muku kallon masu soyayyar jinsi ba, ashe da gaske ne soyayyar jinsin kake ina zaka kai..." "Dalla ka min shiru, ka bude banzan bakin ka sai maganar banza kake yaron nan mata maza ne!" Ya fada da karfi, zaro idanu Mutallab yayi tare da had'iye yawun. "Kasan me yasa na gaya maka? Saboda ina son Yaron ne kuma zan taimaka mishi ayi mishi aikin ya tsaya a mace, wallahi ina masifar kaunar shi. Please my Friend kai ɗaya ne zaka taimaka min shi yasa na maka maganar please" Ajiyar zuciya yayi yana kallon shi, Kafin yace mishi. "Ban san me zan ce maka ba, amma na tausaya maka. Kuma idan na boye maka yadda rayuwa take yana da hatsari, idan yaron nan yana son ganin shi a mace falillahamdu idan kuma ya fison ganin kanshi a matsayin mata maza TOH karka tirsassa mishi ayi abin da zai saka kowa damuwa." Riko hannun shi yayi sannan ya ce mishi. "Na sani, amma abin mafi alkhairi shine a dawo dashi jinsin da ya fi karfi idan aka ce lallai sai an jira ra'ayin shi ba zai yarda ba." Shiru yayi na wani lokaci kafin ya cigaba da cewa. "Tukun kasan inda yaron nan yaƙe? Kasan a inda yake rayuwa? Yana tare da dan primer minister ne, kuma abin takaicin tunda yagan shi ya makale mishi. Wallahi ina tsoron kar yaje a lalata goben shi! Ina tsoron kar abin duniya yasa a lalata mishi mutuncin shi, don Allah ka taimaka min ta yadda zan shawo kanshi." Shiru Mutallab yayi yana gyada kai kamar kadangaren da ya sha rana. "Yaushe kenan zamu hadu da Almamoon din, tunda kaga kun kusan komawa makaranta?" Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanun shi yana kallon yadda Almamoon shi zai koma da yan nonuwa a kirjin shi yana takun kauna a dakalin zuciyar shi. Tashi yayi zaune yana faɗin. "Insha Allah ranar friday" Wani irin murna yake ji sabida yana hango yadda zai yi da Almamoon indan Allah ya nufa ya zama nashi. Kuma yadda zai sarrafa santalelen cinyoyin shi,(da gaske ashe su Mom Sayeed da Maman Sadeeq basu yi karya ba hauka kake tuburan team Ansar 🤣🙆🏾‍♂️😭) *** Zaune take tana ta haɗa aikan da ka kawo mata daga gidan ministan harkokin wajen tana gani tana murmushin mugunta domin haɗin na musamman ne, dan haka ta kira Babban matakin mai tuka jirgin saman fadar. "Maza ku shirya gani nan zuwa Maradi zani" Kashe wayar tayi tare da ɗaukar jakarta tana me jin a ranta shi kenan daga wannan haɗin Insha Allah Mohan Mamman Nasir Aghali ya tafi har abada. .... Dakin Hajiya Lateefah ta shiga daga bakin kofar ta shiga matse kwallar fuskarta tana faɗin. "Hajiya yanzun don Allah ba zaki ki ga jikin Mohan ba? Hajiya abinda kike fa Allah" "Fitar min a d'akina!" Inji Hajiya Latifah, tana nuna mata hanya. Kamar da gaske ta saka kai zata fita. "Inda yaso ya mutu ko ya rayu, ohon shi" ta faɗa da karfi tare da jin kamar zuciyar ta zata buga dan bata kaunar a kira sunan Mohan a kusa da ita balle kuma sauran Yaranta. Da wani shu'umin murmushi ta bar falon tana jin a ranta shi kenan ta karewa Mohan Mamman Nasir, zata biya yaron da yake tare dashi kudi na fitan hankali. Tana fitowa ya hadu da Primer minister, da Manyan yan jam'iyyar shi. Dake tana shirye da ta tozartashi tace mishi. "Yallabai ina son zuwa na duba jikin Mohan" Wani irin duba yayi mata tare da cewa. "Ba yau ba" Ya cigaba da abinda yake, juyawa tayi tare da komawa gida, har ta nufa gidan ya dawo tana cewa. "Yallabai sai yaushe?" "Jibi Insha Allah" "Dama magani zan kai mishi, kuma yana da muhimmanci, tun da laluran nan hauka ce ai dole a duba lamarin don Allah ka barni na duba shi" "Ba zaki ba nace" ya daka mata tsawa da yasa ta juyawa da gudu, Caaa suka mishi da ido, yana jin numfashin sa yana hawa da sauka. "Yallabai Mohan...." D'aga hannu yayi alamar baya son jin koda kalma Daya ce daga bakunan su. Mik'ewa yayi yana me d'aga wayar shi ya mikawa Mai bashi Shawara na musamman. "Ka musu bayani gobe zamu zauna yau bana jin dad'i." Ya nufi hanyar da zai sada shi da cikin gidan shi. Yana jin kamar zuciyar shi zata buga. Daga kasar zuciyar shi kaunar danshi yake kokarin tasowa mishi amma kuma k'iyayyar yaron yana kara danne mishi kin yaron. Yana shiga falon shi ya zube akan sofa, yana jin wani irin kewar yaron a ranshi, amma Yarasa me yasa yake jin zafin yaron. Chef Judge ya fado mishi a rai, baya mantawa ko wancan juma'ar sai da yace mishi. "Yallabai munufarka tana da kyau sai dai kuma da na jikinka ake maka yankan baya, sannan ake niman ganin bayanka, Yallabai nasan ba ilimina ya kawo ni nan ba, Allah ne ya kawo ni nan, kai a tunanin ka bayan mun hadu a Saudiya na gaya maka wannan yaron da kuke tafe dashi zanen ƙaddara zata iya raba tsakanin ku. Kuma kai ma baka manta ba, na gaya maka yaron ka yana da taurari masu karfi da zai hadu da wanda yake da irin taurarin shi da duniyar su. Yallabai Yaron ka yana cikin mawuyacin yanayi wanda a cikin gidan ka aka fara, sai dai kuma Allah yana sane dashi kuma yana sane da kome, idan yaso sai ya kawo mishi dauki kuma ya bashi wanda zai tsaya mishi. Ina tausaya mishi, duk da na daina na tuba amma bana jin dadin yadda rayuwar d'anka ya koma. Allah ya hada shi da mutanen kirki masu tsoron Allah. Yallabai Yaronka shine jigon mulkinka kayi wani abu akanshi ya dawo kusa da kai, Yallabai ina ga baka tab'a jin ana fadin Yan baiwa ba ko? Toh d'anka yana cikin su, domin kuwa idan yana tare da kai kowa tsoron shi yake babu wanda ya isa ya takaka, idan baya tare da kai kuwa wallahi jikin su na rawa zasu nemi bataka idan ka shirya zan duba Al'amarin shi Insha Allah za a dace" Duk da yana jin zafin kiran sunan Mohan da Shugaban alkalan alkalai yake amma haka bai hana shi jin abin a ran shi ba .toh waye yake niman bayan shi? MEYE! Mik'ewa yayi bayan sun idar da sallah jumma'a ya mika mishi hannun shi. "Nagode idan ina son karin bayani zan Nime ka, alkalin alkalai" inji Primer minister, "Nagode sosai Allah ya tsare gaban ka da bayanka" Lumshe idanun shi yayi yana kara nazarin abinda yake faruwa, na farko tunda Mohan ya fara jinya mutane dayawa suka shiga rayuwar shi kuma suna abinda suka gadama bai isa ya hana su ba Na biyu tunda babu Mohan aka fara mishi bore kamar zasu shi Office din shi. Na uku kowa niman daura mishi laifi yake kome ya faru niman a cutar dashi ake? Ya rasa gane abinda yake faruwa,.ya rasa gane dalilin da yasa aka juya mishi baya, a yanzun yana da shekaru masu yawa akan mulki amma bai tab'a jin ko ya cutar da kowa ba, amma shi kullum niman hanyar cutar dashi ake, kasa fahimtar kome yayi, sai ma dage kirjin shi da yayi yana kara tausayin kanshi. Yana kuma jin kamar akwai masu bibiyar rayuwar shi da ta iyalin shi, idan ba haka ba me yasa za a mishi wannan abun? *** Maradi. Addu'a ake mishi yana kara mingirawa kamar maciji, duk ya jima kamshi ciwo, sai rike kanshi yake, da sauri na mike zan kai mishi dauki domin yana cutar da kanshi, rike ni Malik yayi cikin wani irin sassayan kallo, ya rike hannuna. Fisgewa nayi na fada kan Mohan, wani irin duka ya kaiwa kirjina, sai da naji kamar raina zai fita sakamakon dukar nonuwana baki daya da yayi. "Hyaiiiiiiii! Haaaah" na sauke wata irin numfashi tare da jin kamar an cika min iska a bakina da kirjina, tafiya nayi zan zube Malik ya tare ni, daidai shigowar Dan Ba'are, shima ya kai mun wani irin riko, suka kwantar dani a kasa, yayinda Mohan yake ta amai. "Alhamdulillahi yau zamu bari zuwa gobe ku kula da Yaron yayi kokari wallahi" Bai kai aya ba,Dan Ba'are ya dauke ni da gudu ya fita dani Sakamakon jinin da nake fitarwa ta hanci da baki, baya ganin gaban shi domin kamar dirka yake a step din, har asibiti ya kai ni. A guje ya fita dani, Yaran shi da suka rako shi suna ganin shi aka bude kofar motar da sauri ya saka Ni sannan ya shiga yana me daura kaina akan cinyar shi. "Taka motar" Ya fada da karfi, haka suka fincike ta a guje. Daidai fitowar Malik da Malam. "Yanxun ya za ayi da mara lafiyan?" "Zan kula dashi" ya faɗa kamar zai fashe da kuka, domin wani irin yanayi yake ji na takaicin yadda Dan Ba'are ya mishi shigan sauri haka kawai zai wani dauki Almamoon ai haka bai dace ba ina laifin ya kuka da Mohan shi ya kai Almamoon toh idan kuma wani abu ya faru da..... .......... Chaiiii.....🙄 Ga masu bukatar a tallata musu Hajar su kofa a bude yake a tuntube wannan Number,08130269641 [7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... _*SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya.... _Gaisuwar wannan shafin naku ne baki dayan ku Makarantar BRRJI👏 Nagode sosai_ BABI NA SHA SHIDA. Iskar bakin shi ya furza domin yasan dai duk abinda zai ayi almamoon namiji ne, dan haka ya juya tare da sallamar malamin, ya shiga cikin gidan. Yana me kara jin babu dad'i baki daya, ji yaƙe kamar yayi ta kurma ihu. A yau yayi danasanin fara aikin soja, domin yana ganin kamar kasancewar shi a aikin ne ya ja mishi kaddararren wahala,haka ya taimakawa Mohan sannan ya koma bakin aikin shi dan bai ga dalilin da zai saka shi zama a jikin Mohan ba, tunda shi ya janyo haka. *** Muna isa asibitin da gaggawa aka amshe ni, yana rike da gadon da ake turani har bakin kofar shiga dakin da za a duba ni. Tambayar shi nurse tayi yayi mata bayani, sannan ta shiga cikin dakin, suka mai da hankali akan duba lafiyar ta, rigar Jikinta suka nime tsagawa, likitan ya ce musu. "Ku dakata ba sai an raba shi da kayan shi ba, idan aka duba daga wajen ma yayi." Inji likitan yana ƙoƙarin had'a alluran da zai mata, haka suka gama abinda zasu har suka sami nasarar farfaɗowa ta, amma take likitan yayi min alluran barci. Lokacin da aka fito dani, mikewa Dan Ba'are yayi yana kallon su. Kamar me ciwon baki yace musu. "Ya......ya.... Ya...." "Yallabai da sauki ya samu barci, idan ya farka zuwa jibi zamu sallame shi" Gyada kai kai yake tare da kallon keken majiyanta, har dakin da aka kwantar da Almamoon ya shiga. Zama yayi yana kallon fuskar yaron, wanda kullum yake zagaye da saje, kusan ma dabi'ar shi, sajen har kusan kumatun shi. Yana barci kamar wani mage, ya samu auduga. Dan cuter face din shi ya kuma fitowa sosai, gwanin ban sha'awa. A hankali ya shafa dan bakin shi nan (Ni kuwa nace bakin tsiwa ba🙄😩da bakar magana) haka yayi ta shafa bakin shi yana murmushi, bakin yayi mishi kyau dan karami kamar bana namiji ba, murmushi ya sake tare da shafa kanshi yana me kallon window dakin yana kallon mutanen da suke shige da fice daga asibitin. Yana jin ina ma da ace Almamoon mace ce, da yau zai gabatar da kan shi sabida kar yayi sake reshe kama ganye, kuma idan ma bai yi haka ba, taya yana ganin dama zai wuce shi, murmushi yayi sannan ya zauna tare da riko hannun shi yana kara jin wani irin nutsuwa a tare da Yaron, haka kawai yake kara kallon nasibin yaron, yana kara jin yaron a cikin zuciyar shi lungu da sakon cikin zuciyar shi. Wani irin bugun zuciya yake ji a duk lokacin da ya kalli fuskar yaron ji yaƙe kamar dan shi aka halicci Yaron,. Shafa kanshi yayi tare da jin wani sabon nutsuwa akan shi. Yaron baki daya yayi tafiyar bazata da rayuwar shi. Murmushi yayi. --- Kallon shi tayi kafin tace mishi. "Malam Ansar ko zaka kai Ni naga Mamoon ne zuciyata taki yarda da halin da yake ciki, ko zaka kai ni" Yadda ta damu sosai ya kalli Baba Mari kamar zai yi kuka, yace mata. "Baba idan muka je ba lallai su barmu mu shiga ba, amma tashi muje" Babban mayafinta ta yafa, tare da bin bayan shi, har Jacader. Lokacin da ta ga gidan da Almamoon yaƙe zuciyarta sai da ta girgiza, dake sun san Ansar basu hana shi, shiga gidan ba. Asalima kamar an bashi pass ne, yana shiga suka haɗu da Malik kallon juna suka yi kafin Ansar ya fito daga motar shi yana faɗin. "Ina Almamoon na kawo kakanshi ta gan shi ne dan ta damu" Murmushi yayi irin me ciwon nan, sannan yace mishi. "Yana asibiti babu lafiya" Cakume wuyar Malik yayi kamar idanun shi zasu fado. "Me Mahaukacin ku yayi mishi? Kunga abinda nake gudu ba? Kunga dalilin da ya sani nake gudun zaman Almamoon a cikin gidan nan ko? Wallahi idan wani abu ya same shi. Sai na kashe wancan Mahaukacin" Dukar da aka kai mishi a baya yasa shi sake Malik. "Kyale shi Fahad, ba laifin shi bane yana da iko da Almamoon." .wayar shi ya ciro tare da kiran dan Ba'are ya tambaye shi suna ina ga kakan Almamoon tazo ganin shi. Yana gaya mishi asibitin ya gayawa Ansar. Shima yayi amfani da kalmar kaka ce saboda yasan idan suka ji haka zasu bar shi ganin Almamoon. Yana gaya mishi sunan asibitin ya shiga motar shi da sauri, ya bar gidan kamar zararre, dama kuma ai zararren ne (🙄🤸😁🤣) Koda ya iso asibitin, dakyar ya sami dakin da aka kwantar da Almamoon bayan ya gama shan bakar wahala, yana shiga ya kura mishi ido, yana mai da numfashin sa, tare da goge gumin goshin sa, kafin ya kalli dan Ba'are, kasa mishi tijara yayi domin irin karfaffan mazan nan ne, da shi da Mohan fadi kawai Mohan zai nuna mishi da cikar halittar jiki irinta mazan da suke daukar karfe. Idan Mohan ya saka mata matukar ta kama shi idan zai d'aga hannun, toh rigar zata iya darewa, sabida tarin kwanjin shi. Takowa yayi tare da kai hannun shi zai dauki Almamoon, yaji an rike hannun. Tare da mai dashi baya, sake kai hannu yayi zai dauki Almamoon, ran Dan Ba'are ya b'aci dunkule hannun yayi zai sauke mishi naushi Nurse ta shigo. "Nazo duba mara lafiyar ne zamu mishi allura" Sauke hannun shi yayi yana kallon Almamoon, Nurse tana gama abinda zata yi ta fita, wani azazzaben dambe ya kaure a tsakanin su, karan buge buge ya farkar dani. Kallon su nake kafin na tashi dakyar. Na nufe su tare da riko malam Ansar. Bakina yayi nauyi ina son nayi magana amma na kasa, dakyar na koma bayan shi na rungume shi. Tare da zaga hannuna kirjin shi. "Ya isa Hammah ANSAR" na fada a hankali, kamar ba zan iya magana ba, cak ya tsaya kamar an zare mishi duk wata kusarin shi. Ji yaƙe kamar tunda yake ba a tab'a kiran shi da suna Yaya ba, baki daya gwiwar shi tayi sanyi sama da kullum. Yau shi Almamoon ya kira Hammah ko mafarki yake ne? Anya ba mafarki yake ba? Indai da gaske ne shi Hammah ANSAR ne, toh tabbas Almamoon yana rungume dashi kenan. Wani bahagon naushi Dan Ba'are ya kai mishi. A fuskar shi sai da ya kufa a kasa, tare muka fadi. "Almamoon rabu da munafuki" inji Dan Ba'are, "Hammah Khalil! Ka daina dukar shi, bana jin dadin haka." Na shiga tsakanin su. Muna kallon juna. Tafiya nayi luuuu zan fadi suka tare ni dukkan su biyu, ɗauka ta suka yi tare da mai dani gadon, suna kallon fuskana. Lumshe idanun nake ina kuma buɗe shi. "Ya Hammah Mohan yake?" Na tambaye su a gajiye, gyara kwanciya na suka yi sannan Dan Ba'are yace min. "Ana ta lafiyar ka waye yake ta Mohan?" Sam ban ji dadin abinda ya faɗa ba, dan haka na tashi zaune. "Zanje naga halin da yake ciki" "Baka isa ba, wallahi sai na falla maka mari, kuma mun zo da Baba Mari ne" Komawa nayi na kwanta, haka ya fita can sai gasu tare sun shigo d'akin, suna shigowa dan Ba'are yana fita. "Sannun kaji, Allah ya baka lafiya ashe baka da lafiya ne" Gyada mata kai nayi ina jin kwalla na cika min idanuna, shafa kaina tayi tare da cewa. "Zan zauna da kai kaji" Gyada mata kai nayi, muna cikin haka Malik ya shigo tare da kallona. Murmushi ya sakar min, na maida mishi nima. "Ya jikin naka?" "Da sauki" "Allah ya baka lafiya" "Amin Ya Allah, ina ka baro Hammah Mohan? Kasan bai da lafiya kake barin shi babu wani a kusa dashi? Kasan yadda rayuwar shi take cikin hatsari ka bar shi shi daya a gidan? Ku mai dani gidan kawai nayi jinyar a can" "Ba zaka kuma komawa gidan ba, domin ina kaunar ka" juyawa nayi na kalli Malam Ansar. "Ba zaka tab'a samun yadda kake so ba,dan haka babu ruwanka dani." "Kayi hakuri dama nazo duba halin da kake ciki ne, kuma Alhamdulillahi, zan koma domin na bar Fahad a jikin shi." Gyada mishi kai nayi, tare murmushi. Haka ya tafi ba tare da na yarda mun kuma magana ba, sabida bana son yadda yake kallona. Hankalin su Baba Mari da Hammah ANSAR ne ya dawo kai na. "Baba Kinga shi taurin kan bala'i ce dashi dan haka ki saka baki mu koma gida dashi." "Hmm" na fada ban kuma magana ba sai ga Dan Ba'are da manyan ledojin shi guda uku, ya ajiye min. "Sannun bawan Allah Ubangiji ya saka da Alkhairi, Sannun da tallafan rayuwar shi mun gode" Cikin wani irin murmushi yake kallon mu, irin yayi katon bajinta. Dariya ya bani irin wanda ake yin shi a cikin rai haka, na kalle shi nayi murmushi. Zuba hannu Yayi a cikin aljuhun wandon shi yana kallona. Janye idanuna nayi daga kanshi ina kallon Malam Ansar da ya cika ya batse. "Hammah Khalil ka tafi ka duba halin da Hammah Mohan yake ciki kaji" "Toh babu damuwa, duk yadda kace haka zamu yi, Baba sai an jima. Kai kuma be careful" ya saka kai ya fice daga d'akin. "Baba kin gani ko? Hidima suke mishi waye ya sani ko wani abu ne yake shiga..." Fisge ruwan hannu na, nayi tare da sauka a gadon na shiga tura shi har kofar dakin, ina kai shi gurin na ce mishi. "Kar na kuma ganin ka a nan idan ba haka ba hmm" Na nuna mishi hanya tare da banke kofar.. "Mamoon,.kayi hakuri nasan babu dad'i." "Baba kina ji yana zargina shi din waye shi? Meye na tsare mishi da yake zargina? Ina dalili zai saka Ni a gaba" "Kayi hakuri" haka tayi ta rarrashinsa, dakyar yayi hakuri, sannan ya shiga ban daki yayi alola da wanka ya fito, tare da gabatar da sallah. Yana idarwa ya zauna yana kallon kayan da Dan Ba'are ya kawo shi. Flast da ruwan zafi. Sai kayan ciye ciye. Haka na zauna na ci kadan sauran na turawa baba. Tana ci tana kallona. "Me yasa meka?" Kasa magana nayi tare da kasa kallonta. "Ina tambayar ka? Kasan jikinka ba karfi ne dashi ba, kai asalima baka da nau'in karfin maza, don Allah ka daina saka kanka cikin kasada kaji, ka daina cilla rayuwar ka cikin damuwa, malam Ansar yana da laifi gurin sakawa lallai sai kayi abu dole amma ka tab'a bibiyar me yasa yake maka haka? Sabida yana kaunarka gani yake baka cancanci zama a inda za a tab'a lafiyar ka ba. Don Allah karka tab'a min zuciya, wanda aka yi na shekaru sha ma bai warke ba, idan wani abu ya same ka ba zan tab'a yafewa kai na ba.[7/15, 4:04 PM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1099611906?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=B2xbg56NQ%2Bj7itiadIMLq5S6mXv9S%2FsKyYdkh0H8PJKgwqgLqD%2Fo961ZM5LierkVHLwx3qEwMnG%2BOkvdE6rc9D1tbKk2fSwjLb0oWove1cVKshUkIo7LVOxrft0MhTCk 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... _*SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya.... BABI NA SHA BAKWAI. Kwalla ne suka cika min idanuna, na kalli Baba cikin kuka nace mata. "Amma ko ma yayya ne dole yayi min uzuri, tunda nima mutum ne me rayuwa, taya zai dinga jifana da abinda ya fito bakin shi? Shin wannan adalci ne ko son Zuciya? Baki daya na kasa gane mishi bai da aiki sai gaya min maganar da ta fito bakin shi wallahi ki gaya mishi ya daina ko na kafta mishi rashin mutinci." Na fada ina share kwallar da sune zubo min, "Kayi hakuri" Baki daya malam Ansar yaci uwar rena min hankali, dan yaga bana mishi magana ne wannan karon ya isa haka. Kuma zai ga yadda ake rashin mutunci, sai dai bai gaya min magana ba sai na rama. Haka na share kwalla na, na cigaba da sauraron Baba, har dare yayi. Shigowar Mohan da su Dan Ba'are ya sani mik'ewa zaune ina kallon shi, fuskar shi a sake. Kallona yake kamar me cikakken lafiya. Murmushi nayi mishi tare da nuna mishi gurin zama. Kallona yake kamar yana son gano wani abu a tare dani, amma bai ce min kome ba, tunda ba magana ce yake ba. Sauka nayi tare da nufar shi na kawo shi bakin gadon ya zauna, zama nayi a kusa dashi ina me kallon kayan ciye ciyen da yake dakin na shiga mika mishi ina cewa. "Ci karka damu Ayya naga ka rame da ba nan Anya Hammah Khalil kana kula dashi kuwa?" Wani kallon banza ya watsa mishi tare da cewa. "Ba aiki Mohan ya dauke ni ba, dan haka dan banza idan ya dagama yaci abinci idan bai gadama ba ya zauna da yunwa banza dan iska Allah ya baka lafiya kace zaka fito da halin ka cin mutuncin ka zanyi" Kallon shi nayi cikin kankace idanu nace mishi. "Wannan cin mutuncin da me yayi kama? Ka saka mara lafiya a gaba da wulakancin meye yayi maka" Sake hararan shi dan Ba'are yayi yana me dauke kai tare da gyara tsayuwar shi. Abinda ya faru kuwa ba kome bane, tun suna yara suka da wata muguwar wasa da sukewa junan su, idan mutum ya duka, dai ka sake mishi dundu a baya, shine bayan ya koma gida yana ƙoƙarin su tawo asibitin, kawai Mohan ya ganshi ya duka yana saka takalmin shi ya samu gadon bayan shi ya sakar mishi dundu sai da ya kwara amai. Kuma da ya juya ya saka fuska kamar bashi ba, shine abun yake bashi haushi yake ta zagin shi tun a mota, ya kwashe mishi albarka yakai sau dari tare da jan Allah ya isa kamar zai fasa ihu, domin dai da yaji bayan ya kame kafin ya mike tsaye kai Mohan..kwafa yayi ya kuma ce mishi. "Dan iska mugun banxa kawai" "Amma ba na hana ka zagin nan ba?" Kallona yayi sannan yace min. "Mamoon dundu yayi min a baya fa" .kamar zai fashe da kuka. Kallon Hammah Mohan nayi, "Me yasa kayi mishi haka? Kana son ka zama mugu ne dodo me ban tsoro?" Na mishi wani iri da hannuna ina gwalallo idanuna waje. Girgiza min kai yayi tare da kwantar da kanshi yana jin babu dad'i. "Toh karka kuma kaji" na fada mishi ina kallon Hammah Khalil ina me Cigaba da bashi hakuri. "Kayi hakuri" "Shi kanan nazo na zauna kusa da kai?" Matsa mishi nayi Baba bata ce min kome ba, sai bayan da suka gama suka fita, sannan tace min. "Karka kuma haka babu kyau" "Toh ba zan kuma ba" *** Washi gari sai ga shugaban marasa zuciya. Shi da abokin shi suka shigo d'akin. "Sannun ku ya masu jikin?" Inji Abokin Hammah ANSAR, Kallon baya nayi tare da kallon su nace. "Da sauki" na fada a takaice, "Ashe baka ji dadi ba" "Eh" Yadda nace eh din a takaice Yasaka su shan jinin jikin su, tabbas na shirya musu. Fita baba tayi zata nimo goro. Zama Mutallab yayi tare da kallon Hammah ANSAR da yake tsaye. "Hmm! Almamoon mun zo da wani abu me girma bamu sani ba ko zaka yarda da shi?" Ya tambaye ni bayan ya kai aya. "Ina sauraron ku?" Gyara zama yayi tare da fara kalkalo min iyayi, ina kallon shi. Kafin yace min. "Ansar yayi min bayanin waye kai so ina son muyi amfani da wannan damar domin nima maka lafiya?" Kallon bayana nayi, kafin na kalli gefena, na kuma kallon saman kai na, kafin na sauka a gadon ina leka kasar gadon kafin na ce musu. "Toh ni dai na nime lafiyar ban gan shi ba" Na fada ina kallon su. Kafin na zauna. "Ya kake mai da kome da wasa ne? Wannan batun lafiyar kace da? Kuma zaka mai dashi wasa? Ai ba wasa da lafiya" "Wai ma tukun waye ya gaya maka bani da lafiya kazo ku nima min lafiya? Ku Allah ne?" "A'a Almamoon taimako bai zama tashin hankali ba" ya faɗa yana kallona. "Toh zakewa da shishigi ba tashin hankali bane?" "Almamoon karka mana rashin kunya" inji Malam Ansar, "Sai dai na muku bindin akuya, karshen rashin kunya" "Amma kai babu manya ne a gidan ku?" Inji Mutallab, "A'a yara ne a gidan mu irin ku." "Kai waye ne da zaka gaya mana bakar magana?" Inji Malam Ansar, "Toh kayi hakuri zan gaya maka farar magana yadda zaka ci ka koshi" "Kai" "Dalla sauke muryan ka, ba zaka min tsawa ba ana zaune lafiya dan ban cika gane seven da seventeen ba, zaku iya cigaba bujejjunku iska kar na kuma ganin ka" Na fadawa malam Ansar a gadarance, "Kai kasan waye kake gayawa magana?" " Na sani mana? Waye ban da namiji a gabana, na miji ne a gabana nake gaya mishi maganar da tafi to bakina! Ko bai kai bane na gaya mishi?" "Ka kai ka isa idanun ka ya bude ana bin bayanka ba, dole kartin maza sun lalata maka rayuwar ka, sun koya maka mugun nufinsu. Allah ya dawo da kai kan hanya domin nasan tunda suka san kai mata maza ne shi kenan sun lalata ka" "A'a sai dai maza mata ba mata maza ba, Sharrin da kai min kuma ya kare kalau ba zan maka baki ba Allah ya shirya ka shiryar jigida" "Almamoon kaf garin nan baka da gata sai ni" ya faɗa a fusace, "Ayya sabida ka fado cikin mutane ni kuma na fito kalgo, ko nace na diro daga sama, masu asali." Na gaya mishi ina kallon fuskar shi. "Ni kake wulakantawa sabida Mahaukaci wallahi sai na hana ka sukuni gaka ga mahaukacin nan" "A'a akan me zan wulakanta ka ni din banza, kawai gani nayi rayuwar da ka dauka bai dace bane, amma kuma kato da kai na wulakanta ka, abin dubawa ne" na fada ina kallon farcena. A fusace ya taso min, na d'ago kai ina kallon shi. Yana zuwa ya kifa min mari. Dai-dai shigowar Dan Ba'are, kura mishi ido nayi tare da jin kwalla yana cika min ido. Cikin wani irin zafin nama ya nufi malam Ansar. "Kyale shi!" Na fada ina shiga tsakanin su. "Ban san me yasa kake haka ba. Amma ina son wannan ya zama na farko da na karshe, Yaron nan ba bawanka bane da zaka addabi rayuwar shi." "Ina ruwanka? Ni na kawo muku shi. Kuma Ni nake da hurumin tafiya da shi kai har ka isa ka gaya min magana akan shi, wallahi sai na dauke shi." Dan Ba'are zai magana na hana shi, tunda nima ba maganar zanyi ba, haka ya fita a fusace. Suna fita dan Ba'are ya ce min. "Meye alakar shi da kai?" Ya tambaye ni yana tsare Ni da ido. "Malamina ne kuma na zauna a gidan shi" "Shine yake maka hauka kamar shi ya haifi ka." Shima ya tadda min nashi rigimar, kamar zai dake ni har da cewa Ni na bar Malam Ansar. *** Washi gari. Kai malam Ansar bai da zuciya domin da asuban fari sai gashi, duk sai ya bani tausayi. Nuna mishi kusadani nayi, domin na fahimci yana cikin kad'aici. Tunda ya zauna ya kalle ni. "Almamoon" shiru yayi tare da tagumi. "Me yasa kake wulakantani? Almamoon duk wanda yace yana son ka ba makiyin ka bane, Almamoon ka duba girman kaunar da nake maka wallahi jiya dakyar na rintsa." Ya fada yana kallon fuskana. "Malam kaga" "Ina laifin Hammah ANSAR" ya faɗa kamar zai yi kuka. "Amma kasan dai ni din ba mace bane?" Sauka yayi daga gadon ya rike hannuna. "Ina masifar kaunar ka, kuma zan iya kome domin ka sami lafiya Mamoon kawai aiki za a maka akan matsalar jinsin ka a dawo da kai jinsin mata, kaga zaka haihu zaka yi rayuwa irinta mata, zaka zama." Dariya ya bani sannan na kalle shi. Kafin na kuma kwashewa da dariya, domin kuwa mamaki yake bani. "Na zata hauka kake ashe turu kake bukata, Allah ya shirya ka. Idan akan jinsi ne ba zan tab'a yarda a yi min aikin ba" Matse hannuna yayi tare da kallon cikin idanuna. "Kayi hakuri Hammah ANSAR, kai Yaya na dauke ka ba wai soyayya ba, Hammah ANSAR soyayyar nake maka ta yan uwanta ka ce, na gaya maka ba yau ba, ni ba kamar yadda kake tsammani bane" "Na yarda zan zauna da kai haka. Don Allah ka so ni" Tausayi ya bani, na rike hannun shi. " Ba zan iya wannan lamanin ba" Na gaya mishi ina me dauke kwallar da ta cika min idanuna. Rarrashina yake amma bai tab'a sani jin ko zan iya yarda da bukatar shi, kawai dai na dai ki amsa mishi ne, haka ya gama abinda ya ga zai yi, har ya fita bayan ya tunatar dani an kusan komawa makaranta. *** Kwana hudu a tsakanin aka sallame ni, Muka koma tunda daga bakin kofar nake, kallon gidan kamar ka shekara ban gidan. Yana tsaye sanye da riga da wando na Adidas, kallon fuskar shi nayi naga ya kara kyau, shima kuma ni ya kura min ido. Da murmushi na isa gaban shi ina dariya kallon shi. "Hammah Mohan" Wani irin kallo yake min daga kasa har sama. Tare da bina da ido, sake baki nayi kawai ina kallon shi. "Baba ga Hammah Mohan" na fada mata a sanyayye, "Ayya Allah ya baka lafiya" riko hannun shi nayi, shima sai bina yake da idanu. Haka na kai Baba d'akina tayi sallah tare da zama ta ga gidan, bata bar gidan ba sai da Magarib. Lokacin da na raka ta, dake ban kawo ana bin bayana ba, kawai ina juyawa nayi karo da mutum. "Wayyooo" na tafi da baya zan fadi. Hannun shi naji a bayana zuwa k'uguna. Kura min ido yayi yana kallon yadda nake zare idanuna. "H...a...m..m..a..h...Mo...h...a..na" na kira sunan shi a rarrabe, ina zare idanuna, ga wani lugude da nake ji a raina, tare da rike rigar shi, kafaffuna suna dangafe da kasa. Sake ni yayi na zube da timmmm, na kwalu da kasar. Yayi tafiyar shi, tunda ya shiga dakin shi ya rike kanshi, yana wani irin jiri yake daukar shi kamar zai fadi, Kwanciya yayi tare da lumshe idanun shi. Dakin na shiga na kwanta, can na tuna dashi na shiga dakin shi, yana kwance yana juyi, ina shiga na d'ago shi da sauri ina ƙoƙarin d'aga shi. Ya tashi zaune, "Sannun Hammah Mohan" Mik'ewa nayi tare da tab'e goshinsa, kafin na fita na dubo mishi magani, ya sha tare da kwanciya. Zama nayi akan shi ina shafa kanshi har barci ya dauke shi. Tashi nayi tare da fita. *** Satin farko na koma makaranta, sai dai kuma tunda na koma makaranta bani da lokacin shi sosai. Kullum ina dawowa a gurguje zan kula da shi na. Sai dai haka kawai nake ganin kamar akwai wani abu da yake faruwa da Hammah Mohan.... *Kuyi hakuri bani da cikakken lokacin kai na ne, kunsan sallah ya kusa ga masu yawan rai, don Allah ku min Uzuri Insha Allah sai bayan sallah. Yau ma dakyar na muku wannan.* #Mai_Dambu...... [7/18, 8:39 AM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... _*SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya.... BABI NA SHA TAKWAS. A sanyayye na shiga cikin dakin yana tsaye kamar ba zai shigo ba, fita nayi na shigo dashi dakin ina cewa. "Zauna a kan na shiga ban daki na fito." Na zaunar dashi na shiga ban dakin na gama uzurina na fito, sannan na dauko mishi maganin shi, na nutsu na tofa mishi addu'a kafin na mika mishi, wani irin duba yakewa maganin cike da kyankyame. "Ka sha maganinka ne" na fada ina tura mishi maganin a bakin shi, dakyar ya sha yana yunkurin amai, sororo nayi ina mamakin shi. Dafa goshinsa nayi naga ya rintsa idanun shi da karfi, alamar baya son na tab'a shi. Janye hannun nayi ina kallon shi, koda na dauko wanda nake shafa mishi ma, kamar ala dole nake mishi. Ina gama shafa mishi nace mishi. "Kayi hakuri kaji magani ne da alamun kafara samun lafiya shi yasa baka son ina tab'a ka, amma Insha Allah idan ka samu lafiya zan tafi na koma inda na fito, sabida kai nake nan" na fada ina shafa mishi ayatul shifa a kafar shi, kwalla na zuba akan gwiwar shi, ina gamawa na mike na mai da maganin sannan na fita niman abinda zamu ci. Ina gamawa dan Ba'are yana shigowa gidan shi da Malik. Abincin na gabatar musu, kallon Hammah Mohan suka yi da yake tsaye astep ya kura musu ido, yaki saukowa. Mik'ewa nayi cikin rawan jiki zan tafi gurin shi Dan Ba'are ya dawo dani. "Rabu da dan iska kar yazo taci ya zauna da yunwa dan Ubanshi" Juya nayi gurin Hammah Mohan Gandhi tsaye, kan shi a sunkuye. Kwace hannun nayi tare da nufar shi, yana tsaye bai matsa ba, gaban shi na nufa na tsaya tare da kamo hannun shi muka tawo gurin cin abincin. Na ja mishi kujera ya zauna, sannan na zuba mishi abincin. Kallon abincin yake yana kallon nasu, kamar ba zai ci ba. "Banza dan iska karka ci dan kaniyar ka" haka yayi ta juya abincin sai da na hakura da cin nawa na fara bashi, yana yatsina fuska. "Ayya abincin babu dadi ko?" D'ago kai yayi yana kallona, kafin ya ture hannuna ya shiga amsa dan ya lura da yadda kwalla yake cika min idanuna, sosai yake cin abincin yana gamawa ya mika min na kara mishi, shafa kan shi nayi tare da cewa. "A'a ba zaka ci dayawa ba, kaji sha ruwa haka ya isheka kana magani ba a son kana cin da ya fita Muslunci." "Ai da kin bashi, tunda shi ya zama tumbi iza hana gaya rub'a." "Auchewww" inji Dan Ba'are, yana kallon Hammah Mohan, cikin takaici da zafi. "Lafiya?" Na tambayr shi a rud'e. "Ban da wannan dan iskan zai karya min yatsu shege ciwo bai saka ka daina mugunta ba, Mahaukacin banza kawai" ya faɗa lokacin da ya tashi a kujeran yana dingishi. Rike kunnen shi nayi tare da zaro mishi ido, kawai sai ji nayi ya dauke ni cak ya daura akan cinyar shi da hannu daya. Ya saka ya matse ni. "Sake ni! Kyale Ni bana son haka" na kwace kai na ina ajiyar zuciya. Make keyar shi nayi tare da kwashe kayan da aka ci abincin. Na nufi kitchen da shi. Haka dai yanayin shi yayi ta sauyawa har Hammah Khalil ya bar garin, ina kuma kula dashi. Wannan karon karatu yayi zafi bana iya dawowa da wuri sai Malik ya je ya dauko ni, ga Malam Ansar ya taso ni gaba. Kamar zanyi kuka haka yake disgani a gaban jama'a. Bai tab'a sani naji a raina zan mishi yadda yake so ba. Yau ma da wuri na shigo makarantar, na nufi ajin mu. Ina shiga na same shi yana karatu, dan haka na shiga tare da sallama. "Zoka fita min a aji" "Malam kayi hakuri na san sai bakwai da rabi kace zaka..." Ban idar da abinda yake bakina ba ya kifa min mari, tare da daka min tsawa. "Fitar min a cikin ajiye, dan iskan Yaro kawai" ya turo ni waje tare da rufe min kofa, gashi ana wucewa tare da kallon mu,haka na juya na bar makarantar sabida ko ina na zaga dariya ake min, danne kuka na nake har ba samu abin hawa, na nufi Jacader. Ina isa na samu sun bude min gidan, ina shiga na taradda sabon tashin hankali. Domin Matar ranar ce ta zo, ina shiga na same shi kamar Almajiri a gabanta yana zaune. "Sannun da zuwa Hajiya" na fada ina danne kuka na, "Takowa tayi tare da kifa min mari." Sai da na zube kasa. "Akan me zaka na barin shi a gida bayan kasan bai da lafiya? Toh wannan ya zama na karshe kar a kuma, ga kuma maganin nan ka tabbatar ka yi amfani dashi maza dauka ka kai daki" jikina yana rawa na kwashe kayan na nufi sama dashi, "Kai kuma a haka zaka kare, saura kiris burin mu ya cika ba sai kana raye zaka iya taimakawa iyayen ka ba, idan ka isa ka hana mu kashe Ubanka da ita mahaukaciyar Uwarka" ba iya Ni na kad'u ba hatta shi dai da naga ya girgiza, balle ni domin a haukace yake kallon shi, ai kuwa ta shiga marin kyakyawan fuskar shi, da sauri na iso gurin tare da had'a fuskar shi da kirjina, ina bata hakuri. Nima duka na ta shiga yi tana gaya min. "Idan baka min aikina ba, tabbas sai na kashe ka kai ma bayan na samu ka kashe shi matsiyata." Can kuma ta mike tare da ajiye min kudi tana faɗin. "Kayi hakuri raina ne ya b'aci ka dauka kayi min amfani da kome zaka gan shi a rubuce,kaji yaron kirki ka kula min dashi zan maka babban kyauta." Gyada mata kai nayi ina kallon ta, bayan ta gama ta fita. Zama nayi a gurin na fashe da kuka, sosai. Sabida yau iya maruwa na maru. A hankali na mike tare da riko hannun shi, muka nufi sama, yana kallona, muna shiga ya ga na fidda kayan baki daya, na zazzage shi a kasa. Daidai hancina yana zubda jini. D'ago Ni yayi yana me lakutan hancin nawa. "Kaga babu kome kawai jini ne yake diga." Na kwace kai na, tare da kwasar maganin kaf na nufi ban daki dashi na juye a masai na tura musu ruwa suka tafi, sai wata yar karamar mutunmutumi a kwalba, ta rubuta. *A saka a kasan gadon shi ko a yaga rigar katifar shi a cusa maganin lafiyar shi ce* Dauka nayi tare da nufar bayan gidan yana biye da ku, na nimo fetur na watsawa kwalbar wanda aka soka allurai a jikin abin na watsa mishi fetur na kyasa Ashana. Na jefa bayan na yi kabbara, kwalbar ce ta fashe tare da wani irin bakin hayaki ya tashi sama, ihu hayakin yayi wanda ya haifar min da wani irin ciwon kai da daukewar gani na, na tafi zan fadi yayi maza ya taro ni, daukata yayi tare da nufar cikin gidan dani, da sauri. Yana isa dakin kasa ya kwantar dani. Yana kallon yadda gefen fuskana ya sha mari, shafawa yayi. Yana kallon yadda nake kwance. Tashi yayi ya ma rasa me zai min, kawai ya fita can sai gashi da ruwan sanyi ya samu fuskana ya juye min baki daya, a firgice na farka tare da dafe goshina, kai na yana mugun sarawa. Zama yayi tare da riko hannuna yana kallon yadda nake ajiyar zuciya. Tashi nayi tare da nufar ban daki na, hada ruwan wanka, sannan na cire kayana na fara, tunawa nayi ban dauko wani abu ba, na fito daure da towel a kirjina. Da sauri na nufi inda dama kayana yake na dauki yar abin da zan dauka na na koma ban d'akin. "Karka je ko ina ganin nan fitowa" Na gaya mishi ina turo kofar, na cigaba da abinda nake, lokacin da na fito kusa gashina me bala'in yawa ban daure shi ba, na fito haka zube a kirjina, zama nayi ina tattara su,sannan na daure su baki daya, na kuma gyara shi yadda ba zaka tab'a dauka ina da sumar a kaina ba. Kallon inda nake bai yi ba, alola na koma nayi sannan na zo na sashi yayi. A tare muka yi sallah, muna idarwa na fito falo da niyyar niman abin da zamu ci na rana, sai ga Malam Ansar ya shigo gidan, daidai ba fito ina gyara wandona, kallona yake cike da tashin hankali lokacin da Hammah Mohan ya fito zip din gaban wandon shi a bude. Rigar shi botir din a balle. Cikin fusata ya nufe ni tare da zare belt din wandon shi. Wani irin mugun tsoro ne ya shige ni dan ba a tab'a duka na ba, kawai ya dage ya tsulla min belt din shi a gadon bayana sai da na daka tsalle, lokaci guda ya haukata Ni da duka. Rarrafawa nayi ina ihu tare da cewa. "Don Allah Hammah Mohan ka taimake ni" na nufi ne shi tare da k'amk'ame kafar shi. Jikin yana rawa, tare da kerma ilahirin jikina b'ari yake kamar za a zare ruhina, sabida yau ne karon farko da aka zane ni ban san dukkan ba. Jin bulalar bata kuma dauka a jikina ba ya sani kara k'amk'ame shi ina kuka me shiga jiki. A hankali ya janye kafar shi daga rikon da nayi mishi, ya murɗe malam Ansar da bulalar a wuyar shi kamar zai kar shi, idanun shi sun yi wasu irin jajjur, jijjiyar goshinsa sun mike rad'a rad'a, jikin shi wani irin rawa yake kamar an saka mishi mazari. Kakarin malam Ansar ya sani, d'ago kai na, ganin yadda Hammah Mohan ya shake shi, da sauri na mike. "Sake shi ya hakuri bar shi na yafe mishi." Na fada ina kuka. Sake shi yayi ya fadi, sannan Hammah Mohan ya dawo bayana ya rungume ni yana kallon Malam Ansar. Tare da mishi gargadi da idanun shi da suke cike da b'acin rai. "Wato dan na hukunta ka shine zaka saka ya kashe ni?" Bude baki nayi zan yi magana ya juyar dani muka koma cikin dakin. Zama nayi a bakin gadon ina kuka kamar me, ban san ya aka yi ba sai mika min hannu yayi tare da jana zuwa ban daki ya nuna min ruwa, gyada kai nayi. Na fara ƙoƙarin cire kayana ya fita daga ban ɗakin. Ashe fita yayi bayan ya cire key din dakin ya rufe Ni ta baya, ya samu malam Ansar bai bar gidan ba, damke wuyar shi yayi tare da jan shi kamar kayan wanki ya watsa shi a waje, sannan ta nufi yake ya shiga kwallo shi, baki daya Sojojin ganin abinda Mahaukacin mai gidan su yake yasa kowa ya shiga hankalin. "Yallabai karka kashe shi." Inji Malik yana rungumo Mohan. Ture su yayi domin ranshi yau yakai kololowar baci, haka ya wulakanta Ansar kamar yadda ya zane Almamoon. Sannan ya nufi cikin gidan lokacin na fito daga wanka zazzaɓi ya rufe ni, na kwanta tare da rufa bargo. Ina rawan sanyi. Fita yayi daga dakin ya nufi dakin shi, can sai gashi dauke da wasu abubuwan yana zuwa ya damu ina kwara amai zazzaɓi yayi mugun rike ni, kai hannu yayi zai ja bargon na rike ina girgiza mishi kaina, kyale Ni yayi tare da ajiye min maganin, har zai tashi na rike hannun shi. Tare da juya mishi baya ya sha fa min. Musamman yadda bulalar ya fasa min jikina, yadda ya lakato maganin yana shafa min sai da naji hannun shi har cikin jini na yake yawo, tun daga tsoka har ɓargona ina jin hannun Hammah Mohan, yana gama shafa min ya mike tare da barin d'akin mik'ewa nayi na na cire towel din. Ina shafa maganin daga Ni dai pant, ina bin ko ina inda Bulalar ya fasa ina shafawa, sai a lokacin wani tunani ya zo min taya Hammah Mohan ya fahimci ina bukatar man zafi... Na d'ago kai zan yi nazari shi kuma ya bude kofar sai shigo baki daya na fasa wata irin ihu domin dai tsirara nake........😁🤣😜 Ayi sallah lafiya wallahi ko bashi naci sai haka kai Jama'a.... Babu ranar da ba zan ga Sakon Auta ba🙄🙄🙄 ga Yan Bororoji fans ga Mama Mai Voice! Ga Kawar Mommy na, ga Jikar kulu, Aunty Safiya Jos, Sister Fatima Sabo, Aunty Zully, Da My Kawata Mom Abdul, Da Rano 🤣 😂 Lalalala Aunty Mamieh shekaranjiya har da fushi, A'isha Durling har da kirana tsohuwa, Aunty Khalil kan cewa tayi ta hakura dai na gama rashin daraja na ta karanta😁🤣😂🤣😂 Wallahi wannan labarin da alamu sai ya ci kaniyar Kwarkwarah... Fatan Alkhairi 👏 ayi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ina jiran goron sallah....💞💓❤️Team One Love 😍😘❤️ Mai_Dambun ku ce har kullum. [7/20, 9:06 AM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... *Barka da Sallah Ubangiji ya maimaita mana* BABI NA SHA TARA. Da mugun gudu na danne kofar, tare da sake wata irin kara, me had'e da kuka. "Ashhhhhh! Ohhhh Auwshhhhhhh" ya faɗa tare da banging kofar, sai da na kuma faduwa, ashe na rufe da hannun shi ne, ina jin ya bar jikin kofar na koma ban dakin na dauko kayana, na saka kafin na fito da sauri. Yana zaune tare da zubawa hannun idanu, zuɓewa nayi akan gwiwa ta, na sake wani irin kuka tare da jin nadamar me yasa na matse mishi hannu, riko hannun nayi tare da sakawa a bakina ina tsotsa su, can na kuma mik'ewa zuwa kitchen na dauko kankara na saka a cikin towel na nad'e shi sannan na shiga matse mishi hannun. Duk abinda nake idanun shi kumshe bai bude ba, sai leka fuskar nake jijjiyar goshinsa sun mike sosai. Mik'ewa nayi ina kallon shi kafin na shiga inda first aid box yake na dauko na mishi dress din hannun sannan na koma na shiga duba hannun. "Kayi Hakuri" sai lokacin ya bude idanun shi tarr akai na. "Kayi hakuri kaji" Lumshe dara daran idanun yayi, tare da gyara kwanciyar shi, haka nayi ta kula da hannun a binka da farin fata sai gashi gurin yayi jajjur bayan ya kumbura, shafa mishi man zafi zanyi yayi maza ya rike hannuna. Idanun shi har lokacin bai bude ba. Sai tauna bakin shi yake tare da lumshe idanun shi duk da a rufe suke, amma haka bai hana shi yin yadda zan Fahimci yana jin matsanancin zafi ba. "Kayi hakuri ka ji, nasan da zafi amma haka shine mafita domin zaka ji dadin hannun" a Sannun a hankali yake zare hannun, tare da kauda kanshi yana me jin kamar ya kurma ihu, domin shi kad'ai yasan yadda yake ji. Shigowar Hammah Malik yaga halin da muke ciki. "Subhanallahi taya haka ya faru" "Eh wallahi garin garin garin" nayi ta maimaitawa sabida wani irin kallon da yayi min wanda ya sani jin saura kiris fitsari ya zubo a wandona, kai ban tab'a ganin mugun kallo irin na yau ba. Sannan ya juya ga Malik, ya zuba mishi ido. Shima kuma kamar mara gaskiya shan jinin jikin shi yayi tare da cewa. "Sir ko zamu kai ka asibiti ne?" "Ok bari na kawo mishi jacket din shi ya daura akan kayan zai fi kyau kam a kai shi asibitin." Da sauri na haura sama na dauko mishi rigar Black yayi mishi kyau sosai, ga gashin nan irinta buzayen asali ta wani nad'e akan shi, ba zaka tab'a kallon fuskar shi ka dauka bai da lafiya ba. Saboda kullum cike yake da kwarjini da kamala, haka muka nufi asibitin domin yaki bin Malik sai da nace mishi. "Toh muje" Haka ya saka kai ya biyo mu, baki daya ina walwala ne amma bani da nutsuwa domin kuwa ina tsoron malam Ansar sosai,haka aka gama duba mishi hannun shi, sannan muka dawo gida. Zuwa dare sabon zazzaɓi ya rufe mu dukkan mu, dakyar na shiga dakin shi tare da taimaka mishi yayi wanka, amma yana fitowa yanki jiki ya fadi, gashi tikeke, haka nayi ta jan shi. "Ko zan kira Hammah Malik ne baka da lafiya" lumshe min idanu yayi yana kallon yadda nake son kuka nima zazzaɓi nake ji. A hankali ya dafe jikin gadon tare da rike Ni da karfi sai da na kusan faduwa, sannan ya mike dakyar ya faɗa gadon, tare da fisgo ni jikin shi. Hakoran shi suna haduwa da juna. A hankali na saka kafana na janyo bargon na lullube shi, sannan na gyara kwanciyar shi, kafin na fara ƙoƙarin zamewa a jikin shi, wasu irin kananun surutai yake tare da faɗin. "Zasu harbe ni, karka bari su same mi." Ya fada tare da matse ni a jikin shi, yana ƙoƙarin boye fuskar shi a jikina, tsoron kar ya cutar dani ya sani fara mishi addu'o'in, can naji yana sauke ajiyar zuciyar, sai barci me mugun karfi ya tafi dashi. A hankali na gyara mishi kwanciyar shi, kafin na fara ƙoƙarin saukowa a gadon ya rike hannuna, haka na dawo na kwanta a gaban gadon, hannun shi cikin nawa, haka nima barcin ya dauke ni. -.02:30am farkawa yayi yaji hannun shi da na Almamoon a sarkafe da juna, a hankali ya zare nashi tare da mik'ewa ya nufi ban daki yayi alola sannan yazo ya gabatar da sallah da yake kanshi, zama yayi yana addu'o'in wanda duk kusan rabin shi kuka yake hannun shi a sama, bayan ya idar yaji Almamoon yana nishi a hankali a hankali. Tare da kuka yana surutu shima. mik'ewa yayi tare da nad'e abin sallah. Yana ajiyewa ya nufi gaban gadon, a hankali ya durkusa zai dauke shi, bakin Almamoon ya sauka akan kuncin Mohan, tare da sauke mishi wani irin nishi me tab'a jiki da jini, sabar shi yaji sama yana kallon fuskar shi, musamman yadda ya daura kanshi a daidai kahon zuciyar shi, wannan ne first time da ya tab'a ɗaukar wani a hannun shi. Ko mace bai tab'a rikewa ba indai ba jarirai bane. A hankali ya haura gadon ya kwantar dashi, yana me gyara mishi kwanciyar shi,,.bayan ya ja mishi bargon shi, ya zo zai dai fuskar shi zai gyara mishi kwanciyar shi musamman wuyar shi da ya kwanta a karkace, sai ji yayi Almamoon ya kuma damke wuyar shi. A hankali ya kwace rikon ya gyara mishi kwanciyar shi ya fita daga dakin yana mamakin meye ya kawo mishi wani jikin shi? Yasan ya samu lafiya amma baya son koda wani a cikin gidan ya san lafiyar shi lau. A hankali yake takawa cikin wata irin kasalalliyar yanayi, ya fita daga dakin ya nufi dakin shi, ya zauna tare da dafe goshinsa yana jinjina karfin k'iyayyar da Hajiya Safeeya take mishi meye yayi mata da zafi haka? Ba dan Almamoon din ya zubda maganin ba tabbas da wani mara imanin ne zuba mishi maganin zai yi, meye ya tsarewa mutane da suke burin su kashe shi? A iya sanin shi dai bai da matsala da kowa amma meye ya kawo haka? Akwai dalilin da yasa Almamoon yazo ina Khalil da Malik? Amma ko yau kwana biyu yasan Khalil ya tafi amma zaman me yake a cikin gidan nan da yayi shi domin ya kawo matar shi gidan, wato wacce zata zama mallakin shi. *** Tun da asuba na tashi jikina babu dad'i, dan haka na sauka a gadon na shiga ban daki ina mamakin taya aka yi na dawo sama gadon ni da na ke kwance a kasa. Lumshe idanuna nayi bayan nayi alola zan yi sallah ya shigo. Shima ina ga alolan yayi yazo tadda ni. Kallon yayi na wani lokaci kafin ya juya ya fita, rufe kofar nayi na gabatar da sallar, ina idarwa na mike tare da nufar kitchen na mana abun karyawa, ina gamawa na kawo zan ajiye, na hango shi zaune ya daura dogayen kafaffun shi a saman hadaddiyar center table din falon yana kallo. "Hammah ina kwana?" Na dai fada ne amma ban sani ba ko zai amsa, Bai kalle ni ba ya cigaba da abinda yake, mik'ewa nayi na nufi gurin shi da abincin, ya kawar da kanshi, Cigaba nayi da tsayuwa. "Ga abincin ka ni tafiya makaranta zanyi" na fada ina tura mishi baki..share ni yayi ya cigaba da kallon shi. "Wai ma waye ya kunna maka tv? Bana ce kayi ta kallon Tashoshin musulunci bane, na kuma ganin ka kunna labarai sai na cire kunnen ka" na fada ina zare mishi ido. Kallon Yaron yayi daga sama har ƙasa. *Wannan Yaron akwai karfin hali!* Ya fada tare da mik'ewa yana me nufar hanyar table din, sake baki nayi tare da nufar shi da abincin. "Ina wasa da kai ne? Wato zaka mai dani karamin mutum na kawo maka abincin ka taso ka bar ni dashi" na fada da karfi ina zare mishi ido sannan na cigaba da cewa. "Sai na gayawa Hammah Khalil dan na lura kafu shakkar shi, tunda ka rena ni" *Kan Uba! Wato Dan Ba'are ya gaya mishi ina shakkar shi kenan dan Uban shi? Lallai zan ci kaniyar ku daga kai har dan Ba'aren* ya faɗa tare da bin Almamoon da wani mugun kallo kasa kasa. "Maza dauki cokali kaci abinci." Na fada a ikonce, irin nice gaba da shi. *Wai Ni dan abun nan yake min ihu? Abinda bai fi nayi loma daya da shi ba! Zan kama dan Ba'are sai naci Uban shi dan banza mara mutunci* Babu musu ya dauka ya fara ci yana kallon fuskana, tari ya fara na bashi ruwa ya sha, sannan nima na dibe nawa na dawo falon ina ci, kad'an yaci sanan ina gamawa na nufi hanyar kitchen na ajiye kayan, a gurguje na gyara gidan, sannan na tawo tare da rike hannunshi muka haura sama, na bashi magani da addu'o'in da nake tofa mishi. Dakyar yasha yana niman kwara min amai. Ko ta kanshi ban bi ba, na dauki jakata na fita ina me shafa sumar kanshi na fita da sauri. Sabida na kusan makara. Lokacin da na iso makaranta, an kusan shiga aji dan haka ina isa bakin kofar shiga naga dalibai sun tsare hanyar. "Lafiya kuka tsaya a tsatsaye kamar mama maza?" Na tambaye su ina nufar hanyar shiga aji.. "Ai har kai Almamoon malam Ansar zai nemi ya taimaka maka ka saka a mishi dukar kawo wuka?" "Haka ya gaya muku?" Kallona suka yi tare da cewa. "Idan na haka ba toh meye kayi mishi?" "Tunda ku nan uwayen shi ne me zai hana ku rama mishi" ban tab'a zata zasu iya duka na ba, amma dai gashi sun rufe Ni da mugun duka. Dakyar aka kwace Ni na sha mugun bugu, kasa zama nayi domin abokan malam Ansar sun goyi bayan daliban, dan haka aka kore ni zuwa gida, kuka yana cina amma kuma na kasa yi,tafiya nake kamar wanda kwai ya fashe mishi a cikin shi. Ina isa bakin get na samu motar haya, ya kai ni gida, ina isa bakin get din farko aka dauke ni a wani motar zuwa cikin gidan, ina shiga gidan na hango shi yana tsaye ya zubawa dabbobin shi ido hannun shi a cikin aljuhun farin jeans din shi na kamfanin Next, sai bakar riga me kyau me dogon hannu, ya daura wata mara nauyi akan rigar cikin fari tass na saman. Hadaddiyar gashin kan shi ya dauka har keyar shi, Kwalla ne ya shiga zuba min ina jin kirjina yana bugawa da mugun gudu. Na shagala da kallon shi kwalla na zuba min. Yayi nisa gurin tunanin yanayin da ya tsinci kanshi, da yadda yake rayuwa babu lekowar iyaye. Lumshe idanun shi yayi lokacin da yaji kamar ana kallon shi, a hankali ya juyo tare da kallon yadda yake tsaye kamar an dasa shi a gurin. Takowa yayi har inda yake ya hango Bakin Almamoon a fashe. Kura mata ido yayi tare da kasa motsi sakamakon tawowa da Almamoon yaji ya wani rungumo shi yana kuka kamar ranshi zai fita. "Hammah Mohan, don Allah ka mai dani ni gurin Innata, bata tab'a duka na ba, amma sabida malam Ansar na sha dukka sau biyu." Na fada ina kuka tare da jin ko ina na jikina yana ciwo, janye ni yayi a hankali yana kallon yadda fuskana ya kumbura, sai jinin da yake fita ta hancina. Ga goshina da ya fashe, cire rigar saman yayi tare da saka min a bayana sabida yadda suka yaga min rigar jikina, ya lullube ni da shi, dake saman rigar ce, rike hannuna yayi tare da wucewa dani cikin gidan. Ruwan sanyi ya dauko ya bani na sha, na sauke ajiyar zuciya. Bai magana balle ya ce min nayi hakuri, haka ya zuba min ido, sosai sannan ya mike tare da nufa sama, can sai gashi ya kuma saukowa da kayan first aid box. Duk da hannun shi yana ciwo bai hana shi nutsuwa ya shafa min idean ba, lokacin da ya saka min spirit ne na shiga tsalle ina wash da rike hannun shi. "Don Allah ka barni na huta, idan na huta sai ka saka min" na fada ina matsar kwallan, bai saurare ni ba, ya kuma dangwala audugar ya manna min. "Wayyo Allah na zaka kashe wallahi sai na huta kafin ka kuma saka min wayyo ni wayyo zafi don Allah ka saka min a hankali." Kamo ni yayi tare da juyar dani, ya matse ni yadda ba zan iya motsi ba, yana wanke min ciwon ni kuwa sai kuka nake da rikici. Shigowar Malik zai gaya min Ansar ya zo, ya tsaya baki sake yana raba idanun shi akan mu, d'ago kai Hammah Mohan yayi tare da d'aga mishi gira alamar lafiya. Cikin wani irin yanayi da ban mamaki ya kame guri guda ya sara mishi tare da cewa. "Jami'an soja mai lamba C210 mai igiya uku Malik Moussa Abzin yake magana Yallabai" Lumshe idanun shi yayi yana jin wani abu yana yawo a jikin shi tun daga tafin kafar shi har tsakiyar kanshi, tsigar jikin shi sai mik'ewa yake, d'ago kai nayi ina kallon fuskar shi wacce take kara fidda wata irin kwarjini. Shagala nayi ina kallon shi. Bayana yana jingine da kirjin shi, hannun shi daya yana tsakanin cikina da kirjina, daya hannun shi kuma yana rike da almakashi. Jinjina kai yayi tare da kallon Malik irin ina jinka. Nutsuwa Malik yayi a karo na biyu ya fadi abinda ya kawo shi, da sauri na fara ƙoƙarin mik'ewa a jikin shi, kai hatta sunan malam Ansar tsoro yake bani, balle kuma nayi ido biyu da shi. Gyada kai yayi alamar ya shigo da shi. Yana makale dani, har lokacin bai barni na mike ba, fuskar nan ta kuma had'ewa shigowa malam Ansar yayi yana dingishi. Tun kafin ya idda sallamar shi kalmar ta makale a wuyar shi yana kallon ikon Allah. "Almamoon" ya faɗa a sanyayye, cikin wani azzababben kishi, ya tako da karfi ya manta da ciwon kafar shi, yana zuwa ya tsaya a gaban mu jikin shi yana kerma, kokarin fisgo ni yayi amma ya kasa. "Tashi ka haura sama" a mugun kidime na juya ina kallon shi, fuskar ku kusan tana gogan juna, hancin shi har yana gogan goshina, d'ago kai nayi ina kallon bakin da yayi magana, tare da kura mishi ido, ina jin sautin Muryan shi har cikin jinin jikina. "Nace tashi" kara ware idanuna nayi ina kallon shi bakina cike da mamaki. Can kuma sai gashi ya daure fuskar sama da baya, da sauri na mike na haura sama. Nunawa malam Ansar guri yayi tare da kallon shi. "Ba zama nazo yi ba, abinda na kawo na zo dauka" Cikin renin hankali irin ta namijin duniya yace mishi. "I thought abinka yana jikinka" ya faɗa cikin wani irin isa, kamar ba shi yayi maganar ba. "Poor" inji Malam Ansar. Kamar bai ji abinda yace ba, ya kuma Cigaba da kallon yatsun hannun shi. " Malam ka bani yaron can domin ni na mishi hanyar samun damar zama a cikin ku." Ya fada cikin karaje da fusata. Juyawa yayi tare da kallon inda zai ga yaron, bai ga kowa ba. Ya juya tare da tab'e baki yace mishi. "Ban ga yaron ba, yana ina?" Ya fada yana kallon malam Ansar wanda ya cika kamar an watsa mishi yiest. A fusace ya mike Mohan ya mike tare da sakala hannun shi dukka biyu a k'ugun shi, suran shi ta zaratan sojoji ta kuma bayyana sama da farko, ya fito giant din shi, ya tsaya a gaban Ansar duk da shima ba kad'an bane amma Mohan ya kere shi. "Akan me yasa kake cutar da shi bayan kasan kana bukatar shi a tare da kai?" Wani irin duba yayiwa Mohan sama da kasa, kafin ya fashe da dariya. Mai karfi sosai sannan yace mishi. "Ina son shi! Ina kaunar shi! Tun daga lokacin da na fahimci shi mata maza ne, na fara kaunar shi dan haka matsa min a hanya na dauko shi" Shiru yayi tare da matsa mishi a hanya ya wuce sama, bai hana shi ba, komawa yayi ya zauna yana tuno abinda ya faru jiya, ok dalilin da ya sa kenan ya datse mishi kofa a hannun? Lashe bakin shi yayi yana kallon yadda zasu kaya. Can kuwa sai gashi nan ya fito da Almamoon yana jan shi, shi kuwa sai kuka yake yana faɗin. "Ni kam ba zan je ba, ka kyale ni" na fada mishi ina kuka. "Ba zan ba zan cigaba da ganin ka cikin suffar maza ba muje idan ka ga gatar da na shirya maka iya ni da kai a duniyar mu sai kasha mamaki." "Bana son" na fada da karfi ina kwace hannuna. Na nufi gurin Hammah Mohan, yana zaune ya aza daya kan daya yana jin mu,. Rike kafar shi nayi ina kuka. "Don Allah karka bari ya tafi dani". Na fada ina kuka. Malam Ansar yana zuwa ya fisgo ni, tare da d'aga hannu zai mare ni, Ya rike hannun. "Masoyin gaskiya ba tab'a dukar abinda yake so, manufar ka mai kyau ce, amma dukar ba zai iya canza kome ba. Kai kuma ka bishi ku tafi." Ya fada min yana kallon yadda na sake baki, jikina yayi mugun sanyi, haka ya nuna min hanya. Had'iye yawun da ya tsaya min a wuya. Ina kallon shi, na kasa magana, kawai saka kai nayi zan fita. "Amma irin wannan al'amarin iyayen shi sun sani?" Ya tambaya yana kallon yadda Ansar yake jan hannuna. Cak muka tsaya, wasu irin kwalla ne suke zubo min, a hankali ya mike tare da takowa gaban mu. Ya zare hannun malam Ansar da ya rike hannuna. Sannan ya saka hannun shi ya riko k'uguna. "Hatta kare idan yana tarayya da shi ba zan tab'a barin shi yayi haushi ba balle kuma shi Yaron ka koyi yadda ake martaba dan adam sai ka dawo na baka shi...... _Barka da Sallah! Na cika muku alkawari.......😘😍saura kuma ku nuna min naku alkawarin.... Karku saka rai zaku samu update nan kusa domin sha'anin aikin sallah_ #Mai_Dambu... [7/21, 6:14 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ASHIRIN. Wani irin sanyin naji tun daga kafana har tsakiyar kai na, kokarin mai da kuka na, ina kallon shi. Kara kawo hannun Malam Ansar yayi,.da sauri ya kifa kaina a kirjin shi tare murɗe hannun shi sai da yayi kar'a, so nake naga abinda yake faruwa amma fir ya matse kai na a kirjin shi, dan haka baki daya na kasa aikata kome. Cire kaina nayi tare da kallon yadda ya murɗe hannun. "Sake shi kaji" na fada ina kallon shi. "Almamoon! Ni ka ciwa zarafi? Ni ka wulakanta? Almamoon ko yagar namar jikinka nake bai dace ka min haka ba. Amma babu kome." Ya kwace hannun shi yana me barin gidan. Yana fita Hammah Mohan yana kara birkice min, domin kwanciya yayi min alamar bai da lafiya, baki daya na tsora ta. Ya ciwon shi ta dawo sabo fil, sai shegen taurin kai kamar tsohon jaki.. daga rana zuwa dare kamar zanyi hauka, domin sai yayi kamar zai fadi kasa, ina tare shi zai ture ni ya falla a guje. Washi gari. A dararre na wullakila idanuna ina niman shi, hango shi nayi a saman table din cin abincin gidan. "Sauko ko na zane ka" na fada ina gyara hannun riga, "Dama ciwon bai kyale ka bane shine jiya har da..." "Assalamu alaikum!" "Yawwa Hammah Malik dubi abinda mutumin nan yake yi, kana ganin shi kamar wani robot sai rashin mutunci wallahi kayi wani abu ko na sab'a mishi sauko idan ba haka ba zan zane ka" Kallon shi Malik yayi da alama ciwon ne ya kuma dawowa, dan haka ya kira malamin ranar, yayi mishi bayani. Riko hannuna yayi tare da jana gefe yana fadin. "Kaga ka tafi makarantar ka, zan ji da kome" gyada mishi kai nayi na nufi daki na dauki kayana, kallon shi nayi cikin tausayawa nace mishi. "Allah ya baka lafiya" Na fita daga gidan. Motar da yake kai ni makarantar na shiga, duk da bani da nutsuwa, amma zuciyata bata so zuwa ba, naso na zauna a jikin shi har naga halin da zai yi. Hana motar aka yi ta shiga makarantar, ina zaton basu san darajar me motar bane, dan haka na sauka a bakin get na shiga makarantar da kafa. Ina shiga aji na zauna a nutse, ina sauke ajiyar zuciya. "Almamoon ashe kuma likafa ta cigaba ashe ka fara aikatau a gidan manyan mutane shin aikatau na aikin gida ko kuma aikatau na bin bayan ka?" Duk sai na muzanta, sunkuyar da kai nayi ban ce kome ba, haka malamin ya shigo yayi mana darasi bayan fitar shi. Naji ana ta dariya a cikin ajin. Sosai fa, Mik'ewa nayi na kuma jin sun kwashe da dariya, da sauri na fita daga ajin duk inda na wuce dariya ake min. "Almamoon Isma'il Wodaadabe, tsaya ka ciwo abinda aka rubuta a bayan ka" cak na tsaya ina jin wani irin tsoro yana kamani, nasan dai ba haila bace tunda sati Daya da ya wuce nayi gama. Cire min takardan da aka rubuta Kalmar Mata maza da manyan Haruffa. Jikina har wani irin rawa yake, na juya zan bar gurin. "Mamoon" juyawa nayi na kalle shi. "Kad'an daga cikin abinda kayi min kenan, kuma baka ga kome ba domin yanzun aka fara." Dariya ya bani na tsaya sosai a gaban shi ina faɗin. "Idan na kula ka ban san darajar kai na bane, amma idan har ka cika namiji ka tari Mohan Mamman Nasir Aghali ka ga yadda ake wasan kura da lusari irinka." Na juya zan bar gurin ya fisgo ni,cikin fushi na kai hannuna zan mare shi, sai kuma na fasa ina kallon cikin idanun shi. "Wallahi kaci albarkacin girman ka da nake gani da yau na mare ka a cikin makarantar nan, kuma na rantse da Allah sai na baka mamaki." Nayi tafiya na na barshi tsaye cikin mamaki. "Dan daudu zai bani mamaki" murmushi nayi na cigaba da tafiya, domin bani da abin da zan gaya mishi, koda na gaya mishi ba zai ji haushi ba, kuma koda ma mishi a aikace ba zai damu ba, duk wanda ya cutar da kai ba zai tab'a jin zafin dan ka rama a lokacin barshi ya manta abinda ya aikata, haka na kyale shi. Sake tare ni daliban shi suka yi. "Kai dan dan daudu, me bin maza kawai lalatacce mara hallaci." Ban kula su ba, sai ma keb'ewa da nayi zan bar su a gurin dan basu min kama da masu hankali ba. Ina barin gurin su, na samu kasar bishiya na zauna, ina son nayi kuka amma ba zan iya ba, bana son nayi kuka yanzun so nake na iya shanye kuka na, gashi ban san halin da Hammah Mohan yake ciki ba. Bayan an koma aji na mike tare da shiga aji, na zauna ina sauraron darasin shi. Har ya gama zai tafi. "Dalibai ku kasance masu tsentseni da sanin ya kamata, karku zama butulu marasa halacci." Murmushi nayi ina kallon shi, sabida ya daina bani mamaki sai dariya. "Kai waye kakewa dariya?" Ya tambaye ni, ware idanun nayi cikin dariyar renin hankali nace mishi. "Ina dariyar yadda mutane suke manta waye su? Kamar Ni dai." Na nuna kai na ina dariya. Mik'ewa nayi zan fita, ya tare hanyar fita. "Ansar Yusuf, ka bani hanya na wuce na Barka kayi rayuwar ka baka isa ka hanani tawa rayuwar ba, Ansar kayi yadda kaga ya dace amma karka shiga cikin abinda babu ruwan ka" na fada ina me barin ajin. Da sauri na fita a makarantar. Ban samu motar da yake zuwa dauka na ba, dan haka na tari abin hawa, sai dai ina shiga da malam Ansar nayi tozali, kamar zan fasa dan wani irin tsoro ne ya kamani, sai na shiga na zauna ina kallon shi. Kamar da wasa madadin su kai ni inda na faɗa sau suka wuce dani wani gurin. Wani asibiti muka nufa, ban mishi musu ba, har muka shiga cikin asibitin. Tare da nufar office din wani likita, kamar Balarabe ne. Muna zuwa ya mika mishi hannu suka gaisa, Kafin ya fita. "Ko zamu je na duba ka?" Murmushi nayi domin a yanzun nake kara hango Malam Ansar shi ya dace da kasungumin mahaukaci ba Hammah Mohan ba. Mik'ewa nayi zan fita ya mike shima. "Kazo ka zauna na duba ka." "Ba zan iya ba, kuma wallahi ka kuskura ka tab'a ni sai ka yanke ka." Na fasa wata Kwalba da tasa shi tsorata, na fita abina daga dakin. Na samu baya nan da haka da sauri na fita a cikin asibitin. Kamar zan tashi sama haka na bar harabar asibitin, ina isa bakin hanya ana kiran sallah la'asar, Dakyar na sami abin hawa. Na fada mishi inda zai kai ni. Ina shiga malam Ansar yana isowa da gudu ya biyo mu. "Malam karka tsaya sace ni yake son yi don Allah mu tafi" na fada mishi ina me jin kwalla na cika min idanuna, ai kuwa driven ya taka motar da gudu, muka bar ganin shi. Tafiyar kusan minti arba'in ya kawo mu unguwar lokacin da ya tsaya na bashi kudin shi na juya zan tafi. "Malam kudin yayi yawa" "Jeka kawai" na fada mishi ina ƙoƙarin shiga cikin kofar get din farko. Rike hannuna malam Ansar yayi, a tsora ce na juya. Ina ido hudu dashi na fasa ihu, ina ƙoƙarin kwace kai na. "Don Allah ku fito ku taimake ni, zasu sace ni" kafin sojojin su fito ya shaka min abu a hancina, komawa nayi tare da zuɓewa a jikin shi. A hankali na fara ganin kome yana juya min bibiyu kafin na koma tare da lumshe idanuna. "Hammah Mohan" na fada a hankali. Fitowa sojojin suka yi lokacin har ya saka Ni a motar shi, ina da gudu ya bar Unguwar. Danna wani abu suka yi take ilahirin sojojin gidan suka fito. Suna masu hango motar tana tashi da kura. "Meye ya faru Fahad?" "Wallahi wani da bamu sani bane ya dauki Alm.." "Haukar banzan kuke kenan? Tsayuwar Uwar me kuke?" Inji Malik, Ai kuwa kamar wanda ya ankarar da su, suka rufawa motar baya da hilux, amma kafin nan ya b'ace musu, kamar zasu yi hauka. Koda suka dawo sun sami Major General Mohan Mamman Nasir Aghali a tsaye yana kallon su. Baki daya aka rasa wanda zai sauko a cikin motar zunzurutun yau sun ganshi a cikin unifoam. Yana jingine da bike kanshi sanye da hular yaki, fuskar shi tayi jajjur. Yana kallon agogon hannun shi. Tab'a bluetooth din shi yayi. "Ina jin ka? Number guy din? Ka gayawa dakin iko, su bani bayanin inda yake nan da minti biyar" A fusace ya kuma daka mishi tsawa. "Dan Ba'are! Wallahi na rantse da Allah sai na harbe duk wanda ya kuskura ya shiga tsakanin mu da My Maid idan ka sake na kuma kiranka wallahi sai na dakatar da kai" Ai sojojin da basu nimo Almamoon ba sai gasu sun zube a gaban shi cikin tashin hankali. "Yallabai wallahi" yatsar shi ya saka a bakin shi, tare da nuna musu hanya. A hankali ya hau kan bike din, tare da saka hular kwanon shi, ya taka machine din ya jata da mugun gudu, yana bin bayanin da ake gaya mishi. Sai da yayi tafiyar minti Talatin kafin ya isa asibitin da Almamoon ya gudo, cikin isa ya tsaya yaran shi suka iso, tare da taka mishi baya da bindiga a hannunsu, irin duk wanda ya kawo mana wargi zai sheka lahira. Wani irin tafiya yake cikin jarumta da Izza, tare da jin shi din a bakin aikin shi yaƙe. Matashin sojan da yayi zarra sama da sauran manyan sojojin da suke saman shi. Duk inda suka wuce bin su ake da idanu, sabida yadda suke takon a nutse baka jin kome sai karan takun takalmar su, kai.daga dakuna sai leken su ake, cikin isa da jin kai ya isa bakin kofar da aka gaya mishi nan Almamoon yake, dukar kofar yayi da kafiran takalmin shi, budewa kofar tayi daidai ana ƙoƙarin cire kayan Almamoon wanda yake kwace kamar gawa. Wata Ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tsaya cak yana kallon fuskar Almamoon da kwalla ta bushe akai. A hankali ya ja wani kujera ya zauna yana kallon yadda Nurse din cikin dakin da kuma likitan suka yi tsuru tsuru. "Ina yake?" Fitowa Malam Ansar yayi tare da da kallon shi babu tsoro a fuskar shi ko nadama. Mik'ewa yayi tare da nufar shi. "Wannan shine kashedina da kai na karshe karka tab'a Yaron nan tunda ba kai ka kawo min shi ba" inji Malam Ansar, "Idan na ki fa?" Ya tambaye shi a gadarance. Tare da nufar Almamoon, yana ƙoƙarin daukar shi. Wani allura ya dauka ya suka a wuyar Almamoon, kafin ya juya ruwan. Mohan ya kai mishi wani irin duka akan hannun..sai da kashin hannun shi tayi kara, yayi maza ya zare alluran. Takowa yayi gaban shi yana kallon shi. Da hannun daya ya d'ago shi. "Idan ka kuma tab'a ko inuwar shi, wallahi na rantse da Allah sai na aikaka lahira, ina kyale ka ne sabida karatun shi nasan zai fi son shi a matsayin shi ne ba kowa ba, idan ka sake raina ya b'aci, hmm" ya faɗa tare da barin gurin shi ya juya zai dauki Almamoon. "Wallahi ka rubuta ka ajiye, sai na raba ka dashi, wannan alƙawari na ne" Daukar maid din shi yayi tare da tsayawa cak, yace. "Ni kuma nayi maka alkawarin barinka a raye domin ka ga yadda zan yi da Yaronka." "Wallahi baka isa ba! Ni zan Barka a raye domin ganin yadda zamu yi dashi." Inji malam Ansar, "Hhhh! Ni Mohammed Mamman Mohammed Nasir Aghali Mohan na kara gaya maka na maka alkawarin kana raye zaka gan mu da idanun ka, kai ba kai ba hatta shaidanin zuciyarka sai ya gan mu a tare balle kai banza irinka... 2k Words 😁 _😌😌😌 Anya zan cigaba kuwa wallahi Vote yayi kad'an ko na ajiye shi ne na fara Kishi a tsakanin zubda jini ne dan na ga kuna mutuntta labarin kuɗi sama da free book_ [7/22, 9:49 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ASHIRIN DA D'AYA. Cikin ihu da masifa yake bin bayan Mohan tare da niman riko rigar shi, amma zaratan sojojin da suke bin bayan MG Mohan suka cafke shi, tare da shiru suna jiran Umarnin shi. "Ku kyale shi ya rayu. Na barshi ya rayu domin idan kuka dake shi sai ya leka lahira ya dawo." Ya fada tare da cigaba da tafiyar shi, Ganin Almamoon baya motsi ya sashi karawa da sassarfa, yana kallon fuskar shi, hular kanshi ne ya zame, lallausar gashin sa da yake tufke baki wuluk wanda yake warware. Kallon shi yake yana kara mamakin yadda namiji dashi yake da uban gashi haka. Yana fitowa ya ajiye shi a cikin motar su, kallon Fahad yayi tare da kallon bike din shi, sara mishi yayi sannan ya koma, gurin bike din ya ja machine din da gudu, yayi da suma suka rufa mishi baya. Tab'a bluetooth din shi yayi tare da cewa. "Malam turo min wani likita daga barikin sojan maradi." Tab'e abin yayi tare da sauke wani irin ajiyar zuciya. "Yallabai an tura masu wani motar da zata kwaso su." "Hmm" ya faɗa, yana me kallon zoben hannun Almamoon, a hankali yake me jin kamar ya rufe Ansar ku baki daya, amma bai san girman da yake dashi a duniyar Almamoon ba, sai ya farka. Suna isa gidan ya sauke shi cak, har yana mamaki. *Dube bakin shi da ya iya zungure min goshi, nan kuwa tsiwa ce zallah babu wani karfi dube shi kamar ba namiji ba* Ya fada a kasan ranshi, yana jin wani dariya yana niman kwace mishi, yanzun ma idan ya farka zai koma kamar da yadda zai cigaba da rena mishi hankali, dan yana son haukar yaron baki daya ya kam manta da batun shi din wani ne yayi ta shirme. Shigowar wani likita tare da wasu mata biyu, suka fara aikin su a kan Almamoon, tashi yayi ya bar musu gurin. Can suka ci-gaba da aikin su, sai kallon juna suke musamman bayan da likitan ya gama nashi suka fara nasu. Abun mamaki ya basu. Me yasa haka? Dan gulma sai da suka yi ta duba shi har cikin, tsoro ne ya kama su lokacin da Mohan yayi gyaran murya, da sauri suka bar shi. Juyawa suka yi. Likitan ya fara magana. "Yallabai mun debi jikin shi, zamu bincika muga abinda yake cikin shi. Nan da awa daya." "Amma Likita mara lafiyan yana" "Na Fahimta muje Insha Allah zamu kara dawowa, sannan na sami sauran birbidin maganin da aka shaka mishi zamu yi bincike akai." Suna barin gidan likitan ya balbale su da faɗa, yana gaya musu. "Dan baku da hankali taya kuna gaban MG na soja zaku saka bakin ku a cikin maganar mu kusan waye shi?" Shiru suka yi dan sun san halin shi masifaffen ne, har suka isa asibitin, cikin abinda bai fi awa daya ba aka gama binciken. Yana karanta abinda ya kusan da sauri ya kira Dan Ba'are ya gaya mishi. "Don Allah ku tawo da majiyancin nan rayuwar shi tana cikin hatsari" Zunzurutun tashin hankalin da dan Ba'are ya shiga kamar zai dira a maradi, dan haka ya kira Mohan a hanzarce. "Yaron nan yana cikin hatsari a kai shi asibiti gani nan zuwa." Kashe wayar Mohan yayi mishi. "Hello Hello! Kai kai katsaya mana" babu shiri ya dauki kayan shi bai tsaya wata wata ba. Ya kira wata wayar da take cikin Office din shi, ya faɗa musu abin da yake bukata, cikin kankanin lokaci suka hada mishi kome, yana fita ya daga Office gidan shi ya nufa, ya haɗa abinda zai hada, .... A dakile ya watsar da wayar tare da shimfid'a dogayen kafaffun shi a samar table, yana kallon Almamoon da fuskar shi yayi wani irin fayau kamar wanda aka kwashe mishi jinin jikin shi. Bakin shi kuwa fari yayi fayau. Idan ya cigaba da rike yaron mutuwa zai yi, dan haka a zuciye ya dauke shi, yana fitowa dauke da Almamoon, sojojin da suke gidan suka mike, tare da nufar inda motar aikin su yake, suka yadda saka shi yayi tare da shiga ya zauna ya daura kanshi a kan cinyar shi. Lumshe idanun shi yayi yana tuno yadda ya birkice yau ganin halin da ya shiga, duk yabi Cameras na cikin gidan yaga yadda yaron yayi ƙoƙarin kula da lafiyar shi. Da yadda aka yi ta had'a mishi mugun abu a cikin gidan a saka Hajiya Safiya tayi ta dukar shi. Ya rasa inda zai saka zalincin Hajiya Safiya baki daya. Sai dai wani abu daya da ya lura dashi. Bude fararren idanun shi yayi akan kofar asibitin. Ga Nurse da suka tsaya suka jiran fitowar su, a hankali ya fita tare da bude inda Mamoon yake kwance. Ya fitar dashi, Tunda aka shige dashi wani daki bai kuma ganin wani ya fito ba. Tun yana kirga lokacin da aka shiga har ya kai ya daina duba agogon lokacin sallah nayi suke fita da Malik. Bayan awa biyu sai ga Dan Ba'are, kallo daya Mohan yayi mishi ya dauke kai Kamar bai tab'a ganin shi ba. Asalima haushin yadda yake bashi umarni yake sai kace irin shine a kasar shi. Wani b'ata rai yayi yana shan kamshi kamar bashi ba. Shi kuwa bawan Allah bai fahimci halin abokin shi ba, abu daya zuwa biyu ya tambaye shi. "Ya jikin ka? Ya jikin Almamoon?" Wani basarwa yayi tare da mai da smart watch din shi hannun shi yana wani cin magani, dakyar bakin shi ya motsa da cewa. "Da sauki" Ka sake Dan Ba'are yayi yana kallon shi. Kafin jikin shi yayi wani iri, komawa gefe yayi ya zauna tare da ɗaukar wayar shi yana latsawa,shi kuwa Mohan sai wani tsare gida yake irin ba zai yiwu ba. Fitowar likita ya sa dan Ba'are mik'ewa ya mikawa Dr Faruq hannun suka gaisa. "Faruq meye a ke ciki?" "Yallabai rayuwar shi ta fita daga matakin tsari, sai dai bamu da kayan aikin da zai tacce jikin shi." "Dama kunsan baku da kayan aikin uban waye ya ce kuce a kawo ta?" Ya fada tare da watsar da su baki daya gefe yayi wucewar shi cikin dakin. "Mohan ka tsaya ayi magana kaji yace idan da za a fita dashi kasar waje ko Saudi za a dace." "I fuck nonsense words, taya zaka gaya min maganar banza kaniyar kasar waje hell You da kasar wajen" ya faɗa a tsawa ce. Yana bankawa dan Ba'are hararar. Dan ya tsani duk wanda zai mishi iyayi akan Mamoon. "Amma dai meye na zagi? Kamar wanda aka mishi wani abu? Yaron nan dai ni na kawo shi dan lura da lafiyar ka, so it's my responsibility na tsayawa rayuwar shi if not me kake tsammani za a dauke ni, don Allah kayi hakuri a dauki matakin da ya dace." Kura musu ido yayi cikin nutsuwa ya juya zai fita daga asibitin, zuciya kawai yake dawainiya da shi, yana fita ranshi ya kuma b'aci dan haka bai tsaya a asibitin ba ya nufi gidan shi, dakin motsa jikin shi ya cire kayan shi ya rage daga shi sai farin wando. Daukar karfe yayi yana nazarin yadda dan Ba'are ya nuna mishi fin karfi akan Almamoon ne. Ba zai kuma shiga damuwar su ba. Dan haka abinda yake gaban shi zai yi ya cigaba da boye matsalar shi,.kiran Malik yayi tare da zubawa kofar idanun shi. Wanda suke cike da masifar rikici. Yana zuwa ya zuba mishi wasu files a gaban shi, tare da kamewa ya sara mishi tare da yin alamun yana da magana. "Humm" yace a hankali, "Yallabai! Na gama tattara bayanan baki daya, sai dai yaron bai da matsalar kome, kuma ba shi da alaka da Ansar Yusuf. Wancan kuma akan case din su.." D'aga mishi hannu yayi tare da kafe kofar shiga da idanu. Sara mishi ya kuma sannan ya juya tare da barin d'akin, yadda kan shi ya dauko zafin nan idan ya cigaba daukar magana ji yaƙe kamar zata fashe shi yasa ya bar asibitin dan ranshi ya fara b'aci. A hanyar fita suka haɗu da Dan Ba'are. "Ina mara mutuncin yake." "Yana dakin motsa jiki" A fusace ya shiga tare da banke kofar, ya d'aga ruwa yana sha. "Kai wani irin mutumin banza ne haka? Akan wannan maganar sai kayi zuciya da Yaron?" " Kasan kanin Ubana ne da zan zauna muku" ya faɗa bayan ya ajiye goran ruwan, "Banza kawai waye ya kawo batun Iyaye?" Bai kula shi ba, zama yayi tare da sassauta murya yana faɗin. "Mohan yaron yana bukatar kulawa" "And so what?" Ya tambaye shi yana zare mishi ido, "Jinin shi bai da karfi, kwayoyin sinadirin kulorin da kuma Cocin aka hada ya shaka, Kuma shi sinadarin yana lalata huhu da makogaro, don Allah kayi wani abu a fitar dashi kar ya rasa rayuwar shi, gashi ban san inda Iyayen shi suke ba Ansar Yusuf ne kawai ya san inda yaron ya fito" A matukar tsoro yake amma kuma a yadda ya nuna rashin mutunci akan fuskar shi sai ka rantse zuciyar shi bata rawa akan abinda aka gaya mishi. "Wani hali yake ynzn?" Ya tambaya fuska a daure, Gyara zama ɗan Ba'are yayi Y Tare da cewa. "Yana nan dai sai a hankali, ina tsoron kar wani abu ya same shi ne wallahi" Mik'ewa yayi ya fita tare da nufar dakin shi ya shiga ban daki, wanka yayi sannan ya fito ya bude wardrob din shi ya dauki kayan shi wani riga da wando, rigar ja ce sai wandon baki. Sakawa yayi tare da rufe closet din shi,bai cika amfani dashi ba, kasancewar akwai Abubuwan sirrin shi. Lumshe idanun shi yayi lokacin da ya gama shiryawa ya fito, yana saukowa tare da nufar inda Dan Ba'are yaƙe. Ya dauke kai Kamar bai ganshi ba. Haka yasa dan Ba'are jan tsaki me ƙarfi. Bai kula shi ba dan yasan ya shaka ne yasa yayi tsaki. Ko a motar babu wanda ya kula wani asalima dauke kai suka yi dan kowa da jin haushin dan uwan shi, suna isa asibitin Office din likitan suka shiga, suka samu yana duba wasu sojoji.fita suka yi tare da zama. "Ko zamu je kaga yadda yake?" Kamar ba dashi ake ba, shiru yayi yana latsa agogon hannun shi. "Amma kai kan anyi dan iska idan ba zaka ba kayi min bayani mana ka tashi ka share ni kamar wani abu mara daraja" kallon shi Mohan yayi tare da tab'e baki yace mishi. "Idan kai ne da kafana dauke ni ka kaini" "Ok ince kai maganar bakin ka kashi yafi shi daraja" Sanin bai son magana yasa shi dauke kai yana kallon yadda Asibitin yake. Mik'ewa yayi tare da nufar hanyar da zai kai shi cikin asibitin Dan Ba'are yana gaya mishi bi nan can zamu shiga har suka shiga inda Mamoon yake, Ya kai hannu zai bude kofar Dan Ba'are shima ya kai nashi hannun, a lokaci guda suna kalli juna. Tsuke fuska Mohan yayi dole Dan Ba'are ya cire hannun shi, koda ya shiga cikin dakin, rufe kofar yayi yana me jan tsaki. Jingina yayi da kofar tare da kura mishi ido, tausayin yaron yake ji. Haka kawai ƙaddara ta kawo shi inda bai da muhalli, inda yana da gata babu me tozarta shi, amma yau gashi ana watangaririya da rayuwar shi. A sanyayye ya mike daga jikin kofar, ya nufi inda yake a Mamoon yake kwance, ya dafa kujeran da yake gaban gadon, tare da juya shi a hankali sannan ya zauna yana fuskarta shi. Riko hannun shi yayi tare shafa, shi a hankali yana me jin tausayin shi a ranshi, kara rike hannun yayi yana kallon shi zara zara, kafin ya kai hannun fuskar shi. Yana tuno abinda ya faru kafin wannan lamari d'azun da safe. Musamman yadda yake zaro mishi ido, murmushi yayi tare da cewa., "Allah ya baka lafiya" ya faɗa a can ƙasar makoshin sa...... *Har na bude data sai naga Yan Baroriji fans 😂 suna nimana ido a rufe kamar ka sace Mamoon na b'oye🙄😠😏 ku gode yau bana jin rashin daraja da ban muku typing ba🙄 Insha Allah na kusan fara muku rashin darajar nan.... Ban sani ba ko zan sami damar typing gobe, idan nayi zakù gani idan bai yi ba toh na tafi leka Gyatuma ce kusan abinka da mai kaka sai anayi ana leka su thank You so much 💓💞* [7/23, 8:24 PM] Hafsatu Hafs: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ASHIRIN DA BIYU. Karar bude kofar yasa shi maza ya mike tare da mai da hannun Almamoon, daidai shigowar Dan Ba'are. Wani irin b'ata rai yayi kamar wanda aka zo amsar wani abu a gurin shi.sai wani hura hanci yaƙe. Dariya yaso bawa dan Ba'are amma ya share shi dan bai da lokacin sa. Gashi ya wani tsare inda Almamoon yake sai wani b'ata b'ata rai yaƙe irin me kazo yi? Ƙoƙarin leka Almamoon yake ya wani tare shi. "Meye kake nufi?" Ya wani fada yana hararan dan Ba'are, "Kai bana son Iskanci ka bari na ga halin da dan mutane yake ciki indai na so kake a fara sintiri munyi kisar kai" Matsa mishi yayi tare da zama yana kallon su,.kai hannu Dan Ba'are yayi zai tab'a Almamoon yayi maza ya dauke kan shi saboda har cikin zuciyar shi yaji haka amma bai wani nuna a fuska ba. Kamar ance ya kalli inda Mohan yake yaga bai wani damu da abin da yake ba, dan haka ya sha jinin jikin shi bai kai hannun ba ya fasa tare da kallon Abokin nashi da yayi mishi mugun sani. Idan ya fahimtar kamar dai kodayaushe baya son mu'amalar wani da abinda yake tare da shi yanzun sai ya iya cire abin a ranshi yayi mamaki da bai yi haka akan Mamoon dan yasan sun tab'a yin haka akan wata budurwan shi, yarinyar ta makalewa Mohan ba laifi ya fara kula ta, ba wai dan yana son ta ba, kwatsam sai Dan Ba'are ya fara kula yarinyar irin wasan abokin saurayin nan. Har su zauna su sha hira. Tunda aka yi haka a kan idanun shi ya b'ata rai bai ce kome ba. Aka kuma ba biyu bai yi magana ba. Yana tare da su. Wata talata ya dawo daga tafiya yana shiga gidan su yaga yarinyar me suna Sayyidah tare da dan Ba'are suna jiran shi, yana sauka a motar Mohan ya tattara kashin su ya watsar suna mishi Barka da dawowa, amma fir yaki kallon inda suke asalima kamar bai gansu ba. Allah Sarki kallon Dan Ba'are tayi sannan tace mishi. "Ko na mishi laifi ne?" Ta tambaye shi a dame, tab'e baki yayi sannan yace mata. "Babu abin da kika yiwa ɗan iska" ya faɗa tare da mik'ewa zai bar gurin, "Ko zaka raka ni na tambaye shi?" Cikin takaici yace mata. "Dalla can sai kace ba mace ba dan banza ya dawo dan bai kula ki ba sai ki damu karki sake ki fara nuna miki zakalewarki tun ynazun dan wallahi zaki wahala da Mohan." "Toh uban munafukai zaku fitar min a gida ko sai na watsa ku a waje?" Ya fada yana daure fuskar shi alamar babu wasa da sassauci. "Mohan yarinyar nan tun safe take jiranka kuma ka dawo ka watsar da ita, ai ko babu kome zaka girmama soyayyar da take maka" Kallon mamaki yayi mishi kafin ya gyara tsayuwar shi bayan ya zuba hannun shi dukka biyu a cikin aljuhun wando shi domin wandon unifoam ne a jikin shi sai wata shimi ta soja. Kallon yarinyar yayi daga sama har kasa kafin ya mai da idanun shi kan Dan Ba'are. "Kanin Ubana ka gama?" Ya tambaye shi tare da mishi kallon kurilla. "Ayya Ayya Mohan wallahi ina kaunarka da dukka zuciyata karka wulakantani" "Ka dauki wannan abin ku bar min gidana idan kuka sake na fito sai na saka bindiga na harbe yan iska mara sa mutunci irin ku masu cin amanar Abota." Ya juya a fusace kamar zai wuce dakin, yarinyar kamar zata yi hauka, amma Mohan bai saka shi jin ya hakura ba, Dan Ba'are yayi mishi bayani amma fir yaki kula zancen kuma ba iya ita ba yan mata dayawa sun sha wulakancin shi. Ajiyar zuciya Dan Ba'are ya sauke lokacin da ya koma bayan shi ya tsaya tare da cewa. "Kayi duk abinda ya dace, Ni zan tafi dashi kai ka koma bakin aikin ka" ya faɗa tare da mik'ewa yana gyarawa Mamoon fuskar shi da take kara tsutsewa. Cike da mamaki yake kallon Mohan, "Amma kuma" "Na baka umarni a matsayin shugaban ka." Ya fada tare da barin d'akin baki daya domin idan akwai abinda ya tsana ya zauna daki daya da wani, bayan wanda yake tare dashi, shi yasa ya bar dakin domin zuciyar shi ba zai dauka ba. Kuma baya son ya kaftawa Dan Ba'are tijara, sannan shi wani irin mutum ne da baya son raba kome da wasu,idan zai yi abu akan shi yake tsayawa shi yasa yake jin haushin Dan Ba'are da ya zake akan Mamoon. Yana fita aka bude mishi mota ya shiga, tare da zama yana kallon cikin asibitin ran shi yana kara b'aci sosai sama da farko. Ko minti biyar bai yi ba daga barin asibitin ya danna wayar shi tare da sakawa a kunne. "Ku kai shi ya gan shi" Sannan ya kashe wayar yana cizon lips din shi, tare da lumshe idanun shi, sam bai kaunar zalinci shi yasa har kwanan gobe yake yaki da azzaluman mutane. Bude ido yayi kar akan wayar shi da yake tsiwa. "Hmm" ya saka a kunnen shi, "Mohan kai ka turo Fahad da mutumin nan?" "Hm" Ya fada tare da kashe wayar ya cillar gefen shi. Yana kallon agogon shi, turawa dan Ba'are sako yayi. *Kar mu wuce kasa da awa biyu* _Mohan dan Ubanka Ni ba dan ka bane dan Bante Ubanka idan zaka zo kayi kome kazo idan ba zaka zo ba dan Ubanka ka zauna dan iska mara mutunci ai gwara ka zauna a haukarka dama abinda nake gudu kenan ka samu lafiya ka ishi mutane da mulkin Bala'i, dan kaniyar ka ba zan shirya kome akan lokaci ba sai dai yaron Ya mutu_ Dama yana cike da shi kuma Allah ya bashi sa'a ya gaya mishi maganar banza shi kuma ya tura mishi zungurerriyar wasika. Yana son wannan halin na Dan Ba'are, murmushi yayi sannan ya kuma tura mishi da cewa. *Nagode sosai ka hada min akan lokaci* _Toh Kanin Babana ba zan shirya ba ka tsine min na shiga duniya_ *Ko daya sai dai dole kayi yadda nace* Gajiya yayi da mai da sakon ya kashe wayar baki daya ma, domin idan yabi na Dan Ba'are sai iya saka shi ciwon kai. Lumshe idanun shi yayi yana me daukar wayar ya duba wani sako sannan ya kashe ta Cigaba da lumshe idanun shi. Tausayin Mamoon yake sosai shi yasa ya kasa hakuri akan sawa a kama malam Ansar. Bayan sun gama waya da Fahad, suka dauki malam Ansar suka fito dashi, basu yi wata wata ba suka watsa shi a cikin motar su. Tare da kawo shi asibitin. Kallon cikin Barrack din yayi jikin shi ya fara tsuma dan ya yi tunanin an kawo shi ne a ci kaniyar shi. Ganin sun wuce Asibiti ya sa shi sauke Ɓoyayyen ajiyar zuciya har suka isa cikin asibitin ward din da aka kwantar da Almamoon suka shiga VIP babu hayaniyar mutane babu cunkoson mutane sai dai Nurse da likitoci. Dakin aka bude mishi ya hango shi cikin kaya blue irinta ta majinyata, ga sumar kanshi da yake Baje a saman matashi,. fuskar shi ya wani irin motsewa sabida karfin gubar da aka shaka mishi. Kallon shi ɗan Ba'are yayi sannan ya turawa Mohan sako ya dawo mishi har suka shiga fada dashi. "Shigo" ya faɗa tare da kallon Ansar, a hankali ya nemi guri ya tsaya a tsora ce ganin yadda yaron ya koma lokaci guda, tausayin shi da na iyayen shi ne ya kama shi. Bai san lokacin da kwalla ya shiga zuba mishi ba. "Duk abinda zaka so matuƙar ba zaka ririta duniyar shi ba, toh ba kauna bace k'iyayya ce soyayya bata sakawa a lalata goben wani sai dai ya saka a gyara goben wani. Wannan Yaron karami ne kuma bai damu da kan shi ba matukar zai maka abinda zaka ji dadi me yasa kake cutar dashi? Me yasa baka tab'a tunanin yadda zai ji idan ka mishi wani abu? Ina ga kamar ba laifi bane dan kaso shi amma kuskuren shine tirsassa mishi, kayi ƙoƙarin raba kanka da cutar dashi domin shirun Mohan bai da Alkhairi idan ka sake yayi magana ko ya saba umarnin akan ka wallahi zaka kad'e har buzunka yanzun haka Saudiya zamu fitar dashi nan da awa daya meye amfanin abinda ka aikata? Sannan idan iyayen sun suka ji abinda kai mishi zasu ji dadi kuwa? Gaskiya ka sake lalle wannan ba adalci bane domin masoyin gaskiya baya cutar da abinda yake so" Hawaye sosai yake zubdawa tare da tausayin halin da ya jefa Mamoon a ciki, kuma kamar wanda aka rufe bakin shi ya kasa magana, dan haka Fahad ya juya dashi kamar kayan wankin suka fita da shi, yana kallon halin da Almamoon yaƙe ciki yau yake nadamar abinda ya aikata domin da bai aikata haka ba tayu da Almamoon yana cikin nutsuwar shi. Juyawa tare da barin d'akin kicibis suka yi da Mohan, kallon juna suka yi tare da jin wani irin abu a ransu, kowannen su yana jin kamar shi yafi cancanta zama da almamoon ba dayan su ba. Dauke kai Mohan yayi cikin wani isa da jin kai, irin na wuce yadda kake kallona, tare da mai da hankalin shi kan wayar hannun shi. Wani gani gani yakewa Ansar tare da kallon shi daga sama har kasa. "Kayi fatan Allah ya bashi lafiya" ya faɗa tare sake murmushin gefen baki, inji Mohan, "Kai ka isa ka shiga tsakani na da shine? Ok bari kaga ikon Allah" inji Ansar, Ya faɗa tare da wuccewa bai kuma magana ba, shima Mohan yayi gaba abinshi. Shiga dakin da Mamoon yayi. "Amma baka isa gida ba ko?" Shiru yayi yana kallon Almamoon, tare da jan kujerar yayi tare da zauna, tare da harde kafa daya akan daya. Yana kallon Dan Ba'are. "Dama zaman ka nake?" "Matsalata da kai bakar magana" "Hmm" ya faɗa tare da wani b'ata rai, yana kallon Dan Ba'are. "Dan iskan can ya taba shi ne?" "Kai haba ko kusa dashi bai zo ba" Mikewa yayi tare da zuba hannun shi a cikin aljuhun wandon shi. "Zaka iya tafiya" Ya fada tare da mai da hankalin shi window dake d'akin. "Amma Mohan me yasa kake katange Ni da Yaron?" "Sabida na san lafiyar kai na, bai zama dole kowa ya iya sarrafa kanshi ba, so ka bar ganin laifina akan Yaron" cike da mamaki Dan Ba'are yake kallon Mohan idan ya fahimta Mohan yana gaya mishi shi zai iya zama da Almamoon ba tare da ya ji kome a ranshi ba, sannan shi yana da lafiyar da ba. "Mamman kana nufin ba zan iya rike kai na bane sai na hakewa dan mutane?" Ya tambaye shi tare da kankance fuskar shi. Murmushin cusa haushi yayi mishi kafin ya zauna yana me daura kafa daya akan ɗaya, ya kalli Dan Ba'are, bayan ya nad'e hannun shi a kirjin shi. Ya d'aga mishi gira. "Kasan idan ina tare da abu bana son zakewa? So ba wani abu bane dan dai kasan mata basa gabana balle kuma da namiji so kawai manta zan maka bayani" Ya fada yana kallon Dan Ba'are da idanun shi suka yi jajjur, "Da wani ne ya zarge ni zan iya mishi kome amma kai Mohan? Kasan Yaron nan namiji ne kuma akan me zan?" "Ba akan kome bane, naga abinda kake adanawa a ƙwayar idanun ka, Naga chemistry a cikin idanun ka don Allah karka zama kamar wancan Mahaukacin." Ya fada cikin tattausar murya da lafazin, yadda shi kan shi dan Ba'are ba zai ji zafi akan Mohan ba. "Amma me yasa?" Ya tambaya a sanyayye kamar zai sake kuka, "Saboda shi Yaron na musamman ne shi din ba kamar sauran Yarana bane, please karka kawo kanka cikin lamarin Yaron" inji Mohan, jikin dan Ba'are ne yayi masifar sanyi yana kallon Mohan, karon farko da yaga ya damu da abu a ranshi..... #Mai_Dambu [7/24, 10:23 AM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1104788648?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=q5d7yQUTBcJ8BdXrs84PaortqtGlVo0sxj15rZPXOdrLAxFvWQgJa%2BsauKrirmCAI6CTRR9OwqxP0GgCqsNrnu%2B64lqmFiENdCsHVuJcnC%2Bq1rbT7zaXMbV7vn44ciXw 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... _Ban san Meye Ansar ya tsare muku ba kowa sai haushinsa yake ji...😌😠_ Fatan Alkhairi ga Baroriji fans 😂 kuna abinda ya dace!💞💓😍😘Much love.... BABI NA ASHIRIN DA UKKU. "Mohammed Mamman Nasir Aghali akwai abinda kake boye min" ya faɗa tare da kallon Almamoon da yake barci, dauke kai yayi yana kallon yadda Mohan yake kokarin barin gurin da Dan Ba'are yake. Rike hannun rigar shi yayi cikin damuwa yace mishi. "Ko akan matsalar shi ne na jinsin mata maz..." Fauce hannun rigar shi yayi tare da nuna Shi da yatsar shi. Kamar wanda aka gaya mishi wani magana mara dadi. "Karka kuma, kayi abinda na saka bana son kowa ya rab'e shi ne, ni nace ka nisance shi idan kuma ba zaka iya min wannan Alfarmar ba thanks you can go away." Mamaki ne ya kuma rufe Dan Ba'are, sama da baya. Kafin ya kalli Almamoon. "Shi kenan, but i'm in your side babu wanda ya isa shiga tsakanin mu ina tare da kai." Bude mishi hannun Mohan yayi suka rungumi juna, duk da kowa yasan Dan Ba'are dan uwan Mohan ne ta gurin Uwa kuma sun tashi tare, kome nasu daya ne. Amma haka bai hana Mohan kafkafta mishi rashin daraja ba. Kuma bai tab'a fushi yace ya rabu da Mohan ba, domin kaunar su daga Allah ce. "Toh sake ni zan tafi maganar tafiyar ku, duk da mun gama rabin aikin kawai saura naje na karasa sauran ne" inji dan Ba'are, "Ok Yaron kirki kayi abu me kyau maza kaje" inji Mohan ya faɗa cikin zolaya, Wani banzan kallo yayi mishi tare da barin d'akin, shi kuma ya koma jikin window yana kallon yadda ake training ta baya, kasancewar asibitin a cikin Barrack yake. Tsayawa yayi sosai yana kallon kome. Shigowar Dan Ba'are yasa shi juyawa yana kallon shi. Mika mishi wasu takardu yayi sannan ya kuma fita. Bayan kamar minti talatin sai gashi dauke har da jakar Mohan da kayan shi ya mika mishi. Sannan yace mishi. "Toh na gama maka kome, Allah ya bashi lafiya" Bai rufe baki ba sai ga Nurse sun shigo da gadon marasa lafiya, daukar shi suke son yi, Mohan ya dakatar dasu ta hanyar daukar shi cak ya fitar da shi daga cikin ɗakin, lokacin da ya fitar dashi kallon su Dan Ba'are yayi tare da jin idanun shi na cika da kwalla. *Karka manta Mohan yayi maka kome a rayuwa Mohan ya baka kome da kake nima! Dan haka ka bar shi da Yaron ko zai sake kamar kowa kafi kowa addu'o'in Allah ya sauya mishi murɗaɗɗiyar hali dan haka zaman shi da Yaron sai ka ga an dace* Inji wani shashi na zuciyar shi yake bashi shawara. Ajiyar zuciya ya sauke tare da taka musu baya. Har gurin motar shi tun kafin Mohan ya isa sojoji sun bude motar tare da sara mishi kwantar da Almamoon yayi sannan ya shiga cikin motar dan Ba'are ya shiga gaban motar suka bar asibitin. Cikin abinda bai wuce awa daya na suna isa airport din, shi ya fidda Mamoon yana daukar shi tare da daura kanshi daidai kirjin shi. Mamoon ya sauke ajiyar zuciya. Cak ya tsaya tare da kallon fuskar shi jikin shi yana wani irin yanayi. Kallon fuskarshi yayi na few seconds kafin ya nufi cikin airport din dashi. "Kamar yayi motsi ko?" Dan Ba'are ya tambayi Mohan, karamin murmushi yayi tare da gyada mishi kai, "Alhamdulillahi don Allah idan kuka isa ka saka ido akan shi kaji" Wani banzan kallo yayi mishi tare da dauke kai kamar ba shi ba, haka yasa shi jan bakin shi yayi shiru tare da murmushi. Suna shiga dama kamar su ake jira. Dan haka suna bashi keken majinyata suka tura shi a kai, sai cikin jirgin, tare da Dan Ba'are. Mika mishi wata jaka yayi tare da kallon shi. Da idanun Mohan ya tambaye shi. *Meye a cikin shi?* Shima ya mai da mishi da cewa. _Idan ka tafi ka duba_ Gyada kai yayi tare da mika mishi hannun suka yi musabaha, kafin suka rungumi juna. Babu laifi sun ji babu dad'i da zasu rabu da juna. Leka Almamoon yayi da yake kwance a kujera. "Allah yasa a dace" Mika mishi hannun yayi a karo na biyu. "Amin Friend zaka iya tafi" ya faɗa mishi tare da tsare gida dan yaga yadda yake leka Mamoon, shi a son shi kar wani yace zai kula Mamoon. Dan haka Dan Ba'are ya juya yana dariya. "Khalil Ibrahim Dan Ba'are Nagode da kome" "Allah ya tsare ya kuma saka a dace." Dakyar suka rabu, (sai kace masu aljanun kafin zuwa wani lokaci cutar sanyin su ta motsa 🤣 Wallahi sun cika fada kamar masu ganin hanjin juna) bayan fitar Dan Ba'are, basu jima ba jirgin ya tashi. Ya juya a hankali yaji an bangaje shi ana dariya cike da mamaki ya juya, aikuwa Yarinyar ta koma bayan shi. "Hammah kace kar Didih ta dake ni ba zan kuma tsokanar ta ba" d'ago kai yayi tare da tsare yarinyar da bata wuce shekara goma sha biyar ba ido sai hura hanci take tare da rike k'ugunta, ranta yana kara b'aci sosai. Sake baki yayi sabida wani abin mamaki yanzun yayi sallama da Mohan da Almamoon, amma ga wata yarinyar nan me kama dashi har da tsayin fuskar. Cikin tsiwa ta juya shiga ƙoƙarin kamo yarinyar bayan shi ya kai hannun shi tare da kare ta, wani irin haduwa jikin su yayi tare da bada Wani sabon rikittaccen al'amari na daban. Kallon cikin idanun shi tayi, sai gashi ta kasa ko magana yayi mata Kwarjini. Idanun ya ne ya cika da kwalla. "Wallahi Yumnah zan kama ki, sai na fasa bakinki mara kunyar banza kawai" ta faɗa tare da kwace hannunta. "Toh Didih ba naga hoton ki da na Paul bane sai ki ce min solayinki ne Kinga ga Appa can muje." Inji Ita Yumnah, Juyawa Yar budurwan tayi tare da barin gurin, shafa kan shi yayi yana kallon ikon Allah hatta tsayin da tafiyar. Daure fuskar sai dai ita wannan fara ce sosai. Kuma da alama girman kasar Turai ce domin kanta babu dan kwali riga da wando ne a jikinta sai jacket din da ta daura a k'ugunta. Idanun shi ne ya sauka akan Boom ɗinta, da sauri ya rintsa idanun shi. "Yumnah" ta juyo tare da kiran yarinyar, aikuwa idanun shi ya dauka akan dukiyar fulaninta, had'iye yawu yayi, tare da kura mata ido.. da gudu Yumnah ta fito a bayan shi zata wuce ya rikota. "Meye sunan ta." "Benazir!!" Ta fada a hankali, "Daga ina kuke?" "Paris" ta faɗa tana kallon shi, "Yumnah" wata mata ta kira ta, wacce zaka ga dai ba wata babba bace dan ba zata wuce talatin da yan kai ba. "Na'am Nanny" ta amsa da gudu, rike hannun matar tayi tare da juyawa ta d'aga mishi hannu. Murmushi yayi mata. Da sauri yabi bayan su tare da kallon Number motar. Shafa kanshi yayi yana murmushi. "Yar kwaila" shi da kan shi kuma ya kama dariya, tare da gyada kan shi. Yana tab'a gefen kirjin shi kodan kama da Almamoon zai iya sashi bibiyar rayuwar yarinyar. "BENAZIR!" Ya ambaci sunanta yana kallon motar su, yarinyar tayi karama kuma fa, amma kuma ai bata mishi kadan ba, indai zai sake ta zai iya kuma zai koya mata son, a tunanin shi ba zata wuce 15 to 16 ba, dai dai ya kafa gwamnatin shi kenan. Dan bakin nan da idanun. Jan hancin shi yayi, Allah sarki ya rasa Mamoon Allah ya bashi Benazir! Gyada kai yake kamar kadangaren kafin ya isa gurin motar shi ya shiga tare da rufewa suka bar gurin. *** Niamey. Babban Ofishin primer minister, yana kallon Chef Judge. "Yallabai Insha Allah kome zai wuce, sai dai ban da ikon Allah na gama kome Insha Allah babu abinda zai kuma faruwa kuma matsalar na gaya maka daga cikin gidanka ne idan har zaka iya taimakawa na gidan ka zai zama tarihi." Mika mishi hannu yayi tare da mik'ewa yana faɗin. "Nagode sosai, sai dai har yanzun bai tuntube Ni ba" ya faɗa a dame, "Kai ka tuntube shi." Gyada kai yayi yana kallon shi. "Ina kewar shi a kusa dani,.Insha Allah yana dawowa aure zai yi" "Allah yasa a dace, zan koma." Ya fada tare da mik'ewa. "Alkali ka tawo da Iyalinka muci abincin dare mana yau" sunkuyar ka dai yayi cikin sanyin murya yace mishi. "Bani da iyali" "Ikon Allah sun rasu ne?" "A'a Allah ne bai nufa ba" "Sai yaushe? Baka kasan ka girma bane?" Idanun shi ne ya cika da kwalla, tare da jin tausayin kan shi da kanshi yace. "Insha Allah zanyi" ya faɗa tare da barin Office din, cikin sanyin jiki. *** Tafiyar awa uku ya kai su garin Dubai, kafin suka tsaya na tsawon awa daya, kafin jirgin su ya tashi daga birnin Abu Dhabi zuwa Riyadh, sun isa ƙarfe goma na dare, motar asibitin yana jiran su, tunda ya sa shi ya nufi wata motar ya shiga domin akwai wani kamfanin da suka bude shi da wani Yariman saudiyar anan kasar, dan haka suka nufi masaukin bakin su da yake cikin Kamfanin. "Mohan kai a ƙasar?" Inji abokin shi. "Abeed gani nan." Bai gaya mishi gaskiya abinda ya kawo shi ba,.wanka tayi tare da saka jallabiyar shi cream colour..sannan suka nufi babban asibitin Riyadh, yana zuwa suka shiga tattaunawa da likitocin, kafin aka shigar da shi aiki. Tun da yayi Sallah yake zaune a gurin,.har kusan asuba. Basu fito ba, ya tafi masallaci ya dawo, har gari ya waye kafin suka fito dashi babu laifi. A yanzun yana mai da numfashin sa. Wani daki akai shi. Tare da sauya mishi kayan shi. "Alhamdulillahi mun yi aikin cikin nasara,. An tacce jinin shi yanzun sai huhun shi shima an saka allura da maganin zasu yi flushing dattin ko yayi amai ko yayi bayan gari." Gyada kai yayi sannan yace. "Mun gode" ya faɗa tare da kallon Mamoon. Tun daga ranar kome Mohan ya dauka, ranar Alhamis ya shiga macca yayi aikin Umrah, ya dawo ranar juma'a da dare, rabin addu'o'in shi akan Almamoon da iyayen shi ne da yan uwan shi. Amma karfin addu'o'in shi akan Almamoon ne. Duk da Asibitin ba a zama amma shi saboda yadda suka ga ya damu da majinyacin yasa suka kyale shi, yana kula da duk motsin shi. Amma ta bangaren goge mishi jiki Nurse ne suke aikin nan, dan har zuwa lokacin bai yi amai ba bai yi kuma kashin ba. Ranar Asabar yana zaune ya kifa kanshi a gaban gadon. A hankali na fara bude idanuna, ina jin amai rike zanin gadon nayi tare da yunkurin tashi, amma na kasa jikin babu karfi. Dan haka na dan juya kadan nayi ta amai, kakarin yaji ya farka. Yana tashi ya rungume ni, na cigaba da sheka mishi amai a jikin shi da jikina, sai da nayi aman tas a jikin mu, sannan ya daura kaina a kirjin shi ina jin kwalla na zuba min. Shafa bayana yake tare da cewa. "Sannun" Murza kai na nayi a kirjin shi, ya tab'a wani abu, sai ga nurse sun shigo, dan haka ya basu guri suka gyara min jiki shikam fita yayi daga asibitin ya koma gida yayi wanka tare da wanke kayan, sannan ya mai da wasu kayan, ya dawo asibitin ya same ni jingine. Gashi kayan ya fidda kirjina, sau daya ya kalle ni bai kuma kallona ba, ya mai da hankalinsa gurin rubutun da suka yi. Kallon shi nake bako daya ya cika min idanuna. Hada min tea yayi tare da zama yana diba da karamin cokali yana bani a baki, amsa nake ina me kallon shi. Har ya gama ya bani magani, sannan ya dawo inda kafana yake yana matsa min su. Mamaki yake bani babu ruwan shi da magana tun sannun da yace min bai kuma magana ba....... _🙄 Wallahi Na kusan fara rashin Daraja hmmm bana son na dauke labarin daga Wattpad kuma wallahi idan na cire zan dakatar da rubuta shi baki daya ne na Fara na kuɗi na shi kuma zai kai Okada Insha Allah ku bani had'in kai bana son ma fara book din kudi na dakatar da Wannan kuma bana son na sayar da labarin! Idan kuka bari na dakatar tabbas zamu ji babu dad'i bana son haka shi yasa nace kuyi comments da Vote idan babu Insha Allah Ranar Monday Zan fara KISHI a tsakanin zubda jini........iya comments da Vote kawai na bukata domin akwai mutanen da suke buƙatar Bororoji ya koma na kuɗi amma nace a'a kuyi wani abu ko nima na fara rashin Daraja kuma ba iya Pagen nan ba all Pages da masu zuwa👏🙄 Wallahi na iya rashin Daraja na fitar hankali musamman akan Zanen kaddara ta 🤸😒😏😡_ [7/25, 9:44 AM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... _Eh toh nayi ritaya daga Rashin Daraja! Sai dai kuma an koma Gaba gad'i🤫_ BABI NA ASHIRIN DA HUƊU. Kura mishi ido nayi, ina son ya kuma ce min koda Sannun ne amma fir yaki kallona, da na gaji da zaman kurame yana miko min tea din na dauke kai na. Sake tura min cokalin yayi na kauda kaina. Ajiye kofin yayi tare da mik'ewa yana duba maganin da zai mika min. Shima naki kallon shi sai ma ƙoƙarin sauka akan gadon da nake yi. "Ina zaka?" D'ago kai nayi ina son kallon shi amma yalwataccen gashin kaina ya hanani ganin shi sosai. Sake yunkuri nayi tare da zamowa zan fad'i, cikin wani irin kulawa ya tare ni. "Gida zan koma" na fada mishi ina maida numfashi. "Ok ince kana da kudin jirgi?" D'ago kai nayi ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, tare da kokarin kwace jikina, a hankali ya mai dani saman gadon, sai shesshekar kuka nake? Daukar rigar shi yayi tare da wayar shi ta fita. Bai damu da halin da nake ciki ba. Koda ya fito shekar isa yayi tare da fesarwa. Sam bai iya rarrashi ba, asalima kanen shi basa rikici wannan da alamun shine auta a gidan su, shi yasa bai rena kuka. A hankali yake walking a cikin harabar asibitin hannun shi zube cikin aljuhun rigar shi. Karar wayar shi yaji sannan ya dauka. "Ya?" Ya tambaya, "Ya me jikin?" "Am think da sauki" "Mohan anya kana kula da lafiyar shi kuwa?" Inji dan Ba'are, "A'a Alhaji ina ganin me zai hana ka kwashe min albarka tunda ka bani aiki na gaza" ya faɗa tare da shafa kanshi, "Toh tunda haka ne ai gwara Ansar yazo gare shi" ya caka mishi bakar magana yadda shima zai ji zafi, tsaki yaja tare da katse kiran, yana me jin haushin Dan Ba'are kuma yadda yake ji da zai same shi dan Ubanshi sai ya kirb'a mishi naushi a fuskar shi. Da dan sassarfa ya nufi cikin asibitin. Yana shiga ya same ni na cusa kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka, banging kofar yayi da dan karfi wanda ya razana ni. Na d'ago kai ina kallon shi wani b'ata rai yayi sama da koyaushe. "Oya dauki tea ko na zane ka" ya nuna min kofin, kallon shi nayi naga yana niman inda zai zauna. Bayan ya leka inda yake saka cajin shi. Wayar cajin ya dauko. Ban manta ranar da Malam Ansar ya zane ni ba, jikina yana rawa na dauki shayin. Na kafa kai na fara sha, yayi sanyi toh kuma sai na fara jin zan yi amai. "Idan ka sake ka min amai sai na zane ka" ya zaro min idanun shi. Gyada mishi kai nayi tare da kurb'an ruwan tea din, ina sha ina shafa wuyana. Ina gamawa na je ajiye cup din kawai ya fadi kasa, ya tarwatse. Kafe ni yayi da ido. "Kayi hakuri ba da gayya bane" " A cikin albashin ka" ya faɗa min tare da dauke kan shi. Tunawa da nayi, ina aiki dashi ne dan na saya mana gidan da zamu zauna na budewa Babana shafi saura kadan na karasa kudin gidan ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Domin nasan kawo ni asibitin ma da kudina ne. "Hammah Mohan" a masifance ya kalle ni, sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa. Share ni yayi ya cigaba da duba wasu takardun shi, yana turawa a Laptop din shi, da na gaji kwanciya nayi ban san lokacin da barci yayi gaba dani ba. Jin ya daina sauraron kananun kukan shi ya sashi d'ago kai, sai ganin shi yayi yana barci.mikewa yayi tare da gyara mishi kwanciyar shi, ya lullube shi sannan ya koma ya cigaba da aikin shi. Wayar shi ce ta dauki kara, ya kurawa Number ido, wanda ya saka. "Abbu" cikin sanyin jiki ya dauka tare da sallama. "Babana ka kyauta? A ce tsawon lokaci bamu nime ka ba kai ma ba zaka nime mu ba? Toh duk inda kake ina son ganin ka cikin sati me zuwa kana jina?" Gyada kai yayi kamar yana gaban shi yace mishi. "Afwa Abbu Insha Allah" "Khalil ne ya bani Number ka da ba zaka tab'a niman mu ba, ina kewar ka." "Nima haka" ya faɗa a sanyayye, kafin suka yi sallama, Har zai ajiye wayar yace mishi. "Abbu don Allah karka gayawa kowa na sami lafiya kawai ka bari na zo da kaina." "Insha Allah" ya faɗa a sanyayye kamar Mohan din, kashe wayar yayi tare da kura mishi ido, yana kewar shi sosai. A fisge ya kalli inda Almamoon yake kwance yanzun dai ganin likitan da yake son ya kai Almamoon ya fasu kenan. Tunda sun tattauna da Dr Hisham Hadid, ya haɗa shi da wani likita a China Dr Zenrog Chuo a garin Yunnan, amma babu kome insha Allah zai fara tuntubar iyayen yaron dai yana komawa dashi gida gaban iyayen shi zai kai shi kuma su saka idanu akan shi. Kaf idanun shi yayi akan hotunan da Dan Ba'are ya gama hada mishi kome, murmushi yayi sannan yace. "Best friend like no other" yana gama abinda zai yi ya Laptop din ya fita tare da zaga garin. Bayan fitar shi da awa daya na farka, tashi nayi sakamakon ciwon cikin da ya dame ni, sosai nake jin ciwon kamar zan yi hauka. Haka nayi ta fama har nurse biyu suka shigo. Ganin basu shawo kan matsalar ba suka fita, sai ga likitan sun zo dukkan su mata ne.. Sun jima a kaina kafin suka shiga tambaya na. "Al'adar ki dama haka yake miki da ciwon ciki?" Gyada masu kai nayi. Tambaya ma marasa kan gado sai dai abinda na Fahimta suna min kallon mace ce sai da Dr Hisham Hadid ya shigo ne suke gaya mishi. Nan take gaya musu matsalar da nake fama dashi na jinsi biyu sai na zama abin al'ajabi a cikin asibitin domin sun gama tare da saka min ruwa da allura, na fara barci. Bai shigo ba zai karfe bakwai na dare. Lokacin kuwa ina jin kamar na jika jikina baki daya, kuka nake sosai domin babu kowa a tare da ni, kuma bana son daurawa nurse din damuwa, shigowar shi ya same ni ina shashekar kuka. Takowa yayi a hankali yana kallon fuskana. "Ya ilahi sowie me kake bukata?" Ya tambaye ni, "Ban daki zan shiga ina son na gyara jikina." "Ok ok!" Ya shiga ban dakin ya gyara min ko ina, sannan yazo ya d'aga bargon tare da taimaka min zan sauka idanun shi ya sauka akan farin zanin gadon. "Me...me...me.. zan gan..." Kura mishi ido nayi domin bai san halin da nake ciki ba. Sai yau ban san yadda aka yi kunya ta kama Ni ba, na fashe da kuka tare da komawa zan zauna. Cak ya d'agani tare da nufar hanyar ban dakin ya ajiye Ni a bakin jacuzzi tub din da ya cika da ruwa me zafi, sannan ya fito cikin kyankyame ya tattara zanin gadon, ya bude wardrob din dakin ya ciro wani ya shimfid'a min sannan ya kawo ban dakin bayan ya buga kofar, gyaran murya nayi. Na nutsa ruwan zafi ina jin wani irin dad'i kamar zan yi ihu domin jikina ciwo yake kamar an murkad'e ni. A hankali nake wanke jikina bayan na gama na daura babban towel, a hankali na bude kofar bayan na rufe kaina, ganin zanin gadon nayi tare da tsugunawa na dauka. Sannan na shiga ban dakin na fara ƙoƙarin wankewa. Hannun shi naji a saman nawa. "Ba aikinka bane, ko nace ba aikinki bane aikina ne ko kina kokarin b'oye yanayin ki ne?" A hankali na fara ƙoƙarin tashi a tsugunon, amma dake shi din Kamar bishiyar kuka ne sai wani kewaye juna muke. Da sauri na juya, kamar zamu shige jikin juna. Ya tsare min hanya, jikina ne ya shiga rawa, "Relax!" Ya fada min yana niman kwayar idanuna, babban damuwar hannuna daya yana kan towel din kaina da na rufa daya kuma yana rungume na kirjina, domin har kwanjina yake. Lallubar hannu na yayi tare da daura min pant da audugar matan, yana ƙoƙarin na d'ago kai na yaga yanayin da nake ciki amma fir naki asalima kokarin rike towel din nayi tare da cewa. "Hammah" ƙaran wayar shi ya sa shi juyawa zuwa waje, da sauri na jingina da kofar jikina yana wani irin rawa, tare da lumshe idanuna, na dauki Pant ɗin na daura audugar na saka, sannan na bude kofar da niyyar fita, ashe shima yana bakin kofar yana son ya buga kofar dai gashi ya buga goshina, cikin wani irin tsoro naja da baya tsantsi ya kwashe ni. "Hammm!!!" Na fada da karfi tare da sake towel din kaina, na tafi da baya na kirjina kuwa na rike gam, wani irin riko ya kaiwa k'uguna, a tsorace na fada kirjin shi tare da sauke wata irin ajiyar zuciya. Cak ya d'ago ni, wani irin rawa jikin shi yake karon farko da ya kusanci wani abu me sunan kusanci. Shima din na mata maza, a sanyayye ya kai ni bakin gadon yana kallon yadda gashin kaina ya baza fuskana na da jikina baki daya naki yarda mu kalli juna ma balle naga katob'arar da muka yi, wucewa ban dakin yayi ya wanke kayan da na b'ata, kafin ya fito har na gama shiryawa kuma ina kyautatta zaton ya bani damar ba shirya ne, dan haka ina gamawa ya fito. Ya shanya kayan a ban dakin, ya zo ya zauna yana kallon yadda nake juya kafana, mik'ewa yayi yana me zama a bakin gadon ya shiga tausa min kafar, kwanciya nayi tare da lumshe idanuna, a hankali barci yayi gaba dani. *** Niamey. Yana wayar ta shigo bata san da wa yake ba, dan haka yana gamawa ya zuba mata ido. "Mai gida dawa kake waya haka ka saukar da kanka kamar shine sama da kai?" Bai yi mamakin maganar ta ba amma yayi al'ajabin yadda take Mantawa da halin da Yaron su yake ciki. "Kina waya da su Haddir kuwa?" B'ata rai tayi tare da cewa. "Idan ma sabida su ka tsayar dani sai an jima, Lateefah" cak ya tsaya. "Kaga Ni zan tafi bikin yar gwamnar Jahar diffa wacce dan ministan ilimi ya aura sun turo min katin dinner zan tafi!" "Allah ya shirya ki" ya faɗa cike da mamaki, domin kuwa yasan halinta. "Assalamu alaikum! Sannun Yallabai, kai ɗaya ne?" "Eh Safiya" "Yallabai ga wasu takardu ko zaka Duba mana su na kwangila ce." "Toh kin san dai na dauki hutun karshen shekara idan na sami lokacin xan duba." "Yallabai yana da kyau ka duba, nasan da ace Hajiya Lateefah ce da ka duba amma dake Ni bani da arzikin ka duba shine ka ajiye min." Ta fada tare da mik'ewa tana me son fita. "Idan Allah ya kai mu nan da wata me zuwa zanje duba Mohan" ta faɗa tare da kallon shi ko yanayin shi. Bata rai yayi tare da mik'ewa yana jan tsaki, murmushin jin dadi tayi tare da bin bayan shi da ido. "Har yanzun tarkona yana kan kama kurciya." Ta fita daga falon, tana me jin lallai tana da Sa'a shi yasa ta rike wuyar primer minister. *** Damagaram. "Malam yau watan Almamoon biyu bai zo ba bayi aike ba?" Inji Innar shi. "Insha Allah duk inda yake zai dawo cikin amincin Allah" Shiru suka yi sannan suka shiga wani zancen duniya, Sosai yake nuna mata fa'idar yarda da ƙaddara me kyau kalmar kyau, tare da labarta mata abinda yake faruwa. **** Riyadh. Wasu kwanakin da suka tawo Alhamdulillahi naji sauki sosai asalima kokarin barin kasar muke,domin dai ina fita waje daga haka bana zuwa ko ina. Ranar wata Alhamis aka sallame ni, sannan muka shiga cikin garin Makka nayi Umrah, bayan mun gama muka juyo. A hankali nake takawa shi kuma sai sauri yake, wani dan kasar Mali ne ya riko hannuna. "Kai dan kasar Mali ne?" Juyawa nayi ina kallon Hammah Mohan yayi nisa. "A'a Ni daga Nijar nake!" Na fada mishi ina ƙoƙarin kwace kaina, "Toh me ka zo yi?" Ya tambaye ni, yana ja. "Sake ni na tafi" ina kara bin hanyar da Hammah Mohan yabi, dake lokacin dare ya fara, domin bayan sallah isha ne. "Hammah Mohan!!!" Na kwala mishi kira ina tsalle, haka mutumin ya cigaba da jana haka kawai ban san shi ba. Bai juya ba, amma haka kawai yake jin kamar akwai matsala dan haka ya juya tare da dubawa ko ina bin shi. Da sauri ya ware idanun shi babu Yaron shi. Baya ya dawo yana niman shi, can nesa yajiyo muryan shi. Da sassarfa ya isa gurin lokacin da mutumin yake kokarin shigar dani wani lungu, bayan ya daki kafana wanda naji karan shi har cikin ruhina. "Wayyo Allah Hammah na ina kake" na fada da mugun ƙarfi,d'aga hannu mutumin yayi zai mare ni, aka rike hannun shi, tare da murɗa hannun sai da yayi kara, sake murɗe hannun yayi tare da cewa. "Kafin ka zalinci mutum ka fara duba waye a tare da shi, ba iya shi ba!" "Hammah kyale shi na yafe mishi." Sabida yadda naga zai cire mishi hannu, sake jijjiga shi nayi ina magana. "Karka kashe mana" na fada ina zaro idanu, sabida yadda mutumin ya kai kasa baya motsi, "So What! Idan wani ya tab'a hannun ka hukuncin shi a cire hannun shi, idan yayi kuskuren tab'a jikin ka wallahil azim mutuwa ya cancanta ba rayuwa ba." Ya fada min da karfi, a tsora ce naja baya, ina girgiza kai. "Ban yi deserved haka ba matsayina mai maka aiki ne kuma na gama, don Allah karka janyowa ƙaddara ta, wata masifar." Cikin fushi ya fisgo ni, "Wayyo kafana" a rikice ya kuma durkusawa yana kallon kafar, musamman wuyar kafana da ya kumbura sosai, a hankali ya ciro min cambus din kafana, sannan ya mika min, ina shirin mik'ewa nayi yayi sama dani. A tsora ce na kalle shi. A raina ina faɗin. *I do not know how you are destined to bring me into your world, but one thing I know is you are my life, I will continue to follow you like a slave I will stay by your side like a dog and my Lord, I will stay with you until you open for me the door of your heart to respect your cause* (Ban san yadda aka yi ƙaddara ta kawo ni duniyar ka ba, sai dai abu daya na sani kai ne rayuwata, zan cigaba da binka kamar baiwa zan zauna a gefen ka kamar kare da Ubangida, zan ta zama da kai har lokacin da zaka bude min kofar zuciyar ka girmama al'amarin ka) Tafiya yake hankalin shi kwance, bai damu da ina da nauyi ba, bai damu da ni din ina da tsayi ba, kawai abinda ya sani yana tafiya ne a tsakanin wasu abubuwan na musamman, sannan bai ji kome ba sai ma wani irin nutsuwa da yake samu, abu daya yake damun zuciyar shi baya iya hakuri idan yaga wani ya taba Yaron har cikin zuciyar shi yake jin abin, sabida shi yake dauke kai akan Ansar dan haka yana shiga masaukin abinda yayi ajiye shi yayi, Ya koma cikin dakin ya dauko katin shi ya fita, can sai gashi da kayan dauri, a hankali ya tako har gabana ya zuba kayan sannan ya koma dakin shi yana me rage kayan jikin shi ta fito sanye da wandon Nike, sai farin Singlet ya fidda tarin muscle din shi, da sauri na sunkuyar da kai na, yana zuwa ya durkusa tare da janye kafar wandon jikina sama. Sannan ya cire min daya takalmin, ya zauna sosai bai kuma min magana ba, ya haɗa kankaran a cikin wani towel, ya koma gefe yana mai kallon tv, had'iye yawu nayi cikin tsoro, karar kofa muka ji ya mike, can sai gashi da kayan abincin, ajiye min yayi tare da cewa. "Oya cinye min" Kallon abincin nayi tare da kallon shi kamar zan yi kuka nace. "Hammah ko jaki ne ni ai zaka tausaya min balle cikina ba zai iya dauke abincin nan baki daya ba," Da wutsiyar ido ya kalle ni, tab'e baki yayi sannan yace. "Lokacin da kake min rashin daraja ka manta ai?" Da sauri na kalle shi. "Amma ai ban tab'a dura maka abinci ba!" Na tambaye shi ina zare ido, "Ci domin ina da abun yi" babu musu na kalli Chinese bomb din da yake gurin dakyar na had'iye yawun bakina, tun ba aja min kafar ba, na Fahimci akwai dirama. Tab'a abincin nayi tare da turawa ina jin faduwar gaba. "Meye alaƙar ku da wannan gayen?" Da sauri na kalle shi tare da cewa. "Wallahi ban tab'a ganin shi ba sai d'azun kuma na rantse maka da Allah ban san." "Bashi ba wanda ya ce zai maka aikin ka dawo mace?" Ji nayi wani abu ya tsaya min a wuya wallahi na manta dashi baki daya, sosa kai nayi tare da cewa. "Malamina ne kuma kamar Dan uwana yake, bayan haka ina girmama shi." "Me yasa ya dage sai yayi maka aiki?" Sunkuyar da kai nayi, ina kallon yadda yake hada maganin shi. Har ya dawo gabana, tare da d'ago kai yana kallona, kafin yace. "Ina jiranka?" Ya fada bayan ya rike kafar da hannun shi. Ya manna min ƙanƙara har cikin tsakiyar kaina naji sanyin. "Sabida yana sona" cak ya tsaya tare da kura min ido, "Ya tab'a rungume ka?" Wani irin hautsinewa cikina yayi ina kallon shi. Fuskar shi tayi jajjur, ajiye kankaran yayi tare da kama kafar ya wani irin fisgar shi sai da na fasa kara, tare da hada hannuna biyu na dafe kafad'ar shi. "Idan ina magana na tsani ayi banza dani, ya rungume ka?" "Wayyo Allah na, eh sau sau ...sau.." na kasa fada ina jikin ilahirin jikina yana b'ari, ga hawayen da yake zuba min daga ina nuna. "Kasan waye kai?" Ya kuma jan kafar baki daya na fado kanshi..... (Yo Ni a ganina ba a fara Chakwakiyya ba, amma kunce an fara wasan 🤔 🙄 Wallahi indai da gaske zanyi rubutun nan ban yanke shi ba, Billahi azim ba a fara kome ba, wasan ba a fara ba don Allah mu lallab'a juna domin ba ayi kome ba kuma ba a fara ba..... Keep comments And Vote ni kuma na muku typing gaba gad'i 🤫 domin an hanani ambaton Rashin daraja ba wai na daina bane kawai idan ya motsa🙄🤣 Alqur'an zan yi kuma zan kafta... #Mai_Dambu.... [7/25, 9:01 PM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1105333540?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=wFWlz0rB5vLnDHBBsgwmy16HrEu27aKV%2BLrvZEc4HZOQhPxrhzXfAzebs68cEFXa4%2BKxqKR8E%2F8iKJMh4QpPwlUHdawDA%2FOu0EVnwQVQ5hDmkOaB8%2Bq4IYKg9xcPDk7D 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ASHIRIN DA BIYAR. Kifa kaina nayi a kafadar shi ina kuka Sosai, kafar yana hannun shi. Kasa aikata kome yayi ya d'ago kaina. "Kai ba irin sauran yara bane, kome kashin kuskure ya faru da kai babban tashin hankali ne, rayuwarka abar dubawa ce, ina bukatar ganin ka zama wani abu, dan haka duk dan iskan da ya kusanci inda kake sai na kashe shi." Ya kuma murɗa kafar sai da yayi kara nima na sauke ajiyar zuciya tare da kifa kai na a kafadar shi, dif na dauke wuta. A hankali ya d'ago kai na yana kallon yadda kwalla yake sauka ta gefen idanuna, mik'ewa yayi ya kwantar da ni, sannan ya koma hada sauran maganin ya shafa min, tare da gyara min kwanciya na, a kujeran ya shiga dakin ya dauko duvet ya lullube ni sannan ya rage hasken dakin ya zauna tare da mai da hankalinsa kan aikin da yake yana waya da Dan ba'arensa wanda kusan rabin wayar bakar magana sukewa juna. "Ina Mamoon?" Juyawa yayi ya kalli yadda yayi wani lufff a cikin duvet, sai sauke ajiyar zuciya yaƙe. "Yana barci" "Ok amma kana kula dashi kuwa? Kuma idan ya tashi ka bashi wayar mu gaisa mana" Datse wayar yayi tare da kashewa baki daya, yana jan tsaki, Kasa aikin da yake yi, yayi ya cigaba da kallon Laptop din shi, yana ma rasa me zai yi, mik'ewa yayi tare da mika, sannan ya koma saman kujeran da yake fuskar Mamoon ya kwanta. .. Mafarkin mutumin nan nake, da ya kamani d'azun sai kuka nake ina kiran "Hammah na zo tafi dani" na fada ina kuka, dake barcin shi bayi nauyi ba, bude idanun shi yayi tare da tashi yana kallon shi, a hankali ya mike tare da zuwa gaban shi ya zauna a ƙasa, a hankali bakin shi yake karato ayatul kursiyu, yana tofa mishi a fuska, tare da shafa gashin kanshi, har yaji ya fara ajiyar zuciya. A hankali ya mike bayan ya koma barcin, rike hannun shi yayi tare da gyara kwanciyar shi, ya cusa hannun kasan kanshi. Tsayawa yayi yana kallon yadda yake marairaice fuska yake. Saukar numfashin sa yake ji tare da jin wani irin yanayi yana kara tab'a gangan jikin shi. Da sauri ya zame hannun shi yana kallon shi. Kasa komawa kwanciya yayi ya nufi ban daki ya sakarwa kanshi ruwa, yana me dafa bangon ban ɗakin. *Anya Yaron nan namiji ne? Anya mata maza ne? Mata maza ne mana baka ga akwai gashin baki ba? Mtseew!* Yaja tsaki tare da kallon hannun shi, a hankali ruwan yake ratsa shi har ya samu nutsuwa sannan ya fito daure da towel, ya kwanta a gadon tare da rub da ciki, sabida yadda yake jin babu dad'i. A yanzun ya kai matakin da ya dace ya ajiye matar auren shi da iyalinsa tunda shi ba yaro bane, tunda ya haura talatin da bakwai, ya wuce a kira shi da saurayi sai dai tuzuru. Toh wacece zata dace dashi? Wacce mace ce zata iya jure bakin halin shi ba Sannun ba Nagode. Dakyar barci yayi gaba dashi. *** Washi gari. A hankali na mike tare da nufar ban daki nayi wanka da alola na fito na shirya, ina gamawa yana buga kofar dakin. Fitowa nayi tare da kallon shi. "Ina kwana Hammah" share ni yayi tare da juya min baya na nufi falon. Rufe kofar nayi tare da gabatar da sallah, sannan na fito. "Ka shirya?" Gyada mishi kai nayi, sannan kuma mai da hankali kamar bai da abin fada kafin yace min. "Ga abinci" wuce shi nayi na zauna na fara cin abincin bayan ya kalli kafar. Ban tab'a kawo zai jifo min tambayar da ta sani kusan kwarewa ba, sai da na furza da shayin bakina. "Kana son Cigaba da zama da jinsi biyu ne ko kana son tsayuwa akan jinsi daya?" Had'iye yawu nayi ina goge bakina. Ganin naki bashi amsa ya sashi mik'ewa, tare da nufar dakin shi ya fito da kayan shi. Yana kallon agogo kou bai gaya min ba nasan ya shirya. Nima da sauri na tashi ina tafiya ina dingishi. Kallon agogon yayi sannan ya ajiye kan shi ya nufi dakin ya dauko min kome sannan ya fita da shi, kallon shi nake kawai, can sai gashi sun kuma dawowa da wani mutum ya kwashi kayana shi kuma ya kalle ni kad'an yana me takowa gaba na, a tsuguna ya saka min takalmina, sannan ya dauke ni can, ta mike hana na lumshe idanuna. Shi kan shi wani abu yake ji a ranshi, idan yana tare da Yaron shi kuma ba wai dan Iskanci ba a'a kawai yana yin su kawai kamar sunyi raja'a akan abu daya ne, shi yasa yake ririta al'amarin yaron yake kuma kokarin tsayawa yaron, Har waje haka muka yi ta ratsa mutane. Har gurin motar da zata kai mu jidda, lokacin da zai sauke ni ne wani karamin abu me matuƙar tasiri. Domin a hankali yake sauke, yana isowa daidai fuskar shi ee shiga niman nawa, cikin wani irin yanayi, ya zuba min idanun shi cikin nawa, ina iya hango wasu sirrika na shi amma babu damar fadar su, ina ganin wani abu na musamman a cikin ƙwayar idanun shi, amma karfin dakiya irinta zaratan maza ya sashi boye min haka, hancina ne ya gogi nashi, bakin shi ya sauka akan goshina. Wani irin yarrr naji kamar tsutsa na tafiya a jikina, shi kan sa wani abu yaji suna mishi yawo,bai san lokacin da ya sauke ni ba, tare da bude min kofar motar na shiga, ya koma gaban motar ya zauna. Tunda muka nufi Jidda da motar, yana waya da wani har muka isa garin kusan tafiya me dan tsawo, airport muka nufa, anan muka hadu da Abeed, kallona yayi musamman yadda Mohan yake kaf kaf dani. "Yaushe ka fara bin maza?" Kallon juna suka yi kafin yace mishi. "Shine yaron da na gaya maka na kawo shi." "Kai haba na zata lover kane." Daure fuska yayi sakamakon ganin Abeed yana mikomin hannu, yasan larabawa da fitina yanzun sai ya iya makale mishi akan Yaron shi. Dan hka ya buge mishi hannu yana faɗin. "Hannun shi yana ciwo" ya faɗa tare da ɗaukata zuwa cikin airport din, shi kuma Abeed yana dauke da kayan mu, sai zuba yake, shi kuwa yana jin shi dan har ya gundura da halin shi. Haka suka zauna yayi ta mana surutu yana haɗawa dani, nan kuwa Hammah Mohan harara na yake tare da dauke kai, har lokacin tashin mu yayi. "Mohan gaskiya ina son Yaron nan naka" ya faɗa lokacin da yaga Hammah ya dauke ni zuwa inda ake duba kome har kayan mu, ana gama dubawa muka wuce, ya kai ni ya ajiye ni sannan ya fito suka kuma sallama. "Mohan baka ce min kome ba, kasan an Cigaba zaka iya mai da namiji mace please ka bani Yaron wallahi ba zaka sami matsala da Ni ba". Murmushi yayi mishi sannan yace mishi. "Akwai lokaci" daga haka ya juya tare da komawa cikin jirgin yana yaba girman haukar Abeed. Tab'e baki yayi bayan yazo zama ya hango wani dan kasar Philippines a kusa dani, wani daure fuska yayi tare da mikar da mutumin. Yana me zabga mishi harara, tare da nuna mishi hanya. Zama yayi kusa dani, ni kuma na mai da kaina window, ina kallon yadda jirgin zai tashi, cewa aka yi kowa yasa belt, a hankali ya sunkuya kamar zai hade bakin mu, kafin yaja belt din ya saka min. "Wato idan nace bana son abu ba zaka kiyayye ba?" Kallon shi nayi tare da sunkuyar da kaina. Huci yake tare da mai da kallon shi kan magazine din da aka ajiye Mishi. Ina jin jirgin zai tashi ban san lokacin da na kai mishi cafka ba, na boye fuskana a gefen damtsen hannun shi, shafa bayana yake tare da cewa. "Nutsu tashi zai yi!" Jirgin na daidaita a sama, na mike a jikin shi. "Matsoraci kaji kunya." Tura baki nayi ina cewa. "Toh meye laifina?" Dan na razana ya kama ce min matsoraci. ---- Karfe biyu na asuba muka isa dubai, anan ya jani har kasuwa zamani muka yi sayayya, kayan da yayi ta dauka min sune suka bani mamaki. "Ko baka sone?" "Allah ya kara budi" na fada ina amsar kayan, wani wando ya miko min crazy pant, da wata ƙatuwar rigar da nake son saka irin su, amsa nayi ina murmushin jin dadi, sai da na d'aga naga wandona na mata ne, kallon shi nayi. "Ba zan maka dole kasancewa jinsin mata ba, amma wannan wandon yayi min kyau ne, ka amshe shi a kyautana" Murmushi nayi tare da sunkuyar da kaina, ina gyara zaman gashin kaina. "Amma meye amfanin barin gashin nan?" D'ago kai nayi ina kallon shi. "Muje can a yanke maka " ya faɗa tare kallon yadda na firgita. "Tsoro kake ji?" Had'iye yawun bakina nayi tare da marairaice fuska nace mishi. "Iyayena zasu min faɗa" murmushi yayi sannan yace min. "Dama kana tsoron iyayen ka wancan banzan ya dake ka? Sai na kareraya mishi kafa wallahi." A tsora ce na ware idanuna, daga min gira yayi tare da cewa. "Meye?" "Babu" na fada ina girgiza kai, wato shi bai damu da abin da zai ja min ba, kawai yayi hukunci kawai. Kamar yasan ina tunanin da nake kawai ya tako gabana. "Kai na musamman ne, ba yau ba na gaya maka kai kyauta ne na musamman, dan haka dole na gaya maka" Kallon shi nake kamar wanda aka sanya mishi battery sai magana yake kamar bashi ba. "Rufe bakin" da sauri na rufe bakin nayi da hannuna. "Muje" ya faɗa. Idanuna ne ya sauka akan tv ana nuna wani jirgin kasa, wanda yake bin karkashin ruwa da mutane, dafa shi nayi ina nuna mishi tv. Underground railroad. "Hammah Mohan dama an a Dubai ne kawai akwai wannan jirgin" kallona yayi sannan yace min. "Akwai a china, akwai a Singapore, akwai a Japan. Akwai wani dakin da yake bujr Arab dakin yana karkashin kasa ne kuma kina hango kifi mana ko zamu d'aga tafiyar ne muje ka gani" wani ware bakina nayi ina dariya. "Zan je ko sau daya ne" Ja na yayi tare da biyan kudin kaf, sannan ya juya muka fita, wato baki daya rayuwata a Damagaram da Maradi ya kare kai ko Niamey ban tab'a zuwa ba, sai gani a karkashin ruwa ina kallon yadda jirgin kasa yake shiga cikin ruwa, ga kifi yana ta yawo. Cikin wani irin farin cikin nake kallon jirgin tare da kallon shi. "Hammah ka tab'a zuwa nan? Kai wajen da ban sha'awa yake." Na fada ina hada hannuna, murmushi yayi tare da sako kanshi kafadana. "Ya burge ka?" Gyada mishi kai nayi kamar wacce aka zabure ni. "Hammah Mohan! Kasan me gaskiya garin nan yayi kyau kane kar na koma gida," na daura hannuna a kafad'ar shi karku ga yadda na kara har da dagelgel. "Hmm" ya nuna min kafad'ar shi, "Ai kayi hakuri" na fada ina kallon wata irin kifi me rabi mutum rabi kifi. "Wayyo Allah, Hammah Mohan? Wannan shine , mermaid?" Jan bakina yayi tare da nuna min wani kifi shima kato, yana zuwa gurin Meemaid din suna watsewa, dariya na saka ina dawowa ta daya window. "Hammah sun gudu sun ga babban su." Na fada ina wani irin dariya, kukan da cikina yayi ne na kalle shi kamar zan yi kuka nace. "Hammah cikina yana jin yunwa?" Na fada a shagwaɓe, murmushi yayi sannan yace min. "FwpMuje ayi sallah sai a karya" nan ma wancan hotel din ya kai ni, lokacin da ya biya kudin dakin sai da na tambaye shi. "Hammah nawa kudin dakin? Kuma naji kace wuni daya ne?" Na fada ina kallon shi. "Kudin ba yawa sai dai zai iya daukar nauyin abincin wata iyali na tsawon wata uku." Ya fada tare da nufar hanyar da zai kai mu kofar elevator...... _Ban zata zan gama da wuri ba wallahi na zata zan kai karfe goma na dare Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka Sosai kuyi hakuri da rashin editing, Insha Allah gobe zai iya kaiwa karfe biyu na rana kafin nayi Posting Insha Allah sabida na goben ne na baku yau da daddare_ Karku manta sharing 😘👏 #Mai_Dambu.... [7/26, 11:18 AM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1105787433?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=Ja9wL7QqFEErjgU2q%2BSBeLU5C48TPF6alEcOeA68MXjwsxZkfzIB%2B1qokdEbQ55KLRjZ93ztdNSly6DP588o1P6bkl7taWFOl0ee6BP9d%2B%2F0Yz5SwmP2bjWvOwHDMKnB 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ASHIRIN DA SHIDA. Shan gaban shi nayi ina kallon fuskar shi. "Kace zai dauki tsawon watanin yana ciyar da wasu iyalin?" Tura ni cikin elevetor yayi yana me faɗin. "Na gaji da tambayoyin, ba sai ka nuna min Dalibin lauya ne." Ya fada min tare da tsayuwa yana kallon gaban kofar, shiru nayi kafin nace mishi. "Kasan me? Kawai garin nan ya hadu, amma ya abin yake komawa ƙasa?" Na fada ina kallon shi, gajiya yayi da tambayar toshe min baƙi yayi tare da kallon yadda nake zare ido ina ƙoƙarin sai nayi magana. Haka muka shiga dakin tare da kallon ko ina, dakyar na shiga ban dakin nayi wanka da alola bayan na fito na samu baya d'akin amma ga kayana akan gadon dauka nayi na shafa mai, tare da saka kayan sannan na fito ina saka takalmi, kallon shi nayi domin yayi kyau cikin riga da wando sai gyara gashin da yayi, kallon shi nayi sannan nace mishi. "Kayi kyau, amma kuma kayan nan ya mai da kai wani babba dayawa, ka saka kananun kaya zaka fi ka kyau" Na fada ina kallon shi, bai kula ni ba sai aikin gaban shi yaƙe. "Hammah, zo nan" na kira shi ina a kujeran sa yake falon. Daure fuska na nayi, sannan na kuma kallon shi, na mishi alama yazo da hannu na. Shi kan shi mamaki ya gama kama shi abinda yaron nan ke mishi wallahi yana wuce gona da iri, bai musu ba. Domin ya lura Yaron na jin farin ciki ne dan haka ya nufi gurin shi cikin sauki da salama, ya tsaya yana kallon shi. "Kawo kunnen ka!" Wallahi a tunanin shi abin arziki zai gaya mishi dan haka ya sunkuya tare da kallon bakin shi. "Kunne nace" ya gaya mishi haka, mika mishi kunne yayi. Sai da ya gama ja mishi kunne kafin yace mishi. "Wani ya taba gaya maka kai kyakyawa ne? Toh wallahi kai kyakyawa ne gaka kamar dan dambe gingimemme da kai kamar tsohuwar bishiyar kuka." Wato haka nayi ta yabon shi ina kuma rage mishi wani abun. Kallon fuskana yayi tare da cewa. "Da alamu yunwa ce ta saka zuba kamar tsohuwar rediyo?" Had'iye yawu nayi tare da shafa cikina, ina kallon shi. "Idan ka taimaki dan cikina Allah zai gina maka katon gida a aljanna domin yunwa nake ji, kuma Ni kamar mareniya ce" na fada ina had'iye yawun yunwa. Jan hannuna yayi muka fita, muna fita ya hango wani mutum da alama shima dan Afrika ne, wani irin juyar dani yayi tare da had'a ni da bango, kafin kaina ya kai bango ya kai hannun shi, tare da daidaita tsayin shi, ya kai fuskar shi kan nawa, kamar zai sumbaci bakina, zato idanu nayi ina kallon shi. Jikinsa ya matse nawa numfashin sa yana dukar nawa, kwayar idanun shi yana cikin nawa, baki daya na kasa cire idanuna cikin nashi mamaki yake bani yadda ya iya juyar dani cikin zafin nama, *Ka manta shi din soja ne* kuma haka ne fa? . Haka mutumin yazo ya wuce da wata baturiya a gefen shi. Sai da ya tabbatar ya wuce sannan ya d'ago ni. A tsora ce nake kallon shi jikina yana kara sanyi. Kuma na kasa magana, baki daya kamar wacce baya cinye min bakina. "Rediyo me jini ya kai yi shiru?" Tura baki nayi ina me Cigaba da tafiya. "Abokina babu magana ne?" Kara dauke kai nayi ina kallon cikin Elevetor da muka shiga. Daukar wayar shi yayi tare da dannawa ya manna a kunne, kafin ya fara magana, Buzanci ya juya baki daya kamar babu Hausa a bakin shi ko French, haka yayi ta hiran har muna fito, ganin kofar ta bude naka hannun shi mu tafi wayar ta fadi kafin na dauka ya taka, kamar zai bugani da kasa ya dauki wayar yana kallon yadda screen din shi yayi daga daga, gashi suna magana me muhimmanci ne da Hammah Khalil. Ranshi yayi mugun b'aci, "Kasan abinda ka aikata min? Kasan Meye kayi? Me yasa baka da hankali ne? Kalli wayar yadda kayi min da ita? Wallahi baka jin magana mara hankali kawai, kuma a cikin albashin ka zan cire kudin wayata na baka sauran canjinka" A mugun tsora ce nake kallon shi jikina yana rawa, sabida har jijjiyar kanshi mik'ewa yayi, da sauri na fita tare da yankawa da gudu, saka wayar yayi a cikin aljuhun shi yabi bayana, yana fitowa bai ganni ba, sake fitowa yayi ya hango ni, ina tafiya ina share kwalla. Bin bayana yayi tare da da karamin gudu, har ya isa jin ina kuka sosai ya sashi kallon yadda nake kokarin share kwalla da suke zubo min. Abinda na Fahimta shi mutum ne da bai iya rike ka ba, a lokacin da yayi fadar a lokacin yake manta kome. Rike hannuna yayi tare da cewa. "Abokina kuka kake?" Ya tsare Ni da manyan idanun shi. "Don Allah ka mai dani gida zan ga Innah" na fada tare da fashewa da kuka, na fada ina fisge hannuna, ganin na saka hannuna dukka biyu a cikin aljuhun wandona yasa shi bina tare da gyara tsayuwar shi, kauce mishi nayi, ban san mota na zuwa ta bayana ba, sai da naji ya fisgo ni tare da had'a ni da jikin shi. Yana bin fuskana da idanu. Musamman yadda na razana.. hannuna daya a kirji ina zare idanun. "Zan cigaba da baka kariya daga yau har ranar da zan mai da ka gaban Innah." Mai da kaina nayi gefen kirjin shi ina kuka. "Toh kukan na me?" A tsiwa ce na d'ago kai. "Baka ce zaka tab'a min albashi" na ba" na fada ina tura baki. "Really" "Kwarai" na fada ina kallon shi, ga kwalla na zuba min. Shi kam ya manta da wata batun albashi, amma dake yana niman rigamar ya kare sai ya kura mishi ido, sannan yace mishi. "Toh Yanzun kai me zaka yi da kuɗin da baka so na tab'a" da sauri na dawo gaban shi tare da rike k'uguna. Sam na manta da abinda zai fito bakina. "Zan biya sauran kudin gidan da zan saya mana, zan budewa Baba na kanti, zan sayi Laptop zan sayi waya. Kuma saboda wasu yan iska ne zamu bar unguwar dan dayan ya tab'a tab'a." Wani irin caccuma yayi min wanda ya sani tuna abinda Shege yayi min. Jikin shi yana rawa yace min. "Gaya min ina ya tab'a maka" "Hammah sake ni idan har da gaske kai abokina ne!" A hankali ya sake ni, fuskar shi tayi jajjur. Cikin wauta na fara kallon shi sannan nace mishi. "Idan kana min haka wani sai ya dauka kana jin haushin dan an tab'a ni, kuma ai ba wani gurin ya ta b'a ba, duw..." Toshe min baƙi yayi tare da kallon cikin idanuna,, yana wani irin haki. Hannuna ya lalluba tare da sakawa a kirjin shi, yadda zuciyar shi take bugawa kamar zata fito. Dakyar yace min. "Anan na saka ka! Ajiye ka nayi anan karka kuma bani labarin anyi muka wani abu domin babbakewa zanyi a cikin kirjina" "Toh Yanzun idan ka babbake taya zaka rayu? Zaka gaya min gaskiya ko sai na tara maka jama'a" na fada ina had'a index fingers dina yana dan bubbuga su da juna, ina mishi kallon tsokana. Kura min ido yayi cikin damuwa kafin ya riko hannuna, muka koma hotel din, muna shiga kai mu gurin cin abincin, inda ya kai ni babu mutane a cikin gurin, an rubuta VIP. Waiter ne ya tawo tare da memo na abincin, ya ajiye mana cikin girmamawa. Dauka nayi ina kallon abincin da yake rubuce, shi kuwa Hammah ya harde kafa yana kallona. Kallon Hammah nayi sannan na tura mishi memo din ina faɗin. "Ban ga kome" dubawa yayi sannan yace mishi. "African dishi" ya nuna mishi kome sannan ya ce mishi. "Da fruit" haka ya juya kuwa can ba shafa cikina ina faɗin. "Hammah Mohan, wallahi yau sai na biya bashin yunwar da cikin yake bina, kuma ko zai fito sai na dura." "Cikin ka zai fashe" gwalallo idanu nayi waje kafin nace Mishi. "Inji wa? Ai danyen fata bata fasuwa" na fada ina kara tabbatarwa. "Danyen fata yana fasuwa, sosai kuwa amma waye ya gaya maka?" Ya tambaye ni yana kallon fuskana, "Innah ta mana." Murmushi yayi karami sannan yace mishi. "Innah tafi ni gaskiya" sabida yaso ya gaya mishi wata magana amma sanin cewa Yaron shi bai da cikakken kirki yanzun sai ya kuma kara tambayar shi, zuwa an jima reni ya shiga tsakanin su. Ya sa shi gasgata Innah da yaso tace mishi. Akwai a jikin kuma tsaf zai fasu sai ya share zancen. Bai gama nazari ba aka kawo abincin, kallon shi yake yana kallon yadda yake had'iye yawu, dan haka ana gama shirya musu table din yace mishi. "Don Allah karka cinye da table din" gyada kai nayi, ina me daukar cokali, ina faɗin. "Bismillah" na fara diban abincin wani irin motsi kunnena yayi, bayan hanjin cikina yace kururu. "Karka damu ku gama ihun ku, yau zan cakaku da Abincin" ba fada ina kara cika bakina da Abincin. Wato abin ya fahimta, yaron yana da barkwace sai dai rashin abokin da zai zauna da shi suyi hira tare da raba matsalar shi da shi, Yaron yana da kuruciya da wauta, gashi da ban dariya duk fushin sa idan yayi mishi abu zuwa an jima zai bashi dariya, d'ago kai nayi ina kallon Hammah Mohan da yake kallon yadda nake cin abincin.kunya ce kuma ya kamani, na ajiye cokalin ina faɗin. "Ya hakuri na manta da kai ne baki ɗaya." Girgiza min kai yayi sannan yace mishi. "Cigaba" Murmushi nayi mishi tare da ware fararren hakorana. Girgiza kai yayi ya fara shan fruit din yana kallon hannun shi, wayar hannu shi take haske amma babu halin dauka sabida ya bugu da kasa. Har muka gama kallon abincin nayi ina sauke ajiyar zuciya. "Yanzun haka zamu bar abincin?" Na fada ina kallon shi. Bai kula Ni ba, ya fara kokarin mik'ewa nace mishi. "Hammah kawo kunnen ka" na fada ina yafito shi da hannu, ya gaji da shirmen yaron nan, zama yayi tare da kallona. "Kawo mana shawara zan baka" .kawo kunnen shi yayi na kai bakina ina dan karewa kar maganar ya fito. "Kaga mu ce su biya mu rabin kudin mu tunda bamu cinye abincin ba ko me ka gani?" Tashi yayi yana kallon shi idan ya bashi amsa kamar ya biye mishi ne suyi ta hauka, idan kuwa ya kyale shi ya manna mishi haukar shi daya ne dan haka ya mike tare da ciwo kudin ya saka a cikin memo din ya tawo inda nake ya d'ago ni, yasan sai na iya raba kudin biyu, aikuwa bai gama d'aga ni ba, nace mishi. "Wallahi sai na raba biyu." Jana yake ina kai hannuna. "Wallahi zan sab'a maka" kwace hannun nayi ina tura baki. "Haka kawai mutum bai cinye abinci ba ace sai ya biya Alqur'an Ubangiji da na koma sai na kwashe kuɗin." Na fada ina tura baki. Bai san ƙaddara da ta haɗa shi da Mamoon ba, amma baki daya ya hautsina mishi lissafin shi. Daga nan fita suka yi cikin garin Dubai, inda suka nufi wani shagon sayar da waya, anan ya hango irin tashi, a ciki kuwa akwai inda ake gyaran waya Sosai dan haka ya nufi gurin ya mika musu, basu jima ba suka gaya mishi abinda za saya. "Kai haba kudin a kasa kake diba? Gaskiya gwara ka sayi sabo kawai" na fada ina hararan mutanen. "Kasan Allah, karka hada ni da mutane." Ya fada min kamar zai make ni, dan ya fara gundura da halina. Juya mishi baya nayi tare da kallon wayoyin da suke jere. Juyawa nayi gurin Hammah Mohan na janyo shi ina nuna mishi wayar. Na sake shi tare da nuna mishi wata Sumsung S4. "Yayi maka ne?" Kallon shi nayi sannan nace. "Eh amma nasan ko dukkan albashina na dauka ba zai saya min ba. Ba yanzun ba idan na koma gida zan Nime wata yar Vivo, dan naji kace sai ba biyaka kudin wayar ka, shi yasa ba ce maka kawai ka sayi sabuwa." A hankali ya kalli me sayar da wayar ya nuna mishi, yana daukowa ya mika min. "Karb'a" "Hmm, kawai ka barshi domin ka ga idan na koma Maradi zan koma makaranta ne, kuma hostle zan koma. Sannan kuma zan je ganin gida iyayena ina kewar su." Na fada kai na a ƙasa. "Karb'a." Ya mika min lokacin ya mika master card din shi, kamar yadda nayi tsammani haka ce, domin kuɗi ne me mugun yawa, tura baki nayi bayan naga yawan kuɗin. Can nace mishi. "Ina fatan kyauta ka bani? Domin ni dai ba zan iya sayan wayar nan ba, tunda ba kudin ce dani ba" "Zaka zauna dani na wata uku kafin nan na fanshe kudin aikina." Ya fada min yana tafiya kamar ba a bakin shi maganar ta fito ba, wani Jahilin tsalle nayi, tare da dawowa gaban shi, ina raba ido. "Ba ka sami lafiya ba?" "Eh amma ai na saya maka waya kuma na biya kudin gyaran wayar toh me?" "Ungo maza mai da musu bana son Alqur'an bana son, kawai ka bani sauran canjina na koma gida." "Auw haba?" Aikuwa na takarkare murya na fasa mishi kara, sai da ya toshe min bakina, tare da ɗaukata ina, watsal watsal da kafana kamar Yaro dan shekara uku. Haka ya fitar dani daga shagon. Aikuwa na koma inda ya tsayar dani na fashe da kuka. "Wallahi ba zan yarda ba, sai dai ka rike wayar haka kawai zaka tab'a min kudina saura dubu dari bakwai na gama biyan kudin, kace ba zaka kyale Ni ba sai ka fanshe?" "Kwarai sai na fanshe kudina." Ya kuma faɗa min, kuka ne ya kwace min, muna tafiya sai kallon mu mutane keyi. "Kaga akwai wani wasa da ake yi casino zan baka aron kudina idan kaci zaka iya samun sama da dallar Amurka dubu dari uku a lokaci guda, amma sai ka nutsu zan na gaya maka Number kana sakawa, sannan kuma idan aka canza shi zuwa CF kudi ne ne shegen yawa, sai ka biya kudin gidan ka." Kallon shi nayi naga nima yake kallo. "Caca zan buga bayan haramun ne?" Janyo Ni yayi jikin shi. "Karka damu akwai abinda nake son muyi a gurin muje ko ba zaka yi amfani da kudin ba amma kuma zaka ga sabon rayuwa" ya shigar Kawata min gurin babu shiri na amince, muka nufi wani hotel tare mu aka kayi tare da nuna mana inda zamu sauya kaya. Kallona yayi sannan yace min. "Almamoon ina son tausaya min kayi shigar mata?" Wani tsalle nayi kamar wani dan biri. Ina rufe kirjina. "Kai haramun ne" na fada mishi, "Toh babu damuwa bari na fita na nimo wata baturiya" ya juya zai fita da sauri na rike hannun shi. "Amma daga yau karka kuma sani nayi shigar mata, domin ni ba mace bane" na fada mishi ina me sunkuyar da kaina. "Good boy" ya faɗa min, wani daki ya nufa bayan ya buga kofar dakin, wani dan daudu ne ya bude kofar. "Dame zan taimaka maka karjejjen kato" "Sauya min shi a cikin nan da awa daya" ya tura ni. Shiga katon dakin muka yi, da yan mata kafin kace me sun taru a kaina, sai da suka kwashe min albarka kafin suka nuna min wani daki na sauya kaya, haka nayi ta sakawa idan na kalli madubi da sauri zan dawo mishi shi. Dakyar ka sami wata gown iya kwanjina, golen sannan suka dauko takalmin da yar pose, yan kunnewa, aka saka min wato dan daudu nan da ya rike fuskana ya shiga min paint, sai da naji kamar abu ake loda min a fuskar dakyar ya gama. Sannan ya dauko wata jacket ya daura min a ƙafadana yana faɗin. "Kin fito kamar wata Jaruma." Murmushi nayi mishi sannan na fito, ya juya bayan shi yana waya kamar kuma me muhimmanci ne. "Eh mana shi ne daidai da aikina kafin na iso inda zan kammala baki daya, kawai zan yi amfani da hakan ne ka gane kawai ka saka ido akan sauran sai mun iso Insha Allah." Karan sautin takalmi da yaji ne ya sashi juyawa. Tare da zubawa sarautan Allah ido, duk da yasan cewa Yaron mata maza ne amma wallahi yau ganin shi cikin kayan mata ya kara kwadaita mishi son lallai yaron ya koma mace. Takowa yayi tare da mika min hannun, a hankali na saka a cikin nashi, muka fita a hankali domin ban iya tafiya da takalmin ba kamar zan fad'i. Shi yasa ya kange ni a jikin shi har cikin inda ake buga wasan. Kamar zanyi kuka haka nake kallon gurin, saka min abubuwan da zan buga wasan aka yi ya ajiye Dalar Amurka har guda bakwai, sannan ya saka a gabana. Yana faɗin. "Kai me Sa'a ne kayi amfani da sa'ar nan idan suka baka wasan ka dauki wancan silallar." Gyada kai nayi, a hankali yana gaya min ina bin abinda yace kafin minti talatin cinye gasar, a hankali ya shiga tara min kudi ko awa daya ban yi na na zama attajira a gurin an cika min kudi a gaba na. Tab'a kunnen shi yayi tare da cewa. "Ba'are fara" Nan kuwa wani katon mutum ne ya fito, tare da kallon shi. "Dama tunda na ga ana ta cin mutuncin gasar nasan Mohan ya farmake mu. Barka da zuwa." Ya fada cikin French, mika mishi hannun yayi tare da cewa. "Wasan bai kare ba, ita Yarinyar zaka saka nima kuma zan saka abinda na mallaka. Domin zamu gwada kwanji ne?" "Thomas jefferson ba wannan ne ya kawo ni ba, kawai akwai abinda ya kawo ni sai dai matuƙar kasa ni magana zan karya kashin hakarkarinka na kuma Cigaba da wasa na, na jima da ajiye aikin soja kawai ina da yakinin wata rana kasata zata bunkasa." Ya fada yana kallon mutumin. "Toh haba, lallai ku tattara mishi kudin shi, na zata kana aikin ne har yanzun, muje ka sha ruwa" ya faɗa mishi. "A'a kasan bana son giya." Haka ya ja hannuna muka nufi inda mutumin yake zaune, a hankali hira ta sarke a tsakanin su, ina gefe duk a takure nake. "Cire rigar jikinka ka nufi wancan table din, ka zauna" A hankali na cire jacket din na kudi inda yace na zauna, ina zaune sai ga wani dattijo, zama yayi yana kallona. Matsowa kusa dani yayi tare da cewa. "Yan mata daga Afrika?" "Eh" na bashi amsa ina kallon yan matan da suke rawa naked, nan ya zauna yayi ta min shirme da shiririta, har wasu mutane suna shigo gurin. Mikewa yayi suka fita. Mikewa yayi tare da zuwa inda nake ya mika min kofi tare da wani kwaya ya mika min bayan ya bar gurin dai ga mutumin. Ajiye kofin nayi bayan na zuba lemon Kwalba a cikin kofin, na mika mishi sannan nima na sha nawa, a hankali muka hira dashi har ya mike tare da mika min hannu, kallon Hammah Mohan nayi ya gyada min kai. Bin bayan shi nayi, muka tafi yana tangadi har dakin da yaƙe, muna shiga ya zube akan gado. Bayan kamar minti goma, naji an buga kofar, budewa nayi na gan shi. "Babu abinda yayi maka? Toh maza wuce gani nan zuwa." Yana shiga na bar gurin domin da kayan aikin ma'aikatan hotel din ya shiga ya gama abinda zai yi ina club ɗin sai gashi, ya mika min hannun na mike tare da nufar inda muka ajiye kan mu, muka sauya. Kallona yayi bayan na saka kayana na fito rike da jakar da ya saya min waya. "Me yasa baka da account Number? Yanzun da kudin nan sai dai na tura maka" kallon shi nayi sannan nace mishi. "Kudin nan zan kai asibiti da makarantun gwamanti tare da gidan marayu, akwai mutane masu makamanciyar rayuwata basu ci sau uku a rana ba, ma idan na basu zasu yi farin ciki." Jan abinda na daure gashina yayi dashi bayan ya cire hular gashin mazan da yake saman kan nawa, ya zare min gashin. Ribom din da na kama gashin da shi ya ha, gyararren gashin ya sauka har gadon bayana. "Me yasa baka son ayi maka aikin komawa jinsin mata?" Saka hannuna nayi tare da hautsina gashin kaina ina murmushi. "Nafi son wannan yanayin" na fada ina kallon shi. Shima hautsina gashin yayi yana faɗin. "Kuma kayi kyau ba a jinsin mata" Tsayawa nayi ina kallon shi kafin nace mishi. "Ai kafi ni kyau" "A'a ba dai fika farin fata ko" "A'a kawai ba zaka fada bane" "Gaskiyar kenan" Na gaji gashi lokacin sallah yayi dan haka muka nufi inda muka kama, muka yi sallah bayan mun isar yace min. "Pizza kake so ko Shawarma" Mika nayi tare da cewa. "Duk wanda aka kawo min matukar ba zan yi asarar shi ba yayi min" na fada ina shafa cikina. Yayi a waya can dai gashi an kawo min, shi kan Coffee ya sha abin shi. "Kayi sauri domin an jima zamu bar kasar nan." "Hammah duk dai saurin unguwar zoma dole sai an haihu dan haka ka jira na gama cin abincin mana" na fada ina koda pizza a bakina. Share ni yayi tare da mai da hankalin shi kan yanayin da yake ciki, na son lallai ya shiga Nijar yau din nan. Haka na gama dakyar shima dan yayi min barazana zai tafi ya bar ni, yasani mik'ewa da sauri na bi bayan shi, muka nufi hanyar gida. Tunda muka iso airport, yake yawan kallona, "Yanzun idan muka koma dole sai na maka aikin ne?" Na tambaye shi. "A'a bai zama dole ba tunda kayi kudi sai ka rike kudinka kawai." Ya fada min magana mara dadi. Hararan shi nayi tare da cewa. "Wayar ka fa?" "Zan cire a albashin ka" Zama nayi ina kallon shi, har jirgin mu ya tashi, fushi nake dashi. *** Alhamdulillahi mun sauka a garin Niamey. Jerin gwanon motar gidan Primer minister ne ya zo daukar mu. "Hammah karka manta da addu'a" Na fada mishi ina ƙoƙarin bude motar. "Malam ga motan da zaka zauna" juyawa nayi na kalle shi. "Haris kyale shi P.A ne" "Toh Kaji ai ni personal Assistant din shine ɗan haka daga yau nima Yallabai za a kirani ki kuma ba bawa kowa gurin hucin gadi." Girgiza kai yayi yana me shiga bayan an buɗe mishi kofar, nima na bude nawa gurin zaman. "Hammah Mohan! Kai ne primer minister ko kai dan uwan shi shine?" Hannun shi ya kai bakin shi, nima na ja nawa na rufe, a haka muka nufi cikin garin Niamey, ina kallon garin bude min window yayi na juya tare a sake mishi murmushin jin dadi, na cigaba da kallon yadda garin yaƙe. Sai da muka nufi fadar shugaban kasa, na gane cewa Allah yayi arziki, tun daga bakin kofar ake sarawa Hammah Mohan, sabida zuwan shi yau an dauke aikin yan gidan baki daya. Haka muka yi ta ratsa manyan kofaffen gidan har muka isa babban gidan, Wani farin dattijo idan ka gan shi ba zaka zata ya kai shekarun shi ba, haka ya fito da wasu yan yara ƙanana, suna tari Hammah Mohan, sai murna suke, yana fitowa ya rungume Dattijon. "Soja na Barka da dawowa, ina kewar markabu iyalin yaƙi, Barka da zuwa barden Baban shi." "Nagode Abbu" Sake juna suka yi, sannan ya kalli Baban shi yace mishi. "Wannan Yarona ne Almamoon." Murmushi yayi sannan yace. "Khalil ya gaya min mu shiga daga cikin gidan." Kafin kace me har an gama kome, kallon shi yayi sannan yace mishi. "Khalil da yardaddun Yaran ka suka gyara gidan ka, sannan abincin daga mahaifiyar Khalil aka kawo maka, Baba na ina tsoron Allah ina tsoron mutanen da suke tare dani, daga kai sai Khalil nake iya yarda da ku don Allah ka saka ido akan rayuwar ku, yana da muhimmanci...... Naji wani yace yana niman kari 🤔🙄 ku gode kwana biyu ina jin daraja..... Ranar da na rashin shi ya shigo zaku ga aikin gaba gadi....4k wata cewa zata yi kamar kiftu....ta gama #Mai_Dambu... [7/27, 2:39 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI. Juyawa yayi tare da yafito ni,da dan sassarfa na isa bayan su, suna tafiya ina take musu baya har cikin gidan, ba dan na je Dubai nayi kallon duniya ba, ba mamaki sai an daure ni, har falon Primer Ministan na shiga inda ya zauna tare da jan dan shi a jikin shi kamar zai mai dashi cikin shi. A hankali na zauna a kasa, kallona Primer ministan yayi tare da cewa. "Ga key din inda zaka zauna sabida na saka an ware maka maka shashin." "Abbu dalibi ne kuma ina son dawo dashi nan da karatu sabida zan fi sanin meke yi." Da sauri na kalli bakin Hammah Mohan da yayi magana kamar bashi ba, domin yana gaban Abban shi kamar wanda yake daukar karatu wani irin nutsuwa yayi kamar ba shi ba. "Ka tuntubi iyayen shi? Ko ka tuntubi yaron? Kar karfin ikon da Allah ya bamu yasa kayi tunanin kome mana," a hankali ya juya mishi buzanci. Kallon Almamoon yayi da ya nutsu kamar baya gurin yace mishi. "Tashi kaje gurin Harisu zai nuna maka inda apartment dina yake ka gyara kome kafin na iso." "Toh" na ce tare da mikewa, na bar falon. "Yaron nada cikar kamala, yana da nutsu. Amma bai da kwaɗayi?" Primer minister ya tambayi Mohan, gyara zama yayi sannan ya gaya mishi kome akan Yaron, amma bai gaya mishi akan jinsin shi ba, murmushi yayi irin na manyan mutane. "Amma kai me ka gani akan Yaron ni dai a tunanina ka mai dashi makarantar shi, sannan ya koma hannun dangin shi, tunda jinya yazo maka." Duk da sanyin Ac bai hana shi jin wani mugun zafi ba, kurawa Abbu idanu yayi sannan yayi kasa da kanshi. "A'a dama zan cigaba da aiki na a maradin kawai, domin yadda kake ganin yaron ba wani wayo ne dashi ba, kuma akwai wani da yake takura mishi, hmm hmm kuma kuma kawai hannun kawai nake bukata." Kallon mamaki yake mishi domin idan ya fahimta Mohan ba zai iya rabuwa da yaron ba. Sake kishingide yayi yana kallon shi kafin nan yace mishi. "Toh ba laifi amma ba zaka zauna da namiji a gida babu mace ba, tunda ka sami lafiya idan Latifah tazo zamu san abinyi kafin ka koma Maradin." Da mugun sauri ya d'ago kai, ganin fuskar abbu babu wasa yasa shi cewa. "Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Ya fada kamar zai yi kuka. "Zaka iya tafiya kayi wanka idan yaso sai ka turo shi ya amsa maka abincin ka." A hankali ya kara nutsuwa yana faɗin. "Nagode Abbu" ya mike a hankali, ya fita, yana sauke ajiyar zuciya. Bai san lokacin da ya gwammace da ya zauna yayi ta gadin Mamoon har ya gama karatun shi. Ina gama gyara ko ina yana shigowa, jallabiyar ce a jikina me hula. A hankali ya tako har inda nake tsaye, ya zaunar dani. Sannan ya durkusa a gabana. "Wata satin zamu koma Maradi, sama an karb'a maka excuse, toh yanzun zamu koma kuma sunyi korafin kayi wasa da wancan zango, dan haka na mai da hankali sosai ganin na dawo da kai Niamey amma Abbu yaki dan haka idan na gama hutawa zamu koma tare" "Amma nace ba? Kai ɗaya ne ki kana da wasu yan uwan? Naga kai kawai abbu ya damu dashi sai boye ka yake kamar wani abun da za a sace mishi" na fada ina mishi gatsine, tsaki yayi tare da mik'ewa yana faɗin. "Ina da kane maza uku mata uku mu bakwai ne, amma nine babba." "Auw shi yasa ka zama tikeke ashe haka abin yake? Toh Gskiya idan nine kai ba zan yarda a haife ni a farko ba sabida kar na zama tikeke irinka" na fada ina kallon shi. Girgiza kai yayi yana faɗin. "Kai kan wallahi baka da lafiya kana bukatar likitan ƙwaƙwalwa ko zaka samu lafiya." Kallon shi nayi kafin nace mishi. "Babu kyau dai cin mutuncin mutane. Idan bai gaya maka gaskiya ba waye zai gaya maka sai kayi kuma" wucewa yayi tare da barina ina ta mita yace min mara lafiya. "Ina wayar ka?" Dai dai zai shiga wani daki. "Oh toh gashi nan dai ban san ya zanyi dashi ba kuma na kasa kunna shi" juyowa yayi ya zuba min ido. "Wallahi idan ka b'ata wayar nan sai na cire a kudin aikinka" Kura mishi ido nayi ina kallon shi, kafin na kumbura baki ina hararan gefe da gefe na, na juya mishi baya. "Dube shi dan daudu kawai" ya faɗa yana daukar wayar, ai ban san lokacin da kuka yazo min ba. Ina yi ina shasheka, haka ya wuce yayi wankan shi sannan ya fito ya samu ina zaune na zuba tagumi.. "Abokina! Meye Labarin?" Ko kallon shi ban yi ba. "Toh tashi muje ka gaida Ammina" haka na mike tare da zuwa kitchen na wanke fuskana, sannan na tawo na rufa mishi baya. Koda muka shiga falon hannun shi da casbi irin ta yana zikiri, zama yayi ban san lokacin da ya fito dashi ba, sai na ji ya kara burge ni, domin tabon sallah shi har baki yayi na gaban goshinsa. Dinning ya nufa, na rufa mishi baya, dai dai shigowar wata hamshakiyar mace, zuba mata ido nayi, kallon mu tayi. Sannan ya tsaya turus tare da kura mishi ido. Tana son tuna yaushe rabon ta saka shi a idanun ta. "Mohan kayi tafiya ne?" Ta tambaye shi tana niman gurin zama, ina tsaye a kan su. "Ammin kin manta dani, haka nayi jinya babu ke babu Abbu sannan ki tambaye ni kice nayi tafiya ne" ya faɗa kamar zai yi kuka, ya mike zai bar gurin cin abincin sai naji ya masifar bani tausayi. Rike hannun shi nayi tare da kallon shi. "Kaci abincin mana" na fada kamar zanyi kuka, tab'e baki tayi sannan ta mike abinta. "Kai tafi can sake shi ta tafi dan gidan su, kuma ka shirya sosai domin ka dawo sai aure babu b'ata lokaci" Ta fada cikin carelessly, wani irin tausayi ya bani kamar ba uwar da ta haife shi ba, haka ya fita tare da kowa ma apartment din shi, daukar abincin nayi tare da dauka a tire. Yana fita lokacin itama ta dawo daga nata yawon tazubar, suna yi kicibis. Sake jakarta tayi yana kallon shi, baki sake. "Mohan kai ne da lafiyar ka?" Ranshi a b'ace yake dan haka bai bi ta kanta ba yayi tafiyar shi, ina fitowa ta tare ni. "Bakin algungunmi haka zamu yi da kai?" Da sauri na wuce ban kulata ba, ina zuwa na samu baya falon, ajiye abincin nayi na shiga duba dakunan da suke gurin. Can backyard na same shi ya zuba hannun shi dukka biyu a cikin aljuhun wando shi ya kurawa lambun idanu. A hankali na isa tare da tsayawa na kalli yadda fuskar shi tayi jajjur. "Iyaye suna da matukar muhimmanci a rayuwar mu, sannan duk wanda ya rayu da iyayen shi guda biyu bai kyautata musu ba, tabbas yayi asara duniya da lahira. Ban san meye ya sanya ka damuwa ba, amma ka tuna cewa. Kome uwa zata maka ba zaka iya biyan ta ba, Uwa wata irin halitta ce da ba kowa yake iya daukar kasadar da take dauka, Uwa wata duniya ce ta y'ayanta,. don Allah karka yi fushi da Ammin ka" "Ka min shiru!" Ya daka min tsawa, a tsora ce na ja baya, tare da kallon shi, ina jin wani irin tsoron shi. "Kasan yadda Soyayyar uwa take? Kasan har yanzun ban sami soyayyar uwa ba? Daga Anne Mahaifiyar Khalil sai Abbuna sai Alhaji Ibrahim Ibrahim Dan Ba'are,.mahaifin Khalil Ibrahim Dan Ba'are sai Khalil iya mutanen suna tsayawa rayuwata. mahaifiyata bata da cikakkun lokacin dan ta, bata damu da dan ta ba, bata damu da kowa ba sai daukaka da kyakyawan nasaba! Tun ina yaro na taso cikin kad'aici da rashin walwala. Kasan me yasa Uwata bata samu dani ba, idan na zauna bata tab'a tambaya na matsalata. Shine zaka gaya min soyayyar da tuntuni ta kashe shi fita ka bani guri.". Da sauri na juya ina kuka. Duk sai naji babu dad'i, har kusan karfe goma, bai fito ba dan nima ban sami damar sallah isha ba sai karfe tara, yunwa ce ta dame ni na fito ina raba idanu. Haske na gani a wani korido, dan haka na kama Bin hanyar, murmushi nayi da naga dakin motsa jiki ne. Zama nayi akan inda ake d'aga karfe. Na fara kiciniyar d'agawa amma na kasa, hararan karfen nayi tare da tura baki. "Dan banza karka mike mana." Na koma kan abinda ake dan gudun nan, na kunna aikuwa na saka da mugun gudu sai ji nayi na maku da kasa, timmm. Da sauri na mike ina zare idanu. Da suke cike da kwalla. Tare da juyawa ina dubawa ko yana gani na. .... Fitowar shi kenan daga ban daki ya tsaya a gaban tv da yake hade da Cctv, aikuwa yaga abinda Almamoon yake da farko bai maida hankali kai ba, amma lokacin da ya tiku da kasa bai san lokacin da takaici ya sashi jan tsaki, can kuma ya sake murmushi ko babu kome ya sha kasa, kai wannan yaron yana da kayan ban haushi. A hankali yake bin yaron da ido duk wani motsin shi, sam bai yi kama da cikakken namiji ba, inji wani shashi na zuciyar shi. .... Tana shiga d'akinta tayi zaman yan bori, tare da sake kuka kamar karamar Yarinya. "Ni sahiya yau aka tozarta, sai naci kutumar kaniyar wancan bakin Yaron dani yake batu." . Nan ta kira waya tayi ta bayani kamar zata yi sujada ga mutumin da take waya dashi kafin ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya. ... Gyaran murya yayi daidai na balla wani karfe, da sauri na ajiye ina kallon shi. Wato karatu da rashin abin yi yasa Yaron nan ya soma rashin ji baki daya baya jin magana, yanzun haka karfe biyu ya karya mishi a cikin ɗakin. Washe baki nayi ina faɗin. "Hammah na, Sannun ka gama kukan ka?" Na tambaye shi ina leka fuskar shi, Nad'e hannu yayi a kirji nima na nad'e tare da had'e fuska. "Hammah Mohan cikina yana kukan yunwa, kuma idan da hali muje kaci abincin" na fada ina wani tsare gida, takowa yayi gabana na fara ja da baya, ina cewa. "Kaga ka tsaya a gurin yanzun yunwa nake ji idan na koshi zan iya samun damar tanka maka" ban san na kai jikin wani karfe ba sai da nayi da baya zan fadi naji ya saka hannun shi a bayana ya zagayo dashi k'uguna. Hannuna dukka biyu suna kirjin shi idanuna a waje kamar zasu fado kasa. "Baka jin magana, kuma a cikin albashin ka zan cire kudin gyaran kayan motsa jiki na." Ya fada tare da juyar da Ni, sannan ya cire hannun shi yana me niman hanyar fita. Da gudu na tare kofar. "Kasan Allah yau zan bar aikin nan na fasa tunda dai haka ne kuma na daina abotar daga yau" na fada ina hararan gefe da gefe. "Ok haka ne?" "Am preety sure." "Baka jin yinwa ne?" Ya fada tare da niman hanyar wucewa. "Kuma fa haka ne wallahi yunwa nake ji muje na saka nawa na ci tunda kai baka ci" "Canza kayan ka mu tafi mu ci a waje" kallon shi nayi kafin nace mishi. "A wannan tsohon daren ina zamu sami abincin Hammah ka cika tone tone, Ni babu inda zani kawai zan ci wannan ya ishe ni." Na nufi hanyar falon. Na shiga bude kulolin abincin, sun Huce babu wani zafi sai dai dumi. Dan haka na zauna na fara zuwa, zama yayi yana kallon yadda na lakwashe kafa tare da zuba abincin na fara ci, ina gamawa na kalle shi kafin nace mishi. "Hammah kamar akwai magana a bakin ka" na fada ina kwashe kayan. Nufar kicin nayi na ajiye, sannan na dawo. "Jeka kwanta dare yayi" ya faɗa min, babu musu na mike ina karawa da mika. A hankali na barshi gurin bayan na mishi sai da safe. ** Da asuba bayan ya buga min kofa, nayi sallah ina idarwa na koma na kwanta. Domin har yanzun da gajiya a jikina. Mafarkin wata mata muna fada da ita, lallai sai tab'a Hammah Mohan,.na hana ta shine ta zaro hannun ta masu kama da kusa ta yakushe ni, sai da na farka, ajiyar zuciya nayi lokacin da naji muryan Dan Ba'are yana magana kamar rarrashin Hammah. a hankali na fito daga dakin ina kallon su. "Barka da safiya Hammah na, Hammah Khalil ina kwana?" "Alhamdulillahi, Mamoon ka shirya kayan ka zamu koma tare." Mai da idanuna nayi kan Hammah Mohan, dauke kai yayi kamar baya gurin gurin kulolin abincin na nufa ba irin na jiya bane. "Mohan ba wani abu bane idan yarinyar bata maka ba sai a hakura meye na b'ata rai? Kawai ka shirya muje." Kallon su nayi tare da cewa. "Hammah Mohan aure zaka yi?" Na tambaye shi a sanyayye, gyada min kai yayi tare da lumshe idanun shi, alamar yana cikin damuwa. "Toh baka son matar da zaka aura ne?" Na tambaye shi ina cika cokali da madara. "Eh bayan son ta, shine yake son lalata niman auren" murmushi nayi tare da cewa. "Toh Allah ya kyauta." Mikewa Hammah Khalil yayi tare da cewa. "Bari na je na dawo kafin mu tafi gidan ministan Noma." Gyada kai nayi mishi, kallona yayi ba tare da yayi magana ba, ya fice daga falon. Dawowa kusa da Hammah Mohan nayi zan mishi magana kawai naji ya fisgo ni da karfi, sai da ruwan shayin ya zube, karb'an kofin yayi yana kallon yadda nake zare idanuna. Daura ni yayi akan cinyar shi tare da juyar dani, idanun shi sun yi jajjur. "Idan muka je haka zaka min." Jikina da yake rawa, kuwa sai gyada kai nake alamar Eh. A hankali ya sauke ni a jikin shi tare da barin gurin, zama nayi a kasa tare da zubawa shayin ido. Ban san me yasa idan Hammah Mohan ya tab'a ni har cikin jinin jikina nake jin shi. Numfashi na sauke tare da tuna yadda ya juyar dani ina fuskarta shi. Ina jin tasirin hannun shi a cikin ruhina da jikina. *** Karfe hudu na yamma muka shirya mu uku, sai kallona yaƙe tare da karfaffan min gwiwa, har muka isa gidan tun daga parking space na Fahimci irin gidan da Hammah Mohan ya shigo. Falon gidan aka so ya shiga yaki dole aka tura mu garden. Muka shiga tare, Hammah Khalil kuwa yayi tafiyar shi akan idan mun gama ya kira shi. Muna zaune aka shiga kawo abin tab'awa, babu abinda muka tab'a, can kuwa sai ga Yarinyar doguwa kyakyawa da ita kamar bugun injin, tunda na hangota. Na kalle shi lumshe idanun shi yayi tare da gyara zaman shi, kafin ta iso na haura cinyar shi tare da kai hannuna wuyar shi, fuskar mu kamar zata had'e, idanun shi cikin nawa....... Ku more abunku kuma ranar da kuka min rahin daraja na bar ku na bawa WhatsApp 🤣😛😜🤣 suma Rahin daraja suka min..... #Mai_Dambu [7/28, 10:10 AM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1106571155?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=MGSTqUwhvG4fBdc8Tqj6OqYqeY7iy%2Bvg8ZVvU9exRM%2FT3GQPgpgjcFkI2rY8w%2BnUMqLJf147FJNMo%2B9%2FQjDN7znC%2BTjtiS3PBxbASme2UWXXFcEf8ltwj%2F4SXO5evwr1 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... _Ina ganin Comments din ku da Vote din ku Nagode sosai, amma kuma yadda kuke son wani abun ba zai iya samu ba dole sai anyi hakuri da yadda tafiyar take! Allah yasa kuna fahimta_ BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS. Hannun shi dukka biyu ya saka tare da rike Almamoon gam, yana goga mishi hancin shi kan nashi hancin, ganin yadda Almamoon ya rintsa idanun shi yasa shi kara sauke hannun shi zuwa cinyar shi. "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji yayi min tsari da wannan kazamtar." Ta fada tare da toshe bakinta. Cikin wani irin tsana da kyamar su tace. "Ku tashi ku bar min gidan mu na tsane ka dama ba son ka nake ba, aka sani dole kuje bana son ganinku." A hankali na mike ina kallonta a raina kuwa dad'i naji tare da kallon yadda take matsar kwallan. Mikewa yayi sannan yace mata. "Lover na ne, yayi miki" kamar wacce zata yi amai ta fara yunkurin amai haka muka bar gurin ya saka hannun shi daya a aljuhun wandon shi, hannu daya riƙe da waya yana niman dan Ba'are. "Kai Man har ka gama abinda ya kawo ka?" "Kasan sarauniyar kyau ce da zan zauna kallonta mun gama kome saura kai da Ammin ku ji da sauarn." Ya fada tare da kashe wayar yana kallon yadda na takura a gefe guda, sai harde hannuna nake baki daya na gama kosawa na koma gida. Takowa yayi har gaba na, tare da d'ago kaina. "Meke damunka?" "Babu" "Ka tabbatar?" "Eh" na fada tare da gyada mishi kai kwalla na zuba min. Fuskar shi ya kai kamar zai sumbaci bakina, nayi baya da kaina. "Toh meye matsalarka?" Ya tambaye ni a gajiye da abinda nake mishi. "Don Allah ka mai dani gida na gaji Ni ba makaranta ba ni ba gida b..." "Baka son zama dani ne?" Cikin wani irin sarewa na zuba mishi idanuna da suka yi jajjur. "Ba haka nake nufi ba" "Toh nace ba zan kai ka gida bane? Ko so kake mutane suce na maka wani abu! Kayi min shi kafin raina ya b'aci." Yana rufe baki sai ga Dan Ba'are ya iso a masifance ya bude motar ya shiga,.nima na shiga. Tunda na shiga na had'a kai na da gwiwa ta, sai kuka nake. "Meye ya same shi?" Inji dan Ba'are,ya tambaya kamar zai tsaya. Banza Mohan yayi mishi kamar baya cikin motar. Katse kukan nayi tare da cewa. "Hammah Khalil zaka mai dani Maradi ko?" Na tambaye shi ina kara sake kuka, "Eh zan mai da ka." Ya fada min yana kallona ta cikin madubi. Duk da idanun shi a lumshe yake bai hana shi dakawa dan Ba'are tsawa ba. "Dalla can ka kalli hanya karka ja min magana, ya faɗa tare da gyara zaman shi jikin kujeran. Tare da lumshe idanun shi. Haka yayi ta masifa shi daya tare da fadin. "Wallahi na rantse da Allah idan baka min shiru na sai na ga wanda zai kai ka Maradi" had'iye kukan da nayi kenan ban kuma ko tari ba har muka isa gidan. Muna shiga ana kawo mana abuncin daga ɓangaren Hajiya Sahiya. Ina karb'a kitchen na kai na juye abincin. Sannan na fito tare da nufar dakina na hada kayana. Kwalla ne ya shiga zuba min, ina had'a kayan. Har na kusan gamawa na ji motsin mutum a bayana, a hankali na mike ban juya ba. Wani irin fitar numfashi na ja, tare da sake kayan hannuna. Kwalla na kara zuba min. Hannun shi dukka biyu da ya sakalo su akan cikina, na kalla. Kwallar da suke zuba ne suka kara yawan fita tare da zuba akan hannun shi, juyar dani yayi yana mai daura kaina kan kirjin shi. Ina jin yadda zuciyar shi take bugawa very faster. Kanshi yana saman kaina, a hankali ya shafa bayana. "Karka zama stupid, ka mai da hankali akan abinda ya kawo ka niman Insha Allah Wata sati zan shigo duba ka.". Gyada kai nayi sannan na janye jikina, amsar kayan yayi tare da fitar dashi, ina bin bayan shi. Yana fitowa falon ta mika min wayata da jakar Laptop, sai ta card din bankin shi. Kallon shi nayi domin kuwa idan na tafi da wannan kayan gida mai hana Innah ta min Yankan rago Allah da ya halicce mu ne, na bude baki zan yi magana ya daura min yatsar hannun shi a bakina. "Na tsani musu" ya sanin katin a cikin hannuna. Sannan ya nufi Hammah Khalil, ya cakume wuyar rigar shi cikin fushi yana faɗin. "Dan Ubanka idan kayi mishi magana sai na karya maka muƙaminka, Allah ya tsare hanya." "Sake ni don Allah idan baka yarda ni ba, kazo muje." Ya fada mishi cikin jin haushi. Haka ya sake shi tare da shigewa dakin shi bai kuma fitowa na har muka bar gidan. Yana kallon motar ta dakin. Bai san wani irin mugun kaunar Yaron yake ba? Bai san lokacin da kaunar yaron ya mishi kamun kazar kuku ba. Abinda ya sani kawai yaron yana burge shi, toh bayan nan sai ya fahimci ko tab'a Yaron aka yi sai yaji kamar zuciyar shi aka tab'a. A cikin haka ya fahimci baya son yaga yaron yana mu'amala da kowa shi, yayi imanin yadda ya koyawa yaron yadda zai iya hakuri dashi. Ya koyawa yaron wani mugun sabon shi, wanda idan ba shi ba ba zai tab'a hira da kowa me tsayi ba sai shi, ya sakewa yaron zuciyar shi yadda ba zai iya jin dadin Kowa ba sai shi. ... Wani irin numfashi yake saukewa kamar wanda yayi aikin wahala, lumshe idanun shi yayi tare da bude su akan hoton shi da Almamoon da yake manne jikin wallpaper na Laptop din shi. Shafa hoton yayi tare da jin wani irin kewar Yaron, kamar yace mishi ya dawo amma babu halin haka. Dan haka ya kwanta yana kallon hoton. .---. Tunda muka bar gidan na kame kaina, haka muka yi ta tafiya da tsakiyar sojojin da suke bin bayan Dan Ba'are. Kallona yayi yaga ina ƙoƙarin share kwalla. "Baka son rabuwa da Mohan ne?" Gyada mishi kai nayi, tare da kallon gefen hanya. daga haka bai kuma min magana ba, har Allah ya kai mu Maradi, wani Unguwa da take kusa da makarantar mu ya kai ni daidai kofar wani gida, horn yayi aka bude kofar gidan, a hankali ya tura hancin motar zuwa cikin gidan. Sannan ya tsaya tare da budewa ya fito, sojojin suka tsaya a kofar gidan. Daukar jakar Laptop din nayi sannan na fito, cikin gidan nake bi da kallo har muka shiga asalin cikin gidan, ko ina gwanin ban sha'awa. Sannan ya kalle ni. "Gashi nan inji Mohan, idan ya dawo zaka koma gidan da yake jecader wannan kuma ya saya maka ne dan yaji kace kana son sayawa iyayen ka. Wancan motar da muka zo dashi kuma na kane, ka shiga cikin gidan zaka ga kome ya saka maka. Fatana kayi karatu karka b'oyewa abokan banza dan Mohan bai da saurin fada amma idan zai yi wallahil sai ka sha mamaki, Ni zan tafi." Gyada mishi kai nayi domin kamar wanda aka rufewa baki haka na kasa magana, ina ganin ya fita wayata ta fara kara, kallon Number nayi, ina niman sanin Number waye? A hankali naja shi zuwa kan koren na saka a kunne na. Wani irin huci ya sake min. A hankali na zube akan sofar da take falon, ina me kumshe idanuna. Wata irin kasala da gajiya nake ji. "Kun isa lafiya?" Sai da naja numfashi sannan na iya bashi amsa a hankali. "Alhamdulillahi!" "Kayi sallah ka ci abincin yanzun za a kawo maka, sannan akwai sojojin da zasu na gadin kofar gidan, akwai wanda zai na zuwa aka hidima kama daga shara da wasu abubuwan, sabida karatunka. And second And the last karka ji kar na gani wani abu ya shiga tsakanin ku da Ansar idan kuma kana son ganin gawar shi bismillah." "Don Allah bana son kana fadar haka, zan kiyayye amma karka kara furta kalmomi marasa dad'i akan ka." Na fada ina lashe bakina, kashe wayar yayi. Tashi nayi nayi wanka tare da gabatar da sallah da take kaina da wanda zata zo, ina idarwa ana kawo min abincin. Bude kofar nayi naga Hamma Malik. Murmushi muka yiwa juna, sannan nace mishi. "Kwana biyu?" "Yaron Oga ai kayi wuyan gani ya jikinka?" "Da sauki, shigo mana" Girgiza min kai yayi sannan yace min. "Ina nan Oga ya bani umarni daga haka laifi ne" "Toh" na fada, ina kallon shi bayan ya ajiye min abincin yayi tafiyar shi. A hankali na dauka na shiga cikin gidan, ina mamakin Hammah Mohan. Ya hanani mu'amalar kowa toh me yake nufi? Toh ba mamaki ko dan saboda Matsalata ce. *** Washi gari. Da wuri na shiga makarantar, tare da nufar hanyar Office din shugaban makarantar, muka yi magana dashi ya tabbatar min Bani da matsala daga sama an yi min kome kawai na maida hankali nayi karatu kawai. Sati biyu Tunda na dawo babu labarin malam Ansar, bawai baya makarantar bane yana nan kawai sabgar gaban shi ta ishe shi, kuma Bama haduwa, haka yasa min nutsuwa gashi sojoji ke rakoni makarantar, yau da wuri na fito sabida muna da test. Ban damu na bi mota ba, kawai ina son tafiyar kafa, ina rataye da jakar makaranta, dan haka na mai da hankali na sosai a tafiyar da nake har na kusan shiga makarantar, na juya baya naga sojojin Hammah suna bina, cikin jin haushi na harare su. Kafin na ciro wayar dake aljuhun jakar na fara kiran shi. "Ya dai abokina?" "Hammah kacewa mutanenka su daina bina, sun hana Ni shakar iska me dad'i kowa gudu na yake, don Allah kace..." Ji nayi kamar an d'agani sama anyi gefe dani motar ta shiga cikin makarantar da mugun gudu, baki daya na zata motar ce tayi watsi dani, sai dai har yau hancina bai daina banbanta kamshin sa dana kowa ba, D'ago kai nayi ina kallon Ansar Yusuf. "Ka nutsu ka daina waya akan hanya, rayuwar ka tana da amfani." Ya fada yana kallon yadda na razana. Da gudu sojojin suka iso suna mishi godiya. Ni kam na kasa magana sai kallon Malam Ansar nake, ya kara kyau da girma. A hankali yayi tafiyar shi tare da barina a tsaye. Sai lokacin na tuna da wayata da take ya she, dauka nayi ina ganin yadda take magana. Sakawa nayi a kunne na. Hucin shi naji alamar ran shi yana b'ace. "Meye ya faru da kai naji muryan Ansar Yusuf." "Hamm" "Kayi min shiru" ya buga min tsawa har yana dukar wani abu, kashe wayar nayi, can ga daya daga cikin sojojin yana mishi bayani, ban ce kome ba na nufi makarantar. Bayan an fito test naga motar da ta bangaje,. Ina zuwa gudun na duba wani dutse na dauka ina juyawa kafin mutanen gurin su fahimci ma'anar abinda zan yi na fasa gaban motar, tare da kallon yadda kowa ya razana. Sannan na daki kofar motar da kafana. Nayi tafiyata, ina jin duk wanda ya isa ya tare ni. Fitowa suka yi da Kawayen ta, dukkan su yarane bana zasu fara jami'a. Tana zuwa taga motar da Appa ya saya mata ko wata biyu ba ayi ba. "Waye ya min wannan barnin." Darewa suka yi tare da nuna musu Almamoon yana tafiya a nutse, da gudu ta kwasa tare da shan gaban shi. "Uban waye ya ce ka fasa min motana" "Ubanki ne!" Na bata amsa a nutse, "Kai dan gidan Uban waye a makarantar nan?" "Dan gidan Ubanki" D'aga hannu tayi na rike mata shi. Ina murmushi. "Yarinyar karya kika yi, ba'a tab'a ba mace ta mari Mamoon karya ne" Karan da waya ta tayi a karo na biyu na duba, Number Hammah ce. "Hammah" "Me yasa ka fasa motar?" "Na koya mata yadda ake tuki ne?" Na fada mishi. "Baka jin magana ko? Akan me yasa?" "Hamma yadda tayi tukun saura kanta ta kashe ni, sabida rashin sanin hakkokin dan Adam?" Na tambaye shi ina kallon yadda take kallona, "Benazir zo mu tafi zamu hadu kuma dole ya biya kudin motar dan shima kamar Uban shi kwaro ne" Kashe wayar yayi bayan ya gama masifar shi, itama kuma yarinyar tayi tafiyar ta, bayan ta gama huci. Oho ban san ya aka kare ba, sai dai washi gari bayan malam Ansar ya gama darasi ya tura naje. Bayan na shiga ya kalle ni sannan ya ce min. "Zauna" Babu musu na zauna, sai da ya gama abinda yake sannan yace min. "Kayi hakuri da abinda ya faru, sharrin shaidan ne insha Allah ba zai kuma faruwa ba, amma ina son niman wata alfarma daya ?" Duk sai naji ya cika min idanuna. Sunkuyar da kai nayi. "Ina jinka" "Zamu iya zama abokai" da sauri na d'ago kai. "Don Allah, nasan ba zaka tab'a sauyawa ba, kuma babu wani abinda zai bayyana bayan kasancewar ka namiji, so ina son mu zama abokai na har abada." Kallon shi nake ina mamakin yadda ya sauya baki daya, yayi laushi. Murmushi nayi tare da mika mishi hannu, muna gaisa. Tun daga lokacin muka dinke tsakanin mu akwai kyakkyawar fahimta, da kanshi ya kawo min Baba Mari ta zauna dani, karatu yayi zafi dan haka koda muka fara jarabawa babu wani lokaci, Alhamdulillahi kuma kamar ina nan akayi darussan baya. Benazir kuwa ban san ya akayi ba sai dai naga ta gyara motar ta, bayan tayi mako biyu bata zuwa dashi, ranar da tazo ita da kawayenta. Suka tako har gabana zasu min Iskanci na dauki wani dutsen. "Kuna cewa tak zan rushe wancan sabon glass din"' na fada ina kallon su. Babu wacce tayi magana. "Matsalar ku baku da tarbiyya ni kuma na tsani renin. Na fada ina kallon su, mik'ewa nayi na bar su, a gurin ban san me yasa nake iya dauke kai a tsiyar da Benazir take min ba, dan ko tayi min bana kulata. Muna gama jarabawa, ban gayawa kowa ba, kawai na nufi Damagaram tare da jin kamar karna je, sabida tsoron Innah. Da yamma likis na isa gidan, ana gama sauke min kayana, na shiga cikin gidan gabana yana faduwa. Baba na samu a tsakar gida, Inna tana daki. "Almamoon" Baba ya kira sunana a hankali, da sauri Innah tafito tana bina da wani sassanyar kallo, sunkuyar da kai nayi. Tare da isa cikin gidan. Ban yi aune ba sai ji nayi an kife ni da mari, sai da bs zube. "Haba Aminatu murna zamu yi Allah ya dawo dashi lafiya, ba duka ba." Cikin kuka ta sake rufe ni da duka. "Malam kafi kowa sanin har hawan jini aka ce ina dashi sabida wannan Yaron, kafana shida A cikin Maradi ina niman shi, makarantar su ma since basu gan shi ba, maza mike min ka shiga daki ka kuma cire kayan ka gani nan shigowa." " A'a Aminatu karki zarge shi mana kiyi hakuri zai gaya miki inda ya shiga." "WALLAHI har gwajin juna biyu sai na mishi dan abin kunyar shekaru shatakwas ma ban gama fita ba a cikin shi balle ya ajiye min dan daka kuka...... 🤣🤔 Ra uba inji Hamzan zaranda ana wata ga wata.... Mohan ko ka afkawa mata maza ne, ga rubutu ya dauko tafiya ni kuma wani babban uzuri yana taso min ya damu yi kenan...... Kuyi hakuri da rashin editing... #Mai_Dambu... [7/29, 10:27 AM] Hafsatu Hafs: https://www.wattpad.com/1106761947?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=96bc8j7ajP40xeHpU1lx3Iq9KNgJDweWbOsQ2t4marCDkKriXYt89TwgT%2BmS3tOH%2FA0PvkmbeXh9jXQ8GnCAYeKrGW2Uqpce1Fx0xCDcXJXOV%2BHIdFegRFE9fS%2FUP7i8 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... *Wannan shafin gaisuwar kune Mutanen Jikar kulu 💞💓😍 da Masoyan BOROROJI Novel tare da Masoyan MOHMOON da MOONSAR* TeamOneLove❤️😘 BABI NA ASHIRIN DA TARA. A wani firgice na kalli Innah, jikina yana rawa, ta daka min tsawa. "Ina kuka je?" Dakyar na sami bakin magana na gaya musu abinda ya faru. Cike da mamaki take kallona yau dan da ta rena shine har da bin wani namiji wata ƙasa. Zama tayi tana nazarin ta ina ta gaza a tarbiyyar da tayiwa Mamoon. Cikin kuka ta nuna kanta. "Ta ina ma Gaza? Meye nayi maka da zaka zabi bin namiji? Mamoon wata biyu bana barci cikin sa'ida kullum mafarkin mahai...." Rufe mata baki baba yayi tare da mika mata ruwa. "Kisha" karba tayi tare da sake wata irin kuka. "Gaya min meye yayi maka? Ko kuma na saka wuka nayi maka yankan rago" "WALLAHI bai min kome ba na rantse da Allah, ki duba jikina." Na fada mata, wani irin kuka take sannan ta riko hannuna da yake b'ari, ta rungume ni. "Daga yau ba zaka kuma komawa bokon ba, ina tsoron sanadin boko karka bijiro min da tashin hankalin da zai hanani sukuni" "A'a ki bar shi yayi karatun." "A'a malam, tsoro nake ji ina son shi kamar yadda nake son dan uwana." Ta fada tare da kallon shi bayan ta rungume kan Mamoon a kirjinta. Cikin hikima take bugun cikin Almamoon, wanda tsoro ya sashi ya fadi gaskiya ba tare da yasan dabaranta ba. "Kuka kwana daki ɗaya? Ban san iya abinda yayi maka ba Almamoon anya kayi mana adalci." "Innah kiyi hakuri" na fada a tsora ce, sai da ta gama jin abinda muka aikata, sannan ta kama kunne na ta buga min katon kashedi tare da cewa. "Ka gama zama a wani gurin, sannan kudin da ya baka da kayan shi zaka mai da mishi kwadayayyen banza irin haka ake cutar da ku saboda mugun kwaɗayin ku, baku zama inda Allah ya ajiye ku, burin ku kawai kuyi ta bin masu kudi suna baku abin hannun su, ana amfani da ku. Waye ya sani ko ya gama abinda ya gadama da kai malam bani guri na duba shi" Duk yadda Baba yaso ta hakura Innah fir taki, sai da ya fita ta jika wani saiwa, ta mika min masha, sannan ta sani na cire kayana, ta kwantar dani ta duba lafiyar jikina, sosai wani irin ajiyar zuciya take saukewa bayan ya sani na juya baya ta duba mazaunaina, sujada tayi tare da mika min kayana bayan ta mike. "Kana barin ana tab'a maka kirjin ka ne?" A tsora ce na lalle kirjin. "A'a kawai na sayi wanc.." na bude jakar na ciro mata bra ɗina, kifa min mari tayi. Tare da cewa. "Ina yadin da na baka?"jikina yana rawa na dauko tare da mika mata, ganin ma na daina amfani dashi yasa ranta yayi mugun b'aci. "Waye na shi da ys canza maka duniyar ka? Nasan ba Ansar bane, waye shi da idanun ka suke nuna min kana bukatar shi anan?" Ta fada cikin kuka, anan ne kuma na kasa mata magana, duk yadda taso na gaya mata waye ne shi naki. Ta dake ni a ranar kamar bata kaunata, tayi juyin duniyar nan na gaya mata waye haka, naki naki karshe ma kin magana nayi sai kuka domin idan na bude baki nace mata Mohammed Mamman Mohammed Nasir Aghali ne toh ba makawa ba zata kuma barina saka shi a idanuna ba. Fita tayi tana kallon Malam Umaru zuɓewa tayi a kasa tare da fashewa da kuka. "Almamoon Malam, abinda Mahaukacin nan ya faɗa gaskiya ne naga tarin kauna a idanun shi, yaki gaya min kome akan shi." "A'a camfe ne ba kauna bane, kawai shakuwa ne muyi mishi uzuri nan gaba." Kuka take kamar ba ita ba, *** Niamey. Yana zaune gaban Hajiya Latifah, cikin bakin ciki da takaici take mishi. "Idan nayi maka maganar aure sai ka kauce? Kallon ka zan cigaba da yi ko dafaka zan yi? Toh wallahil baka isa ba, ka tafi gidan Hammad Hamidu Dogo, Akwai Yar autar shi Hanan ka amshi address ɗinta tana London ka tafi niman soyayyarta. Tana degree dinta na biyu kenan, kuma bata da matsala an gama magana da iyayenta nan da shekara daya da rabi zata dawo, amma kaje can din ku gana kafin ka koma bakin aikin ka." Gyada kai yayi sannan ya mike tare da barin d'akin, yana jin kamar zuciyar ta fita ya gaji. Bayan tafiyar Almamoon yan mata biyar kenan, ana hada shi dasu, karshe yana kin su ba tare da sun cewa shine yake lalata kome. Tunda ya shiga shashin ya zauna yana kallon wayar shi. Haka kawai yake jin kamar Almamoon yana cikin matsala da damuwa. Daukar wayar shi yayi ya fara kiran layin shi yana kara amma bai dauka ba. Hankalin shi ya tashi, domin yasan anyi hutu kuma zai tafi gida bai san ko ya tafin ba, dan yace mishi idan zai tafi ya gaya mishi sai su tafi tare. Kiran Dan Ba'are yayi cikin masifar da ya rasa waye zai saukewa sai shi, sai da ya gama masifar shi tas sannan Dan Ba'are ya kashe wayar, ya kira Malik, nan ya sanar mishi ai Mamoon ya tafi gida, shi kuma ya kira Mohan, ya gaya mishi. Zama yayi yana kallon yadda garin yake, murmushi yayi sannan yace. "Insha ALLAH gani nan zuwa." Dan haka tafiyar da aka sashi zuwa London, ya kwashe kwanaki yana shirya tafiya London Damagaram, har da dauke kafa na yan kwanaki, kafin ana gobe zai tafi ya nufi gurin Hajiya Latifah, bayan sun gaisa ya gaya mata zai tafi London amma bai da number Hanan, tana mika mishi wayar ya goge na cikin wayarta sannan ya koma gurin kira yasa ka yarinyar a blacklist, sannan yayi reply din shi da number shi na kasar waje wanda idan ta kira za ace wayar a kashe yake.(tantiri 🤔🙄 aji tsoron Allah) haka ya gama kome sannan ya fita ya barta yana murmushin jin dadi.. Yana fita ya nufi cikin gidan shi tun bai shiga ba, ya fahimci akwai wanda ya shiga cikin gidan, dan haka bai shiga ta kofar da aka shiga ba, ta kofar baya aka shiga. Yana shiga ya nufi dakin shi. Tv ya kuna yana kallon Hajiya Saheya. Tana gama abinda zata yi ta fita, shi kuma ya kira masu kula da gidan suka gyara kome tare da fita dashi, sannan ya tattara kayan shi bayan yayi odar wasu kayan gidan wanda ta zuba abubuwan jikin su yasa aka kwashe ma'aikatan gidan suka raba baki ɗaya. Bai iya kwana a cikin gidan ba, karshe gidan su dan Ba'are yaje ya kwana. --- Hanan Hammad Hamidu Dogo, mahaifiyar ta Hajiya Karime da Hajiya Latifah halin su daya, domin mutane ne masu mugun son nasaba da mulki, Hajiya Karime ita ke bin Hajiya Nuratu Mahaifiyar dan Ba'are, ita kuma take bin Hajiya Lateefah, kasancewar babu wani ratan shekaru a tsakanin su. Mahaifiyar dan Ba'are Nuratu bata da halin su, mace mai hakuri da sanin ya makata, bata da damuwa da abin duniya, kuma abin burgewa har matakin Phd gare ta a ilimin kimiyyar musulunci, wato (Islamic Science) kuma mace ce da take da'awa domin mijinta malamin jami'a ne, itama haka. Idan ka ganta dasu Hajiya Latifah ba zaka ce Abu daya bane, domin sun fita rawan kai, ita ta zab'i karamin rayuwa ne. Duk da mijinta a jami'ar ma shugaban jami'a ne, haka yasa suke babban matsayi. Ibrahim Ibrahim Dan Ba'are, abokin Alhaji Mamman Nasir ne, abokin shine tun ma Yaranta, kuma Alhamdulillahi har yau abokin shine domin duk abinda ya taso mishi me taya shi murnar ko bakin ciki, Dan Ba'are ne. Duk da yaso bashi matsayin minista, amma yaki amsa yace mishi. "A'a duk abinda zaka bani duniya tace sabida Ni amininka ne, amma idan ka ajiye shi muka rike amintar mu babu me magana, kasan me zan iya yin kuskure ba zaka gaya min ba, amma a yanzun babu kome da zai sauya mu sai idan kai ne kaso haka." Wannan haka ya kara musu dankon aminta, kuma har kwanan gobe a gidan Dan Ba'are Alhaji Mamman Nasir yake karyawa da abincin rana, sabida bai aminta da abincin da ake dafawa a cikin gidan shi ba. Wannan shine halin da yake ciki da kuma nasabar da take tsakanin Mohan da Dan Ba'are, sai Hanan HH Dogo. Kwanciya yayi a dogon kujera, ta shiga turo min sako. _Me yasa nake kiran ka bana samun ka? Ina son jin a Damagaram a ina kake ina son ganin ka_ _Almamoon ka dauki kirana, ina son rakiyar ka zuwa London ne! Ka shirya gani nan zuwa_ Can ya kuma kiran layin amma bai shiga ba. Kwanciya yayi sannan ya kuma tura wani sakon. _Kayi min magana idan ka bude wayar lafiya?* Cikin damuwa yake kallon wayar, yau kwana biyar baya samun shi a wayar kuma koda ya shiga baya dauka. *Insha Allah gobe ina hanya* Ya kuma tura sakon, yana jin kamar yabi sakon shima *** Damagaram. Duk abinda na gayawa Innah da wanda Hammah Mohan ya bani ta amsa, amma wayar da ya saya min da ita zan ji muryan shi naki nuna mata, duk da tana min kallon akwai abinda nake boye mata. Ina kwance naji wayar tana nishi, tashi nayi dan na hango ta a waje, tana ta sintiri. Tun ranar da tayi min shegen duka ko fita waje bana yi, dan haka ina kwance na duba wayar, sakon shi da na gani babu adadi yasani mik'ewa. Tare da ɗaukar kayana na saka. Sannan ya fita kofar gida tana kallona, bayan gidan mu na nufa, na kira layin shi duk da dare ne. Dauka yayi yana sauke ajiyar zuciya. "Hammah Mohan don Allah karka zo" "Akan me?" "Nace karka zo" na fada cikin kuka, sannan na kashe wayar na koma cikin gidan, kallona tayi bata min magana ba, nima na wuce d'akina, nayi kwanciya ta. Amma kamar yadda naga rana haka naga dare, domin bani da cikakken nutsuwa, ga bugun zuciyar da nake ji. ... Kallon wayar yayi tare da mik'ewa, bai yi wata wata ba ya gyara kayan shi tsaf, ban daki ya shiga yayi alola. Ya fito ya gabatar da sallah nafilla, tare da addu'a Allah ya bashi sa'a a tafiyar da zai yi. Ya kuma nemi tsari daga mugun ji da mugun gani. Sannan ya koma ya kwanta. ... Gari na wayewa ba fita niman layin shi bata shiga, Tunda na koma cikin gida na zauna tare da fashewa da kuka,bata damu ba kuma bata tambaye ni dalilin kukan ba, ni dai ta zuba min ido da na isheta ta rufe Ni da duka domin Baba da yake karb'ana baya gida, kai Innah ta cika zafi. Ita ke dukana ita ke kuka. Haka wunin ranar nayi shi kwance da zazzaɓin. Karfe bakwai bayan an fito masalaci har da rabi, na fito a hankali domin zazzaɓi yake damuna, kiran layin shi na fara naji tana ringing. Yana dauka na fashe da kuka. "Hammah" "Kayi shiru, gani nan yanzun na idar da sallah..." "Idan zabuwa tana yawo kare na yawo dole a riski juna, Mata maza yau zan ji dadi na da kai" inji Shege. Zaro idanu nayi tare da cire wayar, na kalle shi yana tsaye sai wari yake. A hankali na raba gefen shi zan wuce, ya kai min cafka tare da matsa ni a jikin bango. "Dan gani asarare sai na bari ka kwace min? Yau nake son kaji yadda nake, idan ba haka na maka ba, ba zaka Fahimci yadda nake kaunar ka ba, na ci bayan ka na kuma duba gaban ka naci ramin nan da yake kara maida ka wani na musamman." Kuka ne ya kwace min nayi ta naushinsa ko zai bar ni, amma bai saka ya barni ba, sai ma ciro abin shi da yayi yana gogawa a bayana. Kiran Hammah ne ya shigo na hada karfina da nake da shi na ture shi sannan na fita a lungu da gudu, ya rufa min da gudu har zauren gidan mu. Tare da saka min kafa, ashe Hammah yana hango mu, fita yayi a motar da mugun gudu shima, ya shigo zaune , wayar ta fadi can nima kuma ina kwance a kasar sabida gwiwata da ta Bugu. Yana shigowa ya sauke ajiyar zuciya lokacin da yaga Shago ya kamo ni. "Ina ga tunda uwarka ta haife ka bata tab'a baka matsayi na musamman ba, Yaron da nake ji da shi zaka tab'a." Ya tsaya tare da jingina bayan shi da kofar gidan, sannan ya tako inda Shago yake, sannan ya kalle shi bayan ya ciro gaban shi. Wani irin Mahaukacin naushi yayi mishi a fuska sai da ya zube akan gwiwar shi, ya kuma kai kafar shi ya daki shugaban karamar hukumar wandon shi. Wani irin ihu ya saka tare da zuɓewa yana shure shure, jan kafar shi yayi ya fitar da shi daga zauren, dakyar na mike ina dingishi, ina kallon Yadda Mohan yake dukar Shago. _idan mutum ya tab'a ka hukuncin shi a cire hannun shi, idan kuma kaddarar shi ta saya rungume ka hukuncin shi kisa ce..._ Ban san lokacin da wani karfi yazo min ba, da gudu na rungume bayan shi, kaina a bayan shi. "Ya isa, karka kashe shi? Karka janyo min wata kaddarar da ba zan iya dauka ba, ya tuba" Bai fasa ba sai da nayi karan Shago shege alamar Hammah Mohan ya mishi wani ba, na juya da sauri gaban shi na ture shi. "Nace Ya isa haka? Me kake so dani? Wannan irin rayuwa ce haka? Zaka kashe shi ne?" Na fada da karfi ina kuka. Ji nayi ya riko hannuna, ya saka a kirjin shi. Sai numfashi yake saukewa yana kallona, ji nayi an fisgo ni, tare da kifa min mari, "tassss" gurin ya dauka. Da hanzari ya d'ago kai yana kallon Innah da ta kuma d'aga hannu zata dake ni yace mata. "Kiyi hakuri, Yaro ne bai san kome ba." Ya fada a sanyayye.. "Kai ne ko? Kai ka sauya mishi alkibla? Kar na kuma ganinka a kofar gidan nan ka tafi ko kuma wallahil na dauke shi na nisanta shi da ko ina, kaje bana son ganin ka karka lalata min rayuwar shi." Haka ta ja hannuna har zuwa cikin gidan, yana tsaye bai tafi ko ina ba, Yan uwan Shago shege ne suka zo suka dauke shi bude motar shi yayi ya ciro kudi ya wurga musu, suka bar gurin. "Wato shine ya sauya kama tuni na? Wannan abin na waye?" Ta nuna min wayar da yake yashe a wajen. "Innah don Allah karki." Buge min baƙi tayi, sannan tace min. "Wallahi sai naci mutuncin ku daga kai har shi" Hada kayan tayi tare da fita dashi ta mika mishi kayan shi. "Bana son na kuma ganin kafarka a kofar gidan nan, idan kuma haka ya faru, zan cika kalmata da maganata da abinda zai dame ka. Ka rabu min dashi. Kayi tafiyar ka bana son ganin ka a rayuwar shi, bana son kukan shi." Tana gama fadar haka ta juya tare da komawa cikin gidan .. kuyi comments da Vote Insha Allah yau zaku samu next page da dare....💃 Amma sai na gani a ƙasa #Mai_Dambu [7/29, 8:27 PM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1107324574?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=4ugJdhgGa4BvbsExr19Jvhrf8LWxJfS%2FSxI1B7ZzbxI65y3FAC%2F%2Bp5dONKBm%2FARRS1nZwKrYHg3%2FBE6YQ7n4aR6rGLUDTKvkAvezukOoIJGO6fac4VkMX5uB5%2FHWvZsK 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... Wannan shafin gaisuwar kune Mutanen Wattpad Nagode sosai..❤️💓💞 BABI NA TALATIN. Har malam Umaru yazo ya wuce Mohan yana jikin motar shi kayan yana gaban shi, bai saka yayi fush ba, haka yana tsaye har dare yayi sosai yana tsaye a gurin. ..... Bayan Baba Ya dawo, bata gaya mishi ba, kuma bata nuna mishi wani abu ya faru ba, domin ta gargadi ni da babban murya, ina kallon su suka kwanta,wato suka shiga dakin su, nasan yana kofar gidan bai tafi ba, dan haka na tashi a hankali na fito tare da dauko wani abu na saka a jikin katangar gidan mu, na haura katangar na diro. Sannan na kwasa da gudu, sai gurin shi. Ina zuwa na fada a jikin shi ina kuka. Bude min hannun shi yayi tare da shiga cikin jikin shi. "Hammah kayi hakuri, ka tafi" D'ago kaina yayi tare da kallon yadda nake kuka. Sake maida kaina yayi, yana shafa bayana. "Ina nan har sai Innah ta barni nayi magana da ita." Ya fada tare da dauke kan shi. Kallon shi nayi da gaske yake fa. Dan haka na gyara tsayuwa na a jikin shi. "Hammah" "Hmm! Mamoon" "Hammah" "Na'am My Golden Boy" ya faɗa tare da shafa kaina. Bayan ya riko hannuna, ya nufi kofar gidan mu dani. "Don Allah karka buga musu kofar zata zane ni ne, don Allah karka bari tasan na fito ta katanga, please Hammah Mohan" bai saurare ni ba, ya buga kofar yayi dakyar aka bude. Baba ne ya bude. A hankali ya ciro ni daga bayan shi. "Maza shiga ka kwanta, ina nan har gobe." Ya fada yana tura ni cikin gidan, tsoron Allah da tsoron Innah yasa Ni jin fitsarin tsoro, haka Baba ya kalle shi tare da cewa. "Nagode!" "Baba kar a dake shi don Allah." "Idan aka dake shi zaka karya mu ne kamar yadda kayiwa Wancan Yaron?" Bai ce kome ba, ya tsaya a gurin har suka rufe kofar gidan, zama yayi a kofar gidan bayan ya ciro ƙaramar bindigar shi, ya gyara kunamarta. Ganin yadda ina take niman abin dukana yasa Baba ya sha gabanta. "Ya isa haka! Meye laifin shi, Kinga dukar nan da takurawa, wallahi shi zai lalata miki shi, tunda na dawo kika ki gaya min abinda ya faru nace miki wani abu ya faru ne? Kika ce min a'a, amma a can inda nake zaune aka gaya min Shago ya hadu da wanda ya fi karfinshi inda yabi Almamoon, na nuna miki na sani? Toh bari na gaya miki matukar Shago yana unguwar nan wallahil azim abinda kike boyewa zai fitar miki dashi domin ba dan Allah ya kawo shi ba sunan tattalin ki na shekaru sha takwas zai tashi a banza tsanani baya gyara sai lalatawa ba yau na fara gaya miki ba. Sabida ina son auna girman abinda yake faruwa ne, dan haka karki sake Almamoon ya fahimci dalilin ki na hana shi abinda yake so domin kuwa goben sa zai lalata da hannun shi. Ya ga yadda zakiyi, kai kuma wuce ka bani guri." -- Haka muka kwana zuciyar kowa babu dad'i, Allah Sarki. Hammah Mohan anan kofar gidan ya kwana. Da asuba suka nufi masalaci da Baba, sannan suka yi hira bayan ya fadi abinda ya kawo shi da abinda ya faru a baya, malam yayi godiya sannan yace mishi. "Mun gode, sai dai kawai abar aikin nan idan hankali ya kwanta za a yi miahi kaga mahaifiyar shi hankalinta yake s tashi, sannan ina son Yaron ya koma makaranta sabida kwazon shi don Allah kayi hakuri zan kula da kome, ina son Rayuwar Almamoon ya bunkasa sosai." "Insha Allah Baba nayi mata alkawarin ba zan kuma takura mishi ba, Yaron yayi jinya na, dan haka zan kula dashi sosai kamar kanina, kabawa Innah hakuri ba zan lalata mata Dan ta ba, wannan kudin shi da kayan shi ba zan iya kome dashi ba, ka bashi Don Allah." "A'a yaro" "Baba ka ɗauke ni d'anka ne, idan ba zaka nuna min iya Almamoon ka haifa ba" amsa Malam Umaru yayi yana mishi godiya da saka Albarka, Sannan ya shiga cikin gidan,, ina kwance ya d'aga labulen tare da cewa. "Kaje yana son zai tafi yanzun." A hankali na mike tare da fitowa waje, na same shi yana tsaye dake garin bai gama wayewa ba, a hankali na tsaya a gaban shi. Ina wasa da hannuna. "Zaka dawo school ko? Domin ina son zan tafi wani course na shekara daya da rabi lokacin ka gama karatun ina ga zaka attechmen lokacin." D'ago kai nayi ina kallon shi, kafin na sunkuyar da kaina. "Innah tace ba zan koma ba" d'ago kai na yayi yana share min kwalla, "Zata bari idan bana tare da kai zaka yi karatun ka cikin salama, idan kuma muna tare ba zan iya hakuri ba." Gyada mishi kai nayi ina wasa da hannuna. "Amma me yasa zaka tafi?" "Baka son na tafi ne?" Ya fada yana bude min hannun shi, a hankali na shiga tare da lumshe idanuna, kwallan yana zuba min. "Hammah na" "Mamoona, kayi karatu me kyau zan baka kyauta ranar da ka gama karatu da attechmen." Hannun naji akan lips, da sauri na bude idanun na, sai cikin nashi. Sumbatar goshina yayi, sannan ya cire ni jikin shi bayan ya bar Ni tsaye ina me jin sassanyar lips din shi a goshina, har zuwa lokacin ban bude idanuna ba, domin ina jin shi kamar an kunna min wuta ne a jikina, tashin motar shi yasa ni bude ido ina kallon yadda ya figeta a guje.. Yasan idan ba haka ya gaya mishi ba, Almamoon ba zai yi karatu ba, yayi danasanin koya mishi sabo da shi, yasan yaron tunda ya iya dira ta kantagar gidan babu makawa next abinda zai faru ba zai yi kyau ba, amma bari ya gani ko zai iya hakuri na shekara daya da dari bai saka shi a ido ba kai ma wata daya ma tukun. Amma babu inda zashi yana Nijar kuma yana nan yana kare Kayan shi. *** Anyi gwagwarmayar kamar za'a tashi sama kafin Inna ta amince na koma makaranta bayan ta gama ja min kunne, na dawo makaranta bayan nayi wani irin laushi kamar bani ba.. kawai karatu na saka a gabana. Malam Ansar yana taimaka min sosai, gashi ya tattara duk kulawar shi a kaina, wata na daya da kwana ashirin sai ga Hammah Mohan a makaranta. Sanye da unifoam, murza Idanuna nayi tare da kallon shi, yazo a cikin motar lamborghini aventador. Kasa magana nayi ina kallon shi, bude min motar yayi da sauri na nufi inda ya bude min na shiga, sannan ya dauke ni muka wuce. Yana tuki yana murmushi.. "Hammah Mohan yaushe ka dawo" jan hancina yayi tare da mai maida hankali akan tukin da yake. Wani gida muka nufa a cikin Barrack din gidan ya hadu, gashi da alamar an ware gidan yafi na sauran sojojin kyau, bude min yayi, tare da cewa. "Ina zuwa, ka shiga." A hankali na nufi cikin gidan, tare da bude kofar, babu haske a cikin falon shiga cikin gidan nayi tare da lallubar inda makunin gidan yake, ina kunna wutar wani karamin sauti na wakar. "Happy Birthday to you" yana tashi falon, ga wani abu da ya fashe yana fidda wasu yan kyali, an saka katon baloon na 19, sai wasu cake guda biyu, daya Blue And Pink daya kuma fari ne. Juyawa nayi tare da kallon shi. Yana jingine da kofar. takowa yayi tare da kallona. "Barka da cika shekara goma sha tara." "Taya kasani?" "Takardun ka na makaranta da wasu abubuwan suka gaya min haka." "Hammah Mohan!" Na kira sunan shi. "Ina jin ka Mamoon" "Nagode" A hankali ma'aikata suka shiga fitowa tare da shirya mana falon, haka muka ci abincin tare, muka yi game. Kai na kuma jin farin cikin tun bayan dawowar mu daga Dubai, kaina na kafad'ar shi . "Ina son xan gaya maka wata magana amma ban san ya zaka dauke shi ba, sai dai idan na samu lokaci zan gaya maka" jan hancina yayi yana faɗin. "Anan zaka zauna, ina kai kaa makaranta akwai su Hurayyah zasu kasance da kai. Bana son kana zama a can domin naji an ce min Ansar yana kulawa da kai. Ni ba zan yi faɗa akan ka ba, amma zan nisanta kowani dan isa akan ka." Murmushi nayi domin ina jin dadin yadda yake nuna min kome nawa special ne, haka muka sha hiran mu, da dare ya nuna min d'akina, na kwanta naga ya saya min kome. *** Tunda suka fita yake bibiyar layin Almamoon, amma babu alamar zai dawo, dan haka ya mai da hankalin shi kan abinda yake amma kuma Toh. ..... Zama na a gidan Hammah Mohan ya kuma kara mana shakuwar mu, shi yake kai ni makaranta idan na tashi zai zo daukana, karshen wata da kan shi ya ke kawo ni Damagaram ya sauke ni a wajen gari na shiga cikin gari a wata motar.. Tattalin duniyar nan ya dauka min, tunda nake dashi bai tab'a kawowa min wata manufa ba, bai tab'a min wani abu da zai sani cewa yana niman wani abu a jikina ne, asalima babu wannan tunanin a ranshi. *** Bayan shekara daya Yau muka gama jarabawar mu ta wanda daga shi sai zuwa horon da zanyi na dawo na karasa wata shidan da ya rage ina da shekara ashirin. A hankali na fito ina kallon makarantar, ina fitowa na hango Hammah daga min hannu yayi, na nufe shi da sauri. "Mamoon!" Naji muryan Benazir, Kallonta nayi. "Nagode sosai, ba dan kai ba da an kore ni" Murmushi nayi mata, sannan na mika mata hannu. "Kinga ni kamar kanwa nake jinki dan haka ki daina biyewa yaran nan basu da hankali." Sannan na wuce ta, tare da nufar gurin Hammah Mohan, bude min mota yayi na zauna, sannan na kalle shi. "Kace min congratulations" "Ba zan fada ba" "Toh kuwa zan fita a motar." "Ok" ya faɗa bayan ya shiga. A hankali na maida kai na jikin kujeran, ba yau ba ina son muyi magana da Hammah Mohan, ina son na gaya mishi gaskiyar kaina, ina son nayi rayuwa kamar kowa ina son Yancina. A dame na kalle shi. "Hammah Mohan, ina son muyi magana da kai ban san yadda zaka dauka ba." Kura min ido yayi sannan yace min. "Idan ba zaka iya fada ba toh dole ne?" "Eh dole ne" Tab'e baki yayi na rasa gane yadda zan gaya mishi. "Nifa lafiya ta lau, kuma yadda kake gani na ba haka nake ba." "Dama na ce ina son sanin yadda kake mata maza" "Hammah ka daina mai da zancen wasa mana" "Ok na na mai da shi babba." Baki daya ya ki saurarona, ni kuma ba kome bane yasa nake son gaya mishi halin da nake ciki ba sai fadar da muka yi da Hurayyah, ta kuma sha alwashin sai ta haɗa ni dashi. Toh ina son na gaya mishi amma da kuma abu me muhimmanci akai na. Bayan mun isa gida na wuce dakin nayi abunda zanyi na fito, gabana ne ya fadi lokacin da naga sun zura min ido har da shi. "WALLAHI tallahi Azim, mace ce Almamoon ba namiji bane." Kura min ido yayi tare da niman sanin ba'asi. Ranshi ya kai kololowar baci, domin na kasa magana, jikina yana rawa. "Yallabai shekaranjiya na shiga ban daki na ga audugar jinin, sannan na sami wannan bra din a ban dakin, idona idon Mamoon mace ce kuma idan nayi karya gata nan ka tambaye ta." Kallona yayi tare da niman me zance, "Meye gaskiyar abinda ta faɗa?" "Hammah Mohan!" "Gaskiya zaki gaya min?" Ya daka min tsawa. "Abinda nake son gaya maka." Bai saurarre ni ba, ya fita da wani e sauri, bin bayan shi nayi. Ko kafin na isa ya shiga mota tare da fita a haukace, haka nayi ta bin shi da mugun gudu. Na rasa gane dalilin da yasa yaji haushina. Numfashi na sauke ina kallon motar, domin nasan ba zai tab'a saurarona ba. Ina shiga cikin gidan naga ma'aikatan gidan suna min dariya, naji babu dad'i dan haka na koma daki na zauna ina nazarin su. Sam ban san meye na tsare musu ba, baki daya sun tsane ni sun tsani alaƙar mu, karo na farko da naji bana mubaya'a da boye min jinsina da Innah take koma me zata yi ba zan cigaba da boye kaina ba. ..... Har dare ban ga Hammah ba,asalima kin shigowa yayi sai da yaga alamar nayi barci ya shigo. Haka ma washi gari yayi fucewar shi. Gashi ina son tafiya gida, dole tasa na hakura da abinda nake so na jira shi. Haka kwanaki ya tafi babu shi babu alamar, karshe na tattara na koma gida. Da tarin tambayoyi a bakina. ** Niamey Kallon shi Ɗan Ba'are yayi dariya ce ta cika mishi ciki, amma sanin bai da daraja yanzun zai kafta mishi rashin daraja yasa shi kura mishi ido. Yau kwana goma tunda yazo ya kasa gaya mishi gaskiyar abinda ya kawo shi sai dai ya zauna yayi ta busa shisha. Ya sha kamar ba gobe. "Amma dai ƙasan ina da abun yi ka tarani a gaban ka kamar mai daukar darasi" Ajiye bututun shishar yayi tare da saka hannun shi a tsakanin cibiyiar shi kamar mara gaskiya, ya sunkuyar dai kai. "Mohan bana ciki da Bura Uba, zaka gaya min meye ke damun ka saka Ni a gaba kamar me niman gafara." Shiru yayi yana kallon Dan Ba'are, kafin ya kura mishi idanun shi da suke maiko alamar ruwa ce ta taru a cikin shi tace mishi. "Kasan Yaron nan ya ninke mu ne baibai" Ya faɗa yana jin karin b'acin rai sama da na kullum, kafin yace mishi. "Kamar Ya?" "Kamar yadda ka sani!" Na fada a zafaffe, "Toh Ni ban san kome ba?" "Allah yasa karka san kome dan Ubanka, dan iska Yaron nan dai." Shiru yayi yana kallon shi. Ya ma rasa yadda zai da ranshi. Sai jingina kan shi yayi da jikin kujeran, kan shi yana kallon sama. ** Damagaram. Lokacin da na koma gida zunzurutun tsoron Allah da tsoron Innah kasa tambayar ta kome nayi, sai wani mugun shakkar ta ya kuma kama ni, dan haka na hadiye kome nayi shiru, har yanzun bani da zarran tunkarar Innah, har yau bani da kwarin gwiwar mata magana kai tsaye sai na nime taimakon Baba, shi yasa na ajiye batun bayyana kaina. ..haka nayi ta kome suku suku, na turawa Hammah Mohan sako yafi sau dari bai dawo min da shi ba, na kira shi bai kirani ba, karshe ma kin daukar kiran nawa yayi, na rasa meke min dad'i. ** Yau ma kamar jiya yana son gaya mishi abinda ya faru amma ya saka bude baki. "Wai kai dan iskan ina ne? Meye ya had'aka da Mamoon? Nayi imani da Allah da za a gwada jininka sai an samu ya kai dari uku meye yake damun ka haka." Sake jan bargon yayi tare da lumshe idanun shi, yana kara jin takaici na murkusa shi. Kasancewar likita ya zo har gidan ne yake duba shi, yasa Dan Ba'are rufe shi da masifa, bayan likitan ya gama auna shi, ya rubuta musu magani tare da mishi gargadin. "Yallabai ka kula da kanka jininka yayi mugun hawa,..... #Mai_Dambu https://www.wattpad.com/1107772645?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=It8W%2FoFtRBNmtv626Ht7hoebrG%2FLVlSJZLNfj7SZVFb70I%2BU8R57oeYt0nQfprrru5On2xw2q9Wa9DKvsVlrhYzw3HNW938T6zol7nYvstpRTnu2EztkBZZewXp3wWvE 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA TALATIN DA D'AYA. Dafe goshin sa yayi tare da lumshe manyan idanun shi, ya bude tar akan likitan. "Karka bari iyayena su sani" Ya fada yana me gyara kwanciyar shi a jikina matashin, yana jin kamar ta cire zuciyar shi ya huta. Ya gaji da damuwar Almamoon, allura likita yayi mishi wanda zai sanya shi barci. kuma anyi nasarar haka, domin yayi barci cike da mafarkin Mamoon tana sanye da wasu shegun kaya. Ga kai yake tare da mika mata hannu. Amma sai wani ja mishi rai take tana wani yauki. ** Kallon juna suka yi tare da Amincewa da bukatar su, kafin suka ce. "Idan muka bar shi zai cigaba da kare Ubanshi, idan muka tab'a shi zai iya daukar kasadar tab'a mu, amma idan muka saka Ubanshi ya kashe shi wannan alfarma ne kuma samu. Ranar da kasar mu ta samu yancin kai ranar zamu basu kyauta da ya dace dasu, daga dan har Uban zamu bashi kyautar da zasu iya daukar shi." Sannan ya cigaba da tsara musu kome, cikin nutsuwa da sanin ya kamata, kafin ya mike kamar mutumin kirki, ya bar dakin da suke taron sirrin. ** Yau kwana biyu. "Wallahi Yaron nan mace ce ba namiji ba" inji Mohan. "Kamar Ya?" Ya tambaye shi a rud'e. "Mace ce kamar yadda ka sani, taya hankalina ba zai tashi ba yaron ya gama cutar dani." Kasa magana yayi yana kallon Mohan, "Ban san yadda zan yi ba, amma ina cikin tashin hankali" ya faɗa a sanyayye, "Tashin hankalin Uban me? Malam kana son Yarinyar nan tun tana namiji, dan haka yanzun ya dace ka fidda abinda yake ranka, idan kuma ka b'oye toh wallahi damar da wasu suke nima kenan, ka tafi ka tambaye ta meye yasa ta boye kanta na tsawon lokaci haka? Yaron bai iya karya ba, sai dai idan bai dagamar fada ba, sannan ban ga abinda zaka daurawa kanka yawan jini ba, kana son ta sosai duk wanda yake tare da kai yasan kana son Yarinyar." "A'a ba soyayya bane, kawai shakuwa ce. Na shaku da yaron kuma ina matukar tausayin shi. Ashe mara mutunci bai damu da yadda na damu dashi ba." "Komo meye malam me taurin kai mun san kome, tunda har ka iya hana mu mishi magana yana namiji shine yanzun zaka kawo min gulma me ciwon soyayya kawai." Gyara kwanciyar shi yayi tare da Lumshe idanun shi, yana kara tabbatar da kanshi yanawa Almamoon wani irin mugun SO ne kuma shi kanshi bai san da me yake son Yaron ba, idan yace da zuciyar shi ce toh ba mamaki karya ne amma idan yace da ranshi ne wannan gaskiya ne. Dan haka ya cigaba da sauraron shawarar da Dan Ba'are yake bashi. Murmushi yayi sannan ya mike da karfin shi, ban daki ya shiga yayi wanka sannan ya fito k'ugun shi daure da towel, hannun shi rike da wata karamar towel yana goge kanshi, murmushi ya sake irin gashi ga Mamoon suna cikin farin ciki. Shiryawa yayi cikin jamfa da wando kaftani, sai wata hular dara wacce ya murza akan shi, yau yake jin shi kamar zai tafi zance. Dan haka ya shirya kai yadda yake shiryawa kamar ba shi ba, domin kuwa shi kan shi yasan yayi kyau. Privet jet zai bi domin idan ba shi ba zai isa Damagaram a kan lokaci ba. Kiran Dan Ba'are yayi ya gaya mishi. shi kuma ya kira sojojin da suke Damagaram akan ga Mohan nan zuwa. Yana kashe wayar shi Ammyn na kiran shi. "Ina ka shiga ne yau kwana biyu ina niman ka, toh duk da dai babu damuwa, kaje Hanan tazo kuyi magana da ita." "Toh" Ya fada tare da duba layinta ya ajiye ya a blacklist, koda zata kira shi ba zata sake shi ba. Bai bi takan wata hanan ba, yayi fitar shi, anan Khalil ya bashi sakon da ya samu. "Dama meye shirin ka?" "Kyale su, haka nake bukata ka kula da kanka." "Abbu da?" Khalil ya tambaye shi, "Karka damu zan mishi bayani." "Batun Hanan fa?" Kallon shi yayi na wasu lokuta kafin ya mai da kallon shi bisa titin. "Yarinyar ta cika tsani, sannan siririya ce tana da kyau amma ba Matsalata bane kyanta, ka duba yanayin su da yanayin Almamoon. Koda ban sonta matukar zata zauna dani nasan zan sami yara masu tarbiyya, ban sami soyayyar Uwa ba, sai gashi na samu soyayyar Mace da tausayina, dan haka ba zan iya auren Hanan ba domin daga uwarta har uwar da ta haife ni halin su daya, itama zata iya tashi da mugun halin su, Yarana su tashi a wahale, gwara wanda zan ajiye guri daya duk inda zanje zan dawo na ganta cikin Yayana, zata zame musu gata da jin kai. Ita kuma gata yayi mata yawa ba zata san hakkina da yake kanta ba." Ya fada tare da lumshe idanun shi. "Nima shekara daya da wani abu ne hadu da wata yarinya a Maradi, sai dai har yau ban kuma haduwa da ita ba, gashi Nanna ta matsa min na fidda matar da zan aura, wallahil ina cikin damuwa da soyayyar Yarinyar." Dafa hannun shi yayi tare da cewa. "Insha Allah zaka ganta, zaka same ta." Da wannan ya ajiye Mohan a airport, shi kuma ya koma gida ya cigaba da aikin su. Yana isa jirgin yana tashi da shi sai Damagaram. . Kawai a raina nake son kuka dan haka ina tashi ban tsaya ba, nayi ficewa ta, domin Innah tana barci tun ranar da Hammah ya daki Shago na samu hutu a cikin Unguwar mu, kowa mutuntani yake. A hankali nake tafiya so nake na bar cikin unguwar baki daya, motar sojoji ne ya tsaya a gefen Hanyar. "Dan saurayi? Don Allah kasan gidan su Almamoon" kallon shi nayi yana cikin Hilux, a hankali na sunkuyar da kai tare da jan hancina. Hular kaina na cire bayan na gyara tsayuwa ta, na warware mayafin da yake jikin hular tare da baza gashina har ƙafadana. "Eh nasan dai gidan su Maimunari Isma'il Wodaadabe" na fada tare da rike k'uguna. "Toh ya shigo zance ko ta shigo" "Anya yanzun duniya babu yarda da fatan ba harbe ni za ayi ba." Saukowa yayi tare da takowa gaba na. Sai na ganni yar cakwai, a gaban shi. Bude min kofar yayi na shiga, sannan ya shiga shima. Kallona yake kawai ina gyara mayafin kaina. "Dama nasan da wannan, amma me yasa" murmushi nayi sannan na cigaba da wasa da hannuna. Riko hannun yayi yana faɗin. "Moonah kin min adalci?" Sunkuyar da kai nayi ina gyara zaman mayafina. "Ba haka bane, naso nayi maka bayani amma baka saurare ni ba, ka mai da batuna shirme." "Moonah!" "Na'am Hammah na." "Me kike ji a kaina?" Kallon shi nayi kafin na mai da hankali na, kan yatsuna. "Alkalamin ƙaddara ta zana kaddarar mu tare, sai Yau da nake tare da kai sai nake ga kamar nayi shishigi da son kaina dayawa, na zake dayawa. Sam na manta da akwai irin wannan lokacin, gani nake kamar ni din Yar kaina ce, sai yanzun da gari ya waye na Fahimci wacece ni." Na kai hannu zan bude kofar motar, rike ni yayi yana kallona. "Me yasa kike son kawo wani damuwa kuma?" Juyawa nayi na kalli hannun shi da yake rike da hannuna. Wani irin kallo na mishi wanda yasa shi saurin sake mayafin. Murmushi nayi domin ya burge ni yadda yayi saurin fahimtar yanzun ba da bane. "Ni da kai muna da banbanci fa, Kai dan Shugabanan kasa ne, ni kuma ko dagaci Ubana bai rike ba, dan haka yana da kai ka fahimci wani abu, kawai alaƙar mu a iya abota ne bayan haka bana jin akwai wani abu da za...." "Bana son jin haka!" Ya fada da karfi, "Kin san yadda maganarnki yake kona min rai?" A hankali na bude motar na fito, ina kallon waje, shima fitowa yayi tare da zuba hannun shi cikin aljuhun wando shi. Sai yanzun na kare mishi kallo ya hadu sama da kullum. Dauke kai anyi ina wasa da hannuna. "Me yasa?" "Ban sani ba, amma koma meye ai suna da hujjar bani abinda ya dace, koma meye suna da ikon sauya min ra'ayina." "Amma basu da ikon sauya miki ƙaddaran ki, basu da ikon sauya miki goben ki, ki tsaya a matsayin mace kamar arziki ne" murmushi nayi sannan nace mishi . "Gobe na? Ƙaddara ta? Yau nake dashi gobe bani da kome sai abinda Allah ya bani." Rike hannuna yayi sabida ya lura tafiya zan yi, juyawa nayi tare da zame hannuna cikin nashi. "Ka gane yanzun da baya akwai banbancin, idan da shaidan bai samu galaba akan mu ba, a yanzun da muka san kan mu zai iya samun damar shiga rayuwar mu." "Har ila yau ba ki faɗa min me kike ji a kaina ba" murmushi nayi sannan na juya ina faɗin. "Bana jin kome a raina akanka, asalima sai yanzun na fahimci kai Mutum ne mai matukar gundura da hawa kai" Cafko ni yayi tare da sake dariya, yana mai d'aga ni sama, dariya nake kamar zan zauce. "Tun ba yau ba na gaya miki yadda nake jin ki a rayuwata Me yasa ba zaki gaya min yadda kike jina ba?" Sauke ni yayi yana kallon yadda nake wani jijjiga, tare da mai da kaina kamar mazari na nakasa rayuwa guri daya. "Idan na gaya maka yadda nake jin ka me zaka bani?" Na hada index fingers dina ina buga su. "Kawai zan tafi gidan tv na basu labarin kaunar da nake miki ne" " A wannan shekarun naka?" Na tambaye shi ina wani hararan shi. "Ayya kuma ta nan kika ɓullo min? Me kika fito yi toh" Ya tambaye ni, Tab'e baki nayi ina kallon shi, kafin na yatsina fuska ina faɗin. " Kuka na fito yi, amma da na ganka sai na ji na hakura. Ban cika damuwa da kome bane kaje idan na san me nake ji zan kira ka na gaya maka." Shiru muka yi tare da kallon juna, kafin ya juya tare da shiga motar yana faɗin. "Ubangiji yasa karki gaya min, aikin banza aikin wofi" ya buga motar. Dariya ya bani, san haka ina kallon suka bar unguwar gyara zaman mayafina nayi tare da saka hula, na nufi gida. Lokacin da na shiga cikin gidan, Innah tana kallona ganin na shigo da walwala yasa tace min. "Me ka samu?" "Babu" na wuce dakin. "Mamoon!" Da sauri na fito, "Meke damunka?" "Babu" "Zo ka gaya min?" Cikin tsoro da abinda zan tambaye ta, yasa Ni zare ido. Kirjina yana mugun bugawa kamar zai b'alle, "Me yasa ka damuwa?" Shiru nayi ina kallon ta, kafin ba ce mata. "Innah me yasa?" Shiru nayi, "Me yasa me? Ina jinka ?" "Innah ai ni ba namiji bane? Me yasa na." "Mutumin nan shi yazo da motar sojoji ko?" Ta tambaye ni tana murmushi. Girgiza mata kai nayi jikina yana rawa, "Kin Fara soyayya ko Maimunari? Maimunari gaya min soyayya ko? Da nace ki rabu dashi baki rabu dashi ba? Toh bari na gaya miki ba sonki yake ba jikinki yake bukata, idan ta gama dake ba zai kuma kula ki ba, Yaran masu kudi haka suke." "A'a Innah Mohan ba haka yake ba?" Dukar bakina tayi tare da cewa. "Baki isa ba wallahi" Cikin fushi na mike tare da cewa. "Na isa na gaji..... Wayyo Allah na Nepa suna wahalar da mu fa😭😭 wallahil babu wuta. #Mai_Dambu [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1107772645?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=It8W%2FoFtRBNmtv626Ht7hoebrG%2FLVlSJZLNfj7SZVFb70I%2BU8R57oeYt0nQfprrru5On2xw2q9Wa9DKvsVlrhYzw3HNW938T6zol7nYvstpRTnu2EztkBZZewXp3wWvE 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA TALATIN DA D'AYA. Dafe goshin sa yayi tare da lumshe manyan idanun shi, ya bude tar akan likitan. "Karka bari iyayena su sani" Ya fada yana me gyara kwanciyar shi a jikina matashin, yana jin kamar ta cire zuciyar shi ya huta. Ya gaji da damuwar Almamoon, allura likita yayi mishi wanda zai sanya shi barci. kuma anyi nasarar haka, domin yayi barci cike da mafarkin Mamoon tana sanye da wasu shegun kaya. Ga kai yake tare da mika mata hannu. Amma sai wani ja mishi rai take tana wani yauki. ** Kallon juna suka yi tare da Amincewa da bukatar su, kafin suka ce. "Idan muka bar shi zai cigaba da kare Ubanshi, idan muka tab'a shi zai iya daukar kasadar tab'a mu, amma idan muka saka Ubanshi ya kashe shi wannan alfarma ne kuma samu. Ranar da kasar mu ta samu yancin kai ranar zamu basu kyauta da ya dace dasu, daga dan har Uban zamu bashi kyautar da zasu iya daukar shi." Sannan ya cigaba da tsara musu kome, cikin nutsuwa da sanin ya kamata, kafin ya mike kamar mutumin kirki, ya bar dakin da suke taron sirrin. ** Yau kwana biyu. "Wallahi Yaron nan mace ce ba namiji ba" inji Mohan. "Kamar Ya?" Ya tambaye shi a rud'e. "Mace ce kamar yadda ka sani, taya hankalina ba zai tashi ba yaron ya gama cutar dani." Kasa magana yayi yana kallon Mohan, "Ban san yadda zan yi ba, amma ina cikin tashin hankali" ya faɗa a sanyayye, "Tashin hankalin Uban me? Malam kana son Yarinyar nan tun tana namiji, dan haka yanzun ya dace ka fidda abinda yake ranka, idan kuma ka b'oye toh wallahi damar da wasu suke nima kenan, ka tafi ka tambaye ta meye yasa ta boye kanta na tsawon lokaci haka? Yaron bai iya karya ba, sai dai idan bai dagamar fada ba, sannan ban ga abinda zaka daurawa kanka yawan jini ba, kana son ta sosai duk wanda yake tare da kai yasan kana son Yarinyar." "A'a ba soyayya bane, kawai shakuwa ce. Na shaku da yaron kuma ina matukar tausayin shi. Ashe mara mutunci bai damu da yadda na damu dashi ba." "Komo meye malam me taurin kai mun san kome, tunda har ka iya hana mu mishi magana yana namiji shine yanzun zaka kawo min gulma me ciwon soyayya kawai." Gyara kwanciyar shi yayi tare da Lumshe idanun shi, yana kara tabbatar da kanshi yanawa Almamoon wani irin mugun SO ne kuma shi kanshi bai san da me yake son Yaron ba, idan yace da zuciyar shi ce toh ba mamaki karya ne amma idan yace da ranshi ne wannan gaskiya ne. Dan haka ya cigaba da sauraron shawarar da Dan Ba'are yake bashi. Murmushi yayi sannan ya mike da karfin shi, ban daki ya shiga yayi wanka sannan ya fito k'ugun shi daure da towel, hannun shi rike da wata karamar towel yana goge kanshi, murmushi ya sake irin gashi ga Mamoon suna cikin farin ciki. Shiryawa yayi cikin jamfa da wando kaftani, sai wata hular dara wacce ya murza akan shi, yau yake jin shi kamar zai tafi zance. Dan haka ya shirya kai yadda yake shiryawa kamar ba shi ba, domin kuwa shi kan shi yasan yayi kyau. Privet jet zai bi domin idan ba shi ba zai isa Damagaram a kan lokaci ba. Kiran Dan Ba'are yayi ya gaya mishi. shi kuma ya kira sojojin da suke Damagaram akan ga Mohan nan zuwa. Yana kashe wayar shi Ammyn na kiran shi. "Ina ka shiga ne yau kwana biyu ina niman ka, toh duk da dai babu damuwa, kaje Hanan tazo kuyi magana da ita." "Toh" Ya fada tare da duba layinta ya ajiye ya a blacklist, koda zata kira shi ba zata sake shi ba. Bai bi takan wata hanan ba, yayi fitar shi, anan Khalil ya bashi sakon da ya samu. "Dama meye shirin ka?" "Kyale su, haka nake bukata ka kula da kanka." "Abbu da?" Khalil ya tambaye shi, "Karka damu zan mishi bayani." "Batun Hanan fa?" Kallon shi yayi na wasu lokuta kafin ya mai da kallon shi bisa titin. "Yarinyar ta cika tsani, sannan siririya ce tana da kyau amma ba Matsalata bane kyanta, ka duba yanayin su da yanayin Almamoon. Koda ban sonta matukar zata zauna dani nasan zan sami yara masu tarbiyya, ban sami soyayyar Uwa ba, sai gashi na samu soyayyar Mace da tausayina, dan haka ba zan iya auren Hanan ba domin daga uwarta har uwar da ta haife ni halin su daya, itama zata iya tashi da mugun halin su, Yarana su tashi a wahale, gwara wanda zan ajiye guri daya duk inda zanje zan dawo na ganta cikin Yayana, zata zame musu gata da jin kai. Ita kuma gata yayi mata yawa ba zata san hakkina da yake kanta ba." Ya fada tare da lumshe idanun shi. "Nima shekara daya da wani abu ne hadu da wata yarinya a Maradi, sai dai har yau ban kuma haduwa da ita ba, gashi Nanna ta matsa min na fidda matar da zan aura, wallahil ina cikin damuwa da soyayyar Yarinyar." Dafa hannun shi yayi tare da cewa. "Insha Allah zaka ganta, zaka same ta." Da wannan ya ajiye Mohan a airport, shi kuma ya koma gida ya cigaba da aikin su. Yana isa jirgin yana tashi da shi sai Damagaram. . Kawai a raina nake son kuka dan haka ina tashi ban tsaya ba, nayi ficewa ta, domin Innah tana barci tun ranar da Hammah ya daki Shago na samu hutu a cikin Unguwar mu, kowa mutuntani yake. A hankali nake tafiya so nake na bar cikin unguwar baki daya, motar sojoji ne ya tsaya a gefen Hanyar. "Dan saurayi? Don Allah kasan gidan su Almamoon" kallon shi nayi yana cikin Hilux, a hankali na sunkuyar da kai tare da jan hancina. Hular kaina na cire bayan na gyara tsayuwa ta, na warware mayafin da yake jikin hular tare da baza gashina har ƙafadana. "Eh nasan dai gidan su Maimunari Isma'il Wodaadabe" na fada tare da rike k'uguna. "Toh ya shigo zance ko ta shigo" "Anya yanzun duniya babu yarda da fatan ba harbe ni za ayi ba." Saukowa yayi tare da takowa gaba na. Sai na ganni yar cakwai, a gaban shi. Bude min kofar yayi na shiga, sannan ya shiga shima. Kallona yake kawai ina gyara mayafin kaina. "Dama nasan da wannan, amma me yasa" murmushi nayi sannan na cigaba da wasa da hannuna. Riko hannun yayi yana faɗin. "Moonah kin min adalci?" Sunkuyar da kai nayi ina gyara zaman mayafina. "Ba haka bane, naso nayi maka bayani amma baka saurare ni ba, ka mai da batuna shirme." "Moonah!" "Na'am Hammah na." "Me kike ji a kaina?" Kallon shi nayi kafin na mai da hankali na, kan yatsuna. "Alkalamin ƙaddara ta zana kaddarar mu tare, sai Yau da nake tare da kai sai nake ga kamar nayi shishigi da son kaina dayawa, na zake dayawa. Sam na manta da akwai irin wannan lokacin, gani nake kamar ni din Yar kaina ce, sai yanzun da gari ya waye na Fahimci wacece ni." Na kai hannu zan bude kofar motar, rike ni yayi yana kallona. "Me yasa kike son kawo wani damuwa kuma?" Juyawa nayi na kalli hannun shi da yake rike da hannuna. Wani irin kallo na mishi wanda yasa shi saurin sake mayafin. Murmushi nayi domin ya burge ni yadda yayi saurin fahimtar yanzun ba da bane. "Ni da kai muna da banbanci fa, Kai dan Shugabanan kasa ne, ni kuma ko dagaci Ubana bai rike ba, dan haka yana da kai ka fahimci wani abu, kawai alaƙar mu a iya abota ne bayan haka bana jin akwai wani abu da za...." "Bana son jin haka!" Ya fada da karfi, "Kin san yadda maganarnki yake kona min rai?" A hankali na bude motar na fito, ina kallon waje, shima fitowa yayi tare da zuba hannun shi cikin aljuhun wando shi. Sai yanzun na kare mishi kallo ya hadu sama da kullum. Dauke kai anyi ina wasa da hannuna. "Me yasa?" "Ban sani ba, amma koma meye ai suna da hujjar bani abinda ya dace, koma meye suna da ikon sauya min ra'ayina." "Amma basu da ikon sauya miki ƙaddaran ki, basu da ikon sauya miki goben ki, ki tsaya a matsayin mace kamar arziki ne" murmushi nayi sannan nace mishi . "Gobe na? Ƙaddara ta? Yau nake dashi gobe bani da kome sai abinda Allah ya bani." Rike hannuna yayi sabida ya lura tafiya zan yi, juyawa nayi tare da zame hannuna cikin nashi. "Ka gane yanzun da baya akwai banbancin, idan da shaidan bai samu galaba akan mu ba, a yanzun da muka san kan mu zai iya samun damar shiga rayuwar mu." "Har ila yau ba ki faɗa min me kike ji a kaina ba" murmushi nayi sannan na juya ina faɗin. "Bana jin kome a raina akanka, asalima sai yanzun na fahimci kai Mutum ne mai matukar gundura da hawa kai" Cafko ni yayi tare da sake dariya, yana mai d'aga ni sama, dariya nake kamar zan zauce. "Tun ba yau ba na gaya miki yadda nake jin ki a rayuwata Me yasa ba zaki gaya min yadda kike jina ba?" Sauke ni yayi yana kallon yadda nake wani jijjiga, tare da mai da kaina kamar mazari na nakasa rayuwa guri daya. "Idan na gaya maka yadda nake jin ka me zaka bani?" Na hada index fingers dina ina buga su. "Kawai zan tafi gidan tv na basu labarin kaunar da nake miki ne" " A wannan shekarun naka?" Na tambaye shi ina wani hararan shi. "Ayya kuma ta nan kika ɓullo min? Me kika fito yi toh" Ya tambaye ni, Tab'e baki nayi ina kallon shi, kafin na yatsina fuska ina faɗin. " Kuka na fito yi, amma da na ganka sai na ji na hakura. Ban cika damuwa da kome bane kaje idan na san me nake ji zan kira ka na gaya maka." Shiru muka yi tare da kallon juna, kafin ya juya tare da shiga motar yana faɗin. "Ubangiji yasa karki gaya min, aikin banza aikin wofi" ya buga motar. Dariya ya bani, san haka ina kallon suka bar unguwar gyara zaman mayafina nayi tare da saka hula, na nufi gida. Lokacin da na shiga cikin gidan, Innah tana kallona ganin na shigo da walwala yasa tace min. "Me ka samu?" "Babu" na wuce dakin. "Mamoon!" Da sauri na fito, "Meke damunka?" "Babu" "Zo ka gaya min?" Cikin tsoro da abinda zan tambaye ta, yasa Ni zare ido. Kirjina yana mugun bugawa kamar zai b'alle, "Me yasa ka damuwa?" Shiru nayi ina kallon ta, kafin ba ce mata. "Innah me yasa?" Shiru nayi, "Me yasa me? Ina jinka ?" "Innah ai ni ba namiji bane? Me yasa na." "Mutumin nan shi yazo da motar sojoji ko?" Ta tambaye ni tana murmushi. Girgiza mata kai nayi jikina yana rawa, "Kin Fara soyayya ko Maimunari? Maimunari gaya min soyayya ko? Da nace ki rabu dashi baki rabu dashi ba? Toh bari na gaya miki ba sonki yake ba jikinki yake bukata, idan ta gama dake ba zai kuma kula ki ba, Yaran masu kudi haka suke." "A'a Innah Mohan ba haka yake ba?" Dukar bakina tayi tare da cewa. "Baki isa ba wallahi" Cikin fushi na mike tare da cewa. "Na isa na gaji..... Wayyo Allah na Nepa suna wahalar da mu fa😭😭 wallahil babu wuta. #Mai_Dambu [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1107772644?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=bf4OKGFXFm%2BbTBcRYFtIWwkeTpAjYWx%2Ft%2B8piwgYnGj%2BHz02%2BCq8Olw61eWGNCGWLrWoWOYkU9DLRDRLwKRvQ2vFDZM4QGfJKL8gnNicMhI2rfKBsb98bQg%2Fv%2BXS7kmh 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA TALATIN DA BIYU. "Na gaji wallahi na gaji, ina son na rayu da abokin tarayya, babu amfanin boye ni da kike yi. Don Allah ki barni na rayu kamar sauran Yan matan don Allah kinji na had'aki da Allah dan girman Manzon Allah karki hanani rayuwar da ta dace dani" na fada cikin kuka, ina me rokon ta ina kuka ina. Bata hakuri amma bai saka Innah tausaya min ba, duk da tana dukana amma ban fasa rokonta ba,, sai yau zancen Baba nasiru ya dawo mata. Lokacin da Malam ya ke gaya mata zancen sai yanzun ta kuma kara fahimtar dalilin da yasa Munari take sake kin zama wajen ta,ashe soyayya ya faɗa. _Duk abinda zai sanya shi bayyana kanshi tabbas shi zai sanya shi kuka! rayuwar shi zagaye take da zanen ƙaddara dan haka babu wanda ya isa sauya ƙaddaran wani_ Kura min ido tayi sannan tace min. "Ba zan baki damar ki salwarta da rayuwar wasu sabida naki ba. Soyayyar da zata zame miki masifa? Ko ba soyayyar da zata zame miki Bala'i ba, Munari ina miki kallon mutuniyar kirki ashe idanun ki sun bude har kina yarda namiji ya dauke ki ko ya rungume ki, Munari tunda kika iya haurawa katanga ya sani fahimtar soyayyar da ta saka ki kika iya haurawa katanga, soyayyar da tasaki kika tambaye ni zaki rayu akan jinsin ki ba karamar abu bace ko ya kwanta dake ne? Kike tsoron kar ya gudu ya barki" Dariya nayi domin yanzun kam na fara hango tsagwaron zalinci da son zuciya na fara fahimtar abinda Innah take nufi dani?. "Innah zargina kike dan ina son shi! Abinda na sani na haukace akan shi. Innah ina son Muhammad ina mishi mahaukaciyar so ne. Amma duk da haka ban tab'a kusantar zina ba, Innah wallahil billahi azim ban tab'a zina ba, amma kike tambaya na ko ya kwanta dani? Innah tun ina yar miciciya nake kare kaina, Innah na shiga jami'a na kwana a dakin da maza suke ban yi zina ba sai yau rana tsaka ai wallahi ko wani ne ya gaya miki zan iya bazaki yarda ba, balle balle kuma ke da kika da na dauke ki kamar Uwar da ta haife ni" Da mamaki take kallona, kafin taja wani itacce ta rufe ni da duka. Tana kuka tana dukana, ban yi mamakin dukar ba, amma yadda nake jin zuciyata ko zata kashe ba zan fasa ba. "Ki dake ni, ki zage ni matukar zaki barni a raye toh wallahil ba zan fasa ba, kuma ba zan bar kaina a matsayin namiji ba, Ina son rayuwa dan haka duk abinda Kiyi min matukar zaki bar ni da shi ba zan tab'a zama a ?matsayin namiji ba da bakinki kike kirana karuwa bayan ban tab'a ba, ko ciki nayi na kawo miki bazaki kirani da karuwa ba sai dai ki min Uzuri. Innah kawai rayuwa nace zanyi mike min haka ina kuma da nace zan gudu sai kin kashe ni duk abinda zaki yi kiyi "Ni zaki tozarta kamar yadda Iyayen ki suka tozarni, ni zaki wulakanta kamar yadda iyayenki suka wulakantani, bakar ƙaddara, ai tunda iyayenki suka gudu suka barki babu wanda zai iya zama dake, Shegiya yar iska, ni zaki watsawa kasa a idanu?" "Nasan da iyayena suna raye ba za su bar ni haka ba, kuma da suna nan ba zasu wulantani haka ba, zasu bani abinda nake so ki dake ni idan har dukar zai cire miki bakin cikina Innah ki dake ni, na gaji ina son Yancin." Shigowar Baba yaga yadda take dukana kuma ban fasa fadar abinda yake raina ba, yasa shi amsar itaccen. "Baki da hankali ne? Kan me zaki tirsassa mata? Dole ne?" Ya fada da karfi, tare da tasowa ya d'aga ni. "Baba don Allah ka barni na rayu kamar kowacce mace, wallahil zan kama kaina, don Allah ka Amince min na rayu." "WALLAHI ba a cikin gidan nan ba, sai dai a wani gurin ba zaki zauna min a gida ba, sai dai ki zab'a mu ko shi wanda kike son?" "Innah korata kike?" Na tambaye ta hawaye na zuba min, shiru tayi, ba ita ba hatta Baba sake baki yayi yana kallon ta. "Ina kika ce na fita na bar miki gidan dan kawai nace ina son Mohan? Innah ba zan tab'a tafiya ba, ba zan zama butulu ba. Amma zan baki lokaci idan kika huta zan dawo." Na saka kai na shiga d'akina na hada kayana, har bana ganin gaba na. Wayata na dauka na shiga niman Number Mohan, amma da na tuna kar wata rana yayi min gori yasani kiran Ansar, na tambaye shi yana ina? "Ina diffa!" "Ok gani nan a hanya" kawai so nake na nisanci Innah ne, dan haka na fito da kayana, hijab ne da katin bankina da Mohan ya bani. Ina fita na sami Innah ta kafe idan ban hakura da Mohan ba na bar mata gidan ta, sake kiran shi nayi, tare da tambayar shi a ina Baba Mari take, ya gaya min tana gidan shi na Maradi, dan haka na duba jaka na, na dauki key din gidan da Mohan ya saya min, na nufi Maradi dan na gaji bana son na cigaba da zama da Innah dan zan gaya mata magana.. *** Niamey. Karan cikala a yadda ake gudanar da cin abincin ban da Mohan, domin juya cokalin yake. Har suka gama, Kallon shi tayi kafin tace mishi. "Mohan meye yake damunka?" Murmushi yayi sannan ya mike tare da cewa. "Babu" Ya bar gurin su, tare da kara sauri. "Meye alaƙar ka da Yaron nan? Naji an ce mace ce ko mata maza ce" cak ya tsaya ya kasa motsi, a hankali ya juya tare da kallon ta. "Hmm hmm, kawai karya mutane ne" ya faɗa tare a barin gurin da sauri, "Yallabai Mohan yaki zuwa gurin Hanan, ita yarinyar tana son shi amma shi yaki zuwa ban san me yake nufi ba!" Ta fada a dame. "Babu abinda yake nufi sama da ki bar shi ya zab'i macen da yake so Mohan ba yaro bane, kuma tunda yaki zuwa yana bukatar matar da yake so ne" ya bata amsa yana kallon tv, "Amma ai zab'in shi bai zama dole ba, tunda yarinyar da zai kawo bai zama dole ta cika abinda ake bukata, ina ga kawai a fara shirya kome kafin zuwan ranar da kasa zatayi murnan zagayowar samun yanci" kallon ta yayi tare da cewa. "Toh! Amma ke me yasa baki son ya zabi wacce yake SO?" "A'a kasan bai zama dole ya kawo yar masu kudi ba, ko wata yar manyan nafi zargin yaran talakawa yake niman kawo mana" "Meye banbancin mai kudi da talaka? Gani nayi dukkan mu bayin Allah ne amma sai ki ta nunawa kamar baki yarda da Allah ba." "A'a nifa ba haka nake nufi ba, kawai dai bana son ya dauko mana yar karamar gida ce, kawai kome ayi shi a cikin harkan arziki." "Latifah kenan,gani nayi ba a haifi kowa da dukiya ba a duniya ya samu me yasa kike nuna son kan ki dayawa, me yasa baki tuna gobenki?" Dariya da tayi sosai, kafin ta mike tana faɗin. "Wallahi ina da buri akan Mohan, matar da Mohan zai aura ba karamar mace bace, matar da Mohan zai aura zata kasance mai nasaba wacce duk inda zan shiga da ita ce kyawawan tsaro zan hada shi da ita, wacce duk inda muka shiga za a gane yar babban gida ce kamar Hanan" Abinda ya fahimta matar shi tayi nisa a don duniya, matar shi tana da mugun son kai, dan haka ta mike bai kulata ba ya barta tsaye tana bayanin abinda take son akan Mohan. .... "Munmohan" ya kira sunanta a sanyayye, "Na'am Hammah na" ta amsa a hankali, tare da jan hancinta alamar tana kuka, ko kukan yana son zuwa mata. A rud'e ya shiga tambayar ta. "Babu kome, kawai dai ina hanyar Maradi ne na ma kusan shiga." "A ina zaki sauka?" "Gidan nan na kusa da Makarantar" "A'a zan kira malam ya dauke ki." Ya fada can kuma yace. "A'a ki kirani idan kin isa" Baki daya ya rude, ya rasa gane wanda zai kira ya gayawa ya dauki mishi Moonah, "Moonah! Insha Allah kome dare zan zo gare ki" "Toh ina jiranka" Kashe wayar yayi, tare da niman Dan Ba'are. "Kai zoka kaini Maradi" "Professor Ibrahim Dan Ba'are, idan ban kai ka ba zaka iya tsine min ne? Dan Ubanka a yanzun ne zamu tafi Maradin ko ce maka akayi Ni sallamamme ne. "Kazo idan ba a sallame ka ba ai ni na sallame ka, dalla kazo muje ina jiranka" "Mohan bana ciki da Iskanci, a wannan daren zamu fita?" "Kayi hakuri" karon farko da Mohan ya bashi hakuri tabbas ba karamin abu bane. Cikin sanyin jiki yace mishi. "Ina zuwa Insha Allah" domin tunda ya iya bashi hakuri yasan ba karamin abu bane, dan haka cikin wani irin yanayi, ya shiga had'a kayan shi. Kafin dan Ba'are yazo har ya gama, koda yazo babu wanda yasan baya gidan dan sun fita daga cikin gidan. ** Karfe tara na isa garin Maradi, dan ma mun tsaya a hanya, gidan da yake kusa da makarantar na isa, ina ganin kiran malam Ansar. Da kamar ba zan dauka ba sai na dauka. "Kana ina ne?" "Na shigo Maradi zan tafi gidana da yake kusa da makarantar, kuma Hammah Mohan zai iso an jima" na faɗa a sanyayye, "Ok toh idan dai da wani abu ka min magana." "Allah Sarki nagode sosai, Insha Allah idan da wani abu zan maka magana." "Toh" ya faɗa min. "Da fatan ba wani abu bane ya faru?" "A'a babu kome" kiran Hammah Mohan ne na ga ya shigo min. "Don Allah kashe zan dauki wani kiran."kashe wayar yayi na dauki kiran Hammah Mohan, "Kina ina ne?" "Hammah yanzun na shigo Maradi." "Insha Allah zuwa sha biyu saura zan shigo kinji" "Toh Allah ya kawo ka" na fada tare da tare abin hawa, ya kai ni har kofar gidan, na biya kudin sannan na shiga cikin gidan har yau da jami'an tsaro a kofar gidan. Ina shiga cikin gidan wanka nai tare da salallolin da suke kaina, babban addu'a ta, Allah ya sanyayya min zuciyar Innah, amma ban ji dadin yadda tayi ta min miyagun kalamai ba, ko babu kome Innah ce ta reneni, ita ta min kome, Innah ta min gatar da babu wanda zai min bayan shi. Dan haka na zauna nayi kuka nayi kuka har sai da kai na ya fara sarawa ban san ya akayi ba wani irin jiri ya kwashe ni a sallayar na zube.....kuyi hakuri wallahi na gaji ne.... *Nagode sosai Maman Humairah da kawo min ziyara Allah ya bar zumunci 😍💃💞 Ubangiji ya bawa Humairah lafiya Nagode sosai* #Mai_Dambu.. [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1108262550?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=cavWiGGyBrCAo%2BWqCLglY3Gs%2BgN1rFoDPpKB0zWz6PoxIH7kodf8pwkn%2Bapj%2BNu2jcr3lLRQ1jZyx3x0Y0w3eVNqEUJhy%2FQFfQ%2FqU6I47IboRfk%2Fq6JpeUV04y6Fe%2BIf 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA TALATIN DA UKU. Ban tashi sanin inda kaina yake ba sai a gadon asibiti, a hankali na bude idanuna. Da nake ganin dishi dishi, d'aga hannu nayi kamar zan yi wani abu. Naji ana magana kamar daga can nisa, maganar ma amo take min kamar yadda nake tsammanin amsakuwa na saka. A hankali naji an kuma tsikara min allura, nace. "Wash" daga haka ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai washi gari da safe. Na bude idanuna na hango Baba yana zaune. Kokarin tashi nake, Baba Mari ta mai dani. "Koma ki kwanta yar nan Sannun ai kin auna arziki, tunda gashi kin farka da kanki." Kallonta nake tare da kuma kallon dakin. "Sannun Maimunari, Allah ya baki lafiya yasa Zakkar jiki ne, inji Innarki wai a gaishe ki" inji Baba, na san ya fada ne kawai amma bawai dan Innah ta saka shi bane, dan haka na mike dakyar na nufi ban daki. Da taimkawar Baba Mari nayi wanka da alola. Sannan ta mika min doguwar riga na saka, kafin ta kuma taimaka min na fito waje. Sallah nayi da wanda yake kaina, ina cikin yi Hammah Mohan suka shigo tare da dan Ba'are. Gaida Baba yayi fuskar shi a daure tam, sai harara ta yake. Yaki min magana. Tea ya hada min sannan ya mikawa Baba Mari, ta fara kokarin ganin na sha, ture tea din nayi. Tare da kallon shi, takaici ne ya kuma kama shi. Ya mike tare da zuba hannun shi dukka biyu aljuhun rigar shi. "Me yasa ba zaka min magana ba?" Kura min ido yayi sannan yace min. "Duk abinda zan yi a rayuwa ina niman albarkan iyaye ne me yasa da tace bata son alaƙar mu kika dage?" Ya tambaye ni, tare da zuba min ido, wanda suke cike da b'acin rai. "A'a Hammah Mohan, kai ne nake ganin zan samu nutsuwa da kai kace zaka d'aga min hankali? Sai na wuce diffa, kuma wallahi gurin Malam Ansar zan tafi" na gaya mishi ina kuka. "Sai me? Ki wuce diffa ki tafi duk inda yayi miki. Ina can ina faffutikar rayuwar da zamu yi saboda ke zaki b'allo min wata tashin hankali, Toh ki sani da kinyi kuskuren tafiya diffa da har abada kin rasani kenan, dan haka zaki tashi kibi Baba Damagaram, kuma kika sake ki kayi wani shirme." Mikewa nayi akan Abin sallah, na tako gaban shi ina kallon shi. "Idan ka sani na koma can toh na rantse maka da Allah zaku nime ni ku rasa." Na gaya mishi, Kasa magana yayi sabida yadda na kafe shi da ido, ina ƙoƙarin ganin ya yarda da abinda zan aikata. Kasa magana yayi sannan ya juya tare da cewa. "Nag." "Mohammed ka kyaleta ta zauna a nan Maradi tunda ga Iya Mari, ina ga idan ta zauna a nan hankalinta zai kwanta, itama Innarta hankalin ta zai kwanta. Babu amfanin a maida ita gida dole, tunda ga shi akwai inda zata zauna babu wani abu." "Baba nawa Moonah take da zata bawa mutane zab'i? Ita wacece da zata bawa mutane zab'i?" Ya fada a sanyayye, abinda na lura nice yake Zafaffa min murya amma duk wanda ya fishi yana ƙoƙarin gaya mishi kowacce kalma cikin sanyi da nutsuwa. "Bance dole ka zauna dani ba, duniya tana da fad'i zaka iya tafiya akwai Dubun ka da suke buƙatar rayuwa dani, ka gane" na fada ina ninke kayan da nayi sallah dashi, a yanzun da nake jin haushin kowa, wallahil billahi azim duk wanda ya kuskura ya tab'a Ni zai ji magana me tsada. Fisgo ni yayi tare da fitar dani a dakin yana zuwa gurin motar shi ya wulla ni cikin motar, sannan ya zaga ya shiga cikin motar, ya bata wuta. Muka bar asibitin, kaina yana gefe. Tunda ya saka ni yaga ina kallon waje, kuma ina kuka. Haka yayi ta gudu, bai tsaya ba sai da muka isa doso, anan ya nima min abinci ya bani, bayan ya tafi masalaci. Wayar shi ya dauko tare da kiran Dan Ba'are, gaya mishi zai kai ni gidan su, gurin Umman Dan Ba'are, idan ya barni a Maradi wallahi yasan wancan jakin zai iya daukar nauyin wannan gangancin ba. Ina jin shi yana fadan haka na juya ina kallon shi, dan haka ya maida Baba Damagaram, Iya Mari a maida ita gidan ta. Ina kallon shi ban yi mamaki ba, amma nasan ranshi a b'ace yake dan haka nima na had'e raina ina jin lallai ba zan tab'a yarda ya rena min hankali ba. Bayan mun gama abinda zamu yi , muka wuce Niamey. Mun isa ana sallah magarib, gidan su Dan Ba'are ya wuce dani, ana sallah. Masalaci ya wuce bayan ya kai ni babban falon gidan. Yayi tafiyar shi, basu san na shigo ba, sai bayan da suka idar da sallah, suka fito. Da mamaki suke kallona kanen shi. Amma Ummar shi tasan da zuwa na, komawa cikin dakin kanen shi suka yi tare da gaya mata ga bakuwa. Tana fitowa ta amshi ni hannu bibbiyu. A d'akinta nayi sallah aka kawo min abinci naki ci, kuka ne kawai yazo min, dan haka na cusa kaina a tsakanin cinyoyina, na shiga kuka. Bata hanani ba, sai ma barina da tayi nayi kukan. Kallon tausayi ta mana, domin indai ba wani ikon Allah ba, tayi Imani da Allah yar uwarta ba zata tab'a yarda ayi wannan al'amarin ba. Amma ta yarda da al'amarin Ubangiji shine mai kowa me kome, zai iya shirya kome yadda yaso, ya kuma had'a al'amarin shi babu shawaran kowa. * Kwana na uku da zuwa gidan ya dauke kafar shi babu shi babu alamar shi, kai ko waya bana samun shi, abin ya bani mamaki sosai. Dan haka na sami Umman Dan Ba'are a kitchen tana aiki, na rasa inda zan saka damuwa ta. "Sannun da aiki Umma, dame zan tayaki?" Juyowa tayi tare da murmushi. "Zaki iya fere dankali?" "Eh" ta bani kayan feran, na fara ban jima ba kuwa na fere cikin hannuna. "Kai daga aiki?" "Laa babu kome umma bari na wanke na saka magani." Haka na wanke hannun, ina me dangwala magani, sannan na manna plastic, na dawo zan cigaba da aikin ta hanani, bayan takira Nazirah yarinyar da take mata aiki ta amsa. Shiru ne ya ratsa kitchen ɗin, kafin na yanke shirun da tambayar ta. "Umma ina Hammah Khalil?" Murmushi tayi sannan tace min. "Yana can da Mohan a part din shi" "Dama Hammah Mohan yana nan ne?" "Eh yana nan" shiru nayi dan bana son na fidda damuwa ta, dan haka na shiga taimaka mata da shirya wasu abubuwan. Shigowar Jalilah Kanwar Dan Ba'are yasa ni matsa mata, domin yarinyar bata da mutunci. "Umma me kike dafa mana ne Hanan zata zo" ta faɗa tana kallon inda nake, fuskarta dauke da murmushi. "Waye ya saki kiran Hanan? Wato kin zama munafuka ko? Kin gaya mata Mohan ya kawo yarinyar da yake so ko? Hmm zaki hadu da shi indai Mohan ne" "Umma ina ruwa na? Babu abinda ya shafe ni, kawai tace zata zo ne" marin bakin ta tayi. Tare da kallonta cikin zafin rai. "Karki gaya min maganar banza, yanzun nakira Khalil yayi min kwallon dake munafukar banza, Allah yasa wani abu ya faru sai na baki mamaki." Ta fada tare da nuna mata hanyar ta, tana zuwa bata yi wata wata ba, ta bangaje ni. Sai akan idanun Hammah Mohan shi da Hammah Khalil. Ashe suna jin abinda Umma take faɗa. Ganin su a tare ba karamin firgitatta yayi ba, a tsora ce tayi gefe zata wuce. "Idan na miki wani abu kamar na sayawa Moonah k'iyayyar kuce, amma Insha Allah ba zata kuma zama a cikin gidan nan ba, ai na zata idan na kawo mahaukaci nace ina so a kula dashi ke mai bashi kulawa ce ashe ba haka bane, munafuka ce ke har kina." Kasa magana yayi domin bakar zuciya ce dashi. "Karka yarda ka fitar da ita daga gidan nan kaji ko" juyawa yayi a fusace, shi kuwa Khalil ya bi ta da kafa zai tokare ta. "Kiyi hakuri kinji" "Babu kome" Na gaya mata, haka muka gama aikin sannan na nufi dakin nayi wanka da sallah azhar, ina zaune sai ga su tare da wata kyakyawan Yarinya irinta ba ita daya bane su uku ne, Hanan,Jalilah , Hilal. A tare suka shigo d'akin. Suna kallona, wayata na dauka tare da turawa Hammah sako, sai naga babu amfanin haka tunda akan shine gwara na tsaya na cigaba da fada akan shi. "Jaliy wai ba kin ce min guduwa tayi daga gaban iyayenta ba ta biyo saurayi?" Kallon ta nayi kamar yadda yake kallona. "Eh mana, an ga dan masu kudi an haukace da baki kamar zunubin" inji Hilal. Ban yi musu magana ba, sai ma cigaba da nayi da amfani da wayar hannuna, abu na farko fada ba nawa bane, amma dole na koma gida, duk abinda za ayi zan fi samun damar kwatar kaina. Ban da anan dan haka suka gama cin zarafina ban tanka musu ba. Sai da zasu tafi Hanan tace min. "Karuwai ke bin maza har cikin gidan su, matar da tasan ciwon kanta nima mata miji iyayen ta suke." "Tabbas haka ne, amma macen da ta isa da kanta namiji baya kin ta, walo kyakyawa ce ko mummunan ce, sannan idan mace ta isa mace tayi karya a tallatawa namiji Ita sai dai namiji yayi ta haukar niman ta, dan haka ki tambayi waye Almamoon a gurin Mohan? Idan ya gaya miki ni kuma Moonah zan gaya miki girman furashin kaunar da yake min. Koda zai aure ki, sai dai ya aura kawai amma nice rayuwar shi." Na fada mata ina me shiga ban daki, na rufe bayan na bude pampo na fashe da kuka, ashe suna fita ta kira mahaifiyarta, Hajiya Karime bata dauka ba. Dan haka suka yi ta shirya tsiyar su kafin su had'a da iyayen su. *** Tunda ya bar gidan ran shi yake b'ace, dan haka bai dawo ba sai yamma, ina zaune ya turo min sako. _ki fito ina jiranki_ Allah yasa wayar tana hannuna, na sha kuka har nagodewa Allah, na saka mayafi a saman abayar jikina na fito a hankali, hango shi nayi a sabuwar motar shi. A hankali na isa gurin shi. fitowa yayi tare da bude min motar lokacin su Hanan sun fito suma, sannan ya zaga ya zauna, yaja motar muka fita. "Me yasa ki kuka?" "Ina son zuwa gurin Innata ne?" "Ok Insha Allah gobe zaki tafi, sun fitar da inda zaki yi horon aiki." Kallon shi nayi kafin nace mishi. "A ina suka kai Ni?" "Maradi suka barki amma na dawo dake Niamey hedkwatar kasar Niger." Kallon shi nayi kafin nace mishi. "A ina kenan?" "Babban Kotun kasar nan, zaki yi aikin wata shida ne, sauran zaku koma makarantar kuyi karatun wata shida, sannan a kammala jami'a, sai maganar auren mu" kallon shi nayi kafin na dauke kaina daga gare shi. "Moonah kina fushi da ni ko? Nima ina jin babu dadi, karki kuma barin gida saboda ni, duk abinda Innah zata miki kiyi hakuri zai wuce, kuma kiyi ta addu'a, domin shine makamin mumini, Moonah ina sonki dayawa, amma bana son kiyo abinda zai rabaki da danginki, bana son a goranta miki, ina son ganin ki cikin farin ciki." "Zan baka rayuwata da kome da na mallaka, idan har ka d'aga darajata, zan kare ka na zame maka garkuwa, Hammah Mohan ina jin kamar bazan yi nisan kwana ba, ina ji kamar akwai babban abinda zai saka ni mutuwa lokacina bai yi ba, Hammah idan haka ya faru, don Allah karka manta da Ni, idan wani abu yafi to nawa mara kyau karka guje ni, Amma ina jin tsoron lokacin da zaka juya min baya, ina jin tsoron lokacin da ƙaddara zata shiga tsakanin mu, ina tsoron tafiyar ƙaddara. Ina tsoron b'ankad'o wani shashi na rayuwata da zata zaka kowa ya guje ni. Hammah haka kawai nake ji bani da kyakyawan background haka kawai nake ji akan ka soyayyar ka zan iya zab'an ka na bar tawa rayuwar, Hammah idan nace bana sonka nayi karya, idan nace ina sonka nayi karya Amma kullum zuciyata da kai take bugawa, Hammah wata rana zaka tuna da na gaya maka haka." Na fada tare da fashewa da kuka, d'ago kaina nayi tare da kallon shi. "Kasan me? Da Malam Ansar yake fadar wasu abubuwan dan ina cikin jinsin mata maza na zata kawai iya shine mai wannan yanayin halin, amma da Innata ya bude bani ta fadi cewa Ni bakar ƙaddara ce sai naji duniya ta yi min dabaibayi, Hammah Mohan ina son jan numfashi m, sai na tokare kirjina da matashi, idan ina son kuka sai na ta dukar gefen zuciyata. Hammah tausayin kaina nake ji, ban san kome ba sai soyayyar ka, me yasa soyayyar ka yazo min a bazata? Me yasa soyayyar ka ta zame min kamar guba. Hammah Mohan don Allah ka tsaya a gefen titi ka rungume ni, ina son naji dumin wani a kusa dani ina son dumin uwa ko Uba a kusa dani, kai kuma kamar Dan uwana ne nake jin ka, don Allah just hug me" a hankali ya sauka a gefen titin, ya fito tare da bude kofar da nake ya mikar dani, sannan ya kai hannun shi baki daya ya rungume ni, kaina na saka a kirjin shi ina jan kuka na, kuka nake sosai yana bubbuga bayana. "Insha Allah ba zan tab'a juya miki baya ba, ba zan tab'a rabuwa dake ba, Maimoon ina tare dake har karshen rayuwata, Kece farkon kuma kece karshen har abada ba zan tab'a yarda na juya miki baya ba, Ina rokon Allah ko a gidan Aljanna ce ki zama uwargidana a can a nan ki zama matatta ta har abada. A shirye nake na gabatar dake a baikona da za ayi nan da wata uku insha Allah. Ki zauna dani kinji kiyi hakuri dani ina da kishi da fushi, ina da bakar zuciya, amma ko..." "Ko kuda ne ba zan taba barin ya tab'a ka" "Tab'aki!" Muka kai karshen alkawarin mu tare, dariya na saka bayan na cire kaina a kirjin shi ina kallon fuskar shi. " Me yasa kika saka baki alƙawari na?" Janye jikina nayi ina kallon shi, kafin na zauna a motar ina sauke ajiyar zuciya. Shima shiga motar yayi muka bar gurin, duk inda yasan ana bude ido sai da ya kai ni, mun shiga babban Mall muka yi sayayya, sannan muka fito. Tare muna nufi wani gurin cin abinci, muka zauna aka kawo mana abincin. A tare muka ci muna hira. Muna gamawa ya riko hannuna muka fita, a hankali muke tafiya. "Hammah Mohan" "Na'am!" "Me yasa baka tab'a yunkurin niman yi wani abu dani ba?" Dariya yayi sannan yace min. "Kamar Ya?" Cire hannun shi nayi tare da gyara zama ina kallon shi sannan nace mishi. "Kamar irin soyayyar zama Ni, irin sumbtar nan a baki da tab'a ni". Dariya yayi sannan yace min. "Koda nake rungume ki a da can baya kina sani nishadi ne, kuma kallon namiji nake miki, amma bawai bana sha'awar ki bane fa, a'a ranar da aka miki kwalliya a Dubai dakyar nayi barci, amma kin san me? Ke matar da zan aura ce bana son na kwashe albarkan auren mu a hanya ne, idan na fara sumbatarki kafin mu kai ga aure, na lalata mutuncin ki. Ni ke nake so ba wani abu ba a kan me zan yarda na lalata goben mu, gaskiya ni ko rike hannunki ina yi ne abisa al'adar turawa da muka Ara. Bayan haka ba zan iya sumbatar bakin ki ba, goshinki ma ya isa " Kwalla ne ya cika min idanu ban san lokacin da nace mishi. "A wannan shekarunka kake kokarin kare hakkin Allah..... Kunsan weekend ne shi yasa ban baku da wuri ba... Nagode sosai #Mai_Dambu [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1108559379?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza. BABI NA TALATIN DA HUƊU Murmushi yayi sannan yana me kallon hanya. "Sabon Allah ba a girma yake ko a shekaru ba, abu ne da kowa yanka iya aikatawa idan Allah ya zare mishi imanin shi, duk wanda kika ga bai sabawa Allah ba Toh Allah ya tsare imanin shi ne, dan haka ki daina tunanin zan miki wani abu dan kawai ina son ki. Idan har kina mata masa ban ji wani abu ba." A hankali na jingina kaina a jikin kujeran motar, kwalla yana zuba min, na kalli rayuwata tun daga farko har zuwa yau, akan tsarin Innah yake, ko sau daya ban tab'a bijire mata ba, Toh me yasa ba zata fahimci abinda nake ji ba? Me yasa ba zata gane yadda nake ji ba? A iya sani na ban tab'a sha'awar na kwatantata kwanciya a tare da namiji, sai da ya zama dole lokacin ina mata maza ya sani kwana daki ɗaya da maza, ban tab'a tsayawa sun shirya a gabana ba, ban tab'a yarda mun shiga wanka tare ba, kafin su tashi sallah Asuba na riga su. Bana sallah a tare su, kome ma bana yi a gaban su, amma haka Innah ta jefe ni da kalmar karuwanci. Kofar wani katafaren gida ya tsaya tare da danna horn, da sauri sojojin suka bude gidan, ya tusa kan hancin motar cikin gidan, ashe gidan shi na Maradi wasa ne, a hankali yake jan motar har muka yi ta tsalleke get by get, sannan muka shiga cikin gidan. Kallona yayi sannan yace min. "Wannan gidan shekara biyar kenan da na fara gina shi, da Alamu kece zaki fara bude min shi. A da ban shirya kome ba, amma dawowar mu daga Dubai ya sani kara himma domin kuwa ban sami soyayyar gaskiya bane yanzun kuma na samu soyayyar gaskiya,muna ga gidanki nan da zamu shirya rayuwar mu." Ya fada tare da parking motar shi a wani gefen,. Fita yayi sannan ya bude min motar na fito, ma'aikatan gidan duk suka fito. Tare da gaishe shi sannan suka gaishe ni. Haka muka yi ta ratsa cikin gidan, har zuwa babban falon. Katon hotona ina Almamoon ne a falon sai na shi kusa da nawa. Kallon shi nayi sannan ya ce min. "Tsakiyar nan hoton dan mu ko yar mu na fari zamu saka, gefen can kuma na biyu zamu saka hoton shi a can, amma nafi son idan Allah zai bamu ya bamu Y'a mace, ina son Y'a mace musamman me kama dake" Ya ja hancina, ture hannun shi nayi ina faɗin. "Ni mai kama dakai nake son, idan har na haifa maka."dariya yayi sannan ya nufi kitchen ya samu babu kome amma kuma alamar ana kula da gidan ya nuna, dan gaba da gidan akwai masalaci, kiran sallah aka yi na kalli agogon hannuna. A hankali na mike tare da nufar hanyar kitchen ɗin, ina shiga na same shi ya cire rigar shi ya daura afro, ya mai da hankalinsa kan girki, nad'e hannun nayi a kirjina, ina murmushi. "Hammah Mohan" d'ago kai yayi yana kallona, "Zan yi sallah ashe girki kake?" Na fada ina murmushi. "Nasan Abar kaunar nawa ba iya girki ta iya ba, shi yasa na mai da hankali akan girki mijinki yana son a raya mishi cikin shi." Jingina nayi da bangon ina kallon yadda ya mai da hankali akan aikin. "Sallah" na fada a hankali, "Ok" ajiye aikin yayi tare da kai ni wani dakin ya nuna min, sannan ya dawo ya cigaba da aikin shi, lokacin da na idar da sallah kuka na sha sosai, ina ƙoƙarin tuna ta ina iyayena suke. Ta ina zan gansu? Yaushe zasu zo gare ni tunda Innah ta gaya min gaskiya guduwa suka yi,su kuwa akan me zasu gudu su bar ni bayan ina bukatar su a rayuwata. Karan bude kofar nayi ya sani kallon hanyar da aka bude kofar, shine ya shigo yana goge hannun shi, alamar shima alolan yayi zai gabatar da sallah. Ganin ina kuka bai saka shi ya fasa ba sai da ya gama yayi min magana. "Kukan me kike? Wani abu aka miki ban sani ba?" Goge kwallar nayi sannan na mike akan abin sallah na miki mishi, kafin na koma gefe ina kallon shi, yadda yake cika sallah sai da jikina yayi sanyi, kome nashi akan tsari yake yana idarwa ya mike tare ninke abin sallah muka fita dashi waje. Murmushi yayi min sannan ya kai ni gurin cin abincin har ya gama. "Yau zaki ci abinci me dad'i" kallon shi nayi sannan nayi murmushi kafin na dauki cokali, daukar abincin yayi ya zuba min,. Yana faɗin. "Don Allah kar santi yasa ki cinyewa da kwanon." Kamshi spicys ya sani had'iye yawun, ina da yakinin abincin ya hadu iya haduwa. Haka yayi ta zuba min kome da ya girka,sannan ya dauko cokalin shi, shima ya saka hannu muka fara cin abincin tare, na kasa magana, abincin yayi dadi. Daukar nama naje yi ya rigani dauka,hakura nayi na bar mishi na zata zai ci ne sai kaiwa yayi bakin shi ya d'an hura kad'an sannan ya kai min bakina. A hankali na bude ya saka min. Ba kome ya sa haka ba, sai yadda idan na dibi abincin na kai bakina sai na dafe kirjina, ina jin zafin har gurin. Sai ya kwace cokalin ya shiga bani abincin ina ci, ya hakura da shi sai da yaga zan sha ruwa ya barni haka, daukar cokalin nayi bayan na sha ruwa na shiga bashi, shima yana kallona kawai sai naji a raina duk yadda aka yi. Ya rayu cikin kadaici da rashin soyayya, ya bani tausayi. "Hammah kamar kayi rayuwar kad'aici?" Rike hannuna yayi tare da kallon yadda hannun suke, duba agogon wayar shi yayi sannan ya mike, mai aikin gidan ya shigo tare da tattara inda muka ci abincin. Fita muka yi bamu tsaya ba sai a wani babban shagon saloon. Kawo mishi littafin abubuwan da suke yi aka yi ya fara dubawa, sannan ya nuna musu abinda yake bukata, kafin ya koma gefe. Wani daki na musamman aka kai mu, anan aka fara wanke min kafana bayan an gyara min farcen, sannan aka fara wanke min kaina da mayuka masu sanyin dad'i, haka ake wanke min kan, ana gama min wanke kafar da hannun, aka fara zana min jar lalle, kallon matar yayi sannan yace mata. "Ki huda mata kunne domin babu hujin kunne a tare da ita," "Kai Hammah" na fada ina kallon shi, dage min gira yayi, wayar shi ce tayi kara, a hankali ya dauka sannan ya fita. Koda suka zo hujin kunnen nasan da zafi fir ba hana su, sai da ya shigo d'akin, suka mishi bayani. Yana zuwa ya kura min ido, kafin ya durkusa a gaba, yana kallon zanen da ake min, d'an mik'ewa yayi, ban san taya yayi musu magana ba, amma ya kai bakin shi kamar zai sumbaci ni naji an huda daya kunnen, ihu na saka mishi tare da damke wuyar shi da hannun lalle. Kafin na dawo daga duniyar zafi an huda daya kunnen, kuka na saka mishi. Masu aikin Saloon din sai dariya suke min. "Hammah dariya suke min" juyawa yayi tare da kallonsu. "Akan me kuke mata dariya" "Tayi hakuri" tura baki nayi ya dauko wayar shi, zai dauke ni hoto na ki, ina kallon shi. "Hammah na b'ata maka riga da" "Babu damuwa bari na sauya" Ya wuce wani shashi na cikin shagon, ya sauya sannan ya fito da wanda ya cire. Haka ya zauna yana jirana har aka cire lallen ga gashina da aka gyara, yayi kyau sosai. Fuskana ma suka gyara min, sannan muka fito. Tunda muka fito nake lura da yadda yake zuba idanu a gurin, kafin muka shiga motar, janyo hannun yayi yana kallon shi. "Ina son naga mace da zanen lalle kyau yake min, ki Cigaba da zuwa nan koda ban kawo ki ba, zasu miki kome da kike bukata," "Toh" haka muka bar gurin ina yawan karanta irin wannan abun a cikin Novel ko films ban tab'a kawowa za a wayi gari namiji ya dauke ni domin rage min damuwa ba, wato mun yi yawo sosai bamu koma gidan ba sai dare. Sannan ya sauke ni a cikin gidan, ya taimaka min na kwashe kayan da ya sayo min, muka shiga cikin gidan. Tunda na shiga Jalilah take kallona, Kafin ta dauke kanta gaida Umma nayi, sannan na zauna ina me sunkuyar da kai musamman yadda take min kallon tuhuma. "Ki shiga cikin dakin" A hankali na kwashi kayan na nufi d'akin. "Jalilah kwashe kayan ki kai mata, kai kuma biyo ni d'akina." Ya mike haka ya bi bayanta, har cikin d'akinta. Zama tayi a bakin gadon ya zauna a stool. "Baka da hankali ne? Yarinyar da kake so zaka dauka tun la'asar baka dawo da ita ba Da karfe goma na dare, ko an ce maka so hauka ne? Kar na kuma ji ko na gani, ai ki babu kome ka gaya min zaka fita da ita, idan da wani abu ya same ta fa? Wallahi karka kuma wannan gangancin ko kamanta kana da kane ne masu mugun rawan kai, bana so kar ka yi abinda ka san idan aka maka ba zaka ji dadi ba, kuma kaje Lateefah tana niman ka domin tazo nan ganin Yarinyar." "Toh insha Allah ba zan kuma ba, amma wallahil ban da rike hannunta sai da take kuka tace tana son jin dumin mahaifiyarta na rungume ta, wallahil billahi azim ban tab'a kallonta da mugun nufi ba, don Allah kiyi hakuri ban gaya miki dan na d'aga miki hankali ba, amma ita matar da nake burin ta zama uwar Yarana ce idan na b'ata duniyar mu goben mu ba zata yi kyau ba, shi yasa nake bin kome a tsarin Ubangiji gobe zata koma gida, sati biyu masu zuwa zata dawo ta fara aiki a nan." Ya fada tare da mata sallama. WALLAHI sai yaji duk ya bata tausayi, ya burge ta yadda ya iya fadar abinda ya aikata, Mohan ba yaro bane, amma rashin soyayyar uwa yasa shi tashi a wani irin murɗeɗɗan hali. Sai dai fara soyayyar shi yasa ya sauya fiye da bayan idan da yana Mohan shi ne, zai iya share awa daya bai bata amsa ba, har take ganin kamar bai dace da aikin soja ba. Addu'o'in tayi musu, sannan ta mike tare da fita a d'akin. d'akina da nake ta shigo ta samu ina tattara kayan da Jalilah ta fasa min har da mayunkan da ya saya min, kallo na tayi ta ga ina share kwalla. "Taya aka yi kayan suka watse haka?" Jan hannuna nayi domin ban iya karya ba, kuma ban san yadda zan gaya mata ba, sai nayi shiru. "Jalilah ko?" Gyada mata kai nayi, fita tai can sai muryan ta naji tana kuka, dan Ba'are ya shigo har dakin yana bani hakuri. "Babu kome" na gaya mishi ina tattara kayan. "Naga wasu sun fashe" "Eh ba kome zan gyara su" na dauki kayan na zuba a jaka na. "Ko zan sayo miki wasu ne" kallon kayan nayi domin kayan da Masoyina ya saya min ne, ba zan iya sauya su da wani ba. "A'a kayan da Hammah Mohan ne ya dauka min, dan haka babu wata matsala." Na fada mishi haka, ganin bani da niyyar magana ya sa shi fita daga dakin, yana mamakin wannan yanayin, ko zubar da kayan banyi ba, dan haka yana fita ya kira Mohan bai dauka ba ya tura mishi sako da fatan zai gani. *** Cikin nutsuwa ya shiga cikin gidan, tana zaune a babban falon ta, tana kad'a kafarta. Kallon shi tayi lokacin da ya shigo da sallama. "Waalaikumun Salam" ta amsa tana kallon shi, dama yana ganin yadda take ya fahimci kome,.taji labarin Moonah, zama yayi sannan yace mata. "Ammyn Barka da hutawa" "Yawwa Mohan, Ya Surukar tawa?" Kallonta yayi sannan yace mata. "Tana lafiya" "Dama itace kake so?" Gyada kai yayi sannan yace. "Ammyn itace tayi jinyata kuma." "Yar Uban waye a kasar nan?" Nan ne gaban shi ya fadi, ya rasa abinda yake mishi dad'i. "Waye Ubanta?" Sake dukar da kai yayi. "Ina sonta ne, ban damu da ko yar waye bane, kawai zuciyata tayi na'am da ita, bayan haka ba zan iya jure rashin ta ba, kuma ba zan iya jure tashin hankalin da zata fuskanta ba, zuciyata ta bani ita kuma na amsa hannu bibbiyu." "Mohammed Mamman Nasir! Nace waye Ubanta?" Kallonta yayi sannan ya cigaba da cewa. "Ba yar kowa bace!" "Ba yar kowa bace kake b'ata mata lokaci? Bayan kasan cewar nan da wasu watanin za ayi baikon ku da Hanan?" "Ammyn ni fa bana son hanan, ni matar da bata san darajar arziki da dukiya nake nima, matar da zan bata kudi tace min me zata yi dashi nake nima, matar da zan ce mata gabas tace min toh nake nima, matar da zan ce mata zauna ta zauna ba zan yarda na auri matar da bani da iko da ita ba, ina ji ina gani haka na rasa soyayyar ku shine xan yarda ba fada hannun wata mace? WALLAHI ba zan iya aurenta ba, iya gaskiya na gaya miki" Cike da mamaki take kallon shi, kafin tace mishi. "Yarinyar da ta gudo daga gidan su, sabida namiji zaka ce kana sonta kai ma idan ya gaji da kai guduwa zata yi tabi wani, yarinyar da bata san darajar Iyayen ta ba?" "Eh amma ai duk abinda zata yi domin gobenta yayi ba dan yau ɗinta ba, ita guduwa tayi tabar gaban iyayen ta, idan har na rasata tabbas gawata za a shigo miki da shi, dan haka ki barni da abinda zuciyata take so itace farin cikina, kuma itace hasken idaniyata, don Allah karki tab'a min abinda nake so." "Kai baka san girman darajar ka bane? Ko baka fahimci yadda Allah ya maka ni'imommin rayuwa bane? Ubanta yana da arziki ne?" Ta tambaye shi. "Ko gidan kanshi bai mallaka ba, ni dai a haka nake son abu na" ya faɗa yana kallon ta. Abin mamaki ya kuma bata. Lallai maganar Karime gaskiya ce yarinyar bata bar Mohan haka ba, yaron da mace bata ishe shi kallo ba, shine yanzun yake fada mata itace rayuwar shi. Dama tunda taji ance mata Bororoji ce tasan dole ayi haka mutane masu mugun asirin bala'i, dan haka dole ta mike domin karkato da hankalin D'anta, zata bawa Hajiya Karime damar yadda zasu karkato hankalin shi, ina wannan ai ba zata iya dauka ba. "Baba na, ka rabu da ita kaji ina nan ina shirya maka rayuwa me inganci, wancan yarinyar kuma ba mutuniyar kirki bace domin haka suke yiwa mutane mugun abu. Ka hakura da ita zan nima maka macen da ta dace da kai kuma ban da abinka Baga Hanan ba fara doguwa me kyau ina zaka kai wancan me duhun fatar ka hakura da ita mana. *Nasan kuna kokari wallahi amma ku kara min yawan Vote din kunji dearies idan ba Novel din kudi ba bana hana kaina barcin safe ba, amma gashi ina idar da sallah Asuba na fara typing na gama Pagen 07:16 na cigaba da Next page kunji ku kara min sai muyi tafiyar yadda baku zata ba.... Thank You 😁💞❤️💓😍😘 Nagode* #Mai_Dambu... [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1108770833?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=XvTJ715kPu2X0PivW5mr2ueQhMuyT9VxReszdcWX9iE99sEqXcVLFhnWOGRWovfKLC7i4%2FOUqPMZZ6VWIcVOpGiYhQwcVRmRXaxx6lPfK9GN9UgTFxHmNED7gtVuw37%2F 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA TALATIN DA BIYAR. _Ina mika sakon godiya nagode sosai Allah ya bar Zumunci musamman Team din Hajiya Innah da Hajiya Latifah 😁😛😜🤣_ Murmushi yayi sannan ya mike tare da cewa. "Ba zan iya haihuwar Yara su tashi a wulakance ba, ba zan iya auren macen da bani da ita da ita ba, idan zaki duba alamarina ki duba amma tabbas ba zan iya daukar wannan kasadar ba, Moonah nake so. Kuma itace nake da yakinin zata zame min gata a gurin Yarana gaskiya kenan." "Mohan ni na haife ka fa? Amma kake gaya min baka son zab'ina?" "Ammyn ba haka bane baki daya gidan kin watsar damu, kin tab'a tuno sauran yaran ki? Haba Ammyn sauran duk matan da suke su suka aura me yasa ni ba zaki barni na zab'i abinda nake so ba? Dan tana ba yar kowa ba, ni Ita nake so wallahi" "Mohan ba laifinka bane dama ai Bororoji kowa yasan su da mugun tsafi shi ta maka, dan haka sai na karya da Izinin Ubangiji." Kallonta yayi tare da juyawa ya bar falon domin idan ya cigaba da biyawa Ammyn zuciyar shi zata iya dirowa a kirjin shi. Dan haka ya dauke kai kamar bai ji ba. Tana zaune a falon tana jiran Premie minister. *** A babban falon bakin shi sun hadu baki ɗaya. Chef of Army, Attorney general, Minister of defense, Inspector General of Police, duk sun hadu a falon. "Yallabai ba zai yiwu Mohan ya dawo bakin aikin shi ba, sabida bamu da tabbacin me ya rike shi na tsawon shekara biyu baya nan ba, dan haka ba zamu dawo dai aikin ba gaskiya." Kallon shi tayi cike da mamaki, shekara daya kenan yana bin su akan lallai a dawo da Mohan. Murmushi yayi sannan yace musu. "Zai dawo bakin aikin shi! Matukar ina kan kujerata, tabbas Major Mohan zai dawo idan kun shirya toh idan baku shirya ba, Insha ALLAH nan da wata gudu dai dawo ranar bikin yancin kasa." Ya fada tare da mik'ewa ya barsu a falon. Murmushi suka yi a tare, sannan minister tsaro yace musu. "Shi kenan tunda abinda ya zab'a kenan a barshi yayi yadda yake so" Suka fada tare da mik'ewa suma, suna da yakinin lallai dole a dakatar da Mohan da Ubanshi domin babu adalci akan wannan maganar. Taya zasu yarda su bashi aikin da yana zuwa zai fara musu iyayi kamar wanda aka haifa a cikin soja. Kowannen su da abinda yake tsarawa a ranshi. "Amma nake ga ba wani abu bane dan Mohan ya dawo bakin aikin shi tunda dama ai ba sallamar shi aka yi ba" "Eh haka ne amma yaron ba zamu yarda ya dawo bakin aikin shi bane domin bai da kirki sam bai dan darajar mu ba, shi yasa." "Toh lallai dole mu yi abu daya imma mu dakatar dashi imma mu kore shi." "Bamu da ikon tafiyar da kome sai da Sannun Uban shi." Da haka suka bar gidan, ran su babu dad'i. ** Yana shiga cikin gidan ranshi a b'ace tashi mishi. "Yallabai kaji abinda Mohan yake ciki kuwa?" Wani sabon tashin hankali ya kuma shiga, tare da kallonta zuciyar shi ta gama gajiya da damuwa yace mata. "Me ya same shi?" "Wai soyayya yake da yar matsiyata, nayi mishi magana wai ita yake so ita kuma ya zab'a." Wani irin takaici ne ya kuma kama shi ji yaƙe kamar ya dake ta, ko zai sami sassauci. "Ke da aka tashi miki aure ai ba a miki auren dole ba? Ko an baki ni a dole ne? Babu ruwan ki da rayuwar shi, duk abinda yaga ya dace yayi rayuwar shi ce ita wacce zaki hada ta dashi yaushe zata zauna ta kula da rayuwar shi, dan haka kamar yadda kika gurgunta min rayuwa ba zai yiwu ba ki gurgunta mishi rayuwa, kuma wallahi naji labarin kin yi wani shirme akan yarinyar da yake so zan baki mamaki" Ya wuce tare da barinta a tsaye bakinta bude, dakyar ta ja kafarta ta bar falon ranta yana b'aci, ita zai ciwa mutuncin akan rayuwar dan su? Wallahi sai ta tayi maganin su dukkan su. Dan haka babu wani abinda ya dame ta, haka ya shirya gobe zata kira Karime. ** Washi gari da safe. Ya shigo zai gaishe ta yaji tana waya,abin ya kad'a shi dukda ya fahimci ba halinta bane, amma kuma ta bashi mamaki, dan haka ya gama sauraron ta, kafin ya juya yabar kofarta ya tafi ya shirya bai karya ba, a gidan ya nufi gidan su Dan Ba'are, yana zuwa ya nufi dakin Dan Ba'are yana barci ya dage ya maka mishi duka a cinyar shi, Allah sarki a firgice ya mike, yana sosa gurin. "Dan iska mara mutunci akan soyayyar ka, na shiga gararin rayuwa meye nayi maka da zaka katse min mafarkin da da nake da Benazir" "Yarinya ta na zo dauka dan Ubanka dan iska" a fusace dan Ba'are ya wurga da bargon ya mike, dariya Mohan ya saka mishi tare da nuna mishi wandon shi. "Dan iska rago kawai, da ace kai ne lokacin da Almamoon yaƙe damkata da rungumo ni, tabbas da yanzun ka afka mata, mara mutuncin a mafarki kenan kake barin ruwa ranar da ka sami yar mutane dai an kawo mata dauki, wallhi ka zama me karfin zuciya. Ka daina daura sha'awa sama da soyayyar da kake mata, nasan kana Sonta, amma tsakanin ka da Allah meye ya ja hankalinka akan ta?" Cikin sanyin da damuwa yace mishi. "Wallahi kirjinta da k'ugun ta, shine abinda ya fisge ni." "Kasan me yasa nake son Maimoon? Na farko Addininta! Na biyu haukatar,, na uku gaskiyar ta, kai idan zaka mata wani abu na tambaye ya wallahi zata gaya min, bata iya karya ba. Sannan bata da lokacin kananun magana, ban tab'a ganin suraanta ba, balle har ya d'aga min hankali, amma a baya idan ta rungumo ni, kwana nake ina juyi a gado, domin alamarin da ban mamaki. Dan haka karka so mace domin wani abu bata na jikinta kaso ta domin Allah. Taso min ita zamu tafi." Wucewa ban daki yayi tare da gyara jikin shi, sannan ya fito tare da saka jallabiya, ya nufi cikin gidan, tare da Mohan yana gaya mishi abinda ya faru jiya, ran Mohan ya b'aci sosai. Da sallama suka shigo falon Umma, suka gaishe ta, sannan suka zauna. "Bari na taso ta, ina ga kamar sallah take." Ta fada bayan ta nufi hanyar dakin da Moonah take. Ina karatun Alkur'ani ta shigo min, sai da na kai aya sannan na kalle ta tare da amsa sallamarta. "Ina kwana Umma?" "Lafiya lau, da fatan kin tashi lafiya?" "Alhamdulillahi!" "Masha Allah" Shiru tayi sannan tace min, "Karki kuma aikata irin wannan kuskuren, karki kuma barin gida domin saurayi, ki bar gidan ku akan namiji kuskure ne babba, dan haka ina me baki shawara karki kuma haka, idan baki hadu da me mutunci ba rabaki da martabar ki zai yi, dan haka karki sake irin haka ya kuma faru." Tayi min nasiha sosai, kafin ta fita bayan ta bani umarni na shirya na fito yana jirana a wajen,ta koma d'akinta ta haɗa min shatara na arziki,sannan muka nufi falon. Inda na same shi yana karyawa, zama nayi ina kallon shi, sosai nake tausayin shi. "Ki karya" "A'a na tashi da azumi ne" da sauri ya d'ago kai, ya had'e fuska tare da mik'ewa ya ja min kujeran ya nuna min da idanun shi. Sunkuyar da kai nayi sannan na taso tare da nufar gurin shi, na zauna. A hankali na fara cin abincin shi da ya tura min flet din, ina ci ina kallon shi. "Kin tashi lafiya?" "Alhamdulillahi!" Na bashi amsa, "Meke damunki yanzun?" "Kirjina yake min ciwo" na fada ina diban abincin, "Allah ya baki lafiya" "Amin Ya Allah Nagode sosai" "Dame fa?" Ya d'age min gira, murmushi nayi sannan nace mishi. "Da kome" "Toh sai kin biya" "Toh nawa?" "Duk yadda kika biya" "Toh lallai kuwa zai yi araha kenan" Na fada ina kallon shi, murmushi yayi sannan yace min. "Maza kici babu lokaci ina son na dawo akan lokaci ne." Haka nayi ta cusa abincin har na dan ji na koshi, sannan na mike na gyara gurin, muka yi musu sallama, dake a mota zamu tafi. Haka yayi ta jana da hira. *** Maradi. Haka yayi ta niman Number Mamoon bai same shi so yake yaji da gaske ne mace ce ba namiji ba, toh bai samu layin ba, haka ya tattara ya nufi Damagaram. Bai samu matsala da Inna ba, sai dai kuma. Taki sake jiki dashi kamar baya, dan haka yayi ta damunta ina Almamoon yake. Kasancewar Malam na gida, yasa ta jan bakinta tayi shiru, domin tana fara magana malam zai taso ta a gaba har sai tayi shiru. Haka Malam Ansar ya bar Damagaram. Rai babu dad'i. Bayan tafiyar shi da awa biyar, muka shigo garin Damagaram, kallona Hammah Mohan yayi kafin yace min. "Karki wani shirme don Allah,karki yarda ki yi abinda zai bata mata rai, don Allah ki nutsu ki zuba min ido Insha Allah zan baki mamaki zan shawo kanta cikin sauki." Murmushi nayi domin bana jin zai samu kan Innah a saukakkakiyar harshe, dan haka koda muka isa gidan Baba yana kofar gida. Ina sauka gurin shi naje na zauna, tare da sunkuyar da kaina. "Maimunari kin dawo lafiya?" "Alhamdulillahi, Baba ka yafe min" na fada da raunanniyar murya. Alamar xan iya kuka ko wani lokaci. "Munari baki min kome ba, sharrin shaidan ne da zuciya da bata da kashi, Yaron nan yana sonki sosai,don Allah ki kula da rayuwar shi, samun mutumin da zai damu da kai arziki ne, kin ga tashi ki tafi cikin gidan." Ba dan kome na sai dan kukan da nake sosai. Jan hancina nayi sannan na shiga cikin gidan, ina sallama. Sau daya ta d'ago kanta bata kuma d'ago kai ba, ta cigaba da abinda yake yi. Zuwa nayi bayanta na zauna tare da kwanciya kamar yadda ta kwanta na rungume ta, ina kuka. Kuka nake sosai. Wanda tunda nake a rayuwata ban tab'a yin shi ba, lumshe idanun ta tayi tare da janye jikinta. "Da kin san ke wacece ba zaki tab'a d'aga dokar da na saka miki ba, da kin san wacece ba zaki tab'a kallon da namiji ba. Amma kin makaro ba zan tab'a yarda ki auri wanda nayi imani zaki saka shi kuka, kema kiyi kuka ba. Nayi danasanin biye muku kika tafi Jami'a nayi dana sanin barin ki mu'amala da mutane, kinsan me yasa sabida idan kika dan tushenki zai yi wuya ki amincewa kowa, duniyar tsoro zata baki." "Amma bana kashe maganar nan ba? Ko bana ce kiyo hakuri ba? Ina cewa kika yi tafita tabar gidan yanzun ta dawo kina taso abinda ya wuce shiga Muhammad." Ya nunawa Hammah Mohan hanya, da sauri na shiga cikin dakin na, na dauko taburma yau ce karon farko da ya shigo inda talakawan Baban shi suke rayuwa, kallon yadda nake kaiwa da komowa yayi, har zuwa lokacin ban daina kuka ba. Abun ya dame shi sosai, dan haka yake ta bina da ido, ina kawo mishi ruwa cikin kulawa yace min. "Beauty zauna na gode, ya isa haka kukan nan idan ba so kike na fara kukan ba, ya isa haka." Kallon shi nayi domin ya bani tausayi musamman yadda yake magana a dame kamar zai fasa kuka. Gyada zama nayi ina kallon kasa, Baba yayi min nasiha ba iya Ni ba har Mohan din, sannan ya mike zai tafi ma raka shi, ina kallon shi ya shiga sauko min da kayana, tare da kawo min cikin gida da kanshi ni kuma ina jikin motar shi yace na tsaya. Koda ya shigo zuwa yayi ta zube a gaban Innah, ya gurfanar kamar me niman gafara. "Don Allah kiyi hakuri karki Zafaffa mata, kiyi hakuri karki juya mata baya, tunda ta bar gidan har yau kece a ranta, Innah idan wani yayi mata gori kece zaki fara jin ciwon abin amma ke da kika mata gorin har yau kuka take, Innah da xan iya rabuwa da Maimunari wallahi da na rabu da ita. WALLAHI ba kome nake nima a gurin ta ba, kaunarta da Allah ya daura min ya wadatar dani. Innah kiyi hakuri nasan baki son alaƙar mu amma ni, ina sonta sosai ina sonta kamar na cire zuciyata na bata, Innah wallahi da ki rabani da ita gwara ki zuba min yawan kuɗin da zan biya sadakinta ina son Maimunari ina kaunar Maimunari, ina bala'in kaunarta ina son ta." Kasa magana tayi tana kallon shi yadda yake magana kamar mahaukaci, abin yayi mugun b'ata mata rai dan haka tace. "Ba zan baka ita ba, kaje kayi rayuwarta itama tayi nata. Kuna da banbancin rayuwa dan haka kai dan masu kudi ne ita kuma kaga inda muke dan Allah ka fita a rayuwar ta, indai ba wani abu kake bukata ba." "Kiyi hakuri zan cigaba da baki hakuri amma ba zan tab'a sarewa ba, domin ina son Maimoon ce" yana gama fadar haka ya mike tare da nufar hanyar waje. Ina kallon shi ya fito, yana zuwa bai tsaya wata wata ba ya rike kaina tare da sumbatar goshina.. "Kina raina koda yaushe" daga haka ya koma ya shiga motar shi sauke gilashin motar yayi sannan yace min. "Kiyi hakuri idan sati biyu ya cika zan zo daukar ki." Gyada kai nayi ina share kwalla da yake kwaranya a fuskana, daga haka na dauki sauran kayan na nufi cikin gidan, na samu ana rigima tsakanin Innah da Baba, banyi magana ba sai dai tunda na shiga dakin naki kula su, *** Kallon mijinta tayi cikin kuka, wannan shine karo na sha takwas, zuwan shi rugar Alu. Babu iyayenta babu Sumail Wodaadabe da Kanwar shi. "Mommy kiyi hakuri mana, sai kuka kike idan shi wancan baki ganshi ba, Baga mu ba. Kiyi hakuri mana kullum muka zo sai jininki ya hawa. "Benazir baki da hankali ne? Kin san yadda take ji? Sai na sab'a miki mara jin magana" inji Dr Khalid wanda yanzun yake matsayin ministan lafiya. "Dad gaskiya ba fada mata ai idan da tana son shi ba zata tafi ta barshi ba, dad ban san meye ba but wallhi ba zan tab'a barin Yarona a wani gurin ba ko ku da kuka haife ni ba zan bar muku Baby na ba, haka sai kace babu zuciya a kirjin ki." "Keep quiet! Dauke ni yayi ranar aurena yayi" tayi shiru wani irin kuka ne ya kuma kwace mata, tana kallon yaranta guda biyu da kafin Allah ya bata su sai da tasha mugun wahala. Benazir da Yumnah. "He rape me! Sannan ya kashe min mijina, taya zan dauki wannan gagarumin lamari da wasa? Ya rabani da dangina sannan ya ya tafi dani wata duniya inda yayi ta azabtar da ni idan zai kwanta dani, taya kike tunanin zan yafe mishi. Flashing back. _mu tafi baya ne ko mu hakura a yafe rayuwar baya Cigaba abin mu domin tafiyar zata kuma tsawaita amma amsar yana gare ku, maybe mu karkare a page guda idan muka leka bayan🤣🤫😜_ #Mai_Dambu... [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1109232023?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=voxV4XBY%2FnUwatlpE90PRZr0Cb7P5MxReaPUgkD%2Blwo2EZiniMNkAjlJvmFplzmwPYyD1fajKTXN8iPH845IBz%2FlfSldshawiZ5sqrdtJ6HwqYEtA6fZUVlL3erim6GO 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA TALATIN DA SHIDA. Shekaru ashirin baya. Cikin sauri da karfin hali suka isa Paris, tun a cikin jirgi zazzaɓi mai zafi ya rufe Aabuh. Musamman nonuwarta da suka cika har suna zuba ta rigar ta, tun a jirgin yake bata kulawa har suka isa, babban birnin Faransa. Tunda suka bar airport din, masauki suka nufa tare da taimaka mata tayi wanka. Tun a ban dakin yake bibiyarta da bukatar shi bata kula shi ba, har suka dawo dakin,anan dai zancen ya sauya salo, a ruwan sanyi Khalid ya rike matar shi. Tun tana yawaita damuwa rashin abinda ta bari har ta daina sai dai idan baya nan zata yi ta kuka. A hankali kwanakin suka wuce satika suka kawo kai, kafin ce me har wata ta shigo, sai da suka share wata biyar kafin ta samu sauƙin rashin Yaronta. Wani tausayi tana samun cikin daga ranar da ta bude baki tace tana da ciki zai lalace, sai da ta suka shekara uku cif, kafin ta samu cikin Benazir, boye maganar cikin tayi har sai da ya shiga wata biyar kafin ta iya gayawa mutane cewa ciki ne da ita, dama shi kam Khalid ya san da haka. Bayanta haifi Benazir, ta kuma ɗaukar shekara goma kafin ta haifi Yumnah, daga kanta ne aka ce haihuwa ya tsaya sabida mahaifar tana da matsala. Dai dai gwargwado, Khalid yana da rufin asiri, kuma ga aikin da yake ga kuma wanda aka dauke shi. Wasu asibitotin aikin. alhamdulillah za ace domin rayuwar takai musu, sai dai duk da haka ya tsayawa matar shi tayi karatu me zurfi, a wannan shekarun da suka yi sai da ta had'a degree uku kuma a fannin lafiya, dan shi ya zab'e mata. Wani aikin Cigaba da kasan Faransa tayi wa ƙasashen da suke karkashin tsarin harshen ta yasa Dr Khalid haduwa da Prince Minister, wanda ya ji dadin ganin Dr Khalid, har yake ganin idan da zai kawo shi kasar su za a cigaba ta kiwon lafiya, shine bayan Dr Khalid ya gama abu da yake shi kuma ya saka aka bincika Mishi waye Khalid a can da irin aikin shi, domin ba zai dauki matsayi ya bashi ba, ba tare da ya san status din shi can ba. Wannan abin da yayi ya kuma kara Mishi darajar Khalid a idanun shi domin Dakyar aka bashi Khalid, saboda suma turawan Faransa basu so rabuwa da Khalid ba, Khalid ya fara zuwa ya duba kome, sannan ya gyara gidan shi da yake maradi, kafin ya koma can. Yana dawowa ya fara aikin shi Nijar, watan shi huɗu da dawowa Zauna itama ta dawo bayan ta bar Yaran da Nanny saboda yanayin karatun Benazir, ashekaran zata fara jami'a. Suna dawowa ya nima mata Maryam Abatcha University. Kasancewar jami'ar ta Privat ce bata gwamanti bace. Yasa ya nima mata. Duk da haka bai hana Zainab bin gari gari niman danginta da Na Sama'ila ba, suman jaririnta da bata san meye ta haifa ba, koda suke Faransa idan abin motsa mata har suma take, tayi kwana da kwanaki tana coma,. Shi yasa shima Dr Khalid bai tab'a kawowa zai rabata da soyayyar abinda ta haifa ba, dan ko lokacin da Mahaifiyar shi ta rasu, da suka zo sai da tayi ta bin dazuzzukar da Fulani suke, tana niman Danginta da Sama'ila, har ta isa Mali, babu su babu labarin su. ----- Dawo labari... Yadda take kuka ya d'aga musu hankali, tana kallon Benazir take tura baki. "Mommy da shi abinda kika haifa damu wa kika fi so?" Ta tambayi uwar tana kallon ta, "Shi" Khalid ya bata amsa, dan yasan abinda Zainab zata zab'e kenan, kwantar da kai Zainab tayi yana jin hawaye na zuba mata, Yumnah da tunda aka fara abun bata ce kome ba, Mik'ewa tayi ya zo gurin uwar ta kwanta a jikinta. "Kiyi hakuri Mommy" ta faɗa kanta a kafad'ar uwar, abin tausayi. Haka suka isa Maradi, bayan Zainab ta shiga d'akinta, zama tayi ta kuka, idan ta tuna Laifinta na baya. Tafuyar da tayi ta bar baya da kura yakan sata tsanar kanta da kanta, ji take bata yi deserved zama Uwa ba, domin ta gaza tausayin abinda ta haifa. * Can Niamey ana ta shirya ranar samun yancin kai, duk me ruwa da tsaki yana kan wannan shirin, kowa yana kan shiri musamman Primer Minister, sai bangaren Mohan wanda yake cikin damuwa sosai, amma yasa dan Ba'are ya shirya musu masu shirin. .... Gidan Hammad H Dogo. Murmushi Hajiya Karime tayi sannan ta kalli yar karamar Yarta. Saura wata biyu da wani abu, ayi baikon ku, dan haka zan shiryawa Yaya Latifah, wancan maganin da aka kai mata, ita da kanta zata cinyar da danta maganin da zai rabu da ita, nan da kwanaki ƙalilan zai zo ya haukace ana yana niman ki, dan haka ki nutsu ki." Yadda take shirya makircin ba zaka tab'a kawowa zata aikata ba, amma idan kayi dubi da halin dan Adam sai ka yarda zai iya aikata kome akan wanda ya yarda dashi, ita fa Hajiya Latifah hankalin danta take buƙatar a karkato mata ba wani abu can ba, amma baiwar Allah nan ta gwammace gwara ta rabu su da d'anta. ... Tun bayan da yaji abinda Uwar shi take son aikatawa jikin shi yayi sanyi, dan haka ya tsiro daina cin abincin a dinning table, sai dai a kai mishi part din shi, idan aka kai mishi zai zubda ya dafa na shi, dan haka ya zuba mata ido, koda aka kwana biyu suna zaune take ce mishi "Yaushe zaka je gurin Hanan" "Ammyn yaushe kike son naje?" Ya tambaye ta, wani irin farin ciki ne ya lullube ta, dan ta tabbatar da dan ta ya dawo hanya tace mishi. "Ya batun yarinyar nan da kake son?" Kallon mamaki yayi mata, kafin shima dan renin hankali ya yatsina fuska sannan yace mata. "Wata Yarinya? Hanan dai nake so!" Ya gaya mata, "Toh indai haka ne, toh idan kasamu lokaci kaje can ka duba ta" "Insha Allah, zan fita zuwa gidan Umma Nuratu," tab'e baki tayi sannan tace mishi. "Ka gaishe ta" "Zata ji" *** Lokacin da ya sami Umma Nuratu da abinda Mahaifiyar shi da Hajiya Karime suke mishi jikinta yayi mugun sanyi. "Ka cigaba da addu'a, Insha Allah Ubangiji zai tsaya muku, su kuma Allah ya shirya su, nasan dai wannan ba halin Latifah bace barta da son gogaggayya da manyan mutane, amma wallahi ba halinta bane, kawai ƙaddara ce da son zuciya." "Babu kome." Haka yi mata sallama tare da barin gidan, tunda Dan Ba'are baya gari.. kullum zai yi waya da Moonah, sau uku sau hudu. wani lokacin yaji tana kuka wani lokacin kuma tayi ta mishi hira tana gaya mishi yadda take kewar shi. Tausayin ta yake kara cika zuciyar shi, idan ya nutsu sai yaga shi yana mata wani irin Mahaukacin SO ne, yayinda ita soyayyar da take mishi irin mai sanyin nan ne, yadda take son shi bata iya nuna mishi a gaban shi, amma shi yakan iya nuna mata a gaban kowa, sannan yasan Maimunari bawai ta bar gida bane sabida shi, a'a tabar gida ne sabida tana son zama mace. Wannan abun ya rike shi akan shi kamar hadda. * Tunda Hajiya Latifah ta gayawa Mahaifiyar Hanan kome ya fara kyau, suka shiga jifar Hajiya Lateefah kamar me, sai da suka samu ta dawo karkashin kulawar su, sannan hankalin su ya kwanta, a cikin sati biyu kacal suka gama birkita mata lissafi sai yadda suka yi da ita, Yaranta mata ma basu zaman gidan kasancewar Radiyah tana gidan Khausar da zama ita da gidan su sai hutu domin bakin cikin abinda Ammyn su take ne ya sa ta bar gidan, kuma Allah yasa mijin Khausar bai da matsala, dan kasuwa ne babba. Kuma ma'aikacin gwamnati, Nairah kan tana Faransa gurin Salman da yake shima yana da tashi iyalin kuma ya kama Kanwar shi ya rike duk sun watse mata sai Mohan din dai da ta addabi rayuwar shi. Tsakanin Mohan da kanen shi akwai kyakkyawar fahimta, sannan. Sukan hadu da dandalin sadarwa ta Whatsp anan ya gabatar musu da Moonah, tare da gaya musu halin da ake ciki. Dukkan su, sunyi na'am da ita kuma suka bashi shawaran ya tsaya da kafar shi sai inda karfin shi ya ƙare, sannan itama yarinyar kar ya ce zai juya mata baya, suka yi ta rokon shi musamman Khausar da tace idan Moonah tazo Niamey ya kawo mata ita, anan yake kuma sanar musu da abinda Ammyn su tayi mishi na asirin da take mishi. Sun tausaya mishi sosai, kafin suka yi ta turo mishi addu'o'in, da yadda zai nayi su, dake sun san halin uwar su da son nasaba.dan baka basu yi mamaki ba musanman da suka ji batun Yar Hajiya Karime, take suka nuna basu goyan bayan shi ya aure ta. Nan ya gaya musu nashi shirin da yake akan baikon. Abin yayi mugun burge su, dan haka suka yi alkawarin zuwa dukkan su, dake lokacin an saka akan hutune. Tun safe ya shirya bai gayawa kowa ba, sai Damagaram. ** Kallon shi nayi kafin nayi kasa da kaina. "Maimunari ki gaya min me yasa kika iya boye min wannan lamari? Na zata kin dauke ni a matsayin dan uwane? Sai jiya aka nuna min sakamakon ki an sauya miki suna daga Almamoon Isma'il Wodaadabe, ya koma Maimunari I Umar Wodaadabe, meye nayi miki da na cancanci wofantarwaki?" "Ban san kome ba, duk abinda ka ga ya faru ba san kome ba Hammah Mohan ne yake min kome don Allah ka yi hakuri." Na juya zan bar kofar gidan yayi maza ya riko hannuna, kallon shi nayi kafin na cire hannun nawa. "WALLAHI har yau ina kaunarki, don Allah ki duba girman kaunar da nake miki, ki dawo gare ni. Amma idan kika ce baki sona ba zan miki dole ba." Takowa nayi gaban shi, sannan na kalle shi. "Mohammed Mamman Nasir Aghali, shine muradina. Shi din mafarkina ne, domin ina ji a jikina gobe na yana tare da shi ne, shi son shi nake, kai kuma shakuwa ce me had'e da cutarwa don Allah ka hakura dani, kabarni na zauna da abinda nake so. Idan ka dage zaka sani jin tsanarka har karshen rayuwata. Mohan nake SO! Akan shi nasan meye SO! Akan shi nasan dadin SO. Kai kuma a malamina na dauke kuma abokin shawara na, idan ta kama." Daga nesa yake kallon yadda take magana, ranshi yayi mugun ɓaci, har yau parking idanun sa na kansu. Bai yi yunkurin juyawa ba, amma ya fito daga motar ya tsaya yana kallon su. "Ki yarda dani ba zan tab'a zarginki ba, ina mugun sonki da ba zan iya juya miki baya ba, amma idan kika ce min na hakura wallhi zan hakura." Kallon shi nayi domin ya bani tausayi kawai nace mishi. "Ka hakura" sannan na juya zan koma cikin gidan dan nasa Mohan yana hanya, hango shi nayi yana ta latsa wayar shi, gabana ne ya fadi, dan haka na nufe shi, had'iye yawun tsoro nayi. "Barka da zuwa ya hanya?" "Hmm" yace min yana kallon agogon hannun shi. "Ina jiranki" Ya fada min, haka na shiga cikin gidan, na samu Innah na gaya mata zan tafi. "Mohammed yazo ko? Ban isa ya shigo ya gaishe ni bane?" "A'a zai shigo mana" na fada da sauri,idan na gaya muku ina cikin gidan nan ne amma sam bana jin dadin zaman shi, wallahi Innah ta azabtar dani ta hanyar da ban zata ba, amma da nayi hakuri gashi zan tafi samun horona. Mikewa nayi zan fita tace min. "A'a Saurayi yafi iyayen riko, dan haka zaki iya tafiya a dai tuna da akwai Allah kar a sake da namiji dan ya iya samun damar shiga jikin mace, ba iya nan ba sau daya ake hada shimfid'a da wasu. Magana ya ƙare, daga nan dai yawun da amai" Murmushi nayi mata sannan nace mata. "Da zanyi wannan yanayin da tuni nayi tun ina amsar sunan mata maza, amma kuma nagode Ubangiji ya baki ladar rikeni da kika yi, ai kin min gata, kin gama min kome. Tunda kika iya rike ni na tsawon shekaru ashirin haka." Na mike tare da nufar dakina na kwashi duk wani abuna me muhimmanci, ko haya na kama a Maradi na dauko Baba Mari ta zauna dani, amma ba zan kuma dawowa gurin Innah. Har zan fita na kuma dawowa dakin ta. "Innah don Allah me yasa iyayena suka tafi suka Barni?" Wani shegen dariya ta saka tare da nuna ni da yatsa tace min. "Idan kika sani haƙa rami zaki yi ko binne kanki,. Idan kika san abin da ya faru. Wuka zaki saka ki datse wuyarki ko jijjiyar hannunki, ga wannan wukar ki ajiye sabida amfanin gaba, ko ki kashe iyayenki ko, ko kashe kanki" "Wannan wani irin abu ne? Meye tayi miki da zafi? Idan Ni ne baki so zan barta amma da na fahimci itace baki son ta amsa sunanta na mace ya sani jin dud duniya bani da matar da nake so bayan ita. Insha Allah nan da wata biyu daga fadar shugaban kasa zai zo shi da kanshi ya nima min aurenta idan yaso kiyi duk abinda yayi miki." Ya durkusa tare da d'ago ni, ina kallon Innah kamar gumki, kaina ne ya sara, na fara jin jiri, yana rungume dani, haka ya fitar dani bayan ya saka Ni a motar shi ya koma ya kwaso min kayana. Sannan ya shiga cikin gidan ya ce mata. "Insha Allah, sai ta zame miki inuwar gajimare, sai ta zame miki Alkhairi a rayuwar ki, Innah kina raye zaki ganni da Maimunari, Ban san wani irin son zuciya yake dawainiya dake ba, amma tabbas zaki gani abinda kika mata sai kin gani akwaryan cin tuwonki" Daga haka ya fita bai kuma bin kanta ba. "An fada sai ta kashe kanta, kuma sai me duk ihun da kake iyayen ka bazasu Barka ka auri Yar da aka haifa da auren wani ba, Shegiya ce ho Shegiya ce bata hanyar aure aka same ta ba, wannan tambarin shi zai kashe ta ko kashe iyayen ta. Munafuki" haka tai ta faɗa tana fadar abubuwan da ya faru. *** Tunda ya kwantar dani, nake dunkule a jikin kujeran. "Hammah ta gaya maka wacece Ni?" Banza yayi da ita domin yau baki daya an b'ata mishi rai, sai da suka yi kamar zasu dambatu da Ansar ya tafi, sannan ya shiga cikin gidan ya kuma samun na Innah tana buga nata isar, bai san meye Moonah tagayawa Ansar ba, amma kuma abinda Ansar ya gaya mishi yayi mishi ciwo. _Kai a tunanin ka ta zan rabu da Munnah ce? A'a na barta ta huta ne a da sabida ba zan mata dole bane, a yanzun kuwa! WALLAHI idan ina numfashi toh sai na haddasa gaba me zafi a tsakanin ku. Idan ina numfashi kana ji kana gani zata haramta maka kayi fatan na mutu domin shine rufin asirin ka kamar yadda ka rabani da ita sai na rabaka da ita ka zuba ido ka yi kallo akan idanun zan yi kome By now let US started the Game idan nayi nasara zan dauke ta nayi tafiya da ita! Amma kasani idan kayi nasara zan so ka saka bindiga ka harbe ni,. Mohammed Mamman Nasir Aghali idan ka cika cikakken Buzu Bugaje me nasara da Zarra ka amince da game din mu! Kuma zan baka damar choice din shaidu. Ni na zabi abokina Mutallab! Kai kuma ina jiranka idan ka cika da namiji ba lusari ba muyi tsayayya magana ayi wasan rai da mutuwa akan Munnah idan ka gama shawara ga katina zan biyo ka har Niamey mu kulla yarjejeniyar idan muka ba isa namiji ba zaka share. Gani ga kai Ga Munnah Allah ya bamu sa'a sai naji kiranka_ 🙄 Kunji watsassse munahiki meye nufin ka? Shashancin kawai! Amma da gaske game din zai badda citta wallahi🤣🤫 ina team din wanda yayi nasara... Bana team din loser 💃 all the best Ansar Yusuf Abzin. Duk wannan Chakwakiyyar a free book 🙄😠😩 ina laifin da Book ɗin kudi ne 😭 Alqur'an kamar yadda kuka karanta book din nan haka zaku karanta Na kuɗi na kuma ku saya ko na kafta muku rahin daraja 🙆🏾‍♂️😩 #Mai_Dambu [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1109328405?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=f4DtUHMnMYkq7YQxK69EHXzYx4qdYjE9KB3IVp12Bnb%2BzEoaanjkzsPH8vAt9jgM2j%2Blswb6qNSSL7B8%2FPrpejrjetMFg5iT6eRxuTuhL2RSdvHxFf9zphNfPityAhJD 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... _Allah Nagode maka!🙆🏾‍♂️ Tunda Jannart ta da Malik suka mutu na shiga hannun mutane 😭 nace muku zan kashe wani ne?😩_ BABI NA TALATIN DA BAKWAI. Idan na fahimci Innalillahi tana nufin, keb'ewa da nake da Hammah Mohan ba haka kawai bane ina barshi yana wani abu dani? Hmm tashi nayi tare da kallon shi. "Tsaya a can zan sayi abu!" Na gaya mishi. Tsayawa yayi bakin hanya daidai kofar wani shagon sayar da maganin, sauka nayi tare da ɗaukar kudi a jakata, ban san nawa bane kawai ina zuwa shagon nace mishi. "Bani maganin mura" na ajiye mishi kudin, yana gani ya shiga dibo min su, ya tara min, sunan su nake bi, zuba min yayi a laida. Sannan na dauki daya na bude take na shanye a gurin, na ajiye mishi kwalbar, na dauki sauran zuwa motar, tunda na shiga na zauna na juya mishi baya, haka nayi ya shan maganin nan bai tashi sanin abinda nake aikatawa ba sai da na kwalbe Kwalba uku, da na farko biyar yaji karan zuɓewar kwalabe a kasa, wani taka birki yayi tare da birkito ni. Ganin saura Kwalba biyu ina bude ɗaya yayi maza ya gangara bakin hanya, ya kalle ni. Ranshi yayi mugun b'aci, kifa kai nayi sabida maganin ya fara tasiri a jikina. "Ka gaya min me yasa duniyar take shirin juya min? Innah tace kana samun damar kwanciya dani zaka gudu kabarni, Ansar Yace min kana kwanciya dani zaka gudu kabarni me yasa tunanin su yayi daya ne?" Jan numfashi nayi, sannan ba cire hijab dina nace mishi. "Ka tab'a ganin mace a tube? Toh yau zaka ganin ni full naked." Na shiga cire kayana ina faɗin. "Kawai zan baka kaina a wuce gurin, idan nayi haka zamu fi samun nutsuwa daga ni har su." Raba rigar jikina nayi gida biyu, kafin na juya na kalle shi. Kwantar da kujeran nayi baya, kafin na shiga ƙoƙarin cire zanin jikina. Komawa nayi na kwanta, sabida na kasa cire zanin sai na shiga ƙoƙarin cire bra din, anan idanun shi ya sauka akan dukiyar fulanina. Da na fitar da dayan shi. Dayan yana cikin rigar shi. Tausayin ta ya kuma ninka sama da baya, cire rigar shi yayi ya lullube ta, sannan ya motso da fuskar shi, yana kallon yadda take mutsu mutsu da bakinta, kunnen shi ya kai yaji tana faɗin. "Ba zan tab'a kashe iyayena ba, Innah amma zan iya sadaukar da rayuwata domin shafe tarihina, ina son Hammah Mohan!" Gyara mata kwanciya yayi, sannan ya tadda motar tare da barin gurin da gudu, ina son ya isa Niamey akan lokaci. * Damagaram. Shigowa malam yayi ya same Innah tana fadar abubuwan da suka faru, akan rayuwar Moonah, kasakai yayi da bakin shi yana kallonta. "Me ya faru?" Ya tambaye ta, "Waye ban da wadannan lalatattun, yazo ya dauke ta har yana gaya min maganar banza ashe na cancanci wofantarwa Maimuna?" Ta fashe da kuka tana kallon shi. "Baki cancanci haka ba, amma kuma daga ke har Sama'ila kun so kanku dayawa, ai dama na gaya muku dole gaskiya zata bayyana kanta. Ai ba yau aka fara ba. Ai ba yau Sama'ila ya fara ba, ba kuma sabon abu bane. Dan haka ki ha bakin ki kiyi shiru, kiyi addu'a kawai Allah ya takaita hakkin iyaye akan ku. Kin zata yaran da ya raba da iyayen su, hakkin su zai tafi a banza ne? Ba zai tafi ba. Shima gudun tafiyar Ƙaddara yasa shi bai tab'a tunanin aure ba, da ya kuskura yayi auren da yaji yadda ake yinta na gaji da halin ki Allah ya gani, yar dan Uwanki? Zaki wulakanta ta, kamar ba jinin ki. Ai ko da Sama'ila yace ki rike ta karta tab'a bayyana kanta sai ya dawo ce miki akayi zaku yiwa Allah yawo? Ai baba Nasiru yayi gaskiya, dalilin soyayya ta bayyana kanta, yau dalilin SOYAYYA yarinya karama tana kuka. Ki barta ta rayu da abinda take so abu ya ci tura, toh Ni dake muzuba mu gani Allah yabawa mai rabo Sa'a." Daga haka ya juya ya bar gidan ranshi yana soya, sabida zunzurutun bakincikin, ita kanta sai da tayi al'ajabi da abinda malam yayi mata, kasa zama tayi ta kasa tsayuwa. *** Karfe shida na yamma ya shiga babban asibitin Niamey, wayar shi ya dauka ya kira Khausar. "Kina cikin asibitin ne?" "Eh Hammah ina ciki" da sauri ya fito tare da bude motar ya dauke ta, bayan ya rufe motar da kafar shi, ya shiga asibitin da mugun sauri, yana kallonta da yanzun bata da bambancin da gawa, yana shiga suna karo da Khausar. "Ku kawo gado" ya faɗa da karfi, da sauri aka kawo ya daurata, aka Wuce da ita dakin gaggawa. Fitowa tayi da sauri tana niman wasu likitocin, aka nufi dakin da Moonah take, aka shiga ƙoƙarin ceto rayuwar ta, abin tausayi. Yana zaune yayi zugun. Har kusan awa daya kafin Khausar ta fito, ta zauna akan bencin da yake kai, ta daura kan shi a kafad'ar shi. "Alhamdulillahi, Hammah mun yi nasarar ceto rayuwar ta, sai dai karta kuma aikata haka." "Yarinyar tana cikin damuwa ne, kuma ni ne me laifin domin naga ta fita, amma kuma ban san me taje yi ba, ashe maganin mura tayi ta sha." "Ba laifinka bane! Yanayin kaddara ce, mun yi mata alluran da zai lalata tasirin maganin." "Nagode kanwata karki bari sauran su sani don Allah" "Haba ai ciwon ya mace na ya mace ce, dan haka babu wani abinda zai faru, Insha Allah"ta faɗa tare da gyara zama. Suna zaune aka fito da ita bayan an canza mata kaya. Suka kaita wani daki na daban. Zama yayi a jikinta tun karfe shida, Khausar ce ta kira kanin mijinta ya kawo mishi kome, bayan ta gama aiki ta nufi gida wajen karfe tara, ta kawo musu abincin. Lokacin yana addu'o'in. Bayan ya idar da sallah da ake bin shi. Jin ana turo kofar yasa shi juyawa. Murmushi suka sakarwa juna, tare da kallon inda Moonah take. "Hammah Sannun ya jikinta?" Shafa kan shi yayi yana shafa addu'a, yace mata. "Da sauki." Ajiye basket din tayi tare da kallon shi, kafin ta durkusa ta fara zuba mishi. "Karki zuba dayawa, bana son cin abin dan dai naki ne" Ajiye mishi tayi ya kalla kadan sannan ya dauka yana ci yana kallon Moonah. "Hammah kana Sonta da yawa, tun ranar da ka gaya mana da Hammah take kiranka ya sani sauya maka daga Yaya zuwa Hammah, haka kawai nake ganin kun dace da juna" Kallonta yayi sannan yayi murmushi, yana kallon Beauty ɗin shi. Idan ya tuna abinda ya faru kuma sai yaji ranshi ya b'aci sosai, dakyar ya cinye abincin yana ji kamar yayi ta fasa ihu. Domin jin kishinta yaƙe, musamman idan ya tuna yadda ya gansu a yau din nan kamar zasu shigewa juna, ajiye flet din yayi yana jin daci a ranshi. Hiran da Khausar ke mishi ma kamar dole ce, karshe da taga baya son magana, tashi tayi ta mishi sai da safe, har gurin motar ta ya rakata, sannan ya koma cikin asibitin, tunda ya koma yayi alola, duba jakarta yayi ya hango karamin Alqur'ani, ya fara karatu kasa kasa, har kusan karfe biyu na dare, kafin ya ajiye ya kifa kanshi gefen inda hannunta yake. Karfe uku saura ya farka sabida ya saba sallah a lokacin, dan haka ban daki ya nufa yayi alola, ya fito. Ya shiga kaiwa Allah kukan shi dan yayi Imani dashi babu me musu maganin taurarrun iyayen su, sai Allah Sarkin sakarakuna. Yana gurin har karshe hudu, sannan ya nufi masalaci, yana can har aka yi sallah asuba, ya dawo cikin asibitin, yana jin barci amma babu yadda ya iya, dole ya jingina kan shi akan gadon ya fara barci. Karfe bakwai Khausar suka shigo ita da Radiyah, ganin yana barci, ya suka koma tare da rufe kofar. Abin mamakin basu tashi ba sai karfe ɗaya na rana, sai dai Khausar ta shigo tayi abinda zata yi a hankali, tana gamawa zata fita. Kofar ma a hankali take jan shi. Yana tashi ana kiran sallah azhar, dan haka ya nufi masalaci. Zama yayi a can sai karfe hudu ya dawo domin lokacin da zai fita sun hadu da Radiyah. Dan haka ya zauna a masalaci, yana dawowa suka gaisa, tare da zuba mishi abincin, yana ci yana mata yan tambayoyi, tana bashi amsa, haka suka zauna har dare sannan tayi mishi sallama. Wasa wasa sai ga Moonah har ta shafe kwana uku cur, a cikin kwanakin nan kuwa. Idan ka ga Mohan zaka rantse da Allah shi yake jinya domin ya firgita tayi wani zuru-zuru. Sai ka zata shine ai da lafiyar ma. Sam ya manta da kowa sai Moonah, ranar da ta cika kwana uku, likitocin sun taru akanta. Suna tattauwana. A hankali nake bude idanuna. Da nake gani dishi dishi, lumshe su nayi tare da jin wasu irin yarerrika ake a kaina, tsikara min wani abu ya sani cewa. "Wash" suna cewa "masha Allah" sake lumshe idanuna nayi sannan na kuma buɗe su, wani irin haske na gani ya wuce min. Daga nan ban kuma dawowa hayacina ba, Sai washi gari na bude idanuna, yana barci cusa hannuna nayi cikin gashin kanshi, ina wasa dashi. Murmushi nayi tare da jin kome na raina da damuwa ta ya gushe, take kuma abinda na kaita ya dawo min kaina, dafe goshina nayi fa jikina babu kwari. "Hammah" na kira sunan shi, a hankali ya d'ago kai yana kallona fuskar shi a daure. "Kayi Hakuri" na mika mishi hannuna. Tashi yayi ya zauna a bakin gadon sannan ya rungume ni. "Mahaukaciya waye ya gaya miki maganin mura yana rage damuwa, kinsan halin da kike jefa zuciyata kuwa? Kece kike kwance ni nake miki jinyar karki kuma min haka domin zan mare ni, ya faɗa bayan ya had'a goshin mu guri daya." "Kayi hakuri, duk ranar da na rasaka a rayuwata tabbasa mutuwa ce ta dace dani, Hammah na, ina jin tsoro! Ina jin tsoron ranar da ba zaka iya taimaka min da kome ba sai ido, ina ji a jikina abubuwa dayawa suna tunkaro ni, Hammah Mohan kayi hakuri. Idan aka samu akasin ƙaddara karka juya min baya, idan aka samu sauyin ƙaddara karka guje ni, idan aka samu yanayin ƙaddara karka tafi ka barni, Hammah idan ka juya min baya daga zanen ƙaddara ta, wallahi billahi azim mutuwa ita ta dace da rayuwata ba, ba rayuwa ba." Kukan naja tare da kallon shi. "Hammah! Kasan me wallahi wallahi wallahi mutuwa zan yi, domin kirjina kamar yana ci da wuta , Hammah ina da damuwa. Hammah ina ji kamar banbanci zama fa kai ba, me yasa na shiga rayuwar ka? Me yasa na takura maka. Hammah kayi min addu'a idan mutuwa xan yi na mutu a hannun ka, Hammah ina jin kamar nan gaba kowa zai guje ni! Amma kai! Zuciyata ta ki gaya min zaka guje ni. Hammah me yasa nake kuka? Kawai dan nace sai na zama mace ce ko kuma dan nace ina son kane ya kawo haka! Hammah!" Na kira sunan shi ina jin wani irin tari a daga zuciyata irin me kaikayin nan. Tarin na fara tare da jini,, gogewa nayi tare da kallon shi. Kamar wanda aka dasa shi, ya rasa gane meye yake mishi dad'i. Ji yaƙe kamar baya duniyar baki daya. Tarin ya tafi da karfina. Kwanciya nayi a jikin shi. Ya kuma rungume ni. Goge bakina nayi tare da bude baki zan yi magana, ya rufe min bakin da hannun shi. "Ya isa haka, zaki yi dariya wata rana ki daina kashe ni da raina." *HMMM! A KARAN KAINA BANI DA HAUFI AKAN YADDA ALMAMOON KO NACE MAIMUNARI BA ZAN SO TA TAGAYYARA BA! AMMA A YADDA LABARIN YAZO TAFIYAR KADDARA SHINE MADUBIN LABARIN BOROROJI INKIYAR LABARIN CE, AMMA SUNAN LABARIN SHINE TAFIYAR KADDARA! BANCE YA FARU DA GASKE BA. AMMA TOH DAYAWAN MU BAMU SON MUGA JARUMIN LABARI YANA SHAN WAHALA! TOH GASHI TAFIYAR MU NA DAN NISA KUMA KUN FARA SAREWA TAYA ZAKU ZAMU JI RAYUWAR JARUMAR AMMA TOH BANSAN ME ZANCE BA AMMA KUYI HAKURI KUYI HAKURI KUYI HAKURI SHINE ABINDA ZAN CE DA WANDA XAI ZO GABA da wanda zai wuce duk yana cikin tafiyar ƙaddara 💓❤️💞* *Yau lalaci nake ji wallahi! Wai meye nufin Ku? 🙄 Anya ba zan yi rashin daraja ba toh Shikenan mu hadu nan da sati Uku masu zuwa tunda ba zaku yi voting ba🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️ sai na tafi hutun baba ta gani domin dama hanyar tafiyar nake nima kuma kun ki bani damar haka ba* #Mai_Dambu. [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1109544279?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=jfVhi7eN9HoToyWK2IK1Om6sqMtZf1yyZ%2Bne%2FvH0bt9GhZlc9FG1phyPxEZrvJ9chyYJ%2FCfRfvUMri3Zq3pk4FzYixCktvZE2JvpFYpj4wiO1rqTM%2FpB2xa010KtsSOd 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA TALATIN DA TAKWAS. "Hammah" hannun shi ya kai kan bakina, tare da lumshe idanun shi. Yana jin cikar kwalla a kwayar idanun shi. "Ki daina firgita ni, tsorata ni kike. Kina razana ni matukar tsoro nake ji, idan har akwai abinda zaki fada min ya bani tsoro kalmar mutuwa zaki yi! Kina son nayi kuka ne?" Girgiza mishi kai nayi sannan ya shafa gashin gaban goshina yana faɗin. "Masha Allah good Girl, karki kuma fadar haka ina son ganin ki cikin farin ciki." Hannuna na zagaye a jikin shi ina jin wani irin yanayi, tare da saukar kwalla daga idanuna. "Hammah je t'aime" (wato i love You, ina sonka da France) "Moi aussi Moonah!" (Me too Moonah, nima haka) "Zan iya samun damar shiga kowani hali amma idan na tuna da ƙaddara ta sai naji kamar ban dace da kai ba, Hammah kai ne kawai kasan yadda nake ji, Hammah kirjina zafi. Hammah zan yi sallah nayi wanka. Ina son ka fitar dani yawo" Mikewa yayi tare da duba wayar shi, ya nemi Number Khausar, suka yi magana can sai gata da wasu Nurse biyu, ina jingine da jikin shi, suka shigo. "Matar Hammah Mohan, ko zaki tashi su rike ki." D'ago kai nayi ina kallonta, kafin na maida na rufe idanuna. "Hammah na zai kai ni ban daki idan yaso sai su min wankan" kallon shi tayi tana kallon Moonah da take kara kifa kanta a kirjin shi. Alama yayi mata da hannun, suka fita da kanshi ya kai ni ban daki. Zai fita na rike hannun shi. " Ka tayani warware gashin nan yana tsami." A hankali ya zauna ya warware min gashin sannan ya fara wanke min a hankali. Na tuna lokacin da Innata take wanke min gashin har ruwan kanwa take zuba min, domin ya karkarye yadda ba za a fahimci mace ce ni ba, yau gashi ana wanke min shi. Buga kofar aka yi yayi gyaran murya. Gashin ba wai ya fita bane, amma ganin yadda suka uzura ya fito ya sani koran shi, suka samu kan yake wanke min, taimaka min suka yi na yi wanka bayan gama suka bani towel na rufe kaina, muka fito waje na samu har sun fita. Doguwar riga na saka, sannan na kalli inda suka ajiye min abin sallah, sallah nayi musamman wanda na sani, Hammah na shigowa ina sallama. "Kwana nawa nayi ina kwance?" "Kwana uku da wunin yau hudu.". Dama nayi na jiya da yau. kawai na kawo kwanakin da ban yi su ba, tare da niman gafaran Ubangiji, sannan na shiga addu'a Allah ya bayyana min iyayena idan suna raye, idan sun mutu kuma ya jikan su, idan na mu tazo ta kyautatta tamu bayan su. Ina cikin addu'o'in kuka ya kwace min domin sai lokacin nake jin kome yana zuwa min, haka na zauna na cusa kaina a cikin cinyoyina, zama yayi a taburman yana kallona, sai da na gama kukan ya mika min ruwan sanyi na karba hannuna yana rawa, sha nayi sannan na kalle shi. "Ya isa haka! An jima zamu tafi yin hoton zuciyar ki, sabida kin fara tarin jini kuma ba son haka yana da illah." Ajiye kofin nayi sannan na ce mishi. "Toh" Abinci ya diba min da ruwan tea, na fara sha, ina amsar abincin yana kuma bani labarun ban dariya, sai dariya nake, muna gamawa na kwantar da kaina a kafad'ar shi, ina sauke ajiyar zuciya. Shafa hannun yayi yana jin kamar ya boye ni a kirjin shi. Bubbuga bayana yaƙe yana bani labarin ban dariya, wani nayi shiru, wani nayi dariya haka dai har yanzu lokacin da aka ce mu shirya a min hoton, shi da kan shi ya kai ni, yana rike da hannuna, har inda za yi hoton. Duk da mun sami mutane. Ganin mu da Dr Khausar yasa aka ce mu shiga kasancewar an san yar Shugaban kasa ce kuma bata damu da matsayin Ubanta ba, tana aikin ta. Uwa uba an san waye mijinta, haka bai saka ta jin wata ce ita, bayan mun gama muka fito, ina jingine a jikin shi. Kwana na bakwai aka sallame ni, gidan Khausar ya kai ni, na zauna na kara jin dadin jikina. Sannan ya kawo min kome da yayi min har da wani apartment na shi da yake cikin gari, koda muka je apartment din yayi min kyau, ya shirya kome a cikin gidan, juyawa nayi tare da kallon shi. "Duk nawa ne?" Lumshe idanun shi yayi sannan ya bude min, dariya nayi domin haka ya sani farin ciki. "Hammah Nagode" "Tu mérites mieux" (you deserve more, kin cancanci hakan) Kamar wacce aka samin battery, haka nayi ta mazari a gaban shi, kafin ya tako gaba, ya rungume ni. Murmushi nayi domin abinda nake son yi ne, na kasa shi kuma mutum ne da yake saurin d'ago ka. "Bana tunanin banza a kanki, sabida ke Uwar Yarana ce, kullum burina taya zan mallake ki, taya zan samu nutsuwa idan na mallake ki, dan haka bani tab'a saka tunanin wani abinki a raina, ke nake so ba kayan jikinki ba. Ko kin manta ke mata maza ce" mintsinin shi nayi ina me ture shi. "Auchewww, yarinyar nan kin zama kura wannan mintsin fa? Gaskiya sai na rama," fara zagaye falon muke ina dariya, yana bina ina zille mishi. Kafin na gaji na zube a saman sofa ina ajiyar zuciya. "Beauty! Zaki fara aiki a babban Kotun koli na kasar nan, ni dai don Allah ki rufawa zuciyata asiri domin na ganki da wani wallahi." Hannuna na kai bakin shi ina kallon kwayar idanun shi. "Insha Allah babu abinda zai faru, ina tare da kai ne saboda ina raye, idan babu kai tabbas ni matacciya ce, ba zan tsallake dokarka ba" hannun shi ya daura a kafadana yana kallon yadda nake, tab'e baki. Goshina ya sumbata. Tare da shafa bakina yana faɗin. "Insha Allah ina nan zuwa kan ku" Dukar kirjin shi nayi ina dariya. "Hammah Allah ya yaye maka," na fada ina dariya, kitchen ya nuna min, ba laifi kome gidan yayi min, gyada kai nake ina dariya sannan nace mishi. "Amma gaskiya gidan yayi kyau amma yayi min girma, ko zaka iya nima min roommate" jan hancina yayi yana faɗin.. "A yadda duniya ta lalace salon na dauko miki yar iska ta lalata min ke? Tab ba dani ba.". Rike hannun rigar shi nayi ina kallon shi. "Don Allah fa" na fada kamar zan yi kuka. "Wallahi Maimoon ki fita idona, babu wanda zan kawo miki ku zauna tare, gidan bai miki bane na sauya miki?" "Hammah yayi min, amma idan da wani a kusa dani, zan ji dadi da nutsuwa ace babu kowa a cikin gidan, sannan ka duba da kyau bani da lafiya zuciya ta tana ciwo idan ciwon ya tashi waye zai taimaka min kafin wani ya sani? Amma tunda kace ga yadda kake so haka za ayi" na fada a hankali. "Shikenan, zan duba miki koda dattijuwa ce" Washe bakina nayi ina kallon shi. "Nagode sosai" sumbatar goshina yayi yana faɗin. "Tant pis" (wato Never mind, karki damu" haka ya shiga kitchen tare da daura afro, ina kallon shi, ya ciro kaza a frij. Yana kallona yana murmushi ya shiga aikin shi, Bayan awa daya zuwa biyu, ya kammala girkin, sai had'iye yawun nake, ina lashe bakina. "Hammah Abincin nan zai yi dad'i wallahi." "Gashi ba zan iya bawa mai kwadayi ba" "Ayya Hammah na, dan sammin dan kadan mana?" Na mika mishi flet, saka ludayi yayi a miyar ya dangwalo miyar ya saka min a saman flet ɗin. Yana murmushi. "Hammah na, wannan ba halin mutanen kirki bane, samin don Allah wallahi yawuna ya gama tsinkewa." "Toh daure shi tunda ya tsinke" ya faɗa yana murmushin jin dadi. "Kayi hakuri kaji, ka ciyar dani kamar yadda tantabara yake ciyar da matar shi." Na fada ina wani tsuma, Takowa yayi yana kallon cikin idanuna, kafin ya dauki flet din. "Zan ciyar dake sama da yadda tantabara yake ciyar da iyalin shi, zan gina miki sheka kamar yadda tantabara yake gina shekar matar shi, zan kula da ke kamar yadda tantabara yake kula da matar shi, ki yarda dani a Duk lokacin da ƙaddara ta shigo mana kiyi min kyakyawan Fahimta, ki yarda dani, kiyi min adalci. Ki Fahimce ni, karki yarda shaidan da shaidanun mutane da aljanun su rabamu. Kin ji" gyada mishi kai nayi ina jin kwalla na zubo min. Share kwallar nai ina kallon shi. Amsar flet din yayi ya zuba min macaroni da miyar kazar, zuba min ya dauko ruwa ya ajiye min, sannan ya ciyar dani da hannun shi. Ina koshi na dauki cokalin zan fara bashi ya amsa, tare da cewa. "Babu ruwanki dani," haka ya zubo na shi ina kallon shi yaci ya koshi sannan ya shiga min hira, kafin yaja hannuna zuwa ban daki yace min. "Kiyi alola zan tafi masalaci, gidan nan akwai mutane masu haya, kasan shi shaguna ne, sai kuma ko kula da kanki akwai babban falo inda ake hira, ban da shiga harkan kowa. Babu ruwanki da su, kowa yayi harkan gaban shi. Ban hana gaisuwa ki Barka ba, kece kawai bana son ana shigo miki, kuma ban ce ki shigar musu ba, halin dan Adam da wuya karki shiga su sa miki damuwa." "Insha Allah" na fada ina kallon shi, ban daki na shiga ya fita. Sai da nayi wanka da alola sannan na fito ina kallon yadda aka gyara min dakin, a hankali na taka na bude wardrob din da na gani a d'akin. Ikon Allah, gefen dogayen riguna daban, gefen riga da zani dabam sai riga da skirt, sai kananun kaya, masu kyau da inganci. Daukar doguwar riga na saka, tare da wata hijab a naga gefen su daban, abin sallah na dauka na gabatar da sallah azhar. Sannan na shiga addu'o'in, ina idarwa na sha magani, kafin na kwanta. Ina nazarin abinda ya hana shi dawowa. *** A can kuwa fadar shugaban kasa, jarida aka buga shafin Farko hoton Hammah Mohan da Maimunari, abin mamaki magana dai masu matukar zafi aka rubuta. *SHIN ME ZAMU CE DANGANE DA MAJOR GENERAL MOHAN MAMMAN NASIR? ITA WANNAN WACECE MISHI DA YA KE RIKE DA ITA? SHIN ME YA HANA SHI AURE YANA RAYUWAR DA TAYI MISHI* A cikin shafi na biyar na jaridar aka sake saka hoton shi da na Maimunari, wanda suka yi a Dubai tana sanye da kananun kaya musamman ranar da suka shiga club ɗin nan. '''AN CE MANA BAI DA LAFIYA ASHE MUTUM KAWAI WATSEWAR SHI YAKE ABIN SHI TOH ITA YARINYAR YAR WAYE? KUMA IYAYEN TA SUMA SUNA INA?''' Kallon su Primer minister yayi yana faɗin.. "Allah ya kyauta, amma ban ga abin yayatawa ba, sannan kuma ministen labarai zamu tuntubar da wannan abun tunda." Shiru yayi sannan ya kuma kallon su yace musu. "Ku bar zance kawai, Allah ya rufa asiri." Daga haka ya sallame su. Kiran Mohan yayi, can kuwa sai gashi. Zama yayi bayan ya gaishe shi. Tura mishi hoton yayi. Murmushi yayi sannan yace mishi. "Abbu hoton yayi kyau sosai, wannan ne banji dadin ganin shi ba, kuma ban san me zance ba, amma itace Almamoon da tayi jinyata." Ya fada yana sunkuyar da kan shi. "Kana Sonta ne?" Da sauri ya d'ago kan shi. "Eh Abbuna" "Haddir da Salman sun min magana, sai Khausar itama tayi min magana akan na tausassan Mahaifiyar ku, akan ka. Insha Allah zan yi yadda ya dace." Shiru yayi tare da jan fasali kafin ya cigaba da cewa. "Ita Hanan fa?" "Insha Allah zan ji da kome" "Allah yayi muku albarka." "Amin Ya Allah, Abbu!" Sannan ya fita. * Yana fita ofishin Baban shi, wayar Hajiya lateefa na shigo mishi, cikin diriricewa ya dauka. "Ina son ganinka." "Toh Ammyn" A rikice ya nufi gidan, kai jama'a. Ruwan bala'i ya sha na masifa, haka ya zuba tagumi kafin ya ninke ta baibai. "Wallahi Ammyn ni da dud duniya bani da masoyi ya irin Hanan. Daga yau dan na fita da ita har sai anyi baikon mu, ya ga Yar dangi xan kula bare. Ina yar dangina nake so" Anan ya cinye ta da baki, yayi ta rarrashinta, sannan ya mike zai tafi tace mishi. "Abincin ka fa" "Ammyn a kawo min part dina." ** Tun ina saka ran ganin shi, har na cire rai, washi gari sai ga drive yazo ya kai ni babban kotun kasar, anan nayi kome. Sannan na gama zan tafi naga sunan jikin Katsina MAIMUNARI I UMAR WODAADABE, shiru nayi kafin na sake murmushi, sannan na fara gabatar da abinda ya kawo ni. "Don Allah nace ba?" D'ago kai tayi sannan tace min. "Ina jinki" "Suna na Maimunari I Umar wodaadabe." Murmushi tayi sannan tace min . "Rukayya Husain Adam, auta." Mika mata hannu nayi sannan ta mika min nata. "Ofishin justice aka turani, kuma Ni bakuwa ce" Mikewa tayi zata rakani. "Ok tun wancan satin na fara aiki anan nuna turo ni aka yi daga Agadaz, muje na nuna miki" "Yan mata ji mana? Ina niman barista Maimunari" ya fada daga bayana. "Karki kula shi muje niman magana yake." "Kinga kawar mu, ki kulani indai da gaske ne" juyawa nayi a fusace, katon teddy bear na gani, dai dai misali a hannun shi. "Sorry" ya fada min, dauke kai nayi ina kallon shi. "Fiancée dinki ne?" "Kyale shi karki kula shi" "Kiyi hakuri kin sha magani? Kin karya?" Amsar dolin nayi tare da maka mishi ina kuka. "Kasan yadda zuciyata ta kwana da son sanin wani hali kake? Ko kirana baka yi ba, ban sani ba karka kuma zuwa nan dube shi katon mutum kawai, muje Kinji Kawata." "Lallai kaci duka gobe maka kara." "Toh duk wannan fushin name? Da bance zan yi sabuwar budurwa ba" cak na tsaya, tare da juyawa na kalle shi, kamar na rufe shi da dukka, haka na share shi. Bin bayan mu yayi. Har ofishin alkali, muna zuwa muka samu masijan shi, ya shiga ya gaya mishi. Kafin mu shiga Hammah Mohan ya tare kofar, tare da shiga cikin Office din ya rufe, yana ta rubutu. Jan kujeran yayi tare da zama, sannan ya cigaba da kallon shi. "Mai girma alkali!" D'ago manyan idanun shi yayi tare da kallon shi. Yana son tuna inda yasan fuskar shi amma ya manta, "Suna na Mohan Mamman Nasir Aghali, yarinya ta zata zo sanin makamar aiki, toh naji ance baka tab'a aure bane, shine nazo da kaina muyi magana daya, yarinyar a karkashin da'irata take, kai kuma a karkashin da'iran mahaifina kake, ban san yadda zaka dauki batuna ba, amma tabbas zan iya kome akan Beauty. Dan haka zata shigo ayi kome cikin mutunttaka, ba sai na gaya maka ina haukar sonta ba, amma toh gargadi ne ba Shawara ba." Ya fada bayan ya mike tare da bude kofar, shigowa tayi bayan ta, buga mishi dolin tana faɗin. "Kayi min laifi amma haka bai saka ka fahimtar yadda nake ji ba, me yasa jiya baka dawo ba, kasa barci nayi fa. Har sai da nasha magani!" Bude min hannun shi nayi. "Hammah na, ina sonka karka manta dani, idan baso kake na mutu ba...... #Mai_Dambu [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1109846382?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=5APA6mJ8v7GgHSCkDwtNb1XXK%2BVFjYD5JoQuwsUbL%2BoIhl%2B1ELBymj3sVefZSm9hx7T5VudtIwohWKCgDupKfRkENVHC3lkDkAPKgEM%2Fi1YU6rlaxusjnrm2Wbfeg0Md 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... _Merci beaucoup, surtout mes compatriotes nigérs qui parlent français. Merci. Merci. Incha Allah. Nagode sosai ❤️😍💓😘👏_ BABI NA TALATIN DA TARA. "Kinga ga inda zaki yi aiki, domin munyi magana da shi, dan haka ki nutsu kiyi abinda ya kawo ki,ban da shiga damuwar Kowa. Kinji" gyada mishi kai nayi, sannan ya juyar dani, ina kallon alkali, gaba na ne ya fadi. Lokacin da nashi ya fadi ya kura min ido. Cike da mamaki. "Moonah! Gashi nan kiyi aiki da gaskiya karki yarda a hada kai dake a cuci wani ko shi, sannan ki nutsu babu ruwanki da kowa, ki gabatar da kanki." Kasa magana nayi ina kallon shi, haka shima yake kallona, gyada kai kawai nake ina kallon shi, kwarjinin shi da girman shi ya cika min idanuna, sunkuyar da kai nayi kasa, ina kallon kasa. "Itace yarinyar ka?" Cikin karamin murmushi ya gyada mishi kai, "Sunan ta? Ya tambaya zuciyar shi na wani irin bugu. "Maimoon I Umar" ya faɗa. "Toh zaku iya zuwa babban Ofishin majastiri, kuyi cike ciken da ya dace sauran kudawo nan ita daya." "Toh" ya ja hannuna muka tafi, har na manta da Rukayyah Hussain Adam, haka muka gama kome, sannan muka koma ofishin sa, idan ban gaya muku ba. Hammah Mohan so yake ya lalace a jikina, domin baki daya wani ranar haka muka yi ta zirga-zirga, lokacin da na koma ofishin sa, na zauna yana masalaci. Ina cikin Office din ya dawo, ya shigo da sallama na amsa mishi. Ban san me yasa mutum yake min kwarjini da cika ido ba. Zama yayi tare da mai da hankali akan aikin shi. Mikewa nayi tare da cewa. "Yallabai" "Koma ki zauna" zama nayi cikin jin kunya. "Baki da mafadi ne? Ko abinda iyayenki suka turoki kenan? Shi kwalliya ce a tare dashi, ke kuma abin kunya ce a gare ki, ban ji dadin yadda yake rungume a kan idanuna ba, idan mahaifin ki ya ga haka me kike dauka zai kalle ki? Karki kuma kamanta irin wannan shirmen a ofishina, ki cika wannan takardun." Ya ajiye min, jikina yana rawa na dauka, tare da cikawa na mike zan fita. "Dawo?" Da sauri na dawo na zauna. "Kin ci abinci?" Ya tambaye ni cikin kulawa. "A'a. Abie" wayar da can ya danna, yayi magana cikin fulatanci. Murmushi nayi tare da cewa. "Abie anani fulfulde?" Murmushi yayi sannan yace min. "Eh, Wodaadabe Bororo" ya faɗa tare da kallona, kamar na saka ihu." "Laa nima Wodaadabe Bororo ce." "Daga ina?" "Niger" "Libya Mali" "Kai Amma Abie kai ma aiki ne ya kawo ka nan?" Kwankwasa kofar akayi, yace a shigo, katon basket aka shigo dashi, aka ajiye Mishi, tare da mishi gaisuwa, kafin ya ciro kuɗi. Ya bata, tana fita yace min. "Akwai goran fura da nono, ki duba can akwai kofi, sai ki zuba min sai ki kawo min, abincin kuma naki ne" Idanuna ne ya cika da kwalla, na nutsu na fara abinda ya sani, kome na Office din tas yake, na dauraye na kawo, na zauna nayi duk abinda ya sani. Bayan na gama na mika mishi. "Abie me yasa ba zaka ci abincin ba?" Murmushi yayi sannan yace min. "Abincin mata uku naci a duniya na gamsu dashi, Mahaifiyata, mai sunanki dan ke sunan babata ce, sai Kanwata Kabo itama ma ina son girkinta, sai mace daya da tayi tafiyar ƙaddara da rayuwata." Hannuna na had'a tare da kallon shi ina bubuga index fingers dina. "Abie itace Crushed dinka?" Na fada ina kallon shi da yar murmushi. "Ta wuce crushed sai dai rayuwata." "Ta rasu ne?" "Zuwa yanzun kan bana jin tana raye?" "Ayya kayi hakuri, na fama maka ciwon da yake ranka" na dauki abincin zan fita. "Ina zaki? Ki ci anan" "Abie, Hammah yana waje" "Toh jeki" "Nagode sosai Abie" Bai d'ago ba, kuma bai amsa min ba. A duk lokacin da ya kalle ta wani irin abu yake ji akanta, haka kawai muryanta da shiririta yake dibi da ita, idanun shi ce ta cika da kwalla, ya mike tare da tsayawa a bakin window yana kallon yadda mutane ke zirga-zirga. *Jewel* ya ambata a hankali, yana tuno yadda tayi ta kuka da abinda yayi mata, idan ya tuno yadda take daura kanta, a kafadar shi tana kuka. _Wai meye aka miki ne? Kawai dan na tawo dake? Meye na kuka? Toh kiyi shiru zan mai daki gida_ A lokacin dud duniya baya jin zai iya rabuwa da ita, baya jin akwai wanda ya isa raba shi da ita. Sai gashi kai tsaye mahaifinta ya karya karfin shi da yake jikin ta. Itace yarinyar da ya fara ta'adi da ita, yasan ya saka yan mata dayawa kuka, amma baya jin kukanta zai tab'a rayuwar shi sai da ta bar jinjirin da ta haifa mishi, sai da ta tsallake su tai tafiyar shi. Bai san me zai ce ba, amma zuwan yarinyar nan yasan ya shi jin lallai yana bukatar Ahalin shi. "Assalamu alaikum!" Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa yana kallonta, kafin ya mai da kanshi gurin Mohan. "Kayi hankali da rayuwar ka, domin wani lokacin muna tafiya ne da ƙaddaran mu, duk wanda ka ga ya sha Allah ya dibe mishi wani wa'adi ne, ka kuma kara nisanta kanka da mutanen da suke zagaye da ƙaddaran ka, wasu Alkhairi ne ke tafe dasu, wasu kuma sharri ne, malam masoyi zaka iya daukar yarinyar ka tafi da ita, amma kazamar soyayya da ake yin nan a gaban jama'a, ayi hakuri dashi sabida kimar Uwata. Domin naga wani sako a jaridar jiya." A hankali na d'ago kai ina kallon shi, sai naji jikina yayi sanyi. "Ban tab'a rungumar ta ɗan naji dad'i ba, ban tab'a rike ta naji dad'i ba, idan nayi haka ina yi ne sabida yanayin laluranta yana bukatar kulawar da tafi haka, amma a matsayin ka na babba kayi magana Insha Allah zan kiyayye hakkin Allah, gudun fadawa rudin shaidan, sannan karka manta da kashedina." Dariya yabawa Alkali,ya saka hannun shi daya a aljuhun wandon shi, daya yana rike da kofin fura da nono, yana kurb'a. "Toh ai yarinyar ka, Uba ta dauke ni dan haka karka kuma damuwa da ni." takowa yayi gaban shi cikin harshen buzanci yace mish. "Ka kula kana mata mahaukacin soyayya, itace silar kukanku. Kayi fatan Allah ya shiga al'amarin ku. Domin ina hango guguwar da ta tunkaro." Cikin sanyin halin ya kalle shi, kafin ya riko hannunta, yana kallon shi. "Babu wanda ya isa tsakanin mu, domin na shirya zuwan wannan yanayin, tunda na na fara bana jin akwai abinda zai raxanani sai kalmarta kawai nake jin tsoron shi." Daga haka ya riko hannuna,muka fita kallon shi nayi ina son nayi magana, amma tsoron shi ya hanani magana, har muka isa gidan, fushi yake tayi koda zai tafi rike hannun shi nayi. "Kayi hakuri kaji." Na fada idanuna suna cika da kwalla. Shafa fuskana yayi. "Babu laifi dan ya mana magana akan rayuwar mu, amma kuskure ne babba ya shiga al'amarin mu kin gaya mishi wani abu ne akan rayuwar mu" "WALLAHI ka yarda dani ban tab'a wannan gangancin ba." Na fada kwalla na cika min idanuna, "Ya isa, ki kula da kanki" Gyada mishi kai nayi, tare da cewa. "Sai gobe kenan" "Eh nazo miki hira ne? Yawwa gobe Insha Allah Rukayyah Hussain Adam, zata dawo nan da zama. Naga kina son ƙawance da ita" "Eh" na ɗaga mishi kai. "Toh zata dawo nan Insha Allah" Daga haka na rako shi har waje, sannan na koma cikin gidan, na hadu da matan gidan, muka gaisa. *** Baki daya Mohan ya mai da Uwar shi bita can, yana zuwa gurin Hanan amma babu abinda yake hada shi da ita, ta gama haukarta, bai kula ta sai ya gama Gajiya zai tashi ya bar gidan, sannan ya kalle ta, shima bawai dan yana da abinda zai ce mata ba. Bayan kwana goma sha biyu, ana saura kwana uku zayi bikin yancin kai, hankalin shi ya karkata akan wani abu na daban, bai da lokacin kowa sai kanshi. Shi da dan Ba'are dan ya zo gida, kullum suna fita tare da abubuwan kan su. Sau daya yazo a kwanakin nan baki daya ya dauke kafa, a kotu ma ina zance ina fahimta abubuwan da yake faruwa, sai dai ban cika azarbabbin shiga ba, sai Abie yayi min magana nake shiga, dan ma dai ina yawan damun shi da shiririta, da wauta nayi ta dashi dariya, idan kuma muna hira kamar wasu sa'o'in juna, abinda na fahimta a tare dashi Abie ya aikata laifuka da yawa, da suke yawan dawowa rayuwar shi, sai dai wani lokaci zai ta share kwalla, tare da kallona yana fada min wasu kalmomi masu girma da daure kai dan haka tausayin shi da damuwar shi ya kara sakani cikin wani yanayi na daban, shima Hammah Mohan, idan na kira baya dauka duk da Rukayyah Hussain Adam, tana tare da ni, amma bana jin dadin yadda nake kiranshi yana kin d'agawa. Ga wani mugun mafarki da nake yawan yi akan shi. Dan haka ranar na kira shi tare da tambayar shi,yana ina? "Karki zo inda nake kiyi zaman ki kawai" ya kashe wayar. Takaici ya sani bin shi, bayan na kira shi, dakyar ya gaya min. Koda naje sai naga gida ne, dan haka na shiga cikin gidan, hango shi nayi, Hanan tana bashi abu a baki. Wani irin nauyi naji a kirjina, dan yasan na ganshi. Na kira shi waya. "Nagode da abinda ka bukaci na gani." D'ago kai yayi yana kallona, kafin yace zai mike, na juya tare da fita a gidan, ina jin zubar jini a hancina, duk lokacin da raina ya b'aci kai na yake sarawa, kafin nan na fara tari, idan banyi tari ba shine jini zai na zuba ta hancina, lokacin da ya fito har na tari abin hawa, ina kuka. Har na isa gida, shafa kanshi yayi sannan ya kira dan Ba'are. " Ya kome na tafiya?" "Eh amma ita fa tana cikin hatsari domin ana bibiyar kiranta" "Ok gobe da dare Malik ya tafi da ita Maradi, itama Abokiyar aikin ta ta koma garin su, ka tabbatar sun bar garin nan gobe Insha Allah" Sannan ya juya abin shi yana kashe wayar, kara wayar shi yayi sannan ya saka a kunne. "Mohammed Mamman Nasir Aghali, ya kake? Baka saka hannun a wasan ba toh gani nan ina jiran Munnah a gidan da ka bata me kyau da tsada, zaka zo ne ko kuma zaka iya hakura domin nazo ne akan game ɗin." Kashe wayar yayi tare da kiran Dan Ba'are. "Maza kazo gidan Dogo ina jiranka, ina da abu me muhimmanci a gidan Beauty" * Ina komawa gida, tun a bakin get din na hango Malam Ansar, cikin kuka na kalle shi. "Ya isa haka, dama haka rayuwa take, wanda ka damu dashi bai damu da kai ba, wanda baka damu dashi ba yana nan yana hakilo akan ka, shiga mota mu fita." Babu musu na shiga ina goge kwallar da nake, da hanky din da da yabani, muka fito cikin garin, han gyara garin yayi kyau da ado, wani gidan abinci ya kai mu, na kasa cin kome, ruwa kawai na sha, haka yayi ta tsokanata. Tare da jana da wasa. Dole na sake muka shiga hira. Inda ya min odar abincin da suka fi na farko kyau da tsada, ina ci ina bashi labarin gurin aikina. "Hmm! Meye ya had'a ki dashi?" "Babu kome!" Naki gaya mishi, domin a tsakanin masoya akwai yafiya da boye sirrin juna, tun yanzun idan ban iya boye sirrin mu ba, yaushe zan koya dan haka muna cikin cin abinci, aka rike min hannuna. "Ina zaka tafi da ita?" Cikin fushi ya sake hannuna ya zabga mishi naushi dai dai shigowar Alkali. Sai da bakin shi ya fashe. "Mohan!!!" Na kira suna shi da karfi....🤣 #Mai_Dambu [8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110255281?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=DdYNxkS6yN8uhfrR37h62zbfOjOm1OLDDCckdNme%2BKjEwnbGDu4mL6048YMV1h%2B07%2FeXZoIeF7Jb4dl3nS6A6LUJkIqi7ROIE9bf%2BgkMcMKV8M17P9CSRPPYeYAU9QZF 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ARBA'IN. Tsayawa nayi a gaban shi, cikin takaici ina kallon shi, zuba min ido yayi, kafin yace min. "Ba zan miki dole ba, amma kuma yana da kyau ki fahimci suwaye a tare dake, su waye suke son amfani dake, tashi muje gida." Ya fada min, kasa mishi musu nayi ma mike, ashe haka ya b'atawa Malam Ansar rai yace min. "Nagode" juyawa nake son shi yi, amma abun mamaki Mohan ya hanani, muna fitowa ya saka ni a motar shi. Muka bar gidan cin abincin kamar zanyi kuka haka nake bin shi. Baya tafiyar shi, Malam Ansar ta juya zai ya hadu da Alkali, cike da mamaki ya kalle shi. Sannan ya kasa magana, har ya fita yana kara juyawa yana duba alkali. *Taya mutumin nan yake kuma da Munnah? Kamar ta B'aci sosai* shi daya yake zancen zuci, har ya shiga motar shi, wayar shi ya saka a kunne, yana me cewa. "Yaki amsa sabida ya san zai fadi, dan haka duk rintsi ka dauko min ita idan ka sami damar haka, idan ka sake kuma na dauke ta, tabbas zan tafi da ita ne duk inda yayi min." Wani murmushi yayi tare da cewa. "Kwantar da hankalinka, yanzun zaka ji ruwa mai yawa, zan baka abinda baka zata ba, yanzun zan koma diffa, idan na dawo zan kira ka." Kashe wayar yayi tare da sake wani murmushin gefen baki yana faɗin. "Hmm! Ta kare maka Mohan" ya faɗa yana murmushin mugunta, a hankali ya tadda motar,tare da barin Niamey. Abincin ya saya tare da biyan kudin, sannan ya nufi gurin da su Mohan suka tsaya, ganin wayar Maimunari yasa shi dauka, hotonta ne a kai lokacin tana Almamoon, kura mata ido yayi zuciyar shi tana bugawa, da sauri ya kashe wayar baki daya. Abincin da bai ci ba kenan, haka kawai zuciyar shi take raya mishi wani abu akan Yarinyar,duk da ya lura bata da kwaranniya irinta sauran matan, gaskiya da ban mamaki yanayin su da yake gani a tare, abu daya da yake kara fisgan shi a kanta, kafewarta akan abu. Bayan haka baya jin akwai wani abin da ya ke yanayi daya da nashi, sai fuskar shi da kuma yana yin fatar su, sai dai tafi shi washewa kaɗan, kasancewar shi mai duhun fata sosai. Lumshe idanun shi yayi. A da baya tunanin haka sai da wani abokin shi alkali daga tahua yazo da ya ga Maimunari ne yayi ta mamaki. "Wodaadabe wannan yarinyar yar ka ce?" Murmushi yayi sannan yace mishi. "Eh toh kasan ban da iyali dai? Aiki ya kawo ta nan bayan nan kuma gaskiya babu wani abinda ya had'a mu sai dai ina jin ta kamar wacce ta fito jikina" ya faɗa yana murmushin jin dadi. Yau an had'a shi da d'a shi da yayi kuskuren tafiya ya bar baya da kura. Bayan abokin shi ya tafi ya tuna sakon da ya barwa yar uwan shi. _Ban sani ba ko meye muka haifa! Ba zan iya duba shi ba, don Allah ku rike shi da amana, idan namiji ne ku bashi ilimin addinin musulunci, idan mace ce don Allah ki tayani boye sirrinta, dan kar hakkin mutane ya tambaye ni akanta na had'a ku da Allah." Lumshe idanun shi yayi kafin ya bude sunyi jajjur har da ruwa sun cika. "Ina namiji ta haifa, kuma tarihin shi zai rufe,mace kuwa tabbas soyayya zai bude tarihin ta, kuma de ƙaddara zata ratsa tsakanin. Allah kasa namiji ne. Allah kasa kar ya gado mugun halina, ya Allah kasa kar ya dauki halin da na jefa wasu iyayen." Ya fada yana jin saukar kwalla akan fuskar shi, tabbas yayi kuskure sosai, kuma yayi danasanin rayuwa,domin ya cutar da yaran bayin Allah da yayi ka,abun na mishi ciwo. Gashi girma ta cimma shi babu iyali shin Zainabu tana raye ne? Takawa yayi babban falon shi yana kallon yadda rayuwa ta mike mishi, a cikin shekara ashirin yayi faffutikar niman ilimi, yayi karatun boko dan yana da ilimin addini, bayan faffutikar da yayi na yawon karatu kasa kasa, ya halarci yaki da jahilci da yake garin Kano, idan ya damu shekara biyar yana karatu, bayan ya gama ya koma Nijar yayi karamar diploma kan harshen French na shekara uku. Sannan ya nime gurbin karatu ta hanyar wani mutumin da ya tab'a yiwa taimakon sakamakon asirin da aka mishi, akan shi da yaran shi. Mutumin shi ya dauki nauyin shi tafi kasar Faransa yayi karatun lawyer, inda ya shekara takwas yana karatun, yana gamawa ya kuma komawa makarantar horon alkalai anan Faransan, idan ya samu shekara goma sha biyar yana karatun shi bai da lokacin kanshi baki daya ya kuma tafiya jami'ar Madina inda ya karanci Shari'a musulunci a can suka haɗu da Primer minister, inda ya karya mishi asirin jikin shi, sannan ya gaya mishi wasu abubuwan. Akan Yaron shi da suka haɗu dashi wato Mohan. Yana kammala karatun shi, a Saudiya suka dauke shi aiki Nan babban Kotun musulunci, albashin da tabarkallah, haka yayi ta rayuwa ga yan mata da suke bibiyar shi, amma bai tab'a kawo su rayuwar shi, asalima mace daya yake so har kwanan gobe. Lumshe idanun shi yayi idan ya tuna yadda yayi ta yawon niman abokin shi da Kanwar shi kamar ai yi hauka, yayi ta niman Zainab da danginta, kamar Mahaukaci. Haka yayi ta jin kamar ya tsani kowa a duniya, bayan ya dawo Nijar domin Primer minister ba karamin addabar rayuwar shi yayi ba akan lallai ya dawo kasar shi yayi musu hidima, yana dawowa aka bashi alkalin Alkalai na kasar nijar, tare da albashin mai kyau amma bai kai wanda Saudiya take biyar shi ba, idan yanzun zai ga Zainab ko dukkan dukiyar shi ya zab'a ya bata zai sallama mata indai zata zauna dashi. Numfashi yaja tare da d'aga kan shi sama, yana jin babu dadi. Ya rayu a kad'aici gashi Yanzun ma kadaicin ce ta kuma takura shi. Buga mishi kofar gida da aka yi ya sashi bude kofar shiga gidan, manyan mutane ne baki dayan su. Shigowa suka yi bayan sun nime izinin haka. Tashi yayi tare da dauko musu ruwa, ya ajiye musu. Ya zauna yana kallon su, bayan ya daura daya akan daya. "Ina jin ku meke tafe da ku?" "Muna niman goyan bayanka, kan aikin da zamu yi, kuma Alhamdulillahi mun samu nasarar wasu manyan sai dai wasu daga cikin mu sun yi kokarin kin bamu hadin kai." Murmushi yayi yana kallon su. "Kusha ruwa" daukar goran ruwan suka yi tare da kaiwa baki, shima ya dauki nashi yana kallon suka bude tare da kaiwa bakin su. Suka sha, rike musu ruwan yayi, a wuyar su bayan ya damke goran hannun shi. "Kun zo kuyi min tayin na shiga kifar da gwamnati Mamman Mohammed Nasir, bayan baku san tarihina ba, tun ba yau ba nasan zaku zo. Kuma idan kuka tafi zaku iya juyowa gare ni, wannan abin da kuka yi hukuncin kisa zan yanke muku domin wallahi ba zaka yi nasara ba, koda zaku yi faduwa ce zata biyo baya, sake goran yayi suka shekar da ruwan suna tari. "Kafin ka tunkari mutum ka fara dubar waye shi, jarumta ba a jiki yake ba a zuciya yake, idan kuma aka yi katarin haduwa da karfin jiki Magana ya kare maza ku tashi ku bar min gida idan na fito muku a asalina, mutuwa zaku yi domin da bakin ku zaku fadi abinda kuka aikata." Mikewa suka yi tare da barin gidan a guje, domin basu tab'a tsammanin tantiri bane shi sai yau. Murmushi yayi sannan ya fara niman wani layi, bayan sun jima suna magana sannan ya kashe, yana jin wata irin nutsuwa a ranshi. *** Wullani yayi cikin motar ran shi na kara b'aci.. "Dalla malam karka karya musu yar mutane, ka manta kai ka daukota a gidan su? Kishin banza kishin wofi ko ce maka aka yi yar ka ce ita? Baka isa ka hanata kula samari ba, tunda ba aurenta kayi ba. Haba Mohan! Meye tayi maka da zafi haka? Meye ta tsare maka haka? Idan wani abu ta maka zai ka gaya mata. Amma ba kayi ta nuna mata abinda bai dace ba, ta baro gaban iyayenta a wahale, tazo nan kana wahalar da ita" "Kyale shi Hammah Khalil, ban san b'ata min lokaci yake ba, sai da nagan shi da yar uwan shi, ya hanani nayi rayuwa da wani, sannan shi ya kasa fahimtar dani wacece ni? Bayan tashin hankalin da na gani nazo zan shiga gida Ansar yazo, da naso wulakanta ka da a gaban shi zan ki kula ka, na bishi amma kai a rayuwata gaskiya ne baka tab'a min gori ba, nasan kana kishina amma haka baya nufin cewa zaka wulakanta duk wanda yake tare dani ne, Hammah meye nayi maka da zafi? Dama can yar uwarka zaka aura" "Eh ita zan aura" "Mohan ka gaya mata gaskiya mana, meye amfanin boye mata abinda kake?" Inji Dan Ba'are, "Ba zan gaya mata ba, idan ta gadama gobe tana dawowa aiki ta shirya zata koma Damagaram" cikin takaici na kalle shi, ban iya mishi magana ba, na dauke kaina haka muka isa gida, har na fito daga cikin motar na shiga compound na gidan. Ya biyo ni da sassarfa. "Ki hada kayan ki nace gobe" dauke kai nayi. "Maimunari ina magana dake" banza na bawa ajiyar shi. Hannun shi ya d'ago zai rike ni, na buge hannun. "Karka kuma gigin tab'ani, idan ba haka ba, zan mare ka" na fada mishi ina wuce shi. Kasa motsi yayi tare da cizon lip din shi na kasa, furza da iska yayi. Wayar shi ce tayi kara ya dauka. "Malam da alamu kome dai yana tafiya dai-dai, ko ta watsar da kai ne tayi tafiyar ta, ok kasa hannun muyi wasar mana ko kana tsoron zaka fadi ne!" "Kai!!!! Kana ina ne?" "Ina kofar gidan ka mana, kazo domin da shaiduna nake." Kashe wayar yayi, sannan ya fita da mugun gudu ya shiga motar. "Taka muje." "Ina dan Ubanka sai kace aljanu ne suka shafe ka" Bai kula shi ba kallon agogon hannun shi yake. "Gidana mana" da gudu suka bar apartment din, suka isa gidan, ko tsayawa basu yi ba, ya bude motar tare da sauka, yana wani irin ciccira kamar wani lantarki yana spark, takawa yayi zuwa gaban su. Ya daki motar su, "A'a Mohan! Karka lalata min mota na mana." Ya fito yana kurb'an wine. Takardan ya ajiye mishi. "Ka duba mana, meye a cikin shi ban da yarjejeniyar da aka kula idan bai maka ba, sai ka rubuta wanda kake so" Ya fada tare da kallon abokanshi biyu da suke cikin motar. Yana faɗin. "Yan iska zaku fito ku tayani saka hannu ko ya?" Dariya suka yi tare da fitowa suna kallon Mohan. Gira ya d'aga mishi yana nuna mishi takardan daidai fitowar dan Ba'are, tare da ciro bindiga a k'ugun shi. "A'a. A yarjejeniyar mu babu harbi babu fada. Duba mana" Daukar takardan dan Ba'are yayi yana kallon shi. "Ba zai shiga ba" ya riko hannun Mohan. "Hhhh! Kunji dan mace toh tunda ba zaka shiga ba, inji abokin ka nima dai zan maka Yaren da zaka gane" "Zan shiga" "Mohan" "Zan shiga! Bani. Amma idan nayi nasara zan Barka a raye domin ganin mu shi zai kara maka fahimtar kome na Allah ne" Cika gurin yayi, sannan ya juya zai bar gurin. "Mohan ina maka fatan nasara" Cak ya tsaya, sannan yayi gaba abin shi. Bai kuma kula kowa a cikin su ba, har suka shiga motar bai iya magana ba. "Mohan" "Please" Yace mishi, tare da juyar da kanshi. "Idan baka yi nasara ba zai iya daukar ta da?" "Nasara ta Allah ce, ka yarda da faduwa. Don Allah ka barni" Ya fada mishi haka. Murmushi yayi bayan sun bar gurin. "Me yasa ka dage ne? Naga dai baya so kamar tilasta mishi kayi." "A'a yana so mana, da baya so ba zai shiga ba, nasan abinda nake shima kuma ya sani, idan da bai da ilimi ba zai shiga ba, saka ido ka gani." *** Tunda na shiga dakin nake kuka, ban san me yasa kome yake zuwa min haka ba, amma tun haduwa na da Mohan nake kuka, mik'ewa nayi tare da hada kayana ina gayawa Rukayyah Hussain Adam, "Auta tashi ki hada kayan ki, zamu bar garin nan sai bayan bikin yancin kai zamu dawo." "Toh lafiya?" "WALLAHI ban sani ba, Hammah Mohan ya sani haka." Na shiga had'a kayana. Ina ƙoƙarin b'oye damuwa na. Tunda na gama muka kwanta. *1:am Kokarin rike jan numfashi na nake, amma baki daya ya shake ni, ya hanani sakat ban san meye manufar shi ba, sai dai hango shi da nayi ya fad'i kasa warwar ya sani farkawa da sauri ina ajiyar zuciya, ban daki na shiga nayi alola nazo na gabatar da sallah nafilla. Har asuba idanuna yaki barci a duk lokacin da na rufe idanuna abinda ya faru a mafarki yake dawo min, har aka yi sallah asuba,nayi sallah sannan na zauna na cigaba da azkar. A hankali barci ya dauke ni. Karfe tara na bude idanuna, ganin shi nayi zaune, ajiye min kofin shayi yayi tare da mika min brush. A hankali na tashi babu yabo babu fallasa, na nufi ban daki ina fitowa na dauki shayin da magani na sha, sannan na koma nayi wanka ban same shi a dakin ba na shirya sosai, sannan na fito, ina kallon shi suna hira da Rukayyah. "Insha Allah karfe biyu zaku bar garin nan ki gaida iyayen ki," ya mika mata wata jaka, sannan ya kalle ni. "Muje" "Yan mata bari na fita" "Toh sai kin dawo" ta ce min, haka muka fita, gabaki dayan mu jikin mu a mace yake, kamar wanda wani abu zai zame mu, gurin cin abincin ne. na zamani. Kujera ya ja min na zauna. Sannan ya zauna yana kallona, kawo mana kayan abinci aka fara yi. Ina kallon shi. Kasa cin kome nayi ina kallon shi. "Ci mana" "Na koshi" bai ci ba, ya rike hannuna. "Ban sani ba ko zan kai labari, sai dai ina rokonki Abu daya. Don Allah koda na mutu karki auri Ansar ki, Don Allah ki auri Khalil ko Haddir, sune kadai zasu rike ki kamar yadda nake rike dake. Sune kawai zasu soki kamar yadda nasoki. Kasar da Mahaifina nake son bawa kaina don Allah ki taimaka min kinji karki Auri Ansar" Ya fada yana dauke kan shi tare da saka bakar madubi a idanun shi, domin kwalla ce take son zuba mishi. "Me yasa zaka gaya min haka" "Sabida bani da zab'i, rayuwar mahaifina" "Mohan kasan yadda nake ji akanka? Me yasa zaka gaya min haka?" "Sha ruwa" ya mika min. Buge hannun shi nayi, tare da mik'ewa dan kula shi ma, bata lokaci ne. Haka na barshi ya zo ya same ni a gurin. Haka muka fita yayi ta yawo dani, kusan amanar kaina yake bani kar na auri Ansar. *🤔🙄 Toh ya zamu yi daku domin mutanen da suka biya kishi a tsakanin zubda jini sun fara niman shi fa😌😠 🙄 wai suna jiran dan haka zan fara shi ku kuma zan mai da ku posting sai dare sau daya shima sabida nayi alƙawarin shine ɗan haka kuyi hakuri, toh ya na iya an fara tambayana 👏 kuyi hakuri ba laifina bane na mutanen da suka biya kudin su..... Nagode* #Mai_Dambu.... [8/7, 10:04 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110533172?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=aSbcpjgn9asSsm9lZXK1GTYd1hkBoALGTEin2VPj2rrHh0qsHukAEkcdgVB%2Bbd47RHlGBNNnsyrNYAxk4FDLM8zZE%2BhDR1NGlY7Kh7sDrXNrEAQA9XmoAHfTO2Lcqj9H 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ARAB'IN DA BIYU. Gurzawa yake cikin wani irin shauki me mugun dad'i, har yaji shi ya shige cikin jikinta kamar mahaukaci a zauce da ita, ya gigice domin bai tab'a kawowa zata kai mishi ba, dan haka lokaci guda yaji an shake mishi wuyar shi. Ban san yadda zan kwatantata muku yadda nake ji ba, ban san wani irin yanayi nake ciki ba, sai dai duhun da na fahimta yana rufe min idanuna, karar da naji wanda ya tafi da jina da gani na baki daya, daga nan ban kuma sanin me ya faru ba, na ga dai ana tafiya dani da gudu, ina wuce wani irin haske. Sai muryan da ban san ta waye bana yana kirana can da nisa. "Munnah!!!" Cikin wani irin faduwar gaba ta fito bayan ta gama sauya kayan ta, tana kallon abokan. Aikin da da suke mata magana, jin su take amma ba zata ce tana sane da abin da suke fada ba. "Dr Zainab kina lafiya?" Wani irin bugun zuciya taji lokacin da aka shigo da wata mara lafiya, mai da kallonta tayi kan yarinya domin a hannun wani mutum take yana niman agaji. "Ku taimaka min don Allah," da sassarfa ta isa gabanshi. "Ku kawo min gadon dauka marasa lafiya." Ta fada da karfi, yana kawowa aka daura Maimunari, kallon Dr Zainab yayi tare da cewa. "Don Allah ko nawa ne a duba lafiyar ta, don Allah" ya faɗa kamar ya cire ciwon a jikinta ya mai da nashi, da sauri suka wuce da ita d'akin tiyata, aka fara kokarin kunna wutar da zata iya haska inda ciwon yake, domin ta ga yadda mara lafiyan take. Domin zanin gado ce a jikinta, daga haka ya tabbatar mata da zargin da yake ranta, musamman da ta kwaye zanin da ya lulluba mata, kwalla ce ta shiga sauka daga idanunta. Tana kuka kasa kasa, kallon Nurse din dakin tayi tare da cewa. "Kuje kawai ku kira min Dr Fadime da Dr Annah." "Toh Dr" suka fita, a hankali ta mike tare da shafa kan Maimunari, kwalla na zuba mata, kwaso kayan aikin tayi tare da saka Safar hannun, ta fara duba ta sosai musamman gaban da ya fara alamar zai kumbura, yatsin ta gwada sakawa taga bai shiga dukka ba, da sauri ta cire tanadi mamakin yadda aka haka shigowar likitocin biyu ya sata kallon su . "Ban tab'a ganin irin wannan tashin hankali ba, ina ganin cases na Fyade, amma ban san yadda aka yi wannan case din ya tsaya min a rai ba." "Kai Dr meye na rashin hankali, wannan case din ba sabon abu bane, idan kika yi dubi da Yadda ake samun kananun yara ma ana musu fyade balle kuma babban budurwa kamar wannan. Ina ganin ba wani babban tashin hankali bane, kawai a dubata idan aiki ne sai mu hadu muyi mata, amma ki bar kuka haka." Inji Dr Annah. Kallon su Dr Fadime tai sannan tace musu. "Amma ai naga mutumin da ya kawo ta ya biya kome, idan ba ita ta kai kanta ba taya zai sami damar lalata mata rayuwa yan matan mu na yanzun basu da kamun kai, gashi nan ya kai ta ya baro ta. Idan aka gaya musu su kame kansu maza basu da amana su ga kamar karya kake musu gashi nan bata wuce ashirin ba amma dubi yadda namiji yayi mata fata fata, wallahi na fi tausayin Yara kananu da ake musu haka sama da yan matan da ake musu wannan aika aikan, meye amfanin zubda mutunci ne? Shi ba aurenki zai yi ba kin je kin bashi jikinki" "Akwai ƙaddara! Dr ki duba yarinyar mana, dubi fuskarta mana? Dubi yadda gefen fuskar ya kumbura sakamakon dukar da aka mata! Yarinya shekara ashirin, meye tayi mishi? Waye nata ya tab'a yar wani? Kisan yadda fyade yake da ciwo? Karki yi fatan haka ya faru da makiyinki ma balle masoyinki, karki yi fadan wannan mummunar yanayin ta faɗa kan wanda kika sani, wallahi akwai ciwo." Ta rushe da kuka, ta kasa aikata kome,."Dr Bawai muna zargin yarinyar bane, daga Yanayinta ya samu fahimtar halin da ta tsinci kanta amma kuma ai yan matan ne suka zama sai du'a'i," Gyada kai tayi zuciyarta yayi nauyi tace musu. "Muna da y'aya mata, addu'a itace makamin mumuni, Allah ya kare mana su duk inda suke." Tana kallon su, suka gama aikin su tsaf, sannan suka mata sai da safe domin sun tashi aiki. Ita kuma ta Cigaba da lura da Yarinyar. Sai da ta gama gyara gurin tare da rubuta magani sannan ta shafa mata wani cream kafin ta mike, faduwar da gabanta ya kuma ne yasa ta komawa ta zauna dabas, kuka ya tawo mata, sosai tayi kukan da rabonta da tayi tun ranar da ta rasa abinda ta haifa, mijinta abin alfahari ta, Uban Yaranta abin kaunarta. Kallon yarinyar da ta gama dubawa tayi, sannan ta mike, ta sanya mata ruwa da allurai. Ta gyara mata jikinta. Har lokacin kuka take. Tausayin yarinyar da kaunar yarinya ya taru a ranta, har kusan uku na asuba, abun sallah ta shimfid'a a dakin da aka bawa Yarinyar, ta shiga gabatar da sallar nafilla. Tana gayawa Allah kukanta. Zata so ta ga iyayen yarinyar nan kuwa? Waiwaye adon tafiya. Wato masu iya magana suna cewa munafunci dodo ne, yakan ci ubangidan shi. Bari mu dawo tun daga lokacin da Almamoon ya fara aiki a gidan Mohan. Malik bai tab'a damuwa da shi ba, kuma bai tab'a kallon Almamoon da wata manufa ba zai da ANSAR , ko nace Hisham Waadi Ansar ya faɗa a gaban shi Almamoon mata maza ne, a da abin bai dame shi ba, sai dai yadda suka saba da Almamoon ya fara jin sha'awar shi, har ta kai yana kallon shi ina da zai same shi,duk da dama zaman da yake yana cikin mutanen da suke cutar da Mohan, ta hanyar saka mishi sihiri a cikin abincin shi da ruwan shan shi, zuwan Almamoon kuma sai ya kasa samun nasara akan Yaron, sai ya ma shiga taimaka mishi, a hankali kome ya canza, inda Ansar yayi ta cusa mishi kazaman kudi,. Suka fara abota har yana gaya mishi siririn Mohan. Sai gashi duk lokacin da Mohan zai yi wani abu kamar a kunnen Ansar, shi yasa bai damu ba, koda Maimunari ta bayyana kanta sai ya zuba ido ya ga gudun ruwan su, yana kuma bincike akan Familyn Mohan, a haka kuma ya samu labarin Hanan, dan haka ya mai da hankalin shi lallai sai sun yi wannan Game din, da taimakawan Malik. Lokacin da Malik ya tura mishi sakon Mohan yace ya maida Maimunari Damagaram. Tura mishi sakon yayi tare da cewa. *Nawa zan baka ka kawo min ita Maradi?* Dariya yayi sannan yace mishi. _Toh nawa zaka bani?_ *CF Miliyan goma* Tsaki yayi tare da tura mishi cewa. _Ni na matsiyaci bane rike kudinka_ *Nawa kake bukata? Zan baka* _CF miliyan Talatin, sabida abinda kake so ce idan bai maka ba kaje gidan Iyayenta ta_ *Shi kenan ciniki ya faɗa ga miliyan ashirin da biyar sauran idan na iso na dauke ta zan baka shi* Suna gama cinikin ta, ya tafi kiran Mohan, yana zuwa ya mika key motar shi lafiyarta lau, amma suna barin Niamey, ya fara Surutun motar ta lalace, a hankali dai yayi ta jan abin kamar da gaske, har ya yanke shawarar su tafi Maradi su kwana, ya kuma san yadda ya sakata layinta ya daina aiki, koda suka iso, ya kira Ansar ya gaya mishi, sun iso bai yi tsammanin zai biyo daren yazo ba domin shi ya riga su, isowa garin. Shi kuma da iya iso kofar gidan, ya kira wayar shi bai dauka ba, ya kuma kira bai dauka ba, dan haka ya shiga cikin gidan, yana shiga ya hango abinda Malik yake shirin aikatawa, kawai yaja wayar da aka hada na receive ya fincika sai da ya watsar da kome na gurin kayan kallon sannan ya nufi dakin duka daya yayiwa Kofar, yana shiga bai tsaya wata wata ba, ya shiga zarga mishi wayar sai da ya nad'e wuyar shi tam tun yana motsi har ya daina motsi. Jan zanin gadon yayi tare da lullube ta, sannan ya dauke ta. Ranshi na kara b'aci, yana daukar ya koma gaban gawar Malik. "Hukuncin ka kenan, duk wanda ya tab'a Munnah." Kaita mota yayi sannan ya dawo ya kwashi kayanta har da wayarta, a yanzun kan babu amfanin tafiya da ita wani gurin, dan haka. Yana kai ta Asibitin ya basu kayanta akan su bata, sannan ya biya kudin kome, ya bar asibitin. Tare da gudun mafaka, domin yasan tabbas za a nime wanda yayi wannan aikin, shi yasa ya cire Maimunari cikin gida har da kome nata, kar case din ya faɗa kanta. ** Niamey. Wani irin faduwar gaba ce ya same shi bayan ya gama shirya kome, dafe kirjin shi yayi, bayan ya gama daura hannun Fahad, kallon juna suka yi da Dan Ba'are. "Ya dai?" "Beauty tana cikin damuwa?" "Ko?" "A zuciyata nake ji!" Shiru yayi sannan ya dauko ruwan sanyi wanda yayi kankara, ya jefa kafar Fahad a cikin ruwan. Kuka ya fara tare da girgiza kanshi yana mutsu mutsu. "Yanke mishi wancan yar yatsar" Mohan ya gaya mishi, babu wani tausayi ko imani ya yanke yatsar kusa da ta babban, wani irin gurnani ya ke yana ihu, bayan sun toshe mishi bakin shi. "Sake yanke ta karshen" inji Mohan, aikuwa Khalil ya yanke yatsar, "Toh Yanzun gaya min su waye da waye" "Dumm!!!" Garin Niamey ya dauki wani irin ƙarar me mugun karfi tare da daukewar wutar lantarki a garin baki daya, sakamakon faruwar fashewar. "Duba ƙarar me?" Da sauri ya fita, yaji garin yayi wani irin tsit, cire mishi tape din yayi tare da yanka mishi fuska da aska. "Gaya min me kuka Shirya min?" "Zan fada zan fada." "Chief of Army Staff, Attorney general, Minister of defense, Inspector General of Police, tare da Minister of Information, sai Minister of affairs,sune suka shirya juyin mulki, yau Insha Allah. Sannan sun dakatar da babban kwamandan Sojojin sama, domin sun shirya kashe wasu ministocin Babanka, minister Lafiya, minister Ilimi." Cikin tashin hankali ya kalle shi, bai san lokacin da ya caka mishi wuka ba. "Wannan ƙarar fashewar jirgin ne?" "Eh!" Ya fada a wahlarce, "Shaidanun suna ina?" "Suna ina?" "Zasu kashe ka domin sun shirya maka" ya faɗa a wahale, Bai kula shi ba, yayi waya kafin kace me. Har sun fita, kamar yadda suka zauna suka Shirya. Sharrin su haka suma, suka shiya musu, yayin da suka yi ta bin kowani dan banza suna kamewa, basu sami ministan harkokin waje ba ya gudu.. Ba iya shi ba hatta manyan sojojin da suke da hannu akan abin sun gudu, dan haka suka nufi cikin gari bayan sun saka akan kama, munafukan take aka fitar da wani sanarwan me mugun tashin hankali. Akan duk inda aka samu Mohan da Dan Ba'are, a kashe su. Domin suna da hannun akan hatsarin jirgin sama da aka yi, da kashe ministan tsaron ta akayi, tare da mutuwar jami'in tsaro da aka samu gawar shi a Maradi. Domin sun yi kokarin yin juyin mulki ne sai sanarwan mutuwar Fasinjoji jirgin sama har da ministocin kasar biyu Dr Khalid Bashir da Dr Al-Amin Sahabi. Ba karamin tashin hankali dan Ba'are ya shiga ba. "Kai kasan waye ya mutu?" "Waye?" "Malik" "Ya aka yi kasani?" "Idan bai tafi da Moonah Damagaram ba, Tabbas akwai hadin bakin da suke da ANSAR, kuma nasan zai iya kai mishi ita, abu daya nake tsoro kar ya aikata mata mugun abu, tsoron da nake ji kenan." "Babu abinda zai faru, Insha Allah." *** Karfe bakwai na safe ranar da Nijar ta samu yancin kanta Yau ya zamewa wasu iyalan ranar bakin ciki, musamman inda jirgin ya fado, ya kashe mutane da dama bayan fasinjojin cikin dari da ashirin, a nan akayi ta sanarwan mutuwar. Fitowar Dr Zainab kenan, ta hango Benazir da Yumnah, tare da mai renon su. Da gudu suka tawo kanta. "Mommy Daddy sun yi hatsarin jirgin sama." Kamar sauran aradu tashi maganar daga bakin su, kafatan ma'aikatan asibitin, suka sunkuyar da kansu, sabida sun ji labarin ita ce dai basu bari taji ba. Kallon su take kamar wacce ta rasa tunanin ta, a hankali taji maranta yana murɗa mata, lumshe idanunta tayi sakamakon zafin da take ji har cikin ruhinta, mik'ewa take son yi amma ta kasa, haka Benazir ta d'ago ta. Amma ta kuma komawa sai ganin jini suka yi yana zuba daga tsakanin kafaffunta. "Mommy!!!" Yumnah ta faɗa da karfi, baki daya suka rud'e, domin suma tayi. Haka likitocin asibitin da Nurses suka rufa akanta aka mai da ita dakin gaggawa. Inda aka shiga kokarin rike cikin jikinta. Amma ina ya rigada ya fita, shima yabi mahaifin shi. Dakyar suka samu ta farfaɗo. Bayan ta koma barci, sannan suka fita. Bayan kwana biyu. Tun washi gari da abin ya faru dani na farka, sai dai bana magana da kowa, kasancewar babu wanda yake zuwa gurina. Na tsani kaina da kaina, duk da ina samun kulawa a gurin Nurses sosai, na bar haka da sunan taimako ne kawai. Ranar da na cika kwana takwas, aka sallame ni, ina shirya kayana. Ta shigo, kallo daya nayi mata na dauke kai domin Nurses din suna gaya min cewa. "Inji Dr Zainab tana gaishe ki, jikinta babu kwari ne." Ban santa ba, amma kuma ina jin ta a raina, shigowa tayi tare da cewa. "Maimoon" juyawa nayi na kalle ta, sannan na cigaba da had'a kayana na dauka, ina haki. "Ajiye drive zai zo ya dauka zo mu tafi" Kallonta nayi, sai gashi na kasa mata musu a hankali na isa gabanta, ina jan kuka. Jingina kaina nayi a kafadar ta, danne kukanta take amma tabbas akwai al'amari me girma akan Yarinyar. Haka suka fito sai suka ba da sani irin yanayi kamar yaya da kanwa, sabida dan tsayin su kusan daya ne, yanayin jikin su ma kusan iri daya ne banbancin Zainab fara ce kal, kallon su Benazir tayi da take gaban motar. Ta fito da sauri ta bude musu bayan suna shiga. Sai kallon Maimunari take, kamar tasan fuskarta ta. Haka suka zauna. Sai lokacin kukan Dr Zainab ya fito. Rike hannunta Maimunari tayi, sosai irin na rarrashin nan. "Queen Bee, akwai kayan Addarki a dakin da ta kwanta ku kwaso keda Rabil" Cikin asibitin suka shiga tare da kwaso kayan suka fito, a bayan mota suka saka, sannan suka shiga. "Allah Nagode maka! Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka, Allah ka gafartawa Khalid." Ta fada tana kuka. Kamar ranta zai fita, mijinta abin kaunar ta, abin alfaharinta. Ya tafi ya barta da soyayyar shi..... #Mai_Dambu [8/7, 10:04 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110873206?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=w9A2MuNtd%2B622l0%2BjIc2ASPfh3Zd6cFPBnC7ssNginYPPoEFUrAQ6F%2BPyB%2FEL3W27mCWwkzGM1DWmbWijxOkDE%2BgKcaqC15YNh%2Bfbe6kK1ewkr6qPiO5FQd5pOlySlZh 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ARAB'IN DA UKKU. Ta bani tausayi. Amma a yadda nake hango tawa rayuwar taya zan fuskanci Mohan? Taya zan fahimtar dashi? Idan na gaya mishi zai yarda dani ko ba zai yarda dani ba? Yanzun na hango abinda Innah take nufi, yanzun na gane dalilin da yasa ta hanani zama a matsayin Mace, yanzun na Fahimci illar da take cikin rayuwar mata. Ina kallon su kamar masu yanci. Ashe basu da yanci, ina kallon su kamar masu farin ciki ashe kowani dakika na rayuwar su hatsari ne. A haife ka a mace matsala, ka rayu a mace matsala, hawaye ne yake zuba min babu iyaka, dama tana tsoron kar wani mara imani ya min haka ne? Ashe dama can ƙaddara ta a tsare take, dama a shirya min kome nawa daki daki. Daga wannan ƙaddarar sai wata, sai wata. "Hmm!" Naja wani iska mai zafi, sakamakon isowa wani Mahaukacin gida da zai iya cewa yana bayan gidan Mohan na can Jacader. "Mommy ko fito" hannunta naji a samar nawa, juyawa nayi na kalle ta, kafin na bude kofar, ina takawa a hankali, sabida har zuwa lokacin gurin bai warke ba, muna shiga babban falon gidan, mutane ne. Yan gaisuwa, ana ganin Dr Zainab, suka rud'e da kuka musamman yan uwan mijinta. Dangin shi, haka ta zauna a cikin su. Zata yi kuka na matse hannunta a hankali ina murzawa. Jinjina min kai tayi alamar tayi shiru. "Addah muje daki, ki huta" inji Benazir, gyada mata kai nayi. Na bi bayanta muka shiga cikin gidan, dagaske masu ruwa sune da kifi, domin dakin Benazir kamar irin dakin ya'yan Barber's doll ne. Kome na dakin pink da light blue ne, ban daki ta nuna min. Bayan ya shiga ta hada min ruwan wanka, shiga nayi. Na tube kayana. Bayan na zauna cikin ruwan, zafin yana ratsa jikina. Lumshe idanuna nayi ina kara sake ajiyar zuciya, domin dadin da nake ji. Musamman a gabana, domin ji nake kamar an daure ni baki daya. Sai da na gasa kaina sannan nayi wanka da alola na fito, na samu ta ajiye min doguwar riga, dauka nayi na nufi ban daki, ina sakawa hawaye na zuba min, ina gamawa na fito nayi sallah, kusan kwana uku bana cika barci mai dadi, sai mafarkai. Haka ya tab'a min ciwo na, domin kuwa na fara jin ciwon kai da zazzaɓi, tare da nauyin kirji na. Haka na kwanta tare da kifa kirjina, akan matashin na samu barci mai daɗi. Kwanakin da suka biyo baya, bani da lafiya sosai, domin sai da aka danganani da asibiti, inda suka maza suka gano Matsalata. Ciwon zuciya ne ya tashi, gashi babu Number wani nawa da ta sani, domin bata bincika jaka na ba. ** Niamey. "Yallabai yaran nan kokari kare rayuwarka da ta iyalinka suka yi akan me zasu so kashe ka? WALLAHI daga Khalil har Mohan, babu wanda yake da nufin ya cutar da kai don Allah ka saka a janye batun kashe su da zaka yi don Allah" Kallon Alkali yayi sannan yace mishi. "Me nene shaidan ka?" Laptop din shi ya bude bayan ya kunna mishi daukar da yayi na manyan mutanen da suke jikin shi, take ya gamsu tare da yarda da abinda ya faɗa, lokaci guda ya bada sanarwar ta hanyar mai yaɗa labarai na fadar shugaban jamhuriyar kasar Nijar, akan an wanke su Mohan, sannan kuma an saka duk inda aka samu manyan mutanen nan a kama bayan an sake videon su. Sannan ya sauke baki daya manyan sojojin kasar, akan za a tura da sunayen wasu. Da za a basu matsayin kuma matasa masu burin kawo cigaba. Sannan ministoci biyu da suka rasu ta jirgin sama za a kaiwa Iyalin su, gaisuwa. * Kallon Mohan yayi yana murmushi. "Tunda kome ya kammala toh ni ba zan kuma binka muyi irin wannan kasadar ba, aure zanyi idan zan mutu na mutu ina da matar da zata min addu'a dan kutumar Ubanka" Kallon shi yayi ya watsar tare da lallubar wayar shi. Kira yayi cikin Sa'a ta shiga amma ba a dauka ba. Sake gwadawa yayi can aka dauka. "Addah Mommy ta kaita asibiti tana ta aman jini, amma zasu dawo inji Addah Benazir!" "Benazir!!?" "Eh ai kamar su daya da Addana Munah kuma, kullum Addah Munah sai tayi ta kuka tana tari, shine rana na gayawa Addah Benazir, Mommy ta kaita asibiti, sun barni Ni daya na, gashi Daddy baya nan an ce ya mutu a jirgin sama waye kai?" "Mohan Mamman Nasir Aghali!" "Wow, joli nom Où es-tu maintenant? " (Wow, Nice name Where are you now? Wow suna me dad'i, kana ina ne yanzun?" *Tabdijam yau na hadu da tsinkankiyya* ya faɗa a ranshi, ""Alors où est Niamey, C'est ton nom?" (Ina Niamey, kema ya sunanki Cikin shagwaɓe ta marairaice murya yace mishi. "Tout le monde s'appelle Addah, je m'appelle aussi Adda Yumnah" (Kaga kowa Addah ake ce mishi Ni ma ka kirani da Adda Yumnah) dariya ce ta kama shi tace mata. "Toh amma ni katoto ne! Amma zan saya miki chocolat, ina Addah Munah?" "Sunan tafi asibiti" ta faɗa mishi, " Wani gari?" "Maradi" "Gidan waye?" "Dr Khalid Bashir" "Ok baban kune Minister na lafiya" a sanyayye tace. "Eh" "Bani wayar nan, dama bincike kike yi mata? Sai na gayawa Mommy" "WALLAHI ba bincike nake ba, wayar ne take ta kara, Sannun Addah Munah, wani ne ya kira." Amsar wayar tayi tare da cewa. "Me yasa kika dauki wayar? Ince baki gaya mishi inda nake ba?" "Kiyi hakuri na gaya mishi, kuma shima yana jin France" Daka mata tsawa tayi, tare da cewa ta fita,, cillar da wayar tayi tare da jan tsaki. Kashe wayar yayi yana kallon sunanta, mik'ewa yayi ba gobe ba, yau Insha Allah zai tafi Maradi. Bai tsaya na ya fita ai Dole Jelar shi ya bishi da gudu suka fita. Karfe bakwai na dare suka shiga garin Maradi, da location na wayar ta, yayi ta bibiyarta har gidan, dakyar aka Barsu suka shiga dan sun ce ma sun zo ta'aziya ne. Kiran wayar yayi taki dauka, fita yayi zai shiga gidan Dan Ba'are ya rike shi. "Tana cikin gidan zan shiga naji meye nayi mata" "Kayi" banza yayi dashi ya nufi cikin gidan, da sallama ya shiga falon ya hango Benazir, a tsaye tana latsa waya. Dake masifa ya ciyo shi bai tsaya duba ba, kawai ya isa gabanta cikin fada yace mata. "Gaya min meye nayi miki?" Ya fada da karfi, a razane ta kalle shi. Bakinta na rawa, "Mohan Mamman Nasir Aghali, bani bace tana dakina bari na kirata, falon da mutane, Sai lokacin wani mugun kunya ya kama shi, juyawa yayi tare da cewa. "Kuyi hakuri don Allah" Nuna mishi gurin zama Benazir tayi, ya je ya zauna sannan ta haura sama. "Assalamu alaikum! Kamar Almamoon ko?" Murmushi nayi mata, sannan nace mata. "Dama baki gane bane? Tun tuni na Fahimci kawar Almamoon ce ke ai abokiyar fada" "Waw! Kizo Mohan Mamman Nasir Aghali ya zo?" Murmushi nayi sannan nace mata. "Kice ba zan zo ba, yayi tafiyar shi" na fada mata tare da gyara kwanciya na, kasa fita tayi tana kallona. "Addah Munah!" "Bana son jin maganarki don Allah fita" Tana fita na mike da sauri zuwa ban dakin, ina shiga na dauke almashin da na gani a ban dakin na shiga yanke gashina mai mugun tsawo da kyau, na yanke shi kaf, sannan na dauki reza ina kuka sai da na kwashe gashin kaina, sannan na durkusa a gurin ina kuka, kamar raina zai fita. Zan koma gurin Innata, ina mai kama da maza sak. Buga kofar Dr Zainab take amma fir naki kula ta, ina jin ta bar dakin na fito, ashe yana tsaye. Har zan koma ya taso da sauri, abinda ya faru tsakanina da Malik ya dawo min wani irin ihu na saka tare da zuɓewa kasa. A rud'e ya karaso tare da daukata, ya dauko dani, Lokacin dan Ba'are ya shigo gidan kenan, dan ya gaji da zama. "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, d'azun muka dawo asibiti da ita fa, yanzun kuma wani abu ne ya same ta?" Inji Dr Zainab a rud'e. "Mohan kawota Mommy likita ce." "Bani kayan aiki Benazir" sake rikicewa Dan Ba'are yayi jin sunan Benazir, da gudu ta haura zama can sai gata da kayan, ta shiga dubata, kafin tace musu. "Ta firgita ne, zuciyar ta yana bugawa sama da yadda muka dawo, ka firgitatta ne?" "Akan me zan firgitatta, yarinyar da nake kauna? A'a kawai tana ganin na nufeta ta yanki jiki ta fadi bayan ta kwala kara." "Hmm" tace a kasan ranta kuwa tace. *Allah kasa ba sanadin fyaden bane wannan abin ya same ba?* "Dr baki ce kome ba?" Ya kuma tambayar ta, "Akwai abinda ya firgitatta ne, amma babu Matsalar kome" rubutu tayi sannan ta mika mishi. "Kayi hakuri, gashi ka sayo mana maganin da ruwa," ta ciro kudi a jakarta ta bashi. Mikewa yayi sannan ya ce mata. "A'a barshi kawai" Ya fita daga shi har dan Ba'are, kuma zuwan su tare bai zama dole ba, abinda yasa yayi haka dan ya katse mishi kallon BENAZIR ne, kuma yayi dacen haka domin tunda suka fita yake auna mishi maganar banza. "Dan bakincikin da Hassada ina kallon annurin zuciyata zaka ja hannuna." "Kai dan Ubanka yar mutane ba zata iya daukar nauyin ka ba, wallahi yaga musu ita zaka yi" "Allah ya isa tsakanina da kai, wallahi zata iya dauka na, don Allah karka fara." Dariya abin ya bashi bai kuma kula shi ba, har suka sayi maganin a wani Babban kanti. Wayar shi ce tayi kara, ya saka a kunnen. "Yallabai Nagode domin na san aikinka ne" "Karka damu, Mahaifinka yana don magana da kai ka nime shi." "Nagode sosai, Insha Allah zan Nime shi." "Toh babu kome, kayi ƙoƙarin dai." Daga haka suka yi sallama, lokacin da suka isa gidan ruwan aka saka mata a dakin Dr Zainab da yake kasa. Sai da safe suka mata, sannan suka wuce gidan Mohan da yake Jacader. Sun samu babu kowa. Dan haka suka shiga abin su, daga nan suka wuce cikin gidan. *** Karfe biyar na asuba, ina jin motsin Dr Zainab tana ban daki, na mike tare da cire ruwan da yake hannuna, sannan na dauki biro da takarda, na tsaya ina kallon shi. Kuka ne ya tawo min haka na hadiye, ina jin zata fito na koma na kwanta. Fitowa tayi, tare da fara gabatar da sallah nafillah, Ni kuma ba shiga ban daki, nayi alola da wanka. Sannan na fito na bar dakin na haura zama, sai da na gama shiri tsaf na duba jakata babu kome a cikin shi. Ina saukowa kasa na hango jakarta ban tab'a sata ba, amma a karon farko dan nisanci Mohan, na bude jakar na dauki kudin mota da na shan ruwa, sannan na ajiye mata wasikar godiya da fatan Alkhairi tare da laifin da nayi mata na satar Kudinta ta yafe min zan tafi gida ne. Ina isa bakin get na mikawa Baba shima nace mishi. "Bba akwai wasu maza biyu zasu zo zaka ga dayan su kato ne ka bashi wannan wasikar" sannan na fita daga gidan. Ina fita da sauri, babu ababen hawa, dakyar na sami abin hawa. Ya kai ni tasha, ina zuwa na samu mota amma saura mutane biyu, haka na sha zama har karfe bakwai saura, kafin Allah ya taimaka muka tashi. Ajiyar zuciya na sauke lokacin da na Fahimci mun hau kan hanya. Na tsani kome na rayuwa, tun banyi nisa ba, kome ya lalace min. Tun ban yi dogon tafiya ba. Na rasa mutuncina, ina kuma da na matsa kaina, rayuwata zan rasa ba mutuncina ba, tir da wannan soyayyar da bata da riba, daga lokacin da na hadu da Mohan fara fuskar yadda rayuwa take, nagodewa Allah, Innah tana raye. Amma ba zan iya gaya mata wannan mugun labarin ba, domin Mohan zata daurawa...... UZURI💓 *Bai zama dole gobe ku ga Posting da safe ba. Domin wallahi ina jin barci kuma yara sun sami hutu dan haka idan kun gani toh Madalla idan baku gani ba! Sai dare Insha Allah idan ban zama Busy ba kuma sai jibi Insha Allah domin ina da uzuri gobe Insha Allah* #Mai_Dambu [8/7, 10:04 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110763041?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=PYEroEpzcfPkMnsivXwBeeuxpzKGK0fkWNcFQtCIRTayJ6sMVuy4zCFcXax%2BjsXVmcWqYu7JpcasekmM2WVikzyWFlN%2FH2zr4nlW%2F5vRpIWR%2BVC4yv60%2F1T6BeQc23Yo 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ARAB'IN DA HUƊU. Ajiyar zuciya na sauke lokacin da na fahimci na bar Maradi naji burkina ya cika, hankali na ya kwanta. Taya zan fuskanci Innah da wannan abun. Share kwalla nayi tare da alkawarin ko wuta tace na fada sai na shiga saboda na kyautatta mata. *** Karfe tara na safe. Fitowa tayi tare da kallon falon a gyare, zama tayi tana kallon hanyar sama, tana nazarin yaushe zasu fito. Karar sautin takalmin Benazir ne ya sa ta, d'ago kai tana kallonta. "Beenah ina Addah Munah?" Wannan shine tarbiyyar da tayiwa yaranta da ita kanta, indai Babba ne zata kira shi da sunan manyan tare da nuna musu cewa babba ne a bashi girman shi. "Mommy bata dakin ki ne?" Kallonta tayi sannan tace mata, "Kamar ya bata dakina bayan ni nake tambayarki," "Toh ai bata dakina ne, dan ta shigo da asuba tana fita na farka" Wani irin rawa Jikinta ya dauka bata san lokacin da ta nufi waje ba. "Malam Idi bakuwar yarinyar nan tana iya?" "Hajiya ai ta tafi, gashi wannan tace na bawa bakin jiya da suka shigo." Ya mika mata, fararra takardan, ganin har da tambarin Asibitin su yasa ta koma cikin gidan, ta duba jakarta. Samun nata tayi, jikinta a matukar sanyayye ta bude shi. *_Assalamun Alaiki, Dr Zainab. Ina kara mika ta'aziya ta na rashin mijinki, na tausaya miki kamar yar da ta rasa mahaifinta Uwar da ta rasa mijinta. Allah yayi miki ni'imommin rayuwa ta ko ina, na gode da ƙaramcin ki a gare ni. Nagode sosai sai gashi ina tsaka da miki bayanin zan koma gida. Mohan Mamman Nasir ya zo min, don Allah ki taimaka min da rufe sirrina, kisan yadda tafiyar kaddara take, baka shirya mishi. Idan ya same ka haka zaka yi hakuri dashi, sannan kiyi hakuri na miki sata ban tab'a sata ba. WALLAHI ban tab'a zina ba. Kiyi hakuri ki rufa min asiri kodan rayuwar Yaranki nan Benazir da Yumnah. Suma mata ne idan kika boye nawa Allah zai boye naki da nasu, naso ace Mohan shi ya fara ta'adina amma sai gashi ƙaddara ta faɗa min. Ban sani ba ko iyayena dayan su ya tab'a wata ne ko yar wani ne ban sani ba, amma nasan zina Bashi ce. Idan kuma biya aka yi a kaina Ubangiji yasa haka ce mafi Alkhairi aka ina bashin ya tsaya haka kar ya cigaba da tab'a halina nagode sosai ina jinki kamar uwar da ta haife ni Maimunari I Umar Wodaadabe_ Kuka take kamar yanzun aka mata mutuwar mijinta. Wani irin kaunar yarinyar take ji har cikin ranta, ta kasa magana sai kuka kawai take tana karawa. "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji, me yasa? Allah na tuba" "Assalamu alaikum" Mohan da Dan Ba'are suka yi sallama. "Wa'alaikimun salam!" Benazir ta amsa musu itama tana share kwalla, yarinyar tana da hakuri kamar mahaifinta tun rasuwar mahaifinta sai ta nutsu sosai, Tun ba a gaya mishi abinda yake ba, jikin shi ya bashi Moonah ce tayi wani abu. Shiru yayi yana jin sautin kukanta har cikin kanshi, ya tsani yaga mace tana kuka komi kankantar ta kuwa. "Meke faruwa?" Dan Ba'are ya tambaya, "Sai ka tambaya ne? Moonah ta tafi?" Ya fada kamar baya son maganar. Kallon wai haka ne dan Ba'are yayiwa Benazir. Mika mishi takardan da Dr Zainab ta amsa a hannun Malam Idi, shi kuma ya mikawa Mohan. "Ka karanta mana" inji dan Ba'are, "A'a kai ka karanta" kallon shi yayi sannan yace mishi. "Na yarda da kai ne" *_Amincin Allah ya tabbata a gare ka ma'abocin tausayi da taimako ban sani ba ko zamu sake haduwa, amma dan darajar iyyenka karka nime Ni! Idan ka Kuskura ka tawo nima na. Zan tafi zan tafi zan tafi garin nisan nisa! Mohammed Mamman Nasir Mohan Aghali! Nasan kai waye nasan kai dan manya ne! Mohan nasan kana Sona! Amma kuma a yadda kake son ba zai mana amfani ba! Son ba zai mana rana ba, son ba zai amfane mu ba! Mohan ka duba mana yanayin mu! Ni yar talakawa ne futtik kai kuma ɗan shugaban kasa! Gaskiya kayi hakuri bamu dace da juna ba! Nagode sosai daga me kaunarka Maimunari_* Sunkuyar da kai yayi, yana wani irin haki tare da dafe saitin zuciyar shi. "Damagaram" Ya mike dakyar ya nufa hanyar fita daga gidan. Kurawa Benazir ido yayi, sannan yace mata. "Kingan shi nan? Yana kaunarki kimanin shekaru biyu da suka wuce. Dr Khalil mutumin kirki ne. Dr nayi Imani idan ya wulakantatta zan iya saka bindiga na harbe shi, amma ki saka a miki bincike sojan Nijar ne, kuma wallhi zan zame mata Dan uwa, na zan tab'a bari tayi kuka da Khalil ba. Don Allah Karki bari soyayya ta bashi wahala. Bai san wahala ba sai a kaina. Don Allah ki taimaka mishi da Kaunar Benazir yake kwana yake tashi!." Da gudu beenah ta haura sama, bata kuma dawowa kasa ba, Dr Zainab kan hawayen ta ne ya tsaya cak. Wani irin gata Allah yayi mata haka ne? Har gida ana niman soyayyar d'an babban gida, Family Ba'are da yake Agadaz. Masu rike da Wazircin garin. Kwalla ne ya zubo mata. " Sai na yi nazari!" Daga haka ta mike tare da bin bayan beenah. Lokacin da ta shiga dakin ta sami yarinyar a tsakiyar gado, ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta, tana kuka. Zafi biyu ko na ce uku ne ya hadu mata, zama tayi tare da janyo yarinyar a jikinta. "Beenah! Baki son shi ne?" "Mommy. Bi yarinya ce fa, kuma Daddy yace nayi karatu akan me zan yi aure? Ina tsoron shi kar yayi ta." "Kinga kamar ba zai yi haka ba, yan uwan Daddyn ku, tun da na dawo suka watse babu wanda ya zauna min, Nanny ma ta tafi. Beenah bani da kowa sai ke da Yumnah. Bani da dangi, Beenah ki duba idan bai miki ba, ba zan tab'a miki dole ba, abinda kike so shi nake so." "Nagode sosai Mommy" Insha Allah zan duba." Ta fada tana share kwallarta, tun da suka haɗu a airport, ta manta shi ashe shi yana sane da ita, yana nan yana niman ta a ranshi, lumshe idanun ta yi. "Mommy ba zan tab'a yin aure ba, bana son na tafi na barki kina kewar Daddy." Kwalla ce ta zubo mata, turo kofar dakin Yumnah tayi wacce tashinta kenan daga barci. "Mommy ina Addah Munah!" "Ta tafi" "Mommy me yasa baki barta ba? Muna sonta muma tazo ta zauna." "Gashi bani da number ta." "Ina dashi, ranar da wayarta ya fadi a bayan gado ta samin Number na kirata, ina da shi." Da sauri ta fara duba wayar, amma bata samu ba. "Mommy ashe banyi saving ba" "Kara dubawa da karfe nawa kika kira?" "Kamar da dare ne" "Toh duba mugani" Can kuwa ta hango shi kasa can, kiran wayar tayi. Kamar ba za a dauka bata, sai kuma aka dauka. "Addah Munah! Me yasa?" Amsar wayar Mommy tayi. "Na zata ina da iko dake ashe ke yar kanki ce? Me yasa ba zaki gaya min ba zaki tafi?" "Kiyi hakuri." Daga haka ta kashe wayar baki daya, sake kiran suka yi yaki shiga. Shiru suka yi. Haka kawai ta shiga kallon rubutun Maimunari, Wodaadabe? Gabanta ne ya fadi. . Bai tab'a shiga b'acin rai da bakin cikin rayuwa ba irin yau, daga shi har Khalil babu me iya magana, kowannen su da abinda yake damun shi. Har suka bar Maradi. . Karfe biyu na rana muka shiga garin Damagaram, ban isa gida ba, sai da na shiga kasuwa na sayi kayan maza, na tsaya a gidan wanka na sauya sannan na nufi gidan mu da kayan, sallama nayi. Ina tana daki, a hankali na nufi dakin da jakata, ina shiga na zube akan gwiwata, kwalla na zuba min, bata da lafiya ta rame sosai, a hankali na rarrafa na isa gaban ta, ina zuwa na kwanta akan cinyarta, ajiyar zuciya ta sauke. Kafin tace min. "Nayi laifi babba na boye ki, amma yau da kika dawo min kina kuka sai nake ganin kamar nice silar kukanki? " Komawa nayi jikinta na kwanta, ina shashekar kuka. "Nayi ta ja miki jafa'i da masifa bayan wanda kike ciki, na ja miki tashin hankali da damuwa bayan wanda kike ciki, nayi fushi na gaya miki magana, wai dan karki juya. Toh ya za ayi kaddarar mu ce tazo a haka. Mun yi tunanin tunda Allah bai bamu Haihuwa ba, sai mu mayar dake namiji domin gudun ƙaddara, nayi tsammanin dan kina sufar maza ba zaki tab'a jin namiji ya burge ki ba! Ashe gudun ƙaddara." "Innah ki yafe min, don Allah ki yafe min. Wallahi ko wuta kika ce na zauna Innah zan zauna, Innah idan irin rayuwar da kike so ne nayi zan yi don Allah karki kuma barina na tafi wani gurin na hakura da karatun ma." "Mohan da?" Tambaye ni, tashi nayi ina kallonta, zuciyata ta na bugawa da sauri da sauri. Zare hular kaina nayi, taga kwandila tass na kwashe gashin. Cikin sanyin jiki tace min. "Me yasa?" "Bai dace dani ba, iyayen shi masu kudin gaske ne kuma manyan mutane ne, sun zab'a mishi wacce ta dace da shi, idan na cigaba da kula shi akwai matsala ne kawai na hakura." Rike hannun tayi cikin kulawa. " A soyayyar gaskiya ana samun fada da zage zage, amma ba a tab'a rabuwa ba, yayi miki wani abu ne?" "A'a bai tab'a kallona da nufin zina ba!" "Soyayyar gaskiya ce a kwayar idanun shi, kaunar gaskiya ce a jinin shi.yasan kin tawo?" "Na bada sako a bashi." "Tabbas zai zo! Tafiyar Ƙaddara ba a shirya mishi, zai zo domin zai biyo sawunki, zai zo yana biye dake kamar inuwarki." "Innah Ni fa bana son shi" na fada mata kaina a sunkuye. "D'ago ki kalle ni!" Kasa d'ago kai nayi ina wasa da hannuna. "Har yau kina son Mohan" "Nifa bana son shi " "Hmm" Tace min, da sauri na d'ago kai ina kuka nace mata. "WALLAHI bana son shi" "Toh Allah ya kyauta," tace min. Sallah muka yi na kwanta a jikinta, ina jin wani sanyi, sai bani labarin irin taimakon da Ansar yake musu,kuma ba ga haka tun daga cimmar mu, fada tayi min akan askin da nayi, bayan la'asar ta kalle ni. "Ki saka kayan matanki, kin fi kyau da shigar matanki kinji Uwata." "Toh." Na sauya kayana na dauki katin bankina, na nufi bank naje na cire kudi, na yi mana sayayya kafin na dawo,ina sauka a napep na hango motar Hammah Mohan. Shiga cikin gidan nayi, tare da sallama yayi wani irin zama kamar Almajiri, abin tausayi. Dauke kai nayi tare da gaida Khalil sannan na wuce dakin Innah na zuba kayan abincin na dawo na wuce d'akina. "Uwata kizo" inji Baba da yake zaune. a hankali na zauna ina kallon shi. "Uwata ga Mohan, meye yayi miki da zafi?" "Bana! Na gaya maka gaskiya!" "Shi nakeson ji" "WALLAHI bana son shi ne! Yayi hakuri bana son shi" a hankali ya d'ago kai yana kallonta, kafin ya sunkuyar da kai. "Meye nayi miki? Meye nayi miki da zafi?" "Ka gane mana kawai bana sonka ne, idan kuma ka matsa min zan bar garin nan na gaya maka ba zaka tab'a gane inda nake ba" dafe kan shi da yake sarawa yayi, tare da kura mata ido. "Ki gaya min meye ya faru?" "Kai dan Shugabanan kasa!" "Naci kaniyar shugabancin kasar meye matsalar shugabancin kasar da soyayyar mu?ke kiga ya meye nayi miki da zafi?" "Toh Malam an tab'a soyayya Dole ne? Tunda tace bata yi a sake mata mara tayi fitsari mana. Kazo ka saka yarinya karama a gaba da ido kamar cutar haukar ta motsa,." Rintsa idanuna nayi sabida naji ciwon maganar shi, amma ga Hammah Mohan bai kula shi ba, dawowa gabana yayi tare da riko hannuna, yace min. "Gaya min don Allah, meye nayi miki?" "Baka min kome ba, Ni da kai ne kamar bamu dace da juna ba, idan da zaka yi hakuri haka zai fi ace ana takura junan mu nan, Kayi hakuri kana da zafin kishi. Ni kuma mutum ce da Allah ya halicce ni da kaddarorrin mabanbanta,. Ban san yadda zaka dauki kowacce ƙaddara ta ba, soyayyar fatar baki zata iya gushewa daga zaran ka fahimci ƙaddara da yake yawo a kaina, don Allah kayi tafiyarka zan Nime mutum daidai dani." "Maimunari kowacce irin ƙaddara take zagaye dake zan iya zama dake a haka kai koda kuwa ace a gidan karuwai na tsinto ki, toh wallahi zan zauna dake a haka, fatana ki yarda da Ansar Yusuf yana sonki" "Hisham Waadi ANSAR!!!" Ya fada da mugun karfi, tare da mik'ewa tsaye, yana huci. "Karka mana hauka dan kasa mu Ubanka ya wanke ka akan laifin juyin mulki shine zaka zo kana mana ihu, dalla can lusari kawai" Mohan bai iya musayan yawu ba, amma kuma ya iya kirb'awa mutum rashin mutunci, dan haka bai bari Ansar ya kwace mishi ba ya buga mishi wani naushi sai da ya fadi, zai kuma na shiga tsakanin su. "Ya isa haka! Kai Hammah Mohan ka cika saurin fushi wallahi da fatar baki yayi maka magana da shi zaka rama ba da duka ba, kai kuma bari na tuna maka. Ni ne gaya maka koda maza sun kare ba zan tab'a sonka ba, bawai bana son ka bane a'a soyayya ce da kai bana ra'ayi, dan haka ka ji daga yau karka kuma gaya min kana Sona" "Amma. Munnah zan iya zama dake a duk yadda kike! Zan zauna dake a duk yadda kika zo min. Munnah ina sonki babu kishin ki a raina, sonki nake so mai inganci." Inji Ansar, "Ina son shi, amma haka zan rabu dashi, bana jin ko a mafarki xan kuma so wani bayan shi, dan haka ku fita mana a gida kar ka kuma ganin kafarku" na fada da karfi, haka suka fita a zuciye, bin bayan su nayi da harara. Domin sun bani haushi taya ina fama da Matsalata zasu kara min wani, daga Innah har Baba babu wanda iya min magana sai ma shiru da suka yi alamar dai abin yafi karfin su. *** A waje kuwa dokuwa suka yi, sosai sai da aka raba su. Ansar ya daki gefen idanun Hammah Mohan, shi kuma Hammah Mohan ya dake shi sai da ya watsar mishi da hakoran gefen hagun shi. Tare da gaya mishi sai ya karya mishi muƙamiƙi. "Ni kuma ba zan rama ba, amma sai na cusa maka bakin cikin da sai ka kusan mutuwa. Sai na maida mai mara amfani a cikin al'umma Zan sami nutsuwa, ka cigaba da abinda ka gadama, ni nasan kome kai ne baka san yadda kome yake tafiya ba, wallahi ranar da na tashi fitar da kome duniyar ka da duniyar Munnah sai ya jijjiga, sai na maida kai mara amfani ta yadda zaka wayi gari kana fatar da mutuwa kayi da...... Wash... 🙄🤔 Nagode sosai Joindah ba dan ke ba, tabbas da yau bani da wayar charger. Nagode sosai🤝 #Mai_Damby [8/7, 10:06 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1111755716?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ARAB'IN DA BIYAR. Kai Mishi duka Mohan yayi, Dan Ba'are ya rike shi. Ya kuwa fashe da dariya tare da kare kan shi kamar me tsoron duka, cikin fusata ya ce Mishi. "Dake ni! Idan ka cika dan halal idan kai namiji ne ka tsaya muyi damben niman aurenta! Ka tsaya da kafarka bawai ka koma gefe kana ihu zaka dake ba, lusarin banza dan daudu kawai, mara lafiyar gaba." "Ban ce Karku kuma min fada ba?" Na fito waje sakamakon hayaniyar su da nake ji, ganin yadda dukkan su, suka samu rauni. Kallon su nayi kafin nace musu. "Ina cewa kashe ni kuke son yi? Ina ce rayuwata tace kuke bukata?" "A'a Munnah babu haka, zan tafi zan tafi yanzun nan." Inji Ansar, ya shiga motar shi,.tare da d'aga min hannu. Kallon Mohan nayi yana kallona, juyawa nayi zan koma cikin gida yace min. "Baki gaya min meye nayi miki ba, wallahi bani da nutsuwa ki gaya min meye na miki idan yaso idan rabuwar ce zan rabu dake wallahil billahi Azim," Takowa nayi gaban shi, ina kallon shi. "Sabida kai, na rasa kome nawa. Sabida kaina ƙaddara ta fada, sabida kai yau nake kuka. Kasan me? Saboda nasan da kanka zaka juya min baya, zaka kore ni a rayuwarka, me yasa zan damu da kaina a kanka? Me yasa ba zan rabu da kai ba? Don Allah ka tafi ka barni ina son sauran farin cikin da ya rage min na hada na rufawa kaina asiri." Sannan na juya zan tafi, riko hannuna yayi, ya saka a kirjin shi. "Ji yadda yake bugawa! Ko kallon ki nake bugawar shi na daban ne, balle kuma idan ina jin saukar kalaman ki, ba zaki kashe ni ba. Ba zaki lalata min rayuwa ba, Moonah idan laifi naki ki gaya min wallahi zan baki hakuri kamar haka." Ya zuba gwiwar shi dukka biyu a kasa. "Haba Maimunari! Idan yayi laifi ki gaya mishi ke ba abin kunya bane mutum kamar Mohan yana zuba gwiwar shi a gaban ki, meye yayi miki da zafi haka? Idan baki kaunar shi." "Khalil Ibrahim, kyale ta rokonta nake." Ya fada bayan ya mike, kukan da nake yaci karfina. Kwace hannuna nayi cikin tsiwa da masifar yadda zan rabu dashi na kama fada. "Toh dole ne! An tab'a soyayya Dol..." Bakin shi na ji akan goshina. Bayan ya rungume ni. "Ba'a tab'a soyayya Dole ba, kuma akanki ba za ayi ba, Nagode sosai idan na mutu karki min kuka don Allah, kiyi min addu'a." Daga haka ya bude motar su ya shiga, tare da rufewa bai kuma kallon inda nake ba, bai kuma d'aga kai ya kalle ni ba, asalima kamar bana gurin haka sukayi tafiyar su. Durkusawa nayi a gurin ina kuka tare da shasheka, d'aga ni Innah tayi tana faɗin. "Indai laifin shi bai girmama har haka ba baki yi hakuri mana ya a sonki yana kaunarki" "So da kaunar ba zai min rana ba, zai iya gudu na." Kallona tayi tare da rike hannuna. "Me aka miki Maimunari na?" Ta tambaye ni tana min wani irin kallon tsoro, bakina yana rawa na rufe tare da rike hannun ta daya. "Innah!!" Jan hannuna tayi har cikin d'akinta, ta kuma zaunar dani, tare da durkusawa a gabana,ita kuka ni kuka. An rasa me magana a cikin mu. Sai gyada kai yake tana kara kallona hawaye na zuba a idanun ta. "Meye ya faru dake?" "Fy..de.." na fada a tsora ce. Domin nasanta da zafin rai, wani irin riko tayi min tana kuka ina kuka. "Waye ne haka yayi miki wannan wulakancin? Waye ne ya tozartaki? Waye ne ya cutar dake haka? Me kika musu da zafi? Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun,Ya Allah ka tsayar mana haka. Ya Allah ka rufa mana asiri haka." Da sauri ta ja kasan gadon ta, ta shiga niman wasu tarkace, fita tayi domin Baba yana ban daki bata zauna ba, can bayan minti arba'in sai gata, daura tunkuya tayi bayan ta wanke saiwowin da tazo dasu, ta saka a tukunyar ta haɗa mishi wuta. Ya cigaba da nuna. Ni kuma ta shigo d'akin. Tace min. "Bude naga gurin domin nasan ai baki da lafiya." A hankali na kwanta bayan na cire pant dina, dubawa tayi sannan tace min. "Kinje asibiti ne?" "Eh ban san wanda ya kai ni ba, ma dai farka ne na ganni kwance a gadon." Murmushi tayi, sannan tace min. "Da sauki sosai. Babu wani matsala zaki iya aure kuma zaki iya alfahari da kanki da darajar ki" kallonta nayi sannan na cigaba da lumshe idanuna hawaye na zuba, sannan ra gyaran min zanina. Tafita, Tun daga ranar zance ban kuma zaman kasa ba, bana tafiya ba takalmi, gashi ta sani yin azumi uku. Sabida askin da nayi, da kanta tayi ta tattalina, tare da bani. Kulawa na musamman. Haka na share kwana sha biyar. Ranar na sha shida Mohan ya kuma zuwa, ya samu tarba'n arziki a gurin su, Innah amma a gurina ko kallo bai ishe ni ba,. Haka duk inda na wuce idanun shi ne kaina kai karshe sai da na koma daki da zama. Shigowa d'akina yayi ina zaune da Laptop, ina duba wasu takarduna. Jan Laptop din yayi yana kallona. "Na kuma dawowa." Shiru nayi mishi. "Nazo ki gaya min laifina ne? Ina miki son da babu wanda ya isa yace ga karshen shi! Ina kaunarki ainun, me yasa kike bani wahala" Kallon shi nayi ya zabge ya lalace, gyada kai nayi sannan nace mishi. "Yanzun nake karanta wani case wai wata ne suna cikin soyayyar su, ita yar manyan mutane ne shi iyayen saurayin talakawa ne, shine suka fara soyayya, karshe dai anyiwa Yarinyar Fyade kuma tana can kwance saurayin taki zuwa sabida yana kishinta. Na baka labarin ne?" Kura min ido yayi sannan yace min. "Da zafi sosai, amma kuma gaskiya ina da zafin kishi, zan kuma bincika sosai idan ba ita ta bada kanta ba, zan zauna da ita amma har abada ba zan daina kallonta da wannan abin ba, sabida babu namijin da zai so yana tare da mace a keta mata haddinta, duk lokacin da ka kalle ta xaka na tuno da abin da ya faru, shin zata iya zama da kai ko zata na bin saurayin da yayi mata fyaden a karshe ma zaman ba zai yi dadi ba, sabida zargi ya shiga." Kafe shi nayi da ido, tabbas Mohan iya gaskiyar ya gaya min, dan haka bakina a laikum na rabu dashi. "Ni kuwa idan ina son mutum gani nake ko a gidan karuwai yake zan zauna da shi, idan dan ta'adda ne ma zan zauna da shi sabida kaunar da nake mishi. Mohan Mamman Nasir Aghali,kayi hakuri baka tab'a min laifi ba, sai dai ba zan tab'a aurenka bane, kayi hakuri da ban gaya maka akan lokaci ba, akwai abokina na Yaranta shi nake son aura." Juyawa yayi ina ganin kamar ma tangadi yake, oho mishi can ya kare kalau. Haka na cigaba da zaman d'akina, na bashi labarin abinda ya faru dani ya gaya min ba zai iya zama dani ba, toh me zan mishi. Dan haka ya tafi yayi rayuwar shi nayi nawa. *** Allah ne ya maida shi gida lafiya, amma yana fita a motar ya fadi, domin kirjin shi tayi mishi nauyi, haka aka dauke shi zuwa Asibiti. Yana faɗin. "Maimunari! Maimunari!! Maimunari!!!" Kira yake yana kara kira. "Khalil wacece Haka?" "Yarinyar da tayi jinyar shi ce, ban san karfin abinda ya haɗa su ba, sai dai ya bukaci rabuwa da shi." "Tana ina yanzun?" "Tana Damagaram" "Muje" ya kalli Khausar yace mata. "Mahaifiyar ku tana Dubai,.akan baikon shi, ki kula dashi. Insha Allah zan tawo da yarinyar." Haka ya fita Dan Ba'are. Su kuma likitocin suka rufa a kanshi, kallon juna suka yi. "Dr MG zuciyar shi kumbura tayi fa" "Toh meye abin yi? Idan akwai wani abu ku mishi mana," ta faɗa bayan tana kallon su. Haka suka dukufa akan shi, har sai da ya fara barci suka saka mishi ruwa da allurai, sannan suka fita dashi zuwa VIP 012. ** Tunda ya tafi sai bani da nutsuwa kuma, kallon Innah nayi tare da ce mata. "Zan koma gurin aikina." "Toh ai nima bana son na miki dole ne yasa ni shiru, amma zaman gidan kara miki damuwa yake." Innah ta koma Innah da na sani a baya, haka muka yi ta hira. Har bayan isha muna tsakar gida, muna cin tuwo miyar danyen kubaiwa,.Khalil yayi sallama, kallon juna muka yi sannan Baba ya mike tare da amsa sallamar shi. Sannan ya fita can kuwa sai gashi ya shigo da yace. "Muna tare da manyan baki ne shimfida mana babban taburma" Mikewa muka yi tare da kai kayan abincin daki, aka shimfid'a babban taburma, sannan ya shigo dasu, Ni da Innah muka kawo musu abincin, dukkan su basu ci ba, sai da na gaishe shi sannna yace min.. "Almamoon ko?" Sunkuyar da kai nayi kasa, nace mishi. "Abbu kaci abincin." "Toh Almamoon ko Maimunarin Mohan ko?" Murmushi nayi, tare da mik'ewa na kawo roban ruwa na ajiye mishi, sannan na koma dakin Innah na zauna. Sunci abincin kam ba laifi, kallon Khalil yayi sannan yace mishi. "Rabona da naci abinci kamar haka ne manta, Allah yasa Maimunari ce tayi girkin" Kallona Innah tayi tare da sake murmushin jin dadi.. "Kinga da ban ce kizo kiyi aikin tare dani ba, da babu yadda za ayi shugaban kasa ya yaba miki domin sai nace girkina ne" Murmushi nayi bayan sun gama aka kira mu, zuwa muka yi na zauna. "Maimunari bansan wani irin kaunarki Mohan yake ba, amma nayi imanin da Allah zai iya rasa rayuwar shi akanki don Allah ba dan ni ba, ba dan na isa ba. Kije ki ga halin da yake ciki. Nayi magana da mahaifin ki, yace min ya jima da bawa Mohan ke, amma ina son ku kara daidaita kanku Insha Allah zan dawo da kaina niman auren ki da Mohan. Don Allah Karki dauka dole ce, ko kuma karfin Iko ce wallahi a matsayin Uba nazo nan ba a matsayin shugaban kasa ba, don Allah ki rufa min asiri, duk yarana babu me sakani farin cikin da Mohan yake, don Allah ki so shi, yayi rayuwar kunci yayi rayuwar kaɗaici akanki ya fara soyayya." "Insha Allah zata zo ma, dama yau take cewa zata koma bakin aikinta, idan ta shirya ta biku mana" "A'a ta shirya a hankali, za a zo daukarta. Kin amince?" Kuka na saka mishi tare da gyada kaina. Haka suka yi ya farin ciki, Ni kuma aka barni da kuka, bayan ya cika mu da Alkhairi, muka ki karb'a sai da ya nuna bafa a matsayin shugaban kasa ya bamu ba, a'a a wanda ya zo niman yardarmu Yar da tafi kowace ya Daraja yazo niman, yazo ne a matsayin mai nima kuma ya samu, dan haka nashi Alkhairi ne tsakanin mu, shi ba kowa bane. Haka suka tafi rarrashina Innah da Baba suka yi tayi. Dakyar na hakuri tun asuba na gama hada kayana, ina karyawa aka ce ga mai kai ni Niamey yazo..tsoron abinda ya faru ya sani kin binshi. "A'a airport zan kai ki,daga can kuma ai jirgi zaki bi." Shine na samu nutsuwa. Na bi shi muka tafi. Karfe goma yayi min a asibitin,mik'ewa Radiyah tayi tana faɗin. "Yau duk yan uwanmu zasu zo, sabida ke Hammah Mohan yake kwance don Allah karki juya mishi baya." Murmushi nayi mata sannan na wuce dakin da yake yana barci. Daga bakin kofar nake kallon shi. Sannan na juya tare da cewa. "Zan tafi, amma zan zo an jima" "Toh shi kenan." Apartment din mu na nufa, Na samu Har Rukayyah Hussain Adam ta dawo.. "Yar gata sai yau kika gadaman dawowa." Dariya nayi sannan na nafi daki na samu a gyare wanka nayi na ci abincin da ta kawo min, muka shiga hira kamar babu gobe. Da la'asar liss muka nufi asibitin bayan mun yi sayayyan kayan dubayya, sannan muka nufi cikin asibitin, yan uwan shi da mahaifiyar shi sun cika dakin. Rukayyah ce ta samu shiga, ban iya shiga ba. "Hammah Mohan ya jikin ka?" "Da sauki kawarmu" ya faɗa a sanyayye, yana kallon kofar, ido biyu muka yi dashi na juya tare da barin kofar, sunkuyar da kai yayi yana sauraronta. Garin na bar gurin, na ban gaji wata mata ban sani ba, ina d'ago kai ta kwashe ni da mari, ban yi kasa a gwiwa ba, na rama. Sosai ta shige ta. Cikin ihu da masifa ta yo kaina, daidai fitowar shi, domin yana ganina baya fara kokarin cire karin ruwan, yana fitowa yan uwan shi suka biyo shi har da Mahaifiyar su. Ganin Hanan ta cukume ni, ya sashi shi isowa, yana zuwa ya raba mu, sannan ya kalle ni sosai. "Meye ya kawo ki? Kin zo ki karasa Ni ne? Ko kin zo ki bata min rai ne? Don Allah fita bana son ganinki." Ya nuna min hanya. A hankali rukkaya ta tako inda nake tsaye, ina huci. "Muje Kinji Kawata" ta fadi haka tana me rike hannuna. "Sai dai kuma kayi kuskure." Ta fada mishi. Komawa daki suka yi zasu mishi magana ya tsare gida. "Nairah dauki kayan fruit din nan ki wanke min ki kawo min su zanci" Kallon shi suka yi baki daya. "Akan me zaka ci abincin ta, bayan bamu san me ta kulla a cikin kayan abin gaskiya ba zaka ci ba" inji Mahaifiyar shi, "Idan kina son na rayu barni naci abin da ya fito hannunta, idan kuma mutuwata kike bukata shikenan." "A'a me yayi zafi. Ci abinka" ta faɗa, "Toh nagode" "Hammah Mohan ga abinci na kawo maka" shi da yasan ba haka kawai za a kawo mishi abincin ba, ya zabga mata harara. "Uban waye yace ki taba ta? Nace ina sonki ne?" Ya daka mata tsawa, yana dafe kirjin shi. "Daga yau kar na kuma ganin kafarki anan kwashe kayan haukarki kiyi waje dashi" Had'iye yawun tsoro tayi, tana jin kamar zai dake ta, da sauri ta fita, jikinta yana rawa. "Amma Mohan ai." "Ammyn zuciyar shi zata buga idan aka Cigaba da takura mishi." Mikewa tayi da sauri tabi. Hanan, "Amma Hammah ban ji dadin yadda kayiwa Moonah ba" murmushi yayi sannan yace musu. "Zata dawo, sai dai haka da na mata banyi dan na wulakanta ta ba, nayi ne domin kar Hanan da Ammyn su cutar da ita, Ba zan boye muku ba, Ammyn da Hajiya Karime suna kokarin mallake ni, da kunne na naji Ammyn tana bukatar a bata maganin da zai saka na bita na rabu da Moonah, idan ba haka nayi ba, zasu iya cutar da yarinyar, amma banyi dan na tozartatta ba, dan haka ku kyale ni dasu, Moonah zata cigaba da zuwa Ni kuma xan cigaba da koranta, sabida su gamsu bana son ta, idan ba haka na zasu illata mu..... #Mai_Dambu... [8/7, 8:55 PM] Sidrah❤️: https://chat.whatsapp.com/B50yxHYVIcVHx42qCXkmJ9 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ARBA'IN DA SHIDA. "Mun yarda gaskiya da abinda ka fada,.indai haka Ammyn ta koma dai Du'ai amma wallhi Hajiya Karime bata ji dadin ta ba. Karfi da yaji ta lalata mana Mahaifiya, Allah ya isa" Shikam apple yake gutsira a hankali, yana murmushin jin dadi, yana kara tabbatarwa kan shi da Kudinta ta saya mishi, wani irin gutsira yayi yana kara taunawa kamar mai ciwon hakori, ganin ya shiga shauki dariya suka yi ta mishi. "Hammah Mohan yarinyar nan ta maka mugun kamu, kan Uba. Dubi yadda yake murmushi sai kace tana gaban ka" Sake wata lallausar murmushi yayi yana kara jin wani irin dad'i a ranshi. Kwace Apple din Haddir yayi yana dariya. "Salman don Allah kace ya bani kayana" "Ka bashi" Suka hada baki suka yi. * "Insha Allah, Mohan bai da matar da ta wuce ki, karki damu ina tare dake, karki gayawa Mahaifiyarki. Zan sami yarinyar na ci ubanta.". Share kwallar ta tai sannan tace mata. "Babu kome Ammyn nagode" tana gurin har taga fitar yarinyar a cikin asibitin, sannan ta koma cikin asibitin. Tunda ta shiga cikin take cika tana batsewa, su kuwa yaran suka ajiye ta a gefe, domin dama babu wannan shakuwar a tare dasu. ** Tunda muka shiga taxi na ajiye kaina a gefe, ina jin wani irin kuka nason zuwa min, amma ban iya yi ba, har muka isa gidan mu. Ina shiga daki na zube a bakin gado tare da sake kuka me ciwo. Na rasa gane meke min dad'i, mahaifin shi ya tafi ya sa nazo, amma ya tashi yana wulakanta ni, meye nayi mishi da zafi haka? Dama baya sona ne?ko dai ya fahimci abinda ya faru ne?" Haka nayi ta kuka ina tambayar kaina, har na gaji nayi shiru, kafin na kwanta a d'akin, baki daya sai gashi na shiga wani irin kad'aici, bana son magana. Washi gari da na shirya da sunan zan tafi kotu, sai gashi na buge da nufar asibitin, har kofar dakin na isa amma na kasa koda budewa ne, haka na gama nazarin abinda zan yi kafin na leka yana rike da Alqur'ani, na jima ina kallon shi, kafin ba juya zan tafi muka yi kicibis da wata Nurse. "Lafiya!" "A'a babu kome!" Na juya na fita da sauri, bude kofar dakin yayi yana kallonta, kafin ya leka hanyar wajen. "Kana niman wani abu ne?" "A'a babu kome!" Ya fada yana dawowa dakin, itama kallon hanyar tayi tare da kallon d'akin. "Kalaman su iri daya" Shiga tayi ta bashi magani, yana sha ya nufi window ta waje, ya hangota tana mai juyawa bayan ta kalli window, kura mata ido yayi yaga yadda take share kwalla. *Meye nayi miki da zafi? Kika juya min baya* Tsare taxi nayi tare da shiga cikin ina dafe kaina, na juya na kalli window, yana tsaye. Sake labulen yayi tare da juya bayan shi. _Baka min kome ba! Sai dai ƙaddara da ta had'a mu itace zata rabamu! Ni din wani namiji ya wuce iyakar ka ne! Kayi hakuri amma ina kaunarka_ Na fada a raina, tare da jingina kaina, muna isa kotun, biyan kudin nayi sannan na nufi cikin,ina isa Alkali yana fitowa da wasu abokan shi turawa. "Bonjour Abie?" "Lafiya lau, ya jikinki?" "Da sauki Sosai" na gaya mishi. Tare da barin gurin su, "Alkali amma Yarka ce ko?" Dariya yayi yana faɗin.. "Maimunari a'a ba ita bace, amma a ofishina take aiki" "Kai Amma kamar ku ta b'ace, gaskiya." Murmushi yayi sannan ya raka su, suka tafi shi kuma ya dawo. Ya samu ina waya. "Eh Hammah ban san dai me nayi mishi ba, indai akan abinda ya faru ne Allah ya bashi hakuri, a'a bani bace yanzun haka ina gurin aiki ban je asibiti ba." "Toh shikenan" ajiyar zuciya na sauke. Lokacin da kwalla ya zubo min, kafin na fara aikin da yake gabana yana tsaye a bakin kofar. Duk abinda nake jikina na rawa, amsar takardun da suke ta watsewa yayi,tare da zaunar dani. A lokacin na samu damar kuka tun daga kasar zucuyata nake kuka. "Abie me yasa kome yake zuwa min babu sauki? Me yasa ƙaddara ta take da zafi haka? Na zata ko." "Kice Alhamdulillahi" "Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka" na fada tare da zama ina shashekar kuka,ruwa ya mika min nasha. "Iyayen ki suna ina ne?" "Damagaram!" Kura min ido yayi na wani lokaci, kafin yace min. "Kinji abinda bakina suka ce min? Wai muna kama dake?" Da sauri na d'ago kai ina kallon shi. murmushi yai min sannan yace min. "Tashi muje!" "Toh aikin fa?" "Karki damu zan dauki hutun yau baki daya akwai shari'ar da bani zan yi ba. Yau ina son nayi shi da ke ne ko baki son fita yawo dani ne?" "Zan je" Fita muka yi da shi, a hankali driven shi yake jan mu, yana yawo damu. Idan naga abu nace ina so zai tsayar da driven na saya na dawo, haka ya zama duk inda muka je babu abinda bai saya min ba, sai da muka dauko hanyar dawowa gida nayi mamakin da ya kawo ni har gida, da zan fita yace min. "Yau da na fita dake, na sami nutsuwa ya dauke min damuwar da nake da ita. Allah yayi miki albarka ya daidaita ku da saurayinki" sunkuyar da kai nayi ina wasa da laida kayan hannuna, sannan nace mishi amin,sannan na shiga cikin gidan. Sai da ya ga na shiga cikin gidan, sannan ya juya tare da barin unguwar shi da driven shi suna nufi office yayi abinda zai yi ya wuce gida. . "Karka musanta min mana tazo har nan fa! Kuma na ganta a tsaye taga lokacin da na sake labulen kan me yasa zaka kace a ita bace, bayan na ganta da idona." "Kai Hammah sai kace wacce aka sace ta, kawai kayi fatan kasami lafiya domin Ammyn tana shirya maka aiki na musamman. Ta dawo da baikon ku nan da sati daya." Inji Salman yana kallon Mohan, "Kuma da alamun ana baikon ba zai dauki lokaci ba a azayi bikin" inji Radiyah da take mika mishi ruwa. "Allah ya bata sa'a" "Bro me ka shirya mata." Lumshe idanun shi yayi tare da kwanciyar shi,yaki magana. Dan Ba'are ne ya yi amfani da shirun shi ya gaya musu shirin sa. "Amma baku da kirki! Wa Ammyn zamu watsawa kasa a idanu? Zan so naga yadda haka zai faru!" Inji Khausar tana dariyar mugunta ,dukkan su sun yarda akan bawa dan uwansu baya, kuma sun amince da abinda ya shirya musu, kawai abinda suke son gani mahaifiyar su ta amshi abin. Shigowar Primer minister yasa dakin ya kara armashi aka shiga hira. A hankali Nairah da Radiyah suka fitar da wani gown Peach color, suka nuna mishi. "Yayi kyau, amma ba zai mata kyau ba" ya faɗa yana shan kunun gyada da Khausar ta kawo mishi. "Hammah ga wani ja ne?" Mika mishi Tap din suka yi yana dubawa yana kallon kayan a hankali ya tab'a wani tare da mika musu. "Hanan fa?" Khausar ta tambaye shi daidai shigowar Ammynsu. "Tun wancan satin na ba Ammyn kudin gown ɗinta bansan ya aka yi ba" "Eh mun sayo mata Royal blue ne" "Amma Ammyn ita" wani kallon banza ta watsawa Nairah tayi shiru tana tura baki gaba. "Haba a tashi a ba mutum abinda bai mishi ba, sam bata da wani fasali idan ka cire farin fata mutum sai kace 1" Tsaki tai cikin fada da hargagi Ammyn tace mata. "Zan fasa bakinki nan idan kece zaki zauna mishi da ita! Mohan wai baka sonta?" Ta tambaye shi ranta a b'ace.."ina sonta mana" ya faɗa yana hararan Nairah. Haka suka shiga watsewa har dan Ba'are, suka bar mata dakin, nan ta ga shima ya kwanta kamar zai yi barci. Ta dauko magani a cikin jakarta zata saka mishi yana kallonta, tana gama saka maganin a cikin flast din tace mishi. "Kayi barci ne! Bari naje na dawo" tana fita ya mike tare da tausayin mahaifiyar shi, wacce irin masifa ce haka? Bai tab'a ba sai da dan Ba'are ya shigo ya gaya mishi ya shiga ya zubda har kunun yayi wani irin farau a idanu, yana zubdawa ya wanke sannan ya zauna yana bawa Mohan hakuri. Bayan sallah isha Umman Dan Ba'are da Hajiya Karime suka zo, duk da ba tafiya daya bace amma kuma a tare suka shigo dakin a cika. Nima shigowa nayi daga bakin kofar nake kallon shi, ta jinin kofar dake akwai glass, d'ago kai yayi, muka yi ido biyu. "Khalil Maimunari tazo ka tabbatar ka hanata tafiya, idan aka watse ina son ganinta," Da sauri ya fita tare da tsare ta, tana kokarin tare abin hawa. "Mss Mamman Nasir Aghali, ina za a tafi haka? Muje can ki zauna" ya nuna min guri muka zauna ina rike da kulata, kaina a sunkuye. "Gashi ka bashi ka tabbatar yaci abincin ya sha magani" "Toh amma ai shi romeo yace na tabbatar kin jira baki sun tafi na kaiki cikin dakin shi." "A'a Hammah zan tafi kawai bana jin dadin jikina ne" Saka wayar shi yayi a kunnen shi, yana faɗin. "Zata tafi fa" "Bata wayar" Mika min wayar yayi, na masa a sanyayye, sannan na saka wayar a kunnena. "Zaki iya tafiya idan kin so, bakin cikin ki bai kashe ni ba, Kinga kuwa tafiyar ki ba zai kashe ni ba, sai an jima" sannan ya kashe wayar, shiru nayi ina kallon wayar. Kallon Hammah Khalil nayi, sannan na sunkuyar da kaina, ina faɗin. "Zan jira shi" "Me yasa kika bashi wahala?" "Hammah Mohan yana da zafin kishi! Idan yana tare dani zai tsane ni wata rana" " Bazai tsane ki ba" haka ya shiga bani hakuri, har suka fito sannan ya amshi kular yana gaba ina baya har muka shiga d'akin, yana kwance yana waya, yadda yake magana a gadarance ya tabbatar min shi da Hanan ce. Dan haka na sunkuyar da kaina, ina tsaye, ina jin wani abu a raina. "Toh kasha maganin kwari ki mutu!" Kome ta gaya mishi ya caka mata Bakar magana haka oho. "Kina shan wine ai sabida gyaran jiki da gashin ki me zai hana kisha zai saka ki barci!" Kashe wayar yayi tare da sakawa a kasan pillow. "Khalil kasan yarinyar nan tana shan beer! Wallahi na zata sharri ne, Radiyah tayi mata sai d'azun da Nairah take nuna min wani video ɗinta, ina ga ita kanta bata san Nairah ta dauka ba, duba fa kimanin dubu dari uku ake sayar da wannan kwalbar, da na tambaye ta sai ce min tayi ai ba wani babu bane yana taimakawa fatarta da kuma gashin kanta! Don Allah matar da zan aura na ajiyewa Yarana." "Toh kayi hakuri mana, baka kan shirin ka ba, Angon mata biyu" inji dan Ba'are ya zoyale shi. "Zanci Ubanka dan iska, ina wasa da kai ne, mace daya ta ishe ni." "Hanan ko Maimunari?" "Mitsww! " Yaja tsaki,fita Dan Ba'are yayi ya barsu. Saukowa yayi daga gadon, ya tako gabanta, d'ago kai nayi ina kallon shi. Ina matsawa da baya. Har muka kure bangon dakin. Yayi maza Yasaka hannun shi akan karfen da maso buga kaina. "Meye ya kawo ki" "Ba gurinka nazo ba, nazo ganin Khausar ce" "Toh amma kuma shine kike lekena bakin ce baki sona ba?" "Eh... Eh... Amma ai ba gurinka nazo ba" "Toh gurin wa kika zo? Naga dai baki da mara lafiya nan asibitin." "Eh na sani" na fada ina kawar da kaina. "Toh meye kika kawo a kular?" Ya amsa yana budewa. Kamshin kayan miya da kayan kamshi ya daki hancin shi. "Ai kin kawowa mara lafiyar ki ne?" Kokarin kwace kwanon nake amma ina ya kwace abin shi. "Idan kika nace zan baki wahala" kyale shi nayi ina kallon shi, karshe na koma bakin kujeran na zauna ina kallon shi, Mikewa yayi ya wanke hannun shi, ya cinye gurasar da na kaso mishi da miya. "Nasan wannan girkin Kawar mu ce" ban kula shi ba,yana gamawa ya wanke hannun shi, sannan ya dawo ya durkusa a gabana. "Kina nan akan bakarki ko kin zo niman sulhu ne?" "Don Allah kyale Ni" na fada ina niman hanyar mik'ewa, shima mik'ewa yayi kamar zan fad'i, ya saka hannun shi a k'uguna, a hankali ya d'ago ni. "Idan kika ga kin fadi ina raye, Allah ne ya nufa zaki fadi matukar ina raye, rayuwarki zan bawa kariya da tawa" a hankali na janye jikina ina dauke numfashina. Daga Ni har shi muna tsaye rike da juna, kamar ba zamu rabu ba, kafin na janye hannuna na amshi kular na saka a laidar, waya yayi can sai ga Hammah Khalil. "Ka zauna anan zan kaita gida" "Wannan wani irin Iskanci ne? Niman Beenah nake a social media amma ban dace ba!" "Benazir kake nufi?" "Eh man" ya faɗa a fusace, kallon Hammah Mohan nayi ina wasa da hannuna. "Nawa zaka bani na baka Number ta," "Kai Maimunarin Hammah Mohan!" Mika mishi wayar nayi, ina kallon shi ya dauki Number ta, sannan ya koma bakin gadon ya zauna, yana kad'a kafar shi. "Zaka iya tafiya kawai zan ji da kome" Ya wurga mishi key,tunda muka fita escort suke bibiyar shi, sabida bashi tsaro, asali ma a bakin ward din suna tsaye, ciki ne dai basu shiga ba. Hannuna ya lalluba ya hada yana tuki dashi. "Kin razana ni a cikin sati biyu zuwa uku, sabida ban san laifina ba. Kuma ana ta bani wahala." "Ni ban baka wahala ba, Kishin da yake zagaye da ranka shi zai kaika ya baro ka, amma ni kam bani da burin cutar da kai." Juyawa yayi tare da kallona. "Me yasa, kika so juya min baya?" " Ba za a bar maganar ya wuce ba?" Na tambaye shi ina kallon gefen hanya. "Shi kenan" ya fada min, koda muka zo apartment din mu, shima zuba min ido yayi, na wani lokaci. Kafin ya ce min. "Nagode da kulawa?" "Allah ya baka lafiya" na saka kai zan fita, yace min. "An saka ranar baikona" gabana ne ya fadi sosai, kafin na juya na sake mishi wadatacciyar murmushi nace mishi. "Allah ya tabbatar da Alkhairi! Yanzun kan dole mu hakura da juna," "Sabida me yasa? Kika sani ko kizo a Matana na biyu" ya faɗa yana zolaya na." "Hmm" "Allah ya kiyayye ko?" "A'a kawai gani nayi kawai bamu dace." Bakin shi naji a saman hannuna, yayi matukar sanyi bakin shi, a hankali ya d'ago bakin shi. "Next time kika Kuskura kika fadi wani abu a kan soyayyar mu bakin ki zan kaiwa hari, domin shine tanadina na gaba" maza nayi na rufe bakin, yana murmushin mugunta,.hararan shi nayi bayan na fita. "Allah ya shirya ka" na fada ina dariya, haka shima dariya yake tare da cewa. "Tsaya don Allah na nuna miki shiriyar da Allah yayi min yarinya da kin fadi gaskiyar ki" "Ba dani ba gad'a a hurumi." Sai da yaga shiga na sannan ya juya abinshi. ... Ina shiga Auta ta fashe da dariya, tana faɗin. "Munafukai kun shirya kenan da alamun shi ya kawo ki" Dage mata gira nayi, sannan na wuce d'akina. Ina bata labarin baikon shi da Hanan, ban san me yasa ba kodan abinda ya faru dani ne haka kawai nake jin na hakura da Mohan, na cire shi a rayuwata, baki daya sai na rasa meke min dad'i. Har Abie ya fahimci irin halin da nake ciki da kanshi yake bani hakuri har ya bani addu'o'in da zan nayi idan akwai Alkhairi a soyayyar mu, karshe abinda ya gaya min ya sani jin sauƙin Al'amarin. "Idan kina son Mohan zan iya kama miki shi yadda duk duniya babu wanda ya isa ya raba shi dake, amma kuma meye ribarki? Meye zaki samu bayan soyayya kike nima? Gashi nan dai kin samu idan babu kwanciyar hankali fa, kiyi hakuri ki fuskanci ƙaddarar ki, Allah zai baki abinda kike bukata." Da wannan yanayin na hakura tare da cire raina akan shi baki daya. *** A kwanakin da suka gabata an sallami Mohan, inda aka shiga hidimar baikon shi. Da kanshi ya kawo min kayan da zan saka ranar amma naki sai da muka yi faɗa kafin ya ajiye min yayi tafiyar shi.... Zata fashe..... Gaskiya ina jin tashin daraja🤔🙄 idan kuma kayi dace na kafta toh bi ma'ana da Yaren Larabci ba zan yi typing gobe ba, haka kawai nake jin haka💓 #Mai_Dambu [8/8, 10:02 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112247835?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=QQEFDfGekFSRJARqCuAgczdBfyHHQPoGIoXw1TaQOoLLncl9SQq3Zn4Oggvn2k4IOQsrOsZ3SiMt1bhI1OjgktiAuZVMV8ZakJtY1sLTSD8fi3CxlBeppdQp3axJbI3j 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI. _SANNUN MUTANE 🤡🙋🏾‍♂️ INA GAISUWA MUSAMMAN MUTANE ANSAR DA HAJIYA LATEEFAH DA HAJIYA KARIME 💓😘 ANA TARE 🤝_ Kallon gown din nayi ina Kuma juya shi. "Amma ai wannan bai yi kama da gayyatar ki yayi ba, sabida." Kallonta nayi domin bana jin a raina ba gayyatatta yayi ba. Watsar da kayan nayi tare da kwanciya ina jin babu dadi. "Na tsane shi!" "Da gaske" "Allah ina gaya miki na tsani Hammah Mohan!" Na kuma fadar haka ina kallon kayan, "Zan yarda kina jin haushinsa amma banda tsana, meye laifin shi? Dan kawai za ayi baikon shi da wata mace?" Tashi nayi zaune na kuma kallonta. "Amma dai...." Shiru nayi tare da komawa na kwanta, ina jin daci a raina, tsaki nayi tare da juya mata baya, raina na kara b'aci, ina zan iya samun kamar shi, sai dai nasan na rasa shi kenan har abada. Da haka na tsunduma cikin tunani. ** Diffa. Sanye yake da irin kayan sakin nan, yana zaune a kujeran guragu. Ya saka hoton Maimunari a gaba yana kallon ta. "Appa!" Watsar da abubuwan da suke gaban shi yayi, cikin fushi da damuwa. "Yarinyar kawai nake bukata! Amma ka gaza niman soyayyarta, meye amfanin kiranka da sunan D'ana soyayyarta ma ta gaggare ka! Dan ina nakashe" ya faɗa da karfi. Sai da mutanen gidan suka fito. Zuɓewa yayi a gaban shi. Ya rsa yadda zai mahaifin shi ya fahimci abinda yake faruwa. "Yarinyar da tun tana namiji yace min nata sona, duk lokacin da na shirya mata wani abu bata tab'a faduwa sai nasara, yarinyar ta rike Allah sama da yadda kake tunani, Appa Munnah ba gama garin mutane bace domin yar baiwa ce tana da tawwakali don Allah kayi hakuri, idan tana rabon mu zata shigo cikin gidan nan, tunda itace kake bukata zan kawo maka ita indai zaka yi nasara a rayuwar ka." Sanarwan baikon Mohan da Hanan ne ya katse mishi sauran bayanin, murmushi yayi sannan ya ciro wayar shi zai kira Munnah sai ya fasa, dan haka ya shiga garin ciki babu iyaka. Dan haka yake jin yanzun zai iya tura mata sakon da zai saka ta amince da shi ta wata fuskar,dan haka ya tura mata da wata wayar. ** Da Asuba bayan na idar da sallah, ina kwance na janyo wayata na kunna, bayan na bude data. Na duba Internet, abu daya ne wato sake hotonan Hanan da Mohan, babu karya babu hassada sun dace da junar su. Kamar zanyi kuka haka na ajiye wayar, ina shafa kai na da ya fara tohowa da gashi, ina jin haushin kaina. Dan ma ina da kafar gashin ne shi yasa har ya fara tohowa. A hankali na koma na kwanta ina hararan wayar dan itama yanzun haushi take bani, hango sako yasani dauka na bude. Zaro idanuna nayi, cikin tashin hankali da fargaba, tare da jin cikar kwalla a idanuna. Sake wayar nayi a hankali ya fadi kasa, bayan na rike kowacce harafi da kalmomin jikin hoton da aka turo min. *_Ina ga wannan al'amari ya gani ya juya miki baya ko? Toh ina da kuma ya kara fahimtar an shiga cikin an juye bakin mai fa_* Daga Malik Dalhat. Wani irin kuka ne ya kwace min tare da cusa kaina a tsakanin cinyoyina, ina rusa kuka, kamar raina zai bar jikina, haka nasha kuka ma more, har gari ya waye ban fita ko ina ba, ina ganin kiran Mohan naki dauka, karshe goge abin nayi tare da kashe wayar baki daya. Ina jin shi yana buga kofar amma naki budewa, karya kofar yayi ya dame ni zauna akan abin sallah..na takure guri guda, takaici ya sashi takowa har inda nake yana kallona. "Toh wannan haukar da kika min zai sa na fasa abinda nayi niyya ne? Bari na gaya miki koda aurenki nayi wallhi baki isa ki juna ni ba, wacece ke da zan kira wayar ki, ba zaki dauka ba? Dan ina sonki sai ya zama na haukace akan ki? Wacce irin daukaka kike nima ne? Meye zan baki? Meye kike bukata na miki?" Mikewa nayi ina kuka tare da riko hannun shi. "Don Allah ka yarda dani! Shine kawai abinda nake bukata idan kayi min haka har abada ba zan kuma ba, ka amince ba zan maka abinda za a gaya maka ko zaka gani ba, Mohan na yarda da kai matukar zaka saka ni a jerin matanka, koda zaka iya fushi dani don Allah ka yarda dani" Jikin shi ne yayi mugun sanyi, yana kallon yadda nake kuka, janyo ni yayi tare da rungume ni. "Kina boye min wani abu da ya faru dake? Me nene shi?" "Kayi hakuri dani!" Na fada bayan na rike rigar shi. "Insha Allah zanyi hakuri dake" Haka yayi ta shafa bayana yana, faɗin. "Ina tare dake, amma idan akwai wani abu ki gaya min, bana son daga baya muzo muna samun matsala" "Babu matsalar kome Insha Allah" "Ina jiran ki, ki shirya na ajiye ki a gurin saloon." Murmushi nayi tare da kallon shi. "Na aske gashin" na nuna mishi kan. Jan hancina yayi tare da cewa. "Gaskiya ina son gashinki nan me kyau da tsantsi, dan haka muje a hada miki mayukan da zasu fito nan da wata uku insha Allah." Fita yayi na shiga nayi wanka tare da kwalliya, sannan muka fito. Gurin karyawa muka fara tafiya. Bayan mun karya sannan ya kai ni gurin Saloon, aka had'a min mayuka masu kyau, sannan yasa aka min jan lalle, tare da gyara min fuskana. Bayan an gama ya kai ni gurin aiki, yana bawa Abie hakuri. Cikin harshen buzanci suke magana, sai su kalle ni sai su cigaba da magana, kafin yayi mishi godiya da sallama ya fita. "Ashe za yi baikon shi?" "Eh Abie" "Toh Allah ya tabbatar da alkhairi!" "Amin Ya Allah," Daga haka bai kuma magana ba, nima haka sai dai hankalin mu ya raja'a akan abinda yake gaban mu ne. "Me yasa kika sare akan sha'anin ku?" "Abie shi din dan masu kudi ne, kuma uwa uba, dan shugaban kasa ne, taya zan kai kaina gurin shi, kawai ina jin rabuwa dashi shine mafi alkhairi, sabida kamar bamu da ce da juna ba" "Ni kuwa sai nake ganin kun dace da juna, kuma kunsan halin juna, zaku iya zama da juna koma yayya ne, kawai ki daina saurin karaya." Dariya nayi domin yadda yayi min maganar sai da ya bani dariya, Toh Abie kana ganin Mahaifiyarshi zata yarda? Matar da tayi mishi matar da zai aura, kawai daga ni har shi b'ata lokacin juna muke, ka duba al'amarin mana, mahaifiyar shi tana son nasaba ni kuma ko mai kwasar shara bamu dashi ni daya ne nake karatun boko, sannan kuma." "Kin yarda da Allah?" "Sosai ma kuwa!" Na bashi amsa, "Toh ki yarda da ƙaddaran ku, yace na baki hakuri gaskiya yana kaunarki,sosai kuma yana tare dake don Allah karki juya mishi baya" "Abie bani da wannan burin, amma idan ya cigaba da Zafaffa kishi babu bincike alaƙar mu bazata yi nisa ba." Na d'ago kai ina kallon tv dake office din ana kuma saka sanarwan baikon, da Yaren fillaci, anan kan sai da na dauke kaina. "Masu hakuri suna tare da Allah." Ya fada tare da mik'ewa ya kashe tv. "Na sani Abie" haka wunin ranar maganar da zai gaya min na kwantar da hankali ne, da nuna min. Ba wai na d'aga hankali na bane, amma kuma maganar gaskiya, bana jin dadin raina,.kawai ina daurewa ne dan kar na d'aga mishi hankali, Domin abin saura kwana uku, kuma nayi kokarin ganin na dauke kai na akan Mohan, amma na kasa domin komen kashin laifi idan yayi min, yanzun zan tsaya nayi ta balbale shi da masifa, zuba min ido yake na gama masifar sannan na fashe da kuka, toh a nan ne zai ta bani hakuri. Duk da haka bana iya dogon fushi dashi, a cikin saura kwana biyu, har gidan Khausar sai da ya kai ni, ya kuma kai ni gidan yan uwan baban shi da suke yan uba, Alhamdulillahi na samu kyakkyawar fahimta a tsakanin mu dasu, kuma sun mana fatan Alkhairi, dake mutum ne mai matukar ilimin dan adam, bai yarda na tafi hannu rabba ba, domin duk inda zan shiga yana min sayayya yace musu nice na kawo, wannan abin ya kara min matukar daraja a idanun dangin baban shi har suka fara adawa da Hanan. Musamman yan matan family din su, dayawa sun ki marawa Hanan baya, karshe suka shiga rokona. "Don Allah Addah Munari ki amince ki auri Hammah Mohan, don Allah karki ki amincewa wallahi muna sonki". Wannan abin ya kara sani samun kwarin gwiwar son kasancewa da MOHAN. Sai dai abinda basu fahimta ba, duk soyayyar su matukar mahaifiyar shi bata yina ya zama na banza, matukar bata kaunata babu amfanin zama dashi. Haka ana gobe za'ayi baikon ya kai ni gidan su dan Ba'are sabida akwai wasu daga cikin Familyn su da zasu zo, koda suka zo da kan shi ya kai ni. Domin har da Kakar shi ta gurin Uwa. Koda muka shiga gidan. Ba dukkan su bane suka yi na'am da ni ba, sai dattijuwar mai suna Nahnah. Ina shiga cikin dakin da take ta zuba min ido. "Ke bafulatanar ina ce?" Ta tambaye ni, "Libya-Nijar" na bata amsa, "Daga wacce kabilar kike?" "Wodaadabe Bororo" Rike hannuna tayi tsam, tana me lumshe idanunta. Kafin ta bude idanunta. "Ya sunanki?" "Maimunari!" Kura min ido tayi, na wani lokaci kafin tace min. "Allah yayi miki albarka, ya kuma had'e kanku." Na kalle shi, murmushi yayi min tare da lumshe idanun shi, yana gyada min kai. Kafin muka fito tare da mika musu laidar da nazo musu dashi, ita kuma Nahnah na bata katon laida mai dauke da kunshi takarda a cikin shi kilishi ne. Koda muka fito kallon juna muka yi tare da sakarwa junan mu, murmushi. "Gaskiya kai dan babban gida ne, kawai baiko sai kace wanda za ayi bikin shi" Hannun shi cikin aljuhun wandon shi yace min. "Eh ya za'a yi dan ma sauran basu zo ba, amma da kin ga family mu ba karamin yawa ne dasu na, muna dayawa ainun. Kuma duk da haka Abbu yana ƙoƙarin kula dasu baki daya, duk da haka kawai manta." "Idan naki fa? Amma dai gaskiya Allah yana son ka da ya kawo ka babban zuri'a gashi kowa yana sonka." "Sabida nima ina sonsu ba dan yanzun ba, ai da ina zuwa can na zauna. Toh aikin soja ba irin na kowa bane baka da lokacin kanka sai na kasarka. Insha Allah wani sati zan koma office." "Lallai kace mazaje za a saka unifoam!" Na fada mishi. "Wai haka" ya ce min yana murmushi, Baki daya mun kashe lokacin yau a tare da juna, kuma mun yi dogon tafiya, kafin ya kira aka kawo mana mota, tunda ya kawo ni gida nayi sallah tare da cin abincin, muke hira har kusan sha biyun dare, kafin yayi min sallama. Washi gari Baiko... Ina kwance bana jin dadin raina, kawai dai ina kwance ni, gashi Abie ya ce ba sai nazo aiki ba yau, ina jin a raina kamar na rasa Mohan baki ɗaya. Wayata na lalluba ka kira Hammah Mohan. "Hello!" "Hmmm" "Yau ne baikonka ko?" "Eh" Toh Allah ya yasanya Alkhairi, ba zan sami zuwa ba, Innah bata da lafiya zan je dubata a Damagaram" "Karya kike! Ba zaki zo bane kawai nagode, kuma wallahi na fasa" "Hammah Mohan, ka fahimce ni" "Ba zan tab'a fahimtar ki ba, dan haka kiyi tafiyar ki, na gode dana na jima da fahimtar ni nake hauka nake ba, maza jeki Allah ya baki sa'a" Ya kashe wayar, ajiyar zuciya na sauke na fito daga dakina ina sanye da riga da wando. Na kayan barci. Tura baki nayi tare da cillar da wayar na zauna ina dafe kaina. .... Hidimar da ake zaka rantse da Allah biki Mohan din za ayi zunzurutun yadda aka kawata kome, a cikin gidan shugaban kasa ake kome, dan haka Hajiya Latifah an shirya a bangaren Hanan kawayenta ƴaƴan manyan mutane sun halara, *_Gaskiya mura ya sani a gaba! Ba zan samu typing ɗin na dare ba_* #Mai_Dambu... [8/8, 7:33 PM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112326619?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=b5uzlwrsmnjDJy16UxrP%2B6c%2F7MtDoc5iAfHC4HQyJIms0PfUCslcpjPlXla74C0IG9WLlc5Su6cieJVelxnZUaqj64NLFkeQVg24jiQwUO0LftfuKKKLW5VGghOyRdvm 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS. "Toh ki shirya muje mana!" Kallonta Auta nayi a shagwaɓe, "Auta ina jin tsoro ne, kar naje a sami matsala." "Ba gani ba" ta faɗa cikin tsokana, "Kai Auta me zaki iya, keda ba karfi ne dake ba, balle ni" Harara ta tayi sannan tace min. "Baki da mutunci kona miskala zarati, na yarda bani da karfi..dan haka maza ki shirya muje lokacin na tafi karfe biyar za ayi fa!" Buga kofar mu akayi, ita ta tafi a hankali ta bude kofar. "Kina niman waye?" "MG Mohan ya aiko ni nayiwa. Maimunari kwalliyar" "Toh shigo mana" ta bude kofar ta shigo. Juyawa nayi na kalle ta. "Laa! Aunty Uwani shigo mana" "Ya haka karfe hudu saura amma baki shirya ba, gashi can ya addabi rayuwata da kira. Uwani ki tabbatar kin fitar min da ita, Uwani ki gyara min fuskarta." Murmushi nayi domin indai Mohan ne zai rina. "Aunty bari na watsa ruwa." "Ok! Amma tsaya ga wannan" Ta mika min wata jaka. "Ki duba zaki ga yadda ake anfani da shi." "Toh nagode" Tunda na shiga ban daki na shafa wannan, na goga wannan. Kai har su gashin hammata duk dai da na fitar, sannan na yi wanka da wani sabulu na musamman, na fito, zan goge jikina sai ga auta da wasu mai. "Malama zauna na shafe ki!" "Wallahi baki isa ganin jikina ba." "Toh ko nakira Hammah Mohan ne dan nasan shi zai iya gani har can birnin lintsin" ta fada tana min dariya. Bayana na yarda ta shafa min, sauran na shafa da kaina, bayan na gama na saka doguwar riga naje na zauna. Aka fara kwalliyar. Tun karfe hudu aka fara bamu gama ba, sai biyar saura minti biyar, sannan na mike na saka doguwar gown din da ya bani ranar, sai yanzun nake yabawa da shi, dauko min wani set na bracelet diamond ja mai mugun kyau da tsada, dan kunnen shi da abin hannun shi, da wata zobe mai mugun kyau duk nashi. Sai yar siririn agogo duk nashi. Kallon shi nayi da kyau. Ina jin kwalla na cika a idanuna, jan hancina nayi sannan nace mata. "Ban san iy adadin soyayyar da Mohan yake min ba, amma kyautar tayi min girma" "Ke dai Allah ya tabbatar da alkhairi" inji Auta. Wani hula me kyau ta saka min bayan an shirya ni, sannan aka shiga daukar hoton, tare da tura mishi. Sannan ta gyara auta itama tayi kyau sosai, buga mana kofa aka yi. Auta ta bude, "Barka da zuwa Khalil" "Yawwa Auta, kun shirya?" "Eh! Uwani ai ba dan Surukata karta ga nayi azarbabbi ba da na je na dauko Beenah amma babu kom.." Daukar wayar yayi yana faɗin. "Banza kawai idan kayi hakuri zan kawo ta, kafin a saka maka. Shege mayyen mata" "Zan ci Ubanka!" "Na yarda, ku tashi kafin Mohan ya tawo dan ba kunya ce ta ishe shi ba." Takalmin da aka ciro min na gani kamar zanyi kuka nace musu. "WALLAHI tunda Uwata ta haife ni dau daya na saka irin wannan takalmin don Allah ku barshi, zan fad'i" jan kafana Aunty Uwani tayi sai da ta daka min ta daure min belt din, sannan ta mika min yar pose din, sannan ta shiga fesa min turare, sannan ta saka auta ta riko hannuna. Muka fito. Motar da ina da yakinin bai tab'a shigar ta ba, domin naga alamar sabuwa ce, bude min baya Khalil yayi sannan na shiga auta ta zauna kusa dani, muka fara ajiye Aunty Uwani a shagonta. Mika min wata jacket yayi tare da cewa. "Mutumin ki yace ki saka." Amsa nayi, tare da rikewa har muka shiga kofar farko na fadar shugaban kasa. Rike hannuna Auta tayi, tare da cewa. "Sabida ke yau zan shiga fadar shugaban kasa, anya sunanki ba Noor ba!" Murmushi nayi tare da rike hannun ta. Muna shiga yayi parking, sannan ya kira shi. "Gamu nan" "Ok ka shigo da ita" "Toh amma tare suke da kawarta." "Ka hada ta da Radiyah" "Ku fito" haka muka fita, sai da ya kira Radiyah ya hadata da Auta, sannan yayi min jagora, har shashinsa ta baya, muka shiga ya gama shiryawa yana saka links, na shiga da sallama. Duk falon da abokan shi, na wuce su, Hammah Khalil ya nuna min dakin na shiga, tare da sallama a karo na biyu. Kaina a sunkuye, "ki karaso" yace min, a hankali na karasa inda yake. "Me yasa kike wasa da hankalina?" .hararan shi nayi sannan nace mishi. "Ni banyi wasa da hankalin ka ba" "Ok dan ina sonki sai ki ta wulakantani?" Shiru nayi, domin ya fara bani haushi. Wayar shi ya tab'a sannan yace. "Zoka tafi da ita" duk wannan jarabar da yake wallhi ya juya min baya, yana shiryawa. A hankali na juya sakamakon kwankwasa kofar da aka yi. Mamaki na bashi da bance yayi hakuri ba, har na juya zan fita naji ya ce min. "Baki iya bada hakuri bane?" "Kayi hakuri" Na fada, tare da barin d'akin, bin bayan ta yayi da ido, tare da tab'e baki, Munarih akwai ji da kai, hakurin ma a kasaice aka bada shi. Dafe kirjin shi yayi yana faɗin. "Wannan yarinya duk ranar da ta ga girma na.. na shiga uku" "Baka shiga uku ba dan iska. K'ugun kawai na gaya maka a shirye suke ka auna min Ash'aria, ina kuma da macen da take gaban ka. Yarinyar sai kac. " "WALLAHI ka fadi surar matana sai naci mutuncin ka, billahi azim." Ya fada kokarin cire kayan zai daku da dan Ba'are. "Kwantar da hankalinka, wallahi ba da manufa ba, akan me zan fadi wani abu, ai ko lokacin tana mata maza ma banga girman kirjin ba sai yau da aka saka." Cire takalmin shi yayi tare da jifar shi da shi, yana faɗin. "Ka tsaya mana dan Ubanka, na nuna maka rashin arziki. Mayyen mata kawai, kai kan ranar da ka kwana akan mace toh Billahi azim sai mun kaika turu." Daga waje yace mishi. "Eh na yarda ba laifina bane laifin kayan da suke bawa amaren ne, kai kuma ina da yakinin duk ranar da ka tabo dukiyar fulaninta, sai ka kwana goma kana hauka." "Dan Ba'are!!!" "Aghali!!" "Zamu hadu dai na gaya maka rashin mutunci zan nuna maka bani da daraja!" Haka ya shiryo tare da fitowa, yana hararan su, kusan dukkan su abokai ne na family. Wato suna ganin, shi suka kwashe da dariya, tare da cewa. "Hammah Mohan!" Suka kira sunan kamar yadda Maimunari take kiran shi. Cikin nutsuwa da wata irin sanyi, ya yi gaba. Tare da nufar inda ake taron. . Lokacin da muka fito, ya kai ni inda aka tanadar domin mutane su zauna, bayan tafiyar shi dai ga Jalilah. Tana zuwa kawai ta watsa min ruwan a jikina. Allah yasa akan jacket din ta zuba, dai da na bari zata wuce kawai na saka mata kafa, faduwa tai sosai kamar yarinya karama, mik'ewa tayi yana kallona tare da nufo ni, nima na mike, mermaid trappist gown saka, take na taka Jelar gown ɗin tare da kallonta. "Idan kika sake kika yi wani shirme zan ja takalmi na, kuma zai yaga kayan jikinki, ba zuwan ku nayi ba, dan haka wuce babu ruwana dake" A hankali na d'aga kafana kan Jelar gown din, babu musu ta wuce, jikinta yana mugun sanyi,. Sannan na koma na zauna, a hankali gurin ya shiga cika, manyan mutane da ga gwamnatin kasar suna shigowa. A hankali idanuna ya kai kan Abie, lokacin da yake gaisawa da manyan mutane, sannan na ciro wayata na tura mishi sakon. "Abie kayi kyau cikin suite" Duba wayar yayi tare da juyawa yana nima na, d'ago mishi hannu nayi ina murmushin jin dadi, takowa yayi har inda nake ya zauna. "Kinyi kyau" "Nagode sosai" Na fada ina risinawa, "taso muje na gabatar dake a gurin mutane." "Toh " nace mishi, daidai isowar Mahaifiyar Hanan, tare da Hanan tana rike da hannun Mahaifiyarta. Sanye da wani masifaffen gown Royal blue, sanye da whiter gold kan nan babu mayafi balle dan kwali, ganin kishi zai sani na kauce hanya, nayi maza na dauke kai na. Tare da barin gurin baki daya. Na nufi wani gurin na zauna ina jin kwalla na zuba min, ina jin ka fara fadin ga Mohan nan, lokacin da suka saka kidan sojojin kasar tare da taken sojojin kasar, kafin aka fara gabatar da manyan mutanen da suka halarci taron, bayan babban Chef Imam ya gabatar addu'o'in, sannan ya sakawa baikon albarka. Kafin MC din ya bayyana wasu abubuwan da suka danganci Mohan, a katon majigi. Tare da cewa. "Muna bukatar Khalil Ibrahim Dan Ba'are yazo ya gabatar mana da wannan bayanin akan MG Mohan" A hankali ya fito bayan ya gaida iyayen da yan uwa, sannan yace. "Mohammed Mamman Nasir Mohammed Aghali, wanda muka fi sani da Mohan!." Yadda yake bayanin abubuwan Cigaba da ya karu sosai da Mohan, da abubuwan. Sannan ya maida abin maganar. Nan a ka saka kidar taushi, wato (Cool music) kafin aka kira Mohan da Hanan iyaye suka saka musu albarka, tare da bayanin yanzun za ayi baikon tare da musayan zobba. Ina ganin haka na cire jacket din na ajiye musu a gurin, sannan na juya. "Kafin ayi musayar zobe don Allah a bani minti biyar kacal!" Ya fada yana kallon Dan Ba'are. "Khalil tawo min da ita" Nima na ya shiga yi, kafin ya hango ina ƙoƙarin barin gurin, cikin sauri ya tawo tare da riko hannuna, cikin karfin hali da danne kukar da ya taso min na juya. "Yana kiranki" A hankali na juya tare bin bayan shi, muna isa kuwa hasken wutar da aka saka a gurin da na Cameras ya cika fuskana. Tun kafin na isa gaban Hanan ya gama faduwa. "Ammyn ina me baki hakuri da abinda zanyi amma, iyakar gaskiya ce daga zuciyata. Maimunari itace zab'ina amma duk da haka zan amshi Hanan a matsayin zabinki" A hankali ya tako cikin wani irin izza da mulki, uwa uba kwarjini da isar shi tana kara bayyana akan fuskar shi, yana zuwa ya zuba gwiwar shi daya a kasa daya. "Zaki Aure Ni....... *_Wallahi mura ya dame Ni dakyar nayi wannan fa! Hahhhh Hajiya Lateefah! Hajiya Karime! Hanan! Jalilah! Zata fashe fa! Wai ina An Niger ne? Yasin ku fafata ko na tafi jinyar mura🤷🏽‍♀️🤷🏼‍♀️🏃🚶🤸_* #Mai_Dambu...... [8/9, 10:29 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112737045?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=Zioa4Y%2F3Hu%2BHlUSk66YueQO%2BpbPAhg0irEJcowTIrXaYPT9Z1eBnkRuAOXMIzo1imod4QTdXoGp%2FGjSekGkrqI9y9tm6Kgi%2FKpQsmzrrREW8q3mkPoldIzQqc5mqaVfv 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA ARBA'IN DA TARA. _Fatan Alkhairi ga shafin ku nan gaisuwar shi taku ce Yan Uwa Yan Nijar 😘🤝💓💞 sai kun gadama ku bawa wani domin wata miyar sai a makota 🤷🏼‍♀️🏃_ A hankali ya mika min hannun shi, tare da yar karamar kwatin da Haddir ya mika mishi. "Je t'aime tellement! Je t'aime, je te protégerai de tout mon souffle, j'arrêterai de pleurer de toutes mes forces, je te protégerai de toute ma vie. Maimoon, je te critiquerai plus que quiconque, je t'aimerai plus que quiconque, j'arrêterai de pleurer. Je rirai de ton rire, je pleurerai et pleurerai ! crois moi je t'aime même dans mon sang ! Je t'aime de tout mon cœur, Maimunari je t'aime je te supplie de m'épouser !" (Ina son ki sosai! Ina kaunarki ki, zan so ki da dukkan numfashina, ba zan taba barin ki kiyi kuka ba da dukkan karfina, zan kare ki da dukkan rayuwata. Maimoon, zan ba ririta Al'amarin ki fiye da kowa, Zan yi dariya da dariyar ki, zan yi kuka da kukan ki! ni ina son ki da dukkan rayuwata! Ina son ki da dukkan zuciyata, Maimunari ina son ki ina rokon ki da ki aure ni!). Fasali yaja tare da kallon mahaifiyar shi, sannan ya taka har gaban ta, yace Mata. "Ammyn idan ina tare dake Mantawa nake da ita, idan ina tare da ita tunawa nake dake, sabida babu mace da ta cancanci na d'aga darajarta sama dake," sannan na cigaba da cewa cikin Faransa. Tare da komawa gaban Maimunari. "J'élèverai votre dignité et votre valeur devant tout le monde, j'élèverai votre cause devant tout le monde ! je vous respecterai je respecte votre famille aussi longtemps que vous restez avec moi!" (Zan d'aga darajar ki da kimar ki a gaban kowaye, zan ririta Al'amarin ki a gaban kowaye! zan girmama ki na girmama danginki matuƙar zaki zauna dani!) A hankali ya mika min hannu, tare da kallona. Baki daya jama'ar gurin tafi suke mishi, sabida yadda yake amayar da soyayyar shi, kamar wanda aka sakawa wani abu. Idan ka cire Hajiya Lateefah da jikinta yake rawa, bata kaunar ta b'ata kome, Amma tabbas idan ranta ya kai dubu ya b'aci sosai, domin har duhu duhu take gani. "Maimunari! Gani a gaban ki, ga jama'a a zagaye damu. Maimunari ina kaunar ganinki cikin farin ciki da! Bani hannunki na saka miki." Wani irin kuka nake mara sauti,ina kallon shi. Tare da mika mishi hannu nawa, a hankali ya rike tare da saka min zuben danyen zinari wanda aka saka mishi dutse mai daraja akan shi na lu'ulu'u, tafi gurin ya dauka ina kuka tare da kallon shi, mika min karamin akwati Dan Ba'are yayi na cire zoben azurfa har da agogon shi an daura mishi madubin dutse mai daraja, haka na cire zoben na saka mishi, kwalla na zuba min, sanan na cire agogon na saka mishi, tare da kifa kaina ka gefen hannun shi ina kuka, a hankali ya taka har gaban Hanan ya dauki zoben da aka tanadar domin ya saka mata ya riko hannunta, ya saka mata, karfin hali take kawai amma ta gama firgita bata cikin hayacinta, kallon zoben take. Jikinta har rawa yake,. Duk abinda ya bukata ba ita ya bawa ba. Wa wancan kaskantarciyar ya bawa! Hatta kayan da ta saka ita ce ta zab'i na jikinta amma daga baya ta tura mishi kalar jan yaki kulata, ita da kanta ta zab'i jan bracelet diamond, amma ai gashi ta gani a jikin Maimunari. Kallon uwarta tayi hawaye na tsinkewa daga idanunta, da kyar ta samu tabbar gurin ba ita daya ba. Hatta Hajiya Lateefah da take jin kamar ya cire zucuyarta ta huta, kallon mu tayi, tana kara jin tsana da bakin cikin kamar ta shiga filin tayi ta dukar Mohan da Maimunari. A hankali aka saka kida mara sauti dan haka. Ya cigaba da cewa. "A lokacin da duniya ta manta da Alkhairi na, da aikin da nayi dan kasata da al'umma ta, sai Allah ya bani Khalil Ibrahim Dan Ba'are a kusa dani, sannan ya haɗa ni da munafukai a kusa dani wanda dasu ake kashe ni kullum. Sai ga shi Allah ya kawo min matar da ban tab'a zata zan same ta cikin sauki ba. Sai gashi ta shigo rayuwata bayan irin bakar wahalar da tasha a gurin wasu, bayan bakar azabar da tasha a hannuna, Maimunari tayi faman jinya dani ta bauta min sama da yadda nawa na jikina. Ammyn tayiwu kin manta dani amma ita saboda ni sai da aka shaka mata cocin." Ya kura min ido, ganin ina kuka sosai..kafin ya cigaba da cewa. "Sai da tayi wata daya a kwance sakamakon tab'a mata huhu da yayi, duk sabida ni. Ko makaranta ta nufa bata zama sabida ni akan lokaci zata dawo. Ita tayi ta nima min magani lokacin da iyayena suka manta dani, lokacin da kowa ya manta da rayuwar da nake sai Khalil da ita suka fahimci ina bukatar na rayu! Maimoon nagode sosai! Don Allah Karki juya min baya." Ya fada bayan ya tawo gabana yana goge min fuska na. "Dayawan masu son aurena, sai da na sami lafiya suke haukar su a kaina, amma ke da a lokacin aka nime aurenki nayi imani zaki amince, nasan da haka zaki yarda da aurena ba tare da jin ina cikin hauka ba, zaki zauna dani ba tare da kyankyame ba. Duk wacce zata zauna dani ta nuna min kauna bayan kece. Ga Mohan a gabanki ga Mohan baya tare da wata matsayi ko muƙami. Ga Mohan a gaban ki shi ba kowa bane, ga Mohan a gabanki ba dan kowa bane, don Allah ki aureni." Ya kuma dukawa. Wani irin kuka ne ya kwace min, tare da mika mshi hannu ya mike, a hankali na tsaya a gaban shi. "Na amince!" Takowa yayi tare da rike hannuna, yana kallon yadda nake kuka. Kan shi ya kai daidai kunne na. "Nagode!" Hanan kan sulallewa tayi ta bar gidan, da motar su tana wani irin kuka. Ba tare da ta kalli ganbanta ba, ta daki wata mota. Aikuwa na bayan ta da yake Binta ya dake ta, karshe dai can motar ya hantsila. Aka shiga kokarin ganin an ceto rayuwar ta. . Haka aka Cigaba da shagali mutane na bani kyautattaka wanda shi ke taya ni rikewa, mahaifiyar Hanan da mahaifinta suka fita, sannan Ammyn ta bi bayan su. Ba a tashi a gurin ba sai karfe bakwai saura aka tashi, wasu suka wuce masalaci, ni kuma muka wuce cikin part din shi. Anan muka yi sallah tare da cin abincin, muna idarwa sai gashi. "Tashi muje na ajiye ki, zamu wuce asibiti" "Lafiya?" Na tambaye shi a tsora ce. "Wancan mahaukaciyar yarinyar ce tayi hatsari" "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, muje na ganta." "A'a muje na kai ku gida kawai" Haka muka fito bayan ya cire jacket din suit din shi ya daura min, sannan muka fito da kyaututtukan da na samu,muka nufi gidan. Koda muka isa babu wanda yayi wani dogon magana kasancewar mahaifiyar shi tana ta kiran shi. Sai da ya kwashe min kayana tsaf sannan ya kai min cikin, ya fito zai tafi nace mishi. "Nagode" Hannun shi ya zuba a aljuhun wandon shi. "Godiya kawai! Na zata zan samu koda pick ne a goshina" sunkuyar da kai nayi tare da kai bakina na sumbaci daidai saitin zuciyar shi, sannan na juya da gudu ina tattare gown din jikina, rike Ni yayi tare da kai hannun shi dukka biyu, ya janyo ni gaban shi, duk da ina da tsayi amma Mohan kamar mashi yake, domin yana dawo dani gaban shi, d'agani yayi na sumbaci goshinsa. Wallahi a tunanina bakin shi zan sumbata, sai gashi na kare da goshinsa. A hankali ya dire ni. "Ki kula min da kanki" Gyada mishi kai nayi sannan na, tsaya sai da ya tafi, kafin na shiga cikin gidan. ** Wato asibitin kuwa wata shegiyar bala'i ake, domin Hajiya Karime shake Hajiya Lateefah tayi tana kuka. "WALLAHI ba zan yarda ba, idan yarinya ta ta mutu sai na kashe kowa, har dake ban da rashin girman da kika nunawa Yaranki. Ace kamar ki har Mohan zai ajiye wacce zai zab'a baki gaya min ba,ya saka mata abubuwa masu tsada" Sai da Nahnah ta kifa mata mari, tare da cewa. "Eh ya zab'eta, yarinyar da bata kyamece shi ba lokacin da yake laluran hauka itace bata dace da shi ba? Yarinyar da tayi sanadiyar samun lafiyar shi! WALLAHI ban da wannan shirmen da zan ga iyayenta a daren yau za a daura musu aure da Muhammadu, naga ta karshen haukar ku, mahaukatan banza. Ai wallahi idan Muhammadu bai auri yarinyar nan ba,sunan shi butulu, domin duk wacce zata sadaukar da rayuwar ta da karatunta sabida Muhammadu ba karamar son shi take ba, dan haka kar naji kar na gani, matukar ba daga yarinyar za a samu matsala ba, wallahi ban yafe muku ba, duk wanda ya Kuskura ya raba wannan haɗin ko ya shiga tsakanin su, Allah ya isa Ban yafe mishi ba, Ubangiji ya kawo rabon da zai kashe shi har lahira." Ta fada bayan ta zauna tana haki, a hankali ya shigo ya same su sunyi jungun jungu, zana yayi a kusa da Nahnah.. "Ka maida Maimunari?" "Eh! Na kainata" "Kaji tsoron Allah indai zaka juya mata baya, tun wuri ka rabu da ita don Allah" Rike hannun ta yayi, tare da cewa. "Nahnah wallahi ban tab'a. Jin a raina zan juya mata baya ba, ban nime ta dan na wulakanta ta ba, asalima ina mata wani irin kauna ce, mara algus. Nahnah meye ribata idan na wulakanta ta, Ina son Maimuna." Rike hannun shi tayi tare da cewa. "Allah yayi maka Albarka." Daidai fitowar likitocin, a yadda suka yi bayani babu wani abinda ya faru da Hanan buguwa ce kawai tayi a goshinta, sabida da daka seat belt, sai damuwar da yake damunta, Mohan najin haka yayi musu sallama tare da Nahnah suka bar asibitin, Khalil da ya kawo mahaifiyar shi, nan ya same su, ana kulla sharri domin har sun kuma dinkewa, amma suka yi kamar basu ji su ba. Bayan tafiyar su suka shiga tattaunawa, daga Hajiya Lateefah har Maman Hanan a jikinta suka kwana, washi gari tana farkawa tayi ta kuka tana kiran Mohan. Yana barci aka kira shi, babu yadda ya iya haka ya taso yazo, tana ganin shi ta mika mishi hannu, karasawa yayi ya rike hannun ta. Haka tayi ta sauke ajiyar zuciya. Karshe dan Iskanci a jikin shi tayi barci. Iyayen kamar su zuba ruwa a kasa su sha. Da gangan suka sami likita tare da cewa kar ya sallame Hanan bayan an tula mishi kudi me shegen yawa. ** Tun daga ranar da ya dawo dani sai da muka yi kwana biyar bai kirani ba, bai nime ba, idan na kira shi zai ce min nayi hakuri yana Busy. Karshe dai ba tafi asibitin da kaina bayan na mata sayayyan kayan masarufi, ina shiga ward din na same Iyayen a tsaye, suna gani na suka mike. Allah cikin ikon shi sai ga Abbu yazo dubata, shine suka maida kudirin su, cikin sanyin jiki na gaishe su. Sannan na shiga d'akin, na same shi zaune ta zuba mishi kafaffun ta, yana karanta mata story book. Wani irin sanyi jikina yayi a karo na biyu. "Hanan ya jikinki?" Banza tayi min. "Bana son damuwa baki ji tana tambayar ki ba!." " Da sauki" ta faɗa tare da harara na. Ture kafarta yayi tare da ja min kujera na zauna, shigowar Abbu yasa ni mik'ewa, ba kuma gaishe shi. "Ya iyayen ki?" "Suna lafiya" "Masha Allah, Hanan ya jikinki?" "Da sauki Abbu" "Toh Allah ya kawo sauki zan koma. MG Office dinka yana jiranka fa! Nayi hakuri naga kamar baka Fahimci haka ba, dan haka gobe ka shigo Office akwai aiki sunyiwa Khalil yawa." "Insha Allah!" Bayan fitar shi ba kalle su, sannan na mika mishi kayan da nazo dashi. "Allah ya baki lafiya" na mike zan fita ya ajiye kayan tare da fisgo ni. "Meye nufin ki? Ina ta miki magana sai share ni kike!" "Toh kayi hakuri." Na fada mishi ina ƙoƙarin janye jikina, sumbatar kumatuna yayi tare da wuyana duk da hijab ne a jikina, da sauri na ture shi. Dariya ya saka tare da cewa. "Muje na goge laifina da nayi" Haka muka fito, ya kalle su yadda suka cika fam. "Ammyn bari na ajiye ta a gurin aikinta?" Budar bakin Maman Hanan tace mishi. "Toh Hanan kuma fa? Kasan likitoci sun ce ba a son ka barta ita ɗaya." "Idan ta mutu fa kabarinta daban nawa daban, idan ta so.ta Cigaba da kwanciyar ta a nan, babu abinda zai canja. Domin daga gobe zan koma bakin aikintae Insha Allah,tayi ta kwanciya idan Mohan ne zai bata lafiya, ina da abin yi daga yau bani kuma dawowa." Babu abinda ya dame shi duk da mahaifiyar shi tana tsaye bai hana shi fadar abinda yake ran shi ba, yayi tafiyar shi tare da rike hannuna. Muna fita na fisge hannuna. "Wato bani da daraja, shine ka share ni na tsawon kwana biyar, ba dan nazo ba haka zaka Cigaba da jinyarta, ni kuma na mutu ko? Nagode" na fada bayan na juya zan tafi. "Toh kiyi hakuri mana! Ke nifa kina burge ni! Hmm wallahi tafiyar tafi maganar ban sha'awa!" Da sauri na juya tare da bin shi zan buga mishi jakata. Rike hannuna yayi yana dariya. Bayan ya kai bakin shi kunne na. "Insha Allah wata me zuwa Abbu zasu tafi nima min auren ki duk da nasan an bani ke, sauran kuma a daura auren, kinsan Allah! Yadda nake tausayin ki. ba zai hanani amsar hakkina ba, dan haka ki nutsu sosai, domin akwai karamin yaki a gabanki, namiji nake sosai kuma girma nake dashi daga cikin wandon na," da sauri nan juya tare da cewa. "Subhanallahi!" Tare da niman hanyar guduwa, riko ni yayi tare da bude min motar na shiga ina kauda kaina, haka muka nufi gurin aikina, sai dariya yake min tare da kallon yadda kunya ta kama ni. Alhamdulillahi duk wani farin ciki da annashuwa na samu, Mohan yana aiki amma idanun shi yana kaina, kome namu kusan a tare muke, a gurin aiki idan ba meeting ba, ba zaka tab'a ganin mu Bama waya ba, haka tasa har an saka min ido, Abie kuwa bani lokaci yayi, dan na maida hankali akan abinda nake shima kuma yana taimaka min. Gyara rigar shi ta Alkalai yayi tare da kallona. "Yau zan shiga aiki a kotu ko zaki ajiye wayar ki mi shiga tare!" "Toh Abie" na kashe wayar bayan na tura Mohan sako, muka fito tare, ban san me dai ba yana gana ina binshi a baya. "Tsaya" yace min, da guda wani katon kadangare ya nufi kaina,sai da yazo dab dani, kafin ya tsaya cak. Ya kasa motsi. "Koma inda aka turo ka" da gudu ya kuma juyawa, abinda ya kusan sumar dani kenan, sai da ya tab'a ni. "Kuyi hakuri da Typing errors din da suke cikin rubutun domin babu editing 🤷🏼‍♀️🙋🏾‍♂️* Mai_Dambu [8/9, 3:16 PM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112772393?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN. Jan wani irin numfashi nayi tare da niman zuɓewa kasa, ya riko hannuna. "Ke tashi matsoraciya kawai." Kiran wasu lauyoyi mata yayi tare da gaya musu maza su kai ni asibiti, idan kuma zasu iya taimaka min ba sai mun je asibitin ba. Amsawa suka yi da toh suka kaini Office din su, suka taimaka min na farka, sannan suka shiga bani ruwa, kasa sha nayi domin na gama razana, shiru nayi tare da jingina kaina da bango. Har ya fito, hankalin shi yana kaina, yana zuwa ya ce min. "Tashi muje" Haka ya saka ni gaba muka nufi gidan shi, cire kayan shi yayi tare da saka wasu kayan, ya shiga min rubutu a jikin allon karfe, ya nutsu yana rubutun da tawwadar mai zafi,sabida tana tafasa ce ake rubutun dashi, yana gamawa ya wanke min da ruwan zamzam mai zafi dan har yana tiriri. Ya mika min fuskar shi babu alamar wasa yace min. "Nasan kina addu'o'in neman tsari, amma sha wannan makiyan shi sun rub'anyan da! Ta ko ina aika zakina samu, dan haka nake kyautata zaton an fara bibiyar ki, maza sha ba mutum ba ko ifiritu yake, zai ganki ya barki sai dai a kare a makirci da munafunci ba boka ba ko malami ne, idan ya nace zai tab'a miki wallahi kwayar idanun shi tsiyayyewa zasu yi. Idan kuma aka dage na miki sharri hauka mutum zai yi domin da bakin shi zai magana." Sai da ya gama min bayani, sannan ya bani wani Magani nasha, kafin na kwanta a dogon kujeran falon shi, bai tashe ni ba. Sai da aka yi azahar na tashi nayi sallah sannan ya mika min abinci. Awaran madara soyayya sai yaji da dafaffen nama wacce aka dafa ta da madara, har karasa yadda daɗin shi yake, sai shinkafar da aka dafa da ruwan kwakwa. Ina gama ci. Ya kalle ni. "Duba wayarki mutumin ki ya shiga kotu sau uku yana niman ki" A kunya ce na dauki wayar na kunna, sakonni shi kawai suke shigowa, kiran shi nayi. "Kina ina?" "Ina gidan Abie kazo ka ɗauke ni" "Toh gani nan" "Kina son Mohan kamar yadda yake sonki" sunkuyar da kai nayi, ina wasa da cokalin hannuna. .. hira muka sama sama har ya iso, harara ta yayi sannan yace min. "Kin kyauta min!" "Zauna kaci abinci" "Toh Abien Moonah" ya faɗa a zolaye, murmushi nayi na zuba mishi. A hankali yake ci yana kallona. "Muna nake kika yi girkin nan ba? Domin nasan baki iya girki ba" "Subhanallahi! Maimunari, dama baki iya girki ba?" Taka Mohan nayi tare da hararan shi. "Wash ta taka min kafa, Abien Moonah kaga zata cire min yatsu." "Gulmar ka ya ja maka" ya faɗa mishi haka. Wayar shi ya dauka bayan ya danna wata lamba yace. "Akwai yarinyata zata fara zuwa daukar darasi Insha Allah Asabar da lahadi. Sauran ranakun idan ta taso aiki.zata zo" "Abie har da Auta" "Toh su biyu ne" Hararan Mohan nake kamar idanuna zasu fadi kasa, mutum ya zama gulmammame, Haka muka sha hira sannan muka mishi sallama, bayan mun kuma hanya yake ce min. "Yau naji kamar nayi hauka da aka ce min kin suma, ina meeting na fito muje na ajiye ki a gida sai na koma domin ni suke jira." "Toh Sarkin gulma" "Eh na yarda" Haka ya ajiye ni a gidan, na samu auta ta gama abincin, cikin tsokana nace mata. "Kwashe kayan shirmen ki nan ba ci zanyi ba, naci me dad'i a gidan Abie na" "Wallahi baki isa ba har dare shi zaki ci" Haka dai yanayin yake tafiya, ban san wanda ya gayawa Ansar anyi baikona da Mohan ba, sai kirana yayi yana faɗin. "Munnah amana bai ce haka ba, ashe kuma anyi baikon ku baki gaya min ba? Amma har yau ban cire rai da samun ki, domin nasan ke allura ce cikin ruwa mai rabo zai dauka, dan haka ina ban ina miki fatan Alkhairi, amma ban cire rai dake ba" "Ansar ni fa bana son damuwa, dan haka ka bar ni da abinda nq zab'a don Allah ka nime wata mace mana, ina ruwana da kai ne, iya abokin shawara na dauke ka amma na Fahimci kai baka san haka ba, Mohan shi zab'in raina ne kai kuma iya abota kawai na dauke ka. Don Allah karka min abinda zan tsane ka har abada." Na kashe wayar, tare da share batun shi kamar ma babu abinda ya faru. *** Ina ajin daukar darasin girki aka kirani, ban dauka ba. Sai bayan da muka fito na dauka. "Maimunari ce?" Aka tambaye ni, "Eh nice" na bata amsa, "Toh kizo gurin Saloon din Uwani" "Ban gane ba dawa nake magana?" "Idan kin matsu ki" "Toh" *** Hira suke da Khalil da sauran abokan shi, akan yadda za ayi tsarin bikin shi domin nan da kwana uku za a tafi Damagaram niman auren Maimunari. Sako aka turo mishi, yana kishingide ya duba wayar dan a tunanin shi Moonah ce. A hankali ya bude an rubuta a kasar hotunan da videos din. *Ka tambayi matar da zaka aura maza nawa ta sannan dadin su haka! Maza nawa suka kwanta da ita? Ka tambaye ta sau nawa tana zubda cikin? Wannan hujjojin idan basu isa ba, zan kara maka wasu hasken domin ina son na ceto ka daga gurbatacciyar zuri'ar da zaka kai cikin Ahalinka ne."* Mikewa yayi tare da barin falon, ya bude videos da hotunan, zuɓewa yayi akan gwiwar shi, tare da fasa wata irin ihu,, sai da Khalil ya biyo shi. Saka wayar yayi a cikin aljuhun shi. Ya dauki Jacket din shi. "Mohammed Mamman Nasir, lafiya?" Bai basu amsa ba. Ya ja motar shi da gudu ya bar gidan. A sanyayye na sauka a motar, naci kuka har na godewa Allah. A hankali nake takawa har na isa bakin apartment din naji wata irin birki, juyawa nayi naga Mohan ne, fuskar shi babu annuri. Yana zuwa ya fisgo hannu na, ya nufi motar shi dani. Ya cusani sannan ya juya ya koma mazaunin shi ya tadda motar muka bar gurin, ban yi mamaki ba, sai da muka bar garin Niamey, ya faka birki tare da cilla min wayar shi. Yana huci. Bude wayar nayi dake nasan key din, na shiga hango abinda nake b'oyewa. Ban san ya akayi ba kodan zan rabu dashi ne, na sake mishi murmushin takaici, nace mishi. "Meye a cikin dan kawai kaga videon ina holewa?" A birkice ya kalle ni, ya ma rasa me zai min, kallona yake yaga babu wani abu a raina sai ma dauke kai da nayi, tare da fara kokarin barin cikin motar, ya saka lock, sannan ya kuma fisgar motar. Muka dawo Niamey. Lokacin Mahaifiyar shi tana kiran shi, har bakin apartment ya dawo dani, ya bude min kofar da kanshi, na fita ina wasa da jakata. "Ba zan iya miki kome ba, kuma har gobe ina kan baka nason aurenki amma ki sani na tsane ki kamar yadda na tsani abokin gabana, sai na azabtar dake ta hanyar da baki zata ba, munafuka mai fuska biyu." Murmushi nayi mishi sannan sannan na shiga cikin gidan abina, ina shiga na wuce d'akina na zauna tare da rufe kofar, ashe kuka rahama ce, domin an wayi gari na kasa kuka ma. Haka ina ji ina gani barci ya kaurace min. Damuwa tayi min yawa. Ban gaya kowa ba, haka na yi ta shiru ina gayawa Allah kuka na.. ** Yana shiga cikin gidan su, ya zube a falon Mahaifiyarshi, tare da dafe kirjin shi. Mika mishi Tap din tayi. "Yarinyar da ka nuna kana son sama da kowa ita ce ta sayar da Soyayyar ka. Kaji irin hirar da suke da Hanan." Tab'a play yayi tare da kallon murmushin da take.. "Dama ba son shi kike ba?" Hanan ta tambaye ta, "Bana son shi, idan zaki iya sayan soyayyar da nake mishi na karya bani kudi, na bar miki shi har abada" Kallon ta Hanan tayi sannan tace mata. "Yan mata dayawa burin su Mohan ke kuma kin same shi kin watsar." "Mahaukacin zan so? Ina bani kudi domin soyayyar karya nake mishi" idanun shi yayi jajjur, ya mike a hankali, yana kallon aka mika mata chep ta mike tare da barin gurin. Mikewa yayi tare da barin gurin Ammyn shi. Ya shiga dakin shi ya zauna ji yaƙe kamar zuciyar shi zata fashe, ranar ko masalaci bai shiga ba, a dakin shi yayi Sallah. Bayan isha Hanan tazo ta kananeye shi, sai da ya buga mata tsawa ya wurgota waje daga dakin shi. Haka kawai ya tsani kowa. ** A hankali soyayyar mu ta koma k'iyayyar mu, kulawar mu ta koma watsin mu, ban san me yasa Ubangiji ya saka min hakuri akan shi ba. Sai dai ko da wasa bana bin ta kanshi,, a hankali na sauya daga yadda nake na koma shiru shiru, Abie yaso fahimtar halin da nake ciki na ki. A cikin tsakanin na nufi Damagaram, nayi kewar su. Kwana na uku, na dawo gurin aiki na. --- Nazo shiga harabar gurin aikin na hango motar shi, dauke kai na nayi, tare da nufar hanyar da zata kai ni cikin Office din Abie. Ji nayi an riko hannuna, ban yi mamaki ba, dan haka na juya na kalle shi, ja na yayi tare da kai ni cikin motar shi na zauna. Ya shiga, wani gurin shakatawa ya kai ni, inda babu cunkoson mutane, ya nuna min guri na zauna. Zama yayi yana kallon yadda na dauke kai na. "Idan kudi kike bukata me yasa zaki sayar da soyayya ta? Duk fadi tashin da nake akan ki bai isa ba, kin ci Amanata ban miki wani abu ba, ace kuma ke da bakin ki. Kike fada cewa baki sona? Soyayyar karya kike min? Meye nayi miki da zafi?" Ban ce mishi kome ba, sai murmushi nake ina kallon shi. Sannan ya cigaba da cewa. "Na zata ke din kamilar mace ce,, mai daraja ashe ke din watsatsiyar mace ..." Bnsan lokacin da na kifa mishi mari ba, tare da kallon cikin idanun shi. "Wannan ya zama kashedina da kai na karshe karka kuma tab'a kimata" Na mike tare da barin shi a gurin cike da mamaki, ba marin bane ya bashi mamaki, yadda ta iya kare kimarta. Hannun shi ya kai tare da shafa gurin, sannan ya mike yabi bayanta, yana kallon yadda take share kwalla, haka ya tab'a mishi zuciya, yjaa kallon ta shiga motar haya, haka ya bi bayan su, aka ajiye ta a gida. Tunda ta shiga ta zauna take kuka. Tana son Mohan, amma tana ganin kawai kamar yadda mahaifiyar shi ta bukata haka zaa yi. Abinda ya faru kuwa bari mu waiwaya bayan. ** Lokacin da na sauka a bakin shagon Aunty Uwani,.na shiga manyan motocin alfarma na gani ina ganin haka na fahimci daga fadar shugaban kasa ne, dan haka na shiga a sanyayye, na samu babu kowa a shagon sai Ammyn da Maman Hanan, sai Hanan da Jalilah, ina tsaye. A hankali naja kujera na zauna ina kallon su. Tasowa Hanan tayi zata mare ni, ta kasa isowa inda nake komawa tayi ta zauna. Sannan tace min. "Ki cire min zoben hannun ki" kallon zoben nayi tare da sake murmushin farin ciki. "Ai ko mutuwa nayi zai yi wuya a cire shi a hannuna domin zobe ne da Masoyina ya saka min" "Mara kunya! Ba zaki cire zoben ba, domin kasawa ce ta saka abinda kika saka.!" "Allah ko?" Na tambayi Mamanta ina d'ge mata gira. "Nuna mata suwaye wadannan" A hankali suka miko min hoton su Innah da Baba ne. Anan ne zuciyata yayi rauni. "Zaki iya rabuwa da shi ko sai na saka a kashe min iyayenki! Idan har akwai abu me daraja toh wallahi bayan iyaye ne zaki rabu da Mohan ko sai na saka an yanke wuyar su." Mikewa nayi tare da cewa. "Zan rabu dashi, meye a cikin soyayyar shi bayan ina da iyayen da suka fishi. Alhamdulillahi da samun iyaye na gari da nayi, amma ki ajiye a ranki wallahi kin kashe d'anki da hannunki,.kin lalata farin cikin shi!" "'Mika min chep tayi sannan tace min kar na kuma dawowa rayuwar shi " wannan sun ishe ki rayuwa domin iya arzikin da baki taba samun ko gani Bane!" Murmushi nayi sannan nace mata. "Zan dawo miki dashi lokacin da ya dace nagode" Ina gama fadar haka na juya na bar gurin, ina tafiya ina kuka sai da nayi tafiya mai nisa, sannan na samu guri na zauna na sha kuka na ya ishe ni, sannan na mike na nufi gida, ina sauka yana zuwa ban san meye yasa kaddarata take da zafi haka ba...... Wasan yana tafiya fa..... *_Wallahi kuyi Vote yau ina son na baku page 3 Insha Allah amma sai kunyi comments da Vote 🤷🏼‍♀️🤔🙄_* #Mai_Dambu [8/10, 11:13 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112993401?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=lW5RihoQ3v8FZFWeHyymHjbPBLOXqm7aK4EKMuRrfSy%2BfSjbHsNuLRY8JQnuIpGqm8aZk9dQwvCQ4LSVWXgTHbqEvuaBGA%2Ba9UjO%2FHjd0TMtTTHl8QCE2uzXe1MDgaIR 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN DA DAYA. Ina dawowa ya tare ni da wani shirmen shi, taya zan saurarre shi. Bayan ya gama min duk abinda zai kuma yace zai tab'a mutuncina, akan Mohan na fada gararin rayuwa. Yau shi yake zagin mutuncina, saboda ƙaddara ta faɗa min. A hankali na shiga ban daki nayi alola nazo na tadda sallah, ina idarwa na kwanta. Gashi auta bata nan ta tafi gida, bani zuwa ko ina. Tsawon kwana uku ko kofar falon mun ban leka ba, ina kwance. Nasan ban da lafiya amma na rasa waye zan kira, ranar da jikin yayi min tsanani kamar zan mutu. Shine na tashi tare da ɗaukar wayata da ta mutu, dakyar na jonata, tana kawowa na kunnata. Sakon shi sun kai dari dai na Abie da Auta, a hankali na shiga sakon Auta na kirata. "Auta..... Kizo... Zan ... Mutu" na fada mata, kafin na kashe wayar, na kuma kiran Abie. "Abie.. zan.. mutu... kirjina... Numfashina" a hankali na fada tare da komawa na kwanta. ** Ya fito kenan daga Shari'a, suna tattauwana da wani Alkali, kawai ya ga kiran Maimunari, dauka yayi tare da sakawa a kunnen shi, yana faɗin. "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, gani nan" Da sauri ya shiga ofishin sa ya dauki abinda yake da muhimmanci, sannan ya fito. Driven shi ya mike. "Maza kai ni, Apartment din yarinyar nan" Da sauri ya shiga motar, suka bar kotun. Ita kam Auta tana katse kiran Mohan ta kira dan tana da number shi, yana ganin kamar ba zai dauka ba, ya saka a kunnen shi. "Hammah Mohan, Maimunari fa bata da lafiya wallahi ta kira wai zata mutu." Bai san lokacin da yayi watsi da abinda yake ba, ya nufi gidan. Yana isa ya samu ana ta kokarin bude kofar dakin su. Yana zuwa ya daki kofar da kafad'ar shi, amma bai bude ba, cikin zuciya ya ta fi da gudu ya tokari kofar dai da ta balle, ya hangota kwance daga ita dai kayan barci riga da wando, rigar me hannun shimi. Kuma rigar irin shara shara ne. Da wani karfi ya maida Abie waje. "Don Allah ka tsaya, Iyalina ce karka je kanta haka wallahi mutuwa zanyi idan wani ya kuma ganin matar da zan ajiye a Ƴaƴana" ya faɗa idanun shi na kawo ruwa. Murmushi Abie yayi tare da jin tausayin yarinyar, cire ƙatuwar jacket din shi yayi yana faɗin. "Kaji a ranka ni Ubanta ne, ba zan tab'a ganin wani abin da zai d'aga min hankali ba, saka mata bamu da lokaci." Haka ya saka mata sannan ya dauko ta cak, ya fita da ita, motar shi ya saka ta. Suka nufi asibiti da ita, kuma dukkan su. Cikin rawan jiki aka amshe ta, tare da nufar dakin gaggawa da ita, tun da ya dauke ta, yaga yadda take zubda kwalla. Haka ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba, zama suka yi kowannen su da abinda yake damun shi. Lokacin da Khausar ta fito. "Me ya faru ne hakan jinin ta ya hau sosai ga zuciyarta yayi mugun kumburi, wallahi aka Cigaba da haka. Zata iya rasa rayuwar ta, don Allah a kula sosai domin rayuwarta yana cikin hatsari" ta faɗa tare da mikawa dan uwanta, takardan fita yayi da mugun sauri. Kifa hannun shi yayi a fuskar shi, tausayin halin da yarinyar take ciki ya kara raunana mishi zuciyar shi, kaunar yarinyar a jinin shi yake jin shi. Haka ya dawo da kayan da aka bukata, kiran Khausar yayi ya mika mata, ta shiga dashi. Yana zaune a gurin har zuwa azhar, sannan suka fita zuwa masallacin sabida lokacin sallah da ta shigo, bayan sun idar, suka dawo lokacin an sauya mata daki,haka suka zauna a jikinta, aka rasa waye zai tafi ya bar dan uwan shi. Dole Mohan ya kira Radiyah, ita tazo ta zauna. Sai da ta kwana ta wuni sannan ta farka daga dogon barcin da ta samu, tayi. A hankali nake jin zafin da yake kirjina yana raguwa, ina jin sauƙin duk wani damuwa da yake raina ya ragu, a hankali na fara bude idanuna, haske ne ya cika min idanuna kafin na lumshe idanuna, na kuma buɗe idanuna. Lumshe su na kuma. *Indai da haka zaki rayu sai kin mutu sau dubu! Tashi domin ki tsaya da kafarki bude idanun ki! Rayuwa anyi shine domin bautar Allah da kuma faffutikar rayuwa tashi domin faffutikar rayuwar tashi domin rayuwar iyayenki suna tare dake maza tashi* "Aaaah!" Na ja numfashi tare da bude idanuna tar, ina kallon su. Murmushi Abie ya sakar min yana dauke kwallar da yake gefen idanun shi, ya karaso inda nake ya rike min hannun. "Muna sonki! Muna kaunar ki, me yasa ba zaki rayu dan mu ba? Don Allah ki tashi muna nan domin ke!" Ya fada tare da damke hannuna, kwalla ne ya zubo min ina kallon shi. Tare da gyada mishi kai. "Toh tashi, tashi ki nuna min jarumta ki" kokarin tashi nake ya dage goshina. "Da saura amma ki kula da lafiyar ki" Daga haka ya mike tare da barin d'akin, haka Radiyah da Khausar suka taimaka min na tashi, brush ta kawo min da ruwa na wanke bakina, sannan suka bani ruwan zafi nasha, tare da taimaka min na shiga wanka. Ina fitowa naji karfin jikina sosai, sannan na gabatar da sallah da ake bina, tare da wanda ya wuce ni, ina idarwa na fara azkar. Shigowa yayi tare da Dan Ba'are. Ko kallon shi ban yi ba, haka na idar na mike muka gaisa da Khalil, sannan na juya musu baya, ina tari daukar tissue nayi na goge jinin da yake fita ta bakina. Tare da tara su a guri guda sannan na juya ina amsawa likitan da ya shigo duba ni. "Subhanallahi!" Wani abu ya tab'a can sai ga likitocin sun tawo har da Nurses, suka shiga duba zuciyata da abubuwan da yake faruwa. Takowa yayi har gaban su, ya zauna tare da riko hannuna. Ya saka nashi a cikin nawa. "Don Allah!" "MG Mohan kayi hakuri ka bamu guri" Haka ya mike tare da basu guri, ina jin su, suka min allura bayan wasu mintina barci yayi gaba dani. "Zuciyar ya tabu fa, kawai abinda zamu yi mu daurata akan maganin amma zuciyar ta riga da ta sami matsala." *** Bayan kwanaki ƙalilan jikin Maimunari yayi sauki sosai, saboda takanas Abie ya dauko wani likita daga Canada wanda kudin shi kawai da za a dauko shi ba karamin kudi bane, sati daya kawai yayi da izinin Ubangiji sai ga Maimunari tana walwala, ana hira da ita, sannan ga uban maganin da ya daurata akai. Wanda duk Abie ne ya dauki nauyin shi. Lokacin Mohan yayi mishi magana abinda ya faɗa mishi yasa sanya shi jikin shi yayi sanyi. "Ban yi haka da kome ba, sai dai ina jin kamar Maimunari jini nace shi yasa na mata duk abinda ya dace da akan lafiyar ta, meye amfanin dukiyar da ba zata amfane ni ba, bani da kowa sai Allah, dan haka babu kome idan ma na tashi duk wasu abubuwa na zan mai da sunayen ta kai." Ta wani bangaren kuma ya sani a gaba da nasiha, da fada irinta d'a da mahaifi, muka naji dad'i domin sabida haka naji kwarin gwiwar tashi daga ciwon da nake, na cire Mohan da rayuwar shi a gabana, a yanzun kuwa so yake mu dawo kamar da, amma naki sai da nayi sati Daya aka sallame ni lokacin na ji dadi sosai. Tunda na dawo na shiga hada kayana tare da niman haya. Kusan babba gari akwai tsadar dan haka na duba yan canjin da suke cikin account ɗina, ko nace account ɗin Mohan, akwai kudi dan sun wuce canji, na kama wani gida a can wani unguwa daban, sannan na kwashe kome nawa na kai, ko Auta naki gaya, sai da na gama kome na gidan har katifa da kome na bukata, sannan na dauki wayata na danna Number shi. Yana dauka na saka a kunne na. "Assalamu alaikum!" "Waalaikumun Salam!" Ya amsa min. Shiru muka yi tare da rike wayar, daga Ni har shi. "Kana ina?" "Bana gari! Ina Maradi domin ina wani aiki a tsakanin jibiya da Maradi" ya bani amsa, "Toh babu damuwa idan Allah ya nufa ka dawo ina son ganinka! Amma ka kirani." "Toh babu damuwa" ya faɗa min, har zan kashe wayar ya ce min. "Ya jikinki?" "Da sauki" na bashi amsa, "Kina shan magani?" "Eh ina sha" "Toh ki kula da lafiyar ki, babu dogon tunani! Cikin satin nan Abbu zai tafi Damagaram." "Humm! Da an hakura da zuwa can akwai abinda yake da muhimmanci a tsakanin mu. Idan an cimma matsaya sai a kai ga maganar aure ko?" "Maimoon meye nufin ki? Wani matsaya kuma? Bayan mun baiko!" Ya fada a fusace, "Mohammed Mamman Nasir Aghali, idan ka dawo zaka ga koma meye amma idan kana son kome ya tafi daidai ka fara zuwa gurina! Idan ba haka ba kuwa wallahi billahi azim, zan baka kyautar da zata dame ka" daga haka na kashe wayar, ban kuma bin ta kanshi. --- "Khalil ka tabbatar ka nimo min ita, taya za ta bar gidan ba tare da ta sanar dani ba?" Ya fada a fusace, bayan sun gama wayar da Maimunari ya kira Dan Ba'are ya gaya mishi ya duba mishi Ita. Koda yaje ya samu dakin babu kowa, sai kayan Auta. Hankalin shi yayi mugun tashi. Dan haka ya sauke ajiyar zuciya yace mishi. "Mohan meye ya haɗa ka da ita? Haka kawai bazata dauki kayanta tabar gidan ba" "Khalil babu lokaci ne, idan na dawo zan gaya maka amma bari na fara ganinta, tun." Haka suka kasar wayar, tashin hankalin da yake ciki. Allah Allah yake ya gama abinda ya kawo shi, ya koma. Ranar da ya koma bai b'ata lokaci ba. Ya dauki hanyar. * Ina gurin aiki Abie ya kalle ni. "Uwata ina MG ne bana ganin shi?" Sosa wuyana nai tare da cewa. "Baya gari ne, amma ina kyautata zaton zai iya dawowa cikin satin nan." "Allah ya nufa ya dawo dashi lafiya." Ya gaya min, "Amin Ya Allah" na fada ina aikin, ina halkance dashi kawo min hirar Mohan yake amma fir naki kula shi. Har muka tashi naki yarda muyi maganar Mohan din lokacin da na dawo gida abinci na ci tare da kwanciya, ina nazarin matakin da na daukar kallon zoben hannun nayi a cikin kasa da wata daya kome ya ruguje, haka na tattara kome na zuba a gefe bayan nayi sallah. Sannan na gyara kwanciya na, haka lokacin sallah isha, nayi na gabatar da sallah, ina idarwa na zauna a gurin har nayi sallah shafa'i da witirin,. Ina idarwa na kwanta. Nauyin da nake ji kullum ya ragu min. * Lokacin da ya iso gidan, a gajiye ya shiga Part din shi, yayi wanka sannan ya fito, yana share jikin shi ya gama gajiya ko cikin gidan ba zai samu damar shiga ba, dan haka na kwanta yana son gobe lallai ya hadu da Moonah. Kusan barcin ranar kasa yayi shi yayi, yana kara nazarin videon din? Ranar da abin ya faru, ina ta shiga ranar da aka kashe Malik? Sannan Meye ya faru a ranar? Yana niman sanin ba'asi kome, a shagon saloon din Uwani aka yi wancan abin taya aka yi, hakan bai zo mishi tunanin shi ba. Ya manta da Uwani baki daya, bari ya fara haduwa da Moonah sai kafin ya fara diran akan Uwani da Hanan. Tashi yayi ya fito waje, sannan ya d'aga kanshi yana kallon sama, yana mai tuna abinda ya faru a tsakanin su. Lokacin suna dubai, wani irin yanayi yaji na damuwa, ya bada akwai abinda aka yiwa Maimunari haka kawai ba zata aikata kome sabida son ranta ba. Dan haka insha Allah gobe zai ji da kome. ** Washi gari. Ina karyawa naga kiran shi baki dauka, ina gamawa na dauki kome nawa na nufi waje, ina fita na sami abin hawa. Sake kirana yayi na dauka. "Malam ina da abin yi, idan na gama zan kiraka." Na kashe wayar baki ɗaya. Ina shiga kotu wanda ya rage mana kwanaki na kammala shi. Ina shiga na same Abie ya shiga dakin nazari zai shiga wani Shari'a, nima mai da hankali nayi d abinda yake gabana. Karfe biyu na mike tare da yiwa Abie sallama na tafi. Ina fita na kira shi. "Ka same ni a inda ka kaini ranar" "Toh" ya faɗa min a sanyayye, ban damu da jin haka ba, kawai abinda nasani zuciyata, ta gama bani shawarar ta dace. Kuma ina kaunar iyaye na. Dan haka bana jin zan yi nadama ko danasanin abinda na aikata, ko zan aikata bana jin akwai wani kuskuren da zanyi, bana jin zan yi wani cizon yatsa akan abinda na aikata, kawai zuciyata ya bani shawara kuma kamar yadda Mahaifiyar shi ta bukaci na rabu da mata danta ko ta kashe min iyaye na, tabbas zan yi haka. Sai dai ba zan iya cire Mohan a cikin zuciya ta ba, ba zan iya raba ruhina da ruhin Mohan ba, duk abinda zai yi zuciyar mu tana had'e da juna, amma dan ta gane dan ta baya cikin mutanen da idan na rabu dasu zanyi danasani ba. Kawai zan rabu dashi. Zan nisanta kaina da shi, zan tafi nayi tafiyar ba zata dashi, ba zan kuma dawowa rayuwar shi ba, zan nisance shi na tafi kamar yadda bai sanni ba haka nake son na kasance. Ina son nayi tafiyar ƙaddara wanda nasan bai zama dole na waiwaye shi ba, so nake nayi nisar kiwo. Yadda koda zai ganni sai ya gama shan bakar azaba da bakin ciki, tare da cire tsammanin da gani na zan bayya mishi. Ko kasan ban tsani Mohan ba, asalima shi ya tsane ni ya tsane ni tsana mai matukar zafi da cin rai. Baya bukata na a rayuwar shi , yasa baki daya yaki tsayawa ya fahimce ni. Gida na koma tare da watsa ruwa kasancewar ana zafi, ina gamawa na shirya cikin riga da wando na English wear, na saka wata Jacket din da ya taba saya min, rigar cikin fari ne wandon kuma baki ne, sai na daura Jacket din mint color, na daure kaina da mayafi nayi kyau sosai. Sannan na dauki ladies boots shallow shoe, baki tare da gyara fuskana na manna bakin madubi tare da ɗaukar yar karamar pose mai Chain na rataya a ƙafadana. Sannan na nufi waje, na tari abin hawa bayan na fito daga Unguwar. Na gaya mishi inda zai kai ni, bai wani ki ba sabida kudin da ya faɗa min zan biya na amince, ina tafiya a hankali maganar Mahaifiyar shi take dawo min bayan ta sallame ni a gurin saloon din zan fita tace Min. "Dakata!" Tsayawa nayi ta tako har gabana. *_Nasan waye Mohan! Kuma idan ya nemi sanin dalilin rabuwar mu ki nime amsar da zata tarwatsa mishi tunnain shi ki gaya mishi! Idan kika sake haka bai faru ba. Toh wallhi zan kashe iyayenki! Ina son ki saka shi ya tsane ki tsana mai muni! Matsiyaciya yar talaka jinin tsiya da masifa_* Iska na ja lokacin da mai taxi din tace min. "Mun iso yan mata!" Fitowa nayi na bashi kudin shi sannan na wuce inda zan shiga gurin, daga nesa na hango shi. A hankali na cigaba da takawa, sannan na isa gare shi. Zama nayi tare da cewa. "Barka MAJOR GENERAL MOHAN MAMMAN!" Cike da Mamaki yake kallona, kafin ya gyara zama yana d'aga hannu, sai gashi a cika mana gaban mu da abinci. "Bana jin yunwa!" Kallon shi nayi sannan na tab'a zoben hannuna. A hankali na mike tare da dawowa gaban shi na zauna a jikin table din, na shiga zare zoben a hankali, fuskana. Na kai kan nashi a hankali na sunkuyar da fuskana sosai, na hada bakin mu guri daya, lumshe idanuna nayi bayan na kalli cikin nashi, sannan na shiga sumbatar shi, baki daya jikin shi ya mutu. Ya jima yana niman wannan damar amma bai samu ba, ya jima yana dakon wannan al'amarin amma bai ga zuwan shi ba,yau da bai san meye ta shirya mishi ba,ta sumbatar shi nake har nayi nasarar riko hannun shi, na cusa mishi zoben da na cire a hannuna. Sannan na janye bakina. Ina sauke numfashi, kafin nace mishi . "Ubangiji ya hada kowa da rabon shi! Kayi hakuri kaje na samu wanda nake so ANSAR. Allah ya baku zaman lafiya da Hanan, na zab'i Ansar abokin tarayya na, domin bai tab'a zargina ba ko ya cusguna min ba. Ina son iyayena kai ma ka tafi kayiwa iyayenka Biyayya fatan Alkhairi" A hankali na juya tare da barin shi a gurin kamar gumki, ya kasa kome yana rike da zoben..... Breakup *Zaku yi hakuri domin labarin nan yana da mugun tsawo kuma bana son na yanke wani part na labarin dan haka Insha Allah idan na kai Page 60 to 70 zan tafi hutu sai na gama Kishi INSHA Allah zan cigaba dan haka ku Cigaba da bibiyar labarin Yanzun aka fara idan kuma kuna so na yanke babu damuwa wallahi sai na gutsire shi 🤷🏼‍♀️🙄🤣 Alqur'an babu wani abu dan gaskiya ko hudu nake baku bai zama dole na gama shi da wuri ba bana son nayi shi da gudu bana son na yanke shi dan haka Insha Allah na kusan tafiya break na gaya muku ne dan ku sani kar na tafi a fara nima na🚶🚶🚶🏌️* #Mai_Dambu [8/10, 11:13 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1113280247?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=ml%2Bd8%2BtyaNvCS53u6EaYCY0%2BG5P22hSwCFwvGtn%2BKunHRm1zijdp8fID0AwXDh4gnK9vZRZB50KRbcFjAmVYTaXq5PR1XBfOZ44m3%2FgOsffzZwrch908ki14DMntH%2FiK 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN DA BIYU. Dafe kirjin shi yayi tare da kurawa Zoben idanun, a hankali ya shafa bakin shi. Yana jin alamar maikon bakinta, sake juyawa yayi yaga babu ita babu alamar ta. Yason ya tashi amma ya kasa koda motsi ne, wayar shi ya janyo tare da kiran Dan Ba'are. "Khalil kazo" ya faɗa a wani irin murya, cikin rudrwa ya shiga tambayar shi kana ina ne? Ya gaya mishi inda yake, kafin ya katse kiran, saka zoben yayi a gaba, yana kallon shi. Har Khalil ya iso gurin shi. Bai tab'a sanin yana kaunar Maimunari ba sai yau da ya kasa bude baki ta bada labarin abinda ya faru,sai yau da yana ji yana ganin zuciyar shi tayi wani mugun nauyi. Sai yau da kome nashi ya tsaya cak. Yau yake danasani mara amfani. "Mohan ka kirani kuma ka zubawa zoben idanun meye yake faruwa?" "Ta rabu dani!" Ya fada a wani irin yanayi, idanun shi sunyi jajjur. A wani irin kidima Khalil ya ja kujeran ya zauna yana kallon shi. "Meye kayi mata? Wallahi haka kawai ba zata rabu da kai ba, ka gaya min meye kayiwa Yar mutane. Kafin na ci Ubanka dan iska kasan ba zaka iya hakuri da ita ba ka cutar a zuciyarta? Ka koya mata sonka? Karka manta kana da kane mata meye yasa baka da imani ne? Meye yasa baka tunanin kowa sai kanka? Toh shikenan Alhamdulillahi, Allah ta hada kowa da rabon sa, matsiyaci mara mutunci kawai." Tab'a wayar shi yayi tare da cilla mishi videon, dauke kan shi yayi tare da gaya mishi da wani abu daya da yasa shi sanyi sama da farko. "Mohan! Kasan Allah idan har Ina son Beenah aka kawo min ita, tayi ciki an zubar dashi kai a sa ma taxo min da cikin kaunar da nake mata ba zai tab'a barina na duba cikin ba, fatana ita nake so. Kuma ko a gidan karuwai na ganta zan zauna da ita balle kai da ka dauki yar mutane har Dubai ka shiga da ita kuka kwana daki ɗaya, baka lalata musu ita ba, ta zauna tayi jinyar ka, baka lalata ta ba. Sai yanzun da wani jahili ya turo maka hauka? Tun wuri ka kirata kuyi Magana" Allah Sarki jikin shi yana rawa ya kira ta, tare da cewa. "Moonah ki Fahimce mana, kin bar zuciyata cikin tashin hankali! Muna ina sonki dole nayi kishinki!" "Mohammed Mamman Nasir, ina ga kamar mun wuce wannan yanayin ko? Amma ka tambaye ka! Shin da Ni da Budurcina wanne kake bukata?" Ta watsi mishi tambaya, "Munari dukkan ku ina sonku, dake da Budurcin ina sonku" ya faɗa a mugun tsora ce, "Karya kenan, wallahi sai ka zab'e da ni da Budurcin wanne kake bukata?" "Ina son dukkan!" "Toh tunda kana bukatar dukka sai kayi hakuri da Maimunari kake bukata zan iya duba wani abu, amma dake Budurcin kake bukata kaje yana gurin Hanan ni nawa Malik ya rabani dashi kaje na maka tsana irinta k'iyayya da abokan gaba. Mara lissafi kawai. Kuma wallahi ka nime ni sai na illata rayuwarka kaje kaci yar da aka haifa yau ba gobe ba, mara imani da sanin ya kamata, tir da soyayyar da ta had'ani da kai, tir da zama da kai" Kashe wayar tai yana kallon Khalil kamar zai yi kuka, mik'ewa yayi tare da zuba hannun shi a aljuhun wandon shi yana faɗin. "Fatan Alkhairi, idan ka sami damar kashe wutar da kishinka ya kunna ina nan ina jiranka, amma tsakanin ka da Allah, ba iya shi bane matsalar da zata iya hakuri meye ya faru?" Domin dai ba zai iya barin Mohan cikin takaici ba yayi tafiyar shi. "Muje shagon saloon din Uwani." Taimka mishi yayi suka fita bayan ya kai shi motar ya dawo ya biyan kudin abincin da suka saya, sannan ya tafi ya ja shi a motar shi, Mohan Mohan kuma ya kira driven Khausar mai suna Haliru yazo ya kai motar gidanta. .. Cikin bakin ciki ya ke sauraronta. "Wallahi ban tab'a ganin mutane marasa imani irin Hajiya ba, kayi hakuri sunan ita ta haife ka, amma bata damu da abinda ke so ba, sannan ita Hanan din mahaifiyar ta, fadi tashi take sabida ita. Wai Hajiya Latifah ita kuma kashe D'anta take.. nan suka kira yarinyar bayan sun gama bincike akanta sannan suka saka aka dauko hoton iyayen ta, ta rabu da kai ko su kashe ta, haba iyaye ba abin wasa bane, ko kai ne autan maza wallahi na gama zama da kai sannan tayi mata gargadi akan karta bari ka sani ai yarinyar ta bani tausayi." "Mun gode sosai Uwani" inji Khalil, sai yanzun ya fahimci dalilin da abin yayiwa Munari yawa, ga na Mohan yana zargin ta ga Mahaifiyar shi da Kanwar ta suna kawo mata farmaki. "Dole ko nice na rabu da kai, dole na nisanta kai na da kai, wallahi maimuna Yar halak ce, ta nuna maka ita bata da sama da Iyayenta kai kuma sauran naka ka tsaya kayiwa naka iyayen biyayya." Daga haka ya kawo shi gida, sannan ya kalle shi. "Masu iya magana da larabci sunce Alhubbu fihi mararatin, so yana tare da bakin ciki da farin ciki, dan haka kayi hakuri zanen ƙaddarar ku ce, Allah ya baka hakuri rashin da kayi Ubangiji ya tabbatar maka da Hanan a matar ka ita kuwa Maimunari, Ubangiji ya bata wanda zai aure ta babu Budurcin ya zauna ta da ita haka!" Wani irin sanyi jikin shi yayi, a hankali yake d'aga kafa, sannan ya shiga falon ya samu duk suna cin Abinci, kallon Mahaifiyar shi yayi sannan ya tafi inda take ya ajiye mata zoben da Maimunari ta ta dawo mishi da shi, sannan yace mata. "Ita Mahaifiyar Hanan sabida farin cikin Yarta take wannan hidimar, ke kuma sabida ki lalata min farin cikin na kike kome ko? Toh Alhamdulillahi, Maimunari ta fasa aurena, kuma na rantse da Ubangiji Rahama. Kuka hada ni da Hanan sai dai wata ba ita ba, dan zan kashe ta" Ya fada tare da nufar hanyar part din shi, hango Mahnoor yayi da Hindu. Tausayi yaran suke bashi, tun daga lokacin da ya fahimci Hajiya Safiya ita ke mishi wani abu, haka ma Primer minister ya fahimci haka, shine ya kore ta a gidan yanzun haka bin abokan shi take tare da yan uwansa, akan a dawo da ita sharrin Oga shaidan ne. Ya tattara ta ya watsa gefe can, yanzun yaran an saka musu kahon zuga a cikin gidan musamman ma Hajiya Lateefah, shi yasa idan yana gidan suke zama a part din shi, yana son kanen shi. Kuma abinda yasa yake burin Auren Maimunari domin ya tattara Yaran su koma gaban shi. Kama hannun su yayi suka shiga part shi. Abincin gwangwani ya basu. Sannan ya koma uwar dakin shi ya kwanta, kamar wanda aka mintsina. Ya mike tare da surar key motar shi ta fita da sauri, gidansu Hanan ya nufa, tun a cikin motar ya zare belt din shi na aikin soja, yana shiga cikin gidan, ya same ta da Kawayen ta suna maimaita abinda suka yiwa Maimunari, tare da kiran mahaifiyar shi jaka. Wato da bawan Allah nan ya zage yayi ta dukar su, yayi ta kwallon dasu sai da yayi musu kaca kaca, sannan ya nutsu ya juya yana nuna su da dan yatsa. " Ki saka a ranki wannan wasan ba ayi kome ba, domin sai na miki wanda yafi haka." Sannan ta fita ya bar su a gidan domin Hajiya Karime tayi tafiya. ---- "Ban gane abinda Mohan ya faɗa ba! Kina nufin kin sami yarinyar ne domin ta fasa auren shi?" Inji Primer minister, "A'a wallahi sharrin yarinyar ce kawai." "Ammyn sharrin Munari kika ce? Bayan barazanar zaki kashe iyayenta meye na tsare miki da zafi ne haka?" Ya fada a mugun raunane. Dakatar dashi Primer minister yayi yana kallon shi, kafin tace mata. "Ina jinki ko na kira a kawo min Hanan da Karime ne? Na saka a kira Uwani ne?" "A'a Alhaji nayi domin yarinyar bata dace da Mohan ba, kuma ai yar matsiyata ce. Babu karya a cikin shi, waye ke daukar nauyin su banda shi." Yadda take maganar da kwarin gwiwar ta, san zata aikata dan haka ya kalli Mohan. "Ka rabu da Maimunari, ka zauna da wanda Uwarka zata baka, Ni kuma zan yiwa Maimunari mijin ban mamaki." A firgice ya mike tare da dafe kirjin shi, sai zuɓewa yayi a kasa. Duk soyayyar da yake yiwa Mohan, amma yau yaji aranshi bari yabar shi da uwar shi taji yadda ake rayuwa, dan haka ya tsallake su tana ihu a taimaka mata, ya kuma buga kashedin kar a tab'a mishi motocin gidan shi, Mohan din ya mutu yana da wasu Yaran. Ihu da niman taimaka ta gigice, dan haka ta shiga kiran yan uwanta, tana cikin wannan yanayin Hajiyar Hanan ta zo da nata tijarar, ta kuma yi alkawarin sai ta illata Munari da Mohan. Karshe Hajiya Nuratu ta kira Mahaifiyar Khalil, ta gaya mata abinda yake faruwa. Dole ita da mijinta da Khalil suka zo gidan aka kai Mohan Asibiti. Abin tausayi kuka take tana faɗin. "Don Allah ku taimaka min Yarona ya dawo daidai na amince ya auri Yarinyar indai itace rayuwar shi." Dr Khausar da tasan matsalar yayanta kallon mahaifiyar su tayi sannan tace mata. "Ammyn dama farin cikin shi kika watsar shine har zuciyar shi take niman bugawa? Toh Alhamdulillahi. Ki duba d'anki wallahi ba zan duba shi karshe ki kuma wurga shi cikin tashin hankalin da yafi wannan ba. Kunga ku bar mata D'anta ta kula da lafiyar shi." Cak likitocin suka fito, tare da juyawa zasu tafi. "Zuɓewa tayi akan gwiwar ta, na amince na Yarda, Ku duba shi don Allah wallahi da kaina zan tafi niman auren shi da ita don Allah ku rufa min asiri, na tuba nabi Allah da Manzon Allah. Ku duba min shi." "Dr Khausar! Don Allah!" Khalil da Mahaifiyar shi suka masu magana. Dakyar aka samu suka amince, tare da shiga cikin dakin, suka fara aikin su. Har kusan asuba suna tsaye kafin suka fito, zama Khausar tayi tare da fashewa da kuka. Dukkan su tunanin su ya Mutu ne, dan haka Hajiya Lateefah ta zauna dirshan ta fashe da wani irin kuka, tana kuma kara kuka. Shiga dakin Khalil yayi ya hango shi da wasu karafa, kirjin shi yana sama da kasa. Sai na'urar da suke aiki akan shi. Duk karfin zuciyar shi sai da kwalla ya zubo mishi, wani irin soyayya sukewa junan su haka, wata irin kauna ce haka. Soyayyar gaskiya ce, soyayyar gaskiya sukewa junan su, shi yasa kome nasu yake tafiya iri daya, rayuwar su ce ta banbanta amma kaddarata su tafiyarta daya ce. "Ya mutu ne?" "A'a, Umma sai dai a koda yaushe zai iya mutuwa, domin zuciyar shi tayi wani irin laushi har ta tsage, saboda kumburin da tayi lokaci guda. Idan ya cigaba da kasancewa a haka bakin ciki zasu iya masara rayuwar shi, ina ga gwara Ammyn tayi mishi fatan ya mutu kawai domin mutuwar zata iya zame mishi hutu ne a gare shi." Bayansu yi sallah asuba, Khalil da Hajiya Latifah, suka wuce Damagaram.... *** Ina barin gurin Mohan, gida na dawo na hada kayana ina son jin dumin Innata, dan haka na wuce Damagaram. Kome dare alƙawari ne a jikinta zan kwana, dan haka tafiyar dare muka yi bamu iso ba, sai karfe goma sha biyu na dare, dan haka na biya motar ya sauke ni har kofar gidan mu, sanan na buga kofar sosai, Baba yazo ya bude min. "Maimunari kece a daren nan?" "Eh Baba nice" Amsar kayana yayi ya wuce dashi cikin gida, ni kuma na rufe gidan. Nabi bayan shi, Har dakin Innah tana barci na shiga, a hankali na cire takalmi na, na haura bayan ta na kwanta tare da rungume ta. "Waye ya gaya miki ban san kina kusa ba, kwanta ki huta." "Banyi salollina bane." "Tashi muje." Haka ta raka ni nayi alola nazo na gabatar da sallar da suke kaina, sannan na kwanta a bayan ta, sai lokacin na fashe da kuka, na shiga bata labarin abinda ya faru. Shafa bayana take tana faɗin. "Kwanta kiyi barci, ai kina son Mohan, yawan rikicin ku karfin soyayyar ku, yawan makiyan ku. Kafuwar kaunarku. Karki damu Insha Allah. Ubangiji zai daidaita ku kinji." Koda na fara barci mafarkin Mohan nake a cikin mawuyacin hali, yana mika min hannun. Amma naki tare da juya mishi baya. Sai da wasu mutane suka zo tare da kama hannun shi suka saka a nawa. Abu daya nayi ta nanatawa,.karshe barcin da ya ishe ni tashi nayi na Innah ta rakani nayi alola kuma, na gabatar da sallah nafilla, har asuba ni da Innah muna kan abin Sallah. Wayata ce tayi kara na dauka. "Abie ina kwana?" "Lafiya lau. Ya kike?" "Alhamdulillahi! Yau zaki shigo da wuri ne?" "Kayya Abie gani a jikin Innata sai wata sati zan dawo, na tattara wasu bayanan na kai makaranta, tunda sati biyu zamu gama" "Toh babu damuwa ki gaida min Innarki da baban ki" "Zasu ji Insha Allah" katse wayar yayi, nan nake bawa Innah labarin Abie, da irin taimakon da yake min... "Allah ya saka mishi da Alkhairi" ** "Karka Kuskura ka bita zuwa Damagaram, wallahi fushina a ya haura kanka, kuma kika sake kika taka damagaram a bakin aurenki billahi azim. Shi kuma idan zai iya ya tashi domin rayuwa sai da faffutikar. Kaunar da Uwar shi take mishi ne, dan haka ya kwanta a gurin" "Abbu!" D'aga mishi hannu yayi tare da wuccewa, ya shiga motar shi, har zasu tafi yace a dakata. Tare da bude kofar motar yace. "Uwar me kake da ba zaku tawo aiki ba, wallahi idan ban ji labarin ka tafi aiki ba, sai na kore ku daga kai har shi din." Sannan ya rufe kofar suka yi tafiyar su, haka Khalil ya koma gida ya nufi office din shi, kai Abbu ma bai da kirki, domin kuwa haka yayi ta sawa ana duba mishi ko Khalil yana nan. Bayan ya gama abinda zai yi. Babban Aminin shi Professor Ibrahim Dan Ba'are, ne a gaban shi. Yana sosa kai. "Jiya da na ritsa Khalil ya gaya min yarinyar da yake waya da ita har biyun dare, bai boye min ba ya gidan Marigayi Dr Khalid ce, dan haka na yi kokarin na bincika sai na samu yarinyar karama ce, shekaru shatakwas. Amma ina niman alfarma ka barni na nimawa Mohan auren Maimunari,.kayi hakuri tayi laifi ta tuba, kai kuma ka nimawa danka yarinyar can don Allah. Mun girma da yanzun ba da bane, da ake ganiyar samartaka. A duba Yanzun yaran Khausar uku. Yaran Muslima hudu(Kanwar Khalil tana zaune a Saudiya mijinta dan jakadar Nijar ne a Saudiya, daga ita har mijin Likitoci ne, domin tare suka taso da Khausar tare aka musu aure.. mijinta mai suna Miqdad.... *Yau kam babu three pages biyu ne Insha Allah... Masu cewa ko minti biyar basu yi page ya kare Sannun ku🤣🤷🏼‍♀️🤔 🙄 wato jiya dan dad'i har da cewa kuna jiran gud 9ty😏😒☹️🤨 Toh indai ana son haka a fito a nuna min kaunar da ake fadan nan ta hanyar sayan book din Kishi a tsakanin zubda jini idan ba haka ba zan iya kiran Kaunar da Fake na karya ce 🙋🏾‍♂️ dari uku 300₦ ne babu tsada sai Chakwakiyya 🤦🏼‍♀️ Hajiya naji alart ga Number na nan0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank a Turo min shaidan ta nan 08130269641 idan da gaske ana yina naga truelove dinku ta nan 🤷🏼‍♀️😒😏* #Mai_Dambu[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1113306431?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=MylozxK1LL0LZmGH%2BFlqDRo0TQ1Q9yGEG9nFFLmRkE9c1Tezw88rwfc5nN0EYZgvek%2BtvlgPbqgF8xcCF0NBZoEs3rVxEEf5He91kHbbcO253bO6iKoETacuVt1pplyW 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN DA UKKU. "Wannan wayon fa? Kawai ka manta da batun Mohan zan duba al'amarin Khalil Insha Allah. Sai maganar gaskiya, so nake ta Fahimci yarinyar yana da daraja a rayuwar D'anta. Domin nasan Lateefah sanin hakika bai zama dole ta saduda ba, nasa Lateefah kwanton bauna tayi" "Wallahi tayi laushi." Saboda girman juna da suke gani yasa shi hakura, tare da sake musu lokacin, ba tare da iyayen sun fahimta ba, a cikin yan kwanakin Aka nimo Auren Maimunari inda aka biya sadakinta mafi girma da darajar, domin da zinari Baban Khalil ta biya, Itama beenah Primer minister da kanshi ya tafi har Maradi aka nimawa Khalil auren Benazir, inda aka saka bikin su Khalil wata shida masu zuwa, shi kuma Mohan sati biyar sabida halin da yake ciki. A cikin kwanakin suka roki Maimunari tazo ta ga halin da Mohan yake ciki, haka suka tawo har da Innah da Baba, wani abin takaici koda suka iso ta nime Abie wayar shi baya shiga karshe da ta je kotun aka ce yayi tafiya. Su kuma kwana ɗaya zasu yi kamar zanyi kuka haka na hakura. Washi gari har gida Khalil yazo daukar su, dake na mishi kwatancen gidan. Bayan tafiyar su ban kuma bin takan Mohan ba, oho su suka sani. Domin ba zan je ana min kallon wata aba ba. Satin shi biyu kwance, wanda yayi daidai da dawowana kwana goma, Mahaifiyarshi ta kirani. Na gama tattara abubuwan da suka dace ba abinda ya kawo ni. Daukar wayar nayi. "Hmm! Bayan abinda ya faru ne zaki zo ki duba shi ba sai an roke ki?" "Ammyn ni fa banyiwa kowa dole ba, idan yaga zai tashi ya tashi idan kuma kwanciyar ce tayi mishi bismillah, banda ina ganin girman Abban Khalil da Abbu. Allah na tuba ina zan kai sauran hauka." "Kome aka yi da jaki sai ya ci kara," "Hali zanen dutse, kamar yadda aki'data take linzamin na, haka kema ba zaki sauya ba, dan haka ki aura mishi matar da aka haife ta domin darajar duniya, kuma kika kara gaya min magana sai na gayawa Abbu domin ya bani Number shi, sannan wayar da muke dake ina ɗauka, idan kika dame ni na tura mishi, kuma kika iya tunanin balle ni da nake karanta shara'a" Na kashe wayar abuna, na cigaba da aikina. "Maimunari dawa ake rigima?" "Abie mahaifiyar Mohan ce zata zage ni, ni kuma ba zan iya hakuri ba" "Toh ai babba ce! Kar ki kuma mata rashin kunya kinji! Bana son jin haka" "Toh Abie" Mika min wasu takardu yayi, sannan yace min. "Maimunari zaki tafi baki gaya min kome akanki ba, sanan nima kuma ban gaya miki kome a kaina na, wannan takardun dukiyata ce, da wasu kadarorrin duk da ba dukka na tab'a ba, amma gasu nan na saka sunanki a kai, ina da Yaro ban sani ba ko namiji ne ki mace ce, amma na tafka laifukan cin zarafin mata, na nadamar abinda na aikata, Maimunari Yarinyar da naso na wulakantatta ta hanyar daukar ta ranar aurenta." Kasa fada min yayi yana share kwalla da suke zuba min. "Har yau Zainab tana raina, har kwanan gobe ina son Zainab, ta tafi tabar ni da abinda ya haifa, bata kuma waiwaye ba, haka nima na tafi na bar abinda aka haifa ban kuma waiwayen shi ba, don Allah ki sanyani a addu'o'in ki, wallahi na tuba na daina zaluntar al'ummar Annabi." "Abie kunyi Kuskure babba, ta yadda kuka watsarb da jaririn da bai ji ba bai gani ba,. Allah ya yafe mana baki daya, sai dai gaskiya ba zan amsa ba, idan Allah ya nufa zamu yi aure da Mohan zan zo na amsa da kaina, idan kuma wani ne ma zan zo dashi. Nagode zan ajiye shi anan." Na bude wani drowe na saka, sannan na mika mishi key,.nace. "Abie ka bar kuka, Allah yana tare da da masu tuba domin shi. Kuma gashi kaki kayi aure, balle nace zan zo gidanka na kwana biyu. Abie kayi aure don Allah" "Toh ai Zainab nake so" ya faɗa yana murmushin jin dadi. "Toh Yanzun don Allah, a ina zaka samota? A gari me girma irin Nijar?" Dariya kawai yayi tare da rakoni har inda motar shi take yasa aka kai ni gida, ba zan tab'a manta wannan lamari ba, nayi farin ciki nayi bakin ciki. Nayi kuka nayi dariya. Da yamma lis na nufi asibiti, na same su, na gaida Umma bayan mun gaisa da Khausar da Radiyah, gefe can su Salman da Haddir ne, sai matan su. Karasawa nayi na gaishe su, sannan na amshi yar wajen Haddir, mai suna Widad. "Ki shiga ki duba shi mana! Har yau bai san waye akan shi ba, ya shiga coman su Khausar suka ce." Mikawa Matar Haddir yarta nayi mai sunan Nabilah, na shiga jikina a matukar sanyayye, yana kwance mahaifiyar shi tana goge mishi jikin shi.... "Yarinyar tana da nutsuwa da kamala, gashi duk sanda zan ganta cikin shigar mutunci da kamun kai." "Hmm!" Khalil ya faɗa bayan ya kalle su. "Shima bai da mutunci, yarinyar nan tasha wahala da dan iska amma karshe zarginta yake, wai cewa ma tayi su rabu yake kwance, da shi ya kunshi bakin cikin da suka kunsa mata ba mamaki da lahira tayi baki." "Gaskiya Khalil baka da imani, meye na wani cewa da lahira ta yi baki" inji Salman. "Kasan Allah, babu dan iska irin Mohan,ni yarinyar ta min daidai dan Uban shi ko babu kome gashi kwance zuciya tayi laushi" ya faɗa yana dariya. " Da fatan zaka maimaita a gaban shi." "Bar dan iska idan ya tashi zaku ga iyayi da kinibini irin ta shi. Inda nice Maimunari ba zan tab'a yarda na aure shi ba sai ya tashi a jinyar da yake."sake mishi duka Umma tayi tana hararan shi. "Kai dai ka zama sai du'a'i, amininka kake binshi da sharri?" "Kai Umma kina ganin bai da mutunci shima." Fitowar Ammyn yana share kwalla yasa su zuba mata ido. Duk sun fahimci wani makircin ne. "Yanzun sabida nafi kowa laifi idan nayi magana ba za a yarda dani ba, d'azun nakira ta tayi min rashin kunya yanzun ma ta shiga tayi min rashin kunya. Ni da d'ana bani da iko dashi" "Ammyn ai duk abinda zata miki tayi miki da kauna ce, idan wata ce billahi azim ba zata zo ba sai dai ya mutu." Jin abinda Radiyah ta faɗa yasata yin shiru, Nairah tace. "Da nice wallahi ba zan zo ba, kai Ni ba zan aure shi ba, zan yarda ni matsiyaciya ce amma kuma nafi karfin mai kudi ya wulakantani ba Mohan ba, ko Uban Mohan ne ya mutu i don't care" ta wani ware hannunta (🤷🏼‍♀️) "Toh ai abinda zaku duba yarinyar tasan darajar iyayenta da Mana, dan lokacin da Abba ya je, mahaifinta yace shi ba zai hana Mohan Maimunari ba, sai dai matuƙar aka tab'a mishi ita toh wallahi ta rabu da Mohan kenan har abada, ita kuma yarinyar da aka kira ta, cewa tayi duk abinda aka yanke ita mai biyayya ce. Kaji irin yaran da nake fatan Hur ta zama, koda Abba ya kuma tambayar ta, cewa ta kuma ita mai biyayya ce duk abinda aka bata zata amsa hannu bibbiyu, bayan Abba ya kuma tambayar ta, ya kira Abbu ya gaya mishi dama ya tafi Maradi niman auren Budurwan Khalil karshe privet jet din shi ta kuma bi yaje har Damagaram ya tambaye ta, ta kuma cewa. "Abba duk abinda kuka bani ni mai biyayya ce, don Allah ina zaka so rasa wannan kyautar. Sai dai wanda duniya ta aure shi ba laifi zai iya nimar yar da take shan giya." Inji Salman. Da yake basu labarin yadda aka yi gurin Niman auren Maimunari, Hajiya Latifah duk tana jin su, hmm bata ce musu koma ba. (Ni kuwa nace hmm zaku ci kaniyar ku🤷🏼‍♀️😏😒☹️🤨) Lokacin da na shiga na same ta, kallona tayi sannan tace min. "Kun nace!" "Da alamun rayuwar dakin yana cikin hatsari amma bai dame ki ba?" "Hmm!" Shine ta fita. Ni kuma ba zauna a jikin shi tare da rike hannun shi, duk da laifin shi daya ne na zargina da yake amma har yau ina jin son shi yana sosa min zuciyata. Sumbatar hannun shi nayi, sannan na taka a hankali, na isa daidai goshin sa na manna bakina a kai, kafin ya sumbaci idanun shi, na dawo kan dogon lokacin shi ba sumbata, sannan na sauko bakin shi. Jan numfashi nayi sannan daura bakina akan nashi, sai da na jima ina tsotsar bakin shi tare da janye bakina daga na shi, na juya zan fita. Na tuna ranar da aka yi baikon mu, daidai zuciyar shi na sumbata, dan haka na isa gurin na sumbaci inda aka saka wani igiyar da karfe na sumbata, sannan na mike tare da barin. Dakin. "Allah ya bashi lafiya zan tafi" na sallame su, Tana fita a dakin yayi wani irin jan numfashinsa na'urar da suke makale da jikin shi suka bada wani irin sauti. Da gudu Khausar ta shiga dakin tare da kiran likitocin, aka rufa mishi. So yake ya farka amma ina abu daya yake yawo a ranshi da ƙwaƙwalwar shi, sumbatar da ta mishi ranar da zasu rabu, sak irin shi yaji, a wata duniya, yana mishi. Haka suka mishi alluran barci Bayan sun tabbatar da bugun zuciyar shi ya daidaita. "Kun gani ba! Idan ba maita ba meye daga fita zai kama!" "Amma Latifah baki da hankali, godiya za kiyi da Ubangiji ya bashi lafiya ba wai ki zargi wata ba, idan ma itace. Ai ta miki gata tunda ke baki hankali" yaranta babu wanda ya damu da abinda take yi. Fitowar Khausar tana yiwa likitocin godiya dayan yace musu. "Akwai abinda ya tsaya ranshi kafin faduwar shi, kuma ina ga shi din ne ya kuma dawo da bugun zuciyar shi." "Mun gode! Insha Allah zamu bincika" bayan nan ta shiga yi musu bayani tare da gaya musu abinda ya faru. "Dan iska mara mutunci! Zan muku bayanin abinda ya faru, amma ku shiga family room" kallon shi suka yi, take ya bude data yana tura musu hoton emoji na saurayi da budurwa suna kiss, yace musu. *Wannan shine abinda tayi mishi kafin su rabu. Kuma daga shi bata kuma yarda sun hadu ba. Ina da yakinin ta kuma sumbtar shine. Allah ya barsu tare amma gaskiya Ammyn bata hakura ba gani nake kamar akwai abinda yake shiryawa! Amma Allah yana sane da kome* Take kuwa Family room din. Ya kuma hargitsewa. Haka suka yi ta fadan albarkacin bakik su. *** Washi gari kafin na koma Maradi na kuma zuwa asibitin Ammyn bata nan sai Salman da Haddir, a mutunce muka gaisa har nake tambayar su. "Ya jikin na shi har yanzun babu canji." Murmushi suka yi sannan Salman yace min. "Eh toh jiya bamu san me kika bashi ba, daga tafiyar ki kawai malamin mu ya farka, yana barci dai yanzun." _Kar dai sun fahimci na sumbace shi ne? Wayyo Allah na kunya_ "Amma bai ce wani abu ba ko?" Na tambaye su ina zare ido. "Eh toh! Ya dai ce sumbataaaa!" "Ya ilahi!" Na daura hannu a kai. "Amma bai ce muku na sumbace shi ba?"(🙆🏽‍♀️) "Ai ya gaya min kome, kai Maimun!" "Amma me yasa Hammah Mohan yayi min haka? WALLAHI ba sa gayya na sumbace shi ba, ince babu abinda ya faru dashi" "Salman don Allah ka kyaleta haka wallahi ta fadi gaskiya! Shiga abinki Karya yaƙe miki" "Wayyo Allah na, ka sani nayi subul da baka!" Na fada ina shiga dakin da sauri. Har bakin gadon na nufa, tare da rike hannun shi. "Ina jiranka! Ina jiranka a karo na babu adadi! Ni kamar baiwar ka ce! Zan koma Maradi na gama abinda ya kawo ni, amma ina fatan zaka tashi daga dogon barcin da kake min ya isa haka! Maimunari mallakar kace, taka ce har abada ba zaka tab'a raba kaso da kowa ba, Maimunari kason kace! Ina kaunarka da fatan zaka tashi da izinin Ubangiji." Ina gama fadar haka na kuma sumbatar goshin sa, sannan ya juya zan fita naji ya rike hannuna. Juyawa nayi tare da kallon shi, komawa nayi na zauna a bakin gadon, tare da kallon shi. "Karki tafi" ya faɗa min a hankali. "Kayi hakuri! Daga wannan satin sati biyu masu zuwa ina karkashin da'iran mulkin ka ne sai yadda kayi da Ni!" "Zaki Aure Ni?" "Mun wuce wannan maudu'in!" "Da gaske?" "Da gasken gaske!" Na fada mishi ina share kwalla. "Ki tanada min sumbatar ranar da kika min, ki ajiye min duk wani kwarin gwiwar da na gani a cikin idanun ki ranar, ki adana min dukka wani irin nau'in kulawa a daren mu, ni kuma zan gina miki daren da ba zaki manta ba!" Murmushi nayi tare da hade goshin mu. "Na tara maka kome na wannan daren na adana maka kome a wannan daren, zan hada maka kome kuma zan sayo jarunta a wannan daren sabida kar na hanaka sukunin aiwatar da muradinka, Hammah Mohan daga wannan daren karka tausaya min ka fanshe duk wani soyayyar ka, a cikin shi ka nuna min sakamakon kaunar da kake min Ni kuma zan boye kuka na da kome zan baka kyautar daren, zan tsara maka daren ya zama mafi girma da darajar, zan Kawata maka shi. Zanyi kome domin ka, hmmm sannan zanyi kuka da!" Murmushi yayi tare da zungure goshina yana dariya. "Idan kika yi kukan zan rarrashe ki, zan baki kyauta na musamman, nan dan mallaka miki zan baki dukkan shi zuciyar taki ce, zan zame miki farin dare zan raya miki daren da so da kauna, zan shirya miki shagalin da ba zaki tab'a Mantawa, ranar zan baki kyautar kaina baki daya, zaki ganin iya ganin idanunki, zan tsaya a gaban ki na juya ki ga irin mijin da kika aura. Ubangiji ya bamu yawan rai yadda zan share miki kukan ki, Ubangiji ya nuna min yadda zan sanyaki farincikin a wannan daren ya rabbil alamina ya nuna min yadda zan kayata miki daren ki! Ina addu'ar ki same ni a yadda kika sannin kika yi fatan haka, akwai shagali yarinya babu tausayi babu ruwana da Yarantarki! Zaku hadu da katon tuzuru ne!" Rufe mishi baki nayi ina zare ido.... #Mai_Dambu... [8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1113398663?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=%2BxTW4N%2Fi3%2B1dAQX5gbjmfTxgxiRMRb8Nl%2F50OD4pV94UP35Ih%2FrlfzEmYSOqSePFjk4F6wQI4BmDexcUn1v%2B6q7S5wMuA0Uc%2FC5OPGYtcFd9ON0zvTrtgtJg8WkJ5LAn 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN DA HUƊU. *Ana ta zare idanu 🙄🤡🙋🏾‍♂️* Ni a karan kaina nasan ina son Mohan, kuma shima ya san da haka,shi yasa na b'ata lokaci ina hira dashi tare da bashi labari. Kafin na kalli agogon dakin na zare hannuna cikin nashi. "Zan tafi!" Na fada mishi, "Bana son kiyi nisa dani, amma babu yadda na iya, Allah ya kiyayye hanya, ki kula min da kanki" murmushi nayi mishi sannan nace. "Insha Allah! Amma ka godewa Allah da Abbu da Abba da Wallahi sai dai ka nime wacce take." Rufe min baƙi yayi da nashi. "Don Allah a bar zancen kawai, wallahi ina son mata ta haka." Cizon hannunsa nayi tare da kura mishi ido. "Ahhh!" Sannan ya sumbaci gurin, yana murmushi. "Ina sonki" Girgiza kai nayi, tare da ɗaukar jakata na fito. Na same su har wasu sun zo. "Don Allah, ki tuna yana da kane irin wannan sakawa a lungu, baki daya. Toh Allah yasa kar muzo cin shinkafar amarya a hana mu ganin ango." Kasa magana nayi domin Salman yana da raha kamar dan Film. "Toh zan tafi, na gama abinda ya kawo ni Niamey." "Ke dai kice zaki gudu an kusan amarcewa" "Sai anjimar ku" na musu sallama na tafi, sannan suka shiga dakin sun same shi kamar mai barci. "Munafuki idan zaka bude ido ka bude domin yarinyar ka ta nuna mana ka farka." Inji Dan Ba'are Ya fada tare da kallon shi. Gyara kwanciyar shi yayi tare da cewa. "Dan Ubanka idan ban tashi ba sai ka d'aga ni" Nan suka shiga fadar su ta gado, dan zance ta gado. Kafin suka shiga taimaka mishi yayi wanka da alola, yazo ya gabatar da sallah da yake kanshi Allah Sarki. Yana yi yana huta. Haka ya sauke sallah da yake kanshi, ana hira da shi Ammyn ta. Shigo ita da Maman Hanan ko inda suke bai kalla ba, sai b'ata rai yaƙe, A hankali sauki yake samuwa, tare da sanin kulawa daga yan uwan shi, da mahaifin su amma fir yaki amincewa Hajiya Lateefah, sosai yaki sake jiki da ita, idan ya fara waya da Maimunari kuwa kowa sai ya tashi inda yake, domin kasa kasa yake maganar kamar ba zai yi ba, baka tab'a jin abinda yake faɗa. Satin shi daya aka sallame shi saura sati biyu bikin su. Ba karamin shiri ake ba,duk ta inda kake tsammanin abin ya wuce haka, bikin saura kwana tara aka kai kayan lefe, akwati ashirin da hudu (😏😒☹️ saura kuce zuki tamalle🤣😂) tare da kyautar motar sabuwa jaguar, kukan da Innah keyi Allah kadai ya sani, domin babu wani da zata ce danginta ne sai Al'ummar Annabi, sune suka mata kara, dama tun kafin a kawo kayan Radiyah ta turo min, da ranar da za a kawo, tuni na dawo gida na shiga Niman inda za ayi mana abincin alfarma. Tare da kayan ciye ciye dake ban san yadda ake abin ba, sai da ta gaya min. Na kawo kayan drinks aka ajiye, sai da na gama kome tare da bawa Innah kudi me yawa ta basu tukwaici. Aikuwa haka ce ta faru. Amma Innah taki amsar motar da gwala-gwalan cikin kayan. Atamfoffin kuwa kamar shagon sayar da kaya za a bude, haka akayi ta kirga su har suka gaji suka bari, tunda na ga kayan gabana ya tsinke, ban kuma samun kwanciyar hankali ba, ga mugayen mafarkai da suka sani a gaba, a tsakanin kwanakin har saukar Alqur'ani sai da nayi, ana saura sati za a saka ni a lalle na koma gida bani da kawa bani kowa sai su Salihu Muhmuda, sune abokaina dan haka da su muka yi ta zirga-zirga. "Malam ina jin tsoron Allah ina jin tsoron kar wani abu ya faru, ina tausayin yarinyar nan wallahi ba zan iya daukar tashin hankalin da zata ji ko zata gani ba." Inji Innah, "Babu abinda zai faru, sai Alkhairi." Baba ya gaya mata. Shiru tayi tana kallon kasa, kafin ta sauke ajiyar zuciya, tana wasa da abincin da yake gabanta. "Naji tace zai tace zata Niamey, ban san me zata je yi ba." "Eh wannan alkalin zata kaiwa katin gayyata na bikin, kuma Insha Allah zata dawo ana saura kwana kwana uku." "Toh Allah ya nufa, ina tsoron abinda ya faru" "Don Allah idan ba zaki fadi Alkhairi ba kiyi shiru." *** Washi gari da asussuba nayi sammako sai tasha. Ina zuwa motar farko zata tashi Allah ya soni na samu guri. Ina biyar kudin tana d'agawa bakina dauke da addu'a, haka muka dauki hanya. .. Diffa. Juya mishi baya Uban yayi, tare da kin sauraron shi, yana jin yana magiya. "Don Allah ka ajiye kudirinka na cutar da ita, karka manta wallahi ba dan kudirinka nake aikin nan ba, ina sonta don Allah karka cutar da ita don Allah" a fusace ya juya da sandar Azurfan shi ta tsafin ya buga mishi a goshi. "Kai ka isa ka hanani farin cikina! Ka dauko min ita ka kasa, kayi min abinda ya dace ka gaza anya ni na haife ka kuwa? Wallahi da kai jini na ne ba zaka tab'a ɗaukar mace da daraja, macen da rigar sawarka tafita daraja itace kake rokon kar na mata kome!" "Ita nake so ka dauko min ita, so nake ka daukota ka kawo ta nan! Idan ma soyayyar ta kake ji a ranka toh ka daina, domin ita din da ni, gumin mu ake son ya hadu guri guda, daga nan kuma ina zaune mulki zai zo min har inda nake" cike da mamaki yake kallon Mahaifin shi wato abar kaunar shi ce zai kwanta da ita. "Tab wallahi babu wanda ya isa yayi min wannan gangancin na dauka, yarinyar da na gama cin bakar azaba da duka sabida ita, toh ai gwara ka tsine min albarka da na kawo maka ita, kai dai ka kare a gurgunta amma ita wancan kayar tawa ce. Kuma na rantse idan kayi gangancin aikata wani abu, hmm toh wallahi sai na zame maka alakakai, kana ji kana gani zan kashe ka, kaiii Dattijo ban damu ba dan baka dauke ni a d'anka ba. Amma ita ka tab'a inuwarta wallahi sai na binne ka da ranka. Ita din guguwar sauyin ƙaddara ta ce, dama daya tak nake jira kuma Insha Allah na kusan samu idan ka gadama ciwon daji ya kashe ka ko ta zuciya" Daga haka ya juya zai fita ya tsaya tare da cewa. "Daga yau zan zame mata inuwarta duk inda ta shiga ina biye da ita, kai kuma zan zame maka tankar tafiyar Ajali domin duk lokacin da ka ganni tabbas mutuwarka ce tazo maka. Ba zan d'aga maka kafa kana Ubana ba, zan maka kisar munmuke da sai kayi danasanin haifata da kayi. Kaiii Wa'adi Ansar wallahi idan har jininka na mugunta da keta be bin kowa lungu da sako na jikina wallahi na rantse da wanda ya mallaki alrshi sai na maka kisar da ko gawarka sai ta bawa kowa tsoro. Karka tab'a Maimunari domin ita ruhina ce. Idan kuma kana ganin haka da sauki.... Ma gwaji ya gwada" Yasa kai ya fita tare da dukar kofar fita daga gidan, rintsa idanun shi yayi da mugun karfi, yana jin yadda Hisham Waadi ANSAR yake mishi barna duk wani abu me daraja sai da ya lalata a gidan, sai da ya fasa kome har da motocin gidan, sannan ya kwashe kayan shi ya nufi gidan shi da yake wajen gari ya kwanta. Bayan an mintinan wayar shi tayi kara. Kamar ba zai duba ba ya dauka. *_Saura kwana biyar bikin Maimunari da Mohan!_* A zabure ya mike tare da danna wayar jikin shi yana rawa.. ya kira ta. "Maimunari! Meye nayi miki da kika tsane ni? Haba ashe soyayya zata zama k'iyayya? Ina sonki sannan ina miki fatan Alkhairi, naji zaki yi aure. Allah ya cika miki burinki." "Malam Ansar ba wai naki ka bane, sai dai tun farko na gaya maka kai dan uwana ne, Hammah Mohan kuma Masoyina ne, shi na fara so. Kai kuma na shaku da kaine, ka fahimta mana so daban shakuwa daban. Wallahi ban tab'a jin soyayyar ka ba, amma kayi hakuri ba cin fuska bane! Wallahi kasan hali!a bana boye abinda yake raina, kayi hakuri kaji" "Na hakura kanwata, karki manta ki dauke ni abokin shawaranki Insha Allah zan zo daurin auren da duk wani shagali da Ni za ayi." "Kai Hammah na, nagode sosai da ka fahimce ni, kuma naji dadin haka don Allah ka gafarce ni, yanzun haka ina hanyar Niamey ne zan kai katin auren amma ina ganin gobe Insha Allah zan dawo zan bi jirgin sama." "Ai girmanki ce, Surukar shugaban kasa, idan baki biyo jirgi ba ai nayi musu ba'a, karki manta Insha Allah duk abinda kike bukata ki gaya min Insha Allah ni kuma zan cika miki burinki, karki manta da haka ina kaunarki har kwanan gobe, amma yanzun ya koma ba yan uwana" "Gaskiya Nagode da samun babban masoyi irinka, Ubangiji ya baka wacce ta fini don Allah kashe kiran surukinka ya kirani" "Toh!" Ya fada da sauri bayan ya kashe kiran, very sad ya kalli wayar, sannan ya sake murmushin farin ciki, kafin ya mike ya nufi ban daki, yayi wanka sosai cikin nishadi da jin dadin. ** Yana kashe wayar, na dauki wayar Hammah. "Ranka ya dade! Mazaje." "Hmm! Sarauniyar kyan zuciyar Hammah Mohan! Dawa kike waya?" "Kai Hammah! Da abokin karatuna ne fa!" "Ok na zata wani saurayi ne ya kira min mata nasa sojojin kasar Nijar su dira a kofar gidan su, a dauko min shi a kai!" ""Kai Hammah Mohan! Lafiya? Akan me? " Cikin murmushin kasaita yace min. "Sabida ya kula matar Babban sojan" dariya na saka ina kara gyara zamana, ina faɗin. "Toh gani a hanyar garin ku, Niamey" "Don Allah? Toh a ina zaki sauka?" "Toh ai kaji irinta, wallahi sai gidan Abie domin na gaya mishi tun a tasha. Kuma yace min idan zan koma a jirgi zan koma!" "Toh ni dai Allah ya gani na fara kishin wancan tsohon ina dalili ya zake dayawa da!" "Allah Sarki,wallahi kamar mahaifina nake jin shi, idan kace na daina kula shi sai na daina." Na faɗa. "A'a ban isa ba" "Ka isa mana." "Hmm! Har yanzun ban warke ba" "Ayya dama kaji ciwo ne?" Na fada mishi ina dariya. "Gaskiya kin jiwa zuciyata ciwo? Kuma zan rama duk ranar da zan rike ki a hannuna sai kin gane" katse wayar nayi ina dariya, kafin na share zancen shi. Har muka isa Niamey ina jin nutsuwa a raina, Driven baba yazo daukana. Ina isa gidan na sami motar Hammah MOHAN. "Sannun da zuwa Uwata, Sannun Uwata an kusan girma." "Ooh Abien Moonah sonkai tsirara, ina laifin ka min kara ka maidani kamar Bature tunda nazo ruwa kawai ka bani, amma tunda Moonah tayi sallama ake jera wancan table din Abie dan ban gaya maka zan zo bane?" "Abie Hammah Mohan kishina yake, dan yaga kafi sona" na fada ina murguda baki, kwafa yayi irin zamu hadu dake. "Abie kaga tana murguda min baƙi!" "A'a Abie shi yake harara na" "Toh Mohan ya daina Harara. Maimunari ta daina murguda baki." "Abie" "Muje muci abinci sai kiyi wanka ki huta," Haka kuwa ta kasance bayan na gama cin abinci nayi wanka da alola na.gabatar da sallah da ake bina da kuma na magarib da isha. Sannan ya tara mu, yayi mana nasiha akan rayuwar mu da kuma wanda zamu fuskanta, sannan ya kara mana da kyautar da ya bani, tare da wani katon gida a Zurich ƙatuwar gida ce, wanda har kwanan gobe ana tayawa yaki sayarwa. "Ga waɗannan sune wanda na baki su, bansan me zan baki ba, amma ina jinki har cikin jini na, Allah ya albarkaci rayuwar ku." Mun yi hira sai da Abie ya kore Hammah Mohan, amma sai ya tafi zai kuma dawowa, yace yayi mantuwa haka dai karshe Abie ya turo ni, tunda na shiga motar shi na bige da barci. Fitowa yayi daga daya gefen sannan ya bude inda nake, ya dauke ni. Cikin gidan ya wuce dani, Abie yana zaune. Ya shigo dni. "Ina zan kaita?" Nuna mishi dakin yayi tare da shiga da sallama, dakin ta yara ce aka ware shi, domin akwai kayan wasa kala kala. Sannan ya kwantar dani bayan yayi min addu'o'in, Kafin ya ja min kofa ya fita. ** Washi gari. Da wuri na farka, na kuma shiryawa sannan na karya kafin Abie da kanshi ya kai ni. Airport, "Uwata gashi kin kawo katin bikin ni kuma zan tafi Nijeriya taron bita na Alkalai, ban sani ba ko zan sami daurin auren amma duk yadda za ayi zan zo ayi dani." Idanuna ne ya cika da kwalla. "Toh shikenan!" "Kiyi hakuri Insha Allah zan zo" "Toh" nace ina share kwalla, haka kawai nake ji idan da Ubana ne babu abinda zai hana shi zama a daura aurena amma yau sai gashi ina niman ina ma zan ga Ubana su ko tausayina basu ji ne da suka tafi suka bar ni. Ba zan taba barin dana haka ba, har na shiga jirgin yana d'aga min hannu. Bayan tashin shi yake kara jin babu dad'i, idan da yar shi ce babu inda za shi dole ya zauna ayi kome akan idanun shi, Allah sarki. Haka ya fada. Yana komawa gida Mohan na zuwa sosa kai kai yayi sannan yace. "Abie mun ina kwana?" "Toh ta tafi lafiya lau!" "Haba?" " Zan maka wasa ne?" "A'a ya faɗa tare da sunkuyar da kai yana kara jin girman Abie yau sosai. "Toh, Allah ya sauke ta lafiya. Zan tafi" "Ka gaida gida" ** Karfe goma da rabi na isa gida na samu ana ta hidima. ... Biki ake sosai a gidan duk har. Ana gobe daurin aure aka sani a lalle, haka kawai zan zauna nayi ta kuka, sun zata kawai dan zan rabu da Innah ce a'a kawai kukan tausayin kaina nake ji. Ranar sha biyu ga watan Maris aka daura aurena Ni da Hammah Mohan, da misalin karfe sha daya na rana, a babban Masallacin Damagaram, ana daura auren babu b'ata lokaci aka dauke ni a jikin Innata, ina kuka tana kuka. Haka muka nufi Niamey. Ba zan manta da wannan al'amarin ba. Niamey. Tunda muka isa da yamma aka fara wani irin biki na fitan hankali.. ** "Boka kayi wani abu, bana son yarinyar ta shiga cikin gidan." "Ai kin makara, shiga kuwa tuni ta shiga. Ni dai ku tafi bani da abinda xan muku idan kuka nace min kayana konewa zasu yi kutashi kafin masifar da kuka lakato ta same ni" Koran kare yayi musu cikin kunar rai suka fito, kamar mahaukaciya Hanan take kuka tana ihu, garin haukarta ta taka wutsiyar maciji,a fusace ya zabga mata sara, tana ganin shi ta fasa ihu, tare da faduwa uwarta ma ihu ta fasa, haka Bokan ya fito ya same su. Ganin sarar maciji ne ya koma cikin Bukar shi ta dauko magani ya shafa mata, shine ta farka. Ya bata wani tasha. Tayi amai sannan yace musu. "Maza ku tashi, gaba da gaban ta, yarinyar Allah yana tare da ita, idan kuka nace zaku mutu maza ku b'ace min da gani" Jikin su yana rawa ta dauki Hanan suka bar gurin. ** Ana ta shagalin na bikin babu wanda ya damu da kowa, sabida harkan arziki da ake. "Hajiya kinyi bako!" " A wannan lokacin! Kana ganin z a kai amarya d'akinta ne don Allah yayi hakuri Kuma kaga yanzun aka gama liyafa." "Wai abin yana da muhimmanci ne don Allah ki zo" Haka tafita ba dan taso ba, bayan ta haɗu da bakon, ta dawo jikinta yana rawa, tasan ba zasu bata goyan baya ba.dan haka ta ajiye abin a ranta. *** Daga Ni sai radiya da Auta tare muka zauna har angwaye suka zo, akayi abinda ya zame na al'ada, kafin suka mana nasiha,. Radiyah ta riko hannun Auta suna gudu daga bari muyi rakiya. Suna fita kuwa Hammah Mohan yana shigowa cikin ɗakin. Zama yayi a bakin gadon, yana kallona. "Alhamdulillahi gani ga Maimunari, Maimoon, Almamoon! Mamoon! Mata maza" A hankali ya yaye mayafin fuskana, sanan ya matso tare da janyo ni jikin shi. "Tashi muyi sallah" "Toh" Na shiga nayi alola sannan nazo muka gabatar da nafilla kamar yadda Manzon Allah ya umarta ya dage goshina yayi min addu'o'in da aka wajabta, kafin ya ya tashi ya kawo min kayan kwalamar da ake kawowa daren, Alhamdulillahi munci mun sha, sannan muka kwanta, bayan na sauya kayana. "Moonah dawo kusa dani" "Hmm! Barci nake ji" Na fada mishi. "Toh" Ya fada kamar Maraya,matsawa nayi jikinshi na kwanta, a hankali rayuwar da ya tsara mana tare da shirya mana wani irin rayuwa na musamman,. Wannan daren na yarda Mohan namiji ne na gaban kwantaccen, Mohan, Mohan ya kai ni duniyar da ban zata ba, ashe duk abinda nake fada duk cika baki ne, domin kuwa daga yan tab'e tab'e lashe lashe, tsutsa tsotse, sai da Mugun ya fara gangarawa madaidaiciyar hanyar na Fahimci Allah daya ne, yanzun na Fahimci abinda Innah ta gaya min da ban rasa kome na daraja ta ba.(zaku ji bayani nan gaba Insha Allah) domin baki daya abinda aka tura mishi aka gaya mishi a kaina ne a kasan ranshi, dan haka cikin salon kidima da yaji yadda gurin take da dumi bai san lokacin da ya buga iska.(😏🤣🚶🙆🏽‍♀️ Ya isa haka ku hango yadda Mohan ya gigice mana sai nayi fashin bakin har haka!) Na sha bakar azaba a hannun shi nayi kuka na roke shi, na gantsara mishi cizo amma mugun dai da ya mai dani cikakkiyar mace, hankalin shi ya kwanta, ta tattara min gashin kaina ya rasa me zai min ma yaji dad'i. Haka ya haska wutar gefen gadon, ya kalle ni yadda nayi laushi. "Allah yayi miki albarka, kamar yadda kika faranta min Allah ya faranta miki." Tashi yayi ya shiga ban daki. Kasa kasa nace mishi. "Amin mugu!" Dariya na bashi yace min. "Bari na hada mana ruwa sai na kuma ko sau daya ne!" Jan bargon nayi, kawai naji an fisgo shi, da sauri na rike tare da sake kuka zan mishi mita. "Tashi Shegiya bakar munafuka, gurbatacciya! Kin shigo min tsabtataccen Zuri'ata, wanda bamu hada iri da shegu ba, tashi." "Ammyn karki wulakanta ni a shimfid'ar d'anki, don Allah ki rufa min asiri na suturtta jikina!" "Tashi dan Ubanki da ya dauke uwarki ranar aurenta yayi cikin ki aka haifi Shegiya irinki, yar zina. Kazamtar da tafi kowanne muni, ayi zina da matar aure. Aka haifi Shegiya irin ki! Tashi." Kura mata ido nayi kome na kaina ya tsaya, a hankali na fisge Zanin gadon daidai fitowar shi daga shi dai towel, ganin uwar shi a tsaye ya sashi komawa cikin ban dakin da sauri ya dauko rigar wanka ya saka. Sannan ya fito. "Ammyn lafiya?" Kifa mishi mari tayi. "Sake ta dan Ubanka. Shegiya ce mara asali kije ki tambayi Innarki da mijinta ke ba yar su bane maza sake ta kafin na tsine maka ka shiga duniya." Yaki magana yana kallona ina kallon shi. Ni kam zunzurutun na shiga kidima bansan me suke fada ba. "Sake ta nace ko na tsine maka!" Yaki ko guzau. *Kar Allah ya nuna min ranar da ba zan iya amfanarki ki da kome ba sai ido* wani irin hawaye ne yake zuba daga idanun shi, Ni kam kukan ya tsaya min bana jin kome, a hankali ya dauki kayana yana mika min nasa hannuna amsa. Rufe shi da duka tayi, tana faɗin. "Zaka sake ta ko sai na maka baki" "Kiyi hakuri zai sake ki Ammyn! Insha Allah zai sake ni, ba zan kuma dawowa cikin duniyar ku ba! Mohammed kayi abinda tace kaji" A hankali ya fita daga dakin na dauki kayana na shiga ban daki na saka, sannan na fito ina kallon shi. Mika min tai. "Maza Allah ya raka taki gona abinda aka so a lalata mana siyasar mijina." "Ammyn karfe ɗaya ne fa;" "Ba zata kwana ba dan Ubanka, wallahi ka jima baka mutu ba" haka na fito ina jan kafa yana bin bayana, a daren na fita daga gidan shugaban kasar Nijer. Zuciyata tayi sanyi Abu daya zuwa biyu nake son ji.. wacece ni?.... Allura ta tono garma..... *Intermission! Yanzun muka shiga tsakiyar labarin.... Da alamu na fara shinshimo karshe..... Amma haka ba zai samu ba sai na ga ruwan kaunarku da voting 🤣🙆🏽‍♀️🚶🏌️ rashin daraja* #Mai_Dambu... [8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1113774799?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=wttFXwlCWTsu7Xd9brt9PkpuxFS1NA%2FyyAvcpakR2j0eLdqgraAaqKDIsHkdoAh9cMAZ0F3vUQbYnQqanCDd%2B8Ah01MAW4cg9qyzlshahFd%2FF%2Fce11kN%2Fe9K0RRl58%2BM 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN DA BIYAR. "WALLAHI ka kuma taku daya sai na la'anance ka!" Ta fada da karfi, wani irin sanyi ne ya shiga jikin shi, ya kalle ta a hankali sannan yace mata. "Anya ke kika haife Ni? Anya ke kika dauki nauyin cikina? Lallai Ammyn Kinyi abinda kike so ni kuma zan miki yadda kike so! Ba dai Maimunari kika cire a rayuwa ta ba? Alhamdulillahi na hakura da ita koda itace rayuwata Allah ya bata wanda ya fini." "Wallahi naji wannan maganar a kunnen Yallabai sai na tsine maka wanda bai san ciwon kan shi ba, yarinyar da aka haife bata hanyar aure ba." "Bani da lokacin da zan yi magana akan wannan Ammyn wallahi ba zan yi magana akan shi ba, amma Allah zai bi min hakina mata ta ina sonta kina rabani da ita, ina kaunar ta kika rabani da ita Allah yana nan" A hankali ya juya zuwa cin gidan shi, ita kuma ya juya zata shiga cikin gida, ganin wani dogon abu tayi wanda bata hango karshen shi balle farkon shi yana tawowa da mugun gudu, aikuwa ta arta a guje, tana shiga falonta ta yanki jiki ta fadi saboda giftwar shi a falon. Ihu ta saka tare da firgita sosai.ihu take tana kiran mutane. Kafin kace me haka gidan ya cika da jama'a,dole aka rufeta da Addu'a, kafin ta samu barci. me wahalarwa. ** A hankali nake tafiya motar sojojin shi suna bin bayana, a hankali na tsaya a jikin wani mota, na jingina ina sauke ajiyar zuciya, saboda na gaji sosai. Wayata na cire a jakata da ya mika min kafin na fito. A hargitse nake dan haka koda ba kira Number Abie naji a kashe kiran Ansar nayi. "Kana ina?" "Toh ina masaukina ne! Lafiya a tsohon daren nan?" "Kazo ka kai ni Damagaram." "Ina Mohan" "Zaka zo ko ba cigaba da tafiya?" "A'a gani nan zuwa" .ina tsaye a gurin, bayan wasu mintina sai gashi nan ya iso. Da sauri ya bude min kofar, na na ja kafana a hankali, domin zuwa yanzun dan tafiyar da nayi tare da motsa gurin da bai samu kulawa na tasa ina jin nauyin har kirjina. Ina shiga motar kwanciya nayi, ya shiga mazaunin Driven, "ba zan kai ki asibiti ba kuwa naga kina bukatar taimakon?" "Bana bukata Damagaram kawai zaka kai ni." * Abuja. Karfe goma suka gama taron su na majalisar Alkalai ta yankin west africa. Dan haka yana gama abinda zayi ya ga lallai zai iya samun daurin auren tunda ba mamaki tunda yafi tsammanin da tsammanin ranar ne kuma zai iya kasancewa da azhar ne. Dan haka akwai liyafar da aka shirya musu, amma baki daya ya kasa fahimtar kome, karshe gaya musu yayi zai kome gida akwai daurin auren da zai halarta. Haka yayi musu sallama ya bar garin Abuja. ... Yana isowa bai tsaya ba, sai gidan shi ya sauya kayan shi. Sannan ya dauki katin auren da bai duba ba sai yau. Maimunari Isma'il Wodaadabe. Abinda idanun shi ya hango mishi kenan, kan shi yayi wani irin dumm, maganar mutane ne ya shiga dawo mishi. Tare a tunawa da yadda suka yi ta cewa yar shi ce. Wani irin jiri ne ya dauke shi, ya zauna dabas, tare da dafe goshinsa. A hankali yaji kwalla na zuba mishi,.Yar shi ce ya zauna da ita tsawon watanni bai sani ba,.ko dai ba shi Isma'il Wodaadabe bane, mik'ewa yayi ya haɗa kayan shi. Ya fita tare da nufar airport, sai kusan karfe biyar ya samu jirgin damagaram. Dake daurin auren a babban Masallacin Damagaram ne. Shi yasa yana isa gidan bai zame mishi boyayyen gida ba, tun daga nesa ya hango Aminin shi Sanda. Kwalla ce ta cika mishi ido,ana isa kofar gidan mai taxi din ya tsaya, biyan kudin yayi sannan ya fito ya dauki kayan shi. Ya nufe shi, zama yayi a gefen shi suka gaisa. Kafin ya saka hannu a aljuhun shi ya dauko sarewa. Ya fara busawa. Hawaye na zuba mishi. Juyawa Baba yayi. "Sama'ila!" Bai mishi magana ba, ya cigaba da busawa hawaye na zuba sosai, daga cikin gidan Innah taji sautin sarewan ta fito da gudu, a hankali ta isa kusa dashi, ta zauna tare da daura kan ta a kafad'ar shi. Yana busa sarewar yana kuka. "Ina ka shiga shekara Ashirin! Ina ka tafi ka barmu, Maimunari ta girma yau ake aurenta sun tafi da ita" Cire sarewar yayi tare da kallon ta. "Ki yafe min!" "Baka min kome ba." A hankali Abokin shi kuma wanda yake ji kamar dan uwan shi ya dauki kayan. "Sanda na Barka da nauyi" "Babu kome!" Cikin gidan suka shiga har falon Baba, anan aka shiga kuka kuma, kafin aka nutsu. Ya fara magana a hankali. "Bayan na bar ruga, ba zan iya fada muku abinda nake ji ba, amma wallahi ƙaddara jaririn shi ya sa na aikata haka, dan haka ina fita ban tsaya ba na kad'a shanun mu na tafi dashi. Tafiya sosai nayi har na isa Maradi, daga nan na fita daga yankin Nijar na nufi Nijeriya, tafiyar kwana da kwanaki ya kai ni Sokoto. A hankali na nufi kasuwar dabobbin na sayar da su har da naki, nayi fatan Ubangiji ya albarkace shi, sannan na shiga niman sana'ar a zata rike ni, a hankali na sauka a wani gidan gwauraye, na fara fita ina zaga garin. A dan gaba da gidan da na sauka akwai wani attajiri, sai dai kuma daga shi har yaran shi an musu bakin asiri, kullum zaka samu ya zauna yana ta gyangyadi yaran ma basu da abinyi sai yawo da shashancin. Dan haka na same shi muka gaisa ranar mun fito masalaci. "Alhaji Ni kuwa naga wani abu a tare da kai da zaka bani dama da na gwada maka shi" "Yaro xan tafi kasuwa ne, idan na dawo xan maka magana" yana fadar haka ya nufi kofar gidan shi ya zauna daga nan dai barci, ina gurin shi har aka kira sallah ya tashi zai tafi nace Mishi. "Alhaji bana bukatar sisinka kawai ka amince min na taimaka maka, da abinda Allah ya wuwace min." "Toh yaro muje" Bayan mun yi sallah na saka ya sayi kayan aikin da kudin shi dan kar yace zan damfare shi, sannan na hada mishi kome nace ya tafi xan yi daukar Alqur'ani. Haka na kwana akan ruwan addu'o'in nan, washi gari da asuba kafin ya yi magana da kowa ya isa kofar gidan, yana bude kofa na mika mishi zai magana na rufe mishi bakin shi alamar yayi shiru, yana sha ya nufi masalaci, muka yi sallah. Bayan mun fito zai magana nace. "Kayi hakuri! Karka yi magana da kowa, ka dauki kayan ka ka nufi kasuwa Allah yayi mana tsari da muguyen mutane." Haka kuwa ya faru, ya tafi kasuwar. Sai gashi babban abokin shi yana ganin shi yakira sunan shi waye? Meye ya dawo dakai kasuwa? Kai da aka maka iyaka da kasuwa. Sunan kasuwa ma barci zai saka. Yaran ka da suke kula da shagon ka suma haka. Dariya ya fara yana faɗin ai nasan za a rina. Hauka tuburan abokin yayi. Bayan kwanaki nayi mishi na yaran shi, suka sami lafiya suka koma kasuwa. Yayi yayi dani na auri yar shi. Hajara amma naki, sabida zuciyata tana gurin Zainab. A haka na zauna a gidan shi. Har na fara karantarwa. Kafin na shiga yaki da jahilci, Allah cikin ikon shi na samu shekara hudu, kafin na dawo Nijar nayi diploma a harshen Faransa, sannan na shiga jami'a inda na karancin Shari'a, shekarau ashirin din nan ban yi shi karon iska ba, nayi karatu har kasar Saudiyya, kafin na hadu da Primer minister, ya bani babban alkalin Alkalai na kasar Baki daya, har zuwa wannan lokacin zuciyata tana gurinta." Kuka suke suna bashi labarin yadda suka sha wuya kafin suka daura da rayuwar Maimunari. Murmushi yayi sannan yace musu. "Na kasa amincewa ni na haifi wannan doguwar yarinyar, sai yanzun nake kara hango yanayin ta, yanayin mahaifiyarta. Ashe jini na ne, shi yasa da akayi ta jifarta sai da na koma baya, domin kare yarinya na, ko kuka bana son tayi sosa min rai yaƙe, gashi Allah ya bata yaron da zai iya bada rayuwar shi domin ita." "Amma har yau bata san kome akanta ba Hammah Sama'ila ina tsoron kar ta sani ta birkice mana" "Insha Allah Ubangiji zai yayyafa mata ruwa, me yasa kika boye mata al'amari haka? Ko yayya ne ai da kin gaya mata, gaskiya ban ji dadi ba. Koda nace idan ta kasance mace a boye min ita sabida tsoron kar a wulakanta min ita ne, sai ki gaya mata cikin lumana yadda zata gane wacece ita." "Toh ya zanyi mata, bana son ta rasa farin cikin tane." Ajiyar zuciya ya sauke kafin suka shiga hiran da tafi wancan har magarib ta cimma su, suka tafi masalaci. Kusan raba dare suka yi suna hira, da asuba suka nufi masalaci. ... Wani irin azazzaben gudu Ansar yake, karfe shida na safe mun iso garin Damagaram. A kofar gidan ya tsaya, a hankali na tashi tare da rintsa idanuna, kafin na mike na bude kofar a hankali, na sako kafana. Wani kwarin gwiwa nake ji, na dauki jakata, ban mishi magana ba, na shiga cikin gidan ina dingishi. Jini na sauka a kafaffuna. Ina shiga na sami Innah tana abin karyawa sake wukar hannunta yayi tare da mik'ewa. "Lafiya!" A sannun na isa gurin wukar na cire mayafin jikina na dauki wukar ina wasa da shi. "Wacece Ni?" Na tambaye ta. "Ina tambayar ki wacece ni?" "Ke yar dan uwana ne, kuma yana nan yazo kin san shi ma ai ba bako bane!" Ganin zata b'ata min lokaci na ja wukar da karfi akan wuyar hannuna. Aikuwa jini yace gani nan.. "Ki gaya min ni Shegiya ce?" Na daka mata tsawa, "Maimunari Abie!" Da sauri na juya sai yanzun na yarda da cewa da ake muna kama dashi, takowa yake cikin tsawa nace. "Karka yarda ka zo kusa dani! Ko na yanke wuyata" "Don Allah Hammah karka je." Inji Inna tana kuka. "Kiyi hakuri, gaskiya ce abinda kike tambaya kiyi hakuri ƙaddara ce ga fada miki" da gudu ba shiga dakin tare da yanke gefen wuyana, sannan na rufe kofar na fadi a gurin. Gwara na mutu, gwara na mutu kawai da abinda suka ja min. Buga kofar suke ina kwance, jini na malala, a hannuna da wuyata zai kasana da gurin ya kumbura sosai. A kofar gidan kuwa bayan na shigo masalaci Ansar ya wuce yana shigowa, ya samu ana ta kokarin na bude, yana zuwa ya tokare kofar, cikin azama Abie ya shigo, daukata yayi suka nufi asibitin da ni, sai dai abin takaici ganin irin jinin da nake zubdwa suka ki amsata, dole aka nufi Maradi dani, tare da fatan Allah ya ceci rayuwata. Dake a motar asibiti ne Abie ya gama kome. kallon Ansar yayi. "Kar ka kuskura ka biyo mu! Domin idan na tashi zan maka abinda zai dame ne, ka rabu da ita." "Dattijo ka isa ka rabani da ita ce? Kamar yadda ka raba uwarta da mijinta shine na gwada maka ba zaka iya kome..." Kasa magana yayi tare da kakari, "Ka tambayi Ubanka Wa'adi Ansar, waye Sama'ila Wodaadabe Bororo idan ya baka amsa ina jiranka kafin nan ya fara taimaka maka lallai kun tab'a mai tsada, idan tsafi kuke ji ko maita, hmm Ni Alqur'an nayiwa fahimtar zahiri, ka tambaye bashi waye ni" Abie ya ture shi ya fadi sannan suka bar shi gurin, dole idan ya kai ta asibitin ya dawo domin baya da kura, Sun yi tafiya sosai dan ma an saka mata ruwa da allurai, hannun shi yana cikin nata, jikinta yayi dumi, a hankali yake jin kwalla yana zuba mata, duk abinda ka shuka shi aka girba. Yau ya tab'a ba, an tab'a mishi ita. Allah cikin ikon shi suka isa da ita akan lokaci, Ta gama gajiya domin yau mutane uku tayiwa aiki, ban da amsar haihuwar da tayi. "Dr an kawo mara lafiya daga Damagaram." "Toh na gaji wallahi. Ku duba wasu likitocin mana" Shigo da ita da aka yi dan su Inna ma sun iso, an tafiya da ita hannunta me jinin yana zuba. Daga nesa ta hango fuskarta, a hankali ta iso gare su. "Ikon Allah meye ya faru? Wannan case din dole a hada da yan san..." "Zainab!" "Kai! Fita min a cikin asibitina, maza ka fita." Ta fada da karfi. "Idan kin gama haukarki, ga ta nan abinda kika tafi kika bari, Ruwanki rayuwarta ta rayu ruwanki ne ki watsar da ita waje." Ya fadi haka tare da nufar hanyar waje, dauke idanun ta tayi akan shi jikinta yana rawa, da sauri ya kira sauran abokan aikinta aka shiga da ita dakin tiyata, tana kuka ta rasa me zata yi. Ashe tun ranar da aka kawota da abinda aka mata take jinta, har jiya da taga daurin aurenta a Tv, haka kawai taji nutsuwa ya shige ta. Kuka take tana cewa. "Don Allah ku taimaka min ta rayu, don Allah ku taimaka min karta mutu." Jinin da ta gani a Kafarta yasata sake salati. "Ku duba min kasanta" Kai kasa hakuri tayi, tace musu. "Karku tab'a gurin zan dubata, domin akwai aikin da mika mata na angurya." Haka suka gama, ta kifa kai a jikin gadon tana kuka, sai da tayi ya isheta sannan ta ware kafar ta fara dubata bakinta yana ambaton Allah. Tsoro take ji kar wani ne ya lalata goben yarta da mijinta kamar yadda Ubanta yayi mata. Lumshe idanun tayi lokacin da taga yadda gurin ya kumbura, a hankali ya duba taga babu karuwa, sai rashin kulawa da bai samu ba, A hankali ta mike bayan ta gama bata kulawa, sannan tafi to. Bata ce musu kome ba ta bar asibitin, sai yau mutuwar mijinta ya tab'ata sama da koyaushe, tayi kuka har Yumnah da Beenah suka samu sukan su. ** Karfe bakwai na dare ya shiga cikin gidan. bai kula kowa ba yana shiga ya tokari keken guragun da Wa'adi Ansar yake, tare da cewa. "Meye nufin ku! Yar guda daya tal zaku tab'a min ita?" Ya kuma wurgi da keken, tare da shake wuyar Wa'adi Ansar. "Wallahi dukkan mu Bororo ne, idan ka sake d'anka ya kuma rab'an Inuwar ta, sai nayi ajalin shi..... #Mai_Dambu. [8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1113775660?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN DA SHIDA. ___________________________________ Hlo ```Assalamu alaikum sisters,hp everyone is fn🙏 Nazo muku da labarin wani sabulune maiban mamaki🥺wato *mg's herbal whitening black soap*🧖🏻‍♀️ yan'uwa inamasu bukatar sugyara jikinsu fatarsu tayi kyau tazama Babu kuraje,tabo dama dukwani matsalan fata toh Yan uwa kuyi kokari kujaraba mg's Babu tantama zaisharemuku hawaye insha Allah duk wnd tayi using mg's koda roba dayane sai fatarta tagoge tabanbanta Dana saura,Ina maisan yaga fatarshi tayi smooth tana kyalli toh kujaraba mg's domin fatarku zata dinga haskawa tana walkiya da daukar Ido kmn kunsha supplement domin anyishine da ingantattun natural abubuwa masu gyarajiki cikin sauki batare da sunyima fatar mutum lahani ba😘 sister's duk ynd zanbaku lbrn soap dinnan yawuce nan domin zaku iya anfani da zallar sabulun batare da kunma bukaci cream ba🥰Amare gareku akwai hadinku na musamman wnd duk wacce tayi anfani dashi dawuya ango ya iyaganeta😁wani abunma saikungani da idanku👏gamasu nankarwa kuyi kokari kujaraba mg's domin Yana rageta sosai inkuncigaba da anfani da soap dinma saidai kuduba kuga Babushi😊duk wani prblm na skin kugwada soap dinnan Insha Allah zakuyi😂 Kayanmu bana bleaching bn organic ne nagyaranjiki zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkune anyisune d natural abubuwa Soap price:3k Maiso should chat:08062991548 Call 08064532391 Muna maraba damasu siyan daya kosari🙏 Be part of the glow team🤭say nooo to pimples, black spot,acne,sunburn,nd all skin prblms🙏 Mg's lv you guys fisabilillah🤭``` ___________________________________ "Kai tsafe kari ke da wanin Allah, Ni kuma Alqur'an na rike da Allah ka yarda wani abu ya same ta, sai duniya sun ji mu. Gabanka da Mamman Nasir Aghali ya tsaya a can muku yarinya ta kuwa kashe ku zanyi daga kai har d'an ka " Yana gama fadar haka ya juya tare da barin gidan, ina Hisham ya kwaso wannan masifar ai yasan waye Sama'ila Wodaadabe, wannan ai Bala'i ne da kanta, waye ya aike shi niman bala'i. Tabbas duk da yana son zama shugaban ƙasa, ya hakura dan yasan Sama'ila sanin hakika, yasan Waye shi. Ya kuma san dalilin da ya saka shi barin gidan amma bai zata Almamoon Yar shi ce ba, ina zai kai bala'i haka, idan ya kuma zuwa billahi azim sunan shi gawa, ko abinda dan shi yayi mishi bai kai kashedin da Uban Almamoon yayi mishi ba. *** Niamey. Yadda Hajiya Latifah ta hana kowa sukuni da firgice, yasa aka fara mata addu'o'in. "Mohan ka dawo da ita wayyo Allah na, zasu kashe ni. Don Allah ya dawo da ita, wayyo Allah na." "Meye ya faru?" "Alhaji nasa ya saki matar shi ce saboda Shegiya ce an samar da ita ta aure." B'ata ta daina ganin abinda yake gani tare da kallon su. "Meye ya faru?" Gaura mata mari Primer minister yayi sai tayi tambul, kafin ta zauna da kyau.. "Alhaji marina kayi" Cikin tsuma ya mike tare da watsata waje. "Kije na yanke igiyar aurena baki daya akanki, Allah ya bi mishi hakkin shi na cutar da d'anki da kika yi" Ya fada tare da juyawa tana ihu tana kome, kifa hannu Mohan ya a fuskar shi, kamar ba sadauki ba yana kuka me ban tausayi. "Kayi hakuri, baka yi sa'ar uwa ta gari bane." Ya fada tare da shiga dakin shi ya kwanta, kowani dan adam yana da nashi ciwon mai illa ko mara illa, tashi ciwon ya zama tarihi na tsawon shekaru saba'in da wani abu, abinda mutane suka kasa fahimta akan wannan al'amarin shine rashin karban ƙaddara da uzuri. Shi yasa tafiyar Ƙaddara take rugu rugu da zukatar su. ** Kwana biyu ina kwance, ranar da na farka kallon Innah nayi, sannan na dauke kaina. Shigowar Dr Zainab ya sani ce mata. "Mommy don Allah ki taimaka min ina son na tsarkake jikina" "Toh" haka ta taimaka min ta had'a min ruwan zafi, nayi wanka tare da gasa jikina, sannna na fito ina tafiya a hankali, sake mai dani tayi tana faɗin. "Zaki lalace muje na guda ki da kyau." Haka ta dawo dani ban dakin ta dubani sannan ta zuba min ruwa me zafi da wasu magunguna ta sani na zauna a cikin shi. Hawaye ke zuba min, har na gama na fito, sannan ta had'a min shayi me kauri ina sha ina kuka, ina idarwa na wanke bakina, na zauna na gabatar da sallar da ake bina sannan na daura da addu'o'in, wanda badan Ta rufe min bakina ba, Allah kadai yasan Irin Bala'in da zan janyo musu. "Wallahi addu'o'in da nayi ne, Ni na mishi Allah ya juyar da shi kanki, don Allah karki yi addu'a. Ƙaddara ce ta faɗa min amma wallahi na sha zuwa niman ki aka ce sun tafi dake?" "Wacece ke?" "Sai kin tambaya ne? Ai balagazar da ta kasa yarda da ƙaddara ce ta tafi bata kalli abinda ta haifa ba, ta bishi da mugayen fata gashi Allah ba azzalimin sarki bar ga kayan ki nan tunda ta bude ido ta san meye soyayya masifa da bala'i da rashin jin dadin rayuwa suka sakota a gaba, an ce miki Allah abokin wasan kine!" "Ya isa haka Aminatu!" Abie ya daka mata tsawa. "Uwata kiyi hakuri, gamu nan iyayen ki dukkan mu biyu, don Allah kiyi hakuri." Tashi nayi tare da bude kofar, na nuna musu hanya. "Uwata!" "Ismail Wodaadabe da Dr Zainab Mustapha Ja'e, zaku iya barin gurin nan ko sai na fita na bar asibitin?" Na fada ina kallon su. "Zamu fita! Amma kiyi hakuri kinji" "Idan na shigar da karan ku zaku fadi abinda yayi muku kyau a gaban ka, Sai na rusa" Na taka gaban su, ina murmushi na cigaba da cewa. "Sai na saka an muku tofin altsine, sai na hanaku jin dadin rayuwa, kuna kallon jama'a zaku zama abin kyama, sai na saka ku kuka kamar yadda kuka jefa rayuwata. Daren amarcina daren da mijina ya amshi martabata, kuka ja min uwar shi ta kore ni ko wanke janabar jikina banyi ba. Wallahi Billahi azim sai kunyi kuka." "Idan haka zai sanyaki farincikin na shirya taranki, amma karki tozarta mahaifiyar ki" "Mahaifiyar wa? Ni wallahi na tsane ku, bani da Uwa Ni Shegiya ce ku fita bana son ganin ku" haka ayita ihu ina bala'i, tare da koran su. Suka fita baki daya. Idan nace muku bani da lafiya zaku ga kamar karya ce, amma tabbas na haukace. Haka na rubuta karar da nake, na Abie da Mommy, gashi kullum ƙarin ruwa ke min sai da nayi sati biyu. Kafin na uku aka sallame ni, gidana da yake nan Maradin ba nufa, kuma baki musu magana, haka kullum zasu zo. Amma bana kula su. Ranar Asabar na nufi Niamey, tare da maka su kotu, na kafe lallai sai an yi shara'ar, kuma na ce Ni zan tsayawa kaina. A hankali maganar ya shiga yaɗuwa kamar wutar daji, Surukar shugaban ƙasa tayi karan iyayenta sakamakon samarda ita ta hanyar da bai dace ba, haka yayi sanadin da Uwar MG Mohan tasa ya sake ta a daren Auren su. Sannan na samu goyan bayan wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam, tare da goyan bayan yan siyasa, ta kowani gefe an sami taimakon da ya dace kuma sun tsaya min, wannan ya kara min kwarin gwiwa. Shi kan shi Mohan yana can bai da lafiya, bai san wainar da ake toyawa ba, haka na zauna a niamey har ranar da za a saurari karan, Abie a ranar ya ajiye aikin shi, ya shiga kotun. Ina zaune kaina sunkuye, labarin ya zama abin yayyatawa, ko ina na duniya so ake aga shari'ar. A hankali kowa shigo, kafin aka fara gabatar da kara, kirana akayi, bani da lafiya amma dan bakin naci haka ina tashi ina niman faduwa. Na nufi inda zan tsaya, koda na nufi gurin kifa kaina nayi. Ina jan numfashi, gashi har microphone aka saka mana sabida mutanen da sukayi dandali na son jin yadda zata kaya. *** Da sauri ya shiga dakin tare da cilla mishi jaridar. "Matarka tayi karar iyayen ta, a kasar jaridar ka duba" an b'ankad'o sirrin Primer minister ashe ba dan Alhaji Muhammad Aghali bane shege ne. Mikewa yayi tare da ɗaukar jaridar, ya nufi Part din Ammyn. Ya ajiye mata. "Mijinki abin alfaharinki, ya sake ki amma mun roki arzikin ya zauna dake, gashi nan an b'ankad'o sirrin shi, kin b'ankad'o sirrin yarinyar da babu ruwanta, Allah ya bankado namu sirrin, shi yasa hausawa suka ce Kunyar mara kunya asara ce. Dole ya ajiye mulkin domin wannan kadai ya ishe shi zuciyar shi ta buga." Yana fadar haka ya nufi inda motar shi take, ya shiga Office din Abbu ya nufa, cikin kwanciyar hankali ya same shi suna tattauwana ne, da yan jaridu, kuma ya tabbatar da cewa adawa ake dashi shi yasa ake son bata gwamnatin shi. Bayan tafiyar su ya kalli Mohan. "Me ake ciki?" "Kome ya lalace" "A'a mun kira Allah, kuma ya amsa mana, kaje ka dakatar da Yarinyar." "Taya Abbu?" "Tana sonka! Kai namiji ne maza tashi kaje, ko bamu yi aikin gwamnati ba zamu iya rike wasu har da jikokin mu, dan haka zan ajiye aikin da fatan zaka ajiye aikin soja" Murmushi yayi sannan yace mishi. "Insha Allah" .....daga nan yakira Khalil suka nufi kotun, shima kuma primer minister ya kira a dakatar da shari'ar, amma fir Maimunari taki, ta kasa magana sai haki ga hawaye da yake zuba mata,. Duk me Imani idan ya ga yadda take son magana amma ta kasa, sai dukar kirjinta take, tana kuka. Daidai shigowar Mohan. "Ya Mai Shari'a, ka tambaye su Meye nayi musu haka suka rusa min tushe na!" Kafin ta kara sani kalma ya isa gabanta. "Maimunari Isma'il, primer minister ya kira yace wannan matsalar ta cikin gida ce, dan haka kotu ya maida ku gida ku sulhunta a can." "Wannan ba adalci bane, wannan son kai ne.wato dan ban da kome.." bakin shi naji a saman nawa, ya d'ago ni cak yana sumbatar bakina, har ya fito dani daga koyun daukar mu ake, yana zuwa gurin motocin da aka ajiye ya sauke ni, dukar shi nayi tayi. "Ina ruwanka. Meye matsalarka sani Ni, ka kyale ni." Na juya tare da nufar inda motar Ansar yake na shiga tare da cewa. "Mu bar nan." Haka ya fita Mohan ya rufa mana baya, sai da muka kayi tafiya me nisa, sannan na nace. "Sauke ni" gefen hanya ya tsaya na fita tare da nufar cikin sahara babu takalmi, ihu nake ihu nake tare da zama akan kasar ina dukar kasar na rasa meye zanyi, yana tsaye shi kanshi sai da yai danasanin kuntatta mata. Yyi amfani da sirrin ta da yaji a bakin Innah ya kuwa Hajiya Latifah, bai zata idan kome ya fito zata cutar da kanta ba haka dai yanzun. A haukace ya yi parking sannan ya fita, tare da nufar inda nake. Yana zuwa ya rungume ni, kuka nake yana shafa bayana. "Kiyi hakuri" "Hammah Mohan me yasa?" "Soyayyar mu daga Allah ne, wallahi ban ji kome ba akan ki, sau soyayyar ki da yake kara samun matsuguni. Raina," "Hammah na, zan mutu" "A'a bazaki mutu ba, sai dai mu mutu a tare." Kuka nake na rasa meke min dad'i, a hankali ya d'aga ni, daukata yayi cak ya kai ni bayan motar ya shiga ya zauna tare da daura ni a jikin shi. "Khalil muje" Haka muka tafi tare da barin Ansar a gurin, kasa aiwatar da kome yayi, haka yabi motar da ido. Kafin ya shiga nashi yana me barin gurin, shafa wuyar shi tayi yana jin abinda ya rike mishi wuyar har yau yana damun. ** Gidan shi da babu wanda ya san da shi daga Ni dai shi sai Khalil muka san da zaman gidan, ya kai ni, Khalil yana ajiye mu yayi tafiyar shi. Shi kuma ya wuce dani sama, inda dakin shi yake, tunda ya kwantar dani a gadon bana iya kome daga amai sai barcin wahala, kuma shi yake jinyata. Ranar da na cika kwana uku a gidan ya dauko min Mommy, ina ganinta na fara ƙoƙarin Mik'ewa. "Karki matso kusa dani, karki zo inda nake, wato ka dauko min ita ko? Hmm shi kenan." Na fara ƙoƙarin tashi, haka suka min allura tare da ƙarin ruwa, tana kallon yadda na zabge, sai wani bau da nayi tare da cikar da nayi daga Kirjina, ni kaina nasan na kara girma ta kirjina, tunda ta saka min ruwan na ji dama dama, a hankali na cigaba da samun sauki. Kwana na goma sha bakwai, ranar ya fita na bar gidan tare da ajiye mishi wasika. *** Daga nan airport na wuce, na nufi Maradi, na hada kome nawa, sannan na tafi makarantar mu, dakyar shugaban makarantar ya bani transfer, bayan na loda mishi kudi masu yawa, sannan na bi motar dare zuwa Damagaram, na kwashi kayana da takarduna musu muhimmancin, na fito na nime motar da zata shiga Libya. Dakyar na samu sannan yana tashi muka dauki hanya, na bar kome na bar kowa nawa, na mike tafiyar ƙaddara, wanda tunda ba fara ban tsaya ba har yau, na manta rabona da farin ciki. Na manta rabona da nayi dariya, haka kome nawa ya lalace, ina ji ina gani sun lalata min gobe na. *** Yana dawowa gida ya shiga dakin. Akan pillow ya sami yar takardan. *Nagode sosai! Sai dai nasan dama kayi min nisa kuma karambani ne irin nawa yasa Ni fadawa SOYAYYA da mai kyakyawan tushe kayi hakuri na tafi Allah ya had'a mu a darulsalam matar ka Har abada Maimunari* Kaina na mugun ciwo wallahi... #Mai_Dambu [8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1114000208?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=9erIrydatIuPkJseZal69xUkMstLsWx8GyFdlSLeJfq8JZ7%2BWyAuXyBi3TFONZWvmJKNlkO3cngr4M2Sk%2BLQ9DhqVJ2mn36fvlalGIeTBV4qaMAzYIkNfoxokz2fxpjv 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN DA BAKWAI. HMMM NIDAI YAR KALLO CE! Zuɓewa yayi akan gwiwar shi, ya rasa meke mishi dad'i baki daya, wayar shi ya ciro. Ya shiga gurin kira, ya kira Abie. "Abie ta tafi" ya faɗa kamar yaro karami. "Kuka zaka yi?" Ya tambaye shi yana murmushi, "Karka damu, zata dawo Insha Allah ba zata tsallake boda ba, zata dawo." "Abie Mommy tace tana da juna biyu! Abie rayuwar su da abincin ki ta!" "Karka damu zata dawo, baka yarda dani bane?" "Na yarda da kai" "Kwanta kayi barci zata dawo Insha Allah. Sai dai idan ta dawo ka rabu da ita kayi watsi da ita" "Ba zan iya ba" "Zaka iya, domin zata cutar da kai da abinda soyayyarta. Ka cigaba da hakuri Mahaifinka ma kayi ta bashi hakuri. Itama Mahaifiyarka ka bata hakuri." "Toh" ya faɗa, Abie ne ya kashe wayar ma. * Bayan sun gama wayar yayo alola tare da ɗaukar Alqur'ani, addu'o'in kawai ya shiga yi yana ambaton sunanta. Bai tashi ba zai da yaji a ranshi Allah zai amsa addu'o'in shi sannan ya mike tare da turawa Dr Zainab sako. *_Ina kara baki hakuri don Allah ki taimaka mana da addu'a ke uwa ce Maimunari tana bukatar addu'o'in ki._* Sannan ya mike tare da fitowa falo yana labarta musu tafiyar Maimunari. *** Tafiya muka yi bana kare ba, dab zamu fita bodin Nijar, mu shiga hanyar Libya, hukumar shige da ficce suka kamani, nayi juyin duniyar nan amma fir suka ki sake ni, karshe wayata suka amsa suka duba Number Hammah Mohan. Aka kira shi. Kamar a mafarki ya ji kiran dan haka bai b'ata lokaci ba, ya kira Dan Ba'are, aka yi magana da hukumar sojojin sama, aka bada jirgi. Har bakin bodar yazo daukata, sai da yayi kome sannan ya shiga inda aka ajiye ni, na kifa kaina da hannuna. "Tashi muje" mik'ewa nayi a hankali, ya dauki jakar kayana ya fita dashi. A hankali naga yana tafiya. Da gudu na bishi tare da rungume shi ina kuka. Tsayawa yayi yana sauke ajiyar zuciya. Shi kanshi dan Ba'are goge kwallar da yake zuba mishi yayi. Muna shiga cikin jirgin yayi mishi magana da buzanci. "Ka dauki matar ka ku bar kasr nan." "Taya?" "Zaka iya mana" "Zan bar Abbu cikin kad'aici ne" "Toh ai Ammyn tana kan bakanta sai ka auri yar masu kudi." "Toh nagode! Amma ka tattauna da Abbu duk yadda yace" Haka suka yinta hira ina jikin shi a kwance, ina shaƙar kamshi turaren shi, har muka isa Niamey. A hankali ya dauke ni, muka wuce gidan Abie, Khalil na parking ya wuce dani dakin da ya tab'a kai ni, lokacin karfe biyu na rana, haka ya kwantar dani. A hankali ya janye rigar jikina yana kallon shafaffen cikina zuwa maran bai ga alamar kome ba, babu alamar cikin fa. Maida kanshi yayi kirjina da ya cika. Murmushi yayi yana shafa kirjin, su kam ya yarda dan sun dauke kome, har wani kumbura suka yi, addu'o'in yayi mata tare da shafe ta, sannan ya fito ya sami Abie. Mika mishi fura da nono yayi, a hankali yake sha. Shigowar Khalil shima Abie ya mika mishi. "Abie zama haka babu dad'i fa? Kayi aure mana" "Hmm" "Ko Mommyn mu zamu maka bikonta." "A'a Nagode" Duk yadda suka so amma fir yaki, haka suka gama suka bar gidan. .... Karfe biyar na yammacin na farka sannan na nufi ban daki nayi wanka, sannan na fita na nayi sallah, ina sallah naji shigowar shi. Bayan na idar na kulle kofar, haka nayi ta zaman daki ga yunwa ga zazzaɓin da ana magarib nake fara shi dai gari ya waye, nake samun sauki. Cikin dare na farka nayi ta buga kofar dakin, na kasa bude kofar, karshe balle kofar kayi, suka kai ni asibiti. Anan na kwana. *** Washi gari. Ya shiga gaishe da Hajiya Latifah, tana zaune. Abun duniya ya dame ta, sunkuyar da kai yayi sannan yace mata. "Ammyn ki yafe min" "Zan yafe maka amma sai ka min alƙawarin ba zaka tab'a dawo da Maimunari rayuwar ka ba, idan kayi min haka wallahi na yafe maka." Da sauri ya d'ago kai yana kallonta, kafin ya sunkuyar da kanshi. "Naji" "Alhamdulillahi! Allah yayi maka Albarka ka tafi Maiduguri akwai Yar Kawata ka nimo aurenta." "Toh" Ya fada mata, haka ya fita ya nufi shashin mahaifin shi ya gaya mishi, yadda suka yi. "Toh Allah ya kyauta" "Amin amma kafin nace ina son zuwa naga Nahnah naji ance min bata da lafiya." "Karka sake ka gaya mata kome ka barta Allah ya bata lafiya." "Toh insha Allah." Haka ya shirya ya tafi Agadaz babu shiri. Duk da ya samu jikinta da sauki, amma sai da ta mishi maganar Maimunari, yake yayi mata. "Zata zo Insha Allah" "Akwai labarin da zan baka, naji labarin abinda ya sami Mamman Nasir, gaskiya ce babu bincika karya ba. Amma kuma ai Nasir ya rike shi da Amana. Shekaru saba'in da wani abu baya. Duk wanda ya xaga Afrika yasan bayan wasu kabilun babu kabilar da ta kai Fulani yaɗuwa a nahiyar Afirka" Ajiyar zuciya ta sauke nauyin kafin tace mishi. "Karka damu, idan ka shirya kazo kai da iyayenka ka iyayen yarinya, zamu yi magana da kai. Akwai abinda na gani a tattare da Yarinyar. Kayi min fatar na samu lafiya zan gaya maka yadda kome yake har ita yarinyar ta san waye Mahaifinka, sannan itama uwarka ta san waye Mahaifinka." Ba haka yaso ba, amma haka ya bar gidan bayan ya cika ta da Alkhairi, sannan tayi mishi addu'o'in ya tafi. *** Bayan wata uku. Cikina ya shiga na huɗu, ina kwance bana shiga harkan su, amma yau da ya kasance juma'a ina lura da yadda suka ki kallo har wayata dauketa Abie yayi,Ni kuwa ba magana nake mishi ba, Innah tayi fadar tayi rarrashin har ta gaji, shi kuwa zuba min ido yayi. Kuma ban da sakarci naso na kuma guduwa, amma wallahi haka na gama shiryawa, nayi ta yawo a cikin gidan ban fita ba. Haka ya zuba min ido,domin idan yace zai yi magana tabbas zai dake ni, domin zaman da nayi da shi a yanzun wallahi yana da mugun zafin rai, gashi idan yayi magana kamar saukar aya. Bana mishi musu kuma bana mishi taurin kai. Amma kuma bana magana dashi, Mohan shi yake zuwa ya kai ni asibiti, amma shima na lura wani dauke min kai yake,haka ya sani jin na tsane su baki daya. Ina ganin Abie ya shirya zai fita. "Hammah Sama'ila ina zaka?" "Zan tafi Maiduguri ne daurin auren MOHAN" Dama na fito daga cikin kitchen kenan rike da bowl na y'ay'an itacce. Ban san yadda aka yi na yanki jiki na zube ba, jini me mugun yawa ya shiga zuba min kamar an bude fanfo. Tashin hankali,daukata yayi tare da nufar waje dani. Asibitin aka nufa dani, Allah da ikon shi Muka hadu da Khausar. Ita ta amshi ni, shi kuma Abie ya kira Mommy ya gaya mata. .... Washi gari tazo, ita da su Benazir. Abun dariya bata kula Abie a gaban yaran su kuwa dake Abie yana zuwa duba su, Yaran suka makale mishi, ganin halin da nake ciki tacewa Innah. "Ina ga ko zamu fita da ita ne, na gaji da Nijar din nan!" Juyawa nayi tare da cewa. "Babu inda xan bi ki, idan ma fitarwan ne sai dai Baba Mari da Innah su bini, amma ke wallahi ba zaki bini ba" marin cinyata Innah tayi. "Barta Aminatu, shikenan za a kawo miki Baba Mari! Sai ku tafi Zurich." Kin amsa mishi nayi tare da dauke kaina ina kuka. "Mommy Adda Munah sai kace baby. Ta bude baki tana kuka, sai na gayawa Hammah Mohan ya ga kukar ki" "Innah kin ga dake Ita yar Aure ce tana min ab..." Marin bakina tayi. "Amma baki da hankali ko? Ciki ne a jikinki kike tozarta iyayen ki? Haba Maimunari Haba Maimunari" aikuwa na kuma buɗe baki na fashe da kuka. Shigowar Hammah Mohan, a hargitse. Abie yace mishi. "Fita kar na kuma ganin ka, mara hankali kawai. Wallahi ka bani mamaki. Idan ka yi wasa WALLAHI sai na haramta maka Maimunari har abada, dan hauka ka sake yarinya ko gidanka bata shiga ba! Sannan nayiwa Mahaifinka magana yace ba zai maka dole ba" "Ai Abie na zame maka dole, domin dai Maimunari uwar dana ne kuma sau dari idan aka sani niman aure sai ka auro su ba sake su." "Mahaukata kawai." Karasowa yai bakin gadon yana me rike hannuna,.na kuwa fashe da kuka. "Dan ka cuce shi shine kawai zaka zo min jeka ta cinye ka." Takaici ya ishe Abie, dan dole ya kore Mohan, amma dan bakar jaraba yana kofar d'akin. Da yamma haka Hajiya Lateefah ta biyo ni har asibitin taci zarafin mu, babu wanda ya tanka mata, sai dai bayan tafiyarta ne, dake tace min Ni da Mohan sai a lahira idan ana zaman aure mayi. Shine na fara aman jini. Dan haka Abie ya tafi Maradi ya dauko Baba Mari, ya kaita gida dake Innah da Mommy suna kaina, itama kanta wannan karon Mommy tayi kokari, ta saka an daure mahaifar, ita tayi ta shige da ficce, har gurin Primer minister, wanda al'umma suka hana shi barin aiki. Ta nime ya saka hannun, sannan sun tattauna dashi, ya fahimce ta sosai ta koka mishi a matsayin ta na uwa da kuma halin da Yarta take ciki. Kuma ya gamsu. Dan haka tana dawowa lokacin, Abie ya kawo Baba Mari, suka haɗu da Mommy, ta gaishe ta a fisge kasancewar suna tattauwana da wasu likitocin, aka kuma amince da kome sannan ta dawo dakin, kallon juna suka yi, cikin wani irin ta shin hankali Mommy ta rungume Baba Mari. Kuka suke baki daya, kafin suka nutsu. "Ikon Allah! Munyi gudun abin kunya, yau gani na rike abin kunya da hannuna. Gudun abin kunya bayan mun tafi Allah yayiwa Malam rasuwa, tare da fatan zaki nime mu, amma bayan na gama takaba, na dawo Nijar . Naje gidan su Khalid baya na karshe na samu labarin yayi aure sun koma kasar waje da matar, bayan wani lokaci na koma aka ce min sun zo sun. Koma Mahaifiyar shi ta rasu. Ban kuma komawa ba, na barwa Allah duk inda kike zai dawo min dake, shine wata rana ina yawon niman mafaka, Malam Ansar ya buge ni, karshe da yaga bani da matsuguni ya bani matsuguni a gidan shi, har Allah ya kawo min Almamoon, lokacin tana mata maza!" Sun sha kuka sannan suka zauna suka tsara yadda tafiyar zata kasance, tunda su Yumnah sun samu hutu a tafi dasu. Ita kuma Mommy ta zauna a nan ita da Innah tayi tsalle tace bata zama, bakin aikin ta zata koma. Haka kuwa akayi. Suka tattara suka tafi. Ko Mohan bai san inda suka tafi ba, karshe itama Mommy tafiya Saudiya tayi. * Kuka take kamar ranta zai fita idan ta ga yadda Hanan ta koma, sai ta ji zucuyarta yayi nauyi sai ta ga bayan Hajiya Lateefah, Mohan, Maimunari, sam Hanan ta koma kamar wacce ta shekara dari tana jinya, duk inda suka shiga sai ace su koma wanda suka yi niyyar tab'awa ne ya dawo musu da kayan su. Yau ma sun gama wahalar duba inda za a saka mata jini, yaki samuwa, can kuma ta kama amai kore shar, kafin tace. "Aniyata ta zata koma kaina" daga haka bata kuma magana ba, sai warin da ya cika d'akin. Koda aka duba kayan cikinta ne ta kasaye shi, abin tausayi haka Yarinyar nan ta mutu, hauka tuburan uwarta tayi, tana cewa. "Sai na kashe su, sai na kashe su" Itama rufe ta aka yi a daki... (Ramin karya kurarre ne inji bahaushe) ** "Mohan wai ya zan maka ne? Sake ta kayi fa!" Inji Hajiya Latifah, "Toh Ammyn ki kuma nima min wata" "Anya yarinyar nan ba mayya bace? Ya daga kawai an gaya maka ta fadi zaka sake yar mutane..... *KAINA NA MUGUN CIWO A SAKA NI ADDU'A 😓🤮* _KU FAHIMTA MANA SHUGABAN KASA FA AKA BINCIKO LABARIN SHI AKAN SHIMA KAMAR MAIMUNARI CE DAN HAKA A DAINA RUDEWA PLEASE IDAN KUKA YI HKURI ZAKU JI KOME🤭_ #Mai_Dambu [8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... _Don Allah ina niman wata baiwar Allah daga lafia takirani sati daya zuwa biyu da suka wuce idan ta ga sakona don Allah ta min magana 👏🏼_ BABI NA HAMSIN DA TARA ALLAH KA RUFA MANA ASIRI RANAR JIN KUNYA! YA ALLAH KARKA KUNYATA MU RANAR DA BA ZAMU IYA KARE KAN MU BA! DUK WANDA YA NUFE MU DA SHARRI UBANGIJI MUNYI TAWWAKALI DA KYAWAWAN SUNAYEN KA KA KARE MU BA DAN MUN ISA KO MUN KAI BA! YA ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU DA NA YAN'UWA MUSULMAI BAKI ƊAYA 👏🏼👏🏼👏🏼 ASSALAMUN ALAIKUM.... RANAR DA BA ZAN MANTA BA... Na gani a jikin littafin farko da na dauka. _Ba zan manta ba, kasancewar Tabbas ban san kuskuren da nayi a baya zai saka ni kuka a gaba ba, duk da ba laifina bane! Sai dai babu macen da za a keta alfarmarta bata yi abinda nayi ba! Duk inda aka kai aka kawo karshe dai nice mai daukar laifin.... Ya Allah karka kamani da laifin da zuciya ta kai ni! Ina kewar abinda na haifa_ Tsayawa nayi ina kallon kwanar wata da ranar da tayi rubutun, kafin ta cigaba da cewa. _Iyayen mu Fulani suna da kunya da YAKANAH amma basu tsayawa ya'yan su, musamman idan ƙaddara ta faɗa musu! Da ace bai tafi dani ba da babu abinda zai faru! Yayi nasarar juya min duniya ta! Ban san cewa fad'a mishi ba sai da Khalid ya fahimtar dani! Duk da ya cutar dani a lokacin amma dan shi da shi kan shi sune maudu'i na_ Idan na fahimta tana son Abie ne? Idan na gane dama can ta fada kaunar shi! Mutumin da ya cutar da kai, ban da mahaifina ne sai ka kai shi bango. A hankali na bude shafin gaba. _Sai dai kuma zuciya tana son mai kyautatta mata. Khalid yayi nasarar samun matsuguni a raina, na kuma manta da duniyar shi wancan burkina Abinda na haifa na kuma saka shi a ido ko sau daya ne! Burina na daina kuka idan na kwanta, na daina mafarkai akan abinda na bari, ina zanga Iyayena?_ Tayi tambayar kamar tana bawa wani labarinta,a hankali nake bude shafi bayan shafi idan na gama wannan na bude wani, nayi kuka nayi bakin ciki, na tausaya mata. Ina son Mahaifiyata. Duk inda zata yi rubuce-rubuce zata ajiye har da kwanan wata da shekaru, littafin na karshen da na duba shine ya tsaya min a raina. _A ranar da aka kawo ta asibitin akan matsalar fyade ban san ya aka yi zuciyata ya karkata akan ta ba, sai dai kawai na tsinci kaina da son binciken lafiyar ta, a nan na Fahimci tana da angurya, garin a shigeta ne ya fashe har bakin farjinta ya ji ciwo! Abin ya tsaya min a rai shi yasa na roki abokan aikinsa mika mata aiki! Sai dai kuma yarinyar ta kuma tafiya abinta! Ina son ta_ Tsayawa nayi tare da fashewa da kuka, ina rungume littafin. Sai da Yumnah ta shigo. Ta zauna a kusa dani. "Adda Munah! Mommy tana sonki sosai, ki daina kin kulata tace zata zo!" Kallon yarinyar nayi domin ban san me zance mata ba,.banbancin mu da yarinyar ita fara ce kuma tana kama da baban ta, hatta gashin goshinta irin nawa ne, sajenta da (Kai Bororoji fansa musamman matar Sadeeq ko Matar Yau wai na gaya mata spirit din da alamun yake shafawa gashin baki yake tsirowa 🤣🤭 very funny 😂🤣 Wayyo Allah na, wato mutanen nan ba zaku kashe ni da dariya ba🤣😂) "Didi Yumnah jeki wasa zan kiraki anjima" da sauri ta fita na dauki littafin na karshen da nake dubawa. _Ranar da na ga daurin auren yarinyar a tv sai da nayi sallah nafilla ta tsaya min a rai, tausayin ta da Sonta sun cika min zuciya. Ban sani ba ko dan tana yanayi da nice oho! Sai dai kuma washi gari bikinta da kwana biyu aka kawo ya cikin rai kwai-kwai mutu kwai-kwai ya sani jin tashin hankali! Da naga Mutumin nan da ita sai naji kome ya dawo min sabo! Ban tsinke ba sai da ya gaya min ita din Rayuwata ce!_ Kifa kaina nayi a kan littafin ina kuka, Sannan na bude shafi na karshe. _Ta kai mu kotu! Wallahi ban ji tsoron kome ba! Da farko na razana amma dake nasan yanci take nima na bata goyan baya! Allah ka huci zuciyar Maimunari idan ta ga wannan sakon! Ga takardu da risitai na shigowata Nijar nimanki da Iyayena sun tafi sun bar ni! Ban kuma tsinkawa da ita ba sai da ta nime barin mu! Idan Maimunari ta ga sakona ta yafe mana!_ "Ni din banza Ni din wofi! Ni din wacece da ba zan kaunaci iyayena ba! Shi ma da uwar shi ta cutar dashi bai rabu da ita ba, bai tsane ta ba, sai ni Ya Allah ka yafe min" na fada ina kuka, mik'ewa nayi na fito falon, na same su, suna hira. Ina zuwa gurin Abie na zauna tare da kwantar da kaina a jikin shi. "Abie kace ta tashi min gurina ne?" "A'a didi Yumnah! Ki bar Addah Munah ta kwanta kinji!" Inji Benazir. Tura baki tayi tare da cewa. "Abie kace Addah Munah ta tashi a jikinka" "Toh tashi bata so!" Kwalla ne ya cika min idanuna, "Shikenan" na fada tare da mik'ewa zan bar gurin. "Addah Munah!" Kallonta nayi. "Kiyi hakuri, zoki zauna" Haka na koma jikin shi na kwantar da kaina ina kuka. "Abie ina son kane na!" "Toh suma suna sonki" "Abie kayi hakuri" "Ya wuce" "Abie nasan nayi laifi. Shi da yake na miji bai bijirewa mahaifiyar shi ba sai ni, Abie ka yafe min" Murmushi yayi yana dafa kaina. "Babu kome" Haka na sha kuka sosai. Jikin shi sai da barci ya dauke ni, sannan ya gyara min kwanciya, a kujeran. * Auna jininta Khausar tayi cikin tausayawa ta kalli mahaifiyar tatta, "Sannun Ammyn ya jikin naki?" "Da sauki! Khausar kicewa Mohan, yaje Agadaz akwai yar kawu Shagari ya aurota!" "Ammyn ki kyale Hammah Mohan,matukar kika nace zai auro ta amma zai sake ta." "A'a ba zai sake ta ba" ta faɗa tana sauke numfashi. "Assalamu alaikum" suka yi sallama shi da Khalil. Zubur ta mike tare da kallon su. "Yawwa Khalil, gobe Insha Allah ku tafi Agadaz ku nimo auren Yar Kawu Shagari." "Toh Allah ya kai mu" "Mohan kayi ƙoƙari ka ga yarinyar tana da nutsuwa sosai." "Toh" ya faɗa mishi. "Khalil kaina ba yarinyar nan zaka auro ba ko?" Shiru yayi sannan ya sunkuyar da kai. "Me zaka yi da Zuri'ar su! Suna da mummunar nasaba." "Ammyn ita yake so, kuma mahaifiyar shi da mahaifin shi sun amince ina ruwanki da bashi shawara? Iyayen shi sun san abinda ya dace da don Allah ki kashe matsalar mu da kika Kunno mana shi." Inji Radiyah da tafito daga cikin dakin su, "Toh Allah ya baku hakuri, bani na hana Safwan aurenki ba, Allah ne ya nufa ba zai aure ki ba " "A'a Ammyn kece sanadi da baki tozarta sirrin Maimunari ba da babu mamaki babu wanda zai ki auren mu, gashi ko makaranta ban isa na shiga ba, nuna Ni ake da yatsu." "Toh dan an nuna ki laifi ne? Dama can kin fi karfin matsiyaci ke ba sa'ar shi bace!" Cikin jin haushi ta bar falon, domin zata iya yin abinda bai dace ba, baki daya yayunta sun zubawa Ammyn idanun, sai bakin mulki take da rayuwar su, tun ranar da taje aka kafta mata tijara a gidan su mijin Khausar take kwance ba lafiya. "Ammyn zan tafi aiki domin yau aikin dare gare ni" ta shiga hada kayan aikinta ta saka a jaka. "Toh ayi ta kwalliya dai domin ba zaki koma gidan da a san darajar ki ba! Gwara ki samo mijin kera sa'a, wanda zai nunawa Abdullahi yafi karfin shi" "Ammyn nifa ina son mijina, kuma ban ga laifin mahaifiyar shi da tasa shi ya sake ni ba, dan haka babu namijin da zan kula wallahi mijina nake so, ni ba Hammah Mohan bane yaga zai iya, yanzun Salman da Haddir da basu tare damu ai hankalin su kwance domin zasu iya fuskar rayuwar da muke, shima Abbu naji yana niman aure, kuma ya ce min yarinya ce karama yar Sarkin Maradi" Mikewa tayi zubur kamar zata tashi sama, "Yarinya karama? Ya rasa abinda zai sai auren yarinya karama, ai budurwan zuciya ce!" "Allah! Kina iya tozarta matar d'anki ma, balle matar da zan aura ranar juma'a daurin aure, ga katin nan" Ya mika musu yana kallon su. "Mohan naji ance kayanka zasu shigo ta kwatano, Allah ya taimaka." "Amin Ya Allah" "Yallabai don Allah ka saka baki yayi aure" "A'a keda dan gwal dinki! Ai duk abinda kika zab'a mishi zai bi, yaro mai biyayya haka" "Wallahi baya jin magana nace yaje Agadaz yaki min" "Toh kai dan gwal kaji Maman ka" "Insha Allah zan je" Haka ya fita ya barsu, itama khausar ta tafi aikinta, suma suka wuce shashin Mohan, tunda ya kwanta, ya kurawa sama ido bai kuma magana ba. "Khalil nasan kana sane da inda Maimunari take, amma kaki gaya min meye nayi da zafi ne?" "Wallahi ban sani ba, muna chat da kome da Beenah amma bata gaya min ba, sai dai idan na tambaye ta zata ce min da sauki." Tashi yayi zaune, tare da kallon shi sannan yace mishi. "Don Allah ka mata magana ta turo min hoton Matana mana" "Toh bari na dubata." Yana bude data ya fara duba ko tana online, aikuwa ya hango ta, ta daura hoton Maimunari, Mika mishi wayar yayi yana kallon ta, sanye take da doguwar riga, ta yane kanta da farin mayafi. "Ya Allah! Kai kasan dalilin cusa min kaunarta a raina! Ubangiji ka tabbatar da zama na har abada a rayuwar mu" "Amin Ya Allah Mohan" inji dan Ba'are, kwanciya yayi yana kallon fuskarta, cikin sabon kaunar matar shi. "Yar budurburdu dina" "Toh toh ya hakuri bani wayar na yi magana da yar kwailata" "Dan iska" Ya cilla mishi wayar ya cigaba da kwanciyar shi, idanun shi a rufe, yayi tare da tuno daren da ya tsaya mishi a rai, yarinyar ta bashi hadin kai sama da kome a rayuwar shi, ta yi hakuri da shi a daren kuma ta dauke laluran shi, tun daga ranar bai kuma jin wani sha'awa na mace ba, bai kuma kallon mace da sunan bukata ba, mace daya ya so a rayuwar shi bayan ita kuma Allah na tuba ba zai kuma jin dadin wata ba. *** Haka Ammyn ta sashi dole ya tafi niman auren Farisa, cikin girmamawa aka yi bikin, ranar da aka kawo mishi amarya Mohan ya mika mata takardan sakinta cikin mutuntaka, sannan ya shure kama yayi tafiyar shi Dubai, sai da yayi sati Uku me kyau sanan ya dawo. Ya sha masifa babu iyaka, nan ma yace mata. "Idan akwai wata yarinyar ki hadani da ita zan aureta." "Ni na haɗaka da wata ka je ka sake ta, ai na yafewa Maimunari kai ka jira dai duk ranar da ta bayyana sai ka je ka zauna da ita." *** Zuwan Mommy ya rage min damuwa, abinka da likita babba, ita tayi ta daura ni akan magani. Matsowar bikin Benazir da Khalil ne yasa, hankalin su yaso rabuwa biyu, dan haka Abie da dan uwan Baban su, suka tsayar da magana akan ayi hakuri na sauka lafiya, lokacin Itama Beenah din zuwa lokacin ta gama karatun ta. Sosai Iyayen shi suka amince, Kum basu wani d'aga hankalin su ba, haka aka Cigaba da shirya jiran haihuwata. ... Matsa min kafa take, a hankali. Tana bin karatun Alqur'ani karatun Shaikh Jafar Mahmud Adam Marigayi, a hankali take bin shi a cikin suratul Rahama, lokacin da tazo akan wata ta goma, inda Allah yace shin mai dan adam yake bukata wanda Allah bai bashi ba. "Ya bani Uwa ya bani Uba, ya bani kane, ya bani rai da lafiya..... 🤭Kuyi hakuri kunji.... Raina ne ya sosu, Insha Allah ba zan kuma ba🌚🌝 saura Page daya na tafi hutu 👏🏼 Don Allah ina bawa mutanen grp din Kishi INSHA Allah ina gama wannan zaku ji ni 😏🤸 kwana biyu ban kafta rashin daraja ba, wallahi har kaikayi nake ji😂🤣 #Mai_Dambu. [8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN DA TAKWAS. Kura mata ido yayi yana mamakin yadda Allah ya daura mata son kanta, sunkuyar da kai yayi yana kallon shaddar jikin shi. "Zan nima maka maganin ko kurwanka ta kama ta sake maka shi, Insha Allah wannan masifar da me yayi kama." Bai ce mata kome ba, haka dai ta gama masifar ta, yayi mata sallama ya bar gurin. A cikin kwanakin bai da lokacin kanshi domin tun da ya rabu da Maimunari ya ajiye aikin soja, sai ya koma kasuwanci, kuma dama yana kasuwancin bai mai da hankali bane. Amma yanzun da ya mai da hankali yana ganin Cigaba sosai. Yau da la'asar ya shirya zuwa duba Maimunari, yana isa da kayan marmari da ya kawo mata,ya samu basu asibitin. Ya tambaya aka ce ba. A san inda suka tafi ba,bai kuma tabbatar da ya rasa Maimunari ba sai da yake gidan Abie ya samu a rufe nan ya gane cewa sun tafi da ita wani gurin ne, haka ya kira Khalil ya gaya Mishi. Amma babu wani labari, da ya sami Abbu da zancen cewa yayi. "Ban san inda suka tafi ba, amma koma yayya ne ai Mahaifiyarka ta bukaci haka, dan haka idan na isa kuma na haife ka ka kyale musu yar su ta huta, ita ba matar ka bace Yanzun sannan kuma ba zai yiwu uwarka tana tozarta su ba, dan haka na gargade ka da ka fita hanyar ta, ko kuma na sab'a maka." "Amma Abbu!" D'aga Mishi hannu yayi tare da cewa. "Itama iyayenta suna SONTA, kuma babu wanda zai yarda ayi ta wulakanta Mishi d'a. Dan haka ka tafi ka zauna da uwarka ita ka barta da nata iyayen, saboda kai ta saka su a kotu, saboda kai ta wulakanta su, duk sabida soyayyar ka. Indai har zata aikata haka saboda tana son ta dawo rayuwarka amma uwarka taki meye yasa ba zaka kyale ta ba? Me yasa ba zaka hakura da ita ba? Tayi kokari tayi kokari. Don Allah ka kyale ta ta huta Ubangiji ya bata wanda ya Fika kai ma Ubangiji ya baka wacce ta fita." Jikinsa ne yayi mugun sanyi, sannan ya mike a hankali tare da nufar hanyar waje. "Insha Allah na hakura da ita, Nagode sosai Abie" Tun daga ranar yayi wani irin sanyi, magana ma bata dame shi ba, baya harka da kowa sai Khalil shima sai yana gari,.ana cikin wannan yanayin me niman auren Radiyah, suka turo har an gama magana, amma mahaifiyar yaron ta tawo da kanta, har gurin Hajiya Latifah. Bayan sun gaisa tace mata. "Hajiya Lateefah nice Mahaifiyar Safwan kawai jiya Mahaifin shi yace min sun zo nima Mishi auren yarinyar da yake nima bai gaya min ba sai da suka gama magana. Toh gani nan nazo na gaya miki gaskiya. Bana son had'a zuri'a dake! Ba dan kome ba sai dan mijinki shege ne bai da asali" "Keke!" "Ke yi kasa da muryanki! Indai har uwa irinki zata kashe auren danta ranar da ya kwanta da matar shi, meye laifina dan nazo akan a fasa auren dana da Yarki a? Dan haka ita da kika saka ta wulakanta iyayenta. Kin ga ina son kaina da arziki ba zan so dan da na haifa ya maka ni a kotu saboda yar ki ba. A takaice dai ba zan tab'a barin shi ya auri yar ki ba, da ya auri Yarki wallahi gwara ya mutu bai yi aure ba, balle kuma ga mata kaca kaca." Ta mike tana kad'a keyn motar ta, tare da ɗaukar jakarta, har zata fita tace mata. "Wallahi kamar yadda kika saka iyayen Maimunari kuka haka zaki yi kuka ga yara mata gasu nan a gabanki" Sannan ta fita, yadda kuka san gumki haka ta koma, tana cikin wannan yanayin, Khausar ta shigo dauke da jakar kayanta, niki niki. Idanunta cike da kwalla, "Lafiya!" Ta tambaye ta, zama tayi cikin shashekar kuka, tace. "Hajiyarsu Abdullahi tasa ya sake ni" ta faɗa hawaye na zuba mata, daidai lokacin da Radiyah take shigowa da nata kayan, kallon su uwar take cike da mamaki. "Akan me?" Ta tambaya bakinta na rawa. "Ban sani ba." Mikewa tayi tare da fita. Dake dama an ce wanzab bai son jarfa, sai gata har gidan Surukar Khausar, ta samu ma suna magana akan Khausar ne.ta shiga cikin gidan. "Hajiya Marwanatu lafiya Abdullahi ya sake Khausar?" "Zauna mana Hajiya Lateefah,ai abin ba na tashin hankali bane" "Akan me zan zauna" "Toh ita Yar gidan Babban alkalin bata da zuciya ne? Ko ba haihuwarta aka yi ba? Kinga indai har ke zaki iya sakawa dan gwal irin d'anki ya sake yar mutane bayan kuma kuna da abin kunyar meye a cikin dan nace dana ba zai zauna da yar da aka haifi Ubanta shege ba?" "Wallahi karya ne, sharri aka mishi." "Malama fita mana a gida, domin duk nan babu mahaukaci irinki,.dan haka maza a tafi a nimawa yaran ya'yan asali masu kyakyawan nasaba" Asalin koran wulakancin suka mata tare da gaya mata ai ko mata sun kare babu wanda zai auri yar yaranta, taje itama yaji yadda iyayen yarinyan da ta wulakanta take ji!" "Wai dan akan Maimunari kuke wulakanta Ni?" Ta tambaya kamar zata fashe da kuka. "Kai kunna mata wayar nan ta gani" Muryanta ne ya fito fili lokacin da take cin mutuncin Maimunari a asibiti. "Wallahi na rantse da Allah matukar ina raye babu ke babu Mohan. Yar karuwa ribar dadiro. Yar matsiyata an ce miki arzikin iyayenki zai saka na hakura ki zauna d'ana ne? Ko ance miki cikin da yake jikin zan yarda na d'ana ne? Toh ai bari na gaya miki tun wuri gwara ki nemi uban cikin jikinki, yar matsiyata jinin kazamta." "Kai kashe min idan ina jin wannan abin ji nake kamar na tattara yaran da Abdullahi da Khausar suka haifa kamar a watsar da su mota ya bi ta kansu" inji Surukar Dr Khausar, Wani irin abu taji a kirjinta zuwa kanta, dakyar ta d'aga kafarta cikin tashin hankali tace. "Hajiya Marwanatu, don Allah karki wulakanta jikokinki" "Ke kika iya wulakanta abin cikin yar mutane! Bayan d'anki ya yarda na shine? Toh ai dan mu ba jahilai bane da mun baki abinda ya dace, dan haka fitar mana a gida Allah ya wadaranki" Kasa magana tayi ta fita, dakyar ta shiga mota aka fita da ita, baki daya ta rasa fahimtar mene faru, a cikin yan kwanaki ƙalilan kome ya lalace mata. Ji take kamar tayi ta zuba ihu, amma babu hali. ** Tunda suka isa Geneva, wato Zurich, Abie bai da lokacin kan shi sai na sintiri zuwa asibiti. Kuma Alhamdulillahi domin wannan karon ma ya kuma gayyato likitan da ya dubata, shi ya kuma dubata. Amma wannan karon an yi mata aiki a zuciyarta, dan ma damuwar ya hadu da laluran ciki ne. Haka yayi aikin cikin nasara. Bayan kwana uku masu kyau, ta fara motsi, a hankali kuma ta farka baki daya, sai dai tun daga ranar. Abie yake mata addu'o'in yana bata a ruwan zam-zam tana sha, abinda ya haifar mata da komawa tayi sanyi. Magana ma sai kayi da gaske take yin shi. Sai nasiha, tare da bata tarihin magabata, Sannan ya kawo mata irin daukaka ta Khalid bin Walid, wanda Allah ya mishi kirari da saifullahi Ma'asum, sabida yadda yayi adawa da musulunci, sannan ya dawo yayiwa Musulunci hidima yayi adawa da kafirci, tare da kawo mata misalai dasu Nusaiba, Rabi'atul adaweyya, irin su Ummul Salma, karewa ya kafa mata suratul Maryam har dasu mujadala, da yadda mata suka yi gwagwarmaya a musulunci, sai ga Maimunari tana kuka tana rike hannun shi yace mata. "Lokacin khalifancin Umar, Allah ya yarda dashi, yace an taba zuwa yaki aka kamo bayi aka kawo su, yace yana tsaye sai ga wata mata a cikin su, an daure kafarta da hannunta da Sarka na karfe, yace dan matar ne ya b'ata, bata iya tashi tayi tafiya rarrafe take tare da ciro mamarta duk inda ta ga yara na wasa sai da durkusa ta nemi D'anta, wasu malamai ma sunce an ce matar bata gani, haka tayi ta niman D'anta. Balle ke da dukkan mu mun san mun yi miki laifi, mune iyayenki mun baki hakuri amma bamu tsira ba, haba Uwata ai bawa baya wuce ƙaddarar shi." "Abie kayi hakuri." Iya abinda na iya fada kenan na kwanta,.ina kuka mai mugun cin rai, amma a sanyayye. "Kina kukan kin rasa Mohan ne ko kina kukan abinda muka miki ne?" "Dukka Abie" Na fada mishi haka, fita yayi tare da gayawa Baba Mari ta tsaya dani. .... Sai da nayi sati biyar asibitin sannan aka sallame ni, koda na dawo gida ma, gasu Benazir da Abie ya mai da ta makaranta, Yumnah ma haka, idan suka dawo kuma shi yake karantar damu a gidan, a hankali na Fahimci iyayena suna min wata irin soyayya da yasa basu iya tsawata min, musamman Mommy bawai bata fada bane a'a kawai tausayina ne yasa kullum sai ta kirani a waya,kuma koda na dauka daga Sannun sai Sannun da ya jiki da sauki, shikenan. Babu abinda yake hada ni da ita, kuma zata b'ata lokaci tana saurarona, bawai bana son iyayena bane, kawai ni dai ina da yakinin sun tafi sun barni babu wanda ya damu dani sai yanzun da na girma suka damu dani, idan ta ga nayi shiru, tayi min magana nace mata hmm! Sai ta kashe wayar ta kira Benazir ta turo ta d'akina. Duk da halin da nake ciki ban tab'a tsanar su Benazir ba, asalima jin su nake kamar mun fi haka kusanci, bana son naga Beenah tana rab'ewa idan ta ganni da Abie muna zaune, sai naji kamar sabida Ni aka raba su da Mahaifiyar su. Yanzun haka ta shigo dakin tana waya da Mommy, zama tayi tana kallona. "Mommy gata nan dai tana karatu ne" "Toh Toh kyale ta, karki dame ta, amma ya Babyn ku? Yana lafiya?" Dariya ta saka tare da cewa. "Lafiyan shi lau, Mommy baki ga Yadda Adda Munah ta koma ba, zan dauka miki hotonta." Kashe wayar tayi tare da zuwa zata dauke ni na buge wayar ya fadi can, kallona tai tare da juyawa ta dauki wayarta, ta ga ya tsage. "Addah Munah! Ba laifi bane idan kinyi fushi da Mommy, amma kuskure ne babba wulaknta Uwa. ciki ne a jikinki, kuma zaki so idan kina haife shi ya mutunttaki ko? Wallahi da ace Daddy ne ya saya min wayar nan ba zan tab'a miki magana ba, Amma wannan wayar Mommy ce ta bani ranar da na cika shekara sha takwas, ko da wasa ban tab'a barin shi ya fadi haka ba, sabida ina son Uwata duk abinda zai fito daga gare ta mai kyau ne," Fita tayi daga dakin can ta dawo tare da wata jaka, ta shiga zazzage min shi baki daya a gabana, tana kuka. "Dairy ɗinta ne baki daya, labarinta ne a nan baki daya, soyayyarki ce a nan baki daya. Zaki tozarta mana mahaifiyar mu, idan baki sonta Kice baki kaunar ganin mu, yau zamu bar miki gidan Abien ki, domin ba zan cigaba da kallon ki, kina tozarta min mahaifiyar ba." Tana fadar haka ta juya ta fita daga d'akin, tana kuka. Da Abie suka haɗu. Ya riko hannunta har falo ya zauna da ita, goran ruwa yasa aka kawo mishi ya mika mata tasha. Tana shashekar kuka. "Abie ita me yasa bata farin ciki? Allah ya bar mata Mommy da kai! Mu kuma Allah ya dauke Daddyn mu!" Wani irin lumshe idanun yayi, tare da bude su akanta. "Abie a duniya akwai na biyun uwa?" "Babu!" "Toh meye yasa take wulaknta Uwa?" "Sabida laifin da muka aikata? Kuma har yau Mommynku bata zauna da ita ba, kuma tana bukatar kulawar ta." "Wannan shine matsalar ta?" "Eh ina zaton haka!" "Insha Allah zata zo, ta zauna da ita har ta haihu.. *HMM! BAN SANI BA KO A PAGES DA SUKA WUCE NA RUBUTA CEWA HAJIYAR MOHAN TAGA TSIRAICIN MAIMUNARI DA HAR YA ZAMA ABIN MAGANA AKAI KUNGA WANNAN BOOK DIN FREE BOOK NE! SABIDA KANANU MAGANA INSHA ALLAH VERY SOON ZAN KAMMALA SHI AMMA KAFIN NAN NI MUTUM CE DA NAKE TSAYAWA AKAN MAGANA TA DA KUDI NAKE NIMA DA BA ZAN YI BOROROJI FREE BOOK BA. AMMA DAKE WASUNKU BUTULCI BA WANI ABU BANE A RANSU WAI HAR SUNA MAGANA AKAN ABINDA BAN FADA BA INSHA ALLAH WANNAN ZAI IYA ZAMA NA KARSHE! WALLAHI DUK WANDA YAKE BIN BOOKS DINA KARYA YACE NA B'ATA MISHI LOKACI BAN YI POSTING KODA NA KUƊI NE, HMMM MAJI MA GANI AN BINNE TSOHUWA DA RAI. ALHAMDULILLAHI DA KUDIN KU ZAKU SAYI BOOKS SAI AN GADA MA AKE MUKU POSTING WANDA NA B'ATA LOKACI ANA GAYA MIN MAGANA AI BA WANI ABU BANE DABI'A CE TA DAN ADAM BUTULCI ALLAH YA BAKU HAKURI MASU BASIRA NI DA NAKE RUBUTAWA KU YAFE MIN KAR NA LALACE DAN NACE AN GA TSIRAICI YAR UWARKU MAIMUNARI!* Dan haka ina ga babu amfanin na cigaba da Posting a WhatsApp. #Mai_Dambu [8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1114877151?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=z9ZOtX44qohxpFic26GH%2Fsn4B4gALffG4rhIwdZgrEOLvK6sIq9knb%2FFjtTVFnjyKKX0u8D3JU062TWZvHMQK0nMVrMzF9JRvFiItDn%2BYZJxkFtAoVCSwYFXCySTxhIc 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SITTTIN. "Amma" rufe min baƙi tayi, bayan ta kashe karatun. "Me yasa baki da Fahimta? Ki godewa Allah Kinji, abinda ya jarabce ki a kai kuma ki kara mishi godiya yana sane dake, karki yarda son zuciya ya saki, fadawa fushin Allah." Gyada mata kai nayi ina wasa da rigar jikina,sabida ina jin motsin abin cikina, "Kina fushi da Abie har yanzun ne?" D'ago kai tayi tana kallona, "Amma ai kina sonshi, tunda gashi har kina zaune a karkashin inuwar shi, kawai kuma shirya kanku ko kuma wannan abin ya shirya ku" Mikewa tayi sakamakon shigowar shi, tana faɗin. "Allah ya shirya ki" "Amin Ya Allah" ya faɗa bayan ya zauna yana kallona, cikin murmushin jin dadi yace min. "Ga Budurwan da nayi sunan ta, Grace" kallon Mommy nayi wacce ta tsuke fuska, "Don Allah? Na ganta Abie amma ai babba ce ko" na tambaye shi ina leka wayar hannun shi. "Eh talatin da biyu fa" "La ba wata babba bace, toh gaskiya zamu je mu ganta." "Haba Kinga kuwa baturiya ce, sai a haifa miki kane farare" Cikin zolaya nace mata. "Mommy kece babbar kawar Ango, tunda nasan bai da abokai sai ke" "Karki kuma saka ni cikin shirmenku" ta wuce fuuuu, aikuwa muka saka dariya, sannan nace mishi. "Abie me yasa ba zaka gaya mata kana Sonta ba?" "Ina jin tsoron ta ne" Kallon shi nayi kafin nace mishi, "Babu wani tsoro kawai ka gaya mata gaskiya, itama tana sonka fa" "Da tsufana" "Itama ta tsufa ai" "Toh Allah ya sa mu dace" *** Agadaz. Kallonsu tayi sannan tace mata, "Kinsan girman baki uwa? Kinsan yadda Allah yake amsa bakin uwa? Da nace duk wanda ya shiga tsakanin Alhaji da Matar shi ban yafe ba shine kika kashe mishi aure yanzun kin dibo jiki akan Nuratu zata bar D'anta ya auri Kanwar Maimunari" "Nahnah yarinyar da Shegiya ce? Sannan taya ma zan so ya had'a zuri'a da mayu, tunda ya sake ta yaron nan bai kuma samun sukuni ba, dan haka nake zargin kama mishi kurwa tayi" Kallon tayi na wani lokaci, kafin yace mata. "Idan har akan Shegiya ce toh ai kuwa Allah ne ya nufa zan haife ku a silar aure, har na auri buzu. Amma duk wanda yake cikin Zuri'ar mu yasan me ya faru a shekaru baya. Hmm Nuratu ki bashi yar ki Jalilah, Allah ya bada zaman lafiya" "Nahnah wallahi Mohan ba zai zauna da wata mace ba, Maimunari yake so ki saka baki ta barshi ya dawo da matar shi." "Wallahi ba zai sake ta ba, Insha ALLAH ba zai sake miki yar ki ba na rantse da Allah." Ta fada jikinta na rawa. Cikin takaici Nahnah ta kalle ta, kafin tace mata. "Dalla rufe min baki, Ni nace kar ku raba yaran nan amma sake baki da imani shine kika saka ya wulakanta yar mutane. Wallahi ki saka ido kiga abinda Ubangiji zai yi dake tunda baki da imani" shiru tayi cikin yanayin na jin haushi domin duk inda taje niman auren Mohan,kin bashi aure ake. "Ni dai ku taimaka min don Allah" "Hmm! Allah ya gani ba zan yarda ya maida min Y'a bazawa ba, amma babu yadda na iya tunda Nahnah kin saka baki." "Toh nagode" "Nuratu kiyi hakuri" Kamar mahaukaciya ta fado d'akin, tare da shake wuyar Hajiya Latifah, tana kai mata duka. "Kun kashe min yarinya na, wallahi sai kun mutu kuma, ba zan yarda ba." Ta fada tare da rufe Hajiya Latifah da duka, sosai ta haukace musu, sai da maza suka shigo aka fitar da ita. "Wallahi sai na kashe su, tubda suka kashe min Y'a, wallahi sai kashe su wallahi ba zan yarda ba, idan har suka shiga hannuna sai sun mutu." Haka aka yi ta dambe da ita, cikin kuka Hajiya Latifah tace. "Yau na shiga uku, meye nayiwa Karime da zata kashe ni?" "Sharrin da kuka nemi kulawa yar mutane, shine Allah ya maida muku kaidin ku kanku, Alhamdulillahi da abin ya koma kanku. Wallahi Nahnah kin sani abinda ba zan ki ba. Amma da ba zan yarda Mohan ya auri Jalilah ba, yarinyar da tayi jinyar d'anki ma baki kaunace ta ba, sai yar da baki shiri da Uwarta sabida banbancin ra'ayi." "Kiyi hakuri" "Shi kenan Nahnah" ta faɗa idanunta yana cika da kwalla, domin Uwa ce ba zata iya mata musu ba, amma wallahi da Latifah ne ba zata tab'a yarda ta bawa Mohan yarta ba. A cikin kankanin lokaci aka shirya kome, haka Hajiya Nuratu ta kira Mohan ta gaya mishi, sunkuyar da kai yayi sannan yace mata. "Umma ba zan sake ta ba, sai dai har ga Allah wallahi Maimuna nake so, don Allah ki ce karta shige min, karta dame ni. Karta shiga rayuwata. Wallahi zan aureta ne kawai sabida ke da Nahnah da kuma Abba sai kuma Khalil ba zan iya cin zarafin ta ba, domin abotar mu dashi gaskiya ce. Kuma ba zan iya juyawa akan abotar mu ba, ba zan iya cutar da ita ba, dan kamar su Radiyah take. Amma ki bata hakuri domin zuciyata yana gurin Maimuna" Yana gama fadar haka ya juya tare da barin falon, ita kanta ta san gaskiya ya gaya mata, ita kanta ta tausaya mishi, ta kuma tausayawa yarta, dan haka ta ce mishi. "Insha Allah zan kokarta na nuna mata matsayinta." Ta fada mishi. "Nagode sosai" ya mike tare da barin gidan, sannan ta kira Khalil ta gaya mishi, kin yarda yayi da nuna mata gaskiya haka cutarwa ce, domin da a bata mishi abotar shi da Mohan, mutuncin shi da Maimunari take gani ya zube. Bayani tayi mishi tare da gaya mishi gaskiya ita kanta bata son haɗin, dan haka suna gama wayar ta kira Jalilah ta ci Ubanta da kyau sannan ta gaya mata a abinda yake faruwa. Yar banza dai gata tana ihu da murna, tana faɗin. "Nice zan auri Ya Mohan! Wayyo Allah na, dad'i kashe ni" ta faɗa tana ihu, takaici da bakin ciki ya sa Hajiya Nuratu ta kai mata duka, cuno baki tayi tana faɗin. "Ni wallahi ina son shi dama" "Kaniyar ki da soyayyar yaci kaniyarta, toh shi ba sonki yake ba sakarya kawai." "Koma meye ni ina son shi" ta fada tana tura baki, dan babu abinda ya dame ta, takaici kamar ya kashe Hajiya Nuratu, domin bata jin a ranta wannan shine hanya bullaliya, abu uku da yake hana mace zaman lafiya a gidan mijinta K'iyayyar Uwar miji, k'iyayyar dangin miji, k'iyayyar miji, wallahi bata fatan ta zauna da Mohan a wannan yanayin na zuciyar shi tana tare da wata. Amma ya ta iya sam Jalilah bata da hankali. "Umma Idan na aure shi sai na sashi ya manta da Maimunari, wallahi sai na mantar." Make mata baki tayi, "Kin ci gidanku, ana gaya miki gabar kina yamma, dan kaniyarki ba zaki tab'a iyawa ba, sadaukarwa da matar shi tayi shi kawai ya ishe shi mutuwa da rayuwar shi, ke kin san so? Kina son shi ne sabida yana burge ki ko? Toh ita ta sadaukar da kome nata ne domin shi, dan haka kar na kuma jin kince kina son shi zaki mantar dashi kome!" Cikin jin haushi ta mike tare da barin gurin ita ta sha alwashin sai ta mantar dashi kowa ma, balle kuma Maimunari. Dan haka ta juyar da kanta lallai zata mantar dashi kome har da soyayyar Maimunari. ** Diffa. "Ina sonta Baba, wallahi ina kaunar Maimunari, don Allah Baba ka gaya min me yasa kace na rabu da Ita" sunkuyar da kai yayi sannan yace mishi. "Ka hakura da ita Hisham mahaifinta ba zai baka ita ba, koda kuwa zaka mutu ka dawo! Ka kyale su ba zaka tab'a samunta ba." "Baba don Allah ka gaya min meye yasa!" Shiru yayi sannan yace mishi. "Kasancewar shi Baroro, mutum ne da yasan kan shi, kuma yasan abinda zai yi ya kare kanshi. Ni kuma Mahaifiyata bororo ce mahaifina Bazabarme, shima kuma yasan kanshi, sai dai shi yana rayuwa ne a daji mu kuma muna rayuwa a cikin gari, wani shakara ana bikin sallah, na hadu dashi. Wallahi da farko bani da burin zaluntar shi, sai dai lokacin mun nuna mishi muma bororo ne, yasa ya amince da mu. Dan haka bayan sallah mun bishi har inda suke anan muna zauna na tsawon wata shida sai dai muzo cikin gari mu koma, ba dan kome ba sai dai Allah yayi mishi baiwar Ilimi na iya sarrafa Alqur'ani yayi abu dashi, dan haka zaman mu bamu tab'a nuna mishi mun zo cutar dashi bane domin ma bama da wannan alamar a ran mu. Abinda yasa muka shiga wannan al'amarin sai dan yadda muke son mu shiga harkan siyasa da wasu abubuwan. Dan haka muka mai da hankali gurin daukar wasu sirrin Alqur'an, bayan mun gama sai muka fara zuwa muka yi fashi, bayan mun yi fashin shine muka gudu tare da kai cunen shi. Lokacin da ya samu labarin abinda muka yi, shine ya maza ya bar dajin. Aka yi ta niman shi. Bamu kuma haduwa ba, sai a hanyar Mali ya tafi da wata mace, itama kamar bafulatana ce. Dan haka matukar ka matsa kana son Yar shi zai iya tozarta ka, don Allah ka bar mishi yar shi." Cikin bakin ciki ya kalli mahaifin shi, sannan yace mishi. "Toh meye ya had'a ka da Abbun!" Kallon shi yayi sannan yace mishi. "Shi wannan Sa'a yafi Ni, shi yasa nayi alƙawarin sai naga bayan shi" "Lallai ka fini son kai, dan haka koda za a dawo maka da gawata, wallahi sai na auri Maimunari, shi kuma Ubanta dole yayi hakuri ya bar Ni da ita." "Ka hakura ka bar mishi yar shi." Mikewa yayi tare da barin gurin. "Na rigada na yanke hukunci sai dai a kawo maka gawata, amma tabbas sai na tafi ga abar kauna ta. Idan taurin kai da zuciya dabi'ar ka ce, toh ba makawa na gaje ka." Daga haka ya fice daga dakin da Ubanshi yake, yana kara bibiyar layin Benazir, da ya karba a gurin yar ajin su. Tunda ya saka a kan google ya samo kasar, dan haka ya kwantar da hankalinshi ya gama hada kome zai nufi Zurich. *** "Baba Mari Sannun kina ta hutawa!" Na fada ina zama, murmushi tai tare da kallona. "Yo ni da kun mayar dani Nijar da na huta, na gaji da zaman garin nan" ta faɗa tare da kallona. "Hmm! Babu inda zaki muna tare" shigowa Abie yayi Benazir tana kuka tare da fada mishi ita a'a, don Allah ya amince duk da bana jin English amma na Fahimci kamar an b'ata mata rai ne. "Don Allah abie kasa baki wallahi na fasa auren shi" gutsiran apple nayi tare da kallon ta. "Me yasa toh? Idan kinsan baki son shi me yasa zaki bar shi yayi ta wahala?" Na tambaye ta a fusace, "Addah Munah, ban da bakin munafunci me yasa zasu hada kanwar shi da Hammah Mohan? Wallahi na tsane shi baki daya, ba zan kuma aure shi ba" Wani abu naji ya tsaya min a wuya, kafin na had'iye tare da sake murmushin takaici, sannan nace mata. "A'a karki b'ata soyayyarki akan wani banza da bai san hakkin so ba! Dan haka ki gyara tsakanin ku da Dan Ba'are, bai da matsala" na cigaba da cin apple din, shi kan shi Abie dariya yake mata domin tun d'azun take mishi bori ita kuma gashi nan tazo na gwatsale ta. "Addah Munah! Haka zaki ce?" "Toh don Allah me zance miki? Shi yasan me yasa ya gaya miki ai? Tunda Kinga ya iya gaya miki toh sako ya baki, dan haka ki ajiye batun zaki b'ata soyayyar ki dashi, domin babu amfanin haka, tunda yana sonki kuma babu amfanin kiyi fushi dan kawai Mohan zai auri kanwar shi. Sai kiyi fatan Alkhairi ba wai kizo kina cewa kin fasa ba." "Addah Munah!" "Kinga karki b'ata soyayyarki, domin kuwa wasu na niman damar da kika samu amma basu samu ba." Ina gama fadar haka na tashi na bar musu gurin, na nufi can backyard, na zauna a kujeran da yake gurin, kwalla ce ta shiga zuba min ina sharewa amma kamar sake tulo shi ake wato har Mohan yana da kwarin gwiwar aure.. *Don Allah yau ku barni na huta na gaji baki daya👏🏼 wallahi* #Mai_Dambu.. [8/14, 10:44 AM] Joindah: https://www.wattpad.com/1115269487?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=I5OLVif069AImr78w%2FlEumcHUFhhjB3GL%2BklLGDEG2mX72ge1I4j4pFlSrPzq7qgVMUX54J2flC9h4g6fi2m%2FvewJigtCSmbiskTJxpG%2BKNCCPD6AHygfMZwtAY2jz%2F0 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SITTTIN DA ƊAYA. "Wato nice zai tozarta nice zai mai da ba kome ba, bayan faffutikar da nayi dan na same shi amma sake subuce min yayi, meye nayi mishi? Dama duk abinda yake fada min karya ce, dama ba zai tab'a tayani kuka ba, lallai yanzun na gane kuskure na." Sosai nayi kuka nayi bakin ciki tare da zama gurin, naki shiga cikin gidan domin kar a ce min ma nayi kuka dan na damu da Mohan, na san ina son shi amma ban zaci haka daga gare shi ba, wacece irin k'iyayya Ammyn take min haka da ta gwammace ta rabani da abinda nake so! Babu damuwa na bar mata Mohan ba zan kuma damuwa dashi ba. Dafa kafadana Mommy tayi bayan ta zauna. "Bayan na tafi na barki zama cikin kad'aici yana daga cikin abinda Dr Khalid yayi yaki akan shi domin na tsani zama cikin jama'a, bana son magana da kowa. Kinsan yadda nake ji a lokacin. Ismail ya lalata min kome na, ya rabani da iyayena da kome nawa, uwa Uba na rabu da abinda na haifa, sau uku ina samun ciki da zaran nayi mafarkin abinda na bari zai lalace. Ina da yakinin hakkin abinda na bari yake bibiyata, ban wartsae da haka ba, kawai na fara fuskarta matsala daga Mahaifiyar shi, nasan yadda kike ji, amma ba zan iya cewa ga yadda naji ba, Maimunari nayi kuka na roki Allah ya dauki rayuwata da halin da nake ciki da Surukata, ta tsane ni dan ban haifa mata jiki ba,.gashi Yaron nata iya shi daya Allah ya bata, Maimunari ina gaya miki ne dan na yarda dake, amma a lokacin idan da zan ga mutuwa zan so shi sama da kuncin da nake ciki. Khalid sai da ya juya min baya sabida mahaifiyar shi, ba dan kome ba sai dan ya dakata farin ciki, nasha tambayar shi dalilin da yasa yake kin kulani. Murmushi yake kawai, domin karfi da yaji hajiyarshi ta dawo Paris, kuma haka yake kokarin ganin ya kyautatta mata amma baiwar Allah nan, bata fasa gasa ni ba. Haka na hakura da ita har Allah ya amshi rayuwar ta, ban tab'a fushi da shi ba, domin da ya fahimtar dani yana hana ne domin kar ta tsananin ta, k'iyayyar da yake min ya sani kara kaunar shi. Hajiya tayi fatan taga abinda xan haifa sai gashi ina da cikin Benazir Allah ya amshi rayuwarta, kin san me? Tana da kirki amma saboda son da takewa D'anta yasata juya min baya, Maimunari duk tsanani yana tare da sauki, duk wanda kika ga ya zama wani toh kafin ya isa gurin waye shi. Na sha zama na duba wata irin ƙaddara ce take bibiyar rayuwata? Na zata kawai dan abinda ya same ni ba zan kuma fuskarta wani matsala ba, sai gashi bayan rasuwar Hajiya Khalid yan uwan shi sun kuma juya mishi tunani, su dai lallai yayi aure, a lokacin bani da wanda zai tsaya min sai Allah, nafi yarda da cewa hakkin abinda na bari yake bibiyata. A lokacin na kuma bazara rayuwar mutane, ba dan kome ba sai dan yadda nake kokarin na kyautattawa dangin Khalid haka bai saka sun kaunace Ni ba, idan har zamu je hutu Nijar haka xan hada musu shatara na arziki, amma ashe duk abinda nake musu ba, bai musu ba su dai kawai Khalid ya auri yar dangi kin san yadda hankalina ya tashi, haka kawai suka kirkiro bala'i da tashin hankali a tsakanin mu, ina ji ina gani abu kadan zanyi ya fusata Khalid, gashi har lokacin Benazir nake goyo, gashi babu wani nawa, bani da kowa sai shi. Shima ya juya min baya. Munah ina ji ina gani na zama mahaukaciya, karatun da yake biya min ya daina, dan inda nake jin dadi ya katse min, sabida kawai yana son auren wata Yar uwars shi, ban kuma tsinkawa dashi ba, sai da aka gama kome ana jibi daurin auren ya gaya min, haka na saka shi a gaba nayi ta kuka, amma bai saurare ni ba, haka suka yi al'amarin auren su. Ranar da ya tafi Nijar dakyar ya ajiye min abinda xan bukata na sati Uku, amma da ya tafi sai da ya share wata biyu, a lokacin na ga tashin hankali da damuwa, bani da kome sai da ta kai ina fita bakin hanya ina rokon abinda xan ci Ni da Yarinyana, sannan na kawo mana gida a girki. Haka bai saka na samu sassaucin rayuwa ba, domin kuwa idan yarinya bata da lafiya, haka zan ta roko ina Bara." Goge kwallar da yake zuba tayi sannan tace min. "Ban rike shi ba, domin har lokacin ina mishi fatan sauki da salama, ina cikin wannan yanayin wata baturiyar London ita ta taimaka min na samu aiki a wani gurin girki, ban boye mata ba ina karatun likitanci, haka ta kuma nima min damar na koma makarantar, ita kuma Yarinyar da nake goyo ta gaya min na dinga kaita gidan reno, haka ce ta faru da dan albashin da nake samu nake rufa mana asiri, bayan wata biyu ya dawo, ashe ya kamawa matar wani gida mai kyau, dan haka sau daya yake leko ni, haka zai yi tafiyar shi ba tare da nasan yana yi ba, ana cikin wannan yanayin har muka shekara uku, yana zuwa min kullum da yamma, ko da safe. Benazir tana da shekara uku da rabi da watanin ranar yazo min a hargitse,. Yana kuka tare da niman yafiyana haka na yafe mishi. Bayan na yafe mishi muka koma kamar da. Wai ashe fada suka yi da matarshi har ta kai shi ofishin yan sanda, ban gama kaduwa ba sai da naga yan sanda sun kawo sammacin shi nan na gane da gaske sun rabu, amma ban wani damu can ba, domin halin rayuwar da suka jefani dai Allah ne kawai ya sani. Haka suka yi ta sintiri yana ƙoƙarin kare kanshi,kafin matar dai ta bar kasar sai da aka raba dukiyar shi gida biyu, aka bashi rabi, Ke duk wanda ya yarda da Allah bazai tab'a tab'ewa ba, haka dai na zuba mishi ido, bayan haka yayi ta lallabani muka daidaita, amma ban tsira ba a gurin dangin shi, cewa suke nice na raba su. Bani Mantawa bayan haka ya faru da wasu watanni muka zo bikin sallah, wallahi a ranar sai da nayi danasanin kasancewata a cikin su, domin kiri kiri suka yi ta zagina da cin mutuncina. Haka ya shigo gidan ya samu abinda suke min. A ranar na Allah ya dawo min da shi, domin birkice musu yayi tare da nuna musu ai duk aiken da yake musu daga Faransa, ba shi yake turowa ba, Nice shine har suke cin mutumci na, yayi musu bori tare da alqawarin ba zai kuma musu alkhairi ba ya gaji, sannan a gaban mutane ya kira mayar matar shi da suka rabu aka yi magana. Ya gaya musu tunda muke dashi ban tab'a kai karan shi ba, duk da abinda zai min Baba fushi da kawo karan shi, amma ita yar uwar shi ta kai karan shi, wallahi sai da jikin su yayi sanyi sannan yayi alƙawarin ba zai kuma. Dawowa cikin su ba, ba zai kuma waiwayar su ba. Na sha wahala da dangin mijina, amma da yake Allah ba azzalumin sarki bane, sai gashi suna ganin mu, a raye amma babu yadda suka iya, koda ya rasu takardun shaida na filayen shi da wasu abubuwan shi da ta dangance su. Wallahi sun rike, sauran abubuwan kuwa suka matsa lallai sai da aka raba aka cire musu nasu, basu da gadon shi amma haka suka yi ruwa suka yi tsaki, Maimunari. Ina ji ina gani suka addabi rayuwata da na Yarana, zuwan Babanki na samu sauki domin gani suke dan abinda ya rage na hakkin su Yumnah kamar wata tsiya ce yau a kawo min korafin ana niman taimako gobe ma haka, hmm Allah ya taimaka asibitin da nake namu ne tare dashi muka gini badan haka da shima sai sun kwace. Toh ban san meye baban ki ya gaya musu ba, amma naga sun shafa min lafiya, ban sani ba ko zama zai kuma had'a ku da Mohan, amma ki sani dole sai kinyi hakuri da mahaifiyar shi, sai kin dauke kanki daga kanta, matar da zai aura sai kinyi hakuri da ita, mutane sun kashi gida hudu ne. Na farko babu ruwan su da kai idan kayi zasu zage ka, idan baka yi ba zasu zage ka, kuma babu me sauya musu ra'ayin su akan ka, kuma babu ruwan su da alkhairi ko sharrin ka. Dan haka dole ka yi hakuri da su domin can dama ba sa yinka kuma babu mai sauya musu alkiblan su akan ka. Sannan suna iya mu'amala da kai kota wani fuska,. musamman idan suka ji ana maganar baka da kirki zasu biyo ka su bincika basu son ka amma zasu duba wannan labarin da kuma waye kai. Na biyu kuma suna sonka zasu zageka kuma da zasu ganka zasu makale maka, babu domin duk inda suka ganka kai nasu ne, da ka bada baya kai ne tsinannen su sannan idan b'taanci ya fito sune.masu yayyata shi da yadawa a duniya, sannan su addu'a suke Allah yasa kayi ka za domin duniya ta zageka. Babu ruwan su, da kai amma sun fi kowa yayyata sharrin ka, dan haka idan zaka kira makiyi toh su ba zaka kira su makiya ba, su ne ake kira mahassada, suna tare dakai amma basu kaunarka, suna ganin ka zasu ji ran su ya b'aci, ko magana kayi zasu juya zancen ka, ko dariya kai zasu juya shi. Irin wadannan idan kayi sallah biyar da ya wajaba akan ka toh alatilas ne ka saka su a cikin addu'arka wanda zaka hada da falaki da nasi. Sune asalin Original mahassada. Na uku suka kaunar ka da zasu ga an tab'a ka sai inda karfin su ya kare, amma su suna iya kasancewa basu zama tare da kai, kuma ba ka san su ba. Su din masoya ne na hakika, kuma da wani abu zai had'a ka da su zasu biyar duk wani sharrin ka su fadi Alkhairin ka, irin su basu zama a jikin ka, koda zasu zauna a jikinka ba zasu tab'a fadar alkhairinka akan idanun ka ba, kar haka ya zame maka d'agawa sannan wani abinda baki sani ba irin su basu tab'a nuna miki suna yin ki akan idanun ki, sannan idan da zaki yi wani abu na kuskure baki sani ba, su zasu kare ki, idan da za ayi abu dan ranki ya b'aci su zasu hana shi isowa gare ki, su a cikin rayuwar ka baka san inda suke ba, da zaka yi kuskure zasu kiranka su gaya maka haka irin su suke, a duk inda suke suna maka kauna ce domin Allah da Manzonsa. Sai mutane na hudu suna shigowa rayuwarka ce dan su amfana da baiwar ka, ko wani abin ka, sannan babu wani abinda zai saka su kaunaceka domin ba kaunar ce ta kawo su ba, dama sun zo ne domin ribantuwa da kai. Kuma suna gamawa zasu tattara ka su watsa gefe, ba iya a rubutu ba, ba iya a zamantakewar mu ba, ba iya a gurin ayyukan mu ba, a ko ina akwai irin su. Kinga mutane na biyu da na hudu kiji tsoron Allah akansu, domin zasu iya kaika lahira da sawun ka kuma babu wanda ya isa ya dakatar dasu. Muna tare da su yau da kullum. Allah yasa mu dace... 👇🏻 Wannan labarin yana faruwa damu kuma muna tare da irin su ban saka dan kome ba, sai dai idan kana cikin masu irin wannan halin don Allah ka daina. *🤭 bari nayi wani Karambani, wata yar makotar kasar mu, ta tab'a niman Number na, sai aka ce mata wai mai_Dambun kike niman layinta? Matar da bata da mutunci a Media 🤣😂 Wallahi kusan shekara biyu kenan, lokacin ina rubutu masarautan Jordan, kawai sai tace musu eh ita nike nima, sai aka samu wata tace mata kinga ni babu ruwana da ita bana shiga harkan ta, kuma ina ganinta amma saboda ance bata da mutunci yasa bana kulata! Sai tace a bata Number na, maybe zata ji ni indai har yau tana tare dani, sai ta min sallama ba amsa, tace ga abinda take so nace mata to na tura mata MJ na cigaba da uzurina, Alhamdulillahi sai gashi ta kirani tace na ce ki bani book kin bani kuma baki tambaye ne kome ba, wallahi saboda yawan Jama'a yasa na manta ban tambaye ta ba, kuma wani abu anan sai da na kwana biyu ta kuma min magana don Allah taya zan ce mata bani kuɗin, sai nayi dariya nace mata ok bar kudin idan nayi wani book ki saya... Labarin na da tsawo, amma shi alkhairi jifa ce! Dan haka a ranar ban yi mamaki ba da ta gaya min haka. Kuma nayi godiya sai dai wani hukuncin Ubangiji na gama magana da ita, wata baiwar Allah ta min wani Alkhairin da bazan manta da shi ba. nagode sosai domin rayuwa ciken yake da jarabawa da kalubale sai an maka haka zaka san WHO Are You? Allah ka hada mu da masoyan Manzon Allah (S.A.W) domin sune babu tsatsa da lamba a zukartar su* Taku har kullum Ramlat abdulrahman manga #Mai_Dambu... [8/14, 10:44 AM] Joindah: https://www.wattpad.com/1115273030?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=%2FGBnJnXNijQUPspekfVSCvdwVvA67jfZnwBxxbrgfB3mZ707r2j51R%2BtHtXGLFFQhRnwEzTOFYN6wtlFDeefWMBEls9vr15DqQCkIJyDScb3H2il28oON918W3al4mnK 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... Ana harin account ɗina fa, musamman wannan account ɗin... Wallahi 😓 BABI NA SITTIN DA BIYU. Dan haka dole ki koyi mu'amalar irin mutanen wani lokaci ma sa masoyanka kake fada, sai ta kwab'e maka zaka Fahimci haka, sannan da gaske ne dole ki koyi hakuri, domin duk inda zaki zauna dole ki koyi hakurin nan shi yasa Allah madaukakin sarki yace masu hakuri yana tare dasu, dole ki koyi kawar da kai.(🌚🤣wallahi sai ina jin kunya idan na rubuta maganar hakurin nan 🙄domin ban da ita da rashin daraja ce zan iya fada akwai ta buhu buhu 🤨😒😏🌝🤸) mahaifiyar Mohan tana da zafi da fada, kuma irin su dole ka zama ruwan sanyi, sai a zauna lafiya. Bari na gaya miki wani abu, duk yadda aka kai da zaman aure dole ki samu positive and negative, dole cikin biyu ayi daya imma dangin miji su kauna ce ki bawa, umma miji yaki ki. idan aka yi dace kuma kika hada soyayyar dangin miji da namiji kin dace, idan kuma aka yi rashin dace uwar miji taki ki. (Kuyi hakuri bawai babu Yaren Novel bane a labarin amma ina son ku fahimci wani abu ku mata ne! Kuma dole a gaya muku rayuwar wasu dangin mijin baka san da wanda Allah zai had'a ka dasu ba, amma yana da kyau mu fahimci kan rayuwa ba wai nace babu Sex bane a'a kawai labarin na gina shine akan wannan yanayin 🙄🤨 yan buta roro, idan aka barku da shugaban karamar hukumar wandon cinye shi zaku yi. Wallahi ba sex story bane labari ka fahimci sakon labarin shine damuwar, idan naso sai nayi labarin kamar Kwarkwarah 😂🤣 lami kenan a gaban Uban kowa ma za a karanta labarin babu jin kunya ko rufe fuska 👏🏼) Ba wai na gaya miki mugun hali ne ko muguntatta ba, a'a tana da fada amma tana da kirki, kowani dan adam yana da kirki yana da banzan hali, idan Allah yaso halin kirkin ya danne banzan halin ka huta idan kuma halin banzan ya danne na kirki ka banu, domin duk wanda zai fadi wani magana akan ka toh halin banzan zai fada akanka. Ba zai tab'a duba tarin alkhairirronka ba, burin shi ya fadi wancan mugun halin." Rike hannuna tayi sosai, tare da kallona. "Jinki Allah ba zai tab'a jarabtarki ba? Ko yayi dake ne ba zai tab'a jarabtar rayuwarki ba? Maimunari idan har namiji zai dauke ni ranar aurena bayan an daura min aure da wani yaje yayi rayuwa dani meye yafi wannan muni da jarabta? Maimunari idan har zai tafi dani bai tab'a mu'amalata ta cikin nutsuwa ba meye yafi haka cin rai?" Damke hannunta nai hawaye na wasan tsare a fuskana, "kinsan me ya faru? Hatta rayuwar ki nice na lalata miki, domin ba zan manta ba bayan na gama tsine mishi, sai da nayi furucin da nasan shi yake dawainiya dake." Riƙe hannun juna muka yi, kwalla na zuba mana. " Nice na jefa ki a ƙaddara, da a lokacin ban ce wani abu nakanki ba da yau rayuwarki bata cikin matsala. Kiyi hakuri da dangin shi da kuma Mahaifiyarshi." "Mommy ba zan koma gare shi ba, shi daya yayi aure uku bayan Bana nan? Mommy wallahi ina son Mohan, Mommy kinji zuciya tab'a kiji yadda take bugawa, Mommy Mohan wani shashine na rayuwata, amma haka yayi watsi da ni, wallahi ina son shi. Mommy ban san yadda zan gaya miki yadda nake kishin sa ba, shi din mijina ne, Mommy ki min addu'a ko zan sami sauki a zuciyata. Mommy Mohan kamar zinari ne a cikin tsakiyar taku. Shi din Kamar ruwa ce min a zafin sahara, kyauta ne da na samu bayan na rasa kome na, Taya ba zanyi kuka ba, amma nagode zan koyi hakuri zan kuma koyi dauke kai, amma Tabbas ba zan iya hakuri a min irin abinda aka miki ba, ba zan iya dauke kai a cutar dani ba, wallahi zan yi magana, kuma idan ka takani zan rama, sai dai idan ba zan iya ba." Dariya yayi tare da isowa gurin mu. "Yar Baba gaya mata dai ke ba irinta bace, zaki iya yaki dan kwatar kanki. Karki yarda wani ya taka ki, kina da Uban da zai tsaya miki, ko ita uwar Mohan kyaleta nayi sabida Mohan amma da na mata abinda zata nime ki da kanta, amma bana son haka domin xan fi son ki sami soyayyarta da zuciyar ta, shi kuma Mohan ba yadda kike tunani bane, Yaron yana sonki" Mikewa nayi ina kunkuni. "Haka kawai ai da ya damu da Ni, ba zai zauna ba sai ya nimo ni amma bai zo ba yana can ina soyayyar shi da yan mata dama ai nasan nice na takura mishi toh na fita a rayuwar shi. Allah ya bashi hakuri ya cigaba da zama da Kanwa dan Ba'are, Allah zai saka min" Na fada ina kuka. Su kansu dariya na basu domin ba dage sai faɗa nake, zaunar da Ni Abie yayi ya mika min ruwan addu'o'in da kullum yake bani, nasha sannan na sauke ajiyar zuciya. "Kiyi hakuri" kallon shi nayi kafin, nayi kwafa. "Wallahi da zan ganshi sai na sashi ya dauki cikin shi nima na gaji, tunda bai da." "Ai ke kika da hankali tunda gashi zaki sauke mishi cikin ya dauka, rigimammiya kawai" Mommy ta zungure min goshi. Cikin sabon bakin ciki na kuma fashewa da kuka. "Abie ka ganta ko? Ni aka yiwa laifi amma ita haushina take ji, wallahi sai na rama akan Mohan duk abinda aka min tunda ya cuce ni" "Kyale ta, Uwata haka take bata da kirki, kinji babu wanda zai kuma sa min ke kuka kina da Jarumin Uba irina, ko na miki kiranye Mohan din ne duk inda yake ya sussuce ya fito niman ki" "A'a!" Na fada, "Yawwa Yar albarka Ubangiji yayi miki albarka Insha Allah zaki yi kyakkyawan karshe da kyakyawan sakamakon hakurin ki." Gyada mishi kai nayi, tare da mik'ewa a hankali. Wato lallabani da Abie yake kamar wata kwai, amma ba zai hana idan nayi rashin hankali ya taka min birki ba. Ashe Benazir ta haukacewa Khalil. Allah Sarki baki daya ta nuna ba zata aure shi ba. Babu wanda ya sani. *** Niger. Baki daya ya Surkukurce idan ka ganshi ba zaka dauka Khalil din da ka sani ba zaka yarda shine ba. "Mohan yarinyar taki fahimtar ba da gayya aka hada auren ba, wallahi duk yadda naso na mata bayani taki, yanzun haka ta yi ta rufe Ni a WhatsApp ɗinta. Mohan ban san inda take ba balle na je." Wallahi duk sai ya bashi tausayi, ya rasa yadda zai yi dashi. "Khalil ban san me zance maka ba, domin kuwa nima ina cikin yanayin da kake ciki, kuma nasan maganar baki ba zata wadatar ba, dole sai da rarrashi. Kayi hakuri Insha Allah zaku dai-dai ta." "Ba zata yarda ba, wallahi ba zata yarda ba, duk yadda na bata hakuri taki asalima cewa tayi ba zata aure ni ba, ni da zasu amince da sun duba alamarina " "Zasu amince mana." Inji Mohan, "A'a na hakura da ita, sabida itama Umma Umarnin Nahnah take bi, sabida soyayyata ba zan hana Mahaifiyata yiwa nata Mahaifiyarta biyayya ba, Allah ya zab'a min wacce ta fita, akan dangina ba zan zab'e ta, dukda ina kaunar ta, amma na zabi Mahaifiyata na barta" Wani irin sanyi jikin Mohan tare da kallon Khalil, wani irin Tausayin Khalil yayi wani irin mutum ne shi da yake cike da sonka kowa ya zauna dashi sai tayi rashi mai girma, duk wanda ya rab'a sai ya rasa wani na jikin shi yanzun Khalil ya rasa yarinyar da yake matukar kauna. A hankali ya mike tare da barin gidan su, tunda ya shiga cikin gidan su. Ya sami mahaifiyar shi tana fada da Radiyah, zama yayi tare da daura kanshi a zaman gwiwar Hajiyar shi. "Ammyn na amince zan auri Jalilah!" "Haba? Lallai ka kyauta min, Nagode kuma kaga ta samu tarbiyya na gari" "Ammyn don Allah ki so Maimunari mana! Don Allah ki kaunace ta, wallahi zan miki biyayya" "Koda zaka dawo da ita, sai naga yadda ka zauna da ita ta kuma samu kwanciyar hankali a rayuwar ku zan duba yadda zaku zauna." Lumshe idanun shi yayi tare da sauke ajiyar zuciya, a kai akai yana kuma kara jin kamar ya gama rasata kenan, tabbas ba ji bane ya rasata baki daya, domin yasan ya rasa ta baki daya. Kwallar da yake danne shi, a hankali yake jan numfashi, sabida yadda yake jin kirjin shi tayi nauyi, Yana ji yana gani ya rasa yarinyar da ya kaunata. "Ammyn me kike so nayi domin ki Huce!" "Ka hakura da Ita" ta faɗa tana shafa kanshi, d'ago kai yayi yana kallonta. "Ka hakura da ita bata dace da kai ba! Bata damu da kai ba, asalima matar da ta kai iyayen ta kotu meye zata haifa maka tsiya da bala'i, ba matar zama bane." "Amma da baki tozarta ta ba, ai ba zata kai iyayen ta kotu ba, me yasa kike manta laifinki hmm Ammyn Kenan, wallahi abinda aikata shi yake kore min manema na, zan koma gurin Haddir, domin idan na cigaba da zama bakin cikin ki ne zai kashe ni, gashi nan ana zaman lafiya yarinyar da Hammah Khalil zai aura tace ta fasa sabida rashin adalci irin naki, sai ki Cigaba Ni sai ba zan cigaba da zama da wannan abin ba." Ta fada tana kuka, sabida tausayin Yan uwan ta, tana kallon abinda mahaifiyar su, amma babu halin magana, babu wanda ya isa ya dakatar da ita.. Haka ta tasha kuka sosai domin tana son Safwan amma mahaiyarta,, tayi mata sanadin rashin sa, har abada domin ta samu labarin ya kusan aure, shi kan shi ma ya turo mata hotunan amaryan shi, kuma ya gaya mata yana sonta har kwanan gobe, kawai Mahaifiyarshi yake son yayi mata Biyayya, yana son ta rabu da Mahaifiyar shi lafiya, yana son idan zata sauko karta sauko... Wannan Pagen yana magana ne fa akan biyayya ga Uwa.... Alhamdulillahi Ubangiji ya jikan Iyayen da suka rigamu gidan gaskiya, wallahi biyayya ga Iyaye shine babban kalubalen wannan zaman kuyi kokarin rabuwa dasu lafiya! Don Allah Karki yarda karka yarda rayuwar ta tashi babu ka tashi zero! Iyaye ba abin wasa bane, iyaye ba abin yarwa bane, karka yarda aci kasuwa a watse iyayen ka basu ribanci kasuwancinka ba, Karfin nasarata Addu'o'in iyayena, karfin Cigaba na Fatan Iyayena, bani da shekaru masu yawa. Amma Alhamdulillahi na rabu da mahaifana lafiya Yar uwa, ki gwada rabuwa da iyaye lafiya sai ki wayi gari ki rasa me kika yi Allah yake rufa miki asiri..... Addu'ar Iyaye ce.... Alhamdulillahi..... _Kuyi hakuri babu lokaci yau din nan ne, yau addu'ar arba'in makociyata. So dakyar na samu damar typing ɗin su, kuma idan nace sai dare wallahi zan manta daki domin aiki zan shiga_ #Mai_Dambu [8/15, 4:59 PM] Joindah: https://www.wattpad.com/1115798063?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=H4PLUmmQMtRivq0LpRHlS38%2Fr1hLcjzt2XEZ3yHCmyzI3xoWStQC02%2FROcdRbxcPubxgSNp7F%2BbsI7AVD0kyhHL5jlei18XLmYIFmbPXjnlRmUgtZXxtCYJkkmcIRyXT #sun-Aug-2021 HAKKIN MALLAKATA BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA HAMSIN DA UKU. Yana son duk abinda zai yi da amincewar mahaifiyar shi, yana son ita da kanta tace mishi ya je ya auro Radiyah, yana bin duk wani sharadin ta, dan a zauna lafiya. Shi yasa baki daya yaƙi d'aga hanaklin shi, shi yasa yaki damuwa da irin hukuncin da ya yanke, baki daya ya ki mai da hankali kan Radiyah. Burin shi Mahaifiyar shi, ta ji dadin biyayyar da yayi mata, wannan dalilin da yanayin ya saka shi dauke kai akan Radiyah, kuma ita kanta tana mamakin yadda tunda tace bata son ganin su, har yau bai kuma mata magana ba, bai kuma kallon ta da batun ba. Dan koda tace ya nime auren Yar kawarta amincewa yayi jikin shi har da rawa, haka da yayi ne yasa ta jin lallai zata barshi ya auri Radiyah, amma sai ta nunawa mahaukaciyar uwar su basu da hankali zata amince mishi. * Gefe Mohan ya motsa sosai kuma ya maida hankali, duk da yaki zuwa gurin Jalilah da sunan zance haka bai hana a fasa kome ba, Maimunari ce dai yasan ya rasata kenan. Shi yasa ya rungume auren Jalilah bawai dan yana da bukatar haka ba, kuma yau da gobe yana bukatar kulawar mace, idan ya dubi shekarun shi kara hawa suke, matar da yake so baya tare da ita. Dan haka ya watsar da damuwar shi, domin yayi imani da Allah. Tunda mahaifiyar shi taki Maimunari ba zata tab'a kaunarta ba, ya kan zauna yayi dogon nazari akan me yasa kome yazo mishi a jagule! Me yasa kome yake bukata sai ya rasa? Shin ko dan bai kyautatawa mahaifiyar shi ce? Ya rasa gane abinda yake faruwa da al'amarin shi. Da sallama ya shigo falon mahaifin shi, sanan ya nemi guri ya zauna, kafin yace mishi. "Abbu kana jin labarin Maimunari kuwa?" Yayi tambayar a sanyayye. "Baka tambaye ni, me yasa naki auren Yar Sarkin maradi ba?" Sunkuyar da kai yayi yana wasa da capter din falon. "Abbu kayi hakuri, nasan tun wata biyu da suka wuce ya dace a ce anyi bikin kuma Allah bai nufa ba, ban san me ya faru ba. Kuma bana son na tambaye ka kar na shiga abinda bai dame ni ba. Ba wai damuwarka bata dame Ni bane sai dai bana son na cika bincike ne!" Ya fada mishi. "Eh toh da farko yarinyar ta amince amma daga baya taki, wai na mata tsofa, na zata ko wani abu nayi ashe iya kawai girman da nayi ne, shine nace mata toh babu damuwa, kuma Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Ya fada yana kallon Mohan da ya sunkuyar da kanshi. "Mohan Maimunari ta kusan haihuwa, domin cikin ta ya girma. Sai dai kuma tana cikin damuwa ne, domin ko kwana biyu da suka wuce naji labarin bata da lafiya jininta ya haura." Da sauri ya D'ago kan shi yana kallon mahaifin shi. "Abbu don Allah, ka hada ni dasu, dan girman Allah ka taimaka min, ina son sanin halin da Mata ta, take ciki ne idan ma cire abin cikin za ayi a cire. Ta huta wahalar tayi yawa" "A'a yanzun take da wata takwas, idan aka cire karfi da yaji, abin cikin ba zai rayu ba..Insha Allah sunce nan da sati Uku zasu mata aikin shi." Kamar Ya fashe da kuka,yana faɗin. "Abbu don Allah" ya zube gwiwar shi a kasa, idanun shi jajjur. "Kayi hakuri! Insha Allah akwai lokuta da zaka ganta." "Abbu kafin nan na kuma rasata kenan, na rasa ta har abada, ina kara hango nisan da take min, Abbu kayi wani abu, sabida ni Khalil ya hakura da Benazir, an tace ba zata aure shi ba dan zan auri Jalilah, don Allah Abbu kayi wani abu, don Allah ka taimaka min kar ya rasa yarinyar da take so, na yarda zan dauki kome amma ban da na zama sanadin rasa masoyin shi." "Insha Allah ba zai rasa ta ba, ba zai rasa ta ba." Sam iyayen su basu san abinda yake faruwa ba, sai da Mohan yayi bayani, kuma koda Hajiya Nuratu taji labarin bata ji zafin Benazir ba, sai ma burge ta da tayi tana son taga mutum na kishin dan uwan shi, uwa uba son kai ƙarara da aka nuna musu,idan wasu ne zasu ga kamar dama haka shiryayyen al'amari ne. Dan haka ita da kanta ta sami Abban Khalil tayi mishi magana shima ya gaya mata ai ya samu labarin, dan haka suka kira Abie tare da tuntubar shi. Dariya yayi musu sannan yace musu. "Ai shi ya biye mata ne har da d'aga hankalin shi? A'a kar ya damu tana taya yar uwarta kishi ne, shi yasa take ganin idan tayi haka shima zai ji zafi, itama tana can a dame balle shi, dan haka ku kwantar da hankalinku. Insha Allah Benazir matar Khalil ce." "ALHAMDULILLAHI, mun gode sosai da wannan Alfarmar da kayi mana." Haka suka tattauna abin su, sannan suka yi sallama, wani abu da mutane ya dace su fahimta, duk wata tushen matsala daga mace yake, mazajen da suka san ciwon kansu, zai yi wuya su zama tushen matsala, sai dai su zama ƙarshen matsala. Dan haka bayan sun gama tattaunawa ne Abbu da Abba suka kara tattaunawa akan matsalar matan su, shi Abba ya isa da gidan shi kuma ya san matar shi bata da matsala akan wannan maganar, Dan haka bayan sun rabu kowannen su ya koma gida, koda Abba yasa mi Umma da maganar dariya abin ya bata, tace mishi. "Ai tayi mishi da kauna shi yasa naga kamar bai da lafiya, ashe inda matsalar yaƙe kenan! Ai karka nuna mishi kunyi ma, kunyi maganar yanzun ya wani sake ranshi." "Ba zan iya sitirin asibiti ba, idan zaki iya boye mishi ki yi, amma zan gaya mishi wallahi domin ba zan iya kallon shi cikin damuwa ba." Ya fada yana kallon ta. "Toh babu matsala duk inda kace haka za yi. ** A gidan su Mohan. Wayar shi yana kara, duba wayar yayi ya ga babban limamin masallacin Niamey, dauka yayi suka ka gaisa. "Yallabai, na maka karambani, na daura maka aure da kanwata shekaranjiya ta fita takaba, mijinta ya rasu, kuma ba yarinya bace can dan shekarunta talatin da biyu. Kayi hakuri amma bai zama dole ka rike ta ba, idan bata maka ba" Murmushin jin dadi yayi sannan yace mishi. "Babu Matsala Allah yasa haka shine mafi alkhairi, nagode sosai na amshe ta baka gaya min sunan ta ba." "Sunanta Ummu Aimana" "Alhamdulillahi, Nagode sosai Insha Allah anjima zan turo a dauke ta, nagode ka taimaki dan dattijo" Wallahi labarin yayi mishi dad'i, dan haka ya shiga kiran yan uwan shi da yaran shi yana gaya musu, Aikuwa Khausar ta nufi kasauwa aka shiga hidima sosai, zuwa dare Umma suka zo aka dauko amarya, mace mai mutunci da sanin ya kamata. Washi gari kuwa aka buga walima na manyan mutane, anyi nasiha tare da tsoratarwa akan aure, sannan aka yi rabo dan abin yazo a gaggauce, bayan an watse amarya aka kaita part din Hajiya Sahiya, sannan aka watse. Sai fatar Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba,domin bata taɓa haihuwa ba. Da alamu su Mohan za ayi kane (🤣🙄 Wallahi ban ce kome ba) Danne Hajiya Lateefah sosai Umma take domin kuwa, ba karamin haukacewa tai ba, domin kuwa kuka tayi musu. "Ni zai ciwa mutunci? Ya auro sa'ar Salman Meye ya rasa idan yace min yana bukatar hakkin." "Kinga wannan ya zama son kai, bayan baku tare Kice kar ya auro wata, wallahi baki isa ba." "Nuratu! Bayan shi ki ke bi? Toh na fasa aurawa Mohan Yarki wallahi na fasa! Kuma zan kira Nahnah na gaya mata yanzun." Mikewa tayi tare da cewa. "Alhamdulillahi, haka nake so domin ina son farin cikin yarana sama da na kowa musamman Ibrahim akan son zuciyar ki zai rasa yarinyar da yake kauna Kinga maza gaya mata wallahi ban ki mata biyayya ba" "Ni zakiwa rashin mutunci? Toh fitar min a gida, ko na ci mutuncin ki" ta faɗa tare da kumfar baki. "Sai me? Fita kan zan fita wallahi kawai ina farin ciki ne zaki raba wannan sharrin da zaki kula" Fada Sosai suka yi sannan ta kira mahaifiyar su, ta ce ya fasa aurawa Mohan yar Nuratu, sannan Umma ta bar gidan, kusan hauka Hajiya Lateefah tayi a daren, domin bakin ciki ya hanata barci kuma ba auren shi bane a kanta zunzurutun kishi da haukar banza. Washi gari. Nahnah ta kira Abba ta bashi hakuri sannan ta ce su janye maganar auren, bai damu ba domin yasa karshe haka zai iya faruwa a fasa auren, Allah sarki Jalilah ce ma tayi karamar jinya, sabida an fasa auren Mohan da yaji kan shi kamar ya sauke nauyin da ya dace. Dan haka yayi maza ya bar ƙasar domin matukar yana ganin ta tana ganin shi ba zata tab'a barin shi ya huta da batun auren ba. *Kuyi hakuri muna fama da rashin wuta da babu gwara babu dad'i!* *Hmm ku Cigaba da ɗaukar labaruna kuna juyawa! Daga free har na kuɗi bai isa ba? Sai an kwashe wannan ma. Daga yau tambarin littafina zai kasance kwanar Wata Insha Allah idan kuka ga labarin da yayi daidai da nawa Fasaha ta aka dauka! Kowa mai dambu muguwa mai_dambu Shegiya amma kuma labarin mai dambu ba zai tsari ba!? Kome da lokacin sa na saka abinda ya shafi kishi amma haka aka yi ta zagina na dauki fasahar wata Toh wannan karon a bar min labarina! Masarautan JORDAN bai tsira ba, Bahaushiyah bai tsira ba HABEESHAH bai tsira ba! Yau an diro Bororoji na gama shan bakar wahala da asarar data bincike akan abu wasu dan rashin Imani sun dauka! Na hana idanuna barci ina bincike amma ban tsira ba! Ban da ma hauka idan aka dauka ba a sauya tsarin labarin haka za a tafi dashi! Yadda Safina ta shiga Jordan a spy haka aka dauke shi aka rubuta! Yadda Husnah Habib Manga ta shiga Rayuwata Family Abubakar Moddibo haka aka dauke min Bahaushiyah Na Bature Yohanna Chibok labarina ne Dr Yohanna Chibok! Shima HABEESHAH an dauke shi an mai dashi Noorah uku. Kuma ɗan rashin mutunci sayarwa suke! Munafukai da suke karanta books dina suke saya suna shiru ana zuzzuta hauka da jahilci Allah ya isa Ban yafe ba kalmar turanci nayi amfani da shi a Kwarkwarah sai da aka ce nayi satar fasaha 😓 Ni kuma an dauke nawa an hana Ni magana Allah ka bi min hakkina Bororoji ma bai tsira ba haba mana* #Mai_Dambu [8/15, 9:54 PM] Joindah: HAKKIN MALLAKATA #sun-Aug-2021 BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SITTTIN DA HUDU. *ALHAMDULILLAHI. Hhhh ashe nayi kuskuren Pagen d'azun! Mommy Sayeed da Maman Sadeeq Nagode da ankarar dani🤣* Miami. A yadda yake tafiya zaka fahimci ya gaji da tarin ayyukan da yayi baki daya, bude mota yayi tayi maza ta bude tare da zare madubin idanun ta, kallonta yayi sannan ya bude motar ya shiga tayi maza ta zauna a cikin motar tare da kallon shi. "Mohan me yasa nake binka kake wulaknta Ni? Karka manta kana aiki a kasata ce kuma Ni ban damu ba, ina son muyi alaka da kai ne wanda zaka gamsu Ni din mace ce! Kai hadadden namiji ne irin wanda nake bukata" Kallon shi tayi tare da zare jacket din Jikinta, tare da kallon shi tana murmushi, dauke kai yayi tare da Cigaba da tukin shi. Murmushi tayi tare da bude kafarta ta kai hannun yatsunta bakinta ta jika sannan ta shafa gabanta, ta kai hannun bakinta tana tsotsa. "Mohan naga zoben hannun ka, ina da yakinin kana da aure, me zai hana ka mai da ni side chick din ka, ka maidani your slut kaji na rantse maka ba zan tab'a kallon namiji ba." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mai da kanshi yana tuki, yana zuwa kofar gidan su, ya tsaya. "Saka jacket din ki, kin gani nan! Mace daya nake muradi, mace daya tal ta ishe ni, i don't care about you but I caring for her, ina masifar sonta ita daya ce nake jin zata iya wannan shigar ban far mata ba, Moonah ko a ina matukar ta bani haɗin kai zan yi da ita ko a mota, ko a jirgin kasa, ko a jirgin sama. Ko a iya matukar zata ware min tabbas zan shiga jikin mata ta. Ita daya nake jin zan iya rudewa akan ta bake ba. Idan na kuma samunki cikin motana zan baki mamaki." Ya fada mata tare da fita ya zo ya fidda ta yana cewa. "Bana wulaknta mace, amma kar na kuma ganinki a cikin rayuwata." Yana shiga tace mishi. "Ban damu ba, amma wallahi sai nayi fuck dinka sai na sha kome naka, zan saka ka, ka haukace a kaina. Ina son naji jikina a cikin naka na kuma gamsar da kai nima mace ce." Daga haka ya ja motar shi ya bar gurin. Dariya tayi tare da kallon shi yana tsalla gudu, yana isa gida abinda ya fara nima shine magani. Ya hadiya tun bayan rabuwar shi da Maimunari, Allah ne yake kare shi da tausar zuciyar shi amma wallahi yana bukatar mace, ya bisu su gaya mishi inda matar shi take amma fir sun ki. Bayan yai wanka ya shiga closet din shi ya sauya kaya, sannan ya fito ya nime abinda zai ci. *** Hankalin kowa a tashi, ina rike da hannun Mommy, gabaki daya na gama razana, kuka nake son shi amma na kasa, ina ma na samu arzikin kukan. "Mommy! Haka azabar haihuwa yake? Don Allah ke! Mommy don Allah kice ba zan iya ba, su min aiki don Allah, Mommy sau daya yayi wallahi Kinga ya jefa rayuwata, cikin mutuwa" baki daya na gigice na kuma gigita iyayena, dake Mommy ce a kusa dani. "Wallahi bani kuma haihuwa! Idan na kuma Allah ya..." Toshe min baƙi Mommy tayi, tare da shafa kaina tana karanto min addu'a, ina amsawa, sake dubani tayi dake ta gaya musu itama babbar likita ce, kasancewar haihuwar fari yasa ta kawo ni asibiti. Abie sai waya yake mata daga bakin kofar, ita a birkice ni na birkitatta, Abie ya birkitta domin daga waje cewa yayi. "Nayi danasanin karanta shara'a da ba likita na karanta ta ba, Uwata da ana amsar ciwon da na amsa miki." Takaici ya kama Mommy, tace. "Wallahi yanzun na fahimci magana Hajja da tace min sakalci yake addabar rayuwarki, idan baki min shiru ba sai na mare ki." "Wayyo Allah na, Abie Mommy zata buge ni" nafada ina kuka. "Hajja Kinga Ni Ko? Yarinya na fama da ciwo wai Zainabu dukarta zata yi." Cikin jin haushi Benazir tace. "Gaskiya Mommy ki fito karki dake ta, haka kawai Addah Munah tana fama da ciwo zaki dake ta, haba don Allah da wanne zata ji." Ta fada cikin kuka. "Kiyi shiru kinji Beenah ta," ita kam Baba Mari, dariya suke bata, domin tun da aka fara nakudan suka rud'e, musamman yadda ita gwanar take narkewa. Tasan akwai katon aiki, domin daga wash Abie ya rikice kanen ma kuka suke, tunda aka kawo ta Asibitin da asuba,suke tsaye sallah ce take fita dasu. Baki daya sun kidime, kowa gani yake zata mutu, karfe goma na dare, lokacin tayi laushi babu bakin magana sai ya da kai take, kafin Allah ya nufe ta da sauke nauyin da Allah ya daura mata, ta sauke ƙatuwar yarta mace.mai masifar kama da Ubanta, dan har yanayin Hajiya Latifah take dashi. Bayan ni gyara ta aka gyara babyn. Sannan Mommy ta miko min ita. "Mommy nawa ce?" Na tambaye ta,ina son yi kuka. murmushi tayi min sannan ta gyada min kai, tare da mika min ita. Da sauri na amshe ta, ina kuka tare da kirari ga Ubangiji, tare da mata addu'o'in. Albarka nake saka mata, cikin wani irin farin ciki nake mata du'a, har na gama sannan na mata Huduba da Maryam, tare da kallon Mommy. "Mommy sunanta Maryam" murmushi tayi min sannan ta kara mata addu'o'in, sannan ta fita da ita. _Mohan ya tabbata na rasa ka kenan! Ga Maryam tazo na maka gaban kaina. Duk da na tsane ka amma har abada ba zan daina kaunarka ba_ A hankali barci yayi gaba dani, karb'an yarinyar yayi tana kallonta. Kwalla ne ya cika mishi idanun shi. "Rabonta ya tsaga, a wannan lokacin. Da aba ayi auren ba. Da abin kunya zamu gani, soyayyar su mai karfi ce, da ba a mallaka musu junan su ba, karfin rabon zai iya sakawa su aikata abinda zai dame mu! Kai Masha Allah nayi sabuwar Amarya dole ma na gayawa Yallabai." Mikawa Baba Mari yarinyar yayi bayan ya gama mata addu'o'in, yarinyar tasha addu'a. Baba Mari ma haka ta mata, ai a daren ya kira PM ya yaga mishi, sannan ya gayawa professor Ibrahim Dan Ba'are, kafin ya rufe Number shi ya kira Mohan. Bai shiga ba, dole ya kira Dan Ba'are. Canja mata daki aka yi, sannan suka koma dakin bayan sun gama kallon yarinyar, Haka suka mai da yarinyar gurin mahaifiyarta, suka maida Baba Mari dasu Beenah gida, Mommy kuma ta zauna a jikin su, tana kallon kyakyawan Yarta da jikarta, cikin wani irin yanayi. Tashi tayi ta dauro alola bayan ta sallah nafilla tayi, tana jin wani irin nutsuwa ma shigar ta, har kusan karfe biyu, ta kwanta. Da asuba kukan jaririyar ya tashe ta. "Toh Limamiya zaki gaya min lokacin sallah yayi ne?" Ta mike tana kallon yarinyar da take kai hannunta baki, ban daki ta shiga ya dibo ruwan zafi, ta kawo wasu magungunan, ta saka a ruwan tare da auduga ta goge kirjin Maimunari da take barcin wahala, bayan ta gama, ya maida ruwan, ta dawo ta kara goge bakin nonon, sannan ta sakawa Yarinyar yadda ta zoki nonon babu shiri ta bude idanunta. "Mommy!" "Yi min shiru, maza dauki nonon ki bata" cikin jin kunya ta ja mayafin Mommyn ta rufe nonon ta fara bata tana sha. Sai yatsina fuska nake kamar zan fashe da kuka nace mata. "Mommy kuma sai yaushe zata daina shan nonon ni wallahi bana son nonona ya lalace." "Idan baki son nononki ya lalace toh karki na daurin kirji,"(🤣 Joindah ana magana) Aikuwa na zaro mata ido, tare da cewa. "Don Allah! Aikuwa na daina" da taga zan isheta da shirme, ta nufi ban daki kafin ta fito mun koma barci sai da ta gyara mana rufin, Da safe aka sallame mu, bayan likitocin sun dauki hotuna da yarinyar, lokacin da muka iso Baba Mari tayi min wanka bayan ta gama min tayiwa Babyn. Bayan ta gama na yarinyar, Mommy ta shigo da abinci da kuma wasu magungunan ta bani na sha, sannan na gyara na ci abincin kadan, ina kallon su cikin so da kauna, ita da Baba Mari da suke kiranta Hajja. Suna gama shirya yarinyar suna yi suna hira,kamar ba uwa da Y'a ba, domin hiran su me muhimmanci ne kuma da fulanci. Bayan sun gama suka mika min yarinyar, shigowa Beenah tayi tare da ɗaukar hoton yarinyar dani, domin tun aka fasa auren Mohan da Jalilah suka shirya da mutuminta, daukar hoton tayi ta tura mishi,bayan ta gama tura mishi sai ga kiran shi ta WhatsApp. "Maimunari! Barka ashe mun zama Baba" murmushi nayi bayan na gaya mishi fuskar Yarinyar. "Kai Jama'a wannan tadoke Mohan sai dai Ammyn don Allah kuna wata ƙasa ce, muzo ganin princess." "Kayi hakuri kawai akwai lokacin da zaka gan mu. Ba zamu zo bikin ku ba" "Alhamdulillahi!" Addu'o'in yayi min sannan ya gaya min zai turawa Mohan da sauran yan uwan shi. Bayan mun mun gama wayar na kwanta da yarinyar ina jin su Mommy suna hira. "Kinga bakin kishin wancan me karamin kan sun rusawa yaron nan niman auren shi" juya musu baya nayi, domin Mommy zargina take akan nice na ziga Beenah ta saka aka fasa auren Mohan. *** "Mohan ga abinda muka samu tashi ka gani" mika hannu yayi zai amshi Babyn da yake hannun Maimunari, wayar shi tayi kara, tashi yayi zaune, tare da dafe goshinsa. Yau kwana biyu kenan yana yawan mafarki ta, amma na yau ya ganta ta haihu ne, kara wayar shi ya kuma ya duba. "Abbu." Ya gani a rubuce. Dauka yayi tare da sakawa a kunnen shi. "Abbu!" "Alhamdulillahi ina tayaka murna ka zama Uba Maimunari ta haifi Y'a mace, har tayi mata huduba da Maryam." Murmushin jin dadi ya sake tare da shafa kanshi yana murmushi, kafin yace musu. "Abbu! Nine na zama Uba? Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka" ya fada bayan ya kasa cewa kome, kashe wayar yayi tare da fashewa da kuka, yana sujadar godiya, kuka yake, Allah ya azurta shi da yar shi na kanshi babu kazamta babu kome, kiran Khalil yayi bai same shi ba, ya tashi ya shiga ban daki yayi alola bayan ya fito ya gabatar da nafilla, har lokacin sallah asuba yayi, yana gamawa ya kwanta, sai barci, cike da farin ciki dan har zuciyar shi ya tafi gare su. sai mafarkin iyalin shi yake. Kamar zai yi yaya. Washi gari, yana isa gurin aikin shi domin yana aiki da FBI ne, kuma yana isa ya gayawa abokan aikin shi matar shi ta haihu, aikuwa floranse ta tawo cikin murna zata rungume shi ya kauce ta fadi, wajen karfe sha biyu na rana Khalil ya turo mishi hoton yarinyar da uwar Yarinyar, wani irin abu yaji ya taso mishi, kasar hoton an saka mishi Number Beenah. Da sauri ya dauka bayan ya kira, kuwa yaki shiga, tsaki yayi tare da saving Number, ya duba aikuwa tana Whatsp da shi, dan haka yaga ta saka hoton Babyn, murmushi yayi sannan ya tura mata sako. _Beenah Mohan yake magana_ Bata buɗe ba, sai bayan awa daya ta bude sakon dan shima ya saka hoton yarinyar kan Dp din shi ne. *laa Hammah Mohan, kai ne gani ga Addah Munah, na dauko maka hotonta?* _😍😌🤗😍☺️ Zan so haka idan da hali idan kuma babu kice mata ina mata barka_ Voice ta saka, tana jin ta. "Amma dai Addah Munah bai dace ba, kawai dan nace yana ga" "Wallahi zan sab'a miki karki sake ki tura mishi hoton yarinya na, na tsane shi kuma wallahi idan bai daina bibiyar rayuwata ba, ba sai na bashi mamaki shima da yake da uwa take son shi kar ya kuma nima na, idan ba haka ba wallhi sai na bashi mamaki." Ta fada,. murmushi yayi domin babu macen da za a ci zarafinta ta yi hakuri kamar Maimunari, ta dauki kaddarorrin mabanbanta, taga jarabawa kala kala, dan haka bai ga laifinta ba....🙄🙄 Allah yasa labarin bai fara gunduran ku na kamar yadda ya gundire ni 😂🤣 ko mun yanke ne a wuce gurin 😂🤣 Wayyo ni #Mai_Dambu...[8/16, 2:23 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: https://www.wattpad.com/1116236352?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=DqKeHmGUt4S00sTqK6tvHmTwBNce4WSrmwTCLuX9s0%2BZ90klAu0vYuC2%2BG9j3NPu%2BdEkCw%2BpmnVewyRnnYYsyNs%2BbDZEQEPwUVZmfNteR0xffTyfTM0XIqekJsZ5PDHF HAKKIN MALLAKATA #Mon-Aug-2021 BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SITTTIN DA BIYAR. Murmushi yayi yana mai kashe datar, yaso ya ga yadda Maimoon din shi take tsiwa, yasa so yaga yadda take masifa. A hankali ya shafa kanshi yana murmushin jin dadi,yace. "Ya Allah ka zama shedana duk ranar da Maimoon ta shiga hannuna wallahi sai na gyara mata zama yadda ya dace insha Allah" Ya fada yana shafa kanshi, domin yayi wallahi yana jin matukar suka had'e toh ba makawa sai ya bi da ita yadda bata zata ba, sai ya nuna mata shi namiji ne da ba'a rena shi cikin sauki, duk zai iya hakuri da kome amma ya tsani rashin kunya, musamman irin bata da ta rena shi lokaci guda, bayan yana ji a zuciyar shi da gangan jikin shi tana haukar son shi, shafa fuskar shi yayi yana murmushi. *** Ranar beenah ta sha fada a gurina, su Mommy watsar da mu suka yi, ranar da muka cika kwana biyar Abba da Abbu suka zo, abin ya bani mamaki. Amma ganin su bai rage kome ba, sai kara min kaunar Yaron su, na gaishe su ina kuka. "Allah ya miki albarka, Ubangiji ya raya abinda kika haifa, Ubangiji ya shiga al'amarin ku" "Amin Ya Allah, Amin Yallabai" Mikewa nayi na koma dakin ina kuka. "Ka ga ikon Allah! Yarinya ta raba gardama,kaga yadda ta dauko Ubanta, har da Kakanta. " Inji Abba,shi kam Abbu kiran matar shi yayi suka gaisa. Sannan ya gaya mata gashi a gidan su Maimunari, tare da sabuwar Amaryan da yayi, Nan suka shiga wasa,har aka kawo min wayar, sannan suka gama maganar su ne manyan, akan nan da wata wata biyu zasu tawo bikin Beenah da Khalil, anan suka ci abincin rana da na dare, sannan suka wuce, ... Tana gefena tana waya, wallahi bana jin me take cewa, domin maganar ciki ciki ake yin shi da salon shagwaɓa. Make ta nayi tare da kallon ta. "Ki kula min da Widad zan shiga ban daki" na fada mata ina nufar ban daki, juyawa tayi gurin Yarinyar tana mata wasa tana waya, bayan na fito, Naji tana sauke nishi a hankali. Fisgar wayar nayi tare da sakawa a kunnena. "Khalil karka b'ata albarkan aurenka daga waje, duk abin da zaka yi ka jira ta shigo gidanka meye na wasu abubuwa haka?" Na cilla mata wayar ta, mik'ewa tayi tana tura baki. "Idan ke ba zaki kula da masoyinki ba, ki bar ni na kula nawa saurayin" "Zo nan!" Na kirata, tana zuwa na rike kunnenta. "Na makale a zuciyar shi ce, sabida soyayyar mu babu kazamta,ina rungume shi duk lokacin da naso, sau daya na sumbace shi ranar da muka sami sab'ani, ke soyayyar ku shirme ce. Ni tawa dashi guba ce domin idan muka hadu tabbas Allah ka dai yasan me zai faru" sannan ba ture ta, dariya ta saka min tare da cewa. "Matar nan baki da alkibla, shekaranjiya kina ce kin tsane shi yau kuma kina haukar son shi. Duk wanda ya shiga tsakanin kuzari mutu wallahi" Share ta nayi, na cigaba da rarrashin Widad da bata gajiya da rikici. Haka Mommy ta shigo da kayan da aka kawo mana, akwati hudu, tsayawa nayi ina mamakin wannan al'amarin, kayan yarinya kuwa babu laifi, wai dan ba a can na haihu ba, da na ga kayan jaririyar. Har da sarkar farin gold, ** Ranar da suka dawo ya mikawa Ummul Aiman hoton Babyn. "Yallabai yarinyar nan tafi Baban ta kyau, dube hanci har baka. Shine baka kawo mana ita ba." "Wallahi da na turawa Ubanta kamar zai yi kuka. Tausayi yake bani." Ya fada yana cin abincin shi. "Gaskiya ya kamata ka gaya Mishi inda suke haka ba hujja bane." "Insha Allah, zan gaya Mishi meye zaku yi na sunan dan na gayawa Khausar taxo ku tsayar da magana." Ya tambaye ta, "Eh duk yadda kace" Abu ne na kuɗi dan haka ya ware masu kudin da zasu bukata, dan haka aka shirya gagarumin walima,bayan an bawa wata gidan abincin daukar nauyin girkin walima, dan haka gefe guda haka suka yi ta zirga-zirga ita da Yar gidan Babban liman da ya bata, dake budurwa ce, gashi Radiyah bata gidan tana Nigeria, hoton yarinya aka bawa wasu masu yin aikin foste suka masu aikin dake an zuba musu kudi har da kalanda, memo, book, cup ba tangaran, stickers na mannawa a bayan waya, da abubuwa dayawa. Su kuma suka shiga hidima aka raba kaya sosai. Lokacin da Khausar ta nunawa Hajiya Lateefah tace mata. "Ammyn kalli wannan yarinyar ta min kyau!" Kura mata ido tai yana kallon hoton Yarinyar da ya daki zuciyarta. "Wacece ta haifi me kama dani" "Ai baki sani bane, ai gobe gidan nan akwai walima dukda su yau ne suna mu gobe ne zamu yi namu matar da kika tsana ce, jinin ki Allah sai ya raba gardama gashi kowa yasan yadda Hammah Mohan yake kama dake shine Allah ya tashi sai ya sakawa Maimunari jininki me mugun kama dake." Sake wayar tayi tare da dafe kirjinta, tace. "Ta haifi cikin?" "Toh dama kin kifar dashi ne? Ta haifi Maryam Sunan Nahnah, Kinga kuwa dole gidan nan ayi shagali" Kirjinta ne yayi mata nauyi dan haka tana rike da shi, sai kallon ta take. "Ammyn ya dai?" "Babu kawai ina mamakin kamar da yarinyar tayi ne da mu, anya ma Yar Mohan ce?" Cikin bakin ciki da takaici tace mata. "Ammyn Ubangiji ya dube ki da rahamar shi" ta kule dakin ta, domin tana bin na Ammyn zata fadi abinda Allah zai kama ta. Washi gari aka yi walima kuma dake bata da kunya sai gata har a gurin tana gayawa mutane, yar Mohan ɗinta ne, gashi bata san inda yake ba, surutu irin mara hankali tayi ta sake yi shi. Bayan an watse kayan da aka kawo na suna da mugun yawa Khausar da Ummul Aiman wacce suke kira Small Mom, suna ganin kaya, tace mata. "Small Mom, mun hada kudi zamu mishi sayayyan namu kayan, amma ina ganin zata zo bikin Kanwar ta." "A'a dota Abbunku yace ba zata zo ba, domin tana arba'in zata koma makaranta, kuma idan tazo zata zama abin nunawa a cikin dangi dan haka kawai tayi zamanta da yarta, idan zasu koma sai a koma mata da kayan." ** Bayan suna da kwana ashirin, Mommy suka fara hidimar su, da shiga kasuwa sayayyar kayan Beenah da ita amaryan. Jego ya amshe ni, idan ka ga yadda nayi kyau nida yarinya na kamar me,Bama fita Baba Mari jegon da yake min, dan haka na samu kulawa ainun. Lokacin da muka cika kwana arba'in, Abie da Mommy da Baba Mari, da Yumnah aka bari a gida, bayan an kawo min Nanny wacce zata zauna har sai sun dawo. Yumnah suna tsakiyar karatun gama primary school ne,Ni kuma Abie ya nima min makaranta zan cigaba da aji. Duk wanda ya kalle ni ya san na samu nutsuwa kibar da nayi ta boye tsawon da nake da ita. Ranar da na fara karatu, ranar n hadu da Malam Ansar, murna kamar zanyi yayya, har gida ya kawo ni na nuna mishi Yarinya na, haba bawan Allah haka ya dauke ta yayi ta hidima da ita. Washi gari haka ya kawo maka kaya niki niki. A lokacin nake gaya mishi ai mun rabu da Mohan, dan haka karatu ne a gabana, kuma shima ya bani goyan baya, dan haka muka kuma dinkewa sama da baya. ... A can Nijar kuwa bayan an daura aure ne. Anyi shagali sosai ranar budar kai wata Al'amarin ya faru. Domin kuwa Baba Mari ta rike hannun Beenah ta mikawa Nahnah, ita kuma Nahnah ta kurawa Baba Mari ido. "Mariya!" "Mairamu!" Sai suka sake salati tare da fashewa da kuka. "Mariya kina raye?" "Mairamu kina nan da ma?" Komawa cikin gidan aka yi babban falon Abba aka zauna. "Maza ku kira min kowa, har da Mohan da yazo, kowa karku bari har da Wancan kafiran." Bayan minti talatin aka haɗu, kallon Mohan tayi sannan ta kalli Jama'ar falon tace musu, domin har da iyaye mazan. "Mariya kanwata ce Yar baffana." Share kwallar idanun ta tayi sannan tace musu. "Zuri'ar Shehu Usmanu Wodaadabe, babban zuri'a ce fa ta haɗa yammacin Afirka zuwa gabashin Afirka, domin shi din daga kasar Libya yake kuma bafulatani ne na Usul Bororo," (Zaku yi hakuri domin zamu leka 75yrs ne da suka wuce! Da fatan zaku bude kanyar ku, ku fahimci bayani.) ..... 75yrs ago. Shehu Usmanu Wodaadabe ya na da tarin dukiyar dabobbin musamman shanu da raƙuma, ba a batun kananun dabobbin, Yana da mata uku, Maimunari itace Uwargina suna kiran ta da YADIKO Munari, yana da Mai bin mata Hajara Hajjo suna kiranta Yawuro, sai ta Ukun itace Amarya suna kiran ta da Inno, sunanta Ramatu. Dakin YADIKO Munari ita ke da Yara maza, rai shida. Kafin mata biyu. Iro, Kalamu, Isuhu, Dahe, Kabiru, Ya'u, sai Deja da yar karamar su Laure. Dakin Hajo tana da yara mata biyar namiji daya. Kuluwa, Sa'ade, Sakina, sai Rabi'atu, fatsuma, da Garbati. Dakin Amarya tana da yara biyu domin ita wabi take, Sulaimanu da Tanimu, Dukka yaran shi nan doka sha shida, Allah ya albarkace su da tarin ilimin addinin musulunci, kuma suna bada taimako irin na laluran rashin lafiya, dan haka sai ya zama na sun yi shura a rugar baki daya. Domin daga Libya sukan tafi Mali zuwa burkina faso, suna yawo sosai. Sannan Shehu Usmanu Wodaadabe yana da Kane maza biyu, Abdullahi da Abbas, Abbas yana burkina faso, Abdullahi yana Mali, kuma dukkan su da iyalin su. Duk shekara suna zuwa Libya, bikin al'adar Wodaadabe, dan haka lokacin da suka zo aka tsayar da magana yar Abbas aka bawa Iro mai suna Sadiya, shi kuma Kalamu aka bashi Yar gidan Abdullahi mai suna Dayyiba. Haka aka sha bikin su,bayan sun amince da junan su. Sai ya zamana duk shekara ana wannan haɗin,kuma ana zaman lafiya. Bayan wasu shekaru kamar ashirin da Biyar, duk da ana zumuncin amma yayi rauni. Zuwan da suke duk bayan shekara daya, sai ya koma bayan shekara biyu ko uku, ya zama gidajen baki daya uku auren zumuncin da aka a tsakanin su yayi baya, Amma kuma a Zuri'ar Shehu Usmanu Wodaadabe, ba a daina auren ba, a wannan dakunan. Dakin Hajo sun yi aure yaranta a wasu gidajen.. D'ago kai tayi sannan tace musu. " A cikin Zuri'ar iro nice nayi saura, ban sani ba ko akwai wasu dangin nawa! A Zuri'ar Isuhu dakin YADIKO Mariyah ce tayi saura ban sani ba ko a kwai Sauran! Amma a Zuri'ar gidan Ya'u Mamman ne yayi saura ban sani ba ko akwai sauran." Sunkuya da kai Abie yayi tare da cewa. "A Zuri'ar Kalamu Ni da kanwata Amina muka yi saura dakin YADIKO" "A Zuri'ar Sa'ade mune muka saura dakin Hajo" inji Abban Khalil dan Ba'are Take dakin ya dauki kabbara. ( Mu Cigaba) Bayan kamar shekaru ashirin sai iyayen mu suka fara ganin ya dace a hada yaran su aure. Dakin YADIKO da dakin Hajo, aka ware matasa maza da mata. Dakin Amarya aka ware yaran suma. Dan haka aka kira Sa'ido aka ce mishi an bashi auren Hauwa'u, yar gidan Baba Isuhu. Shi kuma ɗan dan Baba Tanimu ne. Kasancewar Baba Tanimu ya rasu, Girgiza kai yayi tare da cewa. "Ni Ummul khairi nake so! Ita zan aura idan ba ita ba sai dai a fasa wannan haɗin" Hauwa kuma yar gidan Baba Garbati ce dakin Hajo. "A'a Ummul khairi an bawa Na'ibi ce." "Hodijam! Wallahi dan anga kasata rufewa Baffana idanu za a bani abinda bana so, toh wallahi ba zan amsa ba. ko a bani Ummul khairi ko kuma na tafi da ita!" Iyayen su tsawatar mishi amma bai ji ba, dan haka suka dauki Hauwa suka bashi, ita kuma Ummul khairi aka bawa na'ibi. Kanwar Sa'ido Aminatu aka bawa dan gidan . Dan haka babu wanda yasan manufar shi, sai ranar da aka daura auren, Ummul khairi da Na'ibi, Sa'ido ya dauke ta ya tafi da ita. Iyayen mu dayawa ransu ya b'aci, dan haka abin sai ya zamana ya tab'a kowani dakin. Domin dakin mu, baffan mu yayi mana fada maza da matan mu, sannan yace kar yaji kar gani. Bawan Allah nan bai tashi dawo da Ummul khairi ba, sai da tasha bakar wahala da tsohon ciki ya dawo da ita. Ana aka gujeta kowa ya gudu ya barta, ashe daman can akwai wani Buzu daga Nijar yana bala'in Sonta shi ya daukota ya dawo da ita Nijar bayan ta haihu ya aure ta, "Mamman kai ne!". Jikin kowa a gurin sai da yayi sanyi. Bayan wata biyar anzo bikin kanwar Sa'idu, dakin su Ummul khairi Ya Ado ya dauke Yarinyar akan idanun Sa'idu, mai suna Deja. Ya tafi da ita, bai dawo ba sai da labarin mutuwar ta, Wannan abin ya fara ne daga dakin Baba Tanimu, sai gashi ya shigo har dakin mu, inda Hammah Babba ya dauke yar Baba Kalamu. Maimunari mahaifiyar (Abie da Innah) Shima Faizo kanin Maimunari ya dauke ni," kin ji ko? Allah ya nufa ba a shegu zan haife ku ba, amma abinda kuke yi dattin zina ce ta lalata min ku! Sabida ita zina masifa ce, kuma dattin ta kashe zumuncin yake kuma ya kashe min zumuntar ku tun mahaifana" Bayan na shekara biyar Allah ya nufa na dawo gida, nima sai ba gudo Nijar gurin Ummul khairi, anan na hadu da mahaifin su Lateefah shima Buzu ne. Sai ya zamana baki daya Zuri'ar mu ta watse, kowa ya kama gaban shi, gwara Maimunari naji labarin Hammah Babba ya aureta kafin suka rasu. Amma ban san inda take ba, ranar da naga Maimunari naji a jikina Yar Uwata ce, domin kamar yadda wancan take haka itama take. Labarin Zuri'ar mu da fadi take amma mu nan yan dakin Iro, Isuhu, da Kalamu duk mun hadu dakin Sa'ade gaka, dakin Tanimu kai ne Mamman, Sulaimanu kuma Yar shi mai sunan. Bilkusu wani Bazabarme ne ya aureta, tana da D'anta shima ban san shi. "Wa'adin Ansar yana nan raye." Inji Abie. Sharce kwalla Baba Mari tayi. Sannan tace. "Baffana yayi saurin aura min Ja'e ne, gudun kar abinda ya faru da sauran ya faru dani, tunda dan Uwana Hammah Babba ya dauke Maimunari, ashe muna namu wayon ne Allah ya shirya mana nashi hikimar, bayan na haifi yara maza da mata, na aurar da su, sai gashi Zainabu ta samu manema dayawa har da wani likita a birnin , mun saka burin son tai karatun boko, abubuwan farin ciki sun faru(babu amfanin dawo da baya muje kawai ba) Bayan ta gama karatunta aka saka Bikinta." Har inda abie ya kwamushe ta, (toh kunji ba kunga illar ramuko kenan wallahi dukkan su zuri'a daya ce) "Haka muka gudu sabida abin kunyar da zamu aikata, idan yar mu ta dawo, bayan mun tafi mahaifinta ya rasu, na manta cewa Allah zai bima kowa hakkin shi, sai gashi dan Maimunari yazo ya dauki fansar uwar shi." #mai_Dambu [8/16, 5:52 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: https://www.wattpad.com/1116237086?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=uJKhfsFaHx1OnFijgRnQ5anbrgbu69dYpl9OGkwca9A2nKghpFbmd3OLH0az9UZXH%2BXwtjoqsjLlfz094p%2BjC%2B2BV7NWPll8LKXfhlmC%2F4I7zE2IA9ygXh%2FB85HrSw%2B0 HAKKIN MALLAKATA #Mon-Aug-2021 BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.. BABI NA SITTTIN DA SHIDA Ya tafi da ita bai tashi dawo da ita ba, sai da cikin shi haka yasa muka gudu, bayan rasuwar Mallam na dawo garin aka ce min suma.basu nan!" Kukan Ammyn ne ya tsannanta, tace. "Nahnah Yayanki ne ya dauke kakar Maimunari? Shi kuma Uban Maimunari ya dauke Zainabu, me yasa ban san tarihin mu na taya zanyi ta d'agawa." "Baki ga kome ba, tunda gashi kin raba zumunci Allah ya haɗa kin raba, dake ke shaidaniya ce" inji Nahnah. Addu'o'in aka yi tare da niman kariyar Ubangiji akan abinda ya faru Shekaru saba'in baya, Sannan Mohan tace. "Don Allah ku taimaka min ku aura musu junan su, ko bayan sallah isha ne," Kallon suwaye aka mishi. "Mommy da Abien mu." Kunyar haka yasa Mommy ta gudu, aikuwa bayan an tashi an rufe taro da addu'a, Aka nufi masalaci, sallah magarib. Mohan ya tsaya waliyin Abie, Khalil ya tsayawa Mommy, Haddir da Salman sune suka biya sadakin.aka daura aure cikin mutumtaka. A ranar kowa yasan matsayin shi, musamman Primer minister, da a daren ya ajiye aiki shi. Mohan kam bai iya magana ba, domin abin yazo mishi bazata, ta ko ina Maimunari yar uwar shi ce, kai ba zai ya jiran ya ganta ba, domin yasan zai bata mugun wahala. An kai amarya d'akinta, bayan watsewar abokan Ango. Wato ma'ana idan na leka gidan Amarya. Duk wani abinda ake na al'ada sun yi (😂🤣🙄 BENAZIR bata san tsohon tuzuru ta aura ba, amma bari mu leka dakin ko🤨😜) Wato shi tuwon girma miyar Nama ce, domin kuwa Khalil ya gaya mata gaskiya (😎🤓 Alqur'an na rasa yadda zan rubuta kome) Yar gidan Mommy da Marigayi ta zata auren shan minti ne, sai da aka gama tab'ayya, sannan ya zaro bayani daga karamar hukumar wandon shi, ya shiga zungure ta,....(na fecce bani da damuwa da ita) *** Washi gari da safe, kiran Umma yayi kamar zai yi kuka. "Umma don Allah kizo" Haka ta nufi shashin su, daga bakin kofar kawai ta tsaya. "Umma ki shigo mana".yana sanye da Jallabiya ruwan milk, tana shiga taga matasai a kasa, ga Beenah can a kuryan gado, ta makure, sai kuka take ta dunkule. "Fita ka bani guri." Ta kore shi ban daki ta shiga ta hada mata ruwa me shegen zafi. Sannan ta zo ta mika mata towel tace mata. "Tashi kinjin" ta juya mata baya,a hankali ya zuro kafarta tana kuka, sannan ya daura towel din, da kifa akan gadon. "Kin gama daurawa" "Eh " tace a raunane, sannan ta juya tare da taimaka mata suka shiga ban daki, sai da ta gasata sosai, ta gabata cire towel din, sannan ta fito ya same shi a falon fada tayi ya mishi tare da cewa "Zan dauke ta, tunda baka da girma sai na jikinka. Kai ko kunya baka ji ba, ka saka yarinya a gaba kamar abinci, wallahi kaji kunyar ka, ina dalilin kasaka yarinya karama a gaba kamar ka samu babbar mace, toh ya kare dan ita ba tuwo bane da zaka saka a gaba kana ciki kamar ba zai kare ba, ce maka akayi haka rayuwar auren yaƙe? Dan haka kar na kuma jin labarin ka adabi rayuwar ta haka" kunya ya yasa shi sosa kanshi. Tana fita can sai gata da magani har zuwa dakin ta kaiwa Beenah,da tea mai kauri. Haka ta sata tasha. Dan ta same ta akan abin salla ne, tana sha ta koma ta kwana, ita kuma ta fito ta same shi a falon yana zare ido, kwafa yayi mishi tare da shigewa ta barshi a gurin yana zare ido. Tana fita shima ya shiga dakin shi yayi wanka ya shirya tsaf, sannan ya fita tare da kiran Khalil suka tafi yawon gaida Surukai, sai wani sheki yake yana wani jim kanshi kamar akan shi aka fara aure (😎🤓 irin yaci sabon d....🤨😜) Ko kallo bai ishe Mohan ba, dan wani cin magani yaƙe. ... Tunda aka daura auren Abie da Mommy, baki daya kowannen su yaki yarda ya hadu da wani, sai ma kara boye kansu suke, musamman Mommy, da take shashin Ummul Aiman, wani kunyar mutane take ji. Shi kuwa Abbu ya sata a gaba yana zoyalarta. "Malama idan zaki fito mu raka ki, toh dan ba zaki bar min dan uwa da kwanan kad'aici ba, ai son kai ne abin" "Don Allah Hammah Mamman ka barni haka meye haka kake, wallahi zaka kore ni a gidanka" "A'a Malama bana son cutar kai idan zaki fito ki fito na raka ki, ina dalilin za a bar mutum shi daya a gida, da iyalin shi." "Assalamun Alaikum!" Mohan da Khalil suka yi sallama, "Waalaikumun Salam," Mommy ta amsa musu cikin kunya domin dukkan su, surukanta ne. "Mommy ina kwana!" "Lafiya lau, ya kuke da fatan an tashi lafiya" sosai goshi Khalil yayi sannan ya damke cinyar Mohan cikin wani irin jin dad'i. "Alhamdulillahi" inji Haddir ya amsa mata. "Kai dan Ubanka sake ni, dan iska sake ni mara mutunci." Mohan ya buge mishi hannu, aikuwa ya kara damke shi. Kamar yara haka suka yi ta rigima Ita kam Mommy da Small Mom sai dariya suke, domin da ga Mohan har Khalil, basu rabuwa da abin fada. Shigowata Ammyn ta zauna tana kallonsu. Domin an maida ita saniyar ware ba. "Maman Maimunari, baku kira min ita ba, ko baki son naji muryan Kawata ce" "Yaushe kika fara sonta haka?" Sunkuyar da kai kowa yayi, domin tambayar da Abbu yayi mata kenan. "Ina ruwanka tunda na kai na tambaya ba" tashi Small Mom tayi tabasu guri dan ta fahimci suna son magana a keb'ence. Kiran layin Zurich din tayi bayan ta dauka tace mata. "Ki bude data zamu yi magana dake kuma ina son ganin hoton me hancin karas" "Toh Mommy kai, Widad din ce mai hancin karas ai irin naki ne, jiya Beenah take gaya min wai an daura auren ku." Kashe wayar tayi tare da bude data, can kuwa Haddir ya dauko Laptop din shi tare da abubuwa connecter, aka had'a tana sanye da riga da wando. English wear. Sai karamin farin gyale da ta yane kanta. Murmushi nayi tare da cewa. "Mommy an gama biki ni da Yumnah muka kewar ku, har da Widad. Please ku dawo" tayi wani maganar a shagwaɓe, kanshi a sunkuye yake bai san lokacin da tsigar jikin shi ya mike ba, tare da kura mata ido, yarinyar jego yayi mata kyau, kuma ta had'u iyaka, dauke kai yayi dan bata lura da shi ba. "Ina me hancin karas?" Dauko mata Widad nayi tana wani yatsuna fuska. "Honey kaka tana miki magana kula ta ko zata ji dadi a ranta taga beautiful baby" "Almamoon ya kake?" Hango Hammah Khalil nayi, na sake murmushi. "Muna lafiya, ya kake kaima? Ya kanwata? Ya Umma da Jalilah." "Alhamdulillahi tunda bata aure miki miji ba dole ki tambaye ta," murmushi nayi sannan na kauda zance haka muka yi ta gaisawa dasu, sannan aka had'a Ni da Ammyn hade rai nayi tare da dauke kai na nace mata. "Ina wuni" Daga haka na dauko abin saka yarinyar na ajiye ta na cigaba da aikina ita kuma, tana fama da jikarta suka hira wai. "Ammyn ki kashe wayar haka baki ga yarinyar tayi barci ba, Mommy kiyi mata magana ta goyeta, tana bukatar dumin jikinta." "Ai ba bayanka bane kuma baka saya ba balle kace ka saya ne dole a maka abinda kake so idan mutum bai fita rayuwar mu ba, wallahi zai sha wahala." Na fada ina murguda baki, na kashe kiran dan ban jira Abinda Mommy zata ce ba. "Kayi hakuri Mohan, sai na sab'a mata Insha Allah, ai baa kanta aka fara rashin aure ba, mara kunyar banza zata ishe mutane bari ka isa Zurich din sai na mata duka.". Haka tayi ta faɗa suna bata hakuri, goggan naku sai wani murmushi yake irin matukar na kama yarinyar nan zata ji a jikinta. Bayan kwana uku. Suka tattara suka dawo Zurich. Baba Mari kan tace bata bin su ko ina, gurin Yar uwata zata zauna. Haka suka tafi aka bar Beenah, wacce suke soyayyar kamar zasu cinye kansu, amma duk da haka bata yarda yace zai shiga aljanna (😎🤓) *** Bayan sun dawo ne suka fahimci Maimunari ta dan sauya, yawan waya fita babu wani kwakwaran dalili, kawai aikin Ansar ne. Kuma bata dawowa akan lokaci haka Yarinyar zata gama kuka kamar ranta zai fita, ranar taga b'acin ran iyayenta, dan kamar zasu dake ta. Ina jin su, suna fada ban kula su ba na dauki yarinyar ina hararanta. Ina shiga cikin dakin na dangwala ta a gado, sannan na wuce nayi alola, haka tayi ta kuka kamar zata shiɗe, koda na idar da sallah, na saka mata mama yarinyar nan taki karb'a. Ruwa na bata garin.daukar waya kawai na tunkud'a mata, yar mutane ta shiɗe. Baki daya ta kafe min. "Wayyo Allah na, Mommy mi taimake yar mutane zata mutu," na fita a haukace karbanta Mommy tayi tare da gwada mata hikima amma fir taki dawowa, ina kuka kamar zan mutu,.haka muka nufi asibitin. Dakyar suka janyo ruwan da ya shiga hancinta, ana ja yana sake wata irin Marayan kuka, nima kukan nake. Likitan ne ya fito yayi ta faɗa tare da cewa sai an hada da hukuma domin wannan cin zarafin yara ne. Dakyar suka hakura tare da sallamar mu. Tun a mota suke fada, Ni dai ban ce kome ba, ina rungume da Yarinyana a Kirjina. "Ance min ana ganinki da wani waye shi? Wato dan bamu nan shine bari ko fara wani rashin hankali ko?" "Abie ba kowa bane fa, Hisham Waadi Ansar ne, kuma naga babu kome a cikin alaƙar mu, sai abo.." tass Mommy ta wanke ni da mari. "Kar na kuma ganin ki dashi, idan ba haka ba, zan miki Yaren da zaki Fahimta, wallhi" inji Abie, da yake tuki. "Toh duk akan me? Haka kawai ban sami farin cikin rayuwa ba, dai da na hadu da shi yanzun shima ace za a rabani dashi." Ran Mommy ya b'aci addu'a take Allah ya kai mu gida, dan haka muka isa ta rigani fita, ta amshi yar tare da mikawa Abie. "Kyaleta mu shiga." Amma ina ta hau dokin zuciya, ta rufe ta da duka, sosai domin ta gaji da Iskancin Maimunari ana cewa wai dan ba a sonta, sai da ta mata mugun duka, sannan ta shige ta barta a bakin kofar, taki shiga kuma taki karbar yarta, dan haka suka kyale ta, ransu kowa ya b'aci. Tunda Mommy ta shiga ɗakinta take kuka, sabida da ciwo a ce baka da iko akan d'anka, har kusan asuba ga yarinyar na ta kuka. Amma Maimunari tana waje, sai da Abie ya fita da belt ya bude mata ido ta dauki yar tare da shiga d'akinta ta, kwanta tana rarrashin Yarinyar. Sam ban san me ya shiga kaina ba, nake jin haushin kowa har da Mohan, ina kwance maganar Ansar ya dawo min. "Ke fa ba a damu dake ba, ƙawai ana damuwa dake ne sabida yar Mohan, ko yayya idan kika bari yarinyar nan wani abu ya same ta zaki ga yadda za a nuna baki da daraja, sai ita." Lumshe idanun nayi wato da gaske ne abinda ya gaya min, sabida ita yarinyar ta hanyar aure aka same ta, shi yasa ake damuwa da ita, Ni kuma Shegiya wacce aka haifa ta zina. Haka na sha kuka na more, da safe na tashi zan tafi makarantar na ajiye yarinyar bayan na shirya ta, na rubuta Musu. *Ba zan dawo da wuri ba sai biyar* Na saka a kasar rigar yarinyar, ina share kwalla. Koda Mommy ta shiga daukarta bayan na tafi ta ga sakona, ko karyawa ban yi ba, haka na bar musu abin su, ranta ya kuma b'aci dan haka ta kasa hakuri ya kira Mohan, ya gaya mishi abinda yake faruwa dauke wuta yayi.... #Mai_Dambu [8/17, 2:03 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA #sun-Aug-2021 BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SITTTIN DA BAKWAI. Duk yadda Abie ya kai ga saka idanu akan Maimunari sai da ya nuna mishi gazawarshi, tare da fita harkan yarinyar tace ta yaye ta,abun yayi musu zafi dama haka take da dan banzan taurin kai yarinya yar wata uku kice kin yaye ta, sai suka shiga Bin ta da addu'a, domin kuwa abin da matukar tashin hankali, ita ba asiri ba balle ya karya zunzurutun daukar zuga. Ranar da Mohan yazo bata gida, ya isa gidan, ya samu yar shi tana ta kuka, rungumar ta yayi yana jin wani irin kaunarta. "Mommy saura wata nawa Mahaifiyar ta, ta gama karatu?" "Saura wata bakwai!" Inji Mommy, gyada kai yayi sannan yace mata. "Toh babu damuwa, ku bar ta. Karku takura mata sai tayi abinda ake bukata, ku cigaba da addu'a, idan na hadu da shi zan ci...." Yayi kwafa. Yana jijjiga yarinyar, Maimoon bata shigo ba, sai karfe bawai a gajiye. Wata tafiya suka yi da Ansar yayi yawo da ita, har suka shiga ruwa, shine ta gaji sosai. Tana shigowa tayi tozali da Mohan, yana bawa yarinyar madara. Wani irin tsalle zuciyata tayi amma na dauke kai kamar ban ganshi ba, kuma wallahi ina matsanancin kewar shi, kawai hakuri nake, yan fita da muke da Ansar ba karamin kama kai na nake ba, domin da zan biye mishi ban san me zancewa Ubangiji na ba, shi yasa kwana biyu da suka wuce ya rungume ni sai da na kifa mishi mari, haka yayi ta bani hakuri. Muka shirya. Shigewa nayi zan rufe kofar dakin ya biyo ni, tare da ajiye min yarinyar a kan gadona. "Ba zan kuma daura igiyar zato akan ki ba, amma kafin ki bata nono ki fara wankar tsari, sabida turaren da kika saka maza suka yi.ta kallon ki da sha'awa." Cikin tsiwa da ban tab'a mishi ba, na kalle shi. "Ba zan bata nonon ba, kuma ba zan kulata ba, kai dalla ficce min a d'akina." Ajiyar zuciya ya sauke tare da soka hannun shi daya a aljuhun wandon shi daya hannun yana shafa kanshi. "Yayi kyau, ina da ɗabi'ar daukar abu tun ina yaro, idan kace min A na dauka idan kace min a'a na dauka, Maimunari, dauki yarinyar nan ki bata nonon ko kuma na kamaki na bata nonon da karfin cin tuwo." "Ba zan bata ba ne fada Mohan" Juyawa yayi na zata fita zai yi na mike ina cire kayana, sai ji nayi ya rufe kofar har da sakata, sannan ya jingina da bangon dakin ya shiga balle rigar shi. "Wannan wani irin Iskanci ne?" Na tambaye shi.a masifance, cire rigar shi yayi ya cilla a gado, sannan ya shiga ƙoƙarin cire wandon. "Kai Malam bana son irin wannan abun ka fita min a d'akina." Bai tanka ni ba, sai da ya gama cire kayansa har da dan karamin boxes din shi, yana me juyar dani. "Na gaya miki zaki ga mijinki, kalle ni da kyau" "Mijin uwar wa?" "Mijin uwar Maryam" Ture shi nayi tare da nufar ban daki, ya biyo ni. Kai Mohan bai za mutunci, kamar wani doya haka yake yawo, ga kiran shi na manyan maza, amma bai hana shi bina kamar jela ba, ina gama tara ruwan zan shiga ya d'aga ni cak ya shiga sannan ya zaunar dani a jikin shi ya kamo hannuna ya saka min.sojar shi a hannuna.da sauri na kwace ina niman fita a cikin ruwan. Ya dawo dani ina fuskarta shi, matsa nonona yayi da suka min tsami, ya kai bakin shi yana zuka, wani katon azaba ce ta kama ni na shiga ture shi bai fasa sha ba. "Dalla sake min abincin Yarinyana, bana son Iskanci wannan ai fasikanci ne" Matsa dayan yayi ruwan ya tsillo mishi ya kai bakin shi yana sha, sai make nonon yake, ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Saboda yana sha yana matse min bakin shi, wallahi ga zafin Bala'i. Yana gamawa da nonon sun yi wani irin fushi, nace mishi. "Allah ya isa min! Ban yafe ba sha min mama da kayi" Murmushi yayi sannan ya mike tare da fita a cikin ruwan, ya fisgo ni, tare da kai ni gurin ya Widad ya zaunar dani, sai da ya tsaya a kaina na bata nono ta sha ta koshi sannan ya koma gurin kayana, ya cire wanda ai cire sannan ya mika min. "Ba zan saka ba" "Toh ko na saka miki?" "Tir" dangwara yarinyar na dauki kayan na saka, sannan ya dauki wata jaka ya zuba kayanta, ya fita sai da ya nimo taxi, sannan ya dawo yatasa keyata a gaba muka bar gidan, ina kallon su Mommy babu wanda yace mishi me yasa. Haka ya shigar dani motar muka bar gidan, a wata hadaddiyar hotel muka sauka, anan ya biya kome sannan ya tawo ya sakani a gaba ina rungume da hannuna, har cikin dakin da ya kama, bai kuma bin ta kaina ba, ya shiga yayiwa yar shi wanka, sannan ya shafe ta da mai da addu'a, sannan ya kwantar da ita bayan yayi mata addu'o'in. Ina zaune, na ga ya shiga ban daki yayi alola sannan ya fito ta shimfid'a abin sallah, yayi Sallah shi, kafin ya idar nima na fara, fita yayi can sai gashi ya dawo masu kawo abincin suka kawo mana, kamar ba zanci ba, haka ya gama abin gaban shi, sannan ya shiga ban daki ya wanke bakin shi ya zo ya kwantar da yar shi a kirjin shi. Bai min magana ba, har na idar na kwanta nima, tare da juya musu baya, bai damu ba zai ma gyara kwanciyar yar shi da yayi, sannan ya koma bayana ya fisgo ni. "Wallahi baki isa ba" "Ka kawo ni ne domin kayi min Fyade? Idan har aka haka ne kayi kuskure." "Bana son rashin hankali, Ansar yake ko waye? Ba kaunarki yake ba, ya saka ki a gaba yana gaya miki maganar banza masoyinki bane." "Hmm karya kenan" ranshi yayi mugun b'aci, dan haka ya fisge rigar jikina sai da ya rabata gida biyu,matsa dukiyar Fulani na yayi sai dana fashe da kuka, ya Cigaba da ya mutsa su, yana matse su. Yana musu wani irin sucking mai mugun shiga jiki, bai fasa ba bai kuma daina ba, wani irin yanayi na mugun kewar shi, amma dake ina son ya kyale Ni haka na shiga ƙoƙarin kwace kaina, amma bawan Allah nan ya nuna min halin shi na mugunta, ya saka min karfi, kome kamar wata inji, sai da ya zo zai shiga gurin na rike shi. "Dama kace min abinda ya kawo ka Kenan, ai da na baka tun a wancan gidan, da nasan shi ya kawo ka da ba zan baka wahala ba, sai dai ka sani wallahi na rufe shafin ka a rayuwata, ka mutu tun ranar da Mahaifiyarka ta ce ka sake ni, maza ka ci amma ka sani kaci abinda zai dame ka, domin Maimunarin da ka sani ba ita bace. Kuma wallahi karka kara rab'an Inuwar yarinya na." Cak ya tsaya yana kallona, kafin ya sauka a kaina, kuka ka saka tare da jan mayafina, ina kuka. Tashi yayi ya shiga ban daki yayi wanka, karshe a doguwar kujera ya kwana, yana jin kuka na, amma bai hana shi juya min baya ba, baki daya ya rasa yadda zai yi da rayuwar shi, domin yana daga cikin matsalar da ya fuskanta bayan rabuwar su,.ya fahimci a da can da bai san mace ba, yana cikin salama, amma a yanzun da yasan mace ya dawo wani irin mutum mara hakuri, dakyar ya kwana yana tashi bayan sallah asuba yayiwa yarinyar wanka. Bayan ya shirya ta, wayar shi yayi kara. "Hello Khalil" nan ya juya Buzanci, ya Cigaba da Yaren shi, ban daki na nufa nayi wanka da alola nazo na gabatar da sallah, bayan na idar ne. Yana cewa, "Eh Yarinyar zan tawo da ita, kawai abinda zaka yi ka gayawa Small Mom ga munan zuwa da Widad." "Karya kenan, wallahi ba zaka tafi min da yarinya na ba" bai kula Ni ba, yayi wucewar shi kamar ba da shi nake ba,. Shan gaban shi nayi, tare da karkaɗa mishi jikina ina zuba mishi rashin kunya, dama Yarinyar tana barci, wani irin rarruma yayi min, sai da ya had'ani da bango, yadda ba zan bugu naji ciwo ba, wallahi tunda ya fara sumbata na,.na manta da kashi saba'in na cikin darin abinda Ansar ya gaya min, wani irin biyar dani yake, d'agani yayi cak tare da matsa ni da bango, ina jin yana aika min da kyakkyawan sakonnin shi masu tsayawa a rai, hannun shi a kofar garin Maradi yana wata irin biyar dashi cikin nutsuwa, ya zare mai girma Gwamnar jahar wandon shi ya ya wata irin goga min(😜🤨 bari mu tab'a rashin kunya da rashin daraja) wani Mahaukacin riko nayi mishi tare da tsotsar harshen shi kamar na samu lillipop,. A hankali ya dawo dani bakin gado, ya zauna tare da ajiye ni akan Babban mutum din shi sai da na sake wata irin kara, ina jin.wasu fitinannun taurari na gani suna yawo a kaina, kai yanxun na fahimta har da kewar shi yake sani masifa, wallahi ina jin shi cikin jikina sauran masifar duk na rasa su. Kwanciya nayi a jikin shi, tare da fashewa da kuka. "Moonah!" "Hammah na" "Kin kara dad'i" "Hammah na kai ma haka" Matse ni yayi a hankali yake jana a karatun shi, sake k'amk'ame shi nayi ya juyar dani tare da dawowa samana, kura min ido yayi yaga yadda nake zubda kwalla. "Yarinya yanzun zaki yi kuka da tushe" a hankali ya zaro a jikina na kara matse shi, ya kuma sakawa a hankali, kai wani irin haukace mishi nayi ina kuka ina rokon shi kar ya daina, bai fasa ba shi kanshi ya matsu ya nutsuwa, aikuwa yana tab'o min Spot dina sai ga ruwan squirt, cizon bakin shi yayi tare da nutsuwa yana tab'owa ruwan na watsuwa ko ina, yana kara tab'awa yana karawa yana kara fita, zarewa yayi tare da kallon yadda nake rawa baki daya kamar wacce aka saka min lantarki,.yana ganin yadda nake zubda ruwan a hankali ya kuma jefa nukiliyar shi cikin babban birnin yan tawayen jikina. Baka jin kome sai sumbatuna,.ina kuka. Kai Mohan yasan yadda ake gudanar da harkan arziki, ba na tsiya ba, cikin ruwan sanyi ya min shegen duka babu bulala babu sanda, domin sai da ya sani na zubda duk wani abinda yake raina, na makalewa Hammah na, sai da ya gama zungure ni da raruke ni, sannan ya dauke a jiyar zuciya. Kafin ya kara matse ni a jikin shi ina kuka tare da bashi hakuri. Haka muka wuni a hotel din,. muna makale da juna, sai dare na kunna wayata, sakon Ansar ne ya shigo min, ina kallon Hammah Mohan ya duba wayar duk zantuttikar batsa ce, dan haka ya zuba min ido, ranshi ya b'aci. "Kinsan zan iya kwana akanki ina abu daya ba tare da ba nemi wata mace ba? Meye gayen nan take gaya miki ne? Wallahi" Amsar wayar yayi tare da fita ta rufe ni,.ya tura mishi sako tare da amfani da wayar shi yayi tracking wayar shi. Yana samun inda yake, yana zuwa ya shiga har club ɗin.ya fito da shi, ya shiga cin Ubanshi, wani irin Jahilin duka yayi mishi tare da kai kafar shi zai daki gaban shi ya tare yana ihu. "Ka ji tsoro? Toh na sake na kuma ganin ka a jikin inuwar mata na, sai na kashe maka wannan abin da yake niman kai mata hari, nasan kai ne silar duk wani abu da yake faruwa damu, amma na baka damar ka rayu lafiyar ka, idan ka gadama ka rabu da ita idan ba ka gadama ba, ka cigaba da bibiyar ta," Kai Mishi duka yayi akan cinyar shi sai da yayi tambul.... Hankalin ku ya kwanta... #Mai_Dambu [8/17, 2:03 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: https://www.wattpad.com/1116738787?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=3wmUfmF%2FKYCEUTT0Or4R8x%2FOHTGp%2Fn%2Fkrfhn%2FB7lHTkzUJhRD5F2rD16co%2BtrR6HblYEBsLqwfg5mD1Uk%2Fkoc73uYq2Ve9MHX7%2F%2BaImoP0o9HmoKgFJY3ZJx0ImK6wgX HAKKIN MALLAKATA #Tue-Aug-2021 BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SITTIN DA TAKWAS. "Wallahi ka sake na kuma samunka kai ba kai ba wani me kama da kai na kuma gani a kusa mata ta, sai na kashe ka." Ya daki kafar shi sai da ya karya. Sannan ya kuma cukumar wuyar shi yana haki. "Wallahi billahi azim, idan na ganka zan b'atar da kai nayi alkawari da rabbil ka'aba!" Ya gwara kanshi da motar da yake gurin, zuɓewa Ansar yayi. Ya dan durkusa. "Ka ci albarkacin zuri'armu daya da sai na yanke maka wadancan abu" sannan ya mike ya bar shi a kwance, cikin bakin ciki ya isa hotel din ina zaune a tsakiyar gadon ya shigo, murmushi ya sake min sannan ya shiga ban daki yayi wanka sannan ya fito sauka nayi a gadon na nufi gare shi na taimaka mishi ya gyara jikin shi ina kallon shi. Zare towel din yayi tare da kashe wutan Dakin, rufe fuskana nayi tare da juya mishi baya, ina jin sojar shi tana gogan bayana. Juyar dani yayi ina kallon shi, a hankali ya dauke ni muka zube a gadon, "Hamma Mohan!" "Na'am" Ya amsa.yana kallona. "Kayi hakuri, naso na maka bayanin yadda Malik yayi yunkurin min fyade." Shafa kaina yayi. alamar yana saurarona. A hankali na fara bashi labarin abinda ya faru, shiru yayi bayan ya zurfaffa tunanin shi, take ya hasko wasu abubuwan masu muhimmancin. Na farko da Mal'ik yana raye tabbas shi zai kare Maimunari dab haka Mohan ya kashe shi. Na biyu y kashe shi ne,.domin kar ya zama shaida akan shi ya saka shi kawo mishi Maimuna, sannan ya kuma ɗauki hoton su da video din su ne dan ya jefa zargi a zuciyar Mohan. Murmushi yayi sannan ya shafa fuskar matar shi, kafin yace mata. "Me yasa kike jin haushina?" Zubur na mike tare da kallon shi ina faɗin yawwa. "Kasan me?" "Ina zan san me tunda ni ba akuya bane" Tura mishi baki nayi tare da cewa. "Toh na fasa gaya maka ma" "Ya hakuri. Yan mata mai nono" buge hannun shi nayi yana wasa da kirjin. "Dama abinda ya dame ni, ka kawo ni nan bayan ka sake ni, sannan kana ta." Juyar dani yayi saman shi yana wasa da fuskana. "Ki koma ki duba takardan dana baki. Amma Ni Muhammad ban isa na sake matar da na sha wahalar samota Dakyar ba, Wallhi ban tab'a sakawa zan rabu dake ba, haka zalika bana jin ma shirya rabuwa dake, amma zan miki cin altsine uwar mai karya" Daga nan ya labarin ya sauya mana, wani fincike rigar jikina yayi tare da makalewa yana tsotse abincin yar shi, har da cewa. "Wallahi Widad yar albarka ce,kiga babu ruwan ta da nono.ta bar Papa yana shan dad'i. Yarinya na, zan baki mamaki," Rike kanshi nayi ina wani lumshe idanuna, tare da gyada mishi kai. Wato Hammah Mohan karshe ne, domin baki daya ya gigita duniya ta, ya gigita min rayuwa sai da ya mantar dani kome, ya kuma dasa min kaunar shi a raina, sama da koyaushe. Kamar yadda ya fada wallahi yayi min cin altsine uwar me karya, domin sai da na kasa magana, sannan ya dauke ni zuwa ban daki. Muka yi wanka tare muka matse junan yau nice a jikin Mohan, kara rungumar shi nayi ina sauke ajiyar zuciya. Bayan mun fito daga ban ɗakin, ina tsaye a gaban madubi ina gyara rigar jikina, tawowa yayi ta rungumo ni. "Maimunari! Kin san me?" "Taya zan san me tunda ni ba akuya bace" Shafa bayana yayi yana goga min yallabai din shi. "Ina Kaunarki, kuma ban gaji ba kullum Ban ki ina tare dake ba, don Allah ki kama kanki, ki tayani rike kanki, ga Amanata nan na baki, kinji Matar arziki yar Albarka wacce haihuwarta ya zama ƙarshen kukan al'umma. Ummul khairi aka fara, Allah ya nufa akanki za a rufe dan haka ina kara niman alfarma a tayani boye wannan manhajar" Rungume shi nayi ina faɗin . "Insha Allah mijina" daukata yayi muka koma gado, ya kama hannu ya daura akan abin shi, murmushi nayi tare da wasa da ita yana bani labarin nasabar mu,nasha kuka sosai tare da haukace mishi. Bayan na tuka shi zuwa kofar Damagaram, kai daren ranar tamu ce dan zan iya cewa amarci muka murza son ran mu. Washi gari bayan nayi sallah, dakyar nayi azkar, sannan na kuma bin lafiyar gado. Yar shi ya wanke tare da saka mata nonon da ya goge ina jin su, dan barci yayi gaba dani. A hankali ta gama sha ya daurata a kafad'ar shi har tayi gatsa, kafin ya Cigaba da kula da ita har barci ya dauke ta, wanka ya shiga ya zo ya shirya. "Nasan kina jina bari na je na dawo" Da hannu na nuna mishi alamar ya dawo lafiya, shima mutum ne da yasan hakkin abokin zaman shi domin idan wani namiji ne haka zai ta uzura min sai na farka. Amma shi kan babu ruwan shi. Barci nayi sosai har da mafarkin Innah muna hira. Ban tashi ba sai da ya dawo ya zauna tare da shafa cikina. "Widad watan ta hudu babu wasu kwanaki me zai hana na ajiye Abie da Abbu da Abba." Da sauri na farka tare da watsa mishi harara, na dira a gadon na nufi ban daki na zubda yawun bakina sannan na fito na fara bubbuga kafa na a ƙasa, ina kukan tare da cewa. "Haka kawai ko tinkiya bata cika haihuwar uku ba, tsannanin ta biyu, Wallahi sai nagawa Abie domin yayi min alƙawarin bani kuma haihu sai ba bukata da kaina." "Toh wallahi uku zaki haifa min Insha Allah" ya fada tare da cire rigar shi bayan ya kira a kawo mana abincin, brush na koma nayi sannan na fito. Zama nayi a jikin shi na ci abincin har na koshi sannan muka shiga wanka tare, muka fito. Shiryawa yayi tare da hada min kayana. "Zan koma inda nake aiki ana nima na, ban san lokacin da zan dauka kafin nazo ba, tayu idan na tafi sai kin kammala karatun ki, zan zo amma a kula min da Widad don Allah karki kuma sauraron Hisham don Allah. Idan kin yarda nike auren karki kuma kula shi." Ya fada yana sumbatar goshina. "Insha Allah tunda kace baka so wacece ni da zan kula shi. Dan haka ka kwantar da hankalin ka" Haka ya taimaka min muka shirya sannan muka fito bayan ya had'a kome na shi, har gida ya kawo ni, ganin Innah nayi na fasa ihu tare da direwa a kanta ina murna, sai dariya take. Mommy da Abie kam sai kallon juna suke, zama Mohan yayi suka gaida har da Baba. "Shugaban masu hankali babu gaisuwa ne" Tura baki nayi tare da cewa. "Hammah na kaji Abie ko?" "Abie babu ruwanka da mu" ya fada yana murmushi, "Innahta yaushe kuka zo" "Da safen nan mijinki ya dauko mu!" Juyawa nayi ina kallon shi tare da sake murmushin jin dadi, kwala mishi pillow nayi ba cigaba da cewa. "Shine ba ka gaya min ba na tashi mu tafi tare." "Toh ai babu damuwa yanzun ma bata b'aci ba, toh ni kam zan bar gari domin ana ta kirana a gurin aikina." Haka ya mike na tashi nima kamar zan yi kuka, ba fito zan raka shi, har gun taxi din na rako shi. "Hammah Mohan! Sai yaushe ka koya min yadda zan dinga tunawa da kai don Allah karka jima sauran wata bakwai karka wuce wannan lokacin, don Allah kazo kaji" Rungume ni yayi sannan yace min. "Insha Allah zan zo ki kama kanki, karki manta da azumin Alhamis da Litinin. Ina tare dake Allah yana tare da mu" Shafa bayana yayi sannan ya shiga mota, ina d'aga mishi. Haka na koma cikin gidan, muka baza hira, kafin na koma dakina na gyara sannan nayi wanka na kuma yi sallah kafin na bi lafiyar gado, haka na wuni ina barci sai biyar na tashi na ci abinci na bawa Widad nono, kafin ba sake gyara jikina na fito, Innah ta saka Ni a gaba na maganin gyaran jiki. Tun daga ranar bani da lokacin kowa sai na karatu da kuma shi kanshi mijin nawa Muna waya, kamar zamu cinye juna ta waya. *** Bayan wata bakwai na kammala karatuna har da su Beenah da tazo da cikinta dan wata shida. Da shi kan shi dan Ba'are, ban ga Mohan ba, kiran layin shi nayi yaki shiga takaici kamar nayi ta ihu. Zuwan Hisham ya sani tafiya gurin shi, yana tayani murna tare da cewa. "Ban ga Mohan ba, yau babban rana ce amma kamar bai damu dake ba? Da yar shi ce da zaki ganshi jikin shi yana rawa" a hankali maganar shi ya fara tab'a zuciyata, ya shiga gaya min wasu abubuwan da nuna min yadda Khalil ya damu da matar shi. "Ki duba ki gani mana, duk nan babu wanda bai zo ba sai shi, ke kin kare kanki,kin kama kanki amma shi.yana can yana cin amanar ki. Hmmm." Wani irin duka aka kai mishi sai da ya fadi kasa, yana rungume da Widad. Shiga tsakanin su yayi ina kallon Mohan. "Meye a cikin maganar shi? Meye laifin shi? Da ka damu dani ba zaka ki zuwa akan lokaci ba, ka samu matan da suka fini." Mikawa Khalil Yarinyar yayi tare da kai mishi duka. "Na gaya maka ka rabu min da matana amma kaki ji, nace ka fita hanyar Maimunari ka ki ji, bari na koya maka yadda ake gudanar da sha'anin rayuwa." "Munnah kina ganin zai kashe ni, karki bari ya ya illatani" Saka karfina baki daya nayi tare da ture shi. "Dalla kyale shi, akan ka aka fara kishi? Ka kyale shi mana, haka kawai zaka saka shi a gaba sai kace bawan ka. Karka kuma dukan shi. Idan ba haka ba zan baka mamaki" Haka ya mike tare da barin gurin, yana dingishi. "Ina sonki shi yasa na kyale shi, amma wallahi sai na illata shi." "Bana son ganinka, ka koma inda ka fito matukar haka ba zai samar min da kwanciyar hankali ba." Haka na gaya mishi tare da barin gurin ina kuka. Shi da Khalil suka kawo mu gida dan su Abie sun rigamu dawowa. Tunda na shige dakina, khalil ya shigo dakin yana kallona, sannan ya zauna tare da bani labarin duk abinda ya faru. *** "Ban damu ba, kome zai faru ya faru, amma ina son a kashe min shi, a kashe min shi bana son ganin shi da ita," "Amma ita yarinyar fa?" "Idan ta kama da ita a kashe ta kowa ya rasa shima ya mutu." "Lallai baka cika mugu ba, ai muguntar da zaka mishi kenan ka kashe ta ya rasa ka rasa," Kallon shi yayi tare da cewa. "Ka kawo shawara, kuma Insha Allah haka zai. A'a a kashe shi kawai ina sonta a raye, ina son Ubanta yaga yadda zan aure yar shi kuma na kwanta da ita a cikin gidan shi. Dan haka daga yanzun har zuwa gobe ku kashe min dan Iska." "Toh amma kasan Unguwar akwai tsaro, idan muka tashi kashe shi ya zamu yi?" "Ku rufe bakin bindigar da salansa" "Toh an gama" Haka suka ci-gaba da bayanin yadda zasu kashe Mohan, a waje kuwa wata yar makaranta ce, taji su dan haka ta fita tare da niman Number Maimoon. Bata samu ba kamar zata yi kuka dan haka ta kai report ga yan sanda, su kuma suka tuntube Maimoon. #Mai_Dambu. [8/17, 2:03 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA #sun-Aug-2021 BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SITTTIN DA TARA. "Kina Fahimta! Ansar ba kaunar ki yake ba, mutumin yake kaunarki ba zai tab'a lalata miki rayuwa da farincikin ba. Bawai ina gaya miki haka a matsayin Aminin Mohan bane, a'a ina gaya miki haka ne a matsayina na dan uwanki, kuma abokin shawaran mijinki.. Wallahi bai aiko ni domin na gaya miki, amma ita wannan ta sani, komi kashin damuwa idan ya gani a tare dake kamar zai zauce haka yake ji, ki duba takardan sakin da ya baki,wallahi bai tab'a kawowa zai sake ki ba." Da sauri na shiga watsi da kayan na fito da takardan a kasar a kwatina. Hannuna yana rawa, jikina sai bari yake na warware takardan. *Ina son mata ta! Ba zan tab'a sake ta ba har abada* Wani irin kuka na sake tare da kallon wayata da take kara, da sauri na dauka. "Kece Mrs Mohan?" "Eh nice!" Na fada ina toshe bakina. "Toh ki kula domin shi bamu same shi ba, amma ana bibiyar rayuwar shi da ke, an saka a kashe shi. Dan haka duk inda yake kice mishi ya kula da rayuwar shi" Sake wayar nayi tare da jan mayafina na rufe kaina, sannan na fita ban iya kula su ba, duk tambayar da suke min. Bani da hankalin da zan basu labarin abinda yake faruwa. Dan haka ina fita na hango shi yana tsayawa a bakin kofar shiga gidan mu, da sauri na isa inda zai bude kofar, ba bude tare da cewa. "Basu maka kome ba? Fito kaji." Bai fahimci me nake nufi ba yana fitowa kuwa suka fara harbi,kwantar dani yayi tare da janyo wata jaka, ya ciro bindigar shi, ya shiga bin su yana harbin su. Sun samu sun gudu dan haka ya fito tare da d'ago ni, hango wani mutum nayi. Yana tasowa ta bayan Mohan, a hankali na juya tare da Mai dashi daidai kofar gidan, sai ji nayi kaifin abu ya huda bayana har ya fito ta cikina. "Hammah Mohan! Na gaya maka rayuwata fansa ce koda ni ba zan more ta ba? Na tab'a gaya maka ina raye ne domin kai? Hammah na, tun kana cikin laluran hauka nake tare da kai, wallahi billahi azim ina sonka da dukka rayuwata..." Na tafi zan fad'i yayi maza ya tare ni, shi kanshi mutumin da fuskar shi take rufe wani irin ihu ya kwala tare da cire abun fuskar shi. "Hisham!" Na kira sunan shi. Ina jikin Hamma Mohan. Sai gyara mata kwanciya yayi a kirjin shi kamar baya gurin. "Na gaya maka cewa, ni Mohan nake so!" Na fada a sanyayye. "Ni shi nake so! Ina son shi baki daya da rayuwata, ko babu kome an kawo karshen rikicin ko? Ni matar Mohan ce, Ina son mijina sosai." Na fada ina share kwalla da ta zubo min. Daidai zuwan motar yan sanda. "Hammah na, karka mishi kome kabar shi da ciwon da ya jiwa ranshi ya ishe shi har karshen rayuwar shi." "Mohan a kaita asibiti mana" "Ko an kaini bai zama dole nayi nisan kwana ba" "Karki damu zaki rayu Wallhi" ya fada da mugun karfi ya nufin inda aka saka motar asibiti yana rungume dani. Bayan tafiyar su, da kanshi yayiwa Yan sanda bayanin shi ya turo ayi kisan, dan haka suka makala mishi ankwa, suka nufi dashi Ofishin su. Hankalin Mommy yayi mugun tashi, dan haka suka nufi Asibitin tunda suka iso suka sami Mohan, ya kasa tsaye ya kasa zaune, sintiri yaƙe, ya shiga Nan ya fita nan hankalin shi a mugun tashe. Allah Sarki baby Widad tana kwance a jikin Abie hannun ta daya a bakinta tana ajiyar zuciya. Bayan awa biyar likitocin suka fito. Tare da nufar inda Mohan yake. "Mun yi kokarin mata aiki, amma gaskiya bamu san yadda zamu gaya maka ba, Matarka koda ta rayu bai zama dole ta mori kafaffunta ba, sabida wukar ta tsinka mata jijjiyar lakanta (spinal Code) abin da muka Fahimta a jikin wukar guba a jikin shi, shi kuma ya tab'a mata ƙwaƙwalwar ta, wanda ya tsayar da aikin zuciyarta. Gaskiya muna baku hakuri domin bai zama dole ta rayu ba." "A'a likita! Wallahi zata rayu. Ina jin haka uwar Ƴaƴana zata rayu, wallahi bana jin mutuwa zata zo mata a wannan lokacin, kaga gaya min ina ne zan kaita a mata jinya, gaya min inda zan kaita. Don Allah kaga wancan Yarinyar watanta goma sha daya. Don Allah na hada ku da Allah ku gaya min ina zan kaita. Bani da amfani matukar ita bata numfashi, rayuwata mallakar ta ce . Don Allah ku gaya min" Ka fada a rikice, abin gwanin ban tausayi, su kansu likitocin share kwalla suke, a hankali suka juya tare da barin gurin. Mommy ta tawo tare da rike shi, ta zaunar dashi. Sannan ta zauna itama tana faɗin. "A lokacin da na haifi Maimunari, ban tab'a jin ko ganin wani zai kaunace ta ba, musamman ta hanyar da na haife ta, naso da a gidan aure na haife ta, sai na kasa amsar ƙaddara a kanta. Nayi ta tafiyar ƙaddara. Mohan ban zata ba yau Maimunari zata fada wannan yanayin ba, domin nafi zargin SOYAYYA ba zai tab'a wasa da rayuwarta sai gashi an samu kishi a tsakanin zubda jini, Imma Maimunari ta tashi, Imma ta mutu. Jininta ya zama sadaukar ce ga Zuri'ar mu baki daya, dan haka ka yi hakuri Maimunari koda yaushe tana ran mu, idan ta mutu muna mata fatan dace da rahamar Ubangiji." Mikewa yayi tare da ɗaukar yar shi suka shiga dakin da aka sauya mata, ya zauna a saman kujeran da yake gabanta. "Kin gan mu, ni da Maryam mun zama kamar marayu, bamu da amfanin kome, gamu dai a raye amma zuciyar mu ta tafi da naki. Don Allah ki tashi muna dakonki, don Allah karki tafi ki bar mu, wallahi zamu tagayyara, idan kika amince kika bamu dama ta biyu zamu." Kuka ya fashe da shi, yana kara rungumar yar shi, tunanin kowa ya tsaya, Abie ma ya saka koda wani abu, kawai yana kallon haka a matsayin da bai tab'a zata ba, yar shi kwaya ɗaya tal itace aka mata wani irin kisar ban mamaki. Meye zai yiwa Hisham ya huta, baki daya ya kassara mishi Rayuwar shi. Haka suka zauna jigun jigun. Mikewa yayi tare da fitowa da yarinyar. Ya mikawa Innah dan itace take cikin nutsuwar ta, duk su Mommy a birkice suke, dan haka ya nufi office din yan sanda, ya mika musu katin shi na FBI, suka sara mishi sannan suka bude kofar da Hisham yake, ya ja kujeran ya zauna, yana kallon shi. Yadda yan sanda suka ci Ubanshi. "Ban san me yasa kayi shura akan lallai sai ka raba tsakanin mu. Shin akwai bashin da kake bin Maimunari ne?" Ya tambaye shi tare da kallon shi. Dariya Hisham yayi sannan yace mishi. "Na riga ka, fara sonta, yin tana siffar maza na fara sonta, zuciyata tana gaya min mace ce a gurin mai dauke da Darajojinta, sai dai lokacin da nake ƙoƙarin biyan bukatan kaina na fahimci kai har tayi nisa akan ka, taya zuciyata zata dauka? Ban san asara ba, ban san faduwa ba, abinda na sani nasara. Kai kuma ka tsaya min a gaba. Dan haka yanzun da ta mutu na rasa ka rasa." Wani banzan naushi ya kai mishi sai da ya tintsira, ya kuma kara mishi duka. Da sauri suka bude kofar. "Kai ku fita Rigimar mu bata ku bace" inji Hisham. "Yallabai ko zaka fita?" "Idan ya fito ya zama lusari. Idan ka fita sunan ka ragon maza, kuma har abada ba zaka tab'a zama cikakken namiji ba, ku fita ku barni dashi ya dake ni. Bari na gaya maka, Ni na biya Malik ya dauko min ita, Ni na saka mishi kawazucin yayi tarayya da ita, ta yadda zan kashe shi babu wanda zai damu. Ni na dauki hoton matar ka na saka shi domin ya ruguza maka rayuwarka ka manta wasar da muka saka ne? Nasan zaka yi nasara yasa ni kaiwa mahaifiyar ka, labarin abinda Kanwar Uban Maimunari ta faɗa na Shegiya ce, tawo k dake ni, itama Mahaifiyarka na gaya mata ta bani goyan bayan zata rabaku ashe tsuhuwar banza ce, shima Babban shegen shima Ubana ya Bankad'o sirrin shi." Lumshe idanu Mohan yayi, sannan ya bude akan shi. "Ko ku fita" Suna fita ya garkame kofar ya shiga gyara tsayuwar shi, kafin suka kaure da wani azzababben fada, suka yi ta jiwa junan su ciwo kamar zasu kashe kansu. Babu wanda yayi yunkurin raba su, sai da Mohan yayi mishi dukar mutuwa yaga baya numfashi, sannan ya daki gaban shi, sai da ya fasa ihu. Kafin ta fita daga dakin, ya saka rigar shi. Sannan ya fita daga Office din yan sanda. ya nufi asibitin yana dingishi. Yana isa ya samu su Mommy, ganin bakin shi a fashe yasa Mohan tambayar shi. "Lafiya" "Wancan dan iskan na koyawa hankali" "Waye?" "Hisham!"ya bata amsa, "Da ka kyale shi" Kwalla ne ya zubo mishi, sannan ya mike hankali yana kallon Mommy. "Ba zan tab'a yafewa kaina ba,matukar na bar Hisham a raye, sabida shi matar da nake so take kwance, taya zuciyata zata nutsu? Bani da abinda na sani sai soyayyar ta, bani da abinda zan yi sai Soyayyar ta, Mommy baki ga halin da Maryam take ciki bane, daga ni har ita mun zama kamar marayu, gashi dai mata tace amma ji nake kamar rayuwata ce take niman kwacewa daga gare ni. Wai kice na yafe mishi, bayan ga lakarta, guba ce ta tab'a kanta da zuciyarta, idan ba dan ke kika haife ta ba, sai nace ko baki kaunarta ne, amma nasan kin fi ni sonta, abin tausayi yarinyar da babu ruwanta tana shirin zama marainiya, wata irin zunubi nayi ne haka? Ban san meye na aikata ba, amma yarinyar nan tana shirin zama marainiya, sannan kice na yafe mishi. Wallahi ba zan yafe mishi ba." Ya fada yana watsa da hannun shi, dan haushin Mommy yake ji, akan me zata ce ya yafewa Hisham, dan banza mutum da ya sani sai ya karya mishi hakarkari. Hankalin shi sai kwanta, banza kawai mara mutunci, a Yanzun haushin kowa ma yake ji, ya tsani a mishi magana dan haka ya dauke yar shi suka shige dakin, kwantar da ita yayi kusa da uwar da aka saka mata na'ura a hancinta,.ya shiga ban daki yayi wanka tare da fitowa, ya ga yarinyar tana barci, fita yayi tare da niman Khalil ya kawo mishi kayan shi. Abie kuwa da Khalil tuntubar likitocin suke ko za a taimaka a fita da ita wani asibitin, dan haka suka shiga zirga zirga, shi kuma yana jikin matar shi. Haka ya cewa Innah. "Innah ku dauki Maryam ku tafi da ita, ni zan zauna anan. Dan ba zai yiwu ina yawo da ita a cikin Asibitin ba, ina ga kawai a yaye ta, tunda tana tsayuwa kuma tana cin abinci, ba sai an bata na Uwarta ba, ita kuma zamu cigaba da addu'a Allah ya bata lafiya." "Son wata goma sha daya yayi sauri me zai hana a barta!" Kamar zai yi kuka yace mata. "Bani da tabbacin Uwar zata tashi, kar a saka mata kawazucin Uwarta tazo mu rasata, Kinga anyi biyu babu, don Allah ku tafi da ita a bata wani abu.... *Toh bari mu gani zuwa sab'ani din nan idan ya wuce sai muyi Barka idan bai wuce ba a wanke hannu a saka facemask Nagode sosai an amana👏🏼* #Mai_Dambu [8/18, 9:55 AM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA #wed-Aug-2021 BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SABA'IN *PAGE 70 NA KAMMALA ZANEN QADDARA TA, AMMA WANNAN KAMAR KUN TOFE NI😭🤣* ----------------------------------------------- *Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida* Kaza Tara bala'i- Gumba bucket ƙarami- Gari- Hatsabibiyar zuma Hatsabibin gari Zobe- Tsumi-, Maina ya rikice Zazzogau Haɗin gigita shi Maƙale mata Sayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku ________________________________ Kallon shi Innah tayi sannan ta maida idanun ta kan Yarinyar, da take kwance jikin Mommy. "Zainabu mu tafi da ita gida." Bata rufe baki ba, Khalil ya isa tare da Abie. "Zamu wuce da ita Germany, akwai likitan matsalar ta, sai dai zata iya daukar wata shida kafin yazo kanta, amma da mu zauna anan jiran gawon shanu gwara mu tafi can ko Allah zai saka ta tashi." Inji Abie, yana kallon Mohan, "Duk yadda kace haka zamu ayi, amma ai shima Mohan din ba zai ki wannan shawaran ba, tunda abinda yake bukata kenan" Kamar kurma haka ya zauna musu, ba tare da yace musu cikanku ba. Dafa shi Khalil yayi ya juya yana kallon Khalil. "Idan hankalin ya b'ata hankali yake nima shi, don Allah kayi hakuri ka saka salama a zucuyarka karka damu Allah zai bata lafiya." Janye hannun shi yayi a kafad'ar shi. "Ni nawa hankalin ya tafi ba tare da nasan ina ya tafi ba, hankalina ya b'ata a jikina tun daga d'azun da naga Maimunari wuka ya fito ta bayanta na fahimci hauka tuburan nake, dan haka ka kyale ni karka dame ni," Ya fada tare da saka hannun a bakin shi yana mishi alamar kar ya tashe ta, haka ya zauna yana kallonta, bani baki daya kome nashi ya tsaya cak, yana tare da ita ne, amma yayi imani da Allah ya mutu ya kai sau dari, kuma da za a tsaga jikin shi babu ruwa a cikin shi zunzurutun tashin hankali da fargaba, a kowacce dakika bugun zuciyar shi yake kara tsananta, ji yaƙe kamar kafin ya bude idanun shi na'urar da yake makale da ita zai daina aiki alamar ya cika, wani irin yanayi mara daɗi yana kara kusanto shi, ya tsani karar abu matukar ba numfashin ta ne, zai fita ba, asalima gani yake kamar kawai yaudarar shi ake shirin yi. Domin bai ga alamar tana numfashi ba, "Zamu tafi da ita Germany da fatan zaka bamu hadinkai.".inji Khalil,cikin wata irin masifa ya juya kan Khalil. "Matar ka ko matata? Karka yarda ka ce zaka min iyayi akan mata ta, wallahi ranka zai mugun b'aci, dalla matsa ka bani guri." Kura mishi ido suka yi baki daya ya fita hayacin shi, gani yake kamar cutar shi zasu yi, dan haka Abie da kan shi ya rike hannun shi tare da cewa. "Karka zama mutumin da bai amsar ƙaddara mana, ka yarda dani babu abinda zai faru da Matar ka Insha Allah." Jikin shine ya shiga rawa tare da karkarwa, ya ce. "Abie da gaske?" Ya tambaya hawaye na zuba mishi, share mishi kwalla yayi tare da cewa. "Insha Allah!" "Don Allah Abie kar wani abu ya faru da ita!" "Da izinin Ubangiji babu abinda ya gaggare shi. Ka yarda dani." Haka suka yi ta rarrashin sa, kwalla na zuba mishi,suka nufi airport aka gama kome, sannan suka dawo, a daren suka bar kasar,.sannan suka bar su Mommy da Innah da Beenah da suka shiga tattara kayansu zasu koma Nijar, inda zasu sauka a Niamey, gidan Abie. Kallonta Innah tayi tare da amsar kayan hannunta tana ce mata. "Sannun Zainabu! Dama baki da lafiya ne?" "Uhmm" tace bayan ta ajiye kayan hannunta da sauri ta nufi ban daki,ta shiga kwara amai. "Subhanallahi ikon Allah, Sannun amma ai baki ci kome ba naga yau tun farar safe, ban da ruwan zafi babu kome a cikinki." Wasu kwallar wahala ne suka zubo mata, wato idan ta fahimta, Abie jika mata aiki yayi, wayyo Allah wannan abin kunyar da me yayi kama? Ina zata shiga ne? Maimunari na haihuwa ga Benazir da tsohon ciki, itama haka zata jera da su, abin kunyar yayi ƙamari. "Sannun Mommy, tashi na wanke gurin" inji Benazir, "A'a barshi na wanke ai kema ba dadin kike ji ba, taimaka mata ki kaita dakin ta." "A'a ba sai ta kaini d'akina ba, takai ni dakin shi, nafi son kamshin turaren shi." Ta fada a wahale, "Ai haka ne? Toh Allah ya raba lafiya, rabo ajali." Ta fada tare da gyara ban dakin, murmushi Beenah take tana kallon Mommyn su. Tana kaita dakin ta riko rigar shi ta daura akan hancinta, wani irin yanayi me dad'i yana ratsa ta. "Mommy ko na duba miki turaren shi ne, tunda kina son kamshin, idan yaso sai kina fesawa." "A'a nafi son na jikin rigar shi" ta faɗa tare da kwanciya, idanunta a lumshe, fita Beenah tai ta barta a dakin suka ci-gaba da tattara gidan, Barci me nauyi ne ya dauke ta, haka tayi barcin da rigar shi a saman fuskarta. ** Wajen karfe biyar na yammacin washi gari. Abie ya kira Mommy, bayan sun gaisa take tambayar shi. "Ya jikinta dai?" "Toh da sauki zamu ce, amma zamu dawo ni da Khalil, shi zai zauna da ita, idan yaso kafin ayi aikin zamu yi ta kokarin ganin mun zo dubata" "Toh amma kashe kudin ba zai yi yawa ba, kawai ku dawo din idan za a mata aiki sai ku je baki daya amma ayi ta sintiri a hanya akwai matsala" "Toh shikenan, amma ya naji muryan ki kamar baki da lafiya?" "Mura yake damuna" "Allah ya baki lafiya" "Amin Ya Allah Nagode" "Ki kula da akanki da yaran Insha Allah jibi zamu shigo" "Allah ya yarda" ta faɗa tare da zuba yawun a jikin wani abu. Sako kafarta tayi kasa, sannan ta mike a hankali,ta nufi hanyar ban daki tayi wanka sannan ta fito daure da towel, zama tayi sannan ta kira Yumnah, shigo tayi da sallama. "Mommy gani" "Yumnah, kice Beenah ta dauko min kayana zan yi sallah ne" "Toh Mommy" Ta juya da sauri,. Kwanciya tayi sai da yarinyar ta kawo mata kayan, sannan ta saka tace mata. "Kicewa Beenah tazo dakin nan ta had'a kayan Abien ku." "Toh" Ta fita da sauri, haka Beenah ta shigo ta had'a kayan tana sallah, tana idarwa tace mata. "Benazir don Allah ki nima min abinda zanci yunwa nake ji" "Toh Mommy me zaki ci?" "Beenah duk abinda kika bani zanci." "Toh" fita tayi dake suna da garin kunun tsamiya, haka ta dama mata da Fanke ta kawo mata, haka tayi taci hannu baka hannu ƙwarya. Tana gamawa ta mike tare da yawo a dakin domin zata iya amai, wayarta ta dauka tare da kiran wani shagon magani ta gaya musu abinda take bukata ko awa daya baayi ba, sai ga shi an kawo mata maganin. Dake ta biya baki daya, sa hannu Beenah tai sannan ta kawo mata maganin. Bata sha ba gudun karta yi ama, sai da taji yunwa tasha. Da kunun. Baki daya kamar an mata iyaka da falo, suna ta had'a kayan tana kwance, kuma zasu yi waya da Abie amma bata gaya mishi ba, kuma ta hana a gaya mishi, kuma irin cikin nan ne mai shegen saka fitina domin ya sakata mugun jaraba, ga laulayi ga fitin. Shi yasa bata son Fitina,. Ranar da zasu dawo haka ta daure ta gyara jikinta, sannan ta kwanta a dakin, basu suka iso ba sai dare, a gajiye suka shigo gidan, shi kan Khalil daukar matar shi yayi suka tafi masaukin shi, Abie kuwa bayan yayi wanka ya fito ya ci abincin dan ya ganta a dakin da yace zai shiga da abinci dakin ta shiga mishi masifa, shine ya fito yaci a waje, yana kallon Kanwar shi da Yumnah. "Wai meke damun ta?" Ya nuna musu kofar dakin shi, "Abie bata da lafiya ne, kuma bata cin abincin sai kunu" Mikewa Innah tayi ta nufi inda Mijinta yake, tana dariya. "Allah ya bamu irin naku ai da mun ware!" Shi da Yumnah suka ci-gaba da hira, bayan ya gama ta kwashe kayan takai kitchen a daren ta wanke sannan tazo ta zauna a kusa dashi. "Abie ya jikin Addah Munah?" "Da sauki karki manta idan kinyi sallah ki sakata a cikin Addu'arki." "Insha Allah, Abiena" rungume ta yayi sannan ya sumbaci goshinta, ya rakata dakin sai da ta shiga ban daki tayi alola da kama ruwa , yana tsaye ta kwanta yayi mata addu'o'in, yana cikin yi tayi ta hamma sannan ya tofa mata, kafin ya fita. Tare da kashe mata wutar dakin, Dakin shi ya nufa a dan tsorace, bayan ya shiga ya same ta tana amai. "Subhanallahi! Sannun" haka tay taimaka mata, ta fito ya wanke ko ina sannan ya shiga jera mata Sannun cikin jin haushi tace mishi. "Zaka kyale ni da Sannun ka ko sai na fita a d'akin" "A'a, Allah ya baki hakuri yi zaman ki, yan mata" ya fada tare da shiga ban dakin yayi wanka, ya a fitowa ya samu ta kashe wutar ɗakin, hango shi da tayi babu kaya ba karamin gigita mata lissafi yayi ba, dan Abie irin mazan nan ne masu kira mai kyau babu ko tumbin, kasancewar yana da tsawo, kuma zamani an Cigaba yana ƙoƙarin kula da lafiyar shi, ta hanyar motsa jiki, dirowa tayi a gadon ta fara rigima, shagwaɓa rikici. Kamar Baby Yumnah, dan ma Innah ta tafi da Widad tana gurinta, domin Yarinyar ta makale mata, itama kuma yadda take son Uwar Yarinyar haka take kaunar Yarinyar. "Hammah don Allah!" Wani irin rikice mishi tayi, a sanin shi tunda aka daura auren, idan ya nime ta bata tab'a yarda tazo. Sai yara sun yi barci, musamman da suka dawo sam taki yarda ko hiran soyayya suna yi a gaban yara, kunyar Maimunari yasa basu sakewa, idan ma ta shigo dakin shi kamar daukar wuta ko mara gaskiya zai ga jikinta har rawa yake, dan haka ya zuba idanu yana kallonta. "Zainah me kike bukata? Jikinki akwai zafi ko zamu je asibiti ne" Yayi kokarin b'oye bukatar shi, cikin kuka me dauke da bukatar shi tace mishi. "A'a kai nake so" "Toh gani a gaban ki" fisge towel din tayi, lumshe idanun shi yayi..yana mamakin sauyin ta, matar da idan ya shiga d'akinta kamar yazo mata da alfasha, tayi ta kuka tana cewa ya rabata da abin kunya, dan haka tallafeta yayi tare da mata matsuguni a saman kirjin shi. "Yau da kanki" Gyada mishi kai tayi sannan, kwantar da ita yayi tare da mata rumfa da faffadar kirjin shi. (😂inji Ubaid yace dan Iya wannan sai dai yar iya) Ajiye kome yayi a gefe ya gurje soyayyar shi, domin ita ta kawo kanta, ya kuma tara mata gajiya sannan ya tashi ya had'a mata ruwan zafi, bayan ya taimaka mata ta shiga wanka. Ya gyara d'akin, bayan ta fito ta samu yana gyara gadon, zama tayi shima yayi nashi ta fito, tana kwance, kayan barci ya saka sannan ya rab'a gefenta, tare da shafa gashin kanta, juyowa tayi tana kallon shi. Janyota yayi jikin shi ina shafa bayanta, ta kuwa narke Mishi, ya gaji sosai dake ya dawo daga tafiya ne amma matar nan haka ta hana shi hutawa. Kallonta yayi idanunta babu barci. "Me kike so?" Ya tambaye ta a gajiye, "Kai" "Toh Zainah" haka bawan Allah nan ya raba dare akan matan nan, sai da suka dauki lokaci kafin ta samu nutsuwa, wanka yayi da ruwan zafi ya zo ya kwanta, karfe shida ya tashi yayi sallah asuba, sannan yayi nafilla da yake kafin sallah asuba. Yana idarwa ya tashe ta, bude idanunta tayi sannan ta zuro kafarta kasa, tare da ɗaukar towel dinta ta shiga wanka. Bayan ta idar ta fito ta gabatar da sallah asuba, sannan ta kwanta a gefen shi. "Hammah barci kake ji?" "Ke kuma rigima kike ji?" "A'a kawai kai nake so" "A'a kayana dai kike so" "Kai Hammah meye haka" ta faɗa a shagwaɓe, "Zainah na gaji wallahi, kuma ina son ma huta koda na awa biyar ne gaya min meye kika sha ne?" Ai kamar ya zage ta, ta fashe da kuka tana faɗa cewa. "Idan ba lalura ba me zai saka na zama haka, ka hada ni da ciki me jaraba kace min ina rigima" Tashi yayi zaune bakin shi dauke da sunan Allah, ya d'agota yana fadin. "Alhamdulillahi! Kanin su Yumnah ne a jikin ki?" Murmushi yayi tare da rufe fuskarta. "A'a ai dole ayi ban ruwa, wannan kyakyawan dashen, Tabbas yana bukatar ruwa domin yayi yabanya" Ai kuwa bawan Allah nan ya dage tare da aikin Alkhairi da aikin lada. .... Khalil ya gaji sosai, dan haka matar shi ta taimaka mishi yayi wanka sannan ta dauko kular da ta kawo mishi na abinci, sai da yaci ya koshi sannan ya zauna suna hira sama sama, ganin zata fara barci ya sashi dole ya taimaka _Zaku yi hakuri a madadin three pages zai zauna a biyu, domin zan cigaba da typing ɗin FREE Pages din kishi._ #Mai_Dambu [8/18, 8:23 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA #wed-Aug-2021 BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SAB'ANI DA ƊAYA. ----------------------------------------------- Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida* Kaza Tara bala'i- Gumba bucket ƙarami- Gari- Hatsabibiyar zuma Hatsabibin gari Zobe- Tsumi-, Maina ya rikice Zazzogau Haɗin gigita shi Maƙale mata Sayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku _______________________________ Cikin kaunar da soyayya mai karfi Beenah ta kula da al'amarin mijinta, shi kuma ya nuna mata yayi kewar ta, anan take shafa mishi Mommy na da ciki. Dariya yayi ta mata, yana cewa. "Eyye kice zamu yi wasu kanen!" Gyara kwanciya tayi a jikin shi tana cewa. "Eh mana, Allah yasa ta haifa mana yara maza dukka." "Kuma kyakyawan irin ku!" "Kwarai Abie ne ko Mommy kasan shi yafita kyau domin shi baki ne ita kuma fara ce, shi yasa Addah Munah tafi mu kyau. Kaga Baby Widad mana yadda Allah yayi mata kyau ba Uba ba Uwa ba, kamar na boye kayan ta." Sumbatar wuyarta tare da rungumo ta, ta baya yana shinshina gashin kanta, har barci ya dauke su. Da asuba bayan sun yi sallah suka kuma komawa, barci. *** Bayan kwana uku, suka tattara sai Nijar, inda suka yadda zango a Niamey, Khalil ya wuce da matar shi. Mommy kan ita dangana ta akayi da asibiti. Domin laulayi take sosai. Yumnah da Innah suka dawo gida, tare da Baby Widad, abin tausayi yarinya da iyayen ta amma ta zama marainiya, dan ma bata damu da nonon uwar ba, ga Innah tana tattalinta haka sata take ganin Innah kamar uwarta. ... Umma Khalil sun je har asibiti suna gaishe da Mommy, sannan suka nemi a basu Widad. Abie bai hana su ba, sai dai yarinyar taki fir musamman da Hajiya Latifah ta nace dai ta dauke ta, nan yarinyar tayi ta kuka. Haka yasa Abbu yace mata, "Kina son Yarinyar kika shegenta ta tun bata bata taka doron kasa ba, ai ban zata da kanki zaki ce a baki ita ba, na fi daukar cewa k'iyayyar uwarta ne zai damammali yarinyar ashe ba haka bane " Wani irin kunya ce ta kama ta, karshe haka ta sunkuyar da kai, bata iya mika hannunta ba. "Hammah Mamman, kayi hakuri ta dauki gudar jinin Mohan, haka zai kara mata imani da tsoron Allah, kuma tayi tuba irin wanda ake son musulmin kwarai yayi." "A'a ai babu amfanin bata, yau Maimunari tana fuskarta rayuwa ce sabida ita, da yau bata rabata da mijinta ba, taya har wani zai samu damar cutar da ita?" Ya tambaye su ranshi a b'ace, "Amma kuma ƙaddara karban shi ma ibada ce" inji Innah. "A'a ban da irin wannan,.domin Kuwa son kai ya shigo cikin al'amarin na yarda da ƙaddara amma ban yarda akan cewa kaddara ce tasa Lateefah kashe musu aure ba a daren idan aka yiwa Nairah ko Radiyah ya zata ji?" "Kayi hakuri duk abinda ya faru ya faru, sai dai a tari gaba. Allah ma muna mishi laifi ya yafe mana balle dan Adam! Dan haka itama Maimunari nasan da tana nan zata yafe mata, ai ba wani abu bane jarabta ce" Abie ya fada tare da sake murmushi, yana kara bawa Abbu hakuri, ita kam Widad tana jin muryan Abie ta shiga mika mishi hannu, daukarta yayi yana cillata. "Ni dai karka karya min kishi ace nice na ƙaryata da gayya!" Inji Umman Dan Ba'are, "Ai da narasa matar so! Wannan fararren idanun kamar na larabawan Libya!" "Abie amma ai tafi Matarka kyau, kuma tafi Ammyn kyau" Inji Benazir da shigowar su kenan. "Nifa dama ina kulata ne sabida tana kama da Mohan, amma ban da haka, akan me zan damu kaina da ɗaukar mummunar mace" rufe baki Benazir tai tare da cewa. "Abie! Da bakinka kake fadar haka? Kaga yar fara balarabiyar Libya da nijar, bafulatanar Mali da Burkina faso. My Bororoji baby" Amsar yarinyar tayi tare da rungumo ta, sannan ta sake sautin kuka me ban tausayi, tana kara rungumar yarinyar a jikinta, tana jin wani irin kaunarta yana cika mata zuciyarta. "Allah ya bawa Mahaifiyarki lafiya yasa ta tashi da kafarta." "Amin Ya Allah, Allahummah Amin." Inji Hajiya Latifah da tayi laushi gwanin ban tausayi, haka suka yi ta amsawa da Amin. ** Bayan kwanaki ƙalilan aka sallami Mommy zuwa gida ya Cigaba da jinyarta, kullum su Benazir suna hanya sai da Mommy tayi mata tas tace bata son ta kuma zuwa mata, taji da kanta itama. Haka ta hakura domin da Khalil ne yayi magana toh sai ya hadu da rigima sosai zata yi ta kuka, tayi ta fushi tare da kin cin abincin, sai idan dan cikin ta ya isheta da juyi nan ne zata shiga niman abinci kamar mahaukaciya,.sai ta gama ci zata zauna tayi ya bakin rai kamar zata fashe. Sai da ya zauna ya gaya mata duk abinda take yaron cikin ta yana dauka. Shine ta rage wasu abubuwan, dan ma tana shiga gurin Umma, kuma itama tana yawan gaya mata tayi ya rage wasu abubuwan na rikici, da saurin fushi domin yaro yana dauka domin har ta kawo mata wata kirsa wanda ya faru lokacin khalifancin sayyidana Umar, Allah ya kara yarda dashi. Yace akwai wata rana yayi tafiyar rangadi izuwa wata shashi na yankin da yake shugabanci, yace sai ya hango wani yaro ya shiga gonar mutane, yana ta musu barna,kuma abin da aka noma bai kai a cire ba, sai ya daka mishi tsawa bai saka yaron ya razana, suka kad'a suka raya yaron nan yaki gonar, sai Amiril Muminina ya tambaya suwaye iyaye nan aka gaya mishi ai iyayen yaron mutanen kirki ne, mahaifiyar shi tana aikin jinya mahaifin shi kuma babban mai koyarwa addinin Musulunci ne. Dan haka yace yana son ganin iyayen yaron, dan haka baka raka shi ya tafi yaga iyayen yaron, nan ya tambaye su Meye yasa dan su ya kasance haka, iyayen suka ce basu yi kome ba, saima bautar Allah da kuma kyakyawan mu'amalar su da mutane, sai ya Amiril Muminina ya dubi uwar Yaron yace mata. "Wannan yaron ba haka kawai yake wannan rashin jin ba akwai wani abu, ko lokacin kina dauke da cikin shi wani abu bai faru dake ba?" Sai tayi shiru, na wani lokaci kafin tace. "Eh wata rana na fito aikin jahadi da nake yi na jinyar mutane da kuma amsar haihuwa, lokacin ina da tsohon ciki, sai na ratsa ta wani gona, anan na hango Randa cikin farin ciki na karo kuzarina dan na isa ga Randa, gashi ana zafin rana sosai. Koda na iso sai na iske randan nan babu ruwa a cikin shi, bakin ciki da takaici ya sani na fusata, har sai da dan cikina ya juya nayi tir da alawadarar manoman da suka bar gurin randan babu ruwa. Daga nan na dawo gida wannan shine abinda ya faru!" Shiru Amiril Muminina yayi sannan yace musu. "Tabbas b'acin ranki shine ya shafi yaron har yake lalata amfanin gona domin babu shafin shaidanu a tattare da shi, lokacin da ranki yab'aci akwai jinin da ta fita ta cikin zuciyarki wanda zai digq akan mahaifar yaron, shi kuma ya wuce dashi cikin jikin yaron shi yasa yake ganin abinda yake aikatawa na wani abu bane." Dan haka Malaman tarbiyya a Musulunci, sun yi kokarin fito da wasu abubuwan da yaro yake dauka, musamman akan matsalar yaron can, wanda suka tabbatar wannan abin ya faru da shine ta hanyar jini , wanda yake had'e da mahaifar shi, da wannan suka kara da cewa. Matukar yaro yana rashin ji ko fitina ko rigima haka kawai, ko yawan kuka da wasu abubuwan, duk Yaronki yana dauka a cikin ki, karamin misali me yasa ake cewa babu kyau sauraron waka idan kina da ciki!( Akwai wata member na grp dina, wacce take gaya mana cewa, babban D'anta sun yana da shekara goma a duniya ya sauke Alqur'ani, ta kara da cewa wallahi yaron ya kasance mai sanyin hali da kyawawan halaye, tace sabida tun ina da cikin shi ', aka bani addu'ar da Annabi Ibrahim yayi lokacin da ya kawo Hajara da D'anta ya roki Allah ya albarkaci Zuri'ar shi. Tace ayar yana cikin suratul Ibrahim, sannan tace sai daya a suratul Maryam,inda Mahaifiyar Nana Maryam tayiwa yarta da kuma bakacen da tayi,tace wallahi ban yi bakace ce ba, amma na roki Allah ya shirya shi tun daga cikina bana jin ko sautin waka, sai karatun Alqur'ani da wa'azi, ta kara da cewa Alhamdulillahi Ubangiji ya amsa min addu'a ta, domin wallahi ko cikin unguwar mu mutuntta yaron ake, ni kaina da nake uwar shi mutuntani ake, Ubangiji ya shirya min shi, dan haka yana da kyau tun daka cikin ki fara nima musu shirya da taimakon Ubangiji Allah zai tsaya miki! Wallahi sai naji matar ta burge ni ainun) Dan haka Umma ta gaya mata gaskiya akan tarbiyya, har take gaya mata idan zata ci abu ta fara da bismillah, idan zata zauna ta zauna da bismillah (🙄😎 gaskiya ya kamata na ajiye rubutun novel haka mu koma Islamiyyan, domin dauko tarbiyya a Musulunci) Duk dani ladubban musulunci, Umma tana daurata, duk da ta lura yarinyar ma ba tayar baya bace akan ilmin addinin Musulunci, amma itama tayi nata kokarin kuma itama Benazir tana dauka. *** Berlin, Germany. Goge mata jiki yake yana kallon yadda take kwance bata ko motsi, murmushi yayi sannan ya gyara mata kwanciya, yana shafa kanta, kafin ya mike tare da nufar ban daki yayi alola. Sannan yazo ya gabatar da sallah, bayan ya idar ne, ya dauko yar karamar Alqur'anin shi ya fara karantawa, idan ya gama kula da ita sai ta dauko Alqur'an ya fara karatu yana rage mishi kewa da kad'aici,. Babu wacce yake tausayawa kamar Yar shi Widad, domin tayi karama da ɗaukar maraici, gashi baya tare da su. Ga halin da Uwarta yake ciki duk sai yaji damuwa yayi mishi yawa, yaji kamar kan shi zata buga, kome ya tsaya mishi cak. Duk sai yaji kamar babu wani amfani a rayuwar shi, tunda wacce yake dominta gata nan kwance, duk fadi tashin da yake yanayi ne sabida ita, amma baki daya. Sai yayi ya sare, tunda suka zo ake gwaje gwajen,, har yau basu ce mishi kome ba, kuma basu kuma dawowa kanta ba, sai dai kuma ana zuwa ana mata allurai da saka mata ruwa. Wannan kawai ya kara mishi kwarin gwiwar suna sane dashi, likitan da zai duba su, ba dan kasar bane kuma idan zai zo yana bin kasashen kusan biyar kafin ya iso, shi yasa suke dakon jiran shi domin duk abinda ake mata shi yake bada umarni, sannan yana daga can ake tura mishi duk wani bincike da aka yi nata, shi yasa ma yace zai zo domin zai tsallake wasu ayyuka masu muhimmanci amma haka ya tsallake su, kuma ya saka zai zo nan da wata biyar da wasu kwanaki. Yana idarwa ya mike tare da rike hannun ta, ya saka a fuskar shi, yana kallon yadda take ko numfashin bata ja, dai na na'ura, baki daya jikin shi yayi sanyi... #Mai_Dambu [8/19, 1:39 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA #thu-Aug-2021 BOROROJI ~The Journey of Destiny💔~ Mai_Dambu Sadaukarwa ga Sajidah Nijar Samirah Nijar OumNass Azizah Hamza.... BABI NA SABA'IN DA BIYU. --------------------------------------------- *Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida* Kaza Tara bala'i- Gumba bucket ƙarami- Gari- Hatsabibiyar zuma Hatsabibin gari Zobe- Tsumi-, Maina ya rikice Zazzogau Haɗin gigita shi Maƙale mata Sayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku ________________________________ Shafa kanta yayi tare da goge mata hannunta. Yana jin saukar kwalla daga cikin idanun shi. Suna sauka a saman fuskar ta. "Ki tashi haka, idan kina cigaba da kwanciya Allah kaɗai san rayuwar da da zasu kwanta, sabida ke? Don Allah ki tashi. Iya haka ma horon ya isa haka, karki cigaba da gana min azaba." Haka yayi ta surutu, kai kusan kullum aikin shi kenan, idan yana kula da ita, baki daya ya koma bai da wani abu me muhimmancin sama da ita, kamar yadda ta badda rayuwarta domin shi haka shima ya ajiye kome, aikin shi da FBI ya ajiye baki daya. Ya zauna a jikin matar shi. Mahaifin shi da yan uwan shi sun zo, sun duba su sai da suka Mishi sati domin baki daya bayi da nutsuwa kuma yaki wani ya zauna a jikinta sai shi kawai. Bayan tafiyar su da wata hudu likitan yazo amma bai fara duba su ba, ya fara da mutanen da suke jiran shi. Sai da suka dauki wata biyu cur, kafin aka shiga aikin farko na bayanta, cikin niman yardan Ubangiji, ana saura sati za a shiga aikin da ita, Mohan ya tura kudi mai mugun yawa aka rabawa mabukata, tare da niman Allah ya amshi bakunar su, yasa ayi aikin cikin nasara, makarantun allo kuwa haka akayi ta kai musu sadaka. Gidan marayu haka aka kai musu motar abinci har gidan, tare da tawwasalin Allah ya kare su ya kuma basu lafiya, musamman Maimunari. Haka aka yi ta rabon nan har aka ya kira yace an shiga da ita aiki. Awa goma sha daya aka dauka kafin aka fito da ita, tana kwance rub da ciki. Mikawa Mohan hannu yayi sannan yace mishi. "Zan tafi, nan da wata uku zan dawo a duba na kanta, Allah ya bata lafiya, kai kuma ya baka hakurin jinya, amma zaka yi hakuri domin ba zata farka yanzun ba, sai anyi na kan Tukun. Shine me muhimmancin. Shi idan ana aikin ma zata fara kokarin farkawa, na fara na bayan ne dan shine Rayuwarta." Cikin karaya yace. "Toh Dr kana cewa zaka tafi sai bayan wata uku, ka duba ta bar yarinyar mu yar wata goma sha daya, dole yasa aka cire ta a nonon, Dr ka tab'a zuciyata ji nake kamar ba zan kai wata ukun nan ba, please ka duba al'amarin, mata ta ce. Ko zaman wata daya bamu cikin soyayyar juna ba" Ya shiga bashi labarin halin da suka tsinci kansu, take jikin likitan yayi mugun sanyi, ya rike hannun Mohan, tare da cewa. "Nayiwa Yarka alqawarin ba zan wuce kwana talatin ba zan dawo na mata aikin karshe ka yarda dani akwai ayyukan masu muhimmanci ne suna jirana, zan mata aiki da Yardan Allahn ku, kuma zata farka da izinin shi, ka yarda da Ubangijinku. Kuma ka nime ya bata lafiya." Duk da ba musulmi bane amma yayi Imani da Allah kuma ya yarda shi ne mai badawa. Bayan tafiyar shi Mohan ya kira gida ya gaya musu, yadda suka yi. Sannan ya kuma ware wasu kudin yace kai gidan marayu, domin yana sauraron wani wa'azain Kabir Gombe akan marayu, dan haka ya ce. "Abbu don Allah a kai gidan Marayu, suna da bukatar shi, a kula da su da matsalar su. Idan bai kai ba Abbu a kirani zan turo, ko ka tambayi Khalil akwai katin bankina na kasuwanci. Duk wani abu idan ana bukata a gaya min INSHA Allah zan turo." Alhamdulillahi a cikin wata biyu Allah da ikon shi aka kuma shiga da Ita aiki na biyu, cikin nasara ana aikin ta fara motsi wannan ba karamin dad'i ya saka su ba, ana gama aikin aka fito da ita, likitan ya mikawa Mohan hannu. "Anyi nasara! Amma zaka yi hakuri kwanciyar da tayi zai saka ta yi ta abubuwa irin na yara, kafin ta gama shan magani zata warware da Yardan Allah ku," Cikin gamsuwa Mohan ya mika mishi hannu, babban burin shi ya ga Maimunari a tsaye tana mishi murmushin jin dadi. Yana tsaye aka kai ta dakin ta,sannan ya bisu. Sai da ta share kwana biyar tana barci, kafin Allah ya nufa zata farka, tunda ta bude take kallon dakin. Ganin haka likitocin suna shigo aka shiga mata abinda ya dace. Sai da suka kai awa daya akan ta, kafin suka fita. Kallon Mohan take kamar wacce ta farka cutar makanta, takowa yayi a sanyayye ya zauna a gefen ta. Ya mika mata hannu. Dauke kai tayi kamar bata tab'a ganin shi ba. "Maimoon" banza tayi mishi. Duk abinda ya dace yayi mata yayi, karshe ma kara mishi ciwon kai take, musamman da suka cire mata na'urar kanta domin tayi wanka, ai kuwa sai da ya kai zuciya nesa, domin wallahi yayi hakuri wata kusan takwas, yana jinyarta, babu abinda ya fisge shi kamar kirjinta, had'iye yawun yayi makwat, tare da kallon yadda take mishi bori. Matseta yayi da bango hannun shi yana bisa duwas ɗinta, yana matsawa yace mata. "Ya isa haka, Hammah Mohan dinki ne" Kallon shi tai a sanyayye kamar tasan meye ya gaya mata kafin ta tura mishi bakinta, aikuwa ya kame bakin ya shiga cinye shi, hannun shi yana yawo a jikinta, kai Mohan dan jaraba ne.(🙄 A jinyar ma ba za kyale ta ba) Dakyar ya iya rike kanshi ya kawo ta waje, ya shirya ta cikin kayan asibitin, sannan likitocin suka kuma kwantar mishi da hankali zata dawo daidai, yayi hakuri, kafin su koma gida da lafiyarta zasu koma. Aikuwa Yar nima tasaka shi a gaba da rikicin banza kukan banza, kuka mara tushe balle makama, amma da zai tab'a yar banza shiru take tana zare idanun kamar tsohuwar mayya, tunda ya gano ta, Malam Mohan kakar shi ta yanke saka, domin tana fara mishi hauka zai kai hannun shi mazauninta. Ko ya riko dukiyar fulaninta,,. Sai dai kuga yar banza tayi luf. Tun tana da lafiya ma Mohan yasan sirrin rigimar ta balle yanzun da take pagal. * Sake shi hukumar gidan yarin suka yi, daga can nesa ya hango Khalil da wasu lauyoyi, cikin isgilanci ya isa gare su.. "Ina labarin Maimunari!" Murmushi Khalil yayi mishi sannan ya shiga motar ya zauna lauyoyi ma haka. "Mohan ya baka damar ka rayu domin kaga yadda za a buga soyayya. Ka rayu domin ka ga yadda Maimoon zata kasance da Mohan, wannan alfarma yayi maka domin yasan zaka so ka ga yadda zasu rayu" "Karya ne wallahi sai ka kashe su dukkan su biyu."ya fada a fusace, "Kuwa zaka mutu" Barin shi suka yi a gurin, Khalil ya kira Mohan ya gaya mishi sun gama kome. "Toh nagode sai dai har yau bata dawo daidai ba domin tunanin ta ya birkice wallahi ina cikin damuwa!" "Karka damu Moha, Allah yana tare da kai, ana kam muku addu'o'in kuma nasan Allah zai amsa." "Nagode sosai, Khalil da tsaya min da kayi da babu kai wallahi da ba zan tab'a tsayawa da kafana ba. Nagode sosai da Aminta mu" "Karka damu nagode sosai nima" Sannan suka yi sallama, cikin nutsuwa Khalil ya koma Niger. *** Bayan wata ɗaya. Alhamdulillahi domin lafiya ta samu, kuma duk wanda ya ga Maimunari ta samu lafiya, domin tunaninta ya dawo, yanzun haka suka kasar Moscow. Inda Mohan ya tafi domin kasuwancin shi. Ina gyara jikina ya shigo d'akin juyawa nayi tare da amsa mishi sallamar shi. Sake towel din nayi ina murmushi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da takowa gabana. "Zaki kashe ni da shagali Matar Mohan" "Burina kenan na raya mijina da shagalina." Karban kayan nayi na watsa a kujeran dakin, sannan na ja hannun shi muka shiga ban daki, tare muka sake wanka, bayan na cinye shi da salona musamman, sannan muka fito daga ban ɗakin, kai Hammah Mohan. Tunda muka fito muke manne da juna, abu daya muke tare da cinye junar mu, sai da ya shiga babban birnin lintsin kafin muka sake ihu lokaci guda, wani irin dad'i da yanayi na musamman, yasa muka haukata kan mu. Bayan awa daya. Ina sanye da doguwar riga, na yane kaina da farin mayafi muka fito cin abinci. Ban san wani irin yanayi na riski kaina ba, amma Tabbas ina cikin farin ciki samun mutum irin Mohan a matsayin abokin rayuwata. Haka muka gama yawo sannan ya kai ni har dubai, wannan dakin dai shi ya kai ni, inda na rasa wani irin dad'i nake ji. Sati biyu muka yi a can. "Wallahi ba mu koma ba, mutane su hnnai sakewa da mata na!" Ya fada yana hararan gefe da gefe, "Hammah na ina kuma zan iya maka Ni fa babu ruwana,idan kace kar na kula su shikenan." "Ni zaki haɗawa aiki? Na manta ban gaya miki ba, wata biyu da suka wuce Beenah ta haihu an sami mace, kuma Kinsan me? Sunanki aka saka. Suna kiranta Jewanah, wato (God gift in Urdu language) dan haka sai ki buɗe bakin aljuhun ki, domin samun takwara da wahala" "Kai Hammah Mohan, me nake dashi sai dai kai, zaka a ra min na yi musu idan yaso na biyaka" na d'aga mishi gira. "Gaskiya kan zaki biya dan ban koshi ba, kuma gaskiya ki biya yanzun sai a wuce gurin" Aikuwa makale mata ya makale min sai da ya samu kanshi muka shiga wanka tare, sannan muka shirya tare da nufar kasuwa, minti sayayya sosai, sannan muka dawo masaukin mu, washi gari. Muka dira a kasar mu ta gado, aikuwa kamar yadda ya fada, sai da muka yi sati biyu bamu ganin juna, saboda jama'a ga Mommy da tsohon ciki, dan ma ina jin wai zasu mata aiki ne, na tausaya mata domin ya hadu da girma da shekaru, kullum cin fada take. Gashi abinda na lura ta tsani ta bude ido taga Abie a kusa da ita, tayi ta kuka tana masifa duk shi ya janyo mata wannan fitinar, tass take mishi, rabonta da haihuwa shekara goma sha biyu,. Amma bawan Allah nan ya cuce ta. Allah Sarki sai yayi ta bata hakuri, kamar zugata yake, haka zata kawo min karar shi, ni kuwa sai nayi ta kuka. Lokacin Yar Jewanah tana da wata biyar, haka muke zama muna rarrashina Mommy, idan muka matsa muyi gulmarta ni da Beenah. "Addah Munah, Mommy gata yayi mata yawa kiga yadda Abie yake rarrashinta amma ba zai hana an jima ta saka shi a gaba da kuka ba, wallahi wancan satin da fushi na bar gidan, haba ta saka mana Uba a gaba da rigima dan bata shiga kauye ne, da ta ga abinda bata tab'a gani ba, matan da suka fita manyanta da ciki." "Toh Magulmaciya Beenah gulmata kike da yar Uwarki?" "A'a Mommy ba gulmarki ba muke ba." Aikuwa ta shiga fada kamar zata dake mu, Abie na zuwa ta fashe da kuka. "Kana jin Yaranka zagina suke wai na samu gata sai abinda na gadama nake" "Uwata ya haka? Beenah zaki daina zuwa gidan nan da"sannan ya lallabata suka bar mu, aikuwa muka sake Dariya. ** Na koma gidan su Hammah Mohan, nan ma sai da muka tafi har Agadaz, lokacin Widad tayi girman ban mamaki,. Daga can muka wuce Damagaram, inda na nimo abokaina Salihu Muhmuda da Amadu Bukar. Sunyi aure har da iyalin su, nasaka Hammah Mohan yayi musu alkhairi bayan ya dauke su aiki, sannan muka dawo. Kwanan mu ashirin da biyar da dawowa aka yiwa Mommy tiyata, tare da ciro mata yaranta Biyu mace da namiji. Tun dare aka yi aikin Hammah Mohan bai gaya min ba, sai da asuba. Kuka na saka tare da kai mishi duka, yana dariya. "Saura ke!" Daukar matashi nayi na rufe shi da duka. Haka muka kasance har bayan mun karya muka nufi Asibitin kamar ba a cire mata Babyn ba, sabida mun samu tana hira tas. Zuwa nayi kan yaran ina kallon su. "Hammah na kalli nafi yaran kyau" "Ina za a gwada! Pure love!" Inji Mohan, "Gaskiya kin fisu kyau, First Love." Inji Mommy Daka tsalle nayi na rungume Hammah Mohan, abinda Mommy ta faɗa. "Ai dukkan su munanan ne, kace karshen kyau!" Inji Abie. Kuka na fashe da shi, ina kara rungumar Hammah Mohan, murna nake ji yadda iyayena suke nuna min. Kamar zan shige jikin Mommy Sai dare muka koma domin an kawo abinci daga gida, na gaji sosai. "Yan mata ya kama ta kiyi wani abu dan wallahi ina son ganin ki da ciki." Dariya nayi na gyara kwanciya ta a jikin shi. "Kayi wani abu" "Ai ina kan yi ko kin sha maganin hana haihuwa ne?" Da sauri na tashi zaune tare da cewa. "Wallahi ban sha kome ba, hutu ne kawai." "Gaskiya bana son hutun nan ya isa haka." Gyada mishi kai nayi sannan na ce mishi. "Toh Hammah na, Allah ya kawo mai Albarka." ** Sai da Mommy tayi sati biyu sannan aka yi suna Bayan sunan inda aka sanyawa yaran Mariya da Mustapha, Inda muke kiran Mustapha da Aneen Mafiya kuma muna kiranta da Anam. Bayan sunan nima na fara nawa. Laulayin kamar yadda Hammah Mohan yaso. Bayan wata tara Allah ya nufa ba sauke katon Yarona namiji, wanda tare muka yi nakudan da Hammah Mohan. Aka saka mishi sunan Abbu muna kiran shi Abul Khair, *** Bayan wasu shekaru. Mun fito makarantar su Yumnah, anyi bikin yaye su, Aneen da Anam suna fada, gefen su Widad ne, tana kallon su. Bata musu magana ba, na shigo motar. "Ummin Abul Khair, Kinga Aneen tana ce min dan lukuti" ya fada idanun shi na cika da kwalla. "Ummi wannan kawu Aneen din bai da kirki zaginta yayi wai munafuka." Inji Widad da take kallon su. "Toh ya isa haka ko na hada mu da Appa yayi min maganin ku" Bubbuga glass din motar aka yi na kalli wanda yake wajen motar tare gabana ya fadi na kuma saka key tare da kiran Mohan, yayi ta buga motar yana ihu, can sai ga Hammah Mohan. Kwallon da Hisham wanda ya dawo Mahaukaci karfi da yaji, sannan aka janye Hammah Mohan, yazo ya fito dani, ya rike hannun. "Mata ta! Maimunari Isma'il Wodaadabe, tana dauke da cikina na hudu a jikinta, inuwarta ka kuma rab'a sai na kashe ka." Sannan ya juya muka bar gurin. * Koda muka dawo gida na razana ba iya ni ba hatta yaran tsoron Baban su, suke sai da na shiga ban daki jini ya tsinke min dole muka nufi asibitin, sai da aka bani hutun wata biyu, yaran suka koma gidan Beenah, dake Su Aneen da Anam sun koma gidan mu gurin Mommy, Allah sarki Abie da kanshi ya haɗa min maganin da na sha cikin ya koma ya zauna, sati na ɗaya aka sallame ni. Mohan ya dauke min kome, haka na cigaba da kula da cikina.. Anyi bikin Radiyah dan sai yanzun Uwar Safwan ta amince sakamakon rashin dadin da matar da ta aura mishi take fuskanta a gurin shi, ita da kanta ta roki Umman shi ta aura mishi Radiyah. Jalilah itama tayi aure a can Saudiya kanin mijin Muslimah ya aure ta, beenah ma Yaranta uku. Mace mai suna na, sai Mai sunan Umman su, sai Mai sunan Baban su da baban shi, ana kiran shi Hanif, mai sunan Umma kuwa ana kiranta Walidah. Sai Jewanah. Nairah itama anyi bikinta ta auri dan Sarkin Kano, an sha biki sosai mune manyan yayyu. *** Cikina yana wata bakwai, Allah yayiwa Matar Salman rasuwa, gurin haihuwa, mugun tsoro ya kamani, babu shiri na shiga nakudar wata bakwai, haka na haifi yarinyar yar karama da ita, aka saka ta a kwalba. Khausar ce a kan mu. Sai da muka yi wata biyu asibitin aka sallame mu, itama ta koma gidan mijinta sai dai Ammyn ce da Allah ya daura mata jinya sosai, kullum ta ganni sai tayi kuka da niman gafarana. Ga Small Mom itama yaranta biyu, Armaya'u da Areeshah. Bayan shekara daya, idan ka ga yarinya na ba zaka dauka yar wata bakwai bane, wacce muka saka mata sunan Ammyn muna kiran ta, Khairat. Zirga zirga muke domin bikin Yumnah da Abie ya bawa Salman ita, bata son shi amma sabida biyayya yarinyar nan ta amshe shi hannu bibbiyu.. Haka muka sha bikin su, dake ya dawo gida da aiki, aka kai ta gidan shi da yake Maradi. Muma haka kawai Mohan ya saka mu muka koma Maradi. Bayan bikin da wata uku aka mai da mata yaran Salman ɗin. Rayuwa cike da kaddarorrin masu kyau da marasa kyau mun amshe su, na cigaba da shiga daji ina wayar da kan al'umma Fulani musamman Bororoji babban burin Baba Mari, ya'yanta da suka b'ace. Su dawo amma babu labarin su. Alhamdulillahi domin duk inda muka samu labarin su muka kai musu kayan tallafi da kulawa. Har da musu burtsaitsai sai makaranta ya'yan makiyaya. Wannan gudunmawar da nake badawa yasa Hukumar Majalisar Dinkin Duniya, suka bani lambar yabo, tare da bani matsayin na musamman inda ake biya na da dallar Amurka, shi wannan kawai ya ishe ni nayi hidimar al'umma. Ganin yadda nake son dakatar da muguwar dabi'ar Hammah Mohan da kanshi ya tafi asibiti da ni, aka dakatar da haihuwar mu, yace min. "Ki bautawa Allah, sannan ki tuna da Al'ummar Annabi, karki manta da igiyar aurena akanki na yarda dake ki shiga ki wayar da kan al'ummar Bororoji." Nayi kuka nayi farin ciki, sannan na cigaba da abinda ya sani. Kuma na yarda da Allah, yana tare da mu. Gefe guda kuwa Hisham yana ganin Cigaban bakin cikin yadda yake ma ya ishe shi, uban shi ya mutu mutuwar wulakancin, sai a anan aka samo gawar mahaifiyar Hisham din da ya tsafeta yana aikin sabo da ita, shi yasa ake son ka gina Alkhairi zaka same shi a gaba. ** Shafa wuyana yayi tare da cewa. "Radiyah ta haihu, baki samu zuwa ba, Nairah kan tace na.miki godiya sako ya isa." "Radiyah Beenah ta je mana amma Insha Allah zamu je da Yaran." "Toh Allah ya kai mu" *** Washi gari Muka je gidan tare da Alkhairi, dan muna hira wata rana, ta tab'a ganin wata mota tace tana so, dan haka ya saya mata motar, na sami yan uwan mijin suna mata dariya, dan Uwar mijin ta mata bawa Uwargidan ta kyauta kujeran Umra, da muka shiga gidan suna mata wannan tsiyar gani na yasa kowa ya shiga hankalin shi, haka tayi ta gaya min abinda suke mata. Mika mata key motar ta nayi, ta fito da guda tana ihu, ai babu shiri suka fito, kowa ganin motar ta sai da jikin shi yayi sanyi, dan haka na nuna mata karta damu, bayan mun koma gida na gaya mishi yayi mata Alkhairi akai mata domin haka zai saka dangin mijin su d'aga mata kafa,. Har sauran yan uwan ta, suna kokarin share mata kuka. Sai gashi hatta mijin shima binta yake yi. ...... Mommy tun daga Yan biyu tace ta yafe a kai kasuwa, sai dai mu yaranta, Yumnah ma da ta haihu ba laifi aka yi hidima. Ta samu ya mace aka saka sunan Mommy. Bayan wani lokaci mai tsawo na ajiye aikin inda na tubure zan kuma haihuwa bai Musa min ba, muka je aka cire min abinda aka saka min a hannu na. Wata na zuwa kuwa Sai ga cikin nayi ta addu'a Allah yasa na samu takwaran Innnah. Ai kuwa Allah cikin ikon shi, na samu cikin, aka nuna mana namiji ne, haka ya kashe min jiki, bayan watanni da na dauka Allah ya sauke Ni lafiya, na samu da namiji ne, aka saka sunan Abie, muka kiran shi Adeel. Watan shi tara na samu ciki. Na sha bakar wahala kamar zan mutu, kafin na haifi yarana biyu mata, Aka saka musu Ummul Khairi sunan kakan Mohan, sai fatar sunan Innah ana kiranta da Meenat. Naga gata da soyayyar mijina, kuma har yau ina alfahari da mijina, domin ya d'aga darajata daga cikin mutane masu yawa, *** Bayan shekara goma sha biyar. Arziki yaci Uban da, na kara kankaro daraja ta, Ammyn kuwa bata moruwa, a cikin shekarun nan muka ji labarin mutuwar Hajiya Karime. Addu'ar barci na tofa musu, sannan na rufe dakin na nufi namu dakin. Karfi da yaji ana niman lalata min miji wai ta fito ta karar siyasa, abinda had'a mu kenan. muke rigima, ina shigowa ya riko hannuna. "Na janye kudirina na bawarwa dan Uwansa Ahmad Bala Raees, daga karamin mataki har zuwa shugaban kasa zan mara mishi baya." "Shima ce maka akayi Halimah Ishrat zata yarda mijinta yayi ta yawo da Gantali irin na yan siyasa? Salon yaje ya hadu da wasu manta su lalata mishi rayuwa?" " A'a karki ce min kema zaki fara kishi a tsakanin zubda jini?" Cikin fushi na ture shi zan wuce. "Mohan mijin mace daya ce kuma ke ce matar shi a duniya da lahira. Kuma nasan shima Ahmad!" "Wai ina ka bar Sheikh Zunnur Bin Jonah(Alhubbuh Fihi Mararatun) da kanin shi Yunus Zunnun bin Jonah? Ko ka manta da Arshan ne(Ruwa a jallo) toh idan ka manta su ka bude idanun ka kaga Malam barci nake ji" Bakin shi a sake yace min. "Nasan Ashraf,.nasan Mehran, nasan Aliyu Asadullah, nasan Malik da Maheer, nasan Dr Yohanna Chibok! Nasan Ahmad Halwani! Toh na kuma san Aalim da Aamil sai wane?" "Yunus mai Nasara tare da Ahmad Roma da Amaan Mandara idan ka manta bari na tuna maka su! Da alamu ka manta Jikar Innah wuro, Sadeeq da Aminin shi Imran" Daukata yayi cak yana faɗin. "Gaya min sirrin Labarin Addah Ramlat!" "Eh toh da zaka ce Dambujebuje da zan fi tuna maka kome, cikin nutsuwa." *Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka sosai da ka bani damar kammala labarin nan akan lokaci kuyi hakuri wallahi bani da lokacin kaina kuma yau ina da zuwa ganin likita amma na tsaya na karasa labarin nan,kuyi hakuri da yadda na kawo shi karshe wallahi ina da uzurirruka masu yawa! Kuyi hakuri! Koda hidimar Muwaddah da Walid aka Barka kasan an baka aiki, balle kuma gana gida ga na miji! And ku ma'abota hankali ne ku duba yanayin, rubutu babu sauki amma Nagode sosai da kuka bani haɗin kai dari bisa dari* Insha Allah October 10! Zan sake muku sabon Free Book dina Alhubbuh Fihi Mararatun! Free ne sabida kaunarku da yake raina. Sai wanda zan yi na kuɗi amma shi babu rana wallahi Ruwa a jallo!!!..... INSHA ALLAH Upcoming books. ALHUBBUH fihi Mararatun!! RUWA A JALLO!!(WANTED) Now Mu hadu a Kishi a tsakanin zubda jini (Ana kan FREE Pages) ga masu bukata zasu biya ta nan 0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank sai su min magana ta Whatsp 08130269641....300₦ ko katin mtn. Kufito kwanku da kwarkwatarku kuzo ku sayi kishi a tsakanin zubda jini, ko kuma nayi ta bori rashin daraja,🙄😭😭😒😏 bari na ga Masoyan asali. #Mai_Dambu