💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ _Bismillahirrahmanirraheem_ *Yan,uwa masoya barkarmu da sake saduwa daku awannan sabon lbr nawa mai suna yaya fahad nawane, kamar yanda na alqawanta muku ayau Allah s w a. Ya cika mana gamu a shafin farko. Ubangiji Allah ya jangorancemu har mu kammala wannan lbrn lfy, tareda fatan xai fadakar kuma ya nishadan tar daku masu karatu Allah yaqara hada kawunan mu ya dai daita tarenmu daku taxamo mai amfani aduniya da lahira ameen!* *•1/5•* Awan qauye ne masuna kukunba wanda yake a qarakar hukumar dukkum ta jihar gomben najeriya ayau kuma nana mota ta saukeni ga dukkan alamu yau yar mutan arkilla tayi nisan kiwo, badan komai ba saidan farauto muku lbr wanda xai motsa kunnuwa da xuciyoyin ku Kubiyoni Dan qarami qauyene wanda awuni daya jal mutum xai iya qirge yan tsirarrun gidaje da bukkokin dake cikinshi a qofar wani dan madaidaicin gida naxo wucewa wanda kaf din qauyen shikadai ne mai dakin bulo da bugun kwana harmada felista da fenti Fatee! Fatee!! Shine sunanda naji wata yar tsakatsakin mata tana qwallawa kira da iyakar qarfinta hakan yasa nakunna kai gidan tareda fatan samun abinda nake nema, aikuwa inashiga naji muryar wata yar matashiyar budurwa wadda aqalla shekarunta baxasu gaxa sha biyar xuwa sha shida ba, Tace na,am goggo gani nanfa, dagani har goggon daga kanmu mukayi sama ta inda mukaji amon muryar yarinyar yafito yasalam na fada inda goggo kuma tashiga rafka salati da sallallami, yanxu fatee kuma rufin daki kika hau? Aina kika taba ganin mace da irin wannan haye2? Hahahhhh wadda aka kira da fateen ta fashe da dariya kai goggo saikace wani abin al,ajani jifa yanda kikayi kamar kinga wani abu dabaki taba gani ba, hmmmm to wake naxo diba kinsan fa baffa yace yaya fahad gobe xai dawo qasar nan, wayyo dadi taqara kecewa dawata irin mahaukaciyar dariya aradun Allah alalen wake xan mishi nasandai dole yaxo gaisa babbfa kai ko baixoba ma ni har gomben xanje inkai mishi ita, Goggo dai shiru tayi dan taga fateen kamar ta xautune ina yarima fahad ina alale? Alalenma na qauye yaronda tuntashinsa ko qauyenma bayyason gani balle abin cikisa tasani sarai inbadan rayuwar mai martaba ba toda xumuncin ma yarima baxaiyi dasuba Tana tausayin yarinyar data dauki ranta ta qwallafa mishi tun yarinta gashi har girma yataso mata sa,oin ta duk anyi musu aure amma ita duk wanda yataso mata da haukan tsiya take koranshi tace ita ta yaya fahad ne yaya fahad kuma nata ne, Ba abin tacemata koxuwa yayi baxaici alalen nan ba, tsaf tasan halin fatee indai tagaya mata hakan kam baqaramin aikinta bane tafado daga saman dan akan yaya fahad dinnan ba abinda baxata iyayiba Girgixa kai goggo tayi taci gaba da wanke kononin datake tace shikenan ai inkalam yaxo yasameki acan kin fada masa, ahab inji fatee wai mutum dai badaman yasakeyayi abu saikaji ance malam inadai malam dinnan baffa nane? To mutum saikace dodo ayita tsorata mutane dashi haba dan Allah Ta duqa taci gabada diban wakenta tana turoshi qasa tana yan waqe2 ta goggo dai bata koma cemata komaiba, tacigaba da aikinta, sallamar baffanta taji a tsakar gidan malam kenan, ai dasauri tamiqe tsaye akan kwanon malam yaxuba mata ido kawai yana kallonta Take jikinta yahau kadi yana karkarwa kwararararararararara naji tasako fitsari yakuwa biyo kwanon jikake yarrrrrrrrrrrrr yasakko al,amarinda ya kusa yasaka malam dariya dattijan yajuya yafita daidai da shigowar bashir yayanta malam yafita yanacewa bashir ka sakkoda ita nanfa fatee tabare baki tahau balla kuka ko,ina anajinta wayyo yaya fahad kaxo katai makeni wayyo yaabaffa xasu kasheni Figigit yarima fahad yafarka daga nannauyan baccin dayakeyi sakamakon kiran dayaji daga muryar dayasaba jin kira da ita akowacce safiya kodare, yana bisa katafaren gadonshi na alfarma daqyar yadaga hannu yakunna bed site yakalli agogo haryanxu su a inda suke dare ne garin bai gama wayewa ba tukunna sweezland kenan kyakkyawar qara waddata wadatu da albarkatu da ababen more rayuwa yakalli gefenshi Sonia ce kwance tana sharar baccinta hankali a kwance Yaja dogon tsaki yarasa meke damunshi tun daga ranarda yaje qauyen kukunba wajan yiwa baffanshi qanin mahaifinshi sallama haryafito xaishiga mota wannan qaramar yarinyar takirashi da *yaya fahad* yajuya yai mata murmushi badan yasoba saidan yakasance halayyarsa ne, Totundaga wannan lokacin yacigaba da jinkira da wannan muryar lokaci xuwa lokaci cikin bacci ko a farke Tsawan shekaru biyar kenan Tofa🤔 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•6/10•* Wani tsakin yakomayi sannan yamiqe bayi yanufa yasalam reader's kuxokuga tsari saikace dakin wata mace macenma ta masu hali, nikam nasmat nace saikace ba gobe? Wai nandaki ne anan brush yafarayi sannan yayi wankan tsarki yaxuro jallabiyya yafito saida yabar dakin tukunna yafada wani tamfatsetsen falo nanfa idona suka nemi sumin yajin aiki dan suna cikin kallon wannan xan maidasu kan wancan masukaratu bansan yaxan keatanta muku tsaruwar wannan falon ba, cos nikam dai tunda nake duk a yan leqe leqena bantaba arba da tsararren wuri kamar wannan da yarima fahad keciki ba, da daya tilo gamai martaba sakin gombe, qaitaccen saurayi mai aji mai taqama da mulki miskili na qarshe mutumin da yaqware wajan sanin halayyar dan adam wannan ne yasaka ayanwancin lokuta inyakalli mutane saikaga yana murmushi cos lokaci daya xai kammale sanin dabi,in dakafiyi da abinda kafi qi dakallo daya, wannan kadan kenan dagacikin baiwarda Allah yayiwa yarima fahad, Baicika yin magana ba galibin maganarshi yanayintane da ido koda hannu, wannan ne yasaka baicika hulda da mutaneba cos indai basanin halayyarshi kayiba to xama dashi xai baka wahala. Mutum ne kaikirki tawata fuskar uwa uba taimakon naqasa dashi bayya son kagode mishi idan yamaka abu xaifikyautuwa ka godewa Allah kalmar yarima kenan gaduk wanda yace mishi yagode Akwaishi da son rayuwar hutu nau,ukan wasanni qalilan ne yake bugawa kuma akowacce wasa dayakeyi sarki ne, fannin mata kuwa ba,a magana domin yarima yana cikin mutanennan masu yawan sha,awa saidai ahakan ma bashiyake neman mataba susuke nemanshi wannan ne yabashi damar amatan ma baoowacce kucaka yake kulawa ba, yanadaga tsarin yarima inya sadu damace sau biyu xuwa uku tagam tashe awurinshi kuma daganan kusadashima bata isa takoma raba ba, komai kyau da nasabarta, Wannan ne yasaka dayawa daga matan jami,ar suke jinjinawa sonia kasancewarta mace tafarko data karya alqadarin yarima ta wannan fannin hartakai watanni biyu yarima na dasawa da ita, sonia takasance yar qasar Indian ce wadda itama yar,sariki ce a garin nagapuran na india, qaramar yarinyace matashiya saidai gogagga akan harkar karuwanci sonia tanada sani sosai akan makamar namiji ga sirrikan tsafi na gado datake amfani dasu wajan qara mallake yarima, wayanda bakowane yasanda hakan ba, Ayanxu itace tagaban goshin yarima fahad wadda yake shanawa da ita kuma cos daya suke karanta da ita Koda namaida kallona ga yarima harya buda qofar wani qaramin daki yashiga ikon Allah🤔 Kunsan me nagani reader's? Hmmmm dakine na musamman wanda aka taneshi domin yin salla ko karatun alqur,ani mai girma Shimfide yake da lallausan cafet gawata yarqaramar sef da akayi mai masaqalar litattafai, litattafaine na addini acikinta kowanne dasunanshi ajikin inda yake yayinda gefe daya yakasance shimfede da wata faffadar sallaya tasha kyau ga laushi da carbi agefe. Can naga yanufa yadai daita akai sannan ya kabbarta salla Duk iskanci dashashanci na yarima baya wasa da salla kokadan yanayin kowacce akan lokacinta Yana nan har time din asuba yayi yagabatar da ita xuciyarshi cikeda tunanin komawarshi 9ja da xamandaxaiyi acan harna watanni uku hmmm yasauke numfashi tareda jan dqn guntun tsaki *A kukunba* Daqyar bashir ya iya hawan rufin kwanon dukda kasancewarshi namiji ai tun daga can yafara ranqwashint yar banxa maikan mangwaro taqara balle baki Yasakko da ita goggodai uffan batace dasuba dan fateema ta cancanci fiyeda hakan ita da a brni taje haihuwa datace canjan ya qkamata yariyar kwata2 bata biyo halintaba balle na malam, ya bashir na janyeda hannunta sun sakko yana tunani sakinta danyasan muddin yasaketa haka saitasami abinda tamishi tunda ita komin qanqantar abu inaka mata wlh saita ram......................, Ai baigama tunaniba yaji saukar lafiyayyen cixo a hannunshi dake riqe da ita bashiri yasaketa tayi waje dagudu tana Allah ya isa ya bashir kam yarfe hannu yahauyi kan ubancan wlh xaki dawo kisameni fatee kam tuni ta shilla waje 😂 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•11/15•* Baffa dake qofar gida yabita da kallo cikeda jimami yagirgixa kai tareda yimata addu,ar Allah shirya, batayi birki ko inaba sai gidansu innawuro shaqiqiyar qawarta wadda tasu taxo daya ko sallama bb haka ta afka maman innawuron taci karoda,ita a xauren adda yanlijam adda dake tsaye a tirken awakanta tana basu ruwa ta dago a ah fatee maubegelle jamfelen noye dadasare modon? Fateen tabata amsa da hausa lfynta qalau Innawuro don sarena ko uburti? A,ah odon tadaga murya ta qwalawa innawuro kira itamadai kamar an cillota yawwa tawan daga ina haka? Tace diga wuro mana, wai kinsan wani abu? Saikin fada ta falle baki jango yaya fahad udon warta sare, inna wuro ta qwalla ihu dan Allah fa? Tace wlh gobexai dawo qawata am dagudu innawuro taja hannunta sukabar gidan sunata ihun murna! Wayyo dadi inatayaki murna fatee To yanxun mekika ganiyadace muyi mishi? Tofa?🤔lallai wayannan iska tana wahalarda mai kayan kara😂 Fatee tadan nisa cikeda damuwa tace wlh ban saniba da alalen wake nayi niyyar yimasa amma harna debo waken wancan baffan yatsoratani yasa aka sakko dani wlh yanxumma gudowa nayi a hannun yaya innawuro ta kece da dariya shagga fatee wlh kinburgeni yanxun yaxa,ayi to? Tace nikam yanxun babu saidai ko ke tayi murmushi bari kawai tawar tashi muje jeji mudebo xobo haddashi mujiqa mishi musiyi cola gun diyeri mai kanti muxuba mishi tajiyo dasauri tarungume qawar tata kai hanijin wadi emiyiduma qawata wlh nagode tashi mutafi najfa suka nausa jeji A gwanar wani yaron mai anguwa suka sauka xobo yayi jajir yayi kyau sosai manya2 suka kalli juna suka fasheda dariya kai Allah kasa wannan ya iya gyaran gwana, kinga yanda sukayi kyau? Hahahhhhh nanfa suka fara yashe xobon kamar xasu cire duka gwanar innawuro ce tace kai fatee wannan fa ya isa haka Allah karmu wuce qarfinmu, itamadai datakalli tulin xobon dasuka tara akan mayafansu dole ta tsaya suka daddaure suka dauka sunci sa,a ba wanda yagansu har suka kai gida amma bata yarda sunje gidansuba gidansu innawuro suka taka birki alokacin adda tafita kaiwa baffan innawuro fura a jeji wajen garken shanunsu, nanfa aka fara aiki babu kama hannun yaro qatuwar tukunyace saida suka cikata nat da xobo suka banka wuta 😂 dayar kuma tatafi karbo bashin cola gun mai kanti, Saiyamma suka samu gama hada xobon suka juye a wani babban bokiti bayan sun tace kamar yanda sukaga anayi a gidajan biki suka rufe dai dai lokacinne adda tashigo gidan da sallamar data gagara iyarwa danganin tukar xobo kqca kaca da gidan ko gidan biki albarka tayi salati fatee kongi aimi? Mexan gani haka innawuro? Nan sukafara raba ido wannan takalli wannan wannan takalli wannan, fateence mai tsaurin idon magana adda jangofa yaya fahad udon warta sare shine mukaga yadace mu hada mishi xobo maimakon adda tayi musu fada sainaga ta tintsire da dariya saida tayi mai isarta suna kallonta sannan ta tsagaita ta kallesu lallai kunan anyi shashashu, shi yariman gombe ne kukesaka rai xaisha wannan kwadon naku? Suka kalli juna 1time fuskar fatee ta canja a ah fa adda a,a. Ni banaso ai dole yashashi wlh kinsan wahalar damukasha kafin muhada wannan? Har bashin cola fa mukaciyo Kuma ma ko yariman inane ai nan ne asalinsa kuma nidashi duk dayani xariya daya shi ya,isama yace baxai shaba? Hmmmm inji innawuro wlh daya gama wulaqanta mu, adda tayi murmushi tace to Allah yasa yasha din Sai alokacin tayi murmushi yawwa adda abinda yadace muji daga gareki kenan Sannan ta kalli innawuro yar,uwa nixantafi gida yamma tayi kixo gobe da sassafe muhada alale kinji tace to Allah yakaimu gobe lfy tarakata har qofar gidan sannan tajuya Itakuwa tana kaiwa daf da qofar idonta yasauka akaj wata kynama taketa xarya a qofar, aikuwa sainaga tayi murmushi sannan taqwalla ihu ta fadi qasa can gefe da kunamar, tayita kwarara uban ihu wayyo ni Allah wayyo qafana jama,a kutaimakeni kunama ya cijeni wayyo qafana, tadinga birgma a qasa da gudu yaya bashir yafito ke lfy tana riqeda qafar tana wutsil wutsil ta nuna mishi kunamar da sauri yadaga wani makeken dutse dake gefe ya maka mata saida ta fashe ta nanike a gurin sannaj yadawo kan fatee sannu fateema taso mushiga gidan aikuwa saitaqara fashewa da kuka nibaxan iyaba qafata xata cire wayyo Kafin yayi magana sukaji kaganar baffansu malam aqofar gidan daga ciki yana cewa to ka dakkota mana bashir yaya bashir ya sunkuya ya tallabeta daqyar yasabata a kafada kasancewar shi lauqa lauqa bawani jikine dashiba malam yajuya suka bishi abaya fateema kuwa dariyace taso ta kubuce mata amma saita gintse tahau dukan bayan yaya bashir da dukkan qarfinta wayyo xafi wayyo qafana nidai ka saukeni qafata xata fadi haka suka isa a qofar inda goggo ke xaune akan taburma ta matsa gefe yasauke fateema akai saboda qaqaro kukan dole datakeyi hartayi gumi sharaf afuska da jikinta kamar dagaske kunamar ta cijeta nan malam yahau yimata kamu sukuma sunabinta da sannu tayi lamo akan ciyar goggo qafar kuma tadora akan cinyar yaya, aranta kuwa sai qyalqyala dariya take dayiwa kanta kirari saini fatee fatar wayau mahassadana fadawa na, hhhahhh dayanxu ance a dakeni 😉 *washe gari da asuba* Lah yaya fahad yaushe ka iso? Qayataccen murmushinnan nashi ya badeta dashi wlh yanxu naxo qanwata yaki k? Lfy qalau toyasu yayabaffa da umma? Yace lfynsu qlau sannan yabita da wani kallo fateen goggo angirma fa yanxunkam sai maganar aure ko? Tayi murmushi tayiqasa da Kanta wai adole taji kunya yaqara murmushi. Kunyarki na qara xaburar da xuciyata ga kuradin aurenki yanxun mekikace ? Meye ra ayinki akan maganar ? Zaki aureni? Ahankali tadago idonta taxubasu anashi fuskarta daukeda ni,imtaccen murmshi xatayi magana kenan taji muryar goggo ke fatee fatee haba mana fateema kitashi kiyi salla tareda kowa Firgigit ta farka gani kanta kwance bisa lfiyayyar katifar tata, yasa ta tabbatarwa kanta abunda ya farunnan mafarki ne, goggo takalleta tace to ya qafar taki tayi saiqi? Wani irin haushi taji ya lillibeta eh da sauqi, to Allah yaqara sauqin, tajuya tafita Itakuma ta sauke ajiyar xuciya wayyo yaya fahad inasonka............. Yarima fahad dake riqeda trolley dinshi yana shirin shiga motar daxata kaishi airport baisan sanda yasaki jakarba domin sautin kiran dayaji yadaki kunnenshi da wannan sababbiyar muryar *yaya fahad* 👉 *nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•16/20•* . Sonia dake maqale a gefenshi takalleshi cikeda mamaki what's wrong with you Prince? Shiru yayi nayan daqiqu batareda yayi maganaba yaduqa yadauki trolley din yasaka a motar sannan yajuyo gareta all my problem is u Sonia I don't want miss u anymore ya marairaice fuska duk da cewa itama tanacikin damuwar amma saita danne tata taqara fuskantarshi hannunta sarqe fanashi tashafa gefen guskarshi u ar main Prince and I am urs , whenever u ar I know I will be in ur heart as u ar, in my on heart Qarajanta yayi yamata kyakkyawar runguma sannan yasauke numfashi I love you Sonia ! Love you too my Prince taqara qanqameshi hawayen dake idonta suka fara kwarara tafara sheshsheqar kuka ahankali yafara bubbuga bayanta dasigar rarrashi don't worry my angel I will be back very soon dear OK? I can't miss u 4 3months I can't, yakaimata kiss a baki lokacinda ya raba jikinshi da nata ta kalleshi cikin ido Prince I don't know how to live with out you. Yakai hannu yashare hawayen nata baisan ya akayiba yanajin Sonia harcikin ranshi itadin dabance da duk wata budurwar da yataba mu.amila da ita bandir din dollars naga yadamqa mata guda biyu take care, baijira komaiba yashige motar Dan kallon hawayen Sonia na Dada karyar mishi da xuciya dama driver yana ciki tayarwa kawai yayi suka tafi Sonia tabi bayan motar da kallo tabbas Rayuwa ba Prince baxata mata dadiba jiki a sanyaye takoma cikin Gidan dama anan xataci gaba da xama harya dawo tunda Gidan da yan.aiki *gombe state international airport* Mai martaba ne dakansa tareda rakiyar fadawansa da xugar motoci sukaxo tarbar yarima fahad a brnin gombe Basufi mintuna biyar datsayuwa ba jirgin ya sauka inda ahankali passenger's dindake cikinshi sukafara fitowa har akaxokan kyakkyawan matashin Wanda yatara abubuwan alfahari dayawan gaske nafarko yarima kyakkyawane na bugawa a jarida, ga isa da qasaita ga kudi ga mulki sanye yakeda sweats yayi red nic dinshi fari haka takalmin qafarshi yayi kyau sosai fuskarnan na daukeda wannan murmushin nashi sumar nan ta fulanin asali tasha gyara ta kwanta sai qyalli take da daukar ido Farin ciki ya lullube mai martaba alokacinda yayi arbada Dan NASA shekara biyar kenan saidai suganshi a video call Dagudu fadawa suka taroshi suka karbe jakar dake hannunshi suna kwasar gaisuwa ya isa ga mahaifinahi sannan ne shima yaxube qasa yakwashi gaisuwa gun mai martaba da kecikin wadataccen farinciki ganin yanda yaron nashi ya girma ayanxu yarima yakai cikakken namiji Yadago yaron yarungumeshi Allah yayi maka albarka yarona , ameen babana nasameku lfy , lfy qlau yarona Daganan suka dunguma xuwa gida wato fada gidankam cikeyake tam da al umma , maxa da mata duk Wanda ka kalla xaka gano asalin farinciki sbd murnar dawowar yarima fahad, kasancewarshi mutum ne mai sanyi a garesu dayawan kyautuka Koda motocin suka tsaya tuni mutanen dake ciki sukayo waje, masha Allah kyakkyawar mace CE fara sanye cikin farar alkebba tasha ado da kuyangi Masu yawa a bayanta , gefenta kuma wata budurwace wadda baxa,a kirata kyakkyawa ba dukda tana cikin Hutu da jindadin Rayuwa itamadai shiga tayi ta alfarma balaifi Kayan dai sunyi kyau amma fa wadda tasakadin 😷 laxeera kenan laxee, yar yayar mahaifiyar yarima fahad CE, dagudu taxo tayi hogging dinsa welcome home yaya prince we miss u a lot, yayi murmushi yajanyeta daga jikinshi shima ya isa ga mahaifiyarshi yayi jogging dinta dukkansu suna murmushi welcome home son we miss you miss you too my mom Itace taja hannunshi suka shiga Gidan gabaki dayansu har mai Martaban 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan Arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•21/25•* Awani qayataccen falo mai fadi da yawan ado na hidan darauta traditional ko ina kaduba akan wata lafiyayyar darduma suka xube wadda akan laushinta har qafar mutum ke nutsewa idan yataka ta, an cika dakin da ita ba kujera ko daya sadai mamya manyan titimmai na sarakuna masu kyau da laushi Bayan sun xauna sai dukkan kuyangin sukayi waje yarage daga mai martaba sai matarsa gimbiya usaina sai yarima fahad dakuma laxeera dakeaqale a gefenshi jerin kayan abici ne dana sha agabansu kala kala laxeera ce tayi saving dinsu cikeda yanga da iyayi Bawanda yayi magana har suka kammala cin anincin wanda baqaramin dadi yayiwa yarima ba, yayi kewar abincin Hausa sosai mai martaba ne yafara magana cikin muryarnan tashi mai dadin sauraro mai tattareda hikima da mulki yace inaqara yimaka barka da xuwa my son tareda fatan kamaida hankali wajan abinda kakeyi acan yarima da kansa yake qasa yadago sosaima kuwa abbana insha Allah saikayi alfari da ilmina, masha Allah Allah yasa hakan Ameen inji mom laxeera kuwa langabe kai tayi gefe yaya Prince mekaxomin dashi saida yayi murmushinan yace abubuwa dayawa qanwata Tayi murmushi yawwa yaya na godiya nake, Mai martaba yace Allah dai yasa a tsarabar yarima bai manta da qaramar qanwarshi ta kukunba ba, Gabanshi ne yafadi damm! Sannan afili yaqaqaro murmushin daya xamemishi jiki yace taya dan,uwa xai mamta da yar,uwa rabin jikinshi kaf fa a duniyar nan namuda wasu kamarsu dangi na jini, yafadi hakan ne badan yayo mata tsarabar ba, saidan yasan mai martaba yana mutuqar jin dadi idan aka nuna soyayya ga dan,uwanshi baffa da iyalanshi, Allah yayi maka albarka cewar mai martaba Fateema ta girma xuwansu yakai uku itada baffanka kuma duk rigimarta ce take kawosu wai ita yakawota taga koda photonka ne, kai daga qarshedai saida aka bata photonka daya ta tafi dashi sannan aoasami xaman lfy Yarinyar ta damu dakai sosai Yakoma yin murmushi sannan yace Allah yaqara maka nasara haka nima na damu dasu duka nayi kewarsu sosai. A qasan xuciyarsa kuma cewa yake ai kam dole ta damu dani tunda gashinan ta hanani kwanciyar hankali badan ita jinina bace danace ko mayya ce ita Maganar mai martaba ce tadawo dashi inda yakecewa wannan yana qara amintar dakai axuciyata nuna so ga ahlina yana dada tabbatarmin cewa kaidin jini na ne, ina alfahari dakai yarima yaji dadi harcikin ranshi dan arayuwa bashida wani burin dawuce yaga ya faranta ran iyayensa musamman mai martaba wanda yafi shaquwa dashi fiyeda mahaifiyarshi domin shi yakasance mai yawan jan yaro ajiki da nuna mishi qauna da kulawa Nagode abbana badan nagaji dayawa ba da ayau xanje na gaida baffa na nayi kewarsu sosai mai martaba yaqara jindadi aranshi wanda hatta fuskarshi saida ta nuna yace bakomai yarona kabari kahuta xuwa gobe dan nasanar musu da dawowarka tun shekaran jiya, duk da bada. Xuciya daya yace xashiba amma yaji dadin farin cikin dayajefa a xuciyar mahaifin shi, Mamanshi tayi murmushi wato mu anmanta damu nida yata ko? Mai martaba yace mun isa? Mantawada uwar gida ai saidai in rai yayi halinsa, tayi murmushin jin dadi yarima ya miqe bari inshiga xanyi wanka indan huta xuwa anjima xan fito Ok afito lfy Allah yayi maka albarka ya karemin kai daga sharrin mutum dana aljan ameen ya amsa cikeda jin dadin addu,oin ya fita laxeera ta miqe dasauri tabi bayansa iyayen suka bisu da murmushi Duk inda suka gifta bayi da fadawa xubewa suke suna kwasar gaisuwa har ya isa part dinsa ko ina tsaf angyare komai an goge, yaji dadin hakan abakin gadonshi yaxauna sannan yakalleta yadai sis? Ta wani shagwabe fuska tsarabata mana yaya Prince, hmmm haba laxee saikace wata baby baxaki bari indan hutaba kinga xuwa anjima sai in baki Sanin halin yarima yasa tace ok ahuta lfy, dan tasan yatsani ayimishi musu arayuwa, saida takai qofa tajuyo ba,abinda kake buqata,? Yace bakomai sannan ta fice Shikuma yarage kayan jikinshi sannan yashige wanka *Asalin su* •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkillalove you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•26/30•* Malam usman ummar shine asalin wannan ahli kuma uba ga mai martaba sarikin gombe bello, da dan uwansa malam aliyu na kukunba, wato asalin su duka a qauyen kukunba ne na qaramar hukumar dukkum ta jihar gombe Shidai wannan qauyen garine mai dimbin tarihi da al,ajabi maxauna cikinshi kuma fulanine xalla babu bare ko wata qabila a garin duk fulani ne masu tarin arxiqi na dabbobi sosai ba dan kadan ba, kowannensu a jeji yake ajiye shanunsa domin yawansu ya wuce ayi kiwonsu gida ko qofar gida, baremma gidan malam usman umar kaf garin ba wanda yayi arxiqinsu na dabbobi dana noma wanda shine aikin mutanen garin rani da damina shidai malam usman ummar shine mai anguwar qauyen awancan lokacin yayinda baffanshi dan,uwan mahaifinshi ke sarauta a birnin gombe, ranan sai Allah yayiwa baffan nashi rasuwa kawai baxato bayan angama kwana ukun, rasuwar margayin mutane suka xowa da malam usman ummar da maganar sunyanke shawara shi xasu nada sarautar gombe sbd can cantarshi bayanda ya iya dasu haka aka nadoshi daga can koda yadawo gida mutane sukayita mamaki dukda cewa ya cancanci hakan,tunda baffan nashi bashida yaya nakanshi Nan yayiwa al,ummar kukunba nisihohi da kuma sabon shugaba daya nada musu wani attajirin bafulatani mai kirki, yayanshi maxa guda biyu kuwa bello da aliyu suna samari alokacin yayiwa kowannesu aure agidanshi na qauye yace baxaiyuwa yakoma birni dasuba al,amarin kiyo da gwanakinshi xai tabarbare yace suxauna nan da iyalansu sucigaba da kula da dukiyarsu, sannan yadauki mahaifiyarsu da rakiyarsu data mutanen gari yakoma nirnin gombe yacigaba da sarauta, yaran kan xiyarcesu lokaci xuwa lokaci Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah matar malam bello ita tafara haihuwa Allah yabata da namiji ranar suna mahaifinsu mai martaba yaxo yaradawa yaro suna fahad, sannan itama matar qanin tahaifo nata akarada mishi suna bashir Sukacigaba daxaman lfy wayannan yan,uwan malam bello da aliyu suna matuqar son junansu, saida fahad yakai shekara goma sha biyu aduniya sannan Allah yaqarawa matar malam aliyu haihuwa inda tahaifo yarta mace ce itama ranar sunanta mai martaba yaxo yarada mata suna fateema Fateema kyakkyawace ta gaban kwatance asalin gulani Allah yayi mata baiwa iri iri, saidai ita takasance irin yarannan ne masu qiriniya batajin dadi inbatayi tsokana ba kamar yanda bata yafe abu idan akamata badaidaiba saita rama haka ta taso tundaga quruciya har girma Shekarar fateema daya a duniya Allah ya yiwa mai martaba malam usman umar rasuwa dashi da matarsa asanadiyyar hatsarin mota aranar mummunan saqo yaxowa al,ummar kukunba ansha kuka babu kamar yayanshi dan sunsan sunriga da sunyi rashin da bayada kama, bayan kwana uku nan ma al,ummar fada sukayanke shawarar nada babban dansa malam bello, aka yi nadi lfy aka rakoshi sallama da yan,uwa Tun alokacin ba yanda bayyiba da dan,uwanshi akan yabiyoshi birni shi xai kawo wayanda xasu dinga oularmusu da gwanaki dakuma dabbobi, amma fir malam aliyu mahaifin fateema yaqi yace sam baxai kauce fadar mahaifinsu ba, dole ya haqura yadebi iyalinsa suka tafi, hakan baikawo tangarda ga xumuncinsu ba sukan xiyarci juna lokaci xuwa lokaci, dakomawar su yabiyawa fahad babbar makaranta anan yafara primary Aqauyen kukunba kuma ansami sauyi sosai mai martaba bello ya gina musu makarantu na primary da secondary da islamiyya, tareda xuba qwararrun malamai ya inganta musu ruwan sha, da qaramar asibiti, Gidan dan,uwansa kuma ba,abinda suka rasa najin dadin rayuwa gida maikyau ya gina musu ginin xamani yaxuba musu kayan amfani da gadaje hatta fateema dakinta daban dakuma lafiyayyar katifar ta, kayan sakawanta iri iri shiyake dinko mata daga can tun tana qaramarta har yanxu datakeda 15years Soyayya ta xahiri da badini yakewa dan,uwansa da jama,ar qauyensa, yarima fahad kuwa tunda yabar qauye rayuwar birni ta shigeshi yamanta da qauye kuma yatsaneshi dole yake xuwa badan yanasoba, Kawai dan mahaifinsa yaji dadi haka mahaifiyarsa dake itama iyayenta sun rasu yarage daga ita sai yar,uwarta itama abirnin gomben take Auren wani mai kudi itace mahaifiyar laxeera umman yarima tace tadawo Gidan ne a wannan dawowar daxaiyi koxasu daidaita yasota Dan taji maimartaba na maganar yimishi aure wannan xuwan nashi . *wannan kenan* . 👉 *nasmy CE*😍. Yar mutan Arkilla love you all😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•31/35•* *Cigaban labari* _washe gari_ Aqauyen kukunba malam ne dakanshi yaketa fama da fateema da innawuro ta biyomata suje makarantar boko Amma fir tace ita baxataba dan kar yaya fahad yaxo har yatafi basu dawoba, tunda baixo jiyaba to tasan dole yau xaixo, kinaji autan goggo tashi kitafi inyaxo nidakaina xan tura bashir yakiraki kinji Shiru taqarayi shimadai shurun yayi dan yafara quluwa gashi ance test sukeyi a makarantar, haryadago daxafinshi saita rigashi magana baffa awadi alkawal tu,awari anoddayam? Tayi tambayar kamar xatayi kuka, Allah sarki saita bashi tausayi wannan yariyar lallai tadamu da fahad sosai take qaunarshi, dan,uwa mai dadi Allah yasa kudore haka, Saida yatausasa murya tukun yace eh nayi alqawari xansa akirakin. Idan yaxo din, sannaj tamiqe a sabule tashiga dakinta ta canxo kayainta xuwa uniform masha Allah kayan sun mata kyau sosai darkgreen colours ne riga da wando sai dan matsakaicin hijab dinta fari, fuskarnan fayau babu digon kwalliya wannan dabi,arta ce batasanyin kwalliya tace to muntafi kumana addu,a test mukeyi wanda dagashi sai final exam, baffa yai murmushi Allah yabada as,a fatee ainasaj kinada qoqari saidai inkinsaka shashancinki. Dan malamanku nagayamin kinada qoqari sosai maida hankaline nakyayi Batace komaiba taja hannun innawuro suka fice, giggo tai murmushi kaga waitayi fushi sukayi dariya yace fateen kenan ai nibansan inatadakko wannan halinna badamar amata magana saita sille wai tayi fushi bari inatashi inkira bashir yaqara gyara babban dakincan kekuma dunda ta tafi tashi kidora kinsan tafiyar wuri sukeyi kuma tareda yaya xasuxo tace to ta miqe tanufi madafinsu shikuma yafita Qarfe goma darabi angaka komai anshare ko ina, gidan yayi fess dashi sai qamshin turarukan wuta ketashi goggo nagani tanufi dakin waje na saukar baqi da qaton tray itamadai ya cancana adonta daidai gwargwado Qarfe shadaya motocin gidan sarki sukafara parking a qofar gidan mota uku daya yarima ne da mai martaba, sai driver sunyi kyau sosai dukkaninsu suna sanyeda kaya na gidan sarauta na alfarma, sauran kotoci biyun kuma duk yan rakiyane da fadawa Malam aliyu naxaune aqofar gidan yataso dasauri yagaida sarki cikeda girmamawa shikuwa mai martaba farincikin ganin dan,uwan nashi yaqi boyuwa fuskarnan faran faran yarungumi qaninshi nayi kewarka dan,uwana fadawama sukafara miqa gaisuwa, saida suka gama tukun yarma ya isa garesu harqasa yatsuguna gaban baffa yana gaisheshi baffa yadagoshi yamiqar dashi alokacinda yake amsa gaisuwar masha Allah, yaronmu shima ya girma ixuwa babban mutum, dai dai lokacinne hashir ya iso wajan dasallama yaje ya suguna yayi gaisuwa a gaban sarki mai martaba ya jashi xuwa jikinshi yawwa yarona yakake ina yar,uwarka? Yakalli baffa banga yata ba, wadda kullum naxo ita nake fara gani? Baffa yace ta tafi makaranta kai bashir jeka kirata bata tafiba saida tasa nayimata alqawari xankirata in yayanta yaxo, damn! Gabanshi yayi mummunar faduwa danyanxu yagano wadda suke magana, yarinyarda take takurashi tahanashi saqat aduk sanda yashigo garin daqyar yake rabuwa da ita, jiyayi ana cewa yarona shigo daga ciki mana saida yadan xabura koda yadago saiyaga kowa yaqarasa cikin dakin baqi da aka. Bude musu saishi kadai awaje Qasa qasa yai tsaki sannan yaqarasa ciki shima yanemi guri yaxauna goggo tashiga suka gaisa sannan ta gabatar musu da abinci da abinsha tafita suka bubbude abincin balaifi anyi tsari maikyau tuwan sakwarane da miyar agushi mai wadataccen kifi, sai lemuka da aka siyo musu Suka faraci suna dan taba hira, ankaiwa fadawa nasu awaje Dagudu tashigo dakin bbu ko sallama saidata taka qafar yarima ta wuce ta isa ga mai martaba data gani kusada baffanta, tafada kanshi kamar qaramar yarinya wayyo Allah yayabaffa, ina yayana yake? Inadai tare kukaxo? Haushi ya tirniqe fahad amma shi mai martaba sai murmushi yake yashafa kanta Allah yayi miki albarka yata taremuke gashinan bayanki sai a lokacin tajuya idonta yasauka akan kyakkyawar fuskarshi wani mahaukacin ihu tatsala takuwa yo kan yarima dagudu 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•36/40•* Jiyayi kamar yayi waje kafinta iso gareshi amma ina badamaryin hakan dole yagyara karbarta karta fadar dashi, aikuwa jikinshi tafada da qarfi ta qanqameshi kai yaya fahad lale lale barkada dawowa Murmushin dole ya qaqabo sannan ya dagata yaxaunar da,ita gefe yakama hannunta yariqe a nashi barkadai qanwata nasameku lfy? Lfy qlau saidai kewarka wlh ba dadi tsayin shekarun nan da bakanan kullum sainaji kamar inbika gabaki daya iyayan sukayi dariya mai martaba yace dan,uwa kenan mai dadi, da yardar Allah kune xaku gajemu dan lura kunadan junanku kaman yanda mukesonjunanku nida dan,uwana, sukayi murmushi dai dai lokacinda fadawa suka yiwa mai unguwar qauyen da yan rakiyarsa iso sunxo su gaida sarki, fateema ta kalli fahad yaya taso muje mudan xaga gari mana kafun su gaisa nafayi kewarka sosai. Jiyayi kaman ya falla mata mari tsabar ta rainashi wai suxaga gari kaman wani sa,anta jinyayi shiru yasa malam cewa haba fatee yanxu daxuwan mutum ko hutawa baiyi ba, mai martaba ya karbi maganar dacewa hutawa saikace wanda yaxo da qafa? Yarima dai baice komaiba yamiqe hannunshi nariqe da nata. Haka yabita cuciyarshi na quna suka fita, kai tsaye hanyar makarantar bokonsu tadauka tanata xuba mishi surutu kamar parrot, iyakacinshi eh kokuma to sai murmushin dole, Cikin makarantar suka shiga yakalleta mekuma xamuyi a school? Ta washe baki xaku gaisa da qawatane dakuma malaman mu, yai murmushi daganan kuma inbinciki kqratunki inkinayi da oyauba, ta qyalqyale da dariya Allah kabincika lbr mai dadi xakaji dan kaf a makarantar nan babu kamar fateema aliyu, tafada cikeda alfahari abinda yabawa fahad dariya yakuwa dan dara kadan Daidai nan kuka suka iso qofar wani aji Tundaga qofar take raraka mata kira innawuro! Innawuro!! Itamadai kaman aiiraye take fit saigata gabansu yawwa qawata ga yayana yaxo innawuro ta rusuna tagaisheshi cikeda girmamawa ya amsa da fara,a yakuke ya karatun tace alhmdullh yace good, ya kalli fatee nan ne class dinku? Tace eh yaduba saman qofar nan yaga s,s,3a madallah kudage da karatu sosai tunda yanxun kuna final year kunji suka amsa da to atare, yakalleta yanxu kuma sai ina? Tace rafi inaso mutafi rafi murmushi kawai yayi baice komaiba ya saka hannu aljihu yaciro kudi yan 1k masu dan dama yabawa innawuro ganin kudin kadai saida yatsorata ta tagirgixakai tace a a nagode takoma aji aranshi yace qauyanci bayyiba, yamayarda kudinshi yaja hannun fatee suka fita school din, Hanyarma sai xuba take suka isa rafi mutanen qauyene samari da yanmata cikeda gurin wasu suna wanki wasu kuma suna wanka a nakin gulbin. Yarima yayi mamakin kawoshi nan datayi dayake kusan duk wanda ke gun yasanshi haka suka ringa daga hannu suna gaisheshi yana amsawa kawai danshi baimasan wasun ba Fatee kuwa saitahau raba ido da,alama wani take nema aikuwa ta hangoshi duqe yana wanki inusa wani saurayi daya taba neman auranta takoreshi kamar yanda tasaba korar sauran saidaishi saida yatsaya ya gaggaya mata magana kusan shekara dayafa amma fatee bata mantaba shine yau taxo ta rama ko ince tamaida martani, shikuwa yarima baisan abinda keranba taja hannunshi bimta kawai yake. Har suka isa bayan inusa dake duqe hannu tasaka ta finciko rigarshi yaxabura adan tsorace yamiqe tsaye ganin fatee da yariman gombe yaqara tsoratashi domin tuna abinda yafaru tsakanin su Gyara tsayuwa tayi taqanqance idanu irin xa,ayi rashin m, tabishi da wani irin kallo na raini inusa gunka naxo shin xaka iya tuna abinda kagaymin abaya kusan shekara daya data wuce? Toyau ranar maida martani taxo inafata daikagane wannan yaya fahad ne dan uwanyariman gombe wanda na gayamaka takalminshi ma yafiminkai afannin so, xaka iya tuna mekace min awaccan ranar? Tobarini intuna maka cewa kai wai koda dan,uwana ne ba,abinda xaiyi dani wai baxai soni ballamtani yakai ga aurena togashiyau agabanka nakawoshi yagaya maka dabakinshi matsayina dana soyayyata gareshi,,, takalli fahad yaya kasanar da wannan yaron cewa ni takace mallakinka kuma kai nawane mijina haskena jagora natafida rayuwata tundaga tashina har girmana kaikadai nakewa kallon namiji daya cancanci yaxama mijina Daga inusa har yariman bawanda yayi magana gabaki daya hankalin mutanen yadawo kansu yarima yafada tunani taredayin danasanin biyota da yayi, ashe haka yarinyarnan take? Yanxun.............. yaxaiyi? Yakalli mutanen dake gun yagaduksu suke kallo sannan yamaida kallonshi ga inusa......................... 👉 *Masmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•41/45•* Cikin murya mai sanyi yace kayi haquri abokina fateema tawace matata uwar yayana, ka kiyaye gaba dan bataran faeema xai iya haifar maka da damuwa, yanagama fadin hakan yaja hannunta sukabar wajan akabisu sa kallo sunburge kowa agun fateema dadi kamar ya kasheta Shikuwa fahad yafadi hakanne dan karya kunyata yar,uwarshi tajini a cikin mutane amma bandashi ai inusan gaskiya yafada inadhi ina auren fateema? Qaramar yarinya yar qauye ranshi yayi bala,in baci da abinda tayi kuma tasakashi yayi yanxun wato qarya abunda ba halinshi bane sam Sunyi nisa sosai ba tsammani taji ya fixge hannunshi dake riqe da nata dasauri ta kalleshi kafintayi magana taji saukar wani lafiyayyen mari a kuncinta wanda ya tilasta mata dafe wajan saidai bata yi yunqurin kukaba dan tsananin mamakin daya tirniqeta wai yaya fahad ne ya mareta, Cikin tsananin fushi yafara magana bakida hankaline wane irin qurciya ne dake? What's nonsense is that? Tayaya nixan aureki ni sa,ankine kokinga mun dace dake? Luck dagayau kar insakejin kalmar sona daga bakinki, karkisake wani yakomajin hakan kisoni amatsayin dan,uwanki mahaukaciya kawai gashi kinsaka nayi qarya dan karemiki mutincinki, xan iyafadar hakannan amma kisani baxan taba iya auranki ba, Marin da yarima yayi mata kokadan baikaimata xafin kalaman bakinshi garetaba, tsananin rudani da tashin hankali tashiga take xuciyarta tayi rauni hawaye sukafara bin kuncinta, taya rayuwa xata xomata tahaka? Itakanta batasan tsawan lokacinda tadauka tana renon son yarima aranta ba, kuma ba ita tasakama kanta ba, kawai tatsinci kanta acikinshi dumu2 taqara kallon yarima taga irin kallon tsanar dayake mata hankalinta yaqara tashi kuka ya awace mata tasaka hannu ta toshe bakinta tafara jada baya dagudu yaga tajuya takoma inda suka fito saidai ba hanyar rafi tabi ba, tagefenta ta dauka yabita da kallo dan yama rasa mexai cemata yadanjima tsaye agun kafun ya kada kai yawuce yanufi gida, Fateema kuwa can cikin jeji tatafi wata gwana mai ni,ima gwanarsuce wadda take kusana rafi hakan yasaka wajan yayi sanyi sosai cikin inuwar mangwaro ta xauna qwaqwalwarta na tariyo mata abinda yarima ya gayamata kukatayi sosai saida tagaji dankanta tayi bacci agun Yarima na karya kwanar gidan gabanshi yqyi mummunar faduwa tunawar dayayi xa,a tambayeshi ina fateema mexaice? Yaji kaman yakoma ya nemota saikuma yaji baxai iyaba dantafiyar dasukayin nan duk ya gaji ga rana tafara xafi agefe daya kuma yanajin haushin yarinyar Yarda ko secondary bata iyarba wai hartasan wani abu SO harmada maganar aure mtsww yaja tsaki shi inbanda igiyar xumunci tama isa ta fuskanceshi balle tamishi irin wannan shirmen Da ire iren wayannan tunanukan ya isa gidan yai sallam dukkansu sunanan indayabarsu sunata hira da mutanen mai unguwa dasukaxo yanemi guri yaxauna bayan yayi musu sannu iyayen suka kalleshi lokaci daya mai martabane ya tambayeshi ina yata? Gabanshi yabada rass! Amma dayake namijine saiya dake ahankali yace wannan yar taka dukta gajiyar dani har rafi takaini sukayi murmushi. Sannan yace acan nabarta dawasu yara nafuskanci shiririta tamata yawa Baffa yace aihaka take fateema kam tafida hakama dagangan kabita sukaci gabada hira har yamma salla kadai ketashinsu suyi sudawo harsuka fara shirin tafiya shirudai ba lbrn fateema Yarima yafi kowa damuwa dahakan tunaninshi kar wani abu yasameta tunda jeji ta nufa gashi kuma tare suka fitadashi Fateema kuwa anayin sallar axahar tafarka dawani irin xaxxafan xaxxabi wanda bata tabajin irinsaba daqyar ta iya kaikanta gidansu innawuro acan ta kwanta inda adda tayita tambayarta kolaifi tayi aka daketa agidan tacemata a,a innawuro kuwa duk hankalinta ya tashi ganin qawarta acikin wannan yanayin Gashi xamutafi amma haryanxu fateema bata dawoba inji mai martaba baffa cikin damuwa yace to allah dai yasa lfy danni hankalina yafara tashi kasancewar tasan kuna nan mawuyacin abune taxauna wani gurin haryanxu bata dawoba indai tana lfy Yayan cikin yarima suka kada hankalinshi ya qara tashi yaya bashir yace bari inje in dubata wajan ina kabarta bros? 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•46/50•* Yayi maganar lokacin da yake miqewa tsaye yarima ya diririce amma sbd gudun xargi saiya dake ya boye tashin hankalinshi yaceda bashir bari intashi muje tare yafadi hakan ne dan bashida amsar daxai bashi axuciyarshi kuwa cewa yake to yanxu ina xai nuna? Can mana inda kaga tabi inji cuciyarsa, suka fita dakin ajere saidai kafin sufita barandar gidan suka hango inna wuro tariqo fateema irin yanda suke tafiya kaidagani kasan na lfy ba, sukaja suka tsaya cikeda makaki sunajiran isowarsu qirjin yarima yahau dukan tara tara addu,a yake aranshi Allah yafiddashi indai ba wani abu yasami yarinyarnan ba acan jejin kar axo a xargeshi Suka iso barandar innawuro tayi sallama suka amsa tare suka hada baki wajan tambayar meyasameta? Bata amsasuba saida taxaunar da fateema tukunna kafun tace wani abu tuni baffa da mai martaba dake ciki suna hangesu sun fito waje sumadai tambayar daya ce meyasameta? Tace wlh tunda rana take gidanmu da xaxxafan xaxxabi shine mukaga yamma tayi adda tace inkawota gida dukda tasha magani amma haryanxu xaxxabin bai saukaba Fuskokinsu cikeda damuwa baffa yace fatee meke damunki? Tayi shiru jikinta sai rawar sanyi yake, mai martaba ya isa gareta yadagata yace yata kohebuma? Meyasameki? Gayamin mana meke damunki Hankalin fahad yaqara tashi cikeda tashin hankali shima ya matsa kusada ita yakama hannunta qamwata meyasameki ne? Kiyi magana mana fateema da koganin yariman batasanyi tajuyarda kanta gefe sannan tafara magana............................. Xaxxabine dama tunjiya yafara mun shine naje rafi nayi wanka shikenan saiya tasomin haka, tana maganar haqwaranta na haduwa sbd sanyi datakeji baffa yafara fada kedai wato baxa,a rabaki da abin asshaba har yaushe yarinya kina girma kinacin qasa kinsan kinada xaxxabi amma baki sanarda kowaba bayan haka kuma kikaje kikashiga ruwa Mai martana yace haba kaikuma bafada xakaimata ba addu,a xakayi wanda yake cikin wannan halin xakamq fada to dawanne xataji? Yafadi hakanne lokacinda yaga hawaye nabin kuncin fateema Allah sarki yarima aj nutsu yakasa koda magana dan yatabbatar da abinda tafada ba gaskiya bane yasan abinda yayi matane yasakata damuwa da kuka har xaxxabin ya rufeta. Sosai yarinyar tabashi tausayi saiyaji abinda yayi matadin sam baikamata ba, dayasani da lallabata yayi da nasiha ya ganar da ita kuskurenta, Maganar mai martabace ta dawo dashi daga tunanin dayake indayaji yana cewa axoda mota akaita asibitin dake garin nandanan akadauko motar suka shiga sudukan innawuro ce ta riqata amotar ma bisa jikinta take sai xubar qwalla take aminiyar tata ta tausaya mata ainun yaya bashir na gefe sai sannu yake mata harsuka isa asibitin Dagaggawa akashigarda ita danganin wayanda ke tafe da ita, sosai likitan yayi bincike akanta tareda yimata yan,tambayoyi tanabashi amsa, saboda tsananin xaxxabi da xafin jiki yajona mata drip, qaramar gora tareda wasu allurai guda uku take bacci ya dauketa likitan yabuqaci abarta ta huta kowayayi waje banda yarima acan wani bare na xuciyarshi tausayin yarimyar yakeji dan aganinshi shine mysabbabin ciwon nata Yaqara matsawa gaban gadon yaja kujera yaxauna a gabanta yaxuba mata ido tunda yake baitaba yimata kallon tsaf haka ba, baccitake amma fuskarta kamar tana murmushi yan qananan pink lips dinta manne da juna haka yalwataccen gashin idonta ya kwanta lip lip kamaryanda nagirartama yake baqi sidik. Ga gashin kanta maikyau da silbi nafulanin asali dukda kanta da dankwali amma xaka iya gane manyan kitsone akan nata, danga jelarsunan kwance akan pilon datake kai kai dagani kasan akwai wadataccen gashi fuskarta kam gwanin sha awa kamar kar kadauke ido akanta Yadda yanayin jikinta yake yanuna nangaba idan taqara girma xatayi dan tsayi da jiki mai kyau, saiya tsinci kansa da murmushi alokacida idonshi yakai qirjinta dominkuwa yan madai daitan nafulaninta yagani kusan rabinsu duk awaje farare sol dasu gwaninsha,awa sunyi luhu luhu tsaitsaye ahakanma basu gama cikana Dasauri Yadauke kanshi yamayar gefe dan gudun faruwar wani bu yasan xuciya xata iya rayamishi yataba dansun burgeshi sosai Wata xuciyarshi ce tace to bandama xuwan lokaci ina wannan yarinyar tasan So dahar ta isa shan wahalarshi? 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•51/55•* Mai martaba ne tadawo dakin da sallama ganin yanda yarima yaxauna agaban fateema cikeda damuwa yaqara tabbatar mishi da irin son dayake hange akwai atsakanin yaran nasu axuciyarshi yayi hamdala yagodewa Allah. Dawannan hadan yake kyautata xatan xumumcinsu xai qara qarfi da dorewa kobayan ransu Ya isa gareshi yadan bubbuga kafadarshi karkadamu yarona in Allah ya yarda xata sami lfy likitan yace data tashi xata tashi da qwarin jiki insha Allah, kaxo mutafi karmuyi tafiyar dare Batareda yace komaiba yamiqe yabi bayan mahaifinshi axuciyarshi yanayiwa yar,uwarshi fatan samun lfy, awajam sukaiyi sallamq dasu baffa a gaggauce nasukoma gidanba dan yamma tayi sosai yasa aka kira wayar sauran motocin dake can yace su shigar dakayan tsarana cikin gida suxo su sakesu anan dayake bakin hanya asinitin take bajimawa sai gasu suka qarayin sallama tareda yiwa fateema addu,ar samun sauqi suka wuce gida Baffa yace yaya bashir ya tsaya gunta shixai koma yasanarwa goggo itakuka innawuro taxo ta wuce gida kar dare yayimata anan, badan tasoba haka tabi bayan baffa suka koma cikin unguwar Bayan sallar magariba yadawo tareda goggo harxuwa lokacin fateema bata farkaba bashir na xaune a gefenta yadawo daga masallaci, goggo taji tsoro yanda taga yar tata ko kotsi batayi ga ruwan da aka saka mata nandanan tafara sharar qwalla ta isa ga fateema yarta daya mace da Allah yabata addu,a sosai tayimata ta tottofa mata ajiki alokacinne aka fara kiran sallaf isha baffa da yaya suka tafi masallaci goggo kuma tayo alwala tagabatar da sallar anan Qarfe goman dare fateema ta farka alhamdllh jikin yayi dan qarfi saidai bata dainajin xigi da radadin kalaman yaya fahad a xuciyarta ba amma batayarda ta gayawa kowa ba,tabarwa Allah lamuranta kafin wa,adin mutuwarta yaxo dan ayanda takeji indai babu fahad arayuwarta tokuwa mutuwa xatayi, tayi qoqarin danne damuwarta dan kwantar da hankalin iyayenta ta nuna taji sauqi Likitan yabasu sallama tareda magungunan daxata rinqa sha safe a yamma, haka suka lallaba suka koma gida cikin duhun dare a dakinta aka ajiyeta sai sannu ssuke mata tana murmushin yaqe ainaji sauqi ba abunda kemin ciwo, sukaja mata qofar kowa ya nufi nashi dakin domin yin bacci Fateema kam naccin ko kusada ita bai rabo ba tashi tayi tafita tayo wanka tadauro alwala sannan tadawo dakinta tafara rankon sallolinda natayi ba, tanayi idonta na xubda hawaye data kammala saita dora da nafila rak,a biyu tayita roqon Allah akan damuwarta Da takammala sai takoma kan katifarta harxuwa lokacin hawaye basu yanke a idontaba, gefen katifar naga ta cusa hannunta ta dauko wani dan madaidaicin hoton yarima na katako ne irin laminated dinnan yayi kyau sosai kamar yayi magana ta qurawa photon ido tana xubda qwalla A,ah dan,uwana abunda kamun sam baidace ba, yayana ina sonka sonda bantabayiwa kowa irinshiba wlh bani nasakawa kaina ba, nimajinshi kawai nake a xuciyata ina qaunarka kuma kasani nasadaukar da rayuwata ga soyayyarka baxan taba daina sonkaba kodai xaixamo dalilin mutuwata ina sonka Ta rungume photon tacigaba da rera kukanta qasa qasa 👉. *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•56/60•* Har gariya waye fateema bata runtsaba idonnan nata sunyi suntum sun kumbura harsunba fuska daqyar tayi sallar asuba takoma ta kwanta qarfe shidda gaggo tashigo dakin a ah fatee a ummaki juludaha joni? Dataga mayafin data rufu murya a dusashe tace nayi salla tindaxu Ayya to sannu yajikin naki? Dasauqi tafada tana maida mayafin a fuskarta goggo taqarasa ta yaye mayafin ganin yanda fuskar yartata takumbura tayi jajir ya tsoratata fatee xaxxabin ne yadawo? Batada xabi shiyasa tace eh jiya da dare ne ciwon kai yatashi amma meyasa baki kirani ba? Bakomai ainaji sauqi tafada da dan qarfi qarfi danta kwantarda hankalin goggon Dai dai lokacin baffa da ya bashir suka shigo sumadai sun damu da yanda fateen takoma lokaci daya dukta canja sukayi mata sannu ta amsa sunashirin fita wayar baffa tayi qara yadaga da sallama ah Allah yataimakeka kun isa gida lfy bamuji me akace a dayan nangarenba nadaiji yace eh dasauqi to tunjiya da dare kukadawo gida ai, to to yace sannan ya miqawa fateema wayar sallam tayi da disheshiyar muryarta ya amsa mai martaba ne, tagaisheshi ya amsa tareda tambayarta ya lfyr jikinta mai makon tabashi amsa saikawai ta fasheda kuka, al,amarida yadada daga hankalin mai martaba kiyi haquri yata wai meyake miki ciwo ne? Yishiru ki gayamin kinji? Itakanta batasan daliliba amma takasa barin kukan saida baffa yakarbe wayar tomeye haka kenan daga tambayar lfyrki sqi kuka ina yanxu kikace mana kinji sauqi, ya dora wayar akunnenshi inajinka yaya Mai martaba yace kuhada mata kayanta anjima xan turo dan,uwanta ya daukota akaita asibitin nan garin koxaifi nacan din to allah yakaimu Allah yabar xuminci yadada girma da daukaka mai martaba ya katse wayar xuciyarshi cikeda damuwa Yafara kiran layin fahad wanda alokacin yake hanyar xuwa turakar mahaifin nashi domin ya gaisheshi, yadaga wayar da sallama yace yarona kana ina? Ina hanyar xuwa wajanka abbana to shikenan bari kaxo din ya katse wayar Da isarshi kuwa bayan sun gaisa mai martaba yasanar dashi buqatarshi tayaje kukunba yadauko fateema akaita asibiti anan yace Allah yakaimu yatashi yafita xuciyarshi cikeda tunanika barkatai shida yake shirin fita garin yau koxai sami dai dai dashi da agaskiya kwana biyunnan haqurinshi yafara gaxawa yanada buqatar mace jiyamadaqyar yayi bacci Qarfe goma shabiyu yarima da yan rakiyarsa fadawa suka isa gidan angama shirya mata komai goggo harda kukanta tanatayi maata addu,a bayan sungama gaisawa yace afitoda ita sam fateema batayi wani farincikin gqninshiba goggo ce ta riqota fuskarta yakalla sqidaya tsorata ganin yanda ta kumbure suntum shidagani yasan kuka tasha bawani ciyoba yayi mata sannu ta amsa batareda ta kalli inda yakeba, Nanfa goggo taqara tsorata da wannaj ciwon na fatee tabbas. Baqaramin ciwo bane ace ga yarima gabanta amma ko kallon inda yake batayiba Hakadai tariqota har bakin motar aka bude ta sakata abaya yarima ma. Yaxaga yashiga sukatafi baffa ne yani goggo da rarrashi aiciwo ba mutuwaba addu,a yakamata muyi mata ba kukaba, Qarfe daya suka isa gombe kaitsaye memorial prvt hospital ya nufa da ita asibityn families dinsi kenan daxuwa aka shigarda ita bayan yan gwaje gwaje likita yakira yarima xuwa office dinshi yagaya mishi qanwarshi fa daftake da kamuwa da ciwon xuciya saida yadan firgita doctor for what? Likitan yace bansaniba amma dai damuwar axuciyarta ne ba mamaki akwai aninda takeso bata sameshina ko kuma bataso ake takurata cikin biyunan dai dole akwai daya sbd haka maganinta badaga garemu yakeba kune xaku gyara inkuma bakusan damuwarta ba toku tambayeta tasanar daku sannan kuyi qoqari da gaggawar sadata da abinda takeso kafin wannan muunan abin yasameta, Yarima ya gama rikicew ya diririce yarasa abinda xaice da dr miqewa yayi yafita yakoma dakinda fateen take xuciyarshi cikeda rudani wannan wacce irin masiface? Yarinya qarama tadauki damuwa ta dorawa rayuwarta yanxu idan takamu da ciwon xuciya tadalilinshi in abbanshi yasani yaxayyi kenan? Bashakka xai tsaneshi Innalillahi 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•61/65•* Tana xaune abakin gadon inda likita yabarta qofa take kallo qkma yana shiga dakin ta dauke kanta tamayar gefe, abinda yanashi haushi kenan wato batama son ganinshi kenan? Lallai yarinyarna wato shibaiji haushintaba itace xataji haushinshi uhum Batareda ya kalletaba yace mata tashi mutafi, baijirata miqeba yayi waje wani irin qololon baqin cikine yatokare wa fateema a maqogwaro tamiqe daqyar tanabin jikin bango harta fita a mota tasameshi sai shan qamshi yake kamar wanda akama wani abu, aka bude mata motar tashiga driver yatayar suka tafi cikin qasaitar nan tashi yaceda driver xamu sayi magani a venga pharmacy, ok sir driver ya amsa cikeda ladabi suka faka a wani makeken pharmacy nan yafita ya siyo dukkanin magungunan da likita ya rubuta mata Da isarsu gidan yafice yayi cikin gida yabarta a motar ahankali ta tako qafarta ta fito daqyar take takawa saidai xuciyarta tagama yanke hukunci akan yarima tafe taje tana cixon lebe, hmmm kawai baisan fatee Bane jina yakeyi wlh dan kawai banida lfy ne amma bari in warke xan nunamishi asalin kala ta, duk a xuciyarta take wayannan maganganun lokacinda take tafiya xuwa cikin gidan sarautar Dayake tasan gidan sosai da mutanen cikinshi suma sun santa tana tafe suna gaisawa da hadiman gidan harta isa sashen gimbiya umman yarima kenan akayimata iso umma tace tajirata anan tana xuwa Takai 20mins bata fitoba dukda angaya mata wadda taxo din can fateema harta fara gyajgyadi tafito cikin takunta na isa da qasaita laxeera na biyeda ita dawasu damammun kaya riga da sket kanta ka dankwali babu, suka iso falon yayinda umma ta hakimce akan doguwar kujera laxeera kuma taxauna a qaramar kujerar dake gefenta fateema tadan xame daga kan kujerar tagaida umman ta amsa da dan kulawa hartana tambayarta su goggo ta amsa mata da lfyrsu qlau, Tace akace bakida lfy keyake daminki? San danki xuciyarta tafada a gajarce, afili kuwa cewa tayi eh wlh yanxunma daga asibiti muke amma da sauqi Laxeera dakejin haushi da tsanar wannan kyakkyawar yarinya takalleta a tsawace tace ke dan iyayenki baki iya gaisuwa bane kobqn isa kigaidani ba? Sosai fateema taji xafin xagin harcikin ranta takalli umma koxatace wani abu amma bataceba, saima cewarda tayi kigaisheta man fateema yayarki ce, itadin yar yayatace Fateema tayi qasa dakanta ina wuni taceda laxee kamar baxata amsaba saican tace lfy Umma takira jakadiya tace takai fateema dakinda xata xauna taceto tqyi gaba fatee tabita a baya van tatsinkayo muryar laxee tanacewa hmm qauyawa kenan anyi marmarin miyar nama, yitayi kamar batajitaba tawuce axuciyarta kuwa cewatake lallai wannan kin tsokalo tsuliyar dodo yoni ko a garimmu ma an isa axageni inqyale balle a birni inda mutum yakeyin yanda yaso tayi qofa xamu hadu ne wlh baxanbar gidannan ba sainayi maganinki yar iska karuwa jibi kayan dake jikinta Dai dai nan suka isa dakinda akabata jakadiya ce takarbi kayanta tabude wardrobe tasaka taja hannunta yaki yata tabude bayin dake cikin dakin ta nunnu na mata yanda ake amfani da komai sannan suka fito Fateema tace ngd jakadiya tace bakomai yata fatee Allah dai yabaki lfy tafita tareda ja mata qofa fateema tasauke ajiyar xuciya taxauna a bakin gadon tafara qarewa dakin kallo yayi mata kyau sosai tanashirin kwanciya jakadiya tayi sallama tashigo dawasu matasan bayi mata gudabiyu abayanta kowacce daukeda faranti ahannu dayar kayan abincine akai dayar kuma kayan lemuka da yayan itace wato pruits, jakadiya tace ga qanwar yarima nan dagayau kuxaku cigaba da kulada ita har ranarda xata komgida bayin suka russuna gareta bayan sun ajiye kayandake hannunsu sukace angama rankishi dade, Sannan tajuya ga fateema tace mata wannan sunanta ummi wannan kuma xaleeha suxasu riqa xama dake suna debe miki kewa duk abinda kikeso ki sanar dasu xasu kawo miki, tamiqa mata ledar magungunan ta tace gasunan idan kinci abinci kisha kowanne daya haka da darema, Allah yabaki lfy tafita tabarta dasu ummi da xalee wayanda dukkausu kusan sa,anninta ne, suka xuxxuba mata abinci da abinsha sukabata tanaci suna mata hira 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•66/70•* To dayake itadinma ba bayaba haka suka dinga hira cikin qanqanin lokaci tasaba dasu ummi wayanda suka taimaka sosai wajan rage damuwarta hankalinta yakwanta da yamma suka hada mata ruwan wanka ummi takalleta kai rankiya dade kibani dama in tsefe miki kanki mana kinada gashi sosai amma xai baciidan bakya gyarawa Fateema tai murmushi dama tanason gyaran dakantane dai baxata iyaba dan agidama goggo ce ke tsefe mata takunce kai suka hadu suka tsefe matashi, suka wankemata da mayukan wankin kai nandanan gashinta yayi fess sai sheqi da walwali yake yaqara baqi ga wani qamshi dakeyi itakanta taji dadinshi Sukabarta a bayin tayi wanka tafito sanyeda hijabinta suka bata towel sukace tagoge jikinta takuwa goge ba musu tashafa mai daya tafita saigata tadawo kata dawata doguwar riga mai kyau da daukar ido rigar pink ce sai akayimata adon red stone sababbin pant da bra suka kawo mata tafara sakawa sannan tasaka rigar masha Allah Ummi ce maiyimata make,up yayinda xaleeha ke taje mata kanta sannan ta busarmatashi da hand drayer masha Allah watabarakallahu ahsanal khaleqeen, fateema tadawo kaman ba itaba, dukda tadauki xubo gashi a gadon baya iskanci ne yau kam tayarda iskancin nayimata kyau sosai jinkanta tayi kaman balarabiya ga kwalliyarda bata tabayin irintaba ga wannan gyaran gashi da aka mata yasha mai sai sheqi yake fuskarta tayi luwaui luwui kaman ta jarirai Kawai saita tuna da wannan laxeeran data xageta daxun, wani shu,umin murmushi naga tayi (nace tofa real fatee ta dawo bari in ruga incewa laxeera ta gudu) Afalo nasami laxee tayi dai dai akan kujera tana cin pruit salad, a yangace tana wani lumshe ido, tashar xee tv take kallo kanaganinta kasan tana cikin farin ciki, wanda ayanxu xaman jiran fitowar yarima fahad takeyi awurin, Ahankali fateema ta tako ganin har tashigo falon laxee batasan da itaba yasa ta buya a bayan kujerar da laxee take kai, dayake kujerun irin dima dima dinnan ne saitashige qarqashinta ahankali tafara xila hannunta tana shafo qafar laxee tun tana dan kada qafar hardai tamiqe xaune amma bataga komaiba, takoma tq kwanta tana mamakin abinda ke tabinta adai lokacinda fateema tasami dan tsinken stick ta tsula matashi aqafa da qarfi tayi ihu ta miqe tsaye amma bataga komaiba ga qafarta sai xogi take mata wurin kaman ya fiddo jini Tafara tsorata nan tashiga dube2 tana qoqarin duqawa qasan kujera ta leqa fateema tayi gaggawar cannja muryarta xuwa kakkaura ta maxa adan tsawace tace karki kuskura ki ganema idonki abinda xai xamo ajalinki ke kin isa kiyi ido biyu da autan jinni Laxee jikinta yahau qyarma dan tunda take bata tabajin irin wannan muryarba aiko ihu bata iyayiba takwasa dagudu harta bige kanta da qofa amma bata tsayaba tabar falon arikice Da gudu fateema ta fito tayi dakinta tahaye gado kaman bata fita ba, dariya tahauyi hadda riqe ciki tana dukan gadonta Jin motsin qofar dakintane yasa tayi shiru su ummi ne dama abinci suka fita kawo mata tayi lamo kaman maison yin bacci xaleeha tace ayya ranki yadade badai bacci xakiyi yanxunba? Ai baccin yamma babu kyau Ummi tace ai warrware baccinnan kitashi yau aljanune a gidannan tadan waro ido alamar tsoro tace aljanu? Eh haka yaya tace gasucan afalo antaru wai anan aka tabata kuma har magana aljanin yayi mata Fateema ta miqe da sauri tafita falon tana ware ido kaman dai batasan komaiba haka suma sukabita abaya fapo cikeda ma aikatan gidan anata dube2 laxee natsaye hannunta riqeda umma sai xare ido take dariya tasota kufcewa fatee amma saita kanne ta isa gareta yaya waidagaske aljani kika gani wata muguwar harara ta wurga mata fateema tayi shiru, maganar datayin yadawo da hankalin mutanen gurin kanta Nanfa sukafara santin kyawun datayi akabar maganar aljani kowa a gurin cewa yake kai masha allah fatee kinyi kyau sosai banda umma da laxeera da abun yayi matuqar qona ransu Ummance tadaka musu tsawa abinda kukaxo yi kenan? Dalla kufita kubani guri nandanan suka fashe jiki na rawa kowa Yakama gabansa yarage dagasu sai fateema a falon laxeera ta qwallawa ummi kira tadawo dasauri ta rusuna a gabanta gani yaya, tace acikinkunnan wacce shegiyarce tayimata wannan adon tareda bata kayan gidan sarauta? Duk sukayi shiru fateema ta daga kai takalleta sannan ta taka xuwa gabanta cikin gadara da rashin tsoro tace nice nan ni ja buqaci suyimin duka wayannan abubuwa laxeera ta kalleta cikeda tsananin mamaki Tamarasa tayanda yakamata tahukunta fateema, hannu tadaga ta sharara mata mari wanda saida yasa ta tangadawa kaman xata fadi ta tirje ta kalli umma dake gefe batacewa laxee komaiba Aikuwa itama cikin shammata da baxata tadaga nata hannun ta wanke laxee da mari har guda biyu 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•71/75•* Tsananin kamakin dataji yafi xafin marin yawa umma tasaya salati yau mexan gani? Ke fatee laxeeran kika mara? Cikin tsananin fushi laxee ta nufo fateema gadan gadan itakuma ko aranta dan batasan tsoroba jirakawai take ta iso gareta su dambace Muryar yarima sukaji daga bayansu inda yadakawa laxee tsawa karki yarda kitaba ta, cikeda mamaki umma takalleshi kasan abinda tamata ne? Laxee kuwa tsayawa tayi tana cixon yatsa Eh ainaga komai agabana akayi baiqara cewa komaiba ya wucesu yakama hannun fateema yakoma sashensa da ita, kallon mamaki umma da laxeera suka bisu dashi kafin umma tajuya takoma sashenta laxeera tabita tana share qwalla baqin ciki kaman ya kasheta A dakin yarima kuwa fateema taqara xama asalin haqauya domin yanda aka tsara dakin dole akalleshi yaxaunar da ita bakin gadonshi shima yaxauna tanakallon tsarin dakin shikuma yana qarewa halittar ta kallo, ashe haka yarinyarnan ta hadu? Hmmm wani iri sha,awa ya qara xaburo mishi sanda idonshi yasauka a lips dinta nandanan idonshi suka sauya yafara shiga yanayi Fatee yakira sunanta lokacinda yakama hannunta yariqeshi acikin nashi ma,am ta amsa batareda ta kalleshiba ta hada rai tajuyarda kanta gefe, hmm yai murmushi mai fidda sauti fushi kikeyi dani qanwata? Tayi mishi banxa ok shikenanma tashi kitafi dama kayan sakawar ne naga yakamata asiyo miki naki kihuta dashan gori, yafada tareda sake hannunta Allah sarki quruciya dasauri tajuyo takamo hannun nashi Allah yaya inaso pls kasiya min yanda tayi maganar cikin farin ciki saiyaji dadi aranshi yajanyota jikinshi yarungumeta tsam dukkaninsu saida sukaji sauyi ajikinsu yawwa qanwata karki koma fushi dani kinji? Taceto, yaushe xaka siyomin kayan? Yace ko yanxuma tasakeshi tamiqe tahau tsalle yeeeeee wayyo dadi xak xama yar birni kuma wlh yaya inada kyau da irin kayan nan kalleni fa taxo gabanshi tasaya tareda kama qugu abin yabashi dariya yai murmushi hmm kinyi kyau sosai jeki dauko mayafi mutafi da gudu ta fita tana ihun murna yabita da kallon mamaki waiharta huce kenan hmmm Agurguje yashirya xuciyarshi fall da farin ciki wanda shikansa baisan dalilinsa ba, yasandai badan xai fita da fateema bane Saidai abu daya daya bashi mamaki gameda ita shine duk tsanani yanayin sha,awar dayake ciki runguma daya yayi mata yaji duk sha,awar tafita akanshi saiyajishi warwar Madalla da fatee nankam yaji dadinta sosai dole yai mata siyayya sosai manyan kaya naji da fada *fans kumin afwa yauba yawa wlh yau banajin dadi kawai dankar kujini shiru ne* _gobe xanmuku dayawa insha allah_ 😘 👉 *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•76/80•* Yana cikin saka botiran rigarshi tashigo, mayafin rigar ne tadauko batayi rolling ba tadai yafa akanta ne sannan ta jefa dayar jelar baya gashinta kuwa ummi tasaka mata ribon tadaure mata shi waje daya saitaqara kyau fuskar taqara fitowa das das, Kai yaya haryanxu baka shiryaba? Tayi maganar cikeda shagwaba tana yanqwane fuska kamar xatayi kuka, hmmm aranshi yace wannan yarinyar akwai shagwaba Rigar takama ta taimaka mishi wajan saka botir din na qasa, suka kammala suka fito tare ajere tamkar wata da xara, kana ganinsu kasan sun mutuqar dacewa da juna abinda haryau fahad yakasa fahimta kenan, haka suka keta gidan fadawa nata xubewa suna gaishesu harsuka isa inda ma,ajiyar motocin take, wata farar farado ya nufa dagudu fadawa biyu suka rugo suka bubbude bayan motar driver yashiga gaba gefenshi kuma wani bafare daya fahad yayi murmushi kuyi haquri nikadai xanfita nida qanwata Dasauri sukafito sunafadin Allah yaba yarima haquri bamusani ba, adawo lfy yakarbi kakullin motar yashiga gaba itama yace tashigo gaban ba musu tashige ayau tanacikin farin ciki irin wanda bata iya kwatantashi jitake kamar su tabbata ahaka itada yayanta Yatayar da motar suka fita fadawan na daga musu hannu dan ladi yakalli lawal yace kai amma wannan fateeman akwai kyakkyawa kuma wlh sun mutuqar dacewa da yarima inamadai............baiqarasaba lawal yace kai dan ladi akwai gulma ashedai kaima ka hango abinda na hango sukayi dariya suka tafa Laxeera kuwa sakin labulen window tayi takoma kan gadonta taxauna xuciyarta namata tafasa kamar wuta aka rura acikinta, kasancewar daga inda taken tana kallon fitowar su yarima har sanda yasallami fadawa yashiga mota daga shi sai ita suka fita, to me hakan yake nufi? Kardai yarima son yarinyarnan yake? Taf him aiko daya sakata a masifa dan wlh xan iya kasheta akan fahad tafada afili tana murxa yan yatsunta *Jifatu and son mall* Nan naga yarima yayi parking suka fito cikin isarnan tashi da qasaita yake takawa fateema nagefenshi kasancewar dayamma ne wurin a cike yake da yan mata da samari kaiharmada masu aure da yayansu mutanene kota ina daban daban saidaifa isassu ne dan baqaramin mai kudine xaije jifatu plaxa ba, Nanfa hankali yan matan dake wajan yadawo kan yarima fahad da fateema saidai duk wadda takallesu shida fateema dauka suke qanwarshice dan kamannin dasukeda shi Nanfa yafara dibar mata kaya iri iri tundaga kan atamfofi xuwa less, dogayen riguna English wear's, takalmi da jakunkuna kyawawan gyaluluwa turaruka kai kayadai kamar wanda xai hada lefe fatee ta kalleshi yaya duka wannan nawane? Yai murmushi duk naki ne qanwata, tayi tsalle ta rungumeshi wayyo Allah nagode yaya fahad thank you ta manna mishi kiss a kumatu, yajidadi sosai na nunafarin cikinta ga abinda yayi mata Nan aka kawo manya2 trolley guda biyu aka loda kayan yabiya kudi suka fita a both aka xuba mishi kayan daga nan kuma sai kusha shagalinku, nankuma gasasshin kaji yasaya musu guda biyu da ace cream da madara suka dauki hanyar wani fitaccen shago sanane kuma qwararre awajan dinki nan yacire duk atamfofi da leses yabar aka gwada fateema kwanahudu mai telar yace xai dinke kayan nanma kudine masuyawa naga ya bawa telan suka nufi gida Yaukam xuciyar fatee farin ciki karma ku tambaya jinta take kamar sabuwa aduniyar nan yaukam yaya fahad yasha godiya harba adadi Sai daf da magariba suka shigo gidan su ummi yakira bayin dake kulada ita yace sukai kayan dakinta su saka a wardrobe tadinga amfani dasu nanfa tabisu abay shikuma yafita xuwa masallacin gidan Suna saka kayan fateema ma tsalle a tsakiyar dakin kamar qaramar yarinya banko qofar da akayi da qarfi ita ta dakatar da ita Laxeera ce tsaye a qofar tana huci fuskarnan ta dada yamutsewa takalli su ummi cikin tsawa tace maxa kubar dakinnan jikinsu na qyarma suka fita xuciyoyinsu cikeda tausayin fatee dansun san yau xata daku, tamaida qofar ta rufe Fateema dai na nantsaye tana kallon ikon Allah tajuyo tawatsa mata wani matsiyacin kallo ahankali ta taka ta isa gabanta ke yar,marasa mutinci mekike nufi? Me iyayen naki suke nufi da turoki nan? Wato kinxone dan ki sami yaya Prince ko? Hmmm lallai kuwa kinyi kuskure dakeda wadancan tsofaffin naki dominkuwa yaya Prince nawane Idanunwan fateema sun canja sunkada sunyi jajur bantaba ganin ranta yabaci kamarna yauba Cikin matsanancin fushi tadago *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *hi my fans I don't know which words can I use to thanks u 4 the true love that you guys show's to me, only god know d way of paying u, not me* *I have nothing to pay u, bt i know you guys are my true lover's thanks all 4d du,a*😘😘 *may Allah make our life be all the best Ameen*🙏 *•81/85•* Tatsura mata ido ko qiftawa babu laxee tadan tsorata da yanayin dataga fateen aciki na sauyin fuskarda tayi lokaci daya Wuf ta cakumi wuyan laxee saidatakaita har bango ta datseta ke ke ke! Abinda laxee ta iya kira kenan tayi duk iya qoqarinta amma takasa raba jikinta dana fatee domin abin yagirmi tunanita sam bata xaci yarinyar nada qwarin qashi hakaba Fatee tafara magana dawata irin murya ke qaramar yar iska akuyar labe yarcin arxiqi ki iya bakinki kisanyawa kalamanki linxami domin samun damar sarrafasu Iyayena dakike gani sunxarce tunaninki sunfimun komai daraja arayuwarnan banxa marar tunani ke bakisan arxiqin iyayena kikeci anan ba? Yaya fahad kuma dakike magana aikinga alama basaina bata yawun bakina wajan yimiki bayaniba shidin nawane mallakina inma tantama kike to bari in tabbatar miki *yaya fahad nawane* kuma nikadai banida kishiya awurinshi banxa mai kamada agwagi ke banda hauka da wautama ina ke ina yaya fahad? Ki kallekifa tafada tana mata kallon rainin wayau daqyar laxee ta sami damar bankade fatee daga maqurar datayi mata tariqe wuyan nata tana shafa dan tsananin xogi da radadin da takeji na riqon da fateen tayi mata idonta sun firfito adan tsorace tafara magana nikikayiwa haka ko? Wlh saikinyi nadama saikinsan wadda kika taba tajuya tafita afusace Fateema tafada kan gadonta tareda riqe kanta gaskiya wannan tabata mata rai bakadanba, wai tana son yayanta hmmm. Lallai laxee kinjawa kanki dan wlh daga yau bake ba xaman lfy, tanacikin tunanin aka koma banko qofar dakin a karo na biyu tamaida hankalinta ga qofar laxeen ce dai tadawo saidai wannan karon hadda umman yarima ido kawai takebinsu dashi ko motsawa batayi daga inda takeba Umma ta kalleta kallon wulaqanci sannu yar masu gida, nace sannu yar masu gida wato keyanxu harkin isa kiyiwa laxeera gori akan gidannan? Iye dake nake magana kiwon qauye, ina kkajemin da yaro? Wato turoki akayi ki lalatamin yaro ko? Fatee kam juyarda kanta tayi gefe kamar bada ita akeyiba dukda cewa tanajin xafin maganganun umma amma haka tadaure dan amatsayin uwa ta dauki umma Tsawa ta daka mata waishin badake nake magana ba? Nanma bata tanka mata ba. Laxeera tace kumafa kalli umma ji uwar siyayyar dayaya mata koni bai taba yiwa irinta ba, kiji har iqirari take wai yaya Prince nata ne, tafada tareda bude wardrobe dinda aka xuba kayan Ido umma ta xaro ganin irin manyan kayan daya siyowa yar,qauye acewarsu😂 Tayi salati tana rafka hannaye nashiga uku sun shanyemin yaro wlh sungama mallakeshi tun yanxu, to wlh barikiji ingaya miki ahir dinku kurwar dana na taku bace dangin mayu kuma kingama xaman gidan nan yarinya daga xuwa yau yau kin tashi hankalin gida da kutanen cikinsa debomin kayannan duka tacewa laxeera, aikuwa kamar jira take tafara fiddo kayan tana jibgewa qasa Laxeera batasan yanda akayiba saijin kanta tayi qasa tim😂 dagowar daxatayi taga fateema tsaye akanta Ta duqa ta tattare kayan tamayar tarufe wardrobe din taxare makulli batareda tace musu komaiba takoma kan gado taxauna tadauki qafarta ta dora daya akan daya tana kallon su *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•86/90•* Mamaki ya hanawa umman yarima magana laxeera kuwa miqewa tayi takoma bayan umma tana muxurai dan al,amarin yarinyar yafara tsorata ta matuqa umma tagyada kai lallai yarinya kin isa naga alamar da shirinki kikaxo shikenan naga wanda yakawoki gidannan daidai nan taja hannun laxeera suka fice Fateema tayi dariyar nan tata ta shaqiyanci kai gaskiya na hadu kajimin mutane ya baqin ciki fatee xata faso gari kuna mata hassada taqara fashewa da dariya to wlh ba inda xani xama daram a gidannan duk na isheku riga da wando ehe, itakuma wannan tsohuwar darajar iyaye tace wlh dasai na nunamata ni fatee ce, amma nakomai yarta tajamawa hukunvi biyu xammata wlh saitabar nan gidan daqafarta Ta dade tana surutai ita kadai kafin ta miqe tayo alwala tayi salla tana gyara shimfidarta yarima yashigo da sallama tadago dasauri ta amsa yaya sannu da dawowa yawwa fatee kinyi salla daiko? Eh nayi toga wannan abinda nasiyo mana daxun takarbi ledar tana godiya yajuya yafita tabi qofar da kallo kamar tadawo dashi takeji Allah yariga ya jarrabeta da son yarima bada wasaba, wannan itace qaddararta tafada alokacinda ta tuno kalaman yarima sanda yake cewa bayya sonta kuma baxai taba yimata sonda ya wuce na yaya da qanwa ba Wasu hawayene masu xafi suka fito daga idonta batadamu data sharesuba taxauna bakin gadon hatta abunda yabatan saitaji yafita akanta Nanfa xuxiyarta tafara axapxalalta da manyan tambayoyi da maganganu akan yarima Shin haka xata qare dason maso wani? Anya baxata rarrashi xuciyarta tabar yarima ba? Dasauri xuciyarta ta gargadeta dabarin wannan tunanin baxata taba barin yarima ba, sam baxata iya rayuwa babushi ba, yaya fahad wani sashene a rayuwarta, wanda bataji xata iya rayuwa babushi kuma koxata mutu baxata taba bari wata ta rabeshi ba koda kuwa bai aureta ba Jinkiran sallar isha yasaka ta tashi tashiga bayin acan tayo alwala tayi salla saida tagama sannan tajawo ledar daya bata tabude kaxace daya gasassa tasha yaji sai qaramar leda dakeda ace cream da madara taware tafara ci Tana cikin ci su ummi suka shigo daukeda abincinta na dare tace suxauna tahade da wannan kaxar tace suci suka xauna sunaci suna hira sunata jinjinama jarumta irin tata. Sunajin dadin xama da fateema garesu tanada kirki sosai Da dare mai martaba dayashigo gidan baikwantaba saida yaje yaga fateema alokacin tayi bacci yayi mata addu,a ya rufo dakin tareda fatan allah yabata lfy Fateema fa tasayawa kanta mutinci agidan dan a yanxu laxee shakkarta take bakadanba kuma dama itakadaice mai takura mata a gidan Abangaren yarima kuma tayi iya qoqarinta wajan Saba mishi daxama da ita dayake baicika fitaba kodayaushe suna tare agida shikanshi yanajin dadin xaman fateema agidan inkukaganta kullum dagwas da ita cikin shiga ta alfarma kamanba fateen kukunba ba tayi shar da ita Duk lokacinda baffa yakira fahad akan fatee tadawo gida saidai yabashi haquri wai abari hutunshi yaqare xai maidata gida, tana debe mishi kewa sosai Shaquwa ce mai qarfi tashiga tsakanin fahad da fatee kusan kullum suna tare yana qaramata haske akan karatunta tana sashi dariya a kowanne lokaci abinda ba halinshiba amma fateema ta koyamishi Sam tunda yaxo baisami damar fita neman mata ba dukda yanajin sha,awa a wasu lokutan amma hirada fateema kadai ta isa ta mantar dashi komai, abinda ke mutuqar bashi mamaki da ita kenan Haka sukacigaba da xama kamar abokai abinda ke matuqar faranta ran mai martaba , umma da laxeera kuwa kusan bayanda suka iya saidai gunaguni da qananun maganganu Yau fateema watanninta biyu agidan tanajin dadin rayuwa sosai dan a kodayaushe tana tareda yariman ta Hausawa sukace laifin dadi qarewa dominkuwa a satinnan ne hutun yarima xai qare yakoma makaranta al,amarinda yajefa xuciyar shi a damuwa kenan dukda cewa harxuwa yanxu yarima bai yardA yanason fateema ba saidai yasan yashaqu da ita xayyi kewarta sosai *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•91/95•* Dakanshi yake shirin maidata gida ayau, bayan tayiwa mai martaba sallama takoma cikin gida tayiwa umma sallama tadan sake mata fuska dan konakomai dai tasan yau xatabar gidan Harmada saqonnin tsaraba tabata takaiwa goggo, laxeera kuwa kallon wulaqanci ta rakata dashi Yarima na gaba tana binshi abaya, harwajanda driver kejiransu, su ummi na bayansu daukeda jakunkunan kayqnta, domin kuwa kaf kayanda yarima yasaya mata batabar ko tsinke ba, haddama qari tayi dan duk kayan make'up dinda ta tarar adakin saida ta yayesu 😂 baya aka bude musu suka shiga, fadawa suka karbi kayan aka xuba a both, tayiwa su ummi sallama harda yar qwallarta saboda sabo datayi dasu Nanfa sukadauki hanyar kukunba, shiru ne yaratsa a motar tsakanin ita dashi bawanda ya iya magana kowannensu da abinda yake saqawa aranshi, saida sukayi tafiya mai nisa sannan a hankali yarima yajuyo ya kalli fatee wadda ta tsareshi da ido ko qiftawa batayi Fateema yakira sunanta a sanyaye shiru bata amsashiba, yakirata harsau uku amma ko ajikinta hakan ya tabbatar mishi bata tare dashi tayi nisa sosai a xurfaffen tunani Yakama hannunta tareda hura mata iskar bakinshi a fuskarta firgigit tadawo hayyacinta nandanan kunya ta lullubeta tayi qasa da kanta yai murmushi mekike tunani haka qanwata? Tayi shiru fateema yakoma kiran sunanta na,am ta amsa qasa qasa, fateema kiyi haquri nasan na cutar dake kiyi haquri kiyafemin fateema nasan kina sona nasani fateema amma inadada baki haquri cos magana ta gaskiya bantaba jin sonki a xuciyata ba fateema ina sonkine kawai amatsayinki na yar,uwata ina fata kema xakiyi qoqarin juya sonda kikemin xuwa haka Yayi shiru fateemadai batace komai ba sai hawaye dake xuba daga idonta domin kuwa abinda yake roqonta tayi abune da baxata taba iyawaba, magana ta gaskiya sonda takeyiwa fahad a xuciyarta kullum qaruwa yakeyi, Kiyi haquri fateema dukda bansan komai akan so ba, nafahimci abin yanada xafi dakuma nauyi amma idan kika dake komai xai daidaita kinji, kiyi haquri qanwata banaso ki koma jefa kanki adamuwa kamar yanda kikayi abaya, dan Allah naroqeki kifitar da komai aranki kinji Tadago jajayen idonta ta kalleshi saitaji tausayin kanta ya qara kamata dominkuwa babu digon soyayyarta a idon fahad, tayi qasa da kanta cikin takaici dajin haushin xuciyarta na nacewa wanda baya sonta Cikin qarfin hali da kannewa tace karka damu dan,uwana insha Allah xanyi qoqarin yaqi da xuciyata kamar yanda kace xan soka amatsayin dqn,uwana tabbas xan aikata hakan nagode da kulawar dakake nunawa a gareni ina maka fatan alkhairi a ilahirin rayuwarka kayafemin yayana bansanba koxamu sake saduwa Mutuqar tausayinta yashigeshi yarinyar tayi hankali yanxun yajata jikinshi ya rungumeta shima dai saida idonshi suka cicciko da qwalla wadda ya tabbatarwa kanshi ta tausayin fateece, nikuma nasmy nace anya kuwa🤔 Hmmmm muje xuwa! *The game is nown started* *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•96/100•* Tayi shiru a qirjinshi tanajin wani ni,imtaccen sanyi na ratsa qirjinta haka shima a bangarenshi dama shi batun yauba yanajin irin haka idan jikinshi yahadu da nata wata irin nutsuwa yakeji a rayuwarshi amma sam baitaba dauka wani abu hakan yake nufi ba, Take nutsuwarta ta daidaita amma saitaji takasa raba jikinta dana Prince, a hakan har suka isa qofar gidan wanda isartasu saida ta haddasawa yarima faduwar gaba wadda baisan dalilintaba Yaya bashir suka fara karo dashi a qofar gidan dagudu ta tafi ta rungumeshi tana murnar ganinshi yai dariya fateen goggo andawo kai qanwata taxama yar birni, tayi dariya tayi cikin gidan da gudu a takiyar gidan ta tararrda goggo nanfa ta cakumeta tana ihu wayyo my goggo nayi kewarki wlh goggo ta mangareta gefe da wasa. ni tafi can karki karyani wanne kewata kikayi aida tuni kika dawo tayi dariya Yaya fahad da bashir sukayi sallama suka shigo kowannensu daukeda qatuwar jakar kayan fateema, goggo ta tareshi da murna aka shimfida musu shimfida suka xauna suka qara gaisawa yake tambayar baffa tace ai yaje xagayen gwana bai dawoba tukanna, yace to gashikuma gobe in Allah ya yarda xankoma aa ah tafiyar ta tashi kenan cewar goggo yace insha Allah, nandai tayi mishi addu,a yaciro wayarshi yakira baffa yasanar dashi xuwan nashi bajimawa kuwa saigashi yaxo dayake gwanar ba nisa, Addu,a sosai sukayiwa yarima yayi musu alkhairi mai yawa sannan yatafi yabar fateema tanata xubda hawaye, yatafi cikeda tausayin yarinyar axuciyarshi Bayan komawarshi gida kuwa saiyaji ba dadi kasancewar yariga ya saba da hira da fateema yawan shirme da shagwabarta suka dinga dawo mishi saiya tsinci kanshi dayin murmushi ahankali yace smart girl Washe gari kuwa jirgin safe yabi qarfe tara nacan yq sauka sweezland tsaf tsaf yasami gidanshi kamar yanda yasaba yasami tarba ta musamman gun sonia kasancewar yasanar da ita xuwan nashi, dayake yakan kira wayarta sudan taba hira sometimes lokacimda yake 9ja, wanka ta tusashi agaba tayimishi sannan ta dauro mishi towel tajawo hanjunshi xuwa danning area shikuma binta kawai yake kamar qqramin yaro duk sai yaji yanda tajeyi dashi din wani iri kasancewar an dade ba,ayiba haka tadinga bashi abinci abaki har saida yace ya qoshi sannan itama taci suka koma toilet sukayi brush to tundaga canfa tafara rikitashi da wasanninta masu daukar hankali abinkada mai nema Prince dama andade ba,ayiba ya dauketa cak sai bedroom dinshi nanfa suka hau aikata masha,arsu nidai nabar musu dakin gun fatee nakoma a kukunba baiwar Allah harya xuwa wannan lokacin tanan takure takasa sakin jikinta da iyayentama dakinta tashige kaj katifarta ta dauko photon nan na yaya fahad tafara kallo tana shafawa kamar wadda ta shekara bata ganshiba, innawuro ce tashigo dakin dagudu tana ihun murna wayyo my fatee oyoyo ta rungumeta itamadai qanqameta tayi dan tayi kewar qawarta ba kadanba Kai fatee awodi kinyi kyaufa wlh kinxama yar birni tafada tana kallon fuskar fateen yanda tadada yin fresh ta goge tayi dariya ba dole inyi kyau ba qawata wlh bakiga yanda yaya fahad yake ji dani ba ta dauko qaramar jaka taxaxxageta kayan mayuka ne kawai sa na make-up tace kallifa irin wannan kayan danake shafawa yanxun tabude mata manyan trolleys dinnan taga irin kayandake ciki innawuro takama baki cikeda mamaki kai fatee wlh kekam Allah yabaki wannan yayan naki yana sonki Allah yasakamu a danshinku 👉 *Nasmy ce* 😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•101/105•* Wasu hawayene masu xafi taji sun cicciko idanunta suna qoqarin xubowa tayi hanxarin maidasu dan hatta qawar tata bataso ta fahimci yaya fahad baya sonta amma agaskiya tana tsananin tausayin kanta Takawar da maganar da yar dariya kai innawuro kema in Allah ya yarda xaki sami naki gwarxon to Allah yasa sukayi dari nan tafiddawa innawuro kala uku masu kyau cikin kayan ta bata. Tayita godiya dan tajidadin kayan sosai da murnarta tanufi gidansu Bayan tadawo daga rakiyar innawuro ne ta dauko kayan duka tanunawa goggo sosai goggo tayi mamakin fahad dayiwa fateema wannan hidimar haka. Aranta tace to kodai yafara son fateen ne? Afili kuwa har kama baki tayi kai fatee wannan kayan haka saikace kayan aure? Tayi dariya hmm kaji goggo wlh ni kayan aurena saisunyi goma irin haka itama goggon dariya tayi to Allah yakawo mijin xamu gani ai inda rai fateema ta kiklnkimi kayanta tashige daki dan itakam miji indai ba yayanta fahad bane ta haqura da aure duka Sati biyu da dawowar fatee ta ware tafara komawq fateen nan mai yawan tsokana fara,a da walwala kullum cikin bawa kanta haquri take akan soyayyar yayanta dukda tasan naxata iya barin sonshiba amma tana neman sauqi akan abin A bangaren fahad kuwa sam baisan fatee wata abace ga rayuwarshi ba saida suka rabu yau kwana biyu kenan daya kori sonia kasancewar duk abinda yakeyi da ita yakasa samun nutsuwa kwatan kwacin wadda yake samu idan yana tareda fatee suna hira, ahalin yanxu yagama yarda da cewa shima yakamu da son fateema, cos tunqnita dayasakashi agaba ako ina, yake kuma akoda yaushe tuna kyakkyawar fuskarta yake mqganar ta, yanayinta, shagwaba, da abin dariya kai komai ma, komai na yarinyar burgeshi yake Yagama tabbatarwa yana sonta kuma ashirye yake daya aureta akowane lokaci dan yanxun shikadai yasan yanda yake axabtuwa da rashinta a kusa dashi idan yaji kewar tata ja neman illatashi sai yakira kawu sugaisa daganan saiya yanemi abata wayar sukan dade suna hira saidai baitaba gaya mata yanxun shima yana sonta ba, yanaso yafara maganar da mahaifinshi ne, Kwanci tashi ba wuya awajan Allah yau wata biyu da tafiyar yarima yakai qarshen haqurinshi da boyon soyayyar fatee dayakeyi aranshi wani lokacin ma jiyake kamar yadawo gida ayi auren yakoma da ita, amma yanxunma yace yasan abinyi Fatee kuwa ayanxun jarrabawa ce ta dauki hankalinta ssce da suke rubutawa wato warc and neco karatu take sosai dan ayanxun tanaso ta ilmantu taxama cikakkiyar yar birni wayayya mai aji burinta kenan arayuwa taxama likita intasami dama, hakan ne yasa ayanxu ko wayar yarima ta daina amsa saidai tace agaisheshi ita karatu take, abinda ke matuqar bashi mamaki da tsoro kenan kardai yarinyar nan tasami wani ta manta dashi Yau takam ranar jummu,a ne babbar rana dayanayin hadari kuwa agarin hakan yasaukarda ni,ima sosai ga maxauna garin, daga can fadar mai Martaba akaturo mota ta musamman aka dauki baffa akaj cewar mai martaba yanason ganinshi cikin shiga ta alfarma baffa yashirya sukatafi da yaya bashir Qarfe hudu nayamma baffa ya dawo cikeda farin ciki tareda rakiyar dinbin mutane da kayan aure yashiga gida da sallama bayanshi kuwa mutane ne dauked kaya goggo ta taresu cikeda mamaki bayan fitar mutanen yaciro kudi dubu hamsin daga aljihunshi ya ajiye agabanta taqara cikada mamaki yace ina fateema take? Tace ta tafi gidansu injawuro, yaceto madalla dama banaso taji me xamu tattauna goggo taqara gyara xama inajinka yace ayau dai Allah yayi andaura auren fateema goggo ta xaro ido tace aure? Baffa yace aure kuwa murya a sarqe take tambaya aure kamar ya malam? Dawa kenan? Yai murmushi yace da dan,uwanta fahad mana nanfa goggo ta hau murna da farin ciki kai alhmdllh yau fateema buri ya cika dama ashe da aure tsakaninta da fahad Allah sarki Allah mun gode maka Baffa yace to ai wani hanxari ba guduba, yaya yace kar asake asanarwa fahad wannan auren harsai ya tabbatar shima yana sonta danfa wannan hasashenmu ne yarima bai taba fada yana son fateema ba saidai mu amatsayin mu na manya mun fahimci akwai so atsakanin su *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•106/110•* Goggo taqara murmusawa akwai so mana malam nima da nadauka ita kadai ke dawainiya da sonshi ashe bahaka bane abaya-bayan nan na fahimci shima yana Santa dan irin kulawa da hidimar dayakeyi da ita ma ai bana wasa bane kai madalla yau fatee xatayi baccin farin ciki Hakadai suka cigaba da tattauna yanda mai martaba yatsara xa,a tafiyarda komai ahankali amma itakam lallaine asanar mata saidai baxa,a gaya mata bada sanin fahad din akayi ba kartaji wani iri, Dai dai lokacin fateeka tayi sallama tashigo gidan sanyeda kayan makaranta ganin manyan akwatunan da ke jibge a tsakar gidan yasata sassauta tafiya takalli goggo wannan fa daga ina? Kayaj me wannan goggo? Tayi murmushi kayan auranki ne, tabata amsa ataqaice ta qara kallonta cikeda rashin fahimta da Neman qarin bayani tace banganeba goggo taja hannunta ta xaunar da ita a gefenta sannan ta kalleta nakine fateema ayau dubannin mutane ne suka shaidi daurin aurenki a garin gombe babban masallacin mai martaba fateema ta xaxxaro ido aurena fa kika ce goggo Nanda nan qwallq suka ciko idonta wannan wane irin hukunci aka yanke mata yanxu shikenan an gurgunta mata burinta nayin karatu mqi xurfi taxama likita hawayen suka gangaro kan kumatun ta goggo tayi murmushi nikaina bansanda xancenba fateema haka Malam ma, wannan hukuncin na mai martaba ne yadaura aurenki da yayanki fahad bisa yarda da tarbiyyarki tareda tabbacin baxaki bijire masaba, nikuwa abin yayimin dadi dan nasan kinason fahad din, kuma koba komai gwara hakan duk sa,anninki a garinnan suna gidan maxajensu wasu hadda haihuwa Sam fateema bata tareda goggo saidai idonta nakan fuskar goggon tanaganin lebenta suna motsi alamar magana take mata saidai ko kasheta xa,ayi batasan me goggon take cewaba, tun daga likacinda taji wai an daura aurenta da yaya fahad, innalillahi Tajuya ta kalli baffa idonta cikeda hawaye saidai takasa furta komai haka tamiqe taja qafufuwanta daqyar ta isa dakinta me hakan yake nufi? Andaura aureta da yaya fahad? Tanaxuwa ta xube kan katifarta nanfa hawayen sukacigaba da surnanowa itakanta takasa tantance wane mataki take ciki shin farin ciki ne ko baqin ciki? Shin yaya fahad din ne dakanshi yanemi aurenta kodai qaqaba mishi ita akayi? Tabbas tasan babu sonta ko kadan a xuciyar fahad kuma bata tunanin xai sota naxaman aure saidai na xumunci kamar yanda akowane lokaci yake tabbatar mata,, Hmmm yanxu inhar tunaninta yatabbata meye makomar rayuwarta a gidan yaya fahad, meye makomar burinta nakaratu daxama cikakkiyar likita? Nanfa wani sabon kuka ya qwace mata Kafin kace meye lbrn auren ya karade gari, domin baffa yaje yasanar da mai anguwar shikuma ya sanar masu jin dadi sujaji masu baqin cikin rasa fateema kuma nayi domin kuwa sosai takeda masoya a garin kawai kulasune batayi Haka mata suka dinga tururuwa xuwa wajan ganin kayan lefen nata abinda ba a taba ganiba wato ba wadda aka taba yiwa kwatan kwacin haka a qauyen adda ma taxo daj goggo ta aika yaya bashir yakirata haka innawuro tabiyo bayanta bayan gama ganin kayan tabi qawarta daki domin tayata murnar wannan al,amarin farin ciki na baxata, fateema tayi iya qoqarinta ta danne damuwarta sundan dade suna hira anan innawuro tace kin gode Allah yau muka xana jarabawar qarshe da an hanaki iyarwa yanxukam sai jiran sakamako ko baffama xai karbo miki tayi wani dan tsaki banda abinki qawata meye amfanin resold din tunda an riga anmin aure ai karatu kam yaxo qarshe tace hakane kam toke fatee ai kema saninki ne ba wani karatu daxa,a barki kiyi agarinnan ba aure, danma Allah ya taimakemu mungama wannan danmafa bakiji yanda ake xagin mu agarin nan bane wlh kin huta nima nasan nan bada jimawaba auren xa,amin sukayi dariya kafun fateema taji kira daga goggo ta tashi tafita wata dattijuwa tasamu xaune a gefen ta, tagaishesu sannan itama ta raba gefe taxauna tace gani goggo ta kalleta tace wannan inna kenan daga yau ba inda xaki koma fita inna itace wadda xata cigaba da kula dake agidannan kuma karki yarda inji tace ga abinda xakiyi kimata gardama fateema ta amsa da to tamiqe xata koma daki dawo aitundaga yanxu xa,a fara tatusa qeyar fateema suka shiga bandaki wasu ruwane dasukaji hadi da kayan qamshi dasu tayimata wanka bayan tasha fama da ita wajan cire kayanta haka ta fito tana sharar qwalla goggo bata kulata takoma dakinta tana gunaguni qasa qasa tasamu innawuro ta wuce hakan yasa tacanxa kayan jikinta tabi lfyr shinfidarta *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•116/120•* Maihaifinne yafara yin sallam yarima ya amsa cikin jajircewa amma dukda haka kuryarshi rawa takeyi cikin kulawa mai kartaba yace yarona lfyrka kuwa yanaji muryarka wani irir haka? Nanfa yaqara narkewa abbana qanwata fateema ce dasauri mai martaba yatari nufashinsa dacewa meyasami fateemar dan shima yaji tsoro akan tabbatarwar dayayi yarima kuka yakeyi Bansaniba abba batason jina koda nace abata waya mugaisa saitace a,a bata karba bansan menamata ba tatsaneni haka abba da tana sona sosai inajin dadin xamada fatee yaqarashe maganar a raunane abin tausayi Abban yayi murmushin farin ciki irin nasu na manya sannan yamaida numfashi yace to banda abin yarima wannan ne wani abun damuwa bayan kasan shirmen yarajta irin nata ai ba lallai saikayi mata wani abin ba, ni wlh ka tsorata ni, inadai kuna gaisawa da baffanka? Yarima yaishuru jiyake kamar ya yadora hannu aka wannan tsohon baxai fahimceni ba, yai shiru Dattijon yaqara yin murmushin gamsuwa yace to share hawayenka bari xan mata magana inafatan dai kanayin karatun dakyau nanmq shuru yarima yamishi baidamuba yacigaba to Allah ya taimaka nagode baijira cewar yarimaba ya katse wayar Abba abba shine abinda yarimq yacigaba dakira kakar xautacce yakoma dannq kiran layin abban yadaga xuciyarshi fall da farin ciki, yadai yarima? Abba kataimakeni bansan yaxanyiba nayita kiran ummana bata daga wayar abba inada damuwa mai martaba ya gyara kishingidarshi yace inajinka meye damuwarka? Itace abba mai martaba yace ita wa? Fateema yafada ataqaice inajinka abban ya buqaci qarin bayani, yai shiru na dan lokaci yana wani guntun tunani, daya tabbata bashida xabin daya wuce yasanarda abban nashi koxai sami sassauci da biyan buqata kumq yasan tabbas abban xaiyi farin ciki dajin xacan Abba dama itace dama itace nakeso in gabatar maka amatsayin wadda nake SO abbana inason fateema sosai ayanxun nafitarda dafin dake raina hukuncinkq kawai nake jira Abba ni wlh karatun mq nadaina fahimtar komai Sainaji daga gareka abba duk abinda kayanke but pls karkaa hanani yarka fateema yana kaiwa nan yakashe wayarshi ya kwanta awurin yana maida numfashi kamar wanda yayi gudun kilometers 50 yakai 15 minutes ahaka sannan yatashi yaxauna yadauki drink daya ya kwankwadeshi tas yakoma yakwanta Mai martaba kuma yana datse wayar yarima yakira layin baffa ya labarta mishi yanda sukayi da yarima dukkansu sunyi farin ciki nan mai martaba yasanya sati mai xuwa ranar tarewar fateema dan baxata yakeso yayiwa Prince Nanda nan goggo tashiga rarraba mintin gayyata dama suna ajiye fateema kuma tsoro da fargaba ne suka qara kanainayeta hankalinta sai dada tashi yakeyi ganin kwanaki na shudewa shirye2 na qara kankama dangi nanesa duk sun fara xuwa gida yafara daukar baqi wasu kuma gombe suka wuce Yau takama ranar assabar ce ranarda akasanya domin tarewar fateema gidan mijinta gidansu kam yacika tnijim da baqi yan yanin biki amarya dawasu tsirarun qawayenta duk suna gidan lalle da gyaran jiki wanda mai martaba dakanshi ya aiko mota da wasu matasan kuyangi guda uku suka daukesu suka tafi can xa ayi komai hadda gyaran kai, Damisalin qarfe uku na yamma mai martaba yakira wayar yarima alokacin su acan yammane sosai bayan sun gaisa yace to yarona danganeda xancenda kaxomin dashi na fateema kayi qoqari duk abinda kakeyi nanda awa daya kasami jirgin 9ja kaxo ayi komai dakai yarima dadi yaji kamar yatashi sama duk dacewa akawi ayyuka dayawa na karatu agabanshi amma Sam baidamu dasuba kaitsaye yahada kayanshi sai airport yafara cuku2 plat yayi sa,a akwai aqasa saidai sujajiran customer's Prince kuwa yana xuwa yabiya duka kudin mutane biyar dinda suka rage musu suka tashi Qarfe hudu na yamma aka dawoda su fatee gida kwaliiyar ma dagacan akayo mata, wohoho fans kuxo kuga kyau,tsari,dakuma haduwa, nikainanasmy nakasa gasgata idona anya kuwa wannan fateen goggo ce? A gaskiya fateema tahadu sunyimata make-up na kece raini fukarnan ta haska sai sheqi takeda walwali wata weading-gown ce ajikinta light pink colour, mai shara2 asama tasha xubin stone's sai daukar ido take sukayimata he'd tied da blue haka shoe's and bag dinta ma, qawayan amaryama ba laifi sunyikyau innawuro ce kan gaba, suma ankon blues din material sukayi wayannan kuyangin ma anan akabarsu suna biyeda ita a baya haka suka shiga gidan nanfahankalin kowa yadawo garesu gida yakaure da ihu da sowa ga amarya ga amarya yar sarki matar yarima Fateema tayi qasada kanta dasauri tashige dakinta koxama basuyiba sukaji ankaureda hayaniya ga motocin daukar amarya sunxo nanfa goggo tashiga dakin taqarayiwa fateema nasiha a gaggauce, Malam kam yakai sati daya kullum saiyayi mata nashar, wata qanwarta taja hannunta suka fita mota biyu aka warewa amarya da qawayanta kasancewar motocin sunadaYawa sosai *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•111/115•* Haka rayuwar fateema ta dore har tsawan wata daya tana samin kukawa ta musamman daga wannan dattijuwar na fannin gyaran jiki saidai duk tsayin lokacinnan sam bata yarda sunyi waya da yarima ba dankuwa bata tunanin jin mai dadi daga gareshi dan baxata manta yanda yanuna mata bacin rai alokacinda tafurta kaomar so agareshi ba, to balle yanxun da aka daura masu aure Allah kadai yasan mexai gaya Mata Aduk lokacinda yakira baffa yace abata wayar saitaqi amsa duk kuwa dacewa tanasonjin muryarshi saidai tana gudun bacin ran daxai haddasa mata, shikuwa baffa dadi abin yayi mishi tunda dama basa son yarima yasanda auran yanxu Shikuwa yarima abangarenshi kusan haukacewa yayi soyayyar fatima da tunaninta xasu kasheshi gashi taqi tabashi damar kodajin muryar tane yarasa yaxaiyi duk yaxama wani iri harma abin yana nema yashafi karatun sa Agidan sarautar gombe kuwa sosai umman yarima ta nunawa mai martaba bacin ranta akan wannan auran daya qulla, dafari ta tashi hankalinta itada laxeera saidai dagabaya yayarta hajiya kaltum mahaifiyar laxeera ita ta kwantar musu da hankalisu tace ai ba,a rama gayya da fushi aure ne dai anriga an daura saidai babu wata macen data isa ta rabi yarima sai yarsu laxee nanfa suka dunguma Neman sirrika wajan bokaye da malaman tsibbo mallakar yarima sukesonyi yadawo sai yanda sukayi dashi tundaga nan ta kwantar dakai tabawa mai martaba haquri akan komai ya wuce saidai tadaina daga wayar yarima idan yakirata dan ita a tunaninta da saninshi akayi auren kasancewar tagani da idonta yanda yake bawa yarinyar kulawa a gida Xaune yake a farfajiyar filin gidan nashi bisa wata lallausar center carpet, kalolin lemuka kusan biyar ne a gabanshi saidai yakasa shan ko daya ya qurawa kyawawan furannin dake xagaye dashi ido kaman mai naxarin fulawa Ahankali naga ya matse ido 😳 fans kunsan me? Qwalla nagani tam a idon yarima kafin ingama tsinkewa saigasu yana matsowa wasu saunabin wasu hawaye sharr kamar wani qaramin yaro abinda baitabayi da wayanshiba, duk kuwa yanda ranshi yakai maqura da baci baya yin kuka yau gashi yanayi a inda bashida mai share mishisu, wai akan mace kacenma qanwarshi fateema yaqara matso ragowar hawayen abin tausayi Ahankali ya kai hannunshi kan wayarshi dake ajiye agefe number mai martaba yayi dialing kai tsaye yaukam ba kodar a xuciyar sa tariga ta dake bashida sauran haquri ko kadan duk yagama qarewa Ringing biyu ana uku aka daga wayar.......................................... *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•121/125•* Sai qanwar goggo dake riqeda hannun ta, Fateema sai kuka take tana waiwayen qofar gidansu yaya bashir taga yana mata murmushi yashiga gabaj motar dake gaban tasu, suma suka shisshiga nandanan xugar motocin suka dauki hanyar gombe Qarfe biyar daidai suka isa gombe fadar tacika tinjim irin cikarda ta dade basuyi ba, wani sashe na musamman aka xarce da fateema wanda yasha gyara da tsari irinnan qasashe waje, kowa ka kalla makaki ne xaka gani qara a fuskarshi cikin wayanda suka kawo amaryar saboda irin tsarin gidan fatee nimadai nace tubar kalla Har quryar daki muka raka amarya aka xaunarda ita bakin narkeken gadonta wanda duk mai kartaba ne yayi matasu, sashen cike yake da bayi kota ina sune suketa hidima da mutane, dattijawan dasuka kawo fateema sunyi mamakin bakowa acikin dangin mahaifiyar yarima bawanda yaxo yataresu koyayi musu maraba haka suka daure suka dauki fateema da taimakon wasu kuyangi biyu suka gane sashen mahaifiyar tashi suka gaisheta haka ta amsa ba yabo ba fallasa suka gabatar mata da yarta akaryar danta dan kar afahimci yanda tadauki lamarin saita janyo fateema jikinta tace fateema ai gida kuka kawota nan dacan duk daya ne ba banbanci Allah dai yabasu xama lfy suka ce ameen suka ja hannunta suka ooma sashenta da ita kasancewar mai martaba yana fada Tsakanin gidan fateema dana iyayen yarima tafiyace mai dan tsayi drivers dinda sukawo yan kai amarya suka turo mutanen sufito amaidasu dan kar,suyi tafiyar dare haka duk manyan matan suka tafi suna qara yiwa faeema nasiha tareda jadda da mata tayi babban dace da auren yarima nan akabar qawaten ta duka sabida ansanar musu da akwai deenar qarfe shida Shiru yaratsa dakin nayan daqiqu qawayen fateema na kukunba sun baxama cikin gidan wajan bawa idonsu abinci wato kalle2 na tsare2 gidan wasu har kitchen wasu bandaki wasu kuma danqaramin lambun dake gidan suka nufa Innawuro ce kadai take xaune da fateema tana bata baki dan har yanxu. Kukaj takeyi sanannin kuyanginta ne su ummi sukashigo da sallamarsu suka xube a gaban fateema suka gaisheta cikeda biyayya sannan sukace ranki yadade uwar dakinmu daga yau mune amintattu kuma bayi mafi kusanci gareki wayanda xasu ringa bawa qananan bayi masu kulada bangaren nan umarnin aiki dakuma isar da saqonninki aduk sanda kika buqaci hakan ahankali tadago ta kallesu saitaji tana murmushi kai kawai ta gyada musu dan muryarta tagama disashewa Dayar tace Allah yataimakeki yanxunka ance mugyara miki adonki sbd lokacin fita deenar yakusanto dagama fadar hakan dayar tamiqe tasga toilet dinda ke dakin ruwan wanka ta hada mata tareda turarukan qamshi nawanka tafito nahada ruwan wankan anty ba musu fateema tamiqe ahankali ta taka tashiga yauten duk wani iri takejin kanta tarasama tunanin daxatayi gameda rayuwarta da auren yarima Itako innawuro kallon sha,awa tabita dashi aranta tace dama nice, Allah yasakamu a danshinki qawata kekam tauraron rayuwarki mai haskene Mintuna kadan fateema ta fito nandanan suka shigoda wasu bayi guda biyu,sukuma aikinsu kenan yakata kwalliya qwararri ne awannan fannin nandanan kuwa suka kama aikinsu Qarfe biyarda rabi girginsu Prince yayi landing a gombe state international airport, shikanshi saida yayi makakin irin tarbar daya samu ta musamman wadda kusanma xai iya cewa baitaba samun irinta ba, kusan mota biyar dasukaxo tariyarshi duka sababbine fil kowacce daukeda sunan masarautar gombe an daddaura musu balons sai qyalli suke ga manyan abokanshi wayanda yasan ko waya bayyi yasanar musuda xuwan nashiba tunda shima baxata ne akq kirashi amma saigasu dayawansu sunxo tarbonshi hakadai sukayita bashi hannu sunacewa congrats aboki yadai daure yashiga motar da sadiq yake ciki suka tafi Baiqara tsinkewa ba saida akafara shiga masarauta yaga ko ina anyi sabin pentee ga gyara na musamman da ko,ina yasha kuma daxuwa abokan nash suka jashi xuwa sashenshi wanda yaga ko ina nagidan ansauya tsari da furniture's daxuwa sukace yayi wanka mai martabq yakirasu yasanar musu inya iso yashirya dakyau xasuje neman aure Nandanan yarima yaqara washewa yafada wanka yasan kukunba xasu tafi dafitowarshi yafara shiri agurguje Sam baidamu da gajiyar dayake tattare da itaba wasu skayblue suit suka dauko mishi yasaka aka saka mishi net da safa da shoes nandanan yafito real Prince gashinan aka tajeshi yakwanta su sadiq sai tsiya suke masa suka fita Yawan jerin motocin dayagani yadan tsoratashi yakalli sadiq wannan shirin haka ina abban nawa? Baice komai ba yanuna mishi wata baqar endofdiscotion sabuwa fill ya bude mishi bayan yashiga yaxauna sadiq yarufa qofar prince kusan mutuwar xaune yayi ganin fatee a gefenshi cikin wata shiga ta alfarma dabai taba tunaninta a haka ba tayi kyau kakarda fenti akamata make-up yasaki baki yaxuba mata ido yayinda itama taxuba mishi nata amatuqar tsorace Saiyafara tunanin kodai gixo fateen take mishi tabbas kuwa yayi nisa a SO tunda har yafara ganin mahaifinshi a kamannin fateema Kafin yayi yunqurin wani abu motocin sukafara tafiya *Nasmy ce*😍 Yarmutan arkilla love you all😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•126/130•* Irin kallonda yatsareta dashi ne yaqara jefata cikin tsananin tsoro tunawa tayi da wancaj lokacin data sanardashi tana sonshi ya falla mata mari har guda biyu, aranta tacr to yaukuma dayaga andaura masa aurena Allah ne kadai yasan abinda xaimin Nandanan hawayendq ke maqale a idonta suka fara fitowa sharr sunabin kuncinta alamun tsoro qara a fuskarta tahada hannayenta guri daya tafara roqonshi dan Allah yaya kayi haquri wlh bansan komaiba kawai jinayi andaura aurena dakai yaya baffa ne dashida baffa kuma wlh ban gayamusu ina sonkaba bawanda ya tambayeni kawai sukq daura auren taqarasa da kuka mai dan sauti Shikuwa yarima hakan yafitar dashi daga waswasi yatabbatar fateeman ce agabanshi kuma a matsayin matarshi wato harma an daura aurensu wani irin dadine Wanda baitaba jin irinshiba yaxiyarci xuciyarshi kyakkyawar runguma yakai mata cikeda marari da xanqi farinciki Mara misaltuwa ya mamayeshi yayinda idonshi yaciko da qwalla lallai abbanshi yayimishi gata mafi girma da daraja a rayuwarshi Ahankali yafara magana cikin digar rarrashi stop crying my teema wlh nayi farin ciki da wannan hadin fiyeda tunaninki ubangiji Allah yasakawa iyayenmu da mafificin alkhairinshi bisa taimako da ceton rayukan dasukayi fateemq nima nakamu da matsanancin sonki ina qaunarki fiyeda tunaninki yaqara sassauta murya yarada mata akunne ina sonki fateema Fateema da jikinta yayi mata wani irin nauyi takasa cewa komai tunda yafara maganar ta dasqare sai takeji kamar a irin mafarke2 datake dashine ba,axqhiri ba, Fahad yafahimci hakan yadagota suka fuskanci juna yace dagaske nake ina qaunarki fateema wlh nayi farin ciki sosai da auren nan Kawai sai fateema tafashe da kuka ta rungume yayanta wanda ko a mafarki bata taba tunanin xaisotaba waiyau itace yake furtawa so haka yaqara dagota yana shafa nayanta tareda umartar ta datayi shiru Dai2 nan motarsu tayi parking yadago yakalli wurin dasuka tsaya mamaki me yai mishi dirar mikiya ganin makeken hotonshi rungumeda fateema anrubuta happy married life son murmushin jindadi ne ya subuce masa yajuyo yakalli fatee kigyara fuskarki mun iso nantarasa yanda xatayi dan nataxoda kayan make-up ba yai murmushi sannan yaciro wani lallausan handcuff daga aljihunshi yabata ba musu ta karba ta share hawayen sama2 fuskarta tadawo nrml tamayar mishi handcuff din yakarba yasaka a aljihun rigarshi fadawa ne suka bude musu motocin suka fito fuskarnan ta Prince yau kaman gwanar auduga yaxahaya yariqo hannun flower sa fateema abinda yaburge daukacin mutanen dake gun kenan hannayensu sarqe har suka isa maxauninsu namma saida yafara xaunar da ita sannan yaxauna atashi kujerar wurin yafarke da tafi raf raf raf. Kujerunsu suka fuskanci wasu manya2 kujeru gaban fahad yayi mummunar faduwa alokacinda idonshi suka sauka kan mahaifiyarshi ta watsa mishi wata harara nanfa yashiga tuno laifinshi ga umman tashi yadade bata daga wayarshi to balle kuma yanxu daya dawo qasar bai nemeta ba yayi qasa dakanshi tareda sake hannun fateema Kallo daya dayaiwa umman mashi saiyaji yafara tsanar fateema yafara wani harare2 xuciyarshi yaji tafara yimishi xafi da xogi akan auren da akayi mishi da fateema yasake kallonta saiyaji wata irin tsanarta ta dira axuciyarshi inannalillahi😳 Jiyayi kamar yatashi yabar wajan saidai yasan hakan baxai yuwuba kasancewar abbanshi yana gun nandanan fuskarshi ta canja yanayinshi yadawo daban da wanda yashigo wajan dashi Ganin nayi umman yarima ta kalli gefen da yayarta da yarta laxee suke xaune suka sakewa juna murmushi tareda kanne ido Tafa🤔 Fateema kuwa kanta na qasa batasan abinda kefaruwa ba hatta canjin fuskar fahad bataganiba balle abinda sukayi Maijawabi ataran sukaji yafara magana a mike yafara koro bayanai da maqasudin taruwarsu agun wanda iyayen amarya da angon ne suka shirya musu nandai aka cigaba da gudanarda bikin iyaye da abokanin ango sunyi nayanai dayawa tareda tarin addu,oi da nasihohi ga ango da amarya daganan biki ya watse qarfe bakwai na yamma kowa yakama gabansa aka dauki ango da amarya kamar yanda akadauko su aka maidasu gida Fateema tayi mamaki qwarai yanda talura da sauyin fuska daga yarima tundasuka shigo motar ko kallonta baiyiba balle yayimata magana haka dasuka iso gidan baiko waiwayetaba yanufi sashensu *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•131/135•* Kai tsaye dakinshi nacikin sashen fateema yanufa wani babban daki danaga aj rubutawa master room yanufa yasaka key dindake jikin qofar yabude yashiga ansauya komai na dakin yayimishi kyau sosai sabon tsarin ya burgeshi saidai har yanxu xuciyarshi tuquqi take mishi da quna Yaxauna a bakin gadanshi yabude wata bedside drower yadauko juice na bost mai sanyi yadaga yashanye qaramar robar duka amma hakan baisa yaji sanyi ko sauyi na xafin xuciyarshiba mahaifiyarshi ce tayomishi sak ga rayuwarshi yamiqe dasauri kamar ana ingixashi yanufi sashenta Dukkansu ukun sunacan sunqure a uwar dakinta wato itada yayarta dakuma yarsu laxeera sai murna suke da farinciki maganin boka yafara aiki akan yarima fahad dama bokan yace musu daxarar ya hada ido da dui wadda tashafa kwallin toxaiji yatsani yarinyar gabadaya daga nankuma duk abinda suka umarceshi xaiyi, ti shinefa ummamshi tashafa ta kalleshi kasancewar tasan acikinsu ba wadda xaiyi saurin hada ido da ita samada ita Hajya takalli umma tace toyakika gani yar,uwa ba fada ba tada jijiyoyin wuya gashi yaro yaxo hannu ai nagaya miki fada da husuma banaku bane kudai kurum kuyi biyayya ga dukkanin umarnin boka Umma tayi wani qayataccen murmushi tace wlh nayarda yaya ai shiyasa akace duk abunda babba yahango yaro koyahau rimi baxai hangoshiba Laxee tai karaf tace toyanxu momy ni meye matsayina banji kunyi maganata ba Ummanta ta harareta kaji shashasha duk wannan fadi tashin damuke danwa akeyi badan keba Harxata kumayin wata maganar sallamar fahad ta katseta tsit tayi shiru sai manyan dasuka wayance da canja xance suka amsa sallamar sai ummanshi ta miqe xatabar dakin bayan ta daure fuskarta tamau dasauri yarima yasha gabanta sannan yakama hannayenta duka niyu yariqe da nashi ya tsuguna akan guiwowinsa duka biyu a gabanta Ahankali cikin murnar tausayi yafara magana dan Allah ummanq kitsaya ki saurareni kar kiyi fushi dani kiyimin rai pls ya qara marairaice murya, anan umman laxee tayi magana haba kekuwa yar,uwa karkiyi fushidashi mana musamman idan kika duba auaren nan dole akamishi komai bada saninshi akayiba Dasauri yaruma ya cafe maganar wlh kuwa umma Allah banason yarinyar nan dole kawai xaisa naxauna da ita amma wlh bana sonta dan Allah umma kiyi haquri idan kikayi fishi dani yaxanyi dawanne xanji? Umman tayi wani irin murmushin mugunta tadago yarima ta miqar dashi suka fuskanci juna tace cikin kissa da iya tuggu son tayaya kakeso inyarda dakai bayan kai namijine ba maceba taya kake tunanin xanyarda auren dole aka maka bana soyayya ba? Naga indai hakane to kanada damar rubuta takardar saki kabawa yarinyar nan Dukdacewa fahad yana cikin sarqaqiya ta asiri da aikin tsibbo amma dayaji ummanshi ta furta kalmar sakin aurenda mahaifinshi ya daura mishi saida yatsorata ainun. Ya kalleta a raxane saki umma? Nanfa takoma tamke fuska tabita gefenshi fuuuuu xata wuce dasauri yasake shan gabanta a karo nabiyu yaxube akan guiwowinshi dan Allah ummana kiji tausayina wlh xan iya rayuwa babu kowa amma baxan iya rayuwa babu keba kifada duk abinda kikeso xanmiki umarninki nakejira mahai fiyata Umman tajuya tayiwa yayarta signal da ido nandanan hajya tabude jakarta taciro wata farar takarda da biro ta taso ta damqawa umma dama can sunshirya wannan umma takarba tamiqaw fahad hannunshi har karkarwa yakeyi yakarba yasake kallonta saki nawa kikeso inmata ummana? Hajya tayi caraf tace uku saki uku xakamata dasauri umman shi tace a,a yar,uwa inyayi uku ai xaidawo sontane kayimata saki daya kace intasami miji tayi aure kawai ya isa Hannunshi na qyarma yana karkarwa yarubuta kaman yanda aka umarceshi sannan ta karba taduba tayi murmushi ta ninke takardar tabashi kayi qoqarin nata ita yau dinnan dan banaso taqara kwana a masarautar nan amatsayin matarka tajanyo hannun laxeera takawo gabanshi wannan yar,uwar taka itace matarka kasaka aranka laxee ce matardatafi dacewa dakai Gamsuwa sosai fahad yaji akan maganar nandanan yaji laxee tasami masauki axuciyarshi yaji wani irin sonta take alokaci daya suka kalli juna suka sakewa junansu murmushi Nanfa yaji gwara yaje yasallami fateema tabar gidan danshi ayanxuma baiqi a daura auranshi da laxee ba Nagode ummana nagode da wannan kyautar dakika min bari naje nasallami waccan yarinyar dan wlh xamanta a gidannan yana dada dagamin hankali baijira cewar taba yajuya yafice da takardar sakin fateema ahannunshi yanufi sashen su *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•136/140•* Dafitarshi dakin suka fashe da dariya da murnar samun nasara hajya tace menagaya miki ai wlh ni nayarda da wannan bokan sha yanxune magani yanxu (wa iyaxu billa) suka hadu harda yar suka tafe hannaye itako murna take sosai yau yaya Prince yaxama nata har godiya yake anbashi ita ta rungume iyayen nata harda qwallar farin ciki tace I really lovo you my mamys baxan taba mantawa dakuba kun ceci rayuwata dan wlh dana rasa yaya Prince da mutuwa xanyi inasonshi ina qaunarshi fiyeda tunaninku sukayi murmushi dukkansu Fahad kuwa yana isa farfajiyar fada yaji ankira sallar isha nanfa yatuna ko sallar magrib bayyiba kaitsaye masallaci yanufa yafarayin magrib kafin akatayarda isha yayi tareda jam,I ciki kuwa hadda abbanshi mai martaba ganin abban nashi yadan karyar mishida xuciya saidai kome xai mishi dolene yasaki fateema dan baya buqatar xama da ita hasalima ayanxun ko sunanta bayasanji ballantana ganinta Baibari sun hadu da mahaifin nashiba suna kammala sallar yafice gidanshi yanufa dashigarshi saiya nufi dakin fateema baikaiga qarasawaba yafarajiyo muryoyinsu natashi itada qawayenta yan kukunba wayanda akabari a gidan sunata hire hirensu suna dariya haka yabude dakin yasamesu cikin farin ciki wani mummunar faduwar gaba yaji da idanunshi suka sauka akan fateema dasauri yakauda kanshi daga kallonta duka yan matan suka gaidashi cikin girmamawa suka fice dakin yarage dagashi sai fateema tatsuguna har qasa tagaishe shi bai amsaba itakuma bata dagoba saidai gabanta dataji yatsananta faduwa shikuwa wani irin xafi da quna yakeji na kasancewarshi da ita a daki daya takardar dake hannunshi ya cilla mata a inda take tsugunen Fateema tadago tana kallonshi da mamaki dan ita ko aranta batamasan yanda ake sakin aureba balle tayi tunanin shi akayimata tace yaya meye wannan? Mexa,ayi dashi? tafada lokacinda tadauki takardar tana qoqarin warwarewa Ke jaka yadaka mata tsawa da wata irin muryar da tajita kamar bashiyayi taba sam batasan fahad ya iya ihu hakaba cikin matsanancin mamaki tadago tana kallonshi Domin jin kamar daya iefeta da ita saidai cin mutunci dacin xarafin data hango acikin qwayar idonshi ya girmi abinda yayi mata nanfa taqara shiga rudu da mamakin dalilin wannan masifa metayiwa yaya tsakanin fitarsu biki xuwa dawowarsu? Mehakan yake nufi? Baitsaya kallon yanayin data shigaba yacigaba da magana ckin sigar masifa basaikin warwareba takardar saki ce daga dareni wadda narubuta ta da hannu na ni fahad yariman gombe ba irinki yakamata ki kasance katata ba wannan kuskuren na mahaifina ne gyaran kuma nawane kije kikoma imda aka daukoki natsaneki bana buqatar sake ganinki fateema!!! Yana kaiwanan yajuya yafice a matuqar fusace yabanko mata qofa bammm! *Nasmy ce* 😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•141/145•* Fateema sulalewa tayi daga tsayen datake xuwa xaune xomin jindatayi qafufuwanta na baraxanar jefarda ita sbd tsananin rawar dasukeyi da dakuma sanyin da sukayi alokaci daya shiyasa suka kasa daukar gangar jikinta Jikin wardrobe tajingina batasami wani tunaniba har tsawan mintuna biyar domin qwaqwalwarta gabadaya ta tsaya ta daina aiki kwata2 tabbas kuka ma rahmane domin kuwa babu yanda fateema bata nemi tayishiba amma yaqi xuwa mata tanaso tayishi ne koxata sami sassauci na wani irin qololo datakeji ya tokare mata a maqogoro yanamata wani daci da tiririn xafi da maqaqi Shiru natsawan mintuna dayawa hatta motsin kirki batayi sai can qofofin tunaninta suka bude alokqcin ne kuma taji wasu xafafan hawaye sunabin kuncinta tabbas ayau *yaya fahad* ya tarwatsa rayuwarta yasakata a nadama da danasani wanda basuda iyaka tayi nadamar saninshi arayuwarta ma ballantana kasancewa yar,uwarshi dakuma son datayi mishi arayuwarta wata irin tsanarshi taji tahuda qirjinta Kaitsaye tunanin iyayenta yafado mata arai Allah sarki goggo uwa kenan tadade tana nuna mata illa dakuma gargadinta akan son fahad data saka a ranta ta tunada baffa dakuma xumunci da irin soyayyar dake tsakaninshi da dan,uwanshi mai martaba gashi tashi daya fahad na nema ya tarwatsa shi Sai kuma tasake tunawa da abinda je tsakaninta da matasan maxan qauyensu yadda take gaggaya musu magana akan fahad yau awayi gari suji ankaita gidan fahad daren farko yasaketa innalillhi abinda tafada kenan data kawo nan a tunanin nata tabbas *yaya fahad* yajefa rayuwata acikin hadari tafada afili sannan tacigba da tunani Kometa tuna oho kaitsaye wani qarfi yaxomata naga tamiqe tabude dorowar akwatunanta da akaxodasu daga kukunba naga ta fiddo tabude bayan aqaramin akwatin takardune naga taciro nakammala karatunta wayanda basufi sati da fitowaba baffa yakarbo matasu tun tana gida tamayar tareda takardarnan da fahad yabata tarufe tasake bude babban akwatin tadauko kayan sakawa guda biyar taloda a qaramin akwatin Wanda ke daukeda kayan gold na sarqoqin aurenta takalmi biyu tadauka da jakunkuna duk tasaka a akwatin tarufe Tadauki mayafi tarufe jikida fuskarta sannan tadauki akwatin tafita ahankali taratsa falon tanajin hayaniya da hirar qawayenta yan qauyensu daga dakinda suke wasu xafafan hawayen ne suka koma silalo mata dasauri taqarasa ficewa daga sashen Batasami matsalar fita gidanba kasancewar dabaqi sosai a gidan shiyasa babu wanda yatareta koya tuhumeta Da isarta titi alokacin qarfe tara tayi dan adaidaita ta tare tacemishi malam tashar bauci xaka kaini batajira cewarshiba tashiga tanq rungumeda akwatinta suka dauki hanya Qarfe tarada kwata yasauketa a tashar inda da isarta yan union sukafara taronta hajiya inaxuwa? Kano ko bauci sokoto saura mutum daya ina xuwa hajya? Batareda wani dogon tunaniba tace sokoto xani badan komai taxabi sokotonba saidan taji yace saura mutum daya dan ita ayanxu dai dai da minti daya bataso taqarayi acikin garin gwambe sam baxata iya jurar baqin ciki da habaice habaicen mutanen kukunba ba, gwara ta tafi koma inane itadai burinta shine tayi nisada duk wanda yataba saninta Jintashin mota shiyadan dawoda ita daga tunanindatakeyi ahankali motar tafita dagatashar sukanufi hanyar fita garin hawaye ne sukacigaba dabin kumatunta yayinda xuciyarta ke dada tsinewa yarima fahad tanabinshi da allah ya isa mara adadi domin yaxame mata tauraruwa mai wutsiya yarabata da iyayenta da yan,uwa da qawaye yakuma rabata da mahaifarta wato jihar gombe Saikawai tafasheda kuka *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•146/150•* Kukanta take hini an sam bata damuda yawan mutanen dake cikeda motarba waiyau itace xata bar gari itace xata nisanta da iyayenta itace xata bar mahaifarta abinda ko a mafarki bata taba kwatantawa kanta ba kai yaya fahad ka cuceni tafada a xuciyarta nasoka ka qini bayan qi ka illata rayuwata illarda batada gyara gabadayan hankalin mutanen dake motar yadawo kanta sbd kukanda takeyi dai daiku daga cikinsune suka shiga rarrashinta yayinda sauran sukebinta da harara na takuramusun datayi aciki kuwa hadda fa,ix wanda tundatafara kukan ba abinda yake sai tsaki ko kallon indatake baiyiba aranshi yana ja jantawa kanshi dajin haushin kanshi na shigowa motar hayar dayayi Wata xuciyar kuma tace dashi ai dai danka kenan saida akace kabi jirgi kaqi kaiga mai ra,ayin riqau to ai kashiga motar hayar kaji abinda ake guje maka Yaidan tsaki jin maganganun da xuciyarshi tayi mishi cikin fushi yajuya danufin yiwa mai wannan kukan masifa da rashin m amma me? Koda idonshi suka sauka a kan kyakkyawar fuskar fateema saiyaji bakinshi yayi shiru xuciyarshi tashiga kai kawo da raya mishi hafix ai wannan ce irin matarda kake nema tsawon lokaci yajinjina kai alamar hakane Yasake qurawa fateema ido ko qiftawa babu ayanda take kukanma abin ya mutuqar birgeshi nandanan xuciyarshi tashiga kaikawo da xarya akan wannan kyakkyawar nudurwar mai daukeda abubuwanda yadade yaja neman macenda ta mallakesu Tundaga kan fatar jikinta har xuwa siffofin fuska da tsarin jikinta kai masha Allah alhmdllh Saikuma yaji gabanshi yakoma faduwa dumm! Dayatuna yanda take ayanxun budurwa kamanta tashigo mota tana kuka wataqilama gudowa tayi daga gidansu kokuma cikin shege tayo iyayenta suka korota wannan tunanin ba qaramin baqanta ran fa,ix yayiba saiyaji duk haushinta yakamashi kaiharma da kanshi atake fuskarshi ta canxa ranshi yayi masifar baci da yayi niyyar kulata yayi mata magana amma saiya fasa yama juyarda kanshi can gefe yadaina kallon inda take Haka fateema tayikukanta saidataji tagaji dankanta tabari alokacin tafiyarsu tanisa sosai dayawa cikin mutanen dake motarma bacci suke amma banda ita da duka duniyar ke mata xafi tayaya xata iya runtsawa? Xaune kawai tayi tajingina da kujerar motar To fa,ix madai kasan rintsawar yayi ga wahala da takuara irin na xaman motar da baisaba ba gakuma tunani dayayi mishi yawa akan wannan budurwa dako sunanta bai saniba 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•146/150•* Kukanta take hini an sam bata damuda yawan mutanen dake cikeda motarba waiyau itace xata bar gari itace xata nisanta da iyayenta itace xata bar mahaifarta abinda ko a mafarki bata taba kwatantawa kanta ba kai yaya fahad ka cuceni tafada a xuciyarta nasoka ka qini bayan qi ka illata rayuwata illarda batada gyara gabadayan hankalin mutanen dake motar yadawo kanta sbd kukanda takeyi dai daiku daga cikinsune suka shiga rarrashinta yayinda sauran sukebinta da harara na takuramusun datayi aciki kuwa hadda fa,eex wanda tundata fara kukan ba abinda yake sai tsaki ko kallon indatake baiyiba aranshi yana ja jantawa kanshi dajin haushin kanshi na shigowa motar hayar dayayi Wata xuciyar kuma tace dashi ai dai danka kenan saida akace kabi jirgi kaqi kaiga mai ra,ayin riqau to ai kashiga motar hayar kaji abinda ake guje maka Yaidan tsaki jin maganganun da xuciyarshi tayi mishi cikin fushi yajuya danufin yiwa mai wannan kukan masifa da rashin m amma me? Koda idonshi suka sauka a kan kyakkyawar fuskar fateema saiyaji bakinshi yayi shiru xuciyarshi tashiga kai kawo da raya mishi fa,eex ai wannan ce irin matarda kake nema tsawon lokaci yajinjina kai alamar hakane Yasake qurawa fateema ido ko qiftawa babu ayanda take kukanma abin ya mutuqar birgeshi nandanan xuciyarshi tashiga kaikawo da xarya akan wannan kyakkyawar nudurwar mai daukeda abubuwanda yadade yaja neman macenda ta mallakesu Tundaga kan fatar jikinta har xuwa siffofin fuska da tsarin jikinta kai masha Allah alhmdllh Saikuma yaji gabanshi yakoma faduwa dumm! Dayatuna yanda take ayanxun budurwa kamanta tashigo mota tana kuka wataqilama gudowa tayi daga gidansu kokuma cikin shege tayo iyayenta suka korota wannan tunanin ba qaramin baqanta ran fa,ix yayiba saiyaji duk haushinta yakamashi kaiharma da kanshi atake fuskarshi ta canxa ranshi yayi masifar baci da yayi niyyar kulata yayi mata magana amma saiya fasa yama juyarda kanshi can gefe yadaina kallon inda take Haka fateema tayikukanta saidataji tagaji dankanta tabari alokacin tafiyarsu tanisa sosai dayawa cikin mutanen dake motarma bacci suke amma banda ita da duka duniyar ke mata xafi tayaya xata iya runtsawa? Xaune kawai tayi tajingina da kujerar motar hawaye nabin kuncinta To fa,eex ma dai kasa rintsawar yayi ga wahala da takuara irin na xaman motar da baisaba ba gakuma tunani dayayi mishi yawa akan wannan budurwa dako sunanta bai saniba jimi jimi saiyaja tsaki a ganinshi tabata wayanta takuma wofantarda kyanta abanxa Can kuma sai wani sashe na xuciyarshi yace mishi to kasani ko dangi takedasu a sokoton? Ba mamaki mutuwa akayi musu shine take kuka wata qilama uwa ko uba kokuma dangi nakusa Allah sarki Sai kuma yaji tausayinta ya mamaye duka xuciyarshi Allah sarki qaramar yarinya abar tausayi nandanan haushinta dayaji daxu yafice aranshi tausayinta ya maye gurbin dayakeshi ajerin kujerun dake gabansu fateema yake saiya juyo a karo nabiyu daya kalli fuskarta saiyaga sabani da akasin daxun dan ayanxu duk fuskarta ta kumbura yayinda idonta sukayi jajir gakuma kumburi sunyi luhu-luhu atake yaji wani irin yanayi na damuwa yashigeshi idonta alumshe suke saidai ya tabbatar ba bacci take ba sbd yanaganin hawaye suna fitowa daga idonta sunabin kuncinta Kaman yayi mata magana saikuma yafasa yajuya yaxauna dakyau shima ya lumshe idonshi kamar yanda tayi yajingina dajikin kujerar xuciyarshi ta dinga kai komo tsakanin fari da baqi wato dalilin fitowar wannan budurwar shin alkhairi yafito da ita ko akasin hakan ? Dahaka mota tayita tafiya dasu kowannensu da abinda yake saqawa aransa Domin itadai fateema ayanxu fargaba da nadamar gudowa daga gidan sunfara yawo a xuciyarta adalilin tunaninta na insuka isa sokoton ina xataje? Ko ya rayuwarta xata kasance a inda ba a gaban iyayentaba? Shikuwa fa,eex qoqarin daidaita xuciyarshi yake akan tayiwa yarinyar tunani mai kyau da kyakkyawar fata akan fitowar tata *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•151/155•* Washe gari misalin qarfe tara nasafe suka shiga kano domin driver din kwana yayi yana tuqi anan yafaka domin akarya masuyin salla kuma suyi duk passengers suka fita kowada abinda yakeyi domin wasu har siyayya sukadanyi a tashar Fateema ma tasauka tanemi ruwa tayi alwala, a akwatinta ta dauko hijaf tamaida mayafindake kanta. tasami dan wuri tayi sallarta sannan takoma motar taxauna dagacan tana hango abokan tafiyarta yanda suketa kacaniyar karyawa saidai ita ko ajikinta sam cin abinci baya gabanta Fa,eex shine kadai mutumin daya damu da fateema a cikin matafiyan gabadayan hankalinshi yana kanta yana lura dakomai nata yanda takeyinshi asanyaye gashikuma bata karyaba, kuma ko tunanin karinma batayiba takoma mota taxauna tabbas tana cikin damuwa yace afili alokacinda yakammala cin abincinda yayo order daga wani babban restaurant dake gun To Allah daiyasa rasuwar akamata dominkuwa in cikin shege tayi baxai iya sontaba domin yatsani maxinata haka yafada aranshi (nikuma nasmy dake gefe nace kaji fa,eex da garaje wayace maka itama xata soka😝 hhh abudai kamar King yaga nadiyya lolx🤣) Takeaway yakarbomata na irin abincinda yaci yashiga motar haryanxu idonta baidaina xubda hawayeba tana xaune kamar andasata komotsin kirki batayi Yai mata sallama da hadaddiyar muryarshi mai tsadarji koga maxa balle matan amma fateema kodagowa batayi takalli mai maiganarba tadai amsa sallamar domin wajabcin hakan agareta kasancewarta musulma fa,eex baidauki hakan datayi mishi amatsayin wulaqanciba saima qara burgeshi datayi arayuwa yanason mace mai aji dasanin darajarta na yamace Yadora dacewa sannu yam,mata nanma bata dagoba kuma bata amsaba yadanyi shiru yana naxarinta kafun yasauke siririyar ajiyar xuciya yace yihaquri nasan bakya buqatar takura a halin yanxu kasancewar naga alamar kinacikin damuwa saidai naga kina qoqarin aikata wani kuskure daya wanda sam baidace ba yadan saurara na yan seconds kafin yadorada duk yanda ranki yabaci baidace ki hori kanki da yunwaba bakya tunanin xata iya shafar lafiyarki? Abinda yafada dinnan yasa fateema dagowa dasauri ta kalleshi tagashin waye wannan? Wanda yadamu da lfyarta? Karaf idonta suka hade da nashi fa,eex wanda dama itayake kallo Kyakkyawan saurayi tagani wanda bataji ta taba ganin maikyawu kamarshi idan aka dauke yarima fahad batasan wani maikyau kamar wannan ba Yanatsaye akanta yariqe kujerar mota da hannunshi daya yayinda daya hannun ke riqeda babbar leda fara Kallon tsaf tayimishi kafin tamaida kanta qasa saitaji mutumin yayi mata qwarjini baxata iya qyaleshiba tace banajin yunwarne kawai fa,eex yai murmushi yace haba beuty taya xakifadi hakan bayan tun a daren jiya muna tare dake anan gashi har tarada rabi nasafe kicemin bakyajin yunwa na yarda saidai in kedin ba kutum bace Fateema taji duk mutumin nan ya cika mata ido tayi shiru kawai tana wasada yan yatsun hannunta yayinda hawaye suka cicciko idonta waye wannan? Meyasa yadamu da ita har yake gudun abinda xai taba lafiyarta? *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•156/160•* Dayake fa,eex ba maiyawan magana bane sai kawai ya ajiyemata ledar akan kujerar dake gefenta yace abinci ne kitabbatar kinci yanxu baijira jin mexata ceba yajuya ya fice daga motar yakoma yaxauna a inda yaci nashi abincin Fateema ta tsurawa Ledar ido xuciyarta na mata wani dar dar toko waye wannan? Mekuma yashafeshi da sakata cin abinci hadda wani cewa taci yanxun kaman wani ubanta taja gajeren tsaki tajuyarda fuskarta gefe, tokodai barawon mutane ne? Nan xuciyarta ta kobeta haba fatee aikodai barawon ne baxai saceki anan cikin dubun mutane ba takoma tambayar kanta to inba hakaba meya dameshi dani takomayin tsaki tareda murguda baki ta harari ledar abincin Kusan mintuna biyar gashi har wasu sun fara dawowa mota dago kan daxatayi kawai sai taga wannan mutumin daya kawo mata abincin yana tsaye akanta ya harde hannaye aqirji ya kafeta da ido kamar maishirin dukanta duk dacewa batasanshiba amma da kallo dayan agane ya tamke fuska alamar ranshi yabaci Nandanan taji jikinta yahau rawa kamar wadda taga wani abin tsoro baice da ita komaiba haka itama batayi magana ba taja ledar tabude tafiddo abincin takeaway ne tabude takalli abincin soyayyar kaxa ce da wata lafiyayyar jolof rice agefe wadda taji hadin vegetables , sai kayan drinks kusan guda uku Badan tanasoba tafara danna abincin abaki ci kawai takeyi badan tanajin dadin abincinba kawai dan tsoron wannan mayen daya kafeta da ido kamar yanda ta saka mishi suna, hmmm wai maye kai fateema Jin abincin take tamkar duwatsu take jefawa a qirjinta sbd tsananin damuwa da tashin hankalin datake ciki tanaci tana xubda hawaye abinda yayi matuqar daurewa fa,eex kai kenan yatabbatar wannan cin dole kawai take ma abincin Ya jijjiga kai yakoma kan kujerarshi yaxauna xuciyarshi cikeda tausayin yarinyar tabbas damuwa ba dadi yatabbatar wannan tana cikin tsananin damuwa to Allah dai yasa ba mummunan tunanin danake akanta ne ya tabbata ba wato tayi cikin shege ne aka kirota daga gidansu Suna cikin wannan halin motar ta tashi fateema ta kammala cin abincin ta window din motar ta wanke hannunta Misalin qarfe biyar na yamma suka shigo babban birnin jihar sokoto (tashehu birnin samu gagara gasa garin malamai da waliyan Allah) a babbar tasha aka saukesu tunda motar ta taso fa,eex bai koma kula fateema ba haka itama tunda dama bata damu dashiba shine yaji yagani Passengers sukafara sauka ahankali duk wanda yaxo wucewa saiya miqawa kondostan dake tsaye a qofar motar dahaka har akaxo kan fateema wadda keta faman raba ido ganin mutane na miqa kudi gashi kuma ita batada su kana kallonta xaka tabbatar da batada gaskiya taxo tatsaya a qofar kondastan ya miqo hannu yaji shiru na,a damqa mishiba yadago ya kalleta yaga ko alamar dauko kudin batayi Ranshi yabaci sisai amma ahakan yadaure yace malama kudinki xaki bayar fateema tarasa ta inama xata fara saikawai tace kayi haquri wlh banidasu wani mugun kallo kondastan ya watsa mata bangane bakidasu ba? Kinsan bakida kudi kika hau motar haya? To wlh saikin bayar tunda motar bata ubanki ceba, banxa irinku ne masu shiga mota dan axo anata rigima to wlh saikin biy.................ai bai qarasa maganarba yaji saukar wani lafiyayyen mari a kumatunshi na hagu Saida abadaya hankalin mutanen dake gun naciki dana waje yaqara dawowa Kansu kowa a wurin yacika da tsananin mamaki tareda jinjinawa iskanci irin na wannan yarinya ke baki biya mutane kudinsuba sannan ki wanke dan tahaliki mari, hatta kondastan kallon mamaki yake binta dashi yqyinda kowa a gun yaxuba ido dan ganin matakin daxai dauka akanta Taf nimadai nasmat tashi guduwa nayi dan ganin fateema ta debo mai xafi lolx *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•161/165•* Harna juya xan gudu naji hayaniya ta kacame dasauri najuyo dan ganewa idona sainaga wuri kam yacika da mutane amma kondastan nan yakasa daga hannu yamari fateema sbd tsorata dayayi dagudun ace yar wani babban mutum ce anan danganin yanda ta iya dqga hannu ta mareshi batareda jin ko dar ajikintaba gakuma yanayinta da shigarta sun isa su tabbatar cewa ba daga qaramin gida tafito ba Shiyasa baiyi gaggawar marinta ba saiyafake da baraxana nikika mara ko? Cikin tsiwa da daga murya tace an mareka kaidin banxa wayekai dahar xaka dqga baki kaxagi ubana to wlh kull ina gargadinka ubana ya wuce axageshi gaban idona duk kuwa wanda ya aikata wannan kuskuren to yaxama dole in ganar dashi kawai dan nahau motarku banida kudi Alokacin drivern motar ya qaraso wurin lokacinda kondastan yake mayar mata da eh din bakyasan xagi meyasa xakici kudin mutane Fa,eex dake gefe ya harde hannaye yacika da mamakinta yaqara gyara tsayuwa kumafa tun kafin su qaraso tashar akaxo daukarshi amma yaqi yatafi dan yayiwa kanshi alqawarin saiyaga inda tadosa dakuma abinda yakawota garin to gashi kuma wai ko kudin mota bata dashi kuma ahakan harda qarfin halin marin masu mota hmmm waishin wacce ce wannan? Ya tambayi kanshi Ai baikaiga nemo amsarba yaqara tsurewa da al,amarinta dan akwatinta yaga ta xuge taciro daya daga cikin sarqoqi na xinarin dake gefe ta miqawa mai motar tace kayi haquri banida kudin motar ne shikuma wancan da baisan darajar iyayeba saiya xageni abinda ya batamin rai kenan a rayuwa natsani xagin iyaye kusayarda wannan ku fanshe kudinku Daga bayanta taji ance mayar mata sarqarta malam juyowar daxatayi saitaci karo da wannan mayen kamar yanda ta liqamishi shine mai maganar ya isa gaban mai motar yaciro kudi dagaaljihunshi yabashi yakarbi sarqar yamayar mata batacedashi komaiba ta karba nagode tace sannan tajuya ta nufi hanyar datagani tafita daga tashar badan tasan ida xata nufaba Fa,eex yabi bayanta da kallo yana mamakin yanayinta da sauri2 yabi bayanta dan harta fita daga harabar tashar Tana futowa taga wasu manyan motoci baqaqe guda biyu dawata hilows mai kalar kayan sojoji bayanta yana cikeda sojoji nanfa gaban fateema yashiga dukan uku uku jikinta yahau bari gar gar gar kamar maxari tunda take bata taba ganin sojoji ido da ido hakaba. Saidai a litattafan karatu na makaranta kokuma a jikin jaridu udan sun siyo qosai a gombe ma ba irinsu take gani a gidan sarkiba Kowannensu na daukeda dirkekiyar bindiga ahannu daqyar ta iyabi tagabansu tawuce takai bakin titi tayi tsaye tarasa yadda xatayi kokuma inda xataje aranta tace komadai yaxanyi yakamata inyi nesa da wayannan makasan mansaniba ko kasuwar sukaxo tashi Haka tadinga tafiya daukeda akwatin ta tayita bin gefen titi ahankali Fa,eex kuwa yana fitowgabadayan sojojin nan sukayi sahu agabanshi suka sara mishi yai musu murmushi tareda cewa thanks dafatan nasameku lfy sukq amsa da lfy yallabai yaje gurin motocinnan yaduba bamai tarbonshi kodaya daga gidansu direbobi ne kawai da ma,aikatan yai murmushi watodai fushi akeyi dashikenan? Ya umarci daya direban dayakoma tareda dayan ya amshi motar yace sujirashi nan yabi bayan fateema Tundaga nesa ya hangota xaune ajikin wata bishiya dake gefen titin tasaka kanta tsakiyar cinyoyinta tana kuka saida yadan wuce inda takedin sannan yafaka yafito daga motar yanufi inda take Jin alamun mutum tsaye akanta yasa tadago dasauri da jajayen idonta dakuku ya canjama clour takalleshi cikeda mamaki meyasa wannan yakebinta tane? Ta tambayi kanta Shikuma gogan tsayen kawai yayi yaharde hannaye ya xubamata ido kamar mai naxarin wani abu akan fuskar tata *Nasmy ce* 😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *5 star's ✨✨ online writer's association*👌 *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•166/170•* Alamomin tsoro ne qarara afuskarta xumbur tamiqe tsaye tasuri akwatinta danufin barin wurin fa,eex yayi hanxarin shangabanta abisa dole taja ta tsaya Har ixuwa lokacin baiyi mata maganaba hakan yasa ita tafara maganar cikin raunaniyar muryata wadda tasha kuka tace dan Allah kayi haquri kafice agabana in wuce naroqeka karka cutar dani kabarni da damuwata ma ta isheni Tana kaiwanan tajuya daya gefen dan cigaba da tafiya kidakata da akwai tambayoyin danakeso nayi miki kuma dakin amsamin su dai dai xanbarki kitafi Fateema bataso tsayawar ba amma saita tsinci xuciyarta da son tsayuwar dominjin wane tambaya xai mata tabashi amsar kawai ta huta dashi, koxai barta tajida abinda ke gabanta saita tsaya batareda ta kalleshi ba tace inajinka Saida yayi taku biyu ya iasa gabanta suna fuskantar juna saida fateema tadan jada baya yai murmushi sannan yace kafin kiji tambayoyin daxan miki imaso kiyimin alqawarin baxakiyimin qaryaba dafatan dai kinsan girma da darajar mutumin dake cika alqawari awajan Allah Fateema tadanyi shiru tana tunanin inda xai dosa to meyasa yakeson quretane? Taya xatayimishi hakan bayan batasan wacce irin tambaya xai mataba? Duk tsayin lokacin nan bawanda yayi magana acikinsu saican tadan juyo tace inajinka saida yakafeta da ido sannan yace kinyi alqawarin? Jitayi qwarjininshi yacika mata ido naxata iya musa mishiba daqyar tayi qasa da kanta tace eh xan fadamaka idan har abinda katambaya wanda nasani ne Fa,eex yanisa yace wacce ce ke? mekikaxoyi a sokoto? Ko ince wurinwa kikaxo? Kinada yan uwa anan ne? Meyasa kikaxo bakida kudin mota? Mekuma yasa kikaxo nan kika xauna kina kuka? Danasani tafarayi axuciyarta akan alqqwarin datayi mishi nafadamishi gaskiyar abinda xai tambayeta domin koda wasa bata xaci xai mata tambayoyin ne danganeda abinda yashafi rayuwarta ba Axatan ta ko wani wajan xai tambayeta saitagaya mishi itama baquwace ba inda tasani To ashe ba haka bane Saitayi shiru tana naxarin abinyi taya xata dauki sirrinta tasanar ga mutuminda bata saniba kuma baisantaba Saikuma taji kira dagacan wani sashe na xuciyar ta yanacewa to amma aikin riga kinyi mishi alqawari xaki gayamishi indai abinda kika sani ya tambayeki nannauyar ajiyar xuciya tasauke kafin wasu xafafan hawaye sukafara xarya akan kumatunta . Takalli fa,exx wanda yakafeta da ido yanamata wani irin kallo wanda sam batasan ma,anarshi ba idonta jage2 da hawaye tace sunana fateema haifaffiyar jihar gombe bansan kowa anan ba ina nufin banida kowa a sokoto asalima bantaba xuwanta ba sai yau maganar kudin mota kuma bantanadesuba kasancewar tafiyar taxomin a baxata Takoma kallonshi wannan karon harcikin ido takalleshi tace inafatan nagama amsa maka tambayoyinka kamar yanda kabuqata to dan allah kabarni hakannan naroqeka katifi abinka bana buqatar kusanci da kowa Tana kaiwa nan tajuya tayi gaba anan tabar fa,eex yasandare dominjin abinda fateema tafada aranshi yace kenan xarginshi akanta ya tabbata babu makawa cikine da ita wato cikin shege tayi aka koreta daga gidansu wani irin haushi da takaicinta suka mamaye xuciyarshi saiyaji xuciyarshi tacigaba da raya mishi karya barta ta tafi wata qila wannan dinma tsautsayine tunda ga yanayinta bawanda xai mata kallon yar iska kartaje tafada wani mugun hannu kota ida xama cikakkiyar karuwa Koda yadago saiyaga fateema harta danyi nisa dashi sosai tama wuce inda yafaka motarshi da sauri yabi bayanta yanaxuwa yashiga motar yatayar yaqarasa inda take yamaxuwa yayi blocking gabanta da motar hakan yasa ta tsaya cak a inda take fa,exx yafito daga motar ya tsaya agabanta Itakuwa ganinshi yahaifar mata da mummunar faduwar gaba axatan ta sun rabu kenan tunda tabashi amsoshin tambayoyin dayayi mata Hasbanallahu wa ni imal wakil abinda tashiga ambato kenan dan ita ayanxu tafara tsoraya sosai da lamarin mutumin nan Shikuwa fa,eex wani irin kallo yakemata dan ayanxu haushinta yakeji kamar ya rufeta da duka aganinshi tariga ta banxartar da rayuwarta nikuwa nasmy nace anya wannan ba kishi bane? Hhhhhh Saiyaji haushin kanshima na bibiyarta to meyasa baxai qyaleta ta tafidin ba? Sai wata xuciyar tace dashi ai wannan taimakon muslumci xakayi dan ba makawa wannan idan tayi gaba rayuwarta xata qara tabarbarewa Yanxu kuma ina kuka nufa? Tambayar daya wurga mata kenan takalleshi da mamaki saitaga yanayin fuskarshi ya canja sosai dukda bawani sani tamishi ba amma ta hango tsanani bacin rai afuska dakuma qwayar idonshi abinka da riqaqqen soja, nanfa hankalinta yatashi tabbas wannan mutumin mugu ne abinda xuciyarta tashiga raya mata kenan Saita farahawaye wlh nima bansaniba amma naroqeka dan Allah karka cutar dani Allah xaibani wajan da xan xauna dan Allah kabarni in tafi wata irin tsawa yadaka mata da wata irin muryar dataji kamar ba daga bakinshi ta fitoba dalla malama shiga mota kina wani kiran Allah kamar kinwani saninshi dakike nunamin tsoro mekike tsoron? Meye baki saniba? Ko meye baki iyaba Wanda kike tsoron a koya miki? Cikin qunan rai yake maganganun wanda kodaya fateema bata fahimtaba kawai abinda tasani shine yau kwanakinta sunxo qarshe a duniya saita fasheda kuka jikinta sai qyarma yake ta tsuguna har qasa danufin ta qara roqonshi amma saiya sake daka mata wata rikitacciyar tsawa wadda tasakata yin fitsari a wando batareda yasake kallontaba yajuya yaxagaya dan ita tuni tafada cikin motar a rikice .dashigarshi saiya tayar ya cilla motar a kan titi itakuwa tana qudundune a guri daya kuka take sosai kamar ranta xai fita nadamace da danasani qarara a xuciyarta saiyanxu ta tabbatar barin gidan datayi shine mafi girman kuskure data tafka a rayuwarta daida nan fa,eex yafaka inda yabar sojojin nan yai musu Horn sannan yasake fisgar motar yayi gaba suka mara mishi baya har ixuwa lokacin fateema bata daina kuka ba shikuwa gogan ko ajikinshi saima qarajin haushinta dayakeyi *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐©(Z.R.A)⭐⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•171/175•* *aslm my lovely fans fans of yaya fahad inafatan xakuyimin afwa abisa rashin jina kwana biyu wannan yafarune Bisa wasu dalilai dasukasha gabana* _farin cikinku shine asalin nutsuwata ku kasance dani xakuyi farin ciki , keep smiling_😍 Sam fateema batasan iya tafiyar da sukayiba balletaga ta inda akebi da ita dan tunda sukafara tafiya kanta yana qasa tana rusa uban kuka tadaiji alamar tsayuwar mota sannan yabude bangarenshi yafita baice da ita tafitoba amma dakanta tasan batada xabin dawuce hakan tabude ta fito hannunta riqeda akwatinta hawaye nacigaba da kwaranya daga idonta duk dacewa tatsayar da kukan na bayyane amma takasa tsayarda hawayen dake ambaliya afuskarta Wani tangamemen wurine tagansu wanda xa,a iya kwatantanshi da kamfani kokuma wata ma,aikata ayarin sojojinda tagani biyedasu yaqara tsorata ta matuqa haryanxu jikinta qyarma yake sosai fa,eex kuwa ko waiwayenta bayyiba tafiyarshi yake cikin qasaita da kwanciyar hankali Ta lura duk wanda tagani awurin da kakin soja ajikinshi wasun kuma da wandunan ba riga wasu kuma babu kodaya hakan yasa ta tabbatar nan gidansu ne wato head cotteer su, tafiya sukayi maidan tsayi cikin farfajiya dakuma layukan dake wurin sannan suka isa ga wani jerin wasu sojojin inda suka jeru suna jiran isowarsu yanaxuwa ya qame ya sarawa mutanen dake gabanshi wani dan madaidaicin dattijo wanda babu kakin soja ajikinshi naga yafito fuskarahi daukeda wani qayataccen murmushi a fuskarshi hannunshi na riqeda wata sarqa wadda ke qyalli kamar da gold aka qerata ajikinta anyi wasu manyan rubutu da black colour kamar haka: canal fa,eex,ma,aruf, ya sakawa fa,eex awuya yayinda gabadaya wajan suka koma sara mishi harshi wanda yasaka mishi din Fa,eex dinma ya sara musu wannan farin dattijo yafara magana cikin ixxa alhamdllh canal fa,eex rundunar sojoji ta jiha dama ta qasa baki daya tana alfahari dakai inamaka barkada dawowa amadadin duka sojojin qasarnan tareda tayaka murna akan gagarumar nasarar daka samu a wannan tafiyar bincikenka yayi fa,eex ina alfahari dakai, da wannan nakecewa kaje kahuta na sati daya kafin kadawo kacigaba da aiki ahuta gajiya lfy Hmmmmm saiyanxu na tabbatar da fa,eex dinnan miskilin mutum nenaqarshe dominkuwa duk wannan yabo da girmamawar da general yayi mishi baiyi magana ba sai wani keeler smile dayayi mishi da rabin lebe sannan ya sara mishi yawuce gaba kaitsaye office dinshi ya nufa Fateema na tsaye taga duk sojojin dasukaxo tare dinnan ba wanda yabi bayanshi hakan yasa itama taji tsoron binshi saita tsaya a inda take rakube agefe daga dan nesa dasu harma tanaji kamar tace suroqa matashi yabarta ta tafi saidai aganinta ai duksune gakuma lura datayi duka kamar sunabinshi ne watodai shi babba ne anan dinma Koya akayi yasan bata bayanshi? Oho saigani tayi yajuyo tareda watsa mata harara ai bashiri tabi bayanshi har tintibe takeyi wata qofa taga yabude yashiga hakanyasa itama tayi shahada tabi bayanshi wani qayataccen office ne wandayasha ado na kayan alatu da more rayuwa kai kace ba aduniya kakeba idan katsinci kanka a wannan wajan abinkada quruciya nanfa fateemq tamanta da damuwarta tashagaltu sosai wajan kallon irin wannan tsari da akayiwa office to inaga gida wajan xama? Ta tambayi kanta saidai kafin takaiga bawa kanta amsa sai jitayi yadaka Marat sawa araxane takalli inda yake yana tsaye aqofar office din dawani babban file ahqnnunshi da alama harya kammala abinda xaiyi yafita amma fateema batasaniba sbd nisa datayi wajan qarewa gurin kallo Batareda yace mata komaiba yaja dogon tsaki yayi waje dasauri tafusgi akwatinta ta rufa mishi baya Wannan karon driver je yake tuqa motar fa,eex da fatee a kujerun baya kanta yana sunkuye aqasa dan ayanxu tsoron mutumin nan takeji sosai shikuwa gogan ya tamke fuskarnan kaman baitaba yin dariya ba, tunanine barkatai axuciyar fateema ko ina xaikaita yanxun? Asace tadago ta kalleshi gabanta yakoma faduwa yaukak nashiga uku tafada axiciyarta wlh wannan sam bayyi kamada masu imaniba ya Allah ka kawomin dauki wani irin kallo ya wurgo mata kafin yace waye baiyi kamada masu imaniba? Fatee ta warwaro idonta duka tq xarosu dan ita asaninta axuciyarta tayi maganar Sam batasan ta bayyana ba yaqara tambayarta nine ko? Tace cikin ina ina wlh bakaibane king nake nufi😂 shikanshi fa,eex saida ya waro ido dan yanayinda tayi maganar yaso yabashi dariya daurewa kawai yayi yace waye kuma King? Bashiri tafara sambado mishi bayani itadai burinta karya fahimci dashi take Tace wani marubucine bashida kirki ko kadan saida yafaro mana lbr maidadi sannan yaxo yabari sunan littafin ma *mijin aljana* amma inaga xaidawo dashi dandai kam yanada qoqarin rubutu sosai Tunda tafara maganar fa,eex yake murmushi badan yasaniba, dukdacewa yariga yasan qarya kawai take xirara mishi amma yanayinta dayanda take maganar abin sha,awane musamman gareshi Baice komaiba sai murmushi dayayi mata cos yariga yasan dashitake ba dawani King ba dai2 nan motar tatsaya aqofar wani katafaren gida mai tananin kyau da ado na furanni dai dai nan driver yayi horn *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐©(Z.R.A)⭐⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•176/180•* Itakuwa fuskarshi tabida kallo tareda ayyanawa aranta baqaramin kyau murmushi yake yimishiba takafeshi da ido haka shima ya xubamata nashi suka sakewa juna wani sabon murmushin batareda sun saniba Wata kyakkyawar budurwa ce madaidaiciya baxatafi sa,ar fateema ba tabude qofar motar dasaurinta cikeda xumudin ganin yayanta nanfa sajida tacikaro da ya fa,eex da fateema sunqurawa juna ido fuskokinsu daukeda murmushi mai wuyar fassarawa jinqarar budar motarne yadawo dasu daga wannan yanayin dasuka shiga fa,eex dai fuskewa yayi ya wayanceda wani kalar murmushin na musamman yace oyoyo my sajjj really miss you yafito daga motar tareda hogging sistershi wadda ta raja,a da kallon kyakkyawar yarinyar da ya fa,eex yaxo musu da ita, itakuwa fateema saitaji abin wani banbarakwai cikin sanyin jiki ta lalubo akwatinta tafito Sajida taxare jikinta daga ja yayanta ta isa gun fateema da murnarta takamo hannunta sannudaxuwa sis ijamiki barka tareda jinjinawa kyawawan dabi,u da halayyarki wanda haryasa kikasami gurbin xama axuciyar dan,uwana jarumin qasata wanda yan,matan qasa da qasa ke daka wawa akansa a gaskiya sis kin........... fa,eex ne ya katseta tahanyar wurgamata da wata irin harara data tilastata yin shiru ba shiri dai dai nan ayarin members na familyn suka qaraso garesu Wani babban mutum ne akan gaba wanda da kallo daya xaka iya tabbatarwa kanka cewa shararrene kuma hakshaqin attajiri mai fada aji a qasarnan alhaji ma,aruf affan kenan fitaccen more ministan ilmi na nigeria kuma sanannen dan kasuwa mai gaskiya da adalci adukkanin al,amiranshi Yana gaba yaranshi yan mata guda biyu suna bayanshi fuskokinsu cikeda annuri kaidagani kasan suna cikin farin ciki dasauri yanufi mahaifin nashi danufin ya rungumeshi saidai sam baisami wannan damarba dan yan matan twins din dasukayi mishi rufff suduka biyun suka rungumeshi oh ya fa,eex munyi kewarka dayawa yai murmushi sannan yashafi kawunansu nima nayi kewarka my sisters fatandai nasameku lfy atare sukace lafy qlau ya barkada sauka yace yawwa .. Ahankali yaraba jikinshi danasu ya isa gun dady dake gefe yana kallonsu cikeda sha,awa ta irin qaunar dasuke nunawa junansu, sukuwa suka wuce inda sukaga anty sajida tsaye da wata pretty acewar sajj, suka yanyameta suna yaba kyauda sa,arta tasamun ya fa,eex dansu atunaninsu budurwarshi ya kawo itakuwa fateema duksaita diririce takasa koda magana saidai murmushi kawai aranta kuma tana godiya ga allah dabai hadata da wanda xai cutar da ita ba, saitaji kunya na irin daukar datayi mishi a fari dady yayimishi side hog yace barkada dawowa son inafatan kadawo lfy alhmdllh dad amma yabanga momyna ba? Dady yai murmushi tace tana fushi dakai acewarta bakiyi kewarmu ba tunda bayan ka kammala abinda xakayima motar haya kabiyo dankar kaxo da wuri wai dankaga ta damu dakaine dashida dadyn duka suka saka dariya dai dai nan su sajjj da yanbiyu safeenah da safeeyah suka qaraso wajansu saj tana riqeda hanun fateema safeenah kuwa akwatinta ta dauko Sai alokacin idon dady yakai kan fateema cikeda mamaki yakalli fa,eex yace ah son baquwa mukayi? Kafin yayi magana saj tayi karaf eh wlh dady budurwar yaya ce yaxo mana da ita dady yaqara fadada murmushin shi yaqara tambayarshi akaro na biyu dagaske take kuwa ? Fateema tadago da Saudi danjin irin amsardaxai bayar akanta shidinma saida yakalleta kafin yamaida kallonshi ga dady yace........................................... *Nasmy ce*😍 Yar mutan Arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐©(Z.R.A)⭐⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•181/185•* No dad yar,uwa dai nasamo musu ku kuma ya' dady yakalleshi kallona rashin fahimta daneman qarin bayani amma fa eex saiya fuske tareda jan hannun dad din suka nufi hanyar daxata sadasu da wannan tamfatsetsen gidan su saj nabinsu abaya sai murna suke su adole yqyansu yayi budurwa abinda aka dade Ana jira Ababban falon suka saketa sai faman xarya take takasa xaune takasa tsaye tanason ganin gworxon danta jarumin qasa babban yaronta fa,eex tayi kewarshi sosai wannan ne dalilin dayasa taji haushin rashin hawo jirgi dayayi saiya biyo mota aganinta kawai dan kar yaxo da wurine Suna shiga falon sukayi arbada ita farar mace kamila mai yawan murmushi saidai tana ganin shigowar tasu saita juya danufin barin falon xuwa dakinta na sama dady yakalli fa,eex da murmushi shikuwa cire dasauri yasha gaban momynshi tareda tsugunawa a gabanta yakama kunnuwanshi ya marairaice fuska kaman xaiyi kuka pls mom inkikayi fushi dani mutuwa xanyi dan Allah kiyi haquri wlh ban aikata hakan dan kiji haushinaba wannan ikone na ubangiji kinganta yanuna fateema rabon kusameta shiyasaka naji nafi sha,awar hawa motar akan jirgi acan muka hadu da ita na lura tana buqatar taimako rarrashi irin naki kafin musan asalin wacce ce ita, kinji dalilin mom pls karkiyi fushi dani yaqarashe kaganar hade da langwabar da kai gefe kaman mai shirin yin kuka Momy datake kallon inda wadda ya nuna mata yake saitajuyo gareshi fuskarta daukeda murmushi akasin yanda suka sameta baxan iya fushi dakaiba son kawaidai nayi kewarka dayawa and I know you do as I do ko tafada lokacinda take dagoshi daga tsugunon dayayi sukayi hogging din juna dadi fall a xuciyar fa,eex haka ma mom kafin tajanyeshi ta isa ga yan matan takamo hannun fateema da kanta yake qasa tanawasa da yan yatsunta tadago da dara daran idaninta suka kalli juna itada mom momy tasake matamurmushi haka kawai taji yarinyar ta kwanta aranta haka fateen ma sosai dattijuwar ta burgeta kai dukkansuma familyn yayimata saitaji inama itace take tareda iyayenta cikin farin ciki irin wannan? Allah sarki saita fara tambayar kanta koya suke ayanxu? Ko lbrn batanta da sakin da yaya fahad yayi mata yariskesu yanxu? Wayyo nawanda tafi tausayawa kaman goggo tasan irin sonda take mata saikawai taji idonta sun fara sirnano da hawaye mom ta qura mata ido kaitsayetagano yarinyar tana cikin damuwa tajata xuwa jikinta cikin dabaru irin nasu namanya tasharewa fateema hawayen sannan tadagota barkada xuwa ya'ta kuxo muxauna tariqe hannunta gefe tariqo na fa,eex kaha tanufi dining dasu inda dady yake xaune yanmatansu suka rufa musu baya Saida momy taxaunar dasu akan kujeru dasuke passing juna kafin itama taxauna kusada dady haka yan biyu ma sajida ce tayi serving dinsu taxuxxubawa kowa abincin sukafara ci amma bamda fateema wadda ayanxu gidansu da iyayenta kadai take tunani momy ce tadafa kafadarta kici abinci kinji ya'ta jitayi baxata iya yimata musuba dan itama matsayin uwa takejinta aganin farko, batareda tayi maganaba tadauki spon tafara cin lafiyayyan abincin wanda qamshi shi kadai ya isa ya qosarda mutum Harsuka kammala ba wanda yakomayin magana saida suka gamane sannan taga mom dakanta tamiqe takama hannun danta tanacewa son muje kayi wanka kasamu ka kwanta ba musukuwa ya miqe sannan takalli sajida tace saj kitafida yar uwartaku can dakinki itama tayi wanka tace to tamiqe takama hannun fateema suka tafi dagudu yanbiyu suka bisu Dady yadan daga murya yace umman twins haka xakumin ko? Shikenan saiduk kutafi kubarni jikadai aishiyasa nace kibari akawa miki qanwa wadda xata ragemiki dawainiyar gida yaqarasa maganar da yar dariya dan dama danufin tsokana yayi maganar yakuwa tsokano dan saida tajuyo ta dalla masa hararan wasa sannan tashige wani daki riqeda hannun fa,eex suna murmushi dady kam dariya yayi sosai Haka su fateema sukashiga dakin saj na riqeda hannunta fateema a ranta tanajinjina irin kudinda aka narka akowanne fanni nagidan agefe daya kuma soyayya da kulawar da iyalan gidan keyiwa junasu ita tafi burgeta Haka suka sakata tayi wanka tafito tasauya kayan jikinta ixuwa wani material mara nauyi dataxo dashi yayimata kyau sosai taxauna agaban madubi gakayan make-up nan irin wanda takeso kala kala saidai batada kwanciyar hankalin daxatayi kwalliyar fateema tanason ado sosai wasu mayuka datagani a wurin sukadai tashafa tagyara kwantaccen gashinta daya dan hargitse takoma tufkeshi da ribon dindake kanta, yan biyu da yayarsu saj sunagefe suna kallonta tanaburgesu sosai danta hadu acewarsu fateema takalli tsararren lallen amarcin da akayimata nanfa tashiga tunano abubuwanda suka wanxu tsakaninta da yayanta fahad burin ranta kuma muradinta mutumin data so tunbatasan kantaba ballatana tasan wani abu na rayuwa takoma tunawa da irin jankunnen da goggo tasha yimata akan son yarima hawayene suka wankemata fuska tacigaba da tuna kalamanshi naqarshe a gareta saikawai ta fasheda kuka yammatan duka sukayi kanta cikeda mamaki na dalilin kukanta *Nasmy ce* 😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐©(Z.R.A)⭐⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•186/190•* Saj tadafata cikin kidima tace yar uwa lfy kuwa? Allah yasa bamu muka batamiki raiba fatee tadago takalleta saitaji tausayinta yakamata yanda tashiga damuwa danganin tana kuka Tashare hawayenta bakomai yar uwa wlh ba abinda kukayimin tace to meyasaki kuka? Fateema tayi shiru safeenah tace pls anty karki kumayin kuka baya yimiki kyau saleema ta karbe allah kuwa amma bakiga yanda murmushi yake yimiki kyauba fatee batasan sanda murmushi ya dubuto mata ba saisuma duka sukayi mata murmushin saj takalleta yar uwa yasunanki? Tadago danufin bata amsa saidai kafintafada saitaji daga qofa ance fateema!!! Dammm gabanta yafadi ya akayi momy tasan sunanta fateema takalli mom din da mamaki qarara a fuskarta suma yaran haka saj ce tafara magana momy dama kinsanta ne bata amsataba ta isa ga fateema xonan ya'ta takama hannunta suka fice daga dakin fateema kam hankalinta a tashe yake bin momyn kawai take harsuka isa wani qayataccen falo ba wanda suka sauka daxuba ganin dady xaune ya harde kan babbar kujera two seeter yasata fahimci wannan falonshine hotunanshine birjik a falon mafu yawancinsu tareda ya'yanshi yadauka wanda sukayi da fa,eex sunfi yawa Kuma sunyi kyau sosai Mom taxaunar da ita gefe akan kujera sannan itakuma ta isa kusada dady taxauna suka fuskanci fateema ahankali taxame daga kan kujerar taxauna dai dai akan capet falon yayi tsit dadyne yafara magana yakira sunanta kamar wanda suka dade da saninta fateema! asanyaye tadago kai tareda amsawa dan amatuqar tsorace take a ina sukasan sunanta? Wannan ba lokacin tunani bane dan kafinma takoma tuno wani abin dady yajeho mata wata dakakkiyar tambaya data kadata tareda raxana qwaqwalwarta waccce ce ke? Mekuma ya fuddoki daga gudanku masarautar gombe? Wannan karon tsoronta ya bayyana qarara a fuska bakinta har rawa yake amma takasa furta komai sai hawayen dake kwaranya daga idonta falon yayi shiru bakajin komai sai sheshsheqar kukanta Fa,eex dake gefe yagama quluwa da ita wata raxananniyar tsawa yadaka mata. Dalla malama kiwa mutane shiru kibasu amsar tambayar da aka miki fateema ta fashe da kuka sosai mai tsuma xuciya duk sukayi shiru kowannensu yakasa magana (Abinda fateema bata saniba shine yanxu yanxunnan aka sako tallan cigiyarta a t'v alokacin dady yana kallon news momy kuma tana xaune a gefenshi kwatsam sai sukaga ankatse labarun ansako cigiyar fateema tareda nuna hotunanta wanda take tareda mijinta wato yaya fahad yariman masarautar gombe ana cigiyarne akan tafita a ranar farko data tare agidan mijinta anaroqon duk wanda yaganta daya taimaka yamaidata masarautar gombe domin itadin ya'ce kuma sarakuwar mai martaba) Saida tayi kukanta mai isarta sannan tatsagaita tafara sheshsheqar kuka Allah sarki tausayin yarinyar yakama momy ta tashi daga inda take taje har gaban fateema ta dagota tareda jan hannunta xuwa inda take xaune taxauna sannan itama taxaunar da ita gefenta tafara rarrashinta saida tayi shiru ta nutsu sannan Momy ta fara yimata tamayar cikin sanyi da alamun tausayawa lokaci mai tsawo tadauka kafin tafara magana cikin sanyi da tsantsar rashin kuxari yanayinta abin tausayi tace: Tabbas sunana fateema kamar yanda kukaji kuma dagaskene ni matar yariman gombe ce a da kafin farawar qaddarata wasu hawaye masu xafin gaske suka silalo daga idonta taja hanci sannan tacigaba shidin yayana ne dan yayan mahaifinane tunda aka haifeni nayi wayan sanin mutane bantaba son kowa samadashiba tun ina yar qanqanuwata nake sanarwa iyayena da yan garinmu dangi da maqota gayamusu nake yaya *fahad nawane* haka nataso tunbansan so ba har Allah yakaimu ga girma nasan so kuma nafahimci anayin aure ga masu son junansu nanfa naqara matsa lamba naqara girmama soyayyar yaya fahad araina lokuta dayawa mahaifiyata na nuna damuwarta bisa irin sonda nake nunawa inayiwa yaya fahad saidai fau niban damuba bankuma tabajin sonshi ya ragu a xuciyata ba dukdacewa a lokuta dayawa idan muka hadu yana nunamin alamu na tsana da rashin so kai akwaima lokacinda yacemin bayya sona kuma sam banyi kamada irin matan da xai iya so ba, amma dayake sonda nakeyimishi ajinina yake bantaba jin xafi ko ganin aibun abinda yake nunamin dinba haka rayuwarmu ta dore har xuwa lokacinda iyayenmu suka yane hukuncin hada aurena dashi*****************************************************************kaf fateema takwashe duk abinda yafaru tundaga lokacinda aka daura aurenta da fahad harxuwa ranar tarewarta da abinda yayimata dakuma dalilinta nabaro gidan wato kunyar da xatasha da habaici da gorace goracen mutanen qauyensu da qawayenta dakuma mahaifiyarta wadda saudatayita kwabarta akan abin tunkan yagirma amma tanace batasan da wane ido xata kaleetaba Tanakaiwa nan takuka fashewa da kuka tarungume momy tsam dan Allah momy kutaimakeni wlh banaso banason komawa garesu dan Allah kubarni inrayu daku nawani lokaci Jikin kowa awurin yayi sanyi shiru yaqara ratsawa hatta dady yakasa cewa komai ballemma gogan fa,eex dajikinshi yahau bari sosai yakejin haushin fahad a lbrn nan dayaji kawai saiyaji tsanarshi ta dira axuciyarshi kaitsaye yayi godiya ga Allah dayasanya lbrn fateema yaxama haka baixoda qaxanta ba, abangare daya na xuciyarshi kuma yalashi takobin kare haqqinta dakuma tabbatarda taxama tashi mallakinshi wato matar aurenshi hukuncin dady sukejiranji dukkansu akan fateemar dan hatta momy data fara ganinta yau tashiga ranta sosai tanaji aranta batason rabuwa da ita *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐ ⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *sallama da fatan alkhairi gareku masoyan nasmat masoyan yaya fahad novel yaudai ga nasmat Allah subhanahu wata,ala yadawomuku da ita cikin qoshin lfy, ina miqa godiyata mara adadi agareku a bisa irin kulawarku gareni tundaga kan masu kirana a waya har ixuwa masu turomin saqonninsu wayanda na mayarwa da wayanda bansami damar yin hakanba nagode ubangiji Allah yabar qauna nasan KUNA TARE DANI kamaryanda nima nake tare daku be with me u will always been in smiling love u all*😍😍😍 *•191/195•* Falon yayi tsit! Banda qarar a.c da shesheqar kukan fateema ba abinda ketashi a wurin jiki asanyaye dady yadago yakalli fateema sosai yarinyar tabashi tausayi wanda damacan halinshi ne koda baitana sanin mutum ba idan yaji yaxo dawata damuwa ko yagani saiyaji abin tamkar a ahlinshi ne Allah sarki Fateema yakira sunanta ta amsa itama asanyaye xuciyarta cikeda fargabar hukuncin da farin dattijan xai yanke akanta gabanta sai dukan uku uku yake dady yace tabbas kina tattareda damuwa dakuma tashin hankali wanda yagirmi shekarunki fateema ke qaramar yarinya ce wadda baxata taba tunani irin na manyaba kisani nimafa ubane nahaifa gasunan bamkuma san ya qarshen rayuwarmu xata kasance ba sbd haka yata ke nasan damuwarki baxata bari kiyitunanin yanda iyayenki xasuji alokacinda wannan mummunan lbr nafitarki ya riskesu ba amma ni xan iya sani sbd nima uba ne Yakike tunanin xasu rayu alokacinda suke tunanin kinshiga duniya kina wajanda bakisaniba sam xuciyoyinsu baxasu taba hutawa da tunani ba shin wane hannu kika fada? Waishinma kina raye kokin mutu? Baxasu taba fidda wayan nan waswasi axukatansu ba har abada wataqila ma tunanin yaxame masu sanadin kamuwa da ciwon xuciya ba mamaki waninsuma yarasa rayuwarshi akan hakan shin kin tanadi amsar daxaki bawa mahaliccinki aranar alqiyama alokacinda xai tuhumeki daxama silar mutuwar iyayenki? Dady yafada yana kallon inda take Fateema jikinta yayi sanyi sosai banda xubda hawaye ba abinda takeyi, ahankali tafara girgixa kai a ah a....ahh....dady baxan iyaba tafada cikin disheshiyar murya kafin tasilale daga jikin momy tararrafa ta isa gaban dady ta tsuguna wlh danayi tunani irin wannan daban yanke shawar barin gidanba dady xama xanyi duk abunda xa,acemin ace koma menene xan jura amma baxan iya jurar ganin mutuwar iyayena sbd wani banxan tunani nawaba Tafasheda kuka nagode dady nagodewa Allah daya qaddara xuwana hannunku tabbas ku iyayene kuma nagari nagode dady momy nagode sannan ina neman alfarmarku akan gobe ku maidani gida xanje in rayu da iyayena gatana kuma farin cikina Dady da momy suka kalli juna sukayi murmushi alhmdllh inji momy madalla da yarinya mai sauqin kai da xurfin tunani insha Allah gobe dakaina xan maidaki gidanku kiyi shiru ki kwantarda hankalinki kinji Allah yayimiki albarka Damn! Yaji saukar maganar a xuci tamkar an buga mishi guduma aqirji yakafe iyayen nashi da ido jiyake kamar yace musu abinda xaku aikata ba dai dai bane wato baya goyon bayan tafiyar fateema *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐ ⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•196/200•* Momy tamiqe idonta tam da hawaye ta isa ga fatee takama hannunta ta dagata tanufi dakinsu da ita tana qara lallami da kwantar mata da hankali suka fice Fa,eex yabi bayansu dakallo saida suka qurewa ganinshi wani irin xafi da qunq yakeji na daban a qirjinshi Wanda baya tunanin yatabajin irinshi a duk tsayin rayuwarshi wata nannauyar ajiyar xuciya yasauke alokacinda yaji andafa kafadarshi yadago saiyaga mahaifinshi tsaye akanshi xai saukarda da kanshi qasa dady yasaka hannu yatare tahanyar riqe habarshi ya qura mishi ido kafin yace yau mexan gani arayuwata? Son hawayene a fuskarka abinda bantaba ganiba son meye matsalarka me ka sirranta aranka gameda wannan yarinyar maimakon yayi magana saima ya fasheda kuka tareda rungume dadyn nashi ikon Allah nanfa dady hankalinshi yakuma tashi Fa,eex yakira sunan dan nashi ahankali cikin sassarqewar murya meye wannan mekefaruwa ne? Cikin muryar kuka fa,eex yafara magana dady inbaxaka mantaba nidakai baxamu iya qirge adadin lokutan dakake sakani agaba kace infitar da matar daanakeso ba, amma haryau bantaba kawo maka koda maganar mace ba dady yanumfasa sannan yace dady wlh bantaba ganin wadda tamin din bane tunda nake arayuwa bantaba arba da macenda nakeso kuma naji nakamu da santa alokaci daya irin wannan ba, dad kwanan mu daya da ita amota amma inaji kamar da ita jafara rayuwata dady inasonta kuma ita kadai ita kadai nakeso dadyna wlh baxan iya bahu ita ba ya kuma fashewa da kuka rairas kamar qaramin yaro Dady yakai maqura da rikicewa yadago fa,eex daga jikinshi suka fuskanci juna tabbas yaronshi akan gaskiyar xuciyarshi yake fada aawayar idonshi yagano hakan, a yau dady yagama sallamawa SO ya ajiyeshi a matsayinda dacan baikaishi ba agareshi tabbas SO daban ne dan tundayake tun fa,eex yana matashin shi baitabayin kuka agabansuba koda yanayi din, duk yanda akakai ga bata mishi rai saidai kaga idanun nan sunyi jajir amma ko hawaye baitaba xubdawa agabansu ba, kai hatta kakaninshi iyayen dady dasuka mutu rana daya tahanyar hatsarin mota fa,eex baiyikukaba Dady yaxubawa dan nashu ido kawai yakasa cewadashi komai tabbas wannan shi ake kira ga qoshi ga kwanan yunwa domin kuwa inda sauran wani abu dayaragewa dady wanda yakeso yayi adujiya kafin mutuwarshi to baifi yaga babban yaronshi yakawo mishi wacca yakeso dakanshi ya daura aurensu ba, to ayau gashi fa,eex yakawo yarinyar saidai yasan ayanda yaji lbrn fateema ya tabbatar tana komawa iyayenta xasu iya maidata gidan mijinta dukda cewa ba santa yakeba amma yalura da iyayen masu son hada kan yayansu ne hmmmmm yasauke numfashi rigiji gabji kenan Momy dake tsaye aqofar dakin tana saurarensu taqaraso dakin jiki ba qwari takama hannun dan nata taxaunar dashi kan kujera itama ta xauna dadyma yaxauna gefensu momy tashafa kan fa,eex kayi haquri yarona kuma ka kwantar da hankalinka babu abinda yagagari ubangiji kakai kukanka gareshi mumanan dukanmu xamu tayaka da addu,a son nikaina inamaka kwadayin samun fateema hankalina ya kwanta da yarinyar kuma insha Allah xanyi iya qoqarina naganin kasameta muddin da akwai rabon aure tsakaninku Da ire iren wayan maganganun ne. Suka dinga rarrashin yaronsu har suka samu yafara sakkowa Fateema kuwa aranar kuka takwana tanayi baji ba gani su saj sunata aikin rarrashi dan momy tagaya musu komai Haka fa,eex ma aranar shima bai samu yarintsaba yanayiwa mayarda fateema ga iyayenta kallon wata hanya daxata yanke duk wata alaqa dayake qoqari qullawa da ita Abirnin gombe kuwa amasarauta wato gidansu yarima hankalin mai martabane kadai yatashi da batan fateema sukuwa iyayen aikin ko ajikinsu saidai shima yariman yanacikin damuwa akan lamarin dominkuwa yaga hacin ran dabai taba ganiba a idon mahaifinshi akan lamarin har marinshi yayi alokacinda yace shibaxaije nemanta ko inaba, mari yasha abinda baitaba tsammaniba mahaifinshi da ko yatsa baitaba daga mishiba wannan ne dalilin damuwarshi aranshi yana jinjina abinda xai faru idan mahaifinshi yaji yasaki auren daya daura mishi da fateema A kukumba kuwa kusan dimuwa ce takama iyayen fatee jin wai tabar gidan bada sanin kowaba duk dacewa bawanda yasanda lbrn sakinta yarima yayi, amma mahaifiyarta goggo tayi amanna cewar fateema baxata bar gidan abanxaba kasancewar ba auren dole suka mata ba Agari kuwa lbrn yaxaga ko ina cewa fateema ta gudu daga gidan mijinda tafi SO fiyeda kowa arayuwarta, wannan ne yasa mafi yawan mutanen qauyen suke fadin wataqila da akwai wata maisonshi acan ita tamata asiri ta fita, dan aganinsu banxa baxata raba fateema da gidanba kuma dayawa sunyi amanna da hakan din wato batanta yashafi asirine wannan ne yasaka duk wani ko wata masu sonta a qauyen suka duqufa dayimata addu,a Hmmmmm nikam dai ina tsakiya, kome readers sukuma xasuce akan wannan?🤔👀 *Nasmy ce*😍 Yar mutan Arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐ ⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•201/205•* Washe garin ranar takasance assabar agidan mai martaba kowa da abinda yakeyi wato mai martaba yanacikin damuwa da tashin hankali na batan yar dan,uwanshi inda abangare daya hjy umma mahaifiyar fahad itada yayarta momyn laxeera suka saka ranar amatsayin ranar daura auren yarima fahad da laxee misalin qarfe tara nasafiyar wanda sam ba,a shiryashi dasanin mai martaba ba a wani babban hotel suka dauro auren tsakanin iyayen laxeera maxa dakuma wasu dai daikun manyan mutane najikin mai martaba wayanda aka gayyata asace Su shida ne suka qure a babban dakin umman yarima wato da ita da yayarta dakuma ita laxee din dawasu qawayenta uku wayanda basa rabuwa, shawarwari sukeyi akan tarewarta da fahad dakuma yanda xa,a gudanarda shagalin bikin tunda komai cikin sirri akeso ayishi sunfiso yakasance saita xauna dashi xamana mata da miji kafin mai martaba yasan da auren yanda bayanda xaiyyi koda yasani sai haquri tunda mai afkuwa tarigada ta afku Dukda cewa suna aikinsune da tsifface tsufface ne da asiri amma umman yarima amatuqar tsorace take sbd gudun abinda xaifaru ranarda mai martaba xaiji wannan lbrn na tayiwa fahad aure batareda saninshiba Momyn laxee ce mai kwantar mata da hankali cewar ta kwantar da hankalinta wannan duk mai sauqi ne idan angama wannan suka tare xasuji da mai martaba ba,abunda ya isa yayi takuwa amince nan suka yanke sutare ayaudin kawai inyaso daga baya idan komai yabayyana ayi shagulgulan bikin Laxee jitake ayau bawanda yakaita murna da farinciki itada uwarta nagani cikar burinsu yaxo kusa, gurin gyaran jiki sukawuni itada qawayenta da yamma aka saka jekadu da qawayen umma dana momy suka kaita sashennan da aka gyarawa fateema acan ta tare yarima kuwa bashida katabus saidai yanda akajuyashi nashi bi ne kawai dukdacewa yanajin wani daci da tuquqi a qasan xuciyarshi amma baya iya tsallake umarnin ummanshi da yayarta ballatana na sabuwar amaryarshi laxeera Qarfe tara dai dai ango yashiga dakin amaryarshi wadda yakegani tamkar tauraruwa idan ya hada ido da ita jiyake tamkar bayan ita din babu wata mace aduniya wannan kuwa yana daga cikin tasirin aikin bokansu, kqmar waina haka taita jujjuyashi domin yanaganinta ya xare buqatarta yake a haukace saida tagama garashi sannan daga bisani tabiye mishi tinda dama abinda takeso kenan dan qarasa mallakeshi gabadaya Fahad haukacewa ne kawai baiyiba daya sadu da laxeera sbd tsumin asurinda boka yayimata dakanshi na wuni daya xaune acikin ruwan tsafi, daganan abubuwa suka fara rincabewa diminkuwa yarima bayaji kuma baya ganin kowa sai laxee Dasafe tayi waya da uwarta take sanar mata yanda abubuwa suke tafiya dai dai momynta tayi farin ciki sosai nanfa tafara bawa yar tata target daban daban nikam danaji saida naxubda hawaye araina nace lallai rashin sani yafi dare duhu domin kuwa hatta wadda sukayi komai da ita basu bariba wato umman yarima sungama shirya makirci da tuggun daxasu rabata da dan nata gabadaya dama shi suke buqata da abinda ke hannunshi Tofa🙊 Gabaki daya wunin ranar yarima bai iya fitaba koda masallaci kai sallarma rabonshi da yinta tun wadda yayi kafin shigowarshi gidan yanan maqaleda laxee ko kadan baiso yadaga kota daga bayaso ta bacewa gajinsa haka kuma inya ganta baya iya haqura saiyajita ajikinshi (tirqashi🤔) Hakasuke nane da juna gidan Qarfe hudu na yammacin ranar ne wata danqareriyar mota qirar jip tashiga qofar fadar bayan angabatarda gajeren bincike akansu mutane hudune a motar sukaxo sukafaka daf dawata farar mota dake fake agurin alokacin bakowa afilin farking din alokaci daya matanenda ke cikin motar suka firfito ikon god! Fateema ce da abban fa,eex da momy dakuma shi fa,eex din masha Allah dukdacewa suna cikin tashin hankali amma kallo daya xakayi musu dole kace tubarkalla Sam fateema batayi kuskuren shiga gidan kaitsaye amatsayin yar gidan ba, iso suka nema akayimusu gun mai martaba tareda bayanin sunxoda fateema ne yarinyar da aka saka cigiyarta agidan tv ai dagudu bafaden yanufi qofar fada har yana hadawa da tintibe badan komaiba sai dan sanin yanda mai martaba yatada hankalinshi akan natan na fateema *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐ ⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•206/210•* Bajimawa yafito tareda wasu mutane daganinsu kasan manya ne masu fada aji afadar daxuwa suka gaisa da dady cikeda karamci da girmama baqo irin na gombawan asali su sukayimusu jagora xuwa dakin baqi na musamman na mai martaba Kusan tare suka isa da mai martaba dan taqofar ciki yabi dashigarshi kuwa idonshi suka sauka ga abin nemanshi fateema tana rakube abayan momy kamar marainiya mai martaba dakanshi yayi tattaki ya isa gareta cikeda farin ciki ya rungumeta wasu hawaye masu sanyi suka kwararo daga idonshi yata fateema! Yafada yana sauke numfashi ina kika tafi fateema? Meya fiddaki daga gidan abbanki? Lock yadagida fuskarta yace kosaceki akayi fatee? Kigayamin gaskiyar abinda yafaru dake yata kinjefamu acikin tashin hankali Mara misaltuwa gayamin yafada lokacinda ya tsareta da ido ko qiftawa babu Fateema kam kuka ne ya qwace mata takoma rungume baffan nata tace kuyi haquri yaya baffa dan Allah kumin afwa abisa kuskuren danayi nufin aikatawa cikin rudewa damuwa da rashin tunani kugodewa Allah baffa kuka kugodewa wannan bawan Allah dashida iyayensa tafada tana nuna yaya fa,eex da iyayensa, sai alokacin idon mai martaba yasauka akan kamilallun mutanen yasake hannun fateema ya isa gaban dady ba girman kai yamiqa mishi hannu cikeda sakin fuska sukayi musabaha dady yayi mamakin hakan tabbas wannan sarkin ba girman kai akanshi yadinga kwararo musu godiya da sa albarka akan wannan alkhairin nasu da baida abinda xai biyasu akan hakan Kowa yanutsu aka xaxxauna aka kawo abinci da abinsha ga baqi fateema kam tanacan maqale agefen mai martaba fa,eex sai satan kallonta yake ahakan saiyaga taqara haskakawa xaman nata gefen mai martaba yaqara fitoda asalin martabar da yadade yanagani a idonta cikin dabara yafitoda wayarshi kamar maiduba wani abu yaita daukarsu photo kasancewar kujerunda suke kai suna fuskantar nasu mai martaba Bayan kamar mintuna talatin sudady sun dan tsakura kadan daga abubuwan ci danasha da aka jibge musu kowa ya nutsu mai martaba yakalli yarshi fateema yace inajinki yata gayamin menene dalilin fitarki daga gidan nan? Karkisake kimin qarya koki boyemin wani abu dukda nasan ba halinki bane Falon yayi tsit nantake abubuwan dasuka faru tsakaninta da *yaya fahad* sukafara dawo mata aqwaqwalwa hawayene suka farabin kuncinta kafin takwashe duk abunda yafaru tagayawa mai martaba sannan tadora mishi dalilan dasuka sakata tunanin barin gidan dakuma rufin asirin da Allah yayimata na hadata da fa,eex dayayi Subhanallah subhanallah innalillahi wa inna ilaihi raji.in abinda suday da manyan mutanen dake gun suka shiga ambatowa kenan fateema kuwa dafe kai tayi tashiga karanto addu.oi da sambatuj rikicewa cikin harshen fulatanci Nikaina danasan hakan xata faru dana hana fateema sanarda mai martaba cewan *yaya fahad* yasaketa domin kuwa mimmiqewa yayi dagakan kujerar jikinshi yahau karkarwa da qyarma hannu da bakinshi duk motsi sukeyi saidai ba.ajin sautin maganarshi da alama magana yakesonyi amma babu damar hakan cos muryarshi bata fitowa kwata kwata daganan kuma saiya shide ya suma yadaina numfashi innalillahi wa inna ilaihi raji.un addu,a suka dauka Dukkansu sukayikan mai martaba cikin kidima da matsanancin tashin hankali *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐ ⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•211/215•* Su waxiri da mai fada ne suka yi gaggawar kinkimarshi hankalin kowa awurin yatashi fateema sai rusa uban kuka take kukanda fa,eex yakejinsa kamar ana gugar qahon xuciyarshi da wuqa, suka shigardashi awani qofan daki dake cikin falon akan wani lafiyayyen gado suka kwantar dashi kafin daga bisani sukayiwa likitanshi waya, tsawan mintuna talatin likitan yayi akansa kafin yasaki nasarar dawowar numfashinsa yabawa mutanen dake gurin umarnin barinshi yasami hutu na awa daya Dady da momy dakuma fa,eex da fateema kaitsaye sashen gidan waxiri aka kaisu kafin cikar lokacin hutunda likita yabuqaci abawa mai martaba dama can matar gidan tasan fateema basu fuskanci wata matsalaba antaresu cikin girmamawa da karamci part daya aka ware musu mai daki biyu da babban falo kowanne daki yanada bayi acikinsa Afalon sukafar yada xango nanma aka koma gabatar musu da kayan abinci dana sha harmada maqulashe kasancewar aqoshe suke yasa basuci wani abin kirkiba suka bige da hira ta jajanta yanda lamarin ya kasancewa mai martaba lurada iyayen sukayi yaronsu yana buqatar ganawa da fateema yasa suka miqe sukashige daya dakin dake gidan sukabar subiyun afalo Hakan yasa falon yaxame masu shiru dan acikinsu bawanda yakoma magana tsawom daqiqu fateema kanta yana sunkuye aqasa fa,eex yakasa haqura domin kaikawo da xuciyarshi take masa abisa tunanin dayayi naganin yau xuwa gobe xasu rabuda fateema rabuwarda yakeganinta kamar shine ganin qarshe daxai mata gashi har yau bai isar mata da saqon xuciyarshi ba, Shine yaqatse shirun tahanyar yin gyaran murya yace fateema! batareda tadago kaiba tace na,am saikuma yakoma yin shiru kafin yadorada fateema kiyi haquri kiyafemin baxan boye miki sirrin xuciyata ba tundaga waccan ranar danafara dora idona akanki naji nakamu da qaunarki xama damukayi dake nakwana daya amota jinsa nayi kamar rayuwata ce tafaro daga wannan lokacin nakamu da sonki fateema, sbd hakanan bbu irin tunanin da banyiba naganin kinbaro gidanku a yanayi da shekarunki sai wata xuciyar tabani kamar kin aikata wani mummunan laifine yasa kika gudo daga gidan iyayenki dukda hakan ban iya rabuwa dakeba saboda tsananin qaunata gareki fateema Saida yadan ja numfashi kafin yacigaba wannan ne dalilin dayasa nadage da bibiyqrki har saida nakaiki gidan mu sannan nasami kwanciyar hankali da nutsuwa fateema tunda aka haifeni banyi soyayya ba nikwata kwata bansan soba saida Allah yahadani dake bayyanar gaskiyar lbrn dakika bamu ayau yaxamo wata iska da taqara rura wutar so da qaunarki axuciyata ina sonki fateema kidaure kisoni kisakani a xuciyarki, idankikayi hakan xaki sami ladar ceton rayuwa dominko ina tabbatar miki rayuwa fankoce indai babuki acikinta idan kikayi kuskuren qina kuwa saiyayi shiru hawaye suka fara bin kuncinshi yadibi dan lokaci ahakan sannan cikin wata disasshiyar murya yace idan kikaqini fateema ba makawa mutuwa xanyi, yaja numfashi tareda share hawayen fuskarshi Allah sarki rayuwa fateema yarinya ce mai matuqar bawa soyayya girma da daraja tayarda da SO kuma tana tausayin duk wanda yafada cikinsa, kuku tafarayi ciki ciki wai yau itace ake bararr soyayya daga gareta itace qasaitaccen mutum kamar wannan yake tabbatar mata xai iya mutuwa sbd ita, yau itace awannan matsayin.................. tsugunawar da fa,eex yayi agabanta itace ta katse mata wayannan tunanikan aganta ya tsuguna bisa guiwoyinsa idonshi na fitarda qwalla yace fateema ni bawane ga soyayyarki ta takurani ta hanani sukuni pls fateema nariqeki kada kibari in rasaki kitaimakeni wlh ina qaunarki fateema wlh nibasan haka SO yakeba dan Allah kisoni wlh inkika qini xan mutu mutuwa xanyi fateema Kuka mai qarfine ya qwace mata ba shakka Allah (s,w,a) yayi gaskiya tabbas shidin mai rahamane ga bayinsa fateema ta taso tana soyayya batada wani burin dayawuce asota amma hakan bata samu ba ayau kuma daga wani wajan Allah yafiddo mata dawani masoyin daban wanda xai iya bada rayuearshi ya ceci tata, aranta tace tabbas wannan damace taxomin wadda xata ceceni daga abinda nake tsoro daga iyayena wato mayarda aurena ga *yaya fahad* haqiqa xanyi qoqarin cusaka araina fa,eex koba komai kana nunamin So abinda nafiso arayuwata kenan xankoyi sonka natabbatar baxansha wahalar sakaka a xuciyata ba Wannan duk maganar xuciyar fateema ce alokacinda ta kafe fa,eex da ido ko qiftawa babu, shikuwa alokacin neyasami damar qarewa fuskar tata kallo alokacin yaqara tabbatarwa kanshi tabbas fateema itace matarda yake muradi komai nata 100% dana matar da yakeda burin yasamu tsawan shekaru Sun qurawa juna ido bamai so yaqifta domin kuwa ita fateema tunani takeyi axuciyarta sam batamasan irin kallonda takewa fa,eex kenan ba, shikuwa hakan datayine yabashi damar kallon nata, duikaninsu sunyi nisa da abinda sukeyin Qarar bugun qoface tadawo dasu hayyacinsu tafirgigit tagyara xamanta akan kujera shikuma yamiqe daga tsugunon dayayi agabanta saida yasaka handkerchief yashare fuskarshi sannan ya isa ga qofar yabude qofar dan aikane daga mai martaba yadawo hayyacinshi yana buqatar ganinsu duka *Nasmy ce*😍 Yar mutan arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐ ⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•216/220•* Daga inda take tanajin abinda dan aikar yake fadi tamiqe xumbur tana sharar qwalla wanda hakan yayi daidai da shigowar dady da momy falon kallo daya sukayiwa yaran suka tabbatar kowannensu yayi kuka ganin fa,eex shiru2 yahaifarwa momy da faduwar gaba kardai fateema bata karbi soyayyarshi ba shikuwa abinda ya susuta shi shine fateema bata bashi kalma kodayaba xuk da cewa bai hango qinshi a idonta ba amma yafiso yaci daga gareta koxai sami sassaucin xogi da radadin xuciya Asanyaye yasanar dasu saqon mai martaba suka ce alhmdllh to ai saimutafi kawai momy ta kama hannun fateema dady yai gaba suka rufa mishi baya Adakin mai martaba kuwa shikadaine kishingide a kan makeken gadonsa sukayi sallama bayan anmusu iso suka shiga duka suka gaisheshi tareda yimishi yajikin ya amsa dasauqi sosai fateema har gabanshi taisa taxauna agefenshi su dady nadan nesa dasu kadan ahankali yafara magana yace yihaquri yata natura akiramin yayan naki sannan nakira baffanki suna hanya insha Allah xuwa anjima duk suna nan yamaida kallonshi ga dady yace alhji nagode ubangiji Allah yasaka maka da mafificin alkhairin sa Allah yabiyaka dady ya amsa da ameen ya rabbi Allah yabawa sarki lfy shima yace ameen Da sallama aka turo qofar dakin gabadaya suka juya dan ganin mai shigowa umman yarima ce dakuma shikanshi yariman Wanda saida tasha fama sosai kafin tasamu yafito daga gidanshi domin amsa kiran mai martaba Bayariman ba hatta umman ganin fateema xaune agefen mai martaba yayi matuqar girgixata harsaida takasa boyewa tace fateema fuskarta cikeda mamaki fatee takalleta kawai amma bata amsa mataba ganin yarima saida yamotsa xuciyar ta saitayi gaggawar kawarda kanta gefe, shikuwa yarima qirjinshi ne yashiga dukan uku uku qwaqwalwarshi taso ta tunano mishi wani abu amma hakan yafaskara saidai dunbin damuwa dayaji ta mamaye duk wani saqo da lungu na xuciyarsa adarare suka qarasa gaban mai martaba suka xaxxauna suka gaisheshi tsoro da firgici qarara afuskar yarima xuciyarshi tahau bugu kamar xata fallo qirjinshi tafito, fa,eex yabishi da kallon raini wanda shi yariman baimasan daxamanshi agunba dattijan ya yunqura ya daidaita xamanshi ya fuskance su sannan yace yarima fahad ayau wani mummunan labari riskeni cewa kasaki auren dana daura maka da qanwarka fateema shin gaskiyane? Hannu yasaka yashare guminda ke yankomasa yagama rudewa amma dayake yasan halin wanda keyimasa tambayar yasa koda wasa bayyi tunanin fada mishi qaryaba wata tambayar yakoma jeho mishi yace kainake sauraro shin gaskiyane kasaketa? Eh abba...........tasss yaji saukar wani raxanannen mari afuskarsa wanda yahaifar mishi da jiri saida kowa adakin ya raxana nandanan lafiyayyar fatar fuskarshi tayi jajir fatarda sam bata taba sanin xafin dukaba idonshi suka kada kamar gauta Yadafe kuncinshi yana jinjina girman abinda yasaka abbanshi ya iya dukanshi xumbur ummanshi tamiqe tahau sababi a ah dakata mai martaba dafa d`afake gani baifi d`a ba akanme xaka dakeshi akan yar dan uwanka tafishi agunkane? To wlh ni tunwuri kasani baxan taba bari aure ya yuwu tsakanin yarima da fateema ba, kuma wani abu dabakasaniba na hada auren yarima da yar yayata laxeera yau kwanaki biyu da daura auransu harma da tarewarsu sbd haka kasanyaya xuciyarka karma kayi wani tunanin gyara auren nan wlh baxan lamunta ba Tunda tafara maganar bawanda ya katseta saidai bawanda baiji abin awani daban ba musamman fateema saita tsinci kanta da jin xafi daciwon auren laxeera da,akace yarima yayi duk dacewa ayanxun ba qaunarsa takeba shikuwa fa,eex maganar umman yarima tafimasa komai dadi arayuwashi na cewar datayi baxata taba bari agyara wannan auren ba, falon yayi tsit kowa da abinda ke yawo axuciyarshi *Nasmy ce*😍 Yar mutan Arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐ ⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•226/230•* Umma Gabaki dayan Idanunta ta War-waro Innalillahi mai Martaba? Mexan gani haka? Mekake nufi? Sakina Kayi wai? Nashiga uku Dangirma Da Darajar Allah Kayi Haquri Kamaidani Kafi kowa Sanin Iyayenmu Sundade da Mutuwa wlh Banida kowa sai yayata Kataimakeni, taja Guiwa ta isa Ganasa sai Alokacin tasamu damar Fashewa da kuka tayi Magiyar Duniyar nan amma sarki ko Kallon Gefenta bai koma yiba, baffa da goggo ma duk jikinsu amace ko Magana sun kasayi, Bashir kuwa jiyake da Dahukunci dayafi hakan dashi Xa,aimata haka tagaji da Gunjin Kukanta ta tashi fita, Lokacinda tafita me Yarima yasami Damar Miqewa Shimadai Barin Dakin yayi Xuciyarshi Cikeda Takaici da Tashin Hankali Tunda yake Abbanshi Baitaba fushi dashiba Ballantana yai Tunanin Dukanshi, Gashi ayau ba wanda bai Samuba, Agaban kowa da kowa yace babushi-babushi harda Korarsa daga Gidan, yasaki ummanshi yasalam! Damuwa tarigada tayimasa yawa Jiyake kamar ya kurma Ihu, yana Tafiya yana Waswasi Kokadan Baya Ganin Abindake Gabansa Ikon Allah ne Kadai Yakaishi Sashenshi, Afalo yasami Sarauniyar tasa Tamiqe Akan Doguwar kujera, tasha make-up taci ado da Wata Damammiyar riga ta roba Gajera ce Bata wuce Cinyarta ba, Tana Ganinshi Tamiqe Dasauri ta Taroshi da Murmushin nan na kissa a Fuskarta ta Rungumeshi kafin takai masa kiss a Gefen Fuskarshi, yasalam! Frnds muji Tsoron Allah kuma Muji Tsoron Asiri, Tabbas Hausawa sunyi Gaskiya dasukace Tsafi Gaskiyar Maiyinsa, Duk Tsananin damuwa da Tashin Hankalinda Yarima Yashiga yanayin Arba da Laxeera Yanemi Damuwar Yarasata Hankalinsa Yakwanta Rayuwarsa Tadawo Tsaf! Sam Yamantada Mahaifin Nasama Ballatana Wani Abu daya Hadasu, Nandanan suka lula Wata Duniyar Baikoma Tunanin Mahaifiyarsa ba Balle Halinda Take ciki Umma Tashiga Rudu hadida Matsanancin Tashin Hankali Kuka take Kamar ba Gobe, Da Lalube tanemo Lambar Yayarta Wato Mahaifiyar Laxeera cikin Kukan Tasanar Mata Duk Abinda Yafaru Saida Tagama Bayanin sannan umman laxee Ta Katse wayar Batareda tace da ita Wani Abu ba, Matuqar Mamakine Yakama Umman Yarima Takafe Wayar da Ido Kamar Xataga Fuskar Yayar tata Aciki, Taxata Yankewa wayar tayi Shiyasa takoma Danna kira wayartayita ringin Harta Yanke Ba,a dagaba, Ganin Abin Xaicimata Lokaci Yasa Tafara Hada Kayanta Tanayi Tana xubda Hawaye Umman Laxee kuwa Tanaganin Wayar Umma Dagan-gan Taqyaleta Aranta kuwa Cewatake Anxo Wajan................... Tadauki Waya Takira Laxeera Tashaida Mata Cewa tayi duk Yanda Xatayi Tafiddo Yarima daga Gidan nan Yadawo Hannunsu Tayanda Xasu Tatseshi Yanda Sukeso. Shikuwa mai Martaba da Hawayenshi yaita Rarrashin fateema dakuma roqonta gafara yace" fateema kiyi haquri bansan fahad xaiyimini hakaba wlh daban hada auren nan ba, yajuya ga baffa shima dai kukan yakeyi yaita bashi baki daban haquri. Agidan suka kwana haka su momy ma sashe daya aka hadesu goggo tayita yimasu godiya Gariya waye har baqi suna shirin tafiya wato su momy da dady dakuma fa,eex amma basu koma ganin fateema ba tun daren jiya taboyr kanta, babuta babu Alamarta. Fa,eex yaga har anmusu rakiya a inda sukayi parking amma babu fateema, gashikuma babu damar tambaya dan mai martaba ne dakansa yayomusu rakiya tareda baffa da bashir yayan fateema, gata babu waya ahannunta balle yayi tunanin kiranta koda sunje gidane Dabaru yayi yakarbi number yaya bashir dan yatabbatar da ita xasu tafi Akayimusu gomasha na arxiqi sukayi sallama suka tafi xuciyoyi cikeda abubuwa daban-daban soyayya, waswasi, mamaki dakuma tausayin fateema....................................................Nikaina Nasmat Abinda ya Mamayeni Kenan Bansan Lokacinda Alqalamina ya Subuce ba *Readers Kumin Afwa Anan Xan Dakata Sai Kutareni After Ramadan, Wato Bayan Salla Domin jin Cigaban Wannan Labarin na Yaya Fahad Nawane, Dominjin Mokomar Rayuwar Fateema, dakuma Qarshen Tirniqin Tsafinsu Laxeera da Yarima Fahad, shin ya Tsakanin Umman Fahad da Umman Yarima Xai Kasance? Hmmm Muhadu A Bayan Salla Dominjin Qarshen Wannan Badaqalar, Fata anan Shine Allah Yasa Munada Rabon Ganin Lokacin* *Nasmat tana muku fatan Alkhairi Gabadaya Madoyana Happy Ramadan Kareem* Masoyan gaske Maimuna Ibrahim isah Sis Hawwa Asiya Isa Baby Maryam Ruqayya Sis Ama Nadiya Zeesah Mmn zee Mom Nasren Action baby Unique *da Gabadaya Members na Nasmat Novel group, Ina sanku kuma ina Alfahari daku Allah ya Albarkaci Rayuwarmu dakuma ta ya'yanmu baki daya, Zanyi akewarku Sosai, love you all*😍 Jinjina ga qungiyar : *Zamani Writers Association* Allah Yaqara Daukaka da Farin Jini Ameen ya Rabbi🙏 *Nasmy ce*😍 Yar Mutan Arkilla Love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐ ⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•221/225•* Mai martaba baiceda umma komaiba yarima kuwa ko motsawa yakasayi daga inda yake sai matsar qwalla yake axajiri wani sashe na xuciyarshi yafara nadama akan abinda ya aikata wanda shikanshi baisan dalilin yinshi ba, fateema kuwa kuka tahauyi baji ba gani momy tajanyota jikinta tana rarrashi, yayinda dady yake bata baki, fa,eex kuwa jiyake kamar ya dauketa subar wajan yaje can wani kebabben guri ya rarrasheta domin yanajin kukan harcikin kwanyar kanshi Adaidai lokacin ne akaturo qofar da sallama baffane tareda goggo dagudu fateema ta tari mahaifiyarta suka rungume juna matsanancim kukan da fateema take yatsorata goggo yayanta bashir ne yajata jikinshi xonan qanwata meyasameki haka? Takasa magana tayi shiru ta kwanta lif ajikinshi abinda yakusa yasaka xuciyar fa,eex bugawa sukanemi guri suka xaxxauna, suka gaisheda mai martaba da umma wadda take faman huci kamar xata fashe goggo taqara tsinkewa da lamarin kardai duka tayiwa fateema,? Kai inaa ai baxaiyiwa ba wannan duk maganganun xuciya ne, yarima yagaishesu cikin wani yanayi ba boye2 sunriga sun fahimci ba lfy ba, saidai koma mene ne to dasauqi tunda Allah ya bayyana musu yar'su fateema Suna cikin gaisawa dasu dady da momy ne aka kuma turo qofar da sallama wannan karon su waxirin sarki ne da shamaki dakuma mai fada. Wayannan sune manyan mutanenda mai martaba yake shawara dasu kafin ya yanke duk wata shawara data shafi fada, ganisu yasaka jikin umma da danta yarima yayi sanyi bashiri tanemi guri taxauna. Suma suka xaxxauna suna sauraren mai martaba Yafara magana Ahankali kamar bayasanyin maganar bakomai bane yasakashi yin hakan saidan tsananin mutuwar jiki da nauyin bakinshi dayakeji adalilin wannan baqin cikin da yarima da mahaifiyarsa suka haifar masa , yace " Ayau kuma awannan lokacin agaban wayannan mutanen masu daraja da mutunci a idona, Na cire yarima fahad daga rayuwata na yafeshi duniya da lahira, sannan na haramta mishi gadon sarautata kobayan rayuwata bana buqatarshi kusada gawata in fact ina buqatar yabarmin gidana dashida mahaifiyarshi sunisanta dani dakuma masarautata ayau basai gobe ba.............innalillahi wa inna ilaihi raji,in abinda gabadaya mutanen dake wajan suke ambato kenan Yarima kuwa baikoma jin komaiba kamar yadda yadaina ganin komai adalilin daukewar da ji dakuma ganinshi sukayi lokaci daya, wani irin bugu xuciyarshi tahauyi kamar xata fallo qirjinshi tafito waje, kanshi yahau sarawa da qarfi Umma kam awurin tasuma daga xaunen datake Fateema ta qara fashewa da kuka Baffa kam miqewa tsaye yayi ya isa gaban yayanshi "haba yaya haba yaya mekake shirin aikatawa haka? Me yarima da hjya sukayi wanda yakai kayanke musu wannan dayen hukunci? Mai martaba cikin daga murya yace "Auren damuka daura masa yasaki tunbaishiga dakin amaryar ba, dan uwana yarima yasaki fateema harma ya auri wadda yake So duk bada saninmu ba Baffa da goggo suka dauki salati shamaki dasu waxiri ma haka, Jikinsu yayi sanyi matuqa yaya bashir kuwa wani mugun kallo yashiga bin yarima dashi dan yariga ya cuci yar,uwarsa qanwarsa ya bata mata suna agari wanda hakan xai iya xama silar rasa mijin aure gareta, ace miji yasaketa a ranar farko data tare gidanshi wannan xai haifar mata da xargin mutane, yana kawowanan atunaninsa yafasheda kuka yaqara rungume fateema xuciyarshi fall da tsananin tausayinta Baffa bakoma cewa komai ba ya silale yaxauna awurin danjin danyen aikin da yarima yayiwa yarshi yatabbatar rayuwar fateema ta tarwatse, yarima yacuceta tunda quruciyarta ba mamaki naxata taba samun mijin aureba harta mutu indai a qauyen kukumba ne sbd wannan sakin da,akamata yanada gagarumar fassara acan qauye Goggo kam kuka take hani'an Mai martaba yarubuta takarda yasaka hannu yajefawa umman yarima wadda tundaxu sanyin a,c yadaketa ta farfado saidai ba laka ajikinta takasayin koda motsin kirki daqyar tamotsa ta dauki takardar Innan lillahi *Nasmy ce*😍 Yar mutan Arkilla love you all 😘 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐ ⭐ *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•221/225•* Mai martaba baiceda umma komaiba yarima kuwa ko motsawa yakasayi daga inda yake sai matsar qwalla yake axajiri wani sashe na xuciyarshi yafara nadama akan abinda ya aikata wanda shikanshi baisan dalilin yinshi ba, fateema kuwa kuka tahauyi baji ba gani momy tajanyota jikinta tana rarrashi, yayinda dady yake bata baki, fa,eex kuwa jiyake kamar ya dauketa subar wajan yaje can wani kebabben guri ya rarrasheta domin yanajin kukan harcikin kwanyar kanshi Adaidai lokacin ne akaturo qofar da sallama baffane tareda goggo dagudu fateema ta tari mahaifiyarta suka rungume juna matsanancim kukan da fateema take yatsorata goggo yayanta bashir ne yajata jikinshi xonan qanwata meyasameki haka? Takasa magana tayi shiru ta kwanta lif ajikinshi abinda yakusa yasaka xuciyar fa,eex bugawa sukanemi guri suka xaxxauna, suka gaisheda mai martaba da umma wadda take faman huci kamar xata fashe goggo taqara tsinkewa da lamarin kardai duka tayiwa fateema,? Kai inaa ai baxaiyiwa ba wannan duk maganganun xuciya ne, yarima yagaishesu cikin wani yanayi ba boye2 sunriga sun fahimci ba lfy ba, saidai koma mene ne to dasauqi tunda Allah ya bayyana musu yar'su fateema Suna cikin gaisawa dasu dady da momy ne aka kuma turo qofar da sallama wannan karon su waxirin sarki ne da shamaki dakuma mai fada. Wayannan sune manyan mutanenda mai martaba yake shawara dasu kafin ya yanke duk wata shawara data shafi fada, ganisu yasaka jikin umma da danta yarima yayi sanyi bashiri tanemi guri taxauna. Suma suka xaxxauna suna sauraren mai martaba Yafara magana Ahankali kamar bayasanyin maganar bakomai bane yasakashi yin hakan saidan tsananin mutuwar jiki da nauyin bakinshi dayakeji adalilin wannan baqin cikin da yarima da mahaifiyarsa suka haifar masa , yace " Ayau kuma awannan lokacin agaban wayannan mutanen masu daraja da mutunci a idona, Na cire yarima fahad daga rayuwata na yafeshi duniya da lahira, sannan na haramta mishi gadon sarautata kobayan rayuwata bana buqatarshi kusada gawata in fact ina buqatar yabarmin gidana dashida mahaifiyarshi sunisanta dani dakuma masarautata ayau basai gobe ba.............innalillahi wa inna ilaihi raji,in abinda gabadaya mutanen dake wajan suke ambato kenan Yarima kuwa baikoma jin komaiba kamar yadda yadaina ganin komai adalilin daukewar da ji dakuma ganinshi sukayi lokaci daya, wani irin bugu xuciyarshi tahauyi kamar xata fallo qirjinshi tafito waje, kanshi yahau sarawa da qarfi Umma kam awurin tasuma daga xaunen datake Fateema ta qara fashewa da kuka Baffa kam miqewa tsaye yayi ya isa gaban yayanshi "haba yaya haba yaya mekake shirin aikatawa haka? Me yarima da hjya sukayi wanda yakai kayanke musu wannan dayen hukunci? Mai martaba cikin daga murya yace "Auren damuka daura masa yasaki tunbaishiga dakin amaryar ba, dan uwana yarima yasaki fateema harma ya auri wadda yake So duk bada saninmu ba Baffa da goggo suka dauki salati shamaki dasu waxiri ma haka, Jikinsu yayi sanyi matuqa yaya bashir kuwa wani mugun kallo yashiga bin yarima dashi dan yariga ya cuci yar,uwarsa qanwarsa ya bata mata suna agari wanda hakan xai iya xama silar rasa mijin aure gareta 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *Assalamu Alaikum masoya na, masoyan "yaya fahad" novel barkarmu da dawowa hutun salla. Da fatan dukkanin ku kunyi salla lafiya, Allah (s.w.a) ya karbi ibadodin da mukayi.* *Fans kumin afwa da rashin dawowa bakin aiki da wuri, hakan yafaru ne a dalilin matsalar dana samu nayi jinya sosai amma yanzu kam Alhmdllh naji sauki kuma insha Allah zan kawo muku karshen labarinku har ma mushiga sabo daku.* *Ku kasance dani u will always been in happiness guys, keep smiling 😀 masoyan Yar'mutan Arkilla* ANA TARE 😍🤝 *•231/235•* Fateema kuwa tana can saman bene daga d`akin mai martaba tana kallon duk abinda ke wakana, tana kallo Fa'eez da iyayen sa sukayi sallama da kowa suka shiga motar, Fa'eez shine na karshe a shiga motar dan tsayuwa yayi yana nazari kamar mai jiran wani abu kai da gani kasan bayason tafiyar ko kuma wani abu ne yake bukata kafin ya tafi, daga karshe dai bisa dole ya shiga motar direba ya tayar suka fice. Sam bataji dad`in kaucewar fuskarshi daga ganin ta ba, a wannan halin da take ciki ta tabbatar a yanzu babu SO a ranta sai dai ta yarda kallon fuskar yaya Fa'eez na d`aya daga cikin ababen dake rage mata rad`ad`i da zogin abinda yarima yayi mata. Tayi nisa sosai a cikin tunanin da take saiji tayi an dafata ta baya juyowar da zatayi sai taga Bilki ce d`aya daga cikin kuyangin dake mata hidima idan tazo gidan. hakan yasaka ta fad`ad`a fuskarta da murmushi domin ta saba dasu sosai "Bilki ya dai, ina Rukayya? " ta fad`a cikin ko'karin ta na boye damuwar da take ciki. Bilkin ma murmushin ta mata kafin tace " ranki ya dad`e wlh ni kad`ai nake kuma wurinki nazo zamuyi magana kafin su goggo su dawo" Fateema ta kalleta cike da mamaki ta ce "magana Bilki?, to ina jinki Allah dai yasa lafiya" Bilkisu ta karayi kusa da Fateema sanna tayi kasa da muryar ta ta fara magana a hankali cikin rad`a tace " wlh anty fatee yarima na matukar kaunar ki, Fateema ta d`ago da sauri dan ko kusa ba abinda tayi tsammanin ji kunnen ta yaji ba. kamar zatayi magana sai kuma Bilki ta katseta ta hanyar cigaba da cewa " wlh yana sonki sai dai an riga an fi karfin sa, alamun mamaki karara a fuskar Fateema take kallon Bilkisu. tace "eh wlh fin karfin sa akayi dan asiri akayi mishi Umma ce da Hajiyar Lazeera ke harma da Lazeeran, anty Fatee nida nake nan nizan gaya miki komai yanda yarima ya tsani anty Lazeera da can wlh ko gunda yake zaune bata isa ta raba ba, idan ya ganta ji yake kamar ya kasheta saboda sha'shanci da rashin kamun kanta." Nan dai Bilkisu ta kwashe duk abinda ta sani ta shaidawa Fateema. Allah sarki hausawa suka ce sauran SO yafi sauran KIYAYYA domin kuwa cikin kan'kanin lokaci tsanar da Fateema ta yiwa Fahad ta juye ta zama tausayi Jikin ta yai sanyi matuka tausayin yayan nata ya kamata soyayyar shi kuma ta dawo sabuwa fill a zuciyar ta, cikin zubda hawaye ta kalli Bilkisu tace "na gode Bilki da kika sanar dani wannan sirrin kafin nabar garin gwambe tabbas ba inda zani har saina ceto d`an'uwana kuma miji na daga wannan halin da yake ciki, na gode da kika gayamin tana shirin rabashi da gidan nan ina tabbatar miji cewar bata isa ba, wannan gidan namu ne, masarautar gombe tamu ce, kuma *YAYA FAHAD NAWA NE* na rantse miki saina karbo Abina" ta fad`a tana share kwallar dake fitowa daga idanun ta. zuciyar ta ta riga da ta dake ta rika hannun Bilki dan su koma babban falon Juyawar da zasuyi sai sukayi kicibis da duka iyayen nata Baffa da Mai martaba Goggo da yaya Bashir dukkanin su sunyi jugun-jugun alamu sun nuna ba abinda basuji ba daga hirar tasu. "Ya Rabbi" Fateema ta fad`a tare da sunkuyar da kanta kasa Bilki kam tsoro ne ya baibayeta. Mai martaba da kanshi yaja hannun Fateema tareda cewa Bikkisu "kema biyo ni" yayi gaba su Baffa suka rufa masa baya kafin Bilki itama tabi su sumi-sumi *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•236/240•* _Wannan shafin sadaukarwa ne gareka fasihi matashin fikira,fasaha, da d`inbin basira dole muyi alfahari da kai autan writers_ *KING BOY ISAH* _Allah ya kara baiwar brain kuma ya kara d`aukaka *ZAMANI WRITERS*🙏 Bai tsaya babban falonshi da suba har d`akin baccin shi ya kure dukkanin su suna biye da shi a baya. haka yaje ya zauna a wata kayatattar kujera dake d`akin sannan ita ma Fatee ya zaunar da ita gefen shi, su Baffa ma zaman suka yi a matukar rauna ne saboda maganar da suka ji ta gama kashe ilahirin lakar jikin su. Mai martaba yayi hmgyaran murya sannan ya kalli Bilkisu yace "shin ki tabbatar abinda naji daga bakin ki gaskiya ne?" Bilki cikin rau'rawar murya tace "eh-eh Allah ya taimake ka, wlh gaskiya ne ba'abinda na dad`a wlh inajin su kuma sau tari ina gani suke aikata wasu sirrukan. tayi shiru, iyayen suka cika da al,ajabi ya yarda dan yasan halin Umma sosai kawai kawar da kai yakeyi a zama da ita kasancewar shi mai sarautar babban birni sakin Aure ba nashi bane, yau d`in ma dan ta kaishi kwano ne. tunani ya shiga yi da nazarin abinyi, d`akin yayi tsit ba abinda ake ji sai karan (a.c) Idan ka d`auke Fateema da Bilki kowa a wurin tunani yake yi na hanyar da za'a bulluwa lamarin, Faeema kuwa tun kafin su shigo d`akin ta samu way out a zuciyar ta, hakan ne yasaka batayi kasa a guiwa ba wajen sanar da iyayen nata sai dai kafin tace wani abu Baffa ya rigata da cewa "to kaji fa yaya yanzu yaron nan duk abinda yakeyi ba bisa hayyacin sa bane, gashi ka yanke masa tsatstsauran hukunci". Goggo tayi caraf tace "to yanzu yaza'ayi kenan meye mafita akan wannan lamarin?" Shirun da taji Mai marta yayi shine ya bata damar amayar da abinda ke zuciyar ta, sai da ta sunkuyar da kanta kasa sannan ta ara magana cikin ladabi da sanyaya murya tace "Ya'baffa tunda abin hakane ni inaganin kayi hakuri kawai kamaida aurena da yaya fahad, kuma ka hanashi barin gidan nan sai afara nemo masa magani da abubuwan karya asiri, ni kuma nayi muku alkawarin zan shanye duk wani wulakanci da cin zarafin da zasu yimin har zuwa lokacin da zamu samo hankalin sa, domin ni a ganina wannan ce hanya mafi sauki dazamu bi mu ceto rayuwar shi. Mai martaba ya kafe yarinyar da ido tsananin tausayin ta da hakuri da kuma zurfin tunanin ta sun burgeshi. Ahankali yayi gyaran murya sanan ya fara magana "Fateema Allah (s.w.a) yayi miki albarka irin tunanin kinan shine ya zomin a zuciya ta sai dai ina nazarin yanda zaki d`auki lamarin keda iyayen ki idan na furta, sai gashi kin fad`a da kanki ba abinda zan ce saidai Allah yayi miki albarka kije d`akin ki zamuyi magana dasu waziri". Fateema ta mike zuciyar ta cike da was'wasin abinda ta ballowa kanta anya zata iya kuwa? haka dai ta fice Bilkisu na take mata baya. Kai tsaye sashen ta ta nufa inda ta fara tarewa har takai ga ko'far Bilki tayi saurin riko hannun ta, tajiyo da sauri a d`an razane Bilki tace "ki gafarceni anty a yanzu Yarima da Amaryar sa ne ke rayuwa a d`akin ki na da kiyi hakuri kishiga d`ayan part d`in tunda shima akwai komai a ciki gyara ne kawai wancan yafi dayan dashi". Wani shu'umin murmushi Fatee ta sake wa Bilki kafun tace " Ai wannan da kika gani shine asalin gida na saboda ni aka gyara shi, kuma ni nafara tarewa cikin sa saboda haka babu wanda ya isa ya hana ni zama a cikin sa, bata jira me Bilkisun zata ceba. kawai saita kunna kai a babban falon dayake shine farkon shiga gidan, subhanallah! Tafad`a da karfi a dalilin abinda idon ta yayi arba dashi ta kawarda kanta gefe Bilkisu kam waje ta koma da gudu tun Yarima bai ganta ba, Yarima ne da Lazeera suketa shagalinsu har sun fara barin duniyar da suke ciki sai yar karar da Fateema tayi ce ta dawo dasu hayya cin su, cikin kad`uwa da mamaki Lazeera tamike zumbur tazubawa Fatee ido taga yarinyar tayi fresh ta goge fuskarta fayau ba make-up amma hakan bai hanawa sihirtaccen kyawunta bayyana ba. Yarima kam kusan d`aukar abin yayi ba gaske ba dan a tunanin shi daga inda yabar ta bazai koma ganin ta ba. Dukkan su dai sunyi nisa Fateema tayi murmushi ganin yanayin data jefa su a tashin farko. Lazeera ce ta daure ta kauda shirun cikin dakewa ta dakawa Fateema tsawa "ke jaka meki ka zo yimin a gida?" Wani irin juyi Fatee tayi da idonta tace gidan ki ko gida na? Ba Laxee kad`ai ba hatta Yarima sai da maganar ta girgiza shi, Lazeera kam zuciyar ta tagama rufewa me wannan yarinyar take nufi? Juyowar da zatayi sai ganin Fateema tayi zaune akan kujera ta d`ora kafa d`aya akan d`aya tana jijjigawa har Lazee ta d`aga baki zatayi magana sai Fateema ta tari numfashin ta da cewa "kinga malama idan kinada abin da kikazo da shi nan to kiyi gaggawar d`auka ki fice dan mai gidan ta dawo shi wanda ya aurekin bashida wani wajan da zai ajiyeki ne? Mintuna biyar su na baki ki tattara kibarmin gidana" ta karashe zancen cikeda gadara da rashin tsoro. Cikin d`aga murya Lazeera tace "kan uban can lallai yarinyar nan kin rainani wlh kuwa yanzu zakiyi laushi a gidan nan" ta daka tsalle tayi kan Fateema da nufin dukan ta sai a lokacin Yarima ya motsa da sauri yasha gaban Lazee yace haba my dear yanzu akan wannan yarinyar zaki wahalar min da jikin ki?, Noo ba sai ke ba barni da ita kawai Ya juya ya fuskanci Fateema yace "ke me kikazo yi a nan d`in? Ko bakisan mata da miji ne suke rayuwa a nan ba? Bai jira amsar taba dan yasan batada abun cewar ya ci gaba "tashi ki kifita" ya fad`a yana nuna mata hanya banza tayi da shi kamar bada ita yake ba, taci gaba da jijjiga kafar ta "keee! Ba da ke nake magana ba" Ya daka mata tsawa saida ta razana a zuci amma bata yarda ta nuna a fuska ba Fahad ya gama cika da takaicin ta dan ya tsani a kawo masa raini a lamuran sa shima dai kanta ya nufa da nufin d`aukar ta ya wurgata waje Tsoro ne ya dirar mata taji kamar ta ruga waje kafin ya iso gareta amma inaaa zuciya ta dake ko gezau batayi ba, baifi taku uku ya rage ya isa gareta ba suka jiyo sallamar Sarkin gida a kofar falon *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•241/245•* Wannan shafin kuma naki ne kawa ta gari abar fahari sis *AMA ALHAJI KABIR* U mean more than a friend to me, u are nown my sister. keep trying sis I believe one day our dream will be come true *INSHA ALLAH* Tsayawa yayi cak ! Sannan ya juya ya nufi kofar ba tareda ya amsa sallamar ba. Daga inda suken suna jin naganganun da sukeyi shida Sarkin gida sako ne daga Mai martaba cewa yazo yanzu yana son ganin sa, ai kuwa kaitsaye yabi d`an aikar suka tafi tare. Nan akabar Fatee da Lazeera suna kallon kallo kafin Kazeerar taja dogon tsaki ta bar falon ta shige bedroom d`inta ta bankowa Fateen kofa, Fateema tabi bayanta da murmushi mai d`aukeda sakon zaki fito ne Tana shiga ta d`auki wayar ta ta dannawa lambar hajiyar ta kira, ringing biyu a na uku aka d`aga wayar da "hello Doughter na" cikin shagwaba ta amsa "momy wai meke faruwa ne Fateema nagani a sashena wai hadda cemin infita in bata gidan ta, badai ta dawo gidan Fahad ba?" Momy tayi shiru na d`an lokaci sannan ta ce "ki kwantar da hankalin ki Fahad kam yanzu ai naki ne sai yanda kikayi dashi yanzu gayamin me ya faru?" Nan ta kwashe duk yanda akayi ta gaya mata. Tace to banda abinki inma dawowar tayi ke ina ruwanki tunda miji ake yiwa kishi kuma yana hannun ki kedai kawai ki dage ki cigaba da amfani da nagungunan da boka ya baki kinji" ta amsa da "to Momy Nah lov u bye!" A d`akin Mai martaba kuma manyan mutane nan ne wayanda ya tara su daga farko dasu Baffa sai Fahad daya shigo daga baya ganin taron ya tuna mishi da abinda ya faru tsakanin shi da mahaifinshi d`azu take idonshi suka kawo ruwa ya nemi guri a d`an nesa da uban ya zauna hawaye nabin kuncin sa. Mai martaba yayi gyaran murya ya kira sunan Fahad ahankali Yarima ya d`ago idonshi tam da kwalla ya kalli Abban nashi tareda cewa "na'am Abba" Mai martaba yace "nasan bakasan dalilin kiran danayi maka ba" ya d`aga kai alamar "eh" yace "to na kiraka ne akan abinda ya faru na hukuncin dana yanke maka d`azu shine zan janye amma abisa wani sharad`i guda d`aya" da sauri Yarima ya d`ago kai bakinshi har rawa yake yace "nagode Abba kafad`i sharad`inka nayi alkawarin zanbi shi ko mene ne shi mutukar bai saba sharu'ar Allah ba" dattijan ya gyara zama sannan yace "to madalla auren ka zan mayar da Fateema wato matarka zata koma gidan ka bayan saki d`aya da kayi mata, kuma inaso kayimin alkawarin zaka rike yar'uwar ka amana zaka zauna da ita ba cuta ba cutarwa, kar ganin hakan yasa ka wulakanta min yarinya Yarima muddin ka tozarta Fatee babu ni babu kai har abada". Gabad`aya d`akin suka d`auka "subhanallah" Yarima cikin kuka yaja guiwa ya isa ga mahaifin nashi kayimin afwa ka gafarceni Abba na wlh bana son bata maka kasani fushinka akaina ba alkhairi bane, nayi alkawari zan rike amanar Fateema Abba xanyi iya ko'karina wajen yin hakan" yana kaiwa nan ya fashe da kuka Mai martaba ya shafi kansa yace Allah yai maka albarka tashi ka tafi. Yarima ya mike ya koma gun Baffa ya tsuguna bakinshi har rawa yake yace "kayi hakuri Baffa ka yafemin wlh har ga Allah ina son Fateema bansan meke damu na ba dazarar naganta sai inji na tsaneta Baffa ka taimake ni kar in komayin wani abinda Abba na zai tsane ni" ya koma fashewa da kuka Allah sarki gabad`aya tausayin sa suke ji, dakyar Baffa ya rarrashe shi da kalamai masu sanyaya rai tareda bashi wasu manyan addu'oi na neman tsari da kariyar Ubangiji (s.w.a) yace yaje yaji da matanshi duka biyun ya kasance mai adalci a agare su". Nan ma yayi godiya ya mike ya fita Suka bishi da kallon tausayi Mai martaba ya kalli Liman yace "gafarta Malam yanzu kuma sauran aikin naka ne kaje ka d`ebi sauran Malaman dake fada kuyi karatu a sauke Alkur'ani mai girma a yanka dabbibi ayi sadaka a gayawa Allah damuwar nan na tabbata zai yaye mana Yarima zai sami kanshi" gaba d`aya suka amsa da "insha Allah" yace "to na sallame ku" suka tashi suka fita d`akin ya rage daga shi sai Baffa da Goggo da kuma Bashir nan suka shiga ja'jantawa juna da godewa Allah daya bayyana musu wannan da wuri daga bisani su Goggo suka koma masaukin su suka bar Mai martaba ya huta. Yarima kuwa tafiya yake yana nazari yarasa inda tunanin sa ke zuwa idan yaga fateema gaba d`aya sai yaji ya tsane ta, idan ta kaucewa ganinsa kuwa ba abinda yake tunani sama da ita yasan yana mutukar Son Fateema amma idan yaganta sai tsanar ta ce take maye gurbin ti meye wannan? Ya tambayi kansa a lokacin da yake shia gidan nashi *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•246/250•* *Wannan shafin kuma naku ne Ilahirin members na NASMAT NOVELS GROUP ina mika d`inbin godiyata gareku sakamakon so da kaunar da ku ke nunawa littafi na, haka ku ma KING BOY ISAH NOVELS bazan manta ku ba Allah yabar zumunci da kauna Allah ya Albarkaci rayuwarmu da ta yaran mu Ameen* 🙏 Kamar yanda yabar Fateema haka ya dawo ya same ta hard`e akan kujera. Da sauri ya kauda kanshi daga kallon nata, dan gujewa jin haushinta. Ita kam ko kallon gefen shi batayi ba saida ya shigeta sannan tabi bayan sa da kallo, sai taga yayi sanyi kalau ko a yanayin tafiyarshi ma mutum zai fahimci hakan. Kai tsaye d`akin baccin Lazeera ya nufa kwance ya same ta ta kifu kan gado tana ta faman aikin na ta wato chat. Jin shigowar tashi ne yasa ta tashi ta zauna tana kallon shi cikeda mamakin yanda yayi sanyi ga wani uban ja da idonshi sukayi wanda ya tabbatar mata da kuka yayi. Mikewa tayi ta taro shi tareda rungumo gefen jikin shi "Ya Prince lafiya kuwa? Ya naganka haka?" dakyar ya d`aga hannu ya shafi gefen fuskarta "bakomai dear Mai martaba ne ya kirani yace yana so...." Sai kuma yayi shiru sakamakon fad`uwar gaban daya riskeshi a lokacin da ta kafeshi da ido sai yaji yanajin nauyi da tsoron gaya mata ance ya maida Fateema "meye yace wai?" Ta tambayeshi cikin d`aga murya, yayi shiru kanshi na sunkuye a kasa. ya Rabbi abinda yake nanatawa a ransa kenan baisan daliliba kawai tsintar kansa yayi da mugun tsoron bacin ran Lazeera. Kanshi na kasa yake gaya mata "kiyi hakuri ki had`o kananan kayanki zamu koma d`ayan part d`in can mubar mata wannan" Lazee ta zaro ido "mene?" "Inbar gidannan nan wai? hmmm ai bazai yuwu ba wlh bazata sabu ba wai bindiga a ruwa, kaje ka gaya mishi bazan fita ba nasan dai ba wanda zai ce haka sai shi to wlh bai isa ba..." Keee! Yarima ya katse ta da wata irin tsawa mai firgitarwa "mahaifin nawa ne bai isa ba?" ya tambayeta yana kallon cikin idon ta. Mamaki ne karara ya bayyana a fuskarta kodai asirin ya karye ne? Ta tambayi kanta sai kuma ta cije dan koma jarrabawa tace "eh shi d`in ko rama masa zakayi?" Yarima yaji kamar ya rufeta da duka amma ina azahiri rarrashinta ya hauyi da ban baki akan ta taimaka masa su barwa Fateema gidan, tare da alkawarin zai kara gyara mata wancan ita ma. Dakyar yasamu shawo kanta, da taimakon shi suka tattare duk wani abu dasuka zo dashi sannan ya fita yashigo da kuyangi biyar suka kwashe kayan suka fita, sannan su Yariman suka fito Lazee na gaba yana binta a baya d`auke da babbar jakar ta, ta wuce tana wurgawa Fateema kallon banza tanaji a ranta kamar ta rufe ta da duka, sosai tabawa Fateeman dariya, ta kuwa dara. sannan itama ta raka su da harara kafin ta make murya tace da yarensu na fulatanci ("kord`o reube") wato "bawan mata" da harshen hausa, a fusace ya juyo "me kika ce min?" Tace ni? Ta fad`a tana yatsina fuska bance komai ba. yanda tayi maganar ma abin kallo ne, ji yayi ta kara fusata shi ya dawo dabaya da nufin dukan ta, ta mike da gudu ta shige d`akin ta tana masa gwalo. ya tura kofar yaji a rufe gam sai kuma ya tsinci kansa dajin haushin hakan yaso ta tsaya yayita ganin ta koda yanajin haushin ta ne Lazeera ce ta daka masa tsawa a fusace to wai meye hakan? Wasa ma zaka tsaya yi da ita? Yarima ya turbune fuska da me zan tsaya wasan? yaja tsaki sannan ya rufawa Lazee baya dan ita tuni tayi gaba zuciyar ta na mata zafi da tiriri. Wai an maida Fateema yanzu zaman kishi zasuyi kenan? ta tambayi kanta uhum tayi wani murmushi inaa wlh bazata sabu ba ta dai dawowa gida amma ba Yarima na ba. Da wannan tunanin suka isa d`ayan part d`in wanda yake kusan had`e da na Fateema suna fuskantar juna ginin duk iri d`aya ne komai da ke nan akwaishi a can banbancin d`aya ne na gyare-gyaren da akayiwa na Fateema kaman sabanta fenti da zuba sababbin furnitures da kayan kitchen. Shine ya nemo wasu kuyangin suka gyare musu sashen tas! Akwai komai a ciki duk ba kowa a sashen hatta kayan abinci babu wanda babu sai dai ba wani dad`in ganin hakan yaji ba kasancewar gimbiyar tashi ba girki take ba a cewarta ba aikinta bane shi kuma Yarima baya iya cin abincin masu aiki sai dai su siyo su ci kullum suna hanyar restaurant abin na damun sa, haka dai aka gyare ko ina aka feshe da turaruka. Lazeera kam zaune take tamkar gumki ba um ba um'um hatta chatting d`inda ta mayar sana'a yau gagararta yayi duk abin duniya ya isheta, tunani take ta inda zata bullowa zaman ta da Fateema hanyoyin dazatabi ta killace Fahad take nema sai saka take tana warwarewa Fateema kam tana shiga d`akin tashiga gyare-gyare dan a cewarta bazata kwanta akan dettin su ba, tana cikin yi Bilki tashigo tareda Rukayya su suka taya ta ta canza was bedsheets ta kwashe kayan make-up dake kan mirror ta zuba wasu sababbi nacikin kayan lefenta, kayan ta kam suna nan ba'a taba mata ko tsinke ba. Lokaci d`aya sashen ya d`auke da kamshi na had`ad`d`un turarukan wuta sannan ne tasami damar fad`awa bayi tayo wanka su Bilki suka can cara mata kwakliya taji da fad`a sannan suka bata wuri tasaka wata doguwar riga ta material wadda awayiwa zubin ado na stones kamar ba d`inkata akayiba Wohoho wani irin kyau da sheki yadin ya kara mata hatta Rukayya da Bilki dasuka ganta saida suka kusan zaucewa gaskiya Fateema kyakkyawa ce ta gaban kwatance abinka da sabon jini kuruciyar ta gabad`aya ta bayyana a wannan kayan. Ta kalli kanta a nadubi tayi shiru a hakan na d`an lokaci kawai saiga hawaye suna bin kuncin ta,, cikin kad`uwa da mamaki yan'matan suka fara tambayar ta Rukayya tace "subhanallah anty Fatee lafiya kuwa, meyasa kike kuka? *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•251/252•* Fateema taja numfashi sannan ta share hawayenta da bayan hannunta tajuyo da jyau ta fuskanci Bilkisu da Rukayya tace "kuka ya zame min dole Rukayya ki kalleni, ki kalli kyan da Allah ya bani wanda ni kaina nasan inadashi, ga farin jini, bazan iya kirga muku samarin da suka soni ba, amma sabida jarraba ta rayuwa ban taba jin son wani namiji samada wanda nakeyiwa *Yaya Fahad* ba tun daga kurciya har girma haka yayita bautarda zuciya ta yana azabtar da idanuwa na, babu wani zuwa dazaiyi kauyen mu batareda ya sakani kuka ba, tun ina karama ya tsane ni, ba abinda yakeso samada ganin hawaye na, ni kuma ganin fuskarshi kad`ai ya ishi zuciyata farin ciki mara misaltuwa, yau takai ta kawo nazama matar auren shi amma duk da haka baya yimin kallon mutum ballantana inkaiga darajar matar shi, taja numfashi tareda share kwalla a karo na biyu tace tunda nake sau d`aya na taba ganin sona a idon Yarima a ranar da nazo nan a matsayin matar shi tabbas na hangi soyayyata a idon shi wannan ranar sai kuma daga baya ta rikid`e ta dawo kiyayya da tsana irin wadda bai taba nunamin ba koda a shekarun baya, wannan ne dalilin daya sa nayarda da maganarki tacewa asiri akayi masa ya ki ni kuma ya tsane ni domin kafin rabuwarmu naga sauye-sauye dayawa a tattare da shi," Tayi shiru kamar mai nazarin wani abu su Rukayya kuwa jikinsu ne yayi sanyi lis maganganun Fateema sun ratsa su hakika soyayyar datakeyiwa Yarima ga'garuma ce kuma abar kwatance. Can ta d`ago ta kalle su tace "shin ku bakuyi mamakin amincewata ta dawowa gidan auren Yarima ba? " gabad`aya sukayi shiru. Tayi murmushi tace "hmmm nasan zakuyi mamakin hakan saidai sam ba abin mamaki bane idan kukayi la'akari da irin son da nakeyiwa d`an'uwa na, sai dai fa kusani inada babban kalubale a gaba na" a tare suka kalle ta cikeda mamakin jin kukanta na neman tsananta cikin kukan tace "wlh yanzu gaba d`aya rayuwa ta abar tausayi ce na sadaukar da farin cikina domin ceto na iyaye na, na sadaukar da rayuwata gayin abinda ko alama banida ilmi da sanin yinshi, ya ake zama da miji ma bansani ba balle takaini yin kishi kishin ma da gogaggiyar mace yar'bariki, maibin bokaye da malaman tsibbo nashiga uku ni fateema na sanya kaina a hallaka" ta fashe da kuka rairas tayita raira abinta dakyar yan'matan suka rarrasheta tayi shiru Bilkisu ce ta fara magana "kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki anty Fatee indai wannan ne nayi miki alkawari zan taimaka mki da akwai wata Hajiya a babban layi take aikinta kenan horarda mata akan zamantakewar aure musamman kanana kaman ke, tana koya musu girke-girke da make-up, sanin makamar namiji, tana gyaran jiki, mace ta goge ta iya kowane irin dressing Hajiya Binta bata tsaya nan kad`ai ba akwaita da sani na ilmin addini a wurinta zaki sami addu'oi da nafilfilin da zaki rike domin kare kanki da kuma ceto mijinki daga hannun waccan shaid`aniyar" Cikin zumud`i Fateema "tace kai amma nagode Bilki a ina wannan Hajiyar take?" Bilkisu tace "a babban layi take nan bayan gidan sarauta saidai matsalar ita ce nan gidan ba'a fita kasafai haka sai dai na tabbata in akwai isassun kud`i Hajiya Binta zata iya zuwa har nan ta koyar dake komai. Fateema tayi shiru tareda kurawa Bilki ido kamar mai karanta wani abu a fuskar ta'ta, sannan ta nisa tace "to yanzu Bilki kamar nawa kike gani za'a bata kuma a ina zamu same su?" Bilkisu tayi shiru tana nazari kafin tace "wurin mijin ki za'ki samu mana, adadin su ne dai ban sani ba". Rukayya tace "kibari gobe idan mun fita zamu tambayo miki ita, kuma ma zamu karbo miki harda lambar wayar ta sai kuyi magana ko?" Fateema batasan sanda ta sake dariya ba tace "banda abinki Rakayya aini ban taba rike waya tawa ta kaina ba, sai dai tazo muje can mu same ta sai ayi maganar koya kuka gani?" Rukayya da Bilki suka kalli juna kafin suka fashe da dariya dukkan su Bilki tace "kai anty Fatee da abin dariya kike shin kin manta yanzu da da ba d`aya bane? Yanzu fa ke matar Aure ce "Rukayya ta cafe da "matar ma ta gudan Yariman gombe" suka koma saka dariya. Abinka da kurciya nan da nan suka manta da damuwar su suka bige da hire-hire, Fateema taji dad`in hakan sosai dan koba komai ta manta da damuwar Yarima. Haka Goggo tashigo ta same su sunata hira taji dad`i sosai da taga yarinyar tata bata saka damuwa a ranta ba, su Rukayya suka fice suka barta daga ita sai Goggo nan ne Goggo ta sami damar zaunar da Fateema tayi mata nasihohi masu shiga jiki tareda jan kunnen ta gameda kiriniya ta jaddada mata yanzufa tariga ta girma ba kaman da bane, harma ta tsorata ta da cewa "muddin ta fita bada sanin mijinta ba kafarta d`aya zatafi d`aya tsawo ta dawo d`ingishi" ai kuwa ta tsoratan dan harda kukan ta. Tace "to dan Allah Goggo ki rokamin shi yadinga barina idan na tambayeshin". Gogga tace "wannan ba matsala bane in Allah ya yarda zai barki" hakadai tayita lallabata har suka tashi tafiya. har wurin mota ta raka su tana makale da Goggo sukayi sallama harda kukanta, sai taji wani iri kamar ba gidan da tasaba zama ba *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•253/254•* Da gudu ta juya tanufi bangaren su,Mai martaba yabi bayanta da kallo na tsayin lokaci kafin ya gyad`a kai ya koma sashen shi. Sosai take bashi tausayi na zaman da zatayi a gidan Fahad saboda tabbatarwa da akayi baya cikin hayyacin sa. Fateema na shiga falon ta ta zube kan Capet ta shiga raira kuka mai ban tausayi, hakika ayanzu nikaina lamarinta ya fara bani tausayi. Tambayoyi ta shiga yiwa kanta a zuci "shin wane irin zama ne zatayi a gidan Fahad? Meye matsayin ta gareshi? Taya zata iya zama batareda fita ko'ina ba?" Sallamar su Bilkisu ce ta dawo da ita daga duniyar tunani-tunanin data tafi, a sanyaye ta amsa musu sallamar idanun ta sharaf da hawaye. wuri suka samu suka zazzauna shiru na d`an lokaci kafin Rukayya ta kauda shirun da cewa "Anty Fatee yanzu fa ba lokacin kuka bane, lokaci ne da zaki tashi tsaye da kafarki kiga kin kwaci mijin ki". Fateema ta kalle ta cikin yanayin rashin fahimta "ban gane ba" ta bukaci karin bayani. Rukayya tayi murmushi domin sanin wace ce Fateema da tayi. tace "da sannu zaki gane" ta kalli Bilki ta kashe mata ido. Bilki ta mike ta shiga bayi na d`akin Fateema ba jimawa ta fito tana Fad`in "na had`a" Rukayya ta mike rike da hannun Fateema suka shiga d`akin kai tsaye bayi ta zarce da ita da shigar su wani dadda'd`an kamshi ya musu marhaba Fateema ta lumshe ido tareda bud`e hancin ta ta shaki kamshin mai matukar kwantar da hankalin wanda ya ji shi, ta sake mata hannu tareda cewa "kiyi wanka ki fito, muna jiranki". tana gama fad`ar hakan nan ta juya ta fice tareda ja mata kofar Fateema ta since kaya ta shiga cikin bahon wankan ta kwanta shiru na wani lokaci mai tsawo dad`i da kamshin ruwan sun hanata tabuka komai, shiru kawai tayi kamar mai nazarin wani Abu. Karar bugun kofar ya farkar da ita daga nisan da tayi daga wannan duniyar wanda batasan abinda ya d`auke ta ba tsakanin bacci da tunani. muryar Rukayya ta ji tana fad`in Anty Fatee kiyi hanzari lokaci na tafiya. Sauri-Sauri ta wawwatsa su tafito badan tana so ba. Sallar azahar suka fara gabatarwa suka ci abinci sannan suka zaunar da ita akan dressing mirror suka fara tsantsara mata kwalliya Masha Allah. Fuskar nan ta fentu tasha kyau harta gode Allah. Bilkisu ce ta fiddo mata wata koriyar riga doguwa asalin rigunan gidan Sarauta tareda mayafin ta suka ce ta saka, sannan suka fice falo suna jiran fitowar ta Masha Allah wa tabarakallahu Ahsanal khalikeen! Bawai su Rukayya ba hatta ni Nasmy baki na sake ina kallon ikon Allah Fateema ce ta fito cikin koriyar rigar nan da Bilki ta fiddo mata tayi kyau tamkar yar'tsana kamar ba Fateen Goggo ba. Rukayya ta dafe hanci tareda rangad`a gud`a "gafara mahassada ga fitila, uwar gida sarautar mata, farar mace alkebbar mata, matar Yarima ikon Allah" gabad`aya suka kwashe da dariya. Yau ce rana ta farko da Fateema taji wani irin dad`i da aka kirata da matar Yarima! Ta zauna akan kujera tana kallon su tace "to ai sai ku gayamin dalilin wannan Uwar kwalliyar da kuka min?" Bilkisu tace "kina dai so ki sami kud`in da zamu biya mu d`auko Hajiya Binta ko?" Tace "eh" cikin zumud`i tana murmushi suma murmushin sukayi kafin Rukayya ta kama kunnen ta ta rad`a mata wani abu Fateema ta d`ago fuska a raunane ta kalli Bilkisu dake gefe tace "anya zan iya kuwa?" Bilki ta d`aga mata kai "zaki iya mana" Lokaci mai tsayi suka d`auka suna karfafa mata guiwa sannan ta mike tasaka wasu hills shoe da suka fiddo mata ta fice daga sashen tana rike bango Wai kar takalmin su yaddata. Kai tsaye sashen dake fuskantar nata ta nufa, kuyangin dake hidima a farfajiyar gidan sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa Da sallama ta shiga falon sai dai ba wanda ya amsa mata kasancewar falon shiru ba kowa. Bata jira komai ba ta nufi kofar da zata sadata da d`akin, shima dai tana murd`awa kofar ta bud`e idon ta fess akan su dai-dai lokacin da Lazeera ta doshi bakin Fahad da nufin sumbata tana kwance bisa kirjin shi akan gado. Wani uban ihu Fateema ta saki tayi tsalle ta hankad`e Lazeera daga kan Yarima tana rafka salati Hatta Yarima sai da ya tsorata ya mike a razane yana kallon ta tareda mamakin abinda ya shigo da ita nan kuma. Fateema bata damu da halin daya shiga ba ita kam Lazee take kallo cikin ido cike da mamaki tace "lallai Anty Lazeera bakida imani yanzu saboda Allah da kika danneshi haka kashe shi kike so kiyi?" Lazeera da ta gama kuluwa ta kalli Fahad dan ganin wane mataki zai d`auka akan Fateema? Ga mamakin kawai sai gani tayi yana murmushi *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•255/256•* Shi gaba d`aya yanayin yarinyar sai ya bashi dariya. Itafa a tunanin ta yanda Lazeera tayi akan shi zai iya cutar dashi, Fahad da baya dariya yau sai gashi yana kyelkyetawa, al'marinda yayi matukar kona ran Lazee ta juya ga Fateema "ke" ta daka mata tsawa "me kika zo yi nan bangaren?" Fatee da ahalin yanzu take jin haushin ta sai da ta murgud`a baki sannan tace "ina ruwan ki? gurin ki na zo?" cikin kuluwa Lazee tace "gurin wa kika zo?" "Gurin miji na" ta bata amsa a takaice "Kutumar uban can" Lazeera ta fad`a lokacin da tayi tsalle da nufin shako wuyan Fateema. Yarima ne yayi gaggawar shiga tsakanin su ya rike Lazeerar "meye haka? dukan ta zakiyi?" "Eh ko zaka rama mata ne?" ta fad`a a tsawance tana kallon shi cikin ido Fateema tace "he ai Wlh in gaya miki ba'a ramawa Fatee duka, da ya barki ki gani hmm" ta juya musu baya tana wani girgiza da karkad`a kafa (ni kuma Nasmy nace "yan iskan kauye sun motsa Liz) Yarima yabi bayan ta da kallo yanajin wani Abu na yawo a ziciyar shi, sai ya tsinci kansa da sha'awar yadda take lamuranta cike da kurciya. Shi kanshi ya san tsanar da yake mata ta ragu a ransa. A hankali cikin sanyin nan nashi ya raba jikinshi dana Lazeera wadda keta faman huci tana jifan Fateema da mugun kallo, ya zaunar da ita bakin gadon ba tareda yace komai ba yaja hannun Fateema suka fice fallo Tirkashi a wannan lokacin Lazeera ji tayi kamar numfashin ta zai yanke, zuciyar ta ta hau bugawa da matsanancin karfi. Fateema kuwa sai da suka kai kofa ta juyo ta dalla mata gwalo. Ta rumtse ido da karfi jitayi kamar an yanki naman jikin ta tabisu da kallon takaici na rashin abinyi ta san Yarima sarai ta kuma san halayen shi, dole ta zauna badan ran ta ya so ba. A falon kuwa sai da ya zauna sannan ya saki hannun Fateema wanda yaji kamar yaci gaba da riki shi, kujerar dake daf da tashi ya nuna mata yace "zauna" ba musu ta zauna tana mai tilasta idon ta barin kallon Yarima ta maida su kan yatsun hannun ta da take murzawa, a ran ta kuwa sake-sake take da tunanin taya zata tambaye shi kud`i?. Yarima Fahad ya zuba mata ido yana mata wani kallo da shi kanshi baisan dame zai fassara shi ba shin so ne, ko sha'awa? Tayi mishi kyau sosai kamar su dawwama yana kallon ta. Zaman shirun yayi mata yawa "Yaya" ta kira sunan kaman mai ciwon baki, shiru bai amsa ba hakan yasa ta d`ago da nufin yi mishi magana karaf idonta suka had`e da nashi daya kafe ta dasu da sauri tayi kasa da nata zuciyar ta na zarya akan lamari na soyayyar *Yaya Fahad* cikin kankanin lokaci jikin ta ke fara shock idan ya tsareta da irin kallon nan take take rasa tunanin ta Ginin girma zai fad`i yasa Yarima ya Kauda kan shi ga barin kallon ta. cikin kasaitar shi yace "kin ce gurina kika zo kuma kinmin shiru" Fateema tace "eh dama kasan ni ban iya komai bane na girke-girke da sauran abubuwa na nan, to shine su Bilki ke gaya min da akwai wata Hajiya mai koyarwa sai dai suka ce zata bukaci kud`i da yawa. Yanayin yadda take maganar ma abin kallo ne baice komai ba ya mike ya shiga bedroom d`inshi bai jima ba ya fito hannun shi rike da jakar hannu ta maza wato briefcase yazo ya zauna kan kujerar daya tashi ya bud`e jakar nan cike take makil da kud`i yan dubu-dubu layi-layi ya mayar da jakar ya rufe duk abinda yake tana kallon shi ta gefen ido Bazato taga ya mika mata gaba d`aya jakar yace "gashi ki ajiye a hanun ki duk abinda kika bukata kiyi, idan suka kare kimin magana" *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•257/258•* Fateema tabi jakar nan da kallo ido waje. Sannan ta d`ago ta kalle shi "Yaya meye zanyi da duk wannan kud`in?" Tana maganar tana zare ido hakan ya burge shi sosai yanayin yarantar ta na bala'in burgeshi, ya kuwa zuba mata ido yana murmushi, a ran shi yace "Wato ita a komai ma haka take" yace "Fateema ai ke yar'uwa tace ko ba komai ai kinfi karfin wannan kud`in a wurina" maganar shi ta shigeta ba karamin dad`i takejiba idan Fahad na magana. itama dai cikin sanyin jiki ta zame daga kujerar tazube kasa tace "na gode Yaya Allah ubangiji ya biya kuma ya saka da alkhairi..." "Shiiiiii ya katse ta ta hanyar d`ora yatsa a baki "No Fateen Goggo" duka hannayen sa biyu yasaka ya tallafo kafad`un ta ya mikar da ita tsaye suka fuskanci junan su a lokacin da idon su suka had`u "huhhh!" Suka sauke wata nannauyar ajiyar zuciya a tare, cos dukkan su ba wanda baiji wani sabon al'amari ba ta dalilin kusanci da had`uwar da idon suka yi. Yarima ya kasa jurewa tunanin shi ya fara dawowa tsohuwar soyayyar Fateema ta motsa masa bai san lokacin da ya kaiwa bakin ta cafka ba ai kuwa yafara tsotsa da tand`a kamar wanda ya sami lollipop, Fateema kam sandarewa tayi a wurin tamkar busashshen itace. Hakan yayi dai-dai da fitowar Lazeera cikin fushi janye da trolley a hannu da nufin barin gidan as tayi fushi zata gidan su. Ai kusan fad`uwa tayi a dalilin abinda idonta yaci karo dashi "Ya Prince" ta fad`a da karfi tareda kolalo duka idanuwan ta waje, da sauri Yarima ya saki Fateema ya maida kallon ahi ga Lazee wadda idon ta yake fess akan shi, kome tayi mishi sai kawai ya tsinci kanshi da fad`uwar gaba tareda jin nauyi da shakkar Lazeera. Fateema kam yana sakin ta ta suri jakar kud`in tayi waje da gudu. bawai dan jin tsoron Lazee ba a'a kawai ganin abin tayi kamar aafarki, tana tafiya tana tuno wani lokaci daya wuce a baya kamar dai haka daya faru yanzu yasha faruwa tsakanin ta da Yarima a babban lambun gidan inda suke zama da yamma a lokacin nan datayi zama gidan. Lazeera kuwa matsanancin tashin hankali ne ya riske ta zuciyar ta kamar zata faso kirjin ta ta fito saboda tsananin bugun da take mata, "me ke shirin faruwa dani ne?" Ta tambayi kanta a fili "inaaa" ta fad`a cikin d`aga murya "this will never be" ta fisgi jakar tayi waje daga ita sai wata tsinanniyar riga doguwa ce amma ta d`ame ta sosai ba ko mayafi haka ta fice Suka bar Yarima tsaye kamar wanda aka dasa shi a gurin, tunanin shi duk ya hargitse yarasa abinyi shikan shi ba zai iya gane abinda yake yiwa Lazeera ba shin So ne ko tsoro? Bakaramin d`aga mishi hankali tafiyar ta'ta tayi ba. Hannu yasaka ya shafi kanshi a hankali ya furzar da wani iska mai zafin gaske. Dakyar ya iya Jan kafa'fun shi ya shiga d`akin baccin shi da zuwa ya zube kan gadon cikin mutuwar jiki ya d`ora hannu akan goshin shi dake yimasa rad`ad`i ya lumshe ido abin uwa na masa yawo a kwakwalwa Lazeera kuwa ikon Allah ne kad`ai ya kaita gidan su, saboda tukin gangancin datayi. Da isarta ko dai-daita parking batayi ba ta fita da gudu ta shiga gidan a babban falon kasa tayi kicibis da Umman Yarima zaune a kan kujera tayi zugum abin duniya duk ya ishe ta tun ranar da ta baro gidan Mai Martaba tasan asalin wace ce Yayar ta, dakan ta ta zauna ta fed`e mata biri har wutsiya akan muguwar manifar su akan tilon d`an ta Yarima da dukiyar gidan sarauta harma da ita kanta sarautar, ranar Umma tasha kuka har ta gode Allah ta kuma yi nadamar goyon bayan data basu suka asirce d`an ta, jitayi a ran ta inama da wata hanya dazatabi ta fad`akar da Iyaye masu hali irin na ta akan su gyara su nisanci duk wata hanya ta asiri da bin nakaman tsibbo domin babu wani alkhairi a cikin ta, hanyace mara billewa itakam tayi nadama yanzu adu'a take baji ba gani akan Allah ya ceto d`anta su kuma ya toni asirin su, tun ranar ita da Hajiya ba mai shiga sabgar wani kowa na bangaren shi ko had`uwa sukayi banda mugun kallo da harare-harare ba abinda keshiga tsakanin su Wani mugun kallo Lazeey ta wurga ma Umma sannan ta haye up tiers tayi saman Umman ta tana kwalla mata kira *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•259/260•* "Momy! Momy!! Mo....." Bata karasa na ukun ba dan ganin wadda take kwallawa kira d`in tsaye a gaban ta, a razane ta fito saboda jin muryar Lazeera da kuma irin kiran da take mata. Tana ganin Uwar ta wurgar da jakar hanun ta ta tafi da gudu ta rungume ta sannan ta fashe da kuka. "Ke lafiya meya same ki? Ina mijin naki yake?" Hajiyar ta ce mai yimata tambayoyin cikin kad`uwa ita kuwa sai ta kara tsananta kukan tareda kankame momyn "Umma na shiga uku yarinyar nan zata kwace min mij......." Da sauri ta kai hannun ta ga bakin Lazeey ta toshe ta hanata karasa maganar a hanzarce ta ja hannun ta suka kure Uwar d`akin ta. Ta kalli yar zuciyar ta na harbawa tace "me kike so ki gaya min Lazeey?". Sai sa taja hanci tace "abinda kunnenki yajiye miki Momy wallahi asiri ya karye ya'Prince ya koma son Fateema" Umma ta koma kallon ta cikeda rashin yarda don tariga ta yarda da Bokan su, samada shekaru Goma suna mu'amala dashi ta harkar asirai amma ba'a taba samun matsala ba da zarar yayi musu aiki kamar yankan wuka haka suke cewa, to baremma wannan da ta tabbatar mishi yafi duk ayyukan da ya saba yimusu muhimmanci kuma ya gamsu harma ya tabbatar musu da babu wata hanya da Fahad zai koma had`uwa da Fateema saboda tsan-tsan tsana da kiyayyarta da akasa Aljanu suka dasa masa a cikin zuciyar shi Tace " to wanne dalili kake dashi wanda ya tabbatar miki da haka?" Nan da nan Lazeey ta bayyane mata duk abinda ya faru tsakanin Fateema da Fahad a d`akin ta. Take jikin Momy yayi sanyi kalau tace "inko haka ne ai zama bai same must ba maza tashi muje mu gurin Boka" ta fad`a a lokacin da ta mike tana ciro mayafi a wardrobe. Lazeey ma mikewar tayi tabi bayanta suka fice Zaune suke a gaban Bokan nasu sunyi shiru bayan sun gama koro mishi bayanin abinda ya faru, shi kanshi Bokan yayi mamakin jin maganar dan a yanayin aikin da yayi musu hatta inda Fahad yake Fateema bata isa ta kusanci gurin ba. Ba tareda ya ce musu komai ba ya bazama ga buga kasa da surkullen tsafin sa. Can kuma sai ya had`e fuska cikin sigar fushi ya fizgo wani d`an karamin shantu baki wulik yana rataye a jikin bangon d`akin ya dire shi gaban sa, ya shiga karanto wasu surkulle na d`alasimman tsafi. Nan da nan d`akin ya kaure da hayaki tareda kuka da kururuwar Aljanu take d`an shantun nan yai bindiga ya fashe ji kake d`uuuu- d`uuuu Hajiya da Lazey suka shiga ihu da bankaura suna gwara kanun su, A gigice Bokan ya daka musu tsawa "Ku asararru marasa nasara maza ku tashi ku fice kafin in hallaka ku, mahaukatan banza kunje kun jangwalo mana masu riko da addini gashi kun saka tsananin addu'ar su ya illata min Aljanu gashi duk sun tarwatsa min fada ta. To kusani wayannan mutanen ayanzu sun riga sunfi karfin Ku babu wani asiri da zai iya tasiri akan su. Haka kuma duk wanda kuka shirya abaya yanzu ya la'lace kutashi Ku fita" yafad`a da wata iriyar murya mai rugugi da gudu suka fice suna had`a hanya Boka kuwa cigaba yayi da sambatu yana cewa "kuje zaku sani na tabbatar idan kowa ya barku Aljani Auhal ba zai barku ba, wannan bakar azaba dayasha saboda aikin ku" *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•261/262•* Abinda su Hajiyar basu saniba shine tun ranar da Mai Martaba ya gano al'amarin na asiri ne, sai yasaka kullum sai an sauke Alkur'ani mai girma tareda manyan addu'oi, sannan a yanka babban bujimi ayi sadaka kuma har yau ba'a daina ba. Addu'oi ake baji ba gani, ba dare ba rana. ana nemawa Yarima da Matar sa tsari da kariyar Allah akan duk wan sharri, na mutum ko Aljan. Wannan kenan Cikin su ba wadda ta kalli ko inda motar su take, da gudu suka nufi hanyar da zata sadasu da babban titi, suka tare napep suka shige. mota kam a gurin suka barta Fateema na shiga sashenta su Rukayya suka mike dan tariyar ta da kuma son ganin ko tayi nasarar samo kud`in?, Sai da ta zauna sannan ta shiga maida numfashi dakyar kamar wadda tayi gudun kilomita biyar. A hankali ta bud`e lumsasun idon ta, wani irin farin ciki takeji Mara misaltuwa, sabon yanayi, sabon Al'amari, mikewa tayi ta rungume Bilkisu cike da farin ciki tace "Allah ya biya wadda takawo wannan shawarar, da badan wadda ta kawo wannan shawarar ba da zaman nisanta da takatsantsan na shirya zanyi da yayana, saboda tunani na yana bani baya sona, amma a dalilin wannan zuwan da nayi gareshi na gano har yau akwai tsagwaron so da kauna ta a ransa. Tsabar tsoron da yakewa Anty Lazeera shi yake hanashi isarwa ko bayyanawa" Bilki tayi murmushi tace "Alhamdulillah yanzu kinga kin kara samun kwarin guiwa na neman horo da gogewar da zaki iya gogayya da kowacce irin mace saboda mijinki" Fateema tace "sosai ma kuwa" ta fad`a tana gyad`a kai, kyakkyawar fuskarta d`auke da murmushi. Rukayya tace "to kud`in fa, an samu?" Bata bata amsa ba ta mika musu jakar kud`in data shigo da ita. Suka kurawa jakar ido cike da mamaki Bilki ce takai hannu ta zuge zip d`in, ai suna d`agawa suka rud`e tare suka kalli Fateema baki na rawa Rukayya tace "A..Anty Fatee baki yayi ko d`aukowa kika yi?, Tayi mata wannan tambayar ne saboda dalilai guda biyu. na farko saboda ganin yawan kud`in da ta yi, na biyu kuma saboda sanin halin kiriniyar Fateen da ta yi, ko a gaban shi zata iya d`auko su ta gudo muddin ta tambaya bai bata ba. Murmushi tayi musu kafin tace "Ku kwantar da hankalin Ku kukam Wlh da kanshi ya bani da hannun shi". Suka rike baki cike da mamaki suka ce amma ya akayi hakan? Hala dai Anty Lazeera bata gurin? Nan fa Fateema ta tintsire da datiya sai da tayi mai Isar ta sannan ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya musu, amma bata gaya musu batu na kissing d`inta da Yarima yayi ba. A ganinta da kuma tunaninta wannan iskanci ne sai dai ba yadda ta iya tunda halin shi ne haka, saboda son da take masa zata dinga rufa masa asiri na duk tabin da zai yi mata. A Sokoto kuwa hankalin Iyayen Fa'eez ne a matukar tashe. Tsayayyen soja jarumi, wanda tun lokacin kuruciya ya taso da jarumtakar sa juriya da zurfin ciki. Amma sai gashi saboda yarinya d`aya ya rasa duk wad`annan Abubuwan. Tun daga lokacin da ya kira wayar Yaya Bashir, ya tabbatar masa cewa Fateema fa ta koma ma mijinta Yarima. To tun daga nan aka rasa kan sa, ya shiga damuwa da rud`u sosai, ba shikad`ai ba hadda Iayaye da kannen shi kai da duk wani makusancin sa Yanzu ma kamar kullum zaune kawai yake kan kujera a falon d`akin shi. Yayi zuruu ya zurawa fankar dake ta faman juyi Ido kamar mai nazarin wani Abu gameda fankar. Momyn shi ta shigo da sallamar ta fuskar ta ba walwala, idonta akan fuskar d`an nata wanda bai ma san da shigowarta d`akin ba. Momy ta girgiza kai a lokacin da take zama kusa da shi idon ta fall da hawaye zuciyar ta cike da tausayin babban d`an nata. Tasaka hannu ta dafa kafad`ar shi a sanyaye ya d`ago da jajayen idon shi ya kalli mai dafa shi, ganin Mahaifiyar shi ce sai Ya koma sunkuyar da kanshi ba tareda yace komai ba sai wasu zafafan hawaye dayaji suna bin kuncin sa. Momy ta rungume shi a lokacin da kuka ya subuce mata. Cikin kukan ta fara magana "a'a son ba zai yiwu ba, sam bazan barka ka kashe kanka saboda mace ba. Ya kamata ka dawo hayyacin ka son, ka zama cikakken musulmi ka yarda da kaddara kayi imani wani ba zai Auri matar wani ba ka yarda Fateema ba rabonka bace" *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *•263/264•* Fa'eez ya fashe da kuka ya kankame Momy cikin yanayin sadakarwa ya fara magana "na hakura Momy, Wlh na hakura pls kar ki koma yin kuka kinji?" Ya fad`a yana share mata hawayen fuskar ta. Momy kuwa dad`i ne ya tirnike ta jin hakan daga bakin sa, ta raba jikin ta da nashi sannan ta zaro wani photon Kati ta Mika mishi. Ya karba Yana kallon photon da alamun tambaya a fuskar shi. Tayi murmushi sannan tace "Sameera ce fa, baka gane ta bane?" Ta tambaya tana kallon fuskar shi. Ya Kara kallon photon da kyau sannan yai murmuhi yace "haba Ina kallon fuskar kamar na Santa, yarinyar ta bace min da gani, mortharn 5years." tace "eh kasan tana landan course din likita, kwanan nan ta dawo yau satin ta daya a garin" shiru ya ratsa d'akin na d'an lokaci Sameera yar'kanwar momyn shi ce duk a sokoto suke, satin ta d'aya da dawowa daga London inda ta dawo a matsayin cikakkiyar likita. Ya sake kallon ta yace "to Momy photon fa" tace "na kawo ka duba ne kafin kaje ku gana, nida hajja mun yi shawara akan had'a ku aure kai da Sameera". Ta takaita maganar tana kallon shi domin ta ga wane irin karba yayiwa maganar?. Ga mamakin ta sai taga yayi murmushi Yana sake kallon photon yace "duk yanda kuka yi da mu yayi Momy na, Ina son Sameera and nasan itama zata soni Allah yayi mana jagora" cikeda farin ciki Momy ta rungume shi "na gode yarona nagode Allah ya yi maka albarka" ta sumbaci goshin shi ta fice zuciyar ta fall da farin ciki. acikin satin aka shirya komai kasancewar duka su biyun sun amince, da sati ya zagayo kuma aka d'aura aure masha Allah ansha biki abin Sai wanda ya gani Auren Soja da likita, abin Dai gwanin sha'awa a cikin abinda baifi wata d'aya ba Fa'eez ya fara saituwa kasancewar Sameera wayayya Mai ilmin boko dana addini ta iya tafiyar da namiji, cikin kankanin lokaci ta goge tabon da soyayyar Fateema tayi a zuciyar shi ta maye gurbin da d'inbin kaunar ta tuni yayi watsi da soyayyar Fateema ya rungumi ta matar da Allah ya kadarta Ita ce rabon sa, ya yarda da kaddara kuma ya karbe ta hannu bibbiyu. Sai Dai ya kudirta a ransa zasu cigaba da zumunci da dangin Fateema. *Garin Gombe* Yarima ne kwance bisa lafiyayyen gadon shi, Sai sheka bacci yake cikin kwanciyar hankali a zahiri amma a bad'ini mafarke-mafarke ne yake tayi akan zaman takewar shi da matan shi duk wani wulakanci da tozarcin da yayiwa Fateema sai da ya gansu. Bangare d'aya kuma bautar dashi da Lazy tayi ita da mahaifiyar ta da Umman shi, har ma da dawowar Fateema gidan shi Sai da yazo inda ya bata kud'in nan ta fita da gudu yai firgigit! Ya farka Yana fitar da numfashi Mai sauti "Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'un" ya shiga Karantowa Yana waige-waige ba makawa tunnin Fahad ya dawo babu abinda bai tuna ba hatta fitar mahaifiyar shi daga gidan da kuma tafiyar Lazeera. Godiya ya yiwa Allah daya kasance ita Fateema tana gidan, da sauri ya mike ko brush baiyyiba ya nufi sashen Fateema. baiga kowa a falon ba, hakan ya bashi damar wucewa kaitsaye izuwa d'akin baccin ta. Kwance ya sameta tayi share-share a kan gadon ta, baccin ta take cikin nutsuwa fuskar nan ta'ta kamar tana murmushi wani irin dad'i ne yaji Yana sakkowa tun daga ko'kon kansa har izuwa tafin kafar sa. Cikin gaggawa ya zube kasa a inda yake ya fuskanci alkibla yakai goshin shi kasa yai sujjada inda ya dinga kwararowa Allah (s.w.a) Yabo yana jinjina da kirari Yana Kiran sunayen sa tsarka'ka Yana gode mishi godiya marar adadi, ya rufe da salatin mazon Allah (s.a.w) ya mike jikin shi har bari yake yi ya Isa gaban ta ya gurfane bisa guiwoyin sa ya zubawa kyakkyawar fuskar ta ido, a ransa Yana dad'a godewa Allah bisa wannan babban rabon da yayi masa na dawo mishi da Fateema wadda a kullam yakejin kanshi incomplete saboda rashin ta a kusa dashi Sai dai bashida damar tunawa ko kuma yin wani katabus na neman ta. ya d'an rankwafa fuskarshi ta dawo daf da ta'ta su na iya jin numfashin junan su Yana shirin Kai Mata sunbata tai firgigit ta farka daga baccin da take, ganin sa yasa tayi baya da sauri, nan fa suka shiga kallon-kallo da ita da shi. *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ 265/266 Cikin in Ina tace "Yaya lafiya?" Ya kalle ta da wani irin kallo Mai d'auke da sakonnin da shi kanshi bai san adadin su ba, "barka da safiya My Princesses" ya fad'a da wata iriyar murya kamar mai yin rad'a. sai da ta d'an harare shi ta kasan ido sannan tace cikin karamar murya "yau kuma? Ko dai batan kai Yayana yayi yau?" maganar yarinyar ta ratsa shi, musamman da ya tuna irin zaman da ya yi da ita tun lokacin da ya aure ta. "a'a Fateen gwaggo, karki soma, pls kizama mai yafiya na roke ki." yayi folding hannayen shi yana kallon fuskar ta, Fateema tayi shiru tana kallon yanayin Prince. tabbas yayi laushi sosai alamu da yawa sun nuna da gaske yake yayi nadama sai dai a ganin ta ba cikin sauki haka ya kamata ta karbe shi ba, ya zama dole ya karbi hukunci. Duk da tana son Yarima hakan bazai hana ta ganar da shi yayi kuskure ba, duk kuwa da cewa ba a hayyacin shi ya aikata ba. Duk wannan dogon tunani da take *Yaya Fahad* yana nan gurfane a gaban ta, yayin da idon shi ya ciko tam da hawaye, yana jiran jin hukuncin da zata yanke masa. "pls Fateema" ya sake fad'a a mutukar sanyaye kamar mai shirin fashewa da kuka. tamkar wadda aka tsikara haka tayi tsalle daga kan gadon ta nufi kofa da gudu tana waiwayen sa. Yarima ya bita da kallon mamaki sam bai san lokacin da Fateema ta cika ta zama babbar budurwa haka ba, kayan bacci ne a jikin ta, rigar iya guiwa mai had'e da gajeren wando sun amshi jikin ta sosai fatar nan ta'ta tayi shar ga laushi ga alamun santsi kamar ta jinjirai tana gudu sassan jikin ta na motsawa tuni ta fice ta rufo mishi kofar amma idon shi na nan kyam akan kofar siffar ta da halittun jikin ta nayi masa yawo a kwakwalwa "huhhhh" ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jiki ba kwari ya mike ya ja kafa dakyar ya nufi d'akin shi dake cikin sashen nata, wanda rabonshi da ya shiga cikin sa tun lokacin da Lazeera tana bangaren. Amma ga mamakin sa sai ya tarar da d'akin fess da shi sai tashin kamshin kalolin tiraruka da yake yi, ya ja numfashi ya fitar cike da shauki. a ran shi yana tuna lokacin da Lazy take sashen, sam d'akin baya samun gyara haka. Ga wannan da ko shigo mata baya yi hakan baisa tayi wasa da gyara muhallin sa ba. "Allah ya albarkace ki Fateema" ya fad'a yana shafa kirjin shi wanda yake ji kamar a cikin sa Fateeman take. Ya nufi toilet zuciyar shi na dad'a yin nitso a soyayyar Fateema ita kuwa tana fita daga d'akin ta shige d'aya d'akin ta saka key, ta shige toilet tayi wanka ta fito ta saka wata doguwar riga ash colour bata tsaya komai ba sai da ta fara gabatar da salla, sannan ta d'an gyara fuskar ta ta zaro wani karamin mayafi black ta d'ora ta fita kitchen dan sama ma cikin ta abinci. Ta samu an gama kammala komai suna ko'karin fita dasu zuwa danning ta tsayar dasu ta d'ebi iya abinda zata iya ci da drinks a babban tire ta nufi d'akin da take. Mintuna kad'an Yarima Fahad ya fito cikin shigarshi ta ya'yan sarakai fuskar nan tashi ba walwala ya nufi d'akin Fateema. Ganin bata d'akin yasa ya nufi d'aya d'akin da yake kyautata zaton can ta shiga da kuzarin sa ya tura kofar amma sai yaji ta a datse gam. "Fateema" ya kira sunan ta a sanyaye hannun shi na rike da handle na kofar. "Fateema dan Allah kiyi hakuri ki saurare ni kinji, wlh nayi nadama Teema ina son ki, ina kaunar ki Fateema." ya saurara da maganar yana tunani ko zatayi magana amma shiru, ya kai mintuna goma tsaye a gurin amma ba ko alamar motsin Fateema. wadda yayi imanin cewa tana jin shi. Sosai yaso ya ganta amma ya zayyi? dole yaja sanyayyin kafafun sa ya fita ko breakfast bai tsaya yi ba ji kawai yayi yau ya tashi da matukar kewar mahaifiyar shi kuma kai tsaye gidan su ya nufa inda take. Umman tana zaune a falon kasa as usual hanunta rike da carbi tana ta yin lazimi, istigfari da hailala. sai ganin su tayi sun shigo a rikice ko sallama babu suka haye saman benen inda d'akunan baccin su suke. kallon mamaki ta bi bayan su dashi a ranta tana jinjina cewa duk abinda ya koro su haka mai girma ne, Wato Lazera da momyn ta. Tana cikin saka da warwara taji dukkanin su suna zunduma ihu sun nufo kasan a kid'ime, ta mike da nufin hawa saman domin ihun da suke bana wasa bane. a up tiers d'in suka had'u da har ta bud'i baki zata tambaye su lafiya suke wannan ihun haka? amma ina a bakinta kalmomin suka makale saboda ganin abinda ke faruwa a saman. gobara ce gagaruma ta taso wacce ta kama dukkan d'akunan bacci hud'u dake saman. rigegeniyar sakkowa sukayi dukkanin su a matukar tsorace suka nufi farfajiyar gidan suna kururuwar neman agaji direba da mai gadin gidan sune sukayi ta maza suka kira ofishin hukumar kashe gobara. domin duka matan ba wadda keda tunanin yin hakan Lazy da Momyn ta sai kuka suke suna ihun kiran duka dukiyar su ta kone domin wutar ci take tamkar ana bulbula mata fetir, haka tayi ta cin kayan dake d'akunan har zuwa lokacin da masu kashe wutar suka karaso, suka fara gudanar da aikin su an sami nasarar kashe gobarar ba tare da ta sakko kasan ba, sai dai a saman kam ta gama lashe komai ko tsinke bata rage musu ba. ganin hakan ya sanya Momyn Lazy kifewa a gurin tana borin hauka had'e da sambatu marar kan gado. A haka Yarima ya same su cirko-cirko a tsakiyar gidan kowa ya watse sai su kad'ai Momyn na ta zuba sambatu Lazy na ta faman kuka tana rarrashin ta Umma na daga gefe tana kallon ikon mabuwayi al'ajabin duniya ya cikata. shuru Yarima yayi daga inda yake yana sauraren maganganun dake fita daga bakin Momyn Lazy wayanda da yawan su duk akan cutar da sukayiwa shi Yariman da Fateema ne, Umma ma ido ta zuba mata domin wasu abubuwan bama da sanin ta ake yin su ba. *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ 267/268 Jiki a sanyaye ya fito daga motar ya nufo inda suke, ganin shi ya basu mamaki dan ba wanda yasan da zuwan na shi. Momy na ganin shi ta fisge jikin ta daga cikin na Lazeera ta isa gaban shi ta tsuguna bisa guiwoyin ta duka biyun tana shirin kama kafafun shi, ya d'an ja da baya yana mata kallo irin na tsana da ala'wadai. Cikin kuka mai sauti ta fara magana "Fahad dan Allah kayi hakuri ka gafarce ni nayi kuskure d'ana wlh nayi nadama ka ceceni yace bazai barmu ba, gashi nan ya fara aibata ni ya saka min wuta a gaban idona ya kona min komai". Ta fashe da kuka mai tsanani "shikenan yanzu banida komai na rasa komai sai rayuwa, na shiga uku gashi yazo nan ma" ta fad'a tana nuna gefen ta da yatsa cikin yanayin tsoro, ta mike tsaye tana ihun wai ga aljanin nan yazo zai kashe ta tanayi tana neman mafaka. Lazeera ce tabi bayan ta cikin kuka ta riko ta tana lallabata, tun daga nan al'amarin ta ya dawo kamar hauka koda yaushe cikin sambatu take abu dai kamar ciwon hauka. Allah ya kyauta haka Fahad yace ya kad'e rigar shi ya isa ga mahaifiyar shi wadda tsananin kunyar shi da dana sanin abinda ta aikata suka lullube ta, ta kasa motsawa daga inda take. hawaye na bin kumatun ta tausayin kan ta ya kara kamata lokacin da ta koma kallon inda yayar ta'ta take, a ran ta tace yanzu da ita ce a wannan matsayin ya zata yi?, godiya tayiwa Allah daya ceto ta kuma ya kare ta daga sharrin su. A fili tace "ya Allah ka kutubar da matan musulmi da suka raja'a da bin bokaye da malaman tsibbo, Allah ka ganar da su sudawo bisa hanyar gaskiya, haki'ka duk wani abin da zaka nema agurin wanin da ba Allah ba to kuskure ne babba" wannan gaskiya ne (Muyi tunani mai zurfi mu dawo hayyacin mu mata, Allah (s.w.a) shine yafi can-canta da mu kai kukan mu gareshi a duk lokacin da muke da bukata mu sanar mishi, mu roke shi shine mai bayarwa, kuma shine mai hanawa. Kisani yake yar'uwa mace zuwa wajen wani boka ko malami neman wata bukata la'lata imani ne. Kuma koman daren dad'ewa karshen ta bazai zamo mai kyau a gareki ba. Allah ya ganar damu baki d'aya). Taku uku Yarima ya kara ya isa gaban Umman shi wadda ta sunkuyar da kanta kasa saboda kunyar abin. "Umma" ya kira ta cikin sanyaya murya sannan ya tsuguna a gaban ta, daga aljihun shi ya ciro wani lallausan handkacip fari mai kamshi ya fara share mata hawayen dake fuskar ta zuciyar shi fall da farin ciki domin hakan ya tabbatar mishi cewa Umman shi ta saduda. Kuka ne mai karfi ya kwace mata ta rungume d'an nata, "Son dan Allah kayafe min kai da Fateema kuyi min aikin gafara wlh son nayi nadama, ka yafe min kaji d'ana" Yarima ya d'ago ta yana kara share mata hawaye yace "babu wani abu a rai na Umma wlh na yafe miki, kuma su d'in ma na yafe musu nasan Fateema ma zata yafe musu. Ina sonki Umma na pls karki koma yin nisa dani kinji" maganganun nashi sun kashe mata jiki sosai domin duk yadda take son zama dasu dole ta hakura tunda Mai martaba ya saketa kuma ya kore ta. ta koma fashewa da wani kukan ta kankame shi "a'a d'ana bazan maka wannan alkawarin ba tunda Abban ka ya koreni daga gidan sa ba yanda na iya, sai dai ka dinga kawomin ziyara kuma dan Allah ka nemamin gafarar Fateema da Abban ka kaji." "ki daina kuka hakan nan Umma pls banajin dad'in shi, Mai martaba ya koreki a lokacin da kike cikin kuskure, yanzu kuma kin gane gaskiya na tabbata zai karbe ki" ya fad'a yana kama hahhun ta suka mike tsaye tare. da kanshi ya gyara mata mayafin ta basubi ta kan komai ba ya sakata mota shima ya zaga ya shiga ya mata key suka fice daga gidan suka nufi gida misalin karfe biyar na yammacin Hajiya Binta mai gyaran jiki ta amsa kiran da Fateema ta aika mata dashi. Sai da ta jira akayi mata iso sannan wasu kuyangi suka shigar da ita babban falon baki dake sashen bayan kamar mintuna biyu da zaman ta Gimbiyar ta fito "Masha Allah" inji hajiya Binta kasancewar basu da wani nisa tsakanin gidan ta da gidan sarauta yasa taji labarin had'uwa da kyawun matar Yarima a wurin matan dake zuwa gidanta koyon abubuwa amma sam bata d'auka kyan yarinyar da kuruciyar ta sunkai haka ba. Ta d'auka zatayi jiji da kai sai kuma taga ba haka bane. Cikin saukin kai da sakin jiki Fateema tayi mata bayanin duk abubuwan da take so ta koya daga gareta. Hajya Binta ta gamsu harma ta karawa Fateen wasu na daban wayanda suma sunada muhimmanci sosai gare ta sun dai-daita maganar kud'i harma sun saka lokacin da zata dinga zuwa (sis hours) zata dinga yi a gidan tana koyar da ita abubuwan, sai dai tace zata na d'an leka gida lokaci lokaci saboda yara *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍. *269/270* Karfe goma da rabi Yarima ya shigo gidan sarautar d'auke da mahaifiyar shi Umma, wadda take ta d'ari-d'ari da shi tunda ta shigo motar batayi magana ba Sai ma shi da yake yi Mata magana jifa-jifa. Kai tsaye sashen ta suka nufa tana gaba Yana binta a baya, kuyangi da ma'aikatan gidan Sai zubewa suke yi suna gaishe su, idan suka wuce Sai abi bayan su da kallo masu masaniya akan barinta gidan su fara kus-kus-kus haka Dai suka ratsa sassan har suka Isa bangaren ta. Jakadiya na ganin ta ta rangad'a gud'a ta shiga antayo Mata kirari da yabo tare da nuna farin cikin dawowar ta. Yanayin da take ciki yasa bata tsaya ta kanta ba, ta wuce uwar d'akin ta. Fahad yabi bayan ta, Sai da ya tabbatar ta zauna sannan ya fice ya nufi sashen mahaifin shi kasancewar time d'in fita fada bayyi ba. Bai tsaya wani boyo ko noke-noke ba Kai tsaye ya sanar da Abban shi komai dangane da mafarkin da yayi, da kuma abinda ya faru a gidan su Lazeeran Sai kuma farin cikin shi daya bayyana wa Abban nashi akan dawowar Fateema gare shi ya tabbatar masa duka aikin asiri ne. yanzu ya dawo hayyacin sa kuma yana son matar sa. Mai martaba yaji dad'in al'amarin sosai har ya dinga sakawa d'an nashi albarka tare da addu'ar Allah ya kare gaba. Daga karshe Yarima ya rufe da rokawa mahaifiyar shi gafara ya sanar da shi cewa ya dawo da ita, kuma tariga tayi nadamar abinda tayi a baya, Yana da tabbacin bazata koma aikata maka mancin sa ba. Tunani mai zurfi dattijan yayi kafin ya d'ago yace na maidata Yarima taci albarkar ka Ina Mata fatan sabuwar rayuwa Mai kunshe da alhairai nan gaba. Yarima yaji dad'in hakan har cikin ran sa bai bar uban ba saida ya tasa keyar sa har sashen Umma suna tafe suna hira cikin raha da walwala ya dad'e rabon da ya rabi mahaifin nashi haka, haka shima Uban ya kyale shi ne kawai amma yaron Yana ran sa Sai yazamana dukkan su suna cikin farin ciki da wannan zaman nasu na yau. Umma kam da tayi ido biyu da Mai martaba Sai ta diririce kunya da takaicin aikin ta na baya suka baibaye ta. Amma dayake mijin nata wayayyen mutum ne Sai ya basar yayi Mata magana kamar wani Abu bai faru ba. Haka Yarima ya barsu suna gaisawa bayan fitar d'an ne yayi Mata nasihohi masu karfi da sanyayar da jiki, Umma kam Sai kuka take tana rokon gafara kuma tace ya saka musu rana suje garin kukunba ta roko gafarar Baffa da Gwaggo. Yace wannan ba komai zasu je nan bada jimawa ba. Zuciyar shi fari kall ya nufi gidan shi sashen Fateema da shigar shi sashen kamshi yayi mishi marhaba, da alama Ana had'a wani delicious ne inji zuciyar shi. Sai a lokacin ya tuna ko breakfast bayyi ba. Da sand'a ya nufi kitchen d'in kamar wani barawo domin yasan Fateema tana da masu aiki Yana so ya gani ne ita ce a kitchen d'in ko ma'aikatan gidan ne Dan magana ta gaskiya Yana so yaga matar shi kewar ta yake ji sosai. A d'an koridon hanyar kitchen d'in ya make Yana lekawa abin mamaki Sai yaga Fateema da wata mace suna shirya girke-girke ga dukkan alamu matar tana koyar da ita ne, farin ciki ya ziyarci zuciyar shi dad'i ya lullube shi. Ya dad'e tsaye a wurin domin kallon da yake mata yana faranta masa, gani yayi sun kammala komai suna shirin fitowa da sauri yabar wajan ya shige d'akin sa. Hajya Binta ta taimaka mata wajan jere kayan akan table wanda shima duk cikin horon ne, daga nan suka wuce d'akin ta inda ta saka ta shiga wanka da wani had'in turaruka na wanka wanda ta bawa Fateen ta had'a da kanta. Tana jin dad'in koyar da yarinyar abubuwa domin tanada brain, da sauri take haddace abu. gaban mirror ta zaunar da ita bayan fitowar ta daga wankan inda ta koya mata yadda ake amfani da hand drayer ta busar mata da gashin kanta mai tsayi da laushi sannan ta nuna mata irin kalolon mayukan da zata dinga amfani dasu a kan nata. daga nan sai aka zarce sashen make-up inda take nuna mata yadda zatayi tanayi da kanta kafin kace me fuskar nan ta d'auki sheki da walwali ga sihirtaccin turaruka sai zuba kamshi take. Suka koma gefen saka kaya nan fa tashiga nunawa Fateema had'in colours na kaya da mayafai, takalmi da jakunkuna ko wanne kalar kaya da kalar mayafi da takalmi da jakar da ta dace da shi. Tana kuwa d'aukar darasin sosai komai yana shiga kanta yadda ya kamata. Doguwar riga ta saka ta wani tsadadde material mara nauyi rigar ta amshe ta matuka tun daga kalar ta data kasance marum ta d'aura mata d'ankwali na wani yadi mai kyan gaske porpul plat shoe ta saka suma porple ta manna mata d'aya daga cikin sarko'kin ta na zinari had'e da yan'kunne da warwaro cikin abinda baifi 30 minutes ba Fateema ta dawo asalin sunanta na tauraruwa (Zara) kyawun ta ya kara bayyana ita kanta Hajya Binta sai da ta bata snap, sannan tayi mata sallama ta tafi har kofar shigowa bangaren ta rakata tana ta yi mata godiya ta tafi. Juyowar da zata yi ne kawai sai ji tayi tayi karo da mutum tayi baya da sauri idonta a kan wanda tayi karon da shi Yarima ne ga dukkan alamu binta yake a baya. Ta tsuke fuska sannan tayi gefe zata raba shi ta wuce wani irin kamshi ya daki hancin sa, sai da ya lumshe ido, baisan lokacin da ya kai mata cafka ba ya kuwa rungumeta tsam a kirjin sa yana sauke numfashi tamkar wanda yayi gudun kilomita biyar. ta shiga kiciniyar kwacewa "Yaya Fahad Allah ka sake ni bana So" ta fad'a tana cinno baki yayi murmushi *i miss you* Fateen gwaggo ya rad'a mata a kunne sai da tayi jim idon ta suka lumshe saboda wani bakon al'amari da taji a jikin ta. bai tsaya nan ba wuyanta ya shiga shaka yana shinshinar ta kamar tsohon maye, ya zagaye ta da hannayen shi ya mata kyakkyawar runguma ta mintuna biyar sai yaji kamar ruhin shi yana dawowa jikin shi wata irin nutsuwa yaji wadda rabon shi da jin makamanciyar ta tun lokacin da yake rabuwa da jikin Fateema. Ya koma sauke numfashi sannan yace "Alhamdulillah" sai z lokacin ya sake ta amma hannun ta yana rike da nashi yaja ta zuwa danning inda yaga an shirya abinci ba musu Fateema ta bi shi suka zauna da kanshi ya zuzzuba musu abincin ya zauna da spon d'aya ya ciyar da kanshi da kuma ita sam bata ki ba taci abincin sai da taji ta koshi sannan ta danne da drinks. Yarima Fahad kam ya raja'a da kallon kanwar shi kuma kyakkyawar matar shi Fateema wadda baya taba gajiya da kallon fuskar ta wani irin fari tayi mishi da ido baisan lokacin da ilahirin gabobin jikin sa suka saki ba kasala da mutuwar jikin suka dirar mishi lokaci d'aya yaji ya kwad'aitu da matar sa kuma abar kaunar sa Fateema sai dai kafin yayi wani yunkuri tuni ta raba jikin ta da nashi ta ruga aguje takai kofar d'akin ta sai a lokacin kuzarin sa ya dawo "Fateema" ya kira sunan ta da sauri murmushin mugunta ta sake mishi sanna ta shige d'akin ta ta leko kanta ta dalla masa gwalo tana dariya "a'a Fateema kar kimin haka pls" ya mike ya nufota da sauri ta datse kofar tamurza key ta barshi a jiki Allah sarki Fahad kuka ne kawai bayyi mata ba amma yayi magiyar duniyar nan taki ta bud'e d'akin dole ya hakura ya kwashi kanshi ya koma d'akin shi ya kife kan gado. Ya dinga matse filo yayin da zuciyar shi ke dad'a afkawa cikin kwad'ayi da sha'awar Fateema. Ita kam tsalle tayi ta haye gado aranta tana cewa "kad'an ma ka gani tukunna ai har marin da kayi min a rafin kukunba sai na rama wlh" ta kece da dariyar nan tata ta shed'anci (niko Nasmy nace anya Fateema bazaki tausayawa Fahad ba) to haka dai rayuwar gidan ta d'ore musu kullum cikin abu d'aya fiye da wata d'aya ya kasa samun Fateema, sai yaga kamar ya kama sai tayi escape. Umma ta roki gafarar ta kuma ta yafe mata yanzu zaman mutunci suke yi da mutunta juna Umma tanajin dad'in Fateema sosai sai yanzu ta fahimci yarinyar tana da kirki kusan kullum sai ta jewa Umma hurar dare wani lokacin hadda Yarima wanda idan suka had'u suna hira ba wanda zai ce da akwai wata damuwa a tsakanin su. Fateema ta kara gogewa ta zama wayayyar mace kimanin watanni biyu kenan tana d'aukar horo a gurin Hajya Binta yanzu ma har ta daina zuwa saboda d'alibar ta'ta ta zama malama ta gama kwarewa ta kowanne fanni tazama tauraruwa a gidan sarautar kuyangi da bayi da ma'aikatan gidan sunajin dad'in ta sosai. Mai martaba na ji da ita kusan fiye da kowa a gidan. Sai da ya tabbatar zaman su yayi dad'i komai ya dai-daita a yau yace musu su zama cikin shiri gobe zasu tafi kukunba, dukkan su sunji dad'in maganar tafiyar amma basu kai Fateema ba wadda tayi kewar gidan su matuka tunda tazo gidan bata koma ba haka suma tunda suka zo sau d'ayan nan suka tafi ba wanda ya dawo sai dai sukanyi waya kodayaushe kasancewar itama yanzu tayi wayar kanta farin ciki ne zallar sa a ranta yau sai rawar kai take ji take kamar anbata kyautar zuwa hajji hatta Fahad yau ya shaidi hakan domin da suka koma bangaren su tsalle tayi ta d'ane bayan shi tana ihun murna Yarima kam ji yayi kamar su dawwama a hakan bisa kuhera ya sauke ta tanata dariya shiko sai kallon fuskar ta yake baki a sake bakaramin kyau dariyar take kara mata ba sai da tayi mai isarta sannan ta tsagaita ta kalke shi "Yaya Fahad, kaima kanajin yanda nake ji ko?" "eh" yace yana kare mata kallo baisan yaushe Fateema zata daina yaranta ba. "Nasan yau kina cikin farin ciki, Fateema dan Allah ki tsaya mu fahimci juna kinada iliminki dai-dai gwargwado shin bakisan akwai hakki na a kan ki ba?" kasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannun ta hakika wasu lokuta Yayan nata yana bata tausayi. Ita kanta daurewa kawai take yi amma tanajin dad'in zama a kusa dash. A ranta tace ya kamata ta tausayawa mijin ta abinda takeyi sam bai dace ba ta d'ago ta kalle shi "kayi hakuri Yaya na insha Allah ya wuce zamu zauna kamar yanda kake so amma fa sai ka cikamin burika na guda biyu tareda bani amsar tambaya d'aya" da sauri ya d'ago ya kalleta *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *271/272* "Meye wad'annan burikan naki Fateema? Wlh zan cika miki su, mece ce tambayar ki? Fateema zan amsa miki" bakin shi har ruwa yake idanun shi a kan ta. tayi murmushi "da fari dai kaga ina son cigaba da karatu, zaka nema min admission ka barni in cigaba" ta tsagaita tana kallon fuskar shi. Murmshi yayi mata sannan ya kai hannun shi ya shafi gefen fuskar ta yace "amma inaga ai kin san dokar ko Fateema?" Kin sani sarai ba'a irin wannan fice-ficen a gidan sarautar nan" Fateema ta bata fuska tana shirin mikewa tsaye yayi saurin rikota ya zaunar da ita "ina son ki Fateema, zan iya yin komai saboda faranta ranki, amma me kike So ki karanta?" sai a lokacin ta saki fuskar ta "ina da muradin na zama likita ne abinda zan karanta kenan, dan Allah Yaya ka taimaka min kaji?" Janyo ta yayi saida ta mannu da kirjin sa yace " I'll do anything for your happiness Teema na, zakiyi karatu amma fa kisani ba dai a gombe ba dole sai in kin lamunta mubar kasar nan da sunan zanyi wani cours kinga sai kiyi karatun ki cikin kwanciyar hankali ko" batasan lokacin da tayi mishi kyakkyawar runguma ba. "Thats my yaya" ta fad'a lokacin da ta kwantar da kanta bisa kirjin sa, shi kuma sai yaji kansa kamar bai taba rungumar wata macen ba sai ita kad'ai. Sbd dad'i da sanyin da yaji a rayuwar sa. Ya d'ago fuskar ta yana fad'in "naji bukatar ki ta farko Fateema, mene ne na biyun?" ita kanta sai da abinda yake ranta ya sakata dariya kafin ta koma d'aure fuska tace "gobe zamuje kukunba, ko zaka iya tuna marin da kayi min a hanyar mu ta dawowa daga rafi?" Yarima yai shiru yana tunani can ya d'ago yace "eh na tuna, lokacin da kika ce kina sona ko?" Ya tambaye ta yana sosa kyeya cike da jin nauyin abin. tayi murmushi "to shi zan rama, kuma a dai-dai inda kayi min a can zan rama" ya zuba mata ido cike da mamakin ta a zatan shi wasa take, amma a fuskar ta sam bai ga alamar wasar ba. hannu ya saka ya tallafo kumatun ta suka fuskanci juna "Fateema, da gaske kike zaki iya marin Yayan ki?" Cike da yaran ta tace "eh ai kai ne ka fara Allah yaya sai na rama" ta karashe maganar cike da shagwaba "to naji na yarda zaki rama, meye abu na ukun?" "uhum dama zan tambaye ka ne akan anty Lazeera ance min ta tafi, shin meye gaskiyar maganar?" Shiru sukayi duka na yan mintuna kafin ya fara magana, ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar mata, daga karshe yake shaida mata ya riga yasake ta saki d'aya, kuma shi da wata macen ma hayatan-hayatan har àbada yana kallon fuskar ta yace "in dai har kika yarda dani kika So ni Fateema to zan zama naki ke kadai har karshen rayuwa, wallahi yanzu ina son ki Fateema fiye da wanda kike yimin dan Allah ki yarda dani ki daure ki karbe ni amatsayin mijin auren ki" ya fad'a lokacin da ya zame daga kujerar ya tsuguna a gaban ta. Tausayin Yarima da mamakin rayuwa suka kama Fateema Wai yau ita ce *Yaya Fahad* yake bibiyar ta yana barar soyayyar ta, Allah sarki rayuwa ba shakka maganar magabata gaskiya ce (mahakurci mawadaci ne wata rana) zuwa yanzu Fateema tariga da ta goge da ilmi na soyayya da sanin makamar namiji. hannayen ta duka biyun ta mika mishi ya rika su cike da farin ciki ta jashi izuwa kan kujerar daf da ita ya zauna idanuwan shi akan fuskar ta. murmushinnan nata ta koma yi mishi hannayen ta na rike a cikin nashi idon su na sarke suna yiwa junan su wani kallo tace "Yaya Fahad a yau kuma a wannan ranar nake yimaka albishir cewa duk wani shirme ya kare, ni Fateema har yau ina son ka kuma zan ci gaba da son ka har izuwa karshen numfashi na, ina son ka yaya na" ta karashe zancen da lumshe ido hawaye suka gangaro daga idon nata da sauri Yarima Fahad yakai harshen sa kan kumatun ta ya lashe hawayen nan tas batare da yabari ko d'aya ya sauka a kasa ba. "Na gode miki Fateema, na kuma godewa Allah daya nuna min wannan rana. Allah ya albarkaci rayuwar mu kuma ya bamu zuriya ta gari". Fateema kam har zuwa lokacin idon ta rufe suke gam tana jin kanta Kamar yau ta fara rayuwa a duniya. hakan ya bawa Yarima damar manna bakinshi a nata yana tsutsar leben ta ahankali ji yake kamar yana shan wata madara wadda bai taba jin mai d'and'anon ta ba lokaci mai tsayi suka d'auka a hakan kafin ya d'auketa cancas ya shige d'akin shi da ita. Suka zube kan lafiyayyen gadon shi Yarima ya shiga wasanni da sassan jikin Fateema wadda ta kwanta lif ajikin na shi ko motsin kirki batayi sam bata hanashi abinda yake yi ba sai ma ta tsinci kanta da jin dad'in yanayin da suke cikin A kunnen ta ya dinga rad'a mata wasu dad'ad'an kalamai na soyayya wayanda ko a mafarki bata taba kawowa zataji su daga bakin Yaya Fahad ba, hakan ya zaburar da ita batasan lokacinda ta shiga mayar mishi da martanin kalaman nashi ba a ranar dai haka suka kwana cikin farin ciki da faran tawa juna, duk da cewa babu wani abu daya shiga tsakanin su amma fa sun shayar da junan su madarar So da kauna washe gari da safe haka suka tashi cikin fari ciki sai tarairayar junan su suke abin dai gwanin birgewa. haka sukayi shirin zuwa kukunba karfe goma na safiyar Mai martaba ya aiko yace su fito Masha Allah haka kowa yake cewa lokacinda suka ratsa tsakar gidan sarautar Yarima da Gimbiyar shi sun sha kyau kamar yau suka fara yin ado da kayan sarauta. Suka shiga sashen iyayen nasu inda suka tarar da Mai martaba da Umma cikin shiri da ado na kasaita. Suka zube suka gaida iyayen suka amsa cikin farin ciki suka sakawa yaran albarka sannan suka mike suka shige gaba yaran na take musu baya suka nufi farfajiyar gidan inda motoci suke a fake an riga an gama shirya komai. *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *273/274* Masha Allah abinda kowane bafade ke fad'a kenan tun bayan auren Yarima basu taba fita irin wannan ba. kana'nan motoci guda biyar ne aka shirya domin tafiyar. d'aya ta Yarima da Matar shi, d'aya kuma ta Mai martaba da Umma. Ukun kuma na security da fadawa ne sannan aka tanadi hillous guda biyu wayanda aka cika su da kayan tsaraba tun daga kan kayan abinci har izuwa kayan sakawa turamen zannuwa da shaddodi da yaduka. bayan duka sun shiga motocin aka tayar suka fara tafiya. Fateema ta kalli mijin ta wanda tunda suka shiga motar bai d'auke idon shi daga kallon ta ba. "to kallon fa?" Ta fad'a Tana kallon shi, Yarima Fahad ya saki lallausan murmushin nan nashi tsadadde ya janyo Fateema zuwa jikin shi yai mata kyakkyawan mazauni a kirjin shi. "Ina kaunar ki Fateema, dan Allah ki daure kiyimin matsuguni a zuciyar ki, ki so ni Fateema, dan Allah ki kaunace ni." mamaki ya cika Fateema jin saukar hawayen Yarima bisa kumatun ta. da sauri ta tashi ta zauna da kyau Tana kallon shi tabbas kuka yake Innalillahi. Hannayen ta ta saka ta tallafe kumatun sa "Haba Yaya na, meyasa zaka yimin asarar hawayen ka akan abinda kake da tabbacin ka samu? Yaya, na so ka tun bansan miye so ba, na kaunace ka tun bansan kaina ba, to meyasa zan ki ka yanzu da na mallaki hankali na? na tabbatar zuciya ta bazata taba aikata wannan kuskuren ba" ta rungume mijin ta Tana share mishi hawaye dad'i da farin ciki suka lullube Yarima "cikin farin ciki yace "na gode Fateema nayi miki alkawarin zama bawa gare ki a wannan rayuwar, na zama rakumi kuma na hannunta miki akalar Fateema *ni naki ne* , ki taimake ni ki cigaba da kasancewa kusa dani kamar haka. dan Allah kar ki koma yin nisa dani kinji" "bazan koma barinka ba *Yaya Fahad* Ina son ka" suka koma rungume juna kowannen su najin dad'in sabuwar rayuwa da sabon yanayi na kusanci da suka tsinci kan su a ciki dai-dai nan suka ji motar ta tsaya ya d'aga ta daga jikin shi sannan ya karbi jakar ta ya ciro bandir-bandir na kud'i guda biyar ya zuba Mata a jakar ta, ga wannan ki rabawa mutanen kukunba Ki tabbatar musu yanzu ke gimbiya ce Matar Yariman Gombe, sauran kayan tsarabar suna mota anjima za'a fito dasu" hawaye ne suka ciko idon Fateema "na gode yaya na, ubangiji Allah ya bani ikon binka in maka biyayya kamar yanda addini ya tanada" ya share Mata hawaye kiyi farin ciki Fateema, ni naki ne har abada" shine ya fara bud'e motar ya fito lokacin ne wani security yazo da sauri zai bud'e gefen da Fateema take Yarima yayi gaggawar d'aga masa hannu, mutumin ya koma baya Prince ya taka da kanshi ya bud'ewa gimbiyar shi ta fito. Sai a lokacin ta fara karewa kauyen nasu da kofar gidan su kallo Mai martaba ma tsaye yayi kamar wani bako Yana kallon gidan d'an'uwan nasa. Sauye-sauye kam kauye ya samu sannan gidan su Fateema an canza mishi gini daga yanda yake da zuwa katafaren gida Mai zagaye da fulawoyi hadda gate d'in mota. Ga manyan shaguna guda biyu a gefe, inda suka hangi yaya Bashir Yana fitowa daga cikin su ya nufo su da saurin shi ya tsuguna Yana gaida Mai martaba. daga cikin gidan kuma Baffa ne ya fito Yana lale marhabi da zuwan su. Farin ciki Mara misaltuwa ya lullube Fateema. da hanzarin ta ta Isa inda suke ta tsuguna har kasa ta gaida Baffa da yaya Bashir suka kalle ta cike da kulawa suka amsa Baffa ya kalli Mai martaba cikin harshen fulatanci yace "yaya yar'ka fa ta girma da alama ta nusu, yau Fateema a kukunba duk dad'ewar nan ba ihu ba tsalle?" dukkan su sukayi dariya har ita d'in hakan yayi dai-dai da isowar Yarima inda suke, ya tsuguna gaban Baffa ya gaishe shi ya amsa cikeda kulawa Yana tambayar shi "yaya hanya" yace Alhamdulillah" Mai martaba ya kalli Baffa "d'an'uwa wannan sauyin gida haka ba sanarwa?" Baffa yayi dariyar su ta manya yace "hana ni akayi yaya, aikin Yarima ne, duk shi yayi komai kuma yace kar in sanar maka Wai duk randa kazo zaka gani" sosai Mai martaba yaji dad'in lamarin domin hakan ya kara tabbatar mishi yaro ya dawo hayyacin sa, Kuma ya d'auki Matar shi da daraja. Umma da Baffa suka gaisa sannan suka d'unguma zuwa cikin gidan inda suka tarar da kyakkyawar tarba daga Goggo tsabagen murna da farin ciki tarasa inda zata saka Fateema taji dad'in yanda ta ganta yarinya tayi jajur da ita ga yadda jikin ta yayi kyau ko manafuki ya kalle ta yasan tana cikin kwanciyar hankali. aka gabatar musu da kayan abinci kala-Kala dad'i da farin ciki sun cike zuciyar Fateema soyayyar mijinta ta dad'a ninkuwa a zuciyar ta gidan su yayi matukar kyau ciki da waje kamar tana cikin Masarauta haka take ji. An dad'a yawan d'akuna a gidan an zuba masu taya Goggo aiki yan'mata guda biyu an kafa fanfuna da ababen more rayuwa a kowane lungu da sako na gidan .... *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *275/276* A babban falon gidan aka sauke su inda suka ci mai dad'i suka sha mai dad'i, a nan ma Fateema ta gano cimakar gidan su ma ta canza, an Sami ci gaba sosai. Bayan sun kammala cin abinci da gaishe-gaishe ne Umman Yarima ta fara rokon gafarar iyayen Fateema tana dad'a basu hakuri akan abinda ya faru a baya. Suka ce ai komai ya riga ya wuce, baya-baya ce yanzu kam Sai dai a fuskanci gaba. Taji dad'i sosai Sai jan Goggo a jiki take ita kuma ba saban ba har yanzu d'ari-d'ari take da ita Yarima Sai kallon Fateema yake ta koma can nesa dashi ta zauna ta d'ora kanta a cinyar Goggo. Sai yaji Ina ma a cinyar shi ta kwanta ya shiga ayyana yanda zai ji. Su Baffa da Mai martaba suka mike suka koma d'akin ajiye baki na kofar gida Wanda shima yanzu an kawata shi da lundum-lunduman kujeru da Kayan kawata falo irin na manyan mutane. d'akin ya rage saura Goggo da Umma, Yarima da Fateema Dan Yaya Bashir kam tun d'azu aka Kira shi waje za'a sayi Abu a shago yanzu ya zama d'an kasuwa domin shi Yarima ya ginawa shagunan kuma ya cika mishi su da Kayan business na bukatun al'umma. Yarima ya mike Yana sosa keya yace "Ina son zaga garin nan gashi bansan ko Ina ba, ga yaya na kuma shago ya rike shi". Iyayen sukayi dariya Umma tace "to ai ga Matar ka nan, Sai ka sakata gaba ku tafi" Fateema kamar jira take tayi zumbur ta mike tsaye "yawwa yaya muje, kaga daga can sai ka cika min alkawari na ko?" "haka ne fa" ya fad'a Yana fita daga d'akin ta bi shi a baya. Iyayen suka girgiza Kai suna murmushi cike da Jin dad'in yanda yaran suke tafiyar da rayuwar su. dai-dai kofar gidan sukayi karo da Innawuro (kawar Fateema) da gudun ta tazo kamar zata tashi sama, tana ganin Fateema ta kankameta sam bata damu da Wanda ke gefen ta ba. Itama ihun murna ta saki suka rungume juna cike da murnar sake had'uwa Yarima kam gefe ya matsa Yana kallon yaranta. Suka saki juna Innawuro tace "Kai Fatee kin ganki kuwa?, ya Salam!,wayyo Allah Fateema wlh kinyi kyau kamar ba ke ba. Wayyo Fatee na" ta koma rungume ta. Fateema tace "kedai bari yanzun ma ta gidan ku naso biyowa in mun dawo, fita zamuyi da yaya" ta fad'a tana kallon inda yake. Sai a lokacin ta lura da Yana wajan ta rusina ta gaishe shi ya amsa da fara'a yace "Ki shiga ciki yanzu zamu dawo" "to" tace ta shige ciki tana cewa Faeema "kar fa ku dad'e Adda tana jira na a gida" "kekam Ki shiga ciki yanxu zamu dawo" ceear Fateema tana washe baki yau dai kam farin cikin ta ya kasa boyuwa dad'i takeji sosai a ran ta. suka fice ita da Yarima a jere suka ratsa garin kukunba duk inda suka bi sai a bi su da kallo samari da yammata duk Wanda ta sani idan ta ganshi sai ta tsaya sun gaisa ta bud'e jaka ta ciro kud'i masu yawa ta basu. da haka har suka Isa dai-dai wurin da Yarima ya mare ta taja ta tsaya cak "yaya a nan ne fa" ta fad'a tana kallon shi Sai a lokacin ta lura da canjin da fuskar shi tayi kamar ran shi ya baci maimakon ta damu sai ta fashe da dariya "kaga yaya da wayau,borin kunya da wayau zaka yi min? Allah ni fushin ka bazai hana ni rama mari na ba". da karfi ya fisgo ta, ta fad'a jikin shi yayi amfani da d'aya hannun shi ya matse bakin ta sai da taji zafi batasan sanda ta saki Kara ba "kaga mugu wani ma zaka dad'a akan wancan? Allah shima Sai na rama" cikin bacin rai ya fara magana "ban damu ba kiyi ta mari na Fateema, amma Sam bazan lamunci ganin kina gaisawa da katti kamar haka ba, shin kin manta da matsayin Ki ne? Kefa Matar aure ce kuma gimbiya Matar d'an sarki ya kamata Ki kula kusan mutuwa nayi lokacin da kike musu murmushin nan" mamaki ya mamaye Fateema lallai ma Yarima wato abinda ya bata mishi kenan tayi rau-rau da ido sai hawaye shar akan fuskar ta da sauri ya sassauta Mata rikon da yayi Mata "meye abin kuka kuma Fateema?, no pls ya Isa haka kiyi hakuri amma Ki dinga tausaya min kinji mata'ta" ta gyad'a Kai tareda cewa "to" ya raba jikin shi da nata suka fuskanci juna yace "gani gaban Ki kuma na baki dama ki rama marin da nayi Miki Fateema" tayi murmushi lokacin da ta d'ora tafin hannun ta bisa lallausar fatar fuskar shi "bazan taba iya marinka ba Yaya na, ka sani na kawo ka nan ne domin ka tuna ranar da na fara furta maka so da kuma tsayin lokacin, Yaya ba ranar na fara son ka ba, na so ka tun banida wayau da wannan nake tabbatar maka bazan taba barin son ka ba" ba karamin dad'i kalaman Fateema suka yi mishi ba ya kasa cewa komai sai dai janta da ya koma yi ya manne ta da kirjin shi "na gode Fateema da wannan nake Kara tabbatar Miki ni *Fahad naki ne* ciki da waje kin kulle ko Ina kanwata" lokaci Mai tsayi suka d'auka a hakan kafin ta raba jikin ta da na shi ta rike hannun shi suka kama hanyar gida zuwa lokacin gabad'aya garin ya d'auka sarki yazo gida da shi da iyalan sa, hakan yasa Mai gari da mutanen garin fitowa domin kawo gaisuwa ga Mai martaba sarkin gombe. An rarraba tsaraba sosai ga yan'uwa da makota harma da mutanen garin sannan aka cika store na gidan fall da kayan abinci Fateema ta bawa Innawuro kaya niki-niki da nata da na Umman ta da kuma na sauran kawayen su sannan ta kara musu da kud'i. Suka yi ta godiya sukayi sallama. Bayan ta gama rabe-raben ne ta kirga ragowar kud'in dubu d'ari uku da arba'in duka ta bawa Goggo su tace ta ajiye ita ma ta fara wata sana'a Uwar tayi ta godiya da d'inbin alkhairi domin nata manyan turamen zannuwa ma daban aka kebe Mata su. Karfe biyar suka yi sallama da kowa suka kama hanyar gombe zukatan Su cike da farin ciki. Tun a mota Fateema ta fara yiwa Yarima godiya akan irin gyaran da yayi wa gidan Su ya rufe Mata baki Yana fad'in "karki d'auki abin da banbanci Fateema, Ki tuna matsayin Baffa gareni ya fi karfin wannan a gurina. a shekarar nan ma duk tare da Su zamuje aikin hajji insha Allah" ta kwantar da kanta bisa gefen kafad'ar shi a hankali tace "ka tare ko Ina da ko Ina yaya na, Ina kaunar ka" yayi murmushi ya shafi fuskar ta "nagode Teema na" lokacin da suka iso fada magariba ta kawo Kai shiyasa Yarima da Mai martaba suka nufi masallacin fada, tareda mutanen da suka tarbe Su. Fateema da Umma ko cikin gidan suka wuce inda suka yi Sai da safe kowacce ta nufi sashen ta *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍ *277,278* Yau kam gaba d'aya rayuwar Fateema fess take, ji take kamar ma bata taba jin farin ciki kamar na yau ba kamar yadda take jin soyayyar mijin ta na tafasa a zuciya da sassan jikin ta kamar dai wannan shine farkon soyayyar inji (Nasmt 😉) da shigar ta d'akin ta rage Kayan jikin ta ta shige toilet tayi wanka da had'in turarukan ta sannan ta d'auro alwala tazo ta fara gabatar da salla bayan ta d'auki lokaci Mai tsawo tana roka musu zaman lafiya da kwanciyar hankali ita da mijin ta tare da neman kariyar Allah akan duk wani Mai nufin Su da sharri. Ta mike ta zauna gaban madubi cikin kankanin lokaci ta rangad'a kwalli fuskar nan tayi shar da ita, kyawun ta da kuruciyar ta suka Kara bayyana a lokacin da ta d'auko wata doguwar Riga ta roba ta saka rigar yar ficik ce mara nauyi irin Masu bin jikin mutum d'innan, tayi wa gashin kanta wani style a gaban sannan ta zubo ragowar baya sai ka rantse baindaya ce. Kasancewar yanzu Fateema take tasowa gabad'aya albarkatun jikin ta sun cike kyakkyawar surar ta Mai fizgar imanin duk wani cikakken namiji ta bayyana ta feshe jikin ta da had'ad'd'un turarukan ta ta kimtsa wurin ta nufi kitchen a can ta Sami Rukayya da Bilki wayanda yanzu sune Masu kula da abincin gidan ta duk da ita take girkawa amma suna taya ta. Yau kuma ganin bata gidan yasa suka d'ora Mata. "Sannun ku da kokari yan'mata" ta fad'a cike da zolaya "Kai anty Fatee, Wai yan'mata sannun Ki da dawowa" suka gaisheta duka ta amsa cikin sakin fuska "yau na barku da aiki ku kad'i" "banda abin Ki anty ai aikin mu ne, Kin Sami mutanen gidan lafiya?" "lafiya lau na same Su Sai alkhairi" Bilki ta canza maganar da cewa "Kai anty Faty tubarkalla wlh kullum Kara kyau kike yi, kin gan Ki yau kuwa?" Tai murmushi "zaku fara ko?" sukayi dariya "ai fad'ar gaskiya baya zama laifi". Ta kyale Su ta shiga duba abinda suka girka. Tuwon doya ne da miyar agushi ta sha kifin hausa busashsshe Sai farfesun kaji daban Sai kuma soyayyen naman shanu Wanda yaji had'in yaji na gargajiya, ta yaba ma aikin Su sannan ta saka plate kowanne ta d'ibi kad'an dai-dai da bukatar Su tace Su d'auki sauran suje Su ci kar Su baci sukayita godiya ita kuma ta d'auki babban tiren da ta jere Kayan ta nufi d'akin Yarima. Bata sameshi a d'akin ba amma taji motsin ruwa a bayi alamar Yana wanka. Hakan ya bata damar Kara gyare d'akin ta feshe shi da turare a cikin wardrobe d'in shi ta d'auko mishi kayan sakawa wasu na Shan iska mara nauyi ta ajiye Su gefen gado bayan ta feshe Su da kalar turaren daya ke amfani da shi. da fitowar shi yayi tozali da ita cikin irin shigar da yafi so a jikin ta Sai da ya lumshe ido yayi godiya ga wanda ya bashi Fateema sannan ya Karaso gare ta inda ta tare shi kamar ba ita ba sosai ta bashi mamaki domin da kanta ta tsane mishi ruwan jikin shi ta shafa mishi Mai da turaren jiki ta taje mishi gashin kan shi ya kwanta yayi luf-luf sannan ta bashi kayan da zai saka sannan ta d'auki Wanda ya cire ta kaisu cikin wata drower inda suke tara Kayan wanki. Ya bi ta da kallo lokacin da yake saka kayan ganin Kayan abinci a d'akin shi yau ya tabbatar mishi cewar da gaske take ta canza komai cikeda zumud'i ya gama saka Kayan inda ya sameta bisa lallausar garass capet dake tsakiyar d'akin tana zuzzuba musu abincin ya zauna daf da ita ya rad'a Mata wani Abu a kunnen ta bansan me ya gaya Mata ba naga Dai tayi murmushi sannan ta ajiye abinda take ta manna mass kiss a gefen kumatu " *I love you* " ta fad'a kanta a sunkuye farin ciki ya Kara lullube Fahad haka Fateema ta zama? ya Tambaya a ransa "Alhamdulillah" ya koma fad'a a fili. Abincin suke ci amma dukkan Su ba Su maida hankali ga abincin ba domin dama ba yunwa suke ji ba wasannin Su suke da tsokanar juna haka dai har suka kammala zuwa lokacin an fara Kiran sallar isha yashiga bayi ya d'auro alwala ya tafi masallaci ita ma tashin tayi ta harhad'a kayan abincin ta mayar kitchen ta kimtsa wurin sannan takoma d'akin ta tayi alwala tayi sallar farilla tana addu'a ya shigo ya zauna gefen ta lokacinda ta shafa addu'ar ta mike domin yin nafila shima ya mike ya shiga gaban ta Yana fad'in "yau jam'i zamuyi Ni da mata'ta" ba musu ta bishi sukayi bayan sun kammala ya koma umartar ta suka mike sukayi wasu guda biyu Inda suka d'auki lokaci Mai tsayi suna godewa Allah bisa barin Su tare dayayi dakuma neman zaman lafiya Mai d'orewa a tsakanin Su daganan Yarima ya fara janta a jiki. da wayau ya kaita bayi da rigima da komai ya rabata da kayan jikin ta ya sake musu ruwa Masu sanyi wanka na farko da ya taba yi tare da Fateema Sai yaji kamar kar Su fito amma daya tuna da muradin shi a yau Sai kawai ya d'auko ta cancas bai direta ko Ina ba Sai bisa gadon ta a lokacin sanyi take ji sosai Sai kudundunewa take a jikin shi shikuwa dama haka yafi so ya shiga sarrafata cikin salo da kwarewa tun suna gano kan Su har suka yi nisa da wannan duniyar suka daina gane komai (ganin hakan yasa na had'a Yan papers d'ina nace bari inabawa yarima guri domin cike burin rayuwar shi, a kunne na rad'awa Fateema asuba ta gari lolz) *Yar'mutan Arkilla* ✍ 💞💞💞 *yaya*💞💞💞 💞💞 *fahad*💞💞 💞💓💞 💓 💞💞💞 *Nawa*💞💞💞 💞💞 *ne*💞💞 💞💓💞 👯💓👯 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Writing by* _Nasmatu Muhammad_✍. . *280* *The* 🔚. Washe gari misalin karfe hud'u na asuba ta farka domin Yarima kam ko baccin bai samu ba tunda ya Sami Fateema bai koma gane komai ba Sai bayan yasami nutsuwa Sai a lokacin ya lura da halin da take ciki da Tsanani wuya da galabaita hankalin shi yayi mutukar tashi sai kuka take mishi tana kiran Goggo, cikin Daren ya Kai ta bayi ya gasa Mata jikin ta bayan ya tsaftace Mata shi har ya kwantar da ita bata daina kuka ba yashiga aikin rarrashi da bata baki Yana lailayeta da hannayen shi a haka yasamu bacci Mai nauyi ya d'auke ta a cikin baccin ma tanata shesheka da sauke manya-manyan ajiyar zuciya Allah sarki Fateema Sai tausayin ta ya mama shi tsananin so da kaunarta suka Kara bin sassan jikin shi, tun da tayi baccin yake makale da ita idon shi kyar akan ta ya kasa bacci har izuwa yanzun da ta farka. Ganin idon shi tamas ya tabbatar Mata da bai rintsa ba tausayin shi ya kamata tana shirin janyo shi jikin ta Sai ta tuna da abinda ya faru a Daren jiya. da sauri ta sake shi sannan ta kudundune fuskarta a mayafi yayi murmushi "feel free Teema na, a yanzu ke cikakkiyar mace ce, ina tayaki murna na samun nasarar kawo budurcin ki gidan mijin ki. Fateema ke babbar mace ce wadda irin ta ke wahalar samu a wannan lokacin, zanyi iya kokarina wajan ganin ban koma rasa kiba kece rayuwar Yarima Fahad" ya fad'a yana had'ata da kirjin shi lokaci d'aya taji duk wani ciwo da rad'ad'in da take ji dun kau, soyayya da kaunar mijin ta suka mamaye ta ta rugume shi tsam Tana hawayen farin ciki da godiya ga Allah da irin tsare-tsaren da yayiwa rayuwar ta. hakika abin farin ciki ne ga kowacce mace ya kasance her first love been her husband. Yarima ya mike ya d'auki matarshi suka shige bayi sukayi wanka suka fito tare suka gabatar da sallar nafila sannan ya fita masallaci ya barta Tana shirin kabbarta farilla. A wunin ranar ko tsinke bai barta d'agawa ba shine ya wuni yimata hidima yana tarairayar t. Bayan kwana biyu yazo mata da passport na barin kasa ya tabbatar mata maganar zuwa aikin hajjin nan ce ta taso kasancewar an fara d'aukar mahajjata an riga angayawa su Baffa suna can suna shirye-shirye. tayi marin cikin jin hakan bayan kwana uku aka kira su su duka suka tafi Mai martaba da Baffa, Yarima da yaya Bashir da Umma da kuma Fateema abin dai sai wanda ya gani. A daddafe ya samu aka gama aikin hajji suka dawo gida domin yayi kewar matar shi matuka ita kuwa ko ajikin ta yanzun ma da suka dawo d'akin Umma ta sauka ganin Goggo a gidan ta sauka kafin gobe a kai su kukunba Yarima sai zagaye yake ya rarasa yadda zaiyi ya sami Fateema bayanda ya iya haka ya hakura ya koma ya kwanta can cikin dare ya ji shigowar ta Umma ce ta korota tace taje gidan ya hakannan da sand'a ta shigo dan tun da suka iso ta lura da take-taken sa. Hmmm bata san idabshi biyu ba ta shige bayi tayi wanka ta fito Tana sand'a saida ta murje jikin ta da mai da turarukan ta sannan ta kwanta a silale azaton ta Prince bacci yake sai ji tayi an rungume ta ta baya ido waje ta juyo Tana kallon shi cike da tsoro sai ta bashi dariya ya kuwa yi mai sar sa sannan yace "yi hakuri kanwata ki taimaka min wlh a hanu nake, kuma bazan miki irin na wancan karon ba i promise" hawaye ne suka ciko idon ta "Allah yaya ni tsro nake ji" ya shiga share mata hawayen yana rarrashinta da haka har ya cimma abinda yake So. Washe gari da kwarin ta ta tashi ba kamar wancan karon ba karfe tara sukayi breakfast suka shiga gida dan gaida iyayen su suka gaishe su. Sun d'an taba hira a nan kafin ya tashi ya fita fada saboda masu zuwa gaisuwar barka da dawowa. Ya barta nan tare da gwaggo da Umma suna shan hira. Karfe uku na yamma aka kai su Umma kukunba. daga ranar Hajiya Fateema da mijin ta suka zama irin masoyan nan da basa son rabuwa ko kad'an, bata so yarima yayi nisa da ita haka shima a nashi bangaren ga wani irin so na Fateema dake kara mamaye ilahirin sassa da gabobin jikin shi jin ta yake kamar ransa tattali da kulawa kam sai wanda ya gani. haka satuttuka da watanni suka shud'e wata shida da dawowar ta su Fateema ta fara laulayin ciki Allah sarki Yarima Fahad sai ya kara zama wani abin tausayi ko motsi tayi sai ya tashi koda kuwa a cikin bacci ne, farin ciki ya lullube iyayen kasancewar Yarima kad'ai suka haifa a duniya. gata na duniya kam Fayeema ta same shi bayan watanni tara ta santalo d'an ta, fari sol mai kamada Uban sa. Farin ciki kam ba'a magana duk inda ka duba yan taya murna ne ga d'aukacin iyalan mai martaba. A ranar suna kuwa mai jego tazama tauraruwa abar son kowa, d'aukacin mutane mota biyu aka ciko daga kukunba na yan'uwa da abokan arziki ina aka sha biki naji da fad'a ilahirin membres na Nasmat novel duk sun halarci bikin haka ma na King boy Isa novel, (King hadda bada babbar jaka yace Hadiza hadi ta ciko masa da kayan makulashe lolz 😝) haka membres na Ama Alhaji kabir novel, ga yan gidan Asmart &deeyart ga na Maryam Ameen kai gaskiya su Yarima sun ga baki yaro yaci sunan Aliyu taron suna kam ya kai taro garin gombe ma ya shaidi hakan. Tun daga wannan ranar alkhairai suka kara kunno kai a gidan sarautar. Bayan shekaru Uku dana koma gidan a falon Umma na sami Aliyu yaron Fateema yanata kiriniya yana wasa da Umma. A sashen Fateema kuwa akasin hakan ba tarar domin samun su nayi suna ta jibga kaya a jakunkunan tafiya kallo d'aya nayiwa fufkarta na gano Tana d'auke da karamin ciki suka gama had'a kayan suka fito cike da annuri a fuskokin su dai-dai kofar fita daga sashen nasu suka tsaya tare suka kalli juna suka saki murmushi ya sanya hannayen sa duka biyu ya tallafo kumatun ta cikin sigar soyayya ya fara magana "Yau na kudur ta aniyar cika miki burin ki matata ina yi miki albishir da cewa lokacin da kafarki zata koma tako nan gidan to kin zama cikakkiyar likita" tayi murmushi Tana fad'in "kai cikakken namiji ne yaya na, na tabbata zaka iya duk abinda kayi niyya, godiya ga Allah daya bani miji mai riko da alkawari sakallahu bi khair" "na gode da yabon ki matata sai alkawari na biyu dazan miki shine na bayar da aikin gina miki babbar asibiti wadda na tabbatar kafin mu dawo an kammala ginin filin yana nan bayan mu direct za'a fitar miki da kofa daga cikin sashen nan zuwa cikin asibitin ki ina kaunar ki matata" farin ciki ya lullube Fateema ta rungume mijin ta cike da murna "wayyo Allah Yaya na na gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairin sa Allah ya biyaka da mafificiyar aljannar sa" "Ameen Teema na Allah ya sauke ki lafiya " yaja hannun ta suka isa sashen Umma da shigar su yaro Aliyu ya rugo gun su da gudu "oyoyo dady na momy ina zaki?" Yarima ya kalle dhi cike da mamakin wayo irin na yaron kamar ba d'an shekaru uku ba ya tsuguna dai-dai tsayin yaron yace "inda nace maka zamuje mana boy, ko ka manta ne?" "Oh na tuna dady, inda zakayo corse kazama babban lacturer ko?" "thats my boy nasan bazaka manta ba" Umma ta fito daga d'aki Tana fad'in "a'a matafiyan har sun fito?" "mun fito Umma" inji Yarima Umma tayi musu addu'a da fatan alkhairi tareda fatan Allah ya bada abinda zaije nema (kamar yanda ya gaya musu zaije wani course ne na shekaru bakwai amma zasu dinga zuwa hutu lokaci-lokaci) shine fa Umma ta dage bazai d'auke mata Fateema kuma ya raba ta da Aliyu ba dole ya bar mata d'aya hakan ne yasa zasu bar Aliyun gida tun jiya sukayo sallama da mutanen kukunba tare da rakiyar mai martaba aka kaisu filin jirgi a gaban iyayen da d'an su jigin su ya tashi suka bar kasar haihuwar su zuwa Ijeep neman ilmin matar sa. A kasar ijip sun sami tarba mai kyau da kyakkyawan masauki gidane sukutum aka mallaka musu dukayi sati d'aya suna hutu a sati na biyu ne ya nema mata admission a wata babbar jami'a wadda aka gina ta musamman domin karantar likitanci duk fanni da mutum yake da bukata Yarima kuwa makarantar horar da malamai ya shiga domin ya samu gogewa akan lacturing bayan yan watanni karatu ya kankama na kowannen su sai dai a bangaren Fateema Tana fama da d'awainiyar ciki cikin da yariga ya tsufa dai-dai lokacin ne kuma suka sami hutun karshen shekara. Sosai taji dad'in samun hutun na watanni hud'u hutun bai Kai sati d'ayaba ta haihu inda Allah ya azirtasu da ya'mace a nan ya d'auko wata likita ta Riga kula da Fateema da babyn ta Su kad'ai suka aha suna inda yarinya taci suna Ameena mutanen gida kam sundai ga baby a photuna da vidio call, yarinya Meena Tasha gata da tattali Sai suke jinta kamar yar'fari bayan watannin hutu baby ta fara kwari yar raino aka samowa Fateema wata dattijuwa musulma Mai suna Aysha raward. Ita ce Mai kula da Meena kafin Umman ta ta dawo daga school karatu kam Fateema ta dage babu kama hannun yaro shine ma yasaka ko hutun shekarar farko basu Sami zuwa ba a hutu na biyu ne suka je Nigeria inda suka sha tattali da tarairaya yaron Su Aliyu ya Kara girma da wayau har an sakashi nursery yaro d'an 5yars soyayyar Fateema da Yarima Fahad kam sai wabda ya gani kullum idan ka gansu Sai kayi zatan ko saurayi da budurwa ne, haka hutu ya kare suka koma egeep rayuwa tacigaba da tafiya satika suna ture watanni su kuma suna ture shekaru hausawa Dai sun ce komai yayi farko zai yi karshe yau Dai Allah ya kawo karshen karatun Fateema Allah yayi ta kammala suk kuma dawo gida Nigeria inda suka zowa da Familyn da wani sabon al'amari wato Fateema ta zama cikakkiyar likitar Mata abin mamaki da al'ajabi bangare d'aya kuma abin fahari domin an kammala ginin asibitin ta Mai suna (Mrs. Yarima women hospital) shi kanshi Mai martaba bakaramin dad'in al'amarin yaji ba gagarumin biki ya shirya musu inda yan'uwa da abokan arziki suka zo taya murna ta Sami cikakkun takardu na shaidar zamanta likita Mai zaman kanta tunda suka dawo busy suke kullum cikin shirye2 suke komai na dangane da Kayan aiki sun gama had'uwa hatta wayanda akayo order sun iso, an gama Diban ma'aikata horses da wasu likitoci Mata Alhamdulillah yau itace ranar da aka kebe domin fara aiki a asibitin Dr Fateema masha Allah jama'a kamar jira suke asibiti ta cika ta tamgatse ayau burin Fateema ya cika a rayuwarta babu abinda ta tsana kamar ta ga Mata musulmi a hannun likita namiji Wanda akasarin Su ma ba musulmi bane. Yau gata ga yan'uwanta Mata Masu neman agajin mace yar'uwar Su. idan tana ganin Su a gabanta Sam bata jin kasala ko lalaci aiki takeyi tukuru Yarima tun Yana damuwa Yana cewa ta huta har ya gaji ya barwa Allah yanzu yaran Su uku Aliyu (littlePrince) yanzu ya zama matashi Mai shekaru goma sha d'aya Sai kanwar shi Meena yar shekara takwas Sai karamin Su Al'amin d' an shekara hud'u yara Yan gata ta gaba da baya duk inda suka yi dad'i da gata suke sha fannin iyayen Su ko na kakanin Su baremma in sunje hutu a gidan kakanin su na kukun ba ko kuma in anclule Fa'eez d'in Su yaxo daga sokoto dashi da yaran sa da matarsa Anty Sameera wadda yanzu kawabce ne Mai karfi tsakanin ta da Fateema haka Yarima da Fa'eez da kuma yaran Su duk da ba koyaushe ake had'uwa ba Su Fa'eez d'inma sune Masu yawan zuwa garin gombe kam sun more sun mance matsalar ciwo takai Su ga likitoci maza sadai jarumar Su Mai burin share kukan Su *Dr Fateema* tammat bi hamdallah dukkan yabo da kuma godiya sun tabbata ga Allah (s.w.a) daya bani dama da ikon kawowa karshen wannan labari na *Yaya Fahad Nawa ne* labarin dake d'auke da sakonni daban-daban jigo acikin Su shine *HAKURI* musamman gare mu mu yan'uwa Mata ma dage mu zama Masu hakuri domin shine solution na kowacce matsala ta duniya duk wani kalubale da zaki fuskanta Ki saka hakuri a gaba Wanda ya jarabce Ki da wannan matsalar zai kasan ce tare da ke ya kuma magance Miki ita in a simple way taku har kullum (yar'mutan Arkilla) nagode da kaunar ku gareni da kuma bibiyar littafi na da kukayi inaneman ggafarar duk Wanda na batawa rai a cikin wannan rubutun nawa ko ta dalilin shi daga karshe kirana ga yan'uwa marubuta mu watsar da girman Kai mu so juna ta yanda hankali da nutsuwar makaran ta zai daidaita garemu aikin mu shine fad'akarwa *Godiya* ga ilahirin members na kungiyar ZAMANI writers association bisa gyararraki da shawarwarinku ga Nasmat Ana matukar tare🤝 Allah ya Kara d'aukaka ZAMANI WRITERS ASSOCIATION makaranta labarin Yaya fahad nasan koda da sunayen groups nayi amfani bazan iya kirga ku ba Sai dai in ce nima Ina kaunarku fatan alkhairi gareku a duk inda kuke. Albishir da zan muku shine mu tafi Kai tsaye ga sabon Novel d'ina na gaba (JA'JIRTACCE) 🙏 *Yar'mutan Arkilla* ✍