AUREN NESA NA KADIJA ABDULLAHI BATURE. K'yiuuuuuuu karar kaucewar motar mu ce ta tasheni daga baccin da ya daukeni shi kansa baccinma kutse ya yi min don ba muhallinsa bane. Wata katuwar motar daukar mai ce taso mu yi taho mugama , ba don Allah ya kiyaye ba dreban motar da muke ciki ya yi hanzarin kaucewa muka koma gefen titin a kayi gefe da gefe. Masu salati na yi masu ihu na yi, har muka yi nisa gabana sai dakan uku uku ya keyi jikina na ta faman kyarma sboda hanta ta da ta riga ta kad'a. Kamal shi ne ya kalleni ya na murmushi "maryam ki samu nutuwa mana ai Allah ya kiyaye "nasa kuka" wai don Allah Kamal yaushe za mu karasa ne yau fa kwananmu uku a hanya, wllh duk na. gaji na k'agara mu karasa . "Ki k'ara hakuri don ba ki Saba doguwar tafiya bane shi ya sa, Amma da mun karasa za ki ji duk gajiyar taki zata warware . Na yi kusuk'wui tare da zabga wani mugun tagumi ina tunani, don na fara karaya da lamarin, kaddai hakkin iyaye ne ya fara kamani. Yau kwana na uku a hanya mai makon a ce a yanzu ina gidana. Babu yadda mahaifana da yan,uwana basuyi da ni ba akan auren nan amma na kekasa kasa na ce ni na ji na gani. Musamman mamana "Maryam ni dai hankalina bai kwanta da aurennan ba tunda mu dai kinga ba wani sanin danginsa muka yi ba, ba Kuma musan garinsu ba in banda sanin sunan garin da muka yi , ga nisa in ba Allah ne ya kiyaye ba in wani a bun ya faru ya ya za mu yi , da mu da ke, daga ya ce ya na yawan zuwa kasuwanci, sai ki bi ki makale masa? " Wllh mama mutumin kirki ne ,ba ki ji yadda yake yawaita yi min wa a zi ba ,kuma kinga tun da ,danayi ta korar samari duk wanda yazo ince baiyiminba har kowa ya dena zuwa yanzu wa ye ya ke zuwa ?, duk k'awayena sunyi aure ,daga mai y'ay'a uku sai biyu har cewa ake ko bazawara ce ni ,to idanna koreshi wa nake dashi da zan kawo muku? A haka na shawo kan iyayena da yan uwana ba tare da son ransuba. Ya aiko wasu maza su uku a cewarsa wai y'an uwansa ne suka kawo dubu hamsin kudin nagani inaso tare da sa rana wata biyu , sai gabda bikin sannan way'annan mutanen da ya kirasu da y'an uwansa suka kawo lefe akwati uku . Babbar akwatin kayan cikinta guda bakwai ne rak , sai mai binta takalma hudu jaka biyu ,karamar kayan kwalliyane yan yaf aciki, ni dai don aurenne kawai a gabana shi yasa bandamu sosai ba , yan'uwa ko da abokan arziki babu wanda bai tausaya min ba ,amma sai suce ai ita ta siyawa kanta , babban fatan dai shi ne Allah ya basu zaman lafiya ya Kuma rike amana. Ranar biki ya zo da kansa ya samu iyayena wai bayason y'an rakiya saboda nisa daga shi sai amaryarsa, da mamana taki yarda mahaifina ya ce ta yi hakuri ta barmu mu tafin insha Allah Allah zai kiyaye ta Haka aka d'aura min aure da zab'ina wa to kamal , ba wani taro akaiba illa yan,uwa da makwabta aka danyi yini da safe kuma za mu tafi ni da ango na kamar yadda ya tsara. Haka akayi kuwa washe gari tun safe na harhad'a yan kayana na sa a kwatunan da ya kawo min tunda kayan ciki basu da yawa, haka na had'a na kulle su. Na shirya tsaf ina ta faman jiran ango ,saican wajan karfe uku na Rana yazo shida abokansa guda biyu wai intaho mu tafi ,haka muka firfito ni da y'an gidanmu sukayi min rakiya har bakin motar da su Kamal sukazo da ita mukai d'an koke- kokenmu na al,ada kamar yadda aka saba in za a kai amarya , ina kallo sukaimin sai wata Rana ,direba ya ja muka d'au hanya, a bakin titi aka sauke abokanansa mu Kuma muka nufi Tasha inda muka hau motarmu ta zuwa Togo. Bayan doguwar tafiya da mukasha Allah ya kaimu Togo lafiya mun sauka da la,asar sakaliya nan muka hau mashina guda biyu wadanda za su kaimu cikin unguwar su Kamal. Tun akan hanya tsoro da mamaki da fargaba duk sun taru sun dabaibayeni ganin muna ta shiga cikin irin gidajennan na ibo da muke gani a( fim) ga mutanen garin na yawo da d'igil-d'igil din kaya kamar ba musulmai ba mamakina ya dad'a fad'ad'a inda na hangi wasu y'anmata su na ta faman wanka a kogi hankalinsu kwance . Banyi aune ba naji mashin din da nake kai ya ja ya tsaya alamun mun karaso. Aka sassauke mana kayanmu daga kan mashinan suka ja suka koma inda suka fito . Mu kuma mukanufi wani gida mai zagaye da karare tun daga waje kana iya ganin cikin gidan mai dauke da bukkoki kamar guda uku aciki. Ni dai sai faman zazzaro idanuwa nake yi bakina na ambaton innalillahi wa Inna ilaihirraji un. Tun kafin mu karasa shiga wasu tub'a-tub'an mata suka rugo daga ciki da gudu suka rukun kumeshi suna wani irin yare , cikin nuna farincikin dawowarsa. Ni kuwa tuni na riga na daskare ,zuciyata cike take da al,ajabi tare da tarin tambayoyi , to wai dama Kamal yare ne ? To musulmi ne? Kuma dama anan yake? Banyi zato ba na ji ya na Kiran sunana , na yi firgigit na farka daga tunanin da na yi nitso a cikinsa. Na lura gabatar da ni yake a wajan su . Babu wadda ta ce dani (ta tafasa sauke) Kamar wanda ya yi musu bushara da ranar mutuwarsu suka koma cikin gidan cikin tsananin bacin rai. Gwuiwata ta dad'a yin sanyi ganin bansamu karb'uwaba a wajan y'an uwansa , ya yi min nuni da mu karasa ,fuskarsa ba yabo ba fallasa ,alamun shima baiji dad'in hakan ba. Haka muka kutsa kai sululu kamar wasu macizai na hangesu sun zagaye wata dattijuwa su na ta faman gwalantu daga gani nasan ana shaidamata isowarmu ne , haka muka karasa na yi saurin zubewa har kasa Ina gaida ita amma ko kallon inda nake batayiba, ban daddara ba a karo na biyu na sake cewa mun sameku lafiya ? Shima ba amsa, a zuciyata na ce toh wannan ai ita hausawa ke kira da ( shewar dila). Nan na samu guri na rakab'e , shi kuma ya tsaya kusa da su ya tayasu cigaba da luguden lab'ba , na zubawa sarautar Allah idanu . Oh ni Maryam yau ga inda Allah ya kawoni. Bayan sun tsagaita ya juyo gareni ya ce "maryama ga kanwa ta nan ya yi min nuni da wata acikinsu wadda na lura ita kamar abin baya yi mata dadi ya cigaba da cewa "zata rakaki daki zanje innemo miki abinci, na amsa da to na mik'e itama ta zo ta dauki kayana muka nufi bukka guda d'aya daga cikin bukkoki ukun da ke tsakar gidan. Bayan mun shiga na karewa bukkar kallo ba komai a ciki face wata yaloluwar katifa da wata tsohuwar tabarmar kaba (karauni), na zauna a gefen katifar Amma nafi bukatar kwanciya sakamakon matsananciyar gajiyar dake damuna, kwatsam naji ta ce "kwanta ki huta mana kamar tasan abin da ke cikin zuciyata ga shi na yi mamakin maganar da ta yi min da hausa . Ganin da ta yi na zuba mata ido cikin mamaki yasatayin murmuhi sannan itama ta zauna kusa dani "kinyi mamaki ko ?ganin na iya hausa , banikad'aiba dukkanmu mun iya saboda babanmu bahaushene mamanmuce y'ar nan shi yasa bamucika hausaba. Ta cigaba da kallo na "baki tambayeniba meyasa y'an gidanmu basu yi maraba da zuwankiba "ba kece basasoba bahaushiya ce basaso sunfi son ya auri yar nan saboda banbancin addini tunda a cewar su dalilin auren da mamanmu tayi da babanmu shiyasa yaja muka rabu gida biyu mu duka matan munbi addinin mamanmu amma Kamal shi yana tare da babanmu wato shi yana cikin musulmai kuma shi yajashi garin Kano inda yake kasuwanci dan shima kafin ya mutu ya gayamana d'ancanne. Muna cikin hira kamal ya shigo dauke da Leda a hannunsa ya ji dadin ganin tana tare dani har zuwa lokan cikin sakin fuska ya ce "yawwa na gode Tokatu ya bud'e ledar ya ce muci , mukaci har da Tokatu , bayan munkare na kashingid'a nan da nan barcin gajiya ya yi awon gaba dani. Bani na tashiba sai da gari ya waye na tashi na fito donyin alwala tare da ramakon sallolin da banyiba na hangi mamansu na tafi da niyyar ingaisheta ta wurgon wata harara tare da dakatar dani ta hanyar dagan hannu nan naja burki, saiga Kamal "Maryam ya akai kinyi sallah ? na girgiza kai ya ce zo ki yi , ya bani ruwa nayi na koma daki na yi sallolina. Bayan na idar saiga Tokatu ta shigo na yi zaton abinci ta kawomin don tunda na tashi cikina yaketa kiran ciroma ,amma abin mamaki babu komai a hannunta ta zauna muka gaisa "broth ne ya aikoni ya ce ingaya miki ya tafi shago inda yake kasuwancinsa nima gona zantafi shi ne na shigo in gayamiki duk sauran yan'uwa nama sunyi gaba muje innuna miki kayan abincinki , na amsamata da to amma na yi zaton in su basubaniba to maiyahana Kamal siyomin kamar jiya tunda ni ai bakuwace. Mukafito muka nufi runbu nayi zaton shinkafa zangani da su taliya. mezangani hatsine na dawa da gero da masara duk a cikin tumunsu , ta kalleni "to mezaki dafa?ganabana ya fadi dam, donni bansan mezanyi dasuba dama a gyarene geron nayi buski ko kunu masarar inyi tuwo ko danbu dawar ma zanyi tuwo ko danbu. Ta katsemin tunanin da nake "nace me zakidiba na kalleta nace babu gyararre? kuma waye zaikaimin inda za'a gyara? ta kallan cikin mamaki "kardai baki iyaba to aiko mama tace kullum ke zakidinga yin girki nayi rau-rau da idanu alamun kuka yana shirin kwacemin, ta nisa" duk da nasan zasuyimin fad'a amma bari yau intsaya in gwadamiki yadda akeyi. Muka d'ebi dawa nan da nan ta sussuke sananan ta gyareta fes ta sa a turmi ta hau daka ni ko sai aikin gwalalo idanu nake yi kamar mazarin tsire , na kasa jurewa nace wai bakwa kai wa na'urane wa to gurinnika ta kallan "duk matan garinnan da kansu suke komai danma broth ya ce abarki ki saba kafin ki fara zuwa gona ,na zaro ido waje gona!! Wayyo Allah wllh ko fatanya bantab'a rikewaba, ta yi dariya" za ki saba. Abinda ni a gurina jan aikine itako cikin sabo nan da nan ta gama tuwo da miyar d'ata, abinda bantab'a ganiba . Ta nunamin yadda zan dinga zubawa kowa nasa , mukad'au namu mukashiga ,d'aki muna cikinci y'an gidan suka dawo, but they may aikuwa Tokatu tasha bala,i don mama har marinta tayi, na tausayamata, wai saboda me zata tayani gashi Kuma bataje gona ba. Tundaga wannan lokacin ya zama kullum sai na yi wannan wahalallan girkin ga gyaran gida da wanke -wanke,kafin d'an wani lokaci na fige na rame na k'anjame, ga Tokatu sun hanata zuwa gurina, abin duniya duk ya taru ya chud'emin ga Kamal kullum sai dare ya yi sosai yake dawowa. Haka nake shiga daki na yi ta kuka ,daga baya na fara tunanin samun mafita ta hanyar guduwa in koma gida , gashi banida kud'in mota. Kwatsam sai na yi tunanin wata dabara ,zuciyata ta amince da shawarar da ta yanke. Da dare ya yi nak'i yin barci har saida Kamal ya dawo nan nake gayamasa ina son na samu sana a ya dubeni da mamaki a tattare da fuskarsa "me zakiyi da kudi ? Na d'an muskuta sannan nace kasan bansaba da irin abincin nan ba shi ne nakeson na dinga siyan wani a bun ba tare da na tambayekaba, ya jinjina kai "nima ramar nan taki tanaban tsoro kijira inyi tunanin abunyi. Na kwanta cike da farinciki. Bayan kwana biyu da maganar kwatsam sai gashi da guma-guman itatuwa tare da yara ana shigowa dasu, cikin sakin fuska yake gayamin wai gashinan idan na gama faskarawa zai turan masu saye, wai shi a nan ala dole ya yi abin a yabamasa, hod'ijam aiki ga maikareka. Na sakawa zuciyata k'warin gwuiwa tare da jajircewa don samun biyan bukata. Haka rayuwata yi ta tafiya lokaci na karewa,duk wahala tare da azaba na jure, ina faskarena kuma ba laifi ana siye, donma in ansiyar acikin Kashi uku Kamal yakan kwashi kaso biyu ni kuma yaban kaso daya , bana kashewa ina ta tarawa har kan hanya nake kai iccen ina siyarwa tunda su a can hakan ba matsala bace. Har sai da na kwashi tsawon shekara guda ina ta wahala, kudin da nake tarawa kuwa sai yawa suke dan nikaina bansan ko nawabane ? A wajan da nake saida itacena a nan na hadu da wata maijin hausa in ta siya ta kan d'an zauna mu taba hira ,a cikin dabara nake tambayarta , ni kuwa daganan in zanhau motar Kano ina zansamu? Ta yi dariya za kije ganin gidane? na ce a'a kawai dai Ina son injine. A take ta fara labartamin cewa "daganan lungunnamu ai kina ganin masu babura na shigowa ko ? Nace eh tacigaba to su za su kaiki har kwatanabor daganan sai su kaiki zuwa bakin bodar Idiyeroko daga nan sai ki Kuma hawa Motar Legas daga Legas Mota dodar har kano. Na yi matukar farinciki don jina nayi kamar naje gida . Ranar wata asabar da wurwuri na tashi na yi ayyukana na gida na gama na debo ajiyata na kulle a dankwali na yi kunzugu da shi na tafi gurin saida itacena ina Allah Allah mai mashin ya shigo aikuwa ba a jimaba sai ga wani ya kawo wata ,na bari saida ya kaita ya ajiye ya dawo ya na karasowa inda nake na yo maza na tsai da shi nace masa kwatanabor ya tsaya nahau gabana sai dakan uku - uku yake yi Ina tsoran kar wani a cikin y'an gidanmu ya ganni cikin sa a har muka kai babu wanda ya ganni, na biyashi hakkinsa . A nan na samu motar bodar idiyeroko ,kamar yadda ta gayamin ban samu wata matsalaba ,har sai da na je Legas na yi tambaya aka nunamin inda ake yin lodin Kaduna Zariya Kano . Na kutsa zan sayi tikiti, mai zai faru!!!!!/ Na lalubi kuguna inda na yi kunzugu da y'an kudadena nan sukace daukarmu inda kika a jiyemu gabana ya yi mummunar faduwa kirjina na wani irin dukan uku-uku zuciyata tamkar za ta yi bunduga ta tarwatse , wani irin duhu ya yi gaggawar ziyartar idanuna , da kyar na yi ta maza na samu gefen hanya kan wani dan dutse na zauna . Wa ni irin ruwa mai dimi na ji a fuskata na sa hannuna na shafa fuskar a she wai hawayene ga yawun bakina ya yi kauri makogaro na ya bushe ga yunwa da kishirwa na addabata ya'yan cikina sai juyawa suke yi su na fidda wani irin sauti kululululuu, a bu goma da ahirin kenan . Wayyo Allah na wannan shi ake kira da tsaka mai wuya. Dakyar daga can karkashin makoshina na kakalo kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji un na yi ta na na ta wa a wahalce hankalina na shirin barin jikina. Ba za to ba tsammani na ji wa ni hannu ya dafani sai a sannan na,urar da ke cikin kwakwalwata ta aikamin da sako, a firgice na juya inda na ji an dafanin na bude jajayen idanuwana masu kama da gauta ga su duk sun fada loko saboda matsananciyar rama da nayi. Wata Mata na gani jibgegiya ta na sanye da wata yar riga wadda iyakacinta gwuiwa kai babu dankwali sai wani himilin gashin doki wai ita ala dole gashintane , cikin harshen turanci take yimin magana "Madam na lura kina bukatar taimako tun farkon zuwanki na lura da hakan, na Kai dubana zuwa inda ta dafani a karo na biyu wasu irin zako-zakon farata na gani na zarce izuwa wuyanta anyi mata wani irin zane maikama da hoton mujiya . Haka kawai na ji zuciyata bata amince da ita ba ga bugun kirjina ya kara tsananta . Ta cigaba" ko kina bukatar a binci ? na yi saurin gyad'a mata kai alamar eh , ta juya cikin wata irin tafiya wadda na kasa ga ne yanga ce ko tsinin takalmine yake hanata yin saurin , hodijan Allah daya gari banban. Bata jima ba na hangota hannunta dauke da Leda ta na karasowa ta mik'amin , na yi wuf na cafa hannuwana na karkarwa kamar wadda ake kad'a mata Gangi na bude ledar shinkaface da miyar ganye har da kifi , yaushegamo ? rabona da cin irin wannan tun ina Kano na ko hauci . Bayan na kammala ne take tambayata a binda ya sakani a cikin irin wannan matsananciyar damuwa, na labarta mata batan kudin motata. Ta ce " kar ki damu ni zan baki amma zan kaiki gidana ki huta sai da safe ki tafi, a zuciyata na ce to yaya zanyi duk da har sannan zuciya ta ta ki a minta da ita, "Bari nad'akko mota ta a gurin fakin ,na amsa mata da to. Barin gurinta keda wuya sai ga wani dattijo bahaushe ya karaso gurina a cikin ujila ,"duk a binda kuke yi da waccan matar ina ganinku na ganki yar arewa a dalilin suturar da kika Sanya Kuma na ga alamun ke musulmace saboda haka ki gaggauta barin gurinnan kafin ta dawo, ni a nan nake yin sana,a ta ina ganin yadda suke zuwa su na yaudarar baki da zummar taimako musamman idan sun lura mutum ya na cikin damuwa don ai saurin amincewa da su. Indai tak'aice miki yan k'ungigar Shan jini ce ,ki yi gaggawa kibar gurin nan , ni kaina ina cikin hatsari in ta ritsani a nan tare da ke , har ya juya zai tafi ya juyo meyene matsalarki ? na ce cikin rawar murya ku ku din mota ta ne ya fadi , ya ciro dubu uku ya mik'omin "ungo wannan ki zagaya can wajan fasinjoji ki naimi taimako ya yi saurin barin gurin na neme shi na rasa ya b'ace tamkar walkiya. Nima na yi sauri na ta shi tunda na samu d'an sassauci a dalilin abincin da ta siyamin, da sassarfa na bar gurin na za gaya ta baya inda fasinjojin suke na shige cikin mutane inda na San da wuya ta ganoni a nan na fara magiya kamar yadda mutum ya bani shawara ina naiman taimako a karo na farko a cikin rayuwata. A bun mamaki saiko naga a nata mik'omin saboda duk wanda ya ganni sai ya tausaya min , musamman da sukaji ina kuka ina cewa kudin motata ne ya fadi daga cikin fasinjojin wani mataship wanda daga ganinsa naira ta zauna ya matso ya yi min magana a cikin tausayi" wane garin Zaki ? na ce Kano ya ce a she tafiyar mu d'aya to ina zuwa, in takaicewa maikaratu nan ya biyamun ba a jima ba muka mika mukad'au hanya . Tunda muka zo Zariya na farajin kamshin garin Kano, na ji nutsuwa ta fara saukar min. Masha Allahu la kuwwata illabillah Shi ne a bunda na fad'a lokacin da na ji matashinnan da ya biyamin kud'in mota na ji ya na cewa mun iso garin Kano ina zaki?, na sa kaina ta taga ina shakar kamshin garina wata daddad'ar iska ta doki fuskata na lumshe idona , bansan lokacin da fatar bakina ta fara furta kirarin garin kanoba da k'arfi , Kano ta dabo tunbin giwa tunjumin gari mai dala da goron dutse mai Mata mai Mota. Alhamdulillah.