💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 0⃣1⃣ I dedicated this page to the jerk that broke my heart into thousands pieces and hand them to me on a plate. Thank you for teaching me how to be strong and never give my scarred heart easily. Shout out to the young writers out there. Tunda abokansa suka rakoshi suka gama surutunsu da kawayen amarya bai ce uffan ba. Asalima bazai iya maimaita magana daya da suka fada ba dan hankalinsa ba akansu yake ba. Kallan yarinyar da take zaune kan gadon ya keyi baima san me zai soma fada mata ba.Ko kalar fuskarta bai sani ba tana zaune kan gadon lullube da mayafin da bashi da niyyar bude mata. A hankali kaman mai koyon magana yace mata. "Sannunki" Tafi mintina biyar a zatansa ma bataji ba sannan cikin rawar murya tace masa. "Nagode" Hannunta tasa tana sake gyara mayafinta dai-dai lokacin da idanuwansa suka sauka kan hannayen nata da suka sha kunshi. A gefe guda kuma zuciyarsa ta dauke shi ta watsa shi wani lokaci can baya. *** *** Da gudunta ta karaso inda yake. "Yayana kaga kunshina yayi kyau?" ta fadi da murmushi a fuskarta. Shima murmushin yai mata yana fadin. "Kai kai gaskiya baiyi kyau ba" Fito masa da idanuwanta tayi lokaci daya ta tabare fuska tana shirin yin kuka. Yana dariya yace. "I am sorry. Just kidding, yayi kyau sosai. Waye yai maki?" Juya bayanta tai alamar tayi fushi. Rufe idanuwansa yai ya bude su a hankali in ba itaba bai fiye son yawan magana ba. "kinga bara nai tafiyata since fushi kikeyi" ya fadi yana mikewa. Riqo masa hannu tai sai da yaji wani abu har cikin kansa. Bayaso tana rike masa jiki musamman in babu tsammani yaji hannayenta a jikinsa. Muryarsa can kasa yace. "let go of my hand huddy" Sake makalo shi tai. Saida yai mata tsawa sannan ta sake shi ta ruga kuma. Yasan tabarar huddy kamar yunwar cikinsa. Kuka zatai kuma bashida zuciyar binta ya lallabata dan tana rikita masa kai da yawa. *** *** Idanuwansa da suke rufe ya bude. Hakan yasa zuciyarsa dakatar da inda ta dauke shi takaishi. Sauke su yai kan yarinyar da take zaune kan tanqamemen gadon dakin. Wani abu yaji ya soke masa zuciya. Jiyai sam bazai iya jurewa ba ya fice daga dakin yaja mata kofar a hankali. * Taji fitarsa. Kwantawa tai kan gadon ko kaya bata da kwarin tashi ta sake. Kuka ne tayi shi har bata zatan tana da sauran hawayen da suka rage mata. "Sannunki" shine kalmar da tunaninsa ya bashi ya furta mata a darenta na farko a matsayin matarsa. Wato kaddara dabance. Bata taba zatan auren wani bayan Ammar ba. Fadar sunansa kawai a tunaninta yasa zuciyarta wani tafasa. Ta gama tsanar mutumin nan tun kamin ma taganshi. Ya rabata da ammar dinta. Wai duk ma matan kano ya rasa wa zai aura sai ita. Dan tsabar rashin adalci da rashin sanin darajar SO. Kunshin hannunta ta kalla da bata ga amfaninsa ba can gefen zuciyarta ta tuno wani lokaci tayi kunshin jan lalle suna zaune da ammar. *** *** "Babyna ina son kunshi sosai. In munyi aure zaki dinga yimin" ya fadi cikin karamar muryarsa da take so. Murmushi tai a kunyace hadi da fadin. "Saika biya tukunna" Dariyarsa yai mata ya wani juya idanuwansa da yasan duk idan yayi yana burgeta sannan yace. "Karki samu damuwa lokaci ne zaki fadamin ma.anar wannan maganar" "Yaushe kenan?" Ta fadi muryarta da alamar dariya. "uhm zakiyi bayani ne yarinya" ya karasa shima da dariya a muryarsa. *** *** Wani radadi taji zuciyarta nayi tasan ta rasa Ammar da soyayyar nan tashi mai tsaya mata a rai. Yanzun duk kulawar nan da alkawurransu sun tashi a banza? A wata daya kacal wani yazo ya ruguza masu soyayyar da sukai shekaru suna ginawa? Ya tarwatsa musu farin cikinsu saboda sonkai irin nasa. Ta tsani koma waye wannan. Kanta taji yana mata wani irin ciwo ga zuciyarta da take mata zafi. Haka tai kwance shiru tana duk wata addu.a datazo bakinta ko zata samu saukin radadin da takeji. A hankali bacci ya dauketa cike da mafarkin Ammar. IF YOU HAVE ANY CORRECTION FEEL FREE. 08074545149. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 0⃣2⃣ This is dedicated to those reading this page. Without you guys i won't be writing this. Much love to you guys at ummie jafar novels group. Your encouragement inspired me and give me the spark to go for chapter two. Allah's blessing. Ya rasa kwanciya zaiyi ko zama ko kuma tsayuwa. A duk yanda yai zuciyarsa sam babu dadi. Auren nan ya sake fama masa ciwukansa yasa suna zubda jini. Da su umma sunsan bashida sauran zuciya mai numfashi ta bangaren soyayya balle kuma aure da basu matsa masa ba. ko da yake harda laifin yarinyar da bata gaya musu bata son shi ba. Shi kam yayi iya kokarinsa na kaucewa auren fin karfinsa akai. Itama yasan kwadayin abin duniya ne yasa ta nace ma aurensa. A wata dayan da akasa na bikinsu. Kin zuwansa yaga kalar fuskarta kawai ya isa ya tabbatar mata da bai amincewa aurenta ba. Amman saboda naci da kwadayi irin na matan yanzun saida ta bari aka daura masa ita. Inda huddy ta sha banban da sauran kenan. Zuciyarsa ta fada masa. Dafe kai yai. Baya son wannan matsayin nasa da wanda yasan yana shirin samunsa a lokaci na gaba. Yasan bakomai bane zai zabarma kansa amman ya dauka cewar atleast matar dazai spending rayuwarshi da ita shi zai zaba. Bawai daukarta za.ai a lika masa bada son ransa ba. Gaba daya kansa yai masa nauyi. Neman wanda zai likama laifin abinda yake faruwa dashi yake kuma a yanzun babu wadda tafi dacewa irin yarinyar can dako sunanta ma bai sani ba. Inma an taba fada a gabanshi bai rike ba dan bata ransa. Baya mata kallan komai sai yar katsalandan da kara masa matsaloli fiye da wanda zuciyarsa take ciki. Gani yai sai juye juye yake yi ya kasa bacci. Ga ciwon kai na damunshi yama manta cewar tun abincin safe ne a cikinshi da ummansa ta takura masa ya zauna yadan ci. Bacci sam yaki yazo. Dan haka ya tashi ya shiga bandakin shi ya dauro alwala. Hakanne kawai zai masa maganin wannan tunanin da ya addabe shi. Kuma yasan zai samu nutsuwa ko yaya take. * Bude idanuwanta husna tai. Kanta ya wani sara mata. Lokaci daya komai ya dawo mata. Dacin da take ji a zuciyarta yana nan daram. Wayarta ta lalubo kan gadon, jikinta ya mata wani irin nauyi. Bata san ta makara ba saida ta duba agogon wayarta taga karge bakwai saura mintina sha biyar. "Lallai nasha bacci" ta fadi a hankali. Sai da kanta yadan saki sannan ta mike zaune. Taja tsaki. Wata kofa ta bude daga cikin bedroom din taga hanya ce. Ta rufe ta nufi wata ta sake budewa taga dakin canza kayane. Ta juya idanuwanta. Ta sake bude wata taci karo da tankamemen toilet. Duk haduwa irin ta gidansu da gidajen yan uwa da take zuwa bata taba ganin kayataccen ban daki irin wannan ba. Duk da tsanar gidan da maishi da tai yawa a zuciyarta bai hana ban dakin burgeta ba. Wanka ta fara yi sannan tai alwala. Sai bayan ta idar da sallah sannan yunwar da takeji ta soma addabarta. Rabon cikinta da wani abu tun safiyar jiya. Sai da ta gama shiryawa cikin wani less ruwan toka duk da ba wata kwalliya tayi ba kayan sun karbi jikinta. Fridge din da yake can gefen dakin ta nufa ta bude cike yake da kayan alatu. Fresh milk ta dauka da apple dan ba ma.abociyar cin abu mai nauyi bace. Musamman da sassafe haka. Bayan ta kammala ta dauki katan mayafi kalar kayanta ta lulluba sannan ta koma kan gadon ta zauna. Ta kudurta a ranta koda wannan Nataccen zai shigo kaman yanda ta yanke shawarar kiransa dashi tunda ba sunansa ta sani ba. Kuma ba damuwa tai da hakan ba. Bata shirya ya kare ma halittarta kallo ba. Auren kaddara ne ta riga ta runguma ko da da hannu dayane. Bata san iya lokacin data dauka ba kamin taji an kwankwasa kofar a hankali. Gabanta taji ya fadi a sanyaye tace shigo. Zuciyarta na dokawa ga mamakinta wata mata ce mai matsakaicin shekaru ta turo kofar hadi da sallama. Amsawa husna tayi. Har kasa matar ta tsugunna ta ce. "Ina kwana. Fatan kin tashi lafiya" Wani irin nauyin matar ya kama husna. Ko bata haifeta ba zatayi kanwa da ita. A kunyace ta amsa. "Ranki ya dade ko kina bukatar wani abu?" matar ta tambaya wadda har lokacin tana tsugunne. Cikin sanyin murya tace mata. "A.a bana bukatar komai nagode. Ya sunanki?" "Sunana asabe ranki ya dade. An shirya abinci ko da kina bukata nazo ingani. Dan lokacin tashin yarima daga bacci baiyi ba." Sai da tai jim sannan tace. "A.a nagode da kulawarki malama asabe. Kije kawai" "Hutawarki lafiya ranki ya dade " Asabe ta fadi tana mikewa ta fita daga dakin. Husna ta yamutsa fuska alamar komai yai confusing dinta. Wannan girmamawar da matar take mata yai yawa. Duk idan tace ranki ya dade din nan sai taji wani iri. "Yarima" Ta nanata tana tabe baki. "Wa abbana ya auramin ni husna?" tai tambayar da batasan mai bata amsarta ba. Zuciyarta tace mata. "da kin maida hankali lokacin da ake miki bayani ai da kinsan kowaye." Girgiza kanta kawai tayi. Tagaji da komai ma. Tagaji da tunani kan wannan auren tunda an riga an daurashi. Takuma gaji da tambayoyin da babu mai bata amsarsu. Hade kai da gwiwarta tai tana sauke wani dogon numfashi...... 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 0⃣3⃣ This page is dedicated to those that ever love and loose. Those that know the pain of getting your hopes high and getting them shattered. Those guys that gets hurt from those they trust. Because that hurt like a bitch. I hope time heals it for you guys. I feel you!!! Bai fito ba sai qarfe Goma na safe. Jikinsa sanye da shadda fara ya dora baqar alkyabba data sake taimakawa wajen bayyana kyawunsa. Kai kawai yake dagawa duk hadiman gidan da suketa zubewa suna gaishe dashi. Yau sarautar yake ji fiye da kullum magana ma wahala take masa. Dining room ya shiga komai a shirye yake. Ya samu waje ya zauna. Kaman yanda suka san tsarin cin abincinsa haka aka shirya masa komai. Kadan yadan tattaba dan kawai kar ya zauna cikinsa babu komai. Amman zuciyarsa bata da wadatacciyar natsuwar dazai ji dadin wani abinci. Baibi takan natacciyar da aka kawo masa jiya ba dan hakan ya yanke hukuncin kiranta. Ya yanke shawara da zuciyarsa babu ruwansa da ita. Tunda bata gabanshi inta gaji zata gane hanyar gidansu da kanta danshi bashida wajen da zai mata a rayuwarsa. Rigimar da yake ciki ma ta ishe shi ba saiya kara da tata ba. Yana kammalawa ya miqe ya fita. Bayan mota ya zauna driver dinsa ya tuqa shi zuwa gida. Tun kamin ya fito daga motar hadimai ke tsugunnawa suna kwasar gaisuwa. Wasu ya dan daga musu kai wasu kuma ya share abinsa. Kai tsaye bangarensu ya nufa ya samu ummansa tana babban falo a zaune. Har qasa ya tsugunna ya gaishe da ita ta amsa masa cike da fara.a ta dora da "Babana har an fito kenan?" Haka take fada masa kasancewar sunan mahaifinta da yaci. "Nazo gaishe dake ne umma" ya fadi yana murmushi duk da zuciyarsa babu dadi ganin mahaifiyarsa kawai ya bayyanar da murmushi a fuskarsa. "Ya kwanan amarya?" Ta buqata sai da yai jim sannan yace "tana lafiya." Ajiyar zuciya tai tace. " babana saika yi haquri komai na rayuwa Allah ya riga ya gama tsarama bawansa. Ka zama mai rungumar qaddara. Kabawa auren nan lokaci sannu a hankali itama zata shiga zuciyarka." Kawai shiga zuciyar data fada saida yaji ranshi ya sosu. In ya saka wata a zuciyarshi ita kuma huddy ya dauketa ya mayar da ita ina? "Nagode umma" ya furta yana ji zuciyarsa na wani tafasa. ya za.aima wannan natacciyar ta shiga zuciyarsa bayan auren kwadayi tayi. Ita kanta yasan badon kudinsa da matsayinsa ba babu yanda za.ai tai wautar auren wanda bata taba gani ba. "Bara na qarasa mu gaisa da mai martaba" ya fadi yana miqewa. "Tam Allah yai maka albarka." "Amin umma." Fada cike take lokacin daya qarasa. Fadawa na ta zuba masa kirari. Gaisuwa ya miqa bai jima ba ya taso abinsa. * Yama rasa ina zaije shi ba ma.abocin yawo bane ba. Babu wata hidima a gabanshi tunda an bashi sati biyu cewarsu ya gama amarci. Duk idan ya tuna wani takaici kara kamashi yake. Yai tunanin zuwa lambu sai dai wajen babu abinda zai qara masa illa rashin huddy. Ashe akwai lokacin da rayuwa zatai masa haka? Lokacin da zai rasa farin ciki. Lokacin da zaiyi murmushi iya fuskarsa bai kai zuciyaba. Akwai lokutta da dama da akan bata mishi rai sosai. Amman huddy tana kwantar mishi da hankali. A haka ya daure aka mai dashi gida. A can qasan ransa yana fatan Allah yasa natacciya na bangarenta dan bai shirya haduwarsu yanzun ba. Bai shirya ganin fuskarta ba. Baiki suyita zama haka ba. Dan ba karamar matsala za.a samu ba inhar tace zatai kokarin shiga rayuwarsa fiye da yanda tai masa yanzun. Yako yi sa.a bata babban falo. Yai maza ya wuce bangarensa ya kwanta. Ta danna wayarta tayi game din harta gaji sam komai baya mata dadi. Ta kunna kayan kallon da suke cikin dakin. Saidai duk wani channel da zata kalla taji dadinshi inta kai kewar ammar zata kara addabarta. Wasu programs din ita ta koya masa kallonsu. Duk idan yai missing ko yana makaranta ko wata hidima yana dawowa saita bashi labari. Haka idan ita tai missing zai bata labari. Wasu lokuttan kuma tare suke kallo. Wasu hawaye masu dumi suka zubo mata. Tasa hannu ta tarbesu zuciyarta na mata wani nauyi. Yanke hukuncin fita ta dan zagaya gidan tayi amman ta kasa. Duniyar ta hadu ta mata kunci. Wayarta taji tana ringing. Ta dauka ta duba. Da hanzari ta daga wayar ganin kausar ce take kiranta. Bata san lokacin da kuka ya qwace mata ba. "Ya salam" kausar ta fadi tana dorawa da "lafiya kuwa? Husna meke ya faru?" Har lokacin kukan bai tsaya ba daqyar ta sami muryar ce mata "kausar bana son mutumin nan bana kaunar wannan auren. Ammar nake so shi na tsara rayuwata dashi." Cikin rawar murya kausar tace "calm down husna please nasani amman kaddara babu yanda bata zuwama bawa dan Allah kiyi hakuri karki kara jan matsala tsakaninki da iyayenki." "Hmm kausar bakisan yanda zuciyata take yiba ne shisa inama mutuwa nai na huta" ta karasa cikin kuka. "Dan Allah ki nutsu zan sake kiranki anjima inkin dan samu natsuwa kinajina?" Jin bata da niyyar amsawa yasa kausar kashe wayar. Ita kam husna jefar da tata wayar tai can gefen gado ta kife kan gadan tana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Sai da tai mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet wanka ta sake yi. Lokacin uku harda rabi dan haka tai alwalar la.asar. Tai mamakin saurin jan lokaci haka. Duk yaushe tai azahar kodan tana jin duk girman dakin ya mata kankanta ne shisa lokaci yake tausaya mata yana gudu? Inama ace yanda lokacin nan yake gudu haka kaddararta ta wannan auren ta nisanceta. Ta jima kan dadduma tana addu.o.i kamin ta miqe. Asabe ta shigo ta sake mata maganar abinci yanke shawarar fita tai kodan taga yanayin gidan da zata kira na aurenta. Gidan da duk lumfashin da zatai a ciki saita fito dashi da wani nauyi a zuciyarta. Asabe ta rakata har qayataccen dining room din. Chips kawai taci tadan sha fruits ta fito zuwa wani tanqamemen falo ta zauna kan kujera. Daya bayan daya hadiman gidan sukaita zuwa suna gaishe da ita. Bata qirga su ba amman tana yaqinin zasu kai su goma sha biyar. Aljazeera take kallo tana ganin yanda duniyar taketa qarewa ko ina yaqi. Ita kanta hatsaniyar ce take faruwa akanta. Saidai su yawancinsu mutuwa suke suna samun hutu da nutsuwa ta har abada. Sabanin ita da take tunanin laifin datai take karbar horonsa da riba haka. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 0⃣4⃣ This goes to those architects that stay up all night designing and drawing. I know how you guys work so hard and think i don't work as much for sparing some time to my writing. I am sorry guys here is the truth, i can go two days without drawing and feel just fine. I feel suffocated if i go a day without writing because i chooses architecture. Writing chooses me!!! Ya sha bacci sosai dan jiya da dare sam bai samu wani baccin kirki ba. Babban falo ya fita hankalin shi a kwance. Bai zaci ganinta a falon ba. Zuciyarshi ta wani doka a yan mintina kadan ya manta da damuwarsa idanuwansa suka natsu wajen aika masa da saqonni kyawun yarinyar da take zaune a falonsa. Hankalinta gaba daya yana kan kallan da take da alama ma bata san shigowarsa ba. Wannan ce natacciyar da aka aura masa kenan to kyawunta bazaisa yaji komai ba yake fadawa kansa. Dan ya tsani makwadaita masu son abun duniya. Kujera ya samu ya zauna can nesa da ita. sai lokacin ta dago ta kalle shi ta sake maida hankalinta kan T.V din kaman baya wajen. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Sam bai saba mace ta kalle shi tai kaman baya nan ba duk min ajinta kuwa. Yana da kyau shima yasan hakan. Duk macen data kalle shi saita qara kallansa amman ta wani basar kaman bashi bane zaune a wajen. Ballantana kuma in tasan koshi waye yanzun zakaga yarinya nasan yai mata magana ta shishshige masa. Well nasan kudina da kuma matsayina yasa kika nace saikin aureni ya fada a zuciyarsa. Yasan zata juyo ne ta sake kallanshi. Ga mamakinsa miqewa tai ta gabanshi ta wuce batare da tayi koda yunqurin nuna yana wajenba tai gaba abinta. Shi ya bita da kallo cike da mamaki yau shi prince Ishaq mace take wucewa kamar baya wajen. Lallai akwai aiki a gidan nan. Zai iya jure komai dan tun daga huddy zuciyarsa ta daina numfasawa kowacce mace amman banda shariya. Izzarsa da mulkin da yake yawo a jininsa bazai jure halin ko in kula ba. Shi ya kamata ya share mata not the other way round. Domin ita ta nace ma aurenshi bawai shi ya nace ma ta ba. * Husna kam ganin natacce da tai a falo ba qaramin girgizata yaiba. Kyakkyawa ne naban mamaki. Kallo daya zakai masa ka fahimci hakan. Duk da kiyayyar da take masa tasan yafi ammar kyau amman hakan bashi bane zaisa ya burgeta. Dan yanaji da kudi da kyau ba shi zaisa yai mata katsalandan da fin karfi ba. Kyawunsa baya gabanta tunda shine silar rabata da farin cikinta. Taga alamar yana ji da kanshi sai dai itama hakan take. Ta dawo dakinta ne tabar masa falon saboda karta sake kallan shi ya dauka burge ta yai. ''Babyna bana son inji kince kina kallan indian film kar kije kiga wanda yafini kyau'' maganar ammar ta fado mata. "Hmm kai bakasan zuciyata ta kulle ba bata ganin kowa sai kai dear idanuwana ne kawai suke ganinsu." Wannan shine amsar data bawa ammar a lokacin amman gashi yanzun tana hada kyawunsa dana natacce. Haushi ta bawa kanta hadi da alqawarin zatai qoqarin qin sake kallan fuskar natacce in Allah yaso ya yarda balle harta dinga hada shi da ammar. * Washe gari da safe wanda shine kwananta na biyu a gidan natacce. Ta tashi zuciyarta da nauyi da wata irin kewa ta ammar data addabeta. Jinta take kaman bata da rai a wasu wajajen na jikinta. Komai tana yinsa ne dan anayi. Tun jiya bata qara ganin natacce ba ko yana ina shi yasani dan baya gabanta. Ta kammala duk abinda zatai ta fita zuwa babban falo ko zata dan shaqi banbantacciyar iska da wacce take a dakin baccinta. Ta tako kenan text ya shigo wayarta. Ganin kausar ce yasa ta dubawa taga tana tambayar ko tana lafiya. Wani murmushin takaici ya tokareta. Reply take rubuta mata tana tafiya. Karo taji takaiwa wani abu dabata san komeye ba saboda rubutun da takeyi yasa bata kallan inda zata saka qafarta. Wani irin qamshi mai sa natsuwa ya doki hancinta. Sai lokacin ta kalla taga inda kafadarta ta doka. Faffadan qirjinsa taci karo dashi da sauri ta daga kanta tako sauke idanuwanta cikin na natacce da yake mata wani irin kallo da yasa ta jin gwiwoyinta sun mata nauyin gaske. Ga wani irin kwarjininsa da taji ya cika mata zuciya. Lokaci daya ta sadda kanta qasa tana kallan takalmin qafarsa. Zuciyarta na barazanar fitowa daga qirjinta. A dake yace mata "ki dinga kallan hanya karkiji ciwo." Wani haushi taji ina ruwanshi da ita shi baisan ta tsane shi bane ba. Ta tsani yanda deep voice dinshi tasa tsikar jikinta tashi. A hasale tace "nagode bana buqatar tunawarka." Kamin ya bata amsa ta wuce ba tare data sake kallan inda yake ba. * Dakinta ta koma ta zauna kan gado tana maida numfashi kamar wadda tai dambe. Duk jikinta ya mata wani iri. Ga idanuwan natacce da takeji har yanzun kaman yana cikin nata. Hakan yasata saurin rufe idanuwanta ta bude su. Wasu hawaye masu dumi suka bi fuskarta. Ta goge in shaa Allah ta daina zubda ma natacce hawayen aurensa dayake kanta. Tasa hannu ta goge hancinta ko zata goge kamshin sa da take ji har lokacin. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 0⃣5⃣ This page goes to you ummie jay. Thank you for solving that calc. My appreciation. A big shout out to my readers. Love you loads!!! Baisan yanda akai bakinsa ya furta masa abinda zuciyarsa take tunani ba. Sam ba kalaman da kunnuwan natacciya ya kamata yaji bane ba. Karon datai dashine ya tuna masa wani lokaci shida huddy hakan yasa shi yin irin furucin da yai wa huddy. A karo na biyu da ta kalle shi ta sake dauke idanuwanta daga fuskarshi tamkar wacce taga wani naman ruwa. Baisan abinda yasa hakan ya sake bashi haushi ba. Meye a fuskarsa da ta kasa jure kallanshi. Who is she da zata kalle shi kaman shi din ba kowa bane. Shin zaima iya tuna tsawon lokacin da wata mace tai masa magana da irin yanayin da natacciya tai masa. Wai me take ji dashine? Kyau? In kyaune shima ai yana dashi kuma bayajin tafishi. Babu macen da zata ki girmama shi ko da bata son shi ballantana wadda ta like ma aurensa. Well koma menene zai sauke mata shi. Ba.ai macen da zata share prince ishaq ba ko da kuwa baya sonta ne dole ita ya burgeta. Kawai ta bata mishi rai. KiranNasir ne ya katse mishi tunanin da yake ya dauka yana fadin "mutanen england." "Yaya ni nayi fushi fa yau kwana nawa baka kirani ba? Tun ranar daurin aurenka" Yasan bai kyauta ba kam. Musamman da nasir din ya fada mishi kwananshi biyu asibiti bashida lafiya ga exams zasu fara. "Afuwan Kanina hidimomi ne sukaimin yawa shisa kaga ban kiraka ba. Ya jikinka?" "Hmm it is alright" nasir ya fada ya dora da "Alhamdulillah naji sauqi. Ya gajiyar biki? Ya in-law dina? Kadai fada mata nace she should take care of you ko?" Sai da yai dim sannan yace "duk lafiya ya england? Ya karatun?" "England gata muna ciki yaya,karatu yayi zafi mun fara exams jiya, na qagu inzo gida duk nayi kewarku." Murmushi yai yana qaunar qaninsa kaman me duk a gidansu jininsu yafi haduwa in baka sani ba bazaka taba cewa baba kawai suka hada mama kowa data shi ba. Shaquwarsu zata baka mamaki. Cikin taushin murya Nasir yace masa. "Are you really ok? I mean is she making you happy? If not yanzun na biyo available flight inyo gida" Duk da wasan da yake yi bai hana prince ishaq yin yar dariya ba. "Nas kai din nan ko!" ya fada da fara.a a muryarshi. Haka suka ci gaba da hira na zuwa wani lokaci kamin suyi sallama. * Rayuwa take badan tanajin dadin ta ba. Jinta takeyi kamar wata zombie. Kaman wayar da take da full charge amman babu ko sim balle kai tunanin samun network. Ga wani ciwon kai da baya sauka bata kuma damu data sha mishi magani ba. Ga kirjinta data soma tunani sai ta dinga ji yana mata wani ciwo dakyar take tsugunnawa. Yau kwananta bakwai cir a gidan natacce amman sau uku magana ta taba hadasu. Shima kuma duk kamawa hakan tayi. Ta wanni fanin ta gode masa dabai yunqurin aiwatar da komai ba akanta da batasan yanda zata dauki hakan ba. Kuma ta tabbata ba karamun rikici zasuyi ba. Ta soma mamakin dalilin da yasa ya aureta. Menene amfanin rabata da ammar ya kawota nan ya ajiye bayan ta kula bama damuwa yai da itaba. Lokaci daya taji ta qara tsanar shi. Yanzun takan fita babban falo ta zauna banda nan bata zuwa kowanne fanni na gidan saikuma in zataci abinci. Idan kewa ta dameta ta gaji da kallo Suna dan hira da su Asabe. Hadiman gidansuna da kirki kuma suna matuqar bata girma. * Yauma kaman ko da yaushe yunwa ce takaita dakin cin abincin. Tana shiga zuciyarta ta doka da qarfi. Ta tsani a gani na hudun nan datai masa zuciyarta ke son fitowa daga kirjinta. Abu na farko da ya fara zuwa tunaninta shine kamshin sa da ta kasa mantawa. Inba sharri bane irin na zuciyarta daga nisan da yake sai taji kaman ta jiyo kamshinsa. Yana zaune kan daya daga cikin kujerun dining room din jikinsa sanye da wata alkyabba Ja. Hannunsa rike da apple din dayake gutsura da wani irin yanga. Ta kula duk ganin da tai masa da alkyabba a jikinsa. Saurin sadda kanta qasa tai kamin ta gama fahimtar kyawun da yayi. Da juyawa zatai ta koma daki idan ya gama ya fita saita dawo. wata zuciyar tace nataccen zaki gudarwa? Qarasawa tai taja kujera ta zauna. Ko kallonta baiyi ba inma yaji alamar ta shigo bai nuna ba ko a jikinsa. Apple dinshi yake tauna hannunsa daya kan tablet din shi da take kan table din wajen. Kawai sai taji jikinta har wani kyarma yake ta kuma rasa dalili. Ga zuciyarta nata dokawa. Yanayin da takeji bata tunanin wani abu zai iya zama a cikinta. Dan jitai ya wani kulle ma. Haka ta dauki kankana guda daya da aka yayyanka da cokali mai yan yatsu tasa a bakinta. Sai lokacin taji idanuwansa na mata yawo a fuska. Bugun da zuciyarta takeyi ya karu. Sam taqi ta dago kanta duk da abinda idanuwanta keson yi kenan. * Yanajin shigowarta da zamanta wajen. Ta kasan ido yaga ta dauki kankana. Ya dago da kanshi ya kafa mata idanuwansa. Kallanta kawai yakeyi yanda take tauna kankanar ma a yangance take yinsa. Kanta a kasa. Badai ta dago ta kalle shi ba ballantana ma yai tunanin zatai mishi magana. He is confused yanzun. Ya soma tababar anya kuwa kwadayine yasa ta nace wa auransa? To inba kwadayi bane menene dalilinta da ba zata nace bata sonshi ba? Kuma inda kwadayine zata dinga shishshige masa tana cusa kanta kaman yanda yan mata sukanyi masa. Sai dai ya kula inda da yanda zatai karta ganshi ma gaba daya datayi. Bata san koda kallan fuskarshi. Tana yi kaman ma bata san yana waje ba duk idan sun hadu. Hakan baqon abune a wajen shi bazai boye ba. Yana daya daga cikin mazan da suke matukar son kulawa. Wata irin zuciya gare shi. Yanajin rashin huddy fiye da ko yaushe ya tuna wani lokaci suna zaune. *** *** "Ke kaman baki taba ganina ba." Dariyar nan tata da yake so tai masa tace "yayana ni bana gajiya da kallan ka fa. Kana da kyau sosai." Murmushi yai miqewa tai idanuwansa a kanta tace "kace fa zaka koyamin doki." "Ban manta ba huddy zan koya maki ba yauba kinga nagaji yanzun ki tafi wajen Nasir." "Um um yaya nasir bazai yi hira dani ba yana karatunsa ne fa" ta qarasa maganar a tabare. Komai na huddy ya masa yana son yarinyar wani irin so da yake ji har jininsa ko dan akwai yan uwanta ka ta jini tsakaninsu ne shisa. Tana rikita shi da yawa ya qagu watanni shiddan daya rage musu ya cika ya dauke kayarsa. * Wata ajiyar zuciya ya sauke. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 0⃣6⃣ This page goes to a friend i learned to love like a sister. A friend i met on social network. A friend circumstances and fate give us nothing more than chat, phobe calls, text messages and sharing pictures. Three good years of sharing secrets, sharing each others ups and down, laughter and happiness, of emotionally being there for each other. And to the mark the exact of three months without hearing anything from you. I have nothing to start from... No address to go and look nothing more than a phone number that is no longer going through and a first name that thousands own. I don't know if you are okay dee...... And i don't kbow if i will ever stop wondering or worrying. Two things are still certain and i mean very certain to me. In will love and pray for you like a sister wherever you are. Dead or alive Dee. And..... And i will never stop searching with the little i have i will never stop searching and hoping!!! Ajiyar zuciyar dayai ne yasa husna dagowa ta kalle shi. A dai dai lokacin da shima ya dago daga tunanin da yake. Ganin ta yasa shi tuna cewar yafa rasa huddy. Wannan wata ce data shigo rayuwarsa ba tare da amincewarsa ba. Kaman ko da yaushe saurin sauke idanuwanta tai kaman irin taso taga wani abune kuma ta fahimci baya wajen. Husna kam bata san dalilin daya sa ya sauke ajiyar zuciya ba haka. Kaman irin ya tuna wani nisantaccen abu. Yanayin yanda ya kalleta da kuma yanda fuskarsa ta sauya lokaci daya ta daure mata kai. Ya kalleta da sanayya a farko kaman taga yaso yai murmushi ne dayan yanayinne bata fuskanta ba. Kema kike wahalar da kanki akan natacce zuciyarta ta fada mata. Miqewa tai tabar wajen ba tare data yarda ta sake kallan shi ba. Ya dafe kanshi. Baya son matsala amman da duk taku daya dazaiyi dan ganin ya guje mata da taku biyu da zatai don samun shi. Dakinshi ya koma da fita zaiyi yaji sam ya fasa. * Kwance yake kan gadonshi maganar mai martaba na masa yawo a kwanya. So yai ya tafi abuja abinsa yadan bar wannan shiga hanci da qudundunen da natacciya taiwa rayuwarsa. Yadan samu nutsuwa ko ciwon kan da ke yawan damunshi zai masa sauqi. Ko zai daina ganin natacciyar yarinyar can tana saka mishi jin rashin huddy. Amman Mai martaba yace bazai tafiyar wata daya ba tare da iyalanshi ba. Ko yaushe ta shigo rayuwarshi da har zata zama iyalanshi oho. Shi baima san ta yanda zai fara ce mata ta shirya zasuyi tafiya ba bayan ko kallan fuskarshi bata son yi. Bakuma ya son shige mata saboda bai manta da yanayin da tai masa magana ba rannan. Komai zai iya faruwa in har ta sake daga mishi murya. Bai saba baba. Ba kuma zai fara daukar hakan daga wajenta ba. Gashi jibi yake son tafiya abuja din. Ya gama shirya komai. Beside akwai abubuwan da yake son aiwatarwa da ba zasu yiwu ya soke tafiyar ba sam. Duk da bata da wani matsayi a wajen sa. Darajar igiyar aurensa da take kanta ya wuce ace ya aika hadimai sun fada mata sako irin wannan. Yanda baya son raini yake ji da izza baya son ya raina wani ta ko wanne fanni. Dafe kai yai ya zama dole ya fada mata duk da baisan kalar zaman da zasuyi ba. "Kalar zaman da kukeyi anan mana. Ko wa yai harkar gabanshi" Zuciyarshi ta fada masa. * Yau satinta biyu kenan a gidan nan da take wahalar kiransa na aurenta. Tun ranar da ta hadu da natacce a dining bata sake ganin shi ba. Hakan yafi mata kwanciyar hankali. * Tana zaune tana kallo kamshinsa ta soma ji wanda tun randa tai karo dashi ta kasa mantawa. Ita kadaima in ta fito babban falo ko taje dining dan neman sharri irin na hancinta sai taji taji kamshinsa. Jin kamshin ya fi na ko yaushe karfi yasata sanin da gasken shine ya shigo. Cike da takaici ta ci gaba da kallonta zuciyarta na dokawa da sauri sauri. Duk da tasan shine ya shigo bata ko motsa ba balle tai yunqurin kallan inda yake. Tadai son nesa da ita zai zauna in zaman yazo yi kenan. Jin zamansa gefenta kan kujerar da take yasa zuciyarta wani irin dokawa da karfin gaske. Hannu tasa ta dafe kirjinta dan zata iya rantsewa natacce dake zaune gefenta yanajin yanda zuciyarta ke dokawa. "Ki shirya zamu je abuja jibi in Allah ya kaimu." Ya furta muryarsa a dake kuma can kasa. Husna kamar zata kurma ihu. Akan me muryarshi zata dinga tayar mata da tsikar jiki. Saboda me zaizo gab da ita ya zauna bayan kamshinsa takurata yake. "Lallaima wannan ya qure rainin hankali sallama bata hadasu,gaisuwa bata hadasu sai yau zai wani ce mata ta shirya zasuje abuja jibi kaman wani ubanta." Zuciyarta ta saka mata. Shiru tai ta kyale shi tai kaman bataji shiba ma. Kanta akan tv. Tasa hannu ta dafe kirjinta kaman yana mata ciwo. * Wani abu yaji ya tokare masa wuya wai wannan yarinyar me take ji dashine haka da zai mata magana ta share masa. Yar wacece ita da kamar shi zai mata magana tai kaman bataji shi ba. Muryarsa a dake can kasan makoshi yace mata "bana magana amin shiru." Miqewa tai da niyyar bar masa wajen gaba daya. Cikin wani irin zafin nama yasha gabanta saida ya tsoratata. Ganinta tai can like da kasa dan ta tabbata in fuskarshi zata kalla sai ta daga kai. Saboda dogo ne. Kanta a faffadan kirjinshi ya tsaya. Kanta ta sadda qasa bata san ganin shi batasan yana mata magana ba taqi ya fita harkarta ba ya kasa gane hakan. "Matsa in wuce ta fada" muryarta na rawa kanta a qasa. "Look at me... ki bani amsar maganar danai miki" Ya buqata yana zuba mata idanuwansa. Ji yake kamar ya kwada mata mari sai ta dago ta kalle shi. Baya son maimaita magana. Ko yaita fadar abu daya ka kasa ganewa. Bata mishi rai hakan yakeyi ba kadan ba. Wannan natacciyar yarinyar ta kasa gane level din hakurin shi yakai karshe. Numfashi yake ja yana fitar dashi a tsanake ko zai controlling bacin ran da yake ciki. Husna tana jin hawaye na shirin zubo mata. Sam bata son takura ya kasa gane takura mata yake. Kaucewa tai ya sake tare hanyar yaga alama yarinyar nan tana gwada haqurinsa. Batasan waye prince ishaq ba harda rashin huddy ya sake mayar dashi haka. Shi ya sashi zama so cool din nan. Da kudi akace tai masa hakan ba zatayi ba. Gab da ita ya kara matsawa yau kome take ji saita sauke shi ta kalli fuskarsa. Yanajin hucin lumfashinta a kirjinsa. * Husna kam zuciyarta ci gaba tai da dokawa tunda take bata taba yin kusa da namijin daba muharraminta ba haka. Ammar ne yake mata yawo a kwanyarta ga kuma qamshin natacce daya addabeta so take ya kauce ta wuce yaqi. Taga alama inba abinda yace tayi ba bazai barta ba. "Ba zani abuja ba kabani hanya in wuce." Ta fada da sauri dan batason yaji yanda muryarta ke rawa. Murmushi yai duk da baikai zuciyarsa ba. "I didn't asked you ko zakije ne. Nace ki shirya. And ki kalle ni kibani amsa" Ya fada idanuwansa nakanta. Ta soma qulewa a hasale tana shirin yin kuka tace "wai kai wanne irin natacce ne ka qyale ni nace ba zani ba!" Kuma sam taki dago fuskarta ta kalle shi. Lumshe idanuwanshi yai ya bude su a hankali. Akwai rigima kenan ya fada cikin zuciyarsa. Hannunsa yasa ya dago mata haba cikin idanuwanta ya kalla. Ji tai duk wani karfi na jikinta yana narkewa. Duk wata gaba ta jikinta ta mata sanyi. "In kina so zaman lafiya you have to take note of three things. Ba.amin magana cikin hargowa. Bana magana aimun shiru. Bakuma nason gardama da maimaita abu." Ya karasa yana kallonta deel cikin idanuwa. Husna tana jib dumin hannun shi dayake kan habbarta a ko ina na jikinta. Kamar habar tata tana da wani dangantaka da sauran inda take jin dumin nakai mata. Hannu takai da niyyar ture mishi nashi dai-dai lokacin da mararta ta wani irin murda mata sai da ta ji lumfashinta ya na neman daukewa. Hannunshin da zata ture ta kama ta rike gam tana kiran "Wayyo mamina...." Ji tai abin bawai na wasa bane ta sake kama hannun shi ta riko dam tana yin kasa. Takan sha wuya ba kadan ba lokacin period dinta sai dai yau saura kwana biyu take tsammani ga abin yazo mata a bazata.....! 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 0⃣7⃣ This one is for my mentor and my clients. Thank you for putting up with my shits. Prince ishaq kam hannunta yabi da kallo da wani yanayi a fuskar shi. Gani yai da gaske takeyi cikin alamar tsoro yace mata "ke meya hakan wai?" Ta ma kasa magana kawai wayyoo mami take kira ta dafe ciki da hannu daya. Dayan kuma ya rike da na prince ishaq dam. Baya son ganin wani cikin yanayi. Hakan na tuna mishi abubuwa da yawa. Tsugunnawa yai Allah ya zuba masa tausayi musamman ma mata. Cikin damuwa yace "Are you okay? wai meke damunki?" Daqyar tace masa "cikina..." Wani abu da ya dade bai motsa ba a jikinsa yaji. Koma menene yafi karfin zuciyarshi. Baisan lokacin daya kai hannun shi kan cikinta ba. "Dai-dai ina yake ciwo? Murdawa yake? Zafi?" Kaman bata masan yanayi ba. Pillow din kujera ya dauko ya ajiye kasa ya samu ya zame hannunshi daga nata. Kamata yai ya kwantar. "Stay right here" ya fada ya mike da gudu har kafarshi ta taka step din farko na benen zai hau sama kawai kamar wanda aka dokawa guduma akai. Ya tuna da alkawarin dayai ma kanshi na kin sake taba wani patient a rayuwarsa. Na barin career din daya so tun yarintarshi. Fasawa yai. Ya sauko da kafarshi. Wajen husna ya dawo da take kwance ta hade jikinta. Ya tsugunna. Muryarshi a tausa she yace mata. "Sannu kinji bara na kira doctor? Or we should go to the hospital? Can you walk? Girgiza masa kai tai muryarta can qasa tace. "zai tafi basaika kira kowa ba." Hade fuska yai yace "Ban fada miki ba.amin musu ba? Ko yan aikin gidan nan ne basu da lafiya hospital ake kaisu." Duk zafin ciwon da husna take ji bai hanata harararshi ba. A ranta tace wato ko yan aikin gidan nan. Itama ai ba catai tana da wani matsayi ba. Kaman yanda bata gabanshi bata kuma san me yasa ya aurota ba. Haka itama baya gabanta. Tana kallonshi.Wayar shi ya dauko tana jinsa ya kira. A wajen ya zauna duk motsin da zatai zai mata sannu. Har doc din ya qaraso. Cike da girmamawa taji sun gaisa kuma ya kira shi da prince ishaq. "Prince ishaq" ta maimaita. Daman sunan shi ishaq kenan. Tambayoyi doc din ya soma jero mata yanayin amsarta yasa ya fahimci period ne takeyin nata mai wahala. Yadan rubuta mata magunguna yace bawani abu bane period dinta ne zai dai-dai ta inta sha wannan magungunan. Ya maida hankalinshi kan prince ishaq yace. "You know the rest.... " "I quit. Sau nawa kuke son in fada maku?" Yai maganar da wani yanayi a muryarsa. Murmushi kawai doc din yayi yana daukar jakarsa. Yace ma husna. "Allah ya kara sauki" Ta amsa da amin muryarta can kasa. "ka tafi da prescription din saika sa a kawomana" Prince ishaq ya buqata. "Alright Nabarku lafiya" Doc din ya fadi yana ficewa. * Kallonta yake a nutse. "sannu ya fada a cikin sanyin murya." Tana jin shi. Yanda idanuwansa ke mata yawo a jiki. Shiru kawai tayi masa. Bata so yana mata magana. Ita dazai tashi yabarta ma da taso. Jin tayi shiru ga idanuwanta a rufe ya sashi daukar tayi bacci. Ya sauke wani dogon numfashi. Sam baya son matsala. Auren nan matsala ne a wajen shi. Yanzun idan irin wannan yana faruwa shi ya zai yi ne? Jin tunani zai haye masa yasa shi miqewa ya fita daga dakin. Cikin hadiman gidan ya tura mata guda daya don shi baida lokacin dazai bata yana kula da ita tunda bashi ya ajiyeta ba. Kawai dai wata irin zuciya gareshi idan yaga mata cikin rauninsu. Sai yanzun ma kalamanta suke sosa mishi zuciya. Ya rasa meyasa natacciya bata son kallon fuskarsa kuma bata shakkarsa shi. Wato yanda yake kiranta natacciya shiya bata damar ce masa natacce. Ko dayake yafi ganin laifin mai martaba a wannan karin. Shi ya takura masa ya aura masa ita kaman yanda yanzun ma yasa shi tafiyar nan da ita.. Sam baya son daukar kaya don ya tabbata shi zata zame masa. Abinda zaije yi abuja yana bukatar sirri kuma mai martaba yafi kowa sanin haka. Dashi kadaine zai zauna hotel abinshi. In yaje gida mutanen da yawa na iya sanin yana garin abuja. Dafe kai yai ya sauke numfashi dai-dai lokacin da wayarsa ta dauki qara alamar kira ya shigo.. Sanin kowa keda ringtone din yasa shi fito da wayar daga aljihunsa ya lumshe idanuwansa sannan ya dannan wayar ya kara a kunne. "Yaya wacece wannan data dauke hankalinka haka? Kar kasa in tsaneta tun kafin inzo.....baka da lokacina sam." Cewar nasir da yake maganar kamar zaiyi kuka. Yasan babu macen da ta isa ta dauke mishi hankali daga kan kanin nasa koda huddy ce balle wannan natacciyar duk kyan da take dashi kuwa. Kawai dai damuwa ce tai masa yawa. "Haba mana nasir. Wacece ma ta isa? abubuwane sunmin yawa babu lokaci sosai amman everything is gonna be alright karka damu." "Yaya sune ko? Ba zasu barmu mu huta ma ranmu bane wai? Ko in dawo gida?" Prince ishaq zai iya jin tsantsar damuwar da nasir din ya shiga. Don haka yai kasa da muryarshi yace. "No! Ka tsaya ka gama exams dinka kana jina ko? I am okay! Komai zai tafi dai-dai in shaa Allah" "To fadamun what is going on? " nasir ya bukata. Prince ishaq ya dafe kai.Sanna yace. "Drop it nasir. I am serious ka kyale maganar nan" "Hmm" kawai ya furta ya kashe wayar. Prince ishaq ya soma tunanin kila dai saiya dinga rubuta abubuwan daya kamata yayi saboda yawan mantuwar da yake yi these days. Ya saba kiranshi a kullum yaji lafiyarsa da yanda komai na rayuwarsa yake tafiya amman a satikan nan ko dan text din baya samun damar tura masa. Bayan damuwar da take zuciyarsa baya buqatar wata damuwar kuma dan haka text kawai ya tura masa ya kwantar mada da hankali. Ji yai iskar wajen ta masa kadan. Ji yake kamar kar nasir su gama exams dinsu ya dawo Nigeria. Zaman shi a England yafi masa kwanciyar hankali. Yasan masu farautar ransu da son gadon mulkinsu duk abinsu zasu bar masa kaninsa in yana can nesa... 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 0⃣8⃣ This one is for you safiyya galadanci. And know that prince ishaq said yes to you being his lil sis. He LVY loads. A big thank you to the readers. Writing this will be boring without you guys. Asabe tai zaune a wajenta har doc din ya dawo da magungunan daqyar ta tashi tasha. Bata jima ba ta samu bacci cike da mafarkin ammar dinta. Bata farka ba sai da yammaci sosai. A hankali ta bude idanuwanta....yanayin yanda taji jikinta ne tasan cewa ta baci ta dan gyara kwanciya da niyyar tashi taga Asabe a zaune cikin ladabi. Tasan ita ta shigo wajenta bayan fitar natacce. "Badai tun dazun kina nan ba?" Husna ta tambaya da mamaki a muryarta. "Ranki ya dade ina nan koda zaki farka ki buqaci wani abu....ya jikin naki?" ta amsa a ladabce. Ita kam bata son wannan girman da suke bata nauyinsa takeji a kunyace tace "da sauqi zaki iya tafiya abinki nagode." "Ki huta lafia" Asabe ta fadi ta mike ta fice,ciwon da takeji yayi sauqi sosai tashi tai ta nufi dakinta. Kanta tsaye toilet ta nufa ta soma yin wanka don ta tsaftace jikinta. Ta wanke kayan data bata ta dauro towel ta fito. Wata er jaka data zubo abubuwan da tasan zata buqata ta dauko Always dinta ta duba saura guda biyu. Ta dauki daya ta shafa farin almiski a jiki saboda yana dauke karnin jini kuma yana maganin ciwon sanyi da qwayoyin cuta da dama. Bayan ta gama shiryawa tunani take tasan dole ma ta fita shopping tana buqatar kanan abubuwa na amfani. Tsaki taja a fili tasan ba zata taba tambayar natacce zuwa unguwa ba don bai kai wannan matsayin a wajenta ba. Shiru tai tana sake sake. Dazun da mararta ke ciwo sai taji kamar yasa hannu ya taba mata ciki. Wani zafi taji kirjinta nayi. Inba tsabar naci ba inama ruwanshi da ita da har zai taba mata ciki. Tama manta shi nashi hannun data kama ta rukunkume. Dan rainin hankali wato jibi zamu tafi abuja ta nanata a zuciyarta wallahi yama rainani ta furta a fili. Inba raini ba shi yana ma da qafafuwan dazai kwaso yazo wajenta yana fada mata zaiyi wata tafiya kuma har ma da ita. Tunda a nata tunanin bata ga me yasa zai sanar da itaba. Babu ruwanshi da ita. Ko gaisawa basu taba yi ba. Sai tai kwanaki bata ganshi ba. Tome zatai masa in sun tafi taren ko kuma dai salon ya qara takurata fiye da wacce take ciki ne a yanzun? Gabanta taji ya fadi. Kar dai ace so yake sai sunje abuja yace zai hada shimfida da ita. Tunanin hakan kawai yasa taji hawaye sun cika mata idanuwa. Goge su tai. Tana tuna alkawarin datai. Cewar ba zata sake zubda ma auren nataccen nan hawayenta ba. Ko me zai faru kuwa. Tadai san akwai rikici kwance in har abinda take tunani yai shirin faruwa. Wata irin kewar ammar take ji kaman zuciyarta zata fito. Wayarta ta dauko. Tun satin bikinta aka qwace wayoyinta duka aka bata wannan aka kuma sake mata sim babu number din kowa saita yan gida da kuma kausar. Ta sake jin wata tsanar natacce a zuciyarta. So take taga karfe nawa. Dan tana son fita sosai. Idonta yakai kan date din wayar. Jitai kanta ya wani sara. Lokaci daya wani irin jiri ya kwasheta. "06-03-2015" Bangon wajen ta dafa tana kiran "Inalillahi wa ina ilaihi raji.un" babu adadi ko zuciyarta zata samu nutsuwa daga yanayin da ta shiga a wani bangaren kuma tunani yakaita wani lokaci can baya..............! *** *** Tana kwance kan gado wayarta ta dauki ruri. Jin kidan kawai ya bayyana murmushi a fuskarta. Dagawa tai ta kara a kunne hadi da yin sallama. Ya amsa mata daga dayan bangaren ya dora da. "Haba mana tawan. Sai anjamun aji za a daga wayar? " Dariya tai wani son shi na sake shigarta tace. "Nawan ni na isa kawai dai..... " "Kawai dai me?" tanajin murmushin dake muryarshi. Itama murmushin take a kunyace tace. "Nayi kewarka ne nawan" Ajiyar zuciya ya sauke da tanajinta har ta cikin wayar kamun yace. "Idan na fadi nawa a fili zaiyi yawa tawan. In shaa Allah 06 ga watan 03 zan dawo" Lumshe idanuwanta tai saboda hawayen da taji suna mata yawo. Muryarta na rawa tace. "Wata ukku kenan nawan" Sai da yai jim sannan yace. "Tawan ki mun addu.a ke dai. Randa na dawo ba zanyi awa biyu ba za.ai maganar aurenmu in shaa Allah." Ba zata iya ci gaba da maganar ba. Dakyar tace. "Nawan zamuyi waya anjima" Shima shiru yai na wani lokaci kamun yace. "Babu damuwa. Ina sonki sosai. Take care of you for me" "You too" ta amsa tana ajiye wayar tasan zai kashe....... 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 0⃣9⃣ This one is for you mumy bilkisu. Allah ya kara dankon soyayya da oga. Allah ya shirya yara ya musu albarka. Cikinsa yaji yana masa qara kuma yasan yunwace tun tea din daya sha da safe bai kuma samun natsuwar qara saka ma cikinsa wani abuba. Abinda ya kara bata mishi rai tunanin waccan natacxiyar yarinyar daya fado mishi cikin jerin muhimman tunanin daya kamata ace yanayi. Fada ma kanshi yake cewar auren shi dayake kanta bashi ya nema ba. Saboda haka ba matsalar shi bace. Ya fita hakkinta tunda ya kira mata doc. Ya kuma tura a kula da ita. So baiga dalilin dazaisa ace yana tunanin ko taji sauki ba. Duk da hakan ba bakon abu bane wajen shi in har akan marar lafiya ne. Ita din daice baya so tana kutso mishi kai cikin tunani. Bai baro inda yake ba sai bayan la.asar. kansa tsaye dining room ya wuce. Plantain da qwai yaci yasha fresh milk ya fito. Dakin shi ya shiga ya watsa ruwa ya saka wani farin yadi marar nauyi. Tunawa yai a dining yabar keys dinsa ya fita ya dauko. A babban falo ya hadu da natacciya kallo daya yai mata zuciyarshi ta wani harba. Rabon dayaji ta numfasa masa haka tun huddy. Tayi kyau duk da bayason fadar haka cikin doguwar rigarta abuja style daurin dankwalinta simple sai mayafi. Tunda can yana son yaga mace cikin shigar kaya purple kowanne irine. Lokaci daya yaja wata qatuwar qofa ya kulle zuciyarsa baima san yanda akai qofar ta soma budewa ba. Da alama fita zatayi don akwai qaramin mayafi a jikinta tasa shade shima purple. Cike da mamaki yake kallonta....kaman koda yaushe kanta a qasa ko inda yake bata kallaba asali ma rabawa tai ta wuce kamar baya wajen. Ficewa tai abinta. Murmushi yaji ya qwace masa ya jima rabon dayaji ya bayyana a fuskarsa haka kawai inba mahaifiyarsa yake tare da ita ba ko suna waya da qaninsa.. Yasan ko qofar farko ba zata wuce ba,babu wanda ya isa ya bude mata gate batare da izininsa ba. * Hanyo yi taita bi. Bata san gidan nada girma haka ba sai yau. Daya daga cikin hadiman gidan ta sa ta rakata har kofar gidan. Sai da ta ganta a wajen gidan tukunna zuciyarta da take dokawa tadan dai-dai tu. Tana saka shade in dai zata fita amman ba kowanne lokaci ba. Yauma ta saka ne saboda ya boye idanuwanta dan kallo daya zakai mata ka fahimci ta sha kuka harta godewa Allah. Date din data gani ne ya sake tunzurata ta fita bada izinin mijin da aka daura mata ta fin qarfi ba....duk da sanin hakan ba dai-dai bane bai dameta ba. Tunda ba tada mota a gidan ta yanke shawarar daukar drop zuwa diamond bank ta ciri kudi sannan kuma ta zo stop and shop ta siyi abinda take buqata. Mamakin girman gidan take yi harda titi a ciki kaman na estate dinsu ta dan soma gajiya da tafiya dan ba sabawa tayi ba. Gate tagani a garqame kuma babu kowa a wajen taji wani takaici ya rufeta takai mintina goma a tsaye a wajen wai ko zataga wani ya bullo tasa ya bude mata amman babu kowa. Juyawa tai idanuwanta cike da hawaye tanata qoqarin tarbesu karsu zubo kenan fita ma in zatayi komin buqatarta saita sauke ajinta ta tambayi natacce kenan. Bata kaunar abinda zai hada su magana da juna. Tana son fitar nan kam ko dan gyaran jikinta ma dole ta fita....tafiya take ga nauyi da zuciyarta tai mata. Ko a wanne hali ammar yake? Allah kadai ya sani tana dai da tabbacin tsakanin jiya da yau ya tsaneta! Tasan abinda ya kamata tayi....duk da kashe di da mahaifinta yai mata. Ta tabbata inda shi ya tsinci kansa a halin data tsinta zai fahimci yanda takeji. Da wani sabon qarfin gwiwar data jima bataji shiba ta juya ta shiga gidan. * Prince ishaq kam keys din shi ya dauka ya shiga dakinshi ya dakko system ya dawo babban falo. Yana zaune a falon hankalinsa akan system dinsa husna ta shigo. Ta tsane shi wata irin tsana dabata san kalarta ba ko ganinsa bata sanyi. Ganinsa kuma datai sai yake kokarin ruguza mata dan kwarin gwiwar da take ji. Abin takaicin ma sai da taji gabanta na faduwa. Ga wani kwarjini da taga ya mata. Tsaki taja cikin zuciyarta. Batason wannan abin da yake mata ko kadan. Cikin muryar dabata gane tata bace tace masa "kazo kasa a budemin gate zan fita." 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣0⃣ In dedication to the reader. May Allah's blessing be with you all. Thank you!!! Yaji shigowarta sarai ya ci gaba da game dinsa. Ya kuma ki abinda tace. Dame take ji da ba zata dauke shi da muhimmanci ba. Dan shi bata gabansa bashi zai bata damar jin hakan game dasji ba. Ba ai macen da zata nuna masa iyakarsa ba. Ko da huddy ce kuwa. Dole ta bashi girma ko bata so. In tana son magana dashi ta zagayo ta kalli fuskarsa. Husna kamar zata saka ihu don takaici. "Magana fa nake maka kazo kasa a budemin gate." Ta sake fadi cikin alamar qulewa. System dinsa ya rufe ya miqe yana shirin nufar dakinsa.....tasha gabansa shade din idonta ta cire ta kalle shi cikin fuska sosai. Tunda yake bai taba ganin kiyayya irin wadda yagani a cikin idanuwanta ba. "Don na tambayeka abu zaka nemi wulaqantani?" Da mamaki sosai yake kallonta. A. Lokaci daya kuma yana tambayar kanshi akan me zata aure shi. Ta tsane shi!!! Yagani cikin idanuwanta bata son shi. Ko da zaka auri mutum dan kudin shi da kalar tsanar datai masa kam zata hakura. Sai dai duk wannan bai bata damar yi masa magana yanda take so ba. Kamar wanda magana ke ma wahala yace. "Not that i care. Ki rubuta ko me kike so aje a siyo miki" Hawayen ta take iya bakin kokarinta wajen tarbewa. Da tana da bindiga harbe wannan nataccen zatai. Me yasa baya ganewa ne. Me yasa yake son kara mata kunci har haka. Muryarta na rawa tace. "Kabarni da abinda yake damuna. Just kasa a bude mun gate" Kallon nutsuwar nan ya tsaya yake mata. Kallon da zaka rantse bashida wani muhimmin abun dazai daya wuce ya zuba mata idanuwan shi yana kallonta kamar yana hango har abinda yake bayan fatar jikinta. Tun da ta kalli idon shi tai magana dazun ta sauke kanta kasa. Tana jin yanda idanuwansa ke mata yawo. Saboda duk damuwar da take ciki bai hana kamshin shi damunta ba. Bai kuma hana bangaren zuciyarta dake dokawa duk idan taganshi ci gaba da aikin shi ba. Ganin suna shirin daukar mintina biyar bai ce komai ba. Yasa ta fadin. "Bana son duk wata alfarma da zata fito daga wajenka zan je da kaina kuma zan shiga motar haya" "Motar haya" ya nanata a zuciyar shi. Bawai bai san akwai bayin Allah da suke hawa motar haya bane. Sai dai har ga Allah ya manta da wani abu waishi motar haya. Saida yazo daf da ita wannan karon ma kanta a qasa hannu yasa ya dago mata da fuska ranshi ya baci. Bakuma ya son ana bata mishi rai saboda bako yaushe yake iya controlling abinda yake aikatawa ba cikin bacin rai. "Ba.a fadamin duk abinda ake so....idan kika qure haqurina ba zai maki kyauba. Daga randa kika tako kafafuwanki cikin gidan nan kike cin alfarmar da duk wanda yake karka shin sa yake ci." Ganin yanda jikinta ke kyarma a hankali ta kuma kasa kallon idanuwanshi. Duk da idanuwanta akan fuskar shi suke. Ya jinjina kai kamun yace. "Ko hadiman gidan nan suke bukatar wani abu fita ake a siyo musu." Ko ina na jikinta kyarma yake. Karo na biyu kenan daya kai hannun shi a habarta. Kuma dumin hannun yana shigar mata wajaje da yawa a jikinta. Hannunta tasa ta ture nashi hannun. Karfin gwiwar da take ji ya gama narkewa. Kawai so take ta samu abinda take bukata. Karo na biyu da yai misalin matsayin yan aiki da nata. Ta rasa abinda yasa hakan ya sosa mata rai. Yana kallonta ta bude jakar hannunta ta dauko dan karamun diary da biro. Ta rubuta always da recharge card. Ta rubuta pin din ATM dinta daga kasa taja masa layi. Sannan ta rubuta 10k da take so a ciro mata. Ta dauko ATM din 3k. Always ta 1k. Katin MTN na 2k. Batare data kalle fuskar shi ba ta mika mishi takardar da kudin da ATM din. Wani irin kallo yai mata sannan ya karbi takardar kawai yabar kudin da ATM din suka fadi kasa. Bai jira amsarta ba ya wuce abinsa ya tsani wannan yarinyar da take ji da kanta. Duk a yanzun ya tabbatar ba kwadayine yasa ta aure shi ba tunda yaga tsanarsa a idanuwanta. Sai dai ya rasa dalilin dazaisa ta aure shi idan tana masa wannan tsanar. Waya yai akawo always din guda goma da katin MTN na 5k. Bai koma dakin shi ba saida ya bar umarnin in an kawo kayan akai ma natacciya bangarenta. Yana shiga dakin shi ya sake duba list din yaga ta saka a ciro mata kudi. Yaja tsaki. Baya son harkar karanta ko kadan da zubda mutunci. Drawer din gadon shi ya janyo ya dauko rappers na kudi yan naira dubu dubu. Na 50k ya dauka dan babu ma kudin sosai. Sai ya kira an ciro mishi. Baya jin zai iya sake fita babban falo. Saboda yanda ranshi yake a bace. Waya yai ma Kamala da yake kula da komai na gidan. Yasa a turo masa wata bangare shi. Falon shi ya fito ya tsaya. Sai da tazo ya bayar da kudin a akaima natacciyar yarinyar can. Kan kujerar falon ya zauna. Ya lumshe idanuwan shi yana karanto addu.o.in dazai samu nutsuwa a bisa koyarwar musulunci. Sallama yaji. Ya bude idon shi. A ladabce hadimar da take tsugunne tace. "Allah ya ja da ran yarima" "Lafiya?" ya bukata muryarshi a dake. A tsorace hadimar tace. "Rankai dade. Uwargida tace a dawo maka da sakon nan" "Kije da shi kawai" ya fada yana kirga 1-10 cikin kanshi. So yake ya nutsu ko yaya ne kamun ya fitar da kafarshi daga falon nan. Cikin rawar murya hadimar tace. "Rankai dade ban fahimta ba" Cikin tsawa yace. "ki dauki kudin nace yaren hausa ne bakya ganewa!!!" Da sauri ta mike tana fadin. "Allah ya huci zuciyar yarima" Tana fita ya saka takalmanshi ya nufi sashin husna da tun ranar da aka kawo ta rabon da ko hanyar ya kalla. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣1⃣ This is for you "Maman Nu.aym. Allah ya raya mana Nu.aym ya albarkaci aurenki. Thank you for being a big fan of wata bakwai 7. Husna kam tana zaune gefen gadonta ta rafka tagumi da tunani kala kala a zuciyarta. Sanda aka zo aka kawo mata kudi wai inji yarima. Wani abu taji tun daga dan yatsan kafarta har zuwa zuciyarta. Waye shi dahar zaiyi zaton tana bukatar kudin shi? Tana kallon mamakin da yake fuskar hadimar data ce ta mayar masa da kudin shi. Kasa jurewa tai. Batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba tasa hannu ta goge su. Kirjinta na mata wani irin zafi. Turo kofar akai da wani irin karfi da saida karar tasa husna zabura. Da yanayin yanda ya turo kofar haka ya mayar da ita y kulle. Tana kallo yasa mukullin jiki ya na shirin kullewa. Gabanta ya shiga dukan uku uku. Murya na rawa tace. "What are you doing? Ka fitarmun daga daki. Bana........ " Ganin ya cillar da mukullin gefe ya nufo gadon. Yanayin fuskar shi ya sa ta hadiye sauran maganarta. Da sauri ta dinga jan jiki tana matsawa har takai karshen gadon. Ta takure jikinta. Gefen gadon yazauna ya fuskanci idan take. Cikin muryarshi da ta kara budewa saboda bacin rai ya kalleta sosai yace. "Zo nan" Yana bubbuga kan katifar kusa dashi. Girgiza kai ta shiga yi tana kara matsawa jikin gadon kaman zata shige cikinsa. "Bazai miki kyau ba inhar na karaso na jawoki da kaina" Ya fadi a gajiye. Muryarshi da yanayin shi sun tsorata husna. Wasu hawaye suka gangaro mata. Kallonta kawai yakeyi. Gani tai bata da wani zabi. Batason me yake nufi da ita ba. Ko menene bata son yazo inda take ya janyota. Bataso hannun shi ya sake kaiwa jikinta. Bataso sam. A yanayin daya fadi maganar tasan zai aikata. Saboda bata ga wasa a fuskarshi ba. Gata Allah ya zuba mata tsoron tsiya. A hankali taja jikinta ta matsa tsakiyar gadon tana hawaye. Kallonta yake yi. Yanda duk ta firgice ga hawaye wani nabin wani. "I really don't want to repeat myself" Ya fada yana kallonta. A yanda yake jin shi komai zai iya faruwa. Matsowa tai inda ya nuna mata. Jikinta ko ina kyarma yake. Yaja wani uban tsaki a zuciyar shi. Daga shi har ita auren nan da akai musu an shiga rayuwarsu ya kula. Kalli yanda jikinta yake kyarma kamar wanda ta ga wani mugun abu. Ranshi ya kara baci. Bason tabata yake ba. Bata jin magana ya kula. Ya kuma rasa dalilin dayasa take da karfin bata mishi rai har haka. Bayason raini. Inhar yan son rage matsalar zaman su dole ya koya mata guje ma bacin ranshi. Duk tsanar datai masa kuwa. Dan haka ya kamo hannuwanta da baisan mai taje ta tababa sukai sanyi karara haka. Hannu daya ya saki. Yakai shi fuskarta ta janye. "Stay still" Ya fadi da wata irin murya da tasa ta tsayawa. Wasu hawayen suka kara zubo mata. Hannu yasa ya goge su yana fadin. "Bana son ganin hawayen nan. Magana nakeso muyi. Kina jina?" Husna kam a tsorace take. Kai ta daga mishi. Tana kokarin tarbe hawayen ta kasa. Hannu yakai ya dago mata fuska. Ya tsani yanda duk da hawayen fuskarta tayi kyau. Cikin idanu yake kallonta dan yana son ya tabbatar da sakon shi ya kai mata. "Yau ya zama ranar farko da zan aiko miki abu kisa a mayarmun. Matsalolin da nake ciki sun mun yawa bakuma nason kara su da gulmace gulmace tsakanin hadimai na, cewar matata ta raina ni" Yanayin abinda tagani a idon shi sai taji sam abinda tai masa din bata kyauta ba. Sai dai shima yanayin da ya saka ta shiga da wanda ta tabbatar yanzun haka ammar yana cikin fin nata bai musu adalci ba. Bata son yanda jikinta yake bin umarninsa. Hannun shi dayake taba mata fuska take son turewa. Saidai bata son bijirema umarninsa. Bata son mai zai iyayi ba. Ga dakin ya kulle hakanma shi yafi daga mata hankali. Kai ta daga masa alamar. "Eh" A dake yace. "Talk to me da bakinki bana son magana da kai" Sai da ta hadiye wani miyau sannan can kasan makoshi tace. "Eh naji" "Good girl" Ya fadi yana cire duka hannuwanshi daga jikinta. "I am waiting" Ya fadi a kagauce. Saida ta sa hannu ta goge fuskarta sannan tace. "Me zanyi kuma?" "Kinmun laifi and bakisan me ya kamata kiyi ba kenan?" Da wata sabuwar tsanar shi tace. "Kayi hakuri" Jinjina kai yai ya mike daga kan gadon. Inda ya cilla mukullan dakin ya dauko. Yana budewa wata hadima zata kwankwasa. Da sauri ta tsugunna kasa tana fadin. "Allah ya kara maka lafiya" Ko kallonta bai ba ya wuce. Tashi tai ta karasa cikin dakin da sallama. Ta tsugunna ta mikama husna ledar hannunta. Karba tai ta ce mata zata iya tafiya. Dan ta kula inba tace su tafi ba haka zasuyita tsugunno. Zuciyarta yanzun bata natacce take ba. Ture shi da abinda yai mata tayi gefe daya sai zuwa anjima. Ta bude ledar ta zazzago kayan ciki. Katin wayar ta dauka ta kankare su duka. Ta lalubo wayarta tai loading hannunta ma rawa yake. Kaman yanda zuciyarta ke rawa. Numbar ammar da take kamar tambari a zuciyarta saboda zaman datai ta saka ta danna kira. Da duk ringing din da zatai da yawan hawayen da suke zubo mata. Sai da ta yanke bai dauka ba. Ta sake kira bai dauka ba. Saida ta jera kira biyar bai dauka ba. Tanajin zuciyarta kamar zata fashe sabo da fargaba. A karo na shidda ya daga muryarshi can kasa yace. "Hello" 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣2⃣ In dedication to my mentor Arc Haidar. Ko a mafarki ko a ido biyu ko a cikin dandazon taron jama.a zata iya gane muryar ammar dinta. Sai yanzun dataji muryarsa tasan kewar sa da zuciyarta tayi. Numfashinta har wani barazanar daukewa yake. Cikin murya mai matuqar rauni tace "Nawan nice." "Husna ta" ya fada tasan shi sosai hakan yasata fahimtar yanayin muryarsa da alamar rashin yarda da cewar ita dince ta kirashi. Shirun da yaji tayi ne yasa shi cewa "husna da gaske kece? Tawan kimin magana dan Allah." Muryarta na rawa tace "nice ammar." "Ya Allah" ya fadi yai shiru. Tasan kuka yake daga yanayin muryarshi. Can kasan makoshi cikin kuka yace. "Husna dan Allah kice mun mafarki nake. Kice abinda suke fadamun ba gaskiya bane." Itama kuma kukan na neman cin qarfinta tasan idan ta kuskura ta fara batasan ranar barinta ba. Dole ta zama mai qwarin gwiwa tai masa magana. "Ka saurareni....wallahi bana son auran nan bana son wanda aka auramin ban taba son kowa ba sai kai ammar ka yarda dani." Tun da take bata taba jin namiji saurayi babba kaman ammar na gunjin kuka haka ba. Kukan shine ya karasa karyar mata da zuciya. Bata san sanda kukan ya kwace mata ba. Sun fi mintina goma sun kasa magana kamun ya samu yace. "me yasa zakimin haka? Ke baki san irin son da nake miki bane? Haba babyna komai da nake nema a rayuwa don na aureki ne." "Nasani nasan haka wlh ta fada" zuciyarta na wani tafasa. Lokaci daya zazzabi ya rufeta ruf. Wani irin kuka take daga zuciyarta yake fitowa dan hawayen ma sun daina zuba. Cikin kuka ammar yace. "To ki kashe auren nan indai kina sona da gaske ba qarya kikemin ba husna" Bata san ya akai ma bata taba kawo ma ranta wannan shawarar ba a tsahon sati biyu datai a wannan qaddararren gidan. Wani sanyi taji a zuciyarta ta wanni fannin. Hannunta tasa ta dafe kirjinta saboda zafin da yake mata. "Ammar zan kashe auren nan na maka alqawari zamuyi rayuwarmu tare." Tanajin yanda ya sauke ajiyar zuciya. Muryarshi harta shige saboda kuka. "Husna ina sonki da yawa nasan ba zaki taba barina ba wallahi tun jiya dana dawo aka fadamin na dauka zuciyata zata fashe ne tunda nazo daki na kwanta jiran mutuwata nake...husna kece numfashina." Murmushi tai duk da halin da suke ciki bai hanata jin son shi har ranta ba wanda ta jima bataji irinsa ba. "Nima kasan ina sonka aiko?" "Da auren wani akanki husna zai wahala zuciyata ta yarda da hakan" Ya fadi a raunane. Da sauri tace. "Zan kashe auren nan. I promise you nawa" Hira sukai tayi abinsu yace mata bara ya tashi yai sallah yai wanka. Bata bari ya tafi ba saida tasa yai mata alkawari zaici abinci tukunna. Duk da taji muryar ammar da alqawurransa masu sakata natsuwa. Itama ta masa alqawarin da bata san yanda za.ai ta cika shiba. Wani farin ciki take ji ammar bai tsaneta ba yana sonta har yanzun. Wani bangare na zuciyarta yana son nuna mata kuskuren abunda suka aikata. Ita kam koma menene bai dameta ba a yanzun da wutar soyayyar ammar take tsarga mata. Kwanciya tai kan katon gadon maganganun su na mata yawo. Sanyi taji tanaji dakyar ta iya sakkowa daga kan gadon ta kashe AC din dakin ta koma ta kwanta. Ta lullube amman jikinta kyarmar sanyi yake saboda zazzabin da ya lullubeta. A haka asabe ta shigo ta sameta. Da gudu ta sauka kasa ta je ta fada a kira kamala a gaya mishi ya kira prince ishaq uwargida ba lafiya. * Prince ishaq kam tunda ya fita daga dakin husna. Ya sa aka kaishi lambu yai zamansa. Dan sam zaman gidan duk da bangaren su daban dana natacce ya fita daga ranshi. Baya son yanda take bata masa rai tana saka shi yana abu dan dole. Yana kishingide kan daya daga cikin kujerun dake lambun ya lumshe idanuwanshi yana tunanin kalar zaman da zasuyi da natacciyar nan a abuja. Wayarshi ta kama ruri. Yanaji ya share sai da tai har sau uku. A na hudunne ya dauko batare daya duba ba ya amsa ya kara a kunne. Cikin ladabi kamala ya gaishe dashi kamun ya fada mishi cewar husna bata da lafiya. Ya bude idanuwan shi a hankali yanajin tamkar duka nauyin duniya aka dora mishi akai. Ina amfanin wannan auren da babu komai a cikin shi sai matsala da takura. Yayi niyyar ya kira doc din kawai yaje gida ya dubata sai dai baya son karanta. Wannan kuma zai nuna cewar bai damu da matarshi ba wanda gaskiyane. Yadai damu da kare mutunci da martabar gidansu. Dan haka ya kira cikin hadiman wajen yace ai ma driver dinshi magana yazo au tafi. * Yana shiga gida bangaren husna ya nufa. Ya sallami hadiman da suke zagaye da ita. Gefen gadon ya zauna. Yanda yaganta sai ta bashi tausayi. Hannu yakai ya taba goshinta yaji shi kamar wuta. Cikin rawar murya tace. "Karka sake tabani.... Bana so" Bai san sanda murmushi ya kwace masa ba. Cikin taushin murya yace. "Save it saikin warke. I am stuck with you like you are stuck with me. Badon ina so hannuna ke kaiwa jikinki ba" Baya son jin kanta. Saboda shi ya kamata ya daga mata kai. Ba wai ita ba. Duk da yasan abinda ya kamata yai mata. Saidai bazai karya alkawarin daya daukar ma kanshi ba. Doc dinsu ya kira. Tashi yai ya shiga toilet dinta. Ya wani yamutsa fuska ganin pants dinta da bra data wanke. Karamun towel ya dauka ya jiko shi ya matse ya fito. Bargon da take lillibe dashi ya janye. "Banaso" ta fadi dakyar. Ko bi takanta baiyi ba. A goshi ya fara dora mata towel din. Ta zabura saboda sanyin da ta kara ji. Hannuwanta duk biyun tasa tana rike nashi. Dayan hannun shi yasa ya rike nata duka biyun gam. A dake yace. "Bana son gaddama. Ba yanda za.ai muyi tafiya bakida lafiya. I am not rescheduling saboda ke" Bata da karfin yin fadan. Ba kuma tason yana tabata. Musamman yau dataji muryar ammar. Sai ta sake tsanar shi. Wasu hawaye suka gangaro fuskarta. Bata manta abinda yai mata ba dazun. Da kuma wanda yake mata yanzun. "Ka sakeni please. Dan Allah ka sakeni" Ta fada tana kallon fuskarshi. Hannuwanta ya saki yaci gaba da dora mata towel din a goshi. Ta bude baki zata sake magana dan taga bai gane me take nufi ba aka kwankwasa kofar. "Come in" Ya fadi dan yasan yace in doc din yazo ya ce a rakoshi bangaren husna din. Da sallama ta turo kofar. Ta gaishe da prince ishaq da ya amsa cikin mamaki. "Kayi hakuri. Doc amir ya samu flat tire a hanya saiya kirani coz ina kusa daku fiye dashi" Jinjina mata kai yai kawai. Ya nuna mata husna da take kwance. Duddubata tai sosai da aune-aune. Tace ma prince ishaq. Damuwace tai mata yawa. Tana bukatar hutu sosai. Ta bada list na prescription din data rubuta. Kira yai akazo aka karba. Doc din ta zauna saboda za.ayi allurai guda uku dan zazzabin ya sauka. Ba.afi mintina sha biyar ba aka kawo. Ai husna na kyalla ido taga allura ta mike zaune. Idanuwa cike taf da hawaye tace. "Wallahi na warke. Dan Allah karka bari taimun allura" Doc din ta kalli prince ishaq. Matsawa yai kusa da husna ya kamo hannuwanta. A tsorace ta rike shi sosai tana magiya. Tun tana karama harta girma sai an riketa ake mata allura. Bata sonta ko kadan. Ko wani za.ayiwa hankalinta tashi yake balle kuma ace ita. Hannuwan shi ya zame daga na husna ya tallabi fuskarta. Ya saba mu.amala da patients irinta da yawan lokutta a baya. Musamman yara kanana. Cikin idanuwa ya kalleta yace. "Pull yourself together. Babu zafi fa" A rikice husna ke girgiza masa kai tana fadin. "wallahi zan bika abuja karka bari tamun allura" Girgiza kai yai a ranshi yana fadin saikace zuwan shi abuja da ita zabi ne. Kamo ta yai. Ya dagota sosai ya rike rungumeta a jikinshi. Kiciniyar da take ta kwacewa ma taso ta bashi dariya. Sake matseta yai sosai a jikinshi hakan yasa ta yin luf. Alama yaima doc din cewar tazo tai mata allurar. Ganin tana kokarin zame skirt din dake jikin husna ya sakashi lumshe idanuwanshi. Yanajin yanda husna ta sake rukunkume shi da shigar allurar. Haka kawai yaji zuciyarshi wani iri. Yanda take rike shi yana saka shi jin wani yanayi da baisani ba kuma bama yason ya fahimta. . "Na gama" Doc din ta fada. Kai kawai prince ishaq ya daga mata. Ya nuna mata kofa. Ta tattara kayanta ta fita. Yana rike da husna har yaji yanayin numfashinta ya canza alamar bacci ya dauketa. A hankalo ya ajiyeta yana bambareta daga jikinshi. Da wani irin yanayi a jikinshi mai wahalar fassarawa ya fita daga dakin yana ja mata kofa. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣3⃣ Precious writer's forum (PWF) we are not the best but we are surely unique for we love what we do!!! Da tunani barkatai a zuciyarshi harya tashi da safe. Tun wajen karfe bakwai daya koma bacci bai tashi ba sai yanzun nan. Yana duba agogo har sha daya tayi. Dakyar ya rabu da katifar yaje yai wanka. Ya shirya cikin wani kaya na karan miski brown. Yayi kyau matuka. Har ya wuce zaiyi dining room din ya tuna da yar mutane da take karkashin kulawar sa bata da lafiya fa. Yaja wani gajeran tsaki sam sam baya son matsala a rayuwar shi. Bangaren husna ya wuce yaga ko taji sauki. Dan bai niyyar daga tafiyar shi ba saboda ita. Yanda aka lika masa aurenta haka aka lika masa tafiya abuja da ita. * Husna kam dayake ba sallah take ba. Tunda ta tashi tai wanka ta shirya cikin wata doguwar riga simple. Suka sha wayarsu da ammar harya shirya zuwa aiki. Dan ya ce mata ya samu aiki a wani gidan mai. Suna gama wayar ta kwanta shiru abinda ya faru tsakaninta da prince ishaq yana mata yawo. Sai taji kaman tanajin kam shi har yanzun kan gadonta. Taja tsaki. Bakin natacce ta fada a ranta. Tanata tunani har bacci ya dauketa. * Kwan kwasawa yai yaji shiru haka yasa shi turawa a hankali yaganta kwance tana bacci. Babu karya tana da kyau. Shi kyan ta baya gabanshi. Gefen gadon ya karasa ya zauna. Ya duba magungunan daya ajiye gefe suna nan yanda suke bata sha ko daya ba. "Yarinyar nan ta rainani" ya fadi a hankali. Sai daya saka aka kawo plantain da fried eggs sannan. Ba inda zai kwashi kaya ya tafi dashi yake fada ma kansa. Hannu yasa ya shafi gefen fuskarta. Da sauri ta bude ido ta sauke shi a fuskarsa. Ganin shi yasa ta saurin tashi zaune tana matsawa. Har haushin yanda take shakkar shi ta ba kanta. Ga jarababben kamshin shi har ya gauraye dakin. Hannu yakai zai sake tabata ta kara matsawa. Bai kobi takanta ba. Ya matsa kusa sosai yaka UK hannu ya taba fuskarta ta rufe idanuwa. Ya taba wuyanta na minti daya yaji akwai sauran zazzabi. Plantain din ya ajiye mata kan cinya da cokali a ciki yace mata. "eat ki sha maganinki" Ya wani hade rai yana kallonta kawai. Husna ta kule. Bata son yana mata shisshigi. Inba naci ba me zai kawo shi dakinta. Girgiza masa kai tayi alamar bata ci. "Ki ci ki sha magani ko kuma ki zauna a dawo ai maki allura. I can't take you ko ina da wannan zazzabin" Ya ce a gajiye. Kaman maganar kawai ta cinye duk karfin jikin shi. A hankali ta dauki plate din. Turawa kawai take badan bakinta nada wani appetite. Dan gara komai da allura. Banda auren natacce babu abinda ta tsana sama da allura. Jitai inta kara amai zatai. Ta ture plate din. Matsawa tai ta dauko magungunan. Ta duba yanda zata sha su. Ta ballo saidai ba ruwa kusa. Ga mamakinta prince ishaq ya tashi yaje inda fridge din dakin yake ya dauko mata swan da cup dayake a jiye kan fridge din. Ya zuba ya mika mata. Saita tsinci kanta da danjin nauyin shi. Ta karba cikin sanyin murya tace. "Nagode" Kai kawai yadan daga mata yanda yakanyi ma wasu cikin hadiman gidan in sun gaishe dashi. Saida yaga ta shanye magungunan. Tana ta yatsina fuska yace mata. "Kina jin ciwon kai?" Ta girgiza kanta. "Dizziness fa? Ko amai?" Ta sake girgiza kai dan ya soma isarta. Shi ba likita ba ya tsare da tambayoyi. Mikewa yai ya karasa daf da ita. Hannu yakai ya sake tabawa yaji yanayin zazzabin. Ta janye fuskarta. Wani abu ya tsaya mishi a wuya. Ya rasa dame yarinyar nan take ji. Baya son ta zame masa kayane dan suna setting kafarsu abuja bashi da lokacin wannan shirmen. Share ta yai ya matsa ya taba kumatunta. Ganin yanda bata so ne yasa shi dora hannun kan wuyanta. Yabarshi akai fiye da yanda yake bukata dan kawai ya takurata. Tadai ki kallon shi harya dauke ya fita. Zanin gado husna ta janyo ta goge kumatunta inda ya taba ta kuma goge wuyanta. Amman da yake kaman yanda Allah ya zuba masa naci haka ma duk abinda yabar mata ajiki yake da naci. Yaki fita sam. Ta ki daina jin dumin hannunshi da yanda tsikar jikinta ke tashi. A fusace ta sakko daga kan gadon ta je wajen dressing mirror dinta. Duk wani collection na turare da take dashi saida ta feshe dakin dashi. Jin turarukanta sunki korar kamshin nataccen nan yasata bude akwati nan da kayan kwalliya ne kawai a ciki da turaruka lefenta datai ma kanta alkawarin ba zata taba ba. Tunda bata son mai kayan ba kuma tason abin hannun shi. Kala uku ta bude daka gansu kasan masu bala.in tsada ne. Ta feshe dakin. Sannan taji yamata kamshi na daban. Tana komawa kan gado ta kwanta ammar na kiranta. "Assalamu alaikum tawan" Ya fada tanajin fara.arshi cikin muryarshi. Ta amsa da murmushi a fuskar ta. Yanda yaji muryarta ya sashi tambayarta lafiya kuwa. Tace. "Nawan zazzabi nake danyi fa" A rikice ya shiga jero mata tambayoyi. "Ya Rabb. Yanzun ya jikin? Kinsha magani? Ko sai kinje asibiti? Husna ko....... " Dariya tai ta katse shi da fadin. "Ya kira likita an dubani har gida. Yanzun ma yazo yaban magani ya fita" Lokaci daya muryar ammar ta sauya. Can kasan makoshi yace. "Husna karki soma son shi. Karya tabamun ke, husna in baki kashe auren nan ba wallahi zan iya mutuwa. Ki tausayamun" Muryarta a tausashe tace. "Relax nawan. Ka yarda dani mana. Ni bansan meyasa ya aureni bama. Wallahi bai damu dani ba. Bai taba yunkurin tabani ba." Wani dumi taji inda ya tabata dazun tamkar waje na neman karyata zancenta. Ta kuma tuno yanda ya riketa da za.ai mata allura. Duk da dumin zazzabin da take ji bai hanata tuno nashi dumin ba. Haka ta samu ta kwantarma da ammar hankali da sake jaddada masa alkawurran da bata san yanda za.ai ta cika shi ba. * Kan kujerar falon shi ya zauna yai shiru. Kanshi ma ciwo yake. Yana so ya hada kayan tafiyar shi gobe duk da yanada kaya acan. Amman akwai yan abubuwan dazai hada saboda yanayin tsaro. Ko da kwana hotel zai kamasu ba komai na can din yake son amfani dashi ba dul da cewar sababbi ne. Wani lokaci yakan godewa halayya irin ta ummarshi da duk matsayinsu tai kokarin koya musu yin abubuwa da dama dakansu. Takance kar matsayin da Allah yai musu ya saka su girman kai ko wulakanta na kasa dasu. Su dauka cewa matsayinsu wani abune mai nauyin gaske da Allah zai musu tambaya akan yanda suka rike shi. Duk da haka kamala ya kira dan ya yarda dashi sosai. Shi yasa ya hada mishi duk abinda yake bukata. Ya kuma ce shine zai kaisu Abuja goben in shaa Allah. Dan haka kawai yake son canji. A mota zasuyi tafiyar. Rabon shi dayai tafiyar fin awa daya a mota harya manta. Ya sanar da kamal baya son security saboda hakanma na janyo hankalin mutane akan su. Normal yake bukata ko da ta rana dayace. Yana son yayi abu kaman yanda kowa yake yi. Yana son ajiye prince ishaq a gefe yai abu a ishaq dinshi zallah. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣4⃣ In dedication to billy galadanchi, safiyya, ummie, dimples, jidderh and all the members of ummie jay novels. Tun wajen karfe tara ya gama shiryawa Sai dai baisan ko ita ta shiryaba ko bata shirya ba. Fitowa yai babban falo ya sami hadima daya dabai san sunanta ba don ba damuwa yai da hakan ba. Har qasa ta tsugunna kanta a sunkuye tace "fatan yarima ya tashi cikin qoshin lafiya?" Lafiya ya amsa a taqaice mulkin na motsa masa. Yana son ya tura a ce mata ta fito sai dai yana gudun zata iya fadar magana a gaban hadimansa. Baya qaunar yarfi da harkar yada girma duk da bawai son matsayin nasa na yanzun da na gaba yake ba. Da kansa ya taka zuwa bangaren ta ya nufi dakinta. A hankali ya qwanqwasa. * Husna kam tunda ta tashi taji jikinta babu zazzabi sam. Tadai yi wanka ne tasa aka kawo mata soyayyen dankali tadan ci. Tasha magungunanta dan bata da bukatar natacce yazo ya maimaita abinda yai jiya. Dan ta kula namiji ne shi da yake yin abinda yaso babu kuma wanda ya isa ya hana shi inya tashi. Chatting suke da ammar a whatsapp dan jiya da dare ya sata tai downloading sabo. Taji an kwankwasa kofar. A zatonta asabe ce ta dawo kwashe kayan data kawo dan haka tace "Shigo" Tura qofar yai tana kwance da wayarta a hannu ta dago. Saurin sadda kanta qasa tayi tana ci gaba da danna wayarta. Wannan nataccen nema sai dai ya gaji da tsayuwarsa a wajen ya shigo ko ya koma. Chatting din da take da ammar ya fiye mata komai na gidan nan. Shi kullum yaita fama da kaya kaman wani dan sarki. Duk da tsanarsa da tai baya hana mayyar zuciyarta ganin yayi kyau. "Ki fito mu tafi." Ya fada cikin wannan muryar tasa ta yanga. Sai lokacin ta tuna yaune yace mata zasu tafi abuja. A kasalance tace "ba zani ba aina fada maka" Wani abu yaji ya tsaya masa a wuya. Inda ba.ai masa umarnin ya tafi da itaba sai dai kawai taga bata ganinsa. Zuciyarsa ta dibe shi ta watsa wani lokaci can baya. **** **** "Yayana ni fa saina bika......yai dariyarsa "huddy kiyi haquri ba dadewa zanyi ba kwana uku kawai Kuma zamuyi waya" Ta sake goge hawayen dake bin fuskarta "bana so kanamin nisa." Sauke numfashi yai "huddy ke kinmin nisa ai" ya fadi a zuciyar tasa. A fili kuma yace "banson jan magana ko bacin rai. Umarni ne na cewar na tafi dake.Ki shirya nan da 15 minutes. I don't want to drag you myself, don't tempt me " Ganin bata da niyyar cewa komai yasa shi ficewa. Ita yanzun kam me zai bata mata rai bayan tana manne da ammar a whatsapp....wuni suke hira ko yana office ma haka da dare suna manne yana rikitata da voice notes dinsa. Da batai niyyar shiryawa ba sai wata zuciyar tace yanzun in ma baki tashi ba dawowa zaiyi. Kuma ta tabbata tsaf zai aikata abinda ya fada. Maganar ma da take yi dashi lokacinta take bashi. Tashi tayi ta sake kayan jikinta. Wani karamun akwati ta dauka badan tasan menene a cikin shi ba. Gara ma ta bishi abuja din dan ya sake tabbatar da baya gabanta. Mayafi kawai ta dora kan kayan jikinta taja akwatinta zuwa falo...inda wata daga cikin masu aikin tai saurin zuwa ta karbar mata. Fita akai dashi. Natacce ne ya fito daga side dinsa sanye da alkyabba ruwan hanta mai cizawa da wata irin hula akansa. Bata so ta tsaya zuciarta ta misalta mata kyawunsa. "Ungo" ya fadi.....hannunsa ta kalla daya miqo mata batare data yarda ta kalli fuskarsa ba. Alkyabba ce mai kalar tasa sai dai wannan akwai ado na mata a jikinta. "Ki saka saboda zamu fara biyawa ta gida sannan mu wuce." Karba kawai tayi. Bata son magana mai tsaho na hadasu inba dole ba. Tanajin idanuwansa na binta har ta saka ba tare data kalle shi ba tace "muje" Gaba daya kamshinsa ne cike da alkyabbar jikinta. Ta kuma tsani yanda hancinta ke jin dadin kamshin. Gaba ya shiga ta bishi a baya har zuwa wajen motar (Range Rover) wata fara mai kyau. Bude musu akai ta shiga shima ya shiga baya. Har suka isa gidan babu wanda yacewa kowa komai. Ita tana ta chatting da ammar abinta. Dan haka bata kula da komai ba sai tsayuwar motar data ji. Aka zo aka bude musu qofa suka fito. Ya zo kusa da ita ya tsaya. "Na iya lokacin da zamuyi a cikin gidan nan kiyi pretending komai normal ne a tsakaninmu." Ya fada cikin muryar da takanji yaima yan aiki. Cike da mamaki ta kalle shi. Bata dai bashi amsa ba duk inda yai nan take binsa suna tafiya. Tana kallon yanda mutanen cikin gida suke tsugunnawa tun kamin ya qaraso inda suke suna gaishe dashi amman ko kallon arziqi balle taji ya amsa. "Ana gaishe dakai ko baka ji?" Ta buqata. Bai bata amsa ba.. Taji haushin kanta ma datai masa magana. Wani irin daki suka shiga da saita wuni a tsaye a wajen bata gama qarema kyawunsa kallo ba. Ya zauna kan daya daga cikin manyan kujerun dakin. "Ki zauna" ya furta a hankali yana nuna mata waje a kusa dashi. Bata musa ba ta zauna. Wata kyakkyawar mata ce magidanciya ta shigo dakin cikin shiga ta alfarma. Sai taga matar ta mata wani irin kwarjini. Kasa taga ya sakko ya tsugunna itama bata san lokacin databi yanda yai ba. Saida matar ta zauna tukunna ya gaishe da ita cike da girmamawa...itama gaishe tan tayi....da fara.a ta amsa musu sannan taga ya koma kan kujerar ya zauna...itama tayi hakan. "Babana an shirya kenan?" Ta buqata. Cikin tausasawar murya yace "yanzun zamu wuce nace saimun biyo ta nan mun gaishe dake." "Aikam ka kyauta sosai ba zaka je da ita taci wani abu ba kuma kudan zagaya ciki?" "Uhm uhm umma sai dai ko inmun dawo muna sauri ne kinsan ba jirgi zamu bi ba" ya fada yana miqewa.. Saita tsinci kanta da sake tsugunnawa tace mata mun tafi. Addu.a tai musu sosai. Kamun su kama hanya su fita. Motar suka koma. Daga su sai driver din. Tun dazun take mamakin yanda cikin motar yake. Ba ta inda driver din zaiga me sukeyi saboda akwai barrier a tsakaninsu. Hannu prince ishaq yakai ya taba goshinta. Ya sake taba kumatunta sanna ya koma cikin kujerar ya zauna sosai. Husna kam batai mamaki ba. Kadan da aikin wannan bakin nataccen. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣5⃣ *I am sorry for the delay. Thank you for reading. May Allah's blessing be with you all. Amin Ya Rabb* IPhone din shin ya dauko ya saka headphones yana sauraran wakokin larabci na Rashid Al Majeed. Ita kam husna suna hira ne da ammar sai dai idan network ya dauke ta tsaya saiya dawo. Can yace "Tawan me kike yine haka?? "Muna hanyar abuja" Ta bashi amsa. "Abuja???" Ya rubuto da alamar tambaya. Tasan mugun kishi irin na ammar koda yaushe saiya tambaya ko natacce yana da kyau tace masa mummuna ne shisa ta kara tsanarsa. Shirun dayaga tayine batai reply ba yasa yace "ke dawa zaku je abuja? Kuma me zaku yi?" "Nima ban saniba ammar haka yace mu tafi ta bashi amsa." Yafi mintina goma bai bata amsa ba sannan yace "husna dan Allah karki bari ya tabamin ke kar ki so shi....ki taimakamin ki kashe auren nan." Wasu hawaye taji zasu xubo na tausaya musu. Hannunta na rawa ta rubuta masa "yanda bana sonshi shima haka bazaimin komai ba...kayi haquri saina kashe auren nan munyi rayuwarmu." "Zanso kina kusa dani yanzun zanyi shirune ina kallon kyawun idanunki masu nutsar dani cikin wani yanayi." Ya rubuto. Ta sauke ajiyar zuciya,yama zata fara zaman aure da wani ba ammar dinta ba mai nuna mata soyayyarsa. Battery dinsa ne ya dauke. Don haka ta sauka akan whatsapp din tana nazarin yanayi na hanyar abuja dan bata taba zuwa ba. Jingina tai da kujerar. A hankali ta juya kanta ta kalli natacce. Ya lumshe idanuwan shi da alama bacci yake. Taja dan karamin tsaki a zuciyarta tana fadin bacci da headphones. Batasan me yasa take jin inta bar masa bata kyauta ba. Hannu tasa ta dauki wayar da take ajiye kan cinyarshi. Yana jinta saboda ba bacci yake yi ba. Ta dauki wayar tana swiping dayake ba password ta bude. Pause ta sakama wakar da yake ji ta ajiye masa wayar inda taganta. Bude idanuwansa yai ya juyo inda take, a kasalance yace. "Saboda me zaki tsayarmun da waka?" Shegen shisshigina mana ta fada a zuciyarta. A fili kuma shiru tai ta kyale shi. Dan bata da abinda zatace masa. Kunnawa yai ya sake komawa yanda yake. Itama shirun tai batama san sanda bacci ya dauke ta ba. Jiyai ta kwanto masa kan kafada. Ya bude idanuwanshi, daman yasan wannan natacciyar kaya zata bala.in zame masa. Kamata yai a hankali ya kwanto da ita kan cinyarshi dan yanayin yanda take yana ganin jikinta zai iya ciwo in ta jima a hakan. Kallonta yake da wani yanayiba zuciyar shi da baigane ba. Kawai kuma ya basar. Gajiya yai shima yaso ya zame kujerar yadan kwanta sai dai bayason motsa wannan natacciyar. Yanda bayason a tashe shi in yana bacci haka bayason ya tashi wani. Saman kafadarta ya dora hannayensa ya dora kanshi. Shima baccin ya dauke shi. * Husna tana bude idanuwanta kamshin shi ya cika kata hanci. Abu taji a kafadarta. Takuma ji dumi sosai inda take kwance. Sai lokacin ta kula da yanayin da suke. Kawai sai taji kasala ta saukar mata. Motsin datai ne ya sashi bude idanuwansa. Muryarshi da take a bude ta sake zama wata babba saboda baccin daya tashi. "Dagani to, tunda kin tashi" Ya fada. Lallai ma husna ta fada a ranta. Shima fa a jikinta yake kwance dan rainin hankali zaice ta wani daga shi. Ita bama tasan me take kan cinyarshi ba bayan alkawarin datai ma ammar dinta. A kufule tace. "Ka dagani tukunna" Murmushi ya kwace masa. Tashi yai daga kafadarta. Ya zuba mata idanuwansa da bata so saboda yanda suke saka ta ji. Gefe ta matsa ta wani daure fuska har taso ta bashi dariya ma. Kujerar ya saukar ya kishingida sosai ya koma baccin shi. Husna ma rakubewa tai can gefe ta koma bacci. Bata tashi ba sai da suka karasa cikin garin abuja. Ta glass din motar take kallo tana yaba kyawun garin. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣6⃣ Yanayin tsari na garin abuja ya burgeta matuqa. Zataso ace da ammar dintane sukazo dataji dadin zuwan. Bude musu mota akai. Tana fitowa takalli yanayin ginin gidan batasan "wow" ta subuce mata ba. Zagayawa tai dan zatonta zaa bude bayan motar ne su dauki kayansu. Ganin ta tsaya yasa shi fadin "Muje mana" "Zan dauki kayana ne" ta bukata tana masa kallon da yake fassara wannan wacce irin tambaya ce? Kallonta yai sosai kamun yace. "Muje za.a shigo maki dashi" Ganin ya wuce abinsa yasa tabi bayanshi Tsakiyar wani qayataccen falo suka isa. "Za.a nuna miki bangarenki. Inkina buqatar wani abu hadiman gidan zasuyi miki" Ya fada mata. Bai jira amsarta ba ya wuce. Wata ce tazo ta rakata har bangarenta. Wajen ya hadu dan duk tsanar mammalakin gidan datai bai sa yaqi burgeta ba. Wanka tayi dan tagaji sosai tunda bata samu tsarki ba balle tace zatai sallah. Ta duba wayarta ammar bai dawo online ba har lokacin. Ta soma kewarshi. Tunawa tai ashe fa kausar na abuja. Wani murmushi ya qwace mata. Wayarta ta dauka ta kirata. Bayan sun gama gaisawa tace "Ke er uwa ina abuja fa" "Wooo bani address zan shigo gobe in shaa Allahu" kausar ta fadi cike da farin ciki. "Ta dora da meye sirrin? Rabon da inji muryarki haka harna manta husna." Dariya tai tace "kausar kin cika zolaya akwai labari saikin shigo ke dai" "Ba damuwa kimin text din address din fa karki manta." "Zan miki yanzun in shaa Allah." Husna ta fadi. "Tam ina jira" kausar ta ce sukai sallama. Ajiyar zuciya ta sauke. Yunwa takeji dan haka ta yanke shawarar sauka qasa ta tambayi address din gidan nan ta tura ma kausar. Daya daga cikin hadiman gidan ta tambaya suka fada mata. Zuwa tai inda aka shirya musu abinci taci wanda yai mata. Bataga natacce ba baya gabanta kuma. Ba.a shigo mata da akwatinta ba tun dazun dan kayan jikinta ta mayar. Ta tsani yanda kamshin nataccen nan yake manne dasu. Sama ta koma tai kwanciyarta dan ammar ya dawo online. Hira sukai tayi bata sake fitowa ba har qarfe goma na dare. Tasan Ammar ya tafi kallon ball yace mata suna da wasa. Ko ya dawo ma ita dai bai kirata ba kuma bata neme shi ba. Duk da gajiyar dake jikinta baisa bacci yazo mata ba. Fitowa tai daga dakin baccin zuwa qayataccen falon dake saman nasu. T.V ta kunna. Channel din yana kan star movies. Bata canza ba dan tasan suna saka films masu kyau sosai. Wani horror ne mai tashin hankali. A tsorace take kallon amman ta kasa tashi ta sauya tashar ko ta kashe. Lokacin da suka gama sha biyu saura. Sai yanzun take dana sanin kashe qwayayen wajen da tayi dan ta dauka ba zata ma fito ba. Ga gidan yayi wani shiru musamman data kashe t.v din. Sanyin AC bai hanata jin zufa ba. A hankali take tafiya zuwa dakinta. Wani abu taji taci karo dashi ta saki wata irin giggitacciyar qara. * Sai juyi yake kan tanqamemen gadonsa ya kasa bacci. Dan yanzun wahala yake masa tunani baya barinsa bacci. Nas ya kira yaji lafiyarsa sukaita hira. Yana fada masa ya shirya fa dan suprised din da zai masa ya kusa. Dariya yai duk da sautinta ne kawai yakan fita ya manta yanda launinta yake a xuci. Sukai sallama. Fridge din dakinsa ya bude duk apple din daya samu ciki ya cinye shi dan yau babu komai cikinsa sai shi. Fitowa yai ya dibi wasu dan dare yayi balle ya sa akawo masa. Mamaki ya cika shi ganin duk an kashe wutacen lungun. Yama manta natacciya tana rayuwarsa ma gabaki daya balle kuma a gidan. Tafiya yake dan ya lalubo switch din ya kunna. Yaji wani abu ya kawo masa karo kuma an saki qara. Tamkar wanda aka dauka aka watsa duniyar tunani zuciyarsa ta budo masa wani yanayi: **** **** Ta baya ya lallabo ganin bataji tafiyarsa ba. A hankali yasa hannu yaja jelar kitsonta guda daya data sauka har gadon bayanta. Wata qara ta saki a razane hadi da juyowa. Shi kansa ta bashi tsoron riqeta yai dam a faffadan qirjinsa yana shafa bayanta. "Huddyna kin cika tsoro daga tsokana." Cikin tabararta tace "Yayana kaban tsoro sosai." * Iya tsoro kam husna ta tsorata numfashinta har barazanar daukewa yake yi. Rungumeta taji anyi cikin wani faffadan qirji. Qamshinsa taji tasan shine. Natacce ne ya tsoratata haka. Kanta yake shafawa "huddyna kin cika tsoro daga tsokana." Ya fada batare daya sani ba. "Huddy?" Ta nanata a zuciyarta. "Ammar" zuciyarta ta sake furta mata. Idanuwansa a rufe suke yanajin duminta dan singlet ce kawai a jikinsa da boxers. Sai dai akwai wani abu daya banbanta. Wannan ba kalar turaren huddy bane. Jin an ture shi yasa zuciyarsa ta sake shi daga duniyar tunanin data watsa shi. "Ya salam" ya furta dai-dai lokacin data kunna hasken wajen. Idanunta ta sauke cikin nashi. Da gudy tabar wajen. Dafe kai yai? Why? Meyasa zuciyarsa take masa haka ne? Saboda me zata dinga kaishi irin wannan wajajen dai-dai lokuttan da qaddara zata jeho masa natacciyar yarinyar nan. Jikinsa ya hada da nata duk da yana qaryata cewar yaji wani abu. Amman abinda ya qona masa rai ba damuwa dayai da natacciya ba son ganinsa da batayi. Sai kace wani dodo ko wanda yake da abin qi a jikinsa. Jibi yanzun tana kunna hasken wajen suka hada ido sai tayi tamkar wadda tai kuskuren kallonshi tabar wajen. Fasa daukar apple din yai ya koma daki ya kwata kawai. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣7⃣ Husna kam dakinta ta koma. Kuka take sosai. Ya zatai ma ammar haka? Wannan cin amana ne. Tunda tasan natacce ne. Kamshin shi kawai taji tasan shine. Bata manta yanayin qamshinsa ba tabari ya rungumeta a qirjinsa. Yanayin rungumar dayai mata batasan ya zata fassara shi ba. Tanajin sawun hannuwanshi akan bayanta har yanzun. Tana jin dumin jikinsa gauraye da nata. Da sauri ta miqe ta shiga toilet. Bathtub ta shiga bayan ta cika shi da ruwa. Soso da sabulu tasa ta durje ko ina na jikinta har ya soma radadi ko zata wanke abinda take ji. Sai dai ga mamakinta yanayine daya samu waje daram cikin zuciyarta bawai iya jikinta bane. Da ace zuciyar nan zata ciru. Data fito da ita ta wanke ta tas. Ta goge ko menene ya dasa mata a ciki. Saboda bata son shi sam. Tai kuka harta gaji. Tunawa tai wayarta a silent take da sauri ta janyota. Missed calls na ammar har 26. Text messages guda 10. Maganar dayai mata a whatsapp 53. Tana cikin dubawane kiransa ya sake shigowa. Da sauri ta dauka "Nawan" Wani nannauyan numfashi ya sauke da har taji ta cikin wayar. "Ina kika shiga haka?" Ta tsani kanta ta tsani qaryar da bakinta yake shirin furta masa. "Bacci ne ya daukeni nawan wayar na silent yanzun na farka naga kana kira." Ta karasa maganar cikin sanyin murya. "Wlh naji tsoro sosai babyna babu tunanin da baizomin ba. Gashi kincemin kin bishi abuja. Husna mutuwa zanyi idan na rasa ki. In ya tabamin ke zuciyata fashewa zatayi wlh kishi kasheni zai husna" Ya qarasa muryarsa na rawa. Hawayen dake bin fuskarta ta goge cike da tausaya mishi. Dayasan abinda ta bari ya faru yanzun........ Da sauri tace "kana karyamin zuciya in kana tunanin zan hada shimfida da mutumin dana tsana. Ni taka ce nawan. Kai kadai bazan taba hada maka jiki da wani ba gara an dauki gawata da hakan ya faru." "Hmm husna ba zaki gane me zuciyata takeji ba inba kashe auren nan kikayi ba naga kin zama tawa tunani kawai zai iya kassarani." Sun jima suna waya kamin suyi sallama. Washe gari tana yin sallar asuba ta koma bacci danko wanka batai ba. Baccin ne a idanuwanta sosai. Wayar kausar ta tasheta wajen goma da yan mintina. Ta fada mata tana hanya. Wanka tayi ta shirya kanta cikin doguwar riga simple ta sakko qasa ta zauna. Hadiman gidan ta fadama tana da baquwa su shirya mata wajen cin abinci na falon sama. Kausar na sallama ta tashi da gudu taje ta ruqunqumeta tana tsalle tsalle. Dariya take sosai "yau mun banu husna kaman wata yarinya." Dai-dai lokacin da prince ishaq ya sakko daga benen. Kausar ta ganshi ita kam husna tsalle tsallenta take yi. * Tunda ya fara sakkowa yake jin dariya da tsalle tsallen husna. Kallonsu yake da mamaki a tsahon ganin da yake mata ko murmushinta bai taba gani ba. Kullum fuskarta kaman zata saka mishi kuka. Sai kuma hawayen tan nan da baya so. Inta fara zubo dasu har wani ciwon kai yake shirin kamashi saboda dagula masa lissafi take. Sai yau tana ta dariya. Baisan murmushi ya qwace masa ba ma. Sai yaga ta qara kyau. Ohh ya fada a zuciyarsa yarinyar da ta tsane shi ya zauna yana ganin ta qara kyau kenan ma ya lura tana dashi. Kauda kansa yai. Muryar kausar qasa qasa tace "dan ubanki ki nutsu." "Wai me kike kallo husna ta fadi tana juya." Lokaci daya fara.ar da take fuskarta ta dauke. Tsikar jikinta ta wani tashi duk da ta janye idanuwanta daga fuskarsa zuwa qirjinsa. Yanayin dumin qirjin ya fado mata a zuciya ta girgiza kai tamkar tana so ta batar da abin ta hakan. Hannun kausar ta damqa da niyyar janta suhau sama ganin natacce ya nufo inda suke. Amman taqi. Cikin qasaita ya iso inda suke. Murmushi ya dora a fuskarsa. Cike da girmamawa kausar tace masa "barka da warhaka." "Barkanki" ya amsa yana dorawa da. "Mungode da ziyara" Murmushi kausar tayi tace. "Bakomai Allah ya kara girma" Kai kawai ya daga mata ya wuce abin shi. Husna ta jata suka wuce suma. Kan hanya taketa faman masifa "meye na wani gaishe dashi harda girmamawa. Ai wlh kin bani haushi ba kadan ba.A hakan ma sai uban yangar tsiya" Shiru kausar tai mata saida suka sami waje suka zauna sannan tace "husna kinsan ko waye shi din? Naga alama baki sani ba koh?" "Kinga nifa baya gabana asalima ke nake jira kizo kiban shawarar yanda zan kashe auren nan. Ammar ya dawo." Sakin baki kausar tai tana kallonta. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣8⃣ To dimples group. "Ba canai ki tsaya kina min wannan kallon kaman na samu haukaba nace miki ammar ya dawo yanzun haka ko yau da safe munyi waya dashi." Husna ta fada tana kallon kausar cikin fuska. Girgizata kausar tai tace "Husna kina da hankali a jikinki kuwa? Kin manta kalar tashin hankali da muka shigane? Tabbas kin manta da har kike son mayar damu." Ganin tayi shiru tana wani kumbura fuska yasa kausar ci gaba da fadin "da aurenki kike waya da gardi???" Cikin bacin rai husna tace "karki sake kiranshi da gardi. Bana qaunar mutumin nan ko na qaramin lokaci. Idan na zauna dashi son ammar kasheni zaiyi. Na tsane shi kausar dole ne na rabu dashi na auri wanda zuciyata take muradi." Husna ta karasa tana goge hawayen da suka taru a idanuwanta. Girgiza kai kausar take cikin tashin hankali: "kin samu tabin kwakwalwa. Kuma kina gab da saka ammar da duk masu sonshi cikin tashin hankali da rudu. Husna kinsan wa kike aure?" Ta qarasa maganar cikin rawar murya. A zuciya husna tace wai natacce din nan waye shine? Fine a yanzun tasan yanada alaka da sarauta ko dan cikin gidansu data gani. Saidai bai dameta ba. Tunaninta bai taba je mata wajem bama. A fili kuwa girgiza mata kai tayi alamar a.a. "Prince ishaq" kausar ta fadi tana ci gaba, "dan sarki kabeer. Wanda yake jiran gadon mulkin garin kano.Husna zaki jefa rayuwar ammar cikin garari inhar ya gane abinda kike. Meyasa ba zaki haqura da ammar bane ki zauna gidan aurenki? Ba kowacce qaddara ake sauyawa ba." Wata irin dokawa zuciyarta take. Idanuwanta cike taf da hawaye tace "kausar ki taimakamin wlh bazan iya haqura da ammar ba. Nayi qoqarin hakan na kasa." Hannunta ta riqe tana fadin "husna babu yanda zamuyi da Hukuncin Ubangiji, ammar ba mijinki bane." Fisge hannunta tai a zuci tana fadin babu wanda ya isa ya rabani da ammar ko sarkin ne ma da kanshi ballantana dansa.Saina kashe auren nan ko ta yaya. A fili kuwa ta goge fuskarta tace Allah yai mana jagora mubar maganar nan kausar sai wani lokacin. Tashi muje ko breakfast banyi ba. "Hmm mudai je nikam a qoshe nake." * Kausar ta wuni gidan. Da zata tafi ma ta sake ma husna kashe di. "Kinga ki rufa mana asiri husna. Har yanzun su abba basu gama hucewa dake ba. Karki jawo wata sabuwar matsalar" Fuska babu walwala husna tace. "Nafa jiki da kyau. Yanzun yaushe zaki kara dawowa? Ko nice zanzo?" Fito da idanuwa kausar tai tace. "Rufamun asiri. Ni yar ubana. Duka satinki nawa da aure daza ki soma yawo. Zan dawo in shaa Allah" Dariya husna tai tace. "Yasan da hakan ya jajibo ni har abuja" Girgiza kai kawai kausar tai ta wuce tana fadin. "Sai munyi waya" * Falon kasa tai zamanta tana ta kallo. Kamun daga bisani ammar yazo online su sha hirarsu. ** Satinsu uku kenan abuja. Husna zata iya cewa tun ranar da sukai karo da natacce. Magana bata sake hadasu ba. Zasu hadu ko a falon sama. Ko na kasa tana zaune. Ko wajen cin abinci. Tun satun da sukazo sau uku a haduwar da sukai zai taba fuskarta da goshinta yaji ko da zazzabi. Badai magana yake mata ba. Wasu lokuttan idan yazo ya ganta a zaune babban falo shima zai zauna. Sai dai taji idanuwansa na mata yawo alamar yana kallonta. * Prince ishaq kam hidimomin shi kawai yake. Yanajin dadin yanda natacciyar can bata damun shi. Bata zame masa kaya ba kaman yanda yake zato. Asalima ya sake kula haduwarsu sai dole. Kawai dai bashida lokacin batawa ne akanta a yanzun. Amman daya dan samu time dole in yana waje ta dinga kallon shi indai tana son zaman lafiya. Badon ya damu da ita bane. Aa kawai ya damu da ta girmama shine bai kuma son dalili ba. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 1⃣9⃣ This is for you Namesake(iLubiee). Thank you for the support and encouragement. May Allah bless you. Tunani yake in ya tafi har kano bai fada ma natacciya ba sam bai kyauta ba. Yasan ba magana take hadasu ba sam. Amman duk da hakan baya son rashin adalci. Beside zai fada matane kawai ko da wani abu ya faru. Tashi yai daga kwanciyar da yake ya fito. Ya koyi sa.a ta rage masa wahalar zuwa bedroom dinta dan tana zaune falon su na sama tana kallo. Gidan ba kaman na kano ba. Da kowa yake da part din shi. Duk da nan dinma dai part dinsu daban amman falo ya hadasu. Sallama yai mata. Yana neman waje kusa da ita ya zauna. * Kamshin shi kawai husna taji tasan ya nufota. Ta lumshe idanuwanta ta budesu a hankali. Batason fitina da yammacin nan. Cikin sanyin murya ta amsa sallamar shi hankalinta na kan t.v. Remote ya dauka da yake kan Centre table din wajen ya kashe kallon da take. Hakan yasa ta fuskantarshi. Idanuwanta a kasa. Shisa bayason mata magana sai dole. Bayason yanda take yin kaman bata son ganin shi. Kaman wata kazanta ce a jikin shi. A nutse yace. "Zanje kano gobe in Allah ya kaimu. But ba dadewa zan ba. Kwana uku zuwa hudu" Shiru tai ta kyale shi dan bataga dalilin da zaisa ya fada mata ba. Asalima taga zuwan shi kano ba damuwarta bane. Ba magana suke ba. Saitai kwana biyunma bata saka shi a idonta. To wacce gulmar zata kwaso kafafunsa yanzun? Kilanma da yai shiru har yaje ya dawo ba kula zatai ba. Bama ta damu ba. * Abu na farko da ya tsana shine yai magana ai shiru. Dafe kanshi yai na yan dakikai. Ranshi ya soma baci. Bayason yanda take bata masa rai sam. Muryarshi a dake yace. "Magana nake miki" Kaman wadda akaima dole tace. "Naji ka" Mikewa yai kawai ya nufi bangaren sa. Dan inya biye ta natacciyar nan zai yi abinda zaizo daga baya yana dana sani. Saboda tagama kure hakurin shi. * Wani karamun tsaki taja ta dauki remote ta kunna kallonta. Share bangaren zuciyarta tayi dake mata fadan cewar ko yankar naman juna suke da natacce dayazo yace mata zai tafiya tai masa addu.a "Allah ya tsare hanya" ta fada a hankali dan tasan ba zata zauna lafiya da zuciyarta ba inhar bata fada ba. Zatai tajin wani irine tunda ba sabawa tai ba. * Tun da yai asuba baima koma bacci ba. Dan jirgin karfe 9 na safe zaibi zuwa kano. Bayason ya kwanta baccin bai gama isarshi ba yai ciwon kai. Tun takwas yagama shiri. Babu wasu kaya dazai dauka. Dagashi sai I.D card sai wayoyi. Driver ya dauke shi daga gidan zuwa Airport. Headphones ne a kunnuwanshi yana sauraren karatun Qur.an. Jiyai kaman driver din na magana kasancewar bai kure maganar ba. Ya saka pause ya zare daga kunnuwanshi yace. "Magana kake?" A tsorace yace. "Rankai dade kamar ana binmu ne. Tunda muka fito gida wannan motocin ukku suke biye damu" Tunda driver din ya soma magana zuciyar prince ishaq ke dokawa. Yasan ba karamar wauta yai ba fitowa babu security. A nashi zaton duk wannan zai kara janyo hankalinsu ne. Bai zata sun biyo shi abuja ba. Addu.o.in tsari ya shiga karantowa dan yadan samu nutsuwa. "Kaci gaba da tuki. Karkai gudu" Ya fada a hankali. Wayarshi ya dauka ya kira kamala. "Muna hanyan airport akwai motoci uku suna binmu. Do what you can and make it snappy" Kamala baima amsa shi ba ya kashe wayar. Ko mintina biyar ba aiba tsakani suka soma jin jiniyar motar yan sanda. Cikin rawar murya driver din yace. "Rankai dade sun sha U-turn" Wata ajiyar zuciya ya sauke. Mutanen nan so suke suga bayansa. Har airport yan sandan suka rakasu. Tukunna. Text ya turama umman shi saboda ya tabbata abinda ya faru a abuja dan kadanne da abinda zai iya faruwa a kano. * Wayar ammar ta tasheta daga bacci. Muryarta can kasa tace. "Hello" Dariya ya kama yi mata. "Tawan koma baccinki" Kamun ta amsa ya kashe wayar. Kwanciya tai shiru dan inta tashi bacci takan dade batai magana ba. Sai da ta wartsake sannan ta tashi. Brush kawai ta sake yi dan tai wanka tun da asuba. Kawai sai take jin mugun kewar yan gidansu. Duk da babu wanda ya kirata har yanzun. Ta kuma son fushin suke basu huce ba. Bayan ita akaima rashin kyautawa aka liqa mata nataccen can da bata so. Wayarta ta dauka ta kira maheer kaninta. Wayarshi a kashe. Ta tuna safiya ce kuma ranar laraba. Yana makaranta. Dining ta nufa ta ci dankali da kwai ta koshi abinta ta koma falo ta zauna. Batasan gulmar datai zuciyarta tunanin ko natacce ya sauka lafiya ba. Kallo ta kunna dan bata son yanda yai mata katsalandan cikin tunani. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣0⃣ To a young girl i have never known and will never get to know. May your gentle soul rest in peace. May Allah grant you endless peace.(XeeXee) Allah ka yafe mana ka jikanmu da Rahmarka(Amin thumma amin) Kwanan shi biyu kano yagama abinda zaiyi. Jirgin yamma yabi zuwa abuja. A falo ya zauna. Sai lokacin duk gajiyar daya kwaso take tambayarshi. Ya sake gyara zama cikin kujerar yana lumshe idanuwansa. Magrib kawai yake jira tayi yai sallah yadan kwanta. * Husna kam tana son fita sosai. Danma ta kira kausar ta kawo mata kayan sawa. Akwatin data dauko shirmene kawai cikinsa. English wears ne da bata tunanin zata iya saka su tsautsayi ya gifta natacce yaganta cikinsu. Sai fama take da alkyabba kullum. Data sakasu saita dora dan ta rufe mata jiki indai zata fito falo. Sai hijab dinta ta sallah. Tasan da wahalar gaske abarta ta fita. Bama tason zubda aji shisa sam bata gwada ba. Zata jira sai ta hadu da natacce inya dawo kenan. Ta sauke ajinta a gefe tai masa magana ko dogayen riguna ne ta fita ta siyo tunda da yan kudinta a hannu taba kausar ATM ta ciro mata. Falo ta fito. Kamshin shi ta fara ji kamun taganshi. Zuciyarta ta wani doka. Hannu tasa kan kirjinta tana so ko bugun da zuciyarta yake zai dan dai-dai ta amman a banza. Kafarta har wani rawa take abin takaici. Karasawa tai inda yake da sallama. Idanuwan shi ya bude ya sauke su akanta da doguwar hijab sanye jikinta har kasa. Amsa mata sallamar yai a kasalance. Sai taji muryarshi ta kara budewa. Bata son yana mata magana saboda tayar mata da tsikar jiki yake. Tana son taji muryar namiji babba haka. Saidai ammar dinta muryarshi yar karama ce. Da sauri kamun kwarjinin dayai mata yasata kasa tambaya tace. "Ina son fita zan siyayyar kaya" Idanuwan shi kawai ya zuba mata. Babu yanda za.ai ta fita saboda yanayin tsaro. Banda kamala babu wanda ya aminta dashi cikin gida. Kudi zai iya siyan kowa yaci amanarsu. Baya son karin matsala. Ko dan darajar auren da aka liqa masa na natacciya. Tana karkashin kulawar shi. Bazai bari komai ya samu yar mutane ba. * Husna kam harta kawo iya wuya. Dole ce tasa ta tambaye shi ya zuba mata idanuwansa yana kallonta. A dakile tace. "Magana fa nake maka" Idanuwan dai su ya zuba mata. Ya gaji sosai. Idan yagaji baya son surutu. Wannan yarinyar bata ganewa ne. Ta kyale shi baya son naci. Yana kallo ta tashi tabar wajen. Ya maida kanshi ya kwantar jikin kujera ya lumshe idanuwanshi. Yana zaune a wajen har aka kira sallar magrib ya tashi yaje yai sallah. A masallacin cikin gidan yai zaman shi. Sai da yai sallar isha.i tukunna ya koma cikin gida. Apple ya diba a dining din dake cikin falon ya wuce dakin shi ya ajiye su kan gado. Jikin shi duk ciwo yakr mishi. Wanka yai sannan ya kwanta. Yana gama addu.a bacci ya dauke shi ko apple dinma bai ci ba. * Wasu hawaye masu dumi ta goge. Dan taje wajen shi ta tambayi alfarma ne zaisa ya wulakantata. Zata hakura tai amfani da kayan da take dasu. Inyaso ta kira kausar taji yaushe zata sake shigowa sai ta sissiyo mata. Wayar da sukai da ammar ne ma ya rage mata bacin ran da take ciki. * Washe gari da safe tun da ta gama baccinta ta tashi wajen goma. Sai da tai wanka sannan tasa aka kawo mata brkfst har daki. Batason fita taga nataccen nan ya sake wulakantata kaman jiya. * Duk da wankan dayai gajiyar jiya bata gama sakin sa ba. Shadda ce a jikin shi dinkin kaftan. Ruwan toka da hula mai cizawa kalar aikin jikin shaddar takalminsa ma haka. Bai manta da abinda natacciya ta tambaya ba jiya. Maganar ce baiga damar yi mata ba saboda yagaji. Bangarenta ya karasa. Ya kwankwasa kofar tace ya shigo. * Abinda take ci taji ya tsaya mata a wuya. Bata zata shi bane. Ca take ma daya daga cikin hadiman gidan ne. Hijab din da take gefe tai saurin dauka ta saka. Kallonta yake yi. Taso tabashi dariya ma. Kome take boye mishi oho. Gefen gadon ya zauna ya mika mata dan notebook karami da biro. Bai jira ta karba bama ya ajiye akan gadon kusa da ita. Kanta a kasa dan bata son idanuwanshi cikin nata. "Ki rubuta abinda kike so. Da sizes za.a kawo maki. You can't go out a yanzun" Yai maganar a nutse. Yama raina mata hankali. Wato sai yanzun yaga dama. Muryarta can kasan makoshi tace. "Kabarshi kawai na fasa" Hannu yasa ya dago mata da haba. Bayason yanda bata iya kallon shi tai masa magana. Ture hannun shi tai kanta na kasa. Tanajin hawayen da suka cika mata ido. Bata son yanda zuciyarta ke saurin karaya a gabanshi. Sake dago mata da haba yai. Wannan karon data kawo hannu ya ture nashi yasa dayan hannunshi ya rike nata gam. "Bana son gaddama. Ki kalle ni kimun magana. And ba tambayarki nai ko zakiyi siyayyar ba. Canai ki rubuta. Akwai bambanci tsakanin biyun" Bata yi kokarin kwace hannunta ba saboda rikon dayai mata bana wasa bane. Muryarta na rawa tace. "Ka sakeni in rubuta" Sakinta yai. Wannan yanayin irin na rannan dabai san fassarar shi ba yake ji. Tafin hannuwan shi ya murza tare yana son ya goge yanayin da yake ji a jikinsu. Bayason tabata. Saidai gaddamarta ce take ja masa wannan wahalar. Yana kallon yanda hannunta ke rawa wajen rubutun. Hakan ya mishi saboda bata da girma da ajin da zata dinga raina shi. Miko masa tai kanta a kasa. Ya tsaya ya zuba mata idanuwa. * Tanajin yanda idanuwansa ke mata yawo ta kuma san abinda yake jira. Dakyar ta dago da kanta ta sauke idanuwanta kan fuskarshi. Ta mika masa littafin da biro din. "Good girl" Ya furta a hankali sannan ya karba ya mike ya fice. Yana ja mata kofar ta diro daga kan gadon. Mukullin tasama kofar jikinta ba inda baya rawa. Ta cire hijab din da kayan jikinta tai toilet. Kwamin wanka ta shiga ta sakarma kanta ruwa. Soso da sabulu ta saka ta dinga gurzar hannunta inda take jin shatin dumin hannun nataccen nan a jiki. Amman a banza tanajin shi har lokacin. Kuka tai mai isarta tana tunanin yanda zata soma bi ta kashe auren nan. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣1⃣ *Rayuwa tana hadaka da mutane da dama. Saidai ko a mafarki ban taba zaton rubutu zai hadani da mutane masu karamci har haka ba.Mutanen da zasu karrama ni. Idan in tsaya lissafo su bansan ta ina zan fara ba.Ummijay da duk yan group dinta. Musamman ita kanta ummin, safiyya galadanchi da anty billy.Dimples da mutanenta. Godiya mai yawa.Anty lubabatu mai tafsir da nata.Musamman ita antin da kanta.Allah ya saka muku da alkhairi.UMMU SABREENA nagode da karamcinki. Wannan page din naki ne* Dakin shi ya koma ya zauna. Saboda yana son duk abinda yake ji yadan tsagaita tukunna. Yakamata ace ya daina taba yarinyar nan. Saidai ita take ja. Hakan ne kawai yake sakata ganin girmanshi. List din ya duba. Riguna ne kawai ta rubuta. Kamala ya kira ya ce masa ya samu wata designer ya tambaye ta tai list na abubuwan da mata suke bukata a turo mishi. Ba afi mintuna goma ba text ya shigo wayarshi. Wani dogon list yagani da karanta shi ma ciwon kaine. Don rabin abubuwa bai san suba. Wasu kuma ana bukatar sizes. Shi bazai iya komawa bangaren yarinyar can ba. Don haka yaima kamala text cewan ya dibi ko nawa yake bukata. A sissiyo kayan su taho da matar ta zabi wanda yai mata a koma da sauran. * Da zundumemiyar hijab dinta ta fita falo ta dibo fruits taji sallama bata mutum daya ba. Haka yasata fitowa daga dining din babu shiri tana amsawa. Hadimaine sunkai shidda da kaya niqi-niqi. Sai wata mata mai matsakaicin shekaru. A ladabce ta gaishe da husna. Ta amsa fuskarta babu yabo ba fallasa. Hadiman suka ajiye kayan husna tace musu zasu iya tafiya. "Ki zauna mana" Husna ta bukata. Da fara.a a fuskar matar tace. "Bama sai na zauna ba. Ki duba kayan nan ki dauki size dinki. Zankoma da sauran" Ta karasa maganar tana ware wasu ledoji. Da mamaki husna ta dauka ta duba. Bra's ne da panties. Ta juya idanuwanta tadan dafe goshi. Har ta bude baki tace bata bukata a mayar ta tuna jan kunnen da natacce yai mata. Ta kuma san tabbas bada wasa yake ba. Dan haka ta duba ta dauki size dinta. "Nagode fa" Tace da matar. "Babu komai. Nabarki lafiya" Ta fadi tana tattara kayan da zata koma dasu ta nufi hanyar benen dan ta sauka. A wajen husna ta tsugunna ta dinga duba kayayyakin. Wasu dogayen riguna data gani sun bala.in burgeta. Gaba daya kayan sunyi kyau. Harda takalma. Flats din kawai ta dauka aka mayar da hill dan ba damunta sukai ba. Gani tai kayan da yawa. Dole ta kira akazo aka daukar mata zuwa bedroom. Wannan karin ba zatai ma kanta karya ba. Kayan sun bala.in burgeta. Harda hijabai aka kawo mata. Taso ta yaba zurfin tunani irin na shi ta fasa. Beside shisshigi yai mata. * Kwanci tashi babu wuya wajen Allah. Haka rayuwar take tafiyar musu. Abin har mamaki yake ba husna. Wai wata na hudu kenan da wannan kadararren auren nata. Zamansun nan yana mata dadi. Balle a satikan nan da zatai kwanaki ko giftawar natacce bata gani ba. Saidai ko in ta fito falo zataji nataccen kamshin shi din nan dayake tsaya mata. Komai na amfani tana dashi. Dan haka bataga amfanin me ganinshi zai mata ba. Sai biyu yazo dakinta. Duk lokuttan yana gaya matane zai je kano. Ta kuma rasa dalilin shi na fada mata hakan. Matsalarta dayace. Ammar ya soma gajiya. Ya soma damunta kan maganar kashe auren nan. Batasan ta ina zata fara ba. Kukantane kawai yake saka shi yai shiru. Banda maheer bata waya da kowa a gidansu. Tayi kewarsu sosai. * Lokutta da dama mantawa yake da natacciyar nan dan abubuwa sun masa yawa. Hidimomin da ya kawoshi garin abuja ya shiga yi. Hakan ya bala.in rage masa tunani har yammaci. A hanyarshi ta dawowa gida yana bayan motar yana tunanin komawarsa. Baisan ko rashin huddy bane yake saka zuciyarsa numfasawa natacciyar yarinyar nan. Yasata yi masa katsalandan cikin tunani. Baya son tuna yanayin dayaji game da ita lokacin da jikinsa ya hadu da nata. Qamshinta. Idanuwanta da suke kallonsa da yanayin tsanarsa da tai. Idanuwanta masu bayyana kome zuciyarta take ji. Har yanzun idan ya tuna sai yaji wani iri. Ya girgiza bai taba ganin tsana da rauni hadi da tsoro irin wanda yagani a idanuwan natacciya ba. Dafe kai yai. Ya Allah! Meke damuna ne haka? Yake tambayar kansa dan yaga daga jiya da daddare zuwa yau gabaki daya zuciyarsa ko ta kawo mishi tunanin huddy zata tattara ta danganto shi da natacciya. Ya rasa wannan naci. Yau yakai kwana hudu bai sata a idon shi ba. Akan me zata dinga cuso masa kai cikin tunani. Wayarshi tahau ringing ya dauka "sweet Qani" yagani a rubuce. Mamaki ya bayyana a fuskarshi. Saboda number din naseer ce ta nigeria. Dauka yai yakara a kunnensa hadi dayin sallama kaman yanda tsarinsa yake. "Yaya ina qofar gidanka!" Naseer ya fadi cike da doki. Murmushi yai. Yakan jima yanzun bai hakan ba har manta kalarsa akan fuskarshi yake. "Qanina babu sanarwa koh?" Dariya yai "Ai nace maka ka shirya zan baka mamaki ko ka manta?" "Hakane harka shiga cikine?" Ya buqata. "Um um yanzun zan shiga wajen antyn nan tawa inga wannan data qoqarta wajen daukemin hankalin yaya." Nas ya fadi cikin siga ta tsokana. "Kai dai bakajin magana zanzo in sameka ne ai." Dariya yake sosai ya furta "Allah ya huci zuciyar sarki ishaq." Baisan lokacin da dariya ta subuce masa ba. Kashe wayarshi yai sai yake jin kaman sabon abu. Ta wani bangaren kuma ya na tunanin kalar tarbar da natacciya zatai ma kaninsa. Kaninsa dayafi so duk cikin gidansu. Dafe kai yai yana sauke wani numfashi. Bayason damuwa sam. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣2⃣ *Kar ka dauka addu.ar da kake bata kaiwa. Karka dauka kai kadai kake cikin kunci a rayuwa. Idan ka samu kaci me kyau ka sha me kyau, me kake nema da rayuwa? Ko kasan akwai wanda idan ya samu yaci sau daya sai kuma washe gari? Ka zamana mai godema Allah. Ka zamana mai wadatar zuci. Alhamdulillah. Allah ka yayema masu damuwa damuwarsu!!!(Amin thumma amin)* Tun dazun da safe da tazo fitowa ta hango natacce da sauri ta koma dan bata son su hadu. Ya bala.in yin kyau cikin fararen kayan daya saka. Komai farine a jikin shi. Bata sake fitowa ba saida tai sallar azahar. Falon saman tai zamanta tana kallo. Pillow din kujerar ta dauka ta gyara ta kwantar da kanta. Kamshin natacce ya cika mata hanci. Da sauri ta zame filon ta cillar kan kujerar dake can nesa da ita. Wani yanayi takeji data kasa fassara shi. Koya maganan natacce ya fado mata sai zuciyarta tayi wata irin dokawa. Kawai kamshin shi dan naci ya tuna yanayin duminsa da maganar shi da komai nashi. Ammar! Ammar kawai! Ammar shi kadai. Haka take ta nanatawa zuciyarta ko zata daina kaita inda bata da buqata ba kuma a buqatarta. Wayarta ta dauka ta duba lokaci.Tai mamakin jan lokaci haka Kusan la.asar sai ta tsinci kanta dayin murmushi ammar ya kusan dawowa aiki. Tana wata irin kewarsa yau. Sallama taji da karfi ana kiran "Anty! Anty!! Gidan ba kowane??? Cike da mamaki ta mike tana sauka benen zuwa falon kasa. Saurayine matashi mai kimanin shekaru sha takwas zuwa sha tara. Duka bazai wuce shekarunta ba ko zata girme shi bazai shige watanni ba. Kallo daya tai masa taga yanayin kama da suke da natacce sosai. Saidai wannan ko hannun rigarsa bai kama ba a kyau. Kyau! Ta nanata, zuciyarta bata ma ammar adalci dahar tama tsaya kula natacce na da kyau. Murmushi yake mata "lallai banga laifin yaya ba" Dariya tai haka kawai taji ya shiga ranta tana son mishi kirki. "Um kaji zolaya. Zuwa babu sanarwa haka?" Ta fadi. Dariya yai shima "Anty afuwa naso in muku bazata ne. Shisa ko yaya ban fadama ba." "Bai jima da fita ba shima ta ce tana qarawa da fatan baka kwaso yunwa ba dan bamu da abincinka gaskia" Zaro idanuwa yai ya dafe qirji da "fadin anty! Ke kin fara sakin na hannuna fa!" Dariya sukai gabaki daya. Sai taji ta duk wani iri duk da dawowar ammar farin cikinta ragagge ne. Amman yaron nan yasataji daban. Da yanayin fara.arsa da wasanninsa. "Bara na kira a shigo maka da kayanka ko" Husna ta bukata. Girgiza kai yai yace. "Suna bangare na ai an shigo dasu" Nas ya fadi yana dorawa da. "Gosh am damn tired. Anty barin watsa ruwa" Kamun husna tace wani abu harya wuce da gudu. Gidan ba baqonsa bane kuma yana da bangarensa a ciki. * Mamaki ya cika husna. Banda falo bama ta taba kula da komai a kasan nan ba. Kodan yaushe ma take zaman kasan. Kullum tana can sama a zaune abunta. Bata son natacce. Amman kaninshi ya mata. Yanayin shiriritarsu iri daya data maheer kaninta. Murmushi tai ya debe mata kewar ganin maheer kadan. * Wanka Nas yai. Ya sake kiran mumyn shi yace mata yana gidan yaya ishaq. Saiya huta sosai zai shigo kano. Mumyn shi bata ma wani damu ba. Tasan tsakanin Nas din da yayanshi sai Allah. Yana iya kwana biyu bai kirata ba ya kira yayanshi. Blue jeans ne a jikinshi matsatse. Sai riga fara kal data kama shi. Fitowa yai ya samu husna zaune a falo tana kallo. Kujerar da take opposite ta husna ya zauna. Ba yanda batayi dashi ba akan yaci wani abu yace mata shi bayajin yunwa. Sunata hira yana bata labarin yan school dinsu. Kalar pranks din da ake playing wa malamai da haukan yan makaranta dai. Zaka rantse sunyi shekara da sanin juna. Kamun daga bisani wani comedy a new world cinema ya dauke musu hankali. Dariya suke tayi ta sha su a gaddama wanda yafi wani shirme cikin yan film din. Sam basuji sallamar prince ishaq ba. Tsayawa yai yana kallonsu. Karo na biyu daya taba ganinta tana dariya haka. Murmushi ya qwace masa dabaisan dalili ba. Qarasawa yai ciki sai lokacin suka ganshi. Kaman qaramin yaro naseer ya ruga da gudu ya ruqunqume yayan nashi. Dariya yake da fadin "Naseeru zaka karyani ne bakasan nagaji ba koh?" Sakin shi nas yai kaman zai kuka yace. "Yaya naseeru fa?" Dariya prince ishaq yai sosai. Yasan ya tsani ace masa naseeru. Kallonsu husna take ya qara kyau dayai dariya. Kaman bashi ba. Sai ta tsincin kanta da son boye halin da suke ciki ita da natacce ko dan yaron nan da taji sunansa a yanzun. Already iya zamansu da bai shige awa daya ba taji kaman ta saba dashi. Duk da hakan bazai hanata kashe auren su da natacce ba. "Sannu da zuwa" Ta furta a hankali. Kallonta kawai yake cike da mamaki saiya tuna nas na wajen dan haka yace "sannunki da gida" Wannan shine magana ta farko da suka fara cikin natsuwa da junansu. Sai takejin daban. Tashi tayi ta basu waje su gana da junansu. Sai da prince ishaq ya haura sama yai wanka ya dauro alwala sannan ya sakko kasa. Dan yaga magrib ta kusa. Hira suke shida Nas ya kalle shi a nutse yace "Yaya matarka na da kirki i know babu mai maye gurbin huddy,sai dai zaka samu wadda zaka so kala daban" Ajiyar zuciya ya sauke nas bazai gane ba yayi yarinta da yawa wajen da huddy ta bari babbane. Babu macen da yake zaton zata so shi kaman ita. Ba kuma ya zaton zai sake samun so irin nata. Komai na huddynsa dabanne. Shi din take so. Tasan shi fiye da kowa. Badon kudi ko matsayin shi ba. Sone na tsakani da Allah. Rayuwa kenan. Ba komai da kake mafarki bane zai zamo maka gaskia. Bakomai daka tsara bane zai faru. Kana ta tsara rayuwarka kana hango abubuwa da dama. Allah ya gama tsara komai. Tsarin shine Mafi cancanta. Murmushi kawai yai ma nas. Hira suka ci gaba dayi cike da shaquwa. * Tana shiga dakinta kiran ammar na shigowa. Dan haka tai kwanciyarta suka soma shan hira abinsu yana bata labarin wani film da ya kalla a office. Sai da aka kira magrib sannan suka katse wayar da cewan zai sake kiranta can anjima. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣3⃣ *Rayuwa ba abakin komai take ba. Shekara biyu cikakkiya zai wuce in wuce. Magana bata taba hadamu ba. Naji wani iri, naso ko da sau daya mun taba gaisawa. Allah ya gafarta maka Dan ladi. Allah ya ya saukaka maka kwanan farko nayau a kabarinka. R.I.J DAN LADI* Ta jima a zaune tana addu.o.i. bayan ta idar da sallar magrib. Dan tana mikewa ana kira. Isha.i dan haka ta sauke nauyi. Jingina kanta tai da gado. Tana sauke ajiyar zuciya. Batasan ta yanda zasu soma magana da natacce ba. Basa magana da ganin juna kullum ma ya ta kare da bugun zuciyarta duk idan sun hadu. Ita da take neman makasar auren nan. Kwankwasawa taji anyi a hankali ta furta. "Shigo" Kaman ko da yaushe kamshin shi ya cika mata hanci. Wannan karin sai taji gajiya ta saukar mata. Batai kokarin fada da yanayin da take ji ba. Kyale kamshin tai ya ratsa ko ina na jikinta. Da sallamar sa ya karasa inda take. A kasalance husna ta amsa. "Nas yace in fada maki saida safe. Ya gaji sosai ya kwanta" Ya fadi idanuwansa na yawo a fuskarta. Cikin sanyin murya tace. "Allah ya kaimu lafiya" Ya amsa da. "Amin" Yana dorawa da "Thank you" Jin tayi shiru ya sashi mikewa. "Good night" Ya fadi bai jira amsarta ba ya fice abin shi. Wani numfashi husna ta sauke da batasan tana rike dashi ba. Wani iri take ji. Wannan kirkin nashi yasata jin daban. Wayar ammar ta katse mata tunanin da take. Dagawa tai tace. "Nawan barin zo. Wanka zan sai mu sha hira" Ya amsa da. "Karki dade" Wanka tai ta rigar bacci marar nauyi. Ta dauki wayarta ta kira ammar. Bai dauka ba ya kashe ya kirata. Sunata hira yace. "Tawan ina jin tsoro fa. Jikina yana bani zan iya rasaki har abada" "Hmm nawan. Dan Allah ka daina karyamun zuciya haka. Believe in us mana" Shiru yai na wani lokaci sannan yace. "Bakomai" Hira sukai tayi har bacci ya soma daukar husna. Hakan yasa suka hakura. Tai addu.a. Bacci ya dauke ta. * Prince ishaq harya kwanta yana mamakin karamcin da natacciya taima kanin shi. Shi mutum ne da baya manta alkhairi ko ya yake. Sannan indai kai masa mutunci komin kankantarsa yakan ji dadi. Yana son Nas sosai. Duk wanda ya nuna ma Nas kauna dole ne ya samu karammawa a wajen shi. Zai kokarin ganin ya mata mutunci gwargwadon wanda taima kaninsa yau. A karo na farko a watannin nan da bacci yazo masa cikin sauki da nutsuwar zuciya. * Sai bayan tayi sallar asuba. Tai wanka tana zaune tana shafa mai, mafarkin da tai jiya ya fado mata a rai. Wani irin dokawa zuciyarta ta shiga yi. Komai ya dawo mata. Mafarki tai ammar da natacce na tsaye kowanne a gefenta. Tana kallon ammar ta nufi natacce ta rike hannun shi gam. Suka tafi abinsu ko juya batai ba duk yanda ammar yake ihun kiran sunanta. Harta gama shiryawa jikinta kyarma yake. Tana ta karyata mafarkin da tai. Ko da ta kwanta. Kasa komawa bacci tai. Tunani ya mata yawa kanta harya soma ciwo. Ko da sukai waya da ammar saida ya tambaya ko lafiya kuwa. Tace masa kawai kanta ne yake ciwo. Zasuyi magana anjima. Fitowa tai daga dakinta zuwa falon kasa. Ganin nas yasa murmushi ya qwace mata. "Um me ake taci haka ba.a neman mutane?" Ta buqata cikin siga ta tsokana. Bakinsa cike yace "Ina kwana anty" "lafiya Nas ya gajiyarka" Tai maganar tana zama kan kujera. Shikam yana zaune kan kafet tsakiyar falon da plate din stuffed cabbage sai mug da coffee a ciki. Saida ya hadiye abinda yake bakin shi sannan yace "haba anty fushi muke fa. Jiya kikai tafiyarki.Inkin manta da yaya ni ai bai kamata a mantani ba. Ko ya kace yaya?" Husna ta mayar da kallonta inda nas yakai nashi sai lokacin ta kula da natacce da haryanzun da tasan sunansa bata shirya daina kiransa da nata ba. Sanye yake cikin wando jeans blue da riga mai dogon hannu baqa. Karo na farko data fara ganinshi da shigar kana nan kaya. Saurin dauke idonta tai daga kanshi kamin mayyar zuciyarta tace yayi kyau. Ga yanda zuciyarta take dokawa fiye da ko yaushe saboda mafarkin da tai ya dameta. Cikin muryarshi dakakkiya yace "Ji bakinka a wajen wato inta mantani kai ba zata mantaka ba. You are nuts" Muryarshi din nan kanta karin matsala ne. Tun dacan ko wani yai magana da muryarsa babba haka saita dago ta kalle shi. Saidai ammar dinta muryarshi sanyi gareta ba kaman ta natacce ba da inyai magana take jin wani abu na miqewa a bayan wuyanta. Sai yanzun zuciyarta ke tattara bangarori da dama da batasan ta kula dasu ba waje daya akan natacce. Hatta yanda yake zama tattare yake da nuna isa da iko irin na jinin sarauta. Dariyar nas ta katse mata tunaninta. "Anty kinji yaya koh?" Ya fadi a tabare da sai da ya sata dariya. "Zo ga waje ki zauna" Prince ishaq ya umarta. 'ki' din da yai amfani da ita yasata fahimtar da ita yake kasancewar babu wata mace a wajen. Sororo tai tana kallonshi da wani yanayi data kasa fahimta. Idanuwansa ya kafa mata yako yi sa.ar sauke su cikin nata, sai taji tamkar tana shirin nitsewa cikin wani irin qaton kogi hakan yasata kauda idanuwanta daga cikin nasa. Hannunsa ya miqa mata alamar ta taho ta kalli nas daya zuba musu ido. Saita miqa masa hannunta yana riqeta taji tamkar wayar wuta ta jata zuwa yanayi na daban. Rikon dayai mata sak da wanda yai mata a mafarki. Ga zuciyarta da take zaton natacce dake zaune yana jin harbawar da take yi. "Oh God this is so gross! Nas ya fadi yana dafe kai. Ya dora da "Inta zauna a jikinka dakina zan tafi" Dariya sukai gabaki daya hakan yaba husna damar qwace hannunta daya riqe ta nemi gefensa ta zauna tana murza inda ya taba ko zata cire duminsa da yanayinsa daga jiki. * Komai yake yi saboda nas ne. Baya son da minti daya qaninsa ya fahimci auren nan bai dame shi ba. Koh dan farin cikin da yaga ya samu na ganin kamar komai ya soma dai daita a rayuwarshi. Ya gaji da qaryata zuciyarsa kan cewa yanajin wani yanayi game da yarinyar nan da baisan meye ba. Sai dai daya kalleta zuciyarsa kan doka da tsanarsa da yagani cikin idanuwanta. Zai iya cewa yana ganin tsana data fi tata a idanuwan mutane akansa. Kan mulkin da sam baya gabanshi. Shisa ma ko tunaninsa bayayi. Asalima da akwai abinda zaiyi ya gujema matsayinsa da tuni yayi. Ya kula taji abinda yaji da jikinsa ya hadu da nata.Hakan ya mishi dadi saboda shine fa. Prince ishaq komin tsanar da zata mishi dole taji wani abu game dashi. Yanzun ma ya tabata ne dan yana son ta fara sanin zai iya duk abinda yaso. Kuma saboda nasir. Saida taba tan ya bude masa shafi a zuciyarsa da ya jima da rufewa. Ajiyar zuciya ya sauke. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣4⃣ *Godiya mai yawa da fatan alkhairi ga duk masoyan WATA BAKWAI* Ta rugasu tashi dan haka bata jira komai ba tai breakfast dinta. Ta samu waje ta zauna. Text ta tura ma ammar taji ko lafiya dan bai kirata ba da safen nan. Kaman ko da yaushe hancinta ya fara jin shi. Bata juya ba. Karasowa yai inda take ya zauna gefenta. Saita tsinci kanta da ce masa "Ina kwana" Cikin babbar muryarshi yace mata. "Kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah" Ta fada tai shiru. Can tace masa. "Nas fa?" Murmushi ya kwace masa jin sunan kanin nashi kawai. Ya kuma ji dadi har zuciyarsa data tambaya. Yana kuma yaba karamcinta na kokarin boye ma Nas halin da suke ciki. A nutse yace. "In yazo adjusting banbancin lokacinmu yana masa wuya. Bacci yake" Su duka zaune suke shiru. Idanuwansu duka kan T.V din yake amman babu wanda hankalin shi yake akai. Kaman yanda komai na jikin husna yake sane da zaman natacce kusa da ita hakan yake a nashi bangaren. Zata iya rantsewa duk da karar t.v bai hanata jin fita da shigar lumfashin shi ba da yake kara ma zuciyarta sauri wajen dokawa. Ba karamun dadin fitowar Nas taji ba dan saiya dauke mata yanayin da take ji. Saida ya karya sannan ya dawo falon. Hira suke su dukansu wayar nas tai ringing. "Ina zuwa pls" ya fadi yana miqewa. Prince ishaq ya maida natsuwarsa kan husna. Cikin muryarsa ya soma magana. "Nakan jima ban ma wani godiya ba. Hakama nema alfarma abune mai nauyi a wajena. Nagode da karamcin da kikai ma kanina. Nagode da boye masa zamanmu. Ina son mu zama friends a iya zaman da nas zaiyi damu. Kome zamu ci gaba bayan nan bai dameni ba." Miyan dake cikin bakinta taji ya qafe. Harshenta ya mata nauyi. Saboda bata ma san me zatace masa ba. Kai kawai ta daga masa alamar ta amince. Hannu ya miqa mata hadi da fadin "friends?" Tayi jim kamin ta karbi hannun nasa "friends" Ta amsa. Cikin wata murya da ta kasa gane ko tata ce. Murmushi tai masa cike da yanayi da yawa. Shima murmushin yai mata data fahimta tamkar yana son gaya mata a can wani bangare na zuciyarsa yaso ace sun hadu a wani lokaci ba irin wannan ba. "Ishaq" Ya fadi yana zuba mata idanuwansa. Daurewa tai ta rike kallon da yake mata cikin nata idanuwan sannan tace. "Husna" Agogon shi ya duba ya kalli husna yace. "Zan fita bazan jima ba. Ki kula da kanki alright? " Dakyar ta hadiye abinda ya tsaya mata a wuya tace masa. "Allah ya dawo dakai lafiya" Amin ya fadi yana mata murmushin da saida dimple dinshi ya fito sosai. Bata taba kula dashi ba. Ko da yake bata kula da abubuwa da yawa akan shi. Sai take jin kaman taci amanar ammar a yanzun nana. Zuciyarta na gaya mata bata kyauta ba. Wani bangare kuma mafarkin datai ya mata tsaye. Haka Nas ya fito ya sameta. Ya tambayeta ina prince ishaq yace ya fita amman bazai jima ba. Nas yace mata zai koma daki zasuyi video chat da friends dinshi ta imo. * Dakinta ta koma tana kwanciya text din ammar ya shigo yana fada mata charge ne baida shi tahau whatsapp suyi hira. "Tawan inajin nisanki da kusancinki a lokaci daya a zuciyata na kasa tantance yanayin kowanne." Ammar ya rubuto. Murmushi tai ta rubuta masa amsa. "naka yanayin mai sauqine tunda har kana iya dorashi akan kalamai nawan. Ni kadai nasan me nakeji." "Bazan iya rabuwa dake ba husna kin zamo ni gabaki daya. Ki tausayawa rayuwarmu ki dawo gareni." Wani daci taji dan a yanzun komai ya kwance mata. Ta rasa mafita. Gaba daya kanta ya kulle. "Hmm ka tayani addu.a ina ta tunani ne nawan." Alama tagani cewan yana recording voice message. Hakan yasata mika hannu ta dauko earphones dinta kan gado tasa jikin wayar. Voice note din farko ta bude. "In aka yarda daso aka amsa shakuwa bataki shiga ba. Tunda nai miki kin mini naji sai mu killace sirrin juna. Abinda zai fita kan harshe da zuciya ya fita. Ki dan matsar da mayafinki ki ganni daina rufa. Idan naganki cikin shauki sai na daina kwafa. Farin cikinki adona ne fushinki shi na tsana" Wani abu taji zuciyarta nayi. Shi ba ciwo ba. Shi ba tsayawa ba. Tasan ammar. Tasan ammar sosai ta kuma san cewar ko hira suke in har ya soma yi mata waka. To abinda yake ji ya girmama. Muryar prince ishaq ta soma sata manta yanda take bala.in son muryar ammar. Musamman in yana mata waka. Mamaki take akan yaushe ya juye mata zuwa prince ishaq a zuciyarta. Wani voice note din taga ya shigo kamun ta gama budewa wani ya sake shigowa. Kuka ya kwace mata. Kuka take sosai da sosai tana jin zuciyarta kaman zata fado. Yanayin muryarshi a wakar karshe tasan ko ba kula yake ba yana jin ciwo fiye da wanda ita take ji. Sam bataji sallamar prince ishaq ba. Dan wayar ma tana gefe ta cire earphone din ta hada kanta da gwiwa tana kuka. * Ya dawo baiga kowa a falon kasa ba. Gidan yayi wani shiru. Zuciyar shi ta bashi shawara yaje ya duba husna. Ko ba komai sun zama abokai. Koda kuwa na iya zaman Nas ne. Ya fison yai komai yanda ya kamata. Ya kwankwasa yaji shiru ya tura hadi da sallama. Ganinta yai kan gado ta dunkule jikinta. Daga inda yake tsaye yana jin saukar ajiyar zuciyarta. Karasawa yai kan gadon ya dafa mata kafada. Cikin taushin murya yace. "Husna" * Sam bataji shigowar shi ba. Ko kamshin shi bata ji ba yau sai dai dumin hannun shi kan kafadarta. Da yanayin yanda yaja sunanta da halin da take ciki bai hanata jin wani iri ba. Dagowa tai ta kalle shi fuskarta cike da hawaye. Idanuwanta sun canza launi saboda kukan datai. Wata irin kewar huddy ta doki zuciyarsa. Ya danne abinda yakeji ba yanzun banne lokaci. Batare da tunanin komai ba yasa hannuwanshi ya tallabi fuskarta yana fadin. "Menene? Are you ok?" Hannun shi tai kokarin turewa ta a sake fashewa da wani irin kuka. Ta rasa yanda akai ganin shi ya kara karyar mata da zuciya. Gyara zama yai sosai kan gado ya riketa a jikin shi yana fadin. "Shhh husna. Komai zaiyi dai dai. Koma menene it will be alright" Baison kukan mace. Yanayin kukan ta ya dagula mishi lissafi. Husna kam duk wani abu da take ji ne yale fita ta hawayenta. Jitai gaba daya ta wani gaji. Ta zame daga kirjin shi. Gaba daya fuskarta kamshin shi take yi. Kallonta yake. Hannu tasa ta goge fuskarta. Ta kalli kirjinshi gaba daya ta jika masa riga da hawaye ne da wanne tsiya. Duk powder dinta ta goge tas a jiki harda jagirar ma. Kasancewar kayan farare. Ta zaro idanuwa. Muryarta a dishe sosai saboda kukan datai tace. "Dan Allah kayi hakuri. Duk na bata maka kaya" Kallon kirjin shi yai. Ya wani bata fuska da taga ya kara masa kyau yace. "Eww. Gross" Kaman zata sake fashewa da kuka tace. "I am sorry please" Da sauri yace. "Wasa nake fa. Enough, do you want to talk about it? I mean nasan ba hurumina bane. A matsayin aboki" Kai ta girgiza masa alamar aa. Ya sauke wani numfashi. Kukanta kadai ya sa mishi ciwon kai. Ganin shirun yai yawa. Yasa shi fadin. "Kinci abinci?" Ta girgiza masa kai. Ya soma gajiya da amsa masa magana da kai da take yi. Baya so sam. Ya share ne yau dan yanayin da take ciki. Mikewa yai sannan yace. "Tam barin watsa ruwa. Ki tashi kema. Kiyi wanka and no more kuka zan dawo ok?" Yanda yai mata maganar cikin umarni zaka rantse da yarinyar da bata fi shekara uku zuwa hudu yake. Karasawa yai daf da ita sannan yadan tsugunno dan ya dai-dai ta fuskar shi da tata. Cikin idanuwa ya kalle ta yace. "Da gaske nake fa. Banda wani sabon kuka zakiyi ciwon kai" Dakyar tace. "Bazan yi ba" Ya furta "Good" Ya fita yana ja mata kofar. Gaba daya ya kara saukar mata da gajiya. Hatta zuciyarta tagaji da aikin tunani. Dakyar ta sauko daga kan gadon ta nufi toilet. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣5⃣ *Babu abinda yakai ciwon rashin wanda ka shaku dashi. Babu abinda yafi tashin hankali sai ya fado maka a rai muryarshi da take cikin tunaninka ta soma dishewa. Saika nemi yanda sautin dariyarshi yake ka manta saboda ya maka nisa. Ya tafi inda zakaje wata rana. Da duk yawan hawayen da zaka zubda da karin tabbacin cewa bazai taba dawowa ba. Sadaukarwa ga duk wanda ya taba rasa wani mai kusanci a tare dashi!!!* Tsaye yake kawai ya sakarma kanshi shower.Yanajin yanda ruwan ke bi masa jiki. Idanuwan shi a rufe. Baisan dalilin kukanta ba amman ya tsaya masa a rai sosai. Da ganin yanayin kukan yasan ko menene ba karami bane. Har ranshi dai yana fatan bashi bane sanadin kukan ta. Mutum ne shi da baya son ya takura ko a takura shi. Dan haka tun randa aka kawota sai dole suke magana. Balle daya sake kula da cewar ko magana kan dole take masa ya kara fita harkarta. Yau kukanta ya dawo masa da abubuwa da yawa. Wankan ya fito ya shirya. Fararen kayan dai ya kara sakawa ya nufi dakin husna. * A daddafe tai wankan ta fito. Doguwar riga tasa milk color. Ta daura mayafin rigar a kanta. Hijab taje dauka kaman yanda ta saba zama da ita. Taji kwankwasa kofar prince ishaq. Cikin sanyin murya tace "Shigo" Ya turo ya shigo hadi dayin sallama. Gefen gadon ya zauna kanshi tsaye yana kallonta. Tayi kyau saidai fuskarta ta kumbura da idanuwanta saboda kukan datai. Hijab din ta zura baice mata komai ba. Abokantakar tasu mai rauni ce sosai. Saitai kwari zai hanata saka wannan hijab din tunda ba kalar matan dabai gani ba. "Muje" Ta ce masa. Tashi yai ya karasa daf da ita. Fuskarta yake kallo sosai kaman me neman wani abu. Muryarshi a dake yace. "Kuka kika kara yi ko?" Da sauri ta girgiza masa kai alamar Aa saboda yanda yake sa gabanta ya fadi. Yanda take jin wani shakkar shi na cika mata zuciya. Kallon ta yaci gaba dayi na yan mintina baice komai ba ya wuce gaba. Kafafuwanta ba kwari tabishi har dining room din. Ta zauna. Zagayawa yai ya zauna kujerar dake fuskantar husna. Plate ya dauka ya zuba mata white rice da miyar nikakken nama. Ya zuba plantain a sama ya tura mata. Kanta a kasa taja plate din. Ta soma ci a hankali dan bayau ta fara cin abinci a gaban shi ba. Kawai dai yaune na farko da shi ne ya zuba mata. Tayi mamaki saboda tana masa daukar mutum maijin kanshi da izza amman ya zuba mata abinci. Kamun taci ko rabi ya zuba fruits yankakku a plate ya sake turo mata da fork a ciki. Dagowa tai ta kalle shi. Shima fruit dinne cike yanata ci. Ba yunwa take ji ba ma. Kawai dai tana cine. Ture plate din abincin datai ne yasa shi dagowa ya kalleta. "Me kike nufi?" Ya tambaya. "Nako shi" tace idanuwanta a kasa. Muryarshi a dake yace. "Tam ki zabi daya. Ko ki cinye abincin nan ko ki shanye fruits din." Yau bata da karfin gaddama ko neman rigima. Cikin raunin murya tace masa. "Nako shine fa" "Just shut up and eat husna. Bana son gaddama, ki zabi wanda zai miki saukin cinyewa." Yana karasa maganar ya maida hankalinshi kan fruits din dayake sha. Da yawan lokuttan da suke daidai ton zama cin abinci waje daya kulewa yake da yanayin cin abincinta. Dan baya son mata magana ne. Ya tsani wasa da abinci duk da shima bawani cin kirkin yake ba. Kallon shi take ya wani hade rai yana tauna fruit din a yangan ce. Dan fa sun zama abokai na wucin gadi bazai sa ya dinga mata wannan shisshigin ba. Fruit din ta dauka ta soma ci. Ta kusan rabi ta ture ta kwantar da kanta a table din. Kallonta yake. With time zata koyi yin duk wani abu da ya umarta. Kyaleta yai bai takurata ba. Yasan limit dinshi. * Satin Nas daya yau a gidansu kasancewar ya kira mumyn shi tace masa yai zamanshi abuja yafi mata kwanciyar hankali. Dan tasan in yana kano bamai kwabarsa. Bamai hana shi fita yawo yaje a samu matsala. Abuja kam tana da tabbacin prince ishaq zai kula da Nas fiye da yanda zai kula da kanshi. Husna ji take kaman sun shekara tare. Yaron ya wani shiga ranta tana jinsa tamkar maheer qaninta sai dai wannan ya girmi maheer. Zasuyi hira. Suyi game. Zuwanshi yasa ta daina wuni da qunci. Da dare zasu sha waya da ammar dinta in kuma yanayin aiki bai riqe shi ba sukanyi chatting. Prince ishaq kaman yanda ta soma kiransa dan a ganinta lokaci yayi da zai zama hakan. Saboda dalilai da dama. Sukan gaisa. Sukanyi hira su uku amman indai su biyune a waje sai su rasa me zasu cewa juna. Duk wani iri kowa saiya daburce. Dan haka suka dinga qoqarin in nas na nan kawai. In baya wajen kowa yai harkarsa. * "Yaya menene idan na fita ni kadai nan ai ba kano bane. Beside babu wanda ma yasan waye ni." Nas ya fadi kaman zaiyi kuka. "In zaka fita wani waje da yake da yawa mutane haka kaman cinema nas you must go with securities.Banson hauka" prince ishaq ya ke maganar cikin qosawa. "I want some normal yaya ka fahimce ni mana. Shisa baso bane banayi inzo inda kuke hakanne yake damuna am 18 fa koda ka manta" "And?" Prince ishaq ya fadi da alamun ranshi ya soma baci. Cikin fuska nas ya kalle shi "hakan yana nufin zanyi yanda nake so da rayuwata. Ba zai yiwu duk inda zani da masu gadina ba kaman wanda za.a kashe" Ya bude baki zai bashi amsa husna tazo wajen.. Kallonsu tai su duka. Tasa akwai abinda yake faruwa. Nas yace mata "anty kice yaya yabarni na fita." Kallon shi tai duk da yana mata kwarjini naban mamaki. Cikin dakiya tace "Kabarshi mana tunda yazo sau daya ya fita" Harararsu yai su duka. "Kibar abinda ba zaki taba fahimta ba. Yaron nan bazai fita gate din farko bama babu masu gadi. Chapter closed" Yanda yai maganar yasa sukai shiru su duka. Yabar wajen kawai. Nas kaman zai kuka yace "I fucking hate this life!" "Calm down kagane kabishi a hankali." Husna ta fadi cikin sigar ban magana. A hasale nas yace "bazai bari ba anty. Wani lokaci rayuwa bata da adalci. Amman wallahi saina fita" Kamin ta samu bakin magana yabar wajen. Zama tayi abin ya daure mata kai. Meke damunsu su duka biyun. Tasan bata damu da prince ishaq ba amman nas kam dan uwa takejin shi a zuci da jikinta gabaki daya. Wajen minti talatin tsakani taji text ya shigo wayarta. Ta duba taga nas ne. "@silver bird cinema" Kawai yace. "Please take care!" Ta bashi amsa. Bai mata reply ba dai. Tana zaune a wajen prince ishaq ya zo. Kallo daya taima yanayinsa taji gabanta ya fadi. Bata taba ganinsa haka ba. Fuskarsa a hade take idanuwansa sun wani canza launi. A dake yace. "Ina Nasir?" Cikin rawar murya tace yana silver bird cinema" "Dammit!!!" Ya furta yana dukan kujeran wajen saida husna ta tsorata. Kallon ta yai da wani yanayi yace. "Saboda me zaki barshi ya fita? Akan me ba zaki zo ki fadamun ba?" Ta bude baki zata amsa shi dan bata ga fa yanda zata fara hana Nas fita ba ya katse ta da fadin. "Forget it" Ya dauko wayarshi kenan. Nata wayar ta soma ringing ta dauka nas ne. "Hello qani yadai?" "Wasu ne suka biyoshi sun ji masa ciwo yanzun haka muna bayan silver bird qarqashin wata mota wannan ne number din qarshe takan kiransa dana gani shisa na kira" Kallonshi kawai tai da bayanannen tsoro cikin idanuwanta fuskarta da alamun tashin hankali ya karbi wayar. Magana sukai da kowaye yake riqe da wayar nas din. Prince ishaq ya miqa mata yana tafiya ta tsayar dashi da "Kana tunanin zaka tafi kabarni anan? Cikin damuwa yace "ki zauna saboda yanayi na tsaro" "Wlh saina biyoka aiba qaninka bane kai kadai" Babu yanda zaiyi kuma baya son yawan surutu a wannan yanayin. Dan haka yabarta taje ta dauko alkyabba ta dora kan kayan da suke jikinta. Gabanta faduwa kawai yake. Jami.an tsaro ne tako ina suke zagaye dasu banda wanda yai waya su isa wajen. Husna bata san kuka take ba saida taji abu nabin kuncinta. Jini ne kaman an yanka qaramar dabba a gurin. Da gudu su duka suka karasa wajen Nas din. Girgiza kai prince ishaq yake cikin tashin hankali ya riko Nas jikinshi da bayama numfashi a rikice yake fadin. "Nas banda kai. Please ka bude idanuwanka" Husna na tsugunne gefe "Nasirr" ta kirashi cikin muryar kuka. Baima san tanayi ba. "Ya mutu koh?" Take tambayar prince ishaq. Shiru yai ya kyale yarinyar nan. Dan shima zuciyarsa zafi kawai take masa ba zata iya daukar wani rashin ba.Na huddy kawai ya ishe su. Wai me mutanen nan suke nema dasu ne? Duk akan mulki. Mulkin da in an tona zuciyoyinsu ba qaunarshi suke ba. Ya Allah! Yake fada a zuciyarsa ya dora da Allah ka tausaya mana. Nas yake jijjigawa. Kasa ya ajiye shi kamun ambulance din da aka kira ta karaso. Hannun shi ya dora kan zuciyar shi yana dannawa. Lokaci daya abinda ya faru da huddynshi yake masa yawo akai. Iska ya soma ba Nas ta baki yana jijjiga shi amman a banza. Baiga amfanin karatun shi ba. Ya kasa saving hudeesa yanzun ma ga Nas. Tare suka shiga motar asibitin su dukansu tare da nas. Kuka husna keyi kaman zata shide ganin qoqarin da likitoci suke tun daga cikin motar na ganin ya farfado amman abin yana neman gagara. Prince ishaq ya kalleta sai yaji zuciyarsa tayi wani irin yanayi. Hannunta ya riqo bata hanashi ba dan bama a hayyacinta take ba. Matso da ita yai jikinsa tako ruqunqume shi dam. Duk da halin da suke ciki bai hanashi jin wani abu na daban ba. Kuka take har lokacin amman wannan karon a qirjinsa take yanajin yanda jikinta ke jijjigasu gabaki daya. Saiya tuna masa lokaci mai nisa. Hannunsa yakai kaman zai riqota amman yana tunanin hakan. Wata zuciyar tace kayi ko babu komai tanajin halin da qaninka yake ciki. Hannuwansa duk biyun yasa ya riqe husna yana lallashinta. A haka har suka isa asibitin. Hana su shiga akai dole suka tsaya suna kallo ta window. Ganin yarinyar mutane na shirin sume masa yasa shi janyeta daga wajen window din suka zauna.Tana maqale jikinsa har bacci ya dauketa. Anfi awa biyu wani likita ya fito daga dakin da Nas yake. Tashin dayai ne yasa husna bude idanuwanta dan yama manta tana jikin shi. Girgiza masa kai likitan yai. Wani jiri yaji ya dibe shi.........! 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣6⃣ TO THE READERS!!! Bango ya dafa dan ya kusan faduwa. Husna ce tai karfin hali cikin rawar murya ta ce ma likitan. "Ya dai?" Ya bude baki zai magana wata Nurse ta fito da gudu ta kirashi.Ai bai saurare su ba ya koma ciki. Prince ishaq gani yai bazai iyaba. Husna yabari tsaye ta jingina da bango ya tura kofar ya shiga. Ihu zasu fara masa ya fita, ya zaro I.D card dinshi ya nuna ma daya daga cikin likitocin. Safar hannu kawai suka mika masa. Baima damu da saka abu ya toshe hancin shi ba. Na.urar dake gefe ya kalla. Addu.o.i yake karantawa dan gaba daya yagama karaya. Bugun zuciyar Nas cikin dari yana kan sha biyar. Yana tsoron taba shi. Saidai yasan bazai taba yafewa kanshi ba inhar bai kokarta da wani abu ba. Rayuwa da mutuwa duk yana hannun Allah. Wani irin ciwo ne gefen kanshi da har kashin wajen kana hangowa. Aikin shi ya ci gaba dayi tare da sauran likitocin na dinke dinken ciwukan dake cikin shi. Yankan wukane. * Husna kam da taji su shiru. Karasawa tai wajen glass din tana kallon su. Kanta wani irin ciwo yake yi. Ga hawayen daketa zubo mata. Bata taba ganin tashin hankali kwatankwacin nayau ba. Prince ishaq take kallo yanata kai da kawowa. Batasan iya awannin da suka dauka ba. Sannan suka fito. Da sauri ta karasa inda prince ishaq yake. Idanuwanshi sun wani canza launi. Sai taga harya rame saboda tashin hankali. Da idanuwanta take rokon shi yace mata Nas lafiyar shi kalau. Yace mata bai mutu ba. Jikin bangon ya jingina a hankali ya zame zuwa kasa ya hade kanshi da gwiwa. Husna ta tsugunna gabanshi. Hannunta na rawa ta dafa kafadarshi. Dagowa yai ya kalleta kyawawan idanuwanshi cike taf da hawaye. Mayar da kanshi yai ya hade da gwiwar shi. Yanda numfashin shi ke fita ne tasan kuka yake. Jitai zuciyarta ta sake karyewa itama zama tai kusa dashi. Batasan me zatai masa ba saboda batasan me yake jiba. Idan har ita dabata hada komai da Nas ba tana jin wannan dacin a ranta. Shi kuma me yake ji. Hannuwanta ta saka kan kafadun shi. Prince ishaq kam wani abune ya tsaya mishi a wuya. Wani irin ciwo zuciyarshi take masa. Kirjin shi ya masa nauyi. Saboda har yanzun zuciyar Nas bata da karfi. Huhunshi bashida karfin taimaka masa wajen numfashi sai da na.ura. A minti daya komai zai iya tsayawa. Yanajin duk abinda yake samun kowa laifin shine. Shi ake turo ma kashe di. Yakamata ace ya janye daga karbar mulkin nan dayai. Tun akan huddy baiji kashe din ba. Gara ya rasa komai. Abar masa kaninsa. So yake wani ya rike shi ya lallashe shi. Har cikin zuciyarsa so yake wani ya girgiza shi yace masa komai zai zama lafiya kalau. Nas zai ji sauki. Za a daina kokarin kashe su saboda za.a kama koma wanene su samu shaida a hannun su. Jin hannuwan Husna kan kafadarshi yasa shi dagowa. Ganin hawayen dake bin fuskar shi ba karamin girgiza husna yai ba. Tasan maza manya na kuka in abun yakai inda yakai. Amman yanayin prince ishaq yakan nuna zai iya daukar komai duniya ta jefe shi dashi. Zai iya jure duk wani kallo da kaddara zatai masa. Batasan lokacin datasa hannu tana goge masa fuska ba. Hannuwanta ya ture alamar ta kyale shi baya so. Kai kawai take girgiza masa tana maida hannunta tana ci gaba da goge masa fuska. Zamanshi ya gyara. Wani irin karyewa yaji zuciyarshi tayi. Hannuwanta ya ture ya dora kanshi kan kafafuwanta. Tsayawa tai tana kallon shi na yan mintina kamun ta dora kanta akan bayanshi. Su dukansu kuka suke. A wannan lokacin ba tare da saninsu ba abinda suke ji ya kulla alaka. Kaman yanda aurensu ya kullu a bisa kaddara haka kaddarar data fada ma Nas ta kulla alaka a tsakanin su. Sun shafe wajen awa daya a hakan kamun husna ta tashi daga bayan shi. Ta daukama bacci yake taga ya motsa. Bayanshi tadan bubbuga muryarta a dishe tace. Ka tashi. Bai mata musu ba ya dago daga jikinta ya sauke mata idanuwanshi da suka kumbura. Abinka da farar fata. Fuskar tai ja. Kayanshi duk jini ne. "Muje gida kai wanka ka sake kaya" Ta fadi muryarta na rawa. Dan bata so hankalin shi ya dawo jikinshi yaga jinin dan uwansa. Girgiza mata kai yai alamar a.a.Dan gani yake yana tafiya daga asibitin Nas mutuwa zaiyi. "Ina wayarka" Ta bukata. Hannunshi yasa a aljihunshi ya dauko wayar ya mika mata. "Wazan kira ya dauko maka wasu kayan?"Ta tambaya. Karbar wayar yai ya lalubo lambar kamala. Muryarshi dakyar take fita yagaya masa ya kawo masa kaya. Yasa a shiga dakin husna ma a dauko mata a hado musu da kafet din sallah. Mintina wajen Ashirin tsakani kamala ya shigo dan saida aka kira prince ishaq sannan suka barshi ya wuto. Yana kawo musu. * Wani kofa ya bude kusa da dakin da Nas yake ciki. Kujeru ne da wani gadon a ciki. Sai kofa ta glass datai connecting zuwa dakin da Nas yake ciki. Nan yabar husna zaune tana kallon yanda gaba daya jikin Nas yake jone da wasu na.urori. Addu.a ta shiga karantowa tana masa fatan samun sauki. Kayan jikinshi kawai ya cire ya ajiye su nan kasa cikin toilet din ya sakar ma kanshi shower. Jin shi yake wani sama sama. Haka ya saka kayan da aka kawo masa ya fito. Kallon shi husna tai. Yana tsaye gefe duk da a hargitse yake yayi kyau cikin black jeans da riga fara. Gashin a harmitse ga suma yana da ita baka duk tai coil. Tashi husna tai ta karasa inda yake. Saman goshin shi da gefen fuskar shi jini ne. Ruwa ya jika shi ya zama kaman lokacin ya goga. "Me kai hakan?" Ta tambaye shi. Idanuwan nan ya zuba mata kaman bazai amsa ba sannan yace. "Wanka" Hannu takai zata goge masa jinin dake fuskar shi ya kauce fuskar shi. "Bana son gaddama" Ta fadi cikin yanayin muryar dayakan mata amfani dashi wasu lokuttan. Ita kanta mamakin yanda take son kula dashi take yi. Dan yau ya zame mata kaman wani yaro karami da yake matukar bukatar kulawa. Kallonta kawai yake dan a yanayin da yake ji kwakwalwar shi bata da lokacin tunani. Hannun shi husna ta kama taja shi zuwa toilet din. Bai mata musu ba ya bita. Towel din dake ajiye sabo fil cikin leda ta bude. Ta jika da ruwa ta soma goge masa fuska dashi. Rufe idanuwanshi kawai yai yana jinta. A gefe daya kuma yana fata da addu.ar samun sauki wa Nas. Hannuwanta sun soma gajiya saboda ya mata tsaho da yawa. Sanda ta gama goge masa fuskar tsaf har wani nishin wahala take. Jin ta kama hannunshi yasa shi bude idanuwanshi. Janshi tai takai wajen kujerar. "Zauna to in fito" Ta bukata. Wani kasalallen kallo yai mata yace. "I am not a kid husna....." Wani guntun murmushi tai masa ta juya zuwa toilet din. Alkyabbar dake jikinta ta cire ta rataye. Kayan daya ajiye ta saka cikin wani bucket dake gefe ta cika shi da ruwa. Sabulun data gani ta fasa ta soma wanke su. Saidai sun rigada sunyi stain. Haka ta wanke iya yinta ta dauraye ta rataye su. Alkyabbar ta mayar ta fito ta zauna gefen shi. Kanshi ya kwantar a kafadar husna. Muryar shi can nesa yace mata. "Ina jin tsoro sosai" Cikin sanyin murya tace masa "komai zaiyi dai dai in shaa Allah.Babu abinda zai same shi." Muryarsa can qasa yace "inajin tsoro sosai husna sunyi sanadin rabani da huddy. Bansan me zancewa su umma ba" Sai lokacin ta kalli fuskarsa. Abinda tagani ta tabbatar ba zata taba mantashi ba har qarshen rayuwarta. Saita samu kanta da sa hannu ta taba fuskarsa. Tana son da duk wani abu da take dashi ta nuna masa komai zaiyi dai dai. Idanuwansa dauke da nisantacciyar damuwa. Tun ba yanzun ba husna ta kasance mai tausayi ko ga dabbobi ballantana kuma en adam. Hankalin prince ishaq ya koma can wani waje wani lokaci. * Riqe yake da hannun huddy suna jiran ambulance tazo ga mutane da suka dabaibaye su. Duk ciwukan da suke jikinshi basu dame shi ba. Huddyn sa yake ji ita kadaice damuwarsa. Duk wani kokari da zai iya ta fannin aikin shi a banza yake saboda baida kayan aiki. Ciwon dake gefen wuyanta yanata zubar jini. Rigar dake jikinshi ya cire dagashi sai singlet. Ya danne mata wajen a rikice yake fadin. "Stay with me huddy. Eyes open. Karki kulle su" "Yaya" ta fadi cikin murya mai dauke da ciwon da takeji. "Huddy dan Allah kiyi shiru karkice komai sannu yanzun taimako zaizo" Yake fada yana tarbe hawayen dake son zubo masa. Bata saurare shi ba tace "yaya karka barsu su sake dauke mana komai. Karku bar musu mulkin da basu cancanta dashi ba........" Tari ya sarqeta wanda tun tanayi harta soma na jini. Hankalinsa ya qara tashi ya tallabota jikinsa "huddy don't give up on me please ki taimaka" Murmushi tai masa "I love you yaya" "Na sani huddy nima ina sonki da yawa dan Allah karki barni." Baiga amfanin karatun shi ba a yanzun. Saboda bashida abinda zai taimaka mata dashi. "Damn....." Ya rasa inda zaisa ranshi yaji dadi. Hannunta ta dago wanda da alamun fuskarta ba matuqar dauriya taiba don azabar da take ciki. Ta taba kuncinsa a hankali tace "karka mantani. Ka zama cikin farin ciki yaya kamin alqawari" Yanzun kam hawaye ne suke zuba a idanuwansa rabon shi da hakan harya manta. "Na miki huddy na maki alqawari. Murmushi tai "La ilaha Ilallah........." Ta karasa muryarta na sarkewa.Lumshe idanuwanta tayi sannan komai ya tsaya cik! 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣7⃣ *Ina godiya mai yawa ga masoyan da suke mun addua ako da yaushe. Allah ya biya muku bukatunku na alkhairi. Amin* Ganin yanayin fuskar shi yasa husna girgiza shi ta dawo dashi daga dogon tunanin da yake yi. Dafe kanshi yai cikin hannuwanshi yana maida numfashi da sauri da sauri. Wayar shi ya dauko. Baisan me zaice ma su mumyn Nas ba. Husna ya kalla idanuwanshi bayyane da duk tsoron da yake ji muryarshi na rawa yace mata. "I don't know what to tell them, mumyn nas ta dauka zan kula dashi........" Kasa karasawa yai ya dafe kanshi kawai yana jin kaman ace kasa ta bude ya shige ya huta da wannan nauyin da yake kanshi. Husna bata san me zatace masa ba ko kuma taya zata rage masa abinda yake ji. Wayarshi ta soma ringing. Ya duba umman shice. Kai ya shiga girgizawa kaman tana ganin shi. Hakan yasa husna duba wayar ta ga wayake kira. Dagawa tai ta mika masa. "Kai mata magana kawai. You can do this" Jikinshi babu wani kwari ya kara wayar a kunnen shi yai shiru. "Babana kana lafiya?" Umman ta fada da rauni a muryarta. Sai yaji ya samu wani dan karfi kadan jin muryarta. Cikin karfin hali yace. "Mungode ma Allah umma...... Mumy fa?" Yanajin ajiyar zuciyar data sauke sannan tace. "Tun dazun kamala ya fada mana abinda ya faru. Mai martaba yace adan dagata tukunna muzo saboda yanayin tsaro. Ita tace tunda kana tare da Nas tabar ma Allah komai" Lumshe idanuwanshi yai yanajin kaman mumyn Nas a gabanshi tai maganar. Yana kuma jin nauyin girman da ta dora masa. "Allah yasa umma. Kuyita addu.a shi kadai Nas yake bukata a yanzun...... " Yanda yai maganar ne yasa tace masa. "Ya Naseer din?" Yasan ma.anar tambayarta saboda yajita a muryarta. Bataso kai tsaye ta tambaye shi idan su saka rai da tashin Nas ko kuma su soma shiryama zuciyarsu hakuri dashi. "Umma zan kiraki in an sami wani ci gaba" Ya fadi yanajin yanda ta furta. "Ya Allah.... " Kamun ya kashe wayar. Dan yana tsoron tambayar datai masa. Tun da suka shigo asibitin nan yake kokawa da zuciyarshi kan wannan tambayar. Jiyai cikinshi ya wani kulle ya gyara zaman shi ya dora kanshi a cinyar husna yai shiru kawai. Kyale shi tai. Tunda batada hanyar da zata rage masa abinda yake ji. Wacece ita da zata hana shi yin abinda yaji zai iya ya samu saukin zuciyar shi. * A asibitin sukai sallar isha.i. Duk yanda likitoci suka bashi magana kan cewa yanayin Nas a yanzun stable ne. Suna kuma addu.a da fatan ya tsaya haka a kuma samu ci gaba kin yarda yai. Da kanshi ya dudduba Nas din dabai masan duniyar dayake ba. Har lokacin bugun zuciyarshi ba wani karfi. Saidai yana dan karuwa da uku zuwa hudu kan dazun sai kuma ya sauka. Amman yaki yarda daya tafi yabar Nas din. Kallo daya zakai masa kasan cewar shi kanshi yana bukatar hutun amman yaki yarda ya tafi gida. Husna ya kalla yace mata. "Idan kamala ya zo kawo blankets ki bishi ya mayar dake gida" Girgiza masa kai kawai tayi. Dan batajin zata matsa kafa daya ma batare dashi ba. Bawai dan bata taba kwana ita kadai sai yan aiki a wannan katon gidan ba. Saidan wani sabon tsoro daya shigeta da kuma son ta zauna kusa da prince ishaq din. Ga tausayin shi daya addabeta. Bazai iya wani surutu mai yawa ba. Dan haka ya kyale husnar. Shima yafi son ta zauna. Yana bukatar wanda zai kula dashi. Tunda ummar shi tayi masa nisa babu wadda zai juya ya kalla yadanji karfi karfi sai husnar. Dakin su suka bari suka shiga inda Nas din yake kasancewar dakin tankameme. Can gefe husna ta shimfida musu bargunan manya masu matukar laushi suka zauna shiru. * Nan inda husna take zaune bacci ya dauketa. Shi ya kamata ya kwantar da ita ya lillibe ta. Addu.o.in tsari ya tofa mata sannan ya koma ya zauna. A haka ya kwana kanshi hade da gwiwarshi. Da duk shigowar da wani likita zaiyi duba Nas tare zasu duba shi. Da asuba saida yai wanka yayo alwala yazo da niyyar tashin husna ya samu ta tashi. Toilet ta nufa itama wankan tai ta saka kayan da aka kawo mata jiya batai amfani dasu ba. Sanda ta fito prince ishaq harya idar da sallah hana zaune yana addu.o.i. Sallar tai itama. Taima Nas addu.ar samun sauki ta koma kan bargunan tai zamanta. Shima nan ya koma kusa da ita ya zauna. Saida taji cikinta na ihu ne ta tuna rabonsu da abinci tun na jiya da rana. Dayan dakin husna ta tashi ta shiga. Prince ishaq kam da ido yake binta. Kayayyakin ciye ciye da kamala ya kawo musu kiya ya zuba a fridge din wajen ta dibo. Fresh milk da snacks ta dibo masa fruits dan a yan kwanakin nan ta kula yana son su. Kome take da ido yake binta. Yana kallo ta miko masa fresh milk da burge. Kai ya girgiza mata dan tun jiya yake jinshi wani iri. Kallon wannan tarkacen ma jiyai amai yake ji. Kyale shi tai tadan samu taci burge guda daya da fresh milk. A hankali tace. "Kaci wani abu please. Ko fruit dinne" Kanshima ciwo yake masa. Bayason magana at all. Dan haka ya karbi apple din data bashi. Gutsura daya dakyar ya hadiye yana wani yatsine fuska. Kula tayi kaman jikinshi nadan kakkarwa. Kallon shi tai sosai. Idanuwanshi sun shige ciki sunyi wani kanana. "Are you okay?" Ta tambaya. Daya daga mata kai alamar eh, sai kuma ya gigiza mata kai alamar a.a dan jinshi yake wani irin sama sama. Apple din dake hannunshi taje karba. Taji wani zafi fiye da yanda takanji jikinshi. Da sauri takai hannu ta taba fuskarshi. Wani irin zazzabine rufe dashi. Ido ta zaro tace. "Baka da lafiya. You are burning up" "Lafiyata kalau" Ya fadi yana kauda kai gefe. "Baka da lafiya bara wanj doc ya shigo" Husna tace tana kallon shi. Batare daya kalli inda take ba yace. "Bana wani bukatar doc saboda lafiyata kalau" "Ka cika gardama" Ta bashi amsa. Kallonta yai cikin fuskata yace. "Kin cika son jan magana" "Bafa kada lafiya" Ta maimaita tana kallonshi cikin idanuwa wannan karin. Yatsina fuska yai a dake yace. "Bana son jan magana and bana bukatan doc" Shiru tai kawai. Ta kula ba wai saurararta zai ba. Dakyar ya iya mikewa saboda jirin dke kwasar shi dan ba karamar dauriya yake ba. "Ina zaka?" Ta tambaya. Baice mata komai ba ya wuce ya fita. Numfashi ta sauke. Batabi bayanshi ba. Yanda baison takura ta saka mishi ido kawai. * Allurar zazzabi akai masa data sake taimakawa wajen kara mishi jirin dayake yi. Da doc din yaga prince ishaq yaki saurarshi kan cewar kodai ya yarda ya kwanta asibiti ko kuma ya koma gida ya huta dan stress ya mishi yawa yasa shi biyo shi har dakin da Nas yake. Husna yaima magana yace prince ishaq din na bukatar hutu. "Ka kira azo a dauke mu kaje gida ka huta please" Ta bukata muryarta a tausashe. Girgiza mata kai yai hadi da fadin. "Ba inda zani" Dafe kai husna tai. Taurin kanshi ya soma gajiyar da ita. A nutse tace. "Nas bazai so kai masa haka ba. Zaiso ka zamana mai kwarin gwiwa yanda zaka kula dashi sosai. Ba ka yarda Allah bane mai bada lafiya?" Shiru yai kanshi a kasa yana saurarenta. Ganin hakan yasa husna cewa. "Duk zaman nan da muke bashi Nas yake bukata ba. Addu.a yake bukata. Please muje gida ka huta.... " A gajiye ta karasa maganar. Yana tsaye inda yake. Kyale shi tai kawai. Ga mamakinta waya taga ya zaro daga aljihunshi. Ya kira kamala. * Saida suka shiga mota prince ishaq ya kalleta na wasu yan mintina. Hannunta ya riko dayasata juyowa ta kalle shi. "Nagode. Nagode sosai da komai da kikai mana" Batace komai ba sai wani dan guntun murmushi datai masa. A haka har suka karasa gida. Kowa bangarensa ya nufa. Saida tai wanka sosai tai brush sannan tama tuna da wayarta. Falon kasa ta sauka nan tabarta kan kujera jiya. Ta dauka ta nufi dining. Irish ta dan ci da soyayyen kwai sannan ta koma sama. Key din wayar ta bude. Gabanta ya fadi. Har ga Allah ta manta da ammar a kwana dayan nan. Hakan ba karamun mamaki ya bata ba. Ya kirata har ba adadi. Ga messages da yawa. Ji tai bata bukatar wani sabon ciwon kan. Ba zata iya magana dashi ba. Text ta tura mishi ta fada masa kanin prince ishaq datake fada masa ne yai accident. Zata kirashi. Ko tsofaffin sakunan daya bar mata bata duba balle ta jira taga reply din dazai dawo mata dashi. Ta kashe wayar ta ajiye gefe. Bacci ya dauketa cike da mafarkin Nas da rayuwa irin tasu. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣8⃣ ALLAH KA YAFEMANA KA JIKAN MU!!! Yana kwanciya bacci ya samu. Sanda ya tashi lokacin zuhr harya gota dan haka saida ya fara yin sallah sannan ya kara yin wanka. Simple yadi yasa fari marar nauyi. Zazzabin daya rufe shi ya sauka sai ciwon kai kawai wanda yasan yunwa ce. Fitowa yai ya samu dakyar ya tura ma cikin shi plantain da irish. A wajen ya zauna yana dan hutawa. Jikinshi ya masa wani nauyi. * Tunda ta tashi bacci ta kunna wayarta suke chat da ammar har saida lokacin sallah yai. Data idar ma ta shirya tai tunanin fita ta duba prince ishaq. Sai taji ba zata iya shiga ba kuma. Ta zauna falon sama tana jira taga fitowarshi. Ga mamakinta daga kasa taga ya hauro sama. Murmushi yai mata da zata iya fahimta a fuskarshi kadai ya tsaya tunda tasha ganin shi yana murmushi. Mayar masa tai ta dora da fadin. "Na dauka kana baccine ai. Ya jikinka?" Saida ya karasa inda take ya zauna. Sannan yace. "Alhamdulillah. Nagode" Kamshin shi duk ya cika mata hanci. "Zan koma wajen Nas yanzun....." Bai karasa ba ta mike tana fadin. "Bari in dauko in sake kaya inzo" Sai lokacin ma ya kula da kayan da suke jikinta. Doguwar rigace loose sosai da mayafinta nade a kanta. Baice mata komai ba. Ko mintina sha biyar ba a cika ba ta fito sanye da atamfa da doguwar hijab. Sai yaga ta mishi kyau. Jakace maidan girma a hannunta ta kalli prince ishaq tace. "Ka dauko kayanka da zaka sake da brush. Kaga in muka tafi basai mun dawo gida ba" Yatsina fuska yadanyi dan wannan tunanin sam baizo mishi ba. Bai amsata ba ya wuce hanyar dakinshi. Itama bata damu da saiya bata amsa ba. Shadda ya dauko fara da brush dinshi ya kawo mata. Karba tayi batasan lokacin da tace. "Baka da kayane sai farare?" Da wani yanayi a fuskarshi ya amsa sata da. "Ina da. Kawai nafison farare ne" Batace masa komai ba ta dauki jakar suka nufi hanyar fita. Cikin sauri wata hadima ta taho ta tsugunna ta karbi jakar husna. Taso ta hanata ma prince ishaq yai mata wani kallo. Hakan yasa ta sakar mata jakar. Kallon dai ya sake mata dayake nuna alaman "Good" Murmushi tai suka karasa waje. * A hanyarsune yake mamakin yanda akai husna ke karantarshi. Ba saiya bude baki yai magana ba. Tana gane duk wani abu daya dora a fuskarshi. Husnar ma bata kawo zancen a raiba. Ita dai inyai abu kawai tana ganewa. * Shigar su asibitin doc ke musu albishir cewar an samu ci gaba. Bugun zuciyarshi yakai 50. Kuma suna saka ran zuwa anjima inbai rage ba zasu iya masa aiki dan a rage pressure din dake kwakwalwarshi. Husna ya raka cikin dakin da Nas din yake ya tabbatar ta nutsu waje daya sannan ya koma wajen likitocin sukai masa bayanin yanda komai zai kasancewa. Tambayarsu yai ko za.a iya moving din Nas zuwa india ai masa aikin acan. Suka bashi tabbacin cewar suma zasu iya. Sunada duk likitocin da ake bukata da kayan aiki. Kuma a halin da Nas yake ciki motsa shi ma zai iya kawo wata babbar matsalar. Amman da yanayin ci gaban da ake samu komai zai dai-dai ta da yardar Allah. * Inda yabar husna nan ya sameta tanata danne danne a waya. Ita kam chatting suke da ammar. Tana jin shigowarshi tace ma ammar din tana zuwa. Duka wayar ta kashe ma. Kujera ya ja a hankali ya zauna kusa da husna. Sun jima a haka shiru. Kaman daga sama yace mata "Bani labari" Da mamaki a fuskarta ta kalle shi tace. "Wanne irin labari" Idanuwanshi ya kafa mata sannan yace. "Kowanne iri ma. Nagaji da sauraren bugun zuciyata ne" Idanuwansa sun sa duk tabi ta wani daburce. Ya kula ta rasa me zatace. "How about in tambayeki abu kina bani amsa" Kai ta jinjina mishi alamar ta yarda. Tunani yake danyi. Kawai saiya samu kanshi da son saninta. "Menene full name dinki?" Wata yar karamar dariya yabata. Ta dauka zai tambayeta wani abu mai muhimmanci. Mutumin nan yakan bata mamaki lokaci lokaci. Saida ta gyara zama sosai sannan tace. "Husna Abdullahi" Jinjina kai yai yace. "Tell me more about you" Kallonshi tai tace. "Saidai kaima zaka amsa mun wasu tambayoyi" Tauna maganar datai yake yi. Ya wani daga girarshi sama alamar anya ya yarda kuwa. Can yace. "Alright" Murmushi tai sannan tace. "Su wa sukaima Nas wannan dukan? Me yasa sukai masa?" Shiru yai saboda tambayar tadan tabashi. Saida tai zaton bazai amsa ba yace. "Me yasa kika aureni?" Tambayar tazo mata a bazata. Da sauri ya dora. "Ina son sani zan amsa miki taki tambayar idan naji dalili and please be honest" Yana son sani ne kamun ya amsa mata tambayarta da take sirrin su. Cikin idanuwa ta kalle dan tana so yaga gaskiyar abinda zata fada. Tace. "Sani akai in aureka" Sai yanzun yasan dalilin dayasa ta tsane shi. Kaman yanda akai masa dole ya aureta itama hakane. "Kaifa?" ta bukata a takaice. "Nima haka" Shiru suka danyi. A hankali yace mata "Asalin sarautar garin kano a hannun kakanin kakaninmu take. Kamin daga baya su sarki saif su karba. Bayan lokutta sun shude ne sarautar ta sake dawowa hannunmu bayan rikici da akai mai yawan gaske. Hakan yasa aka zauna sulhu cewa in wannan gidan sukai mulki suka sauka zai koma hannun dayan gidan. Sai zaman lafiya ya samu. Wannan karon in babana ya sauka sarautar hannun su zata koma. Sai dai mutane sun gaji basa son ai hakan suna so inya sauka a bani ne. Wannan shine dalilinsu na son dauke duk wani jini na gidan kan wannan mulkin. Ban taba son shi ba. Bai taba burgeni ba sun dauke huddy akanshi. Hakan kawai daliline dazaisa na tsani komai na cikinsa,gashi yanzun insun sake nasara zasu dauke min Nas. Ansan sune sukeyi ba yanda za.ayi mu dauki wani mataki tunda bamuda shaidar da zamu bayar a kotu. Ajiyar zuciya husna ta sauke tana mamakin kalar wannan rikicin nasu. "Allah bazai barsu ba" Shiru kawai yai. A wajen Nas suka kwana ranar. Ita kan bargunan shikam a zaune. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 2⃣9⃣ Sati biyu kenan cif. Komai ya sauya musu.A asibiti suke kwana da kusan yini. Ana samun ci gaba a fadar likitoci dan ita kam husna idanuwanta baya ganar mata haka tunda har yanzun nas bai bude idanuwanshi ba. Motsi ma bata ga yayi ba. Harta da numfashi da taimakon na.ura yake yinshi. Abinci sai ta hanci. Husna zatai magana da prince ishaq. Zasu danyi hira tun tanajin wani abu inya riqeta jikinsa harma ta daina. Saboda ba yanda zatayi dashi. Takanji kaman bata kyautawa ammar sai dai a sati biyu harta saba tunda ba wani abun yake mata daya wuce riqeta a jikinsa ba. Kuma ta gaji da qaryata zuciyarta hakan na mata dadi. Tana son qamshinsa da duminsa duka. Ta nemi inda tsanarsa take a zuciyarta ta rasa. Gaskiya mutane da yawa sunyin gaskiya. Karka yanke hukuncin yanda kake ji akan mutum saika zauna dashi tukunna. Ta kula shi din mutum ne mai bala.in yanga. Saidai baya so ai masa. Baya son gaddama. Komai nashi da tsari yake yinsa. Bata san me take ji game dashi ba. Dan yansun komai rudani yake sakata. Tunaninta da yanayin komai. Abu daya take da tabbas a kansa son ammar. Yana nan. Duk da yanzun bata tunaninsa ko da yaushe sai dai da taji muryarsa komai yake dawo mata sabo. Kalamansa nakaita wajaje da yawa da suka kai a soyayya. Danma fadan da suke yawan yi kwana biyu. Ta mishi uzuri saboda ita kanta ta rasa dalilin dayasa take biyo prince ishaq asibitin. Inhar zasu koma gida saiya mata tayin ta zauna itace take kiyawa. Ammar kuma gani yake kaman zai rasata ne. Tsoronshi karta soma kulawa da su. * Prince ishaq kam zai iya cewa abinda ya faru da nas ya tuna masa da alqawarin daya daukar ma huddy a maganarsu ta qarshe a rayuwarta. Yama zai manta. Huddynsa zata so ya samu farin ciki sai dai ko bai mata alqawari ba ba zata mantu a gurinsa ba. Darajar so da en uwantaka ta wuce hakan. Husna baima san me zaice da zuciyarsa a kanta ba. Yakan jima bai yarda ya shaqu da mutum ba. Ko abokai yawanci na karatu ne. Sai na asibitin shi da ya dade da barma Dr.Hashim ragamar komai tun bayan rasuwar huddy. Banda kamala bai yarda da kowa ba da sirrikansa. Shima baban shine sarkin fada. Kusan tare suka taso da prince ishaq din. Zuciyarsa tana da rauni mai yawa ta wannen fannin. Tana da saurin sabo. Koya zakai masa karamci baya mantawa. Yanzun ya saba da hussy kam. Bazaiyi qarya ba sabon da har mamaki yake bashi inyai hange zuwa wasu lokutta can baya. Yanzun aurensu haryana kusan tasarwa wata na biyar. Rayuwar babu wahala. A haka muke ta cinye kwanakinmu. * Sun dan koma gida su huta. Nan husna tabarshi ta shiga ciki abinta. Sai da ta kwanta ta huta sukai waya da ammar sannan. Har zata fito ta tuna. Kausar ta kira ta fada mata abinda ya faru. Ta sha mita cewar batada kirki. Atleast ko da basu zoba zasuyi addu.a. * Yana zaune babban falo yana kallon yanda duniyar take a tashar aljazeera husna ta shigo. Gefensa ta zauna batare data ce masa komai ba. Ya sauke numfashi. Yanayin fuskarsa ta kalla tace mishi. "Yadai?" "Meyasa baki taba kiran sunana bane hussy?Tunda yanzun ana kallon fuskana sunan kuma ya gagara" Ya buqata yana qarasa maganarsa da murmushi. Tun rannan ya soma ce mata Hussy din nan. Sai taji sunan ya mata dadi. Idanuwanta nakan kafet din dakin sai takejin wani iri. Sau uku tana bude baki sai taji sunanshi ya makale akan harshenta. Ba zatai mishi qarya ba dan haka tace "Sunanka yanamin nauyin fadane" Ya wani yatsine fuskarshi mai kyau sannan yace "Nikuma na gaji da zama nameless a wajenki." Murmushi tai bata dago da kanta ba dai. Yanajin dadin yanda yake da tasiri akanta. Koma wanne irine. Muryarshi can kasan makoshi yace. "Uhum inajinki. Ko sunana ko ki zabarmin wani" Iya zaman sun nan tana karantar halayyarsa. Inba abinda ya bukata tayi ba bawai zai barta bane. "Gentle" sunan ya subuce mata da sauri ta dora da "zan kiraka gentle yayi?" Murmushinsa ne ya bata amsa. Bai sake cewa komai. Jingina yai sosai da kujerar yaci gaba da kallon shi. Yanzun harta soma sabawa da wasu halayen nasa. Yanzun zai mata magana kaman zasuyi hira mai nisa sai kuma yai shiru abinsa. Prince ishaq akwai yanga. Wasu lokuttan sai suyi awa biyu zaune baice mata kanzil ba. Yana magana saita kama ne. Ranar cayai mata su kwana a gida. Yai waya yace koya aka samu canji a kirashi. Taji dadin hakan dan hakurin ammar ya kusan karewa. Aikam har sha biyun dare suka kai suna hira. Charge dinshine ya dauke da basu hakura ba * Badan wannan abin daua faru ba da tuni sun koma kano dan wata daya da yan kwanaki kamata ace sunyi a garin abuja Amman yanzun har suna shirin dosarwa wata uku. Taji dadi sosai da kausar tazo har asibiti ita da mijinta suka duba Nas. Dan kam ya zama qani a wajenta. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣0⃣ Ranar da Nas ya cika sati uku a asibiti. Sun dawo gida wajen zuhr. Prince ishaq ya fita yace mata akwai abinda zaiyi. * Kallo take sanda ya dawo. Ya zauna kusa da ita yana wani langabewa. "Gajiya ko?" Ta bukata. Ya daga mata kai. Kallon shi take akwai abinda ya canza mata yau. Fuskar shi tai wani fayau. "Meye babu a fuskarka?" Ta tambaya tana kallon fuskar. Dariya yai. Tajima bataji dariyar nan tashi ba. Itama sai abin ya bata dariya. "Aski nayi fa" Ya karasa maganar yana dariya. Shiru husna tai masa. Haba shisa taga fuskar tai wani fayau. Suna zaune aka kira la.asar. Ya tashi ya nufi masallaci. Itakuma husna tai nata bangaren. Tana yin sallar la.asar tasan zasu iya komawa asibiti don haka ta mike. Wanka ta fito tana kwallia a gaban mirrow ammar ya kirata. Daga wayar tai tasa earphone. Cikin muryarsa mai sanyi yace mata tawan "kaman bakyason kashe auren nan ne ko?" Murmushi tai kaman yana ganinta tace "Nawan ba haka bane.Ka yarda dani wlh na rasa hanyar da zanbi ne har yanzun na kashe auren nan. Kai kasan ina sonka. * Sallah ya dawo. Baiga husna a falon su na sama ba. Dan haka ya nufi bangarenta ya fada mata yai waya da doc din Nas. Komai yana nan yanda suka barshi dazun. Bayajin zasu koma yau saidai zuwa safe inyaso su kwana a wajen shi. Kwankwasawa yai har sau biyu shiru. Ya dauka ma sallah take ya tura dakin da sallama ya shiga. Tana zaune kan stool tana shafa mai jikinta sanye da doguwar riga. Kan kunnenshi take furta komai. * Sam bataji shigowar prince ishaq. Da duk kalma daya da zata fito bakinta sai zuciyarsa tai wani irin dokawa. Lokaci daya ya tuno maganar huddy a wani lokaci can baya "Yayana ka zama mai haquri sai dai karka yarda a wulaqanta mana darajarka ta ko wanne fanni" Yau shi prince ishaq matar da take cikin gidansa da igiyar aurensa ukku a kanta ce take waya da wani qato. Har take fada mishi maganganu iri wa.annan. Inalillahi wa ina ilaihi raji.un yame ta maimaitawa a zuciyarshi. Yana fatan dai-dai ta hankalin shi kamun zuciya tasa shi aikata abinda bashi kenan ba. Husna kam hankalinta kwance taketa wayarta. Tashi tai dan ta dauko dankwalin rigar jikinta. Tana juyawa taganshi tsaye jingine da qofa............! 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣1⃣ Idanuwansa kawai data kalla ya tabbatar mata da yaji kome take fada. Tsaye yake har lokacin ya kafa mata idanuwan na nasa da suke bala.in yi mata kwarjini. Ji take har iskar da take yawo a dakin tsaye take cik. A hankali ya tako ya qaraso inda take. Yanayin yanda zuciyarta ke dokawa ta dauka fitowa waje zatai tsabar kidimewar datai. Bata taba kawoma ranta zai kamata ba. Ko kuma zata ma ji abinda take ji yanzun idan har ya kamata. Baiko kalleta ba. Harya karaso. Hannu yasa ya zare earphone din daga kunnenta. Wayar yazo dauka takai hannu wajen. Ya hada da wayar da hannunta duka ya riqe. Jikin bangon wajen ya turata. Kalar riqon dayai mata a wajen ne yasa batai kiciniyar qwacewa ba. Idanuwansa har sun sauya saboda bacin rai. Bai taba zaton zaiji kishin wata ya mace bayan huddynsa ba. Da huddy baisan kishi kalar wannan ba. Saboda yasan shi kadaine a zuciyarta. A yanzun ma bazaice ga kalar dacin da yake ji a ranshi ba. Yama kasa mata magana. Kallonta kawai yake. Kuma taqi yarda su hada ido. Kanta a kasa da bayanannen tsoro. Ya matsa kusa sosai yana sake hadeta da bangon. Tana jin hucin numfashinsa kan fuskarta saboda kusancin da sukai amman taqi yarda su hada ido. Hannunsa yasa ya dago mata haba. Tako sauke idanuwan nata cikin nasa. Saurin rufe su tai gam. Abinda take gani cikin nasa idanuwan ba zata iya daukar shi ba. Ya mata girma. Dai dai lokacin wayarta ta soma ringing. Karba yai daga hannunta ya duba 'ammar' yagani rubuce jiki da hoton heart qato tsakiyarsa rubuce da 'true love'. Wani numfashi yaja ya fitar dashi. Yakan jima ranshi bai baci ba. Yana duk abinda yasan zai guje masa faruwar hakan. Saboda bai iya shi ba. Dagawa yai ya kara a kunnensa. Hannunshi daya na riqe da husna. Ya janyota ya matseta a qirjinsa sannan yace "Hello" "malam kaba mai wayar abinta" Aka fada daga dayan bangaren. "Mafi munin kuskure da inaji kaf zuri.arku basu taba yinshi ba shine waya da matar aure. Matar kuma ta ishaq" Yanayin muryarshi ya tsorata kafafuwanta har kyarma suke. Badan rikon dayai mata ba dole ta zauna. Ammar kam ranshi ya soma baci yama akai wayar husnar shi taje hannun mutumin daya fi tsana a duk duniya. Dan haka yace "kaine kai kuskuren auren yarinyar da ta jima da miqamin zuciyarta. Ba zata taba sonka ba" Murmushin takaici prince ishaq yai. Yanajin wani sabon ciwuka suna budewa a zuciyarshi. "kai kana sonta kuwa?" Ya bukata da bala.in karfin hali. "Ina sonta son da ba zaka taba iya mata shi ba" Ammar ya fada cikin bacin rai. "Zan iya yarda ka shaqu da ita amman baka taba sonta ba. Daka na sonta ba zaka taba janta zuwa halaka ba. Ni ba qaramin mutum bane akwai dalilai da dama dazai hana na dauki hukunci akanka.........." Katse shi ammar yai da fadin "malami bama son dogon surutu ka saketa mana tunda bata sonka ni take so" Zuciyar prince ishaq har wani daci take ga sabbin raunukan dake ciki suna kara budewa. A hakan ya daure. Cikin kanshi yana lissafa watannin aurensu kamun yace "Zan sake ta! In har bata soni ba nan da *WATA BAKWAI 7* Be a man karka sake kiramin mata har sai wa.adin nan ya cika if not wallahi kaf danginku babu mai gane kurkukun da zan kaika!" Kamin ya bashi amsa ya kashe wayar.Tura husna yai kan gadon dakin ya bude wayan yana qoqarin ciro sim din. Sai lokacin ta taso. "Make shirin yi haka?" Bai kulata ba ya zaro sim din ya karya. "Gentle ka bari kai baka san darajar so bane?" Ta fada tana goge hawayen da suka zubo mata. Ko inda take bai kallaba. Saboda baisan me zai iya mata ba. A yanda yakejinsa komai ma zai iya yi. Wayar ya doka da bango ta tarwatse. Ya tsaya ya dafe kanshi da hannuwansa duk biyun. Yau shine wani yake fadawa maganar da duk ranshi yaso. Yau shine aka tozarta. Tozarci mafi muni. Abubuwa da yawa sun faru da rayuwarsa. Sai dai babu wanda ya taba darajarshi irin nayau. Bai isheta ba ta hada masa da zagi cewar baisan darajar SO ba. "Akanme zaka fasamin waya? Saboda me? Kasan yanda..........." Bata qarasa ba ya dauketa da wani irin mari da saida taga wani haske da wasu kana nan taurari. Ta dafe kunci tana kallonshi. Komai ya tsaya mata. Muryarshi a dake yace "Da aurena akanki husna? Da darajata zakina waya da qato cikin gidana! Qarqashin ikona. Saboda bakisan daraja da haqqoqin aure ba ko? And you dare have the guts to question me? Wallahi bansan tsanar da kikaimun tai girma haka ba" Tsugunnawa tai a wajen tana wani irin kuka. Ya qare mata kallo kawai yana dana sanin wannan auren. Tun farkon shi yasan babu komai sai fitina a ciki. Da karin matsaloli a wajen shi. Fita kawai yai yana doko qofar da qarfi gaske. * Tunda husna take bata taba zaton akwai randa zataji kunyar wani dan adam kwatankwacin tayau bama. Taji ta muzanta. Maganganunsa sun sosa mata rai shisa taso tai tabarmar kunya. Sam marin dayai mata bai dameta ba. Domin ta cancanta yai mata fiye da wannan hukuncin. Ta jima da sanin cewar abinda take bashi da kyau saidai ta kasa dainawa. A kwanakin da suka wuce ta daina kiran ammar saboda tanajin kaman bata kyautawa aurenta. Saidai shi inya nemetan bata iya share shi. Bata san ta inda zata fara ba. Me zata soma gyarawa? Laifukan zunuban da suke kanta taji sun wani danneta lokaci daya. Da sauri sauri take maida numfashi. Tunanin mutuwa da kwanciyar kabari ta ziyarci zuciyarta. Tunanin yanda ta biye son zuciyarta da tunzurar shaidan ta aikata laifi mai girma. Astagfirullah ta shiga jerowa tana wani irin kuka. Bata san da wanne irin ido zata kalli prince ishaq ba. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣2⃣ Falon kasa ya sauka. Baya son ya shiga dakinshi dake cike da hotunan huddy yaga abinda kaddara ta ja masa. Fuskarshi na cikin hannuwan shi yana maida numfashi. Bai taba zaton akwai ranar da zai daga hannunshi wa mace ba. Saidai kuma bai taba zaton abinda ya faru yau zai taba faruwa ba. Hakama ciwon da yake jin zuciyar shi nayi. Yasan ya tsaneta a farko fine. Saboda yana dauka auren kwadayi tayi dashi. Amman wannan bai isa ta hukunta shi ta wannan hanyar ba. Asalima yanzun abinda yake ji game da ita shi kanshi bazai fassara shi ba. Baisan abinda ya kamata yayi ba. Jikinshi har wani kakkarwa yake. * Saida tai kukanta mai isarta sannan. Ko fuskarta bata damu data wanke ba. Ta riga da ta gama yanke ma zuciyarta. Zuwa zatai ta bashi hakuri. Zuwa tai wucewa zuwa bangaren shi. Kaman ance ta kalli kasa ta hango shi. Jitai zuciyarta ta sake karyewa. Da wanne idon zata kalle shi? Me ma zatace ne. * Yanajin zuwanta. Bai dago daga yanda yake ba. Saboda baya son ganinta sam sam a yanzun. Tsugunnawa tai gabanshi a kasa. Ya bude fuskar shi ya sauke jaijayen idanuwanta akan ta. Kasa hada ido tai dashi saboda wani kwarjini da kunyarshi data cika mata zuciya. Kafarshi tazo rikewa ya matsar da sauri yana fadin. "Don't..... Please ki tafi kawai" Girgiza kai tai tasa hannu tana goge hawayen daya zubo mata. Cikin kuka tace. "Dan girman Allah kayi hakuri. Ka yafemun......" Ji yake kaman tana goga masa gishi a sabbin ciwukan dayaji. "Dan Allah ki kyaleni. Just leave me the hell alone!" Duk da ba hayaniya yake ba. Muryarshi a dake take. Bude baki zatai ya katse ta da fadin. "Kibarni husna, laifina ne dana kasa sauke hakkokin ki da Allah ya doramun. Na biyewa son zuciyata. Hukunci na ne wannan........." Da alamaun gajiya sosai a muryarshi. Ga tunani ya masa yawa. Shima ya gane kuskuren daya aikata. Ko da baya son husna bai kamata dan yana gudun karin matsala yaki sauke hakkokin da Allah ya wajabta masa ba. Bai kamata ace yaki duba darajar ibadar da take cikin aure. Shisa Allah yai masa wannan jarabawar. Ya kuma dora masa wani azababben kishin husnar. Yanda husna ta yanke ma zuciyarta duk abinda zaiyi zata jure ta bashi hakuri. Zata sake gwadawa wayar shi dake ajiye jan table din wajen ta shiga ringing. Ko kallonta baiba harta tsinke. Ta kara daukar wani ruri. Ya duba likitan Nas ne. Dagawa yai yana addu.a Allah yasa ba wata jarabawar bace. Karawa yai a kunne yai shiru. Dakyar ya iya amsa sallamar da doc din yai masa. "Nas ya bude idanuwan shi. Saidai baiyi magana ba. Nasan zakaso ka sani......... " Baima bari ya karasa ba. Ya ajiye wayar ya lumshe idanuwan shi yana mika Godiyarshi Ga Allah madaukakin Sarki Mai Ikon rayuwa da mutuwa. Husna ya kalla badon ya daina jin bacin rai ba. Ko abinda ya faru ya wuce. Sai don girmab labarin daya samu yanzun ya danne komai. Hakan yasa yace mata. "Nas ya bude idanuwan shi" Fuskarta ta goge tana hamdala. Mikewa tai muryarta can kasa tace bara in dauko hijab. "Kiyi me?" Ya tambaya yana mata wani kallo daya sata jin ta tsani kanta da abinda tayi. A rauna ne tace. "Muje wajen Nas....." Girgiza kai yai sannan yace. "Believe me, after dazun Nas bazai so ganin ki ba..... " Wasu hawaye suka zubo mata. Ta goge su tace. "Ban roke ka karka hukuntani ba amman ka dubi girman Allah karkai mun hakan da haramtamun ganin Nas" Wuce ta yazo yi saboda yanda take neman karya mishi zuciya. Hannu ta riko masa tana fadin. "Allah idan bakaje dani ba. Ko ta katangane zanbi inba a budemun gate ba" Taso ta bashi dariya ya share. Hannun shi ya kwace yace. "Fine. Karki batamun lokaci" Kusan da gudu ta wuce shi ta hau sama. Ya girgiza kai murmushi na kwace masa. A wannan lokacin ne yasan ko da baya son yarinyar nan gaba daya. Ya soma sonta. Saboda jiyai ya yafe mata. Har zuciyarshi ya yafe mata. Rokar musu gafara yake wajen Allah na laifin da su duka suka aikata. * Har sukaje asibitin ko inda take bai sake kallo ba balle tai tunanin zai mata magana. Saidai sanda suka je Nas din harya koma bacci. Canjin da zaka iya gani an samu da idanuwa shine da kan shi yake numfashi. Babu taimakon komai saina Allah. Zama sukai. Prince ishaq can nesa da ita. Sai take jinta duk wani iri. Mumyn Nas ya fara kira ya sanar da ita da kanshi ci gaban da aka samu. Sannan ya kira umman shi. Sun jima suna waya da ita sannan ta bukaci ya bata Husna su gaisa. Kallonta taga yayi sannan ya tashi ya karasa inda take a dake ya mika mata wayar yace. "Umma nason magana dake" Gabanta taji ya fadi. Hannu na rawa ta karbi wayar. Tai sallama ta gaishe da ita a ladabce. Zata iya jin fara.ar umman ta cikin muryarta tace "Ya mai jiki kuma" A sanyaye ta amsa da. "Alhamdulillah umma" "Allah ya kara sauki. Dan Allah ku kula. Ki rike amana, kinga kalar rayuwar da baban yake fama....." Wata kunya taji don amana ta dade da watsar da ita. Ta daure tace. "In shaa Allah umma. Mungode Allah ya kara girma" Ta amsa da amin tai musu addu.a sosai sannan ta kashe wayar ta mika masa. Karba yai ya koma inda yake ya zauna. * Yau ko da kamala ya kawo musu kayan ciye ciye. Kowa daban daban yaci. Basu koma gida ba sai dare da doc ya tabbatar masa allurai da magungunan dake aiki jikin Nas ba zasu bari ya farka dan ranar ba. Saboda kwakwalwar shi na bukatar wadataccen hutu. Suna isa gida suka hau sama. Yana shirin nufar bangaren shi tace. "Gentle......" Bai juyowa ba amman ya tsaya da tafiyar da yake. Hakan yasa ta fadin. "Dan Allah ka yafemun. Nayi kuskure mai girma. Ka yafemun..... " Yanajin tayi shiru yaci gaba da tafiya abin shi. Yana son sosai ta gana kuskuren abinda ta aikata. Ya kuma yarda da ita cewar ba zata sake ba kamun nan ya soma goge mata wannan yaron a zuciya. Ta lumshe idanuwanta ta bude su hadi da sauke wani dogon numfashi. Bakomai zata ci gaba da kokari tunda ita ta aikata laifi. Dakinta ta wuce itama. Rigar jikinta kawai ta sake dan sunyi isha.i a asibiti. Ta kwanta. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣3⃣ Allah sarki rayuwa. Bata taba zaton zata juya da ita ta wannan fannin ba. Wasu hawaye masu dumi taji sun zubo mata.Sai yanzun girman laifin datai yake dawo mata. Ina hankali da iliminta ya tafi take waya da namijin da ba muharraminta ba da aurenta. Inalillahi wa ina ilaihi raji.un. Wasu maganganu suka dawo mata a daren da za.a kawota gidan prince ishaq. "Husna baki taba bijirewa umarni na ba sai akan auren nan. Ba don bama son yaron da ke kike so bane muka hana shi ke. Sai don mu mun hango abinda baki hango ba. Aure an daura. Ki dauka hakan shine alkhairi a rayuwarki. Inhar kikai abinda kika kaso auren nan Allah ya isa tsakanina dake!!!" "Ya Allah" Ta furta tana sake juyi kan gadonta maganganun babanta na dawo mata. Ta rasa yanda akai komai ya juya mata haka. Lokaci daya farkon abin ya dawo mata. * Husna itace yarinya ta uku cikin yaya biyar da Alhaji abdullahi da matarshi Haj. Baraka suka mallaka. Babbar yarsa mace ce wato haj.fatima. Tana da aure harda yara uku. Sai namijin dake bi mata Aminu. Da shima yana da aure. Sai husna. Akwai tazarar shekaru kusan bakwai tsakanin su da aminu. Maheer sai autarsu aisha. Baban su dan kasuwa ne. Estate guda gare su da gidaje ashirin cif a ciki. Family dinsu ke cikin wajen gidaje goma sha biyu. Sauran ne kawai baki. Sun samu wadatacciyar tarbiya da ilimi na addini dai-dai misali. Husna tagama secondary school da shekaru sha bakwai tai Nasarar samun gurbin karatu a kano poly inda take diploma dinta akan computer science. * Ba zata manta haduwarsu ta farko ba da ammar. Kaya tai loading harda system cikin wata jaka. Tun daga gida mamansu tace mata hannun jakar bazai dauki nauyin data loda masa ba tai gardama. Aikam tai sa.a hannun jakar ya tsinke. Kasancewar bamai zip bane komai yai kasa. System dinta kadai ta iya tarewa. Komai ya watse kasa. Jitai kaman ta saka kuka dan takaici. Bama tasan ta inda zata soma tattara su ba. Ta tsugunna ta soma da maths set dinta. Kaman daga sama taji ance "Dole kiyi bari wannan books din sun maki nauyin dauka" Dagowa tai suka hada ido. Murmushi ya qwace mata. Shi ya tayata ta tattara komai. Haduwarsu ta biyu islamiya zataje anan ne taji sunan shi yaji nata har sukai musayar number. * Ammar kam shine babba gidansu sai kannensa maza. Babansu ba wani mai hali bane. Rufin asirin Allah. Lokacin da ya hadu da husna yana level 2 bawani girman kirki ne dashi ba. Cikin watanni biyu sukai wata irin shakuwa taban mamaki saboda duk wani abu da yake bukata a wajen mace husna ta hadashi. Ba fara bace can. Tana da wani hasken fata mai kyau. Da manyan idanuwanta tubarkalla. Bakinta da hancinta kaman ita ta zaba. Yakan mata tsiya wani lokacin cewan tsayinta bazai wuce damtsen hannun shi ba. Dan kuwa gajera ce da jiki madaidaici. * A shekaru biyu da dori da sukai da ammar duk wani wanda yake tare da ita yasan shi. Duk wani buri na rayuwarshi husna ce. Duk wani mafarki na har abadanta ammar ne. Lokacin data hada diploma dinta ne babansu ya bukaci yaron da take so ya turo manyan shi. Labarin ya daga musu hankali saboda ammar a lokacin yake shekarar shi ta karshe a karatu. Yana da gidan da zasu zauna. Saidai bashida sana.ar da zata rike su. Ko da magabatan shi suka zo basu boye ma baban su husna ba. Sun sanar dansu bashida wata sa.a saidai yana matakin karshe na karatun shi. Sam babansu husna bai musu alkawari ba. Asalima yabar magana ne kan cewar in har yarshi ta samu tsayayye nasu dan bai samu sana.a ba zai aurar da ita. Babu kalar tashin hankalin da basu shiga ba. Husna ke karfafa masa gwiwa cewar saita kula wani ne za.ama ganshi a aura mata. Saidai batasan me kaddara ta rubuta mata ba. * Lokacin da ammar ya tafi bautar kasa ne. Kasancewar estate dinsu yana kusa da gidan wazirin kano. Husna ba zatace tasan wata alaka dake tsakanin babanta da wazirin kano ba data wuce makwabta ka. Asali ma basu ko taba shiga gidan ba. Saidai su wuce shi in hanya ta kama. * Bata san da kaddarar data hada babanta da wazirin kano ba. Alaka ce data samo asali sanadin makaranta. Tare sukai primary school. Lokacin da mai martaba yazo masa da bukatar a samo ma danshi yarinya mai hankali. Ba sai yar sarauta ko yar wani mai kudi ba. Yarinya yar babban gida. Yar manyan mutane. Wazirin yaranshi duk mazane. Macen shi yarinya ce dabata shige shekara goma ba a lokacin ne yaima baban husna magana akan nema ma prince ishaq auren yarshi idan ya amince. Yaji dadi sosai da wannan girmamawa da yai masa dan haka ya amsa shi. * Husna ba zata manta wani yammacin ranar juma.a ba. Kwance take suna waya da ammar. Kasancewar yanzun sai suyi sati biyu ma zuwa uku basuyi waya ba. Wani kungurmin kauye ne yake bautar kasa. Sai yahau abin hawa tafiyar awa daya da wani abu ya shigo gari dan ya samu network yaji muryarta. Aisha ta shigo dakinta tace mata tazo babansu yana kira. Kaman zasu sakama juna kuka sukai sallama. Tun a hanya ta rasa me yasa take jin gabanta na wani faduwa. A haka ta karasa falon babansu ta gaishe dashi. Mamanta ma tana nan. Bayan sun gaisa a ladabce babanta ya sa magama a nutse. "Husna kasancewar ina da tabbaci akanko yasa na amsa neman aurenki jiya da dare. Yau din nan zasu kawo komai. Idan an dade wata biyu..........." Tun daga wajen kalmar "Aurenki" kunnuwan husna suka daina jin wani bayani. Komai ya daskare mata. Zuciyarta na wani mata nauyi. Lumfashinta taji yana shirin daukewa. Cikin tashin hankali tace. "A.a baba.... Wallahi bana son shi.... Mama karku mun haka......." Daga ranar tashin hankalinta ya fara. Babu kalar haukan da batai ba amman a banza. Aka kwace mata wayoyi duka. Wata biyun nan da yan kwanaki shi ya rage musu su cimma burinsu ita da ammar............! **** **** Wani nauyi da zuciyarta tai mata ga numfashinta na fita sama sama yasata tashi zaune. Addu.o.i take karantawa dan Allah ya bata karfin halin hana zuciyarta maidata rayuwarta ta baya. Mayar da ita watanni biyu na rayuwarta da suka fi kowanne kunci. A haka bacci ya kwasheta da mafarkai kala kala. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣4⃣ Da safe tunda tai sallar asuba ta kasa bacci. Ta saba a wannan lokacin ko basuyi waya da ammar ba zai mata text kamun ta koma bacci. Wanka tai tasa kaya. Kwalliyar datai bamai yawa bace. Ta koma ta kwanta. Tuno ammar kawai wani zafi zuciyarta take. Saboda kuskuren da sukai ta aikatawa. Kalar kalaman da suka dinga gaya juna da igiyar aure akanta da ta dabaibayega ga barin ko da daga murya ne ga namijin daba muharraminta ba. Ballantana kalamai masu zafi. Batai kokarin tarbe hawayen da suke zubo mata ba. Qwanqwasa kofar dataji anayi ne ya katse mata tunanin da take. Hawayen dake fuskarta ta goge sosai ta dai daita muryarta sannan tace "shigo" a hankali. Turo qofan yayi. Harya tako yazo bakin gadonta ya zauna bata dago ta kalle shi ba. Batai zaton shi bane saboda tasan laifin datai masa. Da ka yanda ko kallonta baya sonyi duk jiya. "Hussy......." Ya kirata da wani yanayi da saida taji yarr a jikinta. Dagowa tai ta kalle shi. Fuskar shi dauke da mamaki yace "kukan me kike?" Wasu hawayen taji suna shirin zubowa. Kamin tai wani abu ya tallabi fuskarta da hannayensa. Baya son kukan nan ko kadan. Yace "Everything is gonna be okay.....banson kukan nan kinaji!" Daga mishi kai tai alamar eh. Ya lumshe idanuwansa ya bude su. Cikin taushin magana yace "hussy banson ana amsamin magana dakai, idan na miki magana ki bude baki ki amsa ni" "Kayi haquri" Ta fada muryarta na rawa. Sakin mata fuska yai. Duk yanda yake jin son ce mata ya yafe mata ta daina damuwa ya danne. Kwali ne gefe bama ta kula da shi ba. Ya dauko ya dora akan jikinta. Ya soma magana "Kiyi hakuri da daga hannuna danai akanki. Ki yafemun...." Bude baki tai zatai magana dan bataga me yasa yake bata hakuri ba ya daga mata hannu alamar ta saurare shi kawai. Yaci gaba da fadin. Kiyi hakuri da wannan wayar. Akwai sim da komai a ciki. Nasa a kawo miki irin ipad dina.Cikin week din nan. Munyi alqawari da Saurayinki.......! Yanda ya ja kalmar saurayinKI din saida yasa ta dan razana. Kamin ya ci gaba da fadin "so zaki iya daraja dokokin Allah dayake kanki na aure badanni ba dan banda wannan mutuncin a idanuwanki har zuwa lokacin da alqawarinmu zai cika" Shiru husna tai wasu hawayen nason zubo mata. Idan har tace baida daraja a idonta karya take. Tayi shiru ne kawai dan tasan yanzun bazai yarda da duk wani abu dazai fito bakinta ba. Kuma bataga laifinshi ba Jin tayi shiru ta sadda kanta qasa yasa shi saka hannu ya dago da habarta. "Kar hawayen nan ya zubo fa" Ya fadi. Wata sumba mai taushi ya manna mata a kunci. Sannan ya sakar mata fuska. Jin wani dumi da wajen ya dauka yasa husna kai hannu ta shafa ta tabbatar babu abinda ya samu wajen. Yana kallonta gira ya daga sama cikin alamar tambaya sannan yace mata. "Gogewa kikai?" Kai ta girgiza masa. Da sauri tace. "A.a" saboda ta tuno kashe dinshi. Daure fuska yai. Tai raurau da ido kaman zatai kuka. "Ki shirya zamuje wajen Nas" Bai jira amsarta ba ya tashi ya fice. Ta sauke wani numfashi. Dan tun jiya wani tsoro tsoronshi take jima. Yanzun sai taji ya rikita mata lissafi duk ta daburce. Hannu takai zata sake taba kuncinta ta fasa. * Wajen Nas suka wuni. Yauma kaman jiya bacci yake yi har dare da suka taho bai farka ba. Wani sha mata kamshi yake. Tunda yabata wayar magana bata sake hadasu ba. Fuskarshi normal. Kawai dai batajin dadin yanda yake shareta. Sai takejin lefinta like a fuskarta. * Suna hawa sama ta soma takawa zuwa bangarenta ya kira sunanta. Wani yarr taji. Muryarshi ta wani kara budewa ganin ta juyo yace. "Zo" A hankali ta taka inda yake ta tsaya. Matsawa yai kusa da ita sosai ya hade space din data bari. Kan kirjinshi take sauke numfashi. Zuciyarta na wani irin dokawa. Kanta a kasa. Saida yadan kwanto kanshi sannan ya sumbaci kuncinta. Cikin kunne a hankali yace mata. "Ki kalle ni" Yanayin yanda take ji da yanda yai maganar ne ya sata kasa musama umarnin shi. Idanuwanta ta sauke cikin nashi da suka wani shige ciki. Wani irin dumi taji gaba daya jikinta ya dauka da tasan ba zazzabi bane. "Good night" Ya fadi muryarshi tana wani amsawa cikin kunnuwanta. Kamun ta gama sanin me yake faruwa yabar falon. Kujerar wajen ta kama ta zauna. Tana maida numfashi. Batasan meke damunta ba. Tadai san kafafuwanta ne basu da karfin kirki. Takai mintina goma a wajen sannan ta iya tashi ta koma dakinta da wani yanayi da ya dasa mata. * Juye juye kawai yake kan gadon shi. Rabon dayaji wannan yanayin harya manta. Hussy.....huddy ya rasa meye hakane yakeji. Bai taba zaton cewar zai sake samun soyayya ba sai yanzun.Abin har tsoro yake bashi. WATA BAKWAI 7 kawai ya dauka.Alqawari abune mai girma. Bacin raine ya saka shi ya dauki alqawarin da yake jin bazai iya cika shi ba. Abinda yasan ya zama dole a gare shi yanzun shine ya koyawa hussy soyayyarshi. Hakan abune mai matuqar sauqi a wajensa. Duk da kishi yana damunshi. Yana kishin ammar da yasan ta gama furtawa kalamai da baya son zuciyarsa ta soma qiyasta masa. Yanzun daya ganta. Yanayin yanda ta nuna rauni. Idanuwanta....komai nata ya kasa jurewa. So kawai yake yajita a jikinsa. Addu.a ya dinga yiwa huddynsa. Tabarshi da kewarta da yasan har abada bazai daina ba. Sai dai yanzun yana jin ya karbi rashinta a abu rubutacce. Yanzun yakan mata addu.a fiye da da. Kuma yana godiya ga Allah daya bashi damar sanin ta a rayuwarsa. Ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe idanuwansa. Ya so huddy so mai yawa. Ya tuna wani lokaci can baya. *** *** Hawaye yaji suna bi masa fuska. Why? Meyasa za.a canza wannan tsarin a zamaninsu. Bai taba son sarauta ba. Babu komai cikinta sai wahala da rikici. Duk ya gama sakankancewa akan mulki bazai taba juyowa kanshi ba. Duk a ture wannan ai bashi bane babba da za.a nada shi a matsayin magaji. Dafa mishi kafada yaji anyi. Hannunta ya fita daban dana kowa.Don yakanji tabawar da duk zata masa har ranshi. Juyowa yai ya kalleta. Hannu tasa tana goge mishi hawayenshi. "Yaya kana so nayi menene? Ka daina. Komai ya faru akwai dalili. Hikimomi na Ubangiji suna da yawa sosai. Sun wuce tunani. Ba zamu taba fahimtar hakan ba. Sai dai muyi qoqarin gode mishi da addu.a ya kawo mana komai cikin sauqi" Baya taba nuna rauni a gaban mutane. Amman huddy dabance. Duk da qarancin shekaru irin nata in tana wani abun har mamakinta yake Janyota yai ya zaunar da ita gefen shi. Yanda yakeji a kanta yanzun yasa sai dole yake bari jikinsu na haduwa. Idan ita da karancin shekaru a tattare da ita. Shi babu. A hankali yace "huddy ba zasu fahimta ba. Bana son nauyi. Bana son mulkin nan saboda yana da rikici sosai. Zasu iya komai kan shi. Bana so wani abu ya sami........." Kamin ya qarasa ta rufe mishi baki da hannunta. Cikin idanuwanshi ta kalla sannan tace "Allah yasa zabin dayai maka shine mafi alkhairi a lahirarka da duniyarka. Allah ya daukaka ka. Daukaka mai daraja yayana. Karkaja da Ikon Allah. Ka gode masa kawai" Alhamdulillah! Ya furta a fili. Duk da hawayen da yakeji bai hana shi murmushi ba. Allah ya kai Rahma kabarinki hudisa. Zai iya rantsewa yanajin muryarta cikin kunnuwanshi tana masa dariyarta kan abinda yakeji game da hussy Da murmushi a fuskarshi Bacci ya dauke shi cike da mafarkin hudeesa da husna. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣5⃣ Da wuri ya shirya yau saboda zuwan su mumyn Nas. Ya fito zuwa babban falonsu. Wayarshi ya dauko.Ya kira num din husna dayai save tun jiya. Ringing biyu tai ta dauka. Cikin sanyin muryarta tai mishi sallama. Ya amsa "kin tashi lafiya?" Ya buqata. "Alhamdulillah" "Ina babban falo" "Owk tam barin fito" Bai amsa ba ya kashe wayar. Ya sauke wani numfashi da baisan dalilinsa ba. * Shigarta simple cikin doguwar riga irin ta mutanen sudan pink wacce tai matuqar karbarta. Har inda yake ta qarasa. Ta samu waje ta zauna. "Ina kwana ta furta a hankali" Sai lokacin ya dago ya kalleta.Ta mishi wani irin kyau daya kasa fadi. "Hussy" yaja sunanta. Saida taji wani iri kaman ko yaushe. Indai zai kira sunan ta haka. Muryarsa na shigarta har bata son tasirin da take mata. "Mun gaisa yanzun fa" Yace da yanayin gajiya a muryarsa. "Hmm yaushe zamu tafi wajen nas?" Ta tambaya tana sauya maganar. Tunda ta samu yau ya soma mata magana ba kaman jiya ba. "Sai su mumynsa sun qaraso" Ya amsa a taqaice. Jingina tai da kujerar sosai. Kowa yai shiru. Can ya nisa yace "hussy kiban labari shirun nan ya isheni" Yakan bata mamaki haka rannan wai ta bashi labari. Ita kam wanne labari zata bashi. Dan dai yau bata son su wuni irin jiya. Tana son yadan mata magana ta samu damar da zata sake bashi hakuri. "Wanne irin labari kake so?" Ta ce tana maida hankalinta kansa. Gyara zama yai ya kalleta yace "ko wanne iri ma" Yanda yai da fuska ya bata dariya sosai. Ya sake wani tabare fuska. Saita tsinci kanta da son ja masa hancinsa da ya burgeta. Wani irin kallo yake mata data kasa fahimta. Shikuma abubuwa da yawa ne suke yawo a zuciyarsa. Kewar huddy. Yana mamaki yasan soyayya. Amman akan hussy ya rasa ma ko meye a yanzun. Dan wannan ya girmi so. Yakanji yanayi da dama kan huddy. Amman ba koyaushe yake kallonta yaji yana son jin duminta jikinsa ba. Sai in ita ta taba jikinsa. Amman hussy. Ko kallonshi tai da idanuwanta din nan a cikin kwanaki kadan da suka wuce sai yaji jikinsa ya dauki dumi. "Dariya ko? Zo nan" Ya fada yana nuna mata gefen shi. Da sauri ta hadiye dariyar ganin yanda fuskarshi ta sauya babu alamun wasa. Idanuwansa ya zuba mata yana mata wani kallo. Duk sai takejin ta daban. Ga kunya da taji ta rufeta babu dalili. Ammar yakan kalleta sosai haka. Batare da taji komai ba. Amman prince ishaq. Kominsa dabanne. Shi kanshi dabanne. Da ta tsane shi amman yanzun tsanar sake kala take a hankali. Bata taba zaton cewar zata rasa kome take ji game dashi ba. Muryarsa tafi komai tasiri a kanta.Qamshinsa intaji sai taji kaman harda duminsa. Hakan nasa ta son jinta kwance kan faffadan qirjinsa. "Zakizo da kanki ko ni inzo?" Maganar shi ta katse ta. Dakyar ta matsa kusa dashi inda ya nuna mata. Kafarshi daya ya maida kan kujera ya gyara zama yanda zai fuskance ta. Yana son yanda manyan idanuwantan nan ke fitowa waje inta tsorata. Da sauri tace. "Dan Allah kayi hakuri" "Inyin hakuri dan kinmun dariya?" Ya bukata yana kallonta. "A.a kayi hakuri dan girman Allah. Ka yafemun" Sarai tun farkon maganarta yagane me take nufi. Shiru yai kaman yana nazarin me tace. Bayan tun shekaranjiya ya gama yanke hukunci. "Dan Allah..... " Ta sake fadi muryarta na rawa. Dan tana tsoron me zatace ma Allah inta mutu a yanzun. Laifinta mai girma ne. "Fine.... " Yace yai shiru. Ganin bashida niyyar sake cewa wani abu yasata fadin. "Haba mana gentle. Fine fa kawai kace" Wani juya mata idanuwanshi yai a yangance yace. "You need to sweat a bit more....fine for now" Batace komai ba. Zata dauki fine din a yanzun. A hankali zai furta ya yafe mata da kan shi. "Uhum ina jinki" Ya fadi yana sake gyara zama. Muryarta a hankali tace. "Nikam wallahi na rasa labarin dazan baka. Film? Littafi?" Daga mata kafada yai alaman duk wanda yai mata. Muryarta a nutse ta soma bashi labarin "Knock knock by james hardley chase" Tunda ta fara idanuwanshi ne kafe kan labbanta. Yanayin yanda suke motsawa da duk kalmar da take fada. Idan kaganshi zaka rantse wani abu yake karanta daga labban nata. Kula tai kaman ma ba sauraranta yake ba. Fuskarta kawai yake nazari. Hakan yasa tace. "Wai kana ma jina ne?" "Inajinki mana. Massino ya zauna daram kan power yana controlling duka unions" Tai mamaki dan bata ma zata yanaji ba. Langabe kai tayi tace masa. "Zan karasa maka anjima. Bakina ya gaji" Baice mata komai ba kallon fuskarta kawai yake. Labbanta da bai taba karema kallo ba ya zuba ma ido. Ba karamin ja mishi hankali sukai ba. Hannunshi yakai yasa yatsan shi ya zagaye yana dangwalo man dake lebenta. Husna ta wani daskare waje daya. Banda bugun zuciyarta da take ji har cikin kunnuwanta. Kallon yatsan yai. Da man daya dangwalo a jiki. Ita kuma shi take kallo. Ga mamakinta a nashi leben na kasa ya shafa sannan a hankali kaman mai gwada wani abu ya tsotse leben daya shafa ma man. Wani dumi taji jikinta ya dauka. Kawai so yake ya dandana labbanta kuma wannan ba lokacin daya kamata bane. Babu yanda za.ai ya hada bakinshi da yarinyar da bata son shi. Ko ya yake ji akanta kuwa. Hakan ya sashi dandana kalar man da yasa yaga labbanta sunyi wanu pinkish kala mai haske. Zakin dayaji me yasa shi yamutsa fuska. Kallon ta yai cikin ido yace. "Zaqi.... I mean man dake lips dinki" Harshenta tasa ta laso kaman bata taba sanin yanda man leben yake ba. Wani numfashi yaja dayasa kallon shi sosai. Ringing din wayarsa ya katse su daga duniyar da suka shiga.......! 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣6⃣ Wayar ya dauka. Mumyn Nas ce hakan ya tabbatar mishi da isowarsu. Dan haka yace ma hussy ta dauko alkyabbarta ta saka su jira qarasowarsu. Sai bayan ta fito ne ya kalleta yace "me kikaci?" "Bana jin yunwa" ta fadi. Lokaci daya fuskarsa ta sauya zuwa yanda ta saba ganinsa farkon aurensu kamin ta san fara.arsa. "Muje dining room din" Ya umarta. Yanayinsa ya nuna mata ba zai karbi wani uzuri ba dan haka tai gaba yana binta har suka qarasa. Zama yai yace mata "Maza ci wani abu da sauri kamin su qaraso" Babu yanda zatai haka dolenta ta danci plantain da dankalin turawa. Ga kunyarsa da ta tsinci kanta ciki saboda kallon da yake mata. A hankali tace "kai ba zakaci komai ba" "Na sha malt banjin saka ma cikina wani abune" Ya furta yana miqewa. Binsa tai a ranta tana fadin. Wato shi baya son sakama cikinsa wani abu. Sai ita yai ma dole. Suna fita babban falo sukaji sallama. Tare suka amsa. Da fara.ar prince ishaq ya qarasa ya tarbo su yana fadin "mumy sannunku da isowa" Cikin sanyin murya husna tace musu "barkanku da isowa" Mumyn nas ta kalleta tace "Ma shaa Allah. Sannu in-law" Dan bata taba ganinta ba. Sanda akai auren tana england dubo kanwarta da akaima dashen koda. "Ku qaraso ciki mana" prince ishaq ya fadi. Yana shirin juyawa yaji an taho da gudu ana fadin "yayaaaaaa" Kamin ya qarasa juyowa ta ruqunqume shi kaman zata karya shi. Ya lumshe idanuwansa ya budesu a hankali. Wanni aikin sai auta.Baisan da ita za.azo ba. Wani son kanwarshi yaji ya cika masa zuciya fal. Yayi kewarta sosai. "Auta saikin karya shi ke yaushe zaki natsu ne bakya ganin antynki tsaye" mumyn nas ta ke fadi tana murmushi. Auta ta sake prince ishaq tana dariyarta cikin tabara tace "mumy ai na dade banga yaya bane shisa. Laaaa antyyy wlh kin hadu" ta qarasa wajenta tana riqo mata hannu. Shafa kanta husna tai tana murmushi farat daya yanayin yarinyar harya shiga ranta. Tai bala.in kama da nasir. Waisu haka suke da shiga raine? Ta tambayi kanta. * Bayanda prince ishaq baiba ko hutawa su danyi. Mumyn Nas taqi tace suje asibitin dan da sun ganshi ba jimawa zasuyi ba komawa zasuyi. Husna tace "Haba mumy da wuri haka na dauka zaku kwana ne ai" Wai ai kam yau zamu juya in-law. Ba zamanmu nasir yake buqata ba. Addu.a ne. Tunda duk gaku anan din. Da munga yanayin jikin nasa zamu koma in shaa Allah" Haka suka haqura tunda mumyn nas sam taqi jinsu. Suka nufi asibitin. * Suna bayan mota zaune ita da prince ishaq kasancewar mota daban daban ce data su mumyn Nas tace mishi "kana ganin ya kamata auta taga Nas kuwa. Kaman shekarunta sunyi qanqanta taga tashin hankali har haka" Dan autar kam duka bata fi shekaru bakwai ba. Murmushi yai. Hannunta ya riqo.Ya hada yatsun su waje daya. Yace "ki yarda dani hussy a rayuwa irin tamu auta taga abubuwa da yawa. Wannan ba komai bane." Saita tsinci kanta da sake riqe hannunta cikin nasa sosae. Tana mamakin hargitsi dake cikin sarauta. Lallai mutane na kuskure kan mulki. Daga nesa saikaita sha.awarsa har kana jin dama kaine matsayin. Sai yanzun take lura babu komai cikin mulki musamman na sarauta banda rashin kwanciyar hankali da tarwatsar farin ciki. * Har suka qarasa asibitin suna riqe da hannun juna saida suka fito ne sannan. Nas yanata bacci a fadar likitansa. Daqyar ma suka barsu suka shiga gabaki daya da sunce ba.a son hayaniya ta tashe sa anfi so ya farka da kanshi saboda magungunan da ke aiki. Sunkai mintina ashirin zaune shiru kawai. Kamin mumyn nas ta miqe. "Allah ya bashi lafiya" ta furta a sanyaye. Su duka suka amsa da amin. "Is he gonna be okay?" Auta ta tambaya muryarta can qasa. Tsugunnawa prince ishaq yai yanda tsahonsu yazo dai dai. Ya dafa kafadunta cikin taushin murya yace mata "we don't know yet. Amman muna masa addu.a." Husna ta faki ido tadanyi qasa ta mintsine shi a baya. Yaji zafi ya dake kawai ya miqe. Ta riqo hannun auta da idanuwanta suka cika taf da hawaye. Tajata jikinta. A hankali tace "karki damu zaiji sauqi in shaa Allah. Kinga bacci yake. Daya tashi zan kira mumy a waya ku gaisa." Kai kawai auta take daga ma husna saboda kukan da yake neman cin qarfinta. Hada ido sukai da prince ishaq ta galla mishi harara. Duk shi yaja. Wannan yar yarinyar saboda Allah. * A wajen mota sukai sallama da su prince ishaq aka tafi a mayar dasu airport subi jirgin dazai koma kano qarfe 12. Saida suka shiga mota su kadai sannan ta juyo ta kalle shi sosai a dake tace "meke damunka?" "Me nai maki zaki mintsine ni" Ya buqata shima a dake. "Saboda me zaka fada ma auta cewan ba lallai bane nas ya tashi. Baka ga tai qaranta ba?" Husna take fadi ranta a bace. Shi sai yaga ta qara kyau yanda ta dage tanata masifa. Baisan sanda dariya ta kubce masa ba. Ta sake hade rai duk da kyau da taga ya qara mata. Inyai dariya takan bayyana farin cikin a fuskarsa da wani kwarjini naban mamaki. Bata san lokacin data ja mishi hanci ba. Ya ture hannunta yana fadin "oww hussy da zafi fa" Ammar! Zuciyarta ta furta a hankali. Dannewa tai ta kalli prince ishaq dake gabanta. Tace "abinda kai baka kyauta ba sam" Da yanayin muryarta yace "ni bazanyi qarya ba" Dariya ya bata sosai. Ya tsaya yana kallonta. Komai nata yasha ban ban dana huddy. Komai da yake ji a kanta dabanne da yanda yaji akan huddy. A lokaci daya kuma su dukansu sunyi tarayya a zuciyarsa wajaje daban daban. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣7⃣ *Ban taba sanin rubutu zai jamun addu.o.i da fatan alkhairi har haka ba. Nagode sosai da masu kirana da masu mun text. Allah ya biya muku bukatunku na alkhairi. ILYG as much as you love wata bakwai. HUSSAINA uban diya mai "Kaddara ko sakaci" Godiya ta musamman da kauna.* Mintsininta yai a cinya bata zata ba. Tako saki wani qaramin ihu. Dan taji zafin mintsinin. Da sauri ya rufe mata baki yana zaro ido. "Shh hussy bamu kadai bane a motar fa akwai driver" Yake fadi cikin sanyin murya. Duk da akwai iyaka tsakaninsu. Ta rausayar dakai gefe tace "amman kasan da zafi aiko?" Kallonta yai ta qasan idanuwansa "umm qaramin wanda kikamin ne" ya fadi yana daga mata gira. Dariya tai sosai. Ta rasa yanda akai yake yawan sakata dariya. Tasan ammar kan sakata dariya amman ba kaman wannan ba. Yanayin yanda yake canza fuskarsa zuwa yanayin abinda yake so ne yake burgeta. Yana sa ta manta da damuwar da takanji a yanzun. Kewar ammar tana nan daram. Sai dai shi din ya cika wani gurbi da bata son da zamansa ba ma. Kallonta yake yanda tai zurfi cikin tunani. Zaiso sanin me yake yawo cikin kanta saidai shiba mutum bane mai yawan bincike. Muddin abinka bai shafe shiba yakan baka wajen da kake buqata kai taka rayuwar. Hannu yasa ya tallabo habarta ta sauke idanuwanta cikin nasa. Tsoro,shakku da fargaba da wani yanayi da baison meye ba cike da idanuwanta. Sauke su tai a hankali daga nasa idon zuwa fuskarsa. Gara ta kalli komai a yanzun da cikin qwayar idanuwansa da take fisgarta zuwa wata duniya mai zurfi. Hada goshinsa yai da nata. Tana jin hucin numfashinsa kan fuskarta. Ta rufe idanuwanta. Bata son yanayi ko daya da take ji a jikinta. In batai wasa ba prince ishaq zaisa ta manta kanta bama ammar kawai ba. Lokaci daya taji zuciyarta ta fisgeta zuwa wani lokaci. ' *** *** "tawan wlh kewarki ta dameni na ma kasa zama lectures" Na samu na gudo gida fa. Murmushi tai "haba nawan abinda zaka dawo ka sameni saika gudo. Bana son kana saka wasa kaga dai shekarar qarshe kake." Dariyarsa yai mata cikin muryarsa mai sanyi yace "haba kin fiyemin lectures din yau. Inban ganki ba ba fahimtar komai zan ba" Hmm ammar.......! *** *** Bata son ta furta ammar' a fili ba sai wani irin dilla taji mai zafi kan lebenta daya dawo da ita hayyacinta. Owww ta fadi tana ture shi. Lebenta ta taba da dan yatsa ta dawo dashi zuwa dubanta dan zatonta yai jini. Tana shirin yin kuka ta kalli prince ishaq da saida ta tsorata da yanayin fuskarsa. * Wani abu yaji ya tokare masa wuya mai daci dashi bai fito ba shi bai koma inda yake ba. Qirjinsa yai wani zafi. Yana tare da hussy har tunaninta zai kaita kan 'ammar. Hannuwan shi yasa ya janyo gab dashi sosai. Goshinsa ya hade da nata yana kallonta. Numfashi yake maidawa a hankali yana son controlling abinda yake ji. Da aurensa akanta takejin tana da iko ko damar da zatai tunanin wani. WATA BAKWAI 7!!! Kacal yake dasu ta so shi. "I am sorry" ta furta tun kamun abinda take gani a fuskarshi ya fito fili. Muryarta ta katse mashi tunanin da yake. Hannunta ya kamo ya dora saman qirjinsa.Ya hada da nasa ya danna. Tanajin yanda zuciyarsa ke dokawa. A dake yace "kinsa tana bugawa a bangaren da nai zaton ya jima da daina aiki. Zaki iya taimakawa yanayin raunin da ke jikinta. Ki danne son 'ammar'......" Yanda ya fadi son ammar saida jikinta ya amsa. Yaci gaba "sorry na dillar maki lips ko? Ya qarasa yana yatsina fuska.Ta gyada kai alamar eh dan har lokacin wajen yana mata zafi kuma ta tabbata sai jini ya kwanta. Ta sake saka dan yatsa ta taba. Duk yana kallonta. "Good" ya furta ya dora da "inkinzo fadin sunanshi a gabana ki dinga tunawa dan zan maki wanda ya fishi a gaba" Goshinta ta cire daga nashi. Wato wanda yafi wannan ma. Naushin masa kafada tai da qarfi tako ji kaman ta naushi dutse saboda taurin muscles din dake tattare wajen. Ta lanqwashe yatsu. Wayyoo owwhh take fada tana yarfe hannu. Yai dariya dai dai lokacin da motar ta tsaya alamar sun qara so gida. Bude masu qofa akai suka fito. Husna riqe da hannunta tana murza yatsunta har suka qarasa can cikin gidan. Ya wani basar kamar bashi ya gama dariya cikin mota ba. * Cikin gida suka shiga. "Gentle" Ta fadi. Ya juyo yess! Saita rasa me ma zata ce masa saboda yanda ya kafa mata idanuwan shi din nan. Ta kasa sabawa da kalar kallon da yake mata. Kodan koyaushe daban take ganinsa. Intaso ta gane yanayin kallon anjima bada irinsa zai dubeta ba. "Ina jinki hussy" ya fadi a qagauce da son jin me zatace. A daburce tace masa "ina son inje saloon ne daman a wankemin kaina and......." Daga mata gira yai data soma sabawa dan yana yawa yin hakan duk da ma.anarsa yawa gareta a wajensa. Duk ta daburce kaman mai koyon magana. Daqyar ta hadiye miyau ta ci gaba da fadin "Ina son inje wajen kausar in babu damuwa" Sauke ajiyar zuciya yai. "Ki kira kausar ta turo address dinta a kaiki.Masu tsaro zasu rakaki. Su jira ki gama ko yaushe ne su dawo dake gida" "Saloon dinfa?" Ta tambaya tana shagwabe mishi fuska.Ya girgiza kai "Ki haqura ba yauba. Saboda dalilai da yawa" "Amman......." Ta soma yanda ya zuba mata idanuwa yasata yin shiru. Ta rasa me yasa yake bala.in mata kwarjini haka.. "Good Banson gardama..." Bata sake cewa komai ba harya wuce sashinsa. * Itama nata bangaren ta wuce. Kan gado ta kwanta. Yanayin komai da suke ita da prince ishaq na dawo mata. Wani abu na mata yawo cikin zuciya. Ga ammar ta kasa daina jin kome take ji a kansa. Abinda yake bata mamaki yanayi kala daban takeji akan su shida prince ishaq. Shin wanne ne so a ciki? Ko dai qauna, so da kuma shaquwa abubuwane daban bata sani ba wai. Tabbas basukai tsayin lokacin da a tunaninta zasu shaqu da prince ishaq ba. Qaunarsa fa? Tsana na juyewa zuwa qauna ne. Son shi fa? Um to zuciyarta na mata wasi wasi saboda indai yanda takejin ammar a zuciyarta shine so to wani abune daban kan prince ishaq. Abu can cikin zuciyarta manne da qamshin sa kawai intaji yakan tuna mata abu da yawa. Sai ta tuna wani lokaci can baya. Tana kwance kamar lokaci irin wannan a dakinta. Ammar ya kira wayarta suna hira yace "tawan kamar yan gidanku basa na.am da soyayyarmu. Ina tsoro har raina" Duk da itama ta soma tsoron hakan kuma tasan dalilinsu yafi nata qarfi bai hanata son ammar dinba. Cikin taushin murya tace "ba haka bane nawan kaima kasan dalilinsu kuma in shaa Allah zamu samo maganin matsalar kafin abin yai nisa ko?" "Hakane tawan ina tsoro ne kawai. Jiya nai mafarki ana daura aurenki amman da wani bani ba" Dariya tai mishi "nawan mafarkine fa Ba komai ba. Ka manta kawai. Me kake yanzun?" "Um waqa nake ji da wayana na kiraki kuma." Ya amsata. "Wanne waqa?" "Cikin zuciya tana quna da so tai bankwana rabamu da juna soyayya a rai ya bugan naji zafi" ya soma raira mata waqar fitaccen mawaqin nan hussaini danko. Indai waqane kam muryar ammar daban take. Tason waqar jin yai shiru yasa tace "uhm nawan da dadi ka ci gaba" "Hmm" ya fadi ya dora da "waqar ta tunamin da yanayin da muke cikine shisa" Jin ya fadi hakan yasa ta dora dan shiya koya mata jin waqoqin danko "na yarda dakai kadai daya ke saka mini shauqi. Zancen da kake yasa na sarqe ka har a mafarki. Rabani dakai yakan sa na kashe kaina in rufe daki. Zamanmu dakai a zuci nakai ya yarda na mallaka mata kai" Sai lokacin yai dariya "tawan wlh ina shan dariya sosai in kikai waqa a tsayen nan kuma ko a jikinki" Itama dariyar take sam duk yanda ake fadin muryarta nada dadi bata lanqwasuwa indai wajen waqane. Haka ammar zaice tai mishi waqa kawai dan yaita dariya yakance tawan a haka nake sonki da kominki. Hawayen da suka bi mata fuska ta goge. Taya zata manta ammar ne a ranta. Sunyi wata irin shaquwa. A ko ina na rayuwarta yana ciki! Saidai yau take shirin yi masa sallama. Dan ta karbi aurenta da zuciya daya. Ta na fatan Allah ya yafe kata kuskuren data aikata. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣8⃣ Bathtub ya shiga ya sakarwa kansa ruwa masu matsakaicin sanyi. Ko zai daina jin abinda yake ji. Zuciyarsa wata iri ce mai saurin shaquwa. Yana da kishi sosai. Har yanzun qirjinsa zafi yake. Rabon da ya ji haka an kai wata biyar. Tunda radadin rashin huddy ya soma sauqaqa zafin qirjin ya rage. Yakanji shi in yana tunaninta koda kuwa zaiyi murmushi ne. Amman ba irin nayau da yaji sunan ammar kan labban hussy ba. Ya dauki lokaci mai tsayi cikin kwamin wankan kamin ya fito. Towel ne kawai jikinsa ba tare da tunanin komai ba ya qarasa zuwa dakin baccin nasa yai tsaye jikin mudubi yana goge gashinsa da qaramin towel. * Wanka ta sake yi ta shirya cikin atamfa lemon mai dan duhu. Kwalliya tai sosai. Ta zo kiran kausar ta tuna babu lambar a ciki tana wayarta da prince ishaq ya fasa. Mantawa tai randa suka zo asibiti duba Nas ta karba. Amman tace mata zasu dawo ai ta karba tare da address din gaba daya. Ta yanke shawarar ta kira ta fada mishi abar zuwan sai wani lokaci bai dauka ba. Wajen kira shidda. Data share shi saita kasa haqura. Haka kawai taji ta damu tasan ko lafiya. Kamin kwakwalwarta ta gama natsuwa tabi shawarar zuciyarta ta fito daga dakinta ta nufi shashinsa. Duk da bata bata takawa wajenba. Wani dan karamin falo ne a ciki. Kawatacce. Tabi dan lungun da tasan zai kaita bedroom dinsa. Ta qwanqwasa taji shiru ta tura da sallama ba.a amsa ba. Dakin baccinsa gabaki daya kalar blue ne mai haske kaman na sararin samaniya. Da digon taurari yellow mai haske jikin komai. Harta da furnitures din. Kallon dakin kawai ya saukar mata wata natsuwa ta bangaren da bata fahimta ba. Kan gadon ta zauna daga gefe. Hatta zanin gadonsa irin kwalliyar gare shi. Tasa hannu ta shafi pillow din sa. Ko ina qamshinsa yake. Komai neat a tsare sai dakin ya wani burgeta. A nutse take qare ma dakin kallon. Idonta ya sauka kan bangon dake fuskantarta. Qaton hoton mahaifiyarsa ne da mahaifinsa. Dukansu sanye da shiga ta alfarma. Daga gefe ma wani hotonne na mahaifinsa da mumyn Nas shima yai kyau. Ta maida kallonta kan hoton Nas har guda biyu. Tai murmushi a ranta tana masa addu.ar samun sauqi. Dayan bangon ta juya cike yake da hoton wata kyakkyawar yarinya da duka shekarunta ba zasu qarasa goma sha shidda ba. Daya dayafi kowanne girma sanye take da riga da wando na pakistan ta yafa mayafin kan kafadarta. Gashin kanta ya sauka saman kafadarta. Idanuwanta ba kan mai hoton yake ba. Da alama wani take kallo can tasa hannu tana qoqarin rufe bakinta da dariyar da take. Sai husna ta samu kanta da yin dariya itama. Yarinyar a hotuna ne amman tana ji kaman tana qoqarin yi mata magana ne. Duka hotunan hankalinta yana wani waje ba kan hoton ba. Motsi taji dan haka ta juyo. Cik komai ya tsaya mata. Prince ishaq ne daga shi sai towel daure a qugunsa. Sai dan qarami da yake goge gashinsa. In tace jikinsa mai kyaune. To a nata ganin kaman ta rage masa daraja ne. Komai nasa. Tsayi da qirarsa yanda take misalta namijin da zatai rayuwa dashine a can duniyar tunaninta. Abin mamaki yau gashi a gabanta. Bugun zuciyarta taji ya tsaya. Har iskar wajen ma. Shi kawai ta zubawa idanuwa tana kallon yanda Allah yai namiji a wajen. * Jikinsa ya bashi ana kallonshi. Ya juya cike da mamaki ya fito da idanuwa. Lokaci daya mamakinsa ya juye zuwa nishadi ganin yanda husna ta zuba masa idanuwa. Har fitowa yaga idanunta sun qara irin yanda ka keyi inkaga wani bangare na abunka dayafi dayan barin kyau. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 3⃣9⃣ *A duk lokacin da wani zai karramaka. Baka da abinda zaka bashi sai dai fatan alkhairi. Allah ya albarkaci rayuwarki UMMIE JAY. Allah ya karramaki fiye da yanda kika karramani! "Masoya ina godia da sakkoni da fatan alkhairi. Ina kaunarku fiye da yanda kukeson prince ishaq.* Duk ihun da kwakwalwarta take mata a banza dan zuciyarta kan prince ishaq da kyawunsa take. Allah ya qera namiji a wajen. Bata taba zaton namijin da take mafarki a zuciyarta akwai shi bama. Da komai da yanayin jiki. Girma da tsayi haka take son taga namiji. "Hussy" ya kirata da wani yanayi a muryarsa. Hakan ya dawo da ita hayyacinta a kunyace ta sadda kanta qasa. "Lafiya dai ko?" Ya buqata. Duk da bata kalli fuskarsa ba taji murmushin dake cikin maganarsa. Cikin sanyin murya tace "na kiraka ne baka dauka ba shine nazo na duba ko lafiya" Takawa yai har zuwa inda take ya zauna gefen gadon. Kallonta yake sosai. "Ina wanka ne hussy shisa" Tana jin hucinsa a kusa da ita da qamshin da ba zata ce sabulai bane. Abin wanka ne ko na wanke kai. Wani fresh kamshi mai saukar da kasala. Duk ya hautsina mata lissafi so take kawai taji duminsa. Tana kuma so ta taba damtsensa da wata tsoka take dunqule. Cikin rawar murya tace masa "abar zuwa gidan kausar na duba banga number inta a wayana ba. Shine zan fada maka daman" Hannu yasa ya dago mata fuska taqi kallon shi. Miqewa tai da niyyar barin dakin ya riqo mata hannu. "Gentle inka gama shiryawa ina falo" ta furta tana qoqarin qwace hannunta. Muryansa a tabare yace "ke zaki tayani shiryawa tunda kinzo" Sai lokacin ta kalli fuskarshi sosak ta fito mishi da idanuwa tace "haba mana gentle kamin haquri ka shirya kam" Ita kadai tasan me take ji gashi yaqi ya sake mata hannu. Wayarshi tai qara,hamdala husna tai saboda sakar mata hannu yai ya dauko wayarshi. Hankalinsa gabaki daya kan wayar dayake yi ya koma. Hakan yaba husna damar lallabawa ta fice daga dakin. * Falonshi ta zauna harya fito. Suka hada ido tai mishi murmushi. Ya wani yatsina fuska hadi da fadin "shine kika gudu ko?" Dariya ya bata. Ya zagayo ya dauki pillow din kujera ya jefa mata tasa hannaye ta kare tana dariya. "Ka kyaleni ka cika rigima" ta fadi muryarta da alamun dariya. Wani dogon numfashi ya fitar dayasa husna tambayarshi "yadai?" Saida ya fuskanceta sannan yace "nagajine kawai, nagaji da komai ina son zama normal kaman kowa." Tai shiru saboda batasan meya kamata tace mishi ba. Shima shirun yai dan bai tsammaci amsa daga wajenta ba. Yai maganar ne kawai danta tsaya mishi a wuya. "Hotunan huddy ne a dakinka?" Ta tambaye shi cikin sanyin murya. Idanuwanta kan fuskarsa. Tana kallon yanda tambayarta tasa ya rufe idanuwansa na yan daqiqae sanan ya bude su. Da dukkan alamu tambayar ta taba mishi zuciya. Hakan yasa husna fadin "kayi haquri ban........" Katseta yai da fadin "karki damu,hotunantane" * Tare sukaci abinci. Shiru kowa da abinda yake tunani a zuciyarsa. Bayan sun gama ne suna zaune a falonsa take tambayarshi ko zasu koma wajen nas ne. Yace mata "sai gobe in Allah ya kaimu" "Allah ya kaimu" ta amsa mishi. Yatsine fuska tai yace "yadai?" "Gashi na ya isheni bana iya gyarawa da kaina ko a gida saloon nake zuwa ko mamana ta tayani mu gyara" Idanuwansa ya kafa mata yanayin yanda take maganarta yana burge shi. Murmushin sa yai. "Muje ki wanke in tayaki" Ta fito da idanuwa tana dariya "gentle ina ka iya? Ka taba yine" "Sai muyi downloading ingani" Ya fadi muryar sa babu alamar wasa. Hakan ya sake bata dariya. "Lallai barshi i will manage har lokacin da zanje saloon" Yasan zai iya sa a dauko hair stylist ta gyara mata har gida. Bazai yi bane sabo da yana son ta soshi kuma bashida wani wadataccen lokaci. So ba abu bane dake shiga lokaci daya. Musamman nashi a zuciyarta dake dauke dana wani. Hade fuska yai kaman maganarta ta taba mishi zuciya. "Ni ko?" Ya fadi yana tabare mata fuskarshi me kyau. Ta sake yin dariya. Tashi yai. "Ina zaka?" Ta buqata bai kulata ba ya kama hanya. Hannunshi ta riqo ta rasa me yasa jikinshi yake mata dumi haka. Sai kace yana zazzabi. Juyowa yai ya daga mata girarsa duk biyun. "Zo ai downloading din kagani sai mu gyara tare" ta fadi tana kallon idanuwanshi. Murmushin sa yai mata daya kai har cikin idanuwanshi ya samu waje ya zauna sukai downloading yanda ake wanke gashi. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣0⃣ Sai daya gama kallo tsaf sannan ya juyo yace "kinada duk kayan nan na ciki? Ko nai waya a kawo" Ta girgiza kai "tace dryer ne babu irin nasu sai karami na riqewa a hannu...sai clips in nan suma babu" Wayarshi yake dannawa. "Me zakai?" Ta tambaya. Zan wayane akawo. Kamun ta sake magana harya ce "Hello....." Hakan yasa tai shiru tana kallonshi yana bada umarnin akawo duk wani kayan da za.a samu a saloon. Saida ya gama tsaf ta ce "gentle yanda kake fadar nan sai kace saloon zamu bude" Murmushi kawai yai. Ba ai awa dayaba aka kawo kayan. Hadiman gidan suka dauke suka kai bangaren husna. Saida suka gama tsaf suka koma nasu wajen sannan prince ishaq ya miqe tsaye yace ma husna muje. Sai da taji gabanta yadan fadi. Yau akwai rigima kenan gashinta ba wani mai tsaho bane can saidai warwarewarshi ne aiki tunda rubber ne. Takan godema Allah data biyo jinin fulanin babansu ta bangaren gashi. Kanwarta taita cewa daman ita. Dan nata gashin dakyar yake parking. Haka tabi bayanshi har toilet din bangarenta. Duk da ta rage zama da hijab sosai in tana tare dashi. Cire dankwalinta a gabansji ba karamar wahala yai mata ba. Sai taji gaba daya kunya ta rufeta. Da kanshi yaje ya dauko stool din dake dakinta yana fadin ta zauna akai kamun su siyo nasu kujerun wanke kan. Ta zauna wajen abin wanke kai. Prince ishaq yazo ya warware ribbon da ta kulle gashinta dashi. Ya dauko comb ya soma tajewa. Tai mamakin yanda yake bi a hankali kaman ya sabayi daman. Fuskarshi take kallo ta cikin mudubin toilet din yanda ya nutsu sai kace yana wani muhimmin aiki. Sai taji wani yanayi a zuciyarta data kasa fassarawa. Shampoo yasa ya soma cakuda mata gashi. Wayarshi dake ajiye gefe ta soma ringing. Ya share ya cigaba da abinda yake yi harta yanke. Yatsun sa yasa cikin gashinta ya yamutsa hakan yasa tsikar jikinta tashi. Kula yai da hakan yace "da zafi ne?" "A.a" ta fada dakyar muryarta can kasa saboda wani yanayi data tsinci kanta cikinsa. Haka ya wanke gashin tas. Yasa oil ya fara daukar abinda ake maqale gashi yana kallon su. "Hussy" Ya kirata. "Naam" ta amsa tana goge kunnuwanta da towel. "Ya ake maqala wannan abin ma?" Dariya tai sosai tace "ba zaka iyaba kabarshi" tana kokarin karbar clip din daga hannunshi. "Um um" ya fadi yana janyewa ya dora da "ni fa sai nayi ki fadamun yanda zansa kawai Ta kula prince ishaq ba karamin dan rikici bane. Dole a haka daqyar tare suka maqala clips din. Ya dan koma da baya ya kalleta kinyi kyau ya fadi. Tai murmushi a kunyace. Dryer ta shiga suna dan hira da prince ishaq din kadan kadan. Har kanta ya bushe. Clip daya ya cire yako hado da gashinta ouchh! tai yar qara tana kai hannu wajen. "Sannu sannu da zafi ko?" Yake fadi yana shafa mata wajen.A hankali yabi ya cire clips din duka. Tana miqo mishi kalar man dazai shafa mata. Ya gama suka taje kan tsaf tasa abu ta daure. Sannu da aiki gentle. Ta fadi tana kallonshi duk ya wani burgeta. Sauke numfashi yai yace mata "yawwa kinga kin huta da zuwa saloon ko? Tunda na iya" Dariya tai kawai dan tama rasa me zata ce mishi. Suka dawo falonta. Ya dauki wayarshi ya duba. Ya kalli husna yace mata "Zan fita" "Allah ya tsare ya dawo dakai lafiya" Ya amsa da "amin" Miqewa yai kaman zai tafi ya dawo ya sumbaci kuncinta sannan ya wuce. Ta lumshe idanuwa tanajin qamshinsa daya cika wajen. Har lokacin tana jin hannuwansa cikin ko ina nakanta. Zuciyarta tai mata wani nauyi mai wuyar fassarawa. * Har tai sallar isha.i bataji dawowar shi ba. Haka kawai sai taji ta damu tasan wanne hali yake ciki. Ta dauki wayarta ta kirashi wayarshi a kashe. Tai ta trying bata samu ba. Hakan yasa ta shiga tai wanka ta fito tai shirin bacci ta kwanta. Amman zuciyarta dauke take da damuwa musamman da ta sake kiran lambarshi taji wayar a kashe. Tashi tai ta koma bangarensa ta kwanta falonshi kan doguwar kujera. A zuciyarta tana fatan Allah yasa lafiya. Bata san lokacin da bacci ya sace taba. Ji tai ana taba mata fuska a hankali ta bude idanuwanta ta sauke su kan prince ishaq dayake mata wani kallo da ba zatace ga fassarar shi ba. A kunyace ta sauke idonta tana fadin "ka dawo? Inata kiran wayarka shiru" "Chargy na ya kare ban sani ba sai yanzun nagani" Ya bata amsa. Miqewa zaune tai duk kunyarshi ta rufeta saboda yanayin kayan dake jikinta.Shikam ko a jikinsa. Tashi tai tace mishi "saida safe daman dan inji shigowarkane yasa nazo" Kallonta kawai yake baice mata komai ba harta fita daga dakin. Yanda yake ji a zuciyarsa idan ya tsayar da ita komai zai iya faruwa. A hankali yake son ya saka mata sonshi a zuciyarta. Baya son gaggawa a rayuwarsa. Daqyar ya iya tashi ya qarasa ciki ya rage kayan jikinsa ya watsa ruwa. sai juye juye yake kan gado ya rasa abinda yake masa dadi. Ga jikinshi ciwo yake sosai. Ba saba wannan zirga zirgar yai ba. Kasa bacci yai ga yunwa na damunshi. Ya mike ya fito wajen dakin. Da niyyar zuwa ya duba abinda zaici ya fito amman zuciyarsa da kafafuwansa bangaren husna suka kaishi. Saida ya tura dakinta a hankali tukunna yasan me yake. Saidai bazai iya juyawa ba koda yaso. Karasawa yai. Bacci take hankalinta kwance. Ya zauna gefenta ya zuba mata idanuwa kawai zuciyarshi dauke da wani nauyi da ya rasa na menene. Hannu yasa ya shafi gefen fuskarta. Hakan yasata bude idanuwanta cike da bacci ta sauke su kan fuskarshi. "Gentle" ta fadi muryarta ta mishi dadi yanayin yanda taja sunanshi. "Yunwa nakeji hussy" yace mata yana langabe kai. Ga mamakinsa lokaci daya ta mike. Takai hannu ta kunna normal wutar dakin dan marar haske ce bata ma kashe ba bacci ya dauketa. Sai lokacin ya kalleta sosai. Tana murza idanuwanta. Gashinta duk ya hargitse wani ya zubo gefen fuskarta. Dariya yai a hankali. Ta harare shi "ni ko gentle? Zaka nemo mai kawo maka food tunda dariya kakemun" Ta fadi tana komawa kwanciyarta. Dariya yaci gaba dayi yace "Yi hakuri hussy taso ki rakani in samu abinda zanci" Yanda yai da fuska yasa ta kasa mishi musu. Ta miqe zaune tare suka shiga kitchen. Sai tarin snacks. Don haka ya dibi cake da apple sai fresh milk. Su yaci husna na zaune tana kallon shi. Kominshi a nutse yake yinsa. Yanayin taunar abincin ma zaka rantse yanga yake kuma ta kula haka halittarsa take. Saida ya gama tsaf ya sa mata rikici saita rakashi yai brush. Dole ta bishi nasa bangaren yai brush ya dawo dakin baccinsa.Miqewa husna tai ya riqo hannunta. "Ina zakije?" Ya tambaya. Hannunta take kokarin kwacewa tace "bacci nakeji zanje in kwanta" Girgiza mata kai yai alamar a.a sannan yace "nan babu wajen kwanciya?" Fito da idanuwa tai ta langabar dakai gefe guda tana fadin "gentle bana son rikici ka sake ni in tafi" Janyota yai da duk karfinsa ta fada jikinshi. Yasa hannuwa ya rungumeta sosai yana sauke numfashi. Saida ta hadiye yawu yafi sau uku kamun ta samu muryar ce ma "bacci nakeji" Cikin kunnenta yace "hussy........ Yanayin yanda yaja sunan da muryarshi suka saukar mata da kasala. Ga zuciyarta dake dokawa. Ki kwanta anan. Magana take shirin yi ya cizar mata kunne cikin sigar data sa duk wasu kalmomi suka bace mata. Shiru tai. Jin haka yasa prince ishaq gyara kwanciyarshi sosai. Itama ya gyara mata tata kwanciyar. Tanajin shi yana karanto addu.o.in tsari da saida ya burgeta. Ya tofa ko ina na daki. Ya sake yin wasu ya tofa musu shi da ita. Bata ganin fuskarshi yanayin yanda ya kwantar da ita. Bayanta ne a kirjinsa. Sumba ya manna mata a wuya hadi da fadin "sleep well hussy" Yaja blanket ya lullubesu. Bacci mai nauyi ya dauke shi. Husna kam zuciyarta dokawa take da wani irin yanayi da bata saba jin shi ba. Koya tai motsi saiya sake riqeta a jikinshi. Ta jima batai bacci ba kuma ba zatace ga abinda ya hanata bacci ko kuma ga abinda take tunani ba. Tana da tabbacin koma meye yana da alaqa da prince ishaq. A haka har bacci ya dauketa........! 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣1⃣ Bacci take sosai taji ruwa ya digo mata a fuska. Ta bude ido. Prince ishaq ne ya sakar mata murmushinsa mai taushi. "Lazy bones" yace cikin sigar tsokana. Ruwan ya sake digo mata. Ta kalle shi. Da alama wanka ya fito dan rigar wanka ce a jikinshi ga gashinsa nan jiqe da ruwan dayake digo mata. Takan jima batai magana ba inta tashi bacci da safe. Dan haka batace mishi komai ba. Ta matsa gaba ta sauka daga kan gadon. Bandakin shi ta shiga taga brushes da yawa. Ta dauki daya ta bare tai amfani dashi. Tai wanka itama sannan ta dauro alwala ta fito. Ga mamakinta kayanta tagani kan gadon prince ishaq bama guda daya ba ba biyu ba. Sunfi kala goma a ajiye. Shikuma yana tsaye sanye da jeans blue sai riga fara kal har shiga ido take kaman yanda kyanshi yake mata wasu lokuttan. Gani yai tana kallonshi ya daga mata gira cikin alamar yadai? Kaman ya fada a fili tace mishi "kayana nagani anan" "Ni ne na dauko" ya amsa mata a taqaice yana dorawa da "ki saka muyi sallah lokaci na wucewa" Jikinta babu karfi ta dauki doguwar riga daya. Duk yawancin kayan ma sababbi ne.Hanyar bandaki ta nufa taji muryarsa yace "Ina zakije?" "Kaya zan sake" ta amsa mishi a sanyaye. Da murmushi a muryarsa yace "nan zakibi to..." Ta juyo ta kalli inda ya nuna. Bama ta taba kula da kofa a wajen ba. Tazo ta gabanshi ta wuce ta shiga inda ya nuna mata. Dakin canza kayane. Babu komai ciki sai wardrobe da wajen shiri. Inda zaka rarrataye kaya da wajen takalma. Dakin kanshi da tsarinsa abin kallo ne. Dan ta tabbata shagon wani ne a kasuwar sabon gari. Kaya ta sake. * Shi kam prince ishaq har lokacin murmushi yake. Yanzun har mamakin kanshi yake. Yana yawan fara,a kuma yanajin farin ciki har ransa. Husna alkhairi ce a tare dashi. Dole ya tura mata sonshi kamun lokaci ya cika. Da duk ranakun da suke wucewa da kusancin alkawarin daya dauka. Ya sauke numfashi. Dai dai fitowar husna. Ta mishi kyau. Namiji ne shi da baya son kwalliya mai yawa jikin mace. Baiqi yaga fuskarta fayau din nan ba. Babu ko powder balle wani janbaki. "Barin sauri in dauko hijab" ta fadi tana nufar kofa batare data jira amsarshi ba. Murmushi ya sake yi. Batai minti biyarba ta dawo. Shiya ja sallar har suka idar. Husna tai azkar dinta na safe data saba tai addu.o.inta,taima nasir na samun sauki. Saita tsinci kanta da yiwa prince ishaq addu.a da fatan tabbatar alkhairi a zamansu. Abinda bata taba yi ba. Har wata nutsuwa ta daban taji ta shigeta. Mikewa tai takoma kan gadon ta kwanta. Prince ishaq kam Qur.an taga ya bude drawer in kusa da gado ya dauko. Tanata kallonshi ya bude yana karantawa a hankali yanda shi kadai zaiji sautin muryarshi. Sai taji zuciyarta na mata wani iri. Tana son jin muryarshi yana karantawar. Dan haka tace "gentle kayi yanda zanji Kaga kai ka samu ladan karatu nikuma na saurare ko?" Bude murya yai yaci gaba da karatun. Ta nutsu tana saurarenshi. Kira.arsa na burgeta. Muryarshi na shiga wasu wajaje a jikinta da bata san akwai su ba. Harya idar yai addu.o.i sosai ya sauke idanuwansa akanta. "Ina kwana" ta furta a hankali. "Kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah" ta amsa mishi. Bai sake ce mata komai ba. Ya ja kafet din dayai sallah akai ya linke shi. Kan kujera ya koma ya zauna ya zuba mata idanuwanshi. Tama soma sabawa da yanayinshi. Zasu iya awanni a haka. Yana kallonta baice mata komai ba. Ba koyaushe magana ke damunsa ba. Bata san sanda bacci ya sake daukarta ba dan bai wadace taba daman. Saidai tashi tai ta duba ko ina dakin bataga prince ishaq ba. Ta shiga bandakinshi ta wanke fuskarta da bakinta ta fito. Wajen falon ta fita baya nan. Ta duba agogo goma harta wuce. Shisa take jin yunwa na damunta. Dining ta nufa ta dibi iya abinda take jin zataji. Dan har mamaki take. Abincin da ake dafawa bata san ya zasuyi dashi ba. Ko sun kai su goma ya masu yawa. Dan gashi nan kala kala. Saidai suci su bari. Ta gama tsaf. Ta je dakinta ta dauko wayarta. Ta dawo babban falo. Prince ishaq ta kira ringing din farko ya dauka. "Kin tashi?" Ya tambaya. Ta amsa da "um banganka ba ka fitane?" "Ina garden zaune ina kallon tsuntsaye sunata kukansu. Bakyaji ne?" Ya fadi. Sai lokacin ta nutsu take jin kukan tsuntsayen. Cike da mamaki tace mishi "Ina garden din yake?" "Cikin gidan nan zakizo ne?" Ta girgiza kai kaman yana ganinta ta dora da "Kazo mu tafi wajen Nas" "Tam kin shiryane in taso?" Ya fadi daga dayan bangaren. "A.a barin tashi. Nan da minti talatin kazo nagama." Ya amsa da "Tam" Ya kashe wayan. Tashi tai ta nufi bangarenta. Ta sake yin wanka ta shirya. Tana fitowa ta ga prince ishaq ya shigo. Kinyi kyau ya fadi yana matsowa dab da ita. Zuciyarta taji tana dokawa tana jin kamshinsa ya cika mata hanci. Hannuwanshi yasa ya tallabi fuskarta. Sumbatarta yai a kunci sannan yace "Mu tafi ko?" Kai ta daga masa dan bakinta ya mutu. Jikinta ma ba shida kwari. Ya kama hannunta suka fita. * Kan kujeru suke zaune sun tisa nas a gaba kaman kallon da suke mishi ne zaisa ya bude idanuwanshi. Doc dinshi yace musu tun farkawar dayai bai sake ba. Amman babu wata matsala har yanzun. Su duka bamai magana kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa. Husna nata kallon Nas. Can taga kaman ya motsa. Matsawa tai da kujerarta kusa dashi sosai ta sake kallonshi aikam ya sake motsawa. "Gentle!" Yanayin yanda ta kirashi sosai yasa shi dagowa ya kalleta. "Nas motsi yake fa ta sake fadi" Shima matsawa yai kusa suka zuba mishi ido. A hankali ya bude idonshi yana kallon wajaje cikin dakin. Kamun prince ishaq yace komai husna ta fice da gudu ta kira doctors. Husna kam ba zata iya kallon koma menene zasuyi ba. Don haka ta fita ta zauna daga waje. Ba afi minti ashirin ba suka fito. Akace ma husna zata iya shiga. Hamdala suke tayi daga ita har prince ishaq ganin Nas ya nata kallonsu duk da har lokacin baice kala ba. Saidai murmushi dayake ta musu. Amman likitanshi yace ba komai bane. Zai magana idan ya shirya. Sunkai awa biyu a asibitin har saida bacci ya dauki Nas. Daqyar prince ishaq ya lallaba husna su koma gida da yamma su dawo. Suna cikin motane ya kira gida yake fada musu. Kowa yaji dadi ba kadan ba. Anata ma Allah godiya dan babu wanda yaba Nas din tashi. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣2⃣ Suna karasawa gida husna zata fita daga mota prince ishaq yace "zanje wani guri i will call you ok?" Tadanyi jim sannan tace mishi "to please take car" Murmushi ya kwace mishi. Batasan lokacin data sa hannu taja mishi hanci ba hadi da fadin "murmushin me kake?" Ya daga mata girarsa cikin sigar dake kara masa kyau yace "bakomai naji dadine kin damu dani" Dariya husna tai kawai ta juya ta bude murfin motar zata fita. Riqo mata hannu yai yana fito da idanuwa. "Hussy ina zaki? Bawani a dawo lafiya kiss? Kawai zaki barni" ya fada a tabare. Wani lokaci har mamakin shi take. Fuskarshi ta tallabo da hannuwanta ta sumbace a kunci kaman yanda yake mata. Ta hada da fadin "tam a dawo lafiya" "Ko kefa" Ya fadi yana daria. "Saina dawo" Ta fita daga motar bata amsa shi ba. Saboda wani nauyi da bakinta yai mata. Tasan kota tsaya gardama ko dai tai mishi koshi yai mata. Datai masa ma sai yafi mata sauki. Kamshinsa kawai taji. Da shi yai mata kafafunta sanyi zasuyi. Ta kuma rasa dalili. Tana shiga daki alwala tayi. Tai sallah sannan ta sake kayan jikinta ta saka doguwar riga dan duk kayanta sune ta koma babban falonsu ta zauna. Bata jima ba prince ishaq ya shigo. Sallamarshi ta amsa yace kinyi kyau. Ta kalli kanta cike da mamaki. Fuskarta dai ba kwalliya. Karasawa yai inda take ya zauna yana mata murmushin sa. Hannu yasa ya zagaye lebenta sannan yace "yes kinyi kyau. Ban cika son kwalliya a fuskar mace ba" Kallon mamaki take masa a ranta tana fadin. Mutane iri iri. Kowa da kalar nasa ra.ayin. Iska taji ya hura mata cikin fuska ta rufe idanuwanta tana dariya. "Nagaji fa" ya fadi da wani yanayi a muryarshi. "Sannu gentle" husna tace tana kamo hannun shi. Lokutta irin haka ita kanta mamaki take ba kanta. Haka suka zauna shiru dan ta soma sabawa ma. * Sun kai mintina talatin a haka kamun yace ma husn "in tambayeki?" Tace "why not" "Menene burinki a rayuwa?" Dariya tai kawai dan burinta shine ta auri ammar kuma sai komai ya canza. Hannunta taji ya dumtse cikin nashi kamun yace kinyi shiru. A hankali tace "Najima banida wani buri saina ammar ya karasa karatu ya samu aiki muyi aure and komai saiya canza" Lumshe idanuwansa yai yanajin wani daci a zuciyarsa. Duk da hakan bai hana ce mata "i am so sorry hussy" Kallon fuskarshi tai "saboda me?" Ta bukata. Saida yaja numfashi ya sauke shi sannan yace mata "saboda nasan yanda akeji in burin mutum bai cika ba. Zanyi komai dan kauce ma shiga tsakanin wani da burinsa" Hannunshi ta sake dumtsewa sosai tana son fada mishi abubuwan data rasa kalaman da suka fi dacewa ta cikin hannuwan nasu. Muryarta na rawa tace "ba laifinka bane" "Hmm" kawai ya fadi yana sake kwanciya cikin kujerar abinshi. Basu san lokaci yaja ba saida sukaji ana kiran sallar la.asar. Su duka suka tashi kowa yai bangarensa. * Alwala husna take zuciyarta cike da saqe saqe. Sallar la.asar ta yi ta zauna kan daddumar tana karatun Qur.ani. Data idar ma bata tashi ba. Akai tai zamanta tana tunanin abinda ta rasa dakuma abinda takejin ta samu a yanzun. Saidai batasan me zuciyarta take ciki ba game da auren su da ishaq. Kwankwasa kofa taji anyi kamun ma ta amsa ya turo kofar ya shigo. Yai mata kyau sosai cikin shaddar shi light blue da alkyabba dark blue. Kodan bata saba ganin shi da kaya masu kala bane. Shisa taga ya mata kyau haka. Kan gadonta ya zauna. "In shirya ko?" Ta tambaye shi. "Ki dora abu saman kayanki. You are more than ok" ya amsata. Hakan kuwa tayi. Tare suka fita driver ya kaisu asibiti. Suna shiga doc din nas suka gani. Da fara.a yace "yanzun kaizan kira Nas ya tashi yana tambayarku" Basuma amsa shiba da sauri suka nufi dakin Nas din. "Antina" Nas ya fadi muryarshi can kasa. Prince ishaq ya daquna fuska yana fadin "ita ka soma gani Nas?" Dariya husna tai ta juya ta mishi gwalo.Ta karasa ta zauna gefen gadon Nas. "Alhamdulillah Nas sannu kaji Allah ya kara baka sauqi" husna ta fadi muryarta na rawa saboda kukan da taji yana shirin zuwa mata. "If you cry bacci zan koma Nas ya fadi" Sukai dariya gaba dayansu. prince ishaq ya kama hannun Nas yama kasa cewa komai dan farin ciki. Haka sukaita hira kadan kadan kamun wata likita tazo tace musu zasu gajiyar da Nas lokacin allurar shi yayi. Fuska a hade Nas yace "bafa maimun allura. Yaya kwanana nawa a kwance? Kumin alwala in rama sallolin da ake bina tukunna" Husna tace "Nas zaka iya kuwa? Jikinka babu karfi" Prince ishaq yace "yeah kana da gaskia a kira su su ciccire maka wannan tarkacen if motsaka babu matsala" Haka kuwa akai. Daqyar likitocin suka yarda dan Nas din da prince ishaq sun dage. Daga zaune Nas ya rama duk sallolin da ake binshi suna zaune suna hira. Prince ishaq ya kamashi ya koma kan gado. Aka kira doc dinshi. Ana masa allura bacci na daukarsa. Basu suka koma gida ba sai wajen 9 na dare. Kowa ya wuce bangarensa. * Wanka kawai prince ishaq yai dan sunyi sallolinsu tun a asibiti. Ya saka kayan bacci ya kwanta. Wayarshi ya dauka ya kira husna. Ringing din farko ta dauka. "Hello..." ta fadi muryarta da alamar bacci. "Hussy..." ya ja sunanta. "Gentle na fara bacci fa" ta fadi a shagwabe. "Kizo please" ya bukata. Husna ta girgiza kai kaman yana ganinta tace "kayi baccinka nima bacci zan" Kashe wayar yai. Baya son gardama ko kadan. Ta kira yanaji harta gama ringing bai dauka ba. Yakai hannu ya kashe wutar dakin. Yai addu.a yaja bargo ya rufe jikinshi duk da yasan ba baccin zai ba. Yanata tunane tunane abinshi sam baiji turo kofar ba sai motsin mutum dayaji. Hannu yakai wajen switch din dakin ya kunna wuta haske ya gauraye ko ina. Husna ce kwanciya tai batace masa komai ba. Ya rikota jikinshi. Sam taki kallon fuskarshi. Ya sumbaci goshinta yana fadin "haba mana hussy." "Kaine na kira baka dauka ba" ta fadi da wani yanayi a muryarta. Sauke numfashi yai yace . "banason gaddama ne kuma banason takura miki" Shiru tai tana kwantar da kanta a kirjinshi. "Saida safe" ya fadi. Ta daga mishi kai. Saida yai mata addu.o.i ya tofa mata sannan ya kashe wutar dakin yana gyara mata kwanciya a jikinshi. Yana jin canzawar numfashinta alamar bacci ya dauketa. Yai murmushi a zuciyarshi yana lissafa watannin daya rage masa ya tura mata sonshi. Kamun shima ya rufe idanuwansa bacci ya dauke shi. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣2⃣ Suna karasawa gida husna zata fita daga mota prince ishaq yace "zanje wani guri i will call you ok?" Tadanyi jim sannan tace mishi "to please take car" Murmushi ya kwace mishi. Batasan lokacin data sa hannu taja mishi hanci ba hadi da fadin "murmushin me kake?" Ya daga mata girarsa cikin sigar dake kara masa kyau yace "bakomai naji dadine kin damu dani" Dariya husna tai kawai ta juya ta bude murfin motar zata fita. Riqo mata hannu yai yana fito da idanuwa. "Hussy ina zaki? Bawani a dawo lafiya kiss? Kawai zaki barni" ya fada a tabare. Wani lokaci har mamakin shi take. Fuskarshi ta tallabo da hannuwanta ta sumbace a kunci kaman yanda yake mata. Ta hada da fadin "tam a dawo lafiya" "Ko kefa" Ya fadi yana daria. "Saina dawo" Ta fita daga motar bata amsa shi ba. Saboda wani nauyi da bakinta yai mata. Tasan kota tsaya gardama ko dai tai mishi koshi yai mata. Datai masa ma sai yafi mata sauki. Kamshinsa kawai taji. Da shi yai mata kafafunta sanyi zasuyi. Ta kuma rasa dalili. Tana shiga daki alwala tayi. Tai sallah sannan ta sake kayan jikinta ta saka doguwar riga dan duk kayanta sune ta koma babban falonsu ta zauna. Bata jima ba prince ishaq ya shigo. Sallamarshi ta amsa yace kinyi kyau. Ta kalli kanta cike da mamaki. Fuskarta dai ba kwalliya. Karasawa yai inda take ya zauna yana mata murmushin sa. Hannu yasa ya zagaye lebenta sannan yace "yes kinyi kyau. Ban cika son kwalliya a fuskar mace ba" Kallon mamaki take masa a ranta tana fadin. Mutane iri iri. Kowa da kalar nasa ra.ayin. Iska taji ya hura mata cikin fuska ta rufe idanuwanta tana dariya. "Nagaji fa" ya fadi da wani yanayi a muryarshi. "Sannu gentle" husna tace tana kamo hannun shi. Lokutta irin haka ita kanta mamaki take ba kanta. Haka suka zauna shiru dan ta soma sabawa ma. * Sun kai mintina talatin a haka kamun yace ma husn "in tambayeki?" Tace "why not" "Menene burinki a rayuwa?" Dariya tai kawai dan burinta shine ta auri ammar kuma sai komai ya canza. Hannunta taji ya dumtse cikin nashi kamun yace kinyi shiru. A hankali tace "Najima banida wani buri saina ammar ya karasa karatu ya samu aiki muyi aure and komai saiya canza" Lumshe idanuwansa yai yanajin wani daci a zuciyarsa. Duk da hakan bai hana ce mata "i am so sorry hussy" Kallon fuskarshi tai "saboda me?" Ta bukata. Saida yaja numfashi ya sauke shi sannan yace mata "saboda nasan yanda akeji in burin mutum bai cika ba. Zanyi komai dan kauce ma shiga tsakanin wani da burinsa" Hannunshi ta sake dumtsewa sosai tana son fada mishi abubuwan data rasa kalaman da suka fi dacewa ta cikin hannuwan nasu. Muryarta na rawa tace "ba laifinka bane" "Hmm" kawai ya fadi yana sake kwanciya cikin kujerar abinshi. Basu san lokaci yaja ba saida sukaji ana kiran sallar la.asar. Su duka suka tashi kowa yai bangarensa. * Alwala husna take zuciyarta cike da saqe saqe. Sallar la.asar ta yi ta zauna kan daddumar tana karatun Qur.ani. Data idar ma bata tashi ba. Akai tai zamanta tana tunanin abinda ta rasa dakuma abinda takejin ta samu a yanzun. Saidai batasan me zuciyarta take ciki ba game da auren su da ishaq. Kwankwasa kofa taji anyi kamun ma ta amsa ya turo kofar ya shigo. Yai mata kyau sosai cikin shaddar shi light blue da alkyabba dark blue. Kodan bata saba ganin shi da kaya masu kala bane. Shisa taga ya mata kyau haka. Kan gadonta ya zauna. "In shirya ko?" Ta tambaye shi. "Ki dora abu saman kayanki. You are more than ok" ya amsata. Hakan kuwa tayi. Tare suka fita driver ya kaisu asibiti. Suna shiga doc din nas suka gani. Da fara.a yace "yanzun kaizan kira Nas ya tashi yana tambayarku" Basuma amsa shiba da sauri suka nufi dakin Nas din. "Antina" Nas ya fadi muryarshi can kasa. Prince ishaq ya daquna fuska yana fadin "ita ka soma gani Nas?" Dariya husna tai ta juya ta mishi gwalo.Ta karasa ta zauna gefen gadon Nas. "Alhamdulillah Nas sannu kaji Allah ya kara baka sauqi" husna ta fadi muryarta na rawa saboda kukan da taji yana shirin zuwa mata. "If you cry bacci zan koma Nas ya fadi" Sukai dariya gaba dayansu. prince ishaq ya kama hannun Nas yama kasa cewa komai dan farin ciki. Haka sukaita hira kadan kadan kamun wata likita tazo tace musu zasu gajiyar da Nas lokacin allurar shi yayi. Fuska a hade Nas yace "bafa maimun allura. Yaya kwanana nawa a kwance? Kumin alwala in rama sallolin da ake bina tukunna" Husna tace "Nas zaka iya kuwa? Jikinka babu karfi" Prince ishaq yace "yeah kana da gaskia a kira su su ciccire maka wannan tarkacen if motsaka babu matsala" Haka kuwa akai. Daqyar likitocin suka yarda dan Nas din da prince ishaq sun dage. Daga zaune Nas ya rama duk sallolin da ake binshi suna zaune suna hira. Prince ishaq ya kamashi ya koma kan gado. Aka kira doc dinshi. Ana masa allura bacci na daukarsa. Basu suka koma gida ba sai wajen 9 na dare. Kowa ya wuce bangarensa. * Wanka kawai prince ishaq yai dan sunyi sallolinsu tun a asibiti. Ya saka kayan bacci ya kwanta. Wayarshi ya dauka ya kira husna. Ringing din farko ta dauka. "Hello..." ta fadi muryarta da alamar bacci. "Hussy..." ya ja sunanta. "Gentle na fara bacci fa" ta fadi a shagwabe. "Kizo please" ya bukata. Husna ta girgiza kai kaman yana ganinta tace "kayi baccinka nima bacci zan" Kashe wayar yai. Baya son gardama ko kadan. Ta kira yanaji harta gama ringing bai dauka ba. Yakai hannu ya kashe wutar dakin. Yai addu.a yaja bargo ya rufe jikinshi duk da yasan ba baccin zai ba. Yanata tunane tunane abinshi sam baiji turo kofar ba sai motsin mutum dayaji. Hannu yakai wajen switch din dakin ya kunna wuta haske ya gauraye ko ina. Husna ce kwanciya tai batace masa komai ba. Ya rikota jikinshi. Sam taki kallon fuskarshi. Ya sumbaci goshinta yana fadin "haba mana hussy." "Kaine na kira baka dauka ba" ta fadi da wani yanayi a muryarta. Sauke numfashi yai yace . "banason gaddama ne kuma banason takura miki" Shiru tai tana kwantar da kanta a kirjinshi. "Saida safe" ya fadi. Ta daga mishi kai. Saida yai mata addu.o.i ya tofa mata sannan ya kashe wutar dakin yana gyara mata kwanciya a jikinshi. Yana jin canzawar numfashinta alamar bacci ya dauketa. Yai murmushi a zuciyarshi yana lissafa watannin daya rage masa ya tura mata sonshi. Kamun shima ya rufe idanuwansa bacci ya dauke shi. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣3⃣ A hankali komai yake tafiyar musu. Sauqi kam ya samu wajen nas watanshi biyu kenan cif a asibiti. Dan harya soma musu korafin ya gaji shi kam. Saidai likitanshi yace ba zasu sallame shi ba sai sun tabbatar internal injury din daya samu a kanshi bazai bada wata matsala ba. * Prince ishaq da husna kam da duk ranakun da suke wucewa wani irin shakuwa me karfi ce take kara shiga tsakaninsu. Yanzun kam sai tai kwanaki ma bata tuna da wani ammar ba. Zasu kwana waje daya da prince ishaq. Dan tama saba da duk rikicinsa yanzun. Suje unguwa tare, wasu lokuttan in yasan zai fita ya jima saiya dauketa ya sauketa asibiti wajen Nas suyita hirarsu in ya dawo ya biya ya dauketa su koma gida. * Yauma kaman kullum tana zaune falo tana kallon mbc 3 ya fito jikinshi sanye da farar shadda. Da kyanshi da shaddar suka shigar mata ido. Murmushi tai. Ya daga mata gira hadi da fadin Say it hussy" Ta kalle shi cikin ido tace "mezan fada?" Ya sake fadada murmushinsa. "Kice nayi kyau mana" ya fada yana karasawa inda take ya zauna. "Shaddarka tamun kyau" ta fadi tana dariya ganin yanda ya tabare mata fuska kaman karamin yaro. Ja mishi hanci tai tace "sorry gentle kayi kyau kama fi shaddar" Dariya yai shima ya matsa daf da ita ya sumbaci kuncinta. Ya bude baki zaiyi magana kenan wayarshi ta soma ringing. Yasan Nas ne saboda ringing dinshi dabanne dan haka ya zaro wayar daga aljihu ya daga hadi da fadin "Hello Nas..." "Yaya kuzo ku daukeni an sallameni" ya fadi daga dayan bangaren muryarshi cike da farin ciki. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣4⃣ Tare sukaje suka dauko Nas. Su duka ukkun kallonsu zakai ka tabbatar fuskarsu dauke take da farin ciki. Sai hamdala sukeyiwa ubangiji. Haka sukaita hira bayan sun dawo gida. Zaka rantse sun shekara ne basu ga juna ba. Sai can husna ta kalli Nas ta sake duban agogon dakin. Karfe tara harta dan gota. Ka tashi ka sha magani kaje ka kwanta lokaci yayi. Husna ta fadi tana kallonshi. Nas ya wani shagwabe fuska. "Nikam kinga wallahi bangaji da hirar nan ba" "Kana son komawa asibiti ne ko?" Prince ishaq ya fadi muryarshi babu alamun wasa. Aikamun husna tace wani abu nas ya mike da saurinshi yabar wajen. Suka hada ido ita da prince ishaq sukai dariya. Miqewa tai itama a kasalance prince ishaq yace mata "ina zakije?" "Daki" ta amsa mishi yanayin yanda yake kallonta na kashe mata jiki. Hannunsa ya miqa mata alamar taje. Batai masa musu ba tasa hannunta cikin nashi ya dumtse nata sosai kamar zata gudu. A hankali yajata ta zauna jikinshi. kamshin sa na wani rikitata. Ajiyar zuciya ya sauke ya saka hannuwansa duka biyun yana riketa sosai. "Hussy naji tsoro sosai" ya fadi a hankali. Shiru tai dan batasan amsar da zata bashi ba. Jin hakan yasa shi ci gaba. "Allah yaga zuciyata ba zata iya daukar rashin Nas ba shisa yabar min kanina." Ya karasa maganar cikin sanyin murya. Hannunshi ta riqo cikin nata tana kokarin gaya masa kalaman da batasan ta ina zata soma hadasu ba. Sun jima zaune a haka. Kamun tace masa "muje mu kwanta ko?" Kai ya daga mata alamar eh. A hankali ta zame jikinta daga nashi tana miqewa. Shima tashin yai tare suka nufi bangarenshi. Kan gado ya kwanta da full kayanshi yana wani tabare fuskarshi me kyau. Husna ta girgiza kai kawai ta shiga toilet ta watsa ruwa. Ta sakko bath robe ta fito. Prince ishaq ta kalla bacci yake Rabin jikinshi akan gado rabi a kasa. Tai murmushi kawai tasan ya gaji. Gama shiryawa tai tsaf tasa kayan bacci sannan tazo inda yake ta zauna ta zuba mishi ido. Zuciyarta na dokawa. Har kasan ranta batason tashin shi. Saidai yanayin kwanciyar dayai zata iya saka mishi ciwon jiki. Dabara tazo mata nata kamashi ta juyashi ya kwanta kan gadon sosai. Kafafuwanshi ta kama daqyar ta cicciba su ta dora kan gadon tana uban nishi. Komun nauyin baccin dayake kana tabashi saiya farka. Husna na tabashi ya tashi saidai ya rufe idonshi kawai yana jinta da nishin da take. Dariya na son kubce masa. Sake juyashi tai daqyar ta kama hannunshi ta zare alkyabbar dake jikinshi. Ta sake mirgina shi ta zare dayan hannun. Gefe ta zauna tana maida numfashi. Ta kare mishi kallo. A ranta tace Allah ya kera mazaje a wajen nan. A fili kuma fada take tiqa a hankali. "Mutum shi badan dambe ba yabi duk ya tara tsoka. Yanzun da ace baida qiba kamar ni juyashi kawai zan in rage mishi wannan kayan nauyin. Ai shikenan ka huta. Saikaita baccinka da wannan shaddar nikam dai nagaji" Prince ishaq baisan lokacin da dariya ta kubce masa ba. Husna ta zaro ido. Lokaci daya ta hade fuska "ashe kana jina daman" Pillow ta dauka ta kwada masa a kirji tana fadin. "Kasa inata nishi kana jina kai lamo" Ta sake kwada masa a fuska ya tare yana dariya. Kwace pillow din yai ya rama. Husna ta dauki dayan pillow din ta sake kwada masa. Fadan pillow suka ci gaba dayi inta kwada masa ya rama. Yanata mata dariya. Gajiya tai ta ajiye ta kwanta gefe tana maida numfashi. A hankali yakai hannu ya juyo da fuskarta ta kalle shi. Idanuwanta ta sauke cikin nashi tako yi saurin maida nata kan kirjinsa. Murmushi yai. Yanajin dadin yanda idanuwansa ke da tasiri akanta. Bata jure kallonsu. Sauka yai daga kan gadon ya shiga toilet shima ya watsa ruwa ya fito. Ya shiga dakin canza kaya ya fito daga shi sai boxers da farar singlet. Ya hau gadon ya kwanta yana janyo husna zuwa jikinshi. Kaman ko da yaushe sai da taji wata kasala ta saukar mata. Ta kasa sabawa da yanayin nan. "Nagaji da abuja" yace mata. Hannu tasa ta danna mishi kumatu daidai inda dimple dinshi yake. Sannan tace "mukoma gida mana gobe indai babu wata matsala" Ya jinjina kai yace "haka nake planning nima nasa kamala yai booking mana" Saida safe tace mishi tana rufe idanuwanta. Addu.o.i yai musu kamar koda yaushe ya sumbace ta a kumatu da goshi sannan yace mata "Allah ya tashe mu lafiya" 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣5⃣ Washe gari tunda wuri suka hada abinda suke bukata. Dan husna ma akwatinta datazo dashi shi tadan zuba wasu kayan. Wasu kuwa nan tabarsu. Daga prince ishaq har nas babu abinda suka dauka sai kayan jikinsu. Jirgi sukabi zuwa kano. Karo na farko a rayuwar husna data taba hawan jirgi. * Daga airport mota suka samu ana jiransu aka dauke su zuwa gidan su prince ishaq. Husna taga karamci ranar. Takuma ga duk yan uwan prince ishaq masu kyau saidai duk basukai shi kyau ba. Sun jima sosai gidan dan nan sukai sallar la.asar. Komai husna takeyi a kunyace take yinshi. Haka kawai ta tsinci kanta da jin nauyinsu. Musamman mahaifiyar prince ishaq din. Hakan umma ta kula dashi yasa ta kira prince ishaq din tace "Babana kazo ku tafi gidanku ko?" Da murmushi a fuskarshi ya amsa mata ya maida dubanshi zuwa kan husna yace ta taso. Har kofar falon aka rakasu sannan suka fita zuwa harabar gidan inda motar su take ajiye. Bude musu akai suka shiga. Sai bayan an rufene husna tace "gentle banga nas bafa har zamu tafi." "Yana can bangarensu. Zaizo har gida indan Nas" ya amsa batare daya kalle taba. Kanshi ya jingina da kujera yai shiru. Ta kalle shi yau sarautar ta motsa kenan ta fadi a ranta. Duk da yangarshi a jininsa take. Wani lokaci tana kula in sarautar ta motsa magana ma kan dole yake yinta. Sai su wuni shiru saidai yai ta amsata dakai kome zatace inyai kokari yace mata um ko um um ko hmm. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣6⃣ Satin su biyu kenan da dawowa daga abuja. Komai na tafiyar musu yanda ya kamata. Saidai prince ishaq baya zama. Sai ya wuni baya gida wanda husna ke bala.in kula dashi a yanzun. Dan ba zataima kanta karya ba. Ta fara damuwa dashi sosai da sosai. Balle data san masu son illata shin sunfi kusa dashi a kano kan abuja. Duk idan yai cikakkun awa biyu a waje bataji ya kirata ba ita zata neme shi taji ko lafiya. * Ta idar da sallar la.asar ta sake kiran prince ishaq wayar shi har lokacin bata shiga. Tun karfe biyu take nemanshi shiru haka. Ta nemi number din Nas shima a kashe. Ta koma dakin prince ishaq din ta kwanta. Gaba daya a tsorace take. Jitai ba zata iya ba ta fito babban falo ta zauna. Num din shi ta kara nema shiru. Tai rau rau da ido. Saboda bata san wa kuma zata kira taji ko lafiya ba. Ta yanke shawarar inhar magrib tayi zata fita akaita gidansu ta dubo. Ta mike kenan ta sake komawa sama yai sallama. Batasan lokacin data karasa inda yake ba da gudu ta fada jikinshi. Riketa yai yana fadin "Easy hussy....." Hawayen da take ta kokarin tarbewa ne taji sun zubo. Ya dagota daga jikin shi yana kallon fuskarta. "I am so sorry wallahi charge dina ya kare. Hankalina ba a kwance ba. I should have call......" Batace komai ba ya sake rungumeta tsam a kirjinshi yana jin wani abu game da ita daya girmi so yana kara shigarshi. Da ita a kusa dashi sai yake jin komai na masa sauki. "Kinci abinci?" Daidai lokacin dayai tambayar ne cikinta ya zabi yai wani kuuu alamar yunwa. Girgiza kai kawai yai ya kama hannunta suka hau sama zuwa bangaren shi. * Tana nan zaune ya fito wanka ya shirya. Suka sake sauka kasa zuwa dining din. Abinci take ci ita. Shikam tana kula da tun zamansu wasa kawai yake da cokalinsa cikin abincin. Abincin dake bakinta ta hadiye sannan ta kalle shi sosai tace. "Gentle what is wrong?" "Kici abincin ki karya huce" Ya fadi maimakon ya amsa mata tambayarta. Dakyar ta kara cokali biyu saboda ji tai abincin ya fita a ranta. Kallonta yai. Da gajiya hadi da damuwa a fuskarshi yace. "Kin koshi" "Na koshi" Ta amsa shi tana mikewa. Magrib sukaji ana kira. Ta kalle shi yace mata suhau sama kawai. Yai musu jam.i dan bayajin fitar ne kwata-kwata. Sai da suka idar da sallah suka gama addu.o.in da zasuyi. Ya juyo ya fuskance ta sosai yace. "Hussy ban dawo ba yau. Saboda muna asibiti da Nas..... " Yana ambaton sunan Nas taji gabanta ya wani fadi. Katse shi tai da fadin "Me ya same shi kuma? Bayaji sauki ba?" Hannunta ya riko yace. "Ki nutsu kiji ni okay? Just calm down" Kai take daga masa cikin kosawa yaci gaba da fadin. "Tun rand muka dawo yake fama da ciwon kai sosai. Yana ma mumy korafin kanshi kaman ana hura wuta. Sunje asibiti sau hudu dawowarmu. Basu fadamin bane sai yau da abin yai girma" Ajiyar zuciya ya sauke kamun ya ci gaba da fadin. "Yana da wani ciwo cikin kanshi. Buguwane sosai. An bamu 100% tabbacin zai warke. Amman za ai masa aili a kasar india" Bama tasan hawaye sun zubo mata ba sai da taga ya matso kusa da ita sosai yasa hannuwanshi duka biyun ya goge mata fuska. Hannuwanshi tallabe da fuskarta yace. "He is going to be okay in shaa Allah. Ni dakaina naga file din binciken da sukai" Muryar ta can kasa tace. "Yaushe zaku tafi?" Dan husna kewarshi taji ta soma yi. Yanda take jinma ya danne damuwar Nas. Ganin yanda idanuwanta suka sake kawo ruwa ne yasa shi fadin. "Gobe in Allah ya kaimu da yamma. An gama arranging komai....... " Bata iya tace komai ba. Hannun shi ta cire daga fuskarta tana jingina bayanta da bango. Takai tsahon mintina biyar tana kokarin hadiye abinda ya tokare mata a wuya kamun tace. "Allah ya kaimu goben ya bashi lafiya and........ And..... " Kasa karasawa tayi saboda kukan dake shirin kwace mata. Kallonta yai yana dakuna fuska saboda bai san me yake bata mata rai banda damuwar Nas ba. Kokarin karantar fuskarta yake ba saiya tambaya ba. Ya kasa saida tace. "Ka kula da kanka sosai" "Husnaaa..... " Ya fadi da wani yanayi ya dora da. "Kin dauka zan tafi inbarki ne? Kwana talatin fa. Tare zamu tafi" Wani numfashi da batasan tana rike dashi ba ta saki. Duk da damuwar da yake ji bai hana shi sakin mata wani tattausan murmushi ba. Cikin sigar tsokana yace. "Hawayen missing dina ne nan aka zubdo?" Hannuwanta tasa ta rufe fuskarta saboda wata kunya takeji. Tun tana mamakin damuwarta akan shi harta daina. Prince ishaq dinne akwai shiga rai ba kadan ba. Yanayin kulawar shi da komai. Suna nan zaune shiru har akai isha.i. Ta mike dan ya sake jan su sallar isha.i sai taga ya nufi hanyar toilet. "Ina zakaje?" Ta bukata. "Alwala zan" Ya bata amsa a takaice. "Oh...... " Ta fadi da dariya a muryarta. Hakan ya sashi zaro idanuwan shi dan yagama gane me "Oh..." dinta take nufi. Fuskar shi datai wani ja take kallo. Batasan sanda dariya ta kwace mata ba. Gentle da tusa. Abin ne taji shi wani gingirin gin. Ga kunyar da tagani a fuskarshi ta sake bata dariya. Yai tsaye shiru yana kallonta. Bawai dan baya abinda take tunani bane. Yadaiji kunya ne kawai. Kuma taba tan dayaine ya karya masa alwala. Dakewa yai ya soma takawa inda take yana fadin. "Hussy ni kike ma dariya...." Matsawa take tasa hannuwanta tana kokarin tsayar dashi har yakaita bango. Hannuwan ya rike da duk nashi biyun ya matse ta da bangon sosai. Gaba dayanta a jikinshi take. Da kamshinsa daya cika mata hanci. Ya sunkuyo da kanshi saitin fuskarta. Kasa yai da murya sosai dai dai kunnenta yace. "Dariyar me kike?" Jikinta ya dauki dumi. Kafafuwanta na mata kashedin kasa daukar nauyinta. Sumba ya manna mata a fuska da wuyanta ta cikin hijab din dake sanye jikinta. Jiyai abin na neman fin karfinsa. A hankali ya janye jikinshi daga nata batare daya saki hannuwanta ba. Dan ya kula batada wadattacen karfi a jikinta. Daya zuwa goma yake kirgawa cikin kansa. Dan juriyarsa akan husna ta soma kadan. Shi kadai yasan abinda yake ji. Murya a dishe yace. "Wuce mu sake alwala" "Jeka fito tukunna.... " Ta fadi dakyar. Bai mata musu ba ya saki hannunta ya wuce. Bango tabi ta zauna kan gado tana maida numfashi. * Suna tashi da safe. Sukai sallar subh. Husna ta shiga wanka. Data fito wanka prince ishaq taga yana cire bedsheet. Abin ya bata mamaki. "Gentle da kanka. Da saika bari in fito ai. Ko kasa ai maka" Dagowa yai ya kalleta yace "Um um fa. Bamai shigarmun bedroom. Ni nake gyara abuna in share. Iyakacin yan aiki babban falo shima sai da dalili" Kallon shi kawai take cike da mamaki. Ta girgiza kai tace. "What kind of a prince are you?" Tambayarta ta bashi dariya. Shiru yai mata ya karasa cire bedsheet din. Ya dauka ya nufi fita da alamu zai bayar ne a wanke. Mai husna take shafawa sanda ya dawo. Dakin da suke sake kaya taga ya shiga ya fito da wani zanin gadon da rigunan pillow. Man da take shafawa ta ajiye. Ta mike tana fadin "Kawo kaje kai wankan ka" Ba tare daya kalle ta ba yace "Ki sa pillow case din kawai. I will make the bed" Sanin baya son gaddama ne yasa tai abinda yace din. Ta taya shi suka gyara gadon tsaf. Zaka rantse ba tafiya zasuyi yau ba. Hakan daya fado mata a raine yasata fadin. "Bazai yi kura ba kamun mu dawo?" Yadan yi jim sannan yace "Kamala zaizo asa ledoji a rufe komai" Kamun tace wani abu ya wuce ya shiga toilet. Fita tai ta nufi dakinta tana mamakin kalar rayuwarshi. Yana da jin kai amman nasa kala dabanne akan yanda take jin labarin yaran sarauta. * Ita ya bari ta hada musu kaya. Akwati daya suka dauka. Ta zuba duk wani muhimmin abu data san zasu bukata. Yan kana na kuma ta zuba cikin jakar hannunta. Karfe uku yai mata waya ya turo kamala yazo ya tafi da ita zuwa airport. * Nas take kallo a yanayin shi zaka rantse lafiyarshi kalau. Shi kadai yasan abinda yake ji. "Oh sannu Nas. Allah ya baka lafiya" Ta fadi tana jin duk ba dadi. "Antina amin. Yaya har wani murmushi yake. Nifa nace ya taho dake" Kwalo idanu husna tai cikin mamaki. Tace "Allah sarki kanina nagode" "Idan kun gama ku wuce mu shiga ciki" Prince ishaq ya fadi. Dan bashida lokacin tsokanarsun nan. Bayajin maganar. Karfe hudu jirginsu ya tashi zuw india. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣7⃣ INDIA. A bala.in gajiye suka sauka. Musamman Nas da shi kadai yasan yanda yake ji cikin kanshi. Suna sauka airport ya kira doc din suka sake magana. Zama sukai akazo da motar asibitin aka dauke su. Hankalin shi bai nutsu waje daya ba sai da aka shiga da Nas checking. Yaje yagani da idanuwanshi. Gabanshi sukai sedating din Nas din bacci mai nauyi ya dauke shi. Addu.o.i yai mishi sosai sannan ya fito ya samu husna zaune a waiting room tana jiran shi. Murmushi yai mata. "Gajiya ko?" Ya tambaya yana nazarin fuskarta. Kai kawai ta daga mishi dan bata saba irin wannan tafiyar ba. Ga yunwa na cinta. Akwatinsu ya dauka cak. Husna ta bishi da idanuwa tana mamakin karfin shi. Jan akwatin tai dazun amman harda nishinta. Hannu ya mika mata. Ta kama ya dago ta. Har lokacin murmushine a fuskar shi. Yanda yaga gaba daya husna tai laushi. Lifter suka shiga ta saukar dasu zuwa kasa. Suka fita daga asibitin. Hannun shi damtse danata kaman wadda za.a kwace. * Taxi suka hau. Turancin ba ibdiyan mai taxi din dakyar yake haduwa yace mishi ya kaisu wani hotel mai kyau. Amman indai da mai kyau kusa kusa da asibitin yakai su nan. Haka kuwa akai wani dan hotel yakai su. "Hotel ka mubarak" baiyi nisa can da asibitin ba. Kuma yana da dan kyau. Husna sai dai idanu dan tagama gajiya gabaki dayanta. * "Yunwa ko?" Ya fadi yana zama kusa da husna. Kai ta daga mishi ya bata fuska alamar baya so. Hakan ya sata cewa "Eh yunwa fa" Mikewa yai. "Barin samo mana abinda zamuci" Kwanciya tai kan gadon kamun ya dawo. * Yanayin yawancin abincin yagani yasan da wuyar gaske ya ciyu wajensu. Dan haka ya siyo musu kaji da lemuka. Kwankwasawa yai ya tura da sallama ga mamakin shi husna har tai bacci. Badon yunwar da take jiba sam da bai tashe ta ba. Ajiye kayan yai a kasa. Ya zauna gefen gadon. Hannunshi yasa ya shafa kuncinta. Ta ture hannun shi tana sake gyara kwanciyarta. Hannuwanshi yasa duk biyun ya dagota kaman yarinya karama. Ya tallabota jikinshi. A hankali yake jijjigata yana fadin. "Hussy mana. Tashi kici wani abu" Sake langabewa tai jikinshi. Ya lumshe idanuwa yana jin wani yanayi da yake wahalar dashi. Ya sauke numfashi yana sake girgizata. Amman ina gajiyar datai tasa baccin yaci karfinta. Yana son ya tasheta da salonshi sai dai shi zai wahala. Yanda yake ji ma a yanzun kawai ya ishe shi. Dakyar ya samu ta tashi kaman zata saka mishi kuka. Ya kama hannunta zuwa toilet. Ruwa ya zuba mata yace ta wanke fuska da bakinta. Ya sake riko ta zuwa bedroom din. Zaunar da ita yai tana wani murza idanuwa da hannuwanta. Ta wani burge shi. Ya nutsu yana kallonta kamun ya dauko ledar ya bude musu. Tare suka ci. Tana gamawa ta lallaba tahau gadon ta kwanta. Prince ishaq sai da yai wanka sannan yazo ya kwanta. Matsawa yai sosai kusa da husna yanajin wani abu na fisgarsa. Adduo.i yai musu ya dora kanshi a kafadarta yana sauke numfashi. A haka har bacci ya dauke shi. * Da safe da suka tashi. Tana jinshi yana kiran yan gidansu suna gaisawa. Saita tsinci kanta da jin wata kewar mamanta ta rufeta. Yaushe rabon da ko taji muryarsu. In sun waya da maheer ne takan ce ya gaishe mata dasu. Ita ta kasa kira. Su kuma tasan fushin sune bai gama hucewa ba shisa basu neme ta ba. * Magana yake ta mata yaji shiru. Karasowa yai ya zauna kusa da ita. Ya taba mata kafada hadi da fadin. "Hey.... " Dagowa tai ta kalle shi tana sauke numfashi. "Tunanin me kike?" Ya tambaya yana tsareta da idanuwanshi. "Bako..... " Hannu ya daga mata alamar baya son ji. Shirun kuwa tai. Sosai ya kalleta cikin fuska sannan yace "Feel free idan ba zaki iya gayamun damuwarki ba. But yau yaza ma na karshe da zakimun karya" Mikewa yai dan haka kawai yaji ranshi ya baci. Yasan bashida matsayin da zaice saita fada masa komai dake damunta. Yana dai fatan wata rana tazo da bama saiya tambaya ba zata fada mishi. Husna taga alamar ta bata mishi rai. Bawai gaya masa ne ba zata iya ba. Bata son damunshi ne da damuwarta. Hidimomin shi sun masa yawa. A hankali tace "Ba haka bane gentle bana son damunka ne fa" Agogon shi yake daurawa baice mata komai ba. Tasan yana jinta hakan yasa ta ci gaba. "Yanda kake waya dasu umma ne ya sani missing nawa family din. Shine kawai" Yanda ta karasa maganar da wani sanyin murya yasa shi fadin "Crap" Cikin kanshi. Dan baima san yanda akai tunanin suje gidansu baizo masa ba. Ya kamata ace koda sau dayane sunje tare ma. Yaga kalar family dinta ya gaishe dasu. Batare daya juyo ba yace mata. "Zamu kirasu anjima mu gaishe dasu. Idan mun koma gida zamuje" Dan kunyarta ma yaji ta wani saukar masa. Gaskiya bai kyauta ba. Ko da sanda aka bashi ita baya so. Wanda yai maka karamcin aura masa yarka ya cancan ci mutuntawa. "Allah ya kaimu" Ta furta. Baya son maganar don haka yace "Mu tsaya mu karya ko sai munje wajen Nas?" "Muje din. Kaga munbarshi tun jiya karya farka bakon waje" Juyowa yai ya kalleta alamar ta shirya. Ya kuma daga mata kai cewar ya ji me tace. Wani hade fuska tayi yanda yakanyi. Cikin kwaikwayon muryarshi tace "Bana son magana da kai. Ka bude bakinka ka amsani" Towel din dake gefenshi ya dauka ya cilla mata a fuska. Yana rufe tashi fuskar da hannuwanshi. "I love the way you blush" Husna ta fadi tana sake kwashewa da dariya. Kunyar shi na bata mamaki. Sai kaga fuskar nan mai kyau tayi wani ja. Bata ga tahowar shi ba saboda dariyar da take. Jinshi kawai tai kusa da ita sosai. Dariyar ta tsaya mata a wuya. Idanuwanshi ya zuba mata. "Kika ce menene?" Ya fada can kasan makoshi. Ji tai jikinta ya dauki dumi duk wata kalma ta tsaya mata. Fuskarshi ya matsar kusa da tata. Tanajin numfashin shi saman fuskarta. Ya wani ja iska yana lumshe idanuwa. Gaba daya yagama saukar mata da kasala. Sumba ya manna mata a wuya da kumatu da kan hancinta. Tayi luf da ita. Tanajin yanda jikinta ke amsa duk wani sakon da yake tura mishi. Hannu yasa ya zagaye mata lips sannan ya saka hannun a baki yana tasting kalar man leben data saka. Dakyar ya samu ya mike. Yana azabtuwa da yanda yake ji din nan. Sai dai inba tabbatarwa yai da son shi a zuciyarta ba. Bazai iya wuce fiye da yanda yake yin nan ba yanzun. Ko baki bazai iya hadawa da macen da bata son shi ba balle a wuce hakan. "Tashi ki shirya mu tafi" ya fadi yana maida numfashi. Yanda ta amsa "Uhummm" Din dakyar ya sa shi dariya. Yana kallon yanda take sunkuyar dakai a rashi yace good. Yanzun ta sa yaji kunya. * Suna isa asibitin kuwa Nas yace yanzun ake shirin kiransu saboda za.a shiga dashi aiki. Prince ishaq ya kalla idanuwan shi cike da wata kaunar yayan nashi yace. "Yaya ka yafemun. Just incase ko da wani....... " Girgiza masa kai prince ishaq yake. Muryarshi a dake yace "No Naseer. No and i mean NO bana son ji. Allah zai baka lafiya munyi addu.a" "Antina" Ya fadi yana maida hankalin shi kan husna. Kuka take. Nas yace "Haba mana super anty. In kina haka wazai kulamun da yayana" Hannu tasa tana kokarin goge hawayen fuskarta amman ta kasa. Prince ishaq ne ya kamota. Tako yi luf jikin shi tana kuka. Dakyar ta samu nutsuwa ta dago. Tace "Kanina Allah yasa a fito lafiya. Allah ya baka lafiya" Ya amsa da amin. Suna kallo akazo aka tafi da Nas din. Shi kanshi prince ishaq daya tambaya akace masa awanni takwas za.a dauka ana aikin. Sai da yaji jikinshi yayi sanyi. Nan suka zauna husna ta kwantar da kanta saman cinyarshi. Shikuma nashi kan na saman kafadarta. Suna jiran hukuncin Allah. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣8⃣ Anyi ma Nas aiki cikin nasara. Komai na tafiya yanda ake so da yardar Allah. * Yau satin su daya kenan a india. Suna zaune a hotel room dinsu prince ishaq yai zaune shiru. Husna na cin cookies tana game din datai downloading a tablet dinshi. Taga shirun shi ya wuce misali ta dago tace "yadai?" Da wani yanayi a idanuwanshi da ta kasa fahimta yace. "Kinsan sai yanzun nai tunanin kasar nan babu wanda yasanni. Banida wani matsayi sai na koma tawa kasar......" Kallon shi take da mamaki ya ci gaba da fadin "Zan iya kome nake so. Zan iya rayuwata free hussy" Yanayin da yake maganar ya sata fadin. "Me kake sonyi? Kamun mu koma?" Murmushin nan nashi yai mata har dimple din fuskarshi ya fito. "I wanna have fun. Naseer is ok. Ina son living sauran days dina kamun in koma gida to the fullest" Wayar husna ta saka a key. Ta ajiye cookies din gefe tana fadin "Tashi ka shirya to. Muje wajen Nas mu tafi yawo" Mikewa yai ya nufi bathroom. Ta girgiza kai. Yanda yanayinsa yake cike da farin ciki ya mata dadi. Kome yake sonyi ita kam zata taya shi. Kaman yanda ya bata kwarin gwiwa ta kira iyayenta. Dan jiya tai bacci wanda ta jima bata yishi ba. Taji muryar iyayenta. Ta gaisa da kowa. Sun sa mata albarka. Har kuka sai da tai dan farin ciki. To name ita ba zata taya shi ya samu nashi farin cikin ba. Tana nan zaune ya fito. Itama ta tashi tayo wanka. Doguwar riga ta saka loose tai rolling mayafin akanta. Duk da babu kwalliya a fuskarta ta mishi kyau sosai. Fita zasuyi tazo gabanshi ta tsaya. Hannuwanshi ta riko ta sauke idanuwanta cikin nashi. So take yaga yanda tai nadamar abinda tai masa. Muryarta na rawa tace "Har yanzun baka ce ka yafemun ba gentle. Nayi kuskure mai girma nasani amman.......... " "Na yafe miki husna. Na yafe miki tun kamun ki rokeni" Batasan lokacin sata rungume shi ba. Dan ji tai kaman ya sauke mata wani katon nauyi. Hannuwanshi yasa ya rungumeta na wasu dakikai kamun ya sake ta. * Sai da suka biya wajen Nas. Dakyar ma yake musu magana saboda magunguna sun fara dibarshi. Saida yai bacci tukunna suka fito. Su kansu basu san inda zasu je ba. Hannun ta na cikin nashi. Hanya kawai suka diba. Duk titin dayai musu su bi. Wani ad husna tagani na poster din wani film. "O. M. G wallahi ina mugun son actor din can..... " Ta fadi tana nuna ma prince ishaq. Kallon guy din yai. "Vijay yayi fa. Kyanshi wani nutsatse ne. Kaga inyai dariya..... " Mintsininta yai a hannunta da yake rike dashi. Hakan ya katse mata magana ta kwace hannu tana fadin "Ouchhh gentle mana.... " Fuskarshi daya murtuke ta kalla. "Muna tare ne kike kiran wancan tikeken katon nada kyau?" Kwashe wa tai da dariya. "You are jealous...... " Tace tana ci gaba da dariya. Kuma ya wani murtuke fuska zaka rantse bai taba dariya ba. Da gasken kishi yaji. Ya za ai ma suna tare tace wani nada kyau. Son vijay din ya mata sauki. Nashi ne mai wahala. Wucewa yai abinshi ta bi bayanshi tana dariya. Wajen ice cream ta gani da sauri tace "Gentle ice cream" "Nagan shi ai" Ya fadi yana ci gaba da tafiya. Ganin zasu wuce yasa tace "Saimun zakai fa" Tsayawa yai ya dora hannayen shi a kuqu yace "Mu koma wajen poster din vijay ki fada masa ya sai miki" Rau rau tai da ido tace "Yi hakuri. Kawai yana burge ni fa. Kama fishi kyau" Murmushi ya kwace masa. Dan yasan sai dai yafi vijay kyawun zuciya da hasken musulunci. Kama hannunta yai suka tsallaka wajen ice cream din. Guda uku ya sai mata ita kadai. "Kai baka dauka ba fa" Ta fadi tana dandana na hannunta. Ta wani lumshe ido dan bata taba shan ice cream mai dadin shi ba. Ya girgiza mata kai yana kallon yanda take shan ice cream din yana burge shi. Sha kaji da dadi sosai fa. Kamun yace wani abu ta mika masa. Saboda ya mata tsaho yasa ta mika hannu sosai. Ta ko dangwala mishi a hanci da kumatu. Da sauri yakai hannu yana gogewa. Baya son sanyi. Cokalin ya dauka ya dibo ya dangwala mata a fuska. Da sauri ita ma ta goge tana fadin "Bana so fa. Sai ka samun danqo. Ni ka sha karyai melting" Kadan ya diba ya sha. Yace mata "Umm ba laifi" Ta zaro ido "Wallahi da dadi sosai. Bakinka bashi da taste" Gira ya daga mata duka biyun alamar shi dinne bakin shi ba taste. Jiranta yai ta shanye ice cream din sannan. Tace mishi "A karo mu tafi dashi" Ya girgiza mata kai yana fadin "Ya isa haka. Sai kinyi mura ko?" Yanayin yanda yai maganar ne kawai yasa tai shiru ba don ta koshi da ice cream din ba. Fitowa sukai suka sake mikar hanya. Aikam suka shiga wani layi kamar mini market. Ana saide saiden abubuwa a wajen. Wasu bangles ya hango sun mishi kyau sosai. Yaja husna wajen. Ya taba yana cema mutumin. "I want this and that. How much" Da alama banda wanda prince ishaq ya taba da wanda ya nuna da hannu bai gane me yake nufi ba. "ve kitane hain?(nawa suke?)" Husna ta tambaya da yasa prince ishaq ya tsaya kallonta cike da mamaki. "teen hajaar ma'am" (dubu uku) Mai saida bangle din ya fada. "Antim mooly? (gaskiya kenan?) "Yes ma'am" Juyawa tai ta kalli prince ishaq tace "Ka dibo kudi saiya bamu canji tunda ba sanin kan kudinsu mukai ba" Cike da mamaki ya dauko wallet dinshi ya mika mata. Ta dibo kudin ta bashi Ya basu guda biyun da prince ishaq ya nuna ya dibo canji. Sai da ta kamo hannun prince ishaq suka fito daga kasuwar. Kwace hannunshi yai ya tsaya "Daman kina gane wannan jagwalgwalon hindi din kika barni da mai taxi dazun?" Dariya tai tace "Kadan kadan ne fa. Kuma shima dan hindi ne. Mai taxi din dazun urdu yake yi. Ka taho mu tafi" Ya maqale kafada. "Kafafuwana sun gaji. Mu sami taxi mu koma hotel dinmu. Ban labarin yanda akai kike ji" Matsawa tai ta tsaya kusa dashi sannan tace "Ina ganewa sosai saboda ina yawan kallon film dinsu masu translation. Amman kadan kadan nake rikewa fa" Kallonta yake tana kara wani burge shi. Haka suka ci gaba da labari har suka koma hotel dinsu. Wanka yai ya fito. Itama tayi. Sukai ordering nama da lemo dan sun gwada cin kalar abincinsu rannan basu ji dadin shi ba. Ita husna ma kadan taci. Dan duk a hanya yaita siya mata tarkacen duk da tagani tace tana so. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 4⃣9⃣ Yauma bayan sun shirya sai da suka fara biyawa suka ce ma Nas zasu je yawo in sun dawo zasu biyo. Idan doctors din sun yarda wajen shi ma zasu kwana. "Go do your romantic yawo. Nikam am fine. Bama saikun dawo ba munyi waya" Nas ya fadi yana musu murmushinsa yana jin dadin ganin yayan na shi cikin nutsuwa da walwala haka. Saida suka dan kara hira tukunna suka fita. Mai taxi din da suka hau yana gane turanci dan haka prince ishaq yace yakai su inda ake bada renting din mota. Aikam shi ya rakasu. Kasancewar ba yan kasa bane yasa da suka biya kudin renting din motar. Saida ya bada passport dinsu shida husna. Insun dawo da motar a basu abinsu. Sai da suka shiga ne suka dauki hanya husna tace masa "Ina zamuje ne wai? Ka wani kama mota kaman kasan gari" Dariya yai ya daga mata kafadu yace "Mu dauki hanya kawai muga gari. Duk inda muka gaji mu dawo" Rigimar shi din nan tana bata mamaki a lokaci daya tana burgeta. "Kawai ina son yanda nake da damar fita duk inda nake so ba wani fargaba. Ba kallon mudubi ko wasu na biye dani" Ya fadi cikin sanyin murya da yasa ta jin wani abu ya tsaya mata a wuya. Sam rayuwar su bata mishi adalci wani lokacin. Daurewa tai tace "Mu na bin gabas saboda tafi sa.a" Baisan lokacin da dariya ya kwace masa ba. Itama dariyar tai. Suka dauki hanya. Duk inda ya burge shi su fito su gani. Idan wajen siyar da abune su duba su siya wanda yai musu su fito. Sosai yawo suke abinsu. Wani waje suka tsaya inda suka ga masallaci. Gashi nan maza da mata. Fita sukai suka shiga. Sukai alwala. Husna ta wuce inda matan ke bi. Tai sallah. Ta riga shi idarwa ma ta fito wajen motar tana jiranshi. Saida suka shiga yace "Wallahi ji nake kaman muyi zaman mu kar mu koma gida fa" Ta kai hannu ta ja mishi kumatu ya ture yana dariya. * Yamma tayi zagayen gari kawai suke. Hadari ya hado. Iska aka fara sosai hakan yasa shi samun wani waje sukai parking. Zaman su sukai cikin motar shiru. Ya jingina da kujera yana kallon husna da take danne dannenta a waya. Ruwa ya tsuge ba shiri suka rufe gilasan motar. "Yau zamu kwana anan kenan" Cewar husna A kasalance yace mata "Inji waye da ruwan nan ya tsagaita zamuyi tafiyar mu abinmu" Ba ai mintina ashirin ba ruwan ya soma daukewa ya kalle ta yace "You see... " Murmushi kawai tai masa suka kama hanya. Ko tafiyar mintina goma basuyi ba motar ta fara wani slow kamun ta dauke. Suka kalli juna shida husna. Bude motar yai ya fita zaka rantse da Allah yasan abinda ya samu motar. Yana bude murfin wani hayaqi na fitowa da yasa shi rufewa da sauri yana tari. Husna ta fita da saurinta. Ta kalle shi yana kore hayakin da hannu yana tari. "Mechanic gentle. Meye matsalar motar ne?" Ta tambaya cikin tsokana tana danne dariyarta. Hannuwanshi ya ajiye. Yana kallonta fuska a hade. "O. M. G....... " Husna ta fadi tana wata dariya harda dafa mota. Gaba daya hayaqin ya bule mishi a fuska. Bakine har goshin shi kaman wanda kurar gawayi ta bata. Dariya take sosai cike da mamaki yace mata "Wai meke baki dariya. Mun makale a wajen nan kina dariya ko hussy" Dakyar ta iya hadiye dariyar tace masa bakomai fa. Tsaye sukai jikin motar suna jiran wani yazo wucewa ya taimaka musu. Husna ta kauda kai gefe dan data kalli prince ishaq dariya kara kamata takeyi. Wani suka samu ya ko tsaya. Babban mutum ne amman yanajin turanci sosai. Shi ya duba musu motar sukai masa godiya sosai suka shiga suka tafi. Sam bai kula da bakin dake fuskar shi ba. Duhu harya fara sanda suka maida motar. Taxi suka hau suka koma hotel dinsu. * Husna ta kalle shi yanata shagwabe fuskarshi duk baki baki a jiki ta sake kwashewa da dariya. Kamota yai tana kokarin kwacewa ya matse ta jikinshi yana fadin. "saikin gayamun me kike ma dariya" Jan shi tai wajen mudubi ta nuna masa fuskarshi. Ya zaro idanuwa sannan ya kwashe da dariya shima. Hannunshi yasa ya shiga goge fuskarshi yana dariya. "Hussy ke ko...... " "bakai sarkin gyara ba shisa nai shiru ai....... " Gani tai bai gama gogewa ba tace "Akwai fa...... " Yasa hannu ya ske gogewa. Ta girgiza masa kai alamar baiba tana matsawa gab dashi. Hannuwanta takai cikin nutsuwa ta na goge masa. Kallonta yake. Itana tsayawa tai tana kallon shin. Hannunta daya nakan fuskarshi. Kama hannun dake fuskarshi yai da dayan hannu. Ya riko ta yana dora goshin shi saman nata. "Husnaa...... " Ya ja sunanta muryarshi can kasa. Ta kasa amsa shi saboda gani take tana bude bakinta babu abinda zai fito sai karar bugun da zuciyarta take. Koma manene take ji a game da prince ishaq babbane. Yanayi ne da bata taba sanin akwai shi ba. Yanayi ne da babu kalaman da zasuyi adalci wajen bayyana shi. Hannunta ta kwace daga nashi ta dora shi kan wuyanshi yana sake hade goshinsu tare. Lumshe idanuwanta tai tana jin kamshin shi na shigarta yana kara saukar mata da abubuwa masu yawa. A hankali suna goge wasu hotuna na rayuwar ta ta baya ba ma tare data kula da hakan ba. Basu san iya lokacin da suka dauka ba. Dan prince ishaq sam baya son yanayin nan ya wuce. Saboda komai na yanayin ya masa. Haka ya hango rayuwar shi babu hayaniyar mulki a cikinta. Dakyar ya kamata yajata zuwa kan gadon. Kwanciya yai sannan ya rikota jikin shi. Ko kayan jikinsu basu sake bama balle suyi tunanin yin wani wanka. Kwanciya sukai shiru abinsu. Sun jima haka sosai kowa da abinda yake ji. Sallar isha.i suka tashi sukai. Babu mai bakin magana. Wannan karon da suka koma kwanciya. Juya bayanshi yai yana jin wani zazzabin wahalar abinda yake jurewa na saukar mishi. Ya lumshe idanuwanshi dayaji ta matso jikinshi ta kwantar da kanta a bayanshi. Dumin numfashinta a kan wuyanshi. Bai juyo ba a haka yai musu addu.a. Yana jin yanayinta bacci ya dauketa. Ya samu ya janye jikinshi ya shiga toilet ya sakar ma kanshi ruwa mai sanyi shine kawai saukin shi. Alwala ya dauro dan baccin yaga alamar zai wuyar ya samu wajen shi. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 5⃣0⃣ Rayuwa ba ta da wahala. Yau satin su uku a india. Kullum daga wajen Nas babu inda suke zuwa sai yawo abinsu. Da wucewar duk wata dakika ta ranakun nan da shigar wata shakuwa ta ban mamaki tsakanin su. Tare da mulkin dake jiranshi ya hango rikici kwance. Sai dai bai hango shigowar husna rayuwar shi ba. * Randa aka sallami Nas sauran kwana biyu kwanakin da suka diba ya cika. Dan yaji sauki ne sosai. Karfin addu.ar da ake. Taxi suka dauka su duka ukkun. Tare suka koma hotel din aka kama ma Nas nashi dakin kusa da nasu. * Prince ishaq ya dawo daga duba Nas ya shigo yace ma husna ta fito suje waje. Bata musa mishi ba duk da dare ne. Ta dauki mayafinta suka fita. * Kasan hotel din suka shiga wani dan bakery suka siyi coffee suka fito. Takawa suke suka samu wani lilo babu kowa a wajen. Zama sukayi akai. Prince ishaq ya soma rocking dinsu. Husna tace "Gentle karka yaddo mu fa" Dariya yai. "Kin cika tsoro" Saida ta kurbi coffee dinta sannan tace "Um um fa ba tsoro bane. Da gaskiyata" Shiru sukai "Nagode husna" Ya fadi kaman daga sama. "Godiyar me kake mun?" Ta bukata dan ita bataga dalilin yi mata godiyar ba. Itama ya kamata tai masa godiya. Na fargar da ita dayai daga halaka. Na zama dalilin shiryawarta da iyayenta. Hannun shi ta riko. Sannan yace "Nagode sosai husna. For everything" Shiru tai dan batasan me ma ya kamata tace masa ba. Su. Jima sosai a wajen suna zaune ya a rocking dinsu kan lilon kamun yace mata "Dare yanayi mu koma ko?" Mikewa tai. * Washe gari su uku suka fita harda Nas din. Siyayyar tsaraba sukayi. Nas sarkin shiririta. Yaita basu dariya. * Da daren ranar suka hada komai nasu washe gari karfe takwas a Airport tai musu. Karfe tara jirginsu ya tashi zuwa gida nigeria. *** NIGERIA Wannan karon harda mumyn Nas akazo tararsu. Da wasu yan mata su biyu da husna bata taba gani ba. Dayar bakace sosai. Amman tana da kyau. Dayar hasken su zaizo daya da Nas. Bama su bi takan husna ba. Farar doguwa mai matsakaicin jiki ce ta rike nas din tana wani irin kuka. "Am okay. Everything is ok billy" Nas din ke fadi amman kaman ma ba jinshi take ba. Sai da suka sa husna hawaye. Sakin nas tai takama hannun prince ishaq. Hannu yasa ya goge mata hawayen yana girgiza mata kai. "He is okay. Komai zai wuce" Husna dai kallon su kawai take. Ya saki hannun yarinyar daya kira da billy ya janyo husna yace mata. "Hussy ga sister na bilkisu. Tana karatu ne a saudi. Ga dayar kuma fauziyya. Su duka suna karatu ne a saudi. Billy ta gama ita fauzy ne da saura" Murmushi taima husna tace "Mungode sosai da karamci. Welcome to the family. Muna farin cikin shigowarki" "Nima nagode bilkisu" Gaisawa sukai da fauzy fuskarta babu yabo ba fallasa har hakan yasa husna kallon prince ishaq. "Karki damu haka fauzy take da kowa. Baki ga nima kai kawai ta daga mun ba?" Murmushi husna tan dan ta fahimci fauzy irinsu daya da prince ishaq miskilanci. Dukansu gidansu prince ishaq din suka sauka. * Nan ma suka kwana. Saboda maganar bikin billy da duka saura sati biyu. Dan tun tana saudi aka sa rana. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 5⃣1⃣ Husna da kanta ta kira gidansu ta fada sa bikin gidansu prince ishaq din. "Mama ba zaki zo ki ganni ba" Cewar husna Tanajin dariyar maman nata ta cikin waya tace "Husna nikam inzo in miki menene. Idan naji kina kafiya ma ya wadatar" Husna ta langabar dakai tamkar tana ganinta cikin sanyin murya tace "Tam shike nan mama. Ki gaishe mun da abba" "zaiji in shaa Allah. Ki kula banda sakarci husna. Kiyita hakuri zaman yau da gobe sai da hakuri" Ta amsa da "In shaa Allah mama zan kula. Sai anjima" Gaba daya tagaji da kalaluwan abincin da suke ci. Tuwo ma take marmari ita. Dan haka ta tashi da kanta. Tasa asabe ta rakata store. Shakare yake da kayan abinci. Ta dauko semo leda daya tasa aka rakata kitchen din da bata taba sanin hanyar da yake ba. * Asabe ta tayata. Gyaran cefane tai markada a blender. Tuwo tayi miyar danyar kubewa da kaji. Ta saka a warmer abinta tasa asabe ta dauko mata zuwa bangarenta. Saida tabari cewar a bare mata ginger a markada sannan ta wuce. Sallar Asr tayi. Ta fito ta kima kitchen din ta hada ginger drink ta zubo a jug tasaka kankaru ta fito. Tana zuwa babban falo prince ishaq na shigowa. Ga hannuwanta duk kaya. Sallamarshi ta amsa. Ya tako inda take ya na kokarin karbar jug din. Ta fito masa da idanuwa tace "Gentle rufamun asiri kar hadimanka sugani ina saka future king aiki" Dariya kawai yai yace "Nikam kibani abin nan. Ba aiki zan ba. Ya burge ni ne zan sha" Da sauri ta wuce tana fadin bafa abinda zan baka ka taho muje ka dan huta sannan. Ya wani tabare fuska yana binta. Bangarenta suka nufa yasa rikici ai shifa sai ya sha abin nan na cikin jug. Dole ta zuba mishi yasha yana neman kari "Gentle zai kulle maka ciki. Please muje kayi wanka tukunna" Hannun shi ta kama taja shi bedroom dinta. Da kanta ta tayashi ya cire alkyabbar shi ya shiga toilet. Dakinshi taje ta dauko masa wani yadi marar nauyi fari. Ta feso mishi collections din turarukan shi ta dawo. Harya fito ta bashi kayan ta sake fita. Ko minti biyar baiba ya fito falonta ya zauna yace mata "Yunwa nake ji fa" Ya fadi dan duk ranar sunata hidimar auren billy. Bai samu zama ba. "Me zakaci? Sai inje in dibo maka" Ta bukata dan bata tunanin zaici tuwo. "Duk abinda zakici" Ya fadi. Ta ce "um um fa. Ni nagaji da kalaluwan abincin nan. Na shiga kitchen nayi tuwo miyar kubewa" Ai gani tai ya gyara zama yace "amman kin taimaka husna. Kisan rabon da inci tuwo anyi shekaru? Da umma tana mana tun kamun in tafi karatu" Kallon shi take da mamaki tace "Wai da gaske zakaci tuwon?" Daga mata kai yake yace "Nikam ki zubo mun hanjina yana kullewa" Xuba musu tai. Suka sauka kasa kan kafet. Tai mamaki sunci tuwon sosai. Suka shanye lemonsu. Prince ishaq nata mata santi. "Husna gobe ma ki dafa mana wani abu. Na gargajiya" Da dariya a muryarta tace "Zakaci dambun shinkafa" Ya jinjina kai yace "Ban tabaci ba. Amman komai kikai nasan zaiyi dadi" Hira suka shigayi sosai kan abinci. Itama sai taji dadin yanda taga yaci Ta godema Allah taima mahaifiyarta addua data tsaya taga ta koyi girki. Ta dauka niyya a ranta daga ranar kome take zata shiga kitchen tunda ga yan tayi ta dafa ma mijinta duk abinda yake so. Da dare haka yace mata lemon dazun ya masa dadi sosai. Batace komai ba ta tashi taje kitchen ta kara hado mishi wani. Kissing dinta yai a goshi da kumatu. Nan dakinta ya kwanta yace bazai iya zuwa dakinshi ba yagaji sosai. *** Kwanci tashi babu wahala wajen Allah. Ga bikin billy yau saura kwana biyu. * Zaune ya sameta a parlour d'in kasa ta kurawa wayarta ido tana chat da khausar sai uban murmushi takeyi harma batasan yashigo ba. Kamshinsa ne daman take gane shigowarshi dashi. To yanzun kamun ya fita ya gama dakunata itama kamshin nasa take. Ko da taji shi ya cika mata hanci ma ta dauka na jikinta ne daya rungumeta sanda zai fita. Tabayanta ya zago ya warce wayar juyowa tayi gaba daya ta kalleshi. Murmushi tai tace "Gentle yaushe ka shigo?" Dariya ya saka ya wuce abinshi yana fadin "Kinata danna waya ina zakiga shigowata" Mikewa tai ta bishi tana fadin. "Gentle ka tsaya mana. Kaifa nake jira daman" Side dinshinsuka wuce. Ya ajiye wayar kan gado. Yana wani dakuna fuska shi a dole fushi yake. "Waya fad'a maka banji shigowar kaba,naji fa bayan kamanta fushi nake dakai kafita bansaniba" Juyowa yayi ya kalleta kawai ya wuce dakin sake kaya. Ya fito "Ki shirya, umma tamun waya komai naki yana can wai kije tun yau" Wani murmushi ya kwace mata "Inje in dauko hijab dina?" Janyo ta jikinshi yai ya furta "Kina murna zaki barni har kwana wajen hudu. Ko kewana ba zakiji ba ko?" "Waya gaya maka ni baruwana duk inda zakaje zan bikane" Murmushi yamata yace "hargun mai martaba saikin bini?" Waro idonta tayi suka kwashe da dariya dukkansu.... * Biki ya kankama yau ake kamun Amrya Billy da Angonta saeed. Amarya da ango sunsha kyau a taheer guest palace ake bikin kamun. Hussy tashirya tayi kyau iya kyau domin kuwa takanas ta kira belleza, tazo tamata makeup kuma ba laifi tamasifan yi kyau, blue and yellow tayi bawani mayafi ta yafaba. Ashoeke ne blue nakai da na yafawa a kafad'a tayi kyau matuka kai kace itace Amaryar. Prince ishaq ta kira a waya dan yace inta gama shiryawa shine zai kaita. Ga yan gidansu duk za.a tafi gaba daya amman yakiya. Kallonta ya tsaya yanayi domin kuwa ta masifar masa kyau. Murmushin dake karawa fuskarta kyau ta sakar masa tace "Gentle I'm set" janyota yayi jikinshi yashaqi kamshinta mai dad'i ya furta "Hussy anya kuwa zan barki ki fita ahaka kinga yanda kikayi kyau kuwa? Wurin fa da maza" Langwabe kai tayi ta furta "Gentle ba dakai zamuba aiba wanda ma zai kalleni ansan ni matar prince Ishaq ce da anganni" baice komaiba ya sake ta dan yaga mutane nakai kawo. Mota suka shiga. * Wurin ya matukar kayatuwa domin kuwa komi yaji sam barka. kallo ne ya koma sama sanda prince ishaq ya shigo shida hussy domin kuwa sunsha kyau shikuwa sai shan kamshi yake ala dole ana Kallar masa hussyn shi. Ahaka taro ya watse .... * Washe gari dinner akayi a guest house na mai martaba. Nanma sunsha kyau matuka amma antaru sosai wurin ba kama hannun yaro. Zaune prince Ishaq yake shida hussy,shifa duk inda take yananan manne da ita. Wani friend d'inshi zahar yamai waya kancewar yana waje yazo yashigo dashi. Ya nata duba wanda zaisa yaje ya shigo da zahar din bai samu ba. Dan haka yace ma hussy. "Yanzun zan dawo. Karkije ko ina fa" * A hanya taro mutane yayi yawa shikuwa yau mulkin yakeji ahankali yake rabe mutane yana wuceww harya kusan isa gate din da zai sadashi da waje. Ji kawai yayi an cakamai wuka hannu kara yasaka ya dafe wurin dagowar dazaiyi yaga ko waye. yaga ankuma daga wukar zuwa kirjinshi da sauri ya kai hannu dan ya kare. Ya same shina wuya. Ya rike shi dam ya soma ihun kiran mutane. Hankalin mutanen kuwa ya soma yo kansu. Jirin dake dibar shine yasa mutumin ya kubce masa. Amman ina an nasarar damke shi. Prince ishaq kam kasa ya tafi luuu. Ya sume saboda jinin dake zuba jikinshi. * Hussy ta taso domin ta dubashi kasancewar taga wayanshi dayabari kan table nata tsala ihu,da alama wanda yafita ne yashigo dashi basu haduba. Wayar hannunta taga tana ringing. Ganin Nas ne ta dauka tun dazun take mitar bata ganshi ba. "Hello kanina" "Anti fito waje please yanzun nan" Yanayin muryarshi ya tsoratata. Da gudu ta fita waje. Taga komai ya hargitse ga yan sanda sunzo. Nas ta hango ta kara Sa wajen shi. Baice mata komai ba ya kama hanya tabishi. Mota suka shiga gidan baya su dukansu. Sai lokacin take ce masa "Me ya faru. Ina gentle?" Shiru yai kawai. Gani tai yasa hannu yana goge fuskarshi. Ai nan take kuka ya kwace mata. "Dan Allah naseer ka fadamun kome ya same shi" Dakyar ya sauta muryarshi yace "Wani ne ya ji masa ciwo. Amman komai ya kusa karewa. An kama mutum daya yau" Ai tun daga kalmar "ciwo...... " Ta daina fahimtar komai. Kuka kawai take suna hanyar asibiti. So take taganshi ta tabbatar da lafiyarshi kalau. Babu abinda zai samar mata miji. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 5⃣2⃣ A hargitse suka shiga asibitin. Tana ganin umman prince ishaq ta ruga wajenta tana kuka. Sunfi awa biyu zaune likitoci babu wanda ya fito yace musu wani abu. Hankalin kowa a tashe yake. Ko da likita ya fito kusan su duka suka isa wajenshi kaman zasu cinye shi da tambaya. Dakyar ya samu suka nutsu yace musu. "Yana hutawa ne. Ciwukan nashi anyi sa.a ba wani zurfi sukai ba. Ya zubda jini ne shi ya galabaitar dashi" Sai lokacin hankalin kowa ya kwanta. Umma tace azo a tattara kowa ya koma gida dare yayi. Su tafi da husna ma. Abar Nas kawai. Kuka husna ta saka ga shi ta kasa cewa komai. Ganin hakan yasa umma tace abar husna hankalinta zaifi kwanciya. Su duka suka zauna dakin da prince ishaq din yake. Dinkine a hannunshi da wuyanshi. Banda nan babu wani ciwo a jikinshi. Husna taja kujera ta zauna kanta ta dora gefen dagon tana riko hannun shi. Tayi kuka har fuskarta ta kumbura. Bacci kam barawo ne ya saceta. **** Hannun prince ishaq taji saman kanta. Da sauri ta dago ta sauke jajayen idanunta da suka sha kuka cikin nashi. Murmushin shi yai mata kawai. Dan bazai iya magana ba. Makoshin shi ciwo yake masa sosai. Hawaye zatai da idanuwa ya nuna mata alamar baya so. Tako tarbe su. Nas dake kwance gefe ta taso. Yaje ya kira likita. Akazo aka duba shi. Sai bayan ta idar da sallah sannan ta kira gidansu ta fada musu da asibitin da Nas din take. Sukace da gari ya kara wayewa zasu zo. *** Tun da sassafen suke shan baki. Husna kam ba yanda ba ai da itaba ta koma gida ta yo wanka ta sake kaya taqi. Saida umman prince Ishaq tazo sannan tasa Nas ya mayar da ita gida. *** Duk saurin da take yi sanda suka koma mamanta har sunzo sun duba shi sun tafi. Taji kaman zata saka kuka. Waya ta dauka ta kira "Mama ko ki jira in dawo mu gaisa" "Husna zamu dawo gobe in Allah ya kaimu. Kuma su yayanki ma zasu zo da yamma" Ba yanda ta iya. Dole ta hakura. Addu.a tai ma prince ishaq din sosai tukunna sukai sallama. *** Yau kwanan su uku a asibiti. Prince ishaq tunda ya fara samun sauki yake mita shi fa sai a tafi gida. Dole ranar da yamma aka sallame su da warning cewan kar yai stressing kanshi. Ya zauna ya huta sosai. Saima juya idanuwan shi wa doc din dayai hadi da fadin "Zan iya kula da kaina. I know the rules" * Tunda suka dawo gida falonshi ya zauna yanata waya. Husna tana kitchen ta hada masa ginger drink din da yake bala.in so. Farfe sun kifi tai mishi ta zubo ta dawo falo. A plate ta zuba mishi ta zauna ta gyara ta cire kayoyin sannan ta tashi taje ta wanko hannunta ta dawo. Kallonta yai yace "Sannu da aiki hussy" "Kaine da sannu. Ya jikin?" Ya langabar dakai gefe kawai maimakon ya amsata sai yace "Nas ne ya kirani wai an fara zaman court ne kan shari.armu. Gobe sai naje" Plate din ta dauka takai kusa dashi tana fadin "Allah ya kaimu. Allah ne ya kawo karshen mugayen mutanen nan." Ya amsa da amin. Saida ma taita matsa mishi ya dan kara ci. Tun a asibiti yake cewa kifi yake son ci. Amman kaga yanzun an dafa ya kasa ci. "Menene mama ta kawomun dazun da safe?" Kallon shi tai sosai "Dambun nama ne. An kuma hanaka tauna abu for long" Ya tabare fuska "Ni kam zanci fa" Ta sauke numfashi tace "Gentle ka hakura yana nan na ajiye maka. Idan ka kara samun sauki sai kaci" Ya girgiza kai shi bai yarda ba. "Ki tauna saiki dinga bani" Zaro idanuwa tai. Dakyar ta lallabashi. Shifa a dole sai ta tauna ta bashi. Da dare tare suka shiga toilet. Ita ta kama mishi ya cire riga saboda hannun shi. Ya cire har single. Dagashi sai boxers. Wata kunyarshi ta saukar mata. Ta kasa hada idanuwanta da nashi. A hankali tasa towel da ruwan dumi ta goge mishi jikin shi tas. Yai brush sannan ya fito. Wani boxers din ta dauko mishi da singlet ya shiga dakin sake kaya ya canza. Ya fito yasa singlet din zuwa wuyansh kawai. Ta taimaka masa ya karasa sakawa. Magunguna ta ballo da cup din ruwa. Ta mika mishi ya wani girgiza kai yana yamutsa fuska. "Bana sha" Zama tai ta kalle shi sosai. "Bangane baka sha ba. Nika karba ka shanye in tashi in wanke singlet din can daka cire" Gani tai da gaske yake baya shan maganin. "Saina narka a ruwa na dura maka ko?" Dariya ta bashi. Ya tsareta da ido yana fada mata zai so ta gwada dura mishi maganin. "Allah in baka sha ba zan kira umma in fada mata" Da sauri ya karbi cup din da maganin ya shanye. Dan yasan umma sarai. Asibiti zai koma ya zauna sai yagama shan maganin. Dariya tai. Ta wuce ta wanke mishi boxers din. Tai wanka sannan ta fito. Sanda ta dawo har yai bacci. Ta zauna gefen shi. Kallon shi take. Bata tabbatar da abinda take ji game dashi so bane. Koma tace ya girmi so. Sai da nas yace mata anjima sa ciwo. Saida taganta asibiti likitocin sun ki fitowa su bata bayanin. Yanda taji numfashin ta na barazar daukewa. Yanda taji tana son taganshi ta tabbatar da lafiyarshi. Indai wannan ba so bane. Bata san menene ba. Saita tsinci kanta da tofa masa addu.o.i tana fatan Allah ya ci gaba da tsare mata shi. *** Yau ake gama zaman kotu shari.ar su prince ishaq. Da ikon Allah dayai alkawarin biwa duk wani wanda aka zalunta hakkinsa. An nasarar kama masu laifi dumu dumu. An kuma yanke musu hukunci dai-dai da laifukan da suka aikata. Tunda suka fito daga court din jikinshi a bala.in sanyaye yake. Nas ya dafa mishi kafada yana fadin "Yaya komai ya wuce...... " Numfashi ya sauke yace "Nasani nas kawai raina ne bayamun dadi. Duk jimawar nan. Duk abubuwan nan mun riga mun san daga bangaren su Nawaz yake. Amman kamala......... " Yama kasa karasa maganar. Tunda aka kama harda kamala a laifukan nan jikin shi ya gama sanyi. Ko motar su da tai hadari kamala ne ya kwance musu brake. Duk wani motsin dazaiyi kamala da ya yarda dashi shine babban munafukin shi. Kamala shi yai sanadin mutuwar huddy. Shikuma ya so yai sanadin ta Nas. Well Allah kenan. Ga asirinsu duk ya tonu. Ko ba komai daurin rai da rai ne. Shine sassaucin da alkali yai musu. * Gadonta tagama sakema bedsheet. Tana saka pillow case din. Sam bataji turo kofarshi ba. Sai dai taji ya rungumeta ta baya. Kanshi a kafadarta. "It is over hussy. Komai ya kare. We are safe" Hamdala tai wa Mai Ikon Rayuwa da mutuwa sannan ta zame jikinta ta juyo ta kalle shi. "Sarki......... " Gira ya daga mata alamar ta karasa amman sam ta kasa. Sunan shi wani bala.in nauyi yake mata a baki. Janta yai sosai jikinshi. Sumba ya manna mata a wuya. Cikin kunnenta yace "Ina son jin sunana kan lips dinki husna" Kanta ta sake boyewa a kirjinshi tai shiru abinta. Dole ya hakura ya kyaleta. Sakinta yai yana fadin "Jeki dauko hijab dinki zamu fita unguwa" Harta wuce ta juyo tace "Abinci fa?" Ya girgiza mata kai "Na biyo ta gida. Naci nama wajen umma. Kinci wani abu dai ko?" Ta amsa da "Eh naci nima" Hijab dinta ta dauko ta saka. Shi yake tukasu. Saida suka biya ta sahad. Yace mata ta dibi duk wasu kaya na ciye ciye da biscuits. Duk da har yanzun baice mata ga inda zasu ba. Abinda yasa tayi haka ta diba. Basket guda suka cika da kayan ciye ciye. Ya biya kudin suka koma mota. Ga mamakin husna hanyar estate dinsu taga ya nufa. Murmushin datai mishi har ranshi ya jishi. Tama kasa magana dan murna. * Ba karamun dadi su mama sukaji ba. Babban falonsu suka zauna. Bakowa gidan sai mama. Duk suna islamiyya. Abbansu kuma yana kasuwa. Duk abubuwan da aka kawo masa. Dambum nama kadai yaci. Shima dan yaji dadin na kwanaki da maman ta kawo masa. "Mama dan Allah aisha tazo in anyi hutu mana" Cewar husna Mama ta amsa ta da "Wai husna islamiyyar kuma fa. Kinsan suna hadda" "Mama sai a dinga kawota kullum ai" Prince ishaq ya fadi yana ma mama murmushin dayakasan siye mutane dashi. Kwarjinin shi yasa mama ta yarda cewar zata fadama abbansu idan ya dawo. Suna shirin tafiya su aisha suka dawo. Maheer ne ya fara shigowa da sallama. "Anty husna" Ya fadi muryarshi da mamaki da kuma farin cikin ganinta. Ai aisha najin haka da sauri ta ture shi ta karasa ciki. Da gudunta ta fada jikin husna tana ihun murna. Mama tace "Oh ni aisha ki nutsu dan Allah. Baki iya gaida mutane bane" A ladabce suka gaishe da prince ishaq din ita da maheer. "Su maheer ko adan leqo ni" Husna ke mishi mita. Sosa kai yai a kunyace yace "Zanzo in shaa Allah." Hira suka dan taba kadan. Mama tace ya isa haka. Sun tsaida su ga yamma tanayi. Prince ishaq yace ma maheer ya biyo shi mota ya dauko musu abu. Kamun su dawo mama ta shiga kitchen ta ciko musu wata rubber da dambun nama. Sai turarukan wuta taba ma husna. Ganin lodin ledojin da maheer ya shigo dasune yasa mama salati. Cewar hidimar tayi yawa. "Mama ai kune da hidima" Inji prince ishaq. Addu.a tai musu sosai. Har mota su aisha suka rakasu sannan suka koma gida. Husna wani dadi ne da farin ciki fal zuciyarta. Suna shiga mota tace "Nagode sosai gentle. Nagode da karamci" Kallonta yadanyi ya maida hankalin shi kan tukin. Murmushi ya kwace mata. Kawai ya wani kHualleta ya basar. Prince ishaq akwai jin kai. Da zata ce masa yana jin kai. Ko ta kwaikwayi abinda yai yanzun. Zakaga fuskar nan tai ja. Wai shi yaji kunya. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 5⃣3⃣ *2nd to the last page* Da gudunta ta ruga ta sameshi a dakinshi yana kwance yasaka laptop a gaba yana aiki bayanshi ta dare ta zauna abinta ta sakalo hannayenta ta wuyanshi ta kwanta ta furta "Gentle kausar ta haihu ansa mu baby boy" Laptop din ya janye gefe daya. Ya kamo hannunta ta sakko daga bayanshi. Ta zauna gefen shi. Wani yanayi yakeji. Daman ace babyn nan nasu ne. Da ba karamun dadi zaiji ba yau. Da murmushi a fuskarshi ya ce. "Ma shaa Allah. Allah ya raya babyn da mumynshi" Ta amsa da amin kamun yace "Yaushe ne suna?" "Yau aka haihu kaga Friday suna ze kama" bata fuska yayi yace "To yaushe zaki tafi saboda nasan Wanan satin me zuwa ayyukane kaina barkatai bazan samu damar binki abj ba" "Thursday zantafi indawo Sunday" Zaro ido yayi yace "Hussy kwana uku kenan fa ko?" Rau-rau tai da idanuwanta. "Please gentle. Kausar ce fa" "bazan hanaki tafiyaba kinsani, amma hussy kwana uku fa. Ko dan ke ba zakiyi kewata ba?" Murmushi tamasa tana dora kanta a kafadarshi. Ita kanta tasan a daddafe zatai kwanakin nan. Ko bikin gidansu da akai. Dadewa take batai bacci ba. Ta saba duk juyin da zatai ya gyara mata kwanciya a jikinshi. "Gentle kayi hakuri zan dawo saturday.Wallahi nima zan kewarka sosai." Matseta yayi tamkar wani zai kwace masa ita. Yai shiru kawai. Kwanakin daya rage musu yake kirgawa. Yanajin da husna ta soshi da bata soshi ba. A karo na farko a rayuwarshi zai karya alkawari. Da bazai taba iya hakura da ita ba. Koda kuwa ba za.a samu wani ci gaba ba a zamansu. * Da kanshi yai mata booking tun kamun ranar tafiyarta abuja. Ta gama shiryawa tsaf. Shi zai kaita airport ya wuce gidansu. Ya wani tsaya jikin bango ya tabare fuska. "Gentle please. In kana haka da fuska yazan in tafi" Takawa tai ta karasa inda yake tsaya. Hannuwanshi ta riko bai hanata ba. Kawai ya zuba mata idanuwanshi ne. "Gentlee manaa..... " "Kawai bana so ne. Bana sonki da nisa haka har kwana biyu" Ji tai harya kanta ya soma ciwo. Ita kanta badan kausar bace bamai ja mata tafiyar nan. "Ginger dinka na fridge" Ta fadi kaman ginger din data hada mishi zai rage masa missing dinta. "Ki aika mata da ginger din ni ki zauna" Dariya ya bata. Shima kuma sai abun ya bashi dariya. Janta yai jikinshi yau hugging sosai. Ji yake kaman ya maida ta cikin jikinshi kawai ya boyeta. Dakyar ta lallabashi suka fita. * Tana isa abuja ta samu ana jiranta a airport. Saida ta shiga mota sannan ta kira prince ishaq din. Hira sukai tayi har saida taje kofar gidan kausar tukunna. Tace zata kirashi anjima. Kausar kaman tai me dan murna. Ta bala.in jin dadin zuwan husnar. Nan suka shiga hidima basu samu zama ba sai dare. Hira suka sha sosai danma kausar akwai gajiya a jikinta. Hakan yasata bacci da wuri. Husna ta tusa babyn a gaba tana ta kallo. Yaron abun sha.awa. Lokaci daya son mallakar nata yaron ko yarinyar. Sai dai bata san rana ba. A yanayin zaman su da prince ishaq. Wani ajiyar zuciya ta saki tana jin kewar shi. Waya ta dauka zata kirashi kenan. Saiga kiranshi ya shigo. Tana dauka yace mata "Hussy na kasa bacci kuma nagaji sosai" Ji take kaman ta rungumo shi ta cikin wayar. Ko tai tsuntsuwa ta je kano. "Nima inata missing dinka" Shirun shi yai mata tasan shi sarai. Bai gaji bama wasu lokuttan magana na masa wahala. Balle yanzun dayagaji. Labarin baby ta shiga bashi. Saidai yace mata umm. A haka har taji shiru. Sumba ta manna ma wayar sannan ta kashe. Ta ajiyeta gefe tai addu.a sannan bacci ya dauketa cike da mafarkin prince ishaq. * Anyi suna komai yaji husna sai fama take da babyn tamkar ta had'iyeshi. Daukar hoto tayi ta turawa prince Ishaq ta whatsapp aikuwa tasha mita taje tana ta kwalliya. Shi anbar shi shi kadai. * Washe gari tun takwas ya kirata ta shirya dan kuwa jirgin karfe goma zata bi. Kausar ta karbi wayar suka gaisa. Yai maga Allah ya raya. Ta mishi godiyar kayan babies da suka sha. Da husna zata tafi. Fada kausar ta kara yi mata sosai. Ta kwantar da hankalinta. Ta zauna lafiya da mijinta. Dariya tai dan ko kausar bata fada ba. Ammar ya zama tarihi a wajenta. Akwai bangare na zuciyarta da bazai taba manta shi ba. Saboda ta soshi so na gaskia. Yanzun duk wani fata na ci gaba da rayuwarta prince ishaq take gani. * A gida ta same shi. Ya wani basar saboda hadiman da suka shigo mata da akwatinta. Suna barin wajen ya karaso ya rungumeta. Kamshin shi take shaka. Da yanayin matseta dayai yake nuna mata yanda yai kewarta. *** Sam ya kasa bacci. Yana rike da husna. Zuciyarshi cike fal da wani yanayi daya kasa fassarawa. Wani irin daci yake ji. Daren yaune kawai ya rage masa WATA BAKWAI din daya diba ya cika. Sam bacci ya kaurace ma idanuwanshi dan haka ya dauro alwala yazo ya jero sallah raka.a hudu. Zama yai ya bude Qur.ani yana karantawa. Daya idar yai addu.a ya roki gafarar Ubangiji na banzatar da duk hakkokin aure da Allah ya dora masa dayai yabiye son zuciyarshi. Ga alkawari daya dauka cikin bacin rai. Alkawarin da baya zaton zai taba iya cikawa. Duk da yasan hukuncin rashin cika alkawari. Har asuba yana zaune wajen yana sake sake a zuciyarshi. Saida ya sako alwala ya fito. Husna ya taba a hankali ta bude ido. Baice mata komai ba ya zauna abinshi. Yana kallo ta tashi ta shiga bandaki. Shi yaja musu sallah. Suka idar sukai addu.o.i. Wanka ya shiga yayi. Ya dawo gefenta ya kwanta ya lumshe idanuwanshi. * Zaton husna bacci yake yi. Tabon dake jikin wuyanshi na ciwon da aka ji masa tasa hannu tana tabawa. Yana jinta yai luf abinshi. Hannun ta ya ci gaba da mishi yawo a fuska. Harta gaji bacci ya sake daukarta. * Lalubawa tai gefe bataji prince ishaq ba. Ta bude idanuwanta. Baya dakin banda kamshin shi babu komai. Tashi tayi ta shiga wanka. Data fito dakin sake kayanshi ta shiga. Dan akwai kayanta da yawa dakin shi. Atamfa ta dauka riga da zani simple. Ba wata kwalliya a fuskarta sai dan jan baki da ta saka pink. Ta san duk inta saka shi sai prince ishaq ya sa hannu ya dangwalar mata. * A babban falon su na sama ta same shi yana kwance. Gefen shi ta zauna hadi da fadin "Ina kwana" Cikin sanyin murya yace "Kin tashi lafiya?" Ta amsa da "Alhamdulillah" "Ka taso muje muyi breakfast. In kuma kana son wani abune in shiga kitchen in dafa maka" Girgiza mata kai yayi. Dan bayajin zai iya sakama cikin shi wani abu. Gabanshi ma faduwa yake tun safe. Sosai ta kalle shi. Tasan akwai damuwa tattare da yanayin shi. "Meke damunka?" Shiru yai saida ta dauka baiji ta bama sannan ya amsa da "Kije kiyi breakfast dinki hussy" Kasa ta sauka ta matsa saitin fuskarshi. Idanuwanta ta sauke cikin nashi. "Ba abinda zai iya shiga cikina in baka fadamun meke damunka ba" Wayarshi ya lalubo da take gefe ya bude key din. Calendar ya bude ya nuna mata kwanan wata. Da rashin fahimta tace "Gentle bangane ba" Zaune ya mike ya sakko da kafafuwanshi. Wani iri yake ji. Kaman zazzabi zai saukar masa. Muryarshi can kasa yace "Hussy idan nace ina sonki banma abinda nake ji a zuciyata adalci ba sam" Zuciyarta ke dokawa. Tsalle take. Ta sha karantar soyayyarta a idanuwanshi da yanayinshi amman bai taba fada mata ba. Rawa take da tsalle a badininta. A zahiri kuwa idanuwanta ne kafe cikin nashi. Yaci gaba da fadin "Yau naima Ammar alkawari husna. In bakice kina sona ba zan.......... " Shiru yai ya dafe kai. Dan kalmar ba zata karasu ba wajen shi. Furtata a zuciyarshi kawai wani zafi yake ji. Muryarta na rawa tace "I choose you gentle. Ina sonka. Ina sonka sosai" Dagowa yai kallonta yake. Kunnuwanshi na amsa maganarta. Wayarshi ya karba ya bude key din. "Samun number dinshi" Batai musu ba ta karba ta saka mishi. A loudspeaker ya saka. Ringing take ya daga hadi da fadin "Hello" Wasu hawaye husna taji. Ta jima da yima ammar bankwana a zuciyarta. "Hello ammar" Husna ta fadi. Wata ajiyar zuciya ya sauke "Husna..... Ki yafemun dan Allah. Ina mijinki? Bansan ta yanda zan nemo ki ba. Husna munyi kuskure sosai....... " "Ammar" Prince ishaq ya fadi. "Dan Allah ka yafemun. Ka yafe mana. Karka saki matarka......." "Na yafe maka ammar. Allah ya baka wadda tafi husna. Nagode sosai. Daman mun kira ne muyi maka fatan alkhairi" Wani tausayin ammar din yaji har zuciyarshi. Saboda yasan yanda zafin rabuwa da abinda kake so yake. Garama shi lokacin mutuwa ce ta rabasu. Ace a aura mata wani. Bama zai soma hango ciwon abin ba. "Ka riketa da amana. Ka sota sosai. Ka zamana mai yafe mata inta maka laifi. Ka sata cikin farin ciki......" Kasa jiran amsarsu ammar yayi. Ya kashe wayar. Kami husna prince ishaq yai. Ya dagota ya zaunar jikinsu. "I love you hussy" Bude baki tai zata amsa shi ya hada bakinshi da nata. Da sumbar daya manna mata zuciyoyinsu suka hadu. Abinda duk basu da kalaman da zasu fada ma juna ya hadu a lokacin. 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 5⃣4⃣ *Last page* Ringing din wayarshi ya dawo dasu hayyacin su. Saida yai kokarin saita kanshi tukunna ya daga. Mumyn Nas ce tana nemanshi kan maganar komawar Nas makaranta. Saida ya sake sumbatar husna sosai sannan ya fita badan yaso ba. A wajen ta kwanta tana jin wani yanayi na daban. Son shi na kara shigarta. * Bai dawo gidan ba sai yamma likis. Yana shigowa ana sallar magrib dan haka ya fita masallaci bai dawo ba sai dayai isha.i. Jan husna yai dakinshi. Yasa ta sake yin alwala suka gabatar da nafila raka.a biyu. Wanka ya shiga. Ya fito husna ma ta shiga. Mai ta dauka zata shafa ya taso ya rike hannunta. "Nafi sonki haka please" Ajiye man tayi ya jata zuwa kan gadon. Hannunshi ya dora saman kanta ya karanto Addu.ar da Manzon Allah S. A. W yace ayi. ‘Allahumma Inniy as’aluka khayraha wa khayra ma jabaltaha alayhi, wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alayhi.’ Itama husna yana sauke nashi ya dora nata akanshi tana fadin. ‘Allahumma inniy as’aluka khayrahu wa khayra ma jabaltahu alayhi, wa a’uzu bika min sharrihi wa sharri ma jabaltahu alayh.’ Hannuwanta ya riko ya kalleta sosai yace. "Ina addu.a da fatan gina zama da rayuwa ta amana dake husna. Bana bukatar komai daga gareki da ya wuci yarda da aminci" Sauke numfashi tai tace "abu biyu nake rokonka gentle. Ka zama abokina ka zama mijina. Ina son duk randa nake da matsala da mijina inyi magana ta fahimta da abokina" Kai ya jinjina yana fahimtar duk maganarta "Bazan miki alkawarin komai ba husna. Zan iya kokarina" Bai bari tai magana ba ya hade bakinshi da nata. Daren ranar tasha addu.a da albarka. Ya samar musu da wata nutsuwa taban mamaki. * Shi fa yace ta tashe shi karfe goma. Zaije wajen mai martaba. Gashi yanzun shigowarta daki na uku kenan tana tashin shi yaki tashi. Zama tai kusa dashi. Sumba take manna masa ta ko ina na fuskarshi da wuyanshi. Bude idanuwa yai ya fisgota ta fado kan gadon tana dariya. "Gentle dan Allah yi hakuri. Tun dazun inata tashinka kaki ka tashine fa" Bai saurareta ba ya soma aika mata da saqonni cikin salon shi dake tsaya mata a rai. Tun tana masa magiya harya kashe mata bakin magana. * Sanda ya fito wanka tana kwance. "Hussy ki tashi. Yunwa fa nake ji" Tana jinshi gaba daya yagama gajiyar da ita. Tai shiru kaman tana bacci. Gefen gadon ya zauna. "Bara mu kara wani round din....." Kamun ya karasa ta duro daga gadon ta nufi toilet ya kwashe da dariya. Bedsheet din ya cire ya dauko wani ya sake. Da kanta ta sauka kasa ta hado mishi plantain da soyayyen kwai da ruwan Lipton. Tasan baya son madara a tea. Ajiye mishi tai. Ya kamo hannunta. "Zo inji kalar lipgloss din nan" Kwace hannunta tai tana fadin "Sai mai martaba ya aiko fadawa an dauke ka a kafada ba ruwana" Dariya yai sosai. Ya kyaleta. Yaci abincin shi. Bayanda baiyi da itaba tace ta koshi. Taci nata da yana bacci dazun. Mikewa yai yana fadin "yanzun amun a dawo lafiya ko?" Langabe masa kai tayi. "Gentle inzo mu tafi? Zanje in gaishe da umma" Ya girgiza kai alamar aa. Bude baki tai zata sake magana yace "Ba inda zaki fa. Bana son baby na yasha rana" Rufe fuska tai tana fadin "Gentle ka bari please. Cikina ba komaina cikin shi" Kamota yai yana shakar kamshin ta da take cewa ya zama iri daya da nashi tunda turaruka daya duke amfani dashi yanzun. Yakan mata gardama dan shi ji yake nata kamshin daban yake. *** Abinci suke ci suna taba hira. Ta dauki nama ta saka abakinta. Kawai sai ji tai gaba daya kamshin naman ya da taste dinshi ya mata wani iri. Dakyar ta karasa tauna shi. Tana hadiyewa taji wani amai ya taso mata. Da gudu ta tashi ta nufi dakinta. Prince ishaa ya bi bayanta yana fadin "Lafiya. Hussy....... " Bandaki ta shiga ta dinga kwara amai kaman yan cikinta zasu fita. Tana gamawa ya zuba mata ruwa ta wanke bakinta da fuskarta. Kayanta ya tayata cirewa yanata zabga mata sannu. Dakyar tace masa ya fita abinshi zata iya yin wanka. Dole ya kyaleta dan hussyn tashi har yanzun kunyarshi na dawainiya da ita. Tana fitowa wanka sai zazzabi. Kamun kace meye jikin nan rau. Cayai ta tashi suje asibiti takiya. "Me yasa kai ba zaka dubani ba?" Shiru yai. Ya fada mata ya ajiye aikin shi tun randa huddy ta rasu. "Huddy zata so ka ajiye aikinka ne? Gentle ita kanta lokacinta ne yayi. Kaman yanda namu zaiyi muma. Inhar ba zaka dubani ba karka sake mun maganar zuwa asibiti" Tana karasa maganar taja blanket ta rufe ta juya mishi baya. Ya lumshe idanuwanshi ya bude su. Kan gadon yahau sosai ya kamota. "Hussy please ki tashi mu tafi asibiti. Kinga baki da lafiya" Ture shi tai. Duk da jirin da take ji zaune ta tashi. "Akan me ba zaka koma aikinka ba? Ni ka rabu dani. Daka damu dani ai da ka dubani da kanka" Baya son matsala sam sam. Baya son rikici. "Are we fighting?" Ya tambaya yana zuba mata idanuwanshi dake shirin wargaza mata duk abin da tai niyya. Sauke nata idanuwan tai. Tasan meye ba yaso ta soma hawaye. Tasa hannu tana goge fuska. Gaba daya ta dagula mishi lissafi. Hannu yasa ya tallabi fuskarta. "Husna please dan Allah karkimun haka" Idanuwanta cike taf da hawaye ta kalle shi. "kamun alfarmar nan gentle. Ka koma aikinka idan ka zama sarki ba ajiyewa zakai ba?" Sakinta yai ya tashi ya fice. Addu.a husna take har ranta Allah yasa ya koma aiki. Dan Nas ya bata labarin yanda yake bala.in son aikin shi. Tun randa hussy ta rasu a hannunshi ya tsorata. Prince ishaq kam daya fita wajen dakin. Jikin bango ya jingina. Ajiyar zuciya ya sauke. Ya jima yana tunanin komawa aiki amman jikinshi sanyi yake yi. Kamun ya kara kasawa ya dauko wayarshi daga aljihunshi. Dr. Abdul ya kira ringing daya ya dauka. Kalmar shi ta farko shine "welcome back Dr.ishaq" Murmushi ya kwace mishi. Yace "Gani nan zan shigo yanzun" Bai jira amsarshi ba yaje ya fito da husna. Saida ya tabbatar mata dashi zai dubata kamun su isa "Royalty hospital" Da hadin gwiwa ne na su uku. Prince ishaq da kanshi. Dr Abdul sai Dr.muneerat da babbar gynecologist ce. * Da kanshi yaima husna duk wani abu da ake bukata. Hamdala ya shiga yi ganin husna nada shigar ciki sati biyar. Zuwa yai ya dauketa suka tafi gida. Duk da zazzabin dake jikinta bai hana shi nutsar dasu wata duniya ba. Cewan shi celebrating yakeyi. * Wani irin laulayi husna take mai wahala. Kome taci sai ya dawo. Duk wani taimako da kula da take bukata tana samu daga wajen prince ishaq. Catai mishi ya kira gidansu a kawo mata aisha ko dai ba zatai mata wani aiki ba. Idan ya tafi asibiti abinshi sun zauna. Fur yace saidai ta kira da kanta. Shi kunya yake ji dayace bata da lafiya za.a gane ciki ne da ita. Itama ba zata iya fada ba dan haka ta hakura. Ko in sun waya mama ta tambaye ta haka take cewa suna lafiya. Haka taita fama bata dan fara samun sauki sauki ba saida cikin yai wata hudu tukunna. A haka komai yake tafiyar musu a nutse da kwanciyar hankali da wata irin kauna mai burgewa. *** Zaune take da tikeken cikinta tanata faman cin cookies prince ishaq ya shigo. Sam bataji shigowarshi ba. Tsayawa yai yana kallonta. Dariya ta bashi. Dariyarshi taji ta dago kai ta kalle shi. Kokarin tashi take ya karaso da sauri yana fadin "Hussy me zakiyi haka. Kina son wahalar mun da baby" Tabe baki tai tace "Ai yanzun fa komai baby. Sannu da zuwa fa zan maka" Dariya yai. "Na hutar dake. Ya kuka wuni. Inata kiranki baki dauka ba" Sai lokacin ta tuna can daki tabar wayar. "wayata na daki gentle. Nikuma ina nan" Hira suke kadan kadan tace masa ya tashi yaje ya watso ruwa ga abinci ma baici ba. Tashi yai. Dan ba karamar gajiya ya kwaso ba. Yau asibitin nasu cike yake da mutane. * Harya fito tana nan zaune inda ya sameta. Kujera ta dafa tana mikewa dakyar. Yana tsaye yana kallonta. Dan yasan hali. Dayaje tayata zatace bata so. Inbai sa.a ba ma ta tusa rikici ya mayar da ita kaman wata tsohuwa gani yake ba zata iya komai bane. "Gentle dazun......... " Wani amsawa taji kugunta yayi daya katse mata maganarta. Ji tai abin nayi ne ta saka salati. Da gudu prince ishaq ya karaso inda take. "Ya Rabb hussy. Sannu.." Kamata yai ya zaunar. Sun sha karbar haihuwa. Amman data zo kanshi sai yaji komai ya kwance mishi. Wata damqa da husna tai mishi tana salati sai da yai zaton ta tsage masa kashi. Dakyar ya samu ya dauko wayarshi ya kira umma. * Kamun suzo husna ta haifo yaronta kato dashi. Shi ya yanke cibi. Baiji komai ba ya rungume danshi a jiki yana jin kaunar yaron na wani shigarshi. Kiran sallah yai mishi a kunne sannan ya riko husna suna ma Allah godiya tare. "I love you husna" Yake ta maimaitawa. Duk da gajiyar dake jikinta bai hanata sumbatarshi ba. "I more than love you my prince my gentle" 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Wata Bakwai 7 💝💝💝💝 💝💝💝💝 Written by Luβπα Sufyαπ 5⃣5⃣ Epilogue Takai mintina sha biyar tana neman takalmin ta rasa inda yusra ta jefa shi. "Yusra ki zabi wani mana duk takalman kin nan dan rigima sai wannan zaki saka?" "ana la 'urid 'an airtida' bedhm albaed (ni bana son wani)" Yusra ta fada. Husna ta lumshe idanuwanta. Dai dai sallamar prince ishaq. "Amira(gimbiya)" Jikinshi yusra ta makale tana fadin. "Abba aqul laha lileuthur ealaa hadhayiy (kace mata ta nemo min takalmina" Kallon shi husna tai tace. "Ka dinga yima yarinyar nan yaren da nake ganewa" Yusra ya kalla yace "adhhab waleubb mae yasir(jeki yi wasa da yasir)" Fita tai batare da musu ba. Ya karasa inda husna take ya dora hannuwanshi akan kafadarta. Sumbatarta yai a hankali yana shanye duk wani fushi da take da yanayin kaunar shi. Ture shi tai tana maida numfashi. "Seriously gentle in baka gida ni kake bari da wahala. Daga ita har yasir. Garama Nur" Dariya yai yace "Kibarmun yara na. Idan na sake ajiye wani a cikinki zan dinga mishi hausa" Zaro idanuwa tai tace "Gentle ka rufamun asiri. Duka watan yassar nawa? And beside yara ne saika gaji dasu" Murmushin sa yai. Yasan kishi ne yake cinta. Dan a cewarta ya taba ganin sarki da mata daya? Hanci ya ja mata yace "Hussy please mana. Banfa zama sarkin ba. Idan na riga mai martaba mutuwa fa?" Bakinshi ta rufe da hannunta tana girgiza masa kai. "Kar in kara ji" Rungumeta yai a jikinshi yana fadin "Tam kema karna sake jin hangomun rayuwa da wata matar bayan ke. Kin yarda?" Kai ta daga mishi. "You are my now and forever hussy" Ya fada yana hada bakinshi da nata sukaji an buga kofar "Mami. Yassar na kuka" Cewar Nur(dayake hakan suke kiranshi. Shi yaci sunan mai martaba) Da sauri prince ishaq ya saketa. Hannu ta saka ta goge mishi jan bakinta daya bata mishi lips tana fadin. "Gentle ka shiga toilet din su yusra ka wanke fuskarka duk jan baki" Mudubi ya kalla yaga ba komai fuskarshi ta riga da ta goge. Juyowa yai ya nufota yana fadin "Hussy zo nan?" Da gudu ta fita daga dakin ya bita..........!!! ALHAMDULILLAH. Godiya ta musamman ga -ummijay novels -dimples novels -taskar lubiee mai tafsir -exquisite online writers -strictly divorced diaries -Yar baraya novels group -Hausa novels da sauran da ba zasu lissafu ba. Shout out to Architect Ishaq aka bifham. Thank you for being my inspiration throughout WATA BAKWAI. Nagode da kauna da addu.o.in da nake sha daga dubban mutane masoya WATA BAKWAI 7. Allah ya biya muku dukkannin bukatunku!!! Th£ £xceptioπαl. Karshe!!!