Copying and Compiled bay Umar Dalha. 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 BISSMILLAHIR RAHMAN ARRAHIM INA GODIA GA ALLAH MAI KOWA MAI KOMAI DAYA BANI IKON SAKE DAWO MUKU A SABON NOVEL DINA INA FATAN XAKU KARBESHI HANNU BIBBIYU DAN KARUWA DA ABINDA KE CIKI. GODIA MARA ADADI GA DUNBIN MASOYAN SUMYNBASH 💋DA WANDA NA SANI DA WANDA BAN SANI BA INA ALFAHRI DAKU A DUK INDA KUKE. GARGADI BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARINA BA. DUK WANDA YYI HAKAN ALLAH YA ISA. WANNAN NOVEL DIN KIRKIRARRENE BANYI SHI DAN CIN XARAFIN KOWA BA, I DAN YAXO A IRIN RAYUWAR KI/KA BADA NIYA BANE. INA ALFAHRI DAKU AISHAT A MU'HD NAFESAT ANKER RAHENAT UMMA ILA SAFAH SAEED BEBEJI FATY AXLAND MAMAN IHSAN DAMA SAURAN WANDA BAN FADA BA DAN KUNA DA YAWA. ILUSM💋 SADAUKARWA GA LATE ALHAJI SHAREEF KABEER FAMILIES AND ALHAJI SADEEQ IBRAHIM FAGGE A romantic love story 2017 Story & written by ✍🏻 SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 1&2 Qatar "Kyakkyawar budurwa ce kwance take a cinyar mom dinta tana kuka wanda daga gani kasan na shagwaba ne. A hankali ta fara magana da muryarta mai dadi kamar ana busa sarewa,plx mom muyi xaman mu a qatar karmu koma nigeria. Daria mom tayi kai xaljamil rigima ta miki yawa, banda abinki ya xa'ai kice mu xauna a qatar bayan ga country dinmu chan asalinmu yake. Kuma fashewa tayi da kuka, mom ni baxani ba sai dai ku tafi ku barni anan. Baki mom ta saki, eh lallai kina mace ba namiji ba, wane irin iyaye kika dauke mu? Mikewa xaune tayi ta kama hannun mom, mom na miki alkawarin kula da kaina, kinsan bana daga cikin ballagaxaxxun mata, xan kare mutuncin kaina plx, ta fada tana share hawayen dake fuskarta. Xaljamil mai yasameki wai? Ko kin fara shan wani abune, contract ne ya kawo dad dinki kasar qatar kuma ta kare dan haka dole xamu tafi nigeria nan da 2days kuma dake xamu tafi. Maganar mom ta bata ran xaljamil, dan haka ta mike daga cinyar mom ta nufi dakinta tana rusar kuka,. Mom ce ta bita da kallo, sanye take da doguwar riga pink colour wacce taji adon stone, kanta bbu dankwali sai ribbon da tasa ta tufke gashin kanta daya xuba har gadon bayanta. Tana shigewa mom ta mike hade da sauke a jiyar xucia.. Dakin xaljamil ta nufa, kwance ta sameta tayi ruf da ciki tana kuka, da sallama mom ta shiga dakin ta xauna kusa da xaljamil. Habibty mom ta kirata da sigar lallashi, a hankali ta dago kai ta kalli Mom da idonta jajir. Mom ce ta mata nuni data taso ta taho wajen ta, tashi tayi ta nufi jikin Mom ta shige jikinta tayi luf tana kuka. Mom ce ta fara lallashinta dan jin kukan xaljamil take har cikin ranta. Kiyi hkr habibty ki daina kukan nan bashi da amfani. Menene illa a cikin komawarmu nigeria? Kasar mu ce, dolen mu mu koma cikin ta. Kuka xaljamil ta kara fashewa dashi, tana magana, Mom banasan nigeria a yarda nakejin labari rinta baxan iya xama a cikin ta ba.,i can't wallahi, qatar is my country, a cikin ta aka hanani, an mini takardar shedar ni yar kasa ce, ku barni a kasata mom please. Baki mom ta saki tana kallon xaljamil cike da mamaki, ganin da gaske take batasan nigeria,. Xaljamil mom ta kira sunana, na'am ta amsa cikin sheshekar kuka. Kinsan kuwa cewa ke jinin sarautace, da sauri xaljamil ta dago kai ta kalli mom fuskarta dauke da murmushi. Da gaske mom? Yea my habibty.da gaske, grand fa dinki sarkine. Murna sosai xaljamil ta fara, mai yasa baku taba fada mini ba ta tambayi mom? Murmushin nasara mom tayi, menene abin fada tunda nasan xakije ki gani. Tuni annurin fuskarta ya dauke, xanje na gani ta maimaita? Eh mom ta fada tana kallonta. Tinxuro baki tayi ni baxani ba, nama daina murna ma, inama a ce sarkin qatar ne kakana ai danaji dadi amma sarki a nigeria ai bama dadi sarautar. Haba habibty gaskia bakisan nigeria ba, amma sarautar nigeria akwai dadi dan baki gani bane shiyasa, hmm mom duk yarda xaki yabi nigeria ba xata taba yi mini ba. Kuma ko xanje ba xan kalli kowa dan ina ganin su a tv bakake dasu ga muni,kinsan ban saba ganin bakake ba a cikin fafare na tashi fafaren ma larabawa larabawan ma na qatar ta fada tana kara hade rai. Rayuwata xanyi ni kadai a dakina, mom ce ta maka mata harara a karkashin gado habibty. Mom da gaske nake dan kwara ma kuce ba dani kuka xoba.,ko kuce masu bani da lpy banasan ganin kowa a kusa dani. Daria mom tayi, xaljamil kenan wallahi kyayi kya gama gujegujenki kuma daga karshe dole ki saki jikinki ba. Kuka xaljamil ta fashe dashi, mom ynx ba kya sona ko? Hararata mom tayi waya fada miki haka? Nina gani mana.Ina sanki xaljamil, yarda na haifeki haka nima mamana ta haifeni, kuma tanasona, tanasan ganina a kusa da, yaushe rabon dana gata, wallahi ba'a san raina nake xaune a qatar ba. Idon xaljamil akan mom harta gama magana, cike da takaici xaljamil ta mike daga jikin mom ta shige toilet ta rufe. Tagumi mom ta buga tana tunanin yarda xaljamil ta bullo musu da da sabon alamari, duk da tasan laipinsune basu taba xiyarta nigeria ba tunda sukaxo qatar. SUMYNBASH CE 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 3&4 Wacece Xaljamil Kyakkyawa ce mai kama da larabawa, fara ce tas mai manyan idanu da dogon lashes, tana da dogon hanci da karamin baki, ga kuma beauty point wanda ke kara bayyanar da tsantsar kyan xaljamil. She is tall nd slinder a takaice dai xaljamil ta hadu. Ta samu kyakkyawar tarbiyya daga wajen mahaifanta, tayi saukar alqur'ani mai girma, ta kuma kammala haddarsa, miskilace, bata da yawan magana, amma tana da barkwanci. A kasar qatar aka haifeta, anan ta taso amma bata da kawa balle aboki, ita kadai take rayuwar ta a skul. Ta kammala degree dinta a wata babbar university dake qatar, ta karanci anatomy. Xaljamil bata taba soyayya ba dan haka bata san so bama. Tana yiwa iyayenta biyayya bata taba kin yarda da abinda suka xo mata dashi ba sai komawarsu nigeria. Shiyasa mom takejin bbu dadi ganin yarda take masu biyayya kamata suma su mata abinda takeso sai dai bbu dama. Mom ce ta sauke ajiyar xucia ta mike ta nufi dakinta dan gabatar da sallar magrib. A hankali xaljamil ta murda handle din ta fito daga toilet din kirjinta daure da towel tana kuma tsane gashin kanta da karamin towel. Dressing mirror ta nufa ta xauna ta fara shafa mayukanta masu kamshi, ta feshi jikinta da arabian perfume masu dadin kamshi.powder ta shafa a fuskarta ta nufi wardrob. Sanye take da riga milk iya gwiwa da brown din wando pencil, ta dauke kanta da ribbon milk. Har ta xauna a dakinta taji tana san ganin mom dan haka ta mike ta nufi falo ranta a bace. Mom xaune a falo tayi xirfi acikin kallon wani film da akeyi a mbc action mai suna v. Har xaljamil ta karaso inda take, a bayan kujerar da mom ke xaune xaljamil ta tsaya tana kallon itama. Kamshin turaraenta mom taji dan haka ta daga kai ta kalli xaljamil hade da sakar mata murmushi, bata rai xaljamil tayi ta nufi 1cter ta xauna ta cigaba da kallon film din batare da ta kalli inda mom takeba. Door bell aka danna da sauri xaljamil ta mike dan bude wa, dady ta gani dan haka ta buga tsallen murna tayi hugging dinsa, oyoyo dady! Daria dad keyi, kai xaljamil bakya girma ko? yanayin fuskarta ne ya chanja data tuna da dad ne ya bullo da barinsu kasar da take bala'in so, dan haka ta saki dad ta nufi dakinta da sauri. Mom ce ta karaso tayi hugging dad hade da karbar briefcase din hannunsa, peck dad y bata a goshi jikinsa duk yyi sanyi, mai ya samu xaljamil?dad ya tambayi mom. Kasan na mata maganar xamu wuce nigeria gobe shine take bacin rai harda kuka wai baxata jeba,murmushin takaice dad yyi. Mom ce ta kama hannunsa ta raka shi dakinsa hade da taimaka masa har ya shirya, tare suka fito,Direct dakin xaljamil ya nufa. Xaune take a gefen gadon ta ta buga tagumi tana hawaye, da sallama dad ya shiga dakin ya xauna kusa da ita,xaljamil ya kira sunanta, bata dago ba ta kallesa ba dan tafi jin haushin dad. Daga ta yyi chak ya nufi dining area da ita, sai kokarin sauka take amma dad yaki bata dama, sai da ya direta a kujerar dining sannan ya xauna shima,ba yarda ta iya haka ta xauna itama xuciarta na kuna. Mom ce tayi sarving dinsu, xaljamil kam ta xubawa abincin ido kamar mai san tuna wani abu, jellop rice ne da taji hanta da kifi, daya plate kuma farfeson kazane. Sai juya shinkafar take da spoon, mom da dad sun lura da ko spoon daya bata ci ba, tausayin ta ya kamata, basu basa ganin ta a irin mood din ba, kullum cikin fara'a take bata fushi. Dad ne ya jawo kujerar xaljamil ta dawo kusa dashi, daukarta yyi ya daura a cinyarsa. Dago kai tayi ta kallesa bbu yabo bbu fallasa, dan ynx ta gama believing dad baya santa tunda ya kiyi mata abinda takeso. Spoon din ya dauka ya fara bata a baki, a hankali take karba mata harta kusa cinyewa, mom na kallon su tana murmushi dan dad na bala'in san xaljamil baya bukatar ganin bacin ranta. Spoon din ta rike tayiwa dad alamar ta koshi ta hanyar girgixa masa kai.ajiye spoon din yyi ya dakko juice a glass cup ya fara bata a hnkl take sha harta gama. Dad ne ya dauketa ya nufi falo da ita, 3cter ya direta shima ya xauna yana haki alamar ta masa nauyi, tuntsire wa tayi da daria tana kallon dad da yake ta yamutsa fuska. Baki ta tunxiro gaba cike da shagwaba, kai dad yaushe nayi nauyi haka, daria dad yyi ynx habibty bakiga irin abincin da kika ci ba.dad dan kadanne fa, eh na tuna habibty batacin abinci da yawa suka saka daria. Mom na xaune a dining tana kallon su,farinciki ya kamata, tashi tayi ta nufi falon ta xauna a gefen xaljamil suka saka ta a tsakiya suna bata labarai na daria. Tuni xaljamil ta manta abinda ke damunta, ta saki jikinta da iyayenta ta kuma kara tabbatar da kaunarsu agareta , dole ta hakura da kudirinta ta faranta ransu kamar yarda suke faranta mata. Hannu tasa tayi hugging dinsu tana jin kaunarsu na ratsata. Ba karamin dadi mom da dad sukaji ba ganin ta saki ranta,hira sosai sukeyi, mom ce ta duba a gogon dake manne a bangon dakin tym din da ta gani yasata fito da ido waje, omg kunga tym ta fada musu, a tare dad da xaljamil suka duba, 12:58am. Mikewa sukayi a tare suna daria, dad lokaci ya shammace mu hira tayi dadi xaljamil ta fada tana daria, eh lallai kam. Har cikin room dinta suka rakata sannan suka nufi nasu dakin cike da nishadi. Xaljamil bata kwanta ba sai da ta tabbatar ta gama shirya kayanta a trolley na tafiarta nigeria. 8:55am Xaljamil ta gama shirinta cikin arabian gown light blue, wacce taji stones, ta rufe gashin kanta da pink veil, light make up tayi ta feshe jikinta da arabian perfume sai tashin kamshi takeyi. Ta nufi pallow, bata tarar da mom a pallon ba dan haka ta nufi dakin. Da sallama ta shiga dakin Mom, Mom na gaban wardrob tana fito da kayanta tana shiryasu a trolley. Mom ce ta dago kai fuskarta dauke da murmushi ta amsa sallamar xaljamil. A nitse ta karasa dakin ta durkusa har kasa ta gaida mom, dafa kanta Mom tayi habibty kin tashi lpy? Lpy lau mom. Mikewa tayi ta nufi wardrob ta fara taya mom fito da kayan, mom ce ta kalleta, habibty ki barshi xanyi ki shirya naki kayan kema dan dad dinki na dawo wa daga company xamu wuce, Daria xaljamil tayi ai tun dare na hada nawa kayan mom. Ok mom tace suka cigaba da hada kayan,bayan sun gama mom ta shiga wanka xaljamil kuma ta kwashi kayan ta kai pallow ta ajiye. Dakinta ta nufa ta fito da nata kayan ta ajiye ta xauna jiran fitowar mom. Mom ce ta fito a shirye cikin arabian gown black tayi rolling kanta da black veil fuskarta bbu kwalliya sai powder da ta shafa, a hankali ta tako har inda xaljamil ke xaune ta rufe mata ido, wani ihu xaljamil ta saki dan ta tsorata, kamshin turaren mom taji dan haka ta saki ajiyar xucia, mom ta fada tana murmushi, daria mom tayi ta cika idon xaljamil. Kama hannunta tayi suka nufi dining dan yin breakfast,suna xama wayar mom ta fara ringing, hannu tasa ta dauka, murmushi tayi ganin mai kiran nata dan haka ta daga da sallama. Hello jawad! Mom kin manta dani wallahi ya fada kamar xaiyi kuka, daria mom tayi haba dai ni na isa na manta da my one nd only son, kana raina jawad, nayi missing contact dina shiyasa bama waya, ok mom na gane. Mai martaba ya dameni saina koma nigeria da aikina , munyi waya da ammi naji ance dad ma yau xai dawo ya gama contract din daya juyi, eh wallahi an jima xamu biyo flight na karfe 2.ok Allah ya kawo ku lpy. Tunda suka fara maganar xaljamil ke kallon mom, bata ji hirar da sukayi ba tasan yaran su mom ne amma ita bataji daga larabci sai turanci.taji dai mom tace my one and only son, dama tana da da bayan ni, duk a xucia ta ke maganar. Bye mom bye son sukayi sallama. Mom ce ta kalli xaljamil data buga tagumi, murmushi mom ta mata, sannan ta fara bata labarin hirar da sukayi da jawad dan tasan bataji ba. Jawad ta maimaita a ranta,suna mai dadi. Mom wanene jawad xaljamil ta tambaya tana shan xaxxafan tea din data hada. Murmushi mom tayi yareema jawad kikasan jin labarinsa, yea ta gyada kai ok bari mu gama breakfast. SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮?🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 5&6 Xaune suke a pallow xaljamil ta xubawa mom ido tana jiran jin labarin yareema jawad. Daria mom tayi xaljamil kin cika san labari amma inasan kafin kisan jawad ki fara da sanin asalinmu gaba daya dan anan ne xaki samu labarin yareema jawad cikakke. Ajiyar xucia xaljamil ta sauke tare da gyara xamanta dan jin labarin. A hankali mom ta fara bata. Asalinsu Babbar masarauta ce wacce duk nigeria ba'a taba masarauta irin wannan ba, masarauta ce mai ixxa da kasaita, suna da arxiki wanda su kansu basu san iyakarsa ba, amma sun fi kauri a noma. Suna da gidajen gonaki a wajaje daban daban. Kakanki alh Abubakar Abdulaziz ya samu sarautar a hannun mahaifinsa, bayan rasuwarsa, mutane da yawa sun yi kokarin a daura su akan karagar mulkin amma yan majalisar sarki da waxiri suka ga bbu wanda ya chanchanta sai kakanki alh Abubakar Abdulaziz da daya tilo ga sarki Abdulaziz, saboda yana da ilimin addini dana boko, kowa yyi amince da nadin waxiri dan haka a ranar da sarki Abdulaziz y rasu a ranar aka nada Abubakar grand fa dinki. Mai martaba Alhaji Abubakar Abdulaziz yana da mata hajia aminatu wacce ake kira da fulani, ita kadaice matar kakanki yayanta maxa biyu farouq da aliyu sun tashi cikin kulawa a wajen mahaifansu har suka kammala karatunsu wanda sukayi a kasar waje. Dad dinki Aliyu shine babba sai farouqkaninsa, bayan kammala karatunsu mahaifinsu ya bijiro masu da maganar aure, dukkansu a lokacin basu da wata budurwa dan haka suka bawa mai martaba damar xabar musu matan aure. Mai martaba yyi farinciki da xabin da suka bashi dan haka ya kira Alhaji usman akan ya nasan ganinsa. Baiyi kasa a gwiwa ba ya nufi gidan sarki dan amsa kiran amininsa. Xaljamil ce ta kuma gyara xamanta ta kalli mom fuskarta dauke da murmushi da alama labarin yana matukar birgeta, mom ki cigaba bana san dad ya dawo baki karasa mini ba, daria mom tayi ok bani ruwa a fridge sai mu cigaba. Da sauri xaljamil ta mike ta nufi fridge ta daukowa mom ruwa ta taho da cup ta xuba mata ta mika mata, karba mom tayi ngd xaljamil, aiki nane mom na kula dake ta fada tana murmushi. Mom na shanye ruwan ta ajiye cup din a gefe,mom wanene Alhaji Usman aminin sarki? Murmushi mom tayi, mahaifi nane. Ok nagane xaljamil ta fada tana jiran mom ta cigaba. Alhaji Usman ya je kiran da sarki ke masa, bayan sun gama hirar su ta abokai mai martaba ya nemawa aliyu da farouq auren ya'yan alhaji usman aysha da maryam, ba tare da bata lokaci ya amince ya kuma shaidawa sarki shi mai bada auren ya'yan ne. Sosai sarki yyi farinciki dan yasan aliyu da farouq sunyi dacen mata masu hankali da tarbiyya. Xaljamil ce ta kalli mom, su waye aysha da maryam, ni da kanwata mom ta bata ansa, gyada kai xaljamil tayi alamar gamsuwa, ok mom cigaba. Farouq da Umar sun yi na'am da xabin sarki dan haka sarki ya saka musu albarka ya kuma shaida musu ba dadewa xasuyi ba xaayi auren. Alhaji Usman da fara'arsa ya nufi gidan sa ya shaidawa matarsa hajia fatima, itama tayi murna dan tasan xumuncin su da fulani ya karu bayan amintaka ga kuma surukuta. Abbanmu ta bawa maman mu akan tasanar damu xabin daya mana, bbu musu muka amince dan bama iya yiwa mahaifan mu musu. Sosai aka fara shirye shirye a fada da cikin gida, bikin yayan sarki su biyu. Muna munyi shiri sosai dan mahaifin mu ya fitar damu kunya. Bayan bukukuwa na alada aka saka mu a lalle aka daura aure ko wacce aka kaita gidan mijin ta da aka gina a gidan sarki. Ni aysha aka aurawa aliyu kanwata maryam aka aura mata farouq. Sosai maxajen mu ke bamu kulawa ana haka maryam ta samu ciki, sosai gidan sarautar ya dauki murna har karamin biki aka hada a gidan nima nayi murna sosai haka ma aliyu. Cikin maryam ya shiga wata tara ta haifi danta namiji.. Mom ce ta kalli xaljamil data kara nutsuwa danjin yarda xata kasance, murmushi mom tayi a tunaninki wane irin budiri xaa yi da haihuwar baby boy a gidan sarki. Murmushi xaljamil tayi eh lallai kam tunda a samun ciki ma anyi bidiri ballantana a haihuwa. Ranar suna aka sakawa yaro suna jawad, anyi kade kade da bushe bushe irin na gidan sarauta an yi hawan dawakai duk saboda murna, sarki Abubakar yyi gayyata har abokansa na kasar waje a cikin su harda sarauniyar england, sarauniyar england ? Xaljamil ta fada mamaki bayyane a fuskarta. Kwarai kuwa kuma ta halarci wannan ranar, dan nima a ranar na fara ganinta. A jiyar xucia ta sauke eh lallai jawad dan gata, daria mom tayi gaskia kam dan gata, dan ya samu kyaututuka na gidaje da filaye harda wanda ya dauki nauyin karatunsa har ya gama. Tunda aka haifi jawad ka bashi kuyangu masu kula dashi, amma ni a wajena yake wuni, ina kaunar jawad sosai ina kuma kula dashi kamar dan cikina. Hakan yasa maryam ta dauke kanta a kan jawad dan tana tausayamin na rashin haihuwar da banyi ba. Jawad ya girma har an sakashi askul amma ni shiru bbu ciki bbu alamunsa, mahaifiyata ma abin ya fara damunta duk da aliyu bai taba nuna damuwarsa akan hakan ba, amma ni kaina ina san naga na haifi baby na. Kwanci tashi bbu wuya a wajen Allah jawad ya kallama yana primary skul yana shirye shirye tafia secondry. A lokacin mai martaba ya bawa aliyu shawara akan muje kasar waje dan duba lapiyata ina haihuwa ko banayi, aliyu kam ransa ya baci har mai martaba ya lura da hakan ya kuma sanar da mai martaba bbu inda xamuje muna jiran ranar da Allah xai bamu. Sosai dad dinki ya kasa xaman nigeria, dan yana ganin kamar ina xaune ne a cikin damuwa saboda rashin kulawar da bana samu a gidan sanadiyyar rashin haihuwar da banyi ba. Muna xaman mu sai dad dinki ya samu aiki a qatar, da kyar mai martaba ya yarda, shiri sosai muka fara a tym din jawad na ss1. Aliyu ya kaini gida mukayi sallama da mamana da babana suka mini fatan alkhairi,.a daren na shiga wajen fulani da mutan gidan nayi Sallama dasu dan gobe da safe xamu wuce. Jawad kam xama yyi a part dina yana kuka wai saina tafi dashi qatar da Ni kaina saida nayi kokan rabuwa da jawad saboda shakuwar da suka yi kyar aka lallashe hi akan xamu dawo mu tafi dashi. Mom ce ta kalli xaljamil kinji yarda muka rabu da yareema jawad, a jiyar xucia xaljamil ta sauke mom ki cigaba ina jinki. Ok habibty! Da asuba muka bar gidan sarki aka kaimu airport, karfe 8:00 jirgin mu ya tashi sai qatar. A gidan nan muka sauka sai da muka huta sannan dad dinki ya tafi yyi reporting ya sanar da xuwansa. A kwana a tashi mukayi 3 month a qatar, rashin lapia na farayi sosai kamar baxan yi ba, hankalin dad ya tashi harda kuka, daria xaljamil ta fara harda rike ciki, eh lallai soyayya, hararata mom tayi eh ai kadan ma kikaji. uhum romeo nd juliet ta fada tana daria. Hmmmm mom tayi murmushi,, muna xuwa hospital doctor ya tabbatar mana da ina da ciki wata 2,wani tsalle dad ya biga a office din ya fara rawa, doctor din daria kawai yake masa. Kudin dake jikinsa gaba daya ya cire ya bawa doctor. Muna dira gida aliyu ya fara bige bigen waya yana sanar da yanuwa da abokanan arxiki. Mai martaba sai da yaxo qatar ya ganni shida fulani da maryam da farouq, amma baaxo mini da jawad ba dan kar ya makale,. Sallama dady yyi ya shigo pallon, duk da xaljamil taji dadin dawo warsa amma bata ji dadi ba dan tasan anan labarin xai tsaya. A gurguje suka shirya dan flight din ya kusa tashi suka nufi airport. SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P. M. L. W A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 7&8 "Xaune suke a airport suna jiran a kira sunan su su wuce, dad ya gano wani friend d'insa ya tafi suna gaisawa. Xaljamil ta kalli mom fuskarta dauke da damuwa,murmushi mom tayi dan ta gane damuwar xaljamil,dan haka ta cigaba da bata labarin. Haka nayi ta renan cikin ki har na haife ki, dad d'inki yyi murna kamar ya mai da ke cikin sa haka yake ji, waya ya dauka ya kira gida ya sanar musu da haihuwar. Mai martaba da fulani sunxo ganin baby,kuka sosai yyi. Aliyu ashe dama xanga jininka kafin na bar dunia,dad ma sai da yyi kuka. Yareema jawad munyi waya dashi in kinga murnar da yyi xaki sha mamaki, har walima ya had'a a nigeria ya tara friends d'insa,su tayashi murna yyi kanwa. Haka nayi ta renan ki, muna baki kulawa ni da dad d'inki, bayasan yaji kinyi kuka ko kad'an ynx xakiga hankalinsa ya tashi. Jawad kam always muna waya,sai yasa a saka miki waya a kunne yana miki wasa ke kuma kina tuntsira daria. Daria xaljamil ta fara yi tana rufe fuskarta wai kunya. Daria mom tayi eh lallai kamata kiji kunya amma ta jawad, nasan xaiyi murna sosai da ganin ki, b'ata rai xaljamil tayi, ai mom xaiyi murnar sa ma ya gama d'an bbu ruwana dashi. Kallon ta mom tayi hmmmm xaljamil kenan. Sarki Abubakar Abdulaziz ya gaji da mulki dan dama lokacin da ya karbi mulki shekarun sa da yawa, gashi kuma y'a'yan sa sun girma dan haka ya yanke shawarar yin murabus. Bbu wanda ya kamata a bawa mulki sai dadyn ki Aliyu, dan yafi farouq shekaru ya kuma fishi wayo da sanin makamar mulki, dan haka mai martaba ya bugawa Aliyu waya akan ya baro qatar xa'a masa nadin sarauta, dadyn ki bayasan mulki dan yace yana da hadari dan haka yace ya ce ya hkr a bawa farouq. Ba haka sarki yaso ba amma dan kar farouq yaga baya san a bashi mulkin yasa ya janye bawa aliyu ya daura farouq. Ajiyar xucia xaljamil ta sauke, fuskarta d'auke da murmushi, mom wato da tuni dad ne sarki? Yea xaljamil mom ta bata amsa. Gyada kai tayi na gane. Mom ki cigaba mana, hararta mom tayi, haba xaljamil mai kike san ji a tarihin rayuwar ki bayan wannan. Murmushi tayi har sai da beauty point d'inta ya lotsa, hakane mom wannan ma thanks alots, I really appreciate. Ko? Mom ta tambaye ta. Yea ta fad'a tana murmushi. Kiran sunan su aka fara dan haka suka nufi jirgi. Tafiar 4 hours sukayi a sararin samaniya, suka sauka a proudly nigeria. Gaban xaljamil ne ya shiga fad'uwa, baiwar Allah duk ta rud'e dan haka ta rike mom sosai a jikinta. Mom ma rike ta tayi dan taji jikin xaljamil har rawa yake, kiyi du'a mom ta rad'a mata a kunne. Bayan wasu lokuta kalilan aka bud'e masu kofar jirgi, nan aka fara fita, still xaljamil rike take da mom har suka sauka a jirgi suka fito farfagiyar wajen. Xaljamil sai raba ido take dan airport d'in ta mata kyau, wata irin magana taji a wajen kuma bata mutun d'aya ba. Fadawa ne suka xube a gaban d'an sarki Abubakar Abdulaziz, sai kayi d'an sarki jikan sarki,Allah yaja xamanin ka ranka ya dade. Hannu dad ya d'aga musu nan suka dawo kan mom itama suka fara mata kirari, gaishe ki gimbiya aysha, gaba salaman baya salaman. Murmushi mom tayi ta d'aga musu hannu. Xaljamil da Tunda taji maganar nan hankalin ta ya tashi ta kuma runtse idonta tana hawaye kirjinta na bugawa da karfi. Kamar an tab'a dan haka da sauri ta bud'e idonta, tar suka bud'e akan fadawa da suketa bud'e babbar riga,wata kara xaljamil ta saki dan ba karamin tsorata tayi ba ganin fadawan nan, gasu bakake munana ga kuma wasu kaya da bata taba ganin su ba. A hankali numfashinta ya d'auke, ta sulale kasa ta fadi sumammiya. Tofa. Fadawa kam tun daga ihun da tayi suka rikice, mom ce tayi kan xaljamil tana jijjigata amma ina ta suma, dad cikin tashin hankali ya dauki xaljamil ya xura a cikin motocin da aka xo d'aukarsu,shiga yyi mom ma ta shiga duk sun rikice. da gudu driver ya d'auki hanyar gidan sarki, wanda kafin su karasa har xance yaje wai gimbiya xaljamil ta suma. Ina xaka kaimu naga ka d'auki hanyar gidan sarki? Aliyu ya tambaya cikin tashin hankali. Gida muka nufa ranka ya dad'e, a'a hospital xamu wuce. Ba fadan ne ya russunar da murna, Allah ya taimakeka kasan yareema jawad ya dawo d'axu mai martaba yace a kaita gida. Ajiyar xucia dad yyi ok muje, mom kam fuskarta ta jike da ruwan hawaye, Dad ne yake ta lallashinta. Kofar fada ta cika makil duk anyi jigum jigum,, harda mai martaba Abubakar da sarki farouq sun kasa xaune ballantana tsaye. Motar na tsayawa sarki farouq da kansa ya dauki xaljamil ya nufi part d'in da aka tanadar musu. Mom da dad ma suka bi bayan su. Har cikin part d'in ya kaita ya nufi d'akin da aka tanadarwa xaljamil, a kan gadon ya ajiyeta. Wayarsa ya d'auka ya kira jawad, bugu biyu ya d'aga cikin rissinawa. Sarki farouq ne ya lullube shi da fad'a, jawad kana ina haka? Gashi har sun karaso baka xo ba. Gani ya fad'a bayan ya murd'a handle d'in dakin. OMG! Phone d'in hannuna naji tana baraxanar rabuwa da hannuna, da sauri na rike ta dan gano muku rahoton abinda na gani. Kyakkyawan guy na gani wanda xan iya ranteswa baiyi kama da d'an nigeria ba, fari ne dogo yana da dan jiki amma ba sosai ba, sumar kansa a gyare sai kyalli take, wani kamshi mai dad'i ne ya doki hancina. Sanye yake da labcourt fuskarsa dauk'e da farin glass. Sarki farouq ne ya juyo ya kalli shi, jawad mai kake jira? Da sauri ya karasa jikin gadon sannan ya basu umarni su fita ya dubata, mai martaba Abubakar ne ya kalli jawad, kaci gidan ku, ina kakeso muje ina ganin jikata a cikin wannan yana yin. B'ata rai jawad yyi ya kalli iyayensa Aliyu da farouq, murmushin mugun ta yyi sannan ya juyo alamar xai bar wajen, sarki Abubakar ya kalla ok xoka dubata. Sarki Abubakar ne ya kalli jawad dake kokarin fita daga d'akin,da sauri ya riko hannunsa kai tsaya mana, idan ka tafi waxai duba kanwar taka, murmushi jawad yyi wanda ya kasheni a xaune. gaka a tsaye, yau naga ja'irin yaro bari mu fita sai ka dubata. Duk da suna cikin tashin hankali sai da suka murmusa.Fita sukayi gaba d'aya suka rufe kofar. Yareema jawad ya mai da hankalinsa ga kallon xaljamil,kallon fuskarta yake tayi kyau sosai kamar mai bacci, a hankali ya dawo kan pink lips d'inta masu kyau da fasali, wow beautiful ya fad'a yana wani shu'umin murmushi yana shafa sumar kansa.dama haka yarinyar nan ta koma?gaskia ta girma sosai. Jawad ka duba ta mana xuciar sa ta tuna masa abinda yaxo yi. Sosai ya fara dubata, baisha wahala ba xaljamil ta farfado a hankali ta bud'e idonta tana salati,lumshe ido jawad yyi jin daddadar muryar xaljamil. Fes ta bude idonta ta d'aura su akan jawad, gaban ta ne ya fad'i ta ganin balarabe a gaban ta, a hankali take bin d'akin da kallo, eh lallai tabar nigeria, ganin haduwar dakin. Idonta ta sauke akan jawad da ya xuba mata ido yana kallonta. Doctor ina Mom da dad dina ko basu biyo mu qatar din ba? Kallon ta yyi da mamaki amma bai ce komai ba. Doctor suna nigeria ko?duk da larabci ta tambaye shi., jawad kam yyi mutuwar tsaye, muryar xaljamil ta gama tafia dashi.shiru ya mata ya fara ra, idon xaljamil ya kawo kwalla ta fara yarfa hannu cike da shagwaba xatayi kuka,jawad na kallon ta ya dake yana kara yaba siffar xaljamil a xuciar sa, kukan da take niyar yi ta kara masa kyau. Plx doctor bana san allura ta fad'a da larabci, ganin ya nuna kamar bai jitaba ranta ya fara baci, wannan wane irin mutun ne? Tund'a xu nake tambayarsa ya mini banxa. Ko baya magana ne? Xuciar ta ta bata. Jawad na gama hada allurar ya juyo ga xaljamil da ta fara kuka ma, Mom dad kawai take kira, jawad bai daina kokarin tsira mata allura ba dan haka ta rike hannunsa tana kuka mara sauti. Kallonta ya tsayayi gani xata b'ata masa lokaci yasa ya kwace hannunsa, sexy eyes d'insa ya xuba a cikin na xaljamil yana kallonta, gaba d'aya ji tayi jikinta yyi sanyi. Cikin lion voice d'insa ya mata magana, ki tsaya kar kiji ciwo, da larabci ya fad'a mata, wayyo Allah, xaljamil gaba d'aya mutuwar kwance tayi, jin voice d'in jawad, batasan tym d'in da jawad ya juye mata allurar ba. Magani ya ajiye mata a gefe ya kwashi tarkacensa ya fita daga d'akin. Ido xaljamil ta bishi dashi tana yaba kyawun gayen . Xaune ya tarar da iyayensa a pallo sun buga tagumi suna jiran feed back. Murmushi yyi ya kalli sarki mai murabus da ya buga tagumi shima, ganin jawad yasa suka mike suna tambayarsa ya jikin nata? Ta farfad'o amma tana bukatar hutu dan haka basai kun shiga ba ku bari sai anjima idan tayi bacci ta tashi. Sarki Abubakar da kyar ya tafi, sarki farouq ma ya wuce, xasu dawo anjima. Jawad na fita ya nufi part dinsa. Uncle! Uncle!tsayawa yyi chak, murmushi yyi ba tare da ya juya ba dan yasan wacece, da gudu ta karaso ta rungume kafarsa ta baya. Da fara'arsa ya juyo ya d'auketa y chillata sama, daria suka sa gaba d'aya. Nawal ya furta yana kallon fuskarta, uncle ta fad'a tana murmushi, kinyi nauyi mai fulani take baki? Daria nawal tayi, bbu abinda take bani. Hancinta ya lakace au haka kikace ko? Saina fad'a mata. Hannu tasa ta tushe bakinta, la! Uncle karka fad' a mata plxxxxx, murmushi yyi ok chanja xancen ki. Fulani na bani abinci mai dad'i, harda ice cream da chocolate ma tana bani. Daria sosai jawad keyi kai nawal kin cika surutu, haka kowa yake cewa ta fada tana kokarin sauka daga jikinsa, ina xaki xaljamil? Ya fad'a yana kallonta, d'ago kai nawal tayi tana kallon jawad cike da mamaki, uncle! Wacece xaljamil. Sai lokacin ya tuna abinda ya fad'a,, tabarbarcewa yyi ya sauke nawal, oppsss I mean nawal ok? Gyada kai tayi tana murmushi. Uncle! Na'am nawal, bari naje na duba aunty na mai irin sunan daka fada ynx, sun dawo daga qatar fulani tace bata da lpy? Eh haka jawad ya fad'a bayan ya tuna kyakkyawar fuskar xaljamil. Ok nawal kiyi sauri kije ko? Inasan naje nayi wanka xan fita unguwa. Ok uncle karka manta ice cream ni da aunty na, shafa kanta yyi insha Allah baby nawal. Da gudu ta nufi part din Mom dan duba xaljamil. SUMYNBASH CE 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P. M. L. W A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 9&10 "Cike da takun k'asaita da isa ya ke tafia har ya karasa part din sa, bayi na ganin sa suka fara xubewa suna k'wasar gaisuwa, ransa kam duk ya gama b'aci dan ya tsani wannan haya niyar. Bai tanka musu ba ya shige ciki. "Rantsan tsan palour ne wanda yaji kayan alatu, ya hadu iya haduwa wanda idan kana ciki xaka iya manta cewa a nigeria kake. Cike da k'asaita ya nufi bedroom d'insa, yaxo shiga Bala kuma yaxo fita, dan haka Bala da sauri ya matsa baya kamar wanda aka tsikarawa shocking. Hannunsa ya dun k'ule ya kalli yareema jawad yana murmushi, ranka ya dad'e yareema jawad, d'an sarki jikan sarki, gaisheka magajin sarki, gaisheka............ Is ok jawad ya buga masa wata tsawa mai raxanar wa. Da sauri Bala ya kama bakinsa ya tsuke yana jiran irin hukuncin da xa'a yanke masa. "Cike da b'acin rai yareema jawad ya kalli bala, cikin lion voice dinshi ya fara magana. U are very stupid bala, who d hell are u da xance banasan wannan surutan banxa amma ka dinga mini, jikin bala kam har rawa yake yi, ayi mini afuwa ranka ya dad'e hakan baxai kara faruwa ba. Dogon tsaki jawad ya ja ya shigewarsa dakin. "Ajiyar xucia ya sauke jin daddad'an k'amshi na tashi a d'akin, ko ina fes yake a g'yare. D'akin ya cigaba da bi da kallo yana murmushi, komai na d'akin white colour ne tun daga furnitures, rug, paint, tiles.Komai kal kamar yau aka saka su, murmushi yyi, Allah sarki bala kana k'ok'ari wajen bin duk wasu dokoki dana kafa maka. Bala shine bafadan da yareema jawad ya aminta dashi a b'angaren d'akinsa da kuma abincinsa, ya yarda da tsaftar bala dan shi mutun ne mai tsantsami baya san k'axanta. "Sallama bala yyi cike da ladabi ya shigo d'akin, a hankali ya taka kusa da yareema jawad ya fara cire masa labcourt d'in jikinsa. Bayan ya gama ya durk'usa ya fara cire masa takalmin k'afar sa, yana gama wa ya nufi toilet dan had'awa yareema ruwan wanka. "Bala na shiga toilet yareema jawad ya cire kayan jikinsa ya saka rigar wanka, xama yyi a gefene bed d'insa yana jiran bala. A gurguje bala ya hada duk wani abu da yareema xai bukata ya fito a toilet din, yareema jawad ya kalla yana murmushi, ranka ya dad'e xaka iya shiga, mik'ewa yyi ba tare da yace komai ba ya shige toilet din. "Murmushi bala yyi, ranka ya dad'e d'an rigima, banda abin yareema Allah ya baka sarauta amma kace baka san kirari, wayyo Allah ina ma nine, ai da k'asa ma baxan taka ba sai dai mutane. Hmm kunji bala. A gurguje bala ya kuma tattare d'akin yareema jawad had'e da sake feshe shi da airfreashner masu k'amshi,sannan ya nufi wardrob ya ciro wa yareema jawad wasu k'ananun kaya. "Yareema jawad bai fito a toilet ba sai da ya d'auki almost 1 hour sannan ya fito daure da towel a waist d'insa, hannunsa da wani k'aramin towel yana tsane sumarsa. A hankali yake takawa kamar wanda kwai ya fashe wa a ciki ya nufi dreesing mirror. "Da sauri bala ya nufi mirror, rissinar da kai bala yyi sannan ya kalli yareema jawad dake k'ok'arin shafa , ranka ya dad'e fatan an fito lpy?sai da yareema jawad ya d'auki wajen 3minutes sannan ya amsa da lpy. "A hankali yareema jawad ya gama shirin sa, kayan da bala ya dakko masa ya gani a gefen bed dan haka ya nufi kayan yana duba wa.bala kam yyi mutuwar tsaye yana jiran feedback daga wajen yareema. Kayan sunyi masa, gaskia brain din bala tana aiki ya fad'a a xuciar sa. murmushi yyi dan haka bala ya gane komai yyi dai dai, da sauri ya fita daga d'akin dan bawa yareema damar shiryawa. "Yareema jawad a gaban mirror yana karema kansa kallo, yyi kyau sosai cikin white tshirt nd black trouser. Ya taje sumar kansa ta kwanta luf, man pride dinsa ma sai wani sheki yake yi, bakinsa kamar ya saka pink lipstick. Hannunsa daure da agogo mai bala'in tsada wanda ba a ko wane hannu ake ganin irin sa ba sai irin su yareema jawad. Perfumes masu dad'in k'amshi wajen kala 5 ya fesa a jikinsa, murmushi yyi dan shi kansa yasan yyi kyau. "Bedside drower ya nufa ya kwashi wayoyinsa da key din motarsa ya fita, a palour suka hadu da bala, wanda yana jin an murda handle din dakin ya mike tsaye. Yareema jawad ya kalla yana murmushi had'e da sosa keya, ranka ya dad'e wannan wankan da kayi kamata ace xance xakaje. "A fusace yareema jawad ya juyo ya kalli bala rai a b'ace, to hell with u bala, kasan abinda kake fada kuwa? Budurwa, xance, menene su kuma bala, dan a dictionary din rayuwata bbu su a ciki, numfasa yareema jawad yyi ya kuma kallon bala da takaicin kalamansa, karka kara mini shishigi a lamurana idan ba haka ba wallahi ranka sai ya baci. Bala kam duk ya tsure ganin yanayin yareema jawad ya chanja in minute, tuba nake ranka ya dad'e insha Allah ba xaka sake samuna da irin wannan laifin ba. Murmushi yareema jawad yyi wow his smile kill wallahi. Good ya fad'a kamar mai rad'a. A hankali ya fara takawa cikin kasaitar sa ya nufi hanyar fita. " Part din fulani ya nufa dan basu gaisa ba, tafia yake cike da k'asaita, tunda ya doshi hanyar part d'in fulani bayi maxa da mata suka fara xubewa a kasa suna gaida yareema jawad , abinda ya tsana a rayuwar sa dan yana ganin hakan takurawa rayuwar sa ne. Baya ansa musu sai dai kawai ya wuce abinsa sannan sai su tashi su wuce, har ya karasa palour fulani ana masa haka dan haka a fusace ya shiga pallon nata da ko arxikin sallama bata samu ba. "A kishingid'e take ta sha ado da alkyabba, fara ce tas kyakkyawa, kamar su daya da mom din xaljamil, sai dai fulani tafi mom jiki saboda xaman waje daya da rashin motsa jiki da batayi kullum. Kuyangu 5 ne a xagaye da ita, daya na tausa mata kafa daya na bata labari, daya na bare mata ayaba, daya kuma tana mata fifita da maficin sarauta. "Tana ganin yareema jawad ta tashi xaune tana masa murmushi, da sauri kuyangun suka tashi suka nufi hanyar fita, sai da suka xube kasa suka gaida yareema jawad sannan suka fice . "Fulani ta lura da b'acin ran da yareema ke ciki dan haka gaba daya hankalinta ya tashi, tsaye yake yaki kara sowa wajen fulani dan haka da kanta ta tashi ta jawo hannunsa suka xauna a karagar ta. "Cikin rawar murya take tambayar sa, d'an sarki yareema jawad mai yake faruwa ne? Bata rai ya kuma yi ya kalli fulani. Ammi xan bar k'asar nan, xan koma london na cigaba da aikina a chan, xaro ido fulani tayi, yareema jawad mai kake cewa? Mai aka yi maka haka? Naga dai d'axu ka sauka a kasar nan,mai yake faruwa ina san sani. "Kwalla ce a idonsa yana kokarin hanata fitowa amma sai da ta fito, salati fulani ta fara tana tafa hannu duk ta shiga rud'ani, girgi xashi ta fara yi yareema jawad ka fad'a mini mana. " Ammi xan bar k'asar saboda ba xan xauna bayi su kashe ni ba, ido ta xuba masa dan ta rasa inda xancen jawad ya dosa. Kisa kuma ta maimaita, yea kisa Ammi, ace mutun bashi da sakewa, duk inda ka d'aura k'afa sai dai ka dinga jin ihun mutane wai sunan kirari suke maka, bana san hayaniya Ammi, nafi san naji silient a ko ina, bana san surutan nan wallahi Ammi ciwon kai yake sakani, ynx haka kaina ne ke ciwo. "Fulani gaba daya ta gama fusata da maganar yareema jawad amma ta basar gudun kar yyi fushi da ita. Hannunsa ta kama cikin sigar lallashi tana kallon fuskarsa, yareema jawad ta kira sunan sa kamar mai rad'a, d'ago kai yyi ya kalli fulani ba tare da ya amsa ba. "A hankali ta fara magana , sarauta baiwa ce wanda ba kowa Allah yake bawa ba sai xab'abb'e, ana siyan komai a dunia banda sarauta, sarauta aba ce mai daraja kuma kariya ga wanda yake da ita,sarauta a jininka take yareema jawad bbu wanda xai iya chanja maka ita, bayi dole su maka biyayya sbd akwai taxara mai nisa tsakanin yan'ci da rashin yan'ci. Kana tunanin kowa akeyi wa kirari ne? Shi kansa wannan miliyoyin mutane n nema a musu amma basu samu ba, amma yau abin takaici da mama ki, dan sarkin da duk fad'in k'asar nan bbu kamarsa yace bayasan bayi su dinga masa kirari. "Yareema jawad kayi hkr ka janye kudirinka kuma karka kuskusa wani a gidan nan yaji wannan xancen , indai ni fulani nice na haife ka. D'ago ido yyi ya kalli Ammi da itama shi take kallo, gyada kai yyi a fili alamar ya yarda, amma a xuciar sa ji yake kamar kamar ya shak'e kansa. "Mikewa yyi yana duba agogon dake d'aure a wrist d'in shi, kallon sa Ammi tayi ina xaka yareema jawad naga ka mike, kallon ta yyi yana murmushi xanje wajen areef ne inasan na bashi suprise dan bai san xuwana ba yau. Ok Ammi ta fad'a ka gaida mini da hajiar su, xataji ya fita da sauri daga part din, a jiyar xucia fulani ta sauke tana jin kaunar jawad na kara shigar ta, murmushi fulani tayi a karo na biyu data tuna maganar da sukayi da yareema jawad, tasan ansar daya bata bata kai xuciar sa ba, amma ya amince dan ya mata biyayya. Allah sarki jawad ta fad'a a fili, Allah ya maka albarka. "Yana fita ya nufi inda aka tanada dan ajiye motoci, cruiser prado golden colour ya hau ya bar gidan . "Nawal da gudu ta shiga part din su xaljamil tana kwa'lawa mom kira, kamar yadda taji fulani ta fad'a data tambayeta sunan bakin da suka xo tace mata mom da xaljamil. Mom ta fito daga dakin xaljamil taji ana kwalawa mata kira, xubawa babyn idon tayi tana kallon ta ta nufi mom da gudun ta, murmushi mom tayi ta bud'e hannunta gaba d'aya nawal na karasowa ta dauke ta chak ta dagata sama suna daria. Mom ykk? Ya gajia,l? nawal ta fada tana kallon fuskar mom,lafia lau babyna . OMG nawal ta fad'a tana murxa idonta da hannu ta, mom wallahi kamarku d'aya da fulani, har murya ku fa ta fad'a tana k'ara kallon fuskar mom. Daria mom tayi eh babyn mom, she is my sister ta fad'a tana murmushi. Wow gaskia mom kin had'u ni saina ga ma kamar kinfi fulani kyau, ita fulani tayi k'iba da yawa ni kuma banasan naga mai k'iba, kinsan ni nan gidan ma xan dawo, sosai mom ke daria ganin yarda nawal ke xuba mata surutu bbu comma. " Babyn mom ya sunana? Ni sunana nawal, ni marainiyace mamana ta rasu tunda ta haife ni, ynx fulani itace mamana. gaba d'aya nawal yanayin fuskarta ya koma abin tausayi, sosai mom taji bbu a ranta, jikinta gaba d'aya yyi sanyi. Allah sarki baby nawal Allah ya raya ki kinji, kinga ynx kin sake samun mom ga kuma fulani, ynx ke yar gata ce, kar na karajin kin kira kanki marainiya kinji nawal? Gyada kai tayi shikenan mom ina aunty xaljamil? Tana room dinta mom ta fad'a tana sauke nawal daga jikinta, ok bari naje na duba ta naji ance wai ta suma? Eh mom tace. Da gudu nawal ta nufi dakin xaljamil,nawal mom ta kirata, yes mom ta amsa,auntyn ki batajin hausa ki mata magana da turanci, ok mom ta fad'a ta cigaba da gudunta. mom binta tayi da kallo tana jin tausayin yarinyar na ratsata, Allah sarki Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i. "Xaljamil xaune tana naxarin d'akin da take ciki, gashi ta kasa tambayar mom qatar suka koma ko kuma suna nigeria, da karfi nawal ta banko kofar d'akin wanda sai da ta tsorata xaljamil. Xubawa yarinyar ido xaljamil tayi tana kallon ta, kyakkyawace itama sak larabawa, gashin kanta baje a bayanta, tana gudu gashin na yawo a bayan ta. Sanye take da yellow gown wacce ta tsaya iya gwiwarta, tana karasowa ta shige jikin xaljamil, oyoyo my aunt, how was ur body? Fyn dear xaljamil ta fad'a tana shafa fuskar nawal.xama tayi a cinyar xaljamil tana wasa da xoben dake hannun xaljamil,ita dai xaljamil ta xuba ido tana kallon ikon Allah. Aunty ya qatar? Kallon ta xaljamil tayi cike da mamaki, qatar ta maimaita, yes qatar fulani tace daga chan kuka xo, fulani xaljamil ta fad'a jin wani bak'on suna, eh matar sarki ce. Wayyo Allah xaljamil ji tayi kamar ta d'ora hannu aka tayi kuka, wato suna nigeria to amma Kyakkyawan guy d'in data gani da wannan beautiful gal din daga ina suka fito? Aunty uncle d'ina yace na gaishe ki yace na gaishe ki, murmushin yake xaljamil tayi ina ansawa ta fad'a tana kallon nawal. SUMYNBASH CE 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P. M. L. W A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ DAN ALLAH INA BARAR ADDU'AR KU INA KWANCE BANI DA LAFIYA. ILYSM💋 Chapter 11&12 "Gaba d'aya ta shiga rud'ani, ynx ta yaya xata cigaba da rayuwa a cikin mahaukata, ita dai mutanen data gani sun bata tsoro. Nawal ce ta kalli xaljamil! Aunty su waye mahaukata kuma? Da sauri xaljamil ta kalli nawal, sai sannan ta gane maganar da tayi a fili ne ba'a xucia ba. Murmushin yak'e xaljamil tayi tana kallon nawal, baby ya sunan ki? Daria nawal tayi, ni sunana nawal, wow nice name, murmushi nawal tayi thanks my aunt. Mom ce ta turo k'ofa hannun ta dauk'e da coffee, a kusa da xaljamil ta ajiye sannan ta mikawa nawal nata.wow mom thanks alots, daria mom tayi dan manyancen nawal na birgeta, yarinya ce da bata wuce shekara 5 ba amma wayonta ya mata yawa. "Xaljamil ce ta kalli mom duk ta shagwabe fuska kamar xatayi kuka, cikin yaren larabci ta fara magana,mom wai muna nigeria ne? Kallon ta mom tayi cikin rashin fahimtar tambayar da xaljamil ke mata. Cikin yaren larabcin mom ta bata ansa, yea muna nigeria akwai matsala ne? Hawaye ta fara yi dan tasan ta rasa rayuwa mai yanci, ta daina fita, shikenan ita a d'aki xata kare rayuwar ta. "Nawal ce ta kalli mom da duk jikinta yyi sanyi ganin aunt dinta na kuka, mom mai ya samu aunty xaljamil? Murmushi mom ta kirkiro ta kalli nawal, baby nawal kinsan bata da lafia shiyasa take kuka. Eyyah sannu my aunt, xaki samu sauki very soon kinyi? Gyad'a kai tayi tana gunguni a xuciar ta, nifa gaskia wannan yarinyar ta takura mini da yawa. Tashi nawal tayi daga jikin xaljamil, mom, aunt bari naje na duba uncle dina idan ya dawo, ok nawal mom ta ce nawal kam ta fita da gudu. "Xaljamil ta kalli mom fuskarta na xubar da hawaye, mom baxan iya xama a nigeria ba, dan Allah ku mai dani qatar, murmushin takaici mom tayi ta kalli xaljamil, hmmmm xaljamil kenan, naga alama so kike ki jawo mana maganar da xama a gidan sarki sai ya gagare mu, duk ranar da aka gane bakyasan jinsinki, jininki wallahi xaljamil kin jawo mana tashin hankali, ko wane tsuntsu kukan gidan su yakeyi, ke yar nigeria ce kuma baxaki tab'a chanja wa daga hakan ba. Bbu maganar komawa qatar xaljamil kina nigeria harki mutu a nan xa'a binne ki inda aka binne yan'uwanki da danginki, kina bani mamaki xaljamil, sai na rasa ina hankalinki yake da ilimin ki suka tafi, kin chanja gaba d'aya daga yarda na sanki, ya kamata ki tattaro nutsuwarki ki da tunanin ki gaba d'aya kamata ki rungumi k'addarar ki, ki saki jikinki sai ki huta. " Da bak'i da fari halittar ubangiji ne, kuma bbu wanda yake xabar yarda xa'a halicce shi da kuma a k'asar da xa'a halicce shi. Kuma indai yaren hausa ne indai kina gidan nan xaki iya, daga ranar da kika fara fahimtar hausa xaki gane ba shirme bace, shiru mom tayi tana kallon yarda xaljamil ta nitsu tana sauraran maganar ta. "Jikin xaljamil kam yyi sanyi, sai dai itama bayin kanta bane, amma xata daure tayi kokari ta fara sakin jikinta da gidan ko xata samu xuciar ta ta xauna lpy. Ajiyar xucia ta sauke ta kalli mom da itama xaljamil d'in take kallo, mom insha Allah ba xaki kara jin irin haka daga gareni ba,ta fada hawaye na xuba a idon ta. Rungumeta mom tayi itama sai da tayi kukan saboda tausayin xaljamil,Allah ya miki albarka xaljamil. Ameen ta amsa tana goge hawayen fuskata. "Ga coffee dinki ki sha sai kishiga wanka kinji, yes mom ta fada tana murmushi. "Yareema jawad, tafe yake a motarsa wacce sai shik'e takeyi ya nufi gidan su areef xuciar sa fal nishadi, a wani tangameman gida yyi parking fita yyi daga motar ya taka da kansa har jikin gate d'in, knocking yyi gate man ya lek'o dan duba waye, ganin yareema jawad yasa ya bud'e gidan jikinsa har rawa yake yi, bajewa yyi a gaban yareema yana kwasar gaisuwa, sosai ran jawad ya b'aci amma ganin tsofan gate man yasa ya d'anyi murmushin da bai kai xuci ba, kud'i ya cire a a aljihunsa ya mik'awa gate man yyi gaba cikin takun kasaitarsa, a hankali ya k'arasa har inda xai sada shi da cikin gidan. Hayaniyar masu gidan yaji a babban palour d'insu, jin muryar tayseer yasa yareema jawad yaji kamar ya juya, dakewa yyi ya tura kai cikin palourn da sallama. Hajia binta, areef da tayseer xaune suna hira, gaba d'aya hankalin su yyi jikin kofar jin muryar yareema jawad. Wani ihu tayseer tayi ta nufi yareema jawad tana murna, mutuwar tsaye yyi dan yasan tayseer rungumar sa xata yi, dan haka yyi saurin durk'usawa k'asa ya fara kokarin cire takalmin kafarsa, hakan kam ba karamin bata ran tayseer yyi ba, amma tana tsaye bata tafi ba, a hankali ya gama cire takalmin nasa sannan ya mik'e ya nufi cikin palourn, caraf tayseer ta rik'e hannunsa, d'aga idonsa yyi ya kalli hajia da areef da suka xuba musu ido, murmushi ya kirkiro amma a xuciar yana Allah wadarai da irin tarbiyyar tayseer. "Areef kam gaba d'aya ya kasa magana dan mamakin ganin yareema jawad yake,bai sanar dashi xaixo nigeria ba, amma ya sanar dashi ya kusa dawowa. Cikin tafiar k'asaitarsa dake tafia da tayseer ya karasa gaban hajia bayan yyi kokarin raba hannunsa dana tayseer. Durkusawa yyi har kasa ya gaida hajia cikin girmama wa, dan yareema jawad mulkin sa bai dame saba, yana bada respect ga duk wanda ya girmeshi. Da fara'a hajiar areef ta amsa tana tambayar sa fulani, cikin murmushin sa wanda ba kowa ke ganin sa ya bata ansa, tana gaishe ki. Ina ansawa yareema jawad ta fada tana murmushi. Tayseer kam xama tayi ta xubawa yareema jawad ido cike da so da kauna. "Areef ne ya tashi bakinsa yak'i rifuwa dan farincikin ganin yareema jawad, hannunsa ya kama suka nufi part din areef. Xaune suke a palourn areef wanda a ka cika gaban yareema jawad da kayan tab'awa. Wallahi yareema jawad ka matuk'ar bani suprise, murmushi yareema yyi ai dama haka nakeso, eh ka kyauta. Kasan ku manya masu sarauta komai naku daban ne, hararasa yareema yyi yana murmushin sa mai birgewa. Areef xaka fara ko? Wallahi ynx sai na bar maku gidan ku, daria areef yyi tuba nake ranka ya dad'e suka sa daria gaba d'aya. "Areef ne ya kalli yareema jawad wanda ya lumshe idonsa yana xuba murmushi,yareema jawad da alamu a kawai wani abin farinciki daya sameka, bud'e idonsa yyi tar a fuskar areef still da smile a face d'in shi, a hankali ya furta baby xaljamil sun dawo nigeria, areef kaga xaljamil kuwa, ta girma sosai tayi wani kyau, wallahi xaka rantse cewa bata had'a jini da nigeria ba. Baki areef ya saki yana kallon yareema jawad duk da yasan akwai soyayya mai karfi da yareema jawad kewa xaljamil, amma daga ganin yarda yake nishadi da farinciki ya fara xargin wani abu. Kai masha Allah areef ya fada, gaskia naji dadi sosai yareema jawad, kace auren ka ya kusa kenan? Juice din da yareema jawad ya xuba a bakinsa ya fito dashi, yana hararar areef, god 4 bid, xaljamil ai kanwa tace, kana tunanin xan iya auren ta, tun ba yau ba kasan irin san dana kewa baby xaljamil amma ta yan'uwan taka ce kawai, murmushi areef yyi daya tuna wani abu, ok yareema jawad, gaskia na gane manufarka amma idan bbu damuwa inasan ka hadani da xaljamil mana,cup din hannun yareema jawad ne ya fadi a kasa wanda sai da ya fashe, duk ya wani rikice, cikin rawar murya ya kalli areef, wai, wai xaljamil kake so? Wani shu'umin murmushi areef yyi eh ya fadawa yareema jawad. Wata xufa ce ta lullube shi, da kyar yyi controlling temper d'insa ya kuma kallon areef, gaba d'aya yanayin sa ya sauya, sai da ya had'iyi wani yawu mai d'aci sannan yace, sai ka iya larabci kafin kaje, murmushi areef yyi kai nayi murna babban yaya dan dai larabci ai mun iya haxa da haxihi.wani kallo yareema jawad ya watsa masa wanda bai masan yyi ba. SUMYNBASH CE💋 KUYI HKR DA WANNAN WALLAHI BA K'ARAMIN K'OK'ARI NAYI BA NAYI TYPING D'IN NAN, LUV U MASOYAN SUMYNBASH 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P. M. L. W A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ PLX MY FANS UR PRAYER IS NEEDED IM SICK, PLX KU SANI A DU'A DINKU, INA KAUNAR KU A DUK INDA KUKE MASOYAN SUMYNBASH 💋💋💋💋 Chapter 13&14 "Yareema jawad ji yyi gaba d'aya hirar ta ishe shi, dan haka ya mike yana duba watch d'in dake d'aure a wrist d'insa, wata iska ya furxar sannan ya kalli areef, gaba d'aya yanayin sa ya chanja, xan wuce ya fad'a da sanyin murya, tashi tsaye areef yyi sannan ya kalli yareema jawad yyi murmushi, ok babban yaya muje na rakaka gida dan ina san na fara ganin my heart desire, ya fad'a yana shafa sumar kansa. "Yareema jawad ji yayi kamar areef ya soka masa mashi, dan haka bai iya cewa komai ba ya d'auki hanyar barin palour, bayan sa areef yabi yana daria k'asa-k'asa. Yareema jawad shiga motar yyi yana jiran k'arasowar areef su wuce, areef na karasowa ya sunkuyo da kansa dai-dai yareema jawad fuskarsa d'auke da murmushi, babban yaya baxan samu damar binka yau ba, amma gobe xanxo xance wajen my heart desire dan Allah a gyara ni a wajen ta, wani k'ululun bak'in ciki ne ya a tukarewa yareema jawad a mak'ogaro, da kyar yyi murmushin da bai kai xuci ba, ya ansawa areef da ok. "A takaice suka yi sallama yareema jawad ya ja mota da gudu ya nufi gida. Wani shu'umin murmushi areef yyi wanda shi kad'ai yasan manufarsa da haka ya shige cikin gida. "Yareema jawad kam Allah ne ya kai shi gida, bai tsaya ko ina ba sai a part d'insa, a nan ya ajiye motar yyi ciki. Gaba d'aya ransa a b'ace yake kuma ya rasa dalilin b'acin ran, to mai yake shirin faruwa dashi ne. "Bala ya fito daga kitchen yaga shigowar yareema jawad a fusace, daga gani yasan bbu lpy, dan haka ya rud'e dan yasan abin sai ya shafe shi. "Yareema jawad bedroom d'insa ya nufa yana shiga ya cire kayan jikinsa ya saka na wanka ya nufi toilet, dan wani bala'in xafi yake ji da baxai iya jiran bala yaxo ya hada masa ba. "Da sallama bala ya shigo d'akin yana rarraba ido, jin saukar ruwa a toilet ya k'ara firgita shi, shikenan yareema jawad ya gaji da jirana har ya shiga toilet da kansa. "A gurguje bala ya kwashe kayan da yareema jawad ya cire ya nufi wardrob ya dakko masa wata red riga mai karamin hannu, sai wando 3quater black colour ya ajiye a gefen bed, da sauri bala ya fita ya nufi kitchen dan kar girkin daya d'aura ya k'one, dan wannan yafi masa komai tashin hankali saboda yareema jawad bayasan yaji k'auri ko kad'an ballantana ace abincin da xaici ne yake k'aurin. "Yareema jawad kam banda sakarwa kansa ruwa bbu abinda yake yi, a hankali yaji sanyin ruwan ya fara ratsa shi dan haka ya hak'ura ya fito d'aure da towel a waist d'insa. Wajen standing Ac dake d'akin ya nufa, a hankali ya kaita karshe dan yaji sauki a ransa,sannan ya dawo ya nufi dressing mirror. "Kayan da bala ya d'akko masa ya saka ya fada luntsumeman gadonsa yana kallon ceilling, knocking bala yyi sannan ya shigo d'akin hannunsa d'auke da tray, gaba d'aya yareema jawad ya tafi duniar tunanin da bai san ma abinda yake tunanin ba. Ranka ya dad'e bala ya fada cike da ladabi, firgigit yareema jawad yyi ya d'ago kai ya kalli bala,na'am bala akwai matsala ne? a'a ranka ya dade ga abinci na kawo maka, ok ajiye bala ya fada bayan ya lumshe idonsa. Jiki bbu kwari bala ya ajiye abinci ya fita daga d'akin yana naxarin yarda yareema jawad ya shiga damuwa irin haka, ko mai ya same shi Allah masani. "A bangaren xaljamil kuwa tana gama shan coffee ta fad'a wanka, tsayawa kallon kyau da tsarin toilet d'in, gaskia dakin nan da toilet d'in nan sunyi masifar birgeta, dan a gidan su kad'ai xata iya bada labari. "Ta dad'e a bathtube sannan ta fito d'aure da karamin towel d kad'an ya rufe mata cinyoyinta, gashin kanta a jik'e alamar ta wanke shi,sai faman gogesa tak'eyi ranta duk a bace,duba d'adin tayi taga ba kayanta dan haka ta shiga rud'ani, ita ba sanin kan gidan tayi ba, nd batasan fita ta had'u da kowa,gashi ba'a sai mata layin nigeria ba ballantana ta kira mom. ido na xaro waje nace ok xaljamil dama bata janye k'udirinta ba? "Tunda ga dakin ta fara sand'a, a hnkl ta murd'a handle d'in kofar ta lek'a, OMG! Xaljamil ta fad'a a fili, ganin kyau da tsarin palour d'in ya birgeta, ga sanyin Ac da ya had'u da airfreshner, sosai xaljamil ta bud 'e kofar hanci ta tana shak' a. Da sauri ta tuna abinda ta fito yi dan haka a hankali ta fara k'arewa palour kallo, wani murmushi ta saki ganin trolley d'insu a chan gefe, cikin sand'a da kallon hanya xaljamil ta k'arasa gaban trolley d'in. " Duk abinda xaljamil ke yi mom na kallon ta ta window d'in d'akinta, sosai xaljamil ta bawa mom daria, hmmmm xaljamil kenan xakiyi ki gama. "A hankali xaljamil ta fara jan trolley d'inta tayi hanyar d'akinta,ji tayi an bankad'o curtain d'in palour, wani bugawa xuciar xaljamil tayi tana baraxanar fita daga kirjinta. Tsayawa chak tayi dan ta kasa d'aga k'afarta tayi. Batasan sanda hawaye ya fara fita a idon ta ba, shikenan yau ta shiga uku, ko wane irin mutun xata gani. "Aunty xaljamil! Nawal ta kirata, da gudu ta nufi xaljamil ta rungumeta ta baya, wata ajiyar xucia xaljamil ta sauke wanda sai da nawal taji, dan haka ta xagayo gaban xaljamil tana kallon fuskarta, OMG nawal ta fad'a aunty xaljamil waya saki kuka? Da sauri xaljamil ta fara goge hawayen fuskarta dan ta manta sun fito. Murmushi ta k'irkiro ta kama hannun nawal, bbu komai baby nawal xo muje cikin na shirya, ok my aunty. Xaljamil ta kama trolley d'inta ta shig'e da sauri dan kar tsautsayi yasa wani ya shigo. "Handdryer ta fara d'akkowa ta xura a socket ta fara busar da gashin kanta, nawal kam sai surutu take mata xaljamil na kwasar daria, a hankali taji kaunar nawal ta shiga ranta. "Bayan gashin ta ya bushe ta fito da mayukanta na shafa da gashi, sosai xaljamil ta gama da shafa ta kuma nufi trolley d'in ta dan chanja kaya, wata purple gown tasa wacce aka mata ratsi da yellow, abinka da farar fata sun bala'in karbar jikin xaljamil,ga rigar dai-dai ita bata mata yawa ba batayi kad'an ba. "Nawal sai yaba kyan da aunty d'in nata take, wallahi aunty xaljamil kinyi kyau, dama a kwai mata irinku a duniar nan nawal ta fad'a hannunta a kan bakinta irin mamakin nan takeyi. Kamo hannunta xaljamil tayi tana tunxira daria, chiiiiiiiiiiii gaskia baby nawal xamu cire bakin ki mu aje a gefe, ido nawal ta fito dashi, i'm sowi my aunty kinsan haka uncle jawad yake fad'a? Ji tayi gaban ta ya fad'i a xuciar ta ta mai-maita jawad, badai wanda mom d'inta ta bata labari ba? Gaba d'aya ta shiga tunani, indai shine ta nasan ganin sa, amma ya yake, bak'i ne ko fari, mai kyau ne ko mummuna, a hankali labarin mom ya dawo mata, yareema jawad kyakkyawan gaske ne, au my aunt na manta sarki mai murabus ynx yace mini xai taho duba ki, nasan ma yana hanya kinsan ya xama old man tafiar sai a hnkl. "What! Xaljamil ta fad'a da karfi wanda sai da nawal ta tsorata, kallon aunt d'in nata tayi, aunty xaljamil layin? Idonta ne ya kawo kwalla dan haka hankalin nawal ya kuma tashi, my aunty ki fad'a mini mana, xaljamil kam banda innalillahi wa'inna ilaihi rajiun bbu abinda take nanatawa a xuciar ta. Dabara ce ta fad'o mata dan haka tayi wa nawal rad'a a kunne, daria nawal tayi hhhhhh my aunt karki samu matsala. "Jin an fara murd'a handle d'in d'akin xaljamil yasa nawal da xaljamil suka kashewa juna ido, da gudu xaljamil ta haye gadonta ta runtse Idonta ta fara hawaye dan dama xaljamil hawayen banxama fita yake a Idonta ballantana na kare kai, nawal ce ta koma kusa da xaljamil data d'aura hannunta a kan cikin ta tana kiran, wayyo mom cikina! Mom cikina. "Kofar d'akin aka turo da karfi, sarki Abubakar ne mai murabus da matarsa fulani da itama d'aga so kafar ta tayi ta taho duba xaljamil. "Ganin xaljamil na juyi tana kiran cikinta yasa hankalinsu gaba daya ya tashi, harda mom dan batasan plan bane, innalillahi wa'inna ilaihi rajiun shine abinda sarki keta mai mai tawa, mom da fulani ma haka, sarki ne yyi karfin halin tambayar nawal, tun yaushe take haka? Ynx bbu dad'ewa ta fada tana jan majina. Sarki mai murabus ne ya kalli bafadan sa da suka xo tare kira mini yareema jawad, rissinar dakai yyi bani da ita ranka ya dad'e. Ok kira mini farouq maxa a waya da sauri ya kira mai martaba sarki farouq ya sanar dashi halin da ake ciki, cikin rawar murya farouq ya ansa bari na kira jawad d'in. "Wayar yareema jawad ce ta fara ringing, kamar baxai duba mai kiran ba sai kuma ya dauka wayar ya duba, mai martaba ya gani dan haka yyi saurin dagawa dan ta kusa yin missed call. "Hello! Yareema jawad ya fad'a cikin kasalalliyar murya, sannu jawad ashe dama baka koma ka sak'e duba jikin xaljamil ba, ynx baba ya kirani akan gata chan tana ciwon ciki, haba jawad mai ya sa kake haka, xaljamil ce fa, xaljamil d'in jawad amma naga kamar baka damu da ciwon nata ba. "Sunan da mai martaba ya fad'a yareema jawad ya maimata a hnkl, jawad d'in xaljamil, ji yyi tsigar jikinsa ya tashi, he is speechless dan haka, bari naje ya fad'a wa mai martaba, yawwa jawad nima gani nan. " Jiyay gaba d'aya hankalinsa ya tashi, a gurguje ya dauk'i first aid box ya chanja shigarsa xuwa blue jeans, labcourt d'insa ya xira ya fita da sauri. Ba wai wani sauri chan ba, amma a yarda yareema jawad ke taka k' asa kamar baya so na tabbar cewa sauri yake. SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P. M. L. W A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ NAGODE SOSAI DA ADDU'AR KU MY FANS ALLAH YA BAR XUMUNCI ❤💋 Chapter 15&16 "Da sallama ya shiga part d'in, ba kowa a palour dan haka direct d'akin xaljamil ya nufa, ganin yarda take juyi tana murk'ususu yareema jawad yaji hankalinsa ya tashi, da sauri ya k'arasa gaban ta ya fara bud'e first aid box, sarki mai mirabus da fulani da momy suka fita dan barin yareema jawad yyi aikinsa. "Nawal na gefen xaljamil tana ta mata sannu, xaljamil idonta a runtse yake tana hawaye. A hankali yareema jawad ya fara duba xaljamil, kallon ta yareema jawad yyi dan ya fara xargin ciwon cikin da xaljamil keyi na k'aryane kawai pretending ne.idan ran jawad yyi dubu sai da ya b'aci, dan haka ya tattara kayansa ya fice daga d'akin ransa a b'ace. Yana fita ya dan saisaita yanayin fuskarsa sannan ya karasa inda su sarki mai murabus suke xaune duk hankalin su a tashe, jawad ya ake ciki? Jiyayi gaba d'aya sun bashi tausayi, lallai yarinyar xata gane kurenta. Murmushin takaici jawad yyi eh na mata allurar bacci sai dai ku bari gobe kwaxo ku ganta. Shikenan yareema jawad Allah ya bata lpy, bai amsa ba yasa kai ya fice daga palour xuciarsa da bak'in cikin xaljamil. "Part d'insa ya nufa, yana shiga palour bala ya tashi da sauri ya karb'i first aid box d'in. Barka da xuwa ranka ya dad'e, yareema jawad bai kalli bala ba dan gaba d'aya ransa a b'ace yake, bedroom d'insa ya nufa yana takun k'asaitarsa. Bala na biye dashi a baya, suna shiga bala ya cirewa yareema jawad labcourt a ajiye a cikin wardrob. "Xama yareema jawad yyi a kan carpet tare da bawa Bala umarnin xuba masa abinci. Durkusa Bala yyi ya jawo tray d'in ya fara xuba masa,jellop spagetti wanda taji kayan lambu,sai farfeson kaxa, mixed fruit d'in da Bala yake had'a masa dan bayasan shan ko wane irin juice, xuba masa yyi ya ajiye, tashi yyi ya koma gefe. "Kamar bayaso haka ya dinga cin abincin, har ya kammala, Bala ya tattare wajen ya gyara komai.Pajamas bala ya dakkowa Yareema jawad ya ajiye a gefen bed ya masa sai da safe ya fita. Kayan ya saka ya haye luntsumeman gadonsa, yana runtse idonsa ya tuna alkawarin da yyi wa nawal na ice cream, tunawa yyi yana dashi a fridge dama saboda ita yake ajiyewa, nd kuma yana san kara ganin kyakkyawar fuskar xaljamil, duk da dai ta b'ata masa rai d'axu. "Tashi yyi ya cire pajamas d'in ya xira jallabiya, wayarsa ya dauka ya kira layin momy, bugu d'aya ta d'aga kiran, hello yareema jawad wallahi fushi nake dakai, wato ta xaljamil kawai kake ka manta momy ko? Murmushi yareema jawad yyi yana shafa sajen fuskarsa, i'm sorry momy na kinsan mara lapia na bukatar a bashi kulawa shine kawai amma kun kwanta ne? A'a dan dad d'in naka ma bai dawo ba yana chan wajen sarki farouq da mai martaba. Daria yareema jawad yyi cike da kasaita, eh lallai baxaki ganshi da wuri ba. Nawal ta tafi ne? A'a tace tare da xaljamil xata kwana dan fulani taxo duba xaljamil amma nawal taki binta, murmushi yareema jawad yyi eh lallai yarinyar nan wai menene manufarta ne? Momy gani nan. Ok sai kaxo. "Fridge ya bud'e ya ciro rubar ice cream guda biyu ya nufi part d'in su xaljamil, da sallama ya shiga palour, mom na xaune tana kallon labarai a aljaxeera, cike da fara'a ta amsa ya shigo ya xauna a gefen momy. Hira sosai sukeyi suna daria abin sha'awa. "Xaljamil da nawal xaune a bed suna hira, aunty xaljamil dan Allah ki tashi muyi pillow fight, haba nawal ki bari sai gobe mana, plx aunty ki tashi muyi, nawal ta bata fuska kamar xatayi kuka, karki mini kuka tashi muyi. "Yes, dats my aunty, tashi tashi suka dauki pillow suka fara guje guje a d'akin, daria suke sosai xuciar su cike da nishadi. "Yareema jawad ne ya kalli momy, mom ina su nawal? Tana d'akin xaljamil, ok bari naje na dubata,mikewa yyi ya nufi d'akin, tun kan ya bud'e d'akin yaji hayaniyar su, nawal ta biyo xaljamil da gudu ta nufi hanyar k'ofa yareema jawad ya murda handle d'in ya bud'e, da sauri xaljamil ta durk'ushe a wajen ta rike cikinta. Baki da hanci yareema jawad ya bud'e yana kallon xaljamil cike da mamakin wannan alamari,nawal kam da gudu ta nufo jawad ta rungume shi, I miss u sooooooo much uncle jawad, miss u 2 baby. "Ice cream d'in hannunsa ta karb'a yawwa uncle thanks, baice komai ba xaljamil kawai yake kallo, da yaga ta kasa d'aga kai ballantana ta tashi daga inda take. Juyawa yyi ya murda handle ya fita, still momy na xaune a palour, dan haka ya mata sai da safe ya fice. "Bedroom d'insa ya shiga ya chanja kaya ya haye gado, wayarsa ya jawo yana dubawa yaga missed call din " xahra" tsaki ya ja ya gyara kwanciyar sa yyi rigingine, tunani ne iri-iri ya addabi brain d'insa. Phone d'inshi ce ta fara ringing, dubawa yyi yaga "xahra" kamar baxai dauka ba sai da ta kusan katsewa sannan ya daga. Shiru yyi yana sauraronta, hello! Yareema jawad ykk? Tunda ka tafi baka nemeni ba, idan na kira baka d'agawa, sanin halinsa ba tanka mata xaiyi ba yasa ta cigaba da xancen ta, ya kakeso inyi da rayuwata, batun yau ba na fada maka ina sanka, wallahi yareema jawad I can't do without u, kuka ne yaci karfin ta, shiru tayi tana sheshekar kuka. Da kyar ya iya bud'e baki cike da ixxa, xahra xahradden, mai yasa kike san takura wa rayuwata? Mai yasa kike san abinda baxai taba sanki ba, baki da muhalli a xucia ta, bakya cikin type din matar dana keso na aure, so plx ki taimakeni ki fita a rayuwata, kinsan halina ai, tsaki yaja ya kashe wayar cike da takaicin xahra, gaskia matan ynx sun lalace, ace wai macece xatayi ta bibiyar namiji akan ya sota. Ajiyar xucia ya sauke ya lumshe idonsa ya kuma gyara kwanciyar sa ya lula duniar tunanin rayuwar sa a london. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P. M. L. W A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ I proud to dedicate dis page 2 u hyxarana halliru, thanks 4 love nd care, I really appreciate. Much love 😍💕💕💕💕💕 Chapter 17&18 LONDON "Yareemah jawad karatune ya kai shi london, ya karanci physiology ya kammala ya samu aiki a chan, aiki yake sosai and sunajin dadin aikin nasa dan yasan mai yake yi. "Haduwarsa da xahra xahradeen a london ne, watarana ya fita xaga gari kamar yarda ya saba duk week end, shi kadai yake tafia kasancewarsa bashi da friends a london, tun yana skul wasu da yawa ke san abota dashi Amma yaki basu dama,saboda ixxa irin ta yareema jawad da kuma rashin son hayaniya. Abinda ya rabashi da gidansu kenan baya san hayaniya. "Xaune yake a gefen wani beach yana shan drink, hankalinsa kwance yana cike da nishadi, sbd yana son kasancewa a irin wannan yanayin. "Hello! Yaji wata murya mai d'auke da kissa ta daki dodon kunnensa, kamar baxai juya ba , dan duk nishadin da yake tare dashi ya dauke in seconds. Ya koma yareema jawad dinsa na asali, ya hade girar sama da kasa, cike da gadara ya dago sexy eyes d'insa ya kalleta. Omg! Xahra ta fad'a tana wani gyara tsayuwa,gaskia guy diinnan ya hado, fari tayi mai da ido kasancewar ta yar dunia. "Riga body hug orange sai trouser purple, sai dan wani siririn veil data xagaye wuyanta dashi, kanta a bude yake, hakan ya bawa gashin kanta damar xuba gadon bayanta. Fara ce, mai matsakaicin tsaho, kyakkyawace ajin farko, banda maganar da tayi masa da hausa xai iya cewa kareena kapoor khan ce. "Please xan iya xama? Ta fad'a tana masa wani shu'umin murmushi , bai tanka mata ba ya cigaba da shan drink d'insa a gayen ce.ganin bashi da niyar mata magana yasa ta nemi waje ta xauna. "A hankali ta fara magana, sunana xahra xahradeen, mahaifina babban attajiri ne a k'asar nigeria, ni kadai ce yar'sa mahifiyata ta rasu ina karama, hakan yasa mahaifina ya kara daukan son dunia ya daura mini, ya kuma dauki nauyin kula dani duk da yawan ayyukan dake gabansa. A cikin family a kwai masu maganar xasu rikeni amma dad yaki yarda da hakan, sai kawai ya yanke shawarar kawo ni london yarda xan samu better life bbu mai takura. A time d'in na gama secondry dan haka university na fara a london, samari da yawa na kawo mini tayin soyayyayrsu amma duk basu mini ba cux mai aji nake nema irinka. Nan wajen xuwana ne, na tab'a ganin ka a nan na taho da sauri dan yi maka magana wayata tayi ringing, ganin precious dad ne yasa na kyaleka ka tafi da addu'ar Allah ya kara hadani da kai.duk daga ranar kullum sai naxo wajen nan ko xan ganka amma haka xan gaji na tafi , suddenly kawai na hangoka dan haka Ban tsaya bata lokaci ba na taho gareka, akan ka amince da soyayya ta gareka, hakane xaisa xucia ta ta xauna cikin kwanciyar hankali. "Sosai ya d'ago ido ya kalleta up nd down, tsaki yaja a ransa yace "mace har mace amma bbu aji, wai a haka take neman mai aji irin yareema jawad ya so ta, tabbas ta had'o amma bata dace da irin matar da yake bukatar ya aura ba. " Mikewa yyi tsaye tare da ajiye tin d'in drink dake hannunsa, wayoyinsa ya kwasa da mukullin mota ya xuba a aljihu, hannu daya ya xuba a aljihu ya fara tafia. Mikewa tayi itama "please ka taimaka mini ta fada tana matso hawaye,wallahi ina sanka" . Tsayawa yyi chak dan ya tsani wannan kalmar ta fito daga bakin xahra, d'ago wa yyi ya kalleta da sexy eyes d'insa da suka kara rud'a xahra, cikin husky voice d'insa ya firta"ni kuma bana sanki "kamar mai ciwon baki. " Juyawa yyi ya cigaba da tafia cike da k'asaita, da gudu xahra ta bi bayansa, "dan Allah ko sunan ka ka sanar dani" "jawad "ya fad'a a hankali ya nufi motarsa.Badan ran xahra yaso ba ta hakura ta kyale jawad, tana tsaye har ya tashi mota ya bar wajen,ajiyar xucia ta sauke, tayi wani murmushi tana lumshe ido, a hankali ta firta jawad, wow nice name, sunan yyi kama da sauki mai shi. "Yareemah jawad da takaicin xahra yaje gida, yana shiga ya baje a palour yana dan hutawa, wayarsa ta fara ringing yana dubawa yaga mai marta ba, cik'e da ladabi ya d'aga ya gaida mahaifin nasa,sannan yyi shiru yana sauraronsa. "Yareemah jawad lokaci yyi daya kamata ka dawo gida, na xuba maka ido dan ganin hankalinka amma naga baka san xuru ba, to ynx na fad'a maka k'asar ka tafi bukatar ka akan london, kwara kaxo ka bautawa k'asar ka ka samu lada, fatan ka fahinci abinda nake nufi "gyada kai yareema yyi kamar a gabansa yake," dan haka na baka xuwa one week ka ajiye aikin london ka dawo nigeria. "To mai martaba, insha Allah xan taho a lokacin da kace" "Shikenan yareema jawad Allah ya maka albarka "ameen ya amsa, sallama sukayi ya kashe wayar. " Jingina yareema jawad yyi da jikin 1cter d'in daya ke xaune ya lumshe ido, yana jin dad'in xaman k'asar amma kuma ya xama dole ya barta tunda mai martaba baya so. "Yareemah jawad mutun ne daya san darajar iyayensa, baya iya tsallake maganar su. Tagumi yyi hannu bibbiyu na rashin sanin ta ina xai fara. "Ganin baxai iya tunanin komai ba a tym din yasa na nufi bedroom yyi wanka ya shirya cikin pajamas ya haye bed hade da du'a ya ja blanket ya kwanta da tunani kala kala. Sunday "Kamar ko yaushe misalin karfe 5:00pm ya bar harabar gidansa, ya nufi beach, xaune yake a inda ya saba xama yana cike da nishadi a ransa. Sanye yake da blue tshirt mai karamin hannu sai trouser red, sun glass ya saka da ya kara k'awata kyansa, sumar kansa a kwace luf ya mata style mai kyau sai kyalli take, wrist d'insa d'aure da watch mai bala'in tsada,jikinsa sai tashin k'amshi yake na turaruka masu tsada daya fesa. "Idonsa a lumshe yake yana shan drink, jiyay daga chan nesa an kwala masa kira, a fusace ya waiwaya dan ganin mai wannan ikon, xahra xahradeen ya fad'a a ransa, harga Allah ya manta da ita, ballantana labarinta,. Da gudu ta karaso kusa dashi tayiwa kanta maxauni. "Cikin fara'a ta mika masa hannu su gaisa, amma me? Ko kallon inda take yareema jawad bai kalla ba, marairaice murya tayi ta wani langwabar da kai tana masa shu'umin kallo, plx jawad mu gaisa mana. Yi yyi kamar bai jita ba ya cigaba da shan drink d'insa.wayarsa ce tayi ringing yana dubawa yaga fulani ce, wato "ummi" kayataccen murmushi ya saki wanda yasa xahra murxa idonta ko ba gaskia ta gani ba. A xucia ta fara magana, "dama guy d'innan yana murmushi? To ko dai buduwarsa ce? Turkashi, nan da nan taji wani kishi ya lullubeta kirjinta ya fara bigawa da karfi. Daga wa yyi suka fara gaisawa, daga yarda yake wayar ta gane ba buduwa bace maman shi ce, hhhhh! Kaji xahra da shishigi, ke da bama a tataki amma harda su kishi. "I donta akan lips d'in yareema jawad, yarda yake magana gaba daya ya tafi da ita, ganin yarda yareema jawad ya shagwabe fuska sai abin ma yaso ya bawa xahra daria, ya xa'ai wannan guy d'in da ya kamata yyi aure da ya'ya amma ya ke shagwaba. Amsar daya baya ita ta dawo da xahra daga tunanin da takeyi, "eh ummi mai martaba yace nan da 1 week na dawo nigeria" kai alhmdlh wallahi naji dadi, dama yaushe rabon naga yareema nah, wajen shekara daya kenan fa"murmushi yareema yyi wallahi ummi na nima ina kewarki, kawai yanayin aiki nane sai a hankali, amma komai yaxo k'arrshe tunda monday xanje nayi reporting, kinga kafin friday na gama komai saturday sai na biyo jirgi. "Murmushin jin dadi ummi tayi, to yareema Allah ya kawoka lpy, ameen ummi ya fada yana murmishi. Sun fi 30 mints suna waya da ummin sa ,cike da so da kauna na uwa da d'a. Waowayowar da xaiyi ya hada ido da xahra data kafe shi da idanunta, take annurin fuskarsa ya dauke dan ya manta da wata xahra a xaune. Take ya koma yareema jawad d'in da tssani yyi kicin kicin ya bata rai. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P. M. L. W A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ I proud to dedicate dis page 2 u guys, pure moment of life writers, tunda nake ban tab'a ganin group masu san juna da had'in kai irin sa ba, Allah y karama soyayyar juna ya d'aurar da xumuncin mu har abada. Ilysm 💞💞💞💞💞much love sisters. Aisha Ali garkuwa, u are like mtn line now, every where u go😂😂karki damu sis daukaka ce Allah ya miki ya kuma bayyana miki makiyanki a fili, namiji baya kadan ynx aka fara sambado mana shi, ki cigaba da gashi sis muna jin dadin novel😍😍😘😘 Chapter 19&20 "Ajiye phone d'in sa yyi a kan table d'in gabansa, yana duba watch d'in dake d'aure a wrist d'insa, watch ne mai tsada wanda ba'a ko wane hannu ake ganinsa ba sai a wajen su yareema jawad. Bai ankara ba yaji ta kawo hannu ta d'auki phone d'insa mai tsadar gaske iPhone 8, yana kallonta ta gefen ido yyi kamar bai ganta ba. "Operating wayar ta fara yi cikin kwarewa, ta shiga nan ta shiga chan tana ta masa bincike, number d'in ta ta saka a cikin phone d'in yareema jawad tayi dialing sim d'inta ya shiga, saving tayi masa a number d'in "Zahra" murmushin nasara tayi, "ai tunda na samu number d'inka, to xaka sha naci yareema jawad" sai ka xama mallakina, sai na aureka, tunda ina sanka ya xama dole kaima ka so ni "tunda nake a rayuwata ban tab'a neman abu na rasa ba kuma baxan fara akanka ba. " Bata mayar masa da phone d'in ba ta cigaba da operating, gallery ta shiga, pictures d'insa ta fara gani, sanye yake da kayan sarauta, kansa sa rawani, daria yake a pic d'in, wanda ya bayyanar da kyawun yareema jawad. Wani murmushi Zahra keyi,"dama guy d'in nan jinin sarauta ne? No wonder ashe abinda ke dawainiya da shi kenan"ji tayi ya kara shiga ranta, a dunia "Zahra" nasan sarauta sai dai Allah bai basu ba. Lallai da suna da mulki da anga ixxa, Idan ta auri yareema jawad ta xama gimbiya kenan, aiko xata shinfida mulki da ko sarkin albarka. Ido na xare ina kallon Zahra dan duk burina na auren yareema jawad ta fini"lol" "Watch d'in hannunsa ya kalla, 6:30pm amma bata bashi wayarsa ba, gashi tym d'in tafiarsa gida yyi, gashi kasaitarsa ta hanashi ko kallonta ballantana ya mata maganar phone d'inshi. "Zahra ta lura da hakan dan haka ta cigaba da danne-dannenta a phone d'in, watch d'in ya kuma dubawa 6:45pm mikewa yyi ba tare da ya kalli Inda Zahra take ba ya fara tafiarsa cike da k'asaita irin tasu ta ya'yan sarakuna, tafiarsa yake hankali kwance ya nufi motarsa. "Tashi tayi da gudun tatabi bayansa, please jawad ga phone d'inka, ko kallo bata ishe shi ba ya karasa jikin motarsa. Budewa yyi ya shiga xaija kofar motar ta tare da hannunta, kunnenta ta kama tana masa wani shu'umin murmushi,"kayi hakuri jawad baxan kara ba, banxa yyi da ita ya fara yiwa motarsa key, ganin yaki karba kawai tayi sauri ta xura masa a aljihun gaban rigarsa, da karfi yaja murfin motor ya bar wajen. "A tsaye ya barta cike da mamakin girman kai irin na jawad, wato dayace ta bashi phone gwara ya tafi yabar mata phone d'in a nan. "lallai ina da aiki babba a gabana". "Gudu yake tamkar shi kadai ne a road d'in, har ya karasa gida. A fusace ya shige gidan cike da takaicin abinda Zahra Zahraden ta masa. " Lallai Zahra xata gane kuranta, ta sansa amma batasan halinsa ba, amma xai ganar da ita Idan bata fita a harkarsa ba, tunda yake bbu macen da ta tab'a gigin tab'a masa waya sai yau, dole ya bar London ko dan saboda tsinanniyar yarinyar nan, saboda Idan ta cigaba da bibiyarsa to kwa lallai da ita da baban nata da take takama dashi xaiyi maganin su. Tsaki yaja ya nufi bedroom d'insa dan yin wanka, saboda xufar data tsatsafo masa, bayan ya fito ya shirya tsaf kamar yarda ya saba. "Kitchen ya nufa ya hada coffee, parlour ya dawo ya xauna ya kunna TV yana kallon news a aljazeera, bayan ya gama shan coffee ya tashi ya rufe ko ina yyi switching TV da Ac ya nufi bedroom d'insa. Light ya kashe ya rage Ac ya haye bed d'insa, blanket yaja ya rufe har kirjinsa, addu'oin kwanciya bacci yyi wanda suka xo a hisnul Muslim ya shafe jikinsa, bbu dadewa bacci ya d'auke shi. "Da asuba alarm d'in dake kan bedside ya fara k'ara, ya saita ne cux ba Kiran sallah xaiji ba. "Tashi yyi ya kashe alarm d'in yyi addu'ar tashi daga bacci ya nufi toilet. Alwala da wanka yyi ya fito daure da towel a waist d'insa, da small towel yana goge sumar kansa daya jik'e. A gurguje ya shafa mai ya xira jallabiya dan kar tym d'in salat d'in ya wuce, prayer mat ya shinfida ya tada sallah, bayan ya idar yyi addu'oin kamar yarda ya saba ya shafa. System d'in shi ya dakko ya fara aikin office dan baxai koma bacci ba, ranar Monday ne akwai aiki. Bayan ya gama ya nufi kitchen dan hada break fast, yareema jawad expert ne a wajen girki, tunda yaxo London da kansa yake girki, kasancewarsa mutun mai kyankyami. Ba wani abu mai wuya yyi ba Irish and egg ya soya sai tea da yyi boiling d'in shi a kettle in minutes ya kammala, bayan ya gama ya jera a dining ya duba wall watch, 7:00am ya gani dan haka a gurguje ya nufi toilet ya sake wanka yyi shirin office. "Sanye yake da English wears kamar yarda ya saba, t-shirt ce yellow mai karamin hannu, sai trouser pencil black wrist d'insa daure da black watch, yyi kyau sosai ya nufi dining. SUMYNBASH CE 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P. M. L. W A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 21&22 "Xama yyi ya fara breakfast hankali kwance, wayarsa ce ta fara ringing, d'auka yyi ya duba mai Kiran, Peter ne abokin aikinsa, shima doctor ne. Daga wa yareema jawad yyi yayi shiru yana sauraran peter. cikin rawar murya jawad "jawad where are u? Please we need to see u in hospital now" a rikice jawad ya tambayi Peter, "what's happening Peter? Cikin sark'ewar harshe Peter ya fara magana" we have a patient pregnant women, please jawad is an emergency operation need to see u "a rikice yareema jawad ya ajiye cup d'in tea dake hannunsa, parlour ya nufa ya d'auki laptop bag dinsa ya rataya a kafad'a ya dau hanya, gudu yake sosai har ya karasa gate d'in hospital, horn yake ba tsayawa har ya firgita gate man, da gudu shima ya taso ya bude gate d'in. Motar ya fixga ya shige surrounding d'in hospital, waje ya samu yyi parking car d'in ya d'auki laptop bag dinsa yyi cikin da sauri. Office ya nufa ya ajiye laptop bag ya d'auki lab court ya saka, yana fita da sauri suka ci karo da peter, tsorata yyi da ganin yareema jawad a hospital kuma a shirye, kallonsa yareema jawad yyi "ina patient d'in?" jawad ya katsewa peter tunani. Duk wani singing da xa'ayi an gama dan haka yana shiga hand clove yasa a hannunsa ya fara operation d'in, bai d'au wani long time ba yayi nasarar cire baby girl a cikin matar. "Yana fita ya tarar da mijin matar tsaye a kofar theater room d'in, da sauri yabi bayan yareema jawad yana tamayarsa a wane hali matarsa ke ciki,labari ya bashi matarsa ta haihu kuma baby girl, yyi gaba, ya bar mutun da rawa. Office dinsa ya nufa ya huta kafin yaje wajen director ya sanar masa tafiarsa Nigeria. "Da kyar director ya yarda da tafiar jawad, dan yace ya sanar dasu ko salary d'in da suke basa ne yyi kad'an ya sanar dasu ko nawa yakeso xasu bashi, a hankali ya warware musu abinda ke faruwa, shima ba asan ransa bane tafiar. Sunyi ciwon rai dan samun doctor kamar jawad abu ne mai wuya. "Bbu matsala doctor jawad amma ko ya koma yyi kokari ya dinga xuwa, ya amince da hakan ya kuma ji dadin yarda suka nuna masa kauna, "Xaune yake a office d'in sa yana duba wani file, wayarsa ce tayi ringing, mai martaba ya gani dan haka da ladabi ya daga, sun gaisa nan yake masa tuni cewa yau Friday gobe ne ranar daya kamata ka dawo, "eh mai martaba insha Allah goben xan taho" to shi kenan Allah ya maka albarka "ameen yareema jawad ya amsa. " A ranar Friday karfe 8:00pm aka hada dinner saboda tafiar yareema jawad, suna so su karramashi, duk doctors d'in hospital d'in sun hallara a wani babban waje da ake ji dashi a London, yareema jawad yyi farin ciki da hakan. "Karfe 8:00pm yareema jawad ya bayyana a wajen, yyi masifar kyau, suit ce a jikinsa black, sai red longslip, black necktie ya saka, fuskarsa dauke da farin glass wanda ya karawa shigar sa kyau,wani daddad'an k'amshi ke tashi a jikinsa. Da takunsa na k'asaita ya karasa kan high table da aka tanadar masa, nan waje ya kaure sa tafi, raf-raf-raf, cikin farin ciki ya daga kai yana karewa mutanen dasukazo wajen, waxai gani, Zahra zahradden ya maimaita a xuciarsa. Sanye take da wani mini skirt orange,sai karamar riga mara hannu, ta saki gashin kanta a gadon bayanta, xaune take a cinyar wani bature sai wani shafa fuskarsa take tana wani narkewa a jikinsa, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shine abinda ya nana ta a xuciarsa. A hankali yaji kuncin da yakeji ya bar xuciarsa. Neman yareema jawad akai akan yyi jawabin godia da kuma sallama ga friends dinsa,tashi yyi ya karbi loudspeaker ya fara bayani, dum Zahra taji xuciarta ta buga jin murya yareema jawad, a hankali ta juyo da kanta tana kallon mai magana, shi ne ta fada a ranta, gaba daya ta tsure, Dan tabbas tasan ya ganta, tashi take kokarin yi daga cinyar baturen amma yaki barinta, haushi ne ya kamata ta fara kunkuni, "ynx Idan yareema jawad bai ganni ba wannan sai ya tuna mini asiri" duk abinda take jawad na kallonta yana murmushin mugunta. Da kyar ta samu ya cikata bayan ta masa rad'a a kunne akan tana da uxuri ne, tana tashi ta nufi high table Inda yareema jawad ke bayani, tana wani kwarkwasa da karairaya. Tunda ta tunkaro shi ya xuba mata ido yana kallonta cike da kyama, sai yatsina fuska yakeyi. Gaba daya Zahra tasha jinin jikinta da kallon da jawad ke mata, duba jikinta ta fara yi ko a kwai matsalar daya hango,a haka ta daure ta karasa kusa dashi, bude baki tayi xatayi magana yareema jawad ya tushe hanci yana kakarin amai, security ya fara kira yana nuna Zahra da hannunsa hancinsa da bakinsa a tushe, da sauri kam suka bayyana a wajen suka d'auki Zahra chak suka nufi waje da ita. Baturen da sukaxo yana gani ya basar dan a tunainsa ganin jawad yasa ta rabu dashi, ga kuma irin wulakancin daya mata dan haka ya nuna kamar bai Santa ba.wani murmushi yareema jawad yyi bayan mutanen wajen sun kewaye shi suna masa sannu. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P. M. L. W A romantic love story 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 23&24 "A hankali yake amsa musu bayan ya gama kakarin nasa, d'aya bayan d'aya suka dinga tashi suna masa sannu. Xuciar yareema jawad fal farinciki dan yasan yyi wa Zahra abinda har ta mutu baxata manta dashi ba. "Zahra security na fita da ita suka direta a gate d'in wajen suka yanka mata warning akan kar suga ta dawo cikin wajen,durkusa wa tayi a wajen ta fashe da wani kukan bakin ciki," lallai yau ta tabbatar yareema jawad baya santa, amma duk da haka baxata rabu dashi ba sai ta mallaki zuciarsa" Xama tayi a wajen tana jiran fitowar yareema jawad, dan tanaso suyi sallama dan taji yace gobe xai wuce a bayaninsa, Allah sarki Zahra. "Sai 11:35pm aka tashi a dinner party d'in, bayan an bawa yareema jawad award da kyaututuka aka fara watsewa. Cikin tafiarsa ta k'asaita yake takawa shida Peter suna tafe suna hira, Peter yana bayyana jimaminsa na tafiar jawad, a hankali ya karasa jikin motarsa, kokarin budewa yake yaji an kama kafarsa, wani tsalle yareema jawad yyi yana kallon k'asa wani tsaki yaja na bacin rai ganin Zahra zahradden ce, tabbas banda shi d'in namiji ne to da bbu abinda xai hanasa ihu a wanna lokacin. "Kuka take shabe shabe still hannunta a kafarsa, "please jawad ka taimakeni ka yarda da soyayya ta, ynx abinda ka mini daxu ka kyauta?? Ka tuxartani a cikin mutane, mai nayi maka?" ta cigaba da kuka. Wayyo yareema jawad jiyay kamar yasa k'afa ya hambare ta, wani k'ululun bakin ciki ne ya tukare masa xucia, wannan kalmar ta ina sanka data fita a bakin Zahra ta tafarfasa shi. " Kallon ta yyi da sexy eyes d'in sa wanda sun koma ja dan tsabar bacin rai,wata iska mai xafi ya fitar daga bakinsa cikin husky voice ya fara magana "to hell with you Zahra, wallahi na tsane ki na tsani halinki, baxan taba soyayya dake ba dan bakya cikin type d'in matan da nake bukata nayi rayuwar aure da su ba, ba mu dace da juna ba, ina miki nasiha ki rabu dani tun muna mu biyu" "Mik'ewa tsaye tayi ta kama k'ugu cik'e da fitsara ta kalli yareema jawad, "wallahi sai ka aure ni kuma sai ka so ni, ban taba neman abu na rasa ba, kuma baxan fara a kanka ba, ina sanka ya xama dole kaima ka so ni, kuma nima nigeria d'in xan taho, muyi ta achan mu k'are,I ayi auren mu mu xauna a chan ko jawad" ta masa dab dashi tana masa wani kallo. "Mamaki ko al'ajabi xaiyi a maganar Zahra, tabbas yana ganin brain d'in yarinyar ya fara samun problem, bai tanka mata ba dan bashi da lokacin ta. Peter na tsaye a wajen kamar an dasa shi yana kallon yarda xa'ayi so dole, yasan wahalar da kanta kawai take dan yareema jawad ba sauraran ta xaiyi ba, ya sha gayyatarsa club dan su shana da yan mata amma yareema jawad yaki bashi dama, Peter har ya fara xargin ko yareema bashi da lapia ne?. "Bude motarsa yyi ya shige, da sauri Zahra ta matso ta kuma fashewa da kuka, Dan Allah karka tafi, inasan ka sanar dani kana sona please, cikin xafin nama yaja motarsa ya bar wajen dan ko sallama baiyiwa Peter ba. "Zahra kam durkushewa tayi a wajen ta cigaba da kukanta, Peter ma motarsa ya nufa y bar wajen. "Sai da tayi mai isarta sannan ta Mike ta shiga nata motar ta bar wajen. "Hawayen bakin ciki yareema jawad ke xubar wa, Zahra taci masa mutunci da baxai barta ba, "sai ya wulakanta ta, duk dunia ta rasa wanda ya mata sai shi"tsaki yaja ya daki steering motar da hannu biyu yana jin zuciarsa na kunci da d'aci. Yana isa gida ya fara hada kayansa a daren da sassafe ya nufi airport sai nigeria, Dan yana ganin xai samu sassauci a chan. "Tsaki yaja dan ransa yaji yakuma baci lokacin daya dawo daga duniar tunaninsa, da kyar bacci barawo ya sace yareema jawad a wannan daren. "Kiran sallar asuba ne ya tashi yareema jawad, wanda xai iya cewa a d'akinsa aka saka speaker d'in dan k'arar da yaji, a hankali ya bude ido yayi addua sannan ya shiga toilet, kamar yarda ya saba sai da yyi wanka sannan yyi alwala ya fito, a gurguje ya xira jallabiya dan yaji masjid suna neman su tada sallah, yana fita ya tarar da bala na jiran fitowarsa, durkusa bala yyi yana gaida yareema jawad, lpy yace ya d'auki hanyar fita bala na binsa a baya. Suna xuwa ana tayarwa dan haka suka shiga sahu. Bayan an idar ya fita daga masjid ya tarar d sarki mai murabus (grand fa) d'in sa a kofar masjid d'in. Charaf yyi ya rike hannun yareema jawad yana murmushi," xonan d'an nema, muje ka duba mini jikata"yareema jawad ne ya harare sa," kai dai tsohon nan rikicin tsofan ka ya isheni, naga alama ma akaina yake k'arewa, to baxani ba cika mini hannuna ". " Sarki abubakar chanja rik'on da yyi wa yareema jawad yyi daga sakwasakwa xuwa da karfi, tuni xafin rik'on ya xagaye ilahirin jikin jawad, wata k'ara ya saki da bai masan yyi ba dan axaba, hhhhh yaji hannun maxan jiya. Da kyar yareema jawad ya tattaro jarumtarsa ya kalli grandfa ya wani b'ata rai kamar gaske , "kai tsohon nan bari mana, so kake ka karyani?" daria sarki abubakar yyi "ai Idan kaga na sakeka munje ka duba mini jikata" to xani"yareema jawad ya fad'a yana wani bata rai. Daria sarki abubakar yyi ya kalli jawad "akace bakaji" banxa yareema jawad ya masa suka d'auki hanyar gidan farouq a lokacin gari ya waye. "Bala ne yyi knocking, farouq ne ya bud'e dan bai dad'e da shigowa gidan ba shima, ganin mahaifinsa yasa ya durkusa k'asa ya dunkule hannu yana gaida sarki, murmushi sarki abubakar yyi "tashi farouq" tashi yyi ya basu hanya suka shiga. A parlour suka xauna bala na tsaye a gefe, xamewa yareema jawad yyi daga kujerar ya gaida yayan mahaifinsa, cikin sakin fuska farouq ya amsa masa cike da kulawa. "Momy xaune a bedroom ta jiyo muryar mai martaba, dan haka ta sako hijab d'in ta dan kwasar gaisuwa, bayan ta gaida shi sarki abubakar y kuma sa musu albarka. Nan ya tambayi jikin xaljamil sukace da sauki. Sarki abubakar ne y kalli jawad da yake ta cika yana batsewa"wannan ja'iriin yaron na sako a gaba ya duba mini jikata"daria sukai gaba daya banda jawad daya makawa grandfa harrara. "Farouq ne ya kalli mom"ta tashi ne? "eh ta tashi ita da nawal" ok jawad ka fara shiga kafin mai martaba ya tashi shima y shigo. Tashi jawad yyi ya kuma makawa mai martaba harrara gaba daya suka sa daria, "xan kamaka ne jawad a hannuna xaka maimaita" daria yyi ya shige ciki. "Xaune take a kan prayer mat, hannunta d'auke da alqur'ani mai girma tana karatun ta a bayyane, suratu yusuf take karantawa, murda handle d'in yyi yaji ana karatu, baiyi tunanin kunnensa gaskia ya fada masa ba sai da ya bude kofar dakin ya shiga, chak y tsaya ganin ta sanye cikin pink hijab mai hannu, daddad'an muryar ta da yarda take fitar da harufan had'e da tajweed ya birgeshi, ji yyi inama su dawwama yana jin wannan daddad'an karatun nata mai sanya nutsuwa, ji tayi kamar ana kallonta dan haka ta daga ido ta kalli kofa, idonsu sune ya had'e wani irin shock yaji aa jikinsa ganin idon xaljamil, ita kuma da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, dan wani nauyi da kunyarsa take ji ganin daya mata suna pillow fight d nawal alhali tace cikin ta ciwo. "Yareema jawad ya lura da yanayinta na kunyar da takeji dan haka dan ya kara bata wata kunyar ya xuba mata ido yana kallonta, a hankali taji voice d'in sa ya daki kunnenta, "mai ciwon ciki y jiki? Fatan ya daina ciwon?" wayyo xaljamil ji tayi kamar k'asa ta tsage t shige ciki don kunya, ita kam duk rashin kunyarta ai baxata ansa masa ba. Nawal ce t fito daga toilet, da gudu ta nufi jawad, hannayensa ya bude ya dagata sama, kamar wata baby,kiss ya mata a baki had'e da shafa gashin kanta, "I missed u soo much uncle jawad" missed u 2 baby nawal. Hugging d'in sa ta kara yi,xaljamil na kallon su sai taji sun birgeta inama gaba daya yan gidan kamarsu daya da wadan nan kyawawan da taji dadi , sosai ta shagala da kallonsu tana murmushi har beauty point dinta ya lutsa, yareema jawad na kallonta dan shima nashi hankalin na kanta. "Xaljamil ji tayi an turo kofar dakin da muryar da taji ance grandfa din ta ne, da idonta ta rufe ruf tayi k'asa da kanta, gaba d'aya jikinta ya d'auki bari kamar maxari, kallonta yareema jawad keyi da mamaki da kuma San sanin damuwar xaljamil, "Wato jawad a wajen nawal ka shiririce baka duba mini jikata ba, da turanci grandfa ke magana dan an fada masa xaljamil bata jin hausa, jin tturancin tayi wani iri dan haka batasan lokacin d ata bude idonta ba tana San ganin tsohon, duk da ta gane mai yake nufi amma turancin nasa na yan da ne. Idonta tar akan tsohon, kamar su daya da dadyn ta farouq, shima fari ne amma dad ya fishi fari tana tunanin tsofane da ranar nigeria ta maida shi haka,duk abinda take yareema jawad na kallonta,mamaki duk ya ishesa, ji tayi soyayyar grandfa ta shiga ranta ganin yarda ya damu da ita, tausayinsa ne ya kamata yarda ta dinga pretending bata da lapia duk hankalin sa ya tashi, tabbas da tasan haka yake da bata wahalar dashi ba. "Sarki abubakar ne ya kalleta, ganin tana daria, murmushin jin dadi yyi yana kallonta, kamarsu daya da farouq sai dai ta debo momy ta wani wajen, "masha Allah jiki yyi sauki xaljamil" murmushi tayi ta daga kanta alamar yea, hannunsa ya bude alamar taje ya rungumeta, a nitse ta tashi ta ajiye alqur'anin hannunta ta nufi grandfa, tana murmushi, Hugging d'inta yyi sai ga hawaye a fuskar sarki mai murabus. Nawal da jawad na tsaye suna kallon su, mom da dad suka shigo d'akin suma, sukaga xaljamil rungume a jikin sarki abubakar, dad'i ne ya kamasu suma mom harda hawaye. "Allahu akbar ashe xan ji dumin jikata a jikina kafin na bar dunia, Allah ya raya ki xaljamil ya baki miji na gari " ameen suka amsa harda nawal. SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 Pure moment of life writers p. m. l. w A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Alhamdulillah I'm back, fatan munyi axumi lpy, ina wa dukkan musulmai barka da sallah, fatan anyi lpy, and sai naxo karb'ar happy sallah na😁 Chapter 27&28 A fusace yareema jawad ya nufi part d'insa, banda tafasa bbu abinda xuciarsa keyi, banka k'ofar shiga part d'insa yyi da k'arfi, bala dake xaune yana kallo ya mik'e a firgice yana duba hanya, ganin yareema jawad a fusace yasa ya tattaro nutsuwarsa yabi shi da idanu, jawad kam baibi takan bala ba ya nufi bedroom. Jikin bala yyi sanyi dan yasan ba k'aramin abune ke tafarfasa ran yareema jawad ba, bai kammala tunanin abinda ya samu jawad ba yaji an sake banko k'ofar, da sauri bala ya juya dan ganin mai shigowa, areef ne fuskarsa d'auke da murmushi, wajen bala ya nufa "ina sarkin rigimar yake?" nuni bala ya masa da hannu xuwa d'akin jawad, dan haka da sauri ya nufi d'akin. "A tsaye ya taradda yareema jawad, sai safa da marwa yake, bak'in ciki da takaicin zaljameel ya masa katutu a xuciya, tunanin yarda xai ladaftar da ita yakeyi, dole sai ya ganar da ita ynx ba a Qatar take ba a Nigeria take, baisan da shigowar areef ba sai jiyay ya dafa kafad'arsa, yasan waye dan haka yak'i juyowa, wani bak'i yaji xuciarsa tayi ganin areef, duk shi ya jaxa masa wannan b'acin ran, da bai ce xaije duba zaljameel ba ai da haka bata faru ba. "Haba yareema jawad dan sarki guda d'aya tilo, yareema mai jiran gadon mulki, "cikin lion voice jawad ya bugawa areef wata tsawa," is ok areef, please leave me alone, mai kake buk'ata kuma bayan jawowa dakai aka b'atan rai"harara ya kuma makawa areef sannan ya xauna a gefen bed d'insa, dafe kansa yyi dan jiyay yana sara masa, bayasan b'acin rai shiyasa baya shiga sabgar kowa. Murmushi areef yyi ganin yarda yareema jawad yad'au xafi, dan haka ya yanke shawarar tafia ya bashi waje ko ya samu sanyin xucia. "Natafi jawad sai gobe"areef ya fad'a bayan ya nufi k'ofa, jawad bai d'aga kansa ba ballantana areef yasa rai xai tanka masa, fita yyi yaja k'ofa. Bala na tsaye bakin k'ofa yakasa shiga d'akin, ganin areef ya fito yasa shi gyara tsayuwa, yallabai mai ya samu uban d'akina, murmushi areef yyi, "kasan jawad d'an rigima ne sai da lallaba, so shida zaljameel ne yarinyar uncle aliyu," nan areef ya kwashe labarin abinda ya faru ya fad'a ma bala, ajiyar xucia bala ya sauke "na gode yallabai, ynx ina xakaje?" gida"areef ya fad'a yana tafia,"ka gaida gida yallabai "ok bala nagode". "Da sallama bala ya shiga d'akin, yareema jawad bai amsa masa ba dan haka ya nufi toilet dan had'a masa ruwan wanka, bayan ya kammala ya sanar dashi,still yareema jawad bai amsa masa ba dan bayasan magana mikewa ya yi ya nufi bathroom d'in. As usual Bala ya d'aukowa yareema jawad kayansa ya ajiye gefen bed ya nufi kitchen dan had'o abinci. " Yareema jawad, shirye yake cikin English wears, blue jeans and orange shirt, kansa d'auke da P cap ya bala'in yin kyau, watch d'in dake d'aure a wrist d'insa ya duba, bedside ya nufa ya d'auki phone d'insa da key d'in mota ya nufi parlour, cin karo sukayi da Bala hannunsa d'auke da tray, murmushi Bala ya k'irk'iro "yallabai ga abincin" a yatsine jawad ya kalli tray d'in a hankali ya furta" bana ci Bala"yayi gaba abinsa, Bala kam binsa yyi da ido har ya fita daga parlour d'in. Fulani maryam ma kam ta tsorata amma ta basar, sosai hankalinta ya karkata ga jawad dan fitar da yayi tasan ya fusata ne, sai dai tasan tunda areef yabi bayansa komai xanxo da sauk'i. Zaljameel kam jitayi kunya ta kamata, cikin ladabi ta durk'usa har k'asa ta gaida Fulani maryam, da fara'a ta amsa mata ta kuma tambayeta jiki, zaljameel jitayi xaman parlour ya isheta dan haka ta nufi bedroom d'inta, sosai ta shiga dana sanin ihun da tayi duk kuwa da cewa ba tana sane bane tsorata tayi, fitar yareema jawad a fusace ta shiga tunawa, omg tasan ihun ne ya b'ata masa rai. Kwanciya tayi a bed d'inta tana kallon ceiling, a hankali bacci yyi awon gaba da ita duk da uwar yunwar da takeji sai taji ta koshi. Mom da Ammi xaune a parlour suna hirar yaushe gamo, amma hankalin Ammi ya karkata ga jawad, tasan sa da mugun xucia, tasan yana chan yana fushi, a daddafe suka kammala hirar Fulani ta nufi part d'inta da kuyangunta. Aikawa tayi a kira Mata jawad, dan aiken ya dawo da bayanin jawad bayanan, hankalinta ya kuma tashi dan haka ta d'auki phone d'inta ta fara neman layinsa, wayar ya shiga sai dai baiyi picking ba hakane ya k'ara tashin hankalin fulani. Yareema jawad a wani katafaren garden, wanda yaji kayan fruits da korayen bishiyu, xaune yake a k'asa kan grass carpet, iska mai sanyi da dad'in k'amshi na kad'awa, sosai yaji dad'in xamansa a wajen jiyay duk bak'in cikin dake ransa ya yaye, nishad'i yakeyi. Sai daf da magrib ya bar garden d'in ya nufi wani babban mall, a lokacin ya tuna da phone d'inshi daya bari a car d'in, dan haka da sauri ya d'auka ya duba, 50 missed calls ya gani a raxane ya danna dan ganin waye, Ammi ya fad'a a bayyane, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, xuciarsa ta damu tasan abinda ke faruwa Ammi ta masa wannan missed calls d'in , juya kan motar yyi dan bayajin xai iya xuwa mall d'in. Wani wawan gudu yakeyi a titin burinsa ya ganshi a gida, yana isa gida kam part d'in Ammi ya nufa, tun daga parlour ya fara kwala mata kira, Ammi! Ammi! Ammi, sauri tayi ta mik'e ta nufi parlour jin muryar jawad, dama xaune take ta buga uban tagumi tana tunanin inda jawad ya shiga da yakasa d'aga kiranta. Tana fitowa ta rungumeshi, had'e da sauke ajiyar xucia, kuyangunta kam tuni sukayi waje dan basu guri, breaking hug d'in yareema jawad ya yi ya kama hannunta suka xauna a 2cter dake parlour n."Ammi na mai yake faruwa naga missed calls d'inki da yawa?" Kallon sa Ammi tayi bata gano b'acin rai a tare dashi ba sai damuwa, hakane yasa ta gane ya sakko daga fushin da yayi. Murmushi tayi "bbu komai jawad kawai na aika a kira mini kai akace baka nan, shiyasa na nemeka naji a ina kake" murmushi yyi had'e da kama hannunta "my Ammi ki daina d'aga hankalin ki haka, I'm not a small boy, kuma na manta phone d'ina a mota that's why banga call d'inki akan lokaci ba" ok my jawad, please ka dinga yayyafawa xuciarka ruwan sanyi, ka rage saurin fushi bashi da amfani kaji"gyad'a kai yyi, ya gane inda maganarta ta dosa amma ya share. Watch d'insa ya duba jin kiran sallah magrib, dan haka ya mik'e yayi ma Ammi sallama ya nufi masjid. After two weeks "Yareema jawad yayi tafia xuwa Egypt dad d'insa ya turashi ganin lapiar company d'in su dake chan. Areef kam ya samu damar xuwa gidan dan samun had'uwa da zaljameel, yau ma kamar kullum, tafe yake cikin motarsa sanye yake da manyan kaya, shadda milk colour kansa bbu hula k'amshi mai dad'i ke tashi a jikinsa, driving yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wani wani Bash Bakery ya shiga ya siyo snacks da ice cream, tsarabar nawal ce dan yasan tana san ice cream and yaga yanayin shakuwarsu da zaljameel. Direct part d'in su zaljameel areef ya nufa, xaune suke a bakin swimming pool suna wasa da ruwa, "nawal inasan na iya hausa gashi kema naga baki iya sosai ba ballantana ki koyamin" daria nawal tayi "wallahi kam my aunt, nima ba iyawa nayi sosai ba sai dai na fiki" daria suka saka, "ok haka kikace ko?" yeah" nawal ta fad'a," gashi uncle jawad bayanan daya koya miki "shiru zaljameel tayi jin sunan jawad, ok dama guy d'in nan baya nan, ai naxata fushi yayi shi yasa naga ko wajen mom baya xuwa." Assalamu alaikum "sallamar areef ta katse musu hira, da gudu nawal ta mik'e ta nufe shi tana murna, uncle areef oyoyo, ledar hannunsa ya saki a k'asa d'aga ta yyi chak yana daria." Nawal yan mata, kin girma sosai "daria tayi" haba uncle dubani fa "hancinta areef yaja ya sauke ta, hankalinsa ya karkata ga zaljameel da duk ta dururuce, sanye take da English waers riga mara hannu sai igiya da ake d'aurewa a wuya rigar iya gwiwa ce, sai tree guater pencils gaba d'ayansu pink colour ne, a kame suke a jikinta,gashinta xube a gadon bayanta. Wani mugun yawu areef ya had'iya, zaljameel ta gama tafia da imaninsa, jiyay sha'awarta ta kamashi, areef kam dama bbu dama a wannan fannin, sai dai ko jawad bai san yana harkalla da mata ba, sirrinsa ne shi kad'ai. Sumyn Bash ce💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 Pure moment of life writers p. m. l. w A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Nan gani nan bari, Idan kaji wane ba banza, ina kuke yan'uwa yan PURE MOMENT OF LIFE WRITERS, yabon gwani ya xama dole, gaskia tsarin ku dana novel din ku abin birgewa ne, Allah ya kara kaifin basira ya kuma kara had'a kanmu ameen, much love sister ❤ Chapter 29&30 "Gaba d'aya ya zuba mata idanu, a hankali ta mik'a hannun ta inda ta ajiye k'aramin mayafin data fito dashi, kafin takai areef ya rigata ya kai hannunsa ita ma takai, wani irin shock taji jin haduwar hannunsu, da sauri ta saki veil d'in, wani killer smile areef yyi sannan ya d'auki veil d'in, matsowa yyi dab da zaljameel ya durkusa a gabanta, tuni kirjinta ya hau dukan uku uku, d'aga idonta tayi tana dube-dibe cikin fad'uwar gaba, ganin bbu nawal a wajen ya k'ara tashin hankalin ta, murmushi areef yyi ya yafa mata veil d'in a kanta , jin hakan yasa ranta ya d'anyi sanyi, zama yyi a inda take xaune ya zura k'afafunsa a cikin swimming pool d'in,cikin mamaki ta d'aga ido ta kalleshi, idonsu ne ya had'u dan dama beautiful face d'in ta yake kallo, wani shu'umin murmushi yyi a hankali cikin salonsa na yaudara ya furta "zaljameel"bata juyo ba ta cigaba da wasa da zara-zaran yatsunta," oh ni zaljameel na shiga uku, waye wannan yake k'ok'arin shiga rayuwata, gashi dai handsome, sai dai ya jawad ya fishi kyau "my aunt nawal ta nufo wajen da gudu, sanyin dad'i zaljameel taji dan haka da sauri ta samu kwarin gwiwar mikewa tsaye, cikin sassarfa ta bar wajen tana mai jin kunyar ganin da areef ya mata. " Nawal binta tayi da kallo, juyowa tayi ga areef, "uncle dan Allah ka koyama aunt zaljameel hausa, tace tana son ta iya gashi uncle jawad baya nan da ya koya mata" Murmushi areef yayi dan ya samu damar shiga rayuwar zaljameel, hannun nawal ya kama suka fara tafia, "baby nawal kice mata zan koya mata, kuma gobe zamu fara" wani tsallen murna nawal tayi ta rungume areef," thanks uncle areef, Allah ya biyaka "bbu komai nawal ai mun zama d'aya, sai da suka k'araso part d'in su zaljameel ya cika hannunta," kije gida nawal zamu had'u gobe, ki gaida mom kinji "ok uncle areef zata ji,da gudu ta shige part d'in. " Jawad zaune a office d'insa na cikin company, files ne masu yawa a gabansa, da kagansa kasan aikin yasha kansa, cikin nuna gajia ya ajiye wani file, kansa ya dafe dayaji yana sara masa, watch ya duba 9:55pm,tsaki yaja ganin dare yyi, tun 7:00am yake wajen yana fama da files, gaskia banda maimartaba bbu mai bashi wannan aikin yayi. Cikin nitsuwa ya fara tattara abinda xai tafi dashi hotel din daya kama, motar company ce ta kaishi har hotel din. "Zaune yake cikin shirin bacci, laptop a gabansa yana typing, green tea din daya had'a yake sha, tunanin zaljameel ya fad'o masa, tsaki yaja dan tana d'aya daga cikin abinda yasa yake jin dad'in zama a Egypt dan ko fuskarta bayasan gani, yana gama tunanin sa ya buga wani tsakin, jiyay ransa ya baci dan haka ya tattara ya kashe laptop din ya nufi bed. "Tunda nawal ta bawa zaljameel labarin koya mata hausa da areef zaiyi taji abin bai kwanta mata ba, ita dai tafisan ya jawad ya koya mata, and waye wannan din daya keson shiga rayuwar ta, "nawal wanene areef?" daria nawal tayi ta d'ane cinyar zaljameel "my aunt areef frnd din uncle jawad ne kuma amininsa tun suna yara, uncle jawad ya yarda dashi sosai kowa a masarautar nan ya San areef, mai martaba sarki mai murabus yana ji dashi"ni kaina uncle areef yana birgeni, saboda yarda ya iya zama da uncle jawad, kin sansa da saurin fushi ga izza, bbu mai iya zama dashi sai areef d'in, fulani ma naji dashi, dan ita duk mai san jawad mai kuma kula dashi to fa tana sansa shima,kinji matsayin areef a gidan nan. Ajiyar zuciya zaljameel tayi, sai ynx hankalinta ya kwanta kuma sai ynx ta fara murna za'a koya mata hausa, rungume nawal tayi," thanks my proudly sister, I luv u so much"love u 2 "nawal ta fad'a tana murmushi. Areef zaune a parlour d'in mom yana jiran fitowar zaljameel, sanye yake cikin kananun kaya, sun karb'i jikin sa, zaljameel tafe cikin tafiar ta mai daukar hankali, da sallama ta shigo parlour, jin muryarta ta daki kunnensa ya sashi d'agowa bbu shiri, "wow" ya fad'a a zuciyarsa, sanye take cikin Arabian gown blue black an mata ratsin pink colour, pink veil tayi rolling kanta dashi, flat shoe ne a kafarta, k'amshi mai dad'i ke tashi a jikinta, a hankali ta k'araso har inda yake zaune ta zauna a gefen kujerar dake kusa dashi, areef kam baisan da k'araso war zaljameel kusa dashi ba"gud afternoon "zaljameel ta gaida areef, firgigit yayi ya dawo daga duniar tunanin daya tafi, murmushi ya k'akaro sannan ya amsa mata. Bayan sun gaisa areef ya fara koyawa zaljameel hausa cikin kwarewa, tun daga( a e i o u) sosai zaljameel ke ganewa and tana jin dad'in karatun, a cikin 2 weeks zaljameel ta iya hausa sai dai idan tanayi daria take bawa mutane har mom, duk da ana gane abinda take fad'a, sosai mom taji dad'in yarda areef ya koyama zaljameel yarenta, gaskia yyi namijin k'ok'ari, wani irin shakuwa ya shiga shakanin areef da zaljameel, indai areef baizo ba zaljameel bata jin dad'i, yana bata duk wani lokacinsa dan kula da ita, shi kansa areef ynx ya rasa mai yake masa dad'i, a da kam san daya kema zaljameel yana tattare ne da kyan fuskarta da jikinta, amma ynx kam soyayyarta yakeji har cikin ransa, kuma aurenta yake buk'ata. "Yareema jawad na Egypt duk da ya kammala aikin da mai martaba ya turashi amma baya jin xai dawo a wannan lokacin, dan Nigeria tafita a kansa, dama ba'a san ransa ya dawo ba. "Soyayya mai karfi ta shiga tsakanin zaljameel da areef, wanda tun sunayi a boye har ta fara fita fili, nawal dama ita tasan komai dan da ita zaljameel ke shawara, mom ma ta lura da hakan amma bata nuna farincikin ta ba dan ita ta da zaljameel zata bi tsarinta da sai tace ta mata miji. SUMYN BASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 Pure moment of life writers P. m. l. w A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ I dedicated dis page 2 u Sumyn Bash novels group thanks for your love and support. Ilysm Chapter 31&32 Zaljameel xaune a parlour, sanye take cikin top and jeans, gashin kanta baje a bayanta, light make up tayi, hannun ta dauke da jotter tana duba karatun da areef ya mata, taunar chewing gum take ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya, mom xaune a gefenta tana watching film, Nawal ta tafi part d'in fulani, phone d'in Zaljameel ya fara ringing, cikin zumud'i ta d'auka wani k'ayattacen murmushi tayi sannan tayi picking call d'in. Kallonta Mom tayi tana nazarin farin cikin daya ziyarci babyn tata. Cikin muryarta mai dad'i ta masa sallama, sai da ya lumshe idonsa ya bud'e a hankali, ajiyar zuciya yayi wanda ta daki dodon kunnen Zaljameel, "wa'alaiki salam sarauniyar kyawawa, murmushi tayi, cikin shaukin so areef ya kira sunanta," Zaljameel "yarda yaja sunan nata ya bala'in birgeta.. " Sarauniyar kyawawa Zaljameel, ina sanki,ina matukar kaunarki, burina bai wuce ki amince da soyayyata ba ni kuma na bayyana miki tsantsar kauna Zaljameel" Duk da tana san Areef sai da taji zuciyarta ta buga, bazata ce bata sansa ba tunda bata san so ba amma tasan tana jin feelings a kansa, "Kinyi shiru Zaljameel, ina san na sanar da jawad akan maganar ya kika gani? " ras taji gabanta ya fad'i jin an ambaci Jawad, "Jawad" ta maimaita a ranta,"Yeah Areef ka sanar dashi," dam gaban Mom ya fad'i" mai Zaljameel ke shirin yi? Badai Areef zata bawa dama ba"shiru tayi tana kallon Zaljameel." Ok my dear insha Allah yau zamuyi magana dashi naji yarda za'ayi, dan ina buk'atar ganin ki a kusa dani Zaljameel " murmushi tayi ta lumshe ido ta bud'e, jin ta take kamar ba itaba bata tab'a tunanin a kwai wani wanda zata so ba, amma yau gashi har ta amince da wani. Sallama sukayi cikin shaukin so, cikin nutsuwa Zaljameel ta hang up d'in call d'in sai a lokacin ta tuna da Mom a parlour, ji tayi kunya ta kamata ganin Mom na kallon ta , hannu tasa ta rufe fuskarta tana daria mara sauti, zumb'uru baki Zaljameel tayi cikin shagwaba, "kai Mom mai yasa kike kallona" murmushi Mom ta k'irkiro 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 Pure moment of life writers p. m. l. w A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 33&34 Wayarce ta subuce a hannunsa ta tawarwatse a k'asa, banda innalillahi wa'inna ilaihi raji'un bbu abinda bakin Jawad keyi, Allahumma ajirni fi musibati wayukulifni khairan minha, zama yyi a k'asa yana bin wayarsa da kallo, kirjinsa ne yaji ya masa nauyi, wani irin tashin hankali ya tsinci kansa a ciki, maganar Areef ce ta dawo masa "eh budurwatace and my wife 2 be insha Allah" "nayita jira ka dawo na sanar dakai amma najika shiru dan mun gama dai daitawa da ita". Yareema Jawad ya rasa irin tunanin da zaiyi, wato Areef abinda ya masa kenan? Tunda aka haifi Zaljameel nake kaunarta, Amma Areef ya zama sanadiyyar rabuwarsa da farin cikinsa, wata zuciyarce ta tunasar dashi, "Jawad Areef bashi da laifi, cux kai ka bashi damar yin hakan, zamanka na Egypt bai amfane ka da komai ba sai dana sani" wani kukane ya kwace masa da baima san yana kukan ba, cikin sanyin jiki ya tattara phone d'in shi ya zuba a aljihunsa ya nufi room d'insa na hotel, juwa ke d'ibansa yana dafa bango ya shiga, bajewa yayi Akan bed d'in sa yana mai da numfashi, addu'oin ya cigaba da karantawa a zuciyarsa a hankali, ya fara samun nuts uwa,tunani ne ya fad'o masa a rai, wayarsa ya had'a ya kunna "dole ya d'au revenge amma ko son Zaljameel zai kashe shi ba zai sanar da kowa ba,amma ya k'udiri niyar bai komawa Nigeria sai ya samu matar aure shima. Contact d'insa ya shiga ya fara scrolling, dai dai sunan daya tsaya yana kallo nima sumyn Bash naketa dogon wuya dan ganin waye, "Zahra Zahradden" na gani a rubuce, ba tare da b'ata lokaci ba ya danna kira. Zaune take a wani restaurant taje yin dinner, gaba d'aya tayi sanyi kamar ba Zahra yar rawar kai ba, takai spoon d'aya bakin ta taji ringing a phone d'in ta, cikin sauri ta zira hannu cikin hand bag dinta ta d'auka wayar, sunan data gani yasa ta mutuwar zaune da har phone d'in ta katse bata sani ba,sai a lokacin ta lura kiran har ya katse,"Yareema Jawad "wani ihu Zahra tayi ta fara taka rawa a wajen gaba d'aya hankalin mutanen dake wajen yayo kanta, bata damu da hakan ba dan bata su take ba, cikin zumud'i ta danna kiransa dan dama bata sa rai zai sake kiranta ba. Sai da phone d'in ta kusa katsewa sannan yayi picking bai bari tayi magana ba ya fara "Zahra Zahradden" ajiyar zucia ta sauke jin muryar Jawad da kuma sunan ta daya kira, lallai yau duk dunia babu kamar ta" "Zaki aureni?" Zahra ji tayi kamar zata shid'e, mamaki da al'ajabi zatayi amma bbu dama, cikin zumud'i ta amsa da eh Jawad wallahi zan aureka, ina san........ Bai bari ta k'arasa ba ya d'aura, kina ina yanzu? London ko Nigeria? Cikin rawar murya ta furta ina London Jawad, "ok ki baro London London ki same ni a Egypt xamu wuce Nigeria. 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 Pure moment of life writers p. m. l. w A romantic love story 2017 July 2017 Aishat A muh'd, tabbas ke dashen Allah ce, murucin kan dutse, karyar mak'iyi ballantana mai hassada, nan gani nan bari, littafi kuma yanzu kika fara shi, yarda kika tsaro shi haka zaki kammala, bbu wata shegiya da zata chanja miki ra'ayi, wuce gaba hajia ta, kina tafe muna binki da petrol, YAYI SAKE muna jiran page 3😁👍🏻 Chapter 35&36 Bai jira mai zatace ba ya katse wayar, Zahra tattara kayanta tayi ta bar restaurant d'in zuciyarta fal farin ciki, yau mafarkinta ya zama gaskia, Yareema Jawad d'in da yace bazai iya auren ta ba, bata cikin type d'in matan daya ke so ya aura, mai ya chanja ra'ayinsa? Cikin sauri ta shiga motar ta ta nufi gidanta. Tun a daren Zahra ta fara shirya kayanta, dan gobe take san ta sauka a Egypt, dama tayi missing d'in Jawad. Tana gama shirya kayanta a trolley ta fad'a toilet dan yin wanka,bakin ta a bud'e yake ta rasa inda zata tsoma ranta. Tana fitowa ta tarar da missed call a wayarta, dad d'in ta ne jikin ta na rawa ta bi kiransa, bugu d'aya ya d'auka. " Hello my Baby!" " Hi precious dady" "Dady yau ina cikin farin ciki, Dad ina Yareema Jawad da nake baka labarin sa wanda muka had'u a nan London" "Eh na gane shi Baby na kin ya dawo London d'in ne?" "A'a Dad" Nan ta bashi labarin wayar da sukayi da Yareema Jawad, cikin murna Dad d'in Zahra ya fara hamdala. "Yaushe zaki wuce Egypt d'in?" "Gobe Dad, bana so na b'ata masa rai yace ya fasa" "Eh Zahra kina da gaskia, kije da wuri kam" " Ok Dad, ina buk'atar kud'i ka tura mini yau" "Ok Zahra yanzu zan aika mansur bank ya tura miki" "Thanks alot my Dad, I love you so much" "Love you too Baby Zahra" idan kin isa Egypt let me know, cuz I want talk to Jawad akan maganar auren naku" "Dad! Zahra ta fad'a a razane, please Dad karka masa magana yanzu, Dad kasan waye Yareema Jawad kuwa? Wallahi zai iya cewa ya fasa aure nah, ni kuma indai haka ta faru wallahi kashe kaina zanyi" "Zahra kiyi hakuri, kije duk lokacin daya ke son gani na sai ki fad'a mini kinji baby" Gyada kai tayi da alamar ta gamsu, a haka sukayi sallama. Egypt Yareema Jawad ya dake zuciyarsa, duk da tana azal zala masa son Zaljameel amma yana k'okarin dauk'e ta a zuciyarsa, ya hakura da Zaljameel har abada, ya barwa Areef dan bbu abinda Areef zai nema a wajensa ya rasa. Zaune yake a bakin swimming pool, bayan ya gama wanka, towel a hannunsa yana tsane kansa, fuskar Zaljameel ke masa gizo,beautiful face d'inta, smile d'inta da slow voice d'inta komai nata abin birgewa ne, iska mai fitar da takaici ya fitar daga bakinsa, ya kamata yayi gaggawar sanar da yan gida akan maganar Zaljameel da Areef, dan ya cire Zaljameel a ransa. Phone d'insa ya d'auka ya fara neman layin mai martaba sarki farouq, bugu d'aya ya d'auka. "Yareema kak'i dawowa ko? Na rasa zaman mai kake a Egypt, ina san sanar dakai munyi maka mata, gaban Yareema ne ya buga da karfi, ji yay zuciyarsa na barazanar fita a kirjinsa saboda tsabar tashin hankali. Cikin rawar murya ya fara magana, " Mai martaba, tuba nake, amma ina san sanin yarinyar daka zab'a mini a matsayin matar aure?" "Yar uwarka ce Zaljameel" " Bana sonta mai martaba, bazan aureta ba, ya fad'a a hassale" "Karya kake Jawad, mun riga mun gama magana kuma bazamu chanja ba" "Zaljameel tana da wanda takeso mai martaba, dan Allah karku hanata aurensa, nima akwai yarinyar da mukayi alkawarin aure da ita, please mai martaba karku raba soyayyar mu" Yana gama fad'in haka ya fashe da kuka. Gaba d'aya jikin mai martaba yayi sanyi, sarki mai murabus da Aliyu suna zaune, kasancewar wayar a speaker take yasa suka ji duk abinda Yareema Jawad ya fad'a. "Kayi hakuri mai martaba, yanzu ma abinda yasa na kiraka ina san sanar dakai maganar Zaljameel, munyi magana da ita ta sanar dani Areef abokina dashi suke soyayya and shi take buk'atar aure, dan Allah mai martaba kar amana auren dole" Aliyu ne ya karb'i wayar hannun farouq, dan yaga yayi mutuwar zaune, "Yi shiru Yareema Jawad ka share hawayenka, bbu mai maka auren dole, wacce kake so ita zaka aura" , Godia Jawad ya fara yiwa Aliyu," ngd Dad, Allah ya saka maka da alkhairi" Zaljameel a gaban mirror sai faman make up take, dan yau zasu je ta gaida umman Areef, batasan abinda yake faruwa ba, Mom ce tayi sallama dakin Zaljameel, da fara'a ta amsa, ganin yana yin Mom yasa jikin ta yayi sanyi, A gefen gadon ta Mom ta zauna dan haka Zaljameel ma tabar jikin mirror d'in ta zauna a kusa da Mom. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©pure moment of life writers P. M. L A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 37&38 Zama tayi a gefen Mom ta d'aura kanta a kafad'ar ta, hannun Mom ta kama ta rik'e a nata. "Mom meya sameki?" Shiru Mom tayi ta fara tunanin maganar da sukayi da Dad, "Aysha munyi magana da Jawad, mun kuma sanar dashi maganar aurensa da Zaljameel" Nan Dad ya labarta mata yarda sukayi, Mom kam gaba d'aya bata ji dad'in hakan ba,sai dai family d'in basu da al'adar auren dole, sun fi so kowa ya fitar da wanda xai aura. "Sarki mai mirabus ba baiji dad'in shirin da iyayen sukayi ba, amma shi bashi da wani buri daya wuce yaga auren Zaljameel da Jawad. Ajiyar zucia Mom tayi ta kalli Zaljameel," Baby na wannan kwalliyar ina zaki? " Rufe fuskarta tayi tana murmushi, " Mom hajiar Areef ce ta damu naje mu gaisa " " Ok ke dawa zaku? " " Nida Nawal " " A'a Zaljameel, ba zaki je ke kad'ai ba, kinsan ke jinin sarauta ce, akwai kuyangu daya kamata su rakaki, bari muyi magana da Fulani " " Ok Mom " Zaljameel ta amsa ba dan ranta ya so ba, dan bata son bac'in ran Mom. " Mom ce ta kira Fulani ta sanar da ita maganar zuwan Zaljameel, "Eh gaskia taje amma shawarar da kikai ta zuwan ta da kuyangu yayi, dan sarauta ba k'arya bace, zan tura miki Annah da yan mata guda biyu" "Ok Fulani" Sallama sukayi Mom ta zauna tana nazari. Sallama Annah tayi a cikin parlour,Mom na zaune, cikin ladabi suka durkusa k'asa suna kwasar gaisuwa. Da sauri Mom ta mik'e ta nufi inda Annah ke durkushe, hannu biyu tasa ta d'agota, fuskarta d'auke da fara'a ta kalli Annah. "Haba Annah, maiyasa kike haka, ai ni yarki ce bai Kamata ki dinga durk'usa mini ba" Murmushin jin dad'i Annah tayi,kanta a k'asa ta fara magana "Tuba nake ranki ya dad'e amma durk'usawa miki ya zama dole, a matsayina na baiwar ku" "Baiwa? Annah kina so kice mini har yanzu ke baiwa ce a masarautar nan?" Murmushi Annah tayi, "Sarauniya Aysha ni baiwa ce kuma a baiwa zan mutu" Cikin hassala Mom ta fara fad'a, "Gaskia Yareema Jawad ya bani mamaki, shin bashi da labarin kece kika renesa har ya girma?" Ganin yarda Mom ke huci yasa Annah ta fara bayani cikin ladabi," Sarauniya Yareema Jawad ya bani duk wani gata, ya kuma yi iya k'ok'arinsa wajen ganin ya y'anta ni amma nak'i dan bani da burin daya wuce na kyautata muku, dan kun mini hallaci, idan na yarda kuka y'anta ni zanji kamar na zama kai d'aya daku, ni Kuma bana fatan haka a rayuwata " " Annah ni Aysha na miki alkawarin zan y'anta ki, kuma zan cigaba da yi miki kallo a matsayin uwa ba kuyanga ba" Annah ce ta fara hawayen farin ciki, ita dama Allah ya sani jinin ta ya had'u dana Aysha, dan ta kasance bata dauki dunia a bakin komai ba, kuma bata tak'ama da mulki da daular da take ciki, a ko yaushe mai arziki da mara arziki nata ne. "Godia nake ranki ya dad'e Allah ya raya miki zuria" "Ameen Mom ta amsa" "Ina gimbiyar take" Annah ta tambaya tana murmushi. "Tana d'akinta" Mom ta musu nuni da hannu. Cikin sauri yan matan biyu suka nufi d'akin Annah ma tabi bayansu. Da sallama suka shiga d'akin, Zaljameel zaune a gefen bed d'in ta, ta lula duniar tunani, jin sallama yasa ta amsa, a hankali ta juyo da kanta, ganin bak'in fuska yasa ta mik'ewa zaune, da gani bbu tambaya sune kuyangun da za'a had'a su tafia tare, ba laifi sunyi. Bajewa sukayi a k'asa suka fara gaishe ta, "An gaishe ki gimbiya Zaljameel, yar wazeeri jikar sarki, takawarki lafia" Sosai Zaljameel abin ya bata daria, au dama abinda suke cewa kenan, gaskia rashin jin hausa ya sata a matsala, daria take sosai harda rik'e ciki, tunanin shirmen data dinga yi take. Annah da sauran bayi kam sun bi Zaljameel da kallon rashin fahimtar dariar da take musu, to ko dai Zaljameel tana da matsalar kwakwalwa ne ba'a fad'a musu ba, cikin dauriya Annah ta fara magana. "Tuba muke ranki ya dad'e ko zamu iya sanin dalilin dariar nan? " Kallon Annah tayi, ji tayi tsohuwar ta shiga ranta, cikin murmushi da kuma maganar ta cikin yaren hausa da bata gama kwarewa ba ta fara magana. "Na tunane a tym d'in da nazo Nigeria bana jin hausa, danaji ana magana irin wanda kuka yi yanzu dan razana da rashin sanin abinda ake fad'a har suma nayi" Yan matan biyu suka fara tushe bakin su, dan yanzu suma Zaljameel ta basu daria, ganin yarda take gurbatacciyar hausa amma tana ta iya hausa. "Allah sarki uwar d'akina gimbiya Zaljameel, ina tayaki murnar iya hausa" cikin jin dad'i ta amsa ma Annah da nagode. Cikin sauri Annah ta sanar da Zaljameel zasu gyara mata kwalliyar ta, bbu musu ta yarda suka fara shiryata, cikin mintina kalilan Zaljameel ta fito cikin alkyabba mai bala'in tsada da kyan gani, tasha ado sosai, tsaye take a gaban mirror tana yaba kyan da tayi, tana kuma jinjima su Annah . "Ranki ya dad'e kinyi kyau" murmushi tayi ma Annah dan bama ta kalli sauran yan matan ba, ita tsohuwar ce kawai ta mata. Wayar Areef ce ta shigo, cikin sauri a cikin yan matan ta dakko mata, karb'a tayi murmushi tayi da sai da beauty point dinta ya luba, tsantsan kyanta ya k'ara bayana. "Hello my Queen kin gama shiryawa gani a kofar gidan ku" "Na gama habibi sannu ka da zuwa" " Yawwa amaryar Areef"ji tayi kunyarsa ta kamata, shiru tayi tana daria k'asa-kasa. A gurguje suka fito bayan Annah ta koyawa Zaljameel irin tafiar da zatayi, ba tare da b'ata lokaci ba Zaljameel ta iya, ita kanta yana yin tafiar da takeyi a yanzu ta birgeta. A parlour suka tarar da Mom, sallama sukayi mata suka fita, a wajen Areef suka tarar da Nawal, dan haka ba b'ata lokaci Areef yaja suka tafi. Kyakkawar tarba hajiar Areef tayi masu, dama an tanadi kayan ciye ciye, da shaye shaye, kamar yarda Annah ta fad'a ma Zaljameel kar taci komai aka bata haka tayi. Shigowar tayseer cikin parlour tana way yaja hankalin su, har Zaljameel. Sanye take cikin wani material black, dinkin fitet gown, kayan ya kamata kamar a jikinta aka d'inka shi, siririn veil ta yafa hannunta d'auke da jaka, daga ganin alama daga unguwa ta dawo. "Hajia ta I'm back" abinda tace kenan ta wuce ciki ba tare data kalli inda su Zaljameel suke ba. Sosai hajiar Areef ta had'a ma Zaljameel tsaraba, sukayi sallama Areef ya maida su gida. Egypt Yareema Jawad zaune a dakinsa na hotel yana tura ma Zahra kwatancen inda zata same shi a Egypt, a ranar zata sauka. Ya matsu tazo su wuce Nigeria, dan bashi da burin daya wuce ganin Zaljameel. Sosai Zahra ta gane kwatancen hotel d'in, dan Egypt ba bakonta bane tana zuwa shakatawa. Waya ta mishi tana reception, ok yace mata ya kashe wayar. Waya yayi ya sanar da zuwan Zahra ya kuma bada umarnin a bata key d'in d'akin da yayi mata bucking, ranta bai so ba taso ace a daki d'aya zasu zauna da Jawad, ta karb'i key d'in ta nufi room d'in. Wasa wasa bbu Yareema Jawad bbu alamunsa, tunda yaji ta je room d'in daya kama mata yyi switching phone d'insa. Har dare bbu Jawad tayi ta ta kiran layinsa amma shiru, zama tayi taci kukanta ta gode Allah, wato dama Jawad so yake ya wulakantata shi yasa ya kirata. Haka Zahra ta kwana bata ga Jawad ba, shi kam yana daki ya dasa tunanin Zaljameel har bacci barawo ya daukesa. Washe gari Yareema Jawad sanye cikin suit red and black, tsaye yake a gaban mirror yana kallon Kansas, sauri yayi ya d'auke kansa daga mirror dan pic din Zaljameel ke masa gizo, ya rasa wane irin so yakema Zaljameel, kamata ace yanzu ya hakura da tunanin ta, d'akin da Zahra take ya nufa cikin takunsa na kasaita. Zahra najin knocking ta fito jikinta na rawa, tana bude masa ya wurga mata wani kallo da tasha jinin jikinta, kallon kanta tayi, sanye take da sleeping dress iya gwiwa, kanta bbu dankwali gashinta baje a gadon bayanta, cikin hanzari Yareema Jawad ya juya zai bar wajen Zahra ta rike hannun sa. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©pure moment of life writers P.M.L A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 39&40 Hannu ya d'aga zai kwad'a mata mari, komai ya tuna ya sauke hannun sa yana huci. Tsawa ya daka mata, "Zahra" firgigit tayi ta saki hannun sa, gaba d'aya yana yinsa ya chanja. Nuna ta yayi da yatsa, "Zahra" karki k'ara mini irin haka, ko da wasa karki k'ara gigin rik'e hannu na.jikinta a sanyaye ta saki hannun sa,kallonsa tayi cike da so da kauna, k'ank'antar da murya tayi. "My dear Jawad ka shigo mana" Sai da ya runtse ido dan jiyay kamar ya hambare Zahra, anya baiyi dana sanin zabarta ba a matsayin matar aure? Mai ma zata d'aukesa mai magana biyu? Yace bazai aure taba amma yanzu ya nemeta akan ta auresa, lallai dole ya k'ara kama mutuncinsa dan kar Zahra ta kawo masa raini.wucewa yayi cikin room d'in ya zauna sai wani yatsina yake yi. Zama tayi a gefensa yana kallonsa kamar zata cinye shi dan so, k'aramin tsaki yaja ya fara magana. "As u know, zamu wuce Nigeria, kuma a gidan mu zamu sauka, kin san ko ni waye, jinin sarauta ne, masarautar mu bbu masu d'abia irin taki, dole ki koyi sa manyan kaya, dan bazaki dinga mana shigar da kika ga dama ba a chan, ina gargadin ki da rawar kai da fadi ba'a tambaye ki ba, yana zuwa dai dai nan ya kalli Zahra, ganin ta yayi ta zuba tagumi hannu biyu tana sauraransa, sosai taso bashi daria amma ya basar. Mikewa tsaye yayi y kalleta, "Zahra" "Na'am my dear Jawad" ta amsa tana murmushi, dan ita Jawad duk abinda zai mata zata jure matuk'ar zai aureta. " Ki shirya zamuje shopping na dogayen riguna da after dress," dam gaban Zahra ya fad'i, wai dama Yareema Jawad da gaske yake yi ita zata iya cewa tunda tazo dunia bata tab'a sa doguwar riga ta mutunci ba ballantana after dress. Ita ai sun mata nauyi ina zata kaisu. Katse mata zancen zucinta yayi, "Kinji mai nace ai, and gobe zamu wuce Nigeria, ya kamata ki zubar da duk wani iskancin ki a Egypt, dan wallahi idan mukaje kika jamin magana, gyad'a kai yayi alamar zata san sauran kenan yayi gaba. Dabas Zahra ta zauna a kasan carpet, lallai ta d'auko ruwan dafa kanta, bbu komai zata jure tunda tana sonsa, tashi tayi ta nufi toilet. Yareema Jawad yayi handing over da company, washe gari suka dauki hanyar Nigeria. Already yayi waya ya kuma sanar dasu tare da matar da zai aura yake, an shirya komai akan tsari an kuma tura fadawa tarar su. Jirgin safe suka biyo dan haka 11pm suna airport, ba tare da b'ata lokaci ba aka d'aukesu sai fad'a. Zahra gaba d'aya ta rud'e, duk yarda take jin labarin gidan sarauta da yarda akema mutun biyayya kamar za'a lashi k'afarsa, sosai kan Zahra ya fara rawa dan dama abin nema ya samu, Yareema Jawad tun a mota ya lura da Zahra ta fara zubar da fad'an daya mata, gashi ba damar magana saboda fadawa. A part d'in Fulani aka sauke Zahra, da kyar ta yarda zata zauna wai Yareema Jawad zata bi part d'insa, wani kallo ya mata tuni Zahra ta shiga taitayinta ta bi fadawan. D'aki guda aka bama Zahra da kuyangu masu kula da ita, jin kanta take so high, dama haka sarauta take? Komai sai dai a maka, kai ita dai taji dad'in had'uwa da Jawad. Sai da ta huta sannan aka kaita wajen Fulani. Fulani kam yak'e kawai take yi da hausawa sukace yafi kuka ciwo,gaskia Jawad ya gama bata kunya, bata tab'a tunanin haka zata ga Zahra ba, a tunanin ta zata fi Zaljameel komai da komai, sai gashi abin haushi tarbiyar kwarai ma Zahra bata dashi dan akan kujera ta zauna ta gaida Fulani. Bala bakinsa yaki rufuwa saboda dawo war Jawad, kitchen ya shiga ya dafa masa favorite food d'insa, Yareema Jawad kam yaji dad'in tarbar da Bala ya masa, cikin sakin fuska suka gaisa, "Yallabai ya madam ance da ita kuka taho?" eh yace ya fad'a toilet. Fes ya shirya cikin wani farin yadi mai tsadar gaske, ya gyara sumar kansa, kamshi mai dad'i ke tashi a jikinsa, man's pride d'insa ya shafa wanda ya k'ara ma fuskarsa kyau, wani k'ayattacen murmushi yayi jin zuciyarsa yake fes bashi da matsala dan ya dawo kusa da abar kaunarsa Zaljameel, burinsa bai wuce ya ganta ba. Fitowa yayi ya nufi part d'in Fulani. Zaljameel kwance tayi pillow da cinyar Annah, a wani babban garden, ita da Anna da kuyangun nan guda biyu, tun daga ranar da suka je gidansu Areef Fulani tace su cigaba da kula da ita. Labaran daria Annah ke bata Zaljameel kam daria take bbu saurarawa,fuskarta tana kallon bakin Annah kamar zata fad'a ciki dan dama Zaljameel akwai san labari, sosai take jin dad'in zama da Annah dan yarda suke da ita ta dauke ta kamar granny d'in ta. Yareema Jawad tafe cikin kasaitarsa kamar bazai taka k'asa ba, kuyangu da bayin sarki nata kwasar gaisuwa yana basar wa, wucewa yazo yi ta dai dai garden d'in, kamshin perfume d'in daya ji ya d'auki hankalinsa zuwa wajen, sanyayyar ajiyar zucia ya sauke yana godia ga Allah daya sa yaganta a lokacin da idanunsa ke buk'atar kallonta, da yake garden d'in babba ne sai ya shiga ya zauna chan nesa dasu, ganin yarda Zaljameel ke daria ya daure masa kai, gashi yaji tana dabura hausa, abin ya bashimamaki, waye yayi kokarin ko yawa Zaljameel hausa? Gaskia ko waye yayi kokari. Ya shagala sosai da kallon Zaljameel, gani yayi ta Mike zaune an miko mata wayarta, cikin zumud'i da fara'a ta d'auka, jiyay wani mashi ya soki gefen zuciyarta, ranshi gaba d'aya ya baci, wani kishine ya tokare masa kirji, cikin sauri ya tashi zai bar wajen yaji an rike masa riga, da sauri ya juyo, "Uncle Wana kama, wato dan kaji ance ina neman ka shiyasa ka gudu garden ko? Hannun ta ya kama suka fara tafia dan shi bai da burin daya wuce ya bar garden d'in kan zuciyarsa ta tarwatse. Part d'in Fulani ya nufa, a dakin ta ya sameta abin dunia ya isheta, daga ganin Zahra yar dunia, idonta a bud'e yake, bata dace da Jawad ba, ita dai batasan mai ya gani ba a tare da ita. Bayan ya gaida Fulani bai samu wata fuska da zaiyi hira da ita ba, dan bala'in haushinsa take ji, haka ya tashi jiki bbu kwari ya nufi part d'in Mom dan yasan ita kad'ai zata faranta masa. Tafe suke shi da Nawal suna hira, yakusa part d'in Mom ya gano abinda zai iya sawa zuciyarsa ta daina aiki, Areef tare da Zaljameel a jikin mota, sai hira suke cikin annashuwa da jin dad'i, tsayawa yyi chak daya tuna wani abu, phone d'insa ya d'auka ya fara neman layin Zahra, bugu d'aya ta d'auka, "hello baby" "ki fito ina waje, kuma na fad'a miki ki ajiye duk wata rawar kanki, wallahi Zahra zan iya fasa aurenki"bakinta na rawa ta fara bashi hakuri, katse wayar yayi ya tsaya jiran Zahra. Cikin rangwada da karairaya Zahra ta tunkaro inda Jawad yake, yana yin fuskarsa ya chanja ya fara fara'a, jerawa sukayi suka nufi wajen, kai kace arziki suke da Zahra, sai wani kallonta yake yi, baki ta saki tana kallon ikon Allah, a haka suka k'arasa har inda su Areef suke. Basu san da zuwansa ba suna ta hira, hakane ya k'ara kular dashi, amma ya basar. "Sannan ku romeo and Joliet" , tare suka d'ago kai suka kalli Jawad, Zaljameel ji tayi zuciyarta bugun ta ya k'aru, kallon Zahra tayi daga sama har k'asa, ganin yarda ta tsaya kusa da Jawad kamar zata rungumesa, ji tayi haushinta ya kamata, wannan kuma wacece mai matsayin tsayuwa kusa da Yareeman da bbu irinsa? SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Wannan page d'in naku ne SUMYNBASH NOVELS NOVELLAS LODGE AUNTY AND SADDY NOVELS P.M.L WRITERS FANS ZEE AND HUSSY NOVELS FUTHUHATUL KHAIR 1 FUTHUHATUL KHAIR HOME OF HAUSA NOVELS HAFSAT MUSA NOVELS (INDON KAUYE) MACEN GABAN GOSHI BARI IN DAKATA HAKA DAN KUNA DA YAWA AND I LUV YOU ALL ❤😍 Chapter 41&42 D'auke kai Zaljameel tayi sakamakon had'a idon da sukayi da Jawad, wani kallo ya watsa mata wanda bazata ta iya fassara abinda yake nufi ba, gaba d'aya jikinta yayi sanyi, cikin sanyin muryarta ta gaida Jawad. "Ya Jawad ina yini? Fatan ka dawo lpy?" Ba tare daya kalleta ba ya amsa a dak'ile, "lpy " Areef ya bud'e baki zaiyi magana Jawad ya d'aga masa hannu "stop it" Ya kalli Areef, kasaitarsa gaba d'aya ta tashi, ya koma Yareema Jawad d'in sa. "Meet me in part, kasan I don't want to talk in front of kids " ya kalli Zaljameel yana yatsina fuska. Wucewa yayi yabar su a tsaye a wajen, Zahra kam da, kishin Zaljameel ya hanata kata b'us tabi shi suka jera, jinta take so high, lallai Jawad yana santa, ji yarda ya tsalama zankad'ed'eyar budurwa rashin mutinci, ita kam taji dad'i abinda yama Zaljameel, dan da har kishin yarinyar ya shiga ranta, dan Zaljameel takai ayi kishi da ita, saboda ta had'u ta ko ina. Tunda suka tafi Jawad bai k'ara kallon Zahra ba har suka shiga part d'in Mom. Annah zaune a k'asan carpet suna hira da Mom, sallamar Jawad ta katse su, cikin farin ciki da zumud'i Annah ta mik'e tsaye tana washe baki a nitse ya shigo parlour, bayan ya tattara duk wata shagwabarsa, yana shiga ya nufi cinyar Mom da itama fara'ar take masa. Zama yayi kusa da ita ya d'aura kansa a cinyarta, fuskar sa kamar zaiyi kuka ya fara magana. "Mom bakya missing d'ina ko? Duba yarda wuya ta maidani a Egypt, duk na rame nayi bak'i, amma Mom kalli yarda kikayi k'iba, ni wallahi keda Fulani kun daina sona" Ya k'arashe maganar fuskarsa d'auke da damuwa. " Baiwar Allah shigo mana" Annah ta bawa Zahra dama. Zahra kam mamaki ya gama cikata, dama haka Jawad ya iya magana ga kuma shagwaba kamar baby. Shigowa tayi parlour ta zauna tana k'are ma parlour kallo, gaskia akwai arziki a gidan nan, ji yarda suke decoration kamar bada kud'i suka siya ba, ta saba ganin manyan gidaje, masarautar su Jawad tasha kanta. Sai da Annah tama Zahra iso sannan Jawad ya tuna da ita, Mom sai shafa gashin kansa take yi, idonsa a lumshe ya fara magana "Mom ga Zahra, itace my 2 be d'in" , ya fad'a yana murmushi. "Kai masha Allah, ok ashe itace wacce ta tafar mini da zuciyar Yareema, gaskia Zahra kina da babbar sa'a, samun dan sarki Yareema Jawad" Wani killer smile Jawad yayi ya shafa man's pride d'in shi. Sai a lokacin Zahra ta gaida Mom, itama a kujera ta hard'e ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya. Cikin kulawa Mom ta amsa, "Zahra kinzo lpy? Lpy lau Mom," ta fad'a kamar yarda taji Yareema ya fad'a. Duk da Annah bata jin turanci amma taji labarin Yareema yak'i auren Zaljameel cuz yana da wacce sukayi alkawarin aure da ita, indai ko wannan ce ita bata ga abin so a tare da itaba,dan kuwa Zaljameel ta fita komai. Yan matan nan biyu Mom ta basu umarnin kawo wa Zahra abin tab'awa, da hanzari suka nufi kitchen. " Yallabai uban gidana ina mik'o gaisuwa" Jin muryar Annah yasa Jawad mik'ewa da sauri, ganin ta yasa ya saki wani smile da yake k'ara masa kyau, "Annah" ya fad'a yana kallonta. "Na'am Jawad kazo lpy?" Annah fushi nake dake, Annah ai nazata kin manta sunana ma, Annah bakya nemana, ko a waya ai kya ara ki buga mini mugaisa ballantana gaki a kusa da Mom d'ina " Ya k'arashe maganar yana wani b'ata rai. " Tuba nake Yareema Jawad, Allah ya huci zuciyar maza, wallahi kana raina ko yaushe, ya za'ai na manta ka Jawad, ai har a gidanka sai na zauna, yarda na rene ka haka zan raini d'anka idan Allah ya ara mini rai da lpy" Wani kallo Zahra ta watsa wa Annah mai kice da tsana, wannan tsohowar ce zata raini d'an da zata haifa, Allah ya kiyaye, ji tayi har ta tsani Annah, ai ita masu renon ya'yanta a London zata samo su, turawa take bukata. Sosai Jawad yaji dad'in maganar Annah, cikin jin dad'i ya amsa da " Allah ya nuna mana Annah "Ameen Annah ta amsa. Zaljameel gaba d'aya hirar tasu da Areef tak'i mata dad'i, lura da hakan yasa Areef ya mata sallama ya nufi part d'in Jawad dan jiranshi yana son sanin wacece wacce suke tare da ita, ko Jawad ya fara harkar bariiki ne, banda haka har ya kawo Zahra cikin gidan nan, bayan duk wanda ya kalleta yasan yar dunia ce, gaba d'aya ransa a b'ace yake, ga kuma wulakancin da yama Zaljameel. Mik'ewa Jawad yayi yama Mom sallama suka tafi. A gurguje please Wasa wasa lokaci tafia yake yi, yayin da aka fara shirye shiryen biki, Dad d'in Zaljameel shi yayi ja ragamar bikin ya kuma sanar da Zahradden mahaifin Zahra, shima kam like father like daughter haka suke da Zahra, duk wani yanayi na dan duniar mutum ya bayyana a tare da baban Zahra, dama ance barewa bazata yi gudu ba d'anta yayi rarrafe. Wai ina sarki mai mirabus sarki Abubakar. Tunda Jawad ya sanar dasu bazai auri Zaljameel ba wani abu ya tokarema grandfa a zuciya, gaba d'aya ya rasa sukuni, ko Aliyu da farouq ya daina sakar musu, ganin sun goyi da bayan ya'yansu zasu basu wanda suke so, sosai ya hango alheri a auren Jawad da Zaljameel,amma Allah bai nufa ba.Ganin yarda ake shirye shiryen bikin yasa sarki Abubakar ya fara rashin lpy, gaba d'aya hankalin families d'in ya tashi, aka nufi hospital dashi, cikin gaggawa da sanin matsayinsa aka kwantar dashi a emergency, likitoci biyar tsaye a kansa, a gadon asibitin ya fara aman jini, sosai suka bashi taimakon gaggawa suka masa injection for sleeping, dan gaskia he have to rest, cuz akwai damuwa a ransa, wanda yay cussing masa heart attack. Cikin dare abin ya faru hakane yasa Yareema Jawad baima san an tafi da grandfa hospital ba. Kwance suke shi da Areef a bed d'aya, dan tunda aka fara maganar auren su ya dawo gidan dan su shirya komai akan tsari. Yareema Jawad ya tafi duniar mafarkin Zaljameel wanda ya zame masa jiki kullum sai yayi. Zaune suke a wani babban garden suna hirar su ta soyayya, Zaljameel sanye da wani wedding gown red colour, tayi kyau sosai, kanta bbu veil sai dai gashin ta yasha gyara sai shining yake yi, zaune take a cinyarsa suna tazuba hannayenta a kafad'arsa, gaba d'aya sun kafama juna ido cik'e da so da k'auna, bakinsa yakai kan nata ya fara romancing dinta cikin kwarewa, sauri tayi ta kwace kanta ta tashi a cinyarsa tana ja da baya, tashi yyi shima wahale dan romance d'in bai ishe shi ba, tafia take da baya da baya tana d'aga masa hannu, cikin azama ya fara binta da gudu,"Zaljameel please ki tsaya don't go, you know I love you, can't do without you Zaljameel, dan Allah ki tsaya, u mean alot to me, yanzu aure xakiyi ki barni, wallahi Zaljameel zuciyata dab take da bugawa, na tabbata duk ranar da aka d'aura miki aure ranar numfashina zai tsaya". Bata tsaya ba saima b'ace masa daya ga tayi cikin razana ya fara kiran sunan ta da karfi, "Zaljameel................... Zaljameel....fashewa yayi da wani kuka mai cin zuciyar maiysaurare. Areef dake kwance a gefen Jawad tuni ya farka jin maganganun da yake yi, ganin he is dreaming yasa hankalin Areef ya kuma tashi." Zaljameel? Dama Jawad yana son Zaljameel kamar haka, zama Areef yayi ya fara hawayen tausayin Jawad, shegen girman kai da izzarsa suna so su kaishi ga barin dunia, daga yarda yaji mafarkin da Jawad yake yi yasan ba k'aramin so yakema Zaljameel ba, dan shi zai iya cewa bai tab'a mafarkin Zaljameel suna soyayya ba sai dai suna sex, hakan yasa ya gane har yanzu sha'awar Zaljameel yake yi ba sonta ba idan kuma ya aureta baima Jawad adalci ba, ita kanta Zaljameel tunda Jawad ya dawo ya rasa walwalarta, ya kuma lura da chanjin yanayin ta, ta daina bashi wata kulawa and ya lura akwai damuwa a ranta, shi kuwa ko shed'an ne ya kamata ya cece zuciyoyi biyu, hawayen fuskarsa ya goge sannan yasa hannu ya goge na fuskar Jawad daya gangaro. A hankali Jawad ya bud'e idonsa ya d'aura a fuskar Areef, cikin basar wa da nuna baiji abinda ya faru ba Areef ya sakar ma Jawad murmushi,"Jawad barka da tashi,Yareema Jawad kasa magana yayi dan a tunanin sa Areef yaji mafarkin sa, ya naga kwalla a idonka ko duk na farin cikin gobe za'a d'aura maka aure da habibatyn ka Zahra ne? Cikin hassala jin an ambaci sunan Zahra yasa Jawad mik'ewa zaune ya d'auki pillow ya rungume a kirjinsa yana tunanin mafarkinsa, wato da gaske Zaljameel ta masa nisa kuma baya cikin zuciyata, uban tagumi ya buga yana tuna yanayin da suka kasance a dream d'in, wani k'ayattacen murmushi ne ya sub'uce masa batare da yasan yana yiwa. Areef zaiyi magana wayarsa ta fara ringing, dubawa yayi yaga mai martaba mahaifin Jawad, cikin ladabi ya d'auka, cikin girmamawa suka gaisa, sannan sarki Farouq ya fara bashi bayani akan ya same su a J&Z special hospital, kai kad'ai zaka zo kuma bana son Jawad yasani, shikenan Yallabai gani nan. Tunda ya fara wayar Jawad ke kallonsa bai bari ya gane dawa yyi waya ba ya tashi ya fad'a toilet, Jawad ma nasan tambayarsa amma miskilanci ya hanashi, mik'ewa yyi shima ya fara shirin wanka. A gurguje Areef ya nufi hospital d'in. Ganin, Aliyu Dad d'in Zaljameel da Fulani, mahaifiyarsa hajia Binta da kuma baban Zahra, Alh Zahradden da ita Zahra. sosai jikinsa yyi sanyi ya kuma fara b'ari, ganin fuskarsu bbu walwala, k'arasawa yayi cikin d'akin ya zauna. Cikin ladabi ya gaida iyayen nashi, hankalin sa ne ya koma ga wanda ke kwance a gadon hospital d'in. Grandfa kwance ansa masa oxygen a baki, numfashinsa sa na fita a hankali, k'arasawa yayi jikin bed d'in hankalinsa a tashe ya kama hannun grandfa, tuni hawaye ya cika idonsa dan Areef akwai tausayi, juyowa yayi ya kalli parents d'in nasa ya fara tambayar su abinda ke faruwa, Alh Zahradden ne ya fara masa bayani tunda ga tahowa da grandfa hospital har lokacin da doctor yace ya samu heart attack, an kuma tambaye shi meye dalili yace saboda rashin had'a auren Jawad da Zaljameel. Mik'ewa Zahra tayi tsaye dan ba'a bata labarin komai ba an dai aika direba ya kawota, ja da baya ta fara yi idonta ya cika da kwalla, kai ta rik'e tana furta no...... Dats is impossible, kunsan waye Jawad a wajena da kukesan rabani dashi, Dad harda kai ta nunashi da hannu, Jawad shine rayuwata, kunsan irin wahalar da nasha kaifin na samu soyayyar Jawad, ranar da Jawad yace zai aureni wallahi banyi bacci ba saboda murna, naso ace ya fad'a mini yana sona tun kan ranar, ina san Jawad wallahi ina sonsa, idan na rasa shi wazai aureni? d'irkusa Zahra tayi ta fashe da kuka mai tab'a zuciyar duk wani mai jinta, iyaye matan kuwa Hajia Binta, Mom da Fulani tausayin Zahra ya su zubar da hawaye. Areef tsaye yyi yana k'arema Zahra kallo, tunda tazo sai yau ya kalleta sosai, tunda ta fara magana yake kallonta, gaba d'aya ta tafi da shi, murmushi yyi lallai yyi mata,dan Zahra ba baya bace a kyau, matsalar ta rashin tarbiyya amma tunda tasan so, to son nan zai gyarata. Areef ne zai aure ki, sukaji muryarsa, ita kanta Zahra d'aga kai tayi ta tsaya da kukan tana kallonsa, yarda yayi shiru sai taga kamar maganar ba daga bakinsa ta fita ba. Gira ya d'aga mata had'e da kashe mata ido d'aya ya sakar mata wani murmushi, Yes Zahra ina sonki kuma zan aure ki,ni dama na hakura da auren Zaljameel tun banzo hospital d'in nan ba. Gaba d'aya sun maida hankalinsu ga Areef dan jin dalili sa, labarin mafarkin Jawad ya basu da kukan da yake yi yana kiran karta tafi ta barshi yana sonta, "Tunda naji haka na bawa zuciyata hakuri, dan nima Zaljameel tunda Jawad ya dawo ta chanja mini gaba d'aya, hankalin ta yafi karkata ga Jawad. Zahra ke meye ra'ayinki akan Areef, Dad d'in ta ya tambaye ta? Kallon Areef tayi shima ita yake kallo ya hard'e hannunsa biyu a kirji, gani tayi ya mata wani kwarjini ya kuma birgeta dan Areef akwai kyau shima, Ina sonshi Dad na amince zan auresa. Wani dad'i ne ya lullube duk wanda ke wajen harda grandfa da yanzu fitar numfashinsa yyi normal, hawayen farin ciki ya fara bin gefen fuskarsa. Sosai iyayen suka musu addu'a da kuma sadaukarwar da sukayi, tare direba ya maida su gida. Duk abinda ya faru Jawad da Zaljameel basu sani ba har aka fara biki, dan ance ya zama sirri tunda duk tare za'ayi bikin karsu bari a gane. NIMA KAM SAI SHOKIIII NAKE KWASA SABODA MURNA💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 SUMYNBASH CE💋 CE💋 ?🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L A romantic love story 2017 July 2017 Ina kuke masoyan littafin yareema jawad da ni mai rubutashi Sumyn Bash, na matuk'ar k'aunar ku fiye da yarda bakwa zato, ina alfahri daku masoyana, ina godia da addu'oin da kuke mini kuma ana tare#One love❤ Chapter 43&44 Zama Jawad yyi a kujerarsa da irin babbar nan ta sarauta, wani irin annushuwa yake ji aransa, yau dream d'insa ya tabbata, ya mallaki Zaljameel cikin sauk'i, bai tab'a tunanin hakan ba, gaskia grandfa ya masa k'ok'arin da bazai da hakan ba, a hankali ya furta "luv u grandfa, how will i forget u in my life ka min komai a rayuwata". Fuskarsa ya d'aga sama yana kallon ceiling, ya lumshe idonsa fuskar sa d'auke da murmushi. Sallama Bala yyi a parlour, ganin Yareema Jawad zaune a karagarsa yasa ya k'arasa, a gaban sa ya zauna a k'asan k'afarsa. Fara'a ya fara magana! "Barka da hutawa ranka ya dad'e" "Barkan ka dai Bala" ya fad'a fuskar sa d'auke da murmushi. Mamaki bayyane a fuskar Bala, dan rabon da Jawad ya k'ira sunan sa har ya manta, hakan ya bashi damar cigaba da zancen sa! Ina taya ka murnar Aurenka, ina rok'on Allah ya baku zaman lpy kaida gimbiya Zaljameel, ya azurtaku da salahan ya'ya masu biyayya ga iyayen su" Wani dad'i ya ratsa zuciyar Jawad, Bala bai tab'a faranta ransa ba sai yau, tunda Bala ya fara magana idonsa a rufe yake, dag'o kai yayi had'e da gyara zaman sa, tar ya d'aura idonsa akan Bala dake zaune! Sai da yyi wani murmushi sannan yace! "Bala na 'yanta ka na kuma biya maka aikin hajji, na d' auki dawainiyar aurenka na kuma baka gidan da zaka zauna, kai na daban ne yanzu a wajena, tunda aka d'aura mini aure Areef shine wanda ya fara faranta ta raina da kyakkyawan labari, sai kai Bala" Mutuwar zaune Bala yayi dan jinin dake jikinsa jiyay ya daskare, anya abinda kunnensa yaji gaskia ne?D'aga ido yayi ya kalli Jawad wanda shima d'in Bala yake kallo, Bala gani yay kamar maganar ba daga bakinsa ta fita ba, tsantsar mamakin da Jawad ya gani a fuskar Bala yasa ya nanata masa abinda ya fad'a a baya. Fashewa da kuka Bala yayi dan bakinsa ya gaza gode ma Jawad, kuka sosai Bala yayi ba tare da Yareema Jawad ya lallashe shi ba, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana muryarshi a shak'e! "Ranka ya dad'e godia nake, duk da bakina ya rasa kalmaomin da zanyi amfani wajen gode maka, akwai alfarma da zan nema a wajen ka, Dan Allah ka barni a matsayin bawanka, ina son na dawwama ina maka hidima, bana son rabuwa dakai ranka ya dad'e. Cikin kulawa Jawad ya d'auke idonsa akan Bala ya maida part d'in Zaljameel, ji yake inama zata fito ya ganta, Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fara magana! "Muna tare Bala, bbu wanda zai iya d'aukar dawainiyata sai kai, kasan komai nawa, dakai kad'ai na yarda, ina ganin' yanta ka ba matsala bane". Bayan ya gama yi ma Jawad godia ya nufi bedroom d'insa dan had'a masa ruwan wanka. Zaljameel zaune a d'akinta, tana jiran shigowar Areef da friends d'insa dan taji muryar su, jin shiru yasa ta sauke mayafin kanta tana k'arema d'akin kallo, babban d'akine an masa decoration da Arabian furniture, design d'insu irin na sarauta ne,gefe cushion ne white colour an masa ado da golden, sunyi kyau, a gefe wata shegiyar plasma ce bango d'aya ta cinye, kamar ta fad'owa mutum dan girma, a hankali Zaljameel ke bin d'akin nata da kallo, gaskia iyayen ta sunyi k'okari. Wall clock ta kalla, 11:56pm hankalinta ya tashi, to ina Areef ya shiga? Ni sumy nace yana wajen matarsa suna rak'ashewa. Lol Wasa wasa bbu Areef bbu alamunsa, ganin haka yasa Zaljameel ta fara shirin bacci, kayan jikinta ta cire ta nufi toilet dan yin wanka. Bayan ta fito ta shirya cikin wasu tsadadden sleeping dress red colour, silk ce, rigar iya gwiwa tabi jikinta ta lafe,duk surorin jikinta ya bayyana, a hankali ta taka gaban standing Ac ta rage ta nufi bed ta kwanta, tunanin inda Annah take Zaljameel ta fara yi, badai Annah ta tafi ba, dan bata tunanin akwai wanda yayi saura a gidan, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ina Areef ya shiga? Anya bazata kira gida ta sanar dasu ba, wata zuciyar tace ki bari anjima ko akwai abinda ya tsare shi bai shigo da wuri ba, phone d'in ta ta jawo ta hau online, messages ne suka fara shigo mata na congratulations, a wani group da take ciki, na class mate d'in ta dake Qatar. Ta gama yi musu reply ta sauka zuciyar ta fal damuwa, dan ma Zaljameel bata da tsoro hakan yasa tayi kwanciyarta tana jiran dawowar Areef, a haka bacci ya d'auke ta. Areef da Zahra kam sun raya daren su sosai cikin farin ciki da k'aunar juna, da yake Zahra duk wayewar ta bata tab'a yarda wani d'a namiji ya kusanceta ba, hakan yasa Areef daya dan tab'a bariki ya birkice mata gaba d'aya, su Zahra ansha kuka kamar rai zai fita, sai da suka raya daren sannan suka yi bacci. The next day Jawad ya tashi da asuba yayi wanka ya shirya cikin jallabiya ya fito zai nufi masjid, kamar yarda suka saba yana fitowa yaci karo da Bala a tsaye yana jiran fitowarsa, d'urkusawa Bala yayi ya gaida Jawad, bayan ya amsa masa cikin kulawa suka nufi masjid. Bayan sun idar Yareema Jawad ya hango grandfa a gefe yana tasbihi, wajensa ya nufa fuskar sa d'auke da fara'a. Grandfa na ganin Yareema Jawad ya nufeshi yayi kicin kicin da fuska, ganin hakan bai hana Jawad k'arasa wa ba. A gabansa ya zub'e yana dariar ganin yarda grandfa ke cin magani, zama yayi a kusa dashi ya fara gaida shi! "Grandfa nawa ni kad'ai" Harararsa Grandfa yayi! "Ina kabar Zaljameel? Da zaka ce naka kai kad'ai ". Daria Jawad yayi dan dama yasan zasu fafata da grandfa, saboda abinda ya masa, sai da yajanyo yayi rashin lpy. " Dan nema! Wato kana so kana kaiwa kasuwa ko? Yanzu badan na tubure ba da tuni ka rasa farin cikin ka ko? Zaljameel alheri ce a tare da kai na dad'e da gane hakan, burina ya cika Jawad dama shi kad'ai ne ya rage mini a duk buri kana, sai kuma fatan na cika da imani. Cikin barkwanci Jawad ya bawa grandfa hak'uri, abinka da jika da kaka tuni grandfa ya saki jiki sukayi magana da Jawad. Nasiha sosai grandfa ya masa akan ya rik'e Zaljameel da amana, ya bata duk wata kulawa data kamata, nasihar ta ratsa Jawad sai dai a zuciyarsa bashi da wani buri da zai bama Zaljameel damar shiga rayuwarsa, kamar yarda yayi alkhairi bazai tab'a bayyana mata yana sonta ba, yanzu ma kam haka za'ai, lokacin bayyana mata soyayya baiyi ba, so yake sai ta gama kamuwa da sonsa shima dan zata fi sanin darajar sa, sallama yayi ma grandfa, anan grandfa ya bashi sak'on gaida Zaljameel. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ I proudly to dedicated dis page 2 u guys u are so special in my heart. Aishat A Muh'd (Aunty) Aunty cute Zahra Bukar Ummi hambali Rahma(momyn sultan) Faridat sweery Maryam s bello Maryam Abdul Hafsat musa(indon k'auye Aunty kausar Aisha Ali garkuwa Feedy luv Dama sauran wanda ban fad'a ba, duk ina sonku. Ina kike Aunty na Zahra Uba Leader Ina matuk'ar alfahri dake ina kuma godia da k'aunar da kike nuna ma littafin yareema jawad, # much love 💋 Chapter 45&46 Wani doguwar mik'a Zaljameel tayi tana salati, a hankali ta fara bud'e idonta, a zabure ta mik'e zaune ganin gari yayi haske, phone d'in ta dake a gefenta ta jawo ta duba time, ganin lokaci yasa ta fito da idonta waje a tsorace ta hannu tasa ta dafe kanta, omg! Yau wane irin bacci nayi, ace har 12:00 pm tana kwance, zata iya cewa rabonta da bacci irin haka tun kafin a fara shirye shiryen bikinta. Addu'ar tashi daga bacci tayi ta fara duba d'akin, so take taga alamun Areef ko ya shigo d'akin da tana bacci amma yarda ta kwanta haka tata shi, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ta fara nanatawa a ranta, mai yake shirin faruwa da ita ne, ina Areef yake, kar dai sace shi a kayi. Zuciyarta ta gama yarda da Areef ya b'ata hakane yasa ta d'aura hannu aka ta fara kuka, shikenan ni Zaljameel na shiga uku, Ya Allah ka bayyana Areef, Allah kasa yana hannu nagari, ni kam daria Zaljameel ta bani, ya za'ayi ace sauri kamar Areef ya b'ata. Kukan da Annah taji shi yasa ta fito daga kitchen da gudu ta nufi d'akin Zaljameel hankalin ta a tashe, murd'a handle d'in Annah tayi ta fad'a d'akin, wajen Zaljameel ta nufa da ke rusar kuka mai ban tausayi, cikin kid'ima Annah ta fara tambayar Zaljameel meke faruwa. Rungume Annah Zaljameel tayi tana kuka, cikin sheshek'ar kuka Zaljameel ta fara yima Annah bayani cike da shagwaba. "Annah ya Areef bai dawo ba, tunda aka kawo ni ban ganshi ba, Annah zama nayi jiransa har bacci ya sace ni, yanzu ma na tashi ban ganshi ba, ta sake fashe wa da kuka. Turk'ashi! Annah tace a zuciyarta, wato dama Zaljameel bata san Yareema Jawad aka aura mata ba? Lallai akwai matsala. Dama tasan Jawad bazai zo wajen Zaljameel ba, saboda ba ita yake so ba dole aka masa. jin Annah tayi shiru yasa Zaljameel d'agowa ta kalle ta, fuskar sharkaf da hawaye, basar wa Annah tayi ta fara tafa hannu,"Kai amma Areef da shiririta yake, ai na zata ya miki waya tun a jiya". Zaljameel ta tsaida hawayenta ta zubawa Annah ido tana sauraron ta. Annah ta cigaba "jiya bayan na fita waje sunzo da abokanan sa, ina tsaye ina gaida shi aka masa waya hajiarsa bbu lpy, an kwantar da ita a hospital, to shine fa hankalin sa ya tashi ya fita bai fad'a miki ba. Ajiyar zuciya Zaljameel ta sauke, wayyo Allah sarki ai bai fad'a mini ba shi yasa hankali na ya tashi, Allah ya bata lpy. "Ameen" Annah ta amsa. Annah Zaljameel ta kalla, "Annah yaushe zamu je duba ta?". Wani zufa ne ya yankowa Annah ta fara magana, "Haba Zaljameel, waya fad'a miki amarya na fita, ai ita kanta mara lpy idan taji cewa kinje bazata ji dad'i. " Shikenan Annah Allah ya bata lpy "Ameen" Annah ta kuma amsawa. Annah tabawa Zaljameel labarin nan ne dan ta kwantar mata da hankali, sai dai abinda Annah bata sani ba tarewar Areef a kusa da gidan Jawad, shin Areef da Zahra zasu k'i shiga part d'in Zaljameel ne ko yaya zata kasance. Wayarta ta d'auka zata kira Areef Annah ta lura, Gimbiya mai zakiyi? Kallon Annah tayi, cikin sanyin murya tace! "kiransa zanyi Annah" Kirjin Annah ne ya buga ta kalli zaljameel! "Aa Zaljameel, ni dai a gani na karki kirashi, saboda bai kiraki ba, ina tunanin yana wani abun ne shiyasa kika jishi shiru, amma nasan duk inda yake hankalin sa yana kanki Gimbiya Zaljameel". Sanyar yar ajiyar zuciya Zaljameel ta sauke ta d'auke phone d'in a kunnenta ta fara k'ok'arin tashi a bed d'in, yatsina fuska tayi jin cikin ta ya murd'a she's feeling hungry, Annah ta kalla!. "Annah yunwa nake ji" baki Annah ta washe, Gimbiya Zaljameel ai dole kiji yunwa, gaskia kinsha bacci, dubi har rana tayi" Sake kallon window Zaljameel tayi, rana ta fito ta haske dunia. "Ai break fast d'inki ya kammala sai ki yi wanka kizo kice" "To Annah" mik'ewa Zaljameel tayi ta nufi toilet, sai da ta d'au wajen 30mint tana wanka sannan ta fito d'aure da towel a kirjinta, mirror ta nufa ta fara shafa, light make up tayi ta nufi gefen bed d'inta ta duba kayan da Annah ta zab'o mata, wani swiss lace ne, mai tsadar gaske, an mata d'inkin riga da siket, sun kama ta sosai, sun bayyanar da tsantsan kyan Zaljameel, d'auri ta kashe ta d'auki chewing gum mai k'amshin pineapple ta zuba a bakinta ta na tauna a hankali,dining area ta nufa. Nan ma yaji kayan alatu ya tsaru iya tsaruwa. Tana fitowa kuyangu suka fara bajewa suna gaishe ta, da sakin fuska ta amsa musu! parlour d'in ta k'arema kallo shima ya tsaro, an mishi decoration har yaso ma yayi yawa,ko ina fes sai kamshi dake tashi. murmushi Zaljameel tayi dan tana son taga ko ina tsaf kuma tana son k'amshi. Kuyanga d'aya taja mata kujera ta zauna cike da k'asaita, d'aya kuma tayi sarving nata abinda take so, bayan ta k'oshi ta nufi parlour ta zauna kuyangun ma suka zauna a k'asa. Yareema Jawad Zaune a fada gaban mai martaba, sanye yake da wani yadi irin shara sharan nanAsh colour, kansa da hula sumar sa ta kwanta luf, yayi kyau sosai. "An gaida Yareema mai jiran gado" bai kalli inda suke ba bai kuma ansa ba! ya gaida sarki cikin kulawa mai martaba ya ansa, a hankali ya fara magana irin ta sarakuna. "Yareema Jawad na kira ka ne dan in sanar da kai ya kamata ka karb'i hospital d'in nan dana sa aka gina maka ka cigaba da kula dashi, dan dama na rabo ka da London dan ka taimaka wa talakawan mu ne". Mamaki bayyane a fuskarJawad ya kalli sarki! "ranka ya dad'e dama an gina hospital ne?" "Eh Yareema nasa an gina hospital ansa masa sunan kai da Zaljameel, J&Z special hospital" Ji yayi gabansa ya fad'i jin sunan Zaljameel beautiful face d'inta ya bayyana a fuskar sa, wani smile yyi sannan ya gyara zama ya kalli sarki! " Nagode mai magana, Allah ya k'ara girma da d'aukaka" "Ameen" Sarki ya amsa, fadawa ma suka amsa. Tashi yayi bayan sun gama magana da sarki nan da one week zai fara zuwa aikin. Tafe yake ya nufi part d'insa Bala na biye dashi, phone d'insa da ke hannun Bala ta fara ringing, Bala ya duba yaga Areef, cikin sauri ya d'aga dan kar ya katse, ya mik'awa Jawad, karb'a Yareema yayi ya kara a kunnensa. "Ango! Ango! Ango na amarya" Areef ya fara tsokanar Jawad, murmushi Jawad yayi wanda sai da beauty point d'in sa suka lotsa ya fara magana!. " Areef ya a kayi ne? Ai banyi tunanin zaka kirani yau ba dan nasan ana chan ana kwasar soyayya" Areef da ke zaune a parlour sa Zahra Rungume a kirjinsa ya k'ara matseta a jikinsa, yana daria," Ha Jawad ai kaima kasan fad'a b'ata baki ne ya Amarya Zaljameel? Sai da Jawad ya d'auke wuta ya saci kallon Bala dan yasan bai maga Zaljameel ba, amma kuma bai san dalilinsa nayin hakan ba. "Tana lpy" To ka gaida ta, dama ina son fad'a maka ka shirya zamu je gaisuwar surukai da yamma, "Surukai?" "E surukai " " Gaskia Areef baka da hankali, Mom da Dad d'in zanje gaisarwa, gaskia bazan iyaba, sai dai na raka ka mu gaida Alh Zahradden " " Ok bbu damuwa tunda ka zama dan kanka, su d'au yarsu su baka kace baka zuwa ka gaida su, ka shirya kawai malam dole muje " Shiru Jawad yayi jin hakan Areef ya kashe wayarsa dan yasan Jawad bazai ce ya yarda ba zashi ba, amma shirunsa ya tabbatar masa daya gamsu. Alh Zahradden suka fara gaisarwa sannan suka nufi part d'in su Zaljameel. Mom zaune a parlour ita da Nawal! Nawal nata zuba mata rigima sai an kaita wajen Zaljameel, tana cikin bata hak'uri akan ta bari anjima zata sa akaita, sukaji muryar Jawad! Da gudu Nawal ta nufeshi tana "Oyoyo Uncle, wallahi sai ka tafi dani gidan ka naga Aunty Zaljameel, sai hawaye" D'aukarta yyi yana share mata hawaye, "haba Nawal! Indai akan zuwa ne to karki k'ara kuka dake zan tafi" Peck ta bashi a kumatu "Thanks my Uncle, dats why i love you". Sauke ta yayi ya nufi cikin parlour dan Areef da sauran Friends d'insu har sun zauna. Bajewa yayi a k'asa ya gaida Mom kansa a k'asa, kunyar Mom yake ji,bayan sun gaisa suka yi sallama suka tafi, tare da Nawal. Zaljameel zaune a main parlour d'in gidan tana duba pic d'in biki, sanye take da wani material green colour d'inkin doguwar riga, ta amshi jikinta, high neck aka mata duk boobs d'inta a rabinsa a waje yake, d'auri tayi emergency, jikinta na tashi k'amshi. Muryar da taji ta nufo parlour yasa numfashinta ya kusa d'aukewa, bata gama tunani ba taji sallamar sa a parlour ya shigo hannun sa rik'e da Nawal,Zumbur tayi ta mik'e tsaye tana kallon bayan Jawad ko zata ga Areef ya shigo, kallo d'aya ya mata ya d'auke kai ya nufi part d'insa, da gudu Nawal ta nufi Zaljameel da tsanin farin ciki, gaba d'aya tunanin Zaljameel ya birkice, to mai Jawad yazo yi part d'in ta,? wata zuciyar tace wajen Areef yazo, Areef d'in da bayana nan ta sake tunani! To ko ai koshi yayi ya d'auka masa wani abu, "Yeah hakane ma, ai ko shi yayi" zuciyarta ta gasgata hakan. Rungumar da Nawal ta mata ya dawo da ita tunanin ta, nan ta fara murna ta kuma kama hannun Nawal suka shiga ciki dan bata b'ukatar sake had'uwa da Jawad. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L A romantic love story 2017 July 2017 Wannan page d'in naki ne maman khady, Allah ya bar k'auna ya kara zumunci 👌🏻❤ Ina mik'a gaisuwa ga yan pure moment of life writers, kungiyar da bbu irin ta, Allah ya kara had'a kanmu ya k'ara mana son juna, Allah ya k'ara mana basira ameen. #ana tare💋. Chapter 47&48 Yareema Jawad na shiga room d'insa ya fad'a kan katafaren bed d'insa yana sauke ajiyar zuciya, surar Zaljameel yake hangowa cikin wannan rantsantsan material d'in, komai nata bayyane, boobs dinta daya hango cikin riga sun fi tafia da imaninsa, ni ko nace Jawad daga kallo d'aya,lol.pillow ya jawo ya hugging d'insa tight yana jin wani feelings na shigar sa, how long zai mallaki Zaljameel da gangar jikin ta? Tambayar daya dad'e yana yima kansa amma bbu amsa , a hankali yaji relief hakan yasa ya mik'e a bed d'in ya nufi toilet. Bayan ya fito yaji phone d'in sa na ringing, duba yayi ya ga Fulani, dan haka ya tattaro nutsuwarsa cikin fara'a ya d'aga. "Fulani barka da yamma" Murmushi Fulani tayi dan itama burinta ya cika Jawad ya auri Zaljameel, zama take gyara a kujerar ta ta karaga! "Jawad ina fatan zaka rik'e Zaljameel da amana, tunda kana sonta, kaga Zaljameel yarinya ce ba komai zata maka kace sai ka d'au mata ki ba, nasan ka sarai da d'aukar fansa, matar kace, duk wani responsibility nata yana hannun ka!" Jawad"! Fulani ta sake kiran sa, b'acin ran Zaljameel b'acin raina ne, wallahi kar naji kar na gani " Gyada kai yayi kamar tana ganinsa, "Insha Allah Fulani bazaki ji wani abun ba daidai ba "a zuciyar shi kuwa cewa yake haba Fulani, indai ba biyayya kike so nayi ma Zaljameel ba, kyace kar na b'ata mata rai? " tana ina Zaljameel d'in" Muryar Fulani ta dawo dashi daga tunanin daya keyi. Tashin hankali dabar bar cewa yayi ya fara kame kame," Am... Uhmmm dama sun fita ne parlour da Nawal ni ina d'aki amma ki kashe sai in kai mata" "A'a Jawad basai na kashe ba, kai mata kawai". Cikin rawar murya ya fara bayani! "Fulani yanzu na fito a wanka, ina son shiryawa ne sai na kai mata ". " Ok bbu matsala" ta kashe wayar zuciyar ta fal farin ciki, daga jin yarda Jawad ya amsa mata tana ganin sun samu jituwa da Zaljameel. Zaljameel zaune ita da Nawal akan sofa suna hira,"Aunty dama zaki iya tafia ki barni? "Ta had'e rai, ta juyama Zaljameel baya, daria Zaljameel keyi," Haba my sweery, ni dake ai bama b'aci, kinsan kullum tunanin ki nake, dama da kaina nace zanje na d'akko ki sai gaki kinzo " Juyowa Nawal tayi ta kalli Zaljameel,"Aunty ni zaki yima dad'in baki, gaskia ni ban yarda ba" ta cigaba da k'unci. Zaljameel ce ta fara yi mata chakul kuli, hakan yasa Nawal ta fara daria tana k'ok'arin guduwa, da gudu itama Zaljameel ta bita Nawal ta nufi k'ofa tana k'ok'arin fita sukaji an murd'a handle an turo! Yarda Zaljameel ke gudu ta rasa control hakan yasa taci karo da Jawad, sosai ta fad'a jikinsa tana koma k'ok'arin fad'uwa yayi saurin rik'e ta, "wani yar sukaji a jikinsu hakan yasa Jawad jikinsa ya mutu ya kusa sakinta ta fad'i, sai da ya tattaro nutsuwarsa sannan ya sake ta! Zaljameel tak'i d'aga kai duk a tunaninta Areef ne, jin k'amshin perfume d'in da bazata manta k' amshin sa ba yasa ta d'aga kai ta kalle shi, wani irin zabura tayi ta fara ja da baya, tsayuwarsa ya gyara yayi crossing hands fuskar shi bbu annuri. Tunawa da Nawal a room d'in yasa Jawad ya kalleta yana smiling," Baby Nawal je parlour akwai ice cream a fridge ki d'auka " Wani ihun murna Nawal tayi ta fita da gudu. Cikin tashin hankali Zaljameel ke ja da baya tana nuna Jawad da hannu, ganin ya fara takowa ciki yasa ta fara hawaye, cikin sanyin murya da ba komai zaka ji ba ta fara magana! " Ya Jawad mai kake yi a gidan nan, dan Allah dan annabi ka fita, kasan fa ni matar abokinka kace, duk da kai dan uwana ne shiga bedroom dina ya haramta a gare ka, komai kake nema kaje sitting room ka zauna gani nan" Cigaba yayi da binta har ta dangana da bango, hakan ne ya k'ara tashin hankalinta ganin bashi da niyar tsayawa, sai da yazo daf da ita har tana jin saukar numfashinsa, idonta ta runtse tana hawaye, wani irin k'arfine yazo mata ta ture Jawad da k'arfi ta fara k'ok'arin gudu, ji tayi ya rik'e hannun ta hakan yasa ta hassala, dan taga Ya Jawad na neman zubar mata da mutunci, Yanzu idan Areef ya shigo ya tarar dasu a haka mai zaice?. "Ya Jawad wallahi zan maka ihu idan baka cikani ba"jin sallamar Annah yasa taji dad'i a ranta, takarkare wa tayi da dukkan k'arfinta zata kwalama Annah kira Jawad yayi saurin rufe mata baki da hannunsa, k'ara tsorata tayi shi kuma ganin hakan yasa ya wullata gefen bed d'inta tana k'okarin tashi ta gudu ya k'araso! Cikin lion voice d'insa ya fara magana! "kar ki kuskura ki tashi, a tunanin ki mai zan miki, mai zanyi dake ballantana jikin ki, Kuma karki k'ara kiran Areef a matsayin mijinki tunda bashi aka aura miki ba, ni Jawad ni aka lik'awa auren ki, ya wani runtse ido alamun takaici ya cigaba!baki da gurbi a zuciyata, Zahra nake so an hanani aka bani ke, dan haka ki daina tunanin akwai abinda zai shiga tsakani na dake"wayarsa ya mik'a mata kin karb'a tayi dan tunda ya fara magana ta daskare a zaune, duk ilahirin jikinta rawa yake, idonta kuma na kallon fuskar Jawad, allahumma ajirni fi musibati, wa yukulufni khairan minha.hawaye ya gagari idonta, dan shima samun damane! Bata k'arasa tunanin ta ba taji muryarsa cikin tsawa "Karb'i mana" hannun ta ya mata nauyi hakan yasa ya d'aura mata wayar a hannun ta, Fulani zata yi magana dake, saura ki fad'a mata abinda zai tada mata hankali, idan haka ya faru Zaljameel! Gyada kai yayi alamun she will suffer. Zaljameel zaune kamar an dasa ta a wajen, zuciyarta na bugawa da k'arfi, taji phone d'in ta fara ringing, kallon phone d'in tayi amma bata da niyyar d'aga wa hakan ne ya hassala Jawad dake tsaye a kanta, phone d'in ya d'aga ya kuma gaida Fulani, "Jawad baka je wajen Zaljameel d'in bane na jika shiru" Hannun sa d'aya ya zura a aljihu ya kalli Zaljameel da idonta ke kallonsa har a lokacin, wani killer smile yayi ya cema Fulani, "Gatanan Fulani sai rigima take min wai bazata gaisa dake a phone ba sai dai na kawota" Murmushin jin dad'i Fulani tayi "A'a banda abin Zaljameel waya ce mata amarya na fita, ta bari dai ta kwana biyu sai ka kawota. Zaljameel da mamaki da al'ajabin abinda Jawad ya fad'a ma Fulani yasa Zaljameel ta rasa irin tunanin da zata yi, miko mata wayar yayi lokaci guda kuma ya b' ata rai karb'a tayi ta fara k'okarin saisaita nutsuwarta. Cikin dashewar murya ta gaida Fulani, jin muryarta ta chanja yasa Fulani ta zata ko dan Jawad ya hanata zuwa ne, nasiha ta mata sosai mai ratsa jiki akan tabi Jawad tayi masa biyayya a matsayinsa na mijinta , sannan ta kashe wayar. Sakin wayar Zaljameel tayi a k'asa ta kwanta a bed dinta ta fara kuka mai fidda tsantsan bakin ciki da damuwa, shikenan ta tabbata Jawad mijin ta ne, ita yau ta shiga uku, ina Areef yake? Mai ya hanashi auren ta ya bari aka aura mata wannan mara imanin, keeeeee......... Jawad ya kirata, dagowa tayi ta kalle shi, taso ki bani wayata ko a k'asa kika d'auka.mikewa tayi zaune ya kalle shi tunda ga sama har k'asa ta fara k'okarin mikewa ta sakko k'asa ta tsaya," Ya Jawad ka sani ni ba baiwarka bace, dan an aura maka ni baka sona ni an fad'a maka sonka nake, ban ma son kaine wanda kaddara ta zab' a mini ba sai yau, mai kake ji dashi kud'i ko sarauta, kasan nima a sarautar nake kuma a jinin jikina take yaw......... Bai bari ta k'arasa ba ya d'auke ta da kyakkyawan mari, bata dago kanta ba ya sake d'auke ta da mari. GANIN HAKA YASA NA KOMA GEFE NIMA NA DAFE NAWA KUMATUN DAN ZALJAMEEL TA MARU😰😢😳🙄🤔😭 SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Kuyi hakuri najin na shiru kwana biyu, hakan ya faruwa ne sanadin wani uzuri. Chapter 49&50 A gigice Zaljameel ta d'aga kanta hannun ta dafe a kumatun ta, hawaye ne masu zafi suka fara zarya a fuskarta, tunda take bata tab'a ganin anyi mari a gaban ta, amma yau ita aka mara, kuma ba Mom ba ba Dad ba, Jawad wanda Mom d'in ta ta bata labarin irin k'aunar da yake mata. Cikin dauriya Zaljameel tace, "Marina fa kayi Ya Jawad?" A hassale ya kalle ta," An mare ki d'in, ko zaki rama ne? "ya cigaba da magana. Keeeeee.... Zaljameel kike ko wa? Daga rana irin ta yau karki kurkura ki sake gangancin fad'an magana, wanda ya fiki ma yayi kad'an ballantana ke da wata hausar ta kamar an mata dole sai tayi, yana kaiwa nan ya ja tsaki ya fice a d'akin ransa a mugun b'ace. Fad'awa bed d'in ta tayi ta fashe da wani irin kuka na ban tausayi, mai yasa parent d'in ta suka mata haka, wane irin laifi ta musu da suka hanata Areef suka d'aura mata aure da Jawad ? mai yasa Anna tayi mata k'arya?. Duk tambayo yin nan Zaljameel ta rasa ansar su, hakan yasa ta tashi ta nufi parlour inda taji muryar Anna da Nawal. Yareema Jawad na shiga bedroom d'insa ya saka ke ya zauna akan sofa ya dafe kansa da hannu biyu, tuna marin da yama Zaljameel yayi da hawayen daya zuba a fuskarta saboda shi. Runtse ido yayi yana jin zuciyarsa na tafasa mik'ewa tsaye yayi dan jiyay zaman ya gagare sa, hannun sa ya kalla, yana jin kamar ya cire hannun, wannan hannun shi ya mari Zaljameel! Sunshine d'insa,no...... Ya furta da k'arfi ya sake zama a sofa yana mai da numfashi, yayi dana sanin abinda ya aikata,a hankali ya mike ya nufi bathroom. Annah tsaye a kitchen tana had'ama Zaljameel dinner, ita da Nawal sai hira suke, ji sukai an bankad'a kofar kitchen d'in, a firgice Annah ta juyo, ganin Zaljameel da hawaye a fuska yasa kirjin Annah ya buga, barin abinda take yi tayi ta nufi Zaljameel hankalinta a tashe, zub'ewa Zaljameel tayi a k'asan kitchen d'in ta zauna dab'as, Annah na zuwa ta lura da fuskar Zaljameel da tayi ja ga kuma alamar hannu, abinka da farin mutum. Cikin kid'ima Annah ta durkushe gaban Zaljameel tana tambayar ta wanda ya mareta,Nawal ma zama tayi a jikin Zaljameel ta fara kuka. "Gimbiya Zaljameel waya mare ki?" Cikin sheshek'ar kuka Zaljameel ta fara yima Annah magana! "Annah, dama Ya Jawad aka aura mini ba Areef ba?" Dam kirjin Annah ya buga ta kalli Nawal da hawaye ya wanke mata fuska "Nawal je parlour ki zauna gamu nan zuwa" Badan ranta yaso ba Nawal ta nufi parlour tana share hawaye. Gumi ne ya tsattsafowa wa Annah ta, bata damu ta share ba ta fara bayani, "Eh Zaljameel shi aka aura miki" "Annah dake aka Had'a,baki aka aura mini Jawad, Anna mai yasa baki fad'a mini ba na nemi yanci na tun kan a d'aura mana aure da azzalim.......Anna bata bari Zaljameel ta k'arasa ba ta rufe mata baki, Allah ya huci zuciyar Gimbiya, karki manta Jawad mijin ki ne yanzu, magana irin wannan bata dace ki fad'a masa ba, ina jiye maki fushin Allah. Kallonta Zaljameel tayi cike da tuhuma,"Annah da wane suna ya kamata na rika shi banda hakan?, Anna tunda aka haife ni ba'a tab'a marina na ba sai yau da Ya Jawad ya mare ni" Shiru Annah tayi, "Jawad d'in ya mare ki,?" E Annah "Zaljameel ta fad'a ta d'aura hannun ta a fuskarta tana tuna saukar hannun Jawad a fuskarta. KUYI HAKURI DA WANNAN ZAN MUKU TYPING MAI YAWA INSHA ALLAH. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Kuyi hakuri my fan's, akan jina shiru da kukayi kwana 2, hakan ya faru ne sanadin uzuri da ya sha kaina, duk da ban gama ma amma wannan page d'in naku ne dan sanya ku nishadi.💃🏻 Ilysm ❤ Chapter 51&52 Wani kuka ta sake fashewa da shi,"Annah ki taimaka mini ki sa a raba aurena da Ya Jawad, bazan iya zama dashi ba". Annah jikin ta yayi sanyi, marin da Jawad ya yi ma Zaljameel ya b'ata rai, ai marin mace bashi da kyau ballantana, tana matsayin matarsa, wani dogon numfashi Annah taja ta kalli Zaljameel! "Wallahi Zaljameel ban san komai game da aurenki ba sai bayan an d'aura auren ku da Jawad, kinsan matsayina a gidan nan, duk da sarauniya Ayshat ta bani dama ta 'yanta ni amma ban daina muku hidima ba, babu yarda zanyi na hana abinda Allah ya tsara, Allah ya rubuta Jawad shine mijin ki,ina me baki hak' uri Zaljameel, tabbas ba'a baki dama ba, sai dai dama budurwa bata da 'yancin zab' ama kanta miji sai dai iyayenta su zab'a mata, Zaljameel, ni na san Jawad na san halin Jawad, dan ko Fulani maryam bazata fad'a mini halin Jawad ba, xan sanar dake hanyoyin da zaki bi ku zauna lpy, ki kuma shawo kansa, Jawad namiji ne, namiji kuwa yaro ne a hannun matarsa, ke zaki yima Jawad sabuwar tarbiyya Zaljameel, ke zaki d'ora shi akan hanya kuma dole yabi" Shiru Annah tayi tana kallon Zaljameel data zuba tagumi tana sauraron ta. Murmushi Annah tayi ganin yarda Zaljameel ta bada attention tana sauraron ta, hakan ya bawa Annah damar cigaba da magana. "Zaljameel bani kunnen ki kiji" matsowa Zaljameel tayi Annah ta mata rad'a, wani shu'umin murmushi Zaljameel tayi tama Annah godia. Mik'ewa tayi ta nufi bedroom d'inta,a parlour ta tarar da Nawal ta gama kukan ta ta b'ige da kallon cartoon harda tuntsira dariya, tana ganin Zaljameel ta mik'e tayi wajen ta da gudu suka shige ciki. Annah kam dad'i ya kamata ta shawo kan Zaljameel, sai dai abinda Annah bata sani ba, yayin da take bama Zaljameel shawara a kunne a yayin Zaljameel ta tuna da nata idea d'in,tayi watsi dana Annah, hakan ne yasa ta murmushin jin dad'i. After one week Tunda ga ranar da Jawad ya mari Zaljameel basu k'ara had'uwa ba, cuz ya fara zuwa hospital, hakan yasa ya shiga damuwa ya kuma fara tunanin taya ya zai had'u da sunshine d'insa. Zaune yake a office d'insa na alfarma, yayin da sanyin Ac ke kad'ashi,sanye yake da maroon suit gashin kansa ya sha gyara sai kyalli yake, glass cup a gaban sa wanda aka zuba masa hot coffee a ciki, sha yake kamar baya so dan tunanin Zaljameel ya hanashi sukuni, zuciyarsa na azalzala shi akan yaje ya nemi forgiveness d'inta, a hankali ya furta no.. It will never happen, ace na bama Zaljameel hak'uri ai na siyama kaina raini, zan cigaba da jurewa har ranar da Allah zai sanya mata sona a zuciyar ta". Zaljameel zaune a parlour, sanye take da Arabian gown peach colour da taji stones, tayi rolling kanta da light blue veil, tayi make up sosai a fuskarta, jikin ta sai tashin k'amshi yake kamar kullum, tayi wani fresh da ita dan Annah na matuk'ar k'ok'ari akan Zaljameel tana kuma k'ara kwantar mata da hankali, hakan yasa Zaljameel ta saki jikin ta tayi dan ki'ba abinta. Tsaye take ta bama door d'in parlour baya tana kashe selfie, sai chanja style take yi tana kama waist da hannu d'aya tana d'auka pic d'in, tayi kyau sosai, sai da ta dauki yakai 50sannan ta fara k'ok'arin hak'ura dan ta fara gajia, tana kashe selfie na last ta duba pic d'in wa zata gani! Ya Jawad tsaye da phone a hannunsa d'aya hannun da briefcase, Murmushi a fuskarsa, a pic d'in amma Zaljameel na juyawa ya had'e rai, mak'ala phone d'in yayi a kunnen sa ya fara magana "Bala mai yasa kake hakane, sau nawa kake so na fad'a maka," tsaki ya ja ya kalli Zaljameel data yi mutuwar tsaye, a hankali taja k'afa ta fara tafiyarta mai d'auke da jan hankali,duk wani sassa na jikin ta kad'awa yake yi. Ganin ta fara tafiya yasa Jawad ya daka mata tsawa," keeeeee..... Zaljameel zo zo nan "tsayawa tayi chak amma bata juyo ba, hakan ya hassala Jawad, cikin zuciyarsa ya fara magana" Anya Zaljameel bata ganshi ba kuwa lokacin da yake kallonta? "rasa amsar tambayar yayi hakan yasa ya cigaba da magana. Baki iya sannu da zuwa ba baki iya k'arbar briefcase na miji ba? Ya fad'a fuskarsa a had'e. A hankali ta juyo ta kalle shi,eyes to eyes sukayi da Zaljameel for some minutes! Wani far Zaljameel tayi da ido tayi wani shu'umin murmushi duk da k'irjinta na bugawa dan bata san abinda zaije yazo ba ta fara magana! "Eyyah ya Jawad, laifin ka ne da baka fad'a mini tun wuri kana da buk'atar hakan ba, so yanzu gaskia bani da time d'in wannan cuz baya cikin agender na na yau da kullum, ina ganin ka tara next time" Murguda masa cute mouth dinta tayi ta bar wajen da sauri kar tasha bugu. Mamaki bayyane a fuskar Jawad akan maganar da Zaljameel ta fad'a masa, ko a mafarki bai tab'a tunanin Zaljameel ta iya magana haka ba, lallai sai yayi da gaske, in ba haka ba raini zai shiga tsakanin sa da Zaljameel. Bedroom d'insa ya nufa ransa a dagule. Zaljameel na shiga d'akin ta ta lek'o taga ko Jawad ya bi bayanta, ganin bashi yasa tayi saurin zura key ta nufi bed dinta ta kwanta tana murnar abinda tama Ya Jawad, tasan yarda yake dan girman kai da jiji da kai yana chan ya hassala, wata dariya ta fashe da ita, "Ya Jawad" ta furta a hankali, ji tayi sunan ya mata dad'i hakan yasa taji tana sha'awar sake kiran sunan, "Ya Jawad" ta sake maimaita wa, shiru tayi kamar mai nazarin wani abu sai kawai ta d'auka wayarta ta fara ganin pictures. Pictures ta gani nata birjik da ita da Ya Jawad, yarda tayi fara'a haka shima, babu wanda zaiyi tunanin ba tare suka d'auka ba, sunyi kyau sosai, tsayawa tayi tana kallon face d'in Jawad, murmushin da yayi ya k'ara ma fuskarsa kyau, cikin zuciyarta take magana! "Dama Ya Jawad ya dad'e da shigowa parlour amma bata ji shigowarsa ba?" Zuciyarta ta bata amsa,! " Yeah Zaljameel ga alama kin gani a pic " " To murmushin mai yake yi?" maybe da fara'arsa ya shigo aka yi sa'a kika d'auka pic d'in". Yes.... Hakane ta fad'a tana kuma kallon pic d'in,sallamar data ji yasa ta d'aga kai dan ta tabbatar. "Zahra" Zaljameel ta fad'a da karfi ta mik'e tsaye, bata bari Zahra ta k'arasa shigowa room d'in ba ta tare ta da gudunta!" Zahra where are you?, Zahra ina nemanki ina son a warware mini dalilin aurena da Ya Jawad da kuma dalilin daya hana aurenki da shi ". Kallonta Zahra tayi tana murmushi, ohhh... Ni Zahra, Zaljameel dama haka Mom ta koya miki ki dinga karb'ar bak'i, Zahra ta fad'a tana rik'e baki. Kunya ce ta kama Zaljameel, hannun Zahra ta kama suka zauna a kan sofa,Zahra yi hak'uri, na dad'e ina son ganin ki muyi magana amma na rasa wannan damar, gani nake kamar zaki tafi baki bani amsar tambaya ta dats why kika ga na fara tambayr ki". "Babu komai Zaljameel ykk?" " Zahra ba lafiya ba, Zahra ya akai Ya Jawad ya zama mijina shi nake son sami" zama Zahra ta gyara ta fara bama Zaljameel labarin yarda akayi. Mik'ewa tsaye Zaljameel tayi "A'a Zahra, gaskia baki fahimta dai dai ba,babu son ya Jawad a zuciyata, Zahra mai yasa kika hak'ura da farin cikin ki saboda ni, wane hallacci na miki a rayuwa da kika mini hakan,sai dai kash, na so ace kamar yarda ku kayi tunanin ina son Jawad ace da gaske ina sonsa, kuma naso ace da gaske shima yana sona ". Zama tayi tana shartar hawaye, cikin sanyin jiki Zahra taja Zaljameel jikin ta ta fara lallashi," Zaljameel mai ya faru tsakanin ki da Jawad a dan zaman da ku kayi da har kika yanke masa hukuncin baya sonki". Tun daga ranar da aka kawo ta ta fara bama Zahra labari har zuwa yau, shiru Zahra tayi tana nazarin labarin Zaljameel, Murmushi Zahra tayi ta kalli Zaljameel............ Ku biyo ni dan jin mai Zahra zata cema Zaljameel 👂🏻👀 SUMYN BASH CE 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L We don't just entertain we touch the heart of the readers. A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 53&54 Tsaf Zahra ta k'arema Zaljameel kallo, sosai ta k'ara tabbatar da soyayyar da Zaljameel kema Ya Jawad, sai dai ga dukka alamu Zaljameel bata san ta kamu da soyayyar ba. gyara zama tayi ta kalli Zaljameel tana murmushi! "Zaljameel gaskia kinyi mini dai dai abinda kika yima Jawad, kar ki kuskura ki nuna kina tsoron sa, ina san ki dake zuciyarki ki kwaci yancin ki a wajen Jawad, karki yarda ya k'ara marinki ko da wasa, kefa macece Zaljameel, Allah yayi ki da kyan sura, gaki kyakyawa wacce duk wani namiji mai lafiya idan ya ganki sai ya yaba" Shiru Zaljameel tayi tana sauraron Zahra, a zahirin gaskia bata gane mai Zahra ke nufi ba, murmushi tayi ta kalli Zahra "Zahra ban gane mai kike nufi ba, ki fahimtar dani a yaren dazan gane" Daria Zahra tayi, Zaljameel kenan ke yarinya ce, kuma baki son komai ba, amma zan sanar dake yanzu ki gane kamar yarda kika buk'ata" "Zuba ma Zahra ido Zaljameel tayi, matsowa Zahra tayi a dai dai kunnen Zaljameel ta rad'a mata wani abu dani kaina bansan menene ba! A razane Zaljameel ta d'aga kai ta kalli Zahra, fuskarta na bayyanar da tsoro," What are you saying Zahra? I can't gaskia bazan iya abinda kika fad'a ba har abada, so kike ya raina mini hankali? Gaskia bazan iyaba ki bani inason wata shawarar ba wannan ba. Dafa k'afadar ta Zahra tayi a hankali ta fahimtar da Zaljameel, Zaljameel ta yarda da shawarar Zahra ta kuma ce zata gwada, a haka sukayi sallama ta tafi gida. Bathroom Zaljameel ta shiga ta fesa wanka, d'aure take da towel ta nufi wardrobe, side d'in English wears ta fara dubawa dan dama tunda tazo gidan bata saka su ba. Wata ficiciyar riga yellow ta d'auka mai siririn hannu iya gwiwarta take ta kama jikinta sosai, hakan yasa hips d'in ta ya zauna das a rigar, raba gashin kanta tayi biyu, tayi 2 babies, tayi light make up, Arabian perfume ta fesa ta kalli kanta a mirror, a hankali ta furta "Wow" dan ita kanta taga irin kyan da tayi, sai dai bata tunanin zata iya fita Ya Jawad ya ganta a haka! Ta fi 15 mints a tsaye a kofar room dinta amma ta kasa fita, tsoro da fargabar abinda zai je yazo ne ya shige ta, wata zuciyar ce tace mata, "Haba Zaljameel, wannan abinda zakiyi kwatar ma kanki yanci zakiyi, kuma ai mijinki ne" Cikin dakiya Zaljameel ta mird'a handle ta fita. Kwas Kwas take taka tiles d'in parlour da wani high hill a k'afarta, fridge ta nufa ta d'auka ice cream sannan ta zauna a 2cter ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya, kallo take a mbc 3 ana Tom and Jerry tana kwasar dariya, a hankali taji an mird'a handle, Ya Jawad ne ya shigo hannunsa d'auke da briefcase da alama daga office ya dawo, kallo d'aya ta masa ta dauke kai ta maida hankalin ta ga TV, baki da hanci Ya Jawad ya saki yana kallon tsantsar kyan Zaljameel, idonsa ne ya sauka a santala santalan cinyoyinta wanda sai da ya had'iye wani yawu kut! Gaba d'aya yayi mutuwar tsaye Zaljameel ta gama kashe shi. Jin maganar Areef da friends d'insa da suka taho tare ya fargar da Ya Jawad, Zaljameel ma kam ta tsorata da jin muryar maza a baya amma ta share cuz tana son ganin mai zai faru ta cigaba da kallon TV amma a zahirin gaskia kallon take ba kirjijnta ke bugawa yarda k'artar maza zasu ganta a haka. Matarsa Zaljameel ita maza zasu kalla a haka, nan da nan wani mugun kishi ya rufe shi, da yayi niyar barin ta mazan su shigo su ganta haka, amma gaskia bai iyawa. Cikin wani irin zafin nama Jawad ya saki briefcase d'insa a k'asa ya nufi inda Zaljameel ke zaune, sosai buguwar kirjijnta ya k'aru tana addu'oin neman mafita a ranta,yana k'arasawa dai dai ita bai tsaya dogon zance ba ya d'aga ta chak ya nufi bedroom d'inta! A razane Zaljameel ta fara k'ok'arin kwatar kanta tana dukan kirjin sa akan ya sauke ta, "Ya Jawad me haka? Ka sauke ni bana so" bai saurare ta ba sai da ya shiga da ita room d'in dai dai nan kuma su Areef suka k'arasa shigowa dan sun tsaya gaisawa da Bala. Jawad yak'i sauke Zaljameel, tsaye yayi tana hannunsa suna kallon kallo, wani abu sukaji yana tsarga musu tun daga kai har k'afa, idonsa ya mayar kan breast dinta da suka tsaya chak, kwayar idonsa Zaljameel tabi da kallo tana son ganin mai yake kallo, ganin yarda ya k'urama kirjin ta ido yasa ta jin kunya. sun dau wajen 5 mints a haka a hankali ya taka ya shiga sosai cikin bedroom d'in, wani sanyanyan k'amshi ya bugi hancin Jawad a hankali ya lumshe idonsa kasancewarsa mutum mai son k'amshi, kamar wanda aka tsikara yayi firgit ya dawo hanyacinsa. direta yayi a tsakiyar gadonta, idonsa ya rikid'e ya koma ja tsabar b'acin rai, a hassale ya fara magana" Keee waya baki izinin fita main parlour da wannan shigar? " Wani murmushi Zaljameel tayi ta kalli Ya Jawad! " Dama sai an bani damar sa irin suturar da nake so "? tayi wani far da ido, cikin sanyin muryar ta mai dad'in sauraro ta d'aura, "Haba Ya Jawad, maiyasa kake son takurama rayuwa ne, gaskia ka fita a harkata nayi rayuwata yarda nake so cuz ban takura ka ba kaima" ta karashe maganar a ciki. Cikin b'acin rai Jawad ya nufi Zaljameel, tashi tayi tsaye a gadon ta zuba masa idanunta masu mantar dashi damuwa, jiyay ya kasa d'aukar mataki a kanta, hakan yasa ya buga tsaki ya fita a dakin. Wani tsalle Zaljameel tayi a bed d'in ta dire tana murna, "Yes, gaskia naji dad'in shawarar Zahra, Ya Jawad ka shiga uku, sai ka tattara kayanka kabar gidan nan dan bak'in cikin ni Zaljameel, wayarta ta d'auka ta kira Zahra ta bata labari abinda ya faru Zahra ma kam tayi murna da jin haka," yawwa Zaljameel wannan had'uwa ta farko kenan, saura ta biyu, nan Zahra ta kuma bama Zaljameel shawara amma bata bari naji ba. A kunyace Jawad ya fita a part d'in Zaljameel cuz friends d'insa na main parlour a zaune basu shiga ciki ba, suna ganin sa suka fara tsokanarsa, "Kai mutumi na baka da dama, wato tsabar gajen hakuri briefcase d'in ma a bakin k'afa aka yarda ta, Areef ne mai fad'an haka sauran friends suka fara dariya suma. Jawad bai iya cewa komai ba, cuz Zaljameel ta gama tayar masa da hankali, ba surutu yake buk'ata ba yana son ya huta ne kawai,zama yayi shima a parlour ya d'aura kansa a saman cushion yana tunanin Zaljameel. Jin K'ofar part d'in Zaljameel ta motsa yasa Jawad bud'e idonsa tar dan tabbatar da hakan, jin tafiya yayi hakan yasa ya juya da red eyes d'insa suka had'a ido da Zaljameel! Sanye take da brown hijab mai hannu har k'asa, ta nufi parlour. A kusa da Ya Jawad ta zauna dab dashi tana murmushi, d'ago ido yayi ya maka mata harara Zaljameel ta maida masa da murmushi, Cikin sanyin muryar ta ta gaisa da friends d'in Ya Jawad, rintse ido yayi jin muryar Zaljameel na fita tana gaisuwa da friends, muryar matarsa a sadaka wasu suke ji, jiyay zuciyarsa na tafarfasa kamar zata cire, ganin yarda take musu murmushi Jawad yaji kamar ya rufe ta da duka ko zai huce. Mikewa tayi ta nufi kitchen dan had'a musu abinda zasu ci, cuz yanzu Anna bata fiya zuwa gidan ba, kuma kuyangun ma basu zama a gidan dasun gama aiki suke tafiya. KUYI HAKURI DA WANNAN SUMYNBASH CE💋🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L We don't just entertain we touch the heart of the readers A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 55&56 Bayanta yabi sa kallo, duk da babban hijab d'in dake jikin Zaljameel bai hana mazaunan ta juyawa ba, cikin ziciyarsa ya fara magana "Yanzu haka zata d'auka abu ta kuma kawo wa friends d'insa bayan jikin ta na showing, tashi yayi yabi bayanta. Tsaye take a kitchen tana had'a snacks da drinks, a landline ta kira d'aya daga cikin kuyangun ta dan ta jera mata kayan, tazo shiga Ya Jawad yazo shiga, hakan yasa tayi baya jikin ta ya fara b'ari kamar an sa mata shocking ta fara gaida Jawad, bai bi ta kanta ba ya shige kitchen d'in. Jin mutum ya shigo yasa Zaljameel bata waiwayaba ba cux tasan tayi waya, magana ta cigaba, "Yawwa Lantana zo ki tayani had'a kayan nan mijina ne yayi bak'i, wani murmushi Jawad yayi ya nufi inda Zaljameel ke tsaye, ta baya ya zira hannunsa ya kama k'ugunta ya juyo da ita suna facing juna, sosai ta razana amma ta basar,! " Ya Jawad kana buk'atar wani abu ne?, cikani please sai in d'auka maka" ta fad'a da wata irin murya da ita kanta bata san ta iya taba saurin sakinta yayi ya yayi kicin kicin da fuska, ita kam Zaljameel fuskarta d'auke da murmushi da har sai da beauty point dinta duka lotsa, ta zuba masa dara daran idanunta, saurin d'auke kai yayi daga kallonta, hannunsa d'aya yasa ya kama danyatsan ta ya murd'a har sai da yayi k'ara! K'as, ji tayi kamar ta saki ihu dan azaba. Cikin wata irin murya mai wuyar fassararuwa ya Jawad ya fara magana, "Zaljameel baki jin magana yanzu ko? Waya baki izinin zuwa ki gaisa da su ballantana har ki had'a musu abinda zasu ci? Da chan da suke zuwa gidan ke kike basu?" Jin tayi shiru yasa ya kuma murd'a hannun, wata k'arar da bata shirya ba tayi dan azaba, hannun ta ta rik'e ta kalli Ya Jawad cikin muryar tausayi tace "Please Ya Jawad let me go, kaga munbar mutane a zaune, idan sun tafi ko ma menene sai ayi". Tausayi ta bashi ganin yarda idonta yayi ja, hakan yasa ya cikata, bai fita a kitchen d'in ba sai da ta had'a komai a babban tray, Ya Jawad ya mik'a hannunsa ya d'auka d'aya sai da bisa da kallon mamaki sannan ta d'auka nata, jiran ta yayi suka fita tare. Jerawa sukayi har k'afadar su na gogan ta juna suka nufi parlour, a center table suka ajiye! Mazauninsu nada suka koma,hannun ta Ya Jawad ya kama ya rik'e cikin nashi yana wasa da zara zaran yatsunta da suka sha jan lalle,ga wata azurfa mai kyau da ring na gold mai bala'in tsada,sosai tayi k'ok'arin kwacewa amma ta kasa hakan yasa ta hak'ura. Zaljameel ta gama sarewa da al'amarin Jawad,Anya ba talala ya mata ba, gaskia kafin bak'in nan su tafi zata samu ta gudu kar reshe ya juye da mujiya. Kallonsa tayi ta kuma sakar masa murmushi, adai dai kunnesa ta masa rad'a "Ya Jawad ina son na shiga bathroom, please" Kallonta yayi yaga ta wani b'ata fuska kamar gaske, a hankali ya cika hannun ta kamar bayaso, "Thanks Ya Jawad" ta fad'a ta nufi part d'inta da sauri. "Chaiiii Jawad gaskia kunji dad'i kai da Zaljameel, a gaban mu ma baza'a hakura fa soyayya ba?" Murmushi Jawad yayi ya lumshe idonsa yana shafar man's pride d'insa daya kwanta luf, "A bayan idonku kake so muyi?" Dariya Areef yayi a'a Romeo and Joliet kuyi sha'anin ku wallahi. Dariya friends d'in suka saka, Jawad kam hankalin sa na kan Zaljameel, smooth d'in hannun ta ya tuna kamar bata d'aukar komai dashi, a hankali ya furta "Kin had'u Zaljameel". Su Areef basu bar gidan ba sai dare, Zaljameel kam bata k'ara fita ba, key ma ta zuba a room d'in dan kar ya Jawad ya shigo, wanka tayi ta shirya cikin wasu purple sleeping dress, yar yalolowa ce, mai siririn hannu, iya karta cinyar ta. Bayan ta gama shirya wa ta d'ane bed tayi dai dai abinta suna chat da Zahra har bacci ya d'auke ta. Cikin tane ya murd'a mata a cikin bacci, wani zabura tayi cuz bata tab'a jin ciwon ciki irin wannan ba, rik'e cikin tayi tana murk'ususu, a haka ta fad'o k'asa, ji tayi numfashinta na barazanar fita a jikin ta a hankali taja jiki ta nufi k'afa, sai da taje jikin kofar sai ta kasa mik'ewa tsaye ta jingina da k'ofar, kuka take sosai tana rik'e da cikin ta! "Wayyo ciki na! Wayyo zan mutu Ya Jawad" Kamar a mafarki yaji ihun Zaljameel, kwance yake a main parlour dan ya kasa shiga ciki, haka Bala ya gama nacin sa akan Jawad ya tafi part d'insa amma yak'i yayi kwanciyarsa a parlour. Firgit yayi ya tashi zaune, "Please ya Jawad come and help....... Bata k'arasa ba yaji dif kukan da maganar sun tsaya. Wani irin tsalle yayi ya dura ta bayan 3cter ya nufi room d'in Zaljameel, murda handle d'in yayi yaji shi a rufe da key!" Zaljameel! Zaljameel "ya fara kiran sunan ta a kid'ime, duk ilahirin jikinsa rawa yake," Zaljameel bud'e mini mana let me help you "dai dai nan numfashinta daya d'auke ya dawo, ta sauke ajiyar zuciya da yaji ta har kunnesa, ganin tsayuwar babu amfanin da zata masa yasa ya nufi d'akin Bala ya bashi spare keys, cikin magagin bacci Bala ya bama Jawad keys amma ya kasa tambayar sa mai ke faruwa. Da gudu ya nufi room d'in ya saka key ya bud'e, jinta yayi jingine jikin door d'in a hankali ya tura harta bud'e, "Hannu Jawad ya d'aura akai ya furta" innalillahi wa'inna ilaihi raji'un "ganin Zaljameel kwance babu alamun numfashi a tare da ita. Hawaye ne ya fara zarya a idonsa da gudu ya nufi inda first aid box yake dan bata taimakon gaggawa. Allurai ya fara mata yayi mata duk abinda ya kamata na gaggawa, d'aukarta yayi chak ya kaita bed d'inta ya kwantar, tsaye yayi yana k'are mata kallo, "She look sexy ya fad'a a ransa". Tundaga k'afarta Jawad ke k'arema ta kallo har fuskarta, idonsa ya sauka a kan cute mouth d'inta,sunyi pink dasu kamar ta shafa lipstick, idanunta a rufe eye lashes d'in ya kwanta luf ya kuma k'arama fuskar tata kyau. Zama yayi a gefenta yana shafa gashin kanta "I love you Zaljameel, please karki tafi ki barni, can't do without you my sunshine, kece farin cikina, burina bai wuce zuciyarki ta fad'a sona ba , ni Kuma na bayyana miki tsantar san da nake miki" Peck ya bata a lips d'in ta y zauna ya d'aura kanta a cinyarsa yana shafa kanta a haka bacci b'arawo ya kwashe shi. Asuba Idon Zaljameel ya fara bud'ewa a hankali, jinta tayi jikin mutum mik'ewa zaune tayi jikin ta babu kwari, ganin Jawad tayi zaune yana bacci ga kanta a cinyar sa, tsorata tayi, "Mai ya kawo Ya Jawad d'akin ta?" a hankali ta fara resuming komai, "Omg" tace ta kalli Jawad, a zaune ya kwana saboda ita, wane irin matsayi gareta a zuciyar Jawad, kardai abinda Zahra ta fad'a mata gaskia ne? Ta rasa amsar tambayoyinta. Allah sarki Ya Jawad, sosai taji tausayin sa a ranta, man's pride d'in sa ta shafa tana murmushi dan yarda yake masa style yana burgeta, pillow ta saka a hankali ta kwantar da Ya Jawad. Mik'ewa tayi ta nufi toilet, sai a lokacin ta tuna da irin yanyin kayan dake jikin ta, kunya ce ta kamata ta shige toilet da sauri kar Ya Jawad ya farka.wanka tayi da alwala ta fito sad'af sad'af dan kar Jawad yaji takunta ya tashi. Jallabiya ta zuba ta saka hijab ta shimfid'a prayer mat ta tada sallah. Bayan ta idar ta zauna adkar, bayan ta gama ta fara karatun Al'qur'anil kareem, kira'a mai dad'i ta keyi, cikin bacci Jawad yaji muryar Zaljameel na karatu, a hankali ya bud'e idonsa tar, inda Zaljameel take ya kalla, sosai ta masa kyau, hijab d'in ya karb'eta. Yunk'urawa yayi ya tashi tsaye zai bar room d'in yaji k'afarsa ta rik'e, ta masa tsami, ba shiri ya koma ya zauna. Zaman da yayi ya ja hankalin Zaljameel ta kallo wajen, ganin yana ya mutsa fuska yana kallon k'afarsa yasa tana kai Aya ta tsaya, tashi tayi a ajiye Al'qur'an d'in ta nufi bed inda Jawad ke zaune. Had'e fuska yayi ya kalleta, "Lafiya" yace da ita ganin tana kallonsa, "lafiya lau Ya Jawad, gani nai kana kallon k'afarka ko lafiya?" "Eh lafiya lau" ya fad'a yana k'ok'arin mik'ewa tsaye, sauri yayi ya zauna dan azaba. "Sannu Ya Jawad" Ko kallonta baiyi ba ballantana ya amsa mata, hakan ne ya bata haushi amma ta basar cuz ya mata mutinci itama. "Ko zan iya taimaka maka". "A'a babu buk'ata" Zaljameel fa ta fara hassala, hakane ma yasa ta kyale Jawad ta hayewarta bed d'in ta gefe d'aya chan ta kwanta sai dai bacci ya gagari idonta, tasan Jawad ba buk'atar taimakon ta amma shegen girman kansa bai barinsa. Tana sak'e sak'e a kwance bacci ya d'auke ta. A hankali Jawad ya taka ya nufi part d'insa, wanda Bala ya gaji da jiransa k'ofar d'aki ya nufi masjid. Bathroom ya shige yayi wanka yayi alwala ya fito, k'afar ta saki hakan ya bashi damar saka Jallabiya ya tada sallah a gida dan jam'i ya wuce shi. Zaljameel zaune a gaban dressing mirror, ta yi light make up, sanye take da k'arama riga ash colour mai hannu d'aya, tana da tsaga a gefen cinya, kusan rabin breast d'in ta a waje yake, kama gashin ta tayi ta tufke, yunwa take ji hakan yasa ta nufi dining room. Zaune yake a dining table yana yin breakfast, ya shirya cikin wata orange shirt and black tree quarter, sai tashin k'amshi yake yi. Gaban Zaljameel ne ya fad'i "anya zata iya zama cin abinci bayan ga ya Jawad a zaune?" Why not? D'aya zuciyar ta bata ansa. Dake zuciyarta tayi ta nufi dining d'in tana tafiya mai d'aukar hankali harta k'arasa. K'amshin perfume d'in tane ya mata sallama, basar wa Jawad yayi ya cigaba da cin abincinsa, kujera taja ta zauna tayi crossing leg, da k'afarta Idon Jawad yayi tozali, wani takalmi ne mai bala'in tsini yana da igiya an d'aure ta sama,ga cinyoyinta sai kyalli suke, gaba d'aya ya kare mata kallo bai bari ta lura. Jiyay zaman wajen ya isheshi abincin ma ya k'oshi. Kallonsa Zaljameel tayi ta lumshe idonta a hankali tana jin wani abu game da Ya Jawad a zuciyar ta amma ta rasa gane menene. Cikin sanyin muryar ta ta furta "Ya Jawad ina kwana" bai kalleta ba ya amsa da lafiya lau ya mik'e zai bar wajen "Thanks Ya Jawad for saving my life" Chak ya tsaya, juyowa yayi ya kalle ta yana wani yatsina, "Ki gode ma Allah bani Jawad ba" yayi gaba abinsa fuskarsa babu annuri, a ziciyarsa kuwa murna ce ta kamashi wanda indai ya cigaba da tsayuwa a nan to tabbas Zaljameel zata gane shi, part d'insa ya nufa. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (we don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ I DEDICATED DIS PAGE 2 MY FANS, NGD ALLAH YA BAR K'AUNA YA KUMA BARMU TARE #ONE ❤ Chapter 58&59 After one month Zaman Zaljameel da Jawad bai chanja ba, suna nan a yarda sai ma abinda ya k'aru, Zaljameel gaba d'aya ta fita harkansa, duk wani hanya da zai had'asu dashi ta daina, ta koma life inta a part d'inta, shima wannan shawarar Zahra ne. Kwance take a sofa, sanye take cikin wata doguwar riga mara nauyi red ta kama jikinta, gashin kanta baje a bayanta, dama Zaljameel ba mai son yawo da d'ankwali bace,Babu make up a face d'in ta! powder kawai ta shafa sai lip balm mai k'ashin strawberry. idonta na kallon ceiling, She missed her Mom, cuz tunda aka mata aure 2 month kenan bata k'ara sa Mom a idonta ba cuz fushi take da ita, amma yau kam bata ganin zata iya kwana bata sa Mom a idonta ba. Mik'ewa tayi ta fad'a bathroom dan sake wanka. Shiryawa tayi cikin wani lace dark blue mai tsadar gaske, an mishi ratsi da yellow,yellow veil ta yafa a k'afadar ta ta d'auka handbag black da wani shoe mai tsini shima black. Mirror ta kuma kalla taga yarda tayi kyau, ita kanta tasan tayi kyau dan yau make up d'in nata na mussamman ne, sake fesa tsaddaddun perfume tayi ta nufi parlour tana takawa a hankali. Sai da ta gama kashe selfie sannan ta nufi hanyar fita, da happiness a heart d'inta, cuz zata ga Mom da Nawal. Har ta murd'a handle zata fita taji an daka mata tsawa "Keeeeee" Duk da tasan waye hakan bai hanata tsorata ba, cux bata sa rai yana gidan ba. Handbag d'in ta saki a k'asa tsabar tsorata da tayi, jikinta har rawa yake! Had'e fuska tayi ta kalli Jawad! " Harararsa tayi ta tura cute lips d'inta gaba" haba Ya Jawad! Meye haka?tsorata ni fa kayi". "Meye haka" ya maimaita a ransa, lallai Zaljameel ta gama raina sa. Cikin zafin nama ya k'arasa kusa da ita ya janyo ta ta fad'o jikinsa da k'arfi, gashin kanta ya rike data fito dashi bata saka shi a d'aurin taba ya ja, wata k'ara Zaljameel ta saki ta runtse idonta tana jiran hukuncin Ya Jawad. Sosai ya shagala da kallonta, ganin yarda tayi masa kyau dama gashi ya kai wajen 2 weeks bai ganta, kewarta ya dame shi, har wata rama yayi, hannun sa yasa ya fara zagaya mata a face, face d'insa ya had'a dana Zaljameel hancinsa da nata suna gogar na juna,tana jin saukar numfashin sa. wani yarrr Zaljameel taji a jikinta haka Jawad, so yake yayi kissing d'inta amma ya kasa, zuciyarsa na ingizashi amma yana tuna abinda zai je yazo, jin shirun da Zaljameel taji yasa ta bud'e idonta d'aya tana kallon Jawad, k'arema fuskarta kallo yake,face d'insa babu walwala, sosai yake jin feelings akan Zaljameel. "Ya Jawad ci kani in tafi" Sosai ran Jawad ya b'aci cikin zafin nama ya tura Zaljameel baya, sai da tayi tangal tangal sannan ta fad'a kan 3cter, wani k'ara Zaljameel kwalla dan a tunanin ta a k'asa zata fad'i, jinta a zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya. Nuna ta yayi da yatsa, "Keeeeee waya baki izinin fita a gidan nan ba tare da kin tambaye ni ba? Ko zaman kanki kike yi a gidan?" Cikin b'acin rai ta mik'e tsaye, Ya Jawad, karka k'ara ce mini keee, you know my name, I'm Zaljameel bana son ka k'ara kirana dake kuma" ta fad'a tana harararsa had'e da murgud'a masa baki. "Kuma fita basai na ganka ba zan fad'a maka, tayi rau rau da idanu, kamar zatayi kuka, na gaji da zaman nan wallahi,menene banbancina da mai zaman kanta d'in, iyaye na sam basu mini adalci ba, da basu had'a ni aure da wanda nake so ba, na rasa irin zunubin dana aikata da k'addara ta had'ani da kai Ya Jawad, yau zan tafi wajen Mom d'ina kuma karkasa rai zan dawo gidan nan " tana kaiwa nan ta mik'e tana goge kwallar dake fita a idonta ta d'auka handbag d'inta ta yi gaba. Mutuwar tsaye Jawad yayi, komai na jikinsa yayi nauyi, yana kallon Zaljameel ta fita amma ya kasa tsaida ta. Ja da baya yayi ya zauna a 1 cter ya rik'e kansa daya ji yana sara masa,addu'oi ya fara karanta a ransa a hankali yaji zuciyarsa ta saki,a zuciyarsa ya fara magana "Mai Zaljameel ke nufi da idan tatafi bazata dawo ba? Hakan na nufin ta barni kenan, No....ya furta da k'arfi, it will never happen Zaljameel, muna tare har mutuwa dan ita kad'ai zata iya rabani dake" Cikin hanzari ya nufi part d'insa ya fara shiri ko ina zashi oho, a gurguje ya shirya cikin shadda mai tsadar gaske coffee colour, ya saka hula ya d'auka key na moto ya fita. Parking space ya nufa ya d'auka motornsa ya ja da k'arfi. Tafiya take a nutse ta nufi part d'in Fulani dan yafi mata kusa, bayi nata tsayawa suna bajewa k'asa suna kwasar gaisuwa, Zaljameel kam da fara'a take amsa musu. Sosai ta fara gajiya, ba tayi tunanin akwai tazara mai yawa a tsakanin su ba shiyasa bata d'auka motor ba. Jin mota tayi a bayanta tayi parking, juyawa tayi ganin waye, "Ya Jawad, mai ya kawo shi nan kuma?" bata k'arasa tunanin ta ba taji an kama hannun ta, cikin zafin nama ta fuzge hannun ta ta hararesa ta cigaba da tafiya, binta yayi da sauri yasha gaban ta, ya kuma kama hannun ta ya langwabar da fuska yana murmushi, har sai da beauty point d'insa suka lotsa. "My wife Zaljameel" a furta in a romantic voice. Yarda ya kira sunan Zaljameel ya tafi da ita, cuz Ya Jawad yafi kowa iya fad'ar sunan ta. D'aga idonta tayi ta sauke a fuskarsa, shima ita yake kallo, sai da suka dau mintuna a haka sannan Zaljameel ta d'auke idonta bata iya jurar wannan kallon, hannun ta ta fara k'ok'arin kwata amma Jawad yak'i sakin ta, a hassale ta fara magana! "Ya Jawad cika mini hannuna let me go please, ko na maka ihu yanzun nan na tara maka mutane". Dariya Zaljameel ta bama Jawad har sai da white teeth d'insa suka fita," ihu Zaljameel, Oya fara mu gani, banda abinki ai babu wanda zaizo cuz kowa yasan you are my lovely wife, so babu ma wanda zai taho cuz ansan wasa muke "D'aga kai tayi ta kalle shi ya kashe mata ido d'aya. " Zaljameel muje rana na dukan mu" ya kalli sama. Itama saman ta kalla,ta tab'e baki, "Ina ruwanka dani, ba rana ba ko ruwa ne ya dake ni mana ya fad'a zata tafi ya jawo ta jikinsa ya rungume, a razane ta fara k'ok'arin ture shi amma amma ta kasa. Kansa ya d'aura a k'afadar ta yana shin shinar k'amshin perfume d'inta dake saukar masa da kasala. Zaljameel ta gaji da ture Jawad tayi luf a faffad'an kirjinsa, idonta ya cika da kwalla dan kunya, tana ganin bayi ta bayan Jawad da sun biyo hanyar suka gansu rungume da juna sai su chanja hanya, takaici ya ishi Zaljameel, mai ya Jawad ke nufi da itane da zai mata haka a cikin jama'a. "Please Ya Jawad ka cikani, kana gani mutane na kallon mu" Sake matse ta Jawad yayi a jikinsa ya sauke ajiyar zuciya, Zaljameel najin yarda bugun zuciyarsa ke k'aruwa. Cikin wani voice mai wuyar fassaruwa Jawad ya fara magana "Mutane na kallon mu" ya maimaita abinda ta fad'a! Hmm su mutanen ai sun san ba matar wani na runguma ba matata ce, so bana tunanin akwai damuwa anan" Zaljameel kam al'amarin Jawad mamaki kawai yake bata, ace lokaci d'aya ya chanja, "muje moto Zaljameel in ba haka ba wallahi zan d'auke ki na saki da kaina, kallon sa tayi taga yarda ya zuba mata ido kamar zai cinyeta, a hankali ta lumshe idonta, zuciyarta na bugawa, bud'e idon tayi ta kalli Jawad, cikin sanyin murya ta fara magana" Ya Jawad cikani zan shiga basai ka kaini ni ba, Kallon ta yayi "Zaljameel you promise?" Yes i promise ". Cikata yayi, yayi crossing hands yana kallon ta, Zaljameel kam tana fakar idon Jawad ta fara gudu tana dariya " Wooooo Ya Jawad na maka wayo " Dariya yayi yabi ta shima, taku kad'an ya kamata, d'aga ta yayi chak ya nufi moto da ita, ita kam sai dukan kirjinsa take tana k'ok'arin kwatar kanta amma ta kasa har ya kaita moto ya rufe ta ya zagaya bangaren driver ya zauna. Kallonta yayi sai hakki take cuz ta dad'e batayi gudu ba sai yau, murmushi ne a fuskarta. Baice da ita komai ba yaja moto sai part d'in Fulani dan nan yaga ta nufa. Tun kan su k'araso an sanar da Fulani zuwan su, tasa an shirya musu abin motsa baki. Jawad da kansa ya bud'e ma Zaljameel ta fita ya kama hannun ta, fuzge hannun tayi tana harararsa "Haba Ya Jawad meye haka wai, naga alama yau so kake kunya ta kashe ni" ta murgud'a masa baki. "Ok d'aukan ki kikeso nayi ko bari na d'auke ki". "A'a Ya Jawad ka bari mana"ta fad'a a shagwabe . Maganar da tayi cikin shagwaba ya matuk'ar tafiya da Jawad, sexy eyes d'insa ya zuba mata ya kama hannun ta suka nufi ciki. Rik'e da hannun Zaljameel Jawad yayi sallama parlour Fulani. A kashingid'e take, sanye take da alkyabba ta mata kyau taci necklace and earing da bangles masu tsadar gaske. Murmushi d'auke a fuskarta ta amsa musu, Zaljameel nata k'ok'arin kwace hannun ta amma Jawad yaki sakin ta, a waje d'aya suka zauna jikinsu na gogar juna. Kunya ta lullube Zaljameel, Jawad kam ko a jikinsa. Bayan sun gaisa Fulani ta sake musu lecture akan zaman aure, sosai ta ratsa su suka mata sallama,Fulani tace ta kalli Jawad " To mak'ale mata kaje waje ka jira ta zamuyi magana" sai da shagwabe fuska sannan ya fita badan ransa yaso ba. wata jaka Fulani ta bama Zaljameel ta fad'a mata kayan mata ne da aka kawo mata daga nijar da kula sosai wajen shansu, godia ta mata a fili aranta kam cewa take, "Haba Fulani, wanda nasha ma kafin auren ma ya isheni". Part d'in Mom suka nufa. Motor Jawad na tsayawa Zaljameel ta bud'e murfin motar ta fita da gudu ko handbag d'inta bata d'auka ba dan zumud'i. Jawad kam binta yayi da kallo yana kallon yarda take budirinta babu abinda ya dame ta, kai baka ce tana da aure ba. Girgiza kai yayi ya d'auka handbag d'in ya rufe moto ya shiga ciki. Da gudu Zaljameel ta shiga, Mom zaune a parlour tana karanta newspaper taji mutum ya fad'o jikin ta, d'aga kai tayi tana murmushi cuz tasan babu mai mata haka sai Zaljameel, Rumgume ta Mom tayi itama tana murnar ganin Zaljameel. Sallama Jawad yayi da handbag a hannun sa, ganin Zaljameel yayi zaune a cinyar Mom, "Inama ace Zaljameel a cinyar sa take a zaune bata Mom ba" Zama yayi kusa da Mom ya d'aura kansa a k'afadar ta yana cin magani, ture Zaljameel Mom tayi ta d'aura hannun ta akan Jawad tana shafa sumar kansa. Zunburo baki Zaljameel tayi, tana b'ata rai, "Mom ture ni fa ki kayi a cinyar ki saboda Ya Jawad ko?". Dariya Mom tayi ta jawo Zaljameel jikinta tana lallashi"Aa Zaljameel ba haka bane, kinsan Jawad shine first born,amma ai kema ina sonki ". Gwalo Jawad ya mata yana murmushin mugun ta! B'are baki tayi ta fara kukan shagwaba, tashi tayi ta nufi d'akin ta tana buga k'afa. Zaljameel na shiga room d'inta ta ganshi fes, babu abinda ya chanja yana nan a yarda ta barshi, k'amshi mai dad'i ke tashi. Wardrobe ta bud'e, kayanta suma suna nan, wani tsallen murna tayi! "Yes zama daram kenan a gidan nan" Kayan jikinta ta cire ta nufi toilet danyin wanka. Zaman parlour ya gundiresa, hirar da suke da Mom ba bajin dad'in ta yake ba, idonsa nakan d'akin Zaljameel ko zaiga fitowarta amma shiru, Mom ta gama lura da Jawad dan haka ta mik'e ta cewa Jawad tana zuwa. Dad'i ne yake mashi tana shiga room d'inta shi kuma yabi bayan Zaljameel. Murd'a handle yayi ya shiga, bai sameta ba sai kayanta daya gani a gefen bed ga kuma saukar ruwa a toilet, hakane ya tabbata masa wanka take yi. Murmushi yayi" sai kace agwagwa" ya fad'a a hankali. Zaljameel d'aure da towel a kirjinta tana brush a toilet, bayan ta gama ta d'auka k'aramin towel ta fara goge gashin kanta daya jik'e, fitowa tayi ta nufi mirror, ta jona hand dryer ta fara busar da kanta. Yareema Jawad yayi suman zaune, ganin Zaljameel a haka, gaba d'aya notin kansa ya kunce, wata irin sha'awar Zaljameel ce ta motsa masa, kyan dirin Zaljameel ya tafi dashi. Bai san sanda ya mik'e ya nufi inda Zaljameel ke tsaye. Bata san da zamansa a d'akin ba duk a tunaninta ita kad'ai ce. Hannun sa ya zura ya sak'alo waist d'inta ya juyo da ita ta fad'a jikinsa, a razane ta dage zata saki k'ara da iya k'arfinta Jawad ya had'e bakinsa da nata..... 🙊 SUMYNBASH CE 💋🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 60&61 Kissing d'inta yake cike da kwarewa,sun dau wajen 5mint Jawad na kissing d'in lips d'in Zaljameel kamar ya samu sweet, cire bakinta yayi daga nasa amma bai cikata ba, hugging dinta yayi yana sauke ajiyar zuciya, dan ba k'aramin d'aure wa yayi ba ya rabu da Zaljameel. Zaljameel tayi luf a kirjinsa tana maida numfashi, cuz taji bak'on lamari a tare da ita, tunda take babu wanda ya tab'a kissing d'in ta sai Jawad. Sake hugging dinta yayi yana ji kamar wani zai raba su. A hankali Zaljameel ke dawowa nutsuwarta, da k'arfinta ta tura shi, kasancewar jikinsa babu kwari yasa yayi baya, ya zuba mata sexy eyes d'insa yana kallon ta cike da sha'awarta. A hankali y fara takowa ya nufi inda Zaljameel ke tsaye, hannu ta d'aga masa! "Jawad dakata, karka kuskura ka matso kusa dani," tuf ta tufar da yawon bakinta, "Ka rasa abinda zaka mini sai ka zuba mini wannan bakin naka a cikin nawa. Runtse ido tayi cike da takaicin abinda Jawad ya mata." Jawad karka raina mini hankali, na rasa dalilin chanja warka lokaci d'aya, I know what I'm doing, i'm not a small gal I'm matured, so na riga na gane ka, I hate you Jawad, kamar yarda kaima you hate me, banson k'ara ganin ka, kaje ka auri wacce kake so ka huta da auren Zaljameel har abada". Jawad kam ya zama kamar an dasa shi a wajen, his brain has already stop thinking anything,banda kallonta babu abinda Jawad keyi. K'ofa ta kalla," Get out Jawad I don't want to see you ". Bashi da zab'i daya wuce ya fita a d'akin kafin zuciyarsa ta tarwatse, a hankali yaja k'afa ya fita a d'akin. Bai tsaya yima Mom sallama ba cuz bazai iya magana ba a halin da yake ciki, bai bi takan motarsa ba ya nufi part d'insa haunkalinsa a tashe, dishi dishi yake gani a idonsa a da kyar yaje guda. Yana shiga bai tsaya ko ina ba ya nufi bathroom, dan ruwa kawai yake buk'ata, jacuzzi ya nufa ya shiga ciki ya sakar ma kansa ruwa,a hankali ya fara dawowa dai dai da har ya fara tuna maganganun Zaljameel, Runtse ido yana jin zuciyarsa na masa rad'adi, a haka ya gama wankan y fito ya baje a kan bed. Binsa Zaljameel tayi da kallon tausayi, fad'a wa kan bed d'inta tayi ta fashe da wani kuka mai ban tausayi," I'm sorry Ya Jawad, wallahi I love you, you mean alot to me, but ina son tabbatar da soyayyata a zuciyarka ta cigaba da kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi zaune, ko me ta tuna ta mai rubutashi da sauri ta nufi wardrobe,shiryawa tayi cikin wani black material, mai ratsin red, d'inkin riga da siket, veil ta yafa ta fita da sauri. Itama bata bari Mom tasan da fitarta ta wuce da sauri, gidan ta ta nufa. A hankali ta shiga parlour dan karsu had'u da Jawad, ganin baya nan yasa ta shige part d'inta tana sand'a, tana waiwaye harda tuntub'e a haka ta shige ciki ta saka key. Zama tayi a gefen bed d'inta ta buga tagumi, Jawad ya shiga uku, wato girman kanshi da izza sun hanashi magana, tsaki taja ta jawo wayarta ta buga ma Zahra, tana fara ringing tayi picking kamar mai jira. Zaljameel ta bama Zahra labarin yarda sukayi da Jawad,"Zahra kaina ya kulle, need your advice please ki taimaka mini. Shiru Zahra tayi tana nazarin mafita, cikin sanyin jiki Zahra ta fara magana! Zaljameel Jawad ya gama dake, ya kuma ruguza miki duk wani shiri da kike yi, karki manta kince tare kukaje wajen parent d'inku ya kuma nuna miki so a gaban so, Zaljameel a tunanin ki mai zaki ce musu su yarda?. Gumi ne ya karyo wa Zaljameel, tabbas Jawad ya gama da ita, "Zahra solution nake nema please help me". "Akwai mafita d'aya Zaljameel, amma tana da had' ari, amma idan kika bi yarda na nuna miki to tabbas zakiyi nasara" "Insha Allah Zahra komai zai tafi dai dai fad'a mini" korata Zaljameel tayi banji me Zahra tace mata ba. A tsorace Zaljameel ta fito da ido waje, "Zahra kina ganin hakan zaiyi kuwa?" "Kwarai kuwa Zaljameel babu matsala" Ihun murna Zaljameel tayi ta fara had'a kayan ta a trolley. Jawad tunda ya kwanta ya kasa motsi, a haka Bala ya same shi, cikin tashin hankali Bala ke tambayar Jawad ko lpy amma bai ce dashi komai ba, ya kawo masa abinci yak'i ci, hankalin Bala kam ya tashi ganin Yareema Jawad a wannan hankali, bai ankara ba yaga hawaye nabin fuskar Jawad. Tagumi Bala ya buga dan yasan duk abinda ke damun Jawad ba karami bane. After one week Zaljameel tayi doguwar mik'a tayi addu'ar tashi a bacci ta mik'e zuciyarta fes ta shiga bathroom, wanka tayi ta d'auka doguwar riga ta saka, batayi make up ba sai kyalli da fuskarta keyi, rub ta samu ta shafa a face d'inta nan da nan face d'inta yayi ja idonta ya fara hawaye, itama ta k'ara da nata kukan, hijab ta d'auka ta saka ta d'auka trolley ta fita. A motar ta ta nufi part Fulani tana rusar kuka. Tana zuwa kofar gida ta fita batare data rufe motar ba ta shiga tana wani irin kuka. Fulani da mai martaba zaune suna hira sukaji shigowar Zaljameel, a razane suka tashi tsaye suka nufeta, fad'awa tayi jikin Fulani ta kuma fashewa da kuka. Fulani ce tayi k'arfin halin tambayar ta," Zaljameel meke faruwa ne? Mai ya samu Jawad d'in" D'ago wa tayi da jan idonta ta kalli Mom, "Fulani babu abinda ya same shi,Fulani koroni yayi gida wai dan ina da ciki, yace sai an zubar ni kuma nace A'a ban yarda ba ina son cikina shine yace nabar gidan. Mai martaba bai son lokacin daya zube a kujera ba yana salati, Jawad d'in ne yace ki tafi gida" Eh mai martaba shi yace na taho. Shikenan Zaljameel, kiyi hak'uri, Fulani shiga da ita ciki. Fulani da ta kasa magana dan takaicin abinda Jawad yayi tana kama Zaljameel suka nufi ciki. KUYI HAKURI DA WANNAN, SAI DA NAYI TYPING MAI YAWA WALLAHI YA GOGE, NA SAKE WANI NE SABODA NA MUKU ALKHAWARI, SAI KUN JINI. SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 62&63 Wani katafaren room Fulani takai Zaljameel, an cika shi da decoration kala kala, sosai ya burge Zaljameel, zaunar da ita tayi a akan sofa tana zauna itama, a time d'in Zaljameel sai matsar hawaye take, kallonta Fulani tayi cike da tausayawa halin da Zaljameel ke ciki, hannun ta ta kama ta rungume ta ta fara lallashi! "Zaljameel kiyi hak'uri ki daina kukan haka, ai kukan ki ya k'are saboda kinzo inda za'a nema maki mafita, duk duniyar nan babu wanda ya isa ya zubar da cikin nan, kin birgeni da baki biyema rud'in shed'an ba saboda soyayya miji ku aikata zunubi, amma ki bar mini komai a hannu na ". Fulani ta cigaba da shafa bayan Zaljameel," Zaljameel a hospital aka fad'a muku kina da ciki?". "A'a Fulani shi ya auna ni dakansa, shine yace wai ina maganin hana d'aukar cikin daya ke bani nace ai bana sha, Fulani da kyar nasha har marina fa yayi" Zaljameel ta sake fashewa da kuka. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,Yareema Jawad haka ya lalace ban sani ba, lallai zamansa na london bai amfane mu da komai ba sai barna" Fulani tayi shiru tana jinjina maganar a ranta. Tashi tayi tsaye, "Zaljameel bari naje, dan zama bai kamani ba" ta fice ta bar Zaljameel zaune. Kuyangu sun cika room d'in Zaljameel sun hau gyara duk da a gyaren yake amma Fulani ta tura su a sake gyarawa, sun had'ama Zaljameel ruwan wanka a bathroom sun kunna turaren wuta mai k'amshi, bayan Zaljameel ta fito daga bathroom ta bada umarnin a d'auka mata kayanta a motar ta,an d'akko kayan an jera mata a wardrobe, coolers na abinci masu kyau da tsada aka ajiye ma Zaljameel, dan takanas Fulani tasa aka shirya mata girki, ga fruits kala kala suma an ajiye, bayan sun gama tsara komai sauran suka fita kuyangun Zaljameel lantana da jummala suka tsaya cuz ta saba dasu. Washe gari Yareema Jawad da kyar ya iya zuwa office, shima fita yayi ko zai samu sassauci, tabbas yasan Mom bazata bari Zaljameel ta zauna mata a gida ba bayan ga gidan mijin ta, kuma yasan duk abinda Zaljameel zata fad'a akansa Mom bazata yarda ba, hakan ne yasa hankalinsa ya d'an kwanta. Meeting d'in gaggawa Sarki Farouq ya had'a a part d'in grandfa, da shi da aliyu sai sai grandfa sai matan su, Fulani da Momy. Mom da Dad k'iran meeting d'in ya tashi hankalin su, suna ta tunanin meke faruwa har suka je, Sarki Farouq ne ya fara magana, bayan an bud'e taro da addu'a. "Assalamu alaikum! Nasan zakuyi mamakin abinda yasa na taramu anan, to ba komai bane sai akan 'ya' yanmu Jawad da Zaljameel". Ras gaban Mom ya fad'i "Wani abune ya same su?" cewar Dad hankalinsa a tashe. Sarki Farouq ya fara jawabi tunda ga zuwan Zaljameel da yayin data zo musu tana kuka da labarin data basu. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shine abinda suke nanatawa a fili, grandfa kam yama kasa magana tsabar takaici, Dad ne ya fara magana, To Farouq yanzu ina Jawad d'in?". Tab'e baki Sarki Farouq yay cike da takaici, haba ai kasan bazai zo ba, sai dai mu mune shi tunda ya riga ya shuka tsiya, al'adar yahudawa, Allah ne ya soni na farga na rasa shi da k'asar nan da bansan abinda Jawad zai aikata ba, amma duk da haka sai ya d'and' ani abinda ya shuka indai nine "Sarki Farouq ya fita a fusace Fulani ma data k'ara tinzura ta bi bayansa. Aliyu da Ayshat zaune gaban grandfa daya kasa magana, Aliyu ne ya fara magana cikin sigar lallashi" Allah ya taimaki sarki Allah ya k'arama sarki tsahon rai". Dan Allah ranka ya dad'e ka kwantar da hankalinka, wannan ai k'aramar matsala ce, kuma shawo kanta bazai yi wuya ba, banson ka saka damuwa a ranka ". Duk maganar da Aliyu keyi sarki najinsa amma ya kasa magana, dan indai zai magana to babu wanda zata yima dad'i, shiyasa yayi shiru yayi koyi da sunnar ma'aiki annabin mu muhammad (S.A.W) daya ke cewa hak'uri yayin fushin farko,idan ranka ya b'aci karka d'au wani action a time d'in sai ka huce, dan zai iya zama hukuncin da zaka d'auka kai kanka sai kayi nadama a gaba. Suma haka suka nufi part d'insu da jimami, Mom kam ta gama hassala da abinda Zaljameel tayi, saboda me Zaljameel zatayi haka? Meye ribanta idan ta had'a Jawad da iyayensa, ita inda tazo ta sanar mata da maganar bata kai haka ba, tsaki taja ta zauna tana tunanin mafita, "Ya Allah ka kawo mana komai da sauk'i" Ameen Dad ya amsa ya shige room d'insa, Momy kam ta zauna a parlour. Jawad ya kasa zaune ya kasa tsaye, komai na duniya ya daina masa dad'i, dumin jikin Zaljameel kawai yake da buk'atar ki gashi ta masa iyaka da ganin ta, aikin Office d'in yak'i samuwa hakan yasa ya nufi gida, part d'in Areef ya nufa bayan sunyi waya ya sanar dashi yana gida. Da sallama Jawad ya shiga gidan, shigarsa ta farko kenan tunda Areef ya tare, zaune ya tarar da Areef yana kallon aljazeera, jin sallamar Jawad yasa ya tashi ya tare shi suka zauna tare. Areef yasan duk abinda yake faruwa cuz bai dad'e da dawo wa daga wajen Sarki Farouq ba, dan haka shima ya gama hassala da Jawad. Zama sukayi a kujera Jawad ya rufe idonsa ya d'aura kansa a saman kujerar yana jin yarda zuciyarsa ke bugu da k'arfi, hawaye masu zafi suka fara fita a idonsa. Areef ne ya kalli Jawad ransa a b'ace, "Kai saurara mana malam, lallai Jawad abin naka ya girmama, harda hawaye saboda Zaljameel tak'i bin umarnin abinda ka sata shi ya saka ka cikin wannan halin, wallahi Jawad ka bani mamaki, kai da ya kamata kayi murna ka gode ma Allah akan baiwar daya maka, amma kake k'ok'arin ja da shi, kasan mutane nawa ne ke neman haihuwa Allah bai basu ba, amma ka samu kai sai ka kasa godiya ka yima Allah butulci. Tunda Areef ya fara magana Jawad ya zuba masa ido yana kallonsa dan bai gane mai Areef ke k'ok'arin sanar dashi ba, sai da ya gama sannan Jawad yayi k'arfin halin bud'e baki ya fara magana "Areef banfa gane mai kake nufi ba, ina son ka fahimtar dani please" "Ok haka kace?, to bari kaji, Zaljameel matar ka tana d'auke da cikin ka a jikinta, wanda kace baka so sai dai a zubar, wallahi Jawad ka bani mamaki a matsayin ka na misulmin kwarai kuma dan sarki, a tunanin ka idan maganar nan ta fita ba cin mutuncin masarautar nan bane? ". Banda zufa babu abinda ke bin jikin Jawad, tashin hankali ya tsinci kansa a ciki da bai tab'a shiga cikin sa, sai yanzu ya tabbatar da da hankalinsa a kwance yake yanzu ne tashin hankali ya same shi. " Areef Zaljameel ce ke d'auke da ciki a jikinta kuma nawa?" wata harara Areef ya makawa Jawad,"Jawad keep jokes a part, karka raina mana hankali, ok wato tanan ka b'ullo, cikin kake so kace bana ka bane? To idan ba naka bane na waye? ". Mik'ewa tsaye Jawad yayi ya fara zagaye parlour," Areef wallahi tallahi bansan maganar da kake yi ba, Zaljameel na dauke da ciki, nace ta zubar, to yaushe ma na mata cikin, ni da ko gado d'aya bamu tab'a had'awa da ita ba " Shiru yayi yana hawaye ya tafi wajen Areef ya zauna dab dashi," Wallahi Areef bamu tab'a had'a gado da Zaljameel ba, ka yarda dani". Areef kam ya shiga rud'u dan shima abin ya fara bashi mamaki, anya Jawad bai fara shaye shaye ba? Taya ma za'ai yace bai tab'a saduwa da Zaljameel ba, to cikin jikinta ta ina ya fito? Shine tambayar data addabe shi. "Jawad ka nutsu ka mini bayani please, kaina ya kulle, ina son na fita daga cikin rud'ani". A hankali Jawad yabama Areef yarda zaman su da Zaljameel ya kasance, Areef kam banda innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, babu abinda bakinsa ke furta wa, Jawad ya kalla da hawaye ya wankewa fuska yana tunanin waya ma Zaljameel ciki? Nikam na koma gefe nace kaine mana Jawad 🤣😜. Areef ya yarda da maganar Jawad, saboda bai tab'a masa k'arya ba a zamansu, nan suka zauna suna tunanin mafita suna zaune Zahra ta dawo daga wajen Zaljameel, bata yima Jawad kallon arxiki ba ta nufi dakinta bayan ta buga masa tsaki.binta yayi da kallo har ta shige. After 2 weeks Zaljameel tana samun duk wata kulawa daga Fulani, sai dai har yanzu Mom bata zo ba, hakan kuwa ba k'aramin tada hankalin Zaljameel yayi ba dan tasan Mom bata bayanta. Zaljameel kullum da hijab kamar wata munafuka haka take yawo. Kamar kullum zaune take a bed dinta bayan ta tashi daga bacci, dan bata da aiki yanzu sai bacci, kayanta take son d'auka a gidan ta dan wanda ta d'ebo ya k'are, kuma bata son ta aika da kanta take son zuwa, shiri ta fara ta nufi room din Fulani, da sallama ta shiga. Fulani zaune kuyanga na matsa mata k'afa, jin sallamar Zaljameel yasa suka fita, zama Zaljameel tayi a jikin Fulani ta shagwabe fuska, "Fulani zanje gida na dauka kayana sun k'are," Shafa kanta Fulani tayi," Zaljameel ki aika mana ai basai kinje da kanki ba" sake shagwabe fuska tayi, " Fulani ba komai zasu d'auka mini yarda nake so ba, please naje na d'auka da kaina" Ok Zaljameel sai kin dawo, ki bi a hankali kinji "Rungume ta Zaljameel tayi ta bata peck a kumatu ta fita. Binta Fulani tayi da kallo tana murmushi, Zaljameel na matuk'ar birgeta, tana k'aunar yarinyar,amma Jawad yana nema ya cuceta, itakam banda takai zuciya nesa ai da tuni ta dad'e da tsine ma Jawad. Zaljameel motar ta ta shiga ta nufi gidan ta, cikin sanyin muryarta tayi sallama, Jawad na kitchen yana had'a coffee yaji sallamar Zaljameel, mamaki bayyane a fuskarsa mai ya kawo ta, bai amsa ya gano ta tana takawa a hankali, tana sand'a ta shige room d'inta. Wani murmushin mugun ta Jawad yayi ya fito a kitchen d'in ya bi bayan Zaljameel. Zaljameel ta manta bata rufe k'ofa ba ta nufi wardrobe ta fara d'ibar kayanta tana zubawa a trolley, jin an murd'a handle yasa Zaljameel tsorata, dan bata tunanin da wani a gidan. Ganin Jawad tayi ya shigo ya maida k' ofar yasa key, yayi crossing hands yana kallon ta. Tsorata Zaljameel tayi ganin ramar da Jawad yayi, yayi bak'i, sanye yake da singlet sai boxers, sajensa ya cika fuskarsa dan bai samu kwanciyar hankalin yin aski ba, a hankali ya fara takawa zuwa inda take tsaye ita kam tausayinsa yasa ta fara zubar da hawaye. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Kuyi hakuri naji shiru, hakan ya faru ne sanadin wayana daya lalace, har yanxu ma ba gyara ta a kayi ba, amma insha Allah zaku jini. Ina kuke masoyan Yareema jawad, ina alfahri daku a duk inda kuke,ngd da so da k'aunar ku gare ni. # much love 💋❤😘 Chapter 64&65 Fara ja da baya tayi tana hawaye, har ta bud'e baki zatayi magana taji takai bango tsaida maganar tayi ta cigaba da hawaye. Tuna abinda Zaljameel ta masa yasa ya ja da baya da sauri yana kallonta fuskarsa k'unshe da tsantsar b'acin rai da damuwa, zuba nata narkakkun idanunsa yayi yana mata wani irin kallo da ta kasa fassara shi, maganar Areef ke masa yawo aka, "Matarka Zaljameel na d'auke da cikin ka a jikinta wanda kace ta zubar" rintse ido yayi, a take yanayin Jawad ya chanja, idonsa ya rikid'e yayi ja, sai huci yake, Zaljameel ya nufa gadan gadan ya fincike hijab d'in dake jikinta, yana k'are mata kallo tun daga sama har k'asa, cikin ta ya zubama ido yana nazari, "Zaljameel cikin waye a jikinki?". Wani kallon rainin hankali Zaljameel ta masa, ta yatsina fuska, "Haba Ya Jawad mai kake nufi da cikin waye a jikina? Ina da mijine bayan kai?". Cikin zafin nama Jawad ya tamk'i gashin Zaljameel ya rik'e kam yana huci,. Wata k'ara Zaljameel ta saki dan azaba, ta fara k'ok'arin kwatar gashin ta, kuma ja yayi da k'arfi hakan yasa ta saki hannunsa tana hawaye "Please Ya Jawad" Keep quiet Zaljameel, banson jin magana daga bakin ki indai ba ansar tambaya na zaki bani ba. "Ya Jawad gaskia fa na fad'a maka, please ka cikani". D'auke fuskarta Jawad yayi da wani kyakyawan mari, dan a yarda zuciyarsa na bushe tofa zai iya zubar da cikin dake jikin Zaljameel amma ya bama zuciyarsa hak'uri, cika kanta yayi ya fita a room d'in amma sai da ya d'auka key ya rufe Zaljameel a ciki. Zama tayi ta zura fuskarta cikin cinyoyinta tana rusar kuka, "Anya bazata fad'a ma Jawad gaskia ba, ganin sa cikin tashin hankali yafi komai d'aga mata tunani, ji tayi an cire key d'in ya shigo, bata d'aga kai ba ta cigaba da kukan ta, cikin sauri ya k'arasa inda take ya fisgo hannun ta ta mik'e tsaye, bai tsaya jiran mai zatace ba ya ja hannun ta suka fice a room d'in. Zaljameel batayi yunk'urin kwace hannun ta cuz bata da wani kuzari a jikinta suka fita, parking space ya nufa ya d'auka wata golden Prado ya tura Zaljameel a front sit ya dawo ya shiga motor d'in ya fara driving, ganin ya nufi hanyar fita daga masarautar yasa Zaljameel ta tsure, kallonsa tayi idonta da hawaye, tana son tambayarsa inda zasu amma yanayin fuskarsa bai bata dama ba, hakan yasa ta tsuke bakinta ta cigaba da kuka mara sauti. Gudu Jawad yake kamar mai shirin tashi sama, Zaljameel ta gama tsorata da al'amarin Jawad, ta runtse idonta dan a zahirin gaskia bata tunanin zasu je inda yayi niya ba tare da sunyi accident ba. A dai dai wani babban hospital Jawad yayi parking, sai da ya harari Zaljameel sannan ya fita yaja hannun ta suka nufi ciki. D'aga kanta tayi taga inda suka zo, ganin Jawad & Zaljameel special hospital tayi rubuce a jiki, a razane Zaljameel ta fara k'ok'arin kwace hannun ta dan tasan tabbas Jawad ya shiga da ita hospital d'in asirinta ya tuno kenan. Dakewa tayi dan taga tsoro babu inda zai kaita, cikin d'aga voice ta fara magana "Ya Jawad leave me let me go," ta fara kokawar karb'ar hannun ta. Bata ishi Jawad kallo ba ya nufi office d'insa da ita, doctors da nurses nata gaida Jawad amma bata so yake ba. Gwaje gwaje yasa wata doctor tayi ma Zaljameel na gane idan tana da pregnant, doctor ladi kam bata ga komai ba, ga results kala wajen 4 tayi printing, cuz Jawad bai yarda da test d'in ba har sai da a kayi sau 4, wani kallon tuhuma ya watsa ma Zaljameel, ji tayi kamar tayi fitsari,ga kunya ta lullub'e ta, tsaki Jawad yaja ya kuma kama hannun Zaljameel suka nufi motor, wata unguwa silient Zaljameel taga ya shiga, duk gidajen dake wajen abin kallo ne, daka gani kasan naira ta zauna, a k'ofar wani katafaren gida yayi parking, horn d'aya yayi gate man ya bud'e k'ofar ta sauri yana washe hak'ora, Jawad ya shiga da motor d'in ciki yayi parking. Da gudu gate man ya k'ara so kusa da Jawad ya zube yana kwasar gaisuwa, babu yabo babu fallasa Jawad ya amsa masa. K'in fitowa Zaljameel tayi tana ta zare ido kamar shege a rabon gado, lol. Fincikota Jawad yayi ya nufi cikin gidan da ita, sai da ya danna password a jikin k'ofar sannan ta bud'e suka shiga k'ofar ta rufe da kanta. Tsaye Zaljameel tayi tana k'arema gidan kallo, ya bala'in burgeta, yanayin ganin irin na turawa ne, ta shagala da kallon parlour taji an watso mata papers a jikinta, firgit tayi ta kalli k'asa inda suka zube ta kuma kalli Jawad dake zaune a 2cter ya yayi crossing leg yana ma Zaljameel wani irin kallo na kin shiga uku. Gaba d'aya ya koma Yareema Jawad d'insa na asali, ya manta fara'a ballantana smiling, hankalin Zaljameel fa ya tashi, cike da izza Jawad ya fara magana. "Keeeeee d'auka papers d'in nan kizo nan" ya nuna mata k'asa inda k'afarsa take. "Kasan ta kalla ta kuma kalli Jawad, ganin babu alamun wasa a tare dashi, gasu a wani gida da bata son ta ina zata fita ba ballantana ta gudu yasa ta durk'usa ta d'eba ta nufi inda ya nuna mata sai dai ta kasa zama a k'asan kamar yarda ya umarce ta, dan Zaljameel itama akwai izza,hakan yasa take ganin bazata iya zama a k'asan k'afarsa ba. Ganin bata da niyar zama yasa ya tashi tsaye yana zuba hannu a pocket yana kallon Zaljameel. Wata iska ya fitar a bakinsa mai bayyanar da takaicin dake zuciyarsa ya fara magana "Zaljameel? Kinyi k'ok'ari sosai a abinda kika aikata, kuma na gane abinda kike nema, tun farko da kin fad'a mini da baki bamu wahala ba" tsayawa tayi tana kallon sa dan bata gane inda ya dosa ba. " Zan baki abinda kike nema Zaljameel, ciki kike buk'ata na miki ko, to zan miki kuma ke da gida sai kin samu cikin gaske Zaljameel" yayi wani killer smile ya kashe mata ido d'aya. Cikin rawar murya Zaljameel ta fara magana "Ya... Ja.. wa.. d! Please karka mini haka, wallahi ni ba haka nake nufi ba, dan Allah kayi hakuri, wallahi na tuba, please ka maidani gida, wallahi zan janye abinda ya fad'a ma iyayen mu " ta fashe da kuka. Dana sanin abinda ta aikata, itakam Zahra ta cuceta data bata wannan shawarar, gashi bata taho da phone ba ballantana ta buga mata waya ta bata wani advice d'in. Upstairs Jawad ya shige ya bar Zaljameel na kuka. SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 July 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 66&67 Jin takunsa tayi yana sakko wa, a hankali ta d'aga fuskarta da tayi ja saboda kuka tana kallonsa, kyau sosai ya mata, sanye yake da pink shirt and blue jeans ne a jikinsa ya d'aura p cap, fuskarsa d'auke da sunglass,sai tashin k'amshi yake. ta shagala da kallonsa sai jin muryarsa tayi a kusa da ita, firgit tayi ta kalle sa, tsugunna wa yayi dab da ita yana kallon cikin idonta, itama zuba masa nata idon tayi,wani yarrr taji a jikinta, dan yau kallon na Ya Jawad na musamman ne, janye idonta tayi ta kalli gefe tana hawaye, duk da zuciyarsa bata masa dad'i ba ganin Zaljameel a ya nayi na tashin hankali, amma bai bari ta gane hakan ba ya fara magana "As you know Zaljameel yau ke amarya ce, ina son kisa ranki cewa yau aka kawo ki gidan Jawad, so kukan ya isa haka zan fita na siya abinda ake kaima amarya a daren farkon ta". Yayi wani murmushi ganin kukan Zaljameel ya k'aru, "Zaljameel!" Ya kirata, bata iya amsawa ba dan maganar da Jawad ya fad'a mata ta bala'in d'aga mata hankali, kallonsa tayi idonta na zubar da hawaye,"Ki tashi ki hau upstairs akwai room na farko ki shiga zaki samu duk abinda kike buk'ata a ciki, kinsan ya kamata ki shirya kanki kafin Angon ki Jawad yazo" yana gama fad'in haka ya mik'e da sauri y nufi hanyar fita, binsa tayi da kallo har ya fice. Tashi tayi ta fara zagaye gidan, tana kallon kyau da tsari da yayi, upstairs ta nufa nan ma duniya ce, an zuba kayan decorating kamar ba kud'e ne yayi aiki ba, room d'in daya fad'a mata ta shiga, shima a tsare yake, ganin wardrobe ta nufa ta bud'e, ganin kaya an mace a ciki ya firgita Zaljameel, gaba d'aya English wears ne a ciki, tana son dubawa amma kyankyami ya hanata tab'a su, a zuciyarta ta fara magana, dama Ya Jawad dan iska ne, har room ya ware saboda mata, shine zai fake mata da abinda tayi itama ya raina mata hankali, wai tana buk'atar ciki? Eh lallai zaiga ciki Amma a jikinsa. Tsaki taja ta rufe wardrobe, zuciyarta taji tana harbawa da k'arfi, duk wani tsoro ya fita a ranta, murmushi tayi, "Ha Ya Jawad bazaka tab'a cin nasara akaina ba, ba kuma zaka tab'a samun kwanciya da ni ba ta dole, har sai ka firta da kanka kana buk'atar kuma kana d'auke tsantsar sona a zuciyarka. Wardrobe d'in Zaljameel ta kuma nufa zatayi shahadar tab'a kayan, white top ta d'auka tana dubawa, daga ni ba'a tab'a saka ta ba hakan yasa hankalin Zaljameel ya kwanta ta kuma duba wani mini skirt ta d'auka shima sabone hakan yasa ta ajiyesu gefen bed ta rufe wardrobe d'in tunda ta samu na sawa. Mirror ta nufa taga cream and lotion masu kyau da tsada, ga perfumes kala kala, harda powder da lipstick, ga eyeliner, abin ya d'aure mata kai, lallai a gaida Ya Jawad, yayi k'ok'ari wajen ajiyewa yan matansa abinda suke buk'ata. Bakin ciki taji ya tsaya mata a rai, a hassale ta nufi bathroom danyin wanka. Fes ta fito d'aure da towel a kirjinta, gashin kanta na d'igar da ruwa ta nufi mirror, bayan ta gama tayi make up sosai harda Eye Shadow, white top ta saka wanda bata da baya kuma ta gaba cibiyar ta a waje take, yellow mini skirt ta saka shima bai rufe mata cinya ba, ta gyara gashin kanta yayi baya ta fesa perfumes a duk wata gab'a ta jikinta ta fita parlour ta zauna jiran Jawad. Kitchen ta l'eka taga fridge, bud'e wa tayi taga chocolate ice cream, cikin zumud'i Zaljameel ta d'auka ta nufi parlour ta zauna tayi crossing leg tana kallon film tana shan ice cream d'inta hankali kwance. Tun tana jiran dawowar Jawad har ta gaji ta shanye ice cream d'in ga wani bacci ta take ji, bata son lokacin da bacci b'arawo ya sace ba. Jawad bai dawo gida yana part d'in Areef suna tattauna akan maganar, Jawad ya sanar ma da Areef Zaljameel na gidan sa, Areef ya tsorata da abinda yayi, amma d'aya fad'a masa dalilinsa nayin hakan Areef ya bashi goyon baya 100 percent,a haka sukayi sallama ya fice dan dama bai shigo da motor ba. Fulani taji shirun Zaljameel yayi yawa, hakan yasa ta tura kuyangu su duba mata ita, sun dawowa da Fulani da labarin da yasa zuciyarta ta kusa tsaya wa, part d'in Mom ta aika a duba mata Zaljameel, Mom kam tace rabonta da Zaljameel ai ta dad'e, nan da nan labari ya karad'e masarauta akan rashin ganin Gimbiya Zaljameel, hankalin kowa ya tashi harda grandfa dan labari yaje garesa, gate akaje aka tambayi masu gadi ko sunga fitar Zaljameel suka ce a'a, duk wani sak'o da luko a gidan nan an duba babu Zaljameel babu alamun ta,Fulani kuka take sosai, ina Zaljameel ta shiga ita kam ta shiga uku, a haka a kayi report a duk wata station dake garin. Mom ma abin ya d'aure mata, a lokacin ta d'aura fitar Zaljameel daga gidan sanadiyar kin goya mata baya da tayi, tayi watsi da ita gaba d'aya. Dana sani mara amfani Mom keyi, itama taci kuka kamar ranta zai fita. 10:2pm Jawad ya danna password ya shiga gidan, ganin Zaljameel kwance tayi dai dai a kujera tana bacci, skirt d'in da tasa ha dan dag'e har white pant d'inta Jawad ya gano, binta yayi da kallo mai cike da so da k'aunar Zaljameel, ga kuma sh'awarta data masa katutu, sai dai bazai tab'a kusantar Zaljameel ba tare da yarda ta ba, yayi alkawarin hakan, dama duk abinda ya fad'a mata barazana ce. Step ya k'ara yaje dab da Zaljameel ya tsugunna yana k'arema beautiful face d'inta kallo, "make up d'in da tayi ya bala'in birgeshi,gashin kanta daya rufe mata fuska ya mayar gefe da hannunsa, baison lokacin daya bata peck a pink lips d'inta ba, ganin zata motsa yasa Jawad ja baya, ganin ta cigaba da bacci yasa, d'aukar ta yayi chak ya nufi upstairs da ita idonsa akan kirjinta daya cicciko kamar an hura balloon, wani sanyayyar ajiyar zuciya Jawad yayi ya shiga room d'in daya ware saboda Zaljameel. Kwantar da ita yayi a bed ya saka mata pillow, blanket yaja ya rufeta ya rage gudun Ac, parlour ya sauka ya d'auka ledar daya zo dasu ya nufi room d'in Zaljameel, baccinta take ba tare da damuwa ko kad'an ba a tare da ita, murmushi Jawad yayi ya ajiye ledojin ya d'auka memo yayi note ya ajiye a gefen ledar, "Idan kin tashi kici abinci, dan bana son ki wahala nafi so ki k'oshi tukunna kafin komai ya gudana a tsakanin mu ki samu abinda kike so" yana kaiwa nan ya fice a room d'in ya tafi nashi. Room ne daya amsa sunan sa na Yareema Jawad, ya tsaru sosai ya kuma ji manya manya frames masu d'auke da pictures kala kala, pic d'in dana gani shi ya tsorata ni, pictures d'in Zaljameel ne manne tun tana k'arama har girman ta, duk ya cika dakin dasu, sai ma mai martaba da fulani, sai nashi wanda kana shiga yana kallo ka, akan doki yake yaci alkyabba da rawani yayi murmushi a pic d'in, sai da y gama bin pictures d'in da kallo fuskarsa d'auke da murmushi, ya shafa gefen fuskarsa ya furta, "I LOVE YOU MY NISFUL HAYAT" Bathroom ya nufa yayi wanka ya chanja kaya ya d'auka key sai da ya lek'a Zaljameel sannan ya fita ya nufi gidan sarki. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 August 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 68&69 Gidan sarki Jawad ya nufa, hankalin sa kwance, tun a gate ya lura da yanayin masu gadin gidan yasan babu lpy, tsayawa yayi suka gaida shi, a dak'ile ya amsa ya tambaye me ke faruwa, d'aya daga cikin su ya bama Jawad labarin b'atan Zaljameel, baice dasu komai ba yaja motarsa da k'arfi ya k'ure speed ya nufi part d'in Fulani. Cikin tashin hankali Jawad ya shiga parlour yana kiran Fulani, Ammi nah! Ammi nah!, zumbur Fulani tayi ta mik'e daga zaunen da take tana kuka ta nufi inda taji muryar Jawad, har tuntub'e tayi ta fito. Tsaye ta tarar da Jawad ya rik'e kansa yana hawaye, sororo tayi tana kallonsa dan ita ta gama believing Zaljameel na tare da Jawad, to mai yasa taga yana kuka. Inda take tsaye Jawad ya nufa ya rumgume Fulani ya fashe da kuka, "Fulani wai Zaljameel ta b'ata, wannan wane irin tashin hankali ne yazo mana da rana tsaka, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ya Allah ka bayyana mini Zaljameel" ya kuma fashewa da kuka. Duk da haushin da Fulani keji na Jawad sai da ya bata tausayi, amma ta dake, a zafafe ta ture shi a jikinta, tana nuna sa da yatsa, "Kul Jawad, karka kuskura ka k'ara zuwa kusa dani, bana son ganin ka Jawad, har kana da bakin kuka saboda rashin ganin Zaljameel, gaskia Jawad rashin kunyar taka takai, duk abinda ya samu Zaljameel da hannun ka a ciki Jawad, wallahi indai kaga na sakar maka to Zaljameel ta dawo gare ni da dan dake cikin ta, tun wuri Jawad, tun raina bai b'aci ba ka dawo da Zaljameel, nasan kai ka d'auke ta. A razane Jawad ya d'ago ya kalli Fulani, sosai kirjinsa ya buga dan yayi tunanin asirin sa ya tuno, amma ya basar. "What?! Fulani what are you saying, kina nufin nasan inda Zaljameel take? Ba haka bane Fulani, nasan nayi kuskure na korar Zaljameel da nayi wallahi Fulani ina son Zaljameel ina kuma son abinda ke cikin ta dama sharrin shed'an ne, amma bani da sa hannu a b'atan ta "Jawad ya durkusa ya cigaba da kuka. Binsa Fulani tayi da kallo, Jawad na kuka, abinda ta dade bata gani ba kenan, a kalaman sa ta tabbatar da gaskiar sa, to ina Zaljameel ta shiga, shine tambayar data damu Fulani,ja da baya tayi ta zauna a karagarta jin kanta na juyawa. Jawad ta kalla, "Jawad! Kamar yarda na fad'a maka baka fa sauran sakewa a gidan nan in har Zaljameel bata dawo ba, na d'aura maka alhakin neman Zaljameel duk inda ta shiga a duniyar nan" tana gama fad'in haka ta mik'e tabar Jawad a durk'ushe, mik'ewa yayi ya fita, direct part d'insa ya nufa zuciyarsa fal farin ciki, Allah ya taimake shi shima zai bar gidan, dan dama yana ta tunanin yarda zai dinga zirga zirga daga gidan sarki zuwa gidansa inda ya ajiye Zaljameel, room d'insa ya shiga ya kira Bala akan ya had'a masa abinda yake buk'ata. Mamaki bayyane a fuskar Bala, ganin yarda Yareema Jawad ya nuna halin ko in kula da b'atan Zaljameel, sanin halin Jawad bayason shishigi a lamarinsa yasa Bala ya kama bakinsa, ya had'ama Jawad kayansa ya fita kawo masa dinner. Washe gari Ana idar da sallar asuba Jawad ya bar gidan. Gidan sa ya nufa ransa fes zaiga Zaljameel. Horn yayi gate man ya bud'e masa, parking motar yayi ya shiga ciki,sai fara'a yake. Tunda Jawad yabar gidan Zaljameel bata tashi ba, baccin ta kawai take cikin kwanciyar hankali. Jawad na shiga upstairs ya haye, ya nufi room d'in Zaljameel, yarda ya barta haka ya same ta,sai dai ta yaye blanket d'in, tayi d'ai d'ai tana bacci, gashin kanta ya rufe mata fuska. Murmushi Jawad yayi ya nufi bed idonsa na kanta, duba ledar daya kawo mata yayi, komai na nan,hakan ne ya tabbatar masa da Zaljameel bata farka ba, juye juye Zaljameel ta fara alamun zata tashi a bacci, hakan yasa Jawad ya fita a room d'in da sauri, yana fita Zaljameel na bud'e ido, gani tayi gari ya waye hakan yasa tayi du'a ta mike ta shige toilet. Wanka tayo ta fito tayi sallah ta nufi mirror tayi shafa da light make up ta nufi wardrobe, sai a time d'in ta lura da kayan gaba d'aya new ne, hankakinta ne ya kwanta hakan yasa ta kuma duba kayan ta d'auka wata red gown mai k'aramin hannu iya gwiwa, ta gyara kanta, zama tayi a sofa ta buga tagumi dan ta fara jin yunwa, idonta ne ya sauka a kan ledojin da Jawad ya ajiye ga kuma paper kamar an bar Note, tashi tayi ta nufi wajen, letter d'in ta fara karantawa sannan ta fara bud'e kayan, gas chicken ne guda biyu, sai yoghot guda biyu shima,d'ayan kuma kayan chocolate ne da sweet,murmushi Zaljameel tayi, "Ha Ya Jawad kenan, ana so ana kaiwa kasuwa". Sai a time d'in ta tuna bacci ya d'auke ta ne a parlour, to waya kawota kan bed, "Ya Jawad" ta fad'a tana murmushi, tashi tayi ta nufi kasa ko zata ga kitchen, ta dan gasa chicken d'in a macro wave. Jawad zaune a parlour yana watching film a mbc bollywood , Bajrangi baijaan, film d'in ya masa kyau ya bada duk wani attention nashi, hannun sa d'auke da hot coffee yana sha. Jin k'amshin turaren Zaljameel yasa Jawad juyawa da sauri, itakam bata lura dashi ba ta fara neman kitchen, ganin ledar dake hannun ta yasa Jawad gane inda take nema, murmushi yayi ya mik'e ya nufi inda Zaljameel ta nufa cuz ba hanya bane. Tafia take tayi tana zare ido, cuz ta fara ganin kamar tabi wrong way dan ta rasa kitchen, wani door Zaljameel ta bud'e tana lekawa taga duhu, gashi tana ganin alamar mutun a ciki, gani tayi kamar mutun d'in ya nifo ta, ai da sauri daja door d'in ta kwalla k'ara ta fara neman hanyar gudu,gudu take sosai tana kuka tana kiran Jawad "Ya Jawad! Ya Jawad! Please need ur help. Ji tayi tayi karo da mutun wata razanar niyar kara Zaljameel ta kwala ta fara k'ok'arin kwace kanta, hugging d'inta Jawad yayi yana shafa bayan ta" Relax Zaljameel its me Jawad ". Jin muryar Jawad yasa Zaljameel ta kara shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Shafa bayan ta Jawad ya cigaba dayi, ji tayi wani yarr a jikinta haka shima, fara kokarin kwace kanta tayi amma Jawad yak'i bata dama, sai da tayi tayi ta gaji sannan ta hak'ura ta d'aura kanta a kirjinsa tana jin bugun zuciyarsa. Perfume d'in da ta saka yayi ma Jawad dad'i hakan yasa ya fara shinshina wuyanta yana shakar k'amshin ta, kissing dinta ya fara yi tako ina har ya sauka a kan lips d'inta nan ya fara sha. Jikin Zaljameel banda rawa babu abinda yake yi, Jawad kam ya birkice sai kissing d'in ta yake, cika lips d'in yayi ya kuma hugging din Zaljameel yana buga bayan ta, saboda kukan da take. "Please Ya Jawad ka sake ni yunwa nake ji". Banza ya mata ya kama hannun ta suka fara tafiya, "Ina kike nema?". Kallonsa tayi taga kamar bashi yayi maganar ba cuz hanya kawai yake kallo. D'auke kanta tayi, "kitchen nake nema" "To gidan ki ne da bazaki nemi mai gidan ki tambaye shi ba, kinsan kuwa ba mutane ne kad'ai ke rayuwa a gidan nan ba amma kika fara shiga inda bai shafe ki ba,da banzo ba Zaljameel kinsan mai zai faru?". Rike Jawad tayi kam tana girgiza kai, please Ya Jawad take me home, ina son ganin Fulani da Mom, nasan basu san da zamana a nan ba, please ka dauke ni a gidan tun wani abu bai same ni ba, bazan iya zama ba"ta fashe da kuka. Hugging dinta yayi, jin tausayinta yayi aransa, "Zaljameel keda da Mom da Fulani sai ranar da nai miki ciki ya fito ya zama k'ato kika haife dan dake cikin ki sai muje gare su, a tunanin ki wace irin murna zasuyi?" A firgice Zaljameel ta kalli Jawad tana hawaye, "Ya Jawad kasan mai kake fad'a kuwa? Please karka mini haka, wallahi zaka kuntata rayuwata, komai na duniyar nan zai daina mini dad'i, taya zan fara rayuwa a gidan nan ni kad'ai Ya Jawad a tunanin ka ka mini adalci?" D'ago fuskarta yayi ya had'a ta tasa, "I'm here for you Zaljameel, karki damu da komai kinji" Yarda ya mata magana ya bata mamaki d'aga kai tayi ta kalle sa, shima ita yake kallo,sun dau lokaci a haka, sannan Jawad ya hura ma Zaljameel iska a idonta, lumshe idonta tayi tana jin wani sabon yanayi na shigarta,mai da kanta tayi kan kirjinsa tayi luf. SUMYNBASH CE💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 August 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 69&70 Jawad wani nishad'i yake ji jin Zaljameel rungume a kirjinsa, "Ya Jawad yunwa nake ji". "Ok Zaljameel muje muci,an kammala break fast sai kici". Kallonsa Zaljameel tayi, "Ya Jawad waya girka?". Nine mana ya fad'a yana murmushi. Hararasa Zaljameel tayi, "Haba dai Ya Jawad, ai nasan baka iya girki ba". " To shikenan Zaljameel zan baki mamaki "cikata yayi ya kama hannun ta suka fita parlour, dining area ya nufa da ita," Gashi nan sai ki duba abinda ya miki " bai jira mai zatace ce ba ya nufi upstairs. Binsa Zaljameel tayi da kallo har ya b'acewa ganin ta. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin dad'in yarda Ya Jawad ya fara chanjawa Jawad wanka ya sake yi ya shirya cikin wata light blue shadda, half jumfa, tayi masa kyau, ya fashe jikinsa da perfumes ya d'auka key da phones d'insa ya sauka k'asa. . Bayan ta gama break fast ta koma main parlour ta zauna tana tunanin gida, ita duk takaicin ta phone d'inta ai da tayima Zahra waya ta sama mata mafita, tsaki taja ta dan kishingid'a tana tunanin maganar Jawad, "Ba mutane kad'ai ke rayuwa a gidan nan ba" tashi tayi zaune tana duba gefenta, dan tayi matuk'ar tsorata, gani tayi parlour ya mata girma gashi kamar za'a kamata, mik'ewa tayi tana shirin fara gudu taji mutun a bayanta, a razane ta juya suka had'a ido, ganin sa a shirye yasa gaban ta ya fad'i, cikin rawar murya ta fara magana "Ya Jawad ina zaka je haka?" kallonta yayi yana mamakin abinda ya bata tsoro yayi crossing hands yana murmushi "Aurena kike da zaki tambaye ni inda zani?" Zan fita ne zaga gari, akwai matsala ne? ". " matsala d'aya ma kenan, wallahi Ya Jawad bazaka barni a gidan nan ka fita ba, gaskia sai dai mu tafi tare, ka maida ni inda ka d'akko ni", ta fashe da kuka. Jawota Jawad yayi ya rungume ta tsam a jikinsa yana shafa gashin kanta sigar lallashi, "Zaljameel ki zauna mana, babu abinda zai kamaki, abinda na fad'a miki d'azu I'm joking fa". Mak'e kafad'a Zaljameel tayi "Ni dai a'a gaskia sai dai mu tafi tare" ta cigaba da kukanta, kukan dake ratsa duk wani sassa na jikin Jawad, bayason jin kukan Zaljameel ko kad'an, zama yayi a kujera tana manne a jikinsa yana jin son Zaljameel na kuma k'aruwa a zuciyarsa. "Zaljameel ki barni naje mana, kinga baki da kayan kwarai, ko da wannan kayan na jikin ki zaki fita, kayan ma da bakisan na waye ba kika d'auka kika sa a jikin ki". Wayyo Mom! Fulani "ta fad'a a tsorace, Ya Jawad kayan waye?" naki ne Zaljameel" ya fad'a yana yana shafa bayanta "Nawa kuma?" Yeah naki mana Zaljameel , na dad'e da siyansu " Tashi tayi a jikinsa ta kalle shi, sun dau time suna kallon juna, shagwabe fuska Zaljameel tayi," Ya Jawad ina da hijab sai na saka" "Ha Zaljameel mai yasa rigima ta miki yawa, ni babu inda zani dake sai dai na fasa fitar" Kwantar da kanta tayi a kafad'ar sa "Yawwa Ya Jawad, haka nake so". Shiru sukayi for some minute, a haka Zaljameel tayi bacci, kallonta Jawad yayi, kwanciya yayi ya gyara ma Zaljameel kwanciya itama a kirjinsa yayi hugging d'inta a haka bacci ya d'auke shi. 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 August 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 71&72 1:06pm Zaljameel ta farka daga bacci, jin ta tayi jikin Jawad yayi hugging d'inta kamar mai tsoron kada wani ya kwace masa ita, murmushi tayi ta shafi gefen mans pride d'insa, "wicked man, Allah yasa da gaske ka you change ur habit, heart d'inka ya zama clean makar beautiful face d'inka" takai bakinta zata masa kiss taga ya bud'e idonsa ya zuba mata su cikin nata, da sauri ta fara k'ok'arin mik'ewa daga jikinsa dan ji tayi kunya ta kamata, rik'eta Jawad yayi yana murmushin nan nasa gwanin birgewa. "Oya kiyi kissing d'ina mana ya kika fasa?". Shagwabe fuska tayi, "Haba Ya Jawad, ni fa ba kissing d'inka zanyi ba, mans pride d'inka kawai nake kallo". Murmushi Jawad yayi ya shafa gefen fuskarsa, "Ok ya birge ki ne?".ya fad'a yana kallon jikinta, gani yarda ya zuba ido a wajen yasa Zaljameel ta tsargu, a hankali ta kalli inda Jawad ke kallo, ji tayi kunya ta kamata, ganin rabin breast d'inta a waje, sauri tayi ta gyara rigar sannan ta dungurema Jawad kai ta wani b'ata rai ". Dariya Jawad keyi ya kama hancin Zaljameel yaja har sai da tayi k'ara" Wato Zaljameel bakyajin magana ko? Dungure mini kai kikayi? ". Harararsa tayi," Ha Ya Jawad ka gode Allah dungure maka kai kawai nayi". Binta yayi da kallon mamaki, "Lallai yarinyar nan kin fara raina ni, ina ganin sai kinji nauyi na sannan zaki shiga hankalin ki". Kallonsa tayi" Nauyi kuma? Meye nauyinka? ". Dariya Jawad yayi har sai da white teeth d'insa suka fito ya wani lumshe ido," Zaki sani ne ranar dana d'aura miki ". Tashi tayi ta fara zumb'ura baki cike da shagwaba, hannun ta ya rik'e shima ya tashi. " Ina zaki ki barni "kallon mamaki ta masa ta kama baki" OMG, yau naga ikon Allah, ya Jawad dama tare muke tafiya ne ban sani ba? ". Harararta yayi," Aa yau dai zamu fara ". Wall clock ta duba 1:40 pm, fito da ido tayi waje," Ya Jawad duba time, tun d'azu na tashi ka hanani sallah ko?" kalla yayi ya mik'e da sauri, tare suka hau upstairs kowa ya shige room d'insa. Zaljameel toilet ta shiga tayi wanka ta d'aura alwala, ta fito d'aure da towel, wardrobe ta nufa ta fara duba kayan da Jawad yace nata ne, gaba d'ayan su babu kayan kwarai, half best ta d'auka, maroon sai tree quater black, ta ajiye a gefen bed, doguwar riga data zo da ita a jikinta ta saka ta sa hijab d'inta dan duk ta wanke su saboda sallah. Bayan ta idar ta gabatar da komai na ibadah ta mike ta nufi mirror, shafa tayi tayi simple make up ta saka kayan ta duba kanta a mirror ta tufke kanta da ribbon maroon, ta feshe jikin ta da deffrent perfumes, fita tayi a room d'in ta nufi room d'in da Jawad ya shiga, tana murd'a handle d'in ya bud'e, ji tayi wani k'amshi mai dad'i ya daki hancinta, sai da ta lumshe ido sannan ta bud'e tana k'arema room d'in kallo, frames d'in dake manne, Fito da ido tayi ganin pictures d'inta tayi kala kala, baki ta bud'e tana kallon ikon Allah, dan ita wasu pic d'in ma bata san dasu ba. Mutuwar tsaye tayi dan jikinta ya gama sanyi, mai pictures d'inta keyi a room d'in Ya Jawad? Me hakan yake nufi "Sonki da k'aunar ki mana" zuciyarta ta bata ansa, ji tayi idonta ya cika da kwalla ta zubama pic d'in Jawad ido, wanda yayi murmushi, hawaye take tana murmushi, dama da gaske Ya Jawad yana sonta, amma mai yasa bai tab'a fad'a mata ba, izzarsa da k'asaitarsa sun hanashi bayyana abinda ke ransa, tana tsayen nan taji yana k'ok'arin bud'e door d'in toilet, da sauri ta goge fuskarta ta fara tafiya zata bar room d'in. "Zaljameel" taji ya kira sunan ta, tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba, ta cigaba da hawaye, ganin bata da niyar juyawa yasa Jawad ya taka har inda take tsaye, yayi hugging dinta ta baya,ya d'aura kansa ta cikin wuyanta ruwan kansa na diga a wuyanta, ajiyar zuciya ta sauke jin saukar ruwan, cigaba da kuka tayi. In a romantic voice Jawad ya fara rad'ama Zaljameel magana a kunnen ta " Baby Zaljameel meya saki kuka"Ji tayi wani abu ya tsarga mata tun daga kai har k'afa Ajiyar zuciya tayi, ta cigaba da kuka,juyo da ita yayi cike da tashin hankali, dan baya k'aunar kukan Zaljameel. Harshe yasa yana lashe hawayen nata har ya sakko kan pink lips dinta da yaji lipstick ji tayi jikinta ya fara rawa ta ta fara ture Jawad amma yaki bata dama, d'aukar yayi chak ya sauke a bed d'insa, still yana shan bakinta, tun tana k'ok'arin kwatar kanta har ta kasa jikinta yayi sanyi ta fara maida masa martani, sai da ya tabbatar ya mantar da ita damuwar da take ciki sannan ya d'aga ta ya kwanta gefe yana maida nunfashi. Itakam Zaljameel rigar ta daya d'aga take k'ok'arin gyarawa tana maida nunfashi itama, sosai Jawad ya saukar mata da kasala hakan yasa ta kwanciyarta itama. Matsowa yayi dab da ita ya fara magana. SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L A romantic love story 2017 August 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 73&74 "Zaljameel my wife,menene yasa kike kuka haka?kinsan yarda kukan ki ke tab'a mini zuciya? Jinsa nake har raina, please Zaljameel wipe ur tears", Bata kalle shi ba ta runtse ido tana jin zafin Jawad, Dama yana sonta, amma ko da wasa bai tab'a nuna mata ba, sai ma wata k'irk'irarriyar kiyayya da yake nuna mata, juya masa baya tayi ta cigaba da kuka. Jawota yayi ya d'aura ta a saman kirjinsa yana shafa bayanta, k'ok'arin kwatar kanta ta fara yi,ya kuma k'ank'ameta, "Ya Jawad ka cika ni mana". Murmushi yayi,a hankali ya fara magana kamar mai rad'a!. "wai wannan fushin na menene?" Zumb'uru baki Zaljameel tayi, "Ni ka rabu dani". Kara hugging d'inta yayi, "wallahi bazan cika ki ba indai baki fad'a mini ba". Ganin bashi da niyar cikata yasa Zaljameel ta fara magana cikin kuka "Ya Jawad mai pictures d'ina keyi a room d'inka?" In a romantic voice, Jawad ya fara magana, cuz baya tunanin a yanzu zai iya yima Zaljameel b'oye b'oye dan ta riga ta gane sirrin dake rasa. "Zaljameel" "Na'am" ta amsa tana sauke ajiyar zuciya. "Sonki da k'aunar ki su suka sani jera pictures d'inki a room d'in nan, a duk lokacin da naji kewar ki nan nake zuwa na saka pictures d'in nan a gaba ina kallon beautiful face d'inki,tun ranar da aka haife ki zuciya ta ta kamu da k'aunar ki, kinsan yarda naji lokacin da Areef ya kirani ina egypt akan kin yarda dashi zaki aure shi? Dakin ganni Zaljameel dakin tausaya mini, ramuwar gayya yasa na kira Zahra na sanar da ita zan aureta, Zaljameel kinsan tsawon wane lokaci Zahra ke neman soyayya ta akan na amince da ita amma nak'i yarda dan bata da gurbi a zuciyata, amma nayi kasadar taho da ita na nuna ta a matsayin itace zab'ina, tunda nake ban tab'a yima mahaifina musu ba a duk abinda ya bani umarni sai a kan auren ki, na hak'ura ki auri Areef saboda naga shine zab'inki, nafison farin cikin ki fiye da nawa, bana tunanin ina da sauran farin ciki idan babu ke, wallahi Zaljameel can't do without you ". Ya d'aga fuskarta yana kallon yana yin ta, hawaye take tana murmushin jin dad'in kalaman Ya Jawad, rumgumeshi tayi ta had'a fuskarsa da tata, hancinsu na gogar na juna. " Ya Jawad i'm speechlees, Ya Jawad I love you, wallahi I really love you,ban tab'a tunanin ina sonka ba sai ranar dana ganka dana ganka da Zahra, wani irin kishi ne ya taso mini da ban san inada shi ba, ji nake kamar na shak'e Zahra, a lokacin banson dalilina nayin hakan ba, sai daga baya Ya Jawad nasan na fad'a tarkon sonka, sai dai ko k'ad'an banson ka gane hakan saboda gudun wulakanci ". Wani sanyin dad'i ya ratsa zuciyar Jawad, jinsa yake kamar a wata sabuwar duniya, Zaljameel ta furta masa tana sonsa, wannan ranar is unforgatable to him, bakinsa yasa a nasa ya fara kissing, sun dau wajen 5mint suna faranta ran juna,sannan suka samu nutsuwa. Tashi Jawad yayi zaune yana godia ga Allah daya nuna masa wannan ranar, Zaljameel ya kalla da idonta ke a rufe tana murmushi, murmushin yayi shima ya nufi toilet,wanka ya sake yi ya fito, sai dai bai tarar da Zaljameel ba a room d'in ba, shiri ya fara zuciyarsa fal nishadi. Zaljameel kam Jawad na shiga bathroom ta nufi room d'inta, itama zuciyarta fes, tana godia ga Allah daya mallaka mata Ya Jawad a matsayin mijinta mai k'aunar ta. Bathroom ta shiga itama ta fesa wanka, tana fitowa ta nufi wardrobe ta shirya cikin, wata doguwar riga ash mai dogon hannu, an mata tsaga tunda ga k'asa zuwa cinya, tufke gashin kanta tayi da yellow ribbon, feshe jikinta tayi da perfumes masu k'amshi ta d'auka wani earing mai kyau ta saka light make up tayi ta kuma kallon kanta a mirror, sosai tayi ma kanta kyau, murmushi tayi ta fara tafiya taji an bud'e door d'in room d'inta, zubama door d'in ido tayi, Ya Jawad ne ya shigo, sanye yake da tshirt black da white trouser, hannayen sa ya bud'e mata ya mata alama da ta taho, murmushi tayi ta fara takawa a hankali, cikin sigar shagwaba ta k'arasa wajen Jawad, fad'awa tayi jikinsa Jawad ya rumgume ta. A kunnenta ya rad'a mata, "Baby Zaljameel kinyi kyau sosai, kamar in d'auke ki na gudu". Dariya ya bata "Haba Ya Jawad, ka gudu dani ka kaini ina? Naga dai ai gamu tare a gida d'aya ko?" D'ago kanta yayi ya shafa cikin ta, "Zaljameel cikin nan yunwa yake ji, muje nayi feeding d'inki" yaja hannun ta suka nufi waje. Tsayawa tayi, juyowa yayi yana kallon ta cik'e da mamakin abinda ya tsayar da ita "Zaljameel akwai matsala ne?" Girgiza kai tayi, "Ya Jawad, mai zamu ci bayan banyi girki ba?" Akwai masu girki Zaljameel, nasan sun kammala komai yanzu mu tafi ". Hannun ta yaja suka sauka k'asa, dining suka nufa. Ya labarin gidan sarauta. Hankali kowa a tashe yake, Mai martaba sarki mahaifin Jawad ya aika a kira masa Jawad ya masa tatas Fulani take sanar dashi yarda sukayi da Jawad,hankalin sarki ya tashi, dan hukuncin da Fulani ta yanke baya tunanin shine mafita, sai dai ta riga tayi "Ina Jawad d'in sarki ya tambaya?" Ai tun ranar da dana fad'a masa maganar ya dad'e yana kuka a parlour na daga baya ya fita, to tunda ga ranar na tambayi kowa a gidan nan sunce basu k'ara ganin sa ba, har Areef ma baisan inda Jawad ya nufa ba. Sosai aka zuba malamai akan suyi addu'a Allah ya bayyana inda Jawad da Zaljameel suke, dan yanzu su biyu ake nema. Iyayen su ba'a barsu a baya ba, wajen addu'oin kariya ga y'ayansu, Mom ma taji haushin hukuncin da Fulani ta d'auka, yanzu gashi ta jawo babu Jawad babu Zaljameel, tun tana kuka harta dangana. After one month Zaljameel da Jawad soyayya babu kama hannun yaro, ji suke kamar su shige jikin juna su huta, gaba d'aya Jawad ya cire ma Zaljameel batun zuwa gida, sai dai tana tambayarsa jefi jefi yaushe zasu koma, sai yace mata ba sun kusa. Har lokacin babu wata mu'amala ta aure data shiga tsakanin sa da Zaljameel, lallab'ata yake kamar kwai, sai dai hak'urinsa ya k'are yana buk'atar Zaljameel. Jawad kwance a bed d'insa, yana kallon cielling tunanin yarda zai k'arbi hakk'insa yake cuz bai son sa babyn nasa kuka, amma ya ya iya, dan yana tunanin in har ya wuce yau, zai iya samun matsala. Murd'a handle Zaljameel tayi ta shigo room, dan yanzu a d'aki d'aya suke kwana, tana shigowa ta tsaya tayi crossing hands tana b'ata fuska, kallonta Jawad yayi, sanye take da sleeping dress, black iya cinyarta ce transfarent ce, hakan yasa ake ganin komai dake ciki, white bra da white pant d'in data sa, murmushi Jawad yayi ya mik'e ya nufi Zaljameel, dan yasan abinda take nufi, yana zuwa ya zuba mata sexy eyes d'insa zira hannun sa ya kama k'ugunta, "kinyi kyau matar Jawad". Murmushin jin dad'i Zaljameel tayi, "thanks mijin Zaljameel". Rumgume ta yayi ya fara kissing, a haka suka iso jikin bed, suka zube akai,suna zuba soyayya, a hankali Jawad yayi nasarar raba Zaljameel da kayan jikinta, a takaice dai a ranar Jawad ya maida Zaljameel cikakiyar mace. SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 August 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Happy marriage Aunty kausar luv, ina taya ki murnar auren ki, Allah yasa kin shiga a sa'a ya baku zaman lpy ke da angon ki ameen. Chapter 75&76 Jawad kam yasha mintsini, yak'ushi daga Zaljameel. Zaljameel kam ansha kuka an gode Allah, dan idonta har kumb'ura yayi. Asubar fari Jawad ya bud'e ido, a time d'in Zaljameel baccin wahala ya d'auke ta, zuba mata ido yayi cike da so da k'aunar ta, gashin kanta ya gyara daya rufe mata fuska, bacci take hankali kwance, sai dai tana sauke ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci, tausayinta yaji ya kamashi cuz shi kansa yasan tasha wahala,mik'ewa yayi ya nufi toilet. Wanka yayi ya d'auro alwala, ya fito ya zira jallabiya ya nufi masjid. Bayan ya dawo ya tarar Zaljameel ta tashi tana kukan shagwaba, sai wani yarfe hannu take, tana jin shigowar Jawad yasa Zaljameel ta ja blanket d'in ta rufe fuskarta, dan wani kunyar Jawad take ji yanzu. Murmushi yayi ta tako gaban bed d'in, zama yayi ya fara jan blanket d'in, rikewa Zaljameel tayi gama ta hanashi ja, ta cigaba da kuka! "I'm sorry sweetheart, nasan na wahalar da baby na tuba nake" "Ni babu ruwana da kai, sai da ka gama mini mugun ta sannan zaka bani hak'uri, ni lokacin da nake baka ai baka saurareni ba". Dariya Jawad kesan yi amma ya k'unshe," Please baby na muje na taimaka miki, banza ta masa, hakan yasa ya hawo bed d'in ya d'auke ta chak ya nufi bathroom, da kansa ya gasa ta tana ta koke koken shagwaba, a haka ya kammala mata wanka ya fita ya barta tayi na tsarki. Kanta fito ya d'auke bedsheet ya shinfid'a wani, ya gyara ko ina ya fita had'ama Zaljameel coffee. Tana fitowa taga baya nan, a hankali ta d'ingisa ta fice daga room ta nufi nata, wardrobe ta nufa ta d'auka wata pink d'in doguwar riga, tabi jikinta, ba tayi make up ba dan babu lpy, ta dai shafa powder da lipgloss ta shimfid'a prayer mat ta zira hijab ta fara sallah, bayan ta idar tayi azkar ta shafa ta koma gefen bed ta zauna tana tuna muguntar da Jawad ya mata,ji tayi an murd'a handle, zama ta gyara ta wani yi kicin kicin da fuska, ta maida kanta gefe. Murmushi yayi ya sosa k'eya, ya k'araso ciki hannun sa d'auke da hot coffee, zama yayi dab da Zaljameel jikinsu na gogar na juna ya mik'a mata coffee, "my darling gashi ki sha please" hararsa Zaljameel tayi "Bana sha" , ta cigaba da k'unk'uni, tausasa murya Jawad ya sake yi, "Haba mana baby na idan baki shaba zamu b'ata". Kallonsa Zaljameel tayi" Ok har kana tunanin wani b'atawa bayan wacce mukayi, ni ka rabu dani "ta tura baki gaba. " Ok na gane kina b'ukatar mai mai, kallonsa tayi saboda rashin sanin mai yake nufi da mai mai, "tambayarsa tayi," Ya Jawad mai kake nufi da mai mai, "dariya yayi," abinda ya faru jiya tsakanin mu nake so ya k'ara faruwa indai baki shaba "bai k'arasa zancen sa ba Zaljameel ta k'arfi coffee tana harararsa, dariya ya fara mata takai masa duka ya goce" matsoraciya kawai, jiya duk kin cika mana gida da ihu, wayyo Allah na Mom, wayyo Allah na Fulani, "ya fad'a yana kwaiwayon muryarta. Pillow taja a kusa da ita ta shiga buga masa, shikam banda dariya babu abinda yake yi. Sai da ta shanye coffee sannan suka sauka main parlour na k'asa, kasa tafiya tayi sai Jawad ne ya d'auke ta chak suka sauka. Zaune suke a parlour, Jawad ya d'aura kansa a cinyar Zaljameel ya lumshe ido kamar mai shirin yin bacci, hannun su a cikin na juna,jJawad na duba lallen da Fulani tasa aka mata, "Zaljameel henna d'in nan yayi kyau sosai, waya miki?" hannun ta kalla, "Fulani ce tasa aka mini, kasan Fulani na bala'in sona" hodijan Zaljameel aini zan fad'a miki gaka, "haba Ya Jawad kaima ka gani ko?" kai ya gyad'a mata," Zaljameel bacci nake ji, ki sani bacci please "." Ok Ya Jawad, gashin kansa ta fara chakud'awa tana shafawa a hankali, wani bacci mai nauyi ya d'auke shi, kiran sunan sa tayi a kunnensa taji shiru, hakan ya tabbatar mata da yayi bacci, gefen fuskarsa ta shafa tana Murmushi, "sleeping beauty, dan a zahirin gaskia zaka iya cewa Jawad ba bacci yake ba. Zaljameel zaune har Jawad ya tashi, yana bud'e ido ya sauke shi a a cikin na Zaljameel, wani k'ayattacen murmushi ya sakar mata sannan ya mik'e zaune," Mata ta baki tashi ba kenan, na wahalar dake ko? "murmushi tayi aa Ya Jawad," Ok, tashi yayi ya d'auke ta suka nufi uptsairs, room d'insa ya nufa, a bed ya sauke Zaljameel y shiga toilet, 15mint Jawad ya fito daure da towel a waist d'insa, faffad'an kirjinsa a byyane, runtse ido Zaljameel tayi ta kwanta a bed d'in, murmushi Jawad yayi ya nufi mirror, sai da yayi shafa sannan ya nufi wardrobe, white shadda ya d'auka ya dauka ya saka,perfumes kala kala ya fesa, duk shirin da yake Zaljameel na jinsa amma ta basar, ji tayi anyi sama da ita, a razane ta bud'e ido, ganin Ya Jawad yasa ta fara dukan kirjinsa "Kai ko, ri gimar ka tayi yawa, haka kawai ka bama yar mutane tsoro" Dariya Jawad yayi, "Ok ashe tsoron bashi da wuya, ?kinsan ina d'akin nan ai babu abinda ya isa ya kamaki Zaljameel sai dai ikon Allah". Binsa tayi da kallo cike da so da k'auna," thanks Ya Jawad, I really appreciate ". " Don't mention my darling, u are mine for ever, dats means u deserved more my baby" u mean a lot to me, I love you nisful hayat. Hugging din Jawad tayi, saboda murna ta rasa mai zatace masa, kissing d'insa tayi a wuya, dariya yayi ya sauke ta. "Baby Zaljameel zan fita please karki hanani" Ya Jawad ai ban hanaka fita ba amma dai tare zamu tafi? "Aa Zaljameel kishin ki nake yi wallahi ko k'uda banda dole bazai ganki ba" shagwabe fuska tayi, Ya ina da hijab fa sai in saka in mun fita sai na sayi kayan kwarai dama ai kai ka ajiye mini wannan kayan dan ka hanani fita "murgud'a masa baki tayi dariya yayi," ha Zaljameel zanyi maganin rashin kunyar nan, naga har yanzu baki yi hankali baa"Aa Yaya ni kuwa nayi hankali "suka saka dariya gaba d'aya. Room dinta ya rakata ta d'auka hijab suka fita zuciyarsu fal nishadi. SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 August 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 77&78 Room d'inta ya rakata ta d'auka hijab, da kansa ya sama mata ya d'auke ta chak suka sauka, bai ajiye ta ba sai a gaban prado d'insa, bud'ewa yayi ya saka a ciki ya zagaya shima ya shiga. Zaljameel ta zuba masa white eyes d'inta masu kama da madara, masu kuma saukar wa da Jawad kasala. Yana shiga ya saka key zai tada motar ya lura da kallon da Zaljameel ke masa ta gefen ido, juyawa yayi ya suka had'a ido, wani kallo ya watsa mata mai bayyanar da tsantsan son da yake mata, lumshe ido yayi ya bud'e ya sakar mata murmushi. "Sweetheart wannan kallon fa?sai kace yau kika fara gani na, kinga handsome guy ko? ". Dariya Zaljameel tayi ta d'auke kai tana murmushi k'asa k'asa," Haba Ya Jawad ina wani handsome anan, kawai dai ina kare yawa ne da kai ". Ta tsuntsire da dariya. Ido ya fito dashi da alamun mamaki. " Eyyeh Zaljameel ni kika fad'a ma haka ko? Ba matsala zaki gane cewa ni handsome ne, guy d'in da yan mata ke yayi ". Dariya suka saka Jawad yaja mota suka fita. A wani babban mall Jawad yayi parking ya fito, Zaljameel ma ta fito tana kallon mall d'in, ya birgeta sosai, dan tunda tazo Nigeria bata je tayi shopping ba, hannun ta Jawad ya kama suka nufi ciki yana takunsa na k'asaita. Basket ya d'auka suka fara zagaya wa, bangaren Arabian gowns masu kyau, ga wasu galilas d'inkin dubai ready made, Zaljameel binsu tayi da kallo dan kayan sun mata kyau, Jawad ta kalla shima ita yake kallo, kashe mata ido d'aya yayi, "Oya mrs Jawad a bata zab'a". Mak'e kafad'a Zaljameel tayi "A'a ni dai kai zaka zab'a mini". Murmushi yayi "wannan ai shi yafi komai sauk'i ranki ya dad'e, gimbiya Zaljameel matar Yareema Jawad " Dariya Zaljameel tayi, "Kai mijin Zaljameel Allah ya shirye ka" Ameen "Jawad ya fad'a yana dariya shima. Nan Jawad ya shiga d'aukar kayan, sai ya kara mata a jikin ta yaga yarda sukayi mata sannan yasa a basket. Ya mata shopping sosai na kayan sawa, shoes, handbag, jewellries masu kyau, da kayan make up, har sai da Zaljameel ta b'ata rai sannan Jawad ya hak'ura suka bar wajen, suka nufi side d'in chocolate da ice cream suka siya, sai da suka cika basket uku, Zaljameel ta cema Jawad tana zuwa, "Gyada mata kai yayi ta koma baya da sauri. Side d'in hand watch ta nufa, ta zab'a ma habibinta mai kyau da tsada sannan ta taho. Tana b'ullowa inda ta bar Jawad ta wani ci birki jin k'afarta ta mata nauyi, mai zata gani? Jawad tsaye da wasu kyawawan yan mata, da kagansu kasan kud'i ya zauna, sai wani kwarkwasa suke masa suna fari da ido, shikam Jawad ko kallo basu isheshi ba, amma yana duba gefensa ko Zaljameel ta taho, yana ganin ta kam, ya fara musu murmushi, ya yarda suka gaisa sai dai suma abin ya basu mamaki ganin sun dad'e suna masa magana yak'i responding, amma shine harda murmushi. Zaljameel kam ji tayi kamar zuciyarta zata fito dan kishi, wani k'arfi taji yazo mata, da saurin ta ta k'arasa, yarinyar dake washe ma Jawad baki Zaljameel ta d'auke ta da gigitaccen mari, bata dawo dai dai ba Zaljameel ta kuma d'auke ta da mari. Yarinyar ce ta d'ago hannun ta a fuskarta tana mai jin zafin marin da Zaljameel ta mata, idonta duk ya ciko. Wata da suke tare ce ta fara magana wacce daka ganta kasan babu kunya a tare da ita ta nuna Zaljameel da yatsa "Ke yar iskar inace da zaki mari sister ta, dame kike tak'ama?". Zaljameel ce ta kalli Jawad, ganin ya wani crossing hands yana kallon ikon Allah, yana kuma mamakin kishi irin na Zaljameel da k'arfin halin harda mari, ganin yana murmushi bayan yaji ana ci mata mutinci ya b'ata ran Zaljameel, hannu tasa ta d'auke Jawad da mari ta fashe da kuka ta fara tafiya. Yan matan ne suka bishi da kallo suna son ganin action d'in da zai d'auka, sai ganin Jawad sukayi ko a jikin sa, kuncinsa ta mara ya shafa da hannun sa yayi kissing, da sauri yabi bayan Zaljameel yana kiranta, amma bata bi ta kansa ba, gudu kad'an yayi ya tadda Zaljameel, hugging d'inta yayi ta baya, itakam sai k'ok'arin kwatar kanta take amma Jawad yak'i bata dama,juyo da ita yayi suna facing juna ya shiga goge mata hawayen dake bin fuskarta. "Haba my sweetheart mai yayi zafi haka, kika mari yar mutane,?". Banza ta masa tana harararsa tana kuma jin zafin tambayar daya mata, lalle Ya Jawad, ya raina mata hankali "murmushi yayi, yayi k'asa da murya kamar mai rad'a" kefa ki kace ni ba handsome bane, bayan nasan mata rushing suke a kaina ". I'm sorry dear, ba magana muke dasu ba fa, nayi hakane kawai dan abinda kika fad'a mini d'azu," kallonsa tayi dan ita gaba d'aya ma ta manta da maganar da suka yi,lallai Ya Jawad wato ramawa yayi?. Kunnensa ya kama,"Baby na idan bakiyi hak'uri ba, ganin ta masa banza ya yasa Jawad ya tafi zai d'urk'usa a gaban ta, da sauri tasa hannu biyu ta taro Jawad, "A'a habibi na hak'ura". Tashi Jawad yayi da tsananin murna ya rungume Zaljameel "Thanks my baby". Ji sukai wajen ya dauk'i tafi, cikata Jawad yayi suka fara waiwaye, mutanen da suka gani zagaye dasu suna tafa musu ya basu matuk'ar mamaki, Sosai suka birge mutanen wajen, dan a Nigeria basu t'aba ganin masoya kamar Jawad da Zaljameel ba, ciki kuwa harda wacce Zaljameel ta mara. Dariya Jawad da Zaljameel keyi, itakam Zaljameel ta rufe fuskarta da hannu saboda kunya, shikam Jawad ko a jikin sa. Gaisawa da mutanen wajen sukai, sannan Jawad yaja hannun Zaljameel suka nufi yarinyar data mara, cikin jin nauyi Zaljameel ta bata hak'uri, ta hak'ura ta kuma yi dana sanin kula Jawad, sunayen su Zaljameel ta tambaya, d'aya siyama,wacce aka mara kuma khairat, "Wow nice name, can we be friends?" khairat ta tambaya, kallon Jawad Zaljameel tayi, alama ya mata data amince, "why not sister" dariya sukasa sukayi exchanging number, bayan an gama buga musu balance Jawad ya bada atm card aka cire kud'in su, suma khairat da siyama Jawad ya biya musu kud'in suka fita tare. Sallama sukayi siyama da khairat suka nufi motarsu, Zaljameel da Jawad ma haka. SU ZALJAMEEL ANSAN KISHIN MIJI 😂😂🤔🤔 SUMYNBASH CE 💋 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMAH JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 August 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 79&80 Bayan an loda musu kayan da suka siya a boot Zaljameel ta b'ata fuska kamar zatayi kuka, kallon ta Jawad yayi gaba d'aya hankalinsa ya tashi. "Zaljameel me yake faruwa kuma? Ki fad'a mini please" Please Ya Jawad muje gida dan Allah, ko ba zamu zauna ba mu gaida su sai mu tafi, idonta ya kawo kwalla. K'aramin tsaki Jawad yaja, yayi wani kicin kicin da fuska, bai sake kallon Zaljameel ba ya nufi gidansa, Zaljameel ji tayi wani bak'in ciki ya tsaya mata, wato ma bashi da time d'in bata amsa yake nufi ko me. Kallonsa take tana hawaye amma ko da wasa Jawad yak'i juyawa ya kalli fuskarta , dan bayason yaga hawayen ta, yasan zasu saka masa rauni a ransa. A haka suka je gida, motar ma bata gama tsayawa ba Zaljameel ta fita da gudu tana kuka,bin bayanta Jawad yayi da kallo, ya sauke ajiyar zuciya, Zaljameel yama za'ai mu koma gida yanzu, ai sai ranar da alkawarina ya cika tukunna zamu je ga iyayen mu, nasan zasuyi murna da hakan, dan haka da sauran time, fita yayi a motar ya bama mai gate man umarnin shiga da kayan main parlour, ya shige ciki duk ransa babu dad'i. Room d'inta ta shiga ta saka key, kan bed ta fad'a ta cigaba da kukanta, Jawad ma yazo wucewa yaji kukan hakan yasa yaga bazai iya wucewa ya barta a haka ba, door d'in ya shiga knocking,ya murd'a zai shiga yaji a rufe da key. "Zaljameel" ya kirata in a romantic voice, "ki bud'e door d'in mana I want to talk to you kinji ". Tana jin shi amma tak'i bud'e wa, cuz tana son ya yarda su koma gida dan taga inhar ta biye masa to fa a gidan nan zasu mutu. Tashi tayi ta nufi bathroom, wanka tayi had'e da alwala sannan ta fito, wardrobe ta nufa ta d'auka sleeping dress pink colour, transparent ce iya karta cinya ta d'aure kanta da ribbon, sai da feshe jikin diffrent perfumes sannan ta kwanta a bed d'inta tana tunanin Jawad, jinta take wani iri coz ta saba kwanciya a faffad'an kirjinsa, anya yau kam zata iya bacci? Sake juyawa tayi taja pillow tayi hugging d'insa a kirjinta, a haka bacci b'arawo ya sace Zaljameel. Jawad kam ya kasa zaune ya kasa tsaye,sai juyi yake a kan bed ya kasa bacci, ya shiga damuwa bad'an kad'an ba, yanzu ya zai da Zaljameel, bazai iya jurar rashin ta a kusa dashi ba, gangar jikin sa ya saba dana Zaljameel, ga wani sha'awarta da yake ji, tabbas yasan ance bacci b'arawo ne amma baya tunanin bacci zai d'auke shi. Tashi yayi ya sauka main parlour ko zai ga alamun Zaljameel ta fito amma, duk wani da suka siya yana nan, gashi ya tabbata bata ci komai ba, gashi yasan halin Zaljameel da zuciya duk irin knocking d'in da yayi ba bud'e masa zatayi ba, murmushin k'arfin hali Jawad yayi, amma kuma yunwa itama ai bata bari ayi bacci, kwanciya yayi a kujerar main parlour yana tunanin Zaljameel. Zaljameel kwance a bed sai juye juye take, da alama yunwa ke d'awainiya da ita, tun tana iya d'aurewa taga abin yaci tura, zumbur tayi ta mik'e ta fita neman abinda zata ci, dan bama ta gani sosai tsabar yunwa. Tana sauka ta nufi ledojin da suka yi shopping, ta chocolate da ita cream take nema, Jawad kam yana jin takun Zaljameel ya sauke wata sanyayyar ajiyar zuciya, had'e da murmushi mai bayyanar da farin cikin daya samu kansa a ciki. Bata lura da Jawad ba, ta d'auka ledar ta fara duba cikin ta, chocolate d'in ta fito dasu ta baje a k'asa ta fara sha, ta d'auka ice cream shima tasha, sai da taji ta k'oshi ta huta sannan tayi fara k'ok'arin barin parlour, ji tayi an hugging d'inta ta baya, amma razane ta bud'e baki zatayi saka ihu Jawad yayi saurin juyo da ita ya had'a bakinsa da nata ya fara kissing, Zaljameel kam ganin Jawad ne yasa ta saki jiki tare biye masa itama, dan itama bak'aramin missing d'insa tayi ba, sai da yayi romancing d'inta yarda ya kamata har ya samu nutsuwa sannan ya cikata yayi hugging d'inta a kirjinsa yana jin sonta na k'ara ratsa shi. Zaljameel kam anyi luf a kirjinsa sai wani lumshe ido take kamar mai jin 3bacci, gaba d'aya Jawad ya mantar da ita b'acin ran da take ciki da salon soyayyar sa. Kunnen ta Jawad ya kama da bakinsa ya cijeta kad'an, k'ara ta saki tana wani yarfe hannu na shagwaba, daga kai tayi ta harare sa, had'e da turo bcute lips d'inta gaba "Ya Jawad mai nayi maka ka cijeni ?" kallonta yayi itama shi take kallo, sun dau wajen 3mint a haka, sannan ta hura ma Jawad iska a ido. " Ya Jawad wannan kallon fa? " In romantic ya fara magana, yana shafa gashin kan Zaljameel, fuskarsa d'auke da murmushi. " Zaljameel rashin ki kusa dani shine babban hukunci mai wuyar gaske da bazan iya jurar sa, bana tunanin zan iya cigaba da rayuwa a gaba bayan bana tare dake, ina sonki matuk'ar so" Hannun ta ya kama ya d'aura a kirjinsa saitin zuciyarsa ji tayi tana bugawa da sauri da sauri. Zuciyata na harbawa ne saboda ke kad'ai Zaljameel, zata iya tsaya da aiki a duk lokacin da kikayi k'ok'arin guje mata, a da na jure rashin ki Zaljameel amma a yanzu bana tunanin zan rayu idan bake. Hugging d'insa Zaljameel tayi ta fashe da kuka, "please Ya Jawad kabar maganar nan, nima bazan k'ara barinka ba, na hak'ura na barka har sai lokacin da kaso mu koma ga parents d'in mu sai mu koma. Rik'e ta yayi sosai shima yana jin dad'in maganar Zaljameel, harshe yasa ya lashe hawayen ta. " Its ok my baby kukan ya isa haka ko?, bana son ki k'ara yi mini asarar hawaye na kinji " "Insha Allah my habibi, d'aukarta yayi chak ya nufi bed room d'insa, a ranar ma Zaljameel da Jawad an rab'ashe soyayya, sai dai bata sha wahalan na farko ba. After 3 month Babu abinda ya chanja a son da suke ma juna, suna tattalin juna sosai, Zaljameel ta chanja tayi wani fresh tayi k'iba kad'an, tsaye suke a kitchen, suna h'ada lunch, dan Zaljameel tace bata yarda wata ta dinga ciyar da mijin ta ba da kanta zatayi, hakan yasa Jawad ya sallami mai masu girki. Zaljameel sanye da gajeran wando na mata pink colour, sai wata black half best,ta d'aura apron akai, ta tufke kanta da ribbon, Jawad sanye da boxers, sai white singlet yana taya Zaljameel aiki,(shifati) take so tayi, snacks ne na larabawa, duk ta b'ata masa fuska da fulawa, shima ya zuba mata har jikinta, ta bishi zata rama ya d'iba fulawan ya zuba a jikin sa, dariya suka sa gaba d'aya. bayan ta gama h'ada sos taji zuciyarta na bala'in tashi, da gudu ta fita a kitchen d'in ta nufi toilet,bin bayanta Jawad yayi hankalinsa a tashe, amai tayi sosai kamar zata fito da kayan cikin ta, ta jigata sosai, bayan Jawad ya wanke mata ya d'auke ta suka nufi upstairs, a bed d'insa ya ajiyeta yana jera mata sannu, Zaljameel kam sai maida numfashi take, idonta yayi ja tsabar azaba. In minute jikin Zaljameel ya dau zafi ta fara rawar sanyi, lura da hakan yasa Jawad ya lullube ta da blanket, dakinsa ya nufa ya d'auka first aid ya fara auna Zaljameel, ya bata treatment ya mata allurai amma da kyar dan sai da yayi da gaske Zaljameel ta bari akayi mata. Bacci mai nauyi ya d'auke ta . Sai dai me, gaba d'aya Zaljameel bat son k'amshin girki, ko abinci Jawad ya dafa sai dai yaci shi kad'ai, batama son ganin sa, sai dai tayi ta fama da chocolate da ice cream, shine abinda idan Zaljameel tasha babu maganar vomiting,ga yawan bacci da take yi, kuma batason ko wane perfume sai na Jawad shi d'in ma ba shinshina shi take direct ba sai dai kayan da Jawad ya cire, shi zata d'auka ta rufa a fuskarta to anfi zaman lpy,ga zafin rai da take ji dashi, abu kad'an ke hassala ta. Kasancewar Jawad kwararran likita ne yasa ya gane Zaljameel na d'auke da juna biyu sai dai banson kwana nawa bane ko wata nawa,dan bashi da kayan aiki wani private hospital ya kaita, anan aka shaida masa Zaljameel na d'auke da ciki na 3month. Kallon doctor d'in Jawad yayi, "Kana nufin nan da 6 month zan zama dady?" murmushi doctor yayi "Yes my brother, congratulations". Jawad d'aga Zaljameel yayi sama yana juyi da ita, godiya yayi ma Allah daya masa wannan kyauta, haka suka nufi gida da tsantsar farin ciki. After 6 month Cikin Zaljameel yayi girma ya zama k'ato,ga watan haihuwar ta ya tsaya. banda tsokanarta babu abinda Jawad yasa a gaba, wai cikin ta kamar randa, Zaljameel kam dariya ma yake bata. Kamar kullum, kwance suke a bed, bayan sunyi yan dabaru sun faranta ran juna coz cikin Zaljameel ya hana Jawad sakewa. Kwance take tayi tana kallon ceiling, fuskarta d'auke da fara'a, Jawad kam an samu akasin haka, dan wayar da Areef ya masa, akan rashin lpy grandfa, jikinsa yayi tsanani kuma babu sunan da yake ambata sai Jawad da Zaljameel. Hakan y tashi hankalinsa ya kuma sa ya fara kokarin janye k'udirinsa na sai Zaljameel ta haihu, ajiyar zuciya yayi to meya ma marabar tambe da fad'a, tunda Zaljameel d'in ma ai watan haihuwar ta ya tsaya, hakan yasa ransa ko yau Zaljameel ta haihu to tabbas daga hospital sai gidansu kuma zasu nufa direct. Zaljameel ta lura da yanayin Jawad ta kuma tambaye shi yace mata lpy, duk da tasan babu maganar lpy amma ta gyale shi dan bata son tirsasashi kuma itama taji abinda hankalin ta zai tashi. Ta zuba masa ido tana kallonsa taji wani irin ciwon mara ya taso mata, batason lokacin data furta "innalillahi wa'inna ilaihi". SUMMY NACE ALLAH SARKI ZALJAMEEL, YAU ZA'A D'AND'ANI ABINDA MOM TAJI.........🤧😰😭😔 SUMYNBASH CE 💋 COMPILER:AISHA AMINU SHUGABA. 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 YAREEMA JAWAD 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮 ©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L (We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers) A romantic love story 2017 August 2017 Story & written by SUMAYYA SALEES SADEEQ Chapter 85&86 END A GURGUJE PLEASE Ganin sakin fuska a tare da iyayen nasa yasa hankalinsa ya d'an kwanta, tashi yayi tsaye ya nufi inda suke tsaye ya durk'usa gaban su, cikin sark'ewar murya wanda yaci kuka kuma yana cikin tashin hankali Jawad ya fara magana "Dan Allah dan Annabi kuyi hak'ur" Dad bai bari ya k'arasa ba ya d'ago Jawad,"tashi son, ba wannan ne ya kawo mu hospital d'in nan ba, ya jikin Zaljameel"?. Waiwayawa yayi ya kalleta ya sakar mata murmushi, itama murmushin k'arfin hali ta masa,"da sauk'i Dad! Allah ya k'ara sauk'i? "Ameen suka amsa har iyayen mata. Zahra kam baki har kunne, ita ta kawo ma Sarki da Dad babies d'in suka d'auka, an musu kud'uba da sunan Mom da Fulani, Maryam da Aysha kenan. Zaljameel na samun taimakon doctors, hakan yasa ta warware da wuri, Fulani da Mom dama hospital suka dawo da zama suna kula da d'iyarsu. Ana gobe suna aka sallami Zaljameel, dama already Zahra ta gama shirye shiryen shagalin suna, ranar suna mai jego da babies sunyi kyau, ana ta yaba kyawun yaran wasu suce kyan uwarsu sukayi wasu suce baban su, coz a tsakanin Yareema Jawad da Zaljameel kowa ji yake da kyau babu na kushewa. Anyi suna lpy anci ansha kunsan abu na manya.yara sun samu gift kala kala harda kyautar gidaje aka basu, kowa ya watse. Grandpa ya watssake, murna kawai yake na ganin jikokinsa da akayi, yana godiya ga Allah, sai dai ga dukkan alamu Zaljameel da Jawad basu wahala ba, a duk inda sukaje. Bayan suna iyayen da yaran suka had'a meeting. Bayan an zauna anan iyayen ke tambayar su yarda suka had'u, cikin jin kunya da danasani Jawad ya bayyana musu shi ya d'auke Zaljameel, ya kuma sanar dasu irin k'aunar da yake mata. Zaljameel ma ta bada labarin k'aryar da tama Jawad, inda take bayyana musu a lokacin ma Jawad bai tab'a kunsantar ta ba. Iyayen su da grandfa kansu y d'aure, lallai anyi chakwakiya ba k'arama ba, sunyi masu nasiha sosai suka kuma saka musu albarka da yaran su, taro ya watse. AFTER 3 MONTH Zaljameel kwance a part d'in Mom tana danna wayarta, cikin sand'a Jawad ya shiga parlour,Zaljameel bata san da zuwansa ba sai ji tayi an d'aga ta sama, a tsorace ta saki k'ara, tana k'ok'arin kwacewa, riketa Jawad yayi, yana dariya, "Kai my darling, a gaskiya tsoron ki yayi yawa" Harararsa Zaljameel tayi, ta fara k'ok'arin kwace kanta "ni cikani, haka kurum ka tsorata ni" ta turo baki. "Haba maman Hanan da Hanfa, kiyi hakuri mana "Jawad ya shawo kan princess d'insa ya zauna a kan three sitter ya d'aura kan Zaljameel a cinyarsa suna jirar su ta soyayya "Zaljameel yaushe zamu koma gidan mu ne, nifa gaskiya hak'urina ya fara k'arewa" Harararsa tayi tana murmushi, "Kaji ka mijina ai ni naxo kenan babu inda zan sake zuwa kuma". "Wallahi kam baki isa ba, dan kinga nayi shiru bance a bani matata ba, shiyasa kika samu bakin magana ko? ". Kallonsa tayi" Sannu mai mata ". " Yawwa" Jawad ya amsa yana dariya. Yarda tayi dariyar ya tafi da Jawad, bai san lokacin daya h'ada bakinsa da nata ba ya fara kissing,Zaljameel kam an manta a ina ake aka biyewa miji coz itama tayi missing d'insa. Mom ce ta fito daga bedroom tana jijjiga Hanfa data dame ta da kuka zata kawo wa Zaljameel ta lallasheta dan ita kad'ai ke iyawa da rigimar Hanfa, turus tayi ganin Jawad da Zaljameel an lula wata duniyar, da sauri tayi baya ta koma d'akin tana jin haushin fitowar da tayi, lallai yaran nan babu kunya a tattare dasu, kwara ta had'a ma Zaljameel kayanta su tafi tun ba'a mata mai gaba d'aya ba a gida. Sun d'au dogon lokaci a haka sannan Jawad ya kyale Zaljameel, yana maida numafashi, "Gaskiya Zaljameel ki fara shirin tafiya, dan zanyi magana a bani matata" yana gama fad'in haka ya fice a parlour, binsa tayi da kallo tana jin sonsa da k'aunar sa na ratsa duk wani sassa na jikinta, sai a lokacin taji kukan Hanfa, dan haka da sauri ta nufi dakin Mom. AFTER 5 YEARS Tun daga nesa zakaji hayaniyar su a field , sanye suke da sport wears, Zaljameel da Hanfa iri d'aya, Jawad da Hanan iri d'aya, kowannen su da P cap a kansa. Basketball suke bugawa, sai dai Jawad yafi Zaljameel ci hakan yasa Hanfa da Zaljameel ke jin haushin su, ita kam Hanan murna ta isheta team dinsu yafi nasu Hanfa sai kwalo take mata. Jawad ya sake bugawa yaci,dama shine bugawar k'arshe, aikan yaci, wani ihu suka saka shida Hanan suna murna, Jawad ya d'aga ta sama, "Bravo my Dad we deed it" ta bashi peck a kumatu. Zaljameel da Hanfa sai cika suke suna batsewa. Jawad yaje inda Zaljameel ke tsaye tana ta harare harare, "Haba Queen of beauty, wannan fushin bai dace dake ba, ayi zuciya a iya basketball" ya lakace mata hanci. "Bazan iya ba d'in, amma dai kasan nima akwai inda nake winning ba, zaka gani in mun had'e a cricket sai na kaika k'asa ". " Yes haka ne Mom a time d'in mu zamu musu dariya Wallahi "rumgumeta Zaljameel tayi," kad'ai bari my Hanfa, losers zasu zama ". " Losers," Hanan ta maimaita, "ai mu mun daina wasan cricket coz babu dad'i basketball yafi dad'i shi zamu dinga yi ko dady"hakane my proudly Hanan ". "Momy we are feeling hungry a bamu abinci mana"Jawad ya fad'a ya wani shagwabe fuska. Dariya ya bama Zaljameel, suka nufi cikin gida zuciayrsu fal farinciki,sun jera suna tafiya Jawad ya mata rad'a," Zaljameel yaushe zaki bamu Baby ne "hararsa tayi," Baby kuma? Gasu Hanfa da Hanan nan ai sun ishemu ". Zaljameel na ajiyewa Hanfa da Hanan suka d'auka," A'a mom Wallahi bamu isa ba muna son bro or sis please ". Dariya Jawad da Zaljameel sukayi coz basuyi tunanin yaran sunji mai suke cewa ba. D'urkusa Jawad yayi ya kama yaran," Yawwa babies ashe kuma Kuna so, "eh dad muna so" to ku kwantar da hankalinku baby ya kusa zuwa "yeeee suka shige parlour da gudu suna murna. Zaljameel kam cikin ta ta shafa, coz ita tasan akwai ciki a jikinta sai dai bata son months d'in ba,d'aukar ta Jawad yayi suka shiga parlour suma suna hirar su mai dad'i. END, THEY LIVE HAPPILY. JINJINAR BAN GIRMA GA: PURE MOMENT OF LIFE WRITERS, A ZAHIRIN GASKIYA BANI DA KAMARKU, U ARE SPECIAL TO ME GUYS. AISHAT A MUHAMMAD KE TA DABAN CE A ZUCIYAR SUMAYYA, INA MATUK'AR ALFAHRI DAKE MY TWINNY. ZAHRA BUKAR(AUNTY CUTE) KEMA TAWA CE KUMA ANA MUGUN TARE. KAWALLIYA HAPSAT MUSA(INDON KAUY'E, BAN MANTA DAKE BA ALWAYS KINA RAINA. AISHAT AMINU SHUGABA U ARE SUCH A DARLING, KE D'IN TA DABAN CE YAR UWATA TA JINI, INA TAYAKI MURNAR ENGAGEMENT D'IN KI, ALLAH YA KAIMU LOKACI MISHA BIKI💃🏻 SUMYN BASH NOVEL YAREEMA JAWAD FANS FUTHUHATUL KHAIR1&2 ZEE&HUSSY NOVELS ONLINE HAUSA WRITERS WASH HANNUNA WALLAHI KUNA DA YAWA WAD'ANDA SUKA DACE NA JINJINA MUSU, AMMA KUNA RAINA, ZUCIYAR SUMAYYA NA HARBAWA NE SABODA KU MASOYANA. WALLAHI I SOO MUCH LOVE YOU ❤💛💚💙💜🖤 KU CIGABA DA BINA A SABON NOVEL D'INA DAZAN FARA IDAN NAYI SABIWAR WAYA. NIHLAH NIHLAH NIHLAH 💖💖 Karku bari a baku labari. SUMYN BASH CE💋