[12/02, 21:41] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. TSOKACI: Labarin ya faru a gaske, sai kwaskwarima da na yi masa. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA ƊAYA Gumi ne yake keto mata ta ko ina, saboda yanayin tsananin zafin garin da ake busawa. Sai dai zafin da take ji bai kai rabin wanda yake ɗamfare a birnin zuciyarta ba, duba da zafi, zugi da raɗaɗin da ke kwance kane-kane a cikin ranta. Wanda a kullum cigaban da yake samu, shi yake kuma dakusar da ƙwarin gwiwarta. "Fauziya! Ke Fauziya, ki fito ki rufe mana gida. Kin san dai gidan matan aure ne, za ki bar mu a yashe salon wani ƙaton ya faɗo mana." Kiran mafarautar da A'ilo take yi mata, ya katse igiyar tunanin da ta zabarto ta ba tare da ta sani ba. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita tsakar gida, tana shirin magana A'ilo ta sake katse ta. "Allah dai ya kusan raba yari da ɓarawo, don masifa a ce kullum sai ka kwanta a ishe ka da bige-bigen ƙofa. Haƙƙi dai na zaman maƙotaka, wallahi ana shiga haƙƙinmu. Baban Walid ya shigo tun ɗazu ki je ki rufe mana ƙofa. Idan mijin naki ya dawo, ki riƙe hannunsa ki kai shi har ɗaki. Don wallahi idan ƙaton mashayi ya sake faɗo mini ɗaki sai mun sheme shi." Ko kaɗan ba ta ji zafin maganganun A'ilo ba, domin kusan duk maganganunta a hanya suke. Don haka ta gagara furta koda kalma ɗaya, ta ƙarasa soron mai cike da duhu ta haska da 'yar ƙaramar wayarta ta rufe ƙofar. Sai da ta haska yaranta da ke kwance a ƙofar ɗaki, ta gyara musu kwanciya sannan ta koma ciki. Domin zafin da ake yi ne ya sa ta yi musu shimfiɗa a waje, kamar yadda ragowar matan gidan kowacce take yi wa 'ya'yanta shinfiɗa a ƙofar ɗaki. Idan dare ya tsala gari ya ɗan saki, sai kowacce ta mayar da yaranta ɗaki. A hankali ta zauna, bayan ta kashe fitilar wayarta ta latsa lambar mijinta Kabir. Sai dai tashin farko aka tabbatar mata wayar a kashe take, ta mayar da kallonta wurin agogon wayar ya nuna mata ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare. Gyangyaɗi take yi daga zauna, don haka ta kishingiɗa da gefen gadon. Don kada ta kwanta nannauyan bacci ya ɗauke ta, daga baya Kabir ya zo ya yi ta bugun ƙofa da ƙarfi yana ja mata zagi a wurin matan gida. Da yake baccin yana kanta, nan taka ya yi awon gaba da ita. "Wayyo Allah ƙafata! Mami ƙafata cinnaka ya cije ni." Kururwar Fatima ta katse mata daddaɗan baccin da ya yi awon gaba da ita, a gigice ta fita tsakar gidan ta shiga kiciniyar haskewa da hasken fitilar wayarta. Inun Fatima ya cika gidan, saboda azabar harbin kunamar da yake ratsa ta. "Mene ne Fatima? Me ya samu ƙafar ki?" Fauziya ta shiga jera mata tambayoyi tana haska ƙafar tata. Ba ta ga komai ba, sai dai wurin da Fatima ta riƙe ya yi wani irin ja. Da hannu ta janye ta gefe, sai kuwa ta ci karo da wata ƙatuwar baƙar kunama za ta gangara wurin da Na'ima take kwance. Da sauri ta suri wani takalmi da yake gefenta ta buga mata, nan take kunamar ta mutu. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, sai ta rasa taimakon da ake yi na gaggawa idan kunama ta harbi mutum. Ga Fatima da ke sakin kuka kamar za ta shiɗe, duk ta gama gigita ta. Hijabinta ta ɗauko, ta ɗauki Fatima mai kimanin shekara uku ta goya. Wani irin nauyi ta ji, saboda tsohon cikin jikinta da kuma goyon Fatima da ta yi. Kan mudubi ta fara dubawa saboda a nan take ajiyar kuɗi, amma ita kanta ba ta da tabbacin za ta samu kuɗi masu yawa. Naira ɗari biyu taci karo da ita, da sauri ta ɗauka ta fita tsakar gida, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Lawisa tana yin sallama. "Salamu alaikum. Lawisa! Lawisa." Cikin bacci Lawisa ta amsa mata, Fauziya ta gyaya goyon Fatima ta ce. "Don Allah ko zan samu aron dubu ɗaya a wurinki? Zan leƙa na miƙa Fatima kemis, kunama ce ta harbe ta." "Subhanallah kunama fa? To bari na dubo miki, amma dai ba za a samu dubu ɗaya ba." Lawisa ta furta tana daga ɗaki. Fauziya tana nan tsaye, Lawisa ta ɗaga labule ta miƙe mata kuɗin hannunta, "Fauziya wallahi ɗari da hamsin kawai aka samu ga ta." Fauziya ta karɓa tana faɗin. "Don Allah zan tura ƙofar gida idan na fita, koda na dawo idan an rufe Lawisa. An ce ba a son barin harbin kunama da sai na bari zuwa safiya." Lawisa ta furta, "Shi kenan sai kin dawo, Allah dai ya tsare mu. Wallahi shi ya sa kullum na kwantar da su Siyama hankalina yana wurinsu, wannan zafi Allah Ya sa mu ga wucewarsa lafiya." Fauziya ta amsa sannan fita. Kemis ɗin da ke bayan layinsu ta zagaya, tun ba ta ƙarasa ba ta hango shagon a rufe. Ta kalli yagulallun canjin hannunta ɗari. 'Bayan kemis ɗin Bala ina zan kai Fatima?'' Fauziya ta raya a ranta, sai wani tunani ya faɗo mata. Da sauri ta sake ɗaga waya ta kira lambar Kabir, amma har lokacin a kashe take. Don haka ta yanke shawarar zuwa shagonsu, don ta fi tunanin ba shi da caji ne ya sa wayarsa take kashe. Bakin titi ta nufa, a lokacin babu mutane sosai sai tsirari da suke kai-komo. Zuciyarta a cunkushe take tafiya, saboda kukan da Fatima take rairawa ga ciwon ƙafafuwa da bayanta suke yi. Ta ɗan jima a bakin titi babu adaidaita sahu, har ta yanke shawarar fara tafiya da ƙafa. Saboda shagon su Kabir ana iya zuwa da ƙafa, sai dai akwai 'yar tafiya sosai. Tana tafe tana saƙa da warwara a cikin ranta, ga shi duk lallashin da take yi wa Fatima ta ƙi yin shiru. Wani mai adaidaita sahu ta hango, da sauri shiga ɗaga masa hannu. Har ya wuce ta, ganin goyon da yake bayanta ya sa ya dawo. "Baiwar Allah wannan yarinyar da take kuka daga ina?" Mai ɗan sahun ya tirke ta da tambaya, yana wurga mata kallon tuhuma. "Yata ce, shagon Babanta zan je kunama ce ta harbe ta zan kai ta kemis." Fauziya ta furta a gajiya, kallon da yake yi mata na rashin yarda ya sa ta ɗan waiga ta ce. "Fatima ki faɗa masa me ya samu ƙafarki." Fatima ta sake sakin ihu cikin kuka ta ce, "Cinnaka mai allura ne ya harbe ni, wayyo Mami ƙafata. Don Allah ki cire mini allurar cinnaka." Sai da mutumin ya haska Fatima, sannan ya ga zallar kamar da suke yi da mahaifiyarta. Ya ce Fauziya ta shiga, bayan ta zauna ya wuce da su. Ba su yi wata tafiya mai mugun nisa ba suka ƙarasa, ta miƙa wa mai adaidaita sahu ɗari biyun don ya ɗauki kuɗinsa. Ya ce mata ta je kawai, bayan ta yi masa godiya ta nufi layin da shagon ɗinkin su Kabir yake. Tana gab da ƙarasawa shagon, ta ga wani ya fito daga ciki da mukulli yana shirin rifewa. "Assalamu alaikum." Fauziya ta yi masa sallama, mutumin ya amsa mata yana saka mukullin ƙofar. "Don Allah Kabir fa?" Kallon tsaf ya yi mata, yanayinta ya ga ba ta yi kama da masu karɓar ɗinki ba. Kuma koda ɗinkin za ta karɓa, tana mace har sha biyu saura yana ganin dare ya yi. "Hajiya lafiya?" Fauziya ta dafa bango a gajiye ta ce, "Matarsa ce." Sai a lokacin mutumin ya ɗan faɗaɗa fara'arsa. "Ah Allah sarki, ai ban gane ki ba. Wallahi Kabir ya fita tun bayan sallar isha'i, ni kaɗai na rage a shagon ni ma yanzu zan tashi." Wani abu ya tsaya a zuciyar Fauziya, amma don kar ya fahimci wani abu sai ta saki fuska ta ce, "To shi kenan na gode." Kamar ta karɓi aron kuɗi a wurin mutumin, sai kuma ta haƙura. Don ba ta san duk wani abu da zai taɓa mutumci, da martabar Kabir. Kemis ɗin da ta hango a farkon shigowarta layin ta nufa, ta sake zaro ƙaramar wayarta ta latsa lambar Kabir ko Allah zai sa ta shiga. Bugun farko ta ji an ɗauka, don haka ta yi saurin faɗin. "Hello." Ita ma sai ta ji an ce hello da muryar mace, amma sai ta yi tunanin ko network ne ya maimaita abin da ta faɗa. "Abban Na'ima kana jina?" Daga can ɓangaren ta ji an ja dogon tsaki an kashe. Dam! Gabanta ya yi wani mummunan bugawa, wanda ya sa juya ta fara zabarin ƙafafuwanta har take yunƙurin wurgar da ita. Da sauri ta sake latsa lambar amma sai ta ji ta a kashe, haka kawai ta ji zuciyarta tana yi mata wasu-wasin ko kuskuren lamba ta kira. Kamar wacce take bitar hadda, haka ta fara karanta lambar Kabir a fili tana saka wa a cikin wayarta. Ta sake latsa lambar ta kira saboda ta fita daga kokonton da take yi, amma sai ta ga duk lamba ɗaya ce da wacce ta kira da farko. Wani irin abu ta ji ya tokare mata maƙoshi da ƙirji, ta haɗiyi yawu mai ɗaci har ta ƙarasa shagon mai Kemis ɗin da yake ƙoƙarin rufewa. Da sauri ta ƙarasa ƙofar shagon tana faɗin. "Don Allah ka taimaka ka duba yarinyata kafin ka rufe, wallahi kunama ce ta harbe ta." Tausayinta ne ya kama shi, ya zare kwaɗon ƙofar ya koma ciki. Saboda tsabar gajiya, da ƙyar ta iya sauko Fatima ta miƙa masa. Bayanin abin da ya faru ta yi masa, sannan ya yi wa Fatima allurai. Ya ɗebo magunguna ya yi mata bayanin yadda za a ta dinga ba ta, jiki a sanyaye Fauziya ta ce. "To nawa ne kuɗin?" Sai da ya sake duba magungunan ya ce, "Hajiya gabaɗaya kuɗinki dubu huɗu da ɗari biyar." Kirjin Fauziya ya buga, ta dubi wayarta da ko dubu huɗu ba za a saye ta ba ta ce. "Don girman Allah ka yi mini wata alfarma, don Allah ka yi mini haƙuri zuwa gobe da safe. Yanzu haka shagon mahaifinta na zo ba ya nan, wallahi ɗari biyu ce kawai a hannuna." Cike da takaici yake wurga mata wani kallo, ya furta. "Haba Hajiya, yanzu ni kin yi mini adalci kenan? Tun farko ai da sai ki ce mini ba ki da kuɗi, ni ma fa ba shagona ba ne. Yanzu idan Oga ya zo me zan ce masa? Kin san dai gari ba gaskiya, magana ta Allah ba zan iya ba ki kayan dubu huɗu da wani abu ki tafi da su ba." Wayar hannunta ta miƙa masa ta ce, "Na san ban kyauta ba, amma don Allah ka yi haƙuri. Ga wayata ka riƙe, zuwa gobe In Shaa Allahu zan kawo maka cikon kuɗin..." "A'a gaskiya, ba zan karɓi wayarki ba. Zan dai karɓi magungunan, ki je gobe da safen sai ki kawo kuɗin. Idan ma ba ki dawo ba, ni a aljihuna na biya kuɗin allurar da na yi mata." Mai kemis ɗin ya katse ta yana kwashe magungunansa, sannan ya miƙe mata wayarta ya ƙoƙarin fitowa daga ciki. Duk yadda Fauziya ta kai ga roƙonsa fir ya ƙi amincewa, saboda ya jaddada mata shi ma ba shagonsa ba ne. Idan aka samu matsala a aljihunsa yake ciko. A wannan karon ma haka ta dinga tafiya a ƙafa, sai dai wannan lokacin har ta ƙarasa gida ba ta samu adaidaita sahu ba. Sai tsirarun motocin gida da suke kai kawo a titi. Ta ci sa'a kamar yadda ta janyo ƙofar haka ta same ta, ta yi mamaki sosai da har sha biyu da kusan rabi amma Kabir bai dawo ba. Ba yau Kabir ya saba kai dare da sunan yana shago ba, amma bai taɓa haure sha biyun da rabi na dare a waje ba. Wannan ne ya sake tabbatar mata da zarginta. "An ya Kabir ɗina zai iya zuwa wurin wata mace a tsohon daren nan?" Ta furta tana sake tuna muryar wacce ta ɗauki wayar. "Kabir ɗina babu macen da take gabansa." Fauziya ta faɗa tana girgiza kanta. Da haka ta miƙe ta sake yi wa su Na'ima shimfiɗa a tsakar ɗaki, ta kwantar da su don ta samu Fatima ta tsagaita da kukan. Bugun ƙofarsa ta ji, ta ji wani ɓacin rai ya lulluɓe ta. Kamar ba za ta tashi ba, tuna gidan ba su kaɗai ba ne ya sa ta yunƙura ta fita ta buɗe masa. Saboda haushinsa da take ji, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce ciki. Suna shiga ɗaki ta ɗebo kayan abincinsa ta ajiye ba tare da ta tanka masa ba. "Ummu banat lafiya kuwa? Na ga kamar ba yadda na saba ganinki ba." Kamar tana jira a ƙule ta ce, "Ta ya za ga gan ni dama? Bayan kana can wurin 'yanmatanka, yanzu Abban Na'ima cin mutumcin da wulaƙancin har ya kai ka tafi wurin wata har na kira ka ba ta waya." Idanunta suka ciko da hawaye tana jin wani maƙaƙi a cikin zuciyarta. "Ai duk wulaƙancin da za ka yi mini ban cancanci haka daga gare ka ba, amma babu komai akwai Allah." Ta ƙarasa maganar cikin shasshekar kuka. "Innalillah wa inna'ilaihir raji'un! Yanzu ni kike zargi Fauziya? Ni Kabir ɗinki kike zargi da yawon gidan 'yanmata? Yanzu ko wani ne ya jefe ni da waɗannan kalaman, ashe ba za ki iya wanke ni ta hanyar shaidata ba?" Shiru Fauziya ta yi tana mamakin kalamansa, tana kallon rainin hankalin da yake shirin yi mata. Ita kanta da wani ne ya sanar da ita abin da ta ji a lokacin, ba za ta taɓa yarda ba. "Kana nufin wacce ta yi mini tsaki ɗazu ba ka santa ba? Ko kana nufin ba wayarka ba ce? Don Allah Abban Na'ima kada ka mayar da ni wacce ba ta san me take yi ba." Kabir ya sake marairaice murya ya ce, "Haba Fauziya, mene ne nawa ba ki sani ba? Kina tsammanin akwai wata mace da zan ɓata lokacina a kanta? Wallahi abin da kike faɗa ban san shi ba. Haba Fauzeena, yau fa da farinciki na ƙaraso gida saboda 'yan canjin da na samo." Ya yi maganar yana sakin murmushi ya cigaba da cewa. "Wallahi yau aiki ne ya sha mini kai, mun jima ba mu yi ɗinki irin na yau ba." Girgiza kai Fauziya ta yi tana jin ɗaci a ranta, a ɓangare ɗaya tsoron Kabir ya fara kama ta saboda ita da Kabir ba sa ɓoyewa junansu komai. "Abban Na'ima yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki? Yaushe ka fara yi mini ƙarya?" Ƙirjin Kabir ya buga da ƙarfi yana shirin yin magana ta katse shi. "Ko minti talatin ban yi da baro shagonku ba, kuma an tabbatar mini da tun bayan sallar Isha'i ka bar shagon. Ashe kullum ninke ni kake yi? Ina nan yashe da baki ban sani ba." "To ai fitar da na yi daga shagon gidan Alhaji Musa na je, kaya na kai wa iyalinsa kin san duk cikin shagonmu ya fi yarda da ƙwarewa ta. To lokacin da na je ƙofar gidan na kira wayarsa a kashe. Da na ce a yi mini sallama da shi, sai yaran gidan suka ce yana ganawa da wasu abokan kasuwancinsa, sai dai da na jira su kammala. Ganin zaman ya yi yawa ya sa na bayar da wayata aka jona mini caji a gidan, lokacin da Alhaji ya sallame ni har na kusa zuwa gida, na tuna na bar wayata a gidan shi ya sa na koma na karɓo." Kabir ya janyo ledojin da ya shiga da su ya ce. "Ki dubi wannan sayayyar da na yi, duk da kuɗin da Alhaji ya biya ni ne. Wannan shinkafar kwano ɗaya ce, ga taliya da makaroni guda bibbiyu sai wake kwata da na ƙaro mana." Ya sake buɗe ɗayar ledar ya ce. "Wanna kuma fulawa ce kwano ɗaya, ga sabulun wanka da omo dama na ji kin ce za ki yi wanki. Sai biskit da alawar yara." Sai ya sakar mata murmushi ya miƙa mata wata ledar ya ce, "Ga shi har tsire na sayo mana mu da yara, kin ga da safe sai mu sha da shayi tun da har madara na sayo." Har a ranta ta ji daɗi, domin duk halin Kabir mutum ne da ya tsayu a kan ciyar da iyalinsa. Shi ba mai ƙarfi ba ne, amma indai a ɓangaren ciyarwa ne ko wani mai kuɗin ba zai nuna masa komai ba. Amma haka kawai ta ji zuciyarta ba ta aminta da abin da ya faɗa mata ba, duk da ta ji kaso mafi yawa na daga damuwarta ta yaye. "Ina jin a cikin gidan Alhaji ne aka ɗauki wayar da kika kira, amma kin san babu wata mace da zan ɓa ta lokacina a kanta. Haba Fauzeen KB, har kya kawo wani abu ki sa a ranki don Allah?" Jin sunan da ya faɗa mata ya sa ta saki murmushi, nan take ta aminta da shi. Ganin ya shawo kanta sai ya miƙe ya sauya kaya, ya zura jallabiyarsa ya ɗauki ƙatuwar butar da ke cike da ruwa ya ce. "Bari na watsa ruwa wannan zafin ya yi yawa." Har zai fita ta katse shi. "Yau fa kunama ce ta harbi Fatima a ƙafa." Da sauri ya juyo ya ce, "Garin ya ya?" Ya ƙarasa tambayar yana duba ƙafar da Fauziya ta haska masa. A nan ta sanar da shi duk yadda suka yi da mai Kemis, ya ɗan yi jim ya ce. "Wallahi ciki da waje dubu ashirin ne suka rage mini, nake son na adana ta na samu cikon dubu goma sha biyar na haɗa. Domin na sayi ƙofar da za a saka mana a ginin can. Ko ba mu samu ta ɗakuna ba sai mu yi haƙuri zuwa wani lokaci." Sai ya ɗan yi jim ya ce, "Amma daga wurinki babu wani abu da za a samu?" "Wallahi babu Abban Na'ima, sai dai zuwa gobe Dillaliya za ta zo mu ji nawa za ta yi wa firjin nan kuɗi, ni babban tashin hankalina wa'adin kwanakin nan da suke ƙaratowa. Tun da yau saura wata guda cif, kuma na tabbata Alhaji Mudi ba zai taɓa ɗaga mana ƙafa ba. Da ya zo ya yi mana korar kare gara na sayar da firjin, a yi abin da ba ya rage mu koma. Tun da ba wutar nepa muke samu ba, ka ga yafi ajiyar da ake yi da shi." Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce, "Allah zai kawo mana ɗauki, amma gaskiya ba na son ki sayar da firjinki Fauziya. Ki bari dai mu ga yadda Allah zai yi da mu, idan muka koma can wataƙila a dinga samun wuta sai ki yi sana'a da shi." Fauziya ta gurgiza kai, "Kai fa ka ce mana ya ce ranar da notice ɗinmu ya ƙare duk wanda bai tashi ba zai fitar masa da kayansa titi, tun da har muna da abin da za a ɗaga a sayar ɗin ya fi zaman wulaƙanci Abban Na'ima. Na gaji da gidan nan, na gaji da zaman takurar da nake yi ni da 'ya'yana a ciki." Fauziya ta ƙarasa maganar tana jin ɗaci a ranta. "To shi kenan Fauzina, amma dai aro zan karɓa idan Allah Ya hore na ba ki kuɗinki ko jari kya ja." Daga haka ya saka kai ya fice, ta bi bayansa da hararar wasa ta ce. "Ko ba aro ba? Lallai Abban Na'ima." Da yake hanyar banɗakin, da hanyar fita duka kusan hanya ɗaya ce. Da sauri Kabir ya yi soron gidan, ya latsa lambar Surry don tun bayan da ya baro wurinta ya saka wayar a blacklist ta yadda ko ta kira shi ba za ta yi ringing ba idan ba shi ya duba ya gani ba. Murya ciki-ciki ya ji ta ɗauka tana faɗin. "Na gode Kb har ni za ka yi blocking saboda ka koma gida, ai na gwada kiranka da wani layin na ji ya shiga." Kabir ya yi ƙasa da murya ya ce, "Kin san bala'in da kika kusa ɓallo mini kuwa? Wai Sury dama bayan kin shiga gida da wayata matata ta kira kin ɗauka? Gaskiya ban ji daɗi ba kada ki sake yi mini haka." Ganin ran Kabir ya ɓaci sai ta kwantar da murya cikin kissa ta shiga ba shi haƙuri, da yake duk ba a nutsuwarsa yake ba sai ta fahimci haka. "My Kb wai lafiya na ji muryarka haka? Kamar a tsorace kake?" Kabir sai da ya ɗan leƙa don kar ataho bai ji ba ya ce, "Ke ina soron gidanmu fa, yanzu haka wankan da kika jaza mini zan yi shi ne na raɓe a soro. Kin ga yanzu dai sai da safe, kada ta ji ni shiru ta biyo bayana." Har zai kashe ta shagwaɓe murya ta ce, "Baby don Allah kada ka fasa zuwa kai ni ganin ginin da kake yi mini, ka san yadda na gama ba wa ƙawayena labarin gidan kuwa? Gaskiya dole na yi bidiyo na nuna musu." Kabir ya saki murmushi ya ce, "Haba love, ai tun da na yi miki alƙawari kin san ba zan saɓa miki ba, yanzu dai ki yi bacci da tunanina..." Motsin da ya ji a bayansa ya sa shi saurin waigawa, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi sakamakon tozalin da ya yi da Fauziya. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [12/02, 21:42] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA BIYU Irin kallon da take wurga masa, ya shi saurin sauke wayar daga kunne gabansa yana faɗuwa. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, tana bin sa da kallon tuhuma. Duk da ba ta ji wayar da yake yi ba, amma tana da tabbacin da mace yake yin wayar. "Abban Na'ima wankan kenan?" Fauziya ta furta murya babu walwala. Kallo ɗaya za ka yi wa Kabir ka fahimci ba shi da gaskiya, a ɗan diririce ya ce. "Wallahi wata amarya ce ta dame ni da kira, wai gobe ɗaurin aure ban gama mata ɗinki ba." A wannan karon ita kanta Fauziya ba ta aminta da shi ba, duk da a cikin duhu ne amma hasken fitilar wayar ta fallasa sirrin zuciyarsa. "Abban Na'ima!" Ta furta kamar za ta yi kuka, saboda sauye-sauyen halayensa a kullum ƙara ba ta tsoro suke yi. "Abban Na'ima, yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki?" Kabir da har lokacin ƙirjinsa yake bugawa, ya ɗago wayar da yake har lokacin bai kashe ba ya ce. "Ga ta ai ban kashe ba, kina iya yi mata magana Fauziya." Kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta karɓi wayar. Saboda ta fahimci kamar akwai abin da yake ɓoye mata. "Hello!" Fauziya ta furta cikin sanyin murya, daga can ɓangaren Sury ta amsa. "Uwar gida sarautar mata!" Kusan lokaci ɗaya zuciyoyin Kabir da na Fauziya suka buga da wani irin ƙarfi. "Ban da abinki uwar gida, Oga ai ba na ki ba ne ke kaɗai." Maganar Sury ta katse su, nan take jikin Kabir ya ɗauki karkarwa saboda ya yi tsammanin Sury za ta rufa masa asiri. Fauziya tana shirin yin magana Sury ta cigaba da magana. "Idan kika riƙe Oga ke kaɗai mu costomers ina muka kama? Kin ga gobe ɗaurin aurena, a haka ma sai magiya nake kada ya jirga ni, shi ya sa na kasa haƙuri na kira yanzu na yi masa tuni." A fili Fauziya ta sauka ajiyar zuciya ta ce, "Shi kenan, Allah Ya sanya alheri." Sury ta amsa da Amin, sannan ta katse wayar. Butar ya ɗauka ya wuce banɗaki, ita kuma Fauziya ta wuce ɗaki duk sai ta ji ba ta ji daɗin abin da ta yi masa ba. Fauziya tana da kishi sosai a kan Kabir, sau tari sai ta yi wani abin sai kuma ta ji ba ta kyauta ba. "Allah ka rage mini raɗaɗi da zafin kishin bawan Allahn nan, ina tsoron kada zuciya ta sa na fara zargin mijina." Ta furta a raunane. Washegari tun da gari ya waye, Fauziya ta fito ƙofar ɗaki ta fara haɗa musu kayan karin safe. Da yake kowacce abin girkinta yana ƙofar ɗakinta, kasancewar babu kitchen a gidan. Gidan da su Fauziya suke zaune, gidan haya ne mai ɗauke da ɗaukunan mata biyar. Kowacce daga mai yara biyu sai zuwa uku, kuma dukkansu ɗakunansu falle ɗai-ɗai ne sai banɗaki ƙwaya ɗaya da suke amfani da shi. Dalilin da ya sa su A'ilo suka kafa wa Fazuiya ƙahon zuƙa saboda, duk cikinsu mijinta ya fi nasu rufin asiri. Domin ta fi su yawan sauyin tukunya, don Kabir idan da 'yan kuɗi a hannunsa haka zai sayo musu nama ko kifi ko ba can mai yawa ba ta sarrafa. Kuma indai Fauziya ta yi sauyin girki duka sai ta zuba a 'yan robobi ta aika masu, saboda fita haƙƙin maƙotaka. Duk cikin gida Lawisa ce kawai ta su ta zo ɗaya, ba ta yi mata irin cin kashin da su A'ilo suke yi mata. Don haka Fauziya da Lawisa suka haɗa kai, su kuma su A'ilo suma su uku suka haɗe kansu. Da yake ita Lawisa ba ta da haƙuri, sai ya zama suna shakkarta don suna yi mata kan kara take yi musu na itace. Saɓanin Fauziya da ta kasance mace ce mai sanyi, tsananin haƙuri da kawaici. Duk abin da za su yi mata ko su yi wa yaranta, sai dai ta yi shiru idan kuma yara aka yi wa sai dai ta zaunar da su a ɗaki. Babu damar yaranta su fita wasa tsakar gida, sai yaran su A'ilo su doke su da yake kusan duk sun girme su. Ita kuma Fauziya ƙiris suke jira ta yi wani kuskuren, ko ta taɓa kayan wani daga cikinsu sai su hau ta da faɗa. Don haka gidan suke zaune kara zube babu haɗin kai, hatta shara kowacce sai dai ta share iya ƙofar ɗakinta. Banɗaki ma kuwa sai dai kowacce idan mijinta zai yi wanka, ta ɗauki buta ta je ta wanke masa. Shara ce kawai idan ta cika suke haɗawa, idan ta cika wannan ce za ta biya idan wani karon ta sake cika sai wata ma ta bayar da kuɗi a kwashe. Maman Sabir tun da ta fito tsakar gida take leƙen abin da Fauziya take dafawa, ana cikin haka Kabir ya fita ya sayo musu ƙwai guda huɗu. Nan take gidan ya cika da ƙamshin suyar ƙwai, baƙinciki da hassada suka ƙara cika zuciyoyin su. Bayan ta gama sai da ta gutsiri kaɗan-kaɗan ta saka a leda kowacce ta miƙa mata, sannan suka shige ɗaki ita da iyalanta suka karya. Da yake ranar Lahadi ce babu makarantar boko ya sa bayan sun gama ta yi wa yaranta wanka. Kabir ya ɗauki Fatima ya mayar da ita kemis, ya karɓo mata magunguna sannan ya wuce shagonsu na ɗinki. Su Fatima ne suka fita tsakar gida wasa, abin ka da yaro duk kyarar da yaran su A'ilo suke yi musu da sun ga suna wasa haka za su je su shiga cikinsu. Zaman su a wurin babu wuya kenan sai Nabila ta fisge abin wasanta a hannun Na'ima ta ce, "Umma ta ce na daina wasa da ku, babanku ɗan shaye-shaye ne." Duk da ba su san me kalmar take nufi ba, amma tun da suka ji suna yawan faɗa musu cikin tsangwama sai suka ƙyamace ta, Na'ima ta ɓa ta fuska ta ce. "Ba dai babanmu ba, sai dai babanku. Abi yana siyo mana alewa da biskit, ba ɗan shaye-shaye ba ne." Duk cikinsu Sabir yayan Nabila ya girme su, don kusan shekararsa goma. Ya fi su wayo don haka ya ce, "Ke mu babanmu ba ya shaye-shaye, Ummanmu ta ce mu daina wasa da ku kada mu zama 'yan'iska. Wai babanku har shiga ɗakin matan aure yake yi."Yaron ya ƙarasa magana yana dariyar tsokana. Abin sai ya yi wa su Na'ima ciwo, don haka suka shiga mayar da martani abin har ya zame musu faɗa. Suna cikin kokawa su Nabila suka tararwa Na'ima da duka, da ta ji zafi ita kuma sai ta ciji Hafsa a hannu. Nan take iyayensu suka fito, dama kamar jira suke yi. Cikin masifa Maman Sabir ta fisge Fatima tana ƙwalawa Fauziya kira, Fauziya da ke ɗaki ta yi saurin fitowa tana shirin yin magana Maman Sabir ta katse ta. "Wallahi wannan shi ne na farko na ƙarshe, ko da wasa idan Fatima ta sake cizar mini 'ya'ya sai na ɗauki hannunta na tura musu a baki sun rama. Ƙarya aka yi uban na su ba mashayi ba ne? Na ga rannan da ya yi mankas ɗakin A'ilo ya faɗa." Fauziya ta yi shiru ta rasa bakin magana, Lawisa ta ɗaga labule tana faɗin. "Haba ku kuwa kamar ba ku san faɗan yara ba har za ku shiga? Wallahi indai yara ne kuna zaune za su ba ku kunya..." A zafafe Abu ta katse ta. "Sai ki bari idan an ciji naki 'ya'yan sai ki faɗi haka, za ki fito ki yi wa mutane gwalangwaso. Don sun ce ubansu ɗan maye ne shi ne za ta cije su. Shekaran jiya waccan, ina ce butata ya ɗauka ya yi mini wurgi da ita ta fashe." Lawisa za ta sake magana Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta girgiza mata kai sannan ta ce. "Don Allah ku yi haƙuri, In Shaa Allahu ba za su sake cizonsu ba." Kusan lokaci ɗaya suka taɓe baki, Fauziya ta yi wa su Na'ima magana suka wuce ɗaki. Jiki a sanyaye ita ma ta wuce ɗaki, tana jin su A'ilo suna ci gaba da yadda mata magana da habaici haɗe da yin dariya. "Mami wai mene ne shaye-shaye? Me ya sa kullum su Sabir suke ce mana Abi yana shaye-shaye?" Tambayar Na'ima ta katse dogon tunanin da Fauziya ta faɗa. Ras! Ta ji gabanta ya faɗi, da sauri ta kamo hannunta fuska ɗauke da alamun tsoro ta ce. "Kul Na'ima yara ba sa faɗan irin wannan maganar kin ji! Babu kyau kada na sake jin kun faɗi haka." Lokaci ɗaya suka gyaɗa mata kai, sai Hidaya ta ce. "Mami to ki faɗa wa su Hafsa su daina faɗa kada Allah Ya ƙona su a wuta." Fazuiya ta yi murmushi ta ce, "Su ma mamansu za ta faɗa mu, sannan don Allah Hidaya ku daina zuwa cikinsu kuna wasa. Ba ga kayan wasanku nan ba, ku dinga zama a ɗaki kuna yi kun ji." Lokaci ɗaya suka amsa mata, tana nan zaune ta ji sallamar Sadiya facalarta. Daga wurin da take zaune ta amsa mata, Sadiya ta shiga tana faɗin. "Uwar huɗu, wai har yanzu ba za ki kotse ba ne?" Fauziya ta miƙa mata fulo ta ce, "Zauna uwar 'yan sa ido, ni kaina kullum jiranta nake yi." Sai da suka gaisa Fauziya ta ce, "Ina zuwa haka da tsakar rana?" Sadiya ta yi dogon tsaki tana kallon su Na'ima da ke wasa ta ce, "Ai tun da akwai radiyo mai jini dole na gyara zancan. Wallahi Fauziya komai ya yi mini zafi, kin san dai halin wancananka. Yau haka ya ƙare mini zagin cin mutumci, saboda kawai na ce ya biya ni kuɗaɗen da nake bin sa bashi. Ke dai shaida ce kin san ba yau ya fara zagin iyayena ba, ni ma yau na gaji na rama. Ke faɗa har sai da ya kaimu tsakara gida, shi ne fa o'o (Inna) ta shigarwa ɗanta suka yi mini zagin ƙare dangi. Abin da ya sake ɓata mini rai kwanana uku kenan ina zazzaɓi, kullum nace ya ban kuɗin magani sai ya ce mini yake ba shi da kuɗi. Amma ina duba wayarsa a chart ɗin da suke da budurwarsa, na ga ya tura mata dubu shida kuɗin ɗinki wai bikin yayarta ake yi." Sadiya ta furzar da iska mai zafi, tana tuna ɗacin abin da mijinta ya yi mata ta cigaba. "Kin san fa shi indai a kan 'yanmata ne duk arzikinsa a nan yake tafiya, ni kuwa ina gida ko oho wani lokacin na omon wanki ma gagarata yake yi." Fauziya ta girgiza kai cikin damuwa ta ce, "Ke ma Sadiya tun tuni kin san halinsa, da kin sani ba ki biye masa ba kun yi ba daɗi a gaban yara ba. Ita kuwa dama kin san yaranta ba sa laifi, kwanaki fa a gabanta ya mare ki amma sai cewa ta yi ai ɓata masa rai kika yi." Kamar Sadiya za ta yi kuka ta ce, "Idan ban biye masa ba Fauziya ya zan yi? Kina ga fa haka zai tsallake ya bar mu indai akwai tsaba babu ruwansa da kuɗin kayan mahaɗi, duk ni nake fafutukarsu. Ga shegen kule-kulen mata har da na hauka, don wallahi da kuɗin da yake kashe musu ba gara mu ya kashe mana ba." "Eh to haka ne, lamarin ne sai haƙuri kawai. Ni dai ta nan fanin sai dai na ɗaga hannu na gode wa Allah, domin gaskiya babu macen da ta sha gaban Kb da har zai tsaya ɓa ta lokaci a kanta..." Murmushin da Sadiya ta yi ya katse furucin Fauziya. "Ban ga laifinki ba, da kika faɗi haka. Domin ruwan da ya dake ka shi ne ruwa. Amma ni dai a wannan gaɓar da zamantakewata da Ali, ta koma irin da zaman cin kunamar ƙadangare. Na rantse da Allah ko me aka ce mini ya yi ba zan musa ba, ki bar cin alwashin namiji saboda ko yaya basa rasa 'yanmatansu ke dai ki ga rijalu kawai." Fauziya ta yi dariya ta ce, "A'a Sadiya, dole na bigi ƙirji wallahi ko a gaban mutanen duniya Kb ɗaya a cikin dubu, ya zamo mini tamkar zara a cikin taurari. Ni shaida ce wallahi-wallahi tun daga ranar da ya muka fara soyayya, har kawo yanzu babu macen da yake kulawa." Sadiya ta miƙe tana gyara hijabinta ta ce, "To ni bari na zo na wuce, ko ba komai mun ɗan tattauna na rage zafin da nake ciki. Kada na daɗe uwar masu gida ta fahimci na fita, na ƙara wani laifin." Har soro Fauziya ta raka ta, Sadiya ta yi ƙasa da murya ta ce. "Wai mutanen gidanku har yanzu zaman naku sai a hankali ne? Na ga da na yi sallama A'ilo ba ta amsa mini ba." Fauziya ta furta, "Hmmm ke dai bari, wallahi shi ya sa zaman gidan duk ya gundure ni." Fauziya da Sadiya sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Sai da ta tabbatar da yaran sun tafi makaranta, shi ma Nazir ya tafi kasuwa. Sannan ta shige uwar ɗaki, ta buɗe drower kayanta. Daga can ƙasa ta zura hannu ta ciro 'yar ƙarama wayarta, ta koma gefen gado ta zauna sannan ta kunna ta. Ba a ɗauki lokaci ba wayar ta kunnu, nan take ta latsa wata lamba ta kira, daga can ɓangara aka ɗauka. "Barka da safiya sarauniyata!" Maimuna ta saki murmushi cike da kissa ta ce, "Barka dai jarumin jarumai." "Wai sai yanzu ya matsa ya ba mu wuri ne? Wallahi tun safe nake jin ƙishirwar muryarki." Jafar ya furta cike da sha'awa. "Hmmm to ya za a yi? Ka san abin ka da mai iyali ko ya fita ai dole sai na sallami yara." Jafar ya yi murmushi ya ce, "Me zan samu? Don wallahi yau kwana biyu kenan, na kasa kataɓus da waccan sakaryar." Dariya sosai Maimuna ta yi ta ce, "Wallahi babu ruwana, kai da Maman Nana." Jafar ya sake kwantar da murya cikin wani irin yanayi ya ce. "Moon!" Yadda ta ji ya ambaci sunanta ya sa har sai da ta ji tsikar jikinta tana tashi, ta janyo filo ta rungume cikin wata irin murya ta amsa. "Na'am Abban Nana!" Ajiyar zuciyarsa ta ji har a fili, ya sake narke murya ya ce. "Ba na son ki dinga kirana da wannan sunan, tun da ita ma waccen haka take faɗa. Don Allah ki saka mini sunan da zai dinga faranta mini rai." Maimuna ta lumshe ido, ta ɗan shagwaɓe murya ta ce. "Baby ya yi?" Shi ma sai ya yi irin muryarta ya ce, "To ya zan yi? A dinga faɗa mini hakan, amma dai har yanzu kin ƙi ki ba ni dama na nuna miki zallar soyayyar da nake yi miki a cikin zuciyata." Jafar ya sake kwantar da murya cike da shauƙi, kamar wanda yake waya da matarsa ya ce. "Moon! A gaskiya Naziru ba ƙaramin dace da sa'a ya yi ba. Wallahi da ace ke na fara gani kafin Sumayya, da babu abin da zai hana ban aure ki ba. Don Allah ki ba ni dama koda sau ɗaya na nuna miki salon tawa kulawar." Wani farinciki ne ya lulluɓe Maimuna, tabbas ko bai faɗa mata ba. Ta sha ji a bakin Maman Nana, cewar Jafar gwani ne a fagen kulawa da soyayya. Don da bakinta take ba ta labarin Jafar irin maza nan ne masu buɗaɗɗan ido, don cewa ta yi wani lokacin wayewarsa har tsoro take ba ta. A duk lokacin da Maman Nana take ba wa Maimuna labarin mijinta, sai dai ta yi ta sha'awa tana jin ina ma ita ce ta yi dacen samun miji wayayye mai rifin asiri kamar ita. Kafin daga baya kuma su tsunduma kogin soyayyar da suka yi nisan kiwo ba tare da sun ankare ba. "Moon! Ba ki ce komai ba." Jafar ya katse mata tunani, Maimuna ta yi murmushi sannan ta ce. "Ina tsoron kada Maman Nana ta gano mu, ka ga a cikin unguwa ɗaya muka." "Haba My Moon, ai dama ko don magulmata ba za mu haɗu a unguwa ba. Wallahi ko hotel zan iya kama mana..." Cikin razani Maimuna ta ce, "Hotel!" Kafin Jafar ya yi magana daga can falo ta ji motsi, da sauri ta katse wayar ta zare batirinta. Jikinta har karkarwa yake, ta tura wayar cikin drowerta. Tana waigowa ta ga Naziru yana tsaye a bakin ƙofa ya harɗe hannuwa a ƙirjinsa. "Maimuna da wa kike magana?" Ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi, cikin firgici bakinta yana rawa ta ce. "Ni... ni... kuma?" Fuska ta ga ya ƙara haɗewa, bai tanka mata ba sai gyaɗa mata kai da ya yi. Kabir yana fita daga gida tun bai ƙarasa titi ba, ya kira Sury. Cikin muryarta mai fisgar hankalinsa ta ce, "Matsoracina! Wato sai yanzu ka samu damar fita daga gida?" Kabir ya saki murmushi ya ce, "Kin gan ki ko?" Sury ta ɗan haɗe fuska kamar tana gabansa ta ce, "Kb ni fa jiya abin da ya faru ka sa na fara jin tsoron ko yadarata kake yi. Ka duba fa ka gani tambaya ɗaya matarka ta yi maka amma duk ka birkice, yanzu a haka za mu yi auren har ka kai ni gidan da kake gini?" Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Haba baby, me ya sa kike kawo wasu-wasi a cikin soyayyarmu ne? Kin san dai ina sonki ina ƙaunarki. Ko soyayyar da na nuna miki jiya ya ci ki fahimci irin soyayyar da nake yi miki. Ki ajiye maganar aure, wannan wani lissafi nake yi a kansa kin san ke ba kalar zaman gidan haya ba ce." Sury ji ta yi kanta ya sake girma, ta lumshe ido cike da jin soyayyar Kabir tana sake nuƙurƙusarta. Domin Kabir irin mazan nan da suka iya nuna zallar soyayya, duk cikin samarin da ta yi babu wanda take yi wa mutuwar so kamar Kabir. Sun jima suna hira sannan suka yi sallama, suka tsayar da magana a zuwa bayan la'asar zai kai Sury gidan da yake gini ta gani. Har zai saka wayar a aljihu sai ya ha wata lambar ta shigo, guntun tsaki ya saki kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka. Yana ɗauka ya ji ta fashe masa da kuka, shiru ya yi yana jin kukanta har cikin jikinsa. "Kukan na mene ne?" Kabir ya furta cikin tattausan lafazi. "Na gagara jure rashinka ne, na gagara jure horon da ke raunatar da zuciyata. Kabir! Ka san na saba da hutawa a lambun ƙaunarka, sai da ka bari zuciyata ta yi nisan kiwo a ƙaunarka sannan kake ƙoƙarin fincike ta da ƙarfin tsiya. Me ya sa kake azabtar da ni Kabir?" Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Hafsa kenan! A kullum haka kike faɗa a fatar baki, amma kin gagara nuna mini zallar soyayyar da kike faɗa. Hotuna biyu kawai na ce ki ɗauka ki turo mini, amma kin ƙi yarda ko ba ki yarda da ni ba ne?" Jim Hafsat ta yi tana nazari zuwa can ta ce, "Shi kenan, zuwa dare zan turo maka matuƙar za ka sauka daga dokin zuciyar da ka hau." Kabir ya cije baki yana murmushin samun nasara ya ce, "Haba ko ke fa Hafsyna, da sai nake ganin kamar ni nake wahalar da kaina a kanki." Hafsa ta ce, "Hmmm ba za ka gane halin da nake ciki ba, yanzu dai yaushe za ka zo." Shiru ya yi yana nazari, don Sury ta kwaɗaitar da shi irin salon tata soyayyar. Kuma ko babu komai ya san idan ya kai ta kangon da yake gini, zai iya samun fiye da abin da ta yi masa a soron gidansu a daren jiya. Don haka ya ce, "Ammm yau dai gaskiya ɗinki ya yi mini yawa, saboda akwai kayan amaren da ban kammala ba. Bayan haka ma, Oga yana raba mana ɗinki saboda gobe za a tafi da su Abuja. Ina jin sai zuwa gobe za ki gan ni." Hafsa ta narke murya ta ce, "Wallahi na yi kewarka, kwana ukun da ka daina ɗaukar wayata ji nake kamar mun shekara ɗari uku." Kabir ya yi murmushi sannan suka cigaba da hira, bayan sun gama ya wuce shago. Bayin Allah wasa farin girki kenan, me kuka fahimta a game da rayuwar Kabir? Kabir yana da 'yanmata amma ya aka yi Fauziya ba ta sani ba? Kuma me kuke tunanin ya sa ta ba shi yarda 100% a kan babu budurwar da yake kulawa. Ga dai Maimuna tana soyayya da mijin maƙociyarta, shin wacce amsa za ta ba wa mijinta Naziru? Sai na ji daga gare ku.😄 Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [12/02, 22:13] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA UKU Tun da yamma ta kawo kai Sury ta fara doka wa Kabir kira, saboda zumuɗi tun bayan Azahar ta gama shiryawa. Kasancewar akwai ɗinkunan da Ogansu ya tara na 'yan wunin biki ya sa shi tsayar da ragowar yaran shagon ya raba musu ɗinkunan domin su yi saurin gamawa. Wannan dalilin ne ya sa da Sury ta kira shi ya sanar da ita, a zuwan ya ɗaga mata ƙafa ko zuwa gobe ne. Ko kaɗan ba ta ji daɗi ba don haka ta nuna masa ɓacin ranta. "Kb shi ya sa nake tsoron soyayyarmu, wallahi sai na ga kamar yaudarata kake yi. Na kai kwana nawa ina son ka kai ni na gano ginin nan, amma yanzu ka zo kana tsara ni." Kabir ya miƙe ya fita zuwa ƙofar shagon ya ce, "Kin gane Sury, wallahi da gaske nake yi miki. Amma tun da haka ne ki ba ni zuwa nan da bayan Sallar magriba, duk yadda zan yi na san yadda zan ɓullowa Oga koda ban gama aikina ba." Sury ta ɗan yi jim sannan ta ce, "Amma ka san bayan magriba Yaya Umar ba ya barinmu fita, sai dai na san dabarar da zan yi masa." Kabir ya yi saurin faɗin, "Yawwa Suryna, kamar ba mace ba. Don Allah ki shawo mana kansa ba za mu daɗe ba, muna gama gani za mu wuce." Sai a lokacin Sury ta ji daɗi, ganin ya lallaɓa ta ya sa shi yin sallama da ita ya koma cikin shagon. Ɗinkin kusan mutum uku ne a gabansa, don haka ya ci gaba da ɗinkin cikin sauri don ba ya son abin da zai sake ɓa ta ranta. Girgiza kai Maimuna ta yi, don har cikin ranta gani take kamar Nazir ya ji kalaman da suke tattaunawa. Amma gudun ta yi saurin bada kai bori ya hau, ya sa ta ce. "Gaskiya sai dai idan kunnenka ne." Shiru ya yi yana kallonta kamar mai nazari, har sai da ta sake tsarguwa. Domin a lokacin da ya shiga ji ya yi kamar waya take duk da bai ji abin da take faɗa ba, amma da yake ya ga wayarta tun a falo sai ya basar. Yana shirin yin magana ta ce, "Ko dai waƙar da ka ji ina yi ce?" Cikin halin ko inkula ya ce, "Wataƙila! Ina wayarki take?" Ya tambaye ta don Nazir mutum ne mai bin diddigi da tsanani a kan iyalinsa. "Tana falo!" Ta ba shi amsa a taƙaice. Falo ya koma ya ɗauki wayarta, sai da ya yi shige-shige sannan ya saki muryarsa ya ce. "Wallahi mantuwa na yi, na manta hulunan mutane ɗauko mini suna drowerta." Sai a lokacin hankalin Maimuna ya kwanta, ta shiga ciki ta buɗe drowersa ta ɗebo masa hulunan ta ba shi, sannan ya sake fita. Ajiyar zuciya ta sauke a fili, sannan ta furta. "Dole na sauya taku, tun da mutumin nan yana da key da yake buɗe ƙofa. Ya zama dole na yi takatsantsan, idan ba haka ba a samu matsala." Gate ɗin ta sake komawa ta saka sakata a gidan, sannan ta koma ta zaro ɓoyayyiyar wayarta. Mayar da batirin ta yi bayan ta kunnata ta sake kiran Jafar. "Hello!" Ta furta cikin kashe murya. Daga can ɓangaren Jafar ya ɗauka murya a can ƙasa, sai kuma ta ji muryar Abdul yana kuka. "Wai kana nufin ba ka fita kasuwa ba? Na ji kamar muryar Abdul ko?" Murmushi Jafar ya yi ya sake jan bargo ya ƙudundune, wani shauƙi yana fisgarsa a kan Maimuna ya ce. "Ya za a yi na iya fita? Bayan ina lulluɓe da bargon bege da kewarki. Don Allah Moon ki nemar mana mafita mana, ki tausaya mini wallahi muryarki ba ƙaramin gigita nutsuwata take yi ba." Shiru Maimuna ta yi, tana nazarin hanyar da za ta ɓullo musu domin ita kanta ta kwaɗaitu ta ga irin soyayya da Maman Nana take faɗa mata. "Ka san dai halin Nazir mutum ne mai shegen kishi, ga shi da zargi da bin diddigin duk abin da nake yi. Kana ga hatta unguwa ba ya iya barina na je ni kaɗai, shi yake kai ni duk inda za ni. Wallahi kaina ya kulle ban san ya zan yi ba." Nazir ya kwaɓe murya kamar wani mace ya ce, "Wallahi ni sai na ga kamar ma ba kya yi mini irin soyayyar da nake yi miki. An ya kin san yadda zuciyata ta kamu da mutuwar sonki kuwa..." Salatin da Maman Nana ta saki ya sa Jafar ya yi sauri ɗagowa, nan take gabansa ya faɗi. Maman Nana da kishi ya gama tirniƙe ta ta ce, "Na gode Abban Nana, yanzu wulaƙanci da tozarcin naka ya kai har ka haye mini kan gado ka kira wata shegiya kuna waya da ita? Yanzu ka yi mini adalci kenan? Ashe duk alƙawarurrukan da kake ɗaukar mini na ƙarya ne." Sai kuwa ta fashe da kuka. Hamdala ya yi a ransa da ya fahimci Sumayya ba ta gane da wacce yake waya ba. "Don Allah ki yi haƙuri My love, wallahi duk wani abu da kika ji na faɗa wa yarinyar nan a fatar ba ki ce. Wata yarinya ce ta nace mini, ni kuma ba na son yi mata rashin mutumci kin san wulaƙanci babu kyau shi ya sa nake son mu rabu lafiya." Wani irin mugun kallo take jifansa da shi, rai a ɓace ta ce. "Idan kai ba za ka iya yi mata rashin mutumci ba ni zan iya, ka kira mini ita in zazzage ta ko wacece." Kamar gaske Jafar ya ɗago wayar ya kira ta amma sai suka ji a kashe, ya saki murmushi a cikin ransa. Ya rungumo Maman Nana ya ce, "Kin ji wayar a kashe take, amma riƙe ki yi blocking ɗinta da kanki. Dama ni ban taɓa kiranta ba, ita take kirana amma tun da an yi haka babu ni babu ita. Munafuka haka kawai za ta haɗa ni faɗa da iyalina ina zaman lafiya da ita." Har a ranta ta ji daɗi, don haka ma ta ɗan saki fuskarta. Ta karɓi wayar ta saka ta a blacklist, sannan ta ce. "Abban Nana wallahi wannan ita ce ta farko ta ƙarshe, kada ka mata kwanaki ma haka na yi yaƙi da kai a kan Fati wacce ka ce wai ƙanwar abokinka ce. Wa ya sani ma ko ita ce wannan, wai yanzu duk irin kulawar da nake ba ka amma sai ka kula 'yanmata." Maman Nana ta ƙarasa maganar cikin ɗacin rai. "Don Allah ki daina dawo da bara bana, waccan ta wuce kuma wannan ma In Shaa Allahu ta wuce ba zan sake ba." Ruwan wanka ta juye masa ta dawo ta ce, "Lokacin fitarka yana tafiya ga ruwan wanka can na juye maka." Yanayin da yake ciki na tunanin Maimuna ya sa shi janyo hannunta ya ce, "Wai kwana biyu ba ki da lafiya na ga ko gayyatata ba kya yi!" Murmushi ta yi masa ta ce, "Ai na ga ba ka dawowa da wuri ga gajiya shi ya sa." Da yake ta kwantar da Abdul ya yi bacci, sai bayan da komai ya gifta a tsakaninsu sannan suka faɗa toilet lokaci ɗaya. A gurguje ya shirya ya tafi kasuwa ganin har sha biyu saura, Maman Nana ta cigaba da aiki cikin sauri tana alla-alla ta gama ta leƙa gidan Maimuna. Tun lokacin da Maman Nana ta fara magana, Maimuna ta yi shiru tana sauraronta. Lokacin da ta ji Jafar ya ce zai kira layin Maman Nana ta zage ta, sai ta yi sauri ta kashe wayar gabaɗaya. Haka kawai ta ji wani irin kishi ya rufe, ta shiga hango irin rarrashin da Jafar zai mata. Domin Maman Nana ta sha ba wa Maimuna labarin idan Jafar ya yi mata laifi, matuƙar shi ne ba shi da gaskiya har kusan tsugunna mata yake yi. Sai da Jafar ya shiga mota yana driving sannan ya kira Maimuna amma sai ya ji ta a kashe, guntun tsaki ya saki ya ajiye wayar sannan ya cigaba da driving. Sai da ya shiga cikin shagonsu yana duba wayarsa ya ga misscall ɗinta. Hannunsa har rawa yake ya kira ta ya ce, "Wallahi Sumayya ta yi bala'in ba ni haushi, ina tsaka da jin muryarki ta zo ta yi mini tsaye a ka." Ya yi maganar yana sakin tsaki. "Hmmm bayan da ka gama ba ta haƙuri kenan, ai na san yadda kake bala'in jin tsoronta." Jafar ya saki dariya ya ce, "Kamar wani matsoraci, idan muka haɗu ai za ki gane ni jarumin gaske ne " Maimuna ta yi murmushi za ta yi magana ya katse ta. "Yanzu dai ba wannan ba, na lura haɗuwa za ta yi mana wahala. Amma me zai hana na saya miki babbar waya sai mu dinga chatting da ita, na fi so na dinga ganinki ina jin daɗi ko na samu nutsuwa." Shiru Maimuna ta yi ta ce, "Kana ganin ba za a samu matsala ba?" "Matsalar me Moon? Ai kin ga wannan layin da muke waya babu wanda ya sanki da shi, kuma ke ba kowa za ki yi wa magana ba sai ni. Ba sai mu dinga magana ba." 'Maimuna me kike shirin aikatawa ne? Wai ko kin manta kina da aure?' Wata zuciyar ta raya mata a rai, sai ta ji sam zuciyarta ta mata babu daɗi. "A gaskiya sai na yi nazari, sai an jima zan dafa wa yara abinci." Jin sauyin muryarta ya sa shi saurin faɗin, "Lafiya My Moon, ko kina da wata damuwar ne? Turon lambar asusunki sai na turo miki dubu ashirin ko kati ki saka." Da sauri Maimuna ta ce, "Dubu ashirin fa?" Jafar ya yi murmushi ganin kamar tarkonsa ya kama ta ya ce, "My moon, na rantse da Allah, zan iya ɓatar da ko nawa ne a kan samun farincikinki. Idan ba za su ishe ki ba, ki faɗa mini sai na ƙara miki." Bugun ƙofar da Maimuna ta ji ana yi mata ya sa ta ce, "Ana buga ƙofa, zan turo maka account number ina zuwa." Daga haka ta katse, tana zuwa gate da ta buɗe ta ga Maman Nana ta shigo da alama ranta a ɓace yake. Kabir yana idar da sallar magriba, bai tsayana ko ina ba sai ƙofar gidansu Sury. Waya ya zaro ya kira ta, tana ɗauka ya ji muryarta a can ƙasa tana faɗin. "Mu haɗu a bayan layinmu ta ɓangaren hannunka na dama, idan ka zagaya ka same ni a bakin layin ƙarshe." Kabir yana jin haka ya amsa mata sannan ya katse wayar, kwatancan da ta yi masa ya bi. Yana zuwa a daidai wurin ya shiga waige-waige, daga bayansa ya ji ta ce. "Lah bai gane matarsa ba." Da sauri ya waiga, cikin mamaki yake bin ta da kallo. "Wai baby ke ce?" Sury ta saki murmushi ta ce, "To ya za a yi, ai idan hagu ta ƙi sai a koma dama. Ƙarya na yi zan je dubiya, shi ya sa na ɓoye niƙab ina zuwa bayan layi na saka. Yanzu dai mu yi sauri kada a ga na daɗe." Kabir ya kanne mata ido ɗaya ya ce, "To shi kenan amaryar Kb, amma daga jiya zuwa yau na yi kewarki." Bakin titi suka ƙarasa ya tsayar musu adaidaita sahu, shi kansa ya ji daɗin yadda Surayya ta ɓatar da kamanni. Domin har a cikin ransa yake fargabar wani ya gan shi, kuma a yanzu kowaye ya gansu yana iya ce masa ƙanwarsa ce. Tafiyar kusan minti ashirin suka yi, da yake sabuwar unguwa ce gidajen tsilli-tsilli haka suke. Tun daga farkon layin Kabir ya ce mata. "Ki jira a nan zan je na buɗe ƙofa na shiga, bayan wani lokaci zan taɓo ki a waya sai ki biyo bayana. Kin san mutane da munafunci, ba za a rasa 'yan tsurku ba. Kina miƙe layin nan da zan bi idan kika yi kwana gida na farko za ki ga ba fulasta ƙofarsa ta langa-langa ce." Sury ta amsa masa shi kuma ya yi gaba. Lokacin da Kabir ya shiga layin gidan babu kowa a waje, don haka jikinsa har rawa yake ya latsa lambar Surayya ya ce mata ta ƙaraso. Yana nan tsaye ta ƙarasa ciki, kunna fitilar wayarta ta yi saboda duhu ta shiga haske cikin gidan. Ciki da falo ne guda ɗaya, sai fallan ɗaki da banɗaki a ciki. A gefe banɗaki ne da kitchen sai ɗan ƙaramin tsakar gida. Kusan an gama komai, sai daɓe, fulasta, fenti, ƙofafi da winduna su suka yi saura. Farinciki ya sa Sury ta rungume shi tsam, tana faɗin. "Gaskiya gida ya yi masoyina, amma kana ganin wannan ƙarashen zai iya kai wata nawa ba a gama ba?" Tun da ta rungume shi ya ji duk yanayin jikinsa ya canza, jikinsa a mace ya shiga yawo da hannunsa a jikinta. Da wata irin murya ya ce, "Kin san samun namu lokaci-lokaci ne, amma dai ina fatan har aurenmu ba zai haure shekara ba." Ganin saƙon da take aika masa ya fara tasiri a jikinsa ya sa Sury ta cigaba shi ma yana mayar mata da martani. Dogon hijabin jikinta ya zame mata, dama Surayya kafin ta fito sai da ta faki idon mahaifiyarta ta zuro dogon wando da ƙaramar riga a ciki, sannan ta zura zumbulelen hijabinta har ƙasa. Duk zuwan da Kabir yake yi wurin Sury wani abu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, bayan rungume-rungume da shafe-shafen da suke yi wa juna. Don haka da ya ji Sury za ta zo ganin gidansa, ya ci alwashin saninta a wannan ranar. Yana tsaka da yawo da hannunsa a jikinsa, ya ci karo da abin da bai yi tsammani ba. "Mene ne wannan?" Kabir ya faɗa ransa a ɗan ɓace. "Gabannin magriba period ɗina ya zo!" Ta furta masa, don dama ta ƙi faɗa masa ne saboda kada ya fasa kawo ta. Domin ta san matuƙar suka zo gidan ta san sai ya nemi koda taɓa wannan ɓangaren ne. Cikin wata irin murya ya raɗa mata a kunne, "Yanzu ya za ki yi da ni?" Murmushi ta sakar masa ta ce, "Dabarun mu na mata mana, ko ba ka san idan macen aure tana wannan halin akwai dabarin da take yi ba?" Ya sani sarai, domin Fauziya duk a halin da take ciki tana ƙoƙarin faranta masa. Amma shi sam ba haka ya so ba, ita ma Sury ta fahimci haka amma ta basar. Babu kunya Surayya ta shiga sarrafa shi, tamkar yadda macen aure take yi wa mijinta. Suna cikin wannan yanayin kiran Fauziya ya shigo cikin wayarsa, kamar ba zai ɗauka ba tuna matsalar da aka samu a daren jiya da ta je shagonsu aka ce ya fita da wuri, ya sa ya ɗauka don ya ji abin da za ta faɗa masa. "Hello!" Daga can ɓangaren Fauziya ta ce, "Abi barka da yamma!" Ya ɗan yi gyaran murya don ka da ta fahimci sauyinsa ya ce, "Barka dai Ummu Banat, ya jikin?" Ta amsa masa tana wurga masa tambaya. "Amma ba ka shago ko? Na ji ban ji ƙarar ɗinki ba?" Duk da ya san zai yi wuya Fauziya ta gane a inda yake, amma sai da ya ji gabansa ya faɗi. Ya janye jikinsa daga jikin Surayya yana faɗin, "Na'am eh na je karɓo wa oga kayan ɗinki ne, ina zuwa an zo kaina za a sallame ni." Daga haka ya katse, tun da ya fara waya Surayya take wurga masa harara tana shirin yin magana ya ce. "Ayi mini afuwa." Juyar da kai gefe ta yi cikin fushi, ya shiga lallashinta sannan Surayya ta cigaba da sarrafa shi. Sai da suka ɗauki lokaci a haka sannan Kabir ya samu nutsuwa, da yake gidan akwai rijiya sai kawai ya ja ruwa da guga ya yi wanka da ita sannan suka fito daga gida. Ummou Aslam Bint Adam🌚 +2347062062624 [12/02, 22:24] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA HUƊU Fauziya tana gama waya da Kabir ta tashi da sauri ta faɗa banɗaki ta sheƙa wanka, bayan ta fito ta ciro wata doguwar riga ta saka. Jikin rigar roba ce, ba ta da tsayi har ƙasa. Daga iya gwiwarta ta tsaya, ta ɗauko kum ta fara gyara gashinta. Fauziya irin dogayen matan nan ne, sai dai tana da ɗan kauri. Tana da ƙira sosai sai dai ba fara bace tas, tana dai da haske da kuma yalwar gashi. Faka gashinta ta yi jelar ta sauka har gadon bayanta, ta ɗebi turarruka masu ɗaɗin ƙamshi ta feshe jikinta da su. A gaban mudubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, su Na'ima sai zagaye ta suke yi suna cewa ta yi kyau. Ita kanta ta san ta yi kyau, don haka take ta ɗokin Kabir ya dawo ya ga kwalliyarta. Dafa tsohon cikin jikinta ta yi ta saki murmushi, domin ta san Kabir mutum ne mai san ƙananan kaya. Jin kiran sallar Isha'i ya sa ta saka zumbulelen hijabinta har ƙasa, ta tasa su Na'ima suka gudanar da sallar Isha'i. Bayan sun idar sai da ta yi wa yaran tilawar Alƙur'ani, sannan ta zuba musu abinci suka ci. Da suka gama suka ɗan yi wasa sannan ta yi musu shimfiɗa a tsakar ɗaki, don ta ci alwashin duk zafi ta daina fitar da su waje. Kabir da Sury tare suka tafi har unguwar su Surayya. Ita ta sauka ta wuce gida, shi kuma ya wuce shagonsu. A lokacin da ya koma Ogansu ba ya nan, don haka shi ma bai zauna ba ya fice daga shagon. A madadin ya wuce gida yana fitowa sai kiran abokinsa Abbati ya shigo masa. "Ya Abbati kana iya?" Kabir ya furta bayan ya ɗauki wayar, daga can ɓangaren cikin muryar maye Abbati ya ce, "Ga mu a majalisa, kai fa muke jira kwana biyu nan ba ma gane maka sai wani eh yane kake yi wa mutane." "Don Allah mijina ka daina wannan shaye-shayen, a yanzu matsayinka na uba ne. Idan za ka yi sara, ka dinga lura da bakin gatari kana wasa shi. A yanzu da muke rayuwa, kamata ya yi ka duƙufa a neman ciyar da mu halali ba shaye-shaye ba. Allah Ya yi mana arzikin 'ya'ya mata, ina gudun kada watarana idan suka girma a dinga goranta musu. Ka yi mini alƙawarin ba za ka sake shan komai ba Kbna." Kabir ya tuna kalaman da Fauziya ta yi masa, bayan ya dawo hayyacinsa a ranar da ya faɗa ɗakin A'ilo yana cikin maye. Murya a can ƙasa ya ce. "Ku sha kawai Abbati, Fauziya ba ta san shaye-shayen da nake yi." "Ɗan abin rage zafin shi ne za ka ce Fauziya ba ta so? Kai yanzu kana namiji mace ce za ta zauna tana yi maka ƙabali da ba'adi? Haba bros kada ka bayar da maza mana, don Allah ka taho muna jiranka." Daga haka Abbati ya kashe, har zuciya ta ce masa ya yi tafiyarsa gida, sai kuma wata ta ce ya je ya sha ko kaɗan ce. Saboda shi kansa kwana biyun da ya yi bai sha ba, har jin sa yake yi wani iri. Don haka daga nan bakin ƙofar shagon ɗinkinsu ya wuce bayan wata makarantar firamare, wacce iren-irensa suka laɓewa a lungunta suke shaye-shaye. Kabir yana zama T-boy ya miƙa masa wata 'yar roba haɗe da da wata baƙar leda, nan take Kabir ya fara shaƙa yana ɗaɗɗakar ruwan robar kafin wani lokaci tuni ya yi wa kansa caji. Jin shiru har ƙarfe goma da rabi Kabir bai shigo ya sa Fauziya ta ɗauki wayarta ta latsa lambarsa. Sai dai wayar ta ƙari ringing har ta katse bai ɗauka ba, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi. Zuciya ta shiga raya mata ko dai Kabir yana wurin shaye-shayen da ta hana shi, girgiza kanta ta yi cike da ƙwarin gwiwa ta ce. "In Shaa Allah a wannan karon ba zai sake ba..." Maganarta ce ta katse sakamakon jin mummunan bugun ƙofar da ake yi, wanda ya gigitata saboda tsoro, firgici da tashin hankali. "Fauziyataaaaaa! Fauzeeeee, zooo ga ni na zo." Kalaman Kabir cikin maye suka doka sallama cikin dodon kunnenta, ba yau ta saba jin haka daga gare shi ba. Amma a wannan ranar sai ta ji wani irin ɗaci, ɓacin rai da baƙinciki ya mamaye ta. Ta kalli su Na'ima da ke kwance a ƙasa, haka kawai ta ji tausayinsu a ya kamata. Hawaye ne bibbiyu suka fara zuba daga kwarmin idonta, tana nan zaune ta sake jin ya buga ƙofar da ƙarfi yana cewa. "Don Allah... kar ki min faɗa... ni babu abin da na shaaaa..." Sanin halin mutanen gidansu ya sa ta yunƙura da ƙyar ta fita, inuwa ta gani a bakin ƙofar Maman Sabir da alama a tsaye take tana leƙen ganin abin da zai faru. "Ni fa... ba na shan... komai, Fauziyaaaaaa ko kin sha kin bugu ne... kika yi bacci... ki zo ki buɗeeee." Ta sake jin muryarsa a daidai lokacin da ta tura ƙofar gidan, tana buɗewa ya faɗo jikinta da yake ya saki jikinsa a kan ƙofar. Hannu ta saka ta kare cikinta, tana shaƙar ƙamshinsa ta ji yana wani irin warin hayaƙi. "Fauzinaaaa." Ya furta yana shafa fuskarta, takaici ne ya gama maƙure ta. Ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta dube shi tana jin kamar ta rufe shi da duka, a wannan ranar ji ta yi da ace su kaɗai ne a gidan tana buɗe masa za ta bar shi a wurin. Idan ya ga dama ya shiga ko ya kwana a nan, amma gudun kada ya shiga ɗakin matan aure ya sa ta kamo shi. Suna tafe yana layi tana dafa bango, tana shiga tsakar gida ta hangi A'ilo da Maman Sabir suna magana ƙasa-ƙasa. Duk da ba ta ji me suka faɗa ba, amma jikinta ya ba ta maganarta da Kabir suke yi. Ta girgiza kanta cike da tausayin irin rayuwar da take ciki, sannan suka shiga ɗaki. Suna ganin Fauziya ta shiga ɗaki suka saki shewa haɗe da tafi A'ilo ta ce. "Ke dai Maman Sabir a kullum maraɗinki ba ya kunya, wato yau kuma da haka kika shigo. Sabon salo kiran salla da usur, ai gara haka da ki faɗa ɗakin da ba na ki ba." Maman Sabir da tuni ta fahimci zancan ta ce, "Ke kuwa ai dukan da kuka yi mini ban ji da daɗi ba. Abin dariyar ma, baban Sabir tunkur yake zama bai yi bacci ba yana jirana." Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya. Lawisa da take ɗaki take jin su kamar ba za ta tamka musu ba, sai kuma ta yi zaraf ta leƙo ya ce. "Sai ki yi takatsantsan kuwa, domin babu ruwan Ubangiji. Ba abin mamaki ba ne ki ga Sabir ya gado ki. Ni ina fata da roƙon Ubangiji, tun da har fatan da kike yi wa kanki kenan Ubangiji Ya sa Sabir ya gaji abin da kike yi wa izigili." Tana faɗar haka ta koma ɗaki. "Wallahi sai dai ki gani a kanki, aniyarki ta biki mai mugun baki." Maman Sabir ta furta cike da tsoro. Fauziya suna shiga ɗaki, bayan ta saka shi ya tsallake su Na'ima da ke kwance sai kuwa ta sake shi rai a ɓaci. Daga gefen gadon ya faɗi, kansa ya bugu da katakon gado. Cikin azaba ya runtse ido yana shafa wurin, takaici ya sa Fauziya ta zauna a gefen gadon sai kawai ta fashe da kuka. Sai da Maimuna ta tura ƙofar ta rufe sannan ta waigo tana bin bayan Maman Nana da harara, ganin za ta waigo ya sa ta saki fuska cikin wayancewa ta ce. "Uwar gida kuma amarya a gidan Baban Nana, ke kaɗai ki sha kurumki daga ke babu ƙari." Maman Nana ta saki guntun tsaki ta zauna a kan kujera, sai kuma Maimuna ta sha jinin jikinta duk da Jafar ya tabbatar mata da ba ta gane da wacce yake wayar ba. Amma sai ta ce, "Uwar Nana ko dai kin samo wa Abdul abokin wasa ne? Na gan ki duk a sanyaye." Maman Nana ta zaunar da Abdul da bai wuce shekara ɗaya ba ta ce, "Ni da wannan ne ai da sauƙi, sai na saka shi ya ɗauko mini mai aiki ta dinga komai kamar lokacin da na yi cikinsa." Cikin bugar ciki Maimuna ta ce, "To! Me yake damunki?" "Wallahi ban tabbatar namiji munafiki maci amana ba ne ba sai yau, wai har ni Abban Nana zai munfurta?" A razane Maimuna ta dube ta, tana shirin yin magana ta cigaba. "Wai har ni zai dinga yin waya da budurwa a ɗaki? Tsabar wulaƙanci ya saka ni aiki, ina can ina haƙilo ko yaro ya ƙi riƙe mini ashe soyayya zai sha. Wallahi ta ci sa'a ban same ta a waya ba, da sai na ƙare wa kaf danginta zagin rashin mutumci. Sai da na raini mijina yanzu kuma 'yan'iskan mata za su fara kawo mini hari, wallahi duk yarinyar da ta yi gangancin auren mijina sai na lahantata." Ras! Ƙirjin Maimuna ya buga, don ta san halin Maman Nana akwai ta da baƙin kishi. Amma duk baƙin kishinta ba ta ji ko ɗar ɗin za ta iya rabuwa da Jafar ba. Dalilin haka ya sa ta dafa ta ta ce. "Gaskiya ni Abban Nana ma ya ba ni mamaki, saboda Allah duka shekararku nawa da zai dinga wani kule-kulen 'yan'mata?" Maman Nana ta wara hannu tana taɓe baki alamun kema dai taya ni gani, don Maminuna ta sake zuga ta sai ta ce. "To ai ko ni me shekara goma da aure Nazir ba shi da budurwa, ina laifin ma ya bari ku shekara ko sha biyar ne kin ga lokacin ke da yaranki kun samu jindadin da kuka samu bakin gwargwado. Amma kina zaman zamanki a kwaso miki gayyar tsiya, gara dai tun wuri ki san abin yi." Ai kuwa nan take Maman Nana ta sake cika, rai a ɓace ta ce. "Ai wallahi bari ya dawo, dama ai na faɗa masa sai ya kira mini budurwar idan ba haka ba zai ga ɓacin raina." Wani irin farinciki ya mamaye zuciyar Maimuna, saboda a yanzu babu abin da yake damunta sama da ta ji Maman Nana ta ce suna cikin daɗi ita da Jafar. Ta sake taɓe baki ta ce, "To ni ban da ma abin namiji, mace har mace kamar ki me zai yi da wata kuma. Dirin nan bakin gwargwado kina da shi, gashin nan kina da na zaman falo. Ke dai a fuska ba za ce miki mummuna ba, to don Allah me namiji yake so da ba ki da shi." Maman Nana ta yi caraf ta ce, "Jaraba fa irin ta namiji, ki duba ki ga irin magungunan da ke ɗurawa cikina Maman Dija, ke kanki shaida ce saboda Abban Nana na fara shafe-shafen man bilicin, tun da na lura yana leƙe-leƙen fararen 'yanmata." 'Ba dai leƙe ba, sai da faɗawa. Jafar ai ya yi nisan kiwo a kan alkyabbar mata.' Maimuna ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "A toh ga shi kina ƙoƙari a turaka ma na ji kin ce ba kya sanya, to wai da ba kin ce har zauce miki yake ba?" Maman Nana ta yi ƙwafa ta ce, "Yaushe rabo? Ni yanzu rabona ma da shi ai mun kusa sati, Abban Nana da yake da jaraba wai shi ne har yake sha mini ƙamshi jiya. Ƙiri-ƙiri mutumin nan ya ce mini ba shi da lafiya..." "Sati fa Maman Nana? Ke kuwa kina me? A gaskiya ki dawo nutsuwarki, ni fa ba don kar na faɗa ki ji haushi ba da na ce wani abu." A zabure Maman Nana ta dafa Maimuna ta ce, "Faɗi mana, ni da ke ai kin san ba ma haka." "Astagafirullah ba wai zargi nake ba, sai na ga ko dai budurwar tashi ce ta ɗauke masa hankali? Kin san fa 'yan'matan yanzu wallahi idonsu a buɗe yake, ba abin da ba sa yi wa sauraye ke kina can yashe a baki suna harkarsu." "Bantan uba! Ai kuwa sai yanzu kika kamo mini bakin zaren." Maman Nana ta furta jikinta yana karkarwa, sannan ta cigaba. "Ai kuwa zan saka ido a kansa, wallahi idan na gano wani abu a tsakaninsu sai an maimaita yaƙin dunuya na biyu." Maimuna ta cigaba da zuga ta, sai ta gama yi mata famfo sannan ta yi mata sallama ta tafi. Tana fita Maimuna ta saki shewa, cike da ƙeta ta ce. "Sakarya wawiya marar lissafi, in dai ni ce wallahi baƙinciki yanzu kika fara ƙunsa. Sai na raba ki da jin daɗin, da kike hura wa 'yan unguwa hanci kina faɗar ke mowar miji ce." Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [12/02, 23:08] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA BIYAR UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Maman Nana ta fita babu jimawa yaran Maimuna suka dawo daga makaranta, hankalinta yana kan wayarta saboda so take Jafar ya turo mata kuɗin ta goge alert ɗin. Sai da su Asiya suka ci abinci suka wuce Islamiya sannan Maimuna ta sake lalubar wayarta. Kamar ya san wayar tana hannunta nan take ta ga alert na dubu ashirin, wani irin tsalle ta buga tana riƙe baki. Jikinta har rawa yake ta shiga ɗaki ta ɗauko ƙaramar wayarta ta saka batirin ta kunna ta, a gaggauce ta shiga kiransa sai dai bai ɗauka ba don dama ta san ba lallai ya ɗauka ba sai dai ya kira ta. "Baby yanzu na ga kuɗin ya shigo." Maimuna ta furta muryarta har rawa take yi, jin sautin murmushin da yake yi har cikin zuciyarta ta yi. Ta mayar masa da martanin murmushin sai ta ji ya ce, "Yanzu saboda dubu ashirin kika kira? Haba my Moon, don Allah kada ki sake yi mini haka." Maimuna ta saki murmushi, tana shirin magana ta ji ya shagwaɓe murya ya ce. "Ni fa na gagara haƙuri gaskiya, na biya ta kasuwar waya na saya miki sabuwar babbar waya wacce za mu dinga ganin hotuna da bidiyon juna." Maimuna ta ji daɗi sosai, amma tana tsoron kada asirinta ya tonu Nazir ya gano ta. "To ya za a yi ta zo hannuna? Kuma ni ina jin tsoron kada Nazir..." "Idan muna magana ba na son ki dinga ce mini kina tsoron Naziru, wai wanne irin zama yake yi da ke da kike mugun jin tsoronsa." Jafar ya katse ta cikin sauri, shiru Maimuna ta yi sai ya cigaba da cewa. "A gaskiya alamu sun nuna ba kya jin daɗin zama da shi, a haka ka gan shi kamar na gari yana sunkuyar da kai ƙasa. Amma ya zo a jiye kyakkyawar mace, yana azabtar da ita." Sai kuma Jafar ya ɗan kwantar da murya ya ce. "Haba my Moon, ki duba irin kulle da takunkumin da yake yi miki? Wai a haka kika iya zama da shi har tsawon shekara goma? A gaskiya an ci amanar kyau wallahi." Jin maganganun Jafar sai suka soso mata mikin da yake ɗamfare cikin zuciyarta, kalamansa suka yamutsa zuciyarta tana jin ɗacin yaudarar da Naziri ya yi mata a shakarun baya. "Hmmm ai Nazir ya dasa mini mikin da zai jima a zuciyata bai goge ba, lokaci kawai nake jira my baby." "Kada ki jira lokaci Moon, kamata ya yi lokaci ya jira ki. Saboda yara uku rak ba za su hana ki rawar gaban hantsi ba. Wai ma kina kallon kanki a mudubi kuwa?" Tambayar da Jafar ya yi mata, ya sa Maimuna ta yi saurin matsawa gaban mudubinta tana ƙarewa kanta kallo. "Ni fa tun ranar da na fara ganinki na san Allah Ya zuba halitta, kuma wallahi duk wanda ya ganki ba zai ce kin taɓa haihuwa ba. Ba kamar waccan sakaran da ta yi shaɓar da jiki ba, dubi ƙirjinta ba kyan gani duk ya saki ya tamushe kamar an tsoma leda a ruwa." Dariya Maimuna ta shiga ƙyaƙyatawa har da riƙe ciki, sai da ta yi mai isarta ta ce. "An ya ba faɗa kake ba Baby don na ji daɗi, ka san fa babu laifi ƙawar tawa tana mayar da hankali wurin gyara." Jafar Ya saki tsaki ya ce, "Hmm ke dai a yi sha'ani kawai, yanzu dai wayarki zan ba wa Maman Nana ta kawo miki gobe..." Tun bai gama magana ba ta katse shi, "Maman Nana fa? Ka san me kake faɗa kuwa Jafar?" Dariya ya yi a fili ya ce, "Saboda zan ba wa Maman Nana waya ta kawo miki har shi ne ya sa kike kiran sunana gatsal? Zan ba ta ta kawo miki kamar yadda na faɗa, zan ce mata mijinki ne ya ba ni sautin waya daga kasuwa. Sai na ce ta miƙo miki, amma sai na kintaci lokacin da Naziru ba ya gida don kada a samu matsala. Idan kuma na samu wata mafitar shi kenan, ko kina da wata shawarar?" Kamar Jafar yana ganinta ta girgiza kai ta ce, "A'a babu." Sun ɗan ɗauki lokaci suna waya sannan suka yi sallama cike da kewar juna. Fauziya tana nan zaune a gefen gado tana hawaye ta fara jin sautin munsharinsa, wanda hakan ne yake tabbatar mata da tuni bacci ya yi awon gaba da shi. Haska shi ta yi da wayar hannunta, tana ƙare masa kallo. Ta kawar da kai gefe cikin sanyin murya ta ce. "Ya Allah Ya Ubangiji ba don ni ba, ba don halina ba. Allah ka shirya mini mijina." A inda yake ta bar shi, ita kuma ta haye gado ta kwanta zuciyarta a cunkushe da ɓacin rai, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da asuba ta yi cikin bacci ta ji Kabir yana tashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune. Sai ta ga ya yi mata kalar tausayi ya zauna a gefenta, ya saka hannunsa ta bayanta ya riƙo ƙugunta. "Don Allah ki yi haƙuri Fauzina!" Kabir ya furzo kalamansa ƙasa-ƙasa. "Zuwa yanzu ya ci ace na haddace waɗannan kalaman naka, ka sake ni Abban Na'ima zan je na yi sallah." Ta ba shi amsa rai a ɓace, Kabir ya riƙo ta a jikinsa tsam ya ce. "Wallahi ba laifina ba ne, su Abbati ne suka ingiza ni amma In Shaa Allahu wannan ne ƙarshe." "Ashe idan su Abbati suka ce ka shiga wuta sai ka bi su ko? A yanzu babu wata magana da za ka faɗa mini na yarda da kai a kan shaye-shaye. Su Abbati sun isa su yi maka dole idan kai ma ba ka so ba?" Kabir ya yi shiru har sai da Fauziya ta gama sannan ya shiga lallashinta. Alwala ya fita ya yi, ya wuce masallaci. Bayan ya dawo cike da daɗin baki ya ce. "Ni kuwa ya maganar Dillaliya? Allah Ya sa ta taya kayan da mutumci." Da yake a lokacin Fauziya ta ɗan sauko ta ce, "Ta taya shi dubu saba'in har ta bada rabin kuɗin." Fauziya ta miƙe ta buɗe drower kayanta, jakar ratayarwa ta ɗauko ta zura hannu ta zaro kuɗin ciki ta miƙa masa. "Ragowar ta ce sai bayan kwana uku za ta bayar, an jima idan gari ya waye ta ce za ta zo da wanda zai ɗauka." Kabir ya janye hannunsa daga jikin kuɗin ya ce, "A'a ki ajiye a wurinki ko jari sai ki ja da su" Girgiza kanta ta yi ta ce, "A'a ka cika ka sayi wani abin na aikin gidan can, ka ga an rage wani abu. Idan ta kawo cikon kuɗin, kafin nan kai ma ka samu wasu sai ka haɗa da na wurinka kafin dai ranar tashinmu an rage abin da za a rage." Fauziya ta ɗan kalli ɗakinsu da shinfiɗar su Na'ima cikin damuwa ta ce. "Na gaji da zaman da muke yi ɗaki ɗaya Abban Na'ima. Yaranmu sun fara wayo kwana da su a ɗaki ɗaya zai iya haifarwa tarbiyyarsu matsala." Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Haka ne Fauzina, amma kuɗaɗen da kike ba ni a ginin nan ina gudun wani abu a nan gaba." Yanayin yadda ya yi mata maganar cikin sanyin murya ya sa jikinta ya yi sanyi, ta dube shi a sanyaye ta ce. "Me kake gudu Abban Na'ima?" "Ina gudun kada watarana wani abu ya haɗo mu ki yi mini gori, sannan tarin kuɗaɗen da kika ba ni lissafinsu nake yi. Idan Allah Ya buɗa mana nan gaba zan biya ki kuɗinki." Maganar Kabir ba ƙaramin ɓa ta ranta ta yi ba, domin duk abin da take yi wa Kabir tana yin sa tsakani da Allah ne. Tun da a ganinta rufin asirinsa tamkar rufin asirinta ne. A irin kalubalen rayuwar da ta fuskanta a kaf faɗin duniya, gida biyu ne ya zame mata gata kuma madogararta. Daga gidan mahaifinta sai gidan mijinta, gidan mijin da take fatan sai dai mutuwa ta ɓamɓare ta daga ginin turɓayarsa. Gidan mahaifinta kuwa a yanzu ba ta fata ko burin kawo wata ƙaddarar, da za ta kwashe ta daga gidan mijinta kuma aljannar duniyarta zuwa ƙangin bautar gidan mahaifinta. Amma sai ta ji Kabir yana faɗar kamalan da take jin, tamkar bai ba ta matsayin da ta ba shi a cikin zuciyarta ba. Don haka a ɗan ƙufule ta ce. "Shi kenan tun da kai abin da ka ɗauka kenan sai ka lissafa abin da nake bin ka, tun da ai da na ba ka cewa na yi na ba ka aro." Murmushi ya yi don ya fahimci ta ji haushi, sai ya gyara zama ya ce. "Tuba na ke uwargida kuma amarya a gidan Kb babban tela. Haba Fauzin Kb fushin na mene ne?" Fauziya ta ɗan kwaɓe murya a shagwaɓe ta ce, "To ai kai ne da wata irin magana." Hira suka ɓarke da ita har gari ya ƙarasa wayewa, gabanin Kabir zai fita ta ce masa za ta je gida ta gaida mahaifinsa. Amma sai ta fara biyawa ta wurin Inna ta gaida. Fita ya yi ya sayo mata ɗan omo, sabulu da magi ƙulli bibbiyu. Ƙulli ɗaya ya ce ta miƙa wa mahaifiyarsa, ƙulli ɗaya kuma ta kai wa mahaifinta. Godiya ta zuba masa sosai, ta sake ba wa Kabir wani matsayi a zuciyarta. Domin kusan duk ranar fa za ta je gaida mahaifinta sai ya sayo wani abin ya ce ta kai masa, har turare sayo mata yake ya ce ta kai masa. Kyautatawar da yake wa mahaifinta ya sa Kabir ya sake samun fada a zuciyarta da zuciyar mahaifinta har ma da matan babanta. Don ba ta taɓa zuwa gida haka, idan ya saya wa mahaifinta abu. Ita kuma da ɗan canjin hannunta na kuɗin kitso, ko na ɗan gyare-gyaren kayan da take yi sai da saya wa matan babanta ɗan magi ko tsintsiya. Wani lokacin kuma ƙannenta take sayawa alewa ta tafi musu da shi, haka idan za ta leƙa gidan mahaifiyarsa Inna ko bai ba ta komai ba da kuɗinta take saya mata omo da ɗan abin da ba a rasa ba. Shirya su Na'ima ta yi tsaf cikin ankon atamfa dogayen riguna, sannan ita ma ta shirya cikin doguwar rigar abaya ta ɗora babban mayafi ta yane kanta. Lokacin da za ta fita Lawisa kawai ta yi wa sallama, saboda magana mai daɗi ba ta taɓa haɗa ta da su A'ilo. Koda ita ta yi musu mai daɗi, sai sun san yadda suka yi suka mayar mata da martanin baƙar magana. Duk wanda ya ga Fauziya da 'yan'matanta uku sai sun birge shi, saboda kusan gabaɗaya kansu ɗaya tazararsu babu yawa. Daga gidan su Fauziya zuwa gidan Inna babu nisa sosai, don a adaidaita sahu bai fi naira ɗari ba. Idan mutun bai sa ƙyuya ba ma zai iya zuwa da ƙafa. A lokacin da Fauziya ta yi sallama a gidan Inna, Sadiya tana tsakar gida tana wanki. Inna kuma tana zaune tana ɗaurin tsintsiya. Sadiya ce ta faɗaɗa fara'arta ta ce, "Yanzu uwar biyu ba ki rufe fita ba sai kin haife mana ɗa a titi?" Murmushi Fauziya ta yi mata, ta ƙarasa gaban Inna ta tsugunna ta ce. "Barka da hutawa Inna." Inna ta ɗan taɓe baki ta ce, "Wane hutu Fauziya ana fama da rayuwa." Fauziya ta sake yin murmushi saboda idan da sabo ta saba da halin Inna, domin irin matan nan ne da ba su da godiyar Allah. Saboda bakin ƙoƙari 'ya'yanta suna kyautata mata, amma duk lokacin da suka haɗu sai ta yi jajen tana cikin wani hali. A cikin yaran Inna mijin Sadiya da Kabir ne marasa ƙarfi sosai, don haka ta fi ji da matan 'yan uwan Kabir. Kuma a haka ma tana nannan da Fauziya saboda kyautatawar da take yi mata, amma Sadiya da yaranta da suke zaune a gida ɗaya kullum cikin tsangwama da kyara suke. Su Na'ima suka zube ƙasa suka gaida Inna, Inna ta taɓe baki ta ce. "Ai dama ku ba na ganinku sai idan uwarku za ta zo, ko ban isa a turo mini ku ba ne oho." Sadiya da Fauziya suka haɗa ido suka saki murmushi a fakaice, Inna ta sake leƙen hannun Fauziya ta ga ba ta ga komai ba sai kuwa ta sake cewa. "Kabirun ma kusan sati guda kenan ban gan shi ba, tun ranar da ya kawo mini garin tuwo da taliya. To dai nan ɗin da ba kwa son zuwa, nan ne dai gidanku tun da ubanku ma a nan ya tashi. Kuma ni na haifi Kabiru babu yadda kuka isa ku yi da ni." Shiru su Na'ima suka yi, saboda dama babban dalilin da ya sa ba sa son zuwa wurin Inna yawan faɗanta. Sau tari Fauziya za ta shirya su musamman ranar Juma'a ta ce su zo su gaida Inna, amma suna zuwa ko zaman minti talatain ba sa yi suke tafiya. Wani lokacin ne ma suke zama su yi wasa da yaran Sadiya. "Kai Salim ku zo ku ɗauki tsintsiyoyin nan, ke kuma Zainabu ga mafitai ki ɗauka. Yau idan kika sake ki yar mun da kuɗi wallahi sai ubanki ya biya ni kuɗina." Inna ta furta wa 'ya'yan Sadiya tana tura musu farantan da aka jera tsintsiya da mafici. Sadiya ko kaɗan ba ta jin daɗin tallan da Inna take ɗora musu, don dai babu yadda za ta yi ne amma ba ta son tallar musamman ga Zainab da ta kasance 'ya mace. "Inna ga wannan a yi wanki da shi babu yawa." Fauziya ta zaro ledar daga kan cinyarta. Ina sai da ta ɗora wa su Salim farantin tsintsiya, sannan ta waiga wurin Fauziya riƙe da baki ta ce, "Oh ke dai Fauziya ba kya gajiya, to an gode madalla. Ai kuwa kin ce na sha wanki, dama kayan sawata duka sun ƙare sai masu datti. Ai ka ga masu abin kirki, amma wasu kuwa ko ƙullin gishiri ba su san su ba ni ba. Ke dai Allah Ya yi miki albarka, wannan ciki da kike ɗauke da shi Allah ya sauke ki lafiya ya sa ki haifo wa Kabiru magaji." Fauziya ba ta amsa ba, suna nan zaune suka ɗan taɓa hira. Fauziya tana son su keɓe da Sadiya amma tana tsoron fassarar da Inna za ta yi musu. Sun ɗan jima suna hira Inna ta ce. "To yanzu ni dai ragowar Taliya ɗaya gare ni ballantana na dafa mana abinci, ko da wuri za ku wuce ne Fauziya?" Girgiza kai Fauziya ta yi tana mamakin rayuwar Inna, Fauziya ta miƙe ta ce. "Yanzu za mu wuce Inna, da ma zan je gaida Baba ne na ce bari na zo na gaishe ki." Nan take kuwa Inna ta hau washe baki ta ce, "To shi kenan ku gaida gida, shi kuma Kabiru ki ce masa ina son ganinsa." Fauziya ta amsa sannan ta nufi hanyar fita, da sauri Sadiya ta bi ta tana faɗin. "Wai har za ku tafi, bari mu fita tare dama zan miƙa wa Mariya kayan wankin da na yi mata." Da biyu Sadiya ta bi Fauziya suka fita, suna fita Fauziya ta ce. "Wai dama har yanzu su Salim ba su daina tallar muhucin nan ba?" Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai na kusa barin gidan nan Fauziya, wallahi na gaji haƙurina ya kusa ƙarewa." "Idan kin tafi yaran kuma fa Sadiya?" Cikin halin ko'inkula ta ce, "Allah zai raya su, wasu ma suna tasowa babu iyayen kuma su yi rayuwa kamar kowa." Fauziya ta tsaya tana bin Sadiya da kallo, duk ta lalace saboda rashin kwanciyar hankali. "Don Allah ki daina wannan maganar, addu'a za ki cigaba da yi har Allah Ya hore muku ku bar wa Inna gidanta. Kin san zama wuri ɗaya dama yana kawo haka, ki cigaba da addu'a sai ki ga watarana sai labari." "Hmmm ba za ki gane ba Fauziya, ni na san takaici da baƙincikin da nake ci a gidan." Cikin ƙarfafa gwiwa Fauziya ta ce, "Babu abin da ya fi ƙarfin addu'a." Fauziya da Sadiya sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama, Fauziya ta wuce ta tari adaidaita sahu suka wuce gidan mahaifinta. A tsakar gida ta samu mahaifinta yana ta bambamin faɗa, a kan 'yan nefa sun zo karɓar kuɗin wuta. Har ƙasa ta tsugunna ta gaida shi, sannan ta miƙa masa saƙonsa, nan take Baba ya shiga washe baki yana saka mata albarka. Ɗakin Inna Sakina ta shiga da yake a nan ɗakin aka raini Fauziya, bayan sun gaisa ta fara bin ƙannenta da alawoyi tana danƙa musu. Su Nai'ima kuwa dama tun a tsakar gida suka fara wasa da ƙannen mahaifiyarsu. Kabir yana fita daga gida kai tsaye wurin masu sayar da ƙofa ya nufa, ƙofofin ba ƙaramin tsada ya ji sun yi masa ba. Ya cika da ragowar kuɗin wurinsa ya sayi guda ƙofofin guda uku, ƙofar farko ta ƙofar gida. Sai ɗakin da yake a tsakar gida, da kuma ƙofar falon gidan. Daga nan wurin can gidan nasa ya nufa, ya kira masu saka ƙofofi suka fara aiki. Ba su suka gama ba sai yamma liƙi, gabanin zai fito daga gidan kiran Hafsa ya shigo masa, zama ya yi a bakin dandamalin rijiyar sannan ya ɗauka. "Gimbiyar mata!" Ya furta cike da kashe murya, daga can ɓangaren Hafsa ta ce. "An ya kana jin abin da nake ji na soyayyarka kuwa?" Kabir ya sake kwantar da murya ya ce, "Haba Hafsyna, don Allah ki daina faɗin haka." Hafsa ta ce, "Ka duba whatsapp ɗinka na turo maka da hotuna." Jikin Kabir har rawa yake ya katse wayar, sannan ya yi saurin buɗe datarsa. Yana shiga whatsapp ya fara cin karo da saƙonninta, buɗe hotunan ya yi ya ga ta ɗauko masa hoton ƙirjinta da ƙasanta kamar yadda ya buƙata. Cikin wani irin yanayi ya sake kiranta, a kunyace Hafsa ta ɗauka sai ta ji duk muryarsa ta sauya. "Baby kin yi kyau sosai, amma don Allah ki yo mini bidiyo mana." Hafsa da duk ta ji nauyinsa ya kama ta ta ce, "Baby gaskiya ka yi haƙuri, wallahi wannan ma da ƙyar na iya turo maka." "Guda ɗai-ɗai fa kawai za ki yi mini, kuma kin san ai aurenki zan yi ko ba ki yarda ba?" Shiru ya ji Hafsa ta yi, ya ɗora da cewa. "Akwai kuɗin da nake saka ran za su shigo mini nan da kwana uku. In Shaa Allah a satin nan za a kawo kuɗin aurenmu." Daɗi ya lulluɓe Hafsa, jikin yana rawa ta ce. "Zan turo maka amma don Allah kana gani ka goge." Cikin sauri Kabir ya ce, "Wallahi ina gani zan goge." Kashe wayar Hafsa ta yi ta shige ɗakinta ta yi masa bidiyo ta tura masa. Kabir yana ganin bidiyon a ruɗe ya shiga yi mata replay da kalaman batsa, tun tana jin nauyinsa har ta fara biye shi. Yamma liƙis Fauziya ta koma gida ta ɗora musu girki, a wannan karon ma ana yin magriba ta kira Kabir ta sake tuna masa maganar da suka yi, game da alƙawarin da ya ɗaukar mata ba zai sake shan komai ba. Sannan ya ce ta tsala masa kwalliyar domin a cike yake da kewarta. Zuciyar Fauziya fes ta tsala wanka cikin wata doguwar riga marar nauyi, ta raba gashinta gida biyu kamar wata 'yar baby ba ƙaramin kyau ta yi ba. Suna nan zaune ita da yara kimanin ƙarfe tara suka ji sallamarsa. Kusan lokaci ɗaya ita da yaran suka rungume shi har ita suna faɗin. "Abi oyoyo." Rungume su ya yi gabaɗaya, sai Fauziya ta saci kallon yadda suke nishaɗi ita da yaran, saboda dawowarsa da wuri kuma a cikin nutsuwarsa, sai ta ji ƙwalla tana shirin zubo mata. Ɗaya bayan ɗaya ya tsugunna yana sumbatar yaran a goshi, sai ya ɗago ya dube ta suka haɗa ido. Rungumo ta ya yi a jikinsa yana kashe mata ido ɗaya, irin kallon da take bin sa da shi ya sa shi hura mata iska a fuska. "Wannan kwalliyar zan biya tukwicinta an jima." Ya furta mata a hankali, ta sakar masa murmushi ta ce. "Na fa tsufa da yawa." Kafaɗa ya maƙale mata cikin kwaikwayon muryarta ya ce, "Ni ban yarda ba." Duk da yaran ba su fahimci me suka tattaunawa ba, jin yadda mahaifinsu ya maƙale murya ya sa suka fara ɗariya. Hula, agogo da wayarsa ya ajiye a gefen gado ya ɗauki bokiti ya zuba ruwa ya tafi yin wanka. Kabir ya manta shaf da abin da Hafsa ta turo masa bai goge ba, har ya iya ajiye wayarsa. Kuma ya bar hotunan ne saboda idan ya keɓe ya dinga kalla yana jindaɗi. Fatima ce ta ɗauki wayar ta shi, da yake wani lokacin idan yana gida ya kan kunna musu game ko cartoon su kalla. Shige-shige suka fara yi masa har suka shiga cikin gallery ɗinsa, Na'ima ta zura kanta ta danna ɗaya daga cikin bidiyon da Hafsa ta tura masa. Fauziya da ke tsugunne tana jera masa kayan abinci ta ji muryar mace raɗau a kunnenta tana faɗin. "Baby kana gani, wannan bidiyon..." A gigice Fauziya ta fisge wayar daga hannunsu jikinta yana karkarwa, sakamakon ji irin bayanin batsar da buduwar take yi. Domin a bidiyon hafsa tana yi masa tana bayanin komai dalla-dalla. "Lah Mami mene ne wannan?" Na'ima da ta fi su wayo ta tambaya, sai da Fauziya ta saita nutsuwarta ta ce, "Bidiyon wata marar lafiya ne da take neman taimako, za a haɗa mata kuɗi a yi mata magani. Na sha faɗa muku idan mutum ya ajiye abu, sai an tambaye shi ake taɓawa ko?" Gabaɗaya suka gyaɗa mata kai, Fauziya da take jin wani abu yana taso mata a ƙirji ta yi ƙarfin halin faɗin. "To daga yau, ko da wasa ka da na sake na ƙara ganin ku taɓa wa mutum wayarsa. Idan ba haka ba ranku zai ɓaci." Su Fatima suka amsa mata. Ear pices ta ɗauko ta saka a kunne, ta shiga bidiyan ta kunna shi. Jikinta ya ɗauki karkarwa gabanta yana wani irin bugu da ƙarfi, lokaci ɗaya hawaye ya wanke fuskarta domin bidiyon ya matuƙar ƙazanta. Da sauri ta shiga whatsapp ɗinsa, ta ga yawanci masu saƙon duk maza ne, don haka take mamaki a inda Kabir ya samu wannan bidiyon. Har za ta fita ta ga an saka costomer Hafsa lace bubu, tana shiga ta ci karo da emojin heart ta turowa Kabir. Can sama ta haura ta fara cin karo da saƙonnin batsar da suka tattauna, a nan ta gano wannan bidiyon na Hafsa ne tun da ga muryar ta nan ta kunna voice ɗinta ta ji." Jikinta yana rawa ta kifa wayar, sai ta jingina da bango tana jim wata irin tsanar Kabir ta mamaye ta. Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [13/02, 21:15] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA SHIDA UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Tun tana zubar da hawayen zuci don kada yaranta da ke zaune su fahimci halin da take ciki har ta gagara sarrafa zuciyarta saboda wani irin zafi da ɗacin da take yi mata. Hawaye taka sosai tana shassheka tamkar za ta shiɗe, saboda wani irin kakkarwa da jikinta yake yi ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri-sauri. Ganin halin da mahaifiyarsu take ciki ya sa suka ƙarasa wurinta suna tambayarsu, ba ta iya tanka musu ba sai ma wani irin kallo da ta dinga bin su da shi kamar ta ga sababbin hallita. A ranta ta ayyana ƙila yarinyar da suke musayar munanan kalamai da Kabir ko kaɗan iyayenta ba su san abin da take aikatawa ba. Sai kawai ta rungumo su jikinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, ganin haka ya sa su Fatima su ma suka rairai kukan su ma. Duk da ya san ba hali ko ɗabi'ar Fauziya ba ne binciken wayarsa, haka kawai yana wanka da ya tuna ya bar wayar a kan gado ya ji gabansa ya faɗi. Nan take ya yi sauri ya kwakkwara ruwa ya fito, don ba ya so Fauziya ta fahimci irin alaƙar da ke tsakaninsa da su Hafsee. Kamar wanda aka kifa haka Kabir ya faɗa cikin ɗakin har yana tuntume, Fauziya ta ɗago tana kallonsa ta ƙura masa ido. Ganin yanayin da ya same ta ita da yaran da kuma mummunan kallon da take wurga masa, ya sa ƙirjinsa ya buga da wani irin ƙarfi. Da gudu yaran suka tafi wurinsa cikin haɗin baki suka ce, "Abi Mami ce take kuka." Yanayin yadda ya ga hankalin yaran ya tashi ya sa ya kalli wurin da ya ajiye wayarsa, rashin ganinta a wurin ya sa shi tabbatar da tabbas mai afkuwa ta riga da ta afku. Ya san duk irin saɓanin da za sh samu da Fauziya ba ta iya zubar da hawayenta a gaban yaran, duk abin da za su yi ko wata tattaunawa ce sai ta bari sun tafi makaranta ko kuma idan sun yi bacci amma gudun kada ya bada kai bori ya hau sai ya yi kamar bai san dalilin ɓacin ranta ba ya ce. "Ummu banat lafiya kike hawaye a gaban yara?" Tamabayar da ya wurga mata ta ji ta yi tamkar ya zuba mata ruwan dalma, ta dube shi cike da mamakin wai ita Kabir zai raina wa hankali. Murmushin takaici ta saki sannan ta miƙa masa wayar ta ce, "Ungo wayarka, cikina ne yake ciwo." Ya san ta faɗi haka ne saboda gudun yaran su fahimci shi ya yi mata wani abin, Na'ima ta ɗauko kwalmar maganin tarinsu ta miƙa mata ta ce. "Ammi riƙe ki sha magani ba na son na ga kika kuka!" Ƙuri ta yi wa yarinyar tana kallo, murya a dashe ta ce. "Wannan maganin yara ne Na'ima, cikin nawa ya sarara idan na tashi zan ɗauko maganina a cikin jaka." "Amma za ki daina kuka?" Na'ima ta sake wurga mata tambaya, gyaɗa mata kai Fauziya ta yi. Dai kuma ta ƙarasa gaban Kabir ta ce, "Abu ni dai ka kai Ammi asibiti, ba na son ta dinga kuka ni ma zan yi." Ta ƙarasa maganar tana janyo hannunsa. Tamkar wanda aka liƙewa ƙafa da super glue, haka ya ji ƙafarsa ta manne ta ƙasa wata irin shakkar Fauziya ta kama shi. "Ko... ko... za mu... wuce asibiti..." Ya furta bakinsa yana rawa, sai dai tun bai fire kalamansa ba Fauziya ta wurga masa mugun kallon fa ya sa shi haɗiye kalamansa. "Ai jikin mamanku da sauƙi Na'ima, ba sai mun je asibiti ba. Yanzu dai bari na yi muku shinfiɗa kun ga gobe kuna da school." Tana gee har lokacin idonta yana kan Kabir, da take yi masa kallo kamar tana som gano wani ɓoyayyan abu daga jikinsa. Shafa jikinta take yi don ta tabbatar ba mafarki take yi ba, ta saka hannu ta mintsini cinyarta jin zafin ya ratsa wurin ya sa ta tabbatar da zahiri ne. Tana kallo Kabir ya kashe wayar gabaɗaya, jikinsa gar rawa yake ya ɗebo kayan shimfiɗa ya yi wa yaran. Yana gama shimfiɗar ta ga ya ɗauki wayarsa ya fice daga ɗakin alamar fita ma zai yi daga gidan gabaɗaya. Tun da ya fice Fauziya take saƙa da warwarar hukuncin da za ta yanke, ban da kai wa da kawowa babu agim da take yi. Hat yanzu zuciyarta rawa take yi a kan ko dai idanu da kunnuwanta ba su jiyo mata daidai ba. Babban abin da ya sake ɓata mata rai, yadda ta ga ya ɗauki wayar ya fice daga gidan wato duk ma abin da za ta yi ta je ta ƙarata. Ta jima tana ƙoƙarin dakatar da hawayen idonta, amma ta kowanne ɓangare ya gagara ba ta haɗin kai. Shinshina jikinta ta fara yi tana son gano ta inda ta gaza, ta ɗaga rigarta tana kallon mamanta ko za ta ga hango aibun na jikinta. Domin Allah ya yi mata baiwa duk da haihuwarta uku ga ta huɗu za ta yi amma mamanta bai lalace, ballantana ta ce ko nata ne suka zube har yake hangen na wasu. Kuma idan ma lalacewa suka yi a tsawom shekaru bakwai da aurensu bai ci ace ya ɓoye mata ba. Har gara ya faɗa mata domin ta san matakin gyaran da za ta ɗauka. Ta matsa gaban madubi tana bin kanta da kallo, sai dai har ta gaji da tsaiwa ba ta gano makusar da za ta sa Kabir ya dinga musayar munanan kalamau da hotuna da 'yanmata. Gajiya ta yi da tsaiwar ta zauna a gefen gado, sai ta shiga tausayin kanta da 'ya'ya matan da ta haifa. "Wannan wacce irin rayuwa, aai yaushe zan sanu kwanciyar hankali? Sai yaushe zan samu nutsuwa kamar kowa? Sai yaushe..." Wani sabon kukan ya sake ƙwace mata, a wannan ranar da take jin kamar zuciyarta za ta yi fiffike ta ɓullo daga ƙirjinta, ba ta shayi ko kunyar bayyana kukanta a sarari domin gurin ɗabi'u da halayen Kabir ba a ranar suka fara yi mata ba. Kamar kuwa Fauziya ta sani, su Ai'lo da ke ɗaki duk sun kasa kunne suna son gano dalilin kukan nata. Don sun san fa wuri ya dawo gida ba a buge ba, ballantana su ce takaicin rashin dawowarsa ne ya saka ta kuka. Lawisa da ke ɗaki har sun kwanta ita da mijinta ta gagara haƙuri, ta fito zuwa ƙofar ɗakin Fauziya. "Maman Na'ima! Maman Na'ima ke jaɗai ce zan iya shigowa?" Fauziya da muryarta ta gana dacewa ta ce, "Shigo ni ɗaya ce." Tana shiga ɗakin ta ɗan ƙasa fa murya ta ce, "Me yake faruwa MamAn Na'ima? Tun ɗazu nake jiyo kukanki lafita kuwa?" Ta san Lawisa tana ƙaunarta tana ba ta kulawa, amma wannan wani gingimemen sirrin mijinta ne da ba za ta iya furta mata ba. "Mahaifiyata na tuna Lawisa, mahaifiyata cw ta faɗo mini. Akwai abubuwa da dama da nake ganin iyaye mata suna yi wa 'ya'yansu Lawisa na rasa wannan gatan. Ban san wa zan raɓa na ji danshi da sanyin mahaifiyata." Jikin Lawisa ya yi sanyi, da jin kalaman Fauziya. Domin ta taɓa ba ta tsakure kaɗan daga cikin labarinta, da irin baƙar wahalar da ta sha a hannun matan babanta. Sai ta yi tsammanin ko wani abin suka yi mata bayan ta je gidan, don haka ta dafa kafaɗarta ta ce. "Ba kuka za ki yi mata ba Mamam Na'ima, addu'a ya dace ki yi mata. Ki yi haƙuri watarana sai labaru."Fauziya ta gyaɗa kai sannan ta yi mata godiya Lawisa ta koma ɗakinta. Tana nan zaune kimanin sha biyu da rabi na dare Kabir ya shiga gidan, a ɗarare ya zauna ya san Fauziya sarai da zafin kishi. Duk sai ya ji haushin kansa da tun yana gama gani bai goge ba. A tsammaninsa Fauziya za ta kula shi amma ga mamakinsa sai ga ko ƙurarsa ba ta kalla ba. "Fauziya don Allah..." "Ba na buƙatar jin komai daga gare ka." Ta furta a kausashe tana ɗaga masa hannu. Shiru ya yi ya kasa cewa uffan, Fauziya ta miƙa ta koma gefen yaranta ta kwanta ta shiga nazari da lissafin takaicin da mummunan ganin da ta yi. Bayan Maman Nana ta koma gida haka ta sake cika fam, don tana aiki amma zuciya tana raya mata abubuwa da dama har aka yi sallar Magriba Jafar ya dawo. Yana zura ƙafarsa cikin gidan ya bi ta da wani kallon cike da ƙyama, ya saki guntun tsaki sannan ya wuce ɗaki. Yanayin fuskar Maman Nana ce ta sa ya tuna abin da ya faru kafin ya fita, don haka shi ma ya yi watsi da ita. Kaskon turaren wuta ta ɗauka har za ta fita Jafar ya ƙwala mata kira, fuska a haɗe ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ce. "Ga ni." Sabuwar wayar ya ɗauko gal a cikin kqalinta ko buɗewa ba a yi ba, ya miƙa matasa sai kuwa ta saki fukarta ta hau washw baki don ta yi tsammanin ita ya sayo wa sabuwar waya. "Idan kin fita ki miƙa wa Maman Asiya, idan Naziru ya dawo ta ba shi saƙon sa da ya ce a taho masa da shi." Murnar Maman Nana ta koma ciki, nan take ta haɗe rai don kusan sati uku kenan ba ta da waya tun da Abdul ya jefa mata wayarta a ruwa. Ta yi nacin Ya sayo mata waya kullun da zancan da zai ɓullo mata. Gidan Maimuna ta ƙwanƙwasa da yake Maimunan ta san da maganar wayar da sauri ta je ta buɗe ƙofar, tana ganin Maman Nana ta ji wani farimciki ya lulluɓe ta. Wayar hannunta ta miƙe mata, sannan ta ce. " A ɗan sammun gawayi zan yi turaren wuta." Maimuna ta ce, "Wannan wayar kuma fa?" "Baban Nana ne ya ce ki ajiye wa Abban Asiya." Kamar Maimuna ba ta san kwanan zancen ba, ta saki fuska cikin murna ta ce. "Allah Ya sa Abban Asiya suprise zai yi mini, don bai yi mini zancen za a taho masa da waya ba." Maimuna ta saka cokali tana ɗiba gawayi ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Wai har yanzu ba ki gama girki ba Maman Asiya? Kai gaskiya masu girkin gawayi kuna ƙoƙari ina zan iya wannan jidalin?" Wani takaici ya maƙaure zuciyar Maimuna, ta bi bayan Maman Nana da harara a ranta ta ce. 'Ni za ki yi wa iskanci kenan? To wallahi daga wannan karon kema kin daina aiki da gas ɗin, ba dai ni za ki yi wa iskanci ba? Za ki ga muna ƙoƙari ganin idonki.' Maman Nana tana gama ɗiban wutar ta yi wa Maimuna sallama ta fice, a ta cikin riga Maimuna ta sakaya ledar wayar ta shige uwar ɗaki ta ita. Kayan sakawarta ta ɗaga daga can ƙasa ta tura wayar, ta ciro ƙaramar har za ta saka layi ta kira shi sai ta mayar saboda ta fi son sai zuwa jimawa idan ta sallami yaranta sun yi bacci ta kira shi su sha hira kamar yadda suka saba daddare kafin Nazir ya dawo. Tun da dama can shi Nazirba mutum ne mai dawowa gida da wuri ba, idan ma ya dawo ɗin mafi yawa lokaci hankalinsa yana kan wayarsa bai cika ba ta lokacinsa ba. Hatta su Asiya sai da suka lura da farincikin da take ciki, amma sai ta nuna musu ba komai. Da yake a ƙage take da ta ji muryarsa, ana idar da sallar Isha'i ta yi musu shimfiɗa. Sai da ta tabbatar da bacci ya kwashe su sannan ta shige ɗakinta ta ciro ƙaramar wayar da suke waya ta kira shi. A ɓangaren Jafar kuwa tun bayan da ya lura da haɗe ran da Maman Nana take yi, shi ma sai ya yi watsin iska da ita. Hakan kuwa ya sake ɓata mata rai, don haka ta ci alwashin za ta gasa masa a ya a hannun ta cikin ruwan sanyi. Yana gama cin abinci ya fice daa gidan, ya tafi can nesa da layinsu wurim da ya saba waya da Maimuna ya zauna. Ya jima yana dakon flashing ɗinta har sai da ya fara cire rai, sai ransa ya ɓaci da ya ayyana ko dai Naziru ne ya dawo shi ya sa ba ta smau damar kiransa ba. Yana nan zaune ya ji flashing ɗinta, a fili ya saki ajiyar zuciya. Hannunsa har rawa yake ya latsa layin nata, tana ɗaga wa ya ji ta fashe masa da wani irin kukan kissa. Wani abu ya ji yana zarga masa wanda ya kashe masa ilahirin jijiyoyin jikinsa. Sai da ya yi ƙarfim hali sannan ya iya fisgar maganar bakinsa. "Wannan shagwaɓar taba gigita ni my Moon, idan ba kya son hana ni bacci a ɗan daga ta da kukan nan haka." Daga can ɓangaren Maimuna ta sake yin wata shasshekw wace ta sake birkita shi, murya can ƙasa kamar wacce take waya da mijinta ta ce, "Ina kukan farinciki ne my J. Haƙiƙa ka faranta mini rai domɗn wannam wayar ba ƙaramin tsada gare ta ba." Murmushi ya yi mata ya ce, "Ko nawa zan iya ɓatar mini Moon, fata da burina kawai ki mallaka mini kanki." "Idan hat ni ce kamar ka samu J, kada ma ka sake wasu-wasi a kan soyayya ta." Har Jafar zai yi magana Maimuna ta katae shi a shagwaɓe. "Ɗazu matarka ta ci mutumcina bayan ta zo ɗiban gawayi, a gaskiya raina ya ɓaci domin an daɗe ba a ci zarafi kamar na yau ba. Duk da ba cikin faɗa ta yi mini magaanar ba, amma a wasan dare ta ƙare mini cin mutumci. Har takw yi mini ƙafafa a kan ita amfani take yi da gas." Sai kuwa Maimuna ta rushe da kuka, kukanta yake ji har cikin ransa. Don ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cikin rarrashi ya ce, "Ya isa haka baby Moon. Wallahi tun ranar da na fara ganinki ba ki kalar amfani da gawayi ba. In Shaa Allaha na san yadda za a yi na saya muki gas ki daina amfani da gawayi. Ita kuma ki bar ni da ita na rantse miki da Allah daga gobe ta daina amfani da gas gabaɗaya. A yanzu ma don dai dare ya yi, da a daren nan zan siyo masa kurfoti da buhun gawayi." Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA BAKWAI UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Wani irin farinciki ne ya lulluɓe zuciyar Maimuna, saboda dama ba a ranar Maman Nana ta saba zuwa tana yi mata fariya, tana baje mata jin daɗin da Jafar yake yi mata ba. Wani abin ma sai ta lura kamar da gayya Maman Nanan take yi, saboda mijinta duk ya fi ragowar mazajen layin rufin asiri. Wannan ne dalilin da ya sa Maimuna ta ci alwashin sai ta tarwatsa farincikinta, tun da ita ba ta samu kwatankwacin abin da Maman Nana take samu a wurin miji ba. "Na ji kin yi shiru ko hukuncin da na ɗauka bai yi miki ba?" Jafar ya furta jin Maimuna ta yi shiru, Maimuna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Hakan ya yi Baby J, to amma ta ya ya zan mallaki gas ɗin? Ni dai ba sana'a nake yi ba ballantana na cewa mutumin nan saya na yi." "Wannan mai sauƙi ne Moon, zan san yadda zan ɓullowa lamarin." Hirar soyayya suka cigaba da yi tamkar ma'auratan da suke nesa da juna, kowanne yana cike da kewa da begen ɗan uwansa. Suna gab da yin sallama Jafar ya ce, "Wayar nan da na aiko ba ta buƙatar caji, na saka mata caji ɗazu. Abin da ya rage kawai don Allah ki ɗaukar mini hotunanki." Maimuna ta ce, "Sai zuwa gobe idan Nazir ya fita, amma ka ɓoye su ta yadda matarka ko wani ba zai gani ba." Murmushi Jafar ya yi ya ce, "Kada ki damu akwai folder da nake ɓoye hotuna, a nan zan ɓoye naki." Yana faɗin haka daga gefensa ya ji Nazir ya yi masa sallama yana daga kan mashin, duk da ya san Nazir ba zai taɓa fahimtar da wacce yake magana ba. Amma sai da gabansa ya faɗi, ya cire wayar daga kunnensa ya ce. "Ale Nazir barka da shigowa." Nazir ya ɗan rage gudun mashin ɗinsa ya ce, "Barka dai Alhaji Jafar, ka na nan a bayan fage kana waya ko? Ai sai na aika na faɗa mata." Nazir ya yi furucin cikin barkwanci. "Tuba nake kada ka sa a rufe mini ƙofa." Jafar ya furta yana kama kunnensa, dariya Nazir ya yi ya wuce gida. Ganin ya tafi ya sa Jafar ya ja dogon tsaki yana mayar da wayar kunne ya ce, "Ina tsaka da farinciki wannan mutumin zai datse mini, don Allah Moon ki rage ba shi kula a turaka. Wallahi haka kawai kishinsa yake nuƙurƙusata." Maimuna da ita kanta haushin Nazir ya kama ta ce, "Ai yau duk bala'insa babu ma abin da zai haɗa mu, dama na kwana biyu ina juya masa baya." Kamar ba za su rabu ba haka suka yi sallama. Maimuna tana gama wayar ta yi saurin mayar da ita wurin da take, ta yi sauri ta haye gado ta kwanta ta rufe ido. A kan kunnenta Nazir ya shiga gidan, ya ɗan jima a falo sannan ya tashi ya shiga ɗakin. "Maimuna! Maimuna!" Ya furta yana bubbuga filonta, yamutsa fuska ta fara yi tana miƙa kamar wacce ta jima tana bacci. "Sannu da zuwa." Ta furta masa tana sakin hammar ƙarya. "Yawwa sannu ya gida?". A hankali ta zuro ƙafafuwan ƙasa, ta jinginta kanta da fuskar gadon ta ce. "Lafiya ƙalau." Ya yi mamakin a 'yan kwanakin nan da Maimuna ba ta yi masa ƙorafi, domin kusan kullum idan ya dawo gida sai ta yi masa ƙorafi a kan kai wa daren da yake yi a waje. Miƙewa ta yi ta fito falo, Nazir ya rufa mata baya. Kayan abincinsa ta ɗebo ta ajiye masa har ta miƙe za ta koma ɗaki ya riƙo hannunta. "Maimuna kwana biyu na ga duk kin sauya, me yake damunki ne?" Fuska babu walwala ta ce, "Me ka gani?" "Na ga kwana biyu kamar ba ki damu da ni ba, kuma ni dai na san ba wani abu na yi miki ba." Nazir ya furta a sanyaye. "A'a babu abin da yake damuna kawai dai baccin da na tashi ne!" "Ba haka ba ne Maimuna, a 'yan kwanakin nan ko ƙarfe nawa na dare zan kai ba za ki kira ni ba, idan na dawo kuma ba za ki tambaye ni dalilin kai wa daren da na yi ba. A yanzu ko zan kwana ina chatting uffan ba za ki ce mini ba, ni sai na ga kamar haushina kike ji." "A'a ni babu wani haushinka da nake ji, ai kowa rayuwar da ya ga dama ita yake yi. Tun da na lura kulawar da nake ba ka ce ta sa kake yi mini wasu abubuwan, don haka na bar wahalar da kaina." Maimuna ta sake yin maganar tana shirin tafiya. "Zauna mana, yau fa hira nake son mu yi. To yanzu dai ki yi haƙuri, ga biskit da chocolate nan na taho muku da shi ke da yara." Ta fahimci sarai hirar da yake nufi, domin dama ba ta cika amfani a wurin Nazir ba sai yana buƙatarta. Sau tari idan hakan ta taso babu wata kulawa da nuna soyayya haka kawai zai afka mata, ta kawar da kai gefe ta ce. "Ai kuwa sai dai ka yi haƙuri zuwa gobe kaina matsanancin ciwo yake, shi ya sa ma na sha magani na kwanta ɗazu." Tana gama maganar ta janye hannunta ta wuce ɗaki, kamar sakarai haka yake bin Maimuna da kallon mamaki. Ya san dai Maimuna ba shiga gidan kowa take ba, ballanta ya ce maƙota ne suke zuga ta. Kuma ya santa da ƙorafi matuƙar ya ɓata mata rai ko bai san laifin ba za ta fito ta sanar da shi. Da sauri ya tashi ya bi ta ɗakin a lokacin har ta ja bargo ta rufa, ransa ya sake ɓaci amma sai ya saita nutsuwarsa ya ce. "Magana nake yi miki fa Maimuna kika shigo ɗaki." Tana daga kwance ta ɗago ta ce, "Ni ma ai amsa na ba ka Abban Asiya." Ƙwafa ya yi ya juya ya fita, ya zauna ya cigaba da cin abincinsa. Sai da ya gama uzurinsa sannan ya shiga ɗakin ya kwanta a gefenta, juyi yake shi kaɗai yana mamakin sauyin halinta. Don haka ya so danne buƙatarsa amma sai ya gagara, hannu ya kai ta janyo ta kamar tana jira ta ture shi tana faɗin. "Haba Abban Asiya, wai me kake yi haka na ce maka ban da lafiya fa." "Kin sauya Maimuna, Me ya sa kike son horar da ni ne? Yau rabona da ke kwana nawa, rannan kin ce mini zazzaɓi kike. Shekaran jiya kin ce ciwon baya, yanzu kuma kin ce mini kanki yana ciwo. Idan kina ganin ba za ki iya ba ni haƙƙina ba sai na ƙara aure." Nazir ya furta cike da barazana saboda ya san Maimuna tana da kishi, amma cikin halin ko in kula ya ji Maimuna ta ɗago ta ce. "Sai me don ka yi aure Naziru? A kaina za ta zauna? Ko ni zan ciyar da ita, ruwanka ne ka ƙara aure kuma ruwnaka ne ka bari na samu lafiya. Idan kuma ƙarin auren ka ga shi ya fi maka mafita wallahi ni ko a gefen takalmina." Tsoro ne ya kama shi saboda ya ji an ce idan mace ba ta ba ka kulawa, ba ta nuna kishi a kanka kawai zama take yi da kai ba don soyayya ba. Da a ce a shekarun ba ya ne ba zai yi mamakin jin haka daga gare ta ba, amma yanzu da shekarun aurensu suka tura ya lura duk ta zubar da makamanta. "Au haka kika ce?" Nazir ya faɗa a zafafe. "Eh haka na faɗa, tun da kishiya ba a kaina aka fara ba." Tana gama faɗa ta sake gyara kwanciyarta. Cike da kewar Maimuna Jafar ya nufi gida, a lokacin da ya shiga ƙarfe goma sha ɗaya da rabi. A zaune tunkur ya samu Maman Nana da alama jiransa take yi, ya shiga ɗakin kamar bai ganta ya fara rage kayan jikinsa. "Abban Nana wato fitar da ka yi gidan su budurwarka ka tafi ko?" Bai waiwayo wurinta ba ya ce, "In ji wa?" "Sai an faɗa mini?" "To tunaninki bai harsaso miki daidai ba." Shi ma ya faɗa fuska a haɗe. Hakan kuwa ya sake harzuƙa ta, rai a ɓace ta ce. "Wai Abban Nana me kake nufi ne? Ka bi ka sauya mini lokaci ɗaya na rasa gane kanka, da idan ka shigo gidan bayan sallar Isha'i ba ka sake fita sai washegari. Amma yanzu kana gama cin abinci sai ka fice ba za ka dawo ba sai dare, na gaji fa wallahi na gaji da irin cin kashin da kake yi mini." "To idan ba za ki iya ba sai ki nemawar kanki mafita." Ta riski miyagun kalamansa a cikin kunnuwanta, ƙirjinta ya buga da ƙarfi. Cike da tsoro ta dube shi amma sai ta nuna masa ba ta fahimci abin da yake nufi ba ta ce. "Me kake nufi?" "Ina nufin idan ba za ki iya zama da ni da ki kama gabanki." Wani irin dum! Ta ji kamar an kwaɗa mata guduma, da sauri ta runtse idonta ta buɗe su a kansa. Ta taka gabansa muryarta tana rawa ta ce, "Abin da za ka ce mini kenan Abban Nana? Dama ka gaji da ni ban sani ba?" "Ko ban gaji da ke ba wulaƙancin da kika tarko ne ba zan ɗauka ba, na lura samu ma yana saka mace ta yi iskancin abin da take so. Amma babu damuwa tun da irin zaman da kike so mu yi shi kenan." Shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta, ta shiga nazari daga safiyar ranar zuwa dawowarsa ko za ta iya tuna laifin da ta yi masa amma ba ta iya tunawa ba. "Don Allah ka faɗa mini laifin da na yi maka Abban Nana?" Bai tanka mata ba ya saki tsaki ya ɗauki fulo ya koma kan kujera ya kwanta. Abin duniya ne ya haɗe wa Maman Nana, sai ta ji ya fara ba ta tsoro domin lamarin nasa ƙara yin gaba yake yi. Don haka ta shiga alla-alla gari ya waye ta leƙa gidan Maimuna ko ta ba ta shawarwarin abin da za ta yi. Washegari Tun da Jafar ya yi sallar Asuba bai koma ba, gari yana yin haske ya shiga cikin kitchen ya ɗauke tukunyar cilinder gas ya fice da ita. Da yake Maman Nana ba ta tashi da wuri ba, saboda a daren bacci bai ɗauke ta da wuri ba ko kaɗan ba ta san wainar da ake toyawa ba. Sai da ta ji alamun buɗe gate ta tashi ta fito, a tsammaninta Jafar fita ya yi kasuwa. Banɗaki ta shiga bayan ta fito ta shiga kitchen za ta shirya wa su Nana abin breakfast da na makatanta. Amma sai ta ga wayam babu clinder, ba ta kawo komai a kanta ba; sai ta yi tsammanin ko ƙaro musu gas zai yi saboda idan ya ga ya kusa ƙarewa yana ɗauka ya ƙaro mata. Tana daga ƙofar kitchen ta hango shi yana kokawar shigowa da ƙaton buhun gawayi, sai da ya ƙarasa ya jingine shi sannan ya sake fita gate ya sauke mirgino buhu na biyu. Maman Nana tana tsaye ya gama dire buhunnan gawayin har guda biyar, sannan ya ɗauko kurfoti ya dire a gabanta. Fuska a haɗe ya ce, "Daga yau ga abin da za ki dinga girki da shi, gas ya sake tsada ba zan iya sayensa ba. Cilnder ma na sayar wa mai shagon da nake sako mana gas, sai a ci gaba da malejin rayuwa tun da komai tsada yake sake yi." Jafar yana gama faɗar haka ya shige ɗaki. Kabir kwance ya yi a kan gado, yana jin haushin kansa a kan abin da ya aikata. Fushin Fauziya ya fi komai ɗaga masa hankali, don Fauziya mace ce mai haƙuri da sauƙin kai. Amma idan ta yi fushi ba ta iya zuciya ba, juye-juye ya fara yi yana hangen ta da take kwance idonta biyu tana hawaye. A hankali ya tashi zaune ya tsugunna a gefenta murya a sanyaye ya ce. "Fauziya! Don Allah ki tashi mu yi magana, ba na son ki saka kanki a cikin wani hali saboda yanayin da kike ciki." Ɗagowa ta yi ta dube shi, tana jin sautin muryar martanin batsar da yake mayarwa da Hafse a cikin kunnuwanta. Zuciyarta ta shiga zafi, wani abu ya tokare ƙirjinta. A hankali ta fara jin mararta tana tsira mata, ta cije bakinsa tana girgiza kai. "Don Allah ki yafe mini..." "Idan ka sake yi mini magana zan fice daga gidan nan na ba ka wuri." Ta katse shi da wani irin sauti, kamar sabon munafiki haka Kabir ya ja jiki yana sunne kai ƙasa ya koma kan gadon ya zauna. A cikin wannan daren daga shi har Fauziya bacci rabi da rabi suka yi, sai bayan Asuba ta samu bacci mai hauyi ya yi awon gaba da ita. Tun da Kabir ya tashi bai koma ba, saboda ya san ya yi wa Fauziya laifi a hankali ya dinga aiki don kada ya tashe ta. Shi ya dafa wa yara abinci, ya shirya su suka tafi makaranta. Sannan ya shiga ɗakin ya share mata, kwanukan wanke-wanken kuma ya ajiye a bakin rariya zai wanke mata. Lawisa tana sanye da hijabi tana girki a bakin ƙofarta ta hango shi ya tsugunna zai yi wanke-wanke, miƙewa ta yi ta ƙarasa wurin ta ce, "Baban Na'ima ka bari zan wanke mata, ko jikin Maman Na'iman ne." Kabiru ya ɗan sosa kai ya ce, "Eh ta tashi ba ta jin daɗi ne, shi ne ta ɗan kwanta zan rage mata aikin." "Subhanallah! Allah Ya raba lafiya, bari na ƙarasa girki sai na haɗa na wanke da nawa." Godiya ya yi mata sannan ya koma ɗakin, tun da ya shiga yana son ya tambaye ta abin da za zai girka musu da rana yana shakkar tashinta da ɓacin ranta. Tukunyarta ya buɗe ya ga akwai sauran miya, sai kawai ya ɗora taliya ya dafa musu. Kafin Fauziya ta tashi tuni Kabir ya gama komai, hatta turaren wutar da take sakawa ya saka musu. Ya shiga ɗakin ya same ta a bakin gado a zaune ta tashi, fuskarta ta sauya sosai daga jiya zuwa yau duk ta rame. "Ga ruwan wanka zan sirka miki sai ki yi wanka." Kabir ya furta yana satar kallonta, ko kallonsa ba ta yi ba har ya sake maimaita mata. "Don Allah ka matsa daga gabana Kabir." Da sauri ya fice daga ɗakin, ya shiga banɗaki ya yi wanka. A inda ya bar ta a nan ya same ta, bayan ya shirya ya tambaye ta abin da take buƙata a wannan karon ma banza ta yi da shi. Don haka ya zaro dubu ɗaya ya ajiye mata, bayan ya fita ta bi bayansa da kallon tsana. Miƙewa ta yi ta ɗauki wata 'yar babbar leda ta ɗebo kaya a drowerta, sai da ta yi wanka ta ɗauki kular abincin su ta zuba, sannan ta saka wata doguwar rigar atamfa ko man kirki ba ta shafa ba. Bakin ƙofar Lawisa ta ƙarasa ta ce. "Lawisa ga abincin yaran nan da kayan makarantarsu, idan sun dawo don Allah su wuce makaranta." Lawisa ta karɓa tana faɗin, "Ai na leƙa kina bacci, wai ko abar ce ta zo." Fauziya ta girgiza mata kai ta ce, "Ga wannan mukullin kuma koda babansu zai dawo." Da mamaki Lawisa ta bi Fauziya da kallo, don ba ta taɓa tafiya unguwa ta ajiye mukulli ta ce a ba wa Kabir ba, amma sai ta haɗiye abin a ranta don tun daren jiya ta fahimci akwai abin da yake damunta saɓanin maganar da ta faɗa mata. Sallama Fauziya ta yi mata ta fice daga gidan, tana fatan wannan fitar da ta yi daga cikinbaƙin gida ya zame mata ita ce fita ta ƙarshe da za ta yi masa. +2347062062624 [14/02, 17:27] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA TAKWAS UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Kabir tun da ya fita daga gidan ba a nutsuwarsa yake ba, kwata-kwata ya rasa me yake yi masa daɗi. Zuciyarsa ce ta shiga wassafa masa laifin abin da ya aikata, har yake jin kamar ya rabu da su Hafsee ya rungumi matarsa ita kaɗai. Ɗaya tsagin na zuciyarsa kuma, ya shiga kwaɗaita masa haɗe da harsaso masa surorin jikin Surayya da Hafsat. Nan take ya ji sam ba zai iya rabuwa da su ba, koda a ce bai auri su duka ba. To tabbas dole zai auri ɗaya, domin zuciyarsa ta jima tana kaɗayin dandalar ni'imar da Allah ya yassare musu. Rashin walwala da sukunun da yake ciki, ya sa mutanen cikin shagon suka lura da shi. Har suke tambaayarsa ko ba shi da lafiya, saboda Kabir mutum ne mai faram-faram yana da sakin fuska sosai. Ganin ya gagara gudanar da aikin da yake yi, yamma liƙs ya yi wa Ogansu sallama ya ce zai koma gida saboda ba ya jin daɗin jikinsa. Lokacin da ya tunkaro gida, kamar ya kira Fauziya a waya ya tambaye ta ko akwai abin da take buƙata ya sayo mata. Sai kawaa ya haƙura, saboda ko sunanta ya tuna gabansa faɗuwa yake yi. Lokacin da ya ƙarasa gida kusan shida saura, su Na'ima suna jin sallamarsa suka fito daga ɗakin Lawisa da sauri suka rungume shi. Mukulli ta ba wa Fatima ta ce ta kai masa. Kabir turus ya yi a bakin ƙofar ganinta rufe da kwaɗo, kamar yaran sun san tambayar da take cikin zuciyarsa Hidaya ta ce. "Mami ta je unguwa!" Gabansa ne ya faɗi, ƙafafuwansa har rawa suke yi saboda tashin hankali. Da ƙyar ya iya saita nutsuwarsa hannunsa yana karkarwa ya buɗe ƙofar ɗakin suka shiga, yana shiga ɗakin ya fara kiran layin Fauziya sai dai tashin farko ya ji an ce masa a kashe take. Kamar zai yi hauka, haka ya fara zagaye ɗakin da sauri-sauri. Wani tunani ya faɗo masa cikin sauri ya sake riƙo hannun yaran, ya kai su ƙofar ɗakin Lawisa ya ce su shiga zai je ya dawo. Rufe ɗakin ya yi ya sake ba wa Lawisa mukullin sannan ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama. "Ina Fauziya ta tafi? Ko dai ta tafi gidansu ne? Fauziya ba ta taɓa yin yaji ba, ko ƙarata ta kai gidansu? Yanzu haka za su dinga yi mini kallon mutumin banza? Kai Fauziya ba za ta yi mini haka ba, ina da tabbacin ba za ta bankaɗa labulen sirrina ba." Haka Kabir ya dinga tafiya yana surutai kamar sabon taɓin hankali, domin kafin ya ƙarasa bakin titi gani ya yi hanyar ta ƙara yi masa nisa. A gurguje ya tari adaidaita sahu ya nufi uguwarsu Fauziya, yana zuwa ya samu mahaifinta a ƙofar gida yana sallar magriba. A hargitse ya zube a gabansa yana faɗin, "Baba barka da yamma." "Baba ya yi masa kallon tsaf ganin ƙafafuwansa duk sun yi butu-butu, da mamaki ya ce. "Barka dai Kabiru, kai ne da doshin magriba haka? Ya Fauziya da yaran?" Turus! Kabir ya yi ya ɗan sosa kansa, gabansa ya cigaba da faɗuwa saboda fargaba. Amma gudun kada Baba ya gano shi sai ya ce, "Duk lafiyarsu ƙalau, dama wucewa zan yi na ce bari na biyo mu gaisa." Baba ya saki murmushi ya ce, "To Ma Shaa Allahu, ai jiya mun ga abin alheri. Allah dai ya raya zuri'a." Jiki a sanyaye Kabir ya amsa sannan ya cewa Baba zai wuce. Haka Kabir ya cigaba da tafiya yana kiran layin Fauziya har lokacin a kashe, gidan ƙawarta Jamila ya je suka gaisa. Ita ma ta wurga masa tambayar Fauziya, don ta yi mamakin ganinsa a ƙofar gidanta. Saboda rabon shi da gidanta, tun tana amarya da suka zo mata shi da Fauziya kusan shekara biyar kenan. "Kabir ko ƙawar tawa ce ta haihu?" Jamila ta jefe masa tambaya tana gyara mayafinta. "Amm dama na ɗauka ta ƙaraso nan ne, da yake ta fita ɗazu ta ce mini idan ba ta yi yamma ba za ta biyo ta nan. To mukullin yana hannunta, kuma akwai ɗinki wata Mai jego da aka zo karɓa daga nesa, ga ɗakin ta rufe shi. Na kuma kira wayarta a kashe." Ita ma Kabir ya zabga mata ƙarya, Jamila ta ce. "Ai kuwa ba ta biyo ba, ina jin ko kun yi saɓani a hanya tun da magriba ta yi." Amsa mata Kabir ya yi suka yi sallama. Tunanin duniya ya shiga yi a kan inda zai je ya lalubo Fauziya, saboda tun da suke duk faɗan da za su yi ba ta taɓa yi masa irin haka ba. Wayarsa ce ya ji ta fara ƙara, da sauri ya ciro ta a tsammaninsa ita ce sai ya ci karo da lambar Surayya. Guntun tsaki ya saki ya ƙi ɗauka, amma sai ta cigaba da kira. A ƙufule Kabir ya ɗauka yana faɗin, "Wai Surayya me ya sa kin fiye naci ne? Idan kika ga ban ɗauka ba ai kin san ina uzuri." Daga can ɓangaren Surayya ta kwantar da murya ta ce. "Haba sweet..." "Babu wani sweet, Surayya ba na cikin nutsuwata yanzu haka duniyar ta yi mini zafi." "Me yake damunka baby? Ko za ka zo na rage maka damuwa?" Kamad Kabir ya buɗe baki ya faɗa mata abin da ya faru, sai kuma ya tuna idan ya yi haka kamar ya rusa soyayarsa ne, idan Surayya ta ji labarin hotunan tsiraicin da hafsa ta tura wa Fauziya ne ya sa ta fita daga gidan. "Wannan ba damuwarki ba ce, family issuesne." Daga haka ya katse wayar, sai ya sake lalubar layin Fauziya amma a kashe. Gida ya ƙarasa ya laɓe a soro, don kada mutanen gidan su fahimci akwai matsala tsakaninsa da ita. Ganin har lokacin ba ta dawo ba ya sa Kabir ya nufi gidan Inna domin ya sanar da ita halin da ake ciki, a lokacin da ya shiga gidan har an fara kiraye-kirayen sallar Isha'i. Yana shiga ɗakin Inna ya nemi wuri ya zauna haɗe da haɗa kai da gwiwa. Inna da ta gama alwala ta shiga ɗakin ta ce. "Kabiru nake gani da daren nan?" Kabiru ya share ƙwallar idonsa ya ce, "Inna ni ne." "To ashe Fauziyan ta isar maka da saƙona, amma ba ka samu zuwa ba sai yau. Yau kuma me ka kawo mini, saboda dama garin tuwona ya ƙare." Inna tana yin gama magana ta ji Kabir yana shasshekar kuka, a ɗan kaikaice ta leƙa fuskarsa ta ce. "Wai kuka kake yi Kabiru? A cikin yaranka wata ce ta mutu?" Kabir ya girgiza mata kai, Inna ta sake cewa. "To Fauziyan ce ta mutu?" A nan ma ya sake girgiza mata kai. "To uban me ya sa ka kuka tun a farkon daren nan? Ni dai na san rabon da na ga kukanka tun ranar da mahaifinku ya mutu." "Inna gida na koma na ga Fauziya ba ta nan, na je gidansu da niyyar tambayarsu sai mahaifinta ya tambaye ni ya take, kin ga kenan ba ta je can ba. Ga shi dama ba ta tambaye ni ba, ban san inda ta tafi ba." Kabir ya ƙarasa maganar yana zubar da ƙwallah. Wani takaici ne ya maƙure ziciyar Inna, ta dube shi a wulaƙance tana sakin dogon tsaki ta ce. "Mttssswww amma dai Kabiru ka yi asara wallahi, yanzu a kan mace kake zubar da ƙwalla? Ashe abin da ake faɗa gaskiya ne, yarinyar nan ta gama wanke hannu a kanka." Inna ta koma bakin gado ta zauna ta cigaba da cewa, "Yo wai ma Fauziyar yarinya ce? Da za ta fice har ka dinga neman saboda ta ka ganɗma lalacewa" Cikin damuwa Kabir ya ce, "Wallahi Inna ni ne da laifi, ni na ɓa ta mata rai, duk macen da ta ga abin da na yi fiye da haka ma za ta iya aikatawa." "To ai sai ka yi ta yi tun da wahala ta aure ka, yanzu kuma a ina ta bar yaran?" Kabir ya ce, "Suna ɗakin matar gidanmu." "Amma wannan yarinya an yi baƙar munafika, haka kawai ina zaune ƙalau ta ɗaga mini hankali. Sai ka fita ka kai cigiyarta gidan radiyo, tun da lalacewarka ta kai haka." Daga haka ta saka hijabinta ta tayar da sallah. Kabir da ya lura zamansa a wurin Inna ba mafita zai kawo masa ba, sai ya miƙe ya fice. Kasancewar Sadiya ta ji duk abin da yake faɗa, sai ta tsayar da Kabir tana tambayarsa. A nan ya zayyane mata duk abin da ya faru, duk da bai fito ya faɗa mata laifin da ya aikata ba. Shiru ta yi tana nazari, amma har cikin ranta take ji Kabir ne bai kyautawa Fauziya ba, domin ta san tana da haƙurin gaske. Saboda damuwa Kabir haka ya dinga takawa a ƙafa, yana tafe yana jimamin halin da take ciki da tsohon ciki a wannan lokacin. A haka har ya ƙarasa gida. Tun lokacin da Fauziya ta tashi daga bacci ta ji mararta da bayanta suna ciwo, don haka ta yanke shawarar zuwa asibiti. A ranta tana fatan koda haihuwar ce ta zo mata, tana fatan ta kasance silar tafiyarta lahira. Duk haihuwa ukun da ta yi Kabir ne yake kai ta asibiti, daga baya kuma sai ya kira matar mahaifinta ya sanar da ita idan sun je. Amma da yake zuciyarta a cunkushe take da haushin Kabir, ya sa ta ɗauki duk wani kaya da za a buƙata a asibiti. Ta ƙi sanar da Lawisa ne, saboda ta san idan suka tafi ita da Lawisa asibiti babu a inda su Na'ima za su zauna ballantana su ci abinci. Sai da ta fara biyawa ta gidan Dillaliya ta roƙe ta, da ta ba wani abin daga cikin cikon kuɗin firji, bayan ta karɓi kuɗin ta fice daga gidan. Fauziya ba ta damu da kallon da mutane suke yi mata ba, tana tafe tana hawaye haka ta dinga tafiyar ƙafa domin ya taimaka mata wurin samun saurin naƙuda. Ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu adaidaita sahu ya kai ta asibiti, a lokacin da ta je asibiti ana duba ta aka ga tana 5cm. Wayarta ta ciro ta fara kiran ƙanwarta da suke uba ɗaya ba ta same ta ba, ta kira ta matar babanta ita ma a kashe. Na'ima ba ita ta haihu ba sai bayan sallar magriba, ta haifo jaririyar 'yarta mace kyakkayawa mai kama sak da Kabir. Ido ta ƙurawa jaririyar tana kallo, saboda tsananin kamar da suke yi da mahaifinta. Wani irin takaici ya kamata sai kawai ta fashe da gunjin kuka, Midwife ɗin da ke gefe ta dafa ta ta ce. "Maman baby kukan kuma na mene ne? Ai farinciki ya kamata ki yi, tun da Allah Ya raba ku lafiya." Murmunshin yaƙe Fauziya ta yi, sannan ta ciro wayarta ta sake kiran lambar ƙanwarta Shukura. A wannan karon ta ci sa'a an ɗauka, a nan ta sanar da ita asibitin da take. Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba Shukura ta ƙarasa asibitin, bayan an gama duba ta da jaririyarta aka sallame ta suka wuce gida. Lokacin da Fauziya ta yi sallama da gudu yaranta suka fito daga ɗakin Lawisa suna faɗin. "Mami oyoyo." Turus! Lawisa ta yi ganin Shukra tana rungume da jaririyar Fauziya, tsalle Lawisa ta buga ta ƙarasa gabanta ta ce. "Wai dama matar nan abin da kika fita kenan? A gaskiya kin shammace ni Maman Na'ima, shi ma kuma Abban Na'ima abin ka da namiji bai ce mini haihuwa kika fita ba. Barka-barka uwar 'yan'mata, In Shaa Allahu matar gwamna kika haifo mana." Fauziya ta saki murmushi, tana shirin shiga ɗaki su A'ilo suka fito suka yi mata barka sama-sama kowacce tana yamutsa fuska. Sai da Shukura ta yi mata ɗan abin da ba a rasa ba, sannan ta wuce gida. Kafin wani lokaci tuni Lawisa ta ɗora mata ruwan wanka, sai da ta surka mata sannan ta karɓi jaririyar ita kuma Fauziya ta shiga wanka. Bayan Fauziya ta gama Lawisa ta haɗa mata ruwan shayi ruwan bunu. Karamcin da Lawisa ta yi mata ya sa ta dinga zabga mata godiya, har sai da Lawisan ta nuna ɓacin ranta. Sai da ta yi wa su Na'ima shimfiɗa, ta tambayi Fauziya ko akwai abin da za a yi mata ta ce a'a, sannan Lawisa ta yi mata sallama ta tafi ɗakinta. Lokacin da Kabir ya shiga gidan hango ɗakin ta ya yi a kunne da fitila, wanda hakan ne ya ba shi tabbacin ta dawo gidan. Ƙafarsa har harɗewa take saboda sauri, a haka ya faɗa ɗakin. A zaune ya same ta jingine da gado, yanayin fuskarta babu yabo babu fallasa. A fili Kabir ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, saboda farinciki kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha. Fauziya yi ta yi kamar ba ta gan shi ba, sai dai kallo ɗayan da ta yi masa ta fahimci duk ya fita a kamanninsa. Ƙafafuwansa sun yi futu-futu kamar wanda aka tuno daga rami, a gefenta ya zaune murya a raunane ya ce. "Fauziya!" Ido ta zuba masa tana kallo sai dai ba ta amsa masa ba, ya riƙo hannunta a sanyaye ya ce. "Hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba da na dawo na ga ba kya gidan nan, don girman Allah ki yi haƙuri ki saurare ni. Na san na yi kuskure amma don Allah ki yafe mini." Ajiyar zuciya Fauziya ta sauke tana janye hannunta daga cikin nasa ta ce, "Da a ce ban yafe maka ba, da fitar da na yi ba zan sake tsoma ƙafata a cikin gidan nan ba." Lumshe ido ya yi cikin farinciki ya ce, "Wallahi wannan yarinyar da kika ga maganarmu ban jima da haɗuwa da ita ba, kuma kin san akwai shaiɗanun mata da suke jan hankali maza. Wannan ne nan farko da ƙarshe, In Shaa Allahu haka ba za ta sake faruwa ba..." "Wannan ba damuwa ta ba ce Kabiru! Amma ka sani, ka zabtare kaso casa'in da tara na daga cikin yarda, ƙauna da amincin da na damƙa maka. Ka shayar da ni ruwan mamaki Kabir, mamakin da har zuwa numfashina na ƙarshe ba zan daina yin sa ba. A kullum ina son ka dinga tunawa, kai ma uba ne. Uban 'ya'ya matan da kake yunƙurin ɓa ta tarbiyyar 'yar mutane." Shiru Kabir ya yi yana jin kalamanta suna ratsa shi, ko babu komai ya ji daɗi da ta furzo abin da yake cikin zuciyarta. Ya sake marairaicewa ya ce, "Duk abin da kika faɗa haka ne, In Shaa Allahu zan kiyaye. Amma don Allah ki daina fushi da ni, wallahi fushinki shi ne abin da ya fi komai ɗaga mini hankali." Kabir ya faɗa yana jiran amsarta, kukan jaririya ya ji a bayanta. Fauziya ta juya ta ɗauko ta tana yunƙurin ba ta mama, wani irin abu ne ya tsarga masa kamar wanda aka yi wa shocking. Da wata irin murya cike da ruɗewa ya ce, "Wai dama kin haihu Fauzina?" Fauzina da ta ji ya faɗa ya sa kalmar ta ƙara ba ta mata rai, ta tuno boyis ɗin da ta saurara wanda ya yi wa Hafsa da ta ji yana cewa, duk duniya bai taɓa yi wa kowacce mace soyayyar da yake yi mata ba. Ganin ba ta za ta ba shi amsa ba, ya sa shi saurin karɓar jaririyar ya rungume a ƙirjinsa. Kamar mutum-mutumi haka Maman Nana ta daskare a tsaye tana kallon Jafar har ya shige ɗaki, ita abin ma mamaki ya ba ta. Domin tun da suka yi aure ba ta taɓa amfani da gawayi ba, duk da a shekarun baya ƙarfin Jafar bai kai na yanzu ba. Rufa masa baya ta yi cikin ɗakin, yana ganin haka ya sake haɗe fuska. "Abban Nana wai me yake faruwa? Me ya sa kake son cusguna mini? Me na yi maka duk ka canza kake ƙaƙalo abin da za ka cusguna mini?" Maman Nana ta yi maganar muryarta tana rawa. "Me kuma na yi miki?" "Amma clinder fa ka ɗauke mini ka kawo buhunhunan gawayi ka ajiye mini." Sai da ya ɗaura towel ɗin wankansa sannan ya ce. "Su waɗanda suke amfani da gawayin mutuwa suka yi? Ko kuma taɓo ya yi musu a goshi? Am sorry to say na ga ke gidanku ma da itace suka amfani." Saukar kalaman Jafar a kunnenta ji ta yi tamkar an buga mata guduma. Maman Nana ta haɗiyi wani irin abu mai ɗaci a zuciyarta, idonta ya ciko da ƙwalla. "Gori za ka yi mini Abban Nana? Ko dai ka daina ƙaunata ne? Wane ne yake zuga ka a kan iyalinka ne?" Jafar ya matsi toothpaste kamar ba zai tanka mata ba, sai da ya je bakin ƙofa ya waiga ya ce. "Babu ɗaya daga ciki, kawai ke kika yi zargin haka. Yanzun ba ni da ƙarfin saka gas ne..." "Wallahi kana da shi Jafar, sai dai idan wani ne yake zuga ka kuma wallahi ba zan yi amfani da gawayi ba." Maman Nana ta furta cikin kuka, jin hayaniyarsu ya sa Abdul ya rarrafa ya riƙe ƙafarta ya saka kuka shi ma. Ɗaukarsa ta yi tana hawaye ta ji ya ce, "Ke dai Sumayya wallahi ba matar rufin asiri ba ce, ban da haka saboda na kawo miki gawayi, za ki yi mini hayaniya har maƙota su ji." Wani irin sak Maman Nana ta yi, tana jin wata irin juwa tana yunƙurin taɗe ƙafafuwanta. Hawaye ya shiga kwarara daga kwarmin idonta, cikin ƙunan zuciya da sarewa ta ce. "Yau ni kake kira da ba matar rufin asiri ba Jafar?" Cikin halin ko inkula Jafar ya ce. "Mata nawa ne a nan unguwar suka amfani da gawayi? Su sun yi wa mazajensu irin abin da kika yi mini? Idan kina son rufin asirina ba hannu bibbiyu za ki karɓa ki sarrafa ba, mata ku dai halinku sai Allah. Da kun samu sake a gidan miji sai ku manta halin da kuke ciki a gidanku." Baƙaƙen maganganun Jafar suka sake baƙanta ranta, zama ta yi a wurin ta ci kuka ta more saboda ɗacin da zuciyarta take ciki. Tana nan zaune har Jafar ya fito daga banɗaki, sai da ya gama shiryawa sannan ya ce mata. "Idan kin gama ki miƙa su Nana makaranta ni ina da uzuri da wuri zan fita." Yana gama maganar ya fice. Kamar ta ga sabuwar hallita haka ta bi bayan Jafar da kallo, zuciyarta ce ta shiga yi mata saƙa da warwara. Sai ta fita ta fara yunƙurin kunna kurfitin, amma ta ƙona ashana ta fi goma ba ta kama ba. Sannan ta ɗauki wata ledar pure water ta kunna da ita A nan ta samu wutar da kunnu, da yake tana da ruwan tea fulas sai ɗumame kawai ta yi, bayan ta sauke ta ɗora doyar su Nana ta makaranta. Saboda rashin sabo Maman Nana ba ta gana suyar doya ba sai kusan ƙarfe tara na safe, da yake bayan su Nana sun gama breakfast shirya su ta yi ta miƙa su. Sai daga ba ya ta kai musu abin break, da ta koma ta ɗora abincin rana. Wuni ɗaya da ta yi gidan gabaɗaya ya ɓaci da toka, hannuwanta sun yi baƙi da gawayi. Sai kusan azahar ta gama girki sannan ta gyara gidan. Ranta ya ɓaci sosai da ta ga cikin faratanta duk baƙin gawayi, gyara gidan ta yi bayan ta gama ta faɗa wanka. Sai da ta yi wa Abdul wanka sannan ta shiga gidan Maimuna, a harabar gate ɗin ta same ta sanye da hijabi ta ce. "Sai ina kuma uwar Asiya?" Maimuna ta gyara saka hijabin ta ce, "Wallahi almajirina ne bai zo ba, ga lokaci ya ƙure yara sun kusa dawowa kuma gawayina ya ƙare." Maman Nana ta saki tsaki ta ce, "Hmmm wai kin san ni ma yau Abban Nana buhunnan gawayi ya dire mini? Wallahi namiji ɗan kunama ne. Kin ga cin zarafin da ya yi mini yau a kan na ce ba zan yi girki da gawayi ba?" Maimuna har cikin zuciyarta ta ji wani irin daɗi, a cikin zuciyarta ta raya. 'Ƙaryar banza ashe ke marar kunyar ƙarya ce?' Amma a fili sai Maimuna ta ce, "Ikon Allah, ni kam lamarin Abban Nana kullum ƙara gaba yake, wai ni ko dai neman aure ya fara ne? Maman Nana sai fa kin tashi tsaye, ba na son dai ki yi mini wata fassarar da sai na ce gaskiya sai kin haɗa da neman taimako." Maman Nana ta yi shiru tana juya kalaman Maimuna a ranta. Ummou Aslam Bint Adam🌚 +2347062062624 [17/02, 19:53] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA TARA UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Ganin kamar tarkonta ya kama Maman Nana ya sa ta saki murmushin gefen baki, ta ɗan taɓo ta da tuni ta dulmiya kogin tunani. "Na ga kin yi shiru Maman Nana, amma fa kada ki yi mini mummunar fahimta. Lamarin ne nake ganin kamar ba banza aka bar shi ba, tun da ke da bakinki kike cewa a duniya Abban Nana ba ya son abin da zai sa ki wahala ko ya ƙuntata miki. Kwanaki na ji kin ce har girki yake taya ki da rainon yara, shi ya sa na ce ko za ki haɗa da neman taimako." Maman Nana ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan girgiza kai, don ko kaɗan ba ta da ra'ayin zuwa wurin malaman a kan duk wani abu da ya sha mata kai. "Kai an ya kuwa Maman Asiya? Gaskiya ba zan iya ba, saboda malaman nan idan ka fara zuwa wurinsu sun fara kunto maka matsaloli kenan. Bari dai mu gani zuwa nan gaba." Maman Nana ta ƙarasa maganar tana dafa ƙofar, ba haa Maimuna ta so ba. Don haka ta taɓe baki a fakaice ta ce, "To ai shi kenan, Allah Ya yi mana magani. Kin san akwai malamai akwai kuma muna malamai." Maman Nana ba ta tanka mata ba, suka fito ita da Maimuna. A madadin Maman Nana ta koma gida sai ta shiga gidan ɗayar maƙociyarsu da ke ɓarin hannun hagu, buga ƙofar ta yi babu jimawa Maman Sudais ta buɗe mata. Daga bakin ƙofa Maman Nana ta tsaya ta ce, "Maman Sudais kwana biyu." Maman Sudais da ba ta cika shiga shirgin maƙotan ba ta taɓe baki ta ce, "Lafiya ƙalau, daga ina haka?" "Gidan Maman Asiya na leƙa." Maman Nana ta furta, nan take Maman Sudais ta haɗe rai sannan ta ce. "Aminan juna kenan, ki gaishe ta idan kun sake haɗuwa." Maman Sudais ta faɗa cike da ƙagauta, ganin haka ya sa Maman Nana ta fita ta wuce gida. Maman Sudais ba ta da shige-shigen maƙota, idan har ta shiga gida to sai dai idan abin jaja ko murna ne ya kai ta. Ba wai dom mijinta ya hana ta ba, sai don tuntuni haka tsari da ra'ayinta yake. Koda cefane ta fita sai dai ta sayi abin da za ta saya, idan sun haɗu da maƙotan a bakin hanya sai su gaisa. Har gara idan ta ga an ɗauki kwanaki tana iya leƙawa a tsaitsaye su gaisa ta koma gida, dalilin da ya sa ba su cika ga maciji da Maimuna ba tun watarana da Maman Sudais ta kama Maimuna da ƙanwar mijinta suna gulmarta, da yake ko kaɗan dangin mahaifin Baban Sudais ba sa son ta. Yau da gobe shigar da take yi gidan Maimuna ya sa suka yi sabo har da ƙanwar mijinta, a ranar da za ta kama su bayan ƙanwar mijin tata ta fito da niyyar tafiya gida, sun yi sallama tun da jimawa sai ta faɗa gidan Maimuna. Ashe ita take ƙara hura wuta tsakanin Maman Sudais da dangin mijinta, duk wani sirrinta take kwashe take faɗa musu. Dalilin da yake da a kullin suke ƙara kafa nata ƙahon zuƙa, Maman Sudais ta fito sayen ashana ta ga Salma ta fito daga gidan Maimuna tana faɗin. "Ai wallahi daga yau yaya ya daina saya wa mahaifinta maganin hawan jinin, gara da kika faɗa mini. Ina zuwa wallahi kamar Umma ta ji labari..." Maganarta ta maƙale sakamakon ido huɗu da suka yi da Maman Sudais, murmushin takaici ta sakar mata ta ce. "Maimuna kenan, na ba ki yarda da aminci ashe cin dunduniyata kike? Idan kuwa ni ce yadda Annabi ya bar duniya na bar ki kenan." Cike da borin kunya Maimuna ta ce, "To zancenki ake yi da za ki faɗa wa mutane magana? Idan kin bar ni Baban Asiya ne ya bar ni ko me? Ai dama ba zamanki nake yi ba." A ranar haka suka rabu baram-baram dutse a hannun riga, tun daga wannan ranar idan ba abin jaje ko gaisuwa ba ne babu abin da yake haɗa su da Maimuna. Gaisuwar ma sai da Abban Sudais ya takura mata da yake ta sanar da shi komai, kuma shi mutum ne mai fahimta ya ce ta kiyaye zamanta da maƙota. Don haka take takatsantsan da gabaɗayansu, tsakaninta da su sai hirar duniya ko ta yara. Kuma tun daga lokacin ta rage ba su fuska, shi ya sa yawanci suka daina shigar mata sai Maman Nana da take leƙa mata sama-sama. Sai da Maimuna ta sayo gawayi bayan ta ɗora girki, ta sake shiga ɗaki ta ɗauko sabuwar wayarta da Jafar ya aiko mata, dama tun bayan fitar Nazir ta ciro ta haɗe da saita komai ta yi masa Salam ta whatsapp. Saboda farinciki kamar Jafad zau taka rawa haka suka ɓa ta lokaci suna musayar kalaman soyayya, domin a ranar Maimuna ba ta yi aiki gida da wuri ba. Don haka a yanzun ma da ta koma ta kira shi voice call ta whatsapp da yake ta ga yana online, yana ɗauka suka dasa daga inda suka tsaya. Daga ƙarshe ya ce ta ɗauki hotuna masu kyau ta tura masa. Wannan ne ya sanyaya mata jiki, kuma tsoro ya kamata. Har ta shiga wasu-wasin kada ta zo tsautsayi ya ratsa Maman Nana ta gani, duk da ta ji ya ce mata zai ɓoye amma haja kawai ta ji tana tsoron tura hoton. A ɓangaren ɗaya kuma ta ji kamar ba ta kyauta masa ba, domin shi ya zuba maƙudan kuɗinsa ya saya mata wayar saboda haka. Jin ta shiru ba ta tura masa ba ya sa shi kiranta a waya ya sake tunasar da ita, sai da Jafar ya yi da gaske sannan ra iya tura masa tana sake jadadda masa da ya san yadda zai yi ya adana hoton ta yadda kwaɓarsu ba za ta taɓa yin ruwa tsululu ba. Nazir irin bauɗaɗɗun mazan nan ne, kuma yana ɗaya daga cikin mazan da ba su damu da ba wa mace haƙuri ko lallaɓa ta ba idan ta yu fushi ko idan sun yi mata laifi. Idan har Maimuna ta ga ya ɗan sakar mata fuska to a ranar yana buƙatar kusantarta ne. Abin da ya fi ci wa Maimuna tuwo a ƙwarya bai wuce rashin ba ta kulawa ba, idan Nazir ya dawo gida ba shi da abokiyar hira sai wayarsa. Koda hira Maimuna ta zauna tana yi masa sai dai ya dinga ba ta amsa sama-sama, amma kaso casa'in cikin ɗari (90%) hankalinsa yana kan wayarsa. Da yake Maimuna tana da ɗan surutu ta dinga yi masa mita kenan, tana nuna ɓacin ranta. Hakan ne ya sa wani lokacin Nazir ba ya dawowa gida da wuri, sai ya gama uzurorinsa a waje. Ya kasance mutum mai takura, bin diddigi da rashin yarda. Don hatta maƙota ba ya barin Maimuna shiga, su ma kuma a ɓoye suke shigo mata bai sani ba. Duk inda Maimuna za ta je shi zai kai ta, kuma bai cika kai ta da rana ba har sai ya dawo daga kasuwa. Kuma idan ya kai ta duk taron da ake yi sai dai ya jira ta a ƙofar gida agama ya tafi da ita. Maimuna tun tana zama ta ci kuka bayan aurensu har abin ya zame mata jiki, kuma sannu a hankali Nazir ya aurensa ya sure mata har take jin Allah Ya kawo sanadin da za su rabu wala mutuwa ko sakin aure. Sakamakon halinsu da ya yi hannun riga da ita, tun da har babbar waya ya hana ta riƙewa a cewarsa duk wani abu da zai buɗe idonta ba zai lamunra ba. Tun da ai sai mace ta yi mu'amala da mutane ake ba ta munanan shawarwari, ko a zuge ta ta sauya halaye. Idan kuwa aka ɗora mace a doron da ya ɗora Maimuna, a ganinsa hakan ne zai daidaita mace ta zama kamila tun da idonta bai buɗe ba. Tarihin Maimuna Maimuna 'yar asalin garin Dutse ce da ke jigawa, mahaifi da mahaifiyarta duk 'yan can ne. Kuma su biyar ne a wurin iyayensu, yayanta Sadik shi ne babba sai ita take binsa ƙannenta mata uku suke biye da ita. Maimuna ta yi karatunta na addini daidai gwargwado, ha boko kuma ta tsaya a secondary. Domin mahaifinsu mai sauƙin ra'ayi ne, idan yarinya ta samu miji zai aurar da ita ra'ayin mijinta ne ta cigaba ko ya hana ta. Idan ba ta samu miji ba kuma ta cigaba da karatu, kuma hakan ce ta faru da Maimuna. Tun tasowar Maimuna 'yar gayu ce mai sosai, tana son ƙwalisa. Uwa-uba tana da wayewa, don ƙawayen da take hulɗa da su duk masu buɗaɗɗan ido ne. Maimuna tun tasowarta take da tsari, don ra'ayinta ne auren namiji mai kuɗi da iya soyayya. Kuɗin ma bai cika tasiri a ranta ba matuƙar namiji zai ba ta kulawa da soyayya koda mai rufin asiri ne za ta iya zama da shi. Dalilin haka ya sa ta gama tsara rayuwar da za ta gudanar a gidan aurenta, ita da mijinta. Tarihin Nazir Nazir haifaffan garin Kano ne, sai dai mahaifi da mahaifiyarsa asalinsu 'yan garin Katsina ne. Neman kuɗi ne ya kawo mahaifinsa garin Kano, a nan duk aka haife su shi da ƙannensa. Mahaifinsa yana da mata biyu da 'ya'ya takwas, ƙannensa da suke uwa ɗaya guda uku ne duka maza. Sai waɗanda suke uba ɗaya su shida kasancewar shi ne babba a wurin mahaifinsa. Nazir kasuwancin hulunan maza yake a kasuwar kwari, shagonsa babba ne kuma yana da rufin asiri bakin gwargwado. Nazir ya haɗu da Maimuna ne a wurin dinner wani abokinsa da suka yi a garin jigawa, da yake tana daga cikin manyan ƙawayen amarya. Tun da Nazir ya ganta ya maƙale mata har aka tashi daga taron, amma kafin su a watse sai da suka yi musayar lamba sannan ya kai ta har ƙofar gidansu ya sauke ta. Ko kaɗan Nazir bai kwanta a ran Maimuna ba, don tun daga yanayinsa bai yi mata kalar irin mijin da take burin zama da shi ba. Shi kansa Nazir ya fahimci haka, don ko kiran wayarta ya yi wani lokacin ba ta ɗauka. Da ya yi bincike a kanta, sai aka yi masa bayanin halinta tsaf da yanayin waɗaanda take mu'amala da su. Hakan ne ya sa Nazir ya lulluɓe kura da fatar akuya, sai da ya tabbatar da da ya siffantu da irin mijin da Maimuna take muradi sannan ya koma mata tsamo-tsamo. Tun Maimuna tana share shi har ya fara karkato da hankalinta kansa, don tuni ya saye zuciyarta ta hanyar ƙyale-ƙyale da kayan ƙawa. Ya shiga shayar da ita romon zallar soyayya tana sharɓa, har sai da ta dinga gina musu irin rayuwar da za su gudanar a gaba. Hakan ya sa Nazir ya bijirowa Maaimuna da maganar turo magabatansa, kafin ta amince da ta suka yi yarjejeniya a kan bayan sun yi aure za ta cigaba da karatu. Don tana da burin yin aiki a gaba, tashin farko Nazir ya amince mata. Hakan ya sa aka tsayar musu da lokacin aure, da lokacin ya ƙarato Nazir ya yu mata bajimta ta hanyar kama manyan kuma ƙayatattun wuraren taro na alfarma. Matsalar farko da Maimuna ta fara fuskata a ɓangaren ƙawayenta ne, domin ko wata ba su yi ba da aka tashi bikin wata ƙawarsu ya ce ba za ta je ba. Lamarin da ya kai su ga yin faɗa, saboda Samira aminiyar Maimuna ce ta yi mata ƙoƙari a sha'anin bikinta. Wannan faɗan har sai da ya kai su gaban iyaye, a nan kuma kowa ya ba wa Maimuna rashin gaskiya da cewar mijinta yana da damar da zai hana ta zuwa bikin kowacce ƙawa, kuma mahaifinta ya jadadda mata idan har ta kashe aurenta ba tare da wani dalili ba sai dai ta nemi wani wurin ba gidansa ba. Wannan ikon da Nazir ya samu ya sa kai tsaye ya yanke alaƙar Maimuna da ƙawayenta, tun suna yin kara suna zuwa wurinta har kowa ya janye jikinsa saboda ba zuwa wurinsu take yi ba. Hatta garinsu sai ta shafe lokaci mai tsayi.ba ta je ba, idan sun tashi tafiya kuma shi zai kai ta ya zauna a ƙofar gida idan yamma ta yi ya ɗauko ta su dawo gida. Sannu a hankali Nazir ya dinga bijirowa Maimuna da ɓoyayyun halayensa, tun daga wani faɗa da suka yi ya karɓe babbar wayarta ya ba ta ƙarama. Sannan makarantar da suka yi yarjejeniya ya ce ba za ta cigaba da karatu ba, da ta kai ƙararsa gida kuma sai iyayenta suka nuna mata tun da aure gaba yake da komai gara ta zauna ta yi ibadar zaman aure. Da zaman aurensu ya yi zama ne Maimuna ta fahimci kuɗin da yake mata facaka da su ba su kai haka ba, don a farko kallon mai kuɗi take yi masa sai daga baya ta gane duk munfurtarta y yi. Tun daga wannan lokacin Nazir ya sire wa Maimuna, tana dai zaune da shi ne saboda biyayyar mahaifinta. Da zaman haka ya ishe ta sai ta nuna wa Nazir tana buƙatar yin kasuwanci, amma fir ya ƙi ba ta dama. Wata irin ƙaunar Fauziya ce ta lulluɓe Kabir, yana daga tsaye ya zauna a gefenta ya haɗe ta ita da jaririyar ya rungume su cike da so da ƙauna. Ƙwace kanta Fauziya ta shiga yi, ya riƙe ta tsam sai suka saki ajiyar zuciya kusan lokaci ɗaya. "Don Allah ki bar ni na ji ɗuminku!" Kabir ya furta cikin shauƙi, fa sauri Fauziya ta fisge zuciya tana ɗaci ta ce. "Ni a wa da za ka ji ɗumina? Ka bari ka je wurin Hafsa ai tana da abubuwan da ba ni da su." Kabur sam bai ji daɗi ba, ya marairaice murya ya ce. "Duk fa wasu kalamai da kika ji ina na fatar baki ne, babu abin da ya taɓa haɗa ni da ita. Ni ko gidansu ma ban sani ba." Fauziya ba ta tanka masa ba, ta taɓe baki tana bin sa da harara. Tun daga wannan ranar Kabir ya shiga nannan da Fauziya, ita kuma har lokacin ba ta ba shi fuska. Ya yi mata ɗinki kala uku masu kyau, sai jaririya da saya mata rigunan kanti kala uku. Su Na'ima kuma suja tashi da atamfa ɗaiɗai, ba ta yi wani taro ba. Tsirarun mutanen da ba a rasa ba, ta yi kyau sosai kamar ka sace. Kabir da ya shiga gidan ya ganta sai ya shiga rawar ƙafa, ganin kada mutane su fahimci ba sa shiri ya sa ta saki jiki 'yan uwa suka shiga ɗaukarsu hoto. A wannan lokacin Kabir bai samu damar yanka wa jaririya hakika ba, sai haƙuri da ya ba wa Fauziya da yake ta san yanayin samunsa ya sa ba ta damu ba. Sannu a hankali Kabir yake ta shawo kan Fauziya har ta saki jiki da shi suka dawo kamar da, amma kafin nan sai da ta tasa shi a gabanta ya kira Hafsa ya ci mata mutumci don a ganinta duk budurwar da za ta tura wa namiji tsiraicinta ba matar aure ba ce. Saboda kafin ta sa ya kira shi sai da ta tambaye shi idan auren Hafsat zai yi ya ce a'a, don haka ta hura masa wutar sai sun rabu idab ba haka va ta bar masa gidan ya zauna da ita. Wannan shi nw dalilin rabuwar Kabir da Hafsa, saboda duk rashin zuciyar mace sai ta ji haushin irin wulaƙancin da ya yi mata. Don Kabir yadda ya dinga cin zarafinta nuna wa ya yi kamar dama can Hafsan ce ta maƙale masa, a yadda ta fahimta ma nuna wa yake ba su da dpguwar alaƙa ita da shi. Ranar da Kabir ya je ƙofar gidansu ba ƙaramin cin mutumci ta yi masa ba, duk yadda ya kai ga son lallashinta ko kaɗan bai shige ta ba. Saboda a ganinta Kabir ba mijin aure ba ne tun da bai isa da matarsa ba, domin ya bayyana a fili ba zai iya adalci ba. Ranar Juma'ar da suka wayi gari ita ta yi daidai da saura kwana biyu rak su tashi, don tun ranar Laraba Lawisa ta tashi suka kama haya a unguwar rimin kebe. Ranar Juma'ar kuma ita ma A'ilo ta tashi, sai su Maman Sabir da suka haɗa kayansu su ma washegari Asabar za su tashi. "Abban Na'ima ban gane maka ba, har yanzu fa ba ka ce mini komai game tashinmu ba. Ka san halin mutumin nan ba sho da mutumci, mutanen gidan nan duk sun fara tashi. Saboda gudun tozarci fa na sayar da firjinmu domin mu samu mu ƙarasa abin da ba a rasa ba." Fauziya ta yi maganar zuciya babu daɗi tana ƙoƙarim danne ɓacin ranta. Saboda tun da kwanakin tashinsu ya ƙarato, ta ga wata alama daga wurin Kabir. Kuma idan ta yi masa naganar ko dai ya bagarar, ko kuma ya fara faɗan ta cika gajen haƙuri. Haɗe rai Kabir ya yi ya miƙe yana shirin fita ya ce, "Eh haka ne, amma duk tsiya ai ba za mu rasa wurin zama ba." Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai dama ba ina nufin za mu rasa wurin zama bane ina maganar ginin can ne. Ko a rana ɗaya za mu kwashe? Amma ko rana ɗaya za mu kwashe sai dai ko zuwa gobe, tun da jibi na tabbata sai ya zo da masu fitar da kaya." "Wai me ya sa kin fiye mita da takura ne Fauziya? Mtsww Allah Ya sawaƙe da wannan halin naki, ai ki kammala haɗa kaya gobe za mu koma gidan Inna kafin na ƙarasa." Kabir yana gama magana ya fice daga gidan. A yi haƙuri da errors kwana biyu kuma ban zauna ba ne, shi ya sa ban yi typing ba. Ummou Aslam Bint Adam🌚 +2347062062624 [18/02, 18:45] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA GOMA UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731 *** Kamar wacce ta ci karo da sabuwar hallita haka ta bi bayan Kabir da kallo, nan take ta cigaba da nanata kalaman da ya faɗa mata kamar mai yin hadda. Ba ta yi aune ba ta ji murfin idonta ya buɗe, hawaye ya shiga kwarara kamar idaniyar ruwa mai gudana. Duk yadda ta yi hoɓɓasar dakatar da shi sai abin ya gagara, maƙogaronta ya shiga ɗaci tana jin wani abu ya tokare mata ƙirji. Nan take ta ji ƙirjinta ya hau ciwo, don tun daga mummunan ganin da ta yi a wayar Kabir da ranta ya ɓaci sai da ta ji wani abu ya tokare mata ƙirji, sai bayan wani lokaci kuma ta ji ya lafa mata. Don bala'in da yake cikin zaman gidan Inna ba abu ne mai sauƙi ba, duba da irin abubuwan da take gani tana yi wa Sadiya. Da kuma wanda ita kanta Sadiyan take faɗa mata, wani tunani ne ya faɗo mata don haka ta yi saurin janyo wayarta ta latsa layin Kabir. Sai fa ta kusa katse wa ya ɗauka yana faɗin. "Ina hanya." Tana jin yana shirin kashewa ta ce, "Magana nake son mu yi Abban Na'ima." Kamar ba zai amsa mata ba, sai kuma a daƙile ya ce. "Ina jin ki." Gaban Fauziya ya shiga faɗuwa, tana fargabar irin fassarar da zai yi wa kalamanta. Jin shiru ya sa Kabir ya ce, "Kin san ba ki da abin faɗa kika kira ni?" Maganar da ya yi ba ƙaramin bugun zuciya ta saka ta ba, ta yi ƙarfin halin faɗin. "Abban Na'ima don Allah ka kama mini haya!" "Saboda me?" Ya wurga mata tambaya a gaggauce. "Haka kawai, ina ganin kamar za mu fi sakewa. Na ga gidan Inna kamar babu ɗaki, ga kuma yara." Guntun tsaki ya yi ya ce, "Duk ɗakunan gidan Innar ne za ki ce babu? Ko dai zama da mahaifiyar tawa ne ba kya so?" Kamar Fauziya za ta yi kuka ta ce, "A'a na ga ɗakin da ya rage ba kowa shirgi suke ajiyewa." Ajiyar zuciya Kabir ya sauke ya ce, "Na sa yara sun gyara ɗazu, idan Allah Ya kai mu da sassafe akwai mai motar da na yi wa magana zai zo ɗaukar kaya." Murya tana rawa ta ce, "Ko na kira dillaliya ta sayi keken ɗinkin nan nawa? Idan ya so kafin jibi sai mu nemi ɗaki." A hassale Kabir ya ce, "Wai me kike nufi Fauziya? Mahaifiyar tawa ce ba kya ƙaunar zama da ita? Ko kin manta ita ta ɗauki cikina wata tara ta haife? Saboda raini har ni kike cewa za ki kamawa haya, a kan ki zauna da mahaifiyata?" Nan take ta rikice, don ta san dama ba lalle ya fahimci irin abin da take gudu ba. Tuni hawaye ya wanke fuskarta, tana shirin magana ta ji Kabir ya katse a fusace. Kuka Fauziya take yi wanda take jin ɗacinsa yana fitowa daga ƙasan maƙoshinta, tsakar gidansu ta ƙura wa ido tana hangen ɗakin Lawisa. Tana ji a ranta yadda zuciyarta take zafi, da ace Lawisa tana nan ita ce mutum ta farko da za ta fara faɗawa halin da take ciki ko ta ji sanyi. Duk da wannan ba ɗabi'arta ba ce, amma tana jin idan ba ta sanar da wani ba zuciyarta za ta iya bugawa. Tashi ta yi ta fara kai wa da kawowa domin neman mafita, amma gabaɗaya kanta ya cushe. Tunanin tafiya gidan mahaifinta ta yi, a nan ma ta ga sam ba mafita ba ce domin mahaifinta ba zai taɓa goya mata baya ba. Da wannan tunanin Fauziya ta wuni har sai da zazzaɓi ya rufe ta, haka daren ranar ya zo mata cikin ƙunci. Da Kabir ya dawo ta ga yana fushi ba ta tanka masa ba, da ta miƙa masa abinci kuma ya ce ba ya ci. Ita ma da yake a cike take da haushinsa, ba ta sake bi ta kansa ba ta kwanta. A daren ranar kwana ta yi tana miyagun mafarkai a kan zamanta da Inna har gari ya waye. Tun da farar safiya mai motar da Kabir ya yi wa magana suka yi sallama, ya fara fitar musu da kaya. Fauziya tana haɗa kaya tana hawaye, Na'ima da Fatima tun da suka ji mahaifiyarsu ta ce gidan Inna za su koma duka walwalarsu ta dusashe, amma da yake Hidaya ba ta san dawan garin ba haka ta dinga tsalle tana murna. Sai da aka gama kwashe kayan tsaf sannan ta leƙa ta yi wa Maman Sabir sallama, da neman yafiyar juna. Tun da suka doshi layin ƙirjinta yake bugawa, tana fargaba irin zaman da za su gudanar a cikin gidan. Tsayuwarsu a ƙofar gidan, ya yi daidai da tsala ihun da Salim yake yi. Jiki a sanyaye Fauziya ta tsoma ƙafarta cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama. Inna ta hango a zaune ta maƙure Salim a ƙasan ƙafafuwanta tana tsala masa dorina yana sakin ihu, sai da ta gaji don kanta sannan ta ce. "Don ƙaniyarka gobe ma ka sake zubar mini da kuɗin tsintsiya, wallahi dukan da zan yi maka sai ya ninka wannan." Sai a lokacin ta ɗago ta dubi Fauziya ta ce, "Baƙin safe ashe kun ƙaraso, ga ɗaki can sai ku fara jera kaya." A ɗarare Fauziya ta gaishe ta, su Na'ima da dukan Salim ya tsorata su ya sa duka suka riƙe zanin mahaifiyarsu a tsorace suna leƙen Inna. "Ku kuma leƙen me kuke yi mini kamar ba ku sanni ba? Ku dama uwarku ba ta koya muku gaida mutane ba ko? Kai shi ya sa 'ya'yan Mudam suke birge ni, uwar su Zaliha akwai tarbiyyar. Ai kuwa ga yaranta nan gwanin birgewa, duka tarbiyyarta suka gado." Ita dai Fauziya ba ta kula ta ba, ta wuce ɗakin da aka nuna mata. A bakin ƙofa ta tsaya tana ƙarewa ɗakin kallo, ɗan ƙanƙani ne ko gadonta ta haɗa ba zai zauna a ciki ba. Ballantana a kai ga saka keken ɗinki, kwanuka, manyan robobi da akwatunan kayan yara. Sadiya ce ta ƙarasa wurin fuskarta cike da jimami ta ce, "Fauziya kun ƙaraso?" A madadin Fauziya ta amsa mata sai kawai ta fara zubar da ƙwalla, a tsorace Sadiya take waigen wurin Inna tana girgiza mata kai. Ita ma girgiza kan ta fara yi cike da tausayin kanta da 'ya'yanta. Da ƙyar ta ja ƙafa ta faɗa cikin ɗakin. Sadiya ce ta rufa mata baya ta yi ƙasa da murya ta ce, "Fauziya ba ta son tun daga zuwanki Inna ta fahimci ba kya son zaman gidan nan. Don Allah ki yi haƙuri ki mayar da komai ba komai ba, ni ban ma san yadda aka yi kuka gagara tarewa a gidanku ba. Allah na tuba indai aka yi rufi ko a ya yake ai gidanka ne, sannu a hankali sai a ƙarasa." Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce. "Sadiya!" Ɗagowa Sadiya ta yi jin yadda Fauziya ta kira sunanta, Fauziya ta share hawaye mai ɗaci ta cigaba da cewa. "Kabir ɗin da na sani a baya kamar ba shi ba ne yanzu ba, Kabir ya sauya mini Sadiya. Ina tsoron kada wani abu ya biyo bayan tariyarmu, domin a yanzu ban cika gane gabansa da bayansa ba." A fili Sadiya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Tabɗijam! Lallai da alama tura ta kai bango Fauziya, tun da har yau ke kika fito kika faɗi aibun Kabir, tabbas an kusa zuwa daidai gaɓar da nake son a zo." Sadiya ta kamo hannun Fauziya ta ce, "Shi ya sa ba tun yau ba, nake nuna miki ba a ɗaukar yarda ɗari bisa ɗari a damƙa wa ɗa namiji. Ki zauna da shi saffa-saffa, ta yadda idan ya yi watsin iska da ke abin ba zai ɗaɗa ki da ƙasa ba. A duk lokacin da na ga kin nuna wauta, sau tari ina son na ankarar da ke amma ina gudun ki ga kamar ina son haɗa ki da mijinki. Ko kuma ki ga ina kushe shi, don haka na kawo na mujiya na zuba miki." Fauziya ta share ƙwallar idonta ta ce, "Haka ne Sadiya, amma don Allah kada ki ga laifina. Idan kika cire mahaifina Kabir shi ne mutum na farko da na shaƙu da shi, na kuma damƙa wa ragamar rayuwata." Sadiya za ta yi magana daga can waje suka ji Inna ta ce, "Ke Sadiya me kike yi a ɗakin Fauziya tun ɗazu ne? Ko munafurcina za ki kai mata, ga tuwo can kin bar shi yana kamawa sai ki je ki kwashe mana." Jiki yana rawa Sadiya ta amsa mata, sannan ta kalli Fauziya ta ce, "Sai na sake shigowa bari na je kada na ja miki karantsana a wurinta." Daga haka ta fice. Shiru Fauziya ta yi tana ayyana ita ma kenan irin wannan rayuwar za ta fara. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fara jan kayan tana lodewa a gefe, sai ta ɗauko katifata ta shifiɗa. Ragowar wurin da ya rage bai fi kwanciyar babba mutum ɗaya ba, keken ɗinkinta, mangal ɗin girki da abin zuba ruwanta ba su samu wuri ba sai a ƙofar ɗaki ta ajiye su. Sannan ta ɗora musu abinci, bayan ta gama ta zuba wa yaranta sannan ta zuba kaɗan a roba. Ita kuma Inna ta saka mata a plate ta rufe, Sadiya ta miƙa wa na robar sai kuma ta ba wa Inna nata. A yatsine Inna ta dubi farantin har Fauziya za ta miƙe Inna ta ce, "Au ashe fa ke ba ki san tsarin gidan nan ba ko?" Fauziya ta gyaɗa kai. Inna ta saki murfin ya faɗi ƙasa a wulaƙance ta ce, "Abincin rana a gidan nan haɗa shi ake a yi girka gabaɗaya, girkin safe da na dare ne kowa yake yin nasa. Sannan daga yau kada ki sake zuba mini abinci a ciki shatalallan faranti, saboda mu a lokacinmu kwanon uwar miji daban ake yi mata don haka ki kiyaye wannan ma ai wulaƙanci ne." A sanyaye Fauziya ta amsa mata, ta koma ɗakinta. Tana shiga ta ga Zainabu, 'yar wurin Sadiya ta cika hannu da ƙatuwar lomar abincin su Na'ima ta tura a baki, tana ganin Fauziya ta sake kwasar ƙatuwar loma ta fita a guje tana dariya. Hidaya da Fatima suka saka kuka suna faɗin, "Ta cinye mana abinci, Mami tun ɗazu take kwashe mana abinci." Shiru Fauziya ta yi sai ta ji duk zuciyarta babu daɗi, buɗe tukunya ta yi ta ɗebo daga cikin wacca ta rage za ta ci ta zuba musu. Ta zauna gefen katifa ta janyo tukunyar ta fara ci a ciki, tana nan zaune ta ga Zainbu da ƙaninta Faisal ɗan shekara ɗaya da rabi suka dinga leƙensu sai su tafi da gudu. Tun daga wannan ranar, zaman Maman Nana da Jafar ya koma irin zaman doya da manja. Sakamakon rashin kyakkayawar alaƙar da take shiga tsakaninsu. Kuma har kullum zaman nasu ƙara tsamari yake, don Jafar ya jima da ƙaurace mata. Idan dare ya yi sai dai ya ɗauki filo ya tafi falo ya kwanta, gari yana wayewa kuma ko breakfast ba ya yi yake fita. Idan ta ce abu ya ƙare sai dai ya ba ta kuɗi ta sayo kaɗan, saɓanin a baya da komai idan ya tashi dire mata yake yi mai yawa. Wani abu da Jafar ya tsiro mata da shi sai suna zaune ya ɗauki waya ya yi ta latsawa yana sakin murmushi, ita kuma da ta yi magana kamar jira yake sai ya rufe ta da faɗa. Watarana tana suna zaune da safe, da yake ranar ba ta ga alamar zai fita da wuri ba. Waya ta ga ya latsa yana kai wa kunnensa, tsam ya tashi ya wuce uwar ɗaki sai ta ji ya kashe murya yana faɗin. "Barka da hutawa My Moon." Ƙirjin Maman Nana ya buga da ƙarfi, don a yanayin maganar da ta ga yanayi ta fahimci da mace yake waya. Ta jinjina kai tana sauke ajiyar zuciya ta ce. "Wato duk wannan cin kashin da yake yi mini saboda mace ya yi mini fana? Ai kuwa ba zan lamunci ya dinga yi mini waya a ɗaki ba." Tuni zuciya ta ɗebe ta, ita ma ta faɗa cikin ɗakin a daidai lokacin ta ji ya ce. "Wallahi tallahi Moon babu wata 'ya mace nake jin kewa da muradinta a yanzu, ganin hotunanki kaɗai suna iya hargitsa ni har na gagara gane kaina." Tsaye Maman Nana ta yi hawaye ya gama wanke idonta, baki yana rawa ta ce. "Abban... Nana... ashe a kan wata 'yar iskar kake wulaƙanta ni?" Ɗago kansa ya yi ya kalle ta, ga mamakinta sai ta ga ya ɗauke kansa gefe ya cigaba da cewa. "Na rasa abin da zan yi miki don ki yarda da abin da nake faɗa, kin san Allah ke ta daban ce a cikin mata..." Shiru Maman Nana ta yi tana ƙura masa ido cike da hawaye, har gani take kamar ba Jafar ɗinta ba. Domin a baya Jafar ba ƙaramin shakkarta yake yi ba, amma a yau wai shi yake yabon wata a gabanta. A haukace ta fisge wayar ta yi wurgi da ita, cikin matsanancin kishi haɗe da ƙaraji ta ce. "Jafar ni za ka mayar mahaukaciya? Da wacce 'yar iskar kake waya a ɗakina..." Maganarta ce ta katse sakamakon wani gigitaccan mari da ya sakar mata, idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai. Ya dube ta a hargitse ya ce, "Kada ki sake ce mata 'yar iska, idan kuma ba haka ba wallahi sai na ɗauki mummunan mataki a kanki." Wani irin sanyi jikin Maman Nana ya yi, sai kuma tsoro ya kama ta. Har take ganin kamar Jafar ba a hayyacinsa yake ba, ta sake matsawa gabansa ta riƙo rigarsa tana jijjiga shi, a ganinta ko hakan zai sa ya dawo hayyacinsa. Hawaye yana zuba ta ce, "Kana cikin hayyacinka kuwa Jafar? Ni kake mari saboda na cewa wata 'yar iska?" Kamar yana jira ya yi saurin faɗin, "Na mare ki Sumayya, wallahi idan kika kuma faɗar mummunar kalma a kanta sai na yi miki abin da ya fi haka." Maman Nana ta ji kamar ya watsa mata ruwan zafi, zuciya a ƙeƙashe ta ce. "Na faɗa 'yar iska karuwa don Allah ka kashe ni a wurin nan." Kamar wancan karon haka ya sake tsinke ta da mari, sai dai a wannan karon tagwayen mari Maman Nana ta samu. Wayarsa ya ɗauka, da yake dama ya yi wanka sai kawai ya shiga ɗaki ya saka kayansa ya fice daga gidan. A wurin Maman Nana ta durƙushe tana kuka kamar ranta zai fita, sai da ta yi mai isarta sannan ta sauya kaya. Ta ɗauki Abdul da yake bacci ta goya shi ta fito daga gidan, duk wanda ya ganta kallo ɗaya zai yi mata ya fahimci ba ta cikin nutsuwarta. Gidan Maimuna ta shiga ta same ta zaune a falo, Maimuna tana jin shigarta ta saki murmushin ƙeta saboda duk abin da suka yi a kan kunnenta, tunda wayar ba mutuwa ta yi ba a lokacin da ta yi wurgi da wayar Jafar. Amma a fili tana ganin Maman Nana ta dafe ƙirji ta ce, "Lafiya kuwa Maman Nana? Me ya samu fuskarki ta kumbure haka?" Da yake har lokacin da ɗacin abin a ranta, sai Maman Nana ta rushe da kuka mai cin zuciya. 'Na rantse da Allah kuka ma yanzu kika fara, mu je zuwa wai mahaukaci ya hau kura." Maimuna ta faɗa a ranta, amma a fili cikin ruɗewa ta ce. "Maman Nana ki yi magana don Allah, kin ɗaga mini hankali. Daga gida ne aka kira ki wani abu ya faru, ko Abban Nana ne?" Maman Nana ta girgiza kai, Sai Maimuna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "To mene ne? Don Allah ki yi mini magana, wannan kukan da gani dai ba na lafiya ba ne." "Wai yau ni Jafar ya mara saboda wata maman Asiya, Jafar ya zama wani iri wallahi asiri aka yi masa, don Jafar ɗina ba ya cikin hayyacinsa." Maman Nana ta yi maganar cikin kuka. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Kada ki ce mini tun yarinyar da muka yi magana da ke kwanaki? Ai kin ga sakacinki Maman Nana, tun wancan karon na ce ki ɗauki mataki amma kika tsaya sanya. Yanzu ai ga shi kina gani ƙarfi da yaji yarinya ƙarama ta shanye shi." Cikin ƙaguwa da neman mafita ta ce, "Yanzu mene ne abin yi Maman Asiya?" Shiru Maimuna ta yi kamar mai yin nazari, sai ta ɗago da sauri ta ce. "Gidanku sun san abin da ya faru?" Girgiza kai Maman Nana ta yi, sai Maimuna ta ce. "Yanzu abin da za ki yi kai tsaye ki wuce gida, ki sanar da iyayenki a san halin da ake ciki. Saboda wallahi matuƙar ba a ɗauki mataki ba abin ƙara gaba zai yi, kin san aka ce idan namiji ya ji daɗin dukanka ya samu wuri kenan. Kar ma ki faɗa masa za ki tafi, ki bari sai dai ya dawo kawai ya ga ba kya nan. Idan aka yi muku sulhu daga baya sai ku daidaita ki dawo, amma ina mai tabbatar miki da sai kin tashi tsaye." Shawarar Maimuna ba ƙaramin kwanciya ta yi a zuciyar Maman Nana ba, haka ta dinga ba ta shawarwari daga ƙarshe suka yi sallama ta fita. Da yake makarantar su Nana a bakin titi take, sai ta da ɗebi kayansu sannan ta wuce ta makarantar ta ɗauke su suka wuce gidansu da ke unguwa uku. Tun bayan da Maman Nana ta yi wa Maimuna sallama da ta ji fitarta daga gida, ta kira Jafar ta kwashe ƙarya da makirci ta faɗa masa. Don har cewa ta yi Maman Nana tana ta zaginsa kuma ta ce ta tafi gidansu kenan, domin ta gama zaman aure da shi. Maganar da ta fi tsaye masa a rai da Maimuna ta ce wai Maman Nana tana kuka tana cewa, ta yi dana sanin haɗa zuri'a da shi, domin shi ba miji kuma uba nagari ba ne. Da irin waɗannan miyagun huɗubar, Maimuna ta samu yin galaba a kan Jafar. Har shi ma ya hau dokin zuciya da cewar ba zai taɓa nemanta ba, kuma ba zai je biko ba tun da ba shi ya ce ta tafi ba. Ya kuma ci alwashin ko a ranar ta nemi takardar saki, a shirye yake da ya miƙa mata kayarta. A ranar tun yamma ya dawo gida saboda ya san Maman Nana ba ta nan, kuma har cikin zuciyarsa da zai samu yadda yake so kuma da babu 'yan gulma tsaf zai ce Maimuna ta zagayo su sha soyayya. Amma da yake ya san akwai matan maƙota da suke kai kawo, sai ya haƙura da buƙatarsa. Ya shiga ɗaki ya rage kayan jikinsa sannan ya jira Maimuna a waya, ya ce ta kunna data za su yi magana. Ita ma da yake ta gama girki ta kuma sheƙa wankan ƙananan kaya, sai wayar ta shi ta zo mata a daidai. Ta whatsapp ya kira ta video call, ta ɗauka a kunyace tana sunne kai ƙasa. "Wai wai wai, wannan wankan duk ni aka yi wa? A gaskiya baby za ki hargitsa ni." Sai kuma Jafar ya shagwaɓe murya ya ce, "Don Allah idan babu damuwa ki zagayo mana Moon. Wallahi babu wanda zai gane, domin a cike nake da ƙishirwarki."Maimuna ta yi shiru tana nazari, domin ita kanta wannan lokacin ta jima tana buri da fata. Tun da dare ya yi bayan ta kwantar da yaran ta yi shiru tana ƙare musu kallo, Na'ima da Fatima ne ta yi musu shimfiɗa daga ƙasan katifa. Hidaya da Humaira kuma ta yi musu shimfiɗa a kan katifa, tana nan zaune Kabir ya shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa ta yi ta mayar da kanta gefe, saboda haka kawai haushin Kabir take ji. Shi kansa shiru ya yi ganin yanayin kwanciyar da suka yi, sai kuma jikinsa ya yi sanyi tausayinsu ya kama shi. Kayan abincinsa ta ajiye a gabansa, ba tare da ta ce masa uffan ba. Shi kansa ya fahimci fushi take da shi, sai ya ɗan saki fuska ya ce. "Haba Fauzina yanzu wannan fuskar da kika haɗe duk saboda za ki zauna da mahaifiyata ne, zaman nan fa ba na dindindin ba ne. Don Allah ki daina ɓata ranki ba na so." Fauziya da dama ciki take da shi ta ce. "Ni ba ina fushi da zaman da zan yi tare da mahaifiyarka ba ne Abban Na'ima, domin Inna tamkar mahaifiyata haka na ɗauke ta. Kawai yanayin zaman ne bai yi mini ba, dubi a inda yaran nan suka kwanta. A gaskiya sam babu tsari wallahi, don girman Allah ka bari mu koma gidannmu idan ya so ko a hankali sai ka ƙarasa." Kabir ya ɗan yi jim ya ce, "Ummu banat kin san dai muna da maƙiya, waɗanda suke son ganin cigabanmu, wallahi ba na son na koma a ga gidana ko fulasta babu. Kin san idan aka ce shago ba naka ba ne sai haƙuri, Oga ba wata kyakkaywar sallama yake mana ba. Kin ga Allah Ya taimaki Sani da yake shi kekensa ya kai shagon, shi yake cin gashin kansa. Sai dai ɗan kuɗin da yake bayarwa duk shekara, wanda Oga yake cikawa ya biya kuɗin shago. Ni ma kin ga da ina da keken kaina rufin asirin da zan samu sai ya fi haka." Shiru Fauziya ta yi, ta kallo keken ɗinkinta da ke waje. Ta tuna ba wani ɗinki take samu ba, mafi yawa sai ɗan gyare-gyare da mata suke kawo mata. A yadda take jinta kamar kwance cikin ƙaya, babban burinta bai wuce ta ga sun tashi daga wannan gidan ba. Don haka ba ta yi dogon tunani da nazari ba ta ce. "Indai hakan zai sa ka yi ka ƙarasa mana, ga kekena nan ka ɗauka Abban Nana. Babban fatana Ubangiji ya rufa mana asiri." Tana gama magana Kabir ya rungumo ta jikinsa, sai ya shiga sakar mata kiss a duk ilahirin jikinta. Cikin wata irin murya ya ce, "I love you my Fauzee." Fauziya ta saki murmushi ta ce, "I love you too Abi." Gani ta yi Kabir yana yunƙurin wuce gona da iri, don haka ta janye shi daga jikinta ta ce, "Ga abincinka fa." Kafaɗa ya maƙale mata yana bin ta da wani irin kallo ya ce. "Idan da ke abinci da komai ba ne." Tana shirin sake yin magana Kabir ya janyo ta jikinsa, ya shiga yawo da hannuwansa a cikin jikinta. "Wallahi kunya nake ji, magana ta Allah ba zan iya wani abu a cikin ɗakin nan ba. Don gani nake kamar Inna tana jin duk abin da muke yi, tun da kaga ɗakinmu a jikin ɗakinta yake. Kuma ka dubi kusancin kwaniya da muka yi da yaran nan." Kabir ya zame hannun rigarta ƙasa, ya ɗora kanta a saman cinyarsa cikin wata irin murya ya ce. "Babu abin da za ta ji, don haka kada ma ki..." "Kabiru! Kai Kabiru ashe kana ciki?" Maganar Inna da bakaɗa labulen ɗakin da ta yi ne ya sa maganar da Kabir yake yi ta maƙale, cikin tsananin jin kunya Fauziya ta tashi tana jan rigarta sama. Inna ta saki baki haɗe da riƙe baki ta ce. "Dole na ji ku shiru a ɗaki mana, ku dai wallahi an yi jarababbun yara. Don masifa tun a farkon dare? Ko tara fa ba ta yi ba, shi ne za ki saka yaro a ɗaki ki ƙadandane kamar alkaki." Shi kansa kunya Kabir ya ji, ya ɗan sosa kai ya ce. "Amma Inna ai da kin yi sallama kafin ki shigo." "Ba zan yi ba, na ce ba zan yi shashashan banza da wofi. Ina ganin jarabar su Sadiya da duk asuba za ka ji su suna karafniya da ruwa kamar kifaye, ashe nasu shafar mai ne tun da ga ku; ku tun garin bai nausa ba. To idan ka gama shinshine-shinshinen sai ka zo ka same ni a ɗaki." Inna ta ƙarasa maganar tana sakin tsaki sannan ta wuce ɗakinta. Bayin Allah na kusa kammala free pages, masu son littafin za su biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [19/02, 17:43] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA SHA ƊAYA GIDAN INNA Wani irin ɓacin rai ne ya lulluɓe zuciyar Fauziya, rai a ɓace ta miƙe tsaye tana ɓalle maɓallin rigarta. Shi kansa Kabir bai ji daɗi ba, cikin tausasa harshe ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri Fauziya." Fuska babu walwala ta ce, "Babu damuwa." Ya ɗan leƙa fuskarta ya ga har lokacin babu alamar fara'a, duk sai ya ji babu baɗi. "Kin san iyaye wani abin sai ana haƙuri da su." Ya furta a sanyaye. "To ni me na ce Kabir? Ka je idan ka gama sai ka ci abincin." Fauziya ta furta bayan ta zura doguwar rigar bacci, can gefen katifa ta koma ta kwanta. Kamar Kabir zai yi mata magaba sai kuma ya fasa ya nufi ɗakin Inna. A bakin gado ya samu Inna da alama ta gama cika, ya zauna a ƙasa ya ce. "Gani Inna." "Kai ma ashe sakarai ne Kabiru ban sani ba? Don Allah kai ba ka ji kunyar kanka ba, a ce tun farkon dare ka naniƙe 'yar mutane a ɗaki? Kai Allah dai ya sawaƙe da wannan jaraba ta 'yan zamani." Shiru Kabir ya yi, sai ya ji kunya duk ta kama shi. Inna ta taɓe baki ta ce, "To dama kuɗinka na wurina nake son na ranta, idan ba amfani za ka yi da su ba. Na ji an ce barkono ya sauko a ƙauye zan saro na dinga ƙulla wa yaran nan." Da sauri Kabir ya ɗago ya ce, "A'a Inna, dama na ce ki adana mini su ne saboda ban samu ciko ba. Amma zaman da muka yi da Fauziya, yanzu ta ba ni keken ɗinkinta, idan na sayar da shi sai na haɗa kuɗin suka cike dubu ɗari. Idan ya so sai a tura su Yaya su kai kuɗin, don Allah Inna kada ki taɓa ko sisi, wallahi yayan yarinyar nan ne ya ba ni sati biyu. Idan ban tura ba zai iya aura mata wani." Inna ta wara hannu ta ce, "Ai ka ga matar rufin asiri, wallahi da Sadiya ce sisi ba za ta ba shi ba. To idan an kai kuɗin auren wai a ina za ka saka ta, ban da abin ka ai da bari ka yi ka kammala gidanka tukunna. Ka ga lokacin hidima ta yi maka sauki, don ma kai Allah Ya haɗa ƙashin arzikinka da na matarka" Tagumi Kabir ya zuba da hannuwa biyu ya ce, "Wallahi ni ma haka na so Inna, to yayanta ya matsa ne. Haka ta kira ni tana kuka wai zai aura mata wani ɗan uwansu idan ba ta fitar da miji ba." A gwasale Inna ta ce, "To dama mene ne ribar yawan zancen idan ba aure za a yi ba? Ai gara a yi wacce za a yi a wuce wurin." Kabir ya tashi daga wurin da yake zaune, ya hau kan gado gefen Inna ya riƙo hannunta, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce. "Amma wata alfarma nake nema a wurinki Inna, don girman Allah ki cewa su Yaya kada su faɗa wa matansu. Don ina gudun kada Fauziya ta ji labari, da so samu ne ma har sai bikin ya matso tukunna." "Idan ta ji uwarka ce da za ta hana ka aure? Ko kuma ƙanwar uwarka ce ita?" Kabir ya miƙe tsaye cikin tsoron kada Fauziya ta ji ya ce, "Don Allah Inna ki yi shiru kada ta ji, kin san fa yadda aka yi wurin sayen filin gidan can da kuma ginin. Wallahi idan ta sani tana iya cewa Surayya ba za ta zauna a gidan ba, tun da haɗa su nake son yi.." "Mtsswww." Inna ta ja dogon tsaki ta cigaba da cewa, "Amma dai wallahi an yi lusarin namiji, shashasha da bai san ciwon kansa ba. Saboda ta sayar da firjinta ta ba ka ka sayi ƙofofi, sai ta hana ka yin aure? Wai me ya sa kake son zama sakarai hotiho ne Kabiru? Kai ne fa miji ba ita ba, wai dama haka ka lalace a wurin yarinyar nan ban sani ba?" Kabir ya saka hannu yana kare bakinsa alamar Inna ta yi shiru, ya sake kwantar da murya ya ce. "Ba fa kuɗin firji nake nufi ba, wannan ai na ƙarshe-ƙarshe ne da ta ba ni. Kin manta na ce miki kuɗin gadon wurin mahaifiyarta ne, ta ba ni muka haɗa da kuɗin wurina muka sayi filin, to a ginin ma akwai kuɗaɗen da ta ara mini sai daga baya ne ta ba ni na firji." Jin kalaman Kabir ya sa Inna ta taɓe baki ta ce, "To sai me? Kai dai an riga da an shanye ka wallahi." Kabir da ya lura Inna ta ɗauki zafi kuma tana iya tsula wa kwaɓarsa ruwa, sai ya shiga rarrashinta. Sannan ya nuna mata da ta gargaɗi 'yan'uwansa a kan maganar auren, har ya samu ya shawo kanta. A lokacin da ya koma ɗaki Fauziya tuni ta yi bacci saboda gajiyar aikin da ta sha, cikin sanɗa ya sake jan ƙafa ya fice daga ɗakin sai ya nufi hanyar fita. A bayan layinsu ya tsaya ya zaro wayarsa ya latsa lambar Surayya, bugu ɗaya wayar ta yi ya ji ta ɗauka muryarta da alamun bacci. "Baaabyyy." Jin yanayin muryarta ya sa jin wani irin yanayi, ya kwantar da murya yana raɓewa a jikin bango ya ce. "Baby wannan muryar tana azabtar da ni." Surry ta saki murmushin ƙeta ta ce, "Kamar yadda taka take hargitsa ni ba." "Albishirinki zumata." Cikin sauri Suryy ta ce, "Goro My." "In Shaa Allahu a satin nan su Yaya za su kawo kuɗin aurena gidanku." Farinciki kwance a saman harshenta ta ce, "Don Allah da gaske?" "Zan yi miki wasa ne?" Kamar tana gabansa ta girgiza masa kai, Kabir ya cigaba da cewa. "Ina tunanin har da rana za a saka, kafin nan da shekara guda In Shaa Allahu na gama haɗa lefe." Surry ta sake kanne murya ta ce, "Na ji daɗi sosai sadaukina, ina ƙaunarka masoyi." Shi ma Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Na yi kewar komai naki." "Surayya da komai mallakinka ce Kbna." Wata sabuwar soyayyarta ce ta sake mamaye shi, ya gyara tsayuwarsa haɗe da sakarwa wayar kiss kamar yana tare da Surayyan. Sun jima suna musayar daɗaɗan kalamai, sai da dare yayi sosai sannan suka yi sallama Kabir ya koma gida. Yanayin da Surayya ta jefa shi a ciki ne ya sa bayan ya gama cin abinci, ya lallaɓe jikin Fauziya domin ya rage zafi. Duk da ya so a ce Surayya ce a maƙale a gefensa, amma a haka ya samu da ƙyar Fauziya ta ba shi haɗin kai. Domin gani take ko yaya suka yi motsi Inna za ta iya gane halin da suke ciki. Washegari tun da farar safiya ta fara jiyo hayaniyar Sadiya da mijinta, tun suna yin faɗan da cacar baki a cikin ɗaki har suka fito tsakar gida. Kamar Fauziya ta danne kada ta fita, sai ta ji kamar dukanta Sadiya Yaya Nura yake yi. "Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, Allah sai ya saka mana." "Kada ki yafe mana, ai wallahi na yi nadamar aurenki." Cikin kuka ta ji Sadiya ta ce, "Ni zan faɗi haka don wallahi na gama zama da kai har abada." Da sauri ta fita tsakar gidan tana faɗin, "Subhanallah me yake faruwa haka?" Wurin Sadiya ta ƙarasa da ke yashe a ƙasa tana kuka, a daidai lokacin Yaya Nura ya fito yana faɗin. "Ki tarkata komatsanki ki koma can baƙin garinku, na ƙarashe ragowar igiyar aurenki a kaina. Na saki, yau zan yi bacci da saleɓa." Sadiya ta fisge hannunta daga jikin Fauziya ta ce, "Sai me? Ai wallahi da wannan ƙaddararran auren na ka gara na ƙarasa rayuwata a haka." A wannan lokacin Kabir ya fito daga banɗaki ya ce, "Haba Yaya, a gaskiya abin da ka yi sam bai dace ba. Aunty Sadiya ba ta cancanci haka daga wurinka ba, ga duka ga saki abin ya yi yawa." "Ɓarauniyar za ka ce na cigaba da zama da ita? Me ake da mace ɓarauniya ana zaune ƙalau, ni wallahi da na san haka zuri'arsu take ta ɓarayi; wallahi da ban auro ta ba. Haka kawai ta zo ta gurɓata mini zuri'a da mugun hali." Inna da tun farko take ɗaki tana sauraronsu, sai a lokacin ta leƙo ta ce. "Ai wallahi ya yi mini daidai, saboda Allah Sadiya duk ta raina yaron nan. Miji wasa ne? Abin ya kai har da sata, yara gasu nan su uku ne Allah ya raya su." Mamaki ne ƙarara ya lulluɓe Fauziya, don son zuciyar Inna a bayyane yake ƙarara. Duk wanda ya ga Sadiya ya ga halin da take ciki ya san ba ta jin daɗin gidan aure. Cikin tsantsar tsana Sadiya ta miƙe ta isa gaban Inna zuciya tana suya ta ce, "Ai dama 'ya'yanki ba sa laifi, amma ki sani ki bar ganin 'ya'ya maza duk gare ki. In Shaa Allahu sai kin ga sakayyar son zuciyar da kika nuna mini, shi kuma yadda ya azabtar da ni da yunwa haƙƙinmu ba zai bar shi ba. Sata kuma da ake iƙirari ko gaban malamai na je hukuncin sata ba zai hau kaina ba. Saboda abinci ya hana mu, ni kuma na shiga rumbunsa na ɗiba zan girka mana shi ne ya rufe ni da duka. Allah Ya ba ni wanda ya fi ka, domin kai ba mijin aure ba ne." Yaya Nura ya saki dariyar izgilanci ya ce, "Kina fama da gajartar ne za ki samu wanda ya fi ni, ai ni ma tsautsayi ne ya taɗe ƙafafuwana har na faɗo kanki. Ki tashi ki fice mana daga gida, kuma kada ki sake ki ɗaukar mini 'ya'ya." Tuni hawaye ya wanke Fuskar Fauziya ta ce, "Sadiya wai mene ne haka kuke yi a gaban yara ne?" Ta kalli yaran Sadiya da su Na'ima da suka yi carko-carko, wasu daga cikinsu suna hawaye. "Waɗannan mutanen da kika gani ƙarshen butulaye ne, ba su san karamci da hallaci ba Fauziya. Hakan shi ya fi mini alheri In Shaa Allahu." Sadiya tana gama magana ta miƙe ta shiga ɗaki, kayan jikinta ta sauya. Ta ɗauko wata ƙatuwar jakarta ta loda kayanta a ciki, hijabinta ta saka ta fice daga gidan. Maƙota ta dinga bi tana karɓar kuɗaɗen waukau da take bi, sannan ta ƙarasa titi ta taro Mai adaidaita sahu har ƙofar gida. Kusan a inda ta bar Fauziya a nan ta koma ta same ta, suna ganinta gabaɗaya suka yi kanta cikin sanyin jiki. Ɗaki ta shiga ta jango ƙatuwar jakartata, Salim da Zainabu suka ƙarasa suka rungume ta suna kuka. "Don Allah kada ki tafi Umma." "Umma idan kika tafi Inna dukanmu za ta yi." Suka furta cikin kuka, hawayen da Fauziya take riƙewa ne ya fara zuba. Ta saka hannu ta toshe bakinta tana kuka, Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci hawaye masu zafi suka shiga tsiyaya daga idanunta. Cikin tausasa lafazi ta riƙo hannunsu ta ce, "Zan dinga zuwa ina ganinku lokaci-lokaci, Allah Ya yi muku albarka Zainabu." "A'a mu dai ki tafi da mu." Zainabu ta faɗa tana hawaye. Da sauri Yaya Nura ya ƙarasa a fusace ya fisge hannunsu yana faɗin, "Duk wanda na ƙara jin muryarsa sai na taka wuyan yaro." Fauziya ta ƙarasa cikin kuka ta ce, "Don Allah ka bari ta yi sallama da 'ya'yanta cikin salama, wannan hawayen da ka ga suna fitarwa har abada ba za su manta da shi ba." "Da ta san tana ƙaunar yaran take ƙin yin haƙurin zaman gidan ubansu." Sadiya ta dube shi cike da tsana ta ce, "Kada ki damu Fauziya, ni uwa ce na tabbata duk daren daɗewa za su nemo ni. Hakan da ya yi ba shi zai sa su kankare ni a matsayina na mahaifiyarsu ba, ba don na san halin mugun halin gidan nan ba. Da sai na damƙa miki amanar 'ya'yana, amma na san wacece ke Fauziya da kyakkyawar zuciyarki. Ina fatan Allah ya sada mu da alheri. Fauziya ta rungume Sadiya tana hawaye, a hankali ta janye jikinta tana jan jaka har ƙofar gida. Ganin haka ya sa su Salim suka saki matsanancin kuka suna ƙwala mata kira. Sadiya ba ta waigo ba sai ma hawaye da take zubarwa, jakar ta saka a cikin adaidaita sahun. Har ta zauna a ciki tana jin ihun Zainabu da take ƙwala mata kira tana ihu, sai kawai ta kifa kanta a kan cinyoyinta ta saki gunjin kuka mai cin zuciya. GIDANSU MAIMUNA Shirun da Maimuna ta yi ya sa Jafar ya ce, "Kin yi shiru My Moon." Maimuna ta ce, "Gaskiya tsoro nake ji, kada tsautsayi ya sa Nazir ya dawo bai same ni a gida ba. Ka san akwai matsala tun da ba barina fita yake ba, ni dai ina ganin mu cigaba da yin video call hakan zai fi." Ba don ya so ba ya narke mata ya ce. "To ya na iya baby? Amma dai gaskiya ki rage mini kayan jikinki, na fi son na ganki sosai bari ni ma ki ga." Jafar yana gama maganar ya jingine wayar a gefe, ya zame ragowar ƙananan kayansa. Ita ma Maimuna babu kunya, ta zame rigar jikinta. Ya rage daga ita sai rigar mama, can saman gadonta ta haye sannan ta ɗauki wayar ta ce. "Baby ka gama kuwa." Ido suka haɗa ta cikin wayar, Jafar ya ji wani irin abu ya tsarga masa. Bakinsa yana rawa saboda shauƙi ya ce, "Mooooonnn." Yanayin yadda ya kira sunanta ya sa ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe ido, sai ta buɗe su tana ƙura wa faffaɗan ƙirjinsa mai cike da yalwataccan gashi da kallo. 'Haƙiƙa dole Maman Nana ta dinga ɓarin zancan a kanka, tabbas! Jafar ba irin ragowar sauran mazaje ba ne.' Maimuna ta raya a ranta, tana shirin yin magana Jafar ya ce. "Baby wai dama haka Allah ya zuba miki sura? A gaskiya Nazir ba ƙaramin dace ya yi ba." Maimuna ta shagwaɓe murya ta ce, "Nazir ne ya yi dace ko Maman Nana? Allah Ya sani ba zan ɓoye maka ba Baby J. Wallahi za a daɗe ba a samu ingarman namiji kamarka ba." Kalaman Maimuna suka sake kashe masa jiki, ya kwantar da murya cikin shauƙi ya ce. "Ina ma yanzu haka a tare muke, da na shayar da ke romon soyayyar da ba ki taɓa sharɓa ba. Ina kewarki Moon, ina ƙaunarki komai ina ji a kanki Habibtee." Maimuna ta saki murmushin jan hankali, suna cikin haka Jafar ya nemi Maimuna da ta cire rigar da ta rage mata, kamar ba za ta iya ba sai sheɗan ya sake ingiza ta. A hankali ta cire komai na jikinta, suka shiga musayar munanan kalaman batsa. Suna nuna wa junansu duka sassan jikinsu, Daga Jafar har Maimuna ba ƙaramin gigicewa suka yi da ganin surar junan ba. A haka har Jafar ya yi galaba a kanta, ta amsa masa gayyatar da ya dinga yi mata magiya. Maimuna ta amsa masa da cewar za ta shiga wurinsa washegari idan Nazir ya tafi kasuwa, tun da yaranta suna makaranta. Ya so ta shiga a ranar amma ta nuna masa yamma ta yi, yaranta za su iya dawowa daga makaranta. Daga ƙarshe suka yi sallama cike da kewar juna. MAMAN NANA Tun bayan da ta fita daga gida take tafe tana hawayen baƙinciki, ta biya ta makarantar su Nana ta ɗauke su suka wuce gidansu, yaran sai tambayarta suke yi ta ce musu ba ta da lafiya. Lokacin da ta je gida mahaifinta ya fita kasuwa, ta sanar wa mahafiyarta duk abin da ya faru. Ko kaɗan ba su ji daɗin abin da Jafar ya yi ba, amma ita ma sun yi mata faɗa sosai kuma suka ba ta rashin gaskiya. Daddare bayan mahaifinta ya dawo, mahaifiyarta take sanar da shi abinda ya faru. Kiran Maman Nana ya yi, ta tunkari ɗakin gabanta yana faɗuwa. "Amma ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yau Sumayya, an faɗa miki miji wasa ne da za ki cakumi wuyansa a kan yana waya da budurwa." Mahaifinta ya rufe ta da faɗa bayan ta zauna. "Baba marina ya yi fa a kan na ce mata 'yar iska, kuma don wulaƙanci a ɗakina yake waya da ita." Mahaifinta ya girgiza kai ya ce, "Idan ya yi waya a ɗakinki Sumayya, tambarin wayar ne zai fito a goshinki? Tun da kin faɗa da baki bai ji ba me ya sa ba za ki bar masa ɗakin ba? Kin san maza kowa da irin halinsa ai, wani har ya gama neman aurensa mace ba za ta sani ba. Wani kuma a gabanta zai yi komai, to yanzu da kika yi hakan me ya rage shi?" Maman Nana ta saka kuka, Baba ta nuna ta da yatsa ya ce. "Daga yau kada na sake jin kin aikata wannan ɗanyan aikin Summaya, idan kin ji yana wayarsa ki bar masa ɗakin ko ki kama aikin gabanki. Kuma ko da wasa kada na sake jin ki kira budurwarsa da 'yar iska, ke ba a auren aka aure ki? Namiji ai mijin mace huɗu ne, bayan ita ma yana ikon neman guda biyu ya aura." Cikin shasshekar kuka ta ce, "Baba ba za ka gane ba, Jafar duk ya canza mini kamar ba shi ba. Yanzu fa ko abinci bai cika ci ba, ga shi gas ɗin da nake aiki ya ɗauke sai buhun gawayi ya dire mini. Da na yi masa magana har gori ya yi mini, wai su Umma ma da itace suke amfani." "Ƙarya ya yi? Ai ba ƙarya ba ne, ko ɗazu ma da shi kika ga na yi girki ai. Yaran yanzu ba ku ajiye komai ba sai baƙin kishin tsiya." Mahaifiyarta ta yi maganar cikin faɗa. "Tun da har yana ciyar da ke yana tufatar da ke, duk abin da ya kawo miki matuƙar ba guba ba ne sai ki karɓa, da hannu bibbiyu ki yi godiya ki sarrafa shi. Haba Sumayyan Baba ina ganin ki kamar mai wayo ashe ba haka ba ne, don Allah ki kiyaye gaba. Shi kuma zan kira shi ya zo na yi masa faɗa don a sharuɗɗan aure babu dukan mace a ciki." Baba ya ƙarasa maganar cikin tattausan lafazi, sai ya ciro wayarsa ya latsa lambar Jafar ya ji ta a kashe. Ya mayar da kallonsa wurin Sumayya ya ce. "Na kira mijinki wayarsa a kashe, yanzu dai dare ya yi babu damar ki tafi. Amma idan Allah Ya kai mu gobe da safe, ki shirya yaranki ki koma ɗakinki za mu yi magana da Jafarun." Maman Nana ta gyaɗa masa kai, Mahaifi da mahaifiyarta sun jima suna yi mata nasiha sannan ta tashi ta koma ɗaki. In Shaa Allah gobe za mu gama free pages, masu son littafin za su biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Idan kun ba ni haɗin kai zan yi ƙoƙari na kammala shi kafin Azumi🥹 idan kuma na ga kun wankacalar da ni, sai na bari zuwa bayan Sallah idan muna da yawancin kwana.🥸 Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [20/02, 19:45] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA SHA BIYU GIDANSU MAIMUNA Ganin irin miyagun ɗabi'un da Maimuna ta ɓullo wa Nazir, ya sa shi tattara ta gabaɗaya ya yi watsi da ita. Dama can ba ya dawowa gida da wuri, don haka ko da ya kai dare idan ya ci abinci hakan ba ya hana shi ya sake fita. Har mamakin Maimuna yake, saboda gabaɗaya halayenta sun sauya. Maimunan da ya sani a baya ko kara ya ajiye ba ta isa ta ƙetare ba, duk da taurin zuciya irin nata sai da ta kai ta kawo ya sa ta yi laushi, ta yadda ko musu ba ta isa ta yi masa ba. Amma a yanzu Maimuna ta yi masa rainin da ko ƙannensa ba su yi masa ba, ya hana ta shiga mutane ya hana ta hulɗa da maƙota. Ya hana ta riƙe babbar waya, ya hana ta shige cikin danginta sosai. Ya hana ta cigaba da karatu duk don kada ta saba da shiga jama mata su zuga masa ita. Amma sai ga shi a rana tsaka tana shuka masa rashin mutumci son ranta, don a yanzu ba ta shakkun idan ya faɗi magana ta mayar masa. Dalilin haka ne ya sa ya tsiri zuwa majalisar gaban gidansa, da yake wasu maƙonsu suna zama shi ma ya bi sahunsu. A ɓangaren Maimuna kuwa hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, saboda tana jin fitarsa take yin zaraf ta ɗauko wayarta ta kunna data su fara shan soyayya ita da Jafar. Maimuna bayan whatsapp har sabon Acc na facebook ta buɗe, amma ba da sunanta na ainahi ba sai kawai ta rubuta 'Matar Mai Rabo' ta cigaba da fantamawa tana harkokin gabanta. Zaman Nazir a majalisar kenan, ya samu maƙocinsa Adam yana nuna wa ɗayan maƙocin wani rubutu da ya ga an yi posting ya ce. "Ni ban san me matan aure suka ɗauki aure ba, bini-bini za ka ga rubutu ace wai a bata shawara ga halin da take ciki. Don Allah dubi wannan, wai mijinta ya hana ta cigaba da karatu bayan an yi yarjejeniya a ba ta shawara." Lawan ya saki tsaki ya ce, "Sakarcin fa, ai mata wasu a cikinsu mahaukata ne. Na tabbata a nan wasu za su zuge ta har ta kashe auren." Haruna ya ce, "A'a ba lalle ba, ka san wasu matan suna jin nauyin tambayar 'yan'uwansu neman mafita. Sai suka zaɓi a ɓoye sunansu tun da ba wani ne zai gane su ba." "Kai wannan fa ba magana ba ce, shi ya sa tun matata tana budurwa na ce mata ban yarda da wannan hawa soshiyal midiyar ba." Adam ya faɗa cikin ɓacin rai. Jin haka ya sa Nazir ya yi zaraf ya ce, "Ai wallahi tun farko shi ya sa na datse duk wata alaƙa da za ta sa a hurewa iyalina kunne, ba sai ta fita ko tana hawa soshiyal midiyar kanta zai sake wayewa ba? Don lalacewa kwanaki haka na ji ana maganar wata matar aure tana soyayya da wani matashi. Shi ma kuma a onlayin ɗin suka haɗu." Haruna ya yi dariya ya ce, "Wallahi ina faɗa muku mace fa kariyar Ubangiji ce, wallahi duk kaffa-kaffarka idan mace ta so ninke ka a baibai wallahi ba za ka taɓa ganewa ba. Kai tsanani fa ba shi ne ba, ka yi ƙoƙari iya iyawarka a kan kula da iyalinka. Kada ka saki gidanka sakaka, kuma kada ka tsananta. Sauran sai ka bar wa Allah, shi zai tsare maka su." Ya ƙarasa maganar yana miƙewa, sai sauran ma suka miƙe. Nazir ya kaɗe rigarsa ya ce. "Ai wallahi wannan zance ne, kai dai kawai kowa ya ji da gidansa. Amma ka saki mace take walwalawa ai ka riga da ka daɓa wa kanka wuƙa, musamman ma ace ka bar ta tana aiki ko sana'a kuɗi yana juya mata. To kuwa sai abin da ka gani, don matan auren yanzu wallahi mafi yawa sun gama lalacewa." "A'a gaskiya Alhaji Nazir, waɗannan zantukanma bai kamata mu dinga danganta su da iyalanmu ba, Allah Ya nesanta mana su da dukkan wani abin ƙi." Adam ya furta, sannan suka yi wa junansu sallama. Gida Nazir ya nufa sai kuma tunanin Maimuna ya faɗo masa, don haƙurinsa yana gab da ƙarewa. Tun da ta yi watsi da shi, a duk lokacin da ya neme ta sai kawo masa wani uzurin. Maimuna tana kwance ta ji motsin shigowar Nazir, da sauri ta ɗauki wayar ta ɓoye ta koma ta kwanta. Haka kawai ya ji kamar ba bacci take yi ba, don haka ya zauna agefenta yana bubbuga hannunta. "Maimuna! Maimuna." A yatsine ta tashi tana faɗin, "Ya aka yi?" Mamaita kalaman ya yi yana jin ɓacin rai, ya ɗan haɗe fuska ya ce. "Ki tashi mu yi magana." "Ni bacci nake yi sai da safe ma yi maganar." A ɗan tsawace ya ce, "Ki tashi na ce, yanzu nake son mu yi maganar." A hankali ta tashi yana sakin guntun tsaki. "Me ya sa kike ƙaurace mini, me ya sa duka kika canza kin raina niMaimu kada ki bari ki kai ni bango." Murmushi ta saki cikin halin ko inkula ta ce, "Wane kalar ɓacin ranka ne bn sani ba Nazir? Ai sai dai ka faɗa wa wata macen idan ka sake aure." Idanunsa suka kaɗa jawur saboda ɓacin rai, ya matso kusa da ita ya damƙi hannunta yana faɗin. "Uban waye yake zuga ki da yake hure miki kunne har kika raina ni?" Ido cikin ido ta kalle shi ta ce, "Sai ka fara sanar da ni wanda ya zuga ka har ka tauye ni, ka kuma dakushe burikana saboda zalinci ka ƙuntata mini ta hanyar tsauwalawa. Sannan ni kuma na sanar da kai wanda ya zuga ni." Shiru ya yi yana kallonta kamar a ranar ya taɓa ganinta, cikin rashin damuwa ta ce. "Idan kuma ba ka da abin magana sai na yi kwanciyata." "Ni kike faɗa wa haka Maimuna." Nazir ya tambaye ta a zafafe, sai kuwa ta mayar masa da martani cikin sauri kamar tana jira. "Na faɗa maka Nazir, na fa jima ina tara ka a zuciyata. Wlalahi-wallahi daraja ɗaya kake ci a wurin, wato mahaifina. Da ace mahaifina ba ya raye, wallahi da na jima da datse alaƙar auratayyata da kai." Tas! Ta ji ya sauke mata mari a fuska, zuciyarsa tana suya ya nuna ta da yatse. "Duk rashin mutumcin da kike tunƙaho da shi, wallahi daidai nake na sauke miki su. Kin san wane ne ni sarai, ba zan ɗauki wannan iskancin ba." Maimuna ta dafe kumatu tana bin sa da kallon tsana, har zai fita ta ce. "Allah Ya isa ban yafe maka ba, kuma wallahi indai ni ce ba zan taɓa komawa yadda nake a baya ba." Nazir bai kula ta ba ya fita, kai tsaye cikin store ɗin ta ya shiga. Ya ɗauko wani ƙaramin mukulli ya rufe shi, sannan ya ɗauke ƙaramar wayar Maimuna da ke falo ya koma ɗakin. Duk abin da yake yi tana jin sa, don ba sabon abu ba ne idan sun yi faɗa ya rife store ɗinta na kayan abinci. Sai dai kullum idan zai fita ya ɗebo mata wanda za ta dafa. Fulo ta ga ya ɗauka ya tafi falo, ta taɓe baki tana nuna ko a jikinta. Don ta sake ɓa ta masa rai sai ta furta. "Ko a jikina, wai an tsikari kakkaura." Ta gyara kwanciyarta, tana ayyana irin abin da za ta yi wa Nazir don ta huce takaicin marin da ya yi mata. GIDAN INNA Tun bayan fitar Sadiya gidan Inna ya kacame da iface-ifacen kukan yaranta, Inna ban da kyara da hantararsu ba abin da take yi. Fauziya ce ta janyo su ta rarrashe su, da ƙyar Zainabu ta ta yi shiru. Zazzaɓi ne ya rufe Fauziya, saboda duk cikin matan 'yan'uwan Kabiru Sadiya ce ta hannun damanta, suna ba wa junansu shawara musamman da ya kasance Sadiya ba ta da kowa a garin. Sai su rufe su binne ba tare da wani ya ji labari ba, domin dama Kabir da Yaya Nura sune masu ƙaramin ƙarfi. Gudun raini ne ya sa su Fauziya suka kama kansu, don haka ma ya sa matan su Yaya Tasi'u ko gidansu ba sa zuwa. Abincin kari Fauziya ta haɗa gabaɗaya har yaran Sadiya, bayan ta gama ta zuba wa yaran. Suka fara ci, sai dai ta lura har lokacin sun gagara sakin jikinsu. Kabir kafin ya tafi sai da ya kira Mai adaidaita sahu ya fita da keken ɗinkin Fauziya, kai tsaye shagonsu ya wuce da shi. Ya yi sa'a Ogansu yana nan, yana ganinsa ya washe baki ya ce. "Allah Ya taimaki Oga" Oga ya faɗaɗa fara'arsa ya ce, "Kb namu." Janyo keken ɗinki ya fara yi har ya samu ya shigar da shi cikin shagon, sai ya ce, "Oga ya ka ga keken? Ay na faɗa maka sabo ne bai ji jiki ba." Tasowa ya yi daga mazauninsa ya sake leƙa keken ya ce, "Gaskiya ne kuma na ga butterfly ne. A ajiye shi a gefe, zan sa a yi masa service sai ku cigaba da amfani da shi." Kabir ya matsar da keken ciki, sai kuma ya saki murmushi ya ce. "To Oga cittar fa?" "Idan za ka tafi an jima ka yi mini magana, zan ba ka rabin, rabin kuɗin kuma sai zuwa nan da rana ita uku." Ba haka Kabir ya so ba, ya so ace duka kuɗin ya samu. Amma duk da haka ya san idan ya karɓi kuɗin, za su cika a haɗa a kai gidansu Surayya. Tun daga wannan ranar zaman Fauziya da Inna ya fara ɗaukan sabon salo, sai dai Fauziya tana bakin ƙoƙarinta don ganin wani abu bai haɗo su ba. Duk safiya idan ta yi abinci tana bakin ƙoƙarinta, don ta ga ta ba wa su Zainabu abinci ko yaya ne duk da ciyarwarsu ta koma hannun Inna kacokam. Kwana biyu da tafiyar Sadiya, har gida Yaya Tas'u ya zo ya ƙarewa Yaya Nura faɗa a kan sakin da ya yi wa Sadiya. Don wani lokacin idan suka yi faɗa tana zuwa ta kai ƙararsa wurinsa, shi kuma sai ya je ya yi masa faɗa. Idan aka yi haka sai Sadiya ta samu sassaucin rashin mutumcinsa, bayan kwana biyu kuma ya ɗora daga inda ya tsaya. Duk aikin da Sadiya take yi wa Inno sannu a hankali ya dinga dawowa kan Fauziya, lokaci ɗaya ta yi wani irin duhu ga rashin hutu daga wannan sai wannan. Murmurewar jegon da ta yi duk sai ta zuge, a ɓangare ɗaya ga tunanin halin da gininsu yake ciki. Saboda halayen Kabir sun dawo mata sababbi, don tana yi masa magana yake rufe ta da faɗa. Idan Inna ta jiyo sai ta ƙarasa bakin ƙofa ita ma ta cigaba da tofa albarkacin bakinta. Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali, bai wuce yadda ta lura da take-taken Inna tana son fara ɗora wa su Na'ima talla ba. Duk da ba ta fito ta faɗa ba, amma ta lura da yanayin shaguɓen da take yi. Hakan ne ya sa ta shiga takura wa Kabir a kan ya saka su a makaranta, amma sai dai ya ce mata ba shi da kuɗi. Kuma ta rasa wurin da yake zuwa, a kullum ya dawo gida da wuri haka zai buga wankan ƙananan kaya ko manya ya fice daga gidan. Wani lokacin ma sai ta yi bacci yake dawowa, saboda gajiya ta sa ana yin sallar Isha'i take yin bacci. Watarana suna zaune bayan magriba yana tsaka da shiri ta ce. "Abban Na'ima!" "Ina jin ki." Ya amsa mata yana saka belt ɗin wandonsa. "Wai kasuwar ɗinkin ce yanzu ba a samu ko yaya? Zaman yaran nan babu makaranta baya zai mayar da su, don Allah ko Islamiya ce ka saka su." Sai da ya ƙarasa komai sannan ya ce, "Islamiyyar ma ai ba kyauta ake zuwa ba, ki bari idan na samu kuɗi zan saka su. Kin san dai yadda abubuwa suke ƙara tsada." Saboda takaici ba ta tanka masa ba, ya gama shiryawa yana fesa turare, a daidai lokacin wayarsa ta kawo haske da yake a silent take. Da sauri ya ɗauke wayar ya saka a aljihu har zai fita Fauziya ta ce, "Abban Na'ima ni fa ban gane wannan shige da ficen nan da kake yi ba. Ina za ka je ne da daren nan?" "Haifata kika yi da za ki tsare ni da tambaya, ina ruwanki da wurin da za ni? Kin san dai yanzu na daina shaye-shaye ballanta ki kafa mini zargi." Sai kawai ya saka kai ya fice daga ɗakin, shiru Fauziya ta yi tana nazari. "Tabbas ruwa ba ya tsami banza, wallahi akwai abin da Abban Na'ima yake ƙullawa." Ta faɗa a sanyaye, tana jin nadamar ba shi kekenta. Saboda ta san da ko da kuɗin gyaran da take yi ne za ta iya samu ta biya musu kuɗin makaranta, a nan take tunani ya faɗo mata a kan ta fara yin wankau tun da yanzu Sadiya ba ta nan. Sai kuma ta ga sam ba za ta iya wankau ba, don wani lokacin ko wankin yaranta ta yi wuni take bayanta yana ciwo. Sai kuma dabara ta faɗo mata a kan ta fara yin kitso, da wannan shawarar ta bar wa zuciyarta a kan idan gari ya waye za ta shiga maƙota duk ta faɗa musu. Kabir yana fita daga gidan ya ciro wayarsa ya latsa lambar Surayya yana faɗin, "Na fito fa baby." Surayya ta akashe murya ta ce, "Tun ɗazu fa nake ciki da muradin son ganinka gwarzona." Amsa mata ya yi sannan ya kashe wayar. Adaidaita sahu ya tara kai tsaye ya wuce unguwarsu Surry, waya ya ciro ya kira ta sannan ta fito. Kamar kullum idan za su yi zance a soron gidan suke yi, hakan ce ta sa yanzu ma ta shimfiɗa musu dadduma a soro. Rungumo Surayya ya yi, ita kuma ta kamo bakinsa ta fara sakar masa kiss. Nan take Kabir ya fara birkice mata, ya shiga kai hannunsa cikin sassan jikinta. Jingina suka yi da bango, ita ma Surry ta fara sarrafa shi da hannunta tamkar ƙwararriyar matar aure. "Baby na gaji fa!" Kabir ya furta cikin wani irin yanayi. "Kamar yau ne fa, ba yanzu saura wata goma ba. Ni fa ba don 'yan gidanmu ba, da ko ba lefe tsaf za a sha biki. Don tun lokacin da aka tsayar da rana na so a saka wata shida." Janye kansa ya yi daga cikin ƙirjinta ya ɗago yana kai hannunsa ciki jikinta sannan ya ce, "Amma kafin lokacin me ya sa ba za ki ɗan dinga rage mini zafi ba dear?" Surry don ta zolaye shi sai ta ce, "Ba kana da mata ba, ya kake abu kamar wanda bai taɓa aure ba." "Mtswww." Ta ji Kabir ya ja dogon tsaki sannan ya ce, "Ana maganar matan da suka cika cikakkun mata, kina sako mini zancan waccan abar. Don Allah ki taimaka mu dinga zuwa gidan can kina yi mini dabaru." Wani irin daɗi Surry ta ji, saboda ta jima da fahimtar matarsa ba komai ba ce a wurinsa. Ta sake maƙale shi ta ce. "Shi kenan my love, zan yi ƙoƙari na dinga yi wa su Yaya dabarar fita, kasan tun da aka saka ranarmu yake saka mini ido sosai." Sake haɗe bakinsu Kabir ya yi sai da suka ji alamar motsin za a fito, da sauri ya sake ta yana sauke numfashi, Surry ta wayance da cewa. "Hasko nan mu ga ko can azurfar taka ta yi." Wayarsa ya zaro ya fara haska mata, kamar masu neman azurfar gaske. Suna cikin haka Yaya Umar ya yi musu sallama ya fita daga gidan. Ya so sake yamutsa Surry ta nuna masa ya yi haƙuri za ta dinga zuwa can gidan, saboda tana tsoron kada yayanta ya sake dawowa ya kama su. Cike da kewar Surry Kabir ya fito daga soron gidan, yana fitowa babu jimawa ya zaro wayarsa. Misscall ɗin Farha ya gani har sau uku, ya latsa layin nata yana karawa a kunne ya ce. "Ina fatan sarauniya ba ta yi fushi da ni da." "Idan na yi ma ai ka saba kanainaye zuciyata har ta yi maka afuwa." Farha ta furta cikin shagwaɓa. Murmushi ya yi yana jinjina baiwar da yake da ita. Kabir irin mazan nan ne masu iya tsara zance da kanainaye zuciyar 'yanmata. Ya ƙwarai sosai wurin iya yaudara da kife mace, kuma yana ɗaya daga cikin maza masu kule-kule da ƙoƙarin dandanlar arzikin jikin budurwa. "To yanzu dai ayi mini afuwa cajina ya ƙare, zan kira ki da asuba. Ina fatan za ki yi bacci da ni a zuciyarki." Kafin su yi sallama sai da suka yi musayar kalaman soyayya sannan ya katse. Lokacin da ya ƙarasa gida tuni Fauziya ta yi bacci, don haka ya ɗauki buta ya faɗa banɗaki ya tsarkake jikinsa sannan ya koma ɗaki. Sannu a hankali haka rayuwa ta cigaba da tafiya watanni suna shuɗewa, Fauziya ta fara kitso babu laifi tana samun ɗan kuɗin kashewa. Da kanta ta saka yaran a wata makaranta da ake yi boko da Islamiyya, sai dai duk da hakan ba su tsira ba sai da Inna ta fara ɗora musu tallar barkono ranar Alhamis da Juma'a. Tun Fauziya tana kara har ta gagara haƙuri ta yi wa Inna magana, a lokacin faɗa ta rife ta da shi amma da shi ma Kabir ya nuna yaransa ba za su yi talla ba sai ta kawo ido ta saka masa. Fauziya da karanbami har magana ta yi a kan su Salim, a nan ne Inna ta ce daga Kabir har ita ba su isa ba matuƙar ba mahaifinsu ne ya hana ba. Wannan dalilin ne ya ja wa Fauziya da yaranta baƙin jini a wurin Inna, ko fita suka yi tsakar gida wasa ta dinga zaginsu tana hantarasu wani lokacin har da duka. Daga ɓangaren Kabir shi ma zamansa da ita tuni ya sauya salo, don babu abin da za ta yi masa haka kawai zai ɗauki fushi da ita. Ko kuma magana kaɗan za ta yi masa sai ya rufe ta da faɗa, daga haka ma sai ya ƙaurace mata. Domin a zaman da suke yi sun tafi kusan wata biyu ba tare da wani abu ya gifta a tsakaninsu ba. Ana cikin haka watarana Kabir ya dawo da daddare a lokacin sha ɗaya saura, a zaune ya samu Fauziya ta yi shiru tana nazari. Tsakin da ya ja ne ya sa ta ɗago tana kallonsa, karaf idonta ya sauka a kan damɓareren jambakin da ke gaban rigarsa har zuwa leɓensa. Ta haɗiyi wani irin yawun takaici, amma ba ta tanka masa. Kamar yadda ta yi tsammani, buta ta ga ya ɗauka ya tafi banɗaki. Ba tun ranar ba, dama ta lura da shi kusan kullum idan ya dawo ya yi wanka ya fita, to bayan ya sake dawowa daga yawonsa sai ta ji ya ɗebi ruwa yana wanka. Ya tafi banɗaki ba jimawa ta ji kira ya shigo wayarsa, a kan windo ta hango wayar jikinta har rawa yake ta saka hannu ta ɗauka. Wannan ce rana ta farko da zuciya ta ingizata a kan ta ɗauki wayarsa, ƙirjinta yana bugu ta ɗauki kiran da ta ga an ributa 'Sec wf' Ɗauka ta yi sai ta yi shiru daga can ɓangaren ta ji an ce. "Baby don Allah idan za ka yi wanka ka turo mini hoton lovely ɗina, ni ma na turo maka ina wanka ka duba whatsapp ɗinka." Da sauri Fauziya ta katse, ta ci sa'a wayar babu key tana duba whtaspp ta ga sakon lambar da aka kira. Ƙazantaccan hotun surorin jikin Surry ne, sai ta yi sama a nan ta ci karo da hotunan al'aurar Kabir ya tura mata hotuna. Sai kuma wasu hotuna da ta gansu rungume da juna hannun Kabir yana saman ƙirjin Surry. A yadda ta gani babu riga a jikinsa, ta ga kuma ita ma Surayyan ko ɗankwali babu a kanta. Amma sai ta lura wurin da suke kamar ba gida ba ne. "Innalilla wa Inna ilahir raji'un." Fauziya ta furta tana jin kanta yana sarawa, idabunta suka fara ganin dishi-dashi. Ɗakin da take ciki ta ga ya fara juya mata. GIDANSU MAIMUNA Saboda fushin da Nazir yake yi da Maimuna ya sa koda gari ya waye bai bi ta kanta ba, wanka kawai ya yi ya ɗebo shinkafa kofi huɗu ya tsiyayo mai wata 'yar roba ya ajiye mata sannan ya fice kasuwa. Maimuna tana kallonsa duk abin da yake yi har ya fita, da yake a lokacin tuni yaranta sun tafi makaranta, wanka ita ma ta shiga ta tsala a banɗaki. Bayan ta fito ta zaro wayarta ta ga misscall ɗin Jafar, goge hannunta ta yi za ta kira ta ga wani kiran ya sake shigowa. Tana ɗauka cikin zumuɗi ya ce. "Baby ke fa nake jira." Murmushi Maimuna ta yi ta ce, "Na gama komai kayana zan saka." Katse kiran ya yi. Maimuna ta jima a gaban drower kayanta, sai ta ɗauko wasu figaggun ƙananan kaya ta saka, ta zaro zumbulelen hijabinta ta zura. Ƙaramar wayarta ta gani Nazir ya mantata a falo, don ta tabbatar da ya yi nisa da gida sai ta kira shi. Har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka. "Ina jinki." "Na ga ka ajiye mana shinkafa, har dare ko iya rana." Ta furta tana sauraron yanayin wurin da yake. Daga cikin wayar ta ji alamar yana cikin kasuwa, don ta ji ana tambayarsa hula lamba ashirin (Size 20). "Har dare za ku dafa." Ya ba ta amsa a zafafe yana katse wayar. Tsalle ta buga sannan ta ɗauko mukulli ta rufe gidanta, kamar yadda Jafar ya ce zai bar mata gidan a buɗe haka ta same shi. Duk da ta san Maman Nana ba ta nan, haka kawai ta ji gabanta yana faɗuwa. Tana shiga ciki ta hango shi daga shi sai gajeren wando, da sauri ya ƙarasa ya rungume ta yana zame hijabin jikinta. Wata irin kunyarsa Maimuna ta ji ta sunne kanta ƙasa, shi kuwa ya shiga laluben jikinta kamar waɗanda suka jima da sanin juna. A kan gadon Maman Nana suka yada zango, Jafar ya shiga rage mata kayan jikinta har ya raba ta da su gabaɗaya, ya shiga gwaɗa mata zafaffiyar soyayya. Abin da ya birge ta, ya kuma ba ta mamaki yadda ta ga Jafar ba ƙyamar komai na jikinta. Abin da Nazir bai taɓa yi mata ba, don shi ko kiss bai damu da ya yi wa mace ba. Sai da Maimuna da Jafar suka gigita juna sannan komai ya wakana a tsakaninsu, cike da so ya rungumo ta a jikinsa ya ce. "Don Allah ki cigaba da ni haɗin kai zumata." Gyaɗa masa kai ta yi har lokacin hannun Jafar yana cikin jikinta. Bayan gari ya waye sai da Maman Nana suka ci abinci sannan ta yi musu wanka, ta nufo hanyar gidanta. Mahaifinta ya yi mata nasiha sosai, ya sake tabbatar mata da zai kira Jafar ya yi masa faɗa. Da yake ita ma tana da mukulli a hannunta, tana zuwa bakin gate ta saka key ta buɗe jamlock ɗin. Ta yi mamaki da ta ga motarsa a gida har lokacin, amma sai ta yi tsammanin ko lalacewa ta yi bai fita da ita. Don haka ba ta yi wata-wata ba ta nausa kanta ciki, tun daga tsakar gida ta fara jiyo sautin dariya da wasannin da suke yi a cikin banɗaki da ruwa suna wanka. AlhamduLIllah a nan ƙarshen free pages ya ƙare, ba sai na tsaya bayanin irin cakwakiyar da za a riska a gaba ba. Mai son cigaba zai biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 In Shaa Allah Jibi Asabar zan cigaba da posting a paid group Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624