+++++++ YARENA ADDININA +++++++ FARKON LABARI Garin Doko gari ne mai yalwar jama'a masu sana'u daban-daban wasu Manoma, wasu *yan kasuwa suna yawan zuwa cin kasuwanni a garuruwa daban-daban. *Yan garin yaren Hausa suke yi saboda haka Hausawa ne yawancinsu, sai wasu kadan Fulani a garin. Garin yana karkashin karamar hukumar Garki dake Jihar Jigawa. Yau daren goma sha hudu don haka garin ya gauraye da hasken farin wata, ko kwandalarka ce ta fadi a kasa zaka iya ganinta saboda hasken farin wata. Matasan Samari da *yan mata wadanda shekarunsu basu wuce goma zuwa goma sha biyar ba sune suke shawagi suna tsalle-tsalle suna wasanni kala-kala da alama suna jin dadin yanayin garin a yau. Ga hasken wata tar ga wata iska mai sanyi na kadawa. Suhaif saurayin da babu mai iliminsa, kyau, nutsuwa, hankali da tsantsar iya kwalliya da gayu, yana fitowa daga gidan Kakarsa sai ya tsinci kansa da samun wani dan dakali a kofar gidan ya zauna yana kallon yaran da suke wasanni kala-kala yana murmushi shi kadai. Yana tuna baya lokacin da suke kamar haka suma sunyi duk irin wannan. *Yan maza suna wasan langa, wasu na wasan *yar buya. *Yan mata kuma gada suke yi. Wata zabiyar yarinya ce mai zazzakar murya ta ware murya ta fara rero waken gada ta ce. "Uwar miji ta zagen na durkusa ina ta neman gafara. Uban miji ya zagen na durkusa ina ta neman gafara. Da kishiya ta zagen na lillisata na kaita Ofishin *yan sanda sun lillisata sun juyata sun kaita lahira sai gata a duniya. Iyaraye nanaye aiye raye iye nanaye *yan mata. Dariya ta kubcewa Suhaif ya fada a bayyane ya ce "Kai mata, mace bata son kishiya. Sai ga dandazon mata *yan kai amarya sunzo wucewa za'a kai amarya gidan mijinta. Mata dauke da kwallayen alkaki da nakiya na gara. Wata guda daya daga cikinsu ta goya amarya a baya, sai rera waka kawayen amarya suke yi. Suhaif ya bisu da kallo har suka wuce. Gefensa kuma wata kanwarsa ce (cousin) dinsa mai suna *Yar Hajja tana zaune da fitila a gabanta tana sayar da kwai ana *yar fashe, duk wanda aka fasa nasa an cinye shi sai ya bawa wanda ya fasa kwan ya cinye. *Yar Hajja ta ware murya ta rada tallar gyada da karfi ta ce "Ta soyu da manda rangadau. Tayi arewa da filin dakata amaro, Sai ta sake rerowa, "Goro goriye goro daushe, goro dan Kano dan Kaduna wanda bai ci ba yaci sabo. Cikin tsokana Suhaif ya ce da ita "Ke zabiya rufe bakin kar sauro ya fada miki. *Yar Hajja uwar son kudi bayan tallar Koko da kike da safe, kiyi ta dan wake da rana da daddare ma sai kin sayar da goro da Kwai da gyada amaro. Bari inzo inci alakoro. Ya taso ya zo gaban farantin *Yar Hajja ya tsaya. "Yar Hajja ta ce "A'a bana bayar da alakoro sai dai ka saya, wallahi Babangida ka cika son kudi duk kudin da kake jidowa idan kaje Kano kace baza ka saya ba sai dai alakoro kai ko tausayina baka ji. Suhaif ya kyalkyale da dariya ya ce "Kaji ta wai kudin da nake jidowa a Kano kamar wani barawo, kudin ma jido shi ake yi a Kano? Ai kin fini son kudi, lashe money sunanki fa. Ya kai hannu zai dauki kwai daya sai *Yar Hajja ta janye farantin ta ce "Wannan Kwan nawa ne na kashin kaina amma gyada da goro na Hajja ne kakata kuma kakarka ce babu abin da zata ce maka. Ya ce "Ni ai ba tsoho bane bana cin goro. Bana cin gyada kuma tunda ni ba mayunwaci ba ne kwai ni zanci. *Yar Hajja ta dauko kwai daya ta mika masa, ya karba ya mikawa wani yaro a kusa dashi. Sai ya fisgo kwan gaba daya farantin ya ce da yaran dake wajen "Ku shirya yanzu zan rarraba muku kwai ku ci kyauta sai kuyi mata wakar yayi kwantai. *Yar Hajja ta fashe da kuka ta tashi da gudu zata shiga gida taje ta fadawa kakarsu cewar ga Suhaif nan zai rabar mata da kwanta. Suhaif ya kwalla mata kira ya ce tazo ta karbi kudin kwanta zai siye ya bata kudinta. Ta dawo tasha kunu ta rike kugu. Ya zaro *yan dari-dari guda uku sababbi fil ya mika mata ya ce "Kudin kwan nawa ne? Nasan baifi dari biyu ba ga dari uku nan ki rike, uwar son kudi. Ta kyalkyale da dariya ta rafsa buda tana murna ya saye kwan duka harma ya kara mata kudin. Suhaif ya dinga rabawa *yan mata da yaran dake zazzaune a zagaye da fitilar *Yar Hajja kowacce ya mika mata sai farinciki ya rufeta daya bayan daya yake binsu. Daga karshe sai ya hango wata budurwar yarinya a can gefe a zaune da jakar kayanta a gabanta. Ya ce "Waccan kuma wacece ta tafi gefe ta zauna ita kadai? *Yar Hajja ta ce "Mu ma bamu santa ba, bamu taba ganinta a garin nan ba, tun dazu tazo ta sauna tana kallon mu. Munyi mata magana tayi shiru. Suhaif ya karasa gareta, ya mika mata sauran kwan dake hannunsa guda biyu. Tasa hannu ta karba. *Yar Hajja ta dauko fitila da sauri ta zo tana haska wannan baiwar Allah, sai taja mayafinta ta rufe fuskarta, Suhaif ya yiwa *Yar Hajja tsawa ya ce ta daina haskata sannan ta tafi da fitilar. Suhaif ya durkusa a gabanta ya ce "Yan mata ya sunanki ne? Ta yi shiru bata amsa ba. Ya sake cewa bamu sanki a garin nan ba, haka baki yi kama da *yan garin nan ba. Daga wanne gari kika zo? Tayi shiru bata amsa ba. Yana shirin jeho mata tambaya ta uku sai yaji ta rushe da kuka mai tsanani. Yaji hankalinsa ya tashi ya hau lallashinta yana cewa "Daina kuka Allah Ya baki hakuri na daina tambayar ki. Can da kukan ya tsagaita sai ta dago da wasu dara-daran idanuwanta farare sol ta dube shi cikin wata sanyayyiyar murya ta ce "Ina so insha ruwa ko zaka taimake ni da ruwa? Ya ce "Zan taimake ki da ruwan sha *yar uwata. Ya tsura mata ido yana kallonta yana mata murmushi, sai ta sunkuyar da kai kasa. Ya kwallawa *Yar Hajja kira ya ce taje cikin gida ta dauko kwanan shan ruwan Hajja Kakarsu sabo, ta kawo masa ruwan sha mai sanyi na tulu. *Yar Hajja ta tashi ta nufi gida don dauko ruwan sha. Suhaif ya sake duban Yarinyar ya ce "Idan na taimake ki da ruwan sha, zaki taimakeni ki fada mun sunanki da kuma inda kika fito? Ta gyada kai kai tana jujjuya kwai biyun dake hannunta. Ya nisa ya ce "Kawo kwayayen in bare miki. Ta mika masa ba tare da ta kalleshi ba. Kafin ya gama barewa *Yar Hajja ta kawo ruwa a cikin kwanan sha, mai sanyi kuwa tamkar daga firij ya karba ya mika mata. Lallai ta kwaso kishirwa kusan kwanan shan duka ta shanye, kadan ta rage. Ya mika mata kwan sai yaga ta karba tana ci bayan kishirwar data kwaso da alama akwai jin yunwa ma a tare da ita. Suhaif ya ce "Gashi kuwa kwan ya kare dana suyo miki wani sai dai gyada da goro. Ta girgiza kai ta ce "Ya isa na gode. Har yanzu a durkushe yake a gabanta. Ya nisa ya ce "Ina jiran amsar tambayata. Tayi narai-narai da ido ta ce "Sunana Fatima ana cemin Iman. Daga tashar *Yankaba na hau motar Gumel, kudin motata bai cika ba shine masu motar suka saukeni anan garin suka ce anan kudina ya kare. Ya ce "Ke kuma Gumel kike so kije suka sauke ki anan Doko? Yanzu idan aka baki kudin motar zuwa Gumel shi kenan matsalarki? Iman ta rushe da kuka ta ce "Gumel din ma idan naje bansan inda zani ba, bansan kowa ba kuma. Suhaif ya gyara tsugunansa ya ce "Iman ban gane ba, baki san inda zaki ba kenan? Ta kara rushewa da kuka mai tsanani tana cewa "Ban san in da zani ba, ban san kowa ba a duniyar nan. Ya bude baki yana mamaki can ya ce "Iman yi shiru ki daina kuka in tambayeki. Ina Iyayenki? Cikin kuka ta ce "Ni a Makka a ka haife ni, uwata ta rasu kwanannan, ubana kuwa tun ana goyo na ya rasu. A Makka muke zaune, sune kadai suka rage min bansan danginsu ba. Shine askarawa masu kame a Makka suka kamoni. Suhaif ya girgiza kai cike da tausayi ya ce "Oh my God! Yi shiru Iman insha Allah zan taimakeki. To amma abunda ya daure mun kai shine daga jin Hausarki kun dade a Makka baku da takardar shaidar zama (igama)? Iman ta sharbe hawaye ta ce "Wahala da wulakanci nake sha tunda iyayena ba su bar min wata dukiya ba, aikin gidan larabawa suke yi kuma daman bamu da takardar zama, ina yawo askarawa suka kamani suka kawo mu kasar, bansan kowa ba a Nigeria. Kukan ya sake kece mata. Ya girgiza kai yayin da tausayinta ta sashi kwalla. Ya nisa ya ce "Iyayenki *yan asalin wanne gari ne? Iman cikin shesshekar kuka ta ce "Sun ce su Fulanin Sokoto ne, Suhaif ya ce "Allah Sarki *yan Sokoto kuwa suna da kirki, zo in kaiki cikin gida wajen Kakata in shaida mata. Ya rike mata jakar kayanta tana biye dashi suka nufi cikin gidan. *Yar Hajja da kawayenta suka bi su Suhaif da kallo suna *yan gulmammakinsu. *Yar Hajja ta ce da kwayenta "Babangida zai kai mana wannan bakuwar gida karfa aljana ce ko mayya ta cinye mu cikin dare. Kwayenta suka ce "Wallahi, dan kuwa lokacin da kika haskata da fitila mun ganta kyakkyawa ce, kamar aljana don kyau. *Yar Hajja ta ce "Dalla, waye ya ce muku aljanu kyawawa ne? An ce har kaho garesu da kofato a kafarsu. Suhaif na shiga suka iske Hajja Kakarsa a tsakar gida yayi sallama ya shiga. *Yar tsohuwa ta amsa ta ce "Wa nake ji kamar Babangida, dawowa kayi, tsokanar da kayi mun dazu bata isheka ba? Ya yi dan murmushi ya ce "Daman ban tafi ba ina kofar gida, Hajja ga wata marainiya na tsinto a kofar gidanki tana zaune tana kuka bata san kowa ba bata san inda zata ba. Iman shigo ki zauna akan tabarma. Hajja ta ce "Marainiya ka tsinta a kofar gidana? Suhaif ya ce "Gata kuwa kina ganin mu tare. Iman ta zo ta zauna a gefen Hajja ta duka ta gaisheta. Hajja ta amsa gami da sa hannu ta shafa kan Iman ta ce "In shafa kan marainiya in samu lada. Allah Sarki daga ina kike? Iman ta rushe da kuka mai cike da tausayi. Sai Suhaif ya fara bawa Kakarsa labarin Iman kamar yadda ta fada masa. Hajja ta ce "Sokoto, wai akwai nisa da sai kaje ka nemo *yan uwanta su taimaka su rike yarinyar nan, tunda babu iyayen a raye marainiya ce, su riketa tunda sune jininta. Suhaif ya ce "Ai Hajja babu zancen akaita a roke su tunda bata taba zuwa Nigeria ba a can aka haifeta bata san su ba. Kuma ko da ace tasan inda suke, yanzu duniyar nan mutane basa abu sabi Allah komai na ganin ido suke yi, sunga babu ran iyayenta wulakantata za su yi, yanzu idan muka ki riketa yaya za'ayi taje garin? Allah Ya kiyaye ai barin yarinya budurwa kamar wannan hatsari ne sai ta fada hanyar banza a garin ta sami abunda zata dinga cin abinci. Kawai ta zauna anan garin Allah Ya rayata, mu bama wulakanta *yan uwanmu Musulmai, muna son Musulmi kuma ko yaya yake. Hajja ta yi murmushi ta ce "Babangida sarkin zuciya har ranka ya baci yanzu ka farajin haushin danginta kenan? Bi a hankali Babangida kasan yaran yanzu wai so nake a bincika ko auren dole aka yi mata ta gudo kasan yaran nan basa so su fadi gaskiya. Iman ta rushe da kuka ta hau rantse-rantse ita ba auren dole za'ayi mata ba. Ta sake shaida musu bata san *yan uwanta ba, da taje wajensu. Da man kuma ita kadai iyayenta suka haifa don haka yanzu da ta taho ma babu mai nemanta. Suhaif ya ce "Hajja kinji ko, kinji wannan abun tausayi to yanzu tayaya zamu dauki yarinyar nan mu kaita inda bata san kowa ba? Ga Hausarta nan ma bata fita, babu alamar karya a labarin Iman. Iman ki kwantar da hankalinki kinzo gida, kinzo wajen mutanen da suke sonki. Mune danginki, zamu taimake ki insha Allah. Ta dago ta dubi Suhaif ta ce "Nagode madalla. Suhaif ya nisa ya ce "Babu komai Iman yanzu zan tafi in barki anan gidan zaki kwanta, gobe da safe zan dawo, Hajja ki bata tuwo taci don ta kwaso yunwa. Hajja ta ce "Ai dole ne yanzu zan zuba mata tuwo. Iman ta ce "Na gode madalla, sai dai kafin in ci abincin ina son inyi salloli tukunna. Suhaif ya nuna mata buta da bandaki, yayi musu sallama ya tafi. Reedwan Suraj Isma'il YARENA ADDININA CI GABAN LABARIN Suhaif na isa gida ya iske mahaifinsa Alh. Hayatu suna kofar gida a zaune shida wani bako yazo neman na cefane. Bayan ya gaishe su sai ya sami waje ya zauna a gefensu. Baba yace da Suhaif ya shiga ya aunowa wannan bawan Allah gero kwano uku Suhaif ya je ya auno ya kawo. Mahaifinsa ya hadawa mutumin da kudi dari biyu ya bashi, Mutumin yana ta godiya ya dauka ya tafi. Alh. Hayatu ya dubi Suhaif ya ce "Yaya na ganka duk kayi sanyi kalau kamar marar lafiya? Suhaif yayi murmushi ya ce "Lafiyata kalau Baba, sai dai ina tausayin yadda nan gaba talakawa zasu ci gaba da rayuwa a kasar nan. Yanzu Allah ne kadai Yasan yawan magidantan da suke cikin halin rashi ga iyali da yawa haka suke kwana da yunwa sabo da babu, sun buga ko ina basu samowa iyali komai ba, su kuma ba musakai ba ballantana suyi bara. Taimakon irin wadannan yana lada tunda baza su iya yawon bara ba, su kuwa musakai zasu iya bara a basu. Alh. Hayat ya girgiza kai don tausayi ya ce "Hakane Suhaif, kasar nan sai addu'a, talaka yana wahala Allah Ya canja mana wannan rayuwa. Suhaif ya ce "Amin Baba, amma kaga da za'a sami iri-irinka, masu hali su dinga taimakawa marasa hali da kan musulmai ya hadu, sun so junansu musulmai, da masu yin bara sun rage bara. Abu ne mai wahala kaga wanda wanda ba Musulmi ba yana bara duk yawancin masu bara Hausawa ne kuma Musulmi kaga bama kishin YARENMU DA ADDINIMU. Amma sai kaga mai kudi ya tara abincin da zai iya ciyar da iyalinsa har tsawon shekaru, makwabcinsa kuwa bashi da ko kwayar shinkafa. Alh. Hayat ya yi murmushi ya ce rufin asiri dai Alhamdulillahi tunda duk shekara ina samun amfanin gona wanda zai isheni in ciyar da iyalina har wata shekarar, amma nima wataran na cefane sai mun harhada da mahaifiyarka da kai kanka dan abinda ka samo a Kano. Daman mutum ba zai ga Allah yayi masa wata baiwa ba sai ya dubi wanda yafi, amma muddin yana duban na sama dashi wanda suka fishi ba zai godewa Allah ba. Yanzu me yasa na dage na hakikance na ce sai kayi digiri? Duk garin nan waye ya taba wani karatu me zurfi kamarka? Ai dan a sami ilimi a garin wanda wataran in Allah Yasa ka zama wani kusa a gwamnati ka tuna da *yan garinku ka zo ka taimakemu. Dan haka abunda nake so da kai shine kaga ka gama karatunka na digiri kuma ka fito da sakamako mai kyau (First class). Bautar kasa ya rage muku kuje kuyi shikenan ka samu aiki ka fara. Duk garin da aka kai ka bautar kasa kaje babu komai dan ina jiyo ka rannan kana hira da dan uwanka Najib kana cewa idan ba Kaduna ba ko Kano aka kai ka babu in da zaka je kai baza kaje Kudu ba. Suhaif yayi murmushi ya ce "Baba ba kudun ne bana so ba, saboda bana so in shiga cikin mutanen da Yarena, addinina ya bambanta da nasu, kaga ko a B.U.K bana zama dasu a daki daya saboda bana sonsu suma basa son Bahaushe Musulmi. Baba kawai ka taya ni da addu'a Allah Yasa a kaini arewa. Alh. Hayatu ya ce "Zan taya ka da addu'a amma fa kai ka fada mun cewar *yan Kudu arewa ake turosu, *yan arewa kuma a kai su kudu sai dai idan mutum yayi sa'a. Ni dai ina baka shawara karka dauki wannan sanadiyyar raunana karatunka kace baza ka je bautar kasa ba dan an tura ka kudu. Ina da kyakkyawan zato a kanka Suhaif ka rike karatunka ka nemi aiki ka taimaki al'ummar garin nan, naga kana son taimako kana kishin Yarenka da Addininka. Suhaif ya gyara zama ya ce "Baba ai barewa ba zata yi gudu danta yayi rarrafe ba, abunda duk kaga ina yi a wajenka nake koyi kamar son taimakawa mabukata da kishin YARE da ADDINI. Alh, Hayat yayi dariya ya ce "Ai shi yasa ake son iyaye su zamana masu kyakkyawar dabi'a don duk abinda suke yi shi *ya*yansu suke kwaikwaya, Allah yayi maka albarka ya taimakemu baki daya. Suhaif ya ce "Amin Baba, yanzu ma daga gidan Hajja nake naje gaisheta. To ina fitowa kofar gidan sai naga *yar Hajja da kwayenta a kofar gida suna sayar da goro da kwai. Suka nuna min wata yarinya bakuwa ce bata san kowa a garin nan ba tana kuka tana neman taimako bata san inda zata je bama. Da nayi mata tambayoyi sai ta ce ita marainiya ce bata da uwa bata da uba ita kadai kuma suka haifa. Danginta kakaf bata sansu ba Nigeria ma bata taba zuwa ba, a Makka aka haifeta shine aka kamota don bata da takardar zaman kasar ba tare da tasan inda zata je ba. Baba idan kaga yarinyar sai kayi mata kuka abun tausayi, shine na kaita gidan Hajja na ce su bata abinci ta kwana gobe inji shawarar da zaku yanke. Alh. Hayat yai shiru can ya ce "Suhaif waye ya ce maka ana irin wannan gangancin? Da daddaren nan ka tsinci yarinya ka dauke ta ka kaita gidan tsohuwa kace ta kwana, ba ka kaita gidan me gari ba shima idan yaga bazai iya riketa ba a kaita wajen hukuma su riketa. Bakasan duniya ta lalace ba, ka taimaki mutum shi kuma ya cuceka. Yanzu idan ka bibiya ma yarinyar karya take yi. Ko aure aka yi mata bata san mijin ta gudo. Suhaif ya ce "Baba ba haka bane duk wannan tambayoyin Hajja tayi mata nima nayi mata ta rantse ba auren dole aka yi mata ba. Kuma yarinyar kintsattsiyar yarinya ce Baba, ko daga maganarta zaka san yaran Hausa bai ishetaba, Baba Musulma ce tana neman taimako mu taimaketa mana. Yanzu idan muka kyaleta tayi gaba zata iya fadawa wani hannu a cuceta a matsayinta na mace budurwa akwai hatsari. Daga jin Hausarta zaka san ba girman nan ba ce. Alh. Hayat yayi shiru can ya nisa ya ce "Suhaif tunda kace haka na amince kaje ka taho da yarinyar nan gidan yanzu, don ba za'a bar tsohuwa ta kwana da wacce ba'a san asalinta ba, duniyar nan a bar tsoro ce. Ni kuma zan shiga gida in sanarwa Mahaifiyarka da kannanka kafin ku karaso. Suhaif har zaiyi magana ya ce a bari sai gobe, sai yayi shiru ya amsawa mahaifinsa da "To madalla Allah Ya kara arziki da wadata. Ya tashi ya nufi gidan kakarsa, Babansa kuma ya shiga cikin gida. Suhaif yayi sallama a gidan Hajja ya tarar da Iman ta gama cin tuwo tana wanke hannu, Hajja kuwa tana kishingide akan shinfidarta. Tana jin muryar Suhaif sai tayi zunbur ta tashi zaune ta ce "Muryar wa nake ji kamar Babangida, daman baka tafi ba ko dawowa kayi baka gama tsokanar daka saba bane? Suhaif yayi dariya yazo ya zauna a kusa da ita ya fara koro mata bayanai kamar yadda suka yi da Babansa a hankali suke maganar ba tare da sun bari Iman taji ba. "Zancen banza yarinya mai hankali da nutsuwa har na fara jin dadin zama da ita shine kake so ka dauke mun ita? Gata wayayyiya tafi *yar Hajja wayo ko talla suka je ba zata ajiye kayan tallar ba ta hau wasa da kawaye kamar yadda *yar Hajja take yimin. Suhaif ya kwashe da dariya ya ce "Ai ba'a yayin dorawa *yan mata talla yanzu Hajja, yayin karatun boko ake yi. Kinga Iman bata yi kama da *yan talla ba da mai ilimi take kama. Anyi-anyi kibar dorawa *yar hajja talla kinki, taci makarantar kwana anan Garki babu nisa kinki yarda a kaita ai lokaci zan samu inzo in sace ta in kaita makarantar dole ta zauna tayi karatu. Takaici ya hana Hajja yin magana saita gyara filo ta kwanta. Suhaif ya juya dubi ya dubi Iman wacce ta takure a gefe kan tabarmar da tayi sallah tana jan carbinta yayi murmushi ya ce "Iman ki dauko kayanki kizo mu tafi can giddanmu su Baba suna so su ganki ku gaisa. "Bata kara ko sakon daya ba ta tashi cikin ladabi gami da amsa masa ta nufi dakin da ta ajiye jakar kayanta ta fito. Suhaif ya mike tsaye yana yiwa Kakarsa sallama, kamar yadda ya sani daman baza ta amsa ba saboda tana jin haushin dauke Iman kuma yayi mata maganar makarantar *yar Hajja wacce da zarar yayi mata in ranta yayi dubu sai ya baci. Iman ma tazo ta durkusa a gaban Hajja tayi mata sallama gami da yin godiya, Hajja ta amsa dakyar. Suhaif fuskarsa cike da murmushi ya shige gaba Iman na biye da shi suka fice. Sun danyi nisa Suhaif ya juya ya kalli Iman ya ce "Af kawo jakar kayan in taya ki rikewa. Ta sunkuyar da kai kasa ta ce "Ka barshi nagode zan rike babu komai. Suhaif ya sake mika hannu ya ce ta bashi ya rike mata. Sannan ta mika masa jakar suka ci gaba da tafiya. Suna isa gidan a tsakar gida suka iske Baban Suhaif da Babarsa. Bayan sunyi sallama sun amsa musu sai suka shigo Suhaif ya dubi Babansa ya ce "Ga Iman din na taho da ita. Iman tazo ta durkusa a gabansu ta gaishesu suka amsa dukkansu. Mahaifiyar Suhaif ta ce da Iman ta dawo gefen tabarma tazo ta zauna. Iman tayi godiya cikin ladabi ta zo ta zauna a kusa da mahaifiyar Suhaif. Suhaif ma ya sami waje ya zauna. Alh. Hayat yayi gyaran murya ya dubi Iman ya ce "Yarinta ki fada mana gaskiyar dalilin da yasa kika bar garinku, karki boye mana idan kina so ki zauna damu anan baza mu kore ki ba sai mu zauna tare. Kuka ne amsar tambayar da yayi mata, tayi kuka har ta godewa Allah, su duka lallashinta suke yi, dakyar ta tsagaita da kukan. Cikin shesshekar kuka ta ce "Duk abunda na fadawa Suhaif shine gaskiyata ban boye muku ba, ina neman alfarma ku yi min sutura ku taimake ni in zauna daku babu inda na sani, babu wanda na sani. Tausayinta ya rufe su Goggo mahaifiyar Suhaif har hawaye take yi ta ce "Iman yi shiru daina kuka zamu rike ki tamkar *yarmu ta cikinmu. Goggo ta kwallawa Naja'atu da Zubaida kira suka fito daga dakinsu suka zo suka sami waje suka zauna. Alh. Hayat ya shaida musu ga *yar uwa kuma kawa tazo zata zauna dasu, ya shaida musu marainiya ce tana neman taimako don haka kada su wareta su riketa tamkar *yar uwarsu jinin su domin haramun ne cusgunawa maraya. Sun dauki alkawarin cewa zasu zauna da Iman lafiya tamkar *yar uwarsu. Daga karshe Goggo ta ce su dauki jakar kayanta su tafi da ita dakinsu suyi mata shimfida kusa da shimfidarsu. Farin ciki mara misaltuwa ya rufe Iman ta sake durkusawa ta yiwa su Alh. Hayat godiya. Naja'atu ce ta dauki jakar kayan Iman na biye dasu har cikin daki suka yi mata shimfida ta kwanta. Daga karshe Suhaif ya yiwa Mahaifansa sai da safe ya tashi ya nufi shagonsa dake zauren kofar gidan. Bayan Alh. Hayat da Goggo sun taba hira suma suka shiga dakinsu suka kwana. Mahaifin Suhaif Alh. Hayat dan garin Doko ne haka ma Mahaifiyarsa Raliya. Raliya ita ce matar Alh. Hayat ta farko kuma tun daga kanta bai sake aure ba. Hayatu yana son Raliya sosai don sunyi soyayya mai wahala dakyar iyayensu suka yarda suka daura musu aure, kasancewar Raliya kyakkyawa ce duk garin babu mai kyanta a waccan zamanin, samari da dattijan garin masu kudi da masu sarauta sun fito neman aurenta. Ita kuwa ta ji bata son kowa sai saurayinta Hayatu shi kuma a lokacin maraya ne ba uwa ba uba sai kakansa ne yake rike dashi amma yana da sana'ar yi, da gonar gadonsa makekiya yana nomawa kuma yana da tumakan da yake kiwatawa. Yana da ilimin boko daidai Junior secondry school ya kuma sauke kur'ani yafi a kirga. Ba karamar gwagwarmaya aka sha ba wajen neman auren nan. Kakar Suhaif Hajja ita ta haifi Raliya Mahaifiyarsa. Ta kekashe idanuwanta ta ce ita fa *yar ta ba zata auri dan yaku bayi ba sai mai kudi. Mahaifin Raliya lokacin bai rasu ba shine ya takura Hajja ya canja mata wannan tsattsuaran ra'ayi nata ya ce dole a aurawa Raliya saurayin da take so tunda bai sabawa shari'a ba. Shi musulmi ne kuma yana da sana'ar yi. Dole bada son ran mahaifiyar Raliya ba aka daura musu aure da Hayatu. Allah Ya albarkace su da *ya*ya mata har uku sai dai kash, da sun fara dan wayo sai su rasu, daga baya ne suka haifi Suhaif. Raliya tayi ta addu'a tayi kuka, tayi fargaba akan tana tsoron ko shima Suhaif mutuwa zaiyi kafin ya girma amma Allah mai komai mai kowa sai Ya raya musu shi har sai da ya shekara shida, sannan akayi masa kanwa mai suna Nadiya ana yaye Nadiya itama ta rasu. Bayan nan ta kara haifar *yan biyu suna rarrafe suka rasu. Hakika wannan rasuwar yara guda shida ba karamin tayar da hankalin Raliya da Hayatu yayi ba suka dukufa da yin addu'a suka rungumi dansu kwaya daya Suhaif, tamkar su hadiyeshi don kauna. Alh. Hayatu su uku ne a wajen iyayensu akwai Furera itace Babba tana Garki tana aure. Sai Alh. Hayatu sannan kaninsa Usman. Allah ya yiwa Usman arziki don haka yana da katafaren gida a Kano a Unguwar *Yankaba da matarsa Usaina ana kiranta Usai ita *yar Gumel ce suna da *ya*ya uku. Babban dansu sunansa Najib, sai na biyun Sagir sai *yar autarsu Zubaida. Don haka Alh. Hayatu yayi shawarar gara ya dauki dansa kwaya daya jal ya kaishi Kano wajen kaninsa Usman ya hadasu da Najib dansa a saka si a makarantar boko me kyau yadda zaiyi ilimi sosai. Haka kuwa akayi tun daga Nursiry har suka shiga primary tare ajinsu daya Suhaif da Najib kuma daman kamarsu daya tunda iyayensu kamarsu daya kamar an tsaga kara suma kuma kowa da mahaifinsa yayi kama sai dai Suhayf ya dauko farar fatar Mahaifiyarsa da gwarzagwarzan idanuwanta. Suhaif yana firamare aka yi masa kanwa Naja'atu Raliya bata ma dora rai akan Naja'atu ba don taji a jikinta ba rayuwa zata yi ba ita ma. Amma babu wanda yasan gaibu sai Allah Ya raya Naja'atu har ta girma. Naja'atu Hayatu da Zubaida Usman suma sa'anni ne duk da Naja'atu a garin su Doko tayi karatun firamare sai daga baya ta koma Kano aka hadata da Zubaida a makarantar Sakandire daya wato F.G.C Kano nan suka gama shima Suhaif da Najib F.G.C Azare suka gama suna fita daga sakandire suka wuce Bayero University Kano inda Suhaif ya karanci Enginearing, Najib kuma ya karanci Physic. Sun gama cikin wannan shekarar sakamakonsu ya fito, bautar kasa zasu wuce. Raliya kuwa su biyu mahaifinsu suka haifa ita da kaninta Nasiru shima ya haifi *ya*yansa da yawa duk suna mutuwa sai Rabi ce kawai tayi saura wato *yar Hajja tana karama mahaifinta ya rasu Hajja ta dauketa shine yanzu take rike da ita. Naja'at Hayat da Zubaida Usman sun shaku bayan *yan uwantaka ta jini ga kawance, don ko a makaranta ba sa rabuwa har *yan biyu ake kiransu daman kuma kamarsu daya suma sai dai Zubaida ita kuma ta danfi Naja'atu haske. Yanzu ma haka basu fi watanni biyu da kammala karatun sakandiren su ba shine kuma suka dungumo Doko suka zauna har suka shiga makarantar Islamiyya. Kullum da safe daga karfe tara zuwa sha biyun rana, ranar alhamis da juma'a ne kawai basa zuwa makaranta. Sai su zauna a gida suyi ta hira da mahaifiyarsu Raliya wacce suke kira da Goggo tamkar wasu kawayenta. Suyi labari suyi dariya su tafa haka suhaif ma yake zama da mahaifiyarsa yayi ta hira, wasa da dariya, sai dai son girmansa yayi yawa bai cika zama da kannensa Naja'at da Zubaida yayi hira dasu ba. Wani lokaci idan *yan fara'ar basa kusa ko kallansu yayi sai su hau makyarkyata suyi wuf su shige daki. Amma wasu lokutan yakan yi hira dasu, amma yana taka musu birki idan yaji hirar tasu ta fara shiga raini. Yafi yin wasa da *yar Hajja saboda dariya take bashi, bayan kauyancin daya addabi halinta gata rikon Kaka ce, saboda haka tabargazarta tayi yawa. Fargabar Suhaif da Mahaifansa daya, ita ce a zaman Iman da su Naja'at sun san dole sai Iman ta fuskanci wariyar launin fata don sai sun hade mata kai su biyu sun wareta duk da sa'anni ne su duka ukun. Ba sau daya ba, ba biyu ba Naja'at da Zubaida sun sha yiwa kawayensu halin ko in kula baku damemu ba, kanmu kawai muka sani, bamu san ku ba. Duk kawar data rabesu sukan shareta har ta gaji ta kama gabanta kansu a hade yake su biyu basa son su sami ta uku. Haka kuwa aka yi suka ware Iman suna wani kaf-kaf da junansu ita kuma tana binsu, idan suna hirarsu tazo ta zauna ta tsoma musu baki. Idan aiki suke yi tazo ta sa hannu suyi tare. Suhaif yasa ido sosai yana kula da yanayin zamansu, ya gane abinda ke faruwa. Bai wata-wata ba ya kira Naja'atu da Zubaida dakinsa ya ja musu kunne sosai yayi musu fada, yaci layar muddin basu canja halinsu ba, sunja Iman jikinsu tamkar *yar uwarsu, kawarsu to lallai su guji hukuncin da zai yanke a kansu. Ko tantama basu yi a zuciyarsu ba sunsan zai aikata abunda yace zaiyi musu in har suka kuskure gargadinsa. Suna daurewa suna jan Iman a jikinsu badan sun saba da ita ba, sai don dolen da Yaya Suhaif yayi musu. Ko da suka fara zama da Iman sai suka ji sun fara sonta har cikin zuciyarsu, saboda Iman mutum ce mai tsananin dadin zama. Mai hakuri, mai fara'a tasan me take fada, mai son aiki ga tsananin ladabi da biyayya bayan tsantsar ibada ta rike addininta. Gason Reedwan da ta ke .....lolx =)) *yaudara* ni na ma mance ko wacece Matawata,,,, na daina sonta ga daidai dani Iman...............reed1 Ehem to gwauraye a huta anan sai kuma gobe da yardar Allah. Reedwan Suraj Isma'il INA KWANAN KU? _____________________ YARENA ADDININA CI GABAN LABARIN Ba su Naja'at kadai ba har su Goggo da Babansu nan da nan suka ji Iman ta shiga ransu saboda wadannan kyawawan dabi'unta. Inda tafi burge Babansu shine tunda Iman tazo gidan nan ya huta da bugun kofar dakin su Naja'at da asuba, kafin yazo ya tashesu sai ya tarar Iman ta tashesu tuntuni har sunyi sallah. Haka kuma take zama ta bude alkur'ani tayi ta kwarara karatun alkur'ani da kira'arta da muryarta mai dadi har garin Allah Ya waye. Dole su Naja'at suka fara koyi da ita. Goggo kuwa Iman ta kara shiga ranta saboda rashin son jikinta akwai aiki ko an hanata bata hanuwa. Kafin su ankara ta gama aikin gidan kakaf, har aikin da basa yi kullum Iman ta kirkiro shi kamar cire yana, da wankin bandaki kullum. Su Naja'at masu son jiki sunyi farin ciki da zuwan Iman gidan nan saboda hutawarsu kawai suke yi. Ko Goggo ta korosu ta ce su zo su taya Iman aiki sai ita Iman ta hana su ta ce su bari kawai zata yi. Ko kuma idan tana gudun kada Goggo tayi musu fada sai ta ce su sami waje su zauna su dinga yi mata hira tana aikin. Nan da nan suka ji sun shaku da Iman. Matsalar daya ce wacce take kawo musu illa wajen kara shakuwa da juna ita ce Hausa bata ishi Iman ba. Tana so ta fadi wani abu da yawa da yaren Hausa bata sanshi ba, haka idan suka fada bata cika ganewa ba. Harshenta yafi kama da na Fulani, wani lokacin kaji kamar Larabci ne yafi yawa a bakinta, Hausa dai kadan-kadan take yi. To inda Allah Ya tarfawa wannan matsalar tasu ta bambamcin yare ruwan sanyi shine da ga baya sai Iman ta fuskanci Goggo tanajin fulatanci, itama ashe fulatanci ne yarenta sai suka fara yarawa. Sannan sai suke turanci tsakaninta da Zubaida da Naja'atu da Suhaif. Babansu kuma daya fuskanci tana jin larabci sai shima suke yarawa, duk da bazai iya doguwar hira da ita ba sosai da Larabci bai kware ba. To fa yare ake zubawa a gidan nan kala-kala. Suhaif yayi-yayi Iman ta saki jiki dashi su saba su dinga hira abu ya faskara taki yarda su saba. Kunya ce da ita sosai, daga gaisuwa babu abinda take kara ce masa sai dai idan yayi mata tambaya ta amsa, ta mike ta shige daki. Saboda ita nema ya fara zama da kannensa yana hira idan yazo ya same su suna hira, amma dif zaiji Iman ta dauke wuta ta daina zuba labari ta hau gyara nayafi tana tura gashi cikin dankwali. Idan ta sunkuyar da kai kasa ba zata kara dagowa ta kalleshi ba, balle suyi hira. Bayan zuwan Iman da wata guda ta nuna sha'awarta ta shiga makarantar Islamiyyar su Naja'at da Zubaida. Bayan sun shaidawa shugaban makarantar cewa zasu kawo sabuwar daliba ya ce su biya mata kudin wata sai ta fara zuwa. Iman da Zubaida da Naja'at suna tashi da sassafe suyi aikin gida suyi wanka duk da ba kayan makaranta (uniform) suke sawa ba sai su saka manyan hijabansu wani lokacin Iman takan saka katuwar (nikaf) ta rufe fuskarta, su dauki jakar littattafansu su tafi. Ajinsu daya kasancewar nan ne ajin manya wadanda suka yi nisa, sun sauke alkur'ani tuntuni hadda ake koya musu. Da aka gwada Iman don asan wanne aji za'a saka ta sai suka ga Iman harta wuce *yan manyan ajin saboda tayi nisa sosai a hadda. Haka a fannin hadisai da zauransu. Tunda babu aji na sama dana su Naja'at sai suka sakata a ajinsu. Iman bata wasa da karatunta akwai hazaka a gida da makaranta koda yaushe ka ganta da littafinta a hannu tana karantawa idan bata da aiki. Haka take kara koyowa Zubaida da Naja'at inda suka kakare. Goggo ma ba'a barta a baya ba, ta yarda da hankali da nutsuwar Iman don haka take zama da Iman tana koya mata karatun kur'ani. Yau Alhamis babu makaranta bayan duk sun tashi da asuba sunyi salla, kamar yadda *yan makaranta suka saba sai kowacce ta zauna akan abin sallarta ta bude kur'aninta tana karantawa har saida gari ya washe. Naja'at da Zubaida suka gyara shinfida suka sake kwantawa suka bude wani sabon barcin da basa samu suyi saboda makaranta. Iman ta mike ta fito tsakar gida don ta gaishe da Baba da Goggo sai taji tsit babu kowa da alama dai sun koma barci. Ta juya zata koma dakinta sai taji karar bude kofa. Tana jiyowa sai taga Baba ne ya fito daga daki dauke da wata bakar leda a hannunsa. Ya yi wanka ya yi kwalliya yana ta kamshin turare. Tayi sauri ta durkusa har kasa ta gaisheshi cikin harshen larabci. Ya amsa mata cike da fara'a ya shaida mata yau Kano zaije sai gobe zai dawo idan su Naja'at sun tashi ta fada musu ya wuce. Ta amsa masa da to, sannan tayi mas fatan Allah Ya kiyaye hanya. Ya fita ita kuma ta koma daki ta cire hijab da doguwar riga baka dake jikinta ta daura wani tsohon zaninta wanda ta mayar da shi na aikin gida ta sanya wata yaloluwar riga fara (tea shirt) ta daura dankwali ta fito tsakar gida don fara aikin gida. Tsakar gida kaca-kaca saboda sunsha hirar dare anci gyada ansha rake duk an zubar a tsakar gida. Kwanukan da aka cicci tuwo ne a watse a tsakar gida. Wasu a kicin, wasu kuma an kaisu wajen wanke-wanke kusa da rijiya. Iman sarki tsafta, ta tsaya kawai tana kallon tsakar gidan saboda mamaki da takaicin daya dameta a zuciya tana fadin "Daman haka muka yi da tsakar gidan nan jiya da daddare a duhu ban share ba, yanzu a dattin nan muka kwana? Ga babban abun kunya a haka Baba ya fito yaga tsakar gidan nan, zaice bamu da amfani a gidan. Tama rasa ta ina zata fara, wanke-wanken zata fara ko shara? Sai ta tsayar da shawarar ta hada kayan wanke-wanke ta fara share tsakar gida da kicin. Haka kuwa tayi ta share gidan ral a binka da Siminti ya fita yayi tas ko tsinke bata bari ba ta tattara ta kwashe. Sannan ta dauko kujera da omo bayan ta jawo ruwa a rijiya ta zauna ta fara wanke kwanukan da suka bushe da tuwo miyar kuka. Suhaif ne ya dawo daga rakiyar mahaifinsa, ya rakashi har bakin titi ya hau mota sannan ya dawo gida. Yana sako kai cikkin gidan saiya ga Iman a zaune tana wanke-wanke kanta a sunkuye a kasa bata ganshi ba, kuma karan kwanukan da take wankewa basu barta taji motsin shigowarsa ba. Ya tabbata Iman bata zaci zai shigo a dai-dai wannan lokacin ba kuma bata zaci yana kallonta ba data ruga daki ta saki hijabinta. Ba zata zauna da damammiyar rigar nan a gabansa ba, saboda bata bude ko wutsiyar gashinta a gaban wani namiji. Iman ta san addininta, tasan darajar ta *ya mace gata da kunya. Daya tabbatar bata ganshi ba sai bai bari ta ganshi ba yaja da baya a hankali ya koma. Wani dan karamin wundo ya tsaya yana lekenta domin yana kokonto ko ba ita ba ce bama. Saboda shi har yanzu baima kare mata kallo ba balle ya santa sosai, tsakaninsa da ita ya ganta a lullube cikin hijabi ta durkusar da kai ta gaishe shi, wani lokaci ma fuskarta a rufe da nikaf kafarta da safa. Yasan fara ce amma bai dauka tas-tas kamar haka ba. Ya kurawa fuskarta ido yana kallon hancin dodar, ga wani lumshasshen ido mai dauke da far tas da bakar kwayar ido dara-dara. Gashin girarta mau taushi a kwance dodar bakinkirin. Bakinta karami dai dai ita ga lobawar kumatu ko magana take balle tayi murmushi ko dariya. Ga wata *yar siriritar wushirya a tsakiyar fararen hakoranta. Fatar jikinta abar kallo ce farinta mai kyau tas da ita kama daga fuskarta har tafin kafarta jawur da ita. Suhaif ya shiga tunani a zuciyarsa "Anya kuwa wannan ba *yar Larabawa ba ce? Kai dole ruwa biyu ce ko uwarta ko ubanta a sami balarabe. Tana da tsananin kyau wadda ko a mata sai sun tsaya sun kalleta sun kara kallonta balle namiji. Suhaif ya nisa ya ce a zuciyarsa "Lallai dole ki boye wannan kyawun naki saboda mu anan kasar bakake zaki zame mana tamkar wata zinariya abar kallo abar sha'awa wanda kowa yake fafutukar tara kudi ya mallaka domin zinare abun ado ne ga mata, kadara ce ga da namiji shiyasa kowa yake son ya mallakeshi. Allah Ka bani Iman, Allah Ka sani inason Iman tun ranar dana fara ganinta har cikin raina. Dankwalin kanta ne ya sulmiye zai fadi duk da hannunta da bakin tukunya tayi kokarin sa bayan hannu ta dafe dankwalin don kada ya fadi abun ya ci tura, kasancewar yana da santsi sai ya sulale yayi kasa yayin da idanuwan Suhaif ya dira akan wani lallausan gashi dogo baki wulik. Ya sake murtsike idanuwansa yana kallo. Gashi ne dai Suhaif ba karya idanuwanka suke nuna maka ba. Ta lunkube gashin ta tufke bai san iyakar sa ba amma ko ba'a fada masa ba yasan zai tabo gadon bayanta. Gashin kanta bashi da alaka dana bakar fata daga gani wannan tsatson jajaye ce. Suhaif ya fada a ransa "Dolo Iman ta hada jini da farar fata ko Uwa ko Uba, amma bari mu saba zan binciketa a hankali. Ko da ta mike tsaye ta dauki kayan data wanke tana mikawa kicin sai Suhaif ya bi kira da dirin jikinta da kallo. Wai!! Allah Yayi halittarsa ance mutum tara yake bai cika goma ba ko ta ina aka ragu wannan? Mai madaidaicin tsawo ce. Ta fi kiba daga kugu daga sama siririya. Kafarta abar kallo ce saboda anyi mata shape mai kyau wanda shi ya taimaka wajen kara dirar jikinta. Tea shirt din dake jikinta bata da kauri don haka ta sake fito da cikar kirjinta. Ya ja dogon numfashi ya shafa kirjinsa ya fada a bayyane "Allah Ka bani wacce nake gani yanzu, kasa ta soni kamar yadda nake sonta. Bayan ta gama kwashe kayan wanke-wanken sai ta zo ta wanke bakin dake hannunta da ruwan kyau da omo. Sannan ta dauki dankwalinta dake kasa a cikin ruwa ta kade ta daure kanta, ta dauko tsintsiya da ruwa da omo ta fara wanke wajen. Yaji zuciyarsa ta hau dukan uku-uku saboda ya sake sarkewa da son abunda ba lallai bane ya samu sai ya shiga tausayin kansa kamar ya rushe da kuka. Yasa hannayensa biyu a aljihu ya jingina goshinsa a jikin bango ya runtse idanuwansa yana zulumi da takaicin ta yaya ma zai saba da Iman balle ya sami soyayyarta? Yarinyar da ko hada ido sau daya bata yarda su yi, zaman minti uku bata yarda suyi, magana jimla biyar basu taba yi ba. To yaya zaiyi? Yana tambayar zuciyarsa yana tambayar kansa. Motsi ya ji a bayansa ya juyo da sauri, sai yaga Iman ce dauke da tsintsiya a hannunta daya hannun kuma dauke da abun kwashe shara da kanzo a ciki tazo zata zuba a abun zuba sharar dake ajiye a zauren. Saboda tsananin firgita Iman ta zubar da abubuwan dake hannunta. Ya sake zare wadannan manyan idanuwansa ya kalleta sai taji wani abu yarr a cikin jikinta, taji kamar a tsirara take, hankalinta ya tashi yau wanda take tsananin kunya da jin nauyinsa ya ganta a haka. Ta fisgo dankwalin kan ta tana so ta rufe jikinta sai taji ta tuje gashinta ya zubo a fuskarta da bayanta yaraf, ta fara ja da baya. Yana kallonta ya durkusa a hankali ya dauki tsintsiyar da abun kwasar sharar ya fara tattara kanzon data zubar a gabansa. Sai gabanta ya fadi tana gudun ko tayi laifi ta zubar da kanzo yana kwashewa ta hau in ina ta ce "I'm sorry. Ya sakar mata wani lallausan murmushi ya girgiza kai ya ce "ba mishkila, tafi kawai. Abunda ya bashi mamaki sai yaga tayi masa murmushi ta duka ta ce "Thank you ta sunkuyar da kai kasa ta juya ta tafi. Ya ajiye tsintsiya da abun kwasar shara yazo ya jingina ajikin kofa yana kallon yalo-yalon gashin nan nata har sai da ta shige daki sannan ya dawo ya kwashe kanzon daya zube ya shiga dakinsa ya kwanta tamkar bashi da sauran laka a jikinsa. Babu abinda yake hangowa a idanuwansa da zuciyarsa sai Iman. Tun daga wannan rana Iman ta sake kara jin kunyar Suhaif sai kara gudunsa take, haduwa tayi musu wuya sai wasan *yar buya in dai ba kure musu tayi ba bata yarda ta tsaya su gaisa. Abun yana damun Suhaif babu yadda zaiyi ya hanata wannan hali, kuma duk gidan shi kadai take yiwa haka duk sauran ta saki jiki dasu rai-rai yake jiyo hirarta amma a gabansa sai tayi shiru, a hankali sai ta zame ta gudu daki shi kuwa a zuciyarsa ya saba da ita don tunaninta da sonta ya zame masa abokinsa na yau da kullum, tana zuciyarsa koda yaushe yana tunaninta, son kuma karuwa yake yi. A yau da yamma Najib ne ya dira a garin Doko daga Kano, ya iske Suhaif a dakinsa yana zaune kan katifarsa ya jingina a jikin filon daya jingina a jikin bango. Tunanin Iman ne yake damunsa ya saka wannan ya cire, ya saka wancan. Sallamar Najib ce ta katse masa tunani ya amsa a sanyaye yayin da hankalinsa gaba daya ya tattara ga kallon mai shigowa. Kasancewar yamma tayi ga babu wuta, dakin ya fara duhu. Suhaif bai gane fuskar mai shigowa ba duk da yaso ya dauki muryar amma yana kokonto anya kuwa Najib ne zai zo da yammar nan. Kuma a yadda suka yi da Najib ba zaizo yau ba, ya ce zai je Bauchi ya dawo tukunna. Najib ya karaso kan katifar da Suhaif ke zaune ya kama masa hannu suka gaisa sannan Suhaif ya gane ko wanene. Cikin mamaki Suhaif ya ce "Malam Najib kaine, kasan kuwa ban ganeka ba? Gaskiya mutumin nan kayi min zuwan bazata. Najib yayi dariya ya sami waje ya zauna a kusa da Suhaif ya ce "Haba dai, ba dai tun shigowata baka gane ni ba. Na dauka zaka gane muryar? Suhaif ya ce "Naso in dau muryar saina ce kai ba kai bane yaushe ka dawo daga Bauchi? Ko dai *yar Bauchin za'a samo mana ne? Ka cika yawan zuwa Bauchi. Su duka suka tuntsire da dariya. Naji ya ce "Kai wallahi ka cika rudu, bana gaya maka bikin Aliyu Bauchi course mate dina muke ba? Kasan ni ai sai Samira Tukur, bayan har yanzu yarinyar nan garani take ban samu shiga ba ina ni ina jijjibo wata kuma? Samira ta cika yanga da yawa. Suhaif ya fada yayin da yake tabe baki.. Najib ya kwashe da dariya ya ce "To meye kake tabe baki? Suhaif ya ce "Ai haka take idan zata yi magana a wani tabe baki a yatsune fuska kafin ta gaishe da mutum shi yasa ban cika rakaka ba wajenta. Yanzu a label nawa take ne? Najib ya ce "Lebel two ta shiga tana Micro-biology anan B.U.K Old Side. Najib ya gyara zama ya ce "Daman labari na kawo maka da dimi-dimi, da sai gobe zanzo naga kai gara in zo yau in fesa maka wannan abun farin cikin. Kasan kamar akan kaya nake Allah-Allah nake su turamu bautar kasa nan muje muyi mu dawo mu sami aiki mu ma a dama damu a gwamnati, Babana yana da abokai a kusoshin gwamnati. Last week ma ya kirani falonsa ya dubeni ya ce, "Wai kai da dan uwanka Suhaif yaushe zaku je bautar kasa ku fara aiki har na yiwa abokaina maganarku fa. Na ce "Mun kusa tafiya Baba. Suhaif ya harareshi ya ce "Kai mayen kudi ne wallahi baza ka iya aikin banki ba. Ni har yanzu baka fada mun labarin da ka kawo min da dimi-diminsa ba. Najib ya ce "Ina dawowa daga Bauchi na shiga School na tarar an kafe sunayenmu kowa da garin da zaije bautar kasa. Suhaif ya zabura ya dafe kirji ya ce "Kaga nawa? Najib ya ce "Ba dole ba ai kafin in tsaya in duba nawa naka na fara dubawa an turani Kaduna kai kuma Ogun. Suhaif ya daka tsalle ya mike tsaye ya ce "Bazai yuwu ba, danme za'a turani kasar inyamurai? Ai nafadawa Baba, indai kudu ne ba inda zani don haka kayi shiru karma ka bari su Baba su sani dan ba zanje ba. Najib ya mike ya nufi kofar fita yana cewa "Kai wallahi dan yawa ne, bari in fadawa Baban da kaina dole ma kaje. Suhaif ya damko Najib ya rike shi, Najib kuma na kokarin fisgewa. Baba ya zo wucewa ya gansu suna kiciniya. Ya daka tsawa ya ce "Meye hakan, kamar wasu *yan yara kuke wasan kunce? Najib ya kyalkyale da dariya ya durkusa ya gaishe da Baba sannan ya gaya masa abunda yake faruwa. Suhaif kuwa sai bata rai yake yana tsaye yana hararar Najib. Baba ya fusata ya sharba masa Carbin dake hannunsa ya rufe shi da fada fafafafa "Sai kaje wallahi. Ko na mutu na bar wasiyya a tura ka. Yaro ka gama karatu bautar kasa ta gagareka wai kai sai arewa, kudun zaka je dole ne ai. Najib ya yiwa Baba sallama ya ce ba kwana zai yi ba. Reedwan [[f9.heart]] Iman [[f9.heart]] Matawata ....... Mai mace daya aminin Gwauro. Su wa'e a dage ai aure.. SAI GOBE IDAN ALLAH YA KAIMU Reedwan Suraj Isma'il 08098715332 @watsapp _____________________ YARENA ADDININA CI GABAN LABARIN Washe gari ranar Juma'a su Iman basu da makaranta don haka su Zubaida baccinsu kawai suke yi har karfe takwas na safe babu kowa a tsakar gidan. Iman a kwance take juyi kawai take ko itama ta samu ta danyi baccin safe yau taji yadda masu iya baccin safe suke ji don ita bata iya komawa bacci ba, bata san yaya suke ji masu yinsa ba. Ta duba agogo taga takwas ta dan gota sai ta mike ta cire *yar yaloluwar rigar baccin dake jikinta ta saka kayan da ta mayar da shi na aiki. Ta fito tsakar gida duk da ta share tsakar gidan da daddare tas yake babu datti amma ai ba za'a rasa kura ba. Sai ta shiga hado kayan wanke-wanke. Bayan ta wanke tas ta kawar da kayan saita share wajen ta kwashe kanzo da gayan tuwon da aka ci aka rage. Ta nufi zaure inda abun zuba shara yake. Akan wani dan dakali dake kofar gidan ta hango kafafuwan Suhaif bata hango gangar jikin ba amma ta jiyo dogon tsakin da yake ta ja da alama yana cikin damuwa, damuwar tasa ba zata rasa nasaba da zancen tafiyarsa bautar kasa ba, an tura shi garin da baya so kuma mahaifinsa ya ce dole yaje. Ta taho a hankali ta leka inda yake zaune ta ganshi ya dukar da kansa kasa ya rike kai da hannu biyu yana girgiza kai saboda tsananin damuwar da yake ciki. Iman ta ji tausayinsa ya kamata, ba don tana kunyarsa ba data bashi hakuri ya daina damuwa da yawa amma baza ta iya tsayawa tayi magana ba. Ta juya a hankali ta shige cikin gida taje ta karasa wanke wajen da tayi wanke-wanke ta koma daki ta zauna sai taji ta kasa zaman, ta tashi ta fito tsakar gida ta tsaya taji ta rasa sukuni lallai wani abu yana damunta a zuciya. Ta rasa meke yi mata dadi a ranta kuma yanzun nan abin ya fara nukurkusar zuciyarta don kalau ta tashi a safiyar yau zuciyarta cike da farin ciki. Can ta tuna ashe halin da Suhaif yake ciki ne ya shafeta itama ta kasa sukuni. Sai ta shiga mamakin kanta da kanta. Yaya haka? Meye wannan? Yaya na shiga damuwa don Suhaif yana cikin damuwa? Inji zuciyarta. Sai wata zuciyar tace "Ai ya kamata ki taya Suhaif duk halin da yake ciki ko farin ciki ko bakin ciki. Ki tuna fa shine ya taimakeki a lokacin da kike neman taimako, kin shigo kasar da baki san kowa ba gaba da baya. Ya tsaya tsayin daka sai da ya ga kin sami wajen zama daram sannan hankalinsa ya kwanta. Ya kamata a ce kin taya shi bakin ciki, sai ta koma daki ta kwanta tayi shiru a kan *yar katifarta. Can a cikin zuciyarta taji ance "Gaba daya wannan ba mafita bace kinzo kin kwanta ranki ya baci shi wanda kike dominsa bai san me kike yi ba kuma ko da ya sani babu abinda zai kara masa kije ki tare shi ki bashi hakuri ki gaya masa kalaman kwantar da hankali ki bashi misali da hadisai in da Annabi ya fada mana mu bi maganar iyayen mu kuma yarda da kaddara. Sai Iman tayi zunbur ta tashi zaune tayi shiru tana tambayar kanta da kanta tayaya zata iya tarar Suhaif tayi masa magana har tayi masa kalaman da zai gamsu ya kwantar da hankalinsa bayan kunyarsa take matukar ji, kwarjini yake yi mata sosai. Sai taji ranta ba zai yiwu ta tare shi don baza ta iya ba, to amma tana tunanin me zai hana ta rubuta masa wasika ta kai masa. "Hakaa kuwa za'ayi. Ta fada a bayyane. Ta tashi cak daga kan katifarta ta dauko jakar makarantar islamiyya dake rataye a jikin kusar dake manne a bangon dakin, ta dawo ta zauna akan katifarta ta bude jakar ta dauko littafi da biro, ta ciro takarda ta fara tsantsarawa Suhaif wasika cikin harshen turanci don shi tafi iyawa fiye da Hausa sai kuma fulatanci yarenta wanda shi tafi ji amma ai shi wanda zata yi dominsa baya ji. Da farko ta gaishe shi, gaisuwa irin ta addinin musulunci da kuma girmamawa. Sai ta nuna masa irin halin damuwar data shiga sanadiyyar ta ganshi yana cikin damuwa to amma ya bar damun kansa saboda abun bana damuwa ba ne in har zai barwa Allah zabinSa. Ta kara da cewa ya bi maganar mahaifinsa ya yi biyayya a gare shi hakika idan yayi haka zaiga budi a rayuwarsa. A ko ina yake ya sawa ransa Allah Yana tare dashi, kudu da arewa duk daya ne Allah yana ganin ko ina. Kada ya damu mutum yakan so abunda ba shine alheri a gare shi ba sai Allah Ya zabar masa abunda zai ji baya so kuma ya zama shine alheri a gareshi. Yayi hakuri yaje tayi alkawari zata zamanto mai yin addu'a a gare shi, insha Allah zaije lafiya ya dawo lafiya. Ta jawo wasu ayoyi a cikin littafi mai tsarki ta fassara taja hadisai tayi masa misali dasu. Ta kara yi masa nasiha daya kwantar da hankalinsa kada ya damu. Data gama rubutawa tsaf sai ta linke ta jawo zirmikeken hijabinta ta saka ta fito. Ta leka kofar gida ta hango Suhaif yana nan a zaune inda ta barshi sai ta tsaya tayi cak tana tunanin yaya za'ayi ta bashi wasikar. Mummunar faduwar gaba ce ta afko mata yayin da ta ga Suhaif a gabanta ba tare da ta ji motsin tafiyarsa ba. Shi ma yayi kicibus da ita, sai yayi kasake yana kallon ta bai zata zai ganta a nan ba, ya yi matukar mamaki da sassafen nan "Ina Iman za ta je, yau Juma'a kuma babu makaranta, bayan makaranta kuma babu inda Iman take zuwa? Wasu lokutan ne ma takan raka su Naja'at su je su gaishe da Hajja Kakarsu. Ta durkusa ta gaishe shi ya amsa ya ci gaba da kallon ta a zuciyarsa cike da alamomin tambaya. Ya ga Iman dai a tsaye ba ta shige gida ba, ba ta kuma fita waje ba, kanta a sunkuye a kasa. Ya ce "Iman unguwa za ki ne? Ta girgiza kai ta ce "A'a. Ya ce "Kawai kin leko kofar gida ne? Sai ta yi murmushi ta dora takardar da ke hannunta a kan wundon da ke kusa da inda suke tsaye ta juya ta shige cikin gida. Suhaif ya bita da kallo yana cewa: "Wasikar tawa ce ko kuma wani zan kai wa? Ba ta iya juyowa ta bashi amsa ba saboda kunya. Ya yi ta mamakin irin wannan kunya ta Iman, amma babu mamaki kunyar Fulani ta wuce haka. Sai ya sa hannu ya dauki wasikar da mamaki da kuma zumudi, wani bangaren cike da fargaba, Allah Ya sa ya ga abin da yake fita a cikin wasikar, ma'ana, Allah Ya sa ita ma ta fahimci son da yake yi mata, ita ma a ce tana yi masa. Ya shiga dakinsa ya sa makulli ya rufe ya zauna a kan wata tsohuwar kujerar da ke dakin. Ya yi bismillah sannan ya bude wasikar ya fara karantawa Suhaif ya tsinci kansa da tsananin farin cikin abin da ta fada kana kallon fuskarsa za ka iya ganin farin cikin da ya lullube masa zuciya, daman Hausawa sun ce. Labarin zuciya a tambayi fuska. Nan da nan ya ji mugun bakin cikin da tsananin damuwar da ke addabar zuciyarsa sun ware. Ya gamsu kwarai da bayanan Iman. Ya ji ya sake son ta fiye da son da yake yi mata a da. Ya maimaita karanta wasikar nan fiye da sau goma saboda ta yi masa dadi. Murna yau ba za ta misaltu ba a zuciyarsa. Can ya dau biro da takarda ya fara rubuta amsar wasikar. Bayan ya yi mata sallama irin ta addinin Musulunci sai ya nuna mata jin dadinsa da ta kula da halin da yake ciki har ta damu ta dauki biro da takarda ta rubuta wasika ta yi masa nasiha. Ya yi godiya sannan daga karshe ya yi mata alkawari zai yi amfani da shawarwarin da ta ba shi zai kuma bi abin da mahaifinsa yake so sannan shi ma ya yi mata alkawarin zai zamo mai yi mata addu'a a ko yaushe Allah Ya ba ta miji na gari mai tsananin son ta, saboda haka shi ma kuma yana rokarta a cikin addu'ar da ta yi alkawari za ta dinga yi masa ta ce Ubangiji ya ba shi wata yarinya da yake tsananin so da bege. Ya sa yarinyar ta san halin da yake ciki ita ma ta so shi, saboda wacce yake so din ba ta san yana yi ba. Ya bayyana mata cewar wannan dalili yana daya daga cikin dalilan da ya sa ba ya son tafiyar. Da ya gama rubutawa sai ya nade wasikar ya ajiye biron, ya dade a zaune yana tunanin a inda zai gan ta ita kadai ya bata wannan wasika. Ya dubi agogo ya ga karfe tara daidai, sai ya ji a jikinsa ai *yan gidan ma ba su tashi daga barci ba, tunda sukan kai karfe goma suna barci. Yayi zumbur ya fito tsakar gida ya tarar babu kowa, sai yaji motsin kwanuka a kicin, ya nufi kicin sai ya tarar da Iman ce take damun koko. Tana dagowa ta ga Suhaif suka hada ido sai dukkansu suka sakarwa junansu wani sanyayyen murmushi. Ta yi sauri ta sunkuyar da kanta kasa bata yarda sun kara hada ido ba. Ta ajiye ludayin da take juya kokon tayi sauri ta saka hijabin data cire ta dora akan cinyarta. Suhaif yayi murmushi ya jefa mata wasikar kan cinyarta ya ce "Ina daki ina jiran amsa nasan baza ki iya kwankwasa min kofa in fito in karba ba to sai ki dora akan wundon da kika ajiye mun dazu. "Bata ce masa komai ba kanta a durkushe a kasa tana ta murmushi. Ya dakko kofi a kwando ya mika mata. Ya ce "Zuba min kokon. Ta karba ta zuba masa ya karba ya tafi. Zumudin karanta me Suhaif ya rubuta bai barta ta gama juye kokon a kwanukan sha ba sai kawai ta rufe da faifai ta mike ta shiga daki. Ta tabbatar su Naja'at har yanzu barci suke haikan sannan ta zauna kan katifarta ta bude wasikar ta fara karantawa. Fuskarta kawai zaka kalla kasan tana farin ciki. Ta karanta ta sake maimaitawa, sai tayi doguwar ajiyar zuciya ta lumshe ido. Ta dade tana tunanin me zata rubuta masa. Bayan ta gama tunano meya kamata ta rubuta, sai ta jawo jakarta ta dauko biro da takarda ta fara tsantsara masa wasika. Ta fara da yi masa godiya game da alkawarin da yayi mata addu'a Allah Ya bata miji na gari mai sonta. Sannan tayi masa addu'a Allah yasa wacce yake so ta soshi sai dai ta bashi shawara ya kamata ya sanarwa wacce yake so kafin ya tafi kada yaje tunaninta ya dameshi. Ya kuma cire tsoro da fargaba da gudun ko ba zata soshi ba, ta tabbatar masa da cewa shi saurayi ne irin wanda kowacce *ya mace take addu'a Allah Ya bata kamarsa don haka tana tabbatar masa yaje ya tareta zata soshi kowacece yarinyar. Daga karshe ta bashi shawara ya guji zurfin ciki da yawa musamman a fagen so, domin a bari ya huce shi ke kawo rabon wani. Ta linke wasikar ta fito zaure, taga takalmansa abakin kofar dakinsa da alama yana ciki. Sai ta je ta dora wasikar akan takalminsa ta kwankwasa kofar sannan ta shige cikin gida. Suhaif na bude kofa sai yaga babu kowa yayi sauri zaisa takalminsa ya leka waje ko mai kwankwasa kofar ya fita sai yaga wasika. Ya durkusa ya dauka ya koma daki ya zauna ya bude ya fara karantawa. Wanan karon farin cikin daya lullube shi ya wuce yayi murmushi sai dai dariya. Ya kyalkyale da dariya shi kadai, ya mike tsaye yana kai kawo a tsakar dakinsa yana sake karanta wasikar. A zuciyarsa yana tambayar anya kuwa Iman ce ta rubito masa wannan wasikar ko kuwa shine bai karanta daidaiba. Ya sake murtsike idonsa yana karantawa yaga da gaske ne abun da yake gani. Sai ya koma ya zauna ya dauko biro da takarda ya fara rubuta mata wasika. Fargabar da yake a zuciyarsa ta kau, kai tsaye ya fayyace mata abunda yake ransa na game da soyayyarta data damki zuciyarsa. Sai dai yana rokarta don Allah taji tsoron Allah, Allah Yana kallonta kada ta boye masa ta fada masa gaskiya menene ra'ayinta game da soyayyarsa. Idan bata amince ba ta fada masa wannan ba zaisa ya damu ba kuma zumuncinsu na nan a matsayin kanwarsa ya dauketa. Daya gama rubutawa sai ya nade wasikar ya fito. Kafin ya fito tsakar gida sai ya hango Zubaida da Naja'at a bakin rijiya suna brush. Don haka sai yaji duk ransa ya baci bai so suka tashi daga barci yanzu ba. Ya koma daki ya dauko kofin daya sha koko ya fito. Maimakon ya kai wajen wanke-wanke da ya hango Iman a kicin sai ya nufi kicin din ya mika mata kofi, ta karba sai taga wasika ce a cikin kofin. Ya juya ya fita, Naja'at da Zubaida suka yi sauri suka duka suka gaishe shi. Ba tare da sakin fuska ba ya amsa musu, ya wuce ya fita kofar gida Iman ta zare wasikar ta soke a cikin zaninta sannan ta fito takai kofin wajen wanke-wanke. Ta shaidawa su Naja'at ga kokonsu nan a kwanan sha, suka amsa mata da "To mun gode. Iman ta shiga daki cikin sauri ta dauko wasikar ta bude ta karanta. Sai ta tsinci kanta da tsananin farin ciki, sannan ta sake tabbatarwa da kanta ashe wannan tsananin kunyarsa da take yawan ji ashe so ne, sai dai kash yanzu su Naja'at sun tashi sai dai wani lokaci. Ta bude can kasar jakar kayanta ta boye wasikun. Hankalin Suhaif ya tashi yaga har azahar Iman bata rubuto masa amsar wasikarsa ba. Duk motsin da yaji a jikin kofarsa sai ya leko yaga ko Iman ce ta ajiye wasika amma sai yaga wayam babu komai. Ya sake duba kan wundon dake zaure inda ta ajiye masa wasikar farko nan ma babu komai bata ajiye ba. Sai ya sake shiga damuwa da zulumi. Ya shiga cikin gidan baya ganin Iman tana daki a zaune. Da yamma ne ya hangota a kicin tana dora tukunyar tuwo. Naja'at tana daka daddawa, Zubaida na wanke-wanke. Gwaggo kuma na zaune a tsakar gida. Yazo ya zauna yaji duk hankalinsa baya jikinsa, Gwaggo na magana bai cika fahimtar me take ce masa ba. Ta dala masa duka a kafada ta ce, Wai kai yau meke damunka ne tun zancen tafiyar jiya ka bi ka susuce, kayi hakuri mana kasan fa halin mahaifinka sarai idan yace sai anyi to fa sai anyi gara ka kwantar da hankalinka kawai. Suhaif yayi murmushi ya mike tsaye ya ce "Ke ta tafiya kike Gwaggo ni abunda yake damuna yafi karfin damuwar tafiya. Ta ce "Meke damunka ka fada mun mana. Bai iya ce mata komai ba ya fice. Har dare bai ga amsar Iman ba sai ya tabbatarwa kansa Iman bata amince ba kuma tana kunyar rubuto masa a'a sai ya zauna ya bude sabon tunani mai dauke da tsananin bakin ciki. Bai iya cin abincin dare ba ko loma daya da yaga barcin ya gagara sai ya daura alwala ya dinga nafilfili yana addu'a yana kai kukansa wajen Ubangiji Ya taimake shi yayi masa agaji ya sami soyayyar wacce yake so. Hawaye ne ke kwaranya daga idanuwansa yayin da yake ganawa da Ubangijinsa. Shi kansa yana tsoron halin da zai shiga muddin Iman ta kishi har asuba yana zaune yana addu'a. Da yaji ana kiran assalatu sai yaji motsin mahaifinsa yana bude kofar gida zai je masallaci, yayi wuf ya fito suka dunguma suka tafi tare. Bayan an idar da salla wasu na zama suyi zikiri a masallacin har sai gari ya waye. Suhaif da mahaifinsa suka zauna suma aka yi zikirin dasu har sai da gari yayi tangaran sannan suka fito daga masallacin. A hanyarsu ta tahowa gida ne Suhaif yake bawa mahaifinsa hakuri akan zancen tafiyarsa bautar kasa da ya nuna baya so amma yanzu yayi tunani yaga yayi kuskure yanzu ya sawa zuciyarsa ba komai zaije din. Mahaifinsa yayi farin ciki ya dora masa da nasihohi masu ratsa jiki na kwantar da hankali. Suhaif ya wuce dakinsa, mahaifinsa ya shiga cikin gida. Suhaif na shiga daki sai ya kwanta ya runtse ido zatonsa zai iya barci saboda kansa yayi masa nauyi, idanuwansa suna masa tsaki-tsaki da alama dai barcin daya kwana bai yi ba ne yake tambayarsa. Amma ina! Barci ya gagara yazo, mummunar faduwar gaba data addabe shi idan ya tuna Iman bata amince masa ba. Bakwai da rabi dai-dai ya jiyo muryar Iman tana yiwa Gwaggo Sallama akan zata tafi makaranta saboda taron da za'ayi yau a makarantarsu har ana sa ran Mai Martaba Sarkin Gumel Alh. Ahmad Mohd Sani zai halacci taron bude wasu sababbin ajujuwa da masallaci da za'ayi a makarantar. Kasancewar Iman itace aka nada shugabar dalibai saboda kwazonta da kulawa da makarantar da take yi shine yasa, aka ce tazo da sassafe tasa yara su share filin makarantar a kamo bencina su fito dasu su shirya wajen da manyan baki zasu zazzauna. INA MUKU BARKA DA SALLA !!! Am sick, pls i need Ur prayers Reedwan Suraj Isma'il _____________________ YARENA ADDININA CI GABAN LABARIN Iman na fitowa zaure saita debi tsintsiyoyin dake wajen zuba shara ta kara gaba ta fita. Suhaif yayi firgigit ya tashi ya bude labulan Wundon dakinsa yana lekawa. Ya hangota sanye da hijabinta tasa nikaf ta rufe fuskarta da tsintsiyoyinta a hannu tana tafiya a nutse. Ya ce a ransa "Duk wanda yaci sa'a Allah Ya bashi mace mai addini irin Iman hakika yaji dadin duniya da lahira don ko yaki Allah Iman zata tuna masa hanyar bin Allah. Ya sake murtsike ido yana kallonta. Can a cikin zuciyarsa yaji ance "Ka bita ka tareta kuyi magana gar da gar mana karka cuci kanka. Ka tuna fa ita da kanta tace ka rage zurfin ciki musamman a fagen soyayya. A bari ya huce shike kawo rabon wani. Sai yayi wuf ya fito da sauri zaisa takalminsa ya bita. Abun daya bashi mamaki sai ga wasika a ajiye akan takalmansa. Yaji ajiyar zuciya sannan ya tsuguna ya dauka ya bude ai kuwa rubutunta ne. Sai ya koma daki ya zauna ya fara karantawa. Layin farko na wasikar gaisuwa tayi irin ta so da kauna. Suhaif ya lumshe ido yayin da lumfashin kauna ya fara dira a hunhunsa. Ya ci gaba da karantawa, yakan tsaya yayi dogon tunani harya tattaba jikinsa ya tabbata shine kuwa da gaske ko kuwa a mafarki yake jinsa. Sai yaga shi din ne ba mafarki ba ne. Iman ta fayyace masa sirrin zuciyarta cewar ta amince masa tana kuma sonsa fiye da tunaninsa. Ta bashi labari cewa ashe wannan kunyar data ke ji bata komai bace illa so da kauna, amma bata tantance ba sai bayan daya shaida mata yana sonta, sannan tasan ashe itama ciwo daya ne yake damunsu. Farin ciki da yayiwa Suhaif yawa sai ya kalli gabas ya yiwa Allah sujjada ya gode masa. Yayi masa kirari ya ce "Allah Mai jin kan bayinSa. Allah Kaine mai badawa a duk lokacin da kaso. Allah mai amsa addu'ar bayinsa, Allah kaine abin godiya, Allah na gode maka daka amsa addu'ata ka bani Iman. Sai yaji a ransa ya tsaya yana rubuta wasika ma ai bata lokaci ne yanzu sai dai yaje ya tari Iman gar dagar suyi magana. Amma a ina zai iya tsayawa da ita ba tare da *yan sa 'ido sun gansu ba? Sai ya tuna ai yanzu ba aji zata shiga ba share-share zasu je suyi me zai hana ya bita makarantar yaje suyi magana tunda kannensa suna gida ita kadai ta tafi. Sai ya fito yasa takalminsa ya nufi makarantar su Iman. Kananan yara ya tarar suna ta share farfajiyar makaranta. Ya waiga ko ina bai ganta ba sai ya tambayi wata rayinya ko ina Iman. Yarinyar ta ce "Yanzun nan muke yin shara sai tari ya turnike ta ta shiga ajinsu ta zauna. Suhaif ya ce "Ina ne ajin nasu? Ta nuna masa da hannu, ya nufi cikin ajin da sauri gabansa na faduwa yana tunanin meye sameta take tari? A can a karshen aji ya hangota ta kifa kai akan Tebur. Ta karasa gareta, yayi mata sallama ta dago da sauri gami da yaye nikaf din data rufe fuskarta ta mike tsaye ta gaishe shi taci gaba da sauraronsa a zatonta ko kiranta ake a gida. Yayi murmushi ya ce "Koma kiyi zamanki zuwa nayi in duba ki ance kina shara tari ya turnikeki kin shigo aji kin zauna. Lafiya kike tari? Ko kura ce ta yi miki yawa ta saki tari? Ko daman kina da asma? Iman tayi murmushi ta koma ta zauna. Suhaif ma ya zauna akan kujerar da ke gaban teburinta yana fuskantarta. Ta nisa ta ce "Kura ce ta sani tari bani da asma amma ina da ciwon kirji. Suhaif ya ce "Ai da baki tarki shara ba da kinbar yaran sunyi kina zaune kina kallonsu, ko da yake neman lada kike yi kema, nasan baza ki bar ladan nan mai tsoka ya wuce kiba ko? Tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa. Ya kara ce wa "Naga wasilarki wacce ta sani farin ciki naga ya dace in rubuto godiya sai naga biro da takarda baza su iya zana mun irin godiyar da nake miki ba gara inzo da kaina in gode miki. Domin ba karamin ceto raina kika yi ba da kika amince mun. Iman tayi shiru sai murmushi kawai take yi. Ya ce "Nasan a yanzu baza ki iya bani amsa ba amma nagode da kika iya zama kike fuskantata kika bude fuskarki nake kallon kyakkyawar fuskarki har kike min murmushi. Sai su duka suka kyalkyale da dariya. Sai tai sauri ta saki nikaf din ta rufe fuskarta. Suhaif ya mike tsaye ya ce "To nabar ki lafiya sai anjima idan mun zo ganin Sarkin Gumel. Naji ance kece za kiyi wa manyan baki tafsiri ko? To zamu zo muji. Kin ga dana iya karatu da sai in dinga ja miki baki kina fassarawa. Ba tace komai ba kuma ta rufe fuskarta balle yaga yanayin fuskarta amma daga dukkan alamu murmushi take yi, ya juya ya fara tafiya har ya kai bakin kofa sai ya juyo ya ce "na tafi fa. Sai yaga ta daga masa farin hannunta. Shima ya daga mata hannu sannan ya fita daga ajin ya nufo gida cike da farin ciki. Ya wuce cikin gidansu ya tarar da Gwaggo a zaune a tsakar gida tana cin dumamen tuwo. Naja'at na wanka, Zubaida kuma tana goge hijabinsu da abun gugar gawayi. Zubaida ta duka ta gaishe shi. Da yake yau yana jin farin ciki ya amsa mata da fara'a harda tsokanarta ya ce, "Lallai yau dole a fesa wanka a goge hijabi tunda za'aga Mai Martaba Sarkin Gumel ko Allah Zaisa dogari daya ya taya. Gwaggo ta harareshi ta ce "Dogari fa kace? Amma ka cika wulakanci ina laifin hakimai amma a Dogari zasu tsaya wadannan kyawawan *yan matan nawa danma Iman tana sa abu ta lullube fuskarta ai da duk bakin sai sun taya. Suhaif ya ji wani kaikayin kishi ance duk bakin zasu ce suna son Iman yayi sauri ya ce "Ai banda Iman da Naja'atu da Zubaida ne naga ana fesa wanka da guga. Gwaggo ta ce "Ko suma sunfi karfin dogarai karma kayi musu baki. Zubaida tayi dariya tace "Yaya Suhaif kasan Dogarai baza su tare mu ba sun san mu ba kalar su bane, kai ko *yar Hajja tafi karfin Dogarai. Suka kwashe da dariya. Gwaggo ta ce "*Yar tawa *yar Hajja kika raina? Suhaif ya ce "Aikuwa *yar Hajja ta fiku kyau abu daya zaku nuna mata kunyi sakandire ita kuma bata yi ba. Naja'at ce tayi sauri ta fito daga wanka don ta mayar da martani tana jiyo hirarsu daga ban daki. Tana fitowa ta ce "Wallahi *yar Hajja bata fimu kyau ba fari kawai ta fimu. Yaya Suhaif ya ma za'a yi ka kallemu kace dogari ne zai taya? Suhaif ya tsuke fuska ya gallawa Naja'at harara ya ce "Ke wuce ki bani waje. Idan ana wasa daku sai ku wuce gona da iri. Gwaggo ta ce "Kai kuwa wallahi shegen son girmanka ne yake hadani da kai inda Najib ya fika kenan. Idan baka yi wasa da kannenka ba da wa zaka yi? Yaje ya wanke hannunsa ya zo ya zauna a gaban Gwaggo ya sa hannu suke cin dumaman tare. Naja'at da Zubaida suka kama bakinsu suka yi sim suka shige daki ba su kara cewa komai ba. Bayan sun shirya tsaf suka fito suka yiwa Gwaggo sallama za su tafi makaranta. Suhaif ya tabe baki ya bisu da kallo ya ce "Kalli dalla har da goge kafa da sa sabon takalmi wai don za su ga Sarki. Gwaggo ta ce "A'a, wai ina ruwanka ne? Ka takurawa *ya*yan nana nawa shi yasa har yanzu sun kasa sakin jiki da kai suna ta dari-dari da kai. Har Iman ta zo ta tarar da yadda suke yi maka ita ma ta shiga wasan buya da kai, a ce kai da *yan kannenka babu maganar arziki sai gwasala da harara da tsawa da tsare gida, haba Babangida ka zamar musu dodo a gida kana tsorata su. Naja'at da Zubaida suka wuce suka nufi kofar fita ba tare da sun tsaya sunji abin da Gwaggo za ta fada musu ba, kafin Suhaif ya huce fadan da ake yi masa a kansu. Gwaggo ta yi ta yi masa fada bai iya ce maya komai ba tsananin yunwar da yake ji kasancewar bai ci abincin kirki ba jiya saboda fargaba da tashin hankalin rashin ganin amsar Iman. Yau kuwa ya ji dadi hankalinsa ya kwanta da ya ji amsar ta don haka fadan da Gwaggo take yi bai bata masa rai ba ko kadan don ba kasafai yake jin abin da take fada ba. Zuciyarsa na can na tuno masa da dadadan kalaman Iman da ta rubuto masa da kuma kyakkyawar fuskarta da lallausan murmushinta, sai ya tsinci kansa yana murmushi da annashuwa da annuri. Gwaggo ta yi mamaki tana yi masa fada yana ta murmushi yana fara'a ta ce "Ka zamar da ni kakarka ko Babangida wato dariya nake ba ka? Ya nisa ya ce: "Gwaggo yi hakuri ki kwantar da hankalinki in sha Allah a gidan nan na daina bacin rai balle *ya*yanki su dinga ba ni haushi wallahi daga yau za ki ga ina ta farin ciki da fara'a. Ko ba haka kike so in dinga yi ba? Ai shi ne yanzu na fara fara'ar don ki san na ji fadanki. Su duka suka kyalkyale da dariya ta ce "Ka dai zamar da ni Kakarka kana min shakiyanci iri-iri. Suhaif ya mike yana sudar hannu ya ce "Da gaske nake zaku ga canji a gidan nan daga yau sai farin ciki da annashuwa za ki ga ina ta yi. Ya karasa wajen wanke-wanke ya wanke hannunsa ya juyo ya dubi Gwaggo wacce har yanzu take zaune da kwanan tuwo a gabanta ya ce "Bari in shiga dakina in dan yi baccin awa daya sannan in tashi in yi wanka in tafi makarantar su Iman wajen taro. Gwaggo ta ce "Wanne irin baccin ne na awa daya kuma, yaushe garin ya waye da za ka yi wani bacci kuma? Suhaif ya ce. Don dai ba ki san irin baccin da nake ji ba da kin ce in yi ta bacci har azahar. Ya nufi dakinsa. Ya sa hannu zai bude dan karamin kwadon da ya sakale kofar dakin sai ya ga wata takarda an soke a jikin kwadon kofar dakin, ya yi matukar mamakin ganin wannan wasika. Ya ce a ransa "A'a Iman ce ta dawo ta sake sakale masa wannan wasikar ko kuwa aikowa ta yi aka kawo masa? Ya bude takardar da sauri ya ga lallai wasika ce kuma tasa ce. Tashin farko ma abin da aka rubuta My Dear Yaya Suhaif. Ya yi murmushi yayin da farin ciki ya lullube shi marar misaltuwa. Ya girgiza kai ya ce a ransa. "Lallai Iman ta kamu da sona ba da wasa ba, Allah ya kara mata fiye da haka don na san ko kama kafar son da nake yi mata ba ta yi ba. Ya linke wasikar ya bude kofar dakin ya shiga ya tura kofar ya rufe ya haye shimfidar ya kwanta zuciyarsa cike da farin ciki. Yasan babu tantama wannan wasikar zata kara masa armashin dimbin baccin daya addabi idanuwansa. Zata sa masa kayatattun mafarkan so da kauna. Ya gyara filon da yake kwance sai mamaki mai dimbin yawa ya sake hawa kansa ganin wasikar an rubuta da harshen hausa kuma Iman bata iya rubutun hausa ba. Yaushe ta iya hausar ma balle ta rubuta? To amma bai yi mamaki ba watakila ta iya ko bai sani ba, ko kuma tasa a rubuta mata ne saboda kawai tana sha'awar yarensa hausa, daman idan kana son mutum duk wani abu nasa kana sonsa. Wasikar kamar haka:- [[f9.heart]] My Dear Yaya Suhaif. _____ "Gaisuwa irin ta addinin Musulunci, hade da ta *yan uwantaka da tsananin so da kauna. Yau Allah Mai kowa Mai komai ya bani ikon in bayyana maka sirrin zuciyata. Wani boyayyen al'amari mai ban mamaki da firgitarwa daga karshe kuma mai farin ciki. A matsayina na *yar uwarka kanwarka na kasance na dade ina dauke da wani ciwo mai illar gaske ga lafiyata, wanda ya dade yana cutar dani yana damuna ina ta sake-saken ina zan samo maganin cutar nan sai naga babu likita ko malami ko bokan da zai iya warkar dani sai kai saboda ciwon a sanadiyyarka ne kuma kai ne kasan maganinsa. Yaya Suhaif na dade ina sonka tuntuni na rasa yadda zanyi in fada sai yanzu naga ya dace in fada maka don naga zaka tafi bautar kasa kusan shekara guda gara kasan kabar marar lafiya a gida. Mai sauraran ka kawo mata maganin da zata warke shine ka amsamin bukatata ka agajeni ka kaunaceni jini daya ba wasa bane. Kanwarka a da, Masoyiyar ka a yanzu Zubaida Usman {Mrs. Suhaif} [[f9.heart]] Yai firgigit ya wurgar da wasikar ya tashi zaune ya fada a bayyane "Zubaida! Zubaida!! Zubaida kike sona? Kin cuce ni, kin cusgunawa rayuwarmu da Iman. Zubaida dan me zaki dauko hanyar sa za'a bata zumunci da Iyayenmu? Bana sonki Zubaida ba zaiyu ba. Ya ji kwalla mai radadi tana zubo masa ya mike tsaye a fusace yana kai kawo daga karshen bangon dakin zuwa kofar dakin yana zancen zuci wani lokaci a bayyane. Ya dunkule hannayensa biyuu yana dukan bango. Ai mun afuwa sakamakon yanayin jikina ya sa ban yi da yawa ba. Ina tare daku Reedwan Suraj Isma'il _____________________ YARENA ADDININA CI GABAN LABARIN Ya shafa keyarsa ya juyo ya leka wundo yana duban hanya yaga ta ina su Zubaida zasu bullo yanzu yayi wasan kura da ita har Naja'atun yasan bakinsu daya. Ya ce a ransa "Muddin Gwaggo da Baba suka ji wannan maganar to fa kashinsa ya bushe dan kamar anyi an gama kada ma iyayen Zubaida suji labari ai sai sunfi kowa murna saboda suna son Zubaida sosai. Da wanne ido zan kalli Najib dan uwana kuma abokina ince bana son kanwarsa uwa daya uba daya? Dubi irin kauna da mutuncin da Babansu, Baba Usman ya nuna mun kamar shi ya durkusa ya haifeni tun daga Nursiry har Jami'a shi yake biya min ya rikeni tsakani da Allah. Bani da kwabo, bansan yadda ake samowa ba duk daga aljihunsa nake samu, Duk sanda naji rashin kudi kawai sai in nufi wurinsa zai bani ko nawa nake so har wani lokacin ya hana dansa Najib ni ya bani. Da wanne ido zance bana son *yarsa Zubaida? Zubaida me yasa zaki mun haka? Danme sai ni kike so ba wani ba? Yaya zanyi da son Iman din daya ke kokarin ya lahantani gashi na furta mata itama ta kamu sai ta dauka yaudararta nake, bata da uwa ba uba ba dangi ni kadai zan aureta in rufa mata asiri in zama farin cikin rayuwarta. Na zame mata uwarta, ubanta, mijinta, danginta. Bazan so wani ya auri Iman ba in bani ba. Ba zai yuwu ba, bazan iya rayuwa ba Iman ba abar kaunata, bazan iya auran *yar uwata kuma in wahalar da ita ba. Don babu wannan soyayyar a tsakaninmu. Haka Suhaif ya kasance a daki shi kadai kamar zautacce, ya kasa zama ya kasa tsayuwa ya kuma kasa kwanciya yana magana shi kadai. Idonsa yayi jajawur kamar tattasai ga rashin bacci ga tsabar tashin hankali. Zuciyarsa tafasa take kamar zata kone. Jiran isowar su Zubaida yake kawai ya dirar mata don zai iya kacaccalata yake ji kamar yadda take shirin kacaccala rayuwarsa yanzu nan. Karfe biyu dai dai taro ya watse kowa ya kama gabansa. Yana tsaye a kofar gida bayan ya fito daga masallaci sunyi sallar azahar yana duban hanyar da zasu bullo. Sai ya hango Iman ita kadai ta nufo gida. Murmushin dole Suhaif ya kirkiro ya yiwa abar kaunarsa. Ta gaisheshi ya amsa mata, tayi kamar ta tambayeshi me yasa baije wajen taron ba don bata gan shi ba sai taji ta kasa yi masa magana ta wuce cikin gida kawai yaci gaba da tsayuwa yana dai ta sauraran isowar su Zubaida. Yaji shiru har biyu da rabi, ya juya zai shiga cikin gida zai tambayi Iman a ina tabar su Zubaida sai ya hango suna tafe. Suna karasowa inda yake tsaye ya kula da irin kallon da Zubaida take yi masa mai kunshe da kauna da tsananin kunya. Ya buga musu uwar harara lokaci guda suka dukar da kansu kasa. Naja'at ta ce "Sannu Yaya. Bai amsa mata ba suka wuce sum-sum zasu shiga cikin gida. Ya juyo a fusace ya ce "Ku shiga dakina ina son ganinku. Nanfa suka ji gabansu ya yanke ya fadi don yadda suka ga fuskarsa ba annuri lallai baiji dadin wasikar ba dole ne shima ya bata musu rai kamar yadda suka bata nasa. Gashi Gwaggo bata san sun dawo ba tana dakinta balle tazo ta taimake su. Me kwatarsu yau sai Allah. Cikin rawar jiki suka shiga dakin, ya biyo bayansu ya shiga ya mayar da kofa ya datse. Ya juyo a fusace ya kallesu yaji haushinsu ya kara kamashi musamman Zubaida. Ya daka musu tsawa mai firgitarwa ya ce "Duk kumin knell down ku daga hannu ku rufe ido. Ya dauko ashar ya narka musu. Sai suka hau rawar jiki suka yi abunda ya umarcesu. Ya koma kan kujera ya zauna yana fuskantarsu, yayi shiru ya rasa ta inda zai fara. Can yayi wani dogon tsaki ya girgiza kai ya gyara zama ya ce "Naja'atu da shawarar ki Zubaida ta rubutomin wannan wasikar? Kada ki kuskura kimin karya zan tattakaki idan baki fadamin gaskiya ba. Cikin rudani da fargaba Naja'at ta ce "Zubaida ta dade da fadamin tana sonka nayi mata nasiha na bata shawara karta kuskura ta shaida maka nasan ma ba zaka yarda ba kuma idan ka ji ba ita bama ko ni sai raina ya baci muka bar zancen. Kwannannan muka tace gaskiya ko zaka kasheta zata rubuta maka don ita tana sonka. Shine muka yi shawara ta rubuta ta soka a jikin kofarka. Ya juya ya dubi Zubaida ya ce "Na miki kama da sa'anki da zaki ji kina tsananin sona a ranki? Ta yi shiru bata yi magana ba, sai hawaye da yake zubowa daga idanuwanta. Ya daka mata tsawa da karfi mai firgitarwa ya ce "Ki bani amsa ba kukan munafunci nace kiyi mun ba? Cikin shesshekar kuka ta ce "A'a Suhaif ya ce "To dan me zaki dubi kwayar idona ki ajiye mun wannnan wasikar ta soyayya. Kamar yadda ba za ki iya rubutawa Najib ki ce kina son sa da aure ba, haka kamar yadda aure ya haramta tsakanina da Naja'atu ina so ki sa wa ranki babu zancen aure a tsakaninmu ko soyayya. Idan na sake jin wata kalma ta so daga bakin ku sai na lahanta ku munafikai. Sai shesshekar kukan Zubaida ne yake tashi. Can bayan *yan mintoci babu wanda ya iya magana sai Suhaif ya ce "A cikin iyayen mu wa kuka sanarwa da wannan maganar? Naja'at ta yi caraf ta ce "Wallahi babu wanda ya sani ko Gwaggo ba mu fada mata ba. Iman ma ba ta sani ba ni da ita ne kawai muke maganar. Suhaif ya ce "Ko a Kano ba ku fadawa kowa ba? Naja'atu ta ce "Ba mu fada wa kowa ba. Suhaif ya yi ajiyar zuciya mai dauke da kwanciyar hankali, can ya nisa ya ce "Alhamdulillahi, babu wanda ya ji ko? To ba na son in kara jin wannan kalma ta so daga gare ki Zubaida balle wani ya ji, ka da ku kuskura ku fada a cikin gida a nan ko a Kano saboda abu ne marar yiwuwa ni ba sa'anki ba ne da za ki ce kina sona muddin kuka daga zancen wani yaji, hakika za ku ga bacin raina, kunga yanzu sakwa-sakwa na yi muku. Don haka ku tashi ku tafi zance ya wuce, kada a sake. Naja'at ta mike da sauri ta duka ta yi godiya ta fice. Zubaida ce take tafiya a hankali tana harare-harare tana bata rai, har ta fita. Suhaif yana harararta cike da tsantsar takaici, bayan ta fita ya rike baki yana girgiza kai ya ce a ransa "Lallai yarinyarnan daga dukkan alamu ba ta hakura da ni ba, ba ta ji fadanda na yi mata ba. Wai yaushe na sakar mata fuska har ta shaku da ni ta fara so na? Yarinyar nan za mu sa kafar wando daya da ita a gidan nan. Suhaif da Iman sun ci gaba da son junansu amma babu wata alama da *yan gidan za su gani su ce akwai soyayya a tsakaninsu, sai dai a boye suke rubuta wa junansu wasiku. A rana daya sukan musayar wasiku kamar sau biyar. Kowanne na fayyace me yake ji a ransa. Kafin ka ce kwabo kwayoyin sinadaran so sun yi yado a zuciyoyinsu. Kowannensu yana jin ba zai iya rayuwa ba idan babu dayan. Yadda Iman take burge Suhaif haka Suhaif yake burge Iman. Duk da kalar fatarsa baki ne yana yi mata kyau sosai. Halayensa ma sun yi mata, yana da ilimi a dukkan bangarorin, ga shi da fara'a, ga rikon addini ga tausayi, ga bin iyaye, ga shi ya iya kalaman soyayya. Kwanci tashi, lokacin tafiyar su Suhaif bautar kasa ya karato don haka, kafin ranar dole Suhaif zaije Kano ya je makaranta ya karbo takarda, sannan ya wuce. Kallo daya za ka yi wa Suhaif ka san hankalinsa a tashe yake, ba bacin ran tafiya kudu ne ya dame shi ba, rabuwa da gida da iyayensa da *yan uwansa da uwa uba wacce yake matukar kauna da bege a zuciyarsa wato Iman. Matukar damuwa ta tabbata a zuciyar Iman, amma sai ta danne ba ta fito da shi a fuskarta ba, gudun kada *yan gidan su gane. Tana kicin tana dumamen tuwo ta jiyo muryar Suhaif a tsakar gida yana yiwa su Gwaggo sallama. Zubaida da Naja'atu suka yi farat suka fito daga daki suka nufi wajen Suhaif bayan sun gaishe shi sai suka yi masa fatan Allah Ya kiyaye hanya. Iman ta ji wani mummunan faduwar gaba da bacin rai ya kuntso zuciyarta, ta gyara hijabinta ta fito a sanyaye, yayin da Suhaif ya zuba mata ido yana duban ta. Ta sunkuyar da kanta kasa ta duka ta gaishe shi ya amsa gami da cewa. "To Malama Iman mu dai zamu tafi sai a saka mu a cikin addu'a Gwaggo tayi murmushi ta ce "Ai kuwa kasan inda ya kamata ka roki addu'a domin Iman gwanar addu'a ce zata yi maka kuwa. Su duka suka yi dariya harda Iman din cikin sanyayyiyar murya Iman ta ce "Insha Allah addu'arka ita ce farko a cikin jerin Addu'o'in da nake yi. Suka sake yin dariya dukkansu. Suhaif ya ce kinyi alkawari? Iman ta ce "Insha Allah na dauki alkawari. Zubaida da Naja'at suka hada idon gulma, sunyi mamakin yadda Yaya Suhaif yake ta yiwa Iman fara'a haka da kuma yadda Iman duk wannan kunyar tata ta tsaya suke magana haka wasa da dariya. Yaushe suka saba? Alamar tambayar da suka ajiye a zuciyar su kenan sai sun kebe zasu tsarge amsar. Iman ta durkusa ta karbi Jakar hannunsa ta ce "Kawo in tayaka. "Naja'at da Zubaida tace. Zo muma mu dauki hijab dinmu mu raka shi bakin titi. Suka shiga daki da sauri suka sako hijabansu kafin su fito Zubaida ta radawa Naja'at ta ce. "Wannan Iman din ta cika feleke da shisshigi da cusa kai. Kalli yadda ta shigewa Yaya Suhaif har suka saba itace ma zata rakashi ba mu ba. Naja'at tayi ajiyar zuciya ta ce "Zo muje rakiyar mu dawo mu tattauna. Suka fito daga daki suka iske Iman da Suhaif da Gwaggo a tsakar gida bayan sun fito sai suka dunguma suka fice "Soron kofar gida Gwaggo ta tsaya da rakiyar sai addu'a take yiwa Suhaif da fatan Allah Ya kiyaye hanya ya kareshi daga sharrin Mutum da aljan. Yana amsawa da amin, suka juya suka tafi ita kuma ta shigo gida tana sharbar kuka na bakin cikin rabuwa da danta. Zubaida ta mikawa Iman hannu ta ce "Kawo muma mu dauka ko tunda rakiya muka fito yi muma "Iman tayi murmushi ta ce "Haka ne, to gashi. "Wata uwar harara Suhaif ya dakawa Zubaida ransa ya baci amma baiyi magana ba suka ci gaba da tafiya. Naja'atu ta zo gefensa Zubaida ma ta dawo daya gefen nasa suka sashi a tsakiya. Iman ta koma baya tana biye da su. Naja'atu ta ce "Yaya Suhaif awa nawa ne zuwa Ogun? Naga akwai nisa ko? Suhaif ya tsuke fuska ya ce "Oho. Zubaida ta ce "Dama kai aka kai Kaduna, aka tura Yaya Najib Ogun din. Ya kalleta ya kawar da kai yasan dadin baki kawai take masa, ta kula da abin da yafi so, ya juyo ya dubi Iman ya ce "Ya kika tsaya daga baya? Matso kusa da *yan uwanki mana. Iman tayi murmushi ta karasa ta jeru da su suka ci gaba da tafiya. Har suka isa bakin titi babu wacce tayi magana. Basu dade da tsayawa ba sai ga Bus zata je Kano Suhaif ya tsayar da ita sannan ya mika hannu ya karbi jakar kayansa daga hannun Zubaida. Ya dubesu su dukkansu yayi murmushi ya ce "To na tafi, sai Allah Ya sadamu da alheri. Abunda nake so da ku kuyi karatu sosai kuyi amfani kuma da abunda ku ka koya, don kunyi babbar sa'a da Allah Ubangiji ya baku ilimin kur'ani. Kun sauke, kun sake saukewa yanzu kuna hadda kun kusa haddace littafi mai tsarki. Zubaida da Naja'at kuna neman admission a B.U.K kuje ku karbo sakamakon jarabawar Secondry. Kafin ku sami admission ku dinga dauko littattafanku kuna bita. Sannan ku hada kanku ku duka ukun bana so a ware daya, idan nazo na tarar da wata magana sabanin yadda nace rai zai baci. Su duka suka amsa da "To a cikin ladabi. Ya dubi Iman yayi murmushi tayi murmushi ta daga masa hannu. Ya juya ya tafi ya nufi cikin mota Zubaida da Naja'at suka ce "Allah Ya kiyaye hanya, a gaishe da Yaya Najib da Mama da Baban Kano kafin muzo. Ya shiga mota ya tafi suka juyo suka nufi gida. Sun zo daidai wani lungu Zubaida ta dubi Iman ta ce "Ki je gida ki fadawa Gwaggo zamu je gidansu Raiha kawarmu. Iman tayi murmushin nan nata da yake kara fito da kyakkyawar fuskarta ta ce "To sai kun dawo, ku gaishe min da Raihar dan Allah, suka amsa mata da "Zata ji. Suka shige lungun ita kuma ta mike ta nufi gida. Ana saura kwana biyar Sallar azumi Suhaif ya dira a Kano. Ko zama baiyi ba saiga Najib shima daga Kaduna yazo Sallah suka iske Mama a falo, Mama tayi dariya ta ce "Af kamar tare kuke? Amma fa kunci sa'a da suka barku ku ka taho tun yau. Suhaif ya ce "Aini ko basu barni ba na fadawa Oganmu tahowata kawai zanyi. Ta ce "Ai gara dai da ka bari suka barka baka taho ba, ai komai yana da doka. Najib ya gaishe da Mamarsa, Suhaif ma haka. Sai suka mikawa juna hannu suka tafa. Suhaif ya ce "Kalleka dan Allah har wata uwar kiba kayi daga zuwa bautar kasa. Najib yayu murmushi ya ce to kai kuwa ai Kaduna gida ce YARENMU daya ADDININMU daya. Su duka suka kyalkyale da dariya. Mama ta ce "Wannan dai tsokanar Suhaif kake dan kasan baya son kudu. Suhaif ya ce "Kyaleshi Mama yazo Ogun yaga Musulmai, hausawa, duk yadda nake tunani ashe ba haka bane. Ramar da nayi bata komai bace Azumi ne. Najib ya ce "Ai nima ina Azumin, kai duk tsiyarka na fika jin dadin garin da nake ka ji ko, komai yawan Musulman Ogun basu kai arewa ba. Suhaif ya dubi Mama ya ce "Baba ya fita ne? Mama ta ce "Ya tafi Umara, ai ba a Nigeria zaiyi sallah ba. Ga kudin kayan Sallarku can ya bari, ya ce idan kun zo sallan a baku idan baku zo ba a suyo a dinka muku idan ya dawo zai kai muku ziyara sai ya tafi muku dasu. *Yan Doko ma tun kafin ya tafi duk an diddinka musu an kai musu. Suhaif ya ce "Allah Sarki, Allah Ya saka da alheri. Ba dan yamma tayi ba da yanzu nan zamu kasuwa mu sayo dan mu sami dinki. Najib ya ce "Sai dai gobe muje da wuri mu suyo saimu wuce wajen mai dinki ai ko ana gobe sallah Tijjani tela zai yi mana dinki. Suhaif ya ce "Sai dai in dawo gobe muje kasuwar amma ni yau in Allah Ya so a Doko zan sha ruwa. Mama ta ce "Dan wahala? Kaje yau ka dawo gobe ba zaka bari gobe daga kasuwa ka wuce ba? Suhaif da Najib duka suka kwashe da dariya. Suhaif yadau jakarsa ya nufi dakinsu, Najib ya dauki tasa jakar suka nufi daki. Najib na cewa "Ke dai Mama yi shiru baki san me yasa yanzu Suhaif yake son Doko ba. Sallar la'asar kawai Suhaif yayi ya dauki Jakar kayansa ya fito Najib ya rako shi. Har yanzu Mama tana falo a zaune, ta kira *yan aikin gidan tana zanawa kowacce aikin da zata kama yi na hidimar kayan shan ruwa. Suhaif ya duka ya ce "Mama na fito zan tafi sai gobe in Allah Ya kaimu zan dawo, direba na nan ko ya tashi zai mika ni tasha? Mama ta ce "Kai dai ka dage saika tafinko? Danlami direba baya nan saboda Azumi da wuri nake cewa ya tafi. Ka dauko makullin motar a dakina kan fridge ka tuka ka tafi tunda gobe zaka dawo. Daman Babanku ne baya so in dinga baku mota yafi so ku gama bautar kasa, kuna samun aiki ya rarraba muku mota. Cewa yayi yanzu kawunanku samari rawa yake amma idan kun gama bautar kasa kun fara aiki kun mallaki hankalin kanku. Suhaif ya ce "Ba komai Mama zan hau achaba inje tasha har na kai gida ba'asha ruwa ba, gobe kuma tunda Motar Kano bata wuya zan dawo. Ai mun kusa gamawa har a bamu tamu ta kanmu. Najib ya ce "Wallah Baba yayi mana yawa, wai sai mun fara aiki zai bamu mota. Me kenan? Ai a lokacin zamu iya saya ma da kanmu. Yanzu ya kamata a bamu, duk mun kode a motar haya. Aini da in zauna kwam direba na tukani gara in tari achaba in hau, shi yasa ma bana shiga motocin gidan nan. Mama ta ce "Ka santa kuma. Ni dai na yi iya kokarina Babanku ya ki yarda ya saya muku yanzu. Suhaif da Najib suka fita zuwa bakin titi. Ana kiran Sallar Magruba Suhaif yayi sallama a gidansu Doko. Gaba dayansu suna tsakar gida kowa yana kacaniyar buda baki. Sallamarsa ce ta ja hankalin kowa yana duban mai shigowa. Duk da sun so su dauki muryar. Baba yayi alwala ya dauki carbinsa zaije masallaci, Iman tana alwala a wajen rijiya, Zubaida tana tace zobo, Gwaggo ta gama suyar kosai tana rabawa, Naja'atu kuma tana zaune tana shan kunun tsamiya. Sai gaba suka hau cewa sannu da zuwa yau kaine a gari? Na ji dadin Addu'o'in ku gareni sosai Allah Ya bar zumunci na gode. Sai kuma wata shawara, dan Allah kada a ce wani abu, da yawa daga cikin masu rubuta sunan Allah anan page ba sa son farawa da babban baki dan Allah a gyara saboda sunan Allah ba abin wasa ba ne. Na gode Na ku angon Iman jini da hanta..... Lolx Reedwan Suraj Isma'il >>>>>>>>>>> YARENA ADDININA ____CI GABAN LABARIN Iman ta gama alwala sai ta zauna tayi shiru tana tunanin irin farin cikin da taji na ganin Suhaif abun baya misaltuwa. Ya ajiye jakar kayansa ya dauki dabino guda daya a kayan shan ruwa da aka jere a tsakar gida yaci. Ya gaishe da Babansa da Gwaggo. Naja'at da Zubaida suka gaishe shi. Ya karasa wajen rijiya ya dubi Iman yayi murmushi ya ce "Iman ba gaisuwa? Maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin data tsunduma. Tayi murmushi ta ce "Ina jira ku gama gaisawa ne sai in gaisheka. Ta gaishe shi ta dauki buta da sauri ta cika masa ta durkusa ta mika masa sannan ta wuce daki ta tayar da ikamar sallah. Bayan kowa yayi sallah aka zauna aka sha ruwa tare a tsakar gida. Gwaggo kwananta daban. Iman, Naja'at da Zubaida kwano daya suke ci. Baba da Suhaif tare suke ci, ana ci ana hira. Suhaif ya ce "Wannan sallar me aka fi yayi ne? Naja'atu tayi farat ta ce "Yaya Suhaif ai mu wannan sallar munfi kowa chabawa kayan sallarmu kala biyar ne tsadaddu. Dadi ya rufe Suhaif daman ya lura Iman bata da wasu hadaddun kaya na kwalliya duk da dai shigar dogon hijab tafi yi. Amma ai tana sako riga da zani masu kyau a ciki idan ta cire hijabin ana gani. Ya ce "Haba! Dakko in gani, lallai ku *yan gata ne kayan sallar kala biyar? Naja'atu ta tashi ta shiga dakin Gwaggo ta dauko wata katuwar leda a shake da kaya ta zazzage akan tabarmar da Suhaif ya ke. Dai dai lokacin da aka kawo musu wutar lantarki dan da sai fitilar kwai. Suhaif ya ce lallai *yan Nepa ma sun san zanyi kallon kayan sallah shi yasa suka kawo wuta. Sai gaba daya suka kyalkyale da dariya. Suhaif da Naja'atu suka fara warware kaya. Naja'at ta ware kala uku-uku guda biyu ta ce wannan kala uku-ukun ni da Zubaida Baba na Kano yayi mana. "Ta ware wata atamfa Nichem guda biyu iri daya ta ce "Wannan Hajja Kakarmu tayi min ni da Zubaida. Sannan ta ware wata atamfa Code Boire ta ce "Wannan mu uku Baban nan gidan yayi mana ni da Zubaida da Iman. Suhaif ya ce "Kala daya na gani na Iman ina nata na wajen Baban Kano kala uku da kala daya wanda Hajja tayi muku? Naja'atu tayi shiru can ta ce "Mu biyu suka yiwa banda Iman. Iman ta sunkuyar da kai kasa, Baba da Gwaggo ma sai kunyar Iman ta rufesu. Suhaif yaji ransa ya hau tafasa don bakin ciki. Ya dubi *yan matan ya ce "Ku tashi ku shiga daki, ku bamu waje muna magana. Naja'at ta tashi ta hada kayan sallarsu ta nufi dakin Gwaggo inda suka ajiye, Zubaida da Iman suka kwashi kwanukan abincinsu suka shiga dakinsu. Suhaif ya ce "Haba Baba, haba Gwaggo yanzu *yan marainiyar Iman din nan baza'a riketa tamkar *ya ba? Wa take dashi a duniya yanzu wanda ya wuce ku? Baba ya dakatar dashi ya ce "Kai tsaya Malam kafin kayi mana wa'azi sai ka tambaya. Shin a cikin kayan da aka nuna maka baka ga kala dayan dana yi musu su duka ukun ba? To abunda Allah Ya horemun kenan ban ware Iman ba. Bani da hujjar da zan aikawa Usman Baban su Zubaida in ce suyi kayan sallah da wata bakuwa. Aka bibiyama bai san da ita ba. Dan duk zuwan da yake yi yana ganinta su gai gasa bai taba tambayar wacece wannan ba dan bai kawo aka wai a gidan ake rikonta ba. Gwaggo ta ce "Hajja kuwa su uku ta sayawa atamfa na dauka da Iman ashe dayar ta *yar Hajja ce tayi musu iri daya. Na yi magana ta ce min bata yi niyya ba baza ta dinka da Iman ba. Ya zanyi mata? Suhaif ya tashi daga cin abincin, bacin rai yasa ya fita daga ransa. Ya leka dakin da suke zaune ya kwallawa Naja'atu kira ta fito. Ya ce ta dakko masa *yan kwalayen kayansa guda hudu da ba'a yi da Iman ba. Ta je ta dauko da sauri ta kawo masa ya karba, ya dauki jakar kayansa ya wuce dakinsa. Naja'atu taje gurin Gwaggo tana tambayarta "Me zaiyi da *yan kwalayen? Gwaggo ta ce "Watakila sayo mata zaiyi. Baba yayi dariya ya ce "Ina yaga kudi? Zai je dai ya kara gani. Washe gari da sassafe Suhaif yayi sallama yace zaije Kano. Bai dawo ba sai ana gobe Sallah. A daki ya sami Gwaggo ita da Zubaida, Naja'atu da Iman an aike su. Bayan sun gaisa saiya zazzago kayan ledar da hannnunsa. Saiga kayan mata a dinke irin nasu Naja'atu kala hudu. Sak irin na su, dinkin wannan ma yafi nasu kyau da tsada. Surfani ne tsadadden gaske. Zubaida ta ce "Kai wadannan dinkunan na waye? Sun yi kyau gaskiya. Suhaif yayi murmushi ya ce "Da gaske sun yi kyau? Zubaida ta ce "Wallahi sunyi kyau sosai daman irinsu nafi so Mama tasa aka yi mana wadancan. Na waye wadannan din? Suhaif ya ce "Na Iman ne. Kamar an watsa mata wuta haka ta zabura ta wurgar dana hannunta ta tsuke fuska ta hau harare-harare. Zaka iya ganin bakin cikinta a baiyane. Gwaggo ta yi murmushi ta ce "Allah Ya saka maka, kaga yanzu sai su fito dukkansu ukun kayansu iri daya. Amma fa ka iya rigima Babangida ina ka samo kudi haka? Ince dai kai ka sami kayan sallar kai? Suhaif ya mike ya fita yana cewa "Idan tazo ki bata ni ai ba yaro bane, ba sai na saka kayan sallah ba. Da Iman ta dawo aka nuna mata kayan sai ta fashe da kukan murna. Su Naja'atu da Zubaida kuma yanzu suka tabbatar da abunda suke zargi Yayansu son Iman yake don haka sun dasa tsanar Iman a ransu, sai harararta suke. A boye Iman ta rubuta wasikar godiya mai dauke da kalaman so da kauna ta turawa Suhaif daki. Dolen su Naja'at suka saka kaya iri daya da Iman ranar Sallah saboda tsoron Suhaif. Da niyyarsu duk ranar da ta sa wannan su kuma sai su ki saka irinsa sai su saka wani. Amma babu yadda za su yi kayansu iri daya ranar sallah haka duk inda za su je tare suke zuwa, amma fa suna raina kansu idan suka jera. Iman ta yi kyau sosai, kyawun da duk garin babu wanda idan ya kalle ta ba zai sake juyowa ya sake duban ta ba. Dolensu suke jerawa da ita saboda Suhaif ya ce, su je tare, sai dai Zubaida ta sha yarwa Iman bakar magana a hanya, ita kuma sai ta yi shiru ba zata rama ba, babu wanda zata fadawa kuma. Suhaif ya kashewa Iman kudin kayan sallarsa kakaf har da neman ciko ya yi a wajen Najib. Haka yayi sallar babu sabon kaya, nasa ya wanke ya goge ya sa ya je Idi ya dawo ya ci tuwon sallah ya kwanta a daki yana karanta wasikun Iman shi ne babban farin cikinsa a yau ranar sallah. Ya ba wa kannensa sababbin kudi da ya canjo daga Kano. A takaice hoton Iman yake so yadda ta yi kyau da sallar nan ya fake da wai su hadu su dau hoto su uku su kawo masa. Bayan Sallah da kwana uku aka ce su Suhaif su koma Ogun, idan ya tafi ba zai dawo ba sai sun gama. Suhaif ya tafi ya bar Iman a gida duk *yan matan sun tsaneta, biyayya take yi musu tun karfi, amma komai ta yi sai a ce ta yi laifi, sai ta yi sauri ta ba su hakuri don ta zauna lafiya da kowa. Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah, su Suhaif sun kammala bautar kasarsu. Allah cikin ikonSa sai ga Suhaif yana bakin cikin rabuwa da *yan Ogun saboda ya saba da su, mutane ne masu kirki. Sun yi masa mutunci ya saba dasu su ma haka. Bayan dinbin kyaututtukan da suka dinga ba shi, sun dauki hotuna saboda tarihi, dukkansu ba a son ransu suka rabu ba. Suhaif ya dawo gida ya iske su Iman lafiya kalau. Kamar yadda Iman ta saba tafiya makaranta da wuri, haka yau ma ta tashi da wuri ta gama aikin gida ta yi wanka ta sa hijabinta ta dauki jakar makaranta ta yi wa Gwaggo sallama, ta nufi makaranta ba tare da ta jira su Naja'atu ba, don sai fitowarta ma suka shiga wanka. A wajen wata mai kosai ta hango Suhaif da wani abokinsa suna saya. Yana hango Iman ya nufo inda take cike da fara'a yana cewa "Ka ga masu himmar makaranta, har zaki tafi? Iman tayi murmushi ta ce "Ai kuwa yau ma ban fito da wuri ba, tara fa har ta gota, wata rana kafin tara na je. Ta gaishe shi, gami da *yar harara ta ce "Kosai ma ka zo saya ko? Tuwon gidan namu ba za ka ci ba, shi ke nan, na yi fushi ma mu ma mun daina dafawa da kai, tunda ba ka son namu babu dadi ka fi son na sayarwa. Suhaif ya bude baki yana salati fadi ya ke: "Yi hakuri wallahi ba ni zan ci kosan nan ba, ni kosai bai dame ni ba. Tunda nake da ke kin taba gani na ci abincin wani gida? Ai sai naki balle kuma abincin sayarwa. Iman ta yi murmushi gami da yi masa wani sunkuyayyan kallo ta ce "Yau na ga ikon Allah ga ka a gaban mai kosai tun daga nesa naga ka mika mata kudi kana jira a zubo maka, kuma har da rantsuwa ba ci zaka yi ba, me za ka yi dashi sadaka? Su duka suka kwashe da dariya ya ce "Kin cika mantuwa, dazu kina damun koko na ce ki cika min kwanon sha mu biyu za mu sha, na shaida miki yau Najib zai zo daga Kano takanas don ya zo ya ganki, ku gaisa. Saboda bai taba jin na yi budurwa ba, sai kuma yaga na kwana ina bashi labarin ki da na je Kano, sai ya ce bari ya zo takanas ya ga wannan mai rabon. Dariya ce ta kubce musu su dukkansu. Iman ta maimaita "Lallai kuwa ya zo ya ga wannan mai rabon Suhaif ya ce "Au ba ki da rabo da kika sameni? Iman ta rike baki alamar mamaki ta ce "Ni na isa ince haka? Ai nafi kowa rabo dana sameka. Suhaif ya ce "Da gaske kike ko zolayata kike yi? Iman tayi dariya gami da rufe ido ta ce "Ai babu zolaya tsakaninmu. Suna tafe a hankali har suka isa makaranta Iman ta shiga ajinsu Suhaif kuma ya juyo ya dawo wajen me kosai. Iman ta iske kawayenta biyu a aji Rakiya da Laure suna shara, gaba dayansu suka hada baki suka ce "Iman yau kin makara mun rigaki zuwa. "Iman ta ce "Yau na makara gaskiya gashi nan har kunyi rabin shara. Bari inzo in tayaku. Rakiya ta ce "Gyara mana bencinnan karki shigo kurar nan yanzu ki turnike mana da tari. Iman ta hau gyara bencina kamar yadda suke a layi-layi. Muryar Malam Yahaya ce tasa dukkanninsu suka juyo suka kalli wundo da suka ji sautin maganar ya ce "Sannunku da shara, suna ganin Malaminsu sai dukkansu suka durkusa suka gaishe shi, ya amsa musu cikin lankwashasshiyar murya mai dauke da jimami. Kallo daya zaka yi masa ka san yau hankalinsa a tashe yake. "Malam yau kuwa lafiya? Iman ta tambayeshi. Malam Yahaya ya nisa yayi shiru yana tunani na wani dan lokaci. Sai gaba dayansu gabansu ya hau faduwa suka bar abinda suke suka nufo inda yake tsaye jikinsu na karkarwa. Malam Yahaya ya ce "Ku yi hakuri ku koma gida yau baza'a yi makaranta ba. Ku tari masu zuwa a hanya kuce sai nan da sati guda za'ayi makaranta. Rakiya ta dafe kirji ta ce "Lafiya? Iman kuma tuni hawaye ya fara kwaranyo mata babu abunda take sai karkarwa tana fargabar taji me zai fito daga bakinsa ya ce "Kamar yadda kuka sani dukkan mai rai saiya dandana mutuwa, Allah Ya yiwa dan uwanmu abokinmu, yayanku rasuwa a jiya da daddare yanzu muka dawo daga binneshi. Iman taji kafarta bazata iya daukarta ba saboda tashin hankali sai ta durkusa ba tare da ta iya bude baki ta yi tambayar da take so tayi ba. Waye ya rasu? Malam Yahaya ya ce "Malan Hadi ya rasu "Innalillahi wa'innailaihirraji'un suke karantawa yayin da Iman ta dora hannu aka tana jin jiri yana jujjuyawa da ita, hawaye kuwa daya na bin daya. Ya ce "Kar kuyi kuka addu'a zaku yi masa, ku tashi ku rufe ajin ku tafi gidanku. In ya so ko da yamma sai ku hadu kuje kuyi wa iyalansa ta'aziyya. Ya wuce ya tafi da sauri yana share hawayen da ya cika masa ido ganin kukan da Iman take shi yasa shi kuka. Rakiya da Laure suka goge guntun hawayen daya cika musu ido suka zo kan Iman wacce kukanta ya ribanya nasu, suna lallashinta dakyar da sudin godhi suka lallasheta ta tsagaita da kukan da take ta tashi daga tsugunan da tayi ta fito suka rufe ajin suka nufi hanyar komawa gidajensu. A hanya suka dinga cin karo da dalibai, suna ganinsu Iman suna dawowa sai suyi turus su tsaya. Sai suyi masa bayanin cewa ba makaranta saboda rasuwar Malam Hadi. Nan dai kowacce ta rafsa salati ta juya gida. Su Rakita suka yiwa Iman Sallama da suka zo lungun gidansu, suka shiga Iman kuma ta wuce ta nufi hanyar gidansu. Dai dai kan kwanar da Iman zata shiga gida ta ci karo da dandazon *yan ajinsu su biyar suna tafiya makaranta Iman ta tsaya suka gaisa. Talatu ta ce "Ah Iman mantuwa kika yi kika dawo? Iman ta girgiza kai hawaye ya zubo mata ta ce "Ba ayin makaranta yau saboda Malam Hadi ya rasu. Raiha ta ce "Wai yaya malaman makarantar nan suke ta rasuwa haka a jere a jere? Kunga ba'ayi sadakar arba'in din Malam Nayaya ba sai Malam shehu ya rasu. Ga shi ba'a fi wata biyu ba da rasuwar Malam Shehu Malam Hadi ya rasu. Allah na tuba. Mai jidda ta ce "Kuma dukakansu lafiya-lafiya ake rabuwa dasu sai dai aji sun mutu, babu ciwo. Ku kalli Malam Hadi jiya-jiyan nan fa ya zane *yan ajinmu ya farfasa mana baya. Lallai da yasan zai mutu da baici zalinmu ba. Dan ba laifin fari bare na baki ya hau dukanmu. Iman ta girgiza kai yayin da wasu hawaye masu zafi suka zubo mata ta ce. "Ya *yan uwana musulmai ku yadda da kaddara, kuma duk mai rai saiya dandana mutuwa, ko da ciwo ko babu ciwo sai an tafi. Allah Baya barin wani don wani yaji dadi. Ikon Allah Ya wuce haka ba mutuwar malamanmu a jere ba idan yaso zai iya hada garin nan koma kasar nan ko duk duniya ya kashe bazai karuba ba zai ragu ba. Shine Ya haliccemu kuma ya rayamu haka kuma zai kashemu a duk sanda Yaso fatan mu Allah Ya sa mu cika da Imani. Cikin sanyin jiki da gasgata maganar Iman ta ratsa zuciyoyin su dukkansu suka ce "Amin. Iman ta dafa kafadar Maijidda ta ce "Maijidda babu kyau fadar abu marar kyau akan mamaci domin shaidar duniya ita ake masa a lahira. Ku fadi abun alheri ko kuyi shiru. Domin Musulmi dan uwan Musulmine, kuma abunda kaso wa kanka kasowa dan uwanka. Muma za muso idan mun mutu ayi mana shaidar kirki. Dan Allah mu yafewa Malam Hadi koma me yayi mana. Allah ya yafe mana gaba dayanmu. Gaba daya suka ce "Amin mun yafe masa kuma Allah Ya jikansa. Zaka iya ganin farin cikin da Iman taji a fuskarta tayi addu'a, dukkansu suka daga hannayensu sama Iman na kwararo addu'a suna amsa mata da amin suka shafa. Sai Iman ta ce "Da yamma bayan la'asar dan Allah mu hadu a bakin ajinmu mu dunguma muje gidansa muyi musu ta'aziyya ko ba haka ba? Dukkan su suka ce "Haka yayi in Allah Yaso zamu je. Ummi ta ce "Mungode Iman kina gaya mana gaskiya, shiyasa muke son zama dake muna karuwa. Akwai ki da hankali, tunani, hakuri, ga ilimin addini, Iman sai na ganki nake tunawa da wani abun addini. Dubi yadda kike shiga kamar a Makka shi yasa nake kokarin in dinga koyi da ke. Iman ta yi murmushi ta ce "Na gode Allah Ya shige mana gaba to sai anjimanku saida yammar. Ta juya ta tafi. Maimuna bakuwa ce a garin jiya tazo gidan su Raiha *yar uwarsu ce Mamakin Iman ya hanata yin magana tun dazu cikin zumudi bata bari Iman tayi nisa ba ta ce "Wai wacece take burgeku saboda addininta? Iman ta ce muku sunanta? To karya take muku, taudararku take a nan garin dan tasan baku santa ba. Rafkatu sunanta, bama musulma ba ce arniya ce bata da addini. Har cikin shege tayi ta haihu a kashe Dan. Bata da kunya har danbe take da mahaifiyarta akan idona, kai in takaice muku tana cikin kungiyarnan ta matsafa masu shan jini wato (secretSociety). Sai karaf a kunnan Iman, Iman ta juyo a fusace ta kalli Maimuna suka hada ido, sai ta juya taci gaba da tafiya ba tare da tasan inda take jefa kafafuwanta ba saboda tsananin hankali da rudanin data shiga. Hmmm Sai Allah Ya Kaimu Gobe Da Yardar Allah. Reedwan Suraj Isma'il >>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA _____CI GABAN LABARIN Tana tafe tana layi ta shiga wani gida mai *yar gajeriyar katanga ginin kasa mai dauke da daki guda daya dan karami. Gidan wani tsohon mahaukacine wanda Allah Yayi masa rasuwa. Tun bayan mutuwarsa babu wanda ya gyara gidan ya shiga duk da bashi da mata balle da ko jika da zai gada. Danginsa kuma suna tsoron su shiga gidan don sun canfa gidan wai aljanu ne a ciki duk wanda ya shiga zai mutu. Kan kace kwabo gari ya rude da maganar. Duk gidan da kazo giftawa zancen ake wai annoba ta shigo garin nan. An shaidawa mai gari halin da ake ciki. Suhaif kuwa tamkar mahaukaci zaka iya kiransa babu abin da yake sai fada da zage-zage da duk wanda ya kira Iman mayya. Yasa iyayensa a gaba sai magana yake yana cewa duk su suka tonawa yarinyar nan asiri da suka koreta gashi ta shiga wani hali ta shiga gidan da babu wanda yake iya shiga ya zauna, kuma karyane babu maye a duniya. Tun suna bashi amsa har suka kyaleshi yana maganarsa shi kadai a tunaninsu baya hayyacinsa damuwa ce ta fara taba masa kwakwalwarsa. Yaga abu ya faru baro-baro kowa ya gani ace karya ake mata sharri ne. Haka Suhaif ya kwana bai runtsa ba. Najib yayi iya kokarinsa ya kwantar masa da hankali abun ya faskara. Karfe uku dai-dai na tsakar dare Suhaif na zaune akan katifarsa daram-dakam babu ko alamar bacci a idanuwansa. Najib yana kishingide yana gyangyadi don shima ya kasa kwanciya ganin Suhaif ya ki ya kwanta. Suhaif ya taba Najib, yayi firgigit ya bude ido. Suhaif ya ce "Najib bansan halin da Iman take ciki ba a cikin wannan mugun gidan da aka canfa shi. Babu makwabta gaba da baya, amma Allah sai Ya sakawa yarinyar nan. Najib ya murtsike ido ya ce "Suhaif ka nutsu ka duba maganar nan akwai kamshin gaskiya, ka ji ance yarinyar data tona mata asiri mutuwa tayi a lokacin. Sannan ance lokacin da samari suka tareta zasu daketa suffarta canjawa tayi, idonya yayi jajawur, gashinta ya mimmike, hannunta yayi cako-cako, uwa uba ance tafiya take akan babban *yan yatsunta. Ka duba kaga wanne mutum ne zai iya tafiya akan yatsan kafarsa guda daya? Ka tuna maganar data fada maka ta ce kada ka zama makaho alhali kana gani. Kada ka zama kurma alhali kana ji. Daga karshe ta ce kada ka biyewa abunda zuciyarka take tsananin so alhali ba alhairi bane a tare da kai. Har ka damu ka dinga tunanin ko me take nufi to yanzu ga amsar da take nufi, ta ce ka kiyaye kaki kiyayewa. Suhaif ka zama makaho alhali kiri-kiri kaga abubuwan da suka faru, ka zama kurma alhali kana ji ana fada, kabi son zuciyarka alhali ita ba alhairi bace a tare da kai, ko wannan ka tuna kasan ta fada maka da bakinka ga yadda take. Suhaif ya harareshi ya ce "Ban gane ga yadda take ba? Najib ya ce "Ah ta fada maka a fakaice ita mayyar ce. Suhaif ya daka tsawa ya dakatar da Najib da hannu ya ce "Ya isheni haka Najib, zagin ya isa na dauka kana bayana ashe kana bin maganar *yan gari kana kiran Iman da mayya a gabana. Danme zan yadda da bayaninka? Najib ya dafa kafadar Suhaif ya ce "Dakata kaji dan uwana. Suhaif ya fisge jikinsa ya mike tsaye fada yake tun karfinsa "Babu abinda zanji daga gareka kawai ka kyaleni Malam. Najib na kallonsa yaje ya dawo daga wannan bango zuwa wannan a cikin daki sai fada yake. Najib ya gyara filo ya fara shakar baccinsa don yaga wannan abu na Suhaif ba kararre bane. Can yayi juyi ya kalli Suhaif ya ganshi akan abun sallarsa yana ta nafilfili yana addu'o'i, ya koma yayi kwanciyarsa ya ci gaba da baccinsa ya ce a zuciyarsa "Haka yafi maka alhairi idan ciwo ne Allah sai ya yaye maka. Da safe karfe takwas Suhaif ya jiyo muryar mahaifinsa a tsakar gida sai yayi farat ya fito bayan sun gaisa, mahaifinsa ya dubeshi shekeke ya ce "Me kake so kace naga bakin ka na son magana. Suhaif ya sosa keya ya ce "Eh Baba ina son magana, daman abunda ke faruwa dazu da asuba bayan masallaci mai gari ya aiko aka yi kirana akan zancen Iman ance tana cikin dan dakin nan har yanzu, mutanen dake kusa da nan duk sun kasa kwanan gidajensu. Ya ce mun yaya za'ayi a fitar da ita daga garin? Shine nake so ku bani izini ni zan je wajenta inyi magana da ita ta fito ta tafi. Goggo ta yi wuf ya fito daga kicin ta ce "kaje ina? Bazai yiwu ba gidan da ba'a iya shiga ko bata a ciki balle tana ciki, masifa biyu kenan. Baba ya dakatar da ita da hannu ya ce "Raliya kwantar da hankalinki yanzu Suhaif ba yaro bane karami wanda bai san ciwon kansa ba tunda har suka yi magana da mai gari ki barshi yaje in har zai iya magana da ita ya ce ta fito ta bar garin to alhamdulillahi. Suhaif ya duka yayi godiya ya juya ya tafi Goggo ta rushe da kuka yayin da kannansa ma su Naja'atu suka sa kuka suna "Yaya Suhaif kar ka je. Ko juyowa bai yi ba balle mahaifinsa ya canja shawarar hanashi zuwa. A zaure ya hadu da Najib a tsaye yana jiyo maganar da ake a tsakar gida. Ya dubi Suhaif, Suhaif ya dube shi sai Suhaif ya kawar da kai yace gaba da tafiyarsa ya nufi kofar fita. Maganar Najib ce ta dakatar dashi cak ya tsaya a inda yake ya ce "Suhaif yaushe Maigari ya kiraka ya ce ka shiga ka fito da Iman daga gidan nan? Ina tare da kai tun jiya haka da suba tare muka je masallaci muka dawo daki yaushe kaje gurin Maigari? Suhaif ya hasala ya ce "Nayi karyane don su cire mun takunkumin da suka yimin na kada inje wajen Iman. In har kana so ni da kai mu daina gaisawa har abada to kaje kace musu karya nake. Najib ya ce "Muna sonka ne kuma duk mai kaunarka bazai so ka jefa kanka cikin halaka ba. Suhaif ya yatsine fuska ya ce "Inhar kuna sona sai ku so abunda nake so, amma duk kun ki Iman gudunta kuke, tun daga magaruba kowa ya rufe gida haka da asuba kusan kowa yaki fitowa masallaci. A tunanina babu mai kaunata a garin nan tunda kun ki Iman Alhamdulillahi tunda kaina zan jefa a halaka ba wani ba, yaci gaba datafiya ba tare daya kara sauraron maganar da Najib yake fada ba. Najib ya fito yana kiran Suhaif amma ko juyowa bai yi ba yayi tafiyarsa, hawaye mai zafi ne yake zubowa daga idanuwan Najib don bakin cikin halakar da dan uwansa yake jefa kansa. Suhaif na isa kusa da gidan yaga jakar kayanta a yashe a cikin kasa da takalmanta da hijabinta ya durkusa ya tsince ya karkade ya nufi cikin gidan. Ya yi bismillah yayin daya jefa kafarsa a cikin gidan gami dayin sallama a kofar dakin, yaji shiru ba'a amsa ba. Mutanen da suka hango shi a lokacin da yake shiga gidan suka tsaya daga nesa suna kallon ikon Allah suna sauraron abunda zai je ya dawo tsakanin Suhaif da wannan Dodanniya. Dodanniya mana Iman ta zamar musu a garin nan duk a firgice suke. Ya ji gabansa na faduwa kasancewar dakin da duhu bai hango kowa ba a cikin dakin. Ya sake kwada sallama gami da kara tura kai cikin dakin ya shiga ba'a amsa ba kuma baiga kowa ba. Ya ajiye kayan dake hannunsa ya bude windon dake dakin, nan da nan haske ya gauraye dakin sai ya waiga kowacce kusurwar dakin babu abinda yake hangowa daga kura sai yana a jikin bango. Yayi matukar razana daya hango idanuwan Iman a bayan kyauran dakin tana kallonsa. Ya shaki numfashi yayi ajiyar zuciya da karfi don ganin Iman cikin wannan hali ya tsorata shi. Gashi kanta buyu-buyu babu dan kwali. Daga yadda yaga idanuwanta suna wurwurgawa yasan ba lafiya ta ke ba. Ya dan matso kusa da ita yayi mata sallama, bata amsa ba. Kallonsa take tamkar hoto. Ya nisa ya ce "Ga hijabinki kisa, ga takalminki kisa da jakar kayanki kizo mu tafi wani garin ba anan garin ba. Bata tanka masa ba, ya sake matsowa ya mika mata hijabin ya ce ta karba ta saka ko gezau bata yi ba sai kallonsa take tayi. Yayi magana harya gaji bata amsa masa ba, ya kira sunanta wajen sau ashirin bata amsa masa ba. Daga karshe ya ajiye mata kayan a gefe. Ya ce "Ko yunwa kike ji bari naje in suyo miki kosai da koko. Ya je ya suyo ya zo ya ajiye mata a gabanta ya koma ya ciko mata ruwa a botiki da kofi ya kawo mata yayi-yayi taci kosai ta sha kokon, tasha ruwa. Idan zata yi alwalla ga ruwa a bokiti taki magana. Yayi da Hausa, yayi da turanci, ya burkuta mata dan abunda ya sani da Larabci da Fulatanci wai ko ta daina jin Hausa abu ya faskara Iman dai kallonsa take. Daga karshe ya fashe da kuka, yayi kuka har ya gaji ya tashi ya taho gida. Mahaifinsa da Najib sun yi masa tambayar duniyar nan yaya Iman? dan takaici yaki amsa musu, ya kwanta yayi shiru sai shi sai abunda yake damunsa a zuciyarsa. Haka abincinsa na rana ana kawo masa ya dauka ya kai mata na safen nanan ko taba shi bata yi ba, tana nan zaune a bayan kofa inda ya barta. Ya dauke na safe ya ajiye mata na rana ya tafi. Daya kawo na dare sai ya tarar dana rana shima bata ci ba. Abun yayi matukar tayarwa da Suhaif hankali musamman irin duhun dakin daya barota dare yayi. Ita kadai ya shiga wasi-wasi anya kuwa Iman dinsa ce wannan ko kuma ba mutum ba ce daman? Ina son Iman, Iman ina sonki. Karki min haka Iman. Karki koma wata halittar da baza mu iya zama tare ba. Suhaif ya fada a baiyane yayin da yake kwance a dakinsa hawaye yayi masa kawanya. Najib na gefensa sai kawai ya dube shi ya girgiza kai don tausayi. Haka Suhaif da Iman suka kasance kullum zai kai mata abinci sai uku a rana haka kuma zai dawo ya dauki kayansa ko loma daya bata yi ba. Haka zaiyi maganar duniyar nan baza ta amsa ba. Yanzu kanta a sunkuye yake ko idonta bata dagowa ta kalleshi balle yasa rai zata yi masa magana sun kwana biyu a haka a ran na ukun ne ya shigo gidan da yamma ya tarar da abin al'ajabi. Tun daga bakin kofa ya ga warin takalminta daya da wani abu kuma a jikinsa ja kamar jini. Ya tsaya yana kallon takalmin saiya wuce ya shiga dakin sai yaga warin takalmi a rataye a daure yana lilo ajikin azarar da ke rufin dakin shima jan abu a jiki. Iman na zaune ta juya bayanta wannan karon ta fito daga bayan kofar. Sai Suhaif yaji jikinsa ya dau karkarwa. Muryarsa na rawa ya ce "Iman meke faruwa, me nake gani haka? Kada ki cemun zargin mutane gaskiya be. Ya daka tsawa kamar zararre ya ce "Ki fada min, kimin magana ko ke wacece? Shin ke mutum ce ko ba mutum ba ce? Yau bazan bar dakin nan ba sai kin kasheni na huta. Kina wahalar dani kina tsorata *yan garin nan. Naki yarda a zarge ki, na kasa hakura da sonki. Ki kashe ni na huta da bakin cikin nan, sai ki bar garin ki bar *yan uwana a garinsu. Ko motsi bata yi ba balle ta juyo ta kalle shi. Wannan karon jama'ar dake taruwa suna hangen kofar dakin da Suhaif yake shiga sun fara razana saboda suna jiyo muryarsa da karfi yana fada. Cikin fushi ya sa hannu ya finciko Iman da karfi ya juya fuskarta. Amma me? Baisan sanda ya ji shi fuk ya fadi kasa ba ya gwara kai da bango. Shin taba ta din da yayi shine ya fadi kasa ko kuwa fuskarta ce ta bashi tsoro ya fadi da kansa don razana? Oho! Fuskar Iman ta razana Suhaif ya sake gwala ido yaga lallai Iman ce duk da fuskarta ta canja zaka iya hango kamanninta. Idota jawur, jan kyalle a wuyanta jan kyalle a gashinta, jajayen kyalle a daure a hannunta da kafafuwanta. Suhaif ya gyara zama cikin fidda rai da sake yin numfashi a duniya ya ce "Iman da gaske ne abin da mutane suke fada kenan? Ta nuna masa kofar fita da hannu alamar ya tashi ya fita da sauri. Suhaif ya mike yana layi kamar zai fadi ga zafin da keyarsa take yi masa inda ya fadi ya doka kai a jikin bango, ya juya zai fita kamar daga sama yaji muryar Iman ta ce "Suhaif! Suhaif!! Suhaif!!! Da karfi ya juyo da sauri ya dubeta. Ta ci gaba da cewa "Ina baka shawara yau kada ka yi bacci ka kwana kana addu'a, ka kwana kana sallah, ka nemi tsari daga makiya, munafikai da shaidanu. Suhaif ya tambayeta cikin mamaki "Kamar yayafa? Ta daka tsawa ta ce "Kada ka bincikeni, kada kaki bin umarnina, kada ka karyata ni, kada ka shagala da barci ka ki yin addu'a idan ba haka ba zaka mutu a daren yau. Ba na son ka mutu don kana da kirki. "Mutuwa? Waye zai kasheni? Ya sake tambaya. Ta yi kara mai tsanani ta ce ya fita ya bata waje. Suhaif ya fice hawaye na zuba a idanuwansa yana nanatawa a zuciyarsa abu kamar wasa ashe da gaske mutane suke. Wannan lamari na Iman ya caja masa kai, har ta kai ta kawo hankalin iyayensa ya tashi sun ga Suhaif kamar mahaukaci yana tafe yana magana. Sai mahaifinsa ya kirawo wani malami bayan sallar isha ya zo yasa Suhaif a gaba yana tofe shi. Bayan Malamin ya tafi sai Suhaf ya yi alwala ya ce zai je Masallaci acan zai kwana. A'a hauka ta bayyana sai *yan uwa suka dau kuka. A kayi-akayi ya dawo yaki dawowa ya shiga Masallaci yayi ta sallah yana addu'o'i. Cikin gida mata da *yan uwa da ubansa suma addu'a suke yi Suhaif ya tabu. Shi kadai yasan dalilinsa na kwana sallah da lazumi. Sai karfe tara na safe aka samu Suhaif ya fito daga masallaci suka nufo gida da mahaifinsa da Najib suna wani sashi a tsakiya wai dan karya koma Masallacin tunda suna tunanin aljanar Iman ita take kaishi Masallaci sai dariya ta kubuce masa idan ya ga sunyi wani abun. Dan shi da hankalinsa ras suke tunanin bashi da hankali. Idan yayi dariya sai su sake razana sun dauka haukar dariya ce ta kamashi. Sun kusa isa gida sai ga wasu motoci guda uku bus biyu da motar *yan sanda biyu ta zo ta wuce. Wani yaro ne ya rugo yana fadawa abokansa cewar Maigari da jama'arsa ne suka je Dutse suka shaidawa Gwamna abun da yake faruwa game da maganar Iman, cewar a kawo musu agaji annoba ta sauka a garin Doko a zo a fitar musu da ita shine aka ciko motoci biyu da malamai da kuma *yan sanda. Idan bata fito ba za'a saka mata tiyagas ko a kona dakin. Ai kafin yaron nan ya rufe bakinsa Suhaif ya arta da gudu inda Iman take, Najib da Mahaifin Suhaif binsa suke a guje suna "Jama'a ku tare mana shi. Suhaif ya isa kofar gidan ya iske cin-cirindon mutane da Maigari da *yan fadarsa, ga *yan sanda na kokarin hada tiyagas zasu jefa cikin dakin. Malamai na bin katanga suna tofa addu'a. Amma an rasa mai shiga ciki saboda an riga an fada musu irin bala'in da suke cikin dakin. Suhaif na isa wajen, mutanen gari suka ce "Yauwa ga mai iya shiga wajenta. Suhaif ya ce "Ku dakata zan shiga in fito da ita karku saka mata tiyagas. Kafin su Mahaifinsa su iso Suhaif ya shige dakin sai suma suka tsaya a gefe suna kallon ikon Allah. Ya shiga ya iske Iman zaune tana duban bakin kofa amma jajayen kyallayen nan babu a jikinta. Ya karasa gareta yayi mata sallama bata amsa ba sai ya durkusa a gabanta ya fara mata bayani akan ta fito zasu tafi wani gari. Ta bude baki ta bashi labarin abunda ke faruwa a waje ta ce "Babu garin da zamu tafi. Malamai da *yan sanda ne zasu fita dani daga garin, kaje ka basu labarin bazan fita ba sai dai su kasheni. Mutuwa nake so. Mutumin daya kashe hukuncinsa a kashe shi nafi so a kasheni. Hawaye ya kwararo daga idanuwanta, sai Suhaif ma ya fashe da kuka ya tashi ya fita wajen jama'a ya shaida musu sakonta. Wani Malami daga cikin Malamai ya ce "Kaje ka ce mata ta fito za'a kasheta in har an bincika hukuncin kisa ya hau kanta. Suhaif kuka yake haikan ya koma cikin dakin da Iman take ya shaida mata ta fito sun ce zasu kasheta. Wannan karon murmushi ta yi. Suhaif ya dauko mata hijabinta ya ce ta saka saboda akwai maza da yawa a waje. Iman ta girgiza kai ta ce "Ni da za'a kasheni maye abun saka hijabi? Ba zan saka ba. Suhaif ya girgiza kai don tausayi ya cukuikuye hijabin ya dauko mata jakar kayanta da takalmanta. Iman ta mike, tafiyarta da kamanninta sun dawo dai-dai ta dubi Suhaif ta ce "Har yanzu ni Musulma ce idan aka kashe ni aimin wanka, a yimin sallah, a yi min sutura irin ta addinin Musulunci ina son Musulunci. Sai hawaye ya zubo daga idanuwansu su duka "Suhaif ya ce "To naji amma ki saka hijabinki sai kifi kama da Musulma sai su yadda muyi miki Sallah. Ta karba ta saka hijabin suka fito. Jama'a sunyi mamakin Iman sanye da hijabinta a nutse yadda take da, *yan sanda da Malamai sai jikinsu yayi sanyi suna fadin yarinya nutsattsiya haka ace mata mayya? Watakila ma bakin ciki ne yayi mata yawa ta shiga wannan hali. A gindin katuwar bishiya aka shimfida tabarmi da kujeru aka ce ta zauna za'ayi hira da ita ayi mata tambayoyi kafin a kasheta din. Iman taki zama ta ce ita dai kawai a kasheta babu hirar da za'ayi ta gaji da duniyar. Malamai suka ce babu yadda za'ayi su kasheta basu ji wa da wa ta kashe ba, don sai wanda ya kashe wani sannan a kashe shi. Da kyar Suhaif ya lallasheta ta zauna akan wata tabarma Suhaif ya ajiye jakar kayanta yazo ya zauna a kusa da ita. Mutanen gari mata da maza suka dinga diddukowa, a ciki harda Goggo dasu Naja'at. Kuka kawai Iman take ta kasa magana. Anyi mata tambaya kala-kala tayi guda ASHIRIN DA HUDU taki amsawa tamkar da GANGAR JIKINTA ake magana Ruhinta baya wajen. Ba karamin yi da baki aka yi ba kafin Iman ta bude baki ta fara magana. LABARIN IMAN........... Wash gaskiya na gaji da shige da fice dan ganin na kawo muki labarin nan. clap 4 me.... Kunsan na cika jarumi da har nabi bayan Suhaif na ambalo muku abin daya faru tsakanin su. Su wa'e ko Oho. Lolx... Reedwan Suraj Isma'il >>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA ____CI GABAN LABARIN _LABARIN IMAN_ Ta ce "Makasudin shigata wannan mummunan hali na dangantashi da Iyayena. Su suka jamin wannan bakar rayuwa. Tun kin maganar Allah da abinda Annabi ya zo dashi sai bata, sai kuma kuncin rayuwar duniya da lahira. Mahaifina mutumin Gombe ne bafillatani ne gaba da baya kallo daya zaka yi masa kaga kamannin Fulani. Fari ne tas dogo sosai sunan Mahaifina Lamin kuma shine babba a gidansu sai kannensa mata guda biyu Hajara da Gambo, mahaifinsu ya rasu tun suna kanana Mahaifiyarsa ce kawai take kula da su sunanta Fatima. Sun sha wuyar rayuwa kasancewar duk dangin mahaifinsu basa kulasu, sun bar Mahaifiyarsu da wahalarsu. Ta jajirce sai sunyi karatu musamman mahaifina ganin shine babba namiji babu abunda zata masa irin ta bashi ilimi gara ma matan dake su aure zasu yi shine ya kamata yayi karatu ya sami babban aiki ya riketa ya rike kannensa. Ta sayar da shanunsu ba adadi da gona don Lamin ya sami ilimi. Allah cikin ikonSa ya gama sakandiren dai-dai lokacin yayi nisa a karatun alkur'ani gashi da hazaka a duka bangarorin biyu. Ya sami admission a Jami'ar dake Bauchi wato ATBU suka bashi Engineering course din masu kwazo da kokari. Haj. Fatima Mahaifiyarsa ta hada masa duk abunda zai bukata na makaranta ya tafi. Mahaifiyata kuwa sunanta Patrica ba Musulma bace. Mahaifiyarta Inyamurace mutanen Onisha, Mahaifinta kuwa bature ne jar fata. Yazo nan ya ganta suka yi aure daga karshe ya tafi da matarsa can kasarsu Maziko acan Allah Ya basu haihuwa suka haifi Mahaifiyata Patrica. Ai dole tayi kyau don ta biyo Mahaifinta sak farinsa da gashinsa da hancinsa, idanuwanta ne irin na Mahaifiyarta dara-dara duk da Mahaifiyar ma farar Inyamura ce tas amma farin Patrica kana gani kasan na farar fata ne. Mahaifiyata na shekara uku Mahaifinta ya rasu. Cikin dare Mahaifiyarta ta saceta suka gudo Nigeria don taga alama dangin mijinta na kokarin kwace mata *yarta. Mahaifiyata na da shekara tara Mahaifiyarta ta rasu a garin Onisha sai kaninta ya dauketa mai suna Uncle Sunday. Aiki ya kaishi garin Jalingo wato Taraba State nan Mahaifiyata tayi karatun sakandire dinta ta samu admission ita ma a nan ATBU Bauchi inda Mahaifina yake suka bata courst din Architecture wato zane da tsara gine-gine. A lokacin Mahaifina yana shekara ta uku wato lebel 3 Mahaifiyata ta shiga label 1. Allah cikin ikonSa tun sanda Mahifina yasa ido akan Patrica yaji duniya babu wacce yake so sai ita. A hankali suka saba musamman a lokacin Jarabawa wajen karatunsu daya, kasancewarsu su duka masu nacin karatu ne har yake koya mata abun da bata sani ba. Bayan sun saba sai ya fito mata da bukatarsa cewar yana sonta kuma da aure. Abunda ta fara nuna masa ya za'ayi yace zai aureta bayan YARENSU da ADDININSU ba daya bane? Ta nuna masa tayi zurfi a addininta, uwa-uba kawunta murikinta babban mukami yake dashi a wajen bautarsu sune masu bin kauyuka suna kira azo cikin addininsu. Ta ce tayi nisan da babu wani abu da zaisa ta canza addininta. Mahaifina ya nuna duk wannan mai sauki ne shima bazai bar Musulunci ba ya dawo addininta ba, don shima yayi nisa a addininsa amma zasu iya aure kowa yayi addininsa. Ta nuna masa wannan abu ba mai yiwuwa bane ya bar maganar kawai. Yaran da zasu haifa fa ai zasu iya shiga addininsa. Yayi mata alkawari duk yaran da zasu haifa ya yarda subi addininta idan sun ga shi suke so. Tambayar da tayi masa ita ce "Ka yarda da *ya*yanka su bi ADDININA kai kaki yarda ka bi ADDININA meye dalilinka nayin haka? Ya kasa amsa mata wannan tambayar. Amsar ita ce idonsa ya rufe yaga wacce yake so baya tunanin rayuwar *ya*yansa yadda zata kasance nan gaba. Wanne irin bacin ran Mahaifiyarsa da danginsa zasu shiga idan suka ji ya auri wacce ba Musulma ba? Patrica a kullum tana nunawa Lamin bata son wannan soyayyar tasu domin abune mai wuya musamman idan aka koma bangaren Iyaye. Iyayensa da nata ba zasu yarda ba don haka su hakura su auri wadanda YARENSU DA ADDININSU yake daya. Amma Lamin ya makale shi dai yaji ya gani ba gudu ba ja da baya. Tayi masa wulakancin da ko kare bazai dauka ba don yaji haushi ya rabu da ita, duk da tana tsananin sonsa itama amma tana tunanin gara su hakura domin ita babu mutanen da ta ki jini irin Musulmai da addinin Musulunci. Lamin ya gama karatunsa ya tafi bautar kasa ya bar Patrica a ATBU ita bata gama ba. Allah cikin ikonSa aka turashi Jalingo garin su Patrica acan yake bautar kasarsa. Lokaci-lokaci yake zuwa ya gaishe da kawunta marikinta ya shaida masa shi abokin Patrica ne a makaranta. Wani weekend Patrica tazo gida ta iske Lamin da kawunta har sun saba hira suke haikan. Tayi matukar mamaki ya aka yi Lamin ya nemo gidansu harya shisshigewa kawunta haka suka saba? Bayan ya gama bautar kasarsa ma saiya nemi aiki a garin saboda abar kaunarsa Patrica. Duk inda take yana biye da ita, duk sanda ya shiga Gombe garinsu sai ya karasa Bauchi wajenta haka idan aka yi hutu ta dawo jalingo Lamin yana Jalingo kullum saiya zo gidansu Patrica. Abun ya fara bata tsoro don kawunta ya fara fuskantar akwai soyayya a tsakaninsu ba kawance bane. Tasan abune marar yiwuwa tunda tun tana yarinya yake yi mata fada tasan kawayen da za tayi a makaranta ban da Musulmai domin zama da Musulmai zasu dinga saka mata wata akida har wataran taji tana son addinin Musulunci. Amma me? Sai taga kawunta da kansa yake nuna mata ta kula Lamin tabar wulakanta shi, don yaro ne mai hankali da nutsuwa. In har yace zai aureta ta yarda ta aure shi. Patrica ta tsorata da maganar kawunta. Ya za'ayi da bakinsa zaice ta auri musulmi. Ya fada mata manufarsa ita ce watarana zasu iya jan hankalin Lamin ya shigo addininsu. Tunda ya nace yana matukar sonta kamar ransa, har ya yarda *ya*yansa su bi addininta shima zai iya canjawa. Patrica ta yarda da zancen kawunta daman kuma tana matukar son Laman sai ta sakarwa Lamin fuska suka yi ta tafka soyayyarsu. Aka tsayar da lokacin aure da zarar ta gama karatunta sai tayi bautar kasa a dakin mijinta. Duk wannan shirye-shirye tsakanin Lamin da Patrica da iyayenta ne kawai ake yi, Iyayen Lamin basu taba sanin akwai wata halitta a duniya ba wai ita Patrica balle zancen aure a tsakaninsu. Don su a bangarensu har sun tanadar masa wacce zai aura a dangi. Yarinya mai kyau *yar Fulani Hauwa'u sunanta ta gama Sakandirenta a F.G.C Azare tana kiransa. Sai hanya-hanya yake yi musu har ta kai ta kawo ya fara dauke kafarsa daga garinsu don ana damunsa da maganar auransa da Hauwa'u. Idan mahaifiyarsa ta tuntubeshi game da zancen aurensa sai yayi ta hanya-hanya yana cewa a jinkirta akwai wasu shirye-shirye a gabansa yana so ya kamala. Haka mahaifina yayi ta shammatarsu har lokacin aurensa da Patrica, suka yi bikinsu ba tare da danginsa sun sani ba. A nan garin Jalingo ya samo wasu tsofaffi suka shige masa gaba aka yi aka gama. Amarya ta tare a gidan angonta a cikin Jalingo wata unguwa da gidajen ma'aikata suke wato G.R.A. Mahaifina yayi ta nuku-nuku ya kasa shaidawa mahaifiyarsa da danginta cewar ya auri wacce ba musulma ba amma duk daren dadewa abun boye zai fito fili haka duk nisan dare gari zai waye. Wani dan uwansa ne yazo Jalingo kuma aka fesa mata labari cewar Lamin fa ya yi aure tuntuni wacce ya aura kuma ba Musulma bace kuma taki Muslunta. Bai yi wata-wata ba ya garzaya garin Gombe ya shaidawa Kakata da danginta halin da dansu Lamin yake ciki. Aka ce Mahaifiyarsa faduwa tayi fuk ta suma. Dangi gaba daya kuka suke yi tamkar gidan mutuwa. Ko da labari yakai kunnan Lamin cewar yazo maza-maza a gida ana nemansa sunji labarin auren da yayi sai yaki zuwa garinsu kwata-kwata. *yan uwansa da yawa sun zo sun iske shi har Jalingo suyi fadansu su tafi babu abunda ya ragu a jikinshi don shi yanzu ya fara zama da matarsa babu mai rabasu. Allah Ya albarkacesu da samun haihuwa suka haifeni ko ban fada ba kunsan nayi kama da Mahaifiyata ne tunda jama'a da yawa suna mun kallon farar fata ce *yar kasar jajaye. Duk da idan ka karemun kallo zaka iya ganin ina kama da Babana amma nafi kama da Mahaifiyata. Ta radamun suna RUFKATU. Mahaifina kuma ya tara Musulmai ya yanka rago ya radamun sunan Mahaifiyarsa Fatima. Nan aka sha rigima da mahaifiyata wai ita babu mai kiran *yarta da sunan Musulmai Fatima. Shi kuma ya ce ba zai kira *yarsa da suna Rufkatu ba. Mahaifina yana kirana da Fatima. Mutanen gari suna kirana da Prety ma'ana mai kyau. Kowanne suna ina amsawa, amma da aka sakani a makaranta Rufkatu Lamin Mahaifiyata tasa ake rubutawa. Ina da shekaru hudu aka haifi kanina kamarmu daya aka saka masa suna Bobby, mahaifina ya rada masa suna Abubakar. Bayan ya shekara biyu aka haifi *yar autarmu, mahaifiyata na kiranta da Rebecce Mahaifina yasa mata sunan kanwarsa mai binsa Hajara. Bacin rai sosai ya dasu a zuciyar mahaifiyata danme mahaifina yake yanka mana rago yake rada mana sunayen Musulmai baya kiranmu da sunayen data radamana. Bayan dashi aka yi yarjajjeniya *ya*yansu zasu bi addininta, ya ce ya yarda. Me yake nufi kuma yanzu? Fadan safe daban na rana daban. Ya shaida mata shi ba wai yana nufin *ya*yansa dole sai sunyi sallah ba, amma shi abun kunya ne wataran su shiga danginsa aji sunayensu bana Musulmai ba. Mahaifina yana ta aike a nemar masa gafara wajen Mahaifiyarsa, ace ta yafe masa yasan yayi mata laifi. Dakyar ya samu ta aiko masa da magana mai dadi ta ce ta yafe masa kuma tana masa fatan Allah Ya shirye shi ya kare shi daga barin addininsa kamar yadda ya yarda ya haifi arna a cikinsa. Da ya dauki hutu a wajen aiki, Mahaifiyata ma tana aiki a banki itama ta dauki hutu mu ma aka yi mana hutu a makaranta saiya cika mu a mota muka nufi Gombe muje muga danginsa, dangi kuma su ganmu. Munsha wulakanci, munga takaici iri-iri domin baro-baro ake nuna mana tsana da zafuta da hantara. Ko randar Kakarmu muka je muka bude muka sha ruwa sai an fasa randar an sayo wata wai marasa tsarki sun saka mata najasa. Bamu isa mu zauna akan tabarmarsu ba balle abun sallarsu sai ayi ta yayyafa ruwa koma a wanke gaba daya. Mahaifiyata taji haushin wannan wulakanci da ake yi mata da *ya*yanta sosai, tasha alwashin har abada ba zata sake zuwa Gombe ba. Mahaifina ma baiji dadin yadda aka yi mana ba, amma ya kasa tarar danginsa balle yajawa kansa. Muka har-hado muka dawo gidanmu Jalingo. Yaren Fulatanci shine yaren da yawancin *yan garin suke yi don haka fulatanci Mahaifina yake yi mana. Mahaifiyarmu ma haka amma tafi yi mana magana da turanci wasu lokutan da yarenta Igbo. Me rainonmu da mijinta maigadinmu suna zaune a boy's qoutern gidanmu su kuma yarensu Tangala ne mutanen Billiri karamar hukumar Gombe. Tun muna yara suke yi mana yarensu na tashi ina jin tangalanci. Rayuwata tana cike da rudani nakan kasa tantance wazan bi uwata ko ubana. Na tashi naga Mahaifina na yin sallah sau biyar a rana. Haka kuma na tashi naga Mahaifiyata tana zuwa wani waje suna bauta kullum. Gata ma'aikaciyar Banki ce tana fita aiki da sassafe sai da yamma likis take dawowa gida amma da zarar ta dawo ko hutawa bata yi saita shirya ta nufi wajen bauta har dare suna addu'a. Ranar Asabar da Lahadi kuma saita shiryamu ayi mana ado ni da kannene mu tafi wajen bautarsu. Mu bar Mahaifinmu a gida yana karatun Jarida wani lokaci yana karatun kur'ani mai tsarki. Nafi son Mahaifina fiye da Mahaifiyata saboda nafi zama dashi don haka munfi sabawa. Idan ya fita wajen aiki karfe tara na safe shima baya dawowa sai da yamma likis. Yafi Mahaifiyata sakin fuska da wasa da janmu a jiki musamman ni yafi jana a jiki fiye da kannena, su kuma sunfi son Mamarmu. Ina wasa da Mahaifina kamar wani abokina, ya goyani, muyi wasan *yar tsanata dashi, yasa mana kida da waka ya tashi ni dashi muyi ta rawa. Amma baya garajen ya koya mun karatun kur'ani saboda gudun bacin ran Mahaifiyata. Watarana ne Mahaifina yana sallar la'asar baisan ina bayansa ina binsa sallah ba. Mu dai munji muryar Mahaifiyata kamar zata tsaga gidan don kara muka juyo a firgice mu dukkanmu ni da shi. Sai ta ci gaba da fadace-fadacenta da zage-zage wai ashe daman idan bata nan sallah yake koyamin? Yayi mata rantsuwa da Allah shi bai san ina bayansa ba ina binsa Sallah. Ranar naga tashin hankali a wajen Mahaifiyata tayi min dukan da tunda nake babu wanda ya tabamun irinsa har jikina ya fashe, masu aikin gidanmu da mahaifina suka dinga riketa suna rokarta tayi hakuri tace sai tabar gidan ita da *ya*yanta baza suyi addinin Musulunci ba kuma zamanta da musulmi ya kare. Dakyar ta hakura, bayan Mahaifina yayi mata alkawarin irin haka ba zata sake faruwa ba. Shekaruna basu wuce tara ba a lokacin amma kwakwalwata tana da kaifin hankali da tunani. A kullum kuma a koda yaushe bani da abun yi sai tunani ina so in tantance me yasa kowa da abunda yake bautawa? Haka kuma nake bi ina tambayar manyan da shekarunsu sukafi nawa wai shin su me suke bautawa, bayan sun fadamun musulmai ne ko ba Muslmai ba ne. Sai ince me yasa suka zabi wannan addinin basa yin dayan? Sukan rasa amsar da zasu bani sai suyi dariya kawai. Huzaifa wani saurayine makwabcinmu shine baya taba gajiya da bani cikakkiyar amsar duk tambayar da nayi masa akan addininsa da ma wanda ba nasa ba. Idan na tashi da safe, Tabita me aikinmu sai ta shiryamu mu tafi makaranta. Mahaifiyarmu na da mota ita zata sauke mu a makaranta sannan ta wuce wajan aikinta. Mahaifinmu kuma sai ya dauko mu daga Makaranta shima dai-dai lokacin yake dawowa daga aiki sai mu dawo gida tare. Tabita ta bamu abinci muci, sau da yawa bayan Mahaifinmu ya ci abinci saiya fita wajen abokansa can wata unguwa mai nisa. Kannena kuma sai su kwanta suyi ta barci ko su fita kofar gida wajen abokansu. Da Tabita nake zama muyi ta hira a hankali sai take nuna mun abunda take bautawa. Abunda take bautawa kuma yasha bambam da abunda Mahaifiyata da Mahaifina suke bautawa. Wani sassakekken itace ne anyi mutum-mutumi da shi an rataya masa kahunhunan rago da wasu gashi-gashi. Sai suzo ita da mijinta su durkusa a gabansa suna rokarsa duk abunda suke so wani lokaci har suce nima in zo in durkusa in rokeshi zai ba ni. Wa'iyazubillah. Haka kullum muke yi da su. Idan kuma na gaji da zaman gida sai in sa takalmina in fito in tafi wajen kawayena da muke yin wasa tare, wadanan kawaye nawa ba wasu bane illa arnan daji. Zaka iya hango bukkokinsu daga can nesa da gidajenmu, sunan yaren mumuye. Ehem,, gaskiya na gaji da zama, za kuji komai daga bakin IMAN..RUFKATU..PRETTY..FATIMA zuwa gobe da yardar Allah. Reedwan Suraj Isma'il >>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA ____CI GABAN LABARIN Kauyen Mumuyawa ne wajen wasana, mun saba da *ya*yan mumuyawa sosai tun bani da wayo muke tare. Har takai ta kawo ina jin yarensu sosai suma kuma suna jin yaren Fulatanci. A lokacin mutanen kauyen mumuyawa basa saka sutura matansu da mazansu yara maza da mata fata suke daurawa a tsantsarsu su rufe al'aurarsu kawai. Budurwar da batayi aureba ita ke daura fata a kirjinta. Matan aure kuwa kirjinsu a bude haka suke yawo. Ranar Juma'a ne ranar kasuwar Jalingo ranar ne kawai idan zasu shiga kasuwa su sayar da giya, burkutu suke daura zani su cire fata. Karku dauka zani da riga sosai irin na mutane suke daurawa a'a wani dan fatarin siket ne suke dinkawa iya guiwarsu kirjinsu a bude su dau tukunyar giya burkutu a kansu su biyo layi-layi suna tafiya, suna karyar kubewa a gonakin da suke giftawa suna ci gayau-gayau. Masu goyo suna yin goyo da fata. A kasuwar Yalwa suke cin kasuwar giyarsu a karkashin wata katuwar bishiyar mangwaro suke zama da fulatanci ana kiran wajen (La mangwaro). Babu abunda suka sani sai tsafi kuma wani dodo suke bautawa. Ma'ana wani mutum suke zaba a cikinsu su nada shi abin bautarsu. Yana saka wata riga duk jikinta gashi ne zaro-zaro ko fuskarsa baza ka iya gani ba shi suke bautawa. Matansu da mazansu kansu a aske yake. Haka hudar kunnuwansu da hanci barka-barka. Duk lokacin da amfanin gonarsu ya nuna wato lokacin cin doya akwai biki da suke na musamman na godewa dodansu daya sa doyarsu ta nuna, tayi yawa. Wa'iyazubillahi basu san Allah ba kwata-kwata wanda shi Ya haliccesu, Yasa amfanin gonarsu ya nuna yayi albarka. Kafin ayi wannan bikin cin doyar sai an nemo kai, ma'ana sai sun yankawa dodo mutum sun bashi jini yasha sannan a fara kade-kade asha biki. Idan dan uwansu ya mutu suna jera itatuwa sai su shimfida tabarma akan itatuwan su lillibe jikin su fito da kai da kafafuwa a waje su dora aka suna gudu a titina suna wake-wake. Haka ranar da za'a binne gawar sai suyi tsafin da gawar zata tashi da kafarta tana layi suna biye da ita ana tafi ana wake-wake taje ta fada a kabarinta sannan su rufe kabarin. Iyayena duk suna wajen harkokinsu babu mai nemana balle susan ina nake zuwa su hanani. Akwai lokacin da idan na tafi tunda rana sai magaruba in dawo muna ta wasa da *ya*yan mumuyawa, wani lokaci har kayana nake cirewa in daura fata kamar yadda suke muyi ta gadarmu sai zan tafi gida in canja. Idan na kwana biyu banje wasa garin ba kawayena su Mungai su Maho sai su biyoni har gida amma ba shigowa suke ba suna labewa a jikin wunduna suna mun busa da hannunsu da bakinsu sai in gane sunzo sai in saci jiki idan iyayena na gida in fita da gudu wajensu mu dunguma mu tafi gidansu. Ina da shekaru goma dai-dai na gama makarantar Primary muka dauki jarabawar (common interance examination) kafin jarabawar mu ta fito har zaman gida ya ishe ni. Kannena sun tafi makaranta, iyayena sun tafi wajen aiki saini kadai a gida da mai aikinmu Tabita. Ina bata labari cewa "Ina so muci makaranta daya ni da kawayena. Sai Tabita tace mun inzo in roki abunda take bautawa zaisa muci makaranta daya da kawayena. Inje muyi ta rokar sassakekken itacen nan. Idan naje wajen kawayena mumuyawa suma sai na fada musu bukatata ina son muci makaranta daya da kawayena. Suma sai su ce muje wajen abunda suke bautawa a rokeshi, nan ma muje mu durkusa mu fadawa dodon bukatar sai ya ce mun an gama. Na dawo a hanyata ta tahowa gida dai-dai kofar gidan makwabtanmu wato gidan su Huzaifa na hadu da Bilki, da Amina kannen Huzaifa ne kawayena ne zasu tafi makarantar Islamiyya. Sanye suke da hijabansu har kasa da kur'anansu a hannunsu sun bani sha'awa matuka. Bayan mun gaisa sai nace musu "Inzo muje makarantarku? Wani kallo suka min na wulakanci Amina ta ce "A haka zaki bimu? Kalli riga shimi ce a jikinki da dan karamin siket iya cinya, kanki ba dankwali gashinki a waje. Ance miki makarantar arna ce? Bilki ta ce da Amina "Ke kike mata bayani ma ko tasa hijabi ai ba zata iya binmu ba tunda ba Musulma bace sai anyi mata wankan shiga Musulunci. Suka wuce abinsu suka barni anan a tsaye. Ashe yayansu Huzaifa na gefenmu a zaune akan abun sallarsa ya idar da sallar la'asar yana karatun kur'ani. Nazo zan wuce jikina yayi sanyi babu abinda nake nanatawa a raina sai magnar Bilkisu da Amina. Kaina ya daure ina tunanin su kuma wadannan me suke bautawa da har zasu ce bazan iya zuwa a haka ba sai nayi wankan shiga Musulunci. Muryar Huzaifa ce ta katsemun tunanin dana ke, daman daga shi sai Mahaifina suke kirana da Fatima. Na juyo da sauri sai naga Hamma Huzaifa ma'ana Yaya Huzaifa da fulatanci. Na karasa wajensa na cire takalmina na zauna akan takalmin a gabansa, fara'ar da na saba yi yaga sai kadan yasan lallai maganar da kannensa suka fadamun tayi min ciwo. Ya ce "Fatima yau bakya fara'a lafiya? Na gyara zama na ce "Hamma Huzaifa wai shin a addininku wa ku ke bautawa? Huzaifa yaji dadin tambayar dana yi masa yayi murmushi ya ce "Fatima ni Musulmi ne kuma duk wani Musulmi Ubangiji yake bautawa Shine Allah Shine Ya halicci Duniya da Lahira, Ya halicci dukkan mutanen duniya da aljanu, shine Ya ke mana ruwan sama amfanin gona ya fito mutane su girba suci, Shine Yake rayawa kuma Yake kashewa, Shine Ya ke sa rashin lafiya kuma ya bada lafiya, Shi Ya ke azurtawa kuma yake talautawa. Bai haifa ba ba'a haifeShi ba. Ma'ana baShi da uwa baShi da uba bashi da da ko jika. Baya bacci kuma baya gyangyadi. Duk abunda mutane suke a duniya yana kallonmu mune baza mu iya ganinsa ba. Ya aiko mana da Annabi wato Annabi Muhammad (S.A.W) da sallah, azumi, zakka da Hajji idan kana da hali. Duk wanda bai yadda cewa Allah guda daya bane kuma Annabi Muhammad (S.A.W) Manzonsa ne to idan ya mutu zai dauwama ne a wuta. Allah Zaiyi masa azaba har abada. Kamar hayaki haka naji zuciyata ta turnike nayi minti uku bance uffanba, can na shaki numfashi na ce "Hamma Huzaifa wa Mahaifina yake bautawa? Huzaifa yayi murmushi ya ce "Mahaifinki Musulmi ne, addininmu daya Allah guda daya yake bautawa kuma ya yadda Annabi Muhammad (S.A.W) Manzonsa ne. Na ce "Wa Mahaifiyata take bautawa? Huzaifa ya ce "Mahaifiyarki ba Musulma ba ce, bata yadda da Annabi Muhammad (S.A.W) ba. Nayi shiru can na ce "Wa Tabita me aikinmu take bautawa? Ya tambayeni "Yaya take addinin nata? Na fada masa yadda take sai ya girgiza kai ya ce "Tabita ta bata, tayi shirka tana bautawa itace ne kawai ba Allah ba. Itacen da da kanta ta sassako ta gina ta ce Ubangijinta ne kuma ko yanzu aka dauko shi aka ce ya biya bukatarta bazai iya ba, baya gani, baya magana, da za'a jefashi a wuta konewa zaiyi daman kuma itacen dafa abinci ne kawai. Nayi shiru ina tunani a raina na ce "Tabbas zancen Huzaifa gaskiya ne, itace ne kawai Tabita take bautawa ko motsi bayayi. Na sake gyara zama na tambayeshu "To me su Mungai suke bautawa kawayena mumuyawa? Yayi min tambaya tsaf yaya suke bautarsu? Na fada masa saiya kyalkyale da dariya ya ce "Wannan mutum ne kamarki, suke nada shi suke saka masa rigar gashi. Babu abinda zai iya basu shima Allah ne Ya halicce shi kuma Allah Zai kasheshi. Bai isa komai ba kuma Allah Zai kona su. Daga nan ban sake cewa komai ba sai nasa takalmina na yiwa Huzaifa sallama na nufi gida zuciyata cike da wasu-wasi ina tafe ina kallon shukoki da bishiyoyi cike da *ya*yan itatuwa ina nanatawa a rai na duk wadannan Allah su Huzaifa ne yayi su. Ban tsaya a ko ina ba sai a boys' quarters mu don nasan Tabita ta gama abincin dare da share-share, ta rufo gidan ta koma dakinta. Ita kadai na samu a tsakar gidan tana cin tuwo. Ina isowa na zauna a gabanta zansa hannu inci abincin sai ta rike hannuna tace inje in wanke hannuna nayi wasan kasa na taba fatar mumuyawa. Naje na sami ruwa na wanke hannuna na dawo zan zauna, ta ce kar in zauna in shiga in roki abunda take bautawa cewar zanci abinci ya samun albarka a abinci. Duk a cikin yarenta muke maganar wato tangalanci. Ban ki ta tata ba amma ko dana shiga dakin bautar sai na tsaya kawai ina kallon sassakakken itacen nan cikin nutsuwa sai naga ashe kawai gunki ne, yayi min kama da *yar tsana. Nasa hannu na taba shi sai naji itace ne. Nayi masa tambaya na ce "Kana ganina ko bana cikin gidan nan? To fadamun da ina da ina naje yau? Shiru bai amsa mun ba. Tabita ta leko ta kwallamin kira ta ce me nake yi har yanzu, in fito ai ya ji saina fito nazo na zauna muke cin tuwo. Munyi nisa da cin tuwo saina gyara zama na ce "Mama Tabita kinga wancan abunda kike bautawa itace ne kawai baya magana, baya ji baya gani. Idan na jefashi a wuta konewa kawai zaiyi daman kuma itacen tuwo ne. Kema ki dinga bautawa Allah daya wanda ya halicci duk mutanen duniya, Ya halicci duniya da lahira da shuka da bishiyoyi. Yana jinmu, Yana ganinmu mu bama ganinsa, kuma baya bacci ko gyangyadi. Kamar yadda Huzaifa ya fada mata ta haddace tas. Tabita ta kwalla kara ta zabura ta mike tsaye a tsorace ta ce "Pretty kece kuwa? A ina kika san duk wannan? Nayi murmushi na mike tsaye naje na wanke hannuna na dauki mukullin gidanmu a gefenta, murmushi kawai nake yi mata na daga mata hannu na fice na tafi na barta tamkar sassakakken gunki irin wanda take bautawa. Iman ta surnano da hawaye tayi ajiyar zuciya. Mutanen dake wajen gaba daya sun sami wajen sun zauna daga dukkan alamu labarin Iman yana da shiga jiki. Cike yake da ikon Allah, Suhaif babu abinda yake sai girgiza kai. Reedwan kuma ya kasa kunne sai copy din labarin ya ke. Malamai sai fadi suke "Allahu Akbar" Iman ta ci gaba da cewa. Misalin karfe bakwai na dare Mahaifina ya dawo ya iske ni a zaune a falo ina kallo. Ya tambayeni "Mummy bata dawo ba? Na ce "Bata dawo ba ta tafi da su Rabecca wurin bauta da yamma. Ya hau kan dinning table yana cin abinci, sai nazo na jawo kujera daya na zauna na dube shi nayi murmushi yayi murmushi shima ya ce "Fatima kina da magana ne? Na ce "Eh Daddy, wai shin Daddy wa kake bautawa ne? Ya dubeni cike da mamaki sai ya tambaye ni me yasa nayi masa wannan tambayar? Na fara bashi labarin addinai daban-daban. Na ce "Wasu na bautawa sassakeken itace. Wasu na bautawa dodo mai gashi duk jikinsa, wasu na taruwa a wani waje suna bauta, wasu kuma suna sallah. Sun yarda Allah daya ne, wanda Ya halicci sama da kasa da mutane da aljanu, da bishiyoyi da komai na duniya. Ya aiko Annabi Muhammad (S.A.W). Sai ya ajiye cokalin da yake cin abinci ya dube ni cike da mamaki ya ce, "To wanne ne addinin gaskiya Fatima? Na ce "Shi ne nake son in sani, sai yayi shiru yana kallona. Na mike tsaye na fara tafiya zuwa falon da kujeru suke, na juyo na ce "Daddy ina ganin addinini Musulunci shi ne addinin gaskiya. Na wuce kan kujera na ci gaba da kallona. Mummy da kannena Bobby da Rabecca ne suka shigo gida. Kannena suka taho da gudu suka dane ni. Rabecca ta ce min cikin harshen Turanci "Sister mun je wajen bauta mun yi addu'a bakya nan, Mummy ta aiko direba ya zo ya tafi damu. Mun ci kek da lemo ban da ke. Wata uwar harara Mahifiyata ta sakar min kamar yadda ta saba kullum, na san laifin da nayi na kin tafiya wajen bauta, an zo daukar mu bana nan, na tafi yawo. Sai na sunkuyar da kaina kasa, ta gaishe da Mahaifinmu ta wuce dakinta. Tabita ta shigo kamar yadda ta saba ta yi mana wankan dare muka sa rigunan baccinmu ta raka mu dakinmu muka kwanta, ta kashe mana fitila ta zo ta wuce boys' quarters. Juyi nake fiye da awa daya na kasa bacci zancen Huzaifa na ta caka min kwakwalwa, na san addinai kala-kala amma ban tabajin irin wanda ya ratsa mini zuciya kamar addinin Musulunci ba. Na dade ina wannan tunani cewar kowa abin da yake bautawa ne ya halicce shi? Idan aka mutu sai in yi ta tunanin yaya za a yi mutum ya mutu shi kadai. Har ma Huzaifa ya wayar min da kai yau. Duk da yake ban gama gane abin da Huzaifa yake nufi ba. Na tashi cimak daga kan gadonsa na fito falo sai na sike Mahaifina a zaune a falo yana kallon talabijin. Na tamabaye shi ina Mummy? Ya ce "Tana dakinta. Na wuce zuwa dakinta. Na kwankwasa kofar na shiga na iske ta sanye da tawul ta fito daga wanka. Ta yi mamakin ganina ta ce "Lafiya ko don bakya zuwa makaranta shi ne kika ki kwanciya da wuri? Ina fatan ba ki hana kannenki bacci ba ko? Don su zasu tafi makaranta gobe da safe. Na ce "Sun yi bacci tun dazu, na zo ne in yi miki tambaya. Ta tattara hankalinta tana saurarona. Na gyara durkusan da na yi a gabanta na ce "Mummy wa kike bautawa ne? Cikin harshen Turanci na tambayeta ta zazzare ido tana kallona can ta ce "Ban gane tambayarki ba Rufkatu? Na sake maimaita mata cikin harshen Fulatanci "Mummy moi atokirta? Sai ta tsuke fuska ta ce, wato baki san abin da nake bautawa ba shi ya sa kike gudowa daga wajen bauta? Ke yarinya yaushe aka haife ki da har sai kin binciki me nake bautawa, sannan ki bauta masa? Ta yi ajiyar zuciya ta dafa kafadata ta fara cusa mun ra'ayinta a nutse yadda addininta yake. Da ta gama sai na mike tsaye na girgiza kai na ce "Allah guda daya ne shi ya halicci mutanen duniya gaba daya ya halicceki ya halicci Daddy. Ta amsa min da Eh na yarda da hakan. Sai na ce "To me yasa bakya sallah, shi kuma yake yi, me yasa ba za ku bautawa Allah Shi kadai ba? Ta daka min tsawa ta ce, tambayar ta ishe ta haka in tafi in kwanta. Har nakai bakin kofa zan fita sai na juyo na dube ta na ce "Allah guda daya ne, ba shi da uwa ko uba haka ba shi da da ko jika, ba ya bacci ko gyangyadi, yana kallonmu, mu ba ma iya ganin Sa. Na fice na bar Mahaifiyata, don mamaki saita dora hannu aka kamar me shirin kwala ihu. Ta kwana bata rintsa ba ta shigo dakinmu ta rike hannuna tayi min addu'a ta fita taje suyi fada da Mahaifina wai shi yake cusa mun addininsa bazata yarda ba. Tun baya kulata har ta isheshi ya biye mata suka dinga fada kamar zasu daku. Saita sake dawowa dakinmu ta sake yimin addu'a haka ta kwana tana yi har bacci ya daukeni. Bayan ta sauke su Rabecca a makaranta ta wuce wajen aikinta ta dau izini zata je unguwa, sai ta wuce dani wajen bautarsu tana kuka tana shaidawa babbansu halin da *yarta take ciki. Sun juya suna magana yana fadin addu'a za'ayi min na sulale na arce ban tsaya a ko ina ba sai garin mumuyawa wajen kawayena muka ci gaba da wasanmu. Nake shaida musu su daina bautawa wanda suke kira Ubangiji, ubangiji Shine Allah wanda Ya halicci duniya da lahira. Sai karaf a kunnan Maho Mahaifiyar Mungai abokina ta taho da sauri ta jamu daki dukkanmu ta bubbugemin baki ta jajjawa sauran kunne tace karta kara jin nayi wannan maganar suma kuma kar su fadawa kowa, idan ba haka ba dodo zaisa a kashemu a kashe iyayenmu. Tace maza insa takalmina in tafi gida wasan ya isa haka. A kofar gida naga Hamma Huzaifa a zaune akan mota ya dawo daga Yola a inda yake neman addimission zai shiga jami'a FUTY. Na karasa wajensa na gaishe shi cikin harshen Fulatanci kamar yadda muka saba da yaren fulatanci muka yin magana sai wani lokacin ne muke yi da turanci. Yayi murmushi ya ce "Pretty kin cika yawo wato dan bakya zuwa makaranta ko? Nan dai nima na dane kan mota kusa dashi na zauna ina ta jero masa tambayoyi game da addininsa kuma addinin da yafi shiga raina. Amma ban isa in bishi ba saboda tsoron Mahaifiyata. Musamman sallah ina sha'awar yadda mata suke saka hijab suna sallah. A lokacin Hamma Huzaifa ya dinga cusawa raina inji tsoron Allah kome zanyi. Ya ce kada in kuskura in yi zina, Allah baYa son mai zina. Allah Ya ce "Kada ku kusanci zina barema ku aika ta. A cikin kur'ani. Allah Yana kallon kowa, mutum ko ya kulle daki, ya kashe fitilarsa a duhun Allah na kallonsa. Kada kiyi sata, ko gulma, zaluntar wani duk ya hana bayinsa suyi, zai konani duk wanda yayi idan na mutu. Na yi shiru ina tunani can na ce "Yanzu ko karkashin motar nan na shige na kwanta nayi luf Allah Zai ganni? Hamma Huzaifa yayi dariya ya ce "Zai ganki mana. Na ce "Idan na zura da gudu na shige dakinmu na kulle na shige can cikin toilet dinmu zai ganni? Karshen kwatancen da yayi min shine ya ce ko cikin Mahaifiyata na buda na shiga aka mayar da cikin aka rufe ta daura zani ta saki rigarta ta dauko mayafi ko bargo ta lulluba Allah na ganina. Saina fara jinjina ikon Allah a zuciyata, lallai Allah Mai girma ne kuma Shi Ya cancanci a bautawa ba dodo ba da sassaken itace. A ranar Hamma Huzaifa ya fara fasalta min yadda ni'imomin aljanna suke, ya ce idan na bi Allah zan shiga aljanna. Sai kuma ya zano min azabobin wuta, ya ce idan naki jin tsoron Allah Zai konani bayan mutuwa. Hmmm, ba sai na fada ba wallahi duk wanda bai bi Allah ba, maganar Huzaifa haka take. Allah Yasa mu dace. Ameen. Hai jango........ Nasan su wa'e basu gane ba, sai gobe nake nufi. Reedwan Suraj Isma'il >>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA ____CI GABAN LABARIN A nan kan mota Mahaifiyata ta zo ta sameni. Ta jawoni a fusace zata dakeni ashe tuntuni ta karada gari nemana ta rasani sama ko kasa ita da *yan wajen da take bauta. Hankalinta a tashe yake musamman yadda na nuna mata karfi da yaji naki addininta. Dakyar Hamma Huzaifa ya hanata dukana. Ya durkusa har kasa yana rokarta kasancewar tana ganin mutuncinsa saboda yana da hankali ga ladabi a unguwar, kunyarsa tasa ta hakura. Amma a lokacin tayi rantsuwa ko jarabawata ta fito naci inda nake so inje ni da kawayena ba zanje ba, wata makaranta zata nemarmin a kudu makarantar koyar da addininta. Kona ki kona so dole inso addininta. Ta dakamun tsawa ta ce in shiga mota mu koma can. Na shiga mota a tsorace yayin da hawayen takaici ya dinga surnanowa daga idanuwana. Hamma Huzaifa ya bini da kallo cike da tausayina saiya dagamun hannunsa sama da alama addu'a yake yimin, sai naga hawaye yana zuba daga idanuwansa, ta ja mota suka tafi. Iman ta sharbe hawaye mai radadi, Malamai da mutanen da ke wajen suka dinga hawaye. Suhaif ma ya surnano da hawaye, ya dauko hankici daga aljihunsa ya mikawa Iman ta goge hawayen idonta. Sai Allahu Akbar suke kira. Wasu na girgiza kai don tausayin Iman. Ta dade tana sharbe hawayen idonta sannan ta ci daga da basu labari. Tace "An kaini wajen bautarsu anyi min addu'o'i, cikin lallami shugabansu yayi min nasiha ya cusa mun ra'ayin son addininsu shine addinin gaskiya. Sai kaina ya sake cunkushewa na sake dabarbarcewa tunanina ya hautsine na kasa tantance addinin gaskiya. Haka kuwa akayi mahaifiyata ta samo min makarantar da ake koyar da addininsu dake Enugu. Raina baya son kudu nasha kuka Mahaifina bai so ba amma Mahaifiyata ta ce saina je. Hamma Huzaifa ma yasha bacin rai, kawayena Mumuyawa sunsha kuka zamu rabu haka aka kaini garin Enugu. Nasha bakar wuya a makarantar saboda yadda nake jayayya da Malamai a duk sanda aka zo darasi akan addininsu, ana fara wa'azi duk sanda suka fadi wani abu sabanin yadda Hamma Huzaifa ya fadamun saina tashi na karyata Malamin a aji. Ince Malam ba haka bane baka fada dai-dai ba, Allah baShi da uwa baShi da uba baShi da da ko jika. Sai suyi ta mamakina tun suna bani amsa a hankali suna kawomin hujjoji daga littafinsu amma bana dandara ko gobe Malami yazo aji ya fadi wani abu sabanin abunda Hamma Huzaifa ya fadamun zan tashi in karyata shi. To sai suka shiga dukana kamar Allah ne ya aikosu har da farfasamun jiki. Dalibai ma suka tsane ni. Seniors su kayi ta dukana suna zagina a hostel wai daman banyi kama da su ba watakila ni ba bafillatana bace dama balarabiya ce nazo in yada addinin Musulunci. Takai ta kawo duk an tsane ni duk da haka ban canja ra'ayina ba sai dai idan ba'a shiga ajinmu ba an fadi wata kalmar da bata yimin ba akan addini sai na musa. Malamai suka ga zasu kasheni saboda duka kuma baisa na daina ba, sai aka kaini kara wajen shugaban makaranta aka zauna meeting. Aka kirani ofishin suka zagayeni dukkansu tambayar da suka yi min shine "meye addinina? Na ce musu ban sani ba. Suka sake tambayata meye yarena? Nan ma bansan yarena ba, na dinga zano musu yare kala-kala da nake ji. Suka bugawa Mamana waya aka shaida mata tazo ta dauki *yarta don wannan makarantar koyar addininsu ce, *yar kuma ba irin addinin take ba Musulma ce. Mummyna ta fashe da kuka don takaici tace ba Musulma ba ce. Suka ce sun tambayeni yarena shima nace ban sani ba na zano musu yare iri-iri sufa sun kasa gane wannan wanne irin abu ne? Ta ba su hakuri ta ce kuma za ta zo karshen sati. Mummy ta zo makarantar ta ba wa Malamai da shugaban makarantar hakuri ta yi musu bayanin cewar Mahaifina ne Musulmi yake hure mun kunne da addininsa shi ne ma ta ga gara ta kawoni makarantar koyon addininta. Ta ce ni yarinya ce mai kaifin basira dukan da suke yi mini ba zai sa in canja ra'ayina ba, amma in har za su zaunar da ni cikin hikima da dabaru su karanto min addininsu a hankali, to tabbas zan rike a zuciyata sai in sawa zuciyata son abun. Ta zayyano musu yadda zasu bini har ta ce zata dinga biyan wani kudi na musamman ga Malamin da zai dinga ware lokaci yana yi min darasi na musamman ni kadai a kan yadda zan fahimci addinin sosai wato (extra Lesson). Ta kira ni gefe cikin dabara ta dinga lallaba ni tana yimini wa'azi har naji zuciyata ta fara karkata ga addininsu. Na tsayar da hankalina a waje daya na sa karatu a gaba na yarda da abin da suka cusa min a zuciya. Ta kai ta kawo idan aka yi jarabawa akan addinin na fi duk *yan ajin cinyewa. Mahaifiyata tana jin dadi sosai, hankalinta ya kwanta. Idan na fara zayyano mata abin da yake kwakwalwata wanda aka koyamin a makaranta na game da addininta, mamaki yana rufeta tamkar na haddace littafin a kaina sai ta yi murna. Mun gama shekarar farko har mun shiga shekara ta biyu a makarantar. Wata rana ranar Asabar da rana a makarantarmu na fito daga hostel zan tafi hall karbar abinci, na zo wucewa ta dakin seniors sai wata daliba *yar aji shida ta kirawo ni ta ba ni wata roba ta ce in karbo mata abinci daga hall. Na durkusa na karba don girmamawa don muna matukar tsoron *yan ajin gaba damu. Musamman ni da na yi kaurin suna a makarantar sun tsane ni ana min zargin ko ma ba addinin nake yi ba, na tafi hall sai na tarar teba aka yi da miyar danyar kubewa dama ni duk ranar da aka yi teba ba na ci, sai na karbi wacce aka aiko ni na fito, na kusa karasowa dakin sai na hango ta ta bude wata katuwar lokar da ke kusa da gadonta. Lokar cike take da kayan makulashe kai ka ce katafaren kanti ake shirin budewa. Biskit kala-kala, alewa, cingam, madara, milo, corn flakes, da dai sauransu. Senior ta kalle ni ta yi murmushi da taga ina kallon kayan lokar, na mika mata robar teba na juya zan tafi sai ta kirani na dawo. Ta dauko leda ta dinga damko biskit da alewa kala-kala tana zubawa a ledar ta cika ta taf ta mika min, na kalle ta cike da mamaki na tambaya. "Wa zan kaiwa? Sai ta yi murmushi ta ce "Na ki ne, ki je ki ci ke yarinya ce mai hankali, ga shi ba ki da kiwa. Na yi murmushi, farin ciki ya rufeni, sai na duka na yi mata godiya na fito daga dakin. Ta fito har bakin kofar dakin tana dagamin hannu, ni ma ina daga mata. Duk waigowar da zan yi sai na ganta a tsaye a inda take tana dagamin hannu, har sai da na shiga dakinmu, ina ma da biskit kala-kala a akwatina, amma ba ni da irin wadannan tsadaddun, alewa kuwa ba ni da ita don *yar kadan mamana ta saya min, ta ce na cika shan zaki ida na ga alewa ko biskit ko abinci bana ci sai shan alewa. Don haka tuni na shanye alawowin a kwana kadan. Na haye kan gadona na lankwashe kafa na bude ledata cike da farin ciki don yau na huta da cin abinci tunda na sami alewa da biskit. Na dauko wata katuwar alewa wacce aka yi ta da cakudadden bonbita da madara, daga gani zata yi dadi. Tun kafin in kai bakina har yawuna ya fara tsinkewa. Ledar alewar kadai abar kallo ce da sha'awa tun kafin ka bude. Nakai ledar bakina zan cisga in yaga sai na dakata cak ina tunani. Abunda ya fado mun a raina nasihohin da labarun da wasu Malamai da prefect suke bamu a Makarantar kasancewarmu kanana, sababbain suwa bamu san abunda yake faruwa a makarantar ba. Ansha ja mana kunne akan mu guji cin abun wacce bamu sani ba, saboda akwai dalibai da suke kungiyar matsafa a makarantar, suna nan jifge guda har sun kafa kungiyarsu suna kuma jan *yan uwansu dalibai cikin kungiyoyinsu a boye. Wadannan daliban ba'asan ko su waye ba kuma babu wata shaida da zaka gani a jikinsu kace sune wadannan balle ka gujesu. Amma dai koda yaushe ana samun wadanda aka tsafe, wasu a sume, wasu kuma an kawar da hankalinsu sai dai a mayar dasu gida don basa iya tuna abunda ya faru. Duk yadda suka boye kansu amma ansan wasu daga cikin daliban ana korarsu amma koda ankori iri-irinsu sai kaga sun sake yaduwa fiye da da. Kullum a tsorae muke musamman da daddare, anan ana tsoron fitar dare saboda aljanu, acan kuma haka ake tsoron fitar dare saboda matsafa. Idan kaga yarinya ta kwanta bacci anzo an tasheta bata tashi ba, a girgizata, a dauko ruwa a sharara mata bata farka ba. Daga karshe a dauko reza a tsattsaga jikinta ko motsi baza tayi ba. To *yar kungiyar ce kuma gangar jikinta ce anan ruhinta ya tafi wajensu. Sai sanda kurwarta ta dawo sai tayi firgigit ta tashi taji tsumu-tsumu cikin ruwa taji radadi wajen da aka tsaga mata. Duk a gabanmu muke ganin irin haka dan haka kusan kowa bai yarda da kowa ba, ko kawa ba'a cika yi ba kuma ba maicin abun wani. Sai dai in tuntuni kasan mutum. Wala gidanku daya ko *yan uwa ko gari guda, ko kun zauna kun saba ka karanci mutum ka yarda dashi. Sai na mayar da alewar hannuna cikin leda na daure ledar na jefa ledar na jefa kan akwatina na fasa sha. Ga bakar yunwa ina ji amma wani barci mai nauyi na ba gaira ba dalili ya ruftomin ko idona bana iya budewa, tun ina jingine akan filo harna mike na kwanta akan gado nayi ta barci mai nauyi. Bazan iya fasalta yadda naji ba kamar a mafarki, kamar a ido biyu naga wasu irin mutane sun zagaye gadona mata da maza, manya magidanta ba dalibai bane, da kuma daliban har da uniform irin namu. Sannan *yan kananan yara *yan primary duk suna ta dariya da karfi mai tsoratarwa. Babbansu wani tsoho tukuf cikan harshen turanci ya ce mun "Rufkatu sannu da zuwa cikinmu, yanzu kin zama mu mun zama ke. Zamu yi miki arziki, farin jini, mu kara miki kyau da kwarjini da ilimi zaki ji dadin rayuwarki. Amma kada ki bi ko wanne addini domin bama son addu'a kowacce iri ce. Sai naji na ce "Bana sanku kuma bazan shiga cikinku ba. Ya jawo wata budurwar yarinya gabansa ya ce mata bude idonki ta ganki. Sai budurwar ta yaye wani gyale da ta rufe idonta sai naga wannan senior ce da ta bani biskit da alewa dazu. Sai ta ce "To meya sa kika ci alewa da biskit dina, ki biyani. Saina nuna mata kan akwati na ce gasu can ban ci ba, dauki kayanki. "Suka kwashe da dariyar mugunta suka ce "Rufkatu aikin gama ya gama ki bamu uwarki ko ubanki mu kashe. Na firgita amma na rasa addu'ar da zanyi a cikin addinina na kasa tuno addu'a daya da zanyi dan babu addini daya dana tsayar har in koyi addu'ar neman tsarin makiya da akeyi, sai na fara kwalla kara mai firgitarwa. Babbansu yasa hannuna ya kama gashina ya dinga cukurkudawa ina ihu kamar raina zai fita. Ni dai na bude ido naga *yan dakinmu gaba daya a kaina ana tambayata ihun me nake yi. Ban iya basu amsa ba naci gaba da ihu kamar zan tsaga kunnuwansu don a firgice nake ba zan iya tuna abunda ya faru ba ga tsananin ciwo da jujjuyawar da kaina yake mun. Dalibai suka dunga zazzagamun addu'a, ban daina ba sai aka je staff quarters aka kira malamai suma suka zo suka fara tasu. Saina daina ihun na fara wani bacci mai kama da mutuwa. Kwanana daya da yini daya a gadon asibiti ana karamun ruwa ban farka ba. Aka nemi wayar gidanmu ba'a samu ba a lokacin an rufe layin. Sai aka daukeni aka kaini wurin addu'a a garinmu ana ta cigiyar Iyayena. Nan da nan Mahaifiyata taji labari ta garzaya wurin taga ni din ce kuwa. Sai ta fashe da kuka, ganina cikin wannan hali . Ta tambayesu meya sameni suka bata labarin abunda ya faru. Sai tasan wannan ciwon nawa bana asibiti bane. Saita daukeni ta tafi dani wajen bautarsu. Nan fa suka dukufa da yi min addu'a ba kakkautawa ba dare ba raba ga karin ruwa ana yimin saboda bana ci bana sha a sume nake kawai a kwance kamar gawa numfashi kawai nake yi da an binneni, har tsawon kwananki biyar a haka a kwance. Mahaifina da yaga haka shima ya hado Malamai musulmai suka hadu har Hamma Huzaifa duk suka dauki Alkur'ani suka yi ta saukewa a kofar gidanmu. Ana yanka ana sadaka, addu'a bata faduwa kasa saina farka na bude idona. Iman ta fashe da kuka haka *yan wajen sai hawaye ya dinga zubo musu. Sai girgiza kai suke dan tausayi. Ta jima tana kuka kafin taci gaba tace. Nasha wuya, nasha wuya a wannan lokacin domin sai dai ban kwanta barci ba na dinga ganin wadannan mutane suna firgitani. Daga karshe Mamana ta hakura da makarantar aka dawo dani ta jeka-ka-dawo a nan jalingo ina zuwa ina dawowa gida a hankali-ahankali kuma ana yimin addu'a daga dukkan bangaran uwata da ubana, Hamma Huzaifa har rubutun kur'ani yake min yana kirana a boye yana bani ina sha yace kada in fadawa Mahaifiyata. Sannan nabar ganinsu a mafarki na dawo hayyacina kamar da. Naci gaba da harkokina kamar kowa kuma ina jin dadin sabuwar makarantar ta jeka ka dawo. Amma naci gaba da bincike akan addinai kuma ina zuwa wajen kawayena Mumuyawa kullum bayan na dawo daga makaranta, haka ban daina zuwa dakin bautar mai aikinmu ba Tabita ina ganin yadda ake bautarta ina yi mata tambayoyi. Kuma dolen-dolena in bi Mahaifiyata wajen bautarta duk ranar yin bauta. Musamman yadda Mahaifiyata ta sami karin girma ada aka bata mukami saboda saninta, da kwazo a bin addininta. Dukiyarta, jinin jikinta da duk lokacinta duk ta sadaukarwa addininta. Ta kai ta kawo duk ranar bauta bayan an tashi daga wajen bauta su Mahaifiyata suna shiga motoci su shiga kauyuka da burane suna wa'azi suna kira zuwa ga addininsu. Na fara zama budurwa na kara wayo da hankali. Ina zama da Hamma Huzaifa a kofar gidansu lokaci-lokaci da yamma idan na dawo daga makaranta naga Mummy bata nan, kuma idan bana son zuwa wajen kawayena da abokaina Mumuyawa. Shi daman Hamma Huzaifa kullum da yamma idan yana gari bai koma makaranta ba a kofar gidansu yake shimfida darduma ya zauna yana karatun kur'ani, a lokacin yana karatu a FUTY jami'ar dake Yola. Sai inzo in zauna in yi ta sauraronsa domin karatun yana yimin dadi kuma ina sha'awa in koya. Idan ya shafa addu'a sai mu shiga hirar duniya a hankali sai mu gangaro hirar da muka saba ta addini. Na ce "Hamma Huzaifa ka bani addu'ar kariya idan abun tsoro ya tunkaroni. Sai ya koyamun ayatul kursiyyu, falaki da nasi, duk da nasha wuya kafin in koya amma na nace dakyar na koya da sudin goshi kuma na dauki lokaci mai tsawo kafin na iya sosai. Watarana ina aji hudu na secondry ni da kawayena mun fito daga get din makaranta an tashi zamu gida saina ji dik mutum ya diro a gabana ina tafiya na tsaya cak sai naga wannan budurwar data bani alewa da biskit amma a suffar abun tsoro tazo mun, farata zaka-zaka da hakora. Ta mika hannu zata tabani na tsorata na fadi kasa ina karkarwa, sai Allah Yasa na tuno da addu'ar da Hamma Huzaifa ya koya mun saina fara karanto ayatul kursiyyu ta kasa tabani saita bace. Wadanda muke tafiya basu ganta ba ni kadai na ganta sunga kawai na fadi kasa ina karkarwa har sun wuce suka dawo suka tashe ni muka tafi. A lokacin na sake sakawa raina ina son Musulunci addinin gaskiya ne. Na ci gaba da bincike da koyon abubuwa a cikin addinin a wajen Hamma Huzaifa ko kannensa idan baya nan. Ko kuma kawayena Musulmai. Watarana in shiga library makaranta bangaren littattafan addinin musulunci in buya inyi ta karantawa. Ina da kokari a makaranta sosai don haka ina S.S 2 na zana jarabawar S.S.C.E tare da *yan S.S 3 kuma na cinye dukka. Mahaifana sunyi murna sosai, ba tare da bata lokaci ba Mahaifina ya samarmin addimission a ATBU yace can zanje idan naje Yola bazan yi karatun kirkiba saboda akwai *yan Jalingo da yawa kuma kusa da gida ne gara nesa. Da farko na damu sosai kawayena Harriet da Janet suka ce kar in damu dukkansu jami'ar ATBU zasu tafi saimu hadu kawai a can, sannan naji hankalina ya kwanta. An bani course din da Mahaifiyata ta karanta achetecture naji dadi Iyayena ma sunji dadi. Kafin inje registration saida Mahaifiyata da Mahaifina dani muka je London da China yawan shakatawa kamar yadda koda yaushe suke yimin alkawari idan na gama secondry naci jarabawata zasu kaini kasashen waje. Munyi sati hudu acan sannan muka dawo. Alokacin har naso in makara saboda an koma makaranta har an kusa rufe rigistration. Cikin gaggawa Mahaifina ya hadamin kayan tafiya kamar sababbin dinkuna na zamani, privision. Takalman gayu akwatina masu tsada littafi biruka, Pencil da dai sauransu. Ya kaini har Bauchi Da kansa ya tayani muka yi registration saida ya tabbatar ya kammala mun komai. Ya biyamun kudin daki a hostel dake cikin makarantar. Yayi min fada sosai in tsaya inyi karatu kamar yadda shi da Mahaifiyata suka yi suka fito da first calass degree. Har ya zazzagaya dani wasu wurare a makarantar yake nunnunamin inda suke zama da Mahaifiyata suyi karatu tare. Don haka kar in biyewa kawaye marasa son suyi jaratu. Abu daya Mahaifina ya bani mamaki da bai taba yimin fada akan in rike addinina ba, har yayi min fadan ya gama ya shiga mota zai tafi naga baiyi min zancen addini ba. Sai na ce "Daddy baka ce in rike addinina ba. "Ya tsaya yana kallona kwai ya kasa magana. Sai hawaye ya zubo daga idanuwana, na ce "Daddy ko dan ba addininmu daya ba? Jikinsa yayi sanyi hankalinsa ya tashi sosai. Cikin harshen fulatanci na yi magana na ce "Bakar saniya mai cin ciyawa koriya ta bada farin nono. Ya sake zare ido yana kallona, saina juya na tafi hostel ina daga masa hannu. Ya kifa kai akan sitiyarin motarsa, yafi minti goma sha biyar bai tafi ba yana tunani da hawaye. Ina lekensa ta daki, sannan ya share fuskarsa ya ja mota ya tafi. Daga Bauchi sai ya shiga Gombe garinsu don ya gaishe da Mahaifiyarsa da danginsa, duk da yana gani a fuskokinsu basu bukatar ganinsa sun ma cireshi a dangi haka kuma ko kyautar kudi ya yiwa Mahaifiyarsa bata karba kome ya sayo bata ci. Kuma duk sanda ta ganshi sai tayi kuka, dan haka hankalinsa yana tashi idan yaje Gombe sai ya rage zuwa sosai jifa-jifa. Allah Ya tsaremu daga sa6awa Iyaye maganarsu. Ameen Sai kuma Allah Ya kaimu gobe da yaddarSa. Ina cigiya wanda yake da wannan littafin a hannu pls. Reedwan Suraj Isma'il """""""""""""""""" YARENA ADDININA ____CI GABAN LABARIN Na hadu da kawayena Harriet da Janet suma kuma duk cours dinmu daya. Ranar da muka fito daga lecture farko su Janet suka cemun ga wani abokinsu sunansa Micheal yazo daukarsu zasu je suga gidansa dake New G.R.A. Wai inzo in rakasu. Na ce meyasa zasu tafi bayan da yamma muna da lecture? "Suka ce "Ai yana da mota zai dawo damu kafin lokacin. Fadan da Mahaifina yayi min shiya fado min a rai, ya ce kada inyi kawance da wadanda basa son yin karatu. Sai nace su je ni ba zani ba. Suka takura mun, Micheal din ma ya zo yasa baki wai in daure inje yanzu zamu dawo a matsayinmu na baki a Bauchi shi kuma dan gari shine yake so ya nuna mana gari da gidansa. Ko ba komai dai mun san wani, koda muna bukatar wani abu, shi kuma zai rikemu a matsayin kannensa zai taimaka mana. Naji lafazinsa masu sanyi na shiga mota muka tafi. Ashe daga wannan tafiyar ba zamu sake dawowa mu shiga lecture ba. Gidansa mai kyawun gaske mai dauke da dakuna uku kowanne da bandakinsa. Falo babba, kicin cike da abinci kala-kala ga kuku mai dafawa ya jera a dining area. Ko'ina a gidan sai sanyin A.C, wannan gidan daya ne daga gidajen Micheal da babansa ya mutu ya bar masa ne, ga tulin dukiya. Sai yace mu zauna a gidan kawai ba sai mun koma zaman hostel ba, shi kuma zai tafi sauran gidajensa daman ba'anan ya fiya zama ba, ya ce mu zauna mu kadai kowacce da dakinta. Ina son gidan amma nayi tunani naga ba yadda za'ayi haka ta yuwu domin hostel Mahaifina ya kaini. Na ce musu ni tafiya zanyi bazan zauna ba. Harriet ta dinga mun masifa wai danme zance bazan zauna ba, bayan mu kadai ne a gidan ba iskanci za muyi ba, ga direba zai dinga kaimu lectures. Ni dai nayi shiru ina tsoron masifar Harriet amma ba dan raina ya so ba. A hankali su Harriet suka je suka kwaso mana akwatinan kayanmu daga makaranta kowacce tasa a dakinta. Sai mun shirya tsaf da litattafanmu zamu je lecture direba yazo ya daukemu sai inga anyi ZARANDA HOTEL. Sai in tambaya "A'a ba makaranta zamu je bane? Sai suce wai Micheal zasu gani a dakinsa na hotel yanzu zamu fito mu tafi. In zauna a mota ina ta jiransu su shiga ciki su dade sai ni sai direba a zaune a mota ina tsaki ina duban agogo. Can sai inga Micheal ko wasu abokansa su Debid, Solomon, Gibreal, Emeka da sauransu su zo suyi ta rokona wai in shigo ya zan zauna a mota, ga rana inzo mu shiga. Su dameni dole sai sun takura mun na shiga. A dakin hotel din nan ake zama ana hira ana ta ciye-ciye. Abin yana ba ni mamaki yadda na ga kawayena Harriet da Janet sun saki jiki ko fargaba ba sa yi, sun saba da mazan nan har tafawa suke yi, suna cin abinci tare suna kwantowa akan cinyarsu. Ashe daman ni suke yi wa dabara, samarinsu ne tun sanda suka fara zuwa. Ni dai ina makale da littattafaina na takure a lungu idan raina yayi dubu ya baci. Duk wanda ya matso kusa dani a cikin mazan sai inyi zumbur in mike ina shirin buda kofa in arce, sai Micheal ya yiwa abokansa tsawa ya ce, su kyale ni. Kome a ka kawo gabana na ci ko nasha sai in ki ci ko sha, suka yi ta roko na in ki. Idan suka gama ciny-ciye da shaye-shaye har da giya sai su ce za su shiga dakin disco su yi rawa inzo mu je, in ki zuwa. Micheal ya miko min jarida wai in kwanta in yi ta karantawa kafin su dawo, su fice su bar ni. Na fashe da kuka mai tsanani, na yi tunani bari kawai in tashi in fita in hau acaba, in yi tafiyata makaranta, sai in ji ashe sun datse ni ta baya, na dawo na zauna na sharbi kukana. Sai da yamma likis sannan direaba ya mayar damu gidan da muke. Ina shiga na hau hada kayana zan tafiyata makaranta su Janet suka hanani tun suna rokona da lallashi har ta kai ta kawo sun fadamun baro-baro ba zan je ba ni in je inyi karatu, idan na koma Jalingo in yada su a gari in ce ba karatu suke ba iskanci suke. Suka karanto min manufarsu shine in kwantar da hankali muci kudi kawai ba wahalar karatu. Idan muka sami kudin sai mu biya lecturers dinmu su ba mu marks. Akwai yarinta a tattare da ni ga rashin sani don a lokacin shekarata goma sha biyar kacal duk sun girmeni. Sai na yarda na saki jikina a gidan mukayi ta cin dadi. Kuku ya dafa mana abinci kala-kala. Micheal ya zo ya daukemu ya yawata gari damu, super markets kala-kala kowacce ta dauki abin da ranta ke so na ci ko kayan tsukewa jeans, t-shirt, takalma da dai sauransu. Amma ko alama ban taba ganin wani daga cikin samarin nan ya neme ni da iskanci ba za su zo gidan mu zauna a falo mu yi ta hira. Dama ni ba na binsu Zarandah Hotel. Idan zasu je club su yi rawa. Su yi su yi da ni sai na ki, in shige dakina in kulle, ina kallon films. Su Harriet da Janet dai suna zuwa, kuma ko alama ba sa nuna min suna iskanci da mazan nan. Na san dai suna fita su dade su kai har sha biyun dare. Kwanci tashi first semester ya kare *yan makaranta suka yi jarabawarsu suka gama mu kuma muna can muna hutawa. Micheal ya bamu mota da direba ya kaimu garinmu Jalingo. Sai dai kawai Mamana da Babana suka dawo daga wajen aiki suka tarar da ni a gida na dawo. Sun sha mamakin ganin yadda na yi kiba, na yi fari da kyau sosai. Abin da Babana ya fara cemini da ya dube ni sai ya ce min, Mamana kina karatun nan kuwa? Na yi murmushi na ce "Daddy ina yi. Mummy ta sake kallona ta ce "Ina sakamakon jarabawar? Nan fa na ji gabana ya fadi na zazzaro ido sai Daddy ya ce "Ai ba yanzu ba sai sun yi second semester exam za a kafe musu result. Na yi ajiyar zuciya don dadi, don ni ban san ma haka akeyi ba. Hutunmu yana da tsawo don haka muna zama da Hamma Huzaifa sosai mu yi ta hira. Shi kuma a lokacin ya gama karatunsa na degree har yayi bautar kasa, don haka kullum yana gida ba inda yake zuwa. Saboda ni ya sayo wasu kujerun roba ya ajiye a bayan gidansu karkashin wata katuwar bishiyar mangoro, anan muke zama muyi ta hira. Kallo daya Huzaifa yayi min yaga na canja sai ya shiga jero min wasu tambayoyi masu wuyar amsawa ya ce da ni "Amma makarantar nan ta karbeki pretty. Nayi murmushi na ce "Meka gani? Ya ce "Kamar ba karatu kike je ba hutu kika je yi. "Nayi murmushi kawai, sai ya shiga baromin tambayoyi akan course din da nake karanta, nayi sauri na canja salon hirar. Ya sake dawowa da hirar karatu, yace in je in dauko masa litattafaina zai ga abunda ake koya mana. Nanma na amsa masa da "To sai gobe zan dauko maka. Hankalina ya tashi ainun na shiga fargaba. Abun mamaki Iyayena basu sani a gaba ba sun bincikeni haka sai Huzaifa saboda haka naga gara na rike shi mai sona ne na kuma nuna masa sha'awata ta Musulunta. Allah cikin ikonSa a cikin hutun ne na karbi kalmar Shahada, Hamma Huzaifa ya Musuluntar dani a boye ba wanda ya sani. Iman ta sharbe hawaye mai wuyar fita. Taci gaba da cewa "Ya koyamin yadda zanyi wankan shiga Musulunci, wankan haila da janaba. Bayan na koyi duk wanna sai ya fara koyamin sallah da karatunta, bayan nayi wankan Musulunci sai na kulle kaina a daki nayi sallah. Kullum haka nake yi, amma duk ranar da Mahaifana suke gida sai naje gidan su Hamma Huzaifa in yi aboye don suma bana son kannensa su ganni balle zance ya fito aji a gidanmu. Mahaifiyarsa kawai muka sanarwa, sai ta boyeni a dakinta ta datse in shiga inyi sallah. Itama ta koya mun abubuwa da dama kuma tayi matukar farin ciki dana Musulunta. Haka danta Huzaifa har kukan dadi ya yi. Inda gizo yake sakar kuma Mahaifiyata sai ta ce in shirya inzo muje wajen bauta inyi ta hanya-hanya har sai ranta ya baci ta zazzageni sannan in shirya in bita. Hankalinta ya kara tashi don da ta dauka na rungumi addininta ba wasa, yanzu taga na dawo da halina na da. Hamma Huzaifa yayi min wa'azi sosai ya bani tarihin Annabawa ba adadi, na karu sosai nasan abubuwa da yawa wadanda ada duk bincikena ban sansu ba. Daga karshen nasihar da yake min sai yace inji tsoron Allah. Allah Yana ganin duk abunda nake, kada inyi zina, in guji zina, kada in kusanci zina. Ko ina na shiga komai duhun daki Allah Yana kallona, sai in amsa masa da "To zan kiyaye. Hamma Huzaifa ya fito min da komai baro-baro baya kunya, baya boye mun abin addini. Idan na fara jin kunya kamar su wankan haila da janaba sai ya ce kada inji kunya ba'a kunya a wajen koyan ilimin addini. Hutu ya kare zan koma makaranta, Hamma Huzaifa ya bani carbi da littafin addu'o'i saiya dauko kudi ya bani me yawa. Da farko naki karba ganin ba aiki yake ba, shima a jikin Mahaifinsa yake samu duk da Mahaifinsa mai hali ne. Sai ya ce kada inki alhairi, Musulmi dan uwan Musulmi ne. Kyauta tana kara dankon zumunci. Ya karamun da cewa in zama mai kyauta da son mutane duk da yasan halayena ne. Yayi min nasiha da in rike sallah kada inyi wasa da ita kuma inyi akan lokacinta. Mahaifana sun hadamun duk abunda zan bukata. Zasu sa direba ya kaini nace kawayena su Harriet zasu zo su daukeni a motar gidansu kamar yadda suka shirya min suka ce in fada, amma Micheal ne ya zo ya daukemu muka tafi. Ko makaranta bamu nufa ba gidansa kawai ya ajiyemu. Kowacce ta shigar da kayanta dakinta, muka ci gaba da zamanmu cikin jin dadi. Abunda yake bani mamaki shine yadda Micheal da abokansa suke kashe mana kudi kamar ruwa. A ina suke samun wannan uwar dukiya Oho? Nafi shakuwa da Micheal fiye da sauran, saboda kyautata min din da yake yi. Idan Harriet da Janet basa nan sai yazo ya kawo min kayayyaki kala-kala da damin kudi yace kyauta ya bani. Ban san me zan saya da kudin ba ko kuma wanda zan bawa ajiya. Hankalina ya tashi ince bazan karba ba. Ya ce dole in karba, ya fita ya barni da himilin kudi. Inyi sauri in sami lungu a dakina in boye. Dan ko zan hadiyi laya idan nace ina zamana ya dauko ya bani ba zasu yarda ba, naga shima a boye yake bani karsu sani. A hankali Micheal ya fara fito min da manufarsa, ashe shi sona yake yi yamin bayani ya ce babban makasudin da yasa ya bamu gida muka zauna saboda ni ya bayar kuma duk wannan hidimar da yake mana ya ciyar damu, ya shayar damu, ya saya mana saboda tsananin son da yake min ne. Amma baya so in fadawa su Harriet abunda ke tsakaninmu. Sai kawai naji na fara jin haushinsa saboda bani da ra'ayin soyayya, ban iya ta ba kuma, ban taba yi ba, kuma bana so nayi. Amma kunya dajin nauyin Micheal bai iya cewa bana sonsa ba sai dai kawai in dinga amsa masa sama-sama. Harriet da Janet basu cika yinin gida ba yanzu, da sassafe sai in ga sun shirya mota tazo ta daukesu basa dawowa sai dare. Ni kadaice a gidan sai wasu sababbin kawayenmu Fadila, Ngozi da Elizebeth suke zuwa mu yini muna hira da ciye-ciyen kayan dadi. Suma *yan matan abokan Micheal ne. Micheal koda yaushe yana zuwa ya taya ni hira haka kuma yake ajiyemin damin kudi duk sanda yazo. Na tambayeshi wai ina su Harriet suke tafiya yanzu basa zaman gida. Idan na tambayesu sai su ce in kyalesu tunda idan sun fadamun ba zuwa zanyi ba. Micheal ya ce min ai yanzu a wani sabon Guest house dinsa suke yini ko zanje ya kaini? Na ce "Ba zani ba. Watarana ina zaune a gida ni kadai da yamma tunani nake yi yayin da kuka ya rufto min saboda kawai bana jin dadin wannan rayuwar dana tsinci kaina a ciki. Micheal ya zo ya same ni hankalinsa ya tashi ganin ina kuka yayi ta bani hakuri gashi da iya lafazi masu dadi nan danan naji damuwar ta fara gushewa a zuciyata. Ya ce zaman kadaici ne yake sani damuwa inzo ya zazzaga gari dani. Muka fita ya kaini wajen shakatawa kala-kala. Daga karshe muka shiga Zaranda Hotel. Ya ce zai dauki wata takarda a dakinsa in raka shi ciki, ganin tunda nake dashi bai taba nunamin wata alama ta iskanci ba sai na yadda muka shiga daki. Naga mutum yasa mukulli ya datse kofa. Na ce "Ya haka, ba takardar zaka dauka ba mu tafi? Sai ya hau dogon turanci wai yadda muka gaji ya kamata mu huta wajen dare sai mu koma gida. Na ce bazai yiwu ba ni tafiyata zanyi. Kamar yadda na ce Micheal saurayine son kowacce budurwa saboda dan gayu ne na karshen zamani ga uwa uba kyau fari ne dogo sosai, hanci, ido ga iya magana mai dadi. Yayi ta lallashina yana roka na wai inzo in zauna a gefen gadon muyi hira, naki zama. Har durkusawa yayi akan gwiwarsa yana hawaye yana rokata. Hankalina ya tashi na kasa gane wannan al'amari "In zauna muyi hira. Kamar yaya? Ina ganin mutuncin Micheal ga hidimar da yake yi mana musamman ni sai nazo na zauna a gefan gado na takure. Ya zo ya zauna shima a gefe guda muna kallon talabijin din dake dakin. Yana ta yimin hira tun bana amsa masa har na fara kula shi da ke hirar duniya ce kawai, yana ba ni labarin kasashe daban-daban da al'adunsu da ke ya zauna a kasashen wajen. A hankali Micheal ya matso kusa da ni, hirar kasashe ta fara komawa ta soyayya. Ya fara yabon halayena ina da hankali, ga nutsuwa ga ladabi da tausayi sai kuma ya koma yake yabon kyawuna yana suffanta ni wai irin macen da kowanne da namiji yake so na yi dan murmushi na ce masa "Na gode. Sai ya ji dadi ya sake matsowa kusa dani ya ce "Priety irinku ba su da yawa a Africa, kai a duk nahiyoyi. Na yi dariya na ce . "Kai haba ni din me? Ya ce, "Kin fi ma haka, kalli hannunki kamar na jarirai masu laushi ga kyau. Sai ya riko hannuna. Na ji wani yar a ranar namiji ya taba rike min hannu. Na janye hannuna da sauri. Ya sake rikewa ya fara marairaice mun yana rokona wai ban san yadda yake ji ba saboda so na. Na ce "To me zan yi maka? Ya yi murmushi ya gyara zama ya jawo ni jikinsa yana fadamin dadadan maganganu, na lumshe ido don maganganunsa suna sosa min zuciyata. Kalma daya ya fada ta zaburar da ni da yace in yarda ya nuna min irin kaunar da yake min, idan mun kwana tare babu wanda yasan muna nan ba wanda zai ganmu, ba wanda zai gane wani abu ya faru a tsakaninmu. Na mike tsaye zumbur na dauki jakata cimak na nufi kofar fita, na ce tafiya zan yi. Babu abin da ya fado min a raina sai kalaman Hamma Huzaifa ya ce "Kada kiyi zina ko kun rufe kun kashe fitila Allah Yana kallon ku. Ya taso ya biyo ni ya sa hannu zai rungume ni, yana min dadin baki, sai naja gefe na ce "Kar ka taba ni, bude min kofa in tafi gida. Ya zaro mukulli a aljihunsa ya ce "Kin ga mukullin ba zan ba ki ba ki balla kofar ki fita. Ya juya ya tafi kan gado ya kwanta ya boye mukullin a karkashin filo. Raina ya baci sosai nan da nan na kasa controlling kaina. Abin da da ke jikina wato matsafan nan da suke kokarin jana cikinsu suka motsa. Idona ya yi jawur, karfi ya zo min, hankalina ya gushe, tafiya nake akan yatsan kafata guda daya. Na tunkari inda yake. Ya firgita ganina a wannan hali, hannu daya nasa na fisgo shi na wugar gefe ya fadi ya buga goshi da bango goshin ya fashe. Na dauki mukullin kofar dakin na bude na fita, ni kaina sai da safe na ganni a kwance a falon gidan da muke ba zan iya cewa ga yadda na yi na zo gida ba. Su Harriet sun ga goshin Micheal a fashe sun tambaye shi bai fada musu dalili ba, amma ya fada wa abokansa wadanda tun tuni sun san irin son da yake yi mini. Su kuwa abokan suka zagaye suka gulmata wa kawayena, wai ni na fasa masa kai don ya ce yana so na. Ni ban taba sanin ashe ni yake so a rashina yake kulata. Ashe sabon gidansa yake turasu su yini don ya sami damar zuwa wajena ba tare da sun sani ba. Ina kwance a dakina daya amma sai na ji Harriet ta shigo a fusace na tashi firgigit na zauna kafin in bude baki in gaisheta na ji wani wawan mari tas a kumatuna. Na rike kuncina na yi shiru, radadi ya hanani magna, balle in tambayi dalilin marin. Sai na fuskanci dalilinta a zage-zagen da take yi. Micheal nata ne, ita yake so shi ne daman nake sadan-sadan kamar ba ruwana, ashe gulama ce son sa nake yi, ina lallabawa in je wajensa. Na yi na yi ta bari in yi mata bayani ta ki saurarona, dakyar Janet ta janye ta suka fita daga dakina. Na kwanta na rushe da kukan da na sa ni, na sake ji an banko kofar dakina da karfi, na daga kaina da sauri na duba sai naga Micheal wannan karon ransa a bace yake sosai. Na dubi goshinsa naga ansa masa plaster ashe ba karamin buguwa yayi ba goshin yayi loto tamkar dan jinjirin Jaki. Hmmm Allah Yasa mu dace, Amin Sai kuma gobe da yardar Allah. Reedwan Suraj Isma'il YARENA ADDININA ____CI GABAN LABARIN Nayi zumbur na tashi a tsorace na shige lungu ina makerketa. Cikin rawar murya cikin harshen Turanci na ce "Micheal yi hakuri bada gangan nayi maka ba, ban zata zaka ji ciwo ba. Ya daka min wata tsawa wai in rufe masa baki. Ya karaso inda nake yasa hannu ya damko gashin kaina ya fisgoni daga lungun. Na durkusa kasa na rike gashin don karya fisge. Cikin tsawa ya ce "Ina kudina, bani kudaden da nake baki. Na nuna masa inda suke da hannu. Ya sakeni, na tashi jikina yana bari naje na bude lokar da nake ajiya na dinga zaro dami-damin kudi. Harriet da Janet suka shigo sai kawai suka bude baki suna mamaki, ashe daman kudi Micheal yake cusa mun haka? Ko su da suke fita suna bariki haikan don su sami kudi basu kama kafar wannan kudin ba, gani ni da nake kunshe a gida kullum na tara wannan makudan kudi. Ya fisgo hannuna ya fegeni farfajiyar gidan. Yace kar in kara shigo masa gida in kama gabana. Harriet da Janet suka zo wajen da nake durkushe ina kuka. Saina hau rokarsu su tayani bashi hakuri idan ya koreni ba inda zanje, idan na koma gida ansan ba'a yiwa *yan makaranta hutu ba sannan makaranta ma bansan kowa ba, dakin da muka kama da nasan wasu sun shiga babu yadda zanje ince bed space dina ne. Abun kunya ne yanzu in shiga makaranta, ince nazo yin me? Ko kuma ina nasan inda *yan ajin namu suke lecture nida ko I.D card bamu dashi. Su Harriet suka yi shewa suka tafa suka fara zazzaga mun wulakanci wai ba cin amana nayi niyyar yi musu ba, ni me wayo nazo na tara kudi na barsu to ai gashi nan don haka babu ruwansu. In san nayi karma in gansu a hanya ince na sansu. Micheal daman saurayin Harriet ne nake so in kwace shi. Na fara rantsuwa na ce ban sanma saurayinta bane don ban taba ganin wani abu ya faru tsakaninsu ba. Nasan dai duk ana zama ayi hira kuma ni ba soyayya muke yi dashi ba ranar ne kawai ya nuna yana sona ban yarda ba kuma. Ban rufe baki ba naji jiff Micheal ya watsomin akwatinana kakaf waje, kayana suka zubo daga cikin akwatinan suka watse a kasa. Ya ce "Good bye pretty, I don't want to see you near my house again. Ya juya ya shige gidan. Su Harriet suka sake yin shewa suka juya suka ce "Muma kinga shigarmu babu ruwanmu da inda zaki tafi. Sun saka kafarsu daya a cikin gidan zasu shiga sai Micheal ya turosu waje ya fito ya tsare kofar shiga yasa hannu a bakin kofa ya kare. Suka dubeshi cike da mamaki "Ya haka, me yasa ya hanasu shiga gida? Sai yayi murmushi yace "Kuna nufin ku zaku ci gaba da zama anan gidan bayan na kori pretty? Suka tambaya "Bamu gane ba? Ya ce "To don ita na baku gida, ci da sha da sutura don tun farko ma ita nake so, tunda bata sona bata yarda dani ba ku ma sai kun bar gidana kamar yadda ta bari "Harrie ta fusata ta kai masa mari ya rike hannunta ya sharara mata wani sharbeben mari. Ni dai ina gefe ina linke kayana ina kuka ina kallonsu Janet ta fusata ta fara fada masa bakar magana sai ya zaro belt din jikinsa ya dinga dukan duk wanda ya samu. Da naga haka sai nima na zubar da kayana nayi ta kaina. Ya bimu da gudu muka nufi get kafin me gadi ya wangale get ni da Janet mun kama get mun dirga. Harriet ce ta kasa haura get din da yazo ya sameta ya dinga tafka mata belt din dakyar me gadi ya bude mata get Micheal ya angazota waje ta fadi kasa, muka rirriketa dukkanmu kuka muke tamkar Iyayenmu ne suka mutu. Me gadi da Micheal suka dinga jido kayan mu suna watso mana kofar gida bakin titi. Harriet tace "Micheal to albishirinka har yanzu wannan cikin daka yimin yana nan ban zubar ba don haka kasani idan ba haka ba kaji kara a kotu. Yace "Cikin banza kije kisan yadda zaki yi dashi. Kinzo kin takura min kin makalemun, bana sonki kinsa na miki ciki. To sai inga uban da zai kawo da ko *ya yace kin haifar mun saina fasa dan. Ya jawo get din gidan sa ya rufe me gadi yasa kwado ya bame. Sai gaba dayan mu muka sulale muka zauna, sai kuka muke rusawa. Na nanata a raina ciki, ciki, Harriet ciki tayi? Mun shiga uku mun lalace, cikin kuka Janet ta ce "Ku hada mana kayanmu gefe guda bari in je in nemo mana wajen zama zama ko Boy's quarter da Segun yake zama ya bamu daki daya mu zauna. Na ce "Waye Segun? Ta ce "Wani mutum ne me sayar da giya, mun saba da shi. Bashi da mata shi kadai ne kuma tsoho ne, ina masa kyautar kudi sosai idan ya kawowa su Micheal giya. Nasan Boy's quarter da yake zama don mun taba zuwa da su Micheal rannan da daddare muka taso shi ya sayar mana da giya shima a nan cikin G R A yake wajan Bauchi Club ku jirani yanzu zan dawo, na amsa mata da "To sai kin dawo. Ta tafi da sauri ni kuma na hau harhada mana kayanmu da suka watse a titi. Harriet kuwa bata iya komai ta takure a jikin get sai kuka take kamar ranta zai fita. Na gama hada kayan kenan sai ga Janet ta dawo akan achaba tace mu kwaso kayan mu tsayar da wasu achaba mu tafi ta shaida mana ta samu Mr. Segun din ya amince muzo mu zauna a daki daya, muka tare wasu achaba muka hau mu da kayan mu, muka tafi. Hankalinmu ya yi mummunan ta shi ganin wannan banbararriyar Boy's quarter. Sumintin kasa duk ya ciccire, ba finti ba filastar kirki. Muka shigar da kayan mu dakin daya ko gilashin wundo babu, wasu daga cikin silin sun ciccire. Kura da yana sun cika dakin. Da sauran kudi a jakar Janet ita ta biya *yan acaba suka tafi. Sai muka fara tunanin yadda zamu fara gyaran dakin, Mr. Segun ya zo ya tsaya a bakin kofar dakin ya fara zano mana dokokin da dole mubi idan muna so muci gaba da zama a gidansa. Ba kawo maza, ba kazanta, kada muyi masa sata, kuma ba ruwa a fanfo mu zamu dinga dibo masa. Muka amsa masa da mun yarda zamu kiyaye. Muka roke shi aron tsintsiya ma yace bazai bayar ba muje mu siya ya kara da cewa na manta ban fada muku ba babu aro a tsakanin ku da ni komai ku nemi naku. Ya dauki kayan giyar sa ya tafi talla bayan ya kulle dakin sa da kicin. Nan dai muka tambayi wajan da ake saida tsintsiya muka siyo muka hau shara da cire yana da goge-gogen kura, wundunan dakin dai a wangame suke ba gilas muka dinga tsinto guntun katakwaye da langa-langa muna karewa mukayi labule da zannuwan mu san nan muka shiga tunanin akan me zamu dinga kwana. Ko waccan su ta zazzage dan kudin da yake jakarta ashe ba masu yawa bane, sun baro masu yawan a dakunan su a gidan Micheal wannan kuwa kwalelen su. Ba yadda za ayi su shiga wannan gida su dauko kudin su, sun sha takaicin kudadan su domin suna da yawa tun farkon zuwan su suke tara kudin nan wanda suke samowa a harkar barikin su. Domin sun yarda da wannan kalmar ta ayiwa maza wayo a karbi kudi, in sun fita daga daki a sata haka zakaji suna fada a hirarsu. Janet ta dube ni ta ce ke baki da ko sisi ma ko? Na ce "Eh. Ta ce "To badan halinki ba zamu suyo tabarma guda uku kwannen mu dai-dai. Amma cinki, shanki ke zaki nemo dan yanzu kowa yayi ta kansa. Ko sabulun wanka babu me baki ba wai kina wani kam-kam da jikinki ba, ke ba *yar iska ba mune *yan iska ko? To dole ki fito ki nemo maza ku sami kudi idan kinki yunwa ta kasheki ba ruwanmu. Na fashe da kuka na ce "Yanzu ina zan fita in sami mazan da zasu bani kudi? Janet ta harareni ta ce "Kullum da daddare dole mu fita mu tsaya a titina wato Good evining ko muje hotels mu sami me daukarmu mu kwana dasu su biyamu. Amma fa duk inda kika san zaki hadu da Micheal ki gudu bashi da hankali har bindiga gare shi, zai iya harbe ki. Nayi ajiyar zuciya nace "Yaushe za'ayi hutu ne mu tafi gidajenmu mu huta? Su duka suka harareni suka ce "Au ke yanzu gida zaki koma, kicewa iyayenki me idan suka ce ki kawo result? Na rushe da kuka nace "Ba cewa kuka yi ba zamu sami kudi mu bawa Malamai su bamu marks ba? Janet ta mike tana tsaki ta ce "Ke ta boko ma kike. Wanne lecture ne zai karbi kudinki ya baki marks? Ni kinga tafiyata acahaba zan hau inje kasuwa wunti in suyo mana tabarmi, tukunya da plates na cin abinci. Ta fice ta barmu. Na dora hannu aka ina rusa kuka ina fadin yaya zanyi? Me zan fadawa iyayena? Harriet wacce kamar duk ta fimu damuwa ta rasa yadda zata sa rayuwarta, cikin dake jikinta shi ya dameta gashi yayi girma da akwai hatsari cire shi. Ita daman ta barshine don Micheal ya aureta, wato ai dai sun haihu tare ba yadda zaiyi saiya aureta taci kudi tana daga kwance. Yanzu ga irin wulakancin daya yi mata. Ta dafa kafadata itama kukan take tace "Pretty, yi hakuri duk wannan tunanin result bazai gagara ba idan da kudi, ki yarda mu fita mu nemo maza masu kudi zasu bamu kudin da zamu biya lectures su bamu marks. Idan baki yarda mun fita mun nemo ba ko kudin motar Jalingo babu mai bamu. Na dakata da kukan na dubeta na ce "Kema a haka da cikin zaki je wajen wani? Ta sunkuyar da kai kasa sai ta rushe da kuka. Tace "Pretty yaya zanyi? Wa zai bani idan na zauna? Muka rungume juna muna ta kukan dana sani. Washe gari da daddare suka shirya suka sani na shirya muka tsuke da dan karamin siket din jeans da *yar riga ba dankwali da takalmi me tsini sai jaka kowacce ta rataya, muka fita. Janet ta ce da masu achaba su kaimu Hotel. Nayi mamakin yadda aka yi suka san in da zamu sami *yan iskan maza suma himili guda manyan masu kudi. Suna ganinmu suka yo kanmu kowannensu yana cewa ni yake so daga karshe dai wani mutum ne ya daukeni, bana jin dai Musulmi ne kuma a kalla ya bawa shekaru hamsin baya. Suma kawayena duk suka sami nasu costomers dakunan da muka shiga dukka ukun ajere suke. Su Janet sun fahimci a tsorace nake ko hannuna ya rike sai in fisge kafin mu shiga dakin Janet ta kirani gefe ta zazzageni tace saura kuma idan na shiga in ki yarda dashi, dole in saki jiki in faranta masa. Kafin ayi wani abu in tabbata ya bani kudina nasa a jaka. Na amsa mata jikina yana karkarwa sannan na dawo wajensa itama ta koma wajen nata kowacce da nata, mu ka shiga dakuna. Ya mayar da kofa ya datse sai gumi ya keto min na hau karkarwa. Ya zauna akan gado ya jawo hannuna na zauna a kusa dashi kamar ace kule ince cas in zura da gudu dan tsoro. Ya dubeni yayi murmushi ya ce "Wai ke wannan ya haka, ko dai sabon shiga ce? Ya miko hannu zai tabani nayi zumbur na mike tsaye na goce. Ya sake kallona cike da mamaki ya ce "Lafiya kike guduna, to nawa zan biya kwana daya? Nayi shiru can na ce dubu biyu. A ganina na ballo wasu makudan kudi masu yawa. Ya kwashe da dariya harda buga kafa. Ya ce "Haba baby ai kinfi dubu biyu ko kallon fuskarki da nayi ai na biyaki dubu biyu balle mu kwana tare, na kara miki zan baki dubu goma. Na zazzare ido don mamaki na fada a bayyane na ce "Dubu goma? Yasa hannu cikin wata *yar jakar hannunsa wato (brief case) ya zaro bandir din Naira dubu goma ya mikomin, na karbi kudin nan ina jujjuyawa don mamaki, murna ta kamani. Na ce a raina "Na sami kudin da zanje in biya Malamina su bani sakamakon Jarabawata sannan inyi kudin mota in koma gida. Nasa kudin a jakata. Ya jawo hannuna nazo na zauna a kusa dashi. Yasa hannu zai shafa wuyana sai naji maganar Hamma Huzaifa a karkashin zuciyata. "Kada kiyi zina, kiji tsoron Allah duk inda kike ko ina kika shiga kika buya Allah na ganinki. Saina zabura na mike tsaye na ce "Malam yi hakuri bude mun kofa tafiya zanyi bazan iya ba. Na bude jakata na dauko masa kudinsa na ajiye masa a gefensa. Ya bude baki yana kallona. Yace "Me yasa? Na ce "Kawai bazan iya ba, ina tsoron Ubangijina bazan iya zina ba. Ya kyalkyale da dariya ya ce "Ko ki karbi kudina ko karki karba babu yadda za'ayi in yadda ki subuce min gara ki tsaya in miki a hankali kafin inyi miki da karfi. Na rataya jakata na nufi kofar fita, daman da mukullin a jikin kofar zan murda in bude, sai naji cimak an daukeni ta baya sai naji ni a tsakiyar gado yana shirin ya afkamin. Naji raina ya fara tafasa don tsananin bacin rai, nan da nan na rasa hayyacina, muyagun dake jikina suka tashi. Na lalubo wata katuwar kwalbar lemo dake ajiye a gefen gadon na rotsa masa akai. Ko sakon daya ba'a kara ba jini yayi masa hijabi a fuska. Ya rike kai sai ihu yake zanbadawa. Na yar da jakata da takalmi na bude kofa zan fita da gudu naci karo da jama'ar da suka jiyo ihunsa suka rugo suga meke faruwa. Caraf suka damkeni. Suna lekawa cikin dakin suka ganshi cikin jini. Suna kokarin yimin duka abinka da ba yin kaina ba naji na fara zubar da kartai a kasa suka sakeni ba shiri na arce waje na fita daga hotel din da gudu. Harriet ma da nata saurayin dai-dai lokacin ya gaggalla mata mari ya kwace kudinsa ya tunkudota waje daga daki saboda ya tarad da ita da rusheshen ciki, itama ta lallabo ta fito waje. Janet itama dakyar tasha da nata yaga abunda nayi saiya korota ba tare daya bata ko kobo ba, da dabara da haure-haure ta fito daga hotel din ance sai an daketa tunda tare muke. A gida muka hadu wannan na shigowa sai kaga waccen itama ta shigo a guje a galabaice. Ranar naga tashin hankali a wajen kawayena zagi da dungure kai nasha, wai duk ni nake jawo musu masifa. Har wayau basu daddara ba washegari suka sani dole na shirya muka fita amma muka canja hotel. Aka sake kwatawa duk yawan kudin da zasu bani bana iya yarda inyi zina domin tsoron Allah ya shigeni tun ina karama, Hamma Huzaifa ya cusa mun haka a raina. Allahu akbar Allah Yayi masa albarka ya sami ladana ta wannan bangaran. Ga tsananin bukatar kudi ina yi amma tsoron Allah ya hanani in aikata sabon Allah in sami kudi. Su kuma mazan idan naki yarda da su sai su kasa hakura dani su yi kokarin zasu yimin ta karfi daga nan san hankalina ya gushe raina ya baci in fita hayyacina in farfasa musu kai. Don barnar da nake musu ta yau tafi ta jiya, ta gata tafi ta citta kullum mune a guje an biyomu na fasawa maza kai, laifina yana shafar kawayena. Da kansu suka hanani binsu suka sha zagina suka ce sai in zauna a gida na dinga dafa musu abinci tunda haka nake so. Tafi nono fari daman haka nafi so. Haka na kasance duk sanda zasu tafi su bani kudin cefane su zano mun abubuwan da suke so in suyo in dafa musu. Jikina yana rawa nake karbar kudin cefanen in hau achaba inje kasuwar Wunti ko Mudalawan da ke nan Bauchi in sissiyo in dawo. Da murhu da itace in dafa musu abinci idan da daddare suka fita to da sassafe nake dafa musu abinci kafin su karaso, idan kuma fitar yamma suka yi kafin dare na kare musu girkin dare. Duk da ba sabawa nayi da aiki ba, girkin ma ban iyaba balle hura wuta haka nake daddagulawa ina yi ina rugawa da gudu wani gida dake kusa damu ina tambayar matar gidan yadda zanyi kafin in kare girkin duk nayi wujiga-wujiga na fita hayyacina. Hawaye, majina, gumi, bakintukunya a rigata kaca-kaca. Amma duk da wahalar nan basa godewa, Janet ma saita yi fada da zage-zage kafin ta fara cin abincin. Ni dai hakuri nake basu don kar suyi fushi suce sun daina bani kudin cefane nima in fita in nemo. Wata rana da yamma ina ta riki-riki da itace da tukunya sun hadani da babban aiki wai tuwan shinkafa miyar taushe suke so. Ina gudun bacin ransu sai ban fada musu cewar ban iya ba fargaba ta isheni bansan yadda zan hada miyar taushe ba, ga dai kayan taushe reras na cefano. Na dora ruwan zafi ya tafasa na wanke shinkafar tuwo na zuba tana ta dahuwa. Daya daga cikin kawayenmu da muka saba a sanadiyar abokan Micheal wato Fadila dadiron Gibrel ce abokin Micheal a gidan Gibriel din take din-din-din ya tsare mata ci da sha da sutura. Ya saka mata takun-kumin fita wajen wasu mazan. Amma abunka da ba maganar Allah ba, zama ne na sabon Allah tana satar jiki ta fita ta hole da wasu mazan idan yayi tafiya. Ran da aka sami akasi ya dawo bai isketa a gida ba to fa ranar saiya fasa mata wani wajen ajikinta don duka. "Excuse. Sallamar arna tayi min. Na daga ido na dubi me shigowa duk da boy's quater a wangale take babu zaure ba tsakar gida don ba'a zagaye da katanga ba ko zana a fili muke wangal sai dakuna biyu a jejjere da dan karamin bandaki a tsurkukin kicin. A filin bakin kofar dakin nake girki. Ina zaune akan wani katan bulo na saka rigar aiki iya gwiwa. Hayaki ya cika mun ido sai hawaye nake shar-shar. Na tashi da sauri na rungume Fadila don munyi wata guda bamu hadu ba tun muna gidan Micheal. Wa'iyazu billah,,,, Allah dan girman Ka da tsarkin Mulkin Ka, Ka tsaremu daga rayuwar bariki. Allah Ka da Ka sanyamu a jerin ta6a66u duniya da lahira. Uhmm gaskiya ni bana son Iman din ma,,,, cikin biyu za'ai daya ko Naja'at ko kuma Zubaida ehe...... @watsapp__ 08097365237 YARENA, ADDININA..... CIGABAN LABARIN Na tsashi da murna na rungume Fadila don munyi wata hudu bamu hadu ba tun muna gidan Micheal. Amma tunda muka dawo nan bata zoba. Sai a ranar tazo shima da tambaya ta samu gidan. Nadauko mata tabarmar kwanciyata daga daki nazo na shimfida mata a gefe yadda hayaki bazai dameta ba nace ta zauna. Amma fadila ta kasa zama, tayi tsaye kawai tana kalle-kalle gidan da muke zaune. Ta dubi ko ina harda daga labulen kofar dakin da mukayi da zani ta leka dakin sai girgiza kai take ta juyo tadubeni cike da tausayi tace "cafdijam pretty haka kuka zama? Yanzu kune acikin gidan nan haka harsu janet da harriet agidan suke zaune haka?' Na sun kuyar dakaina kasa na kasa bata amsa. Taje tazauna a tabarmar dana shimfida mata nan ma kafinta zauna saida ta karkade tana wani yatsuna kamar wacce zata zauna akan kashi. Kirjinta da kunnuwanta da yatsun hannunta da hannuwanta da kafarta tsadaddu. Kanta babu dankwali anyi gyaran gashi a saloon anyi karin gashi har baya an zubo dashi, sai kamshi da kyallin mai. Nace "Gabrel yana sakar maki kudi fadila.' Nafada mata haka yayinda nake dubanta ina murmushi. Nanfa tahau feleke tana wata kwalmada tana iyayi daman gwanace awajen feleke. ita ta koyamun hausa na iya magana da hausa sosai domin ita bahaushiya ce gaba da baya kuma musulma bakatsiniya. Tace "wai dan kinga nasa gold aiba komai kika ganiba pretty. Gibrel fa ya bude mun account yana zuba mun kudi sannan duk sanda yaje lagos zai suyo mun kayan tsukewa da leshina. Idan yayi tafiya infita inje wajen wasu mazan duk haka muke dani da kawayena su Ngozi. Wallahi pretty bakida wayo bakima san abunda kikeyiba. Koda yake yarinta na damunki gaki kuma 'yar fari. Micheal fayafi su Gibrel kudi da kika kwantar da hankalinki da kinji dadin rayuwarki. Naji labarin abunda ya faru kinban kunya ko tsoron harriet kike? Danshi fa ba sonta yake ba ita take sonsa shike yake SO duk mun san abunda yake faruwa. jiya ma har karfe dayan dare yakai a gidan da nake yana baiyana mun har yanzu yana sonki ki yarda dashi, zai canza miki rayuwarki. Harriet din banza inhar kin yadda zai kaiki gidan dako get din gidan su harriet baza su iya tabawa ba balle su shiga suyi miki wani abu. Yace ashiye yake ya kashe miki duk abunda ya mallaka don shi arayuwarsa bai taba jin yarinya da yaji yana kauna ba kamarki." ta dafa kafadata tace "haba kawata dubeki yadda kika zama duk kinyi duhu. Wannan gashi naki har baya kamar na turawa duk ya cukurkude kodan mai bakya shafawa. Da yar gayu dake, kala ce sai an wanke hannu kafin a tabaki yanzu kin zama kamar bola. Wai girki da murhun itace haba pretty kinci baya. Garaki shigo bariki kiji dadin rayuwa hajiyata. "NA fisge kafadata natashi daga kusa da ita ina girgiza kai, kallo daya tayi min tasan ta bani haushi, raina ya baci sosai. Najuya na dubeta nace" fadila ki kularmin da abincin nan zanje cikin ginin can yanzu zan dawo.' Na nuna mata wani tsohon ginin benen da ba'a kareshi ba, babu kowa a cikin. Ta harareni tace 'me zakiyi aciki? To gaskiya kiyi sauri idan baki dawo da wuriba zaki tarar bana nan, donni ban saba girki a gas cooker bama balle murhu kece dai wahalalliya.' Nayi murmushi nace "yanzu zan dawo bazan dadeba." nadauki buta natafi kamar tafiyata da minti goma nadawo. Fadila takalleni awalakance tace 'oh kashima bakuda wajenyi sai kun shiga kwango? Gaskiya pretty kin shiga uku. To in fada miki gaskiya kece abar tausayi don jannet har yanzu tana tareda solomon abokin micheal kudi sosai take samu shiyasa bata cika kwana anan gidan ba kawai tana ciyar dake don ki kulada kawarta harriet wacce tadauko ciki ba zata iya fantamawa ba. Amma da harriet garau take bazasu yarda su zauna dake a gidan nan ba. Ke kuma wawuya kin tauye rayuwarki kin kunshe anan ki taho kawai ki biyoni. Nida nice da kyau irin naki daba saina buga tsiya agarin nanba.." Nakoma kan bulon dana zamar dashi kujera na zauna na bude tukunyar girkina naga har yanzu ruwan shinkafar bata tsotseba na rufe na gyara itace. Najuyo na kalli fadila wacce ta zuba min ido tana sauraron amsar da zan bata. Nayi ajiyar zuciya nace "fadila hankalina yana tashi jikina yana sanyi duk lokacin da muka hadu. Zaki ga kome janet,Harriet dasu Ngozi kawayenki zasuyi na bariki da tabewa da maza bana ko daga ido in dubesu saboda nasan ba musulmai bane." fadila ta zazzaro ido tana kallona cike da mamaki tace 'pretty nadauka duk addininku daya dasu, nikadaice musulma acikin ku? Meyasa jikinki yake sanyi idan kika ganni? Nasake zubo da hawaye daga idanuwana. Nasa gefen rigata na sharce. Nace fadila a matsayinki na musulma gaba da baya musulmar ma bahaushiya, bahaushiyar ma bakatsiniya hausawan asali masu al'adu irin ta larabawa. Nayi mamaki da rayuwarki ta zama haka fadila na zauna da masu irin addiniki kala- kala na tantance addininku addinin musulunci addini ne me tsafta. Har mamaki nake idan naga musulmi yana bin arna yana bata. Domin dani na samu Allah yayini a musulma hausa fulani tsantsan na sami tarbiyyar musulunci tun ina yarinya banga dalilin dazaisa na sabawa ubangijina ba.... YARENA ADDININA....CIGABAN LABARIN..., Jikin fadila ya fara sanyi ta dubeni cike da nadama tace 'pretty ban fahimcekiba. "na nisa nace ina mamakin yadda yar musulma zata iya buda jikinta tayi zina nasan ko batada ilimin QUR'ANI sosai duk inda take duk abunda take tasan Allah yana kallonta. Ina sha'awar musulmai domin sun san darajar mata sai dai mace ta wulakanta kanta domin addini yazo musu da cewar mace ta killace kanta a gidan mijinta. Idan ya kama zata fita unguwa ta suturce jikinta, hijab har kasa mace musulma bata tsayawa da maza atiti kotaje gidan wani suyi shakiyanci kota yarda wani da namiji ya taba jikinta ko su tafa hannu. Duk inda zata shiga ita kadai ta saka tsoron Allah a zuciyarta Allah na ganinta don Haka mijinta baya fargaba hartaje inda zataje tadawo shiyasa nake sha'awar addininku fadila. Amma ke kin zubar da duk wannan gatan, don duk wanda Allah yayishi musulmi dan musulmai ba karamar kyauta Allah yayi masa ba kuma Allah yaso shi da rahamarsa. Bai kamata ki zubar da wannan baiwar ba fadila." sainaga idonta ya cicciko da hawaye, ta zauna tayi shiru tana tunani. Naci gaba da cewa "kina musulma fadila ban taba ganinki kintashi kinyi sallah ba saboda karki batawa wani arne rai Gibrel da kawayenki su Ngozi kin shiga cikin arna gaba da baya kin bar addininki. Ga sabon Allah da kike ciki tsantsa. Cinki da shanki da suturarki duk haramun ne. Ga uwa-uba hakkin iyayenki, kin fadamun aure za'ayi miki kikace bakya son mijin kika kai musun Gibrel suka ce czaki aureshi ba kika hado kayanki kika biyo shi ku kazo kuke holewarku? Iyayenki duk inda suke suna chan suna tunaninki, kin dauki alhakinsu kin rusa duk tarbiyar dasuka yimiki fadila. Kece mutum ta uku da zan fada mata wani boyayyan sirri; daga hamma huzaifa sai mamarsa saikuma keda zan fada miki yanzu. Fadila ni musulma ce, kuma nakarbi musulunci a boye duk ranar da mahaifiyata taji ina sallah zata yankani ne kawai." fadila ta zazzaro ido tana mamaki. Naci gaba dayi mata bayani, nace "butar nan da nake dauka in shiga ginin chan salla nake shiga in buya inyi. Hijabina da abun sallata da carbina duk suna ciki aboye banaso kowa yasan ni musulma ce shiyasa nake mamakinki, karfi da yaji kinbar addininki addinin tsafta da gaskiya. Kiji tsoron Allah fadila, ki saka aranki duk inda kike Allah yana ganinki, akwai mutuwa, akwai hisabi, akwai wuta da aljanna. Kafin in rufe bakina fadila ta rushe da kuka ta rungemeni tsam-tsam, nima kukan nakeyi. Cikin kuka fadila tace mun "ban taba tunanin akwai wa'azin da zaisa inyi nadama ba, inji na tsani abunda nake sai yau. Pretty kin fimu wayo ashe, nake miki kallon wawuya?" dakyar na lallashi fadila na mayar da ita wajen zamanta tazauna. Nadauko muciya nafara tuka tuwona. Tambayoyi fadila take mun wai yanzu yaya nake gani? Inbata shawarar yadda zata canja rayuwarta. Shawarar dana bata nace ta tuba ga Allah shita sabawa kuma Allah mai rahama ne, mai jinkai zai karbi tuban wanda ya tuba. Sannan tabar zinar da take, ta hada kayanta ta koma gidansu ta nemi gafarar iyayenta, ta rike salla ta shiga islamiya tanemi ilimin QUR'ANI da hadisi tayi addu'a Allah yafito mata da miji nagari musulmi tayi aure ta hayayyafa ta bawa ya'yanta tarbiyar addinin musulunci. Ta tambayeni toni kuma akan kaina yazanyi da rayuwata tunda na fada mata mahaifina musulmi ne amma mahaifiyata ba musulma bace. Gashina musulunta a boye,? Nayi shiru ina tunani nikaina bansan yazanyi ba. Ina fargabar komawa gida tunda karatu aka turoni banyi karatun ba, kuma yadda zanje in zauna a gidan da sabon addinina. Na faiyace fadila labarin da bata saniba na game da rayuwata, na shaida mata wani dan makwabcinmu shine ya cusawa zuciyata tsoron Allah. Shine ya musuluntar dani. Abunda yafito daga bakinta shine ki auri hamma huzaifa mana shine mai sonki zai kula dake ya kuma kara koya miki addimin." najuyo da sauri na dubeta can na tambayeta. "tayaya zan aureshi? Kuma yaya akayi tasan inason huzaifa." tayi murmushi tace ai karshen so yana miki kema kuma haka daman ginshinkin so shakuwa kin shaku da huzaifa fiye da iyayenki. Huzaifa yana burgeki saboda addininsa da halayensa shi yaja ra'ayinki zuwa musulunci kawai ya daukeki kuyi tafiyaku wani garin kuyi aurenku tunda mahaifiyarki ba zata yarda ba." zance fadila haka yake babu namijin da naji ina so nake sha'awarsa a matsayin mijina irin hamma huzaifa amma nasawa raina bazai yuwu ba. Nayiwa fadila bayani hamma huzaifa yanada tarbiya yana yiwa iyayensa biyayya bazai yarda ya daukeni mu gudu wani gari muyi aureba. Na dai cewa fadila ta tayani da addu'a amma rayuwata tana cikin wani hali don haka nema nake sha'warta domin uwarta da ubanta dukka musulmai ne kuma musulmi zasu aura mata, bahaushe YARENSU DA ADDINNISU daya. fadila ta tausayamin sosai kuka nake tamkar idona zai fita naji na tsani rayuwata, naji haushin mahaifina daya auro mahaifiyata wacce addinin suba daya ba suka sakani a cikin rudani. Fadila tayi nadama ta gamsu da shawarwarina ta shaida min in Allah yaso ko.. Surayya Abubakar Surayya Abubakar ________________ YARENA ADDININA. ___CI GABAN LABARI part 2 Nan da nan na nemi yawun bakina da makogarona na rasa sun bushe kamas don tashin hankali, sai zuciyata ta lalubo min addu'ar da Huzaifa yake karantawa a duk lokacin da bala'i ya tunkaroshi. Naji kafata ba zata iya daukar jikina ba da dan Jaririn dake hannuna sai nima na sulale na zauna kamar yadda tashin hankalin ganina yasa Mahaifiyata ta sulale ta zauna. Karkarwa suke suna nuna Jaririn dake hannuna, nima hannuna na karkarwa idanuna na zuba tamkar ruwa a famfo ina nuna gagarumin tashin hankali da nake hange a tare dasu. Mahaifina yayi karfin hali yasa hannu ya tashi Mahaifiyata tsaye yana goge mata hawayen daya wanke mata fuska. Ya ja hannunta da kyar suke jefa kafafuwansu suka shiga gida suka barni a nan zaune cikin kasa turmus. Na kalli gabas na juya yamma, na kalli kudu na juya arewa, na kalli sama, na kalli kasa gaba daya duniyar tayi min zafi ji nake kamar ba a duniyar nake ba, dama a dau raina. Hankalina ya gushe, kaina ya dau zafi gumi ya keto min hade da hawaye mai radadi na rasa inda zan nufa inji sanyi a raina. Babu mai lallashina, babu wanda zanwa bayani ya gane halin da nake ciki bani da sauran gata sai Allah. Shi kadai nake ambato, kowa ya watse ya barni. Na kurawa Jaririn da ke hannuna ido ina kallonsa, sai tsala kuka yake har da hawaye kamar yadda nake hawaye, na fashe da kuka na rungumeshi tsam ina tausayin kaina amma na fi tausayin Jaririn, shi da baisan komai ba na rayuwa. Tabita naji ta tabani na dago da sauri na kalleta itama hawaye take, ta rungumeni da dan Jaririn dake hannuna mu duka ukun kuka muke. Ta mika hannu ta karbeshi tasa hannu ta tasheni tsaye tana karkademin jikina, tace inzo mu shiga gida. Na girgiza kai, na sharbe hawaye nace "Mama Tabita ba zan iya shiga gidan nan ba da sunan in ci gaba da rayuwa. Tabita ta ce "Rufkatu me kike nufi da baza ki shiga gidanku kici gaba da rayuwa ciki ba? Ga Mahaifiyarki ga Mahaifinki su basu koreki ba, ke zaki kori kanki. Ina zakije ki zauna wanda yafi nan gidanku ga ki da dan Jariri. Na sake rushewa da kuka na ce "Ni ba zancan dan Jariri bane ya daga min hankali. Mama Tabita bakya ganin yadda Mahaifina ya zama? Tabita ta bude baki tana mamakina can tace "Na dauka babban farin cikinki ne yanzu hankalinki zai kwanta binciken da kika dade kina yi akan addinai kala-kala, me yasa kowa da abinda yake bautawa ba'a bautawa abu daya Mahaifanki suna bin addinai daban-dabam, yanzu Mahaifiyarki da Mahaifinki da ke da kannanki kun zama abu daya kuke bautawa. Allah Yasa Baban wannan yaron shima ya zama yana bautawa abun da kuke bautawa. Tasa hannu ta dafa kafadata ta ce "Zo mu shiga gida in kintsaki ke da danki daga ganinku kunsha wuya. Na fisge kafadata naki tafiya na tsaya cak na rasa abun yi, jin zuciyata nake tamkar ana kwankwatsamin don takaici, wani jiri ne yake daukata yake shirin ya yar dani kasa. Tabita na lallashina bana fahimtar abunda take fada. Ukuba tayi ukuba, tashin hankali yayi tashin hankali na zura da gudu gidan su Hamma Huzaifa inje in tambaye shi, ya akayi yana raye ya bari haka ta faru da Mahaifina. Sai Mahaifiyarsa ta ce min ai a lokacin dana ganshi dinann a bakin mota kayansa ake zubawa a mota tafiya zaiyi Saudia. Jami'ar koyan addinin Musulunci ta Madina ya tafi karo ilimim addinin na tsawan shekaru hudu. Ta dauko min wasikar daya bari a bani. Na bude na karanta, ashe Hamma Huzaifa yana tsananin sona bai fadamin ba sai a wasika. Na sulale na zauna a tsakiyar dakin su Maman Huzaifa ina ta sharbar kuka. Maman Huzaifa tayi ta bani baki ta ce "In kwantar da hankalina in daina kuka duk abun daya samu bawa jarrabawa ce daga Allah. Na ji dan sanyi a raina dana samu mai lallashina mai nuna min akwai Allah. Na share hawayena da gefen mayafina nayi ajiyar zuciya. Mama ta matso kusa dani ta ce "Fatima, Huzaifa ya shigo dazu yana hawaye ya shaida mun dalilin hawayensa ke ya gani da dan Jariri kin haihu. Yayi tsananin bakin ciki da bacin rai da kika watsar da duk abubuwan da ya koya miki tun kina yarinya, yace mun tunda yake bai taba ganin yarinyar da take da matukar hankali da tunani da sanin ya kamata kamarki ba, ya shaku dake yana kuma godewa Allah da Allah Yasa kika Musulunta ta sanadiyyar sa, yasan kuma ba karamin riko zaki yiwa addininki ba. Amma hankalinsa yayi mummunan tashi da yaga abun da bai taba zata ba a gareki. Nasan duk inda yake yanzu yana can yana tunani da bacin rai. Da kyar na lallashe shi ya tashi ya tafi shi da direba za'a kaishi filin jirgi. Iman ta girgiza kai ta ci gaba da cewa "Sai ajiyar zuciya nake na kasa yiwa Maman Huzaifa bayani. Nayi shiru na kasa magana. Sai ni sai zuciyata da Ubangijina muka san gaskiya, babu abin da zan fada su yarda dani, tashin hankalin da nake ciki ba zai barni in iya bayani ba. Ni da Maman Huzaifa muka yi shiru muna tunani can na daure na bude baki nayi magana na ce "Mama nazo wajen Hamma Huzaifa ya aka yi ya bari haka ta faru da Mahaifina? Maman Huzaifa ta kalleni ta ce "Meya faru da Mahaifinki Fatima? Sai na rushe da kuka na ce "Mahaifina na gani sanye da kayan bauta irin na Mahaifiyata, da alama ma wani babban mukami suka bashi a wajan bautarsu. Mahaifiyata ta ja Mahaifina ya bar addinin Musulunci ya bi nata. Cikin shesshekar kuka na ci gaba da cewa "Har yanzu ni Musulma ce ban bar addinin Musulunci ba, yanzu ma nake kara zurfafa a cikinsa, nazo da niyyar in tunkari Mahaifina in shaida masa na karbi addininsa, na Musulunta kuma zan bishi koda kuwa Mahaifiyata zata yankani. A yanzu nake son tsananin taimako da shawarwari daga Hamma Huzaifa sai gashi Allah mai yadda Yaso ya dauke min Huzaifa lokacin da nake tsananin bukatar taimakonsa, wanda bana fargaba bana kokonto, da jikinsa da dukiyarsa zai taimake ni in rike addinina. Bugun kirjin da nake ina tinkaho Mahaifina Musulmi ne zan iya binsa in Musulunta, sai gashi komai ya canja min. Bani da sauran mai karfafa min gwiwa inci gaba da bin addini Musulunci sai Allah. Meya sa Babana yayi min haka? Danme ya bari suka rinjaye shi ya bar addininsa, addinin gaskiya, addini mafi tsafta mafi can-canta a bishi? Bayan tsawan shekarun da aka dauka yana rike da addininsa, yaki shiga nata yanzu kuma kwatsam ya bari ta rinjayeshi. A tunanina shine namiji ni kuma babbar *yar mu zamu hadu mu hada kai mu rinjayeta ta shigo Musulunci sai gashi shi ta rinjaye shi. Allah ne kadai gatana, shine jagorana, Shi zai tsareni Ya kareni, don bazan iya canja addinina ba saboda Mahaifina ya bar addinin, ko don Huzaifa ya bar kasar. Na sake kifa kai akan gwiwata kuka mai radadi ya ketomin. Maman Huzaifa ta matse hawayen daya cika mata ido ta dafa kaina ta ce "Fatima kinyi gaskiya kada kibar addininki komai ukuba. Dare da rana, safe da yamma Huzaifa yana tunani, gashi zai tafi wazai ci gaba da taimakonki akan addininki, yana ta sake-sake yana neman shawarata. Sai muka yanke hukunci kafin ya tafi yaje ya sami Mahaifinki a boye ya sanar da shi cewar kin Musulunta ya ci gaba da baki goyon baya ki rike addininki. Kafin Huzaifa yaje ya fada masa sai rashin lafiyar ciwan kafa ya dami Mahaifinki bayan tafiyarki makaranta. Kafar ta rure, ta kumbura ko fita baya iya yi, ganin halin da yake ciki shi ya hana Huzaifa ya je ya sanar masa na ce ya bari ya samu sauki tukunna don ya dade yana jinya. Anyi maganin asibitin, anyi na gargajiya abu ya faskara kullum kafar sake suntumewa take. Aka rasa kan ciwon musamman idan dare yayi ciwon yafi damunsa ihunsa har gidan nan. Baban Huzaifa ma yayi masa kokari, duk inda ya samu labarin mai magani zai je ya dauko shi ya kawo shima yayi bajintarsa ya tafi, ciwo dai yana nan danye sharaf. Ciwo daga Allah babu wanda yasan sanadiyyar ciwon, haka kuma babu wanda yasan maganin ciwon. Iman ta sharbe hawaye, suhaif ya sake sa hannu a aljihunsa ya dauko mata wani hankici ya mika mata, ta karba ta goge hawaye. Jama'a sai sake gyara zama suke suna jin wannan abun al'ajabi. Taci gaba da cewa "Na dakata da kukan da nake na tattara hankalina gaba daya ina sauraran Maman Huzaifa, zuciyata cike da fargaba da tsananin tausayin Mahaifina da kuma kaguwa inji karshen labarin. Me ya hada ciwon kafa da canja addini? Maman Huzaifa ta ci gaba da cewa "Kinsan tsakanin mata da miji sai Allah, ashe Mahaifiyarki koda yaushe tana lallashin Mahaifinki ya yarda ta kaishi wajen bautarta, a kwai wasu turawa da suka shigo garin nan suna yada addininsu. Allah Yana basu iko su warkar da mutum duk tsananin ciwo, amma fa da sharadi kafin su warkar da mutum. Zasu saka masa doka idan ya warke dole ya koma addininsu. Wanda bashi da rabo, hankalinsa ya gushe, ciwo ya tsananta so yake ya rabu da ciwon ya huta, sai idonsa ya rufe ya manta magani da ciwo duk yana hannun Allah, sai kaga mutum ya amsa musu da "Eh na yarda idan na warke zan koma addininku. Kuma babu mahalukin daya isa su warkar da shi ya tsere yaki shiga addininsu, kana warkewa abu na farko da za su yi maka shine su baka babban mukami a wajan bautarsu, su baka kudi masu yawa idan kana dashi ma sai su kara maka lunkin naka, su zamana koda yaushe suna tare dakai suna koya naka addininsu har sai sun tabbata addinin ya ratsaka ka manta da naka na da, kafin su daga maka kafa. To irin haka ne ya faru da Mahaifinki. Da tsananin ciwo ya dame shi ya amincewa Mahaifiyarki, wacce take member ce a cikin kungiyar, ta dauko wadannan turawa suka zo suka dinga zano masa sharuddan gaba daya ya amince. Allah Ya basu iko suka warkar da shi a cikin sati biyu kacal yayi garau, duk da ransa bai so ba dole ya dulmiya ya bar addininsa. Wato ranar da muka ji labarin haka ta faru da Mahaifinki hankalinmu ya tashi musamman Huzaifa ke yafi tausayawa, babu yadda zamu yi dukkanmu. Huzaifa ya so ya fasa tafiya Madina ya zauna saboda ya taimaka miki ki rike addininki amma babu yadda za'ayi ayi haka, tunda ya gama komai na tafiya har sun turo masa da takardar an dauke shi, suna nemansa a wannan lokacin za'a fara karatu. Mahaifinsa ya ce lallai ya zo ya tafi. Iman ta ce "Nayi kuka, nayi takaici har kamar zan zautu. Daga karshe na dangana, na yiwa Maman Huzaifa sallama ita kuma taci gaba da bani baki tana kara karfafamin gwiwa akan ko ba Huzaifa ita zata maye gurbinsa iya karfinta zata taimaka min duk abinda ya cushe min na game da addini in zo in tambayeta zata warware min. Sannan duk lokacin sallah in dinga yin wayo ina sulalo jiki ina zuwa dakinta ina yin sallah a boye a ranar da Mahaifanki suke gida. Na mata godiya na fito na nufi hanyar gidan mu. Kafin na iso gida nake jiyo kukan dan Jaririna a Boy's quater, da alama wanka Mama Tabita take yi masa. Hankalina ya tashi na nufi inda suke da sauri ina tunanin idan an gama yi masa wankan wanne kaya za'a saka masa gashi bani da kudi. Na isa inda suke kan baranda na zauna a gefe ina kallonsu sai wanke shi take da sabulu. Ta juyo ta dubeni ta ce "Ashe ko wankan haihuwa ba'ayi masa ba. Yau ki ka haife shi ne? Na sunkuyar da kai kasa na ce "Jiya da daddare aka haifeshi. Tabita ta maimaita abunda na fada, "Jiya da daddare aka haifeshi. Ban sake cewa komai ba. Ta ce in shiga dakinta cikin akwati in dauko wankakkiyar atamfarta in kawo ta lullubeshi. Na tashi na shiga dakin na dauko zanin na kawo mata ta lullebeshi. Sai tsotsar hannu yake saboda yunwa. Ta jawo dan kwandon kayan kwalliyarya ta dauko mai basilin tana shafa masa. Ta ce "Bari in gama shafa masa mai sai ki karbe shi ki bashi nono ya sha yunwa yake ji. Ko babu ruwan nonon bai fara zuba ba? Nan fa gabana ya fadi na ce "Eh bai zo ba. Cikin rawar murya na fada. Tabita ta kalleni ta ce "Pretty ki kwantar da hankalinki, ki rungumi danki, ba'a kanki aka fara ciki ba a haihu, ashayar da dan ko ruwan nono bai zo ba dole ki bashi ya dinga sha har ruwan ya zo. Nan ma gabana ya sake faduwa na ce "Mama Tabita ba sai na bashi nono ba, ina laidar da kika karba a hannuna akwai Madararsa a ciki. Tabita ta nuna min inda ta ajiye ledar. Na tashi na shiga kicin na dauko kofi da cokali na tarar da wata katuwar tukunya cike da ruwan zafi akan murhu yana ta tafasa, wai ruwan wankan jego ta dora min. Na dibi kadan a kofi na zo na zauna a kusa da ita na dama madarar na firfita ya huce sannan na mika mata, ta dinga tarfa masa yana sha har ya koshi. Bacci mai dadi ya kwashe shi, ta tambayeni ina kayan sawarsa a saka masa na ce "Bashi da kaya. Cike da mamaki ta sake tambayata "Ina Mahaifinsa? Nayi shiru can na ce "Yana Bauchi, ta ce "Baisan kin haihu bane, ko bai karbi cikin bane ya kyaleshi tsirara? Na sake yin shiru can na ce "Yasan an haifeshi mana. Tabita ta girgiza kai don tausayi ta tashi ta shiga daki da jaririn, ta kwantar dashi akan katifa ta dauko Jakarta ta fito. Ta kalleni ta ce "Bari inje kasuwa na siyo masa riga ko guda daya ce kafin muga yadda za'ayi. Na laluba cikin ledar da na zo da ita na zaro sauran kudina daya rage na bata na ce ga sauran kudina ki hada ki siyo masa. Ta karba ta zuba a jaka sai ta ce min "Ga ruwa can a murhu idan ya tafasa ki juye kiyi wanka. Ko baza ki iya juyewa ba saboda jikinki ba kwari in zauna idan ya tafasa in juye miki in miki wanka yadda zaki gasu sosai? Nayi sauri na ce "Yi tafiyarki zan iya juyewa, zanyi wankan da kaina. Ta amsa min da to ta tafi ta nufi kasuwa. Tana fita na tashi na debi ruwa dai-dai wanka, na kwalfe sauran na zubar a rariya na kashe wutar. Na shiga nayi wankana da soso da sabulun sosai saboda nayi datti da yawa. Bayan na shafa mai nake tunanin kayan da zan saka, don kayana kakaf na baro su a can Bauchi, kuma sauran da na bari suna cikin gidanmu a dakina, bazan iya shiga gidan ba ina tsoron arangama da Mahaifana. A gefen katifa na takure daure da tawul ina kallon kyakkyawan jariri mai kama da Ubansa sak, sai addu'a nake tofa masa Allah Ya sa kada ya biyo halin uwarsa da ubansa. Allah Yasa Musulmi ne mai yiwa Musulunci hidima. Shigowar Mama Tabita ce ta katsemun tunanin da nake. Ta shigo dauke da leda, tana shigowa ta mikomin ledar na karba na bude. Riguna ta siyo masa kyau kala biyu, da *yan wandina (panties) na manya shima biyu. Ta ce "Wandinan manyan naki ne, "Na yi murmushi na ce "Na gode Mama Tabita. Ta farke riga da wando daya ta sakawa Jaririn ta sake kwantar da shi tana jijjigashi har ya sake komawa bacci. Muryar Mahaifiyata ce ta daga mana hankali tazo bakin kofar dakin tana ta bugun kofar tana fada "Tabita yau ba zaki fito ki dora mana abincin rana bane? Yanzu karfe goma sha biyu da rabi na rana ga yara sun fara jin yunwa. Aikin abinci na dauke ki ko aikin jego? Tabita ta hau rawar jiki tayi wuf ta fito tana bawa Mahaifiyata hakuri. Ita kuma kamar sake zugata ake sai fada take. Fadan dai Tabita ake yiwa amma maganar duk tawa ce. Wai ita babu ruwanta in rube mana ni da Jaririn kada Tabita ta sake makara bata dora abinci ba kuma ta tabbatar ta gama musu kowanne aiki kafin ta je ta fara gyara wani shegen Jariri. Na yi shiru sai kwalla nake nasan sai mun wulakanta ni da yaron nan, in ma ba'a koremu ba daga gidan. Ina zan je in zauna ni da Jaririn nan idan aka kore mu? Nake tambayar kaina da kaina. DUK WANDA BAISAN AN QARA DA YAMMA BA YA SHIGA WAJEN "SHOW MORE" ZAI GANI Sannan ba'a kammala na 1 ba yau da yammacin insha Allah Surayya Abukar zata karasa. Reedwan Suraj Isma'il YARENA ADDININA CIGABAN LABARI. Fadila tayi nadama ta gamsu da shawarwarina ta shaidamin in Allah Yaso ko kwana uku bazata karayiba agarin nan zata kwashe kayanta ta gudu ta koma garinsu tanemi gafarar iyayenta tarike addininta. Nima na shaida mata da zarar anyiwa yan jami'a hutu zan lallabasu janet su bani kudin mota in koma gida duk da bansan mezan fadawa iyayena ba dakuma yadda zamu karke da mahaifiya akan sabon addinina. Fadila ta zage tadaura zanina tazo ta tayani girki. Ita tayi miyar taushenan tas. Harriet ce ta shigo tana tafe tana layi idonta sharkab da hawaye. Muka tashi muka tareta muka rirriketa mun dauka ma ko nakuda takeyi domin watanni cikinta tara cifcif. Muka zaunar da ita akan tabarma muna tambayarta meke damunta, dakyar ta iya bamu amsa tace na tsani rayuwata,rayuwata ta dagule, nafi sha'awar mutuwa da inci gaba da rayuwa. Karuwanci ba rayuwar alkhair bace. Ina labe tundaxu abayan wundo inajin hirarku, pretty kin fimu hankali kin fimu sani ciwon kanki, kinfimu jin tsoron Allah. Naji natsani kaina. Ni jahilace wace basan addinin da nake cikiba saboda wurin bautar iyayen nawama bana zuwa. Nagamsu da addininku addinine me tsafta addinin gaskiya. Zan karbi musulunci in mutu a ciki musulunc." gaba su suhaif suka dau kabbara. Iman ta fashe da kuka taci gabada cewa "nida fadila da harriet muka rungume juna muna ta kuka. Aranar na musuluntar da harriet ta zabi suna khadija. Na sata tayi wanka kamar dai yadda hamma huzaifa ya koyamin. Nafara koya mata karatun salla da yadda ake yinta. Abincin da bamu iya ciba mu dukka hankalinmu a tashe muna nadama. Bayan munyi sallar isha'i. Fadila tace zata tafi gidan gibrel ta hado kayanta washe gari zataje banki ta kwashe kudinta ta gudu garin su amma kafin ta tafi zata zo tabamu kudin mota muma mukoma gida. Sai dai fatan Allah yasadamu da alhairinsa. Ta tafi ta barni da harriet abu kamar a mafarki harriet ta musulunta. Ta zauna zaman dirshen wai ita adole yau saita koyi karatun sallah. Har sha biyun dare ina koya mata karatun dana iya, ta tashi tayi alwalla ta sake yin magariba da isha'i sannan muka kwanta. Nafara bacci kenan harriet ta daka min duka na tashi figigit saina ganta a durkushe tana murkususun zafi. Na kunna fitilar lantarkin dakin sai naganta afujajan sai zufa take tana cije baki wai cikinta ciwo. Nace ko nakuda ce? Tace eh.' gabana yafadi nahau salati na rirriketa nida ita dukka yarane bansan yaya zanyi mata ba. Nafita da gudu na kwankwasawa mr.segun daki naga kwado a datse abakin kofar shima yau bazai kwana a gida ba. Ga janet ma bata dawo ba, na dawo wajen harriet sainaga wani ruwa yana fitowa daga jikinta ciwan kuma kara karuwa yake sai ihu take tana kuka. Nima na fashe da kuka jikina yadau karkarwa. Nace "yaya zamuyi yau? Na tambayeta akwai kudi ajakarta ne inje insamo mota? Tace naira ashirin ce kawai a jakarta, fitar da take aiba namijin dayake daukarta da wannan tsohon cikin. Wani waje take samu tazauna tayini cur sannan ta dawo gida bakin cikin rayuwane kawai ya isheta. Nace to bari in dauki naira ashirin in nemi achaba inje in kirawo micheal yazo yakaita asibiti ko yaki ko yaso shiyayi mata cikin ai. Harriet fadi take inyisauri in kirawo shi yazo yakaita asibiti kafinta mutu. Nadauki naira ashirin na fita da gudu. Dare yayi sosai bbu yan achaba, na tuna akwai wani dan achaba. dakinsa awata boy's qauter dake kusa datamu. Naje da gudu na kwankwasa masa kofa nace yataimaka yazo yakaini wani wajen nan cikin G.R.A. ne zanbiyashi, yafito da babur dinsa nahau ahanya yake tambayata "lafiya? Na shaida masa "harriet ce zata haihu zan kira wanda yayi mata ciki. Yace aida asibiti nafara kaita kafin akirashi. Nace bazata iya hawa babur ba dan a durkushe take kuma bamuda kudin zuwa asibiti saiyazo. Ya figa ya kaini kofar katafare guest house din micheal inda ina kyautata zaton anan zan sameshi don fadila ta shaidamun yanzu anan yafi zama. Nace hadi dan achaba yajirani in shiga inji yadda zata kaya. Nakwankwasa, mai gadi yaki bude mun yace in tafi inbashi waje bazai iya kirawo mai min micheal ba. Narokeshi nace yace pretty ce. Ya tafi dakyar yafadawa ubangidansa. Koda yaji sunana nanda nan micheal yace yaje yashigo dani. Afalo na iskeshi 'yan mata biyu karuwai a zagaye dashi. Yana ganina ya kuramin ido yana kallona, kallo irin na 'yan iska. Sai a lokacin ma na kula da cewar rigata yar yaloluwace shara-shara 'yar karama iya gwaiwa, ta barci, kaina ba dankwali. Takalmin kafata wari da wari don gigicewa. Nasa hannayena nadinga kare jikina don kunya. Yayi murmushi cikin harshen turanci yace "you are well come pretty. I'm glad to see u my baby come and hug me". Ya yiwa yan matan nan biyu nuni da hannunsa alamar su matsa daga kusa dashi, suka koma gefe. Na matso kusa dashi a tunaninsa zanzo in rungumeshi sai yaga na durkusa a gabansa. Yayi murmushi yace 'common stand-up baby feel free, relax don't shy i am your lover, i love you my baby yasa hannu zai jawoni jikinsa na goce gefe muryata na karkarwa nace "zance harriet ne ya kawoni." ya bata rai yaji an ambaci harriet yace fadi meye inji" nace ka taimakemu kazo ka kaita asibiti zata haihu..dan bazaka jeba kabamu kudi da direba. Bamuda kowa agarinnan saikai kuma danka ne za'a haifa." uwar tsawar daya daka mun bani ba 'yan matansa ma sun razana sunja da baya. Na mike da gudu nayi bakin kofa yace "fita daga gidan nan kar in kara ganinki indai zancen harriet zaki dinga yimin. Ina ruwana da haihuwarta ta mutu mana." ya kira 'yan matan sa ya rungumesu a gabana suka dinga aikata masha'a. Ban daddara ba na rushe da kuka naci gaba da rokarsa yataimaka ko cikin banasa bane yataimaka ya kaita asibiti. Yace ya tuna alkawarin daya yimana yace shi kadai muka sani agarin nan duk abunda muke so zai taimaka mana. Maganar daya sake yicewa yayi idan zan yarda in shiga dakinsa inbashi minti uku mu kebe zai yarda yakai harriet asibiti, idan kuwa bazan yarda ba na fice nabashi waje. Na ishe shi da magiya akan basai nashiga dakiba yadaure yakaita asibiti tunda shi yayi mata ciki. Yazaro belt ya biyoni aguje. Gudun da ban tabayin irinsa ba, na bude get nayi waje ba shiri. Na cewa hadi maza ya kunna babur mubar kofar gidan nan. Tambayoyin da hadi yakemun "ku arna inda ake kwararku kenan ba kamar mu musulmai ba kuje kuyi ta iskanci da mazan banza suna muku ciki wai dan dakan kuka a haihu ba aure. Ku acikin arnan ma karuwai ne ai munada labarinku, makaranta iyayenku suka turoku kuka falle kuka kiyin karatun. Kebakiyi kama dasu ba kamar bafillatana kike ko balarabiya ko shuwa. Bai kamata ki shiga cikin arna ba kina tacewa. "nasake rusa kuka naji na tsani kaina na tsani rayuwata. Abakin dakin mu ya saukeni nace ya tsaya in shiga in rikota ko zata iya hawa achaba mu kaita asibiti. Nashiga natarar da harriet wanwar a tsakar daki cikin jini kaca-kaca kan da yafara lekowa ta galabaita ko maganarta bata fita sosai. Na kwalla kara na fito da gudu a gigice nace da hadi dan achaba "taimaka min kazo mu daukota jini ne yake zuba daga jikinta." ya yatsuna fuska yace "to da jini zan dauketa, yaya ma zatayi ta iya zama akan babur? Gaskiya mota yakamata ku samo, kuma da ace matar aure ce zata haifi dan sunna da saimu bugawa wani kofa yafito da mota yakaiku asibiti ace ya taimaka amma duk an sanku a unguwar nan karuwai ne babu me sauraronku. Yanzu ki biyani kudina saiki bani wasu kudin inje intaso abokina me taxi yazo ya kaiku asibiti idan yaga an biyashi zaije." namika masa naira ashirin din nan nace "ita kenan garemu kataimaka." ya galla mun uwar harara. Yace "akan naira ashirin kika katsemun barcina dan ubanki? Ya kawo mun mari na kauce, yayi wurgi da naira ashirin din ya buga babur dinsa ya tafi yana zagina. Na koma cikin daki da gudu na tarar da kan da yana sake fitowa waje. Ina kuka narike hannun harriet, tarikeni tace pretty mutuwa zanyi idan na haihu dan yayi rai kidauka kirike minshi amana nima yar uwarki ce musulma ki taimaka ki rikemin dana ko 'yata. Kicewa iyayena su yafe mun. Pretty kici gaba da kyamar zina, ki gujeta kikoma gida kiyi aure, irin wannan rayuwar da muka jefa kanmu ba alkhairi bace." harshenta yafarara hardewa sai gumi take kamar ruwa sai wani nishi take da karfi kamar akuya. Nahau salati da karfi itama saita kamayi sai tayi nishi mai karfi guda daya sai da ya sunbulo ya fado ya cara kuka, yayin da ita kuma nishinta na karshe a duniya ta cika. Abun yafi karfin kuka saina koma na zauna ina kallon bakin dan kankanin jariri yana tsala kuka sai in juya in kalli uwarsa a kwance ta mutu. Jini face-face ajikin su bansan yadda zanyi ba, banida sauran tunani. Harreit data zama gawa ta fini jin dadin yadda nakejina a ranar. "dama nima akamani a harbeni ace nina kasheta. Haka nake addu'a. fakam naji an daga labule an shigo. Fadila na gani sanye da rigar bacci irin tawa harma tafi tawa kankanta iya cinyarta. Ta dora hannu aka ta kwalla ihu ganin harriet da dan ta face-face a kwance a cikin jini. Tambaya take 'harriet ta mutune?" na gyada kai don bana iya magana alamar "eh ta mutu. Saita jawo hannuna tace pretty tashi mubar dakin nan, taso mu tafi tun daga unguwarmu da kafa na taho inzo in shaida miki abunda yake faruwa. " na kalleta cike da fargaba nace "meke faruwa? Jikita yanata karkarwa sosai a tsorace take. Tace "janet ma ankasheta solomon saurayin janet an kashe shi, ngozi da easter kawayena an kashesu. Ta rushe da kuka tace Gibrel saurayina shima yana cikinsu ankashe shi. Yanzu motar yan sanda ta zagaye gidan micheal za'a kamashi shima a kashe shi? "Na zabura na mike tsaye na dafe kirjina nace "me sukayi? Ta rushe da kuka tace ashe duk kudin nan dasu micheal suke kashewa bana iyayen su bane, ba sana'a sukeyiba fashi sukeyi. Micheal ne babbansu shi yake turasu suyo fashi idan sukaje lagos ma fashi sukeyi. Dazu suka tafi jos wai harda su janet suka rakasu sukayo fashi yan sanda suka biyosu suna harbin yan sanda 'yan sanda na harbinsu. 'yan sanda suka harbi tayoyin motarsu suka gangara motar ta kife duk suka mutu. Wani abokinsu ne guda daya emeka bai mutu ba amma ya jijji ciwo, ya fita daga motar kafin yan sanda sukaraso yabi duhu, ya tsere bakin titi ya dane motar daukar kaya. masu motar basu sani ba ya shigo Bauchi duk a cikin daren nan. Ya dibi kudin Gibreal ya ce yanzu zai gudu garinsu Lagos, nima na debo mana kudin mota, taho mu gudu. Zan karasa anjima insha Allah. Surayya Abubakar Masu motar basu saniba ya shigo bauchi duk acikin daren nan. Yazo gidan da nake wujiga wujiga yace inyi ta kaina. Ya dibi kudin gibrel yace yanzu zai gudu garin su lagos nima na debo mana kudin mota, taho mu gudu. Jikina na rawa na dauko zani na daura na yafa wani zanin gadon janet. Fadila ma tasaka wata doguwar rigata. Ta fisgo hanuna muka fito daga dakin. Dan jaririn harriet sa kwalla kuka yake nace mata "ban dauko dan jaririn ba. Ta daka mun tsawa "kidauko shi ki kashi ina? Zomu tafi muyi ta kanmu. Kinsan fa ansan tare muke dasu micheal zasu zo nan nemanmu fa. Harna juya na bita, naji yaron nan sai kuka yake. Nadawo da gudu cikin dakin, fadila ta biyoni tace "me kika dawoyi? Nace dan jaririn zan dauka. Ya zanyi in yanke cibiyar in rabashi da uwar? Tace "dauko reza. Sabuwar reza nabata acikin kayan kwalliyar mu. Fadila ta yanke cibiya, sake bani shawara take tana cewa in ajiye dan jaririn nan idan nadauke shi ina zan kaishi. Nima nayi tunanin haka amma tausayi ya hanani in tafi in barshi. Nadauko zanin mahaifiyarsa na lullubeshi na rungume shi a kafadata. Najawo mayafi na lullube fuskar harriet na tofa mata addu'a Allah yajikanta. Muka sakd juyawa zamu fita wani dan karamin hoton harriet ne a jingine a wajen kayanta tana dariya a hoton tayi kyau sosai. Nakoma nadauko shi. Fadila ta kwalla da karfi tace "pretty idan bazaki tafiba zan tafi ga karar jiniyar motocin 'yan sanda can watakila nan zasu zo neman mu mu yan matan yan fashi. Muka fito daga dakin muna ta gudu muna shiga gonakin mutane. Batare damun san inda muke nufaba. Akwai wani katon dutse a bangaren da za'aje wata makaranta jibrin aminu primary school a jikin dutsen muka labe. Idan muka hango motocin yan sanda saina toshewa dan jaririn baki yanata tsala kuka. Anan a gindin dutshen muka zauna muna rusa kuka tamka ranmu zai fita. Fadila tace mu "pretty kin fadamun gaskiya, rayuwar bariki ba rayuwar kirki bace. Mubi maganar iyayen mu domin muddin kaki bin iyaye bazakaga ci gaban rayuwarka ba, dubemu kiga irin rayuwar da muka jefa kanmu. Ta debo kudi mai yawa daga kudadenta tabani, tace inyi kudin mota intafi gida itama zata shiga mota ta koma gida. Dan jariri ya gaji da kuka sai yayi barci. Bamu fito daga bayan dutse nan ba saida gari yafa washewa muka farajin karar wucewar motoci da babura suna giftawa. Allah ne yakiyaye mu ashe duk ramukan macizai ne a inda muka fake ga kunamai sunata gif-giftawa. Mukayi sauri muka bar wajen muka fito titi muka tari achaba gudu biyu muka ce tashar yankari. 'yan achaba ma hirar 'yan fashi da aka kashe jiya suke bamu, sai cikinmu yakara durar ruwa suna cewa "abun mamaki harda mata acikin yan fashin da aka harbe jiya. "naji kuka mai radadi ya zubo min bamu iyace musu komai ba. Suka kaimu tasha muka sauka muka basu kudinsu. Dan jaririn dai kuka yake tsalawa babu riga ko wando ajikinsa ko jinin haihuwar ma ba'a wanke masa ba ga uwa uba sanyi da yake surarsa da yunwa. Fadila shawarar da take bani itace inyar da yaron nan intafi gida. Natuna amanar da uwarsa ta bani, kuma tausayinsa nakeji idan nayar dashi bansan hannun wandazai fadaba watakila yatashi ba'a musulmi ba. Naji ajikina zai zama musulmi ya amfani musulunci duk da dai bansan inda zan tinkara da dayan jariri ba a yarda arikemu. Na shaidawa fadila bazan iya yarda shiba, zan tafi dashi. Na roketa nace ta rakani kantin dake cikin tashar in saya masa madara in bashi yasha kafin afara sayar da ticket din shiga motocin yankari expressg. Akantin na tambaya ko akwai madarar jarirai akace akwai. Nasaya sai muka je wajen wata mai koko da kosai na roketa Allah annabi ta bani ruwan dimi in damawa dan jinjirina madara. Tabani kadan a kofi da cokali nida fadila muka dinga tarfa masa yana hadiyewa harya koshi, muka yiwa matar godiya muka tafi wajen da ake yankar tiket din shiga motar. Nayanki tikitin jalingo, fadila ta yanki na katsina. Muka rungume juna muna kuka mukayi sallama kowacce tashiga motar garinsu muna dagawa juna hannu muka tafi. Na shiga garin mu, atasha nadauki shatar taxi wacce xata kaini har kofar gida. Na shiga unguwarmu na tarar unguwar shiru ba kowa. Nashi mummunar fargaba da mummunar damuwa yadd zanyi da dan jaririn nan. Ina cikin taxi ina waige-waige ina fargaba jinake kamar incewa dan taxi ya juya dani nafasa zuwa gidan. Akofar gidan su hamma huzaifa na kalla sai kuwa mukayi ido hudu dashi. Ya bude baki yana mamakin ganina. Saiya washe baki yayi min wannan dariyar tasa tanuna farin cikin ganina. Yasa hannu ya tsayar dame taxi gami da cewa "wait-wait." ya tunkaro motar ta tsaya da farin cikin sa. Mummunan faduwar gaba tadasu a zuciyata. Nazaro kudi nabawa dan taxi kafin bude kofar motar in fito hamma huzaifa da kannensa sun karaso wajen motar yasa hannu yana bude mun kofar cikin harshen fulatanci yake tsokanata. Yace inye pretty 'yan makaranta, yanzu angama level 1 an zama yan level 2 ko, point nawa kika buga mana? Nasan dai kin bugo samada 3 points ko mutuniya? Yana fada yana bude mun kofar mota.... Amin afuwa plz YARENA ADDININA....CGBN LBRN Nasa kafata daya awaje ina kokarn fitowa dakyar don jikina yayi sanyi. Huzaifa ya sake kallona cike da mamakin ganin yadda na zama kamar baniba. Bayan rashin fara'a gashi na yafa wani burgujejen zanin gado na lulluba, baki abushe, ido a kode sanadiyar kuka. Gashin kaina biyu-biyu a cukurkude. Alamar tambaya zaka iya gani a idanuwansa. Zai bude baki yayi min tambaya meke damuna yaga nazama haka? sai kukan jaririn dake hanuna ya mayar da hankalinsa ya kalli abunda na rungume, fuskar sabon jariri ya hango. Nanda nan ya canja zaka iya ganin fargaba da tashin hanakalin da suka rufto masa, yaja da baya da sauri jikinsa yayi sanyi sai kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'un yake karantowa, kaji musulmin kwarai. Muka hau kalon-kallo, ya kalleni ya kalli jaririn hanuna. Abunda ya sake fadomin arai shine nasihar da yakemun tun ina yarinya. Yace "kada kiyi zina, Allah ya hana zina, yana kallon ki zai konaki, kiji tsoron Allah. Shima kuma daga dukka alamu abunda yake tunowa a zuciyarsa kenan. Wato na manta nasihar da yayi min? Ina tsoron Allah da yake ganin alamar yashigeni? Sai naga hawaye daga idonsa guda daya ya surnano. Ya girgiza kai ya juya ya tafi ya nufi gidansu yabarni anan a tsaye. Bakina yahau kaikarwa inaso inyi magana na kasayi domin nasan babu bayanin da zan iya yi masa awannan lokacin ya yarda dani me taxi yaja motarsa ya tafi. Kannena na hango sun taho da gudu zasu tareni sainaga sunyi kicibus sun tsaya ganin dan jinjiri a rungume a hannuna sukayi gefe suna kallona, nazama abar kallo. Mahaifina da mahaifiyata nahango awajen mota da alama motar zasu bude su shiga su fita, sai suka tsaya suna hange suna so su gaskata abunda suke hange gaskiyane ko kuwa gizau idanunsu suke musu. Jariri ne a rungume a hanuna ba gezau bane gaske ne. Na tunkaro inda suke a tsaye. Mukullin motane a hannun mahaifina saiya fado kasa don razana. Haka jakar dake rataye a kafadar mahaifiyata sai data sulmiyo fadi kasa. Mahaifiyata ta sulale ta zauna akasa tsabar tashin hankali. Muka hau kallon-kallo dasu yayinda nima idanuwana suka haskomin mummunan tashin hankali a tattare dasu wanda yafi tashin hankalin da suke hangowa a tattare dani. Naji tsananin bakin cikin da nake ciki tamkar shafar mai ne akan bakin cikin daya tunkaroni a yanzu yanzun nan. Shin gizau idanuwana sukayi min ko kuma gaskiya ne. Hakika gaskiya ne ba gizau bane. Turkashi, nanda nan na nami yawun bakina da makokarona na rasa sun bushe kamas don tashin hankali sai zuciyata ta lalibo addu'ar da Huzaifa yake karantawa a lokacin dabala'i ya tunkaro shi. Naji kafata bazata iya daukar jikina ba da dan jaririn dake hannuna sai nima na sulale na zauna kamar yadda tashin hankalin ganina yasa mahaifiyata ta sulale ta zauna. Karkarwa suke suna nuna jaririn dake hanuna, nima hannuna na karkarwa idanuwana na zuba tamkar ruwa a famfo ina nuna gagarumin tashin hankalin da nake hange a tare dasu..... Toh littafi na dayan yakare da iznin Allah YARENA ADDININA. ___CI GABAN LABARI Mahaifiyata ta wuce tana fada, Tabita tana rawar jiki ta shigo ta dauki mayafinta ta fita. Har ta fita, na tashi da sauri na ce "Mama Tabita ki dauko min kayana set daya a durowata zan saka, ta amsa min da to ta tafi. Bayan tafiyar Tabita da minti biyar sai ga kanwata Rabecca ta shigo ta tsaya, ta kalleni ta kalli jaririn cikin harshen turanci ta ce min "Aunty Rufkatu kizo inji Daddy ki dauki kayan da kanki, Mama Tabita ba zata dauko miki ba. Na amsa mata da "To ina zuwa. Ta fita ta tafi, a zaune nake ina tunani wai me suke nufi da inzo da kaina? Shiguwar Mama Tabita ce ta katsemin tunanina, ta shigo da sauri ta ce "Pretty dauko yaron ki fito kizo muje gidan ki roki Mahaifanki gafara tun da sunyi fushi dake. Duk fadan da zasu yi miki suyi miki yanzu ki huta. Babu yadda za'ayi keda jaririn nan ku zauna cikin kunci da rashin gata. Na girgiza kai na ce "Ba zan shiga gidan ba "Tabita tayi ta lallashina dakyar na yadda na dauko mayafi na lulluba, ta mikamin Jariri na karba muka fito. A kicin Tabita ta labe ta ce in shiga cikin falon. Na kwankwasa kofar na shiga, gaba daya suka dago ido suna kallona na sunkuyar dakai kasa na wuce sum-sum cikin dakina, ina shiga na kwantar da Jaririn akan gado na bude durowa ta kayana na dauko wani leshi yellow riga da siket da dankwali na saka. Mahaifiyata ta shigo a fusace ta harari dan Jaririn dana kwantar akan gado, ta juyo ta harareni ta ce "Ki kwaso kayanki kakaf ki koma wancan dakin ki barwa Rabecca dakinta, kije can ki karata keda buhunhunan abinci. Na zubo da kayana kakaf akan gado na warware wani dan kwali na zuba na daure. Ta sake daka min tsawa "Kizo ki dauke wannan yaron kafin ya jikawa yarinya gado da fitsari. Na taho da sauri na dauke shi zuciyata cike da bakin ciki. Muryar Mahaifina naji ya kugamin kira cikin kakkausar murya, jikina na rawa na amsa na fito Mahaifiyata na biye da ni. Ya nuna min tsakiyar falo kan kafet ya ce inzo in zauna shi kuma yana zaune akan doguwar kujera. Mahaifiyata tazo ta zauna a kusa da shi. Ta juya ta kalli kannena ta ce "Su tashi su fita, ko su shiga dakinsu suyi kallo. Cikin fushi Mahaifina yake magana, cikin harshensa na fulatanci ya ce min "Fatima kin bani kunya, kin bani mamaki. Abunda kika yi kin kyautawa kanki kenan? A kwai wani yaro dan nan garin ne, dan abokina ne ya sanki, kece baki sanshi ba shima a ATBU yake tun wancan satin ya dawo gida sun gama jarabawa, na tambaye shi ko yana ganinki a makaranta? Ya shaidamin bakya makaranta, ya takaicemin yace sunanyenku na nan kafe an fitar da result an rubuta an koreku kwata-kwata, bakwa cikin makaranta kuna can kuna yawan iskanci. Baki taho min da result din jarabawa ba sai kika taho min da result din yawan iskanci kamar shi muka turaki. Kaina a sunkuye a kasa hawaye nake. Tun da nake da Mahaifina bai taba nuna min bacin ransa ba balle ya fada min bakar magana, tsakani na da shi sai wasa da dariya da nasiha. Ya dakamin tsawa gami da kawo min duka da gefen hannunsa na goce ya ce "Ba tambayarki nake yi ba kika yi shiru kina min kukan munafunci? Na ce sakamakon jarabawar kenan kika kamo hanya ki shigo min gida da goyan shege? Na sake rusa kuka, na kasa magana. Mahaifiyata ta tambayeni ta ce min "Waye uban dan? Nayi shiru ban amsa ba. Ta sake daka mun tsawa "Waye yayi miki ciki? Na share hawaye na ce "Ina so inyi bayani. Mahaifina ya daka min tsawa ya ce basa son bayani na, in amsa musu tambayar da ake min. Waye uban dan? Cikin rawar murya na ce "Wani ne mai suna Micheal a Bauchi yake. "Micheal suka hada baki suka maimaita. Na gyada kai na ce "Eh. Mahaifina bai kara magana ba ya koma ya jingina da kujera. Mahaifiyata sai ta hau murmushi. Abun ya bani mamaki. Ta gyara zama ta ce "Meye addininsa? Nayi shiru can na ce "Addinin ku daya. Ta harareni ta ce "Addininmu daya banda ke? Taci gaba da cewa "Naji dadi da Allah Ya sa addininmu daya, kina da labarin Mahaifinki da kannanki mun zama addini daya muke bi, kin ci sa'a kuma ga uban danki addininmu ne. Na daga ido na kalli Mahaifina sai ya kawar da kai gefe. Hawaye mai radadi ya zubomin. Dukkansu sun gane banyi farin ciki ba da wannan sabon labari dana ji, sunsan yadda nake kin addinin tun ina karama, su kan rasa to ni me nake bautawa. Na dora Jaririn akan kafadata ina jijjigashi don ya tsula min fitsari ya jikani ya hika zanin da aka nade shi. Nayi gyaran murya cikin marainiyar murya na ce "Nayi kuskure, nayi laifi, ku yafemin. Nima ba da son raina ba na bar makaranta inda ku ka turani karatu. Wannan yaron da kuke gani ba dana bane tsintarsa nayi. Su duka suka yo kaina kamar zasu cinyeni danya tun ban dahu ba don masifa, kowannensu na zagina da yarensa. Wai in rufe musu baki basa son karyar banza, su zan mayar yara. In tashi in basu waje kafin suyi ball dani da Jaririn. Na tashi cimak ina rusa kuka na nufi dakina da aka nuna min aka ce in koma in bar dakina na da. Tabita ta biyoni dakin ta fara lallashina ta ce inje kicin in zauna bari ta share mana dakin ta kade kura, ta shimfida mana wankakken zanin gado a tsohuwar katifar dake jingina a dakin. Haka kuwa akayi, ni da kayana kakaf na dawo dakin nan. Tabita kullum na shigowa ta yiwa yaron wanka ta bashi madara nima ta kawomin nawa abincin. Sabida tashin hankali bana iya ci sosai. Allah Ya dubi zuciyata Yasa yaron ba mai rigima bane sosai. Baya min kukan dare duk da wataran a dakin Mama Tabita yake kwana idan mijinta yana aikin dare, me gadin gidan mu ne watarana ya kwana wata rana wani ke canjarsa. Tana kula da ni sosai da jaririn. Tana gasa masa cibiyarsa dare da rana da safe don haka a kwana uku cibiyar ta fadi. Mama Tabita tana kula dani, ko kadan bata ga alamar jego a tare dani ba audugar matan data siyo min tana nan ko budeta ban yi ba. Ga fama da take dani saina bashi nono, ni kuma naki sai dai madara. A tsanake take tambayata gaskiyar al'amarin nan. Na zauna na bata labarin abunda ya faru tsaf. Ta gamsu dani ta kuma kara tausayamin da dan Jaririna. Ta ce min ba dan Mahaifana zasu ga laifinta ba, daman yanzu ma harararta suke idan suka ganta da yaron, da taje ta basu labarin abunda ya faru, amma ba zasu saurareta ba, na ce kawai ta kyalesu. Ranar da muka yi sati biyu da dawowa, da misalin karfe daya da rabi na rana, na fito daga gidansu Hamma Huzaifa da goyon dan Jaririna a baya. Na je sallar azahar kasancewar Mahaifiyata tana gida yau asabar bata je aiki ba. Sai naga wata mota katuwa baka kirar CRB tana biye da ni ana min hoon. Na juya na dubi motar sosai sai naga babu abinda nake gani kasancewar gilasan an fentesu sunyi duhu, kuma ban taba sanin me irin wannan motar ba, sai na sawa raina ba dani suke ba. Na juya naci gaba da tafiya na nufi hanyar gidanmu. Dai-dai get din shiga naji an sake matsa hoon an ja burki an tsaya dab da bakin get dinmu. Har na bude karamin get zan shige sai dai na sake juyowa na dubi motar. Sai naga an sauke gilashin. Yanzu ina iya ganin samari guda biyu a cikin motar gabadayansu sanye suke da kwabta-kwabtan bakaken gilasai a idanuwansu. Ina yiwa dayan kallon sani amma na kasa gane ko waye. Suka bude kofofin motar suka fito suka tunkaro ni suna min murmushi gami da kiran sunana "Pretty. Nayi kasake ina kallonsu naga da gaske ni suke tinkarowa sai na tsorata naja da baya, dogon sosai ya zare gilashin dake fuskarsa ya ce "Pretty baki gane ni bane? Kallo daya na yi masa ba gilashin na gane shi Micheal ne. Wata uwar tsana da takaici da tuna baya suka ruftawa zuciyata. Sakon daya yayi yawa annurin fuskata kakaf suka gushe, na bata rai, na murtike fuska tamkar naga kashi mai tsutsa naja dogon tsaki gami da wata uwar harara na kada kai na fada get din gidanmu, suka yi wuf suka biyoni ciki. Micheal na rawar murya yana magiya in saurare shi inji sakon da ya zo min dashi, bai isheni kallo ba balle in saurari maganarsa. Ficik naji an fincikoni inda nake tafiya a arewa naga an juyo dani kudu. Micheal ne ya fisgoni ta baya. Cikin fushi na fara zaiyano masa kalaman batanci, da zagin da ban taba yiwa kannena ba balle kawayena ko balle uwa uba na gaba dani. Ransa ya baci ya dakamin tsawa ya ce "Ya isa haka, kanki ya zare ne, don me zaki ce in bar kofar gidanku bayan ga dana kina goye dashi. Na fusata na ce "Danka? Ya aka yi ya zama danka, daman kana da da? Ya sake fada cikin fushi "Ki bani dana sai kiga nabar zuwa gidanku. Na sake fusata na ce masa "Ban gane abunda kake nufi ba. Ya aka yi wannan yaron da nake goyo ya zama danka? Dan makwabtanmu ne na daukko raino. Yayi murmushi ya ce "Pretty kin dauka bani da labarin Harriet ta haifar min cikin da nayi mata? Ko bani da labarin ke kika dauki yaron? Wannan abokin nawa dan garin nan ne, bayan haka munyi waya da Fadila ta fadamin kakaf abunda ya faru, na nemo wannan abokin nawa a waya na sanar masa na masa kwatancen gidanku na ce ya zo ya bincika mun kin zo da jariri? Ya ganki da idonsa goye da Jariri da yayi kama da ubansa. Ko kin manta nasan gidanku, mun taba zuwa daukarki? Dan haka na shiryo nazo takanas dan inga dana. Nayi shiru tamkar ruwa ya cinyeni na rasa abun cewa, na tsani Micheal bana kaunar ganinsa, amma kuma ina son dansa bana son rabuwa dashi kuma na saba da shi sosai a cikin sati biyun nan. Kamar daga sama naji Micheal ya ce "Pretty me zai hana muyi aure mu rike yaron nan. Kina da labari har yanzu son da nake yi miki yana nan? Na fusata bansan sanda na fisge zanin goyon da nayi ba, na kunto yaron daga bayana na dungura masa dan gami da cewa "Idan danka ne gashi nan, ko bayan raina bana son ka matso kusa da gawata balle ni da kaina in aureka. Na fashe da kuka na juya naci gaba da tafiya. Kukan da yaron yake tsalawa ne naji tamkar mashi ake caka mun a zuciyata. Babu abinda ya fadomin a rai sai idan na barshi ya tafi da yaron nan ko shakka babu sunansa ba Musulmi ba, idan ma ba a ci sa'a ba ya tashi cikinsu *yan fashi ya koyi fashi da iskanci da shaye-shaye irin na ubansa. Sai na ji na tsaya cak, na juyo na dubesu suna nan a tsaye suna kallona. Na juyo na dawo na mikawa Micheal ya miko min dan na rungumeshi ina kuka, har cikin raina bana son rabuwa da dan nan duk rintsi. Aka rasa mai yin magana har tsawon wasu *yan mintuna. Sai Micheal ya ce in zo bakin mota in ga wani abu. Naki tafiya saida yayi ta min magiya sannan na bishi a baya, abokinsa ma na biye damu. Fargaba nake karfa su danke ni da jaririn su wurga a cikin mota, sai baya-baya na keyi. Ya bude mun but din motarsa na kalla babu abinda nake gani sai hadaddun akwatina guda biyu manya-manya. Koda ya budemun ciki sai naga tsala-tsalan rugunan Jarirai ne masu kyau da laushin gaske *yan waje masu tsada, ga pampers katan guda. Daya akwatin kuma leshina ne da atamfofi da shadda har da takalma da jakarsu da turaruka masu tsada. Cikin fushi na ce "Mungode amma ka juya da abunka bama bukata. Na yi gyaran murya na ce "Micheal ka yiwa Allah ka dubi girman iyayenka ka rabu damu ka daina zuwa gidanmu balle iyayena su ganka, ka kuma cirewa ranka zaka aureni har abada, na riga na shaidawa iyayena duk yadda aka yi Harriet ce ta haihu na taho da dan kuma ita kanta bata san wanda yayi mata cikin ba. Kana da kunya yanzu zaka dubi idona kace dan gidan Harriet danka ne? Ka manta lokacin da take sanar maka cewar har yanzu cikin da kayi mata bai zube ba? Kace mata duk ranar da ta kawo maka da ko *ya ta ce naka ne sai ka fasa dan? Ka manta ranar da zata haihu bamu da kudin zuwa asibitim nayi maka magiya ka zo ka kaita asibiti ka ce kai ba danka bane su mutu mana. Ka manta ne Micheal? Hawaye yaci gaba da kwaranyo min yayin da Micheal ya sunkuyar da kansa kasa yayi shiru. Abokinsa na cikin mota a zaune yana saurarenmu, sai gyada kai yake yana sauraron wannan abun al'ajabi. Ma sharbe hawaye na sake rungume yaron na ce "Kamar yadda kace Harriet ta mutu idan har kai zaka kaita asibiti, to baka kaita asibitin ba kuma ta mutu. Amma kafin ta mutu cemun tayi in rike danta amana bata cemun in kaishi wajen Mahaifinsa ba. Micheal ina rike yaron nan ne saboda kawata marigayiya Harriet badan kaiba. Ka cuceni ka hanani karatu amma duk nawa mai saukine tunda baka batamun rayuwa ba ka yaudareni. Wa danda ka yaudara ka rabasu da makaranta, ka yiwa Harriet ciki, Janet ka hadata da abokanka ta zama *yar fashi daga karshe kai musu sanadiyyar barinsu duniya dungurungun. Ka tafi ka bani waje bana son ganinka zan rike dan Harriet amana, kuma in Allah Yaso bazai zama mai irin halinka ba. Na juya na nufi gida ina sharbar kuka nabar Micheal anan tsaye abakin but tamkar an gina shi. Ina shiga ban tsaya ko ina ba sai na nufi dakina da sauri ina shesshekar kuka. Mahaifiyata na wuce a falo tana karatun jarida ita da Mama Tabita tana gogo-goge suka bar abunda suke yi cak suka bini da kallo. Ina shiga daki na datse, na haye kan katifa na bude sabon shafin kuka, yaron ya bude idansa yana ta tsotsar hannu alama ma yunwa yake ji. Nayi kuka ya ishe ni nayi addu'a Allah Yasa Micheal ya tafi ya rabu dani kar Allah Ya sake bashi ikon dawowa. Na tashi na tsiyayo ruwan zafi a flaks na dama masa madara ina bashi. Hirar da Tabita take yi da Mahaifiyata ita ta tsayar dani daga abunda nake, nayi tsai ina sauraronsu. Labarin dana bata na game da Micheal da Harriet take bata. Abun mamaki kafin Tabita takai aya Mahaifiyata harta rufeta da fada wai karyar banza wannan labarin bana kamawa bane. Wai karya nake dana ne. Muryar Mahaifina naji ya shigo sai kuma naji muryar maza da yawa da alama bashi kadai bane da baki yake tafe. Nayi sauri na karasa bashi madarar, na sake daukar zani na sabashi a baya na lallabo na bude mukullin dana datse kofa na bude kofar kadan na leko cikin falon. Gabana yayi mummunan faduwa a lokacin dana hango Micheal da abokinsa a zaune tare da iyayena suna gaisawa. Mahaifina ya ce "Nazo zan shigo na gansu a tsaye a jikin get da motarsu sunyi jigun-jigun, bayan mun gaisa suka ce mun wajan Fatima suka zo taki sauraronsu, ta shige gida ta barsu. Suna cemin daga Bauchi suke saina ce to su shigo. Mahaifiyata ta kalle su ta ce "Cikinku a kwai Micheal? Micheal yayi murmushi ya sunkuyar da kai kasa ya ce "Mama nine. Sai Mahaifina ya ce "Oh kai ne ka hana *yata karatu kayi mata ciki? Micheal ya yi shiru ya sunkuyar da kai kasa. Mahaifina ya rikice da fada inda ya shiga bata nan yake fita ba fada yake tun karfinsa tsakani da Allah. Har fadi yake sai dai kotu ta raba su. Mahaifiyata tana lallashinsa tana bashi baki da kyar ya fara saukowa. Micheal da abokinsa suka durkusa gwiwoyunsu a kasa suna rokon a gafarta masa yayi kuskure. A tunanina da Micheal yaji zancen kotu zai fadi gaskiyar abunda ya faru, cewar bani ya yiwa ciki ba kawata ce kuma ta mutu a garin haihuwa na dauki yaron. Sai naji Micheal ya kaikaice ya narkar da murya yana bada hakuri wai haka Allah Yayi, ya san bai kyauta ba da yayi sanadiyyar hanani karatu. Amma son da yake min ne ya ja haka, yanzu ya zo ne ya ga dansa ya kuma kawo masa kayan haihuwa kuma a radawa dan suna kuma in da za'a yadda a bari ya aure ni don mu rungumi dan mu. Kuma ya dau alkawarin zai rike ni da dana amana cikin wadata da kulawa kuma zai dau nauyin karatuna tun daga degree har sama da haka idan ina so kuma a kowacce kasa kuma ko nawa za'a kashe. Tashi daya kalaman mayaudari Micheal ya sanyaya zuciyoyin Mahaifana, suka ji lallai Micheal ya dace abi shawararsa. Shine kadai mafita tunda ga da waye kuma zai aure ni da dan wani, gara ubansa. Daman babban takaicin shine karatuna dana rasa amma yanzu gashi na samu mai nemomin makarantar fiye da ta da, ai shikenan. Mahaifiyata ta gyara zama ta ce masa "Micheal meye addininka? Ko da ya fada mata, taji addininsu daya sai suka hau dogon kwatance. Daga karshe sai ta gane Mahaifiyar Micheal mai bi ce sosai itama, shugabar wani babban wajan bauta ne a Bauchi. Tun Mahaifiyata tana ATBU nan take zuwa bauta duk ranar bauta. Zata iya tuna Micheal lokacin yana yaro karami. Lallai Micheal ya fito daga gidan manyan mutane, ga arziki ga addini. Farin ciki ya rufe Mahaifiyata daman ita babban burinta taga na auri miji wanda ba Musulmi ba domin ta kula dani bana son addininta. Huldata da Hamma Huzaifa ma bata so, saboda ta fuskanci akwai ranar da zata ji wani labari na game da aure a tsakaninmu domin shakuwar da kaunar junanmu tayi yawa. Ashe ita wannan Jaririn gaba ta kaita wai gobarar Titi a Jos. Hmmm ku huta da karatu anan Wanda ba su ga farkon na biyu ba su shiga wajen "Show More" yayi kasa zai gani Reedwan Suraj Isma'il ________________ YARENA ADDININA. ___CI GABAN LABARI Mahaifina baiyi magana ba daga dukkan alamu wannan labarin auren baiyi masa dadi ba. Baiyi niyyar aurar da ni yanzu ba nayi kankanta a lokacin shekaruna goma sha biyar. Amma yaya zaiyi na dauko goyo? Gara in tafi can da dan mu karata. Mahaifiyata na cikin farin ciki ta kwallawa Tabita kira ta ce "Ta kawo musu ruwa da lemo. Micheal ya cewa abokinsa ya je mota ya dauko akwatina da kwalayen da yayi mana shopping. Matukar bacin rai ya darsu a raina bansan sanda zuciya ta fito dani falon ba na tsaya a tsakiyar falon gaban Micheal da Mahaifana na ce "Micheal karya yake yi bani ya yiwa ciki ba kawata ce. Don haka bazan aure shi ba. Mamaki marar misaltuwa zaka iya gani a fuskokinsu su duka. Mahaifiyata ta daka min tsawa ta ce in tafi in basu waje kar in yiwa mutane rashin kunya. Wana dauka kananan yara? Ai ana ganin Jaririn anga ubansa. Ita kawar tawa bata da hannun rike dan sai ni zan rike mata? Mahaifina ya ce to ai wannan maganar bata sauraro ba ce ya akayi na bar makaranta na shiga gari? Har kuma ina musu ina cewa ban haihu ba. Babu yadda za'ayi in dauko dan wata in tinkaro gidanmu da shi da sunan dan kawa. Micheal ya hau rantse-rantse har da sa hannu a aljihu ya dauko wasu hotunanmu daya ni da shi, daya kuma ni da shi da abokinsa, don ya iya munafunci bai dauko na ni da shi da su Harriet ba. Takaici yasa na nufi gidan Mama Tabita da gudu ina rusa kuka. Babu yadda zata yi da ni sai lallashi ta ce min inyi hakuri. Bubby kanina ya shigo ya iskemu cikin wannan hali ya dube ni duban tausayi ya ce "Aunty Rufkatu ki daina kuka kiyi hakuri, Mummy ta ce ki kawo Jaririn babansa zai ganshi. Tabita ta miko hannu zata kwance shi daga bayana na fisge na ce "Bazan bayar ba, Mama Tabita Micheal mugu ne baya tsoron Allah, shi yayi sanadiyyar mutuwar Mahaifiyar yaron nan yanzu kuma dan zai kashe, daman ya fada sai ya kashe dan duk ranar da aka ce dan sa ne. Bubby ya bude baki yana kallona cike da mamaki. "Kamar yaya Micheal yayi sanadiyyar mutuwar Mahaifiyar dan, ba kece mahaifiyarsa ba? Ya tambaye ni. Na sake rusa kuka na ce "Bani ba ce Bubby yayi wuf ya fice ya nufi gida yana zuwa ya tarar da Micheal da Mahaifanmu a falo a inda ya barsu, ya dubi Micheal ya dubi Mahaifiyarmu da ta aika shi ya ce "Ta ce ba zata bada yaron ba Micheal mugu ne shi ya kashe Mahaifiyar yaron ya ce sai ya kashe yaron shima. Nan fa aka hau kallon-kallo, Micheal ya hau zare guru-gurun idanuwansa tamkar bai gane abunda nake nufi ba sharri nake masa. Mahaifina cike da mamaki ya ce "Wai meke faruwa ne, me yake damun Fatima ne take magana kamar tababbiya? Micheal fada mana gaskiya me take nufi? Mamaki marar misaltuwa zaka iya gani a idon Micheal ya ce shima bai san me Pretty take nufi ba, shi dai abinda ya sani shi ne yayi mata ciki, ciki yayi wata tara, da hannunsa ya kaita asibiti ta haihu yana shirin ya siyo musu kayan haihuwa ya kawota gida, ta gudo tazo tana nunawa kamar bata sanshi ba yanzu. Mahaifiyata ta fusata ta mike ta nufi inda muke tana fada tana cewa "Na zamar dasu kamar wasu yara kanana yaushe aka haifeni da zan musu wayo in nuna ma bani na haifi yaron ba, don haka duk ranar da na kara duban kwayar idanuwansu na ce ba nice Mahaifiyar yaron nan ba saita fasa min baki. Ta tunkaro inda nake tsaye a fusace, a zatona ma dukana zata yi saina rufe fuskata da hannuna Tabita ma jikinta ya dau rawa ta taso tana bata hakuri sai na ji ta fisge goyon daga bayana ta tafi da yaron wajen Micheal. Na sulale na zauna a kasa don takaici da radadin da zuciyata take yi. Tabita na bani baki akan kar in damu kar in sake yin musu akan bani na haifeshe ba in barsu haka. Na ce "Mama Tabita zancen aure fa suke yi, wai tunda ga da a tsakani zai aureni mu rike danmu. Tabita ta ce "To ai babu komai ki aure shi Rufkatu, yaro ne mai hankali mai kyau kuma, kin fada mun yadda yake matukar sonki tun farko ma ke yake so ba Harrier ba zai rikeki sosai tunda yana sonki. Na girgiza kai hawaye bai daina zuba ba nace "Ba zan iya auran Micheal ba Mama Tabita Micheal dan iska ne, macuci ne, bashi da tausayi ko kadan, dan fashi ne, duniya yasa a gaba babu addinin da yake yi. Haka Tabita ta tsaya a kaina tana kallona tamkar sassakakken gunkin da take bautawa, daga dukkan alamu ta fara zargina da yiwa Micheal kazafi saboda kiyayyar da nake yi masa. A can falo suka yiwa jaririn adddu'a irin tasu, suka sakawa yaron suna Citibin. Micheal ya dauko Camara ya daddauki yaron a hotuna kala-kala, ya dauki Mahaifiyata da Mahaifina da Jaririn a hoto, sannan abokinsa ya dauki Micheal da dansa sannan ya dauki Micheal da dansa da Mahaifana a hoto. Daga karshe suka yi addu'a, Micheal yayi musu sallama akan da zarar yaje gida zai sanar da Mahaifiyarsa ya gano inda Pretty take da Jaririnta dan hankalinta ya tashi daya sanar mata Pretty ta gudu kuma baisan garinsu ba. Ya ci gaba da zuba musu karya ya ce itace tace lallai-lallai yaje ya nemo Pretty duk inda take. Yanzu kuwa zata fi kowa jin dadi idan taji labarin ya ganta ita da Jaririn suna cikin koshin lafiya. Kuma zai daukota su zo taga yaron sai ayi zancen aure. Mahaifiyata taji dadi kwarai saboda zata hada zuriya ko kuma ma in ce ta hada zuriya da babbar Malamarta a wajan bauta, mai tsananin yiwa addininsu hidima da dukiyarta da jikinta wato Mahaifiyar Micheal. Dari bisa dari taji aurena da Micheal ya kwanta mata a zuciya. Mahaifina kuwa ba yabo ba fallasa, ba haka yaso ba wai kanin miji yafi mijin kyau. Bashi da zabi tunda matarsa sai yadda tayi dashi, jikinsa yayi sanyi kalau dan yasan ba'a yin haka a addininsa na da, mace ta haihu a titi ba tare da anyi mata aure ba. Mahaifiyata ta kwallawa Tabita kira tazo ta dauki dan Jaririn da lubgin kayan da Mahaifinsa ya sayo mana kala-kala ta ce a kawo min. Nayi farin ciki da kayan Jarirai *yan waje dan daman yana fama da rashin kaya, bayansu kuwa duk sauran basu burgeni ba. Leshinan da atanfofin basu isheni kallo ba, saidai madarar Jarirai suma ya burgeni da yayi tunani ya siyo, dan kuwa yasan yaron ba uwa gareshi ba balle yasha nono. Haka na kasance kukan dare daban, na rana daban, na yamma daban. Ko gidanmu bana son shiga ina nan nane da Mama Tabita, ita kadai ta rage mun mai kwantar mun da hankali ta bani hakuri idan ina kuka, ta tausaya mun halinda nake ciki. Na kanyi kuka na musamman idan na tuna babban rashin da nayi na Hamma Huzaifa, ina tsananin jin takaicin ya tafi da bakin cikina a ransa, na ganina da jariri ba tare da na wayar masa da kai ba cewar ba dana bane, kuma fadan da yake mun, naji fadan ban taba aikata zina ba. Huzaifa ne abokin hirata mai kokarin amsa min tambayoyi, mai kaifin basirar yanke mun kyakkyawan hukuncin duk wata matsala data dameni. Allah baya barin wani dan wani. Ya daukemun Huzaifa. Iman tayi shiru tsabar yin kuka tayi magana ta gaji, gashi babu koshi a tare da ita. Suhaif ya aika wani gida kusa da inda suke ya ce a debo mata ruwa ta sha. Idanuwanta sunyi luhu-luhu tasha kuka ta godewa Allah. Abun tausayi, da aka kawo mata ruwa kurba daya tayi da kyar ta hadiye saboda tsananin rayuwar da ta shiga. Suhaif yayi-yayi ta sake shan ruwan ta ce ba zata iya shaba, ta dauki lokaci mai dan tsawo kafin ta sake cewa wani abu. Ta ci gaba da cewa "A tunanina iya sanina bana zaton akwai yarinya mai irin shekaruna, da ta taba shiga irin kuncin rayuwar dana shisshiga. Amma na sa a raina Allah Ya na sane dani kuma baya bacci. Kowanne bawa akwai yadda Allah Ya ke jarrabarsa, ni kuma ta haka Allah Ya ke jarrabata. Nasha wuya a wannan lokacin saboda kula da jaririn bana samun bacci da daddare kuma dole in bar dakin Mama Tabita saboda mijinta ranar zai kwana a gida domin wani yana canjarsa. Ni kadai a dakin da aka ware mun, tun bansan yadda zan lallashi yaro ba nar na fara sabawa, shima kuma ya saba da jagwalgwalon da nake masa har yayi shiru ya koma bacci. Yana rungume a hannuna, ni kuma ina zaune ina gyangyadi har sai na tabbatar barcin nasa yayi nisa sannan nake kwantar dashi in kwanta. Ana jimawa zai farka in sake katse baccina in bashi madara, idan yaki komawa bacci saina goya shi ina jijjigashi. Ni kadai a zaune cikin dare yayin da duk bil'adama suna bacci. Idan na gaji sai in ta kuka ni da jaririn a rasa mai lallashin wani. Kar kuce da safe zai barni inyi bacci, a'a garin Allah na wayewa zan shiga kacaniyar hada ruwan wanka Mama Tabita tayi masa, ana jimawa in dama masa madara in bashi, a jima yayi kashi, ajima yayi tunbudi, ajima inyi wankin kayansa. Haka dai muka kasance babu hutu ni da Tabita kuma ga aikin gidanmu. A lokacin na sawa raina Mahaifana basa sona ko kadan don ina bukatar taimakonsu da kulawarsu basa mun, ina takaicin wannan al'amarin musamman idan naga kallon da Mahifina yake min, hankalina yana tashi kamar ba shine mai sona ba, yayi hira da ni, yayi wasa dani, yau gashi idan na gaishe shi dakyar zai amsa min a cicciki. Mahaifiyata kuwa daman can ta saba yimin haka tun ina yarinya, kullum muna rigima da ita saboda bana zuwa wajan bautarsu, ta fuskanci bana yin addininta, tayi dukan tayi zagin ta gaji. Ina tsananin jin takaici idan naga Mahaifina tare da Mahaifiyata da kannena sun dunguma za su tafi wajan bauta duk ranar bauta. Nakan gigice inyi kuka saboda takaicin Mahaifina ya bar addininsa na Musulunci. Babu wanda yake cemin in shirya in biyo su wajen bauta. Kamar yadda suka san Tabita da addininta nima sunsan dole da addinina daban ba nasu ba. Jaririn ya fara warwarewa yana girma watanninsa uku a duniya. Mahaifiyata tasa kanwata Rabecca ta kira ni a gidan Mama Tabita, ina yi masa wanka. Mama Tabita ta karbe shi ta ce in je kiran da ake min, ina zuwa na duka na gaishe da Mahaifiyata cikin harshen Igbo. Ta amsa a shelake ta nuna min wata katuwar jaka a makare da kaya ta ce "Ki dauki jakar nan sako ne daga Micheal ya aiko jiya da daddare hade da wasika, wasikar kuma gata na karanta, ya ce ranar asabar mai zuwa yana nan tafe da Mahaifiyarsa da *yan uwansa akan zancen aurenku. Kada ki sake bamu kunya, kada ki kuskura ki bude baki ki fadi wannan bayanin naki na rashin hankali cewar bake ce kika haifi yaron ba, daga karshe kuma kada ki sake ki fito min da wata tsirfar wani addini idan ba irin namu ba. Ni da Micheal da Mahaifinki addininmu daya don haka dole addinin da muke shi zaki bi, haka danki ma. Ranar lahadi zamu dunguma dasu Micheal dukka aje wajan bauta, saura ki ki zuwa ko kuma kije ki faki idanuwanmu ki gudo kamar yadda kika saba tun kina yarinya. Idan ki ka kunyatamu, ki ka ki auransa to fa ke da danki zamanku ya kare a gidan nan, don babu wanda ya ce ki je kiyi ciki ki haihu dole ki aure shi ku tarkata ku tafi. Baza ki jawo mana abun kunya ba, abun fada, ana ganin girmanmu ana mana biyayya kisa girmanmu da mutucinmu ya zube a idon jama'a. Yanzu ma Allah ne Ya dubi zuciyata ya rufa mana asiri Micheal ya zo da kansa yayi zancen aure da bansan me zan fadawa mutane ba *yata ta haifi da marar uba. Jinta kawai nake amma tuntuni tasan bana cikin haiyacina nayi sharkaf da hawaye. Wata uwar tsawa da ta daka min ina tsugune sai da ni mike tsaye ta ce "Kukan me kike yi? Rufe min baki ko in tashi in tattakaki. Mama Tabita ce ta katsemu ta shigo da gudu a gigice dauke da Jaririn a hannunta, zanin jikinta ya fadi a hanya bata sani ba, daga ita sai dan siket da riga. Karkarwa take ta nufo wajen da Mahaifiyata ke zaune tana cewa "Madam ki taimakamin ina sawa yaro riga idanuwansa sun kakkafe sama, babu numfashi, babu motsi. Subhanallahi! Irin bugun da zuciyata tayi a lokacin inda yazo da karar kwana, zuciyata ta fashe na fadi na mutu. Na karaso da gudu na karbe shi ina jijjigashi hakika ko ba'a fadamin ba nasan yaron ya rasu. Mahaifiyata ta gigice gaba dayanmu ihu muke. Mahaifina na kwance a dakinsa yayi wuf ya fito, ya karbi yaron ya jujjuya, sai ya girgiza kai alamar babu. Nayi kuka nayi kururuwa, babu lallashin da basu yimin ba naki yin shiru. Na rike yaron tsam a hannuna, suka yi juyin duniyar nan su karbe shi naki basu. Abun mamaki sai suka ga na sabashi a baya. Suka tambayeni ina zanje cikin kuka na ce "Asibiti Mama Tabita ta rikeni tana cewa ya mutu me za'ayi miki a asibiti, na fisge na shiga dakina da gudu na dauko jakata na fito, kuka nake, tana rokona in hakura in sauke dan, idan mutum ya mutu babu abin da *yan asibiti zasu iya yi. Na ki fur nace ni dai asibiti zan kai shi. Mahaifiyata ta ce da Tabita ta barni inje asibitin in na je ma zan dawo, likitoci suna farfado da matacce ne? Haukar banza da yarinta, manya sun fadamin ya mutu ni na san mutuwa ne da zance asibiti zani. Mahaifina yana ta kwallamin kira na fice da gudu na nufi titi ina kururuwar kuka tamkar tababbiya. *Yan unguwarmu suka firfito suna tambaya "Meya sami Pretty? Aka sanar musu dana ne ya mutu na goya shi na ce asibiti zan kai shi. Sai suyi dariya suce "Yarinta ke damuna ban san mutuwa ba ne, lallai da ban je asibiti ba. Na hau dan achaba ina karkarwa na ce ya kaini asibiti. Daidai get din shiga asibiti naji yaron yana tamin mutsu-mutsu a baya, wani dadi marar misaltuwa ya lullubeni, nan da nan na cewa dan acaba ya sauke ni a nan. Yana tsayawa na diro da sauri daga kan babur na kwance goyon da sauri yayin da nayi ajiyar zuciya gami da ambaton alhamdulillahi a lokacin da nayi ido hudu da dan jaririna. Saboda tsabar gigicewa gami da jin dadi, mantawa nayi ban biya mai achaba kudin babur dinsa ba, na ruga cikin asibitin da gudu. Ina shiga ba tare da na yanki kati ba, haka ba tare da na tuna ana bin layin ganin likita ba, haka na tsallake dandazon matan dana iske a zaune akan bencina suna bin layin ganin likita, sai kawai na tsallakesu na rufta dakin likita, kowa ya bude baki yana kallona cike da mamaki. Ma'aikaciyar jinya (nurse) din dake aiki tare da likitan ta biyoni cikin dakin da sauri tana tambayata "Ke baiwar Allah lafiya kika zo kika iske mutane a layi, wasu a ciki suna ganin likita kika shigo? Nayi guru-guru da ido in kalleta in kalli likita in kalli matan dana iske a gaban teburin likita yana dubasu. Haka shima likita ya zura min ido gaba dayansu suna sauraran bayanin da zai fito daga bakina. Nurs din ta sake tambayata "Ina katinki na ganin likita ko shima baki je kin yanka ba? Na gyada kai alamar eh ban yanka ba. Sai haushina ya rufeta ta hau fada tana cewa in fito kar in bata musu lokaci in likita zan gani inje in yanki kati in bi layi irin na kowa, akwai mutane a gabana saman da talatin. Na rushe da kuka ina rokarsa ya taimakeni yarona suma yake yi yanzu ya farfado. Cike da tausayi likitan ya dubeni sai ya cewa nurse din ta rabu da ni bari ya dubani bata ganin ni yarinya ce watakila bansan yadda ake yi ba. Nurse ta fita ta jawo mana kofar ta rufe. Ya juya ya dubi matan guda biyu da suke zazzaune a kujerun dake gaban teburinsa suma rungume da yaransu ya ce suyi hakuri bari ya duba min yaron. Ya mika hannu ya karbeshi ya fara duba shi yana bude bakinsa, hancinsa, cikinsa da kirjinsa, ya zabura ya mike da sauri ya nufi kan wani gado dake ofishin na kwantar da mara lafiya domin dubawa. Na ji gabana ya fadi na dafa kirji cike da fargaba nake tambayar likita "Meke damunsa? Bai bani amsa ba yaci gaba da aikinsa. Ya dauko wani abun gwaje-gwaje yana auna numfashin yaron, ya sake daukar yaron da sauri ya nufi kofar fita, yayin da kuka ya kece min ina binsu a baya, na tabbatar akwai matsala mai yawa ganin likitan hankalinsa a tashe. Muka fito muka nufi wani daki. "Malama me kike nufi ne kin ruga da gudu baki biyani kudin achabana ba? Dan achabar da ya kawo ni ne yake tambayata a cikin kakkausar murya. Na juya inda sautin maganar ke fitowa naga dan achaban ne ransa a bace. Hannuna yana rawa na bude jakata na dauko naira ashirin na mika masa gami da bashi hakuri na ce mantawa nayi. Na sake runtumawa da gudu na bi bayan likita a lokacin harya shiga dakin. Muna shiga likitan ya cirewa yaron kayansa, ya daga kafafuwansa sama kansa a kasa yana jijjiga shi, yayin da yaron ya shide yana kuka, amai ya fara diddikowa ta hanci ta baki, ya mayar da yaron ya kwanta ya kafa masa wani inji mai doguwar roba ya sakala masa ta hanci da baki. Kukan da nake ina tambayar likita meya same shi? Ya tunzura likitan yayi fushi ya ce in fita waje in jira na barshi yayi aikinsa. Me zaku ce game da Member 2 da suke son zama Admin a wannan page? Na daya zai dinga rubuta littafin SHAFI'U DAUDA GIWA Na biyu shi kuwa WA'AZANTARWA zai dinga yi Ya kuka gani? Kuma me zaku ce? ________________ YARENA ADDININA. ___CI GABAN LABARI Na fito bakin kofar dakin na tsaya ko ban fada ba kowa yasan ina cikin tashin hankali. Ina son Jaririn Harriet tamkar dan da na haifa a cikina. Ina tsoron halin da zan shiga idan aka ce min ya mutu. Fitowar likitan ya katse kukan da nake. Ya ce in shigo dakin, ya fara min bayanin abun da yake damun yaron ya ce "Yaron baya samun kulawa, ma'ana ana bashi madara ko nono ba tare da ana tallafo kansa ba, a kwance ake bashi yadda zai zuraro ta hancinsa ya kware. Haka kuma bayan ya sha ba'a dagashi akan kafada har sai yayi gatsa, sai a barshi a kwance har nonon ya gargara yabi ta wajan da yake shakar iska. Sannan ana bari yana shakar sabulu idan an zo yi masa wanka. Sune suka taru suka hana shi numfashi badan anyi saurin kawo shi asibiti ba an zuke masa, gaskiya daya rasa ransa. Na sulale na zauna kan wata kujera ina rusa kuka, ya dube ni sosai sai ya ce "Danki ne? Na gyada kai alamar eh. Ya girgiza kai ya ce "Fada min gaskiya ba ke kika haifi dan nan ba, ina Mahaifiyarsa? Dole ki fada min gaskiya don kar a sake samun irin wannan matsalar. Saboda rayuwar yaron tana cikin hatsari dole in yi magana da Mahaifiyarsa idan ma yara irinki take barwa danta to ta daina. Cikin sheshekar kuka na ce "Mahaifiyarsa ta mutu. Ya ce "To wacece take rike da shi? Nayi shiru can na ce "Ni ce cike da mamaki ya tambayeni "Ke ce? Ina Mahaifiyarki? Na ce tana gida. Ya ce "Lallai-lallai ina son in yi magana da ita ko wani babba ba ke ba. Na goge hawaye na ce "To bari inje in kirasu. Ya ce "Yauwa gara kije ki kirasu in yi magana da wani babba. Na ce "Zan iya tafiya da shi? Ya ce "Ki dauke shi ai nagama yi masa abunda zanyi masa ya samu sauki Insha Allah. Na saka masa rigarsa da wandonsa, sai tsotsar hannu yake da alama yunwa yake ji, na goya shi. Na bude jakata zan dauko kudi in biya likita, sai naga wayam babu ashe ashirin din dana bawa mai babur din nan ita kenan. A zatona da kudi a cikin jakar sai nayi kasake ina dogon tunani, san nan na tuna ashe na kashe kudin shekaran jiya tsabar rudewa tasa na manta. Na ci gaba da binciken Jakata ina zulumin yau me zan cewa likitan nan, bani da kudin da zan biya shi wannan uban aikin da yayi min, sai na ji na lalubo sarkata ta gwal a cikin aljihun jakata na laluba kunnena na ji dankunnen sarkar a kunnena, zoben a yatsana da awarwaron gwal guda biyu a hannuna. Naga sarkar babbace sosai bazan iya bashi ba, awarwarayen ma sunyi girma sai nayi tunani in cire *yan kunnayen da zoben in bashi matsayin kudin aikinsa tunda bani da kudi. Shi dai yana tsaye yana kallona, na cire *yan kunnaye da zoben na dubeshi na dukar da kai kasa cikin ladabi da fargaba na ce "Likita na duba jakata ashe ban taho da kudi ba, ga dan kunnena da zobena na gwal ka karba a madadin kudin aikinka. Sai naji ya bushe da dariya ya ce "*Yan mata yaya sunanki? Na amsa masa cike da fargaba "Sunana Fatima. "Fatima, Fatima is a nice name, I like this name, Fatima is my Mother's name. Na ce "Na gode, ya ce "Fatima me yasa kikayi tunani bari ki bani gwal dinki a madadin kudin aikina, baki yi tunanin zan iya yi miki kyauta ba? Nayi murmushin karfin hali. Yaci gaba da cewa "Saka dan kunnanki da zobanki, karki damu nayi miki komai kyauta sai dai kamar yadda kika yi alkawarin zaki je ki kira wata babba ku zo tare ina jiranku kafin nan zuwa lokacin da zan tashi. Ina fatan zaku zo? Na amsa masa da "Eh yanzu zan je in kirata. Ya sake dubana cike da murmushi ya ce "Fatima zaki gaya min gaskiya game da jaririn nan, da inda kika samo shi? Domin kinyi kankanta ace danki ne wannan, baki yi kama da wacce ta haihu ba. Kiyi min alkawari zaki fada min komai harda sauran tarihin rayuwarki? Na amsa masa da "Eh nayi alkawari. Maganarsa ta karshe ita ce "Thank you very much my dear. Yayin daya ci gaba da kallona yana murmushi, na sunkuyar da kai kasa na fara tafiya, shi kuma ya fito bakin kofar dakin yana kallona ina tafiya. Kamar daga sama naji an kira sunana na tsaya cak na waiga sai naga likitan ne yake kirana. Na juya na dawo inda yake a tsaye. Yayi min murmushi wanda ko bai min bayani ba nasan ma'anar murmushin. Wannan karon cikin harshen Fulatanci ba Hausa ba da Turancin da muke nagana tun dazu, ya ce "Baki tambayeni sunana ba. Nima cikin harshen na ce "To yaya sunanka? Ya ce "Dr. Hani. Nayi murmushi mai wuyar fita na ce "Dr. Hani na gode. Na juya naci gaba da tafiya bai bar wajen ba har sai da ya daina hango ni na fita daga get din asibitin. Ina fita na kalli gabas da yamma, kudu da arewa bansan ta ina zan fara ba, ina zan dosa? Meye abun yi? Ina mafita? Na farko bani da kudin achabar da zan koma gida, na biyu babu yadda za'ayi in je in kirawa Dr. Hani Mahaifiyata yayi mata bayani akan matsalar yarona, don ita kanta taki tsayawa taji gaskiyar al'amari akan yaron, haka daga ranar data gasgata bani nahaifi yaron nan ba to lallai dole in mayar da shi inda na dauko shi, ni kuma ina sonsa kamar raina. Don haka Dr. Hani zai tsufa yana jirana ba zai ganni ba. Sai babbar matsalata ta uku zancen aurena da Micheal da ya karato, ana zancan sati mai zuwa za'a zo da danginsa a zauna akan maganar auran. Sai naji zuciyata ta cushe na rasa me yake min dadi. Sai na rushe da kuka ina tafiya ina kuka. Na yanki hanyar cikin gari ba unguwar mu ba, bansan in da na nufa ba. Nayi tafiya na gaji likis yaron dake bayana ya gaji da tsotsar hannun, ya gaji da mutsu-mutsu yunwar da ta fara masa illa. Sai ya fara rusa kuka tamkar an zuba masa ruwan zafi. Da sauri na karasa gindin wata bishiya mai inuwa mai sanyi, na kwanto goyon na zauna a karkashin bishiyar na fara jijjigashi. Baya jin lallashin da nake yi masa tamkar tunzura shi nake, shi dai kawai nono ko madara yake lalube. Dole yaji yunwa tun madarar sassafe da na bashi da karfe shida da rabi, har yanzu karfe sha biyun rana. Na rasa abinda yake damuna, na rasa yadda zanyi. Yara *yan makarantar Islamiyya ne suke wucewa an tasosu. Yara kanana guda biyu *yan gida daya mace da namiji, macence babba *yar kimanin shekaru shidda, kaninta dan kimanin shekaru hudu, masu kama daya suka tsaya suna kallon Jaririna yana tsala kuka. Cikin gigicewa da harshen Fulatansi na ce dasu "Kuzo ku yiwa kaninku wasa. Yaran dama haka suke so in ce, sai suka karaso inda nake suka fara yi masa wasa suna shafa kumatunsa. Cikin ikon Allah sai ya fara tsagaitawa da kukan yana kallon yara *yan uwansa. Macen ta ce "Ki bashi nono mana. Nayi murmushi na ce "Yasha nono yanzu. Sai karamin yaron ya ce "Ki bashi ruwa ya sha sai na ce "Bani da ruwa. Ya ce "Ga fanfo nan kusa dake. Ya nuna min gefena. Farin ciki ya kamani na tashi da sauri naje na bude fanfo ina debo ruwa a hannuna ina tarfa masa a baki, sai sha yake kamar wanda ya kai azumi. Yaron ya zo inda nake ya miko min kofin robar ruwansa dake rataye a kafadarsa ya ce "Ga shi ki bashi da kofina. Na karbe cike da murna na ce "Yauwa kana son kanin nan naka ko? Na tari ruwa, na tallafo kansa sosai don karya kware, kamar yadda likita ya kwatantamin na bashi ruwa yasha da yawa. Nima kishir ruwar nake ji, na sha ruwan yayi kofi uku sannan na bashi dan kofinsa. Muka dawo muka zauna a gindin bishiyar tare da yaran suna ta yiwa Jaririna wasa. Ya fara dariya da alama daman kishir ruwan yafi damunsa, da ya sha ruwan sai ya manta da yunwar. Iska mai sanyi tana kadamu. Na dubi yaran na ce "Yaya sunanku? Babbar ta ce "Sunana Aisha, kanina kuma Abubakar sunansa. Na tambayesu ina gidan ku? Sai suka nuna min da hannu babu nisa da inda muke zaune. Gida ne lafiyayye na zamani, an zagaye gidan da kayatattun faulawowi da bishiyoyi, ba a zagaye da katanga ba ko waya. Farfajiyar gidan abude take har kofar da zata kaika falonsu. Naci gaba da tambayarsu ina babansu da Mamansu? Suka bani amsa, "Mamar su ta tafi Islamiyya itama, Babansu ya tafi aiki. Na tambayesu suna da yayye ko kanne? Suka ce su biyu ne kawai a gidansu. Na tambayesu ko suna makarantar boko? Suka ce eh suna zuwa, hutu suke yi yanzu. Daga nan nayi shiru, na shiga yiwa Jaririna sha'awar dama ace shine su Abubakar da uwarsu da ubansu, suje makarantar Islamiyya su je ta boko gata kan gata. Sai hawaye ya sirnano min ina fargaba ina tausayin yadda rayuwarmu zata kasance ni da shi. Kamar daga sama Aisha ta katse tunanin da na ke ta ce "Aunty yaya sunan danki? Nayi duuum na ce "Sunansa Muhammad. Sai suka fara yi masa waka da fulatanci ta yabon Annabi Muhammad (S.A.W) wakar mai dadi, nayi shiru ina sauraransu. Kwatsam naji wani tunani ya fadomin a cikin zuciyata wanda ni kadai sai dana firgita. Zuciyata ta ce "Fatima mai zai hana ki kai yaron nan gidan su yaran nan ki ajiyeshi ki gudu ki barshi, ya girma ya tashi a Musulmai cikin gata. Idan baki kaishi inda zai tashi a Musulmi ba daga karshe dole Micheal zai dauki dansa ya tafi da shi ya tashi a tsakiyar arna cikin *yan fashi, kilama ya gaji ubansa ya tashi ya zama gawurtaccen dan fashi. Sai naji na hau karkarwa hankalina ya kara tashi yaya za'ayi in ajiye yaro in tafi, ai bazan iya rayuwa babu shi ba. Na sake yin tunani idan ban ajiyeshi ba rayuwata da rayuwar yaron tana cikin hatsari, don karshe dole mu koma hannun Micheal sai yadda Allah Ya yi damu. Kuma daman batun Musulunci kuwa babu shi. Na yi ta tunani, karshe na yanke shawarar dole mu rabu da jaririna in ajiyeshi a gidan Musulmai ya tashi a Musulmi. Tunda *yan gidanmu sun dauka ya mutu sai in barsau a ya mutun na bar gawar a asibiti za'a binne. Sannan ni kuma in yi ta kaina. Na dubi Aisha wacce tana tayi wa Jaririna wasa na ce da ita "A kwai littafi da fensir a jakarki? Ta ce "Akwai. Na ce "Bani *yar takarda in yi rubutu. Ta miko min jakar gaba daya na bude na falli tsakiyar takardar na rubuta kamar haka "Sunana MOHAMMAD. Ni Musulmi ne, ku rike ni dan Allah. Na ciro *yan kunnayena da awarwarayena da sarkata na gwal na zuba a cikin takardar na nade. Na ce da su "Kunce gidanku babu kowa yanzu ko? Suka ce "Ba kowa sai mai aikinmu Barira. Na tambayesu yarinya ce ko babba ce? Suka ce yarinya ce. Na ce "To ku tashi kuje gida nima zan tafi gida. Abubakar ya bata rai ya ce "Da Mohammad zaki tafi? Na ce "Dashi zan tafi ko in bar muku? Suka hada baki "Aunty ki bar mana Muhammad kaninmu tun da bamu da kani. Na ji dadi a raina, har na hasko Mohammad ya girma a gidan, ya tashi cikin gata ai kuwa kowa zaice kaninsu ne na jini, domin yana kama dasu farare masu dogon hanci. Na ce "To muje gidanku in ajiye muku shi kun ga kun sami dan kani. Idan Mamarku ta dawo kuce ta rikeshi, karku yadda akaishi wani wajen. Na nuna masu gwala-gwalan nan na ce "Wannan gwala-gwalan ku cewa Mamarku ta siyar ta dinga siyawa Mohammad madara yana sha tunda Mamarsa ta mutu, ni ba Mamarsa ba ce babu mai bashi nono. Suna tsalle suna murna suka amsamin to to. Muka dunguma muka tafi gidansu. Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, na dinga waige-waige kar wani ya ganni ina ta zare ido ina fargaba. Muka isa kofar falonsu, zasu kwan kwasa na ce karsu kwan-kwasa mu zauna akan barandar mu huta kafin Mamarsu ta dawo daga Makaranta. Suka shaida mun mai aikinsu tana ciki ita kadai tana bacci, daman yawanci idan sun taso sai suyi ta bugun duniyar nan bata jiba har sai Mamarsu ta dawo ta iske su anan, sannan ta zagaya ta kwalla mata kira ta wundon dakinta. Na ce "Ba komai yanzu ma su bari idan Mamarsu ta dawo sai su shiga ciki. Na dan taya su zama cike da fargaba suna min hira bana fahimtar me suke cewa, na rungume jaririna tsam. Wani kuka mai radadi ya keto min babu yadda na iya na kwantar da shi a gabansu suna yi masa wasa, na dauko takardar da na rubuta sunansa na nade gwalagwalan nan nawa na ajiye a gefensa cikin zanin goyansa, ya tsaya yana kallona kamar yasan rabuwa zamu yi. Ni ma na dade ina kallansa, nayi karfin hali nayi masa wasa, sai kuwa yayi min dariya ni kuwa na fashe da kuka. Aisha da Abubakar suka hau murna suna cewa "Lah yana dariya, ba tare da sun kula da kukan da nake sharba ba. Na juya zan tafi Abubakar ya ce "Kin bar mana shi da gaske? Na ce "Na bar mu ku shi. Ba kunce kuna son kani ba? Suka hau murna da tsalle. Na juya na tafi ba tare da na iya sake waiwayowa ba. Na koma gindin bishiyar da muka zauna dazu, na kalli gabas da yamma naga babu kowa caraf na haye kan bishiyar nayi luf a cikin ganye ina hango abinda zai faru ga jaririna. Ba dadewa na hango Mahaifiyarsu Abubakar ta dawo daga Islamiyya a motarta. Shigarta ba dadewa naga ta fito ta kira wani saurayi tayi masa magana. Saurayin a gigice cikin sauri ya zo ya wuce ta gabana ya nufi makarantar Islamiyyar su Abubakar da Aisha da yake babu nisa. Ba jimawa sai ga saurayin da manyan dattijai da alama Malaman makarantar Islamiyyar ne da Limamin Masallacin unguwar da *yan unguwa masu salla a masallacin da yake jikin Islamiyyar ya kirasu ya shaida musu abun dana aikata na an tsinci Jariri. Suka zo suka wuce ta karkashin bishiyar dana labe ba tare da sun ganni ba, ina hangensu sun zagayeshi ana ta mamaki da shawarwari. Musamman ganin gwal din nan, sun tabbatar ba talauci bane, ko cikin shege yasa aka yasar da yaron. Uwa uba ga sunan yaron an rubuta har an kara da cewa Musulmi ne ku rikeni dan Allah. Sai suka kawar da zancen a kai shi gidan marayu ba a san baiwar da Allah Ya yi masa ba, gara a sami wani ya rike shi a cikin su, nan dai aka yi ta fafata shawarwari. Mahaifiyar Aisha aka tambaya ko tana so ta rike tunda a kofar gidanta aka tsinta? Ta ce "A'a baza ta rike ba, bata san ko wanne irin da ba ne. Jama'a da yawa suna so su dauka watakila kwadayin gwal ne, ko kuma da man suna son da ne ban sani ba. Wani dattijan Malami shike rungume da Mohammad suka ce su tafi dashi Masallaci aci gaba da shawara. Sun juya zasu tafi sai Aisha da Abubakar suka ce basu san zance ba, kaninsu ne, su aka bawa kuma Mamar Jaririn ta ce ya zauna a gidansu ta basu shi. Haka suke ihu suna birgima ba za'a tafi dashi ba. Hankalin Mahaifiyarsu ya tashi sosai ta shiga kokwanto, ta yi lallashin duniyar nan yara suka ki sun tubure, daga karshe ta musu duka amma basu hakura ba, suka bi wadanda zasu tafi da Mohammad da gudu suna cewa a dawo musu da kaninsu. Dai-dai karkashin biyar da nake, nan suka sake tsayawa suna shawara, Mahaifiyar su Abubakar ta ce kar ayi saurin yanke hukunci inda za'a kai yaron ayi mata hakuri zuwa yamma mai gidanta ya dawo, ta tambayeshi idan ya yarda sai ta karbi dan ta rike, saboda Allah kadai Ya san dalilin da yasa aka wuce kowanne gida aka ajiye mata a kofar gidanta, ga yaranta suna sonsa. A haka aka tsayar da shawara, ta ja hannun yaranta suka nufi gida. Su kuma dattijai suka tafi da yaron Masallaci. Aisha da Abubakar suna rafsa kuka suna kiran Muhammad dinmu. Ina kan bishiya ina rafsa kuka ina "Nuhammad dina. Yanzu na rabu da kai har abada kenan? Na yi fiye da awa biyu a zaune ban sake jin motsin kowa ba. Na sauko daga kan bishiyar na nufi Masallaci don in ga halin da yake ciki, ina ta zagaye ina leke-leke, babu alamar yaro ko zancen yaro duk wadanda suke ciki ibadarsu suke. A kayi sallar la'asar, aka kira Magruba ina ta kai kawo a wajen. Na dawo kusa da gidan su Aisha inga ko Mahaifinsu ya dawo inji hukuncin da aka yanke, sai na iske ya dawo, ya dauro alwala ya zo ya wuce ni ya shiga Masallaci suka yi sallar magaruba ya fito ya nufi gidansa babu wanda ya tsayar dashi yayi masa zancen an tsinci Jariri a kofar gidanka, haka bai tambayi kowa ba ina Jaririn da aka tsinta dazu a gidana, ya shigewarsa gidansa ya mayar da kofa ya rufe. Gari yayi duhu kirin, kowa na gidansa sai mutane kadan a Masallaci, in takaice muku ina wajan akayi sallar Isha'i, aka gama karatu aka rufe Masallaci kowa ya kama gabansa, babu zancen dana. Nayi kuka har na gaji, hankalina ya tashi dan ban san halin da yake ciki ba, nayi dana sanin ajiye shi, haka na kama hanyar gidanmu da kafa, ga uban nisa ga kishir ruwa da yunwa da tashi hankali. Allah Ya tsaremu daga shiga kuncin rayuwa, wadan da suke ciki Allah Ya fitar da su da girman zatinSa da ikonSa. Ameen. Reedwan Suraj Isma'il *************** YAREANA ADDININA ___CIGABAN LABARI Na isa gidanmu da misalin karfe tara na dare, ina shiga na dora hannu aka na kurma kukan mutuwa a falonmu. Mama Tabita da Mahaifiyata suna kicin suka fito da gudu, Mahaifina da ya tafi nemana asibitoci kala-kala sai yanzu ya dawo a gajiye. Suka taru akaina suna tambayata lafiya? Cikin kuka na shaida musu Jaririna ya mutu an binne shi a asibiti. Daga dukkan alamu sun tausaya min su duka, suna bani baki inyi hakuri dama sun gaya min ya mutu na dauki gawa na kai asibiti. Ban daina kuka ba kamar zuga ni ma suke yi. Dole Mahaifiyata ta zaunar dani ta zuba min abinci da ruwa ta ce sai naci. Ci nake amma ban san dandanon abincin ba tamkar dusa nake cusawa ba abinci ba. Ranar Mahaifiyata ta nutsu ta tsaya tayi min nasiha a tsanake yadda rayuwa take, ta ce kada in kuskura in sake bari rayuwa ta subuce min in shiga halin kakanikayi da nadama. Amma daga karshe ta fara cusa min addininta da aurena da Micheal. In da na dauke hankali daga sauraron abunda take cewa dan ba zai yuba. Sai a lokacin Mahaifina ya sa baki ya ce "Tunda danta ya mutu ai kuwa babu zancan auranta da Micheal, babu mai yiwa *yar sa aure tana da shekaru goma sha biyar. Sabon Adimission zai samar min in fara karatu. Ita kuwa Mahaifiyata bata yadda ba wai dole in auri Micheal sai inyi karatu a gidansa. Nan fa ta mike ta fara zuba masifa da yare kala-kala, duk hakurin Mahaifina bai cike biye mata ba idan tana fada irin wannan, amma yau ya biye mata har ma ya fita bugun kirji da jajircewa yana nan akan bakarsa babu mai yiwa *yarsa aure karatu zata yi. Kamar zasu tsagamin kunne saboda daga murya. Na tashi dakyar saboda tsananin ciwan kai da damuwar dake damuna, na shiga dakina na zube kan katifa sharaf. Tunda na kwanta ban sake farkawa ba haka ban sake jin ko kalma daya ba ta maganganun da suke don haka nake tunanin ba barci nayi ba sai dai idan suma nayi, domin yafi barci nauyi. Ban farka ba sai sanda agogon dakina ya buga karfe ukun dare daidai. Nayi karfin hali zan tashi zaune sai na koma yaraf na kwanta. A lokacin wani barci mai nauyi ya daukeni na dora da wani mafarki wanda ban taba yin irinsa ba. Mafarki nayi na ganni a wani gari, mutanen garin gaba dayansu suna sanye da hijabai a jikinsu. Sahun sallah sahu-sahu anata sallah, wasu kuma suna karatun kur'ani. Ina tsaye ina kallonsu, a mafarkin sai wata mata ta saka min hijab ta ce "Fatima shigo cikinmu muyi sallah, mu karanta littafi mai tsarki sai muyi addu'a Allah Ya yaye miki bakin cikin dake damun ki. Sai na ganni tare dasu muna salla, ban iya karatun kur'ani ba sai karatun salla kadai, amma a mafarkin na ganni ina karatun kur'ani babu gargada manyan surori nake ja. Dai-dai nan na farka daga barci, a lokacin ana kiran sallar asuba. Na bude ido na tabbatar mafarki nake, nayi farat na tashi zaune naji jikina yayi karfi. Na daina ciwan kai, zuciyata tayi fari tas. Na tsinci kaina ina farin ciki, babu abinda ya lullube min zuciya sai in tashi in tafi neman wannan gari da ake addinin Musulunci, in nemo ilimi in tsayar da Sallah da azumi. Na yankewa kaina hukuncin gara in raba rigima tsakanin uwata da ubana in bar garin, tunda haka rayuwata ta kasance, bani da sha'awar karatu a rayuwata ba zan iya ba, ganin yadda ta kasance daga zuwana Jami'a, kawayena sun rasa rayuwarsu, nima kuma na fada hatsari da masifa kala-kala. A sanadiyyar karatu aka samu yaron da bai san komai ba ya zo ya fada maraici da rashin gata ga rashin asali. Na fada a baiyane bazan auri Micheal ba, bazan tafi jami'a ba. Ba aure, ba karatu, dole ba zaman gidanmu. Kuma idan na zauna a gidanmu bani babu addinin Musulunci. Zuciyata ta ce min "Tashi maza-maza shirya ki gudu ki bi hanya madaidaiciya. Nayi wuf na mike daga kan shimfidata na nufi bandaki da sauri na dauro alwala na rufe kofar dakina, na gyara labulayen wundo, na kashe fitilar dakin kada wani ya zo ya riske ni ina salla. Na dinga jero sallolin da banyi ba jiya na ramasu kakaf, na idar nayi addu'a sosai akan Allah Yasa karshen damuwata ce tazo barina gaban Iyayena. Na shiga bandaki nayi wanka na wanke bakina da brush, na hada sosona da brush dina a leda na daure na fito da su. Na dauko jakar zuba kayana na saka a ciki. Na zabi kaya kala uku atamfofi na zuba a jakar. Sannan na saka wani leshi pink sai dai matsalar bani da gyale babba bare hijab da zan saka in saje da Musulmai a garin Musulunci. Salla ma dakyar na harhada kananan Mayafaina nayi. Babu komai idan naje can zan samu in siya insa. Af na manta, nan fa matsalar take da na tuna bani da kudin motar barin garin. Amma sai na tuna akwai wata tsohuwar sarkata ta gwal da ta tsinke tuntuni dan kunne daya ya fadi, Mahaifiyata ta ce in ajiye zata karba ta canzo min wata. Na lalubota cikin akwatina da warin dan kunnanta, na saka a jakar kayan tafiya. Na dauko biro da takarda guda biyu na zauna na fara rubuta wasiku, daya ta Maman daya kuma zuwa ga Babana. Na basu hakuri kuma na nemi gafarar su yafe min. Na shaidawa Mahaifiyata tayi hakuri ni Musulma ce bana bin addininta yanzu haka na tafi neman ilimin addinin Musulunci. Na bata labarin rayuwata da su Harriet da yadda aka yi na samu jaririn, amma ban fada mata jaririn bai mutu ba, nace idan Micheal ya zo su fada masa jaririnsa ya mutu. Na shaidawa Mahaifina yayi kuskure babba da ya bar addininsa na Musulunci addini gaskiya. Don haka bazan iya zama da su ba, na tafi wajen *yan uwana Musulmu. Na rokesu da kada su damu kansu su wahalar da kansu su bazama nemana, baza su iya gano inda nake ba don taka maimai nima kaina bansan garin da zan nufa ba, mai yiwuwa ma in bar kasar gaba daya. Bazan fada hannun halaka ba ko mugaye, ko karuwanci tunda Allah Yasan zuciyata da izininsa zai kareni. Na ce su kara hakuri da rashina nima ina cikin tsananin bakin ciki da takaicin rabuwa da su, da kuma kannene dole ce tasa zan tafi don ba yadda zanyi. Ina gama rubuta wasikun sai kuka ya kece min. Na jera wasikun akan katifata a bude yadda suna shigowa zasu gani. Jikina yana karkarwa na yafa dan karamin gyale na rufe jakar kayana na rataya na fito gami da tura kofar dakin na rufe kamar ina ciki na fara sanda don kar suji karar bude kofar falon, na fice na mayar da kofar falon na rufe. Misalin karfe shida na safe ne don haka garin bai gama wayewa ba. Mai gadinmu mijin Mama Tabita bai fito wajen gadi ba yana gidansa shima. Na iske get din a datse da kwado, gashi ban san inda ake ajiye mukullin ba, amma wannan ba matsalata bace duk girman bishiya da tsawon get zan haura, saboda tun ina yarinya ni da kawayena Mumuyawa mun saba hawan bishiyoyi kala-kala. Ina jefa jakata waje, sai na nade siket dina na kama get na haura. Na dauki jakata na kara gaba. Kicibus nayi da Mahaifin Hamma Huzaifa ya dawo daga Masallaci. Nan da nan na kawar da fuskata gefe na rufe da gyale don kada ya gane ni, amma yaso ya gane ni sai kallona yake har da waiwaye cike da mamaki. Na san dalilin da yasa bai tsayar dani ba, yasan babu yadda za'ayi in ce ban tsuguna na gaisheshi ba. Na wuce shi da sauri dan kada ya tona min asiri. Ina isa bakin titi na tsayar da achaba na haye, yana tambayata ina zan kaiki nace muje kawai. A hanya nake shaida masa wuraren zuwan nawa da yawa. Na farko ina so ya kaini duk inda yasan ana sayan gwal zan sayar, sai kuma ya wuce dani tashar da zan tafi wani gari. Yayi murmushi ya ce "Akwai wata Hajiya tana zuwa Saudia tana sana'ar gwal zai kaini yasan zata siya, sannan wanne gari zanje dan yasan tashar da zai kaini? Nayi shiru can na ce "Garin da kasan suna Addinin Musulunci. Ya tuntsire da dariya ya ce "Lallai yarinya nan baki ma san wanne gari zaki ba, ko dai guduwa zaki yi daga gidan Iyayenki, ko gidan mijinki? Nayi caraf na ce "Na yi maka kama da mai guduwa ne? Kawai tambayarka nayi don inji yadda nake zato din gaskiya ne. Shine garin da yafi kowanne gari Musulmai. Ya nisa ya ce "Wanne gari kika dauka yafi kowanne musulmi? Na ce "Kogi state. Dan acaba ya ce "Inah ai yarinya baki canka ba Kano yafi Musulmai. KANO TA DABO TUMBIN GIWA KO DAME KAZO AN FIKA. Na maimata "Kano? Ya ce "Kwarai akwai Malamai, a kwai Makaranta addini, ga masu arziki da suke taimakawa addini da dukiyoyinsu. Ke duk *yan garin Musulmai ne sai dai bakin da suke zuwa zaka samesu da wani addini. Nayi wuf na ce "Ashe nayi gaskiya nima Kanon na nufa sai na bugi cikinka na tambayeka. Ni da shi duka muka tuntsire da dariya. Yakaini kofar gidan Hajiya mai sayar da gwal, saina kafe a bayan babur naki sauka, na ce sai dai in bashi ya shiga ciki ya sayar mun idan ta ganni yarinya zata ki saya ta ce na sata ne, shi kuwa babba ne zata siya. Bai yi musu ba ya kashe babur na debo su daga jakata na hada da zoben dake hannuna na mika masa. Ya aika yaro cikin gidan akayi masa sallama da ita suka tsaya a zaure suka yi ciniki ta shiga gida ta dauko masa kudin. Ina kallonsa bayan matar ta shiga cikin gida sai ya debi wasu kudin ya zuba a aljihunsa ya fito daga zauren ya nufo inda nake, ban nuna na ganshi ba ya mikomin kudin na karba nayi godiya. Ban damu da cutar da yayi mun ba ganin kudin cunkus ya bani. Ya buga babur muka tafi. Na sake mamaita masa "Ka kaini tashar Kano yace "An gama *yan mata. Muka isa tasha na sauko daga kan babur na dauko kudi mai yawa na bashi, ya sani, nima nasan yafi kudin aikin da yayi mun. Yana ta godiya muka yi sallama na nufi wajan motoci shi kuma ya buga babur dinsa yana mai matukar farin ciki shikam ranar kamar danshi na sayar da gwal dinnan, saboda kudin da ya samu. Nayi tambaya ina zanje in hau motar Kano? Aka nuna mun, kwarai kuwa gaskiya ne, Kano garine na Musulmai da Musulunci. Domin matan dana iske a layin yankar tikitin shiga mota sun burgeni gaba dayansu sanye suke da hijabai har kasa wasu harda abun lullube fuska wato (nikaf) nabi layi nima a bayansu. Kamar yadda naga suna yi duk wacce ta mika kudinta aka yankar mata tikiti sai ta dauki jakar kayanta ta shiga cikin zungureriyar mota. Layi yazo kaina na tambayeshi nawa ne? Ya fada mun na zaro kudin na bashi ya bani tikiti saina dauki jakata na shiga mota. Na shiga cikin mota ina ta baza ido ina neman wajan da zan zauna, kasancewar motar tana da kujerun zaman mutane bibbiyu ne a layi-layi. Kowanne layi ya cika da mutane. Hankalina ya tashi ganin zan rasa wajen zama kuma kowa abokin tafiyarsa yake tanadarwa kusa dashi, ni kuwa ni kadaice bansan kowa ba. Amma zuciyata tayi sanyi hankalina ya kwanta ganin kowacce na hada ido da ita sai tayi mun murmushi tace mun "Salamu alaikim. Na wuce can karshen motar saina iske wata mata ita kadai, koda taga na tunkaro wajenta nan da nan ta dauke jakarta ta nuna mun kusa da ita ta ce in zo in zauna. Ina zama a kusa da ita saita mikomun hannu gami da cemun "Salamu alaikim". Muka gaisa. Nayi ajiyar zuciya na ce a zuciyata "Addinin Musulunci kenan, Musulmi suna son *yan uwansu Musulmai. Mota ta cika aka rufe kofar mota, direba ya shiga ya kunna mota ya ja muka fara tafiya, yayin da hawaye ya kece mun. Matar da ta ke kusa dani ta lura da kuka nake sai ta shiga yimun tambayoyi meya sameni nake kuka? Duk ta damu ta rikice tana tambayata. Na rasa amsar da zan bata na goge hawayena na hau murmushin dole. Ta fara mun nasiha tana jawomin aya tana bani musalai da rayuwar da sahabbai suka yi, daman duniya kurkukun mumini ce sai lahira zaiji dadi dan haka duk yawancin masu holewa a duniya su sha giya, suyi zina, suyi sata, su suke jin dadin duniya lahirarsu kuwa tamkar kurkukunsu ne. Nan ma naji na karu da abunda ta fadamun na rike a zuciyata. Sai na fara tambayarta ita *yar Kano ce ko *yar Jalingo ce? Ko da yake naji ta iya Hausa sosai daga dukkan alamu *yar Kano ce. Sai ta ce mun ita *yar Kano ce aure ya kawota Jalingo, amma duk shekara tana zuwa Kano. Na sake tambayarta ganin gida take zuwa. Sai ta ce "Bama ganin gida kawai ba, kinsan wannan watan Azumi ne duk gomar karshe muna shiga Ittikafi a Masallaci har sai ranar sallah muke fitowa muna Masallaci muna ibada. Nayi shiru na kasa magana tunda bansan har an fara azumi ba an yi kusan ashirin. Sai dai duk sanda na shiga gidansu Huzaifa sai suce min suna azumi, bansan Ramadan bane koma na sani ai ba damar inyi a gidanmu. Ina mata tambayoyi tana amsamin duk yadda suke yi. Ta nuna min sauran tawagar tafiyarta ta ce haka suke yi duk shekara a Masallacin BUK old site suke zama har kwana goma suna sallah cikin dare suna addu'o'i. Nan danan na ce mata nima zan bita inje mu kwana goma. Ta dube ni cike da mamaki sai ta tambayeni "Kin fadawa iyayenki sun yadda? Na Marairaice na fara hawaye na ce "Ai ni marainiya ce, aikin wanke-wanke da shara nake a Jalingo suka koreni, shine zan taho Kano ko zan samu wani aikin. Sai naga ta kuramin ido tana min kallon kurilla daga ni har kayan jikina. Da alama taga babu wahala a tare dani, sai ta shiga wani tunani mai zurfi. Dana ga haka dan karta gane ni sai na hau tsarata yadda zata yadda da ni na ce "Sun rike ni amana a gidan aikin tamkar *yar gida tun ina karama, sun saka ni a makaranta, to tun lokacin da mai gidan ya ce yana sona matar gidan ta tsaneni ta kore ni. Nan da nan matar ta gaskata abunda nake fada mata ta ce "Eh kwarai dole ta kore ki karki aure mata miji, to Allah Ya kyauta. Ta yi shiru bata sake cewa komai ba muka ci gaba da tafiya, Jalingo da Kano akwai nisa. Duk inda muka tsaya salla sai matar ta siya mana abubuwan ciye-ciye kona roketa ta bari in siya da kudina sai ta ki. Ganin duk suna azumi nima sai in ajiye in ki ci ina jiran sai an sha ruwa. Amma ta lura bana azumi sai ta ce min "Zan iya ajiye azumin saboda ni matafiya ce bayan sallah sai na rama azumin. Na ce "A'a azumi nake nima. Sai daf da zamu shiga Kano aka kira sallar Magaruba, dukkan mu muka yi buda baki da abubuwan da muka siya. Mun isa Masallacin BUK ana kiran sallar isha'i. Mun iske mata da yawa masu zaman Ittifaki, haka wasu da yawa sun zo bayanmu. Na sha mamaki dana ga wasu harda kayan abincinsu danye da rusho din dahuwa kamar a gida. Sunan matar da muke tare da ita Maman Aisha. Tana da kirki sosai kamar yadda ya kamata, tana kaunata tamkar jininta, naji dadin zama da ita kamar yadda taji dadin zama dani. Ta bani hijab dogo har kasa haka duk wasu ayyuka da suka taso da rawar jiki zan tashi inyi bana barinta ta wanke ko cokali. Muna zaman lafiya da kowa, *yan uwa Musulmi masu neman ladan ciyarwa a cikin wannan watan mai girma na azumi suna ta tururuwar kawo abinci sadaka cikin Masallaci, don haka akwai wadatar abinci kuma idan wasu daga cikinmu suka dafa suna kiran kowa da kowa a taru aci saboda Allah. Muna yini ibada, mu kwana ibada, bayan sallolin farilla da muke bin jam'i, daga karfe sha biyun dare mata suke tururuwa su taru a Masallacinmu ana cika taf har wasu a waje saboda cika. Maza kuma a bangaransu babu mai ganin wani idan aka fara salla har asuba. Allahu Akbar! Lallai Musulmi su suke ibada tukuru da jikinsu kuma duk mulkinka da kudinka. Na sha wuya kafin in saba dare da rana sallah, ga yunwar azumi amma zuciyata a dake take na sawa raina son Musulunci, kafin kwana gomar nan harna saba na daina gajiya. Ba shakka wannan shine mafarkin da nayi, sahun sallah sahu-sahu sannan ayi karatun kur'ani. Ina nacewa Maman Amina tana biyamin karatun kur'ani na kuwa fara koya yadda ya kamata. RANAR SALLAH. !!! ALLAH YA KARA DAUKAKA MUSULUNCI DA MUSULMAI AMEEN Reedwan Suraj Isma'il *************** YAREANA ADDININA ___CIGABAN LABARI RANAR SALLAH !!! Ranar da muka kwana goma, ranar ne ake sauke azumi, ranar ne kuma ranar Sallah. Bayan Sallar Idi sai naga matan da muke tare suna harhada kayansu suna shirin tafiya. Na tambayi Maman Amina ina zasu tafi naga suna hada kaya? Sai ta sanar mun ai yau kowa zai tafi gidansa tunda azumi ya kare. Gabana ya fadi, hankalina ya tashi bani da inda zan nufa, sai jikina yayi sanyi. Maman Amina ta lura da halin da na shiga yanzun nan, sai ta fara mun tambayoyi taji ra'ayina. Ta ce min "Yau nima zan je gidan Iyayena ayi bikin sallah dani sai sati na sama in koma Jalingo. Ke fa Fatima wacce unguwa zaki tafi ne? Hawaye mai yawa ya zubo nace bani da kowa, ban san Kano ba, ban taba zuwa ba bani da dangin uwa babu na uba. Sai na rushe da kuka na fada kan cinyarta ina cewa "Maman Amina ki taimakeni. Hankalinta ya tashi, tana lallashina idonta ya cika da kwalla ta ce min, "Fatima yi shiru kada jama'a su taru kinga sun fara tambayata meya sameki zan taimakeki kamar *yar cikina, Fatima Allah ne Ya hadamu. Naji dadin maganarta sai hankalina ya fara kwanciya ta share mun hawaye ta ce "Zaki yarda ki bini gidanmu na nan Kano idan sati ya zagayo zan koma Jalingo mu tafi tare, ki zauna tare da ni da marayun *ya*yana su Amina? Nan fa daya ai bani ba komawa Jalingo, nayi shiru. Can naji ta sake ce wa "Zabi zan baki, ko kuwa kinfi son in nemar miki gidan aiki anan garin? Nayi sauri na ce "Eh ki samar min gidan aiki anan garin saboda inason garin akwai addini. Tayi murmushi ta ce "Jalingo ma akwai Musulunci sai dai kice akwai yare daban-daban da wasu addinai, ba kamar Kano ba Hausawa ne kuma Musulmai ne dukkansu. Mu duka mu kayi dariya. Wadanda muka saba suna ta zuwa inda muke muna zaune acikin Masallaci suna yi mana sallama, muna musu fatan alheri da fatan Allah Ya hadamu a wata shekarar. Muma muka tashi muka hada kayanmu Maman Amina tayiwa *yan tawagar da muka taho tare sallama cewar ita ta tafi cikin gari sai wani satin zata je Jalingo su kuwa yau zasu koma Jalingo nima nayi musu sallama muka fito. Bana barin Maman Amina ta dauki tsinke idan muna tare dan haka da jakar kayana dana kayanta na dauka muka fito get din makarantar BUK. Naga ta tsayar da tasi ta ce masa TUKUR ROAD zai kaimu. Su kayi ciniki muka shiga. Muna tafiya a hanya take sanar dani zata kaini gidan aiki ne da farko sannan ta dawo cikin gari kusa da gidan Sarkin Kano nan ne unguwar gidan Iyayenta. Ta ci gaba da yi mun bayani, ta ce gidan da zata kaini bama Hausawa bane balle ayi gutsiri tsoma da kananan maganganu. Larabawa ne, larabawan Egypt. Mace da Mijinta sai dansu guda daya. In har zan zage in yi musu aiki ba ha'inci in kular musu da dan karamin yaronsu to lallai zasu rikeni tamkar *yarsu, zanji dadi in huta, gida ne tamkar aljannar duniya. Kamar yadda ta karanci halina dan zaman da muka yi tasan babu matsala halina yana da kyau zamu dai-daita, don haka ne ma taga ya dace ta kaini can. Tana bani labarin yadda suka saba da balarabiyar, Baban Maman Amina ne ya taba yi musu aikin gadi, waccan shekarar baban ya rasu. Dan haka *yan gidansu kakaf sun saba, kuma har yau har gobe kusan su suke ciyar da gidansu Maman Amina. Kayan abinci buhu-buhu suke kaiwa gidansu, kudin cefane, kwancen kayansu na sawa da zakka. Shi yasa itama duk sanda tazo garin alkawari ne tazo ta gaishesu, duk sanda taje sai taji Balarabiyar tana jajen *yar aiki bata jin dadin yadda basa iya kula da danta. Danta guda daya, ga kuma yadda take ji dashi, shekaru goma da aure sai yanzu suka samu haihuwa. Na tambayi Maman Amina sun kauro Nigeria kenan baza su koma kasarsu ba? Ta ce mun zaiyi wuya su koma gaba daya suna dadewa ma basu je ganin gida ba. Duk harkar samun kudinsu da kasuwancin su suna nan Kano. Mijin dan kasuwa ne, matar ma ta bubbude super market da Nursiry ana karatu. Dai-dai lokacin Maman Amina ta cewa mai tasi "Nan zamu sauka. Na bude baki ina kallon kerarren gidan da ban taba arangama da irinsa ba a ido biyu. Ta biya shi kudinsa muka dunguma kofar gidan, kafin mai gadi ya bude get sai da ya liko ta windo ransa a bace zaiyi mana wulakanci ko da yaga Maman Amina ya ganeta sai ya washe baki ya ce "Sannunku da zuwa" da sauri ya wangale get muka shiga riki-riki da jakunkuna a hannuna. Muka tsaya suka gaisa da buzun mai gadin sannan muka wuce cikin gidan bayan mun keto ta lambuna da swimming pool ga ruwa yana bulbulowa ta cikin wasu duwatsu suna bawa grass carper ruwa da fulawowi. Abun tamkar a film ba a ido biyu ba. A Nigeria dai ban taba ganin irin ginin nan ba, sai dai a waje lokacin da muka je da Iyayena. Mun iske balarabiyar matar a katafaren falonta na alfarma tana kallon talabijin tashar Makka ce ana sallar azahar, ta burgeni matuka ganinta sanye da hijabi tana jan carbi a hannunta. Ta amsa sallamarmu, sai ta taso da fara'a da sauri ta tari Maman Amina gami da rungumeta ta sunbaci kumatunta, ina gefe ina kallon sabon salon gaisuwar da ban taba gani ba ina kuma sauraron yaren da ban taba jiba a sarari wato da larabci suke magana. Ban san me suke cewa ba naga Maman Amina tana magana tana nuna ni da alama dai gabatar dani take. Sai naga sun tuntsire da dariya dukkansu, Maman Amina ta juyo inda nake tsugunne ta ce mun "Na mata bayani ta ce kamar kuwa nasan tana tsakiyar neman mai raino. Ta ce kinyi mata dari bisa dari, kinga ko bata nan danta zai ganki kamar ita saboda kema kinyi kama dasu Larabawa, wai kamarku daya anya ke ba balarabiya ba ce? Sai nima nayi dariya, suna Magana Maman Amina tana fassara mun. Matar ta zano dokokin gidan, da abun da zanyi da wanda zan kiyaye. Tana ta maimaita mun in kular mata danta sosai shine burinta. Sannan nawa zata dinga biyana a wata? Nayi caraf na ce "Bana bukatar ko kwabo fata na su rikeni amana kuma su sani a makarantar Islamiyya har in sauke alkur'ani shine burina. Da Maman Amina ta fada mata abinda nace sai ta bude baki tana mamaki. Tace in matso kusa da ita ta mikamin hannu muka gaisa tana larabci tana shafamun kai, Maman Amina na fassara mun abunda take cewa, bata taba ganin yarinya mai hankali wacce ta rike maraicinta ba irina, nayi tunani mai kyau kudi bai kai ilimi muhimmanci ba. Tayi alkawari zata kaini Makarantar Islamiyyar da take yi, ta *yan kasar su ce larabawa ne ziryan a makarantar. Da yamma ake zuwa Makarantar kullum banda alhamis da juma'a ranar asabar da lahadi ayi da safe. Akwai ajujuwan yara, manya tsofaffi, maza da mata, ana biyan kudi da yawa saboda kwararrun Malamai, tayi alkawari zata biya mun har in sauke kur'ani. Naji dadi sosai nayi ta godiya sai ta fada min sunanta Naila, sunan mijinta Abdul-Samad danta kuwa Abdul-Malik. Ta tambayeni sunana na ce mata sunana Fatima, sai ta rike kai ta ce babban suna ne a wajenta ba zata iya kiran sunan ba. Sunan Mahaifiyarta ne kuma sunan uwar mijinta ne zata dinga kirana da IMAN to daga nan na samo asalin suna Iman. Anan gidan na zauna tare da Mummy Naila zaman jin dadi da kwanciyar hankali. Idan kuka ga dakina a gidan tamkar dakin *yar shugaban kasa da ban dakina a ciki. Na saba da danta Abdul-Malik shima ya saba dani har yakan ki zuwa wajen Mahaifiyarsa da Mahaifinsa sai ni kawai. Aikina shi ne kula da Abdul-Malik kawai dan haka na zage ba rana ba dare ina kula da shi matuka ko Mahaifiyarsa sai haka. Shekarunsa biyu kacal a lokacin amma dakinsa daban shima an zuba masa kayan wasan yara kala-kala ba ya iya rabuwa dani, ko Mahaifiyarsa ta ce in kai shi dakinsa ya kwanta to fa da tsakar dare zan tashi in je in dauko shi dakina mu kwana tare ko ni in kwanta a dakinsa. Na kan rungumeshi inyi kuka idan na tuna da dan Jaririna. Haka idan ina masa wanka ko shirya shi, ko ina masa wasa sai dan Harriet ya fado min ina tunanin halin da yake ciki yanzu, inji dama ace shine Abdul-Malik muke tare haka cikin jin dadi, wadata da kulawa mai yawa. Kamar yadda na cika mata alkawari da na dauka na kula da danta, itama ta cika min alkawari ta saka ni a makaranta mai dunbin kwararrun Malamai. A kaimu a mota a dauko mu a mota duk ranar da baza ta samu damar zuwa ba ni da Abdul-Malik ake kaiwa direba ya jira har a tashe mu. An bude ajin kananan yara kamar *yan shekara biyu zuwa hudu anan ajin aka saka Abdul-Malik shima, tun yana kuka ina lallashinsa har ya saba. Ina jin dadin rayuwata sosai amma Mummy Naila ta fini jin dadi, bata da fargabar bar mun danta ko ina zata je. Tana matukar sona da kula dani, babu abunda na rasa, babu wani abu ko wani daki da tayimun katangar shigarsa, komai nake so zanci, ko ina zan shiga a gidan. Ta yarda da gaskiyata. A kwai kuku mai dafa abinci akwai Liliyan me share-share da goge-goge, a kawai Lantana mai wanke-wanke. Isa mai yanke fulawa. Isyaku da Kasim masu wanki da guga, ga masu gadi da masu sharar farfajiyar gidan ba adadi. Dukkansu girma suke bani, rissina mun suke suna kirana da Madam nima, dan su a tinaninsu jinin masu gidance banyi musu kama da *yar aiki ba. Na kara yin fari kal, nayi kiba, nayi fes na samu gyara ga sutura kala-kala, duk da ma nayi kwalliyar zurmikeken hijab nake sawa. Mummy Naila tana dan jin Turanci amma mijinta yana magana da turanci sosai ta haka muke magana. Amma na dage saina koyi Larabci dan haka nake kin yin magana da turanci, nake kwaba larabci. Ita kuma tana rokona in dinga yiwa danta turanci tana so ya koya kafin ya shiga makarantar boko. Na samu shekara guda a gidan larabawan nan cikin ikon Allah larabci ya zauna a bakina saboda a gida larabci, makaranta daman kakaf larabawa ne komai da larabci ake yi don haka siffata, shigata da maganata duk ta larabawa ce. Haka a shekarar na sauke Alkur'ani mai girma, na haddace Hadisai masu yawa, nasan Tauhid da Fikihu. To kunji inda naji yaren Larabci na kuma iya karatun Alkur'ani. Iman tayi hawaye tasa gefen hijabinta ta goge. Su Suhaif sun zuba mata ido suna jin wannan labari mai dinbin al'ajabi kamar almara. Iman taci gaba da cewa "Sai kuma yanzu za kuji dalilin barina gidan. Gidan da ake min gata, ake kaunata tamkar jinin jikinsu. Ta ce "Babu wani mugun hali da suka yimin har nabar gidan, haka nima har muka rabu babu ha'inci ko zamba ko cin amana dana yi musu, illa mugayen matsafan da suke jikina suka rabamu. Tun sanda na kama addinina haikan ba dare ba rana bautar Allah karatun Alkur'ani ya shiga bakina sai kuma na shiga tashin hankali, rayuwata ta shiga barazana. Kullum na kwanta barci sai in ga wadancan matsafan a mafarki kuma kamar ido biyu. Suna kirana kuma suna lallabata, suna bani shawara in fita daga addinnin da nake. Sabida addinin akwai addu'a mai zafi da nake damunsu da ita suna nisanta daga gareni, su kuwa a kullum suna tare dani dan suna sona, zasu bani arzikin da zanfi kowa. Inyi farat in tashi a firgice amma da addu'ata fal baki. Da naga haka sai na shiga bin Malaman makarantarmu daban-daban suna bani addu'o'in tsari daga sharrin mugaye. Na kuma bazama neman litattafan addu'oi iri-iri sune abokan hirata. Haka kuma nake ganina a mafarki inata kona su da Ayar Allah, don haka na fara fin karfinsu. Matsafan ma suka bazama neman abun tsafin da zasu tsafeni suci galaba a kaina, suna kai kukansu kasa-kasa, gari-gari wajen manyansu suce wai yarinya karama ta gagaresu shakara da shekaru. Da Allah Ya kaddara za suci galaba a kaina daga baya sai na zama yin addu'ar yana min wuya. Musamman da daddare sai in kasa addu'a in zan kwanta bacci. Wata rana cikin mafarki sai naga matsafan sun daukoni suna murna, suna tsalle suna waka. Suna magana da duk yaren da nake ji, suka daure ni a jikin wata bishiya, suna waka suna zagayeni. Ina ta zullo ina so in kwace daurin da suka yimin na kasa kwacewa, sun kuma dauremin bakina na kasa ihu balle addu'a. Babu abin da zan iya hanga a wajen sai dokar daji da *yan bukkoki, sai itatuwa waje-waje an kunna wuta, suna rike da wasu itatuwan a hannayensu suma a kunne da wuta. Matansu da Mazansu, yara kanana da manyan dukkansu babu sutura ajikinsu. Gajerun wanduna mazan suka saka sai jajayen kyallaye a daure a kansu da dukkannin gabobin hannayensu da kafafuwansu. Haka suma matan banbancinsu da mazan karamin siket ne maimakon gajeran wando sai dan siririn jan kyalle da suka daura suka rufe kirjinsu. Sunyi zane-zane da farin fanti a goshinsu da cikinsu, kayan tsafi kuwa gasu nan birjik ko ina jifgi guda a gabansu, kamar su kan dabbobin gida daban-daban da na daji, kan kunkuru, kan macizai da kokon kan mutane. Abun mamaki naga wasu mutanen da na sani a cikinsu, naga wannan senior data fara sakani cikin ukuba naga da yawa daga cikin *yan makarantarmu na sakandire harda wani babban mutum makocinmu ne mai suna Mr Izera.. Babban abin tausayi harda yara *yan furamari. Babbansu ya fito suka matsa masa suka bashi hanya yazo gabana, da sauri suka dauko masa abun zaman ya zauna, ya dube ni ya tuntsire da dariya mai karfi da firgitarwa ya ce "Rufkatu! Rufkatu!! Rufkatu!!! Yau gaki a hannunmu amma duk da haka kinfi karfinmu ko yanzu muka bude miki baki zaki karanto addu'ar da zata kona mu. Kinyi nisa mun kasa rinjayarki cikinmu, kuma mun so mu halakar da ke mun kasa saboda karfin addu'arki, da wacce dan Makwabtanku yake yi miki da Mahaifinki. Amma yanzu ladan wahalar da kika bamu zamu zamar dake abar tsana, abar gudu, abar cutarwa a cikin *yan uwanki Musulmai. Yanzu ma zamu gwada miki abunda muke nufi. Sai naga sun dauko wani yaro. Ina duban fuskar yaron sai naga Abdul-Malik dan rainona. Hankalina ya tashi ina ta fisge-fisge ina so na balle na kasa. Suna dariya irin ta mugunta suka bankare yaron sun shake shi zasu kashe shi yana ta tsala kuka. Cikin ikon Allah na daka tsalle da karfi sai na kwance daurin da suka yi min na fusge kyallan da suka rufe min bakina, na dinga karanto addu'o'i, suka fara ja da baya naje da gudu na dauke Abdul-Malik na zura da gudu cikin daji. Sai suka biyoni da gudu. Muna ta gudu ba tsagaitawa, dai-dai nan nayi firgigit na farka daga barci ina ta shesheka kamar da gaske nayi gudun. Jikina gaba daya ya min nauyi yana ciwo zuciyata tana ta bugun uku-uku. Hankalina a tashe, na firgita kwarai da gaske, don ban taba mafarki irin wannan ba. Na gyara fulo na jingina ina mai matukar damuwa da tashin hankali, na fara hawaye ina tunanin yadda rayuwata zata kasance nan gaba. Gashi yadda nake jin yanayin jikina duk sanda zanyi addu'a sai na kasa, nasan dole sun fara samun galaba a kaina. Na tuna irin wahalar da nasha a lokacin da nake Bauchi duk da dai wadanda na farfasawa kai *yan iskane masu san aikata masha'a dani. Nayi sauri na jawo Abdul-Malik da yake kwance a gefena na dube shi, na firgita na mike da gudu yayin dana ga numfashinsa na harbawa sama-sama, jini yana zuba ta hancin sa. "Ina zaki je ne? Kije ki dauke shi a kai shi asibiti, waye yasan abunda kika gani a mafarki? Zuciyata ta fadamin haka. ALLAH YA KAREMU DAGA SHARRIN MAKIYANMU AMEEN INA MUKU FATAN ALKHAIRI Reedwan Suraj Isma'il *************** YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Karkarwa nake tamkar a lokacin hunturu, har hakorana na sama da kasa suna hadewa. Numfashina yana sama yana kasa, kai kace hakar rijiya nake yi. Ina sanda na zo inda Abdul-Malik yake kwance. Na dauke shi da kyar na fito na nufi dakin Mahaifiyarsa ina kuka ina kwankwasa musu kofa. Ta tashi da sauri ta bude kofar gabanta na faduwa, tana ganina tasan ba lafiya. Karar sautin da take tambayata ya firgita mijinta ya fito da sauri shima. Na kasa bayani saina mika mata yaron ko da suka ga jini sai suka rude tana kuka mijinta kuwa ya hau karkarwa, suna sake tambayata meya same shi? Na daure na bude baki nayi musu bayani cewar nima naji yana ta nishi sama-sama dana kunna fitila sai na ganshi cikin wannan hali. Aka tashi direba muka shiga motar har dani muka dunguma asibiti, duk da tsakar dare ne misalin karfe uku na dare likitoci suka dukufa aikinsu na ceto ran yaron da kuma gano mahassadin ciwon. Hankalin Mahaifansa ya fara kwanciya ganin likitoci suna aikinsu, kuma sun yarda da aikin likitocin saboda kwarewarsu, amma ni kuwa hankalina yaki kwanciya, kuka nake naki tsagaitawa. Mummy Naila ta dawo ita take lallashina inyi hakuri in daina kuka zai sami sauki da ikon Allah. Abu kamar wasa Abdul-Malik ya kwana biyu bai farfado ba ana ta kara masa ruwa. Hankalin kowa ya tashi har likitocin don sunyi iya kokarinsu sun kasa gano irin wannan cutar, kuma da wuya ace sun yiwa mara lafiya irin wannan taimakon bai sami sauki ba. Mahaifinsa ya fara shawarar su fita da shi asibitin kasar waje. Na san duk abunda yake faruwa na kasa fada, duk sanda na kwanta bacci zanga matsafan sun bishi asibiti suna jagula aikin da likitocin suke yi suna sake shake shi yadda jikin zai rikice. Suka shaida mun cewar bayan sun gama wahalar da shi sannan su kashe shi ba kuma mutuwa salin alin ba yana kwance, a'a a hannuna zai mutu yadda za'a kamani ace ni na kashe shi. Suna nan suna biye da ni zasu min sharrin da kowa zai tsaneni karshen rayuwata ta kare a gidan yari. Da naji haka hankalina ya tashi sosai nayi kuka har na gaji daga karshe na yanke shawarar gara na bar gidan nan saboda in ceto rayuwar Abdul-Malik. Ina son Abdul-Malik yana sona, haka Mahaifansa ma suke sona. Sun nuna min gata, sun rikeni tsakani da Allah dole ce tasa na bar gidan duk da nasan jin dadi da gata ya kare kuma ban san inda zan dosa ba. Na rubuta wasika cikin harshen Larabci na ajiyewa Mummy Naila akan gadonta lokacin tana asibiti wajan danta, ni kuma na dawo gida zan kai abinci. Da farko nayi mata godiya bisa taimakon da tayi min da kauna da take min tsakani da Allah, na mata addu'a Allah Ya kara mata budi da arziki da wadata Ya kuma karbi addu'arsu ta samun haihuwar *ya*ya da yawa masu albarka, kuma kyawawan halayansu da son taimakawa marayu da talakawa ya bisu har kabarinsu, san nan nace ina mai matukar damuwa dare da rana safe da yamma akan halinda da Abdul-Malik yake ciki, ina yi masa fatan Allah Ya bashi lafiya. Shawarar da nake baku shine ku dauke Abdul-Malik daga asibiti kuma kar kuyi wahalar kaishi kasar waje ciwon Abdul-Malik bana asibiti bane. Ku komo gida ku dukufa ku dinga yi masa addu'a ba dare ba rana, kuma ku hado manyan Malamai ayi ta sauke muku Alkur'ani a tofe kowacce kusurwa a gidanku kada kuyi sakaci, kada kuki daukar shawarata, ina son Abdul-Malik bana son ya hallaka. Nayi alkawari zan zamo mai yi masa addu'a a duk inda nake, kuma ba zan ci gaba da zama a nan gidan ina ganin halin wuya da Abdul-Malik yake ciki ba. Na yi kuka na gaji sannan naje na ajiye wasikar a tsakiyar gadonta a bude yadda zata gani da zarar ta shigo dakin. Ina da suturu na gani na fada kala-kala akwati akwati, riguna da siket kala-kala, riga da wandunan jeans, jallabiyoyi bakake na Larabawa tsala-tsala ba adadi, leshina da atamfofi manya-manya babu kanana mai arha. Takalma da jakunkuna, kayan kwalliya kamar su jan baki da hoda a cike a gaban madubi, wasu kuma jifge a akwati. Babu abinda na dauka sai dogayen riguna guda uku da atamfofi kala biyu. Kudin da ke jakata basu da yawa, na fito na bar gidan. Tafiya nake da sauri fatana na bar unguwar don kar in hadu da idon sani. Kutsawa nake cikin unguwanni ba tare da nasan inda zan nufa ba. Motoci na alfarma suke tsayawa suna rokata wai na shigo su kaini inda zanje, sai naki shiga. Pure water kawai nake tsayawa in saya in sha sai in kara gaba. Dana gaji da tafiya sai na hau bus da naga kowa ya shiga ana cewa "Bata-Bata. Muka isa Bata kowa ya fito daga mota ya nufi inda zaije, ni kuwa na fito, na sake ganin bus ana lodin Dawanau sai na shiga muka isa Dawanau can ma banga wajen zama ba ga dare yayi. In takaice muku a rumfar kasuwa na kwana. *yan iskan maza kala-kala suka yi ta lallabani za su cuce ni, naki yarda dasu ina ta addu'a basu matso kusa da ni ba. Gari ya waye na roki ruwa na yi salla, na kara gaba, haka na yini ina yawo daga wannan unguwa zuwa waccan, duk macen dana gani sai in bita ina rokarta ko zata dauke ni aiki, Allah Baisa an sami wacce ta amince in bita ba. Kudin motata ya raunana, canjin kawai ya rage a jakata a lokacin ina tsakiyar tashar *yan kaba. Abunda ya fado kunnena shine naji wani kwandasta ya ware murya yana ce wa "Gumel! Gume!! Gumel!!! Naje na tambayeshi menene Gumel? Saboda sunan ne kawai yayi min dadi, yayi kama da albarka. Sai yayi dariya ya ce "Malama yanzu duk zamanki a kasar nan bakisan garin Gumel ba? Gumel gari ne mai mata da maza, yara da manya, attajirai da masu Sarauta, masu Mulki da manyan Malamai bayin Allah. Garin da suke da faffadar Masarauta. Sune suke bikin Sallar Mauludi (sallar gani) ake tururuwar zuwa daga gari-gari da kasashe-kasashe daban-daban. Garin da suka taba yin ministan sufuri General I.D Gumel. Sai na tsaya kawai ina kallon bakinsa har ya kai aya. Sai nayi murmushi na ce masa "Zanje Gumel. Ya ce "To shiga zungureriyar bus din nan *yan mata, yanzu kuwa zamu kai ki garin Sarki Amadu. Mota ta cika makil direba da kwandastansa suka shiga aka rufe kofar mota, muka fara tafiya. Yayin da iska mai sanyi take busowa cikin motar na lumshe ido dadi ya lullube zuciyata naji a raina daga lokacin dana shiga garin Gumel bakika damuwata zata gushe da Izinin Allah. "Ku hado kudin motarku. Inji kwandasta. Na laluba canjin daya rage a jakata sai naga basu da yawa, nan fa gabana ya hau faduwa na shiga mota babu cikakken kudin mota, yana fadar yawan kudin motar nasan bani da su. Jikina yana rawa na mika masa abun da Allah Ya hore min. Nan fa tarwatu ya tashi da tonar asiri. Ya kirga kudin dana mika masa sai ya harareni ya ce "Malama ciko kudinki bai cika ba. Na narairaice na ce "Bani da wasu su kenan. Ya ce "A'a wannan zance kike da ganganne haihuwa da damuna inji masu iya magana, falleliyar budurwa kamarki ace baki da kudin mota? Idan ma wasa kike to ya isa wasan ki ciko mana kudinmu. Nayi murmushi na ce "Da gaske nake kudina kenan, ku taimakamin. Ya sake cewa "Ai ba laifin mu bane, mu ma balance muke hadawa mai ainihin motar, da zarar kwabo bai cika ba, za'a daga mana hankali koma akwace motar a bawa wadansu, shi yasa bama wasa da karbar kudin mota. Ko kuma idan Allah Ya sa akwai wanda a cikin motar nan zai yi kudunbala ya biya miki cikon kudin motar ai babu matsala. *Yan cikin motar suna jin mu babu wanda yake da niyyar taimakamin, sai ma tura kai suke cikin wundo suna kallon daji kamar basa sauraran abunda muke fada. Bai daina magana ba, bai kuma hakura ba, shi dai a dole sai na ciko kudin motar nan. Ya ce "Yarinya baki fito da sa'a ba, sa'ar kuwa ita ce, yau da kin shiga motar nan da Haj. Yalwa Gumel da kinga yadda ake taimako, ba cikon kudin mota ba ma kawai da mota zata saya miki kyauta. Ace kin yi sa'a kin hadu da Yusuf Gumael wato Barman Gumel kuma (special adviser) da kinga taimako. Haka kuma yau da kin hadu da Malam Abdul-Salam Mohd (M.D NPA) da bakin cikinki ya warke. Ko kuma Alh. Adam I.D Gumel (Sarkin yakin Gumel) ko kaninsa Alh. Nasir I.D Gumel. Ko kiyi kicibus da Alh. Muhammad Alkali (Sardaunan Gumel) ko matemakin gwamnan Jigawa wato Alh. Ahmad da kin warke. Wannan ina zano miki mazan fa kenan, a mata kuwa da kika hadu da Haj. Fatima da Haj. Rafi'atu matan Alh. Ahmad (depety Govern Jigawa State) ko Haj. Sadiya da Haj. Ummi matan Yusif Gumel wallahi ba tantama zasu biya miki kudin motar nan. Ko Allah Yasa ki hadu da Haj. Maryama I.D Gumel yau da kinji dadi. Da kin fito a sa'a yau a ce a motar nan akwai Haj. Hajara Adam I.D Gumel ko kanwarta Haj. Aisha Nasir I.D ko Haj. Mariya Nasir I.D Gumel da kin huta da takaicin kudin mota. Ke bari inyi miki dungurungun ki hadu da Haj. Binta da Binta matan Malam Abdul-Salam Mohd ko Haj. A'i uwar gidan Alh. Muntari dan Muloniya (darwaton Gumel) ke da kin zama abar kwatance da nunawa a tashar Gumel. Ni dai ina sauraronsa ina kuma kallon bakinsa yadda yake zaro magana baya gajiya, bai yi shiru ko na sakon daya ba tunda ya shiga motar magana yake kowa na sauraransa. Na katse shi na ce "To tunda banyi katarin haduwa da wadannan bayin Allah ba, inci albarkacinsu mana ka yafe mun kudin motar. Ya zabura ya ce "A'a niba dan Gumel bane ni nan da kika ganni Bahadeje ne, baki kula da tsagun ba, ko baki ganni baki wulik ba? A samu Bagumule daya ya biya miki cikon kudin nan mana. Ko babu Bagumule a motar nan? Ya tambayi *yan motar, shiru babu wanda ya amsa masa. Ya ce "Kwarai da gaske ni fa nasan babu dan Gumel a motar nan kirarin da na yiwa Gamulawa da an samu wani ya tofa, to ke *yan mata yau kin fado motar *yan cirani, *yan kwadago, fatake ne daga kasuwa zuwa kasuwa. Ashe fa yau Laraba yau ne Kasuwar Gumel ta ke ci. Sai a lokacin wani daga cikin *yan motan ya tanka masa ya ce "Malam ka ishe mu da bara, har kana kiranmu fatake, ba muyi niyyar cika kudin motar ba, idan ba zaka yafe mata ba ka sauketa a inda kudinta ya kare. Direban ma ya tsoma baki ya ce da kwandantan "Abba dan Allah ka ishemu da magana, tun da a Doko kudinta zai kare sai mu sauketa kawai. Ni dai ina sauraransu, nayi mamakin irin wanan rashin tausayi da tsananin son kudi irin na direba, kwandasta da dukkan jama'ar da suke cikin motar. Ana zuwa Doko, direban ya tsaya kwandasta ya bude mota ya ce "An zo Doko *yan mata anan kudin motarki ya kare, ba rabon ki je Gumel. Ki ga garin Sarki Amadu. Sai naji hawaye ya surnano min, takaici marar misaltuwa ya lullube zuciyata saboda ban je Gumel ba, amma nayi tawakkali na bawa zuciyata hakuri nayi addu'a Allah Ya sa nan ne yafi Alkhairi a gareni. Na sauko daga motar jikina sanyi kalau, suka ja motarsu suka tafi. Na sake saba jakar kayana a lokacin ana kwada rana mai zafi, ga yunwa da kishirwa ina ji. Na hango wasu Fulani masu siyar da fura da nono da *yan mata guda biyu suna sayar da abinci. Na karasa wajansu na gaishesu, saina zauna a kusa dasu. Naji dadin yadda suka kula ina jin yunwa, da kansu suka dama mun fura da nono suka miko min ruwan sha. *Yan matan ma suka zubomin wake da shinkafa na ci na koshi na musu addu'a Allah Ya biya musu bukatunsu, Allah Ya taimakesu kamar yadda suka taimake ni. Ina zaune a tsakiyarsu ina ta hira da su, daga baya ma muka juye Fulatanci da Fulanin har kusan magaruba, sannan suka tashi kowa zai kama hanyar gidansu. Nauyi da fargaba na kasa ce musu zan bisu rigarsu, ina kallonsu suka tafi suka barni. Masu wake da shinkafa ma suka tafi. Da gari yayi duhu shine na kutsa cikin garin Doko, ina tafiya na hangi fitilar *yar Hajja tana sayar da gyada, kwai da goro, ita da kwayenta samari da *yan mata suna wasanni shine na nufi wajansu na zauna a gefensu ina kallansu. Har Allah Ya kawo Suhaif yana rabon kwai ya hango ni. Ya zo ya tambayeni daga ina nake? Ba tare da na shirya karyar da zan yi ba, na bude bakina naji na ce masa daga Saudia aka kamoni kuma ban san kowa a Nigeria ba. Dalilina kuwa don aji tausayina a taimakamin a rikeni. Saboda bana son a mayar dani garinmu. Ina son Musulmai, ina son addininsu, ina so kuma in sami ilimin addini sosai kafin in koma ga Iyayena, in basu hujja mai karfi yadda zasu yarda da ni su bar addininsu, su shigo nawa. Amma ina yi ina tsoron cutar da muyagun Matsafa nan za su yiwa al'ummar Musulmai a sanadiyyata. Da Suhaif yaji bayanina ya tausaya min ya kuma taimakeni ya kaini ga Iyayensa, suma mutanan arziki sun rike ni amana. Na sami ilimin addini mai yawa a garin nan, na karu da abubuwan da a da ban sansu ba. Na sake haddace Alkur'ani mai girma, na sake sanin Sunnonin Annabi Muhammad (S.A.W) da Hadisansa masu yawa. Hamma Huzaifa ne wanda muka shaku sosai, ya taimakeni akan addinina wanda daga baya shakuwarmu ta zama soyayya. Nayi takaicin rashin Huzaifa, na shiga kunci sosai dan ina kaunarsa, na kaddara cewa haka Allah Ya rubutomin na bawa zuciyata hakuri da dangana. Sai Allah Ya mayarmin da madadinsa Ya hadani da Suhaif. Tun sanda na hadu da Suhaif na ji raina na sonsa, da muka zauna da shi muka saba naga yana da kirki matuka kuma yana tsananin sona tsakani da Allah sai nima nake son sa. Babu abin da zan ce sai dai Allah Ya saka masa da alheri tunda tawa ta kare, Allah Ya bashi mata ta gari mai sonsa. Dalilin da yasa jama'arku suka yi ta mutuwa aka ce nice nake kashesu kuma shine, idan baku manta ba na fada muku abinda Matsafan nan suka fada min cewar zan zamo abar tsana, abar gudu a cikin Musulmai har sai na gaji na bar addinin. Yadda suka yimin shine idan wani abu ya hada ni da mutum na rashin jituwa misali da farko Malam Nayaya ya ce yana sona kowa ma a makarantar yasan yana sona, ban tsane shi ba, saboda ina son duk wani Musulmi musamman Musulmi irin Malami wanda yasan ilimin addini, amma kuma gudun kada Matsafan nan su cuce shi shine yasa na guje shi. Da ya takura min da zancen yana sona, sai na fada masa yayi hakuri bana soyayya. A zatonsa da tunaninsa sai ya dauka wulakanci nayi masa irin na *yan mata, sai ya tsaneni kullum zagi da duka. Ban damu ba, a inda ya duke ni a wurin zanyi kuka na share hawayena, na kaddara a raina duk jarabawa ce daga Allah. A daran da zasu kasheshi wani ciwan kai mai tsanani ya kamani tun daga magaruba, na kasa sallar isha'i balle nayi addu'a idan zan kwanta, dan haka na kwanta da wuri saboda barcin da yake wartata mai nauyi ban san meyasa ba. Mafarki abune daga Allah Ya ke saukowa bayinSa don Ya nuna musu wani abun da basu sani ba, ko wani albishir, ko gargadi akan wani mugun hali da suke aikatawa a doron kasa. A lokacin Annabawa kuwa ana saukowa Annabawa wahayi a cikin mafarki. Wani mafarkin kuwa daga shaidan yake, ko *yan tsubbu, Matsafa ko Aljanu. Yayin da wasu bayin Allah suke mafarki da Annabawa ko karatun Alkur'ani da massalatai wasu har aljanna Allah Yake nuna musu, su tashi daga barci suna masu godiya ga Allah da sadaka suna murna suna fadawa masoyansu, ana taya su murna. Ni nawa mafarkin bala'i ne, abun bakin ciki ne da tashin hankali. Ina cikin wannan barci marar kan gado, sai naga Malam Nayaya a mafarki matsafa sun kamo shi sun daudaureshi kuma na ganni sanye da kaya irin nasu suna sanar dani cewa ga wuka da hannuna zan kashe shi. Amsar da na basu itace bazan kashe Malamaina ba. Ban ankara ba naga sun fadar dani kasa sun daure min hannaye suna gana min azaba. Babbansu ya fito dauke da wuka baiyi wata-wata ba ya sokawa Malam Nayaya wuka ya mutu. Na kwalla kara mai tsanani a lokacin na farka daga barci jikina na rawa, zuciyata cike da bakin ciki. Kwatsam sai da safe aka cemin ya mutu. Nayi kuka mai yawa, nayi takaici, amma babu wanda zan iya fadawa gaskiyar abun da ya faru, na dukufa da addu'a ba dare ba rana akan Allah Ya kare mu daga sharrinsu ni da *yan uwa Musulmai, amma duk ranar da Allah Ya yi wani zai mutu ta sanadiyyata gaba daya a wunin nakan kasa addu'a ko da na fara bakina yana yimin nauyi, idan na takura hakorana suna datse harshena. Bacci mai nauyin gaske ya hanani sukuni, dole na kwanta ba shiri, sai naga wanda zasu kashe a mafarki sun dauko shi sun zo sun kashe shi. Don haka a zaman makoki na fi kowa kuka da damuwa. ..... Tofa Matawata ta ce tana gaida Masoyanta da fatan suna cikin koshin lafiya, sai dai bata ji dadin abun da yake faruwa akan Iman ba..... Lolxx. Ehem na fara tara *ya*ya, Junior ta ta haihu, zanso addu'arku akan su.. Nagode. Reedwan Suraj Isma'il *************** YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Dole in damu saboda nasan meye sanadin mutuwar tasu. Shi yasa nake kaffa-kaffa ko da Malamina ko a kawayena *yan ajinmu nake gudun hatsaniya ta hadamu, da zarar sun harzuka sai inyi ta basu hakuri, amma suki hakura lallai sai sun daga murya asan muna fada, rashin sani sai su zazzageni. Zasu kwanta da daddare lafiya zanyi mafarki an kashesu da safe za ace min sun mutu. Da naga anyi haka sau daya, sau biyu, kafin ayi na uku sai na hada kayana cikin dare zan gudu in bar garin. Niyyata kuwa inkaura dokar daji inyi rayuwa da namun daji in sun gaji dani su cinyeni. In shirya kayana in fito inyi ta tafiya, sai naji hankalina ya dauke in fadi in yi ta barci, sai in yi mafarkin matsafan sun daukoni aka sun dawo dani har dakina kan shinfidata. Ina farkawa daga barcin a shinfidata zan ganni, inyi ta mamaki. Mun yi haka dasu yafi a kirga. Da ga karshe dole na hakura na zauna. Amma basu dai na hadani fada da jama'a ba suna kashesu cikin dare. Allah cikin ikonSa jama'a basu gane ba har sai da Maimuna *yar garinmu tazo ta tona min asiri. Ta fadi gaskiya bata yi karya ba, ta sanni sosai duk da ba kawarta ba ce kawar kannen Hamma Huzaifa ce su Bilkisu Islamiyyarsu daya. Bayan na sha kuka da takaicin tona asirin data yi min, sai bacci da ciwon kai ya kamani. Hakika gangar jikina ce a kwance ruhina ya tafi wajansu, ranar raina a bace ina ta zaginsu akan su rabu dani, su rabu da jama'ata. Nayi-nayi inyi addu'a Allah bai bani ikon yi ba, ina ji ina gani suka kashe Maimuna. Su Baba, su Goggo a kaina suna tashina ban farka ba sai da kurwata ta dawo, na farka daman ba bacci bane. Ina tashi kuwa na samu labarin Maimuna ta mutu, daman ko basu koreni ba dole in kori kaina. Bayan na tafi samari suka bini zasu dake ni, to tun daga nan na rasa hankalina, suka turani tsohon ginin gidan Mahaukacin nan na shiga. Sun sami yadda suke so, Musulmai sun koreni, na zama ta su kenan. Na zamo a zaune kawai nake sun zagayeni babu ci babu sha, babu alwala bare salla, bana magana balle inyi addu'a. Gagarumar liyafa suka hada cikin dare a cikin gidan don murna, yau na zama tasu, yau sunci galaba kaina. Mutanen da nake so wato Musulmi sun kore ni daga cikinsu kwata-kwata. Ta kai ta kawo na ma daina ganinsu a mafarki ido biyu nake ganinsu. Suhaif ya ga jini an diddiga tun daga kofar gidan har cikin dakin dana ke, su suka disa akan takalmana, suka daura takalmi daya a akan saman rufin dakin yana diga, daya kuma yashe a tsakar gida da jini a jikinsa. Sunyi haka ne don Suhaif ya gani ya shaida ni mayya ce, suka daura min jajayen kyalle a jikina, sai daga baya na ciccire. Suna fakon Suhaif sosai, sun kudiri niyyar sai sun kashe shi, saboda shine kadai ya rage mai takura musu da addu'a, shine bai tsane ni ba, bai rabu da zuwa inda nake ba. Babu makawa sun gama shirye-shiryen kashe shi tsaf a cikin daren dana ce masa ya kwana yana sallah yana addu'a kada yayi bacci. Da suka je zasu kashe shi suka kasa shiga inda yake balle su ganshi su kashe shi, sai suka kufula a daren kwana suka yi suna gana min azaba. Ban damu ba tun da mutuwa nake nema. Babu wadanda suka jawo min wannan matsananciyar rayuwa sai Mahaifana, tun farko da na hadu da Matsafan da sun hadu sun taru sun rabani dasu da karfin addu'a da haka bata faru ba, duk da nasan kaddara ce. Amma kowannensu addininshi daban, wannan yana jin haushin wannan, idan ya kawo mai addu'arsa yana ganin kara min ciwo ake, kawai sai rigima ta harde su, daga karshe suka kyaleni da ciwo yana bibiyata har girmana. Duk lokacin da waninku ya hadu da dangina ku shaida musu abubuwan da suka faru dani har izuwa mutuwata. Nasihata zuwa ga Mahaifana itace su dawo su rungumi addinin Musulunci, suma su mutu a cikinsa kamar yadda nima zan mutu Musulma. Iman ta rushe da kuka mai tsanani sai jama'a da dama a wajen tausayinta yasa su kuka suma. Cikin kuka ta dukar da kai kasa ta ce "Na gama labarina ku kasheni kamar yadda ku kayi alkawari, na gaji da rayuwar wulakanci da kyama da tsangwama a cikin *yan uwana. Kafin wani ya bude baki yayi magana, ganin Iman akayi ta daka tsalle ta fadi can gefe kamar wani ne yayi ball da ita. Sai ta tashi a gigice tana kallon wani gefe tana magana kamar a kwai wadanda take gani mutane basa gani. Cikin harshen Turanci take magana take cewa "Ku rabu dani, karku matso kusa dani, baku zaku kashe ni ba, ku bar *yan uwana Musulmai su kashe ni. Suhaif yana jin haka ya tashi da gudu ya fisgota ya kawota tsakiyar Malaman yana fassara musu abunda yaji tana fada da Hausa. Sai suka gane cewar matsafan sun zo su kasheta saboda ta tona musu asiri. Yanayin halin da suka lura Iman na ciki shine matsafan suna rike da ita suna shirin su kasheta. A gigice Suhai yake janta yana so ya kwace ta daga hannun matsafan duk da baya ganinsu yasan janta suke yi. Nan da nan manyan Malamai suka bude Alkur'ani suka fara karatu. Ba su kadai ba jama'a da yawa suka ruga gida suka dauko Alkur'ani cikinsu harda Najib ya kwaso Kur'anan gidab gaba daya. Suhaif ma ya karba aka zagaye Iman ana tayi mata karatu. Ta dora hannu akai, ta nutsa kanta cikin gwiwowinta kamar zata nitse cikin kasa, saboda tsabar tsananin zafin addu'ar da take kona matsafan da suke jikinta. Ta mika hannu da kyar ta kamo bishiyar dake kusa da ita ta kankame bishiyar da karfi tana yare wanda babu wanda yake jin yaren. Haka kuma bai hanasu daina ragargazarsu da ayar Allah ba. "Mu muna sonta tun kafin ta rungumi addininku. Ta fada cikin wata kakkausar murya wacce ko kusa bata yi kama da muryar mace ba, cikin harshen Hausa take magana yanzu. Wani Malami ya ce "Karya kuke makiya Allah yau sai munga bayanku azzalumai. Kamar yadda kuka kashe sai an kasheku. Ana ta karatu an zagaye bishiyar da ta rike ta rasa inda zata sa kanta, idonta yayi jajawur sai zufa take keto mata tamkar ana ruwan sama ta jike hagaf. Ta sake cewa "Kuna kona mu kuna kashe mana *ya*yanmu da jama'armu fa. Sai su kuwa masu karatun suka sake daga murya suna karatun da karfi. Ukuba tayi ukuba, zafin kuna yayi zafi, sai Iman ta fadi kasa numfashi sama-sama. Baisa sun daina karatu ba, ana ta jan ayoyi masu karfi. Matsafan ji suke kamar ana musu ruwan wuta. Yau sunga ta kansu sun gamu da gamunsu, a yau suka yi nadamar haduwa da Iman, sun yi dana sanin nacin da suka yi shekara dashekaru. Tuba suke, hakuri suke bayarwa daga yau zasu rabu da ita. Ko hanyar da tabi ma sun daina bi, amma tuba da nadamarsu yau baza tayi amfani ba. Babu mai sauraronsu, babu mai tausayinsu, babu mai shirin sassauta musu. Tun ana jin abinda Iman take fada har ta fara magana a hankali yadda ba'a fahimtar ta har tayi shiru bata ce wa komai ta rufe ido kamar mai bacci. Ba'a tsagaita da karatun ba yi ake tayi. Can Iman tayi magana wannan karon muryarta ce. Ta ce "Gaba dayansu gasu nan sun mutu, sun kone kurmus da wuta. Suhaif yayi ajiyar zuciya ya fada a baiyane "Alhamdulillahi. Ana ta karatun ba a daina ba har saida Iman ta tashi zaune daram tana kallon kowannensu daya bayan daya cike da mamaki. Sai ta tambayesu "Me yake faruwa? Suka tsaya da karatun itama suka tambayeta meya faru tsakaninta da matsafan? Ta yi shiru tana tunowa can ta ce "Na gansu suna ihu suna kamawa da wuta daga karshe suka fadi suka mutu, sun kone kurmus gaba daya garinsu ya kone kayan tsafinsu ma ya kone. Sai gaba daya *yan wajen suka yi kabbara. Malami daya daga cikin Malaman ya ce "Muna miki albishir kuma muna taya ki murna daga yau kin sami lafiya, kin rabu dasu har abada da izinin Ubangiji. Wannan wutar da kika gani tana konasu karatun da muka taru muka yi miki ne don haka mun konesu kurmus da ayar Allah. Iman taji dadin da tunda uwarta ta haifeta bata taba ji ba. Sai ta rushe da kuka tana godiya ga Allah. Wani Malami ya ce "To ai shikenan sai ta dauki kayanta ta koma gidan su Suhaif ta ci gaba da rayuwarta, ku kuma jama'ar gari kunji da kunnuwanku ba laifinta bane don haka banda tsangwama da kananan maganganu. Samun mutum irin Iman sai an tona a wannan zamanin. Ta sadaukar da rayuwarta, ta sallama rayuwar jin dadin duniya saboda ta shiga Musulunci. Sai kowa yayi kabbara. *Yan garin Doko gaba daya suka ji suna son Iman, saboda karfin Imaninta. Da gaske Iman take tana son Musulunci da *yan uwanta Musulmai. Yarinya mai kunya da ladabi, ko a hanya taga mutane zata yi musu sallama ta duka har kasa ta gaishesu. Haka jama'a suka gauraye wajen da yabonta. Suhaif yaji dadi sosai har kamar zaiyi tsalle don murna. Ya dauko jakar kayanta ya dauko mata takalmanta ya ce "Iman saka takalmanki ki zo mu tafi gida kiyi wanka, kici abinci ki huta kinji. Ta sharbe hawaye ta yi murmushin karfin hali ta ce "Na gode Suhaif Allah Ya saka muku da alheri kai da Iyayenka, *yan uwanka da mutanen Doko gaba daya. Ba zan kara ko kwana daya a garin nan ba, yanzu lokaci ne da zan koma gida wajen Iyayena in ga halin da suke ciki. Alhamdulillah abunda na zo nema na samu, na samu ilimin addinina. Zan iya kare addinina in kuma bada hujjoji masu karfi da za'a yarda abunda nake bautawa shine gaskiya. Hakika zan sami Iyayena in musu wa'azin da zai ratsa su, su karkato zuwa ga addinina musamman Mahaifiyata nafi ji, ta Mahaifina mai sauki ne domin yasan gaskiya karfinsa aka fi kawai. Ga Mama Tabita mai kaunata zan so ta kasance Musulma ba mushirika ba. Zuwana Kano da Doko na karu sosai, kuma a sanadiyyar haka na samu lafiyar ciwon da ya dade yana addabata. Malamai su ka ce "Ai haka ya yi gara ki koma garinku ko hankalin Iyayenki zai kwanta, kin bar gida shekaru biyu kenan. Wannan hukuncin bai yiwa Suhaif dadi ba ransa ya baci, jikinsa yayi sanyi, ya shiga damuwa. Baya son Iman ta tafi ta barshi. *Yan sanda suka ce to ta shiga motarsu, su kaita Kano sai su sakata a motar garinsu. Suhaif ya yi caraf ya ce "A'a ku barta gobe zan kaita Kano in sakata a motar garinsu. Babansa yayi wuf ya katse shi ya ce "A'a ka bari tunda ga masu tafiya ka bari a kaita yau mana. Kafin Suhaif ya sake magana Iman har ta shiga mota, dan sanda daya ya karbi kayan Iman a hannun Suhaif ya saka a mota. Malamai suka shiga motocinsu, *yan sanda ma suka shiga, kafin aja motar *yan garin suka baibaye jikin wundon da Iman take zaune suna tayi mata sallama da fatan alheri. Iman tana hawaye tana mika musu hannu suna musabaha da bankwana ko rai kanga rai. Zubaida da Naja'atu suka zo wajen Iman, sai kuka ya kece musu su duka ukun. Zubaida tayi karfin hali ta ce "Iman ki yafe mana abubuwan da muka yi miki, baki taba yin fushi ba, baki taba kai kararmu wajen wani ba, bakya gaba damu. Cikin kuka Iman ta ce "Na yafe muku tuntuni Zubaida ku yafe mun nima. Suhaif da Najib suka karaso jikin wundon Iman, sai kuka ya sake barkewa Iman ganin hawaye daga idanuwan Suhaif. Suhaif yayi karfin hali ya ce "Iman tafiyarki zata iya haddasamun abubuwa guda biyu, na daya zan iya rasa jin dadi a rayuwata har abada, na biyu zan iya kamuwa da ciwon rashinki har ya ja in iya rasa raina saboda damuwa. Iman karki tafi ki barni. Ta ce "Suhaif karka damu, kada rashina ya haddasa maka ciwo, Allah ne ya hada mu, kuma shine zai raba mu a yau. Shine kuma idan Ya so da izinin Sa zamu sake haduwa. Zai yi wuya in manta da kauna da halaccin da kayi mun a rayuwata, babu wani mahalukin daya taba sadaukar da rayuwarsa a kaina irinka. Ka soni a lokacin dana zama abar tsana, abar tsoro, abar gudu. Ina sonka nima bazan daina ba ko zai zamanto bazan sake ganinka ba har karshen rayuwata...... Ba ta karasa maganarta ba aka ja motar suka tafi. Tana hangen Suhaif yana ta bin motar da gudu yana ce wa "A tsaya! A tsaya!! Kuka mai zafi ya rufto musu ita dashi. *Yan gari suna ta dagawa Iman hannu har saida suka daina hango motar. Gwaggo da *yan matanta kuka suke tukuru na rabuwa da Iman. Haka jama'a da yawa basu shirya yin kuka ba, amma sai suka ji hawaye ya kece musu saboda bakin cikin tafiyar Iman. Sabo turken wawa, Iman ta shiga ransu sun saba da ita, ta saba dasu. Zaku tausayawa Suhaif idan ku kaga halin da yake ciki, a cikin kasa ya zauna turmus yana damkar sawun tayar motar da Iman take ciki. Najib ya dade yana bashi baki amma kamar zugashi yake. Kowa ya watse ya barsu shi da Najib a wajen. Suhaif yaki tashi su tafi shi kuma ya kasa tafiya ya barshi, Suhaif sai rokon Najib yake Allah Annabi yake, ya tafi ya kyale shi anan shi ba zai koma gida ba, Najib yaki tafiya. Baba ya fito sallah Masallaci ya hangosu a zaune sunyi jugum-jugum ya zo ya same su, ya tambayesu me suke yi. Najib ya fada masa abunda yake faruwa. Ya shiga bawa Suhaif baki akan yayi hakuri ya manta da Iman Allah zai iya bashi wacce tafi ta. Suhaif yana dagewa shi fa Iman yake so gashi bai karbi adireshinta na garinsu ba, babu inda zai ganta. Haka Baba da Najib su kayi ta lallashin Suhaif da kyar Suhaif ya tashi suka nufi gida. Iman ta tafi tabar Suhaif da tunaninta, begenta da tsantsar kaunarta. Baya walwala, baya son shiga mutane balle yayi hira dasu daga Masallaci sai dakinsa. Abincinsa kuwa idan yayi cokali daya, biyu, baya iya yin na uku sai yaji ya kasa ci. Babu abinda yake yi sai tunaninta wani lokaci ya debo wasikunta da hotunanta yana kallo. Sai ka ga hawaye ya surnano masa saboda tsananin damuwa. Abunda yafi tsaya masa a rai, shine irin wahalhalun da tasha a rayuwaarta shima yasa yaji ya kara sonta yana kuma tausaya mata yadda rayuwarta zata ci gaba da kasancewa bayan rabuwarsu. Yana ganin abu daya zai sa hankalin Iman ya kwanta a rayuwarta shine idan Allan Ya bata miji na gari mai tsoron Allah, mai sonta tsakani da Allah. Wannan mijin kuwa ba kowa bane illa Suhaif. Ina son Iman tamkar yadda nake son rayuwata, yadda bazan iya wulakanta rayuwata ba haka bazan wulakanta rayuwar Iman ba. Allah ka bani Iman. Ina zan sake ganinki Iman? Na rasa Iman na rasa mace ta gari, mai kirki, mai addini, mai kunya da tsananin tsoron Allah. Suhaif yana fada yana kuka. Najib bai daina yiwa Suhaif nasiha ba har lokacin da ya shirya ya koma Kano. Mahaifan Suhaif basa jin dadin yanayin damuwar da Suhaif yake ciki. Suna ta bashi baki da nasiha kala-kala. Daga karshe Mahaifin Suhaif ya bashi shawara ya shirya ya koma Kano ko hankalinsa zai fi kwanciya, har Allah Yasa aikin da ake nemar musu ya fito. Suhaif bashi da zabi yasan Kano da Doko duk daya ne tunda ba Iman zai gani ba. Bai ki yarda da shawarar Mahaifinsa ba, ya shirya kayansa kakaf ya tafi Kano. Can ma bata sauya zani ba cikin damuwa yake, amma yana samun dan sanyi a ransa tunda koda yaushe Najib yana tare da shi dakinsu daya, su kwana su tashi tare. Ko zasu yi fada Najib bazai fasa fada masa gaskiya ba, yana cewa wannan damuwar daya saka a ransa babu abinda zata kara masa illa ciwo. Iman dai ta tafi zai yi wuya ta dawo dan haka gara ya barwa Allah komai, idan Allah Yaso zai sake hadasu kamar yadda itama Iman din ta fada sai su hadu. Tamkar dalmar wuta kalaman Najib suke yiwa Suhaif a zuciya, su Suhaif da Najib suyi ta fada wai dan me zai ce ya daina damuwa Iman ta tafi kenan. Daga baya Suhaif ya fara yadda da zancen Najib gaskiya ne babu alamar dawowar Iman, gashi wata da watanni. Sai ya fara bawa zuciyarsa hakuri yana daddaurewa yana fita wasu harkokin. Baba Usman Mahaifin Najib ya shigo da wasu motoci guda biyu iri daya kalace kawai suka banbanta, daya kalar ja, daya kuma shudiya ce, motocin sababbi dal-dal a ledarsu, irin na zamani da kowanne matashi mai ji da kudi ko Mahaifinsa mai ji da Naira yake mafarkin samunta. Aka yiwa Najib da Suhaif albishir cewa ta su ce. Wai!! Wayyo Allah Najib yaji dadi har da ihu. Suhaif ma ya ji dadi sosai, suka je wajen Baba suka yi godiya suna baiyyana farin cikinsu. Baba yafi su jin dadi ganin yayi musu gwaninta kuma wadanda yayi dominsu sun gode. Wai meya sanya wasu suke cewa ba'a tashi inda aka tsaya ne? Wa ya fada musu ana tsallake? Gimbiya Zarah Matawata kenan ta ce ta ji dadi da ba'a mance da ita ba a wannan dandali..... lolxxx *************** YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Dole in damu saboda nasan meye sanadin mutuwar tasu. Shi yasa nake kaffa-kaffa ko da Malamina ko a kawayena *yan ajinmu nake gudun hatsaniya ta hadamu, da zarar sun harzuka sai inyi ta basu hakuri, amma suki hakura lallai sai sun daga murya asan muna fada, rashin sani sai su zazzageni. Zasu kwanta da daddare lafiya zanyi mafarki an kashesu da safe za ace min sun mutu. Da naga anyi haka sau daya, sau biyu, kafin ayi na uku sai na hada kayana cikin dare zan gudu in bar garin. Niyyata kuwa inkaura dokar daji inyi rayuwa da namun daji in sun gaji dani su cinyeni. In shirya kayana in fito inyi ta tafiya, sai naji hankalina ya dauke in fadi in yi ta barci, sai in yi mafarkin matsafan sun daukoni aka sun dawo dani har dakina kan shinfidata. Ina farkawa daga barcin a shinfidata zan ganni, inyi ta mamaki. Mun yi haka dasu yafi a kirga. Da ga karshe dole na hakura na zauna. Amma basu dai na hadani fada da jama'a ba suna kashesu cikin dare. Allah cikin ikonSa jama'a basu gane ba har sai da Maimuna *yar garinmu tazo ta tona min asiri. Ta fadi gaskiya bata yi karya ba, ta sanni sosai duk da ba kawarta ba ce kawar kannen Hamma Huzaifa ce su Bilkisu Islamiyyarsu daya. Bayan na sha kuka da takaicin tona asirin data yi min, sai bacci da ciwon kai ya kamani. Hakika gangar jikina ce a kwance ruhina ya tafi wajansu, ranar raina a bace ina ta zaginsu akan su rabu dani, su rabu da jama'ata. Nayi-nayi inyi addu'a Allah bai bani ikon yi ba, ina ji ina gani suka kashe Maimuna. Su Baba, su Goggo a kaina suna tashina ban farka ba sai da kurwata ta dawo, na farka daman ba bacci bane. Ina tashi kuwa na samu labarin Maimuna ta mutu, daman ko basu koreni ba dole in kori kaina. Bayan na tafi samari suka bini zasu dake ni, to tun daga nan na rasa hankalina, suka turani tsohon ginin gidan Mahaukacin nan na shiga. Sun sami yadda suke so, Musulmai sun koreni, na zama ta su kenan. Na zamo a zaune kawai nake sun zagayeni babu ci babu sha, babu alwala bare salla, bana magana balle inyi addu'a. Gagarumar liyafa suka hada cikin dare a cikin gidan don murna, yau na zama tasu, yau sunci galaba kaina. Mutanen da nake so wato Musulmi sun kore ni daga cikinsu kwata-kwata. Ta kai ta kawo na ma daina ganinsu a mafarki ido biyu nake ganinsu. Suhaif ya ga jini an diddiga tun daga kofar gidan har cikin dakin dana ke, su suka disa akan takalmana, suka daura takalmi daya a akan saman rufin dakin yana diga, daya kuma yashe a tsakar gida da jini a jikinsa. Sunyi haka ne don Suhaif ya gani ya shaida ni mayya ce, suka daura min jajayen kyalle a jikina, sai daga baya na ciccire. Suna fakon Suhaif sosai, sun kudiri niyyar sai sun kashe shi, saboda shine kadai ya rage mai takura musu da addu'a, shine bai tsane ni ba, bai rabu da zuwa inda nake ba. Babu makawa sun gama shirye-shiryen kashe shi tsaf a cikin daren dana ce masa ya kwana yana sallah yana addu'a kada yayi bacci. Da suka je zasu kashe shi suka kasa shiga inda yake balle su ganshi su kashe shi, sai suka kufula a daren kwana suka yi suna gana min azaba. Ban damu ba tun da mutuwa nake nema. Babu wadanda suka jawo min wannan matsananciyar rayuwa sai Mahaifana, tun farko da na hadu da Matsafan da sun hadu sun taru sun rabani dasu da karfin addu'a da haka bata faru ba, duk da nasan kaddara ce. Amma kowannensu addininshi daban, wannan yana jin haushin wannan, idan ya kawo mai addu'arsa yana ganin kara min ciwo ake, kawai sai rigima ta harde su, daga karshe suka kyaleni da ciwo yana bibiyata har girmana. Duk lokacin da waninku ya hadu da dangina ku shaida musu abubuwan da suka faru dani har izuwa mutuwata. Nasihata zuwa ga Mahaifana itace su dawo su rungumi addinin Musulunci, suma su mutu a cikinsa kamar yadda nima zan mutu Musulma. Iman ta rushe da kuka mai tsanani sai jama'a da dama a wajen tausayinta yasa su kuka suma. Cikin kuka ta dukar da kai kasa ta ce "Na gama labarina ku kasheni kamar yadda ku kayi alkawari, na gaji da rayuwar wulakanci da kyama da tsangwama a cikin *yan uwana. Kafin wani ya bude baki yayi magana, ganin Iman akayi ta daka tsalle ta fadi can gefe kamar wani ne yayi ball da ita. Sai ta tashi a gigice tana kallon wani gefe tana magana kamar a kwai wadanda take gani mutane basa gani. Cikin harshen Turanci take magana take cewa "Ku rabu dani, karku matso kusa dani, baku zaku kashe ni ba, ku bar *yan uwana Musulmai su kashe ni. Suhaif yana jin haka ya tashi da gudu ya fisgota ya kawota tsakiyar Malaman yana fassara musu abunda yaji tana fada da Hausa. Sai suka gane cewar matsafan sun zo su kasheta saboda ta tona musu asiri. Yanayin halin da suka lura Iman na ciki shine matsafan suna rike da ita suna shirin su kasheta. A gigice Suhai yake janta yana so ya kwace ta daga hannun matsafan duk da baya ganinsu yasan janta suke yi. Nan da nan manyan Malamai suka bude Alkur'ani suka fara karatu. Ba su kadai ba jama'a da yawa suka ruga gida suka dauko Alkur'ani cikinsu harda Najib ya kwaso Kur'anan gidab gaba daya. Suhaif ma ya karba aka zagaye Iman ana tayi mata karatu. Ta dora hannu akai, ta nutsa kanta cikin gwiwowinta kamar zata nitse cikin kasa, saboda tsabar tsananin zafin addu'ar da take kona matsafan da suke jikinta. Ta mika hannu da kyar ta kamo bishiyar dake kusa da ita ta kankame bishiyar da karfi tana yare wanda babu wanda yake jin yaren. Haka kuma bai hanasu daina ragargazarsu da ayar Allah ba. "Mu muna sonta tun kafin ta rungumi addininku. Ta fada cikin wata kakkausar murya wacce ko kusa bata yi kama da muryar mace ba, cikin harshen Hausa take magana yanzu. Wani Malami ya ce "Karya kuke makiya Allah yau sai munga bayanku azzalumai. Kamar yadda kuka kashe sai an kasheku. Ana ta karatu an zagaye bishiyar da ta rike ta rasa inda zata sa kanta, idonta yayi jajawur sai zufa take keto mata tamkar ana ruwan sama ta jike hagaf. Ta sake cewa "Kuna kona mu kuna kashe mana *ya*yanmu da jama'armu fa. Sai su kuwa masu karatun suka sake daga murya suna karatun da karfi. Ukuba tayi ukuba, zafin kuna yayi zafi, sai Iman ta fadi kasa numfashi sama-sama. Baisa sun daina karatu ba, ana ta jan ayoyi masu karfi. Matsafan ji suke kamar ana musu ruwan wuta. Yau sunga ta kansu sun gamu da gamunsu, a yau suka yi nadamar haduwa da Iman, sun yi dana sanin nacin da suka yi shekara dashekaru. Tuba suke, hakuri suke bayarwa daga yau zasu rabu da ita. Ko hanyar da tabi ma sun daina bi, amma tuba da nadamarsu yau baza tayi amfani ba. Babu mai sauraronsu, babu mai tausayinsu, babu mai shirin sassauta musu. Tun ana jin abinda Iman take fada har ta fara magana a hankali yadda ba'a fahimtar ta har tayi shiru bata ce wa komai ta rufe ido kamar mai bacci. Ba'a tsagaita da karatun ba yi ake tayi. Can Iman tayi magana wannan karon muryarta ce. Ta ce "Gaba dayansu gasu nan sun mutu, sun kone kurmus da wuta. Suhaif yayi ajiyar zuciya ya fada a baiyane "Alhamdulillahi. Ana ta karatun ba a daina ba har saida Iman ta tashi zaune daram tana kallon kowannensu daya bayan daya cike da mamaki. Sai ta tambayesu "Me yake faruwa? Suka tsaya da karatun itama suka tambayeta meya faru tsakaninta da matsafan? Ta yi shiru tana tunowa can ta ce "Na gansu suna ihu suna kamawa da wuta daga karshe suka fadi suka mutu, sun kone kurmus gaba daya garinsu ya kone kayan tsafinsu ma ya kone. Sai gaba daya *yan wajen suka yi kabbara. Malami daya daga cikin Malaman ya ce "Muna miki albishir kuma muna taya ki murna daga yau kin sami lafiya, kin rabu dasu har abada da izinin Ubangiji. Wannan wutar da kika gani tana konasu karatun da muka taru muka yi miki ne don haka mun konesu kurmus da ayar Allah. Iman taji dadin da tunda uwarta ta haifeta bata taba ji ba. Sai ta rushe da kuka tana godiya ga Allah. Wani Malami ya ce "To ai shikenan sai ta dauki kayanta ta koma gidan su Suhaif ta ci gaba da rayuwarta, ku kuma jama'ar gari kunji da kunnuwanku ba laifinta bane don haka banda tsangwama da kananan maganganu. Samun mutum irin Iman sai an tona a wannan zamanin. Ta sadaukar da rayuwarta, ta sallama rayuwar jin dadin duniya saboda ta shiga Musulunci. Sai kowa yayi kabbara. *Yan garin Doko gaba daya suka ji suna son Iman, saboda karfin Imaninta. Da gaske Iman take tana son Musulunci da *yan uwanta Musulmai. Yarinya mai kunya da ladabi, ko a hanya taga mutane zata yi musu sallama ta duka har kasa ta gaishesu. Haka jama'a suka gauraye wajen da yabonta. Suhaif yaji dadi sosai har kamar zaiyi tsalle don murna. Ya dauko jakar kayanta ya dauko mata takalmanta ya ce "Iman saka takalmanki ki zo mu tafi gida kiyi wanka, kici abinci ki huta kinji. Ta sharbe hawaye ta yi murmushin karfin hali ta ce "Na gode Suhaif Allah Ya saka muku da alheri kai da Iyayenka, *yan uwanka da mutanen Doko gaba daya. Ba zan kara ko kwana daya a garin nan ba, yanzu lokaci ne da zan koma gida wajen Iyayena in ga halin da suke ciki. Alhamdulillah abunda na zo nema na samu, na samu ilimin addinina. Zan iya kare addinina in kuma bada hujjoji masu karfi da za'a yarda abunda nake bautawa shine gaskiya. Hakika zan sami Iyayena in musu wa'azin da zai ratsa su, su karkato zuwa ga addinina musamman Mahaifiyata nafi ji, ta Mahaifina mai sauki ne domin yasan gaskiya karfinsa aka fi kawai. Ga Mama Tabita mai kaunata zan so ta kasance Musulma ba mushirika ba. Zuwana Kano da Doko na karu sosai, kuma a sanadiyyar haka na samu lafiyar ciwon da ya dade yana addabata. Malamai su ka ce "Ai haka ya yi gara ki koma garinku ko hankalin Iyayenki zai kwanta, kin bar gida shekaru biyu kenan. Wannan hukuncin bai yiwa Suhaif dadi ba ransa ya baci, jikinsa yayi sanyi, ya shiga damuwa. Baya son Iman ta tafi ta barshi. *Yan sanda suka ce to ta shiga motarsu, su kaita Kano sai su sakata a motar garinsu. Suhaif ya yi caraf ya ce "A'a ku barta gobe zan kaita Kano in sakata a motar garinsu. Babansa yayi wuf ya katse shi ya ce "A'a ka bari tunda ga masu tafiya ka bari a kaita yau mana. Kafin Suhaif ya sake magana Iman har ta shiga mota, dan sanda daya ya karbi kayan Iman a hannun Suhaif ya saka a mota. Malamai suka shiga motocinsu, *yan sanda ma suka shiga, kafin aja motar *yan garin suka baibaye jikin wundon da Iman take zaune suna tayi mata sallama da fatan alheri. Iman tana hawaye tana mika musu hannu suna musabaha da bankwana ko rai kanga rai. Zubaida da Naja'atu suka zo wajen Iman, sai kuka ya kece musu su duka ukun. Zubaida tayi karfin hali ta ce "Iman ki yafe mana abubuwan da muka yi miki, baki taba yin fushi ba, baki taba kai kararmu wajen wani ba, bakya gaba damu. Cikin kuka Iman ta ce "Na yafe muku tuntuni Zubaida ku yafe mun nima. Suhaif da Najib suka karaso jikin wundon Iman, sai kuka ya sake barkewa Iman ganin hawaye daga idanuwan Suhaif. Suhaif yayi karfin hali ya ce "Iman tafiyarki zata iya haddasamun abubuwa guda biyu, na daya zan iya rasa jin dadi a rayuwata har abada, na biyu zan iya kamuwa da ciwon rashinki har ya ja in iya rasa raina saboda damuwa. Iman karki tafi ki barni. Ta ce "Suhaif karka damu, kada rashina ya haddasa maka ciwo, Allah ne ya hada mu, kuma shine zai raba mu a yau. Shine kuma idan Ya so da izinin Sa zamu sake haduwa. Zai yi wuya in manta da kauna da halaccin da kayi mun a rayuwata, babu wani mahalukin daya taba sadaukar da rayuwarsa a kaina irinka. Ka soni a lokacin dana zama abar tsana, abar tsoro, abar gudu. Ina sonka nima bazan daina ba ko zai zamanto bazan sake ganinka ba har karshen rayuwata...... Ba ta karasa maganarta ba aka ja motar suka tafi. Tana hangen Suhaif yana ta bin motar da gudu yana ce wa "A tsaya! A tsaya!! Kuka mai zafi ya rufto musu ita dashi. *Yan gari suna ta dagawa Iman hannu har saida suka daina hango motar. Gwaggo da *yan matanta kuka suke tukuru na rabuwa da Iman. Haka jama'a da yawa basu shirya yin kuka ba, amma sai suka ji hawaye ya kece musu saboda bakin cikin tafiyar Iman. Sabo turken wawa, Iman ta shiga ransu sun saba da ita, ta saba dasu. Zaku tausayawa Suhaif idan ku kaga halin da yake ciki, a cikin kasa ya zauna turmus yana damkar sawun tayar motar da Iman take ciki. Najib ya dade yana bashi baki amma kamar zugashi yake. Kowa ya watse ya barsu shi da Najib a wajen. Suhaif yaki tashi su tafi shi kuma ya kasa tafiya ya barshi, Suhaif sai rokon Najib yake Allah Annabi yake, ya tafi ya kyale shi anan shi ba zai koma gida ba, Najib yaki tafiya. Baba ya fito sallah Masallaci ya hangosu a zaune sunyi jugum-jugum ya zo ya same su, ya tambayesu me suke yi. Najib ya fada masa abunda yake faruwa. Ya shiga bawa Suhaif baki akan yayi hakuri ya manta da Iman Allah zai iya bashi wacce tafi ta. Suhaif yana dagewa shi fa Iman yake so gashi bai karbi adireshinta na garinsu ba, babu inda zai ganta. Haka Baba da Najib su kayi ta lallashin Suhaif da kyar Suhaif ya tashi suka nufi gida. Iman ta tafi tabar Suhaif da tunaninta, begenta da tsantsar kaunarta. Baya walwala, baya son shiga mutane balle yayi hira dasu daga Masallaci sai dakinsa. Abincinsa kuwa idan yayi cokali daya, biyu, baya iya yin na uku sai yaji ya kasa ci. Babu abinda yake yi sai tunaninta wani lokaci ya debo wasikunta da hotunanta yana kallo. Sai ka ga hawaye ya surnano masa saboda tsananin damuwa. Abunda yafi tsaya masa a rai, shine irin wahalhalun da tasha a rayuwaarta shima yasa yaji ya kara sonta yana kuma tausaya mata yadda rayuwarta zata ci gaba da kasancewa bayan rabuwarsu. Yana ganin abu daya zai sa hankalin Iman ya kwanta a rayuwarta shine idan Allan Ya bata miji na gari mai tsoron Allah, mai sonta tsakani da Allah. Wannan mijin kuwa ba kowa bane illa Suhaif. Ina son Iman tamkar yadda nake son rayuwata, yadda bazan iya wulakanta rayuwata ba haka bazan wulakanta rayuwar Iman ba. Allah ka bani Iman. Ina zan sake ganinki Iman? Na rasa Iman na rasa mace ta gari, mai kirki, mai addini, mai kunya da tsananin tsoron Allah. Suhaif yana fada yana kuka. Najib bai daina yiwa Suhaif nasiha ba har lokacin da ya shirya ya koma Kano. Mahaifan Suhaif basa jin dadin yanayin damuwar da Suhaif yake ciki. Suna ta bashi baki da nasiha kala-kala. Daga karshe Mahaifin Suhaif ya bashi shawara ya shirya ya koma Kano ko hankalinsa zai fi kwanciya, har Allah Yasa aikin da ake nemar musu ya fito. Suhaif bashi da zabi yasan Kano da Doko duk daya ne tunda ba Iman zai gani ba. Bai ki yarda da shawarar Mahaifinsa ba, ya shirya kayansa kakaf ya tafi Kano. Can ma bata sauya zani ba cikin damuwa yake, amma yana samun dan sanyi a ransa tunda koda yaushe Najib yana tare da shi dakinsu daya, su kwana su tashi tare. Ko zasu yi fada Najib bazai fasa fada masa gaskiya ba, yana cewa wannan damuwar daya saka a ransa babu abinda zata kara masa illa ciwo. Iman dai ta tafi zai yi wuya ta dawo dan haka gara ya barwa Allah komai, idan Allah Yaso zai sake hadasu kamar yadda itama Iman din ta fada sai su hadu. Tamkar dalmar wuta kalaman Najib suke yiwa Suhaif a zuciya, su Suhaif da Najib suyi ta fada wai dan me zai ce ya daina damuwa Iman ta tafi kenan. Daga baya Suhaif ya fara yadda da zancen Najib gaskiya ne babu alamar dawowar Iman, gashi wata da watanni. Sai ya fara bawa zuciyarsa hakuri yana daddaurewa yana fita wasu harkokin. Baba Usman Mahaifin Najib ya shigo da wasu motoci guda biyu iri daya kalace kawai suka banbanta, daya kalar ja, daya kuma shudiya ce, motocin sababbi dal-dal a ledarsu, irin na zamani da kowanne matashi mai ji da kudi ko Mahaifinsa mai ji da Naira yake mafarkin samunta. Aka yiwa Najib da Suhaif albishir cewa ta su ce. Wai!! Wayyo Allah Najib yaji dadi har da ihu. Suhaif ma ya ji dadi sosai, suka je wajen Baba suka yi godiya suna baiyyana farin cikinsu. Baba yafi su jin dadi ganin yayi musu gwaninta kuma wadanda yayi dominsu sun gode. Wai meya sanya wasu suke cewa ba'a tashi inda aka tsaya ne? Wa ya fada musu ana tsallake? Gimbiya Zarah Matawata kenan ta ce ta ji dadi da ba'a mance da ita ba a wannan dandali..... lolxxx :::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI A falon Baba suka hadu ana ta hira, wasa da dariya ga Mahaifiyar Najib itama tana taya su godiya. Ta ce "Baban Najib sauran *yan matan Naja'at da Zubaida gashi suma kwanan nan zasu fara zuwa B.U.K kamata yayi suma a saya musu *yar karamar mota irin ta *yan mata koda guda daya ce su biyu a daukar musu direba ya koya musu. Bai musa mata ba sai ya ce "Suma na aika Germany a cikin motocin da za'a auno min za'a taho dasu Civic kowacce tata daban saboda idan ma aure suka yi su tafi da kayansu gidan mijinsu. Gaba daya falon ya hargitse da murna. Suhaif ya sake dukawa yayi godiya ya tashi ya nufi dakinsa, yana murmushi a baiyane kada a gane labarin da yake zuciyarsa. Hakika Suhaif yaji dadi sosai da wannan abun arzikin da Baba na Kano ya birgesu shi da *yan uwansa, amma babu wacce ta fado masa sai Iman dama da ita zasu ci arzikin nan tare, yaji a ransa dama Iman tana nan su shiga motar tare, a zahirin gaskiya yaji baya son motar nan tun da ba Iman. Sai ya ji kuka ya kamashi ya kulle kansa a daki ya sha kukansa shi kadai yayi ya gaji. Bayan Doko daya tuka yaje ya nuna musu ya dawo babu inda yake hawa motar yaje kullum yana gida a kwance a daki. Ba kamar Najib ba ai shi tun ranar da aka danka masa mukullin motar idan ya fita da safe sai da yamma zai dawo ya ci abinci, yayi wanka, ya canja kaya ya sake fita sai karfe goma na dare kuma. Har yawon Najib ya fara damun Mamarsa tana masa fada tana masa misali da dan uwansa Suhaif baya fita ko ina kullum yana gida. Don an saya maka mota cewa akayi ka fita yawo da abokai? Sannan Najib ya fara dan zama a gida. Shi dai Suhaif ya zama tamkar mutum-mutumi a gidan bashi da tunani, bashi da abun yi sai ina zaiga Iman? Dama ya ganta, ko a wanne hali take ciki yanzu, yaya za ta kasance da Iyayenta? Aikinsa kenan tunaninta. Suhaif na kwance kan gadonsa, daya daga cikin masu aikin gidan ta kwankwasa masa kofa ta ce da shi ya zo Baba na kiransa. Ya tashi ya nufi falon Baba ya iske shi shi kadai bayan sun gaisa ya tambaya "Ina Najib? Suhaif ya ce "Baya nan, Baba ya gyara zama ya shaidawa Suhaif cewar Naja'at da Zubaida sun sami admission a B.U.K. Zubaida ta sami Geography, Naja'at kuma Biochemistry. Suhaif ya yi murmushi gami da yi musu addu'ar fatan alkhairi da sa'ar farawa da gamawa lafiya. Sai Iman ta fado masa arai saboda su uku suke tare, gashi su biyu zasu fara Jami'a ya yiwa Iman sha'awar dama da ita. Jikinsa yayi sanyi idonsa ya ciko da kwalla amma bai bari Baba ya gane ba. Baba ya ci gaba da cewa "Don haka ka shirya kaje Doko ka dauko su Naja'at domin an ce min har an fara bayar da admission letter. Suhaif ya amsa da "To Allah Ya kaimu goben, sai Baba ya sake cewa "Ga wani sabon albishir din, na so ace kai da Najib kuna tare ku bani goran albishir. Suhaif ya tattara hankalinsa gaba daya yana sauraran abinda Baba zai fada cike da zumudi, babu abinda yake fata irin dama ya ce masa Iman ta dawo Doko. Amma sai ya tuna ashe Baba na Kano bai san Iman ba, sai dai Mama ta bashi labarin abubuwam da suka faru, da yake bashi da son labari a nan ya watsar bai sake tayar da maganar ba. Baba ya katse masa tunani ya ce "Kun sami aiki kai da Najib. Kai a Nigerian Port Authority Lagus, Najib kuma a Union Bank Kano Branch. Suhaif ya kurawa Baba ido yana kallonsa tamkar hoto. Wani tunani ne ya fado masa, yana tuna ranar da Iman ta hada masa takardunsa na neman aikin a wani file. Da hannunta ta rubuta masa takardar neman aiki da Baba ya ce su rubuta, ita kuma da kanta ta zaba masa inda zai zaba. Har Iman tana tsokanarsa tana cewa "Idan suka daukeka aiki a NPA kafin shekara ka zama mai kudin gaske, zaka yi mana wahalar gani sai mun cike form. Yau ga aikin ya fito amma Iman bata nan. "Kai lafiya, meke faruwa? Ka zama kamar gunki, tunanin me kake? Baba ya tambaya. Suhaif ya sunkuyar da kai kasa yayi shiru ya kasa magana, "Suhaif wai me yake damun ka ne, kwana biyu naga alamar akwai abinda yake damunka har ya shafi walwalarka baka son shiga mutane kullum kana kwance a daki shiru? Baba yake tambayar shi. Suhaif ya boye masa ya ce "Babu komai Baba, Baba ya ce "Akwai wani abu Suhaif, karka boye min ka fada min ko maye. Ko sai Baba na Doko kake fadawa matsalarka? Suhaif yaji zancen Baba banbarakwai yana nufin dai ko dan bashi ya haife shi ba. Suhaif da yaji haka sai yaga bari ya fada masa kada ya dauki wani abu daban. Sai ya gyara zama ya bawa Baba labarin Iman tun daga farko har karshe ya kuma shaidawa Baba son Iman ne kadai matsalarsa da damuwarsa. Baba yayi murmushi ya ce "Ai duk wannan ba matsala ba ce zamu je garinsu mu nemo maka auren Iman. Suhaif ya ce "A kwai matsala Baba saboda ban san adireshinta ba Baba. Baba ya gyada kai ya ce "Lallai tunda babu adireshi babu zuwa amma duk wannan ba zai sa ka ci gaba da damun kanka ba ka barwa Allah komai. Ya yiwa Suhaif nasiha kala-kala, ya bashi hakuri. Hakika Suhaif yaji dan sanyi-sanyi a ransa, yayi godiya ya tashi ya nufi dakinsa. Sun bar maganar aikin akan gobe za'a ci gaba da maganar idan Najib yana nan. Washe gari da sassafe Suhaif ya shirya ya fadawa Najib idan *yan gida sun tashi ya ce musu ya tafi Doko dauko su Zubaida. Najib ya tambayeshi "Lafiya? Suhaif ya amsa masa "Lafiya kalau munyi magana da Baba ne ya ce a daukosu sun sami admission a BUK. Najib yayi murna ya ce "Lallai yaran nan sun faso gari. Wai wa yaga idanuwansu a Jami'a? Suka yi sallama Suhaif ya fita, a motarsa ya tafi Doko. Da la'asar likis suka shigo Kano sun kuwa ci sa'a Baba da Najib suna gida, da Mama dukkansu zuna zazzaune a babban falo. Bayan sun gaggaisa suka tambayi lafiyar mutanen Doko. Sannan Baba ya sanarwa da su Zubaida cewar sun sami admission kuma ya aika Gemany a shigo musu da motocinsu, suka yi ta murna suna godiya. Ya juya ya dubi Najib ya ce "Najib kai kuma wata mai zuwa za ka je Jos yin interview, Suhaif kuwa sati mai zuwa zaka je Lagos domin tantanceku. Alhamdulillahi abun alheri ya samu lokaci guda, ina rokon ku dan Allah masu karatu ku rike karatunku ku mayar da hankalinku ku ci jarabawa, ku gama karatunku akan lokaci. San nan ku kuma da Allah Yasa ku ka gama karatun lafiya, Allah yasa ku ka sami aiki kuyi kokari ku rike aikinku, har Allah Yasa kuyi iyali ku rikesu. Mama ma ta ce "Gaskiya ku godewa Allah Ya kara budawa Mahaifinku, ya sassaya muku motoci, ya yi kokari ya samar muku aiki, matan kuma ya taimaka kun sami admission a Jami'a duk lokaci daya. Suhaif ya gyara zama ya ce "Haka ne, mun godewa Allah kuma mun gode muku, ku Iyayenmu da ku ka bamu ilimi. Kuma Insha Allah zamu rike aikinmu, ku kuma *yan makaranta ku san abin da ya kai ku jami'a, karatu ne ya kai ku ba zance da samari ba. Najib ya karba ya ce "Ku sani a jami'a zaku hadu da jama'a kala-kala kowa da dabi'ar gidansu, da al'adar yarensu don haka ku kiyaye ku san irin kawayen da zaku yi, ku guji mayaudaran samari, *yan matan suna amsawa da to. Bayan Suhaif ya koma dakinsa sai ya nemi bacci ya rasa ya shiga tunanin inda zaiga Iman shine matsalarsa, yayi tunani da kwakwalwarsa iya kokarinsa ya tankade ya bakace yaga kawai ba zai iya zuwa wajen aiki ba, domin rayuwarsa gaba daya ta sukurkuce saboda rashin Iman, babu aikin da zai iya a rayuwarsa. To amma ta ina zai kubce, ya ya zaiyi, wacce hujja zai bawa Baba akan ya rabu da shi ba aiki? Ana gobe ranar da za'a tantance su Suhaif a Lagos, tun da daddare Baba ya bawa Suhaif kudin Jirgin da zai tafi Lagos ya ce ya shirya da sassafe a kaishi filin Jirgi ya tafi. Ran Suhaif bai so ba amma ya rasa ta inda zai fara yiwa Baba bayani. Ya kwana yana juyi yana tunani, yaji a ransa ba zai iya lulukawa ya tafi har Lagos ba, ba tare da yaje neman Iman ba don haka ya yanke hukuncin da yaga ya dace da rayuwarsa. Kudin Jirgin da Baba na Kano ya bashi na zuwa Lagos da sauran kudaden ya hada ya daure a cikin jakar kayansa daya shirya tafiya Jalingo neman Iman ba wajen aikin zai jeba. Ya rubuta wasika ya ajewa Najib a kan gadonsa yayin da yake ta shakar bacci da sassafe misalin karfe bakwai. Al'adar gidan ce bayan sallar asuba sai a koma bacci, sai dai idan akwai mai uziri ya tashi ya shirya ya yiwa masu aikin abinci magana suyi masa nasa kalacin ya ci ya tafi, sauran kuwa sai sanda yunwa ta addabesu za kaga suna fitowa daya bayan daya. Daman Suhaif tun asuba yayi wanka ya shirya daya tabbatar kowa ya koma bacci haikan sai ya kinkimo jakar kayansa ya je ya saka a motarsa ya tashi mai gadi a hankali ya bude masa get in zai fita. Ya shiga mota ya na sanda ya kunna, ba tare da ya bata wuta ba, ya sulale ya fita don kar Baba yaji fitarsa. Misalin karfe goma sha daya Baba ya fito yana tambayar mai gadi "Ina Suhaif ya ce zai je ne tun karfe bakwai saura? Ashe ya ga fitarsa ta wundan dakinsa. Mai gadi ya ce "Bai fadamin inda zaije ba amma na ganshi da jakar kaya. "Jakar kaya, ina zaije da jakar kaya ba dai Lagos din zai tafi a mota ba, bayan na bashi kudin jirgi? Baba ya fada yayin da mamaki ya kamashi, Baba ya juya ya nufi gida da sauri ya shiga dakin su Najib shi ai zai san inda Suhaif din ya tafi, tunda bakinsu daya. Najib yayi dai-dai akan gadonsa yana shakar bacci bai san ma inda yake ba, sai da Baba yayi ta dukan hannunsa sanna ya farka. "Ina Suhaif? Baba ya tambayeshi. "Gashi can a gadonsa yana bacci. Najib ya fada cikin magagin bacci. Baba ya ce "Kai bude idonka. Ina Suhaif din yake? Ba ga gadon nasa babu kowa akai ba. Sai Najib ya tashi ya zauna yana murtsike ido yana soshe-soshe ya ce "To ban san inda ya tafi ba. Baba ya fusata ya fara fada yana cewa "Na fara gajiya da irin wannan rashin jin naku, kamar wasu kanana. To idan baku gyara halin nan naku ba zan cire hannuna akan ku kowannenku yaje ya nemo aikinsa. Yanzu yanzun nan daga Lagos aka yi min waya yau ake neman su Suhaif, tun jiya ya kamata yaje ya kwana acan yau litinin za'a tantancesu amma ya shiga mota ya tafi yawonsa kawai. Najib ya yunkura zai tashi sai yaji ya dafa wata takarda a gefensa, ya dauko ya bude yana karantawa sai mamaki ya kamashi gami da fargaba. Baba ya dube shi ya ce "Me aka rubuta? Najib yayi shiru can ya ce "Suhaif ne ya bar wasika ya ce ace maka ba zai iya aiki ba saboda tsananin damuwar da take damunsa ko ya fara aikin ma zasu gaji su kore shi. Don haka ya je nemo maganin damuwarsa shine ya tafi garin su Iman nemanta. Yadda ku kasan ruwan zafi ake watsa masa haka Baba yake jin labarin da Najib yake bashi. Sai ya hau balokoko yana fada, ya fito daga dakin ya nufi dakin matarsa itama ya hada da ita cewa yake laifin ta ne, ita ta sakarwa yaran suke abunda suka ga dama. Naja'at da Zubaida suma suka fito Mama ta kasa bawa mijinta hakuri saboda ransa yayi matukar baci. Suhaif dai ya kama hanya sai tafiya yake haikan ya tafi neman abar kaunarsa, ya bar *yan gida da shan fada ko ruwan shayi ya gagaresu kurba a safiyar yau, yau dai laifin wani ya shafi wani. Suhaif ya isa Jalingo da magaruba, baiyi wata-wata ba ya zabi hotel din da yake so ya biya aka bashi daki, bayan anyi masa odar abinci yaci yasha, sanna yayi sallah yayi wanka ya kwanta amma tunani da murna sun hanashi bacci. Murnar ita ce yau gashi a garin su Iman dan haka yana da 50% din tabbacin ganinta. Tunanin kuwa shine ta ina zai fara nemanta? Gari kamar Jalingo ace an zo neman mutumin da ba'a san inda yake ba. Shi ba attajiri ba, ba dan siyasa ba wanda da zarar an fadi sunansa kowa ya sanshi. Allah gani gareKa. Suhaif ya fada lokacin da yake ta juyi akan gado. Washe gari da sassafe Suhaif ya shirya ya fito neman abunda ya zo nema, da farko cewa yayi a nuna masa G.R.A. An kaishi G.R.A sunfi a kirga amma Allah baisa ya ci sa'ar ganin gidan su Iman ba. Ya yi kwatancenta, ya nuna hotonta, ya fadi sunayenta da ake kiranta dasu kakaf amma bai sami wanda ya santa ba. Har dare ya yi sanna ya koma dakinsa na Hotel ya kwanta, cike da bakin ciki. Haka washe gari ma da sassafe ya fita, amma yau wajen bauta ya nema ya dinga zazzagawa yana fadar sunan Mahaifiyarta da Mahaifinta basu sansu ba. Washe gari kuma ya nemi asibitoci yana tambayar Dr. Hani ko Allah zaisa yaga Dr. Hani ko a lokacin daya zukewa yaron Iman abu daga hancinsa ya rubuta adreshinta, bai samu inda Dr. Hani yake ba, anan ma har dare. Washe gari kuma kauyukan Mumuyawa ya yini, anan ne kuwa yafi shan wuyar banza. Ba sa jin yarensa, baya jin nasu, basu fahimci kalma daya ba daga cikin abubawan da yake tambayarsu. Sai suka zamar dashi a bin kallo, wasu kuwa ganin ya tunkaro su a mota sai su zura da gudu. Dole ya hakura ya dawo dakinsa na Hotel cike da takaici da dacin bakin ciki. Bai hakura ba sai ya shirya washegari ya nufi kasuwanni ko Allah zaisa yaga Iman, nan ma ya yini yana kallon masu saye da sayarwa babu Iman babu mai kamarta. Ranar da ya cika sati guda a Jalingo ya saduda ya hakura ya hada kayansa a jakarsa ya biya masu Hotel ya fito ya nufi hanyar Kano. Hawaye sharaf-sharafa fuskarsa saboda bacin rai gashi a garin su Iman amma ya rasa inda take. Ya iso Kano da misalin karfe shidda na yamma saboda irin gudun da yake zurawa don bacin rai, bai damu da ko motar zata fadi ba, ko yayi karo da wasu motocin, ya fitar da rai da son ci gaba da rayuwar duniya. Mai gadi yana bude masa get ya kutsa ya shigo cikin gida a fusace. Yaga *yan gida kakaf har da *yan Doko suna zazzaune a farfajiyar gidan, daga dukkan alamu tafiyarsa ta tayar musu da hankali, da rashin dawowarsa kwana da kwanaki. Ya je inda ake ajiye motoci yayi parkin ya dauko jakar kayansa ya rataya ya nufo inda suke ransa a bace yake kamar yadda yaga rayukan iyayensa a bace har da masu wurgo masa harara. Ya karaso inda suke ya duka ya gaishesu, babu wanda ya amsa masa, sai Naja'at da Zubaida ne suka yi masa sannu da zuwa Najib ma dauke kai yayi baya ma kallon inda yake. Shima sai ya share, zai wuce cikin gida, Mahaifinsa Baba na Doko ya daka masa tsawa ya ce "Kai sha-sha-sha ina zaka je ne? Da wo nan kayi mana bayanin daga ina kake, suhaif ya dawo ya tsaya yayi shiru bai ce komai ba. Baba na Kano ya ce da Suhaif "Zo nan gabana, Suhaif ya zo ya durkusa, suka fara masa fada su duka hudun wato har da Goggo da Mama, har ma baya gane abun da suke fada domin carin yayi masa yawa. Naja'at da Zubaida suka tashi suka shiga gida suka labe, saboda kada a gama masa fada ya huce a kansu, gannin wata uwar harara da yake jeho musu. Najib ma yake tsoma baki a fadan. Suhaif ya zabura ya ce "Dalla Malam ka rufe mana baki ka bar wadanda suka isa suyi min fadan ba kai ba, Najib ya ce "Ai gaskiya ake fada maka, gashi nan akan Iman ka rasa aikinka, wata kilama baka ganta ba. Baba na Kano ya ce "Ni dai ka kunyata ni, abokina ne manajan na rokeshi arziki ya daukeka aiki, ya kukuta ya soka ka amma shine ka gudu a ranar da ake nemanku. Baba na Doko ya ce da Suhaif "To kar ka shiga cikin gidan nan ka koma inda ka fito kaje can ta baka aikin tunda ka rasa wancan aikin da aka sha wuyar nemar maka, babu gidan wanda zaka je ka kwanta ana ciyar da kai. Suhaif ya ce "Kuyi hakuri dan Allah, nasan nayi laifi ku yafe min, Baba na Doko ya ce "Babu zancen hakuri wallahi sai kabar gidan nan yau, kuma kar ka je Doko, Suhaif ya mike ya saba jakarsa ya nufi wajen motarsa ya shiga. Uhmmm to jama'a Angon Matawata ya gaji da daddanna hannunsa. Sai na ce muku sai Allah Ya kaimu Monday, gobe da jibi kunsan "Weekend ne,,, ina tare da Matawata da Amaryata Zulaihatu... Lollxxxx. Reedwan Suraj Isma'il ::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Da alama wannan hukunci da Baba na Doko ya yanke akan Suhaif bai yiwa kowa dadi ba musamman Mahaifiyar Suhaif, sai ta fashe da kuka tana cewa "Idan bai zauna a nan ba, bai je Doko ba ina zai je? Baba na Doko ya ce "Ina ruwana ya koma garinsu Iman. Baba na Kano ya yunkura zaije ya tsayar da Suhaif kada ya tafi Baba na Doko ya jawo shi ya ce ya koma ya zauna tunda ya rantse sai Suhaif ya tafi. Mama da Najib suka dinga rokar Baba na Doko yayi hakuri yabar Suhaif tunda yayi nadama ya ce yayi kuskure a hakura. Baba na Doko ya ce "Da gangan yayi, yayi tafiyarsa, dadi ne yayi masa yawa yana daga kwance ake ciyar da shi shiyasa bai san zafin nema ba, amma idan ya je yasha wuyar nema, gobe idan an samar masa aiki ba zai yi masa rikon sakainar kashi ba. Suhaif ya ja motarsa ya fice ba tare da yasan inda zai tafi ba. Bakin ciki goma da ashirin, yana ta yawo a gari daga wannan titi zuwa wancan, har karfe tara da rabi na dare sannan ya tuna da wani abokinsa Rabi'u wanda suka gama makaranta tare yanzu yana lecturing a B.U.K, yana zaune ne a staff qauters na B.U.K. Suhaif ya nufi gidan Rabi'u ta ci sa'a kuwa ya same shi daman bai yi aure ba, kai tsaye ya shiga gidan. Rabi'u ya yi murna da ganin Suhaif musamman da ya ce masa kwana ya zo taya shi. Sun dade suna hira sannan suka gangaro hirar dalilin daya kawo shi, Suhaif ya zaiyana masa labari kakaf. Rabi'u yayi masa fadan bai kyauta ba, dan me zai bar aikinsa ya tafi dole hankalinsa ya tashi. "Yanzu meye abun yi? Rabi'u ya tambaye shi. Suhaif ya ce "Bazan koma gidanmu ba saina sami aiki saboda haka gobe da sassafe zan bar garin nan duk inda aiki yake zanje in samu. Rabi'u ya bawa Suhaif shawara ya zo suje gidan gobe ya taya shi bawa Iyayensa hakuri tunda suna da hanya zasu iya samar masa wani aikin. Suhaif ya cewa Rabi'u ya manta da zancen bawa Iyayensa hakuri, domin ba zasu sauraresu ba, shi dai zai kara gaba neman aiki. Daga karshe Rabi'u ya bawa Suhaif shawarar yaje Lagos wajen abokin Baba wato M.D na port Authority ya duba yaga ko akwai yadda za'ayi a saka sunansa a cikin wadanda su kayi interview saboda akwai sanayya zai taimaka. Suhaif ya yarda da shawarar Rabi'u, ya yarda goben zai shirya ya tafi Lagos. Washe gari da sassafe Suhaif ya shirya, bayan sun karya kumallo sai ya yiwa Rabi'u sallama, Rabi'u yayi masa fatan alheri da fatan Allah Ya kiyaye hanya. Suhaif ya kama hanyar Lagos tafiya yake ba ji ba gani, ya isa cikin dare sai ya wuce ma'aikatar N.P.A. A cikin motarsa ya kwana, da gari ya waye ya shiga Masallacin kusa da nan yayi sallah, da ma'aikata suka fara zuwa wajen aiki sannan yayi kokari aka yi masa iso wajen Manaja. Duk da sanin da Manaja ya yiwa Suhaif sai da ya sake tambayarsa "Daga ina? Suhaif ya gyara zama ya yi masa bayani. Manaja ya bata rai ya ce "Na gane ka ai, meke tafe da kai? Ai kasan mun gama tace wadanda zamu dauka ko? Infact na kira Babanka several times cewar ya ban ganka ba, tun yana boye mun har ya fada mun gaskiya cewar an rasa inda ka tafi baka son aiki. Suhaif ya hau soshe-soshe ya ce "Ranka ya dade nasan nayi kuskure, and I realize my mistake, am sorry ran Iyayena ya baci har sun ce in bar musu gida. Sun ce in je in nemo aiki da kaina, dan Allah a taimaka min ranka ya dade. Manager ya yi sauri ya ce "Actually nayi iya kokarina in baka aiki kaine kaki, yanzu ba yadda zanyi maka kayi hakuri. Suhaif ya rike kai ya yi shiru. Manager ya ci gaba da cewa "Naga alama a gajiye kake bari in sa direbana ya kaika gidana ka huta. Suhaif ya ce "Na gode Baba kamar kasan a gajiye nake na yini na kusa kwana ina tafiya. Bayan Suhaif da direba sun tafi gida, Manager ya kira Baba na Kano yake shaida masa ga Suhaif ya zo, ya zaiyana masa duk yadda su kayi aiki dai babu sun gama dauka. Baba na Kano ya roki Manager ya taimaka ya ajiye Suhaif a gidansa tun da akwai wajen ajiye baki ko Allah zai jeho wani aikin daga wani bangaren. Manager yana ganin mutuncin Baba na Kano ba zai iya kin yi masa duk abunda ya tambayeshi ba, ya amsa da "Ba damuwa za a binciko Insha-Allah ko a wani bangaren ne. Suhaif yana zaune a gidan Manager har na tsawon wata biyu babu abinda yake yi sai kwanciya, babu aiki babu alamarsa. Sai dai Suhaif yana taimakawa Manager akan harkokinsa, yana aikensa wurare kuma yaje ya aiwatar masa da duk abunda yasa shi babu kuskure. Idan harkar kudi ne kuwa babu munafunci, ko kwabo ba zai dauka ba. Da gangan Manager yake hana Suhaif kudin kashewa kuma yasan bashi da kudi, yana son gwada hankalinsa ko zaice duk wannan wahalar da nake yi masa bai biyani ba, ko kuwa zai rinka rage kudin da yake aikensa. Sai yaga Suhaif ba haka yake ba kuma bai damu ba. Dan haka Manager ya cure Suhaif ya kudiri niyyar nemar masa aiki ko a wane waje ne. Amma a hirar da suke da Suhaif ya bugi cikinsa yaji ra'ayinsa game da aiki. Suhaif ya nuna baya son aiki kwata-kwata saboda a fadarsa yana da matsalar da ta dami zuciyarsa baya so ya fara aiki ya je ya zauna a office yana tunani ya kasa aikin yadda ya kamata. Da dai zai sami jari yayi business ko kwangila da yafi so. Duk da Manager bai gane damuwar da Suhaif yake ciki ba amma ya kudira a ransa zai yiwa Suhaif yadda yake so. Zai bashi kwangila da kuma kudin da zai yi kwangilar tunda bashi dasu. Suhaif na zaune a bangaren da aka sauke shi a gidan Manager, shi kadai yana tunanin abar kaunarsa kamar yadda ya saba wato Iman. Ya ji wayar dake ajiye a gefen gadonsa tayi ruri ya dauka da sauri. Manager ne yake magana ya ce da Suhaif ya zo office ya same shi. Suhaif bai bata lokaci mai yawa ba ya je ya sameshi a office. Manager ya mika masa takardun wata kwangila mai tsoka ya ce "Ga wannan taka ce. Suhaif ya hau dogon tunani "Ni da bani da ko sisi ya zanyi in yi kwangilar miliyoyi? Manager ya bashi amsar tunaninsa "Mu zamu ranta maka kudi kayi, sannan mu biya ka akan lokaci "Tsarki ya tabbata ga Allah (S.W.A). Suhaif ya fada yayin da ya sulale ya zauna dan murna da mamaki, lallai wannann shine arziki a dare daya. Allah mai azurta duk wanda Yake so a duk lokacin da Ya so. A cikin shekara daya Allah Ya azurta Suhaif fiye da tunanin mai karatu. Kwangilolin da yayi ta yiwa port Authority ake biyanshi akan lokaci ya sami makudan miliyoyi. A shekara ya kama hadadden gidan haya duplet a unguwar manya (victoria island) wanda kudin hayar ma kadai zai iya siyan wani gidan. Kafin ya samu a hankali ya binciko inda zai sayi fili ya gina gida irin wanda ya keso, a garin da ya keso, da unguwar da yake so. A lokacin Suhaif ya canja mota kirar zamani wacce ake tsakiyar yayinta a lokacin. Nan fa Suhaif yaga ikon Allah da abunda yafi karfin idonsa, wato cincirindon *yan mata da suke sonsa HAR DA SU WA'E . Shi kuwa basa burgeshi ko daya baya son su, soyayya bata gabansa har yau har gobe Iman ce a zuciyarsa. Ya hado tara ta arziki ya zo ya gaishe da Iyayensa, a Kano ya sauka. *yan gidan sun sha mamakin yadda Suhaif ya zama a shekara guda. Duk da bai yi kiba ba amma yayi fari, kallo daya zaka yi masa kasan yana cikin daula, ni'ima da wadata. *Yan gidan gaba daya sunyi farin ciki da zuwan Suhaif, saboda sun dade basu ganshi ba. Yana musu gizo kamar ba shi ba. Gara Baba na Kano, Baba na Doko da Najib sunje Lagos sun ganshi kwanakin baya, amma Mama, Goggo, Naja'at da Zubaida shekara guda cur kenan basu ganshi ba. Shima farin cikinsa baya musaltuwa dan haka nema ya sakarwa kannensa fuska ya daina musu muzurai. Har a kwano daya suke cin abinci shi da Naja'at da Zubaida, bayan zama akan kujera daya ana wasa da dariya har yana tsokanarsu wai ina samarinsu, bayan manya-manyan leshina daya siyo musu, mamaki ya ishi Zubaida da Naja'at ganin yadda Suhaif ya sauko wanwar. Kwanan Suhaif biyu a Kano sannan ya shirya ya ce zai je Doko ya kwana biyu. Najib ya so su je tare amma shi yanayin aikinsa na Banki ke hana shi sukuni. Wata raba har asabar da lahadi ma sai sun je banki. Suhaif cikin dandatsetsiyar motarsa ya isa kofar gidansu na Doko. Tuni kafin ya fito daga mota matukar mamaki ya rufeshi a lokacin da ya yi ido biyu da motar Zubaida a kofar gidansu. Yana fitowa direban gidansu Zubaida ya taso da sauri ya zo ya karbi jakar hannun Suhaif gami da yi masa sannu da zuwa. Cikin fara'a Suhaif ya tambaye shi "Malam Dauda yaushe ka zo, ba dazu-dazun nan na ganka a zaune a kofar gida ba a Kano? Malam Dauda ya yi dariya ya ce "Ranka ya dade ai kana fitowa mu ma muka fito muna binka a baya, sai kayi hanyar cikin gari mu kuma muka zarto nan. Isowarmu kenan Allah Yaja zamaninka. Suhaif ya ce "Kai dawa ku kazo? Malam Dauda ya ce "Ai Hajiya Zubaida na kawo, ai da niyyar makaranta zan kaita muka fito sai kawai ta ce in kawota nan ta fasa zuwa makarantar. Suhaif ya yi shiru mamaki ya rufeshi ya yi minti biyar bai motsa ba, ya kurawa kofar gidansu ido kawai yana tunani yana tambayar zuciyarsa. "Shin me Zubaida ta zo yi Doko da rana tsaka ba tare da ta fadawa kowa ba? Kada fa a ce zancena ta zo yi, son da take yi min bata hakura ba? Malam Dauda ya katse masa tunanin da ya ke, ya ce "Ranka ya dade a shigar da jakar nan ciki? Suhaif ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ka kai ciki ka ce musu zan je in gaishe da Hajja Kakata zan dawo yanzu. Malam Dauda ya amsa ya nufi cikin gida. Abokan Suhaif, *yan uwa da yaran unguwa suka zo suka kewaye shi suna kwasar gaisuwa gami da taya shi murnar sayen wannan dalleliyar mota. Sun cika da mamakin ganin yadda Suhaif ya zama gagarumin mai arziki a shekara guda, tare da sha'awar dama sune Suhaif ganin yadda yayi kyau yana kyalli shi da kayan jikinsa. Suhaif baya kyamarsu, baya daga musu kai ko dan saboda yayi kudi, kamar yadda suke da, haka suke hira suna musabaha. Ko wannensu da irin nasa kokekoken da suke kawowa Suhaif. Wannan ya ce matarsa ta haihu bashi da ragon suna. wancan ya ce gidansa ya burma, katanga ta dare. Wadansu basu da na cefanu ga iyali ga yara kanana. Suhaif ya amsa musu da cewa da izinin Allah zai taimaka, amma ba yanzu ba su dawo gobe tunda yana gari har kwanaki uku. Da yawa suka shige motarsa wai zasu rakashi inda zaije. Suka dunguma suka nufi gidan Hajja. "Oh *yar Hajja ke har yanzu babu ci gaba a tattare dake balle ki waye kina nan jiya iyau. Suhaif ya fada tun kafin ya fito daga mota. Ya na fitowa daga cikin motarsa ita kuma tana kofar gida tana suyar wainar fulawa ta sayarwa. *yar Hajja ta bude baki tana kallon motar da mai motar dan bata gane shi ba har yanzu. Ta zabura ta tashi da sauri ta ce "Lah Babangida kaine? Haka ka zama? Ba'sabanba, kudi kayi? Suhaif ya tuntsire da dariya ya ce "Ni fa nasan kullum a rana sai kin ambaci kudi yafi sau dari saboda tsabar son kudinki. Ta zura cikin gida da gudu ta shaidawa Kakarta cewar ga Babangida ya zo. Suka yo waje su duka, Hajja tayi murna da ganin jikanta har da kukan dadi. Suhaif ya jawo hannun Kakarsa suka shiga gida. *yar Hajja kuwa jikinta na rawa taje ta kashe wutar wainar, tasa yara suka tayata ta shigo da kayan cikin gida. Ta fasa wainar tunda taga Babangida dole zai bata kudi, ko bai bata ba zata warta. Bayan sun gaggaisa, Hajja tayi masa fada bai kamata ba ya tafi Lagos ya shekara guda cur bai zo gida ba ganin Iyayensa da *ya uwansa, musamman ita tsohuwa wacce ake saka mata ran mutuwa yau ko gobe. Ta bashi shawara ya rage fushi da zuciya da zafin rai irin nasa, ya yi hakuri da rayuwar duniya. An bani labarin duk yadda akayi Babanka ya koreka, amma tunda Baban naka yayi nadama yaje har Lagos din ya ce ka zo gida ai sai ka zo. Anan Mahaifiyarka take zuwa ta zauna, ita kuka ni kuka tana cewa ita Lagos din zata bika idan shekara ta cika baka zo ba. Suhaif ya amsa laifinsa kuma yayi mata alkawarin zai yi amfani da shawarar da ta bashi. Albishir na farko daya fara fadawa Hajja shine ta shirya da ita da *yar Hajja da su za'ayi aikin HAJJI bana in Allah Ya so. Kuma idan *yar Hajja ta sami miji ayi masa magana ko tsinke kada wani ya saya shi zaiyi komai na aure. Sannan kafin su dawo daga Hajji zai sa a rushe wannan gidan nata na kasa a mayar da shi na siminti. *yar Hajja ta daka tsalle ta dira tana murna, Hajja kuwa sai ta rushe da kuka tana godiya. Nan dai Suhaif ya fito ya barsu sun rikice kamar zasu suma don murna. Da kyar ya samu ya lallashi dinbin jama'ar da suke jiransa a kofar gida sun kewaye motarsa, ya basu hakuri akan yanzu ya shigo garin amma su sameshi da daddare a gida. Ya shigo mota ya nufi gidansu. Ya iske babu motar Zubaida a kofar gidan, babu Malam Dauda da alamar sun tafi. Ya yi sallama ya shiga gidansu ya iske Mahaifiyarsu a tsaye a tsakar gida ta yafa gyale. Mahaifinsa kuwa a zaune akan kujera. Suhaif ya tambaya "Goggo unguwa zaki je ne? Ta harareshi ta ce "Unguwa wacce iri? Ance mun ka zo tun dazu ka aiko da jakarka ban ganka ba, na leka kofar gida aka ce mun ka sake shiga mota ka tafi, shine zan fita in tambaya ina aka ga ka nufa. Babangida meyasa kake yin haka ne? Ka shekara cur ban ganka ba, sannan ka zo garin amma ka sake tafiyarka. Suhaif ya ce "Malam Dauda bai fada muku ba? Na ce ya ce muku na tafi gaishe da Hajja. Mahaifin Suhaif ya ce "Kin gani ai, na fada miki yaran yanzu basu damu da Iyayensu ba. Iyayen ne suka fi damuwa da su. Goggo ta ce "A'a Babangida ba haka yake ba, bacin rai ne yasa shi yin hakan amma da haka kawai ne ba zai shekara bai zo gida ba. Suhaif ya karkade kujera ya zauna yana sauraronsu. Bayan Goggo ta sami waje ta zauna Suhaif ya durkusa ya gaishesu. Suma abu na farko da suka fara masa fadan shine danme ya shekara bai zo gida ba. Suhaif ya basu hakuri, yasan ya yi kuskure su yafe masa. To fa! Cafdi!! Rigiji gabji!!! Budar bakin Mahaifinsa keda wuya sai ya ballowa Suhaif wani danyen aiki. Da ya fesa masa labarin da yake tafe da Zubaida. Baba ya ce "Da kuka Zubaida ta shigo mana wiwi a zaton mu ma wani ne ya mutu a Kano. Mahaifiyarka kuwa tuni ta zata kaine kayi hatsari tunda an ce mana gaka nan zuwa. A gigice muka tare ta muna tambayarta "Waye ya mutu? Ta ce "Ba mutuwa aka yi ba, bayan mun lallasheta, ta daina kukan muka takura mata da tambaya meya faru sai take shaida mana cewar Babanta ya ce zai musu aure. Naja'at tana da saurayin da take so itama Zubaidar tana da saurayi amma bata sonshi kai take so. Suhaif ya yi shiru ya sunkuyar da kai kasa tamkar ruwa ya cinye shi, ya kasa magana. Goggo ta ce "Ban da abun Zubaida wannan ai ba abun daga hankali ba ne, tuwo na maina. Na san kai ma zaka fi son hakan *yar uwarka, jininka. Mun ce mata ta kwantar da hanakalinta insha-Allah ba zaka koma Lagos ba sai da daurin aurenku. Suhaif ya zabura ya mike tsaye kamar cinnaka ne ya cijeshi. "A'a kai! Lafiya kake zubure-zabure kamar kayi gamo? Baba ya tambayeshi "Allah Ya kyauta "Suhaif ya fada yayin da ya dauki jakarsa ya nufi dakinsa dake zauren kofar gida ya bar Mahaifansa suna kallon-kallo. Suhaif kwance yake akan yaloluwar katifarsa yana tunanin mafita "Kai babu mafita Zubaida tayi min da baibaiyi da sakar karfe mai wuyar tsinkawa. Wanda hakori ko wuka ba zasu iya cizgewa ba, da dai na tsumma ne, inji zuciyar Suhaif. Ba na son in auri Zubaida, ina sonta a matsayin na kanwa, bana so ta tsinci kanta a matsayin matata saboda zata wulakanta, zata sha wuya ba zata samu soyayyata ba. Tamkar GANGAR JIKINA ZA TA AURA, zuciyata da ruhina yana wajen Iman har abada. Kamar na Ramla da Haisam, Suhaif ya fada a baiyane. Nima dai na ce GANGAR JIKINSA zata aura zuciyarsa da ruhinsa yana ga Iman. Ehem anya ba zamu sasanta da Suhaif ya ce a aura min Zubaida a MADADInsa ba? Reedwan Suraj Isma'il 08097365237 @watsapp :::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Da daddare a tsakar gida Suhaif da Iyayensa suna cin tuwo suna hira. Baba ya sake tuntubar Suhaif da zancen Zubaida sai Suhaif yaji ya kasa kai lomar dake hannunsa bakinsa, yayi shiru bai ce komai ba. Goggo ma tasa baki suna ta yi masa nasiha, suna nuna masa alhairin hakan. Yana jin nauyi, yana jin tsoron bacin ran da zai afku a zuciyar Iyayensa idan suka ji amsar da zai fada. Amsar ita ce "A'a bana so. Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce "Ka fadi alhairi ko kayi shiru. Dan haka Suhaif ya yi shiru bai ce musu komai ba. Yaran unguwa ake ta aikowa daga kofar gida "Wai Suhaif ya zo inji abokansa. Ya san mutanen da ya yiwa alkawari ne, suka taru a kofar gida. Ya ce da *yan aike su ce musu yana zuwa. Hajja da jikarta suka shigo da kuka, hankalin Mahaifan Suhaif ya tashi Goggo ta tare su da gudu tana tambaya "Waye ya mutu? Suhaif bai damu da yasan dalilin kukan ba, ba zai wuce godiya suka zo yi ba. Ya je ya wanke hannunsa a wajen rijiya. Hajja ta ce "Ba mutuwa aka yi ba godiya muka zo muyi, dadi ne yayi mana yawa har muka yini muna kuka. Suhaif ya tuntsire da dariya ya ce "Shegiya *yar Hajja kema har dake kukan? Bari in haskaki da fitila, na san kukan karya kike yi. Hajja ta ce "Ni na ce tayi kuka ko ba hawaye saboda wannan abun arzikin yafi karfin mu shigo ba kuka. Suhaif ya kwashe da dariya yayi ta dariya har cikinsa yayi ciwo, ya fice kofar gida wajen abokansa, bayan ya shiga dakinsa ya ciko aljihunsa da kudin da zai raba musu. Hajja ta mike kafa ta zaiyana musu abun arzikin da Suhaif yayi musu alkawari. Iyayensa su ka ce su basu ma sani ba, bai fada musu ba. Sun ji dadi sosai har fiye da Hajja da jikarta, yau ga dansu ya zama mutum yana abun alkhairi da dukiyarsa. Suka hadu suna ta shi masa albarka. Suhaif bai dawo gida ba sai da misalin sha daya na dare. Shi da abokansa sun nutsa cikin gari gaishe-gaishen *yan uwa da abokan arziki da aka dade ba'a haduba. Har Garki suka je wajen Babbar yayar Mahaifinsa Iya Furera. Itama ta yi masa kukan danta zai yi aure kuma bashi da kudin hada lefe. Suhaif ya yi alkawari zai hado masa lefen. Ya dauko kudi mai tsoka ya bata, tayi murna sosai. Lokacin da Suhaif ya dawo gida Iyayensa har sun kwanta, su Hajja sun tafi gida tuni, ya rufe kofar gida ya shiga dakinsa ya kwanta. Bacci ya gagari idanuwansa yana ta kwatanto Zubaida a matsayin matarsa, ya ga ko zai hakura, ya danne zuciyarsa ya aureta, sai ya ga ina! Bazai iya ba, Iman ce har yau a cikin lissafinsa. Gashi babu Iman amma ya kasa hakura ya auri wata, ba Zubaida kawai ba *yan mata da yawa suna sonsa amma ya kasa sonsu. Manyan dalilan shine duk wadanda yake haduwa dasu basu da nutsuwa da halaye irin na Iman, ko kusa bai taba samun mace mai hankali da biyayya irin na Iman ba. Ya sha daurewa zuciyarsa ya fara zuwa zance gidajen *yan matan da suke rokarsa ya je amma idan yaje sau daya, sau biyu baya komawa na ukun. Saboda *yan boko ne, yanzu wayewa ce ba'ajin kunyar saurayi sai su saki jiki da saurayi kamar mijinsu. Daga zuwa zance wata budurwa ta tubure masa wai sai ta bashi abinci a baki. Tun daga ranar ya rabu da ita. Wata kuwa daya gwada zuwa gidansu, da gyale a jikinta da ta ganshi sai ta cire tasa matsattsan kaya. Wannan rashin kamun kan ne yasa ya barta, don ba haka Iman dinsa take ba. Daga karshe ya hadu da mai saka hijabi har kasa kamar Iman, har ya fara murna ya samu mai hali irin na Iman. Ashe hijabin ne iri daya ba zuciyarsu daya ba. Sun yi watanni tare har yana saka ran zai yi maganar aure da manya a rashin Iman. Wata rana yayi mata zuwan bazata gidan da ake rikonta, gidan yayarta. Ya isketa da kananan kaya (english wares) matsattsu. Tana zance da wani dan caburos har yana kai hannu yana taba ta. Tana ganin Suhaif kafin ta iya motsi ya shiga mota yayi tafiyarsa. Tasha kuka tasan ta rasa Suhaif, daman hijabin yaudara ne, ta lura yana zon mace mai hijab shine take yaudararsa da hijab. A zamanin nan ina zan samu mace kamila mai tsoron Allah irin Iman? Suhaif ya fada yayin da hawaye yayi masa kawanya yana kwance. Washe gari misalin karfe goma na safe, bayan Suhaif yayi wanka ya fito tsakar gida ya gaishe da Iyayansa. Bayan Goggo ta bashi koko yana sha sai ta dube shi sosai taga idanuwansa a kunbure suke. Ta tambaye shi, "Babangida kuka kayi, ko kuwa rashin bacci ne idanuwanka suka kunbura? Suhaif yayi murmushi bai ce komai ba. Goggo ta dauko masa zancen abun arziki da ya yiwa Hajja Mahaifiyarta. Tayi ta shi masa albarka, ta ce ya ci gaba da taimako irin wannan. Amma ya kamata ya dinga samunta ko Mahaifinsa yana fada musu abun alherin da ya yiwa wani ko neman shawararsu akan abunda yake so ya bawa wani domin ya kamata su sani kar a zo yi musu godiya su hau zare idanu basu san akan me ake yi musu godiya ba. Suhaif ya amsa mata da "To daman gani nayi saboda Allah na yi, shiyasa ban fadawa kowaba' Mahaifinsa ya ce "Haka ne, amma mu dai ya kamata ka fada mana. Suhaif ya shaida musu yana so ya biya musu Makka amma yaga Baba na Kano ya biya musu waccan shekarar sai yayi tunanin ya rushe gidan nan ya sake gina musu na siminti, na zamani. Amma yaya suka gani? Suka ce haka yayi tunda sunje Hajji wancan shekarar ya musu gyaran. Baba ya ce "Kafin ka fara yi mana gini na fi son ka bani kudin da zanyi noma sosai wannan shekarar in dauki ma'aikata, in sayi takin zamani da magungunan kwari. Goggo ma ta ce jari take so ya bata tana so ta dinga saro atamfofi daga Kano tana rabawa ma'aikata. Suhaif ya ce "Duk mai sauki ne zan baku kafin in tafi. Baba ya gyara zama ya sake dauko zancensa da Zubaida, ya ce "Muna magana tun jiya ka ki cewa komai ka barmu muna bolokoko mu kadai. Ni yanzu da ka ganni Kano zan je ko in aikeka Kanon ka kiramin Usman Mahaifin Zubaida, mu zo a hadu da Mahaifiyarka da Yaya Furera ta Garki a yi magana. Suhaif ya yi caraf ya ce "Baba ya kamata ku gane abun da nake nufi, tunda amsar da zan baku ta yi min nauyi a bakina, na kasa ce muku a'a bana so. Dan Allah Baba ku yi hakuri ku bar zancena da Zubaida. "Sai wa kake so ka aura tunda baka son *yar uwarka? Baba ya tambayi Suhaif a shelake. Suhaif ya ce "Babu wacce nake so takamaimai, amma ina gudun a bani *yar uwata in zo in wulakantata. Goggo ta ce "Kai Babangida kaji tsoron Allah, har ka iya kallon idanuwanmu ka ce baka son Zubaida. To kar ka sake ka dubi Mahaifanta kace baka son *yarsu, duk halaccin da suka yi maka, tun kana yaro har ka girma ka zama mutum sak. Suhaif ya ajiye kofin koko ya ce "Oh my God, Dad, Mum kun kasa gane abunda nake nufi. Akwai wacce na yiwa alkawarin aure bana so in zama mayaudari. Baba ya fusata ya ce "Kai dalla rufe mana baki Dad kake cemin da kuma Mum kake cewa Goggo? Wai kai dan boko ko? To badan Mahaifin Zubaidar ba ina zaka san sunan uwa da uba da turanci? Da ba kana kauye kana noma ba? Goggo ta ce "Wacece wacce kake so din, kasan yanzu duk wacce zata ce tana sonka badan Allah za ta so kaba saboda abun hannunka zata so ka. Ba gara ka auri *yar uwarka ba. Suhaif ya ce "Wallahi waccan ma don Allah take sona tun bani da komai. Goggo ta ce "Iman din dai har yanzu? Baba ya yi jan ido ya ce "To bari kaji maganar karshe ita ce ka auri Zubaida ka gama, ko bayan raina a daura musu aure. Kar ka kara kawo mana zancen banza, a garin neman Iman ka rasa aikinka. Idan ka sake kiran sunan Iman a gidan nan saina bata maka rai. Yanzu ka shirya ka kaini Kanon in je in yi magana da Usman. Ran Suhaif ya yi mummunan baci, ya rasa abunda yake masa dadi, sai wata kwalla mai zafi ta cika masa ido ya gwammace bai zo ba ma kwata-kwata. Tun da suka shiga motar suna tafiya babu wanda ya sake magana shi da Mahaifinsa, har suka isa Kano. Suhaif ya wuce dakinsu ya kwanta babu abun da zuciyarsa take sai bugun uku-uku. Babu wacce yake tunowa a ransa sai Iman, baya fitar da ran zai ga Iman kuma ya aureta. Kamar daga sama ya sake jiyo muryar Mahaifinsa da Baban Zubaida. Bayan Baba na Doko ya gama fadawa Baba na Kano duk abunda yake faruwa tsakanin Zubaida da Suhaif da kuma hukuncin daya yanke. Yanzu kafin Suhaif ya tafi, dole ya bayar da sadaki koma ba'a daura auren ba, tuwona maina. Baba na Kano yana bude baki cewa yayi "Har yanzu banji kalma daya da Suhaif din ya ce ba. Naji na Zubaida, naji naka. Me shi Suhaif ya ce? Baba na Doko ya zabura ya rufeshi da fadan da ya saba ya ce "Kai! Kai dakata bana son kwakwa ni dai na gama magana, aure zan daura shi ko baya so yarinya dai tana so, ni da Mahaifiyarsa muna so. Ya tashi ya fito yana kwallawa Suhaif kira. Suhaif ya fito da sauri, ya ce da Suhaif "Zo ka mayar da ni Doko suka tafi. Maman Zubaida ma taji dadi sosai, haka Naja'at ba kamar ita Zubaida kamar zata zuba ruwa a kasa tasha. Amma banda Najib, yayi shiru bai ce musu komai ba, amma shi da Mahaifinsa sun san ra'ayin Suhaif har yau Iman yake so. Balle shi Najib da suke hira ta waya, kuma Najib ya je Lagos ya ga yadda Suhaif yake gudun *yan mata, shi har yau Iman yake so, yake kuma jira yaga ta ina zai bullo ya aureta. Suhaif ya kara kwana daya a Doko, sai ya dawo Kano. Zubaida da Naja'at wasan *yar buya suke da Suhaif, tunda ya zo bai gan su ba, sai dai ya tsinkaye su suna shigowa gida ko suna fita a motocinsu in zasu tafi makaranta ko suna dawowa. Daga nan kuma bai san ta ina suke tsallakowa cikin gida ba. Watakila ko zagayawa baya suke ta wundon dakinsu su haura. Fara'ar Mama da kirkin da take yiwa Suhaif ya karu, amma bata yi masa maganar ba. Baba ma bai ce masa komai ba, haka Najib ma bai ce masa komai ba, shima Suhaif bashi da abun da zai fada musu. Don haka duk gidan suna hira da Suhaif akan wani abu daban, ba'a hirar aure. Suhaif ya kara kwananki uku a Kano sannan ya shirya zai koma Lagos. Suhai ya iske Baba a falonsa da sassafe misalin karfe bakawi. Bayan ya gaishe shi, ya shaida masa ya fito zai koma Lagos yanzu. Baba na Kano ya zaunar da Suhaif ya yi masa nasiha akan ya rike gaskiya akan aikinsa da al'amuransa na yau da kullum da abokan aikinsa. Musamman ma Manager da suke aiki tare, in har ya rike gaskiya duk kwangilar daya bashi yayi tsakani da Allah, to hakika zai sami alheri a wajen Manager nan sosai zai zama abun kwatance a kasar nan. Domin Manager mutumin kirki ne haka kuma wajen ana samun kudi sosai. Suhaif yayi godiya gami da yin alkawari zai yi amfani da shawarwarin daya bashi. Sai Suhaif ya zaiyana masa irin kyaututtukan da yayi a Doko da kuma alkawuran da ya yiwa Hajja, Iyayensa da kuma Iya Furera. Baba na Kano ya ji dadi ya kara karfafa masa gwiwa yana da kyau yayi kyauta, ya kuma ci gaba da taimako. Suhaif ya yi masa sallama ya mike zai fita daga falon. Baba ya kira sunansa "Suhaif, suhaif ya waiwayo, Baba ya ce "Kar ka damu da hukuncin da Mahaifinka ya yanke akan ka, zan lallasheshi ya janye. Kunya da nauyi ya rufe shi. Ya ce "Baba wannan ba matsala ba ce, hakan da yayi din yayi dai-dai ai kanwata ce. Suhaif ya juya ya fice. Baba yayi shiru yana tunani yasan Suhaif a kwai kunya da kara dole zai yiwa kansa ko zuciyarsa bata so. Suhaif ya shiga falon Mama ya isketa ita da me aikinta. Ya yi sallama ya shiga ya gaishesu, ya shaida mata ya fito zai tafi. Tayi masa fatan Allah Ya kiyaye. Ya dauko kudi mai yawa ya ajiye a gabanta. Ya ce ta kara jari ya kuma shaida mata ya bawa Mahaifiyarsa jari itama. Ya bawa mai aikin ma kudi mai tsoka, suka yi ta murna da godiya da fatan Allah Ya kiyaye. Suhaif ya fito ya nufi in da motarsa take, dauke da jakar kayansa. Sunyi sallama da Najib tunda asuba kasancewar aikin banki Najib yake yi ya fita tuntuni. Kamar daga sama yaji ana jan jakar kayansa. Ya waiga da sauri yaga mai jan jakar, sai yaga Zubaida ce, Naja'at a bayanta. Wani kululun bakin ciki ya darsu a zuciyarsa da dacin takaici. Ba abinda ya dauki zancen Zubaida illa raini. Ta yaya zata dubi kwayar idonsa a matsayinsa na yayanta ta ce tana sonsa da aure? Shima son yayi garaje daya kama zuciyarta, yayi kuskure. Ya rike jakarsa tsan a hannunsa yaki sakar mata. Ya bata rai kai kace bai taba ko murmushi ba balle dariya a rayuwarsa. Ya tsaya cak yana galla mata uwar harara. Sai ta saki jakar ta ja da baya, gabanta ya hau faduwa. Ya waiwayo ya dubi Naja'at sai taji kamar ta rafsa ihu dan tsoro, tana rawar murya ta ce "Yaya Suhaif Allah Ya kiyaye hanya. Ya ja wani dogon tsaki, ya juya ya tafi ya shige mota, ya ja ya fice. Ya tsaya a bakin get suma masu gadi da direbobin gidan ya rarraba musu kudi masu tsoka sannan ya tafi. Kuka wiwi Zubaida ta shigo gida dashi. Mahaifiyarta ce daman ta sa su raka shi. Baba yana daga falonsa yana jiyo duk hayaniyar da suke yi. Zubaida tana cewa "Uwar hararar nan tasa ya sakar mana gami da tsaki, ya juya ya tafi ya bar mu. Baba ya fito ya iske su a babban falo, Naja'at da Mama rike da Zubaida tana zabura tana faduwa share-share akan kafet. Ya tsaya cak yana dalla musu uwar harara fiye da wacce Suhaif yayi mata har take kuka. Tayi zunbur ta tashi ita da Naja'at suna shirin guduwa daki. Ya ce su zo su zauna a gabansa. Mama ta zauna itama. Bayan sun zazzauna ya fara zayyanowa Zubaida laifuffukanta ya ce "Akan abubuwa uku ki ka bata min rai, kallonki nake dama ina jiran Suhaif ya tafi tukunna. Na farko baki taba fada mana cewar Suhaif kike so ba har kika kawo Muslim gidan nan, nan falon kuke hira rimi-rimi har ya taba zuwa muka gaisa, na ce za muyi magana da Mahaifinsa customer na ne a kasuwa. Mahaifinsa ya sameni munyi magana sosai akan auranku, amma dan kin iya gulma kika je Doko kika canja Muslim ki ka ce Suhaif kike so, ni nake son in miki auren dole. Abu na biyu kinsan sarai Suhaif yana da wacce yake so, yana jira har kuka yake, har addu'a yake cewa inyi masa Iman ta bayyana, zaki sa a cusgunawa yaro a ce sai ya aureki. Abu na uku kuma zaki raba mana zumunci, wato yaki yarda ya aureki mu ce mu ya yiwa rashin mutunci ba ke ba, mu kullace shi. Ko kuma mu ki yarda da auren Mahaifinsa ransa ya baci, a yi kaca-kaca a rabu, zumunci ya watse. To daga yau idan na kara jin zancen aurenki da Suhaif a gidan nan ran kowa zai baci. Kamar yadda daga makaranta kika saci hanya kika je Doko kikai gulma, yau ko gobe ki saci hanya kije Doko kice musu da kanki kin fasa auren Suhaif, Muslim zaki aura. Kada ki sake ki nuna saki aka yi dole, ki nuna ke kikayi tunani kika fasa. Daga karshe kuma ki bugawa Suhaif waya ki bashi hakuri domin ko ba komai kin daga masa hankali. Mama ta bude baki zata yi magana, ya daga mata hannu ya dakatar da ita gami da cewa. "Duk wannan kisisinar ke kika koya mata kada ki sake ki cemin komai idan ma baki warware mata ba daga karshe ku zata kwabewa. Ya tashi ya koma falonsa ya rufe kofa. Zubaida ta rushe da kuka ta nufi daki, Naja'at ta bita tana lallashinta. Mama na zaune ta kasa motsawa abun duniya ya isheta. Najib na dawowa daga aiki karfe shida dai-dai na yamma ya iskesu su dukka a babban falo. Ya ce "Yauwa Zubaida dama so nake Suhaif ya tafi inci Ubanki. Yaushe Suhaif ya zama sa'anki da zaki ji yanzu shi kike so, dan kawai ki caza masa zuciya aga laifinsa bayan kinsan wacce yake so. Mama ta dakatar da shi ta ce "Ya isa haka dan Allah, yarinyar nan ta ce tayi kuskure a yafe mata. Da safe Babanku yayi mata fada zance ya wuce zata auri Muslim din wanda aka yiwa alkawari. Daman matan nan haka suke....... Lolxxx Reedwan Suraj Isma'il :::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Duk abun nan da ake Suhaif bai sani ba, yana can yana ta lallashin zuciyarsa ya zaiyi dole ya hakura ya auri Zubaida. Amma yaji shiru babu wanda ya taba kiransa a waya yayi masa zancen auransa da Zubaida. Baba na Doko ma ya taba kiransa suka sha hira, har suka yi sallama bai yi masa zancen auren ba. Sai abun ya fara bawa Suhaif tsoro har ya damu, yana tsoron ko Baba na Kano yayi fushi ne yana ganin baya son *yarsa. Haka Suhaif yake ta wasi-wasi shi kadai a ransa. Ya kira Najib ta layin office suka gaisa suka sha hira Najib bai nuna masa alamar damuwa ba, babu alamar akwai wani laifi da yayi masa. Aka kwana biyu Suhaif ya kira Mama, ko daya bata canja masa ba. Sai ya kira number gidan makwabtansu, bayan sun gaisa da matar gidan Maman Faruk suke kiranta sai yace a kira masa Naja'at zai sake bugowa. Faruk ya zo kiran Naja'at bata nan sai Zubaida ce kawai a gidan. Ta tambayi Faruk "Waye yake kiran Naja'at? Ya ce "Yaya Suhaif ne ya ce ta zo ta dauki waya, mamaki ya rufe Zubaida ta fara tunanin ko dai wayar gidansu ta samu matsala ne ya kasa kamawa. Sai ta dauki kan wayar taji lafiya kalau tana yi. Ta ce da Faruk "Je ka ce gata nan zuwa. Zubaida ta suri gyale ta nufi gidan makwabtansu. Tana shiga falon gidan ko gaisawa basu yi da Maman Faruk ba, waya ta hau ruri. Maman Faruk ta ce "Ina jin Suhaif din nema. Zubaida ta karasa wajen wayar a hankali, gabanta yana faduwa. Ta dauka ba tare da ta iya cewa komai ba. Da Maman Faruk ta ga Zubaida ta kasa magana sai tayi tunanin ko wani sirri za suyi sai ta ja hannun yaronta suka fita daga falon. Bata san fargaba, tsoro da tsananin son Suhaif ne ya hana Zubaida magana ba. Lolllllxxxxx na 2 ya tafi kenan YARENA ADDININA (III)-------> 3 PART 1 Suhaif yana ta magana shi kadai ya ce "Naja'at ce? Ta amsa da cewa "Eh" ya ce "Wai bakya magana ne? Ko baki iya gaisuwa ba ne? Ba'a ce miki Suhaif ba ne? Muryarta na karkarwa ta gaishe shi, sai ya gane muryar Zubaida ce. Yayi ajiyar zuciya ya ce "Naja'at ce ko Zubaida? Ta ce "Zubaida ce, Naja'at bata nan. Suhaif yayi shiru kamar ruwa ya cinye shi, ya rasa mai zai ce mata, kawai sai ya ajiye kan wayar. Bai so Zubaida tasan ya kira Naja'at ba, cikin sirri yake so ya tambayeta halin da ake ciki game da maganar auransa da Zubaida. Suhaif yayi dogon tunani yaga mafita ita ce ya kira Baba na Kano suyi maganar, hakika kamar yadda Mahaifansa suka fada gaskiya ne bai dace ya dubi idon Baba na Kano ba ya yi kirmisisi ya ki aurar *yarsa. Bayan ta fada shi take so. Ya ci sa'a kuwa ya sami Baba na Kano a layin wayarsa na office. Bayan sun gaisa sun taba *yar hira akan harkokin kwangila da kasuwanci, sai Suhaif yayi gyaran murya ya ce "Baba ina tunanin zan zo Kano karshen watan nan akan maganar da muka yi da kai. Baba ya tambayi Suhaif ya ce "Wacce maganar fa? Suhaif ya hau kame-kame can ya ce "Zancena da Zubaida. Baba yayi murmushi ya ce "Ai wannan zancan ya wuce tuntuni. Ba su fada maka bane? Karka damu kanka ka ci gaba da harkokinka, Zubaida ta yarda zata auri Muslim. Daman munyi maganar aurensa tuntuni da Babansa. Suhaif ya ce "Amma Baba ai.... Baba ya katseshi ya ce "Na ce ka kwantar da hankalinka, ka manta zancen ya wuce. Baba na Doko ma ya gamsu da hujjojin da na bashi. Ba komai Suhaif karka damu. Su kayi sallama suka ajiye kan waya. Suhaif ya shiga halin damuwa mai tsanani yana ganin anya Baba na Kano ko dai ya dauka baya son *yarsa ne? Sai Suhaif ya kira Najib ya tuntube shi da zancen aurensa da Zubaida. Irin kalaman da Baba ya fada masa haka Najib ya fada masa. Hankalin Suhaif a tashe ya hayo jirgi ya zo Kano babu shiri. Ya iske Mama ita kadai a gida, tayi matukar mammakin ganin Suhaif. Bayan sun gaisa sai ta ce "Amma baka ce min ba zaka zo kwanan nan ba. Suhaif ya ce "Wallahi nima ba shiri na taho. Bayan ya zauna tasa masu aiki suka kawo masa ruwa da abinci, ya tambayeta ina *yan gidan? Ta ce "Duk sun tafi harkokinsu sai ita kadai. Suhaif ya gyara zama ya zaiyana mata abunda ke tafe da shi, ya zo akan maganar aurensa da Zubaida. Ya fada mata yadda suka yi da Baba da Najib, sun ce ya kwantar da hankalinsa kar ya damu Zubaida zata auri Muslim. Sai yake ganin kamar fushi suka yi ko suna ganin shi ya ki aurenta. Shi kuma ba haka bane tabbas Iman yake so. Amma ina Iman din take yanzu? Kuma ko tana nan ai wata kusan tafi wata, gara ya auri kanwarsa Zubaida. Haka Suhaif ya karka ce yana yiwa Uwar *ya dadin baki, alhali har ga Allah Iman ya fi so ya aura. Mama taji dadi sosai da kalaman Suhaif dan sauran kullatar da ta yi masa ta goge. Ta yi dariya ta ce "Haba haba Suhaif karma ka kawo wannan a ranka. Mun san ba zaka ki aurar kanwar ka ba, kai da idan ba ranmu kai zaka zabar mata miji na gari wanda zai rike ta amana. Ta zayyanowa Suhaif dalilan da suka sa Mahaifinta ya ce ta auri Muslim tunda har anyi magana da Mahaifinsa. Shima yaro ne mai hankali, mai sonta. Suhaif ya ji dadi tamkar an sauke masa wani kaya dingimeme mai nauyi a kansa. Yayi ta addu'a akan Allah Yasa haka shi yafi alheri kuma Allah Ya basu zaman lafiya. Mama tana amsawa da amin. Ya ce ta bashi mukullin motarta zai je Doko gobe zai dawo, jibi kuma zai koma Lagos. Suhaif ya isa Doko ya ci sa'a ya iske Mahaifinsa da Mahaifiyarsa a gida. Ya zauna ya tambayesu dalilin da yasa aka fasa aurensa, shi dai ga yadda suka fada masa a Kano, ya Zaiyyana musu yadda suka yi da Iyayen Zubaida. Har ya nuna baiji dadi ba da aka ce an yiwa Zubaida miji don shi yanzu ya zo da shirin aurenta. Mahaifinsa ya ce "Ai daman Zubaida ta wuce ka, bayan har an kawo min kudin aurenta na karba sai dai ka nemi wata. In kuma har yanzu Iman kake jira sai ka yi ta jiran yarinyar da baka tabbatar bama ko tana raye ko ta mutu. Yanzu nan da watanni uku za'ayi auren Zubaida, Naja'at da Najib. Shima ya ce min ya sami mata zaiyi mana magana lokacin da zamu kai kudin auren. Ka zauna kana turo hula gaban goshi za ka tsufa baka yi aure ba kannanka zasu yi aure su haihu. Suhaif yayi dariya ya ce "Lokaci dai Baba. Goggo ta hau lallashin Suhaif akan yayi hakuri ya nemi wata ya hakura da jiran Iman shima nan da wata ukun a hada da na *yan uwansa. Bayan komawar Suhaif Lagos da wata biyu Najib ya kira Suhaif a waya. A lokacin Suhaif ya tare a dankareran gidansa na Abuja. Yana zaune a bakin swimming pool din gidan a kishingide kan kujerar hutawa yana sanye da dan dajeren wando da yamma. Masu yi masa hidima duk maza ne suna ta kai kawo suna ta jera masa kayan makulashe akan teburin dake kusa dashi. Yana shafa gashin burgujejen Karen daya suyo daga England. Suhaif ya amsa wayar Najib cikin fara'a ya ce "Najib ka ki zuwa sabon gidana ko, balle ka kawo su Mama da Baba da Goggo, Hajja, *yar Hajja, Zubaida da Naja'at da sauran dangi suzo su sa albarka ko? Najib yayi dariya ya ce "Ai ni zuwa Abuja zai yi min wuya, kasan yanayin aikina. Amma nan da wata guda zan dauki hutun bankina, a gidan zamu zo muyi honey moon ni da amaryata. Suhaif ya tuntsire da dariya ya ce "Kaji Sarkin makaryata, karya kake yi kana cewa ka samu mata har yau babu wanda ka taba nunawa ita. Najib ya ce "Wallahi da gaske nake, yau kuwa zaku gaisa da ita da bakinta zata fada maka sunanta. Suhaif yaji muryar mace ta karbi waya a hannun Najib ta gaishe da Suhaif, suhaif ya amsa cike da tunanin kamar ya san mai muryar. Sai ya ce "Amarya yaya sunanki? Ta ce "Sunana Naja'at, Suhaif ya zabura ya tashi tsaye ya ce "Wacce Naja'at? Babu tantama har muryar Naja'at kanwarsa ce. Ta bawa Najib wayar, ta zura daki da gudu itama sai yanzu ta gane Suhaif ne, dan Najib bai fada mata ko waye ba. Najib ya karba yana dariya ya ce "Ita ce matata, wallahi ita zan aura insha Allah. Mamaki ya rufe Suhaif ko kadan babu wanda yasan Najib da Naja'at suna soyayya. Bayan wata guda Suhaif ya zo Kano aka sha bikin Zubaida da Muslim, Najib da Naja'at. Suhaif yayi musu hidima da dukiyarsa abunsa, mutane suka yi ta mamaki duk wanda ya zo bikin ya kunshi goma ta arziki. Gidan Amare ya kawata da gadaje da kujeru, show glass da kayan kicin duk na Italy ne Dubai da London. Baba na Kano ya sayi wasu, Suhaif kuma ya sayi sauran. Bayan ansha shagalin biki Suhaif ya koma Abuja, cike da damuwa kan damuwa. Yasan yanzu idon kowa ya dawo kansa dole za'a dame shi da zancen aure a dangi. Hankalinsa a tashe duk ya bi ya sukurkuce yana cikin tashin hahkali. Tunda ya kasa zabar wata ya aura wacce yake so, yake jira kuma shiru ba ita babu labarinta. Suhaif ya dubi sama da kasa a gidansa babu abinda ya nema ya rasa na rayuwar jin dadin duniya. Ya jawo wata brief case ya bude babu abinda ke cikin ta sai Dallers, ya wurgar da akwatin, kudin da ke ciki ya watse a tsakiyar dakin, ya buga kai a jikin gadon da yake zaune. Ya ce "Babu abinda na nema na rasa a duniyar nan amma bana jin dadin rayuwata saboda na rasa Iman, na rasa farin cikina. Kwanci tashi shekarar auren su Najib uku. Su Naja'at har sun gama bautar kasa. Zubaida ta haifi *yan biyu mace da namiji aka saka musu suna Hauwa da Adam. Amma Naja'at da Najib Allah bai basu haihuwa ba, suna neman haihuwa ido rufe. Suhaif da Najib suka je Umara a watan Maulud. Ba su cika zama a katafaren Hotel din da suka sauka ba, koda yaushe suna Harami. Babu abin da suke sai ibada, babbar matsalar Najib shine Allah Ya basu haihuwa shi da matarsa Naja'at, sai kuma Allah Yasa a kara masa girma a wajen aiki. Suhaif kuwa bayan ya nemawa kansa da Iyayensa gafara, sai addu'ar Allah Ya hada shi da Iman kuma ya aureta. Domin ya kasa aure har yanzu bayan duk abokansa da kannansa sun yi aure sun hayayyafa. Dawafi suke tayi, Suhaif ya daga hannu yana addu'a fadi yake "Allah Ka jeho min Iman ina zuwa Nigeria, Allah Ka sa in auri Iman. Allah Kai ka halicceni ka halicci Iman Allah Kasa Iman ce matata. Allah Kai ka hadani da Iman Ka rabamu Allah Ka sake hada mu alfarmar Annabinka Muhammad (S.A.W). Najib dake kusa dashi ya karasa salatin. Suhaif ya juya ya kalli Najib ya ce "Daman kana jin abunda nake cewa? Najib ya ce "Wanda yake nesa da kai ma zai ji balle ni da nake kusa dakai, ai a fili kake fada baro-baro. Ina jinka wannan shine zagayenmu na shidda amma abu daya kake roko Iman! Iman!! Iman!!! Kawai kake ambato. Ba gara ka dinga sirkawa da idan ba ita ba wata da ta fita. Wani tsoho Bahaushe a bayansu ya ce "Ai ina bayanku duk zagayen nan da kuke yi Iman kawai kake kira. Wasu mata larabawa guda biyu a gabansu kawaye ko kuma ya da kanwa suma tare suke zagayen sai suka waiwayo suna kallon Suhaif kamar sun san su ko kuma suna jin abunda suke cewa. Duk da dai bakaken kayane a jikin matan tun daga sama har kasa babu abinda zaka gani sai farin tafin hannunsu. Sun rufe fuskarsu da nikaf. Hawaye ya kwararo daga idanuwan Suhaif ganin ya fara zautuwa har ya zama abin kallo saboda ambaton Iman. Son ta ya zame masa tamkar numfashinsa, yadda dole zaiyi numfashi haka dole Iman tana ransa. Da suka kewayo na bakwai kenan, sai suka yi kokarin fitowa daga wajen dawafin zuwa bayan mukami Ibrahim dan suyi sallar Nafila raka'a biyu wacce ake yi idan an gama dawafi. Tare suka fito da Bahaushe tsohon nan na bayansu da matan larabawan nan guda biyu na gabansu suma sun yi zagaye bakwai. Suka yi nafila a waje daya. Dai-dai lokacin aka kira sallar magruba. Suka jira aka yi sallar Isha'ai. Suhaif yana addu'a, sai Najib ya ce da Suhaif "Muna jinka fa har yanzu. A zuciyarsa yake addu'a amma baya sanin sanda addu'ar take fitowa, Iman dai yake kira. Tsohon nan ya ce da Suhaif "Yaro wacece Iman? Najib ya ce "Wacce yake so ya aura amma bai san inda take ba, kuma ya kasa daina sonta. Tsohon ya ce "Allah Sarki sannu yaro, Allah mai amsa addu'a ne zai bayyana maka ita kaji ko Insha Allah. Suhaif ya kasa magana amma a zuciyarsa yace amin. Daya daga cikin larabawan nan biyu ta matso tayi musu sallama, su duka ukun suka amsa. Tayi magana da larabci, su duka ukun basu gane abunda take cewa ba. Sai suka ji tayi Hausa ta ce "Allah mai karbar addu'a ya hadaka da Iman. Sai suka zazzare idanu suna kallon-kallo, su kalli junansu su kalleta babu wanda ya iya bata amsa ko kuma ya tambayeta me take nufi. Babban abun mamaki Balarabiyar Saudia da ta iya Hausa radau. Bayan wannan ma ya akayi tasan sunan Suhaif. Tasa hannayenta farare tas ta bude nikafin dake fuskarta sai ga fuskar Iman. Iman ce Allah ya hada Suhaif da ita inda bai taba tsammani ba. Su duka ukun suka hada baki suka ce "ALLAHU AKBAR! Kafin Suhaif ya ce komai sai da ya tashi yayi sallar nafila raka a biyu ya idar sannan ya ce "Iman! Iman!! Kece? Ta yi dariya nan tata mai kayatar da mai kallonta. Ta ce "Yaya Suhaif ni ce. Cike da fargaba yana in-ina ya tambayeta ya ce "Iman kin yi aure? Kafin ta bashi amsa na kusa dashi zai iya jiyo bugun zuciyarsa saboda fargabar irin amsa da zata bashi, ba Suhaif kadai ba har da Najib da tsohon nan zuciyarsu bugawa take uku-uku Allah ya sa amsar ita ce bata yi aure ba. Iman tayi murmushi gami da rufe ido don kunya, can ta dago taga sun zubo mata ido suna jiran abunda zai fito daga bakinta. Ta ce "Banyi aure ba, Najib kai fa kayi aure? Najib ya ce "Eh nayi aure amma Suhaif baiyi ba, su duka suka yi dariya. Najib ya ce "Ai nasan Suhaif kike so ki tambaya ko yayi aure ko baiyi ba, to baiyi ba. Shi kuwa gogan sai murmushi yake kawai dadi zai kashe shi. Najib ya zunguri Suhaif ya ce "Ta shi ka sake yin nafila raka'a biyu bata da aure. Suhaif ya tashi ya tayar da ikama, ita kuma Iman sai dariya take yi musu kawai. Kamar yadda su Najib suka saba idan suka idar da sallar Isha'i sai su koma Hotel su ci abinci, su yi wanka, sannan su kwanta ba tare da sunyi shafa'i da wutiri ba. Su tashi karfe biyun dare su dawo masallaci suyi ta nafifili har sai kusan asubah sai suyi shafa'i da wutiri, suyi sallar asubah tare da Liman. Bayan an idar sai suyi ta dawafi har gari ya waye. Sannan su koma gida suci abincin safe sai su sake kwanciya suyi barci har sai da azahar suke tashi suyi wanka suci abinci sannan su koma Harami ayi sallar azahar dasu. Suhaif, Najib, Baba tsoho, Iman da kawarta suka fito daga Masallaci zuwa bakin titi. Iman ta ce "Ya kamata mu je ku ga gidan da nake zaune, Najib ya ce "Tare da *yan garinku ki ka zo? Iman ta ce "A'a ni ai yanzu shekara ta hudu kenan a kasar nan ina karatu a jami'ar koyar da ilimin addini. Na kammala karatun waccan watan muka gama, akwai gidan da nake zama, anan kurkusa babu nisa, mu je ku ga gidan. Suhaif yayi sauri ya amsa mata da "To muje. Baba tsoho ya mikawa Suhaif da Najib hannu suka gaisa ya ce "To na barku lafiya zan tafi masaukina naga hanyar ba daya ba ce. Suhaif yasa hannu a aljihu ya dauko Riyad da yawa ya bawa tsohon. Mamakin kudin nan mai yawa ya rufe tsoho sai godiya da addu'a yake yiwa Suhaif Allah Yasa Iman rabonsa ce. Suhaif yaji dadin adu'ar baba tsoho. Ya sake ciko hannu da Riyad ya sake bawa tsoho. Tsoho ya sake rike baki yana mamaki. Suhaif ya dauko katin da yake dauke da adreshinsa da nambar waya ya bawa tsohon ya ce idan sun koma Nigeria ya nemeshi zai yi masa alheri. Najib cewa yake "Ai kai dan tsoho Allah Ya hadaka da arzikinka tunda Allah Yasa a gabanka Suhaif yaga Iman. Iman da kawarta suna gefe sai murmushi Iman take kawai. Suna tafiya a hanya Najib yake cewa "Af ban tambayi sunan kawar taki ba ko gaisawa ba muyi ba. Iman ta ce "Sunanta Zainab ai bata jin Hausa kuma bata jin turanci Balarabiyar baharain ce. Da kyar Iman ta yarda suka jera da su Suhaif saboda girmamawa sai take tsayawa a bayansu. Saida Suhaif ya roketa sannan ta yarda suka jera. Farin ciki ya hana Suhaif magana sosai, Najib da Iman ne suke hira. Idan za'a auna yawan farin cikin Suhaif da Iman ban san na wanda zai rinjayi na wani ba. Yo aini bakin ciki ne ya rufe ni, na san ba na da wani abin katabus da na shiga takara, tunda har yanzu Hamma Huzaifa ya na sonta,,,, uhmmm wayyoni Masoyiyata!!! Reedwan Suraj Isma'il :::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Sun isa katafaren gida mai kyawun gaske. Iman ta ce su shigo ciki babu damuwa. A katafaren wurin cin abinci suka iske mutanen gidan an shake teburi cike da abinci kala-kala da abun sha iri-iri. Abunda zai fi daukar idon mai kallon teburin bankararrun dakwalan kajin da suka yi bake-bake akan plates. Teburin mai daukar kujeru goma sha biyu ne don haka akwai sauran kujeru birjik. Su Suhaif suna tsaye, Iman ta karasa wajen wadanda suke zaune tayi musu wata magana. Maza ne guda biyu, daya balarabe daya kuma bakar fata ne amma shima sai kayi masa kallan kurilla zaka san ba balarabe bane, hancinsa, farar fatar, laushin gashin, dogon gemun duk irin na larabawa ne. Sannan da wata mata balarabiya itama tana zaune. Maza biyu suka taso suka rungume su Suhaif irin gaisuwar larabawa. Bakar fatar yayi musu Hausa ya ce su zauna su ci abinci. Najib da Suhaif suka zauna kusa da daya matar, suka hadu su bakwai kenan suna cin abinci. Balaraben nan mai fara'a yana so suyi hira da su Suhaif toshi ba turanci, su babu larabci, haka sauran matan ma larabawa ne ba turanci. Su Iman sun bude fuskokinsu sun daga nikaf din sama don haka Suhaif yana ta satar kallonta, ya ga ta kara kyau da fari har tana kokarin fin larabawan kyau. Wayyo dadi kan dadi yau zuciyar Suhaif sumul sai farin ciki. Iman ta katse tunanin Suhaif ta ce "Af na manta ban gabatar muku dasu ba ko? Ta dubi Suhaif ta nuna bakar fatan nan ta ce "Wannan shine hamma Huzaifa dana baku labarinsa. Hamma Huzaifa? Suhaif da Najib suka maimaita. Numfashin Suhaif ya dauke cak saboda tashin hankali domin yasan akwai tsohuwar soyayya tsakanin Hamma Huzaifa da Iman. "To koma dai har ya aureta ne ta boye musu? Suhaif yake tunani a ransa. "Babau tantama mijinta ne dan haka ma Iman ta kauro Saudia, idan ba haka ba ta yaya zata dawo Saudia da zama haka kawai? Iman ta nuna kawarta Zainab ta ce "Zainab kuma matar Huzaifa ce. Sannan numfashin Suhaif ya diro zuwa kahon zuciyarsa don saboda kwanciyar hankalin daya samu. Iman taci gaba da cewa "Yanzu Hamma Huzaifa yana koyarwa a wata Jami'a a kasar Baharain, a can ya hadu da Zainab ya aureta, Allah Ya albarkace su da *ya*ya biyu mace da namiji. Macen aka sa mata sunana Fatima, namijin kuwa aka saka masa suna shima Huzaifa. Suhaif ya nanata sunan a ransa Fatima! Lallai har yanzu Huzaifa na son Iman kenan? Amma kwalelensa matata ce. Iman ta nuna balaraben ta ce "Shi kuma sunansa El-Sadik, dayar kuma matarsa ce, sunanta Na'ima. El-sadik abokin Hamma Huzaifa ne tare suka gama karatu a Madina, shi kuma anan kasar yake koyarwa, nan ne gidansa, Allah bai basu haihuwa ba. Suhaif da Hamma Huzaifa suka sake yin hannu suka gaisa. Iman ta ce da Huzaifa. Kamar yadda na fada maka na taba zama a gidansu, Huzaifa ya ce "A Kano suke kenan? Iman ta ce "A wani gari sunan garin Doko. Najib da Suhaif sunyi mamakin yadda aka yi Iman bata bawa Huzaifa labarin rayuwarta ba, bayan rabuwarsu saboda shakuwar da su kayi tun tana yarinya. Amma daga baya sai suka daina mamaki da suka tuna Iman ba ta da surutu, suma dalili ne yayi dalili yasa ta basu labarin Huzaifa. Domin tunda ta zo bata taba labarinsa ba saida ta kwabe gaba daya. Suna cin abinci suna hira El-sadik kam yana so ayi hiran nan dashi ba Hausa, ba turanci sai Huzaifa ne yake fassara musu, sun ci sun koshi sosai. Iman, Zainab da Na'ima suka fara kwasar kwanuka suna kaiwa kicin. Huzaifa ya tambayi su Suhaif yaushe zasu koma Nigeria. Suhaif ya ce ranar lahadi suka yi bukking. Huzaifa ya yi dariya ya ce "Ku ce ma rana daya zamu tafi. A wanne jirgi? Suhaif ya ce "EGYPT. Hamma Huzaifa ya sake tuntsirewa da dariya ya ce "To ashe ma jirginmu daya, a Abuja zaku sauka ko? Suhaif ya ce "Eh a Abuja zamu sauka Hamma Huzaifa ya ce "Alhamdulillah! Tare zamu tafi kenan. Ina fatan za kuzo jalingo idan muka gayyace ku bikin mu ko? Najib ya ce "Insha Alla, mai zai hana zamu je. Suhaif ya gyara zama ya ce "Har da Iman zaku tafi? Huzaifa ya ce "Tare zamu tafi, daman itama shekara hudun nan data yi anan sau daya taje gida saboda karatu yanzu kuma ta gama. Ga matata ita ma sau daya na taba zuwa da ita Nigeria. Shine kuma yanzu daga Bahrain muka biyo mu dauki Fatima sai mu dunguma. Iman ta zo ta kwashi plates ta nufi kicin, ita da Suhaif sai kallon-kallo suke. Suhaif ya bar sauraron hirar da Huzaifa da Najib suke yi yana kallon abar kaunarsa. Kamar aradu ce ta fado daga sama haka Suhaif yaji sautin maganar Hamma Huzaifa a kunnensa ya ce "Ai bikina da Fatima zamu je, za'yi nan da sati biyu. Iman ta fito daga kicin itama kunnenta ya jiyo mata, sai ta tsaya cak. Wai! Wai!! Wa yaga zare ido wajen Suhaif? Ya kurawa Iman ido kem yana mata kallon "Haka zaki min? Najib ya hau doguwar addu'a yana tofawa Suhaif a zuci saboda tsoron halin da dan uwansa zai shiga. Huzaifa bai san muzuran da ake yi ba shi dai yana ta zuba musu labari. El-sadik ya fito daga cikin daki ya zo ya sami su Huzaifa cikin harshen larabci yayi masa magana. Huzaifa ya dubi su Suhaif ya ce "Ya kamata muje inga masaukinku kun ga ranar da zamu tafi sai mu biya mu daukeku. Najib ya yunkura ya tashi ya jawo hannun Suhaif domin yasan Suhaif baya fahimtar komai tunda tashin hankalin nan ya rufta masa. Suka dunguma su hudu suka nufi wajen mota Iman na rakasu a baya jikinta yayi sanyi. Suhaif kallonta kawai yake wannan karon ba kallon kauna bane, amma kuma bana tsana bane tabbas yafi kama da harara. Ya kasa kwatanto halin da zai shiga a rayuwarsa nan gaba. Yasan tabbas ya gama samun sukuni har abada. Ga Iman baro-baro sun hadu amma ta subuce ya rasa ta har abada. Suhaif, Najib, Huzaifa da El-Sadik suka shiga mota suka nufi katafaren Hotal din da su Suhaif suka sauka wato Darul Tauhid yana daf da Harami. Har dakin Huzaifa ya bisu domin yaga dakin saboda ranar lahadi su biyo su dauke su. Ga duk wanda yasan Suhaif kuma yasan halinsa kallo daya zai yi masa yasan yana cikin halin damuwa, dakyar yake iya bude baki yayi magana. Najib da Huzaifa ne kadai suke hira. Huzaifa bai dauki komai a ransa ba, saboda haka ya dauki Suhaif a matsayin irin mutanen nan ne wadanda halittarsu ce haka basa son suyi magana. Huzaifa da El-Sadik suka yi musu sallama suka tafi. Tunda Suhaif ya jawo filon dake kan gadonsa ya dora kansa ya kwanta kai ka ce bacci yake yi mai nauyi, nan kuwa idonsa biyu tunani ne yayi masa yawa harma yake jinsa tamkar ba'a wannan duniyar yake ba. Najib yayi waya kicin din Hotel ya fadi irin abincin da abin shan da za'ayi musu order, bayan ma'aikatan sun zo sun jera musu akan darning table. Najib ya dinga tashin Suhaif, Suhaif yayi shiru kamar baya jinsa. Najib yasa hannu yana girgiza shi Suhaif yaki tashi, Najib ya fisge filon ya ce "Malam ka tashi mana meyasa ka cika damuwa ne akan kaddara da Allah ya jarrabceka? Kaifa Musulmi ne kuma Malami. Suhaif ya tashi zaune a fusace ya ce "Dalla Malam rabu dani, bana son bayaninka ko lallashinka, ka rabu dani kawai. Najib yayi murmushi ya ce "Har abun ya kai haka, nifa dan uwanka ne kuma ciwon da namiji ai na namiji ne, Suhaif ya harare shi ya ja dogon tsaki ya ja filon ya dora akai yana ta juyi yana tunani. Najib ya ce "Abinci zamu ci fa kuma saboda kai nayi order naga baka ci komai ba dazu, kadan ka caccakula amma baka ci ba. Suhaif ya ce "Ban ci ba kuma bazan ci ba. Najib ya wuce kan tebur yana cin abincinsa, ya dauko waya ya dannan lambar abar kaunarsa Naja'at. Ya kashe murya ya kirata da sunan da ya saba kiranta "My life, ta amsa da "Na'am my heart. Suka rincabe da hirar soyayya kowannensu yana bayyana halin da yake ciki saboda rashin ganin dan uwansa. Suhaif ya tashi zaune yana sauraran Najib dake kan dinning area yana waya babu abinda ya fado masa sai dama shine da Iman. Washe gari kamar yadda suka saba tunda la'asar suna Harami har bayan sallar isha'i, sannan suka fito suka nufi masaukinsu. Sun sha mamaki kafin su hau lift ta kaisu dakinsu sai suka iske Iman a reseption. Ba su gane ta ba sai da ta yaye bakin nikaf din da ta rufe fuskarta. Ta na murmushi ta ce "Sannunku da zuwa, na dan dade da zuwa, ince a can cikin Masallacin ku ke shi yasa baku fito da wuri ba ko? Najib ya ce "Wallahi muna can kusa da Liman shi yasa fitowa tayi mana wuya. Suhaif wanda ya zama tamkar wani gunki yana tsaye yana kallon Iman, idan zata kalleshi sai yayi sauri ya kawar da idonsa. Najib ya sami kujera ya zauna a gefen Iman. Suhaif kuwa sai ya wuce ya hau lift ya haye sama. Yana shiga dakin sai ya nufi gadonsa ya kwanta zuciyarsa cike da damuwa. Wato duk begen Iman da yake da bata nan, ashe wannan ba komai bane sai yanzu da ya ganta. Sonta ya karu a kokon zuciyarsa, haka bugun da zuciyarsa take abun ya kazanta. Hakika halin da Suhaif yake ciki abun a tausaya masa ne, kuma abun a tsorata masa halin da zai shiga nan gaba idan ya rasa Iman har abada. Najib bai shigo daki ba sai bayan awa guda, tunani ya ishi Suhaif da mamakin wai shin ina Najib ya zauna haka? Ko ya bi Iman gidansu ne? To ita Iman din me ya kawota Hotel din da suke? Najib na shigowa dakin, Suhaif yayi zunbur ya mike tsaye ya tari Najib yana tambayarsa "A ina ka tsaya ka dade? Ina Iman din take? Najib ya samu abinda yake so, so yake Suhaif ya dinga tambayarsa, yana ta binsa ya bashi labarin yadda suka yi da Iman, shi kuma yana sharewa yana basarwa yana ja masa rai. Lallai badan labarin Iman za'a bawa Suhaif ba da har abada ba zai sake tambayar Najib ba. Najib ya shiga wanka ya fito ya dauki waya ya buga kicin ya fadi irin abincin da za'ayi musu odar. Sannan ya juya ya kalli Suhaif wanda ya na zaune yayi tsuru yana kallon Najib. Tausayinsa ya rufe Najib ganin yadda ya zaku yana jira a bashi labarin Iman. Da Najib zai cewa Suhaif sai ya bashi guzirinsa gaba daya, ko tantama babu Suhaif zai bayar da duk abinda yake da shi don a bashi labarin Iman. Najib ya ce "Ai na dauka baka son labarin Iman saboda wulakancin da kayi mata kamar baka son ka kara ganinta a rayuwarka. Ka haye sama ko magana baka amsa mata ba. Ban ji dadi ba nima balle kuma ita, har kuka tayi. Ta shaidamun saboda kai ta zo amma ta fuskanci yanzu baka son ganinta, Suhaif ya zabura ya ce "Saboda ni ta zo, da gaske haka ta ce? Najib ya ce "Of course, da saboda ni ta zo? Suhaif ya yi ajiyar zuciyar zuciya ya ce "Me ta ce? Najib ya ce "Ta zo kawai mu gaisa ne, sai kuma ta tambayeni da gaske har yanzu baka yi aure ba kuma saboda me baka yi aure ba har yanzu? Shine nace mata lokaci ne baiyi ba. Suhaif ya zabura ya mike tsaye ya rufe Najib da fada yana cewa dan me yasa bai fada mata cewar ita yake jiraba dalilin da yasa bai auri wata ba? Najib ya ce "Naga kamar za'a fasa mata kai, kai kasan mata. Ko kanta zai ragargaje karewar fashewa ka fada mata haka, tasan ina sonta dan haka ba abun kunya bane dan Iman tasan banyi aure ba saboda jiranta. Najib ya ce "To sai hakuri, ni dai boye mata nayi, duk tambayar da ta yi min sai ince ba haka bane ban nuna mata kana sonta ba har yanzu. Suhaif ya dakawa Najib tsawa ya ce "Malam ka rufemin baki kawai ka cuceni, idan gani kake ka karamin aji, to zubar min da aji kayi, najib ya mike ya nufi darning table daman har ma'aikata sun jera musu abinci, najib ya ce "Kasan zanyi maka shirme dan me yasa baka tsaya kai da ita kunyi magana ba? Ita ai kai take so kuyi magana a rashinka ne ta fada min abunda take so taji. Ni kuma gani nayi an gama maganar aurenta da Huzaifa babu makawa auren za'ayi tun da gashi nan zasu dunguma suje ayi biki, na ga babu fa'ida da zan zubar maka da aji, ince sonta ne ya hana ka aure har yanzu, tunda da tana sonka yadda kake sonta da bata amsawa wani ba, ko da yake Huzaifa ma ba wani bane shima yayi mata halacci a rayuwarta. Yanzu dai ka zo mu ci abinci sai in rakaka gidan da take ko kuma ga nunbar wayarta mu kirata mu gyara bayani. Suhaif yayi dogon tsaki ya ce "Na ce ka rabu dani bana son bayaninka, da wata banzar shawararka wacce ba zata amfane ni ba yanzu. Najib ya dauko waya ya bugawa matarsa Naja'at yayin da ya make murya ya ce "My life ya kika yini yau? Suhaif ya zo a fusace ya fusge wayar ya kashe ya ce "Ba zaka yi wayar ba kaji idan da dadi. Dariya ta kubucewa Najib ya girgiza kai yace "Allah Yasa Iman matarka ce ko muma ma huta. Suhaif da dan Uwansa Najib basu fasa nafilfili ba da dawafi suna addu'ar Allah Ya zaba abunda yafi alheri tsakanin Suhaif da Iman. Har ranar da su Huzaifa suka zo suka dauke su zuwa filin jirgi. Tun bayan da Suhaif ya gaishe da Huzaifa da El-Sadik, Iman ma da matar Huzaifa suka gaishe shi, Suhaif bai sake cewa komai ba har suka shiga jirgi. Ya tafi can nesa ya samu kusa da wani ya zauna. Najib da Huzaifa ne suka zauna kujera daya, Iman da matar Huzaifa a bayansu sai Fatima da Huzaifa *ya*yan Huzaifa suma an balla musu belt din kujeru suna zaune a bayan kujerun su Iman. Har zuka iso Abuja Suhaif bai ce uffan ba haka ko kallon abincin da ake rabawa a jirgi baiyi ba. Zuciyarsa ta nausa ta tafi uwa duniya tana tunanin Iman. Haka Iman ta kasance bata magana sosai saboda damuwar da ta shiga ganin yadda taga Suhaif yana damuwa, ta rasa abun da yake damunsa ga Najib ya ce ba damuwar rashin aurenta ba ya shiga. Tasan Suhaif, tasan halinsa ba haka yake ba ada. Najib da Huzaifa kuwa hira ce ta rincabe a tsakaninsu suna yi suna kyalkyala dariya suna tafawa kamar da can sun san juna. Har mutanen jirgin duk suka yi shiru sai su kadai suke magana. Ko gyangyadi basu yi ba suna labari har aka iso Abuja. Bayan doguwar mota ta debe su daga bakin jirgi zuwa arrival. Huzaifa yana kokarin saka layinsa na Nigeria ya kira kanwarsa Bilkisu zata aiko da direba ya zo ya daukesu. Sai Najib ya hana shi ya ce ya bari sunyi waya tun kafin su taso, za'a zo da motoci a daukesu tun da tsakar dare ne sai su kwana a gidansu washe gari sai a kaisu inda zasu je. Huzaifa yaje ya sanarwa Iman abunda Najib ya ce, tayi murmushi ta ce ba komai su je su kwana gobe sai su je gidan Bilkisu kanwarsa din. Motoci guda hudu na alfarma ne suka biyo layi suka zo taryar uban gidansu Suhaif. Tun daga nan Iman da Huzaifa suka fara mamaki kafin suga gidan da za'a kaisu. Sun sha matukar mamaki a lokacin da suka gansu a cikin katafaren gidan Suhaif wanda kirarsa da zubinsa irin na turawane tamkar a America. Amma ba su tantance gidan na Suhaif ne ko na Najib ne. Najib ya kai Huzaifa wani bangare a gidan masaukinsa, ya dawo ya kai Iman da matar Huzaifa da yaran bangaransu. A cikin gidan suke su duka amma wani ba zai ga wani ba saboda girman gidan. Kowanne bangaren yana dauke da tafka-tafkan falo mai dauke da maka-makan bandakuna na alfarma. Lallai gidan Suhaif gida ne kayataccen gaske, ko daga wacce kasa kake sai ka dubeshi ka sake duba, kuma da wuya idan baka ga abunda baka taba gani ba. Iman ta kwana tana tunani ko wannan gidan waye a cikinsu amma bashi ya fi damunta ba irin halin damuwa da Suhaif yake ciki har yaki ya kulata balle ya dubi inda take har yayi mata magana. Washegari da safe Najib yaje bangaren Huzaifa ya kwankwasa kofa, bayan ya bude sai ya shiga suka gaisa ya ce idan ya kintsa ya fito babban falo zasu karya kumallo. Najib ya fito ya nufi bangaren su Iman, nan ma Iman ce ta leko bayan sun gaisa ya ce suna jiransu a babban falo idan sun kintsa su zo suci abinci, ta amsa da "To gamu nan zuwa. Najib ya wuce bangaren maigida Suhaif dan shima a bangare daban ya kwana. Najib ya shiga ya iske shi a zaune a falo yana kallo da alama ya dade da tashi daga bacci. Bayan Najib yayi masa sallama, Suhaif ya amsa. Ya mika masa hannu suka gaisa sai ya sanar da shi ya fito falo za'a hadu a ci abinci. Suhaif ya dan yatsine fuska ya ce "Bana jin zan iya cin komai yau. Najib ya zauna a kan kujerar dake fuskantar Suhaif ya ce "Gaskiya Suhaif bai dace irin wannan basarwar da shariya da kake yiwa wadannan bayin Allah ba, idan kayi musu haka a Makka amma nan gidanka suka zo. Ba su san maye a ranka ba, basu yi maka laifi ba, to meyasa ba zaka daure zuciyarka ba don karsu dauki wani abu a ransu. Ko baka ci dole ka zauna ayi wasa da dariya, kuma lallai-lallai dole muje Jalingo bikinsu, ka dauki kaddara matar mutum kabarinsa. Hakika abun da Najib ya fada gaskiya ne amma fa bugun da zuciyata take yi, tsananin bakin cikin daya addabeni ba zai bari in zauna a tsakiyar Huzaifa da Iman ina kallonsu ba. Suhaif yake tunani a zuciyarsa. Najib ya katse shi ya ci gaba da cewa "Zancen wasa ya wuce ina gaya maka gaskiya da gaskiya nasan yadda kake ji, duk wani masoyinka zai jiye maka, amma ikon Allah Ya wuce haka, duk yadda Allah Ya so haka ya keyi da bayinsa, ka zubawa Sarautar Allah ido kaga irin matar da zai sauya maka a madadin Iman. Suhaif ya yi ajiyar zuciya ya mike tsaye ya dafa kafadar Najib ya ce "Na ji abun da ka fada, mu je falon ba komai. Cab! Allah Ya kiyaye,,,, gaskiya soyayya wata wahala ce babba, hmm * Reedwan Suraj Isma'il ::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Sun isa falon da yake dauke da tafkeken dining area me kunshe da zungureren table da kujerunsa. Huzaifa kawai suka iske ya iso, Suhaif cikin fara'a ya mika masa hannu suka gaisa. Suhaif ya ce "Jiya ina jinku a jirgi kuna ta hira ciwon kai ya hanani magana. Huzaifa ya girgiza kai ya ce "Ayya! Allah Ya sawake, wallahi ban sani ba, kuma Najib bai fadamin ba da nayi maka sannu. Yaya ciwon kan yanzu? Suhaif ya ce "A'a yanzu na warke da nayi bacci. Huzaifa ya ce "Alhamdulillahi Allah Ya sawake. Shigowar su Iman ce ta katsesu sai dukkansu hankalinsu ya koma ga duban bakin kofa suga masu shigowa. Iman da matar Huzaifa dukkansu suna sunke a cikin burgujejiyar bakar riga daga sama har kasa amma yau basu saka nikaf ba fuskokinsu a bude. Fatima da Huzaifa suma fes dasu Iman tayi musu wanka ta caba musu ado da wandon jeans da riga shirt iri daya banbancin kawai ta Fatima anyi adon irin na mata a jiki na Huzaifa kuwa anyi ado irin na maza. Yaran kyawawan larabawa ne babu abu daya da zaka gani a halittarsu kace sun hada jini da bakar fata, duk da dai namijin kamarsu daya da Mahaifinsa amma gashinsa da fatar duk na larabawa ne. Suhaif ya fara dimaucewa yana kokarin rikicewa irin wacce ya saba yi idan suka hadu da Iman. Yayi yaki da zuciyarsa ya daure ya saki ransa kamar baya jin komai. Iman ta dubi angonta Huzaifa wanda tun shigowarsu ya zuba mata ido, ta gaishe shi da larabci, matarsa taje ta rungumeshi sannan ta sumbaci kumatunsa yaransa ba irin gaisuwar da suka yi masa kenan. Ya yiwa yaran magana da fulatanci ya ce su je su gaishe da su Suhaif. Fatima da Huzaifa suka je suka yi musu sallama suka mika musu hannu suka gaisa. Matar Huzaifa ma ta dubi su Suhaif tayi murmushi tayi musu sallama, suka amsa cikin fara'a. Iman ta karasa kusa da Najib ta gaishe shi tana mai fargabar gaishe da Suhaif tana gudun kada yaki amsawa. Suhaif ya katse kokonta ya ce mata "Amarya Iman ina kwana. Sai abun ya basu mamaki da dariya ita da Najib. Ta ce "Amarya Iman ka saka min? Huzaifa ya ce "Ai kuwa sunan yayi dadi daga yanzu ma Amarya Iman zan dinga kiranki. Wai shin ina kika samo suna Iman ne? Sunan yayi min dadi tun ran nan nake tambayarki baki fada min ba. Iman ta dubi Najib ta juya ta dubi Suhaif, yayin da su duka suka zuba mata ido tayi murmushi ta ce da Huzaifa "Tambayi Yaya Suhaif ko Yaya Najib. Sai su duka suka kyalkyale da dariya suka dunguma kan teburin cin abinci. Irin kayan alatun da aka jera yafi karfin cikin mutane shida, mutane ashirin zasu iya ci su koshi su rage, babu abin da babu kai har da dumamen tuwo miyar kuka duk an hado musu sai wanda kake so zaka zaba. A waya Suhaif ya zanowa Kukunsa abubuwan da zasu daddafa tun jiya da daddare suke aiki har wayewar garin yau. Lallai kuwa wannan kayataccen Breakfast ya burge wadanda aka yi dominsu. Suhaif yana dan cin abinci duk da dakyar yake iya hadiyewa saboda kallon soyayyar daya fuskanci Huzaifa yana yiwa Iman. Ita kuwa kanta a sunkuye a kasa ta kasa kallon kowannensu. Suhaif ya fake da yiwa yara wasa da yake Babansu ya koya musu turanci da fulatanci don haka da turanci Suhaif yake musu magana. Najib da Huzaifa sun barke da hirar da suka saba yi tun jiya, hirar dai bata wuce halin wahala da talauci da masu mulkin kasashe suka jefa talakawansu ba. Iman da matar Huzaifa suma sun juya harshe suna ta larabci. Haka suka kasance suna cin abinci amma kowa da abokin hirarsa. Bayan sun gama sai suka dunguma zuwa kujerun falo inda suka zazzauna. Wayar Huzaifa tayi kara kanwarsa ce Bilkisu. Bayan ta gaishe shi cikin yarensu fulatanci ta shiga nuna bacin ranta da damuwa akan kin zuwansu jiya. Ta ce har sha biyun dare ta hana direbanta tafiya dan yaje ya daukosu idan sun karaso amma taji shiru. Yanzu ma kamar da wasa ta gwada lambar taji ta shiga, wato da bata kira ba ma baza su bugo suce mata sun karaso ba ko? Huzaifa sai dariya yake yi ya dannan speaker yadda Iman zaya ji. Ya ce da kanwarsa "To kin gama tutsiyeni? Ga Iman tana jinki ita zata baki amsa. Iman ta ce "Bilkisu kiyi hakuri, ba haka bane. Ai yanzu zamu zo. Bilkisu ya ce "Kuzo ina? Aini yanzu haka ma bana gida, gani nan har zamu shiga jirgi zan tafi Lagos. Huzaifa ya kashe speaker, ya tashi ya fito baranda suna magana da kanwarsa ta sirri. Matarsa ta bishi barandar bayan ya gama waya ya juyo ya dubeta ya kirata da sunan masoyiyarsa cikin harshen larabci ya tambayeta me yake damunta ne? Ta shakwakkwabe ta ce ta gaji duk jikinta ciwo yake, haka kirjinta yana mata ciwo. Yayi mata sannu yayin da ya jawota ya rungumeta. Ya jawo hannunta ya ce ta zo ya rakata daki ta kwanta ta huta yanzu zai fita zai sayo mata magani. Iman tayi-tayi da yaran su zo wajenta su zauna kada su dami Mahaifiyarsu, suka ki suka bi Mahaifiyarsu daki. Bayan dan wani lokaci Huzaifa ya dawo ya ce da Najib "Bani mukullin mota zan je Gwarunfa yanzu zan dawo. Suhaif ya ce "Akwai direbobi a waje, mukullan motar na hannunsu ka zabi daya ya kaika. Huzaifa ya ce "Ba komai zan je da kaina, nima fa dan gari ne bazan bata ba. Sai su duka suka kyalkyale da dariya. Suhaif ya ce "Muje wajen motocin sai in karbar maka mukullin. Bayan Suhaif ya bawa Huzaifa mukullin motar, Huzaifa ya shiga suka yi sallama akan yanzu zai dawo ba dadewa zai yi ba sako kawai zai karbo. Suhaif ya dade annan a tsaye ya rasa me yake yi masa dadi, hakika idan ya ci gaba da zama kusa da Iman zai iya kasa controlling kansa ya fadi abunda Huzaifa zai gane halin da yake ciki. Sai kawai ya yanke shawarar ba zai koma cikin gidan ba sai ya nufi katafaren lambun da yake bayan gidan, ya samu lungu ya zauna yana tunani. Najib da Iman ne kadai ke zaune a falo suna *yar hira. Iman ta ce "Ina Yaya Suhaif, ko ya bi Hamma Huzaifa ne? Najib ya ce "Anya, naga giftawar Huzaifa shi kadai ne a motar, bari in leka watakila ya tsaya da masu aiki ko direbobi suna lissafi. Najib ya leko farfajiyar gidan yaga babu kowa, sai ya dawo falo ya zauna. Ya dubi Iman ya ce "Baya area nan ban san inda ya kutsa ba, yayi wani bangaren. Iman tayi ajiyar zuciya ta ce "Najib na tambayeka ka ki ka fadamin tsakani da Allah abunda yake damun Yaya Suhaif. Nasan dole akwai abunda yake damunsa, wallahi da kasan yadda na shiga damuwa da ka tausaya min. Ban san dalili ba tun ina Doko idan naga Suhaif yana cikin damuwa sai naji na damu. Kaga kamar lokacin da zai tafi bautar kasa ya ce baya so yaje kudu, Baba ya ce sai ya je damuwar da yayi tasa na rasa abunda yake min dadi. Zan tafi da damuwa a sanadiyyar damuwar da na bar Yaya Suhaif a ciki. A tunanina, na dauka dan zanyi aure ne ya sa shi damuwa, amma kace bashi ne damuwarsa ba. Yaya Suhaif mai fara'a, ga son wasa, ga shi da bayar da labari. Yanzu fa? Dubi halin da yake ciki, kace min kuma babu komai. Huzaifa dauke da Invitation card din bikinsa da Iman ya sako kansa cikin falon abun da kunnensa ya jiye masa shine Najib yaji yana cewa. "Iman kamar yadda kika sani Suhaif yana tsananin sonki tun kafin ku rabu, to ko bayan rabuwarku Suhaif ya kasance yana matukar kaunarki, kaunarki tasa ranar da za'a tantancesu a wajen daya sami aiki ya ki zuwa ya tafi garinku nemanki. Satin Suhaif guda a Jalingo yana nemanki bai ganki ba, ya dawo a lokacin angama daukan ma'aikata. Duk tsawon shekarun nan Suhaif ya kasa daure zuciyarsa ya auri wata, a koda yaushe yana fadin Iman yake jira, saboda na kasa son kowacce *ya sai Iman. Mun bashi shawara ya hakura ya barwa Allah idan ke rabonsa ce ko bayan yayi aure sai ku hadu kuma ya aure ki. Ya ce duk *yan matan da yake haduwa dasu basu da hali irin naki don haka idan bake ya aura ba ya hakura da aure a duniya. Ya mallaki komai na rayuwa, wannan gidan da muke ciki nasa ne amma shi kadai yake rayuwa a cikinsa saboda rashinki. A koda yaushe yana addu'a Allah Yasa ya ganki, haka makasudin zuwanmu Makka yanzu takanas don yayi addu'a Allah Yasa ya ganki. Allah Ya amsa addu'arsa ya ganki, amma a kurarran lokaci. Ma'ana a satin bikinki don haka ya shiga damuwa fiye da ta da kafin ya ganki. Iman ta runtse ido sai hawaye sharr-sharr yake zuba daga idanuwanta. Najib ya dubeta yayin da hawaye ya surnano masa ya ce "Ba kuka za kiyi masa ba addu'a da nasiha za kiyi masa a matsayinki na Malama ki nuna masa kaddarace da jarabawa daga Allah, a matsayinsa na Musulmi dole ya yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau amma ni kaina ina tsoron halinda Suhaif zai shiga nan gaba, in dai ba Allah bane Ya saka masa dangana. Iman ta hau karkarwa jikinta da bakinta da kyar maganarta take fita ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hakika na tausayawa Suhaif kuma bani da abunda zan bashi ko in fada masa yaji damuwar da yake ciki ta gushe. Illa nayi alkawari zan dauwama har karshen rayuwata, ina mai yi masa addu'a Allah Ubangiji Ya yaye masa ya kuma bashi macen da zai so fiye da ni. Bayan rabuwata da Suhaif sannan na sake gaskatawa na tabbatar Suhaif mai sona ne, so na hakika kuma tsakani da Allah. Ya soni a lokacin da kowa ya ki ni, Suhaif ya tsaya a lokacin da kowa yake guduna. Suhaif ya lallasheni lokacin da kowa yake hantarata. Suhaif ya kirani da masoyiya a lokacin da kowa yake kirana makiyiya. Suhaif ya kira ni da Iman lokacin da kowa yake kirana da Mayya. Sannan Suhaif ne ya fara fahimtata, yayi kokarin fahimtar da jama'a har saida suka fahimta ba laifina bane. Yana kuka da hawayensa lokacin da yaga ina kuka. Haka yana dariya lokacin da nake dariya. Ya hana kansa abu ni ya wadatar dani don kawai kada in banbanta da kawayena. Ya ki yadda in yi kukan maraici a lokacin dabani da Uwa ko Uba, babu dangin Uwa babu na Uba. Allah ne kadai gatana sai Suhaif. Sai kuka ya ci karfinta ta kasa magana. Najib ma hawaye ne yake kwarara daga idanuwansa. Hankalin Huzaifa ya tashi yayi shiru ya kasa motsi tamkar daskararriyar kankara ya zama a wajen da yake labe. Yayin da ledar dake hannunsa mai dauke da invitation card din bikinsa da Iman ta rikito ta fado kasa saboda ciwon rashin laka da ya kama shi yanzu-yanzu. Karar faduwar ledar ita ta ja hankalinsu su dukka suka dubi bakin kofa amma sai basu ga kowa ya shigo ba. Najib ya tashi ya leka baranda sai ya ga Huzaifa a tsugune yana kwashe katinan da suka watse a kasa. Najib yayi sauri ya goge idanuwansa don kada ya gane halin da yake ciki, ya karasa da sauri inda yake tsugune, ya ce "Ranka ya dade bari kayi ne? Huzaifa yayi karfin hali ya saki ransa yana murmushi ya ce "Zan hawo barandar nan kawai ledar ta subuce ta fadi. Najib ya harhada masa yana zubawa a leda. Bayan sun tsince suka shigo falon tare. Iman wacce tuni ta goge fuskarta ta hau murmushi tamkar ba itace mai kuka yanzu ba, ta fake da matsa remote ita a dole kallo take. Ta dubi Huzaifa fuskarta cike da annashuwa cikin harshen Hausa ta ce "Sannu da zuwa, ina fatan baka sha wuya ba wajen gano gidan ko? Huzaifa yayi murmushi ya ce "Ko a Bahrain ba za'a batar dani ba balle a kasata Nigeria. Najib ya ce "Sai a kasa batar da kai a Bahrain amma a batar da kai a Nigeria, kai Nigeria fa da yawa. Huzaifa ya ce "A'a Najib ba dai ni ba, ai duk inda zan shiga saina fito. Nan dai suka dinga musu Iman na taya su, tana bayan Najib cewar gaskiya za'a iya batar da Huzaifa don dai iyakacin yawonsa bai wuce Jalingo, Yola, Kaduna ba. Suhaif wanda ya shiga lambu cikin fulawoyi ya buyar da kansa don takaici sai yanzu ya fito. Yana shigowa falon ya dubi Huzaifa yayi murmushi ya ce "Ah ango yaushe ka dawo ne? Ina fatan baka bata ba? Su duka suka kwashe da dariya. Huzaifa ya ce "Au kaima zancen batan zaka yi min? Nima fa dan Nigeria ne, dan kunga na dade a Madina, na kaura Baharain daga can? Ai yanzu Najib suke min musu wai zasu iya batar dani a Nigeria. Suhaif ya samu kujera ya zauna. Najib ya ce "Sai da Suhaif ya ce ango na tuna kamar katin aurenku na gani a cikin ladar nan ko? Huzaifa ya ce "Af kaga na shagala na manta ban nuna muku ba. Najib ya ce "Baka nuna mana ba ko baka bamu namu ba? Muma da *yan gayyarmu fa. Zuciyar Suhaif ta hau dukan uku-uku, wata zufa ta gangamo masa, yayin da huhunsa suka yi ta dauki ba dadi da numfashinsa yana kokarin ficewa gaba daya saboda tashin hankali. Katinan bikin sun kawata matuka, an yi su irin na zamani, irin na masu hannu da shuni saboda ita kanta ambulan din da katin yake ciki abar kallo ce. An buga katinan da yare kala-kala anyi da Hausa, Turanci, Fulatanci da Larabci. Huzaifa ya ce "Gashi nan kowa ya dauki yadda zai yi masa da kuma yaren da yake ji. Najib ya debi guda shida na turanci biyu, na Hausa guda biyu, na Larabci daya na Fulatanci. Ya dauki adadin haka ya mikawa Suhaif. Suhaif wanda tuni karfin jikinsa ya kare, da Najib ya miko masa sai ya ajiye a gefensa yayi shiru. Ta ido Najib yayi masa sigina sai ya fahimci abun da Najib yake nufi. Wato ya daure ya bude katin ya karanta, sannan ya taya su murna kar su gane halin da yake ciki. Suhaif ya dauki katin ya bude amma tsabar rudewa, da daman kawai ba karantawa yake yi ba, bai san upside-down ya juya katin ba sai da Huzaifa ya kula ya karba ya gyara masa gami da cewa "Malam Suhaif yaya dai ciwon kanne yake damun ka, ka juya katin Upside-down kana karantawa? Suhaif yayi ajiyar zuciya har guda uku a jere ya kirkiro wani bushasshen murmushi ya ce "Kamar ka sani kaina ne yake ciwo. Najib wanda ya kurawa Suhaif ido yana masa nuni akan ya daure ya sake daurewa ya cije kada a gane shi. Suhaif bai san Najib ya fadawa Iman halin da yake ciki ba, don baisan ta sani ba, haka su duka basu san Huzaifa yaji ba. Sai kowa yake dannewa yana nunawa babu komai a ransa. Kallo daya Suhaif ya yiwa katin yaga an rubuta Huzaifa Ahamed Jalingo weeds Fatima Lamin Jalingo sai yaga ganinsa ya raunana ya koma hatsa-hatsa tamkar yanar ido ce ta tsuro a idonsa yanzu-yanzu. Sai yayi sauri ya mikawa Iman kati ya ce "Ke amarya baki karanta ba. Iman ta karbi katin ta kasa budewa sai ta ajiye kan tebur ta rufe fuska. Huzaifa ya dubeta ya ce "Waike har yanzu kunyar fulanin ce bata sake ki ba? Kunsan da fa ana fara zancen auran take tashi tabar wajen. Wai nan dagewa tayi ta zauna a wajen da ake rabon katin bikinta. Najib da Suhaif suka yi dariya. Ina tunanin sai jibine zan ci gaba idan Allah Ya kaimu Reedwan Suraj Isma'il >>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Huzaifa yayi gyaran murya ya ce "To Alhamdulillahi! Mun gode Allah, mun gode muku akan matukar kokarin da kuka yi wajen dawainiya da ni da bataliyata, ga Uwa Uba wahalar da zan baku ta gayyatarku da nayi zuwa wajen daurin aurenmu tun daga Abuja har Jalingo Allah Ya saka da alherinSa. Najib ya yi sauri ya katse shi ya ce "Haba mai gida meye abun wannan doguwar godiya? Mu da ku ai mun kulla zumunci har abada kuma duk kasar da kuke zamu kai muku ziyara balle daga nan zuwa Jalingo ai babu nisa. Suhaif ya yi gyaran murya ya ce "Iman *yar gidanmu ce, kanwarmu ce, tamkar jinin jikina take. Idan a bangon duniya za'ayi daurin aurenta zamu je. Kai kuma mai gidanta kun zama daya, mun zama daya da ku. Huzaifa yayi murmushi ya ce "To mun gode mun ji dadi muma zamu rike ku kamar yadda ku ka dauke mu *yan Uwa, jinin jikinku kuma dan Allah ku cika alkawari, kamar yadda ku kayi alkawari, nasan zaku cika alkawari ku zo daurin auren nan kada a samu matsala wani daga cikin ku yaki zuwa. Najib ya ce "Haba Huzaifa ai mu da Iyayenmu mata da maza da kannan mu duk zamu zo insha Allah. Huzaifa ya ce "Lallai kuwa zan zamo mai farin ciki. Yanzu zamu kama hanya zuwa Jalingo ina ga zai fi kyau mu tafi Yola ta jirgi. Nan ma zamu raba kati, sai mu wuce Jalingo. Iman ta ce "Ba da Bilkisu zamu tafi ba, ko ita ba yau ba? Huzaifa ya ce "Duk zancen nan da muke baki gane ba? Nafisa ta tafi Lagos tun karfe bakwai na zafe zata sayo ankon da za suyi kuma zata karbo dinkunanki, dukka lefen naki can takai a dinka miki. Tace sai wajen jibi zata je Jalingo shine ta bawa direbanta katinan daurin auren ya kawo min, ta bani lambarsa nayi masa kwatance, yanzu muka hadu a bakin titi ya bani, ta ce ko zamu fara rabawa kafin ta zo. Iman ta ce "Ai da ban gane ba, na dauka tana gidanta zan zamu je sai mu dunguma mu tafi. Huzaifa ya ce "Na rasa yadda zamuyi wannan tafiyar ina so in tsaya a Kano akwai abokaina da *yan Uwana da nake so in gayyata. Najib ya yi caraf ya ce "Muma Kanon zamu tafi dan *yan gida ba su san mun dawo jiya ba. Me zai hana mu dunguma a mota muje Kanon kayi rabon katinan, Iman ma ga kawayenta su Naja'at ta gayyacesu da bakinta. Ku kwana gobe da sassafe in saku a jirgin Yola ku isa Yola da wuri kuyi rabon a nutse sannan ku wuce Jalingo. Tun da yau bikin saura kwana shida babu lokacin da zaka je Yola ka dawo Kano kuma. Huzaifa ya ce "Gaskiya ne. Ya dubi Iman ya ce "Haka yayi miki? Ta gyada kai ta ce "Haka yayi Hamma Huzaifa. Suhaif dai yana zaune yana kallonsu tamkar ya rusa ihu dan tashin hankali. Ya rasa haushin wanda yake ji. Haushin Iman yake ji? Ko na Huzaifa? Ko kuwa haushin kansa da kansa yake ji oho? Haka kuwa aka yi, mota daya direba da Huzaifa a gaba Iman da Zainab matarsa a baya. Daya motar direba da Najib a gaba, Suhaif da yaran Huzaifa a baya. Suka dunguma suka kama hanyar Kano. Tafiya suke a titi, tamkar a jirgin sama suke saboda dadin motar. Kujeru lausasa hade da sanyin A.C da kamshin turaren dake manne a kowacce kusurwar cikin motocin. Huzaifa ya juyo ya dubi Iman cikin harshen fulatanci yace mata "Fatima bani labari, wanne labari Hamma Huzaifa? Labarin da kika taba bani can kwanaki na abubuwan da suka faru da rayuwarki bayan tafiyata. Kin fada min inda kika zami jariri da yadda ki kayi da jaririn. Kin tsaya a inda kikabi matar nan Masallacin B.U.K baki karasamin ba. Iman ta ce "Duk tsawon lokacin nan baka tambayeni ba sai yau? Huzaifa ya ce "Ai kin san komai kamawa yake yi, kinga yanzu da kin karasa mun labarin da nasan su Suhaif kafin ki gabatar mun dasu kamar yadda suka sanni kafi ki musu bayanina. Iman tayi murmushi ta ce "Haka ne amma kasan ban cika son yin hira da kai ba a gaban matarka ko? Babu dadi za taga kamar cin fuska ne kasan mata da kishi. Huzaifa ya ce "Ke kike ganin haka laifine ita tasan zan aureki yanzu haka ma katunan daurin auren duka suna wajenta saita hana mu hira? Bani labari bata jin fulatanci shima direba baya jin fulatanci. Iman bata yiwa Huzaifa musu, duk abunda Huzaifa zaisata komai wahala zata yi masa balle labari ai ba zai zama matsala ba. Ta gyara zama ta fara rangadowa Huzaifa labarin duk abunda ya faru. Musamman da taga barci ya kwashe matarsa sai ta saki jiki tana ta zuba. Ta bashi labarin zamanta a gidan larabawa wato Mummy Naila, bata boye masa ba duk yadda suka yi da Matsafan akan Abdul-Malik dalilin da yasa ta bar Kano kenan ta nufi Doko garin su Suhaif. Tana hawaye tana fada masa halinda ta tsinci kanta da irin halaccin da Suhaif yayi mata. Amma har yanzu Huzaifa bai ji kalmar da yake son ji ba daga bakin Iman, bata kira kalmar so ba tsakaninta da Suhaif. Sai take kiran Suhaif da Yayanta. Huzaifa ya tausayawa Iman matuka, kuma ya jinjinawa Suhaif da irin taimakon da yayi mata. Haka suka dinga hira har suka shiga Kano. Motar su Suhaif na gaban ta su Iman dan haka su suke bi a baya. Basu tsaya a ko ina ba sai a Hadeja Road unguwar Iyayen Najib. Suka shiga gidan suka iske Mama da Baba suna nan. Sai Baba ya dubi Suhaif da Najib ya ce "Wai yaran nan kun zama *yan Saudia ne, na ganku da larabawan mata har da *ya*yansu? Suka yi dariya dukkansu. Suhaif ya ce "Kwarai kuwa Baba muma mun zama *yan kasar Makka tunda gamu da *yan kasar mun taho muku dasu. Najib ya ce Baba wannan itace Iman *yar Jalingon nan da ta zauna a Doko. Sai Suhaif ya yi sauri ya ce "Ga kuma mijinta gobe zasu wuce Jalingo bikinsu. Kallo daya zaka yiwa Baba da Mama kasan sun shiga damuwa sabida tausayin Suhaif. Idan kasan Suhaif kasan shi da kaunar Iman. Huzaifa ya zaro kati ya mikawa Baba ya ce "Baba ya amsa da insha-Allah. Akayi-akayi a kawo musu abinci Najib ya ce a gidansa zasu ci abinci ya yiwa Naja'at waya ta hada musu abinci kala-kala. Gidan Najib a Badawa Layout yake, suka dunguma sai gidan Najib. Naja'at tayi mamakin ganin Iman murna ta kamata suka rungume juna. Daga karshe Naja'at ta damu har taso a gane damuwarta da taji labarin Iman zata auri Hamma Huzaifa tana tausayawa dan Uwanta Suhaif tana tunanin halin da zai shiga. An jera musu abinci kala-kala sunci sun sha sun koshi. Bayan sunyi sallar la'asar sai Suhaif yayi musu sallama ya ce zai tafi Doko yanzu haka yana yi musu fatan alheri sai ya zo Jalingo daurin aure kenan. Najib, Naja'at Huzaifa da Iman suka raka shi har bakin mota ya shiga shi kadai zai tafi ba tare da direba ba. Ko kadan baya garajen duban gefen da Iman take ita kuwa babu abunda take sai satar kallonsa, ko tantama babu tana so tayi masa magana amma babu dama dan haka maganar da tayi masa ta karshe shine ya gaishe mata da Goggo, Baba, Hajja da *yar Hajja. Ta ce ya cewa Goggo dan Allah ko kowa bazai zo bikinta ba ita ta zo. Suhaif ya amsa mata da "To zan fada musu yaja mota ya tafi yayin da hawaye ya zubo a idanuwansa, Iman ma haka amma sai tayi sauri ta shige gida. Misalin karfe biyar na yamma Najib da Huzaifa suka shirya fita gidajen *yan uwa da abokan Huzaifa. Iman da Naja'at suma suka ce zasu je NNDC quater sharada gidan Zubaida su kai mata nata katin. Don haka gidan ma rufeshi aka yi tunda babu kowa. Najib da Huzaifa a motar Suhaif wacce suka zo da ita suka fita. Naja'at, Zainab da Iman da yara su kuma suka fita a ta Najib tunda tafi girma. Naja'at ke tukawa suka nufi Sharada. Sun iske Zubaida itama shigowarta kenan ko fitowa daga mota bata yi ba, daga gidansu take Hadeja Road. Daman tana da labarin Iman ta zo. Ta tare su da sauri cike da mamakin ganin Iman. Itama Iman tayi mamakin ganin Zubaida saboda yadda tayi uwar kiba haka. Iman ta rungumeta suka gaisa ta ce "Zubaida me kike ci kika yi kiba, nima in ci, ina mamakin kibar Naja'at ashe ita ba kiba tayi ba akan ki. Zubaida ta kyalkyale da dariya ta ce "Ke dai kina nan yadda kike Iman dama ni ce, kamar kara dawowa yarinya kika yi, kin zama *yar siririya kin dada fari da kyau, kiyi zamanki a haka ni ai bana son kiba. Oh! Iman sai naga katin aurenki da Hamma Huzaifa ya aka yi? Naja'at ta ce "To uwar tambaya ai sai ki kaimu cikin gidan mu zauna sai ayi labarin, ga bakuwa da yaranta suna tsaye. Sannan Zubaida ta ce "Lah ashe da wata ban kula ba, wannan balarabiyar fa? Iman ta ce "Matar Hamma Huzaifa ce da yaransa. Zubaida ta gaisheta da turanci, Iman ta ce "Ai bata jin kowanne yare sai larabci, *ya*yanta ne suke jin fulatanci da turanci. Iman ta fassarawa Zainab abun da Zubaida take cewa wato sannu da zuwa. Zainab tayi murmushi ta mikawa Zubaida hannu suka gaisa. Zubaida tayi gaba suna biye da ita har cikin gida tana cewa "Ku shigo ku zauna, ashe yau akwai labari kala-kala. Ga Iman ga Hamma Huzaifa sannan ga matarsa balarabiya, ga kuma Yayana Suhaif wai ya za muyi? Naja'at ta ce "Ai kuwa baza ki sha labarin komai ba dan kuwa Iman bata iya surutu ba. Katin biki kawai zamu baki mu tafi a gidana suka sauka. Suhaif da Iyayensa zaune suke a dandasheshen gidan da Suhaif yasa aka rushe gidansu na da aka mayar dashi na zamani. Ya zuba musu kaya na alfarma na zamani, idan ka shiga gidan baza ka taba zata a Doko kake ba, sai ka fito kofar gida. Goggo ta dube shi taga a hautsine yake kamar wani abu yana damunsa. Ta ce "Baban gida kamar kasha wuya a Umarar nan, naga ka rame duka ka hautsine kamar ba kai ba. Shi yasa na ce ka bari muje da Azumi, kace ta Mauludi tafi rashin cikowa. Mahaifinsa ya ce "Da gaske ne ai ta Maulud tafi rashin jama'a. Wane irin wuya zai sha kamar wani wanda ya je babu guzuri? Goggo ta ce "Allah ganinsa nayi kamar ba shi ba. Suhaif yayi ajiyar zuciya ya ce "Babu wata wuya da muka sha kawai dai yanayin rayuwar ce haka. Suka dauki lokaci mai tsawo suna hira sai Suhaif ya bude wata *yar jaka a kusa dashi ya zaro katina guda biyu ya mikawa Baba daya, Goggo daya. Baba ya iya karatun Hausa, Goggo kuwa babu ko ABCD ta jujjuya katin ta ce "Shegantaka zaka yi mun, ka fada min da baki ko katin meye. Ko auren aka dauro daga Makka bamu sani ba, ka samu wata ne? Suhaif yayi murmushi ya ce "Baba ya karanto da karfi kiji. Baba ya ce "Daurin auren Huzaifa Ahmad Jalingo da Fatima Lamin Jalingo. Su duka suka hada baki "Wacece Fatima? Suhaif ya yi ajiyar zuciya ya ce "Katin daurin auren Hamma Huzaifa da Iman ne. Sai Goggo ta dau salati mai hade da kuka kamar an fada mata mutuwa. Baba ya cabki kunnan Suhaif yana ja yana fada cewa yake "Shin na fada maka ko ban fada maka ba? Na ce ka hakura ka auri wata, ko ban fada ba? Daman banda hauka a ina ka taba jiran mutumin da baisan ana jiransa ba. Nan sai suka dinga yiwa Suhaif nasihohi kala-kala cewar kada ya sake ya ce zai tsangwami kansa ya shiga damuwa, ya dauka haka shine yafi alkhairi, ya nemi wata ya aura. Shi kuma ya rokesu su yiwa Allah suyi masa alfarma su shirya aje bikin nan dasu saboda Iman ta zama *yar gida. Goggo bata musa ba, ta ce zata je harma da *yar gudunmawarta, Iman ai *yarta ce. Baba ne yake dujewa da kyar Suhaif ya lallasheshi gami da yi masa alkawari da zarar sun je bikin Iman sun dawo a watan shima zasu ji nasa auran. Yayi musu alkawari ya yadda da kaddara zai nemi wata ya aura. Sunji dadi sosai sun yi masa addu'a Allah Ya yi masa albarka ya musanya masa da ta gari. Suhaif ya dauki jakar kayansa ya nufi dakinsa hawaye ne ke zuba sharr-sharr daga idanuwansa. Ya kwanta yana tunani haka kuma yake kuka, saboda ya kasa bacci ya kasa daina son Iman har yanzu. Sai ya tashi cikin dare ya yi ta sallah, ya yi azumi ya roki Allah Ya kawo masa karshen damuwar nan da ta haddasu a zuciyarsa ta Iman shekara da shekaru. Washe gari Iman, Huzaifa matarsa da *ya*yansa suka shirya suka fito dan kama hanyar tafiya Yola. Najib da matarsa Naja'at suka musu rakiya har filin jirgi. Najib ne ya biya musu kudin tikitinsu duka, Huzaifa yayi-yayi ya bari ya biya ko rabi ne. Najib yaki ya ce shima bashi ya biya ba, tun jiya Suhaif ya bashi ya ce ya biya musu. Suka yi ta godiya suka shiga jirgi suka tafi, sannan Naja'at da Najib suka dawo gidansu. Ana jibi daurin auren Iman da Hamma Huzaifa. Suhaif ya yi waya Abuja aka kawo masa wasu sababbin motocinsa fil-fil a ledarsu guda uku da ya shigo dasu daga GERMANY. Motocin duka ukun irinsu daya, kalar fentinsu daya bakake kirar zamani wadanda ake yayinsu a lokacin. Ana gobe daurin aure kuma da sassafe suka shirya a daura dasu. Idan da wuri aka daura su juyo a ranar idan kuma an samu African time su sake kwana. *Yan Doko sun hallara a Kano gidan Baba na Kano, Najib da Naja'at sun iso da sassafe sai Zubaida da mijinta Muslim da *yan tagwayenta da mai renonsu Lantana suma sun iso akan lokaci. Ana shirya yadda za'ayi tafiyar, wannan ya ce a shiga babbar mota daya tafi, wancan ya ce araba a shiga kananan motoci a jeru a tafi da direbobi. Suhaif ya ce dalilin da yasa ya aika Abuja aka kawo masa sababbin motocin nan iri daya guda uku, sai dan su tafi dasu zai fi tsari, kuma suna da saurin tafiya, gasu da tudu dan haka nisan nan bazaisa su gajiba. Yana so idan sun tashi dawowa suje filin jirgin Yola su dawo ta jirgi. Babansu ya ce "Ban gane muje a mota ba mu dawo a jirgi waye zai dawo da motocin, direbobin? Idan haka ne mu tafi a jirgi mana. Suhaif ya ce "A'a so nake in bawa amarya kyautar daya, angon ma kyautar daya sai in tuko dayar in dawo ni da wanda baya son hawan jirgi. Baba na Doko ya zabura ya ce "A'a Suhaif har kyautar motoci biyu zaka yi? Haba-haba sunyi yawa irin wadannan motoci masu tsada galla-galla dasu a ledarsu. Baba na Kano ya dakatar da Baba na Doko ya ce "Kyaleshi karka hanashi alheri. Suhaif mai kyauta ne, kuma duk wanda harkarsa ta taso Suhaif yana yi. Da dai ace bai wadata gida bane zai wadata na dawa shine zamu hanashi, ai abun farin cikinmu ne har muka samu yayi hakuri ya dangana, har zai halacci wajen bikin har ma ya dauko kyauta ya basu yayi musu fatan alkhairi. Suhaif hakan da kayi yayi, Allah Ya saka da alkhairi kaci gaba da hakuri da dangana Allah Zai saka maka da alkahirin sa. Mota daya Muslim ne yake tukawa, Zubaida agaba. Kujerun baya kuwa mai aikin Zubaida ce da *yan tagwayenta. Daya motar kuwa Najib ne yake tukawa, Naja'at a gaba, Mama da Goggo a baya. Sai daya motar Suhaif yake tukawa Baba na Kano a gaba, baya kuma Baba na Doko shi kadai. Suka yi addu'o'i sannan suka kama hanya. A jere suke tafiya, suka nufi garin Jalingo. Jalingo Ja garin Baba, shiga da kaya ka fito da gammo. Inji masu kirari. Nima sai na dana kirarinmu. KANO TA DABO TUMBIN GIWA KO DAME KAZO MUN FIKA Ko da musu ne???????????????? Reedwan Suraj Isma'il >>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Tafiya suke babu ji, babu gani taki ta kare. Sunyi sallar azahar a hanya, haka la'asar ma, suna yi suna tsayawa suci abinci, sannan suci gaba da tafiya. Basu jigata sosai ba, kasancewar motocin lafiyayyu ne masu sanyin A.C, ga lausasan kujeru kamar akan gadonka kake. Kasancewar Huzaifa ya basu kwatance a rubuce basu sha wuya ba, suna shigowa Jalingo sai suka yi tambaya ba tare da bata lokaci ba aka samu wanda yayi musu jagora har kofar gidan su Iman. Iman da Mahaifiyarta suna zaune a daki. Falon gidan da sauran dakunan da farafajiyar gidan duk mata ne suke ta aikin abinci. Dangin Mahaifin Iman ne jingim, suka taho mota-mota daga Gombe cikinsu har da Kakarta wacce ta haifi Babanta, sauran kuma *yan uwan Mahaifiyar Iman ne da kawayenta, da makwabta suka taru ana ta soye-soye da dafe-dafe saboda masu zuwa daurin auren gobe. Wata yarinya ce karama ta shigo har dakin da Iman take ta sanar mata ta zo waje ana kiranta, tayi baki daga Kano. Tana jin kalmar Kano ko tantama babu tasan su Suhaif ne, don haka tayi zumbur ta tashi da murna ta bude labulen windo ta leka. Ta juyo ta dubi Mahaifiyarta da fara'a cikin harshen turanci ta ce "Mummy da gaske su din ne kuwa. Mahaifiyarta tayi dariya ta ce "To jeki maza ki tare su, gidan nan ba zai shigu ba ki kaisu can gidan da aka gyara na saukar baki. Ni kuma zansa a hada musu abinci a kai, sai nima in zo mu gaisa. Iman ta ja mayafinta ta fito da murna ta nufi wajen motocin su Suhaif. Kafin ta karasa ta hango Hamma Huzaifa har ya gansu yaje wajensu suna gaisawa. Iman ta nufo inda suke, ido mai kalle-kalle, idon Suhaif ya hango masa Iman ta tunkarosu. Ya ji gabansa ya yanke ya fadi, sai yake kokarin dimaucewa. Duk wanda ke wajen zai iya gane halin da Suhaif ya shiga yanzun nan. Ba Suhaif kadai ba duk wanda ya ga amarya Iman sai ya sake kallonta, wato kyau ta kara yi kamar yau aka cirota daga leda, ta sha kunshin bakar fulawa a fararen kafafuwanta da hannayenta, ga wasu siraran kitso anyi mata yisin-yisin kai ka ce ba da hannu aka yi su ba. Da yake yau mayafi ta yafo, kuma atamfa ta saka super anyi mata dinkin riga da siket. Tana zuwa sai ta je wajen su Baba ta zube har kasa ta gaishe su. Cikin fara'a suka amsa gami da sanya mata albarka a cikin auranta. Ta wuce wurin su Goggo ta durkusa nan ma ta gaishesu. Goggo ta kamo hannunta ta ce "Taho nan Iman *yata mu gaisa sosai, gaisuwar yaushe gamo. Sai Iman ta fara hawaye Goggo ma tana nata. Iman ta karasa wajen su Naja'at ta karbi Hauwa a hannun Zubaida suma tana fara'a tayi musu sannu da zuwa. Huzaifa ya mikawa Iman makulli ya ce "Jeki ki bude musu can gidan su shiga su huta sun sha hanya. Suhaif ya ce da Huzaifa "Su Baba sunce a nuna musu Hotel baza su iya zama anan ba, mata sun yi yawa. Huzaifa ya ce "Ah! Daman matan ne kawai anan mun riga mun kama dakuna a Hotels. Bari su gaisa da Babana da Baban Iman suna falon gidanmu, mu je in kaisu. Huzaifa na gaba, Baba na Doko, Baba na Kano, Suhaif Najib da Muslim suna biye dashi a baya har falon da Mahaifin Huzaifa da Iman suke a zaune a gidan su Huzaifa. Iman da su Goggo tuni sun shiga gidan saukar bakin, shima kusa ne a tsakanin gidan su Iman da Huzaifa yake. Shima gidan irin gidajensu ne na gwamnati. An share shi an shimfida sabon rog carpet da sababbin katifu, filillika da sababbin zannuwan gadaje. Bandakuna kuwa sababbin bokitaine da butoci. Babu abunda su Goggo suka fara yi sai sallar magaruba da isha'i, daga nan sai suka dinga shiga wanka. Bayan nan sai suka hallara a falo suka fara cin abincin da aka jera musu kala-kala. *Yan Uwan Huzaifa da *Yan Uwan Iman suna ta shigowa suna gaishe su. Da yawa daga cikinsu ko Hausa basa ji sai fulatanci. Iman tana zaune tana fassara, tana kuma gabatar da su. Suna ganin kanwarta Hajara (Rabecca) kafin ta gabatar da ita Zubaida ta ce "Amma wannan kanwarki ce ko? Don kuna kama. Haka Mahaifiyar Iman tana shigowa su Goggo suka ganeta. Ta zo ta zauna bayan sun gaisa sai ta shiga yi musu godiya, ta ce Iman ta fada mata duk abun arzikin da suka yi mata, don haka sun zama *yan uwa. Duk da ba Hausa sosai take ji ba. Su Goggo suka ce babu komai. Zuciyarsu cike da tambaya ai Mahaifiyar Iman ba Musulma ba ce a labarin da ta basu. Yaya suka ganta da hijab har kasa tana kiran Allah da Annabi? Suhaif, Huzaifa, Najib da Muslim ne suka shigo. Goggo ta ce "Ina kuka shiga ne? Ga abinci fa jifgi ku zo ku ci ku kaiwa su Babanku suma. Huzaifa ya yi sauri ya ce, "Ai su har an kaisu masaukinsu a Hotel sun kwanta, sun ci abinci tare da su Babanmu. Su kuma su Suhaif mun ci tare, sannan suma sun je masaukinsu sunyi wanka sun ajiye kayansu. Yanzu ma zuwa muka yi su gaishe da Mummy (Maman Iman). Su Suhaif suka durkusa suka gaisheta cikin harshen turanci, tayi ta godiya da shi albarka. Mama, Goggo, Zubaida da Naja'at babu wanda bai kawo wa Iman gudunmawa ba. Suka firfito da gudunmawarsu suka jifge a gaban Iman da Mahaifiyarta sai godiya suke. Daga karshe Mahaifiyar Iman tayi musu sallama, ta ce zata aiko yara su zo su kwashe kayan, ta fita Mahaifiyar Huzaifa da kannensa ne suka shigo, suma aka gaggaisa suna godiya suma. Bayan sun tashi sun fita sai Zubaida ta taba cinyar Iman ta ce "Iman bayan kin bar Doko meya faru? Na ga Mahaifiyarki da hijab, ta Musulunta ne? Najib ya ce "Wannan Zubaidar akwai shegen surutu da tambaya. Mama ta ce "Zubaida ta baci da magana na rasa dalili, gashi ke ba bangaren jarida kika karanta ba. Naja'at ta ce "Kun manta mijinta Muslim dan jarida ne? Sai su duka suka kyalkyale da dariya. Goggo ta ce "A'a ku bar su kawaye ne fa, suyi hirarsu. Ba tare ku ka gansu ba? Gida daya, daki daya, ajinsu ma daya a Doko. Iman ta ce "Lah ai ba laifi bane dan ta tambayeni, idan ma babu wanda ya tambayeni a cikinku sai in ce baku damu dani ba. Ranar da na bar Doko a motar *yan sanda, tashar unguwa uku suka kaini, suka saka ni a zungureriyar mota mai zuwa Jalingo. Suka bani kudin motata a hannuna, nayi musu godiya suka tafi. Ina ganin sun fita daga tashar na fito daga motar na tari tasi sai gidan Mummy Naila dan in ga Abdul-Malik kuma in mata sallama nasan idan na bar Kano na bari kenan. Da na je sai tayi matukar mamakin ganina ita da sauran ma'aikatan gidan da suka sanni da. Abdul-Malik ya warke ras har ya girma yayi wayo abinsa. Kamar zai gane ni sai kallona yake tayi ba kiftawa. Mummy Naila ta hau tambayata ina na tafi ne? Kuma meyasa na tafi? Kamar wata jahila zan hada kaya in bar gidan, in ce bana son ganin Abdul-Malik cikin wannan halin. Ina ruwan Allah, Zai iya yanke HukuncinSa akan bawansa yadda yaso. Na kasa amsa mata wadannan tambayoyi sai hawaye nake na rungume Abdul-Malik. Ta sa aka kawo min abinci na ci, sai ta ce in shiga dakina in yi wanka in shirya, taga alamar a gajiye nake. Na shiga dakina na bude dirowata, abun mamaki kayana suna nan babu wanda ya taba, an hada min su a waje daya. Bayan nayi wanka na zabi bakar doguwar riga a cikin kayana na saka. Sannna na dinga jero sallolin da ake bina. Abdul-Malik ne yake bude kofar dakin da nake yana lekowa, ya kalleni sai ya koma da gudu. Mummy Naila ta leko da kanta ta ce in fito falo idan na gama muyi kallo da hira. Na fito muka zauna a falo taci gaba da tambayata. Babu fa'idar in boye mata komai, duk da ba komai ba ne zai iya faduwa. Na gyara zama na fara neman gafararta, kuma na bata hakuri saboda zata ji labari sabanin na farko dana bata. Na zaiyano mata makasudin barina garinmu, saboda in zo in rungumi addinin Musulunci ne nabar gidanmu, kasancewar Mahaifiyata ba Musulma ba ce kuma ta rinjayi Mahaifina shima ya bita ya bar Musulunci. Na fada mata dalilin da yasa na bar gidanta kuma don kawai ina jin tausayin Abdul-Malik na matsanancin halin da yake ciki na rashin lafiya abun yake ta damuna, saboda ina son Abdul-Malik. Sai na bata labarin rayuwata a Doko, na ce na kara samo ilimi. Yanzu kuma nabar Doko zan koma garinmu Jalingo in je in sami Iyayena in yi amfani da iya ilimim dana samo in musu nasiha, in wa'azantar, in kuma tunasar dasu su rungumi addinina. Duk wannan bayanin da nayi mata babu in da na sako zancen Matsafan da suka addabeni, domin zaiyi wuya ta fahimceni. Ita ba *yar Nigeria ba ce, wata kila ma basu taba jin labarin tsafi ba, ko kuma irin wanda suka sani ba irin namu ba ne. Mummy Naila ta fahimceni sosai, ta ce kuma ta kara sona da tausayina fiye da da, ta shaida min tunda take a zamani irin wannan bata taba ganin wacce ta sadaukar da rayuwarta ba, ta shiga wahala da halaka dan kawai ta rike addininta, sai ni. Ta nuna damuwarta akan rabuwa da ni, ta ce ba dan dole ba da baza ta barni in koma gida ba. Har yau har gobe bayan tafiyata bata samu mai rainon danta ba tsakani da Allah irina. Na yi mata godiya da alkawarin zumunci tsakanin ni da ita ba zai rabe ba, ko da bata kasar nan zan je duk inda take. Na karbi lambar wayarta, ta dauko kaya da kudi masu yawa ta bani. Washe gari ta hadani da motarta da direba ya kawoni har nan garin, kofar gidanmu. Naja'at ta ce "To ya kika tarar da Iyayenki? Iman tayi ajiyar zuciya ta ce "Kannena da *yan unguwa sun rude da murna, da ihu suka zo suka tareni. Mahaifiyata da Mama Tabita a guje suka fito suka rungumeni muna kukan murna. Kanina ya ruga ya kira Babanmu a Masallaci. A bin daya fara farantamin rai shine da naga Mahaifina rike da carbi a hannunsa, haka kuma shi da kanina Abubakar dukkansu abun salla rangadede a goshinsu. Bayan na kintsa na ci abinci, nayi wanka, nayi salloli. Mahaifina ya kirani falo shi da Mahaifiyata da kannena, duk suna zaune. Ya tambayeni ina na shiga shekaru biyu? Na fara musu labari tun daga farko har karshe. Mahaifina ma ya bani labarin abunda ya faru tun daga farko har karshe. Ya ce "Allah ne Yayi zan dawo in same shi tare da Mahaifiyata har sun rabu, yayi shekara guda cur a garinsu Gombe shi da kanina Abubakar. Yana karanta wasikar dana bar masa ranar da na gudu na rubuta masa dalilan guduwata sai yaji nadama da danasani sun rufe shi, a take ya yanke hukuncin dawowa addininsa koda za'a kashe shi. Haka kuwa aka yi ya Musulunta, akayi ta rigima da shi da Mahaifiyata da *yan wajen bautarsu, suka takura masa wai dan me zai dawo Musulnci, bayan sunyi da shi ba zai bar addininsu ba har abada, dan haka nema suka yarda suka warkar da shi. Shi kuwa ya ce ya yarda su mayar masa da ciwonsa ya dauwama a cikin ciwon, daya koma addininsu. Abubakar kanina yana bayan Mahaifinmu, shima ya Musulunta, babu wahalar da Mahaifiyarmu bata gana masa ba dan ya bar Musulunci. Ya ce shi Musulunci zai bi daman ya dade yana sha'awar addinin, kuma ya yi bincike mai zurfi akan addinin, ya yiwa Musulunci kyakkyawar fahimta bashi da ibu. Rigima taki ci taki cinyewa Mahaifina da kanina suka hada kayansu suka bar garin gaba daya ma suka kaura Gombe wajen danginsa. Mahaifina ya nemi gafarar danginsa musamman Mahaifiyarsa, suka yafe masa. Mahaifiyata ta je Gombe nemansu da taji da gaske ba dawowa za suyi ba shi baima san ta je ba. *Yan Uwansa suka hanata ganinsa suka yi mata kaca-kaca da cin mutunci, suka koreta ta tafi. Sai bayan da Mahaifina ya tabbatar komai ya lafa, sannan suka hado suka dawo Jalingo wajen Mahaifiyata. Najib ya ce "Bayan sun dawo Mahaifiyarki bata Musulunta ba? Iman ta girgiza kai ta ce "Duk wannan baisa ta Musulunta ba. Mahaifina da Abubakar suna addininsu, ita da kanwata Hajara suna addininsu. Amma su duka sun dukufa suna addu'a Allah Ya bayyana ni, sun damu matuka da rashina, su kan hadu su dukka wani lokaci su zauna suna kukan labarina, a rasa mai lallashin wani. Duk wannan labarin da Mahaifina yake bani, Mahaifiyata na zaune a wajen tana kallon talabijin, bata ce mana uffan ba. Tamkar ba labarinta muke ba. Sai na shiga fargabar lallai zan sha wuya duk sanda na tunkareta da zancen Musulunci. Bayan zuwana, babu abinda take cemin game da addinina a gabanta nake salla ko kuma muyi jam'i ni, Abubakar da Mahaifinmu. Suma a gabanmu suke shiryawa suje wajen bautarsu ita da Hajara kanwata, bamu ce musu komai. Ina bude alkur'ani inyi karatu a gabanta so nake tayi min magana, na sami fuska in dauko mata zancen Musulunci, amma bata ce min komai. Duk lokacin da Mama Tabita bata aikin komai, to muna tare ina mata wa'azi ina fahimtar da ita Ubangijin daya hallicceta da Annabinsa. Kusan kullum da yamma ina tafiya hira kauyen kawayena Mumuyawa. Ina zama da kawayena maza da mata muyi ta hira kamar yadda muka saba. Yawancinsu sun yi aure sun hayayyafa amma su kansu basu san me suka zo yi duniya ba balle su koyawa *ya*yansu. Gida-gida nake shiga har yara da tsofaffi duk mun saba har yanzu ban manta yarensu ba kamar yadda na iya nawa yaren. Sai da na gama shammatarsu ta hanyar suyo musu duk abunda nasan suna so. Kamar farkata-farkatan *yan kunne da fallen atamfofi wanda dashi suke dinka siket din da suke sawa. Duk ranar dana kwana biyu ban je ba, sai sun aiko yaransu su zo su tambayeni lafiya kuwa kwana biyu ban zo ba. Sun saki jiki dani, sun yarda dani, sun san ba zan cucesu ba. Sai na fara bin masu hankali a cikinsu ina shigo musu da manufata, ita ce su yarda da addinina a cikin sigar dabara da wayo. Tun suna kushewa, wasu suna dariya, wasu kuwa cewa suke bani da hankali. A hankali suka fara saurarata har takai ta kawo suna min tambayoyi idan basu fahimta ba. Wata rana da yamma na dawo daga kauyen Mumuyawa nazo na gaishe da Mahaifiyata a zaune kan wata kujerar roba tana karatun jarida a farfajiyar gidanmu. Mama Tabita a gefe tana bushe gyada. Na gaishe da Mahaifiyata na jawo abun zama na zauna ina tayata aikin. Cikin yarenta muke hirar wato Tangalanci, Mahaifiyata bata jin yaren Mama Tabita sai kadan-kadan, dana fuskanci bata ganewa ni kuma so nake taji sai na juya na koma yaren fulatanci saboda su dukka suna jin yaren fulatanci. A boye Tabita take so mu dinga yi kada Mahaifiyata ta gane tana shirye-shiryen shiga Musulunci. Domin a kashi dari na ci galabarta kashi sittin, ita da kanta wani sa'in take zuwa ta tambayeni akan addinina. Wani bangare a zuciyarta yake gaya mata karya shine ya hanata ta karbi Musulunci amma na ci gaba da yaki akanta da zuciyarta. Oh,,,, wadansu har so ake a koyi yarensu fulatanci sunki su koya ma mutum.... **zagi a kasuwa nayi ehe** Sai hakuri kunsan halin gwauro,, sai yanzu na tashi,,, ba kuga post da wuri ba. Daga Angon Iman da Pretty Matawata Reedwan Suraj Isma'il >>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Cikin harshen fulatanci na cewa Mama Tabita "Annabin farko shine Annabi Adam, bayanshi an yi Annabawa da yawa sannan daga karshe Allah (S.W.A) Ya turo Annabi Muhammad (S.A.W) sai wasu mutane suka ki yarda da shi. Don haka Annabi Muhammad (S.A.W) ne Annabin karshe shine ya zo da addinin karshe wato addinin Musulunci. Mahaifiyata na karatu sai naga ta rufe jaridar, ta cire gilashin dake fuskarta tayi shiru na lokaci mai tsawo sannan ta juyo ta kalleni muka hada ido sai tayi sauri ta juya ta ci gaba da karatunta. Na gyara zama na cewa Mama Tabita "Ki na da labarin wata rana da ake kira ranar lahira ko kuma tashin kiyama? Mama Tabita ta amsa mun a shelake ta ce "Haka naji wai-wai a gari ana fada. Nayi murmushi na ce "Yafi karfin wai-wai a gari gaskiya ne. Rana ce wacce ita ce ranar karshe, ranar da Allah (S.W.A) zai yi hisabi dan wuta ya shiga wuta dan Aljanna ya shiga Aljanna. Rana zata sakko kasa-kasa a lokacin da kwakwalwa zata dinga tafasa. Babu wata inuwa da mutane zasu shiga su fake sai inuwa guda daya itace karkashin Al'arshin Ubangiji. Jama'a zasu kagu ayi musu hisabi susan matsayinsu saboda wahala da azaba tayi yawa. Allah (S.W.A) bai kula kowa ba, sai mutane su dunguma wajen Annabin farko Annabi Adam su ce masa "Ka rokar mana Ubangijinka ya kula mu yayi mana hisabi. Sai Annabi Adam ya ce "Nima bazan iya tunkarar Ubangijina ba domin ina fargabar nayi masa laifi a lokacin daya hanemu cin wata itaciya, shedan ya zuga mu muka ci. Sai mutane su tafi wajen duk sauran Annabawa suma za su ce sun yiwa Allah laifi ba zasu iya zuwa wajen Ubangiji ba a wannan rana. Daga karshe sai mu dunguma wajen Annabin karshe Muhammad (S.A.W) sai ya ce ku zo mu je wajen Ubangiji. Ya roki Allah, Allah Ya amsa masa. Mahaifiyata ta zuramin ido tana kallona sai tayi murmushi ta kira ni, na je na zauna a gabanta. Nan fa muka hau fafatwa ni da ita, ta ce wannan in ce ba haka bane. Kar kuce tana niyyar yarda da ni, a'a tana nunamin ba gaskiya bane. Akwai tambayoyin da taimin masu tsaurin gaske wanda ilimina bai kai nan ba don haka na kasa amsa mata. Haka muke ni da ita kullum muna muhawara. Sai naga ashe har yanzu da saurana, bani da ilimin tunkararta, ta fini ilimi tasan abubuwa da yawa a cikin littafina kamar yadda tasan littafinta yarda ne kawai baza tayi ba ta Musulunta. Wata rana kanin Hamma Huzaifa ya zo ya ce in zo in ji Hamma Huzaifa. Naji gabana ya fadi murna ta rufeni na zabura na tambayeshi na ce "Hamma Huzaifa ya dawo ne? Ya ce "A'a waya yayi, kullum yana tambayarki aka ce bakya nan shine yau ya kira aka ce kin dawo shine ya ce in kiraki zai sake kira. Ko sakon daya ban bata ba na zari gyalena sai gidan su Huzaifa. Bayan na gaishe da Mahaifiyarsa ko zama banyi ba, wayarsa ta shigo. Na dauka bayan mun gaisa sai yake min fada danme zan tafi a neme ni a rasa har tsawon shekara biyu, matsayina na mace, karamar yarinya. Ban iya ce masa komai ba har ya gama sannan na bashi hakuri na yarda nayi kuskure, muka yi sallama na tafi gida. Duk ranar da yayi waya sai ya aiko a yi kirana mu gaisa. Har takai ta kawo nima ina kiransa mu gaisa. A cikin hirar da muke yi ne ya lura nasan kur'ani da hadisai har ina jan aya in fassara. Yake tambayata ya akayi na koyi duk wannan. Sai a lokacin na bashi labarin yadda akayi na samu ilimi. Na shaida masa ina da matsala wacce take damuna. Cikin sauri ya tambaye ni "Wacce irin matsala? Na shaida masa har yau bani da ilimi, ilimin da nake dashi bai isa in tunkari Mahaifiyata wacce take da tsananin sani a addininta. In bata hujjojin da zata gamsu dani har ta yarda da addinina. Zan bazama in nemi ilimi cikin duniya daga nan har Birnin Sin. Hankalin Hamma Huzaifa ya tashi da ya ji nace zan sake bazama duniya neman ilimi, sai ya shiga bani shawara yana bani hakuri ya ce in ci gaba da wa'azantar da ita a hankali har Allah Yasa ta yarda watarana. Na girgiza kai na ce Mahaifiyata tana da ilimi sosai, tasan wasu bangarorin na kur'ani, idan ta kawo min wata tambayar bana iya amsawa ita take amsa min. Na fada masa Mahaifiyata ta shaida min cewar duk abunda na sani ta fini sani tuntuni, Musuluncin ne ba zata yi ba. Kamar wani dutse ne ya tokaremun a zuciya, kamar wani gungumemen dutse aka dora mun akai, haka nake jina. Bacci wani sa'in yana gagarata ina tunanin hanyar da zanbi Mahaifiyata ta Musulunta. Nayi masa misali da Mama Tabita da Mumuyawa wadanda ba su san ma wanda ya haliccesu ba ma balle su san Akwai Annabawa, na fara samun galaba akansu sosai na wayar da su sun yadda akwai Allah Shine Ya haliccesu saura kiris su yadda dani su karbi addinina. Amma Mahaifiyata har yau har gobe babu jijyarta guda daya data fara rissinawa balle zuciyarta tayi marmarin shiga Musulunci. Hamma Huzaifa ya ce in kwantar da hankalina tunda na ce ina so in koma in nemo ilimi, zai karbo min form ya aiko ta hannun dan uwansa daya masa hanya tafiya, nima sai inje Jami'ar koyan addinin Musulunci ta Makka ita ce mai mata da maza. Wacce yake ta Madina maza ne kawai. Ya tambaye ni zan iya yin shekara uku ne karatun tunda na iya larabci kuma na iya rubutawa. Wanda bai iya larabci ba ne zai yi shekara hudu, shekara daya cur za'ayi ana koya masa magana da rubutun larabci kafin ya fara karatun. Da gudu nace masa ina so ya aiko min da form din zan je. Ya yi min alkawari zai aiko amma in fara neman shawarar Mahaifina. Ashe a lokacin Mahaifina yana ta fafutukar nemo min admission in samu in hada digirina. Koda na shaida masa zan je karatu Saudia sai ya shaida min yana nemar min admission, me zai hana in hakura in zauna in yi digirin a nan tunda Allah Ya sa na sami abinda na samu na ilimin addinin? Na shaida masa manufata har yau ilimin da nake da shi bai isa in gamsar da Mahaifiyata ba ta rungumi addininmu. Bai hanani ba, sai ma yayi min addu'a Allah Ya taimaka ya bani sa'a. Sai bayan da Hamma Huzaifa ya kusa kammala min komai na tafiya har ma sun aiko sun dauke ni sannan na shaidawa Mahaifiyata cewar zan je karo ilimin addini a Saudia. Kafin ta ce komai sai da tayi dariya sannna ta ce Allah Ya bani sa'a in je in dawo tana nan tana jirana, amma kafin in tunkareta in tabbatar na san komai a cikin addinina idan ba haka ba zai zamanto ita zata dinga kure ni. Kamar yadda Huzaifa yayi da zarar Ambasadan kasarku yasa maka hannu shikenan babu abinda zaka biya, kyauta zasu baka visa da tikiti, gidan zama, abincin da zaka ci hatta kudin jrigin da zaka zo ganin gida kyauta ne. Ba tare da bata lokaci ba aka aiko aka ce in taho. Na shirya na yi sallama da kowa da kowa. Alhamdulillahi kafin in tafi na Musuluntar da Mama Tabita da kanwata Hajara har na koya musu karatun salla, na Musuluntar da mutane uku a garin Mumuyawa maza biyu mace daya kawayena, suna Sallah a boye. Tun sanda na je kasa mai tsarki na dukufa da karatu haka komai ya zo min cikin sauki sai da takai ta kawo na zama a bar kwatance a makarantarmu saboda kokarina. Bamu cika haduwa da Hamma Huzaifa ba sai in ya shigo Makka ko kuma nima idan na je Madina Ziyara kabarin Annabi Muhammad (S.A.W) a lokacin aikin Hajji ko Umara muke haduwa mu gaisa. Kafin in je kasar Hamma Huzaifa yayi aure shi da matar suna Madina. Na je ban dade ba Hamma Huzaifa ya kammala karatunsa a turasu Bahrain a matsayin Teaching Practice, daga nan suka rikeshi suka daukeshi aiki. Shi Bahrain ta zamar masa gida domin matarsa *yar asalin kasar ce. Don haka sai yayi zamansa a kasar Bahrain gaba daya. Sai bayan dana cika shekaru biyu da fara karatu sannan na dauki izinin zuwa ganin gida gaishe da Iyayena, aka barni na zo. A lokacin ina jin kaina kusan babu tambayar da za'ayi min a cikin addinina ta gagareni amsawa ko kuma babu fejin da za'a bude a cikin littafi mai tsarki a ce in karanta ban karanto ba, har in fassara kuma in yi karin bayani, in tafi lokacin da aka saukar da ayar da kuma dalilin da yasa aka saukar da ayar. Don haka bani da fargabar tunkarar Mahaifiyata kai tsaye. Bayan zuwana da sati guda muka fara gwagwarmaya da Mahaifiyata ta ce wanan ince ba haka ba wancan ne. Tayi-tayi ta kureni ta kasa na mata tambayoyi da dama ta kasa amsawa, haka na zaiyano mata hujjoji babu adadi, na mata wa'azi mai ratsa jiki har jikinta sai da yayi sanyi da alama ta fara tantance gaskiya da karya. Na kutsa kauyen Mumuyawa da karfina ina ta wa'azantarwa duk da ban tunkari shi ainihin shugaban nasu ba, kuma bai san abunda nake aiwatar masa a gari ba. Ya dauka har yanzu wasa nake zuwa wajen kawayena su Maho. Cikin ikon Allah suna ta yarda dani suna karbaar Musulunci da yake duhun kan nasu ya ragu naga yanzu suna saka sutura ba fata ba, sannan sun fara shigowa gari suna gina gida su zauna masu halinsu. Harma suna shiga wasu Addinai ba nasu na gadon-gado ba. Mama Tabita da kanwata kuwa Musulunci ya ratsa su, suna sallah da Azumi. A lokacin kanina Abubakar ya tafi Jami'ar Jos shine yake koya musu karatun Al-Kur'ani kuma daman Mahaifina ya sa shi a makarantar Islamiyya har ya sauke. Abu duk ya cushewa Mahaifiyata duk jikinta yayi sanyi da alama ta gane gaskiya nauyi da kunyar *yan wajen bautarta ne yake damun ta yadda zata kallesu ta ce musu ta Musulunta bayan girma da mukaman da suka bata take rike da shi, watanni uku nayi a kasar nan kafin in koma, Ana sauran sati guda in tafi Allah Ya taimakeni. Mahaifiyata ta karbi shahada, dadin da naji bazai misaltu ba. Sai su Goggo suka yi kabbara. Muslim ya gyara zama yana sauraran Iman cike da mamaki. Iman taci gaba da cewa "Mahaifina yafi kowa mamaki ko a mafarki bai zata akwai wa'azin da zai ratsa Patrica ta karbi Musulunci ba, domin yayi iya kokarinsa da ilimin da Allah Ya bashi tun ba yau ba ya musuluntar da ita taki yadda fur. Yayi murna tamkar ya goya ni, yayi min addu'ar alhairi wacce bai taba yi min irin ta ba tunda aka haifeni. Na tafi na barshi da ita yana koya mata addini. Bayan sun tambayi Malamai yaya matsayin aurensu yake a yanzu? Malaman sun yi musu bayanai da gyara akan aurensu. Tun bayan dana koma bansake dawowa ba sai wannan dawowar da muka yi gaba daya, duk da tun waccan shekarar na kammala karatuna. Sai Hamma Huzaifa yasa na sake yin wani karatun na shekara guda wato Masters, shima na gama. Hamma Huzaifa ya tunkareni da maganar aure, sai naji ba zan iya aurensa ba, saboda ya zama tamkar dan uwana na jini, wato Babban wa magajin Uba haka Hamma Huzaifa ya zama a wajena. Ga Uwa Uba matarsa Zainab ta zama kawata in dai sun zo Makka tana wajena tare muke kwana mu tashi, nima kuma zuwana Bahrain biyu wajen su. Sai na nuna masa ba zan iya ba. Suhaif ya dago ya kalli Iman, kallo mai hade da harara. Don tunda ta fara bada labarin sai yanzu ya dago ya kalleta, tun dazu kansa a sunkuye yana murda agogon hannunsa. Yana sauraron labarin Iman yana jin muryarta a kunnansa tamkar ana busa sarewa don dadi. Iman ta kalleshi sai ta sakar masa wani tsantsareran murmushi da yake tayar masa da dankararriyar soyayyar data daskare a zuciyarsa. Ya ji kamar a yanzu ya fara sonta, son da yake mata a da duk ba so ba ne akan yadda yake ji yanzu. Nan da nan ya ji zuciyarsa ta hau bugawa, sai ya mike da sauri ya nufi kofar fita. Najib ya yi sauri ya ce "Suhaif ina zaka je ne? Dare yayi fa yanzu zamu tafi mu kwanta a masaukinmu. Suhaif ya ce "Idan kun gama ku sameni a waje. Tun daga lokacin Iman ta ji ta rikice ta kasa ci gaba da labarin tama manta in da ta tsaya, hankalinta ya koma wajen Suhaif. Zubaida ce ta fito daga ban daki ta ce "Babban aiki ya same ni gashi dare yayi. Duk suka juya suka dubeta "Kamar yaya babban aiki ya sameki? Mama ta tambaya. Zubaida ta zo kunnen Iman ta rada mata cewar audugar mata take so. Sai Iman tayi dariya ta ce "Shine aikin daya sameki? Kar ki damu bari inje gida in dauko miki yanzu-yanzu. Huzaifa ya kalli Iman cike da shaukin so, kauna da bege, yayi murmushi ya ce "Ko kina jin tsoro in zo in raka ki, naga wajen da duhu. Iman ta dan harareshi ta ce "Haba dai tsoro, aini baka sanni da tsoro ba mantawa kayi, sai dai Zainab matarka ita ce mai tsoro. Najib ya ce "Je ka rakata. Huzaifa yayi dariya ya ce "Tsokanarta nake yi ai bata da tsoro ko kadan, wannan sai dai ta dinga rakanu ma ni da Zainab din gaba daya. Duk kansu suka yi dariya. Goggo ta dora musu labarin rashin tsoro irin na Iman a zamanta na Doko. Iman tana dariya ta fita. Tana fita ta mance da sakon Zubaida sai ta shiga wurwurga ido ko zata ga Suhaif, amma bata ganshi ba, har motocinsu ta lelleka baya ciki. Ta zagaya bayan gidan kamar da wasa, bata yi tunanin zai shiga cikin ciyayi da duhun nan ba sai kuwa ga Suhaif ya rike kai a tsugune. Ta tunkaro shi da sauri tana kiran sunansa gami da tambayarsa "Lafiya? Me ya faru? Me ke damunka? Ya zabura ya daga hannu biyu ya dakatar da ita kada ta karso in da yake. Ya kara da cewa ta yiwa Ubangijinta ta tafi ta kyaleshi babu abin da aka yi masa shi. Iman ta rushe da wani kuka mai turiri tun daga kahon zuciyarta zuwa idanuwanta, ma'ana kana jin kukan kasan yana dauke da bakin ciki mai tsanani ba irin wanda ake kirkirowa bane wato kukan dadi ko na kissa. Tsananin damuwar da Suhaif yake ciki, zazzafan kukan da ya labe yana sharba sai ya lafa, hankalinsa gaba daya ya tashi ya dira akan halin da yaga Iman ta shiga yanzu-yanzu. Iman me ya saki kuka? Me aka yi miki? Suhaif ya fada a lokacin daya je ya tsaya a gabanta. Ta kasa magana kuka take tayi abinta. Ya gigice gaba daya, ya hau lalube-laluben aljihu ya lalubo mata wani farin hankicin ya mika mata yana mai tsananin bata hakuri, har sai da kukan ya lafa. Ta dago ta dubeshi cikin sanyayyiyar murya ta ce "Na yi zaman mutunci da amana ni da *yan uwanka, iyayenka, da jama'ar garinku. Mun yi zama ni da kai zaman amana, ka taimake ni, ka tsaya tsayin daka har sai da na yi rayuwar jin dadi da kwanciyar. Mun rabu kana kuka ina kuka, na tafi na barka da sona da tunanina, na tafi da tunaninka da sonka. Ko da yaushe kana addu'ar ka ganni, nima ina addu'ar in ganka. Kamar yadda Najib ya fada min kazo garin nan nemana, nima na taba zuwa Doko nemanka da daddare na aika Yaro gidanku aka ce ka kaura Lagos, takanas don kai naje Doko tun daga filin jirgin Kano lokacin da zan tafi Makka karatu. Tunaninka ne yayi min yawa dole na je ganinka koda jirgi zai tafi ya barni. Ina gani na a Kano naji bazan iya barin kasar nan ba tare da naje na ganka munyi sallama ba kafin in wuce. Duk sanda naga mai sunanka, ko mai kamarka sai naji gabana ya fadi in zata kai ne. Mun hadu ni ina murna kai kana bacin rai, duk da dai mun hadu a cikin wani yanayi na babu zancen soyayya tsakaninmu. Suhaif ina sonka ne kawai a raina amma nasan bazan aureka ba saboda har tsinuwa Mahaifanka suka ambata idan baka rabu dani ba. Amma ina son muyi rabuwar arziki yadda idan mun hayayyafa *ya*yanmu zasu yi zumunci ko kuma ma suyi aure tunda mu bamu yi ba. Suhaif bani da niyyar in yaudareka, ba yaudararka nayi ba. Kaji dalilin da yasa zan auri Hamma Huzaifa ba kai ba. Mun rabu a zatona ma kayi aure ka manta dani. Sai kuka ya kece mata. Sai nima kuka ya kece min domin na tuna tsumammen tsumin so da kauna wanda na sha nai tatul daga karshe........... Gwalo... Bazan karasa ba ehe. Reedwan Suraj Isma'il ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ YARENA ADDININA ___CIGABAN LABARI Suhaif ya matse idanuwansa ya ce "Daina kuka, kar kiyi kuka. Kukan nan naki zai iya dasuwa a raina ya zamarmin damuwa. Iman nasan baki yaudareni ba, nasan ba mu isa mu gocewa kaddarar Ubangiji ba. Damuwata ita ce yadda rayuwata zata kasance nan gaba. Sai ya yi shiru ya kasa magana. Iman ta ce "Kamar yaya? Suhaif yayi shiru ya girgiza kai ya ce "Kimin addu'a duk lokacin da aka ce miki na mutu kada ki sake ki bari Huzaifa yasan ina sonki. Ya juya ya tafi, ya dafe kirjinsa da alama zuciyarsa ce ta matsa masa da ciwo. Da kyar yake iya jefa kafarsa ya nufi cikin mota ya zauna ya kifa kansa akan sitiyari. Iman ta kalli gabas yamma, kudu da arewa ta rasa mai taimakonta, ta ji kamar ta zauna tayi ta kwala ihu sai ta kamo kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ta taho ta nufi hanyar gidansu kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki, dakyar take tafiya. Ta zo dai-dai motar da Suhaif ya shiga ya kulle kansa ta kwankwasa masa glas, ya dago ya dubeta, ta ce ya sauke gilas. Ya girgiza kai alamar a'a, yayi mata nuni da hannu alamar ta tafi. Hawaye mai radadi yake zubowa daga idanuwansu. Sai ta daga masa hannu ta ce "Good bye Suhaif I miss you. Shima ya daga mata hannu ya ce "Bye-bye Iman I miss you too. Ta tafi tana waiwayansa tana daga masa hannu, shima yana daga mata hannu su duka kuka suke har ta kure ya daina ganinta, ta daina ganinsa. Iman tasha mamaki da taga Hamma Huzaifa a zaune a cikin get din gidansu akan wani benci kusa da dakin mai gadi, shi da ta bari a gida tare da su Najib. Yaushe ya fito? Ta ina ya biyo basu ganshi ba? Mai ya zo nema? Sai tayi sauri ta goge hawaye ta hau murmushin karfin hali. Taje wajensa tana tambayarsa ita ya zo nema? Yayi dariya ya ce "Na zo in ganki kafin inje in kwanta, yau kwana zan yi a zaune, ba zan iya barci ba saboda farin cikin daurin aurenmu gobe. Zan auri macen da na taba so a rayuwata, wacce nake so a rayuwata, wacce na fi so a rayuwata, wacce zan ci gaba da so har karshen rayuwata. Sai Iman ta fashe da kuka ta zauna a gefensa a sanyaye. Huzaifa ya rikice ya tambayeta kukan me take? Sai ta ce masa kukan me zata yi wanda ya wuce kukan dadi. Ita kuwa ji tayi hankalinta yayi mummunan tashi, ta taho da tausayin Suhaif ga kuma Huzaifa. Duk sun yi mata halacci a rayuwa, kuma ta saba dasu su duka. Najib da Muslim sun zo sun iske Suhaif zaune a cikin mota. Sun nemi Huzaifa basu ganshi ba, sai suka shiga mota suka tafi, daman sallama zasu yi masa. Sun shiga katafaren Hotel din da aka sauke su, dakinsu yana kusa da dakin Babansu. Sauran dakunan ma duk bakin su Huzaifa ne daga garuruwa daban-daban, wasu kuwa abokansa ne daga Saudiya da Bahrain har da abokin nan nasa El-Sadik shima ya zo. Najib ya taba kofar dakin Babansu yaji a kulle daga ciki, munsharinsu na tashi, shi ya tabbatar masa sun dade da yin bacci. Su Najib sun shiga sun kwanta yayin da gajiya ta dannesu kan kace kwabo Najib da Muslim sun yi bacci amma ban da Suhaif. Idonsa biyu ya kurawa fitila ido yana tunani. Tambayar anan shine shi bai gaji bane kamar yadda sauran suka gaji? Amsar ita ce Suhaif ya gaji shima yadda sauran suka gaji, amma wani yakin yafi wani, damuwar da yake ciki tafi gajiyar damunsa. Idan ya gaji da kwanciya sai ya tashi ya zauna. Ya sauko kasa ya kwanta kan kafet. Ya gaji ya hau gado duk juyi yana ambaton La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntum minal zalimin, da dukkan addu'ar data shigo bakinsa. <3 ______RANAR DAURIN AURE______ <3 Da misalin karfe goma sha daya na safe za'a daura auren Hamma Huzaifa da Iman. Misalin karfe tara Huzaifa ya shigo dakin su Suhaif cike da fara'a kai ka ce an masa albishir da Aljannah ne, hannunsa dauke da wata katuwar leda. Bayan yayi sallama ya shigo Najib ya je da fara'arsa ya mika masa hannu suka gaisa ya yi masa kirari ya ce "Ango kasha kamshi. Ango na Fatima da Zainab. Baban Fatima, kai ne Huzaifa Baban Huzaifa. Angon Fatima kuma Baban Fatima. Huzaifa ya kyalkyale da dariya ya ce "Najib a ina ka iya kirari haka kamar wani maroki? To na nadaka sarkin maroka a wajen daurin auren nan. Suka kwashe da dariya su duka dakin har da Suhaif. Huzaifa ya mikawa Muslim hannu suka gaisa, sannan ya mikawa Suhaif hannu. Gaban Suhaif sai da ya yanke ya fadi da yaga Huzaifa. Babu abinda Suhaif ya keji yau sai faduwar gaba da tashin hankali. Yasa hannu ya rike bangaren kirjinsa na hagu inda zuciya take. Shi kadai sai Ubangijinsa yasan halin da yake ciki a safiyar yau. Hamma Huzaifa ya zazzage kayan cikin ledar akan gado. Sai ga wasu dandatsa-dandatsan shaddoji farare sol a dinke set uku iri daya. Riga da wando da babbar riga sunsha dinkin surfani da brown din zare. Hade da hular data shigo da kayan itama guda uku. Najib yana dagawa yana gwadasu yana yaba kyawun da suka yi. Hamma Huzaifa ya ce "Kaifa Suhaif sun yi maka kyau? Suhaif ya matso ya daga yayi murmushi ya ce "Kyau kai! Ai dole ma a kalle ka Ango. Amma yaya har guda uku iri daya? Huzaifa ya ce "Ni da kai da Najib na dinkowa saboda kuma abokan ango mu fito fes iri daya. Sai su duka suka ce "A'a bai kamata suyi anko dashi ba ai an fi so ango yafi kowa caba ado saboda ya bambanta, kowa ya ganshi yasan shine. Muslim ya na taya Huzaifa rokar su Suhaif akan su yadda suyi ankon babu komai shi daman haka yafi so. Daga karshe Suhaif suka yarda zasu saka. Huzaifa ya dauki nasa kayan ya saka a leda yayi musu sallama yace zai tafi gida sai sun hadu a wajen daurin auren kar suyi African time. Najib ya lura da Suhai baya cikin hayyacinsa sosai, da alama akwai ciwon da yake damunsa asafiyar yau. Baya jin dadin jikinsa da asuba ma ya lura da kyar yayi salla yana yawan cije baki ya dafe kirjinsa. Abinci ma da aka kawo bai ko dandana shi ba. Najib ya dube shi ya ce "Suhaif ta shi ka fara wanka muyi mu shirya kar mu makara. Yayi minti biyar a zaune sannan ya yunkura zai tashi sai ya koma ya zauna ya kasa mikewa, da sauri Najib ya tare shi. Ya ce "Lafiya Suhaif, ko in kaika bandakin? Suhaif ya girgiza kai alamar a'a, ya tashi yana tafiya a hankali ya shiga ban daki hannunsa dai a dafe da kirjinsa. Yana shiga suka ji ya ce "Subhanallah" Najib ya shiga a guje yaga Suhaif daure da tawul yana tsugune yana rike da hannunsa. Najib ya tambaye shi "Lafiya? Suhaif ya ce famfon ruwan zafi ya bude ya manta ya tara hannunsa shine ya kone. Najib ya ce "Wai tunanin me kake yi haka har ka budewa kan ka ruwan zafi, ga hannunka nan ya sale? Haba Suhaif kayi hakuri mana ka barwa mai duka komai. Najib ya surka masa ruwan wanka, ya ce ya shiga yayi wankan. Najib ya fito daga ban dakin hankalinsa a tashe. Muslim wanda bai san abunda yake faruwa ba sai ya hau tambayar Najib "Wai me yake damun Suhaif ne? Najib ya ce "Baya jin dadin jikinsa ne. Bayan Suhaif ya fito Muslim ya shiga wankan. Kayan ma Suhaif ya kasa sawa a dai-dai sai karkarwa hannunsa yake Najib ne yake gyara masa. Najib yana ta bawa Suhaif baki ya kwantar da hankalinsa kada ciwo ya kama shi. Budar bakin Suhaif sai ya ce "Dan Uwana Najib kayi min addu'a, yau za'a daurawa Iman aure nima kuma yau zaku yi taron jana'izata. Najib ya ji gabansa ya fadi ya zabura ya dafe kirji. Ya ce "Suhaif, haba Suhaif meye duniya? Daman nasan abunda yake damunka kenan. Ko kuma ka hakura da zuwa wajen daurin auren ka kwanta. Suhaif ya girgiza kai ya ce "Zanje, zan iya zuwa karka damu. Najib ya zauna kan kujera yayi shiru ya zurawa Suhaif ido ya rasa yadda zai taimake shi. Dame zan taimaka masa ya rage damuwa? Babu! Iman ce kawai maganin, babu Iman kuma. Muslim ya fito daga wanka ya ce da Najib "Yayana shiga, na fito. Najib ya tashi dakyar yake tafiya saboda damuwa. Yana shiga shima ya kwalla kara. Muslim ya shiga da sauri sai ga Najib a tsugunne ya rike hannu, tunani yasa shima ya budewa hannunsa famfon ruwan zafi ya kona hannnu. Muslim ya ce "Yau lafiyarku kalau kuwa? Ya yi masa sannu ya fito ya jawo kofar ban daki ya rufe cike da tunani ya kasa gane kan Suhaif ga Najib shima yana kokarin rikicewa. WAJEN DAURIN AURE ---- <3 Karfe goma sha daya dai-dai sai ga Suhaif a wajen daurin auren, daman su Babansu sun dade da tahowa goma ma anan tayi musu, suna tare da Baban Huzaifa a falon su Iman. Wajen daurin aure ya cika dankam da jama'a duk lungun da ka waiga mazane. Yare iri-iri ke tashi a wajen daurin auren, dangin Huzaifa da dangin Mahaifin Iman daga Gombe yaren fulatanci suke. Wasu jama'ar yaren Hausa suke, abokan Huzaifa daga Saudia da Baharain larabawa ne dan haka yaren Larabci suke. Abokan Iman Mumuyawa suma sun hallara suna yaren Mumuyanci, wasu daga cikin dangin Mahaifiyar Iman sun zo suma suna nasu yaren Igbo. Huzaifa ya fadawa masu daurin auren cewa su daura auren da Hausa saboda ba kowa ne yake jin Fulatanci ba amma yawancin Fulanin suna jin Hausa. Ango Huzaifa, Suhaif, Najib suka jero suka taho kayansu iri daya, hula iri daya, tsayinsu daya, dogon hanci dukkansu, dara-daran idanuwa dukkansu, fararen hakora cas idan suka yi dariya dukkansu, farar fata dukkansu. Duk da Huzaifa ya fisu fari, shi fari ne sosai. Jama'a sun yi mamaki da suka ga ango da wasu sun yi anko, har wasu suka shiga tunani ko daurin auren mutane uku ne. Maroka sai kirari suke musu, makada sai buga ganga suke suna wakesu su duka ukun, bayan sun tambayi sunayen su Suhaif. Suhaif tsaf da shi, ga mutum har mutum amma a zuci dai ba mutum bane, domin zuciyarsa ta nutsa ta tafi tunani mai tsanani. Dai-dai lokacin da aka hallara ana daf da fara daurin aure Suhaif ya ji numfashinsa yana kokarin kakarewa saboda tsananin damuwa. Ba ya so Suhaif ya gane halin da yake ciki, sai ya faki idon Huzaifa da Najib yayi wuf ya bar wajen ya tafi can bayan wani gida da yake gefen gidansu Iman ya jingina a jikin katangar ya runtse ido. Yana bude ido Iman ya gani da dandazon mata kawayenta da *yan Uwanta. Amarya ta cancada ado kamar wata India suna take mata baya kamar wata sarauniya. Za su shiga gidan da Suhaif yake jikin katangar, a nan zata zauna ita da kawayenta saboda duk gidajen sun cika da mutane. Haka aka hau kallon-kallo shi da Iman har suka wuce. A cikin kawayen har da Zubaida da Naja'at suna shiga get din gidan sai Iman ta fashe da kuka, Naja'at da Zubaida ma kuka suke kamar ransu zai fita. Sauran suka yi ta basu hakuri amma suna ta mamaki, kansu ya daure meke faruwa ne haka suke kuka? Can gidan su Huzaifa kuma Mahaifiyar Huzaifa da kannensa suke fama da matar Huzaifa Zainab, ta dauki *ya*yanta da kayanta wai ita kasar zata bari kasarsu zata tafi ta fasa auren tunda yayi mata kishiya. Da tana ganin wasa ne yau ta tabbatar da gaske ne da ta leko kofar gida ta wundo ta ga taron *yan daurin aure da gaske kuma daurawa za suyi baza su fasa ba. Maman Huzaifa da sauran mata dukkansu babu larabci, ita kuma babu Fulatanci babu wanda yake gane abunda take cewa. Aka aika wajen daurin aure a kira Huzaifa ba a samu ganinsa ba saboda taro. Sai aka aika aka kira Iman don ta fassara musu larabci abunda Zainab take cewa. Kafin Iman ta fassara musu abinda Zainab take fada, sai suka ga Iman ta fashe da kuka itama. Hankalinsu ya sake tashi dakyar aka lallashi Iman ta tsagaita da kukan, sannan ta shaida musu abun da Zainab take fada. Shine fitowar Imar da Iman tayi da kawayenta a cikin tashin hankali kuma ta hadu da Suhaif a irin halin da take ciki koma fiye da nata. Abu ya hadu duk yayi mata yawa, tana shiga ciikin gidan sai ta shiga daki tayi ta fusge kwalliyar da aka cancara mata tana rusa kuka ana bata hakuri. Najib da Huzaifa suna ta waige-waige ko za su ga Suhaif basu ganshi ba. Najib ya cewa Huzaifa "Bari in je in kira shi. Huzaifa ya ce "To" Najib ya tafi ya kutsa cikin jama'a yana ta neman Suhaif, sai Muslim ya gani. Ya tambaye shi ko yaga Suhaif? Muslim yake shaida masa yaga Suhaif ya wuce ta gabansa, ya nuna masa in da ya nufa. Suka nufi wajen da ya nufa, sai suka hango shi a zaune cikin ciyawa ya hada kai da gwiwa. Suna karasawa wajensa ya zabura ya tashi yana cewa "Kar ku karaso wajena, ku rabu da ni. Idanuwansa sun kumbura, kallo daya zaka yi masa kasan yana cikin tashin hankali kamar mai shirin zautuwa. Najib ya durkusa a gabansa yana lallashinsa yana bashi baki, dakyar Suhaif ya yarda ya zauna. Muslim ya ce da Najib "Ko in ke in kira su Baba ne? Ni na kasa gane abunda yake faruwa. Najib ya ce "A'a ba zaka iya ganinsu Baba ba, suna can cikin falon su Iman wajen masu daurin auren. Dai-dai lokacin suka ji lasafika ana sanarwa ana cewa "A saurara za'a daura auren yanzu. Suhaif ya zabura zai tashi a gigice. Ko ina zai je? Najib da Muslim suka rike shi suka mayar da shi ya zauna. Haka zuciyarsa take ta bugawa fuf-fuf-fuf yayin da numfashinsa yake sama yana kasa, ya dafe kirjinsa saboda tsananin ciwon da zuciyarsa take yi masa da tsananin ciwon kai. Yana rungume da hannun Najib da kirjinsa, Najib ya tsuguna a gefensa, Muslim ma a daya gefen suna tofa masa addu'a suna masa firfita da babbar rigarsa da suka cire masa ganin gumin da yake hadawa. Suhaif ya daga ido ya dubi Najib ya ce "Dan Uwana Najib mutuwa zan yi, ciwon da yake kokarin kama ni sana diyyar rashin Iman shine zai zama ajalina. Na dauka zan iya daure rabuwa da Iman ashe bazan iya ba. Kar kuji haushina, kada kuga laifina, kar ku dauka ni na dorawa kaina. Allah ne Ya dora min Shi zai cire min kuma bai cire min ba. Nayi addu'a da kaina Allah Ya yaye min tun ba yau ba sai gashi sai kara son ta nake. Na rasa Iman na rasa ta har abada, haka kuma zan rasa rayuwata. Mutuwata ita ce hutu, Najib kumun addu'a gara na mutu da in zauna na dauwama a cikin wahala da kunar rai. Na rasa farin cikin rayuwata har abada, gara na bar duniyar. Dan Allah kada ku bari Iman tasan sonta ne yayi sanadiyyar mutuwata. Kada ku bari Huzaifa ya san halinda na shiga har yayi sanadin ajalina. Huzaifa ya na da kirki, yana son Iman zai riketa. Na godewa Allah da Iman ta samu miji irin Huzaifa, ina son Iman ta huta a rayuwarta saboda tasha wahalar rayuwa. Najib na gode da kokarin da kayi min da taimakona da kasha yi dan na samu Iman Allah ne Bai yi ba, na gode. Najib ya rushe da kuka ya rungume Suhaif suka kankame juna suna kuka su duka. Muslim yayi tagumi ya sa su a gaba yayin da idanuwansa suka cika taf da hawaye dan tausayi, yanzu ya gane makasudin damuwar Suhaif. Sai kawai Suhaif ya mutu. Labarin ya kare daga nan......... Lolx Daga wannan Tuzurun na ku mai suna Reedwan Suraj Isma'il [[[[[[[]]]]]]]-----------YARENA ADDININA ***CIGABAN LABARI Ana ta magana da fulatanci, a fassara da Hausa haka dai ake ta bayani a wajen daurin auren. Liman mai daura aure da waliyan ango da amarya duk sun hallara. Aka sanar cewa ga sadaki nan waliyan ango za su mikawa waliyan amarya, za'a daura auren akan sadaki naira dubu ashirin. A lokacin da mai sanarwa a lasafika yayi sanarwa karshe sai da kowa ya gigice. Iman da kawayenta suka fito waje da gudu. Goggo da Mama da suke zazzaune a dakin Maman Iman da Maman Iman din da sauran mata suka kado da gudu falo. Maman Huzaifa da kannensa da danginsu mata a cikin gida sun yi wuf sun fito kofar gida. Najib da Suhaif da suka kankame juna suna kuka suka yi firgigit suka rabu. Shin meye ya gigitasu ne haka? Me aka ce da kowa ya firgice ya fito? Maza kawai aka sani a wajen daurin aure. Amma wannan daurin auren ya zama na maza da mata a cakude. Suna zaton wanda yake sanarwar ne bai jiyo dai-dai ba, ya yi kuskure sai suka ji ana mai-maitawa, wani ma ya karbi lasifikar yana sake mai-maitawa da Hausa, da fulatanci ba kuskure bane gaske ne an daura auren Fatima Lamin Gombe da Suhaif Hayatu Doko ga sadaki nan lakadan an mika, har aka kara salati goma da kulhuwallahu da sauran addu'oi aka shafa. Kowa ya kasa tafiya gida sai ya ji kwakwaf. Waye Suhaif? Kowa Huzaifa ya sani, kuma saboda shi aka zo daurin auren. Huzaifa yana ta yiwa jama'a bayani cewa kada su damu haka Allah Ya rubuto, ya barwa Suhaif ya aureta. Saboda Suhaif ya zama dan uwansa duk daya ne shi da Suhaif din. Haka jama'a suke watsewa suna tafe suna sake jinjina wannan abun al'ajabi. Wasu kuma suna ta rububin zuwa kallon Suhaif mai tsananin rabo tsuntsu daga sama gashasshe. Masu daukar hoto da bidiyo suna ta bin Huzaifa da maroka, Huzaifa yayi dariya ya nuna musu Suhaif ya ce "Ga ango can ku bishi. Huzaifa ya mikawa Suhaif hannu suka gaisa ya ce masa, "Congratulation. Haka Suhaif yake kallon Huzaifa tamkar gunki ya rasa kalma guda daya da zai fara yiwa Huzaifa ta godiya. Mamaki marar misaltuwa a fuskar Suhaif da Najib. Suhaif a cukurkudansa yake, babbar riga a hannunsa takalminsa a hannun Muslim, hularsa a hannun Najib haka suka yi wuf suka fito daga dan sakon da suka labe. Sai Huzaifa ne ya ankarar da su ya ce "A'a yaya ango a haka ku saka masa rigar da takalmin mana. Huzaifa da jama'ar da suka baibayeshi ya na ta musu bayani suka dunguma suka yi can bakin titi inda suka ajiye abubuwan hawansu. Baba na Doko, Baba na Kano, Baban Iman da Baban Huzaifa ne suka fito daga falon su Iman. Najib ya tare su ya ce "Baba ya aka yi haka ta faru? Sai Baba na Kano ya ce "Yauwa, ina Suhaif din? Ku taho gaba dayanku. Ku aika akira Iman, Mamarta, Mamanku Goggo duk ku zo mu hadu a falon Baban Huzaifa za muyi magana. Suhaif ya kalli Najib, Najib ya kalleshi. Suhaif ya ce "Tabani ko mafarki nake yi. Najib ya mintsine shi a keya ya ce "Ka ji zafi? Suhaif ya shafa wajen ya ce "Eh naji zafi da gaske ne kuwa ashe, Najib kaganni na warke na daina jin ciwon komai. Najib da Muslim suka kwashe da dariya. Yadda mamaki ya hana Suhaif sakat haka ya yiwa Iman wanna illar ta kasa sukuni, ta shiga ta fita ta tambayi kawayenta anya kuwa kunnuwanta sun jiye mata dai-dai, Suhaif aka ce? Kowa yana shaida mata abunda taji gaskiya ne, Suhaif ne angonta. Sai take tambayar su Naja'at wadanda murna ta cika musu ciki wai ya akayi haka ta faru? Suka amsa mata suma da suke a nan cikin gida tare da ita basu sani ba. Hajara kanwar Iman ce ta zo tayi kiranta ta ce ta zo za'a shiga meeting da Iyayensu, Naja'at da Zubaida ma suka bita. Gaba daya sun hallara a falon, Huzaifa kadai ake jira. Duk wanda ka kalli fuskarsa a wajen yana cike da tsananin mamaki da jinjina ga Allah bisa ikonSa daya nuna yanzu-yanzu nan. Ikon Allah ya wuce haka. A jima Goggo ta ce "Allah mai iko. Mama ta ce "Ikon Allah. Baba na Doko ya ce "Allah mai girma, Baba na Kano ya ce "Allah Ya wuce haka. Suhaif ya girgiza kai ya ce "Cafdijam, Allah kenan, Najib ya ce "Ka godewa Allah ka sake gode masa. Mamar Huzaifa tayi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne komai da yadda Allah yake tsara shi. Iman ta sunkuyar da kai kasa, a jima tayi ajiyar zuciya ta ce "Uhm. Huzaifa ya shigo da fara'arsa ya ce "Don Allah kuyi hakuri na barku kuna jirana, mutane nake ta sallama. Ya tafi kusa da Suhaif ya zauna, yayi shiru yana sauraron abunda Mahaifinsa ke cewa. Bayan Mahaifin Huzaifa ya bude taro da addu'a cikin harshen Hausa yake magana ya ce "Ba mu kadai ba yau duk wanda ya halacci daurin auren na ya tafi da dimbin mamaki, har wanda za'a bawa labari a wani waje zasu yi mamakin abinda ya faru yanzu-yanzun nan. Amma duk abunda aka ce Allah ya wuce mamaki. Gaba daya suka dauka "Haka ne, gaskiya ne. Baban Huzaifa ya ci gaba da cewa "Kamar yadda ku kaji haka, nima haka naji. Cikin daren jiya misalin sha biyu, har dakina Huzaifa ya je ya tasheni ya shaida mun yana ganin zai hakura da Fatima ya barwa Suhaif. Na rasa meye Suhaif? Ya ce suna ne Baba, Suhaif bakin da suka zo daga Kano. Na tambayeshi kamar yaya zaka bar masa Fatima? Kamar wata shadda ko yadi ko atamfa da ya gani a jikinka ya ce yana so. Yayi min bayani mai tsawo har sai da na gamsu. Na shi masa albarka akan tausayawar da yayi, ya sani a gaba cikin dare muka taso Mahaifin Fatima, shima da kyar ya gane abunda muke fada masa. Ga bacci a idonsa ga wani cukurkudaddan labari. Bayan ya gamsu da hujjojin Huzaifa sai yayi addu'ar Allah Ya zaba abunda yafi alheri. Dashi muka dunguma a mota zuwa Hotel din da Mahaifan Suhaif suke, suma da kyar muka tashe su suka bude mana kofa muka shiga muka zauna. Mun kayi musu bayanin abin dake tafe damu sai suka ki amincewa da farko. Suka ce baza'ayi haka ba, su da suka zo daurin aure sai a buge da daura musu. Huzaifa yayi musu bayani cewar babu damuwa, karsu damu Allah Ya sani tsakani da Allah ya yiwa Suhaif wannan kyauta daga yanzu sun zama madauri daya. Suma suka yi ta godiya dashi albarka. Huzaifa ya rokemu kada mu bari wani ya sani musamman mata, idan aka daura zasu ji don haka har ita Fatima da Suhaif din basu sani ba. Najib ya yi gyaran murya ya ce "Baba wanne bayani Huzaifa yayi muku haka har ku ka gamsu ku ka yarda? Baban Huzaifa ya yi dariya ya ce "Waka a bakin me ita tafi dadi, gaka ga Huzaifa a kusa da kai. Huzaifa yayi dariya yayi gyaran murya ya gyara zama ya ce "Na kasance tare da Fatima tun da aka haifeta, ina daukarta har ta fara girma a wajena take yini. Idan tana kukan makaranta ni nake mayar da ita in bata alewa sannan ta zauna. Haka bayan ta fara girma ta fara sanin meye duniya, meye matsalolin duniya, ni take tara tana tambaya. Da kanta ta tambayeni addinai daban-daban, na wayar mata da kai, na dinga cusa mata addinina da yadda zata yi da kuma yadda zata yi taka tsantsan da rayuwar duniya. Har ta girma tasan ciwon kanta, tasan abu mai kyau da marar kyau. Na tafi Madina makaranta na tafi da son Fatima amma na tafi da tsananin bakin cikinta, a tunanina Jaririn dana gani nata ne. Haka baisa na daina sonta ba, ko na tsaneta, ko nayi tunanin fasa aurenta. Ina karatu, har bayan shekara guda cur da tafiya ban samu nayi magana da mutanen gidanmu ba, a lokacin gidanmu babu waya sai dai idan na hadu da wanda na sani a can in rubuto wasika. Na hadu da matata Zainab *yar kasar Bahrain sun zo aikin Hajji ita da Mahaifinta, ta nuna tana sona har ta shaidawa Mahaifinta. Abu kamar wasa, da farko naki yadda saboda ina ganin da wacce na ajiye anan ina tunanin ita zan aura, domin ina ganin nine kadai zan iya aurenta da da, in kuma tsaya tsayin daka in ga ta kula ko taci gaba da addininta tun da Uwa da Uba duk ba Musulmai bane. Mahaifin Zainab ma ya ki yadda ya ce ba zata aureni ba, amma ita ta dage har sun koma kasarsu sai naga sun dawo. Ni da Mahaifinta muka zauna muka yi magana sosai ba yadda na iya, da ya amince sai nima na amince. Mahaifina da *yan uwansa suka je can Madina muka hadu muka tafi Bahrain zancen auren. Daga Bahrain muka dungumu da ita da Mahaifinta mu ka zo Nigeria suka ga gidanmu da asalina. Anan aka daura mana aure, amma kafin aurenmu na shaida mata akawai wacce nake so kuma munyi alkawarin aure da ita sunanta Fatima, rayuwata kankat ita nake da burin aura kuma ko yau idan Allah Yayi zan iya auranta. Zainab tana sona tace duk ba matsala. A lokacin da na zo ban samu Fatima ba ance ta tafi an rasa inda take. Mahaifiyata tayi min bayani tas akan jaririn Fatima cewar ba danta ba ne. Nayi takaicin, nayi kukan batan Fatima har bayan na koma na dauwama a cikin yi mata addu'ar Allah Ya kareta duk inda take, duk da nasan neman ilimi take da kuma inda zata zauna tayi addininta. Na haifi *yata ta fari na saka mata suna Fatima saboda son da nake mata. Kamar yadda dukkaninku ta baku labari na mata hanya ta je Saudiya karatu muka sake haduwa acan, duk da ni a lokacin na kaura Bahrain amma koda yaushe muna waya kuma muna zuwa Hajji da Umara mu hadu. Na fada mata ina son in aureta sai taji banbarakwai domin ta daukeni tamkar Yayanta, ta nuna min ba zata iya aurena ba, badan bata sona ba sai dan wani girma da matsayi da take jina a zuciyarta. Ga kuma matata kawarta. Na nuna mata duk abubuwan data zano bai haramta aure tsakaninmu ba. Ta amince daga baya, tun a waya muka shaidawa Iyayenmu, babu wanda bai yarda ba a cikinsu Mun hadu da Suhaif da Najib a satin da zamu taho daurin aurenmu. Bani da masaniya akwai tsohuwar soyayya a tsakaninsu, na dai kula Najib ya fi Suhaif fara'a da son hira. Sai na zata halittarsa ce haka, sai ban damu ba. Muka dunguma muka taho Abuja, to a ranar na fara sanin halin da ake ciki. Zan shigo kenan cikin falon da Najib da Fatima suke zaune sai na ji suna hira Najib yana shaida mata damuwar da Suhaif ya ke ciki a sanadiyyar sonta. Itama tana kuka tana fadar halaccin da Suhaif yayi mata. Abunda ya fi dagamun hankali shine da aka ce yaki aure saboda jiranta, kuma ba zai yi aure ba har abada idan ya rasata. Ban nuna musu naji hirarsu ba, a mota hanyarmu ta zuwa Kano nake tambayarta yadda suke da Suhaif ta bani labari tas zamanta a garin Doko, da taimakon da Suhaif yayi mata har da yadda suka yi da matsafan da suke cutarta. Amma bata ambaci kalmar soyayya da take tsakaninsu ba saboda kada in sani raina ya baci. Na ci gaba da kula da Suhaif da halin damuwa da yake ciki, tun daga Kano har zuwasu daurin auran nan. Tuntuni nake tunani ko na bar masa ita tunda yana tsananin sonta? Sai na shiga kokonto ina zulumi domin ina sonta nima, idan na bar masa ita kuma zan cutu. Naci gaba da addu'ar Allah Ya zaba mana abunda yafi alkhairi kuma duk sanda zan kwanta barci sai nayi istahara Allah Yasa inji zabi mafi alheri da yafi kwantamin a zuciyata. Jiya da daddare ana hira sai Suhaif ya tashi ya fito, Fatima ta biyo shi, ni ma sai na biyosu. Na ji duk abunda suka fada, yana kuka tana kuka har Suhaif ya ce tayi masa addu'a idan ya mutu. Ya roketa kada ta bari in san ciwon son ta ne ya kashe shi. Dukkanmu nan Musulmai ne, duk Musulmu ya san Hadisin Annabi da ya ce "Imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya sowa dan Uwansa abunda ya sowa kansa. Ina son Fatima, Suhaif ya na son Iman fiye da ni, har yana kokarin haramtawa kansa aure gaba daya a rayuwarsa, yana kokarin rasa ransa saboda sonta. Itama tana sona amma kuma tana kukan rabuwa da shi tana tausayinsa, zata dauwama cikin tausayinsa musamman idan ya rasa rayuwarsa a kanta. Nayi koyi da hali, dabi'a, kirki da karamci irin na mutanen Madina. Yadda suka yiwa Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da yayi Hijira daga Makka zuwa Madina shi da Sahabbansa. Mutanen Madina da murna suka tare shi, su raba gidajensu suka basu rabi, wasu su saki matansu suka aura musu. Don haka ko da ace na auri Fatima zan iya sakinta in bawa Suhaif ya aura. Idan na auri Fatima na so kaina da yawa saboda ina da mata guda daya, shi kuma Suhaif ba shi da ko guda daya, yana cikin ukuba da tashin hankali ya rasata, ni kuma ina cikin walwala da jin dadi zan aureta. Sai naga bazan iya yiwa dan uwana Musulmi haka ba. Na yanke hukuncin na barwa Suhaif Fatima ya aura ni na hakura. Alla Ya dubi zuciyata Ya san dan shi nayi, sai Ya yaye mun damuwa da bakin ciki. Yanzu haka ni da Ubangiji ne kadai nasan dadin da farin cikin daya rufe min zuciya. Gaba daya suka dauki kabbara, Iyayen Suhaif, Mahaifansa Huzaifa, Mahaifan Iman suka dinga shi masa albarka. Hawaye ke zuba a idanuwansu su dukka harda Huzaifa. Suhaif ya rungume Huzaifa ya kasa magana sai hawaye kawai ke zuba. Iman ta rungume Mahaifiyarta su dukka kuka suke. Mahaifiyayar Iman ta share hawaye ta ce "Lallai sai yanzu na sake gaskatawa, na sake rungumar addinin Musulunci da karfina, zuciyata, da dukiyata gaba daya. Hakika Musulunci addini ne mai salama, addini ne mai girma, addinine mai karamci. Ya koyawa Musulmai son junan su, su hana kansu su bawa dan uwansu, a taba Musulmi daya suji kaman su duka aka taba. Suna da kishin addininsu, na kara gane gaskiya, gaskiya ce, na kuma gane addinin gaskiya. Allah Ya sanar dani hakan ta hanyar *yata ta cikina. Tun da cikinta kafin na haifeta ina mafarkan da suke min nuni da hakan zata faru nan gaba, sai na ki ganewa. Bayan na haifeta sai naga fassarar mafarkaina Musulma na Haifa, mai kira zuwa ga addinin Musulunci, duk naki yarda da gangan na danne sai daga baya naga da gaske Malama na haifa a cikina kuma tana kira zuwa ga gaskiya sai na yarda na bita. Na godewa Allah, Huzaifa na gode, Allah Zai saka maka sakayya da gidan Aljanna dalilin wannan abunda kayi. Huzaifa ya amsa da "Amin na gode Mummy. Mahaifiyar Huzaifa sai yanzu tayi magana ta ce "Huzaifa dana, na yarda da kai dari bisa dari. Nasan tausayinka, kana kaunar *yan uwanka da ma sauran Musulmi gaba daya. Nasan zaka iya haka, zaka iya abunda yafi haka. Mutane suna ta mamaki amma ni dana haifeka banyi mamaki ba. Tunda na sanka fiye da kowa, nasan halinka Allah Yayi maka albarka, Allah Ya saka maka da Aljannah. Hawaye a idon Huzaifa ya amsa da "Amin Fetal" yadda suke kiranta kenan. Wayyo Allah! Ruwan kaina zai kare nima mutuwa zan kawai kowa ya huta tunda na rasa Iman ....... Lolxxx.. Amma dai bari na sa dangana in taimaki Hajara (Rabecca) in aureta.... Lolxxx Reedwan Suraj Isma'il _____________________ YARENA ADDININA ___CI GABAN LABARI Huzaifa ya dubi matarsa Zainab cikin harshen Larabci ya ce mata "Zainab kinga rayuwa ko? Kinga muhimmancin hakuri ko? Kawayenki a can suna zuga ki wai danme zaki yarda ayi miki kishiya bayan ku a kasarku ba'a cika yin haka ba. Kika dauki zuga kina cewa saidai in sake ki, dakyar na shawo kanki to kin gani komai sai Allah Yayi. Idan ba wata kaddara ba mai tsanani bani ba kara aure har abada, daman ita ce kadai wacce nake tunanin zan aura. Zainab tayi murmushi ta gyada kai ta ce "Hakika na ga muhimmancin hakuri, kuma na sake gane zaman duniya. Na yi nadama ku yafe min. Ta dubi Iman ta ce "Ki yafe min. Iman na kuka suka rungume juna Iman ma ta cewa Zainab ta yafe mata. Mahaifin Suhaif yayi ajiyar zuciya ya ce "To mun godewa Allah, Huzaifa! Suhaif ya taho muku da gudunmawarsa zai bawa ango da amarya. Motoci ne guda biyu yake da niyyar idan zamu tafi ya baku, daya ta amarya daya ta ango. Huzaifa da Mahaifansa suka yi godiya, Iman da Iyayenta ma suka yi ta godewa Suhaif. Nan dai suka zauna suka yi ta magana ta farin ciki da godewa juna har zuwa lokaci mai tsawo, sannan suka fito dan za'aje aci gaba da gudanar da shagalin biki. Huzaifa ya shiga gidansu kannensa su Bilkisu sun yi tatul sun cika da bakin ciki. Suna ganinsa suka hau yi masa korafi don me yasa zaiyi musu haka bayan sun shirya sun zo tun daga Abuja zai ce ya fasa ya barwa wani, ga anko har Lagos taje ta kai dinki, ga robobi da memo da kalandu duk sun bugo yanzu sun yi asara kenan. Suka bashi labari har Aljanu Amina ta tayar dan bakin ciki, dakyar ta sauka. Huzaifa yayi ta dariya yana tsokanar Amina yana cewa "Wato suma Aljanun sun yo sabon dinkuna zasu sha biki suka ji an fasa shine suka ji haushi kenan? Sai a lokacin suka bashi labarin tataburza da suka sha yi da matarsa Zainab tana kuka ta hada kayanta da *ya*yanta zata tafi suna riketa. Shi dai dariya yake tayi. Ya zauna ya wayar musu da kai ya fada musu dalilai masu karfi har saida suka gamsu suka saki ransu. Ya rokesu karsu fasa yin hidimar bikin da suka yi niyya, duk abunda suka yi niyya suyi, Fatima dama ai kawarsu ce. Kalandu ne kawai da memo mai hotonsu za'a kona robobi da kufuna kuwa sitika kawai za'a ciccire aje a sake bugo wata da sunan Fatima da Suhaif, zan baku kudin sitikar a lillika a raba. Suka amsa cikin fara'a suka ce babu damuwa sun huce. Sai yanzu farin ciki ya cika zuciyar Iman, hankalinta ya kwanta saboda sanda taji da Suhaif aka daura bata yi bakin ciki ba amma abun ya daure mata kai ta rasa dalilin wannan sauyi, amma yanzu da taji haka daga bakin Huzaifa sai taji hankalinta ya kwanta farin ciki ya lullubeta. Bata da zargin kowa a kanta, don da tana damuwa saboda Suhaif yana ganin bata sonsa dama shine yake sonta. Ga matar Huzaifa ta damu tana kuka dan zata aure mata miji duk ta tsangwami kanta, tasan kuwa har abada damuwar tana ranta. Yanzu Huzaifa ya wanketa bata bata da kowa ba. Zumunci tsakaninsu yanzu ya kullu, haka tsakanin Iyayenta da nasa da Iyayen mijinta Suhaif Alhamdulillahi! Aka sha biki! Budiri!! Birede!!! Babu kwabon Suhaif balle na Iyayensa duk Huzaifa ne yayi komai. Babu abinda Huzaifa bai tanada ba kuma bai fasa duk abunda yayi niyyar yi a bikinsa ba. Anyi liyafu kala-kala, haka duk abunda ake kaiwa gidan Iyayen Amarya na al'ada Huzaifa yasa an kai gidan su Iman a matsayin Suhaif ne ya bayar. Da aka kammala biki sai Suhaif da Iyayensa suka fara shirin komawa gida wato Kano. Yadda suka tsara tafiyar za'a kai su Baba, Goggo, Mama, Zubaida, *ya*yanta, mai aikinta da Naja'at Yola su hau jirgi su tafi. Sai Suhaif, amaryarsa Iman, Najib da Muslim su tafi a motar Suhaif. Huzaifa ya ce karsu damu su Suhaif su hau motarsu su tafi shi zai kai Iyayen nasu Yola su hau jirgi. Huzaifa da Iyayensa, kannansa, matarsa, Mamar Iman, Babanta, kannanta, Mama Tabita da kawayenta Mumuyawa duk sun rako ta bakin mota ana ta koke-koken rabuwa. Huzaifa da Suhaif suka yi musabaha suka gaisa Suhaif ya na masa godiya ba adadi. Huzaifa ya girgiza kai ya ce "Nasan dadin da kaji dan haka karka damu. Saboda Allah nayi, shi zai saka mun da alhairinsa. Huzaifa ya zaga wajen Iman yana mata nasiha ta bi mijinta sau da kafa suk da yasan ita me biyayya ce kuma ta sani amma tuni yake mata, cikin kuka take amsa masa yayin da kwalla ta cika masa ido shima. Iman ta rungume *ya*yansa Fatima da Huzaifa tana yi musu sallama tana kuka. Dakyar Iman ta shiga mota kannenta Abubakar da Hajara sai kuka suke suna rike mata hannu. Haka Mahaifiyar Iman ta damu dan rabuwa da *yarta, ba kamar Mama Tabita tayi kuka har idonta ya kunbura. Akwatinan lefenta guda takwas kadai aka saka mata a but. Suhaif da Iman a bayan mota, Najib ne yake tukawa, Muslim a gaba suka ja suka tafi, suna daga musu hannu suma suna daga musu hannu. A sababbin dalla-dallan motocin da Suhaif ya bawa Huzaifa da Iman wacce ana bata ita kuma ta bawa Mahaifinta kyauta, a ciki za'a kai Iyayen Suhaif Yola inda za su hau jirgi, *yan rakiya suka dunguma wajen motocin. Matan ne kawai suka cika motar Huzaifa, su kuma su Baba suka shiga ta Mahaifin Iman. Mahaifin Iman ke tukawa suka dinguma filin jirgin Yola. Suna da kudin yankar tikiti amma Huzaifa ya hanasu su biya, ya biya musu gaba daya. Su Huzaifa ba su baro filin jirgin ba har saida suka tsaya suka ga tashinsu. Suhaif da amaryarsa Iman suna zaune kawai suna kallon-kallo, farin ciki da kauna fal a zuciyarsu, sun bar Najib da Muslim a gaba suna ta zuba. Najib magana yake ba kakkautawa har saida Suhaif yasa baki ana hirar da shi daga nan Najib ya gangaro tsokanar Suhaif ya ce "Oh! Suhaif da tuni ka mutu, har ranka ya zo makogaro, ya aka yi ya koma? Dariya suke tayi har sai da cikinsu yayi ciwo ballema Iman. Muslim ya ce "Aini ban san farin ciki yana sawa a fasa mutuwa ba sai akan Suhaif. Suhaif dai dariya yake yana cewa "Kwaji da shi, ku ce duk abunda zaku ce ni dai na warke babu ciwo har abada. Su Baba sun rigasu isowa Kano, kafin su Suhaif su karaso har an gyara musu wani bangare in da amarya zata sauka. Kwanan su uku a Kano amma Suhaif baya iya ko leka bangaran Iman saboda kunyar Iyaye sai dai su hadu a falo da safe su gaisa. Daga Kano ya dauketa suka tafi Doko nan ma a bangaren Suhaif aka sauketa. A bangaren akwai falo, daki, bandaki a ciki. Suhaif kacokan shi da kayansa ya kaura gidan Kakarsa Hajja acan yake kwana saboda kunyar Iyaye. *Yan garin Doko sun sha mamaki lokacin da aka fesa musu labarin Suhaif ya auri Iman gashi ya zo da ita. Suka dinga tururuwar bin layi waccan na fita waccan na shiga suna zuwa suna gaishe da Iman. Kawayenta na da duk sunyi aure da *ya*yansu suke zuwa su sha hira da Iman. Daman *yan garin Doko suna son Iman tana birgesu, abunda ya faru yasa suka kita da suka ji labarinta tun asali sai suka daina ganin laifinta. Suhaif da Iman satinsu guda a Doko, dangi sunga Iman, itama ya kaita taga dangi na cikin Doko da kauyuka. Da suke je Garki wajen Iya Furera sai Suhaif ya ce da Iman "Ko in kaiki Gumel ki shiga garin Gumel yadda kika ci burin zuwa Gumel Allah bai yi ba. Iman ta ce "Kaini in ga Gumel tunda gani a motata ma bata haya ba. Suhaif ya kai Iman Gumel daman su Suhaif suna da *yan Uwa dankam a Gumel, yini guda cur suna zagaya Gumel. Iman ta ce "Gaskiya naji dadin yadda Gumulawa suke karbar baki, sun karbeni hannu bibbiyu. Bayan sun yiwa kowa da kowa sallama sai suka fito suka kama hanyan garin Abuja kai tsaye, suna tafe suna hira amma idan Suhaif ya dauko mata hirar soyayya sai ta rufe ido ta kasa bashi amsa, har yanzu kunyar nan tasa da take ji tana nan. Sun isa Abuja lafiya, kai tsaye suka kutsa cikin katafaren gidansa. Masu gadi da ma'aikatansa sun fito taron Suhaif. Amma sai suyi turus su tsaya a lokacin da suka ganshi rike da hannun Iman. Kamar yadda Suhaif ya saba hira da su yana yi musu wasa sosai. Sai suke tambayarsa "Oga yaushe ka samu matar da zaka aura bamu sani ba? Suhaif yayi dariya ya ce "Ku biyoni falo zan baku labari. Gaba daya ma'aikatan gidan ya ce a kira su zo ya na da magana dasu. Suka hadu reras sunyi su ashirin, gaba daya maza ne. Ya sanar musu da cewa Iman matarsa ce yanzu haka daga Jalingo yake can aka yi bikin. Ya musu gargadi, ya ja kunne ya fada da kakkausar murya cewar su kiyayi bata mata rai, idan ta ce a yi to ayin, in ta ce a'a to a bari, saboda zai iya yanke kowanne irin hukunci akan wanda ya bata mata rai. Ya sanar musu da cewar zasu iya yi masa laifi sai dubu ya hakura amma idan suka yiwa Iman sau daya ba zai yi hakuri ba. Ko shakka babu sun ji ajikinsu da gaske yake yana son matar nan ko ba'a fada musu ba. Akwatinan Iman direba daya kwaso daga but ya shigo da su falo sannan Suhaif ya sallamesu, kowa ya koma wajen aikinsa. Iman ta dubi Suhaif tayi murmushi ta ce "Yaya irin wannan fada da kake yi musu a kaina kamar ka auro *yar gwal? Suhaif ya ce "Ai kinfi *yar diamond ma Habitti (masoyiya). Tayi murmushi ta ce "Yanzu duk wadannan ma'aikatan gidan nan ne? Suhaif ya ce "Idan bakya sonsu sai in koresu a dauki wasu. Iman ta ce "A'a duk zamu zauna dasu ba kora, sai dai ina son a karo mata kamar guda biyar naga gaba daya maza ne. Suhaif ya ce "An gama Madam, za'a samo miki mata tunda gidan da mace yanzu, da ai gidan gaurone. Suhaif da kansa yake kai kawo a cikin falon. Ya dauko juice a firij da kofi ya kawowa Iman. Ya koma ya dauko yagot ya kawo, yayi waya kicin ya ce a kawo mata kaza, aka kawo yasa anata kawo abubuwa ana jerewa gabanta har ta gaji ta ce ya isa haka. Suhaif ya zo ya dinga kinkimar akwatin kayanta yana hawa dasu sama, daya gama kaiwa ya dawo sai ya kama hannunta ya ce ta zo ya nuna mata dakinta. Suka dinga tafiya lungu da sakon a cikin gidan, dakuna barkatai da falo kala-kala. Ya kaita wani katafaren daki mai girman gaske ya ce mata "To ga dakinki kuma dakina, ni da ke babu raba daki har abada. Suhaif ya dinga zagayawa da Iman ciki da wajen gidan, duk falon da suka shiga su kan dan zauna su kunna talabijin suyi kallo ko su bude computer. Daga karshe suka shiga shimfideden lambun da ke dauke da fulawoyi da bishiyoyin kayan marmari. Ba su fito ba saida magaruba. Suka yi sallar Magruba da Isha anan falon kasa. Kai tsaye suka wuce kan tafkeken teburin cin abinci da aka shake shi taf da abinci da abin sha kala-kala. Daman tun asalin Iman ba mai cin abinci ba ce da yawa, idan taci kadan sai tace ya isheta. Amma yau Suhaif ne yake bata a baki ko ta ce ya isheta sai yayi mata dubara ya sake saka mata a baki. Duk abubuwan dake teburin nan saida ya bata taci ta sha. Da suka kammala sai Suhaif ya rufe kofar falon ya kama hannun Iman suka hau sama sun gama da kasa sai shirin bacci. Iman dai tayi tsuru a gefen gado, mutumin nata kuwa ya shiga ban daki ya hada mata ruwan wanka. Ya zo ya isheta da magiya sai ta tashi ta shiga wanka. Ta ce "Naga ikon Allah, dakuna sunyi guda goma a gida ina aka taba zuwa aka cusu a daki daya ance bazan zabi dakina ba. Suhaif yayi dariya ya ce "Nan ne dakinki, nima nan ne dakina mu biyu kenan. Amma tunda kina kunyata bari in tafi wani dakin inyi wanka, shiga kiyi. Suhaif ya fice san nan Iman ta shiga tayi wanka. Ya shigo ya iske Iman a zaune ta takure a gefen gado tana sanye da galleliyar rigar bacci *yar karama mai kyau mai laushi. Ya kalleta yayi murmushi ya ce "Daina takurewa, karki damu kwanta ki juya gabas ni kuma zan juya yamma muyi kai da kafa, kinga ba ruwan wani da wani. Ya kashe fitila suka kwanta. Bayan wata guda cur da bikin su Iman, Huzaifa ya shirya shi da matarsa da yaransa zasu koma kasar su Bahrain. A jirgi suka zo Abuja ya sanarwa da Suhaif ta waya, shi da Iman suka daukosu a filin jirgi. Kwanansu daya a Abuja gidan su Iman sannan suka wuce Bahrain. Suhaif ya yiwa Huzaifa alkawari zasu zo Bahrain idan suka je Saudia a Umarar Azumi. A lokacin azumi saura wata biyu. Suhaif da Iman suna zaman jin dadi da kwanciyar hankali, haka ma'aikatan gidan suke cikin farin ciki. Saboda tun lokacin da Iman tazo gidan nan, kawai idan Suhaif ya bushi iska sai ya tarasu yayi ta raba musu kudi kyauta ba albashinsu ba kuma kudin masu yawa yake basu. Suhaif ya kan je Lagos wajen hidimominsa amma kafarsa kafar Iman da ita yake tafiya. Duk in da zata je shine direbanta, baya bari kowa ya kaita. Iman tana mamakin irin wannan kulawa da Suhaif yake mata itama kenan balle jama'ar da suke ganinsu. Watan azumi na kamawa Suhaif ya biyawa Iyayensa, Iyayen Najib, kannensa Naja'at da Zubaida, Iyayen Iman da kannenta, Mama Tabita da kuma Iyayen Huzaifa sannan shi da Iman kacokan suka dunguma suka tafi Umara har sai bayan salla za su dawo. Kafin su je Suhaif yasa an tanadar musu Hotel wanda ke daf da Harami, kowa bangarensa daban, ma'ana duk mata da mijinsu dakinsu daya. Haka zalika basu san sayan abinci ba. Bayan kudin tsaraba daya rabawa kowannensu. Azumin shekarar gaba daya a Makka suka yi shi. Ranar salla suka wuce Bahrain sai su Huzaifa suka gansu reras kamar a mafarki. Satinsu guda a Bahrain suka shirya juyowa Nigeria, yayin da Suhaif da amaryarsa Iman suke rike da Visa tafiya kasashen biyar a hannunsu. Daga Bahrain London suka fara zuwa, yawon amarci sauran kuwa suka dawo Nigeria, *yan Kano suka sauka a Kano, *yan Jalingo suka runtuma garinsu. Iman da Suhaif sun yi wata guda a London. Sannan suke wuce America, bayan sati uku suka wuce France. Bayan sati biyu suka je Dubai. Bayan wata guda suka taho Cairo suka yi sati guda suka iso Nigeria. Lallai sun huta, hutu kan hutu. Babu abinda Iman bata gani ba a kasashen nan. Babu abunda take so bata ci ba. Babu abinda tayi sha'awa bata suyo ba. Haka babu hamshakin Hotel din da basu shiga sun kwana ba. Iman bata da sauran matsala a duniya sai guda daya. Musamman idan taga yara kanana sai jaririn Harriet ya fado mata a rai. Tun tana boyewa Suhaif bata fada masa damuwarta har ya isheta da tambaya ta fada masa. Ya ce ta kwantar da hankalinta daman suna dawowa zasu je Kano, Doko da Jalingo sai su nemo Muhammad duk inda yake. Haka kuwa aka yi bayan sun dawo daga tafiya da sati biyu suka taho Kano, suka kwana biyu a Kano. Sai a lokacin Iman tasan ashe Suhaif gini yake yi mata a Kano. Sun je sunga gidan har anyi nisa an kusa kammalawa. A unguwar su Najib ake ginin wato Badawa Layout. Gida har gida mai kyawun gaske ga ginin da ake yi mata. Dandatsetsan gida flat house da get dinsa shima an yi nisa da gini har an kusa kammalawa. Nima ya gina min gida na mu ni da sweety Matawata.... Lolxx.. Reedwan Suraj Isma'il YARENA ADDININA CI GABAN LABARI Sun isa Jalingo Iman ta sauka a gidansu shi kuwa Suhaif a Hotel ya sauka. Nan ma yasha alwashin wataran zai yi gini a garin saboda idan suka zo su dinga sauka. Bayan sun huta gajiyar hanya sai Iman ta shaidawa Iyayenta gaskiyar magana akan jaririn Harriet cewa bai mutu ba don haka yanzu zata bazama nemansa har sai ta samo shi. Suhaif ke tukata suka nufi gidan da aka ce mata marikan nasa nan suka koma. A bakin get din gidan Suhaif yayi parkin. Ya ce zai raka Iman ciki ta ce "A'a ya bari ta shiga ita kadai tunda gidan matan aure ne. Iman ta shiga cikin get bayan ta gaishe da mai gadin ta tambayeshi "Matar gidan tana ciki kuwa? Ya amsa mata "Eh tana ciki" ta tambaye shi "Yaran fa? Ya ce "Sun tafi Islamiyya. Iman ta ce "Su duka ukun? Ya ce "A'a su biyar dai. Iman ta ce a ranta "Su biyar? Anya kuwa gidan ne Abubakar da Aisha ne kawai ai sai Muhammad suka zama su uku, to ko Mamar tasu ta kara haihuwa tayi? Haka Iman take tunani har ta isa kofar falon gidan. Tayi sallama matar gidan mai suna Salma ta amsa gami da yin izini ga mai sallamar ta shigo. Iman ta shiga, tana shiga ta gane fuskar matar Mahaifiyar su Aisha ce domin taganta lokacin da ta haye kan bishiya, ita kuwa matar bata taba ganin Iman ba. Iman sai fara'a take yiwa Salma kamar ta santa, Salma cike da mamaki take kallon Iman tana tunanin anya ta san wannan matar kuwa? Ta gama tunanin duniyar nan taga bata taba ganin Iman ba. Ta nunawa Iman kujera ta zauna suka gaisa. Ta kwallawa mai aikinta kira ta ce ta kawowa bakuwa ruwa da lemo. Iman ta gyara zama tayi murmushi cikin yaren fulatanci ta ce "Baki sanni ba ko? Salma tayi murmushi ta ce "Gaskiya ban gane ki ba. Iman tayi gyaran murya ta ce "Ba zaki gane ni ba amma ni na gane ki. Shekarun baya nazo mai gadinku ya ce min kun tafi Umara ku duka gidan harda yaranki. Salma ta ce "Oh daman kece kika zo? Ya fada min wai nayi bakuwa ya ce wata fara tas. Ya ce ta tambayeni ta tambayi Muhammad . Ya ce har kina tambayarsa Muhammada ya girma, yana tafiya yanzu? Na dinga mamaki sai na zata ko ma Mahaifiyarsa ce ta zo, ta fada a hankali. Iman tayi shiru can ta dago ta kalli Salma ta ce "Haka aka yi nice na zo. Da Aisha da Abubakar sun ganni me yiwuwa su gane ni amma ba lallai bane su gane ni saboda tun suna kanana. Salma ta gyara zama ta tsurawa Iman ido tana sauraranta cike da mamaki. Iman ta ci gaba da cewa "Yanzu ma na zo ne mu gaisa tunda na zo garin. Salma ta ce "Ko zaki min dalla-dalla don in gane ki sosai? Iman ta ce "Maganar gaskiya nice na ajiye muku Muhammad, amma nasan nayi muku laifi ku yafe min, babu yadda zanyi a lokacin. Salma ta zabura ta tashi tsaye ta dafe kirji ta ce "Ke ce? Iman ta nisa ta ce "Labarine mai tsawo. Salma ta ce "To bari na taso mai gidana Ibrahim, yana bacci a daki wannan lamarin babba ne. Ta shiga daki bayan *yan mintina suka fito tare, a zabure ya fito. Iman ta gaishe shi sai taga ya na mata kallon tara saura kwata ya amsa da kyar. Ta nisa ta ce "Dan Allah idan baza ku damu ba zan iya shigowa da mijina shima ayi maganar a gabansa? Matar ta ce "Kwarai kuwa ya shigo. Ibrahim ya ce "Bari na aika a kira su Malam Shehu tunda suna nan aka tsinci yaron duk a hadu aji labarin. Tunda sune shaidu. Iman da mijinta, haka ga Salma ga mijinta Ibrahim sannan ga Malam Shehu da sauran Jama'ar da suke nan ranar da aka tsinci dan. Aka cika falon ana sauraran Iman. Ta fara basu labari tun daga farkon yadda Harriet ta haifi yaron har ranar data yarda shi. Babu shakka duk yadda ta kwatanto yadda ta yar da dan haka ne babu karya. Sai suka tambayeta yanzu meke tafe da ita, da kuma dalilin zuwanta yanzu. Iman ta ce ta zo ta ganshi ne ta tabbatar da inda yake sannan ta nemi izini su yarde masa ta dinga zuwa ganinsa. Sai tausayinta ya rufe marikan yaron da sun dauka cewa zata yi zata dauke shi. Iman taci gaba da cewa idan da hali tana son ta sami wasu su rakata a je wajen Mahaifin yaron a Baucji yaga Babansa saboda watarana. Suka amsa mata da "Haka ne gaskiya ne. Duk ba abun damuwa bane. Yata *yan makaranta sun taso sai surutunsu ake ji kafin su karaso. Iman ta baza idanuwanta gaba daya tana duban kofar shigowa tana so taga Muhammad dinta. Suka shigo kofar sai suka durkusa suka gaishe su dukkansu. Daga gani babu tambaya, babu wanda ya nuna mata shi ta gane shi. Kamar kaki Micheal yayi, kamarsu daya da Ubansa. Ya girma sosai gashi da tsaho kamar ubansa. Iman ta fashe da kuka, ta ce ya je wajenta su gaisa. Ya tsaya yana kallonta bai santa ba. Sai da Mamarsa Salma ta ce masa "Muhammad jeka ku gaisa da Aunty. Sanna ya je wajen Iman, ta rungume shi tana kuka. Iman ta tambaye shi da turanci ajinsa nawa a makarantar boko? Ya amsa mata ya ce "Primary 2. Ta tambaye shi shekarunsa nawa ya ce bakwai. Tayi masa larabci ta ce Islamiyya fa ajinsa nawa? Ya ce uku. Ta ce kur'ani izunsa nawa? Ya ce izufi biyar. Iman tayi dariya ta fada da Fulatanci "Kai Muhammad har ka yi izufi biyar? Malamin ajinsu yana wajen ya ce "Ai ma har ya rage yanzu a izufi goma yake. Muhammad yaro ne mai hazaka har tsallaken aji ake yi masa saboda kokarinsa. Kafin ya gama primary zai iya sauke Alkur'ani. Iman taji dadi ya rufeta. Aisha da Abubakar sun girma ga kannensa nan kanana da aka haifa dukka maza. Iman ta dinga tunawa su Aisha tana cewa "Yanzu kun manta ni Mamar Muhammad da ku kace in ajiye muku shi kuna son kani. Aisha ta tuno amma Abubakar bai tuna ba saboda bashi da wayo a lokacin. Daga karshe Iman ta dauko musu kayan da ta kawo musu, alawa da biskit kala-kala na kasa shen waje da ta dawo. Suka hadu aka tsayar da shawarar gobe da sassafe su zasu zo su dauki Ibrahim, Malam shehu da shi Muhammad dina a tafi Bauchi wajen Micheal. Washe gari da sassafe Iman da Suhaif suka shirya suka fito tafiya Bauchi. Suka biyo daukar su Muhammad. Iman na shiga gidan ta tarar an shirya su kawai suke jira. Suka dungumo suka fito wajen mota. Salma tayi musu rakiya duk jikinta yayi sanyi, hankalinta ya tashi gani take idan Mahaifin Muhammad ya ganshi zai dauke shi ya hana a dawo da shi. Iman ta lura da halin da Salma ke ciki sai ta shiga kwantar mata da hankali cewar babu matsala yadda suka dauki Muhammad yanzu haka in anjima zasu dawo mata da danta Insha-Allah. Sannan Salma ta saki ranta tayi murmushi ta ce "Allah Ya kiyaye hanya. Suhaif ne yake tukawa, Iman a gaba. Ibrahim da Malam Shehu a baya Muhammad a tsakiyarsu a kujerun baya. Suka tafi, Salma da *ya*yanta suna daga musu hannu har suka yi nisa. Babu in da suka tsaya tunda suka fara tafiya sai a garin Bauchi. Bauchin Yakubu! Inji masu kirari. Iman ta shiga tunani ina zata fara neman Micheal a cikin garin nan, shi me gidaje kala-kala. Sai ta ce su fara zuwa gidansa na G.R.A kusa da gidan Gwamna. Tana nunawa Suhaif hanya har bakin get din gidan. Iman ta fito daga mota tace su jira bari ta tambaya. Ta kwankwasa get, mai gadi ya fito da sauri ta karamar kofa dan yaga ko waye. Iman tayi murmushi ta gaishe shi ta ce "Dan Allah maigidan yana ciki? Ya ce "A'a ya tafi kasar waje da sabuwar amaryarsa yawon shakatawa, uwar gidansa ce kawai a ciki ita kuwa bama iya tunkararta saboda yanzu tana tsakiyar kishi sai ta huce a kanka. Kamar zata mare mu haka take mana, sai kace mu muka sa Alhaji yayi mata amarya. Iman ta ce Alhaji? Yaya sunan Alhajin ya ce "Alhaji Musa! Waye a garin nan baisan shi ba, ko dai batan kai kika yi? Iman ta ce "Ina mai ainihin gidan Micheal? Ya ce "Oh Micheal wannan tantirin yaron? Ai tuni ya tashi, ya sayar da gidan ko ince hukuma ta kwace gidan daya dunguma wani fashi aka kwace kadarorinsa. Iman ya ce "Yanzu a ina kake ganin zan iya ganinsa? Ya ce "Ke kuwa Hajiya ina kike neman kungurmin dan fashi, kina Musulma nai mutunci ko wani abu ya dunguma muku? Koda yake ba ruwana. Gaskiya idan na ce ga inda zaki ganshi nayi karya, don nima labarinsa nake ji ban sanshi ba. Iman tayi godiya ta shiga mota. Ta ce da Suhaif su tafi daya gidan nasa baya nan. Suna tafiya Iman tana hawaye idan ta waiga ta kalli dansa Muhammad, sai hawaye yayi ta zuba daga idanuwanta saboda tausayinsa. Suhaif yana kallonta ya rasa kalmar da zai fada mata da zata daina kuka. Yasan tausayin yaron take ji idan ta tuna da yadda aka same shi amma haka Allah Ya rubuto, uban wani baya haihuwar dan wani. Duk in da Iman tasan gidan Micheal ne ta je sai su tarar an sayar da gidan wasu ne a ciki. Sun je gidajen abokansa gaba daya, suma ba sune a ciki ba. Daga karshe ta ce suje zaranda Hotel ko har yanzu yana zaman Hotel. Suka je, ma'aikatan Hotel suka duba sunayen Jama'ar dake ciki da lamabar dakunan da suke babu mai suna Micheal. Hankalin Iman ya tashi kwarai, ita dama ace ta sami wanda ya sanshi ma ya bata labarin idan mutuwa yayi hankalinta zai fi kwanciya. Idan yaron ya girma a shaida masa Uwarsa da Ubansa sun mutu yafi sauki. Suna shiga mota zasu fita daga Hotel din sai ga wani wanda ta sani abokin Micheal ne sunansa Mansir. Yana tafe yana kallon Iman harda tuntube yana yi mata kallon sani. Iman ta fito daga mota da sauri ta kira sunansa. Nan da nan ya dawo wajen da take tsaye jikin mota. Ta ce "Mansir ne ko? Cike da mamaki ya ce "Ni ne kamar preety ce ko? Iman tayi murmushi ta ce "Ni ce. Sai ya girgiza kai yayi shiru hawaye yana zuba daga idanuwansa. Ya ce "Preety kinga yadda rayuwa ta zamar mana ko? Wato duk abokan mu da kika sani an harbesu. *Yan matanmu su Janet duk sun mutu. Irina da ba'a kamamu ba, mun tuba da fashi mun zama abun tausayi. Yanzu haka sana'ata haka rijiya da yasar masai ko kwata. Iman ta tambaye shi cike da fargaba ta ce "An kashe Micheal ma? Ya ce "Micheal ba'a kashe shi ba, amma wadanda aka kashe sun fishi kwanciyar hankali duk da ban san halinda suke ciki a can ba amma duk karshen mutum mutuwa kowa sai ya mutu. Gara ni dinnan da kika ganni da tsumma akan Micheal. Ni ina haka ana biyana shi ba zai iya ba saboda ya nakashe, ga shi ya tsiyace komai nasa ya kare. Kin sanshi mafadacine shine ya je Lagos ya yo tsokanar wasu gungun *yan fashi ko kudin da suka yi fashi ne ya kwashe ya hanasu? Ban dai sani ba shine suka biyo shi Bauchi zasu kashe shi basu same shi ba suka je suka kashe Mahaifiyarsa. Da yaga haka shima ya je yayi musu barna shine suka biyo shi suka sare masa kafa. Ba na da lafiya ne kun ga labarin kadan yau, ina bukatar addu'ar ku. Reedwan ===============YARENA ADDININA CI GABAN LABARI Iman ta runtse ido sai hawaye ya zubo ta ce "Yanzu ina Micheal din yake? Ya ce "Yana gidan Mahaifiyarsa, nan ne ba nisa cikin G.R.A nan yake. Ya zama tamkar tababbe babu shiga gidan, yanzu sai ya farfasa maka kwalba a kai, abincinsa giya da taba. Iman tayi ajiyar zuciya ta ce "Mansir ka rakani, shi na zo nema garin. Mamaki marar misaltuwa a fuskar Mansir ya kalleta ya kalli *yan cikin motar da alama dai mai tukawar mijinta ne *yan bayan kuma Babanta da wanta. Me za su je wajen Micheal suyi? Mansir ke tambayar zuciyarsa. Ya ce "Ba matsala muje in kaiku. Ibrahim ya dora Muhammad akan cinyarsa suka matsawa Mansir ya shiga suka tafi yana nuna hanya har kofar gidan Mahaifiyar Micheal. Mansur ya ce "Ga gidan ni zan koma, shawarar da zan baku kuyi a hankali domin farfasa kai yake da kwalbar giya, ni bazan shiga ba. Iman ta ce "Mansur ba zaka tafi ba ka dai tsaya tukunna. Zan baka linkin kudin da kake samu a rana idan kayi hakuri, ina so ka taimake ni kai ka san gidan nan da halin da Micheal ya ke ciki, yanzu yaya zamu yi mu ganshi? Mansir ya ce "Ba ki nayi ba Pretty amma me yasa kike so lallai-lallai sai kin ganshi mutumin daya zama haka? Iman ta nuna masa Muhammad ta ce "Kalli yaron sosai. Mansur ya zurawa Muhammad ido ya ce "Kai! Ai kamar su daya da Micheal sak. Iman ta ce "To dan sa ne. Cikin mamaki Mansur ya ce "Tare kuka haifa? Iman ta girgiza kai ta ce "Tare da Harriet suka Haifa amma ta mutu garin haihuwarsa ni na dauke shi, shine na zo in nunawa yaron Ubansa. Mansur ya ce "Kwanaki a garin nan naga Harrit din ai. Ko ba wannan kawar taki ba? Iman ta zabura ta dafa kirji ta ce "Kaga Harriet a ina? Kai Harriet ta mutu ba dai ita ka gani ba mai kama da ita dai. Ya ce "A'a ita ce. Ba ita ce bakatsiniyar nan ba yarinyar Gabriel da nake gidansa? Iman ta ce "Okey! Fadila zaka ce min. A ina ka ganta? Ya ce "Tayi aure harda *ya*yanta, naje gidan nayi musu haka, itama ita ta fara gane ni. Iman ta ce "Allah Sarki dan Allah ka kaini in ga Fadila idan mun gama da nan. Suhaif, Ibrahim da Malam Shehu suna zaune a mota suna kallon Iman da Mansur suna sauraran abunda suke fada. Sai yanzu Suhaif yayi magana ya ce "Wai ku fada min yadda zamu shiga gidan mai fasa kai da kwalba. Iman ta ce "Yaya Suhaif ni da Mansur zamu shiga, ku jira mu anan. Suhaif ya girgiza kai ya ce "Bana so ki shiga ki barmu mu maza mu shiga. Malam Shehu ya ce "Mu shiga kawai da ayar Allah ba zai iya daga kwalbar ba balle ya rotsawa wani kai. Suka fito daga mota su duka suka dunguma cikin gidan. Mansur da Suhaif ne a gaba. Iman rike da hannun Muhammad a tsakiya. Malam Shehu da Ibrahim a baya kowa yana karanto addu'ar dake bakinsa. Suna tafe suna kalle-kalle, gida kamar babu bil'adama a ciki bayan dogayen ciyayin da suka rufe farfajiyar gidan, kofar shiga cikin gidan ma da kyar mutum zai samu ya shiga ciyayi sun yi tsawo kamar bishiyoyi. Suna shiga falon kuwa kujeru ne kowacce ta kalli kabilarta. Talabijin a kife a kasa T.B stand an rabata biyu. Yi suke suna waiwaye-waiwaye kada ya diro musu ta inda basu zata ba. Suka yi ta magana shiru, wannan ya ce Hello, wancan ya ce Hi, wannan ya ce ka fito kayi baki. Babu motsin kowa a gidan kamar ma babu mutum a gidan. Sai suka shiga bubbude kofofin dake falon suna lellekawa, dakuna ne da bandakai babu kowa a ciki sai yana da kura. Mansur ya shiga kicin ya bude kofar store din kicin babu komai sai duhu ko tafin hannunka ba zaka iya gani ba. Su Suhaif a falo sai suka ji Mansir ya kwalla kara a lokacin da yaji an cafke shi. Suhaif Ibrahim da Malam Shehu suka kutsa cikin store da gudu sai suka ga Micheal ya shake Mansir a jikin bango yana shirin kwakwale masa makogaro. Nan dai maza suka saki karfi suna jan Micheal amma gamgam sun kasa fusge hannunsa daga wuyan Mansur. Kokari yake ma ya wawuro daya daga cikinsu ya hada ya matse. Iman na falo rungume da Muhammad kam suka shige wani lungu sai sharbar kuka take. Taji shiru har yanzu ba su fito ba sai kakarin Mansir take ji kamar mai shirin tafiya lahira. Su Suhaif na cewa ja shi ta nan, rike hannun, a'a kafar za'a ja, sun kasa fisge Mansur daga hannun Micheal. Iman ta ce da Muhammad ya zauna a lungun kada ya fito, tana zuwa. Tun daga cikin store suka fito kicin ana ta dambe. Cikin rudani da tashin hankali Iman ta kuga da karfi ta ce "Micheal! Sake shi mana karka kashe shi. Micheal ya waiwayo da sauri ya dubi mai wannan muryar wacce tayi masa kama da muryar abar begensa Pretty. Sai kuwa yaga Pretty ce. Mansur da kansa ta fusge hannun Micheal daga wuyansa saboda Micheal yana ganin Iman sai jikinsa yayi sanyi. Sannan su Suhaif suka sake shi shima. Ya dade yana kallon Iman can ya ce "Pretty! Pretty!! Are you Pretty!!! Iman ta gyada kai ta ce "Yes I am. Micheal ya sulale ya zauna ya rike kai da alama tunani yake mai tsawo kansa ya daure. Mansur dai ido yayi masa jawur ya fita bakin baranda yana shan iska. Suhaif da Ibarahim suna tsaye suna kallon Ikon Allah. Malam Shehu kuwa yana jan carbi yana ta tofa addu'a kusurwa-kusurwar gidan. Iman ta durkusa a gaban Micheal cikin harshen turanci ta fara yi masa nasiha da wa'azi mai ratsa jiki. Micheal ya kwalla kara ya daki wata dorowa ya ce "Ke rabu dani, bakya ganin yadda na zama? Zaki ce min in yi hakuri rayuwar duniya sai a hankali. Na saraki, na rasa dana, na zo na rasa Mahaifiyata. Bayan dukiyata da abokaina dana rasa na rasa kafa guda daya. Dan me zan dauki duniya a hankali? Yanzu na fara kisa, yanzu na fara datsewa jama'a kafa, kowa sai ya rasa kafa a garin nan. Iman ta ce "Micheal yi hakuri duniya a sannu a hankali ake bin ta kaga da ka dauketa da karfi shi yasa ta zo maka a haka. Idan kayi hakuri za ka ga rayuwarka ta gyaru ka dawo rayuwar farin ciki fiye da tada. Ya gallawa Iman wata uwar harara ya ce "Ki gaya min yadda rayuwar da zata dawomin? Ko kin fara dawo da matatattu duniya? Ko kina iya dawo min da kafata da aka gutsire aka yar? Ko zaki iya auran mahaukaci ki zauna da shi? Don ada da nake cikakken mutum ma kin kini balle yanzu. Wani dacin kishi ya darsu a zuciyar Suhaif. Iman tayi murmushi ta ce "Duk wannan abubuwan da ka zano min amsar ita ce "A'a amma Allah Zai iya musanya maka da madadinsu gaba daya. Ya sake zabura ya fisgi kanannadadden gashin daya zama Dada saboda rashin aski ya ce "Da a ce wata ce bake ba, da yau sai na kasheta. Dan me zaki sani a gaba kina fada mun tatsuniya, dan kin daukeni mahaukaci ko? Kina so ki ce min zan iya samun wata uwar bayan uwata? Kina nufin zan sake samun wani sabon da bayan dana na wajenki daya mutu koma nace kika kashe min shi, daga baya na samu matsala likitoci sun ce bazan sake haihuwa ba. Na yi aure shekarun baya matar taga ba zata iya zama ba ta haihu ba ta gudu. Don haka karki sake kallona ki fada min wata maganar da hankali ba zai dauka ba, na san a bunda nake. Iman ta fashe da kuka. Sai Micheal ya tsaya yana kallonta can ya tambayeta "Kuka kike yi? Me yasa kike kuka? Kina tausayina ne bayan kin ki ni da? Kin guje ni bakya sona, kece kika sakani a cikin wannan halin. Domin son da nake miki, dana aureki zaki iya canja ni. Pretty me kike so yanzu? Fadi meke tafe da ke? Kinzo kiga mahaukaci ne ki tafi? Ko wadannan mazan ne suka satoki yanzu in kashe su? Duk abunda kike so zan yi, fada min. Iman ta share hawaye ta ce "Gaba daya rayuwarka ce bana so kaci gaba da irinta. Ina so ka canja, ka dawo addinina, zaka ga yadda Allah zai canja maka rayuwarka. Micheal ya tuntsire da dariya ya ce "Addininki! Ni zaki fadawa addini? Kin manta Mahaifiyata shugaba ce a wajen bauta? Iman ta ce "Addinina ba addinin Mahaifiyarka ba. Micheal ya ce "Wannene addininki? Iman ta ce "Musulunci. Ya ce "Ke Musulma ce? Iman ta ce "Ni Musulma ce shi yasa kaga bana zina, bana shan giya, bana fashi saboda tsoron Allah. Addinin Musulunci ya haramta duk wannan. Micheal yayi shiru yana tunani "Lallai gaskiya ne halin Pretty ya banbanta da namu tun a da, har muna tunanin bata da lafiya shi yasa bata zina. Yanzu ga makomar mu ita kuwa kalli yadda ta koma da alama tana cikin jin dadin rayuwarta. Iman ta ci gaba da yi masa wa'azi mai ratsa jiki yana sauraronta. Suhaif, Ibarahim, da Malam Shehu suma suka tsuguna a gaban Micheal suna taya Iman wayarwa masa da kai suna nuna masa karshen tayuwarsa bai zo ba, haka farin cikinsa a duniya bai kare ba. Ya yarda da Allah daya ne Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon ne. Can Micheal ya ce "Na yadda da Allah daya ne kuma Annabi Muhammd (S.A.W) Manzonsa ne. Sai gaba daya suka dau kabbara. Iman tana masa kalmar Shahada yana maimaitawa. Ta fashe da kukan dadi ta cewa Micheal "Ka zama Musulmi zaka ga alhairi a rayuwarka ta duniya da lahira. Daga yau ba sunanka Micheal ba zabi sunan da kake so a sunayen Musulmai. Ya ce "Sai yadda ku ka yi dani, ki zabar min kawai. Iman ta ce "Daga yau sunanka Ibrahim. Ta dubi Ibrahim marikin Muhammad ta ce "Saboda Muhammad tun a makaranta da sunanka ake kiransa ko? Su duka suka ce "Eh haka yayi. Iman ta dubi Micheal ta ce "Ibarahim yanzu tunda ka dogara da Allah, ka yarda shi kadai ne mai iko, mai bayarwa, mai hanawa. Bari ka gani ma tun daga yanzu. Iman ta tashi ta fita ta je lungun data boye Muhammad ta kamo masa hannunsa suka zo wajen Micheal. Micheal ya kurawa yaro ido, yaro ya kurawa Micheal ido. Micheal ya ce a ransa "Ya aka yi wannan yaron yake kama dani? Cike da mamaki Micheal ya dubi Iman ta ce "Waye wannan yaron? Iman ta ce "Dan Harriet ne kuma danka ne bai mutu ba. Micheal ya dora hannu aka ya fasa kuka share-share da hawaye. Jikinsa ya dau karkarwa yana yiwa Iman godiya ya ce "Yadda na zama dana ba zai iya taba ni ba dana rungume shi naji sanyi a raina. Ni kadai na rage a duniya yanzu Pretty bani da Uwa ba Uba, babu dangi. Ashe ina da da a raye? Na gode Pretty. Iman ta ce "Ka godewa Allah. Iman ta dubi Muhammad ta ce yaje ya gaishe da babansa, Muhammad ya yatsune fuska ya ce "Wannan ne Babana? A'a ga Babana nan. Ya nuna Ibrahim, dakyar suka kamashi suka kaishi wajen Micheal. Micheal ya shafa kansa yana kuka. Micheal makale da sandarsa biyu ya rako su bakin mota suna ta bashi baki da shawarwarin yadda zai gudanar da rayuwarsa. Da yadda zai aiwatar da addininsa. Iman ta dubi Mansur wanda har yanzu yana shafa wuyansa inda yasha shaka. Ta ce "Mansur yi hakuri, ka taimakeni ka taimaki rayuwar Micheal, kaga kai Musulmi ne. Micheal ya Musulunta, ka shiryu shima ya shiryu ya daina fashi ka zama abokinsa don rayuwa baza tayi dadi ba mutum daya bashi da kowa babu mai zuwa wajensa. Ka koya masa wankan shiga Musulunci, sai ka koya masa alwala da sallah. Idan kaima baka iya ba ka kaishi a koya masa ko kuma zan baku kudi a dauki Malami ya dinga koya masa. Zan baku kudi ku gyara kanku da muhallinku. Ta juya ta kalli Micheal ta ce "Ka yi min alkawari baza ka kara shan giya ba, fashi, neman mata, balle ka datsewa mutane kafa ko kisa. Kamin alkawari baza ka bar Musulunci ba kuma zaka rike addininka duk abunda Musulmai suke yi kamar salla, azumi, da hakuri zaka yi. Sannan kamin alkawari kudin da zan baka zaka gyara gidanka da jikinka da kuma abinci mai kyau. Micheal yayi murmushi ya gyada kai ya ce "Nayi alkawari zan yi duk yadda kika ce, ko bayan idonki ne. Iman da Suhaif suka shiga mota suka yi shawarar nawa ya dace a bashi. Kudi mai dumbin yawa suka bawa Micheal ya bude baki yana mamaki sai juya damin-damin kudin yake yana godiya. Iman ta ce "Ka sayi wayar hannu zan baka lambar mijina idan ka hada wayar sai ka kiramu. Ya amsa mata da "To zan saya. Mansir ma ya hau murza hannu don har kaikayi hannunsa ya fara yi tun kafin nasa kudin ya shiga hannunsa. Iman ta mika masa nasa duk da na Micheal yafi yawa amma yayi murna bai taba zata zai sami haka ba. Shima yayi mata alkawari zai tsaya tsayin daka ya ga ya taimaki Macheal akan komai ma ba addini kawai ba. Mansur ya shiga mota su Iman ma suka shiga suka tafi. Micheal yana daga musu hannu har suka tafi. Gidan Fadila Mansur zai nunawa Iman. Suka isa bakin get din gidan, lallai kuwa attajiri Fadila take aure. Iman ta ce su jira bari ta shiga ciki ta gani. Iman na shiga falon gidan ta tarar da Fadila a zaune a falo tana da tsohon ciki, ga karamin yaro zaune akan cinyarta da samari guda biyu suna zazzaune dukkansu suna kallon talabijin. Fadila ta amsa sallama gami da dago ido tana kallon mai shigowa. Fadila ta zabura ta sauke yaron dake cinyarta ta mike tsaye cike da mamaki ta tambaya "Wa nake gani kamar Pretty? Iman ta ce "Ni ce Fadila. Suka rungume juna saboda murna. Fadila ta kama hannun Iman ta ce "Zo ki zauna kawata Allah mai iko, ba dan ikon Allah ba da koda kudina ina zan nemeki? Iman ta ce "Kafin na zauna bari na shigo da baki a waje, mai gidana ne da wasu guda biyu. Fadila ta ce da samarin nan "Bishir jeka waje ka shigo da baki maza ka kaisu falon Babanku ka nuna musu bandaki. Iman ta ce "Sai ka shigo min da karamin yaron nan. Bishir ya amsa da "To Aunty, ya fita waje. Fadila ta ce "Kafin mu gaisa bari nasa masu aiki su harhado muku abinci. Bayan shigar Fadila kicin ba dadewa ta dawo wajen bakuwarta. Iman ta ce "Sallah nake so in fara yi. Fadila ta ce "To bari mu shiga daki. Suka dunguma zuwa katafaren dakin barcin Fadila, Fadila ta dubi Muhammad ta ce "Pretty danki ne wannan kuwa? Kai bayan rabuwarmu bai ci ki haifi wannan ba. Iman ta ce "Bari inyi salla zaki sha labaru. Kafin Iman ta idar da salla masu aikin Fadila sun jere musu abinci kala-kala da abun sha. Haka suma su Suhaif an kai musu nasu. Wash! Idan ba na gaji da rubutun nan ba. Lolxxx ashe ciwon S? ne ya kamani jiya ban sani ba...... uhmm Daga gwauron ku. Reedwan Suraj Isma'il ===============YARENA ADDININA CI GABAN LABARI Iman da Muhammad suna idar da salla sai suka fara cin abinci. Fadila ta sa Iman a gaba tana jiran labari. Abu na farko da Iman ta cewa Fadila shine "Dubi yaron nan Fadila da wa yayi miki kama? Fadila ta gama kallon Muhammad sai ta ce "Kinsan ban san Babansa ba, ke dai bai yi kama da ke ba. Iman ta ce "Baiyi kama da mai gidana ba, amma yayi kama da Mahaifinsa sai dai baki gane ba ne. Kin tuna dan gidan Harriet da suka haifa da Micheal? Fadila ta zabura ta sake dago kan Muhammad ta ce "Kwarai kuwa gaskiya kamar su daya da Micheal. Allahu Akbar. Pretty Allah Yayi miki albarka. Yanzu da dan nan kika je gidanku har ya girma? Wallahi kusan kullum sai Mahaifiyata tayi miki addu'a, da yake na bata labarin yadda kika yi min wa'azi har na koma gida na shiryu, na shiga Islamiyya. Babban abun al'ajabi bayan na shiryu ina gida samarina na da duk suka ki aurena wai ni karuwa ce, ko kuma Iyayensu su ki amincewa su aure ni. Tsohon da naki aura shine bai daina sona ba, kuma shi na aura yanzu. Kishiyoyina biyu suna Katsina har da *ya*yansu aurarru. Wadannan samarin da kika gani a falo suma *ya*yan sa ne, suna karatu a ATBU. Aiki ya kawo shi Bauchi ya taho dani, ashe da sauran shan ruwana a Bauchi. Ina matukar yin biyayya ga mijina, yana jin dadin zama da ni fiye da sauran matansa. Pretty zaman mace a dakin mijinta yafi komai dadi, yafi mutunci. Nayi rayuwar bariki na ji, ba rayuwar mutunci ba ce. Babu abinda ke cikin rayuwar bariki sai wulakanci da tashin hankalin duniya da lahira. Na godewa Allah na gode miki da kika yi sanadiyyar shiriyata. Na haifi dana na fari ga shi can Aliyu sunansa, sannan ga wani cikin, hankalina a kwance har na shiga ATBU nima yanzu ina Level 2 zan hada degree dina. Ke fa Pretty yaya rayuwarki ta kasance? Ina Hamma Huzaifa, shi kika aura? Waye ya kawo ki gidana? Iman ta fara zaiyanowa Fadila labarinta tun daga ranar da suka rabu har rana irin ta yau. Suhaif ne yake wa Iman aike in ta gama su fito su tafi kada dare yayi musu a hanya, a yau zasu juya Jalingo. Iman ta bawa Fadila number ita ma Fadila ta bata tata. Iman ta karbi account number Fadila domin ta ringa aiko da kudi idan bukatar hakan ta taso a bawa Micheal. Fadila tayi alkawari zata hada dan mijinta da Mansur su je gidan Micheal saboda kai masa sako idan Iman ta turo din. Fadila sanye da hijabinta ta rakosu har bakin mota don ta gaisa da su Suhaif. Nan dai suka yi bankwana da Fadila da Mansur. Fadila tayi alkawarin duk sanda taje Abuja zata nemi Iman, don tana yawan zuwa Abuja. Cikin dare sosai suka isa Jalingo suka fara zuwa suka sauke Ibrahim, Malam Shehu da Muhammad. Iman tayi alkawarin zata zo gobe su yini su sha hira da yara, yayin da ita da Suhaif suka nufi Hotel din daya sauka. Ranar da Iman suka yi sallama da Iyayenta wato sun fito zasu taho Kano daga nan su wuce Abuja. Sai da suka biya ta gidan su Muhammad suka yi musu sallama. Kudi na mamaki Suhaif ya bawa Ibrahim gami da bashi adireshinsa na Lagos da number waya ya je zaiyi masa hanyar samun saboda sunyi magana da Ibrahim ya nuna masa ya sami matsala wajen aikinsa. Haka Iman ta yiwa Salma kyautar kudi na mamaki, suna ta godiya tare da yiwa Iman alkawari zasu kawo mata Muhammad da kansu har Abuja idan anyi musu hutun makaranta. Muhammad ya fara sabawa da Iman shima, ta rungume shi tsam a jikinta yayin da kuka ya kece mata don kauna. Sannan Suhaif da amaryarsa Iman suka nufi garin Kano. KANO TA DABO TUMBIN GIWA, KODA ME KA ZO AN FIKA, in ji masu kirari. Bayan shekara daya da bikin su Iman Allah Ya bata haihuwa ta haifi santalelen da namiji mai kama da Mahaifinsa, aka radawa yaro Huzaifa. Allahu akbar sun cure Huzaifa gam saboda taimako da abun alhairin da yayi musu a rayuwa. Mutane da yawa suka dinga cika zungura-zunguran motoci, wasu a jirgi suna zuwa taya Iman da Suhaif murna. Anyi kayatacciyar liyafar suna a katafaren gidan Suhaif na Abuja wanda ya kara kayata shi saboda suna. A cikin *yan suna harda Salma da yaranta dukka su Muhammad. Bayan suna kowa ya hau shirin komawa gida, Iman ta marairaice ta roke su su bar mata Muhammad ya dawo wajenta da zama zata dinga kawo musu shi hutu. Basu hanata ba tunda sun zama daya ga dinbin alherin da Ibrahim yake samowa daga Lagos a wajen Suhaif. A shekarar Suhaif ya kantara gidaje uku iri daya a jere a wata sabuwar unguwar attajiran garin suka zamar da ita small London a cikin garin Jalingo. Gida daya na Iyayen Iman ne, daya na Iyayen Huzaifa, daya kuwa na Iman ne inda zata dinga sauka idan ta zo garin. Alhamdulillahi! Irin dadin da mutanen nan suka ji a lokacin da Suhaif ya danka musu mukullan gidan kamar su zuba ruwa a kasa su sha. Iman bata manta da Mama Tabita ba, gida sukutum ta saya mata ita da mijinta da basu jari mai tsoka yanzu sun daina aikin wahala an dauki wasu *yan aikin. Iman da Suhaif sun gamsu da shiryuwar Micheal. Ya nutsu, ya rike addininsa, ya gyara jikinsa da gidansa, ya bar shaye-shaye. Koda yaushe Micheal suna gaisawa da Suhaif a waya, kuma yana fada masa abun da yake bukata idan matsala ta taso masa kamar yadda suka bashi izini ya dinga tambayarsu. Suhaif ya shirya ya tafi Italy ganin likitansa sai ya hada visar sa data Micheal sai a waya Suhaif ya ce da Micheal ya shirya ya taho Abuja ya same shi zai tafi Italy da shi ayi masa kafar roba, wacce zai dinga takawa kamar yadda kowa yake takawa. Hakika Micheal yaji dadi, farin ciki yayi masa yawa har ya rasa ta inda zai fara godiya, yau ya sake tabbatar da zancen Pretty data fada masa cewa farin cikin rayuwa bai kare masa ba in har ya yarda da Allah daya ne kuma ya rike addinin Musulunci. Iman ma taji dadi da Suhaif ya sanar mata abun alkairin da zai yiwa Micheal. Suhaif a koda yaushe arzikinsa kara lunkuwa yake na yau tafi na gobe. Saboda kyakkyawar niyyarsa ta taimakon talakawa masu karamin karfi masu neman taimako, danginsa da kuma sauran al'ummar Musulmi gaba daya. Suhaif yana matukar kaunar Iman a zuciyarsa gaba daya, musamman dadin zaman da yake ji da ita. Babu abun da take dorashi akai sai hanya madaidaiciya tana matukar bashi shawara ya kyautatawa Iyayensa *yan uwansa, talakawa masu bukata, da kuma ma'aikatan da suke yin aiki a karkashinsa na gida dana wajen aiki. Kamar yadda Suhaif yayi kudi, Iman ma tayi kudi, domin kayan Suhaif na Iman ne. Bai yi mata Katanga ko iyaka da dukiyarsa ba. Ya bata izinin fitar da kudi duk yadda take bukata. Iman bata da matsala bata da abunda zata yi da kudi komai an ajiye mata naci ko na sakawa, haka kafin tayi tunani siyawa Iyayenta wani abu tuni Suhaif ya saya musu dan haka bukatarta da kudi shine tayi amfani dasu wajen yada addininta. Tana shiga lungu-lungu, sako-sako, gari-gari. A jirgi ko a mota inda mota bata shiga ta hau keken shanu. Allah Ya dubi kyakkyawar zuciyarta da tsananin addu'ar da take yi yana cika mata burinta. Allah ne yasan dunbin jama'ar da suka Musulunta a hannun Iman saboda wa'azin da take musu a nutse cikin sassanyar muryarta har sai ya ratsa zuciyarsu ya shiga jijiyoyin jikinsu. Iman bata gajiya kuma bata fushi da masu zaginta tana ci gaba da basu hakuri, tana musu wa'azi har sai sun ji su da kansu ta fisu gaskiya. Bayan Musulunta sai ta bisu da dinbin dukiya wacce zasu dade basu ce babu ba. Allahu Akbar ita kuma haka Allah Ya halicceta tana tsananin son addininta ta kuma rike shi da karfinta. A zuciyarta da dukiyarta, a shirye take ta yada addininta ko za'a daketa ko a jefeta koma a rabata da rayuwarta. A shirye take da ta karar da duk abunda ta mallaka dan yada addininta, haka mijin ta yake taya ta son abunda take so, yana taimakonta da dukiyarsa da karfin jikinsa. Katafaran kanfani Suhaif ya bude a Kano ana yin leda, man-gyada da kuma atamfofi. Kusa da nan Suhaif ya bude katon wajen sayar da manyan motoci (tifa) bayan hamshakan super market da a kowacce state ya bude branch. Najib tuni yabar aikin wahala wato aikin banki, dan uwansa Suhaif ya danka masa kacokan kula da kanfanoninsa na Kano da sauran harkokinsa. Zubaida da Naja'at suma Suhaif ya basu babban aiki a kamfaninsa. Haka Micheal bayan kafar roba mai kama da ta gaske da Suhaif ya kaishi aka yi masa a Ilaty suna dawowa Nigeria Suhaif ya bashi Upper ya dauke shi aiki a kamfaninsa akan albashi mai tsoka. Ya bashi zabi ya zabi duk garin da yake so kanfanin Lagos ko Kano. Micheal yana son Musulmi da addinin Musulunci nan take ya zabi Kano. Suhaif ya sa Najib ya samar masa gidan haya mai kyau zai biya masa hayar shekara biyu, kafin ya saya masa gida kyauta in har ya ji dadin Kano yana son ci gaba da zama a Kano. Micheal yayi farin ciki marar misaltuwa, godiya ba adadi. Ya shiga Bauchi cike da murna ga kafa ras yana takawa kamar kowa ya zubar da sanduna. Babu mai cewa ba kafarsa ba ce, ga aikinsa a hannu. Micheal yana ta godiya ga Allah, godiyar da ya yiwa Ubangijinsa shine Allah Yake kara masa. A satin ya hadu da wata zankadediyar bazawara wacce mijinta ya mutu bayan sun haifi yara biyu mace da na miji a sanadiyyar natsarin mota. Sunanta Khadija Bahaushiya ce gaba da baya Musulma mai asali, sune Bauchi domin Mahaifinta na da sarauta a garin. Khadija fara ce sal doguwa mai kyau ga Uwa Uba ilimi domin ta kammala karatun degree din ta a University of Maiduguri (Uni Med) ita ta fara nuna masa so da farko ya ki amincewa kasancewar yana da tabo a garin bai boye mata ba, ya bata labarinsa kakaf tun da har zuwa yanzu. Ta nuna masa duk babu damuwa tana sonsa haka tunda muna yiwa Allah laifi ya yafe mana. Tunda ya tuba ya gyara halinsa hakika Allah Mai karbar tuba ne. Khadija da Micheal sun shaku sosai soyayya ta hardesu, cikin dubara ta rurrufa ta tsara Iyayenta har suka yadda suka amince ta auri abin kaunarta Ibrahim (Micheal). Bayan haduwar Micheal da Khadija da wata hudu suka yi aure, an kai amarya gidan angonta a nan Bauchi gidan Mahaifiyarsa da ya gada. Kayan daki na gani na fada aka shiryawa amarya. Dakuna uku ne duk an zuba gadaje, kujeru na alfarma a falon, kayan kicin na haduwa a kicin, sannan kayan bandaki na burgewa a bandaki. Iman ta zo biki ta sauka a gidan Fadila, ta taho da Muhammad dan Micheal. Micheal ya ji dadi sosai ya nunawa amaryarsa dansa, ya kuma gabatar mata da Pretty daman ya dade ya na bata labarinta. Iman ta bawa amarya da ango gudunmawa mai ban mamali, kyautar dalleliyar mota ta basu kirar Camry. A bauchi Ibrahim (Micheal) ya bar matarsa Khadija shi yana Kano wajen aiki, sai dai duk karshen sati Bauchi yake zuwa. Itama amarya takan bishi Kano tayi *yan satittika. Zumunci mai karfi tsakanin Micheal da matarsa da su Naja'at, Zubaida da Najib a Kano. Muhammad ya kaura Abuja kaco kan wajen Iman. Ta saka shi a makaranta mai kyau mai tsada wacce *ya*yan manyan Nigeria suke yi. Yaro mai hazaka da son karatu, a bangaren karatun addini kuwa Iman ta daukar masa Malamai masu koya masa. Amma ba shi da Malamin da ya wuce Iman, Iman ta tsaya tsayin daka tana koya masa ilimin kur'ani da hadisai. Dai-dai Lokacin da Muhammad ya gama primary yana shirin shiga Secondry a lokacin ya sauke alkur'ani, babu inda za'a bude masa ya kasa karantawa. Iman ta ga ya dace ta hada masa kayatacciyar walima yadda *yan Uwa da abokan arziki gaba daya za'a hadu dan a kara dankon zumunci. Ta buga kati masu yawa ta rarrabawa dinbin kawayenta da abokan arziki da suke mutunci a Abuja. Ta tashi Rashida mai aikinta da direba mai zuwa Kano da Doko ta kai musu nasu katin. Sannan ya aikawa *yan Jalingo nasu, na gidan Iyayenta, Iyayen Huzaifa, Kawayenta Mumuyawa da gidan Ibrahim da Salma marikan Muhammad. Iman ta jajjadawa Salma lallai-lallai a taho da Aisha, Abubakar, Aliyu da Usman in ji Mohd. Alhamdulillahi! Duk wanda Iman ta gayyata babu wanda bai zo na harma da wadanda bata gayyata ba suma sunzo dan su ganewa idanuwansu. Da misalin karfe hudu na yamma za'a fara gudanar da shagalin walimar saukar karatun Muhammad a katafariyar farfajiyar gidan Suhaif da Iman na Abuja. Dan haka tun misalin karfe uku mutane suka fara hallara. Wadanda suka zo daga nesa kamar *yan Jalingo tun jiya suka karaso suka kwana a gidan, amma *yan Kano da *yan Doko a ranar suka kamo hanyar Abuja, karfe biyun rana tayi musu a Abuja. Ma'aikata na musamman mata da maza sune suke rarraba riguna ga duk wanda zai shigo cikin get din gidan, maza a basu farar riga fara sol mai dogon hannu, hirami ja da bakin kokoro irin na Larabawa da suke dorawa akan hirami. Mata kuwa doguwar riga ake basu baka mai dan kwali (open) wacce ko wanne irin kaya kika saka zaki iya dorawa aka. Kusan dole ne duk wanda zai shiga wajen walimar ya saka wannan riga. Nima dai sai da na ziyarta.... Lolxx Reedwan Suraj Isma'il ===============YARENA ADDININA KARSHEN LABARI Aziza ta dubi mai gidanta Ashraf tayi ajiyar zuciya ta jujjuya rigar da aka bata. Ta ce "Dadina da zuwa gidan Iman kenan, kullum sai ta wahalar da mutum dole sai ya canja kaya, idan karamin gyale na sa dole sai ta bani hijabi na saka kafin na fito daga gidanta, yau kuma da doguwar riga mai dankwali ta hadamu. Saboda bana son kaya mai nauyi ne fa na saka material ban sako atamfa ba ko leshi. Ashraf ya yi dariya ya ce "Ai ni Iman tayi min daidai hakan da take miki shi yasa duk kawayenki nafi sonku tare kamar yadda kawarki Hanna Haisam take koya miki hakurin zama da mutane. Bai rufe bakinsa ba sai ga Hanna da Haisam sun fito daga motarsu, kai tsaye suka tunkaro inda Aziza da Asharaf suke tsaye, suka gaisa kowannensu cike da farin ciki. Suka ma'aikatan masu raba riguna suka dubi yanayin jikinsu suka dauko musu size dinsu. Kowannansu ya zura goguwar riga suka dunguma cikin farfajiyar gidan. Iman da Suhaif suna tarar baki suma suna sanye da dogayen riguna irin wadanda ake rabawa. Iman da sauri ta zo ta tari kawayenta Aziza da Hanna, bayan sun yiwa juna sallama su kayi musabaha sai suka rungume juna. Suhaif ya gaishe da Ashraf da Haisam game da nuna musu wajen zaman maza, suka je suka zauna. Iman ma ta kai su Aziza bangaren da aka warewa mata suka zauna. Aziza ta yamutse fuska ta dubi Iman da Hanna ta ce "Gaskiya na takura da aka raba min wajen zama da mai gidana Ashraf. Mu fa bamu rabuwa, duk inda zamu je ga kafata ga tasa, ga hakarkarina ga nasa. Bama iya rabuwa ta secon ashirin da hudu, ko awa ashirin da hudu balle ace KWANA ASHIRIN DA HUDU rasuwa kawai zamu yi. Dukkansu suka yi dariya. Iman ta ce "Yau dai kuyi hakuri, idan ku ka zauna tare sauran mutane fa? Wata matar wani ce, wani kuma mijin wata ne babu dadi a gauraya mata da maza ba maharraman juna ba, kunsan ina kishin YARENA ADDININA. Aziza ta ce "Wa'azi dai kullum, daman nasan yanzu zaki fara wa'azi da an zauna a kusa dake zaki fara yiwa mutane wa'azi. Hanna tayi dariya ta cewa Iman "Kinsan halin iyayin Aziza, ki daina kulata kina mata bayani. Ta tashi ta je kar ta zauna a kusa damu din, ta je wajen mijin nata. In ba iyayi ba zaman awanni sai ta ce ba zata iya ba sai a kusa da mijinta dadi miji. Dukkanmu nan muna tsananin son zama a kusa da mazanmu amma muka hakura, don GANGAR JIKINA ce kadai anan zuciyata na wajen Haisam. Iman ta ce "Ai shine, ni naga Hanna da Haisam wadanda soyayya ta kusa hallakasu. Aziza ta ce "A'a dakata Hanna, karma a hada soyayyarmu da ta ki, ke fa ba ke kadai ba ce. Yau idan ya kwana biyu a wajenki, gobe kwana biyu zai yi a wajen Ramla, ni kuwa fa kullum muna tare. Iman taga surutun kawayenta ya ki ya kare ga baki sai duddukowa suke yi, ta tafi wajen jama'a suna ta gaggaisawa. Micheal da amaryarsa suma sun karaso. Sai ga Huzaifa da matarsa Zainab suma sun shigo. Iman da Suhaif sun yi mamakin ganin Huzaifa domin ko da wasa Huzaifa bai ce musu zai zo ba, sun dai sanar masa a waya ya taya su murna. Dinbun jama'a mata gaba daya kayansu iri daya yaransu da manyansu bakar riga doguwa mai dan kwali. Maza kuma yaransu da manyansu farar riga doguwa da hirami a kansu. Idan ka kalli mutanen wajen tamkar a kasar Saudia kake, babu abinda yake tashi sai sallama kowa na yiwa na kusa dashi sallama. Masu daukar hotuna da masu daukar bidiyo suna daukarsu. Muhammad wanda ake taron dominsa ya caba ado da farar doguwar riga, farin harami, da farin takalmi da bakar alkebba tsadaddun gaske. Ya fito dauke da katon hoto lamination hoton Harriet Mahaifiyarsa. Hoton Iman ta dauko a ranar da Harriet ta haifeshi ta mutu. Babu dan kwali akanta a hoton amma Iman tasa an yafa mata mayafi a computer tamkar da mayafinta tayi hoton. Aka yi katon enlargement. Mohd ya dafa hoton aka dauke shi a hoto. Iman ta ce ya je wajen Babansa Micheal a daukesu a hoton tare da hoton Harriet. Cikin sanyin jiki da nadama Micheal ya tsugunna, Muhammad yana tsaye duk sun daddafa hoton Khadija (Harriet) aka dauka Micheal ya kurawa hoton Harriet ido cike da tausayi da nadama, ya juyo ya dubi Iman yayi dan murmushi yayin da hawaye ya sirnano daga idanuwan sa ya ce "Allah Ya jikan Harriet. Ku yafe min a madadinta ke da danta, kiyi hakuri karki fadawa danta abubuwan da suka faru idan ya girma. Iman tayi murmushin karfin hali yayin da ta zubo da hawayen daya cika mata ido ta ce "Harriet ko Khadija? Ai Khadija sunanta, domin itama ta musulunta kafin ta rasu, ta zabi suna Khadija da kanta. Kar ka damu a kullum kuma a koda yaushe ina cusawa danka Muhammad ya so ka kaine Mahaifinsa. Na yi alkawari duk hutu zan yi kokarin in dinga kawo shi wajenka hutu yadda zai shaku ya saba da kai. Micheal ya gyada kai ya ce "Na gode Pretty, na godewa Allah da Ya hada ni dake. Micheal ya je gaban Mahaifi da Mahaifiyar Iman ya durkusa ya gaishe su. Kamar yadda Iman ta basu labarin Micheal hakika gaskiya ne Micheal ya canja ba kamar da ba, sanda yake saka dan kunne, sarka da kaftara-kaftaran zobuna a yatsu. Ya zama nutsattse, mai kunya da ladabi da biyayya. Su ka amsa masa cike da fara'a, ya kira matarsa itama ta zo ta gaishe su. Iman da jama'a sai hotuna ake dauka, ta dauka ita da danta Huzaifa, Muhammad da Suhaif. Iman ta dauka da Mahaifanta da kannenta, Muhammad rike da allon saukarsa a tsakiyarsu. Aka dauki Iman, Muhammad, Marikan Muhammad, wato Ibarahim da matarsa Salma da *ya*yansu Aisha, Abubakar, Usman da Aliyu. Aka dauki Iman da Muhammad da Iyayen Huzaifa. Aka dauki Iman, Suhaif da Hamma Huzaifa. Aka dauki Iman, Suhaif, Muhammad Baba na Doko, Baba na Kano, Mama da Goggo. Sannan aka daukesu su duka wato Iman, Suhaif, Muhammad, Micheal, Marikan Muhammad, Najib da Matarsa Naja'at da dan Jaririnta a hannunta, sai Baba na Doko, Goggo, Baba na Kano da matarsa, Zubaida da mijinta, Iyayen Iman da Iyayen Huzaifa, MATAWATA da Reedwan,, lollxxx. Laillai hoton nan zai yi matukar kyau, """GASKIYA YA DACE IN WANKARWA MAKARANTA LITTATTAFAINA DOMIN SUMA SU GANEWA IDANUWANSU WADANNAN MUTANEN DA NAKE BASU LABARINSU"""" inji tauraruwar marubutan Hausa wato "J.U.T". Matan kayansu iri daya, maza ma yaransu da manyansu kayansu iri daya, shigar larabawa. Sai Iman tasa aka dauketa a hoto ita da Mama Tabita da Mijin Mama Tabita wanda shima a yanzu haka cikakken Musulmi ne. Iman taje tsakiyar kawayenta mata da maza Mumuyawa wadanda tuni suka rungumi Musulunci a hannun Iman. Wadanda suka yi sallama da jahilci, duhun kai da talauci a sanadiyyar Iman. Ta canja musu rayuwarsu gaba daya, ta basu izinin duk matsalar da ta taso su gaya mata, a shirye take ta taimaka musu. Iman, Muhammad, Fadila, mijin Fadila, da *ya*yansu suma aka daukesu. Iman da masu aikinta mata da maza aka dauka gaba daya. Suhaif, Iman, Kakarsa Hajja da *yar Hajja da Iyayenta aka dauka. Iman, Suhaif, Aziza, Ashraf, Hanna da Haisama ma aka dake su. EH LALLAI DOLE IN WANKARWA MAKARANTANA WADANNAN HOTUNA. In ji "J.U.T". Cancadi! Sun zuba kyau ainun a hotunan nan. Iman tayi alkawari zata wanko hutanan nan masu dinbin yawa dan a rabawa masu son ganinta su ganta. Muhammad aka kira aka bashi lasifika ya fara rangado karatu mai dadin saurara da kira'a mai dadi irin ta Iman. Jama'a duk suka zazzauna suna sauraren Muhammad. Ma'aikata suna ta raba abubuwan da aka buga da hotunan Muhammad kamar, kalandu, memo, jakunkuna, sallayu, atamfofi, hijabai kur'anai littafin rubutu masu kyau, tun daga wani kamfani a London suka sa aka buga musu ma musamman. Abinci da abin sha kuwa babu wanda aka yiwa iyaka, kowa da kansa zai zuba abunda yake so yadda yake so. Komai akwai babu ce kawai babu, a jere akan zungureren teburan da aka cika da darukan abinci. Daga karshe Iman ta je ta zauna kan wata kujera Muhammad shima a kusa da ita akan tasa kujerar da teburi a gabansu wanda ke dauke da kur'anai akai. Iman ta dubi dunbin jama'ar da ta tara, gaba daya sun zagayeta suna sauraranta. Ta tuna mutane da dama wadanda a da ba Musulmai ba ne a yanzu kuwa sun Musulunta. Kukan dadi ya keto mata, sai ta share hawayenta tayi murmushi cikin harshen Hausa ta ce "Gaba dayanmu nan addinin mu daya, Allah daya muke bautawa mun yarda Annabi Muhammad (S.A.W) Manzonsa ne. Amma kuma yarenmu daban-daban. Shin da wanne yare zan yi magana yadda kowannen ku zai ji, zai fahimce ni? Idan na yi magana da turanci wasu basa ji, idan fulatanci ne da yawa basa jin fulatanci, balle in yi magana da Igbo, Tangalanci ko Mumuyanci wadanda suke ji a cikin ku kadan ne. Sai su duka suka dau dariya waje ya hargitse da hayaniya, kowa yana ambaton tayi magana da yarensa. Iman tayi dariya ta ce "Ina ganin kusan kowannen ku anan yana jin Hausa a ganina muyi amfani da yaren Hausa a matsayin yarenku kuma YARENA. Iman tayi gyaran murya tayi bismillah sanan ta fara karanto Hadisai tana fassarawa da Hausa, ta dauko tarihin Manzon Allah (S.A.W) tun daga ranar da aka haifeshi har ranar da yayi wafati. Ta gangaro rayuwar Sahabbai har zuwa rayuwa irin tamu ta yanzu. Ta ce "Shin ba zamu yi koyi da rayuwa irin ta lokacin Annabi ba? Yanzu duk kan Musulmai sun rarraba, masu hali basa tausayin marasa hali. Masu mulki basa tausayin talakawansu. Talaka baya hakuri da talaucinsa, *ya*ya basa tausayin Iyayensu, Iyaye basa bawa *ya*yansu tarbiyya yadda ya kamata. Ba'a soyayya dan Allah sai dan wani hali. Musulmi ya kashe Musulmi saboda kudi ko neman mulki ko dan ya fadi gaskiya. An danne gaskiya an daukaki karya. An daukaki duniya tamkar ba za'a mutu ba. Sace-sace sunyi yawa. Gulmace-gulmace sunyi yawa, cuta, danfara, hassada ba babba ba yaro. Kowa baya tausayi, burinsa ya samu wani ya rasa. Iman tayi kira, tayi roko ga *yan Uwa Musulmai su gyara halayensu. Su ji tsoron Allah, su so junansu saboda Allah. Suyi aure saboda Allah. Hawaye ne ke zuba daga idanuwan Iman da gaba daya masu sauraronta. Kowa yayi shiru, wasu sun doka uban tagumi suna sauraren Iman hawaye ne ke ta kwaranya daga idanuwansu. Hakika Iman ta hadu da ilimi, ta iya wa'azi mai ratsa zuciya kaji tunaninka da rayuwarka gaba daya sun kaura lahira. Mahaifiyar Iman sai kuka take tana duban irin baiwar da Allah Ya yiwa *yarta da ta haifa a cikinta. Ta godewa Allah daya bata *ya irin Iman har Allah Yasa ta Musulunta a sanadiyyarta. Daga karshe Muhammad ne yake karanta kur'ani Iman tana fassarawa. Ayar da suka karanta ta karshe wacce daga ita za'a rufe taro da addu'a saboda magruba ta kawo kai, ita ce Suratul Kafirun: Mohammad:- "Bismillahir-Rahmaanir-Rahiim Iman:- "Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai. Mohammad:- "Kul yaaa- ayyuhal KAAFIRUUN! Iman:- "Ka ce, "Ya ku kafirai! Mohammad:- "Laaa'a -budu maa ta - buduun. Iman:- "Ba zan bauta wa abun da kuke bauta wa ba. Mohammad:- "Walaaa'antum -aabiduuna maaa'a'a-bud. Iman:- "Kuma ku, ba ku zama masu bauta wa abun da nake bauta wa ba. Mohammad:- "Wa laaa 'ana 'aabidummaa 'a'maa abbattum, Iman:- "Kuma ni ban zama mai bautawa wa abin da kuke bauta waa ba. Mohammad: "Wa laaa antum 'aabiduuna maaa'a -abud. Iman:- "Kuma ku, baku zama masu bauta wa abin da nake bauta wa ba. Mohammad:- "Lakum Diinukum wa li-ya Diin. Iman:- "Addininku na gareku, kuma ADDININA yana gareni. Sai aka dauki kabbara gaba daya wajen. Aka rufe taro da addu'oi sannan aka tashi. KARSHE!!! ALHAMDULILLAH. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya sanya na kammala muku karshen littafinnan lafiya, na gode da bibiyata da kukai. @ watsapp 08097365237 @2go............reedwan2021