[26/02 16:05] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲 MAKARANTAR MATSAFA 2☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta *FCWA*☀️ ________________________ 01 A gajiye na dawo gida,ina ta ƙoƙarin haurawa sama amma yarana suka rugo tare da rungume ni suna faman faɗin “Mamy! Mamy!” Mohamed na ɗauka shi da ke ƙarami ina mai cewa “yeee! Ɗan gidan Mama,mene ne ka ci duk bakinka yayi shanana?” Cikin gwarancinsa ya ce “Mama ta bani fura,Inna wake da shinkafa” “Ƙarya yake Mamy ɗan wake ne Dijo ta yi mana kuma ke ma ta ajiye miki naki ” cewar Abdallah yana mai kallona tsakiyar ido,da sauri na sauke Mohamed ina mai jawo shi na ce “mene ne ya samu idonka?” “Da muna makaranta ne aljanu suka taso shi ne...shi ne...” sai kuma yayi shuru yana kallon Abidah,ni ma juyawa na yi na dube ta. Gabana na ɗan dokawa na ce “me ya faru?” “Wai tana da jinnu in ji Madam ɗinmu” Abdallah ya faɗa yana wani ɓata rai.“Jinnu kuma? ” na yi tambayar da salon mamaki. “Eh Mamy inda kin ga yadda Abidah ta dinga yi tana tashi sama kamar tsuntsuwa” Abdallah ya ƙara furzo furucin da ya kusa tsinka raunataciyar zuciyata,duk gajiyar da na kwaso ce na ji ta ɓata na zauna dirshen ƙasa ina tambayar ƙarin bayani amma duk sai suka yi min shuru suna kallona cike da tsoro.Ganin ba za su yi magana ba yasa na ɗauki waya na soma ƙoƙarin kiran Abbansu,bugu biyu ya ɗauka yana mai cewa “babyn Uncle ya...” ban bar shi ya ida ba na ce “Abban Abidah ka tawo gida babu lafiya...” sai kuma na fashe da kuka. “Subahanallah! Meke faruwa ?” ya tambaye ni ina iya jiyo tashin hankali a cikin maganar tasa. Cikin kuka na ce masa “wai Abidah ke da aljanu yanzun nan Abdallah ke faɗa min” “Don Allah ki kwantar da hankalinki,ki jira gani nan zuwa ” sai ya kashe kiran. Haka na saka su a gaba ina kuka su ma suna taya ni,hakan ya jawo hankalin Mama da Inna A'i da suka fito na koro musu ba'asi su ma suka shiga zullumi.Kamar minti goma sai ga Uncle Salem ya shigo sanyen da kakinsa na soja,direct wurin Abidah ya nufa wacce ta rikice lokaci guda da ya ɗauke ta.Ƙoƙarin kwantar mata da hankali ya fara kafin ya ɗauki ruwa ya karanta suratul fatiha⁷,ayatul ƙursiyu ¹,amanar rasulu² sai ya bata ta sha ko minti biyu ba a ɗauka ba jikinta ya fara fitar da zufa,sai dai fa ba irin wacce muka saba gani ba wannan zufa haɗe take da wani koren gumi sannan iskanta bai da daɗin shaƙa. Uncle Salem yasa hankici fari ya shafi gefen fuskar Abidah nan take yayi datti,sai ya kalli hankicin ya kuma maido dubansa gare ni.Kallo ne mai cike da zargi da kuma son sanin ƙarin bayani. “Mene ne ke damunta? Ka yi shuru ba ka ce komai ba” Mama ta tambaya. Uncle Salem ya ƙara haɗe fuska tamau,murya cike da tuƙuƙin baƙin ciki ya ce “Nafisa za ki tambaya ba ni ba” Duk sai suka maido hankalinsu a kaina,a ɗan rikice na ce “ni kuma?” “Kin ga ki faɗa mana abin da kika yi wa Abidar kafin maganar ta yi nisa” Mama ta faɗa , wannan karon cikin zafi amon muryar nata ya fita. Wasu hawaye masu ɗumi suka surnano min,ba na komai ne ba sai na baƙin cikin yadda na ga suna jingina ayar zargi a kaina alhalin sun fi kowa sanin cewa a cikin ƴaƴan nawa uku soyayyar Abidah ta daban ce a zuciyata. “Auta meke faruwa? Ban gane mene ne suke nufi ba” Inna A'i ta faɗa cikin sanyin murya,da sauri na je gare ta don na ga alamu ita ɗaya ce kawai tudun tsirana.Murya na rawa na ce “Innarmu ki tambaye su ni ma ban san me suke zargina a kai ba,wallahi banda laifin komai...” ban ida rufe bakina ba Uncle Salem ya wani fizgo ni tare da miƙar da ni tsaye ya wanke min fuska da wasu lafiyayyun marika guda biyu waɗanda suka tsinkar da igiyar majiyar sautina,yayin da idona suka yi ɗif ban ganin komai sai baƙin duhu da ya turnuƙe ganina. Ban ida dawowa daga hayyacina ba na ji yana feso min wasu baƙaƙen kalamai waɗanda ko a mafarki ban taɓa tunanin zai faɗa min su ba ballantana a zahiri. “Ki sakar wa ƴata ruhinta kafin na yi miki illar da har abada ba za ki taɓa moruwa ba.Duk yadda na yi ƙoƙarin nakasa maitarki wato sai da kika fito da ita fili kuma ki rasa wacce za ki kama sai ƴar cikinki” Idona da suka yi min mugun nauyi na soma buɗe wa a hankali,sai dai ban ganin komai sai buji-buji.Kafin nan Mama ita ma ta feso min nata,“dama tun can ka san mayya ce ka yarda ka aure ta?” “Mayya???” na maimaita kalmar a bakina..... [26/02 16:06] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲 MAKARANTAR MATSAFA 2☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta *FCWA*☀️ ________________________ 02 “Mayya? Ni ce mayyar ko wa?” na ƙara yin tambayar wannan karon na yi nasarar buɗe idona na sauke su kan fuskar Uncle Salem wanda yake ta ƙoto kamar wani kumurci. “Tabbas ke mayya ce kamar yadda ya faɗa” muryar Daddy ta ratso falon namu,duk sai muka mayar da dubanmu a gare shi har ya ƙaraso ya zauna kan kujerun da ke nan falon. Hawayena ne suka ƙara gudu wurin zuba jin mahaifina ma wanda ya kawo ni duniya ya gaskata maganar da nake jin gwara ace ajalina ne ya riske ni kan a ce gaskiya ce. Na rairafa wurin Daddy tare da kamo dukkan ƙafafunsa,kaina na shiga girgiza masa murya na ɗan rawa na ce “don Allah Daddy ka bar faɗar haka zuciyata za ta yi bindiga” Yasa hannu ya kamo kafaɗuna kamar wata ƙaramar yarinya kafin ya ce “ Nafisa ana haifar wasu ne don su zama bala'i da annoba ga al'umma,ke kuma an haife ki ne don kawar da wannan ɓarnar ki kuma kawar da kambun maita.Tabbas na san na yi babban kuskure na nisanta ki daga cikin garin Victoria Falls,domin a can ne kawai za ki iya yin rayuwa ba tare da kin fuskanci ƙalubale ba don akwai ire-irenki da yawa” “Ire-irena kamar ya? Don Allah Daddy kar ka ce min Mayu domin ni ba mayya ba ce” na faɗa ina mai fashewa da wani matsanancin kuka mai taɓa zuciya. Daddy ya ce “sai haƙuri Nafisa amma ba za a taɓa canza wa tuwo suna ba,alƙalamin ƙaddararki ya riga da ya bushe. Yanzu kuma lokaci yayi da za ki fara fuskantar kanki ” A hankali na zame daga jikin Daddy na miƙe tsaye na soma ja da baya ina girgiza kai,ko kaɗan ba zan taɓa yarda da wannan tashin hankalin ba .Kamar wata mahaukaci haka na ruga zuwa kitchen na ɗauki wuƙa,ba tare da wani tunani ba na yanka hannuna daidai babbar jijiya ta magudanar jini. “Gwara na mutu da na dinga amsa sunan mayya wallahi ba zan yarda ba” na faɗa ina ƙoƙarin jan ƙofar kitchen na rufe,sai dai tuni Uncle ya rige ni.Wani irin mugun riƙo yayi min ya fitar da ni daga kitchen ɗin,duk yadda na so kashe kaina hakan ɗin bai faru ba don tuni ya tsayar min da jinin tare da ɗura min maganin da ya saba bani. Tun ina kuka tare da suratai har na soma gajiya ,a hankali kuma idona suka fara lumshe wa alamun bacci na son ɗaukata. UNCLE SALEM ya ja wata irin ajiyar zuciya yana kallon fuskar Nafisa wacce lokaci guda har ta faɗa,sai yanzu kuma yake ganin bai kyauta ba sam da ya ɗauki mataki kai tsaye ba tare da wani tunani ba. A kunyace ya dubi abokin nasa kuma surukinsa ya ce “mu je daga ciki”sai duk suka haura sama ,a falon Uncle ɗin suka zauna kafin kuma su yi shuru. Daddy ne ya fara yin magana,“aboki kana tune da cewa fatalwa ba za ta taɓa yi wa mutum wata hidima ko taimako ba dole da sai da wani sharaɗin? To Deborat ta ƙara bayyana a ɗakina yau a karo na biyu,sannan ta sanar da ni cewa kai ma ka san da dole za ta zo tun da ta shigar ma faɗa ” Uncle Salem ya ja wata ajiyar zuciya kafin ya ce “to amma mene ne na sako Abidah a ciki? ” “Saboda Nafisa ta fi sonta a cikin ƴaƴanta” Daddy ya basa amsa. “Mene ne mafita yanzu?” Uncle ya tambaya . Daddy ya ce “da dukkan alamu akwai wani kuskure da ka yi ,ko kuma aikin kawar da matsafan nan bai kammalu ba” Daddy ya faɗa. Uncle Salem yayi shuru yana nazari kafin ya ce “ yanzu dai abu na farko da za mu yi shine ganin mun disashe kambun maitar da ke jikin Abidah kamar yadda na dinga yi wa Nafisa tun tana ƙarama zuwa yanzu.Amma abin da ya fi ban mamaki bai wuce yadda cutar ta yi saurin bayyana a jikin Abidah ba alhalin duk wani ƙarfin iko na power yana bayyana ne a shekaru sha uku zuwa sama” “Mu saka ido kawai sosai”Daddy ya faɗa tare da miƙewa tsaye , Uncle yayi masa rakiya suka sauko ƙasa har zuwa yanzu Nafisa na ta yin bacci ita da Abidah. A nutse yake kallon su duka biyun,wani abu yake gani suna masayen ta bacci mai kama da kambun maitar ido sai dai bai san ta yaya zai yi ya dakatar da su ba. Ragowar ruwan addu'ar ya ɗauka ya zuba wa Abidah,da wani irin bala'itacen ihu ta tashi daga baccin tana kiran “ina son sha jini! ” [26/02 16:07] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲 MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta *FCWA*☀️ ________________________ 03 “Jini! Jini! A bani jini na sha! Ina son shan jini! Mamy ki bani jini!” muryar Abidah ta ratsa dodon kunnena ,a hankali kuma na buɗe idona na ware su a kanta,yanayinta kawai na kalla na tabbatar da eh tana da buƙatar shan jinin,kuma jinin iya nawa ne kawai za ta sha.Na lumshe ido ina mai tuna Madam Lee ba zan manta ba ita ce ta farko da na saba gani cikin irin wannan halin. “Mama ki jiƙa ganyen magani a yi mata wanka,sannan ki haɗa maganin zazzaɓi kar ki manta ki ɗiga ruwan floris ”na ji muryar Uncle Salem cikin ruɗani,sai na ware idona a kansu ina kallon yadda yake ƙoƙarin lalaɓa Abidah amma sam ta ƙi saurarensa sai ma wani juya idonta da ta fara suna canza kala daga fari zuwa ja kamar garwashin wuta. Jikin Mama har rawa yake ta yi aikin da Uncle Salem ya bata,sai dai tana kawo robar mai cike da ruwan magani Abidah ta canza murya ta soma magana cikin salon gargaɗi “jini na ce ina so shine kuke wani ƙoƙarin haɗa magani? Ku bani jini ko kuma na kashe ku ɗaya bayan ɗaya” “Abidana ki yi haƙuri ki bari na yi miki wanka sai a baki jinin”Mama ta faɗa tare da kama rigarta,da ƙafa Abidah ta shure Mama ta yi sama tare da faɗuwa can gefe kanta ya bugu ga table nan take jini ya soma zuba, Abidah ta fara yin dariya cikin wata shaƙaƙar miya ta ƙato majiya ƙarfi kafin ta ce “yaushe aka haife ki da har za ki yi min wayo? Ki yi hankali da ni yau kanki na fasa in kika ci gaba da yi min ƙarya nan gaba wuyanki zan karye na cire shi na baiwa tsuntsayena namanki su cinye” Cikin zafin rai Uncle Salem ya tsumbula Abidah cikin ruwan ba tare da ya cire mata kaya ba,ai kuwa ta shiga tsala ihu tana kirana “Mamy?Mamy?” ban sani ba ku su ma sun fahimci cewa aljanin da ke jikinta ya bar tunaninta a halin yanzu ita ce ke jin azaba ba shi ba. Da wani irin sauri na diro daga kan kujerar na zo gaban robar,sai dai ko kafin na taɓa ta Daddy ya wani jawo ni baya.Tun Abidah na iya kiran sunana har ruhinta ya galabaita,idonta suka kafe wuri guda sun koma farare tasss kamar na fatalwa,yayin da fatar bakinta ta soma bushewa tamkar itaciyar da ke neman a yi mata ban ruwa ba ta samu ba. “Daddy ka sake ni na ceci ƴata kafin ta mutu”na faɗa zuciyata na yi min wani nauyi don tuni na yarda kuma na aminta da cewa eh ni ɗin mayya ce,haka ma ƴata sai dai na lashi takobin zan tarwatsa rayuwar duk wani wanda ke da hannu a kawo wannan ƙwayar maitar a cikin ahalinmu. “Ki bari Abbanta na bata taimakon ne” Daddy ya faɗa . Na girgiza kai na ce “duk abin da yake yi mata ga banza ne,domin kuwa iya fatar jikinta kawai zai yi wa aiki amma ruhinta jini yake buƙata” Uncle Salem ya juyo yana yi min wani irin kallo,sam kuma ban damu ba ni dai burina kawai shine na ceto Abidah.Daddy na sakina sai na lalaba cikin gashina na fito da wani tsinke mai tsini kamar allura,a yatsana manuniyar na caka shi nan take jini ya fara tsirta sai na yi saurin kai shi kusan bakin Abidah a hankali jinin ya soma kwarara cikin maƙoshinta yana shiga hanjinta nan take kuma idonta suka fara dawowa daidai haka ma bushewar da bakinta yayi duk ya dawo normal. Sai da na tabbatar ta sha jinin yadda ya kamata kafin na janye yatsana,a nan take kuma kamar na kashe pampo jinin ya bar zuba.Daga cikin ruwan na tsamo ta na rungume ta gam a ƙirjina,ina jin ƙaunarta na sake huda ɓargon zuciyata tana ƙara samun matsuguni. Miƙewa na yi da ita a jikina na haura sama,ina jin Mohamed na kuka amma ko waiga wa ban yi ba.Ina shiga ɗakina na cire mata kayan jikinta na yi mata wanka da kaina,sannan na shafa mata mai .Kayanta suna can ɓangaren Mama don a can suke kwana su duka ukun wurin kakarsu,wani kallabina na atamfa na ɗaura mata na kwantar da ita kan bed sannan na shiga toilet na sakar wa kaina shower.Duk abubuwan da suka faru suka soma dawo min ,wani irin ciwo zuciyata ta soma tuna marin da Uncle yayi min na soma yi wa kaina tambayar ‘ya bar sona ne ko me? Duk tsawon shekarun da aka ɗauka kenan ya san ina da wannan cutar amma bai taɓa faɗa min ba,don me sai yau? Saboda kin fara tsufa!’ wani ɓangaren zuciyata ya bani amsa. Ina nan tsaye na ji an turo ƙofar toilet ɗin an shigo,na san in ba shi ba to babu wanda zai iya yin haka.Amma duk da haka ban juyo ba,sai ji na yi ya rungume ni ta baya tare da yi wa cikina zobe da hannuwansa yana mai ɗora kansa kan kafaɗata,cikin wani sauti marar hayaniya ya furta “ki yi haƙuri babyn Uncle ” ji na yi kamar ya watsa min ruwan zafi,wato ya san abin da yayi min bai kyauta ba? Da wani irin ƙarfi na ture shi ina mai juyowa muna facing juna,cikin masifa na ce “na ƙi na yi haƙurin! Ba zan yi ba! Ka fita ka bani wuri zan yi wanka” Ya matso yana shirin kamo hannuna amma na buge shi ina mai cewa “kar ka taɓa ni ! Ka fita ko kuma ni na bar ma toilet ɗin” A cikin idonsa ina iya hango damuwa,a haka ya fita ni kuma na ɗauki soso da sabulu na soma wanka ina yi ina kuka har na gama.Ko da na fito ban ga Abidah ba,na san kuma shi zai ɗaukar ta ya sauka da ita ƙasa.A gaggauce na shirya tsaf kamar wacce ba ta da damuwar komai na sauko,ina isa falon Abdallah ya zo ya rungume ni yana mai cewa “Mamy ?” Na ɗan ƙaƙalo murmushi na ce “ka ci abinci ne?” kai ya girgiza,na kama hannunsa ina mai kallon inda Mohamed ke bacci fuskarsa duk ta yi sawun busassun hawaye.Tausayinsa na ji,don na san saboda ni ce duk gidan ya hargitse.Can inda aka ware domin cin abinci na ja Abdallah na zaunar da shi kan kujera na soma basa da hannuna shi kuma yana yi min surutunsa wanda babu laifi na ji nauyin zuciyata ya ɗan rage.A hankali na ɗaga idona saboda yadda nake jin kamar ana ankare da duk wani motsina,Uncle na gani ya harɗe hannuwansa kamar ya samu tv yana kallona... [26/02 17:28] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲 MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta *FCWA*☀️ ________________________ Masu jiran book ɗin *MAKARANTAR MATSAFA* to ya kammala za ku iya tura kuɗinku kai tsaye ta wannan account 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ku turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 04 Da sauri na fidda hannuna daga cikin plate ɗin abincin na miƙe, kitchen na shiga na fara wanke hannuna kenan na ji ƙamshin turarensa ya cika wurin.Na haɗe fuskata tamau kafin na juyo na banka masa wata muguwar harara,shi kuwa murmushi ya sakar min ya buɗe baki da niyya yin magana na bangaje shi na wuce ina jin sawun takunsa alamun ya biyo bayana amma ban juya ba har na soma taka step,muryar Mama na ji tana kiransa “Sadauki zo nan ” a yadda na ji amon muryarta na tabbata ranta a ɓace yake. Shi kuwa ce mata yayi “ina zuwa Mama ɗan jira ni don Allah ” Ina shiga ɗakina na fara ƙoƙarin rufe ƙofar da key amma ya wani bangazo ƙofar har sai da na kusa faɗuwa na yi tangal-tangal amma yayi saurin cabko hannuna,bayan na tsayu daram kan ƙafafuna na yi ƙoƙarin fizge hannuna amma ya ƙi sakina sannan na kasa ƙwatar kaina don ba ƙaramin riƙo yayi min ba. “Naf don Allah wannan duk na mene ne?” yayi tambayar cikin sanyin murya. Idona ya kawo ruwa,shi kuwa sai ƙoƙarin ɗago haɓata yake sama don na kalle shi amma na ƙiya.“Na ce ki yi haƙuri ko?” ya ƙara faɗa. Sai a lokacin na ɗaga kaina sama na sauke masa idona masu cike da masifa na ce “na ƙi na haƙura ɗin,ba zan yi ba.Ni za ka tozarta gaban ƴaƴana? Ni ka kira mayya? Na ji gaske ita ce ɗin,amma kai yanzu ba abin kunya ne a gare ka ba ka kira matarka da wannan sunan? Kuma gaban ƴaƴana...” kukan da ya kubce min ne yasa ni yin shuru ban shirya ba. Ya ce “kar fa ki manta su Abdallah yara ne ba su san abin da kalmar ma take nufi ba,sannan Mama da Inna A'i sam ba za su taɓa tada zancen ba” Ƙirjinsa na soma duka da dukkan ƙarfina kafin na soma magana cikin ɗaga murya har jijiyoyin wuyana na tashi,“kasancewar tasu yara yasa na fi damuwa,don za su iya fitar da maganar su ce sun ji Abbansu ya cewa Mamynsu Mayya.Kenan me za ka ce in ƴan unguwa suka fara guduna? ” Ƙara riƙe ni yayi gam na soma zillewa ina son raba jikina da nasa,ya ce “don Allah Naf ki yi haƙuri wallahi na san Abdallah ba zai taɓa faɗar haka ba ballantana Mohamed da ko magana bai iya ba” “Shi kuma zargina da ka yi ka ce ni na kama ruhin Abidah?” “Naf ki fahimce ni na faɗi haka ne saboda ke ma farkon ciwon jinnunki haka suka fara nunawa,tun gwajin farko na gane kina ɗauke da kambun maitar aljanu amma na yi ta fafutukar ganin na toshe duk wata ƙofa da za ta iya yin galaba a kanki har ki fara aiki da ita.Ina son ki Naf, wannan dalilin yasa duk wani lokacina na ƙarar da shi wurin kula da ke.Na san na yi kuskure a ɗazu amma ki yi haƙuri ki yafewa Uncle ɗinki” Kalamansa sosai suka daki zuciyata,amma ba zan sauko da wuri ba na fi son na nuna masa zunubinsa mai girma ne don ko kowa ya kira ni da sunan mayya shi bai kamata furucin ya fito bakinsa ba. Na goge hawayena da bayan hannu kafin na ce “na ji yanzu dai ka cika ni ” “Sai kin ce kin yafe min kin haƙura” “Zan faɗa amma ba yanzu ba” “Don me?” “Sai na yi tunani” na fara tare da ci gaba da yin mutsu-mutsu ina son ya rabu da ni.Ya na sakina na yi saurin yin gaba na shige bedroom,kan bed na haye tare da yin rub da ciki har yanzu hawaye na zubo min.Na kasa gane me ake nufi da Maitar aljanu sam,ta gado ce ko kuwa jinnun ne ke Mayu sai su liƙawa mutum? Ban sani ba! “Tashi ki ci abinci ”na ji muryarsa bayan ɗan lokacin da na ɗauka a haka.Ina jin yunwa hakan yasa na tashi zaune,a halin yanzu kuma Naf ɗin Uncle ce kawai na wai matarsa ba haka nake ji wannan yasa na shagwaɓe masa kamar tun can farko da muna gidan Daddy kafin aurenmu. Murmushi ya saki mai sauti kafin ya zauna gefena ya soma ciyar da ni da kansa har sai da na ƙoshi.Ina shirin komawa na kwanta amma ya taro ni tare da kafe ni da ido,na turo baki gaba na ce “ni ka bar kallona da jajayen idonka” “Irin naki ne ai” ya faɗa tare da kaiwa lips ɗina sumba,da sauri dai na janye don ban son abin yayi nisa.Ƴar dariya yayi tare da miƙewa tsaye yana cewa “da dukkan alamu wata dai tsoron haihuwa take shi yasa take gudun mijinta” Na yi masa hararar wasa na ce “su waɗanda na haifa ai na ga kai ka riƙe ni suka faɗo” “Har da faɗan magana? Zan kama ki ne haba yarinya” “Ni ce yarinyar?” na faɗa cikin jin haushi,ya ɗaga min gira yana mai cewa “ko ba ita ba ce?” “Ita ce” na basa amsa ina shirin kwanciya sai na ga wani ƙaton ɓera kan dressing mirror yana kallona ƙuri.Gabana ya bada wani irin sautin dasss,na zabura zan sauka amma ɓeran ya ruga.Na ja ajiyar zuciya ina mai cewa kaina ‘ kai Nafisa ki cire tunanin matsafan nan a ranki,ki bar shirme’ Uncle kuwa tambaya ta yayi “mene ne?” Na ce “babu komai ” kawai sai ya fice ya bar ni a nan . Duk yadda na so ture tunanin ɓera sai dai abin ya cuttura don kuwa da zarar na rufe ido shi nake gani yana yi min murmushin mugunta.Na shagala sosai a duniyar tunani barkatai sai na ji an dafa kafaɗata, na zabura ina ɗan ihu sai dai ban ga kowa ba amma tabbas na ji ɗumin tafin hannu.Babu shiri na zuro ƙafafuna ƙasa da niyyar sauka,amma sai na ji na laɓa wani abu mai taushi kuma mai gashi na yi ƙara tare da koma kan bed sai na leƙo ƙasa.Ɓeran ɗazu ne dai na gani,yanzu ma muna haɗa ido ya ruga ya shige ƙarƙashin gado.Wannan karon kam na tabbata ba zargi nake ba,kawai zahirin gaskiya ce ta fito .Wani irin tsalle na yi na diro daga gadon tare da falfalawa da gudu sai dai ina kai wa ƙofar fita daga falo ta rufe kanta ruf tare da motsa kanta tana saka key wanda a gaban idon handle ke juyawa da kuma gidan key kafin daga ƙarshe key ɗin ya ɓata gaba ɗaya. Wasu Mayun idanuwa na ji suna kallona,cike da tsoro na juya bayana a hankali nan na yi arba da wata mummunar siffa sanye da fararen kaya waɗanda ba su rufe ƙafafunta irin na ƙofaton doki ba. Wani irin luuuu ruhina da ke can cikin ɓargon jikina yayi,ko tantama babu FATALWAR DEBORAH ce a zaune a kan kujerata tana yi min wani kallo mai cike da tsana da kuma son kawo ƙarshena..... [27/02 02:13] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲 MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta *FCWA*☀️ ________________________ In ba ku manta littafin MAKARANTAR MATSAFA ainahinsa ci gaban book ɗin MUTUWARE ne,sannan tun a can yayi magana kan DEBORAH wacce ke babbar hatsabiyaya.In mutum yana so zai iya karanta iya FATALWAR DEBORAH in kuma yana son sanin duk abubuwan da suka shafe ta ne sai ya koma ya samo littatafan farko wato MUTUWARE da kuma MAKARANTAR MATSAFA. 05 Ban taɓa ganin fatalwa ba cikin siffarta ba sai yanzu ,ko Andre da na gansa yana cikin siffar mutum ne sannan sam jikinsa bai fitar da warin gawa ita kam wannan har wani iska marar daɗin shaƙa jikinta ke fesar wa. Kamar ƙyaftawar ido haka gangar jikinta ta ɓata sai doguwar rigarta kawai da ke zaune kan kujera.Daga bayana na ji shuuu ,da sauri na juya sai na ga wayam.Dariya na ji daga can sama ,ina ɗaga kai sai na hange maƙale da fanka ashe duk jikinta ƙwarangwal ne rigar ce ta rufa masa asiri. Bakinta ta buɗe ta shiga dalalo da yawunta wasu koraye kafin ta soma magana cikin wata shaƙaƙiyar murya wacce kana ji ka san ta matattu ce. “Wajen ƙarni uku ya shuɗe,amma har yanzu ba a yi jaruma irin DEBORAH ba,ni ɗin ta daban ce.In na so na mayar da ruhina mai kyawu ko akasinsa,kin ga zamanin Kakarki Ayodele muguwa ce Ni amma ta iya sarrafa kambunta ta kuɓutar da al'ummarta sannan duk yadda na so na ɗauki mataki a kanta ban yi galaba ba.Ke kuma lokacin zamaninki haka na fito a salihata amma kika kasa taɓuka komai sai mijinki ne yayi, wannan babban abin kunya ne kika tabka kin fita zakka a kaf sarakunan da Victoria Falls ta samu.Wannan dalilin yasa na yi tattaki tun daga ɓoyayyar duniya na zo nan,ki sani daga yau an fara ƙirga kwanakin ƙuncinki da wahalarki.Sai na kawar da duk wani farin cikinki,hatta shi mijin naki zan mayar da shi nawa Hahaha ! Ya iya soyayya ba? Zan zama karuwarsa Hahaha ” ta ƙarashe maganar tana wata irin dariya wacce ta saka fankar fara juyawa da ita yayin da kuma amon muryarta duk ya hargitsa dodon kunnena. Rigarta ce ta wani miƙe tsaye tare da soma yin tafiya kamar wani mutum sai faman wuwulniya take tana doso ni,ni kuma ina ja da baya har na dangane ga ƙofa. Sai a lokacin kuma siffarta ta bayyana cikin rigar,sai na ga ashe ta fi muni in tana kusa. “Ni zan tafi ba za ki sake ganina ba,amma shi mijinki iyeee! Iyeeen! Za mu dinga soyewa” sai ta wani tashi sama ta fice ta rufin ɗaki.Ƙiiii! Ƙofa ta buɗe kanta,a wahalce na fita ina dafa bango har na sauka ƙasa ina mai ƙwala kiran sunan Mama ya fi a ƙirga amma babu ko ɗaya da ta amsa alhalin tana zaune daram a falo. Ina isa na ƙara marairaice murya na ce “Mama yanzu nan ...” saurin katse ni ta yi “don Allah ban tambaye ki ba,kin ga ki yi rayuwarki yadda kike so tun da hakan kike gani daidai ne.Sai dai ki sani ni kurwar ruhina ta fi ƙarfinki ko kin kame ta sai kin sake ta,saboda ɗaci ne da ni shi dai tun da ya zama malaho sai ya je can ki ci gaba da juya shi” tana gama faɗar haka ta ajiye kofin madarar hannunta ta tashi ta bar min wurin. Ji na yi kamar na ɗora hannu a kai na ƙwala ƙara haɗi da kuka,bayanta kawai na bi da ido har ta shige sashenta. Inna A'i wacce shigowarta kenan ta dube ni ta ce “auta lafiya?” Hawaye masu ɗumi suka zubo min na ce “babu komai Innarmu,daga ina kike?” “Gidan Dijo na tafi,kin san ba ta jin daɗin jikinta ɗazu da mai aikinta ta kawo ɗan wake ta sanar da mu shine na je.Na yi tunanin ma ko ciki ne da ita ashe zazzaɓi ne kawai” “Allah ya bata lafiya” “Amen! Faɗa min meke faruwa na ga uwar sadauki kamar ranta a ɓace” Na sunne kai kawai don ban san me zan ce mata ba, Uncle Salem yayi sallama yayin da kuma Abdallah da Mohamed ke yin dariya suna biye da shi.Kallo ɗaya kawai na yi musu na janye idona,ko zama bai yi ba sai ga Mama ta fito fuskar nan a murtuƙe ta ce “in ka gama abin da kake ina son yin magana da kai” “Ba na yin komai Mama” ya faɗa yana mai miƙo min leda,ina ganin yadda Mama ta bi ledar da ido kafin ta koma ɗakinta.Uncle ya dube ni ya ce “me kuma aka yi ? Na ga kamar Mama na fushi da ke, sannan su wannan hawayen na mine ne?” Ban basa amsa ba sai Mohamed da na jawo wanda tuni an yi masa wanka an canza masa kaya.“Ina kuka je yarona?” na tambaye shi,dariya yayi ya soma yi min surutu yana sanar da ni sun je wani Mall Abbansu ya saya musu abubuwa masu daɗi. “Naf da ke fa nake” Uncle ya faɗa ,na ɗaga kai na dube shi na ce “Mama na kiran ka” Matsowa yayi kusa da ni ya wani kamo ni kamar wata yarinya ya ce “ki faɗa min don Allah kafin na je” “In ka dawo za mu yi maganar” na faɗa ,“ok na ji bari na je” ya faɗa tare da yin gaba na bi bayansa da kallo ina jin tausayin kanmu ganin wata masifar na tunkaro mu ta uƙubar uwar miji. Uncle Salem na shiga ɗaki ya tarar da Mama a zaune ta cika fam kamar za ta fashe,gefenta kuma Abidah a zaune yanzu ta tashi daga bacci. Cike da girmamawa ya gaishe ta tare da cewa “Mama ga ni ” sai kuma ya samu wuri ya zauna. Cike da izza ta ce “dama tambayarka nake son yi wace ce uwarka?” “Subahallah! Mama wacce irin tambaya ce wannan?” Uncle Salem ya faɗa yana jin wani iri a zuciya . Mama ta ce “eh ai gwara na ji da bakinka wace ta haife ka ni ko Nafisa?” Kansa ne ya soma sarawa,cike da ladabi ya ce “Mama don Allah ki yi haƙuri duk da ban san laifin da Naf ta yi miki ba” “Ai ita ba ta laifi matar gwal ce,ina ce duk abin da ta yi daidai ne ta mayar da kai malaho sai abin da take so ake yi a gidan nan tana ƙaryar ita jinin sarauta ce an wani kawo bayi suna yi mata ayyukan da ita ce ta dace ta yi su.Ko kunya ba ta ji ƴan aiki ne ke yi wa mijinta girki yana ci ita kuma tana can tana yawon ta zubar tana gogayya da ƙatti da sunan aiki.To daga yau in dai ni ce uwarka to ya zama dole a kori bayin can daga gidan nan,a bar iya A'i” “Mama kar ki manta Inna A'i ko can ba ƴar aiki ba ce,kuma Nafisa yarinya ce ba za ta iya yin ayyukan gidan nan ba ita ɗaya a bar ko mutum ɗaya ne sai ya dinga kama mata” “Ba dai a cikin bayin Victoria Falls ba,ka sallame su ni nan da kaina zan nemo ma ƴar aiki ka tashi ka tafi Allah yi ma albarka” Ya miƙe yana mai cewa “amen” kafin ya fice.... [27/02 02:52] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲 MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta *FCWA*☀️ ________________________ 06 Ina nan zaune tare da yara Uncle Salem ya fito,a yanayin fuskarsa kawai na fahimci ba abu mai daɗi ne Mama ta sanar da shi ba amma na basar na ci gaba da fitar da chocolat da ke cikin ledar da ya bani ina nunawa Abdallah shi kuma yana karanta sunayensu. Bai ce komai ba yayi sama,ni ma na ƙi tanka shi na yi zamana dukkan sallolina ma a ɗakin Inna A'i na yi su har isha'i.Abinci kuwa kasa ci na yi sai su Abdallah da na saka gaba suka ci na kuma umarce su da su wuce can ɗakin kakarsu tun da a can suke kwana,na yi Inna A'i sallama na fito. Tun da na soma taka step nake jin tamkar ana take min baya har wata guguwa-guguwa nake ji haɗi da wani numfashi kamar na kumurci,amma a haka na daure na haura sama direct kuma ɗakin Uncle na shiga. Kiciɓis muka yi da shi ya fito daga bedroom ɗinsa ƙugunsa ɗaure da towel yana goge kuma sumar kansa da ɗan ƙarami. Na ɗan ja ajiyar zuciya kafin na je na karɓi towel ɗin na zauna da shi ina goge masa ruwan. “Naf!” ya faɗa can ƙasan maƙoshi,na ce “uhum!” “Mu je ki yi wanka” ya faɗa tare da tashi tsaye ya ja ni muka shiga can uwar ɗaka,sai da yayi mana addu'a sannan muka shiga toilet ɗin.Ruwan ɗumi ya cika min bahon wankan da su na shige,sai a lokacin ya fita ya bar ni na soma wanka ina ayyana abubuwa da yawa a raina har na gama na fito ɗaure da towel ɗinsa. Bayan na shafa lotion da turare na saka kayan baccin da ya fitar min,sai a lokacin ya rufe laptop ɗinsa yana tsokana ta.“A zo a sama wa Mohamed ƙanwa” Murmushi kawai na yi , ya rungumo ni tare da ja na muka yi baya muka zube kan bed.“Wai kin san da ina mahaukacin son ki?” yayi min tambayar da bai bani damar basa amsa ba saboda bakinmu da haɗe wuri guda yana kissing a hankali kuma yake shafar cikina zuwa ƙasa.Dakyar na aro jarumtar fitar da duk damuwata na ajiye hankali muka faranta ran juna,a yau ma Uncle ya ƙara dasa min wani sonsa na musamman a zuciya .A ɗan kunyace na yunƙura zan tashi amma ya mayar da ni tare da yi min raɗa a kunne,a shagwaɓe na daki ƙirjinsa na ce “uncle kana ƙara girma amma kana abubuwan yara” wata shu'umar dariya yayi ya ce “au kar dai a ce kallon tsoho kike yi min? Baby duka nawa nake da ba zan kasance da ke sau biyu ba?” “Ni dai a bar ni na huta bacci nake ji” na faɗa ina ƙara ƙoƙarin tashi amma ya ɗora hannunsa kan cikina yana mai cewa “ki jira na haɗo miki lafiyayen abinci dai baby sai ki ji ƙarfin kula da mijinki” Yana gama faɗar haka ya tashi ya kimtsa tare da fita,ni kuwa na lafe cikin blanket ina murmushi. Uncle Salem kuwa shi kansa yunwar yake ji don kalaman Mama kasa barinsa sukuni suka yi ballantana har yayi tunanin cin abinci. Ƙasa ya sauka tare da shiga kitchen,tray ya samu ya soma ɗora duk abin da za su ci yana tsaka da yin aikin gabansa Mama ta shigo hannunta riƙe da na Abidah. A ɗan kunyace ya ce “Mama fitowa kika yi?” “Eh Abidah ce tace min yunwa take ji shi ne na zo kitchen don sama mata abin da za ta ci” ita ma Mamar ta faɗa tana mai kallon trayn da ya zuba fruits kamar yadda Abidah ke kallo. Shi kuwa ƙaramin plate ya samu ya soma yayanka mata yana mai farawa da Bismillah kamar yadda abin ya zame masa jiki babu abin da zai yi ba tare da ya ambaci sunan Allah ba. Yana miƙawa Abidah amma ta ƙi karɓa a ƙarshe ma dai cewa ta yi ba ta jin yunwar,da Mama ta kama hannunta don su koma sai ta tsira kuka tana mai cewa “ni wurin Abba zan tafi” Uncle kuwa sanin halin da ya baro Nafisa ,sannan da wanda shi kansa yake ciki na larurarsa sai ya kuwa ya murje ido ya ce “Mama ki tafi da ita ki rarrashe ta za ta bari,Abidar Mama ki bar kuka kin ji ko ? Gobe zan saya miki zuma” ya faɗi haka ne saboda duk rigimar da take in ambaci zuma tana yin shuru. Da wani irin kallo Abidah ta bi bayan Uncle,wanda kuma a zahiri ba ita ce ɗin ba ruhin DEBORAH ne ke juya gangar jikinta.Ta so ace ya tafi da ita can ɗakin don hana shi ƙara kusantar Nafisa,amma babu yadda ta iya dole ta haƙura ta bi Mama. Ina nan yadda ya bar ni ya shigo,jikinsa har rawa yake kamar kullum muddin dai yana da buƙatar kasancewa da ni to duk wani control rasa shi yake. Fruits ya soma ciyar da mu,sai ya saka a bakinsa yana ɗura min kamar wasu tantabaru ko kuma ya saka a bakina sai ya dinga sha yana gamawa da sumbata ta a haka muka ƙara shiga wani shauƙin soyayyar muka samawa juna nutsuwa a karo na biyu.Duk yadda na so kuma na kwanta bacci Uncle bai bari na zauna da najasa ba sai da muka tsabtace jikinmu,a shagwaɓe nake yi masa mita sai ya ce “Baby babu kyau fa kwana da janaba,in mutum bai iya yin wanka to Manzon rahama ya ce ko alwala ce ka yi kafin ka kwanta don nisanta kanka daga sheɗanu” Ambatar sheɗanu da yayi shi ya dawo min da tashin hankalin ɗazu na gamdakatar da na yi da FATALWAR DEBORAH,cike da tsoro na ƙanƙame shi ina shigewa ƙirjinsa haɗi da ɓoye fuskata shi kuwa karatu na ji ya soma yi min yana min wata irin shafa wacce ta mayar da tsikar jikina da ta tashi. A hankali na soma lumshe ido saboda karatun da yake yi min yana kashe min jiki ne ruhina na yin wani sanyi liƙis,ko gama ida rufe ido ban yi ba na ga Deborah a tsaye a cikin mafarkina ta yi kicin-cikin da fuska,ba ta kuma ɗauki dogon lokaci ba ta shaƙe min wuya.... [27/02 15:49] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲 MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta *FCWA*☀️ ________________________ 07 Ko a cikin miyagu ita Deborah ƙarshe ce wurin iya mugunta,na sha jin labaranta a cikin littafin sirrin Kakata Ayodele na MUTUWARE.Wannan yasa ban ma ɓata wa kaina lokaci ba wurin ƙwatar kaina ta ƙarfi ba,sai dai furucin baki wanda nake feso ayoyin Alkur'ani duk wacce ta zo min wata ma ko ƙarshen ayar ban kai wa nake kamo wata.Amma tsabar taurin rai na fatalwa haka ta daure azabar da nake yi mata domin kuwa karatun Alkur'ani na ƙona ruhinta ne kamar yadda yake ƙona jinnu. Cikin ikon Allah dai na samu na ci galaba a kanta ta bari na tashi daga baƙin baccin nan.Kan fuskar Uncle na sauke idona wanda ke sharar bacci,a hankali na sauka daga bed ɗin na nufi farantin da ya shigo mana shi don ɗaukar ruwa na sha sai dai ina taɓa gorar da hannuna nan take ruwan suka ƙwafe ki ɗigo ɗaya babu alhalin da idona na gansu. Ƙishi nake ji sosai,maƙoshina ya bushe kamar wacce ba ta taɓa shan ruwa ba.Don dole na zura hijabi tare da fitowa,wani abin mamaki ne ya faru da ni,a daidai lokacin da na sauke ƙafata daga step ɗin ƙarshe sai duk ƙwayaƙwayin lantarki suka fara disashewa suna wani lummm kamar rana za ta faɗi,ko kafin ƙyaftawar ido kuma suka dinga tarwatsewa ji kake tatatseeee ! Rasss! Duk sun mutu ɗakin ya dawo baƙi ƙirin ko tafin hannuna ban iya gani,iska ne ya soma kaɗawa a hankali-a hankali kafin kuma ƙofae fita falo ta yi wani ƙiiii ta buɗe kanta daidai nan wata murya irin kamar ta wanda ya ɓata ta soma kiran sunana. “Naf? Naf zo gare ni! Naf zo mana za su tafi da ni” muryar da na ajiye hankali sai na ji ta Uncle ce,kamar wacce ake yi wa jagora haka na soma bin wani hasken jar wutar kyandir har na fita daga gidan baki ɗaya.Tafiyar ƙasa na soma yi a cikin duhun sararin samaniya wanda ya ɗauki wani yanayi kamar lokacin damina,duk taurari sun ɓata sai giza-gizai ke faman gudu. Ba zan iya cewa ga iya adadin lokacin da na ɗauka ina tafiya ba,ni dai kawai na gan ni a bakin ƙofar shiga wani jeji ina dab da saka ƙafata ciki na ji an jawo ni ta baya.Sai a lokacin kawai tunanina ya dawo jikina,a tsorace na juyo ina kallon shi.Farin dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekara ɗari da wasu ƴan kai. “Me ya kawo ki wannan wuri?” ya jefo min tambaya cikin wani yare wanda ba nawa ba amma tabbas na fahimci me ya ce. Samun bakina na yi da irin nasa Yaren na ce “ina ne nan?” “Keɓaɓiyar duniya ce wacce aka tanada domin ɓatattun ruhika waɗanda suka kasa gane inda za su dosa” ya bani amsa. “Kana nufin nan ba Zimbabwe ba ne?” Wani kallo yayi min na wani lokaci kafin yayi ɗan ƙyaci ya ce “wannan duniyar da taku abubuwa biyu ne mabanbanta,iya ruhi kawai ke shigowa a nan amma ke ban san ta ya aka kika zo nan ba alhalin babu wani tabo da ke nuna kin aikata wani zunubin” “Don Allah ka taimaka min na koma gidana” na faɗa ina hawaye. Ya ce “dole sai na san wanda ya turo ki izuwa nan” “Kamar yaya?” “Ina nufin matsafi,aljani ko bokan da ya cillo ki nan” “Deborah ce” Ina faɗar sunanta sai yanayin fuskarsa ya canza ya bayyanar da razani,amma ban san me yasa ba ya kwantar min da hankali wurin cewa “ko ma dai wace ce za ki fita in kin so sannan in kin yi niyya don babu abin da ya fi abin bautar Musulmi ƙarfi ” Wata ajiyar zuciya na sauke da tunanin a yau zan koma gida amma sai na ji yana mai ci gaba da cewa “za ki biyo ni mu je can gidana in kin huta sai na faɗa miki hanyoyin da za ki bi ki koma duniyarku” Duk da ban so haka ba amma na yi yadda ya ce ɗin na take masa baya har muka isa wani kogo,ko kafin na kai ga tambayarsa me za mu yi a nan sai na ga ya rikiɗe ya koma maciji .Na yi baya da sauri ina waro ido,yayin da shi kuma ya soma magana “kar ki ji tsoro domin ni ɗin aljani ne ba mutum ba,ki kama kogon gam za ki tsinci kanki a ciki” Na girgiza masa kai don ba zan yarda na shiga cikin wuri tare da aljani ba. “Ba ki da sauran lokaci ki yi sauri ki shiga na fara jin ƙamshin Deborah muddin ta tarar da ke nan to shi kenan fa ba zan iya yi miki komai ba” bai gama rufe bakinsa ba na soma jin sawun takunta,jiki na rawa na yi yadda ya ce kamar ƙyaftawar ido sai gani cikin kogon wanda ke ɗauke da abubuwan ban mamaki. Daga inda nake ciki na ji muryar Deborah na cewa “Baba tsoho ba ka ga wani ruhi yana shawagi ba ta nan wurin?” “Babu wani baƙon ruhi da ya shigo nan duk yau” ya bata amsa,sai ta yi gaba shi kuma ya shigo yana mai kallona kafin ya rikiɗe ya koma mutum.Wata step ya soma takawa ni ma na take masa baya har muka isa can saman ƙatuwar bishiyar,na waro ido ina kallon duniyarmu ya bil'adama. Ya tsinko wani fure ya murza shi yana mai furta wasu harufa sai ga gidana ya bayyana,haka yayi ta tafiya da tunanina har muka shiga babban falo Uncle Salem na gani a zaune duk hankalinsa a hargitse,yayin da bokanyar gidanmu ke zuga shi kan cewa babu wani ɓata da na yi akwai dai inda na je na ɓuya abin da ya fi ban mamaki jin wai tana faman cewa sati guda rabona da gida.Baba tsoho kamar ya san abin da ke raina sai cewa yayi “kin yi doguwar tafiya ne shi yasa,kika yi kwanakin nan” bai ida rufe baki ba duk komai ya ɓace daga idonmu wanda na lura yayi daidai ne da shigowar wata baƙuwar fuska a falon wacce alamu suka nuna kuma ƴar aiki ce.... [28/02 08:22] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲 MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta *FCWA*☀️ ________________________ 08 “Da matsala fa,ina ga Deborah ce ta ɗauki siffar bil'adama ta je gidanki da sunan ƴar aiki” Baba tsoho ya faɗa fuskarsa cike da damuwa. Cike da tashin hankali na ce “ta ya aka yi ka gane?” “Ita kaɗai ce mai ƙarfin ikon da za ta iya katse min dubana kai tsaye daga shigowarta,yanzu abin da ya kamata a yi ki je ki kwanta ki huta zan fara binciken hanyar da za ki bi ki koma gida kafin nan da wata uku” “Wata uku kuma? Ni da nake son na koma tun yau” na faɗa a rikice. Wani kallo yayi min kafin ya ce “kina tunanin tafiya daga ɓoyayyar duniya zuwa duniyar bil'adama abu ne mai sauƙi? To tsaya ki ji ita kanta Deborah farkon ranar da za ta keta hijabin da ke tsakaninmu da ku sai da ta ɗauki kusan shekara guda currr.In taƙaice miki zancen a ƙaramin misali sai kin yi tafiyar wata biyu kafin ki isa can,shi ma sai in na samu aljani mai matuƙar gudu” Wani gumi ne ya rufe ni nan take,a duniyarmu na sha jin cewa aljani na iya yin abu kamar ƙyaftawar ido amma a nan ga shi yana yi min zancen watanni biyu.Sam ban yarda da shi ba,don haka na ƙudurta a raina zan fita daga kogon nan na je na nemi hanyar da kaina. Kan wani gadon ganye na je na kwanta kamar yadda ya ce,na lumshe idona amma ba da niyyar yin bacci ba.Sai da na bari hankalinsa ya ɗauku kan aikin da yake yi jikin wani allon ƙarfe sai na yi saurin sauka daga gadon na je na dafa kogon nan take na tsinci kaina a fili. Gudu na soma ina waiwaiye har sai da na yi nisa sosai sannan na tsaya yin tafiya,cikin ikon Allah na hangi hanyoyi biyu daga nan ma ina tsinkayen kwalta.Na saki murmushi don kuwa na san in ba a duniyarmu ba babu inda ke da kwalta ina dab da bin ɗaya daga cikin hanyoyin kwatsam wani dodo ya bayyana a gabana.Tsoro ya kama ni ,ga shi ina son yin baya amma tamkar shukar da aka dasa haka na kasa motsi. “Barka da zuwa hanyar tsirar ruhin da ya ɓata” dodon ya faɗa yana wangale min baki nan muninsa ya ƙara bayyana,hanya ya bani da nufin na wuce.Abin da ya faɗa na maimaita a zuci sai na fahimci eh lalle ina kan hanyar daidai kenan, wannan karon ina cira ƙafata sai ta bar ƙasa haka na bi hanyar nan na soma tafiya duk yadda nake tsinkayen kwaltar amma na kasa kawowa a gare ta. Ga yunwa ga ƙishi ga gajiya,sai na ɗan sunkuya ina mai riƙe gwiwaina kamar mai yin sallah daidai nan idona yayi tozali da wani ɗan rame kamar gurbin tanda sai ruwa ke ɓulbulowa.Jikina har rawa yake wurin duƙawa na soma sha,sam ban farga ba na ji ni tsundum cikin ruwa na nitse ciki hatta kaina.Ina ɗaga kaina sai na ga wasu ƴan masu mugun kyawu suna wasar kos,yayin da kuma ɗaya daga cikinsu ke gefe tana saƙar hannu.Ido muka haɗa da ita sai ta sakar min murmushi kafin ta yi min alama da hannu na zo,ƙafafuwana a sanyaye na soma tafiya kwacal! Kwacal ! Cikin ruwan har na isa gare ta. Duk ƴan matan suka maido hankalinsu gare ni,suna masu karon baki wurin cewa “waooo! Bil'adama a duniyarmu?” “Ku yi min shuru ku ci gaba da wasarku,ke kuma zauna nan” ta dube ni tare da nuna min wani Kunkuru🐢 ni tsoronsa ma ya kama ni ganin yadda yake ziro kai yana maida shi kuma ciki, amma a haka na daure na zauna. Tsakiyar idona ta kafe da kallo har sai da na ji wani abu na huda fatata yana ratsa ɓargona,a nan take kuma tsikar jikina ta tashi duk gashin da ke hannuna yayi wani tsiri-tsiri da shi ban gama yin mamaki ba na ga wani abu ya soma fita daga hudodin yana zubewa... Ga waɗanda ke son shiga paid group sai su yi min magana kai tsaye ta WhatsApp numberta +22795045822. A page 10 zan dakata da free page in sha Allah [28/02 10:07] MRS SADAUKI: *FATALWAR DEBORAH*🐲 MAKARANTAR MATSAFA 2 ☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga malaman makaranta *FCWA*☀️ ________________________ 9_10 ★DEBORAH Ta daɗe tana kwaɗayin dawowa duniyar bil'adama tun shekaru ɗari da ashirin da suka gabata,sai dai ba ta samu ƙwaƙwaran dalilin da za ta faɗawa al'ummarta na ɓoyayyar duniya waɗanda take mulka ba.Sai a ranar da idonta suka yi gamdakatar da Uncle Salem ta ji wata hatsababiyar ƙaunarsa ta shiga ranta,ta yi ƙoƙarin danne muradinta sai dai hutar sonsa sai ƙara azalzala take yi a ranta.Yanayin yadda yake kula da Nafisa shine abin da take so tun lokacin da ta na raye,sai dai babu namijin da ke da jarumtar tunkararta da zancen so ballantana har ya kai ga ririta ta dukkan hatsabiban matsafa da bokaye tsoronta suke. A ranar da ta zo ta shigar da Uncle Salem faɗa da niyyar dama don ta kasance matarsa ta dare ne a duniyar mafarki,shi yasa ta sanar da shi cewa dukkan komai yana da farashi. A yanzu da ta faso duniyar bil'adama ba ta ga abin da zai mayar da ita ɓoyayyar duniya ba,farkon zuwanta a jikin Abidah ta yi wa baƙin ruhinta masauki.Cikin shu'umancin da ta saba yi ta juyar da kwanyar Mamar Sadauki ta saka mata kishin Nafisa,don sai in rikici ne ya shiga a tsakaninsu ne za ta samun yadda take so.Korar bayi masu yi wa Nafisa hidima duk tsarinta ne,kuma birninta ya cika duk an sallame su. A wannan ranar ce kuma ta bazama neman gangar jikin da za ta ɗauka,dole tana buƙatar na cikakkiyar mace mai hankali wannan yasa ta fita tsakar dare neman raunatacen ruhin da za ta nakasa ta ɗauke gangar jikin. Gida-gida ta dinga bi har Allah ya kai ta gidan Sakina ƙawar Nafisa,tun kallon farko ta gane ta.Tsaye ta yi tana kallon yadda Sakina ke zazzaga wa mijinta ruwan masifa tana cewa “ wallahi sai ka sake ni,ba zan zauna kullum kana tafiyarka daji kana barina a gida ba kamar wata mai gadi .Ka sake ni na je na auri wani wanda ya san mutumcina,ai MIJI GOMA BA UBA GOMA BA NE(littafin Sadiya AbdulRak kenan)” Cikin rarrashi ya ce “Sakina ki ajiye hankalinki da kyau ki yi wa kanki karatun tanutsu don kar ki je ki yi BONONO(Mom Afra) daga baya ki zo kina cizon yatsa” “Wa ya faɗa maka ƘWAƘWALWAR KIFI( Emilia) ce da ni da ban san abin da zai fishe ni dare ba?” Yayi ɗan murmushi don kwantar mata hankali ya ce “ ba ki san kusan duk kowanne gida NAUSHIN WUTA (Ameera Adam) mazajensu ke yi ba?” “Kar ka yi ɓarnar bakinka don wallahi ba zan yi BIYAYYA(Mai ƙosai) a gidan auren da ake cutata ba” ta yi furucin tana mai banko ƙofar ɗaki ta fito ba tare da ta yi la'akari da tsawon dare ba,FATALWAR DEBORAH wacce tun ɗazu take tsaye ƙiƙam ta yi wuf ta shige gangar jikin Sakina nan take kuma ta ɗauki controling tunaninta,cike da iya tsafi ta ƙarawa jiki da fuskar Sakina shekaru ta yadda ba kasafai za ka gane eh ita ce ba. Daga nan direct gidan Uncle Salem ta zo,ba ta wani sha wahalar fiddo Mamar Sadauki tsakar gida ba sai kuma ta fara buga ƙofa.Baiwar Allah Mama ta zo ta buɗe mata ,kawai sai ta fashe da kuka tana cewa ta taimaka mata ba ta da kowa.Abin ka da dama an juye ma kwanya haka Mama ta shigo da ita cikin gidan,a washegari kuma ta gabatar wa da Uncle Salem da ita a matsayin ƴar aiki,shi sam hankalinsa ba kwance ba saboda tashi da yayi ya ga Nafisa ba ta kan shimfiɗa har ɗakinta kuma ya je nan ma ba ta nan. ★Nafisa A hankali duk kambun maitar da ke jikina ya fice na dawo normal,sai dai kafin ma na kai ga yi mata godiya na ji tana cewa “zan ara miki ƙarfin ikona ta yadda za ki yaƙi abin da ya fito da ke daga duniyarki izuwa nan,ban son gardamar nan taki ki riƙe a barki ” ta faɗa tana mai yi min wani kallo na tsakiyar ido kafin ta ci gaba da cewa “ki faɗa min wacce siffa kika fi so? Ina nufin cikin dabbobi me kika fi so?” “Ban son ko ɗaya” na bata amsa. “Me kika fi tsoro to?” “Ƙadangare” na bata amsa. Sai ta saki wani murmushi kafin ta yi wa ƴan matan nan magana ta aike su wata maƙabarta tana son su tono mata kabarin wani su kawo mata shi. Babu jimawa suka je suka dawo ɗauke da wani abu cikin farin ƙyalle,kan teburi suka ajiye shi tare da buɗe shi.Gawar wani ƙadangare ce na gani har ya bushe kana iya ganin ƙasusuwansa. Wasu harufa ta fara lissafowa yayin da kuma ta saka ƴan matan suka yi wani cercle suka kewaye mu suka sa mu tsakiya,wani furucin su ma suke yi cikin salon ɗaga murya yayin da ita kuma nata take yinsa a sauti ƙasa-ƙasa “Lazaaar! Laaazaaar! Ōÿānīÿēmį ” a hankali na ga ƙadangaren yana dawowa ɗanye haɗi da ɗan kumbura nan take tsoro ya kama ni,daidai wannan gaɓar ne kuma ta kama yatsana ta tsaga shi jini ya soma tsirta yana sauka kan jikin ƙadangaren kai kace dama jinin nawa ne yake so nan take ya soma motsi yana buɗe bakinsa. Kalmar farko da ya furta ita ce “Gimbiya Sarah” a nan ne kuma na san sunanta,sai ta saki murmushi a lokaci guda kuma ita da ƙadangaren suka kalle ni. Tsoronsa nake ji sosai,don haka da sauri na je bayan Sarah na ɓuya amma ta wani matsa ta yadda dole dai na fuskanci ƙadangaren wanda ke kallona da ƙattin idonsa. “Shugabata!” ya furta,na waro ido jin wai ni ce shugabarsa. “Nafisa wannan shi ne Lazar,wata ƙawata ce da muka yi rayuwa da ita duniyar bil'adama ta ƙyarƙyare shi ta hanyar tsafi.Yana da matuƙar power na san zai taimaka miki sosai,abin da nake so da ke dai shine kawai kar ki yi gardama har mu kammala aikin nan kin ji ko?” Kai kawai na gyaɗa mata,sai ta ƙara bani umarnin na zauna.Jikina na ɗan rawa na yi zaune ,yatsana ta kamo wanda ta tsaga ɗazu.A gaban idona ba mafarki ba ta kamo shi Lazar ɗin ta saka min shi ta cikin ƴar tsakar da ko allura sai an yi da gaske ta wuce amma ƙaton Lazar ɗin ne ya shige tsaf,wani iri na ji bayan ta gama shigar da shi. “Ki lumshe idonki me kika gani?” Sarah ta faɗa . Na kuwa lumshe su nan na hangi FATALWAR DEBORAH tana shayar da Abidah wata gubar maita,so take a dole dai sai ta cutar da ƴata.Ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba,abin da na gani ɗin na sanar da Sarah ita kuma sai ta ce “ƙarfin ikon fatalwa yana ƙaruwa ne ta hanyar shan jini kawai, wannan dalilin yasa ta zaɓi Abidah matsayin wacce za ta dinga yi mata farautar rayukan mutane tana kamo kurwarsu ita kuma sai ta tsotse jinin.Yara da yawa Mayu na amfani da su don yi musu bauta,saboda shi yaro sam ba za a zarge shi ba amma hakan tana faruwa ne ga iyaye masu sakaci wurin yi wa ƴaƴansu addu'ar bayan asubah kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yayi mana umarni da mu dinga karanta musu wannan addu'ar *A'UZU BIKALMATILLAHI TAMMA,MIN KULLI SHAITANIN WA HAMMA,WA MIN KULLI AYNIN LAMMA* ” Idona ba su bar fitar da hawaye ba na ce “in kuma mutum bai iya karanta Larabcin ba?” Ta bani amsa da “ sai yayi da Hausa don Ubangiji yana jin kowanne Yare sannan yana amsar addu'ar bayinsa ” “To ki faɗa min da Hausar don halin yanzu ma ji nake kamar ban yi karatu ba” “Ina neman tsari tare da tawwasali da kyakkyawan zantukan na Ubangijina da ya kiyaye Ni daga sharrin dukkan dodanni,daga sharrin dukkan wasu dabbobi masu dafi da kuma sharrin dukkan wata ido mai cutar maita ” “Na gode! Yanzu wacce hanya zan bi na koma gida?” na tambaya,shuru ta ɗan yi kafin ta ce “gaskiya ba zan yi miki ƙarya ba,komarwaki ba yanzu ba sai dai kina iya balaguron ruhi ki je kuma ki dawo” Ban gane abin da take nufi ba,da na tambaye ta kuma sai ta ja ni muka wuce can gidansu.Sosai na yi mamakin yadda duniyar ƙasan ruwa ma take ɗauke da gidaje da kuma iyalai,iyayen Sarah suna da kirki sosai na samu tarba mai kyau na ci na sha sannan muka wuce ɗakinta mai ɗauke da gado da komai na buƙatar mace. Kasancewarmu cikin ruwa ba shi ke nufin ka yi wanka ba a'a,har da toilet ke da kwai da kuma abubuwan gyaran jiki.Haka na shiga na yi wanka ina ta mamakin duniyar,bayan na fito sosai na ƙara wani mamakin ganin kayan jikina a saman gado. “Ki yi sauri ki shirya domin ki ziyarci mijinki,in kin je ki sanar da shi duk abin da ya faru zai fahimce ki sannan ki aje hankali ki sama masa nutsuwa” Ni dai banda kallonta babu abin da nake yi,ban bari ta yi min kwalliya ba sai da na yi sallolina sannan na shirya cikin wata haɗaɗiyar rigar bacci.Turare na fesa sannan na ce “yanzu ya za a yi na je can ɗin?” “Kin fiya sauri kamar zawo,ki jira mana ina haɗa jirgin balaguron ne”Sarah ta faɗa tana mai zana gidan gizo-gizo,bayan ta gama ne ta umarce ni da na lumshe idona sannan na ratsa ta cikinsa haka kuwa aka yi. Ina yin yadda ta ce sai na tsinci kaina a gidan Uncle Salem,a cikin ɗakinsa ban bayyana ko ina ba sai a cikin madubi.Ya fito daga wanka ƙugunsa ɗaure da towel yana goge gashinsa da ɗan ƙarami,sai na ga ya fara buɗe ƙofofin hancinsa alamun ya ji ƙamshi jikina kenan .Na saki murmushi na ce “kawo na taimaka maka na tsane ma jikin” da sauri ya juyo muna kallon juna,kafin ya ce “Naf?” na yi murmushi na ce “ka taimaka min na fito” Hannunsa ya miƙo ni kuma na ɗora nawa ya jawo ni,na yi tsalle na ƙanƙame shi.Ya ce “ina jin ki a jikina amma na bar ganin ki” “Dama ba za ka iya ganina ba saboda ni ruhi ce” na basa amsa ina mai kai wa lips ɗinsa sumba,kan bed muka zube da dukkan alamu shi ma yayi kewata na san halin Uncle sosai muddin yana gida to kowanne dare sai mun kyautata shimfiɗar aurenmu.Cikin shauƙi da bege muka raya daren,ina dab da yi masa bayanin abin da ke faruwa na ji Sarah ta fizgo ruhina na koma can ƙasan ruwa.Na buɗe ido ina kallonta cike da takaici na ce “ya kuma za ki yi min haka?” Ita ma rai ɓace ta ce “kafin ki je sai da na faɗa miki da kin je za ki yi masa bayani amma kika fara da wata sumbatarsa,sannan tuni hasken alfijir ya keto inda na ƙara ko minti guda ne za a samu matsala don duniyar ruwa ba irin taku duniyar ba ce nan muna da ƙa'ida” tana gama faɗa ta fice ta bar ni nan. ★Gidan Uncle Salem Shi ɗin ya yarda da akwai ɓoyayyar duniya wannan yasa bai yi mamakin ziyarar da Nafisa ta kawo masa ba.Sosai ya ji daɗin kasancewa da ita don babu wani banbanci tsakanin mu'amalar ruhi da kuma ta gangar jiki, washegari cike da walwala ya fito kusan kowa ya ga canjin amma ba wanda ya san dalili hatta kuwa Deborah wacce take jin kwaɗayinta a kansa ya ƙaru. Yau girki na musamman ta yi wa ƴan gidan wanda ko kaɗan ba ta wani shan wahalar kunna gas,cikin iya tsafinta take yin komai.Da dare bayan ta faki idon mutane haka ta haura sama,ɗakin Nafisa ta je ta buɗe drowerta ta ɗauko kayanta sai ta shiga toilet ta tsoma kayan cikin ruwa.Da wannan ruwan ta yi amfani ta yi wanka,nan take jikinta ya fara rikiɗa ya koma irin na Nafisa.Cike da makirci ta shirya cikin wasu fitinanun kayan bacci ta fesa turare sannan ta nufi ɗakin Uncle Salem ta je haye bed ɗinsa,shi kuwa bawan Allah yana toilet yana wanka sai tunanin moments ɗinsu na jiya yake. Yana fitowa yau ma da ƙamshinta ya fara cin karo irin na jiya,ya washe baki yana kallonta jikinsa har rawa yake ya haura gadon yana mai cewa “Naf?” Ita kuwa FATALWAR DEBORAH wacce ke ɗauke da siffar Nafisa cike da zaƙuwa ta rungumo Uncle Salem.Daidai nan free page ya ida mai son ci gaba 500 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 *NB:* lokacin posting sai bayan shan ruwa in sha Allah. [28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 01 Ra'ayi riga in ji ƴan magana, wannan haka yake a lokacin da matasa sa'anina ke sha'awar fita waje domin yin dogon karatu tare da burace-buracen ababen ƙyalƙyalin duniya ni kuma shiga ƙauyuka ne ra'ayina domin koyar da yaran da ke cikin duhun jahilci.Sunana Nafisa,matashiyar budurwa ƴar kimanin shekara ashirin da biyu a duniya.Na fito gidan sarauta,a jinin masu izza da taƙamar dukiya sai dai ni sam ba wannan ne a gabana ba.Duk da na sha wahalar shawo kan mahaifina kan ya bar ni na yi karatun zama malamar makaranta amma kuma fafur ya hana ni fita aiki wanda hakan ba ƙaramar barazana ba ce da cikar burin nawa. Fuska shaɓe-shaɓe da hawaye na nufi ɗakinsa,shine kaɗai tilo da na san zai iya yin magana mahaifina yayi amanna da ita ba tare da gardama ba.Ko sallama ban yi ba ballantana neman izini kawai na tura ƙofar,kamar kullum yana zaune kan dadduma yana jan casbi.A gabansa na zube kamar raƙumar da ke jin ƙishi,ya ɗago fararen idonsa ya zube su a kaina kafin cikin tattausan furuci ya ce “Naf !” Baki na turo gaba idona na sake zubo da wasu sabbin hawayen. “ Yau kuma wa ya taɓa ki?” ya tambaye ni cikin nutsuwarsa wacce ke ƙara masa ƙwarjini. Cikin kuka na ce “Daddy ne wai ba zan yi aikin gwamnati ba” Yayi murmushin da ya bayyana fararen haƙoransa waɗanda kullum suke shan gugar asuwaki kafin ya ce “ki je zan yi masa magana” da sauri na girgiza masa kai na ce “ a'a Please uncle ka tashi mu tafi yanzu kafin masu hura wuta su ƙara masa ƙaimi” na faɗi haka ne saboda ahalin gidanmu suna da ɗagawa sosai ta yadda suke ganin kamar ƙasƙanci ne a ce jinin gidan ya je yana aikin gwamnati,aikin ma koyarwa. Ya buɗe baki zai yi magana na yi saurin kamo tafin hannunsa wanda yake lutuf da tsoka sai taushi kamar na mace,hannun nasa ya duba da sauri na sake shi saboda ba tun yau ba ya yi min hani da hakan ba wai iya gare shi ba kawai a'a hatta ƙannaina maza ya hana ni raɓar su ko kuma taɓawa a tsakaninmu. Na sunne kai wasu hawayen na sake surnano min suna ɗiga kan farin hijabina. “Nafisatu?” ya kira ni cikin wani salo,ba tare da na ɗago ba na ce “ na'am uncle” “Me yasa ra'ayinki ya banbanta da sauran danginki? Me yasa kike son yin aiki alhalin mahaifanki sun tanadar miki komai na rayuwa?” Na ɗago na dube shi kafin na ce “ uncle kai ma ba ka son na yi wannan aikin jahadin na shiga ƙauyuka ina wayar da kan al'umma? Saboda me uncle? Kawai don iyayena suna masu arziki shi kenan sai na yi kwance na dogara da dukiyarsu? Me yasa ni ba zan yi aiki ba?” “ Saboda ke mace ce!” ya bani amsa yana kallon idona,ji na yi kamar ya watsa min ruwa zafi kawai sai na tashi na fita a guje ina gwanjin kuka.Ina shiga babban falonmu duk sai na tarar da ƴan uwana kuwa suna ta cece-kuce akan maganar,ɗakina na wuce direct na haye gado na kwanta rub da ciki amma abin mamaki sai na ji tamkar kan cinyar mutum ne kaina yake amma sam ban bai wa hakan muhimmancin ba na ci gaba da rera kukana,har na fi jin haushin rashin goyon bayan Uncle Salem kan na Daddyna.A hankali na soma jin ana shafar gashin kaina wanda ke luluɓe da hijabina,ido na soma lumshewa ba tare da na shirya ba yayin da kuma na soma sauke numfashi akai-akai.Ban sani ba ko na shiga duniyar mafarki ne ko kuwa zahiri ne amma sai na tsinci muryar wata dattijuwa na yi min gatana haɗi da bani tarihin ababen tsoro kamar yadda na fi ƙaunar kallon horror film. ★A can ɓangaren Uncle Salem kuwa Nafisa na fita da gudu yayi saurin tattare littafansa kafin ya gyara zaman hiramin kansa ya fito.Direct ƙofar da za ta sada ka da babban falon ya nufa bakinsa ɗauke da sallama,tsit duk falon ya ɗauka kafin duk su yi ƙasa da idanunsu saboda yadda yake da matuƙar muhimmancin da kuma girma a idonsu.Cike da girmamawa suka soma gaishe shi “ Barka da fitowa Daddy ƙarami“ domin haka suke kiransa in ka fidda Nafisa da take ce masa Uncle ita ma ɗin shine da kansa ya koyar mata da hakan. “Fatan dai ba ƙara ta ba aka kai wurinka,a toh don na san ba kasafai za a gan ka a nan ba” cewar Daddy yana ɗan murmushi yana kallon babban abokinsa,amininsa kuma ɗan uwansa.Uncle Salem ya ce “tun da ma ka sani ai shi kenan sai a fara shirya mata abubuwan da za ta buƙata in ta je can” Daddy ya ɗan nisa yana kallon yaran wurin duk sai suka tashi suka kama gabansu,sai a lokacin kuma Uncle Salem ya zauna suna fuskantar juna. Duk shuru suka yi na wani ɗan lokaci kafin Daddy ya ce “ ba wai yadda kake tunani ba ne aboki,ina da dalili na daban da yasa ban so Nafisa ta yi nisa da gida” Uncle Salem ya murmusa ya ce “tun muna makaranta ake faɗar wannan kalmar akan kana da dalilin ƙin yin wani abu amma har yanzu ba ka taɓa faɗa min mene ne dalilin ba.Abdul Hameed ka sani cewa su yara da kake gani sun fi son bin zaɓinsu kan na iyayensu,kuma kai ma in ba ka manta ba...” sai kuma yayi shuru. Yanayin fuskar Daddy ta ɗan sauya kafin ya ce “babu damuwa zan bari ta je ɗin, Allah ya bada sa'a ya kuma tsare ta akan abin da nake tsoron faruwar” da “amen“ kawai Uncle Salem ya amsa kafin ya miƙe tsammm ya nufi ɗakin Nafisa,ya tura ƙofa tare da yin sallama sai kuma yayi tsaye cak yana buɗe ƙofofin hancinsa saboda kalar wani ƙamshi da ya dake shi da bai taɓa jin irinsa a wannan duniyar ba.... [28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 02 Tsaye yayi yana kallon yadda take bacci tana wani taɓe baki kamar mai kuka yayin da goshinta ke fitar da gumi.Ya furzar da wani huci kafin ya ƙarasa ya zauna bakin bed ɗin,a hankali ya cire mata hijabin nata wanda ya ɗan jiƙe saboda zufa.Sumar kanta wacce take baƙar ƙirin ya soma shafawa yana tofe ta da addu'a,a hankali ta soma sauke ajiyar zuciya tana wani motsa idonta kamar mai son buɗe su. Kamar wanda ke wasa da maciji haka ya soma shafa farar fatar fuskarta wacce ta yi ɗan ja saboda kukan da ta yi.Wata irin azababiyar ƙaunarta ce yake jin tana bijiro masa,ji yake tamkar ya ɗauke ta ya haɗiye tsabar so. Sam bai san abokin nasa ya shigo ba don ya lula sosai a duniyar tunanin muradun ruhinsa,sai jin saukar muryarsa yayi “ sai yaushe ne za ka sanar da ita ɓoyayyen sirrin da ka binne abinka?” Uncle Salem yayi saurin ɗagowa ya dubi Daddy ya saki ɗan murmushin da ya zame masa jiki kafin ya ce “ har yanzu Naf yarinya ce aboki,zan ƙara mata lokaci ” sai kuma ya mayar da duban nasa ga fuskarta a iya kallon da yake jifar ta da shi ya isa ya fallasa ma sirrin da ƙunshe a zuciyarsa. “ Shekarunta ashirin har da biyu fa,lokaci na ƙurewa girma na sake zuwar ma amma har yanzu ba ka ajiye iyali ba aboki” Daddy ya faɗa cikin rashin jin daɗi. “ Shi aure ai ba sauri yake so ba,a'a fahimtar juna aboki.Ka yi tunanin yadda Naf za ta ɗauki lamarin ne in ta ji cewa ni mijinta ne alhalin a uba ta ɗauke ni?” Daddy yayi murmushi kafin ya ce “ to ai kun fi kusa,ban iya na sani” Uncle Salem na shirin yin magana aka shigo haɗi da sallama,Ammy ce hannunta riƙe da kofin ruwa.A mutumce ta gaishe da Uncle Salem wanda a girme ya girme mata sannan ta dubi mijinta hasken idaniyarta ta ce “ ga maganinta yau ba ta sha ba sam” ya karɓa ita kuma sai ta fita. Kan dakalin gado Daddy ya ajiye maganin yana mai kallon Nafisar wacce har zuwa yanzu take baccinta yayin da kuma hannun Uncle ɗinta ke kan sumarta. “ Aboki me kake ɓoye min dangane da Naf?” yayi tambayar cike da kulawa. A ɗan rikice Daddy ya ce “ no babu komai zan je na duba wasu takardu in ta tashi ka bata maganin” yana gama faɗa ya fice,shi kuwa Uncle Salem kai ya girgiza tun suna yara suke tare amma har izuwa yanzu bai san dalilin da yasa abokin nasa ke ɓoye masa wani babban sirri da ke ɗawainiya da rayuwarsa.Tun da Nafisa ta soma tasowa yake lura da yadda hankalinsa kocokwam ke kanta hatta makaranta in ta je ya dinga kiran waya kenan yana tambayar labarinta,yana ɗaya daga cikin abin da yasa kuma ya basa aurenta tun ba ta san kanta ba amma har yau ya ƙi sanar da shi mene ne sirrin. Ganin kamar baccin nata irin wancan ne da ta saba yi ,sai Uncle Salem ya ɗauki kofin maganin ya cika bakinsa da shi kafin ya taɓe bakinta yana ɗura mata shi kamar yadda tantabaru ke ciyar da junansu,a hankali kuma take haɗiye ruwan maganin da shi ne ya haɗa mata shi a haka har ta shanye shi tasss.Da ya kai ƙarshe sai da ya ɗan lashe mata lips kafin ya miƙe ya fita,sashensa ya nufa ya rage kayan jikinsa yayi wanka ya fito ya shafa turare kawai sai ya ɗauki system ɗinsa ya soma aiki yana duba saƙonnin sojawan da shine ya tura su mission a daji.Reppot ne iri-iri wasu na murna wasu na jimame,tuni kansa ya soma yin hayaƙi yana jin cewa da buƙatar ya je can ɗin da bada wata sabuwar atisaye. ★ NAFISA Ban san iya lokacin da na ɗauka ina bacci ba,ko da na tashi da ƙamshin turaren Uncle Salem na soma cin karo wanda ya game ko ina na ɗakin.Na turo baki gaba kafin na dubi hijabina wanda na san da shi ne ya cire min shi ko shakka babu.Wanka na shiga,bayan na fito na yi sallar azahar don sallah na ɗaya daga cikin abin da na fi so a kaf cikin abubuwan ibada ita da azumi wannan kuma horarwa Uncle Salem ce tun ina ƴar shekara sha uku yake saka ni yin azumin Litinin da Alhamis,tun ina kukan yunwa har na kai na saba. Ina zaune kan dadduma Ammy ta shigo,“yawwa kin sha maganin ashe ” shi ne abin da ta fara cewa. Shiru na yi ina tunanin yaushe na sha magani amma ban tuna ba,amma tabbas da na tashi na ji bakina na zaƙin zuma.Na sake turo baki don kuwa tuni kwanyata ta hasaso min ina baccin ya bani magani. “ Ammy ni yunwa nake ji” na faɗa kamar zan yi kuka,“ Sai ki je ki ci mana,ki taso ki kaiwa Daddy ƙarami abincinsa” ta faɗa tare da ficewa .Ina kukan sangarta na fita zuwa falo,cikin gunguni nake cewa Ammy “ duk ga ƴan aiki nan amma shine ba za su kai masa ba sai ni ” Ta dube ni da mamaki kafin ta ce “ au! Dama can ƴan aiki ke kai masa abinci?” Ba tare da na ce komai ba na nufi dianing na ɗauki ƙaton tray ɗin da aka jera komai nasa,na ɗauka tare da fita ina tafe ina turo baki har na isa sashen nasa dakyar na lalubo sallama can ƙasan maƙoshi na yi. Bai amsa ba sai ɗagowa da yayi yana kallona kafin kuma ya mayar da dubansa kan system ɗinsa.Hakan yasa na ji haushi na ajiye tray kan table har na juya zan tafi na ji ya ce “ Naf!” na tsaya cak ba tare da na juyo ba ina jiran abin da zai ce sai kawai na ji tsayuwarsa a bayana.Da sauri na juyo muna fuskantar juna,idona tab tsoro nake kallon nasa da nake hango tsantsar ɓacin rai a cikinsu. “ Ka yi haƙuri!” na faɗa murya na ɗan rawa.Bai ce komai ba ya kamo hannuna ya zauna da ni kan kujera,“ ki zuba abinci ki ci” shi ne abin da ya faɗa sam babu wasa a maganar sai ya je ya zauna ya ci gaba da aikinsa. Ni kuwa kallo na soma ƙarewa kyakkyawar fuskarsa mai cike da yalwatacen saje da ɗan madaidaicin gemu,kan jajayen laɓansa na tsayar da ƙwayar idona waɗanda ke yin furucin da babu sauti da alamu wani abu yake karantawa. Tamkar wacce aka yi wa dole haka na ƙanƙance ido ina karanta bakin nasa,na waro ido jin tamkar har da muryarsa ke yi min raɗa a kunne tana sanar da ni abin da yake cewa ɗin. “ Ba ki ji abin da na ce ba?” ya jefo min tambayar,da sauri na mayar da hankali kan abincin haka na zuba na soma ci lokaci-lokaci ina satar kallonsa har na gama. “ Kawo min wanda kika rage ɗin” ya faɗa ,sai na dubi plate ɗin yadda duk abincin ke cakule saboda miya da na zuba dayawa don ina son haka. “ Uncle bari na zuba ma wani” na faɗa tare da ɗaukar wani sabon plate ɗin. Ya ce “ wanda kika rage nake so” Na ɗan ɓata fuska cike da kunya na ɗauka na kai masa,ya amsa ya ajiye shi kan system ɗin kafin ya soma ci hankali kwance . “ Uncle wannan wane ne?” na tambaya ganin wani matashin soja baƙi an naɗe kansa da bandeji. “ Wani ne” ya bani amsa,da ido na ƙara kafe hoton don kuwa ni dai yayi min kyau sosai har ban san lokacin da na ce “ yana da kyau sos...” yadda Uncle ya ƙware ya shiga yin tari ya hana ni ƙarasa abin da nake son faɗa,da sauri na je na kawo masa ruwa ya karɓa tare da rufe system ɗin ya soma sha kafin kuma ya miƙa min kofin ya je ya kwanta kan kujera mai zaman mutum uku yana wani jan numfashi tuni na tsure wuri guda ina kallonsa.... [28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 03 Jikina na ɗan rawa na isa gare shi ina mai zube wa ƙasa daidai kusan kansa na ce “ Uncle?” shuru yayi min bai ce komai ba haka ya ƙi buɗe idonsa,hakan sam ba ƙaramar barazana ba ce a gare ni don gani nake na yi masa laifi ne har ya sa shi ƙwarewa amma ban san taƙamaimai mene ne ba. “ Uncle?” na ƙara faɗa wannan karon ina mai kai hannu ina gwale fatar idonsa a dole so nake ya buɗe su ya kalle ni,na kuwa ci nasara ya buɗe su sai dai yadda suka yi ja sosai har sai da na ji tsoro na ɗan ja baya. Murya a disashe kamar wanda ransa zai fita yana kokowa da numfashinsa ya ce “ Nafisa me na faɗa miki? Ban ce kar na saki ko da wasa kin ce wani namiji yana da kyau ko kuma ki kalle shi ba?” Na ɗan ja ajiyar zuciya tare da matsowa na ce “ ka yi haƙuri Uncle ba zan sake ba,amma saboda me Uncle? Ka ga fa duk ƙawayena suna da samari ni amma ka hana ni kuma...kuma kamar mai baƙin jini maza sun tsane ni ” shaaa hawaye suka zubo min tuna yadda ko a makaranta ƴan ajinmu ba su shiga duk abin da ya shafe ni,kusan kuma malamanmu maza ma haka ba kasafai suke saka ni yin wani abu ba,in an zo nan ta wurin ƙannaina da kuma mazan da suka zo karatu a gidanmu su ma duk hakan ce ke faruwa. Ba tare da ya ce min komai ba ya tashi zaune haɗi da ɗan duƙewa ya dafe saitin zuciyarsa,ina ganin haka sai na miƙe da sauri har ina tuntuɓe na nufi bedroom ɗinsa na ɗauko masa maganinsa.Na cika kofi da ruwa tare da ɓallo ƙwaya biyu na miƙa masa ya karɓa tare da sha,cikin ƙanƙanin lokaci ya soma yin wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ ki je ki haɗa kayanki,zuwa jibi sai na kai ki can ƙauyen da za ki koya” Duk ƙuncin da ya cunkushe min zuciya ne ya tafi ban san lokacin da ƙawa zuci ya ja ni ba kawai na rungume shi ina cewa “ na gode sosai my Uncle,kenan har ka yi magana da Daddy ya amince wayyy!” na yi ihun murna ina jijiga bayan Uncle da na rungume tsam a ƙirjina kafin kuma na sake shi da gudu na bar falon. Ina shiga ɗaki na tarar da family na cin abinci,ɗakina na nufa na shiga sauko da akwatina ko taimakon masu aiki ban nema ba na soma shirya kayana ina yi ina murmushi ina jin daɗi na luluɓe min ruhi.Sai hoton kaina nake gani a cikin aji ina koyar da darasi wa ɗalibaina,ban zauna ba sai na haɗa duk kayana na jiki da kuma jaka da takalma. Takardu da littafaina ma trolly daban na ware musu kafin na miƙe ina yawo cikin ɗaki ina magana ni ɗaya kamar irin yadda malamai ke yi.A hankali na soma jin ciwon kan da ya zame min aboki tun na ƙurciya na ziyartata,tun ina daurewa har na kai na kasa jurewa na haye bed na kwanta.Mafarkin da na jima ban yi ba tun shekaru kusan uku shine na soma yi kamar ana jirana. Tsaye nake kan ƙafafuna na mage ina juya idona masu matuƙar haske da hange nesa tamkar na Alhuduhudu. Manyan-manyan dabbobin daji ne a tsaye a gabana suna buɗe min bakunansu masu manyan haƙora yayin da ni kuma ke ankare da kowanne daga cikinsu kafin mu soma yin dambe ina jibgarsu duk na yi musu jina-jina da jini kafin wata halitta mai siffar babban sauro ta caka min bakinta daidai cikina .Azabar da ta ratsa ni ce yasa na saki wani razananen ihu,daidai nan na farka sai dai abin mamaki daidai wurin da aka cake ni ɗin har a zahiri ciwo yake yi min. “ Lafiya Nafi?” Ammy ta faɗa wacce ta shigo yanzu hankali tashe,ido na soma juyawa amma na kasa faɗa mata don ko na ce zan faɗi abin da na gani a mafarki kamar abin tsayi sam bakina ba zai iya furtawa ba. Hawaye kawai nake yi,sai shi ma Daddy ya shigo yana tambayar lafiya.Kai kawai na girgiza masa ,ya zo ya kamo hannuna ya ce “ kina ji na Nafisa faɗa min mafarkin me kika yi?” da sauri na janye hannuna daga cikin nasa,na diro daga kan bed na nufi ƙofa. Sai kuma na yi tsaye ganin Uncle shi kuma zai shigowa gemunsa na ɗigar da ruwa da alamu alwala ce yayi. Haɓata ya tallabo ta yadda zai iya kallon fuskata da kyau ,tsakiyar idona ya dinga duba yana wani motsa baki kafin ya ce “kin kuwa yi Azkhar yau?” Idona na soma juyawa ina son kauce kallon nasa da ba ƙaramin takura min suke ba,sam babu daɗi ji nake kamar yana zuƙo raina ne. “ Kin yi Azkhar na ce?” ya sake tambayata. Kai na girgiza alamun a'a,don kuwa ban yi saboda tun asubah na samu saƙon cewa sunana ya fito a jerin waɗanda za su je bautar ƙasa wannan zumuɗin ya shagaltar da ni yin Azkhar kamar yadda na saba. Ya sake ni kafin ya ce “ biyo ni” sai ya juya,haka na take masa baya ina waiwayen su Daddy muka fita zuwa can sashensa da yake waje. Ɗakin Uncle Salem ciki biyu ne da falo,ɗakinsa guda na bacci guda kuma wanda yake zuba kayan maganin aljanu na ruƙiya.Direct ɗayan ɗakin muka shiga,kaina ne ya juya da na shaƙi warin magani iri-iri yayin da gefen cikina daidai inda aka soke ni ya soma motsi har sai da na danne wurin. “ Zauna a nan” Uncle ya nuna min wata doguwar kujera,babu muso sai na zauna ɗin.Wata kwalba ya ɗauko tare da zuwa kusa da ni ya zauna kafin ya buɗe ta,tun kafin ya ce min na sha na soma hawaye don ni kaɗai na san irin abin da nake ji a duk lokacin da ya bani ire-iren maganin nan. Bakina ya taɓe tare da ɗura min maganin,jikina ya ɗauki rawa kafin cikin fitar hayyaci na soma basa labarin mafarkin da na yi tiryen-tiryen.Kwantar da ni yayi yana mai jan doguwar rigar jikina sama,da sauri na rumtse ido lokacin da ya janye hannuna ya ɗora nasa a daidai wurin da ake ta yi min motsi. Teburin da ke ɗauke da tarkacen da shi kaɗai ya san na mene ne ya jawo,ina ji ina gani da raina Uncle Salem ya soma tsatsaga fatata da reza.Banda wani zaɓi banda hawaye don tuni maganin da ya bani ya kashe min dukkan jijiyoyin jiki sai kaina da ke faman juyi tamkar an jefa ƙwarya a ruwa. Wata kwalba ya ɗora daidai wurin ya soma tatsar jinina har ƙarar fitarsa kake ji,kamar minti biyu kafin ya cire kwalbar ya ajiye ta kan teburi.Wani magani ya shafa min a daidai ciwon mai bala'in zafi,har sai da raina ya kusa fita kafin da sauri ya cika bakinsa da wasu ruwa ya zo ya fara shayar da ni su.Duk ɗigo ɗaya na ruwan da zan sha to tamkar ana warware azabar da yake jikina ne , wannan yasa nake shan maganin cike da zalamar da ta haifar min da soma shan yawunsa da kuma laɓansa. Jikin Uncle Salem ne ya ɗauki wata irin rawa jin Naf ɗinsa na sumbatarsa kamar za ta cinye leɓensa,duk wani tsohon feeling nasa da yake faman yin ƙasa da shi a kowacce safiya ya soma taso masa.A daidai gaɓar da ya soma mayar mata da martani kuma tuni bacci ya ɗauke ta,idonsa na fitar da wasu irin hawayen jaraba ya soma sunsunar wuyanta yana jin tamkar ya mayar da ita cikakkiyar mace ko zai samu salamar ruhi. Dakyar ya rareashi kansa ya janye daga jikinta,daɓas ya zauna yana duban yadda take baccin wahala . Ƙonannen jinin mai tattare da guba yayi baƙi ƙirin a cikin kwalba,sai ya ɗauke shi ya je ya zubar toilet ya wanke kwalbar. Sai da ya je ya sake wata alwala sannan ya nufi masjid,a can ya samu Daddy bayan sun yi sallar sun fito ne Uncle Salem ya dubi abokin nasa ya ce “ Abdul Hameed ban san me yasa ka zaɓi ka ɓoye min rufaffen sirrin Nafisa ba,amma hakan bai da wani amfani don kusan na fahimci matsalar junun da ke jikinta ya samo asali ne daga can tushe ba wai gamo ta yi da su ba” Cak Daddy ya tsaya yana kallonsa, Uncle Salem ya jinjina masa kai ya ce “ tabbas ko yau sun ziyarce ta,saboda sakacin addu'ar da ba ta yi ba” Daddy ya ce “ mu je can gida zan yi ma bayani” haka suka wuce suka isa,a keɓaɓen falon Daddy duk suka zauna tare da yin shuru Uncle Salem ya matsu ya ji labarin yayin da shi kuma Daddy ya rasa ta ina zai soma.Can ya nisa tare da furzar da huci kafin ya ce “ to da farko dai kamar yadda na faɗa ma ni ɗana ga sarauniya Ayodele Ayush,kafin zuwan Musulunci a Victoria Falls suna bautar ababen bauta iri-iri ,yin tsafi kuma sai ya zama adon garin.Sai dai sannu a hankali duk komai ya canza saboda yadda mahaifina sarki Ameer ya taka muhimmiyar rawa ganin ya kawar da duk wani fasadi sai dai kash zuwana duniya kuma aka tsiro da wasu sabbin canfi wai alamomi sun nuna za a sake yin maimaici wato daga cikin tsatsona za a samu wacce za ta jagoranci mulkin ƙasar.Amma tabbas ni ba magajin sarki ba ne,sosai na ji tsoro da jin haka don tamkar karatu haka ake biya min maganar nan har na mallaki hankalin kaina” Uncle Salem yayi saurin katse shi da cewa “ haba aboki ta ya za ka yarda da wani canfi?” Daddy yayi murmushi wanda ya fi kuka ciwo kafin ya ce “ dole na yarda mana,duba da tun ina ɗan shekara ashirin a duniya na ajiye iyali saboda yadda kullum nake kasa bacci ina harin neman abokiyar rayuwa wacce zan jefar wa da ƙwan haihuwar shugabar gobe ko zan samu sukuni ” Uncle Salem ya ce “ kana nufin wai Naf?” Daddy ya jinjina kai ya ce “aboki tun lokacin da na yi aure zan ce ma wannan larurar da ka san ni da ita ta mugun feeling ta kau,shi ma tun a daren farkonmu.Sannan kana dai ganin yadda lamarin aurena ya kasance a sirrance sai daga baya iyayena suka sani,har bisa yanzu sarki fushi yake da ni saboda na ƙi yarda na zauna a can Victoria Falls ni kuma ina gujewa Nafisa ƙalubalen da za ta fuskanta ne in ta zama shugaba” “To amma mene yake baka tabbacin cewa hakan za ta kasance?” Uncle Salem ya tambaya . Daddy ya ce “ saboda kama take da wata goggon Mamana ita ce mace ta biyu da ta mulki Victoria,to yadda ka ga Nafisa ita ma haka take kai kace tsaga kara ne aka yi.Hakan kuma babbar matsala ce domin zai iya kasancewa ita ta dawo duniyar nan a gangar jikin Nafisa ” “ Wai ko sarauniya Deborat?” Uncle Salem ya tambaya,don kuwa ita ɗin ba ɓoyayya ba ce a duniyar nan duk kusan labarinta ya karaɗe ƙasashen duniya saboda shahararta wurin iya yin tsafi,sai dai ko kafin Daddy ya ce wani abu tuni tv ɗin da ke manne jikin bango ta soma yin wata tsaga “ƙiiiii!” kafin kuma ta faɗo ga ƙasa ,sai iska kuma mai ƙarfi wacce ta haifar da fashewa ƙwan lantarki ji kake ɗuuu haskensa ya ɗauke sai labulaye suka soma tashi sama suna wulwulwul.... [28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 04 A cikin duhun ɗakin ne Daddy da Uncle Salem suka hango wata mace sanye da fararen kaya wanda ko tantama babu likafani ne.A tsaye take jikin window sam ƙafafunta ba su taɓa ƙasa ba sai wani lilo suke kamar wacce aka rataye,farin gashin kanta kuwa sai yin sama yake iska na naɗa shi. Cikin muryarta wacce kana ji ka san ba ta ɗan adam ba ce ta soma yin magana,“ ko kai ko abokinka babu wanda ya isa ya dakatar da ni daga yunƙurin da nake,Yarima Abdul Hameed ban sani ba ko ka san cewa sunan Deborat ya haramta ga duk wanda yayi hijira ya bar gidansu domin guje abubuwan da allolinmu za su zartar,ka sani cewa Nafisa jaruma ce ba mu zaɓe ta ba sai da sanin za ta iya.Sannan ka godewa Allah da ya kasance aikin alkhairi ne za ta gudanar ba wai na cutar da al'umma ba,sannan kai kuma da kake ta ƙoƙarin dakatar da mu ziyartar ta ka sani akwai lokacin da maganinka ba zai yi aiki a jikinta ba don haka gara ka baiwa kanka lafiya ka bar matarka ta yi aikinta yadda ya kamata.A tunaninka hatta auren naku ba mu sani ba? Mun sani sarai saboda kai ne za ka yi jinyarta a lokacin da ta kammala aikinta na farautar azzalumai ” tana gama faɗa kawai ta bi ta window ta fita yayin da kuma komai ya dawo normal hatta hasken ƙwan lantarki rasss ya koma yana yi . Daddy da Uncle Salem sai suka fara ƴar kallon-kallon ba tare da sun cewa juna komai ba. Can Daddy ya kasa yin shuru ya ce “ aboki ka yarda da fatalwa?” “ Na yarda mana saboda ni ma ita ce ta raine ni” Uncle Salem ya basa amsa . “ Ban gane ba” “ Eh kamar yadda na faɗa ma ni kaina ban san iyayena ba domin a titi aka tsince ni to Inna Delu ta raine ni ta bani dukkan tarbiyya da kuma kulawa ta uwa,sai bayan na mallaki hankalin kaina ne ta sanar da ni ita wace ce saboda za ta koma makwancinta“ Daddy ya ce “ wai kana nufin dama Inna fatalwa ce?” “ Eh sosai ! Bari na je na duba na ga ko Naf ta tashi” ya faɗa tare da miƙewa ya fita ,hankalinsa da tunaninsa na kan fatalwar Deborat wacce kusan duk dare Inna Delu na yi masa gatanarta. Ko da ya shiga ɗaki ya tarar Nafisa na ta yin baccin gajiya ,ya dubi agogo ya ga lokaci sai tafiya yake ga shi kuma ba ta yi sallah ba.Sam bai son ya tashe ta amma sanin sallar asar ma nada ƙurarren lokaci yasa ya soma shafar fuskarta da tafin hannunsa mai taushi da sanyi. Cikin bacci na soma jin sanyi na ratsa min kumatu,ga taushi kamar auduga.A hankali na ware idona na sauke su kan kyakkyawar fuskarsa,ban ida warkatsewa ba ya ce “ lokacin sallah Naf” Jin ya ambaci sallah na yi saurin tashi hankali tashe don na tsani na makara,ya ɗan ja da baya yana mai ci gaba da kallona kafin kuma ya fita.Ni ma fitowa na yi na wuce can sashenmu sai da na fara gabatar da sallar sannan na yi wanka na saka riga doguwa marar hannu na ɗaura kallabinta sannan na fita. Yunwa nake ji hakan yasa direct kitchen na shiga,Ammy ce da A'i mai aiki ke ta faman yin girki da dukkan alamu yau sarautar ta Daddy ta motsa shi yasa Ammy ke aikin da kanta. “Yunwa nake ji” na faɗa kamar zan yi kuka,A'i ta yi dariya ta ce “ oh shagwaɓarki Nafisa ko auta albarka ” Ammy ta ce “ bar ni da ita dai ta ci gaba da sakalcin in ta je can ƙauyen ai na ga wacce za ta yi wa” Kamar wacce suka yi wa allurar zaburar wa kuwa haka na wani kwanto jikin A'i mai aiki wacce nake kira da Inna na ce “ ai tare da Innarmu zan tafi ita za ta dinga kula da ni,kafin na dawo ta yi min girki mai daɗi” A'i ta washe baki don sosai take jin daɗin yadda Nafisa ta ɗauke ta tamkar Kakarta sam ba ta nuna cewa ita ke ƙasa gare ta,haka kuma ita ce ta raine ta tun tana cikin tsumman goyo ko aiki za ta yi haka take goye ta in kuma ka ga sun rabu to Uncle Salem ne ke gidan. “ Ki ma cire wannan a ranki don Inna A'i ba za ta bi ki ba” cewar Ammy tana mai zuba min kunun gyaɗa a kofi. Na ce “ wai Innarmu ba za ki je ba?” A'i ta ce “ ke wasa take yi miki fa,tuni ai na haɗa komatsaina na ƙulle a buhu” cike da jin daɗi na ɗauki kofin kunun gyaɗana na fito falo na zauna,tv na kunna na saka horror film ina kallo ina sha sam ban jin tsoron abubuwan da ake nunawa wani sa'in ma ji nake tamkar ƴan uwana ne. Ƙamshin turarensa ne ya fara yi min maraba kafin shi ya shigo,na ɗaga kai ina kallonsa .Sanye yake cikin kakin soja sun yi bala'in yi masa kyau sai dai ya aske gemunsa da sajensa,da sauri na ajiye kofin hannuna ina turo baki ina kallonsa tuni kuwa ya fahimci dalili don tun ina yarinya nake faɗa masa ina son saje,sannan Inna A'i ta taɓa faɗa min ranar farko da na fara ganin Uncle Salem ya cire sage da gemu haka na yi ta kuka ina ɓata fuska sannan kuma na ƙi yarda da shi . Da sauri na miƙe zan bar wurin yayi saurin kamo tsintsiyar hannuna yana mai cewa “ oyaaa Naf ɗin Uncle kar ki yi fushi zo ki shanyen kununki ki zo mu je na yi miki shopping ” jin ya ambaci shopping yasa na juyo don na san duk cikin shirye-shiryen tafiyata ne. Na sake turo baki a karo na biyu kafin na ce “amma shine ka aske ...” yayi wani murmushi mai sauti yana cewa “ zai fito ai,kin ga kar ki yi fushi da Uncle ɗinki” sai ya zaunar da ni tare da ɗaukar kofin ya ci gaba da bani kunun har na shanye kafin ya ce “ je ki canza kaya ki zo mu wuce” Da murna na koma ɗakina,sai dai ban canza kayan ba kawai dai na zumbulo dogon hijabi har ƙasa.Ina fitowa Uncle Salem ya matso kusa da ni kafin ya ce “ ki canza kaya Naf ” da mamaki na dube shi,ko ta ya aka yi ya gane ban canza ba. Na marairaice fuska na ce “ Please mu tafi kar dare yayi” ya ɓata rai yana kallon ƙirjina,sai na turo baki na koma ɗaki na je gaban madubi na yi tsaye ashe rabon a yi ne ya kai ni don kuwa ina tsaka da tantance yadda saka hijabin bai ɓoye ainihin shap ɗin jikina ba sai na hango wata farar mata tana saka min abubuwa a jaka,ta yi zaune daram kan gadona.Na waiga da sauri sai na ga wayam,ina maida dubana kan madubi daidai nan ta bi ta window ta fice.Da mugun sauri na je bakin windown sai na gan ta a buɗe alhalin kullum a rufe take ban barinta a buɗe . “ Naf wai har yanzu ba ki shirya ba?” na ji muryar Uncle Salem a bayana,na juyo da sauri ina cewa “ yanzu zan shirya“ sai kuma na ga yana buɗe ƙofofin hancinsa ya ce “ wannan wai ƙamshin mene ne kamar na Gawa?” Da ido na tsure shi ina kallo jin ya ambaci gawa,a zuci na ce ‘ kenan dai da gaske ne abin da idona ya gane min? Ko ɗaya daga cikin fatalen da ake cewa sun shigo duniyarmu ne?’ “ Ki yi sauri ina jiran ki a mota” ya faɗa tare da fita.Kayan atamfa na saka kafin na ɗora hijabi sama,sai da na je na shaidawa Ammy kafin na fita can tsakar gida inda yake jirana.Bayan motar na shiga na zauna kusa da shi,waya na tarar yana yi sai da ya bai wa direba umarni sannan ya soma tuƙa mu. Sai da muka hau titi sosai kafin ya kashe wayar wacce duk rabinta turanci ne da kuma sunayen makaman yaƙi.Na ɗaga kai na dube shi daidai shi ma ya dubo ni,sai muka haɗa ido hannuna ya kamo yana murmushi ban san dalilin da yasa ni ya hana ni na dinga riƙe hannunsa amma shi in ya yi niyya haka yake kamo ni. “ Faɗa min me da me kike son saya?” ya tambaye ni yana ɗan matsa hannuna,ko kaɗan ban jin wani abu na daban saboda a matsayin uba na ɗauke shi.Na langwaɓar da kai na ce “ Chocolat da kuma teddy babba,sai turare da kuma ƙumbar kanti,da lipstick,da uhmm yawwa da sabuwar waya Uncle Please ” na ƙarashe tare da ciro ƙafafuna na yo sama da su tare da ɗora su kan nasa,ina jin lokacin da ya ja wani numfashi kafin ya ce “zobe fa?” ya tambaye ni saboda yadda ya san ina son zobe sai dai duk in ya siya min ban san ya ake yana ɓata ba.Na saki ɗan murmushi kafin na ce “ na hannunka nake so” sai na soma ƙoƙarin zare wani zobensa mai shegen kyawu da sauri ya dakatar da ni yana mai cewa “ zan saya miki wani dai” Na turo baki na ce “ Uncle wannan zoben dai kamar a tare aka haife ku ko kuma wani ɗanka sam ba ka son rabuwa da shi,ina ga ma ka fi sonsa fiye da Niii!” na ɗan ja ƙarshen ban shirya ba saboda yadda ya kafe ne da rikatatun idonsa masu matuƙar kaifi . “ Shi zoben?” ya tambaye ni cikin wata irin murya,ban iya cewa komai ba sai kai da na ɗaga masa alamar eh.A gabana ya cire zoben daga babban yatsansa na tsakiya sai ya kamo hannuna na hagu ya zura min shi a yatsana na biyu,a hankali yayi ta shafar zoben yana kallon tsakiyar idona har ya gama daidaita shi,sam tunanin ta ya aka yi zoben da shi kansa a babban yatsa kawai ya tsaya masa amma ni kuma a yatsa na biyu? Wannan tunanin sam bai shigo kwanyata ba sai na shiga yin murna har da wani rungume shi, Uncle Salem ya ƙara jan ajiyar zuciya a karo na biyu. Muna isa Mall ɗin ya ja ni izuwa ciki,ana ganinsa da kakin soja duk a soma basa girmansa,ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin aka haɗa ni da ita muka je tana nuna min kaya masu kyau sam ban san Uncle yayi tafiyarsa ba sai da muka sauko ƙasa ina ta baza ido amma ban gansa ba.Idona ya ciko da hawaye har zan tambayar mai kula da shiga da fita sai ga shi ya shigo ,ya sakar min murmushi kafin ya ce “ zo ki zaɓi wayar kafin a kira sallah” ya wani kama hannuna zuwa inda aka jera wayoyin manyan masu tsada Iphone na ɗauka sai muka zo nan ya biya kuɗi muka wuce mota yayin da kuma aka kawo min kayana har mota. Tun a hanya aka soma kiran sallah ga shi wurin da ɗan nisa, Uncle ya ce “ Jabeeru ɗan tsaya mu yi sallah kar jam'i ya wuce mu,dama da alwala ta” wuri direba ya samu ya parker suka fita suka bar ni nan,ina duba sabuwar wayata na ji an ƙwanƙwasa gilashin mota.Da sauri na dubi wurin sai na ga wata tsohuwa mai ƙusumbi a tsaye tana kallona da manyan idonta da suka shige can ciki tsabar tsufa. Banda ko dala a hannuna tun da ban fito da jaka ba,duk a tunanina almajira ce wannan yasa na buɗe ƙatuwar ledar chocolat da sauran kayan maƙulashe na ɗauko mata cake guda biyu da kuma jus,ina buɗe murfin motar sai ta ɗan matsa gefe na fito .Fuskata ɗauke da murmushi na ce “ ga wannan Kaka banda kuɗi hannuna” Cike da murna ta karɓa kafin ta ce min “ ki san yadda za ki yi ki hana mijinki tafiya dajin nan rayuwarsa na cikin haɗari tarko ne aka yi masa” Na yi dariya na ce “Kaka ai ni budurwa ce banda aure” “Naf shiga mu tafi kin wani fito waje duk ana kallon ki“Uncle ya faɗa tare da buɗe min ƙofa na shiga ina kallon tsohuwar wacce ke tsaye tana yi min murmushi amma abin da ya bani mamaki yadda aka yi sam Uncle bai gaishe ta ba alhalin na san shi da girmama tsofi don shine ya koya min yin sadaka musamman masu rauni irinsu. Sai bayan na shiga motar ne na lura da ashe tun tuni shi Jabeeru ya zauna kan mazauninsa.Har muka iso gida da tunanin tsohuwar nan danƙare a zuciyata amma sam ban faɗa wa kowa ba sallah kawai na yi na fito na soma buɗe kayan ina nunawa Ammy da kuma ƙannaina biyu Abdul da Mubarak,sai kuma sauran ƴan uwana waɗanda suke cousin ɗina ne.Wayar iphone ɗin dai ce duk suka yi ta taya ni murnar mallakarta don su duk sun jima da yinta in aka cire ƙannaina.Bayan an yi sallar isha'i Daddy da Uncle suka shigo a tare nan ne na ji yana faɗar cewa gobe in Allah ya kai mu Jabeeru direba zai kai mu can ƙauyen Ƙwargwam ni da Inna A'i saboda shi zai wuce can mission.Sam kwata-kwata ban kawo zancen cewa akan Uncle Salem wannan tsohuwar ke magana ba shi yasa kawai ban wani damu ba sai ma rigima da na ɗora masa na cewa to dole da zarar ya sauko ya fara zuwa can inda nake kafin ya zo gida. A cikin daren ma sai da na yi mafarkin tsohuwar nan ta sake ce min kar na bar mijina ya tafi,amma na share batunta na soma shirin tafiya don tuni tun jiya ka saka komai namu a cikin mota. Ƙarfe tara tuni mun yi breakfast,sai duk muka fito.Uncle Salem motarsu ce ta wurin aiki ta zo ta ɗauke shi yayin da ni kuma ta gidanmu ce.Duk lokaci guda motocin suka tashi muka hau titi,ta windown mota muke kallon juna ni da Uncle muna sakarwa juna murmushi har aka zo mararrabar hanya motocin namu suka rabu.Sai a lokacin na maido dubana kan titi ina jin abu biyu,kewar Uncle da kuma murnar cikar muradina ba tare na san abin da ke can yana jirana a ƙauyen Ƙwargwam..... [28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 05 Sosai Jabeeru ke sharara gudu kan titin da yake tsit babu kowa kamar an yi ruwa an ɗauke.Kamar daga sama haka na ga tsohuwar nan mai ƙusumbi daga can nesa ta yi tsaye tsakiyar kwalta amma duk nisan tazarar bai hana ni ganin ƙwayar idonta ba wacce ke yi min magana kuma raɗam nake jin sautin muryarta kamar waccan lokacin. “ Me kike jira da har yanzu ba ki sanar da Uncle ɗinki saƙona ba? In wani abu ya samu ɗana sai na ɗanɗana miki azabar da ba ki taɓa tunani ba ballantana gani a duniya” na shagala sosai da kallon ƙwayar idon nata sam ban san lokacin da Jabeeru direba ya kawo dab da ita ba,cikin ƙaraji na ce “ Jabeeru ka taka burkiiii!” sai dai ko kafin in rufe bakina tuni ya ratsa ta jikinta amma abin mamaki sam bai kaɗe ta tamkar dai iska wannan mai kaɗawa haka gangar jikinta take. Jabeeru ya tsayar da motar,ina haƙi ina ƙari na ɓalle murfin motar na fita na je na yi tsaye na duba can gaba a zatona ko zan ganta sheme a ƙasa sai dai wayam ba komai.Kamar wata mahaukaciya haka na ƙara yi a guje na duba bayan motar nan ma babu kowa ko ɗigon jini babu.Da na leƙa ƙarƙashi ma babu komai,tuni sun fito suna tambaya ta lafiya.Kai na dafe kafin na koma cikin mota na ɗauki wayata don na kira Uncle Salem sai dai sam babu network.Zuwa wannan lokacin hankalina ya soma tashi ji nake kamar dai gaske wani abu zai same shi. “ Wai Nafisa lafiya duk kike wannan kai komon kamar mai saffa da marwa?” Inna A'i ta tambaye ni. Ba tare da na dube ta ba na ce “ network nake nema ina son kiran Uncle ne” Jabeeru direba ya ce “ Hajiya fatan dai lafiya?” “ Jabeeru ina son samun network don Allah,mu je ko cikin dajin nan ne mu duba ko zan samu tsauni na hawa” na faɗa kamar zan yi kuka. Inna A'i ta ce “ a'a gaskiya ba zan bari ki shiga daji ba,daga ganin wannan ciyayi ba za su rasa maciji ba.Ki yi haƙuri mu ƙara gaba na san za a samu” Jabeeru direba ya yi caraf ya karɓe zancen“ eh Hajiya wallahi sosai ake samun macizai zo mu ƙara gaba ai mun kusa shiga inda ke da network tun da ga ƙarfen falwaya can ina tsinkaye” jin yadda suke ta tsorata ni yasa na yarda muka koma ciki sai dai juyin duniya motar ta ƙi tashi a dole kuma muka sake fitowa Jabeeru ya soma dubawa. Da wani irin gudu na ratsa cikin ciyayin saboda wasu manyan duwatsu da idona suka hango min.Ina jin Inna A'i na kirana amma ko waigowa ban yi ba ballantana na amsa mata,da isa ta na hau can ƙoli ai kuwa sai ga network ya shigo ko kafin na kira Uncle text ne birjit irin waɗanda ake turowa in an so a kira mutum amma ba a same shi ba.Hannu na rawa na rubuta lambar Uncle Salem wacce ke zaune raɗam a kwanyata,sai na ji yana cikin kira amma ba a ɗauki lokaci ba ya ɗaga yana mai jan ajiyar zuciya yayin da ni kuma na saka masa kuka tare da soma magana “ Uncle Please kar ka tafi tarko suka haɗa maka duk ƙarya ce babu wani kashe sojojinku da aka yi, Please ka koma gida” “ Naf lafiya kike kuwa? Wane irin zance ne wannan? ” ya faɗa .Na ce “ ni ma ban sani ba wata baƙar tsohuwa ce ke son haukata da farko ta ce mijina,yanzu kuma ta ce kai” “ Ya siffarta take?” ita ce tambayar da ya jefo min. Na ce “ tana da ƙusumbi...” ko kafin na ida koro masa sauran bayanan ya ja wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ Ok to” yana faɗar haka aka shaida min kuɗina sun ida,daidai nan kuma na ji muryar Inna A'i tana cewa “ Nafisa zo mu wuce motar ta tashi” tuni na sauko na kama hannunta muka fito daga cikin ciyayin don sai da ta biyo sawuna. Muna shiga motar muka ci gaba da tafiya cikin gudun da ya saba,sai da muka yi wajen awa uku kafin ya tsaya mu ci abinci da kuma fitsari sannan muka ɗora tafiya .Ba mu kai ƙauyen Ƙwargwam ba sai wuraren sallar azahar lokacin rana ta zo tsakiya,muna shiga garin gabana ya soma faɗuwa ina jin wani irin yanayi kamar wacce ta taɓa zuwa dama har da wasu tsofin moments nake gani wanda na rasa daga ina suke ziyartar kwanyata sam ban taɓa kawowa cewa suna ɗaya daga cikin ire-iren mafarkan da nake yi ba tun ranar da na soma ganin period. Kamar yadda tun kafin mun tawo Uncle ya bani duk wasu takardun sheda da ya karɓo daga can makarantarmu haka muka samu wani yaro ya kai mu can gidan shugaban makarantar wanda yake cikin ƙatuwar school ɗin wacce sosai na yi mamakin yadda aka yi ma aka gina ta. Da isar mu can sai muka taras da wasu malaman da alamu suma zuwansu kenan .Tarba muka samu daga wajensa kafin ya nuna mana ɓangaren jerin flat/appartement ɗin da aka tanada domin malaman ƙetare waɗanda ba ƴan ƙauyen ba.Kowane daga cikinmu ya bamu key ɗin ɗakinsa kafin mu wuce ,Jabeeru ya tuƙa mota har zuwa ƙofar ɗaki mai lamba uku wato nawa.Shi ne ya kai mana kayanmu ciki,ɗakin tsaf yake bai da datti kamar an sa da zuwanmu.Ciki guda ne sai toilet da kuma ƴar ƙaramar kitchen,haka duk muka jera komai wajensa Inna A'i ta cire zanen da muka tarar shimfiɗe kan ƴar madaidaiciyar kafitar ta shimfiɗa wata,na shiga toilet bakina ɗauke da addu'a na yi wanka tare da alwala sannan na fito sai na tarar tuni Jabeeru ya tafi ko sallama bai yi min ba .Dadduma na shimfiɗa na gabatar da sallah yayin da ita kuma Inna A'i ta shiga toilet ita ma don yin wanka.Ina zaune ina lazumi na ji ihunta haɗi da yin ƙara,kafin kuma na ji tana magana da alamu akwai abin da take kora can kuma ta fito kamar wacce aka jefo. Cike da kulawa na ce “ Innarmu lafiya?” Cikin masifa ta ce “tsakaka ce na gani kin san ban son ganinta“ ta bani amsa. Na ce “ ai kuwa inda kashe ta kika yi da kin samu lada ” Ba tare da ta ce komai ba ita ma ta zo ta yi sallar bayan ta gama ne muka soma taɓa hira kafin kuma mu ji bugun ƙofa,ita ce ta je ta buɗe sai kuma ta dawo hannunta riƙe da kwanon abinci tana mai cewa “ kin ga shugaban makaranta ya aiko mana da abinci” Na ce “ ban jin yunwa amma in kina ji kawai ki ci ki rage min” Inna A'i ta ce “ ai kuwa ina ji tun da a mota abin turawa ne kawai kika bamu ” tana nufin cake.Na yi dariya tare da ɗaukar wayata na soma saita app don jiya ban samu na yi ba.Ita kuwa Inna A'i hankali kwance take cin shinkafa da miyar kajinta tana santin cewa ashe ƴan ƙauye ma sun iya girki,ashe ba ta san guba ce take ciwa kanta ba. ★ Uncle Salem Tun jiya da ya rabu da zoben hannunsa yake jinsa wani iri tamkar gangar jiki babu ruhi amma babu yadda ya iya haka ya haƙura ya bar wa Naf ɗinsa.Tun asali zoben Inna Delu ce ta basa shi a ranar da ta sanar da shi za ta koma can maƙabarta makwancinta,sam bai san amfanin zoben ba amma yau da Nafisa ta kira shi ta sanar da shi cewa ta ga tsohuwa mai ƙusumbi kawai ya fahimci wato sirrin ganin Inna Delu da yake a duk lokacin da wata matsala ta tunkaro shi ya ta'allaka ne da zoben.Suna tsaka da gudu ya cewa direban da ke jansa yayi su koma gida,cike da mamaki direban ya juyo ya dube shi sai dai babu damar tambaya don bai ma ga fuskar tambayar ba . Suna tafe yana tunanin yadda Naf za ta ɗauki wannan lamari mai kama da wahayi don gudu yake abin ya bata tsoro don ya fahimci har zuwa yanzu kamar ganin abin take a mafarki. Tunani ya soma ta yadda zai bi ya karɓe zobensa ba tare da ya ɓata mata rai ba,a haka har suka isa Company.Ya fita cike da izzarsa wacce ba kullum yake bayyanar da ita sai in yana cikin fushi ko kuma yana son gwada ƙarfin ikonsa akan wasu.Ofis ɗinsa ya nufa tare da buɗe shi,yana shiga ya duƙufa yin bincike. ★Ƙwargwam Sallah kawai ke raba ni da wayata wacce bayan na kira gida mun gaisa na shaida musu mun sauka lafiya sai na soma chating da ƙawayena a whatsapp.Hira sosai muke a group ɗinmu na ƴan makaranta har dare yayi,sam ba mu yi girki ba saboda akwai abinci shi Inna A'i ta ƙara ci kafin ta kwanta ni kuma sam ban jin yunwa saboda dama haka nake muddin ina maƙale da wayata. Kiran Uncle Salem ya shigo a lokacin ne kuma na yi alwala na canza kaya ina shirin yin shafa'i da witiri na kwanta.Na ɗauka tare da yin sallama na gaishe shi cike da girmamawa sannan ya soma tambaya ta hanya ina basa amsa har muka yi hirar yadda muka samu tarba mai kyau. Ya ɗan jan numfashi kafin ya ce “ ina kewarki Naf” Na yi ƴar dariya kafin na ce “ Uncle tun da ka fasa tafiya me zai hana ka zo nan ɗin ka yi kwana biyu?” Ya ce “ kika ce ɗaki ɗaya ne tal inda aka sauke ku” Na ce “ eh amma ai ba za a rasa wurin da za ka kwanta ba ko da hotel ne” Yayi ƴar dariya kafin ya ce “ to zan duba na gani,amma Please ki kula min da kanki sosai banda magana da maza ko da kuwa shugaban makarantar ne ban so” Na ce “ to Uncle in sha Allah,amma yaushe za ka zo?” “ Sai zuwa wani satin Naf,yanzu akwai binciken da zan yi” Kafin na basa amsa sai da na juya na dubi Inna A'i wacce ta zagaya toilet a karo na uku tun lokacin da na soma waya,ina son tambayarta lafiya amma saukar numfashin Uncle a kunnena yasa na ƙara mayar da hankali wurinsa. “ To Uncle zan fara lissafin kwanaki tun yanzu” “Faɗa min me za ki shirya min na special?” tambayar da yayi min kenan wacce na ji wani banbarakwai don har wani salo na daban amon muryarsa ke fitarwa.Kamar zai yi kuka na ji yana cewa “ Please Naf faɗa min mana kar ki ji kunyata ” hakan kuwa ya ƙara ɗaure jijiyoyina na rasa amsar da zan basa,daga can toilet na soma jiyo saurin nishin Inna A'i cikin azaba babu wani tunani na kashe kiran Uncle ɗin tare da nufar toilet ɗin ina tambayar lafiya.Ba ta bani amsa ba sai ƙofar toilet ɗin da ta buɗe ƙiiii da kanta,daga inda nake tsaye na hangi Inna A'i zaune kan wc tuni ta fita hayyacinta don da alamu gudawa ce take ta yi. Tsakaka na gani kan katanga tana saukowa kamar za ta faɗo bisa kanta da mugun sauri na ɗauki takalme ina kiran sunan Allah na kashe tsakar,ta kuwa faɗo ƙasa bindinta ya rabu da gangar jikinta da mugun sauri kuma ta bi ta ƙafafuna shuuu ta fice ta bar guntun bindin wanda sai motsi yake. Daidai nan Inna A'i ta soma kelaya amai kamar hanjinta za su faɗo,ba tare da tsantsani ko ƙyanƙyaminta ba na taimaka mata ta yi wanka ,bayan nan na sa abin kwashe shara na saka bindin tsakakar sannan na wanke toilet ɗin na rufe ƙofa.Ina zuwa tuni Inna A'i ta yi bacci,ni ma sai na raɓa gefenta na kwanta. Washegari bugun ƙofar ɗakinmu ne ya tashe mu,yadda ake jijiga ƙofar kamar za a ɓallata yasa muka kalli juna kafin na miƙe na je na buɗe,da sauri na yi baya ina kallon shugaban makarantar da mamakin abin da ya zo nema a yanzu ko ƙarfe shidda ba ta yi ba.Yadda kuma yake yi min wani kallon tsaf yasa na sha jinin jikina...... Ga mai son shiga paid group 500 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank Sai ya turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 [28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 6-7 Na haɗiye wasu yawu muƙut, Allah na gani ba na cikin mutane masu mugun tsoron nan don za a iya kirana jaruma kai tsaye amma kallon idon headmaster kaɗai sai da suka hautsana hanjin cikina. “ Barka da warhaka shugaba!” na samu bakina dakyar ya furta. Ya saki wani murmushi wanda kana gani ka san ba na jin daɗi ba ne kafin ya ce “ lafiya! Ina son duba toilet ne don ganin ko gyaran da aka yi yayi” ya faɗa cikin wani irin amo. Kamar na ce masa wane gyara kuma amma sai na basa wuri ya shigo,cike da girmamawa ya gaishe da Inna A'i wacce ke zaune har yanzu a inda na bar ta kafin ya shiga cikin toilet ɗin na take masa baya kuwa.Dube-dube na ga yana yi kamar mai neman wani abu amma ban kawo komai ba don na yi tunanin ko gyaran ne a gaske yake dubawa . Fuskarsa duk ta nuna alamun ƙin jin daɗi har zai fito sai kuma ya tsaya cak yana cewa “jinin mene ne can?” Inda ya nuna na duba sai na ga daidai wurin da na kashe katsakakar jiya ne,amma ai na wanke toilet ɗin sosai ta ya aka yi jinin bai fita ba. Yadda ya watso min idonsa masu matuƙar dafi yasa na soma inda-inda,“ dama...dama jiya ne da Innarmu ta shiga ta ga tsakaka...” da sauri ya katse ni “ kenan ita ce ta buge mata bindi? ” Tsuru-tsuru na yi don ina tsoron kar ya kore ni ya ce ba zan koya ba,ya ƙanƙance ido ya ce “mu nan garin ba a kashe ƙwari ban san daga wane wajen kuka fito ba” sai kuma ya fita ni ma na take masa baya,ina kallon yadda ya bi Inna A'i da wani mugun kallo kafin ya fita. Ɗakin na rufe bayan na gama kallon yadda har a wajen sai da yayi ta dube-dube. Ko da na juyo sai na ga tuni ta shiga toilet,sai na jira ta fito sannan na shiga ni ma na yi alwala na fito na yi sallah sannan na zauna na yi Azkhar ɗin safe. “ Ina kwana Innarmu? Ya ƙarfin jikin naki?” na faɗa bayan na gama komai. “ Alhamdullah ai na ma warware,ina ga kajin jiya ne suka buga min ciki don na yi doguwar tafiya” ta bani amsa . Na ce “ ai kuwa dai ,yanzu ki kwanta ki huta dai zuwa an jima sai ki yi mana girki” Ta ce “ a'a na fa warke yanzu zan shiga kitchen“ tana gama faɗa ta miƙe kuwa,ni kuma na ɗauki wayata nan na ci karo da miss call ɗin Uncle Salem ya fi goma duk yayi su ne bayan na kashe kiransa na jiya.Ɓangaren saƙo na duba sai na ga text ɗinsa yana bani haƙuri tare da alƙawarin ba zai sake ba. Kiransa na yi sai dai sam lambar ba ta shiga,duk sai na ji babu daɗi haka na kunna data na soma yin shat ban ajiye wayar ba sai da na ga ta kusa mutuwa sannan na saka ta caji.Ina shirin shiga wanka na ji ana shelar ana son ganin dukkanin malaman da suka zo a ɗakin meeting da ke cikin makaranta da misalin ƙarfe takwas da rabi . ★Uncle Salem Cikin kaɗaicin son kasancewa da Nafisa ya soma bijiro mata da sabbin abubuwan da za ta fahimci shi mijinta ne amma da dukkan alamu ya ga sam ita a iya uban kawai ta yi masa matsuguni.Jin ta kashe masa waya yayi tunanin kunya da kuma fushi ne yasa ta datse kiran,hakan yasa yayi ta jera mata su da ya ga ta ƙi ɗauka sai ya tura mata text tare da kashe wayar ya rungume pilow.Zuwa yanzu haƙurinsa da juriyarsa sun yi ƙasa sosai,yana matuƙar son kasancewa da ita a duk cikin sati ranar juma'a da asabar kawai a bai yin azumi duk don kare mutumcinsa.Sau ɗaya tak ya taɓa neman auren wata wacce dama ita ce take haukan sonsa,amma an zo yin auren aka fasa saboda bai da wani asali. Idonsa sun kaɗa sun yi jajur saboda abu biyu da suka haɗe masa, feeling da kuma fushin Naf wanda a duniya in akwai abin da yake guje ma to bayansa yake shi yasa a kowane lokaci yake yi mata abin da take so.Ko da kuwa iyayenta sun so nuna masa illar gatan da yake yi mata sai ya ce musu har yanzu Naf yarinya ce.Sai dai a jiya da Daddy ya ce masa ya ci a ce ta tare da kuma yadda ya ga surarta cikin doguwar rigar da ta lafe jikinta duk ta fitar da shap ɗinta sai yake ji a ransa eh za ta iya ɗaukar nauyin buƙatarsa. Juyi yayi ta yi a daren,da ya ga dai sam baccin ba fa zai zo ba sai ya miƙe ya je watso ruwa tare da zama kan dadduma yayi ta lazumi bayan raka'o'i biyu da yayi.Sai daf da asubah ya samu bacci,amma duk da haka ana kiran sallah sai da ya je masjid da ke nan cikin Company ya dawo ya ƙara komawa bacci.Bai farka ba sai wuraren ƙarfe goma na safiya,wani wankan ya sake tare da shirya wa cikin wando tree quater na sojawa da kuma rigarsa t-shirt ita ma ta kakin soja.Bai ɗora hulla ba ya dai saka farin gilashi kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ta aiki da kuma wayarsa.Sai da ya fito a hanya ne ya kunna ta,bayan ya shiga mota ne ya ga saƙon cewa Nafisa ta so kiransa amma ba ta same shi ba.Ya ɗan saki murmushi yana jin zuciyarsa ta yi sanyi ko ba komai yana da tabbacin ta sauko daga fushin da take.Kiranta yayi har sau biyu,a na uku ne Inna A'i ta ɗauka ta shaida masa ta fita. ★ƘWARGWAM Ko da na fito daga wanka tuni Inna A'i ta soya min dankali da kuma ƙwai,na yi zaune na ci na ƙoshi kafin na jawo kayan kwalliyata na shafa mai da turare har da hoda.Bayan nan na zaɓo doguwar riga ta tambaya ƴar côte d'ivoire,sosai ta amshe ni sai na zaɓo hijabi da jaka da kalmi duk waɗanda za su hau da ita. Ina shirin fita ita ma Inna A'i ta fito daga kitchen hannunta riƙe da kwanon miya na jiya,ta ce “ ashe ba ki ci abincin nan ba dubi yadda duk yayi tsutsotsi ya lalace” Na dubi cikin kwanon na ga babu kyawun gani manyan tsutsotsi ne ke ta yawo suna shige da fice cikin ragowar naman kajin.Da mamaki na ce “ amma kuma abincin har ya isa lalacewa haka?” “ Ni ma haka na ce,ko ƙila zafi” Inna A'i ta faɗa . Na ce “ kawai ki zubar ki wanke kwanukan sai ki mayar musu ,ga key nan in za ki fita ki rufe ɗakin na tafi sai na dawo” “Allah ya tsare hanya” Na ce Amen ina mai yin addu'ar fita daga gida.Kamar yadda ƴan magana ke cewa in ka yi boko to ƙauyancinka ragage ne hakan yasa duk da ban san ko ina na makarantar ba haka na dinga karanta duk wani allon sanarwa da na gani har na dace da ɗakin meeting. Da isa ta sai na tarar duk kamar ma kowa ya zo ni ake jira,sallama na yi tare da samun wuri na zauna kusa da wata wacce na ga tana sanye da hijabi saɓanin sauran matan da ke wurin duk sun ci uban ado an ɗora mayafi. Babu jimawa kuwa manyan namu suka suka shigo,duk muka miƙe tsaye don nuna girmamawa kafin mu zauna. Ɗaya daga cikinsu ne ya soma yin magana ,su biyar ne huɗu maza sai mace ɗaya. “Yawwa da farko muna yi wa baƙin malaman School Ƙwargwam Barka da zuwa,kamar yadda kuka sani duk faɗin garin nan wannan ita ce kawai makarantar da ake koya karatun boko da sauransu...” sai yayi wani murmushi wanda yake ɓoye wata manufa kafin ya ci gaba da cewa “ Ƙauyen Ƙwargwam na zagaye da ƙauyukan maƙota guda huɗu,shine a tsakiya sannan dukkan sauran ƙauyukan nan a wannan makaranta tamu mai farin jini suke zuwa ɗaukar darasi.Kar dai na cika ku da surutu,ina son waɗanda za su koyawa ƴan sakandari su koma layin nan duk su zauna” ya nuna wani layi,nan duk wasu daga cikinmu suka ware kansu nan ne na fahimci wato ba iya primary ba ce kenan school ɗin. Kamar kuwa ya karanci tunanina sai ya ce “ makarantar ta kashi gida uku ne,da farko Sakandari sai ya nuna layin malaman kafin ya ce wannan shi ne Principal ɗinku ku da ɗalibanku,ƴan primary kuma ga naku shugaban headmaster sai ya nuna mutumen nan na jiya da ya kawo min abinci shi kuwa har da yin wani murmushi.Ina so duk ku basu girmansu,ni kuma mai yin magana ni vice headmaster,wannan kuma vice principal ya nuna ɗayan namiji ,daga ƙarshe sai wannan kuma ita ce Grand Maa mai makarantar ce ofishinta shine dogon nan mai jan penti in kuna da wata matsala ko wani abu da ya shige muku duhu ita ce za ku je ku yi wa magana” bayan duk ya gama nasa jawaban su ma ɗaya bayan ɗaya suka yi nasu kafin su faɗa mana fatansu da kuma tsarin makarantar wanda tun da nake ban taɓa jin irinsu ba amma haka na ja bakina na yi shuru. Bayan an gama meeting sai wasu matasa suka shigo suka soma rabon coffe mai shegen ƙamshi.Ana bani na karɓa ina kallon ruwan coffe ɗin waɗanda a tsakiya aka shatin zuciya,na dubi na maƙwabciyata na ga ita ma nata haka yake. Na yi shuru ina tunanin ko sai yaushe zan fara soyayya oho. “Madam Nafisa ” Muryar headmaster ta katse min tunanin na ɗago muka haɗa ido,ya sakar min murmushi kafin ya ɗaga kofin hannunsa kamar yadda Turawa ke yi mai nufin Bismillah. Na ɗan murmusa kafin na soma kurɓa ina ganin lokacin da ya saki murmushi ,a baki coffe ɗin har ya fi daɗi kan kyawunsa a ido. Bayan mun gama sha ne aka rabawa kowa ajin da zai koya ,sai kuma duk muka miƙe Grand Maa sai ƙara jadadda mana take gobe tun ƙarfe bakwai na safe kowane malami ya tsaya bakin ƙofar ajinsa. Muna fitowa na cewa wacce muka zauna kusa da juna,“mene ne sunanki?” “Adama,ke kuma fa?” “Ni kuma Nafisa”na bata amsa nan muka so yin masayen lambobi sai dai ni na bar wayata can gida tana caji a dole ni na bata tawa na ce sai ta ɗago min hannu. Ina zuwa bakin ƙofar ɗakina sai na tarar da shi a rufe.Sai na zauna kan ƴar matakalar da aka yi bakin ƙofa na tsaya jiran Inna A'i don babu tantama gidan headmaster ta je.Ni kaɗai ce a wurin amma haka nake jin ana magana kusa da ni irin sosai ɗin nan,da na waiga ko ina kuma babu wanda na gani.Shuru na yi ina tunanin ko dai kunnuwana ne amma abin mamaki sai na ji ana dariya,da sauri na dubi inda sautin ke fitowa wani ɗan rame na gani irin na gidan tururuwa tabbas a ciki nake jiyo sautin amma sai aka yi tsit na wani lokaci. Ni kuwa da son jin ƙwaƙwaf na duƙa tare da kai kunnena ƙasa ina saurara,ƙafafun mutum na gani tsaye kusa da ni.Da sauri na tashi sai na ga headmaster ne,yayi min kallon nan nasa kafin ya ce “me kike yi haka a waje?” Na ƙaƙalo murmushin yaƙe na ce “na zo na tarar Innarmu ba ta nan ne shine na tsaya jira har ta dawo” “Kuma kin yarda za ta dawo ɗin?” ya jefo min tambayar wata iri,ni kuma da yake ba wani damuwa na yi ba na ce masa “ eh za ta dawo ai ita ce za ta zauna da ni har mu koma” “Hum!” ya ja wani ƙyaci kafin yasa key ya buɗe min ɗaki,na yi masa godiya tare da shigewa ciki. Har zan shiga wanka na soma jin ƙaurin ƙonewar abinci,da sauri na shiga kitchen na kashe gas ɗin .Bayan na yi wanka na fito na yi mamakin da ban ga Inna A'i ta dawo ba,wayata na cire a caji na duba sai na ga Uncle ya kira ni sai na mayar masa ya ɗauka.Muka fara gaisawa kafin na ce “ Uncle ina ne za ka je na ji kamar kana driving?” “Wurinki mana ko ba ki so?” Cike da murna na ce “ wai Uncle da gaske?“ “ Na taɓa yi miki ƙarya? Ke dai kawai ki shirya tarbena don na kusa zuwa sai an na iso” yana gama faɗa ya kashe,ni kuma cike da zumuɗi na miƙe na soma gyara ɗakin na shiga kitchen na fara duba abubuwan da duk muka zo da su na haɗa masa lemun zoɓo na jona ƴar ƙaramar frigine ɗin da ke nan a kitchen na saka. Haka na zauna na yi ta yin abubuwan da na san yana so kafin isowarsa.Aikin da na duƙufa shi ya mantar da ni wani cewa Inna A'i ta fita,haka na wuni ni ɗaya sai dab magrib ne Uncle Salem ya kira ni ga shi ya iso ni na je na tarbo shi can fara isa makaranta.Gidan gaba na shiga ya tuƙo motar yayi parking nata daidai ɗakina,nasa sabon key ɗin da headmaster ya bani na buɗe sannan muka shiga .A gajiye yake wannan yasa ya soma shiga wanka,ko da ya fito tuni an soma kiran sallah da sauri na ɗauke idona ganin ya fito babu riga daga shi sai farin towel ya ɗaura a ƙugu. A ɗan daburce na ce “ Uncle ga kayan buɗa bakinka” Bai ce komai ba sai gefen katifa da ya zauna haka nan ya ƙi saka kayan,da kansa ya zuba zoɓon don dai ni ba zan juri kallonsa a haka ba na shige toilet na ɗauro alwala . Da zan fito sai da na ɗan ziro kai don ganin ko ya saka riga sai dai karaf muka haɗa ido da shi,yana nan kuma a inda na barsa.Ya sakar min murmushi yayin da ni kuma na fito cike da kunya,kaina sunkuye na ɗauki dadduma na soma yin sallah ko kafin na gama ya canza kaya ,a nan ɗaki shi ma yayi sallah gefena kan nasa daddumar. Hannuna ya kamo da nake ta yin Azkhar ɗin yamma da ban samu na yi bayan sallar asar ba.Wani irin sanyi ne nake ji yana ratsa ni ga tuwon tafin hannunsa sai wani matse min nawa yake . “ An gama yi wa Uncle ɗin fushi?” ya tambaye ni yana murmushi mai sauti. Na ce “ ni ban yi fushi ba” “ Kalle ni” ya faɗa ,a hankali na dube shi ɗin idonmu ya sarƙe cikin na juna ina son kawar da kai amma tamkar wacce ya yi wa dabaibayi na kasa.A hankali na soma sauke ajiyar zuciya ,tsawon lokaci muna a haka kafin ya buƙaci in zuba abin da na dafa mu ci.Jiki duk a sanyaye na zuba muna ci muna aukin kallon juna har muka gama,ana kiran sallar isha'i na miƙe don gabatarwa amma ya katse ni “je ki yi ɗahara ki sake alwala” Ban musa masa ba don ba ya daga cikin halayena yin gardama a gare shi.Da mamakina kuwa da na shiga toilet alwalata ta karye iya ɗan kusanci da muka samu kawai,amma sam ban kawo shi wai don wannan niyyar yasa ya ce na je na sake alwala shi yasa ko da na fito ban wani ji kunyarsa ba na haye dadduma,shi ma sai da ya sake yin wata alwala kafin ya yi sallah. Hira muka soma yana tambaya ta meeting ina basa amsa cike da sakewar fuska kafin na soma jin cikina na yin ciwo,tun ina daurewa har na kasa. “ Je ki kwanta” cewar Uncle ,ina cije leɓe na haye katifa tare da yin rairan ina duban sama dafe da cikina. Jakar da ya zo da ita ya buɗe sannan ya ɗauko wasu kwalabe yayi wani haɗi cikin kofi ,kafin ya cika bakinsa da ruwan ya zo ya ɗora shi kan nawa.Na buɗe bakina na dinga haɗiye ruwan maganin a hankali ina lumshe idona har na shanye duka,ina jin yadda Uncle ya soma tsotsar lips ɗina amma banda wani ƙarfin hana shi dukkan jikina ya saki kwanyata ma tamkar ta rabu biyu tunanina yana gushewa yana dawo wa kamar wani network. Wani irin zazzaɓi ne nake jin yana rufe ni a sunnu,na ware idona a hankali kamar na jariri sabon haihuwa ina kallon Uncle da ya gama tsotse min baki.So nake na faɗa masa ina jin sanyi amma babu bakin magana,tashi na ga yayi yasa key ya rufe ƙofar sai a lokacin ne kuma Inna A'i ta faɗo min a rai. Jakar kayana ya buɗe ya je ya ɗauko kayan baccina,irin rigar nan mai buɗewa ya saka min bayan ya zare ta jikina sai rumtse ido nake don ko bra ban saka ba saboda muddin ba fita zan yi ba takura min take.Shi ma irin rigar ya saka sai dai bai ƙulle tashi ba,ina ganin ya kashe hasken ɗaki ya kunna wutar ƴar ƙaramar waya sai ya ɗauko ƙaton blanket ya rufe ni kafin shi ma ya shigo ciki.Hannuna mai sanye da zobe ya kamo ya riƙe kafin yayi min rumfa da ƙirjinsa mai cike da yalwa gashi ta kwanta sai santsi take. Wannan karon yana ɗora bakinsa kan nawa ji na yi kamar ya jona ni ga lantarki,tuni na ji duk jijiyoyin jikina sun dawo aiki.Na ƙanƙame shi gam ina yin numfashi da sauri-sauri,yayin da shi kuma ya ci gaba da shan yawuna kafin ya soma shayar da ni nasa can kuma ya cire bakinsa ya mayar da shi daidai kunnena yana cewa “faɗa min wa ya baku abinci jiya?” Dukkan jikina rawa yake saboda sabon yanayin da na tsinki kaina,na tallabo bayansa da kyau na ƙanƙame shi ina jin lokacin da igiyar rigata ta since ƙirjinmu ya mannu da na juna sai na ji kamar raina zai fita tsabar shock.Murya na rawa na ce “ headmaster ne!” ina gama basa amsa ya ƙara lalubo bakina wannan karon har da romance yana yawo da hannunsa a duk sassan jikina.Ni dai duk abin kamar a mafarki nake jinsa ba zahiri ba saboda tunanina ba zaune yake daram ba,ban san lokacin da na yi bacci ba bugun ƙofa ne ya tashe ni.Na ware idona a hankali sai na ga Uncle a tsaye bakin ƙofa yana murza key,yana gama buɗe wa sai Inna A'i a tsaye kamar wacce aka fiddo daga rame....... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Zuwa page 10 zan gama free page in sha Allah,za ki iya yin payment ɗinki tun yanzu. [28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 08 Da wani irin sauri na gyara rigar baccina wacce na tuna sosai Uncle ne ya saka min ita .Na miƙe tsaye ina mai ci gaba da kallon Inna A'i wacce ta shigo ƙafafunta fututu kamar wacce aka fiddo daga kabari.Tana shigowa Uncle ya maida ƙofa ya rufe,sannan ya je ya zauna kan dadduma hannunsa riƙe da ƙaramar casbi. “ Innarmu daga ina kike?” na samu kaina da tambaya. Sai ta dubi Uncle Salem,ni ma sai na dubi bangaren da yake ina mai tambayar kaina ‘shi wannan a nan ɗakin ya kwana ko me?’ a nan take kuma kwanyata ta soma kawo min gogagen kilishen abubuwan da suka faruwa sai dai ba su fita sosai ba dishi-dishi ne ban ida tantance taƙamaimai abin da ya faru ba a tsakaninmu. “ Bari har na yi wanka Nafisa, lokacin sallah ma ya gabato ” Inna A'i ta faɗa tare da nufar toilet. Yadda na ji idonsa na yawo a jikina yasa na kai dubana gare shi,sai na ga ashe cinyoyina ne yake kallo bai ƙyaftawa.Duk sai na ji babu daɗi don dai bai saba yi min haka ba,na je na ɗauki hijabina na saka na yi tsaye har sai da Inna A'i ta fito daga wankan sannan na shiga saboda fitsarin da nake ji ya matse ni. Wani irin tsoro ne ya kama ni ganin ina yin fitsari baƙi ƙirin da shi tamkar wani Lipton .Wani kuka ne ya ƙwace min tare da tashi ina yarfa hannu,ban san ta ya aka yi har Uncle ɗin ya ji kukan ba sai gani na yi ya shigo toilet ɗin sam kuma a wannan matakin da nake cikin tsoro ban ga aibun shigowarsa ba . Wani irin sihirtacen kallo yayi min a tsakiyar idona da suke tsiyayar da hawaye kafin ya ce “ ki yi wankan tsarki ki fito, wannan dattin ciwon cikin da kika yi ne jiya ko kin manta har magani na baki?” yayi maganar yana jan ruwa fitsarin ya wuce,sai a lokacin na ji kunya tare da gyaɗa masa kai alamun na yarda. Murmushi ya sakar min kafin ya fita,sai a lokacin na cire rigar baccin da hijabi.Wankan tsarkin na yi kamar yadda ya umarce ni kuma sai na ga ya kyautatu ɗin na yi shi.Bayan na fito sai na ga yana bai wa Inna A'i magani da murfin roba,ya fi kala uku maganin kafin kuma ya miƙe ya fita. ★Uncle Salem Jiya a lokacin da Inna A'i ta ɗauki wayar Nafisa ,a cikin muryarta kawai ya ji hucin wani ruhi da ke jikinta.Bai kuma yi wani dogon tunani ba ya fahimci tabbas da matsala,can gida ya koma ya tattaro duk maganin da ya san zai buƙata kafin ya ɗauki hanyar garin Ƙwargwam.Abu guda ya sani shine ba zai iya rabo su daga ƙauyen can ba tun da har Innarsa Delu ta yarda ta bar su suka wuce alhalin kuma ta fitowa Nafisa a siffar ruhi. Ko da ya zo kuma bai ga Inna A'i bai yi mamaki ba,ita kanta Naf ɗin ƙwayar idonta kawai ya kalla ya hango yadda guba ke son game dukkan jikinta.Abu biyu ne yasa ya bata maganin,na farko don ya ji wane ne ya ciyar da Inna A'i don samo mafita,na biyu kuma don karye abin da aka baiwa Nafisar a cikin shayi ta sha. A jiya ba don yana son ceto Inna A'i ba babu abin da zai hana shi ya mayar da Nafisa cikakkiyar mace,sosai moment ɗin ya ja shi zuwa ƙarshen shauƙi.Ba tare kuma da ya fita ba daga nan inda yake kwance da taimakon zoben hannunta ya lalabo Inna A'i a can wani ƙasurgumin daji tana yi ta tafiya ita ɗaya kamar mahaukaciya saboda tun bayan fitarta zuwa mayar da kwanukan gidan headmaster a nan bakin ƙofar ɗakinsu ta ji kamar ta zurma cikin rame kafin kuma ta tsinci kanta wani wuri.Dukkan detail ɗin nan Uncle Salem ya gansa daki-daki,wanda kuma ko ita Inna A'i aka tambaye ta ba za ta kawo shi ba. Yadda ta ji muryarsa kamar daga sama shi ya sa ta juyo baya ta fara dawowa gida kuma,ko lokacin da ta buga ƙofa daga cikin ramen ta fito sai dai Uncle ya toshe duk wata ƙofa da zai sa A'in ta fahimci wani abu. Yanzu kuma da ya fito, tsugunawa yayi ya ɗiga wasu ruwa cikin ramen kafin ya rufe kwalbarsa ya saka a aljihu. Masjid ɗin makarantar ya nufa wanda ake ta kiran sallah,yana isa ya shiga sawun gaba bayan yayi nafiloli sai ya zauna har lokacin sallar yayi .Tuni kuma masallacin ya cika aka tayar bayan an gama ne Uncle Salem ya juyo yana kallon headmaster wanda ya zauna kafaɗa da kafaɗa da shi.Ya saki wani murmushi kafin ya ci gaba da yin Azkhar ɗinsa,har sai da ya gama kafin ya basa hannu ya ce “ Assalamu alaikum ” Headmaster cikin mazgewa ya miƙawa Uncle hannu suka yi musabaha wacce yayi da na sanin yin ta,don kuwa akwai kumfan magani a hannunsa na karye sihiri. “Wa'aleykum Salam ! Fatan an sauka lafiya?” ya amsa tare da saurin janye hannunsa. Uncle Salem ya ce “ lafiya lau alhamdullah ! Na zo duba wurin da matata ne za ta yi aiki ita da Kakarta sai kuma na ga wuri yayi kyau” Cike da takaici headmaster ke kallon Uncle ,don kuwa tun zuwansa jiya akan idonsa na ɓoye ya sauka.Sannan sarai ya san da shi ne ya warware zare da abawar da ya ƙullawa Inna A'i,amma saboda ya iya munafurci shine zai ce masa wuri yayi kyau. Cike da iya tako shi ma headmaster ya ce “ ai kuwa dai school Ƙwargwam na kula da malamanta har ma da ɗalibai” Uncle wani murmushin ya sake yi kafin ya ce “ ni ne shaida,amma me yasa kuka bata ɗaki mai lamba uku bayan ita sabuwar zuwa ce?” “ Ɗakin nada matsala ne?” “A'a kawai na tambaya ne” “In ba ta sonsa ai sai a canza mata” “ A'a na faɗa ma wuri ne mai kyau,kuma lamba ukun ai ita ce daidai da ita surukar Inna Delu guda” Uncle ya faɗi haka ne ya na saka idonsa cikin na headmaster don yi masa gargaɗi kan cewa kar ya sake cutar masa mata in kuma ya ƙara yin kuskuren haka shi da shi shege ka fasa.Da sauri kuma ya miƙe ya barsa nan. ★ Bayan na gama sallah haka na tsure Inna A'i da tambayoyi sai ta faɗa min inda ta je amma sai kwana-kwana take yi min daga ƙarshe ma ta shige kitchen tana cewa “bari na haɗa mana breakfast ” Na ce “ yau fa Litinin ko kin manta azumi muke ni da Uncle ” “ A'a yau ba za ki yi ba,ki bari har Alhamis ” Uncle ya faɗa wanda ke shigowa.Na dube shi da mamaki jin yau shine ke cewa na ajiye azumi,“ Uncle ina yi fa” na faɗa kamar zan yi kuka ina kallonsa.Ya ɗauke kafin ya ce “a'a akwai maganin da za ki sha yanzu kafin ki ci komai” sai yayi gaba ya ƙarasa gaban jakarsa ya fiddo wata kwalbar zuma. Ido tab hawaye nake dubansa,ya ɗago ya kalle ni kafin ya ce “za ki zo ki sha ko sai na zo nan na ɗauko ki na matse miki baki tare da ɗura miki shi?” Jin ya fito a Uncle Salem ɗinsa mai tsanani yasa na ƙarasa gabansa na yi zaune tare da tanƙwashe ƙafafuna.Da wata ƴar ƙaramar cokali ya soma bani zumar har sai da na sha bakwai da ita kafin kuma ya soma bani wasu sauran maganin,ɗaya kuma ya ce “ wannan kuma sai in kin ci abinci za ki sha” sai ya miƙo min na karɓa ina gunguni. Yayi murmushi mai ɗan sauti kafin ya ce “ Naf sai yaushe za ki girma?” Kamar suɓutar baki na ce “ ranar da ka yi min aure” Shuru yayi bai ce komai ba,ni ma sai na rashin kunyata.Na ɗaga kai da niyyar satar kallonsa sai na ga ashe ni ɗin ce yayi ƙuri kamar mai kallon tv.Zan yi ƙasa da kai yayi saurin tallabo haɓata ya ce “ da gaske kin shirya zaman auren?” Na lumshe ido ina dariya,ya ce “ faɗa min na ji saboda in na koma gida na yi wa Daddynki magana a soma shirin biki” Na ɗan cinno baki gaba na ce “ni da ko saurayi banda” kamar daga sama na ji bakinsa kan laɓana, wannan karon dai kam cikin hankalina nake.Cike da razani na buɗe ido kafin da sauri na tashi daga gabansa jikina na ɗan yin rawa,duk da ba yau ne ya saba yi min kiss ba amma a goshi ne ko a kumatu ya saba min sannan an ɗauki lokaci mai tsayi rabon da yayi. “Nafisa?” na ji muryar Inna A'i,da sauri na nufi kitchen ɗin ina jin daɗin kiran nawa da ta yi.Ina shiga ta yi min wani kallo sai na ji na tsargu na yi tunanin ma ta gani ,a ɗan daburce na ce “ ni ma ban san me yasa Uncle yayi haka ba,shi ba giya yake sha ba ballantana na ce bai cikin hayyacinsa ” “Ungo ni ki je ki sha ya fi wannan surutun da kike yi min marar kan gado,duk duniyar nan akwai mai sonki sama da shi Salem ɗin da har za ki yi tunanin zai yi abin da zai cutar da ke” Inna A'i ta faɗa . Na karɓi kofin kunun tare da komawa can gefe na soma sha sam na ƙi yarda na koma can,ita ma ba ta matsa min amma ina shanyewa sai na fito don tuni gari yayi haske sannan lokacin da za mu je bakin aji ƙarfe bakwai ne. Ina fitowa na gansa a zaune ido rufe yana wani jan numfashi tare da ɗan game fuska haɗi da yamutsa ta.Toilet na shiga na yi wanka,da na fito sai na tarar ba ya nan.A gaggauce na shirya tsaf,na zuba takardun da zan yi amfani da su da abin rubutu. Inna A'i ta fito tana min wani kallo kafin ta ɗauke kai,“ki je yana mota yana jiranki ku yi sallama” Jiki a sanyaye na fita ganin irin yadda ita Innarmu ta canza min fuska wacce nake ɗauka uwa ta biyu.Hijabi na saka kafin na fita,gidan gaba na buɗe na zaune na sunne kai tare da yin shuru ina wasa da zoben hannuna.Kujerar da nake zaune a kai ya ɗan buɗe ta ja baya,da sauri na kalle shi yadda na ga idonsa sun kaɗa sun yi ja yayi bala'in bani tsoro.Murya na ɗan rawa don duk a tunanina kuka ne yayi,na ce “Uncl...” sauran maganar ce ta maƙale jin bakinsa kan nawa abin ma bai tsaya nan ba ya soma shafar hijabina ta sama .Hawaye ne suka soma zubo min ,ba yau ne farkon jin cewa uba yayi mu'amala da ƴarsa ba na sha jin ire-iren labarun nan a kafar BBC amma ban taɓa tunanin akwai ranar da abin zai zo kaina ba don ban taɓa banbance Daddy da Uncle ba.Duk abin da yake yi ko motsi ban yi ba da yatsana ballantana na yi yunƙurin hana shi ,hawaye kawai nake yi don babu bakin kuka saboda Uncle ya mayar da shi sweet ɗinsa.Sama da minti goma kafin ya janye daga gare ni amma ina jin hucin saukar numfashinsa kusan fuskata da na rumtse idona.Shashekar kukansa da na ji ta yi kuma bala'in tayar min da hankali fiye da abin da ya gama yi min,na buɗe idona ina kallonsa shi ma hawayen yake fitarwa kafin ya kama hannuna dukkan biyun ya ce “ don me Naf? Me yasa kike horar da ni da yawa? Me yasa ba ki ganin zazzafar ƙaunar da nake yi miki? I love Naf! Ina sonki,ina buƙatar ki a kusa da ni haƙurina ya ƙare” Tamkar wacce aka bugawa guduma a kai haka na ji ,kalamansa kuwa kusan tarwatsa min kwanya suka yi sam kasa fahimtar abin da yake nusar da ni na yi.“Wuce ki tafi ki kula min da kanki”ko ida rufe bakinsa bai yi ba na ɓalle murfin motar na fito..... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 09 Ƙafafuwana har harɗewa suke saboda kalaman da Uncle Salem ya fesar min,ruhina kuwa yayi wani irin sanyi saboda zazzafan romance ɗin da yayi min wanda ya toni duk wani sirrin zuciyarsa da muradinta na shekara da shekaru.Ta ya zan so Uncle soyayya ta aure? Ta ina ma zan fara wannan cakwakiyar da sam ƙanƙanuwar kwanyata ba za ta iya ɗaukar wannan rikicin ba.Ina shiga ɗaki na tarar da Inna A'i tana jera min takardun da ni ce na fidda su a jaka,ta ɗago ta dube ni kafin kuma ta kawar da kai.So nake na shaida mata kalamai da kuma abin da Uncle yayi min ko zan samu sukuni amma sam ba ta bani fuska ba.Wannan yasa kai tsaye na shige toilet,ga mamakina duk jikina ya ɓace saboda abubuwan da yayi min har sai da na canza pant na kuma wanke fuskata.Ina tsaka da maida kwalliyar fuskata na ji ƙarar tashin motarsa,na ja ajiyar zuciya tare da motsa laɓana kaɗan na ce “Allah ya sauke ka lafiya!” sai na ɗauki wani sabon hijabi saboda wancan duk Uncle ya cukuikuye shi sannan hawayena sun jiƙa shi ta gaba. “Na tafi sai na dawo”na faɗa dakyar,ta ce “a dawo lafiya” jakata na ɗauka tare da fita daga cikin gidan na nufi can ɓangaren makarantar. Ina zuwa gaban ajin da zan koya na tarar tuni ɗaiɗaikun ɗalibai sun zo,haka suka gaishe ni irin yadda ake yi.Wani sanyi ya ratsa ni duk sai na ji ƙuncin ya sauka daga zuciyata har da murmushi,ina nan tsaye kamar sauran malamai bakin aji aka soma kawo yaran sai a lokacin na dinga cewa su shiga aji su zauna.Ina nan tsaye wani ya kawo ƴarsa sai kuka take,da sauri na kama hannunta ina mai rage tsayi na ce “yi shuru mana babyna ko ba ki so na baki alawa?” Cikin murya ƙurciya ta ce “ina so” Na ce “yawwa to yi shuru sai na baki ,me sunanki?” “Firdausi”ta bani amsa,na gyara mata zaman ɗan guntun hijabinta kafin in saɓe ta kamar wata ƴata na ce “to yi wa Daddy bye bye sai mu je aji na nuna miki inda za ki zauna” da murmushinta kuwa ta yi masa alama da hannu,ya ce “na gode Madam ” Na ce “bai komai ai aikinmu ne” sai kuma na shiga aji na zaunar da ita a kujerar gaba ta kusa da kujerar da aka ware domin zamana. Bayan nan na ƙara komawa can bakin ƙofa,ban shigo ba har sai da ajin ya cika zuwa lokacin tuni ƙarfe takwas ta buga.Ina shiga na yi zaune ina kallonsu ɗaya bayan ɗaya ina jin wani sanyi na ratsa min zuciya,kafin kuma na tashi na bi ɗaya bayan ɗaya ina tambayar kowa sunansa.Dukkansu yara ne da ba za su wuce shekara bakwai ba,wasu ma ba su kai ba,ina cikin zagayen ajin sai ga headmaster ya shigo shi da mataimakinsa. Takarda mai sunan ɗalibai ya miƙo min da kuma alli wanda zan yi rubutu da allo,liste ɗin na ɗauke da ɗalibi ɗari cicif.Bayan fitarsu ma sai da na sake kiran sunayen yaran kafin na je na soma yin rubuta a jikin baƙin allon wanda yake goge fesss,kwanan wata na rubutu da kuma ABCD sai na soma koya musu suna yi duk bayan na faɗa.Haka muka ta yi har lokacin shan iska yayi,sai dai kamar yadda meeting ɗin jiya ya sanar da mu dokokin makarantar hakan yasa ban fidda su waje ba. Grand Maa ce ta shigo ita da wata budurwa ɗauke da wani basket,cike da girmamawa na gaishe ta yayin da kuma budurwar nan ta soma raba wa yara abincin da za su ci.Bayan ta gama a gaban idona Grand Maa ta miƙawa wani yaro biscuit kafin su fice. Bayan an gama cin abinci duk suka je suka jefar da abin take away ɗin a shara nan na ci gaba da yin cours ina aika kowane ɗalibi ya zo ya rubuta harafi ɗaya daga cikin ABCD ɗin da na yi musu.Ƙarfe sha biyu na rana cif aka kaɗa ƙarar rawar tashi ,nan aka zo fara ɗaukar yara ba ni na baro ajin ba sai da kowa ya watse . A gajiye na shiga gidan,Inna A'i ta yi min Barka da zuwa na amsa ina mai rage kaya na shiga toilet.Bayan na yi wanka ta gabatar min da abinci,na saka plate ɗin gaba tare da ɗaukar waya na kira Ammy bayan mun gaisa cike da alfahari nake bata labarin yadda ranar farko ta kasance ,sai murmushi take kafin mu yi sallama ina gama cin abinci na ɓingire bacci wanda tamkar jirana ake aka ƙara yi min maimaicin duk abin da suka faru a yau ɗin tun daga lokacin da na je na yi tsaye gaban ajina har zuwa lokacin shan iska na yara.Yaron nan da Grand Maa ta baiwa biscuit na ga yana ta kuka yana kallona yana kiran “madam? Madam cikina ciwo! Madam mutuwa zan yi ,wayyo cikina” amma sam wai na kasa tashi daga kujerar da nake zaune,a gaban idona jini ya soma yi masa zuba ta ƙofofin hanci kafin kuma ya faɗi babu rai bayan yayi wata irin ƙara wacce daga nan na tashi daga baccin. Na yi miƙa tare da duba agogo sai na ga tuni lokacin sallah yayi,kawai na miƙe na je na ɗauro alwala na gabatar da sallar.Sam ban wani bai wa mafarkin da na yi muhimmanci ba sai ma takarda da na ɗauka na soma rubuta abubuwan da zan koyar da su gobe,bayan nan kuma sai muka hau yin hira da Inna A'i lokaci lokaci kuma ina chating abina. Ana kiran sallar magrib na tura wa Uncle saƙo kamar haka “barka da shan ruwa!” Sai ya maido min da amsa da “ azumin da kika yi sanadin karewarsa?” “Kamar ya?” “Eh mana Naf ɗanɗanon yawunki ma kaɗai ya isa ya karya min azumi,uwa uba kuma tattausan ƙirjinki” da ya turo min saƙon nan na karanta shi ya fi sau goma,ina ta juya kalaman cikin tunanina ina jin tabbas Uncle nada buƙatar ganin likita don kuwa na sha jin ana cewa in mutum ya daɗe bai yi aure ba to hankalinsa na yin rauni .Da wannan na yi masa uzuri na ce kawai bai da lafiya ne kuma na yi alƙawarin zan sanar da Daddy a sama masa magani. ★Uncle Salem Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida lafiya,duk yadda azumin nasa ya zama gurgu hakan bai sa shi ya ajiye shi ba.Wanka kawai yayi ya ci gaba da yin abinsa har aka kira magrib ya ajiye shi,ya dawo daga sallah kenan ya tarar da saƙon Nafisa .Cikin son nuna mata fa eh haƙurin nasa ya ƙare yasa duk ya cire nauyi ya soma yi mata magana cikin wannan salon.Yayi jiran amsarta amma shuru,kawai sai ya kira Daddy ya sanar da shi ya kamata a fara shirin yin bikinsu da Nafisa amma sai Daddy ya ce ya je can gida su yi maganar ido da ido tun da tuni ya sanar da shi bai samu damar zuwa dajin ba. Sai bayan sallar isha'i ya tafi can,a babban falo suka zauna Ammy ta kawo musu gasashen naman kaza da kuma shayi.Suna ci suna tuna baya, Uncle ne ya soma da cewa “ Abdul Hameed ka tuna lokacin da muna yara kai ne ke son gashen nama irin haka? ” Daddy yayi murmushi ya ce “a lokacin ai tantabaru ne muke gasawa,sannan muna samari ne ba yara ba” Uncle Salem yayi murmushi ya ce “ai kuwa dai ” “Kamar sati nawa kake ganin ya kamata a sa ranar bikin?” “Zuwa wata uku haka, lokacin an yi musu hutun makaranta a ranar da ta dawo sai a saka ta lalle” Uncle ya faɗa yana hasko tuni ga lokacin nan ya zo. “To babu damuwa ,amma ka samu ka sanar da Nafisar komai?” Daddy ya tambaya. “A'a tukuna dai amma ...” sai kuma ya ji nauyin abin zai ce kawai sai yayi shuru,shi ma Daddyn bai damu ba sai ma kiran Ammy da yayi ya sanar mata ,sosai ta nuna farin cikinta kafin ta fita.Bayan sun gama tattaunawa Uncle ya fito ya nufi flat ɗinsa,an gyara komai an share an goge.Wanka yayi ya shirya cikin bacci sannan ya soma yin wuridin da ya saba a kullum kafin kuma ya ɗauki wayarsa ya soma kallon hotunan Nafisa wanda a iya kallonsu kawai hankalinsa sai tashi yake yana jin buƙatar kasancewa da ita. ★ ƘWARGWAM Yau ma ban ci abinci da dare ba kawai cake na ci da chocolat,sai na saka wasu a jakata wanda zan baiwa Firdausi kamar yadda na yi alƙawari.Ina yin kwance na ce “Innarmu don Allah ki yi min gatana irin ta dogon ƙarni mai abin tsoro” “A'a Allah ya tsare ni Nafisa ,kin ga bacci ma zan yi don gobe ina son yi mana dambu tun da safe” ta faɗa tare da yin kwanciyarta gefe da ni.Na turo baki tare da lumshe ido,hoton abubuwan da Uncle yayi min duk suka dawo min.Sai wani abu nake ji yana bijiro min na shauƙi amma ban ma san taƙamaimai mene nake buƙata ba,amma sosai nake jin daɗin tunanin don abin da nake ji yana bani shauƙi sosai.Sai laɓana nake motsawa kamar wacce ke son Uncle ɗin ya ƙara shan su,a haka bacci ya ɗauke ni mai haɗe da mafarkinsa muna having sex.Yadda duk jikina ya amsa kamar a gaske yasa na buɗe idona dakyar da suka yi min nauyi,na duba lokaci a wayata sai na ga ƙarfe uku da minti uku na yunƙura na tashi zaune daidai nan hasken ɗakinmu ya ɗauke don dama ban iya bacci cikin duhu.Fitilar wayata na kunna sai dai tamkar wata wutar kyandir haka ta soma yin rawa kafin kuma ta ɗauke ɗif.Ban wani damu ba na sake ɗaukar wayar don sake kunnawa wannan karon cak screen ɗin ya ɗauka kafin kuma ta mutu da kanta. Daga bakin ƙofa na hango wata mace mai fararen kaya a tsaye gashin kanta na tashi cikin iska. “Wace ce?” na tambaya. “Deborat” ta bani amsa kai tsaye,kafin kuma ƙyaftawar ido tsundum na ganta kusa da ni a zaune muna kallon juna. Ido sune ƙofar hango ruhi, wannan yasa nake kallon ruhinta tun daga wajensa har cikinsa.“Ke ce kike yi min gatana kullum” na furta bayan na gama lalubo dukkan asalinta.Ba ta bani amsa ba sai jawo ni da ta yi ta kwantar ni kan cinyarta ta soma shafar sumar kaina,na lumshe ido don kuwa shafar irin dai ta matar da nake ji ce tana yi min haka duk dare.Sai dai wannan karon shafar ta babanta don tsintar kaina na yi a wani wurin, dube-dube na soma yi har na ci karo da allon sanarwa inda aka rubuta “DARASIN SANIN RUHANIYA” ina shiga ciki abun mamaki duk sai na tarar da kaf malaman nan da muka yi meeting da su,ga kuma su headmaster da principal su ma duk suna zaune yayin da Grand Maa ke koyar da karatu.Kamar wancan lokacin haka na zauna kusan Adama,na mayar da dukkan hankalina ga Grand Maa inda take cewa “kamar yadda vice headmaster ya faɗa muku lokacin meeting wannan school Ƙwargwam ta kasu kashi uku primary,da Sakandari sai kuma kuma Ajin Ƙwargwam wanda iya malamai ne kawai muke koyarwa” tana rufe bakinta na jefa mata tambaya,“Grand Maa me Ƙwargwam ke nufi?” “Matsafa!” ta bani amsa kai tsaye,sai na yi shuru ina tunanin zuci na ce ‘Ƙwargwam school na nufin MAKARANTAR MATSAFA? to amma su wane ne matsafan?’ Tamkar Grand Maa ta shiga zuciyata kuwa sai ta bada amsa ta hanyar cewa “darasinmu na farko shine chapter ruhi da gangar jiki,ta wannan hanyar ce ake gane matsafi” tana gama faɗar haka sai ta yi wani abu da hannunta nan take sai ga wani table ya bayyana a gabanmu,sannan a samansa wani yaro ne kwance babu kaya jikinsa da na dubi yaron sai na ga ba kowa ne ba face ɗalibina wanda ta baiwa biscuit a ɗazu ..... My book is only 500 vi 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [28/02 10:12] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ Last free page 10 Ganin Grand Maa ta ɗauki wuƙa za ta tsaga cikin yaron na yi saurin rumtse idona,ina jin sautin kururuwarsa yadda yake kuka yana cewa “madam ki cece ni kar ki bari su cutar da ni ” na buɗe idona da suka yi jawurrr na sake zuba su kan Grand Maa wacce ke zuba jinin yaron nan a kofi ta hanyar saka ludayi tana wani kwaso shi. Bayan ta gama sai ta kai kofin bakinta ta sha sannan ta miƙawa principal shi kuma da ya sha ya bai wa headmaster daga nan sai vice principal da kuma vice headmaster.Grand Maa ta ƙara karɓar kofin ta ce “lamba ɗaya sha ka bai wa lamba biyu,haka za ku dinga yi har kowa ya sha” wanda aka kira da lamba ɗaya na duba, kyakkyawan saurayi ne irin sosai ɗin nan kuma sai na ga yana kama da headmaster da dukkan alamu ɗansa ne,bayan ya sha sai ya miƙawa lamba na biyu shi kuma ya miƙo min na karɓi kofin ina kallon yadda jinin ɗalibina yake kwance a ciki mugayen matsafan nan sun mayar da shi lemun sha .Na kai kofin kusan bakina na yi kamar na sha kafin na miƙawa Adama wacce ita kuma ita ce lamba huɗu,so nake na ce mata kar ta sha amma idon Grand Maa ƙurrr suke kanmu ina ji ina gani Adama ta sha jinin kafin ta ba na kusa da ita a haka har kowa ya sha aka mayar da kofin. Daga nan sai Grand Maa ta yi wani siddabarun sai ga yaron da aka feɗe cikinsa ya tashi zaune daram da buɗaɗen ciki idonsa na shatatar da hawayen jini yana kallon tsakiyar idona har yanzu kuma bai gushe da neman taimakona ba sai dai sam ban san ya za a yi na taimake shi ɗin ba. Wasu kwalabe ta jera saman table ɗin,ta yi wani alama da hannu a nan take duk suka buɗe kansu.Bakinta na furta ɗalasiman tsafi ta dinga umartar ruwan da ke cikin kowacce kwalba da su je su shiga buɗaɗen cikin yaron,nan ya soma yin wata irin zabura kamar an jona shi da lantarki abin da na kasa jura kenan na ce “ōvovār̃ī” hakan yana nufin komai ya tsaya wato stop cak duk komai ya tsaya kuwa yayin da dukkansu suka soma amayo jinin da suka sha suna wani waro ido kamar za su mutu.Sam ban wani damu ba sai ma zuwa da na yi na ɗauki ɗalibina ,kamar yadda uwa ke gudun matsala ta samu ga ɗanta ko kuma in ta ga wani abu zai cutar da shi take ɗauke shi tare da ɓoye shi haka na yi wa ɗalibina na ƙanƙame shi gam a ƙirjina ina kallon Grand Maa wacce ke yin ƙarfin hali tana cewa “lamba uku ki ajiye shi kar lokacin kaddamarwa ya wuce duk ki ɓata mana shiri ki maido mu baya” Na girgiza mata kai na ce “ba zan bayar da ɗalibina ba” “Lamba ɗaya je ka ƙwato min abin farauta” Grand Maa ta basa umarni ai kuwa sai ya miƙe tsaye ya tunkaro ni,muna kallon juna cikin ido sai na ga tamkar na san shi yana dab da kawowa wurina kuma sai na tuna a inda na san idon,wato tsakakar ranar nan ce da na bugewa bindi.Na dubi ƙafarsa sai na ga yana yin ɗingishi,“kār̃bās!” na furta nan take kuma ya ɓangwale ya faɗi yana ihu,nan kuwa na ga hankalin headmaster ya tashi ya nufo shi duk da kuwa ƙoƙarin tsayar da shi da Grand Maa ta yi don ba a so kowa ya gusa daga wurinsa sai da umarni. Ta yo kaina za ta ƙwace shi da ƙarfi ni kuma da mugun sauri na bi ta rufin ɗakin na tashi sama cikin iska muka bar wurin.Ban san inda na ɓoye yaron ba amma tabbas na kuɓutar da shi kuma na basa tsaro,daidai nan kuma na tashi daga baccin saboda kiran sallar asubah da aka yi. Dukkan cinyoyina na ji suna yi min ciwo kamar wacce ta yi wasar tsere,dukkan abubuwan da suka faru da ni kuma sai na manta da su .Wanka na yi tare da alwala na zo na yi sallah,bayan na gama na soma yin Azkhar ina lumshe ido alamun bacci ne yake son ƙara yin gaba da ni amma kiran Uncle Salem ya shigo wayata na je na ɗauka tare da yin kwance na kara wayar a kunne. Yau shine ma ya gaishe ni da farko,na amsa cikin mayen bacci ina jin yana cewa “ mafarkin me kika yi Naf ?” Baccin da nake ji ne ya sake ni a nan take tuna na yi mafarkinsa mun haɗa shimfiɗa da shi muna mu'amalar aure ,amma me yasa yake yi min tambayar nan shine abin dubawa .Cike da gyatse na ce “kai wane iri ka yi?” Sai da ya saki murmushi kafin ya ce “mafarki na yi ga shi nan an kawo min ke gidana,muna kwance kan bed duk babu sutura a jikinmu ina yi miki zazzafan romance ke ma kina maido min da kuma na fara kusantarki sai kika fara yi min kuka kina kiran sunana Uncle Sal zafi ka bari ban so.Amma sai na soma rarrashinki har kika yi shuru kika bar kuka,Naf na ji daɗin mafarkin nan sosai kin ga yanzu ma da zan yi sallah sai da na yi wanka” Tun da ya soma magana na rumtse ido,wato shi ko kunya bai ji yayi mafarkin suna sex da ƴarsa sannan har wani labari yake bani.Ina ƙoƙarin kashe kiran ya tsayar da ni,“ Please Naf kar ki kashe min kira faɗa min yau ma kin yi mafarkin tsoro?” Jin ya canza akalar zancen yasa na yi shuru,sosai na tuna na yi mafarkin ban tsoro amma na kasa tuna abubuwan da suka faru. “Faɗa min me kika gani?” ya sake faɗa . Na ce “ni na manta komai” “Kin sha maganinki kuwa kafin ki kwanta?” ya jefo min tambaya,ni sam na ma manta da ya bani magani.Na ce “eh a'a...” “Baby ina ga ke ma kina son na zo kusa da ke shi yasa kike wasa da shan magani,amma babu damuwa duk weekend zan dinga zuwar miki” da sauri na ce “a'a ban so ka yi zamanka ” “Saboda me? Naf me yasa kike son hana cikar burinmu ne ? Haƙurina ya ƙare fa ina buƙatar kulawa kin san abin da nake ji duk dare? Da zazzafan feeling ɗinki nake bacci ina tuna surar jikinki na matsu na ji komai na jikinki a hannuna yana sarrafa shi ...” kuka na saka masa ina roƙonsa don Allah ya bari ban son irin wannan zancen daga ƙarshe na ƙara da cewa “uncle ka je asibiti don Allah likita ya duba ka” “Ke ce likitata domin ke kaɗai kike da maganin ciwona,kin ga yanzu ma duk kin tayar min da hankali ji nake...” ban bari ya ida ba na kashe kiran ina mai ci gaba da yin kuka. Inna A'i wacce ta fito daga toilet ta ce “in kin gama kukan sai ki tashi ki yi sallah” Na ɗaga kai na dube ta ina mamakin yadda aka yi ta canza min,na turo baki gaba na ce “Innarmu kin bar sona ” na faɗa ,ba ta kula ni ba ta haye dadduma.Ni ma tashi na yi na shiga toilet na yi wanka sannan na ɗauro alwala na zo na gabatar da sallah,ina Azkhar ina tuna mafarkin da na yi da Uncle Salem nan take kuma na soma jin jikina na saki har wani sanyi-sanyi nake ji yana rufe ni.Na je na ƙara haye katifa tare da jan bargo na rufa ina lumshe ido,karon farko da na ji ina muradin yin saurayi mu yi soyayya sannan aure ya biyo baya sai yayi min duk abin da Uncle ɗina yayi min cikin bacci.Da wannan tunanin bacci ya sake yin awon gaba da ni sai kuma na ci gaba da mafarkina daga inda na tsaya wato cikin wani daji na tsinci kaina.A gabana kuma wani ɗaki ne na kara,a bakin ƙofa wata tsohuwa ce zaune tana hura wuta amma ban ganin fuskarta. Na matsa kusa da ita na ce “Kaka jiya na yi ajiya a wannan ɗakin cikin dare” ko kafin ta ɗago idona ya sauka kan ƙusumbinta. Ta ɗago tana kallona,ganin mun san juna sai na sakar mata murmushi na ce “Kaka dama ke ce? Nan ne gidanki?” na faɗa ina nuna ɗakin. Ta jinjina kai kafin ta ce “ki shiga ciki yana nan yana bacci amma kar ki tashe ” Na shiga ɗakin sai na tarar da ɗalibina kwance bisan kunnuwan ganye yana bacci,fuskarsa kawai ake gani saboda yadda aka yi masa rufa da wata fatar dabba. “Ya samu rauni sosai Allah yayi sa'a ma kin kawo shi nan kan lokaci da saura ƙiris ya rasa ransa” Kaka ta faɗa wacce ta shigo hannunta riƙe da ƙwayar sai tururi ke tashi. Zama ta yi kusa da shi kafin ta yaye fatar,da sauri na kawar da kai ganin yadda ciwon nasa yake buɗe har yanzu. “Ki matso ki soma ɗinke masa cikin ” ta faɗa . Na juyo da sauri na ce “ni kuma?“ “Eh kin zata wa zai yi miki aikin?” ta faɗa tare da miƙo min wani mashi mai kamar wuƙa da kuma baƙin zare. Jikina ne ya soma rawa haka na zauna ina kallon yadda ta ƙara wanke cikin nasa tare kuma da zuba wani magani,hannu na kyarma na soma ɗinki yayin da ita kuma take faɗar wasu surkullen da ita kaɗai ta san ma'anarsu a haka har na ida. Na yi baya ina mayar da numfashi,ta tashi ta je can gaban wani babban teburi ta ɗauko min zuma ta bani na karɓa ina washe baki saboda ina son zuma kullum sai Uncle Salem ya bani ita tun ina ƴar yarinya. Zumar na soma sha muna kallon juna ni da Kaka kafin ta ce “ban san dalilin Deborat ba da ta zaɓi ta ɓoye miki baiwarki,amma na so a ce kin zama tamkar Kakarki Ayodele ciwon idon Mayu...” sai kuma ta yi shuru yayin da ni kuma na tsaya da shan zumar na ce “wai Granny Mamar Daddyna?” Ta jinjina min kai kafin ta ce “eh sosai ita fa! Kin san ita ma ba ta da tsoro kamar ke take,sai dai ita dukkan aikin da alloli da magabata suka saka ta yi tana sane da komai ba kamar ke ba da yake zuwar miki siffar mafarki” “Yanzu mafarki ne nake yi kenan?” “Kusan haka ne! Sai dai wannan muna kiransa da balaguron ruhi,wasu suna yinsa cikin bacci yayin da wasu kuma ke yinsa ido farke ” “Ita Kakata Ayodele ya take yi?” na tambaye ta,sai da ta saki wani murmushi kafin ta ce “in na tsaya baki labari ai ɓanar lokaci ne kuma ba za ki fahimta ba,amma MRS SADAUKI ta fi kowa iya bada labarinta shi yasa ta fitar da littafi na musamman dominta ungo” ta faɗa tare da miƙo min wani littafi ban kai ga duba sunansa ba na ji muryar Inna A'i na ce “Nafisa ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai fa har ta wuce” da sauri na ware idona tare da yaye abin rufa. “Littafin mene ne wannan babu kyawun gani?” Inna A'i ta faɗa tana yamutsa fuska. Sai a yanzu na farga da littafin da ke riƙe a hannuna,an yi masa cover da hoton matattu har da fatalwa na motsa bakina dakyar “MUTUWARE(Duk mai son jin labarin Ayodele sai ya tuntuɓe ni)” “Ki bar kirawo min mutuwa don Allah ” Inna A'i ta faɗa ,na yi dariya ina saboda na daɗe da sanin babu abin da take tsoro a duniya kamar mutuwa da kuma fatalwa,haka duk kusancinta da mutum ba za ta iya kwana da gawarsa ba. Sai da na yi dariya mai isata kafin na saka littafin cikin jakata sai na shiga toilet,ruwa na sauka a jikina mafarkin da na yi na yanzu ya faɗo min a rai abin da ya fi bani mamaki ta ya aka yi littafin ya bayyana gare ni alhalin cikin bacci aka bani shi? A nan take wani tsoro ya kama ni wanda zan iya cewa wannan ne karon farko da na taɓa jin tsoro game da ire-iren abubuwan nan. A gaggauce na yi wanka na fito na shirya, breakfast ɗina ma cikin kwano mai murfi Inna A'i ta saka min shi kafin na wuce can makaranta. Tuni kuwa dalibai sun soma zuwa,sai da na je na ajiye jakata a cikin aji kafin na fito na yi tsaye. Abun mamaki duk malamin da muka haɗa ido da shi sai ya harare ni,ciki kuwa har da Adama wacce ajinmu ke manne da na juna.Ina son yi mata magana amma sam ba ta bani fuska ba sai wani cijewa take. A haka har lokacin shiga aji yayi,na shiga ina mai yin tsaye tare da fiddo takardar liste ɗin ɗalibai na soma kiran sunayensu bayan na gama na ce “ akwai wanda bai ji sunansa ba?” “Madam ni ” na ji wata murya wacce ta min kama da wacce na sani,na juya inda na ji sautin sai idona ya sauka kan ɗalibina na jiya da dare amma fa sam ban gane wai shi ne ba saboda mafarkin da na yi na manta shi. “Mene sunanka?” na tambaye shi. “Abdul” ya bani amsa,hakan na nufin sunansa na cikin jerin farko na masu A .“Abdul wa me sunan mahaifinka?” nan ya faɗa min amma abin mamaki sam babu sunansa a liste ɗin. Na ce “kuma jiya da na yi kiran sunan ɗalibai ka ji naka?” “Eh Madam ” ya bani amsa. Ban ƙara cewa komai ba sai na fita zuwa ofis ɗin Grand Maa kamar yadda aka ce in wata matsala ta samu can za mu je.Tun daga bakin ƙofa na ji jinin jikina ya daskare yayin da kuma numfashina ya canza salon tafiya,dakyar na danna belt na neman izini ta bani izinin shigowa. Ina buɗe ƙofa na ci karo da lamba ɗaya ɗan headmaster shi kuma zai fita,yayi min wani mugun kallo kafin ya fice ni kuma na ƙarasa na gaishe da Grand Maa.Ciki-ciki ta amsa kafin ta ce “ me kika zo yi kuma?” tambayarta ta ce ta yi min wani iri amma na watsar da ita kafin na ce “ an manta ba a rubuta sunan ɗaya daga cikin ɗalibaina ba bisa liste ” sai na faɗi cikakken sunansa . Wani irin kallo Grand Maa ta yi min na kar ki raina min hankali kafin ta ce “ ai ba mantawa aka yi ba,ki duba liste ɗin da kyau” yanzu ma furucinta sai ya yi min wani iri,amma sai na yi kamar yadda ta ce ɗin na nutsu da kyau na duba liste ɗin sai na ga liste ɗin ta fara da lissafin lamba biyu,sannan a can sama ga sawun rubutu nan mai ɗauke da lamba ɗaya sai dai sam ya goge ba ka ma ganin abin da aka rubuta. “Me haka ke nufi?” na tambaye ta ina mai ɗaga kai ina kallon ta . “Kin ga Malama fitar min daga ofis ki bar yin kamar ba ki san komai ba,ni ba za a yi comedy da ni ba” ta faɗa cikin ɗaga murya tare da nuna min ƙofar fita,ganin yadda tuwon fuskarta ya kumbura har yana motsi ga idonta da suka rikiɗe suka zama kamar na Zombie yasa da sauri har ina tuntuɓe na baro ofis ɗin. Ina shiga aji sai na ɗauki biro na rubuta sunan yaron daga sama,sai na soma yi masu darasi har lokacin shan iska yayi.Kamar yadda aka sanar da mu cewa iya ranar Monday kawai a ba za mu fitar da yara aji ba a nan za su ci abincin da makaranta ta dafa musu,to yau suna da damar fita wannan yasa na ce su je su sayi abin da suke so amma da zarar sun ji ƙarar rawa su dawo. Kowa ya fita daga aji amma banda Firdausi,na dube ta tare da cewa “ke me yasa ba za ki fita ba?” “Babana ya ce bai da kuɗi” ta bani amsa.Abincina na buɗe muka ci tare bayan mun gama na bata chocolat tare da cewa “kullum zan dinga kawo mana abinci mu ci kin ji ko?” kai ta gyaɗa min alamun to.Haka ta yi ta mini surutu har lokacin dawowar ɗalibai yayi. Bayan sun shigo waƙa na soma koya musu sai na ga sun fi mayar ma da hankali a kanta,yadda duk suka shiga nishaɗi sai abun yayi min daɗi. Lokacin tashi ya gabato sai na yi zaune tare da fiddo liste ɗin sunaye,abun mamaki sunan Abdul da ni ce na rubuta shi ya goge babu shi.Shuru na yi ina sauraren bugun zuciyata da yake wani harbawa fiye da ƙa'ida,dakyar na aro jarumtar sake rubuta sunan nasa sai kuma na soma kira ɗaya bayan ɗaya har na gama duk sai aka zo fara ɗaukarsu har kowa ya watse. Ina fitowa muka yi kiciɓis da Adama na ce “madam Adama Barka da warhaka fatan kina lafiya?” “Bayan kin kusa kashe ni shine kike tambayar ina lafiya ? To nan sani ba” ta bani amsa tare da yin gaba fuuu.Na yi tsaye cak ina kallon ta kafin dakyar na ɗaga ƙafata na wuce zuwa gida,sai na tarar da Jabeeru direba muka gaisa a mutumce nan Inna A'i ce ke faɗa min Ammy ta aiko shi ya kawo mana abubuwan buƙata har ƙatuwar frigine wacce aka cika da kaji zuƙu-zuƙu. Bayan ya tafi ne na shiga na yi wanka na fito,ina zaunawa Inna A'i ta miƙo min kofi cike da madara tana cewa “ungo ki shanye ƴar autata ” ganin yadda ta yi min abin cike da soyayya yasa na karɓa na sha ba tare da na tambayi na mene ne ba. Sosai na yi ƙoƙari wurin watsar da duk abin da ya faru da ni a makaranta muka sha hira da Inna A'i kafin ta kawo min naman kaza wanda ta yi wa wani romo na musamman dama tun da na dawo ban ci komai ba sai na zauna na soma ci sai na ji tamkar ɗanɗanon magani amma ban yi magana ba na ci na ƙoshi. Inna A'i ta ce “zan fita na je kasuwa akwai abubuwan da zan sayo ” Na ce “kin san kasuwar ne?” “Taxi zan shiga,ba zan jima zan dawo” “To a dawo lafiya” na faɗa nan ta fice ni kuma saboda kaɗaici yasa na jawo wayata sai dai sam babu network a dole na ajiye ta na ɗauki littafin MUTUWARE ,tun a page ɗin farko na soma jin kaina na juyawa yayin da nake ganin kamar abin da ya faru ya taɓa faruwa da ni,da na tsananta tunani ne kawai idona suka hasko min abin da ya faru da ɗalibina Abdul a daren jiya.Na dafe saitin goshina da ya soma tsira min,ba tare da na shirya ba na kwanta baccin dole wanda ban yi niyya ba. Cikin wata kasuwa na tsinci kaina,sai tafiya nake ina waige-waige kamar mai neman wani abu.Yayin da hankulan ƴan cikin kasuwan duk ya dawo kaina kamar sun ga sabuwar halitta,har tambayar kaina nake mene ne suke kallo a jikina.Ban ɗauki dogon lokaci ba kuma na samo amsar,wato dogayen fuka-fuka ne a bayana sai motsa kansu suke.Ban kuma ɗauki lokaci ba na tashi sama ina baza idona ta ko ina ,can na hango Inna A'i tana ta sauri yayin da wata matsafiya ke take mata baya tana naɗe inuwar Inna A'i tamkar wata tabarma.Shuuu na dira a tsakiya cak matsafiyar ta tsaya tana kallona,“bani abin da ke hannunki ” na faɗa saboda kusan rabin kurwar Inna A'i na hannunta. Da sauri ta saka abin cikin kwagiri (wata jaka ce da tsofi ke ɗaurawa a ƙugu don zuba kuɗi) Ihun Inna A'i yasa da sauri na juya ta ɓangarenta,sai na ga ta faɗi na je da guduna ina kiran sunanta na tallabo ta.Ko da na waiga sai na ga babu matsafiyar babu alamunta,daidai nan na tashi daga baccin saboda kakarin mutuwa da na ji ana yi kusa da ni. Na buɗe idona a hankali da suka yi min nauyi,sai na ga Inna A'i ce kwance tana kakarin mutuwa jini na fita ta hancinta.Hankali tashe na ce “me ke damunki Innarmu?” Numfashinta kamar zai fita take min jawabi “a kasuwa ne wata mata ta bani ƙananun kifi na ci shine kawai na soma jin jiri,jikina kuma kamar ana cire min wani abu” Fatarta na kalla na ga ta yi wani mugun ja ga wasu sawun halittu tamkar dai kifin.Tsam na miƙe tare da saka takalmi,idona har wani rufe wa suke saboda ɓacin rai,ni kaina ban san wa nuna min kasuwar ba haka dai na samu kaina da tunkarar wata hanya har na isa.Allon sanarwar na duba inda aka rubuta ƘWARGWAM MARKET wato kasuwar matsafa,ƙafata na ɗora da niyyar shiga sai dai tamkar akwai wani abu da ke jana a baya wanda ya hana ni shiga ciki.Na gwada hakan ya fi shuren masaki amma na kasa,a ƙarshe ma dai sai zube wa na yi ƙasa a gajiye numfashina na shirin tsinkewa. Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank Sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 NB: Yanzu nake rubuta shi ,so don Allah kar ki zo kina ce min ke complet kike so Ni kaina banda shi. In kuma ya kammala 1k ne kuɗinsa. 30 Janairu 2025 [28/02 10:12] MRS SADAUKI: My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822. __________________________________________________ *PAID PAGE* 11 Daga inda nake yashe a ƙasa fitilun idona ke dallo min abubuwan ban mamaki,komai da ke wakana cikin kasuwar Matsafa .Dariya suke yi min suna zagina da sunan kasashiya,ban san ta ya aka yi ba har nake jin sautikan muryoyinsu alhalin akwai tazara sosai mai mugun yawa tsakanin inda nake kwancen da kuma ƙofar kasuwar. Fatun idona na soma lumshewa don dole,ina jin kaina na mugun sara min daga nan ban sake sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsinci kaina a gida. Da ɗan mamaki nake kallon ɗakinmu,har zan yi magana sai na ji dariyar Inna A'i ita da wata mata.Da sauri na miƙe na je na yi tsaye bakin ƙofar kitchen ɗin na tsura mata ido,ta saki murmushi kafin ta ce “kin tashi?” “Innarmu wannan ɗin wace ce?” na tambayi Inna A'i,ta bani amsa da “wata ƙawata ce ,kin ga je ki yi sallah kafin nake gama girkinki ” Ban ce komai ɗin ba na je na yi alwala na yi sallah,ina tsaka da yin lazumi su suka fito suka yi zaune kan tabarma. Ido na tsura mata ina don karantar wani abu sai ga shi kuwa na lalubo amsa ita ce matar da ta cece ni ta ɗauko ni daga kasuwa ta kawo ni nan,a cikin idonta na ga lokacin da ta buɗe gorar ruwa ta ɗura min su na sha sannan na ga hatta Inna A'i ita ce ta ceto ta daga mawuyacin halin da na bar ta. Yadda ta lumshe idonta ya katse min hanzari daga kutsen da na yi cikin tunaninta ba tare da ni kaina na san abin da na yi ɗin ba. “Mamar Sadauki na ce sai yaushe za ki bani labarinki?” Inna A'i ta faɗa . “Ki bari har zuwa dare in za mu kwanta” ta bada amsa tana mai buɗe ido,suka sauka cikin nawa da suke ɗauke da mamakin jin wai a nan za ta kwana. Na yi tunanin Inna A'i za ta yi ƙorafi akan haka amma sai na saɓani ,murna ma take da hakan. Haka muka zauna jungum har muka yi sallah isha'i,tsaf na shirya cikin kayan baccina na kwanta.Matar nan ta zo kusan kaina tana shafar gashina kafin ta ce “Naf?” wani irin tsammm na ji a jikina,ban amsa mata ba kuma ban juya na kalle ta ba kawai ta ci gaba da cewa “ke ba ki sha'awar jin labarin ainihin garin nan na Ƙwargwam?” Kamar mai tsoron yin magana na ce “ina so” ban rufe baki ba ta cire matashin kaina sai ta maye min gurbinsa da cinyarta. A nan take na ji wata nutsuwa ta shige ni cike da ƙaguwa na ce “Mama ki fara bani labarin mana” Inna A'i ta ce “ta bamu dai don ni ma tun ɗazu na ƙagu na ji” Wacce na kira da Mama ta yi murmushi kafin ta soma cewa “a wasu shekarun baya, lokacin ina da shekara ashirin ba ɗaya an yi wani zamani mai ban tsoro da tarwatsa ruhi.Duk dare na Allah haka za ka dinga jin ihuce-ihuce daga gidaje daban-daban wanda tsautsayi ya ja shi ya fita don kai agaji to ba zai sake dawowa ba ko gangar jikinsa ba za a gani ba.Duk wannan badaƙalar da ake yi babu wanda ya san taƙamaimai mene ne ke faruwa,sai sannu a hankali duk kowa ya fahimci akwai wanzuwar fatalwa a cikin garin namu.Manyan abin harinta su ne maza da ƙananan yara sai kuma ƴan mata,haka ta dinga yi wa garinmu ɗauki ɗaiɗaya har ya kai zawarawa sun fi yawa sannan ƴan mata sun yi ƙaranci.A daidai wannan gaɓar ne iyayena suka yanke shawarar haɗa ni da wani malami na garinmu,duk da ban sonsa haka na yarda na aure shi domin tsira da rayuwata.A ranar da aka kai ni gidana a wannan rana ce kuma wannan fatalwa ta kai hari a gidanmu,cikin ikon Allah na amsa sunan matar aure a wannan daren na zama cikakkiyar mace.Yadda ake buga ƙofar gidanmu haɗi da wani kuka ana cewa “malam taimako ! Taimako aljanu sun taso wa ƴata” shi yasa malam ya zura jallabiya ya fita don dama aikinsa ne yin ruƙiya....” sai ta yi shuru,da sauri na ɗaga kai na dube ta sai na ga idonta sun yi ja jawur ga ƙwalla na haɗuwa a cikinsu. Gabana ya faɗi ,murya na ɗan rawa na ce “kar dai ace shi ma fatalwar ce ta tafi da shi?” Ta jinjina min kai kafin ta ce “tun da ya tafi bai dawo ba,a ranar na yi kuka kamar raina zai fita.Tun ina lissafin kwanaki har na koma yin na wata ,a ƙarshe na tattare na koma gida.Sannu a hankali cikina ya soma girma har ya shiga watan haihuwa,to a lokacin ne fa na fara yin mafarki mai maimaici tun ina ɗaukar abin wasa har na fara jin tsoro na sanar da iyayena nan suka shaida min cewa ana son na sadaukar da yarona domin farin cikin al'umma.A lokacin ban gane abin da ake faɗa ba sai ranar da na haihu na ga Ummana na gyara jariri ta saka shi cikin wani ɗan basket,ta dube ni ta ce “Rumana ki sadaukar domin al'umma ta rayu cikin aminci,kar ki yi jayayya da abin da magabatanmu suka zartar kawai abin da nake so ki yi haƙuri ki daure wata rana yaronki zai dawo miki” sam sai na ƙi fahimtar Umma na karɓe yarona na rungume,a cikin wannan daren kuma muka ƙara samun ziyarar fatalwa .Abun sam bai yi min daɗi ba,a gaban idona ta kashe dukkan iyayena ta tsotse jininsu ta bar su nan.A washegari mutane suka cika gidanmu,sai aka fara zagina ana cewa ni na kashe su kan in ce wani abu aka fara jifana da duwatsu.Dole dangin naƙi tasa na bar gidan,hanyar daji mai tsarki na nufa wanda zamanin Kakani da iyaye suke kiransa da wuri mai tsarki da ruhika masu kyau.Ina ratsa tsakiyar dajin na soma jin wani yanayi na daban a jikina,sai na soma waige-waige can na hango lilo na yara wanda ake kwantar da su haka na je na ajiye jaririna da ko suna ba a saka masa ba.Ina gama ɗora shi sai wani haske mai ƙarfi ya rufe shi har ban iya ganinsa, wata murya ta ratsa dodon kunnena tana cewa “barka da zuwa uwar Sadauki,ababen alƙawari da tsarkakun ruhika na alfahari da ke a bisa wannan sadaukarwa.Ki juya ki koma gida cikin aminci,daga yau kina kan kariyarmu ” ana gama faɗa min haka na juya cike da kewar ɗana,ga mamakina ko da na koma can cikin gari sai na ga ana bani wani girma na musamman.Tare da ni aka yi hidimar yi wa gawar iyayena sutura,bayan nan kuma na zauna ni da sauran dangi muna karɓar gaisuwa” sai kuma ta sake yin shuru. Na dubi ɓangaren da Inna A'i take sai na ga duk ta takure wuri guda tana kyarmar tsoro,na tuntsire da dariya kafin na dubi matar na ce “ to amma Mama ya zancen fatalwa?” “Tun daga wannan lokaci ba ta sake saukowa doron duniyar bil'adama ba,sai dai ta gurɓata mana gari wanda ya koma na matsafa” ta bani amsa. “Ya ake gane matsafi?” na tambaye ta,ba ta bani amsa ba sai ido da ta tsura min har sai da na tsargu na ce “ Mama ya kike kallona haka sai ka ce ni ma dai MATSAFIYA(MRS SADAUKI) ce” “Wane ne matsafi Naf?” ta jefo min tambayar. Kai tsaye na ce “mai shan jini” Sai ta girgiza kai ta ce “a'a ba ita ce amsar ba,a duniyar Ruhaniya sun fassara matsafi cewa duk wanda zai iya juya wani matakin iko ko kuma ya iya karantar tunanin wani to matsafi ne.Sai dai matsafan sun rabu kashi biyu,tsarkaku da kuma masu mugunta.Misali ni da ke ai kin ga aikinmu shi ne ceto al'umma,yayin da kuma tsohuwa mai kifi take muguwa” “Ni da ke kuma? A'a ni ba matsafiya ba ce,Mama faɗa min ita tsohuwa mai kifi matsafiya ce ko mayya?” na tambaya sai dai ko kafin ta bani amsa Inna A'i ta fasa wani uban ihu tana cewa “wayyo idona” Da wani mugun sauri duk muka miƙe tsaye,Mama ta ce “dama ai zuwanki nake jira shi yasa ban tafi gida ba.Ki bayyana kanki kafin na binciko ki ” Na dube ta na ce “Mama ke da wa kike magana?” dariyar da aka ƙyalƙyace da ita ne yasa na samu amsata,na waro ido duk da ina son labarai da kuma horror film amma ai ban taɓa ganinsu a zahiri ba wannan yasa tsoro ya kama ni ashe hakan kuma shine babban kuskurena.Saboda ina firgita duk tsikar jikina ta tashi wannan kuma ya bayyana ɓoyayyar siffata wacce ban san da ita ba sai gani na yi akaifuna na ƙara yin tsayi suna yin tsini daidai nan kuma tsohuwa mai kifi ta bayyana a gare mu.Sai na rasa da wacce matsalar zan ji,dukkan jikina rawa yake. “Hahaha! Ƙaramar matsafiya har ke ce za ki wani je tare ma wani faɗa?” tsohuwar ta faɗa tana kallona kafin ta mayar da dubanta ga Mama ta ce “ oh! Uwar Sadauki ko kashe ni za ki yi irin wannan hassala?” jin furucinta yasa na juya na dubi ɓangaren Mama,wani uban ihu na fasa tare da rugawa can kusurwar ɗaki ganin Mama ta juyar da idonta sun koma farare tasss kamar madara. Nan dambe ta kancame a tsakaninsu har suka iso inda nake , tsohuwa mai kifi ta kama ƙafata ta gantsara min cizo ban san lokacin da na fasa wani mahaukacin ihu ba.Cike da jin haushi na caka mata yatsuna gefen wuyanta,zoben hannuna sai ya soma fitar da wani haske kafin can tsohuwa mai kifi ta ɓace ɓat. Hannuna ya dawo normal sai dai inda ta cije ni ya fasa,da sauri Mama ta nufo ni tare da cire kallabinta ta ɗaure min ƙafar. Ƴar ƙaramar jaka ta buɗe ta fata ta fiddo wasu abubuwa waɗanda na sha ganinsu wurin Uncle Salem.Hawaye na soma saboda ban son shan maganin nan,ina ji ina gani ta sa wata ƴar ƙaramar wuƙa ta tsaga ƙafata na ƙwalla wani uban ihu ina kiran sunan Uncle haka ta saka min magani kafin ta naɗe min ƙafar,sai ta bani maganin nan da ke kashe min jiki yana jefa ni duniya biyu mabanbanta.Baccin na gama ɗaukata kuma na tsinci ruhina a ɗakin darasi na matsafa,ina shiga sai na ji lamba ɗaya na cewa “ƴar rainin hankali sai yanzu kika damar zuwa?” ban kula shi ba na je na zauna kan kujerata na maida hankali kan darasin da Grand Maa ke yi.Yau kuma zane ta yi a jikin allo na wasu halittu maras kyawun gani kafin ta ce “a yau zan nuna muku yadda ake mayar da abin da ba yiyu ba a zai tabbata,sai dai ku sani hakan a iya ɓoyayyar duniyarmu da kuma masu irin ido uku kawai za su iya ganin abubuwan nan.Ba komai ne wannan abin ba sai fitar da abin da ka zana da hannunki izuwa wannan duniyar,wato ka mayar da zane gaskiya ta hanyar saka masa RUHIN ALJAN(MRS SADAUKI) bari na nuna muku kan wannan zanen” ta faɗa tare da taɓa wani zanen maciji tana faɗar formula na tsafi,sannu a hankali kuwa macijin ya soma yin motsi kafin kuma ƙyaftawar ido ya sauko ƙasa yana buɗe baki .Grand Maa ta ɗauke shi da hannu tana dariya kafin ta ce“kun gani babu wuya ko? Principal raba musu takarda da biro kowane daga cikinku ya zana abin da yake so” haka a raba mana takardu kowa ya shiga zanen abin da yake so,ni sai na rasa ma me zan zana can kuma na soma yin zanen ina murmushi ba tare da ni kaina na san mene ne zan zana ba a haka har na kammala. Wasu takardun aka sake raba mana masu ɗauke da harafofin tsafi,Grand Maa ta ce su ne za mu karanta domin kawo abin da muka zana izuwa duniya.Bakina na soma motsawa ina kafen zanen da ido kamar yadda ta koya mana,kamar almara kuwa haka na ga ya soma yin motsi sai dai fa ya ƙi yin sauri kamar na kowa tun da tuni suka fara yin shewa suna jin daɗi wasu har sun fara yi min dariya. Grand Maa ta ce “lamba uku ki nutsu da kyau ki aje esprit ɗinki wuri guda don aikin na son nutsuwa” ba tare da na ɗago na dube ta ba na jinjina kai tare da ci gaba da yin fafutukar fiddo shi amma ya ƙi,hakan ya hassala ni na ɗaga murya ina karanto harufan “huhannn!” zanen yayi wani irin kuka da yasa na zabura yayin da ajin yayi tsit. Kowa ido ya buɗe da baki yana kallon abin da ya fito cikin zanen da na yi,yayin da Grand Maa tsabar tsoro ta ƙanƙame principal. Da sauri na lumshe ido jin Dragon 🐲 ɗin ya soma lasar fuskata yana yin wani kuka kuma,na buɗe idon tare da kai hannuna na soma shafar saman kansa. Headmaster na gani da sauri yana goge dukkan zanen da aka yi kan allo.Yadda na kafe shi da ido ƙila shi yasa Dragon ɗina kallon wurin,yana ganin sauran zanen da ba a goge ba ya fara yin wani kuka da yasa duk halittun da ƴan uwana suka zana suka soma ɓuya yayin da kuma Ajin ya soma girgiza takardu na tashi sama. Headmaster jiki na ɓari ya bar jikin allon ganin my dragon ya soma feshin wuta yana ƙona dodannin da ke jiki.Kafin daga ƙarshe ya soma feshin wuta ta ko ina babu shiri duk suka shiga guduwa yayin ni kuma na yi tsalle na haye bayansa kawai sai ya tashi da ni sama yana shawagi. “Nafisa? Nafisa?” na ji muryar Inna A'i na tashe ni,na buɗe ido dakyar ina kallon ta kafin na ce “lokacin sallah yayi?” Ta ce “ina fa ! Gobara ce aka yi can cikin makaranta shine headmaster ya ce a tado ki” Na miƙe ina kallon bakin ƙofa sai na gansa a tsaye sai gumi yake,na ce “to ni da ba namiji ba mene ne kuma abin tada ni kai agajin kashe gobara?” Wani kallo ya watso min irin yana cike da takaicina ɗin nan,kafin ya haɗiye wasu yawu har sai da na ji ƙarar muƙut .Ya ce “ki zo mana Malama Nafisa duk kowa fa ya fito ke ake jira” Ina shirin yin magana aka buɗe ƙofar toilet sai na ga Mama ta fito hannunta riƙe da bokitin ruwa,ta miƙa min shi tana cewa “ki dai je ai taimako babu ruwansa da mace” na karɓi bokitin na zura takalmina ko hijabi ban saka ba haka na fita zuwa can inda wutar ke ci ,abun mamaki a wuri guda take sannan duk ƙoƙarin kashe ta da suke ta ƙi raguwa amma ina watsa ruwa ɗaya da bokiti ta soma mutuwa ko minti biyu ba a yi ba kuwa duk komai ya tsaya cak sai biɗiɗin hayaƙi da yake tashi.Da yake ni har yanzu doluwa ce sam ban ga abun almara ne ba koma wanda hankali bai ɗauka,sai ma murna da na yi wutar ta mutu.Na juya zan tafi na ji muryar Grand Maa na cewa “ina za ki je? Kin ɗauka haka za mu bar ki ne ki tafi bayan duk uwar asarar da kika yi mana” Da mamaki na ɗago ina dubanta,sai kuma na ga dukkan sauran malaman sun zagaye ni kowane yana murmushin mugunta....