KARNI UKU Book 1 Writing by MANSUR USMAN SUFI SARKIN MARUBUTAN YAƘI 08137237071 ƘASAR MADINATUL-BARNAWIY Kasaitaccen ɗakin taron ya cika ya batse da manyan sarakuna,Bokaye,matsafa haɗe da jarumai. Duba ɗaya zaka yi musu ka fahimci cewa akwai wani muhimmin al’amari daya taru a wajen. Tsawon daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali babu wanda yace ƙala. Daga bisani ne wani dattijo ma’abocin ƙasumba da gemu farare sol!, Mai ɗauke da yanayin ɗaure fuska. Yayi gyaran murya ya dubi jama’ar dake ɗakin taron yace “yaku yan uwana sarakuna da sauran mahalarta wannan taro mai albarka, dafarko ina yiwa kowa Barka da zuwa. Babban abinda ya tara mu anan shine tabbatar da tsafi a doran ƙasa, wanda hakan bazai taɓa tabbata ba face an ɓatar da ma’abota addinin Musulunci a doran ƙasa. Sanin kanku ne cewa dakushe hasken musulmi abune mai matukar wahalar gaske, matukar muna son cimma wannan buri namu dole sai mun jefa musulunci cikin saɓon Ubangijinsu. Daga lokacin da na fara wannan nazari da sauran Yan uwana sarakuna, mun fara cimma nasarori masu yawa, sai dai a halin yanzu ne zamu kama aikin gadan-gadan ta hanyar haɗa karfi da ƙarfe, domin masu iya magana na cewa hannu ɗaya baya ɗaukar jinka. Ubangiji na faɗa a cikin littafinshi mai tsarki cewa “idan Musulmi suka bauta mashi yadda yake so, zai basu rayuwa mai daɗi tare da ‘ya’yansu da jikokinsu. Sannan a sunnah ya tabbata cewa su musulmi kamar ginin daƙi ne mai kusurwa huɗu, kowace katanga tana karfafawa ne da yar uwar ta, ma’ana dazarar rabuwar kai ta shiga tsakaninsu kodai ta fahimtar addini ko kabilanci da al'adun yau da kullum,to daga nan zasu samu nasara murƙushe. Lokacin da dattijon da ake kira da suna urwat ɗan Abbas yazo Nan azancenshi sai dukkan wanda ke cikin ɗakin taron ya cika matukar mamaki jin yana karanta littafin Allah tamkar yakasance musulmi. Urwat ya cigaba dacewa “Dukkaninmu yan uwa ɗaya ne kuma dangi ɗaya, koda akwai babban jinsi da birane,amma kada mu manta abune ɗaya ne ya haifemu shine, tsafi, bautar gumaka. Fiye da shekaru arba’ina lokacin ina samartaka, ina rayuwa. A cikin musulunci,babu wani abu nasu dabani da sani a kanshi walau ta fuskar ilimin addini ko zamantakewa. Lokacin da yazo nan a jawabinshi sai dukkan wanda ke cikin ɗakin taron ya cika da matuƙar farin ciki,urwat ya gyara zama bisa kujerarshi ya, shiru ne ya kuma mamaye ɗakin taron a karo na biyu. Sarki sha’aran yayi gyaran murya yace “Bayan dukkan bayanin da sarki urwat ya kawo yanzu, akwai waɗansu muhimman abubuwa da ya kamata mu lura dasu anan, mafi yawan suna burin ganin sabon al’amari na cigaba a wajen su koda ta hanyar karama(almara). Ko kuwa ta ƙirƙira, bazasu taɓa damuwa ba koda ya saɓa da addinin su zasu ƙarɓeshi hannu biyu, har wasu ma na ganin idan malami baya karama,to bai cika mai tsoron Allah ba. Yanzu dukkan shiryen mu sunyi nisa, mun tura dukkannin mutanenmu izuwa biranen manyan dauloli musulmi, bayan sun samu horo akan dukkan da muka ɗora su akai, daga cikin nasarorin da muka samu. Akwai kwaɗaitawa mata da son wassanni, koyarwa da mata dubarun zama da mazajen su na tsarin zamani da al’adunmu, Domin gurɓata zaman su da mazajensu, Sannan duka Littattafan da muka wallafa Dake yaƙar gaskiyar dake cikin addininsu, yanzu abinda ya rage mana a gaba shine a mako mai zuwa zamu tura rukuni na ƙarshe daga jama’armu ta zasu tafi ƙasashen a matsayin yan gudun hijira, waɗanda a cikin su ne zamu basu muhimman makamai masu barazana ga dukkan wata halitta mai numfashi, gami da sirrikan tsafi. Lokacin da sarki sha’aran yazo nan azancenshi sai yayi kowa dake ɗakin taron ya cika da matukar farin ciki maral misaltuwa. Daga wannan kowa ya tattare tawagarsa ya fice daga ɗakin taron. ***** Yanayin gidan sarautar ya ƙawatu ainun da fiye da misaltawa, idan mutum yakai dubanshi izuwa ga wani ɓangare da yafi ko ina ƙawatuwa zai yi arba da kuyangi,barorin,hadimai gami da dakarun shirye cikin shigar yaƙi na ta kai komo,suna aiyuka. Wata kuyanga ce matashiya ɗauke da kayan marmari dangin ridda, ayaba da jini, a cikin wani kwandon kaba, ta doshi wata turakar, tana iso masu gadi suka bude mata kofar shiga ta kunna kai izuwa cikin gami da yin sallama. Shiru taji batare da an amsa mata ba, kuma tana iya jiyo alamun motsi a turakar,haka dai ta cigaba da tafiya sannu a hankali tana huce kofofin turkar, har ta iso inda take sa rai zataga gimbiya. Salati gami da tasbihi ta dunga karantawa a ranta, har idanun ta sun fara cikowa da kwalla, tana mai runtse su tamkar tayi arba da mutuwarta ƙirjinta na bugawa da sauri,ta saki kwandon dake hannun ta kayan marmarin dake ciki suka tarwatse ta hanyar watsuwa a turkar. Duk da motsin da ya bayyana na tarwatsewar kayan marmarin, bata sanyasu dawowa cikin hayyacinsu daga saɓon Ubangijinsu ba. Da sauri ta juya domin komawa da baya, zuciyar ta cike da matuƙar ɗimauta, taya ya za’a aikata wannan mummunan saɓon Allah a gidan sarautar musulunci, tabbas sai na bayyana wannan al’amari ga mai martaba sarki koda kuwa hakan zai zamo ƙarshen numfashina a duniya. Haka dai ta cigaba da tafiya da sauri har tana tuntuɓe, domin ta isa hanyar da zata sadata da fada. Fadar ta cika ta batse da manyan fadawa, talakawan gari haɗe dakaru, kowa na zaune cikin ladabi da girmamawa. Sarki Anwar na zaune a bisa karagarshi ta mulki,sanye da tufafin alfarma irin na hamshaƙen sarakai, hannunshi riƙe da cazbaha,yana jan addu’o’i, Ana tafiyar da sha’anin mulki cikin lumana. Wani dattijo ma’abocin tarin shekaru da cikar kamala yayi gyaran murya cikin ladabi ya dubi mai martaba sarki yace”ya shugabana ina wani labari da na samu daga shugaban masu kula da hidimar masallaci cewa, kwana biyu an samu raguwar matasan mu wajen fitowa sallar asubahi, Haƙiƙa hakan babban abin takaici ne sosai,a shawarata kodai a faɗakar da iyaye illar Hakan ko kuwa a sanyawa dukkan wanda yaƙi fitowa sallar asubahi haraji matsawar bada wani uzuri da addini ya amince dashi ba. Wani mutum daga cikin fadawan sarki da shekarunshi basu gaza arba’in ba, yayi gyaran murya yakawo Gwauron numfashi ya ajiye ya dubi dattijo mai suna Salman yace” Allah ya shugaban majalissa a rawa fahimtar a cikin littafi da sunna, babu wani waje da ake iya tilasta mutum ibada, ballantana ace idan yaƙi yi a sanya mashi haraji, domin ita ibada ana yin ta ne cikin daɗin rai . Ko da jin wannan batu daga bakin Hakimi urwat sau fadar tayi shiru tamkar mutuwa ta kawo ziyara, duk wannan tattaunawa da ake yi sarki yana ji bai ce uffan ba, sai da ya fahimci tattaunawar zata haifar da damuwa, sai yayi gyaran murya yace” yaku fadawana kuyi sani cewa wannan magana da shugaban majalisa ya kawo na da matukar muhimmanci ainun sai dai ni akwai wata matsala dake ganin tana gaba da wannan kuma dare da rana da ita nake tashi,wannna matsala ba wata ba face yawaitar yan gudun hijira daga waɗansu birane dake zuwa wannan ƙasa tamu, domin samun mafaka, hakan baya rasa nasaba da tashe-tashen hankula da ake samu a birnin Nuraniyyu. A makon da ya gabata labari ya riskeni cewa a wannan makon an kai wani mummunan hari a masallaci a lokacin da ake gudanar da sallar asubahi, tabbas wannan abun baƙin ciki ne da damuwa daya kamata mu kula sosai ta hanyar ƙarfafa tsaro tare da ba wa mayakan mu horon yaƙi. Uwa uba kuma shine tsayawa bisa tafarkin da magabata suka ɗora mu akai…..! Kafin sarki ya ƙarshe maganar sai ya hango kuyanga ihsan ta shigo fadar hankalin ta a tashe tana haki,tamkar numfashinta zai ƙare. Sarki Anwar ya mayar da dubanshi izuwa gareta domin yaji shin mene ne ke tafe da ita. Lokacin da yazamana cewa saura taku huɗu tsakanin ta da karagar mulki sai ta zube ƙasa bisa gwiwoyinta ta kwashi gaisuwa. Sarki ya ƙarɓi gaisuwar cikin annuri. Ihsan ta buɗi baki ta buɗi baki da nufin tace wani abu amma koda ta haɗa idanu da Hakimi urwat sai taji bakinta yakasa furta komai, tsawon daƙiƙa ashirin tana ƙoƙarin hakan amma ya gagara, Al'amarin da ya sanya sarki da sauran jama'a suka cika da mamaki kenan bisa ganin tana magana da Yaren kurame. Sarki ya dubeta yace" yake ihsan shin ina dalilin wannan hali da kike ciki, me kike son fahimtar dani?. Hawaye ne ya shiga shata ta daga idanun ta bisa ganin halin da take ciki, tana mai tambayar kanta akan ranta tana mai mai cewa shin ina dalilin rashin yin maganata, koda wani ne yayi mini wani sihiri, amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenan. Urwat ya saci kallonta gami da murmushin mugunta, wanda waziri ne kaɗai ya lura da hakan. "Ta yiwu akwai wata rashin lafiya ce ta same ta, ranka ya daɗe ina ganin yana da kyau mu tafi zuwa masallaci domin lokacin sallar azuhur yayi. Hakimi urwat ya faɗa cikin ladabi". " Zancen ka dutse yakai urwat". Sarki ya faɗa tare da kallon in da hasken rana ya ratso a fadar. Ya ɗorawa batun shi da cewa "A kai ihsan izuwa wajen 'yar mai ganye domin a duba lafiyarta, Ka dawo da ita izuwa gareni, haƙiƙa na tabbata akwai wani muhimmin al'amari da take son sanar dani, domin na aminta da ita matuƙa. Ya ƙare zancenshi yana duban wani bafade, saurayin mai yanayin kazar-kazar dake tsaye a hannunshi na dama. " An gama ya shugabana Bafaden ya daɗi cikin ladabi, ya juya ya nufi kofar fita daga fadar taɓa mai yafito ihsan da hannu dake yi mata nuni ta biyo bayanshi, Da sauri ta miƙe tsaye tayi koyi dashi suka kule izuwa wajen fadar. Sarki ya sauko bisa karaga ya taka matattakalar fadar ya sauko ƙasa ya durfafi wata kofa ta musamman dogare da sandarshi, dakaru,hadimai tare da hakimai suka mara mashi baya, sauran jama'a sukayi koyi dasu, domin isa zuwa masallaci. Kafin a isa masallaci sai Hakimi shaibat ya shafi wani gurin tsafi a damtsen hannunshi na dama ya ɓace ɓat!. Sarki shaibat ya juya domin ya amsa sallamar da wani mutum yayi mashi, ai kuwa sai idanuwanshi suka sauka a saitin inda Hakimi shaibat ke tsaye a can gefenshi, take yaga wayam Babu alamun shi, Batare da bari wani daga cikin jama'arshi ya lura Bai bayyana ako ina ba sai a daf da kofar fita daga gari, kai tsaye ya durfafi kofar, yayin da dakaru suka hangoshi sai suka miƙa gaisuwa gareshi tare da yi masa sallama yana amsawa, waɗansu dakaru a gefe ya hango sun tare waɗansu samari uku da fuskokin suke ke rufe da bakin rawani suna ɗauke da waɗansu bujjuna a bisa kan amalanke. Sannu a hankali yana takawa har ya isa gare su. Mene ne ke faruwa ana ? Urwat ya tambaya a taƙaice. Wani saurayi mai tarin ƙasumba ya risina gareshi cikin ladabi ya buɗi baki Muryar na rawa yace " ya shugabana muna binciken buhhunan da suke ɗauke da sune domin tabbatar da tsaro. "Shin baka da sanin cewa dukkan kayan daga gareni suka fi to?". Urwat ya tambaya fuska a murtuke. Tuba nake ranka ya daɗe insha Allah hakan bazai sake faruwa ba. Badakaren ya faɗi. Cikin hanzari samarin suka tura kayan suka huce gaba. Badakaren ya bisu da kallo yana ƙarewa buhhunan kallo yana son fahimtar wani abu, har suka ɓace gareshi ya daina hangoshi. Wata unguwa urwat ya nufa data saɓa da wacce samarin uku suka bi, da shigar unguwar ya durfafi wani gida yana isa tamkar an san da zuwanshi aka wangame kofar gidan ya kunna kai ciki. Zaune ya isar dasu suna shan barasa suna ta ƙyaƙyata dariyar mugunta, samarin uku da ya baro a hanyar kofar gari ne Waje ya samu ya zauna bisa wata kujera yana mai fuskantar su a lokacin da suka nutsu domin suji bayanin dazai yi musu. Ina fatan dukkan kayan mu mun kammala yadda ake buƙata? Urwat ya tambaya. Wani daga cikin matasan mai yanayin shiru- shiru shine ya yiwa sauran samarin biyu Indiya ta wutsiyar idanu, da sauri suka miƙe tsaye suka nufi bangare a ɗakin sauko waɗannan buhhunan suka zo suka ajiye a daf da inda urwat yake suka buɗe buhhun. Urwat ya ɗora idanuwashi akan buhunan domin yaga abinda ke ƙunshi a ciki. Motsin alamun sawaye suka ji na kusanto da ɗakin, al'marin daya sanya dukkanin su sukayi turus kenan domin ganin abinda ya bayyana gare su zukatansu cike da matuƙar al'ajabi domin kuwa a iya sanin su babu wanda ya san da wannan gida na sirri face su huɗun kacal. Wannan shi ne abinda ya wakana a ƙasar madinatul-barnawiy. **** Al'amarin Bafade da ya tafi da kuyanga ihsan izuwa gidan 'yar mai ganye domin zartar da umarnin mai martaba na duba lafiyarta. Lokacin da suka kaɗaita a cikin turkar 'yar mai ganye sai Bafaden ya zayyane mata dukkanin saƙon da yake ɗauke dashi izuwa gare ta daga wajen mai martaba. Ko da jin wannan batu sai yar mai ganye ta ƙura wa ihsan idanu kuma ta hanya hannunta ta gwale idanun ta na dama, bayan ta kammala bincikenta, sai ta dubi Bafaden ta buɗi baki cikin murya mai tattare da alamun dattijantaka tace. "Dukkanin ƙoƙarin da nayi domin na gano irin nau'in cutar dake damun ihsan hakan ya fasƙara, Kawai abinda na ɗan fahimta shine an yi amfani da sihiri ne a lalurarta. "Ni kaina ina zargin hakan matuƙa. Bafaden ya faɗi. "Yanzu Ina ganin zan gwada yi mata addu'o'i ku Allah zai sa a dace. 'yar mai ganye ta faɗa, gami da sanya hannunta ta buɗe bakin ihsan, ta shiga karanta Ayatul-kursiyyu tana Tofa mata a ciki. Lokacin da ta kammala karatun bisa mamaki sai suka ji ihsan tayi Atishawa da ƙarfi ta buɗi baki tace "Alhamdulillah. Nan fa Bafaden da ihsan suka cika da matukar farin ciki maral misaltuwa suka yi salati ga Annabi s'a'w domin nuna godiya ga Allah (SWT). Su kayi sallama da yar mai ganye domin komawa ga mai martaba sarki. Kasar Madinatul-barnawiy Wane ne sarki Anwar ? Kuma mene ne dalilin daya sanya Musulmi suka fara samun matsaloli a cikin al'ummar su tun daga tushe? Dalilin haka kuwa shine kamar haka. Sarki Anwar ɗan Adam yakasance mutum mai matsakaicin kyawu da shekaru yana tarin ilimin addini da son ganin ya kyautata al'ummarshi, bisa wannan dalili ne yasanya kowa ke zaune lafiya, manya na tausayawa ƙanana, na ƙasa na girmama manya, babu cuta babu cutarwa, kuma dukkan wani fabatake da ya shigo birni sai limamin dake yankin ya ganshi kuma ya tabbatar da cewa ga daga inda yazo domin tabbatar da tsaro. Miji na sauƙe haƙƙin iyalanshi, mata na yin biyyayya ga mai gidanta, duk wanda ya aikata laifi tsakanin babba, Attajirai da talakawa ana yanke hukunci babu bambanci. Bisa wannan dalili ne yasanya dukkan al'umma ke zaune cikin aminci, kwatsam sai aka wayi gari da waɗansu a yarin fatake dake ɗauke da malaman addinin Musulunci ƙarƙashin wani shehun malami mai suna sheik Habib al-attad. Kansancewarshi malamin addinin Islama ɗaya tara ilimi wannan yasa ya samu shiga a wajen sarki Anwar har ya zama na hannun damar shi bisa wannanne ya sanya sheik Habib yayi amfani da wannan dama wajen jefa sabbin gurɓatattun aƙidoji domin kawo rabuwar kan Musulmi, saboda dukkan wata fatawa ta addini shine ke amsawa. Kafin shuɗewar waɗansu shekaru yanayin al'umma ya canza al'adun su da kyawawan halaye na musulmci sun fara rabuwa dasu Bisa wannan dalili ne yasanya matsaloli ke bazuwa a cikin al'ummar musulmi da aka kasa shawo kansu. Wannan shi ne taƙaitaccen bayani game da sarki Anwar da rayuwar al'ummarshi a shekarun da suka gabata. **** Lokacin da Hakimi urwat da samarin uku suka yi turus! Bisa jin wannan motsi da suka yi na takun sawaye a gidan sirrinsu. Tsaye suka yi arba dashi fuskarshi rufe da rawani idanuwanshi kaɗai ake gani, matashi ne da shekarunshi bazasu haura ashirin da uku ba,sanye cikin sulken yaƙi. "Assalamu alaikum". Saurayin ya faɗi a taƙaice. " Wa'alaika-Salam warahamatullah". Urwat ya amsa da yawun sauran matasan dake tare dashi. Matashin ya ɗora hannunshi akanshi ya cire rawaninhi fuskarshi ta bayyana a fili ƙarara, koda Urwat da samarin uku sukayi ido biyu dashi sai suka sakar mashi murmushi mai taushi. Matashin ya risina ya kwashi gaisuwa gareshi sannan ya buɗi baki cikin ladabi yace"ya shugabana mun sace dukkan fataken da ka buƙata da suka tafi izuwa birnin infaƙul-Maisur domin yin kasuwanci, sai dai anyi rashin Sa'a a cikin waɗanda mukayi garkuwa dasu har da yarima Affan ɗa mai martaba sarki. Ya ƙare batun nashi cikin alamun damuwa. Urwat ya bushe da dariyar mugunta gami da cewa ni a wajena hakan Babban nasara ce a garemu, domin kuwa dukkaninku kun shaida cewa babu wani mai ƙoƙarin kawowa aiyukanmu tazgaro a wannan birni tamkar yarima Affan, kun ga yanzu komai namu zai cimma nasara, Wani abin farin ciki ma baku sani ba shine a gobe ne da safe za'a yanke hukuncin kisa ga manyan 'yan leƙen wannan birni a fada bisa laifin shirka wato (tsafi). Sannan halin yanzu dukkan matasan da muka ɗauka aiki sun shirya fara aiyukan su na zartar da kisa ga dukkan wanda bai yi biyayya ga tabbatar da aƙidarmu ta mujahidul' Haƙ ba. Koda yazo dai-dai nan azancenshi sai samarin huɗu suka bushe da dariyar mugunta har da kyakyatawa. Sannan daga bisani matashi ɗaya daga cikin samarin ya buɗe wannan buhu sai ga waɗansu miyagun makamai da kwalaben barasa haɗe da nau'ikan kayan maye. Koda ganin hakan sai urwat ya cika da farin ciki, sannan ya dora dacewa ku tabbatar da an bawa dukkanin matasan mu waɗansu kayan maye da makaman a daren yau kafin wayewar gari. Yana gama faɗin hakan sai ya miƙa tsaye kawai sai ya shafi wani guru a damtsenshi yakaranto waɗansu dalasiman tsafi ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba. Wannan shi ne abin da yafaru Hikimi urwat. Bayan ya ɓace cikin alƙalumman sihiri a lokacin da Sarki shaibat da tawagarshi zasu tafi masallaci domin sauke farali. Madinatul-barnawiy Kashe gari tunda duku-dukun safiya fadar birnin madinatul-barnawiy ta cika ta batse da jama'a Kowa yayi jigum ana jiran fitowar sarki da muƙarrabanshi،Tsawon daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali, Sai daga bisani aka hango martaba da tawagarshi sun shigo fadar ta hanyar yin sallama. Jama'a suka miƙe tsaye domin girmama agaresu, sai da sarki da tawagar shi suka zauna bisa wajen wajen zamansu, kuma jama'a sun kammala kwasar gaisuwa ga sarki, fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta. Sarki ya miƙe tsaye yayi gyaran murya sannan ya ɗora dacewa "Da farko ina yiwa dukkan mahalarta wannan fada rawa mai albarka Barka da zuwa, Bayan haka a yau ne dukkan jama'ata ke zuba idanu domin suga yadda za'a zartar da hukuncin kisa ga manyan'yan leƙen asirinmu, kamar yadda labarin ya wakana. Sai a wannan karon ba haka al'amarin yake ba, domin kuwa abinda zan sanar daku zai yi matukar girgiza ku, yaku jama'ata kuyi sani cewa a daren jiya ne wani muhimmin sirri da na daɗe ina ɓoye muku zai bayyana a gareku. Fiye da shekaru uku ina tare da Amintattun 'yan leƙen asiri a dukkan wani rukuni na al'ummar wannan ƙasa tawa, tun daga gidan sarauta, Unguwanni da kasuwa da ma manyan ƙasashen maƙiyan Addinin musulunci, kuma a kowa ce rana dukkan aiyukan da na sanya su ya kammala, ta wannan hanya ne a samu nasarar tarwatsa dukkanin shirin maƙiya. Hanya ta biyu dana kawar da hakan shine gabatar da addu'o'i dare da rana tare da keɓaɓɓun mutane, domin kuwa babu wani abu da yafi ƙarfin addu'a, Ubangiji na iya canza dukkan abinda ake ganin ya gagara ta kowace fuska, amma sinadarin wannan canjin shi ne bin dokokin ubangiji (SWT). Sannan wani muhimmin abu da mutane basu sani ba shine a kowa ne dare bana iya rintsawa da idanu na har sai na shiga cikin gari cikin ɓadda-kama ina mai sanya idanu akan aiyukan da na sanya shuwagabanni akansu, kamar yadda na saba wannan al'ada ne ajiya ina yin rangadi a cikin gari na shiga wata unguwa da ake ɗaukar matasanmu mayaƙan Mujahidul-Haƙ, Sai da nayi shiga da siffa irin ta Mujahidul-Haƙ sannan na samu shiga gidan sirrin inda ananne na ganewa idanuna Gaskiyar rahoton da ake bani akan Yan tawayen ƙasarmu. A bisa wannan dalilai na yasanya Ni da kaina na ɗebi dakaru na shiga har cikin Daji na ceto rayuwar Ɗana yarima Affan tare da sauran jama'ar da akayi garkuwa da su, A cikin wannan daji ne muka samu nasara gano wani Ɗakin sirri da dukkan maƙiyanmu wato sarakunan kafirai,bokaye haɗe da Musulmi maciya amana ke haɗuwa suna ƙulla makirci da sharri, mun sha gwagwarmaya dasu ta hanyar fafata arbu tsakaninmu bisa taimakon Ubangiji muka samu sanar hallaka su baki ɗaya. Anan ma mun samu waɗansu bayanai muhimmai wacce da ita ne mu kayi amfani wajen kame dukkan maci amanar mu a cikin dare kafin wayewar gari. Koda yazo nan a jawabinshi sai yayi shiru Kuma idanuwanshi suka ciko da kwalla. Al'amarin da ya jefa ruɗani a cikin zukatan al'umma kenan suka ƙara tattare hankulansu akan mai martaɓa. Sarki ya ci gaba da cewa "Sanin kanku ne cewa fiye da shekaru uku wannan ƙasa tamu na cikin halin matsalolin tsaro da taɓarɓarewar matasan mu, daga lokacin da abubuwan suka fara gudana ina saka idanu tare da tattara hujjoji domin tabbatar da zargin da nake yi domin ya zamo gaskiya ba son zuciyata ba. Sai gashi abinda nake zargin ya tabbata gaskiya, Daga cikin jerin mutanen dake hannu wajen jefa kasar mu cikin tarin matsaloli sun haɗar da Sheikh Ɗayyib babban malamin dake amsa fatawa a wannan ƙasa tamu da sauran biranen musulmi, sai Waziri Utbah,Hakimi urwat, uwar gidana gimbiya Huwailah,sarkin dogarai, sarkin fada,tare da sauran jama'a da yawa waɗanda zaku cika da matuƙar mamaki a yayin da kuka yi arba dasu a lokacin da za'a gurfanar dasu. Sheikh Ɗayyib an kama shi da laifin yin fatawa waɗanda suka saɓa da magabatanmu wanda ta wannan hanya ne yayi amfani wajen zartar da hukuncin kisa ga dukkan Musulmin da ya saɓa da aƙidarsu ta Mujahidul-Haƙ tare da dukkan wanda zai tsananta bincike akan abubuwan da suke gudanarwa. Kusan dukkan Musibun dake wanzuwa a wannan lokaci an samu ne ta hanyar Littattafan addini daya wallafa kuma ya sanya su a cikin addini domin su kawo rabuwar kawunan musulmi, sanin kanku ne cewa Babu wani hukunci da yazo a cikin alƙur'ani da sunnah da ya tabbatar da cewa koda musulmi yayi kalmar shahada a hallakashi idan ya saɓa wa wata fahimta ta wata jama'a a addini, Domin ubangiji shine masanin abinda ke wakana a zukatan bayi kuma shine ke yi musu hukunci. Bayan wannan ma fatawoyinshi sun yi tasiri akan matasan mu wajen samun damar saɓa wa Ubangiji ta hanyar fakewa da rashin aikin yi har su karbi aƙidar Mujahidul-Haƙ, dake Kaɗaita musu aljanna da kyakkywan ƙarshe, Waziri kuwa an same shi da laifin taimakawa waɗanda ke Safar mutane daga wannan birni namu ayi Garkuwa dasu domin a ƙarɓi dukiya mai tarin yawa da za'a bawa matasan Mujahidul-Haƙ. Sannan kuka kuma ya taimaka sosai wajen kawar da ainihin Littattafan magabatanmu da ke da tsaftacciyar aƙida ta addinin Islama. Sarkin dogarai kuwa ya cutar da al'ummarshi ta hanyar ƙarbar cin hanci ga dukkan wani bafatake daya shigo wannan ƙasa tamu, ta hanyar ƙarɓar cin hancin ne masu safarar mutane da shigo da miyagun makamai, da kayan maye suka samu dama akan mu, da kyale dukkan wani nau'in kaya da suka shafi wani attajiri ko Basarake, batare da an binciki mene ne ake ɗauke dashi ba. Hakimi urwat da uwar gida kuwa sun ci amanar Allah da Annabin sa ta hanyar tallata saɓon Allah da yaɗashi cikin al'ummar mu da sauran laifuka, Lokacin da kuyanga ihsan ajiya tazo fada domin ta sanar dani irin nau'in sabon Allah da ake gudanar a gidan sarauta shine urwat ya kurumtar da ita ta daina magana domin kada ta bada hujja, sai gashi ta samu lafiya kuma ta tabbatar mini da hakan tare da waɗansu hujjojin daga wasunta. Daɗin daɗawa kuma Dukkanin dai laifukan suna da yawa bazai yiwu mu bayyana su hakanan ba, domin annabin rahama ya hore mu da ɓoye laifukan yan uwanmu musulmi, domin kuwa da yawan laifukan dake yaɗuwa a wannan zamani na mu Suna da alaƙa da yaɗa alfashar da wasu ke yaɗawa da 'yan uwansu ke aikatawa Bayan wannan kuma ina so jama'a su lura cewa bawai don kana cikin wata jama'ar ba ne Abin da zai sa kaga cewa kai babu hannunka a cikin wannan Musibun dake damun duniyar Musulunci ba, kowanne mu ana akaran kanshi yasan nau'in laifin da yake yiwa Allah to shi ma na iya janyo dukkan wata musiba kamar yadda dai muka sani cewa saɓon Allah SWT shine ke kawo gushewar dukkan ni'ima. Kuma ku lura cewa tabbas Matsalolinmu mu musulmi daga kaɗan suka fara har suka haifar da manya, saboda haka kada ku taɓa raina kuskure komai ƙanƙantarshi. Yayin da bayi suka aikata zunubi sai Allah ya saukar musu da Musibun da zasu kankare wannan zunubinnasu domin su haɗu da Allah (SWT) lafiya. Da wannan dama nake roƙon dukkan jama'ata daga Nan fada kafin su koma gida su yiwa Allah alkawarin zasu daina duk laifukan da suke yi wanda tsakanin su da Allah ne kawai, tabbas ina da tabbacin Ubangiji zai dube mu ya kawo mana gyara a cikin wannan Rayuwa tamu, kuma mu riƙa kallon dukkan Musulmi a matsayin ɗan uwanmu kuma abu ɗaya ne ya haɗamu ita ce kalmar shahada, Ko da kaga ɗan uwanka yana aiwatar da wani abu da ya saɓa da fahimtar ka to kayi mashi kyakkywan zato, domin baka san a ina ya samo hujjar yin hakan ba, saɓanin fahimta ba sabon abu ne a cikin addini ba Kada mu zama masu bincike abinda ke zukatan al'umma,domin Allah shine kaɗai yasan abinda ke zuciyar bayinshi, kuma shi ne zai yi hukunci a gobe ƙiyama. Kuma dukkan abinda musulmi zai yi bazai taɓa kafurtaba face ya yarda da abin azuciyarshi, don haka ne idan mutum ya yi abin da ya saɓa da fahimtar mafi yawan al'umma ake neman shi da ya tabbatar da Mene ne hujjarshi na aiwatar da hakan. Kada muyi watsi da abin da magabatan mu suka rayu akai, kuskuren da sukayi mu nema su gafara wajen Allah. Sannan dukkan abinda kowannen ku zai aiwatar yaji tsoron Allah a ciki. Tsira da aminci Allah su tabbata ga Annabin rahama Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama da jama'ar gidanshi. Lokacin da sarki Shaibat yazo Nan a jawabinshi sai fadar jama'a suka ruɗe da kabbara masu salati nayi, kuma kowa na ƙara jinjina wa sarki, bisa jawabinshi, suna masu cewa munyi yarda mun amince zamu gyara halayenmu da tsakaninmu da ubangiji, a dai-dai lokacin ne aka shigo da waɗanda ake tuhuma da cin amanar addini. Nan fa jama'a suka cika da matukar mamaki a cikin waɗanda basu yi zato da hannunsu a cikin al'amarin ba. Suka shiga yi musu Allah wadai har sai da sarki ya tsawatar sannan komai ya samu dai-dai ta. Duk wanda ya kalli fuskokin su waziri a wannan lokaci zai ga alamun nadama da da nasani, Da yawan su Har zubar da hawayen baƙin ciki da takaici su ke yi, wasu daga cikinsu ma har faɗuwa ƙasa suke yi suna cewa "Haƙiƙa mun tuba munyi nadamar abin da mu ka aikata muna neman afuwa. Sarki ya ɗora da jawabin shi da cewa yanzu dukkan su za'a tafi dasu izuwa kurkuku, waɗanda a cikinsu suka cancanta a yanke musu hukuncin kisa zamu zartar waɗanda kuma waɗanda za'a bukaci tuban su, da waɗanda za'ayi bulala duk zamu zartar a sirran ce, nasan yanzu da kanku kun ganewa idanuwanku waɗanda suka nuna Nadamarsu dama waɗanda basu da alamun hakan, dukkaninsu zamu yi musu adalci Da wannan nake yiwa jama'a fatan alkairi kuma na sallami kowa daga fada. Koda gama faɗin hakan sai sarki ya juya ya shige izuwa gidan sarauta dogarai na biye dashi a baya. Nan take aka tusa ƙeyar maci amanar addini aka nufi hanyar kurkuku, fuskokinsu cike da ƙunci da da na sani, ƙarƙashin jagorancin yarima Affan. Bayan mako ashirin da biyar lamura sun fara dai-dai ta acikin ƙasar madinatul-barnawiy, jama'a na ta ƙoƙarin ganin sun daina saɓa wa Ubangiji (s'w't). Sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba'a je ba, sai gashi dukkanin kawunan ƙungiyoyin musulmi sun haɗu, zaman lafiya da aminci ya wanzu a ko ina albarka gami da ni'imomi suka mamaye al'ummar musulmi. www.littafanyaki.com.ng Kuma sarki da kanshi ya dunga yin hawa izuwa ƙasashen sauran Musulmi yana sai-sai ta musu matsalolin su, tare ƙone dukkanin Littafin addinin dake ɗauke da gurɓatattun aƙidoji, gami da ɗorasu bisa turbar gaskiya. Karshe Alhamdulillah Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaki Wthapp number 08137237071