ABDULFATAH by Fateemah S Umar Jajira PAGE 1-2 A hankali take saukowa daga benan har ta k'araso cikin falon zama ta yi kusa da shi ta na ya mutsa fuska ta ce "Morning my choice." Yana mata kalon tuhuma ya ce "Morning ya gajiyar ki ta jiya?" Baki ta tab'e ta ce "Ba gajiya na yi sauki." Murmushi ya sakar mata ya ce "Okay ya kamata ki tashi mu yi bearkfast sai ki koma ki k'ara hutawa ko." Tana yatsina fuska ta ce "Ka ga my Choice ni fa na yi bearkfast d'ina tun ba ka dawo daga kiran Abba ba, kai dai ka je ka yi na ka." Girgiza kai ya yi ya mik'e ya haura darning table d'in ya fara tsiyaya tea a cup ya k'ara suger san nan ya d'auki spoon yana tonawa, Satar kalon ta yake yi, tun da ya tashi tana rike da waya tana dannawa, Kad'an ya sha tea d'in ya mik'e yana cewa "To My zan wuce office." Kalon sama da k'asa ta masa ta ce "Office fa ka ce My Choice tun yau zaka fara fita na ga yau 2days ke nan da kawo ni gidan nan amma za ka ce za ka fita wani office." Murmushi ya yi cikin rarrashi ya ce "Ayya! hakuri za ki yi My ina da marasa lafiya da yawa da suke buk'atar kulawata, in sha Allah zuwa 2:00pm zan dawo gida." Ya k'arasa maganar yana kamo hannun ta da fuskar tausayi "To na ji amma kar ka huce two d'in don Allah" Kai ya gyada mata ya ce "In sha Allah" Mik'ewa ta yi ta rakoshi har waje hannun sa na cikin nata har ya shiga motar sa sannan ya sake ta ya ce "Ki kulamin da kanki My." "Kai ma haka." Ya tada motar ya fice daga gidan tana d'aga masa hannu har ya fice sannan ta koma cikin gidan, Sama ta haura ta shiga d'akinta ta zauna gefan gado ya d'auki wayarta ta kira wata number, Bugu d'aya zuwa biyu aka d'auka daga can b'angaran a kace "Hello! kawata ya kike? Ya Amarci?" Lokaci d'aya ta jero mata tambayoyi, Murmushi Mufida ta yi ta ce "Amarci lafiya lau k'awata mutumin ki harda rawar kai da yi mun sannu." Dariya sosai Nuratu ta yi ta ce "Ai wallahi Mufida ba k'aramin tada mun da hankali wannan mijin na ki ya yi ba, na d'auka duk shirin da muka yi a banza zai tashi tun da kika ce mun Doctor ne." Murmushi Mufida ta yi ta ce "Haba Nuratu duk shirin da Malam Tanimu ya mana zai tashi a banza ne?" "Hhhhhh haka ne fa k'awata ba shi ya yi kan saba dan haka sai yadda muka yi da shi" "Ashe kin gane k'awata" "Yauwa tun da yanzu mun gama da page d'in maganar mijinki to yanzu ya maganar Alhaji Sani kin san fa dan kin yi aure ba yana nufin kun rabu ba kuma kin san idan Alhaji Sani ya san kin yi aure sunanki sorry ko?" Ajiyar zuciya Mufida ta yi ta ce "Gaskiya ne na san rashin hakuri irin na Alhaji Sani yanzu ya san na yi aure sai ya kashe auran kuma asirina zai tonu a gurin ABDULFATAH dan haka zan ji da shi" "Yauwa k'awata" Nan Nuratu ta ringa ba wa k'awarta ta shawara yadda za ta yi da Alhaji Sani, Har suka yi salama Mufida ta ajiye wayar. Tun da *ABDULFATAH* ya fita yake aikin tunani, har ga Allah bai yarda da Mufida ba amma ya rasa me yasa ya kasa d'aukan mataki a kanta amma duk ya ji ta fita a ransa tun da ta kasa rike mutuncin kanta, Haka yaringa tunane-tunane har ya k'araso Asibitin wadda aka rubuta *ABDULFATAH* *HOSPITAL* Me gad'i ne ya bud'e masa kofa ya shiga, fitowa ya yi ya na nufi cikin Asibitin, gai da shi aka rin ka yi har ya k'arasa office d'in sa, Shiga ya yi ya sa key ya kulle ya zauna akan kujerarsa ya kifa kansa a table d'in gaban sa, Ya jima a haka ya ji ana buga k'ofar, tsaki yaja ya mik'e ya zare key d'in sannan ya ba ta izinin shigowa, ganin wadda ta shigo ba k'aramin b'aci ransa ya yi ba, Budurwace da bazata haura shekara 18 ba sanye take da kaya farare na nurses Kanta a k'asa jikinta na rawa ta ce "Barka da safiya Sir! da fatan ka tashi lafiya?" Ta k'ara maganar tana d'agowa ta kalle shi, ganin irin mugun kalon dayake jifan ta da shi ya sa ta k'ara tsorata, Cikin fushi Abdulfatah ya ce "Sau nawa zan fad'a miki idan na zo kar ki bari naga wannan bak'ar fuskar ta ki, naga alama aikin Hospital d'in nan ya fara isarki shiyasa kike k'etare umarnina." Kai ta girgiza muryarta na rawa ta ce "Ba haka bane sister Hauwa ce bata zoba shine Doctor Rukayya ta ce nazo na fad'a maka akwai matar da kasawa rana zaka mata CS sai kuma ka shiga hidimar biki to matar tazo tun shekaran jiya kuma ta ce a nesa ta ke shiyasa zata koma gida ba zata jira ka dawo aiki." Harara ya watsa mata ya ce "Yaushe gidadancin ki ya fara shafar na kusa da ke, meyasa Doctor Rukayya bazata kirani a waya ta sanar da ni ba ko ita da Doctor Nasir su mata CS d'in har sai an jira na dawo? yanzu ida ban dawo yau ba fa? kuma matar wani abu ya sameta fa? ki je ki ce ta zo ina kiranta kuma wallahi kika bari na k'ara ganin wannan bak'ar fuskar ta ki hmmm ki kuka da kanki." Ko bari ba ta yi ya gama maganar ba ta fice daga office d'in tana haki Ya bita da harara ya tsaki. Islam na fita ta sanar da Doctor Rukayya sakon Doctor Abdul ta d'auki kayata ta fice daga Hospital d'in gaba d'aya. *Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karantawa* *zasu* *biya* #200 *kacal* *Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167 COMMENTS AND SHARE by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 3-4 _____________ Gida ta nufa ranta a dagule, idan da mutumin da ta tsana a duniya to Dr Abdul ne ji take kamar ta kasheshi tahuta da muguwar tsanar da ya mata tarasa me ta tsare masa a rayuwa da ya tsaneta haka, Abunda bata sani ba shi Abdulfatah bak'ar maca ce bayaso a rayuwar sa dan cewa yayi daya auri bak'a gara ya mutu a aure, shiyasa ya auro Mufida sabuda Mufida farace k'all, Shi Abdul ya d'auka farin Allah da Annabi ne baisan na kanti bane, shiya yake mugun son Mufida wai a cewarsa farar wace itace mace bak'a kuma muna mata. Haka Islam ta koma gida ranta a b'ace, a tsakar gida ta zube tana cika tana batsewa, Ummi ce ta fito daga kitchen tana kallon ta ta ce "Lafiya kuwa uwata naga kin dawo yanzu? keda yau aikin safiya kika tafi." Hawaye Islam ta share ta ce "Gaskiya Ummi na gaji da wannan shegen aikin, daga yau ba kuma zuwa zanyi ba ai talauci ba hauka bane" Nunfashi Ummi ta sauke cikin rarrashi ta ce "Haba uwata haba mamana ki dena iskanta aikin da muke cin abunci dashi kiyi hakuri wata rana sailabar." "Amma Ummi dan kana cin abunci a k'ark'ashin mutum saiya ringa wulak'an ta ka, shima fa Allah ne ya bashi ba wayansa ko dabarar sa ba." "Hakane uwata amma wasu basa fahimtar hakan, idai akan likitan kune in sha Allah wata rana zaizo har gaban ki ya duk'a ya baki hakuri kuma zaizo neman wata aifarma a gurin ki da yardar Allah." Ido Islam ta zaro ta ce "Ummi kinsan halin wannan mutun kuwa?" "Ban saniba Mamana amma yardar Allah na ce kuma kinsan lamarin Uban giji ya huca nan." Ajiyar zuciya Islam ta sauke ta ce "Hakane Ummi lamarin Uban giji yahuce nan dan nima ikonsa ne ya kaini matakin dana ke ciki a yanzu." Haka Ummi ta zauna ta ringa tausar Islam tana bata baki har har Islam ta saki ranta ta manta da batun wani Dr Abdul ta cigaba da harkokin gabanta ranta fari k'all. Sai yamma Abdul ya koma gida tun daga waje yake jin k'arar kid'a yana tashi kuma bana hankali ba, Da sauri ya shiga gidan ya tadda Mufida a falo kure kid'a sai rawa ta keyi tana d'aukar Video, Kayan jikin ta ya kala ya ga rigace iya guwa sai wando da kad'an ya huce rogar, Sarai Mufida taga shi gowar sa amma ta share sa, Sai da ta gama video sannan ta juyo tana murmushi ta ce "Harka dawo k'arfe biyu ko?" Harara ya watsa mata ya haye sama ya barta, Itama da Harara ta rakashi ta cigaba da rawar ta. Ya jima a zaune a d'aki yana takaicin abunda Mufida ta masa, ya dawo daga office mai makwan ta masa sannu da zuwa saita bige da tuhumar sa, Tsaki yaja sabuda yadda yaji yinwa tana kwakular sa. Wayar shi ya zaro a aljihu ya kirata ya ce tazo, yana kashe wayar ya bud'e data ya shiga WhatsApp, Status ya fara dubawa da Status d'in Mufida ya yi karo ashe duk videos da pics d'in da tayi posting ta ringayi, jikin Abdul ne ya d'auki rawa sabuda Allah ya zuba masa kishi a rawuyarsa, Ko salama babu Mufida ta shiga d'akin zama tayi kusa dashi ta ce "Gani My Choice." Shiru ya yi na d'an lokaci kad'an kafin ya ce "A gidan ku ba'a koya miki bawa miji abunci ba in ya dawo?" Ido ta zaro ta ce "Abunci fa ka ce? Kana nufin ni zan girka na baka?" Kalon mamaki Abdul yake mata, Tayi murmushin rainin hankali ta ce "Tun huri ma ka nemi wadda zata ringa dafa ma abunci dan ni ba......!" Tsawar da Abdulfatah ya daka mata ne tasa ta had'iye sauran maganar dake bakinta, cikin d'aga murya ya ce "Wallahi ki tashi ki dafa mun abunda zanci tun ranki bai baci ba" Baki ta turo gaba ta kunkuni ta tashi ta fita. Wayar da ta manta yakan gadon ya d'auka ya bud'e ya shiga WhatsApp d'in ta, Comments d'in mutane ya ringa gani akan pics d'in data d'ora wasu suna Amarya tayi kyau harda maganar daba ta dace ba kuma yawanci duk maza ne abokan charting. Bata jima ba ta dawo d'auke da plet a hannun ta ajiye masa tayi, ya kali filet d'in, Kwai ta soya fari fattt dashi ko albasa babu sai k'arni ya keyi. D'agowa ya yi ya kaleta ta had'e rai ta ce "Nifa shi kad'ai na iya soyawa." Takaici da bakin ciki yasa Abdul kasa cewa komai sai tsaki da ya yi ya mik'e ya fice abun sa. Sarah ce ta shigo da salama Ammi ta amsa ta zauna kusa da Ummi ta ce "Ammi kinsan me?" "To uwar kawo k'ara me akayi?" "Baki ta turo ta ce ba wannan Yaya Abdussamad d'in nan bane na gama girki na ya kwashe ya cinye d'an kad'an ya bar mun." "To yanzu tunda ya bar miki ragowa mene na kawo k'ara ba Yayanki bane?" "To amma Ammi....!" "Nifa kin ta kuramun tashi ki bani guru." Mik'ewa Sarah tayi zata fita Ammi ta ce "In anjima ki kiramun Abdulfatah kice Abban su ya ce Jibi zai je ya d'auko Maman Kaduna." "Laaa Ammi taji sauki Maman?" "Taji sauki Jiki Alhadulilah." "Masha Allah, Allah ya k'ara mata lafiya." "Ameen, amma fa kice wayata ce ta samu matsala shiyasa ban kirashi da kaina ba, karya je ya rufeki da fad'an nasa." "Lalai kuwa Ammi na dan Yaya Abdul akwai lafiyar fad'a wannan aunty Mufida tana kokari." Juyawa tayi zata fita suka had'a ido dashi. Ido Sara ta zaro gabanta yana fad'uwa murya na rawa ta ce ........ *Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karan* *tawa* *zai* *biya* #200 *kacal* *Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167 COMMENTS AND SHARE by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 5-6 _____________ "Sannu da zuwa Yaya." Harara ya watsa mata ya huce ta ya shiga ciki, Gaban Ammi ya je ya zauna yana ce wa "Ammi ina huni." "Lafiya lau Abdulfatah ya gidan?" "Lafiya k'alau Ammi." "Dama yanzu nake cewa Sarah ta kira ka ta ce maka Abban ku ya ce jibi kaje ka d'ako Maman Kaduna." "Allah ya kaimu, Ammi dama idan da abunci a zubumin yinwa na keji." Ya k'arasa maganar yana sosa kai, Murmushi Ammi ta yi ta kira Sarah, Shigowa Sarah ta yi ta zauna kusa da Ammin ta ce "Ammi gani." "Yayan ki zaki kawowa sauran abuncin naki da kike fad'a akan sa." Fuska ta marairaice zatayi magana taga Abdulfatah ya rararo ta tai saurin mik'ewa ta fita. Abunci taje ta zubo masa ta kawo masa ta ajiye ta fice, itama Ammi mik'ewa tayi tabi bayan Sarah. Saida Abdulfatah ya ci ya koshi sannan ya yiwa Ammi salama ya fice, Ita kuwa Sara sai wani abuncin ta dafa tana ta mita. Sai 12:30am Abdulfatah ya koma gida lokacin har Mufida tayi bacci, yaji dadi sosai da yaga tayi bacci sabuda yasan damun sa zatayi. Wanka shima ya yi ya kwanta. Washe gari shi ne ya fara tashi a gurguje yayi alwala ya yi salah dan ya makara, har yayi wanka yai shirin office Mufida bata tashi tayi Sallah. Tashin ta ya farayi yana kiranta "Mufida." Mik'a tayi ko salati babu tana hamma ta kalle shi, shima ita yake kallo, Mik'ewa zaune tayi ta ce "Ina zakaje da sassafen nan?" "Hospital zani mana." "Wai meka keso ka d'aukeni ne Abdulfatah? Jiyama fa haka kace ba jimawa zakayi ba zaka dawo da dare ma har nai bacci baka dawo ba sannan kace yau ma zaka k'ara fita da sassafe." Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya ce "Ga kud'i nan akan stool idan kina buk'ata zaki anfani dasu." Yana gama fad'in haka ya juya ya fice daga d'akin, Da kalo Mufida ta bishi a ranta tana ayana irin tashin mutuncin da zata masa. Yau tunda Islam ta shigo Hospital bata bari sun had'u da Abdulfatah ba, har lokacin tashin ta ya yi ta fito domin tafiya gida, Tana sauka daga bene ne kicin rashin sani ta taka b'awan Banana aikuwa ta zame tayi k'asa zata fad'a, ji tayi ta fad'a jikin mutum k'anshin turaran sa ne ya tabbatar mata da waye, Ji tayi kamar ta saki fitsari a gurin sabuda tsoro da firgici, shikuwa Abdulfatah cikin fushi ya hankad'eta ta daki ginin gurin, Saida ta saki k'ara sabuda zafin da taji tana zubar da hawaye, Kallon tsana Abdulfatah yake jifan ta dashi cikin b'acin rai ya ce "Kewace irin jaka ce jahila bagidajiya dazaki fad'owa mutane jiki, ko da gidan ku bakuda bene? Koda yake ina matsiyata sukaga arzikin yin bene a gidan su, to inma da gangan kika tab'ani nafi k'arfin ki domin ni ba irin sauran k'azaman 'yan iskan tasha ki bane ki sake tunani yarinya mtsss." Yaja tsaki ya huce ya barta a tsaye tana sharar kwala. Sauka tayi ta fita daga Asibitin d'an sahu ta tare ta shiga tana faman kuka. Ta madubi yake kallon ta lokaci zuwa lokaci yana kalon yadda take kuka, gyaran murya ya yi ya ce "Haba baiwar Allah komai ya sameki kiyi hakuri ki daina irin wannan kukan, Allah madaukakin sarki da kansa yake sanar damu acikin suratul bak'ara aya ta 155 cewa Allah zina iza asabatuhun musubatu, k'alu inalilahi wa'ina ilaihirraji'un, to meyasa zakiyi anfani da fad'ar ubangiji ba koda mutuwa aka miki ki daure kita maimaita inalilahi wa'ina ilaihirraji'un." D'agowa Islam tayi suka had'a ido da saurayin ta duk'ar dakai a hankali ta furta "Nagode." Daga haka bata k'ara magana ba, shikuma sai nasiha yake mata har suka k'arasa gidan su Islam. Fitowa tayi ta mik'o masa kud'in sa, murmushi ya yi ya ce "Bazan amshi kud'in ki ba alfarma d'aya zaki mun itace kibani Number ki." Murmushi Islam ta yi ta ce "Me zakayi da number ta." "Sabuda kina buk'atar wanda zai ringa kwantar miki da hankali ni kuma zan iya." "Hmmm Ummi na zata iya kwantar min da hankali ai ba saika wahalar da kanka ba." Murmushi ya k'arayi wanda saida fararan hakoran sa suka bayana ya ce "Duk da haka ki bani dama duk wannan damuwar taki in sha Allah zata ragu." Duk yadda Islam ta so ya rabu da ita yak'i saida ta bashi number ta ya ce "Wane suna zansa?" "Islam." "Wow nice name suna me ma'ana, nikuma Sahal." "Masha Allah suna me dad'i." "Nagode fa." Ya fad'a yana dariya Da haka sukayi salama ta shige gida. Wacece Islam Islam 'yar salin garin Meduguri ce ba banta da babarta duk 'yan can ne sunada arziki da wadata sai canji gurin aiki ya samu babanta ya dawo Kano da zama nan Sharad'a ya cigaba da zama da matar sa Amina da yaranta biyu Fateemah (Islam) sai Aliyu yanda shine k'arami. Shekarar su biyu da dawowa Kano Allah ya amshi ran mahaifin su, Sunyi kukan rashi sosai duk da 'yan uwan Baba sun so tafiya da su Islam amma Ummi ta hana ta ce zata iya rik'e 'ya'yanta, gun kar a kwace mata yara yasa tak'i komawa Meduguri tai zamanta a nan duk da nan sai rufin asirin Allah can kuma da masu taimakon ta amma ta fi son zaman Kano. Shikuma Asalin Abdulfatah Baban sa d'an asalin Kano ne amma mahai fiyar 'yar Kaduna ce Baban su yanada mata biyu Hajiya Khadija (Maman Kaduna) ita ce babba tanada yara uku maza Abdulfatah shine babba sai Abdulmalik sai Abdussamad ita kuma Ammi tana da yara biyu Abdallah da Sarah wadda ita ce autar su Rashin lafiya da Mama takeyi na Asuma ne yasa dole ta koma Kaduna gurin iyayen ta da zama duk da ba rasa me kula da ita tayi ba amma ita ta buk'aci hakan Baban su Alhaji Umar yana matuk'ar k'aunar matar sa Khadija sabuda tun bashi da ko sisi take zaune dashi shiyasa duk abunda take so a rayuwar ta komene shi indai bai sab'awa shara'a ba sai yayi mata. Wannan kenan Bayan kwana biyu , yau Sunday ba aiki dan haka Abdulfatah ya shirya ya tafi d'ako Mahaifiyar ta su yana zuwa bai ko bari ya zauna ba ya d'ako Mama suka taho gida. Ita kuwa Mufida dataga yayi asuban ci ya fita kawai takira abokai maza da mata wai zasuyi..................! *Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karan* *tawa* *zai* *biya* #200 *kacal* *Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167 COMMENTS AND SHARE by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 7-8 _____________ party na murnar cikar ta sati d'aya a gidan Abdulfatah, DJ suka sa anata rawa maza da mata ga kayan ciye-ciye dana lashe-lashe kowa yana kaiwa ka k'a warta Nuratu ce taja hannun ta suka shiga d'aki ta na murmushi ta ce "Tun jiya Alhaji Sani yake kiran wayata wai lafiya baya samunki, kawai saina ce masa mahaifin ki ne bashi da lafiya a k'auye kinje duba shi kuma ba network a k'auyan." "Hmmm wallahi Nuratu na gaji da auran Abdulfatah ga ba d'aya baya zama a gida gashi yadda nake zaton zan juyashi abun ya gagara, wulak'an tani ma yakeyi son rasa." Da fata Nuratu ta yi ta ce "Wallahi duk abun da yake faruwa ke kika so kinaji fa Malamin da mukaje gurin sa ya ce ko bayan biki ki koma a cigaba da baki temako sabuda wannan mijin naki taurin kai gareshi." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Yanzu yau she zan samu lokacin da zamu koma." "Duk randa kika shirya yana fita office kema ki fito mu tafi." "To k'awata nagode." Daga haka suka fito falon nan aka k'ara sakin kid'a shiga Mufida ta yi tana rawa da ita da k'awayan nata Maza da Mata. Parking ya yi a harabar gidan sautin kid'an da yakeji na yau yafi na ko yaushe ga hayaniya dayake taji acikin gidan, Fitowa ya yi ya kira Baba me gadi ya ce "Baba suwaye suka zo gidan nan bayan na fita?" "Kana fita Hajiya ta fito ta ce na siyo mata lemuka, nace ba akwai a gidan ba ta ce ba dashi zatayi anfani ba, na amsa na siyo shine naga k'awar ta tazo suna ta shiri harda me DJ aka d'auko duk motocin da ka gani a waje na maza ne da mata da suka zo gidan nan, d'azu na fito naji wata a cikin 'yammata da sukazo tana cewa wai party takeyi na cikarta sati a gidan mijinta." Murmushin ta kaici Abdulfatah yayi ya ce "Okay nagode Baba." Daga haka ya hashiga motar sa ya fice daga gidan dan yasan idai ya shiga raine zai b'aci gara ya rabu dasu su gama haukar su. Islam kuwa tun ran da ta had'u da Sahal, Soyayya me k'arfi ta shiga tsaka nin su kulum suna mak'ale a waya Yauma tana Hospital ta na rike da wayarta tana ta sheka dariya da masoyin nata Daga can b'agaran ya ce "Gaskiya na matsu naga munyi aure Baby na." Murmushi ta yi ta ce "In banda abunka My yaushe muka had'uma da kake zancan aure." "Hmmm bakisan abun da nakeji bane shiyasa kika ce haka amma inaji a jikina kamar kwace mun ke za'ayi shi yasa na keso nayi nai wuf da ke." Dariya sosai Islam ta yi ta ce "Allah sarki My idai ina raye bazan auri kowa ba sai kai." Ajiyar zuciya ya yi ya ce "To Allah yasa." "Ameen My." Nan suka ciga ba da hirar su ta Soyayya. Mama ce zaune ta na kalon Abdulfatah ta ce "Ya naga ka dawo bayan kace ka gaji gida zaka tafi." Kai ya sosa ya ce "Am da na tafi kuma sai na tuna ma ta na da baki shine na dawo nayi wanka a nan." Ido Mama ta kura masa ta na son gano wani abu dan daga ganin yanayin sa ransa a b'aca yake, "To ina ruwan ka da baki ba gidan ka bane." "Eh amma banaso na takura su." "To shikenan kaje kayi wankan a d'akin Abdussamad." "To Mama" Ya ce ya mik'e ya fice ranshi ba dad'i. Badan zai iya wankan ba ya shiga d'akin Abdussamad ya kwanta ranshi ya na suya, Mufida ta gama raina shi ta maida shi wani sauna shashasha wanda bashida iko da gidan sa amma da sannu zai gyara mata zama. Ranar Abdulfatah bai kwana a gidan ba Hotel ya kama yai kwanciyar sa. Bayan kwana biyu Mama ta kira Sara ta ce tazo ta kaita gidan Abdulfatah tunda akayi auran bata tab'a zuwa ba, Shirya wa sukayi zasu tafi. Ammi ta fito same su a falo ta ce "Har kun shirya?" "Eh Ammi." Mama ta ce tana murmushi, "To idan kunje Ku gaida Mufida, Allah ya tsare." "Ameen, zataji in sha Allah." Nan suka fice Abdulmalik ne ya d'auke su a motar sa ya kai su, A kofar gidan ya tsaya ya ce "Mama nidai zan juya bazan shiga ba anjima kad'an zan zo na d'auke ku." "To Allah ya tsare." Maman Kaduna ta ce Suka shiga gidan da Sara. Salama suka ringayi amma shiru har suka gaji suka zauna a parlour, Sun jima a zaune amma bata fito ba Sarah ta kali Mama ta ce "Bari na shiga na mata magana muna zaune." "A'a ki rabu da ita ko bacci takeyi." Shiru Sarah tayi suka cigaba da zama har kusan minti talatin amma shiru har Abdulmalik ya kira ya ce yazo zai mai dasu tunda ganin gida suka zoyi, A fusace Sarah ta ce "Gaskiya Mama nagaji kamar ba mutum acikin gidan nan taya zamuta jiranta ta fito tak'i fitowa nidai tafiya zanyi Islamiyya zani." Murmushi Mama ta yi ta ce "Idan bazaki juraba kije Abdulmalik ya mai dake ki tafi makaranta ya dawo ya d'auke ni." Mik'ewa ta yi ta ce ta tafi, Sarah bata fi miniti 3 da fita ba sai Mama ta ji takun sakowa daga bene anata shek'a dariya, Gaban Mufida fad'uwa ya yi da taga Mama a zaune bata santa a zahiri ba amma ta santa a hoto tunda Abdulfatah yana nuna mata Maman, Amma da yake 'yar duniya ce saita mazai saida ta raka bakwanta har waje san-nan ta dawo tana hura hanci ta ce, "Wace iriyar bakuwa nayi wadda bata iya salama ba." Ko d'agowa kasayi Mama ta yi sabuda bak'in ciki da b'acin rai, Jitake dama tabi Sarah sun tafi tare da wannan b'acin ran da ta gani. Muryar Mufida taji tana cewa "To koma wace ta gaba tar da kanta ban gane ta ba." Mik'ewa Maman Kaduna tayi ta ce "Duk da nasan baki tab'a ganina ba amma inda ke 'yar arziki ce to bazaki kali kwayar idona ki ringa tanbaya ta ni wace ba ko na shigo ba Salama, amma dama Hausawa sunce d'anku ne mai jawa uwarsa jifa." Tana gama fad'in haka tafi ce daga gidan Da kalo banza Mufida ta bita tai haye warta sama. Mama na fita ta fara tafiya a k'afarta dan bata san ida ta dosaba sabuda b'acin rai tunani kawai takeyi a ina Abdulfatah ya d'ako wan-nan mara tarbiyar mara kunya, Bataji kunyar ta ganta da wani a gidan ba amma harda ci mata fuska ita da gidan d'anta. Tarine ya fara sarketa a hanya ta zauna a wanu dakali tana ta tarin, Amma tak'i denawa nufashin ta ya fara sarkewa lokaci duda Asumarta ta tashi ta ringa kokawar yin nufashi harta fara galab'ai ta ta tafi luuuu zata zube a gurin.............! *Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karan* *tawa* *zai* *biya* #200 *kacal* *Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167 COMMENTS AND SHARE by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 9-10 _____________ Jikin wata yarinya ta fad'a cikin tashin hankali yarinyar take cewa, "Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un sannu baiwar Allah." Ganin kamar me asuma ce yasa ta fara laluba jakarta ko zata samu abuda suke shak'a, cikin sa'a kuwa taga inhelar da temakon ta Mama ta ringa shak'a har nunfashin ta ya soma dai-dai ta, ajikin budurwar ta saki baccin wahala, Rasa yadda zatayi da matar tayi kawai dabara ta fad'o mata takira zaro wayar ta takira wata number, Salama tayi aka amsa sannan ta ce "My kana ina na had'u da wata mata Asumar ta ta tashi kuma yanzu tayi bacci a jikina na rasa ya zanyi da ita." "Okay gani nan kina dai-dai ina?" "Ina layin su Sajida." Ba'a d'au lokaci ba sai gashi ya zo a d'an sahun sa da temakon sa suka sa Mama a babur d'in ya tafi dasu Asibiti, Bayan suje na Asibin ne an duba Mama an bata temakon da ya dace suna zaune da ita, ta bud'e ido a hankali tana salati, Da hanzari Islam ta matsa kusa da ita tana mata sannu amsawa ta yi ta ce "Yarinya a ina nake?" Nan Islam ta bata labarin abun da ya faru duk da Maman tana cikin mawuyacin hali ta tuna abun da ya faru tayi murmushi ts ce "Nagode baiwar Allah." Itama Islam Murmushi ta yi ta ce "Ayyah bakomai Hajiya ki d'auka 'yar cikin ki ce tamiki ba bare ba." Ajiyar zuciya Mama tayi ta kalon Islam tanajin dad'i yarinyar tana da tarbiya irin ta ya dace ta samu matsayi suruka ba Mufida ba, Wayar Mama ce ta fara ruri Islam ta d'ako ta mik'o mata, Maman ta mik'e zaune da kanta ta d'aga wayar, "Hello Mama kina ina mu dawo da Sarah amma bakya gidan." "Ina Hospital Abdulmalik matar Abdulfatah ba matar kwarai ba ce." "Inalilahi kiyi hakuri Mama gamunan isuwa wace Hospital kike?" Tan bayar Islam Mama tayi wanda tunda taji an ambaci sunan Abdulfatah gaban ta yake fad'uwa, ta fad'a mata sunan Asibitin ita kuma ta sanar da Abdulmalik, Mintina kad'an suka k'aso, Godiya sosai suka yiwa Islam da Sahal har Sarah ta amshi number Islam d'in dan suringa zumunci. Salama suka musu suka tafi gida. Zaune take ta kurawa Abdulfatah ido shima ita ya kalo tayi ajiyar zuciya ta ce "Gaskiya na gaji da ga fara sa banga k'ahoba Abdulfatah ya da ce nasan matsayi na a gurin ka." Murmushi ya yi ya ce "Marwa kenan zaki gani very soon." "Na gani ai da kayi aure ka barni, to wallahi idan kayi aure kana ganin na rabuda kai ban tanka ba to karka k'ara yaudara ta in bahaka ba kasan wace Marwa dan wallahi saina kashe duk wadda tayi yinkurin shiga tsakanina da kai." Murmushi me k'aya tarwa ya yi ya ce "Kinsan ina sonki Marwa tun farko Kyan Mufida ne ya sa naji ina son auran ta amma yan ba abunda zai shiga tsakanin mu." Harara ta watsa masa ta ce "A bayama haka kake cewa ba son ta kakeba ita take son ka amma sai bikin ka naji a gari, yanzu yaushe zamuyi aure?" Idon sa na kanta ya ce "Yanzu bazan tukari Abba da zancan aure ba tunda wata na d'aya kacal da aure amma bayan wasu 'yan watani zan masa maganar auran ki." "Hmmmm Abdulfatah kenan kar kamun dad'in baki kamar na baya kasani ni ba kawar lasa ba ce na fi k'arfin raini yanzu." Ido ya lumshe ya ce "Ki daina zargin zan rabu da ke Marwa ki sa a ranki kin malaki Abdulfatah na kine ke kad'ai." Murmushi ta yi ta ce "Ko wannan kucakar matar taka saita bar gidan zan shiga." Magana zaiyi kira ya shigo wayar sa, Abdulmalik ne dan haka ya d'auka ya kara a kune. Salama Abdulmalik ya yi Abdulfatah ya amsa yana tanbayar lafiya, nan Abdul malik yake sanar dashi abunda ya ke faruwa, Da sauri Abdulfatah ya mik'e ya cewa Marwa, "Marwa Mama ba lafiya tana Hospital Asumar ta ta tashi." Ya tsina fuska ta yi ta ce "Ayyah ka mata sannu." Bai jira ta k'ara cewa komai ba yabar gurin da sauri. Hospital d'in yaje yaga Mama ma a zaune ajiyar zuciya ya yi yaje kusa da ita ya zauna ya kamo hannun ta ya ce "Sannu Mama ya jikin naki?" "Da sauki." Kalon Sarah ya yi ya ce "Me yasa baku kaita Hospital d'in na ba? ku kirani ba kuka kawo ta nan?" Shiru ta yi kanta a kasa ta na raba ido, Ya bud'e baki zai fara fad'a Mama ta ce "Ba laifin su bane nice na ce akawo ni nan kar a ta dama da hankali." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Da kun sanar dani to da nan basu baki kulawa yadda ya dace ba fa?" Murmushi Maman Kaduna ta yi ta ce "To in sha Allah nan gaba zan sa su kira mun kai." "Allah ya tsare Mama na ya kikaye gaba." "Ameen Abdulfatah." Nan suka ciga ba da hira har Doctor yazo ya bawa Mama Salama dan ta warware. Sai da Abdulfatah ya kaisu gida sannan ya wuce nashi gidan. Sarah ce ta shiga d'akin Mama ta ajiye mata tea d'in da ta had'o mata, ta zauna kusa da ita ta ce "Amma Mama meyasa baki sanar da Yaya Abdul gaskiyar abun da ya faru?" Murmushi Mama ta yi ta ce "Sabuda nasan halin Abdulfatah da zuciyar da yake da ita zai iya zuwa yai wa 'yar mutane ila akan wannan abun amma na bata lokaci zan d'au mataki da kaina dan bazan zuba ido d'ana yana da tarbiya ya auri mara tarbiya ta b'ata mana zuri'a da 'ya'ya marasa tarbiya ba." "Hakane Mama amma wana mataki zaki d'auka?" "Bazan raba Abdulfatah da matar sa ba amma zai k'ara aure dole na nemo mata me tarbiya wadda zata iya gyara masa gidan sa ta haifa masa yara masu tarbiya." Ajiyar zuciya Sarah tayi ta ce " kuma shi Yaya Abdul zai yarda ya yi aure yanzu? bayan bai jima da yin aure ba." "Kinsan Abdulfatah duk abun da muke so da Abban ku idai bai sab'a shari'a ba to zaiyi shi." "Hakane Mama." Nan suka ciga ba da hira da yaba kirki irin na Islam. Mufida tunda ta ga Mama ta fita hankalin ta ya tashi dan ta na tsoran ta fad'awa Abdulfatah a samu matsala. Ta na zaune taji shigowar sa gidan a tsorace ta mik'e ta na zare ido ta ce ................! Free page ya k'are duk meso ya karan ta wannan litafi har k'ar she zai biya #200 ta wannan number 08166077167 *Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karan* *tawa* *zai* *biya* #200 *kacal* *Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167 COMMENTS AND SHARE by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 11-12 _____________ "Am ka kadawo." Ido ya zuba mata ya na mamakin abun da ya rud'ata haka, tsaki kawai ya ja ya haye sama ya barta a gurin. Ganin beyi magana ba tayi ajiyar zuciya ta koma kan kujera ta zauna, aranta ta ce ko Mama bata fad'a masa ta zo ba? "Koma mene tunda na tsira shikenan" A fili tayi maganar dai-dai lokacin da ya sako, tsayawa ya yi da mamaki ya ce "Kodai wani abun kika sha?" Harara ta watsa masa ta mik'e ta shige d'akin ta. Da kallo ya bita ya na mamakin ya akayi Mufida ta zama mara kunya, kafin ayi auransu ko magana bata agawa sama da tasa ko da kuwa zai huni a kanta yana mata fa a amma yanzu har tsaki ta ke masa ko ta harare sa kamar ba mijinta ba ta huce. Girgiza kai kawai ya yi ya shiga kitchen dan ya ora abunda zai ci. Dariya ta ke ta yi tana rike da waya sai kokawar sa talami take, Ummi na tsaye tana kallon ta ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ayi hakuri da wayar nan a bari agama shirin tukuna." Sahal dake bawa Islam labari yana jin muryar Ummi yai sauri ya kashe wayar. Islam ta turo baki ta ce "Kai Ummi ya jiki fa." "To seme Sahal in bakona ne ko me?" "Duk da haka Ummi da ki....!" Da uwa Ummi tai mata ta ce "Nayi maganar yanzu Asibiti zaki ta fi amma kinfi awa guda kina shiri bayine kawai bakije da wayar nan ba, kuma sai a hanani fad'ar gaskiya." Takalmin tasaka ta rataya jakar ta ta ce "To kiyi hakuri nidai na tafi." "Allah ya tsare uwata." "Ameen Ummina." Fita Islam ta yi ta samu babur ta huce gurin aiki. A can ma Sahal yana ta kiranta amma ta i auka sabuda tasan in dai ta aga bazai barta ta yi aiki ba kuma shima bazai fita ba. Mi ewa ta yi ta shiga office in Doctor Rukayya. Salama ta yi, Doctor Rukayya ta amsa da fara'a, zama Islam ta yi ta ce "Dama zuwa na yi mu gaisa yau ban shigo mun gaisa ba." "Gaskiya ne ya gida? Ya Ummi?" "Lafiya alau muke aunty Rukayya." "Masha Allah haka akeso, jiya na baki wata peppers ko ki ajiye mun." "Eh anyi haka amma kiyi hakuri wallahi na manta ta a gida." "Ayyah gaskiya banji da i ba inda hali ki tashi ki gida ki kawota sabuda ta Doctor Abdul kuma yanzu zaiyi anfani da ita." Ido Islam ta zaro ta ce "Meyasa baki fa a mun tun jiya tashi ce ba da ban ansaba wallahi." "Nidai ki daure kije ki ako." Tashi Islam ta yi ta fita da sauri. Suhal ta kira a waya ta ce tayi mantuwa ya zo ya maida ita gida. Ba'a au wani lokaci ba yazo suka koma gida, Takadun ta ako suka dawo Asibiti. Fi towa ta yi daga cikin adaidaitar, shima Suhal fitowa ya yi ya matso kusa da ita ya ce "Gaskiya mukayi aure daina wannan aikin zakiyi." Murmushi ta yi sannan ta ce "Nima haka nake tunani bazan ha a aure da aiki ba." "Kinyi tunani me kyau Baby." Dariya ta yi ta ce "Yanzu dai ka tafi aikin ka Sweetie. " "To Baby ki kula da kanki." "In sha Allah." Ya koma ya tashi babur in yabar gurin Islam na tsaye ta na ta aga masa hannu har ya acewa ganin ta. Duk abuda ke faruwa Abdulfatah yana cikin motar sa ya na kalon su. Hakan nan ya ji ranshi ya aci da kamar zai share sai ya fito daga motar ya nufo ida ta ke, Ta juyo zata shiga ciki ta yi ido hu u da shi yana jifan ta da mugun kallo. Jikinta ne ya auki rawa za ta yi magana ta ji ya ce "Wato iskan cin naki ya huce a waje har Hospital ina kike kawo gardawa ko?" Ran Islam ne ya aci bata ta a tanka masa ba sai yau taji baza ta iya rabuwa dashi ba. Cikin acin rai ta ce "Ya isheka ai batani da kakeyi ba ci kake bani ba sha kake bani ba amma ka takurawa rayuwa ta kulum cikin askan tani kake ka ta a kamani da wani ne da zaka ringa ai batani ni nayi kaina a talaka ko ba a da ka tsaneni duk wannan abun sabuda ina aikine a ar ashin ka ne ko to in sha Allah na daina har abada bazan sake dawomaka Hospital ba arziki na Allah ne muma wata rana zai azur tamu." Tana maganar tana hawaye har takai aya ta cila masa takadun sa tabar gurin. Da kallo ya bita yana jin ciwan maganar da ta fa a masa amma zai au mata ki babba akan wannan yarinyar, Takardun da ta watsa masa ya kwaso ya duba ya ga wanda ya bawa Doctor Rukayya ne, kawai saiya koma motar sa dama su yazo amsa ya juya gida ransa ba da i. Mama na gaban Abba ta na kallon sa shikuma ya na cin abunci, saida ta bari ya arasa sannan ta ce "Dama inaso muyi magana dakai akan Abdulfatah." "Inajin ki." asa ta yi da kanta ta ce "Aure na ke so ya ara." "Me? Aure fa kika ce kwata-kwata kwana nawa dayin auran na sa?" "Nasan da haka amma dole ce tasa na ke so ya ara auran." Nan ta kwashe irin hula an cin da Mufida ta mata ta sanar da Abba sannan ta ara da cewa "Na i sanar da Abdulfatah sabuda karya je yai abuda bai da ce amma duk ran da ya titsiyeni yana san sanin meyasa na ke so ya ara aure zan sanar da shi abun da ya faru." Ajiyar zuciya Abba ya yi ya ce "Amma akan wannan dalilin kawai zai ara aure?" "Bafa a ramun dalili bane, so kake mu zuba ido aita haifawa Abdulfatah yara marasa tarbiya irin matar sa." "Shikenan Allah ya bada sa'a." Cikin farin ciki Mama ta ce "Amin nagode Abban su Sarah Allah ya ara arziki." "Amin, amma za i zaki bashi ya fito da mata?" "A'a sabuda idai na bashi za i to bazai auran ba yata mun kame-kame kenan amma idan na za a masa da kaina ba wani lokaci da zai ata mana." "Gaskiya ne, yanzu wa kika za a masa?" Murmushi ta yi ta ce "Eh na za a masa ..........! by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 13-14 _____________ "Amma sai na gama binkice akan yarinyar tukun." "To Allah ya za a masa abunda yafi alkairi." "Amin." Daga haka suka cigaba da hirar su. Islam na kwance kusa da Ummi ta ji wayar ta na ruri duba wa ta yi taga Sarah ce, ta na murmushi ta auka. "Assalamu alaikum." Ta furta a hankali, muryar Mama ta yi ta ce "Amin wa'alaikum salam." Kin ladabi ta ce "Mama ina huni?" "Lafiya alau Islam ina Ummin ki?" "Gata ma tanajin ki." "Okay bata mu gaisa." Mi awa Ummi wayar ta yi Ummi ta amsa suka gaisa da Maman Kaduna, sannan ta ji Ummi ta ce "To Allah ya kaimu, nagode Allah ya bar zumunci." Ta kashe wayar ta mi owa Islam ta na cewa "Mama ta ce gobe in sha Allah za suzo da Sarah." Ido Islam ta zaro ta ce "Nan gidan za suzo Ummi?" "Eh mana da wane gida muke da shi bayan wannan." Ajiyar zuciya ta yi hakan ta ji hankalin ta bai kwanta da zuwan Mama gidan suba. Komawa ta yi ta kwanta ta cigaba da tunanin sahibin ta Sahal. Ummi na ajiye wayar ta kali Sarah da ke kusa da ita ta ce "Allah ya sa za in da naiwa an uwaki ya yi dai-dai?" "Gaskiya ya yi Mama amma kika sani ko ita Islam in ta na da wanda ta ke so?" Murmushi Mama ta yi ta ce "Nasan da haka shiyasa na dage a addu'a Allah yasa ita ce matar Abdulfatah." "Amin Mama." Ki cewa Ammi ta shiya goban da ita zamu ta fi." "To Mama." Sarah ta ce ta auki wayar ta tafi ce. Zaune ya ke a mota yana kallon Marwa ita ma shi ta ke kallo ya kashe mata ido ya ce "In sha Allah jibi na dawo daga Lego's zan sanar wa Abba maganar aure na da ke." Murmushi Marwa ta yi ta ce "Gaskiya naji da in maganar ka amma fa kar naji shiru a samu matsala." Hannun ta ya kamo ya ce "Al awari fa na miki kuma kinsan zan cika miki." "Okay naji yanzu bari na shiga gida sai ka dawo jibin." "To ki gaida Mommy." "Zataji." Ta ce tana fitowa daga motar, ya ja motar ya bar gurin. Wayar da ke hannunta ta fara danna wa ta kara a kune. Hello Sada yau zaizo yan kin ku, kusa mun ido a kansa dawa zaizo kuma gurin wa yazo da abunda ya zo yi ko maca aya kuga ya fiye shishige mata ku saita mata hanya." Ta na gama fa in haka ta kashe wayar ta na murmushi a fili ta ce "Saura ke Mufida kike ko wa? Tunda kika sake kika auri abunda na ke so to wallahi saina ga bayanki." Ta girgiza kai ta wuce gida. Washe gari su Mama suka shirya suka je gidan su Islam, Ummi ta tarbe su hannu bibbiyu cikin fara'a da sakin fuska hakan ba aramun da i ya yiwa su Mama ba, Bayan su bai sa Ammi ta ce "Gaskiya mun gode sosai da karamci Ummi." Murmushi Ummi ta yi ta ce "Ba komai mun zama aya." "Hakane shiyasa na ke so mu zumunci mu ya ara arfi ta hayar bamu Islam." Dariya Ummi ta yi ta ce "Islam ai ar ku ce za ku iya aukan ta." Ajiyar zuciya Ammi ta yi a hankali ta ce "Ba irin wannan aukan ba inda hali auran ta zaki bawa ana." Cikin razaki Ummi ta ce "Aure kuma?" "Kwarai kuwa, ki mana wannan taimakon." "Bawai zan watsa muku asa a ido ba ne amma Islam ta na da wanda ta ke so." Karo na farko Mama ta ce "Idan hali kuyi mana wannan sadaukar war." Nan ta bata Labarin komai ga me da Mufida sannan ta ce "Dan Allah ki ro a mana alfarma gurin Islam da shi yaron da ta keso tunda manya ba su shiga maganar ba." Shiru Ummi ta yi ka fin ta ce "To zan duba na gani." Godiya sukayiwa Ummi suka huce gida. Bayan kwana biyu Mi ewa ya yi ya tsuguna yana duba jarbin sa na dannawa da ya fa a ar ashin gado, hannu ya zura yana lalubawa a hankali ya ji ya ta o wani kwalin magani. Jawoshi ya yi ya fara dubawa gaban sane yai wata irin fa uwa ganin maganin zubar da ciki ne. To waye ya yi anfani da shi? Ya tanbayi kan sa, mi ewa ya yi da sauri ya fita ta na zaune ta hakim ce a falo ta na kallo. Gabanta ya je ya tsaya ya nuna mata kwalin ya ce "Wan nan maganin na waye? Kuma waye ya yi anfani da shi?" Ya tsine fuska ta yi ta ce "Magani dai na wane kuma ninayi anfani dashi sabuda naje Hospital shekaran jiya Doctor Rukayya ta ce ciki ga reni shiyasa na bawa Nuratu ku i ta siwomin wannan maganin na sha kuma Allah ya taimakeni cikin ya fita bansha wata wahalaba baka gida ma shiyasa baka sani ba, cewa nayi bazan jira saika dawoba sabuda bazan zauna da ciki tun yanzu na haihu na tsofe ba wallahi." Ai Abdulfatah bai san sanda ya...........! by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 15-16 _____________ Zube a gurin ba ya dafe kansa yana karanto "Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un." Baki Mufida ta ta e ta ce "Kayi hakuri idan ranka ya aci amma gaskiya bazan iya haihu yanzu na tsufa ba." Ko kallon ida ta ke beba ya na zaune zuciyar sa tana wata irin tafasa, shi Mufida zata zubarwa da ciki kamar ba cikin sunnah ba kuma har take iya fa a masa da bakin ta. Mi ewa Mufida ta yi ta bar masa gurin duk da cikin zuciyar ta cike ta ke da tsoron ma takin da Abdulfatah zai auka akanta amma ta dake kamar bata damu ba tai shigewar ta aki ta barshi. Yafi awa duda a gurin yana dafe da kansa sannan ya mi e ya nufi akin Mufida ransa ya na suya. Da dare bayan sun gama cin abunci Ummi tali Islam ta ce "Dama ina so muyi wata magana da ke." Cikin nutsuwa Islam ta ce "Inajinki Ummi." Ajiyar zuciya Ummi ta yi ta ce "Yanzu na ce ki auri wani ba Sahal ba zaki amunce." A tsorace Islam ta ce "Meya kawo irin wannan maganar Ummi." "Tabayar ki nayi." asa Islam ta yi da kanta ta ce "Ke Mahaifiya ta ce kuma kin cike mun gurin mahaifi na ba abunda baki mun a rayuwa ta ba dan haka ba abuda zakice na yi a rayuwa na kasayi miki, amma Ummi idan kika ce na auri wani ba Sahal ba ya zanyi da shi?" Cikin nutsuwa Ummi ta ce "Sahal ba magana ya yi da magaba tanki ba kuma koni ina so naga kin auri Sahal kodan son da yake miki amma Mama ta da abokiyar zamanta sunzo neman alfarma suna so abawa ansu auran ki, da naso na share su sai naga magana suke akan tarbiyar ki ce tasa suke so su ha a jini da ke to shiyasa na ce nikuma zan amunce domin wannan shedar da suka miki bazasu hula an ta kiba kuma inaso kema karki basu kunya." Tunda Ummi ta fara magana Islam ta ke hawaye wai da gaske Ummi ta ke wani ta ke so ta aura ba Sahal ba. Da fata Ummi ta yi ta ce "Bazan miki dole ba idai bakyaso to zan basu hakuri." Cikin kuka ta ce "Nasan bazaki ta a za a mun abunda zai cutar da ni ba dan haka na amunce amma kimun wata alfarma guda aya." "Wace alfarma ce?" "Ke zaki sanar da Sahal cewa kinmun miji." Rugumeta Ummi ta yi ta ce "Nagode Allah yaimiki albarka kuma in sha Allah zan kirashi har gida na masa bayani yadda zai fahim ce ni." "Amin Ummi." Islam ta fa a tanajin zuciyar ta kamar zata fashe. Abdulfatah kuwa yana shiga akin Mufida ya tadda ta na kwance ta ora kafa aya kan aya ta na danna waya. Wayar ya fuge itama ya fusgota daga kan gadon ya na huci ya ce "Sabuda kin mai dani sa'an wasanki ni zaki zubarwa da ciki, cikina na sunnah ba na kwararo ba amma kika zubar mun da shi." Mi ewa tsaye ta yi ta ri e ugu ta ce "To sai me dan na zubar da ciki zan zauna ne na haihu da kuru ciya ta na lalace kaje ka auro daleliya ko to wallahi baka isa ba ko gobe nayi ciki saina zubar da tsinane na ga......!" Bata arasa maganar ta ba ya kwashe ta da maruka har biyu wanda saida ta kai asa taka ta ya farayi yana tamole da ita ihu ta ke da kuruwa amma bai rabu da ita ba saida ya mata lilis sannan ya daina dukanta yana huci ya ce "Wallahi sai nayi shara'a da ke akan cikina da kika zubar zaki gane ki aramar ar bariki ce." Ya fice da ga akin ya barta a gurin da tsamin jiki. Washe gari Ummi ta sa Islam ta kira Sahal a waya ta sanar da shi Ummi na ne mansa, Bai jima ba ya zo, Ummi ta sa aka shigo dashi har falo bayan sun gaisa ta dukar da kai ta ce "Wata alfarma na ke nema a gurin ka." Cikin rawar jiki ya ce "Alfarma kuma Ummi ko mene ki bani umarni nayi." Kai ta girgiza ta ce "Kayi hakuri da abunda zan fa ama nima ba haka na so ba amma ba yadda zanyi, ina so kayi hakuri da auran Islam na mata miji." Wata irin fa uwar gaba Sahal ya yi yanajin zuciyar sa na bugawa da sauri da sauri ya ce "T.. To Ummi Allah yasa hakan shi ya fi alkairi." "Amin Allah ya muku albarka." "Amin." Ya mi e jiki a sanyaye ya fita, Islam da ke la e ta najin duk abuda suke tattanawa ta bi bayan sa da sauri. A soro ta kira sunansa ya juyo yana kallon ta da ida nuwan sa da suka koma ja, Jikin ta har rawa ya ke muryar ta ma rawar ta ke ta ce "Yanzu har ka ha ura dani cikin sau i haka meyasa zuciyar ka tai saurin karaya da.....!" Hannu ya aga mata ya ce "Ya isa Islam wana mataki kike so na auka bayan wanda kuka yanke da Mahaifiyar ki, dama tuntuni ina kawowa a raina bazaki auri talaka mejan kafu babur ba amma na i hakura na nace yau gashi naga iyaka ta." Tunda ya fara magana Islam ta ke kuka me tsuma zuciya yana kai aya ta ce "Wallahi ba haka ba ne nima bansan taimako zai shiga tsakanina da kaiba da banyi ba." Nan ta sanar dashi Mama da suka taimakawa suka kai Asibiti ita ce ta zo neman alfarma gurin Ummi ita kuma Ummi ta kasa cewa a'a. "Hmmm dama ina zata kasa hanasu tunda ni me kafu babur ne su kuma masu arziki, kidaina wahalar da kanki Islam komai nufine na uban giji na barki lafiya." Ya juya ya fice ya barta a soran, zubewa ta yi akan guyoyinta ta na wani irin kuka me ta a zuciya ji take kamar ranta zaibar gangar jikin ta shikenan yanzu ta rasa Sahal wannan wace irin addara ce me tsauri haka. Abdulfatah gida ya nufa ranshi a ace, A falo ya tadda Abba da su Abdulmalik suna hira zama ya yi ya gaida Abba, Abba ya amsa ya na kallonsa ya ce "Me yake damun ka Abdulfatah?" Yana huci asa- asa ya ce "Ba komai Abba." Murmushi Abba ya yi ya ce "To shikenan Allah ya kyauta." "Amin." Ya ce yana hararar su Abdulmalik sum-sum suka tashi suka fice daga falon. Ammi ce ta fito da tea a hannuta ta ajiyewa Abba ta na cewa "Abdulfatah lafiya kuwa? na ganka ba a nutsuwar ka ba." asa ya yi da kansa ya kasa cewa komai. Abba ne ya zaro waya ya kira Mama dan yasan ba lafiya a tattare da Abdulfatah. Fitowa ta yi daga akinta ta shigo falon da salama. Duk suka amsa ta zauna kusa da Abba ta na kallo sa ta ce "Gani Abban Sarah." Nuna mata Abdulfatah ya yi ya ce "Ki tanbayi aki me yake damun sa." Sai lokacin ta kula da Abdulfatah da ya ke zaune a falon ta mi e ta koma asa ida ya ke zaune ta ce "Abdulfatah me yake faru?" Hawaye ne suka gangaro fuskarsa Mama ta ara tsorata da lamarin dan rabon da taga hawayan Abdulfatah tun yana yaro. A hankali ya furta "Mama Mufida ta cuceni wai ni zata zubarwa da ciki." Salati duk suka auka Mama ta dafashi ta ce "Kayi hakuri Abdulfatah Mufida ta cuceka amma kai ka siyo hakan da ku in ka tunda baza ka iya binke ce akan mata ba tunda tama shikenan." "Wallahi Mama na gama zama da ita." Abba ne ya ce "Ka daina rantsuwa Abdulfatah dan bazaka saki Mufida ba." Kallon Ammi ya yi wai ta yi magana ta girgiza masa kai, Mama ce ta ce "Kar ka sake cewa zaka rabu da matarka kana sonta laifi tama kuma zai huce amma fa aure zaka ara." Da sauri ya ce "Yauwa Mama dama inada wanda nayiwa alkawarin aur....!" Muryar Abba ya ji ya ce "So kake mu ara baka dama ka auro wadda zasu taru da Mufida su arasa kasheka." Cikin rarrashi Ammi ta ce "Iyayanka sun za ama wadda zaka aura." Da kallo ya ringa binsu tun yana fahim tar abunda suke cewa har ya daina, mi ewa ya yi a razane ya............! by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 17-18 _____________ Zai fice jiri ya kwashe shi ya yi baya zai fa i da sauri Abba ya taro shi yana salati suma su mama salatin suka sa, Abba ya ajiye shi kan kujera yana masa sannu Ammi ce ta ce "Sannu Abdulfatah." Kai ya gyada mata kawai, Abba ya dube shi ya ce "Nene matsalar ka Abdulfatah daga maka zancan aure zaka fa i." Cike da dauriya ya ce "Abba inda wanda zan aura yanzu sunan ta Marwa dan girman Allah ku barni na aure ta ba dan ni ba." Kallon juna Abba da Mama sukayi Mama tai sauri girgiza masa kai, ya kauda idon sa daga kanta ya kali Abdulfatah ya ce "Karka ji komai Abdulfatah zanyi shawara da Mahaifiyar ka." Cikin tsananin farin ciki ya mi e ya yiwa Abba godiya ya huce gida kansa na mugun ciwo dan sai Abdulmalik aka sa ya kaishi gida. Bayan ya tafi Abba ya samu Mama ya ce "Yanzu mene abun yi?" "Nidai na karaya wallahi kawai a rabu dashi ita yarinyar ko Abdulmalik ma bawa." Kai Abba ya girgiza ya ce "A'a baza'ayi haka ba Abdulfatah akayi niyar bawa dan haka bazan canza ra'ayi ba, mun masa adalci ya auri wanda ya ke so to tunda ya kasa za o ar mutunci dole ne mu muza a masa da kan mu." Ajiyar zuciya Mama ta yi ta ce "Amma kana kallo fa uwa ya kusayi a gurin nan sabuda zancan auran." Murmushi Abba ya yi ya ce "Ai dama da acin ran matarsa ya zo gidan nan ba zancan aure ya sashi wannan halin ba sai acin rain matarsa da ta zubar masa da ciki." Kai Mama ta gya a ta ce "Hakane Allah ya tabbatar da alkairi." "Amin." Abba ya ce suka cigaba da hirar su. Yana zuwa gida kwanciya ya yi ko magani bai nema ba haka bacci ya kwashe shi. Cikin bacci ya ji wayar sa na ruri, A hankali ya sa hannu ya zaro ta, Marwa ya gani dan haka ya aka ya kara a kune tare da yin Salama. Amsawa ta yi ta ce "Meyasa kake mun haka Abdulfatah tun safe mukayi da kai zamu ha u amma shiru ban ganka ba ko dan kaga ina son ka da ya wane shiyasa kake hula an ta ni." " Cikin rarrashi ya ce "No ba haka ba ne Marwa ina kwance ba na jin da i." "Ayyah sannu bari na zo na dubaka." "A'a ki barshi kawai nagode." "Allah sai nazo duba mijina dan tun yanzu wannan ku a iyar matar taka tasan da zamana." Zaiyi magana ya ji ta kashe wayar, shiru ya yi ya kasa binta dan yasan idai Marwa ta yi niyar abu to ba wanda ya isa ya hanata, A ransa ya ce ai garama ta zo kodan Mufida ta ji irin ba in cikin da ya ji. Duk yadda Islam taso dane damuwar ta kar Ummi ta gane kasawa tayi dan har ta rame so tari Ummi tana kamata tana kuka amma bata canza ra'ayi ba. Tana yawan kiran Sahal amma baya auka daga arshe ma wayarsa dai na shiga tayi gaba aya. Yauma tana aki a kwance tana ta faman kuka Ummi ta shiga, saurin goge hawayen fuskarta ta yi amma Ummi ta riga ta gani zama ta yi kan gadon tana kallon artata da tausayawa ta ce "Ban sani ba ko namiki laifi dan na rabaki da Sahal amma inaso ki san wani abu, ita rayuwa ba komai kake so kake samu ba kamar ke da kika damu da Suhal Allah zai iya jarbatar ki ta rabuwa da shi, kuma ki sani matar mutum kabarin sa ki godewa Allah da addara rabaku ta yi da Suhal ba kasheshi ta yi ba." A tsorace ta ke kallon Ummi. Ummin ta gya a kai ta ce "Ina mamakin yaran yanzu da baku yarda da adara ba kudai in kuna son abu to ko a mutu ko ai rai shi za'a baku, kun mata da iyayen ku bazasu za a muku abunda zai cutar da kuba, abunda baku sani ba shine yadda iyayen suke sonku ku bakwa son kanku haka amma gani kuke kamar tsanar ku akayi ko?" Kai Islam tai saurin girgiza wa ta ce "Wallahi Ummi ban ta a ji a raina zan sa a miki ba kuma na yarda da za in ki gare ni duk da basan waye ba ban ta a ganin sa ba amma na amunce a haka kawai na kasa man tawa da Suhal a zuciya ta lokacin da Doctor Abdulfatah yana cusgunawa rayuwa ta shine ya ke faran ta mun kuna na yarda so na gaskiya ya ke mun." Dafata Ummi ta yi ta ce "Na sani amma ki duba alfarma da girma irin nasu Mama amma tazo har inda nake ta nemi alfarmar abasu auran ki badan komai ba da sun yaba da tarbiyar ki da iliminki basu duba matsayi ko arziki ba kinga kuwa wannan mutane bazakayi dana sanin ha a zuri'a aya da suba kuma nasan zasu mutun taki shiyasa badan arzikin su ko wani abuba in da a mutun taki nake hange, shi Suhal da kike so zata iya kasan cewa dagin shi ba sa sonki to wallahi idan auran ya yi tsayi sheni ya shekara duk son da yake miki sai sun cusa masa iyayyarki shikuwa wannan kodan son da iyayensa suke miki dole ya rungimeki hannu biyu indai an mutun ci ne." Ajiyar zuciya Islam ta sauke ta ce "Hakane Ummi nagode Allah ya saka miki da gidan a aljana." "Amin." Ummi ta ce tana murmushi tai ta jan Islam da hira har ta saki ranta. Ko salama babu ta shigo falon tana ya mutsa fuska dai-dai lokacin da Mufida ta fito daga akin ta, Kallon juna suka kamayi kowa da abun da yake rayawa a cikin ransa, Tsaki Marwa ta yi ta cigaba da tafiya ta nufi akin Abdulfatah, Gaban ta Mufida ta sha ta ce "To daga ina naga kina shirin shiga akin mijina." Fuska Marwa ta ya mutsa ta ce "Bai ta a sanar da ke yana da wata matar bayan ke ba? To tun wuri ki matsa daga gabana dan ni ko mayan maza an daba tsorona sukeji sabuda sunsan halina zan iya kashe mutum ba wani abu bane." Tsaki Mufida ta yi ta ce "Ni kuma baki isa ki shiga akin mijina ba saidai duk uban da za'ayi ayishi." Murmushin mugun ta Marwa ta yi kafin Mufida ta ankara ta zaro wani arfe a jikinta ta kafa mata a..........! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 19-20 _____________ Hannu amma ba ta yi na sarar samun ta ba taji an rike hannun ta juyawa ta yi ta ga Abdulfatah ne yana watsa mata mugun kallo kafin wa ce "Wannan wane irin haukane Marwa raunata ta zakiyi." Huci ta farayi ba ta ce komai ba ya juya yana hararar Mufida ya ce "Na rasa yaushe zakiyi hankali ki ringa kama kanki mtss." Ya ja tsaki ya cewa Marwa ta biyo shi ya shige akinsa. Saida Marwa ta juyo ta watsawa Mufida kallon banza sannan ta shige akin Abdulfatah. Zubewa Mufida ta yi a gurin ta na kukan ba in ciki, Ganin kukan bazai amfane ta ba ta mi e ta shiga akin ta. Wayarta ta ako ta kira number Nuratu. Tana agawa ko magana Mufida bata bari ta yi ba ta ce "Kina ina nazo na sameki?" Cike da mamaki Nuratu ta ce "Ina gida mana amma da zan fita." "Okay jirani ina zuwa." Mayafi kawai ta zura ta fice daga gidan. Zama ta yi kan gadon tana turo baki, Murmushi ya yi ya ce "Mene abun damuwa kuma?" "Hmmm wai a gaban wannan kucakar matar ta ka kake mun fa a." "Ba haka bane Marwa gidan ta kika zo dan haka duk matakin da ta auka a kanki bata da laifi." "Hakane amma kasan bana aukan raini ko, naso ka barni na ilatata wallahi amma yan zuma zamu ha u zanyi maganin ta." Shidai Abdulfatah bai magana ba sai komawa da ya yi ya kwanta ya barta tana ta mita ita ka e. Da salama ta shiga gidan Nuratu ta amsa tana fi towa daga aki ta rungume ta, Murmushi ya e Mufida ta yi ta ce "Akwai matsala Nuratu." "Wace irin matsala Mufida?" "Abdulfatah ya daina sona Nuratu duk shirin da mukayi ya tarwatse har mata yake kawowa gida yanzu." "What." Nuratu ta fa a da arfi tana zaro ido, Kai Mufida ta gyada ta ce "Yanzu mene abun yi?" "Hmmm abunyi ayane mukoma gidan Malamin daya mana aikin tun farko." "To amma kinsan bani da ku i yanzu ya daina bani komai." "Ke kikayi sake har ta kaiku ga haka, amma zuwa zakiyi gurin Alhaji Sani kice har yanzu haifin ki ba lafiya za'a mishi aiki ya daure ya baki ku i ki biya ku in aikin." Rungume ta Mufida ta yi ta ce "Gaskiya wannan shawara taki tayi awata taso muje tun yanzu ba sai anjima ba." Tashi Nuratu ta yi suka fice daga gidan. Har office in Alhaji Sani suka je ya yi mamakin ganin Mufida gashi ta ara iba ta yi kyau sosai. Bayan sun gaisa ne Mufida ta kalle shi ta ce "Kayi hakuri Alhaji mahai finane ba lafiya shiyasa baka ganina ko a waya baka samu na gashi yanzu ance aiki za'a masa gashi bamu da ku i murasa yadda zamuyi shine na yanke shawarar zuwa gurinka ka taimaka mum." Murmushin rainin hankali Alhaji Sani ya yi sannan ya ce "Bakomai turo account number amma a ina zaki kwana tunda dare ya yi baza ki koma auye yan zuba?" Muryar ta na rawa ta ce "Am dama gidan Nuratu zan kwana." "Okay basai kin ora mata nauyi ba muje gidana ki kwana." Kallon juna sukayi da Nuratu, Nuratu tai saurin gyada mata kai, Fuska ta marairaice amma Nuratu ta harareta batasan sanda ta ce "To Dear nagode amma bari buje na oko kayana gidan Nuratu." "Ba matsala idan kin shirya ki kirani nazo na taho da ke." "To." Ta ce suka masa salama suka fito. Bayan sun hau an sahu Mufida ta ce "Nidai gaskiya gida zan tafi taya zan kwana da wani ato bayan kinsan yanzu inada aure." Tsaki Nuratu ta yi ta ce "Yanzu ba mijin nakine ya kai wata atuwa gidan kiba?" "Hakane amma tsoro nakeji wallahi." "Sai kace ba Mufida da na sani ba ki saki ranki yarinya." Zigata Nuratu ta ringayi har ta amunce da kudirin Alhaji Sani. Duk abunda suke tattaunawa Alhaji Sani yana sauraran su ta wayar Nuratu saida suka sauka ta kara a kune ta ce "Yanzu ka yarda Mufida ta ci amabarka ta yi aure." "Na yarda kuma na gode da kika sanar dani da wuri zan bari naga iya gudun ruwanta sannan na hukun ta ta." "Shikenan sai na jika." Sukayi Salama tai saurin kashe wayar ganin Mufida ta nufo inda take. Bayan kwana biyu da amun cewar Islam Ummi ta kira Mama ta ce sun amunce. Ba aramun farin ciki Mama ta yi ba taringa yiwa Ummi godiya, Ummi ta bata address in dangin uban Islam dan Ummi ta ce acikin satin nan za'aje a gama komai ba taso bikin ya ja lokaci, sukayi salama cikin girma ma juna. Abdulfatah na zaune a falo ya rasa abunda yake masa da i tunani yake ina Mufida ta shiga sai yanzu yake na damar barin Marwa ta zo inda ya ke. Message yaji ya shigo wayarsa ya duba rubutu kamar haka. SALAM BARKA DA DARE ABDULFATA NASAN YANZU KANA ZULUMIN INDA MATARKA TAKE TO KA KWANTAR DA HANKALIN KA MUNA TARE DA ITA A HOTEL ITAMA ZATA RAMA IRIN CIN MUTUNCIN DA KA MATA. Yana gama karan tawa hotuna suka shigo wanda Mufida ta ke shiga hotel gata da wani katon mutun a aki tare...............! by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 25-26 _____________ Ya bu e baki zeyi magana kuma komai ya tuna saiya fara ya juya zai shiga motarsa, ya ara juyowa ya ce "Kuskure mafi girma da zakiyi a rayuwar ki shine ki yarda da aure saina wula anta rayuwarki." Yana gama fa in haka ya shige motarsa ya bar gurin. Sai lokacin Islam taji wani irin hawaye masu zafi sun taho mata ta juya ta shige gida tana o arin oye damuwar ta kar Ummi ta gane. Ranshi a dagule ya koma gida amma wani abun takaicin Mufida ya tarar ta dawo gidan. Tana ganin sa tasha jinin jikinta muryar can asa ta ce "An dawo lafiya?. " Mtsss." Tsaki kawai yaja ya huce yabarta a gurin. Da harara ta rakashi har ya shige akinsa, taja tsaki itama ta samu guri tai zamanta. Yana shiga akin nasa kan gado ya zube, ya na tunane-tunane. Yanzu shi bashida iko da kansa sai abunda akaso shi za'a masa ance sai ya yi aure ya yarda, ya saki mata an dawo masa da ita. To me ake nufi dashi? Ya tanbayi kansa, ka annansa Abdulmalik da Abdussamad ba wanda ya takura su sai shi aketa sa masa ido a rayuwar sa. Kirane ya shigo wayarsa ya duba yaga Marwa ce, saida gabansa ya fa i ya dake ya aga kiran ya kara a kune tare da yin salama. Bata amsa ba sai cewa da tayi. "Abdulfatah kasani kowa yaci tuwo dani miya yasha, wallahi baka ci bulus ba tunda ka yaudare ni kaci amanata to nima saina rama, akan wata ar matsiyata ka rabu dani ko? To nasan komai game da Islam wallahi saina lalata rayuwarta." Kit yaji ta kashe wayar. Jikin Abdulfatah ne ya yi sanyi yasan Marwa batada mutunci ya na tsoron ta cutar da ar mutane da bata ji ba bata gani ba, kiran wayar ta yayi amma yaga tanasa Busy alamun tasashi a black list girgiza kai ya yi, ya mi e ya nufi gidan ta. Gidan Marwa yaje amma ba ita ba alamunta haka ya baro gidan jiki a sali e dan ya na tsoron abunda zaije ya dawo. Anata shirye-shiryen biki har an kai lefan Islam akwatina 8 duk sha eda kaya na alfarma, Mama tafi kowa farin ciki da okin bikin an nata dan gani take kamar auran fari zeyi. Mufida kuwa sai yawan malamai takeyi wai dole sai ta hana auran da taga ba sarki sai Allah saita hakura amma tasa Abdulfatah a gaba masifar yau daban ta gobe daban, shidai baya biye mata rabuwa yake da ita ta araci haukarta. Yau saura kwana biyu biki Islam tasha gyara tayi kyau sai she i da warwali takeyi har kunshi ammata kanan yasha gyara gashi har gadon baya, tana zaune suna hira da an uwansu na Meduguri yaro ya shigo ya ce "Wai Ummi ta ce Islam taje tayi ba i a waje." Tashi tayi tasa hijab ta fita wajan. Wanda ta ganine yasa hantar cikinta ka awa ya sa kar mata Murmushi ya ce "Amarya bakya lefi." Jikin ta ne ya fara rawa, ya matso cikin nutsuwa ya ce "Islam bazan oye mikiba har kwanan gobe ina son ki kuma basan sanda zan daina son kiba, ina tunanin da sanki zan mutu Islam." Duk kansu hawaye sukeyi ya ara da cewa, "Amma Allah bai addaramun auran ki ba duk da ya jabaceni da sonki amma Alhadulilah da na kasance me yarda da wuhuncin ubangiji, koranar da nami wannan abun acin raine amma na fahimceki kuma na gane kema biyaya ce, shine nazo yau namiki salama da fatan alkairi Allah ya baku zuri'a ayiba." Kuka Islam take kamar ranta zai fita ya zaro leda daga aljihunsa, karona farko ya kamo hannunta ya danka mata ledar ya ce "Ga gudun mawa ta nan nagode da Soyayyar da kika nunamun Allah ya ha a fuskokin mu a aljana dan ba lalai ki ara ganina a rayuwar ki ba, nasiha aya zan miki kiyiwa mijinki biyaya ki manta sa Sahal a rayuwarki ki auka baki ta a sanina ba fatan alkairi." Yana gama fa in haka ya shiga kafu babur dinsa yabar gurin. Durkushewa Islam tayi a gurin ta saki wani kuka me sauti har shi ewa take sabuda azabar kukan da take. Wata ar uwarsu ce tazo fitowa taga halin da Islam take ciki, hannunta ta kamo ta mi ar da ita tsaye suka shiga gidan. Inda ba kowa ta kaita cikin damuwa ta ce "Haba Islam yaufa ranar farin ciki ce a gareki meyasa kike irin Wannan kukan kinsan gidan da jama'a ai saiya zama abun magana." Kasa tsada kukan ta Islam ta yi dan ji takai kamar ranta zaifita, rarrashi ta Zahira taitayi har ta samu ta tsagaita da kukan ledar da Sahal ya kawo mata ta bu e, ai batasan sanda tasa wani sabon kukan ba a fili ta ce............! by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 27-28 _____________ "Shikenan na rasaka Sahal me yasa adara zata rabani da kai? Ta ha ani da wanda baisan kimata ko mutuncina ba, inalilahi wa'ina ilaihirraji'un." Ta arasa maganar cikin kuka. Zahira ce ta dafata ta ce "Dan girman Allah kiyi hakuri ki daina wannan kukan haka dan Allah." Mikewa Islam tayi rungume da sarkar da ya kawo mata tashige akin ta. Da kallo Zahira tayi tana bita da kallon tausayi. Kwanan zaune Islam ta yi ranar sabuda bakin ciki ai kuwa ta tashi da ma tsanancin ciwo kai, ko ido bata son budewa. Ummi ce tazo dan Zahira ta sanar mata komai, cikin damu ta ce "Haba Islam kar kizama cikin bayi marasa yarda da adara me kyau ko mara kyau, ki sani komai kiga Allah ya hukunta maki to da hikimar yin hakan dan Allah ba azalimin bawansa bane, shi Sahal da kike so ba shine mafi alkairi a rayuwar ki ba, kulum ina miki wannan nasihar kinajin haushi bazaki gane ba sai nan ga." Cikin kuka ta ce "A'a Ummi wallahi ban a jin haushin ki ba, kiyi ha uri dan Allah." Nasiha Umma tayi mata sosai duk da ita ma zuciyarta ta karaya amma bata nuna ba. Shima Abdulfatah yau da mugun ciwan kai ya tashi har takai ko office ya kasa fita, yana aki a kwance ya na tufka da warwara. Mufida da take jiran fitowar sa ta are masa tadani taji shiru har 10:30am bai fitoba, gajiya tayi da jira ta mi e ta shiga akin nasa. A kwance ta hangosa cike da mamaki ta arasa kusa dashi ta zauna hañnu tasa ta ta a wuyansa taji zafi sosai jikin ta ne yayi sanyi cikin tausayawa ta ce "Dama baka da lafiya Abdulfatah?" Idanunsa da sukayi ja ya bu e a hankali yana kallon ta ya tsana ko kallon fuskar Mufida idan ya tuna salwantar da cikin sa da tayi. Cikin acin rai ya nuna mata hanyar fita ya ce "Fita ki bani guri, in ba haka ba kuma rainkine zai aci." Harara ta watsa masa ta mi e ta ce "Shidai me hali baya fasa halinsa." Ta fice tana kunkuni, duk da cikin zuciyar ta tana son sanin halin da Abdulfatah yake ciki amma baza ta iya rarrashi ko banhakuri ba. Kiran wayar Abba ne ya shigo wayarsa, Da kyar ya iya mi ewa zaune ya kara wayar a kune. Salama ya yi Abba ya amsa da cewa "Lafiya Abdulfatah kasan gobe ne aurin auran nan kuma na sanar da kai ina son ganin ka, amma baka zoba, ko katafi Hospital ne?" Cikin arfin hali Abdulfatah ya ce "Abba ina kwance bana jin da i." "Subahanallah, me yake damunka?" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Kaina Abba kamar zai cire." "Ayyah sannu Abdulfatah Allah ya baka lafiya amma ka rage sa damuwa a ranka sai komai yazo maka da sauki." Kai ya gyada kamar Abba ya na ganin sa. "Ka kira Doctor ya dubaka?" "Nasha magani Abba kuma nasan in na samu bacci zanyi dama-dama." "To Allah ya sawake." "Amin Abba." Sukayi salama ya kuma ya kwanta ya na rintse ido cikin tsananin tashin hankali, wai da gaske wannan ba ar yarinyar za'a aura masa? kuma gobe? Kanshi ya ara dafewa cikin tashin hankali ya na maimaita "Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un!. Har bacci yayi yawan gaba dashi. Wani ranar sukuku Islam ta yi shi duk wata walima da suka ha ama sai hakura sukayi sabuda Amarya ba lafiya. Washe gari Abdulfatah yasai ya tashi kan ya daina ciwo sai dai fa uwar gaba da yaketa fama da ita. Sa anin Islam da ciwo sosai ya kwantar da ita dole tasa Ummi ta sa aka kaita wani gida a makotansu sabuda hayani ya da bakin mutane. Gida ya shirya ya tafi dan Abba ya na ta kiransa. Mama ta ha a taro biki gagarumi har ya nunka na farko a cewarta yanzu tayi sirika. Ya na fita Mufida ta kira Nuratu ta zo gidan, kuka sha e-sha e Nuratu ta ta da ita tanayi cikin mamaki ta ce "Lafiya kuwa?" "Ina fa lafiya yaune bikin Abdulfatah." Zabura Nuratu ta yi ta ce "Me kika ce yaushe ya auroki da yake yin kurin aro wata." Tsaki taja ta ce "Mtsss dalla ba yinkuri ya ke yi ba yanzu haka ya fita aurin auran." Hannu Nuratu ta ora aka ta ce "Mu shiga uku, ya akayi kika bari haka ta faru?" "Tanbaya ta kikeyi bayan dake muke yawan malama mu hana abun." Shiru Nuratu ta yi cikin ranta ta ce Matakin da Abdulfatah ya auka akanki ya yi dai-dai naso iyayensa basu sa ya dawo da keba amma kishiyama ta isheki saura Alhaji Sani ma yarinya. Maganar Mufida ce ta katseta tai saurin cewa "Yanzu ya kike so muyi?" "Kiran da namiki kenan ai." Zama ta gyara ta ce "Tun farko laifin ki ne ya kika bari asirin da kika masa tun kina budurwa ya karye, gashi yanzu wani ya i tasiri a kansa amma idan yasan wata bai san wata ba dole ne kiyi anfani da basira gurin kora yarinyar nan gidan ubanta, duk abuda kika san Abdulfatah ya tsana shi zaki cusa mata shari kala-kala zaki ringa kula mata har ya tsaneta ya saketa." Ai Mufida batasan sanda ta saki wata dariya ba, Suka sa shewa gaba aya. Nuratu ta ce "Yanzu tashi zakiyi mu shirya kayan girki ki kira an uwa da kawaye azo asa ki a a cashe aci a sha, sabuda kar an uwanta suzo suga ba kowa ace bakida dangi." "Hhhhh kuma fa hane, shiyasa nake sonki Nuratu duk irin cakwakiyar da mutum ya shiga sai kin nemo solution." "Kar kiji komai awata in dai ina raye to ba abunda bazan miki ba." Nan suka tashi suka fara hada-hada. Bayan yaje gida suka gaisa da mutanen gida, Abba ya kirashi ya ringa yi masa nasiha me ratsa jiki da ha o in matarsa a kansa, sosai jikin Abdulfatah ya mutu ya na jin wani iri a ransa yayi niyar azabtar da Islam amma Abba duk ya kashe masa jiki. Da haka sukayi shirin arin aure suka tafi Mama tanata musu addu'a farin ciki fal zuciyar ta. An aura auran Islma da Abdulfatah akan sadaki dubu ari lakadan ba ajalan ba. Abdulfatah zuciyarsa kamar ta buga dan ba in ciki kasa zama ya yi a gurin ya sirare ba tare da kowa ya sani ba ya bar gurin. aga kiran da ya shigo wayarta ta yi "An aura auran yanzu Hajiya Marwa." Murmushi ta yi ta ce "Ya tabba ta Abdulfatah ya yau dare ni ko? To ku tabbar Amaryar ta zo hannun ku a lokacin, ku kirani in kun kaita gidan." "To Hajiya." Ta katse kiran ya yi murmushin mugunta ta ce "Zakayi mugun kallon Abdulfatah................. by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 29-30 _____________ Bayan an aurin aure sun gama tafiya, Ummi ta sa wata yayarta Hajjagana ta kaiwa Islam magani kuma tayi wanka ta fito. Hajjagana taje tasa Islam a gaba tasha magani taci abunci tayi wanka ta shirya, ita kanta taji da in jikinta amma gaba daya bajin da in duniyar take ba, ta fito suna gaisawa da mutane zata shiga cikin gidan, wani yazo ya mata salama, amsawa tayi ya ce "Sahal ne ya bani sa o na baki." Kallon Hajjagana tayi ta ce "Hajja ina zuwa, kije zan shigo gidan." "To." Hajja ta ce ta shige gidan Can bayan gidan suka je cikin zumu i ta ce "Me ya aikoka Sahal din bayan yasan yau nazama matar wani." Ta ara maganar tana hawaye "Am sakone ya bani bari kiga." Ya zura hannu a jakar dake sakale a wuyan sa ya ciro wata leda ba zato ba tsamani taji ya ba a mata hodar a fuska a take hankalita ya gushe ta zube a gurin kamar mataciya, da sauri yayi fito wata mota tazo suka kamata sukayi gaba shi kuma ya koma ofar gidan su Islam ya zauna inda yake azu ya ciga ba da har kokinsa. Abdulfatah ne kwance ya na faman tunanin hali da yake ciki yaji kira ya shigo wayarsa ko kallon wayar baiyiba bare ya aga kiran, har ta gaji ta katse. Aka ara kira amma ya i agawa, message aka turo sai lokacin yayi tsaki ya jawo wayar ya duba new number ya gani ya bu e message in. *zuwa yanzu nasan hankalinka a kwance yake kayi aure ko to tsune bata areba ga amaryarka a gurina sai yadda naso zanyi da ita amma zuciyata tafi amunta na kasheta*. Wani message in ya gani hotunan Islam ya gani cikin natsanan ci har gata a aure gurin wasu gardawa. A rayuwar Abdulfatah baisan mene kishiba sai yau da hautsinawa yaji zuciyarsa tana yi, kiran number ya yi amma taki shiga reply message ya yi ya ce "Kai wane?" Aikuwa yaga an turo da amsa *Hhhhh kamanta da Marwa na da nufin fansa a kanka ko to ka arawa kanka laifi kafin na kashe wannan azamar yarinyar sai ta zama ganimar maza Hhhhh* Zabura Abdulfatah ya yi ya fice daga gidan ya hau motarsa da mugun gudu yabar gidan. Gudu yake yama rasa ina zashi idan ya je police station kan suyi wani abu aikin gama ya gama kuma bazai fa a a gida ba hankalin mutane ya tashi amma yayi al awari zai dawo da ar mutane cikin koshin lafiya. Gidan Marwa ya je yauma bai tadda ita ba, dabara ce ta fado basa kawai ya juya ya nufi gidan iyayen ta. A hanya ya ringa kiran number ta har ta shiga. auka ta yi tana dariya ta ce "Haba new ango ya hankalinka zai tashi dan wanine zai angwance ba kaiba, to ka kwantar da hankalinka na fasa amma zan fa a inda zaka auki awar amaryarka." Cikin acin rai Abdulfatah ya ce "Marwa karki cutar da yariyar nan ni namiki laifi ba ita ba ki hukuntani ki rabu da ita." Dariya tasaka ta ce "Hhhhh Abdulfatah kenan ai dan na hukuntaka bazakaji ciwoba amma idan na mata kaine zakaji unar a cikin zuciyar ka kasan bana barin bashi." Yaji ta kashe wayar, jifa yayi da tashi wayar ya tada motar sa a fusace ya nufi gidan su. Acan gidan su Islam kuwa ba wanda ya farga Amarya bata nan tunda kowa yasan tana kwance ba lafiya, Ummi da taga yamma tayi koda yaushe za'a iya zuwa aukan Amarya ta fara nemanta amma ko sama ko asa bata ganta ba tun hankalin ta bai tashiba har ta fara susucewa cikin tashin hankali. Bayan Abdulfatah yaje kofar gidan su Marwa ya zaro wayarsa Mama ya kira cikin sa'a kuwa ta dauka ya ce Ta turo masa number Ummi, cikin farin ciki ta ce "to." Yasukayi salama. Mota ya mu e ya ako jarka ya shiga gidan, me gadi dayake ya sanshi bai hanashi shigaba ya shige falo, Daddyn Marwa da Kakarta da Mamanta duk suna zaune suka amsa salamar da ya yi zama ya yi ya gaida su suka amsa, Dady ya ce "Lafiya kuwa?" Ajiyar zuciya Abdulfatah ya yi ya ce "Ba lafiya ba, yau bikina kuma ar ku Marwa ta sace matata tana ikirarin kashe ta." Salati duka suka saka Dady ya ce "Marwa bazata aikata haka ba yaro kadai bi wani sarkin." Kaka da take tafa hannu ta ce "A'a Sa'idu Marwa ba hankali gare ta ba zatayi abunda yafi haka." Masifa Dady ya farayi wai Abdulfatah ya fice ya basu guri tun ransa bai aci ba. Mi ewa Abdulfatah ya yi ya nufi hanyar fita kofar fita ya daga falon ya sawa sa ata ya kule ya dawo cikin falo fuska ba annuri ya bu e jarkar da ya shigo da ita, Warin fetur sukaji ya rufe ya ce "Zuwa yanzu kunsa abunda yake cikin jarkar nan ko? To ku kira ar kuce ta bani mamata ko na one ku gaba aya." Ai Kaka tanajin haka ta saki fitsari a gurin jikinta ya na rawa, Mama ma kuka ta saka ta na bashi hakuri, Dady ne ya yi arfin halin cewa "Bansa da manufar da kazo gurin mu ba yaro amma ina ro on ka karka cutar damu." "Za i aya gareku ku kira Marwa ta sakar mun mata." Jiki na rawa Dady ya zaro wayarsa a aljihu ya kira number Marwa, Bugu 2 ta auka tare da cewa "Hello Dad ya gidan?" Cikin rawar murya ya ce "Ba lafiya Marwa wani yazo da fetur zai kone mu idai baki bashi matarsa ba." "What, Abdulfatah ne ya zo?" "Basan sunan sa ba, mudai ki temaka ki bashi matarsa dan Allah." Jiki a sanyaye ta ce "Bani shi Dad." Mi awa Abdulfatah waya ya yi jiki na rawa, amsa ya yi ya kara a kune, "Babban kus kuren da nayi a rayuwata shine nuna maka Ahalina Abdulfatah amma ka sani bana barin bashi." Ta kashe wayar message ta masa inda zai samu Islam fita ya yi da sauri yasa mukuli ya kule su Dady ya ajiye shi a wani guri a gidan ya mata reply da cewa *nakule iyayan ki idan na samu mamata zan fa a miki inda mukulin yake sa a nin haka kuma wuta ce zata tashi dasu* Kukane kawai Marwa batayi ba sabuda ta kaici da ba in ciki Abdulfatah ya maida ita shashasha amma zata nuna masa kanta yafi nasa ja. A hanzar ce ya kira number Ummi da Mama ta turo masa kuka yaji tanayi cikin tausayawa ya ce "Afuwa Ummi ni na zo na auki Islam sabuda na kira wayarta naji jikinta ya yi tsanani yanzu haka muna Hospital." "Amma meyasa baku fa a ba da zaku tafi?" "Ayi hakuri nima na ru e ne." "Shikenan, ina Islam in?" "Gata bacci takeyi." "To Allah ya bata lafiya." "Amin Ummi daga can zamu zarce gida." "To Allah ya yi albarka." "Amin." Daya haka sukayi salama ya kashe wayar. Can bayan gari yaje inda Marwa ta ce Islam na can, gurin ya je amma ba kowa. Ya juya zai tafi ya ganta a yashe a gurin babu alamun nufashi a tattare da ita. Cikin hanzari ya arasa gurin ya auko ta amma kamar bata da rai da hanzari ya kamota ya mi e da ita zaibar gurin da ita ya ji.............! by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 31-32 _____________ Saukar arfe a gadon bayan sa, bai ajiye ta ba sai kara a ameta da yayi ajikinsa ya juya ya kali inda yaji saukar dukan wani katon mutum ya gani da wasu a bayansa sai Marwa da ta bulo daga tsakiyar su fuskarta a ha e ta araso har gaban sa ta ce "Dama jiran isowarka nakeyi malam Abdulfatah, ba kaje kayi garguwa da iyayena ba to gashi nan na sakar maka matarka amma kasani daga kai har ita bazaku tsira daga gareni ba, kuma na jawoka nan domin na fara kasheta a gabanka bayan nasa an mata fya e, yadda zakaji ciwo a ranka kafin kaima na kashe ka." Da kallo kawai yake bita yana mamakin taurin rai irin na Marwa, Cikin bada umarni ta ce da yaran ta "Ku kar o mun wannan yariyar a hannunsa." Da sauri suka arasa gaban sa kusan su 6 amma suka kasa a are Islam daga jikin sa, Ganin haka cikin acin rai Marwa ta ce su ta dukan sa har sa ya saduda ya saki Islam. Wayar ta ce ta fara ruri ta duba taga me gadin gidan sune, da sauri ta auka. "Hello Hajiya su Alhaji suna kule a cikin gida inda suke ba isaka sosai kuma bansa ida wannan saurayin da yazo ba ya ajiye mukulin a halin yanzu har Hajiya Kaka ta suma shima Alhaji yanata tari ciwan sa ya tashi itama hajiya sai wani irin nishi takeyi." A tsorace ta ce "Nashi uku yanzu ba yanda za'ayi ka bu e su?" "Gaskiya babu Hajiya, saidai ki nemi wannan saurayin ya fadi inda ya sa mukulin da gaggawa dan zasu iya halaka." Katse wayar ta yi ta da katar da wanda suka fara dukan Abdulfatah taje har gabansa tana wani irin huci ta ce "So kake ka nuna mun kafini kwakwalawa ko? To kar ka dauka ka tsira ko matarka dan saina dau fansa wallahi, ka sanar dani inda kasa mukulin da ka kule iyayena dashi." agowa yayi ya wurgo mata wani mugun kallo ya ce "Baki da kwakwalwar da kika isa kiyi tasiri a kaina daga ke har wa an nan tsirarin yaran naki kunci sa'a da ar mutane a gurina kuma banaso wani abu ya sameta a dalilana da na shafe tarihin ku a doran asa, kuma bazan fa i inda key yake ba har sai na bar gurin nan da wannan yarinyar cikin hayacinta." Kukane kawai Marwa bata saba cikin hanzari ta ce da wani ya kawo ruwa ya shafawa Islam, Abdulfatah ya watsa masa mugun kallo ya ce ba gardin da zai zo kan matarsa ita da kanta zata zuba mata ruwan, Da kin zuwa tayi ganin yadda megadi yake ta kiranta yasa ta arasa banasu ta fara shafawa Islam ruwa a fuska, ajiyar zuciya Islam ta yi tafara bu e idanunta, tana arba da Marwa ta saki wata razananiyar ara ta zabura zata tashi, Abdulfatah ya riketa kuka takeyi tana kallon Marwa cike da tsoro ta na cewa "Dan Allah karki sa a cutar dani ban san me nayi miki ba kike so saikin ga bayana, kiji tsoran Allah karki bari a cutar dani kemafa a mace ce kinsan ciwan kanki, amma kike so dole sai kin cutar dani." Abdulfatah ne ya ce "Malama ki nutsu ba abunda za ta miki yanzu tunda ina tare da ke." Sai lokacin ta kula da shi ashema a jikinsa take a kwance, mi ewa tayi ta matsa daga kusa dashi. harara ya watsa mata ya mi e ya ce "Ki biyoni mutafi in kuma zaki cigaba da zama a gurin ta to ki zauna." Ai da gudu tabi bayansa tana waywayan Marwa wace ba in ciki ya kusa kasheta, tana kallon su suka tafi ba yadda zatayi. Inda ya yi parking in motarsa suka arasa ya bu e ya shiga ita ba ta shiga gurin me zaman banza ta zauna, yaja motar a guje ya bar gurin. Yana barin gurin ya yi wa Marwa message in inda yasaka mukulin sabuda kar iyayen ta su salwanta. Tana ganin message in ta yi saurin kiran me gadi ta sanar dashi, ya bu e su a daran aka kwashe su akayi Asibiti da su. Suna tafe yana ankare da ita yadda taketa sharar kwala baki ya ta e ya cigaba da tafiyar sa, kai tsaye gidan sa ya kaisu ya fito, itama fitowa ta yi tana biye dashi har suka shiga ciki. A falo sukayi karo da Mufida tana ganin su ta mi e tana tafa hannu ta ce "Daga ina kuma a wannan daran? Ko dama saida kuka gama yawan banzar ku shine zaku shigo mun gida da tsakar dare, ke kuma Amarsu ta ango baki da dangi ne da za'a rasa mutum guda da zai rakoki akin miji saidai ki bishi ku gama yawanku ku dawo sabuda bakisan ciwan kanki ba." Ko kula iskanta baiba ya wuce ya bar su a tsaye da Islam. Islam da ilahirin jikinta rawa ya ke ta ce "Haba baiwar Allah ki tsaya kij......!" "Dalla malama rufemun baki har kina da bakin yimun wata bakuwar magana bayan bakida wata kima ko mutunci a cikin gidan nan sakarai jaka wadda batasan ida yake mata ciwo ba." Zaginta sosai Mufida ta ringayi kamar zata daketa gashi batasan inda akin ta yake ba bare ta shige ta barta haka ta naji ta are mata zagi tasss bata kulata ba harta gaji dan kanta tashige akin ta. A falon a takure cikin tsoro Islam ta kwana. Ya fito zai tafi masalaci yaga mutun a kwance dayake gari bai wayeba ya haskata yaga Islam ce a takure a gurin baki ya ta e, ya arasa gurin da ta ke, cikin tsana yakai hannu ya ta ata a tsora ce ta tashi yaja tsaki ya ce "Sama zaki haura a nan akin ki yake." Bai jira ta ce komai ba ya yi ficewar sa. Tashi ta yi ta haura saman nan taga akin da yake a bude tana shiga taga kayan akin ta ne dan haka tayi hamdala ta maida kofa ta rufe ta shiga bayi ta yi alwala tazo ta yi Sallah sannan ta koma ta kwanta. Da gari ya waye masifar Mufida ce ta tasheta, tana ta bugo mata aki kamar za ta ala ofar. Ba shiri Islam ta bud'e ta fito. Kallon raini Mufida ta mata ta ce "To hamshakiya mandiya to ki fito ki ora mana abun kari tunda kece kika kwana da miji." Murmushi kawai Islam ta yi ta koma ta sako hijab ta sauka ta shiga kitchen ta ha a abun karin kumalo ta fito ta kawo musu falo tana ajiye wa zata koma sama yana fitowa, Har asa ta tsuguna ta gaida shi, "Lafiya." Kawai ya ce ya cigaba da tafiyar sa mi ewa ta yi ta fara tafiya juyowa ya yi yana kallon tafiyar ta ta sai yanzu ya lura da ta dai-dai take tafiya ba tana in gisa afarta ta dama.................! by *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 33-34 _____________ Ta kubura sosai, daga gani dukane a gurin kai ya girgiza cike da takaici ya samu guri ya zauna saida yaga ta shiga akinta sannan ya kira sunan ta, "Islam." Yadda naji sunan nata a bakinsa saida tsikar jikinta ta tashi a sanyaye ta dawo falon ta samu guri a kasa ta shuguna ta ce "Gani." Saida ya gama shan kamshin sa ya ce da ita "Kije ki shirya muje Hospital a duba wannan raunin na afarki." Cikin ladabi ta ce "to." Ta mike ta koma aki. Jiranta yayi harta shirya ta fito zasu huce han yayi dai-dai da fitowar Mufida a hasale ta araso inda suke ta ce "Au yanzu duk gan talin da kuka gamayi a rariya jiya bai ishekuba sai kun ara wani yau, ke da ya ke jakace kina biye da shi kuna yawan ta zubar, wai ke ina dangin kine ko a kwararo ya tsintoki shiyasa zaku are a gantali a tit......!" Saukar marin da taji a kuncin ta yasa ta ha iye sauran maganarta ba shiri, Cikin acin rai Abdulfatah ya ce "Kar ki ara dubana kice ina yawan ta zubar sannan kinsa wannan matata ce ci mata mutunci ya zama haramiyarki in ba haka ba kuma zaki koma inda kika fito." Ya juya ya kalli Islam ya ce "Malama huce muje." Binsa tayi suka fice, ita kuma Mufida ta ringa zazzaga ruwan ashar harda saita one gidan kowa ya wuta. Nuratu ce ta kale shi ta na murmushi ta ce "Jiya akayi bikin mijinta na kamala duk wani aiki da kasani yanzu saura ka cika mun alkawarin da kamu sannan ka salame ni." Murmushi Alhaji Sani ya yi ya ce "Gaskiya aikin ki ya yi kyau Nuratu kuma naji da i amma wani hanzari ba guduba bakya ganin yanzu ya yi wuri Mufida tasan inda kika dosa." "Hmmm Alhaji kenan, ai ni yanzu bana tsoran ta mutu balai tai rai kuma ita Mufida da kake magana ba abunda zata iyayi sabuda ko matsala ce ta sameta bata iya magan cewa da kanta saita ne meni kaga kuwa ba abuda ta isa tayi kuma ko ta sani kafin tayi yin kurin ramawa muncita daya i." "Hakane zanji da komai kedai ki kasance cikin shiri." Murmushi ta yi ta ce "Baka da matsala dani Alhaji." Ku i ya ako masu yawa ya bata ya ce "Ga wannan kisa kati sannan ki kirani in kina bukatar wani abu." Amsa ta yi ta na washe baki, ba godiya ta mike tare da aga masa hannu ta ce "bye." Ta fice abunta. Ta na fita ya auki wayar sa ya kara a kune ya ce "Kusamun ido a kanta duk inda zataje da abunda zatayi." Ya kashe wayar yana murmushi a fili ya ce "Harni zakiyi yiwa wayo Nuratu ance miki kwakwalwata irin ta Mufida ce da zakiyi wasa da hankalina." Saiya ara sakin murmushi. Asibiti ya kaita aka duba raunin doctor ya ce da Abdulfatah sai an mata gyara a gurin, "to." Abdulfatah ya ce ya kalli Islam cikin tsana yana watsa mata harara ya ce "Ki matsa zai duba miki afar." Shiru ta yi, ita bata matsaba ita bata ce komai ba, fusata ya yi ya daka mata tsawa "Ba dake akai magana ba." Kawai saiya ga hawaye takeyi, tsaki ya ja wanda yasata goge hawayen ta mi e ta arasa gurin doctor da zai duba ta. afar ya fara ta awa da Islam taji zafi saita kwace afarta ta na yarfa hannu da hawaye, yin duniya ta miko afar ki tayi da Doctor ya gaji sai ya kira Abdulfatah ya sanar dashi ta i tsayawa, a fusace ya zo gurin, ya zata ganin sa zata bari a gyara amma ko gezau, sai kuka da takeyi. Haushi kamar ya kashe Abdulfatah jiyake kamar ya kashe yarinyar nan, doctor ne ya kalli Abdulfatah cikin nutsuwa ya ce "Da alama bazata bada kafar nan a gyara ta da in raiba kawai abunda zai faru ka riketa sai a gyara inba haka ba wahala zata bamu." Da farko Abdulfatah cewa yayi a'a saida yaji Doctor ya ce "Wai ba matarka ba ce in baka rike ta ba wazai riketa." Ba yadda ya iya yanajan tsaki ya arasa gabanta fuskar nan a hade ya ce "Idan baki tsaya kin nutsu an gyara miki afarki ba to zan tafiyata tunda ciwan a jikin ki yake ba ruwana." Hararar sa ta yi tayi kamar bata jisa ba, doctor da zai gyara mata ciwon ne ya araso ya tsuguna dai-dai kafar ya cafkota zabura Islam tayi ta kwala ihu zata kwace Abdulfatah ya sa hannu ya riketa ram yadda bazata iya kwace wa ba. Saida aka gyara tass Abdulfatah najan tsaki ganin kukan da take sakin ta yayi zai miki, yaga tayi baya zata fa i da sauri ya tarota jikinsa, jiya yi jikinta zafi zau da alama zazzab'i ya rufeta a gurin ga nunfashi da take fitarwa da gyar, da jikin bango ya jinginata ya tashi, yaje gurin Doctor ya rubuta musu magani ya dawo ya ce da ita tami e su tafi. Da gyar ta iya tashi amma kafa taki takuwa, dole sai Abdulfatah ne ya kamata suka fita yanata kauda kai war kar ace wannan black girl din ce matar sa. Da kashi ya bude mata mota tashiga ya maida ita gida ya shige office. Ta na in gisa afar ta tashiga falon da salama, ido ta zaro da sauri cikin mamaki ta ce..............! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 35-36 _____________ "Aunty yaushe kuka zo?" Murmushi aunty ta yi ta ce ki shigo mana, araso wa ta yi taga falon a cike duk da an uwan ta, farin ciki ne ya lulu e ta ta zauna suka gaisa sannan ta je ta bu e musu akin nata suka shiga suna yaban tsaruwar gidan. Sun jima a gidan kafin su mata salama zasu wuce duk sunyi gaba, Yagana ar uwar Ummi ta dawo ta same ta a aki ta zauna kusa da ita ta ce "Kafin ki dawo kishiyarki ta wula an tamu amma ba komai ki cigaba da hakuri sannan ki ringa gasa kanki da ruwan dumi idan na koma gida akwai abuda zan aiko miki zakiga yadda zaki afani dashi a rubuce." Kanta a asa ta ce "to aunty nagode." Salama Yagana ta mata ta wuce kai ta girgiza ta san duk aukan su Yagana Abdulfatah ya kwanta da ita abunda basu sani ba tsanar da Abdulfatah ya mata bazai bari ya iya ha a shifi a da ita ba. A aki ta wuni sabuda zazzab'in da ya kwantar da ita amma taji afar ta daina mata zugi ba kamar azu ba. Abdulfatah sai dare ya dawo gida bayan yaje akin sa ya yi wanka ya sauya kaya ya nufi kitchen dan ya samarwa kansa abunda zaici kamar yadda ya saba. Tayi bacci ta farka taji tanajin hinwa tanajin jiri-jiri ta fito ta nufi kitchen. Kanta a asa ta shiga ji tayi ta ci karo da mutu a tsorace ta ago dan ganin waye. Yana tsaye yana kallon ta cike da tsoro ta ce "Kayi hakuri ban kula da kaiba." Bai mata magana ba ya fice daga kitchen in ya rabu da ita. Baki ta ta e ta shiga ha a abunci duk da bata jin da in jikinta. Saida ta gama tass ta zuba a filet ganin girki Abdulfatah yake son yi tayi murmushi ta sauke masa wanda ya fara ta zuba wanda tayi a food filas ta ajiye masa, ta fice. Saida yaga fitar fa daga kitchen in sannan ya koma kanshi girki kawai yakeji amma ya basar ganin an sauke masa nasa girkin ya fusata sosai har zai fita ya hango kula ya koma ya bu e, saida ya lumshe ido sabuda kanshi daya ji ya daki hancin sa, bashiri yasa spoon ya fara cin abunci tun a gurin. Mamaki yake a ransa dama ammatan yanzu sun iya girki haka? To meyasa ita Mufida bata iya ba sai wannan ar tala kawan? Baiyi aune ba yaga ya kwashe girkin tass, sai lokacin yaji haushin kansa ya kamashi to menene ma na ta a abuncin wannan azamar yarinyar, tsaki yaja ya fice da sauri. akinta ya shiga tana zaune tana cin abuncin nata a nutse wani mugun kallo ya watsa mata ya ce "Da izinin wa? Kika sauke mun girki?" Muryar ta na rawa ta ce "Bansan ranka zai aci ba kayi hakuri gani nayi gamu har mu biyu a gidan nan zaka ringa girki da kanka." "Ke a matsayin ki na wa? Ko kin zata matsayin matata kike? kinsa kuwa menene matsayin mata? To ki daina kai kanki inda Allah bai kaiki ba kuma girki tunda kinji kin gani kuma da ma kin saba da wahala to kulum ke zaki ringa yinsa dare da safiya idan kika sake na kamaki bakiyi ba ranki saiya ace." Har ya juya zai fita ya juyi ya ce "idan kin gama zaki iya samuna a aki ki amshi maganinki." Ya fice yabar akin. Ajiyar zuciya Islam ta sauke da taga fitar sa ta ajiye abuncin da take ci ta cigaba da tunanin hali irin na Abdulfatah, shi a rayuwar sa za'a ta a burge shiba. Mikewa ta yi ta zura hijab in ta, ta sauka zuwa akin sa. Da salama ta shiga bai amsa ba kuma bai ko ago ya kali inda ta keba saida ya gama abunda ya keyi a hankali ya ora idonsa a kanta, ta e baki ya yi ya ce "Makaranta zakije da kika sako wannan aton hijab in? ko ance dake akwai wani abu da mutum zai kalla a jikin ki ya burge shi? Haka kike tunani ko." Girgiza kai kawai ta keyi ya watsa mata harara ya ce "Ga maganin nan ki auka idan kinga dama sannan duk girkin da zakiyi kiyi a kitchen din ki na sama amma idan girkin na ne ki sako kiyi a na gida." "To." Ta ce ta auki maganin ta fice daga akin. Akan idon Mufida ta fita hankalin Mufida a tashe ta shiga cikin akin nasa kamar an jefata. Dogon tsaki Abdulfatah ya ja kawai sabuda yaga abun na Mufida kulum karuwa ya keyi, ita kuwa a hasale ta ce "Wai me kake nufi dani Abdulfatah? Tun jiya naga kana rawar afa akan wannan yarinyar kana fifitata a kaina sabuda kaga ina kyaleka ko." Ko ci kanki bai ce da ita ba ya tashi ya shige bayi. Hannu ta ora a kai ta ce "Lalai Abdulfatah ya mai dani ma mahau kaciya to zakayi magana bari naje na targa a wace muna fukar zaka fito." Da sauri ta juya ta nufi akin Islam. A hankali ta kalli Dady da yake ta yi mata fa a cikin acin rai ta ce "Haba Dady in kai zaka iya yafewa ni bazan iya ba taya za'ayi wannan mutumun ya kusa halaka ku na rabu dashi wallahi sai na auki fansar abunda ya muku." Da sauri ta mi e ta fice a fusace, Dady ya na ta kiran ta "Marwa! Marwa." Amma ko juyowa ba tayi ba tai tafiyar ta...........! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fateemah S Umar, Jajira PAGE 37-38 _____________ Da sassafe Islam ta tashi ta ha a musu abun kari harda Mufida tajere a darning table taje har kofar akin sa gaban ta na fa uwa ta buga masa ofar a hankali dan a zaton ta ya makara ne gashi yau ranar aikice. Mufida da take zaune kusa dashi ta tsare shi da korafin da ta saba, taji bogun ofar mikewa ta yi zata fita, ya riko hannunta ya ce "Ina kuma zakije?" Harara ta watsa masa ta ce "Wanda yake buga mana kofa zan ciwa mutunci." Sai lokacin ya tuna da zaman Islam a gidan kafin ya yi magana ta kwace hanunta ta yi gaba da sauri ya mi e ya bi bayan ta ya rikota, dai-dai lokacin da ta bu e ofar, Islam da ta juya zata tafi motsin da taji yasata juyawa. Mufida ta na ganin ta juyo tai saurin shigewa jikin Abdulfatah tana yatsina fuska ta ce "Malama ya haka zaki zo da sassafe ki tashemu a bacci ko ance miki nan irin kangon gidan kune da ba'a baccin safe." Murmushin ta kaice Islam ta yi kafin ta ce "Ai kangon gidan mu ya fi mun wannan gidan so dubu tunda gidan mu gidan katun al-Qur'ani ne ba gidan she a nufa." Abdulfatah ne ya ture Mufida daga jikin sa ya arasa inda Islam ta ke ya kaleta sama da asa ya ce "Waya fa a miki gidana gidan she a nune?" Ta kaici hana Islam magana ya yi ta juya zata bar gurin da sauri yasa hannu ya jawota, ta fa a jikinsa atare suka rintse ido, ita na tsoro shikuma na sauyin da yaji a jikin sa, ya yi baya ya kafeta da ido ya ce "Naga alamar baki da kunya to zan gyara miki zama dan baki isa kizo gidan mu ki aga mana hankali ba." Dariya kawai Mufida ta keyi ranta fari tasss, har Islam zata yi magana da tsiwa kome ta tuna ta fasa ta ce "Kuyi hakuri bearkfast na gama shiyasa na tashe ku." Tana gama fa in haka ta juya da gudu ta haura sama. Komawa ciki Abdulfatah ya yi saida ya yi wanka ya sauya kaya sannan ya zo ya fara karyawa. Mufida ce ta fito ta gansa cikin acin rai ta ce "Haba Abdulfatah girkin wannan yarinyar ka ke ci?" Ko kallo bata isheshi ba saida ya gama tass ya tashi ya rataya jakar aikinsa ya ce "Kila da naki a cikin zaki iya zama kici." "Allah ya kikaye wallahi." Kafa a ya aga alamun ko a jikin sa yai ficewarsa ya barta a tsaye a gurin. Islam kuwa tunda ta hau sama ta ke aikin kuka yanzu haka zata zauna miji ya tsaneta kishiya ta adabeta? wallahi bazata yarda ba saita kwatowa kanta anci in ba haka ba ta naji tana gani zasu maida ita baiwa a cikin gidan. Nuratu hankali a tashe ta ke tafiya a titi har ta arasa gaban wata mota, asa akayi da gilas in motar aka mata magana da sauri ta shiga ciki aka figi motar da uban gudu akabar gurin. Sunyi tafiya me nisa har sun fita wajan gari sannan suka gangara sukayi parking suka fito. A baya tabi mutumin har suka kai wani guri da Alhaji Sani ya ke tsaye gaban motarsa. Durkusawa ta yi a gurin ta saki kuka me sauti, murmushi ya yi ya ce "Nuratu kenan ni ba aramun yaro bane da zaku maidani kamar doll keda awarki tuntuni na gano so kike na cutar da Mufida kuma ki samu wasu ku i masu yawa a gurina ki aure mijinta ta hanyar asiri, saidai duk da ke ka ai kike shirinki na ganoki shiyasa na ce bazan rabuda kuba dagake har Mufida dataci amanata ta yi aure." Cikin kuka Nuratu ta ce "Kai mun duk hukunci da zaka mun amma dan Allah kar ka bari su cutar mun da ata." Dariya Alhaji Sani ya yi ya ce "Nasa aka kawomun ar kine sabuda zaki mun wani aiki." Da sauri ta ce "Ko nene zan maka shi indai zaka rabuda ata." Murmushi ya yi ya ce "Kin oye gaskiyar ke wace a gurin mu bakisan zamu iya gano wa ba to yanzu aiki aya zaki mun, ki kashe auran Mufida ta dawo gidan ki da zama." Kaita gya a da sauri ta ce "Na yarda wallahi." "Shikenan zaki iya tafiya." Da sauri ta mi e da gudu tabar gurin. Alhaji Sani ya kali yaron sa ya ce "Duk sanda kuka tabatar ta gama aikin da na sata kuyi abunda na ce, ni asar zan bari sabuda gudun ko ta kwana." "Okay Sir." Duk suka shiga motar suka bar gurin. Marwa ce zaune kusa da wani mutum ranta a ace ta ce "Ina bu atar taimakon ka Yunus." Kallonta Yunus ya yi ya ce "Shawara aya zan baki Marwa ki rabuda wannan mutumin ya fiki kwanya zaki iya kwana a ciki." Harara ta watsa masa ta ce "Idan bazakayi ba kawai ka fa amun?" Kai ya girgiza ya ce "Zan taimaka miki amma bazanyi da kaina na kwana a ciki ba." "Okay hakan ma ya mun." Nan suka cigaba da tattaunawa akan yadda zasu gabatar da aikin na su. Islam na kwance ta ji salamar Sarah da gudu ta mi e suka rungume juna cikin farin ciki. Zama sukayi Sarah ta ce "Amaryar Ya Abdulfatah ya kike da halin sa kuwa?" Hararar ta Islam ta yi ta ce "Bazaki tanbayi lafiya ta ba sai halin yayanki." "Hmmm Aunty Islam kenan, ai halin ya Abdulfatah zaifi komai damunki idan yaso mugun tarsa." Dariya Islam ta yi ta ce "To nidai halin yayanki ya fi komai burgeni da shi yanada kirki sosai." Ido Sarah ta zaro ta ce "Da gaske kike?" Kaita gyada mata tana dariya "Gaskiya ke ta daban ce aunty Islam." Share zancan Islam ta yi da cewa "Ya Mamata?" "Mama tana lafiya duk sunce na gaidake ita da Ammi." "Ina amsawa." Hira suka sha sosai har yamma Sarah tana gidan sai da sukayi aikin gidan gaba aya sukayi girki sannan Ya Abdulmalik yazo ya tafi da ita. Da gudu ta shiga akin Mama ta rungume Mama tana dariya ta ce "Gaskiya Mama sai yanzu Ya Abdulfatah ya yi aure." Dariya Mama ta ringa yi mata ita kuma sai yabon halin Islam takeyi. Yana zaune a office ya na tunanin halin mata yaji anyi salama an shigo, ganin wanda ya shigo yasa ya amsa salamar, Zama Doctor Salis ya yi yana murmushi ya ce "Ango kasha amshi gashi sai annurin Angonci ka keyi." Harararsa Abdulfatah ya yi bai kulasa ba. Dariya Doctor Salis ya yi yai asa da muryar sa ya ce "Ina fatan dai ka ajiye wannan girman kan naka ka rungumi matarka ko?" Tsaki Abdulfatah ya yi ya ce "Na rasa wazan runguma sai wannan yarinyar." Ido Doctor Salis ya ce "Kana nufin wai girman kai ka tsaya yi har yan zu?" Ganin Abdulfatah baiyi magana ba yasa ya kwantar da murya ya ce.............! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fatima S Umar Jajira PAGE 39-40 ___________ "Haba abokina wataran saika ringa abu kamar bakaje School ba." Wata uwar harara Abdulfatah ya watsa masa ya ce "Amma dai Salis bakada hankali ko? Ni zaka maida aramin yaro, kasa yarinya ta rainani." "Da ina da kai rashin fahimta wallahi, tayaya zata rainaka? Kai ko raini ne a tsakanin ku zata daina sannan ta ringa maka biyaya sabuda ta gane kasan abunda kakeyi ke me ilimine ba irin jahilan mazan nan ba ne." Shiru Abdulfatah ya yi dan yasan indai ya cigaba da biyewa Doctor Salis to zai kashi ya baroshi. Kamar Dr Salis yasan me yake ayanawa ya ce "Nasan cewa zakayi cutar ka zanyi, ni temakon ka zanyi bazaka gane hakan ba sai nan gaba." Shiga ala Abdulfatah bai ara cewa ba, ya share Dr Salis. Shikuwa Dr Salis guri ya samu ya ringa shiryawa Abdulfatah zance iri-iri har Abdulfatah ya gaji ya ce "Wai dan Allah mene damuwarka akan tsakanina da iyalina?" "Hmm kada ka manta ni me aunar ka ne kuma Amininka na ha i a bazan zuba ido kana ganin kashi da rana ka takaba amma tunda baka so shikenan na bari, amma zan maka tunatarwa guda aya ko ba ha in Soyayya a tsakanin ku da Islam akwai na aure kuma idan kayi watsi da su da gangan kaida uban gijin daya haliceka." Yana murmushi ya mi e ya ce "Na barka lafiya aboki." Ya fice daga office in ya bar Abdulfatah cikin damuwa, kifa kansa ya yi a jikin table yana sauke ajiyar zuciya akai-akai yana jujjuwa magan ganun Dr Salis anya ba wayo yake so ya masaba? Ya tanbayi kansa, amsar da zuciyar sa ta bashi shine To mene hurumin ko ala ar Dr Salis da matarka ila da gasken shawara yake baka. Da ya gaji da juya zancan a cikin ransa sai ya mi e ya fice, ya cigaba da zagaye yana duba marasa lafiya da yake da su. Sai yamma likis ya nufi gida yana tafiya yana juya magan ganun Dr Salis yana so ya share zancan daga ransa amma ya kasa, can asan zuciyar sa cike yake da fargaba da baisan ta mece ba. Wata mota yaga tasha gabansa yai saurin taka burki amma motar ta i tsayawa ga ba aya burkin motar ya shanye, salati ya saka yana ambatan sunan Allah, mumunan karo sukayi da motar dage gabansa wanda ya haifar da molewar motar Abdulfatah da shigarsa mawuyacin hali. Jama'a ne suka kawo aukin gaggawa, aka kashe su akayi Asibiti dasu. Wayar sa aka duba ba wanda yasan pin in wayar dan haka aka ajiyeta ko Allah zaisa wani ya kira. Wani daga cikin wanda suka kawosu Hospital ne ya ce "Nifa naga ID cart in sa likitane." ayan ne da sauri ya ce "Masha Allah, ako mu nuna musu ko sunsan inda yake aiki." ID cart in suka nunawa wani likita da suka gani, cike da mamaki ya ce "Wannan ai ID cart in Doctor Abdul ne, yana ina?" Nuna masa inda aka shiga da Abdulfatah sukayi ya shiga da sauri. Ganin halin da Abdulfatah yake ciki yasa ya kira Abba ya sanar dashi halin da Abdulfatah yake ciki, da yake ya san Abdulfatah sosai abokin sane nan suka shiga bashi taimakon da ya dace. Mama ce a zaune Sarah na zuba mata tuwan shinkafa ta ce "Yauwa idan kin gama zubawa kije kiyi Sallah Magrib sai kizo lokacin yayan ku ya koma gida sai na kirashi ya ha aki da Islam." "Yauwa Mama nagode." Cikin zumu i ta kamala zubawa ta ajiye gaban Mama zata fita suka kusa karo da Abba, gaban tane ya fa i gani yanayin da Abba yake ciki har zata huce taji ya ce "Abdulfatah fa yana Hospital yanzu ya samu hatsari a hanyarshi ta komawa gida." "Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un!" Abuda Mama da Sarah suka furta a tare cike da tashin hankali kenan. Salatin sune ya jawo hankalin Ammi itama tazo ta tadda wannan mumunan labari. Nan Abba ya kwashe su suka tafi Asibiti da aka kai Abdulfatah. Lokacin da sukaje angama bashi duk wata kulawa amma yana halin suma a lokacin. Abba ne yaje gun Doctor nan ya sanar dashi matsalar bamai yawa ba ce yadai samu karaya a hannun hagu sai kananan raunika da baza'a rasaba, godiya Abba ya masa ya fito. Mama da kanta tasa Abdulmalik ya je gida ya tawo mata da matan sa dan suga halin da yake ciki. Islam ta kamala Dinner ta yi wanka tasa wata atanfa pink me flowers green tayi kyau sosai, ta sako dan aukan nata abuncin taji salamar Abdulmalik, gaban tane yai wata irin fa uwa a fili ta ce "Hasbunallahu wani'imal wakil." Dakewa ta yi ta amsa salamar tashi ya shigo ya sakar mata murmushi, itama ta maida masa murmushin nasa. "Barka da dare aunty Islam." Kunya taji babba kamar Abdulmalik yake ce mata aunty, dukawa ta yi ta gaidashi ya amsa yana mamaki a ranshi halin dattaku irin na Islam ba kamar Mufida tijarariya ba. Yana tsaka da wannan tunani hakimar ta fito dan ganin wanda ya zo, baki ta ta e ta ce "Sabuda kun aura masa wannan kucakar har kuka samu damar yimana sitiri a gida dama sabuda haka kuka takura masa sai ya aurota ko." Ta ri e ugu tana zaro masa ido, kallon sama da asa ya mata ya ce "Na yarda duk inda shashasha ya ke baya sauya halin sa ke yanzu har wata tsiyar kuke da ita da zakiyi mana gori muna zuwa gidan nan ko mun muki kama da matsiyata." "Aiga ar matsiyata nan." Ta nuna Islam. Tsaki yaja ya ce "Kece babbar matsiya ciya wanda batasan mutunci ba." Wata uwar ashar Mufida ta gunduma, Abdulmalik yaga abun nata ba hankali a ciki ya shareta ya dubi Islam da taketa bashi hakuri ya ce "Jeki sako hijab in ki, kizo muje Hospital Ya Abdulfatah ba lafiya." Dafe iji Islam ta yi tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, hakuri Abdulmalik ya ringa bata ya rarrasheta ta sako hijab suka tafi, ita kuwa Mufida banda ura ashar ba abunda takeyi. Wayar ta da take ruri ta auka ta kara a kune tare da cewa "Hello Yunus ya akayi?" Daga can Yunus ya ce "Hajiya Marwa aiki ya kamala kamar yadda kika bu ata mun cire burkin motar sa yanzu haka ya samu mumunan hatsari yana Hospital, kamar yadda na fa a miki a farko bazan shiga wannan abun na kwana a cikiba sauran aikin kya arasa da kanki." Murmushi ta yi ta ce "Ai kayi me wuyar Yunus nagode sai kaji sa o." Nan sukayi salama ya kashe wayar. Wata number ta lalubo ta tura kora, bugu biyu aka auka cikin isa ta ce "Yanzu haka yana Hospital in ku tabbata kun ilata munshi sosai." "Angama Hajiya." "Nasan zaku iya ai kawai ku kula sosai." "To Hajiya." Ajiye wayar tayi ta fashe da dariya ta ce "Ka gama yawo ABDULFATAH.............! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fatima S Umar Jajira PAGE 41-42 ___________ A daran an uwa da abokan arziki na Abdulfatah suka halara a Asibitin kowa yana jimamin halin da Abdulfatah ya tsinci kansa a ciki. Da dare ya yi Duk suka fara tafiya gida Mama ta ce tunda har yanzu bai farko ba abar Abdulmalik ko Abdussamad wani ya zauna dashi tunda shi Abba bashida cikakiyar lafiya. Doctor Salis ne ya ce zai zauna su kwana da Abdussamad sauran su tafi gida. Haka kuwa akayi harda Islam suka wuce gidan su. Koda suka koma gida Mama taso surukar tata ta kwana da ita amma sabuda kara irin ta Islam ba ta ce a'a ba kawai sai ta ce bari ta dawo taje gurin Sarah ta turo ta gun Mama ta ce tare zasu kwana, murmushi kawa Mama ta yi ta ce "Allah ya tashe mu lafiya." "Amin Mama." Sarah ta ce ta fito suka kwana da Islam. Washe gari Tun kafin su Mama su tashi Islam ta gama aikin gidan ta ha a bearkfast ta ajiyewa su Mama. Sarah ce ta fara tashi taga duk aikin da Islam ta yi ta dubi agogo taga 09:30am cike da mamaki ta ce "Yanzu har kin tashi kinyi duka wannan aikin? Kekuwa tun yaushe kika tashi?" Murmushi Islam tayi ta ce "Kudai zan tanbayi meyasa bakwa tashi da wuri? Nifa a gida idan nayi salar Asuba bana komawa, amma ku sai kukai Goma kuna bacci." "Sannu da o ari aunty Islam, amma nasan yanzu Mama ta tashi sabuda ita indai wani abu mara da i ya faru to bata iya bacci sosai." "Ayyah Allah sarki Mama ta." Dariya Sarah ta yi ta ce "Masu Mama manya." Harararta Islam ta yi zatayi magana sukaji salamar Ammi, amsawa sukayi Islam ta du a har asa ta gaida ita Ammi ta amsa tana murmushin jin da i a ranta ta ce, ashe Mama ita tasan abunda ta hango ta dage akan auran nan, lalai wannan ita ce sirika ta gari a fili kuma ta ce "Sannu da o ari Islam kin gyare mana gidan." Kanta a asa ta ce "Tare mukayi aikin ta Sarah ai." Baki Ammi ta ri e ta ce "Wannan malalaciyar ce zata iya wani abun arziki ai kidaina fa in hakama dan ki kareta kowa yasan halin ta a gidan nan." Baki Sarah ta turo, Ammi ta harareta ta ce "Bari na gida naga Mama naga bata fitoba." "A fito lafiya Ammi." Islam ta ce, Ammi ta mata murmushi ta shiga akin Mamai. Akan gado ta tadda Mama tana kwance da alama bacci ta keyi girgiza kai Ammi ta yi ta juya dan tasan baccin dare ne Mama ba ta yi ba ta keyin na safiya. Sai gurin 11 Mama ta tashi itama ta yiba da abunda Islam ta yi nan ta shirya bayan su Islam sun shirya abunci suka huce Asibitin. Lokacin da sukaje Abdulfatah ya farka amma bacci yakeyi, duk sunyi hamda ga Allah da abun yazowa Abdulfatah da sau i. A fusace ta ke kallon sa ta ce "Kasan baza ka iya aikin nan ba kace zakayi?" "Kiyi hakuri Hajiya jiya akwai abun....!" Tsawa da daka masa ta ce "Ya isheni haka, banason jin komai, tunda bazaka iya ba zan nemi wani." "A'a Hajiya Marwa baza ayi haka ba kiyi hakuri zan yi abunda kika ce yau da dare." Tsaki taja ta fice daga gurin ko kallon arziki bata masa ba. "Hello awata kina ina? inason ganin ki yanzu." Daga can agaran Nuratu ta ce "Ina gida, me ya faru." "Kizo gida na yanzu dan Allah." Saida Nuratu ta yi jimmm sannan ta ce "Okay gani nan zuwa." Ta kashe wayar Ba'a jima sosai ba Nuratu ta zo gidan, ko Salama babu ta shiga gidan tana wani yatsine fuska a ranta ta ce Zamanki yazo arshe a gidan nan Mufida. Mufida ce ta fito taganta ta washe baki ta ce "Lah harkin araso, sannu dazuwa." "Yauwa." Nuratu ta fa a a ta ai ce. Guri suka samu suka zauna nan Mufida ta sanar da ita halin da Abdulfatah yake ciki yanzu ta ara da cewa "Nifa da na share su daga shi har dangin nasa da matar daya kwaso su arata gaba aya dan ba zuwa zanyi duba shi ba." Murmushin mugunta Nuratu ta yi ta ce "Kiyi dai-dai tunda shima ba mutunci gare shi ba, shawara ma kawai ki fito mu sha ata kan ya dawo daga jiyar tasa." "Allah ko?" "Eh mana." Dariya suka saka a tare suka tafa. Nan da nan Mufida ta ha o kayanta suka fice daga gidan. Da dare Abdulfatah ya tashi ya gane kowa, dan haka sunyi farin ciki sosai, Doctor Salis aka kira Matar sa tana na kuda dan haka ya tafi gida. Da zasu ta fi Mama ta ce "Tunda Doctor Salis ya tafi ina ganin kawai abar Abdulmalik da Abdussamad su zauna a gurin sa." Abdulfatah da yake kwance ya na jinta baiyi magana ba sai ya kamo hannun Abba, Abba ya kaleshi yaga ya girgiza masa kai, murmushi ya yi ya kali Mama ya ce "Mara lafiyar da kansa ya ce baya wanda kika za a masa wata ila Matar sa ya koso a kusa da shi." Murmushi Mama ta yi ta ce "To shikenan tunda shi ka ai ne ku Asibiti naga sunada kulawa sosai tunda ku ine yake aiki shikenan sai ta zauna dashi." Wani irin tu u i Abdulfatah ya ji a ransa da hanzari ya bu e baki ya yi magana, amma duk basu ji abunda ya ce ba suka kama hanya suka fice, rintse ido ya yi cikin ta kai ci, sabuda gudun raini ya ce baya so abar masa su Abdulmalik, yaso Abba ne zai zauna dashi, sai gashi an barmasa wannan jaririyar ko me zata iya tsinana masa oho. Ita ma Islam kuka ne kawai ba tayi ba dan ita a yanzu kallon Abdulfatah tsorata ta ya ke sabuda irin kallon raini da yake mata. 02:00am wasu matasa kimanin su shida suka hauri Hospital in fuskokin su a rufe ba wanda zai gane su waye. Kai tsaye akin da Abdulfatah ya ke suka shiga sunyi sa'a a bu e yake dan azu har Islam ta rufe Abdulfatah yasata dole ta bu e ta. Tana zaune akan daduma taji mutane a cikin akin da hanzari ta mi e zata yi ihu wani ya rike mata baki hannun sa ta kalla taga yatsu 4 gareshi tunawa ta yi da wanda suka saceta tabas taga me yatsu 4 a cikin su, tsoran ta ne ya aru ganin sunyi kan Abdulfatah da yake kwance yana bacci da wu a sun sata wuyan shi ai batasan sanda ta...........! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fatima S Umar Jajira PAGE 43-44 _____________ Ta hanka e wanda ya ri eta ba ta kwala ihu da arfi ta nufi inda Abdulfatah ya ke, ganin haka wanda ya ako wu ar ya juya ya saita wuyan Abdulfatah ya fara o arin yankashi, ya kai wu ar wuyansa Islam tai saurin saka hannuta, yanka a maimakon wuyan Abdulfatah. Azabar da tajine yasa ta ara sakin wata razananiyar ara ta janye hannunta wanda yake ta zubar da jini ka ba a autawa tana wani razanan nan kuka. Wanda ya fara ri eta ya ce "Oga yarinyar nan fa ta tona mana asiri gara tun kan azo a tadamu mu fece." Kai Ogan ya gyada suka nufi hanyar waje, amma me? Karo sukayi da police da suke gadin Hospital in, nan fa ido ya raina fata, wannan Police suka tisa eyarsu sukayi gaba. Wasu daga ciki suka dawo gurin su Islam, da sukaga yankan hannun ta babba ne basu kira Nurses in da sukwana suna aiki, sai suka kira babban likintan Asibitin. Kuka takeyi sosai amma ta iyarda ya fito fili wai dan kar Abdulfatah ya farka, lokacin da likitan ya araso yaga raunin saida ya mata inki a hannun sannan ya bata magani harda na bacci dana rake zugi ya tafi. Ta jima a tsaye tana safa da marwa da alurar kashe ciwon da aka mata ta saketa tana so tayi kuka amma bataso ta tashi Abdulfatah, haka ta ringa yarfa hannu har akayi Asuba ta samu tayi sallah a gurin da tayi sallah bacci ya auke ta. Jin kamar ta yi bacci Abdulfatah ya bu e ido yana kallon inda take yama rasa me yakeji a zuciyar sa, tun ihun da tayi na farko ya tashi Allah bai bashi ikon motsawa ba amma yanajin komai lokacin da Doctor yazo ya duba ta komai ya sakeshi har bu e ido ya yi ya kalesu amma bai bari tasan ya tashiba sabuda yaga bata so ya tashi dan kartaji ba da i a ranta ya tashi shiyasa ya i bu e ido. Tashi ya yi ya sako a hankali ya taka har inda take kwance, hannun sa me lafiyar yasa ya agota a hankali ya manta da jikin sa, zabi yaji jikin nata, ya girgiza kai ya matseta da hanun ya mi e da ita, kan gadon nasa ya orata ya rufe ta ya zauna gefan gadon, ya kamo hannun da aka yanke ta, gurin yayi zurfi sosai duk da anyi in a gurin kowa yana gani yasan babban yanka ne, kwatan tawa ya yi da wuyan sa, ajiyar zuciya ya sauke dan ya san da yanzu ya jima a kiyama. Ya jima yana kallon hannun kafin ya tashi ya lalla a ya yi sallah sannan ya koma inta yake zaune. Idon sa a kanta yana mamakin jarumtar da sadaukar da ran da ta yi bacci ya yi awan gaba dashi. Bugun ofar akin ne ya tashe shi, a hankali ya furta "Waye?" Muryar Abdulmalik ya ji ya ce "Ni ne." Tashi ya yi a hankali yana je ya bu e masa ofar ya shigo, ya ajiye abuncin da ya kawo akan table ya ce "Yaya ina kwana." "Lafiya." "Ya jikin?" Saida ya yatsine fuska ya ce "Da sauki." Kallon gadon ya yi ya ga Islam kwance da alamun batada lafiya da mamaki ya ce "Yaya Islam bata da lafiya ne?" Bai bashi amsa ta ya shiga bayi, alwala ya yo, Abdulmalik ya taimaka masa ya shin fi a masa dadduma ya yi Sallah, ya sa Abdulmalik ya zubo masa abunci ya yi bearkfast sannan ya ce "Ina Mama?" "Tana gida ta ce sai zuwa Azahar zata zo tunda Islam ta na nan." Kallon inda ta ke ya yi sannan ya dawo ya dubi Abdulmalik ya ce "Kira mun Abba." Ba musu ya kira Abba ya mi a masa wayar, bayan sun gaisa da Abba ya masa sannu ya ce "Abba akwai matsala fa." "Subahanallah wace irin Marsala kuma Abdulfatah." Dakewa ya yi ya ce "Inda hali kuzo da Mama sai kuga abunda ya faru." Bai jira cewar Abba ba ya katse wayar ya bawa Abdulmalik abar sa. Ba'a wani jima ba su Abba suka zo Asibitin harda Ammi da Sarah. Bayan sun gaisa yaga kowa sai kallon tuhuma ya ke masa cikin girma mawa ya ce "Abba abaya na ta a sanar da kai akwai wadda na yiwa al awarin aure ko?" "Gaskiya ne na tuna." Ajiyar zuciya Abdulfatah ya yi sannan ya cigaba da magana "To ita ce tunda ta ji nayi aure ta zata yau darar ta nayi ta ke tamun baraza na zata kashe Islam, da na auka fa a kawai takeyi bazata iya ba ashe da gaske ta ke" nan ya basu labarin abunda ya faru ranar bikin su da Islam ya ara da cewa, "hakan da tayi bai isheta ba shine ta turo a kwashe ni jiya" ya basu labarin abunda ya faru jiyan. Salati gaba aya suka auka, ita kuwa Mama kuka ta saka, Abba ne cikin ta kai ci ya ce "Amma meyasa tun farko baka sanar da mu an auki mata ki ba?" "Kayi hakuri Abba na zata zan iya maganin abun da kai na." Cikin kuka Mama ta ce "Yan zu da sun kashe ka fa? Haba Abdulfatah ka daina oye mana irin wannan abun." Matsawa gaban gadon ta yi ta kamo hannun Islam ta sake sakin kuka ta ce "Bansan da abunda zan saka miki ba Islam kin ceci rayuwa kin ceci ta ana, Allah ya miki albarka duniya da lahira." Cikin tsanin mamaki Abdulfatah ya ce "Rayuwar ki kuma Mama?" Mama ba ta yi magana ba dan haka Sarah ta samu kwarin kuwar fa a masa duk abunda ya faru ta ce "Dalilin cetan Mama da ta yi yasa Mama ta dage akan saka aure ta sabuda tarbiyar ta da mutuncin ta wanda aka gaza samun hakan akan matar ka Mufida." Gumi kawai Abdulfatah ya keyi, meyasa Mama ta oye masa wannan abun tun farko bata sanar da shi ba, ya fara zalutar baiwar Allah, Allah ya so shima da abun baiyi nisa ba da dawane idon zai kaleta, rintse ido ya yi tuno irin kalaman da yake far fa a mata lokacin da tana aiki a Hospital in sa. Salatin da Islam ta yi ne ya katse masa tunani ta bu e ido a hankali, ganin muta ne a kanta ta yi afin halin mi ewa zaune tana a alo murmushi ta ce "Gaskiya yau na makara da yawa." Murmushi Mama ta yi ta ce "Dama kin kwana da miji ai dole ki makara." Ido ta rufe cike da kunya tanaji kamar ta nutse a gurin, saida naji suna mata sannu sannan ta bu e ido tana mamakin wa ya sanar dasu abunda ya faru, kallon Abdulfatah ta yi wanda sunda ta tashi ya kasa auke idon sa daga kanta zata yi maga sukaji salamar su Ummi da sauri Islam ta duro daga gadon ta koma kusa da Sarah ta zauna ta bawa kowa dariya a gurin kuma kowa ya fahimci bata so Mahaifiyar ta ta fahimci abunda ya ke faruwa, nan suka shigo da Hajjagana. Aka gaggasa cikin mutun ci sukayi wa Abdulfatah sannu basu jima ba suka ta fi. Islam ta ce wa Mama zasu je gida da Sarah, ba musu Mama ta ce to dan shima Abdulfatah ya gama zaman Asibitin likita zai ringa zuwa gida yana dubashi. Bayan sun tafi ba jimawa suma su Mama suka koma gida da Abdulfatah ya so akaishi gidan sa dan ya matsu ya je ya yi wani abu amma Abba ya ce A'a dole suka huce can gidan su. Ita kuwa Marwa..............! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fatima S Umar Jajira PAGE 45-46 ___________ Hankali kwance ta tashi da safe dan tun a daran suka mata wayar sun samu nasarar shiga Hospital in, tana zaune ta ji ana salama Dadyn ta ne ya fita. Bajiwa ya shigo gidan hankali a tashe yana cewa "Maza-maza ki tashi ki gudu police ne suke nemanki na ce bansan inda kike ba isauri Marwa." Mi ewa ta yi ko hijib babu tabi ba ta yan gidan su zata gudu, amma me? Can ma police ne rike da budugu a ufar gidan tana fita duk sukayi kanta. aya daga ciki ya ce indai ta motsa sai sun harbeta hakan yasa dole ta zame ta tsuguna ta aga annayan ta biyu sama tana hawaye. Nan police suka tusa eyarta suka tafi da ita. Dadyn Marwa ya je Police station ya fi biyar bai samu inda Marwa ta ke ba gashi basu tsaya sun saurare shiba tunda ya musu arya. Mama na kusa dashi tana bashi magani ta ce "Wai Abdulfatah bazaka nemi matarka ba?" Yatsine fuska ya yi ya ce "Yawan duniya ai sabon ta ne dan haka bazan ata lokaci na gurin nemota ba, ko da ta dawo ma zama na da ita ya are na jima da sakinta saki uku cif." "Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un, kana da hankali kuwa Abdulfatah? Saki uku fa ka ce?" "Eh Mama, idai akwai sama da haka saina mata wallahi, wasa da rayiwarki fa ta yi." Ajiyar zuciya Mama ta yi ta ce "Duk da haka Abdulfatah saki uku lokaci guda sai kace a zamanin jahiliya." Murmushi ya yi ya ce "Kin mata dai Mama a baya na saketa duk da abunda ta miki kukasa na dawo da ita, mataki na auka na yanke igiyar auran gaba aya kowa ya huta." Itadai Mama fa a ta masa sosai shidai bai tanka ba sai hakuri da ya ringa bata. Ita kuwa Mufida tana can gantalin ta, acan yawan ta ji abunda ya faru da Abdulfatah yanzu haka yana gida. Hankali a tashe ta nufi gidan da rakiyar Nuratu, me gadi suka bugawa ofa, ya fito. Mufida na kokawar shiga ya tare hanya ya ce "Me gidan ya bada izinin kar a sake a barki kishigar masa gida." Kallon juna sukayi, gaban Mufida na fa uwa ita kuma Nuratu tana hamdala a ranta. Duk yadda suka so ya bar su hanawa ya yi dan haka suka yanke shawarar zuwa gidan nasu, suji akan me Abdulfatah zai hanata shiga gidan ta." Duk suna zaune a falo Abba kawai babu, Sarah ce ta mi e ta ce "Bari naga ko aunty Islam ta gama mu wuce kasuwar?" Gaban sa ne ya fa i dan tunda suka dawo daga Hospital bai sata a idon sa ba. Salamar da sukaji ne ya hana Sarah ta fiya dan ganin marasa kunyar da suka zo. Abdulfatah ne ya tashi tsaye ransa a dagule ya ce "Kuskure mafi girma da zakiyi a rayuwar ki shine ki ara so parlour nan, na riga na yanke duk wata alaka da ke na sakeki saki uku kuma kika sake ko a hanya muka gamu da ke saina wula an ta ki." Kuka sosai Mufida tasa wai dan su Mama suyi magana amma taga ko kallon inda take basuyi ba. Hannun sa da yafara samun lafiya ya nuna mata ofar fita, tana kuka kamar ranta zai fita suka juya da Nuratu suka fice. Sarah ta yi murmushi ta mi e ta shige aki. dan dama so take taji kwakwaf ta sha awa Islam. Islam tana kwance taji an fa o jikin ta ana ihu, ture Sarah ta yi ta na hararar ta ta ce "Karya ni zakiyi kike shale a kaina." Dariya Sarah ta yi ta ce "Abun farin ciki ne ya samu, ya Abdulfatah ya saki matarsa Mufida." Saida gaban Islam ya fa i ta dafe girji tana salati, da mamaki Sarah ta ce "Mene na dafe girji lafiya kuwa?" Cikin damuwa Islam ta ce "Yanzu sakin kike wa murna Sarah, Yayanki ya saki ma tarsa wadda yake so ma yau gobe ni ce nida ya tsana ma." Dafata Sarah ta yi ta ce "Ba haka ba ne Islam ai ba halin ku aya da Mufida ba." Nan ta ba ta labarin duk irin abun mufida take aikatawa, Islam ta girgiza amma duk da haka bataji a in wannan sakin ba. Sarah ce ta ringa janta da hira har ta ware suka shirya dan tafiya kasuwar da suka tsara zasuje. Tare suka fito, Mama ce kawai a falon ta zaune suka ce sun fito ta basu ku in mota tunda su Abdussamad basa nan bare su kaisu a mota, salama suka mata suka fita. A harabar gidan sukaci karo dashi yana ganin su ya ha e fuska zasu wuce ya kira sunan Sarah. Amsawa ta yi ta arasa inda ya ke ta ce "Gani Yaya." "Ina zakuje haka?" "Kasuwa zamuje." ara tamke fuska yai ya ce "Wa kuka tan baya da zaku fita?" Saida Sarah ta turo baki ta ce "Mama ce fa ta aike mu." Mi ewa ya yi ya ce "To ku koma ba inda zakuje." Da gudu Sarah ta tashi tana turo baki ta shoge gida, ba yanta Islam ta bi suka koma ciki. Mama Sarah ta fa awa abunda ke faruwa, bata rufe baki ba yashigo cikin falon, Mama ce ta yi magana "Nifa na aike su Abdulfatah ka barsu suje." Saida ya sosa kai ya ce "Ita Sarah zata iya zuwa ta siyo miki koma mene." Bai bari tayi magana ba ya wuce ya bar gurin. Kai Mama ta girgiza ta kalli Islam ta ce "Kece baya so ki fita, kiyi hakuri ita Sarah ta je ta dawo." Murmushi Islam ta yi ta ce "To saita dawo." Sarah ba ta so haka ba, haka ta tafi kasuwar ita ka ai. Abdulfatah yana shiga aki wayarsa ya zaro ya kira police da suka kama Marwa, suka sanar dashi duk sun kama masu hannu acikin wannan abu kuma zasu aikasu kotu nan da kwana uku, godiya ya musu ya kashe wayar, zama ya yi yana tunanin yadda zai samu Abba da maganar komawarsa gida tunda an bagance duk wata matsala. Sosai Mufida ta ke kuka, ita kuwa Nuratu ta zuba mata ido tana jin kamar yau take Sallah, fakar idon Mufida ta yi ta fita soro, ta kira Alhaji Sani, bugu biyu ya dauka ko salama babu ta ce "Na kamala aikin ka yanzu haka gata a gida na tana kuka mijin ta ya saketa saki uku." Daga can Alhaji Sani ya ce "Zaki iya samun yarki a gidan gonata da kika gani ran nan gobe da arfe biyu na rana." Ya katse wayar bai jira cewar ta ba. Komawa ta yi ciki tana cike da farin ciki. Kallon mutumin ya yi ya ce "Ina so kar sukai gobe dukan su zaku kashe su, kuma kar ku bari kubar wata sheda da za'a gane ku............! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fatima S Umar Jajira PAGE 47-48 _____________ "To yala ai." Kashe wayar Alhaji Sani ya yi yana dariyar keta a fili ya ce "Idan aikin ku rainin hankali to ni nafiku iyashi mtsss." Yaja tsaki ya koma ya zauna akan kujerar da yake yana murmushi. Da dare Abdulfatah ya samu Abba a falonsa bayan sun gaisa ya fara kame-kame, Abba ya yi murmushi ya ce "Kanaso ka ce wani abu ko?" Kai ya gyada cikin nutsuwa da girmamawa ya ce "Abba dama gida nake son koma wa tunda har an kama yarinyar nan kuma na samu sauki hannu ne kawai bai gama warke wa ba, kuma ina son kumawa Hospital kaga gidan yafi kusa da gurin aikin." Cikin rarrashi Abba ya ce "A'a Abdulfatah bana son kuma warka gidan nan kai ka ai." Abdulfatah bai iya musu ba duk da yana da tarun maganar da zai fa a amma sai ya yi shiru. Kallon sa Abba ya yi ya ce "Amma tunda son kumawa ka keyi shikenan Allah ya tsare." Cikin tsananin farin ciki ya ce "Nagode Abba, kuma dama na riga na zuba masu tsaro a gidan in sha Allah ba abunda zai faru." Murmushi Abba ya yi ya ce "Ga kuma matarka ta na tsaran ko?" Gaban Abdulfatah ne ya fa i harga Allah ya manta da zaman Islam a gidan sa dai bai nemi komawa ba. Murmushi ya a alo ya ce "A'a Abba da ita ta cigaba da zama har Allah yasa komai ya dai-dai ta." "A'a Abdulfatah baza ka bar matarka a gida ba indai kana son tafiya to tare zaku tafi idan kuma baka shirya tafiya ba to ku cigaba da zama dukan ku." Rasa bakin magana Abdulfatah ya yi yama rasa abunda yake masa dadi. Maganar Abba ce ta katse masa tunani "Baka tsaida mun da magana aya ba, tafiyar ko zaman?" Kanshi a asa ya ce "Tafiyar zanyi Abba." "Allah ya tsare ya yi albarka." "Amin Abba." Saida safe Abdulfatah ya yi wa Abba ya wuce akin sa ya kwanta. Suna wance suna sharar baccin asara sukaji mutane akan su ihu suka saka, wani ya sa mu arfe ya buga musu a kai a take duk suka sume, nan suka yayyafa musu fetur suka cinawa gidan wuta. Suna fita police sukaci karo dasu dan ihun da su Nuratu sukayi ya jawo hankalin su, kama su sukayi nan aka fara o arin ashe wutar, da yake ba kamawa ta yi sosai ba, ko yan kwana-kwana ba'a kira ba aka kashe wutar aka kwashi su Mufida akayi Asibiti da su. Nan ne Doctor ya tabbatar da mutuwar aya daga cikin su ayar kuma tana cikin mawuya cin hali. Washe gari Da safe Abdulfatah ya shirya zai ta fi Hospital, ya fito sukayi karo da Mama. Kollon mamaki ta ke masa ta ce "Ina zuwa haka, da sassafe?" Kai ya sosa ya ce "Hospital zani Mama." Harara ta watsa masa ta ce "Har yaushe aka salamoka daga Hospital shine zaka fara zuwa office." Fuska ya marairaice ya ce "Naji sauki Mama zan iya zuwa aiki." Kallon hannunsa ta yi da har yanzu yake na e sabuda orin da akayi masa, ta ce "To naji amma bari matarka ta shirya ta raka ka ta tayaka aikin." Fuska ya murtuke zaiyi magana Mama ta katseshi da cewa "Kar ka ce a'a Abdulfatah, zata taimaka maka kaga baka gama warware wa ba." Kasa magana ya yi, ya rasa meyasa komai sai an li a masa wannan yarinyar, maganar Mama ce ta katse shi "Idan kuma kafi son tafiya kai kad'ai to." Dabara ce ta fado masa ya ce "Jiya munyi magana da Abba yau zamu koma gida, ta zauna ta shirya kafin da dare mu wuce." Murmushi Mama ta yi ta ce "To shikenan Allah ya tsare." "Amin Mama." Ya wuce Mama na masa addu'a. Mama ta samu Islam ta sanar da ita ta shirya yau zasu huce da mijinta. Jiki a sanyaye Islam ta ce "To." Ita kuwa Sarah murna ta ringayi ta ja hannun Islam sukayi akin ta. Nan ta ringa ba ta shawarwari harda kalar abuncin da Abdulfatah ya fi so da kayan da yafi so da duk wani abu da yake so da wanda baya so, godiya Islam ta mata suka fara shirya kayan Islam. Sai dare ya dawo lokacin Abba ya dawo ya samu Abba ya ce zasu wuce. Kiran Islam da Mama Abba yasa aka masa ya kira Ammi, bayan sun zauna ya yi wa Abdulfatah da Islam nasiha sosai ya nusar dasu darajar aure da Hakokin aure, ya ara da cewa "Ammi da Mama ko da wanda zai arayi musu nasiha?" Ammi ce ta fara magana "Duk da Abba ya fa i duk abunda zan fa a amma tuna tarwa ce, kuyi hakuri kuyi hakuri kuyi hakuri, dan hakuri shine jigon zaman aure sannan biyayya, dan Allah karmuji kar mu gani karku biyewa ru in zamani kuringa auran jeka nayika dan Allah." Ita kuma Mama murmushi ta yi ta ce "Nidai addu'a zan muku Allah ya kauda fitana ya baku zaman lafiya da zuri'a ta gari." Duka suka amsa da ameen Abdulfatah ya musu godiya sosai, ita ma Islam jiki a sanyaye ta musu godiya sosai sannan suka musu salama suka fito. Sarah ce ar rakiya har gurin mota ta raka su tana musu addu'a. Islam ta juyo ta ce "Nagode sosai Sarah ki ara yiwa su Mama godiya bani da abunda zan iya biyan ku saidai na muku fatan alkairi." Murmushi Sarah ta yi ta ce "Bakomai aunty Islam kin cancanci a miki haka ne koma fiye da haka." Abdulfatah ne ya katse musu hirar da cewa "Ko nayi tafiya ta ne?" Sarah ta agawa hannu ta shiga cikin motar suka wuce. Har suka je gida ba wanda ya yi wa wani magana, Islam ta yi mamakin ganin ma'aikata a gidan, kodan abunda ya farune oho. Shine ya bu e musu falon suka shiga, duk ya yi kura. Abdulfatah hucewa ya yi akin sa ya kule. Ita kuma Islam kasa hucewa saman ta yi saida ta gyara falon ta goge ko ina sannan ta haura nata dakin, shi dai ba abunda ya yi sai yar kura data share, falon ma tasan azan tar Mufida ce kafin tabar gidan. Saida tayi wanka ta kwanta sabuda ta gaji ga bacci da take ji sosai. Harta fara bacci ta ji ana.........! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fatima S Umar Jajira PAGE 49-50 _____________ Kiran sunan ta, ta shi ta yi cikin bacci ta kalli a gogon akin ta ga shabiyu saura, da mamaki ta mi e ta fita, aranta tana mamakin kiran me Abdulfatah yake mata acikin daran nan. A tsaye a fallo ta tadda shi, kanta a asa ta ce "gani." Kauda kai ya yi ya ce "Kinsan dai yanzu matar gidan nan bata nan duk wani aiki nata ke zaki ringayi, kina jina." Kai ta gyada ba tare da ta yi magana ba. Cigaba ya yi da magana "Bayan aikin gida kinsan tana da wani amfanin daban ko?" Wannan karon ko motsi Islam batayi ba "Dake fa nake." Kai ta girgiza, ya ta e baki ya ce "Yanzu kan na kwanta ki ha a mun tea ki kawo mun, saina sanar dake sauran aikin naki." "To." Islam ta ce, ta shiga kitchen ta ha a masa tea ta zubo masa a cup ta fito, baya falo dan haka ta shiga akin nasa da salama. Yana zaune gefan gado ta ajiye masa ta juya zata fita, tsaki ya ja ya ce "Ba na ce dakai zan sanar da ke sauran ayikan ki a gidan nan ba." Sum-sum ta dawo ta zauna ya watsa mata harara, ya cigaba da abunda ya keyi. Saida ya gama ya fara shan tea ba tare da ya kulata ba, lokacin har bacci ya fara ibarta ta ji muryarsa ya ce " a'ida ne duk sanda zan kwanta zan sha tea kuma ba kala aya ba kulum da irin wanda na ke bu ata, sannan bana iya kwana ni ka ai dole saida wani a kusa da ni, kuma ba komai na ke iya yiwa kaina ba wani yimun akeyi." Saida ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Da aikin Mufida ne ban takura ki ba amma yanzu ba ta nan dan kaha duk wata wahala da take mun ta dawo hannun ki." Sai lokacin Islam da ke zaune ta yi magana "Allah ya bamu wuyan auka." Tana gama fa in haka ta mi e zata fice, ta ji ya ce "A rayuwa ta na tsani mutum me rainin hankali, kidai ji me nace Allah ya baki ikon fita daga akin nan hmmm." Bai jira abunda zata ce ba ya shige toilet. Tana ganin ya shiga toilet ta fice abunta, Abdulfatah ma ya mugun raina mata hankali wai baya iya kwana shi kad'ai sai kace batasan gantalin da matarsa ta keyi ba zai raina mata hankali, ya gama azabtar da ita a waje nan kuma ya maida ita baiwa to bazata lamunta ba. Dagonta ta haye tai kwanciyar ta hankali kwance. Yana fitowa daga toilet ya ga babu ita, kai ya girgiza ya ciza lips in sa, lalai yarinyar nan ta gama raina shi, kwafa ya yi, ya sauya kaya zuwa na bacci sannan ya kashe komai na akin ya fice. Sama ya haura akin Islam, lokacin da ya shiga akin nata tayi bacci dan haka bataji shigowarsa ba, maida kofar akin ya yi ya rufe, sannan ya haura gadon. Fuskarta ya kurawa ido, bata da hasken fata amma kyakykyawa ce duk da bacci ta keyi amma batayi muni ba kuma a nutse take cib. Tunawa ya yi da lokacin da yake wula anta ta a Hospital in kuma yau gata matsayin matarsa, ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya kai hannu kan fuskarta, da yake Islam bata da nauyin bacci tai saurin ware fararan idanunta akan fuskarsa. A tsorace ta tashi zaune ya ha e rai ya ce "Ba na sanar da ke cewa bana iya kwana ni kad'ai ba? Nace ki zauna a akina ki maye gurin Mufida, amma sabuda kin rainani shine kika sa afa kika futo ko?" Kai ta girgiza masa cike da tsoro ta ce "Allah ba haka bane, bana iya kwana da......!" Sai kuma ta yi shiru, ya watsa mata harara ya ce "Ai bazaki iya arasa maganar ki ba sabuda kinsan baki da gaskiya, in gaskiya ne ki sanar da su Mama bazaki iya kwana dani ba kar a auramiki ni, ko bake bace harda zama jinyata a Hospital?" Shiru tayi takasa magana ya ce "Tunda har baki iya kwana da mutum ba to karkiji komai daga yau zaki daina ki sama da kwana da wani a kusa da ke." Duk yadda Islam ta so ya rabuda ita a wannan dare ya i yadda ta masa garda ma haka ya mata, tasha wahala har takai saida hankalin ta ya gushe ta daina fahimtar komai. Lokacin da hankalin sa ya dawo jikinsa ne ya kula Islam tana halin suma, sai lokacin ya ji haushin kansa, meyasa ma ya biyewa zuciyar sa ya kusanci Islam yanzu, karfa raini ya shiga tsakanin su. Kauda wannan tunani ya yi a ransa ya fara bata taimakon gaggawa kasan cewarsa likitan mata bai shawala gurin bata kulawar da ta dace ba. Har akayi kiran Asalatu Islam bata farka ba shikuwa wanka ya yi ya wuce masalaci. Yana fita ta fara bu e idonta a hankali tana kallon akin abunda ya faru ne ya fara dawo mata, da sauri ta yinkura zata tashi amma takasa, komawa ta yi ta kwanta, tanaji har aka idar da Sallah a masalaci ta kasa motsi, hawaye ne kawai suke zarya a idanunta har ya shigo gidan ya tadda ita tanata kuka ya arasa inda ta ke kwance ya ce "Ya isa kukan haka komai ya wuce ai." maganar sa ma tsora ta ta takeyi tayi asa da kanta dan ko fuskarsa bata son gani murya na rawa ta ce "Shikenan mutuwa zanyi na kasa tashi." Ta bashi dariya ya yi murmushi ya ce "Ba abuda zai sameki ki godewa Allah ma yariya da baki aruba." Sautin kukan ta ta ara, dole tasa ya taimaka mata taje bayi ta yi wanka a zaune ta iya Sallah ga ciwo da kanta yake mata kan kace me zazzab'i ke zafi ya rufe ta. Sosai ta bawa Abdulfatah tausayi tunawa ya yi da lokacin auran Mufida, sai yanzu yasan cewa mata suna suka tara bai ta a tunanin har yanzu akwai matan da suke da sauran mutunci ba sai yanzu, kalaman da ya ringa fa a mata lokacin da yaganta da Sahal suka ringa dawo masa, ya cije lips in sa yana tuna muzanta ta da ya ringayi dan ta kasance ba a ashe halinta yafi nasa haske ma tunda ta sadaukar da ranta akansa. Tunanin da yake ne ya katse jin ana buga ofar gidan, a sanya ye ya mi e ya nufi ofar gidan. Bu e wa ya yi da mamaki ya ke kallon..........! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fatima S Umar Jajira PAGE 51-52 ____________ Doctor Salis, ya ce "lafiya kazo da sassafe haka." Murmushi Dr ya yi ya ce "Amma dai ko mene ka bani guri na zauna sai ku tatttauna ko." Wuce wa ciki Abdulfatah ya yi Doctor Salis ya bi bayansa suka zauna a falo kafin Dr ya ce "Abdulfatah ya jikin naka kuwa?" "Da sauki." "Allah ya sawake." "Amin nagode." "Am dama maganar zaman kotu da za'ayi gobe ne nace ya dace kaje da Islam sabuda ko bincike zai biyo ta kanku." Girgiza kai Abdulfatah ya yi ya ce "Idai zanje amma Islam bazata fita ba." "Sabuda me? Ka barta mana sheda cefa." "A'a Dr bazan bari taje wannan gurin ba kuma ma kobadan hakaba ma batada lafiya bazata iya zuwa yawon shara'a ba." Mamaki ne ya kama Dr kafin ya yi murmushi ya ce "Okay zuwa goban sai nazo muhuce tare dan nima Bauchi zan tafi yanzu sai dare zan dawo shiyasa nazo yanzu na sanar da kai." "Okay Allah ya tsare." "Amin Doctor Abdul, Allah ya bamu sa'a." "Amin." Nan sukayi salama Doctor Salis ya yi waje shikuma Abdulfatah ya kule gidan ya koma ya kwanta a falo yana cigaba da tunanin duniya daya saba. Sai Azahar Islam ta yi tashi lokacin har Abdulfatah ya siyo musu abuncin da zasu ci, itadai kasa ci ta yi dan bakinta ba a i, tea ya dafa mata saida ya aure fuska taga ba sarki sai Allah sannan ta sha ya bata magani. Bayan ya fita ta sako ta fito falo dagyar duniyar ma juya mata takeyi tana zama kira ya shigo wayarta taga Sarah ce ta auka tare da yin salama. Amsawa Sarah ta yi tana cewa "Labari da umi- umi sa kishiyar ki dai taje wayan gida awa gobara ta one su to ita awar tata ma ta she a barzahu ita kuma ta babbake kaga aya." "Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un, Allah sarki, Allah ya bata lafiya ita kuma wadda ta rasu Allah ya ji anta." "Hmm amin dai, abuda ta shuka ne ta fara girbar abunta." "A'a Sarah jarabta ce ta ubangiji muma bamufi karfin Allah ya jarabce mu ba." "Ai koda yaushe muna cikin jarabawa amma itama da mugun hakita." "To Allah ya kyauta." "Amin aunty Islam, mura kikeyi ne naji muryarki haka?" Magana zatayi suka ha a ido da Abdulfatah ta ya shigo yanzu shima kafeta ya yi da ido dan ya ji abunda Sarah ta fa a tuda a speaker tasa wayar, saurin cewa ta yi "Eh." "To Allah ya sawake da fatan kina kula mana da yay......!" Katse wayar Islam tai saurin yi, murmushi ya yi ya zauna ya ce "Ki barta ta fa i abunda ta ke son cewa mana." Shiru ta yi kanta a asa tana wasa da wayar hannun ta "Okay kidai san duk abuda ya shiga tsakanin ki da mijinki ko wane iri ne sirrin ki ne ba'a sanar da wani ko?" Nan ma shiru ta yi ya ta e baki, kunyar Islam har tayi yawa ba kamar Mufida ba da batada kunya ba. Washe gari Doctor Salis ya zo kamar yadda sukayi jiya da Abdulfatah suka tafi kotu tare. Idan shari'a ta yi kyau akan yankewa Marwa da tawagarta hukuncin zama a gidan gyaran hali na shekaru 20. Abdulfatah ya yi godiya ga Allah da ya rabashi da musifa. Doctor Salis ne ya ce yazo ya rakashi wata dubiya, nan suka tafi Hospital inda suka shiga wani aki, warin da Abdulfatah ya ji ne yasa shi toshe anci Salis yaja hannusa suka arasa jikin gadon. Cike da tsoro Abdulfatah ya kali Salis ya ce "Inalilahi Salis wace wannan ta kone haka?" Da fashi Dr Salis ya yi ya ce "Kaleta da kyau baka gane ta ba?" Kura mata ido Abdulfatah ya yi kamar yasan fuskarta amma yadda ta yi baki ta kone ya kasa gane wace, A sanyaye Salis ya ce "Wannan matarka ce Mufida ta gamu da iftila'i gobara ita Nuratu ma ta rasu." "Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un!!" Abdulfatah ya ringa maimaitawa zuciyarsa ta karaya sosai lalai idan baka mutuba ba'a gama ma halita ba dubi Mufida duk kyan nan nata da kwaliya amma ta babbake haka, tsoran Allah ya ara shigar sa yana nadamar abubuwa da yawa a baya." Kukan da yakeyi ne yasa Dr Salis ya fito dashi daga akin ya zaunar dashi a waje, murya a sanyaye ya ce "Abdulfatah kaga yadda duniya take maida me rai ko? Idan idan kaga Mufida zaka ta a tunanin wannan rayuwar zata risketa? Abun tsoron muma zata iya riskar mu ko wadda bata kai haka muniba ko wadda ta zarce haka tunda muna nunfashi, rayuwa batada tabbas Abdulfatah na tsorata sosai danaga wannan abun." Shiru duk sukayi Abdulfatah ya dubi Salis ya ce "Duk da ba aure a tsakanina da Mufida kuma ta aikata mun laifuka da yawa amma ta bani tausayi sosai." "Hakane amma ya kamata ka taimaka mata Abdulfatah tunda bata da kowa sai Allah." "Ina iyayenta?" "Hmm Abdulfatah kenan ai na arya ne ba wanda yasan asalinta ita da Nuratu su kansu basusan asalin junaba." "Wannan wace irin rayuwa ce Salis? Amma duk da haka zai taimake ta muje gurin Doctor da yake dubata." Tashi sukayi sukaje office in Dr Abdulfatah ya biya duk wasu ku i da aike bu ata, ya dawo gida jiki ba kwari. Islam ta na kitchen tana girki ya shiga da salama, amsawa ta yi ta masa sannu da zuwa, ya amsa ya na cewa "Baki da lafiya amma kike wahalar da kanki kina aiki haka." Murmushi ta yi ta ce "Naji sauki zan iya." Kai ya gyada ya ce "Okay idan kin gama ki sameni a aki." "To." Ta ce, shi kuma ya fice. Kamar yadda ya fa a mata tana gamawa ta shiga akin nasa. Yana zaune ya yi ta gumi, ta zauna ta ce "Gani." Ya jima kafin ya iya furta "Abubuwa da dama marasa da i sun shiga tsaka nin mu a baya, kuma nasan nine ban miki adalci ba amma ina fatan zaki ya femun." Mamaki da al-ajabi ne suka kama Islam wai yau ita mutum me aji da izza kamar Abdulfatah ya ke bawa hakuri, a fili kuma ta ce "Ban ta a ri on ka a zuciya ta ba, kuma kadai bani hakuri wallahi komai ya wuce najima da manta abunda ya faru a baya." Rungumeta Abdulfatah ya yi cike da farinci ya ce "Allah ya miki albarka yasa kigama da duniya lafiya." "Amin kai maha." Murmushi ya yi yana kodewa Allah, yana godewa su Mama da suka tsaya tsayin daka ya auri Islam da yanzu ina zai nemota ya nemi gafarar ta. Yana tafe a motarsa yana kallon garin Kano yana Murmushin bankwana ya dubi driver ya ce "Yanzu idan nabar garin nan ba zan kuma dawowa ba sai nan da shekaru 3 lokacin wannan yaran sun zama kwarangwal." Dariya driver ya yi ya ce "Gaskiya ne wannan Alhaji, kaga ba masu zarginka da babbake su." Dariya duka sukasa, sun shagala da dariyar basusan cewa wata katuwar tifa ta fito daga wani logu sai jikawai sukayi..........! By *XAHRA* *ABDULFATAH* Na Fatima S Umar Jajira PAGE 53-60 _____________ Tifa ta yi awan gaba dasu. Mutanan da ke gefan hanya ne suka ta so wasu na salati wasu na ihu sabuda motar su Alhaji Sani tariga ta tashi daga aiki ta mole kamar kwankwani, kana ganin motar kasan ba za'a samu me rai a ciki ba saidai wani iko na Allah amma da wuya. Da kyar aka iya zaro gawar wakin su Alhaji Sani, motar Asibiti ta zo aka wuce da su. Yau Islam ta yi kwanan farin ciki dan taga kulawa da tarairaya gurin mijin nata wanda bata ta a zatan haka daga gareshi ba anan kusa. Da safe ita ta taimaka masa ya yi wanka yai shirin office, bayan ta bashi bearkfast ya ci ya dube ta ya ce "Munyi waya da Mama ta ce mun yau zasu zo da Ammi wata kila harda mayarki Sarah." Murmushi ta yi ta ce "Ai baza su soma zuwa ma ba ita ba, ita ce jagorar ta fiyar." Kai ya girgiza ya wuce tana masa addu'a ya ce "ameen." yana jin wata nutsuwa da da i suna ziyartar zuciyarsa. Sai azahar su Mama suka zo harda Sarah, Islam ta ji da in zuwan su, ta ringa nan-nan dasu, Mama kuwa da i ne ya isheta sai yanzu tasa tayi sirika da zata zo gidan an ta hankali kwance ba'a tashe ba. Sai yamma suka ta fi Islam harda kuka, itadai Sarah dariya ta ke mata, Ammi ce ta riga rarrashin ta, har ta yi shiru, Sara na tsokanar ta suka tafi gida. Bayan wata uku: Yanzu hankali Islam ya kwanta ta yi kyau tayi kiba sosai ta ara haske duk da har yanzu black beauty ce batayi wannan haske ba. Yau ta shirya Abdulfatah zai kaita gidan Ummi tunda akai bikinta bata jeba itama Ummi bata zo ba, shine ta gaji ta ce bari ta je yau daga nan ma saita bawa Ummi IV bikin Abdulmalik da Sarah da za'ayi next week. Suna tafe a mota suna hirar Soyayya Abdulfatah ya ce "Har gobe na kasa mantawa da rayuwar baya Heartbeat, gani nake kamar duk abunda zan miki bazan goge laifina na baya ba." Murmushin ta me narkar da zuciya ta masa ta ora hannunta akan nasa dayake su i ta ce "Ba abunda nake buri a rayuwata irin naga ka manta da abunda ya faru a baya, Allah yana kallo ni najima da mantawa, adama rashin fahimta ne yanzu da muka samu gashi Hospital ima yana hannu na." Tana rufe baki danja ta tsaida su ya kashe motar, ya kamo hannunta ya mana masa kiss ya ce "Ina tausayawa duk namijin da ya yi asarar mace ta gari irinki Heartbeat, na rasa wane irin so zuciya ta take miki, kamar zan moto haka nakeji." Dariya ta masa zatayi magana, wata ba ar mata, tazo bakin window da Islam ta ke tana cewa "A taimaka mun da sada zan siyi magani a Asibiti." Zare hannun ta tayi daga nasa ta bu e jakarta ta zaro ku i ta mi a wa matar. Suna ha a ido taga matar tabar gurin a hargitse, da mamaki ta juya ta kali Abdulfatah ta ce "Meyasa ta tafi kuma?" Jikinsa a sanyaye ya tada motar dan an basu hannu yana cewa "Ai bazata amsa ba sabuda ta sanki." "Nikuma a ina." Bai bata amsa ba saida ya bari sunje ofar gidan Ummi ya yi parking ya juyo yana fuskan tarta ya ce "Wannan matar da ta i kar ar ku iki Mufida ce." Cike da tsoro Islam take kallo sa jikinta na rawa, kasa furta komai ta yi sai kuka. Ha ata ya yi da jikinsa ya ce "Menene abun kuka kuma itafa ta za awa kanta irin wannan rayuwar da ta tsaya tabi aure bata ci amar aure ba da bata shiga wannan halin ba." Kukan da take ta tsagaita ta ce "Yanzu bayan konewar da ta yi bara ta koma?" Kai ya gyada mata, ta ce "Mukoma dan Allah, ka tausaya mata kamai da ita gidan ka koba komai taci arzikin Soyayya." Murmushin takai ci ya yi ya ce "Islam, Mufida ta riga ta haramta a gareni domin kuwa saki uku na mata, ko ba saki uku ma bazan sake gaggaci maida ita gidana ba wallahi dan ni a yanzu bayan ke bana ganin wata mace zata samu guribi a cikin zuciya ta." Ajiyar zuciya ta yi ta ce "To dan Allah ka taimaka mata, inkai bazaka iyaba ni ka bani dama na taimake ta." "To." Yace ta ita ya share mata hawayen, yaringa janta da wasa har saida yasata dariya sannan suka fito suka shiga gidan Ummi. Ummi ta ji da in ganin su, bayan su gaisa, Abdulfatah ya wuce, ita kuma Islam anan gidan ta wuni suka ringa hirar yaushe gamo da Ummi. Sai dare Abdulfatah yazo ya tafi da ita, dan baya bari taje ko ina saidai ya kaita, duk da tanada motar hawa amma baya bari taje ko ina saida rakiyarsa. Ba hanyar gida taga ya yiba, ya kaita wani gida ya dubeta ya ce "Duk da na rubu da Mufida rabuwa ta har abada amma ban daina taimakon ta ba, ban bari tasan ni nake biyan ku in maganin ta ba harta warke ba, da aka salameta tana gararanba ba gurin zuwa ni na bawa wata mata gidan nan nace tace na tane su ringa zama suna kwana tare, ni nake cidasu duk sabuda albarka cin ta ta a zama matsayin mata a gareni, bansan meta rasaba take bara, na kamata yafi sau goma, bansa dalilin ta ba, zaki iya shiga ki taimaka mata kamar yadda kika bukata na miki." Shiru Islam ta yi kafin ta ce "Ina zuwa." Fita ta yi ta shiga gidan, ta tadda su suna cin abuci suna hira da salama ta shiga matar ce kawai ta amsa,ita kuna Mufida tashi ta yi ta na cewa "Lafiya me kika zo yi nan?" Cikin nutsuwa Islam ta ce "Gurin ki na zo." Nan ta zauna ta zayanewa Mufida abunda Abdulfatah ya ke mata ta ce "Na sanar da ke ne badan komai ba sai dan ki gyara rayuwarki kidaina bara ko nawa kike bukata ki sanar dani zan miki banason ganin ki cikin wannan halin shiyasa na yanke shawar na fa a miki gaskiya ko kya nutsu ki daina bara." Kuka sosai Mufida ta keyi ta ce "Bani da bakin gode muku, nagode dan Allah ki yafemun sannan ki roka mun mijinki ya yafe mun." Islam ta yafe mata sannan ta riga yimata nasiha ta ba ta kudi masu yawa ta baro gidan. A mota take fa awa Abdulfatah ta sanar da ita gaskiya, da ya tanbayi dalili ta ce sabuda idan taji haka zataji kunyar fitowa bara, yanajin haka ya ce shikenan Allah ya kyauta. Ansha bikin Abdulmalik da Sarah, su Islam sune kirjin biki, ita takai amarya har akin ta tamata fa a tana tsokanar ta itadai yau Sarah bata da bakin maida martani dan haka ta shareta bata kulata ba. Islam tunda ta gama hidimar biki ta koma gida take rashin lafiya, idan Abdulfatah ya ce ayi mata test, sai ta ce gajiyar biki ce, saida taga da gaske tana neman she a barzahu ta amunce ya dubata ya mata test ya gano tana auke da juna biyu na 2 mouth. Farin ciki gurin Abdulfatah ba'a magana, ya tuno lokacin da Mufida ta masa asarar cikinsa na farko gashi yanzu Allah ya bashi wani. Islam taga gata gurin mijin nata da danginsa kowa ina kasa ina ka ajiye ake da ita, har lokacin haihu ya yi. Abdulfatah da kansa ya amshi haihuwar matar tasa, inda Allah ya azurtasu da Baby boy kyakykyawa me kama da Abdulfatah. Ranar suna yaro yaci sunan Abba suna kiransa da Annur. Islam da Annur suna ganin Soyayya agurin mutane kamar za'a ha iye su. Watan Islam 10 da haihu ta samu wani cikin, Abdulfatah ya sani amma ya oye mata sabuda gun karta masa rigima, aikuwa ranar da asiri ya tonu ta gane yasha kuka, da ya gaji da rarrashinta saiya ce ta tashi suje unguwa. Bamusu ta shirya Annur ya kaisu wani gurin sha a tawa me kyau ai tuni Islam ta manta da batun wani ciki ta saki rai sukariga zaga gurin suna soyewar su, Hannunta ya kawo ya nuna mata wata mata da bazata huce sa'ar ta ba ya ce "Kali wannan daga gani kin girmeta amma har tayi yara biyu amma ke kike cewa bakya so." Kallon matar ta yi da mamaki take kallon mijin matar har ta mutu bazata manta da wannan fuskarba, Sahal ne rike da hannun matashiyar matar da alamu matar shice. Kawar da kai Islam ta yi taja hannun Abdulfatah sukabar gurin tana na jansa da hira me da i dan kai Abdulfatah ya gane Sahal koshi Sahal in ya gata a samu matsala ran mijinta ya ace ita kuma taba son duk wani abuda zai atawa Abdulfatah rai. (Mace ta gari kenan.) ALHADULILAH Duka-duka anan nakawo arshen wannan labari na ABDULFATAH abuda na fa a wanda ba dai-dai ba Allah ka yafe mun. Duk wanda na atawa acikin wannan labari ina ro on ya yafe mun. Ku biyoni a sabon Litafina me suna WATA RAYUWA, free book. Ga masu shawara ko arin haske ga number ta, 08166077167 call or WhatsApp By *XAHRA*