*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA ƊAYA Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu tagwayen hawaye suka fara 'yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. "Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku." Kuka ya sake ƙwace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ƙullin kayan Lami da ke ɗaure a ɗankwali. Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana faɗin. "Lami kin san irin so da ƙaunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan ƙarfi da yaji? Matuƙar za ki tafi gidanku sai dai ki tafi da ni Lami, domin ni na fi maye maita indai a kanki ne." Baba Isuhu ya janyo hannun Lami ya haɗa da na mai sunan malam ya rungume a ƙirji sai ya sake ɓarkewa da kuka. "Don Allah ki haƙura da yajin nan da za ki yi Lami. Matuƙar naman ƙauri ne zai datse igiyoyin so da ƙaunar da ke tsakaninmu ko sayar da kaina zan yi, amma na yi miki alƙawari duk inda zan shiga zan yi koma me ye na nemo miki abin ƙaurin nan Lami." Lami ta taɓe ba ki sannan ta ce. "Wallahi Isuhu ba abin da zai hana ni tafiya a daren nan, don in gaya maka na ce wa Goggo Sala ko awa guda ba za mu ƙara a gidan nan ba. Saboda Allah kamar a kaina tsiya ta ƙare, haihuwar fari a ce yau kwana biyu cir babu kajin ƙauri ballantana na saka rai da ɗan akuya ko tinkiya. Kai tir da halinka Isuhu, wallahi da Isa mai tsire na aure na san nama har sai na ci na ture..." Cikin sauri Baba Isuhu ya katse ta. "Me aka yi aka yi Isa ne Lami? Wai ko kin manta Isuhun Lamisuwa mai hadarin naira?" Lami ta sake taɓe baki ta furta. "Ai a banza man kare, tun da a haihuwar ɗanka na fari guda a ce abin ƙauri ya gagara, kenan haka zan zauna har hakikar sunan ita ma ta gagare ni. Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa." Jin haka ya sake tsuma Baba Isuhu ya zabure haɗe da ɗaga hannu sama ya ce. "Sai ni isuhullen Lamisuwa mai hadarin nairori, sai ni Isuhun da ya sha gaban zaratan mazaje ya samu Lamisuwa." Lami ta ɗan saki murmushi sannan ya kalle ta ya ce. "Wai ina Lami take?" Da sauri Lami ta amsa. "Ga ni mana." "A yau ba sai gobe ba zan kayar miki da tinkiya." Sai da ya kalli hagu da dama ya yi ƙasa da murya sannan ya matsa saitin kunnenta ya ce. "Kin san Allah yau uwar garke zan girke miki." Da sauri Lami ta washe baki cikin zumuɗi ta furta. "Uwar garke fa..." "Ki yi ƙasa da murya mana haba Lami, ko so kike asirina ya tonu?" Baba Isuhu ya katse ta da sauri. "Ɗan Isuhullena ai sai yanzu na fahimce ka, Allah Ya ba ka sa'a kada hatsabibiyar yarinyar nan ta ganka lokacin da za ka ɗauke mata uwar garken nan." Lami ta yi maganar murya can ƙasa zuciyarta fes. "Ai maso abin ka ya fi ka dabara Lamisuwata, dare zan bi na san yadda zan yi da ita. Ke dai kawai ki zuba wannan ki sha kallo." Baba Isuhu da Lami suka kwashe da dariya. "Lami! Ke Lami ki fito mu wuce kin shanya ni ke 'yar daɗi miji, kin san dai idan ana jego ko kyakkyawan zama a wurin miji ba a yi ballantama wannan mijin na ki..." Lami ta yi saurin katse Goggo Sala, "Goggo zo mu je ciki ai tuni mun riga da mun gyaro ta ni da shi." Baki sake Goggo Sala ta bi ta da kallo sannan ta ce. "Hmmm namiji kenan! Ke yanzu daɗin bakin namiji har zai sa ki zauna..." Lami ta yi saurin yi wa Goggo Sala raɗa a kunne, da sauri Goggo Sala ta washe ba ki ta furta. "Ke 'yar nan da gaske?" Lami ta gyaɗa kai tana murmushe. "Haba ko da na ji wannan ita ce harkar arziƙi, ko ni ƙanwar uwarki ai na samu na lasa wa a bakin salati. Ni fa kin san ni dama na fi kwarkwasa kwaɗayi, duk wurin da ake samun mai maiƙo-maiƙo a nan na fi ƙarfi." Lami ta yi gaba tana tafiya cikin ƙwambo tana jin ita ma ta isa, kuma ta tabbata matuƙar aka wayi gari da an yi mata ƙauri da tinkiya ta san daraja da ƙimarta ta ƙaru a idanun facalolinta. CIKIN DARE A hankali Uwani ta buɗe idonta sakamakon jin fitsarin da ya zame mata kamar farilla cikin talatainin dare, sai da ta gama murtsike idanu sannan ta fara tashin Dada. "Dada! Dada don Allah ki tashi ki raka ni fitsari nake ji." Dada cikin takaici ta saki dogon salati sannan ta ce. "Ni kam wallahi Dijen Iro ta cuce ni da ba ta gashe miki mara tun kina zanin goyo ba, wallahi Uwani ki kiyayi haƙƙin tashina tsakiyar dare da kike yi..." "Dada kamar kukan uwar garke nake ji." Uwani ta katse Dada cikin sauri tana sake kasa kunne, don sama-sama take jin kamar kukan dabbobinta kasancewar suna da ɗan nisa da sashen Dada. Dada ta yi mata shiru saboda takaici. "Dada don Allah ta shi mu je ko wani abu ne yake damun su..." "Ai wallahi ko Umaru ne ya dawo daga Lahira bai isa ya fid da ni waje ba, tun wuri ki kama 'yan matan ƙafafuwanki ki yi gaba." Jin takaicin abin da Dada ta faɗa ya sa Uwani tashi fuuu ta suri buta ta yi waje. Tamkar sabon munafiki haka Baba Isuhu yake tafe cikin sanɗa yana waige har ya ƙarasa sashen da awakin Uwani suke, sai da ya karkace maƙogaro ya maƙe murya kamar yadda Uwani ke yin magana sannan ya ce. "Uwar garkeruruna tayya maza mu je ki ci dusa." Shiru ya ga uwar garke ta yi babu alamin za ta motsa, ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya ɗago ta ya fara ja a hankali. Sai da ya ƙarasa bakin katanga sannan ya taka turmin da ke jingin, sama-sama ya ɗan fara jiyo motsi don haka ya yi kasake. A ɓangare ɗaya ƙirjinsa na bugawa don kada uwar garke ta yi kuka asirinsa ya tonu. Yana raɓe a gefen katanga ya ga Uwani ta wuce da buta a hannu sannan ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya, tirmi ya taka a hankali ya leƙa ya hango Mai gari da ke tsaye yana jiransa. "Haba Isuhu tun ɗazu ɗauko tinkiya ya gagare ka, ko so kake asirinmu ya tonu mutumcina ya bi rariya ya tsiyaye tas a garin nan ina matsayin mai garin garin nan." Baba Isuhu ya yi ƙasa da murya ya ce. "Kai Talle ka san dai fita da uwar garke ta ƙofa ba zai yuwu ba saboda tsaro, yanzu ga ta ka matso zan cicciɓo maka ita." Da sauri Mai gari Talle ya matsa jikin katangar. Baba Isuhu ya koma wurin Uwar garke da ke cin dusa, ya tattaro iya ƙarfinsa ya ɗago ta sai ji kake ɓaaaarrrrrrr wata uwar tusa ta ƙwace masa. Uwani da kawo kanta kenan ta saki murmushi ta ce. "Kai da jin wannan tusar ka san su uwar garke bacci ya yi daɗi." Har za ta gota sai ta leƙa garkensu, sai dai haskarwar da ta yi babu uwar garke babu alamunta. Da sauri ta juyo tana shirin fasa ihu ta hango Baba Isuhu rungume da uwar garke, ita kuma uwar garke jin matsar da Baba Isuhu ya yi mata ya sa ta ware baki ta ce. "Meeeeeeeeehhh." Cikin sauri Baba Isuhu ya miƙa wa Mai gari Talle, Mai gari na karɓa ya fara kici-kicin hawa mashin. Uwani na ganin Baba Isuhu ya miƙa uwar garke ta yi caraf ta kama katanga, sai dai tana gani Mai gari shi da wani da ba ta gane fuskarsa ba suka haye mashin suka fita da gudun gaske. A haukace Uwani ta diro daga kan katangar ta ɗora hannu a kanta cikin tashin hankali ta ce, "Wayyo Allah uwar garkena." Sai kuma ta yi sashen Dada a guje. Ganin haka ya sa Baba Isuhu da sauri ya nufi sashensa. A tsakar ɗaki ya sami Lami don haka tana ganinsa ta ce, "Ya dai Isuhullena an dace kuwa?" Baba Isuhu da ke faman haki ya ce, "Maza ki tafi ɗaki ki kwanta, ni ma lamfo zan yi shegiyar yarinyar nan ta kama mu ni da Talle." Zaro ido waje Lami ta yi ta ce, "Mun shige su Isuhuna ya za ka yi?" "Babu lokaci Lami ke dai ki je ki yi yadda na ce miki." Lami ta yi saurin ficewa shi kuma Baba Isuhu ya faɗa uwar ɗaki ya haye gado sannan ya fara sauke numfashi kamar wanda ya jima yana bacci. "Wayyo uwar garke." Uwani ta furta haɗe da ɓarkewa da matsanancin kuka. Ganin Dada na sakin bacci har da minshari ya sa Uwani ta buga tsalle haɗe da faɗin. "Wayyooo uwar garkena!" Sai a lokacin Dada ta ji ihun Uwani. "Kai ni kam Mamman ya cuce ni da ya haɗa Uwani da kiwo tun tana ƙanƙanuwarta. Yanzu ban da masifa a ce yarinya har cikin bacci tana ambatar tinkiya, wannan bala'in da me ya yi kama..." Dada ba ta ƙarasa magana ba ta ji Uwani ta faɗi a gefen ƙafarta tim! Ta fashe da wani irin matsanancin kuka. A razane ta tashi zaune sannan ta kai hannu ta kunna fitilar ɗakin, hannuwa biyu ta sa ta dafe ƙirji a firgice Dada ta furta. "Uwani ke ce nake gani a gabana ko buɗe mini ido aka yi?" Uwani ta ji tamkar Dada ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta fyace majina da gefen zaninta cikin ihu ta ce. "Uwar garkeeeeeena! Baba Isuhu ne uwar garkenaaaa." Dada ta zaro ido waje. "Ke Uwani ko dai gamo kika yi ne? Shi Isuhun ne ya zama uwar garke? An ya lamarinki Uwani babu jifa a ciki?" Dada na gama magana ba ta ji daga bakin Uwani ba ta fashe da kuka tana faɗin. "A'ubikalimatillahi tamma min sharrin ma kalaƙa. Aniya bi aniya wallahi aniyar kowa ta bi shi, Allah Ya kai mu wayewar gari wallahi sai na je gidan Sarkin aska na karɓo miki ƙaiƙayi, ni za a kashe da ƙullutun baƙinciki..." Uwani ta katse Dada daga dogon jawabin da take yi. "Dada wallahi ganin idona Baba Isuhu ya ɗauke mini uwar garke ya miƙa wa Mai gari ta katanga." "Ke yarinyar nan ki ji tsoron Allah, shi Isuhun nawa ne kike jifa da sata? Isuhun da ko yatsa ba za a saka masa a baka ya tauna ba?" Ganin haka ya sa Uwani ta fice daga ɗakin tana faɗin, "Wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ka dawo mini da uwar garkena. Wayyo Allah garkeruruna!" Jikin Dada nan take ya ɗauki karkarwa don haka ta miƙe cikin sauri ta bi bayan Uwani. Kafin wani lokaci wasu daga cikin mutanen gidan suka fara fitowa, kowa ya tambayi Uwani amsa ɗaya take bayarwa 'Uwar garke, Baba Isuhu ya miƙa wa mai gari ta katanga.' Carko-carko suka yi domin ga dukkan alamu sun fara aminta da kalaman Uwani, sakamakon sun duba garken awakinta sun ga babu uwar garke. "Ina shi Isuhun ne?" Baba Idris ya tambaya. Kallon juna suka shiga yi don haka ya bayar da umarnin a je sashen shi a kira shi. Sahabi da Tasi'u ne suka nufi sashen Baba Isuhu, sun jima suna buguwa sannan ya buɗe ƙofa, yamutsa fuska ya hau yi tamkar wanda aka tasa yana bacci ya ce. "Kai waye a tsohon daren nan yake mana bugu haka?" "Baba Isuhu dama Baba ne ya ce a taso ko?" Suka amsa masa. "Ni kuma? A tsohon daren nan? Ko ciwon Yaya ne ya tashi?" Baba Isuhu ya jefa musu tambayoyi kamar bai san abin da yake faruwa ba. Girgiza masa kai suka yi, suka wuce gaba yana biye da su a baya. Yana zuwa ya samu mutane a tsaye carko-carko, tun daga nesa gabansa ke dukan uku-uku amma gudun tonuwar asirinsa sai ya yi hanzarin aro mayafin jarumta ya lulluɓa wa jikinsa. Ya sake aro fuskar mamaki ya ɗora a saman tashi, cikin mamaki ya furta. "Yaya lafiya na ganku haka a tsohon daren nan?" "Uwani ce ta zo mana da wata magana..." Duk abin da ya faru Baba Idris sai da ya zayyane masa sannan ya ɗora da cewar, "Ina Uwar garke take?" Duk da ƙirjinsa bugawa yake amma bai hana shi fututtukewa ba ya ce. "Haba Yaya yanzu duk faɗin gidan nan a rasa wanda za a laƙa wa sata sai ni? Me zan yi da wata uwar garke? Shekarar uwar garke nawa a gidan nan? Amma kawai don yarinyar nan ta shirya ƙaryarta sai a hau kai a zauna, shi kenan tun da ni ne ɓarawon da kuke zargi a faɗa mini nawa ne kuɗinta zan biya." Ganin yadda ran Baba Isuhu ya ɓaci ne ya sanyaya jikin ilahirin mutanen da ke wurin, Dada ta zauna daɓar haɗe da rushewa da matsanancin kuka. "Tsakanina da wannan ɓarawon ni kam sai na kai kukana gaban Ubangiji, ina zaman zamana zai haɗa mini husuma a cikin zuri'ata." Baba Mustafa ya ɗago Dada sannan ya ce, "Yanzu dai duka mu bar maganar nan ni nan zan sayo miki wata ƙatuwar tinkiyar da ta fi uwar garke girma kin ji Uwani." Jin haka ya sa Uwani ta rushe da kuka. "Wallahi ni uwar garke nake so, kuma ko kur'ani aka ba ni zan dafa ganin idona na ga Baba Isuhu da uwar garkena..." Baba Mustafa ya yi saurin katse ta don haka kawai ya ji ya yi na'am da kalaman Uwani, don haka ma ya ce. "To shi kenan ba tinkiya kaɗai zan saya miki ba, kina son ɗan maraƙin sa ko?" Ba don Uwani ta daina jin zafin rashin uwar garke ba ta amsa, sai don son da take wa ɗan maraƙin sa. Saboda haka ta gyaɗa masa kai tana goge hawaye, a gefe ɗaya tana kuma ƙudurtar irin fansar da za ta ɗauka a kan Baba Isuhu don ta yi rantsuwa da Allah jinin Uwar garke ba zai tafi a banza ba. Daga haka gabaɗaya kowa ya watse, Uwani da Dada suka yi sashensu sai dai buta ta sake ɗauka ta fito kamar za ta banɗaki kai tsaye ta wuce sashen Baba Isuhu cikin sanɗa, ta ci sa a bai rufe ƙofa ba don haka tana laɓe daga bakin ƙofar ɗakinsa ta ji Lami na faɗin. "Isuhullena ai ka birge ni da ka ƙaryata shegiya, haka kawai da tuni da tozarta ka a gaban mutane." Baba Isuhu ya saki dariya ya ce. "Ke zan cen da nake miki gobe warhaka mun riga da mun gama ɓarje dabgen kan uwar garke." A gefe ɗaya ta ji muryar Goggo Sala na cewa. "Yanzu dai tun da aikin gama ya gama ai sai ku ja baki ku yi shiru, amma dai Isuhu dole ka badda kama idan za ka shigo da uwar garke don ka san dole a saka maka idanu." Baba Isuhu ya fashe da dariya yana shirin yin magana daga can bayan ƙofa suka ji muryar uwar garke ta ce. "Meeeeeeeeh." A zabure suka kalli juna cikin tashin hankali. "Kukan uwar garke nake ji a tsakar gida Isuhu leƙa ka gani..." Lami ta faɗa da sauri. "Ba ki da hankali Lami, ya za a yi ganin idona Talle ya tafi da uwar garke kuma na ji muryarta ke ki leƙa mana..." Kalaman bakinsa suka katse sakamakon sake jin kukan Uwar garke ta ce, "Meeeeesuhuuuu." Wani abu ne ya tsargawa Baba Isuhu tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa. "Isuhu kamar sunanka na ji a cikin kukan uwar garke." Lami ta faɗa a tsorace. "Meeeeeesuuuhuuuu." Uwani da ke laɓe ta sake maƙale murya ta faɗa da yanayin kukan uwar garke, tana gama faɗa ta dokon ƙauren ɗakin da suke ciki. A zabure Lami, Isuhu da Goggo Sala suka faɗa uwar ɗaki, Goggo Sala da ke ɗaure da ɗaurin ƙirji tun a falo zanin jikinta ya faɗi ba tare da ta sani ba. Goggo Sala da baba Isuhu suka shige bayan ƙofar uwar ɗaki ita kuma Lami ta maƙale a gefen gado, shirun da suka ji ba a ƙara kukan tinkiyar ba ne ya sa suka fara dawowa hayyacinsu. Goggo Sala ta kai idonta jikinta sai a lokacin ta yi ido biyu da tsurar ɗan fatarin (Under wear) da ke ƙugunta, ga ƙirjinta zube a saman kan Baba Isuhu da ke tsugunne a ƙasa. Sai a lokacin ta lura da hannuwan baba Isuhu da ke riƙe da ɗan fatarinta. Cikin matsananciyar kunya ta ce. "Kai Isuhu wanne irin iskanci ne haka saboda Allah za ka nemi shigewa cikin fatarina, ni fa ƙanwar mahaifiyar matarka ce ." Cikin rashin sani Baba Isuhu ya miƙe tsaye sai jin ƙirjin Goggo Sala ya yi a saman fuskarsa, yana ɗagowa suka haɗa ido da ita. Ganin abin kunyar da aka tafka cike da borin kunya ta ce, "Amma dai Isuhu yadda ka kwaso mini ƙirji ina a matsayin sirikarka Allah Ya kwashe maka albarka." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA ƊAYA Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu tagwayen hawaye suka fara 'yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. "Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku." Kuka ya sake ƙwace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ƙullin kayan Lami da ke ɗaure a ɗankwali. Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana faɗin. "Lami kin san irin so da ƙaunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan ƙarfi da yaji? Matuƙar za ki tafi gidanku sai dai ki tafi da ni Lami, domin ni na fi maye maita indai a kanki ne." Baba Isuhu ya janyo hannun Lami ya haɗa da na mai sunan malam ya rungume a ƙirji sai ya sake ɓarkewa da kuka. "Don Allah ki haƙura da yajin nan da za ki yi Lami. Matuƙar naman ƙauri ne zai datse igiyoyin so da ƙaunar da ke tsakaninmu ko sayar da kaina zan yi, amma na yi miki alƙawari duk inda zan shiga zan yi koma me ye na nemo miki abin ƙaurin nan Lami." Lami ta taɓe ba ki sannan ta ce. "Wallahi Isuhu ba abin da zai hana ni tafiya a daren nan, don in gaya maka na ce wa Goggo Sala ko awa guda ba za mu ƙara a gidan nan ba. Saboda Allah kamar a kaina tsiya ta ƙare, haihuwar fari a ce yau kwana biyu cir babu kajin ƙauri ballantana na saka rai da ɗan akuya ko tinkiya. Kai tir da halinka Isuhu, wallahi da Isa mai tsire na aure na san nama har sai na ci na ture..." Cikin sauri Baba Isuhu ya katse ta. "Me aka yi aka yi Isa ne Lami? Wai ko kin manta Isuhun Lamisuwa mai hadarin naira?" Lami ta sake taɓe baki ta furta. "Ai a banza man kare, tun da a haihuwar ɗanka na fari guda a ce abin ƙauri ya gagara, kenan haka zan zauna har hakikar sunan ita ma ta gagare ni. Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa." Jin haka ya sake tsuma Baba Isuhu ya zabure haɗe da ɗaga hannu sama ya ce. "Sai ni isuhullen Lamisuwa mai hadarin nairori, sai ni Isuhun da ya sha gaban zaratan mazaje ya samu Lamisuwa." Lami ta ɗan saki murmushi sannan ya kalle ta ya ce. "Wai ina Lami take?" Da sauri Lami ta amsa. "Ga ni mana." "A yau ba sai gobe ba zan kayar miki da tinkiya." Sai da ya kalli hagu da dama ya yi ƙasa da murya sannan ya matsa saitin kunnenta ya ce. "Kin san Allah yau uwar garke zan girke miki." Da sauri Lami ta washe baki cikin zumuɗi ta furta. "Uwar garke fa..." "Ki yi ƙasa da murya mana haba Lami, ko so kike asirina ya tonu?" Baba Isuhu ya katse ta da sauri. "Ɗan Isuhullena ai sai yanzu na fahimce ka, Allah Ya ba ka sa'a kada hatsabibiyar yarinyar nan ta ganka lokacin da za ka ɗauke mata uwar garken nan." Lami ta yi maganar murya can ƙasa zuciyarta fes. "Ai maso abin ka ya fi ka dabara Lamisuwata, dare zan bi na san yadda zan yi da ita. Ke dai kawai ki zuba wannan ki sha kallo." Baba Isuhu da Lami suka kwashe da dariya. "Lami! Ke Lami ki fito mu wuce kin shanya ni ke 'yar daɗi miji, kin san dai idan ana jego ko kyakkyawan zama a wurin miji ba a yi ballantama wannan mijin na ki..." Lami ta yi saurin katse Goggo Sala, "Goggo zo mu je ciki ai tuni mun riga da mun gyaro ta ni da shi." Baki sake Goggo Sala ta bi ta da kallo sannan ta ce. "Hmmm namiji kenan! Ke yanzu daɗin bakin namiji har zai sa ki zauna..." Lami ta yi saurin yi wa Goggo Sala raɗa a kunne, da sauri Goggo Sala ta washe ba ki ta furta. "Ke 'yar nan da gaske?" Lami ta gyaɗa kai tana murmushe. "Haba ko da na ji wannan ita ce harkar arziƙi, ko ni ƙanwar uwarki ai na samu na lasa wa a bakin salati. Ni fa kin san ni dama na fi kwarkwasa kwaɗayi, duk wurin da ake samun mai maiƙo-maiƙo a nan na fi ƙarfi." Lami ta yi gaba tana tafiya cikin ƙwambo tana jin ita ma ta isa, kuma ta tabbata matuƙar aka wayi gari da an yi mata ƙauri da tinkiya ta san daraja da ƙimarta ta ƙaru a idanun facalolinta. CIKIN DARE A hankali Uwani ta buɗe idonta sakamakon jin fitsarin da ya zame mata kamar farilla cikin talatainin dare, sai da ta gama murtsike idanu sannan ta fara tashin Dada. "Dada! Dada don Allah ki tashi ki raka ni fitsari nake ji." Dada cikin takaici ta saki dogon salati sannan ta ce. "Ni kam wallahi Dijen Iro ta cuce ni da ba ta gashe miki mara tun kina zanin goyo ba, wallahi Uwani ki kiyayi haƙƙin tashina tsakiyar dare da kike yi..." "Dada kamar kukan uwar garke nake ji." Uwani ta katse Dada cikin sauri tana sake kasa kunne, don sama-sama take jin kamar kukan dabbobinta kasancewar suna da ɗan nisa da sashen Dada. Dada ta yi mata shiru saboda takaici. "Dada don Allah ta shi mu je ko wani abu ne yake damun su..." "Ai wallahi ko Umaru ne ya dawo daga Lahira bai isa ya fid da ni waje ba, tun wuri ki kama 'yan matan ƙafafuwanki ki yi gaba." Jin takaicin abin da Dada ta faɗa ya sa Uwani tashi fuuu ta suri buta ta yi waje. Tamkar sabon munafiki haka Baba Isuhu yake tafe cikin sanɗa yana waige har ya ƙarasa sashen da awakin Uwani suke, sai da ya karkace maƙogaro ya maƙe murya kamar yadda Uwani ke yin magana sannan ya ce. "Uwar garkeruruna tayya maza mu je ki ci dusa." Shiru ya ga uwar garke ta yi babu alamin za ta motsa, ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya ɗago ta ya fara ja a hankali. Sai da ya ƙarasa bakin katanga sannan ya taka turmin da ke jingin, sama-sama ya ɗan fara jiyo motsi don haka ya yi kasake. A ɓangare ɗaya ƙirjinsa na bugawa don kada uwar garke ta yi kuka asirinsa ya tonu. Yana raɓe a gefen katanga ya ga Uwani ta wuce da buta a hannu sannan ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya, tirmi ya taka a hankali ya leƙa ya hango Mai gari da ke tsaye yana jiransa. "Haba Isuhu tun ɗazu ɗauko tinkiya ya gagare ka, ko so kake asirinmu ya tonu mutumcina ya bi rariya ya tsiyaye tas a garin nan ina matsayin mai garin garin nan." Baba Isuhu ya yi ƙasa da murya ya ce. "Kai Talle ka san dai fita da uwar garke ta ƙofa ba zai yuwu ba saboda tsaro, yanzu ga ta ka matso zan cicciɓo maka ita." Da sauri Mai gari Talle ya matsa jikin katangar. Baba Isuhu ya koma wurin Uwar garke da ke cin dusa, ya tattaro iya ƙarfinsa ya ɗago ta sai ji kake ɓaaaarrrrrrr wata uwar tusa ta ƙwace masa. Uwani da kawo kanta kenan ta saki murmushi ta ce. "Kai da jin wannan tusar ka san su uwar garke bacci ya yi daɗi." Har za ta gota sai ta leƙa garkensu, sai dai haskarwar da ta yi babu uwar garke babu alamunta. Da sauri ta juyo tana shirin fasa ihu ta hango Baba Isuhu rungume da uwar garke, ita kuma uwar garke jin matsar da Baba Isuhu ya yi mata ya sa ta ware baki ta ce. "Meeeeeeeeehhh." Cikin sauri Baba Isuhu ya miƙa wa Mai gari Talle, Mai gari na karɓa ya fara kici-kicin hawa mashin. Uwani na ganin Baba Isuhu ya miƙa uwar garke ta yi caraf ta kama katanga, sai dai tana gani Mai gari shi da wani da ba ta gane fuskarsa ba suka haye mashin suka fita da gudun gaske. A haukace Uwani ta diro daga kan katangar ta ɗora hannu a kanta cikin tashin hankali ta ce, "Wayyo Allah uwar garkena." Sai kuma ta yi sashen Dada a guje. Ganin haka ya sa Baba Isuhu da sauri ya nufi sashensa. A tsakar ɗaki ya sami Lami don haka tana ganinsa ta ce, "Ya dai Isuhullena an dace kuwa?" Baba Isuhu da ke faman haki ya ce, "Maza ki tafi ɗaki ki kwanta, ni ma lamfo zan yi shegiyar yarinyar nan ta kama mu ni da Talle." Zaro ido waje Lami ta yi ta ce, "Mun shige su Isuhuna ya za ka yi?" "Babu lokaci Lami ke dai ki je ki yi yadda na ce miki." Lami ta yi saurin ficewa shi kuma Baba Isuhu ya faɗa uwar ɗaki ya haye gado sannan ya fara sauke numfashi kamar wanda ya jima yana bacci. "Wayyo uwar garke." Uwani ta furta haɗe da ɓarkewa da matsanancin kuka. Ganin Dada na sakin bacci har da minshari ya sa Uwani ta buga tsalle haɗe da faɗin. "Wayyooo uwar garkena!" Sai a lokacin Dada ta ji ihun Uwani. "Kai ni kam Mamman ya cuce ni da ya haɗa Uwani da kiwo tun tana ƙanƙanuwarta. Yanzu ban da masifa a ce yarinya har cikin bacci tana ambatar tinkiya, wannan bala'in da me ya yi kama..." Dada ba ta ƙarasa magana ba ta ji Uwani ta faɗi a gefen ƙafarta tim! Ta fashe da wani irin matsanancin kuka. A razane ta tashi zaune sannan ta kai hannu ta kunna fitilar ɗakin, hannuwa biyu ta sa ta dafe ƙirji a firgice Dada ta furta. "Uwani ke ce nake gani a gabana ko buɗe mini ido aka yi?" Uwani ta ji tamkar Dada ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta fyace majina da gefen zaninta cikin ihu ta ce. "Uwar garkeeeeeena! Baba Isuhu ne uwar garkenaaaa." Dada ta zaro ido waje. "Ke Uwani ko dai gamo kika yi ne? Shi Isuhun ne ya zama uwar garke? An ya lamarinki Uwani babu jifa a ciki?" Dada na gama magana ba ta ji daga bakin Uwani ba ta fashe da kuka tana faɗin. "A'ubikalimatillahi tamma min sharrin ma kalaƙa. Aniya bi aniya wallahi aniyar kowa ta bi shi, Allah Ya kai mu wayewar gari wallahi sai na je gidan Sarkin aska na karɓo miki ƙaiƙayi, ni za a kashe da ƙullutun baƙinciki..." Uwani ta katse Dada daga dogon jawabin da take yi. "Dada wallahi ganin idona Baba Isuhu ya ɗauke mini uwar garke ya miƙa wa Mai gari ta katanga." "Ke yarinyar nan ki ji tsoron Allah, shi Isuhun nawa ne kike jifa da sata? Isuhun da ko yatsa ba za a saka masa a baka ya tauna ba?" Ganin haka ya sa Uwani ta fice daga ɗakin tana faɗin, "Wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ka dawo mini da uwar garkena. Wayyo Allah garkeruruna!" Jikin Dada nan take ya ɗauki karkarwa don haka ta miƙe cikin sauri ta bi bayan Uwani. Kafin wani lokaci wasu daga cikin mutanen gidan suka fara fitowa, kowa ya tambayi Uwani amsa ɗaya take bayarwa 'Uwar garke, Baba Isuhu ya miƙa wa mai gari ta katanga.' Carko-carko suka yi domin ga dukkan alamu sun fara aminta da kalaman Uwani, sakamakon sun duba garken awakinta sun ga babu uwar garke. "Ina shi Isuhun ne?" Baba Idris ya tambaya. Kallon juna suka shiga yi don haka ya bayar da umarnin a je sashen shi a kira shi. Sahabi da Tasi'u ne suka nufi sashen Baba Isuhu, sun jima suna buguwa sannan ya buɗe ƙofa, yamutsa fuska ya hau yi tamkar wanda aka tasa yana bacci ya ce. "Kai waye a tsohon daren nan yake mana bugu haka?" "Baba Isuhu dama Baba ne ya ce a taso ko?" Suka amsa masa. "Ni kuma? A tsohon daren nan? Ko ciwon Yaya ne ya tashi?" Baba Isuhu ya jefa musu tambayoyi kamar bai san abin da yake faruwa ba. Girgiza masa kai suka yi, suka wuce gaba yana biye da su a baya. Yana zuwa ya samu mutane a tsaye carko-carko, tun daga nesa gabansa ke dukan uku-uku amma gudun tonuwar asirinsa sai ya yi hanzarin aro mayafin jarumta ya lulluɓa wa jikinsa. Ya sake aro fuskar mamaki ya ɗora a saman tashi, cikin mamaki ya furta. "Yaya lafiya na ganku haka a tsohon daren nan?" "Uwani ce ta zo mana da wata magana..." Duk abin da ya faru Baba Idris sai da ya zayyane masa sannan ya ɗora da cewar, "Ina Uwar garke take?" Duk da ƙirjinsa bugawa yake amma bai hana shi fututtukewa ba ya ce. "Haba Yaya yanzu duk faɗin gidan nan a rasa wanda za a laƙa wa sata sai ni? Me zan yi da wata uwar garke? Shekarar uwar garke nawa a gidan nan? Amma kawai don yarinyar nan ta shirya ƙaryarta sai a hau kai a zauna, shi kenan tun da ni ne ɓarawon da kuke zargi a faɗa mini nawa ne kuɗinta zan biya." Ganin yadda ran Baba Isuhu ya ɓaci ne ya sanyaya jikin ilahirin mutanen da ke wurin, Dada ta zauna daɓar haɗe da rushewa da matsanancin kuka. "Tsakanina da wannan ɓarawon ni kam sai na kai kukana gaban Ubangiji, ina zaman zamana zai haɗa mini husuma a cikin zuri'ata." Baba Mustafa ya ɗago Dada sannan ya ce, "Yanzu dai duka mu bar maganar nan ni nan zan sayo miki wata ƙatuwar tinkiyar da ta fi uwar garke girma kin ji Uwani." Jin haka ya sa Uwani ta rushe da kuka. "Wallahi ni uwar garke nake so, kuma ko kur'ani aka ba ni zan dafa ganin idona na ga Baba Isuhu da uwar garkena..." Baba Mustafa ya yi saurin katse ta don haka kawai ya ji ya yi na'am da kalaman Uwani, don haka ma ya ce. "To shi kenan ba tinkiya kaɗai zan saya miki ba, kina son ɗan maraƙin sa ko?" Ba don Uwani ta daina jin zafin rashin uwar garke ba ta amsa, sai don son da take wa ɗan maraƙin sa. Saboda haka ta gyaɗa masa kai tana goge hawaye, a gefe ɗaya tana kuma ƙudurtar irin fansar da za ta ɗauka a kan Baba Isuhu don ta yi rantsuwa da Allah jinin Uwar garke ba zai tafi a banza ba. Daga haka gabaɗaya kowa ya watse, Uwani da Dada suka yi sashensu sai dai buta ta sake ɗauka ta fito kamar za ta banɗaki kai tsaye ta wuce sashen Baba Isuhu cikin sanɗa, ta ci sa a bai rufe ƙofa ba don haka tana laɓe daga bakin ƙofar ɗakinsa ta ji Lami na faɗin. "Isuhullena ai ka birge ni da ka ƙaryata shegiya, haka kawai da tuni da tozarta ka a gaban mutane." Baba Isuhu ya saki dariya ya ce. "Ke zan cen da nake miki gobe warhaka mun riga da mun gama ɓarje dabgen kan uwar garke." A gefe ɗaya ta ji muryar Goggo Sala na cewa. "Yanzu dai tun da aikin gama ya gama ai sai ku ja baki ku yi shiru, amma dai Isuhu dole ka badda kama idan za ka shigo da uwar garke don ka san dole a saka maka idanu." Baba Isuhu ya fashe da dariya yana shirin yin magana daga can bayan ƙofa suka ji muryar uwar garke ta ce. "Meeeeeeeeh." A zabure suka kalli juna cikin tashin hankali. "Kukan uwar garke nake ji a tsakar gida Isuhu leƙa ka gani..." Lami ta faɗa da sauri. "Ba ki da hankali Lami, ya za a yi ganin idona Talle ya tafi da uwar garke kuma na ji muryarta ke ki leƙa mana..." Kalaman bakinsa suka katse sakamakon sake jin kukan Uwar garke ta ce, "Meeeeesuhuuuu." Wani abu ne ya tsargawa Baba Isuhu tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa. "Isuhu kamar sunanka na ji a cikin kukan uwar garke." Lami ta faɗa a tsorace. "Meeeeeesuuuhuuuu." Uwani da ke laɓe ta sake maƙale murya ta faɗa da yanayin kukan uwar garke, tana gama faɗa ta dokon ƙauren ɗakin da suke ciki. A zabure Lami, Isuhu da Goggo Sala suka faɗa uwar ɗaki, Goggo Sala da ke ɗaure da ɗaurin ƙirji tun a falo zanin jikinta ya faɗi ba tare da ta sani ba. Goggo Sala da baba Isuhu suka shige bayan ƙofar uwar ɗaki ita kuma Lami ta maƙale a gefen gado, shirun da suka ji ba a ƙara kukan tinkiyar ba ne ya sa suka fara dawowa hayyacinsu. Goggo Sala ta kai idonta jikinta sai a lokacin ta yi ido biyu da tsurar ɗan fatarin (Under wear) da ke ƙugunta, ga ƙirjinta zube a saman kan Baba Isuhu da ke tsugunne a ƙasa. Sai a lokacin ta lura da hannuwan baba Isuhu da ke riƙe da ɗan fatarinta. Cikin matsananciyar kunya ta ce. "Kai Isuhu wanne irin iskanci ne haka saboda Allah za ka nemi shigewa cikin fatarina, ni fa ƙanwar mahaifiyar matarka ce ." Cikin rashin sani Baba Isuhu ya miƙe tsaye sai jin ƙirjin Goggo Sala ya yi a saman fuskarsa, yana ɗagowa suka haɗa ido da ita. Ganin abin kunyar da aka tafka cike da borin kunya ta ce, "Amma dai Isuhu yadda ka kwaso mini ƙirji ina a matsayin sirikarka Allah Ya kwashe maka albarka." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA UKU Ilahirin ƙarfinsa Malam na Madina ya ware yana cakumar Jafar, idan ya dunƙule hannu sai dai ka ji dum! Ya kai masa dundu a baya. Shi kansa Jafar ya yi mamakin ƙarfin dattijon duk da ba fin ƙarfinsa ya yi ba. Na Madina da ya ga ya ɗauki lokaci bai kai Jafar ƙasa ba, ya zuba wata uwar kabbara tamkar wanda yake tsakiyar yaƙin musulmai da arna yana faɗin. "Allahu Akbar." Da ya yi kabbara sai ya sauke wa Jafar wani dundu a baya. Uwani na ganin haka ta ɗebo ruwa a randa ta fara yayyafawa Dada, babu jimawa Dada ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe idonta. Jafar tun yana ganin dukan da Na Madina yake yi masa wasa ne har ya ga ya cukwikwiye masa wuya, har wani zullo yake yana kabbara yana kai masa duka tamkar mai jifan shaiɗan. Jafar ya haɗa hannuwan dattijon wuri ɗaya ya murɗe su sannan ya ce. "Wallahi Na Madina ko ka sauko daga kaina ko na bi yatsun hannunka ɗaya bayan ɗaya na tsike su kamar yadda ake tsinkar mangwaro." Jin matsar da Jafar ya yi masa da kuma furucinsa ya sa cikin Na Madina ya karta, yana shirin yin magana ya ji Dada na salati daga kwance. Tamkar ɗan biri sai ga na madina ya yi tsalle ya faɗo ƙasa, Jafar ya gyara wuyar rigarsa ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ya wuce ɗakinsa da Dada ta sa aka gyara masa. Malam na Madina ya tsugunna a daidai kan Dada ya ce. "Sannu da farkowa Kulu." Dada ta dube shi luuuu da idanu a shanye sai kawai ta ɗaga ɗan yatsa ɗaya ta ce. "Ashhadu anla'Ila'ha'illahu wa anna Muhammadur Rasulillah." Malam na Madina ya sake cewa. "Mun auna arziƙi Dada wannan yaron ashe harbe ku ya so yi?" Dada ta sake yin luuuu da idanu fuskar na Madina na yi mata gizo ta ce. "Ismi Hauwa kulu wa ana musulima." Jin haka ya sa Na madina ya fashe da kuka, kukan da Dada ta ji ne ya sa ta ɗan wartsake sai a lokacin komai ya fara dawo mata. Zumbur ta tashi zaune ta fara bin su Uwani da kallo. "Uwani kina jin maganata ko kuma da gaske Jafaru ya harbe ni na mutu?" Uwani ta saki dariya ta ce. "Ina jin ki mana Dada ga Na Madina ma a zaune." Dada ta kalli na Madina suna haɗa ido kamar haɗin baki suka fashe da kuka a tare. "Uwani maza ɗauko mini wayata."Dada ta furta cikin kuka. Da sauri Uwani ta ɗauko mata don ta san ba ya wuce ta ce a kira mata baba Mamman. "Maza kira mini Mamman." Uwani ta karɓi wayar ta gama dube-dubenta sannan ta ce, "Lambarsa ce mai hotan zuciya ko?" Da sauri Dada ta gyaɗa kai. Uwani ta kira tana jin an ɗauka ta miƙa wa Dada. "Assalamu Alaikum. Hajiya Dadata yau ke ce da kira da kanki..." "Dakata Mamman! Kiranka na yi ka gaya mini waye shugaban 'yan sanda na duk faɗin duniya?" Dada ta katse Baba Mamman a zafafe. "Shugaban 'yan sanda na duniya? Dada me ya faru kuma?" Ya tambaya a sanyaye. "Me ye ma bai faru ba Mamman? Ka gaya mini shugaban 'yan sanda na duniya da inda zan same shi, domin a yau ba sai gobe ba wallahi zan ce ya tube Jafaru daga wannan aikin kakin. Kai ni dai Sa'idu ya gama cutata, a ce 'ya'ya duka babu mai aiki ƙwaƙƙwara daga Soja, Rosafti sai Ɗan sabda. Wai kamar ni 'yar limamai jikar limamai ace duka 'ya'yana babu limami ko malamin makarantar allo." Sai da Dada ta fyace majina sannan ta cigaba. "Mamman ko ka sa a tube Jafaru ko kuma wallahi sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba..." "Don Allah Dada me yake faruwa?" Baba Mamman ya katse ta hankali a tashe. Nan take Dada ta zayyane masa duk abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Cikin kwantar da murya ya fara lallashinta har ya samu ta daina kukan sannan ta ce. "To yanzu Mamman yadda aiki yake wahala, idan aka tube Jafaru daga aikin nan wacce sana'a zai fara? Tsorona Allah tsorona kada ya fara ɗauke-ɗauke, ni dai na san Jafaru da tsoron Allah ko mage ba zai iya kashewa ba, to ko dai a Lagas ɗin nan ya fara 'yan zuƙe-zuƙe ne da ya zo zai harbe mu?" Murmushi baba Mamman ya yi ya furta. "Dada da ya kashe mana ke ai gara a tube shin kawai, amma dai ba na jin Jafar yana shaye-shaye ki bar ni da shi zan kira shi yanzu a waya wallahi ransa sai ya ɓaci." Dada ta ɗan yi jim sannan ta ce. "Ni fa Mamman ban ce ka kira shi ka yi masa tijara ba, ina zaman zamana Jafaru ya zo ya cika ni da nunkufurcin tsiya. Ni ban san ma lokacin da Saratu ta koya maka masifa ba, yara irinsu Jafaru sai addu'a da lallashi. Kai kanka Mamman ba don tsayuwar da na yi a Harami ba ai da ban san abin da za ka zama ba, Allah dai Ya shirya mana zuri'a." Baba Mamman ya yi murmushi ya amsa mata sannan suka yi sallama. Uwani sam ba haka ta so wayar ta kasance ba, don haka ta miƙe har za ta fita sai kuma ta wuce uwar ɗakin Dada tana sakin murmushi. A can ƙarƙashin gado ta ciro bankinta ta ƙwaƙulo kuɗaɗen da suke ciki, sai da ta ƙirga su kusan dubu ɗaya da ɗari biyar ne. Ta ɗaure su a ɗankwali haka kawai ta fara sakin murmushi, Dada ta bi ta da kallon mamaki baki a sake. Baba Mamman na kashe waya ya kira Jafar ya yi masa faɗa sosai, tare da nuna masa illar tsoratar da Dada da ya yi musamman da shekarunta suka tura. Jafar ya fahimci mahaifinsu sai dai shi tsokanar Dada yake da ya ce harbe ta zai yi. Can ƙasan akwatinsa ya je ya tura bindigar ya ajiye sannan ya shiga banɗaki ya watsa ruwa ya wuce ɗakin Dada. A nan ya shiga tsokanarta suka fara hira har Malam na Madina kamar ba shi ne ya gama kabbara yana naushinsa ba. Uwani na fita can kantin Ɗan bala ta wuce ta sayo alawa irin da raɗin suna leda biyu, sai ta ƙarasa wurin Ali mai dabino shi ma ta sayo gwangwani uku. Sai da ta tsaya a gefen hanya ta kunce kowacce leda ta zuba kofato biyu da ragowar jelar tumaki ɗai-ɗai sannan ta ɗaure. Tana tafe tana sakin murmushi har ta ƙarasa gida, kai tsaye sashen Baba Isuhu ta nufa za ta shiga kenan ta gan shi ya fito da alama masallaci za shi don an kira sallar Magriba. "Sakaryar banza ke ba kya ganin mutane ne?" Baba Isuhu ya furta yana wurga wa Uwani harara. "Ga shi wata mata ta ce na kawo maka." Uwani ta faɗa tana miƙa masa ledar hannunta. Da mamaki ya karɓa ya furta, "Wata mata kuma? Ba kuma Lami aka ce ki kai wa ba?" Uwani ta girgiza kai cikin alamun tsoro ta ce. "Kai ta ce a kawowa kuma ni fa idanun matar ya ban tsoro wallahi, Baba Isuhu dama mutane suna da kofato ne ban taɓa sani ba sai yau?" A firgice Baba Isuhu ya saki ledar alawar ya ce. "Kofato fa? A ina kika ga kofaton?" Uwani na ganin yadda ya firgice sai ta basar ta ce, "Bari dai na wuce wurin Dada..." "Don ubanki za ki tsaya ki mini bayani ko kuwa?" Baba Isuhu ya yi magana jiki na rawa, don bai jima da barin gidan Talle Mai gari ba, da yaje duba shi sakamakon yana kwance sharɓan. Kuma a dubiyar da ya je ne yake shaida masa abin da ya faru da shi a banɗaki da kuma ɗakinsa. "Eh matar ce na ga ƙafarta da kofato, sai ta miƙo mini ledar nan ta ce na ba ka. Kuma ta ce na faɗa maka idan ka wurgar da saƙon nan a kan mai sunan malam za ta fanshe."Da sauri Baba Isuhu ya tsugunna ya fara tattaro dabino da alawar, a nan idanunsa suka ci karo da kofato, tuno abin da Uwani ta faɗa ya sa jikinsa na rawa ya haɗa ledar ya sa a aljihu ya dubi Uwani ya ce. "Ina matar take yanzu." Uwani ta zuba hannu biyu ta yi tagumi ta ce. "Ni fa tana ba ni ledar nan da na waiga sai ban ganta ba, wallahi ina jin ɓacewa ta yi don kamar ƙiftawar ido haka na neme ta na rasa." Wani irin sanyi ƙafafun Baba Isuhu suka yi, Uwani ta yi kamar ba ta gane yanayin da yake ciki ba ta shige cikin gidansa. Baba Isuhu yana nan tsaye har zai fita ko me ya tuna da sauri ya faɗa cikin gida, yana tafe hawaye na zuba don jikinsa ya gama ba shi ta shi ta zo ƙarshe. Uwani na daga ɗakin Lami ta hango shi nan da nan ta ƙunshe dariyarta, yana shiga ɗakin ita kuma Goggo Sala na sirka ruwan wanka don aiki ne ya hana ba ta yi wanka da wuri ba. "Lami ni kam na shiga uku!" Da sauri Lami ta kalle shi, Uwani na jin haka ta muƙe ta fice. Da yake ta lura hankalinsu ba ya kanta kai tsaye ta bi hanyar banɗakin da Goggo Sala ta bi domin yin wanka. Lokacin da Uwani ta je wurin banɗakin Goggo Sala ta riga da ta tuɓe har ta fara wanka, a hankali ta saɗaɗa ta janye kayan da ta cire. Sannan ta fara wani irin gurnani tana kukan tinkiya. Goggo sala ta riga da ta saɓa sabulu a fuska da sauri ta dakata, jin ta daina wankan ya sa Uwani ta yi wani gurnani mai ɗan tsoratarwa sannan ta maƙe murya ta ce. "Gani gare ki Goggo Sala, ki nutsu ki saurari abin da zan faɗa miki domin zai yi miki amfani a matsayinki na jinsin bil'adam." Nan take jikin Goggo Sala ya ɗauki karkarwa kamar mazari, hannu biyu ta sa ta fara kiciniyar goge kumfan fuskarta amma yajin sabulu ya hanata buɗe ido. "Nan wurin da kike wanka masarautarmu ce, kuma kina tsaye ne akan karagar shugabarmu ga hadimanta nan sai zagaye ki suke yi. Wani abin haushi kin saka su kallon tsiraici, don ma Allah Ya taimake ki aljani Manu ɗan kwarto ba ya kusa da tuni ya haike miki." Jin haka ya sa Goggo Sala ta fashe da kuka, Uwani ta gimtse dariyarta ta cigaba da cewa. "Ni ce uwar garke wacce kika dafa namanta, to yanzu haka na dawo domin ni dama ba tinkiya ba ce. Kuma namana da kika dafa a tukunya na ɗauke shi na kai garkena, sannan zan kafa miki wani sharaɗi matuƙar kika saɓa masa zan ɗauke ki zuwa duniyarmu." Goggo Sala baki na rawa ta ce. "To Babata uwar garke faɗi kowanna sharaɗi ne ni mai biyayya ce a gare ki." Uwani ta sa hannu ta toshe dariyarta ta ci gaba da cewa. "Sharaɗin shi ne kullin za ki dinga goya Isuhu sau uku a rana, safe, rana da kuma dare. Idan kika zo goya shi ki dinga yi kina lasar baki, kuma idan kika kuskure koda na lokaci ɗaya ne ba ki yi ba take zan ɗauke ki ko kuma na tsotse romon kanki." "Wallahi zan yi ba dai goyo ba, ko har da Lami aka ce zan haɗa na goya su." Goggo Sala ta faɗa cikin kuka. "Kin taimaki kanki, yanzu kayan da kika cire zan kai shi garkena amma zan bar miki ɗankwali, kuma kada ki kuskura ki fito sai an kira sallar Isha'i domin anfara tattaunawar fadar aljanu da ke. Sannan ɗan autan shugabanmu ya ce da baya da baya za ki tafi ɗaki kina cewa nasara a kanku Isuhu da Lami." Goggo Sala ta amsa, a zuciyar tana da-na-sanin zuwanta zaman daɓaro gidan Lami. Uwani na gama maganar cikin sanɗa ta koma har lokacin baba Isuhu yana ɗakin don ta hango shi ta cikin labule, ta raɓe a gefen ƙofar ɗakin ta karkace murya ta fara kukan tinkiya. Shiru ta ji sun yi sannan ta yi wani gurnani tana yi tana buga ƙafa irin tsalle-tsallen da awaki suke yi. "Shi kenan Lami ta zo ina jin tafiya za ta yi da ni." Baba isuhu ya faɗa cikin kuka. "Ba zan tafi da kai yanzu ba. Ni uwar garke ni ce na aiko maka da saƙo ɗazu. Ku buɗe kunnenku da kyau, uwar garke ba mutum ba ce. Na zo na kafa muku sharuɗɗana idan kuka bi su zan yafe muku zunubin da kuka aikata mini, idan ba haka ba kuma a gabanku zan yi farfesun mai sunan malam na saka ku cinye shi kuma ku shanye romonsa." "Wallahi ko mene ne kika ce mu yi za mu yi miki biyayya." Lami ta faɗa a tsorace. "Kai Isuhu da farko taimakonka za mu fara yi kafin ka ji sharaɗinmu. Ƙanwar mahifiyar matarka babbar matsafiya ce a ɓoye, kuma dama da biyu ta zo zaman daɓaro gidanka. Idan kuma ka yi yunƙurin korarta za ta halakaka da iyalinka gaba ɗaya. Daga gobe ne wa'adin aikin da take yi a kanka zai fara, don haka yanzu ma za ku ga ta fito tana tafiya da baya-baya tana ambatar sunanku don haka kada wanda ya tanka mata. Kuma gobe za ta zo da sassafe ta ce maka za ta goya ka. Duk rintsi kada ka bari ta taɓa maka jikinka." A zabure Baba Isuhu ya ce. "Goyo fa? Ni Isuhu za a goya da giramana ban da iskanci?" Uwani ta katse shi. "Idan muna magana ba a tankawa. Sannan Sharaɗin da za mu kafa maka ya zama wajibi ka ɗauki rigunan mama na Lami guda uku ka kai wa mahaifiyarka Dada ka ce ta saka su..." "Dadar ce za ta saka bireziya..." Baba Isuhu ya furta cikin suɓutar baki. Uwani ta buga masa tsawa cikin gurnani ta ce. "Idan ka saɓa mana wallahi sai mun hallaka ka da kisa mafi muni." Nan take Baba Isuhu ya ce. "Duk abin da kika ce na bi Inna uwar garke." "Na dawo gare ki Lami. Ke kuma akwai dafin da Goggo Sala ta saka miki a ruwan wanka wanda wa'adinsa gobe zai cika, ko ba kya ganin irin maganin da take zuba miki a ruwan wanka kullin?" Da sauri Lami ta gyaɗa kai. "Idan kika sake shayar da ai sunan Malam daga gobe ke da shi mutuwa za ku yi, domin dodonta zai zuƙe jininku tas." Da yake Lami ta san Goggo Sala da shegen bin malamai nan take ta aminta da kalaman Uwani. "Sharaɗin da zan kafa miki ya zama dole daga gobe ki dinga ɗaukan mai suna Malam kina kai wa Jafar shi yana shayar da shi a sashen Dada." Cikin haɗin baki Lami da Baba Isuhu suka ce. "Jafaru kuma? Shi zai shayar da mai sunan Malam?" "To kada ku kai shi dama ɗan autan Goɗiya kwaɗayin romon jariri yake ji sai na dafe masa shi." Uwani ta faɗa cikin wata irin murya, don ita kanta dagewa take da tuni dariya ta kwace mata. "Wallahi za mu kai shi, Allah Ya kai mu gobe." Gabaɗaya suka amsa. "Kuma ya zama wajibi a gare ka, kai Isuhu ka saka ƙarfi ka danne Jafar domin a shayar da mai sunan malam idan ba haka ba komai zai iya biyo baya. Kuma sharaɗin da zan kafa muku na ƙarshe ko da wasa kuka faɗi abin da ya faru tsakanina da ku, sai na sa wuƙar aljanin mahauta ya yaɗe fatar jikinku sannan na ɗauke ku zuwa duniyarmu a azabtar da ku kamar yadda kuka azabtar da ni." Uwani na daga tsaye ta fara jiyo shasshekar kukan Baba Isuhu. Sai da ta lallaɓa ta ɗauke tukunyar naman da aka yi farfe su ta ajiye a soro sannan ta ce. "Tukunyar namana da kuka dafa ku same ta a wurin garkena, kada wanda ya fito har sai an kira sallar isha'i domin tuni an zauna zaman fadar aljanu da ku. Kuma idan kuka bari namana da kuka dafa ya kwana a garkena cikin dare zan gayyato tawagar jinsinmu su ɗauke mini ku." Uwani na gama maganar ta fara kukan tumaki tana wani irin dire-dire sannan ta ɗauki tukuyar ta tafi a hankali, kai tsaye ta wuce garken awakinta. Da yake duhu ya yi awakin Uwani duka sun kwanta, a hankali ta isa turken uwar garke ta ajiye tukunyar. Ta janyo igiyar uwar garke ta saƙale a jikin ƙafar tukunyar, zuciyarta fes ta wuce sashen Dada don ta yi sallar magriba tana tafe tana dariya kamar sabuwar kamu. Har alla-alla take gari ya waye ta ga irin diramar da za a tashi da ita. A lokacin da ta shiga ɗakin Dada Jafar na zaune ta kofin shayi a gefensa , ga laptop a gabansa yana dannawa, dawowarsa daga masallaci kenan. Uwani na ƙare masa kallo ta tuntsire da wata mahaukaciyar dariya, domin yanayin zaman da ta ga ya yi ne har ta hango yadda Baba Isuhu zai danne shi a shayar da mai sunan malam. Ɗagowa ya yi ya kalle ta sai kuma ya ci gaba da danna laptop ɗinsa, Uwani ta sake kallonsa ta ga yadda yake jin magani sai kawai ta tsugunna a wurin tana sheƙa uwar dariya. "Uban me kike yi wa dariya?" Jafar ya furta a daƙile. Tamkar wacce ya sake ingizawa, sai Uwani ta sake fashewa da dariya har da hawaye da ta tuna duk irin haɗe fuskar da yake yi wai shi za a danne a shayar da mai sunan malam. "Ba tambayarki nake yi ba?" Jafar ya buga mata tsawa. "Dama wani wasa ne muka fara bugawa ni da ƙawata Lantana shi ne na shirya mata yadda zan cinye ta gobe." Uwani ta yi maganar tana ɗan murguɗa baki. "Ba na son shashanci idan wannan iskanci za ki yi ki fice mini ba na son hayaniya." Uwani ba ta kula shi ba ta gimtse dariyarta ta shige uwar ɗakin Dada. Ku kawo wa Jafar ɗauki zai shayar da mai sunan malam🤭🏃🏼‍♀️😂 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA HUƊU Tun da Uwani ta fito daga gidan baba Isuhu daga shi har Lami babu wanda ya kuma motsin kirki, baba Isuhu ya sharɓe hawaye ya dubi Lami cikin kallon tsana da jin haushi ya ce. "Tsakanina da ke Allah Ya isa Lami, kin cuce ni kin cuci rayuwata. Ni ban san ƙaddarar da ta sa na auro ki ba, duk wannan ƙaton bakin na ki ko ina ya je da ban gan shi ba sai yanzu?" Lami ta wurga masa harara ta ce. "Mun dai cuci juna malam ka gyara maganarka. Ni kaina ban azal da kuma rabo me zan yi da kai? Ka san dai duk a samarina kai ne faƙiri matsiyaci." "Wallahi aurena da ke bai ƙare ni da komai ba sai masifa, ina zaman zamana kin jefa ni a jafa'i muguwa mai ƙashin tsiya..." "Dakata malam, kada ka raina mini hankali. An gaya maka ban san dama can kana 'yan sace-sacenka ba? Ko ka manta kajin Yaya Haladu da muka taɓa soyewa?" Shiru baba Isuhu ya yi yana nazari, shi kam ya ci alwashin daga uwar garke har abada ba zai ƙara taɓa kayan wani ba. Dama tun da yake 'yan ɗauke-daukensa ba a taɓa kama shi ba, don haka zai ajiye sata salin-alin ba tare da ta tona masa asiri ba. Suna nan zaune suka ji an rafka kiran sallar Isha'i, babu jimawa suka ji takun Goggo Sala tana tafe da baya-baya, taku ɗaya-biyu idan ta yi sai ta ci karo da kwanuka sannan ta furta. "Nasara dai a kanku Isuhu da Lami." Da hannu Lami ta yafito baba Isuhu ta cikin labule take nuna masa ita, cikin gasgata maganar da Uwani ta gaya musu suka saki baki suna kallonta, a ɓangare ɗaya kuma tsoron Goggo Sala ya kama su. Tana shiga ɗakin da suke kwana da Lami ta banko ƙofa, can ƙuryar bango ta zauna sai kawai ta rushe da wani irin kuka mai cin zuciya. "Kaico kwaɗayina bai amfane ni da komai ba, Allah ka fitar da ni daga wannan gidan annobar. Wallahi nan gaba idan duniya Lami za ta haifa har abada ni da gidanta." Ganin ta shige ɗaki ya sa baba Isuhu ya fita a hankali domin cika umarnin uwar garke, kai tsaye garken Uwani ya nufa yana haskawa kuwa ya yi ido biyu da tukunyar farfesun naman. Nan take ƙirjinsa ya buga, jikinsa ya fara karkarwa sai da ya yi ta maza ya ɗauko tukunyar ya nufi sashensa. WASHEGARI Baba Isuhu tun da ya yi sallar asuba ya gagara runtsawa saboda fargabar goyon da Goggo Sala za ta yi masa, yana zaune a gefen gado ya kallo Lami da ke kwance ita da mai sunan malam. Motsi ya ji a tsakar gida yana leƙawa ya hangi Goggo Sala tana kaiwa da kawowa, abin duniya ya dame ta saboda gari ya fara haske amma har kawo lokacin babu Isuhu babu motsinsa. Cikin sanɗa ta nufo ɗakin da suke ciki baba Isuhu ya leƙo ta windo ya ce. "Munafukar Allah ta'ala ina ankare da ke, wato fakona kike za ki hallaka ni ko?" Goggo Sala ta washe baki tana basarwa ta ce. "Isuhu barka da safiya." Baba Isuhu da ya tuna gargaɗin da aka masa, aka ce kar ya yi mata kora da hali shi ma sai ya yaƙe baki ya amsa. Amma a zuciyarsa ji yake tamkar ya fashe da kuka. Mai sunan malam ne ya motsa Lami ta yi fitgigit ta tashi zaune. "Maza tashi mu je ki kai shi wurin Jafaru." Ba musu Lami ta tashi ta saka hijabinta, baba Isuhu ya manta Goggo Sala da ke waje tana fakonsa ya sa hannu ya buɗe sakata suka fito. Har zai yi gaba ya tuna bai ɗebo rigunan maman Lami da aka ce ya kai wa Dada ba, dama tun a daren ya sa Lami ta ɗebo masa guda uku daga cikin na ta. Komawa ya yi ya ɗebo ya zuba a aljihu sannan ya fito. Yana fitowa Goggo Sala ta yi wata uwar sufa za ta cafko baba Isuhu, a firgice ya zuba a guje yana faɗin. "Wayyo Lami ki zo za ta cafke ni, wallahi tsaf za ta sa a tsotse romon kaina." Goggo Sala na ganin rana ta fara fitowa ga shi ba ta cika umarnin uwar garke ba, ya sa ta rufa wa baba Isuhu baya yana gudu tana bin sa. Da yake ya gama tsorata da ita har gani yake kamanin Goggo Sala kamar har rikiɗe masa suke yi, Goggo Sala irin dogayen matan nan ne, shi kuma baba Isuhu ba shi da tsayi kuma ba shi da jiki. Don haka Goggo Sala ta kusa kama shi amma Allah ya taimake shi ya fice daga gidan, Lami ta rufa masa baya da sauri ya tura ƙofar ya datse ta. Wata gwaruwar ajiyar zuciya ya sauke yana ayyana shi kenan da tuni an bayar da jininsa. Ɓangaren Dada a buɗe yake don haka ba su sha wata wahala ba suka nufi ɗakin da Jafar yake ciki, Lami ce ta fara ƙwanƙwasawa sun ɗan jima sannan Jafar ya buɗe da alama bacci yake yi. Daga shi sai singlet da gajeren wando ya buɗe ƙofar yana murza idanu. Da mamaki yake bin su Baba Isuhu da kallo ya furta. "Ina kwana baba." Baba Isuhu ya washe baki. "Jafaru an tashi lafiya?" Jafar ya amsa sai baba Isuhu ya ce. "Wurinka muka zo Jafaru amma ko za mu ƙarasa ɗakin Dada?" Zuciyar Jafar fes ya ce. "Ok to bari na saka kaya ga ni nan zuwa." Lami da baba Isuhu suka wuce ɗakin Dada a lokacin tana zaune tana jan carbi. Tana ganinsu ta shafa addu'ar, sai da ta cire hijabin ta ajiye carbin ta ce. "Isuhu lafiya na gan ku da farar safiyar nan?" Cikin haɗin baki suka gaishe ta. Baba Isuhu ya ciro rigunan maman hannunsa ya miƙa wa Dada ya ce. "Dada ga wannan a saka." Dada ta karɓa tana yamutsa fuska. "Kai kuwa Isuhu kamar wanda ya kwana da Uwani a rai, tun da farar safiya ka kawo mata wata rigar mama. Wannan dai rigunan ai na manyan mata ne, ina Uwani ina wannan lalacewar." Baba Isuhu ya ɗan sosa kai ya ce, "Ai dama ba na Uwani ba ne, ke na kawowa Dada..." Tun bai ƙarasa magana ba Dada ta katse shi, "Ni fa Isuhu? Ni kuwa me zan yi da rigar mama tsofai-tsafai? Amma dai ka ci mutumcina Isuhu, wai ko dai ka fara 'yan zuƙe-zuƙe ban sani ba?" Idanun baba Isuhu suka ciko da ƙwalla sai da ya share hawaye ya ce. "Don girman Allah Dada ki ɗiba ki shiga ɗaki ki saka." Baki sake Dada take kallonsa, ta rafka salati haɗe da faɗin, "Maza kwashe mini lalatattun kayan nan kafin ranka ya ɓaci. Ni Kulu uban me zan saka a ciki? An ya Isuhu shaɗanu ba su dafa maka kai a cikin bacci ba?" Uwani da ke uwar ɗaki ta sunne kai ƙasa tana dariya. "Haba Dada da farar safiya ki cika wa mutane kunne da ihu." Jafar ya faɗa yana sako kansa cikin ɗakin. Uwani da ke ɓoye a ɗaki ta yi ƙasa da murya ta ce, "Kai ma naka ihun yana tafe." "Ba dole ka ji ihuna ba Jafaru yanzu kamar ni tsofai-tsofai." Sai kuka ya ci ƙarfin Dada sai da ta share hawaye sannan ta watsa wa Jafar rigunan a fuska ta ci gaba. "Wai Isuhu ya rasa me zai kawo mini sai baraziya wai na saka. Yanzu saboda Allah Jafaru ko uwarka Saratu me za ta yi da baraziyya ballantana kuma ni?" Tun Dada ba ta gama magana ba Jafar ya watsar da rigunan sakamakon wani tsami da bashi-bashi da ya ji ya doko hancinsa. "Haba Dada me kike yi haka ne?" Jafar ya faɗa a ƙazance. Kafin Dada ta yi magana mai sunan Malam ya sake tsanyarewa da kuka, Lami ta dubi Jafar ta miƙa masa shi. Kamar Jafar zai yi magana sai kuma ya basar ya miƙa hannu ya karɓe shi, yana bin su da kallon mamaki. "Don Allah Jafaru ka taimaki yaron nan ka ba shi mama ya sha ko ya yi shiru." Lami ta faɗa a ɗan kunyace. Jafar ya kalli Lami cikin sauri ya ce. "Wane Jafarun?" Jafar ya tambaya a hargitse. "Kai mana Jafaru, don Allah ka yi ka ba shi kada ya shiɗe don tun ɗazu yake kuka." Baba Isuhu ya furta. Ran Jafar ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya haɗe fuska ya dubi baba Isuhu. "Baba wannan wacce irin magana ce babu tsari, yanzu idan na faɗa maka magana a ce na yi rashin kunya. Idan har ni zan iya shayar da shi me ya hana kai ba ka shayar da shi ba?" Dada ta saki baki da hanci tana kallon baba Isuhu a tsorace, don ita a yanzu ya fara ba ta tsoro shi da Lami. A hankali ya ajiye mai sunan malam a gefe sannan ya miƙe, yana shirin tafiya Lami ta ce. "Isuhu sai fa mun danne shi..." Tun Lami ba ta ƙarasa magana ba baba Isuhu ya sa ƙafa ya shatalo ƙafar Jafar sai ga Jafar a ƙasa. Dada na ganin haka ta fara tafiya da rarrafe don ta tabbata yau su Isuhu babu lafiya, shi ya sa ta nemi guduwa kafin ita ma su dawo kanta su danne ta su saka mata rigar mama. Jafar ya yi mamakin yadda ya gagara ƙwace kansa a hannun baba Isuhu, don haka jin baba Isuhu ya fara ɗaga masa riga sama ya fara kiciniyar kare kansa, garin yunƙurin danne rigarsa sai ga Jafar yana sakin tusa. Uwani kuwa me za ta yi ba dariya ba har hawaye saboda mugunta. Ganin haka ba zai kai Jafar ba ya sa ya fara ihu. "Wayyo Dada ki kawo mini ɗauki. Wayyo Allah! Mutanen gidan nan ku kawo min ɗauki su Lami za su haike mini." Uwani na daga ɗaki ban da dariya babu abin da take sheƙawa, saboda tsabar dariya har kwanciya ta yi ƙasa. Suna cikin haka sai jin muryar Goggo Sala suka yi a bakin ƙofa ta fara lashe baki tana faɗin, "Allah na gode maka da har yanzu lokaci bai ƙure mini ba." A zabure baba Isuhu ya ɗaga Jafar, take jikinsa ya fara karkarwa ta fara tunkaro shi yana ja da baya. "Wayyo Allah Dada ki zo Goggo Sala za ta sa a cinye ni." A madadin Jafar ya gudu tun da ya samu ya tsira sai ya bi baba Isuhu da kallo, saboda ba ƙaramin mamaki ya ba shi ba. Dada da ke cikin ɗaki ta kai wa Uwani duka tana ce wa. "Dariyar me kike yi Uwani mu da ya kamata mu fara yunƙurin ƙwatar kanmu." Kafin Uwani ta yi magana suka ji baba Isuhu ya zuba ihu. "Wayyo ta shanye mini ƙafafu, Jafaru, Dada ku zo ku kawo mini ɗauki." Goggo Sala ba ta bi ta kan baba Isuhu ba ta shatalo ƙafafuwansa za ta sunkuta shi a baya sai ga baba Mustafa da baba Idris sun shigo. "Subhanallahi kai Isuhu lafiya kuwa?" Suka ƙarasa maganar suna ƙarasawa wurin Goggo Sala, baba Isuhu da yake ya gama tsorata sai ji suka yi sharaf ya faɗo jikinsu da alama ya suma. Suka kama shi suka kwantar a ƙasa sai kawai Goggo Sala ta fashe da kuka. "Yanzu shi kenan rayuwata ta zo ƙarshe." Da mamaki suke bin ta da kallo, Baba Mustafa ya dubi Jafar da ya yi laƙwas a gefe ya ce. "Kai Jafar wane sakarci ne haka ake yi kai kuma kana zaune?" Jafar ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Baba ni ma ta kaina nake da tuni sun haike mini, dube ni wai fa ni zan shayar da mai sunan Malam." "Gara da Allah Ya kawo ku Idirisa, wallahi Isuhu shi da matarsa sun haukace. Ashe ba su kaɗai ba har da Salamatu ita ma, an ya ba gamo suka yi a cikin gidan ba. Ban da haka wai ni Isuhu zai kawowa rigar mama ya ce na saka, sannan su dubi garjejen ƙato kamar Jafaru su ce ya shayar da me sunan malam." Baba Mustafa ya yi farat ya ce. "Shi Jafarun ne zai shayar da jariri?" Dada ta wara hannuwa ta furta. "Ta ya ni ji dai Muɗɗafa, ka ga dai a kan idona aka haifi Jafaru. Kai ƙarshe ma dai ni na yi jinyar shayin da aka yi masa ballantana na ce ko Jafaru ya koma mata-maza, Jafaru ko ka sauya daga baya zuwa mata-maza ne ban sani ba." A ƙufule Jafar ya ce, "Wallahi Dada kar ki ƙara ce mini mata-maza." Kukan da mai sunan malam yake tsanyarawa ne ya sa baba Idris ya yi wa Lami magana, sai da ta share ƙwallar idonta ta ce. "An ce daga jiya kada na ƙara shayar da shi." A daidai lokacin baba Isuhu ya farfaɗo sakamakon ruwan da aka yayyafa masa. "Waye ya hana ki shayar da shi?" Shiru gabaɗaya suka yi, baba Isuhu ya dubi Lami ita kuma ta kalli Goggo Sala sai kawai suka fashe da kuka lokaci ɗaya. Shiru ɗakin ya yi kowa yana bin su da kallon mamaki, ban da Uwani da ke sakin murmushi a fakaice. Sai da suka yi me isar su sannan aka samu da ƙyar Goggo Sala ta ce. "Ni kam na san wannan jawabin da zan yi ƙila shi ne na ƙarshe a rayuwata don na san kashe ni za su yi." Baba Isuhu ya yi tsammanin bayanin 'yan ƙungiyar asirin da take ciki za ta faɗa, don haka ya zuba mata ido sai ya ji ta ce. "Dama dai uwar garke ba..." Kamar haɗin ba ki Lami da Isuhu suka ta fi da gudu suka toshe mata baki, da mamaki mutanen ɗakin suka bi su da kallo. "Ƙarya take yi makira haɗa ni da 'yan uwana za ta yi." Baba Isuhu ya faɗa yana haki kamar wanda ya ci gasar tseren gudu. "Ba ma son shashancin banza da wofi Isuhu, sakar mata baki kada ranka ya yi mummunan ɓaci." Baba Mustafa ya faɗa a fusace. Babu yadda suka iya haka suka koma suka zauna jiki a sanyaye, baba Isuhu ya sunkuyar da kai ƙasa gabansa na faɗuwa. Goggo sala ta fara wassafo jawabi tiryen-tiryen tana hawaye. Tana gama jawabi gabaɗaya ɗakin suka ɗauki salati. "Kaico rayuwa ni Kulu me na haɗa da sata da Isuhu zai janyo mini mugun hali cikin zuri'ata." Dada ta furta tana zubar da ƙwallah. Malam na Madina da ke gefe ya ce. "An ya Isuhu yanzu rayuwar da ka ɗauko mana kenan? Wallahi ka yi gaggawar yin istigifari kuma ka nemi masu kaya ka mayar musu da abin su. Idan ba haka ba muna cikin Firdausi kana Hawiya, atoh faɗar Allah ce ba ya yafe haƙƙin wani a kan wani." Shiru ɗakin ya yi kunyar duniya ta mamaye baba Isuhu shi da su Lami. Baba Idiris da baba Mustafa suka rufe shi da faɗa sosai, don haka ya nuna nadamarsa a fili. Sannan baba Mustafa ya juyo wurin Dada. "Dada ki gafarce ni a game da abin da zan faɗa amma tun farko ke ce kika ɓata Isuhu, saboda Isuhu yana ɗan autanki kika ɗauki son duniya kika ɗora masa. Hatta makaranta da Baba Sa'idu ya saka shi daina zuwa ya yi kuma kika goya masa baya, duk cikinmu shi kaɗai ne bai samu karatun arabi da boko mai zurfi ba. Ga shi nan sana'o'in ma wacce ce ba a nuna masa ba amma kullin a tsalle-tsalle yake ba shi da aiki sai kame-kame, tun wuri ka yi wa kanka faɗa domin kullin girma kake ƙara yi." Dada ta sharce ƙwallar da ke fuskarta ta ce. "Yanzu dama Muɗɗafa ka na da tarin nasihohin nan tutuni ba ka yi mini ba? Ni dai wannan maganar a rufe ta a nan kada Sa'idu ya ji don wallahi sai ya kusa cinye ni ɗanya." Gabaɗaya suka amsa mata. "Dama wannan abin kunyar ai ba za mu bari ya fita ba Dada, yanzu dai a tambayi Uwani tun da haƙƙinta ne ta yafe masa?" Uwani da ke gefe ta saki murmushin ƙeta ta yi saurin cewa, "Ni dai Baba na riga da na yafe musu baba Isuhu ai tamkar mahaifina na ɗauke shi." Da sauri Jafar ya dube ta don haka kawai ya ji bai yarda da kalaman Uwani ba. "Allah Ya yi miki albarka Uwani, dama ɗa ba sai wanda ka haifa ba kaico rayuwa Allah Ya gafarta wa Yaya Umaru." Baba Isuhu ya faɗa yana sharce ƙwallah. Uwani ta saki murmushin ƙeta a ranta ta ce, "Za ka ga ɗa ba sai ka haifa ba." Baba Idris ya yi musu nasiha sannan ya ce shi da kansa a ranar zai kira su Aramma na gangare su yi saukar Alƙur'ani a gidan gabaɗaya. "Baba ni fa gani nake wannan abin da aka yi musu kawai tsoratarwa ne wani ke yi musu, idan aljanun gasken ne ai da tuni sun ɗauki mataki. Kada a yi wasa da hankulan mutane a dai duba lamarin." Jafar ya yi maganar yana zuba wa Uwani kallon tuhuma, don yadda ya ga tana sakin murmushi ya ji sam bai yarda da ita ba. "Koma dai mene ne ai babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji Jafaru. Allah Ya yi mana maganin wannan masifa." Baba Mustafa ya faɗa, gabaɗaya suka amsa da Amin. Uwani na haɗa ido da Jafar ta sakar masa harara, haɗe da murguɗa masa baki. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA BIYAR Kasancewar sunan gidan baba Isuhu ya zo a lokacin hutun zangon karatu ya sa ilahirin zuri'ar gidan sun hallara, musamman da ya kasance baba Mamman ya dawo gida ne gabaɗaya domin lokacin ritayarsa ta kusa. Kuma a wannan kwanakin ne yake shirin tarewa a katafaren gidan da ya gina a nan cikin Unguwar rijiyar zaki da ke jihar Kano. Hajiya Saratu da iyalanta sai shan ƙamshi suke yi suna kallon mutane ɗaiɗai, don ko maganar arziƙi ba ta cika haɗa ta da sauran facalolinta ba. Sanin halinta na raini da wulaƙanci ya sa suma sauran mutanen gidan suke kama mutumcinsu ba tare da sun shiga sabgarta ba. Asalin Tarihinsu Malam Haruna mai shanu shi ne ainihin cikakken sun marigayi malam mahaifin su baba Isuhu. Asalinsa mutumin garin Rigana ne da ke cikin ƙauyen lambar ƙunci, ɗaya daga cikin ƙananan ƙauyukan da ke jihar Kanon Dabon Najeriya. Sunan mai shanu ya samo asali ne tun a wurin mahaifinsa kasancewarsa fitaccen bafulani a wannan ƙauyen, duk girman garin Rigana babu mai albarkar shanu da dabbobinsa. Yana da matar aure ɗaya da 'ya'ya biyu sakancewar duka maza, Malam Haruna shi ne babba sai ƙaninsa mai bin sa Sa'idu wanda bayan su mahaifinsu bai sake haihuwa ba. Bayan mahaifiyar su malam mahaifinsu ya auri mata biyu sai dai ko ɓatan wata babu wacce ta taɓa yi. Mahaifiyarsu ta rasu tun suna samari yayin da mahaifinsu ya rasu bayan da kowannen su ya yi aure a lokacin Malam haihuwarsa biyu. Baffajo tun da ƙuruciyarsa yakan ɗebi shanu da awakinsa su tafi garuruwa kiwo bayan wani lokaci sai ya dawo gida, hakan yake yi har zuwa lokacin da su Malam suka zama samari suma yake nuna musu hanyar kiwon shanu. Sai dai tun suna yara ya fahimci sam ba su da ra'ayin kiwace-kiwacen shanun da yake yi, bayan da mahaifinsu ya rasu sai suka ɗora daga inda ya tsaya sai dai su ba kamar Baffajo ba. Don tun bayan da ya rasu bai fi sau uku zuwa huɗu suka fita da shanu zuwa wasu garuruwan ba. A wannan lokacin ne kuma watarana bayan malam ya fita da shanun su da suka gada a wurin mahaifinsu, ya yi nisa sosai da garinsu sai ya faɗa tarkon wasu 'yan fashin daji. Kasancewar kuma sarkin yawa ya fi sarƙin ƙarfi sai suka yi masa ƙwacen shanu da yawa, kaɗan ya rage ba su hallaka shi ba ya dawo gida da tsirarun shanun da ko goma ba su kai ba. Wannan yanayin da suka shiga wasu sun dasa zargin har da saka hannun mutanen garinsu, yayin da wasu kuma suka ce jarabta ce kawai daga wurin Ubangiji. Dalili kenan da ya sa bayan da malam ya warke suka haɗa kai shi da ɗan uwansa suka bar garin gabaɗaya tare da sayar da shanunsu, suka dawo wani ɗan ƙauye a nan garin Kura suka kafa kasuwancin su. Kuma cikin hukuncin Ubangiji sai Allah ya saka musu albarka. Hauwa kulu Ibrahim mai allo shi ne cikakken ainihin sunan Dada asalinta mutuniyar garin Bauchi ce, baƙar bafulatana ce tana da kyau daidai gwargwado. Mahifinta Malamijo ɗan gidan malamai ne domin a rigarsu gidan su Dada ba ɓoyayyan gida ba ne. Mahaifinta yana da mata biyu da 'ya'ya bakwai. Musa shi ne ainihin sunan malam na Madina, kuma shi ne babban yayansu Dada uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Ya auri matarsa bayan zamansu mai tsawo Allah Ya yi mata rasuwa, sai dai bayan ita ya yi aure-aure da dama bai taɓa samun haihuwa ba. Dada ita take bin shi sai kuma Fatsime take bin Dada sai dai akwai tazara sosai tsakanin Dada da Fatsime. Fatsime ta rasu a wurin haihuwa, ta rasu ta bar 'yarta Abuwa dalilin da ya sa Dada ita da na Madina kaɗai suka rage waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya. A lokacin da mahaifiyar su Dada ta haifi Fatsime har ta cire rai da sake samun haihuwa. Hasiya, Safare, Sule da Gali sune sauran 'yan uwan Dada da suke Uba ɗaya. Malam ya haɗu da Dada ne a lokacin da suka tafi kiwo garin Bauchi tun mahaifinsu na raye, don haka ba a ɗauki lokaci ba aka tsayar da maganar aure bayan wani lokaci aka ɗaura musu aure. Da yake Dada nesa da garinsu za a kai ta sai mahaifinta ya haɗa ta da ƙanwarta Fatsime, a kan bayan wani lokaci idan Dada ta saba sai Fatsime ta dawo. Sai dai ko da Malamijo ya buƙaci Fatsime ta dawo malam da kanshi ya je har garin Bauchi ya roƙi arziƙin a bar musu Fatsime a wurin su. Ganin yadda malam ke kula da Dada da kuma girman da yake ba shi sai ya kawar da kai ya haƙura ya bar masa ita. Dada da malam sun haifi 'ya'ya tara bakwai maza sai biyu mata. Baba Yunusa (Soja ne), baba Mustafa (Road safety ne), baba Idris (Malamin makarantar secondry ne), baba Mamman (Ɗan sanda), baba Rufa'i (Likita), Atika, Halimatu, marigayi Umaru wato mahaifin Uwani sai kuma Baba Isuhu (Sayar da itace yake yi). Baba Sa'idu (Ƙanin malam) Yana da mata ɗaya da 'ya'ya biyar. Biyu maza sai uku mata. Ya auri matarsa ne tun a garin Rigana, kuma tin bayan komawarsu Kura da suka fara kasuwanci shi da ɗan'uwansa, sai ya fara tafiye-tafiye zuwa garuruwa. Sannu a hankali sai nemansa ya fi ƙarfi a garin Zaria, don haka ya ɗauki iyalinsa suka koma can da zama. Cikin ikon Allah kowannensu ya ci gaba da zama da iyalinsa. Da yake Dada kwanika ta dinga yi gabaɗaya 'ya'yanta tazarar su babu yawa, kuma a lokacin da take da cikin Baba Isuhu ne Allah ya yi wa malam rasuwa. Kafin rasuwarsa ne ya biya mata Makka, zuwan farko umara ta je ta yi sai zuwa na biyu da suka je tare suka yi aikin Hajji. Malam Sa'idu ya kaɗu da rashin ɗan uwansa domin ko mutuwar mahaifinsu ba ta bige shi haka ba, daga nan kuma ya riƙe dukiyar ɗan uwansa da amana yana juya musu. Kuma ya ci gaba da tallafa wa Dada ita da yaranta, ya tsaya musu kai da fata suka samu ilimin addini da na zamani kuma har Allah ya ci da su suka samu aikin yi. Sai dai ba da aikin Gwamnati kaɗai suka dogara ba domin suna harkar kasuwancin kayan robobi da harkar kayan abinci. Baba Mamman yana da matar aure ɗaya Hajiya Saratu da yara biyar. Jafar shi ne babba, Ibrahim, Shukra, Jidda, sai Mufida wacce suke kira da Auta. Hajiya Saratu 'yar aminiyar mahaifin baba Mamman ce, ba ta da son mutane ko kaɗan. Mace ce mai faɗin rai da taƙama uwa-uba tana da son kanta, ga ta da tsananin kishi sannan akwai ta son hulɗa da matan masu kuɗi. Wannan halin na ta ya sa ko kaɗan ba ta jituwa da Dada, kuma kusan halayenta ne su Shukra suka kwasa gabaɗaya. Jafar da Ibrahim ne ba su da irin halinta sai Auta don haka har sun fi su Shukra sabo da mutanen cikin gida. Gidan marigayi malam Haruna mai shanu gidan gandu ne da ya haɗa kakanni, iyaye, jikoki da kuma 'ya'yan jikoki. Baba Mamman da Baba Yunusa ne kaɗai ba sa zaune a cikin gidan, kasancewar yanayin aikinsu da sauye-sauyen garuruwan da ake yi musu a wurin aiki. Amma kowannensu yana da ɓangarensa a cikin gidan, idan suka zo hutu suna sauka da iyalansu a ciki. Marigayi Umaru Haruna Mai shanu shi ne mahaifin Uwani, ya rasu tun mahaifiyar Uwani na da cikinta wata bakwai sakamakon hatsarin mota. Maryama Shu'aibu shi ne ainihin sunan mahaifiyar Uwani, dalilin mutuwar mahaifin Uwani ya sa Dada da su Baba Mamman suka ci gaba da kula da ita. Bayan wata tara Allah Ya sauke ta lafiya ta haifi jaririyarta, ta ci burin idan namiji ne ta mayar da sunan mijinta Umaru. Amma da ta haifi mace su Dada suka tambaye ta sunan da take son a raɗa wa jaririyar, da kanta ta ce a saka sunan Dada saboda irin karamcin da suka nuna mata, sai ake kiranta da suna Uwani. Bayan da aka yaye Uwani ne mahaifin Maryama ya nemi da ta dawo gabansa da zama, domin zawarawa suna ta zuwa kai masa gaisuwa da nuna ƙoƙon bararsu a kan aurenta. Ranar da za ta tafi ne Dada ta nemi da ta bar mata Uwani saboda soyayyar da take yi wa mahaifinta, idan tana ganinta za ta dinga jin daɗi. Bayan komawar mahaifiyar Uwani gidansu ko shekara ba ta rufa ba aka ɗaura mata aure da wani mutum, a lokacin yana da aure da mata ɗaya da yara huɗu. Maryama ta aure shi ne ba don tana son shi ba, sai don kawai ta yi wa mahaifinta biyayya amma har lokacin zuciyarta na ga mahaifin Uwani. Garin da take aure yana nesa da garin su Uwani sosai, kuma ta haifi yara biyu da malam Salihu mace da namiji, sai dai ko kaɗan ita da kishiyarta ba sa jin daɗin zama da shi sakamakon mugun halinsa. Uwani ta taso a hannun Dada cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya, tun bayan tafiyar mahaifiyarta baba Mamman ya so a ba shi riƙon Uwani amma fir Dada ta hana shi, lokacin da Hajiya Saratu ta ji ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Shekarun Uwani goma sha huɗu a duniya kuma irin fitinannun yaran nan da suke fita zakka ko a cikin unguwa. Rashin ji, rashin tsoro, kafiya, naci, tsokana rashin yafiya sune halayen da suka mamaye Uwani har mutanen garin suka saka mata suna 'Uwani 'Yar Ƙashin Gwiwa' saboda hatsabibanci da rashin jin ta. Duk cikin gidan mai shanu Dada ce kaɗai ba ta ganin laifin Uwani, don haka ma duk wurin da ta shiga sai dai su bi ta da harara. Jafar ma'aikacin ɗan sanda ne mai ɗauke da muƙamin ASP, shekarunsa talatin da biyu cif a duniya. Ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa matakin degree a jami'ar Bayero University. Miskili ne bai cika surutu ba, sai dai wani lokacin bauɗaɗɗan hali gare shi. Yana da kirki ga wanda suka fahimci juna sai dai wani lokacin yana da saurin fushi. Ba ya son raini ko kaɗan kuma yana da kykkyawar mu'amala da abokan aikinsa. Lokacin da ya fara aiki jihar Kaduna aka tura shi bayan wani lokaci ne ya samu sauyin aiki zuwa garin Katsina daga baya aka mayar da shi garin Lagos, ya kwana biyu a Lagos don bai cika zuwa hutu sosai ba. Ko da ya zo ma a gurguje yake kawo wa Dada ziyara shi ya sa Uwani ba ta wani san shi farin sani ba. Tana yawan jin labarin irin kulawar da Jafar ɗin ya dinga ba ta a lokacin da take yarinya, sai dai a wannan karon sam ba ta ga kalar mutumci a tattare da shi ba. Wannan hutun da Jafar ya samu kusan wata guda zai yi kafin ya koma, kuma ya ji labarin zuwan mahaifansa hutu da tariyarsu don haka shi ma ya yada zango a nan sashen Dada. Mu Koma Labari Tamkar sabuwar munafuka ko ɓarawon da yake sanɗa a daidai gaɓar da yake ɗaukar abin da ba na shi ba, haka Uwani ta shiga cikin ɗakin saɗaf-saɗaf tana tafe tana waige. Sai da ta kai ga ƙuryar ɗakin sannan ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya. "Uban 'yan iyayi ashe ba ya cikin ɗakin, da tuni yana nan a naɗe a kan katifa kamar mai karyayyan ƙugu." Ta furta cikun salon kwaikwayon muryarsa. Motsin da ta ji a bayanta ne ya sa ta yi mutuwar tsaye, zuciyarta ta fara harbawa tamkar za ta bijirewa zama a ƙirjinta, cikinta ya shiga juyawa yayin da zazzafan gumi ya shiga keto mata. Caran zakaran da ta ji a bayanta ne ya sa ta sake sauke ajiyar zuciya, ta saki murmushi a fili sannan ta furta. "Lawan wallahi ka cika binbinin tsiya, yanzu ɗakin Ofisa ma sai ka biyo ni. Idan kuwa ya kama mu wallahi sai ya kusa murɗe maka wuya." Tamkar zakaran ya san da shi take ya ci gaba da takawa yana tafe yana sakin kashi a tsaftataccan ɗakin da ya sha gyara ta ko ina sai zuba ƙamshi yake. Kafin Uwani ta ƙarasa kan katifar ɗakin tuni zakaranta da take kira da Lawan ya yi mata jagora zuwa kan luntsumemiyar katifar da ta sha gyara, a ɗame take da zanin gado kamar gadon sabuwar amaryar da za a kai ɗakin miji. "Lawan ina ka baro Fanteka, uwar 'ya'ya na san tana cen tana yawo ita da 'ya'yan iya." Uwani ta yi maganar kamar da mutum ɗan'uwanta take yi. A saƙale ta hango uniform ɗinsa na kayan 'yan sanda masu bulun riga da baƙin wando. Da sauri ta janyo ta hau kwaɓe kayanta kafin wani lokaci tuni ta saka a jikinta, sai da ta gama soshe kanta da ya cukurkuɗe sannan ta kafa baƙar hularsa a kanta. Cikin ƙwambo ta fara taku ɗaiɗai sannan ta cake a wuri ɗaya. "Ba na son hayani matsa daga kaina, ƙazama mai kwarkwata." Ta yi maganar cikin kwaikwayar maganar Jafar, tana faɗin irin maganganun da yake faɗa mata. Ta jima a tsaye tana surutanta sannan ta ƙarasa gaban mudubin da ke can gefenta, kamar a mafarki haka ta hange shi tsaye ƙyam kamar wanda ya haɗiyi falwaya. Fuska a haɗe kwatankwacin ta fusataccan bujumin sa. Nan take yawun bakinta ya ƙafe, ƙafafuwanta suka ɗauki rawa ƙirjinta ya shiga harbawa. Sai dai dakiya da ƙarfin zuciyar Uwani ya sa ta basar kamar ba ta gan shi ba. "Iya iya iya." Ta ji 'ya'yan kazarta na faɗa yayin da zakaran da ya gama kasaye ɗakin ya fara cara, da sauri kazar ta tunkaro ɗakin da niyyar shiga a fusace Jafar ya sa ƙafa ya yi ball da ita. Wata azababbiyar ƙara Uwani ta ƙwalla kamar da ita Jafar ya yi ball, ta fara tafiya wandon uniform ɗin yana zamo mata. "Innalillahi kashe mini fantake za ka yi..." Uwani ta yi maganar tana shirin fita daga ɗakin, yayin da Lawan (Zakaranta) ya firgice yana tsalle-tsalle a ɗakin, yana jefo masa kwalaben turare. "Gidan uban wa za ki?"Jafar ya wurga mata tambaya rai a ɓace. "Ina da gidan da ya wuce ɗakin Dada..." Jafar ya katse maganarta ta hanyar bige bakinta da ƙarfi. "Wallahi na ba ki nan da minti goma ki gyara mini ɗakin nan, sannan ki yi gaggawar cire mini uniform tun ranki bai ɓaci ba. Kuma idan kin gama zan gauraya da ke." "Sai ka fita na canza kaya." Sororo ya yi yana kallon Uwani don bai san lokacin da ta raina shi ba. Yana shirin sauke yatsunsa biyar a fuskarta wandon uniform ɗin ya zamo mata, gajeren wandon da ke jikinta ya bayyana. Fari ne amma dauɗa da jirwaye sun sa ya dafe saboda ƙazanta. A ƙazance ya kawar da kai gefe haɗe da tofar da yawu. "Ka san dai kallon tsiraici haramun ne, ka fita na sauya kaya. Kuma ni dai ba 'yar iska ba ce..." "Idan ba ki rufe mini baki ba wallahi sai na haɗa miki jini da majina a wurin nan. Sakarya fuska kamar ta aljanu, daga yau ko wani ne ya aiko ki ɗakin nan ba za ki ƙara marmarin shigowa ba." Tun da Jafar ya fara magana Uwani take kallonsa sheƙeƙe tun daga sama har zuwa yatsu biyar na ƙafarsa. Ba ta yi aune ba ta ji ya zuba mata rankwashin da ya sa ta gagara gane muhallin da take tsaye. Cikin sauri ta fisge hular kanta, ta zame dogon wandon uniform ɗinsa da ke jikinta. Jafar na nan tsaye ya ji tuuush! Lawan ya jefo sabuwar kwalbar turarensa, a firgice yake miƙa wuya yana cara haɗe da ci gaba da taka kayan da ke saman mudubin. A zuciye Jafara ya jefa masa takalmin kanbas ɗinsa. Firgitar da Lawan ya yi har cikin ran Uwani don haka cikin ɓacin rai ta ce, "Allah dai ba ya zalinci yana kallon baƙaƙen azzuluman duniya masu baƙaƙen kaya." A fusace Jafar ya yo kanta rai a ɓace, ganin haka ya sa Uwani ta zuba a guje kai tsaye ta wuce sashen Dada Jafar ya rufa mata baya. A daidai lokacin da Jafar ya nufi sashen Dada shi kuma malam na Madina ya kawo kai, cikin rashin sani Jafar ya bangaje shi kaɗan ya rage gemunsa ya taɓa ƙasa. "Jafaru! Kai Jafaru kana ji ka angije ni kamar ka angije dabba? Wallahi duk laifin Kulu ne ni take nunawa 'ya'ya da jikoki sun fi ɗan uwa." Ya ci gaba da tafiya har bakin ƙofar Dada yana kiran sunanta. "Kulu! Kulu kina ina ne..." Cikin sauri Malam na Madina ya datse ragowar kalaman bakinsa jin furucin da Jafar ke faɗa. "Wallahi tun wuri ki wuce mu je ɗakina don har kan katifa..." Uwani ta yi farat ta katse shi. "Amma dai ai ka bari na saka kayana yaya Jafaru, wallahi na fita a haka ka san dai mutanen gidan nan kowa sai ya san abin da yake faruwa." Jafar ya yi ƙwafa yana shirin ba ta amsa daga can waje ya ji muryar Malam na Madina yana sallallami. "Yanzu Jafaru dama munafurcin da kuke aikatawa kenan? Shi ya sa saboda sauri har ka angije ni ko waige na ba ka yi ba. Ba da ni ba, wallahi ba zan zauna ana aikata alfasha ina kallo ba, lokaci ɗaya Ubangiji ya halakar da mu." Sai da Jafar ya fito daga ɗakin Dada ya samu Malam na Madina da ke bin shi da ƙazantaccan kallo. Ficewa ya yi daga sashen Dada ya faɗa ɗakinsa, akwatin kayansa ya janyo ƙiiiiii yana kokawar fito da ita Dada ta sako kai ciki. Jin motsin ya yi yawa ya sa ta fara mita. "Waɗannan dabbobi na Uwani yadda kasan tare aka shayar da su saboda duk hatsabibancinsu iri ɗaya ne..." Ganin Malam na Madina ya janyo akwatinsa ƙiiii ya sa Dada sakin baki, "Wai Muda ne a wurin nan ko Usumanu?" Ta wurga masa tambaya tana ɗan ƙanƙance ido. Sai da Malam na Madina ya fito sannan ya ce. "Ki yafe ni Kulu don kar na tafi da haƙƙin wani a kaina." Baki sake Dada ta ce, "Yaya wani abin aka yi maka ne?" Malam na Madina ya share ƙwallar idonsa, ta waiga wurin da Jafar yake tsaye a bakin ƙofa ya jefa masa mugun kallo sannan ya furta. "Ubangiji aka yi wa laifi, ni dai tsakanina da mutanen gidan idan na ce an yi mini wani abu na ɗauki haƙƙinsu. Amma ni kam ba zan zauna ina ji ina gani a dinga saɓon Allah ba, gara na mutu salin-alin da a tashi idanuwa su bada shaidar baɗala ranar Lahira." Malam na Madina na gama magana ya fara jan akwatinsa ƙiiiii, da sauri Dada ta sha gabansa don tuni hankalinta ya tashi idonta ya fara ciko da ƙwalla. A duniya idan akwai abin ta tsana shi ne a ɓata ran Malam na Madina. Jafar ya kafe Malam da kallo yana jin kamar ya ƙarasa ya shaƙe shi ko ya rufe shi da duka. "A duniyar nan dai Yaya ka san mu biyu kaɗai muka rage, kuma kai ne uwata kai ne ubana kai nake gani na huce rashin su marigayi, (Iyayensu) don Allah ka faɗa mini abin da yake faruwa."Dada ta yi maganar tana share ƙwalla. "Waye wancan a tsaye?" Na Madina ya nuna Jafar a daidai lokacin Uwani ta leƙo don jin abin da yake faruwa daga ita sai gajeren wandon jikinta, ta tuɓe riga ta rufa hijabinta a saman ƙirjinta. Dada ta kai kallonta wurin ta ce, "Jafaru ne sai Uwani da ta fito." "Amma a rigar kwasam na san ba za ki manta Iron Alto ba?" A firgice Dada ta kalle shi, ba ita ba hatta Jafar ya san labarin Iron Alto a bakin Dada. Dada na shirin magana Malam na Madina ya katse ta. "To Ta'adar Iron Alto na ji waɗannan yaran suna aikatawa..." Tun bai rufe baki ba Dada ta saki butar hannunta wacce ta ɗauro alwala da ita jiki na rawa. Yau dai bari mu tsagaita dariyar na ga jiya har da masu shiɗewa 😂 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚