🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕 MALLAKAR ZAINAB DODO STORY AND WRITING BY ZAINAB DODO( FINANCIAL SECTARY OF THE ASSOCIATION OFFICIAL ) Free book 📖 09046495943 Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK ___________________ *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION 💫P.E.W.A💫 Home of perfect writer's together we stand 🤝 ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*pen 🖊️ is mightier than the sword 🗡️* _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 1️⃣ Wani matsakaicin gida ne gidan talaka bawan allah, d'akuna uku ne a jere waje daya,sai wani waje da aka zagaye da alama akwai mutum a 'bangaren,Wata kyakkyawar mata ce na hango tsakar gida hannunta rik'e da tsintsiya,ita ba fara ba ita ba bak'a ba irin dai tsaka_tsakar nan ce ga hanci ga idanu bakinta dai_dai ga diri gareta mazaunan ta mutum zai iya d'ora Kofi a kai ba tare da kofin ya Fad'i ba sanye take cikin wata atamfa,tana tsaye tana daddaga tasharar a hannunta irin mutum yayi shara ta d'an saki, wani mutum ne ya fito daga d'aki hannun sa rik'e da hula, fari ne soll ga hanci, yana sanye cikin wani yadi bak'i " Wai harka fito? " Matar ta fad'a,ya bata amsa da "Eh yau ina san naje kasuwa da wuri "Gashi ko naso muyi magana amman ba komai idan ka dawo sai muyi" Okay to yayi" Muje wajen mama" To" ta fad'a tare da ajiye tsintsiyar hannunta suka nufi wani 'bangare da aka zagaye na cikin gidan, a tare sukayi sallama suka ciga cikin d'akin, wata dattijiya ce zaune saman sallaya tana jan carbi, ganin su yasa ta saki murmushi, bayan sun zauna kowannen su ya gaidata ta amsa musu cikin sakin fuska " Auta har an fito?" Eh wallahi mama yau ina San naje kasuwa da wuri ne "To ubangiji Allah ya taimaka ya kawo kasuwa mai albarka" Amin ya rabbi " su duka suka amsa da amin, ya tashi suka fito hannunsu sark'e cikin na juna har bakin k'ofa ta rakasa tace" zuwa yaushe zaka dawo?" To sai munga yarda yanayin kasuwar ta kasance "Okay ka kulamin da kanka allah ya kaimin Kai lafiya ya dawo da kai lafiya ya kawo kasuwa"Amin amin matata "Bakinta ya d'ora a nata ya tsotsa, Sannan ya bud'e gida ya tafi.............dawowa tayi taci gaba da shararta bayan ta gama ta d'auki tsinke da mashaci tayi 'bangaren mama bakin ta d'auke da sallama "Washhhhhhhhhh" ta fad'a tare da d'ora kanta saman k'afafuwan mama "Sannu "Yawwa mama yau me kike son a dafa ne?" Khadija duk abinda kika dafa "Aah ki za'ba "Aah kiyi kawai"Gaskiya ni sai kin za'ba"ta fad'a tare da bubbuga k'afa irin na shagau'bar nan" To kiyi muna tuwo dan na kwana biyu banci shi ba" To shikenan mama allah nima yau d'in nan da San tuwon na tashi "To kinga shikenan sai kiyi muna shi"Ai kuwa bara na kunce kaina sai naje nayo cefa ne dan ba sauran kayan Had'i "Okay bayan zakiyi ?kawo na kunce miki"Gashi wllh kamar kinsan banasan kunce kitso shiyasama ban cika son yi ba " Ai dan dai kinada gashin ne yasa Baki cika yin kitson ba da bakyada suma dole kije kiyi " Ko mamarmu haka take cewa wai "Ai haka ne ma" ta ciren d'ankwallin sai ga gashin ta ya zuba har a gadon baya manya kitsone ma a kanta kuma ba wani dadewa yayiba, mama ta kar'bi tsinken ta fara kunce mata, ta kunce mata gaba ki d'aya ta shace mata ta kame mata shi........ Bayan sun gama taje tayi Shirin zuwa kasuwa , tazo ta bama mama mukullin d'aya d'akin wanda firij d'in ta suke ciki, dan mace ce mai san Sana'a duk unguwar ita kad'ai keda firij ai kuwa koda yaushe cikin ciniki take, tana siyarda ruwa, zobo, kunun aya,k'ank'arar zak'i........................kuma mace ce da bata dogar ga miji sai ya bata zatayi Abu ba cikin kud'in ta take fitarwa ta siya har cefanen gida ita keyi wani lokaci, ba ruwanta idan ya bata ta amsa tayi godiya idan bai bataba ba ruwanta haka take gareta, yana d'aya daga cikin abinda yasa sadik ke k'ara k'aunar ta,sannan tana bama Mahaifiyarsa girman ta su zauna suyi wasa da dariya wani lokacin idan kaga suna wani abu zaka rantse kace tobassai ne akan shak'uwarsu, yayun mijinta har fad'a suke da mama aka ganin irin sagartar da take mata, sai dai abu d'aya wanda yake damun mama da sadik shine rashin haihuwarta har yanzu kusan shekarar su uku da watanni da aure amman ko 'bari bata ta'bayi ba, ga matar da akayi auren su tare mak'otansu har ta haifi yara biyu amman ita haryanzu Shuru ka ke ji....... Bayan ta kaimata mukullin ta fito ta samun abun hawa tayi kasuwa, cefanen ta tayi mai rai da lafiya, har ta gama cefanenta ta joyo kenan sukayi kaura da wata mata "Subhanallah yi hak'uri dan allah ban ganki ba" matar tayi mata kallan sama da k'asa tare da cewa" Bangane nayi hak'uri ba saboda wawanci kana tafiya bazaka Kalli hanyarka ba "Yi hak'uri dan allah"Khadija ta sake fad'a"Mtsssssssssssssssssss to idan nace bazan hak'ura d'inba fa" yi hak'uri dai" ta sake fad'a duk da ranta ya 'baci na ganin sai faman bata hak'uri take tana gaya mata maganar banza duk da ma ba laifin ta bane dan ita ta jiyo ne ita kuma matar tana tafiya tana dannar waya, " To bazan hak'uraba" Matar ta fad'a irin cikin izzar nan tare da rik'e k'ugu "Bazaki hak'ura ba? "Eh bazan hak'ura ba" khadija ta aje cefanen hannun ta tare da cire nik'ab d'inta ta jefa cikin ledar ta shak'o wuyan matar ta yarfa mata mari tare da fad'in "Dan kutumar ubanki idan kika hak'ura allah bai godeba bura ubar banza kawai dan ma kin samu ana baki hak'uri shi ne harda k'ara botsarewa to ubanki yaci ubansa idan kin hak'ura" nan take idanun matar nan suka kawo ruwa ga Marin da Tasha ga matsarda take sha, ko kafin kace me tuni mutane anzagayensu ana 'ban'barar hannun khadija amman ankasa,wani mutume da yake gefe yana kallansu mussaman ma khadija yana kallan mazaunanta yarda suke rawa akan jijjigar hannunta da akeyi, ya tako a hankali ya tsaya bayan khadija ya zuro hannuwansa ta gaba a yarda ya tsaya yanajin yarda tudun mazaunanta suke sai ki ci niyar rik'o hannuwanta yake wai shi yazo raba fad'a, khadija jin namiji a bayan ta yasa ta saki matar tare da saurin juyowa ta d'auke sa da mari tare da fad'in " Da aure na da yagiyata uku akai dan kana d'ebabben albarka zako kana ta'bani wallahi yanzun nan sai na kullah ma sherin da ba ubanda ya isa ya fitar da Kai dan iskan banza da wofi asararre"ta sake juyowa ta Kalli matar wacce banda Maida numfashi ba abinda take tace" Dan Allah gobe ki k'ara banza y'ar tasha " ta duk'a ta d'auki kayanta tayi gaba abun ta..................... Idan naga anyi comment mai yawa zan rik'ayin typing mai tsawo Bayan ta dawo,ta fara aikin ta,tana aiki ana ta zuwa siyen kaya, duk wanda yazo sai dai tace yaje ya d'auka robar kud'i na ciki ka kad'a kud'i ka d'auka, wasu su kad'a wasu kuma su k'i kad'awa kuma su d'auki kaya............ Cikin k'ank'anin lokaci ta kammala girkin ta sai k'amshin miyar keyi, ta d'auki na mama taje ta kai mata ta dawo ta kai sauran abincin d'aki, ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga,mai kyau,bayan ta gama bada jimawa ba,sai ga sadik ya dawo cin abincin rana, ta tarbesa irin yarda ya dace ta kai masa ruwan wanka a bayi yaje yayi wanka ya fito ta d'auko masa wasu kayan, ta kawo masa abinci, lomar farko sai da ya runtse ido tare da kyad'a kai "Allah dai ya miki albarka ya k'ara miki zak'in hannu kiyita yimin irin wad'an nan girkin mai dad'i" Amin Amin mijina" Yawwa wace maganar ce kika ce kina son muyi?" Daman akan maganar gadon nanne da aka raba aka bani nawa shi ne nayi wani d'an nazari akan mezai hana na arama kud'in ka k'ara cikin Sana'a ka ka juya,tunda ni kaga ina da sana'a bare nace jari zan ja "To matar sadik amman kina ganin ba matsala " Ba matsala" kinyi shawara da inna ne" Aah ai Wannan kud'i na ne ni keda ikon yin duk abinda nake so da su bare kuma nasan inna zata goyi bayana akan wannan abun "To shikenan allah yasa musu albarka"Amin" ta fad'a tare da Mik'ewa taje ta bud'e wardrobe d'in ta ta d'auko wata leda bak'a, tazo ta zauna ta kunce ledar ta fara fito da kud'in " Ga sunan dubu d'ari uku ne"To matar sadik allah ya miki albarka yasa ki gama da duniyar nan lafiya ya k'aro muna zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman takewarmu" Amin ya hayyu ya qayyum " sai da yaci abincinsa ya k'oshi Sannan ya tashi ya wanke hannun yayi shirin komawa kasuwa ya d'auki kud'in yasa aljihu,' bangaren mama ya nufa shi kad'ai ba tare da khadija ba ya barta zata gyara wajen da yaci abinci Da sallama ya shigo wajenta ya gaidata bayan sun gaisa yace" Mama na samu sadakin in Sha Allah da na fita yanzu zan biya na kai musu" Kai ma sha Allah ya sanya albarka, ina k'ara fad'a maka kar ka kuskura ka bari tasan da aure zakayi kadai ji na fad'a maka" Haba mama ai bazan bari ba " To da yafi kam" Ni zan je" To a dawo lafiya "Allah sa" Amin" ya fito ya wuce, Bayan ya wuce khadija ta Had'o kayan da suka cire ta wanke bayan ya fito da gidan ya kira abokinsa usman ya sanar masa ya samu kud'in sadaki yazo ya rakasa suje sukai, usman ya tambesa inda ya samu kud'in bai 'boye ba ya sanar masa inda ya samu kud'in, usman yace" Kana ganin babu matsala kuwa" ba matsalar komai " To shikenan ganinan zuwa Bada jimawa ba usman yazo suka je suka kai kud'in, sadik wani farin ciki yakeji kamar wanda akama bushara da aljanna AFTER TWO DAYS Akasa ranar aure nan da sati d'aya,saboda daman an dad'e da had'a komai sadakin kawai ake jira,ganin ya kawo sadaki suka ce kar a 'bata lokaci ayi a gama, ranar asabar bayan sallahr azahar sadik ya shigo tare da mai gyaran sili, khadija na d'aki,suka wuce suka shiga d'aya d'akin dake manne da nata d'akin ana gyara wajen da ya hude, khadija na d'aki jin motsi yayi yawa yasa ta fito tashiga d'aki,ganin tayi ana gyaran sili ta rik'e k'ugu tare da karkad'a kafa, wata uwar tsawa ta dakama mai gyaran sai da ya tashi Fad'owa saman katakon da yake, hanya ta nuna masa tare da fad'in "Fitar kabar gidan nan tun kafin nakai ga lahanta ka " Mai gyanan jikinsa na rawa ya sauk'o ganin fuskarta ba alamun wasa a tare da ita Sannan da ka ganta kaga zubin majiya k'arfi shiyasa Bai tsaya 'bata lokaci ba ya sauk'o tare da kaushe kayansa ya fito Dubanta ta mayar ga sadik tace" Me nake gani ?"cikin inna inna ya fara fad'in " Daman naga silin ya lalace ne nace yazo ya gyara sa " Kai Kai sadik ba k'aramar yarinya nake ba sili tun yaushe yake haka baka tashi gyaran sa ba sai yanzu to wallahi idan ma wata niyya ce dakai ka cireta daga ranka " ke khadija wai ke ke aure na ne ko ni ke auren ki " Kai ka sani sai ka bama kan ka amsa hmmmmmm" tana gama fad'in haka tayi d'akin ta, harta kwanta ta Mik'e ta fito ta d'auko ta'barya da kujera mai d'an tsawo ta shiga d'akin da sadik ya kawo mai gyara, hawan kujerar tayi tasa ta'barya tana k'ara hude silin sai da duk ta lalata sa sannan taji zuciyarta ta mata sanyi ta........................... 🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕 MALLAKAR ZAINAB DODO STORY AND WRITING BY ZAINAB DODO( FINANCIAL SECTARY OF THE ASSOCIATION OFFICIAL ) Wannan shafin naki ne aunty khadee (Oum sharifat ) Allah ya baki lafiya idan kuma..................ne to allah ya raba lafiya muzo mu caskare waii ai da ranar idan muka fara kausan shoki sai an rik'emu🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 masoyiya koya kika ce?😂 Yan amana Oum sharifat Maryam Naseer Ibrahim ( Jagabar royal star) love you 🫶💔♥️❣️♥️♥️ Free book 📖 09046495943 Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK ___________________ *PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION 💫P.E.W.A💫 Home of perfect writer's together we stand 🤝 ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*pen 🖊️ is mightier than the sword 🗡️* _________________ ________ ________ BISMILLAHI Rahmanirahim ________ Page 3️⃣ Dare yayi ta kama ledar d'akin ta daidai wajen da tasan sadik zai kwanta ta nad'e ledar tabar wajen hok'on siminti, ta k'ara gyara gadonta ta haye, daman tuddin sukayi fad'a to bata bari ya hau mata ledar d'aki bare kuma gado, har ya Saba da haka, shigowa yayi ya d'auki babbar rigarsa ya shimfid'a a k'asa wajen da ta nad'iye ledar, yayi kwanciyarsa Washe gari Ta gama had'a karin kumallo ta kawo masa, amman ba mai cema d'an uwansa ko uffan, yaci abincinsa ya tashi yaje ya gaida Mahaifiyar sa ya wuce, bayan ya fita tayi 'bangaren mama har sun fara fira aka fara zuwa siyan kaya dole ta koma gefensu Sadik shirye_shiryen auren sa kawai yakeyi, amman tun ranar da ta Kori mai gyaran sili bai sake kiranyo kowa ba,gashi lokacin aure na matsowa bai gyara d'akin ba Ana sauran kwana hud'u aure abokinsa usman yazo gidan bayan sun gaisa yace"Khadija wani babban al'amari na Shirin faruwa ba tare da sanin ki ba wanda niko naga idan har aka miki hakan ba'a miki adalci ba shiyasa nazo na fad'a miki" To baban abba wane irin abu ne ke Shirin faruwa da har aka 'boyemin?" Sadik zai k'ara aure in tak'aice miki yau sauran kwana hud'u a d'aura aure amman fa kar kiga laifin sadik Mahaifiyarsa tace kada a sanar dake " Hhhhhhhhhhhhh "khadija tayi wata irin dariyar takaici Wanda ba kowa zai gane ba " Ya naga ina fad'a miki mijin ki zai k'ara aure amman naga kina dariya" Hhhhhhhhhh to baban abba idan banyi dariya ba kuka kake so nayi " Aah" To ka gani badai aure ba allah ya kawota lafiya ya basu hak'uri da juna " Amin ya allah daman haka akeso " ya mata sallama ya wuce, d'aki ta koma ta zauna tare da fashewa da kuka,sai da tayi kukanta mai isarta sannan ta tashi Da rana da yazo cin abinci bata nuna masa komai ba,har suka d'an sha love d'in su ta tambesa tana san taje gida anjima, ya bata izini Bayan ya koma kasuwa ta yi duk aikin da gareta ta shirya tayi gida, ta samu Mahaifiyar ta a d'aki da kuka " Subhanallah khadija lafiya ?meya faru?" Cikin sheshshek'ar kuka take bata amsa da " Inna wai yanzu sadik aure zai k'ara" To dan zai k'ara aure shi ne kike kuka " Inna ni bama auren sa ne yafi 'batamin rai ba kamar irin na k'in sanar dani da basu yi ba wai ma abun takaici Mahaifiyar sa ce tace kar a sanar da ni " Khadija kiyi hak'uri ki barma allah kayanki kada ki wani damu kanki" Haba inna yanzu ace ko kayan fad'ar kishiya bazaimin ba" Kai khadija ana baki kina rok'o tashi ki shirya muje wajen yan koli ki za'bi duk abinda kike so ni zan siya miki" To inna" ta fad'a tare da goge hawayen ta" Yawwa har kinsa na manta daman amina nake jira ya dawo tallah ta je ta sanar miki idan mijin ki zai barki kije " Ina kenan?" Wajen bikin sahura" Wai har bikin ya kawo" Eh gobe za'a fara kinga idan har zai barki kiyi tafiyarki, kije cikin Yan uwa zakima manta da wani zancen auren da zaiyi" To inna in Sha Allah zanje "Allah sa" Amin Zuwa sukayi ta za'bo atamfa manya guda biyu da lace da material guda_guda sai takalmi da sarka, sannan suka dawo tayi gida, bayan taje gida taga dare baiyi ba ta d'auko kud'i ta sake zuwa kanti tasiyoma kanta kala biyar na atamfa da yadi,ta dawo ana gama sallah magrib ta je ta kaima mai d'inkin ta kayan kala tara, sukayi jinga ta biyata Da ta tambayi sadik maganar tafiya bai hanata ba dan har wani murna_murna taga yana yi, ta dai sharesa, tun da safe ta siyo kolin cingum sukutum dan khadija akwaita da jama'a ita kowa nata ne,ta riga rabama mutane tana cewa kishiya za'a kawo mata sai sunzo dannar k'irji Zuwa marece suka tafi wajen bikin sahura ba'a garin ba ne. Sadik jira ce yake da ta tafi dan har cemata yayi tayi zamanta ta kwana a can,taji dad'in hakan duk da tasan ba banza ba, tana wucewa ya kirawo mai gyara aka gyara d'akin akayi fenti har bakin k'ofar ta akayima fenti, khadija ana can ana shan biki tama manta da wani auren mijinta............................... Ango sadik zumud'i kawai ake ana ta shirye_shirye, sabon d'inkin da yayi ya kai d'akin mama ya ajiye kayansa a can, khadija ana gobe d'aurin aure ta dawo, bata iso gida ba sai da taje ta kar'bo d'inkunan ta sannan tazo gida, tana zuwa taga anyi fenti d'aya d'akin Kuma a rufe da alama har anzo anyi jere,taga harda k'ofar ta aka sakema fenti ta yatsina fuska tare da fad'in "Aikin banza wa kare wanka dan nace anmin gaunan ta da ka sanima kabarmin kayana a haka" ta fad'a tare da jan tsaki tayi d'akin ta, wata akwauti ta d'auko ta bud'e tufafi ne a ciki kala hud'u sababbi wad'an da sadik ya ta'ba d'inka mata bata saka ba ga wad'an da inna tayi mata kala hud'u ga wad'an da tayi kala biyar ga kuma k'ananun kayan da ta siyo garin da taje tare da turaruka masu k'amshin dad'i..............................sai da ta gyara kayanta sannan ta fito taje 'bangaren mama suka gaisa ta bata kayan biki ta dawo k'ofar ta,yanzu harda firar da suke zama suyi ta rage zama Washe garin d'aurin aure Tun da safe sadik keta zarya a filin gidan ya rasa ta yarda zai tunkarar khadija da maganar auren nan,wata zuciya na fad'in yaje wata kuma na fad'in kar yaje haka dai ya d'aure ya shiga d'akin ya tarda ta zaune gyaran murya yayi tare da fad'in "Khadija ina san muyi magana" wani kallo tayi masa tare da fad'in ina jinka" Ina san na fad'a miki yau d'in nan za'a d'aura min aure" D'agowa tayi tare da kallan sa ta saki wani murmushin takaici tace"Ina tayaka murna mijina allah ya baka ikon yin adalci a tsakanin mu allah ya kauda sharrin shaid'an Sadik wani irin kallan mamaki yake mata tare da nazarin maganganunta,ya numfasa tare da fad'in "Nagode mama ta allah ya miki albarka" Amin, ka tashi kaje ka shirya kar lokaci yak'ure a tsaya jiran ango " Haka ne fa bara na d'auko kayana wajen mama"Okay, ya tashi ya nufi wajen mama "Hmmmmmmmmm wato ma kayan baza'a ajiyesu a nan ba kaji rashin gaskiya" Zuwa yayi ya d'auko kayansa ya shirya cikin wata shadda fara babba rigar tasha kaud'o na mutumci hularsa da takalmi kusan kala d'aya ya fito khadija ta tsare sa da ido ganin irin kyawon da ya mata" Tabarakallah ma sha Allah mijina wai kama kalli madubi kuwa? Kaga irin kyaun da kayi? Ma sha Allah allah nagode ma " allah ko mamata" Allah kayi kyau sosai" Nagode " yawwa nace ka d'an bani wani abu wanda zan yima mutanena girki " Wallahi ko sisi banada kiyi hak'uri" Hmmmmm to shikenan l" Aha sai na dawo" Allah ya taimaka " Amin Bayan ya fita ta kira inna a waya tana kuka ta fad'a mata harda kud'in abincin da zata dafama mutanen ta yak'i bata yace bayada, inna tayi murmushi irin nasu na manya tare da fad'in" wallahi k'arya ce zance yace bayada kud'i duk Bai taso ba kawai dai yace bazai baki ba, amman karki damu zansa a dafa muku abinci anan amina sai takawo muku" To inna nagode" Karfa ki sama damuwa a zuciyarki taje ta miki illah "ba ruwana inna"Yawwa haka nake San ji sai tazo " To" Koda akace k'arfe goma gayyatar khadija an fara zuwa, taja wanka ko amarya albarka duk inda ta wulga k'amshi ne ke tashi, mutane zuwa kawai suke zuwa shabiyu aka kawo abinci manya_manyan kuloli guda uku da bokitayyen da aka zuba zo'bo, kulolin d'aya dambu d'aya jallop d'in shinkafa d'aya jallop d'in taliya da makroni Khadija tasa aka kiranyo masu kid'i ansha rawa sosai kamar ba gobe, khadija tayi mutane sosai dan ko ango baya nuna mata jama'a, anci ansha an watse k'awayenta biyu suka rage sunce sai an kawo Amarya zasu wuce, kafin a kawo amarya ta sake wani wanka ta had'e cikin material d'in ta mai shegen kyau tayi kyau sosai, k'arfe goma da yan minutes aka kawo amarya, abokan ango sukayi_sukayi akan amarya ta taso suje d'akin uwar gida su gaisa amman tak'i, ganin haka yasa akace d'aya daga cikin abokan ango suje su bama khadija hak'uri tunda tak'i zuwa Usman yaje ya sameta tare da fad'in "Uwar gida ran gida dan allah kiyi hak'uri da y'ar k'anwar nan taki tace bazata zo ba amman nasan ai dole zaku had'u" Haka ta fad'a? Khadija ta tambaya " Eh" Okay muje d'akin nata ai duk'ama wada baya hana ka taso da tsawon ka................................ Suka nufi d'akin fuskarta d'auke da murmushi, k'awayen amarya da abokan ango sune a d'akin tashi bakin ta d'auke da sallama, "Amarya mai butum hankali in tayi wata tazam wagila" Khadija ta fad'a duka d'akin aka d'au dariya, sadik da tunda ta shigo ya kafe ta da ido ganin irin kyawon da tayi ko shakka babu tafi amarya had'ewa Muga fuskar amarya, ta fad'a tare da d'aga mayafin amarya ta lok'o fuskarta " Aah wai ke ce ?" Ta fad'a dan tasan yarinyar y'ar unguwarsu ce " Kai ma sha Allah gaskiya mijina kayi dace to allah ya kawo yan biyu kwanan fari" duka d'akin aka d'auki shewa sunata dariya, k'awayen amarya suna mata murna ganin ta samu abokiyar zaman da ba ruwan ta gata da sa mutane nishad'i Khadija ta mayarda dubanta ga sadik tare da fad'in " To mai gayya idan ka kama ina neman ka daki" Jin ta fad'i haka sai da gabansa ya Fad'i ya dai d'aure tare da fad'in "To " ta fito tayi d'akin ta K'awayen amarya suka wuce abokan ango kawai suka rage suma harsun kama hanya su fita sadik ya dakatar dasu tare da fad'in " Ni wallahi lamarin khadija ya fara bani tsoro ku duba fa kugani wacce na sani da kishin tsiya amman ace tunda aka yi auren nan ba'a abinda tayi wanda za'a ce na kishi ne anya kuwa ku Kuna ganin ba matsala" Wallahi nima al'amarin nan na bani mamaki " ballo ya fad'a" To ba tace tana neman ka ba ko kaje ne? Usman ya tambaya" Aah banje ba ku jirani naje na dawo" To yayi Ya kama hanya yayi d'akin ta, kwance ya sameta tayi ashe_ashe saman gado,ganin sa yasa ta tashi zaune tana kallansa tare da fad'in" Sannu adali uban adallai" Khadija menayi ? Ya fad'a cikin k'asa_k'asa da murya " Au har tambaya kake mekayi" Dan Allah kiyi hak'uri "Hak'uri ai dama sai an gama cutar da kai za'a baka hak'uri, Mik'ewa tayi tsaye yayi saurin ja da baya kad'an tasa hannu ta cukunkume wuyan rigar sa tare da fad'in" Macuci mayaudari wai sadik harni zaka cuta na baka kud'i ka k'ara a jarinka sai ka rasa dame zaka sakamin sai da kishiya saboda kana macuci harda yakan da ake bama mata idan za'a k'ara aure baka bani ba na hak'ura na gyaleka kud'i ka bani nayima mutane na abinci ka hanani kace baka da amman ai kasa an dafa maka abincin yan d'aurin aure macuci kawai" ta fad'a tare da k'ara shak'ar wuyan rigar" Dan Allah kiyi hak'uri nasan ban kyauta ba ki yafemin "Wani irin k'arfi taji yazo mata sai da ta dai_dai ta rigar biyu taja ta har k'asa ta rabata biyu ( allah sarki sadik sabon d'inkin sa an masa fatafata da shi) Sakin sa tayi tajuya tana dube_dube can ta hango wuk'a, taje ta d'auko ganin ta nufosa fuskarta babu alamar wasa a ciki yasa yayi saurin rik'e hannuwan ta duka, can suka fara ko kuwa ta samu ta yanka masa ita a hannu allah ya taimakesa kad'an ne, ganin wallahi da gaske take yasa ya fara kiran suna abokan sa dake waje, Jin yana kiran sunayen su yasa suka shigo d'akin da gudu " Subhanallah! subhanallah meyake shirin faruwa ne subhanallah khadija" Usman ke wannan maganar, dak'yar suka samu suka kar'be wuk'ar " Kuma wallahi ka sani mata ni ka auroma ita dan wallahi baza ka kwana a d'akin ta ba idan kuma kana ganin wasa nake kaje ka kwana kadai san unguwar nan akwai yan black market da yawa wallahi zan fita naje ta samo fetur na k'ona ku sai dai naje gidan yari wallahi mata ni ka auro ma ita baka da ikon cin ta nizan cita dan da kud'i na ka auro ta " Haba khadija dan allah kiyi hak'uri zance bazai cita ba duk bata taso ba amarya ce fa wannan daren shine dare mai daraja a garesu" To ina ruwa na kaji na rantse billahillazi'lah'ilah'ha illahuwa bazai cita ba idan kuma yana ganin wasa nake yaje wallahi sai na bari ya tube ya fara zan shiga na shar'be🍌sa " sadik kamar maraya haka ya koma a wajen "Wallahi sadik duk laifinka ne meyasa zakayi aure da kud'in ta" Ahh to idan yana san matar sa ya bani kud'i na yanzu yanzun nan" akwai kud'in ne? Usman ya fad'a tare da kallan sadik " Girgiza masa kai yayi alamar babu............................. " Khadija dan allah kiyi hak'uri kinga yanzu dare yayi " To ina ruwana da dare yayi ni kud'i na na jama ya bani kud'ina yanzu salin alim na kyalesa " Kud'inan basu yanzu amman da safe duk yarda za'a yi koda rabi ne za'a samosu a baki"Rab! rabi fa kace to wallahi gabaki d'aya nakesan kud'ina ni da zan basa rabi na Basa? " Hak'uri zakiyi " Dallah kun isheni da wannan kalmar hak'uri! hak'uri to bazan hak'ura ba aheeeeeeeeee " Allah ka muna maganin wannan masifar" Au nice ma masifar? Ta fad'a tare da nuna k'irjinta, to wallahi wannan soma ta'bine idan har baka bani kud'i na ba" Amarya jin hayaniya tayi yawa yasa ta fito tare da tunkarar d'akin tun kafin ta isa bakin k'ofa d'aya daga cikin abokan sadik yayi aurin fitowa tare da fad'in" Wallahi juya ki koma d'akin da mijin ki bayada gaskiya tun abun bai shafeki ba" amarya jin haka yasa tayi saurin juyawa tayi d'akin ta Su Usman sai hak'uri suke ta bata, dak'yar suka samu tace yaje d'akin, Usman yace" To kin amince ya kwanta da ita" Hmmmmmm wallahi bazai kwana da ita ba dan bazai cita ba " Khadija ki yi hak'uri su raya daren nan" Usman wai kafira ka d'auke ni ne nayi rantsuwa bazai yi ba Hmmmmm" Bello yayi 'bangaren mama dan ya sanar da ita halin da ake ciki, duk da kusan duk abinda ke faruwa tanaji tak'i zuwane dan tasan idan taje abun zaiyi muni da yawa dan basa da gaskiya, bello na zuwa tun kafin ya kai ga magana ta tare shi da fad'in " Yi hak'uri kawai ka juya Dan bansan abinda zan fad'a ba" Mama da dai kinzo muje nasan zataji Maganar ki " Tabbas haka ne amman idan naje ban mata adalci ba amman ga waya ka duba number sadiya nasan idan tazo in Sha Allah komai zaiyi sauk'i" To mama, wayar ya amsa ya lalubo number kira biyu ta d'aga ya sanar mata abinda ke faruwa tace gata nan tafe, Sadiya yayar sadik ce, khadija na ganin girmanta sosai, Cikin k'ank'anin lokaci aunty sadiya tazo, zaunar da ita tayi tare da bata hak'uri da kalamai masu taushi tana kwantar mata da zuciya, Sannan ta hak'ura, Usman yaje gidan sa ya auno abinci aka fitarma da khadija kolo na rantsuwar da tayi, koda suka wuce ukun dare harta gota, ko wannen su ya bama matarsa labarin abinda ya faru, matan matsuwa sukayi safiya bata waye ba suzo gidan Hadari ne ya taso khadija ta bud'e d'akin ta tayi shimfid'a dai_dai bakin k'ofa tayi kwanciyarta iska na kad'a mata, Sadik zaune yake gefen gado yayi tagumi, amarya baccin ta kawai take cikin kwanciyar hankali, zuciyar sadik cike take taf da tsoro dan har yanzu bai lamun ce da hak'urin da khadija tayi ba, Washe gari Tun da safe yayi wankan sa ya baro gidan, khadija tayi wankan ta ta had'e cikin wata atamfa da ita da d'akin ta sai k'amshin suke zubawa, mutane ta antaru mai kid'i aka sake kira musu suka sa dije, rawa kawai suke tik'a............................. Sun tik'i rawarsu bil'hak'k'i, anci an sha,an watse, da dare sadik bayan ya dawo yaje ya gaida Mahaifiyar sa ya dawo yayi d'akin khadija, fuskarsa d'auke da murmushi ya shiga d'akin, wani k'amshin dad'i ne ya kaima hancin sa ziyara sai da ya lumshe ido, zaune ya ganta saman sallaya da alama sallah ta ida " Ahah uwar gida sarautar mata sai kinyi goma yaro zaiyi d'aya uwar gida ran gida, uwar gidana addu'a akeyi to a rok'a harda mu "ya fad'a tare da samun waje ya zauna, ya tsina baki tayi taci gaba da addu'ar ta sai da ta gama, ta juyo ta gaidasa, ya amsa, hannu yasa aljihu ya ciro kud'i ya sake sa hannu d'aya aljihu ya ciro, ya Mik'a mata, tasa hannu ta kar'ba tare da fad'in " Nawa ne anan?" Dubu d'ari da hamshin ne" su na baka? " Haba khadee ta kiyi hak'uri in Sha Allah zan cika miki saura wallahi wad'an nan ma dak'yar na samesu" ya fad'a cikin mairairaice murya hmmmmm kunsan tsakanin mata da miji sai allah, tausayin sa taji ya kamata, ta tashi taje ta d'auko masa farfesun kayan ciki da inna ta aiko mata, yana ci yana zuba mata albarka, bayan ya gama ta kawo masa waje ya wanke hannun sa yasha ruwa ya Mik'e dan dare yayi, ya nufi d'akin amaryarsa balkisu Yana fita taji hawaye na mata ambaliya a fuska da ta goge sai taji wasu na k'ara zubowa, ga wani k'ololon bak'in ciki da take Jin yana taso ma, wai yau sadik d'in ta ne zaije d'akin wata mata, fashewa tayi da kuka mai ban tausayi, sai da tayi mai isanta Sannan ta tashi ta haye gado tayi kwanciyarta tare da karanta addu'ar bacci Bayan sati d'aya da aure Khadija zaune bakin k'ofar d'akin ta tana d'aura zobo a leda sadik na zaune daga gefe, balkisu ta fito daga wanka d'aure da wani guntun zane, tunda ta fito ta ajiye bokiti tayi tsaye sai ta d'aura zane ta kunce, tana wani tallabe_tallaben nono, khadija ta lura da abinda takeyi ta juya ta kalli sadik taga wandama takeyi dan shi baiko san tana yi ba, wata shewa khadija tayi tare da fad'in "Hhhhhhhhh allah kashe mijin mai kyawo ko bai kashe ba aure ya mutu yo wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwar sa " Ta fad'a taci gaba da k'ullinta, balkisu ta gyad'a kai tayi d'akin ta, sai gata ta fito sanye da hijab tazo tayi tsayen kan khadija ta rik'e k'ugu tare da kad'a kafa "Khadija! Khadija!" Balkisu ta fad'a khadija ta d'ago tana kallan ta, Shima sadik ya d'ago, taci gaba da cewa " Idan kin isa ki sake maimaita abunda kika fad'a d'azu" Okay so kike na maimaita kenan? Khadija ta fad'a tare da Mik'e wa tsaye" Eh " tun kan balkisu takai ga rufe bakin ta khadija ta d'auketa da wasu irin zafafan maruka guda biyu Wanda yasa ta ganin walk'iya tayi saurin ja baya ta dafe kunceta, hawaye rata_rata , sadik yayi saurin tasowa tare da fad'in " Subhanallah meyake faruwa ne wai? Khadija akan me zaki mareta ? " Au bakaji abinda take fad'amin bane saboda tsabagen ta raina ni, wallahi bama laifin ta bane kai ka bata fuskarda zata rainani acikin gidan nan to wallahi kisani, ta fad'a tare da maida dubanta ga balkisu wacce hawaye ke mata ambaliya a fuska dan haryanzu rad'ad'in marin takeji , dai_dai nake dake dan zan saitamiki hanyarki naga tunda kika zo gidan nan kike min wata hikirkitar iskanci to wallahi mai gyaran miki zama ce anan mtsssssssssssssssssssssss" ta fad'a tare da zama taci gaba da aikin ta, juyawa tayi lufff ta shige d'akin ta, sadik har ya kama hanya ya bita yaga wani kallo da khadija ke masa, hkn yasa ya juyo ya koma ya zauna " Hmmmmmm ayi dai mu gani in tusa na hura wuta" khadija ta fad'a Tun da sadik yayi auren nan duk wata hanyar da yake samu ta tushe ko kasuwa yaje haka zaita zama babu kasuwa, ita kuma khadija kamar kar yayi auren nan bud'i ya rik'a zuwa mata kyautukka taketa samu har inda batayi zato ba, yau ma tashin ta daga bacci kenan wani abokin baban su ya aiko mata da buhun d'angote guda biyu da katin d'in taliya biyu da dubu hamshin akai Kalarta biyu na tufafin da ta cire da d'auko zata wanke, balkisu ta taso tare da fad'in " Aunty khadija wanki zakiyi? " Eh" Zauna ki huta kawai kawo na wanke miki" Aah barshi kawai nagode " Nifa nace ki kawo na wanke miki ai ba rok'ana kikayi ba" Ganin ta nace akan sai ta wanke mata yasa ta bar mata................................ *Addu'ar Wanda Al'amari Ya Tsananta A Gare Shi* اَللَّهُمَّ لاَ سَهْلَ إِلاَّ مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً. Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan. Ya Allah! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki Idan ta wanka ita kuma khadija ta d'auraye ta shanya har suka gama, bayan sun gama khadija ta nemi waje ta zauna dan ba aikin da zatayi balkisu a da girki, Kusa da ita ta tazo ta zauna tare da fad'in " Aunty khadija yau me za'a dafa ne" To, khadija ta fad'a tare da mata kallan mamaki " Ki tambayi mijin ki mana" Haba aunty ai babban yatsa ko bayacin tuwo yana kyauwo a miya ai idan baya nan kece matsayin sa a gidan nan. gashi wallahi koda ya fita yace bayada ko sisi bare ya bada kud'in cefane "To ki jira ya dawo"Wallahi aunty ba girman ki bane ace muna da kamar ke a gidan nan amman ace wai sai mun tsaya jiran har ya dawo aunty ki dai duba "Hmmmmmmmmmm naji je ki samo waje ki auno shinkafa" Yawwa aunty ko kefa Allah dai ya biya" ta fad'a tare da Mik'ewa taje ta d'auko wajen da zata zuba tashi d'akin khadija ta auno shinkafar, ta fito "To aunty khadija gashi nan me za'a yi allah ya gani na gaji da cin shinkafa kullum shinkafa " To kiyi muna dambu" Wallahi gashi na jima banci shi ba " To sai kiyi muna " Aikuwa, to kud'in markad'e da kayan Had'i" Ahhh wai kina nufin komai ni zan bayar " khadija ta fad'a" To aunty ni wallahi bani da ko sisi dole kece zakiyi hak'uri ki bayar allah ya baki lada " uhmmmm d'auko jaka na baki kud'in" To, ta d'auko jaka ta Mik'e mata naira dubu tace "gashi a siyo kayan miya da kayan ciki tun da akwai sauran kaya kayan miya ne kawai babu" kar'ba tayi ta fita taje mak'otansu ta samu wani yaro ta aike sa ta dawo takai redar shinkafar, nan tayin su Tun daga lokacin suka shirya, muddin khadija na aiki to balkisu sai tazo ta tayata itama hakan take, sai dai abu d'aya wanda khadija ta lura dashi shi ne, balkisu nada shegen kwaud'ayi, sannan idan taga anata zuwa siyan kaya wajen khadija sai taga tana wani ciccin magani, alamar hassada Sadik ne ya shigo gidan, d'akin khadija ya shiga yaga bata nan, d'akin balkisu ya shiga, yatsina fuska ya rik'a yi tare da bin d'akin da kallo, wai d'aki kamar ba mutum a ciki ya fara k'ura ga wani hanamin bashi_bashin da yake tasowa, ga kaunukan da akaci abinci nan zube tsakar d'aki har sun bushe, balkisu na kwance tana sharar baccin ta, girgiza kai yayi tare da jan tsaki mtsww ya fito daga d'akin, yana fitowa sai ga khadija, kallan ta yayi daga sama har k'asa sanye take da hijab har k'asa Daga ina kike na duba ban ganki ba? " Daga wajen mama"okay, muje ki zubamin abinci " ka manta ba fa girkina bane " ina sane nidai muje " Bata nan ne? " Wani kallo yayi mata bata sake cewa komai ba ta wuce ya biyo bayanta, tana shiga d'aki ta kau'be hijab d'in ta, sanye take da riga da wando, Wandon ya matseta sosai sai rigar y'ar guntuwa idan ta d'aga hannun ta ana ganin cibiyarta, rigar kawai ce a jikin ta ko bre bata saka ba, wasu irin yawu sadik ya had'a, ya kasa jurewa sai da ya taso ya rungumota ta baya tare da zura hannayensa gaba ya d'ora akan na shanunta yana..................... juyowa tayi suna fuskantar juna, ta d'ora hannun ta a kafad'arsa tare da zagayowa, shi kuma hannayensa na kan k'ugunta, gira ta d'aga masa tare da fad'in " Yane nayi kyau" Sosai sosai kayan nan sun miki kyau" ya fad'a yana shin_shinan daddad'an k'amshin dake fitowa a wuyan ta, bakin su ya had'e waye d'aya ya shiga tsotsa ita ma ta biye masa sun d'au yan minutes a haka, ganin yanan san cire rigar da ke jikin ta yasa ta kaunce kanta daga gare shi tare da dai_dai ta natsuwar ta tace" Zauna na kawo ma abincin" wayyoooooooooo sadik ba haka yaso ba................................. *ZUWA GARE KU MATA ✍* Kishin da bazai qara miki.......................... martaba da kima a idon miji ba, kishin da bai sa kin samu qarin kusanci a wajen miji ba, kishin da ba zai sa ki qoqarin gyara da kyautata dabi'un ki ba, kishin da ba zai sa ki qara kusantar miji da mahaliccin ki ba, kishin da zai sa kimar ki ya zube, miji ya nisance ki ko ki nisanci miji da mahaliccin ki ko ki koma bibiyar 'yan tsubbu Tabbas wannan ba kishi bane rashin hankali, rashin sanin daraja da mutuncin kai da qarancin tsoron Allah da son zuciya ne, muddin kika biyema irin wannan kishin tabbas zai kai ya baro ki duniya da lahira ko kiyi asarar duniya da lahirar ki. *🤲YaAllah sa mu gane gaskiya ya bamu ikon binta* _-_Perfectly Pen's_-_~*✊ 2024 *~_-_Perfectly Pen's_-_~*🤟 *Team One.* *🌹 perfectly Pen's together with five Talented's ✍️✊* *Our Ongoing Book's...✍️* *1_PRINCE ASAD.* *Free Book. BY: Zieey Dodo.* *2_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.* *paid 500* *Season one Free. BY: Queen Kainaat.* *3_TSANTSAN SO.* *Paid,500. BY: Nainarh KD Nkd's.* *4_MU ZUBA MU GANI.* *Paid,300. BY: Oum Yasmeen.* *Mun Shirya tsaf domin kawo muku daɗaɗan littattafan mu masu cike da ilmantar wa faɗakarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaɗantar wa.💝* *🔥Kada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters 🔥 Abincin ta kawo masa yaci ya k'oshi, Sannan ya tashi ya koma kasuwa duk da ba ciniki, daya fito ko d'akin balkisu bai sake lek'awaba ya wuce, har yanzu ko tana nan tana sharar baccin ta, Koda ta tashi daga baccin taga lokacin zuwan sa cin abincin harya wuce ta Mik'e ta fito khadija ta zaune tana gyaran waken suya " Aunty sadik bai dawo cin abinci ba ne? " Ya dawo mana ai har yaci ya koma" Okay shine bai tashe ni ba" To kinsan ba dad'i mutum na bacci a tadasa" Uhmmmmmm" ta fad'a ta koma d'aki, bud'e kulolin abincin tayi taga ba abinda aka ta'ba a ciki, ta sake fitowa " Aunty " Naam " kin ce ya dawo yaci abinci? " Eh " To ai ni banga anci komai ba cikin abincin " Eh dayake ba anan yaci ba wajena yaci " Bangane ba" balkisu ta fad'a a tsatstsaye " Kamarya kenan? Khadija ta fad'a tare da ajiye waken da ke hannun ta " Ahh to naga dai bake ke aiki ba taya zai je wajenki yaci abinci ai wannan salon munafurci ne " Yau ga ikon allah shin yazo kina bacci kuma yunwa yakeji yace nazo na saka masa abinci shikenan sai nace masa aah ko tunda ba girkina ba ne sai nabar mijina da yunwa bayan Kuma ina da abincin to wallahi ki sani koda bani da shi yazo wajena yace na saka masa sai naje na nemo masa rainin wayon banza kawai " Ah ah naga kina wani zazzaburomin sai kace wani abun na fad'a bancin kuma gaskiya na fad'a ke idan girkin ki ne namiki hakan zakiji dad'i? " Me zai Hana wallahi dan kinyi haka bazan ga laifin ki ba daga ma kin taimaka min kin basa wallahi ni nace balkisu muddin yazo gidan nan ranar girkina ya tarar da ina bacci wallahi jashi d'akin ki ki basa abinci ke har ruwan wanka kai masa abu d'aya kawai nasan bazan lamunce ba ranar girki na yace ya kwanta dake, bare nasan bazai aikata hakan ba dan yasan haramun ne bancin wannan wallahi ni ba abinda zai damuna " To nidai ban lamunce ba ehhheeeeeeeeeeee kowa yayi aikin sa ranar girkin sa " Ke balkisu wai ma da kika zo kika tasani gaba ni nace kije kiyi bacci sannan ki bari shi wanda ya aika tan idan ya dawo sai ki tasasa a gaba kiyi masa fad'a kar ya sake yin haka " Ai ni bashi yamin laifi ba bare kice na masa fad'a" Ohh wato ni ce nayi laifin ko" khadija ta fad'a tare da Mik'e wa tsaye" Ke naga kina son gayamin magana to wallahi bazan d'auka ba dan mai maganin ki ce a wajen nan ina san muzauna lafiya gidan nan amman daga alamun ke bakyada buk'atar haka muje a hakan duk yada ki ka zo nima dai_dai nake da ke a gidan nan " Magana dai ceee na fad'a ba uban da ya isa ya hanani fad'an abinda nayi niyya" To tsaya daga nan dan bana jurar zagin iyayena idan ba haka ba wallahi yanzu na ma mutum hailar baki " Hmmmmm wai hailar baki" To idan tantama ki ke kiyi ki gani wallahi bakin ki sai ya cika da jini " Balkisu ta bud'e baki ta sake magana khadija ta fere hannun ta wanka mata mari sai da ta fad'i, ta taso tayi cikin khadija, khadija ta samu taja k'afafuwan ta sai k'asa, balkisu ta fad'i khadija ta haye Samanta ta shiga dukan ta, da taji azaba ta fara ihu na neman taimako, Mama da taji ihun balkisu yayi yawa yasa ta taso tayo wajen su, khadija ta gani ta kai balkisu k'asa ta haye sai dukan ta take da sauri ta k'arasa tare da fad'in " Subhanallah! Subhanallah khadija meyake faruwa ne? " Dak'yar mama ta samu ta raba su, balkisu ta koma gefe hawaye da majina sai ambaliya suke a fuskarta " Dan Allah gobe ki k'ara"khadija ta fad'a " Wai meya had'a ku ne ? Mama ta tambaya" Mama wai................................................. khadija ta zayyano mata duk abinda ya faru " Gaskiya balkisu bakya gaskiya ai dan ma abun bai miki dad'i ba ba ita ya dace ki yima magana ba shi zakiyi ma maga cikin hikima amman gashinan yanzu wa gari ya waya bakin ki harya fashe " Eh ina ruwan ki bak'ar muna fuka ai daman nasan goyon bayan ta zakiyi" khadija da mama suka Kalli juna mama ta girgiza kai, khadija tasa hannu zata janyo ta tayi saurin rugawa tayi d'aki tare da rufewa " Ai da kin tsaya k'aramar mara kunya kawai" khadija ta fad'a tare da juyowa tana bama mama hak'uri akan abinda balkisu ta fad'a " Karki damu, amman kema ya kamata ki rik'a hak'uri ki rik'a sassauta zuciyar ki " To mama in Sha Allah........................... Washe gari Balkisu zatayi girkin rana, khadija ta kar'bi girki, gashi sadik bai bata komai na girki ba, da ya riga da ya rabar da khadija zata bayar dan yanzu bayada k'arfin da zai iya ciyar da gidan khadija ke ciyar dasu gabaki d'aya, dan haka yana tashi yayi tafiyar sa, zaune take bakin k'ofar ta tana maganar zuci, Hmmmmm gashi mun samu sa'bani jiya bani da daman da zance naje na kar'bo shinkafa na dafa to ya zanyi mtsssssssww kowa ya ci da kansa to koda ma ance haka ita me zata ci? Ita dai khadija na nan na faman aikin tarbon miji ana had'a kayan gyara ( Kayan mata) bayan ta gama ta aika aka siyo mata cuscus da kayan ciki, tazo ta kashe girki mai rai da lafiya, ta had'a kunun ayar ta Wanda yaji kayan Had'i, su dabino, kwaukwa, kaninfari, minannas, mazark'aula, madara......................................... balkisu ana zaune sai had'iyar yawu ake ( Hhhhhhhh abun ka ga mai kwaud'ayi ).............................. Wannan page d'in sadaukarwa ne a gareku masoya na nakusa da na nesa much love for you fisabillilah ♥️♥️♥️ ♥️ ♥️ 🌹 🥰🥰🥰😍 🌹 🌹🫶💝, ina jin dad'in comment d'in ku i really appreciated, dan hk ku k'ara k'aimi wajen comment nima zan k'ara muku tsawon update 💃💃💃💃💃kun ji a taimakawa mar'atussaliha🧕💔💔♥️ comment d'in ku shine k'arfin guiwarmu😍 love you fisabillilah Bayan ta kammala ta zuba ma mama taje ta kai mata, ta dawo takai sauran d'akin ta, ta fito tayi shimfid'ar ta waje ta zauna, anata zuwa siyan kaya, Balkisu an gaji da zama ta shige d'aki ta kwanta, sadik koda ya dawo ya tarar da khadija tayi shimfid'a waje tana zauna, ya samu waje ya zauna kusa da ita, tayi masa sannu da zuwa tare da fad'in "Ya kasuwa? " Hmmmmmmmmmmm to alhamdulillah za'a ce dan yau an d'an siya abu, ya fad'a tare da sa hannu a aljihu ya ciro d'ari biyu " kingan ta wallahi tun safe ita kad'ai aka yi, ya fad'a tare da nuna mata kud'in" Ohh subhanallah allah ya kyauta hak'uri zaka ci gaba dayi in Sha Allah komai zai dawo dai_dai "Hmmmmmmm to allah yasa khadee ki duba kiga yanzu fa ko gidan nan bana iya ciyar da ku, ya fad'a cikin raunanniyar murya " Ga sauran hak'k'inku da ya rataya akaina amman duka yanzu bana iya sauke ko d'aya allah ka kawo muna mafita" Khadija ta matso kusa da shi ta d'ora kanta a kafad'arsa tare da fad'in"Amin ya rabbi dear kar ka damu muddin ina da shi to kaima kana da komai nawa naka ne duk abinda kake so ka tambaya indai bai fi k'arfi na ba zan baka "Nagode sosai matata ko wannan d'awainiyar da kike damu ta isa bana buk'atar komai allah ya miki albarka yasa albarka a cikin sana'ar ki "Amin ya Allah, ta kai bakin ta dai_dai kunnesa tana magana " Dagaske? ya d'ago yana kallan ta, gira ta d'aga masa tare da kanne ido d'aya" Ki ce yau akwai shagali " Sosai ma" ta fad'a tana dariya na zuboma abinci? " To lallai kam"okay " Tashi tayi taje ta kawo masa tare da kunun ayar da tayi ya d'au sanyi, yana ci yana zuba mata albarka, ita kuma tana gefen sa tana masa fifita, bayan ya gama zai koma kasuwa ta basa dubu bakwai, tace, anjima idan zai dawo ya biyo musu da kaji Balkisu koda ta tashi daga bacci bata tsaya bincikar sadik ya dawo ba ko bai dawo ba dan ko yunwar da take ji kad'ai ta isheta, cikin ta har k'ugi yake, zama tayi bakin k'ofar d'aki sai rabon ido take, khadija na lura da ita, tasan yunwa take ji " Hmmmmm ni dai bazan d'auko nace Miki gashi ba amman idan kika zo da kanki kika nema bazan hana ki ba " khadija ke wannan maganar a zuci, sake Mik'ewa tayi ta shige d'aki tayi tsaye, tana waige_waige cikin d'akin ko zata samu abinda zata saka ma cikin ta, tsaki taja mtsssww tare da fad'in "Kai gwaunda kawai naje wajen ta ko zan samu haka ma za'a yi, ta fad'a tare da fitowa daga d'aki kai tsaye wajen khadija ta nufa tare da zama " Aunty khadija iska ake sha haka"Eh, ta bata amsa a tak'aice " Ko akwai aikin da za'a miki ne " Babu" To aunty khadija daman nace dan allah, tana Fad'a tana sosa kai kamar wata tsohuwar muna fuka, dan allah idan kina da abinci ki sammin wallahi yunwa nakeji sosai " Okay kawo filet" da sauri balkisu ta Mik'e taje ta kawo filet, khadija ta kar'ba ta sako mata, kar'ba tayi tana godiya Khadija ta tashi ta gyara murhu, dan d'aura abincin dare, tuwon d'anyar shinkafa ce zatayi da miyar ganye, cikin k'ank'anin lokaci ta kammala girkin, miyar taji kayan Had'i sai k'amshi take zubawa hmmmmmm khadija badai iya girki ba, k'arfe takwas da rabi sadik ya dawo da gasassaun kaji manya guda biyu, ya Mik'a ma khadija, ta raba d'ayar biyu tace d'aya mama d'aya balkisu d'aya kazar kuma ni da kai, ya d'auki na mama yaje ya kai mata ya dawo ya d'auki na balkisu, koda je d'akin ta har tayi bacci tsaki yaja mtssssww "ita wannan wai bata gajiya da baccin na ne Haba" ledar kaza ya jefa mata, tayi firgita ta farka tana murza ido " Sannu da zuwa"Yawwa ga naki nan " Miye a ciki? " Idan kika bud'e zaki gani, yana gama fad'in haka ya juya ya fita K'amshin da taji yana bugun hancin ta yasa ta saurin Kai hannu ta d'auko ledar ta bud'e, idanuwan ta sukayi arba da kazar ta saki wani lallausan murmushi tare da lashe la'b'banta kamar tsohuwar mayya "Shege ashe dai yana da kud'i " (🙆🙆🙆🙆wai miji ake cema shege balkisu kinga ta kanki hhhhhhh) Tuwo ta kawo masa sai da yaci ya k'oshi, dan yana son tuwon d'anyar shinkafa gashi kuma ta samu lafiyayyar miya, ta kawo masa kazar bai wani ci da yawa ba dan ya k'oshi, ita ma bata ci da yawa ba tasa sauran cikin fridge harda da safe sai ta dumama masa, daga nan suka wuce cikin d'aki suka fara gudanar da ibadar aure, Balkisu an cinye har an fara bacci, kamar wacce aka tsikara cikin baccin ta, ta rik'a jiyo ihun sadik, ta tashi tayi zaune can ta sake jiyo shi, yana sambatu saman khadija tashi daga falo tayi taci cikin d'aki, bangon d'akin su d'aya da khadija taje ta tara kunnen ta kamar wacce za'a fad'a ma magana a kunne, hawaye taji na yawa a saman kumatun da dan abinda kunnuwan ta suka ji baki bazai iya fad'an su ba, ganin idan ta tsaya nan har abinda yafi kuka zata iya yi yasa ta koma falo ta zauna "Babu munafukin Allah kamar wannan mutumen wato ni in yana d'akin nan bayamin irin wannan sambatu nidama nake amarya amman sai wannan wacce ta kwana dubu hmmmmmmmmmmm to wallahi bazata sa'bu ba.......................................... _-_Perfectly Pen's_-_~*✊ 2024 *~_-_Perfectly Pen's_-_~*🤟 *Team One.* *🌹 perfectly Pen's together with five Talented's ✍️✊* *Our Ongoing Book's...✍️* *1_PRINCE ASAD.* *Free Book. BY: Zieey Dodo.* *2_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.* *paid 500* *Season one Free. BY: Queen Kainaat.* *3_TSANTSAN SO.* *Paid,500. BY: Nainarh KD Nkd's.* *4_MU ZUBA MU GANI.* *Paid,300. BY: Oum Yasmeen.* *Mun Shirya tsaf domin kawo muku daɗaɗan littattafan mu masu cike da ilmantar wa faɗakarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaɗantar wa.💝* *🔥Kada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters 🔥* Balkisu ta jima zaune taci kukanta sosai, zuciyarta kamar zata fito, da haka har bacci 'barawo yayi awon gaba da ita, *'Bangaren su khadija* Yau ta kashe sadik da dad'i, ga styles d'in da ta rik'a masa kala_kala wad'an da suka k'ara zautar da shi, ya rik'a mata sambatun dad'i, sun jima suna abu d'aya sannan ya barta suka fito suka yi wanka tare da tsarkake jikin su, suka koma d'aki, khadija kwance saman jikin sa, suna kallan junan su, murmushi ta sakar masa tare da fad'in " Wannan kallan fa? Sai da yaja numfashi kafin yace " Wai daman kin iya irin wad'an nan styles d'in ko koya miki akayi " Sai da tayi dariya sannan tace " Uhmmmm na iya mana ba wanda ya koyamin "Amman shi ne baki ta'ba min ba to daga yau ina expected d'in su gare ki"Kar ka damu dear gobe ma akwai sabbin styles wad'an da na tanadar maka"Dagaske honey ? d'aga masa kai tayi alamar eh " Wayyoooooo allah na shiyasa nake k'ara son ki matata kice gobe zan k'ara Sha dad'ina" ya fad'a tare da kai ta'b'bansa ya d'aura a sana yashiga tsotsa ita ma ta tayasa yaja musu bargo ya rufe su *Washe gari* Bayan ta gama had'a musu breakfast ta dumama kazar jiya, ta bama sadik, balkisu ta fito duk haushin su take ji anyi tsinin da baki kamar ya ta'bo sama, tana lura da khadija da sadik ta zarar sun had'a ido sakarma junan su murmushi wanda ta rasa gane ko na miye, nan take ta k'ara k'uluwa, ko ina kwana batama sadik ba bare kuma khadija, Har ya gama karin sa, yayi shirin fita ganin bata gaidasa ba yasa sa zuwa wajen ta tare da fad'in "Kin tashi lafiya? Tun da ke bazaki iya gaidani ba ni bara na gaida ki ko bakya da lafiya ne? " Lafiya ta k'alau "Ohh iskanci ne kenan " k'ara turo baki gaba tayi, ya kalleta tare da girgiza kai, ya wuce khadija ta taso ta rakasa har bakin k'ofa sannan ta dawo "Komai shafe_shafe munsan tsufa dan duk wanda ya shafa man dallah munsan shi" Khadija najin ta tayi kamar bata ji ba tayi d'aki, tana nan zaune taji sallamar k'awarta safiya da gudu taje ta tarbo ta "Aah yau kece a gida nan"Wallahi kuwa yau allah yayi nazo kuma nazo miki da haja"Kice dai ita ta kawo ki "Aah wallahi daman inada k'udurin zuwa " To muje daga ciki"d'akin suka wuce, firar yaushe gamo suka d'an ta'ba daga nan safiya ta bud'e Jakarta tana fitowa da maganin mata " Amman wallahi naji dad'in zuwan nan naki kamar kinsan ina buk'atar su sai dai kuma banada kud'i a hannu" Ai kuwa ba bashi ba ne, kinga wannan, safiya ta fad'a tare da nuna ma balkisu wata kaulba " Eh nagansa" Hmmmmmmmm wannan shi ake kira da sa kishiya tagumi hana kishiya bacci " Ni kinsan irin wad'an nake so, so nake ki bani wanda ina yana samana har mak'ota sai sun ji ihun sa "Hehehehe idan wannan ne baki da matsala ai da kin kawo ga wannan magana ta k'are ke ba mak'ota ba layin nan naku gabaki d'aya sai anjiyo shi bare kuma muta nen cikin gida ai sai kun hanasu bacci kuma zai zazzage kimi aljihun sa ke da kinyi aiki dashi sau biyu to shikenan sai abinda kika ce a gidan nan kuma duk abinda kika tambayesa koda baya da shi sai yaje ya nemo miki shi" Shegiya k'awata kamar kinsan abun da nake so wallahi " Hmmmmmmm kedai kawai fito da kud'i ki siya kaya kiga aiki nasan sai kin godemin "Haba k'awata mu sasanta mana sai ki bani kinga gobe zan kar'bi aiki idan nayi aiki dashi na samu kud'in sai na baki kud'in ki har ma na miki kari Tab baki shiryar siyaba bari idan kika samu kud'in sai na kawo miki dan gobe barin garin nan zanyi, kinga ko bazaiyi na bada kaya nn bashi ba "Kar muyi haka dake " To mezai hana ki ranto"To ni wazai rantamin ? "Idan kina so akwai wata mata da na sani mai dashe nan take ma cikin unguwar ku tana rantama mutane kud'i "To kina ganin ba matsala "Ba wata matsala "To bara nasa mayafina muje" To, Tasa mayafin ta suka fito, suka wuce, gidan baya da wani jayawa daga gidan su, da suka je ma matar ta gane balkisu dan sunje ganin amarya, bayan ta basu waje suka zauna suka fad'a mata buk'atar da ta kawosu wajen ta matar ta numfasa tare da fad'in " To maganar gaskiya kud'i akwai su amman akwai wacce za'a kwaushe ma dashen ta jibi amman idan kunyi alk'awarin zaku kawo kafin lokacin sai na baku"Eh in Sha Allah kafin nan ma ta kawo dan gobe muke sa ran za'a samu kud'in" to shikenan dubu ashirin kuka ce ko amman dai kunsan talatin zaku mai suwa "Eh "To shikenan, ta tashi ta shiga d'aki ta irko musu kud'in ta Mik'a musu tare da fad'in"Dan Allah ku cika alk'awari "Karki damu in Sha Allah" suka amsa suka fito, safiya ta had'a mata kayan dubu goma, sannan balkisu ta bata dubu biyu kyauta, sukayi sallama ta wuce, kafin ta isa gida sai da ta kusa kashe dubu biyu ta siya awara da madara ta biya ta siyo kilishi sannan tayi gida Koda ta shigo gidan, khadija na bakin murhu tana aiki, ta d'ago ta kalleta dan ita bata ma san bata nan ba " Fita kikayi? "Ai gashi na dawo " balkisu ta fad'a tare da shigewa d'aki, khadija ta mayarda hankalin ta ga aikin da take yi ............................................. Cikin d'aki ta shige ta koma gefen gadonta ta zauna a k'asa , ta bud'e k'afafuwanta tasaka ledar a tsakiya, tun kafin ta bud'e ledar yawu har sun fara taruwa a bakin ta, ledar kilishin ta bud'e ta fara ci, sauri_sauri ta rik'a cin sa kamar wacce ke aikata wani mugun abu batasan a kamata, haka ta rik'a ci, ta cinye ta janyo ta awara ita ma sai da ta cinye tass harda sa harshe ana lasar d'an bad'in da ya lak'e a ledar, zanen gadon ta janyo ta goge hannun ta dashi ledodin kuma ta tura k'ark'ashin gado, ta d'auki maganin tana kallo tare da yin wata irin dariya " Hehehehe sadik ka kusa shigowa hannu sauran k'iris, zan juyaka yarda nake so na tatale dukiyarka koda yake yanzu baka da komai sai dai nasa ka rik'a ciwobashi kana kawo min naci dad'ina khadija taki ta k'are Hhhhhhhhh" Khadija ta gama aikin ta, har tayi wanka ta had'e cikin wata doguwar riga, rigar kamar roba take duk ta kwanta a jikin ta duk yarda ta motsa sai jikin ta ya raya, sai k'amshi take zubawa ita da d'akin ta, abincin balkisu ta d'auko tazo ta kawo mata, tayi tsaye bak'in k'ofar tasa hannu ta k'wank'wasa k'ofar, balkisu dake zaune cikin d'aki tana lissafin abubuwan da zata yi, taji ana k'wank'wasa mata " Wai lafiya? " Idan kika zo zaki gani"khadija ta bata amsa " To naga alkhairi"Shi muke fatan gani a koda yaushe" Uhmm, tana fitowa khadija ba tare da ta sake cewa da ita komai ba ta Mik'a mata kular ta juya, da kallo balkisu tabi bayan ta har ta shige d'akinta, taja tsaki ita ma tashige d'aki tare da fad'in" sai wani kuri da take da d'uwawu sai aka ce mata muma bamada su mtsssww to allah dai yasa kowa nada d'uwawun nan sai dai kawai ace na wani yafi na wani to muma munada namu ehheeeeeee" Khadija ko tana komawa d'akinta ta d'auko had'in da tayima kanta tayi zaune tana Sha.............. Gogan naku koda yadawo cin abincin ganin khadija cikin wannan shigar ba k'aramin tayar masa da hankali tayi ba, ai kuwa yace bazai koma kasuwa ba dak'yar khadija ta lalla'basa ya koma Yau ma kamar jiya koma nace fiye da jiyan, khadija ganin abun nasa yayi yawa za'a iya jiyo su yasa ta dakatar dashi, ta hanyar janye jikin ta daga gareshi ta koma gefe, a hauka ce ya d'ago yana kallan ta yana haki, kamar wanda ya sha gudu, kallan ta yake itama shi take kallo, bakin sa na matsi alamar magana yake son yi amman ya kasa, dak'yar ya iya furta kalmar " Miye hakan ? " Ba mu kad'ai bane a gidan nan ba fa za'a iya jiyo mu " Wani kallo ya watsa mata tare da fad'in"To sai me dan an jiyo mu ba mata da miji bane mu har kike jin kunyar ajiyomu muna raya sunnar ma'aiki( S A W)" Ya fad'a cikin 'bacin rai Khadija ganin kamar maganar ta 'bata masa rai yasa ta dawo wajen sa tare da shigewa cikin sa tana shafa jikin sa a hankali ta furta" yi hak'uri ba haka nake nufi ba "ta fad'a tare da d'agowa tana kallan face d'in sa " To ya kike nufi ? " Sorry zuma na yi hak'uri ka gafarce ni bisa furucin da nayi" zai sake yin magana tayi saurin had'e bakin su waje d'aya, daga nan suka ci gaba da faran tawa junan su................ *'bangaren balkisu* Ko yau ta jiyo su ta tashi tayi zaune tana kitstsima abubuwa a ranta, har bacci yayi awon gaba da ita * Washe gari* Bayan ya dawo sallahr asuba sai da ya sake nemanta dan yasan yau ba a d'akin ta zai kwana ba, ai kuwa ta makara wajen had'a karin kumallo, balkisu ta fito tayi zaune minti d'aya minti biyu tayi tsaki, ganin tsakin yayi yawa yasa khadija ta d'ago ta kalleta tare da fad'in "Balkisu lafiya kuwa? " Ita ta kawo hakan " To allah ya kyauta"Amin mtssww Balkisu allah_allah ake dare yayi tun kafin ayi sallahr magrib ta je tayi wanka, ta kakkamta komai, ta d'auko maganin ta shanye rabi sai d'ayan ta cusa a gabanta ango kawai take jira Sadik koda ya dawo matse take da ya shigo d'akin, ta matsu taga komai ya kankama, al'adarsa ce inda ya dawo sai ya je ya gaida Mahaifiyar sa yayi masa sai da safe sannan idan bake ke aiki ba zai shiga ya miki sai da safe, da yaje d'akin khadija ya d'an jima a can sannan yayi d'akin ta, Abinci ta kawo masa yaci, yana gama ci ya haye gadon yayi kwanciyarsa, tashi tayi ta cire komai na jikinta ta fad'a saman gadon ta kwanta saman sa, bacci har ya fara d'aukar sa yaji ta saman sa, juyowar da zaiyi yakai hancin sa saman kashin kanta, warin kan ta yayi wufff sai cikin hancin sa, ba shiri ya zabura ya tashi zaune, ganin yarda ya tashi yasa ta biyo shi tana fad'in "Lafiya"Girgiza mata kai kawai yayi alamar eh dan yama kasa bud'ar baki, k'ara matsawa tayi cikin sa tana goga masa jikin ta, Khadija kwance tana juyi saman gado, bacci ya kasa d'aukan ta juyi kawai take yi, zuwa can ta tashi zaune tare da jingina bayan ta da gadon,tana tuna moment d'in su na jiya ita da sadik, wasu hawaye masu zafi taji suna zubo mata, tayi saurin sa bayan hannunta tana gogewa tare da furta " Sadik yanzu ba nawa bane ni kad'ai mijin mace biyu ne " Ta k'arshe maganar tare da fashewa da kuka mai ta'ba zuciya " Allah ka zamo gatan mu duniya da lahira" kuka take sosai har bacci yayi gaba da ita, K'ara goga masa jikin ta take Shi kuma idan aka zo wannan fanni ba juriya ce da shi ba, dan haka ya bada kai bori ya hau, balkisu ta baza kunnuwa taji sambatu amman shuru takeji maimakon ma shi yayi sai ita ce ke yi, 'bangaren sadik kuwa haryanzu ya kasa sama ma kansa kamsuwa a wajen ta, Jin ta yake salaf_salaf sai tsakin da yake ja a k'asan ran sa, balkisu ita kad'ai ke jin dad'in wannan harka, har ya sauka a kanta bai samu wata gamsuwa daga wajen ta ba, Balkisu anyi baje_baje an ware k'afafuwa, sadik ya kalleta tare da jan tsaki a ransa a fili ya furta " Tashi muje muyi wanka" Ya tsina fuska tayi tare da fad'in "Wallahi nagaji sosai sai da safe zanyi" Wankan? Ya fad'a cikin jin mamaki da furucin ta "Eh " kad'a kai kawai yayi ya fita dan tsarkake jikin sa, Yana fita tayi zumbur ta Mik'e zaune sai yanzu ta tuna da wani zancen maganin da ta sha " Ah ah nafa sha maganin na to amman banga aikin da yayi ba to kodai ban shasa yarda ake Sha bane ko kuma sai goben idan na sake amfani da shi zai fara aiki, kai haka ne ma inaga sai an shanye baga d'aya zaiyi aikin Hhhhhhhhh allah ya kaimu gobe " Ta koma tayi kwanta sai bacci, koda ya dawo tayi bacci ya kwanta daga gefe, ya runtse idanuwansa, moment d'in su na jiya tare da khadija ya rik'a tunawa, murmushi ya rik'a saki shi kad'ai, a k'asan zuciyar sa yana ta suburbud'a mata ruwan albarka da haka har yayi bacci..........................................