WATA RAYUWA by Fatima S Umar Jajira Na Fatima S Umar Jajira Pree book Episode 1 Murya a sanyaye ta ke magana "Haba dan Allah malam ka taimaka ka saida mun yadi É—aya É—ari uku da hamsin." "Haba hajiya a wannan tsadar rayuwar kike zaton zaki samu yadin hijabi me kyau irin wannan a É—ari uku, ai yanzu komai na rayuwa ya tashi hakuri zakiyi ki siya kan haka." Girgiza kai ta yi ta zaro kuÉ—in sa ta bashi, ya yanko mata yadin hijabin ta baro gurin. Saida ta yi tafiyar Æ™asa mai nisan gaske sannan ta tari kafu babur ta ce ragowar canjinta ashirin ya Æ™arasar da ita kan layin su, saida mai kafu babur É—in ya gama mita sannan ya ce ta hau su huce. DaÆ™arfi ta ban kaÉ—e labulan É—akin ta fito ta riÆ™e Æ™ugu tana karkaÉ—a jiki, a sanyaye ya fito daga É—akin ya zo gaban ta murya atau shashe ya ce "Haba Hauwa'u ya ina miki magana zaki fito ki rabu dani, hakan da kikayi kin kyauta kenan?" Cikin tsawa ta ce "Dakata Yusuf har wata maganar kyautawa kakeyi? Kai kyauta mun kake? Yaza'ayi na ringa ci da kaina da yaranka har dakai katon banza katon hofi sannan kace na maka rashin kyautawa." Yaji ciwan maganar ta amma bai nunaba ya ce "Naji duk abuda kikace, na yarda laifi nane, amma na roÆ™eÆ™i da ki koma ciki muyi magana." "Wallahi ba inda zan É—ara naje daga nan duk abunda zaka faÉ—a ka faÉ—a a nan." Nunfashi ya sauke ya ce "A'a Hauwa ki daure mu shiga daga ciki kinga duk mutan gidan sunajin abuda muke faÉ—a." Kansa tayo da faÉ—a. "Saime dan sunji adalci ka kemun da zaka ce mushiga ciki, ai gara kowa yaji rashin adalcin da kake mun a cikin gidan nan." "Haba Hauwa'u bafa ke kaÉ—aice a cikin irin wannan yana yin ba mata da yawa suna fuskan tar hakan amma suke rufawa maza jansu asiri sabuda sunsan halin da ake ciki a yanzu." "To ni bazan iya ba na gaji." Ganin zata tara masa jama'a yasa ya rabu da ita ya koma É—aki yana tunanin halin daya tsinci kansa a ciki ga talauci ga mata mara mutunci, yanaji tana ta masa habai ci amma bai ko kula iskar ta ba. A Æ™ofar layinsu aka sauketa, ta Æ™arasa gidan nasu ta shiga ciki da Salama, kallon sama da Æ™asa ta mata ta ce "Sannu gan ta laliya kin dawo daga gantalin?" Cikin Æ™unar rai ta ce "Naje siyo yadin hijabi ne tunda next week za'a koma Islamiyya." Wata uwar tsawa ta daka mata "Uban wane zai barki kikoma Makaranta ki cigaba da gantalin naki na hali ko? To baki isaba wallahi." Hawaye ne suka fara zarya a fuskarta ta tsuguna ta ce "Dan Allah Mama karki sa a hanani zuwa Makaranta kiyi hakuri karki hukun tani ta wannan hanyar." "Hmmm Khadija kenan ai azaba kala-kala zan ta gana miki har sai kin yarda da kudirina." Kuka me sauti Khadija ta sa tana girgiza kai "Banzan iya ba walahi kiyi hakuri." A fusace Mama ta warce ledar hannun ta, ta buÉ—a taga yadin hijabi ne ta yi murmushin mugunta ta miÆ™e ta ce "Munafuka zakiyi bayanin inda kika samu kudi kika soyo shi idan Baban ku ya dawo." "Allah Mama kudin taruna ne na gidan su Abida na....!" Ko kulata Mama bata yi ba ta shige warta É—aki. A sanya ye ta miÆ™e ta shiga É—an karamun É—akin su da suke kwana ta samu guri ta zauna, ta yi tagumi. Tana tunani Wannan Rayuwa da ta juya mata baya, da yanzu tana gaban mahaifiyar ta wazai ringa cuzguna mata haka? Hawayen da suka zubo mata ta share a fili ta furta. "Allah sarki Ummi na, ko kina raye ko kin mutu? Allah ne masani, Allah ya kareki a duk inda kike indai kina raye ya dawo mana dake cikin koshin lafiya, idan kuma kin rigamu gidan gaskiya Allah ya kyauta makwanci Ummina." Ta Æ™arasa maganar tana kuka me ban tausayi. ********* Cike da isa ya na tako É—ai-É—ai ya zauna kan dining table É—in yana Æ™arewa kayan kai kallo, fuska ya haÉ—e cikin isa ya fara magana. "Nafisa! Nafisa." "Na'am." Ta amsa da sauri ta na fitowa daga É—aki. Matashiya ce da bazata haura shekara 24 ba fara ce amma bada tsayi sosai amma kyakykyawa ce ga fara'a da tarbiya. Har Æ™asa ta tsuguna na ta ce "Gani Abu Anwar." Kafin ta rufe baki taji saukar ya tsunsa a kuncin ta, dafe kuncin ta yi tana kallon sa hawaye na bin kuncin ta. "Ke wace irin jaka ce da kulu saina sanar da ke abunda bana so? Wace irin jakar kwakwalwa gareki da ba ta riÆ™e abunda ake biya mata, so nawa zance da ke bana son cin wannan Æ™azan tar abuncin naki, me kama da amai. Na sanar da ke inba tea ba ban yarda a dafa wani abu da safe a gidan nan ba, amma baki yarda ba ko? To wannan haukar da kika dafa ita ce abuncin ki na kwana 2 bani mukulin store." Tashi ta yi jiki na rawa ta kawo masa key É—in tana kuka, ya wurga mata harara ya fice daga gidan. Tana masa addu'a amma ko kula iskarta bai ba ya wuce. Tashi ta yi ta share hawayan ta inda sabo ta saba da halin mijin nata, kwata-kwata bashida hali me kyau. ********** Abokin nasa ya tsirawa ido kafin ya ce "Yanzu ya zamuyi da wannan yaron." Dafa shi Salim ya yi ya ce "Karka tada hankalin ka akan Nasir zamu ji dashi, da Æ™afar sa zai gudu ya bar mana company mu muci gashin kanmu." Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Nasani amma tayaya?" Murmushi Samir ya yi ya ce "Zan sanar dakai idan na gama tsara komai." Zaiyi magana sukaji an buÉ—e kofar an shigo, a tare suka miÆ™e suna masa sannu da zuwa. Ya amsa cike da izza harararsa sukeyi Æ™asa-Æ™asa, a fili kuma sunata washe baki. Ya zauna yana cika yana batsewa, suka zauna Samir ya ce "Barka da isowa Alhaji." Kai ya gyada ba tare da ya yi magana ba Isyaqu ne ya ce "Barka da zuwa Abu Anwar." Fuska ya saki ya amsa masa kafin ya ce "Ba wanda ya zo nemana?" "Eh ba wanda ya zo." Kai ya girgiza ya ce "Okay ina son hutawa." Sum-sum suka miÆ™e suka fice. Ya zaro wayar sa ya lalubo wata number ya kara akune. Saida ta kusa katse wa sannan aka dauka murya na rawa ta yi salama tare da cewa "Kayi hakuri Alhaji har yanzu yarinyar nan taki bani haÉ—in kai, na rasa yadda zanyi da ita." "Kinga na gaji da Æ™arairayinki idan baza ki iya ba zan hakura gaba É—aya." "A'a Alhaji yanzu haka na matsa mata har makaranta na hanata zuwa kuma na fara mata sharri gurin babanta kaga wuya zata sa ta amsa da kanta." Cikin isa da gadara ya ce.............! Comment And Share WhatsApp number 08166077167 By *XAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Pree book Episode 2 ___________ "Wannan ita ce dama ta arshe da zan baki, idan kika sake na sake ne manki ba wata tsayayiyar magana hmmmm, basai na sanar dake abunda zai biyo bayaba kin sani." Bai jira ta yi magana ba ya katse wayar. Mama da take kule a aki ta ringa goge gumi kar yarinyar nan ta tona mata asiri fa, tashi ta yi da sauri ta fito tsakar gidan ta fara kiran Khadija. Khadija da ta fara bacci bayan kukan da tasha, taji anata kiranta, ba shiri ta mi e ta fito gurin Mama, jikinta har rawa ya ke sabuda tsoro ta ce "Gani Mama." Mama tana kunfar baki ta ce "Nagaji da rashin mutunci da kike mun kina sawa mutuncina yana zubewa har wani gata gareki da bazaki yarda da kudirina ba to wallahi sai dai ki bar gidan nan." A razane Khadija take kallon Mama, mama ta gyada kai ta ce "Ko kina tantama ne?" Kai ta girgiza alamun a'a "Idan ma kinayi to ki tuna yanzu ina uwarki take? Ta salwanta, to kema kibini a hankali kona sabautaki wallahi." Kuka Khadija ta ke ta ce "Kiji tsoron Allah Mama kisani akwai ranar da zaki koma ga Ubangiji kuma zaki girbi duk abunda kika shuka." Bata rufe baki ba, sukaga shigowar Baba ya na ta ce "Lafiya nakejin maganar ku har zaure?" Kuka Mama ta saka harda majina ta na cewa "Waini Khadija zata zaga harda ni nasa uwarta ta tafi karuwanci ta barta harda zagidana tana cimun mutunci." Zaro ido Baba ya yi ya ce "Yanzu Khadija ce ta ke fa a miki wannan magan ganun." "Allah Baba ba haka na ce ba." "Kaji ko? To na mata arya." A fusa ce Baba ya ako tsabga ya fara jibgar Khadija tana ihu ta na bashi hakuri. Mama tana gefe tana dariya, da taga dukan ya yi yawa sai ta fara bashi hakuri tana cewa "Ni da kasani baka daketa ba kabarta taje taitayi bakin rai bakin fama nan gaba zata haifa ita ma." Sai da Baba ya farfasawa Khadija jiki ya rabu da ita ya ce da ita "Daga yau idan kika ara zagin Lube saikin bi uwarki yawan duniya shegiya me kama da mujiya." Ya fice yana ta huci,ita kuma Mama ta rakashi tana "Allah ya huci zuciyar ka kayi hakuri." Yana ficewa ta joyo ta kalli Khadija ta ce "Khadija naga alama bakya so mu rabu alau da ke amma tunda haka kike so muzuba mu gani." Ta shige aki tana ta rera wa a harda rausaya wa. Khadija jiki na tsami ta tashi ta koma akin na su da duk sako ne a ciki tana cigaba da kuka me ban tausayi, abu buyu ne sukafi tsaya mata a rai, wai Ummi ta karuwanci ta tafi da iskanta ta da Baba ya yi taji ciwan abun amma ba yadda zatayi. ************* Sauke miyar kukan tayi tana ara ice yarinyar ta zo kusa da ita "Umma yinwa nake ji." Ture yarinyar Hauwa ta yi cikin masifa ta ce "Dan ubanki ba gashi kina kallo ina girkin ba, zaki adabe ni, idan biyewa sakaran ubanku zanyi tukunya bazamu ara acikin gidan nan ba." Matar da ke tsakar gidan ta na wanki ta ce "Haba Hauwa kiringa sassautawa kanki mana kulum cikin fa a kiyiwa miji kiyiwa yara sabuda Allah." "To naji ar sa ido mijin ki nayiwa ko yaran ki, da zaki samun ido, ko ba kya ganin laifin sa daya barni da yinwa nida yara saini dan nayi fa a nayi laifi." "Kowa fa zaman hakuri yake dana sa mijin a wannan hali da muke ciki, gara kema ga mijin a kusa dake kya ringa ganinshi kina jin dadi kuma garkuwane a gareku, amma wata ko inda nata mijin ya ke bata saniba." "Mtsss to sai me da zai shiga Duniyar ma ya ne mo ku i da yafi wannan zaman asarar da yakeyi." Girgiza kai matar ta yi ta kasa cewa komai ta kula Hauwa ta yi nisa batajin kira, saidai a tayata da addu'a Allah ya ganar da ita. Habai ci Hauwa ta cigaba dayi tana masifa ita ka ai. Yusuf yana aki duk yanajin ta, yaga alama inba wani mataki ya auka da gaggawa ba fita tsakar gida ma saita gagareshi, duniyar tunani ya lula yadda zai samawa kansa mafuta. ************* Alhaji Nasir yana ajiye waya ya mi e yasa wa office in nasa key ya kule, ya bu e wata ofa a cikin office in sa ya shiga, ya jima aciki kafin ya fito fuskarsa cike da damuwa ya jawo wayarsa akan table ya kira wata number ana agawa ya ce "Akwai matsala ina so mu ha u yanzu." "Okay." Ya ce ya ajiye wayar ya auki car key in sa ya fice daga Company. Ya yi tafiya me nisa har ya fita daga cikin gari, gidaje sai ai- ai, kafin ya parking a ofar wani gida ya fito. knocking ya yi, aka bu e ya shiga har falon gidan ya samu guri ya zauna. Wata hamsha iyar mata ce ta shigo falon, mi ewa ya yi yana mata sannu da zuwa, ta zauna shima ya samu guri ya zauna. Cikin damuwa ya ce "Na fara ganin canji tun yanzu wai meyake faruwa ne?" Wani kallo ta watsa masa ta ce "Haba Nasir meyasa kake son sa kanka cikin matsala muma kasamu, kasan fa idan baka cika al awarin da ka auka ba muma zata shafe mu kajima a harkar nan amma wannan karon kana so ka bamu matsala me yasa?" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Ina iyakar o arina akan haka, yarinyar da nake tunani ta yi dai-dai da a idar abun ta i bamu ha in kai wallahi." "Kuma ita ka ai ce ka gani da wannan sifofin?" Kai ya gya a, ta ce "Okay abunda zai faru yanzu tunda matsala zata baka ka nemi auranta shikenan." Shiru ya yi yana nazari kafin ya ce "Ba matsa hakan." "Eh kawai idan kayi abunda akace ba ruwansu da nasaba ko da Nafisa ce ko Anwar." Gabansa ne ya fa in ba yaso yaji suna ambato sunan Anwar da Nafisa duk da yana azabtar da Nafisa yana son matar sa, gani ya ke idan har aikin su zai shafi Anwar ko Nafisa to duk abunda zai faru saidai ya faru dan bazai ta a lamunta ba. Maganar da tayi ce ya katse masa tunani "Ya kamata ka hanzarta aukan mataki Nasir." "In sha Allah." Ya ce yana mi ewa ya mata godiya sukayi salama ya fice daga gidan. Zazzab'i ne sosai ya rufe Khadija ta ringa rawar sanyi, amma Mama bata duba halin da take ciki ba tasa ta wanki tanayi tana kuka jikinta nata rawa. Mama ce tasa hijib ta fita a ofar gidan ta tadda Alhaji Nasir cike da tsoro ta ce "Me ya yi zafi haka har kazo cikin gidan nan Nasir?" "Tunda kin kasa aikin da na baki bayan magudan kudin dana baki to na yanke shawarar auran ta inya so na saketa daga baya." Shiru Mama ta yi ta ce "Da kayi hakuri, aure nawa zaka kashe akanta." "Ba abunda ya shafe ki da haka ina mahaifinta?" Kafin Mama ta yi magana saiga Baba ya dawo a tsora ce Mama ta shiga gida shi kuma Nasir ya kalli Baba a gadaran ce yace............ Comments And Share WhatsApp number 08166077167 By *XAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Pree book Episode 3 __________ "Malam dama gurinka na zo." Cike da mamaki Baba ya ce "Ni kuma Alhaji." "Eh." Matsowa Baba ya yi suka gaisa da Alhaji Nasir, ya tanbayeshi lafiya? "Naga yariyar gidan nan kuma na yaba da tarbiyar ta ari bisa ari, dan haka nake son a bani auran ta." Washe baki Baba ya yi ya ce "Ai kuwa Khadija akwai hankali da tarbiya masha Allah." Baki Nasir ya ta e ya ce "Bana so maganar ta au wani lokaci, nan da 1 week na ke so ayi komai a gama ko nawa ne zan kashe bakuda matsala." Ya bu e motar ya ako ku i masu yawa a jaka ya mi awa Baba ya ce "Miliyan 2 ce a ciki zata isheku duk hidimar biki, bana bu atar komai daga gurin ku, yarinyar kawai za'a kawo ko spoon karku wahalar da kanku ku siya." Jikin Baba na rawa ya amshi jakar ya ce "Allah ya kai mu, mungode mungode." Hannu Nasir ya aga masa ya ce "Ya isa haka, idan kuna bu atar wa ni abu matar gidan tanada number ta kune meni." Bai jira abunda Baba zai ce ba ya shige motarsa ya bar gurin. Jiki na rawa Baba ya shiga cikin gidan, Mama na ganin sa da jaka ta ce "Menene a ciki wannan jakar." Baba na zare ido ya ce "Ku i ne Lube, arziki ya zo mana." Baki Mama ta washe ta ce "Alhadulilah, amma dai ba gidan nan ka saida ba ko?" Dariya Baba ya yi ya ce "Ko aya auran wannan yarinyar me idon mujiya ya zo, kuma dama neman kai nake da ita shine kawai na amunce." Bu a Mama tasa ta ce "Kayi dai-dai Malam ai dama auran shi ya dace da ita, Allah yasa idan ta je ta zauna karta musu halin nata na tsiya a korota." "Ai wallahi ta kaso auran nan bata isa ta dawo mun gida ba, saidai ta shiga duniya badai gidana ba." Murmushin mugunta Mama ta yi ta ce "Gaskiya ne kayi dai-dai wallahi." Duk abunda suke cewa Khadija dake wanki tana jinsu, ba abunda takeyi sai kuka me sauti, yanzu abuda ta keji wai-wai a gari shine ya ke shirin faruwa da ita, itama iyayenta saida ita zasuyi, sabuda rashin adalci basu san mutum ba basusan asalinsa ba basusan waye shiba, zasu aura mata shi sabuda bata da gata, ba tada Uwa wadda zata kwato mata anci. Dur kushewa ta yi ta saki wani irin kuka me cin rai. A tare suka juyo suna kallon ta, Baba zai fara masifa, Mama ta ce "Rabu da ita Malam, aidai bata isa ta tsalake abunda muka gindaya mata ba ko?" Baki ya washe ya ce "Tabbas ita in banza ai ko Malam Rabe ne (Mahaifinsa) zai dawo Duniya yau ya ce a fasa auran nan wallahi ba zai fasuba bare ita aramun alhaki." Mama ce ta cigaba da zugashi yana hawa kai, ita kuwa Khadija kuka kawai takeyi me ban tausayi. ************* Da murmushi Nafisa ta tareshi zata kar i jarkan hannun sa yai saurin da katar da ita, ya ratsa da gefanta ya wuce, da kallo ta bishi ta rasa yaushe Nasir zai canza hali kulum girma yake yana cin asa, kulum addu'a ta ke masa Allah ya ganar dashi ta daina irin wannan halin nasa. Bayan sa tabi har cikin badroom in sa yana zauna bakin gado tana kallon sa ta ce "Dama jiranka nake ka dawo muyi magana." Bai kalli inda take ba ya ce "Menene kuma?" Saida ta yi jim kafin ta ce "Ina so wannan weekend in muje gida da Anwar, mun kwana biyu bamuje ba." Saida ya gama rage kayan jikinsa ya zauna kusa da ita ya kafeta da ido ya ce "Nagaji da irin abubuwan da kike mun Nafisa, kulum naita biya biki abu kamar karatu, to daga yau na arajin maganar fita a bakin ki ranki zai a." Wannan karon Nasir ya kaita bango dan haka ta ce "Gaskiya Nasir rayuwa bazata yiyu hakaba ka hanani fita cikin mutane sannan zuwa naga iyaye na ma bazaka barni b......!" Kafin ta arasa ta ji saukar mari a fuskar ta cikin tsawa ya ce "Yaushe kikayi girman da har zan fa a kina maida wa, na kula kulum karo wula aci kekiyi idan zaman gidan ne ya isheki to ki kagama gaban ki amma ki sani ko zaki shekara dubu a duniya ba a namijin da zai kaleki da sunan aure shashasha bagidajiya." Ya tashi a fusace ya shige bayi, tagumi Nafisa ta yi har ta saba da tozarcin Nasir, amma ba ta ganin laifin sa tafi ganin na iyayenta da sukaga ku i ba binki ce ba komai suka aura mata shi, tunda ta auri Nasir ba ta gane kan sa mutum ne mara al ibila gashi ba wanda ya sa asalisa ko sirrinsa sana'a ma tasan dai Manager ne a wani Company takalma amma ku in da Nasir ya tara bata tunanin shugaban asar America yana da su, ta rasa ida yake samun ku i, kuma duk lokacin da ta tuhume shi ranar me kwatar ta a hannun sa sai Allah har ta saba da mari da dukan Nasir abun ya zame mata jiki ma. Yajima a bayin ya fito da alama wanka ya yi, tashi ta yi ta ako masa kayan da zai saka ta taimaka masa ya shirya ko dinner bai zauna ya ci ba ya auki motar sa arfe 8:30pm ya bar gidan. Inda sabo Nafisa ta saba da fitar dare da Nasir ya keyi dan wataran har 12 fita yakeyi kuma ba dama ta tanbayeshi jikinta ya fa a mata. Da safe bayan an idar da Sallar asuba Yusuf ya samu wani abokinsa Maniru bayan su gaisa ya ce "Abokina wallahi na gaji da cin kashin da Hauwa take mun a cikin gidana, ni yanzu aiki ko kwasar kashice na samu yi zanyi." "Gaskiya Yusuf kana cikin wani hali, amma inada shawara guda aya, mezai hana kabini Company da nake aiki na takalma muringa aiki tareba suna neman ma'aikata sosai." Baki Yusuf ya washe ya ce "Masha Allah, ai wannan fa uwa ta zo dai-dai da zama naji da in wannan shawara taka nagode abokina sosai da sosai." Nan suka rabu akan cewa gobe Yusuf zaibi Maniru Company takalma dan ya nemi aiki acan shima. Yadda taga dare haka taga rana, zuciyar ta cike da zulumi da tsoron makomar rayuwarta, itadai tasan wannan shirin Mama Lube ne, kardai sa au ta tan da tace zatayi shine ta biyo ta wannan hanya? To amma ina tasamo me ku in haka zuwa aya ya siye Baba da miliyoyin ku i? Tashi tayi cikin dare ta ringa nafila da ro on Allah ya tsareta daga sharin me sharri, Allah ya kawo mata mafuta cikin wannan rikitacan al-amarin. Washe gari da sassafe Yusuf da Maniru suka shirya suka tafi companyn takalma, Maniru ne yaima Yusuf jagora har zuwa office in Alhaji Nasir, bayanan haka suka zauna jiransa har 12:00pm sannan ya zo, nan ma saida suka jira sannan ya ce su shigo. Da salama suka shiga suka zazzauna suka gaidashi bai amsa ba ya ce "Lafiya?" Murya na rawa Maniru ya ce "Dama wannan aboki na ne ya ke neman aiki ko sharace a taimaka yana cikin wani hali." Kallon Yusuf, Nasir ya yi kafin ya ce "Matsayin karatunka fa?" "N.S.E nayi." "Okay wace sana'a kakeyi." "Ba sana'ar da nakeyi ga mata da yara bani da abunda nake basu." Ya arasa maganar yana hawaye Murmushi Nasir ya yi ya ce "Ba damuwa akwai aikin da zakamun, zaka samu ku i sosai amma ka sameni a gida kai ka ai muyi magana." Bakin Yusuf kasa rufuwa ya yi ya ringa yiwa Alhaji Nasir godiya suka masa salama suka tafi. Suna fita Alhaji Nasir ya kira Hajiya Hasina ya ce "Na samu wani miskini nasan zai iya komai akan kudi dan haka ban bashi tayin aikin ki..........! Comments And Share Ga masu gyara ko karin haske WhatsApp number 08166077167 By *XAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Pree book Episode 4 Daga can Hajiya Hasina ta ce "Indai har ya yi aiki na ba wata matsala ka masa ta yin shiga kungiya, amma ka sanar dashi tsarin mu." "In sha Allah, sai kin jini." Salama sukayi Nasir ya kashe wayar sa yana tsara yadda zai shawo kan Yusuf cikin sauki. Yusuf suna fita ya dubi Maniru ya ce "Amma abokina wane irin aiki kake tunanin Alhaji Nasir zai samomin?" Murmushi Maniru ya yi ya ce "Wata kila gadi ne ko aikin gida tunda ya ce ka sameshi a gida." "To amma cewa ya yi fa zan samu kudi sosai." Dafashi Maniru ya yi ya ce "Yusuf wai ba ne man ku i ka fito ba?" "Nema na fito yi mana." "To duk aikin da ya baka kayi ko yankan kaine." Dariya sukayi duka, Maniru ya ja hannun sa suka fice ya rakashi bakin titi ya hau mota shi kuma ya koma bakin aikin sa. Mama ce ta samu Khadija a aki tana zaune ta yi tagumi, dariya ta yi ta ce "Yarinya idan zaki kwantar da hankalin ki, ki kwantar domin aikin gama ya gama ubanki yaga ku i ya badake." Hawayen fuskar ta ta shafe ta ce "Yanzu rashin galibuna har ya kai ayi mun irin wannan auran da ko kaza me gata baza a mata shiba, bakusan mutum ba, sama taka yazo kuma ku bashi aure na." Tsaki Mama ta yi ta ce "Mtssss wa ya ce dake bansa Alhaji Nasir, to na sanshi ciki da bai har dalilin auran ki ma na sani, sabuda ni nace ya zo gurin ki zai samu abuda ya ke so." Kuka sosai Khadija tasaka ta kasa cewa komai, ita kuwa Mama dariya ta ke yi ta ce "Ba yau zaki yi kuka ba sai nan da kwana 6 zakiyi kuka mai dalili yarinya. Bama wannan abun ya kawoni gurin ki ba ubanki ya bar miki gugar kayansa ya ce kan ya dawo kiyi masa, idan kuma bazakiyi ba kedashi idan ya dawo." Tana gama fa in haka ta fice tabar akin tabar Khadija na gurzar kukanta. Suna zaune a tsakar gidan ya shigo gidan da salama, Atine abokiyar hayar su Hauwa ita ta amsa salamar amma Hauwa ko kallon inda Yusuf ya ke batayi ba, girgiza kai kawai ya yi ya shige aki. Tashi ta yi ta bishi cikin akin ta tsaya a kansa ta ce "To me mataciyar zuciya, na auka kayi zuciya ka tafi ne man nakai shine ka dawo hannu rabana." Tashi ya yi ya tsaya a gaban ta ya ce "Hauwa kenan, da kin kwantar da hankalin ki na samu aikin yi yau na wuce gorin da kike mun, yanzu zan iya ri e iyalina da kaina." Shewa Hauwa ta yi ta ce "Ahayee Allah ya nuna mun ranar da zaka kawo cefane a gidan nan Yusuf." Dariya ya yi ya ce "Zaki gani kuwa." Daga haka bai sake kulata ba ita kuma ta zauna sai ana nan magan ganu shidai Yusuf bace mata ci kanki ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Najima da wannan tunanin Salim anya ba zancan ka gaskiya ba ne, Alhaji Nasir yanada alaka da kungiyoyin asiri." Murmushin ta kaici Salim ya yi ya ce "Na jima ina bincike akan sa, kuma bazan daina ba harsai na gano asalin shiwaye." "Amma baka tsoro garin bincike wani abu ya sameka." "Isyaku kenan, kaine kake tsoran wannan yaron ni baya bani tsoro kuma sai na nuna masa mu rigashi zuwa duniya." "To shikenan Allah ya taimaka." "Amin." Salim ya ce suka cigaba da tattauna yadda zasu kawo arshen Nasir. Abida ce ta shigo gidan bakinta auke da salama, Mama Lube tana tsakar gidan amma ko kallon arziki bata mataba. Da yake Abida tasan hali, kawai saita huce akin da tasan anan Khadija take zama. A zaune ta tadda ita tana ta aikin kuka, da sauri ta zauna kusa da ita ta ce "Lafiya Khadija meya faru?" Cikin kuka Khadija ta ce "Ina cikin tashin hankali Abida." "Me yake faruwa, tunda kika zo na baki ku in tarunki kikace zakije siyo hijab in makaranta baki sake komawa gidan mu ba, yau kuma naje school naga baki zoba, shiyasa nace akwai matsala bari na dubaki." Ajiyar zuciya Khadija ta yi ta gyara zama, nan ta sanar da Abida duk abunda ya ke faruwa da auran da za'a mata. Salati Abida ta yi ta ce "Tunda nake ban taba jin irin wannan abun ba, amma ke wane mataki kika auka?" Ajiyar zuciya Khadija ta yi ta ce "Wane irin mataki kuma Abida." "Haba Khadija da zama zakiyi a lalata rayuwar ki a banza, ai ba bari zakiyi ba, akwai hanyar da zamubi mu samu mafita." Cikin zakuwa Khadija ta ce "Wace hanya kike tunani?" Abida zatayi magana, Mama ta shigo ta ce "To hakima, gidan ubakin kine nan da zaki shigo ba salama ba gaisuwa ki shige ciki sabuda kin isa." "Haba Mama Lebe, naga nayi salama kinaji amma baki amsa ba." "To bazan amsabar shugaban marasa kunya, to wallahi tunkafin ranki ya aci ma, ki tashi ki fitar mun daga gida." Khadija ce ta yi magana "Haba Mama dan Allah ki rabu da ita, ko bakisan Abida ba ai bazaki mata haka ba bare kinsanta kinsan matsayin ta a gurina." "Dalla malama rufemun baki, uban ku zan ha a inci, idan bata tashi tabar gidan nan ba." Abida zatayi magana, Khadija ta ce "Dan Allah Abida kiyi hakuri, kije zamuyi magana daga baya." "Hmm to shikenan." Abida ta ce, ta fice suna hararar juna da Mama Lube. Tana fita Baba ya na shigowa ya ce "Wannan ba Abida ce ta fita ba?" "Ita ce mana." "Amma ta wuce ko gaidani ba ta yi ba." "Ai bazata gaida kaiba nima yanzu ta gama yimun rashin kunya ta fita,dan na mata magana, tazo ta sa wannan saunar a gaba tana hure mata kune." Kai Baba ya girgiza ya ce "To daga yau na haram ta mata zuwa gida na, kuma itama wannan yarinyar Khadija ban yarda ta sake fita ko ofar gida ba, kuma aure ba fashi dan ko yau yaron ya kirani munyi maganar abuncin biki duk zai kawo." Murmushi Mama ta yi ta ce "To Alhadulilah, Allah ya nuna mana bikin lafiya." "Amin." Baba ya ce. Mama ta zuba masa ruwan alwala a buta ya amsa ya yi alwalar ya fice daga gidan ya nufi Masalaci. Washe gari. Gari na wayewa Yusuf ya tafi gidan Alhaji Nasir, ba a gida ya kwana ba amma haka ya zauna jiransa har 11:40am sannan ya dawo. Falon gidan Nasir ya sa aka kawo shi ya shigo yana ta kale-kale, bayan sun gaisa, Nasir ya yi ajiyar zuciya ya ce "Malam Yusuf, nasan kana bu atar ku i, Allah ya sa ka shirya samunsu ko ta wace hanya?" "Ranka shi da e indai zan cida iyali ai Alhadulilah burina ya cika." Saida Nasir ya yi jim kafin ya ce "Ni mutum ne da ba kowane yasan ni waye ba, amma idan har ka sake kasan ni waye to dole kashigo cikin tafiyata ka amunce?" Yusuf baiyi tunanin komai ba ya ce "Na amince." "Good, ina da aiki guda biyu da zan baka, aya na wane aya na abokiyar aikina. Kafin kayi wannan kana bu atar kasan ni waye..........! Comments And Share Ga masu shawara ko arin haske ga number ta 08166077167 nagode By *XAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Pree book Episode 5 "Hakane Alhaji." Tashi Nasir ya yi yana zagaye falon kafin ya fuskan ci Yusuf ya ce "Maganar gaskiya ni ba aikin Company Kalama nake ba hasalima company nin na yaro na ne a kungiya. Na kasan ce na taso bani da gatan uwa bare na uba daga baya ma na rasa su gaba aya da ina rayuwa a garin mu can Katsina da zaman can ya gagareni shine da dawo Kano da zama, nayi sana'a kala-kala amma ba nasara, ta hanyar aboki na mukaje Kaduna, nan naga cajin a gurin wani uban gidan mu yana bamu ku i sosai, wata rana ya ta a aika mu gidan sa, da mukaje matarsa ta gani tunda ga lokacin ta like mun, tun ba ta yi nasara a kaina ba har Allah ya bata sa'a taci galaba a kaina, tashiga jikina sosai tasan komai nawa kuma tasan damuwa ta nayi ku i, shine watarana ta jani wani gida ta ce ga ida zan samu ku i ko wane irin ne, mutane ne irina amma kallon Aljanu nake musu har takai, kaina ya juye na rasa abunda ke faruwa dani a gidan, ashe kungiya ce ta asiri ta kawoni, sumun bayani zan samu ku i masu yawa ta hanya me sauki, amma saina kikaye abu guda uku. Dole idan kungiya ta bu aci kayi abu sai kayi, kuma idai ka shiga kungiya ba fita, kuma baza ka fitar sa sirrin kungiyaba, idan ka sake ka karya doka aya daga ciki, to zaka iya rasa rayuwar ka, ko kazama galimar matsafiya, ma'ana zasuyi wani sidabarun da jininka. Na harda da wannan tsarin ban bar gidan ba saida miliyan 10." Ido Yusuf ya zaro ya ce "What miliyan Goma fa." Kai Nasir ya gyada ya ce "Tunda lokacin nayi mahaukatan ku i na dawo Kano da zama sabuda yawanci yan kungiya ba a zaune muke jaha guda ba kowa da inda yake amma duk wata muna zuwa duk wanda aiki ya biyo ta kansa za'a bashi kafin wani watan ya tabbatar ya yi sabuda tsaro, amma ban ta ajin ace abada jinin wani naka ba ko wani saidai ayika masu hadarin gaske, a kano nasamu matar da ta kwanta mun a rai Nafisa na aureta har ma mun haihu da ita, amma ko sau aya banji anyi magana a kansuba, saidai wannan zaman da mukayi, an bani aikin da dole saina samu yariya budurwa da bata ta a sanin a namiji ba, nayi anfani da ita, da wani sihiri da suka bani da bazan sanar da kai shiba, to na samu yariyar amma ta bani matsala shine na yanke shawarar auranta nan da 5days sabuda saura 7days wata na ya cika." Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke, gaban sa na tsananta fa uwa ya ce "Tunda bakwa kisa nima na amunce." Rugume shi Nasir ya yi ya ce "Nagode abokina." Nan ya zauna ya ce "Nan da kwana biyar in zaka kasan ce a gidan da zankai yariyar sabuda tsaro." "Okay ba damuwa." "Yauwa dama shine aikin nawa, aikin Hajiya Hasina zance ta nemi wani." Jaka ya ako fal da ku i ya mi e wa Yusuf ya ce "Gashi ka hau mota." Jiki na rawa ya amsa ya yi godiya sukayi salama da Nasir ya wuce gida. Da salama ya shiga gidan, kamar yadda ta saba wula an tashi bata amsaba, murmushi ya yi ya riko hannun ta har cikin akin ya zaunar da ita. Baki ta ta e ta ce "Da kana abun arziki sai kamun burga kamar wani abun kirki ka kawo." Murmushi ya yi ya danka mata jakar a nannun ta. Amsa ta yi ta zuge jakar, ido ta zaro ta ce "Nashiga uku Yusuf ai ku i ne a ciki, tsita kayi?." Harara ya wurga mata ya ce "Ba ruwanki da inda na samo, badai burinki a samoba gashi to kiyi abunda zakiyi dasu." Idon Hauwa ya rufe kawai saita fara murna harda rungeme shi tana masa godiya, shidai Yusuf hankalin sa ba a nan ya ke ba yanaga yadda zaiyi ya ceci yariyar mutane da akeso ayi tsafi da kuruciyar ta, so yake ya kubutar da ita koda hakan zaiza ma sanadiyar ajalisa, shiyasa ma ya amunce da zuwansa gidan ranar da za'akai yariyar, dan zai tsara yadda zai gudu da ita kafin Nasir ya yi tsafi da ita. A an garan Abida ma hakan take ta ci alwashi baza ta bari rayuwar Khadija ta lalace a banza ba duk yadda za tayi ta hana auran nan sai ta yi, dan tseratar da awar tata. Yana zaune a falo Anwar yana kan ciyar sa, suna wasa Nafisa ta shigo da salama a bakinta. Kasa-kasa ya amsa ta samu guri ta zauna ta ce "Barka da dare Abu Anwar, yau baza ka fita bane?" Kallo ta ya yi ya ce "Kin gaji da ganina ne?" Kaita girguza, shi kuma ya ce "To kar ki kuskura ki ara yimun irin wannan tanbayar tunda ba'a kanki nake zaune ba." Jiki a sanyaye ta ce "Ba haka bane Abu Anwar kawai kwana biyun nan ina mugayan mafarkai akan ka, shine nake so ka rage fitar daran nan kuma ka tsanan ta addu'a." Ransa ne ya aci ya ce "Kai kulum sai kin sa raina ya aci, hankalin ki yake kwanciya, na fara gajiya da halinki Nafisa, na gaji! Na gaji." Ya arasa maganar kamar zai dake ta, Anwar da ke kan ciyarsa ne ya fashe da kuka, dai-dai lokacin da kwala ta sako a idon mahaifiyar tasa. Tsaki Nasir ya ja ya auki Anwar ya shige aki da shi yana rarrashinsa. Da kallo Nafisa ta bisu, halin Nasir ya fara isarta ita ba jaka ba ko baiwa, amma yake azabtar da ita haka, itama a fili ta ce "Na gaji Abu Anwar na gaji wallahi." Da gudu ta ta shi ta shige nata akin ta na kuka. Kwana biyu a tsakani Abida ta je ta shigar da arar Baba a police station a madadin Khadija, har gida police suka zo suka tafi da Baba da Khadija, itama Mama ta ce bataga ta zama ba ta rufa mayafi tabi bayansu. Acan suka tadda Abida aikuwa tasha tsinuwa da zagi, saida police suka takawa Mama burki ta daina magana, nan D.P.O ya ce "Wannan yarinyar ta kawo arar ka, gurin mu sabuda auran dole da zakayiwa arka." Cikin Masifa Mama ta ce "To uwar ta ce, ta haifa mana ita." Nan D.P.O ya ce ayi waje da Mama ya ce da Baba dole a fasa wannan aure. Baba ya na jin haka ya kira Nasir ya sanar dashi duk abuda yake faruwa. D.P.O aka kira a waya nan aka sanar da shi ya salami arar su Baba yan zu subar gurin, ba musu ya salami su Baba suka tafi. Dan bakin ciki, saida Abida ta yi kuka ta na tunanin yanzu wa ce hanya za tabi gurin ceton Khadija. Siyan awara ta fito, tana ta fiya saitaga kamar ana binta a baya dan haka ta tsaya ta waiwaya, abuda ta gani ne ya yi mugun aga mata hankali bata san sanda ta kurma uban ihuba na...............! Comments And Share Gamasu shawara ko arin haske ga number ta 08166077167 nagode By *XAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Pree book Episode 6 Na neman agaji, amma ba wanda ya jita har suka araso inda ta ke suka zagaye ta. Wanda ya zare wu a a hannusa ne ya matsa har inda take ya nuna ta da wu ar ya ce "Dama ina so na samu damar da zan kama wani munafiki me irin halinki na masa kisan gilar da zai zama izina ga masu hali irin naki na munafun ci." Jikin ta na rawa ta ce "Ku suwaye? kuma me na muku?" Tsawa ya daka mata ya ce "Rufe mana baki munafuka, to ko ke oga Nasir ya ce zai aura har kina da kwariñ gwuwar kai iyayen ki ara, bare na shishigi wai ke kin kawo arfi ko?" Sai yanzu Abida ta gane abuda ke shin faruwa da ita, nan ta fara tunanin yadda zata tseratar da rayuwar ta. Mutumin ne ya ce da sauran su rike ta ya yanka ma ogaranta, suka yi yadda ya ce, ya nufota, Abida ta ringa kiran sunan Allah, sai yaji wayarsa ta na ruri ya zaro ya duba yaga Alhaji Nasir ne. Da sauri ya aga Nasir ya ce da shi "Ina yariyar ta ke?" "Gata rakan shi da e." Bata wayar, karawa Abida wayar ya yi a kune, saida Nasir ya jima kafin ya ce "A rayuwata na tsani wanda zai shiga tsakanina da abunda nake so, kina so ki shiga tsakanina da Khadija, to ki sani bazaki kai labari ba. Namiki uzuri yanzu sabuda bakisan ni waye ba amma nan gaba na ara kamaki da irin wannan laifin, hmmm sai kinyi dana sanin zuwanki duniya." Fusge wayar daga kunan taya yi ya kara a nasa kunan ya ce "Kabari kawai mu wanka munafuka yanzu." "A'a ku rabu da ita kawai." "Yadda ka ce haka za'ayi rankashi da e." Nasir ya na kashe wayar yaiwa sauran alama da hannu duk suka watse suka bar gurin. Da mugun gudu Abida tabar gurin. A firgice ta fa a gidan su, da gudu ta shige akin su, ta zube akan kujera tana wani irin nufashi, yau taga mutuwa iri- iri. Ba abunda jikinta ya keyi sai rawa, gumi kuwa kamar wadda aka wanketa da ruwa, hawaye wani na korar wani. Duk da halin da tashiga yanzu bai hanata tunanin ceton awar tata ba, musaman da taga abunda ya faru yanzu, tasan auran Khadija da lauje cikin na i, amma tayi al airin saita gano ko mene kuma ta kawo arshensa. Yau Yusuf ya koma gidan Nasir sabuda ya bu aci ganin sa. Bayan ya je gidan suka fita tare da Yusuf. Gidan Hajiya Hasina sukaje, taji da in ganin su da Yusuf, kuma ta yiwa Yusuf kyautar mota sabuwa, sannan ta ce ya shirya wannan satin zasuje Kaduna meeting za'a gabatar dashi a kungiya, ya yi godiya suka ta fi da Nasir, ba gida suka tafi ba, wani gida sukaje da Nasir suka fito Yusuf ya na arewa gidan kallo har suka shiga falon, gidan ya ha u sosai, Nasir ya kale shi ya ce "Aboki, nan ne gidan da za'a kawo yariyar." Hakan nan Yusuf ya ji gaban sa ya fa i, ya a alo murmushi ya ce "Masha Allah, ya yi kyau." Ido Nasir ya lumshe ya ce "Daga lokacin da nagama anfani da yariyar zan saketa ne, gidan ya zama malakin ka." Dariyar arfin hali Yusuf ya yi ya ce "Nagode sosai Allah ya ara arziki." "Bakaga komai ba, sai munje Kaduna zakaga yadda za'a karamaka." Ya na ya e suka zaga gidan lugu da sako, Yusuf yana karantar gidan ciki da bansa. Bayan sun gama zagaye gidan suka fito Nasir ya maida Yusuf gida ya wuce, driver ya kawowa Yusuf motarsa har gida. Jikin sa duk a sanyaye ya shiga gidan, Hauwa da fara'a ta tare shi, amma ganin yadda jikin sa yake a sanyaye ya sa duk itama jikinta ya yi sakwal. Kusa dashi ta samu ta zauna ta kamo hannun sa ta ce "Lafiya kuwa?" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Ba komai." Bata gamsuba dan haka ta ce "A'a Yusuf akwai abunda yake damunka." Hararar da ya watsa mata ce tasa ta saurin sakinsa, ya mi e tsaye ya na zagaye akin kafin ya juyo ya fuskan ce ta ya ce "Lokacin da bani da ku i burina be wuce na samu ku i ko ta wace hanya bane, amma yanzu na fara gane kuskure na, sabuda na gane wasu ku in masifa ne." Ya tako har inda take ya ajiye mata key in motar da Hajiya Hasina ta bashi ya ce "Jiya na samo ku i yau mota, amma bazan ci komai a ciki ba, ke kika takura na nemo ku i koda sata zanyi dan haka gasu nan ki taci suyi miki maganin da zasu yi miki." Hawaye ne suka wanke mata fuska ta ce "Dan Allah Yusuf karka sakeni dan kayi arziki, ka rufamun asiri abuda ya faru a baya kuskure ne in sha Allah haka bazata sake faruwa ba." Kallo mamaki Yusuf ya ke binta dashi ya yi murmushin ta kaici, ya kula inda yake nusar da Hauwa daban ida tasa gaba daban, itadai ku i take yiwama ba inda ya samo ku i ba. Sabuda takaici kasa cemata ala ya yi yai ficewarsa ya barta a akin. Tunda ga wannan rana Nasir baya fita ko ina saida Yusuf, sabuda ya yarda dashi kuma dama bashida wani an uwa ko aboki, Nafisa ce kawai dashi itakuma girman kansa bazai bari ya zauna ma suyi hiraba. Gobe ne aurin auran Khadija da Nasir. Kulum Khadija cikin addu'a take Allah ya kareta daga sharin mutum da na aljan. Abida tun ranar da abun ya faru bata sake fita ko zaure ba sai yau ta fito tana so duk rintsi taga Khadija dan tana son suyi magana da ita. Gidan ya fara cika da an uwa ana ta gyara kayan miyar biki, ana shewa, Zuruf ba wanda ya sani Abida ta shige akin Khadija. Tana kwance duk ta rame ta ba ance, tana ganin Abida ta tashi da sauri ta rungume ta ta saki kuka me sauti. Itama Abida hawaye takeyi na tausayin Khadija, zama sukayi Abida cikin rarrashi ta ce "Kiyi hakuri Khadija komai yai rintsi maganin sa Allah, kowane bawa akwai kaddararsa a rayuwa me kyau ko mara kyau, kiyi kokari ki cinye wannan jarabawar taki Khadija." Cikin kuka Khadija ta ce "Ina cikin wani hali Abida, gashi bani da me rarrashina ko tausata ba me bani shawara, ya akeso nayi da rayuwa ta, kina kallo mutumin da ban ta a gani ba shine ya kawo miliyoyin ku i gidan nan zai aure ni cikin sati guda, ko mahaukaci yaji haka ai yasan AURAN MANUFA ne wannan, amma idon kowa ya rufe wai arziki ne daga Allah shidama aure lokaci ne." Kamo hannun Abida ta yi ta cigaba da cewa "Nifa auran nan zargin Mama nakeyi, dan abaya ta ta a takura mun akan wani Alhaji yace ya na so na zan rakashi wani guri kwana aya zamuyi mu dawo. Da nace mata bazan iya ba, shine ta sakoni a gaba ta hanani sakat, to tunda wannan bawan Allah ya zo gurin Baba bata sake tada wancan zancen ba." Kai Abida ta gyada ta ce "Tabbas zancen ki gaskiya ne, ba zargi bane hakane, amma zamuyi wa tufakar hanci." Sun jima suna tsara yadda zasuyi, hankali Khadija ya kwata sosai da shawarar Abida, cikin farin ciki sukayi salama Abida ta fice daga gidan ba tare da kowa ya ankaraba. Gabansa ta zo ta tareshi da uban gudu tana huci kamar ranta zai fita ta rirri e shi tana haki ta ce "Ka taimake ni zai kashe ni." Kallon wanda ya biyo budurwar ya yi Mutum ne amma fuskarsa kamar ta aljanu, addu'a ya farayi da karanto ayatul kursiyo, sai yaga mutumin ya fara ja da baya yana cewa "A rayuwata na tsani wanda zai shiga tsakanina da abunda nake so, kana so ka shiga tsakanina da Khadija, to ka sani bazaka kai labari ba, dan kaima kasheka zanyi." Yana gama fa in haka ya watso musu wata wuta kansu................ Gamasu shawara ko arin haske ga number ta 08166077167 Comments And Share By *XAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Pree book Episode 7 A firgice ya farka daga mafarkin da yakeyi, huci kawai yakeyi yana ganin mafarkin da ya yi kamar gaske, gumine kawai yake keto masa cike da tashin hankali, Hauwa da ke kusa dashi tana baccin ta hankali wance ya kalla, janyeta ya yi daga jikinsa, ya gyara mata kwanciyar ta, sannan ya tashi ya yo alwala, ya tada sallah. Nafila ya yi ya auko alqur'ani me girma ya fara karan tawa, saida ya yi izu biyu ya rufeshi, ya daga hannu yana rokon Allah ya tsare shi, da baiwarsa da take cikin wani hali kuma ya bashi ikon cetonta. Lokacin daya gama addu'ar har an fara kiran sallar Asuba dan haka raka'atul fijir ya ora, bayan ya idar ya huce masjid. Saida gari ya waye ya dawo gidan, har lokacin Hauwa bata tashi ba. Tashin ta ya yi, ta tashi ta yi sallah amma saita ara gyara kwaciya, ya kalli agogo ya ga 6:30am tayi rabuwa yai da ita, ya zauna ya yi tagumi, yana jin zuciyar sa na tsinkewa, idan ya tuna yaune AURAN SHIRIN da Nasir ya shirya, duk da sanyin asuba da ke ratsa ko ina amma shi gumi ya keyi, ya rasa wazai samu ya bashi shawara yadda zaiyi ya ceci baiwar Allah, ya fitar da ita daga wannan tugun da ake shirya wa dan a kasara rayuwarta, da baisan RAYUWA ba sai yanzu da ya fita neman halak, sai gashi haram ce ta fara yimasa maraba, idan ya amsheta baiwa kansa adalci ba, dan haka dole ya yi ya i da ita, dan karta kaishi ta baroshi. Zaman duniya lokaci ne an ani kuma da wannan damar zaka gyara lahirar ka da bata da iyaka, taya zai zauna duniyar bai anfane ta ba lahirir ma haka, yau za'a yita ta e dan dole sai ya fito da gaskiyar sa ya rusa tsarin Nasir. Safa da marwa kawai takeyi a cikin akin nata, ta kasa tsaye ta kasa zaune, mugan mafarkan da takeyi akan Nasir na yau yafi na kulum gashi tun jiya bata sashi a idon ta ba, wayar da ke hannun ta taduba kamar ta kirashi amma tana tsoron yin haka. Komawa ta yi bakin gado ta dafe kanta cikin tashin hankali, yazama dole ta gano a hannun wa take rayuwa, idan iyayen ta sun gaza nema mata asalin mijin nata to ita zata nema da kanta dan itace a ruya, yanzu yadda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare kar shima Nasir yana daga cikin masu garkuwa da mutane. Gabanta na tsanan ta fa uwa ta lalubo number sa ta kirashi. Har ta katse bai auka ba, hakan ya sa ta sake kiransa a karo na biyu, sai da ta kusa tsinkewa ya auka. "Lafiya?" Muryarta na rawa ta ce "Umm dama gani nayi baka dawo ba." "Mtssss da yau na fara fita nakai haka ban dawo ba, kinsan basan bana son shishigi a RAYUWA ta ko." Rasa abu da zata ce dashi ta yi, tana tsoron fa a masa gaskiya mafarkin da ta yi daran jiya, tasan ranta ne zai aci a banza. Dabara ce ta zo mata ta yi saurin cewa "Dama Anwar ne yake zazza i kuma naga gari ya waye har sha aya ta wuce baka dawo ba." "Ayyah ki duba aki na akwai maganin zazza i ki bashi." Bai jira ta yi magana ba, ya kashe wayar. Ajiyar zuciya ta sauke, ta ji sauki a ranta yanzu da taji lafiyar mijin nata. Dafashi ta yi ta ce "Lafiya kake Yusuf? Yau duk na ganka wani iri." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Bakomai, kina da number Kawu Ya'u ko?" "Eh ina da ita." Wayarta ya ako ya auki number Kawu Ya'u ya bata abarta, ya ce "Ina son mukoma kura yau." Cike da Mamaki take kallon sa ta ce "Kura fa kace Yusuf, ka manta bada alar da ka baro a can ka dawo nan." "Bazaki gane ba, ki shirya da yara ba tare zamu tafi ba, ku yanzu zaku tafi ni kuma sai zuwa dare, karki sake ki fa awa kowa ga inda zaki je." Baki ta turo ta ce "Gaskiya bazan koma kura da zama ba ma, na riga na saba da nan wallahi." Murmushin takai ci ya yi ya ce "Ina ku in da na baki?" "Gasu." "To bani abuna ki zauna a nan, in kuma kina so ki ri e ku in to zaki koma Kura." Da yake Hauwa shashasha ce, kawai sata yarda zata tafi da ku in, bata tuhumishi dalili ko ku in ma na satane ba a'a ita ta ku i takeyi. Shirya kayansu sukayi da kanshi ya kaisu tasha sukahau motar kura suka tafi, shikuma ya je ya saida motar da Hajiya Hasina ta bashi ya ajiye ku in a inda ba wanda ya sani. Taron biki akeyi amma gaba aya bata fahimtar komai, duk da Abida tana kwantar mata da hankali amma ta gaza samun nutsuwa, Mama Lube, sai shiga ake ana fita, da yake dangin mahaifiyar Khadija basu san da bikin ba, suna can katsina kuma ba wanda yaje ya sanar dasu, dan haka taron na Mama Lube ne ita ka ai sai rawar kai aketayi ana auran yar kishiya. Har aka daura auran Khadija bata sani ba dan tana kule a akin ta, tanata faman kuka. Yana dawowa daga saida motar yaji wayarsa na ruri, na duba yaga Nasir ne, gabansa na fa uwa ya auka ya kara a kune tare da yin salama. Nasir bai amsa ba yace "Naji labarin kakai iyalinka tasha, ko da matsala ne?" Saida nunfashin Yusuf ya auki na wasu an da i u, kafin ya sauke wani nunfashi ya ce "Eh anyi rasuwa ne a kauye." "Ayyah, dama ina gidan da na kai ka ranan kaje da motarka ka aukomun yariyar nan." Muryar Yusuf na rawa ya ce "Ai ban iya tukiba Alhaji, kuma inada shawara mezai hana a tura motoci harda yan rakiyar Amarya sabuda zargi." "A'a Yusuf, iya yaune fa ba a ganina zasuyi ba, kawai ka share, kazo muje tare yanzu ina jiranka a gida." Bai jira amsar Yusuf ba ya kashe wayar. Gumi Yusuf ya ringa sharewa, zuciyarsa ta karaya sosai da lamarin Nasir, tayaya zai iya guduwa da Khadija ba tare da ya gano inda suke ba? Tanbayar da ya kasa bawa kansa amsarta kenan. Har gida ya je suka tafi gidan su Khadija ta re. Yana tsawa a kofar gidan ya kira Mama, fitowa ta yi, ya mata maganar a fito da Khadija. Ba musu ta koma cikin gidan ta kamo hannun Khadija ta na mata waka da keta ta kawota har bakin motar Nasir. Abida da ta jima a tsaye tana jiran fitowar su ta matsa jikin motar ta ce "Inaso na raka Aminiyata har gidan mijinta." Harara Mama take bita da ita shi kuma Nasir da yake cikin motar da ke auke da bakin gilas, karantar Abida ya keyi, shikuwa Yusuf tunda yariyar ta fito hankali sa yake kanta yanajin wata irin fa uwar gaba da bai ta a jin irin taba............... Comments And Share By *XAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Pree book Episode 8 Mama Lube cikin masifa ta ce "To koni uwarta bazan raka taba sabuda daga nan, Abuja sukayi, saike uwar shishigi." Turo baki Abida ta yi ta ce "Ko birnin sin za'a kai mutum ai a ha a shi da an rakiya bare nan-nan Abuja." Mama zatayi magana, Nasir ya bu e murfin motar ya fito ya ce "Abida ko? To bazaki bita ba." Yadda yake kallon ta ne ya sa ta tuna da barazanar da ya mata a baya dan haka ta matsa baya da sauri, shi kuma ya kamo hannun Khadija ya sata a motar ya rufe ya shiga azaunin driver ya figi motar ya bar gurin. Tunda suka tafi ba wanda ya ce ala sai kukan Khadija asa- asa, bamai rarrashinta a cikin su, Yusuf kuwa har cikin ranshi yakejin sautin zazza ar muryar tata da take raira kukan. Parking Nasir ya yi ya fito, shima Yusuf fitowar ya yi, yana kallon gidan da duk ya sauya ga bakin abubuwa da idonsa yake tozali dasu. Nasir ne ya jashi har falon gidan, ya ce "Kada ka damu da mutanan da kagani a nan, sabuda yanayin aikin ne saida haka, zaka zauna mu kwana anan zuwa da safe ka maida yariyar nan gidan su da takardar sakinta." Jikin Yusuf a sanyaye ya ce "Okay to." Komawa Nasir ya yi ya ce Khadija ta fito daga mota, ta biyo shi, a falon suka tadda Yusuf wanda yake tabin Khadija da kallon tausayi, zuwa yanzu duk jikin sa ya yi sanyi, ya sare da lamarin Nasir. Zama Nasir ya yi, ya daka mata tsawa ya ce, ta zauna, ba musu ta samu guri ta zauna, ya ce "Duk da zama ki a gidan nan ba mai tsayi bane, banaso musu ko shishigi, anfanin ki iya yaune zuwa gobe, zaki koma inda kika fito." Cikin kwarin guwa Khadija ta dube shi ta ce "Kana da hali da damar da zakayi duk abun kaga dama a nan duniya, amma kasani akwai lahira kuma akwai hisabi, wallahi duk abunda ka aika ta a duniya dai-dai da sakan aya sai ya yi bayani a gaban ubangiji, kuma ka sani Allah ya halice mu a wannan duniyar ne badan kowa ya zo ya yi abunda yaga dama bane, dan a bauta masa ne, kuma bawa ya nemi lahirar sa. Karka bari karasa duniya lahirar ma haka, kaji tsoron Allah, karka cutar da ni, duk da komai ya sameni laifin iyayena ne amma akwai Allah." Maganar ta, ta daki zuciyar Nasir amma bazai iya ketar ka'idar kungiya ba sabuda idan ya sake jibi, bai cika aikin sa ba, to matakin da kungiya zata dauka a kansa ba mai kyau bane, dan haka cikin acin rai ya ce "Ya isa, waya ce miki duk bansan wannan ba, to ki adana kalamanki dan nan gaba zasu iya yimiki anfani." Yana gama fadin haka ya nuna mata hani aki ya ce "Ga akin ki idan kinga dama kishiga." Daga haka ya fice ya bar su da Yusuf a zaune wadda zuciyar sa ta ke ta bugawa, yana so ya mata magana amma ya na tsoron kar wani tarkon Nasir ya sa musu dan haka ya yi shiru ya rabuda ita. Kamar yadda Yusuf ya yi tunani hakan ce ta kasan ce domin kuwa, Nasir ya na kallon duk abunda sukeyi ta cikin camera. Ya kula yau Yusuf duk ya sauya kuma duk a firgice ya ke dashi, shiyasa ya yi tunanin ya shirya wani abu, da yaga ba abuda suka tattauna Yusuf din ma ya bar gurin sai ankalinsa ya kwanta ya rage zargin da yakeyi akan Yusuf in. Saida Nasir ya dawo sannan Khadija ta tashi ta shiga akin da ya nuna mata azu. arwa akin kallo ta yi ya hadu sosai, kawar da wannan tunanin ta yi ta zauna gefan gado, a jikin ta ta lalubo wata waya, wadda Abida ta bata. Kiran layin Abidar ta yi, bugu biyu ta aga. "Hello Khadija, kun isa gidan?" "Mun isa Abida, amma a garin kano ne ba Abuja ba kamar yadda Mama Lube ta ce." "Nasan za'a rina, kawai ba'aso asan inda aka kaiki ne, amma kiyi kokari ki samo mana wata makama da zamusan a ina kike?" "Okay zanyi kokari yanzu nasan a inda nake." Kashe wayar Khadija ta yi ta zuge window in akin ta fara kale-kale, ta na so ta gano wani abu amma ta kasa. Nasir ne ya dubi Yusuf ya ce "Zanje gidan Hajiya Hasina, zamu taho da su baki aya dan gudanar da aikin mu, kaima zaka shiga ciki ayi da kai, kafin na dawo ka kulamun da ajiya ta." Murmushi Yusuf ya a alo ya ce "To saika dawo." Fita Nasir ya yi Yana fita Yusuf ya leka ta, taga ya tabbatar da fitar sa, da sauri ya shiga akin da Khadija ta ke. Ta na ganin sa ta mi e a tsorace, jikin sa na rawa ya ce. "Ba cutar dake zanyi ba taimakon ki zanyi, me gidan nan ya kawoki ne domin ya yi anfani da kuruciyar ki ya yi wani tsafi da suke samun ku i, amma bazan bari haka ta faruba, ki biyoni akwai hanyar da na gani a bayan gidan nan mugudu, tunkan ya dawo." Girgiza kai Khadija ta yi ta ce "Bazan iya binka ba, ka tafi kawai, ban sanka ba bazan bika ka cutar da niba, nayi hakuri da yadda Allah ya yi dani." Cikin fa a Yusuf ya ce "Ina o arin tseratar da mutuncin ki, kina cewa baza ki bini ba, kiyar da dani wallahi ba cutar dake zanyi ba." Ja da baya ta farayi ta na girgiza zai. Ran Yusuf ya yi matu ar aci, zaiyi yi tafiyar sa ya barta, amma saiya tuna dan Allah, zai taimake ta. Kauda komai ya yi a ransa ya fisgota da arfi ya yi waje da ita. Ta na ganin da gaske fitar da ita zaiyi saita bishi a baya suka fita ta ofar baya. Turus suka tsaya ganin Nasir a gaban su, ya na sakar musu murmushin mugunta. Kafin kace me, an zagaye su. Murmushi Nasir ya yi ya ce "Najima a raina ina wannan tunani saidai, ba wanda yake nasara a kaina, kuma ba wanda ya isa ya hanani abunda naga dama dan haka kashinku ya bushe.............. Gamasu gyara ko arin haske ga number ta 08166077167 Nagode Comments And Share By *ZAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Pree book Episode 9 Acikin arfin hali Yusuf ya ce "Ba abunda ka isa ka mana Nasir ka sani Allah ba zai baka nasara akan wannan yarinyar ba, kuma idai ina raye baka isa ka ida mugun nufika a kantaba." "Idan ka mutu fa?" Nasir ya fa a yana ha e rai "Baka isa ka mun abunda Allah bai munba inkaga na mutu to kwanana ya are." Kafa a ya aga alamar ko a jikin sa. Yai wa yarasa nuni da su kamo masa Yusuf. Khadija da ke rike a hannun sa, ta ara a ameshi ta na Girgiza kai. Mutum biyu ne suka araso inda suke suka fara jan Yusuf, kuka me sauti Khadija ta saka, ta na cewa "Dan Allah karku cutar dashi ku rabu dashi dan Allah." Wani irin tu o in ba in ciki ne ya rufe Nasir gani Khadija ta i sakin Yusuf, a fusace ya fara takowa inda suke. Ihu suka faraji da jiniya ta na tashi, nan yaran gurin suka fara gudu suna barin gurin, motocin police ne suka araso gurin kafin suyi wani abun kowa ya kama gabansa, ba Nasir ba su Yusuf, cike da mamaki, Abida ta sako daga motar police in ta na kallon filin gurin ba kowa, itadai idon ta ya hango mata su Khadija da Nasir, amma kamar wanda sukayi layar zana duk sun ace. Police in ne suka bi bayan wanda suka gudu an kama wasu, wasu sun tsere, haka suka bar gurin ita ma Abida tabar gurin jiki a sanyaye. Hauwa ta sauka a kura lafiya, kai tsaye gidan iyayen Yusuf ta tafi. Da salama ta shiga gidan. Inna da ke hura wuta ta amsa da mamaki ta ce "Hauwa meya dawo daku cikin garin nan?" Baki ta turo ta ce "Nima bansan dalilin sa na cewa mu taho ba." Jiki a sanyaye Inna ta ce "To lalanku." Ta ako musu ta barma ta shiga da kayan su ciki, ta zo suka gaisa, Hauwa ta ce "Ina Kawu da Murja?" "Murja ta je makaranta shi kuma Malam ya je kasuwa." Hirar su suka cigaba dayi ta yaushe gamo. Murja ce ta shigo gidan da kayan makaranta a jikinta, ta sakalo jakarta, baki ta saki ta na zaro ido ta ce "Hauwa meya dawo daku garin nan kura bata gama lafawa ba, wallahi yanzu naga Haliru ya huce ta ofar gidan nan." Kirji Hauwa ta dafe ta ce "Nashiga uku Allah ya sa baisan muzo garin nan ba." "Gaskiya bai kamata kuzo yanzu ba kinsa hali Haliru zai kashe yaya Yusuf akan gabar su, kuma ba abuda za'ayi tunda baban sane megari." Itadai Hauwa duk a tsorace ta ke tarasa ta inda zata fara ma, wayar ta ta lalubo ta fara kiran Yusuf amma a kashe tayi jifa da wayar ta na cewa "Nakirashi a kashe bare nace karya sake yazo garin nan kar wani abu ya sameshi." Jugum-jugum sukayi kowa ya rasa abun da ke masa da i. Sai bayan magrib Kawu ya dawo daga kasuwa, shima ya yi mamakin ganin Hauwa, ya tanbaye ta Yusuf ta ce itama ba tasan inda ya keba itadai ya ce mata ta taho shima zai biyota daga baya. "Allah ya kyauta." Kawu ya ce sannan ya ce kar asake wani ya fa i zuwan Hauwa a cikin gari sabuda tsaro suma yaran nata kar a bari su ringa fita. Da to suka bishi dan kowa ya gamsu da maganar Kawun. Gumi ne kawai yake keto masa, yana kallon Lailah da take zagaye akin, da fashi Alhaji Nuhu ya yi cikin matsanacin tashin hankali ya ce "Yanzu mene abunyi?" Kansa a asa ya kasa furta komai, Laila da ke tsaye ta ce "Haba Nasir ya mun taru a kanka dan mu nemi manufa, amma ka i yiwa kowa magana." Hajiya Hasina da take kusa da Nasir cikin rarrashi ta ce "Bamu da lokaci Nasir, idan wannan yariyar ta kubce a daran yau a samu wata sabuda akwai matsala, idan ba'ayiwa dodo abunda yake so ba." Sai lokacin Nasir ya bu e baki ya ce "Yanzu ku acikin ku ba wanda zamu samu abunda muke nema a gurin Khadija." Harara Laila ta watsa masa ta ce "Taya zaka samu wannan a gurin mu bayan mu ba Yammata ba." Jinjina kai ya yi ya ce "Gara Hajiya Hasina ta yi aure harda yara kefa?" Shiru Laila ta yi, Alhaji Hassan ya ce "Nasir duk bamu da lokacin wannan, maganar mafita mukeyi ba kai ka ai abun ya shafa ba." Kallon Alhaji Hassan ya yi ya ce "Mezai hana ka bani arka nayi anfani da ita, nasan dai ita baka bari talalace ba ko?" Tsawa Alhaji Nuhu ya daka masa ya ce "Haba Nasir ka bamu hankalin ka bafa shirme muka zoyi ba." Sumar kansa ya shafa yanajin zuciyarsa na masa zafi. Magana suke amma baya iya gane abunda suke tattaunawa, hankalin sa yanaga Yusuf da Khadija da irin kisan da zai musu in suka shigo hannun sa. Khadija ya kalla cikin tashin hankali ganin halinda take ci na.............! Comments And Share By *ZAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 10 Na damuwa sai kuka takeyi, jikin sa duk ya yi sanya. Amma cikin ransa godiya keyi ga Allah daya ku utar da su a hannun Nasir, da hayaniya ba ta tashi sun tsereba, da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba, a fili ya furta "Alhadulilah." Ya dubi Khadija dake kuka ya ce "Ya kamata ki daina wannan kukan haka, kiciga da addu'a Allah ya tsare mana gaba, yanzu komai ya huce, bazan maidake gida ba kura zamu tafi gidan iyaye na har komai ya lafa saiki koma gida." Muryar ta na rawa ta ce "Nagode sosai da taimakon ka gareni, Allah yasaka da alkairi." Murmushi ya sakar mata, itama ta maida masa da martanin murmushin nasa. Motar kura suka hau ta kaisu garin kura lokacin dare ya yi sosai dan haka, da suka shiga gidan ba wanda yasan sun dawo, akin sa kawai ya bu e mata tashiga shi kuma yaje masalaci ya kwana. Da asuba bayan an idar da sallah, kawu suka ha u da Yusuf. Har asa Yusuf ya duka ya gaida kawu, kawu ya amsa da cewa. "Yusuf da hankalin ka kadawo cikin garin nan?" "Lafiya kawu, zan maka bayani mushiga ciki bani ka ai ba ne." Shiga sukayi lokacin Khadija ta idar da sallah kenan, Inna ta taso Hauwa. Hauwa na fitowa ta dafe kirji ta ce "Dan Allah tunda da safe kashigo garin nan ba wanda yasan kazo, ka koma kar Haliru ya ganka ko yaransa." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Malama ki zo muyi magana ba hauka ba, abunda na baro acan yafi na nan muni." arasowa ta yi ta zauna kusa da Inna sai lokacin idon ta ya sauka akan Khadija dake zaune kanta a asa. Gaban ta, taji ya fa i, hakan nan taji wani irin kishi na taso mata. Yusuf ne ya gyaran murya ya ce "Ban so dawowa garin nan ba, amma dole tasa na dayo, kuma da yiyiwar daga nan nasake gaba." Kawu ne ya ce "So muke muji dalilin ka na dawowa garin nan da iyalinka harda wata bakuwa ba." Saida ya sake numfashi ya ce "Tunda na bar garin nan, iftila'i yaketa samuna, mun rayu da Hauwa cikin talauci, tun tana hakuri har takai ta fara cimun mutunci dole tasani fita neman halak." Nan ya kwashe komai da yadda sukayi da Nasir da taimakon da yazo yaiwa Khadija, da zuwan sa garin nan. "Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un!" Kawu ya ringa maimai tawa, ita kuwa Hauwa nadama ce ta kamata, yanzu duk itace sanadin shigar Yusuf cikin wannan halin, Khadija ta ke kallo wadda taketa faman rusa kuka, taji tausayin yariyar amma wani angare na zuciyar ta, cike yake da kishinta duk da taje cewa matar aure ce a halin yanzu. Inna cikin jimami ta ce "Lalai kayi jahadi Yusuf, kuma naji da in sadaukar warka. Kekuma yariya Allah ya tsareki." Muryar Khadija na rawa ta ce "Amin Mama na gode." Murmushi Inna ta yi dan lokaci guda ta ji Khadija ta kwanta mata a rai. Kawu ne ya ce "Kayi dai-dai daka kawo iyalinka gida. Ku cigaba da zama anan gidan har muga abunda hali ya yi. Zamu dage aita addu'a a masalatai da tsangayoyi Allah ya tsare ku. Kuma ku dage da addu'a, in sha Allah komai zai dai-dai ta." "Allah ya sa Kawu nagode." "Bakomai amma ka ringa kula sosai, sabuda wannan yaron Haliru." "In sha Allah kawu." Nan suka cigaba da jajan tawa juna. Suna zaune a wani kango suna zuke-zuke aya daga ciki ya kalli wani wanda ga dukan alamu shine, oga a gurin, ya ce "Gaskiya Yarima ya kamata kayi aure, tunda dai ka rasa wannan yariyar ya dace ka samu wata." Murmushi Haliru ya yi ya ce "Nima ina wannan tunanin ga Baba ya kusa mutuwa, kaga yana mutuwa ni za'a na a matsayin mai gari, kuma ba za'a bani mulki ba sai inada aure, dan haka dole nayi aure kwanan nan." Dariya yaron Haliru ya yi zaiyi magana, wani ya shigo kangon da gudu yana haki ya durkusa gaban Haliru yana haki ya ce "Yarima yanzu na samu labari wannan yaron Yusuf da ya auri Hauwa, ya zo an tabbatar mun an ganshi a masalaci da Asuba." Zabura Haliru ya yi ya tashi tsaye ya ce "Ka tabbatar da abuda kake fa a gaskiya." "Na rantse da Allah da gaske nake." Wani irin ihu Haliru ya yi ya ce "Wihuhuuuu saini Haliru a ga megari Usmanu, saini magajin garin Kura, saini yarima sarkin gobe, idan wannan yaron ya ara kwana a duniya to nine bana raye." Yana gama fa in haka ya yi gaba duk tawagar gurin suka taka masa baya. Yaron dake kusa da ita ta kalla, bacci yakeyi hankali kwance, ita kuwa, tun daran shekaran jiya rabonta na rintsawa. Hakan nan takeji ajikinta ba lafiya ba. Tunda take da Nasir duk yawansa na dare dana rana, bai ta a tafiya ya barsu kwana aya da wuni aya ba tare da yazo inda suke ba sai yau, gashi yanzu ko wayarsa bashiga takeyi ba. Tarasa ina zata sa kanta. Wayar ta dake kan stool ta ako ta ara kiran number Nasir amma a kashe. Batasan sanda hawaye suka wanke mata fuska ba. Yanzu ta ina zata fara neman Nasir? Addu'a ya kamata ki masa. Wani an gare na zuciyar ta ya bata amsa. Bako Salama suka banko, ofar suka shigo gidan, Inna ce kawai a tsakar gidan sai Khadija da take mata wanke-wanke. A tsorace Inna take kallon su Haliru da suke shigowa gidan, salati tasaka da arfi, wanda ya jawo hankalin Murja da Hauwa da suke aki suka fito a guje. Hannu Hauwa ta ora a kai tana cewa "Nashiga uku me yakawo ku gidan nan." Haliru da tunda ya shigo yake kallon Khadija da taketa muzurai, ya dubi Hauwa ya ce "Rufemun baki munafuka ba harda ke aka ha a baki gurin yimun shari ba, to yau nazo aukar fansa, ina lusarin mijin naki yake ya aikasa kiya yanzu." Jikin Inna yana rawa ta ce "Yaro jiya yazo kuma har ya koma kano yau kuyi hakuri yariga ya tafi." Murmushin mugunta Haliru ya yi ya ce "Ashe ya gudu ba matsala zan tafi da wannan bakuwar dan nasan tare suka zo idan yaso shi yadawo ya fansheta." A tare duk suka juya suka kalli Khadija wace keta zubar da kwala...........! Gamasu shawara ko arin haske ga Number ta 08166077167 nagode Comments And Share By *ZAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 11 Haliru bai jira ce warsu ba ya arasa inda Khadija take ya kai hannu zai kamota, kawai sai ya ga an rike hannun nasa. Cike da mamaki ya ago yaga wane me arfin halin ne. Ido suka ha a da Yusuf, wanda ya ke huci, shima Haliru hucin ya keyi. Ya warce hannun sa daga na Yusuf ya ce "Nayi wa kaina alkairin duk randa mukayi ido biyu da kai saina aikaka lahira, inba hakaba bancika jinin Megari Usmanu ba." Murmushin ta kaici Yusuf ya yi ya ce "Idai baka kasheni ba, baka cika dan halak haihuwar Saratu da Usmanu ba." WAIWAYE ADON TAFIYA Shekarun baya da suka huce, Haliru da Yusuf aminan junane, har makaranta tare suke zuwa har suka gama. Tunda sukagama Secondary school, Haliru ya ha u da miyagun abokai, tun Yusuf yana masa nasiya har ya gaji ya zuba masa Ido. Haliru yana da wata budurwa da yake auna a rayuwar sa, sunanta Hauwa'u. Duk duniya ba wanda Haliru ke so sama da Hauwa, kulum yana zuwa gurinta hira. Wata rana Haliru zaije ta i gidan su Hauwa, ya taho a hanya suka ha u da Yusuf. "Abokina ina zuwa haka kaci wannan kwaliyar." Murmushi Haliru ya ringayi ya ce "Zanje ta i gidan su Hauwa'u." "Gaskiya ne to a gaida ita." "A'a aboki baza ayi hakaba kazo ka rakani muje kaganta, kaga kar sai anyi baiko kazo kanace mun baka santa ba." Da farko Yusuf cewa ya yi a'a, amma Haliru ya matsa suka tafi tare. Yaro suka sa ya kira musu Hauwa. Tasha kwaliyar ta, ta yi kyau ta fito ta na sakar musu murmushi. Gaida Haliru ta yi, ya amsa yana washe baki. Kamar a mafarki taji zazzakar muryarsa ya mata salama. A tsorace ta ago ta kali Yusuf. Lokaci guda ta ji son Yusuf ya shiga ranta, amma nata nuna ba, suka gaisa da shi. Haliru ya gabatar mata dashi, ta ce "Allah sarki kulum Haliru yana bani labarin ka ashe ganin ka yafi jinka." Ba wanda ya kawo komai a ransa, suka she e da dariya. Haliru ya ce "Ai Yusuf mutumin kirkine sosai." Shidai Yusuf salama ya musu ya tafi, harya kule Hauwa tana satar kallon sa. Tun a ranar Haliru ya fara ganin sauyi amma saita ce kanta ne yake ciwo, da haka suka rabu ta koma cikin gida. Tundaga ranar Hauwa ta daina zancen kowa saina Yusuf, ta ringa wula anta Haliru, ta ce yanzu ba ta sanshi da wanda take so, kuma shi zata aura. Hankalin Haliru ya tashi ya tura Baban sa mai gari ya tuntubi iyaye ta, koda ya je aka kira Hauwa a gaban me gari ta ce tanada wanda ta ke so. Duk yadda aka so Hauwa ta auri Haliru ki tayi ta tubure tanada wanda ta ke so. Iyaye ta ne suka ce, tunda ya i haliru to ta fito da miji kamar jira takeyi kuwa a ranar ta samu Yusuf a gonar da yake shuka shinkafa. Salama ta masa ya amsa da fara'a ta gaida shi ya amsa ya na cewa "Wannan kamar Hauwan Haliru ko?" Kai ta girgiza alamun a'a. Cike da mamaki ya ce "Amma kunyi matukar kama, ke kanwarta ce?" Sai lokacin ta ce "Nice Hauwa amma ba ta Haliru ba." "Tofa, meyake faruwa ne? Mun u dashi ranan nan na masa maganar ki ya kama kuka na tan bayi ba'a si, ya i bani amsa." "Gaskiya yanzu na fasa auransa, kai nake SO." Ido Yusuf ya zaro ya ce "Nifa Hauwa." Kaita gyada, cikin fushi ya ce "Amma bakida hankali Hauwa'u, duk son da Haliru yake miki amma kike son watsa masa asa a ido, yanzu idan na amunce miki naci amanar abokina kuma nima nan gaba zaki iya yaudarata." Kuka Hauwa ta fashe da shi ta ce "Wallahi idan baka aureni ba kashe kaina zanyi." Harara ya wurga mata ya ce "To asarar wa? Idan kin mutu akwai abunda a shafeni a ciki." Kaita gyada ta juya da gudu tabar gurin. Tsaki Yusuf yaja ya cigaba da aikin gonar tasa. Tunda Hauwa ta koma gida, ta haukace kowa ya rasa kanta dagyar aka samu ta fa i abunda ya faru tsakanin ta da Yusuf, kuma ta ce idai ba ta aureshi ba mutuwa zatayi. Ba shiri babanta ya je ya samu Kawu ya ringa magiya a taimaki iyar ta sa. Shikuma Kawu ya ce, sai yaji ta bakin Yusuf tukuna. Yusuf ya dawowa Kawu ya tareshi da zancen, nan ya tubure ya ce A'a shibai yarda ba. Kawu bai matsa masaba ya rabu dashi. Muna fukan garine sukaje suka sanar da Haliru arya da gaskiya aikuwa ya ce saiya kashe Yusuf. Wata rana Yusuf ya na gona, saiga Hauwa ta zo. Yana ganin ta ya ha e rai ya ce "Kibar gurin nan tun rakin bai aci ba." Hawaye ta fara sharewa ta ce "Wallahi na rasaka kashe kaina zanyi." Tafi sukaji a bayan su, duk suka juya. Haliru suka gani ya ce "Sanunku maciya amana, ni zaku ciwa Amana acikin garin nan, to wallahi kunyi arya." Ya na gama fadin haka ya rarumo fatanya ya sarawa Yusuf a baya. A take Yusuf ya baje a gurin ba nufashi, ita kuma Hauwa ta kurma ihu. Barin gurin Haliru ya yi sai wasu manoma ne suka kawowa Yusuf agaji aka kaishi Asibiti. Hauwa da kanta takai arar Haliru police station, akazo kayi gaba dashi. An kashi koto, aka yanke masa aurin shekara uku da ku i dubu ari na diyar wanda ya daka. Tun a gurin Haliru yasha alwashin kashe Yusuf duk sanda ya fito. Yusuf tun baya kula Hauwa, harta shiga ransa, har ya aureta suna zaune a cikin garin. Haihuwar Hauwa ta fari, Haliru ya fito duk da shekara uku aka aureshi amma ko biyu bai rufaba ya fito. Ba wanda yasan ya dawo, sai zuwa da ya yi ya bankawa gidan Yusuf wuta. Allah ya yi sunada kwana a gaba basu mutu ba, amma tundaga ranar basu ara kwanciyar hankali ba. Kulum cikin barazanar Haliru, da Kawu ya gaji, ya ce ya tattara kayasa ya bar garin da iyalinsa. Hakan ta sa Yusuf komawa cikin birnin Kano da zama. ASALIN LABARI Ihu Haliru ya kurma ya ce "Laila yau zan nuna maka ni an halak ne." Wu a ya zaro ya shamaci Yusuf ya...........! Gamasu shawara ko arin haske ga number ta 08166077167 nagode Comments And Share By *ZAHRA* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 12 Zai da a masa, Khadija ta ri e hannunsa ta kurma ihu, wadda ya jawo hankalin makota aka taru a gidan. Jikin Haliru har rawa ya ke ganin mutane sun taru ya arayin kan Yusuf da wu ar, mutanan da suka shigo ne suka riri e Haliru maru salati nayi masu zaginsa sunayi. Wani da tijo daga cikin wanda suka shigo gidan ya ce "Haba Haliru kanada hankali kuwa, ya zaka zo har cikin gidan su kana neman kashe shi. Ance maka mulki hauka ne da zaka ringa addabar mutane." Haliru na huci ya ce "Wallahi ba wanda ya isa ya hanani kashe wannan tsinan nan." "Idan kafi arfin ubanka to bakafi arfin hukuma ba. Ku kamashi mu tafi dashi police station." Ya ce da mutanen da suka ri e Haliru. Aikuwa suka jashi kamar hauka ka ci ya na cewa "Daga kai har wannan bakuwar yariyar da wanda suka aurema gindi, saina ga bayan ku wallahi." Jashi akayi aka fita dashi da tawagar tashi daya ha o, su Hauwa da akayi tsuru-tsuru sai lokacin aka samu bakin magana. "Tsinane la'a nane Allah bazai baka sa'a a kanmu ba." Inna ce ta ce "Ki daina tsine masa, kiyi masa addu'ar shiriya Allah ya shirye sa, ya kare mu daga sharrinsa." "Amin." Murja ta ce tana zama kusa da Khadija da taketa sauke ajiyar zuciya. Yusuf ficewa ya yi daga gidan, dan baya aunar wannan ana nan magan ganun na mata yanzu zasu su fara gutsiri tsoma. "To shikenan ranka shi da e kanada photo shi wanda ya sace ma matar taka ko ita matar taka." Ajiyar zuciya Nasir ya sauke ya ce "Banida photo shi yaron amma, ita yariyar an samu photon ta a gurin iyayenta." Kai DPO ya jin jina ya ce "Karka damu Alhaji zasu shigo hannu zamu kamasu in sha Allah, mun baza ma'ai katan mun, a lungu da sakon jahar nan, harda makotan jahohin mu." Cike da gamsuwa ya gya a kai, yaiwa DPO godiya, ya bashi ku i masu yawa ya tafi gida. Tana rungume da an nata tana hawaye. Zuwa yanzu ta fara fidarai da Nasir, kila ko wani abun ya sameshi ko ya mutu ma, shi ba dangi ba bare ta samu labari a gurin su. Kamar daga sama, taga shigowar tasa ficiki-ficiki, da sauri ta tashi tsaye ta sauke yaron ta kwantar dashi. Ko kallon ta baiba ya huce zai shiga aki, da sauri ta sha gaban sa tana hawaye ta ce "Baka mana adalici Nasir, ina ka tafi ka barmu, bamusan halin da kake ciki ba ka barmu cikin zulimi, ko tunanin halin da muke ciki bakayi." Kawar da kai ya yi dan bashi da lokacin ta yanzu, magana zata sakeyi, yasa hannu ya janyeta daga gabansa, ya shige aki ya kule. Kuka sosai Nafisa ta keyi tanajin tsanar Nasir har cikin ranta. Tana zaune a gurin tana kuka taga ya fito da jaka a hannunsa. Takowa ya yi har inda take zaune yasa hannu ya agota ya kallon fuskarta ya ce "Zanyi ara kwanaki biyu bana nan, akwai ku i a aki ki ibi ko nawa kike so kiyi anfani dashi, amma kar ki sake kifita daga cikin gidan nan har Anwar karki bari ya fita koda school ce har sai na dawo." Bai jira abunda zata ceba ya mi e zai fice. Har yaje bakin ofa ya ji ta ce "Wallahi bazan cigaba da zama a gidan nan ba mudin kasa afa ka fita to nima zan fice na tafi gidan iyayena." Juyowa ya yi ya ce "Okay, ka hanya nan zaki iya tafiya." Yana gama fa in haka ya fice daga gidan yanar Nafisa tana gurzar kuka. Yana fita ya kira security in gidan ya ce asa masa ido akan Nafisa, ko ofar gida kar a barta ta fito sannan kar su bar kowaye yazo ya shiga ya ganta saida izinin sa. Ya auki motar sa a gaggauce ya fice daga gidan. Bayan ya fita Nafisa ta tashi daga inda ta ke, ta rasa wane irin tunanima da zatayi yanzu. Dole ta samawa kanta mafita tun ba in cikin Nasir bai kashe ta ba. Dabara ce ta fa o mata da sauri ta nufi cikin akin ta ta ako wayarta ta fara kira. Sai da akayi magrib Yusuf ya dawo gidan. Hauwa ya tarar a tsakar gidan da Murja suna cin abunci, zama ya yi ya ce "Ina Inna? da Khadija?" Baki Hauwa ta ta e bata kulashi ba, Murja ce ta ce "Inna tana bayi ita kuma Khadija, tana aki tun azu bata fito ba." Hakan nan yaji gaban sa ya fa i, ya tashi da sauri ya shiga akin. Ya duba Khadija, amma ba ita ta alamunta. A firgice ya fito ya ce da su Hauwa "Bata ciki, baku lokacin data fito ba?" Girgiza kai Murja ta yi ta ce "A'a Yaya tunda muka zauna bamuga ta fito ba." Inna data fito daga bayi ta ce "Ka duba sauran akunan mana." Zagaye gidan yarin gayi amma ba Khadija ba labarin ta. Fita ya yi a firgice har suna karo da wani yaro, yaja baya yana kallon yaron. Gaidashi yaron yai ya ce "Gashi inji wata, tagani a hanya ta ce na ara mata biro da takarda. Tayi rubutu, ta ce dan Allah na kawo gidan nan." A firgice Yusuf ya warci takardar yaga abunda ta rubuta. NASAN BAZAKU JI DA IN TAFIYA TA BA AMMA DOLE ZAN BARKU, SABUDA ZAMANA A KUSA DAKU HATSARI NE. INA FATA ZAKA KOMA KANO DA ZAMA SABUDA KAR WANI ABU YA SAMEKE, TUNDA SABUDANI KA DAWO, TO NI NA TAFI KA KOMA DAN ALLAH. NAGODE SOSAI DA TAIMAKON KA GARENI, BISALAM ALLAH YA ADARA SADUWAR MU. Wasu irin hawaye masu zafi ne suka wanke masa fuska, ya dubi yaron ya ce............... Comment And Share Sharhi ko arin haske 08166077167 By Zahra *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 13 "Data baka takardar kaga inda tayi?" "Eh hanyar kasuwa naga tab....!" Bai jira yaron ya ara maganar saba ya zura a guje yai hanyar kasuwa. Har ya arasa kasuwar garin bai ga ko mai kama da itaba, gashi dare ya so mayi duba inda akafara lodin mota yai ko zai ganta. Khadija lokacin da ta faki ido ta baro gida harta ha uda yaro ta bashi takarda, kawai saita nufi tashar garin, motar Kaduna ta tanbaya aka nuna mata. Gurin driver taje bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah Kaduna nake son tafiya nawane ku in motar?" Mutumin daya kura mata ido ya ce "Ku in ki dubu biyu, amma naga kamar ba lafiya ba ko?" Hawaye ta share ta ce "Bakomai amma banda dubu biyu, komawa zanyu." Murmushi yai ya ce "Karki damu ammata zan kaiki kyauta ma, amma ba yau zan tashiba sai gobe." Cikin damuwa Khadija ta ce "Shikenan zan koma cikin gari goban na dawo." "Aa ammata, akwai gida na nan kusa, saiki kwanata tunda asubanci zamuyi." Da farko Khadija bata yarda ba, amma driver ya dage dayaga tana son tafiyar, ta yarda suka nufi gidan nasa. agaran Yusuf kuwa, ba inda bai zagaye neman Khadija ba amma kowa ya tanbaya sai yace bai ganta ba. Ba yadda ya iya haka ya juya ya nufi gida jiki a salu e. Wani gida mutumin ya kai Khadija, saida suka shiga ya rufo gidan, ya nuna mata wani aki ya ce "Ki zauna anan, matar gidan ta lega gidan gaisuwa, amma yanzu zata dawo." Wannan karon Khadija bata yarda da mutumin ba ta ce "A'a bazan iya zama daga ni sai kai a gida ba kowa ba." Murmushin ya e yai ya ce "Kinaji to ki zauna bari na koma waje, idan ta dawo sai mu shigo tare." Girgiza kai ta yi, ta ce "Gaskiya bazan zauna ba." Ran mutumin ne ya aci ya ce "To wai me kike tunani, daga taimako saiki zo kina mun gadama, toga hanya ki fice ki bani guri." Hanyar fita ta nufa, amma tana zuwa taga afar gidan a rufe. Sai yanzu Khadija ta gane kuskure data tabka, daga gani wannan mutumin bashida gaskiya. Jikin ta ne ya fara rawa, ta fara buga ofar da iya arfinta tana cewa "Bakowa a wajen nan dazai bu emun ofar nan." Jabiru driver dayaga zata tona masa asiri, ya yo zauren da sauri, tabaya ya aga Khadija yai cikin gidan da ita. Ihu ta ke da sosai tana masa magiya, amma bai kulata ba ya shiga akin da ita, kan wata tsurar katifa ya ajiyeta, ya haye ta. Bazato ba tsamani aka karya ofar gidan, Yusuf cikin zafin rai shigo akin ya fizgo mutumin yai masa wani wawan naushi saida bakinsa da hancinsa suka fashe, dukansa Yusuf ya ringayu ta ko ina, mutumin da ya rakoshi baiyi yinkurin hanashi dukan tsohun najadun ba. Khadija kuwa ji take kamar asa ta tsage ta shige ciki sabuda kuya da nauyin Yusuf da takeji, tasan ba lalai ya yarda da itaba gani zaiyi kamar ita ta kawo kanta. Yusuf bai rabuda mutumin ba saida ya tabbatar ya sumar dashi sannan ya rabu dashi. Ko kallon inda Khadija take baiba ya juya ya fice, daga gidan. Tashi tayi tabi bayansa tana kuka, ta ce "Wallahi ba laifina bane bansa.......!" Tsawa ya daka mata ya juyo, yana huci Kwarjininsa da nauyinsa yasa ta kasa ha a ido ashi, ya ce "Karki sake ki ara biyoni, ki koma gurin an iskan da kika fito." "Allah ba laifina bane shine.......!" Saukar marin da taji a kuncinta yasa ta kasa ara maganar da takeyi, cike da mamaki take kallon sa. Idon sa yai ja duk jijiyoyin kansa sun tashi, tsabar masifar kishi. Shikan sa mamakin kasan ya keyi yadda yakejin kamar kishi zai kasheshi, abun takaicin shine matar wani ce ba tashi ba amma yakejin kishinta haka. Durkusawa tayi a gabansa ta ce "Nasan nayi kuskure, amma wallahi bani nakai kaina gurin wannan mutumin ba, kayarda dani wallahi basan abuda zai ai kata ba, cewa yai taimakona zaiyi. Ajiyar zuciya, ya sauke ya ce "Bakyajin magana Khadija, yanzu duk fafutukar nan da mukeyi akan tsare kima da mutuncinki mukeyi amma sabuda bakida hankali, kika fito a daran nan zaki gudu. Kin mata ke macace kuma duniya yanzu ba gaskiya ba tsoran Allah, kika taho tasha neman taimako ai kin kawo kanki ne kawai zasu gani. Banda Allah ya somu da rahama, wani yaga lokacin da yashiga dake gidan ya kule, muka ha u dashi a hanya ina cigiya ya sanar dani inda ya ganki, me kike tunanin zai faru?" Kaita girgiza tana hawaye ya ce "Yanzu RAYUWA ta sauya Khadija, zina ta zama ado ba wanda yake shayi ko shakar aikata ta." "Hakane kayi hakuri." Bai ce mata komai ba ya huce yabarta a gurin, ta tashi jiki ba kwari tabi bayansa, suka nufi gida. Tana sintiri a akin ta samu wayar ta shiga jikin ta har rawa yake ta ce "Izatu kina ina yanzu?" "Lafiya kuwa Nafisa? ba gaisu ba komai san tanbayar ina nake." "Da sauki dai nidai ki taimaka mun kizo gidana yanzu." "Tab gidan naki ta sai kasha tanbayoyi kamar kabari ka shiga." Ajiyar zuciya ta yi ta ce "Zanyiwa security magana yanzu, idan kika zo kawai shigowa zakiyi." "To." Izzatu ta ce ta kashe wayar. Ko hijab Nafisa bata nemaba ta fita harabar gidan. Gurin masu gadin ta arasa duk saka gaida ita ta amsa ta ce "Zanyi bakuwa yanzu sunanta Izzatu, kubarta ta shigo." aya daga cikin masu gadin ya ce "Kiyi hakuri Hajiya, Alhaji ya bamu umarni karmu sake mu bari ki fita ko wani ya shigo gidan saida izininsa." Baki Nafisa ta bude cike da mamaki da takaici ta ce...............! Sharhi ko arin haske 08166077167 Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 14 "Amma dai nan gida nane inada ancin kawo an uwana ciki ko? To ka barta ta shigo." "Kiyi hakuri Hajiya, Allah bazamu bariba sabuda gudun fishin oga mubarki mukuma, ranmu ya baci." Sabuda ba in ciki, kasa magana Nafisa tai, ta juya ta shige cikin gidan ranta a dagule. Wayarta ta ako. Ta sake kiran Izzatu. Bugu biyu Izzatu ta aga ta ce "Inajin ki." "Ko kinzo ba zasu barki kishigoba." Cikeda mamaki Izzatu ta ce "What, me kike nufi keda gidanki amma wani naki bazai zo ba." Nafisa da hankalin ta yake a tashe, dan tasan da wata a asa akwai abunda Nasir ya ce shiryawa ta ce "Nidai ba wannan ba Izzatu mene abunyi?" Ajiyar zuciya Izzatu tai ta ce "Akwai abunyi, ki shirya zanzo idan sun hana shigowa ai basu hana bada aikeba ko?" "Eh." "Hmm to ki kwantar da hankalin ki yau zaki baro wannan BAKIN GIDA (my book) ina zuwa." Ta kashe wayar. Zama Nafisa tai ta agu ta fita daga gidan nan, Allah ya gani duk a tsorace take. Nasir kai tsaye Kaduna ya huce, duk a tsorace ya ke da matakin da za'a auka a kansa. Kamar yadda ya zata, kowa ya halara harda uwar akin tasu. Kasa magana Nasir yai sabuda kunya da tsoro. Uwar akin nasu ta ce "Kowa ya shirya, me takanas da kansa zai zo." A tsorace Nasir ya ago yana kallon ta. Ta gyada kai ta ce "Dodo yana fi atar wannan aikin cikin gaggawa ko shima, alkadarin sa ya karye." Zaro ido duk sukayi, ta tashi bata kula kowaba ta rufa wani jan mayafi a kanta, taringa karanto wani yare shiba na caina ba ba kuma indiya ba. Sauketa akayi daga kafu babur in. Tami awa me babur in ku in sa, ya tafi. Juyowa tayi, ta kali gidan. Gida har gida aljanar duniya, amma matar ciki bata cikin kwanciyar hankali. Ajiyar zuciya tai ta fara kwankwasa get in gidan. Me gadine ya leko ya na kallon ta ya ce "Hajiya lafiya." "Dama aike ne, matar gidan tasai kayana a online ta ce na kawo mata hargida." "To ba'a shiga kawo a mi a mata." Bashi ta yi, ya amsa ya koma ciki ya kule. Murmushi Izzatu ta yi, komai ya tafi yadda ta ke so, yanzu abunda ya rage fita da Nafisa daga cikin gidan, cikin sauki. Da wannan tunanin tabar ofar gidan. Da safe, kawu da Inna suka zaunar da Khadija, suka mata fa a sosai sabuda watar da tayi. Hakuri ta basu ta ce "In sha Allah, hakan bazata sake faruwa ba." "To shikenan Allah yai miki albarka." "Amin." Ta ce, ita kuwa Hauwa sai ta e baki ta ke. Zuwa yanzu ta fara zargin Yusuf da Khadija, kuma tasa ido a kansu sosai saita gano tsakanin su. Izzatu na tafiya, me gadi ya sha ciki da salama. Amsawa Nafisa ta yi Ya mi a mata kayan ya ce "Gashi inji wata, wai kin siyi kaya kunta." Tana ansa ta duba ta ce "Eh kayana ne na siya, zaka iya ta fiya." Tashi ya yi yana cewa "To Hajiya a huta lafiya." Itadai Nafisa tabayi magana ba, sai bu e ledar da ta yi. Kayane less masu kyau, sai wani abu a jakar. Waya ta ako, ta kira Izzatu. "Hello, naga kaya na mene?" Daga can Izzatu ta ce "Kaya na wane, abunda ke jarka kuma jini ne." "Me? Mezanyi dashi kuma?" "Dashi zamuyi anfani ki baro gidan, arin ciki zakiyi na bogi." Mamaki ne ya kama, Nafisa ka fin ta ce. "Idan ya kira Nasir fa?" "Bazai same shi ba." "Sabuda me?" "Sabuda kema ba samunsa kike ba." Kai ta gyada cike da gamsuwa ta ce yanzu ya zanyi, nan Izzatu ta labarta mata yadda zasuyi, sukayi salama ta kashe wayar. Bayan minti 20 da yin haka, Nafisa ta fito daga aki da gyar tana nishi. Anwar dake kan kujera ya taho gurinta yana cewa "Ummi meyake damunki?" Cikin wahala ta ce "Kiramun Sada (Megadi)." Da sauri ya fice, ya kira Sada. Tare suka shigo falon da Anwar, ya fa a jikin Ummin tasa yana kuka ganin yadda taketa zubar da jini. Hankalin Sada a tashe ya ce "Sannu Hajiya, dama baki da lafiya?" Tana juya kai ta ce "Ina tunanin ari zanyi, ka ako waya ta, zakaga number kanwata Izzatu, ka kiratu muje Hospital." Ta arasa maganar tana nishi da arfi. Hankalin Sada ne ya ara tashi ya ce "Bari na kira Alhaji na sanar dashi." Da sauri Nafisa ta ce "Aa karabu dashi tunda baya nan, ka taimaka mun zanmutu." Ta cigaba da murkususu. Koda Sada ya ga haka sai ya fala lalubar number Alhaji Nasir. Zagaye suke da matar a kusa dasu ida nuwanta sun koma blue colour ta kalli Nasir, da wata irin murya ta ce "Lalai ka aikata mumunan laifi kuma sai dodo ya hukunta ka, ita kuma yariyar da kake batu ta gudu, zata kawo kanta har cikin gidan nan, sai muyi abunda muke so muyi cikin sauki dan ya zama dole wannan aikin ko duk ta shafemu." Shiru duk sukayi shi kuwa Nasir kansa yana asa ya kasa magana. Wata kwarya ce ta bayana a gabanta, ta ce "Kallo nan." Nasir ya kalli cikin kwaryar. Khadija ce zaune a tsakar gidan su Yusuf tayi tagumi. "Khadija!. Matar ta kira sunanta, a firgice Khadija ta kallo su. " Khadija! Kizo nan yanzu." Ko gama rufe baki batayi ba, Khadija ta taso da sauri ta ta fito ko takalimi babu............ Sharhi ko arin haske 08166077167 Comments And Share By *Zahara* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 15 Ba kowa a tsakar gidan, dan haka ba wanda ya ga fitar ta. Sada yai ta kiran layin Nasir amma a kashe, ga Nafisa kwance male-male cikin jini, tana faman murkusu da rike ciki. Bashi da za i ila yai abunda ta ce, dan haka ya ako wayar tata ya kira Izzatu kamar yadda ta ce. "Hello Nafisa dama kuna duniya." Izzatu ta ce lokacin da ta aga wayar. "Aa ba ita bace, bata da lafiya gata kwance cikin jini kizo a taimaka ma a kaita Hospital yanzu." "Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un, okay ganinan ku jirani." Kashe wayar ta yi, shikuwa Sada ya cigaba da jerowa Nafisa sannu. Yau me gari Usmanu da kansa ya je police station, ya dage aka bashi belin Haliru ya taho dashi gida. Haliru ko zama baiba yai wanka ba, ya fito kangon su inda suka saba zama. Suna ganin sa duk suka mi e suna gaidashi ana murnar dawowarsa. Fuska ba annuri ya ce "Yau lahira zatayi bako acikin garin nan kowa ya shirya." Ihu duk suka saka, ya fara yin gaba suka bishi a baya suna a aga makamai sama suna ihu. Mintina ka an Izzatu ta zo, suka kama Nafisa, aka sata a mota, har zasu tafi Nafisa ta ce "Izzatu kije akin Nasir da ku i masu yawa duk ki kwaso mana su." Ba musu ta koma ciki A jaka ta zubo duka ku in ta kamo hannun Anwar suka shiga motar Sada yaja suka tafi Hospital. Suna shiga Hospital in Nurses suka amshi Nafisa, sukayi ciki da ita. Rufa musu baya Izzatu tayi suka dakatar da ita ta ce "Kuyi hakuri, dole ni zan yiwa Doctor bayani." Barin ta sukayi ta huce ciki. Doctor Maryam ta zo dan duba Nafisa, Izzatu ta ce "Doctor lafiyar ta lau." Da sauri Doctor ta kaleta zata yi magana taga Nafisa ta tashi zaune cikin tashin hankali ta ce "Ki rufa mana asiri Doctor mijina azabtar dani yake ya rabani da kowa, ya hana kowa zuwa inda nake, shiyasa na nemi nayi ciwan wasa na gudu." Girgiza kai Doctor ta yi ta ce "Gaskiya baza'a ha a baki dani ayi mugun abuba kuyi hakuri." Magiya Izzatu ta ringa yi mata amma ta burje bata yarda ba. Nafisa sa ce ta amshi jakar hannun Izzatu ta ciro ku i masu yawa ta ce "Dan Allah ki mana wannan taimakon, kati kawai zaki rubuta mana ki mi awa, wanda ya kawo mu kice ya je ya siyo magani yanzu, mukuma zamu gudu ke kuma kice anan kika barmu, ga dubu ari uku ki taimaka. Amsa doctor ta yi ta ce "Shike nan amma sabuda Allah zanyi." "To mun gode." Rubuta magani doctor Maryam ta yi kamar yadda suka bu ata, ta fita. Sada ta samu a waje ta ce "Dan Allah kaje a samo wannan maganin da ruwa da sauri." Amsa ya yi jiki na rawa ya ce "To in sha Allah." Da sauri yabar gurin. Komawa ciki ta yi ta ce "Na turashi ya siyo maganin da nasan bamudashi a nan saiya fita tafiya me nisa zaku iya tafiya." Godiya suka mata, da sauri suka fito dan su gudu. Wata hanya doctor ta nuna musu dan subi ta gurin. Har sunzo fita Nafisa ta tsaya ta kalli Izzatu ta ce "Ina Anwar?" Sai lokacin suka kula ba yaron. Izzatu ta ce "Ki taho kawai mu tafi." Harara Nafisa ta watsa mata ta ce "Baki da hankali an nawa zan bari." Kasa magana Izzatu ta yi Sai Doctor Maryam ce ta ce "Ki fita ki tare muku abun hawa nida Izzatu sai mu dubo shi." Da farko in yarda Nafisa ta yi, saida Doctor ta tabbatar mata zasu samu yaron. Komawa sukayi ciki ita kuma ta fita ta tare me kafu babur. Shiru Mama Lube tai tanajin fa an da Baba ya ke tayi. Da ta gaji ta ce "Haba Malam, yanzu ni na hana Khadija zuwa gida ko ya?" "Ai kinsan inda take aure ki kaini da kaina naga halin da take ciki mana." "Kaga malam nifa bansan gidan Khadija ba." "To gidan ubanwa aka kaimun ata, ai ke kikasan mutumin wallahi ko ki fito mun da ita konayi ararki gurin hukuma." Mi ewa Mama Lube tai ta ce "Ni nasa ka saida artaka da zaka ringa agamun murya." "Haka ma kika ce ko? To zakiga matakin da zan auka a kanki." Daga haka ya fice daga gidan, mama Lube ta rakashi da harara. Doctor Maryam suna komawa sukaci karo da Sada da Anwar a hannu. Tsuru-tsuru sukayi zatonsu ya ganosu sai ji sukayi ya ce "Naje Pharmacy ban samu maganin ba, bari na fita waje." "Okay kawo Anwar in sabuda rana." Mi a mata shi yai ya ce "Bari naje to." Cikin farin ciki Doctor Maryam ta ce "Kai sauri fa." "To." Ya ce ya juya ya fice. Godiya Izzatu taiwa Doctor da gudu ta fice ta ayar kofar. Kafu babur in ta shiga da Nafisa ta ke suka tafi. Sunyi nisa Nafisa ya amshi Anwar ta rungumeshi a jikinta ta saki kuka me tsuma zuciya, ita da gidan Nasir har abada tunda ta samu ta fito. Cikin tausayawa Izzatu ta ringa rarrashinta harta samu tayi shuru, suka arasa gida. Gayar da Haliru ya ibo kai tsaye gidan su Yusuf suka nufa. Zuwansu yai dai-dai da fitowar Khadija a firgice. Da sauri Haliru ya ce "Ku kamo mun waccan bakuwar da taketa sauri." Da gudu sukafi Khadija, wadda bamata cikin hayacinta............... *Zaku iya samun complete ducment na ABDULFATAH da TAURARI BIYU da AURAN JARIMI akan fashi me sauki.* *Guda aya #200 guda biyu #400 guda uku #500* *Zaku iya tuntu ar wannan number 08166077167 domin malakar naku, karku bari a barku a baya.* Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 16 Batasan abunda akeyi ba balatana ta gudu, har yaran Haliru suka risketa. Rirriketa sukayi har oga Haliru ya zo gurin, ganin irin fusge-fusgen da ihun da take ya ce ya kule masa ita. Nan take yaran nasa suka aiwàtar da abunda ya sa su, sukaja Khadija sukabar gurin da ita. Har sukaje gida, Khadija tana wani irin fusge-fusge da ihu, hakan tasa Haliru ya farajin tsoro ya ce asata a aki a kule. Yusuf ne ya fito daga akinsa. Har zai fita sai ya fara kiran Hauwa, Amsawa ta yi ta fito ta ce "Gani." "Ina Murja ne?" "Ai Murja sun tafi da Hassana awarta dubiya." "To Khadija fa?" Saida ta turo baki ta ce "Tana aki." Kirayomun ita aiki zasumun. Juyawa ta yi ta nufi akin, amma bataga Khadija ba, har akin Inna amma bata nan. Dawowa tai ta ce "Wata kila ta fice yawo dan bata nan." "Khadija ce take fita yawo?" "To ina tashiga inba yawonba tunda dai gashi bata nan." "Mtssss." Yusuf yaja dogon tsaki, ya fara kiran Khadija yana duba gidan amma shiru ba ita ba alamarta. Hankalinsa ya gama tashi sabuda tunu wautar da tayi ranan nan. Fita yai yana cigiyar ko akwai wanda yaga inda tayi. Wani tsoho da kulum yana ofar masalaci a zaune ya kira Yusuf. Har asa Yusuf ya du a ya gaida tsohon. "Yaro naga wannan tantirin an me gari Haliru yazo har nan, ya tafi da wata yariya harda aureta da igiya." A tsorace Yusuf ya ce "Baba wane irin kayane a jikinta? Ko sufarta." "Yarinyace dai amma da hijabi me ruwan asa a jikinta." "Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un!" Abunda Yusuf ya iya furtawa kenan yaiwa Baba tsoho godiya ya koma cikin gida. A gidan Izzatu suka sauka, Nafisa tai wanka ta gyara jikinta, sannan suka zauna a falo. Cikin kulawa ta kalli Izzatu ta ce "Kinsan me yasa nace ki ibo mana wannan ku in?" "A'a." "Sabuda bazan koma gida ba, nasan halin su Baba, zasu iya maidani wannan gidan, wanda da zamansa gara zaman kabari, bazasu duba wahalar da nake sha ba, suna ganin kudi shike nan." Gyada kai Izzatu tai cike da gamsuwa ta ce "Gaskiya ne, yanzu kinga za'a iya bincike ace dasa hannu na kika gudu, kuma in mijina yaji bazaiji dadi ba, dan haka dole mu shirya wata dabarar da zata futar dani." Shiru Nafisa tai kafin ta ce "Hakane amma me yakamata muyi?" "Zaman gidan nan bazai fishe kiba, ki dole zaki koma wani gurin ni kuma duk yadda zanyi na kare kaina zanyi." "Amma ina kike tunanin zanje yanzu." "Akwai wata anwata wadda muke uba aya tana aure a Yobe state, munyi magana da ita mijinta yana America zaki iya zuwa can ki gama kwanakin kima bai dawo ba, kinga saikinfi sakewa mijinta baya nan." Gyada kai Nafisa tai cike da gamsuwa ta ce "Gaskiya ne, nagode Izzatu, bani da bakin da zan miki godiya saidai fatan alkairi." "Karki ji komai awata mun riga mun zama aya." Nan suka cigaba da tsara yadda zasuyi dan a asuba Izzatu take so Nafisa tabar garin gaba aya. Cirko-cirko sukayi a tsakar gidan, Kawu ya ce "Gaskiya lamarin yaron nan ya fara yawa, dole sai mun dauki mataki tsatstsaura akansa." Inna da tai tagumi ta ce "In banda abun Haliru me wannan yariyar ta masa ita da bata san abunda ke faruwaba." Murja da kuka take ta ce "Allah Inna dan yaga ba'a hukun tashine shiyasa yake taka duk wanda ya so." "Idan yafi karfin hukuma aimu baifi karfin mu ba, gani yake kamar tsoransa akeji shiyasa yake wa mutane wannan iskancin, ni yau zanje mu raba raini dashi." Yusuf yana gama fa in haka ya juya yabar gidan da sauri. Hauwa da taketa tabe baki ganin ya fita ta ce "Amma Kawu ku dakatar dashi kar su masa wani abun." Kawu ya ce "Yaga zai iyane kar wanda ya dakatar dashi." Kuka Hauwa tasa, ta shige aki harda ora hannu aka tana cewa "Shike nan na mutu na lalace, takaba ta kamani." Sunajin tanata hauka ba wanda ya kulata. Har kangon da suke zama yaje ya shiga ciki Kamar yadda yai tsamani Haliru yana ciki da yaransa sunata shaye-shaye. Har gaban Haliru ya tsaya yana huci ya ce "Ina ka kai ar mutane?" agowa Haliru ya yi, yana ganin me magana ya mike zunbur ya sa ihu ya ce "Hhhhhh wai yau Akuya ce ta shigo ramin kura." * * * * * * * * * A tsora ce ta yaye jan mayafin da ta rufa a jikinta, Idonta suka koma red ta ce "Akwai matsala." "Wani yana kokarin tar watsa komai namu, ya daure yariyar nan a gidan sa, duk da akwai bakin aljani a jikinta ta kasa fitowa." Tsuru-tsuru duka sukayi ganin lokaci guda komai yana son lalacewa. "Dole ne mu kawo karshen komai tun kafin tsafin mu ya daina tasiri akan mu." Shiru yai yana tuno wani abu cike da firgici ya tashi ya fice daga gidan. Duk da kallo suka bishi na mamaki ganin yana so yaja da ikon dodo ana zama ya fita...............! Sharhi ko arin haske 08166077167 Comments And Share by *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 17 Bai bi takan kowa ba ya hau motarsa ya baro Kaduna. Taron nasu kuwa tashi yai sabuda wanda akayi domin sa ya bar gurin, dan haka suma suka watse tunda shi fushin dodo zai hau kansa. Mi ewa yai ya tsaya gaban Yusuf, yana huci, shima Yusuf din hucin ya keyi. Yaran Haliru kuwa sun zagaye su da maka mansu a hannu. Haliru ne yai kukan kura ya cakumi wuyan Yusuf, shima Yusuf cakumar tasa yai. Yaran sukayo kan Yusuf. Yusuf yai saurin shake Haliru ya zaro huka a jikin Haliru ya saita wuyansa ya ce "Idan baka dakatar da suba wallahi zan yanka ma ogaranka." Ba shiri Haliru ya ce yaran suja baya, suka ja da baya. Yusuf ya ce yaje ya nuna masa inda Khadija ta ke. Kamar ra umi da akala haka Haliru yakai Yusuf inda ya kule Khadija. Aka budeta, sabuda rashin iska har ta suma acikin d'akin. Ran Yusuf ya baci sosai dan haka yana ganin halin da Khadija ke ciki yasa hannu yaiwa Haliru wani wawan duka, saida Haliru ya zube a gurin ba nunfashi. Fita Yusuf yai ya samo me mashin ya taimaka suka dauki Khadija suka tafi gida da ita. Yan gidan kowa yai mamakin ganin Yusuf lafiya kuma gashi da Khadija. Tabarma Inna ta shinfi a aka kwantar da Khadija. Murja ta samo ruwa aka shafawa Khadija. Nan take ta sauke nunfashi "Alhadulilah." Kowa yake furtawa. Amm abun mamakin shine, tunda Khadija ta farka take wani fusge-fusge da ihu tana neman ficewa daga gidan. Kawu yana ganin haka ya kalli Yusuf da yake cikin ru ani ya ce "Daga gani wannan shafar junu ne, ka kira liman yanzu ya mata addu'a." Ba musu Yusuf ya fita ya kira Malam liman Nan Malam liman ya ringa yiwa Khadija addu'a aljanun basuyi magana ba, amma da sukaji wuya sun gudu. Rubutu da tirare, Malam liman ya bada yace abawa Khadija ta ringayi in sha Allah, ba wani aljani da zai sake shiga jikinta. Godiya suka masa, ya koma masalaci. Sai dare Khadija ta tashi shima abunci kawai taci ta koma ta kwanta. Washe gari. Tunda asuba Izzatu ta raka Nafisa tasha ta hau motar yobe state, saida ta tabbatar sun tafi sannan ta koma gida. Nasir da yaga dare ya masa a hanya, bai koma gida ba, ya kama hotel ya kwana sai da safe ya koma gida. Tunda ya shiga gidan yaga duk ma'aikatan gidan jiki a sanyaye kuma duk a tsorace yasan akwai lauje cikin na i. Yana shiga falo yaga Sada ya biyoshi jiki a sanyaye ya zauna ya ce "Ranka shi dade, bayan tafiyarka an samu matsala, Hajiya ta bar gidan nan." "What! Me kake nufi?" Nasir ya ce, cike da tashin hankali. Muryar Sada na rawa, ya zayanewa Nasir komai abunda ya faru. Ajiyar zuciya, Nasir yai ya ce "Tashi ka bani guri." Kamar jira Sada yake ya fice daga falon. Shiru Nasir yai yana nazarin abunda Sada ya sanar dashi, yanzu ta ina zai fara? Neman Khadija da Yusuf da sukaci amanar sa ko neman Nafisa? Da arfi ya gatsa le ansa jikin sa na rawa. Sai 2:17pm su Nafisa suka sauka a Yobe, mota suka hau da kwatance aka kaisu gidan anwar Izzatu. Da salama Nafisa ta shiga gidan, wata datijuwar mata ta amsa mata salamar da fara'a. Murmushi Nafisa tai wa matar, matar ta amshi jakar Nafisan tashiga da ita ciki. A falo suka zauna matar ta shiga da kayan ta sanar da Maryam matar gidan zuwan Nafisa. Itama Maryam kamar Izzatu tanada mutunci. Da fara'a suka gaisa da Nafisa, tana mata sannu da zuwa tasa Mama Karime ta kawo musu ruwa da lemuka da abunci. Sunaci suna hira, bayan sun gama Mama Karime ta auki Anwar suka shiga akinta dashi. Da murmushi Nafisa ta rakasu ta ce "Da alama Mama Karime tana son yara." "Sosai ma kuwa musaman mata, nasha kamata tana kuka idan ta auki yariya ta, na tanbayeta dalili ta ce bakomai." "Allah sarki, wata kila ta ta a haihuwa a baya yaran sun mutu." "Hakane kam." Hira suka cigaba dayi kamar sun jima da sanin juna. Da dare Nafisa tana zaune a akin da aka bata, Mama Karime ta shigo da Anwar ta kwantar dashi tana kallon fuskarsa. Nafisa ce ta kaleta cike da kulawa ta ce "Amma Mama Karime kin ta a haihuwar yara a baya ko?" Hawaye Mama Karime ta share ta ce "Tabbas inada yariya mace amma yanzu bansan inda take ba, amma wannan yaron naki yanamun tsananin kama da wani an uwana a katsina ya rasu can da darewa, amma yanada yaro Nasiru bansan inda yake a halin yanzu ba." A matukar tsorace Nafisa ta kalli Mama Karime ta ce................! Sharhi ko arin haske 08166077167 Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 18 "Nasir sunan mahaifinsa kenan." Itama Mama Karime tayi mamaki ta ce "Ban sani ba ko sunana ne yazo aya amma nawa an a katsina ya ke, kuma na jima banje canba. Amma naki mijin a ina yake." Shiru Nafisa tai dan bata da amsar da zata bawa Mama Karime. Tsawan zaman su da Nasir, ba wanda ya ta a zuwa da sunan an uwansa ne, ko ta tanbayesa iyayensa to ranta ne zai aci a banza. Maganar Mama Karime ce ta katse mata tunaninta. "Ko da yake naji Hajiya ta ce, daga garinsu zakuzo kila shima mijin naki a Kano ya ke, kinga kuwa kamace kawai." Murmushin ya e Nafisa ta yi ta ce "Eh hakane." Hira suka cigaba dayi da Mama Karime ta duniya dan kowa a cikinsu baya so a tanbayeshi ahalinsa. * * * * * * * * * Da salama ya shigo gidan ba kowa a tsakar gidan dan haka ya zarce akin Inna. Khadija na zaune a gefan gadon Inna tai tagumi. Har yai salama batasan ya yi ba, arasowa ya yi gaban ta ya ce "Khadija!" A tsorace ta kalleshi. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya, ta ce "Ina kwana." Bai amsa ba sai ya ce "Tunanin me kikeyi haka? har na shigo baki sani ba." Hawayen da take o arin maidawa ne suka zubo mata ta ce "Ba komai." "Amma kike kuka." Hawaye ta share cikin raunin murya ta ce "Kuka ya zama dole a gareni, ace kwana da kwanaki ina hannunku amma iyayena basu ta a neman inda nake ba." Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke ya ce "A'a Khadija nasan yanzu haka mahaifanki suna can suna nemanki, kawai Allah ne baisa sun riski inda muke ba." Girgiza kai ta yi ta ce "A'a wallah ba wanda ya damu dani da zai nemi inda nake, da dai Mahaifiyata tana raye ne a kusa dani da ita zata damu." Zama Yusuf ya yi a kusa da ita cikin rarrashi ya ce "Kiyi hakuri komai yai farko yanada arshe, zaman mu a nan garin ma zai zo arshe ki koma gaban iyayenki cikin aminci in sha Allah." Kai ta gya a ta ce "Allah yasa." "Amin." Yusuf ya ce, yana cigaba da rarrashinta. * * * * * * * * * Cikin nutsuwa tai faka motarta a ofar gidan, ta zaro wayarta ta lalubo number sa ta kara a kune. "Hello ina ofar gidanka." Daga can ya ce "Okay ina zuwa." Bai auki wani dogon lokaci ba ya fito, sanye da jalabiya ruwan toka a jikinsa, kana ganin fuskarsa ba alamun rahama a cikinta. Murfin motar ya fu e ya shiga. A hankali ta kalle shi ta ce "Nasir!" Kallon ta ya yi cike da damuwa ya ce "Duniyar gaba aya ta isheni Hasina." Ajiyar zuciya ta yi ta ce "Idan rai ya aci hankali baya gushewa Nasir, me yasa ka baro gurin nan, cikin fushi?" "Hasina komai ya dagule mun lisafina ya kwace gaba aya shiyasa na baro gurin dan bana fahimtar komai ma." Jinjina kai Hasina ta yi ta ce "Kasan hakan ba aramun kuskure ka aikata ba, kuma gaba aya kungiya anyi fushi da kai." "Look Hasina, nifa ba sake komawa wannan gurin zanyi ba, na rasa matata da ana dalilin wannan tsinan nan aikin." Cike da mamaki Hasina ta ce "Nasir kasan me kake cewa kowa? Kabar kungiya kenan?" "Haka nake nufi." Gya a kai ya yi, ta jinjina kai ta ce "Ba sai na sanar da kai abunda zai faruba Nasir kasan makomarka." Wani mugun kallo ya watsa mata ya ce "Ba kune a gaba na ba ta matata nakeyi yanzu da wanda sukaci Amanata." "Okay to, amma shawarar da zan baka kacire wannan tunanin a ranka dan ba hanya bace me ilewa ba." "Naji zanyi tunani." Daga haka ya bu e murfin motar yai ficewarsa ya koma gida. Girgiza kai Hasina ta yi taja motarta ta bar gurin. * * * * * * * * * Kawu ya kalla cikin kulawa ya ce "In sha Allah, kan dare zan dawo gida kaga gidan da muke ciki na haya ne kuma kayan mu suna can, masu gidan sai kirana suke suna bu atar gidan su, yanzu dole naje na ibokayan Hauwa." "To shike nan ka kula sosai." "In sha Allah." Daga haka Yusuf yaiwa kawu salama ya huce tasha dan ya hau mota. Lokacin da ya isa gidan da suke haya, azahar tayi dan haka saida ya tsaya yai sallar Azahar sannan ya taro me mota suka loda kayan Hauwa tsaf ya koma gidan ya ako randar kwaro, yana fitowa yaga police sun cika ofar gidan. Gaban sane ya fa i, sai lokacin ya tuno shifa mai laifi ne tafiya da Khadija da ya yi. Police ne suka hangoshi suka tin karo inda ya ke, yana ganin haka ya dire robar ruwan daga hannunsa ya juya a guje yai wata kwana da uban gudu, suma kwalawan suka take masa baya............! Sharhi ko arin haske 08166077167 Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 19 Wata katanga ya gani ai kuwa ba ata lokaci ya ane katangar ya haure, sukuma police in suka huce ba tare da sunga inda ya shige ba. Ajiyar zuciya ya sauke jin sun huce basu ganshiba, da fashi yaji anyi a tsorace ya juya. Ido ya zazzaro ya ce "Kai ne?" * * * * * * * * Suna zaune a falo Mama Karime da kulum tana makale da Anwar bacci ne kawai yake rabasu, tana zane a kan carpet Anwar nakan ciyarta. Wayarta ce ta fara ruri a hankali ta duba me kiran murmushi ta yi ta kara a kune. "Manyan asa dama kina nan kwana biyu shiru." Murmushi Izzatu tayi ta ce "Ai dole ki jini shiru sabuda tsaro badan tsoro ba kinsan me gadin gidanki yaga fuskata dole nayi taka tsantsan." "Gaskiya ne to ya gidan?" "Komai normal, ya Yobe?" "Yobe akwai da i sosai amma saidai kawai matsala." Izzatu dake kwance ta tashi zaune ta ce "Matsala kuma? Wace iri?" Nafisa na kwala ta saci kallon Mama Karime da taga anhalinta ba a gurinta yake ba ta ce "Ciki gareni Izzatu, kuma wallahi banaso na ara hada zuri'a da Nasir." "Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un, yanzu ke wane mataki kika yanke." "Zubar da cikin zanyi." Girgiza kai Izzatu tai kamar Nafisa na ganinta ta ce "A'a Nafisa bazamuyi kisan kai ba, kiyi hakuri ki haihu amma aure ne da Nasir babu shi." "Yanzu Izzatu haka kike so na dawama da auran Nasir a kaina sannan ga a ansa ina yawo dasu a gari." "Ya zakiyi hakuri zakiyi kafin mu samu mafita." "To shikenan nagode Izzatu." "Ki kula da kanki, karki ringa sa damuwa a ranki dan Allah." "In sha Allah." Nafisa ta ce. Sukayi salama ta ajiye wayar. * * * * * * * * * * "Sada wannan itace tanbaya ta arshe da zan maka cikin da in rai, wacece ta gudu da matata." Hawaye Sada ya tsare ya ce "Wallahi ranka shi dade basan sunan ta ba, amma naga akan number ta danakira a wayar Hajiya, Izzatu naga ansa." Kai Nasir ya gyada dan yasan Izzatu farin sani kuma yasan zata aikata tunda komai tare sukeyi da Nafisa kafin ya aureta. Kallon Sada ya yi ya ce "Afuwa aya zanma ta sakacin da kaiyi shine na salameka daga gidan nan." Rokanshi Sada ya ringayi yana masa magiya amma ya tashi yabar gurin, yabar Sada yanata kuka. * * * * * * * * * "Eh nine." "Dama kana nan Maniru." "Ina nan yauma naganka a masalaci shiyasa nakira police sukamaka tunda kazama megarkuwa da mutane." Cike da mamaki Yusuf ke kallon Maniru ya ce "Waye yace ina garkuwa da mutane?" "Waye a garin nan baisan kayi garkuwa da matar aure ba." Cikin tashin hankali Yusuf ya ce "Yanzu kana nufin kai ka kira police su kamani, bayan duk halin danake ciki kaine kasanya ni aciki shine yanzu kakeson ara salwantar da RAYUWA ta." Nan Yusuf ya bashi labari duk abunda ya faru tunda ga kaishi gurin Nasir neman aiki har kawo yanzu da suke tsaye suna magana. Hawaye Maniru ya share ya ce "Kayi hakuri Yusuf duk nine silar shigarka wannan masifar, danasani ban kaika gurin wannan azalumin ba." "Balaifika bane Allah ne yatsara hakan da rabon na ceci yariyar mutane da ake so a lalata rayuwarta." "Hakane amma....!" Maganar matarsa ce tasa ya kasa arasa tasa maganar "Ga an sanda nan a waje wai anga haurowar Yusuf gidan nan." Ido Yusuf ya zaro, Maniru ya dafashi ya ce "Karka damu zanji dasu, kashiga wance akin ka zauna, Raliya zata kawoma abunci kaci karka damu kaji." Kai Yusuf ya gyada, shikuma Maniru yai waje gurin police din. Abuda Maniru ya ce yai shi ya yi gudun samun matsala. * * * * * * * * * * "Barkan ku da zuwa yalabe, lafiya kuwa?" "Lafiya, amma an tabbatar mana da shigowar Yusuf cikin gidan ka." "A'a ranka shidade ba wanda ya shigo gidana." Tsawa ya daga masa ya ce "Maganar banza mu zaka rainawa hankali a tabbatar mana da haurowarsa kace baka ganshiba to inma biyeshi kayi ka fito dashi tun hukuma bata dau mataki akanka ba." Wani daga cikin yan sandan ya ce "A'a Sir Maniru bazai oye me lefi a gidansa ba, sabuda shine ma ya bamu masaniyar zuwan Yusuf." "Gaskiya ne wannan." Sauran ma suka fa a. "Okay to, amma idan ka ganshi ka sanar damu." "In sha Allah." Daga haka suka bar gurin. Maniru bai koma gida ba, sai ya zarce gidan da Yusuf ya zauna, nan ya samu driver da aka lodawa kayan Hauwa ya bashi kudinsa ya amshi labar wayarsa yai masa kwatancan garinsu Yusuf. Yana komawa gida ya sanar da Yusuf abunda ya faru, Yusuf ya yi mamakin ganin yan sandan basu kula da kayan Hauwa ba, dan yasan da sun ga kayan da yanzu sun kama kayan sun tafi dasu. Da dare Maniru da kansa ya raka Yusuf har tasha ya hau motar garin su, saida Maniru ya tabatar motar ta tafi sannan ya dawo gida. * * * * * * * * * Anwar ta kwantar akan gadon sannan ta kalli Nafisa da tai tagumi ta ce "Duk naji wayar da kukayi da Hajiya Izzatu azu." A tsorace Nafisa ta kalli Mama Karime, kai Mama Karime ta gyada ta ce "Matsalarki irin tawace, saidai bansan ba ko kema kishiya ce ta hanaki zaman gidan aure." Cikin damuwa Nafisa ta ce "A'a banda kishiya." Da mamaki Mama Karime ta kaleta ta ce "Iya bakin cikin mijine ya naki zama dashi? Ai taki da sauki, amma har kike ikirarin zubarda ciki." Ajiyar zuciya Nafisa tai ta kasa cewa komai. Mama Karime na kwala ta ce "Ni kishiya ita ta rabani da mijina da ata guda daya Khadija, ta rabani da gidan mijina...............! Sharhi ko arin haske 08166077167 Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 20 "Shekara uku da ta huce ina zaune a garin Kano da mijina da ata Khadija lokacin tanada shekara 14 a duniya, dangin mijina suka takura masa sai ya yi aure, shine ya auro wata me suna Lube, tunda lube ta shigo gidana na dainajin dadin zaman aure, mijina ya daina kaunata da Khadija, har takai wata rana bansan inda kaina yake ba na baro gidan na shigo duniya, nasha wahala sosai kan hankali na ya dawo jikina. Duk da halin da nake ciki baisa na manta da komai daya faru a baya ba amma nakasa sanar da kowa, tun da na ganki naji nauyin dake kaina ya ragu kuma har na iya bude baki na sanar dake komai, yanzu ha zuciya ta cike take da begen komawa gida." Ajiyar zuciya Nafisa ta sauke ta dubi Mama Karime ta ce "Dole ne na koma Kano koda hakan zai sake hadani da Nasir amma saina sadaki da arki da mijinki." Mama Karime na hawaye ta ce "Allah ya miki albarka nagode nagode nagode, har banda bakin gode miki." "Ba komai Mama kamar uwa kike a gurina." Nan suka cigaba da tattauna sanda zasuje kano cikin wannan satin. * * * * * * * * * Lokacin da Yusuf ya koma gida, duk yan gidan sunyi bacci, dan haka saida safe suka ganshi. Da safe ya shigo Khadija da suka fara zuwa makaranta da Murja sun shirya domin tafiya, sukaci karo dashi a kofar gida. Sun gaidashi, Murja tai gaba ita kuma Khadija ta tsaya kanta a asa ta ce "Jiya har dare ina jiranka baka dawo ba, hankali duk ya tashi kar wani abun ne ya sameka." Murmushi ya sakar mata ya ce "A abunda ya faru anwata." Kallonsa tayi ido cikin ido ta ce "Banka ta a yimun karya ba Yayana, amma meyasa kakeso karinga oyemun gaskiyar abunda ke faruwa. Jiya driver da ya kawo kayan aunty Hauwa ya tabbatar mun da police sun kamaka, shiyasa ban iya bacci ba saida naga shigowarka, na zata zaka fa amun gaskiya, tunda duk abunda ke faruwa ya shafeni amma ka oye mun." Nunfashi ya sauke ya ce "Khadija, tabbas muna cikin bala'i, police da laifin garkuwa da mutane suke zargina, kuma nasan Nasir shine ya shirya wannan abun." Cike da tsoro Khadija ta ce "Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un! Ya Yusuf, zamana a gurin ku ba alheri bane, dan haka zan koma gida, na wankeka daga zargin da akema, koda hakan zai bawa Nasir damar cima burinsa a kaina, ai ba akaina aka fara zan jure duk wani wulakanci tunda ba galibu gareni ba. Koda Nasir ya kusanceni da manufarsa, ai ba zina yai daniba akwai aure a tsakanin mu idai tsafinsa zai tasiri a kwaina idan mukaje gaban ubangiji zai mana shara.......!" Saukar marin da taji a fuskarta yasa ta durkushe ba shiri ta saki kuka me sauti. Cikin tsananin acin rai da masifa ya ke magana. "Uban wa yace miki bansan da aure a tsakanin ku, ko kina zaton basan darajar aure ba na nemi salwantar da nawa mutuncin dan na ceci naki, Khadija bazan hanaki tafiya ba wannan karon duk inda zakije kije, koda kanki zaki kawai Nasir bazan dakatar da keba." Yana gama fa in haka, ya juya yashige gida a fusace. Kuka sosai Khadija takeyi duk da tasan Yusuf ya mata halaci amma bazata zuba ido a ringa zargisa da laifin da bashi a aikata ba dan haka dole ta koma gida yau koda hakan zai zamo silar salwantar rayuwarta. Tana tashi bata shiga gidan ba, dan haka tai hanyar da zata sadata da inda zatahau motar garinsu. * * * * * * * * * * * Mama Karime ta fito da jakar tasu, anwar Izzatu dake tsaye ta ce "Gaskiya zanyi kewarki Mama Karime." Murmushi Mama Karime tai ya ce "Ai ba zama zanyi ba, yarinyata kawai zanje na gani, kila na wuce katsina naga lafiyar yaron an uwana Nasiru, ta barsu shekara da shekaru." "To Allah ya tsare." "Amin." Nafisa ta ce, wanda ke rike da hannun Anwar sukayi mata salama suka ako hanyar Kano. * * * * * * * * * * A kofar gidan sukai parking, Nasir ya kali driver ya ce "Nan ne gidan Izzatu, kashiga ka kamun salama da ita, idan taki fitowa to kadawo ka sanar dani." To driver ya ce, ya fito ya shiga gidan Izzatu. Izzatu na zaune a falo dayake mijinta ya yi tafiya sai ita kadai dan haka koda taji salama hijab tasa ta fito dan ganin waye. Ganin bata san shiba ta ce "Lafiya kuwa, ban ganeka ba." "Sunana Kamal, ni driver Alhaji Nasir ne, yana waje yana son ganin matar gidan Izzatu." Zaro ido Izzatu ta yi ta ce "Kaje kace bata nan." Bata jira me zai ce ba ta rufo gidan ta koma ciki. Komawa kamal ya yi ya ce wa Nasir. "Oga wata mata tafito ta ce bata nan." Kai Nasir ya girgiza ya ce "Ya kamanin ta suke." "Fara ce me jiki a shekaru zatayi Hajiya." Murmushi Nasir ya yi ya ce "Bude mun kofa muje tare." Bude kofar Kamal yai, suka shiga gidan tare da Nasir. * * * * * * * * * * Murja ce tai salama, Nasir najin salamarta ya fito daga dakin, dan tunda ya baro Khadija tana kuka yakasa samun nutsuwa. Ganinta ba Khadija ya ce "Murja ina kika baro Khadija?" "Yaya ai ba tare muka tafi ba, tunda na barta a gurinka, natafi kuma ban ga taje makaranta ba." Gabansa ne ya fadi, kenan da gaske ta ke tafiya ta yi. Me yake shirin faruwa Khadija zatakai kanta ga halaka, yasan koda Nasir yayi anfani da Khadija to bazai rabu da itaba tunda ta ata masa komai, zai iya halakata gaba aya. Zuciyarsa ce ta fara tsinkewa, wani irin gumi na keto masa, a hankali ya ce "Okay to." Daga haka ya koma ciki, kaya ya sauya a dauki kudin da zasu kaishi cikin gari, yabar gidan ba tare da yaiwa kowa salama ba. Dan ya kudiri aniyar bazai bari Nasir ya cutar da Khadija ba koda zai kashe su gara ya kashesu tare................! Sharhi ko arin haske 08166077167 Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 21 Har cikin gidan suka shiga tare, driver nashi ya kwankwasa kofar gidan. Izzatu dake zaune tanaji amma tsoro da fargaba sun hanata bude kofar, cikin dakewa ta taso har jikin kofar ta ce "Waye?" Muryar wanda taji yasa ta zaro ido, ya ce "Munason magana dake ko zaki iya bude kofar?" Jiki a sanyaye ta bude, ta gaidashi ya amsa ta ce "Kayi hakuri Nasir mijina baya nan bazai yiyu mu shiga ciki bada izininsa ba, duk maganar da zamuyi muyita a nan dan Allah." Murmushi yai ya ce "Tanbaya aya zan miki, bayan ita bazan sake tanbayarki ba, wata kila tuhuma ta biyo baya, bayan tuhuma kuma abu na gaba bazai da i ba." Baki Izzatu ta ta e ta ce "Ina jinka." "Ina matata da yarona." "Basan ida suke ba, nasan dai ni natayata yakin fita daga gidan ka amma bansan inda ta tafi ba." Wani mayaudarin murmushi Nasir yai ya ce "Na baki nan da awa 1 idan baki ne mota ba, ba lalai ki kasance cikin wannan gidan cikin koshin lafiya ba." Cike da rashin tsoro Izzatu ta ce "Hmmm idan baka fasa, kai ba Nasir bane, har ka isa kaimun abunda Allah bai munba arya kake wallahi. Burin kuya kawai da kana sonta kake hulakan tata." Batajira cewarsa ba ta koma ciki harda rufo kofa da arfi. Da kallo Nasir ya bita cike da mamaki to meyasa kowa ya rainashine? Le anshi ya ciza da arfi yana huci kafin ya juya a fusace ya shige motar subar gurin. Da azahar su Nafisa suka sauka a Kano, kai tsaye mai adaidaita suka tara ya tafi dasu gidan Mama Karime. Khadija tana sauka a cikin gari ta nufo gidan su, duk da zuciyar ta, tana tsanan ta bugawa tsoro da fargaba sun mamayeta, amma ta dake dan ta fitar da Yusuf daga zargin da ake masa. A kofar gidan suka sauka, suka shiga ciki da salama. Mama Lube na daka a turmi taji muryar da bazata ta a mantawa da itaba, A tsorace ta ago dan tabbatar wa kanta, abunda tagani yasata tashi da sauri tana murza ido ko mafarki takeyi, amma me da gaske kishiyarta Karime ce a gabanta, bakinta na rawa ta ce "Karime dama kina raye?" Murmushin takaici mama Karime tai ta ce "Kin zata kin salwantar da rayuwata ko?" Ido Mama Lube ta ringa zarewa, Baba ne ya shigo da salama a bakinsa. Ai kasa arasa salamar yai cikin tsananin mamaki ya ce "Karima!" "Na'am Malama." "Kece ko mafarkin da nasabayi ne naki." "Nice Malam ba mafarki ka ke ba." Amma Baba bai gaskata zancan ta ba, ya matsa kusa da ita ya kai hannu ya ta ata yaga da gaske ita ce saiya fashe da kuka. "Karima rai kanga rai, ina kika shege shekaru da yawa haka, na zata kin mutu dan har na gaji da nemanki ashe zaki dawo." "Gani Malam, ina Khadija ta?" Kallon kallo suka farayi da Mama Lube kafin ta ce "Tayi aure." " arya takeyi ta saida ita ga matsafa." A razane duk suka kale shi. A kofar gidan sukai parking ya dubi driver nasa ya ce "Bani key din motar ka shiga gida." Miko masa yai ya fito ya bude masa motar ya fito ya koma mazaunin driver ya ja motar a guje yabar gurin. * * * * * * * * Gudu akeyi a babur din amma gani yake kamar ba tafiya akeba, sabuda yadda zuciyar sa take bugawa da arfi gani yake kamar wani abu zai faru kafin ya arasa inda Khadija take. *** *** *** *** Nan baba ya basu labarin komai ya ara da cewa "Wannan munafukar matar duk ita taja na zata auran gata naiwa Khadija ashe dan a dauke mun ita ne ba ita ba mijin duk sun ata." Dafe kirji Mama karime tai tana an baton "Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un!" Kafin suyi aune ta zube a gurin sumamiya. Kanta sukayi suna salati, Baba ya fashe da kuka ya na cewa "Kiyi hakuri Karima karki mutu ki barni." Nafisa ce ta karfi gorar ruwan dake hannun Anwar ta fara zubawa Mama Karime a fuska tana tofa mata addu'a. Ajiyar zuciya Mama Karime ta sauke ta bude ido a hankali, Nafisa na jero mata sannu ita kuwa Mama Lube ido kawai take zarewa tana mamakin ya akai duk sihirin da tayi ya karye lokaci guda. *** *** *** *** *** A kofar gidan yai parking har zai fito yaji wayarsa tana ruri, tsayawa yai ya duba, Hasina ce, tsaki yaja har ta katse bai dauka ba. Kiran ne ya sake shigowa, har zai share sai kuma ya daure ya daga. "Hello Nasir kana ina?" "Ina ruwanki da ida nake?" "Akwai matsala duk wani aikin ka an rusa shi yanzu shirin yadda za'a salwantar da rayuwarka akeyi." "Mtsss kinga Hasina ba wannan a gabana ba yanzu haka ina kofar gidan su wannan yariyar dan iyayenta sai sun biyani kudina kuma wallahi saina daure su." "A'a Nasir ka fara kashe wutar gabanka tukun.....!" Wayar ya katse bai shirya ba, abunda idon sa yake gane masa kamar mafarki, Khadija ce a gabansa tana kokarin shiga gida. Da sauri yafito yasha gabanta yana kare mata kallo cike da mamaki. Jikin Khadija rawa ya dauka ganin abunda bata zata ba. Mama Karime na kuka ta ce "Bazan taba yafema ba, tunda ka salwantar mun da yata kuma wallahi sai nayi kararka." Hakuri Baba ya fara bata amma ta tashi fa nufi hanyar fita. Kallon ta yake ido cikin ido ya ce "Kin gama gudun? To yau naga uban da zai kwace ki." Hannu yakai ya fizgota da karfi, ihu ta kurma wanda yai dai-dai da fitowar Mama Karime. Wadda ta saki baki ta ce "Yakubu!" Tare suka juyo, Nasir yana kallon matar wadda ta kirashi da sunan mahaifinsa, ita kuma Khadija kokarin kwace kanta take ta kasa. Nafisa ce ta fito da jakun kunan su, ai sakin su tai a tsaye ganin Nasir rike da wata a hannunsa tsoro da fargaba suka cikata, gumi ne kawai ke tsatsafo mata. Khadija kamar gizo haka take kallon Mama Karime, fuskar da bazata taba mantawa da itaba, wadda ta fida rai da sake ganinta a fili ta furta. "Mama dama kina raye?" Mama Karime kuka kawai take ganin abunda bata taba tsamani ba. Mama Lube da Baba ne suka fito, bakin Baba har rawa yake ya ce "Laaa gashi nan shine munafikin daya sace mun yata." Baki Mama Lube ta saki ta kasa cewa komai dan tasan duk abunda ke faruwa. Khadija ce tai tattara duk karfinta ta kwace daga jikin Nasir, da sauri yakai hannu zai sake rikota yaji an rike hannun sa, d'agowa yai sukayi ido 4 da Yusuf wanda ya hada gumi yai wurjan jan.................! Sharhi ko karin haske 08166077167 Comments And Share By *Zarha* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 22 Ran Nasir ne yai mugun aci ya fusge hannun sa daga na Yusuf, ya kaiwa Yusuf wata shaka, kaucewa yai da sauri Khadija dake kusa da su ta shiga tsakane tana watsawa Nasir mugun kallo ta ce "Duk to zarta rayuwarsa da kayi, da yi masa azafi bai isheka ba sai ka ara da takalarsa da rigima." Nasir da idonsa ya rufe, ga acin rain su da ke ransa kawai ya sa hannu ya shaki Khadija. A take ida nuwanta suka firfito waje ta fara ka karin mutuwa, Nafisa ce tai namijin kokarin zuwa inda yake ta rike hannunsa ta ce "Nasir baka da hankali kashe yariyar mutane zakayi." Sakin Khadija yai yana huci a take tai baya zata zube, Yusuf yai saurin tareta ta fa a jikinsa, tunzura Nasir ya sakeyi zai kara yin kansu Nafisa ta rikeshi sosai ta ce "Meyake damunka ko ka fara shaye-shaye." Kallon ta yai da idanunsa da sukai ja, ya ce "Sakeni malama." "Bazan sake kaba Nasir, me kake kokarin aikatawa?" Cikin tsawa ya ce "Ki sakeni, saina kashe su, naga uban da ya tsaya musu." Ya ara maganar yana nuna Yusuf da Khadija. "Me suka maka? Da kake ikirarin halaka su." Kafin Nasir yai magana, Anwar yazo ya rungume Nasir ya ce "Daddy." aukan yaron yai yai murmushi ya ce "My son ina kuka tafi kukabar Daddy 2days." Ai kowa sakin baki yai yana kallon ikon Allah Musaman Mama Lube da Baba. Mama Karime ce ta ce "Dama jikina yana bani Anwar jinin Yakubu ne." Da sauri duk suka kaleta, ta gyada kai ta ce "Dan Allah mu koma ciki." Mama Lube sai lokacin ta samu bakin magana "Eh hakan zaifi karmu tarawa kanmu jama'a." Shiga sukayi ciki, amma Nasir ya ce bazai shigaba. Cikin rarrashi Nafisa ta ce "Dan Allah ka daure muje, badan komai ba sabuda mama Karime da take ikirarin tasan wani Yakubu, wata kila tasan asalinka." Murmushin takaici yai ya kamo hannun ta ya ce "Na santa." Da mamaki Nafisa ta kaleshi, ya gyada mata kai ya ce "Ina da shekara 8 mahaifiyata ta rasu, ita anwar Babana ce, ita ta rikeni har lokacin da aka aurar da ita lokacin shekarata 13 a duniya, tunda ta baro katsina nasan maraicin uwa, shekararta uku da baro katsina Babana ya rasu, na taho kano ne manta amma ban sameta ba, haka aiki ya kaini Kaduna, amma ban zauna a canba, na dawo kano dan duk na hadu da ita amma ban sameta ba sai yau." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Sabuda wanda sukaci amanata yasa bazan shiga gidan ba." "Suwaye su? Kuma me suka maka haka?" ara an ame hannun ta yai ya kasa cewa komai, dan bazai iya sanar da ita abunda ke tsakaninsu da su Yusuf ba, haka kawai ya ke jin nauyinta. Katse masa tunanin nasa tai da cewa "Nidai kazo kawai mu shiga." Kasa yi mata musu yai taja hannunsa suka shiga ciki. Duk suna zaune, Khadija na jikin Mama Karime ta rasa gidan tsoma rai sabuda da i. Zama sukayi, Baba ne yai gyaran murya ya ce "Yanzu kai Nasiru mun dauki amana mun baka auran yar mu amma ka gudu da ita." Kallon sa Nafisa tai da sauri, yai kasa da kai ya kasa magana. Yusuf ne ya ce "Baba bashi ya gudu da Khadija ba, tana gidan iyaye na." Nan ya kwashe komai ya sanar dasu. Salati duk suka saka, Nasir kuwa in bada gumi ba abunda ke keto masa, Nafisa kuwa kuka take kamar ranta zai fita, tana dana sanin auran Nasir. Baba ne ya taso ya shaki wuyan Nasir ya ce "Allah ya isa tsakanin mu dakai kuma ka sakar mun ata kaje kaida Allah tsinan...!" Mama Karime ce tai saurin cewa "Ka daina zagar mun yaro." Baki duk suka saki Khadija dake jikinta tai saurin tashi tana kallon ta " anane, duk da yai kuskure amma ku masa addu'ar shiriya ba tsinuwa ba, kuma aure shida Khadija ba saki a tsakani." Cikin tsoro Khadija ta ce "Mama a ina kika sanshi?" Nan Mama Karime ta basu labarin Nasir dan yayanta ne Yakubu. Kowa ya cika da mamaki. Nafisa ce ta kama hannun Anwar da sauri ta fice daga gidan Bin bayanta Nasir yai yana kiran sunan ta amma ko kulashi batai ba. Mama Lube ido kawai take zarewa gudun tonuwar asirinta..............! Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 24 Amma bai bari sun fahimci halin da yake ciki ba, yai musu salama ya fice daga gidan. Baba da kansa ya wanke akin Mama aka gyareshi tasss, sannan aka sa mata katifa da kayanta. Bayan sun koma akin, Khadija ta kali Mama murya a raunane ta ce "Mama nidai kiyi hakuri bazan iya tafiya wani gurin na barki ba, kuma kinsan halin wannan mutumin bashi da imani, da zakice na koma gidan sa nai jinyarsa." Dafata Mama tai cikin rarrashi ta ce "Kiyi hakuri Khadija, nima ina tsoran abunda zai faru amma hakuri zakiyi kinji." Gyada kai tai badan zata iya abunda Mama ta ce da ita ba. *** *** *** *** *** Nasir kuwa tunda aka mai dashi gidansa bai san wanda ke kansa ba, gashi duk ma'aikatan gidan sun i kula dashi yana ajiye kamar gawa a yashe ba gata bare galibu. Mama Karime ba yadda batai da Khadija ta koma gidan Nasir tana kula dashiba amma taki sai kuka da take tayi. Dafa ta Mama tai cikin rarrashi ta ce "Khadija ki duba girman Allah dan Allah zakiyi ba dan halin mu ba ko abunda ya faru, Allah ma muna masa laifi ya yafe mu, bare mu da muke neman dacewa, dan Allah kiyi hakuri kije ki kula dashi zuwa gobe zan lala a babanku ya bari muje Katsina acan sai a cigaba da jiyar tasa." Gyada kai Khadija tai ta ce "To bari naje gurin Abida mu tafi tare." "To shikenan Allah ya tsare." "Amin." Ta ce tai wa Mama sallama ta fice. **** **** **** **** **** Koda ta fita gidan su Abida ta huce nan take sanar da Abida abunda ke faruwa. Dariya Abida tai ta ce "Ai dama arshen azalumi baya kyau, amma yanzu ke mekika yanke." "Gaskiya Abida bazan iya zuwaba, kisan halin dan Adam wata kila ma yana sani yai haka yadda idan naje ya cika burinsa a kaina." Girgiza kai Abida tai ta ce "A'a bana tunanin haka, dan kina ganin yanayin ciwansa kisan tsafin da sukene ya fara dawowa kansa, amma nima ban guyi bayan kije wannan BAKIN GIDA n nan nasaba ki zamanki a nan mu kwana gobe maje tare da Mama." Shawarar Abida ta dauka tai kwanciyarta a gidan su Abida. Washe gari Mama da safe ta samu Baba ta ringa masa magiya akan ya bari su kai Nasir Katsina cikin dangi ai masa magani. Saida aka kai ruwa rana kafin ya bari. Mama Lube kuwa taji da in haka dan zata sake samun damar ka a Mama Karime ta koma yawan duniya daga ita har Khadija dan bata kaunar ganin su. Mama tana shiri Khadija tai salama a dakin, cike da mamaki Mama ta ce "A'a meya dawo da ke da safe haka." Kanta a asa ta ce "Kiyi hakuri Mama ban je ba." Ajiye mayafin dake hannunta Mama tai ta dauke Khadija da mari, cikin fushi ta ce "Wato ni ban isa da ke ba ko Khadija, ko da kasheki Nasiru yai kika dawo yaci darajata iya jiya bare ba abunda ya miki, yan zu har kin kawo karfin da zan saki abu ki kiyi ko Khadija? To na gode kin nuna mun matsayina da iyaka ta." Khadija na kuka dafe da kuncin ta, ta ce "Dan Allah Mama kiyi hakuri." Ko kulata Mama batai ba ta fice tabarta a akin. Da kallo ta raka Mama kawai tanajin ranta na mata suya. Da bara ce ta fa o mata, ta koma gidan su Abida ta ce dan Allah tazo ta bawa Mama hakuri. Hijab ta sako, ta zo ta samu Mama ta gaida ita ta ce "Kiyi hakuri Mama bamusan ranki zai aci ba, in sha Allah haka bazata sake faruwa ba." "Hmm na muku uzuri wannan karon amma nan gaba bazan lamunci irin wannan sakarcin ba." "In sha Allah Mama mun gode." "Idan taga dama tashirya zamuje Katsina kai mara lafiya." "To." Abida ta ce, ta sanarwa da Khadija, suka shirya da Mama suka huce gidan Nasir. Abun tausayi yadda suka tafi suka barshi haka suka taddashi duk ya bata gadon da fitsari da yawun bakinsa da yaketa zuba. Jikin Khadija yai sanyi ganin halin da yake ciki kuma zuciyarta me imani ta fara tausayin Nasir. Mama ce ta kira masu aikin gidan tasa sukaiwa Nasir wanka aka sauya masa kaya sannan ta salame su tace kule gidan za'ayi ta biya kowa albashinsa suka tafi, nan tasa aka nemo mata Sada, dan ta tanbayi ma'aikatan gidan sunce shine Nasir yafi amunta dashi kawai matsalar guduwar Nafisa ce tasa ya koreshi, dan haka ta ce tare zasu tafi sabuda dole saida Namiji me kula da Nasir. **** **** **** **** **** Sai yamma likis suka isa Katsina, gidansu Mama tasa aka saukesu suka shiga ciki. Duk gidan ya sauya mata, mutanan gidan sunyi mamakin ganin su amma sunyi farin ciki, anyi gashe-gashe da koke-koken wanda aka rasa sannan aka basu masauki. Mama dakin ta da ban sai wanda akabawa Nasir. Da dare Mama ta ce ita Khadija ta zauna da mijinta shikuma Sada ya koma dakin zaure tunda ba kowa. Kwala ce ta cikowa Khadija amma taga Mama ta hade rai ba fuskar yin magiya ko ban hakuri, gashi ba gurin gudu. Haka ta karaci matsar kwalarta, Mama ta i kulata, jiki a sanyaye ta tashi ta shiga dakin da Nasir ya ke. Can nesa da katifar da yake kwance ta rakube tana kallonsa, da tausayinsa wai yanzu duk izzar nan da fadin rai shine kwance anan an jirkita halitarsa ya koma abun tausayi, kamar a mafarki taga ya bude ido.............! Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 25 A tsorace tai baya ta murza ido, sai lokacin taga gizo idonta ke mata, ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta zauna. Ranar yadda taga rana haka taga dare, a zaune ta kwana sabuda tsoron kar Nasir ya farka a cewarta. Washe gari Da sassafe taje ta taso Sada itace ya kula da Nasir, ita kuma tai kwanciyarta a dakin Mama. Kwanan su biyu a Katsina, Mama suka bazama neman maganin ciwan Nasir. Har Allah ya kaisu gidan wani alarama nan ya tabbatar musu turan aljanu akaiwa Yusuf kuma ba kowa bane sai yan kungiyar Asiri da yake tare dasu, kuma a yanzu rabashi da wannan bakaken aljanu zaiyi wuya. Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta ce "Yanzu ba wata hanya da zamubi ya samu lafiya." "Eh to hanya daya ce, dole duk abunda akasan na tsafine a gidansa aje a kone shi, sannan zaku barshi a nan aimasa magani har ya samu lafiya." Gyada kai Mama tai ta ce "To shike nan ba matsala, amma nawa ne kudin maganin." "Zaku bada dubu dari uku yanzu haka." Shiru Mama tai dan kudin da Nafisa ta bata sun kusa karewa amma zasu isa ta bashi, dan haka ta auki kudin ta bawa Alaraman. **** **** **** **** **** **** Tunda ya koma gida zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa, baisan haka Khadija tashiga ransa ba sai wannan lokacin da bata tare dashi, kulum yana gida ya na tunanin halin da Khadija ta ke a yanzu ita kuma Hauwa sai rawar afa take akansa tunda wadda ta tsokane mata ido tabar gidan. Wata rana Yusuf na kwance a aki, Kawu yai salama ya shigo, amsawa yai yana tashi zaune, kawu ya ce "Yanzu Me gari ya aiko kiranka Allah yasa ba rigima ka arayi da Haliru ba?" "A'a Kawu, saidai in wani abu daban." "To shike nan, ka tashi kaje, Allah yasa lafiya." "Amin." Nasir ya ce, ya tashi ya sauya kaya ya nufi gidan me gari. Shake ya tadda fadar me garin da mutane, salama ya yi yasamu guri ya zauna ya gaida su me gari, da fara'a me gari ya amsa ya ce "Malam Yusufa wannan muta nan ne suka zo gurinka, ka gane su?" Kallon su Yusuf yai ya ce "Kamar na so na gano ku amma na sha'afa." Murmushi wani a cikin su yai ya ce "Sunana Alhaji Munir, can da da ewa na ta a zuwa na siri shinkafa a gurinka kuma Alhadulilah na samu nasibi sosai a ciki, shiyasa da abuki na ya bude company na shinkafa na ce bari na rakoshi gurinka dan kaima ka zama daya daga cikin masu bawa company shinkafa tana sarafawa." Baki Yusuf ya washe ya ce "Masha Allah Alhadulilah, naji da i sosai." "Bakomai, shiyasa muka taho gaban me gari ayi komai a gabansa, kuma idan kana da wani dan uwa ko aboki da kasan zai ringa bamu shinkafa ba ha'inci to kofa a bu e ta ke zaka iya kawoshi gare mu." "Na gode sosai kuma naji da in zuwanku." Nan suka bashi number wayarsu, da address in company sukai wa me gari godiya suka tafi. Me gari sai washewa Yusuf baki ya ke dan yaga arziki ya zo gareshi, yai wa me gari Salama ya tafi gida. Nan aikaita zuwa tayashi murna harda Haliru ba kunya ba tsoran Allah, Yusuf bai nuna masa komai ba suka gaisa ya ce "Munji abun arziki Allah ya sanya alkairi." "Amin, na gode." "Dama naji sunce in kana da wani naka kuje tare, to naga muma muna noman shinkafar nan duk garin kura kowa yasan munfi kowa numa shinkafa dan Allah kasa da sunana." Murmushi Yusuf yai ya ce "Zanyi shawara." Jiki a sanyaye Haliru ya huce, Yusuf ya bishi da kallon mamaki dan Adam kenan, wai yanzu shine mutum har ana zuwa neman alfarma gurinsa. **** **** **** **** **** Mama da kanta ta kira Nafisa ta roki alfarma akan ta je ko ta tura gidan Nasir duk wani abu na tsafi koda kudine a kone su. To, Nafisa ta ce ta aiwatar da abunda Mama ta Sada. Satin Nasir uku a gidan wannan Alarama aka dawo dawo dashi dan ya daina zubar da wannan yahun bakinshi ya dawo dai-dai haka numfashinsa kawai farkawa ce har yanzu ya gaza yi. Dakin da aka fara kaishi Mama tasa aka maidashi Khadija ta cigaba da jinyarsa da dare shi kuma Sada da rana. Tun Khadija tana san ran farkawar Nasir harta fidarai da zai tashi kuma ta sake tana iya bacci amma can gefe take shinfi a ta kwanta. Mama dama ta shirya haka ne dan Khadija ta daina gudun Nasir ta saba da zama dashin tun kafin ya warke dan baza ta bari wannan ha in da Allah ya adara a rabuba. Sun gama cin abuncin dare Mama ta ce "Yanzu Kabiru ya turo matarsa na nakuda Asiya, zanje mu tafi Asibiti yanzu." "Amma Mama gasu Inna Saude suje tare mana." "Tunda har ya tuna dani yazo ya sanar dani ai ya kamata naje matsayina na uwa ko?" "To shike nan, sai kun dawo Allah ya tsare." "Amin." Mama ta ce tasa hijab ta fice. Zaman ta Khadija tai a dakin Mama dan ta ce yau ba inda zata. Sai 9:30pm ta tashi wanka ta yi tashiga dakin Mama, nan ta tuna kayanta suna akin su, tsaki ta ja, ganin ba kowa a gidan tai fitarta daga ita sai zani data daura a jikinta. Kwan akin ta kuna da ya ke da wutar nefa, ta jawo jakarta ta fara duba kayanta. Ba zato ba tsamani ta ji saukar muryarsa a kunanta kamar saukar aradu, a tsorace ta kalli inda ya ke dan aukanta gizon da yake mata ne, amma me a zaune ta kanshi ya zuba mata manyan idanuwansa wanda suka ka a mata hantar cikinta...............! Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 26 Ja da baya ta farayi har Allah ya bata sa'a kafin ya ara magana, ta fita da gudu. Tashi yai ya bi bayanta, hanyar fita yaga ta nufa, wata uwar tsawa ya daka mata wadda tasa saida ta tsaya ma shiri. "Gidan ubanwa zaki fita a haka? Baki da hankali zaki fita waje a daran nan ba kaya a jikinki." Da mamaki ta kalli jikinta dan ta manta da mene a jikinta, kunya da tsoro ne suka ara rufeta taja afa a sanyaye ta shige akin Mama. Hijab kawai ta sako, tana le ensa ta taga, taga ya shiga bayi, Mamaki take taya yasan gidan sosai da haryasan azu hanyar fita tabi kuma yasan bayi ba tanbaya, shida aka tahu dashi kamar matace, koda yake a garin ya rayu ilama nan ne gidan su. Saurin kawar da tunanin tayi, tana san a ta koma akin, kayanta ta ako a guje ta koma cikin akin Mama. Duk abunda take yana kallonta, amma bai kulata ba danshi mamaki yakeyi me ya dawo dashi wannan garin da ya bari shekara da shekaru, kuma ya akai basan ya zo ba? Mama Karime ya ayana a ransa dan tunda yaga Khadija yasan itace zata kawoshi garin nan. Fitowa yai ya koma akin nasa, sai yanzu mutuwar iyayensa ta dawo masa sabuwa fill, kuma yakejin ciwan maraici, da badan maraici ba bazai shiga halin da yashiya ba a rayuwarsa. Hawayen da suke sako masa ya share, yasan ya aikata babban kuskure shiga kungiyar Asiri amma ba yadda zaiyi, basan me yasa yanzu komai yafita a ransa ba, inba Nafisa da Anwar ba, ba abunda yake so ya ra eshi, sai Mama Karime da ta dawo rayuwarsa wadda yasan rashinta ne a baya ya jebashi halin ha'ula'i. Wannan dare shida Khadija kwanan zaune sukai shina tunanin halin da yake, ita kuma na tsoro da bargabar abunda zai je ya dawo. Washe gari Da safe su Mama suka dawo daga asibiti tunda wadda suka kai ta sauka lafiya tun dare. Da salama ta shigo gidan, Khadija najin salamarta ta bu e akin da tun jiya ta kule kanta a ciki, Da gudu ta fa a jikin Mama tana nuna mata akin da Nasir ke ciki. Da mamaki Mama ta ce "Lafiya ko mutuwa Nasir yai?" Da sauri ta girgiza kai murya na rawa ta ce "A'a farkawa yai." Tana rufe baki Nasir yana fitowa dan yaji maganar Mama. Da tsananin farin ciki Mama take kallonsa ta ce "Alhadulilah, Allah na gode ma da ka nunamun wannan ranar." Khadija ta zame daga jikinta ta arasa gaban Nasir ta ce "Sannu Nasiru ya jikin naka?" "Ni lafiya nake yanzu." "To masha Allah." Nasir yana kallon Mama ya ce "Am tunda Allah yasa naji sauki, ni zan koma gida sabuda matata." Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta ce "Bazan hanaka tafiya ba amma zan ha aka da matarka ku tafi, ni sai zuwa jibi zan taho." Shiru Nasir yai kafin ya ce "Jibin kwataho da ita kawai." Mama bata son takura masa dan haka ta rabu dashi ya tafi shida Sada. A hanya Sada ya bashi labarin komai da ya faru da tafiya da iyayen Nafisa sukayi da ita, da jinyarsa da Mama Karime tasha da Khadija, jinjina kai kawai Nasir yai yana ayana abubuwa da yawa a ransa _Kano state_ A Kano Nasir ya samu sallar Azahar ko gida bai jeba ya zarce gidan su Nafisa. Yafi awa 3 a waje ba wanda yafito ya saurareshi a cikin gidan nasu, sai daga baya Babansu Nafisa ya fito, dukawa har asa Nasir yai ya gaidashi, sama-sama ya amsa ya ce "Dama na jima ina zuba idon ganin ka." Da sauri Nasir ya ce "Bani da lafiya amma yanzu naji sauki shiyasa nazo." Gyada kai Babansu Nafisa yai ya ce "Yauwa to yau bazaka bar ofar gidan nan ba saika bani takardar sakin ata." A tsorace Nasir ya ce "Saki kuma Baba, meya kawo zancen saki ana zaune alau." aure fuska tamau Baba yai ya ce "Kada ka maidamu wanda basusan abunda suke ba, taya zan barmaka ata kana cida ita da haram kana shayar da ita da haram kana tufatar da ita da haram, kuma shine sabuda mu bamuna tunani zamu bar armu a sannun matsafi nan gaba yai tsafi da ita." Rintse ido Nasir yai cike da tashin hankali ya ce "Dan Allah Baba ku tausaya mun wallahi bazan iya rayuwa ba Nafisa ba na muku alkairi na daina abunda nake kuma duk abunda nasan nasamu ta hanyar da ba dai-dai ba zanyi sadaka dasu." "Kaga nifa ba sa'an wasanka bane idan zaka bani takardar Nafisa ka bani in bazaka bani ba, to kajira samaci a koto." Ai tuni hawaye sun wankewa Nasir idanu, zaman dirshan yai ya ri e afar Baba yana cewa "Dan darajar Manzon Allah s.a.w Baba karka rabani da Nafisa ina son matata Baba karku rabamu dan Allah." Kwace kafa funsa Baba yai ya ce "Na kula taurin kanka bazaisa mu rabu lafiya ba, dan haka sai kaji samaci." Daga haka Baba ya shige warsa ya bar Nasir a gurin a zaune yana kuka kamar yaro. Abune ya taru yai masa yawa yanzu ina zaisa kansa? Duk abunda ya faru tsakanin Baba da Nasir, Nafisa tana zaure tana jinsu, abunda take tanbayar kanta dama Nasir yana son ta haka yake hula an tata, ya maida ita kamar baiwa? hawayen fuskarta ta share ta koma gida da gudu lokacin da taji alamun tahowar Baba. **** **** **** **** **** A kura kuwa, Yusuf har ya gaji da sintirin da Haliru yake masa kulum yana makale dashi da yaji arziki ya sameshi, duk da Yusuf yasan company da zai ringa kaiwa shinkafa suna bukatar masu kaiwa da yawa amma ba zai kai Haliru ba sabuda yasan halinsa ba mutumin kirki bane. Nasir tun washe gari ya saida duk wata kadara daya malaka ya raba kudin a gidan marayu da nakasasu da masu bukata, ya tashi bashida biyar ta kansa, dan haka ya auri aniyar niman Halakkkk yanzu............... Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 27 Kwanaki biyu da tahowar Nasir Mama taiwa dangi salama ta sako iyarta a gaba suka taho gida. Mama Lube bata ji da in dawowarsu ba dan dai ba yadda zatayi ne. Nasir ya koma kasuwar Singa idan ya samu dako ya yi su sauke kaya a mota a biyasu, da haka yake samun nakai abunci bakin salati, kuma a kulum yana tashi daga Kasuwa, to gidansu Nafisa zaije amma har gobe Baba bai yarda ya sako ba, shi Nasir ma haka ya ce Baban ya yi hakuri baice a bashi Nafisa ba bashida gidan da zai sakata, amma su fahimci ya shiryu yanzu ya zama mutum kamar kowa. **** **** **** **** **** Cikin nutsuwa ya ce da driver n babur in adaidaita sahun ya tsaya, sauka yai ya ce ya jirashi yanzu zai fito su tafi, "to." Me babur din ya ce, shikuma ya arasa ofar gidan. Salama yai aka amsa, ya jira har Maniru ya fito, da mamaki Maniru ya bashi hannu suka gaisa ya ce "Abokina kwana da yawa." "Ina lafiya ya gida?" "Kowa lafiya lau." Cikin nutsuwa Yusuf ya fara magana "Dama Hausawa suna cewa duk dan halak baya manta alkairi, shiyasa nima ban manta da alherinka a gareni ba, na samu aiki da company na rice har mun fara aiki dasu ina kai musu shinkafa, Alhadulilah ina samun nasibi a ciki dan yanzu haka na siyi gida a nan birnin Kano a unguwar Janbulo wadda zamu zauna da matata da iyayena abun hawa kawai ya ragemun yanzu kuma shima in sha Allah muna saran malakarsa nan ba da jimawa ba." Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "Yanzu haka company sun bukaci ma'aikata da wanda zasu ringa kawo musu rice, sun yarda dani 100% shiyasa suka nemi na kawo musu duk wanda naga ya dace, shine naga ya dace na nemeka." Murmushi Maniru yai ya ce "Gaskiya naji dadin wannan al'amari kuma na gode sosai." "Ba komai a baya kaima ka taimake ni, kaso na samu aiki gurin Alhaji Nasir kuma aka samu akasi." Dariya Maniru yai ya ce "Kasan me yake faruwa kuwa?" Girgiza kai Yusuf yai ya ce "A'a." "Naga Alhaji Nasir da idona a kasuwar singa yana dako." Cike da mamaki Yusuf ya ce "Anya Maniru shikagani." "Wallahi Allah shi na gani da idona, na tanbayi wani abokin lebirancinsa ya ce kulum yana zuwa kasu neman na abunci." Gyada kai Yusuf yai cike da gamsuwa ya ce "Allah ya kyauta, ni zan huce duk lokacin daka shirya sai muje company tare." "To na gode na gode na gode." Murmushi Yusuf ya sakar masa ya ce "Karka damu an zama aya." Nan sukai salama Yusuf ya hau adaidaita sahun suka huce. **** **** **** **** **** A jima a ofar gidan yana neman yaron da zai aika ya kira masa mama su gaisa, yanata wage-wage ya gano wata yariya zata shiga gidan. Da sauri ya ce "Dan Allah ammata kice ina samala da Mama Karime." A tsorace take kallonsa duk da taga ya sauya sosai amma ta ganeshi, duk da tana tunanin ita bai tunata ba. "To." Kawai ta ce ta shiga gidan. A tsakar gidan ta tadda Khadija da sauri ta ce "Khadija kinsan wa nagani a kofar gidan nan?" "A'a waye?" "Alhaji Nasir fa na gani wai na kira masa Mama." Baki Khadija ta ce "Saiki sanar da ita." Baki Abida ta saki amma ta kasa cewa komai sai lekawa da tai ta kira Mama. Hijab Mama tasa ta fita gurin Nasir ya gaida ita a ladab ce ta amsa yana sosa kai ya ce "Am dama maganar Nafisa ce naga banda kowa sai ke a duniya dan Allah kije ki bawa iyayenta hakuri." "Shikenan Nasir ba damu zanje na samesu in sha Allah." Godiya ya mata zai huce, adaidaita sahu ta tsaya a gabansu, fitowa Yusuf yai ya araso inda suke ya gaida Mama ya bawa Nasir hannu suka gaisa sannan ya ce "Magana nazo muyi me mihim manci." Duk da Nasir yana tsananin jin haushin Yusuf amma da yaji Mama ta ce to kawai saiya samu guri suka zauna. Cikin nutsuwa Yusuf ya zauna ya basu labarin yadda sukayi da masu company shinkafa ya ara da cewa "Naji labarin kafara zuwa kasuwa dan haka nazo na sanar dakai ko zaka bini mujecan kanemi aiki." Shiru Nasir yai sabuda tsananin kunyar Yusuf data kamashi, Mama ce ta ce "Ai wannan abun alkairi ne bazamuyi wasa da wannan damar ba in sha Allah yanzu ba zai bika kuje tare." Ajiyar zuciya Nasir ya sauke ya ce "Na gode amma da nafison aikin kasuwata." "Haba Nasiru yanzu da sana'ar dakon zaka cida mata biyu harda mahali? Bana son shashanci ka karbi aikinka duk matanka su dawo hannunka ba bin gidajan iyaye ba." Murya a sanyaye ya ce "Mama ina tunanin bazan iya bada mata biyu ba a halin yanzu, kiyi hakuri bazan iya hada Nafisa da kowace mace ba a duniya." Kunya ce ta lulube Mama tama kasa cewa komai, Yusuf da zuciyarsa ta tsananta bugawa kamar zata faso kirjinsa ya ce "Koda mace daya kakeson rikewa ya dace ka samu abunyi me kyau Nasir." Kai Nasir ya gyada ya ce "To na gode Yusuf in sha Allah zan zo muje company." Murmushi Yusuf yai ya ce "Ba komai." Ya kalli Mama ya ce "Mama a sha'ani na aure ba dole a ciki kibar Nasir da zabinsa zaifi." Kai mama ta gyada ta ce "Shikenan Yusuf amma anan zai bawa Khadija takardar sakinta." Gaban Nasir ne ya fadi sai yanzu yaga tsantar rashin hankalin da yai tuno irin dawai niyar da Mama da Khadija sukai dashi lokacin da bashi da lafiya,lokacin da kowa ya gujeshi, lokacin da arziki daya tara yana ganin sune komai na rayuwa bazasu iyai masa komai ba. Girgiza kai yai da sauri dan bazai iya sakin Khadija ba inyai haka ya yi buturci cikin rawar murya ya ce............! Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 28 "A'a Mama bazan iya sakin taba gaskiya." Shiru duk sukayi, ba wanda ya tanka masa har ya mike ya bar zurin. Suka bishi da kallo, Mama ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Yusuf ta ce "To Yusufa mun gode da taimako Allah ya yi albarka." "Amin Mama nima na gode." Daga haka sukai salama ya huce shima. ********** ********** Zaman gida yaiwa Nafisa zafi, batasan haka take kaunar Nasir ba sai yanzu da bata tare dashi, bata ganinsa a kusa da ita, har wata rama tai sabuda tashin hankali na rashin ganin mijin nata. Mahaifiyarta ta kula da halin da take ciki amma ta shareta dan tasa ba abune me sauki ba Baba ya sauka ya barta ta koma gidan Nasir ba amma tana taya iyar tata addu'a Allah ya za a mata abunda yafi alkairi a rayuwata. Koda ya koma gida abun duniya ne ya taru ya masa yawa, yana aunar matarsa ba ya so ya ha a ta da kowace a mace amma yana jin kuyar Mama bazai iya sakin Khadija ba, in ya yi haka yai butulci. Dafa kansa yai yana rintse idanunsa cike da tashin hankali. Yanzu ba abunda yake muradi irin yaga matarsa ta dawo gareshi, ya rasa wace hanya zaibi ya dawo da Nafisa gareshi. Bayan kwana biyu Sunje company da Yusuf kuma ya samu aiki, da yake manager company ma ya san Nasir dan haka baisha wata walaba ya samu aiki da albashi me tsoka. Yusuf zuwa yanzu ya fara cire Khadija acikin ransa tunda yaga alamun Nasir bazai iya sadaukar masa da ita ba dole tasa ya fara shigewa Abida har suka saba sabuda bazai iya zama da Hauwa a hakaba yana bukatar mace me tarbiya ba Hauwa da batasan darajarsa ba. Cikin kankanin lokaci Yusuf ya zama hamshakin me kudi kuma ya auri Abida harta tare a dakinta. Amma har lokacin Nasir yana nan gwaro Nafisa bata dawo ba haka Khadija tana gida duk da yanzu Alhadulilah yana samun kudi amma ya jingine zancan mata a wannan lokacin. Mama ce ta sameshi ta masa nasiha sosai sannan ta ce zata samu iyayen Nafisa in sha Allah. Nasir yaji dadi dan haka ya fara gyaran gidan da Yusuf ya siya masa. Mama taje sunyi magana da iyayen Nafisa, kuma sun fahimceta koma, Mama taji dadi ta musu godiya ta huce gida da farin ciki taiwa Nasir albishir, ai harda ihun murna, yaiwa Mama godiya sosai ya koma gida. A daran Nasir yaje zai taho da matarsa amma Nafisa ta ce bazata biyoshi har saiya tare da Khadija na sati 2 sannan itama zata dawo. Duk yadda ya so da ita kin amuncewa tai dole tasa ya hakura ya koma gida jiki a sanyaye. Washe gari Nasir yaje ya samu Mama da maganar tarewar Khadija Mama taji dadi amma bata nuna masaba, sai cewa tai "Allah ya kaimu yasa albarka." "Ameen." Yusuf ya ce, sannan ya mata salama ya huce. Kwana biyu da haka Khadija ta tare bayan ansha sabon biki da taro aka kai Amarya dakinta............... Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 29 Abida dake kusa da ita a zaune ta kamo hannunta cikin rarrashi da ban hakuri ta ce "Khadija kiyi hakuri komai na rayuwa da kike gani rubutacan al'amari ne, dan haka kiyi hakuri kuma kiyi tawakali a duk halin da kika tsinci kanki a ciki." Dafa hannunta Khadija tai ta ce "Abida tsoro nakeji wallahi, ina gudun ko ya Nasir ba tuba yai ba ya mana hakane dan mu yarda da shi." Girgiza kai Abida tai ta ce "A'a Khadija ki kyautata masa zato kila ba haka bane a cikin ransa, ki maida lamarinki ga uban giji sai Allah ya dafa miki." Gyada kai Khadija tai tana kwanciya a kafadar Abida ta saki kuka me sauti. Rarrashin ta Abida ta farayi tana bata hakuri. Yana rike da hannun amininsa Yusuf suka shiga gidan, duk da cikin ransa ba dadi amma fuskarsa cike take da annuri. A haka suka tadda Khadija da Abida, Yusuf ne ya kara yiwa Khadija nasiha akan hakuri da tawakali, kuma ta manta da abubuwan da suka faru a baya komai na RAYUWA me hucewa ne. Godiya Nasir ya masa Abida ta mike da niyar tafiya da sauri Khadija ta riketa, kallonta Abida tai ta ce "Lafiya?" Murya a sanyaye ta ce "Muje na rakaku." Ba musu suka huce gaba Khadija da Nasir suka musu rakiya har waje saida motarsu ta kule sannan suka dawo gida. Duk yadda Nafisa ta so jurewa zuciyar ta kasawa tai dan dazu Nasir ya kirata ya ce mata yau zai cika mata alkawari zai maida Khadija matsayin matarsa wanda ba da san ransa ba, a bayama badan soyayya ya aure ta ba, har tabar hannunsa yanzu ma sabuda ita kawai zai maida Khadija badan son ransa ba." Hawaye taji sun wanke mata fuska, kishi da bakin ciki suka taru sukai mata katutu, Anwar dake kusa da ita takara rungumewa a jikinta tanajin kaunar yaron nata da ta mahaifinsa tana shigartaaddu' Nasir yasa Khadija tai alwala sukai Nafila raka'a 2 tare da addu'o'i, sannan ya gabatar musu da kayan lashe-lashe, Khadija kasa sakewa tai, shi kuwa Nasir bai damuba yai tafiyarsa dakin baccinsa ya kwanta. Washe gari kafin Nasir ya tashi Khadija ta gyara ko ina ta hada breakfast tayi wanka ta shirya. Bai tashi ba sai 10:30am sabuda bazai je office ba ya dauki hutu. Wanka yai ya shirya, bai tsaya yin bearkfast ba ya ce mata fita zai addu'a ta masa har waje ta rakashi, yaji dadin addu'arta ya hau motarsa ya bar gidan. Kai tsaye gidan su Nafisa ya huce, tayi mamakin ganinsa amma taji dadi sosai hakan ya nuna mata ko nan gaba Nasir bazai juya mata baya ba. Bayan sun gaisa yake tanbayarta yaushe zata komai. Murmushi tai ta ce "Ka manta alkawarin da mukai da kai, sai Khadija tayi 2weeks sannan zan dawo." Fuska ya murtuke sannan ya ce "Bazan iya jiran har na 2weeks ba tare da keba akwai matsala Madam ki taimaka gobe ki koma." Dariya sosai Nafisa tai ta ce "Haba Abu Anwar kai dake da Amarya a gida amma kake rokon tsohuwa ta koma." Harara ya watsa mata ya ce "Na gaji gaskiya da Baba zan hadaki." Baki ta turo ta ce "Naji amma dole Khadija zatai sati dayanta sannan zan koma." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Naji kamar yaune." Dariya ta masa, ya ce "Yauwa madam yinwa nakeji wallahi." Murtuke fuska tai ta ce "Nifa baza ayi wannan son zuciyar da niba, ka baro matarka a gida kazo kana cewa na baka abunci tashi ka tafi na salame ka." Duk yadda Nasir ya so ta bashi abunci ki tai, shi badan komai yaki cin girkin Khadija ba sabuda yana tsoron ko ba dadi kar yaci jagwalgwalo, amma ba yadda ya iya haka ya tashi yabar gidan su Nafisa da yinwa. Haka zamansu ya kasan ce da Nasir har ta cika kwana 4 baya hade mata rai amma baya sakewa su zauna guri daya itama kuma Khadija haka take so sabuda tsoron ganinsa ma takeyi. Yausai gurin karfe 9 ya baro gurin Nafisa wanda saida sukai fadama ya taho, dalilin fadan nasu kuwa dan yace ta taimaka ta bishi ko hotel ne ta sama masa nutsuwa dan yana ganin kamar zama da Khadija a haka ba abunda zai masa amma kwanaki biyun nan ko bacci baya iyayi, duk da ba soyayya a tsakani amma sun banbanta a jinsi dole wani abu ya darsu a ransa. Iskar ya furzar da karfi yana jin haushin kansa da yaje gurinta harta raina masa wayo. Fitowa yai daga cikin motar tasa ya nufi cikin gidan, yana da mukuli a hannunsa amma yaki sawa ya bude ya fara kwankwasawa sabuda Khadija ta fito ya ganta ko zai samu wata nutsuwar. Tana cikin bacci taji ana buga gidan tashi tai a tsorace ta fito cikin muryar bacci ta ce "Waye?" Saida ya dan jima kadan ya ce "Nasir ne." Tanajin muryarsa ta bude masa kofar, saida ya shigo sannan ta maida ta rufe. Juyowa yai yana kallonta ya ce "Yanzu koda bakone a haka zaki fito ki bude masa kofa." Kallon kanta tai ta tabe baki ta ce "To ya Nasir wazai zo da daran nan." Baki ya tabe yana girgiza kai ya ce "Umm gaskiya." Yai gaba tana binsa a baya............... Comments And Share By *Zahra* *WATA RAYUWA* Na Fatima S Umar Jajira Free book Episode 30 Tsayawa yai ta huce nata d'akin sannan ya huce nashi Wanka yai ya sanya jarabiyarsa ya kwanta, amma duk yadda ya so bacci ya sureshi hakan ya gagara juyi kawai yake yarasa abunda ke basa dadi a gidan duniya. Tashi yai saya nufi akin Khadija, sai kuma ya dawo ya yi haka yafi sau 10 tsaki kawai yake ja yanajin takaicin abunda Nafisa ta masa, kuma ya tabbatar yanzu akan Khadija da bataji bata ganiba zai huce. Key ya dauka ya nufi dakin, lokacin dayasa key ya bude dakin Khadija bacci take hankali kwance, batasan da shigowarsa bama. Haurawa yai kan gadon ya fara tashinta. A tsorace ta tashi tana zare ido, tana kallonsa. Fuska ya hade duk da a zuciyarsa wani sanyi ne yake ratsashi iya ganinta da yai yaji zuciyarsa tamasa sanyi sosai. Murtike fuska ya karayi ya ce "Meyasa kinsan hakkin miji akan matarsa amma baki taba sauke koda guda daya ba? Ko bakije Islamiyya ba?" Idon Khadija ne ya kawo ruwa, tai saurin cewa "A'a amma ni bansan abunda banai maka a zaman da mukayi b......!" aga mata hannu yai da yake da fitila dakin yana kallonta tana kallonsa, sai tai saurin rufe bakinta, tana sunkuyar da kai. "Kada ki maidani karamin yaro da bansan abunda nakeba, kinga bazan zauna ina bata lokaci na a gurinki ba minti 3 na baki kizo ina nemanki, idan kuma kika sake na dawo da kaina, hmmm sunanki sorry yarinya." Mi ewa yai ya fice, Khadija ta rakashi da ido kawai tanajin wata fa uwar gaba na ziyartar ta. Ta bata lokaci a zaune kafin ta tashi jiki a sanyaye tabi bayansa. A dakin ma saida yaja mata aji sosai sannan ya dawo kuma ya kulata, cikin da bara ya lalaba Khadija har ya samu ya biya bukatarsa. Kiran sallar asuba ya tayar dashi daga bacci me dadi daya kwasheshi, tashi ya yi yashiga baya yai wanka sannan ya sauya kaya ya huce masalaci. Sada ya dawo lokacin yabi takan Khadija. Wadda duk baccin da yai ita bata samu ta rintsa ba sabuda halin da take ciki gashi ko yatsanta ta kasa dagawa bare ta tashi ta nemi gurin tsira. A hankali ya haura gadon ya dago ta jikinsa, saida ta sauke ajiyar zuciya, idonta a rufe tana zubda kwala. Murmushi Nasir yai yana kallon fuskarta dayaga tana annuri ya ce "Saura kiris nai wani kuskure a rayuwata wadda da hakan ta kasance da bazan yafewa kaina ba." Ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da cewa "Khadija na so lalata rayuwarki ta hanyar da bata dace ba wadda bai kamata aiwa duk wata ya da ka rike mutuncinta na amace kamar kiba, nayi dana sanin abunda ya faru a baya, amma na miki alkawari bazan taba bari wani abu ya taba mutuncin ki ko kimarki ba, na gode my wife Allah ya miki albarka duniya da lahira. Ranar Khadija taga kulawa da tarairaya, dan ko kofar gida Nasir bai laikaba. Saida ya kwana biyu ko gurin Nafisa baya zuwa saidai yakira a waya su gaisa. Haka RAYUWA ta cigaba da juyawa har lokaci dawowar Nafisa yai ta dawo cikin gidan tare da Khadija. Zaman Khadija da Nafisa zamane irin na mutunta juna, basa nuna kishi irin na jahilci kishinsu gurin kyautatawa mijine a turaka, amma baka taba jin kansu, dan sunyi koyi da matan Annabi Muhammad s.a.w, kuma suna ganin rabar hakan dan kulum arzikin mijinsu karuwa da albarka yake da ayi. Zumunci kuwa tsakanin Nasir da Yusuf saidai son barka indai ba sanin su kayi a baya ba bazaka ta a cewa ba uwa aya uba aya suke ba, komai nasu tare suke gwanin sha'awa. Tana kwance a dakinta yashigo da salama amsawa tai tana fa a a fara'arta ta ce "Barka da dawowa mijina." Murmushi ya yi ya ce "Yau matar aljana ya gidan?" "Kowa lafiya aunty ta tafi dakko Anwar a school kaga ni banda lafiya." "Gaskiya ne, ya Babyn nawa." Murmushi tai ta ce "Ya fara motsi fa." Zama yai a kusa da ita ya ce "So yake yaji dumin Babansa bari muyi hira." Nan ya kara kune ajikin cikin nata yana magana shi kadai wai da Baby yake hira itadai Khadija dariya kawai takeyi ganin irin sakarcin da Nasir yakeyi. Yajima a haka kafin ya dago yana kallonta ya ce "Kinsan me nake fata kuwa?" Kai ta girgiza ya ce "So nake ki haifi Baby girl me kama dake sosai na riga kallonta ina farin ciki kamar yadda duk sanda na saki a idona nakejin farin ciki." Murmushi Khadija tai tana shafa fuskarsa ta ce "Allah ya cikama burinka mijina, amma nima zanso haifar me kama da kai." "Zaki haifa abunda yanzu kika fara, kuma duk shekara saikinyi." Ido ta zaro ya gyada mata kai ya ce "Sosai kuwa yarinya." Baki ta turo, yana ganin haka ya fara mata wasa harda kamota nan kamota nan, saida yasata dariya sosai sannan ya rabu da ita. A hankali kwanaki suka ringa shudewa har cikin Khadija ya isa haihu, ya zama aikin gidan duk yana gurin Nafisa duk da itama tanada nata juna biyun amma yaro ne bai girmaba. Ahaka har Allah ya sauki Khadija lafiya, abunda Nasir yake buri shi Allah ya basa baby girl me kama da Khadija ranar suna akasawa Baby suna Nafisa suna ce mata Awara, Nafisa harda kukan dadi an mata takwara, shiyasa ta zama yar dakinta bacci ne kawai ko in tanajin yinwa take kaita gurin Khadija amma tana gunta. Bayan shewara uku Yanzu Nasir yanada yara biyar Khadija nada biyu Nafisa nada uku ciki harda me sunan Mama Karima. Yusuf ma ya hada iyali dan Abida ma yaranta 2 banda yaran Hauwa. Yau suke tsara duk ranar Lahadin karshen wata, za'a hadu a gida daya aci asha ai zumunci. Yauma hakace ta kasance duk suna zaune a gidan Yusuf bayan anci ansha. Hauwa ce da surutu ta ce "Nikuwa Khadija kallon me ciki nake miki wallahi." Khadija kuwa kamar jira rake ta kalli Nasir aikuwa ya kama dariya harda yi mata gwalo. Kwalla ce ta cika mata ido ta ce "Wallahi banason sake haihu." Da sauri Nasir ya ce "Haba yarinya me na ce miki haihuwa yanzu kika fara, saikinyi 12 dozun guda zan barki ki huta ma." Kafin tai magana Abida ta ce "Dan baku kuke haihuwar ba bakusan wahalar da muke shaba shiyasa kuke mana izaya da wai sai mun dinga haihuwa kamar kaji, haka na kusa da kaima ya kecin alwashi." A hankali Yusuf ya ce "A to mene anfanin ku in baku haihu ba." Zatai magana Nafisa ta ce "Kinga rabu dasu zamu dau mataki badai haihuwa bace, to kowane a cikin mu ya hana mijin shiga dakinsa sai muga ta inda za'a cigaba da haihuwar." Ai a tare Nasir da Yusuf suka hada baki gurin furta. "Wallahi baku isaba." Sai kuma gaba daya sukasa dariya harda matan nasu. ALHADULILAH Ina bawa ma'abota bibiyar wannan litafi hakuri na so labarin yai tsayi amma sabuda wani abu daya taso mun yasa dole na takai tashi, kumun afuwa dan Allah. Masoya mu kasance tare daku duk ranar Lahadi da Alhamis da misalin karfe 9:30pm dan sauraran shirin GARIN MASOYI wanda ni Fatima S Umar Jajira zan riga gabatar muku a tashar Raypower 105.6 na gode Sharhi ko arin haske 08166077167 Share please