INTEESAR Story & written by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Wannan kirkirerren labari ne,banyi tunanin rubutashi Dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni da niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* page0️⃣1️⃣ Zaune take akan kujerar tsugunno Tana k'ara itace a cikin murhun wutar da ta hura,wata matashiyar budurwa ce ta fito daga cikin daki,ta karaso gaban mahaifiyar nata dai-dai lokacin da ruwan dake saman wutar ya fara tafasa, ta durk'usa ta ce, "Umma sannu da aiki" Murmushi umman tayi ta bude marfin robar dake gaban ta tayi garin Dan waken da ta kwaba,sannan ta ce, "Yauwa sannu Inteesar" "Umma barshi na tayaki jefawa" "A'a ki barshi kawai nasan yanxun zaki je gidan Hajiya Fatima ne ko?" "Eh umma kindan duk safiya idan bata ganni ba zata fara nema na wai lapiya har yanxun ban shigo ba?" Murmushi umman tayi tare da cewa "Ai na sani don tasha yo aike idan taga k'arfe goma tayi baki shiga ba,kice ina gaishe ta." " To" Ta ce tare da mikewa "Bari to na tafi tunda nagama ayyuka na kuma kin hanani jefa dan waken." Ta Mike cikin nutsuwa irin tata ta nufi hanyar fita gidan.mahaifin ta ta samu a zauren gidan yana karatun Al-qur'ani, Durkusawa tayi ta gaishe sa ya amsa cikin sakin fuska. "Abba zanje gidan Hajiya ta" Kai ya gyada mata tare da cewa "Ki gaishe ta Allah ya tsare a dawo lapiya" Mikewa tayi ta ce, "To Abba,insha Allah" Kofar gida ta fita tare da karanta Addu'ar fita gida. Kasancewar basu da nisa gidan a gaban layin su yakekan hanya.cikin nutsuwa ta karasa gidan cikin nutsuwa ta tsaya dai-dai gaban tangamemen gidan,buga gate din gidan tayi,mallam Ibrahim Mai gadin gidan ya karaso ya bude mata karamar kofar tashigo, Durkusawa tayi cikin girmamawa ta gishe shi. "Ina kwana Baba" Murmushi dattijon yayi tare da cewa "Dama nasan kece kika shigo yanzun,Kin tashi lapiya Inteesar?" "Lapiya qalau Baba" Kai tsaye ta karasa cikin gidan.A hankali ta tura kofar falon tare da yin sallama,dama bata tsammaci ganin kowa a falon ba.kai tsaye ta nufi falon Hajiya Fatima bakin ta dauke da sallama.jin motsi a kitchen ne yasa ta nufi kichen din,Hajiya Fatima dake wanke kayan ciki ne ta kalli Inteesar tare da sakar mata murmushi "Yanxun nake zancen ki a zuciya ta 'yar halak ashe kina hanya"? Murmushi tayi tare da durkawa har kasa ta gaida Hajiya Fatima "Ina kwana mummy"? "Lapiya qalau Inteesar yasu ummanki da mallam?" "Lapiya qalau sunce na gaishe ki." "To Ina amsawa" Mikewa Inteesar tayi tare da kallon mufida dake fere dankalin turawa "Mufida kin tashi lapiya"? "Lapiya qalau Inteesar, Yauwa zoki tayani fere dankalin nan wallahi nagaji." Kallon ta mummy tayi tare watsa mata harara " wani aiki kikayi da zakice kin gaji?" "Mummy har yankewa nayi fa da wukan nan baki sani ba?" Gajeren murmushi mummy tayi "Kece zaki yanke ba tare da kinyiwa mutane ihu da raki ba?" Yamutse fuska tayi tare da cewa, "Wash Inteesar Dan Allah zoki karasa Bari naje nasa spirit da plaster na dawo." Batare da ta jira cewar mummy ba ta ajiye wukan ta ta fita da sauri Girgiza Kai mummy tayi ta ce, " Dama ba son aiki kike ba Don ma ina tursasaki Amma duk da haka ba biyan bukata kidauki dogon lokaci baki gama kwakkwaran aiki d'aya ba." Inteesar ce ta k'arasa gaban dankalin ta dauki wuka ta fara ferewa cikin kankanin lokaci ta gama,ta wanke tasa gishiri kadan ta soya tagama ta soya kwai ta dafa ruwan shayi da yaji kayan kamshi,ta kalli mummy tare da akin murmushi ta ce, "Mummy ki barshi kawai Bari zan karasa" "To Allah yayi maki Albarka bari naje nayi wanka" Ta fita Inteesar taci gaba da aikin ita kadai,cikin kankanin lokaci ta gama ta zuzzuba a flask ta jera a dinning table sannan ta dawo ta tsaftace kitchen d'in, da kayan da suka 'bata,dai_dai lokacin Mufida ta shigo kitchen din tana murmushi. "Inteesar sannu da aiki" Murmushi tayi ba tare da tace komai ba, Mufida tacigaba da magana "Ke bari na fada maki gaskiya bawani yankewar da nayi kinsan bana son aiki aike gara kisaba da aiki don mace ce ke wata rana aure zakiyi kuma haihuwa zakiyi ki zama uwa." Dariya tayi tare da cewa "Ai insha Allah mijin da zan aura bazai zama mai ra'ayi irin na Dady na ba,don Dady baya son a dauko mai aikin da zata dinga dafa abinci sai dai mummy ce damu zamu dinga yi,baki ga gidan nan ga ma'aikata nan ba? suna aiki amma banda shiga kitchen?shi kuma nashi tsarin kenan baya cin abincin mai aiki,ni kuma mijin da zan aura sai na tabbatar ba irin tsarin Dady ne dashi ba ehe."Dariya Inteesar tayi ta ce, "Allah ya shirye ki" Tare suka fito kitchen din dai_dai lokacin da Dady da Mummy suka karasa dinning table din suka zauna,Inteesar ta durkusa ta gaida Dady cikin girmamawa "Dady Ina kwana"? Cikin sakin fuska ya amsa mata "Lapiya Lau Inteesar ya k'ok'ari damu?" Murmushi tayi tare da durkusawa da Kai kasa,mummy ma murmushi tayi tana jin son yarinyar har cikin ranta take kaunar ta, mi'kewa tayi tare da k'arasawa ta zauna akan kujerun da suke falon, Dai-dai lokacin da wayar Dady ya fara ruri,kallon secreen din wayar yayi tare da murmushi ya ce, Ga Muhammad muhdeen na Kira na a waya." Take sai gabn Inteesar ya Fadi jin ya ambaci sunan muhdeen,a zuciyar ta tace Allah yasa mugun ba dawowa zaiyi ba,da na shiga uku.Dady ya d'aga wayar. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & written by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kirkirerren labari ne,banyi tunanin rubutashi da cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Page0️⃣2️⃣ Daddy ya daga wayar tare da cewa " son kana lapiya?yau satin ka daya a can,ko wani irin biki ne yakamata a ce angama,ga Asibiti nan yana jiran ka." Daga d'aya bangaren muhdeen dake kwance saman lapiyayyen godo na alfarma,gyra kwanciyar sa yayi tare da cewa "Eh mungama bikin Dady Amma Ina son kafin na dawo Nigeria zan biya kasar London Naga sumayya." Dady ya katse shi ta hanyar cewa ba wannan lokacin,karka manta ankammala asibitin nan an zuba kayan aiki da ma'aikata tun last week yakamata ka fara zuwa ka ce zakaje bikin abokin ka a kasar Egypt zakayi kwana uku can ka dawo yanzun satinka daya sannan kace mun zaka je wata kasa?bazai yuwu ba." Muhdeen yamutse fuska yayi Don yasan Halin mahaifin sa idan ya fadi magana ya fadi kenan. "To shikenan Dady zan dawo gobe insh Allah." Murmushi Dady yayi tare da cewa "To 'Dan Albarka Allah ya tsare" Ya mik'awa mummy wayar tare da cewa "Ga mummyn ka" Amsar wayar tayi tare da sallama "Son ina fatan kana lapiya"? Daga can bangaren ya ce, "Ina lapiya Mum fatan kema lapiya?" Murmushi tayi tare da cewa "Alhamdulillah kun gama bikin abokin naka me ka tsaya yi a Egypt har yanzun baka dawo ba?" "Mummy na hadu da abokai nane da mukayi karatu tare duk sunzo,kuma kowa daga k'asar da yake shiyasa muka Dan zauna dasu don yanzun idan kowa ya watse mukan dad'e bamu haduba,amma insha Allah zan dawo gobe tunda Dady ya matsa da naso na biya kasar London naga Sumy na ta matsamun wai sai mazo." Shiru mummy tayi kafin tace, "Idan ka samu sarari kaje wani lokacin amma ka dawo yanzun.don idan ka tafi London din nan baka San dawowa sai an matsamaka." "To shikenan tunda haka kuka ce" Mufida ce ta kar'bi wayar ta ce "hellow big bro shine ko ka nemeni a waya ko? Amma Asiya Tana gida da yanzun kace a bata." Dariya yayi tare da cewa "Autar mummy sarkin k'orafi to ai yanzun nake Shirin tambayar ki sai kikayi gajen Hakuri" Tura baki tayi cikin shagwa'ba tace Bawani Nan ai nasan kafi damuwa da Asiya akaina." "Dariya yayi tare da cewa "Karki manta kece fa auta gaba d'aya shalele,hidima ne sukayi mani yawa Amma kiyi Hakuri kinji?" Kai ta gyad'a masa tare da yimasa sallama. Mikawa Dady wayar tayi inda ya K'ara jaddada masa ya dawo bayan sunyi sallama ne mummy ta juya ta kalli Inteesar ta ce " 'yata taso muyi breakfast mana" Kai ta girgiza tana murmushi ta ce "Mummy gida zan koma Umma Dan wake tayi shi zanci* Dariya Mummy tayi tare da jinjina Kai "Kedai Inteesar akwai son d'an wake to shikenan idan kingama ki dawo." Mikewa tayi tare da cewa "To Mummy." Kofar fita ta nufa da sauri Mufida ta ajiye kofin tea din da take Sha ta ce "Lah jirani Inteesar bari na d'auko gyale na mu tafi nima d'an waken zanci" Dariya Inteesar tayi Wanda har sai da wushiryar ta ta fito. "To Ina jiranki kije ki dauko" Bayan ta dauko ne suka tafi,Suna tafiya Mufida ta ce, "kinji gobe Yaya Muhdeen zai dawo ko?" " Wallahi nayi missing d'insa sosai" Ta fadi Tana murmushi Itako Inteesar tunda taji zai dawo kamar taji sak'on mutuwa don har ga Allah bata son dawowar shi saboda ya tsane ta,ba abunda ke hada ta dashi daga yadinga binta da mugun kallo sai kuma ya dinga galla mata harara indai Yana gidan nan bata da sake,ko gaishe shi tayi baya amsa mata sai dai idan akwai idan want wajen mummy ko Dady ko kuma Mufida.idan a gaban Asiya ne Kam baya amsa mata ko kallo bata isheshi ba.dayake Aasiyar ma basu jituwa da Inteesar. Suka shiga gidan bakin su dauke da sallama.Umma dake cikin daki ne ta amsa masu,shiga sukayi suka gaishe ta.ta amsa masu cikin fara'a. "Mufida yau kece a gidan namu?" "Eh Umma naji Inteesar tace 'Dan wake kikayi shine nazo naci." Cewar Mufida Umma ta ce "kema dai kina son 'Dan wake kamar Inteesar." "To yana can nakai mata d'akin ta Don nasan sai ta dawo taci." Mikewa sukayi suka fita suka nufi dakinIinteesar,suna shiga Mufida ta zauna kan katifar Inteesar dama d'akin Sai da tagyara shi fes tasa turaren wuta kafin ta tafi gidan Mummy Plate Inteesar ta dauko ta zuba masu 'Dan waken tasa yaji da man kuli sannan ya yanka kabeji da cucumber da tumatur suka hau ci mufida nata santi,bayan sun kammala sun k'oshi mufita ta kishingid'a ta fara chatting'ita ko Inteesar fita tayi take ta fara Shirin 'Dora masu abincin rana.miyar taushe tayi sannan ta daura tukunyar tuwo,koda ta ahiga d'aki ta tarar mufida ta na barci murmushi tayi sannan ta fita,cikin kankanin lokaci tayi tuwon shinkafa zuwa karfe goma Sha biyu ta kammala komai ta tada mufida tace "ki tashi har na gama girki gashinan idan zakici" Mufida cikin yamutse fuska alamun barci bai ishe ta ba ta ce, " me kika dafa?" Kallonta Inteesar tayi tace tuw....." Tun kan ta karasa ta ce Wallahi bazanci tuwo da rananan ba." Kasancewar Inteesar ma batajin yunwa kuma dama it ba Mai yawan cin abinci bane.ta ce. "To tashi mu tafi" Tare suka fito inda suka shiga sukayiwa Umma sallama suka tafi zuwa gidan su Mufida koda suka k'arasa Kai tsaye Inteesar ta nufi kitchen Don 'Dora abincin Rana. Washe gari ranar da Muhdeen zai dawo kenan bayan sun gama breakfast mummy tasa Inteesar da mufida Sud'an Kara gyara masa d'aki.dama Shima ya hana ma'aikatan gidan suna shigar masa d'aki. Koda suka shiga mufida zama tayi kan side drawer'intesar ta zage ta gayra d'akin ta goge ta wanke masa toilet sannan suka fita,dama d'akin Mummy da na su Mufida Maimuna mai aiki ke gyara masu da fallo Kai tsaye Inteesar ta nufi kitchen Dan taga mummy ta shiga abinci lafiyayyu kala-kala aka shiryar don tarban Muhdeen bayan sun gama sunyi wanka karfe daya na Rana suka nufi airport dan tarban sa, Direban su biyu suka dauki motoci guda biyu inteesar bata so zuwa ba amma da mummy ta matsa mata dole taje, Mummy ta shiga bayan d'ayan motar Inteesar da mufida daya . Suna Isa jirgin su na sauka,ya fito daga jirgin rik'e da akwatin sa da fara'a suka karasa Mufida ta rungume sa tana masa barka da sauka,bayan ta sake shi ya rungume Mummy tare da cewa "Imiss you mum" Murmushi tayi tare da cewa " miss u to." Inteesar ce ta kalleshi ta ce, "Sannu da dawowa ya muhdeen" "Wani kallo ya mata ganin idon Mummy ne ya sa ya amsa "Yauwa" Kai tsaye suka nufi motocin su inda Mufida ta dage sai motar su zai shiga haka akayi kuwa ya zauna gaban motar, da Yana hada ido da Inteesar ta jikin madubin motar ya watsa mata harara,da sauri ta sunkuyar da Kai k'asa. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u ollFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & written by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin Rubuta shi Dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Page0️⃣3️⃣ Yana hada ido da Inteesar ta jikin madubin motar ya watsa mata harara, Da sauri ta sunkuyar da kanta kasa,Direba yaja motar suka bar airport d'in suka nufi hanyar gida,yayin da motar da Mummy ta shiga ya rufa masu baya. Horn sukayi Mai gadi ya wangale masu gate din gidan.bayan sunyi parking direban ya zagayowa da sauri ya budewa muhdeen mufin motar ya fito,yayin da Direban ya dauko kayan da muhdeen din ya dawo dasu daga cikin boot d'in motar,yayin da Mufida da Inteesar suka fito daga cikin motar,mummy ce ta riko hannun Muhdeen cike da son gudan jinin nata,langwa'bar da Kai yayi alamun gajiya. Murmushi mummy tayi tare da cewa , "Ka gaji ko" Kai ya gyad'a mata alamar Eh,hannun shi taja suka nufi kofar shiga part din,yayin da su Mufida suka rufa masu baya,ita dai Inteesar jikin ta duk yayi sanyi kamar an Jefi kaza da gishiri. Kai tsaye Mummy ta raka shi har part d'insa,har bedroom suka shiga yayin da direban ya ajiye kayan a falon sa. Mummy ta ce, " kayi wanka ka fito Muna jiranka muci abinci." kai ya gyad'a yayin da mummy ta fita taja masa k'ofar ta nufi folo inda ta samu Inteesar da Mufida, itama falon ta zauna fuskar ta dauke da murmushin farin ciki. Cikin kankanin lokaci Muhdeen ya k'araso falon sanye yake cikin kananun Kaya farin Riga da bakin wando 3 quarter, Mufida ce taja hannunsa tana murmushi suka nufi dinning area din Mummy ma ta Mike tabi bayan su tare da cewa Inteesar ta taso suci abinci. "Mummy bana Jin yunwa anjima zanci" Mummy ta dakata tare da juyowa tana kallon ta da mamaki,Don tasan cewa tun suna girki take cewa Tana Jin yunwa amma yanxun kuma tace bazataci ba sai anjima. "Ina ce yunwa kike ji sannan yanzun kice bazakici abinci ba,taso ko kadan ne kici . Har ga Allah tana son cin abincin amma kuma tsoron Muhdeen d'in da takeyi ne yasa bazata iya zama dasu taci Abincin ba.mufida ce tace, "Inteesar Dan Allah ki taso Mana tana Shirin mikewa ne taji muryar muhdeen Yana cewa "Ki kyaleta mana tunda tace bazataci ba ko zaki matsa mata dole ne?ba tafiku sanin cikin ta ba?" Mummy bata Kara cewa komai ba taja hannun Inteesar din suka nufi dinning area din kujera taja mata kuje ran dake facing d'in Muhdeen ta zaunar da ita kauda kansa yayi bayan ya jefa wata Mata mugun kallo, Mummy ta shiga bude kulolin abincin ta fara zuba masa nasa.fried rice ne da yaji hanta da Koda,sai kuma farfesun kajin da Inteesar tayi masu,ta zuba masa juice din kwakwa da Madara Wanda Inteesar din ce ta hada.ta kalli Inteesar tace, "'yata me zaki ci?" Cikin sanyi ta ce " ruwa kawai zansha" Ba tare da mummy tace komai ba ta zuba mata jallop din cuscus ta ajiye mata a gaban ta tare da ajiye mata kofin juice a gaban ta,ta juya ta kalli Mufida ta ce, "Ke kuma ki tashi ki zuba abunda kike so, Kulan cuscus d'in a gaban ta.ta zuba a plate ta balle murfin robar ruwa ta zaba a cup Mummy ma nata ta zuba ta fara ci bayan ta zubawa Inteesar farfesun kajin. Inteesar gaba d'aya ta kasa sakewa taci abinci yadda kowa ya sake yana ci,gabanta sai fad'awa yakeyi musamman irin kallon da Muhdeen ke jifanta dashi. Shima kansa a cikin zuciyar sa ya rasa gane dalilin da yasa ya tsani yarinyar,shidai wulak'anta mutane ko kuma kyarar mutane ba dabi'ar sa bace, amma baisan dalilin da yasa ya tsani yarinyar ba.Gashi dai Kullun zata baro gidan iyayen ta taxo gidan su tana taya mahifiyar shi aikace-aikacen gida, gashi tana son dangin shi jininta ya had'u da autar su Mufida amma duk lokacin da yarinyar ta shigo gidan sai yaji gaban sa ya fad'i,ga kuma yawan mafarkin da yakeyi da ita kusan kullun,ko sumayya masoyiyar shi da suka kwashe shekaru biyu suna soyayya baya mafarki da ita sai wannan mayyar,sunan da yasa mata kenan mayya. Yana cin Abincin sa yana tunani kuma gashi yaji dadin abincin sosai don gaskiya Inteesar ba baya bace wajen iya girki.ta kware sosai shiyasa Mummy kullun sai ta jira ta tazo kafin ta d'aura girki,don suna Jin dadin abincin ta sosai. Mummy ce ta zuba mata ido tana nazartar yanayin ta "Inteesar lapiya kuwa me yake damun ki?" Daga kai tayi ta ce "Lafiya qalau mummy" "To meyasa bakici abincin kirki ba kinsaka abinci a gaban ki sai jujjuya cokali kikeyi dakyar taci cokali uku tasha ruwa ta koma falo kan kujera ta zaina, Mummy dai shiru tayi tare da binta da ido suka cigaba da cin Abincin su Muhdeen sai da ya koshi ya Kora da juice din kwakwa sanna ya Mike tare da cewa "Mummy bari na huta" "To son a huta gajiya sai ka fito." Mufida ce ta ce "Yaya tsaraba ta fa?" Murmushi yayi tare da cewa "anjima idan na huta sai na fito maku da tsarabar ku" Kai tsaye ya nufi hanyar part din sa da sauri Inteesar ta sunkuyar da Kai k'asa Don bata San sake kallon sa,sai da ya wuce sannan ta daga Kai. Bayan mummy sun kammala cin Abincin ne Mufida ta kwashe abubuwan da suka Bata ta nufi kichen, Inteesar ta goge wajen ta nufi kitchen dan wanke kwanika da sukayi amfani dashi, Mufida dama dakinta ta wuce, Mummy ce ke zaune a falo tana kallon news, bayan Inteesar ta gama ta fito dai-dai lokacin wayar dake kan dinning ya fara ruri, Mummy ta juya ta kalli wayar tare da cewa "Inteesar Dan Allah d'auki wayar nan na Son kikai masa Ina ganin ya mance da ita ne" Rass gaban ta ya fad'i Jin abunda Mummy tace,ba yadda ta iya haka dole ta karasa ta dauki wayar da haryanzun take ruri sunan da ta gani a wayar shine my happiness, Azuciyar ta ta ce budurwar sa ce ke kiransa cikin fad'uwar gaba ta nufi part d'insa tayi knocking sau uku taji shiru sai tayi tunanin ko barci yakeyi,don haka da sallama ta murda handle din k'ofar ta shiga,ba kowa sai kamshin turare dake tashi ta nufi bedside drawer ta Duk'a ta ajiye wayar dai-dai ya fito daga toilet kenan yana daure da towel a k'ugunshi sai karamin towel dayake tsane ruwan kansa juyowar da zatayi taji taci karo da mutum wani razanannen ihu ta saki cikin tsoro... Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya,to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Page0️⃣4️⃣ Wani razanannen ihu ta saki tsoro ne ya sa ta fad'a jikin sa ba tare da ta sani ba,cikin hanzari ta kalleshi shi,idon ta ne yayi tozali da kwantaccen gashin kirjin sa da suka kwanta luf a faffad'en kirjin sa da sauri ta runtse ido tare da ja baya cikin tsoron sa, mugun kallo ya watsa mata tare da daka mata tsawa cikin d'aga murya yace, "Uban waye ya baki izinin shigowa nan har cikin bedroom d'ina?" Cikin tsananin tsoron sa da takeyi kanta a kasa, ta fara magana cikin in'ina ta ce, "A'a Dddmma in in mu mm mm mummy ce ta ta tace na kawo maka wayar ka." Ta karasa maganar tana nuna masa wayar da hannun ta juyawa yayi ya kalli wayar da ta nuna masa, Tsawa ta daka Mata tare da numa Mata hanyar kofar fita. Cikin daga murya yace, "Get out" Cikin sauri-sauri gudu-gudu tabar dakin,ya bita da harara tare da karasawa ya rufe kofar da key yace, "Mayya" Ya koma cikin d'akin ya karasa gaban dressing mirror ya d'auka lotsion d'in shi ya fara shafawa. Bangaren Inteesar kuwa yadda ta Fado falon Mummy ne yasa ta daga Kai ta kalle ta sauri. "Ke lafiyarki kuwa ya haka kamar an koraki" Girgiza Kai Inteesar tayi ba tare da tace komai ba,sake jin muryar Mummy tayi tana cewa, "Ko Muhdeen d'in ne ya maki wani abun?" Kai ta girgiza tare dacewa, "Babu komai mummy ba korata yayi ba." Shine kika shigo kamar wacce aka koro?" Kanta ta sunkuyar cikin sanyin murya ta ce, "Mummy zan tafi gida" Mummy ce ta kalle ta tace, lapiya yau zaki tafi yau da wuri haka?" Kai ta gyad'a tace "Eh Mummy bari na tafi dan nasan Umma na jira na." Murmushi mummy tayi tare da cewa, "Shikenan ki gaida Mani da umman taki" Kai tsaye ta nufi hanyar fita Mummy tabita da kallo tana murmushi cike da son yarinyar. Da sallama ta shiga cikin gidan, Umma da fitowarta kenan daga band'aki rike da bokiti alamun wanka tayi. "Wa'alaiki Salam Inteesar har kin dawo?" Murmushi ta k'ak'alo akan fuskar ta ta ce, "Eh umma nagaji ne shine nace bari na dawo nayi sallah na d'an kwanta "To shikenan " Cewar ummin yayinda ta d'auki buta ta zauna a kujerar tsakar gida ta Soma alwala . Inteesar ma dakin ta ta shiga ta ajiye hijabin ta,ta fito ta dauki buta ta shiga ban daki ta fito yazauna inda umma ta tashi,ta soma yin alwala cikin nutsuwa. 'Bangaren Muhdeen ma fitowa yayi daga part d'in a inda yasamu Mummy zaune ya kalleta yana murmushi. "Mummy bari naje masallaci ana shirin tada sallah" Mikewa tayi ta ce, "Nima bari na tashi adawo lapiya." Bayan ya dawo daga masallacin ba kowa a Babban falon Kai tsaye part d'insa ya koma don yana son yayi waya da Sumynsa.kwanciya yayi akan gadon tare da daukar wayar say yayi dialing din number ta inda yayi sevin number ta da my happiness. *LONDON* kwance take akan lapiyayyen Royal chair,tana sanye cikin wando 3 quarter yallow da farin singilet kanta tayi Karin gashin attached ya zubo har gadon bayan ta,ga faratan ta zaro-zaro anyi masu fixing tare da ahafa masu shinning sai d'aukar ido suke.wayar ta dake hannun ta ta kalla ganin Kira ya shigo cikin tsananin Jin dad'i tayi picking din wayar tare da kaiwa kunne.cikin shagwaba tace, "Haba my happiness meyasa tun since Ina Kiran ka baka dagawa why"? Ta kara narkar da murya tare da cewa, "Kuma Kai baka damu da ka kirani ba,sannan idan ni na kiraka baka picking sai kaga dama" Murmushi yayi tare da cewa "Sorry my Sumy ki garface ni bana kusa da wayar ne shiyasa.yanxun ma dawowa na masallaci kenan naga kiranki da kuma sak'on da kika turo." Dariya tayi cikin Jin dadi tace, Kaima fa kasan bazan iya jure hours ba tare da naji muryar ka ba." Cikin Jin dadin yadda Sumayya ke nuna masa so yace, "Nima haka ne a wuri na zaro ido tayi tare da cewa "Ba wani Nan nida zan kiraka sau uku kafin ka kirani sau d'aya.wani lokacin baka dagawa ko kuma idan ka d'aga kace I'M busy right now but I will call you letter.kuma bazaka Kara Kira ba sai dai idan nice na Kira, Kai ya girgiza don yasan gaskiya ta fad'a kuma shi idan Yana aiki a Asibiti baya son yawan d'aga waya musamman idan yaga Sumayya ke Kiran sa don yasan dogon fira zasuyi har dai idan Yana tare da patient. "Kinga nasani amma yanayin aikin da nakeyi ne." Dai-dai nan Mummy ta turo k'ofar d'akin tare da sallama.daga Kai yayi ya kalle ta tare da cewa Sumayya Kinga zamuyi magana anjima." Ta'ba fuska tayi tace " meye kuma yanzun?" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Mummy ce ta shigo" Yamutse fuska tayi ta ce, "Ohk to Ina gaishe ta." ta katse wayar.kallon Mummy ya yi Yana murmushi yace "Sumayya ce tace na gaishe ki" Gajeren murmushi mummy tayi Wanda iya fatar baki ta tsaya bata Kai zuci ba,don har ga Allah sumayya bata kwanta mata ba tunda taga pictures d'in ta a wayar Muhdeen taji bata kwanta mata ba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Ina amsawa,kaxo ga Dadyn ku nan ya daw daga mitin d'in da yaje." Ta juya ta fita mik'ewa ya yi yabi bayan Mummy. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DOMIN K'ARIN BAYANI* 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Wannan kagaggen labari ne,ban Rubuta shi Dan cin zarafi kowaba.idan hali ko suna yazo,to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Page0️⃣5️⃣ Mik'ewa yayi ya bi bayan Mummy kai tsaye upstair din suka nufa part d'in Dady,da sallama suka shiga,Daddy dake zauna kan kujera ya daura laptop akan table yana aiki akai,sanye yake cikin farin jallabiya fuskar sa sanye da farin gilashi,d'ago kai yayi tozali da Babban d'ansa mafi soyuwa a gare shi, murmushi yayi tare da amsa sallamar su. "Mutanen Egypt barka da dawowa." Muhdeen d'in ma murmushi ya yi tare da k'arasawa ya ya durk'usa ya gaida mahaifin nasa cikin girmamawa. "Ina wuni Dady?" Cikin sakin fuska ya amsa masa. "Lapiya qalau Muhammad ya gajiyan tafiyar?" Da Alhamdulillah ya amsa tare da zaunawa kan center carpet d'in dake shinfid'e a tsakiyar falon. Dady ya rufe laptop d'in dake gaban sa ya juya ya kalli Mummy dake zaune a gefen sa ya ce, "Ina mufida ce?" "Tana d'akin ta tana barci" cewar mummy Maida dubansa wurin muhdeen yayi tare da cewa, "Muhammad zuwa gobe idan ka huta sai ka leka asibiti ko? Domin gaskiya aiki yana yiwa Jabeer yawa a asibitin." Gyad'a Kai yayi alamun gamsuwa tare da cewa "Dady insha Allah gobe zan koma aiki na" "To Masha Allah.Allah yayi maka albarka." Mummy ce ta amsa da Ameen. Daga nan hira suka d'an taba ,daga bisani ya Mik'e yayi masu sallama sallama ya fice. *WANE NE DADY* Asalin sunan sa shine Alhaji Sani shi mutumin Garin kontagora ne dake nan jihar niger.sunan mahaifinsa Alhaji Mahmud da matar sa Hajiya Hauwa.'ya'yan su uku suka haifa,Babban sunan sa Adam sai mai binsa sunan sa Sani, wato mahaifin Muhdeen kenan sai karamar su Maryam,Babban yayan su Adam yana da 'ya'ya biyu Khalil da Jabir,Jabir ne abokin muhdeen.sai Sani wato mahaifin Muhdeen Yana da 'ya'ya uku Muhdeen ne Babba,Asiya ce ta biyu sai ta ukun su Mufida 'yar autar Mummy kenan,Maryam ita ce kanwar Sani wato itace take bin mahaifin Muhdeen d'in.tana da 'ya'ya biyu tunda ta haifi 'yan biyu bata sake haihuwa ba.daga ita sai tagwayenta Azeeza da Azeema,Adam Babban ma'aikacn gwamnati ne Yana zaune a garin Abuja,yayin da Sani wato mahaifin Muhdeen Yana zaune a Babban birnin jihar niger wato Minna kenan, shahararren 'Dan kasuwa ne da yake kasuwanci kasashe daban-daban yayin da yakai wata ziyara a garin Katsina wajen wani a bokin sa Alhaji Hassan,to a garin ya hadu da Fatima wato Mummy mahaifiyar su Muhdeen kenan,Allah ya k'addara auren su inda ta tare a gidan sa dake unguwar Bosso Estate nan garin Minna,har ta haifi yaran ta guda ukuDuk da a yanxun takan ce 'ya'yan ta hudu har da Inteesar wacce a shekaru uku da suka wuce Allah ya hada ta da inteesar. Shekaru uku baya wata Rana da safe Mummy zataje unguwa direban ta ya dauko ta a mota tsautsayi ya gifta har Direban ya 'Dan kad'e ta da mota ta fadi a k'asa, kasancewar bataji ciwo ba yasa ta Mik'e da sauri yayin da direban da Mummy suka fito suna salati, cikin hanzari Mummy ta k'arasa gare ta ta ri'ke ta ta ce, "Sannu ko zo mu tafi asibiti" Inteesar dake sanye da uniform d'in school ta girgizawa Mummy kai cikin sanyin muryarta ta ce, "Kada ki damu ba abunda ya same ni Ina lafiya,banji ciwo baAllah ya kawo abun da sauk'i" Take Mummy taji son yarinyar har cikin ranta,shafa kanta tayi ta ce, "To muje ga chemist can ko magani ya 'Dan baki saboda tsamin jiki." Girgiza Kai tayi tare da cewa, "Wlh ba komai kada ki damu." Kai mummy ta girgiza tare da cewa, Ina ne gidan KU take? Kallonta Inteesar tayi ta ce "Acan bayan layin ne ba nisa." Mummy tace " To muje na rakaki gida.." Dak'yar Inteesar ta yadda ta shiga motar suka karasa har kofar gidan su Inteesar din,da sallama suka shiga Abba dake zaune kan tabarma yana shan Koko da k'osai yayin da Umma ke gefen shi zaune,tozali sukayi da Hajiya Fatima kamilalliyar mace mai kwarjini,Ummace ta Mi'ke ta d'auko tabarma daga d'aki ta shinfid'e a gefe tare da cewa, "Maraba lale sannu da zuwa" Murmushi mummy tayi ta karasa ta zauna,a gefen tabarma,ta zaunar da Inteesar a gefen ta,sannan ta kalli Abba cikin girmamawa ta ce, "Ina kwana mallam" Cikin sakin fuska da Kamala irin tasa ya amsa Mata da cewa "Lafiya qalau ya aik?" "Alhamdulillah" tace tare da kallon Umma ta sakar mata murmushi kafin ta gaishe ta Umma ce tayi saurin cewa. "Ina kwana Hajiya?ya aiki?" Murmushi Mummy tayi tare da cewa " Alhamdulillah angodewa Allah." Umma ce ta K'ara cewa "Masha Allah Allah dai yasa ba laifi tayi ba naga ankawo ta har gida." Atunanin ummi ta d'auka Mummy malamar su Inteesar ce. Mummy ce ta danyi ajiyar zuciya sannan ta basu labarin Yadda akayi direban ya kad'e Inteesar kuma tak'i yadda suje Koda chemist ne,sannan ta basu hak'uri suka ce kada ta damu ba komai. Abba ne yace to me ya dawo da ita a wannan lokacin ? Cikin sanyin ta take sanar dasu an Kore ta ta kudin school fees ne shiru sukayi yayinda Abba ya dafa goshin sa Mummy ce ta Ciro kud'i a jakkar ta masu yawa kimanin naira dubu ashirin tace gashinan susayi Mata magunguna, Amma fir sukaki karba kud'in nan Babu yadda Mummy batayi ba har aje masu tayi amma Abba ya rantse akan cewa bazasu kar'bi kud'in ba,ba yadda ta iya dole ta tafi tare da yi masu sallama ta tafi. Bayan tafiyar ta ne mallam Ali wato Abba ya kalli Umma cikin damuwa ya ce, "Tun satin da ya wuce nake ta tunanin kud'in makarantar nan Amma na kasa samu wlh." Umma ce ta kalle shi ta ce, "To mallam mai zai hana mu mayar da ita makarantar Gwamnati?" Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) *DON K'ARIN BAYANI* 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin Rubuta ta Shi dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya,to KU gafarceni ni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Page0️⃣6️⃣ Ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da kallon ta ya ce, "A zahirin gaskiya bana son nasaka Inteesar makarantar Gwamnati,zanyi k'ok'ari na naga na samu kud'in nan." Aijyar zuciya umma ta sauke tare da kallon Inteesar. Ya cigaba da cewa "Bari dai naje kasuwar na dawo muga Abunda Allah zaiyi." "To Allah ya bada sa'a ya rufa Mana asiri." cewar umma Abba ne ya amsa da Ameen. Inteesar dai tagumi tayi. To a ranar da yammaci Mummy ta dawo gidan su Inteesar Don ta K'ara duba jikin ta,inda ta kawo masu Sha tara na arzikisannan ta nemi alfarmar cewa tunda unguwa d'aya suke basu da nisa tana son tasa Inteesar makarantar da 'yar ta take zuwa wato mufida dukkan su kusan sa'annin juna ne bazasu wuce shekaru goma Sha biyar ba a lokacin,umma ta ce, " Yanzun ni bazance komai ba idan mahaifin ta yazo zan sanar dashi duk shawara da muka yanke shikenan." Daga nan tayi masu sallama kan cewa jibi zata dawo taji shawarar da suka yanke. Haka kuwa akayi da Abba ya dawo kasuwa bayan yaci abinci ya huta,Umma ta kalleshi tare da cewa, "Yauwa mallam wannan matar da suka kusan Kad'e Inteesar da mota tazo ta kawo mana abin arziki sannan ta nemi alfarmar a wirin mu." Kallonta yayi tare da cewa "Wace Alfarma kuma zata nema a wurin mu kuma?" "Wai dama cewa tayi Tana son ta canzawa Inteesar makarantar boko ce,wai zata saka ta inda 'yar ta sa'ar Inteesar take makaranta.wai zata had'a su su dinga tafiya tare inda Direban ta zai dinga kaisu idan lokacin tashi yayi yaje ya dauko su." Girgiza Kai Abba yayi alamun rashin amincewa "Bazai yuwu ba,bana buk'ata wato don taji Inteesar tace an Kore ta kud'in school fees shine tayi tunanin haka" Gyada Kai Ummu tayi tace , "To shikenan" Yaci gaba da cewa "Insha Allah yadda nad'uki nauyin karatun ta tun daga nursery har primary yanzun Tana secondary jss 3 ,insha Allah bazai gagare ni ba,Allah zai shige Mani gaba." Bayan kwana biyu kuwa sai ga Mummy ta dawo,cikin sa'a kuma ta samau mallam Ali a gidan,bayan sun shimfid'a Mata tabarma ta zauna ne ta kalli malam Ali. "Mallam barka da safiya ya iyali?" Cikin sakin fuska kuwa ya amsa Mata tare da cewa "lapiya qalau Hajiya, ya gajiyan ki?na dawo Naga sako nace meye zakije wani kashe kud'i wajen yi mana siyayya da Ina gidan bazamu kar'bi komai daga gare ki ba ai tsautsayi ne kuma yarinyar da bataji ciwo ba ba buk'atar ki wahalar da kanki." Murmushi tayi tare da cewa, "Ai ba wannan ya kawo ni bama,nasan mai d'akin ka ta sanar dakai alfarmar da muke nema a wajen ka ko?" Kai ya gyada Alamar Eh "Ta sanar dani amma gsky kiyi hakuri kibar maganar nan kawai, d'aukar nauyin karatun Inteesar bazai gagare ni ba insha Allah, kamar yadda a can baya ban kasa ba." Ajiyar zuciya ta sauke don ta fahimci inda maganar tasa ta dosa,yana ganin kamar don ya kasa ne zata d'aura daga yanda ya tsaya,ita kuma ba haka bane a zuciyar ta,soyayyar yarinyar take ji har cikin ranta Allah ya d'aura Mata kaunar 'yar su. Cikin sanyin murya tace, "Bawai ka kasa bace,a'a wallahi Allah ne ya d'aura Mani soyyayar 'yar ku,Ina kaunar ta fisabilillahi har cikin raina.duk da baku sanni ba kuke tsoron amincewa dani ko?" Kai Mallam Ali ya girgiza tare da cewa, "Duk da bansan Halin ku ba Amma da alamu ku mutanen k'warai ne domin inajin yanda jam'ar unguwa ke yabon ku akan kyautatawa da kukewa makwabtan ku,musamman Alhaji Sani mijin ki kowa yabon sa yakeyi akan kyawawan halayyar sa da kyautatawa mabukata musamman watan Ramadan Sai dai Allah ya saka masa da alkhairi." Murmushi tayi cikin Jin dad'i,yayin da Umma ta amsa da Ameen. Mummy ta ce, "Naji dad'in jin hakan,kamar yadda ka sani muna da yara uku da miji na babban wato Muhammad muhdeen Yana can kasar waje Yana karatun masters d'in sayanzun 'yan matan su biyu ne a gaba na Asiya ita ke bin Muhammad Muhdeen,yanxun haka wannan shekaran insha Allah zata kammla karatun secondary din ta sai Auta wacce bazata wuce sa'ar Inteesar ba don Allah ka Amincewa mani da buk'atata kullun da safe idan ta shirya sai tazo Direban ya kaisu tare,idan an tashi yaje ya d'auko su,na d'auki nauyin karatun nata don Allah da soyayyar ka annabi Muhammad S.A.W." Jikin mallam Ali ne yayi sanyi domin duk taurin kansa idan aka had'a shi da Allah da mazon sa angama yace to " Shikenan Allah yasaka da khairan." Waigawa tayi tana neman Inteesar cikin murmushi ta ce, "Ina Yar tawa take?" Umma ce ta ce, "Ta tafi islamiya" Kai ta gyada tare da cewa "Agaida mani ita" Mikewa tayi tare da masu sallama tabar gida. A cikin kwana biyu aka gama shiryawa Inteesar komai na makarantar an basu inda ta fara karatu class d'in su daya da Mufida jss 3 kullun direban gidan su mufida zai kaisu, Inteesar da wuri take shirywa Don idan ta idar da sallar asuba tayi azkar bata kuma kwanciya barci,zata hura wuta tayi wanke-wanke ta gyara d'akin ta da share tsakr gidan idan Koko zasusha ta dama idan kuma d'umame ne tayi kafin karfe bakwai ta gama ayyukan gidan nan ta karya karfe bakwai zata nufi gidan su mufida,kullun idan taje takan samu Mummy a kitchen tana had'a breakfast,haka zataje ta tayata su kammala,ko Mummy tayi ta fama da ita taci wani abun ko tea tasha amma sai tak'i.wata rana ma ita take taya Mufida shiryawa don idan ta Mufida ce sai suyi lettin zuwa school, Ita kuma Asiya tunda ba school d'aya suke ba bata bi ta kansu,ko gaisuwar Inteesar ma Bata amsawa sai dai idan taga idanun mummy,don kallo wulakanci take mata,don bata d'auko halin Mummy ba tana da kyamatar talaka gata mishkila ce,Dady ma ya nunawa Inteesar k'auna da kulawa,musamman da yaga matar sa da kuma autar sa Mufida suna k'aunar Inteesar Shima yake kaunar ta kamar shi ya haife ta,don ko abu zai siyowa yaran nasa guda uku yake siyo komai Asiya, mufida, inteesar.haka 'bangaren mummy komai tar take masu ko Kaya ne dinki ma iri daya ne take masu,haka takalma da d'an kunne,kayan kwalliya gyale ne kawai idan zata siya masu sai ta siyawa Inteesar Hijab kasancewar Bata saka gyale ko ansiye Mata zata a jiye shi ne,Abban Inteesar da Ummata ma takanas sukazo yiwa Dady da Mummy godiyar d'awainiyar da suke da 'yar su, Mummy tana son kowane lokaci Inteesar tana gidan ta, Wata rana Da yamma Inteesar tana zaune a tsakiyar gidan su tana wanke-wanke.Mufidaa tayi sallama ta shigo da far'ar ta ta k'araso cikin Jin dadi take cewa Inteesar Babban yayan mu ya dawo kizo muje ki gansa,dama baki taba ganin sa ba. Cikin Jin dadi tace, "Haba da gaske kikeyi"? Murmushi Jin dadi Mufida tayi kafin tayi magana ne umma ta fito daga d'aki tana kallon Mufida ta ce, "Mufida kece a gidan namu?" Durk'usawa tayi ta gaida Umma "Ina yini Umma?" "Lapiya qalau ya mutanen gidan?" Cikin yanayin da take ciki na jindadi tace "Umma Yayan mu ya dawo shine nazo Kiran Inteesar tazo su gaisa." "Masha Allahwanda yake can kasar turai ko?" Cewar umma "Eh umma" Da-dai lokacin Inteesar ta k'arasa gama wanke-wanke ta saka hijab Mufida taja hannun ta suka tafi tana sallamar Umma. "Umma sai na dawo" "To ki gaishe su." Koda suka karasa gidan a falon ba kowa kowa yayi d'aki,dama sun Dad'e suna fira kasancewar da ya iso Mufida na barci bata sani ba ta farka ne ta gansa take sanar da aminiyar ta. Kai tsaye part din sa suka nufa baya falo, knocking Mufida sukayi yabada izinin shiga.da sallama suka shiga ya na magana da wani a waya da alama abokin sa ne,yana tozali da Inteesar gabansa ya fad'i ya mik'e da sauri tare da cire wayar a kunnen sa,kallon mamaki yake mata,don tabbas itace yarinyar da yake gani cikin mafarkinsa ,nuna ta yayi da yatsa tare da furta " kee!" Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON K'ARIN BAYANI* 09065327995 Love u oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashiubuta ta Shi dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to ku gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Page0️⃣7️⃣ Nuna ta yayi da yatsa tare da furta "Kee!" Inteesar cikin tsananin mamaki take kallon shi ganin yadda yake Mata kallon mamaki,alhalin ita bata ta'ba ganin sa ba, Acikin zuciyar ta kuwa ta ce, "Anya kuwa wannan mutumim Yana da hankali?duk yabi ya rikice har da tambayar ta Wai ni ce?alhalin ban taba ganin sa ba." Muryar mufida ce ta katsae ta Jin tana cewa, "Yaya lapiya kuwa?" K'ok'arin dai daita nutsuwar sa yayi don kada su fahimci wani abu game dashi,sannan ya ce, "Babu komai" Murmushi tayi tare da kamo hannun Inteesar din ta ce, "Yaya wannan itace Inteesar d'in da nake baka labari" Kai ya gyad'a ba tare da ya kalle su ba.inteesar ce tadan durk'usa cikin girmamawa ta ce, "Ina yini?" "Lafiya" Ya amsa Mata a gajerce ba tare da ya kalle ta ba,ta Kara cewa "kadawo lafiya?" Bai kalle ta ba,balle tasa ran zai amsa kallon Mufida yayi tare da yamutse fuska yace, "Pls kud'an fita dan ina son na Dan huta." Kwa'be Fuska ta tare da cewa "Yaya Wai yau nice kake Kora daga d'akin ka abunda baka taba yi maniba?" Jinjina Kai ta yi " Koda kanajin barci sai dai idan nice naga alamun haka na fita? Kuma gani tare da k'awa ta sannan ko gaisuwar kirki baku..." Dakatar da ita yayi ta hanyar daga Mata hannu,sanan ya nuna Mata kofar fita yace "please" Rau rau tayi da idanu kamar zatayi kuka,taja hannun Inteesar suka fice daga dak'in,suna fita ya samu yayi ajiyar zuciya,don har ga Allah baiji dad'in abunda da yawa k'anwar tasu ba,amma ba yadda yadda iya dole yayi hakan ki zai samu sassauci, domin tunda ya kalli Inteesar gabansa yake ta lugude don ya girgiza da ganin ta.fitar nata shine samun sau'kin sa. Bangaren su Mufida kuwa suna barin d'akin sa Kai tsaye d'akin Mummy suka nufa, Inteesar ce kadai tayi sallama Mufida kuwa idanun ta tab da kwallah suke,kadan take jiran tayi kuka, Mummy dake shirya kayan da mai masu wanki da guga ya kawo ne take shiya su a cikin wardrobe din kayana ta. Juyowa tayi ta kalle su ganin su cikin wani yanayin yasa ta dakatar da abunda takeyi ta karaso bakin gadon ta janyo hannayen su ta zauna dasu bakin gadon tare da cewa, "ku lapiya kuwa?me ya faru?" Cikin shagwaba ta da muryar kuka take cewa, "Wai daga mun shiga mu gaida Yaya Inteesar da bata San shi ba sai a photo nace muje ta gaishe sa,shine kawai harda korar mu ko gaisuwar ta bai amsa ba." Ido Mummy ta zuba masu tare da yin tunanin ko me yasa yayi masu hakan? "Kunga wata K'ila akwai abunda ke damun sa ne,kuma kun cika shi da suruta.ke mufida ai kinsan baya son hayaniya,wata Kila shiyasa ya Kore ku,Amma kada hakan ya dame ku kuyi hak'uri kunji?" Ta karasa maganar tana shafar gefen fuskokin su Mufida tayi saurin cewa "Wlh ba hayaniyar da muka damesa dashi,ko gaisuwar kirki basuyi ba. To naji ku saki ranku sai dai idan akwai abunda yake damun sa.cewar mummy kenan." Mik'ewa tayi ta nufi d'akin sa,Murda handle din kofar tayi tare da yin sallama.zaune yake bakin gadon say yayi tagumi.jin muryar Mummy ce yasa ya amsa sallamar tare da amsa sallamar da tayi masa. Murmushi ya k'ak'alo ganin mummy ta zuba masa idanu Tana karantar yanayin sa. "Mummy sannu da shigowa" "Yauwa " tace tare da karasawa ta zauna saman side drawer. "Son lapiyar ka kuwa ko akwai abunda yake damun ka ne ban sani ba?" Murmushi ya k'ak'alo wanda iya fatar bakin sa ta tsaya,bata Kai zuci ba. "Lapiya qalau Mummy kawai dai nagaji ne" Kai ta girgiza tare da cewa, "Akwai mana son,nifa mahaifiyar ka ce idan ma kana cikin damuwa ka sanar dani mana,kada ka boye Mani." "Kada ki damu Mummy gajiya ce,I will be fine." Mikewa tayi tace "To shikenan tunda haka kace,amma baikamta ko Kori kannen ka ba,da suka shigo gaishe ka,musamman ma Inteesar da karon faroko kenan tasan ka,tazo kaishe ka sannan zaka kure su?" Jinjina Kai yayi alamun gamsuwa "To Mummy insha Allah hakan bazata sake faruwa ba,daga ta fita tabar masa dakin." Haka rayuwa tayi ta tafiya yayin da Mummy da Dady da kuma mufida ke Kara k'aunar Inteesar,don har mommy taso a ce Inteesar ta dawo gidanta da zama gaba d'aya,amma ganin cewa ita kad'ai iyayen ta suka haifa kuma tana taimaka wa mahaifiyarta da aikace-aikacen gida gida yasa ta ha'kura.kullun Inteesar idan ta idar da sallar asuba tayi azkar Bata kuma kwanciya zata Fara aikace-aikacen gida,shara wanke kwanuka d'ora masu abun abun da zasuyi kalaci dashi wankin bandaki gyaran d'akunan gidan duk itace.kuma kafin karfe bakwai ta gama komai tayi Shirin zuwa school bayan ta gaida iyayen ta ta sallame su.kai tsaye zata nufi hanyar gidan su Mufida kullu taje zata 9tarar da ma'aikatan gidan nata aiki tunda kan Mai gadi da Mai bawa fulawa ruwa da masu sharar harabar gidan da masu goge windows kowa na aiki harda Mai wankin mota.sai da ta gaishe su sannan ta nufi cikin gidan,nan ta tarar da Mai aikin su tana goge-goge Mummy kuwa kullum tana kitchen Tana hada breakfast din mutanen gidan.Yayin da jummai ke girka na ma'aikatan gidan.don Dady bayason Abincin masu aiki.kullun sai Inteesar sai ta taya mummy karasa hada breakfast tajira mufida tayi breakfast sannan su tafi. A bangaren Muhdeen kuwa sai K'ara tsanr yarinyar yakeyi a cikin zuciyar sa.har ita kanta Inteesar din ta fahimci hakan.cewa baya kaunar ta Wanda ita kanta ta rasa dalilin da yasa haka.don ko had a ido sukayi zai galla Mata harara ko ta gaishe sa sai dai idan a gaban mutanen gidan ne yake amsawa idan basu nan kuwa ki ta gaishe say sai yayi tsaki ko ya harare ta Kwanci tashi asarar Mai rai.har muhdeen ya kammala karatun sa na likitanci ya dawo Nigeria inda Dady ya gina masa Babban Asibiti a nan cikin garin Minna.inda Jabir wato d'an yayan Dady zasu dinga tafiyar da asibitin a tare,don Shima abunda ya karanta kenan. Bayan an zuba kayan aiki an d'auki kwararrun ma'aikata sun fara aiki ba dadewa ne Muhdeen Ya tafi kasar Egypt bikin Abokin saWanda sukayi karatu a tare. *CIGABA LABARIN* Washe gari Monday ne Muhdeen ya shirya da sassafe zai tafi asibiti,kai tsaye ya nufi kitchen,don a tunanin sa Mummy na cikin kitchen din.ya nufi kofar kitchen d'in Yana cewa "Muummy da wuri yau zan fita a hada m"ani breakfast di..." Kasa karasa maganar yayi sakamokon tozali da yayi da Inteesar dake kokarin zuba ruwan shayi a cikin flask.bayan ta gama soya dankalin da kwai. Jin muryar muhdeen yasa ta juyo ta kalle shi tare da sunkuyar da kanta kasa tace "Barka da safiya Yaya" Tsuki yayi tare da niyar barin kitchen din Dai-dai lokacin Mummy ta shigo,ganin ta yasa ya k'ak'aro murmushn dole ya kalli Inteesar din cikin sakin fuska yace "Yauwa k'anwata kin tashi lapiya ko?" Daga kai tayi ta kalle shi ciki mamaki,ganin Mummy ne ta shigo kitchen din yasa tasan dalilin amsa gaisuwar ta da yayi. Don dama mummy tace ya dauke ta kamar Asiya da Mufida itama kanwar sa ce.murmushi mummy tayi tace "Yau da wuri zaka tafi asibitin kenan" Kai ya gyada tare da cewa "Eh kinsan sati daya kenan banje ba saboda tadiyar da nayi,Ga aiki sunyiwa Jabeer yawa" Kai Mummy ta jinjina tare da cewa Hakane, Inteesar had'a masa breakfast ya tafi Da sauri ya girgiza Kai tare da cewa "No ta barshi kawai sauri nake idan naje can zanyi." Ya fita daga kitchen din ransa a bace,Don yayi niyyar yin breakfast a gida ganin cewa Inteesar zata hada breakfast yasa ya fasa haka yayi masu sallama fita. Mufida ce ta fito daga dakin ta cikin hanzari ta shiga kitchen din,ta d'ebi ruwan tea kawai sai slice bread da ta dauki guda biyu.a kichen din ta zauna tayi breakfast din suka tafi suna sallamar mummy don'ton dama yanzun already sunyi late. Bangaren Muhdeen kuwa a office yasa aka kawo masa coffee,Yana zaune akan kujerar office dinsa ga tarin file a gaban say Yana shan coffee din a hankali wayar sa ce dake ajiye akan table din gaban sa ta Soma ruri duban yayi tare da murmushi Don yasan ita ce ke Kiran sa dai-dai wannan lokcin,murmushi yayi acikin zuciyar sa ya furta my Sumy daga wayar yayi ba tare da ya furta komai ba. *LONDON* Tana kwance saman gadon ta Jin yayi picking tace "Morning sweet" Daga can bangaren sa "Kina lapiya"? Lumshe idanu tayi sakamakon Jin muryar sa,sannan tace "Lapiya qalau wlh kana inane yanxun?" "Ina office ne,yasu Mum da Dad?" Ya tambaye ta Amsa masa tayi tare da cewa " suna lapiya yanxun haka ma sune suka sa na Kira ka akan maganar da mukayi dakai kan cewa ka turo magabantan ka ayi maganar auren mu Cikin Jin dadi yace Are you serious?Kai Amma naji dadin Jin hakan daga gare ki. Kinyimun albishir mai dadi da safen nan.ina komawa gida zan sanar da su Dady tunda dad dinki ya amince." Murmushi tayi kafin tace, "Kaima kasan duk abunda nace Ina so shi akaeyi mani,ban taba cewa Ina son Abu Mum da Dad suka ki mincewa ba Koda basa son Abu zasuyi mani don su faranta mani Rai." Jinjina Kai yayi kafin yace "Ai ke 'yar gata ce" Knocking k'ofar akayi sannan yace mata " Kinga I will call you when I'm done." Bata fuska tayi tace, "Oh Allah yanxun ba zaka iya Bari mucigaba da hirar mu cikin jindadi ba." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "Karki damu zamuyi magana," Bai jira cewae ta ba ya katse kiran,sannan ya kalli k'ofar da ake knocking ya bada izinin shigowa. Jabeer ne ya shigo tare da Mika masa hannu sukayi musabaha ya zauna kan kujerar dake facing din muhdeen. Jabeer ne ya ce "Wato ka shigo ko ka sanar dani ko? dan banda nurse Hauwa da take sanar sani." Murmushi yayi tare da cewa "Wallahi nabar gida banyi breakfast ba,Ina shigowa nasa aka kawo mani coffee Ina jiran idan na kammala na Kira ka ne sai kuma na samu labari mai dadi." Ya Karasa maganar Yana sakin murmushi,Shima jabeer dtin yayi murmushi tare da cewa "To Masha Allah wani abun farin ciki muka samu da safen nan?" Fara'ar sa ce ta karu yacigaba da cewa "Sumy ce take sanar Dani cewar mahaifin ta yace na turo magabata na a sa Mana ranar aure" Take fara'ar dake Kan fuskar jabeer ya dauke,ya shiga damuwa nan take.domin yasan sumy sosai tunda dukkan su tare sukayi karatu a America tare,Sam bata da tarbiyya bata San darajar dan aadam ba.yadda kasan ba 'yar musulma ba idan kayi la'akari da shigar ta da dabi'un ta sallah ma Bata Dame ta ba,sunan ta kawai zakaji kasan cewa musulma ce. Ido muhdeen ya zuba masa Yana karantar yanayin sa.kafinya ce "Yadai bro lapiya?" Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wanna kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. Page0️⃣8️⃣ Ajiyar zuciya Jabeer yayi tare da kallon Muhdeen cikin kwantar damurya ya ce, "Amma da zaka bi shawara ta daka rabu da Sumy baby domin bata dace da Kai ba" Wani irin kallo Muhdeen ya watsawa jabeer tare da cewa "Meye dalilin ka?" Jinjina Kai jabeer yayi tare da cewa, "Dalilai da yawa ma kuwa, Na farko, yarinyar Nan bata da kamun Kai Na biyu,Bata da tarbiyya Na uku yarinyar bata San darajar d'an Adam Shigar ta da dabi'un ta sunsha ban-ban da ta 'ya'ya masu mutun..." Muhdeen ya daga masa hannu ta alamun dakatarwa cikin bacin rai ya nuna masa hanyar kofa tare da cewa, "Fice mun da ga office" Kallon mamaki jabeer yayi masa yace "Dan na fadi gaskiya shine kake korata?" Cikin daure fuska muhdeen ya furta "Dama na Dad'e da sanin baka k'auna ta da sSumayya,bansan me tayi maka da yasa ka tsane ta na lura da hakan tunda dadewa.kuma Bari kaji aure na da sumayya babu fashi baka Isa ka hanani auren ta ba." Gajeren murmushi Jabeer yayi tare da cewa, "To meye zaisa na tsane ta hakanan kawai?i ba ita na tsana ba halayyar ta ne kawai na tsana." Tsaki muhdeen yayi "Yaushe ka zauna da ita da har zaka fahimci halayyar ta?don kunyi karatu kasa daya makaranta d'aya shine har zaka fahimci halayyar ta?" Cikin takaici jabeer yace, "Ai ba sai ka zauna da mutum ba,kamannin mutum da halayyar sa da ayyukan da yake aikatawa ma yakan say ka fahimce shi ko wane irin mutumi ne." Cikin Dan d'aga murya ya ce "To koma dai manene abunda na sani kawai shine Tana masifar sona.kuma bazata aikata abunda zai 'bata mani rai ba." Jabeer na ya daga kafad'a alamun bandamu ba,sannan ya furta "Shikenan tunda haka kace,sai dai ina baka shawar ka nemawa 'ya'yan ka uwa tagari wacce zakayi alfahari da it...." Cikin daga tsawa yace "I said out" Kai tsaye ya nufi kofar fita ya fice,yana mamakin abokin nasa da ya makance akan soyayyar Sumayya,tunsa yake da muhdeen bai taba d'aga masa murya ba sai akan sumayya.Bashi da Babban abokin da wuce Muhdeen ko shawara ya bashi yana karba amma yau Karan farko ya 'bata dashi akan mace.haka ya nufi office din sa ransa ba dad'i. Shima muhdeen aikin da baiyi ba kenan,haka ya rufe office din nasa yabar jabeer da tulun aiki. Ya nufi parking space ya tada motar say yabar asibitin. Kai tsaye gida ya nufa. ya tarar da Dady a falo yayin da Mummy ta tsiyaya masa ruwa a kofi ta mik'a masa,da sallama ya Isa da mamaki suke kallon sa ganin lokacin da ya dawo ba lokacin dawowar sa ba. Amsa sallamar sukayi yayin da ya karaso zauna a gaban su bisa center carpet. tare da cewa, "Barka da warhaka Dady." Kallonsa Dady yayi bayan ya ajiye Glass cup din da yasha ruwa a saman center table d'in dake gaban sa. "Yauwa barka dai Muhammad,lapiya Naga ka dawo dai-dai wannan lokacin?" Sunkuyar da Kai yayi tare da Sosa keya "Eh lapiya Dady,dama am... " Sai yayi shiru ya kasa karasa maganar Dady ya tattaro dukkan hankain sa ya maida Kan muhdeen sannan yace, "Kayi magana Mana Muhammad Ina Jin ka." Sunkuyar da Kai Muhdeen yayi tare da Fara magana. "Dma akwai yarinyar da muka dai-daita da ita ne,shine ta kirani Wai mahaifin ta yace na turo magabata na suyi magana." Cikin Jin dadi Dady ya furta "Kai Masha Allah,naji dadin Jin wannan maganar daga bakin ka.don dama buri na kenan naga auren ku." Juyawa yayi ya kalli Mummy tare da cewa. "Bakiji abunda danki ya fada ba?" Jinjina Kai tayi tare da cewa "Naji,Amma ka tambaye sa ya tarbiyya yarinyar take?tana da dabi'u masu kyau da addini? Idan ba mantawa nayi ba akwai ranar da Asiya ta nuna mani photon yarinyar a wayar sa,kuma gaskiya nikam bat..." Abba ne yayi saurin cewa "A'a kada kice komai tunda baki taba ganin ta ba, photo kawai bazaisa ki fassara 'yar mutane ta wace siga ba.baki da hujja,kedai kawai fatan alkhairi zakiyi masu tunda suna son juna." Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Shikenan.Allah ya tabbatar Muna da alkhairi." Ameen Abba yace Sannan ya kalli muhdeen da ya sunkuyar dakai kasa yace "Ita yarinyar 'yar gidan waye kuma a Ina suke?" Cikin Jin dadi yace, "Dady suna zaune ne agarin Abuja sunan mahaifin ta Alh. Tanimu Dan kasuwa ne,kasuwancin Gwal-gwalai yakeyi daga kasar dubai.amma dai yanxun haka suna zaune a London ita da iyayen nata.sai dai ta sanar dani ta hanyar text message Wai gobe zasu dawo Nigeria." Kai Abba ya jinjina alamun gamsuwa Sanan yace, "Zanyi bincike akai,idan yaso sai na Kira Yaya Adam da minina Alh.kabir sai muyi abunda ya dace." Haka kuwa akayi a cikin sati daya aka saka ranar Auren Muhdeen da sumayya nan da watanni biyu masu zuwa.farin ciki a wurin masoyan guda biyu baya misaltuwa,domin abunda suke buri kenan. Wata ranar Asabar ne Muhdeen ya sanar da Mummy cewar zai kawo Mata sSumayya ta gaishe a.mummy taji dadin hakan sosai. Da misalin karfe biyar na yamma sumayya ta gama Shirin ta tsaf da kananun Kaya tasaka saboda dasu ta Saba, mom din ta ce tace ta cire su saboda gidan surukanta zataje tayi shiga na mutunci,zasufi ganin mutuncin ta.dakyar ta yarda ta saka wasu matsatstsun Riga da siket na leshi sun matse ta sosai kamar zatayi numfashi su yage,wayar ta ne tayi ringing Jin ringing din wayar yasa ta sakin murmushi,domin tasan waye ke kiranta ringing d'in sa na musamman ne tasa masada sauri ta daga wayar. "Hello sweet ganinan fitowa" Muhdeen dake zaune a motar say Yana jiran ditowar ta ne ya ce, "Please Baby kiyi shigar mutunci da Kamala,na hanaki saka irin kayayyakin da kike sawa kinki ji ko?" Tura baki tayi tace, "To ni fa kasan dasu nasaba." Muhdeen ya ce, "Ai zance ya kusan karewa da zaran mumyi aure manyan Kaya da manyan hijabai Zaki dinga sakawa,idan kinda kananun Kaya sai dai idan ni zakiyiwa kwalliya" Murmushi tayi sannan ta ce "Ganinan fitowa gashin attached din da akayi Mata Kari ta sake shi baya,tayi daurin Dan kwalin nan da ake cewa ture kaga tsiya,siririn mayafi ta rataya shi a gefen kafad'arta ta tare da rataya handbag dama tayi kwalliya fuska tun daga Kan powder har janbaki ta fesa turarurruka kala uku tasa takalmin ta mai tsini ta dauki wayoyin ta ta rike a hannu.ta nufi kofar fita.Afalo ta samu mahaifiyar ta,sallama tayi Mata ta fice. A cikin mota ta same shi Yana jiranta,bude murfin motar tayi ta shiga ido ya zuba mata yana kallon ta sai sakin murmushi takeyi ta jujjuya ido takeyi tare da cewa. "Baby ya kaga shigar manyan kayan nawa?yayi ko?" Zuba Mata ido yayi tare da cewa "Ba laifi" Zuba masa ido tayi "Cewa zakayi ba laifi? Bayan Kai da mummy ne kuka ce nasa kayan mutunci Amma ki ka Yana Mani?" Murmushi yayi tare da cewa "Sorry my Baby kinyi kyau Amma kike kisaka Koda irin 'dan abayar nan ne da mayafi da mata ke sakawa" Kallon mamaki tayi masa tace, "Tab wlh bazan iya kayan wahala ba duk nauyi ya dameni ga zari ba yanda isaka zai shiga ." Jinjina Kai yayi Taci gaba da cewa "Ni bana ma da abayar ballantana nasaka." Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Ba damuwa zamu siya a hanya sai ki saka mu karasa gidan" "Yakamata ka gane zansha wahala idan na saka" Yace, "Shikenan mu tafi" Baiso haka ba amma ba yadda yadda iya,baiso hakan ba. Horn sukayi Mai gadi ya wangale masu kofa suka fita,basu same ki Ina ba sai gidan su Muhdeen.Bayan yayi horn mai gadin gidan ya bude masa kofa ne ya shiga yayi parking. Atare suka bud'e marfin motar suka fito,Tana tafiya cikin takunta na yanga har suka karasa falo,ba kowa sai Mufida dake zaune a Kan kujera ,ganin su ne yasa ta mike cikin farin ciki ta ce "Sannu da zuwa Aunty Sumayya oyoyo matar Yayan mu" Sumayya ma murmushi tayi tare da cewa "Yauwa Mufida ya karatu "Alhamdulillah" Kasancewar Sumayya tasan kowa a gidan Muhdeen ya tura Mata photon su tun daga kan Dady da Mummy da Asiya da Mufida duk tasansu a photo. Inteesar ce ta fito daga dakin Mummy sanye da Hijab ganin Inteesar sai da gaban Sumayya ya fad'i Inteesar cikin fara'a ta kalle su tare da cewa "Sannu da zuwa,Ina wuni?" Yamutse fuska Sumayya tayi tare da cewa "Wace ce wannan?" Mufida tace kamar 'yar uwa take a wurin mu kullun Muna nan gidan a tare sunanta Inteesar" Sumayya ta Kare Mata kallo ganin irin kyawun da Allah ya mata,gata kamar wata balarabiya Fara ce doguwa mai dara-daran idanu,ga hancin ta dogo sai dan karamin pink lips din ta duk da ta saka hijab Amma Ana ganin yala-yalan gashin kanta da ya kwanta luf a goshin ta take sai taji tsanar Inteesar a cikin zuciyar ta. Dai-dai lokacin Mummy ta k'araso falon,turus ta tsaya tana karewa summaya kallo, Cikin wani irin murya ta ce "Son wannan ce matar da zaka aura?" Muhdeen ya zamo daga Kan kujera ya durkusa akan center carpet din falon Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman ihsa) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa Page0️⃣9️⃣ Muhdeen ya zamo daga Kan kujera,ya durkusa akan center carpet din falon.cikin far gaba ya ce "Mummy itace, na kawo ta ta gaishe ki." Jinjina Kai mummy tayi tana karewa Summaya kallo,gani tayi sam bata dace da Rayuwar Dan ta ba,dan daga gani bata samu tarbiyya mai kyau ba do daga gida ba,kallon Karin gashin da akayi mata ne ya zubo har tsakiyar bayan ta ga uban make up har yayi yawa,suturar jikin ta ya bayyana surorin jikin ta a bayyane, girgiza Kai tayi ta karaso ta zauna kan kujera. Muhdeen idon sa nakan mahaifiyar sa yana karantar yanayin ta. Sumayya daga yanda take zaune Kan kujera ta gaida mummy ta ce, "Barka da fitowa mummy" Cikin sakin fuska Mummy ta ce, "Yauwa sannu da zuwa" Sumayya ce daga yanda take zaune Kan kujera ta Kara da cewa, "Ina wuni Mummy" Ba yabo ba fallasa Mummy ta amsa Mata da, "Lapiya qalau Sumayya,ya mutanen gidan?" Amsawa tayi da duk suna lafiya Dai-dai lokacin ne Inteesar da Mufida suka loda Mata kayan ciye-ciye da lemu da ruwa a gaban ta. Shidai Muhdeen yana zaune a kasa saman carpet,don dama shi idan iyayen say suna zaune a kujera shi yana k'asa a zaune.koda kuwa daga baya suka zo suka tarar da shi akan kujera da zaran su zauna zai sauka kasa.Haka ma sauran kannen sa, Inteesar ma dabi'ar ta ce wannan tun fil'azal. Sumayya ruwa kawai tasha Wanda mufida ta kawo tata,kayan ciye-ciyen da Inteesar ta kawo mata kuwa ko kallon su batayi ba ballantana ta taba. don haka kawai sai taji kishin yarinyar musamman yanda taga Allah yayi mata sura Mai kyau gata Tana zaune a gidan su Muhdeen,kuma tasan dole zai dinga yawan ganin ta.sai tsanar Inteesar ya sake nunkuwa a cikin zuciyar summaya,don tasan tafita komai,abu d'aya zata fita dashi shinec tsayi Don sumayya doguwa ce tafi Inteesar tsayi.bayan nan ba abunda zata n mata,ko hasken fata ma idan Kika kalli Inteesar da sumayya zaki ga Sumayyar ta fita hasken fata.don ita tana karawa da mai maisa hasken fata shiyasa farin nata ya zarce na inteesar.amma da badon mai ba Inteesar tafita hasken fata Ido ta zubawa Inteesar sai taji k'irjin ta na dukan uku-uku,ta juya ta kalli Muhdeen dake zaune kasa saman carpet tace, "Baby mu tafi ko"? Kallon juna sukayi mufida da Inteesar yayinda mufida dariyar da take 'boyewa ne ya kufce mata. Ganin kowa ita yake kallo yasa taja hannun Inteesar suka shige dakin ta da sauri. Mummy ce ta kalli sumayya ta ce, "Tun yanzun gashi komai baki ci ba?" Yamutse fuska Sumayya tayi yayinda ta kalli kayan ciye-ciyen da Inteesar ta ajiye Mata tare da cewa "Mummy am okay" Mummy ce ta Mike tare da cewa "Ina zuwa" Kai tsaye dakin ta ta nufa,ba jimawa ta fito dauke da Leda a hannun ta.d'an kunne da sarka ce sai Turarruka a ciki. Karasawa tayi ta mikawa Summaya karba tayi tare da yin godiya mata sallama suka fita ita da muhdeen Mummy k'arasawa tayi d'akinta zuciyar ta cike da sake-sake ,tana ganin Sam batayi sa'ar suruka ba,ta dad'e tunanin hakan lokutan da take ganin pics d'in ta da Mufida ta nuna mata wasu ka ganta ba dankwali sai tulun Karin gashin wasu ba suturu. Kirki gasu nan dai da sauran su. Tumawa tayi da maganar da Dady yayi mata na cewar tayi masu fatan alkhairi kawai kada tayi tunanin komai,hakan yasa a cikin xuciyar ta tace Allah ya Sanya alkhairi. A bangaren Muhdeen da Sumayya kuwa suna tafiya a mota ne sumayyay ta kalle shi tare da cewa, "Baby na Wai meye alakarku da yarinyar nan ne?" Ba tare da ya kalle ta ba idanun sa nakan tuk'in da yakeyi ya ce , "Wata yarinya kenan?" Yamutse fuska tayi ta ce, "Wadda suka shiga daki da Mufida,Mai sanye da Hijabin nan Mana" "Okay Inteesar kike nufi ko?" "Eh" Ta amsa masa a takaice Dan Jim yayi kafin yace "Bamu da wata dangantaka ta jini da ita" Gaban ta ne ya tsananta bugawa,ta kalle shi tare da cewa "To zaman me takeyi a gidan ku?" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Nima kaina ba son zaman yarinyar nan nakeyi ba,hakanan kawai naji na tsane ta a cikin zuciya ta,wallahi bana kaunar zaman ta agidan nan.ke intakaice maki Zaki zance ban taba Jin tsanar wani mahaluki a duniyar nan kamar yadda na tsani ganin yarinyar nan ba. Sumayya wani irin murmushi tayi wanda sai da hak'oranta suka bayyana,cikin jin dad'in kalaman sa ta ce "Ai da kasa an Kore ta a gidan" Da sauri ya kalle ta tare da cewa "Ke! Kinsan yadda Mummy take k'aunar yarinyar Nan kuwa?To bari kiji zata iya 'batawa dani akan yarinyar nan,don ba k'aramin son ta takeyi ba wallahi,ke ba ma ita ba hatta Dady da Mufida suna matakar son ta nida Asiya ce kawai bamu k'aunarta don ma yanzun Asiya bata k'asar tana can kasar Turkey tana karatu." Shiru tayi tana sauraron sa kafin daga bisani tace, "To ya akayi tazo gidan?" Muhdeen ya ce "Mummy ce zata fita unguwa Direbanta yad'an kad'e ta, mummy ta bita gidan su a bayan layin mu daga nan dai ta janyo yariyar a jikin ta,da taso iyayen yarinyar su bata ita taci gaba da zama a hannunta gaba d'aya,so sai iyayen suka ce a'a ita kad'ai Allah ya basu bazasu iya rabuwa da ita ba.amma fa kwana ne kad'ai batayi a gidan amma nan take ko wane lokaci." Juyawa yayi yana kallonta kafin ya maida hankain sa Kan tukyin da yakeyi sannan ya ce, "Wai me yasa kika damu da sanin ko wace ce it's?" Girgiza Kai tayi tare da cewa , "Bakomai ,kawai dai na tambayar ne dan naganta kuma bansan ta cikin 'yan gidan kuba." Daga ita har shi ba wanda ya cewa kowa komai har suka karasa gidan su Sumayya sallam su kayi inda ya shaida Mata gobe zai shigo.sannan yaja motar yabar gidan Ranar monaday da misalin karfe tara na safe Yana zaune a office din sa yana duba mara sa lapiya, yayin da yake ma wani dattijo tambayoyi yana bashi amsa shi kuma yana rubutu a file d'in da ke gaban sa ne jabeer ne ya turo kofar office din ya shigo,don dama shi kadai ne yake shigo masa office Kai tsaye.zama yayi Kan sofa din dake cikin office din ya zauna,bayan ya sallami dattijon tare da sanar dashi inda zaije ya mik'a file din. Karasowa yayi ya zauna kusa da Jabir tare da mik'awa Jabeer hannu Murmushi jabeer yayi ya ce "Angon Sumayya mai jiran gado, har ka Fara kamshin angonci tun yanzun." Kallon shi Muhdeen yayi tare da cewa "Ai kallon ka kawai nakeyi duk yadda muke dakai banida aminin da ya wuce ka kuma dan uwa a gare Ni dan wan mahaifina amma ace tunda sumayya suka dawo garin nan baka taba zuwa kun gaisa ba har tambayar ka tayi." Rik'e baki Jabber yayi yana dariya yace afuwan aboki yau zamuje tare inasha Allah. yauwa na manta ban fad'a maka ba wannan rigimammitar tsohuwar na kira ta jiya tana ta zagin ka ashe dama baka kiranta ka gaishe ta?tana matsayin mahaifiyar Dadyn ka?" Tabe baki baki Muhdeen yayi tare da cewa "Mahifiyar Dady kace ai ba mahifiya ta ba,matar da duk mutum yayi waya da ita sai ta 'bata masa Rai shiyasa na daina Kiran ta." Dariya yayi tare da cewa "Ai ciwon Kai Kam yaxun zaka Fara don tace jibi tace zata so,kuma kasan idan tazo gidan Dadyn ka take sauka." Had'e fuska yayi tare da cewa "Dama duk cikin jikokin ta tafi saka mani ido wallahi." Jabeer ne yace "Ko kuma tafi kowa kaunar ka ba don wallahi tafi sonka fiye da kowa a cikin jikokin ta." Fira suka 'dana taba kafin ya tashi ya koma office din sa. Bayan kwana biyu kuwa sai Gwaggo ta baro garin Kontagora ta iso garin Minna tun ana bikin Muhdeen da Sumayya saura wata biyu tazo.murna a wurin Mummy da Mufida ba'a magana. Waya ta d'auka ta Kira mu6hdeen tace kada ya dawo gidan nan ba tare da yazo mata da amaryar da zai aura yau d'innan idan ba haka ba ko ruwa bazata bari yasha a gidan nan ba. Sanin rigimamar Gwaggo ne yasa baida wani zabi dole ya Kira Sumayya yace ta shirya zaizo ya dauke ta ta gaishe da kakar sa da tazo. Misalin karfe biyar na yamma Mummy ce zaune a falo yayin da Mufida ke zaune Kan carpet,Gwaggo ta shiga ta watsa ruwa. INTEESAR ce ta turo k'ofar karamin gate din gidan ta shigo gaisawa tayi da Mallam Ibrahim mai gadi sannan ta shige cikin gidan. Bakin ta d'auke da sallama ta shiga falon durk'usawa tayi har k'asa ta gaida Mummy sannan ta kalli Mufida ta ce, "Yauwa Mufida Ina Gwaggon take?kinsan ban ta'ba ganin ta ba,wallahi na k'osa na ganta ba." Mummy ce tayi murmushi tare da cewa, "Karki damu Inteesar yanzun zata fito Zaki ganta" Dai-dai lokacin ne Muhdeen ya shigo da sallama sumayya na biye dashi a baya suka karaso yayin da Muhdeen ya zauna a k'asan carpet ganin Mummy akan kujera, s6umayya ta zauna kan 1 seater dake facing din mummy gaida mummy tayi ba yabo ba fallasa ta amsa Mata, Mufida ta nufi d'akin da Gwaggon take sauka ta sanar da ita cewa Muhdeen ya shigo da matar da zai aura. Da sauri Gwaggo ta nufi falon 'dan kwalinta a hannun ta take fad'in "Ina kishiyar tawa take inga da mai tafini da ya tsallake ya tafi wurin ta" Idon ta ne ya sauka akan Inteesar dake zaune a carpet Muhdeen na gefen ta 'dan nesa da ita. Washe baki tayi tana fad'in " masha Allah wannan had'in yayi ai daga ganin zaren ma kalan yadin ne,gata kyakkyawa kamar shi jikan nawa." Dan Bata lura da Sumayya dake zaune Kan kujera ba.durkusawa tayi ta kamo ha'bar Inteesar tana cewa "Kai kyakkywar kishiya ta dole nayi kishi dake." Gaba d6aya falon tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah.Sumayya Kam ta cika da bak'in ciki tayi fam,idon ta ne yakai kan Sumayya dake Kan kujera wani kallo shek'ek'e take mata sannan ta nuna Sumayya tabce, "Ina kuka samo wannan Mai zubin karuwai?" Muhdeen ne ya ce "Haba Gwaggon ki dinga tsayawa kina tabbatar da abu kafin ki fad'a mana,matar da zan aura kike cewa karuwa?" Ware idanun ta tayi tare da nuna sumayya sannan tace, "Kana nufin wannan zaka kawo a cikin zuri'ar mu? a matsayin uwar 'ya'yan ka?Haba Muhammadu to nikam bada yawu na ba." Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne ban rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo daya to ku gafarceni ba da niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. Page1️⃣0️⃣ Cikin daurewar fuska ya kalli Gwaggo ya ce, "To ni ita na gani nake so, kuma bazan canza ra'ay ina akanta ba". Hannu Gwaggo tasa ta rike baki cikin mamaki ta ce, "Allah buwayi Gagara misali, oh ni yau naga abunda ya ishe ni, to bari ka ji ko Uban da ya haife ka bai isa idan nace a'a yace mun Eh ba, ballantana kai dansa". Murmushi Mai cike da takaici Muhdeen yayi sannan ya kalli Gwaggo yace, "To ai Dama Dady bazai tsallake maganar ki ba saboda ke kika haifesa, "Amma ni kama bak... Tsawar da Mummy ta daka masa ne yasa ya fasa karasa abunda yayi niyyar fada. Cikin bacin Rai Mummy tace, "Kanka daya kuwa? Gwaggon kake fadawa haka, wani irin rashin hankali ne wannan?" Gwaggo ce tace "Kyale shi Fatima idan bai ci mun mutunci ba ai bai isa ba". Sai kuma ta fashe da kuka tana murzar idanu da d'an kwalinta tana fadin "Yanzu D'an nan ni za ka yi wa cin mutunci a bainar jama'a? Ni ka wulakanta ka nunawa duniya ban isa da kai ba? Dan na hana ka bai kamata ka aure karuwa ba ko?" Muhdeen ne a hasale ya bude baki zai yi magana, Mummy ce ta dakatar dashi ta hanyar masa gargadi da idanunta. Shiru sukayi suna kallon Gwaggon, don inda sabo sun saba da Halin tsohuwar da rigimarta, shima Muhdeen din Abunda ya Kara 'bata masa rai shine kalmar karuwar da ta kira matar da zai aura dashi. Ita kanta Sumayya hawayen da ya cika mata ido ne ya samu nasarar zubowa, ranta ya baci matuka tsanar tsohuwar ce tab a cikin zuciyarta. Muhdeen ya je har gida ya dauko ta don tazo ta gaisar da kakarsa amma tazo gaida tsohuwar amma sakayyar da tayi mata kenan kalmar karuwa kawai take ta maimaitawa a cikin zuciyarta. Mikewa tayi aguje ta nufi kofar fita, Muhdeen ne ya bi bayanta yana kwala mata kira, "Sumayya! Sumayya!! Sumayya!!!" Amma Ina ko kallonsa batayi ba ta ta ci gaba da gudu dai-dai takai bakin gate ne tana kokarin fita ya samu nasarar rike hannunta, kokarin kwatar hannun tayi ta kasa, hakan yasa ta fashe masa da kuka tana fadin "Ka sake ni na tafi dama ka kawo ni nan ne dan a tozartani? kukanta ne ya tsananta, bai san lokacin da ya janyota jikinsa ya rungume ta yana d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi, Don ya rasa abunda zai ce. Dai-dai lokacin ne Gwaggo ta fito daga kofar falon tana fadin "ba dai bin ta yay... Turus ta tsaya ganin Muhdeen rungume da Sumayya. Salati ta saka tana tafa hannu cikin Al'ajabi tace "Inalillahi wa'inna ilaihir rajiun ni 'yar Sulaiman yau naga tashin hankali ganin ido na, lallai iskancin ku ya girma, rashin kunyar ku ta balaga, to wallahi ba a gidan d'ana zaku janyo masa masifa da bala'i da ransa ba, ban san yaushe Muhammadu ya lalace haka ba Amma zanyi maganin ka wannan yarinyar mai kai kamar na jemage ba matar aurenka ba ce". Muhdeen ya janye ta daga jikin sa ganin tayi shiru ta daina kukar sai hawaye dake bin idanunta, dama ita bata raina abun kuka, hannunta ya rike suka nufi wurin mota da kansa ya bude mata motar ta shiga, Shima ya zagaya ya shiga ya tayar da motar Malam Ibrahim dake kallonsu ne ya wangale masa gate din ya fice. Gwaggo dake sake da baki tana kallon ikon Allah tasa kai ta shiga falon yadda tabar su haka ta same su, zama tayi tana kallon Inteesar da tayi shiru tana tunani. Nuna ta Gwaggo tayi da yatsa tace "To ita wannan yarinyar da na gani wallahi na dauka ita ce matar da zai aura, saboda sun dace da juna sosai, wallahi it ace ta dace dashi ba waccan tambad'ad'd'ar karuwar ba. Mummy ce ta kalle ta tare da cewa, "Gwaggo wannan fa zargi kikeyi baki da masaniyar cewa karuwa ce, zato kike kuma kin san ance zato zunubi koda ya kasance gask..." Bata karasa ba Gwaggo ta nuna ta da yatsa tana fad'in "Ke Fatima a hir dinki ki fita a idona na runtse, idan ba karuwa ba wace ce ita? Ki nuna uban irin kayan da tasa gaba daya surar jikinta a bayyane suke wannan suturar dake jikinta marabar ta da babu kusan daya ne, hata kirjin ta kusan rabinsa waje suke, ga uban gashin dokin da aka kara mata kamar na sabuwar mahaukaciya ga wani kwalliya dake fuskarta kamar na aljannu". Mufida ce tayi dariya tare da cewa "Ke Gwaggo Ina kika taba ganin kwalliya Aljannu" Harara Gwaggo ta watsa mata tare da cewa, "Ke kiyi mani shiru ba dake na ke yi ba da uwarki gata nan zaune, da ita nake". Sannan ta ci gaba da magana tana cewa, "Yanzu na fahimta wato duk isakanci da suke aikatawa da daurin gindiki suke aikatawa, ni dai bazaku jawo wa dana masifa da bala'i yana zaman zamansa ba". Murmushin takaici tayi sannan tace, "To ni meye nawa a ciki me sukayi na daure masu gindi Gwaggo?" Jinjina kai Gwaggo tayi tare da cewa "Lallai ma zaki ce me sukayi? Yanxun ganin idona na gansu nike da juna kamar zasu shige jikin juna kafin yasa ta a mota suka fita. Allah ya dawo da ubansa wannan kama bata dace da matar da yakamata a aura ba" INTEESAR ce ta Mike tare da cewa, "Mummy bari na tafi dama aiki nakeyi nace bari nazo mu gaisa da Gwaggo". Gwaggo ce tayi saurin janyo hannunta tace "Allah sarki 'yar nan kin tafi bamu gaisa ba?" Durkusawa tayi cikin girmamawa da sanyin muryarta tace "Ina wuni?" Washe washe baki tayi kamar ba ita ta gama sababi ba, tace, "Lafiya kalau 'yar nan, ya kike?" "Alhamdulillah", Inteesar ta amsa Mata. Gwaggo tace "Masha Allah. ya sunan ki?" "Sunana Inteesar" Shiru Gwaggo tayi tare da cewa "Too wannan sunan naki da wahala wai isitas" "Ba Inteesar kadai ba hatta Mummy da Mufida sai da sukayi dariya, Mufida harda kwanciya. Sakin baki Gwaggo tayi tana kallonsu "To meye nayi na dariya da zaku tasa ni gaba daga nayi magana kamar mahaukaciya". Mufida ce tace "Gwaggo ba fa isitas aka ce ba Inteesar" Tabe baki Gwaggo tayi tace "Ni kam bazan iya ba" Daga nan Inteesar ta tafi gida. Gwaggo ta kalli mufida tace "Ita wannan yarinyar daga Ina take?" Mufida ce ta bata labarin Inteesar tun daga ranar da direban Mummy ya kade ta da mota har rana irin ta yau. A b'angaren Muhdeen da SUMAYYA kuwa suna cikin mota duk yadda yayi kokarin rarrashin ta kin sauraren shi tayi a haka har suka isa gida nan ma haka yayi ta bata hak'uri amma ina bata saurare shi ba, dole ya kyaleta idan ta sauka zuwa gobe zai dawo ko zata saurare shi. A can b'angaren Gwaggo kuwa Dady na dawowa ko ruwa bata bari yasha ba, ta Fara basa labarin irin abunda idanunta suka gane mata, ta kara da cewa "sai dai Muhdeen ya fasa Auren Sumayya". Dady ne ya numfasa yace "To Gwaggo meye hujjar ki da kike kiranta karuwa? kin ganta a wani wurin ne, ko kuma kallon da kikayi mata yasa kika gane cewa karuwar ce?" Gyara zamanta tayi akan kujera sannan tace, "Ahaf na nawa kuma? yarinyar da kayan jikinta kusan tsirara ne ko idonta a tsatstsaye alamun na rashin kunya da rashin sanin darajar mutane, da kake tamabaya ta ko na ganta a wani wurin ne to a cikin gidan ka suke badalar su ganin idona na gansu nanike da juna kamar zasu shige jikin juna, yadda na gansu Allah yasa naga annabin rahama, ko mai gadin gidan nan shaida ne, saboda haka ban yarda ka aurawa danka wannan yarinyar mai kama da busasshen crayfish ba". Shiru Abba yayi tare da ciro wayarsa number Muhdeen ya lalubo ya kirasa, bugu biyu ya daga. "Assalamu alaikum" Daddy yace "Wa'alaika Salam kana Ina ne?" Shiru Muhdeen yayi kafin yace "Ina hanya" "To idan ka iso ka sameni a falona". Daga nan ya katse kiran tare da aje wayar. Muhdeen ne jikinsa yayi sanyi don ya san tabbas wannan kiran bai rasa nasaba da Gwaggo. *KUYI HAK'URI DA WANNAN*🙏ÀFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. Page 11 _________Cikin sanyin jiki ya fito daga cikin motar kamar wanda aka zarewa lakka a jikinsa. Kai tsaye part din Dady ya nufa, inda ya tarar da Dadyn da Mummy da kuma Gwaggo, da sallama dauke a bakinsa ya shiga falon, Dady da Mummy ne kadai suka amsa masa sallamar ya yin da Gwaggo ta ta'be baki tare da cewa, "Ga iya sallama rangada sallama kamar na Allah, ya yin da Allah kadai yasan barnar da ta'asar da yake aikatawa a bayan idon al'umma, ka dai dinga jin tsoron Allah ana tunawa da mutuwa yara sai shegen jarabar tsiya". Harara ya gallawa Gwaggo tare da Jan tsuki Cikin daga murya Gwaggo tace, "Bani kayiwa ba uwarka kayiwa gata nan zaune". Ta karasa maganar tana nuna Mummy da yatsar ta manuniya. Ko kallon ta bai yi ba ya karasa gabansu ya zauna kan center carpet din falon, ya kalli Dady yace " Ina wuni Dady?" "Lapiya qalau" Ya amsa Sai ya kalli Mummy zai bud'e baki ya gaisheta kenan sai ta daga masa hannu alamun dakatarwa. Sunkuyar da k'ai kasa yayi yana jiran mai zasu ce masa yana fargabar abunda zai biyo baya, tunda Gwaggo tayi masa mugun fahimta kuma Don tun kafin ya bar gidan ya ji sallallami da kalamanta. Muryar Gwaggon ne ta katse sa daga tunanin da ya ke yi, "Kada Allah yasa ka gaisheni Mana, wadan da suka haifeka sun gaishe Ni d'an banza mai jajayen kunnuwa". Shi dai bai tanka Mata ba, saboda idan suna gaban Dady da Mummy bai cika kula ta har ya bata amsa ba. "Muhammad mai kake aikatawa ne haka? Wani irin labari naji Gwaggo Tana fada da yasa raina ya sosu, ahe kai mutumin banza ne ban sani ba eye?" Dago Kai yayi ya kalli mahaifin nasa ya Fara magana kamar haka "Amma Dady wallah..." Dakatar da shi Dady yayi ta hanyar daga masa hannu sannan yace, "Kai ma kasani Gwaggo ba za ta yi karya ba, idan har bata ganku ba ba za ta fada ba". Gwaggo tace "Da karyatani za ka yi? mutumin banza da idona na ganka manne da kuna ka rungume ta kana sumbatarta Amma zaka karyatani, to uwarka ka karyata bani ba". Muhdeen da ransa ya gama baci da abunda tsohuwar ke fada ya kalli Dady cikin rawar murya yace, "Dady Don Allah ka bani dama nayi magana kafin ka yanke hukuncin da zaka yanke. Zuba masa ido yayi na d'an lokaci, domin shi ma kansa yasan irin tarbiyar da su ka yi wa 'ya'yansu ba tarbiyar banza ba ne, sannan baya jin d'an nasa zai aikata kazamar dabi'a, ga gefe daya kuma ya san Gwaggo mahaifiyarsa ce ba za ta yi masa ƙarya ba, cikin sanyin murya yace, "Ina Jinka Muhammad Fadi abunda kake son fada", Muhdeen ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ba wa Dady labarin duk abunda ya faru tun daga kiran da Gwaggo tayi masa Yana office tace kar na dawo gida sai yazo Mata da matar da zai aura, da yadda ya d'auko ta da irin cin mutunci da Gwaggo tayi mata. Shiru yayi kafin ya cigaba da fadin, Kuma Dady wallahi tunda nake a rayuwata ban taba rike koda hannun wata mace wacce ba muharrama ta bace, ko ita Sumayya da Gwaggo take magana akan ta na rungume ta yanayi ne yasa haka, ganin irin kukan da takeyi na d'aukota har gida na kawo ta anci mata mutunci har da Mata kazafin karuwanci, gashi ranta ya 'baci ta fita tana kuka taki ta saurareni ne sai na d'an rungumeta da sigar Rarrashi kamar yadda kasan Ina rarrashin Asiya da Sumayya idan suna kuka ina son na rarrashesu to hakan ne ya faru tsakanina da ita, kuma maganar cewa na sumbaceta ba sumbatar ta nayi ba rarrashinta nakeyi ta hanyar fada mata kalamai masu sanyaya rai a cikin kunnenta, wallahi Abba ban taba sunbatarta ba". Shiru Abba yayi Don ya fahimci Dan nasa, cikin sanyin murya Abba yace "To shi ke nan naji Amma ka kiyaye kada makamancin wannan ya sake faruwa". Jinjina k'ai yayi tare da cewa "insha Allah" Mummy dai shiru tayi don bata da ta cewa. Dady ne ya kalli Gwaggo yace "to me kike son ayi yanzun?". Gyara dan kwalin ta tayi sannan tace, "Ni dai ban yarda ya auri wannan tambad'ad'd'yar yarinyar ba ehe, sai dai ya nemo 'yar mutunci yo wannan wace tarbiyya zata ba yaran da zasu Haifa? Don ko ita tana bukatar tarbiyya". Wani irin kallo Muhdeen yayi wa Gwaggo, ya bude baki da nufin zai maida mata martanin maganarta, Mummy ce ta yi masa kallo mai cike da gargadi hakan yasa yayi shiru ba tare da ya furta kalaman da yayi niyyar fada ba. Dady ne yayi ajiyar zuciya sannan ya kalli Gwaggo cikin girmamawa ya Fara magana "Yanzun haka Gwaggo idan kika ce fasa Auren nan bayan ni da Yaya Adam da Aminaina mu ka je har gidan iyayen yarinyar nan muka nema masa Aurenta, sun girmamamu da mutuntawa suna muna kallon dattako da kamala, suka dauki 'yarsu suka bawa d'anmu anyi komai an saka rana nan da watanni biyu masu zuwa sannan yanzun muje muce mun fasa aurawa d'anmu 'yarsu munyi masu adalci kenan?". Gwaggo dai ta'be baki tayi tare da cewa; "Uhum". Abba ne ya ya cigaba da maganar da ya ke yi; "To idan sun tambaye mu dalilin fasa Auren Mai zamuce masu?meye dalilin da yasa muka fasa?Babu hujjar da zamu basu, sannan yarinyar nan da kika Kira da sunan karuwa bakida hujjar kiranta da sunan Don baki ganta Tana karuwanci ba ko wajen da karuwai suke zuwa, sannan maganar rashin tarbiyya da kika fada bazaki tabbatar da hakan ba don baki zauna da ita ba, sannan Ana sanin mutum ta hanyar zama dashi da aiyukan da mutum yake aikatawa ba ta suturar da yake sakawa ba, ni dai Don Allah na roke Alfarma a wajenki da ki bari ayi bikin nan kada mu zama kananun mutane". Gwaggo tace "Shi ke nan tunda haka kace, daga kai har matar ka kun goyi bayansa ai shi ke nan tunda haka kuka gani duk abunda dan ku yake so shi kuke so idon ku ya rufe baku hango abunda nake hangowa a tattare da ita ba shi ke nan ai" Daga nan ta mike zata bar falon sai ta tsaya bakin kofar ta dawo ta kallesu tace; "Ba mugun baki nayi ba, amma ku sani akwai ranar da ku da kanku zaku tuna da cewar ni na hana auren saboda akwai abunda na hango, lokacin da zaku gano abunda na hango kuma lokacin kun riga kun makara aikin gama ya riga da ya gama amma lallai sai tazo, Muhammadu ka rubuta ka ajiye duk sai kun yi nadama". Abba ne ya budi baki yace "Gwaggo Don Allah ki daina fadin haka Addu'ar ki kadai muke bukata da Sanya alkhairi". "To shi ke nan ina maku addu'a kowa ne rana, biki kuma Allah ya sanya alkhairi". Tana gama fadar haka ta sa k'ai ta fice. Abba ne ya kalli Mummy da Muhdeen yace "Kada ku damu komai zai tafi dai-dai da yardar Allah". Mummy dai shiru tayi ta wuce b'angaren dama ba wai Tana son Auren Muhdeen da Sumayya ne ba, Amma ba yadda ta iya tunda ya nace ya ji ya gani ita ya ke so. Mikewa Muhdeen yayi jin ana kiran sallar magariba, Mummy ma mikewa tayi tabi bayansa ya yin da Dady ya nufi bedroom din sa Don doro Alwala ya nufi masallaci. Wata Rana bayan Inteesar ta gama yiwa umman ta aiki kamar yadda ta saba.sai ta shigar dakin ta ta kwanta bisa 'yar katifar ta Tana Jin alamun zazza'bi na damunta, wayarta ne tayi ringing ta duna taga sunan Mufida ce ke kira, daga wayar tayi tare da yin sallama. Mufida dake zaune akan kujera Gwaggo na tsaye akanta Tana Mata fadar cewa me yasa har yanzun Inteesar Bata zo ba kuma Bata Kira ta a waya ba? Ita wallahi bazata ci Abincin Mummy ba sai dai a Kira Inteesar tazo suyi girki. Jin Inteesar ta daga wayar ne yasa mufida cewa "Inteesar Don Allah ki zo ko wannan rigimammiyar zata Bari nasha ruwa". "Gaky Mufida gaskiya bazan samu zuwa yanzun ba don har na d'an kwanta anjima zan shigo" Sai ta d'an yi shiru sanin cewar idan har Bata tafi ba Gwaggo zata hana kowa sakat a gidan Nan idan Bata ga Inteesar ba. "Ko kuma kice mata gani nan zuwa yanzun nan insha Allah" Daga Nan ta katse kiran ta Mike tsaye tare da daukar wayarta da Hijab dinta, bayan saka Hijab din ta kai tsaye dakin mahaifiyarta nufa, zaune ta sameta bakin gado Tana ninke kayan wankin da Inteesar ta wanke mata.da sallama ta shiga dakin,Umma ta amsa Mata Tana sakin murmushi cikin son d'iyarta d'aya tilo da Allah ya Bata. "Umma dama zan je gidansu Mufida ne, Gwaggo ce take son wai na je muyi girki tare" Jinjina Kai Ummu tayi "To ke da kika ce bakida lafiya kina jin ciwon k'ai da zazza'bi? tunda kin sha magani kamata yayi ki kwanta ki sanar dasu baki Jin dadi" Ta karasa maganar Tana tausayin 'yarta. Murmushin karfin hali tayi tare da cewa, "Umma baki San Halin Tsohuwar Nan ba wallahi idan ban je ba zata addabe su ne musamman Mufida" "To shi ke nan Allah ya baki lafiya ki gaishesu" "To za su ji" Daga nan ta fice ta nufi gidansu Mufida lokaci zuwa lokaci takan zubar da yawu a bakin ta kamar wata mai ciki, dama haka zazza'bin ta yake saboda bakinta ba taste bata iya had'iyar yawu. Tana isa bakin kofar gidan ta gaida Mallam Ibrahim Mai gadi, sannan ta nufi cikin gidan dai-dai lokacin da ta karasa kan barandan kafin ta shiga falon sai ta juya ta zubar da yuwun bakin ta, kwatsam ta ji ance "keee!" da sauri ta waiga ganin Muhdeen zaune akan kujera Yana kallon yawun da ta watsa masa a Riga.l, cikin kad'uwa ta zaro ido Tana kallonsa kafin ta ankare ya sauke Mata tagwayen maruka biyu, cikin azaba ta kwalla kara wanda ya ja hankalin jama'ar gidan.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne,ban Rubuta shi Dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba .Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. Page1️⃣2️⃣ Cikin azaba ta kwalla Kara Wanda yaja hankalin jama'ar gidan.Mallam Ibrahim Mai gadi da yunusa Mai bawa fulawa ruwa da sauran ma'aikatan gidan cirko-cirko sukayi suna kallon ikon Allah. yayinda Inteesar ke durkushe dade da kuncin ta Muhdeen kuwa na tsaye akanta Yana huci, dai-dai lokacin Mummy da Mufida da Gwaggo suka karaso wajen,ganin Inteesar durkushe Tana kuka yasa Mummy cikin sauri ta karasa tare da mikar da ita tsaye,ganin sawun kumatunta sunyi jajir ga sawun yatsu biyar da Muhdeen ya Mata ne yasa hankain tashi cikin tsananin bacin Rai Mummy ta Fara magana. "Yanzun son Kaine ka daga hannayen ka akan fuskar yarinyar Nan ka mare ta akan meye? Yarinyar da ba ruwan ta Mai gudun 'bacin ran mutane zaka mare ta?" Yana huci ya Fara magana "Mummy baki ga abunda tayi Mani bane,yawun bakin ta ta watsa Mani a jikin Ka..." Kafin ya Karasa maganar sa ne Gwaggo tayi saurin cewa, "To shugaban mugaye na Duniya sai me idan ta watsa maka yuwun bakin ta?ko yawun najasa ne da zaka kama 'yar mutane daga zuwan ta ka Fara dukan ta kamar Allah ya Aiko ka mugu kawai Mai bakar zuciya akan yawu zaka kama 'yar mutane zaka illata.wannan irin mari ai sai ka kurmantawa mutane 'ya ta zama musaka. Gwaggo ne ta janyo Inteesar daga jikin Mummy ta rungume ta a jikin ta Tana Dan bubbuga bayan ta.Hatta Mufida sai da taji kamar zatayi kuka ganin yanda fuskar Inteesar din ta canja. Gwaggo ta dago fuskar ta tare da janyo ta suka nufi kofar falo suna tafiya Tana fadin, "Kiyi Hakuri kinji yarinyar arziki wannan muguntar da ya maki Allah zai bi maki hakkin ki akan sa, Mufida ce tabi bayan su daga Mummy sai Muhdeen a wajen,zuba masa ido tayi tace," "Gsky son ka 'bata Mani Rai sosai akan wannan Hukuncin da ka yanke akan Inteesar ta watsa maka Miyau haba Hukuncin naka yayi tsauri da yawa Don yarinyar Nan bazata ta'ba watsa maka yuwun bakin ta da sanin ta ba na tabbatar Bata lura dakai bane.yanzu idan Asiya ko Mufida ne suka watsa maka yuwun bakin su a bisa kuskure Hukuncin da zaka dauka kenan akan su?" Girgiza Kai yayi Yana fadin, To Mummy so fa jini na ne ta Yaya Zaki hada su day wannan kucak..." Tsawar da ta daka masa ne yasa yayi shiru. "Kai! Kai ka fita a idanuna na fada mak,Yadda na dauki Inteesar haka na dauki Asiya da Mufida bana nuna masu Banbanci,haka ma mahaifin KU ya dauke ta komai tare yake masu sai abunda baza'a rasa ba,Hatta Mufida irin shakuwar da sukayi da Inteesar basuyi shi da 'yar uwar ta Asiya ba.kaima haka nake so daga gare ka ka dauke ta kamar kanwa CE a gare ka" Daga Nan tasa Kai ta shige falon Shima bayan ta yabi . Gwaggo na zaune akan kujera ta daura Kan Inteesar akan cinyar ta, mufida na zaune tayi tagumi ta zubawa Inteesar ido ganin yanda sawun yatsun yayan nata akan fuskar Inteesar gefen dama da hagu sunyi jajir. Mummy ta nufi dakin ta Muhdeen ma part din sa ya nufa nufa yayin da Gwaggo tabisa da harara Tana cewa, "Gaka fari Amma zuciyar ka bakakirin Ga kyawun sura Amma ba kyawun Halayya" Baibi ta kanta ba ya nufi dakin sa ransa a bace.mummy ce ta karaso falon Hannunta dauke da magani fridge ta nufa ta dauko robar ruwa ta zauna ta balle maganin ba bawa Inteesar tare da Goran ruwa,ba musu ta karba ta hadiye.Ba jimawa bacci ya dauke ta ganin haka yasa mummy tace ma Asiya ta biyo ta kitchen suyi aikin tare.bayan tadiyar su ne Gwaggo ta nufi dakin ta Tana cewa, "Dan bakin ciki yarinya tazo tayi Mani girkin ta Mai dadi ya Hana ta da muguntar sa" Muhdeen Yana shiga dakin sa you nufi toilet dinsa kayan ya cire yayi wanka da sabulu Mai kamshi da turaren wanka,ya shirya cikin kananun Kaya jar Riga da bakin wando,Kai tsaye yabar part din sa ya nufi falon ba kowa sai Inteesar dake bacci,Goran ruwa ya bude ya Dan yayyafa Mata ruwa a fuska,a firgice ta farka zatayi masa kuka Dan tsoron sa take ji,daura yatsar sa yayi a bakin sa alamun tayi shiru. "Shhhshhh" Hannayen ta ta saka ta toshe bakin ta Tana kokarin hadiye kukan,sannan yace, "Ki biyoni daki na" Da sauri ta Ware dara-daran idanun ta Tana kallonsa cikin tsoro da mamaki Tana girgiza masa Kai,daure fuska yayi ba Alamar rahama,da hannu yayi Mata nuni da ta biyo shi. Haka ta Mike ba musu Tana gaba Yana binta a baya har suka karasa part din sa cogewa tayi a bakin kofar dakin Tana tsoron shiga sanin cewa ba kowa a dakin kuma Ummanta ta Hana ta ke'bewa tare da namijin da ba muharramin ta ba. Ganin Bata da niyyar shiga ya watsa Mata harara tare da cewa, "Ba Zaki shiga ba?" Kai ta girgiza cikin rawar murya tace, "Ummana ta hanani ke'bewa da namiji mu biyu idan ba kowa" Dariyar raining hankali yayi Mata yana Kare Mata kallo yace , "Dalla shiga uban me zanyi dake ko ina neman Mata bazan bazan taba iya hada jiki da kucaka irin ki ba ke har kinkai macen da Zan kalla naji wani Abu akan ki?" Tsaki yaja sannan yace, "Shiga muje" Ba musu tabi bayan sa har toilet suka shiga,kayan da ya cire Wanda ta watsawa Miyau ya nuna Mata yace, Kindan kudin shaddar Nan da kika 'bata kuwa?kinsan nawa na siye ta?kinsan anko mukayi nida Mai sumy kuwa?kinsan yau ne na Fara saka ta da niyar zuwa wurin masoyiya ta kuwa?kinsan zamuje yawan sha'katawa zamuje muyi photo da kayan Nan kuwa?" Cikin rawar murya tace , "Kayi hakuri" Tabe baki yayi Yana cewa, "Wannan kayan sun fita a Raina bazan iya saka su ba,yunusa Mai bawa fulawa ruwa zanba su,yanzun ki Duka ki wanke su tas ki fita ki shanya su a Rana,kiyi gadin su sai sun bushe kafin kizo ki goge sau" *YAWAN COMMENT DIN KU YAWAN READ MORE*🤷‍♀️Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Wannan kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to kuyi Hakuri bada niyyar yin Hakan nayi ba, arashi ne Mai kashe Auren Wawa. Page 1️⃣3️⃣ "Yanzun ki d'auki kayan nan ki je ki wanke su tas ki fita kije ki shanya su a rana, kiyi gadin su sai sun bushe karin kizo ki goge su" Karasawa tayi gaban washing machine Don dake cikin tangamemen Toilet din, ganin hakan yasa shi dakatar da ita cikin tsawa ya ce, "Keee" Da sauri ta juyo ta kalleshi, "Ina kike kokarin zuwa? Hannun ki zaki sa ki wanke su ba warshing machine za ki yi amfani dashi ba" Yana kallon ta har ta gama wanke kayan da ba datti ne dasu ba,ta d'auraye kumfar sabulun ta fito, ganinan zata bi ta hanyar babban falon gidan ya dakatar da ita. ya nuna wata kofar da bata san da ita ba,koface wacce take cikin part din sa wanda idan kabi direct zai sadaka da garden din gidan.cikin bada umarni ya ce, "Idan kika shanya kayan a garden din ki jira su bushe kafin ki kawo su ki goge su, sannan wannan kofar da kika gani ita zakibi ki dawo" Yana gama fad'ar haka ya koma ciki, direct babban falo ya nufa zaman sa keda wuya sai ga Gwaggo ta karaso falon, ganin babu Inteesar yasa ta Fara waige-waigen neman ta ganin Bata Nan yasa ta Harare shi tare da fadin "Kai ina Inteesar take ne? Nan na barta ita kadai?" Ko kallon ta bai yi ba ya cigaba da danna wayarsa. Cikin daga murya ta ce, "Tambayar ka nake, ina yarinyar da kaci zalinta take?" Still shiru ya mata kamar bai ji ta ba don dama akufule yake da ita yadda a gaban Inteesar ta dinga zagin say Wai salon ta Raina shi, a hasale ta sake tamayarsa a karo na uku sannan ya ce, "Ajiyar ta kika bani ko zaman gadinta na ke yi?" A hasale ta ce, "Haka kace ko?yanzun tsabar balagar rashin kunyar taka takai ka kalli tsabar ido na ka fada mani haka?" Ina mahaifiyar Uban ka? Nina haifi wanda yayi sanadiyar zuwan ka duniya da har ya d'an banza Mai suffar sadaka yalla, dama ance wanda kafi so shi yafi kuntata maka, duk cikin jikokina nafi kaunar ka da son ka Amma kafi kuntatamani da bakanta mani rai. Tunda kace ban Isa ba to bari na Kira mahaifiyar ka ai ita na isa da ita" Daga murya tayi Tana kwalawa Mummy kira "Fatima! Fatima!! Fatima!!!" Da sauri Mummy ta fito daga kitchen d'in da sauri jin yadda Gwaggo ki kwala mata kira tasan ba na lapiya bane,bayan ta karaso ta kalle ta cikin girmamawa ta ce, "Gwaggo lafiya kuwa?" Kallaon ta Gwaggo tayi ta ce, "Ina fa lafiya banga baiwar Allah da nasa aka kirata tun daga gidansu tazo wannan bakin mugun yayi mata dukan kawo ruwa, nan ba barta wance" Ta nuna kujera mai zaman mutum uku "Shine yanzun na dawo ban ganta ba, ina tambaye sa Ina take yana fada mani maganar banza, amma yanzun tunda ke uwarsa ce zai fada maki" Kallonsa Mummy tayi na dan lokaci tana karantar yanayinsa ta ce, "Son ina yarinyar nan take?" Kallon ta yayi cikin kwabe fuska ya ce, "Mummy nima yanzun na fito daga d'aki banga kowa anan ba, wata kila ta shiga dakin Mufida ta kwanta" Mummy ta kalli hijabin Inteesar tare da wayarta akan kujera yasa ta kalli Gwaggo ta ce, "Kin ga Hijabin Inteesar da wayarta ba inda taje ina ganin ta shiga ta kwanta ne" K'ai Gwaggo ta gyada ya yin da Mummy ta koma cikin kitchen d'in, Gwaggo ta ci je lebe tare da ce wa, "Wayyo ciwon kafata ta soma yi mun ciwo" Ta karasa maganar da 'kyar ta zauna Kan kujera tana kallon Muhdeen da kallo daya ya Mata ya dauke kansa ta ce, "To yauwa d'an albarka dama magunguna na sun Kare ka taimakawa tsohuwar nan mana" Kamar bai ji ta ba haka yayi mata shiru "Magana nake maka shalele na" Dariya ce taso kufce masa amma sai ya dake tare da cewa, "To waye kuma shalelen naki a yau?" "Kai mana d'an Albarka likita bokan turai, ai ba ni da shalele bayan kai" Murmushi yayi "Ada ne nake shalelen ki, amma yanzun bani ba ne waccen yarinyar mai kama da Aljana ita ce shalelen ki yanzun, don na lura zaki iya batawa dani in dai akanta ne" Ya Karasa maganar ba tare da ya kalle ta ba, rike baki Gwaggo tayi tare da ce wa, "Waya fada maka ba kaine shalele na ba? Ka ta'ba ganin inda aka canzawa tuwo suna?" Dariyar raining wayo yayi mata sannan ya ce, "Ana ki canzawa tuwo suna sai dai idan bai kwana ba, amma idan ya kwana ya zama d'umame" Gwaggo ta kalle shi "Shalele na ka manta cewa da tsohuwar zuma ake magani?" Murmushi yayi tare da ce wa, "Sanin da ki ka yi na cewa da tsohuwar zuma ake magani Amma yanzun anayi da sabuwa Dan neman karin sinadari" Kallon mamaki tayi masa "Wai kai komai aka fada maka sai ka samu amsar maidawa? to naji don Allah ka kawo mani irin magungunan da saka aika mani dasu nasa da na shafawa" "Babu wani maganin da zan baki wannan karon allaura za ni yi maki" Kallonsa tayi da sauri ta ce, "Ai me za ka yi mani?" Mi'kewa yayi tare da bar mata falon. Bangaren Inteesar kuwa tana nan zaune ta tasa kayan a gaba tana jiran bushewar su, kasancewar akwai Rana har sun kusa bushewa, magana takeyi a fili. "Insha Allah na bar masa gidansu kenan, lokaci yayi da zan nisance su tunda har tsanar da yayi Mani yakai haka, dama dole tasa nake zuwa gidan su bawai son kaina ba ne, mahaifiyarsa ce take sani zuwa sshe lokacin da mahaifiyar sa taje ta samu Umma da maganar cewa na dawo gidanta gaba d'aya da zama Umma da Abba suka Hana Ashe da sun amince da na kad'e a hannun sa in banda su da suke matsa Mani aiba killin zan zo ba, ko ban zo ba zasu kirani a waya ne wai dan Allah nazo wata Rana Mufida ce zata zo tace wai Mummy tace nazo.amma yanzun duk abunda zai faru ya faru ya faru zan dauke kafa ta a gidan nan, ki zuwa school din da nake shiryawa da wuri na biyowa Mufida zan daina shiryawa da wuri ne har sai na tabbatar sun bar gida sannan na fito mu had'u a hanya, duk da cewar Mummy, Dady, Gwaggo, ga kuma Mufida da muka shaku ba za su so hakan da zanyi ba Amma shine mafita a gareni.Yaya Muhdeen kayi hakuri na kusa bar maka gidan ka zuba ruwa kasa kasha, mugu a gaban mutane baya nunamin hantara da kyara Amma da zaran ba idon kuwa kare ma narishi daraja a idonsa" Tana ta magana ita ka dai kamar tanayi da wani ga zazabi naso rufe ta ga azababben ciwon Kai da yasa ta gaba,Tana Nan zaune kayan suka bushe ta kwaso su tabi ta yanda ta fito,har Bedroom din sa ta wuce ta fara goge kayan. Can fall kuwa bayan angama girki Anjera a Dinning table kowa ya hallara Mummy, Muhdeen da Gwaggo ya yin da Dady ne kadai baya nan.Mufida ce ta fito cikin tashin hankali tana fadin "Mummy gaba daya na duba ko Ina banga Inteesar ba Ina ta shiga?" Dai-dai lokacin Inteesar ta fito daga part din Muhdeen dafe da kanta, jin alamar tohuwar mutum yasa suka waiga dukkan su sauka zuba mata ido suna kallonta da mamaki, ya yin da Mummy tayi saurin mikewa ta rike hannunta cikin mamaki tace, "Daga ina kika fito?Mai ya kaiki part d'in son?" Mummy ta kara rungume ta tana fad'in "Subhanallahi jiki yayi zafi, zazza'bi ne ya rufe ta" Janyo hannunta tayi suka karasa dinning room dinta zaunar da ita kan kujerar dake kusa da ita.Ba yadda Mummy batayi ba akan Inteesar taci abinci taki da kyar tasha lemon da Mummy ta tsiyaya mata a cup, Mummy ta kalli Muhdeen ta ce, "Son" D'agowa yayi ya kalleta tare da cewa, "Na'am" "Ka d'auko kayan aikin ka sannan ka dauki Inteesar a motarka ka kaita gida kayi Mata treatment din da ya dace kafin ka dawo,sannan kafin KU nufi gidan su ka biya ka siye mata fruit saboda bata ci abinci ba" Cikin bada umarni tayi maganar, kallonta yayi ganin yanayin fuskar ta ba sauki yasa yace, "To Mummy yadda kika ce haka za'a yi" Kallonta ta maida ga Inteesar ta ce, "Inteesar ga yayanki zai kaiki gida yayi maki abunda ya dace kafin nima na zo" Kai Inteesar ta gyada ba ya yin da gabanta ya ci gaba da fad'uwa.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Wannan kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi Dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM* Page1️⃣4️⃣ Kai Inteesar ta gyd'a yayin da gabanta gaba da fad'uwa. "Uhm wannan marukan da tasha ba dole tayi rashin lapiya ba? Yanzun haka ba Wanda ya ta'ba Mata wannan Marin,ko uwar ta ubanta nasan bazasu yiwa wannan nitsatsiyar yarinya Marin nan ba Amma Rana tsaka wani katon banza ya more ta." Gwaggo ce tayi maganar yayin da karasa bayan Inteesar Tana shafa kyakkywar fuskar Inteesar. Muhdeen ko kallonta baiyi ba yayinda ya Mike ya nafi part dinsa fuskar Nan a muturke.Mufida ce to janyo hannun Inteesar tare da cewa, "Muje na rakaki mota,idan na dawo daga gidan Yaya Jabeer matar sa Bata da lapiya ne zamuje da Mummy mu gaishe ta,idan muka dawo zan biyo gidan naku Allah ya baki lapiya" Inteesar tace , "Ameen " yayin da suka nufi hanyar fita,Kai tsaye parking lot suka nufa Inda Mufida ta bude Mata murfin gidan gabar motar.kai Inteesar ta girgiza tare da cewa, "Baya zan zauna" Ba musu Mufida ta bude Mata bayan motar ta ahiga,zamanta keda wuya sai ga shi Shima ya karaso hannun sa rike da akwatin magunguna,murfin motar ya bude yashiga ganin Bata gefen sa yasa Kai idon sa baya,ganin ta dukunkune yasa yace Mata. "Niba direbanki bane ki tashi ki dawo gaba" Mufida ce tace "Ya Ina ga kamar zatafi yin Balanced a baya tunda nac... " Had'iye sauran maganar tayi ganin irin kallon da yake Mata ne yasa tayi shiru.bude bayan motar tayi ta kama hannun Inteesar Dan ta taimaka ta fito,a hankali ta fito da taimakon Mufida Dan har jiri take ji Yana neman dauke ta.Bayan ta zauna gaban motar ne ya figi motar suka bar gidan. Sai da ya biya ya siye Mata fruits kamar yadda umma ta Umarce shi.Tundaga Kan lemo,kankana,Apple, Abarba inibi da ayaba sannan ya kama hanyar gidan su Inteesar din kasancewar yasan gidan ya ta'ba Kai Mummy. Dai-dai lokacin da ya Isa kofar gidan ya juya ya kalli Inteesar,ganin idon ta a lumshe kamar Mai bacci.Dai -dai lokacin ne kuma Kira Sumayya ya shigo wayar Video call ne.daga Kiran yayi ganinta sanye da shaddar da suka shirya sawa sunyi anko su tafi uawan shakatawa.lumshe kyawawan idanun sa yayi tare da bude su yace, "Mai Baby kinyi kyau sosai" Murmushi tayi tare da cewa, "Thanks Amma ya bangan ka da naka a jikin Ka ba?kayi lettin zuwa waje na yakamata ace minti talatin da suka wuce ka iso Amma shiru" Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, "Ki bani minti talatin zan karaso yanzun Nan insha Allah" Turn baki tayi sannan tace, "Kana Ina ne yanzun?" "Ina kofar gidan su Inteesar" Rasss Gaban ta ya dadi tace, "Wace Inteesar" Saita secreen din wayar yayi dai dai yanda Inteesar ke zaune gefen sa idonta alumshe. Take Sumayya Gaban Sumayya ya Fadi ganin Inteesar a cikin motar Muhdeen yayin da ita Tana can Tana jiran sa Amma shi Yana can wurin wannan yarinyar. Take taji wasu zafafan Hawayen kishi suna kwaranya a idanun ta muryar kuka tace, "Nagode da abunda kayi Mani " Tana kokarin kashe wayar ne yayi saurin cewa, "Kinga dakata ki saurare Ni nayi maki bayanin abunda ya daru" "Want bayanin zakayi Mani?cewa Inteesar tafi Ni mahimmanci a wirin ka ne da yasa ka shanyani kusan awa d'aya Ina jiranka yayin da Kai kake can wajenta" "Kinga ki tsaya nayi maki bayanin yadda akayi" Kara fashewa tayi da kuka,Don dama Tana da zafin kishi Bata tsaya sauraren sa ba ta katse kiran. Juyawa yayi ya kalli Inteesar da ta lumshe ido kamar Mai bacci yayinda duk Tana Jin maganar da suke. "Fita" Ya fada Mata a takaice,yayin da Shima ya fito ya rufe marfin motar.da'kyar ta iya bude marfin motar ta fito jiri ne ya d'ebe ta tayi luuu zata fad'i. a guje Muhdeen ya Karasa gare ta ya tare ta ta fad'a jikin sa. Cikin wata iriyar kasalar da ta dorar masa lokaci guda yace, "Kiyi a hankali" Same jikinta tayi ta jingina da motar saboda ganin takeyi komai na jujjuya Mata. Karasawa yayi bakin kofar gidan tare da yin sallama,Yana Nan tsaye Umma ta fito sanye da Hijab.zubawa kyakkywan saurayin Mai kwarjini da haiba ido, Muhdeen kyautatawa ne ajin farko dogo ne fari fuskar sa zagaye da kwantaccen saje da yayi luf a fuskar sa Gashin kansa ma haka yake kamar ba na bakin fata ba ga madaidaitan idanun sa Mai masu kyau da kwarjini. Durkusawa yayi cikin girmamawa ya gaida Umma. "Ina wuni Umma?" "Lapiya qalau" Ta amsa masa cikin sakin fuska 'Dan Jim yayi Don ya gane cewa Umma Bata sanshiba yasa yace, "Dama Inteesar ce bataji dad'i ba shine Mummy tace na na kawo ta nayi treating d'inta kafin su karaso" Jin haka yasa Umma ta fahimci cewa shine Muhdeen din da ake fadi.nuna mata Inteesar da ta jingina da jikin motar yayi tare da cewa, "Umma jiri takeji shiyasa nayi sallama Don azo a taimaka Mata" Da sauri Umma ta karasa ta tallabota tare da had'a ta da jikin ta suka nufi cikin gidan. Acikin d'akin Inteesar din ta kaita yayin da ta koma tare da bawa Muhdeen izinin shigowa.Har dakin tayi masa jagora hannun sa dauke da akwatin magunguna sai ledar fruit din da ya siya Mata. Tana kwance akan katifar ta ya kalle ta tare da cewa "Tashi zaune Kisha fruits din kafin nayi maki allura ,Kinga ba komai a cikinki da kikaci" Shiru tayi masa tare da tura baki Tana kunkuni .Umma CE to daka Mata tsawa Tana fadin "Wai lapiyar ki Yana maki magana kinyi banza dashi ba taimakon ki zaiyi ba" Hawaye ne ya cika Mata ido tace, "Umaa kiyi hakuri indai taimako ne daga wurin say bana bukata ya tashi kawai ya tafi" Umma shiru tayi ta zuba Mata idanu Don ita a tunanin ta allura ce bata so shiyasa take fad'in hakan. Sake magana yayi a karo na biyu yace, "Dakin daure kinci wani abun ko kadan ne* Cikin tsiwar da Bata San Tana da ita ba ta Fara magana Tana fad'in "Dalla mallam ka tashi ka dauki tarkacen ka bana bukatr ganin ka a rayuwa ta,ko a hanya bana fatan sake had'uwa da Kai.Kuma gidan KU bazan sake zuwa ba idan kaga kafata duk wulakancin da kaga dama kayi Mani Ni na jawowa kaina " Shiru yayi ya zuba Mata ido Yana mamakin yadda har ta iya bud'e baki tayi masa magana gatsai haka... Bai karasa tunani da yakeyi ba ya sake Jin murayar ta Tana cewa. "Ka tashi ka fita bana kaunar ganin ka a rayuwa ta,na tsane ka irin tsanar da ba ta'ba yiwa 'Dan Adam shi ba.Ba zaka sake gani na a gidan KU ba ballantana..." Bata Kai aya ba taji Umma ta daka Mata tsawa Wanda yasa Inteesar fashewa da kuka Tana fad'in " Umma Don Allah ya fita wlh idan na kalleshi zuciyata tafasa takeyi" Numfashi taja alamun maganar ma karfin hali ne,sannan tace, "Da ace Kaine likitan da zakayi Mani treatment na samu lapiya gara nayi ta zama da ciwo" Ledan fruits din da ya siyo ta dauko ta watsa masa su a jikin sa.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Wannan kagaggen labari ne ban Rubuta shi Dan cin zarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba Arashi ne Mai kashe Auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM* Page1️⃣5️⃣ Ledan fruits d'in da ya siyo ta d'auko ta watsa masa su a jikin sa. Umma da ranta ya gama 'baci ne ta fita waje,ba jimawa sai gata ta shigo da zabgegiyar bulala,ta nufi Inteesar da niyyar za ga Mata bulalar Amma cikin zafin nama Muhdeen ya shiga tsakani Yana ba wa Ummi hak'uri. "Ka bar ni da ita yanzun nan taji a jikin ta" Girgiza Kai Muhdeen yayi tare da cewa "Kiyi Ha'kuri Umma zafin ciwo ne yasa haka" "Ba wani zafin ciwo da zai sa ta haka?Bata cikin hayyacin ta ne?ka daina kokarin Kare ta " Ta karasa maganar Tana jifa da bulalar ta fita d'akin ranta a 'bace,Don Bata taba tsammanin Inteesar za ta yi abunda tayi a yanzun ba. Bayan fitar Ummin ne ya juyo ya kalle Inteesar cikin 'bacin Rai ya soma magana. "Wace ce ke?me kike dashi ?me kike ta'kama dashi? Kyawu? Ilimi? Daraja?Dukiya ?ko me?" Haka ya jera Mata wad'annan tambayoyin,ita Kam ko kallon sa ba ta yi ba zuciyar ta cike da fargabar hukuncin da zata d'auka akanta,Don rabon da ta ga irin wannan 'bacin ran a wurin Ummi har ta manta. Muryar Muhdeen ce ta ji Yana cewa, "Kalle ni da kyau ni Muhammad Muhdeen na fi karfin wulakanci wallahi,ke har kin Isa ki wulakantani ?ban da yi wa mahaifiya biyayya da ta umarceni nazo nan meye zai kawo ni wajenki. Wallahi kinci arzikin Mai daraja da na baki mamaki wallahi. Bai sake magana ba Fara had'a Alluran da zai Mata yayi,Tana ganin haka ta Fara kuka ita wallahi Ba ta son Allura magani take so, dariyar mugunta yayi tare da cewa, "Yauwa na ji dad'in sanin haka kasancewar kina masifar tsoron Allura ,da haka zan yi maganin ki" Fashewa tayi da kuka Don A Rayuwarta Tana masifar Jin tsoron Allura fiye da komai,cikin muryar kuka da tsoro tace, "Yaya Don Allah ka yi hakuri wallahi bana son kayi Mani Alluran Nan Don mutuwa zanyi kuma nikad'aice Umma na ta Haifa ka tausayawa Umma na kada ta rasa 'yar ta gudaliya" Dariya ce ta so su'buce masa Amma sai ya Danne yace, 'karamar mara kunya ba Ni kika gamawa yiwa wula'kancin da Tunda nake a rayuwa ta Ba'a ta'ba yi Mani kwatankwacin sa ba,Don Haka dole na hukunta ki" Fashewa tayi da kuka sosai Tana ihun Kiran Umma "Umma ki zo za'a kashe maki 'yarki guda d'aya da Allah ya baki,Umma na kizo wallahi fansa yake da niyyar dauka akaina,Umma kinsan bana son Allura ballanta shi da biyu zaiyi Mani Alluran Nan" Bai kalle ta ba ya ci gaba da abunda yake yi saida ya gama sannan ya kalle ta yace, "Ki d'aga rigar ki sama" Cikin muryar kuka tace, "Wallahi bazan d'aga ba tunda baka da imani" Tana fad'ar haka ta Mike cikin rashin 'karfin jiki ha jire dake d'ibarta ta nufi hanyar fita daga d'akin cikin jirin dake d'ibarta tayi luu zata fad'i Don ganin duhu takeyi,cikin zafin nama ya Karasa ya ri'keta da hannu d'aya,yayin da d'aya hannun yayi amfani dashi wajen soka Mata allurar ba tare ya d'aga rigar ba, yayi Mata Allurar.Gigitaccen Kara ta saki tare da sakar masa jiki taci gaba da ihu Tana Kiran Umma a haka ya yi Mata allurai biyu sannan ta kwanta Tana kuka kamar 'karamar yarinya son Sai ta ji zafin Alluran na daban ne,yasha Bambam da Wanda ta Saba ji.nan ya ajiye Mata magunguna ya Rubuta yadda za ta yi amfani dashi ya tattara kayan say ya fito daga d'akin,a tsakar gida ya samu Umma yayi Mata sallama tare da shaida mata gobe zai dawo.Bayan fitarsa Umma ta shiga ta samu Inteesar inda tayi Mata fad'a sosai akan abunda ta yi wa muhdeen,ita dai shiru tayi tare da bawa Umma hak'uri,fad'a ya sake Mata tare da nuna Mata cewa wannan mummunar d'abi'ar Bata son shi, Inteesar din kuwa hakuri kawai take bawa Umma tare Mata al'kawarin ba za ta sake ba. Lalla'bata umma tayi ta d'aci Abinci kad'a kafin ta kwanta. Muhdeen kuwa Koda ya 'karasa gida Bai samu sun Umma ba sun tafi gidan jabeer gaida matarsa Maryam da tayi rashin lafiya. Wanka yayi ya canza Kaya cikin hanzari ya nufi gidan su Sumayya,Bayan yayi horn Mai gadi ya bud'e masa ne ya shige cikin gidan, Yana zaune a motarsa ya Kira layin Sumayya Yana ta ringing Bata d'aga ba. Sumayya kuwa Tana zaune a d'akin ta da tayi kaca-kaca dashi ta hargitsa sa gashin attached din da akayi Mata Kari ta barbaza shi kamar mahaukaciya sintiri takeyi a d'akin Tana ta suratai ita kad'ai,duk abunda ya tari gaban ta sai tayi jifa dashi gaba d'aya ta yay bedsheet din gadon tayi jifa dashi pillows din ma gaba d'aya tayi watsi dasu a cikin d'akin kayan makeup dinta duk tayi watsi dasu da turarruka,wad'anda suke cikin kwalabe kuwa duk sun farfashe suk abunda tayi tozali dashi sai ta hargitsa sa,hatta sidedrawer sai da ta d'auke sa tayi jifa dashi, Dama ita haka take tun Tana yarinya Iyayenta basa tsawatar Mata sai abunda taga dama take yi basu Hana ta.indai ranta yayi masifar 'baci to duk abunda ya tari gabnta sai taga bayansa,hatta T.v dake kunne Yana aiki Tana kallon wani series a tashar zee word idon ta na sauka Kan T.V ta d'auki 'karfen da handbags dinta suke rataye gadan-gadan ta nufi wurin karfen Bayan ta dauki 'karfen Kai tsaye plasma T.Vn ta nufa ta Fara kwalawa T.V 'karfen har sai da taga seecreen d'in T.V ya ragargaje idonta ne suka sauka Kan dressing mirror jifa tayi da 'karfen ta nufi gaban mirror Hannunta tasa ta naushi mirror d'in take ya ragargaje Hannunta sai zubar da jini yake. Mum d'inta dake ta bubbuga kofar Tana ro'konta ta bud'e dakin kada ta ji wa kanta ciwo Amma Ina Bata ma San tana yi ba,gashi Dad d'inta baya Nan ya tafi kasar Dubai,gaba d'aya mum hankalinta yakai 'kololuwar tashi gashi key din d'akin Sumayyar na jikin kofa ta cikin ballantana ta Nemo spare key ta bud'e Muhdeen da ke cikin mota ya gaji da Kiran layin Sumayya Yana ta ringing Bata d'auka ba,dama wayar na falo ta bar shi lokacin da ta kirashi video call ta gansa tare Inteesar cikin motarsa a guje ta shige d'akin Tana kuka ta saka key karar fashe -fashe ne yasa Iya Ggaje Mai Mata gyaran d'aki ta nufi d'akin Mum ta sanar da ita cikin tashin hankali Mum ta karaso taji 'kofar a datse duk da sai an 'bata Mata Rai sosai take haka,Mum ta rasa gane meye ya Bata Mata Rai haka, Idonta ne ya sauka Kan wayar Sumayya dake kawo haske alamun kira,karasawa tayi tare da d'aukar wayar tana subawa ganin Maaoyin 'yarta ne yasa ta d'aga tare da cewa, "Hello" Muhdeen Jin muryar Mum yasa yiyi saurin gaishe ta. "Ina Wuni Mum" Ajiyar zuciya ta sauke karin ta amsa masa "Lapiya Qalau" Ya cigaba da magana "Mum lafiya Ina ta Kiran Sumayya Bata d'agawa?" Ajiyar zuciya Mummy ta sauke kafin ta cigaba da magana "Ba lafiya kam gata cikin d'aki ta rufe kanta Tana ta kuka da fashe-fashe" Da sauri Muhdeen ya fito daga cikin Motar sa ko rufe murfin baiyi ba a guje ya nufi 'kofar falon Sumayya dake ta sambatu Tana fad'in "Ba zai yi ba 'karya ne wallahi Muhdeen nawa ne Ni kad'ai ba wata 'yar matsiyata da zata rabani da shi, Inteesar 'karya kike baki Isa ki ra'bi abunda nake so ba, Muhdeen nawa Ni kad'ai ne", 'kara fashewa tayi da kuka Tana fad'in "Baby me yasa kayi Mani haka?dama da kake fad'a Mani cewar ka tsani Inteesar baka 'kaunar ganin ta 'karya ka fad'a mani?kai fa ka yi muna d'inki iri d'aya ni da kai kace mu saka yau mu tafi yawan sha'katawa mu sha Ice cream mu yi d'auki pictures,lokacin da ka d'ibar Mani har ya wuce bakazo ba na kiraka kawai sai na ganka da wannan yarinyar 'yar matsiyata zaune a gaban motar ka? Dai-dai lokacin da ya kama ta ace muna tare?Why? Why?zakayi Mani haka?" Ta 'karasa maganar yayin da ta taka kwalbar turaren da ta fasa, Jini hannayenta da 'kafafuwar ta ke zuba duk ta 'bata d'akin,Bata damu da jinin dake zuba a jikin ta ba kishi ya rufe Mata idanu. Daga can falo knocking Muhdeen ya gaji dayi, Don Haka ya Fara dukan 'kofar da kafad'arsa bugu na uku kuwa sai ga kofar Bature ta fad'i 'kasa,Sumayya na tozali da Muhdeen ai ta Fara -waige -waige kwalbar turaren wuta na itace tayi tozali dashi Wanda Bai fashe ba,da sauri ta d'auka tare da saiti dai- goshin muhdeen ta seta kwalbar ta jefa masa a goshin sa. *ZAKU IYA JINA SHIRU GOBE BAN YI MAKU POSTING BA BANI DA LAPIYA NE KUYI MANI ADDU'A DA BAKUNANKU MASU ALBARKA*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan)Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. *BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM* Page1️⃣6️⃣ Kwalbar ta jefa masa a goshinsa, cikin zafin nama ya goce kwalabar ta daki bangon d'akin ta tarwatse, ganin yadda jini ke zuba a hannayenta da 'kafafuwarta ne ya d'aga hankalin Muhdeen da Mum d'inta, cikin sauri Mum ta karasa tana cewa, "Haba Sumayya me aka yi maki da zafi haka da har zaki illata kanki?" Cikin muryar kuka ta soma magana, "Mum wallahi bazai yuwu ba babu maccen da ta isa ta mallaki abunda na mallaka, domin duk abunda na mallaka nawa ne ni kad'ai babu wacc..." Mum ce tayi saurin katseta ta hanyar ce mata "Wai akan wa kike magana ne?" Muhdeen ne ya cewa Mum su kaita Asibiti ganin yadda jini ke fita daga jikinta, Sumayya sai hararar Muhdeen ta ke yi tare da cewa, "Me ya kawo ka nan gidan? Ka koma can wajenta tunda ta fini mahimmanci a wurin ka" Maganar da Sumayya tayi ne yasa Mum gane cewa fushin da Sumayya tayi yana da alaka da Muhdeen, ya yin da Muhdeen ya bud'e baki da niyyar magana ta d'aga masa hannunta dake tsiyayar da jini alamar ya dakata tace, "Bana bukatar jin komai daga gareka, Get out of my room" Takarasa maganar tana nuna masa 'kofar fita tana kokarin karasawa garesa da niyyar hankad'a sa waje cikin rashin sa'a ta saki wani gigitaccen 'karan azaba ya yin da tataka wani fasasshen kwalbar turaren da ta fasa, zama tayi a wajen ta kasa tafiya ganin hakan ne yasa Muhdeen ya kalli Mum tare da cewa, "Mum kada a biye mata mu kaita Asibiti ne kawai, Jin hakan yasa Mum tace, "Okay bari na d'auko mayafina" Ta fita ta nufi d'akinta don d'aukar mayafin nata ya yin da Sumayya keta sambatu cikin muryar kuka tana fad'in "Babu inda zan je ka tafi koma wajen wacce ta fini a wajenka meye damuwar ka dani Auren mu saura wata d'aya da sati uku amma ka barni ka tafi wajen wata banza ka manta dani ina ta zaman jiranka" Muhdeen zuba Mata ido yayi Yana mamakin want irin mahaukacin kishi ne Sumayya take dashi,dahar zata illata kanta akan abunda bata da tabbas akansa zargi ne kawai,bud'e baki yayi tare da cewa' "Duk abunda kike tunani ba haka bane,kinyi kuskuren fahimta ce da zakiyi hakurin saurara ta da nayi maki bayanin komai" Dai-dai lokacin da Mum ta shigo d'akin Tana fad'in kada ya biye Mata su tafi kawai,hakan yasa ya d'auke ta kamar wata jaririya kasancewar Bata iya tafiya sakamakon kwalaben da suka shiga cikin 'kafar ta,sai ihu take Tana Kai masa suka a 'kirjin sa Tana fad'in ya ajiye ta Amma Ina baiko sauraren ta har sai da ya bud'e murfin gaban motar ya direta yayin da Mum ta shigo baya 'ko'karin bud'e murfin motar Sumayya tayi Amma Ina ya riga yayi locked din motar ba Halin ta fita horn yayi Mai gadi ya wangale masa 'kofar gate d'in ya fice a guce. Iya Gaje Mai gyara masu d'aki ne ta shiga dakin Sumayya Don ta gyara 'barnar da tayi,itama tayi mamaki matu'ka 'barnar da tayi ta yau tafi ta kullum yawa ganin jinin dake malale akan tiles d'in d'akin ne yasa ta jinjina Kai tana ta magana ita kad'ai Tana cewa, "Kai amma wannan yarinyar anya kanta d'aya kuwa? ace mutum ya dinga yin abu kamar na mahaukata? yarinya Sam bata da tarbiyya da sanin yakamata waye zai shigo d'akin nan yace mai hankali tayi wannan aikin? Tajawa iyayen ta asara,Koda yake su bazasu damu ba ai sun Saba da halin ta kuma su suka d'auka kome taga dama tayi dai-dai ne uwa Babu kwa'bawa uba Babu harara komai tayi sai dai a zuba Mata ido Ina Bata it's komai ba Ana Shirin aurar da ita wallahi Ina tausayawa mijin da zai aure ki." 'Bangaren su Gwaggo kuwa suna Isa 'kofar gidan jabeer kuwa Bayan direban yayi horn Mai gadin ya bu'de masa ya Cinna hancin motar cikin gidan, jabeer dake Shirin fita idonsa ne ya sauka akan kakar tasa mahifiyar Babansa da sauri ya Karasa ya bud'e Mata murfin motar yayi ta jefo kafa kafarta dakyar ta fito rungume ta yayi cikin farin cikin ganin ta yace, "Uwar gida na sai yau kikaga damar zuwa gidan mijin naki har Ina Shirin zuwa biko" "Dariya tayi Tana fad'in, Ai ko kayi biko ba dawowa zanyi ba,Don tunda kayi Mani kishiya ka rage kula dani " Karasawa yayi gurin Mummy ya gaishe ta cikin girmamawa,ta amsa masa cikin sakin fuska tare da tambayar sa ya Mai jiki,Mufida ma ta gaishe sa daganan suka karasa cikin gidan. A falo suka zauna,shi kuma ya nufi bedroom d'in maryama a kwance ya same ta kamar yadda barta,ya sanar da ita zuwan su Mummy mi'kewa tayi cikin karfin hali Hannunta ya ri'keta suka nufi hanyar falon,Bayan sun Isa falon ganin idanun su Mummy yasa ta zame Hannunta daga nasa,ta karasa ta du'kusa ta gaishe su tare da zama akan center carpet din falon, Gwaggo Dada ce tace, "Wannan kishiyar tawa da alamu cikin nan na wahalar dake ko? Uhmm koda yake gwara haka yanzun zaku San irin wahalar da iyayen KU suka Sha akanku ku Kara sanin darajar iyaye ai yanzun ma aka fara wasan" Jabeer ne da ya 'karaso falon dauke da lemu da ruwa a cikin tray ya ajiye tare da duban Gwaggo yace, "Waishin dubiya kikazoyi ko kuma kin zo kisamun mata a gaba da maganganun ki need?" "Ai gaskiya na fad'a mata Wanda zai hau sama ya taka leda ai baiyi komai ba tukunna, jibi fa yadda take langwa'bewa kamar an tsoma tsumma a cikin ruwa" Dariya sukayi gaba d'ayan su banda Maryam data kwa'be fuska kamar za ta yi kuka, jabeer ya kalleta yace, "Kada ki damu Gwaggo haka take da sannu zaki saba da ita" Umma CE tace, "Ya jiki Maryam" Murmushi tayi tare da cewa, "Da sau'ki Mummy" "Allah ya 'kara sau'ki" Cewar Mummy, fira suka d'an ta'ba kafin sukayi masu sallama, Jabir har wajen mota ya rakasu sai da suka fice sannan ya koma cikin gidan. 'Bangaren Muhdeen kuwa suna tafiya a Kan hanyrsu ta zuwa Asibiti Sumayya tayi-tayi ya dakatar da motar Bai kulata ba hakan yasa ta dinga juya sitiyarin motar ta kowane 'bangaren, hakan yasa motar ta ku'buce masa ta dinga tangal-tangal akan titi Mum said salati takeyi ta gama tsorata da lamarin 'yarta, Muhdeen sai 'ko'karin 'kwace Hannunta yakeyi amma abin yaci tura ababen hawa sai kaucewa suke suke suna sauka daga Kan titin, tsawar da Mum ta daka mata ne yasa ta cire hannunta tacigaba da kuka, sannan ya samu yayi control d'in motar parking yayi sannan ya fito Yana bawa jama'ar dake gefen titi suka parking Ha'kuri ya basu, wasu basu kulashi ba wasu kuma suna zaginsa wai bai iya tu'ki ba ya d'auki mota ya hau titi zai kashe al'umma, bai ce dasu komai ba ya shiga motar Kai tsaye ya nufi Asibitin sa. B'angaren su Gwaggo kuwa daga gidan Jabeer Mummy ta Umarci Direban ta yakai su gidansu Inteesar, Kai tsaye gidan ya nufa dasu, bayan sun gaisa da Umma tayi masu jagora zuwa d'akin Inteesar shigarsu yayi dai-dai da farkawar ta daga d'an gajeren barcin da tayi,Yunwa ce ke kwakular cikin ta yasa ta farka, ganin su Gwaggo da Mummy sannan ga 'kawar ta Mufida yasa ta sakin murmushi,Bayan sunyi sallama ta amsa masu ne suka zauna kan tabarmar dake shimfid'e a d'akin ya yin da sai Mufida ce ta haura kan katifar tare ri'ke hannunta cikin tausayawa tace, "Sorry my besty ya jikin ki?" Kwa'be fusaka tayi kamar za ta yi kuka sannan tace, "Wallahi Yayan ki mugu ne ba yadda ban ro'kesa kara yamun allurannan kum..." Had'iye sauran maganar tayi sakamakon hararar da Umma ta watsa Mata Murmushi Mummy tayi tare da cewa " 'Yata kina tsoron Allura ne haka? " Gyada k'ai tayi tare da sunkuyar da k'ai kasa. Mummy ce ta cigaba da magana tace, "To yanzun ya ciwon kan naki?" "Da sau'ki Mummy tunda na tashi barcin nan naji jikin nawa ya d'an mani sau'ki sosai" Amsar da tabawa Mummy kenan ba tare da ta d'ago Kai ba, don ta lura tunda tayiwa Muhdeen rashin kunyar Nan Umman ta ta canza Mata fuska. Gwaggo ce tace "to Allah ya baki lafiya yarinyar kirki" Inteesar ce ta d'auki jakkar Mufida don tasan Bata rabo da kayan za'ki a cikin jakkar ta hakan yasa ta bud'e jakkar ta Ciro biscuit da chocolate ta Faraci "Dariya Mufida tayi tare da cewa yanzun haka har yanzun bakici komai ba ko?" Murmushi tayi tace "Wallahi bakin nawa ne ba taste shiyasa banci komai ba" Mummy ce tace "Amma sai da na fad'awa son cewa ya siye maki fruits a hanya, kenan bai siya ba kenan ko?" Gabanta ne ya fad'i jin tambayar da Mummy tayi mata, don bazata iya fad'awa Mummy irin wula'kancin da ta yi wa d'anta ba. Waige-waigen tayi inda ta watsawa Muhdeen fruits d'in a jikin sa,taga an gyra wajen tasan aikin Ummanta ne, sunkuyar da k'ai tayi kafin tace, "Ya siyo Mummy" Da yake Mummy bata cika bin Kwakkafi ba yasa tayi shiru, don tasan indai Umarni tabawa d'anta Umarni Yana binta koda bayaso. Fira suka d'an ta'ba kafin sukayi masu sallama suka tafi, amma Mufida tace bazata tafi yanzun ba sai tayi jinyar Aminiyarta. 'Bangarensu Muhdeen kuwa suna isa asibitinsa kujeran keke na d'aura marasa lapiya aka d'orata akai don bata iya tafiya, bayan an shigar da itane ya Fara aikin cire mata kwalaben da suke shiga kafar sai sannu yake ya jero mata amma sai tayi banza dashi kamar Bata jishi ba, cikin kankanin lokaci ya gama mata dressing Mum d'inta na tsaye akansu bayan ya gama Mata duk abunda yakamata yayi Mata ne ya d'auke su ya mayar dasu gida Bayan ya had'a Mata magunguna duk da ta'ki yarda yayi mata allurar da zai rage mata zogi. Kai tsaye gida ya nufa yanda ya samu Gwaggo da Mummynsa a falo ya gaishe su, ya juya zai wuce part d'insa part d'insa Mummy ta lura da d'an jinin da ya 'bata masa riga cikin kid'ima tace, "Son Mai ya faru dakaine?" Cikin son 'boye Mata yace, "Ba komai Mummy kawai na gaji ne, zan je na d'an yi wanka na huta" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa, "karya ba d'abi'ar ka bace kada ka Fara yanzun, nasan yanayin ka idan gajiya ke damunka,hakazalika nasan yanayin ka idan akwai damuwa a tattare dakai,idanunka kad'ai na kalla nasan akwai damuwa a tattare dakai,shin akwai damuwar da d'a zai 'boyewa mahaifiyar sa?" Shiru yayi cikin sanyin jiki yabasu abunda ya faru Tundaga lokacin da ta ta Umarceni shi yakai Inteesar gida da Kiran da Mufida tayi masa Video calla ta gansa da Inteesar har zuwa haukan da tayi a d'akinta da Wanda tayi suna cikin Motar har suka kusan yin Accident bai 'boye masu komai ba. Jikin Mummy ne yayi sanyi ta kasa magana, Gwaggo ce ta dinga fad'a tana cewa, "Ai dama na fad'a maka wannan ba matar auren ka bace, bata dace dakai ba, ashe bayan rashin tarbiyya da take fama dashi harda ta'bin hankali? Yanzun da kwananka sun kare da ta kashe ka, ina fatan dai yanzun zaka rabu da ita ka nemi wacce ta dace dakai" Juyawa tayi ta kalli Mummy da tayi tagumi sannan tace, "Fatima" Mummy ta d'ago ta kalleta tare da cewa, "Na'am Gwaggo" Gwaggo ta cigaba da cewa, "Na san cewa ban isa da d'anki ba ya rainani baya d'aukar maganata da mahimmanci, amma ina mai baki shawara cewa idan har kina son rayuwar d'anki da kwanciyar hankalin sa to ki hana sa auren wannan mahaukaciya tun a waje tayi yun'kurin kashe shi ina ga anyi auran ai sai dai ta da'ba masa wuka tace zata kashe shi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Wannan Kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba Arashi ne Mai kashe Auren Wawa *BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM* Page1️⃣7️⃣ "Nasan cewa ban isa da d'anki ba ya rainani baya d'aukar maganata da mahimmanci, amma ina mai baki shawara idan har kina son rayuwar d'anki da kwanciyar hankalinsa to ki hana shi auren wannan mahaukaciya, tun a waje tayi yun'kurin kashe shi ina ga anyi auran? Ai sai dai ta da'ba masa wuka tace zata kashe shi." Tana kaiwa 'karshen maganarta ta mi'ke ta nufi d'akinta, jikin Mummy ne yayi sanyi, kallan Muhdeen tayi tace, "Idan ka gama abunda zakayi ka sameni a d'akina" Bata jira cewarsa ba ta wuce ta nufi d'akinta, jiki a sanyaye shi ma ya nufi part d'insa Bayan sallar isha'i Mummy tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallah tana Addu'o'i, Muhdeen ne yayi knocking yana jiran ta bashi izinin shigowa, bayan ta idar da addu'a ta bashi izinin shigowa, da sallama d'auke a bakinsa ya shiga bayan ya zauna ya kalleta cikin girmamawa yace, "Barka da dare Mummy" "Yauwa" Ta amsa masa a ta'kaice, shiru ya d'an biyo baya karin ta kalle shi ta Fara magana, "Muhammad" Jin yadda ta kira sunansa da Muhammad ne yasa ya tattara gaba d'aya hankalinsa da nutsuwarsa akan ta, don yasan bata cika kiran sunan sa kai tsaye ba sai dai ta Kira sa da son, ta cigaba da magana tace, "Ba na son nayi maka dole akan abunda nake so nafi son na baku dama ku za'bi za'bin ranku akan koma meye matukar hakan bai sa'bawa addinin musulunci ba, musamman akan magamar aure tunda shi aure ba abu bane na wasa kuma ba ni ce zanyi maka zaman auren ba kai da kanka ne shiyasa nafi son kai da zakayi zaman auren ka neme wacce ka ke so take son ka ba tare da anyiwa ko wannen ku dole ba domin d'orewar zaman lapiya da kwanciyar hankalin ko wannen ku, maganar da Gwaggo tayi fa abun dubawa ne, domin jikina yayi sanyi da lamarin yarinyar nan yakamata kayi nazari sosai akan maganar Gwaggo kuma kayi la'akari sosai akan abunda ya faru, naso ace nitsatsiyar yarinya ka samu mai sanin yakamata mai tarbiyya da ri'ko da addini, ba wai Umarni nake baka akai ba shawara ce idan tayi maka idan kuma har yanzu kana nan akan bakanka to shikenan Allah ya tabbatar muna da alkhairi. Kai ya jinjina dare da cewa, "Ameen ya rabbi Mummy nagode, ki tayani da addu'a" Kai ta jinjina Don ta lura da cewa 'Danta yayi nisa sosai akan Son Sumayya baya jin kira, don ta lura laifinta ma baya son ana fad'a, lura da hakan yasa tace, "Kullum cikin maku Addu'ar nake Allah ya tabbatar maku da abunda yafi zama alkhairi a gareku" Amsawa yayi da Ameenn kafin ya mi'ke ya nufi 'kofar fita, ya juyo ya kalli Mummy yace, "Ina Mufida ne tunda na dawo naga alamar bata gidan nan" Murmushi Mummy tayi tace, "Ina kuwa zaka ganta tana can tana jinya" Kallon ta yayi cikin rashin fahimtan inda maganarta ta dosa yace, "Jinya kuma Mummy?Yaushe ne ta Fara rashin lapiyar ?" Dariya Mummy tayi "Ai ba jinyar kanta takeyi ba,jinyar Aminiyarta ce Inteesar,kasan sha'kuwar dake tsakanin su barci ne kawai yake rabasu" Shiru yad'anyi na lokaci kafin yace, "Amma duk da haka dare yayi yanzum yakamata ace ta dawo gida" Wayar sa ya Ciro daga cikin aljihun jallabiyar daya Sanya a jikinsa, Number Mufida ya lalubo my little sister sunan da yayi serving number ta dashi kenan,Danna Mata Kira yayi tare da Kara wayar a kunnen sa, Mufida dake zaune Ita da Inteesar suna cin tuwon shinkafa da miyar zogale Wanda Umma ta girka,sai Santi take,Don taji dad'in girkin sosai,ita ko Inteesar dakyar taji loma uku Don Bata Jin dad'in komai,Wayar ta CE tayi ringing yasa ta duba ganin sunan Mai Kiran ne yasata sakin Murmushi,My lovely brother shine sunan da tasa masa ,d'agawa tayi tun kafin tayi magana tajiyo muryasa yana cewa, "Me kikeyi a gidan mutane dai-dai wannan lokacin?yanzun Nan kidawo gida" Bai jira cewarta ba ya katse Kira Don Bai Bata damara tayi magana ba,kallon Inteesar tayi cikin sanyin murya tace, "Kinga Yaya Wai ma dawo gida dare yayi," Marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka tace, "Kinji Yaya Wai na dawo gida yanzun dare yayi" Da sauri Inteesar ta kalle ta tare da cewa, "Ba kinyi mani al'kawarin cewa tare Dani Zaki kwana ba?" Shiru tayi ma 'Danyi kafin ta saki murmushi ta kalli Inteesar cikin jinda tace. "Na samu Mana mafita cikin sau'ki,Dady zan Kira na sanar dashi cewa zan kwana tare dake bakida lapiya,nasan bazai hanani ba." Murmushi Inteesar tayi tace, "Gaskiya Kam nima nasan cewa bazai hanaki kwana a gidanmu ba" Wayarta ta d'auka tare da lalubo number Dady,bayn ta Kira number ne ta Kara wayar a kunne bugu biyu ya d'aga tare da cewa " Assalamu Alaikum" Mufida tayi murmushi tace, "Wa'alaika Salam Dady Barka da dare ya aiki?" "Alhamdulillah yanzun ma insha Allah zan kamo hanyar gida" Ya 'karasa maganar Yana 'ko'karin kashe Kiran,Jin muryarta Tana magana yasashi dakatawa Yana sauraren ta. "Dady dama Ina son sanar dakai ne Inteesar ce bata da lapiya Ina gidansu zamu kwana tare da ita ne" Cikin sauri hankali a d'an tashe yace, "Subhanallahi me yake damunta?bakuje Asibiti bane?" Murmushi tayi tare da cewa, "Kada ka damu Dady da sau'ki,Yaya ya dubata ya Mata allura da magunguna" Ajiyar zuciya ya sauke yace, "Okay okay ki bata wayar" Mi'kawa Inteesar wayar tayi,bayan ta ka'bi wayar ta Kara a kunne. "Assalamu Alaikum" "Wa'alaiki Salam Inteesar ya jikin naki da sau'ki ko?" "Eh Abba da sau'ki Alhamdulillah" "To Masha Allah, Allah ya baki lapiya yasa ya zama kaffaran jiki,ki maida hankali wajen Shan magani kinji 'yata Allah yayaye maki,saida safe" Daganan ya kashe Kiran inda ya shiga bayan motar sa direban sa yaja suka kama hanyar gida. Mufida tayi murmushi tana kallon kawarta tace, "Allah sarki yanzun gobe Ni kad'ai zan tafi school,gasky zanyi kewarki sosai Allah dai ya baki lapiya,gashi this time muma Shirin kammala secondary d'in mu zamu zama 'yan matar jami'a" Dariya ta kece dashi Tana fad'in, "Wai waya ganmu a jami'a shikenan fa mun zama manyan Mata,Koda yake mum wuce yara tunda a yanzun dukan mu kusa almost 18 years,yanzun cikin kasashen waje wata 'kasa kike son muyi karatun mu a can?" Murmushi Inteesar tayi tare da cewa, "Waye ubana dazan tafi kasahen waje karatu? niba 'yar kowa ba bazankai kaina inda Allah baikaini ba ko anan Nigeria ma idan nasamu Abba ya..." Bata Kai 'karshen zancenta ba tayi shiru ganin irin 'bacin ran da tagani a fuskar Mufida, Cikin rashin fahimtan fushin nata tace, "Mufida me ya faru Naga kin canza fuska yanzu-yanzu?" Tura baki Mufda tayi tace, "Ba dole na 'bata rai ba tunda kin nuna mun cewa nidake ba Abu d'aya bane,har zakice Wai ke 'yar gidan waye da Zaki karatu waje,bayan kinsan duk abunda Dady da Mummy sukayi Mani zasuyi maki" Murmushi Inteesar tayi tare da fad'in "Mufida nasan iyayenki ne suka d'auki nauyin karatuna lokacin da mahaifina ya rasa kud'in da zai biya Mani School fee suka d'aura daga inda ya tsaya,yanzun muna Shirin kammalawa,Banda suturu da sauran ababen bu'kata wannan ma kad'ai ya Isa Allah ya saka da alkhairi,yanzun kina maganar zuwa wata 'kasa ace Nima dani?ke Ni Koda zancigaba da karatuna to anan Nigeria ne kuma a Niger state, IBRAHIM BADAMASI BABAN GIDA(I.B.B. LAPAI) Marairace fuska Mufida tayi tace, "To muje Al-HIKIMA University na Ilori mana" Shiru Inteesar tayi batare da tace komai ba. Gaba d'ayan su suna zaune a dinning room suna dinner Dady, Mummy,Gwaggo,sai Muhdeen,suna zaune kowanen su nacin Abincinsa Amma banda Muhdeen dake jujjuya cokalin ya kasa cin komai,tunanin halin da Sumayya ke ciki yake, Gwaggo ce ta ta'be baki tace, "Indai tunanine bakama Fara ba yanzun zaka saka 'kafar wando dashi, matu'kar kace wannan mahaukaciya zaka aura," Baice Mata komaiba cikin son kawar da zancen yace, "Mummy Wai har yanzum Mufida bata dawo gida ba?kuma fa har Kiran wayarta nayi nace ta dawo Amma ta kasa dawowa" Dady ne yayi magana yace, "Ta kirani ta sanar dani can gidan zata kwana,tayi jinyar Inteesar sai gobe da safe zata dawo tayi Shirin zuwa school, kuma an amince mata" Shirin Muhdeen yayi Don baiso hakan ba Amma tunda Dady ya amince dole tasa ba yadda za'ayi dole ya hakura sai dai yace, " In Banda abunta meye na wani kwana a gidan mutane,nifa Sam hankalina baya kwanciya da irin haka" Gwaggo tayi saurin cewa, Idan Kai hankalin ka baya kwanciya mu namu Yana kwanciya,tunda tare da Mai cikakken hankali zata kwana,bada Mai cutar kwakwalwa ba ballantana muyi tunanin kada tayi barci mahaukaciyar ta illata muna ita," Ta karasa maganar Tana Kai lemu a bakinta, Muhdeen ransa ya 'baci Don yasa magama take fad'a masa a fakaice wato Sumayya ce mahaukaciyar ,Bai gama tunanin da yakeyi ba ya koma jiyo muryarta Tana fad'in, "Ina tausayawa mijin mahaukaciya" Take Muhdeen yabar wajen ransa a 'bace don Yana shakkar Dadyn sa ne kada yaha yanayiwa mahifiyar sa rashin kunyar,da badon haka ba da yaayar Mata da amsa. Kwanci tashi ba wuya a wirin ubangiji,yau su Inteesar da Mufida suka kammala jarabawar su ta kammala secondary School,kuma yau ne ya rage saura sati biyu bikin Muhdeen da sumayya,kuma yaune Muhdeen da Sumayya zasu dawo daga 'kasar Dubai inda sukaje had'a kayan lefen Auren su,don sumayya for ta'ki yadda Wai Muhdeen ko waning nasa ne zai siyo Mata kayan lefe,ta dage dole sai dai suje Dubai ita dashi su siyo kayan lefen acan,haka duk kayan da Muhdeen ya za'bar Mata zatace ita bayyi Mata ba,sai dai ta za'bo wasu kayan daban ,a cewar ta abunda ya burge wani baya burge ta,Koda ta d'auko kaya taga Muhdeen ya yaba kayan zata mayar dashi,akasarij kayan da d'auka duk Basu kwanta masa ba Amma ba yadda zaiyi da ita,Haka suka cika akwatuna goma Sha biyu da kaya hatta sarka da d'an kunne na Gold ita ta za'ba.koda taga ya siyo wasu dogayen rigunan abaya kala daban-daban masu kyau tace Bata son kayan da zasu takura ta,ya nuna Mata cewa 'kannensa ya siyawa Asiya da Mufida Suma ya cika masu Babbar jaka da tsaraba har da Mummy da Gwaggo duk ya masu tsaraba.koda suka dawo yake nuna masu kayan lefe Mummy dai cewa tayi Allah Sanya alkhairi, Gwaggo ne dai tace Allah wadarai da wannan kayan Don Bata ga kayan arziki a wajen ba. 'Bangaren Inteesar kuwa kamar yadda tayi alwashi hakan ne ta kasance, bata sake taka 'kafafuwar ta zuwa Gidan su Muhdeen ba ko kafin su gama Exam idan ta shirya zata tsaya kan hanya ta jira har sai Mufida da direban Mummy yazo tabisu ko Mummy da Gwaggo sun kirata zata kirkiri abinda zata fad'a masu da zai hanata har sun gaji sun kyaleta. Mufice ta kawo Mata Atamfofi da less da material na ankon bikin tace suje wurin tailorn da Mummy ke kai masu d'inki haka kuwa aka yi ta sallami Umma suka wuce wurin Hamza Tailor, bayan sun za'bi irin wanda suke so ne sukayi masa sallama suka tafi, don dama Mummy ce zata tura masa Kud'in, Har zasu shiga mota inda direba ke jiran su sai Inteesar ta hangi wani makaho ya taho Kan titi da 'yar sandarsa Yana dogarawa ga Mota na zuwa a bayan sa,ba tare da tayi tunanin duna janya ba tahau titin a guje kafin ta ankare bisa tsautsayi sai ji tayi mota ta kad'eta ta Fadi akan titi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta ta shi dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. Page 1️⃣8️⃣ Ba tare da tayi tunanin duba hanaya ba, kafin ta ankare bisa tsautsayi sai ji tayi mota ta kad'eta ta fad'i kan titin, Mufida dake can gefe ce ta kwalla mata kira. "INTEESAR!!!" Ta karaso a guje ya yin da matu'kin motar da ya kad'e Inteesar Shi ma ya karaso direban Mummy sai salati ya ke yi, ya yin da Mufida ke kuka kamar ranta zai fita ganin 'kawarta kwance a sume, rungumeta tayi ya yin da wata mata dake wajen ta d'auko Inteesar d'in ta saka ta bayan motar mutumin da ya kad'eta, jin yana cewa ad'auko ta su tafi asibiti, da sauri Mufida ta shiga bayan motar tare da janyo Inteesar ta rungumeta idonta na zubda hawaye Direban Mummy ne ya shiga gaban motar don baikamata ya barsu su tafi da mutumin da bai sansu ba. Tafiya kad'an sukayi suka 'karasa wani private hospital dake unguwar, parking yayi tare da fitowa da sauri ya hangi masu wasu ma'aikatan asibitin kiran su yayi sai gasu da hanzari sun d'auko gadon tura marasa lafiya, bayan an kwantar da ita suka wuce da ita ya yin da suka rufa masu baya. Bayan an shigar da ita d'akin an kwantar da ita bisa gado sai ga doctor da nurses biyu a bayansa, Doctor d'in ne ya umarci su Mufida da su fita su jirasa a waje, fita sukayi Mufida dai har yanzu bata daina kuka ba, saurayin da ya kad'e Inteesar ne ya kalli Mufida yace, "Ki kwantar da hankalinki ki daina kuka in sha Allah zata samu lafiya" Kai ta gyada masa ba tare da tayi magana ba, ta nufi kujerun dake wurin ta zauna akan d'aya daga cikin su tare da yin tagumi, Ishaq direban su ne ya kalleta yace, "To ni bari naje na d'auki mota na tafi na sanar da su Mummy" Kallaonsa tayi tace, "To" Saurayin da ya kad'e Inteesar dai Yana Nan tsaye wayar Sa ya Ciro daga cikin aljihun sa ya lalubo number mahifiyar sa ya shiga Kiran layin. Wata dittijuwar mata ce Mai kimanin shekaru hamsin tana zaune akan a falon ta, Kan d'aya daga cikin lafiyayyun kujeran dake falon,wayar ta CE to soma ringing dubawa tayi ganin d'anta ne ke Kira yasa ta d'aga da sauri tare da cewa, "Babana har yanzun baka 'karaso ba?" Ajiyar zuciya saurayin ya sauke cikin sanyin murya yace, "Mummy na samu accident ne" Zumbur ta mi'ke da sauri Tana fad'in, "Subhanallahi Babana me ya same ka? Kana Ina ne?" "Ba abunda ya sameni wata yarinya ce na kad'e da mota na kawota aaibiti" Cikin damuwa ta furta kalmar, "Inalillahi wa'inna ilaihir rajiun,wane asibitin kuke" "Muna nan asibitin Top medical dake tunga" Bata 'kara cewa komaiba ta ajiye wayar tare da 'kwalawa autar ta Kira. Khadija! Khadija!! Da sauri matashiyar budurwar ta fito hannunta d'auke da wayar ta,kafin tayi magama matar tace, "Kiyi sauri yanzun Nan ki fito zamu tafi asibiti yayanki ne ya kad'eta wata yarinya da mota" Tana kaiwa 'karshen maganarta ta nufi d'akinta, Ba jimawa tafito dai-dai lokacin da itama Khadija ta fito rataye da handbag hannunta ri'ke da makullin motarta,suka nufi kofar fita. Inteesar cikin 'kan'kanin lokaci ta farfad'o, kasancewar ba wani rauni taji sosai ba,buguwa ne da 'kujewa tayi,bayan doctor ya fito ya basu damar shiga su ganta kwance suka sameta, Mufida na ganinta ta saki murmushi a guje ta karasa jikin ta fad'a jikin ta ta rungumeta,ganin yadda Inteesar ke cije le'be yasa Usman wato saurayin da ya kad'e Inteesar yace, "Ki d'an saketa kamar Tana Jin zafin rungumar da kikayi Mata" Sakinta Mufida tayi tare da zama gefen gadon Tana murmushin ganin jikin Inteesar d'in da sau'ki, Inteesar ce the d'aga idonta ta kalli Usman suna had'a ido ya sakar Mata wani lallausan murmushi,da sauri ta sunkuyar da kanta kasa,Jin muryarsa tayi yace, "Sannu ko, ya jikin naki?" Ba tare da ta d'ago ta kalleshi ba tace, "Da sau'ki" Murmushi yayi tare da cewa, "Allah ya baki lafiya ya kiyaye gaba" Mufida ce ra amsa da, "Ameen ya rabbi" Suna cikin Haka aka turo 'kofar aka turo 'kofar aka shigo d'akin,kusan a tare suka shigo Gwaggo,Mummy,sai Umman Inteesar,suna shigowa sai ga Ammy mahifiyar Usman da 'yarta Khadija ne suka shigo d'akin. Gwaggo ce ta ri'ke hannunta cikin tausayawa tace, "'Yar Albarka Garin yaya hakan ta faru?nidai nasan kina da nutsuwa ba laifinki bane,yanzun haka tu'kin ganganci ne direban Nan yayi ways sani ma ko d'an shaye-shaye ne yasha ya bugu Yana neman illata maki illata muna ke,in bandama..." Bata Kai aya ba Mufida ta Kira sunan ta ganin zatayi 'baran 'barama ga Wanda ya kad'e Inteesar a wajen kuma ba mashayi bane yadda Gwaggon ke fad'a,Hasalima Inteesar ce Mai laifin don itace tahau titin dai-dai motar na kawowa,duk da cewa ita ceton rai tajeyi ganin makaho zai hau titin gashi ba idone dashi ba,dayake tsautsayi akanta yake ba'a kad'e makahon ba ita aka kad'e. Mufida ce tace "Haba Gwaggo ki daina yanke Hukuncin abunda bakida masaniya akansa,bakisan yadda Abu ya faru ba ki dinga bincike" Gwaggo ce ta galla Mata harara tare da cewa, "Dalla rufewa mutane baki magananniya na'ki nayi bincike,kuma duk Wanda ya kad'e Inteesar sai Allah ya..." Cikin sauri Usaman yace, "Mama Don Allah kiyi Ha'kuri nice na kad'eta bisa tsautsayi,kuma ba yadda kike tunani bane Allah ne ya 'kaddaro hakan zata faru ba makawa sai ta faru,KU gafarceni Don Allah" Gaba d'ayan su zuba masa idanu sukayi suna kallonsa. Mufida ce tace, "Wani makaho ne yazo yana dogara sanda zai hau titi ganin hakan ne yasa Inteesar ba tare da ta duba titi ba Kai tsaye tahau titin dai-dai motarsa na kawowa" Gaba d'aya d'akin shiru akayi ana sauraren ta, Gwaggo kuma sai taji kunya saboda su'butar bakin da tayi, kowa sai addu'a da Allah kiyaye gaba,Ammy mahaifiyar Usman CE ta gaishe su tare da gabatar da kanta ta kuma Basu ha'kurin abunda ya faru,suka nuna ba komai . Sun d'an jima suna fira a tsakaninsu,lokaci-zuwa lokaci duk sanda Inteesar ta d'ago Kai zasu had'a Idanu da Usman kuma sai taga ya Mata murmushi,har ta kosa su tafi,zuwa can Ammyn Usman tayi masu sallama Kan cewa zasu dawo gobe,hakan yasa Usman da Khadija sukayi masu sallama suka tafi. Mummy ma tayi masu sallama tace zataje tayi girki ta kawo masu Gwaggo kama tace it's zata kwana da Inteesar tayi jinyarta Umma ma tabita suka tafi gida,Don dama Mufida ma tace Nan zata kwana. Washe gari da sassafe Inteesar na kwance a gadon ta na jinya, Mufida na kwance Kan dogon kujera Mai zaman mutum uku Tana barci,yayinda Gwaggo ke cikin toilet tana brush,Usman ne ya turo 'kofar ya shigo tare da sallama, Inteesar ta juya Kai ta kalleshi murmushi ya sakar Mata tare da 'karasowa ya zauna Kan chair d'in dake gefae gadon ya kalleta yace, "Ina kwana?" Tashi zaune tayi tare da sunkuyar da kanta 'kasa tace, "Ina kwana ?" Fuskarsa d'uke da murmushi ya amsa Mata tare da cewa, "Ya jikinki" "Da sau'ki" Ta bashi amsa fuskarta a sunkuye,idonsa ne ya sauka akan wayarta yasa ya d'auki wayar tare da tambayarta ce ko na Mufida,don photonsu su biyu ne a Kan wayar kowacce fuskarta d'auke murmushi,Kai ta d'aga masa alamun wayarta ce,ganin Babu pin yasashi saka number sa a cikin wayar yakira layinsa Jin vibration a aljihunsa yasa yasan Kiran ya shiga,ajiye Mata wayar yayi dai-dai lokacin da Gwaggo ta fito Toilet,cikin girmamawa ya gaisheta tare da tambayarta ya Mai jiki tace, "Jiki kam Alhamdulillah angodewa Allah d'annan yasu Mahaifiyar taka suka koma?" "Alhamdulillah sunanan zuwa anjima" "To Allah ya kawosu lafiya" Kallon Inteesar yayi tare da cewa, Nima nayi sammakon zuwa ne saboda saboda yanzun haka tafiya zanyi zuwa Abuja, nace bari na biyo na duba jikinta, kafin na tafi, don Doctor ya sanar Dani cewa jibi Za'a sallameta,nazo dubata kafin na tafi," Mi'kewa yayi tare da cewa, "Bari na tafi direba na jirana a waje" Hannu yasa a aljihunsa,kud'i ya Ciro dubu hamsin ya ajiye masu. "Gwaggo tace, Kud'in asibitin ne?" Murmushi yayi tare da cewa, "Na biya Kud'in komai na asibiti sallamar KU kawai za'ayi KU tafi" Washe baki Gwaggo tayi tace Dakyau yaron kirki,da wasu marasa mutunci ne guduwa zasuyi bayan sun kad'e mutum,Amma Kai kayi abunda ya dace, Uwarka ta iya haihuwa" Murmushi yayi ya kalli Inteesar yace, "Zan kiraki a waya Allah ya baki lafiya" Bata san lokacin da ta maida masa martanin murmushin da yayi mata ba, daga nan sai ya nufi 'kofa ya fice fusakarsa d'auke da murmushi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. Page1️⃣9️⃣ Bata sanan lokacin da ta mayar masa marttanin murmushi da yayi Mata ba,daga nan sai ya nufi 'kofa ya fice fusakar sa d'auke da murmshi.Kallon ta Gwaggo tayi ta ta'be baki sannan tace, "Shi kuma wannan da yake murmushi dawa yakeyi ne?" Gyara kwanciyarta tayi ba tare da ta kalli Gwaggo ba,tayi magama can kasan ma'koshi, "To Ni inama zan san dawa yakeyi,oho masa" " 'karya kike munafuka har zaki wani ce baki san dawa yake ba?nan nake ta kallon ku Kuna tayiwa juna murmushi kamar wasu masoya,shi kuma ya zuba maki ido yana ta kallonki ko 'kifta ido Babu kamar wani tsohon maybe,to kidai bi sannu a hankali don samarin bana ba tabbas. 'Yan yaudara sunyi yawa musamman ke da kike sumu-sumu nan ba wani wayau ne dake ba". Tura baki tayi, Gwaggo ta ta'be baki tana cewa, "In banda ma rashin sanin inda kaknki ke maki ciwo mutumin da ya saka ki cikin wannan halin sai ki dinga masa murmushi kamar wata sakarya?" Turo 'kofar akayi da sallama,Mummy ce Da direbanta d'auke da basket da suka jero masu Breakfast a ciki,Direban ya a jiye basket tare da gaida Gwaggo,ta amsa masa yayiwa Inteesar ya jiki ya fice daga d'akin.Mummy ta kalli ta dur'kusa ta gaishe ta. "Gwaggo ina kwana" "Lafiya qalau,ya naganki ke d'aya ina sanin yake?" "Yanana Zuwa anjima ka'an,yace na gaishe ku kafin ya 'karaso nima nayi sammakon ne saboda Breakfast da na taho maku dashi" Jinjina Kai Gwaggo tayi tare da cewa, "Allah ya kaimu anjiman ya kawo shi lafiya" "Ameen ya rabbi" Cewar Mummy da ta kalli Inteesar,sai Inteesar tayi saurin gaida Mummy. "Ina kwana Mummy?" Murmushi mummy tayi tare da zama a gefenta ta shafi fuskarta cikin son yarinyar. "Lapiya qalau 'yata ya jikinki?" Murmushi tayi tace "Alhamdulillah naji sau'ki" "To Masha Allah ga Breakfast ki tashi kici" "Mummy tea kawai zansha" Dai-dai lokacin da Mufida ta farka daga barci, mi'kewa tayi ta fad'a jikin Mummy Tana fad'in. "Morning" Gwaggo ce ta had'o tea ta kawo ma Inteesar ko bread ma bata kula ba balle ayi maganar Dankali da kwai.A ranar Dady yazo ya gaida Inteesar sannan ya tafi wurin meeting d'in da zaije, Abba da Umma ma duk sunzo,sai wasu 'kawayen Inteesar su biyu wasila da salaha sunzo sun gaishe da Inteesar, suna tsakiyar fira ne wayar Inteesar tayi ringing,ganin number tayi ba suna,d'agawa tayi tare da yin sallama,Jin wata ba'kuwar murya yasa tad'anyi shiru Tana tunanin muryar waye wannan? Daga can 'bangaren yace "Ina wuni?ya jikinki? "Lapiya qalau naji sau'ki" Murmushi yayi yace "Masha Allah Allah ya baki lafiya yasa ya zama kaffaran jiki" Shiru tad'anyi kafin tace, "Ameen ban gane dawa nake magana ba" Murmushi yayi yana fad'in "Usman ne Wanda tsautsayi yasa ya kad'e ki da motar" Shiru tayi Tana sauraron sa yaci gaba da maganar sa shi kad'ai wani lokacin tace eh idan na cewa A'a ne tace a'a a haka har suka d'auki tsawon mintuna suna waya har ta gaji ta 'kosa sannan yayi Mata sallama.Bayan ta ajiye wayar ne Mufida ta kalleta tare da cewa, "Wai keda waye tun d'azu kike waya haka?" Yamutse fuska tayi tare da cewa "Wanda ya kad'eni da mota ne ya Kira ni?" "To ina ya samu number ki?" "Yazo da safe lokacin kina barci" Ta karasa maganar Tana kwanciya Don ta gaji. Bayan kwana biyu aka sallame su inda suka koma gida,ana dai ta shirye shiyen biki ta kowanne bangare. A ranar Usman ya Kira Inteesar Kan cewa zaizo gidan su,ta'ki amincewa da hakan,ya nuna Mata cewa ai yakamata bayan dawowar sa ya sake duba jikin ta bayan an sallame su,ta nuna masa cewa ba komai ta warke.Fahimtar bazata bari yasan gidansu bane yasa yace Mata akwai sauran magungunan da Doctor yace a bata saboda idan batayi amfani dashi ba buguwan da tayi ciwon zai iya tashi kowane lokaci,jin hakan yasa ta bashi address d'in gidan su. A can gidan Mummy kuwa, Gwaggo tasa Muhdeen a gaba wai me yasa baije asibiti ya gaida Inteesar ba har aka sallame ta.Mummy ma Bata San da hakan ba don ba wuni takeyi a asibiti ba.Nan ta bashi Umarnin cewa yau d'innan yaje har gidan su ya gaishe ta,ransa baiso ba haka ya amince zaije. Misalin 'karfe biyar na yamma Usman ne a 'kofar gidan su Inteesar,Yana tsaye ya jingina da motarsa yayin da Inteesar ke tsaye sanye da Hijab har 'kasa,kanta sunkuye a 'kasa Tana wasa da yatsun hannun ta.Murmushin nan nasa yayi tare da cewa, "Wai Kunyata kikeyi har haka ne kin kasa had'a ido da ni?" Shiru tayi tacigaba da wasa da yatsun hannun ta, dai-dai lokacin da motar Muhdeen ya karaso 'kofar gidan,idanun sa ne suka sauka akan Usman da Inteesar,kallon mamani yake masu Wanda Shima Usman ya lura da hakan Amma sai ya kauda Kai.Muhdeen mamaki yake Wai kamar yarinyar Nan har ta isa aje saurayi ganin irin kallon da Usman ke Mata yana murmshi yasa shi ta'be baki hakanan kawai yaji gabansa ya fad'i yaji tsanar Usman ya d'arsu a cikin zuciyar sa.Bud'e marfin motar yayi ya fito,jin 'karar murfin motar ne yasa Inteesar d'ago ido ta kalleshi caraf suka had'a ido harara ya watsa Mata Wanda yasata sunkuyar da kanta 'kasa,duk akan idon Usman hakan ya faru Amma ya basar,d'ago ido ta sakeyi a karo na biyu suna had'a ido yayi Mata alamar tazo da hannayen sa,kallon ta ta maida ga Usman tace, "Don Allah ina zuwa" Kai ya jinjina alamun amincewa,sannan ta 'karasa wajen motar Muhdeen,sallama tayi ya amsa Mata can 'kasan ma'koshi tace, "Yaya Ina wuni?" Shiru yayi kamar baiji ba,sai da ta sake maimaitawa nan ma shiru don haka bata sake magana ba dama tasan halin sa.Tsawon 5 minutes baiyi magana ba,ganin baida niyyar magana ga fuskar nan a had'e ba alamun fara'a yasa tace, "To Yaya sai anjima" Tana Shirin barin wajen taji yace, "Kina sauri ki koma wajen saurayin ki ko?karamar yarinya dake Wai har kin iya zance da saurayi,aikin banza Gwaggo ta addabeni Wai nazo na gaida mara lapiya ashe lafiyar ki kalau da na sani ban 'bata lokaci na ba. " Ya karasa maganar yana watsa Mata kallon banza sannan ya juya ya shiga motarsa yabar wajen,shiru tayi tana tunananin maganar sa a zuciyar ta tace Mai hali bazai ta'ba canzawa ba. Karasawa tayi wajen Usaman tace, "Zan shiga gida sai anjima" Ajiyar zuciya ya sauke ganin yanayinta ya canza cikin 'kan'kanin lokaci,yace "Naga yanyinki ya canza na janyo maki 'bacin rai ko?bana son na zama silar 'bacin ran kowa,idan wannan shine wanda zai aure ki ko an tsaida magana a tsakanin ku ki Fad'a mani don naga kamar akwai matsala da ya ganni dake" Bakomai Yayar 'kawata Mufida ne,shine Wanda zaiyi aure next week,d'inkin ankon bikin muka tafi kaiwa har ysautsayi yasa ka kad'e ni da mota " Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi yace, "To Masha Allah" Murfin bayan motar sa ya bud'e ya d'auko manyan ledoji guda biyu ya mi'ka mata yace " ga magungunan ki nan da nace zan kawo maki" Kallon ledar tayi da mamaki tace, "Magungunan ne har leda biyu manya ?" Baibi ta kanta ba ya figi motarsa yabar wajen yayin da ta shige gida zuciyarta cike da mamakin yawan magungunan. Muhdeen yana Isa gida ya iske Gwaggo a falo tana ganinsa tace, "Ina fatan yau kaje ka duba jikin yarinyar nan" Har zai shige part d'insa ya dakata Ya kalleta "Wace yarinyar kike cewa ba lafiya?duk kinbi ki dameni banje gaida ita ba yarinyar da naje na sameta ita da saurayi suna firan soyayya..." Caraf Gwaggo mi'kewa tayi tana fad'a "A'a kaga nifa banason sharri wace yariyar ne keda saurayi?bana son 'kazafi wallahi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. Page2️⃣0️⃣ "A'a kaga nifa banison sharri,wace yarinyar ce keda saurayi?Bana son 'kazafi wallahi" Bai tanka Mata ba Kai tsaye ya nufi part d'insa don bazai iya biyewa Gwaggo ba. Bayan Inteesar ta shiga gida d'auke da ledojin da Usman ya kawo mata ne,Umma ta kalle ta ita da ledan hannunta tace, "Amso magani nan waje shine kika kwashe mintuna a wajen? Sannan wad'annan ledojin ne na magunguna?" Zama tayi akan tabarmar tare da ajiye leda,gabanta ne ya fad'i lolacin da ta zazzage d'ayar ledan ganin Turarruka kala-kala da sauran kayan kwalliya kala-kala masu yawa,juyawa tayi ta kalli Umma da ta zubawa kayan ido tana kallon kayan tana kallon Inteesar. "'Bud'e d'ayar ledan mugani abunda ke ciki" Jiki a sanyaye ta bud'e d'ayar ledan ta zazzage abunda ke ciki a gefe, nan ma zubawa kayan ido tayi ba kowane magani kayan ciye-ciye ne kawai.Snacks ne da su Biscuits da chocolate da sweet,idanu Ummi ta zuba Mata ba tare da cire idanunta daga gare ta ba.Ganin hakan yasa tayi narau-narau da ido hawaye na tsiyaya daga idanun ta cikin rawar murya tace, "Umma wallahi bansan abunda ke ciki ba sai yanzun,nidai Kira na yayi a waya yace mani wai doctor ya bayar da magani a bani shine naje ka'ba duk a tunani na magunguna ne a ciki,wallahi bansa cewa abunda ya kawo ba kenan sai yanzun" Shiru Umma tayi tana nazari kafin daga bisani tace, "Ya akayi ya samu number wayar ki kuma waye ya nuna masa gidan Nan?. " Shiru tayi tana kallon fuskar Umma kafin daga bisani ta bata labarin yadda yazo asibitin da yadda yadda d'auki number ta hanyar saka number sa wayar tata ya Kira number sa har ya samu number ta,da yadda yadda zaizo ta hana shi ya nuna Mata cewar magunguna Doctor ya bada a bata hakan yasa ta kwatanta masa gidan su Bata San cewa uzirin sa zai kawo sa ba. Umma dai shiru tayi kafin tace, "Wannan ya zama na farko kuma na 'karshe kada na sake ganin irin makamancin wannan da ya faru" Kai ta jinjina tare da cewa " insha Allah" "To madalla kwashi kayan kikai d'akin ki" Tattara kayan tayi ta nufi d'akinta da su,Umma ma d'akinta ta shige, Inteesar naman zaune ta fa'd'a suniyar tunani sai ga Mufida ta shigo da'akin bakinta d'auke da sallama tana rik'e da leda a hannunta k'arasawa tayi ta zauna gefen Inteesar ta dafa kafadarta,firgigit ta dawo daga suniyar tunananin da ta shiga, Mufida ta kalleta tace, "Lapiya kuwa? me yake damunki haka haka ?" Murmushi tayi tare da kallon ledar hannun Mufida tana fad'in, "Har kin amso muna d'inkin ankon bikin ne?" "Wannan bashine amsar tambayar da na maki ba, cewa nayi meke damunki idan kuma yanzun mun Fara 'boyewa junan mu sirri ne to shikenan" Murmushi tayi tare da dafa kafadarta tace, "Haba aike ma kinsan ba abunda muke 'boyewa junan mu ba sirrina da baki sani ba haka ma ba naki wanda bansani ba,wani al'amari ne ya d'an sani cikin tunanin da kikaga ina yi." Bata labarin yadda sukayi da Usman tayi har zuwan Muhdeen da yadda Umma bataji dad'in ganin kayan nan ba,duk sai da ta sanar da Mudida.Mufida kam janyo ledojin tayi ta bud'e ta ciro chocolate cake da Biscuit ta Fara ci tana ci tana magana. "To waishi Usman d'in meye nufin shi akanki kodai ya fad'a ne." Ta k'arasa maganar tana dariya,dukan wasa Inteesar takai mata tare da cewa, "Ni yanzun buri na bai wuce nacigaba da karatuna ba gsky dan kwata- kwata bana ma mafarkin aure yanzu. " Caraf Mufida tace, "Yauwa kin ma tuno Mani da labarin da nake son baki,Albishirin ki". Da sauri Inteesar tace goro tana murmushi Don tunanin ta labarin da zai sanyata farin ciki ne,Mufida tace , "Wallahi nayi matarkin auren ki amma yayana kika aura". Take far'ar fuskar Inteesar ta d'auke. "Wani yayan ki na aura?" Kallonta mufida tayi ganin yadda ta sauya lokaci guda tace, "Ina da wani yayan da ya wuce Yaya Muhdeen ne?" Fuskar Inteesar ta kalla taga annurin fuskar ta d'auke cikin mamaki tace, "Meye kuma na 'bata rai dan kawai nace nayi mafarkin kin auri Yaya na? kuma Koda na fad'awa Mummy tace itama duk lokacin da zatayi mafarki da matar Yaya Muhdeen ke take gani a mafarkinta " Ta'be baki Inteesar tayi tace, "Kodayake mafarki ba gaskiya bace k'arya ce, Amma ko a mafarki naga wannan mugun yayan naki na farka sai nayi sadaka." Sake baki Mufida tayi tana kallonta damamaki abun ya d'an Sosa ranta Amma sai ta share tacigaba da shan chocolate,zuwa jimawa kad'an ta kalli Inteesar tace, "Wai ke yayana kikeyiwa k'iyayya har haka?mutumin da Mata suke neman sa da kud'in su,aike wallahi idan ma kika samu miki irin Yaya Muhdeen abun alfahari ne a gurin ki.Domin shi miji ne na nunawa sa'a,wasu ma da suke masa kallon balarabe wad'anda basusan asalin sa ba,domin ya had'u ta ko'ina koke da kike ganin ke wata kyakkyawa ce baki Kai Yaya na ba,har kike wani neman tsari dashi,shi wannan Usman d'in da kike kulawa ko kwatakwacin kyawu da had'uwar Yaya na baikai ba. Inteesar ta ta'be baki tace, "Ni kyau baidameni ba Hajiya yaje yayi ta fama da kyawun nasa 'yan matan da suke ribibin sa suje suyi tayi,ke nifa bana son namiji kyakkyawa " Mufida ce tayi wata dariyar raining hankali. "Eh dole kice baki son namiji kyakkyawa tunda baice yana sonki ba" "Taya Mai zaice yana sona mutumin da ya tsane ni a rayuwa baya k'aunar gani na nima ba Wanda na tsana sama dashi a rayuwa" "Inteesar yaushe kika koyi yiwa mutum sharri? Yaya Muhdeen d'inne ya tsane ki me yayi maki na tsana?" Murmushin yak'e tayi ta kalli Mufida tace, "Ba Zaki Gane bane,tunda ba a gaban kowa yakeyi ba sai yaga ba idon mutane yakemun cin kashin da yakeyi,kuma ko na fad'a maki yanzun ma ba Zaki yadda ba.Amma zan fad'a maki Abu d'aya saboda Yaya Muhdeen na d'auke k'afata da zuwa gidan ku,Amma kukayi bina keda Gwaggo har kuka gaji,Amma yanzun tunda ya kusa aure da zaran yayi aure ya tare da matarsa a sabon gidan sa zaku cigaba da ganina a gidan KU,Amma gaskiya yayan ki ya azabtar dani a baya bana k'aunar ma mu had'a inuwa d'aya dashi." Allah sarki bansan meye ya maki ba,kuma baki fad'a Mani ba Amma inaji a jikina kece matar da Yaya na zaiyi rayuwa da ita. *KUYI HAKURI DA WANNAN KILA KUJINI ANJIMA*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. Page2️⃣1️⃣ "Allah sarki bansan meye yayi maki ba,kuma baki fad'a Mani ba amma inaji a jikina kece matar da yayan mu zaiyi rayuwa da ita. Wani kallo ta watsawa Mufida ba tare da ta sake cewa komai ba ta kanyo ledar da Mufida ta shigo da ita,kayan ta fito dasu wad'anda suka Kai d'inki ranar da Usman ya kad'e ta da mota,duka d'inkin iri d'aya akayi masu tun daga Kan atamfa da material da less d'in duk dinkunan iri d'aya akayi masu, tundaga Kan ankon yinin biki har zuwa na dinner da lunching.harda wani shadda da Mummy ta siye masu su biyu kawai zasuyi ankon , Inteesar taji dad'in ganin kayan sosai tsabar farin ciki rungume Mufida tayi tana godiya.Mufida ta kalle ta tare da zame jikinta daga nata tace, "Nidai sake ni don naga alamar k'arfi ya ishe ki,kuma da kike mani godiya ai ba nice zakiyi wa godiya ba, Mummy ce,don ita ta siye Mana kayan kuma kuma ta biya kud'in d'inkin.Kuma tace tasa akawo mana gyalulluka da takalma jakka wad'anda zasu shiga da kayan." Murmushi Inteesar tayi tana fad'in , "To sai dai kece zaki saka gyale,amma banda ni don kinsan cewa Hijab nake sakawa." Ta janyo less d'in purple colour ne wanda yake da ratsin milk colour tana fad'in, "Kinga Hijab d'in da Mummy ta siye mani last month Milk colour ne dama ban ta'ba Sanya shi ba,kinga zai shiga da less d'in." Harara Mufida ta watsa mata. "Wane irin Hijab kuma?kinsan Allah ba Hijab d'in da zaki saka gyale zamu saka iri d'aya,duk da nasan baki saba ba amma lokacin bikin nan kam dole kiyi hak'uri .Don Wallahi so nake komai namu ba ban banci komai ya kasance iri d'aya zamu saka,Don so nake mu kece raini a bikin nan.Sannan kuma gsky dole ki koma gidanmu da zama har a gama sabgar bikin nan." Da sauri Inteesar ta kalleta da niyyar bud'ar baki tayi magana,amma sai taga Mufida ta had'e fuska ta ajiye Mata kayan ta nufi hanyar fita. Tana jin sanda Mufida ke yiwa Umma magiya akan tabar Inteesar tayi kwana biyu a gidansu kuma Umma ta amince da hakan. cikin farin ciki Mufida tabar gidan. 'Bangaren Muhdeen kuwa Shima sai shirye-shirye yakeyi da abokan sa,dama babban abokinsa d'an uwan sa ne jabir sai kuma abokan su guda biyu Salisu da Bilyaminu,suna ta sabgogin bikin abokin nasu ba kama hannun yaro. Yau ne suka shirya inda zasu had'u da k'awayen Amarya ,don suji abubuwan da suke buk'ata na hidimar biki. Su Hajiya Gwaggo kuwa,gatanan dai ba yabo ba fallasa,ita bata farin ciki da auren kuma bata bak'in ciki.Yayinda bak'i da suka zo daga garuruwa musamman mutanen garin Kontagora da Abuja duk sun iso,k'anwar Dady wato Hajiya Maryam tazo da 'ya'yanta tagwayen'yan mata Azeeza da Azeema suma bazasu wuce sa'annin Mufida da Inteesar ba Asiya ma tazo don bikin yayi dai-dai da hutunta .Hajiya saudat matar Alhaji Adam wato mahaifiyar Jabeer ma ta iso da suran dangi da suke garuruwa duk sun iso. Mufida ce ta janyo tagwayen k'anwar Dady Azeema da Azeeza suka nufi gidansu Inteesar,dama tunda suka iso suke tambayarta ina Inteesar,don sun saba ganin Pic d'inta idan Mifida ta d'ora a status ko a dp don akasari tare suke d'aukar photo,suna kuma k'aunar Inteesar har cikin ransu. 'Bangaren amarya kuwa nan ma shiri sukeyi ba kama hannun yaro, k'awayen ta kuwa sai santin ango sukeyi duk da yawancin su basu ta'ba ganin Muhdeen a zahiri ba sai photo da suke ganin sa, k'awayenta biyu ne kawai suka San Muhdeen a zahiri Jummy da shila, kasancewar sune manyan k'awayenta kuma akasari suna yawan zuwa gidansu Sumayya wata rana su tarar da Muhdeen yazo suna tare,wata rana kuma shine zaizo ya tarar dasu sunso wurinta. Koda Su Mufida da Azeema da Azeeza suka k'arasa gidansu Inteesar sun tarar da ita ta gama wanke kwanukan wanke-wanke ta shiga dasu kichen d'insu dake tsakar gidan tana fitowa suka had'a ido,sallama suka shigo cikin gidan, Inteesar ta amsa masu tare da tunanin ina tasan wad'annan Tagwayen masu matuk'ar kama da juna,take ta tuna cewa a wayar Mufida ce take ganin pic d'in Tagwayen.Murmushi suka sakar Mata yayinda itama ta mayar masu da marttanin Murmushin tace, "Oyoyo manayan bak'i ne mukayi yau a gidan namu haka?" rungume ta sukayi Azeema ta rungumeta ta ta gabanta yayinda Azeeza ta rungumeta ta bayanta tamkar ba yau suka fara ganinta ba.Lokaci d'aya suka saketa fuskokinsu d'auke da murmushi, Azeema tace, "Inteesar mun same ku lafiya?" Cikin farin ciki da jindad'in ganin su ta bata amsa. "Lapiya qalau wallahi,sai dai bansan dawa nake magana cikinku ba Azeeza ce ko Azeema?" Murmushi Mufida tayi kafin ta bata amsar cewa "Kina magana ne da Azeema" "Ayyah Masha Allah sannu da zuwa Azeema" Ta maida dubanta ga Azeeza wacce ke karanta message a wayar ta. "Sannu da zuwa Azeeza fatan kun iso lafiya?" "Lafiya lau wallahi Inteesar,ai muna d'an hutawa kad'an mukazo don muganki" "Aiba Wai saboda ganin ta kad'ai mukazo ba,munzo d'aukarta ne yau zamu tafi da ita gidanmu can zatayi ta kwana sai bayan biki sannan zata dawo gidansu" Murmushi Azeema da Azeeza suka sake tare da cewa " hakan yayi" Inteesar ta fara magana tana fad'in "Ba inda zanje yau sai dai gobe idan za'ayi lunching sai ku biyo tanan mutafi" Harararta Mufida tayi sama da kasa. "Ai baki isa ba,dama na nemi izinin Umma tun wancan ranar,kuma ta amince muje sai bayan biki ki dawo,bayan haka jiya da na shigo na k'ara tuntu'bar ta da maganar tace ba komai har Abba ma ta sanar dashi.Don haka ki tattaro muna d'inkunan bikin mu kizo mu tafi. Shiru Inteesar tayi tana nazari don ba haka taso ba,don kwata-kwata batayi niyar komawa gidan ba,saboda alwashin do da taci Kan cewa ba zata je gidan ba sai bayan Muhdeen yabar gidan,amma yanzun kam ba yadda zatayi don Mufida ta d'aure ta da jijiyoyin jikinta.Mufida ce taja hannun Azeema da Azeeza. "Kuzo mu shiga mu gaida Umma" Binta sukayi harda Inteesar,bakunan su d'auke da sallama,bayan ta amsa masu ne suka shiga,tana kwance kan gadonta dama duk maganar da sukeyi a tsakar gidan a cikin kunnenta yake,zama sukayi kan tabarmar suka gaishe ta cikin girmamawa.Ta amsa masu fuskarta a sake Mufida ta fara magana tana fad'in. "Umma wad'annan 'yan uwa na ne,yaran k'anwar Dady ce,'yan biyu ne Azeema da Azeeza" "To Masha Allah,kunzo lafiya ya hanya?" Dukkan su biyu suka amsa da "Alhamdulillah" "Umma dama munzo zamu tafi da Inteesar" Cewar Mufida yayin da take kallon fuskar Umma, "Badamuwa ku tafi Allah yasa a watse taro lafiya yasanya alkhairi" Ameen suk amsa yayinda Inteesar tayiwa mahifiyarta sallama suka mik'e suka nufi hanyar fita su duka. 'Dakin Inteesar suka shiga inda ta kwaso d'imkunan bikin zata d'aiki kayan sawarta Mufida ta hana Wai tayi amfani da nata,daga nan suka nufi gidansu Mufida. A yammacin ranar bayan suk sunyi wanka sun canza kayan jikin su, Azeema da Azeeza wani material pink colour suka saka riga da siket, yayinda Mufida ta saka doguwar Riga na atamafa, Inteesar kuwa rigar Mufida ta abya ta saka Green wanda Muhdeen ya siyo ma Mufida a Dubai lokacin da suka je siyen kayan lefe,kayan sun burgeshi Matuka amma Sumayya tace bata son kayan,hakan ne yasa ya siyewa K'annen sa Mummy ta raba masu kayan su uku Asiya,Mufida,da kuma Inteesar.Suna zaune akan gado suna suna fira ne Inteesar ta mik'e ta bud'e fridge din d'akin ganin ba ruwa sai lemuka ne yasa Kai tsaye ta fita d'akin Don zuwa kitchen ta d'auko ruwan da zata sha.Dai-dai tana k'ok'arin shiga kitchen d'in Dai-dai Muhdeen ya shigo zai wuce part d'insa Yana rik'e da waya a kunnensa Koda yaga Inteesar zata shiga kitchen a tunananin sa Mufida ce,hakan yasa ya janyo hannunta ba tare da ya kalleta ba yace, "Yauwa Muje ki gyara Mani part d'ina,duk da ba wani iya gyara kikayi ba yafi babu,zanyi manaji hakanan" Bai kalli fuskarta ba yaja hannunta suka nufi part d'insa ,sai da suka shiga falon ya saki hannunta yana cewa, "Ki fara gyara falon" Daga nan ya wuce cikin bedroom d'insa,binsa tayi da kallon mamaki. Daga nan sai ta fara k'ok'arin gyaran falon,cikin k'ank'anen lokaci ta gama gyara falon fess ta kunna turaren wuta take falon ya d'auki k'amshi.Dai-dai lokacin ya fito har wannan lokacin ya fito hannunsa rik'ke da waya yana danne-danne a wayar kallon falon yayi sannan ya maida idonsa akan wayar yace, "Dama kin iya gyara waje iskancine kesa idan an sakaki bakiyi dakyau sai yau da kikaga damako?To shiga ciki ki gyara bedroom d'in" Har yakai K'arshen maganar bai d'aga ido ya kalleta ba.kwatsam sai yaji saukar muryarta a kunnensa sa tana cewa, "Nikam wallahi bazan shiga ba" Da sauri ya d'ago Kai yana kallonta da mamaki,domin shi a zatosa Mufidace ganin kayan da ya siyo Mata a Dubai ne a jikin Inteesar yasa yayi tunanin Mufida ce a she ba ita bace Inteesar ce tasa kayan Mufida.Had'e fuska yayi yana cewa "Kee ubanwa ya kawoki d'akina?" Kallon mamaki take masa don gani take ya raina mata hankali. "Tukunna ma dai ba kince idan na sake ganinki a gidan nan duk abunda naga dama nayi maki ba?ke ga mara kunya fitsararriya ko?to yau zakiga kuwa abunda zanyi maki" Gaban Inteesar ne ya fad'i ganin ya nufota gadan-gadan fuskar nan a murtuk'e ba sassauci a tare da shi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Page2️⃣2️⃣ Gaban Inteesar ne ya fad'i ganin ya nufota gadan-gadan fuskar nan a murtuk'e ba sassauci a tare da shi. Tattare k'asar rigarta tayi da nufin guduwa,kunsan abu ga dogon mutum ai taku biyu yayi ya isa gare ta, kafin ta ankare ganinsa kawai tayi a gabanta yayi mata dirar mikiya.Hannayenta duka biyu yasa ya murd'e mata hannayenta tare da maidasu baya,hakan yasa ta bud'e baki ta saki k'arar azaba da sauri yasa hannunsa d'aya ya toshe mata bakii, yayin da d'aya hannun yana rik'e hannayenta da ya murd'e.Girgiza kai kawai take yi na azaba yayinda Idanuwanta suke tsiyayar da hawaye.girgiza kai taci gaba da yi idanunta na cigaba da zubar da hawaye.Girgiza masa Kai tacigaba da yi amma ko a jikinsa baiji tausayinta ba. Suna cikin wannan halin ne Jabeer ya turo k'ofar falon ya shigo,turus ya tsaya yana kallon Muhdeen cikin tsananin mamaki ya ce "Meye haka?wanna wani irin rashin imani ne?" K'arasawa yayi ya cire hannun Muhdeen daga rik'on da yayi wa Inteesar.yana sakinta ta zube a wurin ta samu damar fitar da kukan zucin da takey.Jabeer harara ya watsa masa . "Yanzun meye kake aikatawa haka? Zaka kama 'yar mutane kana azabtar da ita akan meye?" "Ba azabtar da ita nayi ba tarbiya nake koya mata." "Eh k'warai kuwa tarbiyya kake koya mata irin tarbiyuar da kake koyawa Asiya da Mufida,idan Asiya da Mufida sukayiwa laifi haka kake ladabtar dasu?" Ya k'arasa maganar yayin da yake kallon Muhdeen. "Ai idan sune basasu yi mani irin abunda yarinyar nan tayi Mani ba ballantana har na d'auki irin wannan hukuncin akan su." Girgiza kai Jabeer yayi tare da ce wa, "Duk da bansan me tayi maka ba kuma nansan alak'ar dake tsakanin ku ba,amma da dukkan alamu yarinyar nan bata da rashin tarbiyya ko rashin kunya.Ni nasan halinka fa idan ka d'aurawa mutum karan tsana,wata kila ka kure ta ne shiyasa har takaiga tayi maka haka." Don't tell me that,how dare you gaban yarinya kana gaya mun maganganu tare da bani laifi?salon ta k'ara raina ni ko?." Ba tare da Jabeer ya sake wata magana ba ya durk'usa gaban Inteesar dake ta k'ok'arin mik'ar da hannayen ta amma ta kasa,har lokacin kuka take,cikin tausayawa ya kalleta ya ce, "Sannu ko?" Kai ta gyad'a masa alamun yauwa ba tare da ta yi magana ba. "Cikin tausasawa ya ce, "Me kikayi masa ne?" Cikin muryar kuk ta fara magana. "Nidai haka nan kawai ya tsaneni banyi masa laifin komai ba, shiyasa ma nace bazan sake zuwa gidan nan ba sai yayi aure yabar gidan su Mufida suka matsa nazo." Cikin tausasawa ya girgiza kai. "Kenan ke k'awar Mufida ce?" Kai ta jinjina masa alamar eh,da ya ke shi Jabeer baisan Inteesar ba kasancewar duk lokacin da yake zuwa bayan sallar isaha'i ne,kuma lokacin Inteesar ta riga tabar gidan. "To amma me kikazo yi a d'akin sa?" "Shi ne ya janyoni wai nazo nayi masa gyaran falo" Kai Jabeer ya jinjina. "Okay.yanzun ki tashi ki tafi,sannan ina mai matuk'ar baki hak'uri a madadinsa" Tashi ta yi dak'yar ta dafa hannayen ta mik'e tsaye, ta nufi hanyar fita ta fice Jabeer yabi ta da kallon tausayi.Gwaggo ne ke zaune a falo su day wasu Mata k'awayen Mummy su uku,ganin Inteesar ta fito daga part d'in Muhdeen idanunta sunyi ja alamun kuka yasa ta mik'e dakyar,ta nufi Inteesar ta ce, "Subhanallahi 'yar albarka me ya same ki?me kikayi je yi d'akin Muhammadu?me yayi maki? " Murmushin k'arfin hali tayi tare da ce wa, "Bakomai Gwaggo kada ki damu" Ta k'arasa maganar tana mai nufar k'ofar kitchen,bayan ta shiga kitchen d'in fridge ta nufa ta d'auko goran robar ruwa tare da tsiyayawa a kofi tasha.Sai da ta k'ara koge fuskar ta inda hawaye ya gangaro da bayan yatsunta sannan ta nufi da'akin Mufida. Da sallama d'auke a bakinta ta shiga,kallo d'aya Mufida tayi mata da sauri ta mi'ke ta isa gare ta tare da dafa kafad'arta. "Inteesar lafiya kuwa me ya same ki naga idon ki alamun kinsha kuke?" Murmushin k'arfin hali tayi tana kallon Mufida ta ce, "Kada ki damu kaina ne ke Mani ciwo yanzun zan d'an kwanta,idan na tashi zuwa anjima zai sake ni" Azeeza ce ta ce. Ikon Allah daga fitar ki zuwa kisha ruwa shiru baki dawo ba sai yanzun kika shigo kanki na ciwo.Dama kina kukan ciwo ne kamar k'aramar yarinya?" Ta k'arasa maganar cikin yanyin zolaya.Azeema ce ta d'aura da ce wa. Ni da naga shiru-shiru Bata dawo ba na tambayi Mufida cewa ga Inteesar shiru,take cewa kila ta tsaya wajen mutumiyarta Gwaggo" Mufida ta girgiza Kai tare da cewa, "Nidai nasan bakiyin kukan ciwo sai dai idan 'boye mana zakiyi" Asiya dake tsaye bakin k'kofar hannunta na rik'e da handle d'in k'ofa ce tayi tsuki tare da fad'in "Amma kuma da naci kuke,tace bakomai ta a tafi a hakan mana haba da Allah.yauwa ni ba wannan ya kawoni ba,wace ce ta d'auki chargern wayata? Azeeza ta ce Nice Aunty Asiya na mance da tawa ce,na shiga ban ganki ba shine na d'auko" Ta k'arasa maganar tana nuna socket d'in da tasaka charging. "Okay badamuwa idan kin gama ki kawo mani" Daga nan ta juya ta fice, Inteesar kwanciya tayi akan gadon ta juya masu baya. 'Bangaren Gwaggo kuwa ganin Inteesar ta fito 'bangaren Muhdeen Tana kuka yasa ta nufi 'bangaren nasa.ko sallama batayi ba ta tura k'ofar ta shiga. "To shugaban mugaye na Africa,uban me kayiwa 'yar mutane ta fito tana kuka?" Shiru yayi bai kalleta ballantana ya amsa Mata,bada Kai nake magana ba ka yi mani shiru?nasan dai yarinyar nan bazata ta'ba aikata wani abu da zaisa kayi mata azaba ba,sai dai idan kuskure aka samu,haka ranar ka akan ta watsa maka yayu a rashin sani ka kamata kahau yarfa mata maruka kamar Allah ne ya aiko ka,yanzun ma ka kamata kana jibga to a kunnen ubanka d'an banza mai k'irar yahudawa." Ba tare da ya kalleta ba ya fara magana. "A halin yanzun Ina cikin farin ciki,saboda haka kada ki ruguza farin mani cikin da nake ciki.karki manta nifa ango ne" Harararsa tayi ta ce, Dalla rufe mani baki ina angon yake,sai dai muna angon don ni banga cikakken ango anan ba,wata kila idan zakayi auren da ake kira aure zan ganka cikakken ango Amma yanzun angogo na gani.Dan zaka auri wananna tambad'ad'd'yar yarinyar zaka kira kanka ango. Take ya murtuk'e fuskar sa don ya tsani a fad'i kalma mara dad'i akan Sumayyarsa. Zata bud'e baki da niyyar tayi magana,yayi saurin dakatar da ita da fad'in. "Gwaggo a halin yanzun kin riga da kin 'bata mani rai saboda haka kada ki tunzurani." Ri'ke baki tayi tana kallosa. Muhammadu duka na za ka yi ko me?na tunzura kan d'in,ko uwarka da ubanka za su ce kada na tunzura su ballantana kai.?" Jabeer ne ya k'arasa gaban Gwaggo cikin sigar rarrashi ya fara magana. "Allah ya huci zuciyarki Gwaggo kiyi hak'uri ki tafi kada ki biyewa Muhdeen don Allah kinsan halinsa." "Halinsa na banza ba,yanzun ka fad'a mani gaskiya me yayiwa yarinyar nan?"don nasan ba abunda zatayi masa bak'ar zuciyarsa ce da mugun halinsa ne kawai." Ahljiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa, Gwaggo idan har nace ga abunda tayi masa nayi k'arya,nadai zo na tarar ya murd'e mata hannaye ya lan'kwasa mata su baya tare da toshe Mata baki wallahi iya abunda na sani kenan." Jinjina Kai tayi "To Allah yayi maka Albarka ya sauke matar ka lafiya ta Haifa maka d'anka namiji, mai sanin darajar mutane da neman albarka irinka." Murmushi yayi tare da cewa, "Ameen Gwaggo." "Ni banma tambayeka ya jikin matar taka ba ko?anya ma zata iya zuwa bikin nan kuwa?" Girgiza kai Jabeer yayi yana dariya ya ce, "Ba zata iya zuwa ba Gwaggo saboda cikin nan yana wahalar da ita." Kai ta jinjina tare da ake tambayar sa. "Cikin nan nata wata nawa ne?" "Wata biyar kenan Gwaggo" "Auren KU watanni biyar kenan ko" Kai ta jinjina tana dariya ta ce, "Dakyau namijin gaske,ashe dai jikan nawa ba rago bane,aure wata biyar ciki ma wata biyar lokacin da kukayi watanni tara da aure lokacin cikinta watanni tara sai haihuwa kenan. Wato baka da wasa kana jefa k'wallo kenan ta shige raga lallai yaron nan ka cika namiji ba lusari bane kai.Ai dam..." Muhdeen ne ya katseta ta hanyar cewa. Ba'a irin wad'annan maganganun a gaba na,don na dad'e da sanin cewa baki san alkunya ba." Kallon shek'ek'e Gwaggo tayi masa ta ce, "Ubanwa yace dole sai ka saurare mu ka fita mana." "Kuzo har cikin d'aki na sannan ku ce na fita? ai ba zamanin mulkin mallaka muke ciki ba.Koda yake dama ke nasan haka kike shine ma da ya biye maki." Juyawa yayi ya kalli Jabeer ya nuna sa da hannu ya ce, "Kai baka san waye Gwaggo ba ko? shiyasa har take tambayarka sirrin gidanka kake fad'a mata,sai ta dinga terere da sirrin gidan ka.Idan ka biye Mata cewa zatayi ka fad'a mata me ya faru a first night d'in ku,kaga jata ku tafi can d'akinta ku karasa zancen ku ba'a nan ba." ya k'arasa maganar yana shigewa bedroom.Ta bishi da harara tana cewa, "Ai sai dai ka shiga ciki,kuma saura kuma naga naka k'wazon jarumi ne ko kuma lusari." Daga Nan ta fice daga d'akin tana sababi,Kai tsaye d'akin Mufida ta nufa nufa ganin Inteesar kwance tana barci yasa ta fita ko gaisuwar da su Azeema suke mata Bata amsa ba ta fice. Washe gari gidan ya cika da jama'a 'yan uwa da abokan arziki ana ta shagulan biki.inda kowa yake cin abincin da ransa yake so yasa abunda ransa ke so. Da misalin karfe hud'u na yamma ana ta Shirin zuwa reception kowa ya saka ankon material d'in da aka fitar saboda reception d'in kowacce tana shiga mitoci ana waucewa dasu.Su Inteesar kuwa suna cikin d'akin Mufida su hud'u. Mufida, Inteesar,Azeema da Azeeza.Sunci anko inda Azeeza ta tsantsara masu kwalliya sunyi matuk'ar kyawu sosai sai shek'i da k'amshi suke inda suka inda suka dinga fama da Inteesar akan ta dage lallai dole sai ta saka hijabi ita kuma ta dage,dakyar suka shawo kanta ta har ta amince zata saka gyalen.Gashi kayan sun bayyana tsantsar kyawun surar jikinta kowacce ta d'auki wayarta da posa d'inta suka fito. Koda suka k'araso harabar gidan duka motocin gidan ba ko d'aya duk an tafi dasu tundaga Kan motar Mummy har Motocin Muhdeen ba ko d'aya .Domin duk an tafi wajen reception motar Jabeer kawai suka gani sai motar Asiya wacce fitowarta kenan daga cikin gidan ita da k'awayenta guda biyu,tana k'arasowa ta kallesu tace, "Au kuma baku tafi ba?" Mufida ce ta kalleta tace, "Wallahi bamu tafi ba tunda gaki sai mu biki" girgiza Kai tayi tare da cewa, "Sai dai dukkanku motar ba zata d'uke mu duka ba,don ga friends d'ina guda biyu sannan ga ku hud'u kinga sai dai mutum d'aya ta hak'ura ta hau keke napep" Mufida ta kallesu ta ce, "Badamuwa ni zan hau napep ku ku shiga motar." Kai Asiya ta girgiza "A'a sai dai Inteesar ta hau napep don bazaiyuwu ba kibar su Azeeza baku tare." "Gaskiya Inteesar ba zata hau napep ba." 'Daga kafada Asiya tayi alamun I don't care d'innan sannan ta kalli Mufida ta ce, "Shikenan sai ku tafi daga ke har ita kuhau napep d'in." Dai -dai lokacin Muhdeen ya fito tare da Jabeer,Jin abunda suke fad'a yasa Jabeer tambayarsu. "Wace ce zata shiga napep?" Mufida ta ce "Motar ce bazata d'auke mu duka ba saura mutum d'aya." Idanun Jabeer ne suka akan Inteesar ya zuba Mata idanu ba ko k'yaftawa,gaba d'aya ta tafi da hankalin sa ya kasa d'auke idanunsa akan kyakkywan surar jikinta.Muhdeen ya lura da kallon da Jabeer ke mata hakan yasa ya buge masa hannu Wanda yasa shi dawowa hayyacinsa.Muhdeen ya baibi ta kansa ba ya wuce ya shige bayan motar ya zauna. Jabeer ya kalli Inteesar ya ce, "Inteesar kizo mu tafi a motata" Kallon Mufida tayi,sai Mufida tayi mata alamun taje ta shiga.Hakan yasa tabi baynsa inda ya bud'e Mata marfin gabar motar ta shiga ta zauna.Mufida kuwa suka shiga na Asiya.Cikin sanyi murya ta ce, "Nagode" Murmushi Jabeer ya sakar mata tare da cewa "Bakomai Inteesar." Muhdeen ne ya had'e fusaka ya ce, "Motar da zaka d'auki Amarya da Ango ne zaka d'auki wannan kucakar yarinyar to aiko sai dai ta fita." Jabeer ne yayi masa irin kallon nan na kayi kad'an sannan yace, "Wallahi bazata fita daga motar Nan ba sai dai Kai ka fita." 09065327995Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi ( Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Page2️⃣3️⃣ "Wallahi ba zata fita daga motar nan ba sai dai Kai ka fita." Kallon mamaki Muhdeen yayiwa Jabeer don Bai ta'ba tunananin jin wannan maganar daga bakin Jabeer ba. "Yanzun akan wannan yarinyar kake fad'a Mani magana?don kaga friends d'ina sau d'auki motacina zasuyi amfani dashi basoda nace zanbi naka kai ka isa ka fad'a mani mota?kaima kasan motocin da nake hawa sunfi naka, ballantana ka fad'a Mani magana" Murmushi Jabeer ya ce "Bakomai ai zakaranka rak'uminka,kardai ka 'bata ranka a banza a wofi don yanzun zamuje mu d'auko maka amaryarka tana zaune gefenka yayin da ni kuma Inteesar tana zaune a gefe na." Banza dashi Muhdeen yayi bai tanka masa ba, yayinda Jabeer kan d'an ja Inteesar da fira,duk da ba wani biyeshi yakeyi ba idan daga eh sai A'a, a hakan har suka k'araso k'ofar gidan su Sumayya amarya nan suka tarar da d'aya daga cikin motocin Muhdeen a k'ofar Get d'in gidan,wanda abokin ango Bilyaminu ne ya tukota don d'aukar 'kawayen amarya.Bayan ansaka amarya cikin motar da ango ke ciki ne sauran k'awayenta suka shiga motar da Bilyaminu ya tuk'o,daya nan suka d'au hanya.Amarya kuma ta shiga Motar Jabir inda ta zauna kusa da angonta.K'amshin turarenta ne ya gauraye cikin motar murmushi suka sakarwa junansu .Jabir ne ya kalleta ta cikin mirror d'in dake cikin motar ya ce, "Amarya bakya laifi" Murmushi tayi tana fad'in "Koda na kashe d'an masu gida" Amsa ya maida Mata da cewa, " A'a sai dai idan baki kashe ba," Share shi tayi kamar bataji abunda yake fad'a ba,ta mayar da idanunta wajen duban angon nata cikin tsananin k'unarsa ta sakar masa murmushi cike da son sa ta ce, "Kayi kyau my heart" Murmushi ya mayar mata "Ai ban kaiki kyawu ba" Inteesar ce ta bud'e baki ta gaishe ta "Anty sumayya ina wuni" Dai -dai lokacin da Jabeer yaja mota suka bar wajen,sumayya cike da mamaki da takaici ta ce, "Wannan ba yarinyar nan bace, Inteesar?" Jabeer ne ya bata yayinda idanunsa ke kan hanya yana cigaba da tuk'i ya ce, "Itace mana dama kinsanta ne?" Ba tare da ta bashi amsa ba ta cigaba da magana "To me yasa ta biyo ku batabi sauran jama'ar sun wuce ba?dole sai motar da ango da amarya zasu tafi shi zata bi a matsayinta na wa?" "A matsayinta na mutum 'yar mutuwa,jikar rasuwa,kakar jana'iza.kamar yadda babu Wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yafi tsoron sa." Shiru tayi ta cika tayi fam cike da takaici. Kalaman Jabeer d'in kamar yana jirace da ita.Dama ta dad'e da zargin cewa Jabeer baya k'aunarta a tare da Muhdeen,kuma taci alwashin sai ta raba tsakanin su,bata gama tunanin da takeyi a cikin zuciyarta ba taji maganar Muhdeen yana cewa Jabeer "Wai kai Jabeer me yake damunka ne? so kake sai ka gusar mana da farin cikin da ke cikin zuciyarmu ne? ya kake neman ka dinga gayawa mutane magana san ranka ne?ko ko don kaga an shiga motar ka ne zaka nemi gaya mana maganar banza?dama kace da abokaina su d'auki motocina suyi zurga-zarga dasu ne dan kaci mana mutunci? To yanzun kayi parking nan mu sauka mubar maka motarka,zansa yanzun a kawo muna mota,kana ta faman gayawa mutane magana akan wannan kucakar yarinyar." Murmushi Jabeer yayi tare da cewa, "Idan ko zaka kira Inteesar kucaka ashe ko duka 'yan matan duniyar nan kucakai ne.don idan za'a tara mata d'ari to dakyar za'a samu biyar biyar kamarta." Ganin ransu yayi matuk'ar 'baci ne yasashi cewa "Kuyi hak'uri wallahi banida niyyar'bata muku rai,ku gafarceni." Ba Wanda ya sakeyiwa kowa magana magana har suka k'arasa wajen reception d'in inda aka gudanar da komai cikin tsari,inda amarya da ango suka zauna wajen zaman su aka rera masu wak'a aka rak'ashe aka lik'a nairori.bayan antashi ne, Muhdeen ya ce,shi bazai shiga motar Jabeer ba inda Salisu ya d'auke su a d'aya daga cikin motocin Muhdeen d'in.Inteesar kuwa dole ta sake bin Jabeer Don komawa gida. Akan hanyarsu ta komawa gida ne, Maryam matar Jabeer ta kirashi a waya Wai tana son shan agwaluma dan Allah ya siyo mata.bayan ya gama amsa wayar ya juya ya kalli Inteesar sannan ya maida dubansa ga driving d'in da yake yi ya ce, "Don Allah kid'anyi hak'uri zamu d'an biya wani waje na siyawa mata ta agwaluma sai mu biya nakai mata." Da sauri Inteesar ta kalle shi tare da cewa, "To amma da ka ajiyeni anan sai na samu napep na k'arasa gida don bazan iya binka gidanka ba." "Saboda me kina tsoron kada na cutar dake ko?" Shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta da suka sha jan lalle.Batare da ya kalleta ba ya sake jefa mata wata tambayar. "Zaki yarda ki rakani ko?" Nanma shiru tayi tana tunani, ita dai yau ta fara ganinsa lokacin da ya k'wace ta a hannun Muhdeen.Sai dai taji Mufida ta kira shi da Yaya Jabeer,kuma tana yawan jin sunan sa a bakin Mufida ko ranar da tayi rashin lafiya da su Mummy suka zo gaisheta taji Mufida na cewa daga gidan Yaya Jabeer suke wai d'an wan Mahaifinsu ne.sai dai duk da haka baikamta tabishi gidansa ba to amma kuma yana da mata kuma taji sanda matar take fad'a masa ya siyo Mata agwaluma Amma ya dace ta bishi kuwa?dama tare da Mufida suke ba zata damu ba. Tana cikin tunani taga ya d'auki wata hanya daban ,gani yayi yanayinta ya canza alamar Bata yarda dashi ba.Hakan yasa ya Ciro wayarsa bayan yayi parking a gefen titi.Lambar wayar Mummy ya lalubo ya danna mata kira, lolacin Mummy na zaune a d'akinta ita Mahifiyar Jabeer,kiran Jabeer ne ya shigo wayarta kallon Mahifiyar Jabeer d'in tayi ta ce, "Kinga Jabeer ne ke kira na kodai ya kira lambarki ne bai shiga ba?" 'Daga wayar tayi tare da cewa, "Hello Jabeer kun iso gida ne?" Jabir ya Bata amsa da cewa "A'a Mummy dama lokacin da zamu tafi reception ne naga su Mufida da tagwayen Aunty Maryam, so motar da zasu shiga bai d'aukesu ba hakan yasa nacewa Inteesar da bata samu wuri a motar ba ta shigo motata.Tunda ango da Amarya zan d'auka kad'a,to yanzun Angon ma a motarsa ya koma sai ni da Inteesar d'in mun kama hanyar dawowa Maryam ta kirani Wai tana son agwaluma,nacewa Inteesar bari na siye na Kai mata tunda munfi kusa da gidana,naga hankalinta bai kwanta ba tana tsoron na cutar da ita ne gashi yanzun magariba tayi ko zakiyi mata magana ko hankainta zai kwanta." Murmushi Mummy tayi tare da cewa, "Bata wayar" Mi'kewa Inteesar wayar yayi tare da sakar Mata Murmushi,amsar wayar tayi ta Kara a kunnenta ta ce, "Assalamu Alaikum." Jin muryar Mummy yasa ta sakin murmushi tana cewa "Ina wuni Mummy?" "Lafiya lau Inteesar ki kwantar da hankainki Jabeer kamar yaya ne a wajenki,bari ya siye abunda zai siya idan yakai mata sai ku dawo gida kinji?.Abunda yasa baki sanshi ba lokacin da yake zuwa lokacin ki tafi gida shiyasa baki sanshi ba,ki kwantar da hankalinki Jabeer ba mutumin kirki ne.Allahnya kawoku lafiya." "Ameen" Inteesar ta amsa tare da kashe Kiran,Mik'awa Jabeer wayar tayi taga ya shagala da kallonta saurin kanye idanunta tayi ta sunkuyar da kanta k'asa.Ajiyar zuciya ya sauke tare da amsar wayar,key yayiwa motar suka d'auki hanya.Bayan yayi parking wajen me agwalumar ya juya ya kalli Inteesar ya ce, "Kema zakisha agwalumar ne na siye maki." Cikin sanyin Murya tayi magana "A'a bana Sha." Fita yayi yaje ya siyo ya dawo rik'e da leda cike da agwaluma,dan. Inteesar tayi mamakin yawan agwalumar a zuciyarta tana mamakin yawan agwalumar da mutum d'aya zata sha.Bayan ya tada motar ne sun d'anyi tafiya kad'an sai yayi parking a wani k'ayataccen wajen siyar da abinci.ya kalleta ya ce, "Bari na d'anyo mana takeaway sai mu k'arasa gida."Ba ta ce komaiba ya fita yaje ya dawo da ledoji biyu a hannunsa,d'aya takeaway ne guda uku d'aya ledar kuma kayan tand'e-tand'e da lashe-lashe danginsu chocolate da snacks da ice cream da Biscuits ne a cikin.Yana shiga ya tada motar sai gidansa ya nufa,horn yayi Mai gadi ya bud'e masa gate ya shiga da motar,bayan yayi parking ne ya fito ya bud'e mata yayi don ta fito sai ta mak'e kafad'arta alamar bazata fito ba ya k'ura Mata yadda take tura d'an k'aramin bakinta ne ya bashi dariya ce mata yayi "To shikenan tunda ba zaki fito ba Ni zan shiga ciki kinji ana Kiran sallar magariba ni zan shiga nayi alwala sai naje masallaci na dawo sannan zamu tafi gida.kinsan lokacin sallar magariba gajeren lokaci ne dashi gara ma ki fito.Jin hakan yasa ta fito ,bayan motar ya bud'e ya d'auko ledojin yayi gaba tabi bayansa. A falo sula tarar da Maryam kwance kan doguwar, kujera tayi rigingine ta d'aura hannunta akan cikinta.Jin muryarsa yasa ta mi'kewa zaune don dama agwalumar take jira tasha. Jin sallamar muryar mace yasa ta d'aga kai ta kalli Inteesar,gabanta ne ya fad'i saboda yanzun ta sauka a online kuma tagani a status Mufida ta d'ora videon reception d'in da sukayi taga inda Jabeer ya fito daga gaban motarsa ya zagayo ya bud'ewa Inteesar ta fito daga gaban motar sa yana kallonta yana murmushi.Tare suka shiga wurin tana gaba yana binta a baya.Har tayiwa Mufida reply da cewa wace ce nan tare da miji na?Mufida bata amsa Mata ba don ta sauka online.Zaubawa Inteesar ido tayi tana tunanin meye tsakaninta da mijinta da tun d'azu suke tare har yanzun ya kawo Mata ita cikin gida. Murmushin yak'e tayi tare da cewa, " sannun ku da zuwa" Inteesar ce ta gaishe ta,ta amsa mata fusaka a sake ba yabo ba fallasa.Jabeer ya ajiye lesojin ka center carpet dake tsakiyar falon,ya kalli Maryam ya ce, "Madam ya jikinki?" Murmushi tayi tare da cewa "Da sau'ki." Ledar agwalumar ya d'auka ya ce, "Bari naje na wanko maki su kafin ki Fara shansu hakanan." Kichen ya nufa da agwalumar don wankewa, Maryam ta kalli Inteesar ta ce, "Zauna mana baiwar Allah kinyi tsaye." Inteesar tayi murmushi ta zauna Kan kujerar dake kallon Maryam,zauba Mata ido Maryam tayi tana kallon tsantsar kyawu irin na Inteesar kamar wata balarabiya,sai taji wani abu ya d'arsu a zuciyarta ta kasa gane kishi take da Inteesar ko meye?gashi dai yarinyar ta burgeta amma meye had'inta da mijinta?ta sake duba wayarta taga yanda Jabeer ya fito motarsa ya zagayo ya bud'ewa Inteesar sai kallonta yake Yana sakin murmushi.Jin ya dawo ne yasa ta ajiye wayar ta fara shan agwalumar.kallon Inteesar yayi yace bari nayi sallah sai na maidake gida ko?" Ya maida dubansa ga Maryam ya ce " ta shiga ciki tayi sallah ga takeaway nan idan ta idar da sallah taci abinci zan maidata gida." Daga Nan ya fice Maryam ta zubawa Inteesar ido kafin ta mi'ke dakyar tana yamutse fuska ta ce, "Zo mu shiga ciki." Ba musu Inteesar tabi bayanta har bedroom d'inta ta nuna Mata k'ofar toilet ta shiga ta d'auro alwala,Koda ta fito Maryam ta shimfid'a Mata sallaya ta aje mata hijab.Bayan ta Fara sallah sannan Maryam ta shiga ta d'auro alwala tana tafiya tana d'an dafa bango don jiri takeji. Bayan sun idar da sallah,Maryam tace da Inteesar taje taci abinci kafin ya dawo,tace ita ba zataci abinci ba ta k'oshi.Shiru-shiru Jabeer bai dawo ba Inteesar ta kagara sai da har aka Kira sallar isha'i suka idar sannan ya dawo.A falo ya tarar dasu ganin yadda yadda ajiye ledar takeaway haka ya same shi ya ce, "Me yasa bakici komai ba?" Mik'ewa tayi tare da d'aukar posan ta ta ce, "Na k'oshi,ka kaini gida kawai." Yadda tayi maganar ne ya burgeshi ya zuba Mata ido yana murmushi,Maryam ta lura da hakan sai tayi gyaran muryar da yasa ya kauda idonsa akan Inteesar ya maida kan Maryam.alama ya mata Wai meye?Kai ta girgiza ta kauda kanta gefe,hakan yasa yacewa Inteesar ta zo su tafi.Sallama tayiwa Maryam suka fice. Akan hanyarsu yayi parking dai-dai wani super market.kallonsa tayi ya kauda Kai tare da fita don kar ma ta tambaye shi,bud'e mata yayi tare da cewa "Fito" Kallon mamaki tayi masa tare da cewa " me zamuyi anan kuma?" "Turare zan siya" Ya Bata amsa a ta'kaice,ta koma jefa masa wata tambayar ta ce, "To ka maidani gida idan ka dawo ka siya,ko kuma kaje ka siya Ina jiranka a mota." Kallonta yayi yana cewa "Idan baki fito kin rakani ba bazamu bar nan wajen ba ko zamu kwana ne kuwa." Jin hakan yasa ta fito suka jera dab da zasu shiga taji an Kira sunanta,gabanta ne ya fad'i jin muryar Wanda ya kirata.Juyawa tayi da sauri ganinsa tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu ya zuba Mata ido. *DON K'ARIN BAYANI* 09065327995Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba.Idan suna ko hali yazo d'aya,to you gafarceni bada niyyar yin gakan nayi ba arashi mai kashe auran Wawa. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guii sarrafa mani shi ta kowace siga. Page 2️⃣4️⃣ Juyawa tayi da sauri ganinsa tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu ya zuba mata ido. A hankali ta furta sunansa "Usman" Murmushi ya sakar mata tare da yi Mata alama da tazo,kallon Jabeer tayi taga ita yake kallo ita da Usman.Cikin sanyin Murya ta ce, "Yaya Jabeer don Allah ina d'an zuwa 2 minutes." Kai kawai ya d'aga ba tare da yace Mata komai ba,take kuma fara'ar dake d'auke a fuskarsa suka gushe.Dai-dai lokacin ne wayar Jabeer ya soma ruri,ganin sunan Mummy ce ya saka shi sakin murmushi ya d'aga kiran.Jin muryar Mummy na cewa Ina suk tsaya da basu dawo ba haryanzun? Inteesar kuwa har ta kusan k'arasawa kusa da Usman Jabeer ya kira Sunanta,juyowa tayi ta kalleshi.Cikin bada Umarni yace ta dawo,ganin fuskasa ba wasa yasa ta juya ta koma wajensa,tana k'arasawa ya ce, "Mummy ta kira waya, ki wuce mu tafi." Kai tsaye inda yayi parking ya nufa tana biye dashi, bud'e mata yayi ta shiga sannan Shima ya zagaya ya shige.Sauke glass d'in motar yayi tare da kallon Usman yaga idanunsa nakan su,jan motar yayi suka bar wajen super market d'inda basu shiga ba kenan.Usman bin motar yayi da kallo har ta 'bacewa ganinsa,a ransa yana jin babu dad'i, zuciyarsa cike da tarin tambayoyi,shin waye wannan dake tare da Inteesar? Ita da lokacin da ya ce zaizo gidansu ta hanashi ta ce wai ba'a barinta ta tsaya da saurayi,sai da yayi Mata dabarar cewa maganinta ne doctor ya ce a bata sannan ta yarda ta bari yazo gidansu. Kuma iya saninsa bata da wani yaya ita kad'aice a wajen iyayenta ballantana ace shi yayanta ne, yarinyar da Bata tsayawa da saurayi me zaisa a irin wannan lokacin wani saurayi ya kawota shopping?.Haka ya dinga yiwa kansa tarin tambayoyi sanin bashida mai bashi amsane yasa jin zuciyarsa jin ba dad'i musamman idan ya tuna cewa Inteesar zata k'araso wajensa kenan wannan saurayin ya kirata dan kada tayi magana da shi.Ita kuma sai ta biye masa ta tafi ta barshi,Take ransa ya kuma 'baci haka yaja motarsa ya bar wajen,dama ya gama abunda zaiyi yana shirin tafiya ne yaga Inteesar ta fito daga Motar Jabeer. Jabeer kuwa akan hanyarsu ta komawa gida ne yake tuna irin kallon da Usman yakeyiwa Inteesar,da yadda yadda dinga sakar Mata murmushi babu abunda ya ke hangowa a cikin idon Usaman kamar tsantsar so da yake Mata.Take sai yaji kishi a cikin zuciyarsa.Kallon Inteesar yayi sannan ya maida hankain sa kan driving d'in da yake yi sannan ya jefa mata tambaya. "Waye shi?" Kallonsa tayi cikin rashin gane me yake nufi sanan ta ce, "Yaya Jabeer me kake magana akai?" "Raina mani hankali zakiyi?waye kika rabu dashi yanzun zakije gurinsa?" Ya fad'i maganar cikin d'aga murya kamar Yana fad'a.kallon mamaki take binsa dashi yadda lokaci d'aya yanayinsa ya sauya kamar ba Jabeer d'in da sani d'azun ba. Cikin sanyin Muryarta ta fara magana "Shine wanda ya kad'eni da mota." "Yaushe ya kad'e ki da motar?" "Sati biyu da suka wuce,lokacin da zamu kai d'inkin bikin nan nida Mufida,naga wani makaho yazo kan titi sai na k'arasa don na taimaka masa ya tsallaka Dai-dai lokacin da motarsa ta kawo kai, shine tsautsayi ya gifta ya kad'eni." Sake jefa Mata wata tambayar yayi da cewa "Daga Nan kuma sai akayi Yaya?" "Shine ya kaini asibiti ya biya kud'in komai sannan ya tafi." Wani tambayar ya sake yi mata inda ya ce, "Daga nan baku sake had'uwa ba kenan?" "Mun sake had'uwa saboda yazo gidanmu bayan ya dawo daga tafiyar da yayi." "Ya akayi yasan gidan ku?kuma meye dalilin zuwansa." Tura baku tayi,don zuwa yanzun ta fara gajiya da yawan tambayoyin da ya ke mata ba.cikin k'osawa da tambayoyin sa ta ce, "Lokacin da yaje asibiti ne ya d'auki wayata ya saka number sa ya kira,to anan ya samu number na shine yake kira na a waya,sau d'aya yazo gidanmu gaishe ni." Bai sake cewa komai ba ya maida hankain sa kan driving d'in da yakeyi har suka k'araso. K'ofar gidan a waje yayi parking,da sauri ta riga shi fitowa Shima ya fito,tare suka jera zuwa cikin gidan. A harabar gidan ya tararda Muhdeen da wasu abokan su zaune kan wasu kujeru suna tattaunawa.Ido suka zubawa Inteesar da Jabeer,wani daga cikinsu mai suna Bashir ne yayi magana ya ce, "Tsarki ta tabbata ga ubangijin halittu,gaskiya Jabeer ya iya za'ben kyakkyawar mace mai kyawun sura da diri." Salisu ne yayi dariya tare da cewa "Ai wannan ba matarsa bace." Bashir ya sake cewa "To wace ce ita a wurinsa?kodai budurwarsa ce?" "Bari ya k'araso ka tambaye shi don banida amsar wannan tambayar taka." Kai tsaye Inteesar ta nufi cikin gidan, Jabeer kuma ya k'araso wajen su sallama yayi masu tare da mik'awa kowannensu hannu suka gaisa.Muhdeen ne ya kalle shi ya ce, "Daga ina haka?tun d'azun nake jiran k'arasowarka sai yanzun?" Murmushi Jabeer yayi ya shafi sumar kansa ya ce, "Eh daga wajen reception na biya wani waje ne sannan na tafi gidana dawowarmu kenan." "Kenan tun lokacin kana tare da wannan yarinyar?" "Eh kana da matsala da hakan ne?" Ta'be baki Muhdeen yayi tare da kauda kansa gefe.Bashir ne ya washe baki yana cewa, "Ina ka samo wannan zazzafar yarinyar gaskiya ta had'u ta ko ina,tayi mun." Jabeer ne ya had'e fusaka domin yasan halin Bashir da neman mata kamar bunsuru.watsawa Bashir mugun kallo yayi tare cewa "Bari kaji Bashir wannan ba irin matar banzan da ka saba mu'amala dasu bane gara ma ka kama kanka." Gyara zama Bahir yayi cikin d'aukar maganar da mahimmanci ya ce, Ai wannan ba irin wad'annan can sauran 'yan matan bane,wannan idan na sameta sunnah zan raya don mace ce ta nunawa sa'a." Gaba d'ayansu suka saka dariya banda Muhdeen da ko kallonsu bayayi.salisu kuwa harda tafi yayi don bai ta'ba Jin Bashir yayi maganar aure ba,sai dai ya dinga kawo matan banza a guest House d'insa.Sharholiyarsa kawai yake Bai ta'ba maganar aure ba sai da yaga Inteesar yau. Jabeer ya kalle shi yana cewa "Baka dace da Inteesar ba kwata-kwata,ai ko da girgiza kurna tafi magarya." Daga Nan ya tafi ya barsu wajen. Inteesar kuwa tana shiga falon ta tarar da Bak'i mata 'yan biki sallama tayi ta gaishe su,sannan ta nufi d'akin Mummy nan ta tarar da Mummy da mahaifiyar Jabeer sai k'awayen Mummy guda uku.Gaishe su tayi sannan ta nufi d'akin Mufida. Da sallama ta shiga,suka amsa Mata suna tambayarta Ina suka tsaya ne haka? "Lapiya kika k'i d'aukar Kiran wayar da nake maki?" Cewar Mufida da ta zubawa Inteesar ido,Sai a lokacin Inteesar ta tuna cewa wayar na a silent take,ciro wayar tayi taga Miss call d'in Mufida har guda 5. 'Bangaren Usman kuwa Koda ya koma gida ransa a jagule yake, A falo ya tarar da Ammynsa da Khadija suna kallon news,kallo d'aya Ammy tayi masa ta gane akwai abunda ya faru a can.Don ba yadda yadda yadda fita ba kenan,yanayinsa ya sauya,Khadija ce ta kar'bi ledar hannunsa ta ajiye agaban Ammy.don dama ita ce ta kirashi a waya ta ce idan zai dawo ya biya super market yayo mata siyayya kamar yadda yadda saba duk bayan kwna biyu. "Lapiya kuwa naga yanayinka ya canza?ko akwai abunda ya faru ne?" Murmushi ya k'ak'alo ya ce, "Babu komai Ammyna bari na d'an shiga ciki na huta." Bai jira cewarta ba ya shige ciki tabishi da kallo. Washe gari ranar juma'a Gidan Alhaji sani ya cika mak'il da jama'a.'Yan uwa da abokan arziki na nesa da na kusa,aga abinci nan kala-kala sai Wanda mutum yake so zaici ko yasha,komai sunyishi a wadace. Da misalin k'arfe biyu na rana aka d'aura auren Muhdeen da Sumayya akan sadaki naira dubu d'ari biyar murna a wajen Muhdeen Ba'a magana.Haka 'bangaren amarya ma hakan take Dan tafi kowa murna. Da misalin'karfe biyar na yamma aka tafi d'aukar amaeya don kaita d'akin mijinta Dank'arararren gida ne Wanda akashe naira wajen yinsa.Amarya ma iyayenta sunyi bajinta wajen yo mata order lafiyayyun furnitures.Tunda ga Kan kayan d'aki har zuwa kayan kitchen komai masu tsada ne na kece raini, d'akuna guda biyu aka zuba Mata kaya. Da misalin k'arfe takwas na dare ana ta shirin zuwa dinner wanda za'ayi a JUSTICE IDRIS LEGBO KUTIGI dake daura da Government house a cikin garin Minna. Mai makeup aka d'auko inda tazo ta tsantsara wa amarya lafiyyen kwalliya.Tayi kyau kam sai baza k'amshi takeyi tana kyalli,k'awayenta su Jummy sai kod'ata suke suna k'ara fasa mata kai. A can gidansu Mummy kuwa anata shirin zuwa dinner inda nan ma Azeeza ta sake tsantsarawa Inteesar da Mufida kwalliya,sai faman kod'a kyawun da Inteesar tayi sukeyi,har suna cewa ma ai kila tafi amaryar kyawu.Nan ma sai da suka sha fama da ita akan sanya gyale ba yadda ta iya haka ta biye masu ta fasa saka hijabin da ta saba sakawa.Inda kyawunta da kwarjininta suka sake bayyana don ko mace ce ta kalleta sau d'aya sai ta sake kallonta ballantana namiji. Maman Ihsan ce✍️ 09065327995 Comment and share Love u oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing✍️ Zainab Abdullahi (maman Ihsan) *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to ku gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page 2️⃣5️⃣ Kyawunta da kwarjininta suka sake bayyana,don ko mace ce ta kalleta sau d'aya sai ta sake kallonta ballantana namiji. Ajere suka fito daga d'akin inda suka nufi d'akin Mummy. Da sallama suka shiga d'akin, Mummy ce da Aunty Maryam sai Mummyn Jabeer,amsa musu sallamar sukayi Mummyn Jabeer ce tayi murmushi tare da cewa "Masha Allahu'yan matana kunyi kyau sosai kamar kune amaren,Allah ya nuna mani ranar aurenku musha biki.Kai kyawawan 'ya'yana kuzo na rungume ku mana." Ta k'arasa maganar tana bud'e hannayenta alamar suzo ta rungume su.Mufida da Azeema da Azeeza suka k'arasa suka shige jikinta,yayin da Inteesar ta tsaya tsaye inda take Don Bata san Mahaifiyar Jabeer ba sai sai shekaran jiya ta fara ganinta kuma gaisuwa ce kawai ke had'asu.Hakan yasa ita Bata k'arasa ta rungumeta ba,Murmushi ta sakarwa Inteesar ta ce, "Zo mana 'yata ya kika tsaya can?" Hakan yasa ta tako cikin sanyin jikinta ta rungumeta hakan yasa Mufida ta ciro wayarta tayi masu selfie su duka kowacce tana dariya.daga nan sukayi masu sallama suka ce zasu tafi dinner,nan Mummy ta ce da su Anty maryam su shirya lokacin fara dinner yayi. Dama Direban Mummy ne zai kaisu Mufida idan ya dawozai Kai su Mummy.suna Isa harabar gidan wayar Mufida ya fara ruri dubawa tayi taga yaya jabeer ne,d'agawa tayi taji muryarsa yana cewa sun tafi dinner ne? tace suna gida yanzun zasu tafi,ya tamabayeta Inteesar, ta sanar dashi cewa tare zasu tafi ya ce wai Inteesar ta sameshi waje yana cikin motarsa zai wuce da ita dinner d'in.Daga nan ya kashe Mufida ta zubawa wayar idanu Tana mamakin me ya Jabeer yake nufi?baice suzo ya kaisu ba Wai Inteesar tazo wato daga shi sai ita kenan.Kallon Inteesar tayi ta ce, "Tafiyarmu da ke ba d'aya bane,ya Jabeer Wai kije ya kaiki." "Babu inda zanje ya kaini sai dai idan tare zai kaimu da ku." Dariya Mufida tayi tana fad'in "Ai bada mu ya ce ba ke kad'ai ya ce." Kauda Kai Inteesar tayi ta dage bazata je ba.Jin shiru yasa ya sake kiran wayar Mufida ta shaida masa yadda sukayi.Sai gashi ya zo da kansa yace da Azeeza da Azeema su shiga motar haka ma Mufida yasa ta shiga daga nan ya ce da Ishaq yaja motar su tafi.Inteesar na gani motar ta fice tsabar takaici kamar tayi kuka.kallonta yayi yana cewa "Kizo mu tafi lokaci na tafiya fa." 'Dago ido tayi da niyyar ce masa ta fasa zuwa,amma da ta kalli cikin idanunsa sai taji ta kasa masa gardama,haka nan ta bishi har suka fita Murfin motar ya bud'e mata ta shiga,ya rufe sannan ya zagaya ya zauna mazauninsa.kasancewar haske ne gab d'aya kofar gidan yasa ya zuba Mata ido,domin tasaha kyau har ta gaji.tsawon mintuna biyu taji shiru yasa ta d'ago ta kalleshi,ganin yadda yadda ya zuba Mata ido ne yasa ta d'aga kai ta kalleshi,idanunsa ne suka sark'e cikin na juna da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa murmushi yayi tare da Jan motar yabar wajen. Akan hanyarsu ta zuwa kuwa du yadda Inteesar taso share Jabeer hakan baiyuwu ba.Domim da ya dinga janta da hira yaga bata tanka masa ba sai ya dinga yi mata tambayoyi yadda dole sai ta dinga amsa masa.shima dama burinsa kawai yayi ta Jin muryarta.A haka suka k'arasa JUSTICE IDRIS LEGBO KUTIGI inda nan ne za'a gabatar da dinner party d'in, a harabar wajen wajen suka tarar da su Mufida suna jiran K'arasowar su Inteesar d'in yayinda Mufida sai d'aukar photo da video take kasancewar gurin haske ne ya gauraye shi tamkar da rana ne.Tana ganin K'arasowar su Inteesar ta maida d'aukar zuwa ga gurin motar yayinda Jabeer ne ya Fara fitowa yayi saurin zagayowa da nufin bud'ewa Inteesar ta fito sai dai kafin ya bud'e Mata tayi saurin bud'ewa ta fito tare suka k'araso wajen ta kalli Mufida tana murmushi ta ce, "To sarkin d'aukar photo ko dare ma ba zaki bari camera ta huta ba?" Jabeer dai ya nufi cikin hall d'in inda za'a gudanar da shagalin. Hall d'in ya cika mak'il da jama'a 'yan uwa da abokan arziki wasu ta hanyar amarya wasu ta hanyar ango.Nan dai amarya da ango suka k'araso cikin shiga ta alfarma sunyi kyau sosai.Wedding goun d'in amaryar irin Mai sirrin hannun nan ne kamar singileti sai jan k'asa rigar take ta bayanta ya sauka yayinda fuskarta ke lullu'be da farin net gaban rigar anyita kamar breezier.Yayinda shi kuma ya saka fararen suit. Su Hajiya Gwaggo kuwa tana ganin shigar ta Fara salati tana tafa hannu,Aunty Maryam dake zaune gefenta ne ta kalleta tare da tambayarta "Gwaggo lafiya me ya faru?" Rik'e ha'barta tayi tana jujjuya Kai tana cewa "Oh ni,yau naga abunda ya isheni." Anty Maryam ne ta same tambayar Gwaggo ta ce, "Wai Gwaggo ne kike ma sallallami haka?" "Wai ke mairo ke makauniyar ina ce?ki duba wasu 'yan isakan tsinannun rgar da wannan amaryar tasa,duk surar jikinta a bayyane,ki duba gaban rigar harda gidan da mamanta zasu zauna akyi su,gashi sun zauna ciki kowa na ganin shaidar su ga rigar ko hannu Bata dashi.Wani abun takaicin Wai matar aure kenan,tunda d'azu jama'a da yawa sun shida d'aurin auren su.Gab d'aya rayuwar yahdawa suka d'auko.shi kuma da yake mijin hotiho ne da baya kishin matarsa shine ya barta ta fito a haka,ace mutum sam baida kishi kamar Wanda yaci naman alade." Aunty. Maryam ce da wasu k'awayen Mummy suka saka dariya.Nan dai aka Fara gudanar da komai cikin tsari inda aka wak'e ango da amarya,aka kira dangin amarya inda suka fito suka cashe sukayiwa ango da amarya lik'i. Bayan dangin amarya sun koma ne aka kira dangin ango nan suka fito harda Mummy da su Anty Maryam da k'anwar Dady da Mummyn Jabeer da su Gwaggo da Asiyya da Mufida, Azeema, Azeeza hatta Inteesar sai da Mufida ta janyota Jabeer ma ya fito Nan aka shiga lik'e-lik'en nairori da raye- raye anci ansha sannan aka tashi kowa ya watse. Da misain karfe goma da rabi na dare ne amarya tana zaune a Kan gado,sanye take da wani less golden yellow Mai ratsin fari a jikinsa doguwar riga ce dakyar k'awayen Mum d'inta suka lalla'bata ta yadda take saka,don ita ba ma'abociya Sanya suturar kirki bane.yayinda k'awayenta su Jumy da shila je zaune a gefenta suna ta mata tsiya suna tsokanarta. Ango da abokansa ne suka shigo cikin d'akin.Muhdeen Ango Yana sanye da farar shadda da Babbar riga sai k'amshi ke tashi a jikinsa.Salisu na rik'e da ledar kaji da fresh milk a hannunsa,da sallama suka shiga d'akin Su shila ce suka amsa masu.Nan dai akayi siyen baki inda abokan ango suka wuce da k'awayen amarya.Ko rakiya bai masu ba suna ta tsokanarsa suka wuce.haurawa yayi Kan gadon ya yaye mayafin yadda zai ga fuskarta dakyau.Murmush take tayi domin burinta ya cika na auren Muhdeen kullum fatanta kenan tana sonsa sosai.kitchen ya nufa ya d'auko plata da kofuna guda biyu ya k'araso ya bud'e ledar, kaji ne bank'ararru guda biyu sunji gashi Mai kyau kuwa.d'aya ya d'auka yasa a plate d'in ya tsiyaya fresh milk a baki ya dinga bata tana ci tana shan fresh milik d'in har ta k'oshi.ya kwashe kayan ya Kai kitchen sannan ya dawo ya umarceta da ta shiga tayi wanka ta d'auro Alwala suyi sallah daga nan ya fice zuwa d'akinsa. Zuciyarta cike da farincikin mallakarsa a matsayin mijinta, mi'kewa tayi ta cire kayan jikinta ta fad'a toilet don yin wanka.Bayan ta fito ta goge jikinta ne da k'aramin towel,ta shafa lotion da turare ta saka riga da wando na barci don dama ta d'auro alwala hijab kawai ta saka ta shimfid'a masu sallaya tana zaman jiransa Zamanta bada jimawa ba ya shigo sanye da farin jallabiya a jikinsa.Jansu sallah yayi inda sukayi raka'a biyu,bayan sun idar ya dad'e yana masu addu'a kafin suka shafa.Goshinta ya rik'e tare da addu'a kafin suka nad'e sallayar.Zama tayi bakin gado yayimda shi kuma ya haura saman gadon light d'in d'akin ya kashe kafin ya cire jallabiyar jikinsa. "Bakyajin barci ne kika zauna?ko gadina kike yi?" Kwanciya tayi daga d'an nesa dashi,janyota yayi zuwa jikinsa kai tausassun le'b'bensa yayi a kan goshinta ya sunbaceta a goshi.Lumshe Idanuwanta tayi sakamakon jin tausasan le'b'bensa a goshinta tsintan kanta tayi cikin wani irin yanayi na nishad'i.Shafar gefen fuskarta yayi har zuwa kan wuyanta a hankali ya fara 'balle boturan gabar rigarta kasa hanashi tayi cikin hikima ya rabta da komai na jikinta tare da sumbatar kowane sashe na jikinta.A hankali yake shafa sassan jikinta tare da yi Mata tafiyar tsuka, wani abu Sumayya takeji tun daga tafin hannunta har tsakiyar kanta,la'b'banta kuwa sai tsotsonsu yake kamar ya samu sweet.A daren dai sai da ya mayar da Sumayya cikakkiyar mace. Daga Alk'alamin✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) 09065327995 Love u oll😘😍 Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta cowace siga. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne mai kashe auren wawa. Page2️⃣6️⃣ Wani abu Sumayya takeji tun daga tafin hannunta har tsakiyar kanta, la'b'banta kuwa sai tsotsonsu yake kamar ya samu sweet.A daren dai sai da ya mayar da Sumayya cikakkiyar mace. Bayan awa d'aya ya samu nutsuwa ne ya janyota ya rungume yayinda take ta matsan k'walla.Toilect ya shiga ya had'a mata ruwan wanka sannan ya taimaka mata ta tashi ya kaita toilet inda sukayi wanka. Shi da kansa ya yaye zanin godon inda ya shimfid'a masu wani.ya janyota jikinsa nan da nan barci ya d'aukesu. Kiran sallar asuba ya farkar dashi daga barcin da yakeyi.Tashi yayi ya nufi d'akinsa, toilet ya shiga ya sake watsa ruwa ya Sanya jallabiya ya biya ta d'akin Sumayya ya tayar da ita domin tayi sallah.Masallaci ya nufa,sai da aka idar da sallah ya dawo.Kai tsaye d'akinta ya nufa ganinta yayi tana barci da dukkan alamu ma bata tashi tayi sallah ba.Tashita ya sakeyi domin har gari ya fara haske dakyar ta tashi ta shiga toilet,Don bata saba sallar asuba ba ko a gidansu idan tana barci ba'a tashinta idan tana barci ko lokacin sallah ne kuwa,don sallar ma sai taga dama takeyinta idan bata ga dama ba kuwa sai dai Allah ya kar'ba. A can gidan Mummy kuwa tunda su Inteesar suka idar da sallar asuba su Mufida da Azeeza suka koma suka cigaba da barcinsu, Inteesar kuwa azkar tayi sannan ta mik'e ta nufi kitchen don tasan akwai bak'i a gidan hakan yasa taje don had'a breakfast.Kasancewar tana da zafin nama wajen aiki a cikin k'ank'anin lokaci tayi rabin aikin,don Koda Aunty Maryam k'anwar Dady ta shigo k'araso kitchen d'in k'amshi kawai ke tashi kusan a tare Aunty Maryam ta shigo tare da Mummy.sunji dad'in ganin Inteesar a kitchen tana aiki cikin girmamawa Inteesar ta gaishesu,suma suka amsa mata cikin jindad'i.Lokaci d'aya Inteesar ta shiga ran Aunty Maryam.Had'a hannu sukayi su uku zuwa k'arfe takwas sun gama shirya breakfast kala-kala Inda aka jera wasu a dinning table sauran kuma aka kai d'akunan da Bak'i suka sauka inda Aunty Maryam ta jera wasu a basket tace akai gidan Muhdeen.Mummy ce ta kalli Inteesar ta ce, "Ina Mufida ce tazo direba ya kaiku,gidan Amarya ku Kai masu breakfast." Inteesar ta ce, "Suna can suna barci bari naje na tayar da ita." Fita tayi daga kitchen d'in Kai tsaye ta nufi da'akin Mufida.koda ta shiga duk suna barci tayar da Mufida tayi ta sanar da ita sak'on Mummy.Yamutse fuska sannan ta sanar da Inteesar cewa bari tayi wanka ta shirya. "Har sai kinyi wanka?nima fa banyi wankan nan ba dogon Hijab kawai zan saka mu tafi." "Ke da Zaki iya lullu'be jikinki da hijabi kenan ba Wanda yasan ya kayan jikinki ya ke ba,amma ni da ba hijab zan saka ba fa?haka zan fita a ganni da rigar barci ba." Daga nan Inteesar ta fita ta sanar da Mummy cewa Mufida zatayi wanka ta shirya in da Mummy ta ce, "Ba ta yi wanka ba dama?ita da take dad'ewa a bathroom ne zamu tsaya jira?" Kallon Inteesar tayi tare da cewa, "Daughter Kinga bari in sanar da Ishaq direba ya kaiki,don nasan har zaku je ku dawo bata gama wanka ba." Gaban Inteesar ne ya fad'i jin cewa wai ita kad'aice zata je gidan wancan mugun da sassafen nan,domin ita a rayuwarta ba mutumin da ta tsani ganinsa sama da Muhdeen,gashi kuma ba zata iya yiwa Mummy gardama ba ki ta kawo Mata wani uzurin.Bata da za'bi dole haka ta kar'bi basket d'in breakfast hannun Aunty Maryam inda Mummy ta rakata har harabar gidan.Nan ta sanar da Ishaq cewa yakai Inteesar gidan Muhdeen idan ta shiga ya jirata har ta fito kafin su dawo. Can cikin bacci yaji k'arar k'ofa,a zuciyarsa yace waye haka da sassafe?tashi yayi yabar Sumayya a kwance tana ta barci don ko k'arar k'ofar ita bataji ba. Falo ya k'araso ya bud'e k'ofar,ganin Inteesar yasa ya murtuk'e fusak kamar Wanda Bai ta'ba dariya ba.Itama 'bangarenta haka ne don ba Wanda ta ysani haninsa a rayuwarta sama da Muhdeen.Cikin sanyin Muryarta ta ce, "Ina kwana?" Bai amsa ta ba sai cewa yayi "Lapiya?" Bata kula shi ba ta mi'ke masa basket d'in,baice komai ba kar'bi basket d'n tare da shigewa cikin falon ya barta nan tsaye. Juyawa ta yi don k'arasawa wajen Ishaq koma gida. ******* ******** Har Muhdeen Sumayya suka cika sati d'aya da aure,Kullun sau uku Mummy zata Aiko masu da abinci safe da Rana da dare.Aranar ne kuma ta sanarwa muhdeen za'a daina kawo masu abici,sai dai matarsa ta cigaba da yi masu girki. Bak'i kowa ya tafi gidan an watse daga Dady, Mummy,sai Mufeeda.Asiya dama tunda akayi biki ta koma Gwaggo ce kad'ai ba ta tafi ba. : Bangaren ango da ameya kuwa suna shan soyayyarsu son ransu.Abunda ya tayarwa Sumayya hankali shine jin wai zata Fara girki,don ita a rayuwarta ba ta ta'ba shiga kitchen da sunan girki ba don ko ruwan zafi bata ta'ba d'orawa a wuta ba Babu abunda take a gidan iyayenta,komai 'yar aiki ke Mata ko kauda tsinke Bata iya ba.Nan dai ta nunawa Muhdeen cewar ya Nemo masu Mai aiki don ita ba zata iya aikin komai ba,nan ya nuna Mata cewar gsky bazai iya cin abinci wanda 'yar aiki ta girka ba,haka tsarinsu yake ko gidansu Mahaifiyarsa ce ke girka abinci,don haka bazai iya ba gsky.nan hankain Sumayya ya tashi don bata ma san ta Ina zata fara ba kuma Bata San yadda zatayi ba.nan take sanar da ita abokansa ma zasuzo gobe zasu zo suci girkin amarya.Nan dai ta cire d'an kwalin kanta tana goge zufa duk da sanyin A C daga ratsata Daga Alk'alamin✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) 09065317995 Love u oll😘😍 Comment &shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,Idan suna ko hali yazo daya to gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page2️⃣7️⃣ Nan take ya sanar da ita abokansa zasu zo gobe zasu zo su ci girkin amarya.Nan dai ta cire d'an kwalin kanta,tana goge zufa duk da sanyin A C dake ratsata. "Me ya faru ko akwai wata matsala ce?" Kai ta girgiza tana tunanin ta yadda zata fara,domin kuwa wannan Abu ne mai matuk'ar wahala a gare ta.Bata ta'ba tunananin wannan ranar zata zo ba.Ita da rayuwarta daga taci tasha ta kwanta ba abunda takeyi,Mai mata aiki ce take komai sai da ta tashi barci ta yi wanka tayi kwalliya ta fita Koda zata shigo d'akin sai sai ta tarar an kimtsa mata komai ko kitchen idan ta shiga sai dai idan akwai abunda taje d'auka,sau tari ma tana zaune zata bada umarnin a kawo mata duk abunda ranta keso gashi yanzun mijinta da tayi tunanin zai bi ra'ayinta amma ya ce wai bai yarda da 'yar aiki a gidansa ba.Kukar shagwa'ba ta saka ta ruga a guje ta nufi bedroom d'inta.Shima ya ta shi ya bita a guje kamar sharukhan🤣 Koda ya shiga d'akin kwance ya sameta tayi kwanciyar rubda ciki,janyota yayi jikinsa ya rungume yana d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi.Cikin kwantar da murya ya fara magana. "Haba Baby kukan me kike yi?kinsan na tsani naga kina kuka hankalina tashi ya ke." Cikin shagwa'ba ta fara magana "Haba ya zanyi wallahi bazan iya ba,sai kace jaka?nifa bana aiki a gidanmu kafi kowa sanin ma'aikata ke mana aiki ban iya ba kuma ban saba ba,sannan nayi aure bazan huta ba sai nazo na zama banida banbanci da 'yar aiki?" Cikin sigar rarrashi ya fara magana "Kinga ba wai ke zakiyi duka aikin gidan nan ba,girki ne dai bazan iya cin na 'yar aiki ba.kuma ai tunda kika zo gidannan bakiyi aikin komai ba,nine nake yin gyaran d'akunanmu na share na goge na wanke toilet na gyara kitchen,duk da Mummy ke aiko muna da abinci ko wace rana ni nake wanke kwanoni .Aikin komai ban baki ta'ba yi ba,kuma dama ranar Monday zan koma asibiti wajen aiki, kafin ranar zan nemo wacce wacce zata dinga yin aikin Amma iyakar ta dai ta yi wanke-wanke da ta gyara kitchen da falo da d'akinki Amma ban yarda 'yar aiki ta shigar mani d'aki ta gyara ba.Zanyi da kaina kuma ban yarda 'yar aiki ta shiga kitchen ta girka mani abincin da zanci ba sai dai matata,sannan akwai Wanda zai dinga wanki da goga fatan kin fahimta,girki kawai ne aikinki a gidan nan Zaki iya ko?" Kai ta gyad'a masa alamar Eh.Daga nan salon ya canza aka lula duniyar ma'aurata. Gidan Jabeer kuwa,Matarsa kuwa ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba.Tun ranar da taga ya shigo da Inteesar gidan kuma taga yadda taga Jabeer ya na ta rawar jiki da Inteesar a wurin reception d'in bikin Muhdeen,ta kuma tambayi Mufida wace taga tayi posting a status d'inta ta fito daga Motar Jabeer?sannan washe gari ranar dinner haka taga Jabeer ya d'aukota a motarsa sai wani kallo yake mata mai cike da shauk'i sannan cikin pic d'in ga bugu da k'ari taga photon da Mahaifiyar Jabeer d'in ta rungume Inteesar da su Azeema.Tayi ta sak'a da warwara musamman da ta tambayi Mufida cewar meye dangantaka su da Inteesar ta sanar da ita cewa ba dangantaka sai dai suna mata kallon ita wata sashe ne daga garesu, bata kuma da wata aminiyar da ta wuce Inteesar barci kawai ke rabasu.Nan ta d'aura da cewa wai me yasa da Inteesar zata shiga motar Jabeer ita Mufida bata shiga ba,Mufida ta sanar da ita cewa shi Jabeer d'in ne ya ce su biyu zasu tafi.Har Jabeer d'in ta tsare da tambayoyi ya nuna Mata ba komai a tsakaninsu. Washe gari ranar da abokan Muhdeen zasu zo, Sumayya na kitchen tana shirya masu girkin tarbar su.Waya ta d'auka ta hau internet don ta samu tasan yadda zata girka masu lafiyayyen jallop.da Farfesun naman kaji.wayar na gabanta tana kallo kuma tana had'a abubuwan girki,a zuciyarta tana ayyana wahalar da akeyi a yayin da ake girki.ta kwashe awa biyar a kitchen tana girka jallop d'in shinkafa da Farfesun kaji.Muhden ne da dawowarsa kenan daga masallaci ya shigo kitchen d'in Jin k'amshi na tashi kitchen d'in sai yanon girkin yakeyi tun baici ba. Kira ne ya shigo wayarsa, Jabeer ke sanar dashi sun iso,fita yayi ya masu jagora suka shigo.Su uku ne suka zo Jabeer, Salisu, Bilyaminu.A falon gidan ya sauke inda ya d'an tsaya suka gaisa sannan ya nufi cikin kitchen d'in ya sanar da ita zuwansu.Fridge ya bud'e inda ya kwaahi gorunan ruwa da na lemuka ya Kai masu.Ba jimawa itama ta fito daga kitchen d'in d'auke da tray an jera food flask a kai, dinning table ta nufa inda ta jera su,sannan ta k'araso wajensu tana fad'in "Manyan bak'i sannunku da zuwa" Suka amsa mata cikin fara'a har suna tsokananta da cewa wai ta rik'e masu aboki gana d'aya tunda yayi aure basu sake ganinsa ba.murmushi kawai tayi,don dama ita ba Mai damuwa mutane bane.Hira sukan tan ta'ba kad'an inda Jabir ke ce masa ya dawo bakin aiki don aiki ya masa yawa,kusan sati d'aya yana hutu.Dariya yayi Yana cewa "In dawo ina?" Jabeer ya sake maimaitawa da cewa "Bakin aikinka mana " Dariya yayi tare da cewa "Haba Bross idan ka ce na dawo yanzun ai bakayi mani adalci ba,ina laifin ma nan da wata d'aya kaga lokacin na d'an more amarci ." Dariya suka yi gaba d'ayansu. Salisu ya d'aura da cewa "Allah idan baka dawo nan da one week ba a kunnensa Dady don sai na fad'a masa,ba gara kai ba naka da sauk'i ba,Ni tawa matar Bata da lafiya laulayin ciki take kullun ba lafiya ga kasala da amai ga ciwon Kai da jiri,haka nake fita naje Asibiti ballantana Kai.Ta'be baki muhdeen yayi tare da cewa "Allah ya bata lafiya,idan saboda lailayin mace ne ba zaka je aiki ba kuwa ashe zaka dad'e kana zaune a gida." Gayara zama Jabeer yayi Yana kallon Muhdeen ya ce, "Yauuwa Bross tunda naga tana jin maganarka kaje ka shawo mani kanta mana." Kallon mamaki Muhdeen ke masa yana cewa "Kayi mata laifi ne?sannan Kai baka san yadda zaka shawo kan mace ba har sai na shawo maka kanta?karka bani kunya Mana." "Kai dai bari kawai,abun ya wuce tunaninka,kishi ne kad'ai ke damunta akan abunda bata da tabbas akai." Gyad'a masa kai Muhdeen yayi ya ce, "Kamar ya kishi kuma?dududu watan ku nawa da auren?" "Kishin zance mana kawai don ta ganni da naje gidan tare da Inteesar shine fa..." Bai Kai karshen maganar ba Muhdeen ya ja tsuki tare da watsawa Jabeer harara yana cewa, "Aikin banza ai ta burgeni da tayi maka haka,na lura tun randa ka k'yallara ido akan wannan kucakar yarinyar sai wani rawar k'afa kake akanta sai kace a kanta ka fara ganin mace." "Kar ka sake kiranta kucaka don ita ba kucka bace,kuma da kake cewa akanta na faraganin mace kusan haka ne,domin akanta na fara ganin mace da ta had'a komai da komai da komai 💯 abunda nake buk'ata daga wurin mace.Kuma mata irinta basu da yawa sai ka tara mata d'ari dakyar zaka samu guda uku irinta.Duk namijin da zai kalli Inteesar bai hango qualities d'in da ke tattare da ita ba tabbas idonsa a makance yake. Dariya Salisu da Bilyaminu suka yi yayin da Muhdeen da Sumayya kuwa suka tsuke fuska.Salisu ya d'aura da cewa, "Maganarka gaskiya ce,domin domin yarinyar kan Bata da makusa son kuwa k'in wanda ya rasa." Bilyaminu ya d'aura da cewa, "Gaskiya kam ku duba ranar da muka dawo daga reception muna jiran K'arasowar Jabeer, sai gashi da ita kunsan dai neman matan banza a wajen Bashir kamar d'an akuya baya ma zancen aure sai lalata da 'ya'yan mutane amma ranar da yaga Inteesar ya fara furta maganar aure Wai ya samu matar da zaiyi rayuwar aure da ita." Muhdeen ne ya ya'be baki ya ce, "Kun zauna kuna ta maganar wannan yarinyar idan shi ya kawo ku ta ki tafi can ku k'arata da zancenta amma ba gidana ba." Jabeer ya ce, "Au korarmu kake ko ruwa bamu sha ba?" Sumayya ce tayi magana cikin jin dad'in kalaman mijin nata akan Inteesar ta ce, "Kuyi hak'uri ga Abinci can da abunsa na shirya maku a dinning table." Jabir ne ya fara mi'kewa ya na cewa "Dama yunwa nake ji ne wallahi kasan mai dafa mani abincin ba lafiya,idan ma rowa yasa kake korarmu sai munci.Lokacin da mukayi aure gidan kowannenmu nan sai da kaci abinci sannan munzo gidanka bazamu ci ba?ai wallahi sai munci." Muhdeen yayi dariya yana cewa "Au abun ma bin bashi ne?." Salaisu ya ce, "K'warai kuwa bin bashi ne kaci na amaryar mu don haka muma sai munci." Dariya sukayi gaba d'ayansu yayinda suka nufi dinning area.Bayan sun zazzauna sumayya tayi serving d'insu ta ajiyewa kowa a gabansa,ta zuba masu ruwa da lemu ta ajiye masu.Dai-dai lokacin wayar Muhdeen tayi ringing tashi yayi domin amsa kiran, Mummy ce ke kiransa falo ya k'arasa ya zauna Kan kujera.Bayan ta ajiye masu komai a gabansu ta zuba masu farfesun ne ta zauna tana jiran mijinta ya gama wayar ya k'araso.Jabeer kasancewar a yunwace ya ke ya Fara dibar jallop d'in yakai bakinsa tare da bisimillah,rintse ido yayi tare da ya mutse duska sakamakon uban gishiri da yajin da ya gigita k'wak'walwarsa ga shinkar duk karfi da sauri ya tofar da abincin k'asa tare da d'aukar kofin ruwa sai da ya shanye sannan ya ajiye. Ba Wanda ya lura da Salisu shi kuma farfesun ya fara ci yana Kai naman bakinsa ya yamutse fuska,da sauri ya zaro hanki a aljihunsa ya saka naman da ke cikin bakinsa aciki ya dunk'ule a hannunsa Shima ruwa yasaha rabin kofi.Bilyaminu kuwa yana Kai cokalin abinci a bakinsa ya murtuk'e fuska Amma shi yayi k'arfin halin had'iye abincin Amma sai da ya rintse ido sannan ya Kora da ruwa.Sumayua kuwa duk Bata lura da abunda ke faruwa ba hankainta na Kan Mijinta da wayar da yakeyi.Jabeer ne ya kalli Salisu da Bilyaminu ya ce, "Kunji abunda naji kuwa?" Kai suka gyad'a masa ba tare da aunce komai ba.Ya cigaba da magana "To Alhamdulillah ni kunga tafita." Mi'kewa yayi suma suka mi'ke suka bi bayansa dai-dai lokacin da Muhdeen ya gama wayar da yakeyi,kallonsu yayi mamaki ya ce, "Ya dai?har kun gama cin abincin ne?" Wani irin dariya dariya Jabeer ya shek'e da shi Wanda sai da gaban Muhdeen ya fad'i,don yafi kowa sanin waye Jabeer idan yaji yayi irin wannan dariyar to tabbas ta mugunta ce.Jabeer ya ce, "Eh mun gama cin abincin Alhamdulillah girkin Amarya yayi dad'i,kuje kuci naku aci dad'i lafiya. Ya nufi k'ofar fita yayin da Salisu da Bilyaminu suka bi bayansa, kasancewar a motar Jabeer suka zo horn yayi Mai gadi ya bud'e masa suka fice daga gidan.Shiru muhdeen yayi yana nazarin kalaman Jabeer yasan ba banza ba, dinning area ya nufa abincin da Jabeer ya bari ne ya d'auki cokalin ciki ya d'iba tare da kaiwa bakinsa,da sauri ya tofar dashi k'asa ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun dinning d'in ya dafe kansa yana fad'in "Sumayya kin kunyata ni a wurin abokaina,tunda nake ba'a ta'ba kunyatani irin na yau ba.kima mace ace baki San yadda ake gika abinci ba wannan want irin rayuwa ne?" D'aga masa hannu tayi tana cewa "Dakata haka nan dama ka auro ni ne don ka wulak'antani?,tunda nake a rayuwarta ban ta'ba yun'kurin shiga kitchen da niyyar gika komai ba,ko uwata da ubana basu ta'ba cewa na dafa masu Koda ruwan zafi ba Amma a Kan son da nake maka karon farko a rayuwat na shiga kitchen don na girkawa k'artin banza abinci baka yaba mani ba how dare you zaka ci mutuncina.Kuka ta saka masa,tunawa yayi da yanayin rayuwarta bata ta'ba yin girki ba Amma don ta faranta masa tayi hakan yasa ya rungumeta Yana rarrashinta. Jabeer kuwa sai da ya biya gidajen abokansu ya sajke kowa a gidansa,Kai tsaye gidan Mummy ya nufa don hsky yunwa yake ji Yana driving yana dariyar gidan Muhdeen da suka baro a zuciyarsa Yana tausayawa Muhdeen wani 'bangaren zuciyarsa kuma baya tausayinsa, musamman idan ya tuna cin mutuncin da yayi masa lokacin da ya ce bai goyi bayan ya auri sumayya ba. Da sallama ya shiga falon inda ya tarar da Mummy da Mufida a falon durkusawa yayi ya gaida Mummy, Mufida ta gaishe sa ya amsa.Kallon Mummy yayi ya ce, "Gwaggo fa tana d'akinta ne?" "A'a suma kitchen." Dariya yayi tare da cewa, "Dama yunwa nake ji bari na gyara zama naci girkin tsofaffo." Mufida ce tayi dariya tare da cewa "Ai ba ita ke girkin ba,Mai girki nayi ita kuma tana ta zuba mata surutu." "Okay to wace ce ke girkin?" "Inteesar ce ke girkin." Take yaji wani farin ciki, mi'kewa yayi tare da cewa "Bari na shiga kitchen d'in mu gaisa da Gwaggo." Koda ya shiga kitchen d'in a ya samu Gwaggo akan kujera sai surutu take ta zubawa Inteesar,yayin da Inteesar ke tuk'a tuwon shinkafa.Gaida Gwaggo yayi ta amsa da cewa "Jabiru kaine a tafe?ya jikin wannan lagwanin matar taka?" Murmushi kawai yayi ya zubawa Inteesar ido fa take kwasar tuwo,ji tayi a jikinta ana kallonta d'ago Kai da zatayi suka had'a ido da sauri ta d'auke idanunta tare da cewa "Yaya Jabeer ina wuni?" "Lafiya lau ya kike?' "Alhamdulillah." Gwaggo sai surutu take zuba masa shi kuma duk hankainsa na kan Inteesar har ta gama kwashe tuwon ta bud'e miyar agushi da alaihun da takeyi taga ya nuna,kashe gas d'in tayi ta d'auki food flask da ta zuba tuwo takai dinning table ta dawo ta Kai miyar dama ta had'a juice d'in kwakwa da madara ta zuba a jug ta saka K'ank'ara a ciki ya d'auki sanyi bayan ta kammala shirya komai ne ta kalli Gwaggo dake ta zubawa Jabeer surutu ta ce, "Bisimillah Gwaggo na kammala komai." Wasshe baki Gwaggo tayi tana cewa "Yauwa 'yar albarka gani Nan zuwa kwanan biyu da kika koma wajen Ummanki nayi kewar dadd'ad'an girkinki mai dad'i." Mi'kewa tayi tare da janyo hannun Jabeer tana cewa "Muje kaima nasan wannan matar taka ba iya girka maka abinci zata iya ba." Dinning table d'in suka zauna inda suka tarar da Mummy da Mufida Mufida ce ta zubawa kowa nasa, ta tsiyaya masu juice d'in kwakwa da ta had'a nan kowa ya fara cin girkin Inteesar nan Jabeer ya dinga santi yana yaba dad'in girkin yana korawa na juice kundai san Inteesar a wajen girki wannan ne dalilin da yasa Mummy keson girkin Inteesar.Gwaggo kuwa har gidansu Inteesar take zuwa ta d'aukota don ta tayata girki,bayan kowa yaci ya k'oshi ne Mufida ta tattare kayan ta nufi kitchen dasu,Mummy kuwa d'akinta ta nufa inda Inteesar ta kalli Gwaggo ta ce, "Gwaggo ni zan tafi gida ban gama aikin da nakeyi ba kika zo kika ce nazo mu tafi,zan koma na k'arasa." "To 'yar albarka ki gaida umman taki ko na rakaki ne?" Jabeer ne ya ce, "Dama tafiya zanyi bari na ajiye ta kawai." Sallama yayi wa Gwaggo da Mummy sannan yabi bayan Inteesar, kasancewar a waje yayi parking ne yasa yayi saurin bin Inteesar akan tazo ya kaita amma sam tak'i yarda don ta lura da shige mata da yakeyi kuma ita Bata da niyyar kula ko wane d'a namiji. Cikin k'osawa tayi magana "Yaya Jabeer kada ka damu ba nisa ne damu ba da k'afa zan gangara ." Kafad'a ya d'aga alamar baidamu ba,hakan yasa ta cigaba da tafiya abun mamaki sai taga ya jera da ita yana ta binta,hakan yasa ta tsaya ta zuba masa ido ya sakar Mata murmushi tare da cewa "Kada ki damu zan cika alk'awarin da na d'aukarwa Gwaggo,na cewa zan raka ki." Bata sake ce masa komai ba har suka Isa k'ofar gidansu.Kwatsam sai ganin Usman tayi a k'ofar gidansu ya Kara waya a kunnen sa ya cire yana dube-dube da alama wayarta yake kira.Ido hud'u sukayi da Usaman ya zuba mata idanunsa take ya gane Jabeer shine wannan mutumin da yaga Inteesar dashi a super market,Jaber ma ya ganesa.Ganin haka yasa Jabeer ya kalleta ya ce, "Dama wannan shine aikin da kika ce zakije gida kiyi?to gashi nan sai kije ki sameshi,daga nan ya juya ya tafi cikin wani irin yanayin da mai wuyar karanta. Washe gari ranar juma'a da misalin k'arfe goma da rabi na safe Gwaggo ta matsa akan cewa lallai cewa sai an kaita gidan Muhdeen,Mufida ce zata rakata inda Ishaq ya kaisu har gidan Muhdeen. Koda suka shiga gidan Sumayya suka samu a falo, sanye take da wando 3 quarter da singileti ga tulin k'arin gashin da akayi mata a sake shi a tsakiyar bayanta.Da sallama Gwaggo suka shiga falon kallo d'aya Sumayya tayiwa Gwaggon ta kauda Kai gefe hakan baisa Gwago ta damu ba,ta ce, "Amarya baki amsa sallama ne ko kuma baki ganni bane?" Yamutse fuska tayi tare da cewa "Na ganki mana Gwaggo ko so kike na goyaki ne ko?ki kuma na tashi nayi rawa da tsalle saboda kinzo?" Mufida ce ta kalleta ta ce, "Haba Aunty Sumayya wannan fa kike gani itace ta haifi Baban mijinki fa?" Hannu Sumayya ta d'aga ta ce, "To sai me matar da ba k'aunata take ba,a gabanki taci mutuncina Wai banida tarbiyya,to yau zata ga rashin tarbiyya muraran.Idan kuma ba so take na nuna mata ba to tattara tsummar rayuwarta tabar Mani gida. Gwaggo cikin 'bacin rai ta ce, "Ina Muhammadu yake Ina son ganinsa yanzun Nan." "Barci yakeyi kuma bazan tayar dashi ba." Cikin kakkausan murya ta sake magana ta ce, "Yau nine zanzo gidan jikata a wulak'antani ba ruwan sha ballantana abinci?" Dariyar rainin hankali tayi sannan ta ce, "Kinga mijina barci yakeyi bana son ya farka da hayaniyarki fita kibar mani gida,dama tun ranar da kika ci mutuncina Dan naje gaisheki na sakawa raina cewa sai na rama duk randa na auri Muhdeen kika zo gida na.Dama ni haka nake ba'ayi mun ban rama ba ko waye a duniyar nan yayi Mani sai na rama,naki ma na raga maki saboda albarkaci jikanki." Gwaggo tayi dariya tana fad'in "Yarinya kin d'ebo ruwan dafa kanki,wallahi sai kinyi Danasanin abunda kikayi Mani kuma zaki ga matakin da zan d'auka akanki wallahi matakin bazai maki dad'i ba." "Babu matakin da zaki d'auka akaina,don mijina yana sona Baya son 'bacin raina." Daga Nan Gwaggo tana fita Mufida tabi bayanta,suka shiga mota Ishaq yajasu suka tafi. Tun akan hanya Gwaggo ta kira Dady ta sanar dashi duk abunda yake ya bari yazo ya sameta a gida.Jin yanayin Muryarta yasa yasa hankain Dady tashi ba shiri ya kamo hanyar gida.isowarsu ba gida ba jimawa Dady ya iso nan Gwaggo ta basu labarin rashin mutuncin da Sumayya tayi mata nan ta nuna masu cewa yarinyar nan bata da tarbiyya shiyasa tun farko na hana auren nan amma baku saurareni ba. "Innaillahi wa'inna ilaihir rajiun" Kalmar d Dady ya furta kenan Gwaggo ta ce, "Sani!" Dady ya kalleta da sauri Jin yadda ta kira sunansa ,ta cigaba da cewa "Idan har ni na haife ka kuma na Isa da kai to a yau d'innan ina son Muhammad Muhdeen ya k'ara aure." Dady da Mummy da sauri suka kalleta Jin kalamanta,Dady ya ce, "Amma Gwagg... Dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu ta cigaba da magana "Ba shawara na kawo ba,umarni na bada." Kai Dady ya gyad'a tare da cewa "Yadda kike so haka za'ayi,amma wace ce zamu aura masa?" "INTEESAR" Da mamaki ya kalleta ya ce, "Ita Inteesar d'in tana sonsa ne?" Bata bashi amsa ba ta shiga d'akinta ta fito da handa bag ta kalleshi ta ce "muje" sannan ta kalli Mummy ta ce "sai mun dawo " Mamaki ya hana Mummy magana Dady yabi bayanta basu tsaya ko Ina ba sai k'ofar gidan su Inteesar. Daga alk'alamin✍️ Maman Ihsan 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni, bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page2️⃣8️⃣ Mamaki ya hana Mummy magana,Daddy yabi bayanta basu tsaya ko ina ba sai k'ofar gidansu Inteesar. Dady ya tsaya a k'ofar gida yayinda Gwaggo ta kutsa Kai cikin gidan tana kwad'a sallama.Umma ce ta fito daga d'akinta,ganin Gwaggo yasa ta fad'ad'a fara'arta tana yiwa Gwaggon sannu da zuwa,Gwaggo Bata ita take ba ta bud'e baki ta ce, "Allah dai yasa Mai gidan yana nan?" "Eh yana nan,yana d'akinsa bai fita ba kinsan yau juma'a sai bayan an dawo sallar juma'a yake fita." Gwaggo tayi murmushin Jin dad'i ta ce, "Ai zuwan nawa na wannan lokacin wajensa nazo,ayi Mani magana dashi." Ummma ta shiga da sallama ta sanar dashi sak'on Gwaggo,kusan a tare suka fito ya gaida Gwaggo cikin girmamawa ta amsa masa da fara'a sannan ta sanar dashi tare da 'Danta suke tafe,magana Mai mahimmanci ya kawosu.Jin haka yasa Abba ya buk'aci Umma ta kawo masa tabarma,bayan ta kawo ne ta shimfid'a masu sannan ta koma cikin d'aki ta sanyo hijab,yayimda shi kuma Abba yayiwa Dady jagora suka shigo kan tabarma suka zauna yayinda Gwaggo kuwa tana zaune a kan gujerar tsugunno,Umma kuwa tana daga gefe itama akan kujera.Gaggaisawa akayi yayinda Gwaggo ta kalli Abba ta ce, "Nazo wajenku da k'ok'on barata ne,Allah yasa zakuyi Mani alfarmar da nake nema daga gareku." Murmushi Abba yayi tare da fad'in "Haba Gwaggo don Allah ki daina fad'in haka,wani k'ok'on bara Zaki nema daga wajenmu?ai kimfi K'arfin ki nemu alfarma a wajenmu sai dai ki fad'i duk abunda kike so muyi maki, matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba zamuyi maki shi." Kai Umma ta jinjina tare da cewa "Insha Allah" Shiru tayi na d'an lokaci kafi ta cigaba da magana "Alfarmar da nake nema a wajenku shine,ina son a d'aurawa jikana aure da 'yarku." Umma da abba ba k'aramin mamaki furucin tsohuwar ya basu ba,Umma Kam tsabar mamaki Bata San lokacin da ta mi'ke tsaye zunbur ba,tana kallon Gwaggon da mamaki. "Nasan zaku yi mamaki kwarai da Jin furucina amma Dan Allah ku amince Mani kada kuce bazakuyi ba." Abba da har lokacin bai daina mamaki ba ya ce , "Gwaggo wanne jikar naki kike magana akai?" "Muhammadu Muhdeen" Mamaki ne ya k'ara cika Abba. "Bashine aka d'auraurensa a kwankin baya ba?" "Eh shine " Abba ya cigaba da cewa "To Mai zaisa..." Gwaggo ta dakatar dashi ta ce, "Kun yarda dani?" Abba da Umma suka ce eh sun yarda da ita. "To Alhamdulillah tunda kun yarda dani,kunsan yadda nake masifar k'aunar Inteesar bazan ta'ba aikata abunda zai zama Mai cutarwa a gare ta ba,don haka Ina son a masaallacin juma'a a d'aura auren Muhdeen da Inteesar." Shiru sukayi suna nazarin maganar Gwaggo da irin k'aunar da Gwaggo da Mummy suke nunaw Inteesar.dakyar dai suka fahimci Gwaggo inda suka amince za'a d'aura auren.Nan murna kamar ya kashe Gwaggo ta ciro kud'i dubu d'ari daga ciki kakkarta ta ce ga kud'in sadaki,daga baya za'a had'a Mata kayan lefe anjima a d'aura auren a masaallacin juma'a bayan idar da sallar. 'Baengaren Muhdeen kuwa Yana taahi daga barci k'arfe d'aya saura kwata Yana Shirin shiga wanka Kiran wayar Dady ya shigo wayarsa.bayan ya amsa kiran ne Dady ya sanar dashi ya biyo ta gida idan ya biyo sai suje masallacin Juma'a a tare. Hakanan kuwa akayi,bayan ya shirya sai ya biya ta gidan Mahaifin nasa gaba d'aya falo ya tarar da su Falo ,ya gaida Dady ya amsa masa ba yabo ba fallasa haka ma ya gaida mahaifiyarsa Nan ma ta amsa masa fuska a sake.Kallon Gwaggo yayi da niyuar bud'ar baki ya gaisheta ta d'aga masa hannu rltare da cewa "Ri'ke gaisuwarka mijin Hajiya,Wanda baida kata'bus a gidansa sai abunda matarsa ta ce,yanzun kamar Ni ne zanje gidanka har wannan matar taka Mai ka da busasshen crayfish d'in zata ci Mani mutunci kana ciki gida." Kallonta kawai muhdeen keyi don baisan zancen da take fad'a,don har yanzun baisan da zancen ba. Dady me ya kalli muhdeen ya ce, "Kai kana cikin gida Amma a wulakantani Mani mahaifiyar da ta haifeni a gidanka?" Shiru yayi don baisan lokacin da Gwaggo ta je ba kuma Sumayya Bata sanar dashi ba.Muryar Dady yaji ya ce "A yau d'inman ana idar da sallar juma'a za'a d:aura aurenka da Inteesar." Waige-waige Muhdeen ya farayi don yaga waye za'a d'aurawa aure da Inteesar,ganin shi kad'ai ne yasashi cewa "Dady Wai waye za'a d'aura auren Nan yau?" "Kaine" A zabure ya mik'e tsaye tare da firgici a fusakarsa ya Fara magana "Dady yaushe nayi aur... 'Daga masa hannu Dady yayi "Ba shawararka muke nema ba Umarni ne koma ka zauna." Hakan yasa ya koma ya zauna zuciyarsa na masa k'una sosai,shi kad'ai yasan bakin cikin Amma dayake namijin Duniya be shi sai yayi kamar hakan baidamesa ba.har suka Fara Jin dad'i a ransu ganin bai damuba bazai basu matsala ba. Bayan an idar da sallar juma'a ne dubban jama'a suka sahida d'auri Auren muhdeen da Inteesar.Muhdeen kuwa kamar zai mutu don bak'in ciki. Daga nan Muhdeen gida ya tafi ransa na k'una,duk yadda Sumayya tayi ya fad'a Mata abunda ke damunsa k'in sanar da ita yayi.Tabishi ta nace Amma Sam yak'i fad'a dole ta hak'ura ta kyaleshi.Da aka Kira sallar la'asar yaje yayi ya dawo,haka da aka Kira sallar magariba ya fita yaje masallaci,Nan ya zauna sai da akayi sallar isha'i bayan sun idar ne yaje restaurant ya siyo masu abinci.Tana zaune yazo ya ajiye Mata a gabanta Kai tasaye d'akinsa ya nufa,Nan ya zaro wayarsa number Jabeer ne ya kira,bugu biyu Jabeer ya d'aga tare da cewa Ango ango ango ran Muhdeen ya 'baci da yaji ya ce ango ango ango,shi a tunaninsa Jabeer yasan komai don haka cikin 'bacin rai ya Fara magana "Ka bani mamaki Jabeer wato hada Kai za'a had'a baki a d'aura Mani aure ko?sannan ki ka sanar Dani ko?kawai Dady ya kirani a waya Wai nazo bayan naje Wai yau za'a d'aura Mani aure inaji Ina gani yau aka d'aura Mani sabon aure Alhalin ki wata d'a....." Baikai K'arshen maganar sa ba yaji k'arar fad'uwar Abu tiff da sauri ya juyo yaga Sumayya ce,ashe ta biyoshi Bai sani ba kuma taji komai da ya fad'a *PLEASE KUYI MANAGE DA SHI* Daga alk'alamin✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa, ce don a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne banyi,banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, Idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashine mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page2️⃣9️⃣ Baikai K'arshen maganar sa ba yaji k'arar fad'uwar abu tiff,da sauri ya juyo yaga Sumayya ce,ashe ta biyoshi bai sani ba kuma taji komai da ya fad'a. Baisan sanda ya saki wayar ta fad'i k'asa ba ya k'arasa bakin k'ofar ya durk'usa a gabanta tare da tallabota zuwa cikinsa,ganin ta suma ne yasa ya nufi fridge da hanzari ya d'auko robar ruwa 'balle murfin yayi tare da 'balle murfin ya yayyafa mata, shiru bata farfad'o ba,ya sake yayyafa mata a karo na biyu nan ma shiru bata bata farfad'o ba, hankainsa ba k'aramin tashi ya yi ba a karo na uku ne ya guntsi ruwan a bakinsa ya fesa mata a fuska da k'arfi sai gashi ta saki wani ajiyar zuciya tare da fashewa da wani kuka.Ahankali kalamansa da taji ya yi a cikin waya suka soma dawo mata cikin k'wak'walwarta,wani kuka ta fashe dashi mai cin rai tana fad'in "No no no bazai yuwu ba wallahi babu kishiya a zamana da kai, bazan ta'ba zama dakishiya ba wallahi bazan iya shererin d'inka da kowace mace ba kai nawa ne ni kad'ai.Idan mafarki nake ya kamata na farka daga wannan mummunar mafarkin da bazai ta'ba faruwa ba." Ta k'arasa maganar tana marin fuskarta tana alamun ta farka daga mafarkin da take,cikin muryar kuka ta cigaba da magana ta ce, "Wake up Sumayya ki farka daga mummunar mafarkin da kike, Muhdeen naki ne ke kad'ai har abada ba wace maccen da zata ra'bi abunda kike so.Na San mafarkine Muhdeen bazai iya Maki kishiya ba ya Riga da ya d'aukar maki alk'awarin hakan." Tana maganar kamar da wata takeyi ba akan kanta ba. Idanunta da suka canza kala suka koma jazir ta zuba masa su ta ce, "Dan Allah ka sanar dani cewa mafarki nake ba gaskiya bane,sati biyu kenan da aurenmu ba yadda za'ayi kayi Mani kishiya wallahi zuciyata bazata iya jurewa ba." Ta k'arasa maganar tana mai k'ara sautin kukanta,hannunsa ta rik'e tana cewa "Please talk to me,mafarki nakeyi ba gaskiya bane ko?" Cikin tsananin tausayinta da yakeji ya janyota ya rungumeta ya fara magana "Sumayya ke musulma ce kinyi imani da Allah kin yarda da manzonsa,ina son kiyi tawakkali ga Allah mutum bai Isa ya gujewa k'addararsa duk abin..." Kafin yakai k'arshen maganar da zai fad'a ya daka masa "Ya Isa!" Da mamaki yake kallonta yadda take d'aga masa murya "Amsa d'aya nake buk'ata daga gareka,an d'aura maka aure ko ba'a d'aura ba?" Cikin fargabar abunda zai biyo baya ya ce, "Eh" Take taji wani k'ululun abu ya tokare mata a k'ahon zuciyarta na bak'in ciki wanda tsawon rayuwarta bata ta'ba shiga bak'in ciki irin na yauba.A guje ta fita daga da'akinsa ta nufi d'akinta ta saka key ta rufe. 'Bangaren Inteesar kuwa duk Bata san abunda ke faruwa ba,kasancewar ranar juma'a ne ba Islamiyya hakan yasa tana idar da sallar Azahar ta d'auki Al-qurani tana karantawa,suratul kahfi take karantawa gashi tun safe take jin gabanta na fad'uwa,hakan yasa a zuciyarta da dinga nanata inalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Abba da Umma ne zaune a tsakar gida,Umma ta rafka uban tagumi cikin damuwa da take ciki ta fara magana. "Yanzun Mallam ni na rasa dalilin da yasa ka amincwa wad'annan mutanen akan auren Inteesar,wani irin lamari ne wannan lokaci guda azo neman aurenta kuma a kokaci guda a bayar da aurenta sai kace wata kaza.Kuma bamu tuntu'beta ba munji tana son sa ko ba ta son sa shin shima yana son ta?gaskiya ni Ina jin tsoron abunda zaije ya dawo dangane da wannan auren da za'a zo lokaci guda a nema kuma mu bayar ba tare da munyi bincike akai ba kamar muna neman Kai da 'yar mu?" "Kinga duk wannan maganar ki barshi kawai,aure ne dai an riga da an d'aura shi abu d'aya ne ke mani yawo a cikin k'wak'walwarta shine angon da aka d'aura aurensa sati biyu da ya wuce Mai zaisa ya sake wani auren yanzu?"naga alamun 'bacin rai a idanun Gwaggo lokacin da ta zo neman auren Inteesar,sai dai fargaba na d'aya shine ban sani ba ko shi yaron da aka d'aurawa 'yata aure dashi yana son ta?ban damu akan cewa Inteesar tana son sa ko Bata son sa ba saboda nasan tarbiyar da nayiwa 'yata da kuma biyayyarta a gareni,nasan ko bata son sa zata zauna dashi tayi masa biyayya don nasan 'yata mai biyayya ce kuma tana gudun ta aukata abunda zaisa ta fad'a cikin fushin Allah.Tsoro na d'aya shine idan ya kasance shi baya son ta ya k'untatawa rayuwar ta,wannan shine kad'ai abunda nake fargaba kin gane ko?" Ya k'arasa maganar idonsa nakan Umma,Kai ta jinjina masa alamar gamsuwa da bayaninsa. "Bugu da k'ari ba abunda Family d'in Alh.Sani zasu nema a waje na a ce na kasa yi masu shi ko meye shi matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba.Mutanen arziki ne kowa yana yabonsu a unguwar nan kema kanki shaida ce akan k'ok'ari da k'aunar da suke nunawa 'yar taki,Addu'a kawai zamu bita da shi Allah yasa shine mafi alkhairi a rayuwarta. Umma ta amsa da "Ameen" Gidan Muhdeen kuwa tunda Sumayya ta shige d'akinta ta murza key ta rufe sai suratai take kamar wata mahaukaciya.kayan kwallalliyar da suke jere a gaban dressing mirror ne ta Fara wargazawa tana d'aukar su d'aya bayan d'aya tan jifa dasu masu fashewa na fashewa kallon kanta tayi ta cikin mirror d'in hannu ta dunk'ule ta kaiwa mirror naushi take mirrorn ya tarwatse idonta takai ga T.v dake mak'ale a bango a guje ta k'arasa gaban T.v zaro shi tayi ta bugashi a Kan tiles d'in d'akin ya fashe haka komai dake d'akin ta shiga illata shi, hatta pillows da bedsheet sai da ta yi ta cilli dasu durowar kayanta ta bud'e ta dinga d'ebo kayan tana cillosu waje, a k'asa haka ta dingayi bayan ta gama zuar da kayan ta dinga binsu d'aya bayan d'aya ta yayyagasu ko wanne sai ta rabashi gida biyu sannan tayi cilli dashi gefe wad'anda taji sunyi Mata k'arfi a hannu sai ta saka hak'ori tayi masu hanya sannan ta k'arasa yagawa.bayan ta gama ne ta bud'e 'bangaren da akwatunan kayan lefenta suke,nan ma ta zuzzuge zif d'in akwatunan haka ta dinga wurgi da kayayyakin abubuwan fashewa na fashewa wad'anda ba na fashewa ba kuwa ta tattaka su. 'Bangaren Muhdeen kuwa tunda Sumayya ta fita daga d'akinsa ya zauna a bakin gadon gaba d'aya ya rasa mai ke damunsa.don yasan ko yabi Sumayya Dan ya rarrasheta ba sauraransa zatayi ba,hakan yasa ya d'an barta tukunna.Ya rasa me yasa Gwaggo zata yi masa haka zata sa ayi masa aure ba tare da amincewarsa ba,sannan ta rasa wacce zata say aura masa sai Inteesar yarinyar da ya tsana a rayuwar sa ita ce aka aura masa?lallai kuwa Inteesar ta tabka babban kuskure da ta yadda da wannan auren,Don wallahi sai ta d'and'ani kud'arta,daga ranar da ta shigo cikin gidan nan a matsayin matarsa daga ranar zata zatayi ban kwana da farin ciki.Yana cikin zancen zucin nasa ne yaji wani irin k'ara na tarwatsewar abu,cikin tashin hankali ya fito daga cikin d'akinsa ya nufi d'akin Sumayya. Daga cikin d'akin Sumayya kuwa show glass d'in da aka jera Mata turararruka ne da su kwalaben humra da turararen wuta,lokacin da idonta ya sauka akan show glass d'inne ta nufesa tana k'arasawa ta d'auki k'arfen da da ke ajiye na rataya jakunkuna ,tana d'aukar k'arfen ne ta bugawa show glass ya tarwatse,k'arar show glass d'inne yaja hankalin Muhdeen ya nufo d'akin nata cikin tashin hankali. Yana tura k'ofar yaji a datse ya shiga buga k'ofar Yana Kiran sunanta Amma Ina Bata ma San tanayi ba sai buge-buge da jefe-jefe takeyi tana Sam batu tayi nan tayi can duk abunda ya tari gabanta jifa dashi take,komai na d'akin ta gama hargiza wa ta fargasa duk abunda ya kasance na fashewa abu biyu ne a d'akin Wanda suke zaune a muhallinsu, durowar zuba kayanta sai gado suma don ba zata iya d'aukarsu bane hatta katifa tayi jifa dashi gefe. Muhdeen ne koma d'akinsa ya d'auko key yazo ya bud'e k'ofar,ganinta ya yi kamar mahaukaciya duk ta fita hayyacinta ga hannayenta da taji ciwo.Suna had'a ido dashi ta d'aga masa hannu ta ce, "out of my side" Cikin tashin hankali ya ce, "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Duk'awa tayi ta d'auki wani dogon fasasshen gilashi ta d'aga ta saita shi dai-dai saitin cikinta cikin d'aga murya ta ce, "Kafita!" Had'a hannayensa yayi alamar rok'o ya Fara magana "Dan Allah ki tsaya ki saurareni,wallahi bada amincewa ta aka d'aura Mani aure da Inteesar ba." Zaro ido tayi cikin cikin mamaki ta ce, "Inteesar ka aura?" Girgiza Kai tayi tana fad'in "I said out, wallahi idan baka fita ba zan kashe kaina!" Ta fad'i maganar tana saita tsinin kwalbar a cikinta. Daga alk'alamin✍️ Maman Ihsan 09065327995 Love u oll😘😍 *MAULUD MUBARAK*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa. Page3️⃣0️⃣ "I said out,wallahi idan baka fita ba zan kashe kaina!" Ta fad'i maganar tana saita tsinin kwalbar a cikinta. Ganin kamar da gaske take yasa ya fita falo gaba d'aya ya rasa me zaiyi. Wauarsa ya ciro daga cikin aljihu, number Jabeer ya lalubo ya danna masa Kira,bayan Jabeer ya d'aga wayar ne muhdeen ya fara magana yana cewa "Jabeer don Allah duk abunda kake ka ajiye shi kazo gidana yanzun nan." bai jira cewarsa ba ya kashe kiran.Safa da marwa yake yana zaman jiran Jabeer. Jin sallamar Jabeer ne yasa shi sakin ajiyar zuciya,k'arasowa yayi ya rik'e hannun Jabeer ya ce, "Jabir ina cikin tashin" Kallonsa Jabeer yayi cikin rashin fahimtar inda zancensa ya dosa ya fara magat "Wai meke faruwa ne ne?" "Ai komai ma ya faru" "Kayi mani bayanin da zan gane inda zancenka ya dosa,ka kirani a waya kana cewa wai da sanina akayi maka aure wani irin aure kuma? dan Allah ka fitar dani haske domin kwata-kwata ban gane inda zancenka ya dosa ba." Cikin 'bacin ran yanayin da ya ke ciki ya fara magana "Jabeer aure suka k'ara yi mani,sati biyu da auren mu da my Sumy suka k'ara mani aure,jiya ana idar da sallar juma'a ne aka d'aura aure ba tare da sun nemi izini na ba kawai umarni suka bani inaji Ina gani aka d'aura auren.Jabeer wallahi bana son auren nan ba yadda zanyi ne." Shiru Jabeer yayi yana nazarin maganar shikam baiji takaicin wannan auren da aka d'aurawa Muhdeen ba,don yasan cewa iyayen nasau sun lura da rashin tarbiyar Sumayya ce shiyasa aka nema masa masa wata matar.A cikin zuciyarsa yaji dad'in zancen don dama ba yadda baiyi dashi ba akan kada ya auri Sumayya amma soyayyarta ta riga da ta rufe masa ido ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Wace ce matar da aka aura maka?" Cikin takaici ya fad'i sunanta "INTEESAR" Gaban Jabeer ya fad'i Jin sunan Inteesar,take yaji wani Abu zuciyarsa har sai da wayar hannunsa ta su'buce masa ta fad'i k'asa.Sunanta ya ambata da k'arfi "INTEESAR?" Kai Muhdeen ya jinjina masa alamar eh Shiru yayi na d'an lokaci kafin ya saki murmushi ya ce, "Indai Inteesar ce na Taya ka murna samunta a matsayin mata,duk da na fahimci baka son aurenta amma Ina da yak'inin cewa zuwa gaba zakayi alfahari da ita." Tsuki Muhdeen yayi "Allah ya kiyaye kaima fa na lura da cewa a 'bangaren su Gwaggo kake." Gajeren murmushi Jabeer yayi tare da cewa "Ba zaka gane gata akayi maka ba sai nan gaba." "Ba wani gata ni ba wannan yasa na kiraka ba,tunda my Sumy taji Ina fad'a maka zancen auren Inteesar har suma tayi Kai a rak'aice dai gata can a d'aki dai fashe-fashe takeyi." Da mamaki Jabeer ya saki baki yana kallonsa "Yanzu tana ina Wai?" Tana d'akinta Kai tsaye suka nufi d'akin,k'wank'wasawa suka dingayi suna bata baki amma ina bata saurare su ba.Haka suka hak'ura inda Jabeer ya nuna masa cewa ya barta zuwa anjima idan ta d'an sauko sai suyi magana. Daga haka ne Muhdeen yaja Jabeer zuwa d'akinsa inda Muhdeen ya shiga bathroom room don yin wanka inda yabar Jabeer zaune saman sofa yana jiransa. Daga can d'akin Sumayyay kuwa tunda ta gaji taga bazata iya cigaba da yayyaga kayan ba.Hakan yasa sauran akwatunan kayan lefen auren ta dinga jansu tana kaiwa harabar gidan tana jibgesu,a haka har ta gama jidar kayan lefen auren bayan ta gama jibgasu waje guda ne ta d'aga kai ta hango Mai gadin gidan tare da Zayyanu Direban gidan suna kallonta,harara ta watsa masu tare da yi wa Zayyanu Direban alamun yazo manuniya,gabasa ne ya fad'i ganin ta kirasa don kallon mahaukaciya sukayi mata ganin yadda takeyi tsoro da fargaba ya hana Zayyanu k'arasawa wajenta sai da mai gadin yayi masa da alamar yaje,cikin tsoro ya k'arasa wajenta.magana tayi masa a kausashe ta ce, "Kaje ka kawo mani fetur yanzun nan." Da mamaki ya tsaya yana kallonta, Tsawar da ta daka masa ne yasa yaba r wajen cikin rawar jiki,ba jimawa sai gashi ya dawo da fetur a cikin galan,amsa tayi tare da ce masa ya kawo mata ashana.k'arasawa yayi wajen mai gadin gidan ya amso mata ashana ya kawo mata. Ga mamakinsu gani sukayi ta bud'e robar fetur d'in ta tsiyaya shi duka a jikin akwatunan kayan lefenta,sanan ta kyasta ashana ta jefa kai tsaye cikin gidan ta koma. Jabeer dake zaune saman sofa ne ya hango bak'i ta jikin gilashin windows, mi'kewa yayi tare da d'an zuge gilashin window d'in,ganin hayak'in da ya turnik'e gidan ne yasa shi sakin salati dai-dai lokacin da Muhdeen ya fito daga wanka ganin hakan yasa cikin sauri ya saka Jallabiya suka nufi hanyar fita,don sun d'auka gobara ce. Suna nufar inda suka ga hayak'in na tasowa turus suka tsaya ganin akwatuna da da kaya suna ci da wuta. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Kalmar da Muhdeen ya furta kenan.Jabir ya kalleshi tare da cewa " ta yaya kuma me hakan yake nufi?" Ajiyar zuciya Muhdeen ya sauke tare da cewa "Sumayya ce ta k'ona kayan lefenta " Cikin mamaki Jabeer ya ce, "Kana nufin kayan lefen da kuka je Dubai kuka siyo da akwatunan sune ta bankawa wuta?" Kai Muhdeen ya jinjina masa alamun eh. "Tirk'ashi Shine kalmar da Jabeer ya fad'a,sannan ya d'ora da cewa "Gaskiya duk yadda nake tunananin Sumayya lamarinta ya wuce haka,ta wuce sanin tunanina.wannan ai hauka ne da rashin sanin darajar dukiya.kayan miliyoyin kud'in ne zata bankawa wuta?saboda mahaukacin kishi? Zuba masa ido Muhdeen yayi,kafin ya d'aura da cewa "Haka take duk lokacin da aka 'bata mata rai sai tayi asarar duk abunda ya tari gabanta,amma ban ta'ba tunananin cewa zata iya k'ona kayayyakin lefen nen ba,amma hakan Bai rasa nasaba da cewar kishi ne yasa ta k'ona kayan lefen nata." "Muhdeen zan baka shawara guda d'aya,shawarar kuma ita ce kada ka ajiye Inteesar a cikin gidannan,don idan har ka had'asu gida guda wata rana wannan mahaukaciyar matar taka zata iya kashe Inteesar ko ma ta illata ta,mafita d'aya ce shine ka raba masu gida,ka Kai Inteesar wancan gidan naka." Wani kallon irin Wanda ke nuna alamar bazaiyuba muhdeen ya watsawa Jabeer. "Wani gidan ne zan Kai ta? gidan da na gina da sunan Sumayyata ne zan d'auki waccan kucakar yarinyar na ajiye a ciki?." Da mamaki Jabeer ke binsa da ido jin kalamansa "Kamar ya?me kakae nufi ne?" "Kai nifa wallahi ka daina mani maganar yarinyar nan ba itace a gaba na ba,aure dai an d'aura ko to shikenan tunda haka suka so,amma bazan ta'ba kallon wannan kucakar yarinyar a matsayin mata ba.Yanzun kawai ka sanar dani yadda za'ayi na shawo kan Sumayya." Tsaki Jabeer yayi cikin jin takaicin maganganun da Muhdeen ya fad'a sannan ya ce, "Wannan matsalarka ce ni inada abunyi,nabar aiki a asibiti sakamakon kiranka so zan koma patient na jira na,kaima ka shirya dawowa bakin aiki don ayyuka sun mani yawa." Yana Kai K'arshen zancensa sai ya nufi motarsa ya shige,horn yayi Mai gadi ya bud'e masa ya fice yabar muhdeen yana mamakin me yasa duk 'yan uwansa suka juya masa baya akan Sumayya. Wayarsa ce tayi k'ara sunan Mummy ce ya bayyana a kan fuskar wayar,bayan ya d'aga kiran ne ta shaida masa cewa tana buk'atar ganinsa yanzun a gida.Daga nan ta katse wayar shi kuma ya shiga ciki d'akin Sumayya ya nufa still a kulle k'ofar take hakan yasa ya nufi bedroom d'insa key d'in motarsa ya d'auka ya nufi gidan iyayensa. Koda ya ya isa gidan horn yayi mai gadin gidan ya lek'o ganin motar Muhdeen ne yasa cikin azama ya bud'e masa gate,bayan yayi parking ya fito ne ma'aikatan gidan suka dinga gaishesa amma ko kallonsu baiyi ba hannu kawai ya d'aga masu don ransa yakai k'ololuwa wajen 'baci. Gwaggo ce da Mummy a falon suna tattaunawa sai Mufida dake zaune kan center carpet,don Mufida ma Bata San da zancen auren ba sai yau.Kuma Mummy ta kwa'beta cewar kada ta fad'i ma Inteesar zancen auren,su manya zasu San yadda zasu fad'a mata cikin hikima don kada ta tashi hankalinta. Da sallama ya shigo falon gaba d'ayansu suka amsa masa sallamar, inda ya k'araso ya durk'usa ya gaida Mummy "Ina wuni Mummy" Cikin sakin fuska ta amsa masa "Lafiya lau son ya Sumayya take" Jim ya d'anyi don bazai iya sanar dasu halin da yake ciki da Sumayya ba,cikin sanyin jiki ya ce, "Tana lafiya lau Mummy" Ganin yanayin d'an nata da yanayin maganarsa ta fahimci cewa akwai wata matsala don haka ta d'aura da cewa "Ka sanar da ita zancen auren ne?" Kai ya jinjina "Eh na sanar da ita Mummy" "Masha Allah ina fatan dai ba wata matsala kuma Sumayyar Bata tashi hankalinta ba,duk da nasan kowace mace ce dole zata shiga damuwa kishi kumallon mata ne." Bazai iya yi wa mahaifiyarsa k'arya ba,kuma bazai iya sanar da ita halin da suke ciki ba. Jin muryar Mummy yayi ta cigaba da cewa "Son don Allah ka rarrasheta,ka kwantar mata hankali sosai please." Kai kawai ya jinjina ya kalli goggo cikin jin haushin auren da tasa akayi masa ne ya kauda Kai ciki-ciki can k'asan mak'oshi yayi maganar ya ce, "Ina wuni" Ta'be baki tayi tare da fashewa da dariya tana fad'in "Yaro man kaza,wato fushi kake dani ko?to kaci gaba gausuwarka ma bana so d'an k'wal uba mai zubin sadaka yalla,nayi maka gata amma ba godiya ko?zanyi maganinka ne daga Kai har wannan matar taka gata nan kamar busashshen cry fish." Harara ya galla mata ta ta'be baki tana cewa "Uwarka ka harara gata nan a zaune d'an k'wal uban yaro." Dai-dai lokacin Dady ya sakko ya K'araso wajensu.zama yayin da Muhdeen ya ce, "Dady Ina wuni" "Lafiya lau,sauri nake dama zan fita nace Mummynka ta Kira Mani Kai,kana jina ko?" Kai ya jinjina "Eh Dady" "Abunda nake son na sanar da Kai shine,zancen tarewar Inteesar a ina zaka ajiyeta ne? gida d'aya da Sumayya ko kuma zaka kaita d'ayan gidanka ne?" "A'a Dady gida d'aya zasu zauna." Kai Dady ya jinjina tare da fad'in " Masha Allah" "Zancen tarewarta kuma Nan da sati d'aya zata tare." Kai kawai ya jinjina ba tare da yayi magana ba. Zancen kayan lefe kuma Ni da kaina zan bada kud'i a had Kafin yakai k'arshen zancen Gwaggo tayi saurin cewa "Sani akan me zaka bada kud'in kayan kefe?ai bazai yi wu ba,ita waccan Kai ka bada kud'in kayan lefenta?shi da kansa ya siya,to haka ma Inteesar shi ne da kansa zai siya saboda hakan zaisa ya san mahimmancinta a gare shi." Daga alkalamin ✍️ Maman Ihsan Don K'arin bayani 09065327995 Love U oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari banyi tunanin rubutashi shi dan cinzarafi kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to ku garface ni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa. Page3️⃣1️⃣ "Sani akan me zaka bada kud'in kayan kaya lefe? bazaiyuwu ba,ita waccan Kai ka bada kud'in kayan lefenta ta?shi da kansa ya siyo,to haka ma Inteesar shine da kansa zai siya,saboda hakan zaisa yasan mahimmancinta a gare shi." Kallon takaici Muhdeen ke yi wa Gwaggo sai da ta Kai K'arshen maganarta sannan ya ce, "Banda kud'in da zan siya mata wani kayan lefe yanzu,dududu Yaushe nayi auren?sati biyu kenan fa kinsan miliyoyin da na kashe a lokacin auren nan kuwa?banda wani kud'in lefe yanzun keda kika had'a auren sai ki siya mata kayan lefen." "Dan k'aniyarka ba gata nayi maka ba?" Bud'e baki yayi da niyyar maida Mata da martani Dady ya daka masa tsawa. "Kai Muhammad ka shiga hankainka , Mahifiyar tawa ce kake maidawa magana a gabana?" Sunkuyar da kansa yayi k'asa yayin da Gwaggo ta d'ora da cewa "A'a Sani ba ruwanka da shi ai wannan tsakanin kaka da jika ne ka kyalemu kawai." Jinjina kai Dady yayi tare da kallon Muhdeen ya ce, "To na dai sanar dakai sati mai zuwa Zata tare a gidanka,sannan batun kayan lefe Kai da kanka zaka had'o mata ne ko kuma kud'i zaka bayar?" Hannu ya saka cikin aljihun wandonsa ya ciro A.T.M card d'insa ya mik'awa Mummy. "Ga shinan duk abunda kuka siye sai ku cire ku biya tunda kinsan pin d'in." Amsar A.T.M card d'in tayi tare da sa masa albarka.Dady ya mik'e don dama Shirin fita yayi,daga nan yayi masu sallama ya fita.Mummy ce ta ce, "Bari na shiga ciki na d'auko waya ta na kira Aunty Abla ta shirya gobe zamu je mu had'o kayan lefen." Daga nan Mummy ta mi'ke ta nufi d'akinta,Gwaggo ce ta kalle Mufida ta ce, "Ke 'yar nan tashi ki d'auko Mani magani na nasha don anjima zamuje mu d'auko Inteesar" Cikin zumud'i Mufda ta Fara magana "Gwaggo anjima za'a d'aukota?" "K'warai kuwa anjima za'a d'aukota mu kawota gidannan idan sati d'ayan yazo sai a kaita gidan mijinta." Cikin farin ciki ta nufi d'akin Gwaggo yayin da Muhdeen ya mik'e ya fice, Gwaggo na ce masa "Asauka lafiya" Ko kallonta baiyi ba ya daka Kai ya fice. Inteesar ce zaune a gaban Abba da Umma a tsakar gidansu,Abba ya kalleta cikin nutsuwa ya ce, "Inteesar" Jin yadda yadda Kira sunanta cikin wata irin murya yasa ta zuba mada ido tana jiran Mai zaice. "Kiyi hak'uri na yanke shawara akanki ba tare da na tuntu'be ki ba,banyi shawara dake ba naji r'ayinki ba kiyi hak'u..." Idonta ne ya ciko da k'walla cikin rawar murya ta fara magana "Abba don Allah ka daina bani hak'uri akan koma meye,nice ya kamata na baka hak'uri ba Kai ba,duk shawar ko hukuncin da ka ga ya dace ka yanke akaina dai-dai ne Abba.Ni Mai biyayya a gare ka na ka daina bani hak'uri idan kana bani hak'uri ji nake kamar ban cika 'ya Mai biyayya a gare ka ba." Shiru yayi cikin alfahari da 'yar tasa ya fara magama "Na aurar da ke" Da sauri ta d'aga ido tana kallonsa da mamaki,ganin irin kallon mamamkin da takeasa ne ya sashi fad'in "Kiyi hak'uri" Sunkuyar da kanta tayi k'asa hawayen da suka taru mata ne suka samu nasarar zubowa,cikin rawar murya ta ce, "To Abba " Hawaye ne suka cika idanun Umma Don bata ta'ba kowa wa a ranta cewa Nan kusa zata rabu da 'yarta tilo ba,Amma gashi k'addara tasa lokaci guda ba zato ba tsammani zasu rabu ba,ita da ganinta sai ranar da tazo gaishesu.Abba ya cigaba da cewa "Ki kasance Mai biyayya ga mijinki yi nayi bari na bari duk abunda ya umarce ki da kiyi masa to kiyi masa matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba.sannan ki zauna lafiya da abokiyar zamanki ki bata girmanta a matsayinta na wacce take gaba dake,ki zama mai kauda kai akan al'amarin mijinki da abokiyar zamanki,kiji kik'i ji ki gani kik'i gani ki zama Mai kyautatawa ga kowa mijinki da danginsa da kowa da kowa.Ki zama Mai nutsuwa da kamun kai a duk inda kike,ki girmama mijinki kibi shi sau da k'afa kindai ga irin zaman da mukeyi da Mahifiyarki a cikin gidan nan kiyi koyi da ita." Nan dai ya cigaba da Mata nasiha masu ratsa jiki Umma ma ta d'aura da nata, Inteesar dai kanta a sunkuye yake sai kuka da takeyi.Ganin kukan nata yayi yawa ne yasa Abba ya Umarce ta da ta tashi ta shiga d'akinta. Bayan shigar ta d'akin ne,Abba ta kalli Unma ya ce, "Dama kinsan munyi maganar kayan d'akinta akan zan siyar da dabbobi na a siya Mata kayan d'aki tunda auren ba shiyawa akayi ba." "Eh na sani haka ne" Cewar Umma dake goge hawayent,Abba ya d'aura da cewa "Naje na samu kadintan nan dake bakin titi muna maganar kayan d'akin ne sai naga Alh.sani ,wato mahaifin Muhdeen ya tsaya da motarsa Yana horn,juyawa sai naganshi na k'arasa muka gaisa nan yake sanar Dani cewa kada muce zamu siye ki cokali domin su day kansu zasuyi Mata komai.Shi ya d'auki naiyin kayan d'aki komai zai siya matarsa kuma Hajiya Fatima zata siya Mata kayan kitchen,da na nuna cewa yayi yawa shine yake ce Mani Wai na manta cewa Inteesar 'yarsu ce?ko da ace ba d'ansu ne zai aure ta ba zasuyi Mata kayan d'aki ballantana tuwo na maina." Cikin jindad'i Umma ta sanya masu albarka. 'Bangaren Muhdeen kuwa yana komawa gida Kai tsaye ya nufi d'akin Sumayya,yana Isa k'ofar d'akin kuwa ya samu K'ofar a wangale,Kai tsaye ya tura Kai cikin d'akin amma bata nan ga 'barnar da tayi kaca-kaca.Closet d'in ta ya duba kayayyakin da ta yayyaga kawai ke ciki, toilet ya nufa k'ofar toilet d'in ma a bud'e take,yana makin ina Sumayya ta shiga don dai bata shiga kitchen amma duk da haka ya kutsa Kai a cikin kitchen d'in ya duba bata nan.Gaba d'aya haka ya bincike gidan nan ko wane d'aki lungu da sak'o ba Sumayya ba alamarta,sai yayi dabarar tambayar Mai gadin ko yaga fitarta nan mai gadin ya sanar dashi cewa ta fita bayan fitarsa ba dad'ewa.Nan hankalinsa yayi masifar tashi har ya rufe mai gadin gidan da fad'a kamar zai rufe shi da duka shi dai hak'uri kawai yake bashi,don yasan bashida laifi amma yasa shi gaba da fad'a alhalin shi a matsayinsa na mai gadi ya isa ya hana matar gida fita?haka ya k'araci fad'arsa ya fice. Gurin ajiye motocinsa ya nufa ya figi motar a guje Mai gadin ya wangale masa gate ya fice ya fice daga gidan.Parking yayi a gefen titi yana ta sak'e-sak'e ina Sumayya zata tafi?gashi Dad d'inta da Mum d'inta basa nan sun koma London,dama can suka fi zama ko sunzo Nigeria basa jimawa zasu koma.yanzun ta Yaya kuma ta Ina zai fara? Kai tsaye gidan k'awarta Jumy ya nufa a k'ofar gidansu ya sameta tana zance da saurayinta a cikin mota,bayan yayi parking ne kasancewar Jumy ta hangi motarsa yasa ta fito,bayan sun gaisa ne ya tambayeta k'awar ta sanar dashi bata ga Sumayya ba ya sanar da ita cewa bata gida kuma wayoyinta duka basa shiga,daga Nan dai ya yi Mata sallama ya tafi,gidan Shila ya nufa nan ma bata nan k'arshe dai haka ya hak'ura ya nufi gidan Abokinsa Salisu,daga waje ya tsaya ya kira Salisu a waya ya sanar dashi cewaa yana gida ya shigo ciki. Bayan ya shiga cikin gidan ne ya samu Salisu a fall da matarsa Saliha sai 'yarsu k'arama 'yar shekara d'aya mai suna Hidaya da sallama ya shigo falon. "Assalamu Alaikum" "Wa'alaika salam" Salisu ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya k'arasa wurin Muhdeen ya bashi hannu sukayi musabaha tare da janyo shi ya zauna kan kujera. "Abokina da alama yau dai kayi 'batan hanya ne ko?" Murmushi kawai Muhdeen yayi tare da cewa "Bari kawai" Saliha matar Salisu ne ta gaida Muhdeen "Ina wuni ango?" Murmushin yak'e yayi tare da cewa "Lafiya lau Saliha" "Ya amarya?da Safen nan muka gama zancen zuwa gidanka naga amarya." Murmushin yak'e kawai yayi tare da d'aukar Hidaya Yana Mata wasa. Saliha ce ta nufi kitchen take ta kawo masa abun ta'awa,duk d yunwar da yake ji baya tunanin zai iya kai want abu a bakinsa.ganin Saliha na zaune ne kum ga shi magariba ta kusa yasa ya mi'ke yayi Mata Sallama ya nufi k'ofar fita inda Salisu yabi bayansa suka fice. A Harabar gidan suka tsaya Salisu ya zuba masa idanu ganin yadda yadda gaba d'aya ya canza lokaci guda. "Lafiya kuwa?naga gaba d'aya ka sauya me ya faru ne?" Ajiyar zuciya Muhdeen ya sauke,sannan ya bawa Salisu labarin duk abunda ya faru.A jiyar zuciya Salisu ya sauke. "Lallai kana cikin yanzun abuda za'ayi shine mu bari muyani Ko Sumayya zata dawo idan har takai dare bata dawo ba zuwa gobe da sassafe sai mu san abunyi." Nan dai suka cigaba tattaunawa kafin sukayi Sallama ya tafi. Washe gari ne ya kama ranar da za'aje a had'o ma Inteesar kayan lefe,kuma a ranar ne za'a d'auko ta a kawo ta gidan su Mummy.Da misalin k'arfe goma na safe ne Aunty Abla k'anwar Mummy da kuma k'awar Mummy Hajiya Ameera suka zo don siyowa Inteesar kayan lefe.su uku suka tafi Mummy da Aunty Abla da Aunty Ameera ne suka tafi,aka bar Gwaggo da Mufida a gida. 'Bangaren Inteesar kuwa kwana sukayi ita da Ummanta tana tayi mata nasiha Inteesar tasha kuka kamar ba gobe har idanunta sun kumbura,ita dai bata san waye mijinta ba abunda ta sani kawai ance mata an aurar da ita, kuma an sanar da ita cewa yau zata koma gidan Mummy da zama kafin ranar juma'a akaita gidan mijinta.Bayan wannan bata san komai ba.Haka dai dai tayi ta Addu'a tana Kai kukanta ga Allah akan auren nan yasa ya zama alkhairi a rayuwarta. Da misalin k'arfe biyu na rana Mummy da su Aunty Abla suka dawo nik'i -nik'i da akwatunan da kayyaki a ciki akwatunan guda takwas ne da kayan da duk ake had'awa a cikin lefe,komai yayi kyau masha Allah.Nan dai aka bajewa Gwaggo kayan tana dubawa tana Sanya alkhairi da Addu'a Allah yasa shekara Mai zuwa ta Muhdeen da Inteesar. 'Bangaren Muhdeen kuwa ya yi neman Sumayya har ya gaji,ya Kira layin wayarta bila adadin shida Salisu tun safe suke ta nemanta Amma ba Sumayya ba labarinta,duk inda yasan tana da alak'a da mutanen wajen sun tafi wajen amma basu sameta ba. a cikin kwana d'aya muhdeen yabi ya zabge ya fita hayyacinsa domin hankain Muhdeen yafi jirgin sama tashi. Daga alk'amin ✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DOMIN K'ARIN BAYANI* 09065327995 Love u oll🥰😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne mai kashe auren wawa. Page3️⃣2️⃣ A cikin kwana d'aya muhdeen yabi ya zabge ya fita hayyacinsa, domin hankalin Muhdeen yafi jirgin sama tashi. A yammacin ranar ne Gwaggo da Aunty Abla da Hajiya Ameera suka je gidansu Inteesar dan d'auko ta.Umma ce da k'anwar ta Huraira sai k'awayenta su biyo da kuma mak'ota da suka shigo Umma ta sanar dasu,duk da ba taron biki akayi ba amma za'ayi taron biki ranar juma'a a gidan Mummy.Mama Huraira k'anwar Umma ce ta shirya Inteesar cikin atamfa riga da zani da Ummanta ta d'nika mata sai mayafi fari da aka yafa mata ta lullu'be fuskarta da shi,idan ka ganta sai ka tausaya Mata idanunta duk sun kumbara sunyi jazir hatta fuskarta ma duk tayi ja ta kumbura saboda tsabar kuka.Ita dai gata zata rabu da Abbanta da Ummanta,zata je can wani gida inda zata shirya sabuwar rayuwa gashi ita kanta ba'a fad'a mata waye mikinta ba kuma itama bata tambaya ba, tambayar da taketayiwa kanta shine,shin shima mijin bai santa ba kamar yadda itama bata sanshi ba?shin wace irin rayuwa zata yi?yanzun shikenan ta rabu da Ummanta da Abbanta kenan sai randa yazo gaishe su? Kuka ne yaci k'arfinta dakyar mama Huraira ta rarrasheta tayi shiru ta dakatar da kukan da takeyi.Nasiha sukayi mata Mai ratsa jiki sannan aka ja hannunta don tafiya,nan fa ta coge ta ri'ke hannun Umma tana kuka dakyar aka 'ban'bare hannun Umma daga nata,hakan yasa Umma itama hawayen da ta rik'e suka samu nasarar zubowa.A haka tana kuka suka nufi hanyar fita inda Mama Huraira ta tsaya da ita zauren gidan wajen Abba,shima ya d'ora da nasa nasihar sai kuka Inteesar take yi,haka dai aka ja hannunta suka nufi hanyar fita, inda aka jera motoncin.Motoci guda uku ne aka shiga da Amarya d'aya inda Mama Huraira da k'awayen Ummin suka shiga mota d'a ma'kotansu ma d'aya,yayinda su Gwaggo da Aunty Abla ma suka shiga d'aya.duk da cewar unguwa d'aya ce basu da nisa minti kad'an suka isa gidan,bayan Mai gadi ya wangale masu gate ne suka shiga nan aka firfito Mama Huraira ce ta rungume Inteesar ta gefen kafad'arta suka shiga cikin gidan. Part d'in Muhdeen da ya zauna kafin ya auri Sumayya nan aka ajiyeta,duk da cewar ba dad'ewa yayi da barin d'akin ba sati biyu kenan,ba wani k'ura sosai dama Mummy ta sanya Mufida ta gyara part d'in.Da sallama suka shiga falon ba kowa sai k'amshi ke tashi,har bedroom aka shiga da ita inda aka zaunar da ita bakin gado.kasncewar lokacin sallar magariba ne yasa sukayi Mata sallama akan cewa zasu dawo ranar juma'a,waro ranar da za'a kaita gidan mijinta. Har yanzun Inteesar Bata san waye mijinta ba ta d'auka saboda shak'uwar da ke tsakaninta da 'yar gidan su Mummy yasa aka ce ta zauna nan gidan kafi akaita gidan mijinta. Bayan kowa ya watse ne ita kad'ai ta ragae a d'akin,ido ta zubawa d'akin tana k'are masa kallo a zuciyarta tana cewa d'akin wannan mugun aka kawo ni,mutum sai mugunta da da bak'in hali a haka dai ta nufi toilet ta d'auro alwala tazo ta shimfid'a sallaya ta tada sallah. A can aibitin Muhdeen kuwa Salisu ne ya fito daga d'akin tiyata hankalinnsa a tashe, wayarsa ya ciro Number Muhdeen yayi dialing, Muhdeen na kwance a samam gadonsa ya lumshe idonsa kamar mai bacci tunanin Sumayya kawai yakeyi,ya rasa ina zai same ta faga k'arshe dai ya yanke shawarar zuwa London wata kila can take tafi wajen iyayenta,yana cikin wannan tunanin ne wayarsa ta fara ruri da sauri ya bud'e idonsa don kullun baya cire rai akan Sumayya zata kira sa,ganin Jabeer ne yasa shi sakin tsuki don dama haushin Jabeer ya ke ji akan bai goyi bayansa ba ya juya masa baya.Yana gani wayar ta katse bai d'aga ba,har aka k'ara kira still bai d'aga ba sai da Jabeer ya kira sau biyar sannan ya d'aga don yasan idan Jabeer ya matsa da kira akwai abu mai mahimmanci da yasa shi yawaita Kiran.Daga wayar yayi ba tare da yayi magana ba,ganin ya d'aga yasa Jabeer ajiyar zuciya ya ce, "Muhdeen akwai matsala fa" Tsaki muhdeen ya yi tare da cewa "Kaine bak'on matsala ni tun jiya nake cikin matsala ka sani." Cikin tashin hankali Jabeer ya cigaba da magana "Kaga duk abunda kake ka bari ka taho nan Hospital Emergency ne..." "Kamar ya duk abunda nake na bari nazo?Kai me kake yi da ba zaka yi abunda ya..." Katse sa Jabeer yayi tare da cewa "Ba lokacin dogon magana tunda kayi aure k'afarka bai lek'o Asibiti ba kullun kana gida,ban ta'ba kiranka ba sai yau to tunda kaga na kiraka abun yafi k'arfin mu ne don Allah kazo ba lokaci." Katse wayar yayi tare da mi'kewa time ya duba k'arfe goma na dare wayarsa ya saka a aljihun wandonsa ya d'auki makullin motarsa ya fice don zuwa Asibit. Inteesar kuwa tunda ta idar da sallar magarib bata tashi ba sai da ta idar da sallar isha'i.Bakin gadon ta zauna har mai aikin Mummy ta kawo mata abinci da abunsha,ruwa kawai tasha ta zauna tayi tagumi tare da fad'awa duniyar tunani. Mufida ce tayi sallama "Assalamu Alaikum" Inteesar da ta kwanta akan sallaya ta amsa da cewa "Ameen wa'alaiki salam" Mufida madadin ta shiga sai ta tsaya daga bakin k'ofar tayi shiru,jin shirin yayi yawa ne yasa Inteesar cewa me haka Mufida ki shigo mana,cikin tsokana Mufida ta fara magana. "Wace ni da zan shigo d'akin ma'aurata kai tsaye,na sani ko Angon na ciki?" Ta shigo tana k'unshe dariya a bakinta,kallon mamaki Inteesar ke yi wa Mufida cikin takaici ta fara magana "Nagode Mufida wato ma dariya kike mani ko?ina cikin k'unci ke kina farin ciki ko?me yasa kika canza mun ada tare muke kuka tare muke dariya Amma yanzun Ina kuka ke kuma dariya kike mani ko?" "Ba haka bane Inteesar matsalarki tawa ce tawa ma taki ce, gaskiya ina farin ciki da wannan auren naku sosai ba kad'an ba." Ran Inteesar ne ya 'baci sai ta fashe da kuka tare da fad'awa jikin Mufida ta fara magana cikin kuka. "Mufida bansan yadda zanyi ba anyi mani aure ba tare da na shiryawa hakan ba,banida burin aure yanzun ban sakawa raina aure nan kusa ba,karatu naso nayi Mifida bansan dalilin da yasa lokaci d'aya Abba na ya aurar dani ba.banyi wani abu na rashin kyautatawa ba ko na rashin d'a 'a ballantana nace ko shine dalilin da yasa suka aurar dani kudun kada na kunyata su.Kuma wani abun takaicin ma ki Mijin da aka aura mani bansanshi ba Mufida." Tausayinta ne ya cika Mufida,don tabbas tasan cewa Inteesar karatu tasa a gaba sai gashi Allahu yayi ikonsa sai dai abin da ya d'aure mata Kai yadda akayi Inteesar Bata san waye mijinta ba. "To wai ke ya akayi baki san mijin da aka aura making ba?" "Basu fad'a mani waye mijina ba nima bazan iya tambayarsu ba" Shiru Mufida tayi kamar ta fad'a mata waye mijin Amma sai ta kasa tana tsoron abunda zai biyo baya kada aji mutuwar sarki a bakinta.Rarrashinta ta dingayi har tayi shiru ta nutsu,ganin bata ta'ab abincin da aka kawo mata bane yasa Mufida janyo abincin cikin hikama taja Inteesar har suka ci suka k'oshi sannan mufida ta kalleta tare da cewa "2 minutes" Hanyar fita ta nufa ita dai Inteesar ta zauna tayi tagumi,ba jimawa sai ga Mufida ta dawo da wani k'aramin akwati da kaya a ciki, kallon Inteesar ta yi ta ce, "Wannan kayanki ne ki tashi ki watsa ruwa, Mummy ta ce na kawo maki kuma wai yau ni zan tayaki kwana." Inteesar taji dad'in hakan mi'kewa tayi ta nufa toilet don yin wanka. A can Asibiti kuwa misalin k'arfe biyu na dare Muhdeen ya fito daga d'akin tiyata Kai tsaye office d'insa ya nufa.Bayan ya shiga ne ya nufi bedroom d'in dake cikin office d'in,kayan jikinsa ya rage ya nufi bedroom ya watsa ruwa ya fito jallabiya ya saka ya k'ara gudun A C ya haye gado tare da janyo bargo ya lullu'be. Washe gari ne da misalin k'arfe tara na safe, Muhdeen ya shigo gidan,da Sallama d'auke a bakinsa ya shigo falon,don dama yana so yayiwa Dady maganar zuwansa London saboda baisan halin da Sumayya ke ciki ba.Ba kowa a falon Gwaggo na d'akinta Mummy kuwa tana kitchen ita da Mufida, kitchen d'in ya shiga ya gaida Mummy yayin da Mufida ta gaida shi nan yake tambayar ko Dady na ciki, Mummy ta shaida masa cewa ya fita tun safe.Hakan yasa dole ya hak'ura inda ya ce zaije ya dawo anjima da yamma lokacin da Dady ya dawo.Har ya kai bakin k'ofa Mummy ta kira sa. "Son" Juyowa yayi tare da cewa "Na'am Mummy" Kafin ka wuce ka biya ka gaida Gwaggo sannan kuma Inteesar tana part d'inka can aka ajiye ta kafin ta tare a gidanka,itama ka lek'ata ku gaisa kafin ka tafi." Shiru yayi kafin ya amsa da cewa "To Mummy" Baiso hakan ba amma ba yadda zaiyi,d'akin Gwaggo ya fara shiga bata nan amma sai yaji k'arar saukar ruwa a toilet,hakan ya tabbatar masa da cewa wanka take. Part d'insa ya nufa ba kowa a falon,Kai tsaye ya shiga bedroom d'in. Inteesar kuwa tana tsaye ta juyawa k'ofar baya,photon Muhdeen dake manne a bango yana murmushi ta zubawa idanu hararar photon take tana ta surutu ita kad'ai Bata San da shigowarsa ba shima baiyi magana ba,jinmuryarta yayi tana cewa "Hmm kalli yadda yake murmushi a photo kamar bashine wannan mugun ba,mai bak'ar mugunta.Bazan ta'ba mancewa da marukan da kayi Mani a baya ba,kawai don kuskure da nayi bada sanina na watsa maka yawu ba Amma ka dinga marina wanda tunda nake a rayuwa ko mahaifina da mahaifiya basu ta'ba Mani irinsa ba.gashi banda lafiya lokacin haka ka sakani wankin kayanka a cikin toilet dinka duk da haka bai isheka ba sai kace na zauna a rana nayi gadin kayanka har su bushe na goge.Allah ya isan Mani mugu kawai ka banj wahala." Kamar daga sama taji muryar mutum a bayanta yana cewa "Ban baki wahala ba tukunna ki shiya shan wahalar nan gaba." A firgice ta juyo ta kalle shi,wannan shine karo na farko da ta tsaya ta kalleshi da kyau,kyakkyawa ne ajin farko yana da matuk'ar kwarjini gashi da k'ira da cikar zati irin na cikakken namiji.cikin takunsa na k'asaita da tafiyarsa irin na lafiyayyan maza ya k'araso gabanta. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don k'arin bayani* 0965327995 Love u oll😘😍 Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne mai kashe auren wawa. Page3️⃣3️⃣ Kyakkyawa ne ajin farko yana da matuk'ar kwarjini, gashi da k'ira da cikar zati irin na cikakken namiji.cikin takunsa na k'asaita da tafiyarsa irin na lafiyayyan maza ya k'araso gabanta. Gabanta ne ya tsananta fad'uwa ganin fuskasa a d'aure tamau ba alamun rahama,tasan halinsa sarai lokacin da bata zagesa ba ya suka k'arke ballantana da yanzun yaji tana zaginsa.Tsoro ne yakamata tuna wahalar da tasha a ranar da murd'e mata hannayenta tare da matse mata baki. K'ara matsowa kusa da ita yayi har suna shak'ar numfashin juna,cikin tsoro ta bud'e baki zata yi magana ya d'aura yatsar sa d'aya a bakinsa tare da fitar da sautin shhhh. Hakan yasa ta kama bakinta tayi shiru idonta a k'asa Don bazata iya jurar kallon cikin idanunsa ba,don wani irin kwarjini ne dashi. Baya tayi da niyar guduwa tabar masa d'akin amma inaa kafin ta gudu ya damk'o hannunta.Nan take ta ce, "A'uzubillahi mina shaid'ani rajim" "Ke nayi maki kama da shaid'an ne da kike mani ta'awizi?" Kamar zata yi kuka ta fara magana "Nifa yanzun matar aure ce ka sakar mani hannu." K'ara matse hannayenta yayi wanda saboda azaba sai da idanunta ya tara k'wallan azaba. turo k'ofar d'akin akayi Mufida ce ba tare da sallama ba ta fara magana "Inteesar Mummy ce ta..." Bata k'arasa maganar ba ta tsaya turus sakamakon ganin Muhdeen da Inteesar da tayi tsaye yana rik'e da hannun Inteesar,sunkuyar da Kai tayi tare da cewa. "Ku gafarceni na shigo maku Kai tsaye." Daga nan ta juya zata fice taji muryar Inteesar na cewa, "Yauwa Mufida gara da kika shigo ki fad'a masa cewa ni matar aure ce Kinga yadda yadda matse..." Kafin ta kai K'arshen maganar ne taji ya daka wa Mufida tsawa. "Get out in my room" Da sauri Mufida ta fice a d'akin,don ta tsorata da tsawar da ya daka mata,maida dubansa ga Inteesar yayi yana cewa. "Da kike cewa ke matar aure ce ni zaki fad'awa aure?to ki tantabara ce ke ni ba damuwa ta ba ce." Murd'e hannayanta yayi da d'an k'arfi tare da cewa " ni kika gama zagi ko? wato nine bak'in mugu ko?" Kai ta girgiza masa idanunta na zubda hawaye ta ce, "I'm sorry" Gajeren murmushi ya yi yana cewa "Sorry for your self" Yana rik'e da hannayenta wayarsa ta Fara ruri zaro wayar yayi daga cikin aljihunsa,d'agawa yayi tare da cewa. "Jabeer ya akayi ne?" Jabeer yana shirin bud'e baki yayi magana kenan sai yaji muryar Inteesar ta cikin wayarsa tana kuka tana cewa "Dan Allah yaya Muhdeen kayi hak'uri ka barni haka nan wallahi da zafi,ka tausaya mun haka." ta saki k'ara lokacin da ya k'ara matse hannayenta.Jabeer kusa daga can cikin wayarsa yake Jin maganar Inteesar.Dariya ya kece dashi sosai har ya zauna daga tsayen da yake, shi a tunaninsa muhdeen sex yake da Inteesar da ya ji tana cewa akwai zafi ya barta hakanan ya ji k'aran da ta saki hakan yasa yakewa Muhdeen dariya.sai da ya tsagaita da dariyar kafin ya fara magana. "Lallai namiji bashida kunya wato duk zagin yarinyar nan da kake kana cewa kucakar yarinya Allah ya kiyaye ka tsaneta yanzun ta tashi daga kucakar ne?ko kuma k'iyayya har ta juya ta koma soyayya ce? Hhhhj to kadai bi 'yar mutane a sannu kasan sabon shiga sa..." Tsuki Muhdeen yayi tare da katse kiran,hannun Inteesar ya saki tare da hankad'ata ta fad'a Kan gadon tana sakin kuka. Mummy da Mufida ya samu a dinning room suna Breakfast,Sallamar Mummy yayi tare da sanar da ita anjima zai dawo yana son magana da Dady.Nan Mummy ta nemi yayi Breakfast kafin ya tafi amma ya nuna a office zaiyi Breakfast,hakan yasa ta barshi ya tafi hakanan. Fitarsa kenan sai ga Gwaggo ta fito daga d'akinta,k'arasowa tayi tana fad'in "ina cikin band'aki sai naji kamar muryar Muhammadu ya shigo d'akina shin ya tafi ko yana nan?" Mummy ce ta bata amsa "Yanzun ya fita amma ya ce anjima zai dawo." Kallon Mufida Gwaggo ta yi tana cewa "Ya banga 'yar albarka ba?" Mik'ewa Mufida tayi "Bari naje yanzun na kirata dama lokacin da naje kiranta na sameta ita da yaya ne a cikin d'akin,yanzu tunda ya fita bari na koma." Da sallama ta shiga d'akin,jin muryar Mufida ne yasa Inteesar saurin goge hawayenta,d'agowa tayi ta kalli Mufida tana sakar mata murmushi,da mamaki Mufida ta kalli fuskarta. "Lafiya kike kuwa naga idonki kamar kinyi kuka?" "Bakomai banyi kuka ba,barcin da na tashi ne yasa idanu na sukayi haka." Murmushi Mufida tayi tana fad'in "Tare da ke fa muka tashi barci idonki baiyi haka ba sai yanzun?koda ya ke bazan matsa maki tashi muje muyi Breakfast." "Yauwa Mufida bari na tambayeki mana ." "Ina jinki" "Me yasa aka sauke ni a d'akin nan ne?wallahi banso zama a d'akin nan ba ga mai d'akin ya dawo ya sameni a ciki nifa gasky zan koma d'akinki ko na Gwaggo." Dariya Mufida yayi tana cewa "To ai ba inda Zaki zauna bayan nan nan ne yafi dacewa dake." Tunawa tayi da cewa Kila fa haryanzun ba wanda ya fad'awa Inteesar cewa Muhdeen ne mijinta.Hakan yasa bata sake magana taja hannun Inteesar suka nufi hanyar fita. Koda suka k'arasa dinning table kallo d'aya Gwaggo tayi mata taga idonta ya yi kama da na wacce ta yi kuka.Haka ma Mummy ta lura da hakan, Gwaggo ce ya fara magana. "To 'yar albarka lafiya me ya sameki ne kikayi kuka?" "Banyi kuka ba Gwaggona" Mummy ce ta zuba mata ido "Kada kiyi mana k'arya don ba d'abi'arki ba ce k'arya kada ki fara." Shiru tayi tana nazari,don ita dama duk abunda zai janyowa wani 'bacin rai bata so,hakan yasa ta ce, "Bakomai" Kai Mummy ta girgiza "Kodai da son ya shiga ya 'bata maki raine?idan ya maki abunda ba dai-dai ba ki fad'a mani a matsayina na mahifiyarsa zand'auki mataki aka sa." Murmushin yak'e tayi "Ba komai ya sani kuka ba kawai na tuno da Abbana da Umma ne yasa nake kuka" Kai Gwaggo ta girgiza tana cew, "Kiyi hak'uri kinji kowa haka akayi mata Umman taki mma haka Mata ." Nan dai suka dinga Bata baki sai da suka dinga bata baki har ta hak'ura sukayi Breakfast suka gama.Bayan kammalawarsu ne Gwaggo ta ce Inteesar ta koma d'akin Muhdeen zata zo ta same ta,haka kuwa akayi Inteesar ta ka d'aki ba jimawa Gwaggo ta shigo hannunta d'auke da wani galam da kuma Babbar robar ruwa da wani abu a cikin robar.Inteesar na zaune saman sofa dake ckin bedroom d'i,gefenta Gwaggo ta zauna tare da ajiye su,kofin da ta d'aura saman Galam d'i ne ta d'auko robar k'arami ta bud'e tare da tsiyayo wani abu daga cikin gorar,mik'awa Inteesar tayi "Kar'bi wannan yanzun ki shanye shi yanzunnan." Kar'ba Inteesar tare da zubawa abun ido gashi kamar zuma Amma ga wani garin abu a ciki kamar garin magani a ciki. "Gwaggo meye wannan kuma?" "Zuma ce ta mata da tsumi,kar'bi kisha." Kar'ba Inteesar tayi ta fara sha,dama ita akwaita da son zak'i to zak'in da taji ne yasa nan da nanan ta shanye shi tas.Kar'bar kofin Gwaggo tayi tare da zuba mata tsumin cikin kofin ta mik'a Mata, dai-dai lokacin da Mufida ta shigo d'akin,kafa baki Inteesar tayi ta fara sha sannan ta cire baki tana d'an yamutse fuska ta ce, "Gwaggo naji wannan da d'an bauri bai yi zak'i kaman wancan ba,gaskiya ni ya isheni hakannan" Ta k'arasa maganar tana mik'awa Mufida sauran tsumin kar'ba Mufida tayi zata shawa sai Gwaggo tayi saurin k'ar'ba ta mik'awa Inteesar tana cewa, "Me yasa zaki bata?to ba irin nata bane,itama idan lokacin ta yazo zata sha ne amma ba yanzun ba." "Yaushe ne lokacinta?" "Lokacin da tayi aure kamar yadda kema kikayi." "Gwaggo Wai kina nufin saboda nayi aure kika bani?" "K'warai kuwa kayan mata ne gobe ma za'a kawo maki wasu,don Mummyn Mufida tasa akawo maki wasu." Suna Jin haka sun san inda zancenaGwaggon ya dosa tura baki Inteesar tayi yayin da Mufida ke ta yi mata dariya. "Nidai Gwaggo don Allah ku kyale ni wallahi bana so." Fuska Gwaggo ta had'e "Ke dalla gafara can ana nuna maki ga annabi kina rintse ido,akwai gatan da zamu nuna maki wanda ya wuce wannan ne?ko ba don shi jikana ba zanyi ba ko ba komai ni maiyi maki ne,Ballantana jikana nayiwa." Ita dai Inteesar bata san inda maganar Gwaggo ya dosa ba,Don Bata gane nufinta ba.Turo k'ofar akayi had'i da sallama Mummy ce hannunta rik'e da food flask Aunty Abla na biye da ita a baya, Mummy ce ta mik'awa Gwaggo food flask d'in tana cewa, "Kinga ma na d'auka sai gobe ne zata had'o da sauran kayayyakin ta kawo ashe ma Wai tunda an riga an dafa kazar shine ta fara kawo ta tare da sauran magungunan." Aunty Abla ce ta gaida Gwaggo. "Ina kwana Gwaggo" "Lafiya lau Abla ya Mai gidan da yara duka?" "Lapiya qalau suke Gwaggo." "To masha Allah,amma kazar ce kawai ta samu?" "Eh Gwaggo sauran Wai sai gobe zata had'o su,kuma ina da shwara Gwaggo matar nan k'awata ce munyi magana da ita idan ba damuwa da ankai Inteesar ta zauna a gidanta na sati d'aya yadda zata gyara ta ciki da waje,wallahi idan kika yadda na tafi da Inteesar gidanta na tsawon sati d'aya kawai wallahi sai kinyi mamakin canzawa da zatayi don Wallahi sai ta burge ki." Jim kad'an Gwaggo ta yi tare da kllon Mummy ta ce, "Fatima ya kika gani game da shawar k'anwar taki?" Murmushi Mummy tayi tare da cewa "Gwaggo nima nayi wannan tunanin,nariga ta a zuci ne ita kuma ta rigani a baki,nasan Hajiya Bilkisu k'awar Abla ce tun suna yara,sana'ara ce gyran amare da zaifi idan muka bari suka tafi tare don wasu ma tun biki na wata d'aya saura suke Kai yaransu gidanta." Gwaggo jinjina Kai tayi "To shikenan tunda haka kuka ce na amince ta tafi da ita d'in,amma fa ina ganin sai anyi fama da yarinyar nan, yanzun nake bata tsumi da zumar mata take ce Mani wai bata so mubarta hakanan." "Karki damu Gwaggo zata kula da ita yadda yadda kamata ba zata barta hakanan kawai ba,ki tana so ki bata so sai anyi mata,ni kuma kullun zan dinga lek'awa Ina duba su. Ta k'arasa maganar tana zama gefen Inteesar tana cewa "Tare zamu tafi kinji daughter" jinjina Kai kawai Inteesar tayi don bata son tayi masu gardama ne yasa ta yin shiru,amma ita har ga Allah bata k'aunar zuwa wani gidan gyaran da za'a kaita. Mummy ce ta kalli Gwaggo tana cewa "Yanzun taci kazar su tafi don ta ce sauri take zatayi bak'i." Gwaggo ce ta bud'e flask d'in da aka zuba kazar ta mik'awa Inteesar,ganin gari-garin magani a jikin kazar yasa Inteesar ture baki, Gwaggo ce tayi Mata magana "Zaki tsaya kina tura baki ko kuma zakici kazar ne ku tafi ko kuma zaki tsaya kina turawa mutane baki ne." A shagwa'be ta fara maganar "Wallahi Gwaggo na k'oshi ba wajen da zan saka kazar nan." Jin hakan yasa Aunty Abla cewa "Kada ku damu ku rufe mani flask d'in mu tafi dash,ko tana so ko bata so zata cimye shi tas." Aunty Abla ce ta kar'bi flaak d'in ta rufe tare da kallon Inteesar ta ce, "Tashi ki saka hijabi kid'ebi kayan sawanki na sati d'aya mu tafi." Ba musu duk da a ranta bata so hakan ba amma bata da za'bi hakan ta mik'e ta d'auki hijab d'inta ta saka mummy ce ta ce, "Kid'auki akwatin kayan da Mufida ta kawo maki jiya dadaddare kije dasu gaba d'aya." Mufida ce ta janyo akwatin kayan gaba d'ayansu suka fita har harabar gidan,but d'in motar Aunty Abla Mufida ta bud'e ta saka akwatin kayan sannan ta bud'ewa Inteesar murfin motar gefen Aunty Abla ta zauna,sallama sukayi da juna sannan Aunty Abla taja motar tare da yin horn mai gadi ya bud'e mata suka fice daga gidan. Lokacin da Muhdeen yabar gidan Asibiti ya koma,Kai tsaye office d'in Jabeer ya nufa yana k'ok'arin knowking ne Jabeer ya murd'a handle d'in k'ofa zai fito,ganin Muhdeen ne yasa ya koma ciki yana k'unshe dariya a bakinsa,zama yayi a sofa dake cikin office d'in Muhdeen ya tsaya tsaye ya zuba masa luhuluhun idanunsa yana kallonsa.Jabeer ne yayi k'ok'arin dakatar da dariyarsa ya ce, "A mijin kucaka har ka gama kwasan romon amarcin ne? Dan Allah adai dinga d'aga k'afa kasan sabbin shiga sai a hankali sai ana tausaya masu,duk da nayi mamakin cika bakin da ka dingayi akan Inteesar sai dai abun mamaki a Rana d'aya ka zubar da makamanka,banyi tunanin haka da wuri ba fa nace ashe ashe kucakar yarinyar da ka tsana zatayi maka rana 'Dan iska jarababbe ranar har kana cewa ko Mata sun k'are a duniyar nan ba abunda zakayi da ita,Ashe har matan sun k'are banda labari." Ya k'arasa maganar yana kecewa da dariya, Muhdeen ransa ne ya gama 'baci kuma shi Mai yawan magana ba gani yayi baida lokacin 'bata lokacinsa a kan Jabeer yasa ya mi'ke ya nufi hanyar fita.Da sauri Jabeer yasha ganansa tare da cewa "Sorry friend dama na kiraka ne dan na shaida maka kana da patients suna jiranka" Daga nam Muhdeen yasa Kai ya fice ya bar Jabeer na binsa da kallo. A yammcin ranar ne Muhdeen ya koma gida dan magana da mahaifinsa,cikin sa'a kuma ya same su dukkansu a falo Dady, Gwaggo,sai kuma Mummy,da sallamarsa ya shigo falon,gaba d'ayansu suka amsa masa nan ya gishe da kowa da kowa harda Gwaggo yau cikin girmamawa ya gaishe da ita yana kwantar da Kai Dan kada tasa Dady ya hana shi zuwa London.Harda yi mata alk'awarin kawo mata magungunan ciwon k'afarta Wanda zata ji dad'i haka ya dinga kamfen a wajen Gwaggo don yasan ba k'aramin aikinta bane tasa Dady ya hana sa tafiya. "Muhammad ya akayine ance kana ta zuwa nema na bana nan kuma baka sanar dani a waya ba." Sunkuyar da Kai yayi "Dady maganar ba Bata waya bace shiyasa." "To Allah yasa lafiya ina jinka" "Dady Sumayya ce ta tafi bansan inda ta je ba tun da taji an d'aura aure na da Inteesar ta saka k'afa tabar gidan har yau bansan inda ta tafi ba." Da mamaki Dady ke kallonsa "Subahanallahi shine tun tuni baka sanar da kowa ba sai yanzu?Haba Muhammad ai baikamata kayi shiru ba." "Dady abunda yasa nayi shiru na d'auka zan ganta ne sai na shawo kanta mu cigaba da zamanmu,to gaba d'aya mun zaga garinnan inda nasan cewa tana da k'awa ko dangi ko wani Wanda yake da alak'a da ita amma ko ina bata nan." Mummy ce ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,shine na aka tambayeka ka sanar da matarka kace eh." "Wallahi Mummy na d'auka zan iya shawo matsalar ne,kuma na Kira number Dad da Mum d'inta duk basa shiga." Dady ne ya ciro wayarsa a aljihu ya Kira number Dad d'in Sumayya Yana ringing baj d'aga ba, har sau uku.Nan dai ya kwantar wa Muhdeen da hankali,ya ce su tafi masallaci kasancewar lokacin sallar magarib tayi. *WAIWAYE* A ranar da Sumayya ta k'ona kayan lefenta bayan ta koma d'aki ta Kira Mum d'inta tana kuka ta sanar da ita komai.Ran Mun nata ta ce ta tattara kayanta ta bar gidan wani irin wulak'anci ne zasu bada auren 'yarsu sati biyu da aure a k'ara mata kishiya?bazai yiwu ba.Ta bata shawarar ta tattara kayanta tabar masa gida kada ma ta je wurin da zai nemota ta tafi Hotel washe gari ta jirgi ta taho.Shiyasa da Muhdeen ya gama zaga gidajen duk Wanda yasan Yana da alak'a da Sumayya bai same ta ba.wannan shine abunda ya faru Bayan Dady da Muhdeen sun tafi Masallaci basu dawo ba sai da aka Kira sallar isha'i.Suna zaune a Dinning table kafin su fara cin abinci Dady ya k'ara gwada Kiran number Dad d'in Sumayya.A wannan karon ya d'aga.Kasancewar wayar a amsa kuwa take yasa dukkansu Gwaggo da Mummy da Muhdeen suna jiyo muryar Dad d'in Sumayya. "Me ka kirani a waya ka sanar dani? cewa d'anka ya saki 'yata ko me? Kunsan kuma da matar da zaku aura masa kuka bari ya auri 'yata?to Bari kaji 'yata ba zata zauna da kowace kishiya ba.Tun yaushe tabar gidan da yake baku damu da halin da ta shiga ba shiyasa baku Kira ba sai yanzun ko? Dady ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Alhamdulillah tunda tana wajenku hankalina a tashe yake da naji mijinta wai baisan Ina take ba,dan Allah ka saurareni nayi maka bayani ba yadda kake tunani bane,nasan ranka ya 'baci amma ka fahimcemu." Dad d'in Sumayya fad'a ya cigaba dayi "Babu fahimtar da zanyi maku d'anka ya za'bi d'aya ko 'yata ko wacce kuka aura masa." Daga Nan ya katse kiran wayar. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Domin k'arin bayani 09065327995 *INA BARAR ADDU'ARKU DAN ALLAH KUSA K'AWATA A CIKIN ADDU'ARKU TANA CIKIN DAMUWA ALLAH YA YAYE MATA DAMUWARATA YA KAWO MATA FARIN CIKI A CIKIN RAYUWARTA.DA MA DUKKANIN AL'UMMAR MUSULMI*🙏 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa. Page3️⃣4️⃣ "Babu fahimtar da zanyi maku d'anka ya za'bi d'aya ko'yata ko wacce kuka aura masu" Ran Gwaggo ne yayi maaifar 'baci da jin kalaman Dad d'in Sumayya,don haka ta ta mi'kawa Dady hannu alamun ya bata wayar,ba musu ya mik'a Mata kamar yadda ta buk'ata.Kar'ba tayi tare da karawa a kunnenta ta fara magana. "Waye kai da har zaka ce ya za'ba ko 'yar ka ko matar da ya aura?to bari kaji ninan kakarsa wacce ta haifi ubansa kuma ta aura masa Inteesar nace baka Isa ba kayi kad'an.kai da ka kasa ba 'yarka tarbiyya shine..." Muhdeen ya k'araso gabanta yana had'e hannaye alamun rok'o,a hankali yake mata magana dan kada Dad d'in Sumayya ya jiyo muryarsa. "Kinga Gwaggo ya kike neman ki 'bata komai ne?don girman Allah ki rufa mani asiri ki lalla'basu ko zata dawo,idan bata dawo ba wallahi akwai matsala ." Tsawa ta daka masa "Dalla can rufe mani baki kada Allah yasa ta dawo mana, idan 'yar tasa wata masifa ce ya jik'ata ya shanye." Hannu Muhdeen ya d'ora akai ganin Gwaggo ta dagula komai. Dad d'in Sumayya da Mum d'inta kuwa duk suna jin komai dake faruwa ta cikin wayar. Gwaggo ta cigaba da magana "Idan ma za'ba zaiyi sai dai ya za'bi za'bin da nayi ma..." Mum d'in Sumayya ce ta kar'bi wayar daga hannun Dad ta katse kiran cikin 'bacin rai ta fara magana. Akan me zasu wulak'anta mana 'ya? to bamu gaji da 'yar mu ba?wani iri wulak'anci ne wannan ace aure ko wata d'aya bai kai ba ace anyi mata kishiya,sannan ta dawo gida basu nemeta ba sai yau basu damu da halin da take ciki ba,sannan cin mutunci ne zai biyo baya?wallahi bazai yiwu ba 'yata ba zata zauna da wannan 'yar matsiyatan ba don bata Kai matsayin da 'yata zatayi kishi da ita ba." Kai tsaye ta nufi d'akin da Sumayyar take ciki,tura k'ofar tayi ta shiga zaune ta sameta rik'e da wayarta tana kallon photon Muhdeen tana kuka.kar'bar wayar tayi daga hannun Sumayya Wanda hakan yasa ta d'ago Kai da sauri ta kalli Mum fusrkata da kwalla. "Mum Kinga har yanzun bai biyo ni ba ki?yana can ya tare da wannan matsiyaciyar Inteesar d'in wallahi bazai yuwu ba Muhdeen nawa ne ni kad'ai duk maccen da ta ra'besa sai na kasheta ko kuma na illatata,Bata Isa ta mallaki abunda na mallaka ba." Haka dai tayi ta surutu a cikin tana jifa da pillows d'in dake saman bed d'in, Mum d'inta ce ta rungumeta tana rarrashinta. Muhdeen kuwa tsabar tsabar takaici da bak'in cikin abunda Gwaggo tayi ne ya ishe sa.Bayan Mum d'in Sumayya ta katse kiran ne ta kalli Gwaggo cikin jin haushinta ya fara magana. "Wai Gwaggo meye matsalarki dani ne?duk kinbi ki addabi rayuwata,kin hanani samun nutsuwa a rayuwata wai me nayi maki ne?kullun kika tashi magana Zaki ce wai cikin jikokinki kinfi sona da k'aunata ta,amma a ganina ba Wanda kika tsana kamar ni.Kinbar kowa ya auri matar da yake so ya zauna da ita amma Ni tun ranar da na kawo Sumayyar nan a matsayin matar da zan aura kika fara kushe ta Wai bata da tarbiyya,shin ke Zaki zauna da ita da rashin tarbiyar ta ko kuma Ni zan zauna da ita?na aure ta duk da haka bai isheki ba sati biyu da auren mu kika sa aka d'aura mani aure da wata Wai Inteesar to Bari koji bana so Inteesar Sum..." Kafin yakai k'arshen zancen Dady ya d'aga hannu zai mare shi ne Gwaggo ta daka masa tsawa "Kai Sani!!" Dakatawa yayi daga Marin da yayi niyar masa,don a rayuwa Gwaggo ta tsani abunda zai ta'ba Muhdeen tana k'aunarsa fiye da sauran jikokinta,tun yana yaro take masifar ji da shi Bata k'aunar taga an ta'a mata shi. "Akan me zaka mare sa Sani?" "Haba Gwaggo kina Jin yadda yake magana dake kamar ..." "Ba ruwanka da nu yake bada kai ba ku daina shiga lamarina da Muhammadu." Dallonsa Dady yayi tare da cewa "Tashi ka tafi gidanka" Ba tare da ya ce komai ba ya mik'e ya ya fice,gaba d'aya ya rasa me ke masa k'unci kawai yake ji a zuciyarsa,ga rashin Sumayya ga kuma aurennan na Inteesar dan ko kad'an baya Jin soyayyar Inteesar a cikin zuciyarsa.Yayi da ya sanin maganar nan a gaba Gwaggo gashi ta 'bata masa komai har ran Dady ya 'baci shi da yasa ran Dady zai fahimci halin da suke ciki amma ba haka ba. 'Bangaren Inteesar kuwa tana nan tana shan gyara sosai ciki da waje ake gyarata Hajiya Bilkisu ta daga wajen tsumata,musamman da taji cewa ba auren aoyayya bane baya sonta matarsa yake so hakan yasa ta ninka abunda tayi niyyar mata.magunguna Kam ta shasu naci da na sha ba hali tace a'a sai Aunty Bilki ta titsiyeta tasa ta cinye ko ta shanye ga na gyran fatar da ake mata bilhak'k'i. Bayan kwana biyu abun Duniya duk ya ishi Muhdeen ya rasa yadda zaiyi, aiki ma cikin kwanciyar hankali ya gagara yinsa,zaune yake a office d'insa ya yanke shawarar zuwa ya samu Jabeer don ya rakasa suje su rok'i Dady kan maganar zauwansa London. Mik'ewa yayi ya rufe office d'in,kai tsaye office d'in Jabeer ya nufa. Knowkig yayi Jabeer ya bashi izinin shigowa sannan ya shiga,zaune ya same shi yana shan shayi,yana ganin Muhdeen ya sakar masa murmushi yana cewa "Angon Amare biyu ka tashi lafiya?" Banza yayi masa kamar baiji shi ba,sau uku yana masa magana kafin ya bud'e baki dakyar ya amsa masa da cewa "Ka rakani wajen Dady" Kallon rashin fahimta yayi masa "Kamar ya na rakaka wajen dady?" Cikin yanayinsa na rashin son magana ya ce, "Sumayya ta yi yaji iyayenta sun d'auki zafi,Ina son naje bikonta na bata hak'uri ta dawo." "To kaje mana wa ya hanaka?au sorry na manta fa Kai har yanzun kamar yaro kake,ba zaka yi Abu Kai tsaye ba sai da izinin su Dady." Kur'ban shayin yayi ya ajiye kofin kafin ya cigaba cewa "Yanzun ina Ina zancen Inteesar?" Tsuki ya ja tare da cewa "Ni ba wannan nazo ka tambaye ni ba,ban damu da ita ba su Mummy suka ajiyeta Wai sai ranar juma'a zata tare." "Why not ka bari idan ta tare daga baya sai kaje ka d'auko Sumayya,nifa bana son ka had'asu gida d'aya,don wlh Sumayya ba hankali ne ya isheta ba take ta illata 'yar mutane,Ni wallahi da wannan haukan da tayi ranar kake azar'ba'bin dawo da ita?da nine Kai da sai ta d'and'ani kud'arta sai ta dawo cikin hayyacinta.koda ya ke wanda ya ce zai had'iyi gatari 'bota ake rik'e masa naso ka bari idan Inteesar ta tare kaje kayo bikonta." Girgiza kai Muhdeen yayi "I can't" Murmushi Jabeer yayi "Any way, let's go" Mi'kewa sukayi suka fice a tare,a motar Jabeer suka tafi basu tsaya ko ina ba sai gidansu Muhdeen d'in. Ba kowa a falo hakan yasa Muhdeen ya ji dad'i a ransa,don dama baya son su tarar da Gwaggo a falo.kai tsaye part d'in Dady suka nufa a falo suka tarar da shi da Mummy,da sallama suka shiga Dady da Mummy suka amsa masu bayan sun durk'usa sun gaishe su ne Dady ya kalli Jabeer. "Jabeer ya iyali?" "Tana lafiya Dady" "Masha Allah haka ake so." Mummy ce ta ce, Ya jikin Maryam d'in da sauk'i yanzu ko?" "Eh Alhamdulillah jikin yanzun da sauk'i" "Madallah Allah ya sauke ta Lafiya." Gaba d'ayansu suka amsa da Ameen.Dady ya maida dubansa ga Muhdeen ya ce, "Muhammad ya dai ko akwai wani Abu ne?" 'Dan sunkuyar da Kai k'asa yayi kafin ya fara magana. "Dady dama ina son zuwa London ne na dawo da Sumayya." Shiru Dady yayi kafin ya cigaba da cewa "Muhammad ban hanaka zuwa ka dawo da matarka ba,amma ka d'an k'ara hak'uri Don halin yanzun ita da iyayenta a tunzure suke,ko ka ke yanzun ba zasu saurareka ba ballantana har su fahimci baka da laifi ba.Amma idan suka d'an huce sai aje a samesu,amma ka d'an basu lokaci." Muhdeen baiso hakan ba amma ba yadda zaiyi. "To Amma Dady har zuwa yaushe zan k'ara jira." Ya k'arasa maganar fuskarsa d'uke da damuwa.Yana son ya sake wata maganar ne Jabeer ya d'an bige masa k'afa da nasa cikin dabara.kafin Jabeer d'in ya d'ora da cewa "To Dady hakan za'ayi insha Alla,Mungode" Kai ya Dady ya jinjina cikin gamsuwa da maganar Jabeer d'in. "To shikenan Allah yayi maku albarka." Amsawa suka yi da Ameen sannan sukayi masu sallama suka tafi. ********************** Tun washe garin ranar da Sumayya tayi yaji shim Muhdeen yayi yaji da kwana gidan,domin a ranar ne Jabeer ya kirashi dadaddare akan akwai emergency yazo yayiwa wani tiyata.Kasancewar office d'in nasa akwai bedroom a ciki da toilet.idan ya gama abunda zaiyi sai ya shige bedroom d'in ya wuce toilet yayai wanka ua saka kaya ya hau gado ya kwanta,duk da ba cikakken barci yakeyi ba yawan tunanin Sumayya kawai yakeyi. Gashi yanzun gobe Juma'a ne za'a Kai Inteesar gidansa,gaba d'aya ransa a jagule yake ransa ya gama 'baci kuma ya kudiri niyyar cewa Inteesar sai ta d'and'ani kud'arta,musamman da yanzun haushinta ya ninku a zuciyarsa gani yake ita ce sanadiyar rabuwarsa da farin cikin zuciyarsa Sumayya.Hakan yasa ya k'ara d'aukar d'amarar k'untata mata.koda Jabeer ya ce zai sanar abokansu tarewar Inteesar dan a raka ango d'akin Amarya cewa yayi baya so,dole Jabeer ya hak'ura ya kyaleshi. Gidan Mummy kuwa ana ta shirin taron jama'a a gidan don gobe juma'ar nezasuyi taron walima da k'arfe hud'u a shida,bayan walimar ne za'a Kai amarya gidanta.Bayan ankai Amarya gidanta ne dadaddare za'ayi dinner,wanda dakyar ya yarda cewa zaije dinner d'in dan sam yak'i yarda ya dage ba inda zashi,sai da Jabeer ya sanar da Mummy ne ita kuma ta bashi umarni sannan ya amince don bashida ikon bijirewa zancen uwa. Inteesar idan Wanda Bai santa sosai ba ya kalleta bazai gane ta yadda tayi kyau ta k'ara haske fatarta sai walk'iya da sheki yake ga wani k'amshi da jikinta ke fitarwa,idan ta shiga d'aki ta fita sai d'akin nan ya kwana ya kwana yana k'amshi,ko fitsari tayi k'amshi yake fita daga k'asanta sakamakon wani shu'umin turaran da Hajiya Bilkisu kesawa k'ark'ashin wata 'yar kujera Mai hudi-hudi ta zaunar da Inteesar akai.masha Allah duk Wanda ya ganta bazaice 'yar Nigeria bace,zaka d'auka wata ba indiya ce.Aunty Abla ce tazo d'aukarta domin kaita ayi mata zanan lalle da gyaran gashi. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Domin k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘 Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story& writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa. Page3️⃣5️⃣ Aunty Abla ce ta zo d'aukarta domin kaita ayi mata zanen lalle da gyaran gashi, Mufida ma ta gayyaci k'awayenta da suka gama secondary School tare, Wasila da Saliha suma sunzo ana ta hidimar bikin dasu, Maganar dinner ma Mummy ta ce a barshi kasancewar Muhdeen ya nuna baiso itama Inteesar d'in da aka tuntu'be ta ta ce walima kawai zata yi, kuma dama ba kowa yasan da bikin ba tunda aure ne da aka yi ba tare da shiri ba, ko dangi na nesa ma Gwaggo ta ce suyi zamansu tunda basu dad'e da komawa bikin Muhdeen da Sumayya ba ga yanzun na Muhdeen da Inteesar ya taso ba shiri, hakan yasa ba wani jama'a sosai Muhdeen ma ko abokansa bai sanar dasu zancen auren ba, Jabeer ne ya sanar da su Bilyaminu amma abokansa da ba garin suke ba da na k'asar waje duk basu sani ba. Dama Muhdeen ya sa Direbansa Ishaq ya samo masa mai aikace-aikacen cikin gida, hakan yasa ya samo masa wata Mai aiki duk da cewar ba wani aiki ne a gidan ba kuma Muhdeen har yanzun bai dawo cikin gidan ba, idan mai aikin tazo da safe Ishaq zai bud'e mata k'ofa ta shiga falo kawai da kitchen sai dinning area take gyarawa duk d'akunan gidan a rufe suke. Yau Muhdeen ya kira Ishaq a waya ya sanar masa cewa yasa mai aikin nan ta shiga d'ayan part d'innan ta gyara saboda za'a shiga part d'in, Ishaq ya sanar da ita ta shiga ta gyara falo ta goge da bedroom guda hud'u dake part d'in kamar yadda aka umarce ta tayi to hakan kuwa tayi, bayan gamawarta ba jimawa sai ga wad'anda zasu shirya d'akin sunzo, nan suka Fara sassauke kayan suna shiga dasu ciki nan suka fara had'a kayan, Gaskiya Mummy da Dady sunyi bajinta wajen yiwa Inteesar kayan d'aki, d'akuna guda biyu suka shirya mata aka duk wanda ya kalli gadajen duka biyu sai sun burge mutum komai na kayan d'aki da akewa 'ya mace ba wanda Dady baiyiwa Inteesar ba, Mummy ma tayi mata kayan kitchen masu kyau da tsada komai anjera mata su. Inteesar sai yamma suka dawo daga gidan gyaran jiki idan kuka ganta kamar ku sace ta saboda tsabar kyawu da tayi, ga kanta yasha gyara dama ita akwai tsayin suma har gadon bayanta, ga suman bak'i wulik Mai shek'i da santsai ballantana ya samu gyara sai shek'i yake, Hannayenta da k'afafunta yasha jan lalle da bak'i, a daren ranar ma Inteesar tasha gyara a wajen Hajiya Balki. Washe gari ya kama ranar juma'a ranar da Inteesar zata tare a gidan mijinta, tun da safe Aunty Abla ta zo d'aukar Inteesar gidan Hajiya Bilkisu, Hajiya Bilkisu ma ta shirya ta bisu akan cewa itama ta kashe aikinta na yau saboda bikin Inteesar don itama Allah ya jarabceta da k'aunar Inteesar sosai don dama ita tana da kwarjinin jama'a sosai duk wanda ya kalleta sai yaji ta shiga ransa. A motar Aunty Abla suka tafi sai yaba kyawunta Aunty Abla ke yi tana dad'a godewa k'awarta akan k'ok'arin da tayi wajen gyara Inteesar, Hajiya Bilkisu dariya kawai tayi tare da nuna cewa Inteesar 'yace a wajenta kuma ko bayan auren zata cigaba da kula da ita tamkar 'yarta fira suka dinga yi a tsakaninsu ita dai Inteesar tana bayan motar tayi tagumi zullumi da fargabar wani irin miji Abbanta ya aura mata, da kuma irin zaman da zasu yi. Ba laifi kuwa gidan ya cika da jama'a musamman 'yan unguwar, an girka abinci kala-kala kowa yaci abunda ransa keso ga soyayyun naman kaji da na sa da aka yanka,'yan matan unguwar ma duk Mufida ta gayyace su, koda aka shigo da Inteesar kai tsaye d'akin Mufida ta nufa don dama duka k'awayensu da wad'anda suka gayyata suna nan cikin d'akin, nan dai suka nuna farin ciki da fatan zaman lafiya mai d'orewa, k'arfe hud'u akayi walima inda aka gayyaci manyan malamai suka zo suka yi wa'azi da jan hankali akan zamantakewa aure da haƙƙin miji akan matarsa da haƙƙin mata akan mikinta, da misalin k'arfe shida na yamma aka tashi walimar inda akayi rabon sallaya da hijabai. Da misalin k'arfe takwas na dare aka d'auki Inteesar aka Fara kaita gidan mijinta, nan aka dinga yaba had'uwar gidan da kuma had'uwar dakinta, dangin Umma ba k'aramin farin ciki suka yi ba ganin yadda iyayen Muhdeen suka narkar da naira wajen yiwa Inteesar kayan d'aki Mama Huraira ma k'anwar Umma taji dad'in ganin yadda gidan 'yar 'yar uwarta, ba yadda Inteesar bata yi da Mufida akan su ta kwana amma sam Mufida ta ce a'a amma zata zo gobe, lokacin da taga jama'a na tafiya kuka sosai tayi dakyar Aunty Abla da Mama Huraira suka lalla'bata ta hak'ura suka tafi. Gida ya rage ita kad'ai ce a ciki zama tayi tare da tagumi tana tunanin wace irin rayuwa zata yi waye mijinta hawaye ne kawai ke zuba a kan fuskarta kamar an bud'e famfo. Bangaren Muhdeen kuwa yana zaune a office d'insa kan sofa yayin da idanunsa a lumshe kamar mai barci amma ba barcin yake ba, Jabeer ne ta turo k'ofar ya shigo har lokacin bai bud'e idanunsa ba, Jabeer sallama yayi masa. "Assalamu Alaikum" Can k'asan mak'oshi ya amsa, la'b'bansa ne kad'ai zaka kalla ka gane yayi magana. "Ya kamata ka tashi ka tafi wajen amaryarka k'arfe goma yanzun, tunda ka ce baka buk'atar rakiyar mu ai sai ka tafi Allah ya bada zaman lafiya." Banza da shi Muhdeen yayi kamar baiji shi ba, dama baisa ran zai amsa masa ba don yasan halinsa, amma duk da haka bai damu ba sake magana yayi yana cewa "Kasan wallahi idan har baka tashi ka tafi wajen Amaryarka ba sai na kira Dady yanzun nan a waya na fad'a masa cewar kana nan asibiti zaka kwana ba zaka koma gida ba saboda baka son auren da suka yi maka." Still shiru yayi kamar baiji me ya ke fad'a ba tsawon mintuna biyar bai ce komaiba ran Jabeer ne ya 'baci yana da niyyar yin magana ne wayarsa ta soma ringing dubawa yayi matarsa Maryam ce, dama tana gidansu Mummy wajen taron bikin ganin karfe 10 bai zo ya d'auketa sun tafi gida ba ne yasa ta kiranshi, ɗaga wayar yayi tare da cewa. "Hello My dear kinji ni shiru ki?" Jin muryarta yayi kamar zatayi kuka tana cewa "Dan Allah ka zo mu tafi gida na gaji ina son na huta pls" Dariya yayi yana cewa "Karki damu ganinan zuwa nazo na d'auke ki idan muka tafi gida zan gasa maki jikinki da ruwan d'umi nayi maki tausa zaki ji dad'in barci." Dariya tayi tare da katse kiran, dubansa ya maida kan Muhdeen ganin baima da niyyar tashi sai ma kishingid'a da yayi ne yasa Jabeer duba wayansa yana lalubar number Dady bugu d'aya a na biyu Dady ya d'aga wayar inda Jabeer yasa speaker na wayar Muhdeen najin Muryar Dady na cewa "Hello Jabeer ya akayi ne"? Kafin Jabeer yayi magana cikin zafin nama Muhdeen ya fisge wayar tare da katse kiran, wayoyinsa ya d'auka ya saka a aljihu ya nufi hanyar fita Jabeer yabi bayansa yana k'yalk'yata dariyar mugunta. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi. K.N.T Maman Ihsan Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘 Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Page3️⃣6️⃣ Kafin Jabeer ya yi magana cikin zafin nama Muhdeen ya fisge wayar tare da katse kiran, wayoyinsa ya d'auka ya saka a aljihu ya nufi hanyar fita Jabeer ya bi bayansa yana k'yalk'yata dariyar mugunta.saida suka je inda za su rabu ne Muhdeen ya mik'a masa wayarsa kowanne ya shiga motar sa ya kama hanyar fita asibitin. Jabir gidansu Mummy ya nufa yayin da shi kuma Muhdeen ya nufi gidansa. Inteesar kuwa tana can d'akinta, k'udunduna saman gado ta had'a Kai da guiwa sai kuka take yi har da sheshshek'a,tana tuna Ummanta da Abbanta. Horn yayi mai gadin gidan ya lek'a ta k'aramar k'ofa,ganin Mai gidan ne yasa shi saurin wangale gate d'in gidan,cinno hancin motar yayi cikin gidan a parking space yayi parking,ya fito yakai tsawon mintuna goma yana zaune a cikin motar kafin ya fito ya nufi cikin gidan. Duk da cewa part biyu ne gidan amma bawai suna rabe da juna bane,kusan a had'e suke kuma k'ofa d'aya suke da ita dole sai mutum ya bi ta falon Inteesar kafin ka shiga falon Sumayya,kuma ko wane bedroom guda hud'u suke da dasu,kuma kowane bedroom da toilet d'insa a ciki akwai kuma kitchen da dinning area kowanen su. Turo k'ofar yayi k'amshin turare ne suka tarbe sa,wanda bai ta'ba jinsa ba a gidan,kai ya saka da nufin wucewa part d'in Sumayya sai ya jiyo sheshshek'ar kukan Inteesar,kamar ya wuce sai ya nufi d'akin Inteesar d'in,tura k'ofar d'akin yayi ganinta zaune yayi ta k'udundune ta had'a Kai da gwuiwa sai kuka take kamar ranta zai fita.Bata San ya shigo d'akin ba kukanta kawai take yi kamar ranta zai fita. "Kukan uwar me kikewa mutane?" Muryar da taji ya dakai dodon kunnenta ne yasa taji gabanta ya fad'i rass don idan har ba mafarki take ba wannan muryarsa ce don ba zata ta'ba mancewa da wannan muryar ba,azuciyarta take magana "Kenan wannan mugun mutumin shine mijina? Kai ina bazai yiwu ba,bashi bane." 'Dago kumburarrun idanunta da tayi ne yasa ta d'aura su akansa ne yasa gabanta yayi mummunar fad'uwa ,tabbasa shine. "Kallon me kike mani ne?kin zuba Mani ido kamar mayya,ba ke kika ce kina sona ba?" Kai ta girgiza alamun a'a idanunta na zubar da hawaye ta fara magana. "A'a ni wallahi bani bace nace ina sonka." "To kika yarda kika aure ni?kuma amincewa da aure na da kikayi shine kuskure mafi muni da kika tabka a rayuwarki,dan sai kin gwammace dama baki aure ni ba,tukunna wai me yasa baki bijirewa auren ba kika amince duk da kin San ba k'aunarki nake ba?" Share hawayen fuskarta tayi tare da cewa Ban san Kai ne mijin da aka aura mani ba sai yanzun,kuma Koda na sani bazan ta'ba bijirewa zancen iyaye na ba,domin duk wanda yake son rayuwarsa tayi albarka bazai ta'ba bijirewa zancen iyayensa ba,neman albarkar iyaye da biyyaya a gare su yasa ban bijirewa zancen auren ba." "Ko da hakan yana nufin bak'in cikinki ne?" "Koda hakan yana nufin mutuwa ta ce,bazan ta'ba bijirewa zancen iyaye na na ba." "Good" Daga nan yasa Kai ya fice,ita kuma kukanta ta cigaba da yi don bata ta'ba tinanin cewa Muhdeen aka aura mata ba,haka ta cigaba da kukanta a k'udundune har barcin wahala yayi awon gaba da ita. Shi kuma yana fita d'akinsa da ke cikin falon Sumayya ya nufa kayan jikinsa ya rage ya fad'a toilet Dan yin wanka, K'arfe uku na dare Inteesar ta farka daga barcin wahala da tayi, toilet ta fad'a tayi wanka da ruwa mai d'umi sannan ta d'auro alwala ta fito man shafawan Hajiya Bilkisu Mai k'amshi ta shafa doguwar riga ta atamfa ta saka ta sanya hijab don yin sallah,nafila raka'a biyu tayi sannan ta fara karatun alqur'ani mai girma,tana zaune har har lokacin sallah ta tashi tayi sallar asuba,bayan ta idar ne ta dinga yin azkar har sai da gari ya waye tayi addu'a sosai akan zaman auren nan tare da rok'on Allah ya k'ara mara hak'urin zama da Muhdeen. Tashi tayi ta fito daga d'akinta don tsananin yaunwa ke damunta rabon da ta ci abinci tun karin da tayi jiya da safe,da rana bata ci komai ba haka ma dare yayi ba abunda ta saka a cikinta,ba yadda Mufida bata yi da ita ba amma sam tak'i cin abinci dole ta ha'ura ta kyaleta. Fitowarta falon yayi dai-dai da isowar mai aikin gidan,wato kande wacce take zuwa ki wace safiya tayi share-share da goge-goge,yau tayi sammakon zuwa ne saboda ranar da aka sanar da ita zancen aikin an fad'a mata cewa matar gidan zata dingayiwa aiki da bata ga matar gidan ba sai ta tambayi Ishaq ya sanar da ita cewa tayi tafiya ne,to sai jiya da taji labarin matar gidan zata dawo yasa ta sammakon zuwa,dattijuwa ce mai kimanin shekaru arba'in. Ganin Inteesar ya sa ta durk'usa da niyyar gaishe ta,kafin ta kai k'asa Inteesar tayi saurin d'ago da ita tana cewa. "Haba Baaba ai bai kamata ace kin durk'usa mani ba,ni ce ya dace na durk'usa maki,ina kwana?" Murmushi matar tayi tare da cewa "Lafiya lau sannu Hajiya." Inteesar shiru ta yi tana kallon matar ita dai bata santa ba kuma gashi ta daka sammako wajen zuwa gidan,tana cikin wannan tunanin taga matar ta durkusa tana gaida Muhdeen. "Ina kwana alhaji" Alamu yayi mata da hannu alamun ta tashi tsaye,ba tare da ya amsa gaisuwar da tayi masa ba, Mi'kewa ta yi. "Dama ni ce mai aikin da ke zuwa kullun ina gyara gidan lokacin da baki nan,na ji labarin kin dawo ne yasa nayi sammako ko akwai aikin da zan taya ki da shi." Kafin Inteesar tayi magana ta ji Muhdeen ya fara magana "Ai ba ita ce matar gidan ba,matar gidan bata dawo ba tukunna,so it's wannan bata buk'atar'yar aiki don ita ma 'yar aikin ce." Jinjina kai Baaba kande tayi "To Alhaji zan cigaba da zuwa ina aikin Koda matar gidan bata dawo ba kamar yadda na saba yi a kwanakin baya?" "Ba buk'ata Koda ta dawo wannan ce 'yar aikin da zata dinga mata aiki,sabida haka aikinki ya k'are,amma kafin nan ina zuwa." 'Dakinsa ya nufa, sai gashi da kud'i kimanin naira dubu d'ari ya mik'a mata amsa tayi tana godiya duk da ta rasa aikin ta tasa ran dogaro dashi amma kud'in zata ja jari dasu. "Nagode Alhaji Allah ya saka da alkhairi,ya k'ara arziki da wata wadata." Ficewa tayi tare da yi masu sallama cikin jin dad'i Kallonsa ya maida ga Inteesar fuskar nan a tsuke,yayinda ita ma ta kallesa cikin girmamawa ta ce, "Ina kwana?" Tsuki ya ja tare da cewa "Na sallami mai aikin gidan nan daga yau ke zaki maye gurbinta,aikin da takeyi naki sai ya ninka na ta,don ita falo da kitchen kawai take shiga ta gyara ke kuma daga yau na kafa maki doka wajibi ne a gare ki bayan falo da kitchen da Zaki dinga sharewa kina gogewa duka bedrooms d'in gidan nan guda takwas, da toilets nasu guda takwas wajibine ko wace rana sai kinbi su d'aya bayan d'aya kin share kin goge su kin wanke ko wane toilet,sannan ina son na ga ko ina na gida na a tsaftace banason k'azanta,sannan ba sau d'aya ba safe da yamma Zaki dinga aikin, idan kunne ya ji gangar jiki ya tsira." Shiru tayi tana tunanin uban aikin da wannan bawan Allah ya d'ora Mata,bata gama nazari ba taji muryarsa yana cewa. "Ki jirani nan Ina zuwa" "To" Daga nan ya nufi d'akinsa ba jimawa ya fito hannunsa d'auke da keys ya mik'a mata. "Kar'bi wad'annan makullayen ki Fara da wancan d'akin" Ya k'arasa maganar yana nuna mata d'akin Sumayya,daga nan ya koma cikin d'akinsa ya barta nan tsaye,cikin sanyin jiki ta k'arasa cikin falon Sumayya tare da duban saitin da taga ya mata nuna mata, tsayawa tayi tana k'arewa falon kallo a zuciyarayarta ta ce, "Na fahimci mutumin nan so take kawai ya wahalar dani,ya za'ayi manyan falo guda biyu tare da bedrooms guda takwas ko wanne da toilet da ga kitchen guda biyu kowane falo da dinning romms da table da chairs ko ina sai na shere na goge,kuma safe da yamma harda d'akunan da ba kowa a cikinsu ba datti sukeyi ba tunda ba'a shigarsu amma suma wai safe da yamma." Goge k'wallan da ya gangaro mata tayi tare da cewa "Allah ka ka bani hak'urin zama da shi" Bud'e k'ofar d'akin Sumayya tayi ta shiga bakinta d'auke da sallama,turus tayi tare da dafe k'irji ganin yadda d'akin duk a hargitse komai kaca-kaca ga kgilasai da aka farfasa da kwalaben turarurruka kala-kala ga suturu duk a yayyage,katifa a gefe pillows a watse mirror a tarwatse photon Sumayya da ta gani a manne a bangon d'akin ne ya tabbatar mata da cewa d'akin Sumayya ne a zahiri tayi magana. "Oh ni Inteesar mai ya faru da d'akin nan ne kamar anyi girgizan d'aki?ta ya ya zan fara wanna aikin ne?kuma da dukkan alamu d'akin Sumayya ce to ina ita Sumayyar take ne?kuma me ya faru da d'akinta haka?" Sanin ba Wanda Zai amsa mata tambayarta yasa ta fara tunanin ta Ina zata fara,ganin takalmin dake k'afarta irin masu taushin nan ne idan ta taka kwalba zata iya huda takalmin ta shiga k'afarta yasa ta fita dan canza takalmin da ke k'afarta,ba Ba jimawa sai ga ta ta canza takalmi ta sanya wani flat shoe da da abunda zata zatayi shara ta zuba,katifar ta fara ja ta jingine da gadon ta kwashe pillows d'in abunda ya bata mamaki shine,kayan suturar da ta gani a k'asa ta fara d'agawa abun da ya bata mamaki shine ganin duka suturar a yayyage ba mamora,har cikin closed d'in ta shiga abun mamaki suturan dake cikin wurin duka a yayyage suke haka ta dinga kattara kayan da kwalaben sai dai wad'anda ta ga robace ba kwalba ba da kuma wada'anda suke a gwangwani ba su fashe ba ta kwashe ta jerasu gaban mirror d'in don ba abunda ya same su. Tsawon lokaci ta d'auka tana gyara d'akin Sumayya kafin ta kammala,ta shirya d'akin tsaf ta gyara shi ta wanke toilet sannan ta janyo k'ofar ta fito. Haka tabi sauran two rooms d'in duk ta gyara kafin sannan ya rage saura d'akinsa, k'wank'wasawa ta yi yana jinta yayi banza da ita, har sau uku amma ko gezau yana zaune kan sofa sai da ya ga dama ya ce, "Shigo" Turo k'ofar tayi tare da sallama "Assalamu Alaikum" "Wa'alaiki salam" Tsayawa tayi kanta a k'asa tsawon mintuna goma tana tsaye amma bai ce mata komai ba,tsuki ya yi. "Dalla malama idan ba za ki yi magana ba ki fita ki ban waje" Cikin rawar murya ta ce, "Na gama da sauran d'akunan ne naka ya rage shine na zo na gyara" K'arar k'ofar falo sukaji alamun suna da bak'o,hakan yasa ya fita don zuwa dubawa. Kids ya bud'e k'ofar Mufida ya gani d'auke da basket an jira flasks d'in abinci ciki, murmushi ta sakar masa "Barka da safiya Yaya Shima murmushin ya sakar Mata "Yauwa kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah,dama Mummy ce ta ce na kawo maku breakfast" Yana k'ok'arin kar'bar basket d'n ta ce, "Yaya gaskiya sai naga besty na zan tafi" ,hanya ya Bata ta shiga ta ajiye basket akan center table. Okay tana d'akina zauna na kirata" Zama tayi akan kujerar dake falon tana jiran inteesar.koda ya shiga tana gyara gadon ya sanar da ita cewa ta zo murmushi ta yi cikin jin dad'i ta fito yana biye da ita a baya,Mufida na ganinta ta mik'e ta nufeta a guje ta fad'a jikinta,muryar Muhdeen suka jiyo yana cewa "Ke Mufida meye haka ki bi mani amarya a hankali fa ka da ki yi mani illa baki San ba na son abinda zai wahalar mani da ita ba?ki barta ta ji da kanta." Inteesar ce ta bisa da kallon mamaki,bai gama ba ta mamaki ba sai da taga ya sakar murmushi tare da kashe mata ido d'aya. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T Maman Ihsan Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘 Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Andullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, Idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne Mai kashe auren wawa. *SADAUKARWA* Wannan shafin naku ne masoyan Inteesar 'yan group d'in INTEESAR HAUSA NOVEL,inajin dad'in comment naku na book d'in nan sunayenku bazai lissafu ba,ina godiya da addu'arku gare ni Allah yabar k'auna. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page3️⃣7️⃣ Inteesar ce ta bisa da kallon mamaki,bai gama bata mamaki ba sai da taga ya sakar Mata murmushi tare da kashe mata ido d'aya,mamaki da Al'ajabi suka hana Inteesar motsi kallonsa kawai take kamar gunki,jan hannunta da Mufida tayi ne ya saka ta sakin murmushi tana cewa. "Ya dai wannan kallon haka kamar yanzun kika fara ganinsa ba tare kuka kwana a gidan ba,koda yake ba zaki gaji da kallonsa ba don yaya na na musamman ne samun kamarsa sai an tona." Murmushin yak'e Inteesar tayi tare da cewa "Yauwa Mufida na manta waya ta a gidanku tun kafin a kaini gidan Hajiya Bilkisu,don kwanakin da nayi gidanta ma duka ba waya a hannuna." "Okay to Ina kika aje wayar ne?" "A d'akin Yaya" Murmushi Mufida ta yi tare da cewa "To shikenan zan d'auko maki anjima idan zan kawo maku lunch,amma ki daina kiransa da Yaya don yanzun kunzama 5&6 kamata yayi ki canza masa suna na masoya mai dad'i kin gane ko?" Ta'be baki Inteesar tayi,tare da kallon Muhdeen sai gani tayi ya galla Mata harara sunkuyar da Kai k'asa tayi , Mufida ta cigaba da cewa. "To Ni zan tafi sai na sake dawowa." Fuskar tausayi cikin marairaicewa ta ce, "Mufida tun yanzun zaki tafi ki barni ni kad'ai ki bari ki yini dani mana ko zaki d'ebe Mani kewa, pls aminiya ki tsaya kinji." Kafin Mufida ta yi magana Muhdeen yayi saurin cewa. "Kinga Mufida aiko ki akayi kije ki isar da sak'o kince mungode,zaki iya tafiya ki gaida mani Gwaggo da Mummy." Murmushi tayi tare da kallon Inteesar "Karki damu my besty zanzo zuwa na musamman na wuni dake kinji." Murmushi Inteesar ma ta maida mata tare da cewa. "Shikenan ba damuwa" Zuba mata ido mufda tayi tana nazartar yanayin Inteesar,don tasan Inteesar farin sani yanayin yanda ta ganta da dukkan alamu tana cikin damuwa,amma sai ta share zancen ta barshi kila saboda auren da aka yi mata ne kuma ba lallai tana son wanda aka aura mata ba kuma gashi Bata saba da shi ba kila shiyasa ta damuwa amma a sannu zata saba da shi. Sallama ta yi masu daga nan ta fice,dubansa ya maida ga Inteesar fuskarsa a tsuke ya fara magana "Idan ta zauna a nan gidan uwar me zata yi maki?bari kiji na fad'a maki doka ce bana buk'atar bak'i a cikin gidana,kada ki tara mun k'awayenki bana buk'atar kowace mace tazo mani gida babu wacce zata zo gidan nan da sunan zuwa wajenki,ko wace ce a wajenki kuwa Ina fatan kin gane." Kai ta jinjina "To amma me yasa zaka Hana kowa zuwa wajena?kuma ko a gidan kurkuku nake ai baza'a hana a ziyarce ni ba ballantana gidan aure na." Da mamaki yake kallonta "Ke! Ni kike fad'awa magana lallai kuwa kin samu sake,to bari kiji da kike maganar gidan kurkuku to nan tamkar gidan kurkuku ne a wajenki ki aje wannan a cikin zuciyarki." Shiru tayi kanta a sunkuye idanunta sun cika tab da k'walla. "Maza kije ki gama aikin da zakiyi,ba tare da tsayawa ba har sai kin gama,tukunnah ma d'akuna nawa kika gama dasu?" Yanzun na gama da d'akuna hud'u saura hud'u,sannan na dawo kan falo da kitchens." 'Dan Jim tayi tana son ta yi masa magana tana tsoronsa ganin hakan yasa shi cewa. "Maye kike yi haka kamar wata munafuka,idan zakiyi magana kiyi idan ba zaki yi na ki 'bace Mani da gani." Cikin inda inda ta fara magana kanta a akasa. "Nace amm dama Wai dama ummm" Tsuki yayi tare da daka Mata tsawa "Ke! dalla gafara can,idan zakiyi magana kiyi kin tsaya kina mun munafurci a nan." Kanta a sunkuye k'irjinta sai dukan uku-uku yake ta fara magana. "Dama cewa zanyi kullun zan dinga share da goge falo da kitchen safe da yamma kamar yadda ka ce nayi,sai kuma d'aki guda takwas da kace suma safe da yamma naga yanzun d'akuna uku ake amfani dasu sauran biyar d'in ba'a komai dasu,kuma suna kulle ba datti suke yi ba kuma kace suma safe da yamma shine na ce a dinga barinsu sai ranar juma'a sai na dinga bud'esu ina share su." Gajeren murmushi ya yi "Dani dake waye mai gidan?" "Kai ne" "Dani dake waye mai ikon fad'a aji?" "Kai ne" Dani dake wa ya ajiye wani?" "Kinga kuwa magana ta ce sama da taki,kije ki gama duk aiyukan da na saka ki kafin kizo kiyi breakfast." Daga nan ya nufi bedroom d'insa ya barta nan tsaye cike da tausayin kanta. Haka Inteesar ta cigaba da rayuwa a cikin gidan Muhdeen cikin aikin wahala gashi dai ba aikin da gidan ko d'akunan ke buk'ata amma haka zai ce sai tayi shi,koda duka d'akunan da ba'a amfani dasu gasu fes ba datti ko kad'an amma daboda tsabar mugunta irin na Muhdeen sai ya ce ta goge su ga manyan falo biyu da kitchen guda biyu zata gyara dinning zata goge table da kujerun dinning area d'in,idan ta tashi tun asuba tayi sallah ta fara aikin gidannan tayi wanka ba ita zata samu sararin breakfast ba sai K'arfe biyu na rana. Gwaggo ce zaune a falo tana sababi wai tunda aka Kai Inteesar gidan Muhdeen ba wanda ya je ya duba halin da suke ciki,ita fa zata je gidan ta zauna tayi sati d'aya,dama yau ne suka cika sati d'aya da tarewa. Mufida ce ta fito daga kitchen d'auke da basket zata kaiwa su Inteesar abinci,kallonta Gwaggo tayi tare da cewa. "Ke dama yaune zaki kai abincin k'arshe gidan Inteesar ko?" Kai Mufida ta jinjina alamun eh "Hakane Gwaggo daga yau shikenan" "To idan kinje ki sanar da 'yar albarka cewa rana yata yau zanzo gidan sai nayi wata d'aya zan dawo." Kallon mamaki Mummy ta bita da shi "Har wata d'aya Gwaggo?" "Eh haka nace ko akwai wanda Zai hanani ne?" Girgiza Kai Mummy tayi "A Gwaggo ba wanda zai hana ki ai." "Ato idan ma akwai ne inji bayani." Murmushi Mufuda tayi "Yauwa Mummy na mance ban fad'a maki ban tambaye ki ba, Inteesar ta ce tabar wayarta a gidan nan a d'akin Yaya na duba ban gani ba." Dafe goshi Mummy tayi tare da cewa yauwa namanta ne wlh yana d'akina,tun ranar da suka tafi washe gari na ganshi na d'auka tare da kashe wayan gaba d'aya,ki duba cikin side drawer na ki d'auka ki kai mata." Ajiye basket d'in tayi tare da nufar d'akin Mummy ba jimawa ta fito da wayar a hannunta,sallama tayi masu ta nufi k'ofar fita,inda Gwaggo ta jaddada mata cewa ta shaidawa Muhdeen zata zo ranar juma'a. Inteesar na kwance a saman bed d'inta tana barcin wahala,don gaba d'aya a gajiye take Don aikin da take yi yayi mata yawa,jikinta ma ciwo yake mata, ga hawayen da ya bushe a kumatunta da dukkan alamu kuka tayi har barci ya d'auketa. Lokacin da Direban Mummy ya shigo gidan tare da Mufida lokacin ne kuma Muhdeen ya fito daga cikin gidan,sanye yake da farar shadda tsadadda da ba'kar hula a kansa sai bak'in takalmi da ya sakaba k'aramin kyau yayi ba,kwarjininsa ya k'ara bayyana Ishaq Direbansa ne ke bud'e masa murfin gaban motar, ganin Mufida yasa ya dakata ido ya zuba mata a tare suka sakarwa juna murmushi. "My lovely bros barka da rana" Fad'awa jikinsa tayi tare da cewa "Kayi kyau sosai,ina lovely friend tana ciki" "My lovely sis tana ciki" "Okya me take yi?" Ta'be baki yayi ya ce, "Ki shiga ki gani mana,ni masallaci zanje sauri nake lokaci yayi." "Okay ayi juma'a lafiya,ki gaida mutanen gidan." "A'a Yaya ai wannan karon yini zanyi sai dare zan tafi." d'an jim yayi yana nazari kafin ya ce, "Ba Zaki koma gida ki taya Mummy aiki ba?" "Na fad'a masu sai dare zan dawo,sannan ma Gwaggo ta ce na sanar da ku cewa next week zata zo sai ta yi 1 month sannan zata tafi." Sai da Muhdeen ya d'an razana da jin zancen zuwan Gwaggo,Amma sai ya dake ya ce, "To me zaisa tazo ta yi har wata d'aya a nan?ina laifin ta yini ta koma?" Murmushi Mufida ta yi "To ina laifi Dan tazo ta yi wata d'aya?kar ka mance cewa Gwaggo na k'aunar Inteesar fiye da tunaninka,bata son 'bacin ranta ko kad'an,ina tunanin zuwanta bai rasa nasaba da k'aunar da take mata da kuma k'aunar da take maka,kasan duk cikin jikokinta ta fi sonka." Jinjina Kai yayi tare da cewa " shikenan ki shiga ciki." Nufar cikin gidan tayi yayinda shi kuma ya shiga cikin motarsa,tunani yake idan Gwaggo tazo gidan nan akwai matsala babba. Koda Mufida ta shiga ba kowa a falon,hakan yasa Kai tsaye ta nufi d'akin Inteesar,sallama tayi sau uku bata ji an amsa ba hakan yasa ta tura k'ofar d'akin ta shiga,kwance ta same ta ta k'udundune waje guda alamun a takure take,ga hawayen da suka biye fuskarta sun bushe,idonta ma a kumbure alamar ta ci kuka,ido Mufida ta zuba mata ganin yadda ta d'an rame gashi tana barcin amma bata daina ajiyar zuciya ba, hannunta takai ta ta'ba gefen fuskarta a firgice Inteesar ta farka tana zare ido,ganin Mufida ce bata san lokacin da hawaye suka cika mata ido ba yayinda Mufida ta rungumeta. Daga alk'amin✍️ Zainab Andullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘 Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne Mai kashe auren wawa. *SADAUKARWA* Wannan shafin sadaukarwa ce ga duk matar da ta fuskanci k'alubalen aure da uk'ubarsa ta kuma jure,hak'ika ba wata damuwa da zata d'ore har abada komai loaci ne wata rana sai labari. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page3️⃣8️⃣ Ido Mufida ta zuba mata ganin yadda ta d'an rame gashi tana barcin amma bata daina ajiyar zuciya ba, hannunta takai ta gefen fuskarta a firgice Inteesar ta farka tana zare ido, ganin Mufida ce bata san lokacin da hawaye suka cika mata ido ba yayin da Mufida ta rungumeta. "Inteesar lafiya kuwa? me ya ke faruwa dake ne?" Sunkuyar da kanta tayi tare da goge k'wallan da suka cika mata ido. "Bakomai Mufida me kika gani?" "Gani nayi duk kinbi kin rame daga ganinki baki cikin jin dad'i." "Hasashenki ne haka,amma nikam ba abunda ke damuna." Girgiza kai Mufida tayi cikin rashin yarda da zancenta ta ce, "Kardai ace har kun fara samun sa'bani da Yaya tun yanzun,ai yakamata ne ace kuna cin amarci ba Wai daga aure an fara samun sa'bani ba,duk da ance zaman aure 'dan hak'uri ne amma yayi wuri da yawa." "Karki damu Mufida ba komai ba wani sa'anin da muka samu,haka zaman namu yake tun fil'azal." Da mamaki Mufida ke kallonta. "Ban gane be Inteesar cewa fa kika yi haka zaman naku yake tun fil'azal." Murmushin yak'e Inteesar tayi "Ba haka nake nufi ba,ina nufin haka zaman aure yake tun fil'azal,wato d'an hak'uri ne haka abun yake a ko ina." Jinjina Kai Mufida tayi "To wai shin ma me ya had'aku kece mai laifi ko shi?" Ganin yanayin Inteesar ya d'an canza yasa Mufida yin murmushi tare da dafa kafad'arta. "Sorry k'awata mubar maganar." Zama suka yi dab da juna ido Mufida ta zuba mata tana kallonta,kuma tana nazari a cikin zuciyarta,ita dai a iya saninta duk yarinyar da tayi aure sai taga ta canza ta k'ara kyawu da shek'i har k'iba yarinya takan k'ara,idan kuma ba mai kikin k'iba bace sai ta d'an murmure,Amma ita Kam Inteesar sai ramewa tayi gaba d'aya ta fita hayyacinta,amma sai ta bar hakan akan cewa kila dan Inteesar bata son Muhdeen ne auren had'i akayi masu,hakan yasa bata kwantar da hankalinta ba,iska mai d'umi ta furzar daga cikin bakinta,kafin ta fara magana. "Nasan bakya son Yayana aka aura maki shi,dan Allah kiyi hak'uri ki kar'beshi a matsayin mijinki,ki cire damuwar da take ranki,bakiga shima ya d'auki k'addararsa ba ya rungume ki a matsayin matarsa ba? Wallahi ya burgeni yadda naga yana nuna damuwarsa akanki,ranar washe garin ranar aurenku da nazo kawo maki breakfast kin tuna yadda yadda dinga ji dake?Wai kada na wahalar masa dake nabi a hankali ni a tunani na fa da naji ya ce haka na d'auka ko a daren farkon kun kashe arna ne kin wahala yasa naji ya ce haka." Ta k'arasa maganar cikin sigar tsokana, Inteesar bata ce mata komai ba tana da ta sauraronta,inda Mufida ta cigaba da cewa. "Kamar yadda nake jin labari wai hakane a daren farko?" "Labarin me kuma?" "Wai idan mijinki ya kusance ki akwai zafi?" Kallonta Inteesar tayi tare da cewa, "Me yasa kika mani wannan tambayar?" "Saboda naga ke kika riga aure cikin k'awayenmu kuma ke kad'ai zan iya tambaya" "Nima ban sani ba,ki Bari idan kikayi auren zaki sani." Da mamaki Mufida ta kalleta "Kamar ya baki sani ba bayan aranar da nazo kawo maku breakfast daga d'akin kika fito da alama tare kuka kwana a d'akinsa." Dafe goshi Inteesar tayi cikin k'osawa da zancen ta ce, "Kai Mufida ban sani ba ki na sani bazan fad'a maki ba,domin Allah ya tsinewa matar dake fallasa sirrin shimfid'a aurensu a wajen wani." Dariya Mufida tayi tare da cewa "Hakane fa mallama Inteesar." "Yauwa na mance ban fad'a maki ba Gwaggo ta ce zata zo gidan nan tayi maku kwanaki d'ai-d'ai har talatin." Wani uba tsalle Inteesar tayi cikin farin ciki da jin dad'in da ta dad'e Bata yi shi ba ta tsinci kanta,don ko ba komai idan Gwaggo tazo tasan zata d'an ji dad'i a ranta k'uncinta zai ragu na tsawon kwanakin da Gwaggo zatayi a gidan. "Ikon Allah wannan shine Allah d'aya gari banban,ke kina farin cikin da zuwan da Gwaggo zata yi yayinda shi kuma mijinki yana bak'in cikin zuwan da zatayi." Da mamaki Inteesar ke dubanta "Kamar ya bak'in ciki?" "Ki rufa mani asiri kar fa ki fad'awa mijinki,na fad'i hakane kawai dan naga likacin da na fad'a masa yanayinsa ya canza zuwa rashin jin dad'i yayinda ke kuma yanayinki ya canza zuwa jin dad'in zuwanta." Ta'be baki Inteesar tayi yayinda a zuciyarta take ayyana cewa Muhdeen bazai ta'ba jindad'i Gwaggo ta zo gidan nan ba, mi'kewa Inteesar tayi tana cewa. "Kinga bari na tashi nayi wanka na d'auro alwala lokacin sallah yayi." "Okay je ki fito nikam Allah ya yafe mani." Dariya Inteesar tayi ta shiga toilet d'in. Da misalin k'arfe biyar na yammacin ranar motarsa ta cinno Kai cikin gidan,bayan Direbansa yayi parking ya fito tun kafin ya bud'e masa tuni ya bud'e ya fito da kansa,kai tsaye cikin gidan ya nufa. A fall ya tarar dasu Inteesar sanye take da riga da siket na atmafa,d'inkin kuwa ya zauna mata ya kar'bi jikinta ba wani makeup tayi ba powder ta shafa sai lipsglow da ta shafa,dogon gashin kanta ta k'udundune shi a cikin d'an kwalinta, Mufida na zaune a gefenta inda take mik'a mata wayarta da ta taho mata dashi,kar'bar wayar tayi cikin jin dad'i ko ba komai ta rage kewa da kad'aicin da take fama da shi. "Assalamu Alaikum" Gaban Inteesar ne ya fad'i sakamokon jin muryarsa da tayi,tunawa da tayi cewar ashe fa yau batayi aikin yammacin da yasa ta dingayi ba,zuwan Mufida ne ya mantar da ita, Mufida ce ta amsa masa sallamar. "Wa'alaika salam" Kallon ta yayi yana sakar mata murmushi. "my little one baki tafi ba har yanzun kina nan?" "Sai zuwa 8 ne direba zaizo d'aukana dama mun kawo maku abincin amarci na k'arshe don kafin na tafi gidan nan sai naci girkin amarya na farko a cikin gidan mijinta." Murmushi yayi tare da kallon Inteesar "Amarya baki ga angonki ya dawo bane ko d'an oyoyon nan babu?" 'Daga kanta tayi ta kalleshi da mamaki amma sai taga ya sakar mata murmushi, sunkuyar da kanta tayi ba tare da ta ce komai ba,mamakinsa kawai take wato idan su kad'aine a gida sai ya dinga gallaza mata ya k'untatawa rayuwarta amma idan akwai wani a wurin sai ya dinga nuna mata kulawa,wato fuska biyu ne dashi,tana cikin wannan tunanin bata ankara ba sai ji tayi ya zauna kusa da ita tare da rik'o hannunsa cikin nata,da sauri ta kalleshi sakamakon wani irin shock da taji a rayuwarta wannan ne karo na farko da d'a namiji ya ta'ba ri'ke hannunta ita duk hankalinta a tashe yake sakamakon aiki da bata yi ba Bata San hukuncin da zai d'auka a kanta ba,cikin tsoronsa da take ji ta fara magana. "Dan Allah kayi hak'uri na mance ne yau ban..." Kafin ta k'arasa maganar da zata fad'a yayi saurin d'aura yatsarsa a saman le'benta tare da furta kalmar. "Shhhh" Murmushi ya sakar mata tare da cewa. "Kada ki damu dan baki tashi kin tarbe ni ba ba komai,nasan kinyi bak'uwa ne shiyasa kika mance dani." Kallon Mufida yayi da ta zuba masa ido. "Sister bari na na d'an shiga ciki na watsa ruwa,sai dai fa kiyi hak'uri zamu barki ke kad'ai." "Bakomai tunda nazo gidan sabbin aure ai dole nayi hak'uri." Hannun Inteesar yaja suka nufi d'akinsa ita dai Mufida ido ta bisu dashi,tana murmushi har suka 'bacewa ganinta shi kuma bai saki hannun Inteesar ba sai da suka shiga d'akin sannan ya sakar mata hannu,tare da watsa mata mugun kallo wanda sai da hanjin cikinta suka kad'a. "Wato saboda ki had'ani da dangina yasa kika fara magana a gaban Mufida ko?saboda ta fahimci halin da muke ciki take ta fad'awa Mummy da Gwaggo ko?" Kai ta girgiza kanta a sunkuyar da kanta k'asa ta fara magana "Kayi hak'uri na d'auka zaka mani fad'a dan bany..." Tsawa ya daka mata Dalla rufe mani baki mai zubin munafukai,kiyi ta sunkuyar da kai kamar munafuka,duk wanda yazo gidan nan kika kuskura kika nuna cewa akwai matsala a cikin zamantakewar auren mu ko kuma a kika bar wata k'ofa da wani zai gane yanayin zamanmu sai na lahira yafi ki jindad'i kinsan ni ba sai wani ya baki labari na ba sai dai kina wani labarina,ki shiga kitchen ki samu abunda Zaki girka." Daga nan Nan ya nufi toilet ita kuma ta nufi k'ofar fita. Kitchen ta nufa inda inda ta dafa masu jallop d'in shinkafa da yaji kayan lambu da busashshen kifi kasancewar akwai komai na girki a kitchen d'in,Koda aka Kira sallar magrib ta gama girkin. A dinning table ta ajiye abincin da abun sha,falo tazo ta tarar da Mufida da Muhdeen suna fira,sanye yake cikin k'ananun kaya bak'in wando ta jan riga, murmushi tayi ta kalli Mufida. "To bisimillah Mufida ga abinci can." "Okay sannu da aiki matar Yaya" Mik'ewa Muhdeen yayi "Ni zan tafi masallaci sai na dawo." Mufida da Inteesar suka had'a baki wajen fad'in "A dawo lafiya" Daga nan ya fice, Inteesar ma kuwa d'aki ta koma ta sake yin wanka,ta shirya doguwar riga na material tayi sallar magarib bata tashi ba sai da tayi sallar isha'i,ta yi addu'a sannan ta cire hijabin ta d'aura d'an kwalin material d'in ta fesa turare ta nufi k'ofar fita. Fitowarta ya yi dai-dai da shigwarsa k'amshin turarenta ne ya daki hancinsa,dubansa ya Kai wajenta ganin tayi kyau sosai ga k'amshin turarenta ya tafi dashi,kauda kansa ya yi daga kallonta.d'akinsa zai nufa, Mufida ta ce " Yaya kai muke jira fa muci abinci fa,ba yadda yadda ita dole ya dawo wajen inda ya zauna a d'aya daga cikin kujerun dinning d'in,kusan a tare da Mufida suka zauna,inda Mufda ta yi zuba ma Yayanta sannan ta zubawa Inteesar,itama ta zuba nata ta zuzzuba masu lemo da ruwa a cup sannan suka fara ci. "Ummm ummm Inteesar gaskiya nayi kewar dadd'ad'an girkinki mai dad'i,kinsan ke ta musamman ce." Sai faman santi take shi kuma Muhdeen yana binta da ido komai ta ce ya ce eh hakane,shima kansa ya ji dad'in girkin don ya ci sosai. Suna gama cin abincin ne duk da ita Inteesar ba wani ci tayi ba,suna gamawa ne wayar Mufida ta yi k'ara ganin number direban Mummy ne ya sa ta mi'kawa. "Ni zan tafi anzo d'auka ta." Inteesar sai taji na dad'i akan tafiyar Mufida Amma ba yadda ta iya.hakan yasa ta ta aika mata da sak'on gaisuwa wajen su Mummy. Bayan tarfyar Mufida Muhdeen na koma d'aki wayarsa tayi ringing,ganin mummy ce yasa ya d'auka da sauri. "Hello Mummy barka da dare" Daga can 'bangaren Mummy ta ce, "Yauwa son da kazo d'azun na manta ban fad'a maka ba,duk abunda kake yi ka tabbatar gobe ka je gidan iyayen matarka ka gaishesu." Ransa baiso ba amma ba yadda yadda ita dolensa ya je. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T Maman Ihsan Don karin bayani 09065327995 Love u oll😍😘 Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T Maman Ihsan *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne Mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page3️⃣9️⃣ "Yauwa son na manta ban fad'a maka ba duk abunda kake yi ka tabbatar ka tabbatar gobe ka je gidan iyayen matarka ka gaishesu." Ransa baiso ba amma ba yadda yadda iya dolensa ya je. Inteesar bayan ta gama shirinta na kwanciya barci sai ta d'auki wayarta ta kunnah,kamar jira ake tana kunna wayar sai ga kiran Usaman ya shigo wayar.k'walla ne suka cika mata ido ganin ga shi yana kuranta ta d'auka ne ko kada ta d'auka,tunawa tayi da irin k'aunar da yake nuna mata da yawan murmushinsa a gareta,tunani ta shiga yi Anya ko Usaman yasan ta yi aure kuwa?kai bazai sani ba saboda duk lokacin da zai zo wajenta a gidansu bata ta'ba yarda yazo zuwansa biyu kuma shima na farkon sai da ya yi mata k'aryar magani zai kawo mata,zuwansa na biyu kuma ta sanar dashi ya dakata da zuwa sai nan gaba saboda Abbanta baya bari,daga nan kuma bai sake zuwa ba sai dai kullun cikin kiran waya yake,dama tunda taji labarin an aurar da ita ta kashe wayan gaba d'aya,sai yanzun da ta kunna wayar Kiran Usaman ya sake shigowa tana ji tana gani har sai da ya mata 5 Bata d'aga ba sai kuka take you a haka har ta kwanta barci 'barawo ya sace ta. Kamar yadda ta saba k'arfe hud'u na asuba ta farka,wanka ta tashi ta yi ta d'auro alwala tazo ta yi nafila kamar yadda ta saba,daga nan ta fara karatun al qur'ani kamar yadda ta saba,sai da loacin sallar asuba ta yi sannan ta tashi ta gabatar da sallar asuba,bayan ta idar da sallar ta yi azkar da addu'o'i sannan ta Fara ayyukan gidan kamar yadda aka kafa mata doka. Da misalin k'arfe goma sha biyu na rana ya fito raga cikin d'akinsa,sanye yake da shadda sky blue sai hula neavy blue da ya sanya a kansa da bak'in takalmi a k'afarsa da tsadaddan agogo dake d'aure a hannunsa,ya biyo ta falon Inteesar zai wuce tana zaune tayi tagumi, Jin takunsa yasa ta d'aga kai ta kalle sa sai da ya k'araso ta durk'usa ta gaishe sa. "Ina kwana?" Ko kallonta baiyi ba ballantana ya amsa mata,ta cigaba da cewa. "Ga breakfast na shirya can na shirya maka." Nan ma shiru ganin yana k'ok'arin fita ne yasa ta ce, "Adawo lafiya" Dakatawa yayi tare da jefa mata mugun kallo. "Wai ke wace irin mayya ce?kinyi magna d'aya ban amsa maki ba,ba sai ki kyaleni ba?" Tsuki yaja tare da ficewa,wayarta ce ta soma ringing,duban wayar tayi ganin Mummy ce yasa ta sakin murmushi ta d'aga kiran. "Assalamu Alaikum" Daga can 'bangaren Mummy ta ce, "Wa'alaiki salam Daughter ya hak'uri?" Murmushi ta yi "Alhamdulillah Mummy." "Masha Allah" 'Dan jim ta yi kafin ta d'aura da cewa "Daughter" "Na'am Mummy." "Kuna dai lafiya ko?" "Lafiya lau Mummy" "Ki fad'a mani gaskiya naji muryarki wani iri,idan akwai matsala ki sanar dani,kinsan Ni na haife sa idan akwai bunda ya ke maki wanda baki so ki sanar dani." Sahiru Inteesar ta yi ta kasa magana,ganin kamar akwai want abu da Inteesar ke son 'boyewa yasa Mummy cewa, "Ina son d'in ya ke" "Ya fita yanzun nan." Da zai fita ina ya ce maki zaije?" "Bai sanar dani ba." Shiru Mummy ta yi kafin ta ce, "Ki shirya yanzun nan zan kira shi zai dawo ya d'auke ki,zai kai ki giadanku ki gaida Ummanki sannan ya kawoki gida na." Cikin jin dad'i Inteesar ta ce, "To Mummy Nagode sosai sai nazo." Dagan nan ta kashe wayar ta ajiye a nan kan kujera,sannan ta nufi d'akinta cikin tsananin farin ciki. Muhdeen kuwa yana tsaka da driving Mummy ta kirasa nayan ya d'aga a cikin bada umarni ta yi magana. "Son ka koma gida ka je ka d'auko matarka ka tafi da ita ta gaida mahaifiyarta da mahaifinta kaima ka gaishe su,daga nan sai ku taho nan gidan." Bata jira mai zaice ba ta katse kiran. Dole ya juya akalar motar don kawa gida,dan yau da kansa ya ke driving ba kullun ya ke fita da Direba ba. Koda ya koma gidan bata nan a falo don haka ya nufi d'akinta,ita kuma lokacin ta fito daga wanka kenan tana d'aure da towel iya rabin cinyarta ya rufe gashin kanta da suka jike da ruwa kafad'arta,tana goge suman kanta dai-dai lokacin da ya shigo d'akin da niyyar yi mata masifa,mutuwar tsaye yayi lokacin da yayi arba da ita,tundaga k'asan k'afarta ya fara kallon zara zaran yatsun k'afarta da suka sha zanen filawowi masu kyau,a hankali yake d'aga k'wayar idonsa har zuwa santala santalan cinyoyinta farare masu kyalli da d'aukar ido,surar jikinta masu Jan hankali ya ke kallo gashin ya zubawa ido kamar na wata ba'indiya hand dryer ta d'auko ta kunna ta fara busar da gashin kanta,bayan ta gama ne ta fara k'ok'arin zare towel d'in da ta d'auka ne ta hango shi tsaye ta cikin mirror,cikin zafin nama ta maida towel d'in ta d'aura tare da janyo dogon hijabinta ya saka,ta'be baki ya yi ya fara magana cikin muryarsa da ta sark'e ya ce " ki same ni a mota." Daga nan ya saka Kai ya fice daga d'akin,ita kuma ajiyar zuciya ta sauke tare da hanzarin shiryawa. Yana fitowa falo wayarta dake saman kujera ta Fara ringing,kallon wayar ya yi yaga sunan wanda ya Kira ta,Usaman shine sunar da ya bayyana akan wayar,bai kula ba ya fice abinsa. Yana zaune cikin motarsa ya na jiranta, danne-danne ya ke a wayarsa,ta k'araso sanye take da abaya kalar lemon green ta sa hula ba'ki a ciki kafin ta yafa gyalen,ta yi simple makeup tana ri'ke da posanta da wayarta a hannunta,bak'in takalmi flat shoe ta saka,abayar na d'aya daga cikin kayan da ya siya lokacin da suka tafi Dubai da Sumayya had'o lefe inda kayan suka burgesa ya za'besu ita kuma Sumayya ta ce bata son kayan duk abunda ya burge wani baya burgeta,shi kuma sai ya kawo wa k'annensa Asiya da Mufida Mummy ta cirewa Inteesar wasu daga ciki,son shi dama kayan sun masa. Bud'e murfin motar tayi ta shiga tare da masa sallama,a zuciyarsa ya amsa sallamar,zama tayi ba tare da tayi magana ba,shiru yayi har tsawon mintuna goma bai ja motar sun tafi ba kuma bai ce komai ba,ganin bai da niyyar tafiya ne ya sa ta ce, "Yaya na gama." Shiru ya d'anyi kafin ya fara magana. "Dama kina da baki shine kika zauna mani shiru a mota kamar kurma?" Yaui maganar ba tare da ya kalle ta ba,zuba masa idanu ta yi tana mamaki wani irin mutum ne shi wannan?sai da fa ta masa sallama Bai amsa ba amma wai ya na cewa kamar kurma,shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba. "Bari kiji na fad'a maki wani abu d'aya,idan muka je gidanku ko gidanmu aka tambaye ki yanayin zamanmu kika kuskura ki ka sanar dasu halin da muke ciki da ke wallahi sai na lahira ya fi ki jin dad'i,ki nuna masu ba komai a tsakaninmu muna zaune lafiya cikin jindad'i,kuma bari kiji wannan d'ari d'arin da kike Dani ki ajiyeshi tun yanzun kuma a nan ki saki jikinki dani sosai ki nuna masu ba wata matsala a tsakaninmu,ki nuna muna jin dad'i da k'aunar juna,bari na fad'a maki meye ma sunanki?" Kallonsa tayi tare da cewa " sunana Inteesar" Jinjina Kai ya yi tare da cewa " koma dai wace ce na fad'a maki wallahi kika kuskura suka tambayarka kika sanar dasu zaman da muke yi dake,iya ka dai sai dai suyi mani fad'a,ke kuma idan muka dawo gidan nan Ni kad'ai nasan hukuncin da zan yanke maki,idan kunne ya ji jiki ya tsira,ina fatan kin gane?" Kai ta jinjina tare da cewa "Eh na gane" "Good,sannan magana ta k'arshe naji Gwaggo wai zata zo nan gidan tayi 1 month to da zaran ta maki zancen ki nuna mata cewar ba sai tazo ba tunda kinzo ta ganki." Da sauri ta kalleshi,dan Allah ya sani ba zata iya fad'awa Gwaggo haka ba,amma sai ta amsa masa da kawai. Kunna motar ya yi tare da yin horn inda mai gadi ya wangale masa gate ya bar gidan. Suna tafiya a gefen ya yi kwana ya tsaya a gaban wani tafkeken super market,yana gama parking yana k'ok'arin fita daga motar yaji an k'wank'wasa gilashin motar, sauke gilashin ya yi sai yaga shila k'awar Sumayya ri'ke da waya a hannunta, murmushi ta sakar masu tare da cewa "Barka da warhaka amarya da ango." "Shila kece ya kike?" Kallon Inteesar ta yi tare da watsa mata harara sannan ta ce, "Amarya ta ango ya cin amarci?" Inteesar ta kalleta tare gaishe ta "Ina wuni?" "Lafiya lau ya kike" "Alhamdulillah" Harara ta watsa mata a fakaice tare da cewa "Da alama amarya tasa an mance da Sumayya ko?" Ajiya zuciya ya sauke "Ba haka bane shila abun ne ya fi k'arfina ba yadda na iya ne,kuma ita da iyayenta sun d'auki zafi Amma na da few days komai zai dai daita." Jinjina kai tare da yi masu sallama ta bar wajen,shi kuma fitowa ya yi ba tare da ya kalli Inteesar ba ya fita daga motar. Bayan wani mintuna sai sai ji tayi ana zuba kaya a but d'in motar,karin aka rufe ya zagayo ya zauna ya ja motar suka bar harabar wajen. Bai tsaya ki ina ba sai k'ofar gidansu Inteesar,ganin ya yi parking k'ofar gidansu ya sa ta sakin murmushi mai sauti,Wanda har sai da ya kuyo ya kalleta,cikin farin ciki tayi yun'kurin bad'e motar amma sa taji ya yi lock d'In motar,juyawa ta yi da niyyar masa magana sai ta ga ya had'e fuska ba annuri a fuskarsa,hakan yasa ta turo baki ta cigaba da zama cikin motar,sai da kwashe mintuna bakwai kafin ya ce, "Ki shiga ki sanar da su tare muke." Bayan ya yi unlock d'in motar,fita tayi ta nufi cikin gidan,tun a zauren gidan take kwalawa Ummanta Kira. Umma! Umma!! Umma!!!" Da sauri ta fito daga d'aki jin muryar tilor 'yarta,A guje Inteesar ta k'arasa jikin Ummanta ta rungumeta sai hawaye kawai ke fita daga idanunta "Ummana nayi kewarki sosai,ta kwantar da kanta a kafad'ar Ummanta hawaye kawai ke tsiyaya daga idanunta,kusan mintuna uku suna a haka kafin Umman nata ta janyeta daga jikinta tare da Jan hannunta suka shiga cikin d'akin,Kan gadonta Ummanta ta zaunar da ita,zuba mata ido tayi ganin duk ta rame da alama bata cikin kwanciyar hankali,alamu sun nuna haka amma ko mene ne zata nemi Jin ta baki 'yarta, tasan halin da take ciki,don sanin cewa ba auren aoyayya bane na had'i ne. "Umma ina kwana?" "Lafiya lau Inteesar ya kike?" "Alhamdulillah Umma" "Ya mijin mai gidan naki?" Sai a lokacin Inteesar ta tuna cewa yana waje. "Umma muna tare ya ce nazo na sanar dake kafin ya shigo." "In banda abunki shine da kika shigo baki sanar dani ba?" "Farin cikin ganinki ne yasa na mance da shi,ina Abba ya tafi kasuwa ko?" Murmushi Umma ta yi tare da cewa Yana kasuwa amma idan zaki dad'e ne har zai dawo ya tarar dake,ki je ki shigo da mijin naki ko?" Mi'kewa Inteesar tayi ta fice daga d'akin duk wanda ya kalli fuskarta yasan tana cikin farin ciki. Yana zaune a cikin motarsa ya d'an kishingid'a,idanunsa a lumshe kamar mai barci,sallama ta yi masa a zuciyarsa ya amsa har sau uku tana masa magana amma shiru bai amsa ba. A hankali ya bud'e idanunsa a kanta "Dan tsabar iskanci da wulak'anci kika shanyani ina jirnaki ko?" "Kayi hak'uri" "Bari na fad'a maki abu d'aya mintuna talatin na baki kiyi a cikin gidanku,kada ki wuce haka,kina jina ko?" Kai ta jinjina masa "Dan Allah ka k'ara mani lokaci kaga Abbana baya nan koda awa d'aya ne ka k'ara mani don Allah." "Bana son Musu umarni na baki." Daga nan ta shige gaba suka nufi cikin gidan tana gaba Yana biye da ita a baya. *KUYI HAKURI DA WANNAN BA LALLAI BANE NA DINGA MAKU POSTING WEEKEND DAN BANA SAMUN ISASHSHEN LOKACI* Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page 4️⃣0️⃣ Daga nan ta shige gaba suka nufi cikin gidan tana gaba yana biye da ita a baya. Tun a bakin k'ofar zauren ya yi sallama,Umma ta lek'o ta amsa masa sallamar tare da ce masa ya shigo, takalminsa ya cire a k'ofar d'akin. "Assalamu Alaikum" "Wa'alaika salam" Shiga cikin d'aki. Ya yi ya durk'usa k'asa "Ina wuni Umma?" "Lafiya lau Muhammad ya aiki,ya kuma hak'uri?" Sunkuyar da kai ya yi tare da sakin murmushi "Alhamdulillah" Kallon Inteesar Umma ta yi tare da cewa "Kawo masa ruwa mana" Mi'kewa Inteesar ta yi ta ta fita waje ta d'auko kofin silba da murfin sa tazo ta bud'e randar k'asa ta d'ebo ruwan cikinta mai sanyi kamar na fridge,ta rufe kofin ta nufi d'akin a zuciyarta tana cewa nasan ma ba Shan wannan ruwan zaiyi ba,mutumin da ya saba da shan ruwan gora ta ina ma zai iya Shan wannan ruwan namu bari dai na kai masa. Da sallama ta shiga d'akin inda ta ajiye masa ruwan a gabansa,itama ta zauna daga gefe. "Muhammad ga ruwa kasha" Murmushi ya yi tare da d'aukar bud'e murfin kofin ya d'auki ruwan ya sha,kallonsa Inteesar ta yi don bata ta'ba tunanin zaisha ba kasancewar shi muyum mai k'yank'ami,bayan yasha ne ya rufe kofin,kafin ya d'ora da cewa "Abba baya gida ne?" "Eh ya tafi kasuwa" Kud'i ya ciro kimanin dubu a hamsin daga aljihunsa,ya ajiye a saman tabarmar sannan ya ce, "Umma idan ya dawo a gaishe shi to sai na sake shigowa." Umma ta nuna cewa yabar kud'in sunyi yawa ba za'ayi haka ba,ya nuna ba wani abu bane dan ya yi masu hidima,sallama ya yi ya fita inda Inteesar ta duba agogo saura mintuna ashirin cikin mintuna talatin da ya bata, ajiyar zuciya ta sauke tana tunananin cewa wata irin rayuwa ne wannan a ce a ce mace tazo gidan iyayenta ba za'a badi ta yini ba wai mintuna talatin ya bata. A k'ofar gida kuwa wasu matasan samari su biyu Muhdeen ya gani sunzo wacewa ya kira su,but d'in motar ya bud'e kayan da suka tsaya ya siya a hanya ne ya ce su shiga dasu cikin gidan nan,buhun shinkafa ne da carton d'in taliya da makaroni,sai na semovita da maggi da galan man gyad'a da na manja,haka suka shiga nik'i -nik'i da kayan sallama suka yi Umma ta lek'o ganinsu nik'i -nik'i da kaya da mamaki ta tambaye su. "Samari daga ina da kaya?" "Wani ne da ya fito daga nan gidan ya ce mu shigo da kayan nan." Da mamaki Umma ke kallon kayan har suka gama jidesu,ta juya ta kalli Inteesar ta ce, "Inteesar mijin naki har da d'awainiya kuam?haba ai da baki badshi ya kashe kud'i da yawa haka ba ga kud'in da ya bamu ai d'awainiya ta yi yawa." Inteesar dai bata ce komai ba,suka dinga kama kayan suna shigar dashi cikin d'aki. Nan dai suka zauna suna firan bayan rabuwa,kafin Inteesar ta ankare har ta kwashe awa d'aya, lokacin da ta ankare gabanta ya fad'i rasss da k'arfi. "Na shiga uku" Da sauri Ummanta ta kalleta "Lafiya me ya faru?" Shiru ta d'anyi don bata son Ummanta tasan halin da take ciki kada ta saka damuwa a ranta,hakan yasa ta ce, "Ina sauri ne Umma zan koma" Da mamaki Umman nata ta kalleta "Gida tun yanzun kuma? ba Zaki bari Abban naku ya zo ku gaisa ba?" Murmushin ya k'e Inteesar ta yi "Abunda ya sa zan tafi dama zanyi bak'i ne,lokacin da muna hanya ne suka sanar damu shine muka ce su d'an jira mu mun fita yanzun zamu dawo." Ido Umman nata ta zuba mata,don Inteesar bata iya k'arya ba indai ta fad'i maganar da k'arya ce tsab yanayinta ke nunawa,hakan yasa Umma dai ta yi shiru Dan ta fahimci akwai abunda take 'boyewa,bata son k'ureta ne yasa ta dai yi shiru tare da cewa "To shi mijin naki fa?" "Yana jira na a mota" Kai Umma ta jinjina ta ce, "To shikenan tunda haka kika ce,zan k'ara mai maita maki zaman aure sai hak'uri ki k'ara hak'uri akan wanda kike da shi yi nayi bari na bari dan Allah kibi mijinki sau da k'afa ki zama mai hak'uri da juriya a gidan mininki. "To Umma insha Allah" Hawaye ne suka cika mata ido ta mayar da su day sauri ta nufi k'ofar fita ta fice,sai da ta Kai zauren gidan ta tsaya ta saki kukan da ya taso mata,sanna ta tsagaita tare da share hawayen ta fice gabanta na dukan uku uku ta fita waje,wajen motar ta nufa bud'ewa ta yi ta shiga bayan ta shiga ne ta rufe murfin motar,yana zaune waya ya ke da alama Jabeer ne ya kirasa a waya inda yake cewa. "Badamuwa Jabeer,Kai da wa zakuzo goben ne?" Daga can 'bangaren Jabeer ke cewa "Nida Salisu ne da Bilyaminu,sai kuma Bashir dan har sunyi fushi ganin ko d'aurin auren baka sanar da su ba,na dai basu hak'uri sun ce gobe zasu zo suga amarya." Shiru ya yi na d'an lokaci kafin ya d'aura da cewa "Allah ya kaimu gaben sai kunzo." Daga nan ya katse kiran ba tare da ya kalli Inteesar ba ya ce, "Minti nawa na baki?" Shiru ta yi kafin ta ce, "Mintuna talatiin" Jinjina kai ya yi "Yanzun mintuna nawa kika yi?" "Awa d'aya nayi wallahi muna fira da Ummana ne bansan lokaci ya yi nisa ba shiyasa." Jin muryarta alamun ta yi kuka yasa ya kalleta "Saboda baki son komawa yasa kike kuka?to ai da kin fad'a mata baki son zaman auren Kinga shikenan kowa ya huta,ko an fad'a maki nima son zama nake dake?ala dole ala lalurati yasa nake zaune dake,dama Zaki taimaka yanzun ki koma ki fad'a Mata cewar baki so na ba Zaki iya zaman aure da ni ba sai dai na sauwak'e maki,kuma yanzu. Idan mun tafi gidanmu ki fad'awa Gwaggo cewa baki sona ba Zaki zauna dani ba wallahi da kin burgeni,ki nunawa Gwaggo cewa ita da ta had'a auren tasa na sauwak'e maki wallahi da kin burgeni ni,don sai na maki Babbar kyauta amma da ya ke mayya ce ke kika lik'e." Shiru ta yi tana jinsa bata ce komai ba. "Koda ya ke nan ba da dad'ewa ba zan sake ki ne, saboda Sumy na bata son zama da kishiya,buri na Komai ya dai daita ta dawo gida na a lokacin ke kuma Zaki bar gidan don wuta da auduga basa zama waje guda." Tana jin sa irin munanan maganganun da yake fad'a mata bata ce komai ba,tada motar ya yi ya yin da yake cewa "Isakancin banza daga mintuna talatin ta barni zaune ina jiranta sai da taga damar fitowa ta fito." Gyad'a Kai ya yi tare da yin kwafa "Kinci sa'a ba a gida muke ba da ace a gida muke da kika karya Mani doka wallahi sai kin gane kurenki." Ya cigaba da driving yana ta ta fad'a ita dai uffan ba ta masa ba,har suka k'arasa k'ofar gidansu inda ya yi horn mai gadin gidan ya wangale masu gate. Bayan ya shiga ya yi parking ne ya kalleta tare da cewa, "Ina fatan baki mance da abunda na fad'a maki a baya ba ki? matuk'ar kika nunawa Mummy da Gwaggo wani alamu na rashin jituwa ko na rashin sabo da juna sai kin gane kurenki,kada ki nuna d'ari ko wani shakkata da kike idan kunne ya ji jiki ya tsira. Bud'e murfin motar ya yi ya fito itama ta fito,inda ta tsaya gaida su Mallam Ibrahim Mai gadi da sauran ma'aikatan gidan,inda suka ta ya ta murna da Allah sanya alkhairi,sannnan suka gaida Muhdeen,nan suka nufi hanyar cikin gidan tana gaba Yana binta a baya saida suka k'arasa k'ofar falon sai ji kawai tayi ya rik'o hannunta cikin nasa da sauri ta kalle shi,ji kawai ya ja hannunta suka shiga falon bakinsa d'auke da sallama. "Assalamu Alaikum" Gaba d'ayansu suka amsa sallamar tare da kallonsu, Gwaggo,Dady, Mummy,da Mufida. Kunya ce ta rufe Inteesar ta yi k'ok'arin zame hannunta cikin nasa Amma ina bai bata wannan damar ba, sunkuyar da kanta k'asa ta yi har suka k'araso wajensu,Gwaggo sai washe baki take tana cewa "Lale marhaba da zuwa 'yar albarka,lale lale." Zaunawa sukayi a saman center carpet kusa da Mufida, Mummy ma ta ji dad'in zuwansu sosai da yadda tagansu sai ta yi farin ciki matuk'ar jin dad'i ta nuna,har lokacin bai saki hannunta ba, Gwaggo ta ce, "Dalla sake mani hannun yarinyar albarka mu gaisa,ka wani rirrik'eta kamar za'a k'wace maka ita." Gwaggo ta janyo hannunta ta janyota gaban kujerar da take zaune ido ta zuba mata ma wasu 'yan mintuna kafin ta ce, "Muhammadu haka aka aura maka yarinyar Nan?" Kallon Gwaggon ya yi don ya san me zata ce,kauda kansa ya yi daga dubanta ya maida dubansa ga Dady. "Dady ina wuni." Cikin sakin fuska ya amsa masa da "Lafiya kalau Muhammad ya iyalin? "Alhamdulillah" Dubansa ya maida zuwa ga Mummynsa "Mummy ina wuni?" Lafiya lau son kuna lafiya?" "Lafi..." Kafin ya gama fad'in lafiya lau Gwaggo ta fara magana "Ba wani lafiya da kake k'ok'arin cewa,lafiyarce za'a da'auki 'yar mutane a baka da d'an kumarinta a cikin kwanaki takwas naga yarinya ta rame sannan ka ce wa mutane lafiya?to gara ma ka fad'i gaskiya don banga alamar 'yar nan tana cikin kwanciyar hankali ba, Muhammadu kalleni in kalleka nan ba k'aramar yarinya ba ce ni da zaka raina mani hankali nasan k'ugin ciki nasan na gwaiwa wallahi duk wanda yasan 'yar albarka a baya ya kalleta yanzun yasan ba farin ciki da walwala a tare da ita." Dubanta ta maida kan Dady da Mummy ta ce masu "Kuma da yake ba tsoron Allah kuke ba bakusan laifin d'anku,har zaku kalli Inteesar ya ce maku suna lafiya ku yarda?" Girgiza kai Dady ya yi Dan ya Saba da halin mahaifiyarsa,inda Gwaggo ta cigaba da cewa "Da na ce sai nan da sati d'aya zanzi gidan naku nayi wata d'aya amma yanzun na fasa,jibi zanzo gidan naku dan hankalina ya tashi daga ganinta kasan bata cikin kwanciyar hankali,Amma kuka yi shiru tunda ba 'yarku Asiya bace." Muhdeen ya tanka Mata "Wai ke wannan tsohuwar me ke damunki ne haba mana,kince Bata cikin kwanciyar haankali to ki tambayeta idan ina mata wani abun da bata so." "Me kake ci na baka na zuba? ai ba sai ka fad'a mani ba,da kaina zan tambayeta nasan halin da kuke ciki." Janye hannun Inteesar ta yi tare da cewa " kinga tashi mu tafi d'aki kinji 'yar albarka." 'Daga Kai Inteesar ta yi ta kalli Muhdeen ya yinda shi kuma yi mata wani kallo Mai cike da gargad'i karaf kuwa a idanun Gwaggo. "La'ilaha ilallahu Muhammadur rasulullahi salallahu alaihi wasallam kallon uwar me kake mata haka?wato kada ta fad'a ki?to kada ka damu sai nayi maganinka wallahi da mi kake zancen." Daga Nan ta ja hannun Inteesar suka shiga d'aki don ta k'udurata niyyar sak ta gano tsakanins,dafe goshi Muhdeen ya yi yana ta addu'ar Allah yasa Inteesar kada ta fad'awa Gwaggo komai,muryar Mummy ce ta dawo dashi tunanin da yake. "Son maganar Gwaggo fa gaskiya ne nima na gani kuma nasan ba auren aoyayya kuka yi ba,kana can kana k'untawa 'yar mutane da ba ruwanta fa." Dady ya d'ora da cewa Muhammad Inteesar amanace awuri ka indan kaci amama amana zata cika. *LONDON* Kwance ta ke tana kallon Pics d'in Muhdeen tana kuka,ita kad'ai take magana "Baby me yasa kayi Mani haka?me yasa aka aura maka wannan tsinanniyar yarinyar ne mun tsaka da cin amarci?kasan irin son da nake bazan iya had'a soyyayar ka da wata 'ya mace ba." K'arar shigowar sak'one ya shigo tana dubawa ta ga Shila ce bud'ewa yayi taga Muhdeen da Inteesar a gaban motarsa a bakin super market,wani gigitaccen k'ara ta saki Wanda ya ja hankalin Mum nata da Da wayar take kallo tabbas shine tare da Inteesar sun ci ado ya d'aukota a motarsa,jifa ta yi da wayar ta bugata da bango dai-dai lokacin da iyayen nata suka shigo d'akin,numfashinta ne ke barazanar d'aukewa tayi luuu zata fad'i cikin zafin nama Dad d'inta ya tare ta ta fad'a jikinsa. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) DON K'ARIN BAYANI 09065327995 Love u oll😍😘 Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ki hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page4️⃣1️⃣ Numfashinta ne ke barazanar d'aukewa tayi luuu zata fad'i cikin zafin nama Dad d'inta ya tare ta ta fad'a jikinsa,Mum d'inta ce ta saki kuka tana fad'in "Shikenan mun shiga uku 'yar da muke da ita k'wara d'aya ce muke neman rasa ta akan d'a namiji." "Kinga ba kuma Zaki zauna kinayi mana ba,ki kawo mani ruwa." Fridge d'in da ke cikin d'akin ta nufa ta d'auko robar ruwa ta 'balle murfin ta mik'a masa ya kar'ba ya watsa mata a fuska sau biyu,sai ga ta ta farfad'o da ajiyar zuciya tana cewa. "Wallahi bazai yuwu ba Ni Muhdeen zai ci amana ta Ina nan ina tunanin yarinyar nan ba sonta ya ke ba ashe yana can tare da ita ya manta dani ko?" Ajiyar zuciya Dad ya sauke tare da cewa "Kada ki damu da kansa zaizo har nan da kansa ya same ki." Cikin muryar kuka ta fara magana "Dad wallahi yanzun aka turo Mani pic d'insa ya tafi shopping da wannan matsiyaciyar yarinyar Inteesar,Dad ban ta'ba kisan Kai ba amma Inteesar d'innan matuk'ar tana raye bazan ta'ba samun kwanciyar hankali ba,I will kill her matuk'ar ban kashe ta... "Shut up kinyi hauka ne ko kuma kishi hauka ne? kada na sake jin wannan maganar ko makamancinta a bakinki,dole ne sai kinyi rayuwa da Muhdeen? Cikin d'aga murya ta maida ma Dad d'inta da martani "Yas dole ne!na ce maka dole sai nayi rayiwa da Muhdeen shine mahad'in rayuwa ta bazan ta'ba iya rayuwa babu shi ba da na rasa shi gara a ce na rasa komai a duniyarnan Dad Kai da kanka kayi mani alk'awarin duk abunda nake so a duniyar nan zaka yi mani shi, kuma nima shira ne tunda na tashi naga duk abunda nake so shi kake mani ban ta'ba neman abu na rasa ba duk abunda nake so shi kake so kuma shi kake mani,amma karon farko a rayuwa ta na samu abunda nake son amma yana barazanar su'buce mani." Mum d'inta ce ta yi ajiyar zuciya sannan ta fara magana "Tunda haka abun ya kasance da kake cewa ya za'bi d'aya ko'yarka ko wacce suka aura masa kasan dai yana wa iyayensa biyayya bazai ta'ba tsallake maganar iyayensa ya bi na wasu ba kaima kasan da hakan kuma kaji maganganun da kakarsa ta fad'a maka lokacin da ka kira mahaifinsa kake masa magana,indai zaka bi shawara ta tunda basu suka kori Sumayya ba kuma mijinta bai sake ta ba kuma bai wulak'anta ta ba da k'afarta ta bar gidan ta taho nan,to idan zaka bi magana ta ta koma d'akin mijinta tunda ba zata iya rabuwa da shi ba." "Mum ke da kanki kike fad'in na koma da kaina na zubar da aji na a idonsa da danginsa?da wannan yarinyar da ya aura?." Fashewa da kuka ta yi fad'aj ikin Dad d'inta tana cewa "Wallahi Mum ba inda zan koma wato ma na fahimci baki so na baki k'auna ta baki kishi na,tunda har kike son na zauna da kishiya ke me yasa kike zaune ke kad'ai Dad bai k'ara aure ba?ai da Dad ya k'ara aure kika San zafin kishi ba Zaki ce na koma na zauna da kishiya ba." Da mamaki Mum d'inta ke kallonta "Sumayya ni kike fad'awa haka?" Tura baki ta yi tare da cewa "Ai gaskiya na fad'a kinsan zafin kishin ne?" Mummy ta yi kanta da niyyar marinta Dad ya daka mata tsawa "Ke dakata!" Sumayya k'ara shiga jikin Dad ta yi don ta tsorata da 'bacin ran da ta gani a fuskar Mun nata. "Kada ki kuskura ki ta'ba mai ita don wallahi kika mareta sai kinyi mamakin abunda zaki maki,k'arya ta fad'a ba gaskiya bane?sabida ance gaskiya d'aci ne da ita,da wanne zata ji da 'bacin ran mijinta ko da naki?kinzo Zaki saka yarinya gaba kamar ba kece kika haifeta ba,ke kanki kin sani bani k'aunar ki 'batawa yarinyar nan rai tun tana k'arama ballantana yanzun da tasan me yakamata tasan dai-dai da akasin haka,da ki ta'bata gwanda ki ta'ba ni,idan kuma kina musu da haka ne to ki ta'bata kisha mamaki." Mum bata sake cewa komai ba girgiza kai kawai ta yi ta fice ta bar masu d'akin. A nan k'asa ta kuwa bayan Gwaggo ta ja Inteesar sun shiga d'aki ta zuba mata ido bayan sun zauna ta kalleta ta ce, "'Yar albarka ki fad'a mani gaskiya ya yanayin zamanki da Muhammadu ya ke?" Shiru Inteesar ta yi tana nazari kafin ta ce, "Ba komai Gwaggo muna zaune lafiya" Kai Gwaggo ta girgiza tare da cewa "Ba lafiya ba 'yar albarka akwai abunda kike 'boyewa,kina nufin baya cutarki baya zalintarki yana kyautata maki duk wani hakkinki baya tauyewa?" Shiru Inteesar ta yi ba tare da ta ce komaiba,hakan yasa Gwaggo cewa "Kiyi mani magana mana abunda yasa kika ji na ce ki fad'a mani ya zamantakewarku ta ke shine kinsan ba auren soyayya kuka yi ba,auren had'i ne kuma bawai yana sonki bane kada ya je ya dinga k'untata maki ba. "Shiru Inteesar ta yi tana tunanin zamanta da shi Sam baya mata adalci burinshi kawai ya ganta tana wahal,amma Bata son ta zama sanasiyar 'batawansa da iyayensa don matuk'ar ta ce zata sanar da Gwaggo to tabbas zata sanar da su Mummy da Dady kuma zasuyi fushi da shi, hakan yasa ta ja bakinta ta yi shiru ta k'udiri niyyar hak'uri da juriyar zama da shi,dan haka kallon Gwaggo ta yi tare da cewa "Kada kisa tunananin komai a ranki muna zaune lafiya ba abunda kike tunani bane." "Shine duk kika rame kika lalace?ba komai tunda kink'i fad'a,koma dai mene ne zan gano Allah ya kaimu jibi zanzo na gaishe ku,tashi to muje." Mik'ewa Inteesar ta yi inda suka nufi falo,zaune suka tarar da su kamar yadda suka barsu, Mummy ce ta zubawa Inteesar ido tana karantar yanayinta,adai zaman da sukayi tare da Inteesar barci ke raba Inteesar da gidanta a tsawon shekaru uku zuwa hud'u kenan amma tabbasa yanayin Inteesar ya canza da ganinta kasan akwai abunda ke damunta. "Gwaggo ta sanar da ke ko akwai wata matsala?" Kai Gwaggo ta girgiza yayin da take zama a kan kujera "Ba abunda ta fad'a itama 'yar nema tayi shiru tana rufa masa asiri badai namiji ba ki cigaba da rufa masa asiri shi zai tona naki ne,ba'a goyon bayan namiji don ba d'an goyo bane kuma tunda na tambayeki kika mani shiru to duk ranar da kika zo kika ce ga abunda ya maki na cutarwa ba abunda zance masa sai dai nayi maki dariya." "Mummy ce ta yi ajiyar zuciya "Son Inteesar amana ce aka baka don Allah kada ka cutar da ita kaga k'aramar yarinya ce ita sai kayi hak'uri da ita,idan ta yi abu ba dai-dai ba ka nusar da ita ta lallami da hikima ka yi hak'uri da ita kada ka zaince ta." Kai ya jinjina tare da cewa "To Mummy kada ki damu insha Allah ba zakiji komai na rash... Gwaggo ta yi saurin katse sa da cewa "Ai dole ka ce ba za'aji ba tunda ka hanata fad'a kayi mata barazana me kuwa zamuji?amma ni ba iya ji ba har gani sai na yi dani kake zance." Kallon Gwaggon ya yi tare da fad'in "Me kum zaki gani rigimammiyar tsohuwa?ai ba abunda zaki gani,zancen da kike ma na cewa zaki zo gidana kiyi wata d'aya ban gayyaceki ba kiyi zamanki,ko na wuni d'aya bana buk'atarki ballantana na wata d'aya ki yi zamanki mu zamu zo ki ganmu idan kina buk'atar ganinmu." "Wallahi baka Isa ba sai nazo" Murmushin gefen baki ya yi "Aiko duka ranar da kika zo sai kinyi jinya kin gwammaci da baki zo ba." Da mamaki take kallonsa "To me zaka yi mani" "Ba abunda zan maki amma ina Mai tabbatar making da cewa kika zo gida na sai karen gida na ya yayyaga maki fatar jikinki." Salati Gwaggo ta saki tana tafa hannu tana ceqa "Oh ni Kuluwa yanzun kare ka ajiye a gidanka?saboda me?" "Saboda ke na ajiye duk randa kika saka k'afa gida na sunanki sorry." "Muhammadu haka zamuyi da kai d'an jakkar uba?" Mi'kewa ya yi tare da cewa "Ni zan d'an fita anjima zan dawo na d'auke ta mu koma gida." Mummy ce ta amsa masa da "Adawo lafiya" Dady ya kalli Inteesar ya ce "Daughter ba wani matsala ko? Kai ta girgiza tare da cewa "Bakomai Dady" "Ba wani abunda kike buk'ata ?" "Ba komai Dady" Mi'kewa ya bar wajen. Wunin ranar Inteesar a gidan ta yi shi Mummy ta Kira ta har d'akinta ta yi mata dabara da lallami, ko zata fad'a mata wani abu na rashin kyautatawa da Muhdeen ke mata amma sam tak'i yarda ta sanar da su haka suka hak'ura suka k'yale ta, Mufida ta ji dad'in zuwan Inteesar sun yini suna fira. Bayan sallar isha'i ne Muhdeen ya dawo gidan don d'aukar Inteesar su tafi gida,bayan ya ci abinci ne Mummy ke sanar da shi cewa ya je tana d'akin Gwaggo,da sallama ya shiga d'akin Gwaggo da kezaune kan sallaya tana jan carbi ta amsa masa,kwance ya samu Inteesar ganin Gwaggo ya sa ya fara magana mai dad'i "Sweet heart har kinyi barci kenan tun yanzun?"ashe daren yau ba zamuyi fira ba kenan?" Ita kuma Inteesar cikin barcinta da yanzun ta saba aikin wahala safe da yamma, kuma yaune bata yi ba sai ta mafarkin wai yana mata hukunci me yasa ba tayi ayyukan da ya ce ta dinga yi kowa ne yamma ba?a cikin mafarkin ta wai gata kwance tana barci shi kuma yana tsaye kanta zai dake ta ne ta fara magana,daga shi har Gwaggo suna kallonta tana mutsu-mutsu sai suka ji ta fashe da kuka tana cewa. "Yaya dan Allah ka yi hak'uri wallahi narci ne ya d'auke ni banyi ayyukan da kake sani ba,dan Allah kada ka dake ni wallahi bazan k'ara b... Dafe goshi Muhdeen ya yi tare da sauri ya k'arasa bakin gadon yana jijjiga ta tare da kiran sunanta. "Baby lafiyarki kuwa wani irin mafarki kike yi ne ai mafarki ba gaskiya ba ce." Tana bud'e ido ta ganshi a gabanta sai ta k'ara rikicewa tana girgiza kai tana ja baya idanunta na zubda hawaye,goshinsa ya dafe cikin takaicin abunda ya ke 'boyewa yarinyar nan na fiddo da shi,Muryar Gwaggo da Inteesar ta ji ne yasa ta dawo hayyacinta ta gane ashe mafarki take. "Ba shakka! Ni tunda na kalle ki nasan baki cikin kwanciyar hankali,idan ba haka ba ace barcin mintuna Ashirin ne zaisa ki rikice haka?wannan tsoron da na gani a cikin idanunki da maganar ayyukan da ya ke saka ki kina kuka kina bashi hak'uri kad'ai na fahimci halin da kike ciki saboda abinda mutum yasa a ransa ne ya ke mafarkinsa,don haka tashi kibi mijinki ku tafi." Mi'kewa ta yi tare da d'aukar posanta da wayarta suka nufi k'ofar fita tana gaba yana binta a baya,bayan fitar Inteesar Muhdeen na k'ok'arin fita ne ya jiyo muryar Gwaggo tana cewa "Idan baka kashe ta ba to ba sunanka Muhammadu ba." Kamar ya yi mata magana sai kuma ya fasa ya fice tare da buga k'ofar da k'arfi." "Ai da ka dawo ka 'balle k'ofar gaba d'aya,mutumin banza." A falo suka tarar da Mummy sallama suka mata suka fice. Yana driving ransa a 'bace saboda yasan cewa Gwaggo ta gano halin da suke ciki. "Wato ke bakijin magana ko?duk gargad'i da nayi maki sai da kika bari suka gane halin da muke ciki dake ko?." Kai ya jinjina "Zaki gane kuranki wallahi" Hawaye ne ya fara fita daga idanunta cikin muryar kuka ta fara magana "Wallahi ban fad'awa kowa ba duk yadda suka lalla'bani ban fad'a ba." "Ni zaki raina ma hankali?kina magana a gaban Gwaggo har da kuka kina rok'ona Wai ayyukan da na saki ko?." "Wallahi bansan na fad'a ba mafarki nayi." "Kada ki damu mafarkin zai zama gaskiya idan muka k'arasa gida,bana buk'atata na sake Jin muryarki." Daga nan ba Wanda ya sake magana har suka k'arasa gida,bayan Mai gadi ya wangale masa gate ya shiga ya yi parking need suka fito,yana gaba tana binsa a baya,suna shiga yaga tana k'ok'arin nufar d'akinta ya ce, "Dakata Tsayawa tayi tare da kallonsa,ya cigaba da magana. "Yanzunan ki tabbatar da cewa duka falon gidannan kin goge share su kin goge,sannan duka d'akuna guda takwas dake gidannan ki tabbatar a daren nan kin sharesu kin goge su,duka toilets guda takwas ki wankesu a daren nan toilet na falon nan ma shima haka duka kitchen d'in ma haka fatan kin gana?" Shiru tayi ta kalli time a wayarta ta ce, "Yaya kafin na wuce da safe sai da suka ayyukan nan da ka lissafa na yi su,ba wanda banyi ba a cikinsu,bayan na gama ne muka rufe gidan muka tafi ba wani datti bamu zauna gidan ba kuma kaga yanzun k'arfe goma na dare ya kusa don Allah ka barni da safe sai nayi ba datti suka yi ba wallahi barci nake ji." "Umarni na baki ba shawara na nemi ki bani ba, sannan bari na fad'a maki daga yau bana son uzuri." Yana fad'in haka ya nufi parta d'in Sumayya,ita kuma ta nufi d'akinta idanunta tab da k'walla na tausayin kanta canja kayan jikinta ta yi zuwa kananun kaya yadda zata ji dad'in yin aikin. Da paart d'inta ta soma daga nan bayan ta gama ta nufi part d'in Sumayya,haka ta dinga bin falon da d'akunan da toilets na kowane da kitchen duka biyu dinnan area ko ina sai da ta goge su tas. Dama can ba wani datti sukayi ba fes suke kuma ba amfani ake dasu ba ba kowa a ciki,amma don mugunta sai ya sata ta yi safe da yamma. Bata gama ayyukan da ya saka ta ba sai k'arfe d'aya na dare,duk ta gaji sai hawaye ne kawai ke tsiyaya masu d'umi daga idanunta.wanka ta yi tare da yin addu'ar kwanciya barci ta kwanta, lokacin k'arfe d'aya da rabi na dare. K'arfe hud'u da rabi na asuba ta farka wanka ta yi ta d'auro alwala,ta yi nafila da addu'a ta samun sassauci a rayuwarta, har aka Kira assalatu ta yi sallah da azkar tana son ta tashi ta yi ayyukan safe ne barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita ba tare da ta shiryawa yin barcin ba. Misalin k'arfe tara na safe ya fito daga bedroom d'insa ganin bai ganta a kitchen ba kuma bata shigo ta gyara masa d'aki ba yasa ya nufi d'akinta. Tura k'ofar ya yi ya ganta kwance saman sallaya da hijab a jikinta,alamun daga sallah ta yi barcin,fridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi sosai ya 'balle murfin robr ya tsiyaya mata ruwa tun daga Kan fuskarta har zuwa jikinta, a firgice ta farka tare da fad'in "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Jikinta ne ya soma rawa don ruwan ya yi sanyi da yawa,gashi dama bata son ruwan sanyi ko wanka dashi batayi Amma yau ruwa mai sanyi kamar K'ank'ara aka kwarara mata a jiki,kuka ta fashe da shi mai cin rai,yatsarsa ya sa a baki tare da furta "Shhhhhhp" Ba shiri ta had'ye kukan hawaye na tsiyaya a idanunta. "K'arfe nawa yanzun?" Kallon agogon da ke manne a d'akin ta yi "K'arfe tara da minti biyar" "Shine kike kwance kina barci?" "Wallahi bansan lokacin da barci ya d'auke ni ba." "Tashi kije ki yi ayyukan da kika San ya wajaba a kanki." Mi'kewa ta yi zata shiga toilet taji muryarsa yana cewa "Ina zaki je?" "Zan shiga toilet ne na cire kayan nan sun jik'e da ruwan sanyi, idan na ce zan barsu a jikina sanyi zai kamani ne." "Ya kamaki mana sai me?ba sanyi ba ko k'ank'ara zai kamaki ya kamaki ba matsalata bace,don haka fita ki fara ayyukan da na saka ki." Haka ta fita kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki ta fita ya bita da kallon banza. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa,idan suna ki hali yaso d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi t,arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page4️⃣2️⃣ Haka ta fita kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki,ta fita ya bita da kallon banza. A haka ta da jik'akkun kayan ta dinga aiki da su a jikinta,har suka bushe a jikinta ga sanyin da take ji ba yadda ta iya ahaka ta gama ayyukan gidan. Kasancewar ba ya cin abincinta ya sa bata yi wani girki ba ta ruwan shayi kawai ta dafa ta sha,ta koma d'akinta lokacin rana ta riga da ta yi, wanka ta yi ta Sanya soguwar riga na atamfa wayarta ta soma ringing dubawa ta yi Usman ne daon haka Bata d'aga kiran ba har ya tsinke,wani tunani ta yi kodai ta d'aga ne tunda wannan auren ba mai d'orewa bane shi da kansa ya fad'a mata idan Sumayya ta dawo zai rabu da ita,don ba sonta ya ke ba tunanin hakan ne ya sa ta cewa bari ta d'aga kafin matarsa ta dawo ya ce zai sallame ta,d'aga wayar ta yi ta Kara a kunnenta. "Assalamu Alaikum" Daga can 'bangaren Usman da ke zaune a office d'insa ya saki ajiyar zuciya tare da furta. "Wa'alaiki salam, har naji sanyi a Raina Inteesar azabtar da ni da kike ya yi yawa,baki san rashin ganinki da rashin jin muryarka ya hanani sukuni ba kullun da tunaninki nake kwana nake tashi,tunda muka had'u a sau uku nazo gidanku amma kika hana wai Abba ya hanaki,hakan ya sa na yi tunanin zuwa neman izinin zuwa zance a wurinsa." Da sauri ta katse shi da cewa "Kadai bari zuwa nan gaba kad'an amma ko ka same shi yanzun zai ce ka bari zuwa gaba kad'an ba jimawa,saboda haka idan olkaci ya yi da kaina zan sanar dake." Hira suka ta'ba sosai na kusan mintuna talatinl,sai da ya ji ana knocking sannan ya mata sallama ya ajiye wayar,sannan ya bada izinin shigowa. Ita kuma sanin cewa jiya abokan mijinta suka ce yau zasuzo ne ya sa ta mi'ke ta nufi kitchen don d'aura masu girki. Jallop d'in cuscus ta da white rice and stew da ta ji naman rago,sai pepper chicken da tayi masu da farfesun d'anyar kifi da ta yi masu ga lafiyayyan juice na kwakwa da madara,ta had'a masu girkuna masu gidan ya cika da k'amshin girkinta ya cika gidan. Komawa d'akinta tayi ta fad'a toilet ta sake sabon wanka sake ta shirya cikin doguwar riga na less d'inki bubu ya kar'bi jikinta,dama ita bata damu da kwalliya ba,don haka bayan ta shafa man shafawarta na wajen Hajiya Bilkisu, powder kawai ta shafa sai man baki,ta saka sark'a da d'an kunne,gasjin kanta ta tufke shi a tsakiyar kanta,zama ta yi baki gadon tare da d'aukar wayarta tana buga game. Gidansu Inteesar kuwa koda Abbanta ya dawo kasuwa yammaci ne lik'is hannunsa d'auke da leda mai layin yellow da bak'i, Dankalin hausa ne a cikin ledan da sallama ya shigo gidan , Umma da ke zaune gaban murhun itace tana tuk'a tuwo ne ta amsa masa sallamar,sakin muciyar ta yi da niyyar tashi ta kar'bo ledar,hannu ya d'aga mata alamar ta barshi . "Zauna ki cigaba da aikinki Umman Inteesar" Murmushi ta yi tare da cewa "Sannu da zuwa ya kasuwar?" "Alhamdulillah an godewa Allah." Zama ya yi kan tabarman da ke shimfid'e a k'ofar d'akinsa. Bayan Umman Inteesar ta gama tuk'a tuwon ne ta tashi ta d'auki kofin silver da murfinsa ta d'ebo masa ruwa,a cikin randar k'andar k'asa me sanyi gabnsa ta ajiye tare da k'ara masa sannu da zuwa,bayan yasha ruwan ne ya mi'ke tare da cewa "Bari na tashi nayi wanka na tafi masallaci, lokacin salla ya k'arato. Mi'kewa ya yi yayin da Umma dama ta ajiye masa ruwan wanka a cikin tukunyar da suke dafa ruwan zafi,juyewa ta yi a cikin bokinti ta surkar masa da ruwan sanyi ta kai masa bad'aki ya fito daga cikin d'akinsa ya shiga band'akin Bayan sallar isha'i ne bayan ta dawo daga masallaci yana zaune a Kan tabarma Umma ta kawo masa tuwo,ya ci ya gama ta ce , "Mallam Inteesar sunzo da mijinta d'azun da rana kana kasuwa." Zuba ma Umma ido yayi fuskarsa d'auke da murna duk da bai ganta ba amma ya ji dad'in zuwanta gidan. "Masha Allah da nasan zata zo da na bari sai na ganta kafin na tafi,suna dai lafiya ba wata matsala ko?" "Wannan ne kuma ban sani ba mallam" "Kamar ya baki sani ba da tazo me yasa baki tambaye ta ba ko awai wata damuwa." Shiru Umma ta yi tana tunanin yanayin da taga Inteesar,ita ta haifeta tafi kowa saninta a duniyarnan,amma ganin yanayin da ta ganta ko shakka babu akwai abunda ke damunta,dalilin da yasa bata d'aga hankali ba tasan cewa wasu lokutan auren had'i idan har basa son junansu sukan sawa kansu damuwa da tunani saboda ba wannan ne a zuciyarsa ba,wannan dalilin yasa Mummy kauda ido. "Mallam ta ce mani suna zaune lafiya." Jinjina kai yayi "Masha Allah" Umma ta mik'e ta shiga d'aki ta fito hannunta d'auke da kud'in da Muhdeen ya bata mik'a masa tare da cewa "Mijinta ne ya kawo muna kayan abinci masu yawa tare da kud'in nan." Kallon kud'in Abba ya yi sannan ya kalli Umma ya ce, "Harda d'awainiya haka?da baki kar'bi kod'insa ba" "Nima banso kar'ba ba ajiyewa ya yi" Yana zaune akan kujera Yana jiran isowar abokansa,wayarsa ta fara ruri,dubawa ya yi yaga Dadynsa ne,d'aga wayar ya yi tare da cewa "Assalamu Alaikum" Daga d'aya 'bangaren "Wa'alaika salam Muhammad kana gida ne?" "Eh Dady ina gida ina jiran su Jabeer ne zasu zo." "Okay to ga Gwaggo nan ta shirya kayanta ta ce lallai sai dai na kira ka kazo ka d'auke ta zuwa gidanka." Gaba d'aya hankalin Muhdeen ya tashi,don yasan zuwa sa masa ido kawai Gwaggo zata yi ba wai don ziyara ba,yanzun ya zaiyi da wannan tsohuwar ba,ta zame masa matsala,yana cikin tunani ya jiyo muryar Dady na cewa "Ya kayi shiru lafiya kuwa?" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Gani nan zuwa Dady" Tsuki ya ja tare da d'aukar wayarsa kamar ya ba Direba ya d'auko ta,ya tuna kira Mahaifinsa ne don haka ya ta fi da kansa. Yana driving akan hanyarsa ta zuwa d'aukota ne wayarsa ta soma ruri dubawa ya yi yaga Sumayya ce, ba shiri yayi parking a gefen titi ya amsa wayar cikin farin ciki. "Hello Baby sai yau kika Kira ni tunda kika tafi sai ma kika sakani a blacklist ko?" Jin sautin kukanta ya ke harda sheshshek'ar kukanta,rintse ido ya yi sakamakon jin sautin kukan nata. Kinga kunga dan Allah ki daina kukan nan hakanan muyi magana. "Ba dole nayi kuka ba tunda na tafi ba ka damu Dani ba ka mance dani saboda kana tare da wannan yarinyar da parents d'inka suka aura maka." Kinga da kinsan irin zaman da nake yi da yarinyar nan a gidan nan ko?da baki fad'i haka ba,ni fa wannan auren ban d'auke shi aure ba tunda taso gidan nan wallahi ko kallo bata ishe ni ba zaman gidan nan dai-dai yake da zaman gidan wak'afi a wajenta." Dakatar da kukanta ta yi tare da cewa "Kana nufin ba abunda ya shiga tsakaninka da ita?' "K'warai kuwa ko hannunta ba ta'ba rik'ewa ba ballantana wani abu ya shiga tsakaninka mu,kuma zaman da take a gidan nan ki d'auka 'yar aiki ce na kawo maki,zata kasance mai maki ko wani irin aiki da bin umarninki." Dariyar mugunta ta yi tare da cewa to "Gobe ma zan dawo" Shiru ya ya yana nazari kafin ya ce, "Dawowarki gobe akwai matsala ki bari sai bayan wata d'aya ki dawo?" Sakin baki tayi cikin mamaki ta ce, "Baby anya kuwa kana sona yanzun?" "Ba abunda ya ragu cikin son da nake maki." "To me zaisa ka ce na bari sai bayan wata d'aya na dawo alhalin ina nan na matsu na ganka kana cewa one month." "Abunda ya sa kika ji na ce haka yau Gwaggo zata zo gidan nan kuma idan tazo sai ta yi one month kafin ta tafi,Kinga kuma zamanki da Gwaggo a gida d'aya akwai matsala,kuma kunga matuk'ar tana cikin gidan nan bazan ta'ba k'untatawa rayuwar Inteesar ba dole na d'aga mata k'afa bazan cutar da ita ba har sai bayan Gwaggo tabar gidan." Shiru ta yi tana nazari kafin ta d'aura da cewa "Bakomai amma gaskiya ka samu lokaci kazo na matsu na ganka kafin lokacin tafiyar Gwaggo ya zo." Murmushi ya yi tare da cewa "Karki damu zamuyi waya anjima." Tana zaune a falonta tana tunanin yanayin rayuwar da take ciki,tana kuma tuna yanayin rayuwar da take ciki kafin aurenta. Turo k'ofar aka yi taga Ishaq direba ne da akwati a hannunsa,tana kallon akwatin ne ta ji muryar Gwaggo na cewa "Ina 'yar albarka take?" A guje ta nufi k'ofar tana dariya,akan barandar shiga falon ne taga Gwaggo da Muhdeen, rungume Gwaggo ta yi da k'arfi kamar zata shige jikinta. "Yar albarka bini a hankali k'afar ba lafiya" Jin hakan yasa ta d'an sassauta tare da cewa " Oyoyo Gwaggo" "Okay wato ganin Gwaggo yasa kin mance da ni ko?oyoyon da ake mani ma yanzu ban samu ba saboda Gwaggo ko?" Tsayawa ta yi tana kallonsa cikin mamamki,a zuciyarta ta ke cewa yanzun zai fara amfani da fuska biyu kenan. A falo suka zauna inda Inteesar ta nufi kitchen don kawowa Gwaggo abun ta'bawa Muhdeen kuma ya k'udiri niyyar cewa bazai ta'ba barin wata k'ofa da zaisa Gwaggo ta gane cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da Inteesar ba,zai dinga nuna mata k'auna da kulawa,zai janyo Inteesar a jikinsa yadda zata sake dashi ta daina jin tsoronsa don burinsa ya cika. Inteesar ce ta kawowa Gwaggo ruwa da lemu a faranti,kallonta Gwaggo ta yi tare da cewa "Sannu da k'ok'ari 'yar albarka Allah ya nuna mani 'ya'yanku." Sallama suka ji daga bakin k'ofar shigowa, Muhdeen ne ya amsa tare da basu izinin shigowa, Jabeer ne da Salisu da Bilyaminu sai kuma Baahir. "Jabiru kune a tafe? Dariy ya yi tare da cewa "Eh mune Gwaggo, dama kina nan ne?" "Yanzun nan nazo kuma wata d'aya zan masu a gidan nan,duk da cewar shi Muhammadu bak'in ciki yake da zuwa na ban damu ba,duk tsiyarsa Bai isa ya koreni ba tunda 'yar albarka na maraba da ganina." Inteesar dama tunda taji muryar maza zasu shigo ne tayi saurin ta nufi d'akinta,sai gata da hijabi har k'asa,Su Salisu ne suka gaida Gwaggo suka zazzauna a kujera, Muhdeen ya dinga mi'ka masu hannu d'aya bayan d'aya suna gaisawa,Bashir ne k'arshe lokacin da Muhdeen ke mik'a ma Bashir hannu baima san yana mik'o masa hannun ba,gaba d'aya ya shagala da kallon Inteesar ko k'yaftawa baya yi, Muhdeen ya kalle shi ya kalli Inteesar da bata ma San yana kallonta ba hankalinta na wurin Gwaggo da take tambayarta su Mufida,had'e fuska ya yi tare da kallon Inteesar cikin bada umarni ya ce, "Inteesar ki shiga d'aki" Da sauri ta kalle shi tana kokonton sunanta da ya kira,don tunda take bata ta'ba Jin ya Kira ta da sunanta ba sai dai ya ce ke wata rana ma mayya yake kiranta amma yau karon farko ta ji ya kirata da sunanta da mahaifinta ya saka mata,Bata gama tuna ni ba ta jiyo ya maimata cewa ta shiga d'aki,take ta juya ta koma d'akinta,kowa dake falon zuba masa ido ya yi shi kuma fuskar nan tasa a had'e,yana tuna lokacin bikinsa da Sumayya ranar da Bashir ya fara ganin Inteesar yana ta yaba kyawun surarta da har yana kiranta da zazzafar yarinya wai duk neman matan banza da yake bai ta'ba ganin macen da ta mallaki abunda ya ke so komai a jikin mace ba sai Inteesar. "Bros ya zaka kori amarya ita fa muka zo gani,ko gaisawa ba muyi ba ana muna rowarta." Dariya sukayi Salisu ta d'aura da cewa "Nima abunda na gani kenan,lokacin da mukayi auren mu ai da yazo zama ya yi suka gaisa da amaren mu,amma kunga shi rowar ta ya ke." "Muhammadu mutumce fa ita ba akuya ba ce da zaka rufe a d'aki,wannan ai zalinci ne wallahi bani so takura,haka kawai zaka takurawa 'yar mutane." Bai ko kalleta ba ballantana tasa ran zai amsa mata, "Bisimillah kuzo muci abinci" Jabeer ya tintsire da dariya tuna ranar da suka zo cin girkin amarya Sumayya,Salisu da Bilyaminu ma ta ya shi dariyar sukayi don suma abunda suka tuna kenan. "Nidai wallahi tsoron cin girkin gidanka nake ranar farko da mukazo cin girkin amarya ba Wanda ya iya had'iye ko cokali d'aya gaba d'aya saboda k'warewar Hajiya Sumayya a iya girki." Gaba d'ayansu suka sake dariya,hakan ya sosa ran Muhdeen matuk'a don haka ya zauna ya fita batunsu ko kallonsu Bai sake ba. "Koda yake Sumayya daban Inteesar ma daban ,don Sumayya bata iya girki ba ba yana nufin cewa Inteesar bata iya ba,bari mu tashi dai bakinmu ya gaya Mana." Gwaggo ta zubawa Jabeer idanu tana cewa "Jabiru Wai kana nufin wannan yarinyar bata iya girki ba?" Dariya ya yi don dama ya it's tsokana "Ai Gwaggo idan ana sallah ba'a magana wato ranar da tayi muna girki wallahi gaba d'aya kamar an wanke kai,ni wani d'aci naji na ma kasa tantance want irin test abincin keyi gashi bai dahu ba,dukanmu ba Wanda ya iya cin ko cokali d'aya,na ce wannan girkin na masoya ne." Ta'be baki Gwaggo ta yi tare da cewa "Idan mace bata iya girki ba ki ai ba mace bace,dama sai da na guje masa auren ta amma bai saurare ni ba." "Ya isa hakanan kun zauna Kuna ta cin mutuncin mata ta akan me?" Mi'kewa Jabeer ya yi tare da nufar dinning area. "To ina amarya ta zo ta zuba mana muji ya nata k'warewar take." "Ba zata zo ba kowa ya zubawa kansa ya ci tunda ba cikinta zaku zuba ba." Daga nan ya juya ya nufi d'akin Inteesar,tura k'ofar ya yi inda ya samu tana waya a cikin zancen nata ne ya ji tana cewa "Haba Usman ka daina fad'in haka Usman wallahi nima ina cikin damuwa na yi missing d'inka sosai." Gaban Muhdeen ne ta fad'i cikin tashin hankali ya furta "What?" Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kase auren wawa. Page4️⃣3️⃣ "Haba Usman ka daina fad'in haka, Usman wallahi nima ina cikin damuwa, na yi missing d'inka sosai." Gaban Muhdeen ne ya fad'i cikin tashin hankali ya furta "What?" A firgice Inteesar ta juyo ta kalleshi gabanta na tsananta fad'uwa,cikin sanyi da nutsuwa fuskarsa ba yabo ba fallasa,ya k'araso gabanta yayin da ya mik'a mata hannu alamun ta bashi wayar,katse kiran tayi kafin ta bashi wayar kar'ba yayi tare da cewa "Waye shi?" Shiru ta yi ba tare da tayi magana ba,ya sake tambayarta da cewa "Na ce waye Usman?" Shiru ta yi masa ta kasa cewa komai,zuba mata ido ya yi yana kallonta. "Soyayya kike da wani k'ato da igiyar aure na akanki?saboda baki San darajar aure da martabarsa ba ko?." Sanin cewa Gwaggo na cikin gidan kuma matuk'ar Gwaggo na gidan bai isa ya ce zai mata wani abu ba ko ya yi yun'kurin cutar da ita,hakan yasa ta samu k'warin guiwar cigaba da magana. "Usman masoyi na ne na hak'ika yana k'aunata da kuma burin aure na ya faranta mani rai don yana son farin ciki na." Ji ya yi zuciyarsa na k'una da jin d'acin kalamanta. "Shi baisan kina da aure bane ko kuma rashin sanin darajar aure ya sa ya ke waya da ke?" "Eh baisan na yi aure ba." "Uban me yasa baki sanar da shi cewar ke matar aure ba ce?" Ba tare da ta kalle shi ko ta yi shakkarsa ba ta ce, "Saboda ni ba matar auren ba ce, don wannan zaman da nake ban d'auke shi zaman aure ba,kai da bakinka ka fad'a mani cewar da zarar matarka ta dawo gidan nan ni kuma zaka rabu da ni ba zaka zauna da ni ba,wannan dalilin yasa ban sanar da Usaman cewa ni matar aure ba ce a yanzun,domin zaman jiran matarka ta dawo nake, idan ta dawo ka rabu da ni kamar yadda ka ce sai na je na auri Usman." Gaba d'aya ransa ya gama 'baci da kalamanta,fita ya yi da wayar a hannunsa Kai tsaye ya nufi d'akinsa ransa a 'bace Gwaggo da ke zaune a falo taga ya fito ransa a 'bace yasa ta gane akwai abunda ya faru,su Jabeer da suke a dinning area basu ganshi ba. Yana shiga d'akin ya bud'e size durowa ya saka wayar, zuciyarsa na tafarfasa,zama ya yi akan gadon tare da magana shi kad'ai kamar yana fad'awa wani. "To ni mene ne nawa ne na 'bacin rai haka?to wai ma kishinta nake ko me?idan ina kishinta hakan na nufin sonta na fara? tunda ance kishi ke saka soyayya,kai ina bazai yiwu ba me zaisa naso ta? to wai shin ma ina ruwa na ne da zansawa kaina damuwa?" Tsuki ya ja tare da ficewa daga d'akin ya nufi dinning area. Nan ya same su suna ta cin abinci suna zuba santi,sunci lafiyayyan girkin Inteesar kuma daddad'i da lemun da ta had'a masu,Salisu ne ya ce, "Gaskiya zan kawo Saliha ta nan gidan a koya mata irin wannan girkin." Jabeer ne ya yi dariya yana cewa "Ashe matar ta ka bata iya girki ba kenan." "Inji waye ya ce mata ta bata iya girki ba?da wa ke dafa mani abincin da nake ci?" Dariya Jabeer ya k'ara yi tare da cewa "Oho na sani ko kaima matarka irin ta o o ne bata iya komai ba sai anje restaurant anyo mata takeaway sannan suci." Ya k'arasa maganar ya na kora lemu a bakinsa Muhdeen ne ya kalle shi dan yasan da shi ya ke yi bada kowa ba k'ara tsuke fuska ya yi tare da cewa "Jabeer da wa kake?" Murmushi ya saki "Na kira sunanka ne?fira muke yi idan zaka shiga to bisimillah." Dariya ya sake yi tare da cewa "Oh ashe fa haka ne dama hausawa na cewa mai kaza a cikin aljihu baya jimirin ass." "Jabeer Nagode da ziyara zaka iya tafiya ka gaida iyali" "Korata ka ke yi ?" "Eh ko na kore ka gida na ne ai ina da ikon yin hakan." Dariyar rainin hankali Jabber yayi kafin ya ce "Sannu takobi sarkin gida,ba yadda zaka yi dani na zame maka ciwon ido sai hak'uri,kuma ba yanzun zan tafi ba sai munsha fira da kaka ta Gwaggo sai magariba zan tafi,ka fad'awa Inteesar idan zata yi girkin dare ta dafa har da ni da Maryam ta zuba mana a flask na tafi dashi gida." "Saboda kai ka ajiye ta ko?." Daga nan dai bai sake ce masu komai ba suna ta cin abincinsu suna fira,bayan sun kammala ne suka yi masa sallama tare da cewa wai ya kira amarya su yi mata godiyan girkin da suka ci,ya ce wai zai isar masu da sak'on godiya yanzun ta kwanta ne ba zata samu damar fitowa ba,sun san ya fad'a ne kawai amma ba wani barcin da take yana dai fad'a ne,nan suka dinga masa tsiyarsa bai tanka masu ba,suka sallami Gwaggo suka tafi,nan ya zauna tare da Gwaggotana ta jansa da fira duk da cewar hankalinsa ba wajenta ya ke ba,ya kasa gane dalilin da yasa hankalinsa ya k'ikwanciya akan wayar da ya tarar Inteesar na yi,gaba d'aya ransa a 'bace ya ke da lamarin, Inteesar ce ta fito ta nufi kitchen ta kawo ma Gwaggo abinci tare da Gwaggo suka cin abincin,suna fira ya yinda shi kuma idonsa na kan Inteesar abubuwa da yawa yake sak'awa akanta. Da misalin k'arfe biyar ne Inteesar ta shiga kitchen don d'ora masu abincin dare, Gwaggo ce ta biyo ta kitchen d'in tana cewa. "'Yar albarka me kuma xaki girka ne?" Murmushi Inteesar ta yi tare da cewa " Duk abunda kike so shi zan girka maki Gwaggo na ta kaina." "A'a nikan kada kibi ra'ayina kibi ra'ayin mijinki duk abunda kika san ya fi so shi zaki yi." Shiru ta yi tana tunani ita kanta bata ta'ba zama da shi a inuwa d'aya ba,ta ya ya zata san abunda yafi so? mutumin da ma har yau bai tunda tazo gidan sau d'aya ya ci abincin ta shima ganin idon bak'uwa ne. "Ke ya naga kunyi shiru anya kuwa 'yar albarka kina kula da miji?kar fa ki manta yana da wata matar da ya ke so, ke da ba soyayya ce ta had'aku ba zage dantse zaki yi ki nemi soyayyarsa so nake ki zarce waccan matar a wajensa,kafin ta dawo ma sai dai ta ganki da ciki." Da sauri Inteesar ta juya ta kalli Gwaggo. "Meye zaki jalleni haka?me ye ribar auren idan ba soyayya ba?indai shi jarimi ne ma yakamata ace kina da shigar ciki,shin ma na tambaye ki yana da k'wazo kuwa?idan har baida k'wazo da jarumta ki fad'a mani,akwai wani garin yaji da zan baki ki dinga zuba masa a cikin abinci,ina mai tabbatar maki da zaki zuba masa wannan yajin da kanki zaki mani godiya da addu'a." Ta k'arasa maganar tana dariy,dafe goshi Inteesar ta yi cikin kunya da takaicin maganar Gwaggo,don ta lura Gwaggo sam bata kunyar fad'ar ko wace irin magana,don haka ta yi shiru bata ce komai ba,ganin ta yi shiru ne yasa Gwaggo ta k'ara cewa "Naji kunyi shiru na baki ne 'yar albarka?" Nan ma bata ce komai ba "Bari na je na d'auko maki ko?" Ta k'arasa maganar zata fita daga kitchen d'in sai ta ji muryar Inteesar tana cewa "Kubarshi Gwaggo." Wangale baki ta yi " To masha Allah ni nasan jika na ba ragon namiji bane." Haka Gwaggo ta cigaba da suratanta tun tana tsaye har ta zauna, ita dai Inteesar bata ce komai ba har ta gama girkin jallop d'in taliya ta girka da ya ji kayan lambu da busashshen kifi. Da misalin k'arfe takwas na dare bayan sun idar da sallan isha'i Gwaggo na zaune a falo, Inteesar ta k'araso sanye da duguwar riga na material,kallon Gwaggo ta yi tare da cewa "Gwaggo ki tashi muci abinci" "Ina shi mijin naki ya tsaya an idar da sallah bai shigo ba?" Ta'be baki ta yi a zuciyarta ta ce "Oho masa ina zan sani me ye ruwana da shi?" A zahiri kuma ta ce "Maybe akwai abunda ya tsayar da shi ne." Gwaggo ta sake jefa mata tambaya "Dama ba daga sallar isha'i ya ke shigowa ba?" Shiru Inteesar ta yi don bata da amsar tamayar da Gwaggo ta ke Mata,ita da idan ta gama ayyukan bautan da ya ke saka ta ta shige d'aki bata fitowa sai washe gari,bata sanin fitarsa ko dawowarsa. Turo k'ofar falon aka yi tare da sallma yana ri'ke da leda a hannunsa,amsa sallmar sukayi Gwaggo ta yiwa Inteesar alamun ta kar'bi ledar hannunsa,ba musu ta d'an durk'usa ta kar'ba dan kada Gwaggo ta ga laifinta. Fruits ne a ciki ta nufi kitchen ta wanko su ta zuba a faranti ta yayyanka su ta ajiye a dinning table,Gwaggo ne ta rik'o hannun Muhdeen zuwa dinning table,bayan sun zauna ne Inteesar ta zubawa kowanne abincin da zai ci ne suka fara ci,ita dai Bata ci na kirki ba ta mi'ke zata bar wajen, "Yar albarka ya haka ba kici abinci da yawa ba,har yanzun kina nan da rashi son abincinki?" Shagwa'be fuska ta yi Gwaggo na k'oshi." Daga nan ta koma falo ta zauna, Gwaggo kuma suka dinga fira da Muhdeen,kafin ya ce bari ya shiga ciki ya fito, Gwaggo ma falon ta dawo Inteesar ta je ta tattara kayan da suka 'bata ta gyara wajen. Falo ta dawo ta zauna suna kallon film da Gwaggo, Muhdeen ma ya zo ya zauna, Da misalin k'arfe goma na dare Inteesar ta ce, "Gwaggo barci nake ji zan je na kwanta." Kallon Muhdeen Gwaggo ta ce " A d'akin ka take kwana ne ko kuma Kai ke biyo ta d'akinta?" Shiru ya yi yana kallon Gwaggo don dai bai isa ya ce Mata kowa d'akinsa ya ke kwana ba,don haka ya ce, "Ita ce dai take bina d'aki na." Jinjina Kai Gwaggo ta yi tare da cewa "Hakan ya yi don dama na tambaya ne don nasan inda zan kwana,idan har d'akinka kuke kwana Ni sai na kwana a d'akinta idan kuwa d'akinta kuke kwana na shiga wancan d'ayan d'akin na bak'i." "Tura baki Inteesar ta yi tare da cewa "Gwaggo nikam da ke zan kwana." "Wace ni yarinya kibi mijinki ba ruwa na,in banda salon munafurci irin ta ki da kafin nazo da wa kike kwana a gidan nan?" "Ni kad'ai nake kwana" Da sauri Gwaggo ta kalli bakinta jin abunda Inteesar ke fad'a "Yar jakkar uba to ki bishi ki kwana ke dad'an." Inteesar Bata sake magana ba ta nufi d'akinta tana k'unk'uni,dariya Gwaggo ta yi tare da kallon Muhdeen ta ce, "Amma da dukkan alamu kana fama da yarinyar nan akan shimfid'a ko? alamu sun nuna haka shiyasa take gudunka,to bari na maka kada ka ce zaka raga mata ko kad'an idan ba haka ba mace raina ka zata yi." Baice mata komai ba sai kallonta da yake tana ta zuba suratai. Inteesar kuwa tana zuwa d'aki wanka ta yi ta ta shafa man Hajiya bilki da turarenta,gyara gashin kanta ta yi ta d'aure su kamar yadda ta saba ko wane dare,rigar barcinta ta shara sharan rigar barcinta ta d'auka ta saka iya guiwar ta rigar ta tsaya,gadonta ta haye tayi addur kwanciya barci ta kwanta. A can falo kuwa Gwaggo ta mik'e ta ce "Muhammadu mu kwana lafiya zanje na kwanta." Mi'kewa ta yi ya yin da yake mata sai da safe. Tana shiga d'aki ta saki baki da mamaki ganin Inteesar kwance tana barci,ranta ne ya yi masifar 'baci ta k'arasa ta yaye bargon da Inteesar ta lullu'be jikinta da shi,tare da kai mata duka a k'afarta. "Tashi 'yar jakar uba tafi d'akin mijinki." Tashi zaune Inteesar ta yi tare da cewa "Don Allah ki barni na kwanta a nan." Gwaggo ba ta ce komai ba ta janyo hannun Inteesar tana cewa "Har turaka zan raka ki yau kuma wallahi idan baki fita daga idanuna ba sai naci mutuncinki" Inteesar ganin da gaske Gwaggo ta ke zata kaita ne yasa ta ce "Don Allah Gwaggo ki barni na canza kaya." "Ba kayan da Zaki canza ko tsirara kike haka zan kai ki ai mijinki ne." "To ki barni na d'auki hijanin sallar asuba." Jin haka ne yasa Gwagho sakin hannun Inteesar ta koma ta d'auko hijabinta ta zura a jikinta,har k'asa ya sauka mata,sake jan hannunta Gwaggo ta yi suka fita sai da ta kaita har k'ofar d'akin Muhdeen sannan ta saki hannunta tare da cewa "Shiga" Bata shiga ba sai da Gwaggo ta tura k'ofar ta hankad'ata sannan ta shiga,Gwaggo ta janyo masu k'ofar ta rufe. Baya cikin d'akin ta ji karar ruwa a toilet alamun wanka ya ke, kasancewar barci ne a idonta ya sa ta kwanta a saman sofa dake d'akin, nan da nan barci ya yi awon gaba da ita ta k'udundune kanta cikin hijab. Yana fitowa toilet d'in k'amshin turarenta ne ya sa ya Kai dubansa ga wurin,ya ganta har ta fara barci, ta'be baki yayi tare da goge ruwan jikinsa singileti da gajeren wando ya saka ya fesa turare,hawa saman gadonsa ya yi ya zauna tare da d'aukar wayarsa, Sumayya ya kira bugu biyu ta d'aga tare cewa "Baby da naji shiru baka kira ni ba na d'auka ko ka yi barci ne." Murmushi ya yi tare da cewa "Ina zan iya barci banji muryarki ba,ai sai na kasa barci,ya su Mum da Dad suke?" Murmushi ta yi tare da cewa "Suna lafiya" Nan dai suka cigaba fira har tsawon mintuna arba'in, Inteesar da ke barci ta yi wani juyi sai Hijabin da ke jikinta ya tattare ya koma gefe d'aya,lokacin da idanunsa ya sauka akanta ya yi arba da kyayyawun surar jikinta mai d'aukar hankali,rigar barcin da ke jikinta shara -shara suke hatta pant d'inta da bra d'inta ana hangowa. Ido ya kafe ta dasu yana kallonta gaba d'aya tsigar jikinsa tashi suka yi cikin wani irin kasalalliyar murya a sark'e ya ya yi magana ya ce ma Sumayya "Baby zan aje waya sai da safe." Bai jira cewarta ba ya katse kiran tare da aje wayar idanunsa na Kan Inteesar,wani irin azabbaben sha'awar ta ne ke fisgarsa, Saukowa ya yi daga kan gadon,ya k'araso gare ta kwanciya yayi saman sofan shima duk da wajen ya matse su amma bai damu ba,hannunsa ya zura cikin rigarta yana shafar jikinta,mutsu mutsu ta fara yi sakamakon jin kamar ana shafa jikinta,kuma gashi tana jin iskar numfashinsa akan fuskarta,a hankali ta bud'e idanunta ganinsa ne yasa ta bud'e baki ta niyar ihu amma kafin tana bud'e baki kafin ta yi ihu ya ya kai bakinsa cikin bakinsa cikinta yana tsosan la'b'banta,ganin tak'i sakin la'b'banta ne ya sa ya saki la'b'banta ya Fara kissing d'inta a hankali zuwa wuyanta mutsu mutsun k'watar kanta take amma ta kasancewar rigar barcin mara hannu ce zame rigar ya yi zuwa k'asa,bra d'in ya 'balle ya Kai hannunsa a hankali ya shafa k'irjinta had'i da murza breast d'inta da d'an matsa su,laushi fatarta ne ya zautar da shi gaba d'aya ya fara rikicewa Wani k'arfi ne ya zo mata ta hankad'eshi ta nufi k'ofar fita. *WEEKEND BA ZANYI MAKU UPDATE BA* Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, Arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM Page4️⃣4️⃣ Wani k'arfi ne yazo mata ta hanka'deshi ta nufi k'ofar Cikin sand'a ta shiga d'akinta,maida k'ofar tayi ta rufe,a kasancewar hasken d'akin ba a kashe ya ke ba andai rage haaken ne yasa a hankali ta k'arasa wajen gadon,hayewa ta yi ta matsa can k'arshe a hankali ta ke komai da gudun kada Gwaggo ta farka,kwanciya tayi tare sa yin addu'ar barci. Ta dad'e kwance barci bai d'auke tabba tana tunanin abubuwanda Muhdeen ya mata, tura baki ta yi tare da sanya hannu ta la'b'banta lokacin da ta tuna yanda ya dinga tsotsan la'b'banta kamar ya samu sweet, ta kuma sa hannunta duka biyu da rungume a k'irjinta lolacin da ta tuna sanda ya 'balle mata bra ya dinga shafa mata k'irjinta Azuciyar ta dinga cewa Allah ya isarmun,bayan muguntar ma da alamaa ya k'ware a wajen iya iskanci,mugu kawai. Ita kad'ai ta ke maganar zucinta har barci ya d'auke ta. A 'bangarensa kuwa tunda ya ga ta fice a d'akin bai iya yuk'urin kamota ba,don gaba d'aya jikinsa ya saki kamar wanda bashida laka a jikinsa,gaba d'aya ya susuce daga ganin halittar yarinyar mai jan jankali,ko Sumayya dai da ya fara ganinta ba kaya a jikinta hankalinsa ba d'aga haka ba,ballantana ya susuce amma yarinyar nan gaba d'aya ta rikita shi,a halin yanzun ji yake ita kawai yake da buk'ata,gashi shiru baiga Gwaggo ta turo ta ba,don ya tabbatar da Gwaggo ta ganta ba abunda zai hana bata dawo masa da ita ba,amma tunda yaji ta ahiru yasan Gwaggo Bata ganta ba ta yi barci,dama tana da nauyin barci ita. Ta shi yayi ya nufi toilet,ruwa ya sakar ma kansa bayan ya gama watsa ruwan ne ya guge jikinsa ya fito,jallabiya ya saka tare da kwanciya,ya dad'e kwance barci bai d'auke sa ba,da zaran ya rufe ido ba abuda ya ke ganin sai surar jikinta. A haka dai barci ya d'auke sa,duk mararsa na d'an masa ciwo. Can cikin dare ma haka ya dinga juyi ga wani irin feeling da ke bijiro masa,gaba d'aya yarinyar ta saka shi cikin wani hali,yana zamansa lafiya Gwaggo ta je ta turo masa ita gaba d'aya ta hanasa sukuni, sha'awar yarinyar kawai ke damunsa. Sai wajen k'arfe uku ne uku da rabi ne barci 'barawo ya yi awon gaba dashi,bayan ya samu sassauci,ba shi ya farka ba sai k'arfe biyar da rabi,ganin lokacin sallah ya yi ne yasa ya tashi cikin hanzari ya ya watso ruwa tare da d'auro alwala,sharp -sharp ya shirya cikin farin jallabiya ya nufi masallaci,ko ya k'arasa masallaci an idar da raka'a d'aya. 'Bangaren Inteesar kuwa Gwaggo ce ta farka k'arfe hud'u,ganin Inteesar ne kwance tana barci yasa ta saki salati tare da kai mata duka a kafad'arta,farkawa ta yi tare da tashi zaune,kallon Gwaggo ta yi tare da cewa "Lokacin sallah ya yi ko?" Dak'uwa Gwaggo ta yiwa Inteesar ta ware yatsunta duka biyar ta nunawa Inteesar tare da cewa "Ungo naka nan,na ce ungo nan 'yar jakar uba,anya kuwa yarinyar nan kina son kanin annanbin rahama?" Tura baki ta yi tare da cew "To me kuma nayi Gwaggo?" "Uban me yasa kika gudo daga turakar mijinki?" "Gaskiya ni Gwaggo bazan sake zuwa d'akinsa ba." Kallon mamaki Gwaggo ta yi mata tare da cewa "Saboda uban me yasa ba Zaki sake zuwa ba?" "Wallahi d'an iska jarababbe ne." Duka Gwaggo takai mata a bakin ta wanda har sai da tayi saurin d'ora hannayenta akan bakin,don ta ji zafin dukan. "Kul na sake jin wannan maganar daga bakinki ." Kukan shagwa'ba ta saka tare da cewa "To nifa ba 'yar iska bace,wallahi Gwaggo baki ga abunda ya dingayi ba,ya bi ya damu mutum da tsotse-tsotse sai sunshina ni yake yi kamar d'an akuya." Salati Gwaggo ta yi tare da cewa "La lah ilallahu Muhammadur rasulullahi salallahu alaihi wasallam, yau ni kulu na ga abunda ya isheni bai ishi Allah ba,to Bari kiji abunda kike Kira iskanci shi aka kawo ki kiyi,nace iskanacin kika zo yi,kuma badi kiji wallahi indai baki fita a idona ba sai nayi maganinki,baki zuwa Islamiyya ne?ko kuma ba'a fad'a maki hakkin miji akan matarsa ba?" "An fad'a Mana." "Oho an ma fad'a maku kin sani amma kike take sani?ki gwammaci ki kwana cikin tsinuwar mala'ikun Allah?" duk tunanin Gwaggo ta d'auka cewa Inteesar da Muhdeen suna mu'amalar auratayya ne gajiya da rashin sabo ya sa Inteesar gudowa ta barshi,don haka ta cigaba da cewa "Haka Zaki dinga hak'uri da yanayin mijinki,a haka zaki saba kema ki zama jaruma irinsa ki daina gudowa nan kada nima tsinuwar taking ta shafe ni." Ba tare da ta ce komai ba ta mik'e jin zancen Gwaggo ba na k'are bane, kuma gashi har an tayar da sallah a masallaci,bata tsaya yin wanka ba ta d'auro alwala ta fito,kallonta Gwaggo tayi ta ce, "Banga kinyi wankan janaba ba,ana sallah da najasa ne?" Inteesar dai shiru ta yi bata ce komai ba, k'ok'arin d'aukar hijabinta kawai take,sai jin muryar Gwaggo ta sake ji tana cewa "To ko a can d'akin nasa kika yi wankan tsark?" Nanma bata ce komai ba,har zata tada sallah sannan ta juyo ta kalli Gwaggo ta ce "Gwaggo ki tashi fa kiyi sallah lokaci na tafiya." Daga nan ta tada sallah yayin da Gwaggo ta shiga toilet don d'oro alwala. Koda ya dawo daga masallaci d'akinsa ya koma ya kwanta ya cigaba da barcinsa. Bayan Inteesar ta gama azkar da karatun al qur'ani kamar yadda ta saba fara gyaran gidan ta yi sai dai ba kamar na wahalar da Muhdeen ya dinga sata ba,yanzun idan ta gyara falo da d'akinta da toilet sai kitchen,sai kuma falon Sumayya da d'akin Muhdeen,bayan ta kammala gyara ko Ina ne ya rage d'akin Muhdeen,tana ta tsoro da zullumin shiga d'akin tuna abunda ya mata a daren jiya gabanta ne ya shiga fad'uwa tana tsoron shiga har ta kai hannu da zummar bad'e k'ofar sai ta fasa ta juya ta nufi kitchen dan d'aura masu breakfast, Ruwan shayi ta dafa da yaji kayan k'amshi sai Dankalin turawa da plantain ta soya da k'wai,bayan ta kammala ne ta jera su dinning table sannan ta nufi d'akinta ba kowa a d'akin don Gwaggo ta dawo falo tana kallon T.V, magana ta dingayi a zuciyarta ita kad'ai tana cewa "Sai dai yau d'akinsa ya zauna hakanan ba gyara, don bazan shiga d'akin ba idan yana ciki,salon ya je yayi mani fyad'e ya cuceni tunda ba k'aunata yake ba,gara idan naje na auri mai sona nakai masa budurcina amma bazan ta'ba bari wani mugu ya rabani da shi lokaci guda ba." Haka ta yi ta surutanta ita kad'ai,wanka ta shiga bayan ta fito ne ta shafa man shawanta Mai k'amshi na wajen Hajiya Bilkisu mai gyaran Amare,riga da siket ta saka na atamfa ya zauna mata cif a jikinta inda ya k'ara bayyana kyakkyawar surar jikinta da kyawun dirinta. Wani turare da bata ta'ba amfani da shi ba ta d'auko ta shafa son turaren yana da wani sirri na musamman shiyasa ma Hajiya Bilkisu ta sanar da ita cewa idan har zata fita daga gida kada ta shafa turarenta sai dai idan tana cikin gida ne,bayan ta shafa turaren ne ta fito ta zo falo inda ta tarar da Gwaggo, "Barka da hutawa Gwaggo" "Ke ni ba wani barka wallahi,haka gidan naku yake?" "Me ya faru Gwaggo?" "Tambayar me ya faru kike 'yar albarka ?meye ma bai faru ba?to Ni ban saba da haka ba,ace mutum bazai ci abinci sassafe ba sai k'arfe goma?so kike ki kashe ni da yunwa ko?to wallahi bazan iya ba matuk'ar haka zaki dinga yi to zan kira waya a turo direba ya d'auke ni,ko a gidan Fatima koda ba zata karya da wuri ba sassafe zata kawo mani nawa har d'aki,wata rana ma kece kike kawo mani,amma daga yin aurenki zaki koyi mugun hali na barin bak'o da yunwa to kika sake mani haka zan bar gidan nan." Da sauri Inteesar ta durk'usa tana rok'on Gwaggo akan tayi hak'uri,kada ta tafi don idan ta tafi farin ciki ya k'are mata a gidan. "Tuba nake Gwaggo ki gafarceni bazan sake ba insha Allah." "To shikenan naji,yunwa nake ji kije d'akin mijinki ki Kira shi yazo muyi karin kumallo a tare." Gabanta ne ya fad'i Jin abunda Gwaggo ta ke cewa,don haka ta ce "Gwaggo kamar barci yake,mu barshi idan ya tashi sai ya ci nasa." "A'a kedai kije ki Kira shi,kawai." Ba yadda ta iya ranta baiso ba ta nufi d'akinsa,tura k'ofar ta yi tare da sallama,kwance ya ke kan gado idanunsa a lumshe kamar mai barci amma ba barcin yake ba,ganin kamar yana barci yasa ta k'araso d'akin cikin sand'a, waige-waige ta dingayi tana tunanin ina ya ajiye mata wayarta da amshe a hannunta. Shi kuma tunda ta shigo k'amshin turaren Hajiya Bilkisu ya fara aiki,don turaren na musamman ne mai d'auke da wani sirri wanda idan mace ta shafa turaren namiji ya shak'a kamshinsa sai shauk'i ya kamashi,to kuwa tunda Muhdeen ya ji k'amshin turaren nan gaba d'aya ya rasa nutsuwarsa ji yake kamar ya rungumeta Rasa ina ya aje wayar ta yi har ta nufi closet zata duba sai ta fasa duk yana kallonta, side drawer ta duba takaddu ne kawai zagayawa ta yi d'aya 'bangaren da ta janyo side drawer na jikin gado na sama kasancewar tayi kusa da shi sosai k'amshin turaren ya k'ara hautsina shi, sunkuyawar da tayi ne ya fincikota ta fad'o jikinsa,had'a ta yayi da k'irjinsa ya fara kissing nata ta ko ina,jikinsa sai rawa suke idanunsa sun fara janaza kala zuwa ja tun tana k'ok'arin k'watar kanta har ta kasa don abun nasa na yau yafi na jiya yamutse ta ya dingayi ta ko ina kuma son ransa a haka suka kwashe mintuna talatin,ganin yana neman wuce gona da iri ne kuma ta kasa k'watar kanta don bai bata wannan damar ba yasa ta sakar masa kuka,sakinta ta yi tare da maida numfashi,gashin kanta duk sun yamutse,d'an kwalinta ta d'auka ta nufi hanyar fita har ta kai bakin k'ofa ta tsaya ta goge hawayenta sannan ta jiyo ta kalleshi tare da harararsa ta ce "Wallahi sai Allah ya saka mani abunda ka yi Mani." Mi'kewa taga ya yi ta fita a guje,dariya ya yi tare da cewa "matsoraciya ai da kin tsaya" Fita shima ya yi don bai gaisa da Gwaggo ba. Gwaggo na zaune a falo ta had'a tagumi daga cewa Inteesar ta kira Muhdeen shikenan ba ita ba shi fiye da rabin awa, Inteesar gaba d'aya kunya ce ta kamata ganin yadda duk kayan jikinta suka yamutse haka ma gashin kanta,ba yadda za'ayi ta shiga d'akinta ba tare da Gwaggo ta ganta ba,kuma ita gaskiya tana jin kunyar Gwaggo ta ganta a haka don sai ta zargi want abu, tsaye ta yi a jikin k'ofar da zata sada ta da falonta inda Gwaggon ta ke,ji ta yi kawai an rik'e hannunta ana janta zuwa falon,juyawa tayi da sauri ta kalle shi,kafin ta yi magana ne har ya janyota sun shigo falon,ido Gwaggo ta zuba masu daga shi har ita,kallo d'aya ta ma Inteesar ta fahimci komai don haka kauda kanta kawai ta yi kunya duk ya ishi Inteesar amma shikam ko a jikinsa,gaida Gwaggo ta yi tare da cewa "Ina kwana Gwaggo?" "Ina wuni zaka ce mani ba ina kwana ba,k'arfe nawa yanzun ku shige d'aki kaida matarka Kuna ta jarabarka a d'aki kun banzatar dani ko?kuma kafi kowa sanin cewa bana iya zama da yunwa ciwona zai tashi ko." Kallon Gwaggon ya yi ya kalli Inteesar ya ce "Gwaggo dama bakiyi breakfast ba?" "Lokacin da na tura matarka ta kira mani kai bata fad'a maka ba?" "A'a Gwaggo bata fad'a mani ba" Kallon Inteesar Gwaggo ta yi tare da cewa "To da na aike ki baki fad'a ba ko?kika rik'e shi a d'aki kika k'i fad'a masa ko?ke ga jarababbiya uwar son miji,kinje kinyi muk'us a d'aki kin samu abunda kike so ni yunwa ta kase ni ko?indai ke buk'atarki ta biya ni ko oho ko?'yar yarinya dake sai jaraba,to ba sai ki mani Kora da hali ba kinbarni da yunwa ba tafiya ta zanyi kuje can ku k'arata *KUYI HAKURI DA WANNAN* Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, Idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page 4️⃣5️⃣ "'yar yarinya dake sai jaraba,to ba sai kin mani kora da hali kin barni da yunwa ba,tafiya ta zanyi kuje can ku k'arata." Tsabar takaici yasa Inteesar sakin kuka ta fad'a jikin Gwaggo ta kasa magana sai kuka kawai take, rik'e ta Gwaggo tayi ta rungumeta tana cewa "To me aka maki na kuka tsabar sangarta ne ko kuma me?dan na fad'i gaskiya shine zaki saka ni gaba kina mani kuka haba 'yar albarka me kuma zaki zauna kina ma kuka?ya isa hakanan." Ta k'arasa maganar tana shafa bayanta alamaun rarrashi. "Bana son kukanki wallahi ki daina mana kada ki tayar mani da gankali." 'Dagowa ta yi tare da goge hawayenta ta ce, "To kada ki tafi ki zauna da ni,idan kika tafi nima bazan zauna a gidan nan ba." Kallonta kawai Gwaggo ta yi tare janyeta daga jikinta,ta shi tayi ta janyo hannun Inteesar ta mik'ar da ita tsaye. "Taso muje mu ci abinci." Binta ta yi ba tare da ta ce komai ba,shima bayansu ya bi yana kallon ikon Allah daga magana sai kuka. Kwanci ta shi ba a wurin Allah,a haka har Gwaggo ta cika sati biyu a cikin gidan,kullun tana mak'ale jikin Gwaggo,shi kuma Muhdeen na zuwa Asibiti idan ya tafi da safe sai yamma ya ke dawowa,wani lokacin yakan je gidansu ya gaida Mummy da Dady,Mufida ma ta zo da k'awayensu Saliha da wasila sunzo gidan Inteesar,har ya wannan lokacin Muhdeen bai ba Inteesar wayarta ta ba. Kwance take a saman cinyar Gwaggo suna fira, Mufida ce ta shigo. "Assalamu alaikum" Mi'kewa Inteesar ta yi da fara'arta ta rungume Mufida, Mufida ce ta gaida Gwaggo sannan ta juya ta kalli Inteesar ta ce, "Wai me ya samu wayarki ne?" Ta'be baki Inteesar ta yi tare da cewa "Ba abunda ya same ta" "Mummy na ta kiranki bata shiga, the same thing." "Waya ta tana wajen yaya." Kallon mamaki tayi Mata "Me wayarki yake yi a wajensa?" "Kar'bewa yayi wai bazai bani ba." "Me ya faru haka da zafi da zai kar'be maki waya?" Shiru Inteesar tayi tana nazari don bata jin zata iya sanar da kowa halin zaman da suke yi da Muhdeen,duk da cewar Mufida k'awarta ce amma ai kuma k'anwa ce a gurin Muhdeen,don haka ta ce, "Mubaar maganar kawai" "Me kuma kike 'boye mani Inteesar?mufa aminan juna ne bana 'boye maki komai kema baki 'boye mani,amma tunda kika yi aure kika fara mani 'boye-'boye." Dariya ta yi tare da kallon Mufida. "To ai kema kinsani akwai Banbanci tsakanin matar aure da wacce ba matar aure,kuma ai duk mace ta gari bata fitar da sirrin gidanta." Ta'be baki Mufida ta yi tare da cewa "To mace ta gari,idan miji na gari na ciki kije ki sanar da shi Mahaifiyar k'awarki Wasila ta rasu." Dafe k'irji Inteesar tayi tare de cewa "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,Yaushe ta rasu?" "Jiya" Salatin Inteesar ne yasa hankalin Gwaggo ta dawo gare su,don ta yi nisa waje kallon T.V "Allah sarki Allah ya jik'anta da rahama." Gaba d'ayansu suka amsa, Mufida ce ta kalli Gwaggo ta ce "Dama can gidan rasuwar zanje,na kira Inteesar a waya na sanar da ita amma ban same ta ba,shine na ce bari na biyo ko zata samu zuwa." Kallonta Gwaggo tayi tare da cewa "Gashi mijinki baya gidan bare ki nemi izininsa ki bita ku tafi." Marairaice fuska tayi "Gwaggo ki barni na tafi idan ya dawo sai a sanar dashi." Girgiza kai Gwaggo tayi tare da cewa "Ba nice na ajiye ki ba,ba kuma zama na kike ba,saboda haka ki kirashi a waya ki nemi izininsa,idan ya amince sai ku tafi." Shiru Inteesar ta yi tana tunanin ta ina ma zata fara,dan ita ko kashe ta ma za'ayi bata san lamabar wayarsa ba,Mufida ce ta ce, "Yauwa bari na kira maki shi da waya ta,idan ya barki sai muntafi." Murmushi kawai ta yi a zuciyarta tana addu'ar Allah yasa ya amince ya barta. Mufida ce ta lalubo lambar wayarsa ta kira amma switch off,sau biyar Mufida na kiransa amma the same thing,kallon Inteesar ta yi tare da cewa "Duka lombobinsa fa a kashe,basa shika Wallahi." Dafe kai Inteesar ta yi tare da cewa "To yanzun meye mafita?" "Bari to na gwada kiran layin yaya Jabeer nasan dukkansu yanzun suna Asibiti dukkansu." Lamabar Jabeer ta lalubo ta danna masa kira. Jabeer dake zaune a office d'insa yana duba patient,wayarsa ce take ruri bai kula ba har ta katse,sai da aka sake kira ne ya d'aga tare da cewa "Mufida ya akayi ne ya mutanen gidan?" "Yaya Jabeer dama layin yaya Muhdeen ne a kashe,kuma Inteesar ke son magana da shi." "Okay lafiya dai ko?don ya shiga tiyata ne yanzu." Kai ta jinjina " Okya ba damuwa Allah ya bada sa'ar aiki,idan ya fito ka sanar da shi." "Insha Allah zan sanar da shi." Daga nan ya katse kiran ya cigaba da abinda ya keyi. Bayan sun gama magana ne Mufida ta juya ta kalli Inteesar ta ce, "Gaskiya zan tafi,don mijinki yana d'akin tiyata ,idan ya fito na ce yaya Jabeer ya sanar dashi kinga may be ya kira lambar Gwaggo ya ji dalilin kiransa,yanzun kinsan wayar Gwaggo kinsan bata ajiye waya fili sai cikin kaya ayi ta kira bata sani ba,kinga idan ya Kira sai ki sanar dashi idan ya barki kindai san gidan sai mu had'u a can, amma fa ba dad'ewa zanyi ba zan tafi kitso." Daga nan ta mik'e tare da musu sallama ta tafi. Baya awa biyu ne sai ga wayar Gwaggo ta fara ringing,dubawa tayi tare da d'aga kaiwa a kunne. "Assalamu Alaikum" Muhdeen da ke zaune a office d'insa ya fara magana "Barka da gida Gwaggo." Washe baki tayi tare da cewa "Muhammadu ya aiki?" "Alhamdulillah,naji ance kuna nema na ne." "Eh matarka ce wai mahaifiyar k'awarta Allah ya mata rasuwa,shine Mufida ta biyo mata su tafi tare." Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Allah ya jik'anta,ina ita Mufida take?" "A'a itakam Mufida kam ina zata tsaya jiran matarka,kai da aka ce kana can kana farke cikin cikin mutane ne zata tsaya jiranta?" "Mufida ta tafi kenan?" "Eh sai dai ita matar taka ce ake jiran ka fito ka bata izini ta tafi." "To ban bada izinin ba." "Ban gane baka bata izini ba,gaisuwar mutuwa ce fa zata." "Gwaggo ta tsaya tayi masu addu'a a gida,ita k'awar kuma ta kira ta a waya tayi mata ta'aziyya." Girgiza kai Gwaggo tayi kamar yana ganinta ta ce, "Haba Muhammadu, Mahaifiyar k'awarta aka ce ta rasu,kuma k'awa ce ta sosai ko lokacin bikinku ta yi k'ok'ari har nan gidan ma ta zo sannan sai ka hanata zuwa?bai kamata ba." Shiru yayi na d'an lokaci kafin ya ce "Shikenan ta sanar da Ishaq Direba ya kaita tayi ta'aziyya ya dawo da ita." "Yauwa da'n albarka,Allah ya dawo mani da Kai lafiya." "Ameen ya Allah" Daga nan ta katse kiran ta kalli Inteesar ta ce "Ina fatan kinji duk maganar da mukayi." Kai ta jinjina lamar eh,sannan ta ce "Nagode Gwaggo bari na d'auko hijabi na na kira Ishaq mu tafi." "Amma fa kar ki dad'e" "Insha Allah Gwaggo bazan dad'e ba." Daga nan ta shiga d'akinta,ba jimawa ta fito rik'e da hijabinta tana sakawa,ta rik'e handbag d'inta ta fice. A harabar gidan da k'ara ta ke tambayar mai gadi ko ina Ishaq,inda mai gadin ya shaida mata cewa yanzun nan aka kirasa a waya 'yarsa ba lafiya shine ya tafi gidan Jin hakan yasa ta ce da mai gadin Allah ya bata lafiya,daga nan ta fita zuwa bakin titi ta tsaida mai keke napep ta shiga zuwa gidansu wasila. Har k'ofar gidansu Wasila mai adaidata sahun ya ajiye ta,bayan ta shiga ne ta gaida mutanen sa ke cikin gidan tayi masu ta'aziya sannan ta nufi falon gidan nan ma cike yake da mata masu kar'bar gaisuwa,bayan ta gaishe su tare da masu ta'aziyya ne ta nufi d'akin Wasila,nan ta samu K'awayensu wad'anda suka gama school tare dasu a d'akin,nan dai suka gaisa ta tayiwa Wasila ta'aziyya da addu'o'i,zama tayi suka cigaba da kar'bar gaisuwa. Suna nan har aka kira sallar la'asar,nan wasu suka dinga tashi dan gabatar da sallah,dama koda Inteesar bata ga Mufida a gidan ba batayi mamaki ba dan dama Mufida ta ce ba zata dad'e ba zata tari wajen kitso ne. Bayan ta idar da sallah ne tayi masu sallama dan tafiya gida, kasancewar akwai d'an tazara zuwa bakin titi yasa ta fara tafiya dan neman abun hawa. Wata jar mota ce ta tsaya a gabanta tare da yi mata horn,ko kallon motar ba tayi ba ballantana tasa waye a ciki,tafiya ta cigaba da yi shima matuk'in motar ya dinga binta a hankali yana danna horn,ganin abin nasa ne taga yayi yawa yasa ta juya ta kalli motar,ba kowa bane illa Usman sai murmushi ya ke sakar mata,da mamaki ta kalle shi tare da furta sunansa "Usman" Zaune yake a mazaunin Direba yayin da k'anwasa Khadija ke zaune a gefensa,itama murmushi ta sakarwa Inteesar tare da cewa "Lallai yaya na yayi gaskiya,muna cikin tafiya ya hangoki ya ke sanar dani cewa kece nace ya za'ayi ya sani tunda baiga fuskarki ba?ya ce to bari mu k'arasa na tabbatar,ashe kuwa kece." Murmushi Inteesar ta sakar mata tare da cewa "Nice Khadija da ace ba tare da Usman na ganki ba wallahi bazan gane ki ba." "Saboda kinsan had'uwa ta dake lokacin da na samu accident ne ina asibiti,tun lokacin bamu sake had'uwa ba." "Ni kuma duk inda na ganki zan gane ki,saboda pics d'inki da ke wayar yaya na." Da mamaki Inteesar ta kalli Usma "Ina ka samu pics d'ina awai wad'anda na d'auke ki a asibiti ba tare da saninki ba da wad'anda na d'auke ki a k'ofar gidanku ranar da na je akan magani zan Kai maki." Jinjina kai Inteesar ta yi ba tare da ta ce komai ba,jin muryarsa ta yi yana cewa "Daga ina zuwa Ina?" "Daga gidan rasuwa zuwa gida" "To ki shigo nan gaba kad'an zan aje Khadija sai na k'arasa dake gida." Kai ta girgiza alamun a'a "Ka barshi kawai zan shiga adaidata sahu." Nan dai suka matsa mata akan cewa sai ta shiga,dakyar ta amince ta shiga,tafiyar mintuna biyar ya ajiye Khadija a wani shagon saloon inda ya umarci Inteesar ta dawo gaban motar,dan haka ta dawo gaban motar sannan yaja suka tafi. "Me yasa kullun na kira wayarki bata shiga,tun ranar da muna cikin magana kika katse kiran ban sake samumki ba." Tasao ta sanar da shi ita matar aure ne a yanzun amma kuma wannan ai ba aure bane,tunda da zarar matarsa ta dawo zai sake ta,don haka ta yi shiru ta ce "Bana da waya ne." "Okay badamuwa mun kusa k'arasawa Ubasanjo complex sai mu shiga ki za'bi kalar wayar da kike so." Da sauri ta kalle shi "Dan Allah ka rufa mani asiri,yanzun idan ka siye mani waya me zance idan na koma gida?" Dariya ya yi "Kedai akwai matsoraciya to meye a ciki?nifa so nake su san da ni fa,duk da sun sanni amma ina son susan cewa aurenki nake so." "Naji amma duk da haka ba yanzun ba,kaga yamma ta yi ina sauri na koma gida." Dariya yayi yare da cewa "Kinfi son ki zauna kurma ko?" Da mamaki ta kalle shi "Kamar ya kurma?" "Eh mana ai duk mutumin da bashida waya kurma ne." Dariya ya bata sosai har saida dimful d'inta suka lotsa fararen hak'oranta suka bayyana. Muhdeen dake tsaye daga tsallakensu gaban access bank yana magana da wani,kamar ance ya juyo kwatsam idanunsa suka sauka kan Inteesar da Usman,tana zaune a gaban motarsa sai dariya take masa harda hak'oranta,want abu ne yaki kamar mashi ya soki zuciyrsa,tunda ya ke bata ta'ba masa dariya ba ko da ita da Gwaggo take dariya da ta ganshi zata had'iye dariyar,amma gata zaune gaban motar wani k'ato tana masa dariya,ransa yakai k'ololuwar 'baci,garan gadan ya nufi tsallakowa titin cikin zafin rai da k'unar zuciya. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll 😘😍 Comment &,shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa. *JINJINA* Jinjina ta musamman gare ku masoya na, na yaba kuma nagode da addu'ar da kuke mani Allah yabarmu a tare nayi wannan shafin tukuici ga masoya na na group d'in *INTEESAR HAUSA NOVEL* ina jin dad'in comment da addu'o'i da kuke mani i love you lodi-lodi. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page4️⃣6️⃣ Ransa yakai k'ololuwar 'baci gadan gadan ya nufi tsallakowa titin cikin zafin rai da k'unar zuciya,cikin rashin sa'a ga cunkoson ababen hawa sunyi yawa, kasancewar yamma ne kowa na kiciniyar komawa gida. Kamar ance ta kalli gefenta can ta hangoshi duskarnan tasa a murtuk'e,kuma idonsa na kanta,gaban ta ne ya fad'i dan har sai da hanjin cikinta suka kad'a, cikin tashin hankali ta dubi Usman ta ce, "Dan Allah mubar wajennan yanzun nan" Da mamaki ya kalleta "Lafiya?" "Ba lafiya kaidai mubar nan yanzun nan" Cikin sauri ya tara motar suna barin wajen sai ga Muhdeen ya tsallako,kad'an ya rage bai same su ba,cizon yatsarsa yayi cikin takaici da k'unar,don da ya same ta baisan iya abunda zai mata b. Komawa yayi wajen mutumin da suke magana ya kallesa ya ce, "Kaga zamu yi magana a waya." Bai jira cewarsa ba kawai ya shiga motarsa ya tafi,mutumin na masa magana yana tamabayarsa ko lafiya amma ina bai saurare shi ba ya ja motar ya yi tafiyrsa. Inteesar suna tafiya akan titi sai azalzalar Usman take kan yayi sauri,da taga yabi hanyar gidansu ta ce a'a ba gida zata ba,tayi masa kwatancen inda zai kaita. "Wai lafiyarki kuwa duk kinbi kin fita hayyacinki wa kika gani ne." Bata ce komai ba duk da cewar tana dai jinsa ne amma hankalinta baya jikinta. "To yanzun gidan da zan kaiki gidan waye?" "Gidan yaya na ne." Suna isa k'ofar gidan,ko sallama bata tsaya sunyi ba ta fita,da sauri ta tura gate d'in gidan ta shiga, murmushi kawai ya yana kallonta har ta shige sannan ya juya akalar motar yabar k'ofar gidan ba tare da sanin me ya tsoratata ba. Tana tura gate d'in gidan mai gadin da mai baiwa fulawowi ruwa suna gaishe ta ma bata ji ba,da mamaki suke kallonta ganin yanayin da ta shigo. Ita kuma idan ta tuna yadda ya murtuk'e fuska ne da wahalarsa da tasha a baya musamman idan ta tuna zafin marukan da ya ta'ba mata kafin suyi aure ne ya ke k'ara saka mata tsoronsa. Dai-dai kwanar shiga layin gidan Usman na fita yayi gabas,sannan Muhdeen ya fito ta yamma,basu had'u ba. Da sallama ta shiga cikin falon,ganinta a firgice yasa Gwaggo mi'kewa tare da fad'in "Lafiya kamar wacce aka jefo?" "Lafiya lau Gwaggo." Girgiza kai Gwaggo ta yi tare da cewa "To me ya firgita ki ne?" Shiru ta yi tana tunanin ta ina ma zata fara "Dama dama lokacin da zan tafi gidan rasuwar ne Ishaq Direba naje ya kaini aka ce baya nan 'yarsa ce ko matarsa ce ba lafiya na manta,shine naje na hau ada..." Bata kai K'arshen zancen ta ba ganin yadda ka turo k'ofa da k'arfi,ganinsa ne kuma ita ya ke kallo tare da nufo inda take yasa ta daka wani tsalle aguje ta shige d'akinta ta murza key,tura k'ofara ya yi yaji ta a ride "Idan baki bud'e k'ofar nan kin fito kin sanar da ni gidan ubanwa kika je da kuma wanda na ganki gaban motarsa wallahi sai kin tausayawa kanki." Haka ya dinga dukan k'ofar kamar zai 'balle ta, Gwaggo ce ta k'araso wajen ta ke tamabayarsa. "Kai Muhammadu lafiyar ka kuwa?kodai ka fara shaye -shaye ne ban sani ba?" Maganar da tayi masa ne ya basa takaici don haka ya bar wajen ya nufi d'akinsa,don yaga alamar matuk'ar ta tsaya wajen Gwaggo zata iya sawa ya aikata abunda ba shi kenan ba, musamman idan aka ce akan Inteesar ce to fa zata iya 'batawa da koma waye akanta. Kai tsaye d'akinsa ya nufa,zaciyarsa sai zugi yake masa zama yayi yana tunani,to waye wannan da take zaune a gaban motarsa,sai faman sakin murmushi da dariya take masa da alama taji dad'in kasancewarta da shi,zama ya yi yama nazari ina yasan fuskar wannan Mutumin?don Kan gaskiya ya ta'ba ganinsa a wani wurin,duk da dai yanzun bazai iya tuna inda ya gansa ko ya ta'ba saninsa ba,take sai ya tuno da Usman tabbas shi ya gani a k'ofar gidansu Inteesar suna fira,washe garin da aka sallamota daga Asibiti bayan Mummy da Gwaggo sun saka shi gaba kan tunda baije asibiti dubota ba yaje gidansu,zuwan da yayi ne yaganta tsaye jikin motar Usman shi da ita. Zuciyarsa ce ta fara tafarfasa wato saurayinta taje wajensa kenan?tayi k'aryar zuwa ta'aziyya yayinda ta tafi wajen saurayinta,bayan ya ce ta nemi Ishaq ya kaita ya dawo da ita amma tak'i amincewa da ya kaita, toilet ya shiga don watsa ruwa. Inteesar kuwa da taji alamar tafiyar Muhdeen ta kuma ji muryar Gwaggo ne yasa ta bud'e k'ofar,kallonta Gwaggo ta yi tare da cewa "Me ke faruwa?" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bawa Gwaggo labarin komai,tun zuwanta kiran Ishaq Direba baya nan har yadda ta had'u da Usaman da Khadija suka matsa ta shiga motar har dawowarsu gida bata 'boye mata komai ba. "To naji me yasa da Direban baya nan baki baki dawo kin sanar da mijinki ba?" Shiru tayi tare da cewa "Bakomai Gwaggo naga yana da uzuri kuma ba lallai ya dawo a lokacin ba shiyasa na tafi,kuma wallahi Khadija ta matsa kan na shigo shiyasa na shiga motar." Zuba Mata ido Gwaggo ta yi tare da tuna yadda Muhdeen ya bi ya damu da bak'in ciki ta shiga motar wani, murmushi ta sake a zuciyarta tana cewa kenan ya fara sonta ne tunda har yake kishinta murmushi ta yi tare da hamdala a zuciyarta. Daga nan suka nufi kitchen tare dan d'ora abincin dare . Daga can d'akinsa kuwa bayan ya fito wanka ya shirya ne wayarsa ta fara ruri,d'auka yayi tare da sallama,maimako a amsa sallamar sai jin kukanta yayi a cikin dodon kunnensa. "Haba my baby me kuma ya faru daga kiran waya sai kuka." "Haba tambaya ta ma kake?ya zun yaushe rabon da muyi waya?da kullun safiya sai ka kirani idan ka tashi daga barci amma yanzun shiru,kamar ma ka mance da ni ko?" Ta k'ara sautin kulanta lokacin da takai k'arshen zancen,Wanda har Mum d'inta sai da ta shigo d'akin da sauri Jin kukan Sumayya,bayan shigwarta ne taga waya take da Muhdeen yasa taja tsuki ta fita,don lamarin Sumayya yanzun takaici yake bata. "Kinga dain kukar nan haka please,ta yaya za'a ce na manta dake?ai idan na manta ki to nima zan iya mance kaina kenan." Tsagaita kukan tayi ta ce, "To kwana nawa kenan baka kira ni ba? sai dai ni na Kira ka kuma yadda muke dad'ewa muyi fira yanzun mun daina da mun fara zaka nuna gajiyawarka da ni wallahi hak'uri na ya fara k'arewa,wai yaushe wannan zaman nawa ya k'are?" "Ya kusa saura sati biyi fah ba nisa mai Happiness." "Kai a wajenka ne da nisa amma Ni waje na kmar nan da 2 years nake gani,ji nake kamar na janyo ranar tazo yau." Murmushi yayi tare da cewa "Ba zaki gane bane wallahi da kinsan halin da nake ciki na rashinki da kin tausaya mani wallahi,hak'urin zaman nake Dan ba yadda zanyi ne amma wallahi I missed you so much." Sun jima suna fira kafin suka yi sallama Da misalin k'arfe sha d'aya na dare ne Inteesar tana zaune akan gadonta, Gwaggo na falo tana kallon T.V shi kuma Muhdeen na d'akinsa,tunani take yanzun idan ta kwanta nan Gwaggo na zuwa zata tayar da ita sai taje d'akin Muhdeen dole,ita kuma tsoron zuwa take saboda laifin da tayi masa,tun lokacin da ya dawo ta shige d'akinta ta rufe ya buga bata bud'e ba,tun lokacin bata yarda ta had'u dashi ba sai a dinning table,kuma ta lura da irin kallon da yake mata,alamun yau idan kika shiga hannuna mai k'watarki sai Allah,tasan sarai bazai kyaleta ba yadda yadda taga ransa ya 'baci,bata gama tunaninba sai ga Gwaggo ta shigo da sallama "Ke 'yar albarka me kike har yanzun baki tafi ba?" "Wallahi Gwaggo tsoro nake ji." Bata kI K'arshen maganar ba Gwaggo ta ce "Sai da fafe Allah tashemu lafiya." Gabnta na tsananta fad'uwa saboda tsoro,haka ta nufi bakin k'ofar tare da tunani da zullumin abunda zai biyo baya. *KUYI HAK'URI DA WANNA WAYA TA CE TA SAMU MATSALA* Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Manan ihsa) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by ✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ki hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa. *JINJINA* Jinjina ta musamman gare ku masoya na,na yaba kuma nagode da addu'ar da kuke mani Allah yabarmu a tare nayi wannan sharin tukuici ga masoyana na group d'in *INTEESAR* *HAUSA* *NOVEL* *GROUP* Ina jin dad'in comment da addu'o'i da kuke mani I love you lodi-lodi. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page4️⃣7️⃣ ___________Gabanta ne ya tsananta fad'uwa saboda tsoro, haka ta nufi bakin k'ofar tare da tunani da zullumin abunda zai biyo baya. Tsaye tayi a falon kusan mintuna goma, ta rasa yadda zatayi, zuwa can sai ta tuna da d'aya daga cikin d'akunan dake nan cikin falonta, wato d'akin da aka gyara shima aka zuba mata furnitures komai na d'aki, don haka ciki ta shiga tayi kwanciyarta bisa godon bayan ta karkad'e gadon. Shi kuma Yana can d'akinsa ya gama shirinsa na kwanciya barci, zama yayi Yana jiran shigowarta don yasan tabbas Gwaggo ba zata barta ta kwana a can ba sai ta turo masa ita, sanin hakan ne yasa ya zauna zaman jiranta. Ganin har k'arfe goma sha biyun dare shiru ne yasa ya fara tunanin anya lafiya kuwa har yanzun bata shigo ba, mi'kewa yayi ya don shi a tunaninsa kila Gwaggo tana falo barci ya d'auketa ne bata san Inteesar na d'aki ba. Yana zuwa falo yaga ba kowa don haka ya nufi dakin, ganin alamar cewa hasken d'akin a kashe yake alamun sunyi barci, tambayar kansa yayi mene ne dalilin da yasa Gwaggo zata barta ta kwana da ita?gaskiya bata kyauta masa ba haka nan ransa ba dad'i ya koma d'akinsa ya kwanta, duk da cewar ta 'bata masa rai amma hakan bai hana shi jin kewarta ba, ko ba komai yana jin motsin mutum a cikin d'akin. Kwance take a d'akinta tana danne-danne a waya, Jabeer ne ya fito daga bedroom da alama wanka yayi, kallonsa tayi tare da cewa "Ya maganar da mukayi da kai ne na cewa gobe zaka kaini gidan Muhdeen." Murmushi yayi tare da cewa "Maryam kenan ki bari sai wani jik'on, don gobe da sassafe zanbar gidan nan." "Nifa na kula da kai kamar baka son zuwa ka kaini, sau biyu ina maka magana kana kawo mani uzuri." "Ba haka bane duk lokacin da nake da uzuri shine kike magana." "Ina son ne na tabbatar da gaskiyar abunda naji." Kallon mamaki ya mata sannan ya ce, "Me kike son ki tabbatar a gidan nasa?" Murmushi tayi "Naji ance budurwarka ya aura?" Nuna k'irjinsa yayi da yatsarsa manuniya "Ni kuma?waye ya ce maki budurwa ta ce Inteesar?" "Ba wanda ya fad'a mani,amma ni nasan abunda nakeyi." "To hasashenki ba gaskiya bane ban ta'ba soyayya da Inteesar ba." Dariya tayi "Ko da ace baka ta'ba soyayya da ita ba ni nasan kana sonta,na kalli yadda ka dinga rawan jiki da ita likacin auren Muhdeen na farko,sannan lokacin da ka kawota gidan nan kuka siyo mani agwaluma naga tsantsar soyayyarta a cikin idanunka da irin kallon da kake mata,bayan haka nasaha kamaka kana kallon photonta lokuta da dama,sannan ranar da Muhdeen ke sanar da kai cewa Inteesar aka aura masa bayan dawowarka gida naga yanayinka ya canza sosai ka shiga damuwa da yawan tunani." Shiru yayi yana sauraranta, don yasa duk abinda ta fad'a gaskiya ne, don haka daga nan bai sake cewa komai ba do baida ta cewa yanzun sai ta samu abun fad'a,don haka ya share ta kamar baiji maganar da take fad'a ba. "Kuma nikam gaskiya naji dad'in auren Inteesar da Muhdeen,domin kuwa ko ba komai hankali na ya kwanta,don gaskiya tunda na fahimci cewa kana sonta hankili na ya tashi miatuk'a ban dai nuna maka bane, amma lokacin da naji labarin abokinka kuma d'an uwa a gare ka ne ya aureta sai hankali na ya kwanta. Ta k'arasa maganar tana dariya,ido ya zuba mata yana nazari,tabbas abunda ta fad'a gaskiya ne shima ya san da haka. "Allah ya kaimu goben zan kaiki." Murmushi tayi tare da cewa "Ameen ya rabbi" Da misalin 'karfe biyar na yamma ne ta farka daga barcin da tayi, toilet ta shiga ta d'auro alwala hijabin da ke jikinta ne tasa taji k'arar k'ofar gate alamun an bu'de za'a fita,matsawa tayi kusa da window ta d'an zuge labaulen window ta lek'a,hangosa tayi sanye da farar jallabiya ya fita zuwa masallaci,a zuciyarta ta ce "Nikan nan na samu wurin kwana har Gwaggo ta wuce sannan na koma d'aki na." Matsawa tayi ta shinfid'a sallaya ta tayar da sallah. Gwaggo ma haka ne daga 'bangaren ta sallah take,don ita a zatonta Inteesar na can d'akin Muhdeen kamar yadda ta tura ta. Da misalin k'arfe shida na safe ne ta fito daga d'akin ta nufi d'akinta,da sallamata a bakinta ta shiga, Gwaggo na kwance akan gado bayan ta amsa sallamar, Inteesar ce ta k'araso cikin d'akin ta durk'usa ta ce, "Gwaggo ina kwanana?" "Lafiya lumui 'yar albarka kin tashi lafiya?" "Lafiya qalau Gwaggo." "To ya kwanan mijin naki?" "Yana lafiya lau" Kai Gwaggo ta jinjina tare da cewa "Masha Allahu,Allah yayi maku albarka ya azurta ku da samum yara masu albarka." Tura baki Inteesar tayi tare da cewa a cikin zuciyarta "Ya dai azurtashi da matarsa Sumayya."mi'kewa tayi don fara aikace -aikacen gidan kamar yadda ta Saba kowace rana Bayan ta gama komai ne amma bata gyara masa d'aiksa ba,don tasan yana ciki,kuma ba zata iya shiga yana ciki ba don tasan kila har yau bai huce ba. Kitchen ta nufa don ta girka masu breakfast. Bayan ta gama had'a breakfast d'in ne inda ta dama kunun gyad'a sannan ta soya k'osai,sai Indomie da ta dafa yare da dafaffen k'wai. Fitowa yayi daga cikin d'akinsa ya nufi d'akinta don zuwa gaida Gwaggo,da sallama ya tare da tura k'ofar ya shiga, Gwaggo dake kwance ne ta mik'e ta zauna tare da amsa sallama r "Barka da safiya Gwaggo" "Yauwa barka dai ya kwanan iyali?" Shiru yayi yana kallonta don shi dai kam baima sakasa a idonsa ba ballantana yasan ya ta kwana.yana son ya ma Gwaggo tamabaya shin ya akayi ne tabar Inteesar ta kwana tare da ita,bayan yasan cewa bata ta'ba barin ta kwana amma yau ta barta,sai dai yabar zancen kan cewa kila Gwaggo tabarta ne ta kwana tare da ita saboda ganin yadda ransa ya 'baci har yana Shirin dukanta ne yasa ta barta,don bata son abunda zai 'bata mata rai. Daga nan sai ga Inteesar ta gama ayyukan da zata yi ta shigo,ido ya zuba mata ganin da fara'arta ta shigo amma tana kallonsa sai ta had'e fuska,kamar wacce bata ta'ba dariya ba a rayuwarta,tuna yadda yadda ganta a cikin mota da Usman tana ta masa dariya sosai,amma shi da ta gansa zata had'e fuska kamar taga mala'ikar d'aukar rai, jinjina kai yayi tare da maganar zuci tabbas sai yayi maganin yarinyar nan,badai tana tak'ama da Gwaggo bane nan zata tafi ta barshi da ita sai yayi maganinta. "Gwaggo ga breakfast can a dinning table na kammala." Jinjina kai Gwaggo tayi "To 'yar albarka sannu da aiki." Murmushi kawai tayi ta ce "Yauwa Gwaggo" "To kundai san bana da juriyar yunwa,to don haka ku muje muci da wuri ." "Ta'be baki Inteesar tayi tare da cewa "Gwaggo don Allah kuje ku fara ci,ni sai nayi wanka zanci kuma ba na Jin yunwa " "Ke kenan kowane rana sai anyi da gaske kafin kici abinci?to kiyi sauri zamuje mu fara cin abincin ki tabbatar kafin nabar wajen cin abincin ki kinzo." Kai ta jinjina Mata "To Gwaggo" Hannun Muhdeen taja suka fita daga d'akin,dagan Inteesar ta shiga wanka Daga Gwaggo har Muhdeen ba Wanda yaci Indomie, dukkansu kunun gyad'a da k'osai suka ci, Muhdeen ne ya kalli Gwaggo ya ce, "Yanzun Gwaggo sai ki dinga nuna mani wariya akan 'yarki ko? Murmushi tayi tare da cewa "Wariyar me zan nuna maka.?" "Nagani kinfi son Inteesar akaina" Dariya tayi kafin ta d'ora da cewa "Waye ya fad'a maki haka?" "Ai naga kin fifita soyayyarta akaina ne" "Waya fad'a maka haka?ai gurbin ido ba idon bane,karka manta kaifa shalele na ne kafi sauran jikokina soyuwa a cikin zuciya ta." "Ada kenan Gwaggo amma a yanzun dai kam kinfi son yariyar can a kaina,tun ranar da kika zo kika kyallara ido kika ganta shikenan." "Gaskiya ka fad'a yariyar ta shiga raina sosai,kuma naga dacewarka da ita sosai ba kad'an ba,kuma inaji a jiki na ita ce abokiyar rayiwarka ." "Jiya bata fad'a maki abunda tayi bane?" "Ta fad'a mani gaskiya shine na ce da ta tarar da Ishaq baya nan me yasa bata dawo ta sanar ba ta tafi?sannan wanda ka gansu tare ba kowa bane face Usman Wanda ya kad'e ta da mota a kwanakin baya,shine wajen dawowa shi da k'anwasa suka rage mata hanya." "K'arya ne Gwaggo,k'arya take maki,ba wata k'anwarsa da ido na gansu suzo Ubasanjo complex ina tsaye tare da manager access bank,ita da zata zo gida mai ya had'a ta da complex?sannan zata zauna tayi ta wage masa baki kamar mara kamun kai da aurenta." "To yanzun dai kayi hak'uri ba zata sake ba." Da misalin k'arfe goma sha biyu na rana motarsa tayi horn a k'ofar gidan Muhdeen,mai gadin ne ya bud'e masa,bayan yayi parking ne suka fito, Jabeer ya gaida mai gadin gidan da sauran ma'aikatan gidan sannan ya shiga gaba Maryam na binsa a baya. Knocking sukayi Inteesar ce dake kitchen taji k'arar kofar,tazo ta bud'e ganin Jabeer ne yasa ta saki fara'a. "Yaya Jabeer Kaine?" Ganin Aunty Maryam yasa ta fad'ad'a fara'arta "Oyoyo Aunty Maryam ashe yau muna da manyan bak'i, bisimillah ku shigo mana." Kai Jabeer ya girgiza tare da cewa "Ni yanzun zan koma Ina da aiki,anjima zanzo na d'auke ta, Gwaggo na ciki ne?" "Eh amma tana barci." "Ba damuwa idan na dawo sai mu gaisa." Daga nan ya koma ita kuma Inteesar ta janyo hannunta suka shigo cikin falon ta zauna, kitchen Inteesar ta koma ta kawo mata abun ta'bawa sannan ta koma kitchen ta cigaba da aikinta. Tana cikin aikinta ne a kitchen sai ga Aunty Maryam ta shigo tasa hannu wajen taya ta aiki,duk da Inteesar ta hanata kan cewa bata da lafiya,amma sam tak'i amincewa dole ta barta sukayi tare. Bayan sun kammala ne Gwaggo ta farka fitowarta yayi dai-dai da kammalawarsu,da mamaki ta kalli Aunty Maryam ta ce, "Wannan ba matar Jabeeru bace." Murmushi sukayi dukkansu inda Inteesar ta ce, "Ita ce Gwaggo,ya kawota lokacin kina barci yace idan ya dawo sai ku gaisa." Aunty Maryam ta gaida Gwaggo ta amsa tana 'yar tsokanarta,daga nan Inteesar taja hannun Aunty Maryam tana cewa "Aunty Maryam mu shiga ciki kiyi sallah ko?" Tare suka shiga bayan Aunty Maryam ta d'auro alwala ta fito ne, Inteesar ta ahiga don yin wanka,bayan ta fito ne ta sanya kaya tayi sallah,sannan suka fita zuwa falo. A dinning room suka samu Gwaggo tana cin white rice and chicken soup,zama sukayi inda Aunty Maryam ta tsiyayi ruwa Inteesar ta zuba mata abinci sannan ta d'ebi nata. Da yamma ne Jabeer yazo ya d'auke ta suka tafi gida. Da misalin k'arfe goma na dare ne Inteesar tana Sanya rigar barci da niyyar zuwa d'ayan d'akin ta kwana,sai ga wayar Gwaggo tayi k'ara,tana d'agawa raji muryar Muhdeen na cew wai ta sanar da Inteesar ta kawo masa coffee a d'akinsa.gabanta ne ya fad'i don tasan yau Bata da ma'buya. Bata da wani za'bi dole haka ta nufi kitchen ta dafa masa. Hijabi tasa har k'asa tare da k'ok'arin cire tsoron dake ranta,tura k'ofar tayi tare da shiga da sallama tana shiga ya mik'e ya nufi k'ofar d'akin tare da murzawa k'ofar key ya zare key d'in daga jikin k'ofar,gabanta ne ya fad'i ganin wani irin murmushi akan fuskarsa Wanda bata ta'ba ganin ya mata shi makamancinsa ba. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😘😍 Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page4️⃣8️⃣ Hijabi tasa har k'asa tare da k'ok'arin cire tsoron dake ranta, tura k'ofar tayi tare da shiga da sallama,tana shiga ya mik'e ya nufi k'ofar d'akin tare da murzawa k'ofar key, ya zare key d'in daga jikin k'ofar, gabanta ne ya fad'i ganin wani irin murmushi akan fuskarsa Wanda bata ta'ba amfani yayi mata makamancinsa ba. K'ok'arin dakewa tayi don kada yaga tsoronsa a cikin idanunta, durk'usawa tayi ta ajiye jug da kofin sannan ta mi'ke, ba tare da ta kalleshi ta ce, "Ka bud'e mani k'ofa na fita?" Kamar baiji abunda take fad'a ba ya shareta, ganin baida niyyar mata magana ne yasa tayi shiru don taga yana da niyyar shiga wanka yasa tayi shiru, da niyyar idan ya shiga wanka ta d'uki key d'in ta bud'e d'akin ta fice. Kamar yasan niyarta, da zai shiga wankan sai ya shiga da key. Tsabar bak'in ciki da takaici ji take kamar tayi kuka, tana nan tsaye ne ya fito d'aure da towel a k'ugunsa sai wani k'arami da yake goge ruwan kansa, kallo d'aya tayi masa tagansa d'aure da towel,gashin k'irjinsa da ya kwanta luf ta kalla ta kauda kanta da sauri tare da juya masa baya. Jin alamun ya kammala shirinsa ne yasa ta juyo ta kalle shi, sanye yake da riga da wando na barci ya zauna bakin gadon. "Ki zuba mani nasha ko ni zan zuba da kaina." K'arasawa tayi kusa dashi ta durk'usa ta zuba masa ta saka suga dunk'ule uku, mik'a masa tayi ta mi'ke tsaye ta cigaba da tsayiwarta. "Kin tsaya mani akai kamar wata dogariya" Tura baki tayi tana magana ciki ciki "Wannan bakin da kike tura mani shi idan kika shiga hannu na ko?" "Ni ka bud'e mani k'ofa na fita." "Ki fita Ina?ai kin shigo kenan sai kuma gobe, guje-gujen naki ya k'are?saboda kinsan baki da gaskiya shiyasa kike gudu ko?" Ya k'arasa maganar yana kai kofin coffee a bakinsa. "Ina kika je jiya? sannan waye naganki tare da shi jiya? sannan kuma meye tsakaninki da shi?" "Jiya fa gidan rasuwa naje kuma an fad'a maka Mahaifiyar k'awa ta ce ta rasu." "Da nace kije Ishaq Direba ya kaiki me yasa kika tafi?" "Yana da mara lafiya ne ya tafi gida, shine ni kuma na tafi na hau abun hawa,amma Gwaggo tayi mani fad'a bazan sake ba." "Waye na ganki tare a Ubasanjo complex?" "Usman ne sunan sa." "Yayanki ne ko kuma muharraminki ne?" Kai ta girgiza alamun a'a "To meye zaisa ki shiha motarsa alhalin gidan rasuwa na fito zan samu abun hawa ne sai yayi parking, nagansa da k'anwarsa suka matsa akan sai na shiga, bayan na shiga ne k'an war tasa ya sauke ta ne awani tsago, ni kuma ya kawo ni gida." "Me kuka je yi uba sanjo complex?" "Cewa yayi wai zai siya mani waya." Wani irin kallo ya watsa mata sai da hanjin cikinta suka kad'a cikin tsananin 'bacin rai ya mik'e tsaye, tare da zuba mata ido. "Wato saboda wancan ranar na kamaki kina waya da shi, na kar'bi wayar na 'boye shine kika fad'a masa ya siyar maki wata wayar ko?" Kunnenta ya kama ya murd'e, k'ara ta saki saboda zafin da taji,bata san lokacin da ta shige jikinsa ba tare da rok'onsa ya sake mata kunne, wani irin shock yaji kamar an jona masa lantarki, gaba d'aya sai ya tsinci kansa a wani irin yanayi mai wuyar fassara,ya rasa dalilin da yasa kwanan nan duk lokacin da yayi niyar zai hukunta ta ko ya kad'aice daga shi sai ita sai ya tsinci kansa a wani irin yanayi,gaba d'aya jikinsa ya mace sakamakon k'irjinta da ya had'u da nasa,wani irin ajiyar zuciya ya sauke, ita kama duk ba ruwanta bata ma San halin da yake cikin ba, ita dai taji zafin murd'e mata kunnenta da yayi ne yasa ta shige jikinsa, ya rasa yadda zaiyi gaba d'aya yaji buk'atarta kawai yake yi, a hankali yayi mata magana kamar mai yin rad'a " kina son na yafe maki?" Kai ta gyad'a masa alamar eh Sabon yanayin da ya riski kansa ne ya rasa ya zaiyi, duk da cewar ba wani abu da ya ta'ba shiga tsakaninsa da Inteesar, amma duk lokacin da suka kad'aice ita sai yaji wani bak'on yanayin da bai ta'ba jinsa ba, koda kuwa a tare da matarsa Sumayya ce wacce har sex yake da ita bai ta'ba jin irin yanayin a tare da ita ba, ya sanya harshensa a cikin kunnenta ya shiga wasa da shi a ciki, rufe idonta tayi sakamakon wani abu da taji yana mata yawa a jiki, sai da ya had'a ta da bango sannan yaja wani irin ajiyar zuciya, Wanda hakan yasa ta yi saurin rufe idonta,bakisa ya sa a kunnenta ya hura mata isaka,a kasalance ta d'ago idanunta ta kalle shi,sannan ta cire idanunta daga gare shi tare da tura mata baki, bakinshi yakai cikin bakinta ya fara tsotsa, gaba d'aya k'afafunshi sun kasa d'aukarsa, janye bakinta tayi daga nasa, shi kuma ba abunda yake buk'ata illa ya same ta don mararsa ta fara masa ciwo, janta yayi suka fad'a kan gadon, Hijabin dake jikinta ya cire ya shiga k'ok'arin'balle buturan gaban rigarta, rik'e boturan tayi ta hanshi damar cire wa,hannunsa ya zura cikin rigarta hankalinsa gaba d'aya ya gama tashi lokacin da ya fara shafar fatar jikinta gaba d'aya hanklinsa ya gama tashi saboda taushin fatarta. Kuka ta saka masa tare da kiciniyar kwace kanta daga gare shi, cikin wata irin murya da bata sanshi da ita ba ta ji yana magana. "Don Allah karki Mani haka Inteesar, wallahi ina cikin wani hali idan ban same ki ba komai zai iya faruwa dani, ki taimaka mani." Ya k'arasa maganar yana cije la'b'bansa sakamakon mararsa dake masa ciwo. "Banida abunda zan raimake ka da shi, ko ka mance ne na tuna maka?Kai da bakinka ka fad'a cewa me zakayi da wannan kucakar yarinyar, to me kucakar yarinyar zata maka yanzu?kai fa kace baka k'auna ta ka tsane ni to kenan jiki na ne kake so? Am sorry yaya bazan iya bada jiki na ga mutumin da baya k'aunata da tausayi na ba sai dai ya mori jiki na ba, so kake kawai ka mayar da ni abun biyar buk'atarka a duk lokacin da buk'atarka ta taso maka da zaran ka gama amfani na ya k'are a wajenka, to ni ba cingam bane da zaka 'bare kaci da zarar ka gama ka cillar dashi a kwandon shara, zan tsaya na jajirce dan ganin na kare martabar kaina, bazan tsaya lokaci guda wani mugu ya rab..." Bata kai K'arshen zancen ba sakamakon jin da tayi ya yaga rigar barcin da ke jikinta, kalonsa tayi yadda idanunsa suka koma can ciki sun canza launi zuwa ja gabanta ne ya fad'i bata ankare ba sai ji tayi ya cafki na shanunta ya fara tsotsa kamar d'ayan kuma yana wasa dashi, haka yake tsotsan k'irjinta kamar jarinrin da ya kwana biyu baisha nono ba, zafin da taji sun fara mata ne yasa ta fara kokuwar k'watar kanta abun mamaki hawaye ta gani akan fusakarsa yana cewa "Dan Allah kada kiyi mani haka,kada ki haramta mani abunda Allah ya halatta mani shi, yadda nake jin kaina zan iya mutuwa idan ban same ki ba." "Idan ka mutu kwananka ne ya k'are yaya wallahi nima bazan iya ba." Maganar da ta fad'a masa ne yayi masifar k'ona masa rai, sakinta yayi tare da nuna mata key d'in d'akin. "Fita ki wuce kuma kada na sake ganin k'afarki a d'akin na, saboda kasantuwarmu a cikin d'aki d'aya shine yake saka Ni cikin wannan halin." Mi'kewa tayi ta d'auki hijabinta ta saka, cikin sauri ta suri key d'in d'akin har ta murza zata fita taji muryarsa yana cewa "Wallahi na rantse da Allah Wanda ba wani uban giji sai shi, matuk'ar na sake ganin k'afarki a d'akin nan da sunan kinzo barci, to fa ki sani ranar sai na amshi hakki na na aure da yake kanki, baza kibar d'akin nan ba sai na mayar dake cikakkiyar matar aure, idan kuma banyi haka ba to Ni ba Muhammad Muhdeen Sani bane, karki manta da wannan." Aguje ta fita,shi kuma ya kifa cikinsa ga tsananin ciwon marar da yake ji duk ya ishe sa, sai cizon la'b'bansa yake,dakyar ya iya tashi ya ciro wani magani a cikin bedside drawer, ya d'auki goran ruwa a wajen ya had'iye maganin. Ita kuma tana fita ta shige d'ayan d'akin dake kusa da nata,ruf da ciki tayi ta kwanta sai kuka take kamar ranta zai fita,yanayin da ta ganshi da alwashin da ya d'auka idan ya sake ganinta a d'akinsa ne yake tayar mata da hankali,gefe d'aya tasan halin Gwaggo muddin ta lura da bata kwana d'akinsa sai ta rakata har bakin k'ofar d'akin ba k'aramin aikinta bane, a haka dai barci ya d'auke ta. 'Bangarensa kuwa sai wajen mintuna talatin kafin yaji dai-dai, Dan maganin baya saurin masa aiki, wanka yaje yayo don dama duk da sanyin A.C dake d'akin sai da ya had'a zufa. Bayan ya watsa ruwan ne yazo ya kwanta, ba jimawa barci ya d'auke sa. Da asuba ya ya farka a k'urarren lokaci, don har za'a tayar da sallah hakan yasa alwala kawai yayi ya tafi masallaci, Ita kuwa wanka tayi ta d'auro alwala tazo ta gabatar da sallah, bayan ta idar ne tayi azkar kamar yadda ta saba, tana gamawa kuma sai ta tashi ta nufi d'akinta da sallama ta shiga Kallo d'aya Gwaggo tayi mata ta Gane cewa tasha kuka, ganin yadda idanunta suka kumbura sukayi jazir, duk'awa tayi "Ina kwana Gwaggo?" Bata amsa mata ba sai ido da ta zuba mata, ita Kam Inteesar batayi tunanin Gwaggo zata fahimci kukan da tayi ba. "Dukanki yayi ne naga alamar kinsha kuka?, Kai ta girgiza "Banyi kuka ba Gwaggo,barcin da na tashi ne" "Ni zaki rainawa haankali?nasan idon kuka nasa na barci, idan akwai abunda yake maki da baki so ki sanar dani dan Allah." "Ba komai Gwaggo, hanaki yayi ki fad'a ko?zaizo ya same ni ina nan ina jiransa, tunda ke amana ce." Gabanta ne ya fad'i tana Allah yasa kada ya sanar da Gwaggo idan ta tambaye shi, mi'kewa tayi ta cire hijabin ta Ciro wani kaya zata sauya,idanun Gwaggo ne ya sauka akan rigar da Muhdeen ya yaga gabanta, da mamaki ta kalli rigar amma sai tayi shiru kawai, Dan tasan Inteesar ba zata fad'a mata ba ko ta tambaye ta, Yana kwance a d'akinsa Yana waya da Sumayya, inda yake cewa "Kinga kibar wannan maganar kawai kizo gobe." "Ya zan zauna gida d'aya da wannan tsohuwar why not ba zaka bari ta tafi ba." "Kinga idan har kina sona kuma da gaske kinyi missing d'ina to ki bar London ki dawo gobe." "Ok zan dawo zuwa jibi" Acikin zuciyarta Tana mamakin shi da yace ta bari Gwaggo ta tafi yanzu ya canza magana, ta'be baki tayi dan bata san dalilinsa ba. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😍😘 Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page4️⃣9️⃣ A cikin zuciyarta tana mamakin shi da ya ce ta bari Gwaggo ta tafi yanzu ya canza magana, ta'be baki tayi dan bata san dalilinsa ba. Da misalin k'arfe goma na safe Inteesar ta gama duk ayyukan ta da zata yi na cikin gidan,d'akinsa ya rage kuma yana ciki ba zata iya shiga ba,hatta breakfast ta shirya masu ta jera a dinning table,ta sanar da Gwaggo cewa ta kammala amma Gwaggo Bata tashi ba,yau 'yan fad'a da take yi na rashin breakfast da wuri bata yi ba. Wanka Inteesar tayi ta shirya cikin riga da siket na atamfa, d'inkin ya mata kyau kuma ya bayyana kyawun surarta da Allah ya mata, powder kawai ta shafa bayan ta shafa mai sai turare mai dad'in k'amshi. Gwaggo ce da kanta yau taje d'akin Muhdeen don kiransa,samunsa tayi yana waya dan haka ya sallami wanda suke wayan da shi. "Barka da safiya Gwaggo" "Yauwa barka dai kaga na shigo maka d'akinku kai tsaye ko?to naga ita tana can ne nasan kai kad'ai ne shiyasa." Ido ya zuba ba tare da ya ce komai ba,cigaba da magana ta yi "Nace lafiya dai ko?" Da mamaki ya kalleta don bai fahimci tambayar da take masa ba,ji yayi ta cigaba da cewa "Naga alamar jiya akwai matsala tsakaninka da 'yar albarka." Ido ya zuba mata yana nazari,kafin ya fara tambayarsa kansa cewa kodai Gwaggo la'be take masu ne?Kai ya girgiza Dan yasan da ace taji ba ruwanta da 'boye zata yi magana ne. "Naga da ta shigo yau da safe gaban rigarta a yage take,kamar tayi kokawa da kura kaima ga shi na ganka kamar wanda ya tashi daga jinya,shin bata baka hakkinka na aure ne ko kuwa dai tana iya k'ok'arinta kaine jarabarka tayi yawa bata iya d'aukar nauyinka?" Wani irin kallo ya watsawa Gwaggo wanda ita ma bata san ma'anarsa ba,don ita ba ruwanta da kunya ko wani 'boye-'boye,kauda kansa yayi gefe. "Mtsww matsala ta da kai kenan,idan ana tambayarka kana wani kauda kai saboda mishkilanci,inda Jabeer ya fika kenan da shi na tambaya da yanzun ya bani amsa,amma kai k'aton banza dakai k'aramar yarinya ka kasa yadda zaka shawo kanta,kalli yadda ka koma a dare d'aya lusari kawai, sai Kai ta zama a haka tunda ba zaka fad'a mani damuwarba ballantana na shawo maka kanta, idan kaga dama ka tashi kayi kalaci." Daga nan ta fice daga dak'in, binta kawai yayi da kallo har ta fice bai tanka mata ba. A falo ta samu Inteesar zaune akan kujera, ta tsaya tsaye a kanta ta fara magana. "Ke kuma na dawo kanki, me aka kawo ki kiyi a gidannan? Cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa ta ce, "Kiyi hak'uri Gwaggo ban gane inda zancenki ya dosa ba." "Zaki ce haka mana, to bari kiji ba'a kawo ki nan gidan da kici kisha ki kwanta ba, don idan dan abinci ne gidan iyayenki kina ci, idan sha ne a gidan iyayenki kina sha haka sutura ma, ko ba haka ba?" "Hakane" "To wani abu ne wanda ya zama bak'o a wajenki dole sai a gidan miji ake yinsa?" Shiru tayi tana nazari kafin ta ce, "Wallahi ni Gwaggo bansan inda zancenki ya dosa ba, ban gane me kike nufi ba." "Dan k'aniyarka baki san hakkin miji akan matarsa ba? Ko baki san ki biyawa mijinki buk'atarsa ba ne? kin fi son ki kwana cikin tsinuwar mala'ikun Allah? to bari kiji duk ranar da na sake ganin makamancin hakan ya faru dake da mijinki wallahi ranar zaki ga 'bacin raina, daga nan bata sake magana ba ta nufi dinning area, Inteesar mi'kewa tayi cikin sanyin jiki ta bi bayanta, zuba mata nata tayi dai-dai lokacin Muhdeen ya k'araso, k'amshin turarensa ne ya sanar da ita k'arasowarsa, zama yayi d'aya daga cikin kujerun dinning d'in yayin da ita kuma ta zuba masa nasa, k'ok'arin barin wajen tayi sai taji muryar Gwaggo tana cewa "Ina zaki je baki ci komai ba?" Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba ta ce, "Bana jin yunwa" "Shikenen ke kika sani, idan ma fad'a da na maki ne kike fushi dani, ban damu ba kuma matuk'ar baki sauya ba to ba ruwa na dake." Daga nan Inteesar d'akunsa ta nufa dan gyara masa,dama irin wannan lokacin take jira, idan baya ciki ta shiga ta gyara har ta fito ma bai sani ba. A daren ranar ma haka Gwaggo ta sanya Inteesar ta shirya cikin wasu kayan barci masu kyau, har da k'ara ja mata kunne akan kar ta sake gudun mijinta, ita dai Inteesar bata ce komai ba sai da safe tayiwa Gwaggon ta fita. Tsayawa tayi a falo tana ta sak'e-sak'e matuk'ar ta ce zata tafi d'akinsa ba makawa sai yayi abunda ya ce zaiyi da ita, ita kuma bata k'aunar haka ta faru da ita,don haka ta ce ba zata tafi d'akin ba ballantana ace ya cutar da ita, d'akin da ta kwana shekaranjiya nan ta tafi ta kwanta. Shima a 'bangarensa bayan ya gama shirinsa na kwanciya barci zama yayi a bakin gadon ba abunda yake sai tunanin yarinyar nan, ya kasa gane gaskiya shin son ta yake ko me? shidai a iya saninsa ya tsani yarinyar ada ko son ganinta baya yi, amma a yanzun baya jin tsanarta a cikin zuciyarsa kamar yadda yake ji ada, kuma shi haryanzun baya jin yana sonta, sai dai abu d'aya ne yake basa mamaki wanda kuma ya kasa gane dalili, shine a duk lokacin da ya kad'aice shi da ita a cikin d'aki d'aya sai yaji gaba d'aya sha'awar kasancewarsa da yarinyar yake ji,ko kallonta yayi sai yaji wani yanayi na buk'atuwa musamman idan ya kalli wani sashe na jikinta sai yaji feelings ya taso masa, ga Sumayya matarsa da sukayi auren soyayya da ita Sumayya idan zata kwanta tsirara a gabansa zai iya tsallake ta ya wuce ba tare da yaji wani abu dangane da haka ba, amma idan Inteesar ce ko yaya ya kalli wani sashe na jikinta sai ya rasa nutsuwarsa,koda Gwaggo ke turo ta d'akinsa baida niyyar ta'ba koda yatsarta, amma da zaran ya ganta sai ta nemi wargaza masa lissafi, shiyasa ba ya iya hak'uri sai ya ta'ba ta, idan kuma ba haka ba shine yake shan wahala don sai ya kwana yana ciwon mara, shiyasa ya fad'a mata duk ranar da ta shigo masa d'aki sai ya biya buk'ararsa. Kwanciya yayi yana ta juyi shi kad'ai, zuciyarsa sai tunaninta yake,a wannan lokacin ita Kam ta dad'e da barci. *LONDON* Dad da Mum d'inta suna zaune a falo, ta fito daga bedroom d'inta ta tsaya k'erere akansu. "Dad Mum gobe zan koma gidan miji na" Da mamaki Dad ya kalle ta "Akan me zaki koma gidansa? mutumin da tunda kika taho bai saka k'afa yazo ba shine zaki koma gidansa? bayan kinsan cewa danginsa da kakarsa ba k'aunarki suke ba kiyi zamanki anan, bana son kije inda za'a wulak'anta mani ke alhalin kinfi k'arfin wulak'anci." Murmushi tayi tare da cewa "Kada ka damu Dad mijina yana sona, shi kad'ai ma ya ishe ni ban damu da kowa yak'ini ba, sannan wannan kakar tasa ba zamu zauna inuwa d'aya da ita ba, tun farko bata sona, sannan muna tsaka da cin amarcinmu ta sa akayi mani kishiya, hmm bashi ta d'auka tasa nayi nesa da miji na tsawon wata d'aya, yanzun haka tana cikin gidan ita da 'yar lelenta wacce ta aura masa Inteesar take ko wace ce? oho masu amma bazan sauka a gidan ba sai nan da 1 week da zaran ta bar gidan ni kuma zan koma gida na yayin da zan k'untatawa rayuwar Inteesar, wallahi sai tayi nadamar auren miji na." Sai a lokacin Mum tayi magana ta ce, "Aure dai sun riga sun masa,kuma suna k'aunarta fiye da ke, saboda haka kada kije ki aikata abunda zaisa kiyi dana sani bada yawu na ba." "Hmm ita ce da dana sani bani ba sannan kuma kada ma kiyi yawu Mum, don na lura yanzun baki k'aunata kamar kin janza hali ba Mum d'in da na Sani da ba, kuma wallahi da bakinsa ya fad'a mani cewar ba son yarinyar yake ba, ya tsane ta kada na d'auke ta kishiya na d'auka cewa 'yar aiki aka kawo mani,ita zata dinga mani aiki, shine dalilin da yasa na hak'ura na janye k'udiri na akanta, da badon haka ba da sai na illata ta." Dad ne yayi ajiyar zuciya ya ce "Yanzun ke kad'ai zaki koma daughter?" "Lokacin da nazo ni kad'ai nazo ba tare da kowa ba kuma ra'ayin kaina ne, to yanzun ma ni kad'ai zan koma dan ra'ayin kaina." Tana gama fad'ar haka ta juya ta koma, da ido kawai suka bita don idan ta fad'i magana ba ta sauraron kowa. Washe gari da safe dukkansu suna Kan dinning table suna breakfast, Muhdeen ne ya kalli Gwaggo tare da cewa "Gwaggo zan d'anyi wata tafiya ta kwana biyu, so zaku ji shiru baku ganni ba." Gwaggo ne ta ajiye kofin tea da take sha yayin da Inteesar kuma tayi shiru kamar bata ji ba,inda Gwaggo ta ce, "Wani gari zaka?" "Birnin tarayya zanje?" "To Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya, wani lokaci zaka tafi?" "Yanzun idan na fita zuwa asibiti daga can bazan dawo nan ba,sai bayan kwana biyu na dawo." "To Allah ya tsare ka ya kaika lafiya ya dawo muna da kai lafiya." Ameen ta rabbi kaka ta, Gwaggo ce ta kalli Inteesar ta ce, "Baki ce komai ba kodai kunyi sallama jiya dadare ne." Cikin sanyin murya ta ce, "Allah ya kiyaye hanya" Ta'be baki yayi don har yau yana jin zafin maganar da tayi masa inda yake ce mata zai mutu ta ce masa idan ya mutu kwanansa ne suka k'are,wato k'iyayyar da take masa har ya kai haka?idan ya tuna zancenta kawai sai yaji ransa ya 'baci. Gwaggo ce ta katse masa tunani ta hanyar cewa "Lafiya kuwa ko akwai abunda yake damunka ne?" "Kai ya girgiza tare da murmushin yak'e yace, "Bakomai Gwaggo, bari na tafi" Daga nan ya nufi falo Kan kujera ya d'auki k'aramar jakarsa ya rataya a kafad'arsa,daga nan ya juyo ya kalli Gwaggo da take d'aga masa hannu. "Ke 'yar albarka ba zaki zi ki raka mijinki ba?" Bai kula su ba ya nufi hanyar fita, Inteesar tabi bayansa saboda maganar da Gwaggo tayi mata,yayin da Gwaggo ta zauna a kujeran falo. Yana gaba tana biye dashi a bayansa, yana jin k'arar takun takalminta,bai juyo ba kuma bai tsaya ba, har suka k'arasa wajen motorsa ,yana shiga yayiwa motar key yabarta nan tsaye a wajen ko kallonta bai yi ba. Ita kuma taji zafin share ta da yayi don haka ta juya ta koma ciki. A asibiti ma ya sanar da cewa zaiyi tafiya zuwa Abuja,duk da cewar Jabeer d'an uwansa ne kuma amininsa bazai iya fad'a masa gaskiyar inda zai je ba, shiyasa Koda Jabeer ya tambaye shi ya ce Dady ne ya aike sa. Bayan yabar asibiti hotel ya je ya kama masu d'aki na tsawon kwanaki bakwai, shida Sumayyarsa,isowarta kawai yake jira yaje Airport ya d'auko ta. Da misalin k'arfe d'aya na rana bayan ya idar da salla ne ya nufi Airport d'auko ta. Akan hanyarsu ta zuwa Hotel ne yana Driving ya d'an juyo ya kalleta "Ya su Dad da Mum duk suna lafiya?" Murmushi tayi tare da cewa "Lafiya lau suke suna gaishe ka" "Shine kika tafi kika nisanta kanki da ni ba tare da kinyi tunanin halin da zan shiga ba ko" Yamutse fuska tayi "Baby mubar maganar nan kawai, dan wallahi zaka sa na tuno da abunda nake k'ok'arin cire shi a Raina." "To shikenan tunda bakiso na bari" Hirarsu suke har suka k'arasa Hotel d'in, inda sukayi order na abincin da suke so, ta shiga wanka,bayan ta fito ta shirya ta zauna gefensa, kallonta yayi tare da cewa "Banga kinyi sallah ba? Kada dai kice mani fashin sallah kike ki sakani cikin wani hali." Dariya tayi sannan ta ce "Ba fashin sallah da nake." Murmushi yayi tare da cewa "Alhamdulillah, to banga kin tashi kinyi sallah ba." Yamutse fuska tayi "Sai anjima zan had'a da la'asar nayi gaba d'aya." Dafe goshinsa yayi "Sumayya wai har yanzun baki daina jinkirta sallah ba?" "Shikenan bari na tashi nayi" Mi'kewa tayi ta nufi toilet don d'auro alwala,binta da ido kawai yayi ya ce, Allah ya shirya Tsawon kwanaki biyu yana tare da Sumayya,idan ba lokacin sallah ba ba abunda ke fitar dashi daga Hotel d'in, kullun sai yayi waya da Gwaggo da su Mummy ba Wanda yasan ba Abuja yake ba,kowa ya d'auka yana Abuja, a ranar ne kuma Sumayya ta ce ta gaji da zaman Hotel d'in,tana son su d'an fita, haka kuwa akayi suka fita suka d'an shak'ata, a kan hanyarsu ta komawa Hotel d'inne dai-dai kwanar da zasu shiga Jabeer yazo wucewa ya hanto Muhdeen da mace a gaban Motarsa,da mamaki ya tsaya yana kallonsa har suka shige,sannan yaja motarsa ya wuce cike da mamaki. Bayan ya koma gida yana zaune a falo ya ciro wayarsa layin Muhdeen ya kira, Muhdeen da yake zaune a kujera Sumayya tayi folo da cinyarsa wayarsa ta soma ruri dubawa yayi tare da d'aga wayar. "Hello Jabeer ya akayi ne?" Ajiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa "Kana ina ne?" "Ya kake tambaya ta bayan kasan na tafi Abuja" "Me kaje yi a Abuja?" "Saunawa zan sanar dakai Dady ya saka ni wani aiki" "Shi aikin baida suna ne ko kuma na kira Dady na tambaye shi wani aiki kake masa, nasan dai bazai 'boye mani ba." Cikin d'aga murya Muhdeen ya ce, "Bai shafeka ba, kada ka shiga hurumin da ba naka ba" "Bansan yaushe ka zama haka ba, amma bari yanzun nan naje gidanka na d'auko Gwaggo sannan na biya na d'auko Mummy sai na kawo su ka fad'a masu aikin da kakeyiwa Dady wanda su bazasu iya sani ba." "Ka kawo su Ina?" "Safara Hotel, inda ka ajiye mace da sunan kana Abuja." A zabure mi'ke tsaye Sumayya dake kwance saman cinyarsa har ta fad'i. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09055327995 Loveu oll😍😘 Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ki hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page5️⃣0️⃣ A zabure ya mi'ke tsaye, Sumayya dake kwance saman cinyarsa har ta fad'i. "Look Jabeer ba yadda kake tunani bane, kasan waye ni bazan ta'ba aikata abunda ya kaucewa shari'a ba, duk abunda kaga nayi to bai kauce, hanya ba." "To wace ce ka ajiye a Hotel tsawon kwanaki biyu?" "Mata ta ce" "Wace matarka.?" "Sumayya ce,kasan akwai takun sak'a tsakaninta da Gwaggo kuma zamansu waje d'aya akwai matsala, hakan yasa na ajiye ta anan har zuwa ranar da Gwaggo zata bar gidan." Ajiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa "Idan 'bera nada sata daddawa nada wari, haka zalika idan anbi ta 'barawo abi ta mabi sawu." "Kaga ba wani zancen Hausa zaka tsaya kana mani ba, maganar gaskiya Gwaggo ta tsanar mani mata ne kawai,ba gaire ba dalili." "Itama matar taka harda halinta yasa aka tsane ta, kaima kasan matarka nada matsala." "Ni banga matsalarta ba, kaga sai anjima." Daga nan ya katse kiran, don baya son Sumayya taji maganar da sukeyi. Washe garin ranar ne ya sanar da Sumayya cewa zai koma gidansa, don dama kwana biyu ya ce zai yi, kullun da safe kafin ya tafi Asibiti zai je, ya duba ta, kafin ya tafi Asibiti, kuma idan ya tashi kafin yaje gida zai biyo wajenta. Haka dai ta hak'ura badon ranta yaso ba, shi kuma ya nufi gidansa akan hanya ya tsaya harda 'yar tsaraba ya siye ya tafi dasu gidan, a harabar gidan yaga motar Jabeer yayi parking a gefe, sai da gabanasa ya fad'i don kada Jabeer dai abunda ya ce zaiyi shi yake k'ok'arin yi, don ga motarsa nan a gidan hakan na nufin yazo d'aukar Gwaggo ne ya kaita Hotel inda yake tare da Sumayya? tambayar mai gadin gidan yayi yaushe Jabeer yazo gidan? ya sanar da shi cewa yanzun. 'Daya daga cikin ma'aikatan gidan ya kira, yasa shi ya d'auki ledojin tsarabar da ya dawo dasu,fruit ne da kayan ciye-ciye danginsu chocolate cake da snacks. Tsawon mintuna biyu yana tsaye yana tunani idan Jabeer ya sanar da Gwaggo gaskiyar lamarin ya zaiyi, shidai yasan tijarar Gwaggo, duk da cewar matarsa ya ajiye a Hotel ba karuwa ba. Da haka ya nufi hanyar shiga ta cikin falon,da Sallama ya d'auke a bakinsa ya tura k'ofar, Gwaggo da Jabeer ne suka amsa masa yayin da Inteesar ke kwance a k'afar Gwaggo,tana barci, Duk gashin kanta mai tsayi da bak'i ya bazu ya rufe mata rabin fuskarta, sanye take wata k'aramar riga mara hannu mai kama da singileti pinck colour sai siketa bak'i har k'asa,rigar ya kwanta a jikinta kuma ya kama jikinta,hakan yasa ya bayyana surar k'irjinta,ta kwanta rigingine kanta na saman cinyarsa Gwaggo, ta d'ora hannunta na dama a saman cikinta,barcinta kawai take yi, bayan sun amsa masa sallamar ne ya gaida Gwaggo. "Barka da yammaci Gwaggo." Shiru tayi masa kamar bata ji abunda ya ce ba,kauda kanta tayi tana Mai cigaba da kallon T.V da take, gabansa ne ya fad'i kar dai a ce Jabeer ne yayi masa tonon silili, aiko indai haka ne Jabeer bai kyauta masa ba, kuma sai ya ci mutuncinsa, dubansa ya maida ga Jabeer dake zaune shima ya zuba masa ido tare da d'aga Masa gira d'aya ya dai? kauda kansa yayi daga kallon Jabeer d'in, ya maida zuwa ga Gwaggo ya k'ara cewa "Ina wuni Gwaggo?" "Da ban wuni ba zaka ganni?" Shiru yayi yana kallon Jabeer, yayinda shi kuma Jabeer ke masa murmushi ya ce, "Da alama kayi mata lafi ne" "Nayi mata laifi ko kuma kayi mani munafurci ko?" Sanin inda zancensa ya dosa ne yasa Jabeer shek'ewa da dariya ya ce, "Kasan baka da gaskiya ne shiyasa ka tsargu kanka, ni ba abunda na sanar da Gwaggo, amma wata k'ila dai zan sanar da ita, ka Fara bincikar laifin da kayi mata tukunna." Gwaggo ce ta kalli Jabeer ta ce, "Ka rabu dashi Jabeeru, ba wani bincikar da zaiyi ya sani ai,tunda yasa k'afarsa ya tafi Abuja sau d'aya ya kira mu bayan saukarsa, ga matarsa nan koda sau d'aya bai tambayi halin da take ciki ba." Sai a lokacin Muhdeen ya kula da irin kayan dake jikin Inteesar, bayan ga Jabeer a wajen zaune sun facing da juna, ransa ne ya 'baci ya fara magana "Wannan wane irin isakanci ne kuma?" Da mamaki Gwaggo ta kalle shi tare da nuna shi da yatsa ta ce, "Kai Muhammadu ka kiyaye ni ka fita a ido na,gidan uwar wa ake isakancin?" "Haba Gwaggo kema kinsan ko a addinin musulunci wannan ba dai-dai bane, ta yaya matar aure zata tsaya ta kwanta gaban wani namiji da ba muharraminta ba haka,kalli fa ko suturar arziki bata saka ba,ga gashin kanta a waje ki hula bata m saka ba, ga wata 'yar isakar rigar da ko hannu babu." K'arasawa yayi gabansu ya d'an ja gashin kanta da d'an k'arfi, k'ara ta saki tare da tashi zaune tana mutstsika idanu alamun barcin bai ishera ba,ido ta zubawa Gwaggo don Bata lura da shi ba,tura baki tayi tare da ri'ke kanta ta ce "Gwaggo akwai zafi." "Daina Kallo na ga shugaban mugayen nan da yaja maki gashi, saboda mugunta irin taka, dama ina jiran dawowarka ne idan baka sani ba ka sani, tunda ka saka k'afa ka tafi Abuja ka kirani sau d'aya baka sake kira ba, sannan wayar Inteesar da ka amshe ka maida mata da wayarta kaji na fad'a maka." Dariya Jabeer yayi tare da cewa "Au dama Abuja ya tafi Gwaggo?" Kallonsa Gwaggo tayi tare da cewa, "Ya kake tambaya ta bayan ya ce, daga wajen aiki ne tafiyar ta tashi kuma naga wajen aikinku d'aya, shine baka san ya je Abuja ba?" Dariya Jabeer yayi "Wato mutumi na Abuja kaje ko? to me kaje yi ne dan bansan aikin da kaje yi ba,sannan kaga kamar ba Wanda yayi dogon tafiya ba, Abujan ce kuwa ko dai fad'a ne kawai." Banza da shi yayi dama yasan halin Jabeer da tsokana, kuma yana da tabbacin cewa Jabeer bazai ta'ba tona masa asiri ba, don haka ya maida idonsa ga Inteesar ya ce, "Saboda tsabar wulak'anci shine kika Sanya wannan banzayen kayan a jikinki ko? sannan kika zo kika tsaya gashin kanki a bud'e kika tsaya a falon Nan bayan kinsan za'a iya yin bak'i a gidan ko?" "Nifa bansan kowa ya shigo ba ba daga ni sai Gwaggo nayi barci" Tsawa ya daka Mata "Zaki je ki sauya kayan ko kuma kisa hijabi ne ko kuma zaki tsaya kina bani labari ne." Mi'kewa tayi ta nufi d'akinta, shi kuma ya zauna kan kujera, kallonsa Gwaggo tayi ta ce, "Sai kishin banza da wofi, ka damu da ita ne tunda ka tafi baka iya cewa a bata waya kaji lafiyarta ba?" Inteesar ta dawo sanye da hijab har k'asa, kallon Jabeer tayi tare da gaishe sa cikin girmamawa. "Yaya Jabeer ina wuni?" "Lafiya qalau Inteesar, ya hak'uri da rayuwa?" "Alhamdulillah, yanzun ka shigo ne?" "Eh hanya ce ta biyo dani nace bari na lek'o mu gaisa." "Allah sarki mungode, ya Aunty Maryam?" "Tana lafiya lau" Murmushi tayi tare da cewa "Masha Allah" Mi'kewa tayi ta nufi kitchen ta dawo d'auke da faranti da ruwa da lemu akai, ajiye tayi a gabansu, dama Muhdeen gefen Jabeer ya zauna, bayan ta ajiye ne Jabeer ya d'auki ruwa yasha, sannan ya ce, "Amarya ai ba ruwa kad'ai ba har da abinci, don shi nafi buk'ata." Murmushi tayi ta nufi hanyar kitchen, ba jimawa sai gata ta dawo da faranti Babba, anjera food flask da plates da spoon, a gabansu ta ajiye ganin zata bud'e ta zuba yayi saurin cewa "Barshu kawai hakan ma mungode" Komawa tayi ta zauna a mazauninta, Jabeer ya bud'e food flask d'in,tuwon shinkafa ne da miyar agushi da ganyen ugun da yaji naman sa, d'iba yayi ya sauka ya zauna Kan center carpet ya Fara ci, kallon Muhdeen yayi tare da cewa, "Mutumin Abuja ba zaka ci abincin bane? ko kuma Wanda ka ci a Abujan ya ishe ka?" Ki kallonsa baiyi ba idonsa na kan waya, Gwaggo ce ta ce "Tun Abinci da ya ci na Abuja ai yakamata ace yaji yunwa tunda doguwar tariya yayi." Jabeer ya kece da dariya sannan ya ce, "Ai Gwaggo ba Zaki Gane bane, baki san Abujar da yaje ba wacce kika sani bane wata ce." Kallon rashin fahimtar inda zancensa ya dosa ta ce, "Kai Jabeeru Abujar guda nawa ne?" "Nidai d'aya na sani amma wannan shalelen jikar naki Abujansa ba d'aya bace, wacce yaje shekaranjiya ba wacce kika sani bane wata ce." "Kai Jabeeru zancen ya Isa haka nan don naga alamar santi kawai kake, saboda dad'in girkin Jika ta da tayi, don kasan ita ta iya girki mai d'an Karen dad'i, bansan girkinta na sanya sambatau marasa kai ba sai akanka, dama waccan solo'biyar matarka bata iya girki ba." Jinjina Kai yayi "Shikenan Gwaggo tunda haka kika ce" Yana gama cin abincinsa ya wanke hannu, ganin Muhdeen baida niyyar cin abincin ne yasa Inteesar ta tattara kayan ta Kai kitchen. Bayan ta dawo ne suka cigaba da firar su sama-sama Jabeer ne da Gwaggo suke fira, Inteesar ta lura da tsarabar da aka ajiye d'auka tayi takai kitchen ta dawo ta zauna, Gwaggo ce ta fara Gyangyad'i, fira suka tsakanin Jabeer da Inteesar,inda ran Muhdeen ya sake 'baci kenan,wato da shi da banza duk d'aya a wajenta ko? tasan yayi tafiya ba sannu da dawowa ba komai,bata gaishe shi ba, bata bashi ruwa ba ballantana abinci sannan ta zauna tana hira da wani a gabansa ko kallonsa ma batayi ba, girgiza Kai yayi sannan ya mik'e ya nufi d'akinsa,Yana Jin muryar Jabeer na cewa a fito lafiya Mutumin Abuja, Bai kula sa ba yayi shigewarsa ciki. Daga nan Jabeer yayi masu sallama ya ya fice abinsa. Haka rayuwa tayi ta tafiya, yau alhamis yau ya kama gobe Gwaggo zata tafi, Inteesar ta shiga damuwa sosai har kukanta,Wanda hakan kuwa ki jikin Muhdeen, domin shi so yake ta tafi Sumayya ra dawo gidan,kowa da abunda ke gabansa, Muhdeen na cikin farin ciki Inteesar na cikin bak'in ciki,Wanda Gwaggo duk ta lura da yanayin kowanne a cikinsu, kuma tasan tabbas akwai abunda Muhdeen ke shiryawa da ya matsu tabar gidan sai dai ta kasa gano komai. Zaune suke a dinning table suna Breakfast, Inteesar gaba d'aya ta kada saka komai a cikinta,tana ta tunanin wahalar da tasha a gidan a hannun Muhdeen, dalilin zuwan Gwaggo gidan ne ta samu 'yanci a cikin gidan, to yanzun gibe Gwaggo zata tafi kenan hakan na nufin zata cigaba da wahala ne kamar yadda yake bautar da ita a baya? ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon Gwaggo, Gwaggon ma ita take kallo "Ke 'yar albarka lafiya kuwa?" Girgiza kai tayi tare da cewa "Bakomai Gwaggo" "Akawai komai" Sunkuyar da kanta tayi tana juya cokali a cikin kofin tea, Gwaggo ta sake magana ta ce "Kinga idan akwai wani abu ki sanar dani,Kinga ke amana ce a wurinmu, duk abunda kike buk'ata ki fad'a mani idan ina da halin yi maki shi zan maki, idan kuma banda shi zansa mijinki ya maki idan baifi k'arfinsa ba, amma kada kuce na k'ara kwankin da zanyi a gidan nan." Marairaice fuska ta yi cikin shagwa'ba ta ce, "To ai abunda zan nema a wajenki ne kika ce kar na nema." Dariya tayi "Dama nasan abunda zaki ce kenan, ki nemi wani abun amma ba wannan ba" Satar kallon Muhdeen tayi sanna ta fara magana "To ai banda wayar da zan dinga magana da ke da kuma su Mummy." Kallon Muhdeen Gwaggo tayi sannan ta ce, "Kaje ka kawo mata wayarta yanzun nan." Girgiza Kai yayi sanna ya ce, "To zan bata." "Ba haka nake son ji ba, cewa nayi kaje ka kawo mani wayarta, idan kuma ban Isa ba ka fad'a mani yanzun na kira Mahaifiyarka na sanar da ita." Ba tare da yayi wata magana ya mik'a ya nufi d'akinsa, ba jimawa sai gashi ya dawo da wayar ya mik'awa Gwaggo, amsa tayi ta mi'kawa Inteesar, amsa tayi tana murna tare da godiya. Da misalin k'arfe goma na dare Gwaggo da Inteesar suna zaune a d'akin Inteesar suna fira,na bankwana har k'arfe goma sha biyun dare yayi, Gwaggo ce ta kalli Inteesar ta ce dare ya tsala "Yakamata kije mijinki na jiranki" "Ni Gwaggo ba abunda zan zan masa ki bari mu kwana tare na yau kawai." "A'a duk fira dai idan ba k'arya zamu fad'a ba duk munyi ta, bana son gardama kije kawai d'akin mijinki." Sanin haklin Gwaggo ne yasa Inteesar ta mik'e bayan tayiwa Gwaggon sai da ta fice. A falo ta tsaya ta tabbatar ba Wanda yaganta ta shige d'akin da take kwanciya tana barci,don dama tun ranar da Allah ya k'wace ta hannun Muhdeen ya kuma yo alk'awarin duk ranar da ta shigo masa a irin wannan lokacin sai ya kar'bi hakkin aurensa a kanta, hakan yasa bata sake yarda take d'akinsa dadaddare ba, tana shiga d'ayan dak'in ta tura k'ofar tare da rage hasken d'akin. Washe gari Gwaggo zata tafi Inteesar sai kuka take kamar wacce aka ce sun rabu kenan, haka Gwaggo ta dinga rarrashinta har ta gaji, k'arshe dai haka ta hak'ura ta kyaleta, Direban Mummy ne yazo d'aukarta,haka suka fice Muhdeen da Inteesar dake tsaye a harabar gidan bayan tafiyar Gwaggo suka koma cikin gidan, har suka shiga Bata daina kuka ba, jin muryarsa tayi yana cewa "Ke ki rufe mani baki da zaki sakawa mutane kuka na ba gaira ba dalili, ko mutuwa akayi maki ne? to wallahi ki rufe mani baki kafin kisha mamaki anan." Sanin cewa mai goyon bayanta bata gidan yanzun daga ita sai shi ne a gidan, kum tana tuna irin wahalar da ya gana mata a baya ne yasa tayi shiru. "Ki tashi ku shiga kitchen, ki shirya abinci lafiyayyae mai kyau kafin na dawo da bak'uwa a cikin gidan nan." Da sauri ta kalle shi ta ce "Mummy ce zata zo?" Koma wace ce idan tazo zaki ganta,sannan wancan d'akin ki share shi ku goge shi tas ko Ina yayi fess kisa turaren wuta." Murmushi tayi cikin Jin dad'i don a tunaninta bak'uwa ce wacce zata samu abokiyar zaman gida da fira,don haka ta saki murmushi ta nufi kitchen. Wayarsa ce tayi k'ara ya duba yaga ita ce, d'agawa yayi tare da cewa "Hello Baby na" Jin muryarta yayi tana cew "Wai Baby har yanzun Bata tafi bane?" "Yanzun nan ta tafi,na bada umarni ne a gayara maki d'akinki a girl's maki lafiyayyaen abinci." Yamutse fuska tayi "Wai kana nufin wannan kucakar yarinyar ce zata girka mani abinci? nifa bana son jagwalgwalo." Dariya yayi tare da cewa "Kada ki damu, tunda na iya kema zaki iya, yanzun dai bari nayi wanka nazo na d'auke ki." "Okay l love you" "Love you too baby" Dagana nan ya katse kiran ya nufi d'akinsa don yin wanka zaije ya d'auko Sumayyarsa ta dawo kusa dashi, farin cikinsa zata dawo gidan. Daga alk'amin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😘😍 Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *SADAUKARWA* Wannan sadaukarwa ne a gare ki Autar Ammi (Sakeenah) kece ta farko da kika fara kira na a waya dan jin lafiya ta kwana biyu shiru baku ji ni ba, naji dad'i da nuna k'auna da kulawa, wannan shafin naki ne kiyi yadda kike so da shi, Allah yabar zumunci. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi da cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auran wawa. *JINJINA* Jinjina ta musamman a gare ki members na *INTEESAR HAUSA NOVEL* Nagode sosai da kulawarku a gare ni, Allah yabar zaman tare. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page5️⃣1️⃣ Daga nan ya katse kiran ya nufi d'akinsa don yin wanka, zaije ya d'auko Sumayyarsa ta dawo kusa da shi, farin cikinsa zata dawo gidan. Bayan ta gama duk ayyuukan da zata yi ne ta shiga d'akinta wanka tayi, ta shirya cikin riga da siket na leshi, wayarta ta d'auka tana game, k'arar k'ofa taji ta mik'e da sauri duk da bata san wace irin bak'uwa ce tazo ba amma duk da haka da fara'arta ta bud'e k'ofar. Kwatsam idanunta ya sauka a cikin na Sumayya, sai da gabanta ya fad'i, amma sai ta dake ta k'ak'alo murmushi a fuskarta cikin sakin fuska ta ce, "Sannu da zuwa Aunty Sumayya." Kallon banza tayi mata tare da tare da shigowa cikin falon, saura kad'an ta bangaje inteesar sai tayi saurin matsawa baya ta bata hanya, Muhdeen ne ya shigo hannunsa rik'e da jakkarta, kai tsaye falonta ta nufa tare da zama kan kujera ta ce, "Wash baby na gaji." Ajiye jakkar yayi tare da cewa "Ayyah sorry, yanzun ki tashi kici abinci sai ki kwanta ki huta ko?" Yamutse fuska tayi tare da cewa "Ina yarinyar nan take ne? tazo ta zuba mun abinci naci." Juyawa yayi ya kalli falon inteesar, ganin bata nan ne yasa ya k'wala mata kira, ashe tana kwance akan kujera tana tunanin sabuwar rayuwar da zatayi da Sumayya a gidan, ta ji muryarsa yana cewa "Kina ina ne!" Da jin haka tasan ita yake kira don haka ta mik'e ta nufi falon Sumayya, koda ta k'arasa zaune ta same shi yayin da Sumayya ta kwanta tayi filo da cinyarsa, kallo d'aya tayi masu ta kauda kanta gefe tare da cewa "Gani" Tsawon mintuna uku tana tsaye bai ce mata komai ba, ta d'auka baiganta bane don haka ta juyo ta kalle shi, sai taga idanunsa akanta kallonta yake sunkuyar da kanta tayi ganin yadda idanunsa ke yawo a jikinta, jin muryarsa tayi yana cewa "Baki ganmu bane" Ba tare da ta kalle shi ba ta ce "Naganku" "Okay, wulak'anci ne yasa kika share mu?" Shiru tayi masa ba tare da ta ce komai ba, shi kuma abunda ya tsana kenan yayi magana ayi masa shiru kamar ba'aji ba, hakan yasa ya daka mata tsawa. "Sa'anki ne ni da zanyi maki magana kiyi banza Dani?" "Cikin sanyin muryarta ta ce, "Kayi hak'uri" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Baki ga Sumayya ta dawo bane?" "Na ganta" "Tsabar wulak'anci ne yasa kika share ta baki gaishe ta ba?" Kafin tayi magana ne suka hi jiyo muryar Sumayya ta cewa "I na kuwa zata gaishe ne bayan muna auren miji d'aya tana ganin dai-dai da ita nake, bari kiji na sanar dake abunda kika manta, ni nan mijina yana sona sosai auren soyayya mukayi auren na gani ina so mukayi, ba irin naki ba auren had'i da kwad'ayi irin na iyayenki yasa suka bayar da ke ga miutumin da baya k'aunarki baya sonki da k'aunarki aka k'k'aba masa ke, to bari kiji nan gidan tamkar kinzo aikatau ne, ki d'auka gidan aikinki be ba gidan aurenki ba, dan ba mijin da ya kalle ji a matsayin matarsa, koba haka bane baby na?" Jinjina kai yayi tare da cewa "Duk abunda kika fad'a ai gaskiya ce, ba k'arya " Jinjina kai Sumayya tayi ta d'ora da cewa "Kinji abunda ya ce da kunnenki ko 'yar matsiyata kawai." Kallon Sumayya yayi, kallo mai cike da gargad'i Wanda ta gane manufarsa, amma sai tayi kamar bata gane ba ta d'ora da cewa "Ko ke ba 'yar matsiya... "Tsawa ya daka mata tare da cewa." "Stop" Da mamaki ta kalle shi da niyyar yin magana taga inteesar na wajen, don haka tayi shiru dan yadda taga fuskarsa ya canza tasan zai iya kunyata ta a gaban yarinyar da ta raina, idanun inteesar cike tab da k'walla don ba Wanda ya ta'ba mata irin cin mutuncin da aka mata yanzun, jin muryarsa tayi ya ce "Kije ki kawo mana abuncin mu nan" Ba tare da ta ce komai ba ta nufi dinning area dan d'auko masu abuncin . A babban faranti ta jero masu shi, tazo ta ajiye tare da komawa ta kawo masu ruwanda drinks, ajiyewa tayi ta koma d'akinta tare da fad'awa kan gado ta saki marayar kuka. Bayan tafiyarta d'aki ne Muhdeen ya kalli Summayya tare da cewa "Kada ki zak'e akan yarinyar nan da yawa fa, dan zaki iya fuskantar k'alubale." Kallon mamaku tayi masa tare da cewa "Kodai ka fara son yarinyar na ne?" Gajeren murmushi yayi tare da cewa "Me kik gani" Ya za'ayi Ina mata magana Dan tasan banbancin da ke tsakaninmu, kuma tasan matsayinta zaka dakatar Dani?" "Ba haka bane naga kina neman wuce gona da iri ne, duk abunda zaki mata kada ki ce zaki ci mutuncin iyayenta, ko ki zage su bana so, kuma idan yarinyar ta kura Mummy ko Gwaggo a waya ta sanar dasu abunda kike mata me kike tunanin zai biyo baya? kindai san irin k'aunar da suke mata kema shaida ce, bana son abunda zai janyo muna matsala daga ni har ke " "Amma ai kai ne da bakimka ka fad'i cewa nan kamar gidan aikinta na d'auka 'yar aiki aka kawo mani ba kishiya ba, don na fad'a mata shine laifi na?" "Ba sai kin fad'a mata ba, ai aikinta zata san da hakan" Hannunta ya janyo don ta sauko ta ci abincin, zama suka yi Kan center carpet. "To ka kira ta ko muna zamu...' Hannu ya d'aga mata alamar tayi shiru,inda ya bud'e food flask d'in ya d'auki plate inteesar kuwa tana kwance a d'akinta sai sheshshek'ar kuka take,zagin da Sumayya tayi mata ne ke mata ciwo a zuciya . Knocking akayi a k'ofar falon, inteesar kama tana can kwance a d'akinta sai kuka take bata ma san anayi ba, Muhdeen ne ya tashi ya he ya bud'e k'ofar, k'anwar Mummynsa ce Aunty Abla tare da Hajiya Bilkisu mai gayaran Amarya, Murmushi Aunty Abla ta sakar masa tare da cewa "Son wato ko ziyara baby ko?" Sosa kai yayi tare da cewa "Bisimillah ku shigo Aunty" Shigowa sukayi suka zauna a falon inteesar, gaida su yayi cikin girmamawa, suka ansa masa cikin sakin fuska, daga nan ya k'walawa Sumayya kira tare da cewa "Baby zo ga Aunty Abla ku gaisa, duk da bata so tashi ba haka ta mik'e ta k'araso falon tare da zama kujera ta kalle su tare da cewa "Hy ya kuke?" Kallon juna sukayi Aunty Abla da Hajiya Bilkisu, Muhdeen kuma ya dafe goshinsa cike da takaucin abunda Sumayyar tayi, ganin basu amsa va ta mik'e ta kalli Muhdeen ta ce "Baby bari na kwanta na d'an huta " Baice mata komai ba ta mik'e ta nufi d'akinta, kallonsa Aunty Abla tayi tare da cewa "Son where is my daughter?" Shiru yayi da bai gane wa take tambaya ba, kafin ya ce "Wai Mufida kike tamabaya?" Harara ta watsa masa tare da cewa, "Annan gidan Mufida take da zan tambaye ka? ina 'yata inteesar take?" "Tana d'aki Ina zaton kamar barci ma takeyi doke ta tashi don ita muka zo gani." Mik'ewa yayi ya nufi d'akinta, koda ya shiga kwance ya same ta tana kuka? takaici ne yakama shi don yasan tabbas zasu gane inteesar tayi kuka, tsawa ya daka mata wanda hatta su Hajiya Bilkisu da suke falo sunji. "Ke dalla tashi dukanki akayi ki kuma me?da zaki zo kina kuka ga bak'i munyi salon kija Mani matsala ko?" Shiru tayi tunda ya fara magana "To bari kiji, muddin kika bari suka gane wata matsalar wallahi sai nayi masifar 'bata maki rai, dai kukan da zakiyi mai dalili ne, ki tashi ki shiga toilet ki wanke fuska kizo falo, mik'ewa tayi ta nufi toile shi kuma ya fita zuwa falon, bayanbta wanke ne ta nufi k'ofar zuwa falon. Tana bud'e k'ofar ne taga su Aunty Abla, da sauri ta sauri ta k'arasa gare su ta rungume Aunty Abla, sannna ta rungume Hajiya Bilkisu ta ce, "Oyoyo sannunku da zuwa, durk'usawa tayi ta gaida su cikin girmamawa. "Ina wunni?" Gaba d'ayansu suka amsa da " Lafiya k'alau inteesar" "Ido suka zuba mata ganin yadda ta d'an rame kuma ga fuskarta alamun taci kuka, mik'ewa tayi ta nufi kitchen don kawo masu abun ta'bawa, bayan ta nufi hanyar kitchen ne Aunty Abla ta kalli Muhdeen ta ce, "Ya naga yarinyar nan ta rame? bata da lafiyane." "Kafiyarta k'alau Aunty Abla." Jinjina kai tayi ba tare da ta ce komai ba, inteesar ce ta kawo masu ruwa da lemu ta ajiye zata koma kitchen Aunty Abla ta ce, "Ina kuma zaki?" "Zan kawo maku abinci ne" Murmushi sukayi dukansu inda Aunty Abla ta d'ora da cewa "Kada ki damu yanzun daga gidan Hajiya Bilkisu muke, sai da muka ci abincin kafin muka zo nan." Dawo wa tayi ta zauna Kan center carpet dake shimfid'e a wajen tana murmushi ta kwantar da kanta akan k'afar Aunty Abla sannan ta fara magana "Aunty Abla ba Wanda yazo gani na sai Gwaggo, ko Mummy da Umma na basu zo sun ganni ba." Murmushi Aunty Abla tayi tare da shafa gefen fuskarta ta ce, "Jiya munyi waya da Mummy ta ce da zaran Gwaggo ta koma zata zo ta duba ki, nasan da Gwaggo bata nan da tuni tazo ta duba ki, kuma Ummanki kinsan tana da kawaici ba lallai tazo yanzun ba kiyi hak'uri Mummy zata zo maybe gobe ko jibi" Shiru tayi tare da lamo akan cinyar Aunty Abla, shafa fuskar inteesar tayi abun mamaki sa taji sanyin hawaye a hannunta, kasancewar inteesar ta juyar da fuskarta gefe ba Wanda yaga hawayen da ke tsiyaya, lura da haka yasa Aunty Abla sa hannayenta ta goge mata hawayen, sanna ta ja hannunta zuwa d'aki ta ce, "Taso mu shiga ciki." Ba musu tabita suka shiga d'akin intesar tare da tura k'ofar, Muhdeen dai binsu da Ido yayi yana zullumin inteesar ta sanar da ita wani abu mara dad'i, Hajiya Bilkisu ma bayansu ta bi. A Kan gado Aunty Abla ta zaunar da inteesar ita ma ta zauna gefenta, zuba mata Ido tayi na tsawon mintuna biyu tana nazarinta, dai-dai lokacin Hajiya Bilkisu ta shigo d'akin bakinta d'auke da sallama, gaba d'ayansu suka amsa sallamar ta shigo ta zauna saman side drawer, Aunty Abla ta ce, "Daughter me ke faruwa?" Sunkuyar da kanta k'asa tayi "Bakomai Aunty Abla" Girgiza kai tayi "Akwai komai ki sanar dani, ba haka kike ba duk kin rame ga idanunki ma alamar kinci kuka,da alama kina cikin damuwa, nasan ba sonki yake ba zai iya musguna maki ba Wanda ya sani, shiyasa nake son ki sanar dani wata kila akwai irin taimakon da zan maki, yana dukanki ne? " Girgiza kai tayi alamar a'a "Yana zaginki ko cin zarafinki?" Nan ma kai ta girgiza alamar a'a "Akwai wani abu da yake maki Wanda baki so ne" Shiru tayi ba tare da ta ce komai ba, ganin bata da niyyar magana sai hawaye kawai dake fita daga idanunta yasa Aunty Abla janyo ta jikinta ta rungume ta tare da d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi. "Nasan kina cikin damuwa sosai duk da cewar ni kamar dangin miji ne a gare ki amma ina son ki d'auke ni matsayin uwa a gare ki, kamar yadda nake jinki kamar 'yar da na haifa a ciki na, kamar yadda ba zaki iya 'boyewa mahaifiyarki damuwarki ba haka nima kada ki 'boye mani yadda na same ki a haka zuciya ta taji ba dad'i, inteesar me ke damunki ya zamantakewarki da Muhdeen yake?" Goge hawayen fuskarta tayi ta shiga bawa Aunty Abla labarin zamansu tunda daga lokacin da yake bautar da ita da ayyukan da suka fi k'arfinta har zuwan Gwaggo Wanda lokacin ta samu 'yanci har zuwa yanzun da suke tare. Aunty Abla da Hajiya Bilkisu sun tausaya mata sosai, ajiyar zuciya Hajiya Bilkisu tayi tare da cewa "Kenan ba wani abunda ya ta'ba shiga a tsakaninmu na auratayya? Kai ta d'aga mata alamar eh Murmushi tayi tare da cewa "Ki k'ara hak'uri akan wanda kikayi a baya, da zaran ya shigo hannunki sai yadda kikayi dashi, saboda Allah ya baki wata irin baiwa wanda mijinki bai san da shi ba, amma da zaran ya San da hakan to wallahi kinfi k'arfin wulak'anci a wajensa, domin samun mace irinki yana da matuk'ar wahala kuma duk namijin da ya same ki kingama mallake zuciyarsa sai yadda kikayi da shi." Zuba mata ido Aunty Abla tayi kafin ta ce, "K'awa ta ta k'ara hak'uri zuwa yaushe? sai ta cigaba da zama cikin bak'in ciki da k'unci wanda ba'asan ranar wucewarsa ba?" "Kada ki damu nan bada dad'ewa komai zai zamo labari, idan kinyi nazari a cikin labarin da ta bayar ai zaki fahimci ya fara sha'awar kusantarta, tunda ya fara kuwa bai wuya zai shiga hannunta sai yadda tayi dashi." Kallon inteesar tayi tare da cewa "Duk ranar da ya nemi kusantarki kada ki k'ara guje masa kamar yadda kikayi a baya." Da sauri ta kalle ta "Eh hakan zakiyi ba ki da wani za'bi Daga alk'alamin ✍️ Zainab Abdullah K.N T (Maman Ihsan) Don Karin bayani 09065327995 Love you oll😍😘 Comments and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auran wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page5️⃣2️⃣ "Duk ranar da ya nemi kusantarki kada ki k'ara guje masa kamar yadda kikayi a baya." Da sauri ta kalle ta "Eh hakan za'ayi baki da wani za'bi" Tura baki tayi tare da cewa "Shifa ya ce baya sona kuma da zarar matarsa ta dawo gidan nan zai rabu da ni, to kuma mutumin da baya k'auna ta zan bawa kaina? ya raba ni da budurci na fa kenan sannan ya rabu dani." Ta k'arasa maganar tana sunkuyar da kanta k'asa, Dariya sukayi dukansu, Aunty Abla ta d'ora da cewa "Wa ya fad'a maki zai rabu dake?" "Shine da bakinsa ya fad'a mani fah." "Ya dai fad'a ne amma bai isa ya rabu da ke ba, domin rabuwa da ke tamakar bijirewa iyayensa yayi, kuma nasan shi yana da biyayya bazai iya bijirewa maganarsu ba, don haka idan kina tunannin zai rabu dake be to ki daina, kisan yadda zakiyi ki mallaki zuciyarsa kawai." "Nima fa ba sonsa nake ba, jira nake ya rabu dani kawai na koma gidanmu." Murmushi kawai Aunty Abla tayi tare da cewa "To kiyi ta addu'a duk abunda yafi zama alkhairi a gare ki Allah ya tabbatar maki da shi." Daga nan Hajiya Bilkisu ta bud'e jakkarta ta fito da wasu goruna guda uku, ta mik'awa inteesar d'aya kar'bi ki shanye shi nan da kwana uku safe da yamma zaki dinga sha." Ta d'auko wani goran ta mik'a mata ta ce, "Wannan rubutun kuma ki shanye shi yanzun nan ki bani goran." Ba musu ta kar'ba tare da yin Bisimillah ta shanye ta mik'a mata goran, sai ta mik'a mata cikon ta ukun tare da cewa "Wannan zumar kuma zaki sha cokali d'aya a rana, sai kuma washe gari sau d'aya ake sha a rana saboda yana da k'arfi." Jakarta ta bud'e ta fito da wani turare ta ce, "Wannan dai kinsan irinsa na tsugunno ne, na maki amfani da shi lokacin kina gida na." Ta ciro wasu ta ce "Wad'annan turarurruka ne da sabulun wanka ki dinga amfani da su kowane lokaci." Nasiha suka k'ara mata da shawarwari suka k'ara bata hak'uri, sannan sukayi suka tafi, har zata raka su suka ce ta yi zamanta komawa tayi ta kwanta. A falo suka samu Muhdeen yana waya, ganinsu yasa ya katse kiran tare da cewa "Aunty har kun fito?" Hajiya Bilkisu ce tayi masa sallama ta fice, yayin da Aunty Abla ta zuba masa ido ba tare da ta ce komai ba, tunani ya shiga yi ko dai inteesar ta kai k'ararsa ne? bai gama tunani ba ya ji murayar Aunty Abla na cewa "Son kaji tsoron Allah yarinyar nan inteesar amana ce a wajenka, kamar yadda ba'ayi shawara da kai ba aka d'aura maka aure da ita haka itama, ba'ayi shawara da ita ba aka aura mata kai, hak'uri zakayi da ita ko baka sonta ka kyautata mata ka sauke duk wani hakki nata da Allah ya d'ora maka, kada kaga cewa ita waccan soyayya ce ta had'aku ka fifita ta akan inteesar, Allah yana ji kuma yana ganinka kuma zai tambaye ka, kafa ka tashi a ranar tashin alk'iyama 'barin jikinka yana karkata, ka sani kake sani, bata kowa sai ta baro gidan iyayenta saboda kai kada ka wulak'anta ta." Daga nan bata sake magana ba tayi ficewarta, don har ga Allah taji zafin abunda yakewa inteesar a baya, musamman da ta tuna cewa farkon aurensu ya dinga wahalar da ita ba tausayawan alhalin bata masa laifin komai ba. Cikin sanyin jiki ya koma kan kujera ya zaun, yana tunanin maganganun da Aunty Abla ta sanar da shi kuma yasan tabbas bai kyautawa inteesar ba, a d'an zamansa da ita ba wani abu na kyautatawa ko adalci da ya mata, sai musguna mata da wahalar da ita da yayi, kuma yasan tabbas a halin yanzun idan ya ce zai kwatanta adalci a tsakaninsu to za'a samu matsala da Sumayya, domin sai da ya sanar da ita cewa inteesar kamar mai aiki ce aka kawo mata ba kishiya ba kuma ko kallo bata ishe sa ba sannan ta yadda ta dawo, tunda ba abunda ta iya inteesar ce zata dinga mata. Mik'ewa yayi ya nufi d'akinta, tura k'ofar d'akin yayi ya shiga da sallama, d'agowa tayi da sauri ta kalle shi cike da fargabar me zai biyo baya, ta dai san arziki da alkhairi baya sa ya shigo d'akinta, idan ya shigo to wani muguntar be zai mata, a zuciyarta ta ce, na shiga uku me kuma nayi masa ya biyo ni d'aki na? ko dai aikin wahalar ne zan cigaba tunda Gwaggo ta tafi, sannan wannan ne karo na farko da ya shigo da sallama a d'akinta, cikin sanyin muryarta ta ce, "Wa'alaika salam" K'arasowa yayi gabanta ya ce, "Wace magana kukayi da su Aunty Abla?" Gabanta ne ya fad'i amma sai ta dake ta ce "Bakomai" Zuba mata Ido yayi yana karantarta kafin ya ce, "Akwai yanayin maganarta ya tabbatar mani da cewa akwai maganar da kika fad'a mata, wato ke baki iya rik'e sirrin gidanki ko?" "Ba abunda na fad'a mata ta ce,wai na rame ne " Shiru yayi sannan ya d'ora da cewa "Mata ta dai ta dawo yau, saboda haka kiyi mata biyayya a matsayinta na uwar gida wacce kika zo kika tarar, dole ki girmama ta,bayan haka kuma ko a shekaru ba tsaranki bace ta girme maki nesa ba kusa ba, sannan kuma ita ta taso daga gidan iyayenta bata aikin komai masu aiki ke mata gyaran d'aki da girki bata komai sai dai ayi mata bata iya ba, kuma ni bana son ace 'yar aiki zata girka abincin da zanci, kuma bana son ace 'yar aiki zata shiga ta gyara mani bedroom, shine nake neman alfarma a wajenki da ki dinga taimaka mata da ayyukan tunda bata iya komai ba, kinga matsayin ya take a gare ki shekarunta talatin ke kuma shekarunki goma Sha takwas kinga ai ta cancanci kiyi mata ko?" Shiru tayi tana nazari ba tare da ta ce, komai ba, ganin shirun nata yayi yawa ne yasa shi cewa "Kinsan cewa na tsani shariya ko?" Ahiyar zuciya ta sauke ta d'ora da cewa "Zan iya mata gurkin abincin da zata ci kuma na wanke kwanikan da ta ci, amma gaskiya bazan iya zuwa na gyara mata d'aki na wanke toilet ba." Zuba mata ido yayi kafin ya ce, "Saboda me? kinfi k'arfin haka ne?to ki kafin a aura mani ke ni nake wannan aikin ballantana ke." Murmushi tayi ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "Ballantana ni 'yar talaka ko? nasan abunda zaka fad'a kenan, matarka ta gama zagin iyaye na kaima yanzun zaka d'ora daga inda ta tsaya." Ta k'arasa maganar tana goge k'walla da suka taru mata a ido. "Ki kika fad'i haka, kuma na gama yanke shawara dan haka umarni na baki dole kiyi." Daga nan yasa kai ya bar d'akin, a falo ya tarar da Sumayya da alama shi take nema, tana ganinsa ya fito daga d'akin inteesar ta tamke fuska ranta a 'bace ta ce, "Baby me kaje yi a d'akin wannan kucakar yarinyar?" "Naje sanar da ita ayyukan da zata yi ne." Hannunta yaja suka nufi bedroom d'insa. Haka rayuwa tayi ta tafiya, kullun inteesar idan ta idar da sallar asuba bata kowa ta kwanta, zata fara gyaran gidan idan ta gama ta shiga kitchen da had'a masu breakfast, bayan ta kammala ne lokacin da suka tashi daga barci zata shiga bedroom d'insu ta gyara masu, su kuma su zauna suna breakfast, duk randa zata shiga ta gyarawa Sumayya d'aki zara tarar ko ina a hargitse da kaya hatta kayan jikinta idan ta cire anan zata barsu zube a k'asa, ko kuma a watsa su saman gado. 'Dakun Muhdeen ne dai idan ta shiga bata shan wahalar gyarawa, domin komai a tsari yake yinsa ko kayan datti ne zai zuba a basket dake cikin toilet suke zuba kayan datti, idan mai wanki da guga yazo a had'a masa. Wata rana bayan inteesar ta gama aikin gidan, har da breakfast ma ta kammala masu,shiru shiru taga basu fito ba kasancewar wani lokacin Muhdeen na zuwa Asibiti da safe yasa tayi tunanin ko ya wuce ne, bayan ta gama gyara masa d'akinsa ne ta nufi d'akin Sumayya don ta gyara mata, tunda wani lokacin ko Sumayya na barci inteesar na shiga ta fara wanke mata toilet d'inta, don haka ta tura k'ofar tare da cewa "Assalamu al..." Bata k'arasa yin sallamar ba ta dakata sakamakon abunda ta gani, Sumayya ce daga ita sai Bra da pant tana zaune akan cinyar Muhdeen, yana sanye da boxer kamar zasu shuge jikin junanasu, k'arar k'ofa ne ya dawo da hankalinsu gare ta, kallo d'aya tayi masu ta kauda kanta gefe tare da cewa "Kungarce ni, na shigo maku a lokacin da bai dace ba." Daga nan ta fita taja masu k'ofar,Sumayya ce ta kalli Muhdeen ta ce, "Wannan banzar yariyar jaka haka aka fad'a mata ana shiga d'akin ma'aurata ba neman izini? idan na fita wallahi sai tayi nadama." Kallonta yayi tare da cewa "Baki ga ta baki hak'uri ba?" "Hak'uri da ta bayar bai isa yasa next time kada tayi ba." "To idan ba hak'uri ba me zaki mata?" "Dukanta zanyi gobe ba zata sake ba." "Kada ki ta'ba 'yar mutane kinji na fad'a maki,don banga abun dukanba." Yana fad'ar haka ya janye ta d'aga k'afarsa, jallabiyarsa ya saka ya nufi d'akinsa, a falo ya hange ta zaune tana kallon T.V kallo d'aya yaui mata ya janye idanunsa daga kallonta. Da misalin k'arfe goma na dare Sumayya tana zaune gaban dressing mirror tana kwalliya, k'ananun kaya riga da wando ne a jikinta, kayan sun matse ta sosai duk suffar jikinta a bayyanne, bayana ta gama kwalliyar ne ta d'auki mayafinta k'arami ta yafa ta d'auki wayoyinta ta saka a hand bag tana k'ok'ari ta d'auki hand bag sai Muhdeen ya turo k'ofat ya shigo, rungume ta yayi ta baya tare da cewa "Baby wannan irin kwalliya haka kamar zaki fita?" Janyo ta yayi bayan ya zauna akan gadon sai ya zaunar da ita akan cinyarsa ya ce "Duk wannan kwalliyar ni kikayiwa haka?" Juyo da fuskarta yayi da niyyar sumbatarta sai tayi saurin janye fuskarta ta ce, "Kai fa wallahi ka cika jaraba nifa nan shirin zuwa party nayi?" Da sauri ya kalle ta "Shirin Ina kikayi?" "Party nace Mana, kaga ma su jumy suna k'ofar gida suna jira na." Da mamaki yake kallonta ya ce "Ba zaki je ba saboda ina da buk'atarki." "Ai dama kai kullun cikin buka'ta kake, ka cika takura,ni kuma wallahi tunda na shirya zuwa party sai naje ." "Ina mijinki kike fad'awa haka?" "Ai dole na fad'a maka gaskiya na fad'a, tun kafin ka aure ni ina zuwa, kuma aurenka bazai hanani zuwa ba,don idan nayi niyyar abu sai nayi bana sauraron kowa." Daga nan ta fice da mamaki ya bita da kallo, mik'ewa yayi ya nufi d'akinsa, don dama shi mai yawan buk'atar mace ne, take mararsa ta fara masa ciwo,Kan gado yayi rub da ciki. Inteesar kuwa tana d'akinta tayi shirin kwanciya barci, wayarta ta fara ringing dubawa tayi taga Mufida ce da mamaki ta zubawa wayar idanu ta ji gabanta ya fad'i, d'agawa tayi tare da cewa "Assalamu alaikum, Mufida lafiya kuwa kira da daddaren nan?" Ajiyar zuciya Mufida tayi tare da cewa "Amma bakiji abunda ya faru ba ki?" Cikin tashin hankali ta ce, "Me ya faru Mufida, dan Allah ki sanar dani mana" 'Dan jima tayi sannan ta ce, "Inteesar kinsan kuwa Ummanki ba lafiya sosai tana kwance a gadon Asibiti na general hospital." Gabanta ne ya fad'i rass jefar da wayar tayi duk ta rud'e ta rasa inda zata bi,hijabinta ta janyo ta saka a guje ta nufi hanyar fita har zata fice sai kum ta tuna bata sanar da mijinta ba, don haka ta nufi d'akinsa. Knocking tayi har sau uku shiru, yana nan yana fama da ciwon mara,jin knocking yasa ya gane inteesar ce don yaji k'arar tashin motar Sumayya, hamdala yayi a zuciyarsa don yasan ya samu mafita, dak'yar ya iya cewa ta shigo, da sallama ta shigo d'akin hangisa tayi yana juye-juye daga gani baida lafiya, a guje ta k'arasa ta ce "Yaya baka da lafiya ne?" 'Dago rinannun idanunsa da suka rikid'e zuwa ja ya kalleta, gyad'a mata kai kawai yayi. Cikin tausayawan irin nata ta ce "Sannu yaya Allah zai baka lafiya kasha magani.?" "Cikin muryarsa da bata fita sosai ya ce "Kece maganin" Bata ji me ya ce ba ta ce, "Dama nazo ne na nemi izininka zanje Asibiti Umma ta ce bata da lafiya, tana kwance a Asibiti." Girgiza mata kai yayi "Dare yayi bai kamata ki fita ke kad'ai ba " "Cikin muryar kuka ta ce "Yaya dan Allah ka taimaka mani ka kaini naganta ko hankali na zai kwanata" Da hannu ya mata alama da ta zo kusa da shi, ba musu ta k'arasa hannunta ya rik'e "Zan taimaka maki na kaiki amma bisa sharad'i" Da sauri ta ce "Wane sharad'i Yaya?" "Nima ina buk'atar taimakonki, idan kika taimaka mani nima zan taimaka maki na kaiki, idan kuma kika k'i to ba zan ta'ba kaiki ba kuma ba zakije b kwata-kwata." Kuka ta soma tana cewa "Na amince da kowane sharad'i indai zaka kaini naga Umma na." Hijabin jikinta ya cire ya janyo ta zuwa jikinsa ya rungume, bakinta da nasa yake k'ok'arin had'awa nan ta soma kicinuyar k'wacew, kallonta yayi tare da cewa "Cikin sharad'i kike, bijire mani dai-dai yake da rashin zuwanki wajen Ummanki, ko baki son zuwa?" Kai ta gyad'a masa alamar tana so "To don haka ki barni nayi abunda zanyi sai mu tafi kinji ko?" Cikin sanyin muryar kukanta ta ce, "To na bari?" Daga alk'alamin✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love u oll😘😍 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auran wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page5️⃣3️⃣ "Cikin sharad'i kike, bijire mani dai-dai yake da rashin zuwanki wajen Ummanki, ko baki son zuwa?" Kai ta gyad'a masa alamar tana so. "To don haka ki barni nayi abunda zanyi sai mu tafi ko?" Cikin sanyin muryarta ta ce, "To na bari" Had'e bakinsu yayi wuri d'aya, yayi ya fara tsotson la'b'banta yake shiga yi, matse bakinta tayi yadda bazai samu damar tsotsan bakin nata ba, hawaye ne kawai yake tsiyaya daga idanunta, harshensa yasa ya shiga lashe hawayen dake tsiyaya daga idanunta ya ce, "Pls ki daina kukan nan kinji bana so?" Kai kawai ta gyad'a masa ba tare da ta ce komai ba. "Ki kwantar da hankalinki bazan cutar da ke ba" Kai kawai ta gyad'a masa, tana ji tana gani ya raba ta da kayan jikinta, tana jinsa ta rintse idanunta daga ita sai bra da pant, lokacin da yake k'ok'arin 'balle bra d'inne ta rik'e masa hannu, cikin sark'ewar murya ya ce, "Kiyi hak'uri kinji?" Lokacin da ya rabata da bra d'in hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba, ganinsu yayi kamar an hura balon balon gasu tsaye kyam basu rankwafa ba bare su zube ba irin na Sumayya ba, gasu kamar ya ta'ba auduga, gaba d'aya ya fara fita hayyacinsa baisan sanda ya fara tsotson dukiyar fulaninta ba da suke a tsatstsaye kamar jaririn da yake jin yunwa, haka ya dinga tsotson brest d'inta d'aya yana murza d'aya tsawon lokaci ya d'auka yana luguiguita ta son ransa, cikin hikima da dabara ya raba ta da pant d'in jikinta, shafarta yake yi tun daga samanta har k'asanta, hankalinsa yakai k'ololuwar tashi. Inteesar bata tashi ankarew ba sai da taji yana karanto addu'ar saduwa da iyali, nan ta son k'ok'arin k'watar kanta amma ina aikin gama ya gama, wani razanannen k'ara ta saki, sakamakon azabar zafin da taji a k'asanta, hannayenta tasa tana ture shi amma ina bai san ma halin da take ciki ba, ya lula wata duniyar da bai ta'ba zuwa irinta ba, sai gurnani da sambatu yake yi wanda baima san yana yi ba, tsawon lokaci ya d'auka yana wahalar da ita sai sambatu kawai yake yana sa mata albarka da sambatun dad'i, tun tana kuka tana ture shi har takai ta kasa motsi, bai tashi ankarewa da halin da take ciki ba sai da yaji bata motsi ta suma, ban d'aki ya nufa ya had'a mata ruwan zafi a bahon wanka dawowa yayi ya sungume ta kamar wata jaririya, cikin bahon wankan da ya cika da ruwan zafin ya saka ta wani k'ara ta sake saki zata tasahi ya zaunar da ita tare da cewa "Sannu" Kanta ta kawar gefe tana yarfa hannu alamun zafi take ji. "Kiyi hak'uri hakan zaisa kiji d'an dama damar jikinki." Ruwan ya canza kala zuwa ja saboda jinin jikinta, sau uku yana canza mata ruwan zafi, sai da ya tabbatar ruwan ya ratsa ta har ta had'a zufa sannan ya barta hakanan sai sannu yake jera mata ko kallonsa bata son yi, zuba mata ido yayi sannan ya ce, "Yanzun sai kiyi wankan tsarki, ki tsarkake jikinki kin iya ko?" Kai kawai ta gyad'a masa ba tare da cewa komai ba, sai hawaye da ke zuba a idanunta. "To kiyi wankan Ina zuwa" Fita yayi inda ya koma ya cire zanin gadon da ya 'baci,ya shimfid'a sabo, ya nufi toilet da wannan, koda ya shiga ya same ta ta kammala tana k'ok'arin mik'ewa ya k'ara da sauri zai taimaka mata, sai ta koma da sauri ta zauna tare da sunkuyar da kanta, ya fahimci kunyar ya ganta ba kata take,don haka ya fita ya bata wuri, yana fita ta mik'e a hankali towel da ta gani ne ta d'auka ta d'aura, dak'yar take tafiya tana d'an bud'e k'afa har yanzun bata daina tsiyayar da hawaye ba, a hankali ta bud'e k'ofar ganin yadda take tafiya yasa ya mik'e ya nufi k'ofar toilet d'in d'aukanta yayi kamar jaririya, akan gadon ya ajiye ta ya fita, kai tsaye kitchen ya nufa ya had'a mata tea ya koma bedroom d'in magani ya d'auko ya yazo gefenta ya zauna tare da mik'a mata maganin da tea. "Kar'bi Kisha zai taimaka maki wajen rage zugin da kike ji." Maganin ya 'ballo ya bata ya ce, "Kar'bi kisha ko na baki ruwa ko?" Kar'ba tayi tare da had'iye maganin sannan ta mik'a masa, matsa mata yayi da ta shanye tea d'in sannan ta kalle shi da idanunta da sukayi jazir suka kumbura ta ce, "Ka ce zaka kaini wajen Umma na ida..." Kasa k'arasa maganar tayi don ya mata nauyi a baki, murmushi yayi tare da cewa "Kinsan yanzun k'arfe biyun dare kuwa? ki bari sai gobe." Kuka ta saka masa ta ce, "Amma alk'awari ka d'auka cewa idan na taimaka maka zaka kaini." "Na sani ai zan kaiki da safe amma yanzun ki kwanta ki bari sai gobe da safe muje." Kafin tayi magana ne ya d'auke ta ya kwantar da ita tare da ja mata bargo, toilet ya koma sai da ya wanke zanin gadon sannan yayi wanka ya dawo ya haye gadon, cikin bargon ya shige tare da janyo ta a jikinsa ya rungume, k'ok'arin janye jikinta tayi amma bau bata damar hakan ba, hannu yasa ya rage hasken d'akin sannan ya ce, "Kiyi hak'uri inteesar kada kiyi kuka gobe insha Allah zan kai ki, kinga yanzun dare yayi, amma da zaran kin tashi da safe zamu tafi." Sauraronsa take har yakai k'arshen zancensa, tunda take da shi bai ta'ba mata magana cikin taushin murya ba sai yau bai ta'ba lalla'ba ta ba sai yau, tana cikin tunani ne taji ya ce, "Wani asibiti aka kaita?" "General hospital Mufida ta fad'a mani." "Kada ki damu zansa a d'auko shi daga can a kawo shi Asibitinmu." Cikin sanyin murya ta ce, "To" Ji tayi yana cewa "Thank you so much for your help, Allah ya maki albarka hak'ika ke ta daban ce a cikin mata,kin sakani cikin farin ciki da Nisha'i kin jiyar dani dad'in da ban ta'ba jin makamanciyarsa ba a rayuwa ta, ina son ki fad'a mani duk abunda kike so nayi maki shi zan maki, ko mene ne matuk'ar bai da'bawa Addinin musulunci ba, ko na siya maki." Shiru tayi bata ce komai ba, sumbatarta yayi a goshi sannan ya ce, "Nagode , idan kinyi tunanin tukuicin da zan baki ki sanar dani, dan kin cancanci haka daga gare ni." Haka yayi ta surutunsa shi kad'ai har barci ya d'auke ta, shi kuma yana ta tunanin halin da ya kasance da ita a daren yau,yarinyar da ya tsana ya wulak'anta bai d'auke ta a komai ba ashe 'yar baiwa ce murmushi yayi yana kallonta yayin da take jin wani abu na fisgarsa kan yarinyar, shima barcin yayi basu farka ba sai da aka kira sallar asuba farkawa tayi ta jita kwance a jikin mutum ga towel d'in duk ya warware , ta mance ba kaya a jikinta sai ta tashi zaune da sauri ta janyo towel d'in ta d'aura, idanunsa a kanta wani lallausan murmushi taga ya sakar mata wanda bai ta'ba mata irinsa ba,kauda kai tayi don bata ma son ganinsa, kallon mugu take masa mara tausayi. "Kiyi wanka kiyi sallah bari na d'auko maki wani kaya a d'akinki." Fita yayi ita kuma ta shiga toilet ta watsa ruwan zafi ta d:auro alwala, bayam tayi fito ya mik'a mata kayan ya shiga toilet d'in, saka kyan tayi tana k'ok'arin saka hijab ya fito jallabiyarsa ya saka ya nufi masallaci. Sai k'arfe shida ya dawo,ya tarar da ita tana barci, kitchen ya nufa ya had'a mata breakfast, tea ne da kwai ya soya mata, yana kitchen Sumayya ta shigo, ta bayansa ta rungume shi ta ce "Gud morning my love" Kamar bazai amsa ta ba dai ya ce "Morning" "Me kaje yi a kitchen zan wuce na hangoka, ina wannan yarinyar take ne da zaka shiga kitchen da kanka?" ,A takaice ya amsa mata da "Bata d lafiya" "To nikan ba abunda zan iya yi ko ciwon ajali take ta fito ta had'a Mani breakfast." Wani banzan kallo ya watsa mata ya ce "Saboda baiwarki ce ko?" Cikin tashin fahimta ta ce "Wannan ma sun maka yawa muje muci ko?" Kallon da taga ya mata sai da hanjin cikinta suka kad'a, don bai ta'ba mata irinsa ba, kai tasye d'akinsa ya nufa ya shige. "Wallahi bazai yiwu ba ai kullun tare muke cin abinci sai yau ka ce a'a? sai na bika. Kai tasye ta nufi hanyar bedroom nasa . *KUYI HAK'URI DA WANNAN BA YAWA* Daga alk'alamin✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😍😘 Comments and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auran wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page5️⃣4️⃣ "Wallahi bazai yiwu ba ai kullun tare muke cin abinci, sai yau kace a'a? sai na bika." Kai tsaye ta nufi hanyar bedroom nasa, turewa tayi taji k'ofar a datse alqmar ya rufe daga ciki, knocking ta fara yi tare da cewa "Dan Allah kayi hak'uri nasan na 'bata maka rai, ne yasa kake fushi dani." Yana jinta yayi mata banza,ajiye farantin da ya jero masu breakfast yayi ya zuba mata Ido tana barci amma tana sheshshek'ar kuka, tausayinta ne ya kama shi duk da cewar ya tsani yarinyar baya jin sonta a zuciyarsa amma yanzun baya jin wannan k'iyayyar a yanzun sai ma tausayinta, yana tuna yadda ta dinga kuka tana rok'onsa ya k'yaleta a daren jiya ya tuna sumar da tayi ta daina motsi, shi kansa yasan cewa da badon tana son ya kaita wajen Ummanta ba da bazai same ta cikin sauk'i ba don yasan ba zata batshi ma ya ta'ba jikinta ba ballanta har ya kai ga biyan buk'atarsa da ita, rashin lafiyar da yayi amfani dashi ne ta hanyar nuna mata cewa idan bata barshi ba to baza ta je wurin Ummanta ba. Jin yadda Sumayya ke dukan k'ofar tana kiransa kuma yasan zata iya tayar da inteesar daga barci yasa ya k'arasa jikin k'ofar ya fara magana. "Kinga bana son damuwa don Allah ki kyale ni, idan har kuma kika cigaba da takura mani wallahi idan na bud'e k'ofar nan zaki sha mamaki, ina matsayin mijinki ina da buk'atarki kiyi fatali dani ki fita dadaddare kije party ba tare da izinina ba, ki kwana a can saboda rashin sanin darajar aure da kimar mijinki, a k'ullace nake dake ki kiyaye ni ko nayi maki abunda baki ta'ba tsammani ba." Baki sake take sauraronsa don tunda take dashi bai ta'ba 'daga mata nurya ba sai yau, kuma koda ya buk'ace ta ta hana shi baya fushi da ita da safe zai sake lalla'ba ta don ta yarda dashi, amma yau sai taga baima damu da ita ba, sai maganar banza da yake fad'a mata, tunawa da tayi tasan waye shi da kansa zai dawo yana lalla'ba ta shiyasa ta nufi d'akinta ta kwanta don batayi barci jiya ba. Yana jin k'arar tafiyarta yayi tsuki,k'arawa yayi jikin gadon tare da zama gefen inteesar,gashin kanta ne da ya zubo ya rufe mata fuska ne ya gyara mata gashin zuwa baya tare da shafa gefen fuskarta, firgigit ta farka ganinsa yana mata murmushi yasa ta ja baya cikin tsoronsa tana girgiza masa kai hawaye na fita daga idanunta. Murmushi yayi mata tare da cewa "Kinga ki kwantar da hankalinki ba abunda zan maki,kinji." Kai kawai take gyad'a masa kamar wata k'adangaruwa, don tsoronsa ne sabo ya dirar mata musamman idan ta tuna azabar da ya jiyar da ita a daren jiya. "Tashi kiyi brush kiyi breakfast ko?" "Ni Umma ta nake son gani." "Nasani kuma can zan kaiki yanzun ki tashi kiyi abunda na ce kiyi sai kiyi wanka mu tafi." Mik'ewa tayi dak'yar don ji tayi jikinta na mata ciwo, mudammna k'asanta dak'yar take tafiya, kallon yanayin tafiyar mata yayi ya ce, "A haka zamu tafi kina tafiya a bud'e? duk Wanda ya kalle ki yasan akwai matsala, ko zaki bari naje ni kad'ai ne na duba jikinta zuwa gobe idan kin warke sai mu..." Bai kai k'arshen zancensa ba ta sakar masa kuka mai tsuma zuciya. "Kinga ya isa kiyi hak'uri zamu tafi yanzun nan, je kiyi ki fito." Shiga cikin toilet d'in tayi sabon brush ta bud'e ta fara amfani da shi. Shi kuma wayarsa ya d'auka ya kira Jabeer don ya tabbatar an d'auko Umma daga general hospital an kaita asibitinsu, nan Jabeer ya sanar dashi cewa eh yanzun ma zai shiga ya duba ta, sallama suka yi katse kiran, Janyo farantin yayi ya d'auki k'aramin flask na ruwan zafi ya tsiyaya mata a kofi ya zuba mata milo da madar da suga, dai-dai lokacin da ta fito a hankali ta zauna tana d'an jije le'be, sannubya mata tare da mik'a mata kofin tea girgiza masa kai tayi alamun ba zata sha ba ganin yadda ya had'e fuska yasa ta ka'ba slice bread ya mik'a mata ta da soyayyen k'wan da ya soya. "Zan shiga nayi wanka, ki tabbatar kin cinye su sannan kije d'akinki kiyi wanka ki shirya mu tafi." Daga nan ya shige band'akin,jin zasu tafi yasa ta fara shan tea d'in, duk da bata jin dad'in bakinta amma tasan idan bata ci ba zai iya cewa an fasa zuwa, don haka ta tuttura ta bar sauran, tashi tayi ta nufi d'akinta tana tafiya a hankali har ta isa d'akinta, toilet ta shiga ta k'ara gasa jikinta da ruwan zafi sannan tayi wanka, bayan ta fito ne ta sanya riga da siket na atamfa, ba tayi wani kwalliya ba powder kawai ta Shafa a duskarta, sai turaren da ta fesa ta saka hijab har k'asa ta d'auki hand bag d'inta ta saka takalimi, wayarta ta saka a cikin jakkar ta fara takawa a hankali, ganin yanayin tafiyar nata bata iya tafiya yadda ya kamata ne yasa ta cire wannan takalmin da take da tsini, flat shoe ta saka ta fara tafiya a hankali don har yanzun duk da ta k'ara gasa jikinta da ruwan zafi amma har yanzun tana jin zafi a k'asanta musamman idan tana tafiya, lokacin da ta k'araso bakin k'ofar ne ta bud'e ta fita. 'Dakinsa ta nufa da sallama ta shiga cikin sanyin muryarta. "Assalamu alaikum" Yana tsaye sanye da shadda sky blue, agogo yake d'aurawa a hannunsa ya amsa da. "Wa'alaiki salam" Ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "Na shirya" "Me yasa kika shafa turare tunda kinsan fita zakiyi kuma wasu mazan zasu ji k'amshin turaren ya burge su? ko baki san cewa haramun ne matar aure ta saka turare mai k'amshi yayin da zata fita unguwa ba?" "Na mance ne na fesa" "To kada ki sake matuk'ar ba kina cikin gida bane." Da mamaki ta kalle shi tana tambayar zuciyarta me wannan mutumin yake nufi da ita ne, cewa tayi "Insha Allah bazan sake ba" Murmushi yayi mata tare da cewa 'Dakyau mar'atu saliha" Ita dai bata sake magana ba har ya k'araso wajenta, hannayensa biyu ya sa ya zagaye k'ugunta da su, ido ya zuba mata yana kallonta lokaci d'aya yana jin yarinyar har k'asan zuciyarsa, manna ta yayi da jikinsa har k'irjinsu na gogan na juna, narai-narai tayi da ido kamar zatayi kuka ganin hakan yasa ya sake ta ya ce, "Mu tafi" Tana gaba yana binta a baya yanyin tafiyar tata ya gani sai a hankali, baiso hakan ba amma ba yadda ya iya tunda ya mata alk'awari zai kaita, idan bai kaita ba gaskiya bai mata adalci ba, da kansa ya bud'e mata murfin motar ta shiga, shima ya zagaya ya zai shiga ne ma'aikatan gidan suka k'araso suna gaishe shi, amsa yayi cikin sakin fuska sannan ya shiga yaja motar suka nufi asibitin. A can Asibiti kuwa d'akin da aka kwantar da Umman inteesar na musamman ne, don mutum d'aya ne a cikin gadon mara lafiya da goguwar kujera na zaman mutum uku da da fridge sai T.V dake manne a bangon d'akin ga sanyin A.C dake tashi, gaban gadon mara lafiyar akwai kujera da ake ajewa saboda masu jinyar mara lafiya, Mama Huraira k'anwar Umma ce ke zaune a d'aya daga cikin kujeran, don dama ita ce ta kwana da ita take jinyarta, Umma na kwance tana barci k'arin ruwa aka d'aura mata don har ledar tayi rabi, Mufida na zaune akan doguwar kujera tana chatting da wayarta, don ita ce Mummy ta aiko ta kawo masu breakfast. Turo k'ofar akayi aka shigao tare da sallama, inteesar ce da Muhdeen, Mufida tana ganin aminiyarta a guje ta tashi ta nufe ta tare da rungume ta ta mak'alk'ale ta, janyo inteesar tayi da k'arfi don su shiga cikin d'akin su zauna kan kujera, kasancewar inteesar bata iya tafiya da k'arfi yasa ta d'an wash tare da cije baki ta coge wuri d'aya, ganin hakan yasa Muhdeen dakawa k'anwar tasa tsawa. "Ke mahaukaciyar ina ce haka? kin d'auka yadda kike biri-biri haka kowa yake? ba zaki bita a hankali ba?" Cikin shagwa'ba yasa ta ce, "Haba yaya me nayi na hauka kuma daga na tarbe ta? sai ka fara fad'a? "To haka ake tarbar mutum a garinku? baki san bata da lafiya bane?" Inteesar ce ta k'arasa gaban k'anwar Ummanta cikin girmamawa ta gaishe ta, Mama Hure ta amsa mata cikin fara'a, Muhdeen ma ya k'araso ya durk'usa ya gaida Mama Hure tare da mata ya mai jiki, ta masa masa da cewa da sauk'i, duba ruwan da aka d'aura mata yayi tare da duba magungunan da yaga an ajiye a sama durowar da ke gefen gado, kallon Mama Hure yayi tare da cewa zai d'an fita kafin ta tashi sai su gaisa. "Mufida ya su Mummy da Gwaggo" Kauda kanta tayi tare da tura baki, ya gane nufinta tayi fushi ne fad'ar da ya mata ne don haka ya ce, "My lovely sis ya kika kyale ni ne?" "Ba kaine ba yanzun ka daina so na" Dariya yayi yaja hannunta suka fita, ita dai inteesar zama tayi ta zubawa Ummanta ido tayi tana tausaya mata ganin yadda ra rame. Tana nan zaune sai ga Mummyn Muhdeen da Gwaggo sunzo, mik'ewa tayi da niyyar zuwa ta taro Gwaggo sai taji bazata iya ba saboda yanayin tafiyarta, bayan sun k'araso ne ta durk'usa ta gaishe su, Mummyn Muhdeen ta ce, "Daughter ya kike fatan kina lafiya" Sunkuyar da kai tayi ta ce , "Alhamdulillah" Gwaggo ce ta mik'ar da ita tsaye ta ce, "Tashi 'yar albarka, ya Kuna lafiya ina jikan nawa?" Kafin ta yi magana ne Muhdeen ya shigo rik'e da hannun Mufuda yana cewa "Gani nan kaka ta ya kike?" Fuskarsa d'auke da tsantsar farin ciki, musamman da yaga Gwaggo ya tuna cewa ita ce silar aurensa da inteesar, ada haushin Gwaggo yake kan ta aura masa inteesar amma a yanzun yasan gata tayi masa, ta aura masa irin maccen da yake mafarkin samu, gashi tasan darajar miji bata masa gardama, murmushi yayi Gwaggo ta zuba masa ido ta ce, "Kai kuma fara'ar me kake ne?" Ba tare da ya ce komai ba ya durk'usa ya gaida Mahaukaciyarsa. "Mummy ina kwana?" Lafiya qalau son ya iyali da aiki?" "Alhamdulillah" Umma ce ta bud'e idanunta tare da kallonsu d'aya bayan d'aya, Inteesar ta k'arasa gabanta ta ce, "Umma ya jikinki?" Murmushi tayi tare da rik'e hannun inteesar ta ce, "Naji sauk'i" "Umma wallahi hankali na ya tashi sosai da naji baki da lafiya" Murmushi tayi "Ki kwantar da hankalinki naji sauk'i" Muhdeen ne ya durk'usa ya gaida Umma ta amsa masa cikin sakin fuska tare da masa godiya, don an fad'a mata shine yasa a dawo da ita nan. Jabeer ne ya turo k'ofar ya shigo da sallama, ganin Muhdeen yasa ya ce, "Alhamdulillah, dama zan kira ka ne kazo ka duba wasu patients da suke buk'atar kulawarka." Kallon mamaki Muhdeen ya masa ya ce, "Da banzo Asibitin ba waye zai duba su, to nikam ina..." Kafin ya k'arasa yaji muryar Mummy tana cewa "Dama Dadynka nason ganinka, sau uku yana zuwa asibitin nan baya ganinka sai dai Jabeer, ka fara wasa da aikinka kana barin Jabeer da aiki shi kad'ai, don haka ka koma kamar da bana son rashin mauda hankalinka kan aikinka, ko kana da wani aiki ne bayan wannan?" "Kuyi hak'uri Mummy za'a gyara" Da misalin k'arfe d'aya na rana Inteesar da Mufida suka nufi masallacin da mata suke shiga suyi sallah, bayan sun idar ne kasancewar su biyu ne a cikin masallacin yasa Mufida cewa "Wai ni me damunki ne naga kina tafiya a gwale kamar 'yar kaciya." Kai ta girgiza alamar ba komai "Akwai komai mana sai dai idan bai cancanci na sani ba." "Haba Mufida kinsan ba abunda zan 'boye maki, ina tausayin kaina ne." "Tausayin kanki kuma bayan naga Yaya na yana sonki" "Injiwa ya fad'a maki yana so na?idan akwai waccr ya tsana nine?" "Meye dalilinki?" "Zan fad'a maki amma sirri na ne,kada Wanda ya ji" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Yayanki baya so na ya tsane ni, tun ranar farko da ya dawo daga k'asar waje kik kira ni na gaishe sa naga tsanar da ya mani, dalili na ne ranar kema ya kore ki, duk da cewar kusan kullun Ina gidanku, idan na gaishe sa baya amsawa sai ya buni da harara, sai dai idan yaga idon mutane yake amsawa, akwai ranar da banida lafiya kika kira ni a waya nazo na gidanku wai Gwaggo na nema na, a ranar bansan yana nan ba naje zubar da yawu bisa rashin sani watsa masa, maruka biyu ya bani wanda ban ta'ba jin zafin makamancinsa ba, lokacin da yaga ba kowa falonku ni kad,'aice na kwanta saboda rashin lafiyar da nake haka ya kira ni d'akinsa ya saka ni wankin kayan a toilet nasa, zanyi amfani da washing machine ya Hana na wanke da hannu, sannan yasa ni na shanya kayan a rana sannan nayi gadin kayan a cikin rana har sai sun bushe, haka nayi sannan ya ce na goge su, hantara kala-,kala yake mani baku sani ba a cikin gidan, ki da aka d'aura mani aure da shi ya ce na d'auka zaman gidan kurkuku nake, a daren farkon da aka kaini ba irin cin mutuncin da baiyi mani ba, ya ce kuma sai ya sake ni, haka ya dinga bautar dani da ayyukan da suka fi k'arfi na, baya son na huta idan yaga na kwanta Ina barci ba aiki ba haka zai d'auko ruwan sanyi a fridge ya watsa Mani a jiki na, na farka a gigice, idan zan canza kayan zai hana a haka zasu bushe a jiki na." Mufida ce ta fashe da kuka ta rungume ta a jikinta sannan ta ce, "Shine baki fad'awa kowa ba?" Kuka itama tasa ta ce "Bzan iya ba ina jin tsoronsa ada haka da matarsa ta dawo nice nake komai a gidan na gurka mata abuncin da take son ci, sannan na gyara mata d'akinta da gadonta na wanke mata toilet d'inta." Daga alk'alamin✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😘😍 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auran wawa. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page5️⃣5️⃣ "Bazan iya ba ina jin tsoronsa ada, haka da matarsa ta dawo nice nake komai a gidan na girka mata abincin da take son ci, sannan na gyara mata d'akinta da gadonta na wanke mata toilet d'inta." Tsuki Mufida ta ja tare da cewa "Kina jin tsoronsa shine kika tsaya ya mayar da ke tamkar baiwarsa shi da matarsa, kika zauna kina masu bauta? baki da wanda zaki fad'awa ne ko da ace baki fad'awa kowa ba ai zaki k'watarwa kanki 'yanci ne, amma ki zauna kamar wata mara galihu? Ki ce kina tsoronsa yana da wutar saka ki ne?" Dafe goshinta tayi cike da takaici tace, "Wallahi inteesar ki bani kunya, haba mana idan nice ke wallahi koda a ce ban fad'awa kowa zan iya fad'a maki saboda amintan da ke tsakaninmu, ba abunda zan iya 'boye maki kema na d'auka haka ne a wajenki ashe yanzun bankai can ba kin sauke ni a mizanin da kika d'aura ni ada." Girgiza kai inteesar tayi idanunta cike da k'walla ta ce, "A'a Mufida wallahi ba haka bane, bamu 'boyewa juna komai wannan karan abunda yasa ban fad'a maki ba saboda ke k'anwarsa ce, zaki iya zuwa ki fad'awa mahaifiyarku kuma hakan zaisa ya sami matsala da iyayensa, ni kuma bana son a ce saboda ni ya samu matsala da iyayensa bazan so hakan ba." "Aiko sai na fad'awa Mummy bazan zuba ido ina ganinki cikin damuwa da bak'in ciki ba, dole na fad'a asan abunyi domin rayuwa ba zata yiwu a hakan ba, domin kuwa ke ba baiwa bace." Hawayen da suka cika mata ido ne suka samu nasarar zubowa ta ce, "Kinga wannan maganar da mukayi tsakaninmu ne ki d'auke shi a matsayin sirri, don Allah ina neman alfarma a wajenki da kada ki fad'awa kowa maganar nan, kiyi mani alk'awari don Allah." Girgiza kai Mufida ta yi "Gaskiya bazan maki wannan alk'awari ba, domin a wuri na wani abu ne mai kamar wahala." Hannayenta biyu rik'o cikin nata ta ce, "Kada ki damu yanzun ba kamar da bane, inteesar d'in da kika sani a da to yanzun ba ita bace, cin kashin da sukayi mani a da na d'auka to yanzun bazan d'auka ba na canza." Murmushin takaici Mufida tayi tare da cewa "Yaushe kika canza? ke d'in da na sani ce zaki iya canzawa? bank'i ba dai idan yanayi ya saki canzawa, idan kuma ba ya sonki ne gara a raba ku da ya dinga cutarki a banza a wofi, zaki samu mai sonki ya aure ki kiyi rayuwa mai dad'i, Ina fatan dai ba wani abun da ya shiga tsakaninki da shi na fannin auratayya ko? don a cikin labarin da kika bani banga alamar hakan zai iya faruwa ba ko?" Kuka mara sauti ta saki tare da goge hawayenta ta ce, "Mufida aikin gama ya riga da ya gama." Da mamaki ta kalle ta "Ban gane aikin gama ya gama ba, kina nufin a cikin wannan halin da kike ciki kika iya bashi kanki?" Cikin muryar kuka ta ce "Bani da za'bi Mufida, ko kece a cikin wannan yanayin da nake ciki dole ba yadda zaki iya" Tsuki ta ja "Dalla can gafara, har akwai wani yanayin da nake ciki da zan bari ya mori jiki na irin wannan zamantakewar? shi fa ya ce baya sonki kuma zai rabu dake, wato idan ya ci moriyar ganga kenan sai ya yada koranta ko? idan ya gama dake ya mayar dake fanko sannan zai rabu dake ki koma gidanku, duk mijin da ya aure ki fanko ya aura, wallahi ka fad'a mani haka ne zan amince da kai kina abu kamar ba wayayya ba." "Mufida wannan abun fa jiya ne ya faru, idan kin kula bana iya tafiya yadda ya kamata, kuma bani da za'bi yayi amfani ne da rashin lafiyar Umma ta ya d'auke shi a matsayin makami, bayan kin kira ni a waya kin sanar dani shine naje don neman izininsa, ya nuna mani idan ban amince da shi ba to bazan je na gaida Umma na ba, kuma ina son zuwa na ganta hankali na ya tashi bansan halin da take ciki ba, dole na barshi yayi yadda yake so." "Aikin banza dan ya d'auki wannan a matsayin makami shine kika yarda da shi? ya same ki ne shiyasa." Murmushin takaici inteesar ta yi tare da cewa "Asalin samu kuwa, Mufida wallahi ya wahalar dani a daren jiya nasha azaba a hannunsa har na gwammaci mutuwa ta, tun ina gane komai har nazo bana ganewa ban k'ara sanin me ke faruwa ba sai tsintar kaina nayi a band'aki cikin ruwan zafi, ashe suma nayi tsawon awanni hud'u ya d'auka yana wahalar da rayuwa ta, tun k'arfe goma har k'arfe biyun dare." "Koma mene ne kika jawo wa kanki, lallai namiji ma fa bashi da kunya." Girgiza kai kawai tayi ba tare da ta k'ara cewa komai ba, inteesar dai zuba mata ido tayi tana ganin cewa lallai Mufida k'awa ta gari ce mai son farin cikinta, gashi dai Muhdeen yayanta ne amma bata goyi bayansa ba a matsayin d'an uwanta ba. Hira suka d'an ta'ba daga nan suka mik'e suka nufi komawa d'akin da aka kwantar da Umma. 'Bangaren Sumayya kuwa bata tashi daga barci ba sai k'arfe d'aya da rabi, yunwa ne ya addabe ta sosai don tun lokacin da Muhdeen ya korr ta sai ta koma d'akinta ta kwanta, shine bata fsrka ba sai yanzun toilet ta shiga tayi wanka, bayan ta fito ne ta saka kaya ba zancen sallah ma, ta nufi kitchen don a tunaninta Inteesar ta gama girkin abincin rana. Kai tsaye dinning room ta fara nufa, gani tayi wayam ba'a jera komai ba don haka ta tsaya a falo ta rik'e k'ugu cikin bala'i ta ce, "Lallai ma yarinyar nan wato na tashi daga barci banga ta gyara mun d'aki na ba, kayan da na cire na zubar da su a k'asa suna nan har yanzun, toilet ma bata wanke mani ba,sannan nazo na tarar bata gama girki ba wato yunwa ta kashe ni ko?" Girgiza kai tayi tare da k'walawa inteesar kira cikin masifa "INTEESAR! INTEESAR!! INTEESAR!!!" Jin shiru ne yasa tayi kwafa ta nufi kitchen d'in a fusace, tana shiga tayi turus tayi ganin kitchen d'in wayam ba alamar ma anyi girki, ranta a 'bace ta furta "Lallai ma yarinyar nan wuyanta ya isa yanka, ubanwa ta ajiye da zai mata aikin da bata yi ba? lallai yau zanyiwa yarinyar nan wulak'ancin da ban ta'ba yi mata ba." Kai tsaye ta nufi part d'in Inteesar, dan zuwa d'akinta, da k'afarta ta bankawa k'ofar duka, k'ofar ta bud'e ta shiga ciki tare da cewa "Ke 'yar matsiyata ubanwa za..." Dakatawa tayi da maganar da tayi niyar yi sakamakon ganin k'awatuwar d'akin inteesar d'in, kasancewar yau ne rana ta farko da ta fara shigowa d'akin, ganin furniture's masu tsada da aka zuba mata ga d'akin yasha gyara sosai komai na d'akin abun sha'awa ne, ta'be baki tayi tare da cewa "Ina wannan ba iyayenta bane suka sayi mata wannan kayan d'akin, don ba suda kud'in siye mata su, bayan naji ance uban nata dankali yake siyarwa bazai iya siyen ko kwatankwacin kayan nan ba sai dai idan iyayen Muhdeen da suka had'a auren ne suka siye mata, ganin ba kowa yasa ta k'arasa bakin k'ofar toilet ta k'wank'wasa jin shiru ne yasa ta nufi hanyar fita. Bata zame ko ina ba sai k'ofar d'akin Muhdeen,tura k'ofar tayi tare da shiga,har toilet ta shiga bata ganshi ba tambayar kanta tayi da cewa "Ina yaje ne kuma?" Idanunta ya sauka akan gyalen d'an kwalin inteesar dake gefen gado, sai kuma d'an kunnenta guda d'aya shima a saman gadon, gabanta ne ya fad'i Wanda sai da taji wani abu kmar dutse ya danne mata k'irji. "Me nake shirin gani ne haka? me d'an kwalain yarinyar nan yake yi. d'akin nidai nasan bazai ta'ba nemanta ba don bai d'auke ta a mace ba, wata kila ta shigo gyara masa ne d'an kunnen ya fad'i ta mance d'an?" kwalinta. "To wai Ina my love ya je ne? d'an jim taui tare da k'arewa d'akin kallo tayi sannan ta fice ga uban yinwa da ke cinta kuma ita bata iya girka komai ba ki ruwan zafi ba zata iya dafawa ba, rasa abunyi tayi Dan haka ta nufi d'akinta wayarta ta d'auka wayarta number Muhdeen ta shiga kira yakai sau biyar tana kirnsa bai d'aga ba dan haka ta ajiye wayar ta shiga tagumi tana mamakin sauyawar da Muhdeen yayi daga jiya zuwa yau ya canza mata sosai da sosai, fita tayi tare da Kiran Direban gidan ta aike shi yayi mta takeaway ko zata samu abincin da zata ci. Inteesar da Mufida suna komawa wajen Umma suka tare ta farka, da farin ciki inteesar ta k'arasa wurinta ta rungume ta. "Umma na ya jikinki?" "Da sauk'i kunyi sallar?" "Eh munyi Umma" Mufida ce ta ce "Sannu Umma ya jikinki?" Murmushi ta yi "Da sauk'i Mufida" Kallon gefen su Mummy tayi tare da cewa sannu "Sannunku Gwaggo" Gwaggo da Mummy suka had'a baki wajen amsawa, sai a lokacin idanunta ya sauka akan Muhdeen, tana kallonsa taga ya zuba mata ido yana kallonta tare da sakar mata lallausan Murmushi, da sauri ta d'auke kanta tare da tura baki, karaf akan idanun Ummanta sai dai tayi shiru tunda tana fama da kanta,Mama Huraira ce ta ce da inteesar "Inteesar tunda kika zo banga kinci komai ba, kina ta zama da yinwa." Murmushi ta yi tare da cewa "Mama Huraira na k'oshi" Muhdeen ne ya kalle ta ya ce "Me kika ci da kika k'oshi? biyo ni mu tafi office d'ina kici abinci" Kunyar mutanen da ke wurin ne ya kama inteesar, shi kuma baiga abun jin kunya a wurin ba, fita yayi ta zauna kamar bata ji me ya ce ba, Mama Huraira ce ta kalle ta ta ce, "Ba kiranki mijinki yayi ba?" Tura baki tayi ta ce "Nifa na k'oshi" Had'e fuska Mama Huraira ta yi tare da cewa "Bana son gardama" Dan haka dole ta fita, tsaye ta same shi yana jiranta, Dan haka suna fita ya rik'e hannunta yaja suka fara tafiya hannunsu sark'e cikin na juna sunyi kyau sisai, tayi k'ok'ari ta k'wace hannunta amma ina ta kasa da haka ta bishi suka dinga tafiya a hankali, duk inda suka wuce mutane sai an kalle su yadda suka dace da juna, kasancewarsa Doctor da aka sani yasa mutane ke ta gaishe su, ita dai ko amsawa bata yi, har office d'insa suka nufa suna shiga ya tura k'ofar ya rufe , wayarta ce ta soma ringing ta ciro daga cikin jaka ganin sunan Usman ne yasa gabanta ya fad'i, har ta katse bata d'auka ba sau uku yana kira bata d'aga ba,ganin yanayinya yasa ya gane akwai wani abu . "Ya ana kiran wayarki baki d'agawa." "Eh kiran baida mahimmanci ne." Take sai ga wani kira ya shigo, duba sunan me kran yayi Usman, take ya murtuk'e fuska don ya tuna cewa Usman ne saurayin da ke son inteesar, lokacin da Mummy ta matsa ya je gidansu inteesar ya gaishe ta Usman ya kad'e ta da mota, kuma shine wanda ya ta'ba kama ta tana waya da shi bayan aurensu har ya amshe mata wata gaba d'aya, kuma shine ya gansu ya d'auko inteesar a gaban motarsa tana tayi masa dariya shima yana mata kallon soyayya, take yaji wani d'aci a ransa har idanunsa suka rikid'e suka koma ja, text message ne ya shigo wayar ya mik'a mata hannu tare da cewa "Bani wayar nan" Shiru tayi tare da zuba masa ido banu alamar tsoronsa a tattare da ita kmar yadda ta saba tsoronsa, don haka itama sai ta had'e fuska kamar yadda ya had'e nashi fuskar. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman k'arin bayani* 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa, ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* Page5️⃣6️⃣ --------Shiru tayi tare da zuba masa ido ba alamar tsoronsa a tattare da ita, kamar yadda ta saba tsoronsa, don haka itama sai ta had'e fuska kamar yadda ya had'e nashi fuskar. Fusgar wayar yayi daga hannunta dai-dai lokacin da sak'o ya shigo ya fara karantawa kamar haka. "ASSALAMU ALAIKI YA SARAUNIYAR MATA, DAN ALLAH KI DAINA AZABAR DA NI HAKA, KINSAN HALIN DA NA SHIGA NA RASHIN GANINKI KUWA? YANZUN HAKA INA K'OFAR GIDANKU ANCE BA KOWA A GIDAN, DAN ALLAH KI TAIMAKA KI 'DAUKI WAYA TA KO ZANJI SANYI A ZUCIYA TA, DOMIN RASHINKI A RAYUWA TA TAMKAR JIRGIN SAMA NE BABU MATUK'I, I LOVE YOU." Bayan ya gama karantawa ne ya kalle ta tare da cewa "Wato har yanzun kina waya da tsohon saurayinki da igiyar aure na akanki ko?" Murmushin takaici tayi ta ce, "Igiyar aurenka yana wuyar matarka da ka baro a gida, dan ni ba igiyar aurenka a kaina, zaman da nake a gidan kurkukukun gidanka k'addara ta ce kuma tazo k'arshe da yardar Allah, dan zama da kai ya zama tsautsayi da k'addara, jiranka kawai nake ka sauwak'e mani naje na auri masoyi na mai son farin cikin rayuwa ta ba irinka ba mugu azzalumin mutum mai bak'ar zu..." Kafin takai k'arshen maganar da tayi niyar fad'i sai ta ji saukar mari tass a gefen fuskarta, idanunsa gaba d'aya sun rikid'e sun koma jajir kamar garwashin wuta jikinsa har rawa take ya ma kasa magana sai kallonta take, itama dafe kumatunta tayi tana kallonsa sam bata ji zafin marin da ya mata ba, saboda bak'in ciki da ta k'unsa masa lokaci guda ya gusar da zafin marin, ko ba komai zuciyarta tayi fari tunda ta zama sanadiyar 'bacin ranta, fita yayi a fusace kai tsaye ya nufi office d'in Jabeer. Bayan fitarsa itama ta nufi k'ofar fita ta janyo k'ofar ta jita a datse, ya rufe ta ya tafi da key d'in, komawa tayi ta zauna kan kujera mai zaman mutum uku tare da fashewa da kuka. Jabeer na k'ok'arin fita da file a hannunsa Muhdeen ya shigo, ganin yanayinya yasa ya koma ya ajiye file d'in tare da k'arasawa kan kujerar da Muhdeen ya zauna, dafa kafad'arsa yayi tare da cewa "Bross ya akayi ne? wa ya ta'bo ka ne?" Uffan baice masa ba, shima yasan bazai tanka masa ba, don yasan halinsa dama idan har aka 'bata masa rai baya iya magana duk juyin da za'ayi kuwa bazai ta'ba magana ba idan ransa ya kai k'ololuwar 'baci, ba abunda yake tunawa kamar kalamanta da take cewa jira take ya sake ta ta auri wanda yake son farin cikinta ba irinsa ba mugu azzalumin mutum mai bak'ar zuciya, rintse idanunsa yayi tunawa da kalamanta, shi kansa ya yarda cewa yana jin son yarinyar a cikin zuciyarsa,bawanda baisan sanda son nata ya samu gurbi a cikin zuciyarsa ba. Haka Jabeer ya dinga lalla'ba shi da kwantar masa da hankali har fushin nasa ya d'an sauka, Jabeer ne ya fita yayin da shi kuma ya d'an kishingid'a akan kujerar. 'Bangaren inteesar kuwa tana nan sai da taci kukanta ta k'oshi tukunna sannan ta tashi ta fara dube-dube ko zata samu key ta fita amma ina bata samu ba, ganin akwai bedroom a ciki ne yasa ta shiga, toilet ta fad'a ta d'auro alwala tazo ta yi sallah, bayan ta idar da sallar ne ta d'an jingina da jikin gadon ta lumshe ido kamar mai barci bayan ba barci take ba idanunta biyu, bata san lokacin da ya shigo ba k'arar ajiye abu taji ta bud'e idonta da sauri, ganinsa ta yi tsaye a gabanta fuskarsa ba yabo ba fallasa, kallon ledar da ya ajiye mata tayi takeaway ne yayo mata, fridge ya nufa ya bud'e ya ciro mata lemo da ruwa masu sanyi ya ajiye mata tare da zama bakin gadon ya ce, "Ga abinci nan kici, na tuna tun tea da kika sha da safe baki ci komai ba gashi har yamma tayi." Duk da itama kanta masifaffen yunwar take ji sosai amma sai ta dake ta ce, "Bazanci ba?" Girgiza kai yayi tare da cewa "Kinsan irin 'bacin ran da kika saka ni ciki kuwa? tunda nake a rayuwa ta ba wacce ta ta'ba tsayawa a gaba na ta fad'a mani irin munanan kalaman da kika fad'a mani ba, kece mutum ta farko da kika gaya mani maganganun da suka matuk'ar sosa mani zuciya, kuma na kasa d'aukar matakin da ya kamata na d'auka akanki, saboda kece kawai amma wallahi da wani ne ko wata ce da abinda zanyiwa mutum bazai ta'ba mantawa ba." Murmushin takaici tayi tare da cewa "Ni me yasa ka kyale ni?" "Saboda yadda nake jinki a raina, bansan yaushe ne ko kuma a ina be ba, amma kuma abunda na sani shine ina sonki a yanzun." Da sauri ta kalle shi cikin mamaki ta ce, "Wallahi baka sona ka tsane ni, In banda abunka me zakayi da kucaka? ko ka manta ne?" Dafe goshinsa yayi don ko ya mata bayani ba yadda zata yi ba. "Ki bani daman a karo na biyu zan gayara kuskure na." Bata ce komai ba ta had'a kanta da gwuiwa kamar ba da ita yake magana ba. "Waye wannan Usman d'in tsohon saurayinki? akan me zai dinga kiranki a waya kina matar aure?" "Bai san cew nayi aure bane?" "Me yasa baki sanar da shi ba bayan kinsan hakan ba dai-dai bane a matsayin matar aure ta dinga waya da wani namiji da ba muharraminta ba a waya suna soyayya?" Ta'be baki tayi "Ni wannan ban d'auke shi aure ba, shiyasa ban fad'a masa ba don banyi kama da matar aure ba." Dariya yayi tayi sosai kamar ba shi ba, duk da cewar bai cika dariya ba shiyasa ta zuba masa ido tana kallonsa, ganin yadda dariyar tayi masa kyawu sosai har wushiryarsa sanda suka fito, kwantaccen sajen da yayiwa fuskarsa k'awanya ta zuba ma ido suman fuskar bak'i wulik ya kwanta luf akan kyakkyawar fuskarsa, kansa ma a cike yake da suma Wanda ke shan gayara kwanta tare da d'an kanannad'ewa sai shek'i suke, gaba d'aya ta shagala da kallon kyakkyawar fuskarsa, sai da taji ya tsagaita da dariyar sannan ta d'auke idanunta akansa. "Wato kina nufin baki d'auki kanki a matar aure ba ko? saboda abu d'aya ko? wanda ake aure dominsa, dam ci da sha da sutura da lafiya duka an d'auke maki shi a gidanku ba sune aure ba saduwa tsakanin miji da mata ne kad'ai ya rage wanda matar aure zata nuna maki ko? to kada ki damu Dan wannan shima daga jiya ai kin zama cikakkiyar matar aure ko? to kada ki damu yanzun aka fara, dama bawai ya isheni bane gani nayi kin suma yasa na barki haka nan, kuma yau naga kamar baki warke ba ko kin warke ne yanzun ma na d'ora daga inda na tsaya?" Ya k'arasa maganar yana zare mata hijab tare da janyo ta a jikinsa, kiciniyar k'wace kanta tayi amma ta kasa, kuka ta saka masa kuka tana cewa "Ni wallahi ba abunda nake nufi ba kenan, kuma idan wannnan ne aure to na hak'ura da auren tunda ba farilla bane auren." Daiya yayi "Matsoraciya ko ba farilla bece aure ai sunnah ce mai k'arfi, kuma wahalar da kika sha ranar ma saboda na farko ne a rayuwarki, dole zakiji wannan zafin amma yanzun ba zaki ki ba." Sake ta yayi ya d'auka kedar tekeawa ya bud'e, cokali ya saka ya d'ebo abincin da niyyar kaiwa bakinta ta juyar da kanta gefe, naman kazar ma bata ci ba ba yadda bai lalla'ba ta ba ga yunwa tana ji amma tak'i ci, haka ya k'yale ta ya maida ya rufe sannan ya ajiye. Janyo ta jikinsa yayi tare da yin kissing nata ta ko ina, bata yi aune ba kawai ji tayi ya raba ta da kayan jikinta, k'ok'arin cire mata bra yake yi ta rik'e da k'arfi tare da fashe masa da kuka, ganin ta rik'e bra d'in da k'arfi bata da niyyar sakewa kawai sai taga ya yaga mata bra d'inta, haka ya dinga tsotson breast d'inta kamar ya samu sweet, haka ya dingayi yasha wannan ya luguiguita wannan, haka ya dinga tsotson la'b'banta tare da zura harshensa cikin bakinta, haka ya fara rikita ta da salonsa, tun tana kiciniyar k'wacewa har itama jikinta ya fara amsa sak'onsa, wani yanayi ta tsinci kanta Wanda bata ta'ba tsintar kanta cikinsa ba sai yau cikin wani irin murya ta ce, "Yaya ka bari wallahi bana so, akwai zafi ban warke ba wallahi idan ka k'ara mutuwa zanyi." Dak'yar maganarsa ke fita cikin wata kasalalliyar murya ya fara magana "Ki kwantar da hankalinki ba abunda zan maki, ina son ne na samu relief a jikinki, idan kuma kika nemi mani gardama to zan maimaita abunda anyi a daren jiya da kika ce da zafi, jin hakan yasa ta k'yale shi sai da ya luguiguita ta son ransa sannan ya k'yaleta ya mitgina gefe yana fitar da numfashi mai k'arfi. A can d'akin da aka kwantar da Umma kuwa Gwaggo ce da Mummy suka tashi tafiya, Mufida ma ta ce zata bisu ta dawo da safe, tunda Mama Huraira ce zata kwana da ita, Abba ne ya shigo da sallama, suka gaisa da su Mummy lokacin ya dawo daga kasuwa ya zo, bayan sun gaisa ne su Mummy sukayi masu sai da safe don k'arfe shida na yamma tayi, Mufida ce ta ce, "Mummy ina son naga inteesar kafin mubtafi" "Mufida kenan yanzun Ina zaki ganta, tunda son ya fita ta bishi ai bata dawo ba" "Eh Mummy sun dad'e tun k'arfe biyu yanzun k'arfe shida awa hud'u fa kenan, yakamata ace sun dawo." Kallon mamaki Umma tayi mata ta ce, "To ke ina ruwanki ba suna tare ba ai ba abun damuwa." Girgiza kai tayi tare da cewa "Mummy ki kira shi ya dawo da ita mana." Gwaggo ce ta kalle ta da mamaki ta ce, "Yau naga d'ibar albarka, ke wace irin jidalalliyar d'iya ce? ance suna tare da mijinta ki damu ya dawo da ita, idan ya dawo da ita uwar me zata yi anan d'in? ita fa yanzun matar aure ce ke da baki son kiyi auren sai ki ta galbaro akan titi, so kike ta bar mijinta tazo ta zauna dake kuyi ta karad'in banza?" "Haba Gwaggo daga nayi magana sai ki dinga zaro zance haka? kamar dama kina jira na ne? " Haka dai suka tafi amma Mufida taso taga inteesar kafin su tafi, dan haka da suka kawo dai -dai office d'in Muhdeen Mufida ta kalli Mummy ta ce , "Yauwa ga office d'insa nan ko mu d'an tsaya ne zan bawa Inteesar sak'o." Gwaggo tayi saurin cewa "Yauwa kira shi dama maganin ciwon k'afa sun k'are ya bani wasu." Knocking Mufida ta dingayi ba'a bud'e ba,yana cikin bedroom nasa yana ji amma yak'i bud'ewa ita kuma inteesar tana ta addu'ar ya bud'e k'ofar ta fita, ganin ba shi da niyyar bud'ewa ne yasa ta ce, "Knocking ake fah" "Inaji ai bani da niyyar bud'ewa ne." Daga can waje kuwa Mummy ce ta kalli Gwaggo ta ce "May be baya ciki ne amma bari na kira wayarsa naji ko yana ina." Wayar ta ta ciro ta laluno number sa ta danna masa kira. Yana kwance sai numfashi yake saukewa don ba abunda yake da buk'ata illa Inteesar, tun jiya da ya d'and'ani zumarta gaba d'aya ya rasa nutsuwarsa ba shi da wani burin da ya wuce ya sake jinsa a cikin wannan kogin zumar da bai ta'ba tunanin jin irinsa ba, burinsa ya sake shiga wannan kogin dad'in amma ina dolensa ya barta sai ta warke raunin da yayi mata. Wayarsa ce ta soma ruri, bai duba ballantana yasan wa ke kiransa, sai da aka kira sau uku bai d'aga ba, kallon Gwaggo tayi tare da cewa "Son fa bai d'aga wayar ba mu tafi kawai Gwaggo, idan ya kira sai na sanar dashi ya kawo maki maganin ciwon k'afa." "Saboda ba k'afarki bace kuma baki san ya nake ji ba shiyasa kike fad'in haka ko? to ina nan har ya dawo ya tarar da ni a nan ya bani maganin." Mummy dai bata ce komai ba sai ta k'ara kiransa. Mik'a hannu yayi tare da duba wayar ganin Mahafiyarsa ce yasa ya d'aga tare da cewa "Barka da yammaci Mummy" Jin muryarsa wani iri yasa Mummy cewa "Son kana lafiya kuwa?" "Lafiya lau Mummy" "Ok to kana ina ne yanzun?" "Ina office d'ina " "To gamu a k'ofar office d'in" Daga nan ya katse kiran, k'ok'arin dai daita nutsuwarsa yayi ya gyara zama rigarsa sanna ya kalli inteesar da ke zaune ta had'e fuska ya kalla sannan ya mik'e ya fita, bud'e k'ofar yayi duk suka zuba masa ido, idanunsa sunyi ja na jaraba ga gefen bakinsa da inda janbakin inteesar ya shafi la'b'bansa, zuba masa ido sukayi yauinda Mufida ta ce, "Yaya ina Inteesar?" "Cikin sark'ewar murya ya ce, "Tana ciki, ina ganin kamar barci take yi ne." Mummy ce ta ce "Gwaggo tazo ka bata magani" Daga nan ya juya ya koma cikin office d'in Mufida tabi bayansa, Gwaggo ma haka ganin haka ne yasa Mummy ma ta shiga. Anya ma akwai maganin anan?bari na kira a kawo mani na baki, Kiran waya yayi ya fad'i sunan magungunan da za'a kawo masa, Mufida ce ta ce "Yaya banga Inteesar ba" Tana cikin bedroom barci take, karaf kuwa Inteesar taji maganar Mufida bata ma san tare da su Mummy take ba, da sauri ta diro daga kan gadon ta mane cewa kanta ba d'an kwali rigarta duk ta cukuikuye gashin kanta a yamutse zif d'in rigar ma a zuge take, haka ta k'araso wajensu ganin irin kallon da suke mata na zargi musamman Mufida da ke watsa mata kallon gargad'i,tunawa tayi da yadda ta fito sannan ta kalli fuskar Muhdeen taga shatin jan bakinta a bakinsa sai ta kwa'be fuska cikin shagwa'ba kamar zatayi kuka, Mufida ta ce "Ina nan ina ta jiranki ke miji dad'i kinzo kin tare a office nasa ko? Wato bakiji magana ta ba to kije ke kika sani duk abunda ya biyo baya." Mummy ce ta kalle ta ta ce "Me ke faruwa Mufida?" Kallon Muhdeen Mufida tayi tare da cewa "Komai ma ya faru." *Wash hannuna ya gaji* *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *Don k'arin bayani* 09065327995 Love you oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page5️⃣7️⃣ Kallon Muhdeen Mufida tayi tare da cewa "Komai ma ya faru." Kallon rashin fahimta Mummy tayi mata tare da cewa "Ina komai ya faru me kike nufi?" Kafin Mufida ta bud'e baki tayi magana Jabeer ya shigo office d'in a gigice wata nurse na biye da shi a baya, hannun Muhdeen ya janyo tare da cewa "Pls kazo da sauri an kawo Emergency ne, suna buk'atar taimakon gaggawa." Fita office d'in sukayi cikin hanzari, yayinda Mummy ke cewa "Allah ya basu lafiya ya tashi kafad'arsu." Gaba d'ayansu suka amsa da Ameen, idanun Mufida na kan inteesar kafin ta maida dubanta ga Gwaggo ta ce, "Kinga anyi masa kira gaggawa, gashi yamma tayi yakamata mu tafi tunda bamu San lokacin dawoarsa ba." Dai-dai lokacin da wata ta shigo da leda da magungunan Gwaggo a ciki Mufida ce ta kar'ba tare da mik'ewa Gwaggo "Kinga magungunaki an kawo." Kar'ba Gwaggo tayi tare da kallon Inteesar ta ce "Ke kuma abunda ya kawo ki kenan ko? Ko kunya bakiji wai kinzo duba jikin Mahaifiyarki kenan ko? cikakken mintuna talatin bakiyi ba tare da mahaifiyarki taki, da kika kwanan biyu baki gane ta ba ko?amma shi mijin da kullun kina ganinsa kullun tare kuke kwana amma a asibitin ma ba zakuyi hak'uri ba saboda tsabar jaraba irin..." Kuka inteesar ta sake tare da nufar Gwaggo zata fad'a jikinta ne ta dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu ta ce, "A'a ni kada ki k'araso waje na ki shafa mani najasa nasan ko wankan tsarki ma bakiyi ba." Jin kalaman bakin Gwaggo yasa Inteesar komawa jikin Mummy,rungume Mummy tayi tare da saka kuka, Mummy ma rungume ta tayi tare da d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi, tana shafa sumar kanta ta ce, "Kema kinsan halin Gwaggo ba tun yau ba, haka take kada maganarta ya dame ki." "Wallahi Mummy ba haka bane ba abuda mukayi." "Ba komai ba sai kin rantse ba koda ma kunyi ba laifi kika aikata ba mijinki ne." Tafa hannu Gwaggo tayi tare da cewa "Yau ni kuluwa naga abun mamaki, 'yar albarka yaushe kika zama haka da rantsuwar k'arya? ko makaho ya kalle ki yasan da walakin goro a miya." Mummy ce ta kalli Gwaggo ta ce, "Kinga Gwaggo don Allah kibarta haka nan baki ga yadda taji bane, ai ba komai zakiyi magana aka..." Kafin takai k'arshen maganar da zatayi Gwaggo ta ce, "Dalla ni rufe mani bak, dan na fad'i gaskiya zaki ce me yasa? Yarinyar da tazo dubiya na uwarta ko mintuna talatin batayi ba amma ta tare ta k'unshe a cikin ofishin miji sama da awa uku, tun lokacin da suka dawo sallar azahar fa gashi yanzun k'arfe biyar suna nanik'arki juna, 'yar k'aramar yarinya da ita sai jaraba, ni nasanta ko da naje gidansu nayi wata d'aya akwai ranar da na aike ta ta Kira mijinta muyi Karin kumallo tare, tunda ta shiga bata fito ba har yunwa taci ta cinye ni, sannan suka fito yamutsai yamutsai da ita, tunda yanzun an masa Kiran gaggawa ai sai ki koma wajen Ummanki kafin ya dawo." "Gwaggo nifa ba da son raina na biyo shi ba, cewa yayi yayi mije naci abinci da nak'i zuwa Mama ce tasa na biyo shi, kuma shi ya rufe office d'in da key ya hanani fita." Rarrashinta Mummy tayi har ta daina kukan sannan ta shaida mata cewa ta shiga toilet ta watsa ruwa ta kimtsa jikinta ta koma wajen Umma, idan ya dawo sai su tafi gida, sallama sukayi suka tafi suka barta. Bak'in ciki da takaici ne suka ishe ta,ga yunwa da ya addabe ta duk ta rasa yadda zatayi gaban dressing mirror ta tsaya ta gyara dogon sumanta tare da tufke shi, rigarta ta gyara zamansa ta rufe zif d'in rigar tayi bra d'inta da ya ya yaga gida biyu ta kalla d'agawa tayi taga ba yadda za'ayi ya moru, tsuki tayi tare da d'aukar hijabinta ta saka, ficewa tayi daga office d'in ta nufi hanyar da zara sada ta da d'akin da aka kwantar da Ummanta. Tura k'ofar tayi ta shiga da sallama Abbanta da Mama Huraira ta gani sai Ummanta da ke kwance amma ba barci take ba, koda idanunta ya sauka akan Abbanta farin ciki ne ya lullu'be ta, dama tunda tayi aure bata k'ara ganin Abbanta ba, saboda ranar da suka je Muhdeen cewa yayi ya bata mintuna talatin ta gaishe su ta fito,hakan yasa bata ga Abbanta ba sai yanzun a asibiti. Cikin farin ciki ta k'arasa gabansa tare da fad'awa jikinsa ta kwantar da kanta a kafad'arsa ta ce, "Abba na nayi kewarka wallahi sosai." Murmushi yayi tare da d'aga ta ya ce "Kina lafiya?" "Lafiya lau Abba na." "Masha Allah ko na kira wayarki bata shiga ko kin canza layi ne?" Tunawa tayi da tun ranar da Muhdeen ya kar'be mata waya bai bata ba, sai da Gwaggo ta amsar mata ranar da zata tafi, gashi yau ma ya amshe bata san ranar da zai sake bata. "Abba wayar ce bansan inda ta shiga ba amma da zaran na nemo ta zan dinga Kira muna gaisawa." Durk'usawa tayi ta gaishe da Abban nata ya amsa mata cikin so da k'aunar tilon 'yarsa, sannan ta k'ara gaida k'anwar Ummanta wato Mama Huraira, sannan ta k'arasa gaban gadon Umman nata ta durk'usa tare da rik'e hannun Ummanta ta ce "Umma ya jikinki?" Murmushi tayi tare da gyad'a kai almar da sauk'i, Mama Huraira ta kalle ta ta ce, "Tun d'azu da naga shiru baki dawo ba sai na d'auka ko dai kun tafi gida ne." Sunkuyar da kanta k'asa tayi tare da cewa "A'a Mama ." Tayi maganar a tak'aice tare da zama gefen gadon,fira suka dinga yi har sai da aka kira sallar magariba Abba ya tashi ya tafi masallacin, da ke cikin asibitin, kasancewar yanzun ba mutane a d'akin yasa Inteesar ta shiga toilet da ke cikin d'akin ta d'auro alwala ta fito ta shimfid'a sallaya tayi sallah, bayan ta idar ne Mama Huraira ta shiga ta d'auro tazo ta gabatar da sallar, bayan ta idar ta taimaka wa Umma ta rik'e ta sosai suka nufi band'aki ta taimaka mata tayi alwala suka fito ta saka hijab tayi sallah daga zaune. Bayan sunyi sallar isha'i ne Mama Huraira ta janyo Basket d'in da ke da sauran Abinci da Mummy ta kawo masu, Abba ta zubawa sannan sauran da ya rage ta ce da Inteesar ta d'iba ta ci, ganin abincin ba wani yawa ne da shi ba kuma ga Mama Huraira bata ci ba yasa ta ce ta k'oshi dan yinwar cikinta ma tun yana damunta har taji ta daina jinsa. Mama Huraira ta had'awa Umma tea don dama Mummy ta kawo masu kayan tea Gwangwanin Madara da na milo, da sugar da lipton da K'aton Bread, cewa tayi ba zata sha ba dak'yar dai aka shawo kanta tasha kad'an, sai ayaba da ta d'anci guda biyu, don ko Bread ma bata ci ba, Abba ne ya kalli Inteesar ya ce, "Ke yaushe zaki tafi ne ga shi k'arfe Tara tayi." "Abba ni nan zan kwana." "Mijinki yana da aiki dadaddare ne ko shine ya ce ki tsaya ki kwana a nan?" "Tunda aka kira shi bai dawo ba." Mama Huraira ce ta ce "Idan gana abunda yake zai biyo ya d'auke ki ku tafi." Fira suka dinga yi k'arfe goma nayi Abba yayi masu sallama ya tafi gida, don dama Mama Huraira ce zata kwana da ita Sai misalin k'arfe goma da rabi na dare ne Muhdeen ya shigo d'akin tare da sallama, Inteesar kama har lokacin ma barci ya soma d'aukarta, durk'usawa yayi cikin girmamawa ya gaida Mama Huraira da Umma tare da yi mata ya jiki, bayan sun gama gaisawa ne ya d'an zauna kan kujera tare da kallon Inteesar, yana son ya tayar da ita yana d'an jin nauyinsu Umma, lura da haka ne yasa Mama Huraira ta mik'e ta k'arasa inda take barci ta d'an ta'ba k'afarta tare da kiran sunanta, a hankali ta bud'e idanunta ta sauke akan Mama Huraira, sannan ta kalli Muhdeen tana ganinsa ta had'e fuska, jin muryar Mama Huraira taji ta ce, "Tashi ku tafi gida dare yayi." Tura baki tayi tare da cewa "Anan zan kwana." Had'e fuska Mama Huraira tayi tare da cewa "Tashi ki tafi gobe sai ki dawo" Ganin yadda Mama Huraira ta had'e fuska ne ta juya ta kalli Ummanta, ganin kallon da take mata yasa ta mik'e ta saka hijabinta, ta d'auki 👜 d'inta ta kalli Ummanta tare da cewa "Sai da safe Umma Allah ya baki lafiya" Sannan ta maida dubanta ga Mama Huraira ta ce "Mama na tafi sai da safe." Ta fice shima yayi masu sai da safe ya bi bayanta. Kafin su k'arasa parking space har dak'yar take tafiya don yunwa ya galabaitar da ita gaba d'aya jikinta ba k'arfi, ganin yadda take tafiya yasa ya ce da ita "Lafiya kike kuwa?" Share da tayi kamar bata ji shi ba, rik'o hannunta yayi cikin nasa ya ce "Da alama yunwa ce take galabaitar dake ko?" Nan ma bata ce komai ba kuma bata yi k'ok'arin k'wace hannunta daga rik'on da ya mata ba, don bata da wannan k'arfin don haka bata ce da shi komai ba har suka k'arasa parking lot da kansa ya bud'e mata murfin motar ta shiga, zama tayi tare da d'an kishingid'a ta wantar da kanta jikin kujera, tada mitar yayi yana cewa idan banda yiwa kai mugunta kizauna tun Karin kumallo safe har k'arfe goma sha d'aya ba dole yunwa ta cinye ki ba haka ya dinga magana a zuciyarsa shi kad'ai. Tada motar yayi suka bar asibitin, akan hanya ya tsaya ya siye masu gasassun kaji guda biyu da fresh milk mai sanyi, ita kam dama cigaba tayi da barcinta bata ma san ya tsaya ya siye kaji ba. Horn yayi mai gadi ya wangale masa gate suka shiga bayan yayi parking ne ya rasa ya zaiyi don haka ya sai ya bud'e murfin motar ya fito tare da zagayawa ta 'bangaren da take, bud'e Ganin yadda take ta barcinta ya sa ya sunkuya ya d'auke ta cak kamar jaririya firgigit ta farka tare da k'ok'ari ta sauka ya rik'e ta sosai ga jikin nata ba k'wari don haka ta hak'ura, da k'afarsa ya bud'e k'ofar falon ya shiga bakinsa d'auke da sallama ba kowa a falon, kai tsaye d'akinsa ya nufa da ita bai dire ta ko ina ba sai kan gadonsa, ganin d'akinsa ya kawo ta yasa ta kalle sa da mamaki tana cewa "Akan me zaka kawo ni d'akinka?" "Anan zamu kwana" Da mamaki ta kalle shi ta ce, "Anan zaku kwana kai da way?" "Nida matata mana" Ta juya kalli gabas da yamma ta ce "Banga matar taka anan ba, kuma ka sani ni bazan kwana d'akinka ba." "Badamuwa idan ba zaki kwana d'aki na ba, sai n biki muje mu kwana a d'akinki" "Allah ya kiyaye kaga tafiya ta kuma kada ka biyo ni." Ta mik'e kenan zata tafi sai taji wani jiri ya d'abe ta tayi luu zata fad'i yayi sauri rik'o ta cikin zafin nama ta fad'o jikinsa. "Kinga abunda nake fad'i maki, kink'i cin komai har sha d'aya a ce Karin kumallo na safe?shima ba na kikrki bane." Zaunar da ita yayi a bakin gadonsa tare da cewa "Yunwa ta galabaitar dake,idan kikayi yunk'urin tashi zaki fad'i ki jira ni Ina zuwa" Daga nan ya fice daga d'akin, cikin motarsa ya koma ya d'auko ledojin kazar nan da fresh milk ya ajiye tare da kallonta ya ce, "Sannu ko? ina zuwa ." Kitchen ya shiga ya d'auko plate da wuk'a da kofi ya dawo d'akin, ajiyewa yayi tare da sakar mata murmushi, had'e fuska tayi don wannan murmushin nasa ya ishe ta bata ma san kallon fuskarsa. Tunawa tayi da Sumayya don har ga Allah idan yana tare da ita mancewa ma yake da wata Sumayya, sai yanzun da suka dawo gida. Fita yayi ya nufi d'akin Sumayya da sallama ya tura k'ofar ya shiga, ba kowa sai dai du d'akin a hargitse a yamutse kayan da ta cire da wasu kayan ga sunan zube a Kan gadon, tunda yaga bata nan yasan part ta tafi, don haka ya fito ya koma d'akinsa. Shiga yayi tare d rufe k'ofar yasa key ya rufe tare da zare key d'in, ita dai Inteesar tana kwance yana dawowa ya taimaka mata ta tashi zaune, kazar d'aya ya saka a plate ya yayyanka ya tsiyaya fresh milk a Kofi. 'Dauka yayi zai kai bakinta ta kauda kai tare da tura baki,amsa tayi ta dinga ci da kanta don masifaffen yunwar d take ji ma ya ishe ta,sai da ta k'oshi ta kuma sha fresh milk tayi gyatsa sannan ta mik'e ta nufi k'ofar fita baice mata komai ba don yasan ya rufe k'ofar da key, taja taji a datse ta juyo sukayi ido hud'u da shi, tace, "Ka bud'e k'ofar zan tafi d'aki na." Bai kula ta ba illa rage kayan jikinsa da yayi ya nufi toilet don yin wanka, har ya kai bakin k'ofar toileta d'in ya juyo ya kalle ta ya ce, "Kizo muyi wanka mu kwanta ki, don sai gobe zan bud'e k'ofar nan tare zamu kwana shigi muyi wanka" Tura baki tayi ta ce "Bazanyi ba." Shigewa yayi ya barta nan tsaye. Har ya gama shirinda yasa kayan barci tana nan tsaye, kashe hasken d'akin yayi tare da nufar inda take tsaye, cak ya d'aga ta sai tsakiyar gado ya direta, yunk'urin tashi tayi sai ya d'an danne ta tare da yi mata rufa da k'irjinsa. "Wai me yasa kika cika gardama be? ki daina wahalar da kanki akan abunda kika san bazai yiwu ba, kinda dai ba zaki iya fita d'akin nan ba, why not ki hak'ura tunda kinsan baki da wani za'bi baikamta ki wahalar da kanki ba kinji." Ta bud'e baki dazummar yin magana ya saka bakinsa cikin nata tare da cafkar harshenta ya fara tsotsa, kuka ta saka masa daktawa yayi tare da zare bakinsa cikin nata cikin kuka ta fara magana tana cewa "Dan Allah ka bari yaya wallahi bana so." Meye baki so? ni kum ina so." "Wallahi akwai zafi idan ka maimaita mutuwa zanyi." "Ba zaki mutu ba da hakan zaki saba, kinga yanzun ba abunda zan maki yau zan d'anyi wasa dake ne na samu relief, kinga fa ina tausayinki don naga kinsha wuya sosai kuma zuwa gobe nasan kin warke, yau zan hak'ura amma fa ki sani daga yau bazan kuma hak'uri ba gobe insha Allah zan sake kar'bar hakkin aure na ne, gara ma ki fidda wannan tsoron da ke cikin ranki mu mori amarci, Inteesar bazan 'boye maki ba kinjinyar da ni dad'in da ban ta'ba jin kwatankwacin irinsa ba, ke 'yar baiwa ce a yanzun banida wani burin da ya wuce na sake d'and'anar zazzak'ar zumanki, ke ta dabance a cikin mata, na godewa Allah da ya had'a ni da ke da kuma Gwaggo da ta had'a auren nan da ke, dama ta ce gata tayi Mani ashe ko gaskiya ta fad'a tayi mani babbar gata" Kuka ta saka masa "Kinga ki kwantar da hankalinki ba abuda zamuyi yau sai gobe kinji?" Kwanciya yayi kusa da ita tare da janyo ta jikinsa, ya fara shafa ta tana ture shi tana kuka, shiko ya cigaba da shafata tare da kissing nata ta ko ina, tana ture shi har ya raba ta da kayan jikinta, yana lalla'ba ta ba abunda zai mata haka ya dinga shafa jikinta, da luguiguita ta bai barta tayi barci ba sai tsakiyar dare, shima sai da yaga kukan nata yayi yawa ne, amma fa koda wasa baiyi yunk'urin yin sex da ita ba, iyakarsa wasanni da yayi da ita. Bayan sallar asuba suna kwance suna barci da misalin k'arfe shida akayi masa kiran gaggawa a asibiti don haka sauri yayi ya shiga wanka bai katse mata barcinta ba ya tafi ya barta tana barci. Da misalin k'arfe bakwai na safe ne Sumayya ta dawo gidan kai tsaye ta nufi d'akin Muhdeen don jiya gaba d'aya bata gansa ba, tura k'ofar tayi tare da shiga ciki, taga alamar mutum a cikin bargo ta d'auka Muhdeen ne ta janye bargon gabanta ne ya fad'i ganin Inteesar ce kwance saman gadon Muhdeen, wani abu mai nauyi taji ya daki k'irjinta zuciyarta sai tafarfasa take da k'una ganin Inteesar ma barcinta take hankali kwance suman kanta duk a yamutse ta tuna da jiya taga 'yan kunnenta da d'an kwalinta sai tayi tunanin cewa ko gyara tazo mata ashe kwana take yi yanzun ita Muhdeen zaiyiwa haka? ya karkata hankalinsa akan wannan 'yar matsiyata. Waige -waige ta dingayi tana neman abunda zata bugawa Inteesar, dai -dai lokacin Inteesar ta farka ganin Sumayya n huci yasa ta tashi a firgice ta sauka daga Kan gadon, Idanun Sumayya be ya sauka akan jug na glass dake ajiye a side drawer,ta d'auko shi Inteesar na saukowa ta Sumayya ta buga mata jug d'inan a kanta, k'ara ta saki tare da zubewa k'asa a wurin sumammiya, jini na fita daga cikin kanta. A can gidan Mummy kuwa gaba d'aya Mufida habkainta bai kwanta ba, tunda Inteesar ta bata labarin halin da take ciki a giadan aurenta, don haka ta tashi ta nufi d'akin Mummy dan ta sanar da ita halin da d'anta yake ciki da matar da suka aura masa asan matakin da za'a d'auka akai. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) Don Karin bayani 09965327995 Love you oll😘😍 Comments and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page5️⃣8️⃣ A can gidan Mummy kuwa gaba d'aya Mufida hankalinta bai kwanta ba, tunda Inteesar ta bata labrin halin da take ciki a gidan aurenta, don haka ta tashi ta nufi d'akin Mummy dan ta sanar da ita halin da d'anta yake ciki da matar da suka aura masa asan matakin da za'a d'auka akai. Koda ta shiga d'akin Mummy bata same ta a ciki ba, don haka ta nufi kitchen don tasan yanzun tana kitchen tana had'a masu breakfast, ko da ta shiga Mummy na cikin kitchen d'in tana aiki. "Sannu da aiki Mummy" "Yauwa Mufida kin shiga d'aki kina barci kin barni da aiki ni kad'ai ko?" Girgiza kai tayi tare da cewa "Hmm Mummy Ina naga ta barci wallahi ko jiya daddare banyi isashshen barci ba." Mummy da ke k'ok'arin sauke tunkuyar farfesun kayan ciki ne, ta dakata tare da kallon Mufida ta ce, "Me ke damunki ? Ta kashe gas d'in tare da kallon Mufida ta ce "Ina sauraronki me ke damunki?" "Mummy kun k'ulla auren yaya da Inteesar, kuna zaton suna zaune lafiya amma ba haka bane Mummy, yaya baya son Inteesar kuna za ganin yana nuna maku kamar yana k'aunarta bayan azabtar da ita yakeyi, yanzun haka matarsa da kuke ganin kamar baya tare da ita to tana nan cikin gidansa, tare da ita suke k'untatawa Inteesar sun mayar da ita kamar baiwa mara 'yanci." Zuciyar Mummy ce gaba d'aya ta tsinke, ta zuba ma Mufida Ido ta ce, "Ya akayi kika sani." Gyara tsayuwa Mufida tayi ta bawa ta bawa Mummy labarin da Inteesar ta bata tun daga ranar aurensu har zuwa dawowar matarsa da yadda sukayi amfani da ita wajen biyan buk'atarsu har ya zuwa jiya da suka had'u asibiti. Mummy ki tayi gaba d'aya k'afarta ya gagara d'aukarta, zuciyarta sai tafarfasa take kallon Mufida tayi tare da cewa "Je ki d'auko mayafinki mu tafi." "Ina zamu je gidan son" Fita sukayi gaba d'aya kowace ta nufi d'akinta, ba jimawa Mummy ta fito sanye da hijab Mufida ma mayafinta ta d'auko suka nufi harabar gidan, tun kafin su k'arasa Mummy ke k'walawa direbanta Kira, a guje a k'araso don jin yanayin Kiran yasan ba na lafiya bane, kallonsa tayi tare cewa "Kad'auko mota yanzun ka kaini gidan son." Cikin rawar jiki ya fito da mota suka shiga yaja suka bar gidan A can gida kuwa tunda Sumayya taga inteesar kwance bata motsi tayi ficewarta daga cikin d'akin, karo sukayi da jumy da shigowarta kenan, kallon Sumayya tayi ta ce "Kinga na biyo ki gida da safe ko? waya ta ce na mance a cikin motarki." Ganin yadda Sumayya ke huci yasa ta ce "Sumy what happened" Kasa magana tayi illa waige -waige ta dinga yi kamar me neman wani abu,rik'e ta tayi tare da cewa "Please talk to me waya ta'ba ki yanzu-yanzu? Cikin karaji ta fara magana "Jumy Wai ni za'ayiwa cin amana? ya ce baya sonta iyayensa suka aura masa ita dole, ya ce kada na damu kaina shi bai d'auki aurenta a matsayin aure ba zaman gidansa tamkar zaman gidan kurkuku ne a wajenta, mu d'auke ta tamkar 'yar aiki haka ya dinga Mani dad'in baki har na yarda dashi akan cewa maganarsa gaskiya ce, jiya naga d'an kunnenta da d'an kwalinta akan gadonsa, tunda ita ke gyara mana d'aki nida shi sai na d'auka wajen gyara ne ya fad'i ashe har kwana yake da ita, ni kuma bazan iya sharing nashi da kowace mace ba ballantana ita k'ask'antacciya 'yar matsiyata, wallahi bazai yiwu ba gara ta mutu duk macen da ta ra'be shi sai na kashe ta." Ajiyar zuciya jumy tayi tare da cewa "Yanzun ina suke?" "Da alma baya gidan amma ita na same ta kwance a gadonsa na kashe ta." Cikin firgici da rud'ewa Jumy ta zaro ido waje tana ja da baya ta ce, "Kin kashe ta? ta yaya kuma ya akayi kika kashe ta ba tare da kinyi tunanin abunda zai biyo baya ba?" "Ba abunda zai biyo baya na kashe banza wallahi, don iyayenta ba suda komai da zasu iya ja da Mahaifi na." Girgiza kai Jumy tayi tare da cewa "Kinyi kuskure idan iyayanta basu da komai da zasu tsaya mata ai iyayen mijinki suna da shi, kuma ke da kanki kike bani labarin irin k'aunar da suke mata da har suka aura masa ita, kinsan kuwa ba zasu barki kisha ba, yanzun Ina mijinki yasan abunda kikayi?" Girgiza kai tayi tare da cewa "Bai San na kashe ta ba, da alama baya cikin gidan nan" "To Alhamdulillah yanzun tunda bai san kin dawo ba kiyi gaggawar barin gidan, nan sai kin tabbatar ya dawo kafin ki dawo, cikin ma'aikatan gidan nan akwai Wanda yaga dawowarki ne?" "Mai gadi kawai yasan na dawo" "To shima kija masa kunne kada ya sanar da kowa kin dawo, koda an tambaye sa ya ce baki dawo gidan ba, kiyi masa barazana sosai ta hanyar idan ya fad'a k'arshen aikinsa ya zo." Haka kuwa akayi Jumy taja hannuna suka nufibhanyar fita, Kiran mai gadin tayi tare da masa gargad'i da barazana akan ko an tambaye sa ya ce bata dawo gidan ba, ya kuma tsorata don baya son rasa aikinsa. Motarta suka shiga ta fige ta suka bar gidan. Tafiyarta ba jimawa Mummy suka k'araso gidan, horn direbanta yayi mai gadi ya lek'o ganin su ne yasa ya wangle masu gate, shigowa yayi tare da yin parking suka fito, mai gadin ya gaishe su basu ma tsaya kula shi ba suka nufi cikin gidan. Da sallma suka shiga ba kowa a falon, d'akin Inteesar suka nufa nan ma bata nan, suka duba kitchen bata nan, wayar Muhdeen Mummy ta Kira a kashe don haka ta d'an jira tsawon mintuna goma ba alamar motsi yasa Mufida ta ce "Kodai basu nan be?" Mummy ta kalle ta ta ce, "Ina inteesar zata je da safen nan?" Mufida ta mik'e tare da cewa "Bari na duba d'akin yaya ko yana ciki." Kai kawai Mummy ta gyad'a mata, yayi da ta nufi d'akin Muhdeen, knocking tayi har sau uku shiru, kawai sai ta tura k'ofar ta shiga idanunta ya sauka akan Inteesar dake kwance a sume kanta na zubar da jini, K'ara ta saki Wanda ya razana Mummy ta nufi d'akin da sauri, idanunta ya sauka akan Inteesar k'araswa tayi tare da tallabota idanunta na zubda hawaye tana kuka tana jijjiga ta Mufida ma kuka take yi tana Kiran sunanta bata motsi bata numfashi, ruwa ta umarci Mufida da ta kawo mata da sauri ta k'arasa ta bud'e fridge dake cikin d'akin ta d'auko goran ruwa ciki ta kawowa Mummy, kar'ba tayi ta yayyafa mata mata shiru ba numfashi,sau hud'u tabna zuba mata ruwa shiru. Wayar ta ta duba ta laluno number Jabeer tare da kiransa, fitowarsa kenan daga d'akin tiyata yana kunna wayar sai ga Kira Mummy, d'agawa yayi ko jira batayi yayi magana ta ce "Jabeer kana ina?" "Ina asibiti Mummy" Kayi sauri kazo ka same ni a gidan son kuma kada ka sanar da shi kazo kawai yanzun nan ba sai anjima ba." Kashe wayar yayi ya nufi motarsa yana tambayar kansa ko me ke faruwa yaji muryar Mummy kamar tana kuka, figar mota yayi tare da barin asibitin, gidan Muhdeen ya nufa, Mummy ce tayi wani tunani ta ce kada ya shigo ciki ya tsaya d'an nesa da gidan gasu nan zuwa, sai kuma ta share hawayenta tare da k'ok'arin dai daita nutsuwarta sannan ta fita waje ta umarci mai gadin da ya je bakin titi ya siyo mata bottle of water mara sanyi na gidan duk sunyi sanyi yaje can bakin tati ya siyo a can, tunda yasan Mahaifiyar mai gidansa ne yasa ya tafi yabar gidan. Yana fita ta umarci Mufida ta taimaka mata su d'auki Inteesar su tafi da ita, haka kuwa suka kama ta suka fita Direban Mummy ne yana ganinsu yayi saurin bud'e masu bayan motar suka kwantar da ita. Komawa sukayi cikin gidan suka share fasassun kwalbar suka zuba a mazubin shara suka goge wajen suka tsaftace shi sannan suka janyo k'ofar suka fito suna fitowa sai ga Direban Muhdeen wato Ishaq ya dawo tare da Mai bawa fulawoyin gidan ruwa, gaishe da Mummy sukayi ta amsa cikin nitsuwa kamar ba abunda ya faru, dai-dai lokacin da mai gadin ya dawo, ya kawo mata ruwan ta ce ya barshi suyi amfani da shi an Kira ta suna sauri zasu tafi, shiga motar sukayi direbanta yaja suka bar gidan akan hanya suka had'u da Jabeer yana ganin su ya fito daga motarsa ya k'arasa wajen motar,Mufida ce a gefen dieban Mummy ta zauna baya ga Inteesar kwanace a gefenta, ya bud'e baki zai gaida Mummy idanunsa suka sauka akan Inteesar zaro ido waje yayi tare da cewa "Shbhanallah, me ya same ta haka?" "Shine dalilin kiranka, yanzun ba lokacin bayani so nake ka kaimu wani waje da zaka kula da ita kayi abunda ya dace ko Allah zaisa a samu kanta." "Gaskiya sai dai mu kaita asibiti" "Wane asibitin?" "Asibitin mijinta mana." Kai Mummy ta girgiza alamun a'a sannan ta ce, "Ba za'a kaita asibitinsa saboda bana son yasan halinda da take ciki." Da mamaki Jabeer yake kallonta "Saboda me Mummy?" "Yanzun ba lokacin da zamu tsaya dogon magana bane, ina son wajenda bazai san halin da take ciki ba." Shiru yayi tare da nazari sannan ya ce, "To mu kaita asibitin aboki na" Ciro wayarsa yayi daga cikin aljihu sannan ya kira Doctor Salim, bayanin abunda zai kawo yayi masa sannan ya kalli Direban Mummy tare da bashi umarnin ya biyo shi a baya, daga nan ya shiga motarsa tare da yi mata key yabar wajen, Direban Mummy ya bi shi a baya suka bar unguwar. Suna isa Asibitin da Doctor Salim yake aiki suka tarar da shi a harabar asibitin yana jiran k'arasowarsau, cikin k'anka'anun lokaci aka shigar da ita d'akin da Doctor Salim ya umarce su, nan ya kwantarwa da su Mummy hankali ya ce su jira tukunnah. Nan suka tsaya suna jira har tsawon awa biyu kafin Doctor Salim ya fito ya same su, ya sanar da su cewa sunyi duk k'ok'arin da zasuyi amma har yanzun bata farfad'o ba, doguwar suma tayi zata iya fardad'owa ko wane lokaci. Dai-dai lokacin Jabeer ya fito tare da wani Doctor d'auke da kayan aiki, Jabeer ne ya kalli Mummy ya ce, "Mummy ki kwantar da hankalinki, insha Allah zata dawo hayyacinta,anan za'a kula da ita zaku iya tafiya gida anjima kundawo, koda kun tafi akwai nursess d'in da zasu kuka da ita." Girgiza kai tayi tare da cewa "Jabeer bazan iya tafiya nabarta ba." "Mummy ba yanzun zata farfad'o ba gara ki tafi tukunnah idan yaso sai kibar Mufida ta tsaya, don nima zan koma can Asibiti zuwa d'an anjima zan dawo." Yana kaiwa k'arshen maganarsa kafin Mummy tayi magana wayarsa ta soma ruri, cirowa yayi yaga Muhdeen ne, don haka ya kalli Mummy tuna cewa ta ce bata san yasan da zancen, hakan yasa ya d'aga wayar tare da cewa "Doctor ya akayi ne?" Daga can 'bangare Muhdeen ya fara magana yana cewa "Wai ina ka shiga ne tun d'azun ka fita daga Asibiti baka dawo ba kuma naka sanar da ni ba." "Am not sure zan iya sanar da kai inda naje, amma dai gani nan zuwa yanzun nan." Tsuki Muhdeen yayi tare da katse kiran ya cigaba da duba patient d'insa." Jabeer ne ya kalli Mummy bayan sauran Doctors sun tafi ya ce, "Wai garin yaya akayi hakan ta faru?" Girgiza kai tayi tare bawa Jabeer labarin komai da ke faruwa kamar yadda Mufida ta sanar da ita. Ransa yakai matuk'ar'baci da jin zancen don kwata-kwata baiyi tunanin hakan ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "To waye ya dake ta akai haka?" "Allah masani sai dai idan ta farfad'o ta sanar damu." "To Allah yasa haka" Daga nan yayi masu sallama akan anijima zai dawo, ya tafi zuwa Asibiti. Wayar Mummy ce tayi ringing ta duba taga Dady ne ke kiranta, d'agwa tayi tare da cewa "Assalamu alaikum" Daga can 'bangaren kuwa Dady ne da Gwaggo zaune a falo, jin Mummy ta d'aga wayar ne ya ce, "Wai ina kika tafi ne tun safe gashi har k'arfe goma sha biyun rana, kuma kun fita baku sanar da kowa inda zaku tafi ba." 'shiru tayi tana nazari idan ta sanar da shi cewa ga abunda ya faru da Inteesar anya zai giyi bayan hukuncin da tayi niyyar d'auka akan Muhdeen kuwa? kada tazo ta sanar da shi yazo yak'i bin bayan hukuncin da zata yanke akai, hakan kuma zai iya bata matsala, don hukuncin da tayi niyyar yankewa k'arshenta bazaiwa kowa dad'i ba, kuma tasan Dady yana da sauk'in kai, zai iya lalata mata k'udirinta don haka ta ce, "Yanzun zan dawo na tafi dubiya ne" "Okay Mahaifiyar Inteesar ko?" "Eh ita" "To ki gaishe ta nima jiya daddare naje, Allah ya bata lafiya" Daga nan ta katse kiran ta kalli Mufida ta ce, Zan tafi gida yanzun duk abunda ake ciki ki kirani a waya ki sanar dani, sannan naga restaurant a nan kuda da su yakamata ki nemi abunda zaki ci, koda take bari nasa Direba ya kawo maki takeaway." Daga nan ta tafi Mufida ta samu wuri ta zauna. A 'bangaren Muhdeen kuwa yana zaune a office d'insa gaba d'aya kewarta yake, yana tunanin daren shekaranjiya da ya fara kusantarta yana farin ciki da nishad'i shi kad'ai, don Allah Allah yake ya koma gida ya ganta, gaba d'aya tunaninta ya addabe shi, ji yayi gaba d'aya bazai iya hak'uri ba sai yaje gare ta, don haka ya mik'e don komawa gida ya ganta ko zai samu nutsuwa. Sai da ya fara zuwa d'akin da aka kwantar da Umman Inteesar d'in, shiga yayi ya gaishe ta a karo na biyu, daga nan ya nufi motarsa don komawa gare ta Yana k'ok'arin bud'e motar ne sai ga Jabeer ya k'araso wajensa, kallon Jabeer yayi tare da cewa "Daga ina haka?" Dariya Jabeer yayi tare da cewa "Naji kewar matata ce shine zanje naganta." Dariya Muhdeen yayi lokacin da shima ya tuno da Inteesar d'insa "Kaidai ka sani sauk'in abun ma nima Ina da tawa, yanzun haka wajenta zanje don gaskiya yanzun nasan dad'in aure wallahi don haka da na tuno da ita naji na kasa hak'uri sai naje na d'an kwashi gara tukunnah, wata kila ma sai gobe dan bana jin zan samu lokacin dawowa." Murmushin takaici Jabeer yayi don a tunaninsa akan Sumayya yake magana baisan akan Inteesar bane, don haka sharesa kawai yayi yabar wajen, bunsa da kallo yayi tare da ta'be baki yaja motarsa yabar wajen. Koda ya isa bakin gate horn yayi mai gadi ya wangale masa gate, shiga yayi bayan yayi parking ya fito fuskarsa d'auke da annuri, duk Wanda ya kallesa yasan yana cikin farin ciki. Kai tsaye d'akinsa ya nufa ganin ba kowa a falon, ba Sumayya ba Inteesar, kayan jikinsa ya rage ya shiga toilet don yin wanka, bayan ya fito ya ya shafa turare mai dad'in k'amshi, k'aramar riga ya saka da wando 3 quarter. Shikad'ai yake magana kamar yanayi da wani yana cewa "Bansan yaushe ne ki kuma wani lokaci bane na kamu da sonki, bani da burin da ya wuce na ganni gani gaki, ina jinki tamkar wani sashe na jiki na idan na kasance tare da ke har farin ciki nake ji a cikin raina." Haka ya dinga magana shi kad'ai har ya gama shirinsa ya fito don zuwa d'akinta, yana fitowa ne yayi kici'bis da Sumayya tana dawowa daga waje, kallo d'aya yayi mata ya kauda kansa ya nufi d'akin Inteesar, ganin haka yasa Sumayya ta k'arasa da sauri ta rungume sa ta baya tare da d'ora ha'barta a kafad'arsa cikin kirsa ta fara magana tana cewa "Washh baby nagaji wallahi tun jiya da na fita ban dawo ba sai yanzun duk a gajiye nake baby yunwa ya addabe ni me yarinyar nan ta girka muna ne?" Baice da ita komai ba illa ya janye ta daga jikinsa yayi tafiyarsa, murmushin mugunta tayi ta nufi d'akinta, shi kuma ya nufi d'akin Inteesar. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😘😍 Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by ✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page5️⃣9️⃣ Baice da ita komai ba illa ya janye ta daga jikinsa yayi tafiyarsa, murmushin mugunta tayi ta nufi d'akinta, shi kuma ya nufi d'akin Inteesar. Da sallama ya shiga d'akin bayan ya tura k'ofar, bata cikin d'akin dan haka sai ya zauna a bakin gadon yana jiranta don a tunaninsa tana toilet ne, har tsawon mintuna goma bata fito ba kuma baiji alamun motsin mutum ba, dan haka ya tashi ya k'arasa k'ofar toilet d'in bata ciki tsayawa yayi ya k'arewa d'akin kallo komai tsaf abun sha'awa sai k'amshi ke tashi, murmushi yayi sannan ya fita d'akin. Kai tsaye kitchen ya nufa nan ma bata ciki har store ya duba bata nan, mamaki ne ya kama sa ina zata je ita da bata zuwa ko ina kullun tana gida to ina ta shiga ne? Haka ya dinga duba cikin gidan nan duka d'akunan gidan lungu da sak'o ba inda bai neme ta ba amma bai ganta ba, haka ya bincike gidan nan gaba d'aya ba Inteesar ba alamarta, fita harabar gidan yayi ya samu mai gadi da Ishaq Direba da mai bawa filawa ruwa suna fira. "Cikinku akwai wanda yaga fitar matar gidan nan?" Girgiza kai mai gadin yayi tare da cewa "Hajiya Babba dai tun jiya da ta fita yanzun ta dawo, amma Hajiya k'arama banga fitarta ba gaskiya." Shiru Muhdeen yayi yana nazari duk ya bincike gidan nan amma bata nan, kuma mai gadi baiga fitarta ba, juyawa yayi ya kalli sauran ma'aikatan gidan ya tambaya su ko akwai Wanda yaga fitarta kowa ya ce bai gani ba, dubansa ya maida wajen mai gadin ya ce, "Kuma ba wanda yazo gidan nan yau?" "Eh to Mahaifiyarka tazo ita da k'anwar ka da safe." "Akan idonka suka fita?" "K'warai kuwa akan Ido na suka fita." "Basu fita tare da ita ba?" Nan sauran ma'aikatan gidan suka tabbatar da suna dawowa Mummy zata fita kuma ita kad'aice suka hangeta a bayan motar, sai Mufida dake gefen Direban. Haka ya juya ya koma cikin gidan, kai tsaye d'akinsa ya nufa ya shige tare da zama a bakin gadon, zamansa kenan sai ga Sumayya ta turo k'ofar ta shigo, zama tayi gefensa tare da rik'o hannunsa cikin nata ta fara magana "Ya naganka haka kamar kana cikin damuwa?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Wani lokaci kika dawo gidan nan?" Kwantar da kanta tayi a gefen kafad'arsa ta zagayo da hannunta d'aya ta bayansa ta rungume sa d'ayan hannun kuma tana rik'e da hannunsa ta fara magana "Dawowa ta fa kenan naganka kana k'ok'arin shiga d'akin Amaryarka, gashi naga bata girka muna komai ba yau kuma yunwa nake ji." Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Nima tunda na dawo nake nemanta bansan ina ta shiga ba." Gaban Sumayya ne ya fad'i jin maganarsa don ita dai ta san da cewa ta barta kwance matacciya kodai bata mutu bane? ko kuma dai ta rayu ne, to idan bata mutu ba ai da anganta a cikin gidannan amma shiru? meke faruwa ne? haka take ta tunani tare da anyyana abubuwa dayawa a cikin zuciyarta, ganin yadda ta fad'a duniyar tunani ya tambaya ta "Tunanin me kike yi ne?" Murmushi tayi tare da k'ara narkewa a jikinsa ta ce "Bakomai, kada ka damu maybe wani uzurin ne yasa ta fita." Girgiza kai yayi tare da cewa "Ba uzirin da zaisa ta fita kai tsaye ba tare da sani na ba." "Ok to Allah ya dawo da ita lafiya." "Ameen" "Baby nayi missing naka fa, amma kai naga kamar ba kayi missing d'ina ba, ada baka iya kwana biyu baka neme ni ba amma yanzun kwana biyu shiru baka ma damu da ni ba, ko a jikinka ni gani nake ma kamar ba kai ba wallahi, ka canza mun." Zura hannayenta tayi cikin rigarshi ta fara shafar kwantaccen gashin k'irjinsa tana shafawa, wani yarrr yake ji a jikinsa take yanayinsa ya sauya, ganin hakan yasa ta saki wani shu'umin murmushi, ganin tana son sashi cikin wani yanayi ne yasa ya ce mata, "Pls ki bari, bana cikin yanayin a yanzun so nake nasan halin da Inteesar take ciki." "Kada ka damu ita ba k'aramar yarinya bace, duk inda ta je zata dawo mana cikin k'oshin lafiya." Ya bud'e baki da niyyar magana kenan tayi saurin saka bakinta cikin nasa ta fara tsotsa kamar ta samu sweet, hannunta na cikin rigarsa tana masa tafiyar tsutsa, baisan lokacin da ya fara maida mata da martanin abunda take masa ba,dama ba wata rigar arziki ce a jikinta ba, nan danan ya raba ta da kayan jikinta anan ya k'ara tabbatar wa da kansa cewa lallai mata suna suka da kafin ya fara ganin surar jikin Inteesar idan yaga jikin Sumayya burge shi take amma tunda yaga suffar jikin Inteesar sai yaga yanzu jikin Sumayya ba komai bane, dan fatarta bai kai na Inteesar laushi da shek'i da santsi ba, haka breast d'inta ma bai kai na Inteesar girma da laushi ba uwa uba tsayuwa don breast d'in Inteesar a cike suke kamar an hura balon-balon kuma a tsaye kem basu rankwafa ba bare su zube, ita kuma Sumayya nonuwanta k'ananu ne irin masu tsawon nan dan har sun d'an rankwafa. Haka suka dinga wasanni da junansu daga nan suka afka duniyar ma'aurata, ya d'an samu gamsuwa d ita amma bai kai gamsuwar da ya samu da Inteesar ba, dan ko baiyi sex da Inteesar ba iya wasa kawai yana samun gamsuwar da ko yayi sex da Sumayya baya samunta, lallai Allah ya mata baiwar ni'ima. Bayan sun samu nutsuwa ne ya tashi ya shiga toilet ya tsarkake jikinsa. Ita ko kwanciyarta tayi don dama sai yayi fama da ita kafin tayi wanka kullun haka suke ya zama jiki. Bayana ya canza kaya ne ya kalle ta tare da cewa "Ki tashi kije kiyi wanka lokacin sallar la'asar tayi, daga masallaci zan tafi asibiti naji ki ta tafi wajen Ummanta ne, idan kuma bata nan zanje gida ko ta tafi wajen Mummy da Gwaggo." Bayan an idar da sallar la'asar daga masallaci asibiti ya koma, kai tsaye ya nufi word d'in da aka kwantar da Umma a can, Jabeer na k'ok'arin fitowa daga d'akin shi kuma yana k'ok'arin shuga ciki, komawa baya yayi don yana son magana da Jabeer d'in, kallonsa Jabeer yayi tare da cewa "Har ka dawo ne angon Sumy?" Kauda kansa yayi kamar baiji shi ba, Jabeer ya cigaba da cewa "Kazo ganin surukanka ne ko? jikin nata da sauk'i insha Allah gobe za'a sallame ta." "Ni duk ba wannan ba, a cikin nan da ka fito kaga Inteesar a ciki ne?" Kallonsa Jabeer yayi tare da cewa "Wata Inteesar d'in?" "Ya ina tambayarka kana dawo mani da tambayar rainin wayo, wace Inteesar kasan zan tambaya bayan matata." "Au haba dama kana da mata Inteesar ce?ai na d'auka Sumayya ce kawai matarka Inteesar kuwa 'yar aiki ce a wajenku." Baida lokacin jurara maganganun Jabeer d'in don haka sai ya shige cikin d'akin dan bazai iya jurar maganganunsa ba. B'angaren Mummy kuwa koda tabar Mufida a Asibiti gidan ta nufa, inda ta tarar da Dady da Gwaggo suna zaman jiran dawowarta, koda Gwaggo ta ganta ta fara sababi tana cewa "Wannan wani irin mugun hali ne kike so ki d'auko Fatima? kibar gidan nan tun sassafe ko abinci na baki bani ba kin tashi kin tadiyarki ko a jikinki ko? wato idan ma yunwa ta illata ni ba damuwarki bane ko Fatima? kuma kinsan ina da gyambon ciki bana iya jurar yunwa yanzun nan jiki na sai ya soma rawa ko akwai abunda na tare maki a cikin gidan ne da kika fara gajiya da ni? nan fa gidan d'ana ne ni na haife shi kafin ki ganshi ya aure ki, don haka baza ki hora ni da yunwa ba abincin da d'ana ne yake nemowa." Girgiza kai Mummy tayi tare da murmushin takaici, don inda sabo ta saba da halin Gwaggo haka take dam, shiyasa hakan bai dame ta ce, "Don Allah kiyi hak'uri Gwaggo, wallahi nima tafiyar a ba shiri tazo mani dole ce tasa na fita." "Au dole ne fitar shiysa amma ni ba dole bane bani abinci ko?" "Allah ya huci zuciyarki Gwaggo, na kammala had'a breakfast sannan na tafi sha'afa nayi ne shiyasa, kuma Gwaggo ai da kika ji shiru da sai ki shiga kitchen ki d'ebi kici ." "Da nina saba shiga kitchen na d'ibi abincin naci?" Dady ne ya kalli Gwaggo ya ce, "Kiyi hak'uri Gwaggo insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba." Kallon Mummy yayi tare da cewa "Wai yau sammakon gaida Umman Inteesar kikayi haka? Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin ta sanar da shi ne ki kada ta sanar da shi? Idan ta sanar da shi dole Gwaggo zata sani kuma Gwaggo ba zata iya bata matsala akan shawara da ta yanke musamman idan akayi la'akari da soyayyar da take yiwa Muhdeen. Daga alk'alamin✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don neman k'arin bayani 09065327995 Love you oll🥰😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. Page6️⃣0️⃣ Idan ta sanar dashi dole Gwaggo zata sani, kuma Gwaggo zata iya bata matsala akan shawara da ta yanke, musamman idan akayi la'akari da soyayyar da yiwa Muhdeen. "Eh Asbiti naje tare da Mufida na barta a can zuwa anjima zata dawo." Daga nan kitchen ta nufa dan ta kawo masu breakfast nasu, jin muryar Gwaggo tayi tana cewa "A'a idan saboda mu zaki shiga dawo ki huta, don nariga na cika ciki na ban tsaya jiranki ba nida Sani muka ci." Daga nan Mummy komawa d'akinta tayi, duk da tana jin yunwar amma ji take ma ba zata iya cin komai ba. Koda Muhdeen ya shiga d'akin Umma ya samu zaune a bakin gadon, sai Mama Huraira ce a gefenta sai wasu mata guda uku mak'otan Umma da suka zo dubiya. "Assalamu alaikum" Gaba d'ayansu suka amsa sallama, ya k'araso ya durk'usa ya gaishe su cikin girmamawa tare da k'ara tambayar Umma da jiki, suka amsa masa da sauk'i. Dube-dube yake kamar mai neman wani abu, ya kasa magana da dukkan alamu Inteesar bata cikin d'akin, tamabayar kansa yake ko ina take ko tana toilet ki kuma ta fita tayi sallah ne, to ai kuma ga d'akin yau akwai wajen sallah bai cika ba irin na wancan ranar, Mama Huraira ce ta lura kamar akwai abunda take nema ta kalle shi ta ce, "Muhammad akwai abunda kake nema ne?" Murmushi yayi tare da cewa "Bakomai na d'auka Inteesar tazo ne." Girgiza kai tayi tare da cewa "Gaskiya yau bata zo ba, ka barta a gida bata nan ne?" Ya rasa ma ta ian zai fara mata bayani,magana ya fara yana cewa "Dama munyi zata zo ne, to na d'auka ta iso ne ashe bata zo ba" Girgiza kai tayi "Bata zo nan ba gaskiya." Sallama yayi masu tare da cewa bari ya koma gidan kila bata samu fitowa bane. Mummy tana zaune kan sallaya tana azkar na yammaci, tana ta rok'awa Inteesar sauk'i a wajen Allah, bayan ta idar ne tana cire hijabin taji ana knocking a k'ofar bedroom nata, tasan Dady baya gida Mufida na asibiti Gwaggo na barci a d'akinta, mamaki ne ya kamata waye zai shigo har bedroom bak'o dai iya karsa falo,bada izinin shigowa tayi ta zubawa k'ofar idanu, ganin Muhdeen ne yasa ta tamke fuska dan ranta ya 'baci idan ta tuna da abunda yayiwa Inteesar. "Assalamu alaikum" Wa'alaika salam" Ya k'araso ya durk'usa k'asa ya gaishe ta "Ina wuni Mummy?" "Lafiya lau" Shiru yayi na tsawon mintuna biyar ba wanda yayi magana, d'agowa tayi ta kalle shi taga ya sunkuyar da kai kuma yana durk'she be zauna ba, kauda kanta tayi tare da cewa "Ya dai ina fatan dai lafiya?" "Lafiya lau Mummy, dama na d'auka tazo nan ne?" Kallonsa tayi tare da cewa "Wace ce ta zo nan?" "Inteesar nake nufi." "Ce maka tayi nan zata zo? to nidai banganta tazo ba, amma ka shiga d'akin kakarku ka tambaye ta ko tazo nan tana d'akinta kafin ta k'araso nan." Jinjina kai yayi tare da cewa "To bari naje na gani ko tana can" Mik'ewa yayi ta bisa da kallo ya fice don zuwa d'akin Gwaggo. Gwaggo na zaune a bakin gadonta tana cin goro Muhdeen ya shigo d'akin ba tare da yayi mata sallama ba, kaallon mamaki take masa tare da cewa "Yau naga ja'irin yaro d'akin kafura ka shigo da ba zakayi mani sallama ba? d'an banza mai suffan yahudu da nasara, ko nayi kama da kaba'ira ce da ba zakayi mani sallama ba." Bai tanka ta ba ita kuma bata fasa fad'a da take ba, kallonta yayi tare da cewa "Ba wannan ya kawo ni ba, Ina mata ta take?" Kallonsa take shek'ek'e take kafin ta ce, "Ka d'auke ta inda ka ajiye ta." Kauda kanta tayi ta cigaba da taunan goronta, ganin ta share sa ne yasa ya k'ara mata magana yana cewa "Bata gida kuma bata wajen Ummanta ba inda nake tunanin zata je da ya wuce nan." "Kai ka fita a Ido na, ka kiyaye ni na fad'a maka dan tsabar ka raina ni idan uwarka ce zaka shiga mata d'aki haka ne? ko kuma zakayi mata magana haka? Bansan inda matarka take ba ko ce maka tayi waje na zara zo da zaka titsiye ni da tambayar inda take? wata kila ma ba nisa tayi ba ta koma gida kazo kana damu na, ka fitar mani a d'aki ko yanzun nan na kira ubanka a waya yazo yayi mani iyaka da kai." "Ank'i a fata daga d'akin naki" "Haka ka ce?" "Eh haka na fad'a kuma haka kika ji." Wayarta ta ciro daga k'asan filo tana cewa "Yanzun ubanka zai mani katanga da kai." Tana shirin kiran wayar Dady bayan ta lalaubo number dak'yar tana kashe ido dan bata gane wayar sosai, tana kara wayar a kunnenta. Cikin zafin nama ya fisge wayar, tare da sakawa a aljihu ya kalle ta ya ce "In banda masifa da kika saba da shi daga tambaya ina mata ta sai bak'ar magana?" "Ka bani waya ta kuma kaje can gida matarka nasan tana gida ba inda zata tafi ba saninka." Jefa mata wayar yayi sannan ya nufi k'ofar fita, jin muryarta yayi tana cewa "Ka jefi uwarka Fatima amma ba ni Kulu ba" Har ya tsaya zai bata amsa ya kuma yi ficewarsa ya barta tana ta masifa ita kad'ai. A can gida kuwa Sumayya da taji yunwa na neman illata, ta sai ta kira Ishaq Direba ta aike sa yayo mata takeaway, tana zaune tana ci ya turo k'ofa ya shigo, dube-dube yake ganin bata falon ne yasa ya nufi d'akinta nan ma bata nan, kallon Sumayya yayi tare da cewa "Har yanzun Wai bata dawo ba?" Ta'be baki tayi tare da cewa "Dama ka daina wahalar da kanka akan nemanta." Wani banzan kallo ya mata "Akan me kika ce haka?" Gani nayi akan me kake wahalar da kanka bayan ta fita bata sanar da kai ba, ka fita harkarta kawai "Karki sake mani magana makamancin wannan, ke idan zaki fita sanar dani kike yi? ba gara ma ita da ke ba, nasan dai ba zata ta'ba fita gidan nan ba tare da izini na ba, sai dai idan wani abu daban ne, ke tunda na aure ki dai-dai da rana d'aya baki ta'ba bin magana ta ba, ko kibi abunda nake so bakiyi, kina mani biyayya a matsayi na na mijinki wanda mukayi auren soyayya da ita, ita Inteesar ba auren soyayya muka yi ba, hasali ma na tsane ta bana son ganinta, koda aka aura mani ita haka na dinga wahalar da ita da bautar da ita da ayyukan wahala, bana barin ta huta haka zan dinga wahalar da ita ba tausayawa, hakanayyukan da ba sai tayi ba haka zan saka ta yi bana bari ta huta, amma duk da haka tana kallo na a matsayin mijinta bata ta'ba nuna mani 'bacin ranta ba, kwanakin baya Mahaifiyar k'awarta ta rasu Mufida ta biyo mata su tafi, haka tasa Gwaggo ta Kira waya ta har na bada izini sannan ta tafi, shekaranjiya na same ki d'aki kina shirin zuwa oarty, na nuna maki kada ki tafi, ina da buk'atarki haka kikayi fatali da buk'ata na mijinki kika fita ba tare da izinin mijiki ba, ina cikin halin buk'atar mace kika tadi kika barni, Allah da ikonsa sai ya turo mani ita a dai-dai lokacin da ya dace, gashi bata cikin kwanciyar hankali kuma ga mahaifiyarta kwance ba lafiya, a haka na nuna mata buk'ata ta kuma ba gardama ta amince mani saboda tasan girman hakkin mijinta kan wuyanta tasan laifin bijirwa miji masifa ce, amma ke baki San hakan ba, matar da akan rashin lafiyar Umma bata tafi ba sai da ta nemi izini na sannan ta tafi, wani uzurin kuma zaisa ta fita ba izini na." Kallon mamaki take masa har ya gama maganarsa, sannan ta ce "Kana nufin ta ta fini kenan ?" "Kee Sumayya wallahi ki kiyaye ni, a halin yanzun raina a 'bace yake kada ki tunzura ni, dan idan kika tunzura ni zan aikata abunda daga ni har ke bazai muna dadi ba, Dan haka ki kiyaye ni kafin yanzun nan Kisha mamaki, dan zan aikata abunda daga ni har ke bazai muna dad'i ba, karki manta da wannan." Daga nan ya fice ya barta zuciyarta na tafarfasa, tana mamakin wai yau ita Muhdeen ke fad'awa haka. Mummy na zaune a d'akinta tana tunanin halin da Inteesar ke ciki, wayarta ce ta fara ringing ganin Mufida ce tasa ta d'aga ta rawar jiki kafin tayi magana Mufida ta ce, "Mummy Albishirinki." Murmushin farin ciki tayi ta ce "Goro ta farfad'o ne?" Mufida ta kalli Inteesar dake zaune ta jinjina bayanta da filo ta ce, "Eh Mummy gata nan zaune wallahi na tambaye ta me ya same ta muka same ta kwance cikin jini da kwalabe, tayi mani shiru bata bani amsa ba, amma idan kika zo kila tayi maki magana, duk maganar da nake mata bata ce komai ba kallona kwai take kamar wata kurma." Shiru Mummy tayi tana nazari kafin tace, "Ina Doctor take?" "Yana office nasa" "Yasan ta farfad'o?" "A'a bai sani ba." "To kiyi sauri ki sanar dashi yanzun nan, nima gani nan zuwa." Daga nan ta katse kiran ta d'auki mayafinta da handbag ta nufi hanyar fita. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Don k'arin bayani 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *SADAUKARWA* Wannnan shafin naki ne Faty mannir ina jin dad'in comment naki, don haka na sadaukar da wannan shafin a gare ki naki ne, kiyi yadda kike so da shi, sauran members na INTEESAR ma ina godiya da da comments had'i da add'ar da kuke mani Allah yabar k'auna. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page6️⃣1️⃣ Daga nan ta katse kiran ta d'auki mayafinta da handbag ta nufi hanyar fita. Kici'bis suka yi da Dady wanda shigowarsa kenan daga waje, ganin yadda take sauri yasa ya ce, "Ina kuma zuwa haka?" Shiru tayi tana nazari kafin ta ce "Asibiti" "Waye kuma baida lafiya" Jim tayi kafin ta ce, "Inteesar" A kid'eme ya kalle tare da cewa "Subhanallahi me ya same ta?" A juyar zuciya ta sauke "Alhji dogon labari ne ba lokaci muje kawai." Kallon k'ofar d'akin Gwaggo yayi tare da cewa "Ina Gwaggo" "Tana d'akinta barci take" Fita sukayi inda ta umarci Direbanta ya kaisu asibitin da Inteesar take, shiga sukayi bayan motar aka jasu zuwa Asibiti. Zaune take akan gadon marasa lafiya kanta an nad'e shi da bandeji,Mufida na zaune a gefenta Doctor yana tambayarta yadda take ji ko akwai abunda ke damunta, kai kawai ta girgiza alamar ba komai. Mummy ce ta turo k'ofar ta shigo Dady na biye a bayanta, k'arasawa tayi kusa da Inteesar ta rungume ta hawaye tab a idanunta ta fara magana "Sannu Daughter ya jikin naki?" Take hawaye suka dinga ambaliya daga fuskarta kamr an bud'e famfo, Mummy tasa hannayenta tana goge mata hawayen tana cewa "Ki daina kuka Daughter zaki samu lafiya, insha Allah komai zaizo k'arshe da yardar Allah." Jabeer ne ya turo k'ofar ya shigo, ganin Inteesar zaune yass ya saki murmushi tare da cewa "Alhamdulillah" Kallonta yake yana cewa "Ashe ta farfad'o" Dady dai baisan me ya faru ba kuma baisan dalilin kwanciyarta Asibiti ba, kallon Mummy yayi tare da cewa "Accident ta samu ne?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Sai dai idan mun koma gida muji daga bakinta amma yanzun kam bansani ba." Kallon Doctor yayi tare da cewa "Yaushe za'a iya sallamarta?" "Dama ba wani abu da zamuyi mata tunda ta farfad'o, sai dai ciwon kai da ba'a rasa ba, kuma zamu bata magungunan da zata dinga sha." Fita yayi tare da sanar dasu yana zuwa "Inteesar ce ta fashe da kuka tana cewa, "Mummy dan Allah kada ku mayar dani gidan Yaya wallahi bazan iya jurar zaman gidansa ba." Ta k'arasa maganar tana mai sake fashewa da wani sabon kukan, rungume ta Mummy tayi tana cewa "Daina kukan haka nan ba zaki koma gidansa ba kinji? ki kwantar da hankalinki ba zaki koma can ba, haka Mummy ta dinga rarrashinta saosai har tsagaita da kukan da take, shi dai Dady abun ya d'aure masa kai, don baisan me ke faruwa ba, ganin yadda Inteesar ta rikice yasa yayi shiru yana jiran su koma gida. A cikin mintuna talatin aka sallame su suka koma gida inda Jabeer ma ya bisu. Da sallama suka shiga cikin falon Gwaggo tana zaune kan kujera tana kallon T.V Africa Tv3 inda suka saka wa'azin Shekh Jabeer Sani mai hula. Amsa masu sallama tayi tare da zuba masu ido, ganin Inteesar yasa ta mik'a ta sauri tana salati "Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga uku ni kuluwa me ya same ki 'yar albarka naga anbi an nannad'e maki kai da bandeji?" Ba wanda ya iya magana cikinsu k'arasowa sukayi suka zauna yayin da Inteesar ta k'arasa wajen Gwaggo ta zauna a saman center carpet kusa da kujerar da Gwaggo take zaune, kallonta Gwaggo tayi tare da cewa "Kada dai zargin da nake akanki ya tabbata, mijinki yazo nemanki ya ce baki gida kin fita kada dai a ce hakkinsa ne ya kamaki da kika fita ba tare da saninsa ba kika samu hatsarin mota naga an wani yi maki rawani da bandeji." "Bayan sun zauna ne Dady ya kalli Mummy ya ce wai me ya same ta kuma ina mijinta?" Mummy ce ta kalli Mufida ta ce, "Ki fad'a masu abunda ta sanar da ke." Gyara zama tayi ta sannan ta basu labarin irin zamantakewar da ke tsakanin Inteesar da Muhdeen da duk wahalhalun da tasha a gidansa a hannunsa da matarsa, komai sai da ta sanar da su kamar yadda Inteesar ta bata labarin komai ba abuda ta 'boye masu, da yadda Inteesar ta nuna cewa subar maganar a sirri kada ta fad'awa kowa. Gaba d'aya Falon tsit sukayi kamar ruwa ya cinye su, ran kowa ya 'baci sosai da abunda Muhdeen ya aikata, tausayin Inteesar kawai ke cikin zuciyarsu musamman Gwaggo da ita ce sanadiyar had'in auren nasu, gani take ko wane hali Inteesar ta shiga ita ce ta jefa ta ita ce sanadiyar komai. Dady ne ya kalli Inteesar ya ce, "Mu a iya saninmu matarsa tana can London bamu san cewa ta dawo ba tana gidan ba, tun yaushe ta dawo k'asar?" Cikin sanyin muryarta ta ce, Tun ranar da Gwaggo ta bar gidan, don tafiyar Gwaggo kenan naji yana waya yana cewa zaizo ya d'auke ta, ya ce mani nayi girki na musamman zamuyi bak'uwa sai da tazo naga ashe ita ce." Gwaggo ce ta fara magana "Ke kuma da kina shashasha kika zauna yana wahalar dake da bautar dake ko? sannan har wannan matar tasa zata maidake baiwarta kina ji kina gani ko? ta kwanta da miji akan gado suyi abunda zasuyi su shiga toilet suyi wanka su fito, ke zaki shiga ki gyara masu gadon ki wanke masu toilet d'in ko?" Ta k'arasa maganar cikin k'unar rai, kafin ta cigaba da cewa "Allah ya wadaran naka ya lalace, Inteesar kin bani kunya, wai bata iya girki ba kece zata bawa umarnin ki dafa mata abunda take so, kiyi mata duk wani aiki, bata aikin komai sai dai ta ci ta Sha ta kwanta ko?" K'wallar da suka cika mata idanu ne ta goge tare da cewa "Ni na d'auka zaman aure nakeyi, kuma aure ibada ne, na kudirta cewa duk abunda ya umarce ni nayi zanyi shi ne matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba, saboda neman Aljannah ta nakeyi, kuma shine ya umarce ni da nayi mata duk..." Wani tsawa ta daka nata tare da cewa "Dalla rufe mani baki, tunda nake baki ta'ba 'bata mani rai irin na yau ba, me matar tasa ta fiki da shi kyawu ko kuma diri? ba abunda zata nuna maki wanda ta fiki da shi, wato shiyasa ranar da zan dawo nan ya dinga farin ciki yana Allah Allah na tafi ashe akwai abunda yake k'ullawa." Dady ne ya kalli Inteesar ya ce, "Wannan ciwon na kanki fa ya akayi kika jishi?" Kuka ne ya k'wace mata nan suka dinga rarrashinta har ta tsagaita ta fara magana "Ina kwane ina barci ne shine na bud'e Ido na naganta a kaina, da sauri na sauka daga gadon kawai sai naji saukar abu a kaina daga nan bansan komai ba sai da na farka na ganni a asibiti tare da Mufida." Daga nan suka saka salati suna jimamin abuda ke faruwa, Dady ne ya ce, "Anya kuwa Sumayya kanta d'aya?" Murmushin takaici Jabeer yayi ya ce, "Kafiyarta k'alau Dady ba abunda ya same ta haka take dama ba k'aramin aikinta bane ta illata mutum, shiyasa na sanar da Muhdeen kada ya had'a su gida d'aya bai saurare ni ba." Sakin baki Gwaggo tayi tana kallonsa cikin mamaki "Au dama yasan halinta shine ya had'a su gida d'aya dan ta illata 'yar mutane?" Dady ne ya kalli Mufida ya ce, "Tashi ki raka ta d'akinki tayi wanka ta ci abinci." Mik'ewa Mufida tayi taja hannun inteesar suka shiga cikin d'akinta. Jabeer ne yayi musu sallama zai koma wajen aikinsa, har ya kai bakin k'ofar ne ya jiyo muryar Gwaggo tana cewa "Koda kun had'u da shi kada ka sake ka sanar da shi tana nan gidan." Kai ya jinjina alamar to, sannan ya saka kai ya fice abinsa. Koda Jabeer ya isa asibitin ne ya sallami Umma inda ya ce zai jira su gama tattara kayansu ya kaisu gida, a motarsa ya zauna jiransu, Umman Inteesar ce sai k'anwar ta Mama Huraira, inda ya d'auke su a mota ya kaisu har k'ofar gida sannan ya juyo. 'Bangaren Muhdeen kuwa tunda ya koma gida sai faman safa da marwa yake yi, gaba d'aya ya rasa hankalinsa da nutsuwarsa, ganin yanayin da yake ciki da kuma tunawa da kalamansa da take ne yasa ta kama bakinta tayi shiru bata sake ce masa komai ba, wayarsa ya d'auka ya kira Jabeer, lokacin Jabeer na tuk'in mota ne yayi parking a gefen hanya tare da amsa kiran Muhdeen. "Assalamu alaikum" Muhdeen da ke tsaye a falo cikin tashin hankali ya fara magana "Jabeer ka sallami su Umma ne?" "Eh na sallame su, yanzun nan ma na kaisu gida na ajiye ina kan hanyar komawa ma yanzun nan" "Ok su nawa ne ka kai gidan?" "Su biyu ne" "Wace da wace?" "Umma ce sai k'anwar Umma wacce take jinyarta." "Babu Inteesar a cikinsa?" "Gaskiya bata tare da su." "Jabeer akwai matsala wallahi, bansan inda Inteesar take ba na neme ta banganta ba." Shiru Jabeer yayi kamar baisan komai ba ya ce, "Ikon Allah, to Allah yasa ka ganta." Daga nan ya katse kiran, yana shirin tada motar ne ya kuma jin wani kiran . D'agawa yayi yaji muryar Muhdeen na cewa "Jabeer magana fa nake maka mai mahimmanci, amma naga baka d'auki maganar serious ba." "To banda addu'a me zan maka bayan wannan?" "Haba Jabeer ai da sai kazo ka tayani nemanta muyi duk wani fad'i tashi da zamuyi ko Allah zaisa a ganta, dan Allah kazo gida na gani nan ina jiranka." "Okay gani nan zuwa" Daga nan ya katse kiran ya d'auki hanyar zuwa gidan Muhdeen. Koda ya k'arasa gidan a falo ya same shi kallo d'aya tayi masa yaga har ya fita hayyacinsa, yana ganin Jabeer ya fare magana yana cewa "Jabeer bata gidan nan kuma na je wajen Ummanta bata can bata je na na je gidanmu ko ta je wajen Mummy da Gwaggo duk sun tabbatar mani da bata nan, ta ina zan fara nemanta, Jabeer inacimin tashin hankali." "Kallonsa yayi tare da cewa "Kada ka damu kanka tunda dama ba wai kana k'aunar ta bane, to meye naka na damuwa tunda gaka ga Sumynka abar sonka da k'aunarka, ka manata da waccan kucak..." Kafin ya kai k'arshen zancensa yaji Muhdeen ya kai masa naushi a baki har sai da bakinsa yayi jini, hankici ya ciro daga aljihunsa yakai wajen sai kuwa ga jini ya gani dariya yayi yana kallon Muhdeen da ke ta huci. Kasan irin maganar da zaka fad'a mani a bakinka, dama na lura da kai tunda na kira ka nake sanar da kai abunda ya faru da ni naga kai ko damuwa baka yi ba,ina cikin tashin hankali amma kai hankalinka a kwance, yaushe ka zama haka wannnan sam ba d'abi'arka ba ce, ko dabba na ajiye ai ta 'bata zan neme ta ballantana kuma mata ta, wacce nake jinta a yanzu tamkar wani sashe ne na jiki na." Kallonsa kawai Jabeer yake yana gano irin soyayyar da yake wa Inteesar da zallar k'aunarta a cikin idanunsa, bai ce da shi komai ba illa ya nufi hanyar fita ya kai bakin k'ofar sannan ya juyo ya kalle shi ya ce, "Akan wannan kalmar da na fad'a akan Inteesar ne ka fad'i haka idan kuma a ce ranar da ka gano cewa wata tayi yunk'urin kashe ta zanso ganin wani irin mataki zaka d'auka akanta." Sumayya da fitowarta kenan daga d'akinta jin kalaman Jabeer yasa gabanta fad'uwa, zufa ce ta fara keto mata ta fara tambayar kanta me kalaman Jabeer ke nufi, ko dai yasan abunda ya faru ne da Inteesar yasa yayi wannan maganar? me zaisa ya fad'i haka idan baisan komai ba? sannan kuma ina Inteesar take tana raye ko ta mutu? da dukkan alamu Jabeer yasan komai bisa la'akari da kalamansa, gabanta ne ya tsananta fad'uwa musamman da taga Jabeer ya zuba mata ido yana watasa mata wani irin kallon da bata ta'ba ganin ya mata makamancinsa ba, dawowa yayi ya kalle ta ya kalli Muhdeen yana murmushi kafin ya bud'e baki yana ya fara magana. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON K'ARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😘😍 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page6️⃣2️⃣ Gabanta ne ya tsananta fad'uwa musamman da taga Jabeer ya zuba mata ido yana mata wani irin kallon da bata ta'ba ganin ya mata makamancinsa ba, dawowa yayi ya kalle ta ya kalli Muhdeen yana murmushi kafin ya bud'e baki ya fara magana. "A gaskiya ina matuk'ar tausayinku daga kai har ita Sumayyar, domin dukkanku ababen tausayi ne." Daga nan yasa kai ya fice ya barsu suna masa kallon mamaki, yayinda gaba d'aya hankalin Sumayya a tashe yake, tasan dole akwai abunda Jabeer ya sani, shi kuma Muhdeen tambayar kansa yake mai Jabeer yake nufi? dole akwai abunda ke faruwa, Jabeer da idan ya ganni a damuwa shima sai ya shiga damuwa? farin ciki na shima nasa ne bak'in ciki na ma nasa ne, amma yanzun ina cikin damuwa amma shi ko a jikinsa, lallai akwai wani abu a k'asa. Har k'arfe goma na dare yayi ba Inteesar ba alamunta, Muhdeen kuwa hankalinsa ya fi jirgin sama tashi, ko ruwa bai saka a cikinsa ballantana abinci, ya kira Mufida fiye da sau biyar yana cewa ta kira duk wasu k'awayensu ta tambaye su ko sunga Inteesar, itama Mufidar sai ta nuna masa tashin hankalinta akan rashin ganin Inteesar kamar bata bata san komai ba. Wasa-wasa har k'arfe sha biyun dare yayi yana nan zaune a falo lokaci ne yaji yunwa ta dame sa tun safe rabonsa da abinci tun na safe, hakan yasa ya nufi fridge ya bud'e robar yoghurt ya sha. D'akinsa ya nufa ya d'auro alwala tazo yayi sallar nafila, tare da addu'oi Allah ya bayyanar masa da Inteesar, wajen k'arfe uku na dare ne ya yana zaune akan sallaya ya d'an jingina jikinsa da jikin gado a haka barci ya d'auke shi. Da misalin k'arfe biyar na asuba ya farka daga barcin, toilet ya shiga yayi wanka tare da d'auro alwala, bayan ya saka jallabiyarsa ne ya nufi masallaci. Misalin k'arfe shida na safe ya fito daga masallaci, yana shigowa kai tsaye ya d'akinsa ya nufa key na motarsa ya d'auka ya fito, motarsa ya tada kai tsaye sai gidan iyayensa, horn yayi mai gadi ya bud'e masa gate ya shiga yayi parking, dai-dai lokacin da Dady ya dawo daga masallaci, kallonsa Dady yayi ya kauda kansa ya shige cikin gida, tsayawa yayi yana bin Dady da kallo, don iya saninsa idan dai ya shigo gidan nan Dady ya gansa yana tsayawa ne har ya k'araso su gaisa, amma sai yaga yau yayi tafiyarsa, bai kawo komai a rai ba ya nufi cikin gidan shima a falo Dady na k'ok'arin haurawa sama ne ya ji muryar Muhdeen na cewa "Barka da safiya Dady" Dakatawa yayi da tafiyar har ya k'araso gabansa, durk'usawa yayi ya gaishe shi "Ina kwana Dady?" Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa masa "Lafiya lau, kai ne da sassaden nan lafiya dai ko?" "Gaskiya Dady ba lafiya ba har yanzun fa ban ganta ba." "Wace ce baka gani ba?" "Dady fa tun jiya na sanar da ku zancen rashin ganin Inteesar, ko ka manta ne?" "To ka tafi ka cigaba da nemanta har Allah yasa a dace." Daga nan ya haura sama abunsa ya bar shi nan tsaye sake da baki, mamaki yake yadda mutanen da ya kamata ace sun damu da damuwarsa amma sukayi masa biris da zancen rashin ganin Inteesar d'in. Zama yayi akan kujera don yasan mutanen gidan ba su kai ga tashi daga barci ba. B'angaren Sumayya kuwa tunda taga yanayinsa ta da abunda yayi wa Jabeer ta tsorata da yanayinsa, ta kuma shiga fargabar idan Inteesar tana raye ta sanar da abunda ta mata bata san matakin da zai d'auka akanta, zullumin da take kada ya d'auki mummunar mataki akanta na rabuwa da ita, domin kuwa Allah ya sani ita ba zata iya rayuwa babu shi ba, don tana masifar sonsa da kishinsa, wanda hakan yasa ta aikata abunda ta aikata a kansa, kuma yanzu ta gama tabbatar da kanta cewa lallai Muhdeen ya kamu da son Inteesar, Wanda bata san lokacin da hakan ya faru ba, wani irin sake tayi da har hakan ya faru, haka ta kwana sak'e-sak'e da tunanin yadda zata 'bullowa lamarin. A can gidansu Mummy kuwa Muhdeen na nan zaune har yaga k'arfe bakwai da rabi yayi ba motsin mutum ko alamar fitowar kowa. Haka ya cigaba da zama har k'arfe takwasa tayi, Gwaggo ce ta fara fitowa daga d'akinta tana masifa wai har yanzun ba wanda ya fito ballantana ayi haramar shiga kitchen a d'ora breakfast, ganin Muhdeen tayi zaune ya tafka tagumi kallonsa take tana yamutse fuska ta ce, "Kai kuma lafiya zaka zo ka wani zaunawa mutane gida da sassaden nan lafiya? ka fad'i abunda ya kawo ka ka tafi ka bar mana gida?" Da mamaki ya tsaya yana kallonta, dan dai baiga abun fad'a ba, daga ganinsa ta fara sabibi bayan tasan halin da yake ciki, tunawa yayi da abuda yayi mata jiya kila shiyasa take masifa, Dan haka ya share ta kamar baiji me take fad'i ba. "Nace ka tashi ka fita ko?" "Ni da gidan uba na kike kora ta? to wallahi naki isa ki kore ni na fita sai dai ke ki fita kibarni" Sakin baki tayi tana kallonsa ta ce, "Ni da gidan d'a na zaka ce na fita, ni na haife shi da kaina ba wata ba." "Ko ke kika haife shi baki fini iko da gidan nan ba gidan uba na ne, nine magajinsa." Cikin d'aga murya ta ce "Sannu magaji, na ce, sannu magaji, to bari kaji gidan uban da kake tak'ama da shi to zansa yanzun uban naka ya fitar da kai, idan kuma kana musu ne ka zuba ido ka gani." Dai-dai lokacin Mummy ta fito daga d'akinta, ganin Muhdeen yasa ta d'aure fuska, tsayawa tayi ta zuba masa ido. Durk'usawa yayi ya ce, "Mummy ina kwanan?" "Lafiya lau" "Mummy baki ji labarin ta ba?" ",Labarin me kenen?" "Mummy kada dai ace kema kin manta da maganar 'yar ta ki." "Ban manta ba ya ake ciki ne? An ganta me?" Girgiza kai yayi cikin damuwa kafin ya ce, "Mummy ina cikin tashin hankali sosai, Na kasa cin abinci na kasa barci, yanzun ta ina zan fara nemanta?na sanar da Mufida tayi cigiyarta wajen k'awayensu bata nan in zan same ta?" Mummy dai zuba masa ido tayi tana kallonsa, ganin bata ce komai ba ne yasa ya ce, "Ko na koma na sanar da Ummanta halin da ake ciki ne? sai ta tayamu bincikawa wajen 'yan uwanta, a binciko ta." Girgiza kai Mummy ta tayi tare da cewa "Kada ka sanar da Ummanta ka d'aga masu hankali." Kai ya jinjina alamar gansuwa sannan ya ce, "To shikenan zanje gidan kaaai na gaishe ta, idan tana nan shikenan idan bata nan banganta ba sai na sallame su kawai na nar gidan." Kai kawai ta jinjina masa ba tare da tayi magana ba ta nufi kitchen. Hararar Gwaggo yayi tare da yin tsuki ya mik'e ya nufi k'ofar fita, kallonsa tayi tare da cewa "Kayiwa uwarka gata can ta shiga kitchen, mara kunyar banza mai k'irar yahudu da nasara." Duk maganar da suke a kunnen Inteesar dama ba barci take ba, tunda ta idar da sallar asuba tayi azkar bata kwanta ba fitowa tayi da niyyar shiga kitchen sai, sai ganinsa tayi zaune a falo da sauri ta juya ta koma cikin d'akin Mufida ba tare da ya ganta ba, bayan shigarta ne ba jimawa Gwaggo ta fito. Bayan ta ji fitarsa ne ta fito faga cikin d'akin, zata durk'usa ta gaida Gwaggo sai Gwaggo tayi sauri jan hannunta ta mik'e tsaye, "Kinga 'yar albarka ta shi ba sai kin wahalar da kanki ba, fatan kin tashi lafiya? ya jikin naki? Cikin sanyin muryarta ta ce, "Lafiya lau da sauki' naji muryarsa ya zo gidan nan Gwaggo dan Allah ka da ku maidani gidansa" Ta k'arasa maganar cikin rawar murya kamar wacce zata saka kuka, dafa kafad'arta Gwaggo tayi tare da cewa "Ki kwantar da hankalinki ba mai maida ke gidansa kinji." Jinjina kai tayi alamun gamsuwa ta ce "To nagode" Daga nan ta nufi hanyar kitchen. Jin muryar Gwaggo tayi tana cewa "Ina kuma zaki je?" "Zanje na gaishe da Mummy ne" Daga nan ta nufi kitchen d'in inda ta samu Mummy na fere dankalin turawa, Mummy na ganinta ta sakar mata murmushi ta ce, "Daughter kin tashi" Itama murmushi ta sakar mata zata durk'usa Mummy tayi saurin cewa "A'a Daughter tashi dan Allah" "Ina kwana Mummy" "Lafiya lau Daughter ya jikinki" "Naji sauk'i Mummy" "Ina ke maki ciwo yanzun?" "Bakomai Mummy, ba wurin da ke mani ciwo?" "Kin tabbata" "Eh Mummy" "To alhamdulillah haka nake son ki" K'ok'arin karb'ar wuk'ar take ne sai Mummy ta hana ta tace "Daughter kije ki kwanta ki huta" "Mummy kinsan ban saba kwanciya da safe ba idan ba aiki mayi ba, dan Allah ki kawo zan iya." Mik'ewa Inteesar tayi ta nufi wajen gas don duba ruwan shayin da ta d'ora, Gwaggo ce ta shigo kitchen d'in ganin Inteesar na aiki yasa ta saki salati. "Fatima saboda rashin tausayi yarinyar da d'anki ya gama azabtar da ita daga fardad'owarta kuma sai ki sakar mata aiki? wannan ai rashin tausayi ne muraran." "Gwaggo ba laifinta bane ta hanani nice na matsa mata dole ta barni." "Saboda baki tausayin kanki da kanki ko?" "Gwaggo wallahi zan iya kibarni nayi." "Sai kiyi tayi ai" Daga nan ta saka kai ta fice, Mummy dai uffan bata ce ba don inda sabo ta saba da halin Gwaggo. Muhdeen kuwa da ya d'auki motarsa ya bar gidan, kai tsaye gidansu Inteesar ya tafi, koda ya shiga a zaure ya samu Abba yana karatun al'qur'ani mai girma, bayan ya kai k'arshen ayar da yake karantawa ne ya rufe tare da ajiye shi gefen tabarmar da yake zaune, durk'usawa yayi bayan yayi sallama "Ina kwana Abba" "Muhammad kai ne da safen nan? ka tashi lafiya? "Lafiya lau Abba" "Masha Allah, ya kwanan iyali?" "Lafiya lau" "Masha Allah" Shiru yayi ya kada magana, har abba yayi magana ya ce, "Bari na shiga na duba ko Umman ta tashi sai ku gaisa." "To Abba" Daga nan Abba ya mik'e ya nufi cikin gidan, ya tarar da Umma ta fito daga d'akinta kenan zata hura huta,kallonsa tayi tace, "Mallam ka shigo ne" "Eh ga Muhammad nan zai gaishe ki." "Wani Muhammad d'in" "Surukinki mana" "Murmushi tayi tare da cewa "Tare da Inteesar suka?" "A'a shi kad'ai na gani" Daga nan ya koma zaure inda suka shigo tare Muhdeen na bunsa a baya, suka tarar har Umma ta shimfid'a masu tabarma, durk'usawa yayi ya ce, "Ina kwana Umma?" "Lafiya lau Muhammad" "Ya k'arfin jiki?" "Jiki Alhamdulillah naji sauk'i" "Masha Allah Allah ya k'ara lafiya" "Ameen ka zauna mana" Zama yayi gefen tabarmar kansa a k'asa, muryar Abba ya ji yana cewa "Sannu da k'ok'ari fa mungode da d'awainiyar Asibiti, Allah ya saka da alkahiri." "Bakomai Abba addu'a da sanya albarka kawai nake nema daga gare ku" Murmushi kawai Abba yayi tare da cewa "Ai kullun cikin yi maku addu'a muke Allah ya albarkaci rayuwarku ya kare ku daga sharrin abun k'i yasa ku gama da duniya lafiya." Murmushi yayi tare da jin dad'in addu'a da Abba yayi masu Umma ce ta amsa da Ameen, shiru ne ya biyo baya, inda muryar Umma ta katse shirun da cewa "Halan Inteesar bata san zaka zo nan ba?" Zuciyarsa ce ta tsinke ya rasa me zai ce, amma tuna zancen Mummy da tayi masa da gudun kada hankalin iyayenta su tashi yasa ya k'ak'alo murmushi ya ce "Bata sani ba Umma" "Ayyah nasan da ta sani zata dame ka, ka kawo ta." Fira suka d'an ta'ba daga nan yayi masu sallama ya tafi. Yana driving gaba d'aya hankalinsa a tashe yake ya rasa inda zai saka kansa yanzun ya gama tabbatar wa da kansa cewa bata gidan Ummanta, kai tsaye gidansu ya koma. Suna kitchen sun kammala aikinsu dai-dai lokacin da Inteesar ta fito daga cikin kitchen d'in d'auke da faranti da aka jera foodflask a ciki tana fitowa daga kitchen d'in ta nufo falo, dai-dai lokacin da Muhdeen ke shigowa ya juya falon ya maida k'ofar ya rufe. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON K'ARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😘😍 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page6️⃣3️⃣ Suna kitchen sun kammala aikinsu dai-dai lokacin da Inteesar ta fito daga cikin kitchen d'in, d'auke da faranti da aka jera foodflask a ciki, tana fitowa daga kitchen d'in ta nufo falo dai-dai lokacin da Muhdeen ke shigowa ya juya falon ya maida k'ofar ya rufe, tana ganinsa tayi saurin komawa cikin kitchen d'in da sauri ba tare da ya ganta ba, jin motsi hanyar kitchen yasa ya kalli wajen amma baiga kowa ba. Mummy dake cikin kitchen ganin Inteesar ta dawo da sauri yasa ta ce, "Lafiya kuwa me ya faru?" A hankali tayi magana ta ce "Yaya ne ya dawo" Da sauri Mummy ta nufi hanyar fita kitchen d'in, tana fita kenan sai gashi yana k'ok'arin shigowa kitchen din, tsayawa tayi ta kalle shi fuska a tamke ta ce, "Lafiya?" Cikin karaya yayi magana yana cewa "Mummy na shiga uku wallahi Inteesar bata gidan iyayenta, ku taimaka mani na samota ta ina zan fara, nemanta ban san mutanen da take mu'amala da su ba, ban san k'awayensu ba, suk da cewar jiya nasa Mufida ta Kira duk wasu k'awayensu amma sunce bata nan, Mummy yanzun ba wanda ya kamata ya taimkaa mani a cikin wannan halin sai Mufida tasan mutanen da Inteesar ta sani k'awaye da dangi da 'yan uwa, dan haka tazo mu tafi..." Tun kafin takai k'arshen maganar da zaiyi yaji Mummy na cewa "Kuje ina? kuma tare da wace ce? badai Mufida ta ba kamar yadda bata san mai ya had'a ku har Inteesar ta bar gida ba haka zalika ba zaka saka ta cikin zancen nemanta ba, kaje can ka k'arata duk inda 'yarsu ta shiga ka je ka nemo masu ita." Da mamaki ya ke binta da kallo don kwata-kwata baiyi tunanin jin makamancin wannan zancen daga gareta ba cikin kwantar da muryar ya fara magana "Mummy yanzun ke da bakinki kike fad'in haka? idan da wani ne ya fad'a mani abunda kika fad'a zan k'aryata shi, amma ni naji da kunne na." "Ka ji ka k'ara ji duk inda 'yar mutane ta shiga ka je ka nemo masu 'yarsu, duk yadda akayi akwai wani abunda kayi mata Wanda yasa dole ta fita ta bar maka gidanka, amma ba banza ba haka nan kawai ba zata fita ba an d'auki amanar 'yar mutane an baka kana ta gallaza mata har ya kai ga ta bar maka gidanka, Dan haka zama bai ganka ba ka tafi duk inda take a fad'in garin nan ka nemo masu 'yarsu." "Mummy ba gallazawa ne yasa ta bar gidan ba, domin da gallazawa ne da tuni ta bar gidan a lokacin da nake gallaza mata, amma ba yanzun ba da bana gallaza mata ta bar gidan duk yadda akayi akwai wani 'boyayyen al'marin wanda bansan da shi ba." Ta'be baki Mummy tayi tare da cewa "Sai ka tafi ka nemo ta koma mene ne Kaine sanadi." Zuba mata Ido yayi yana kallonta ya kasa gane dalilin da yasa suka yi biris da lmaarin nan shiru yayi na d'an lokaci kafin ya nufi k'ofara fita ya fice. Yana driving ne ya ciro wayarsa tare da lalunar wayar Salisu, bugu biyu ya d'aga bai jira yayi magana na ya ce, "Kana ina ne Salisu?" Salisu ya bashi amsa da cewa "Yanzun gani k'ofar gida ina shirin fita." "Dan Allah ka jira ni a k'ofar gidan naku, gani nan zuwa yanzun nan insha Allah." Daga nan ya katse wayar tare da maida hankalinsa ga driving din da yake yi. Koda ya k'arasa k'ofar gidaan Salisu ya same sa yana jiransa, Salisu me ya k'araso ya bud'e murfin motar Muhdeen ya shiga ciki, hannu ya mik'a masa suka gaisa kafin ya ce, "Mutumi na lafiya kake kuwa? naga kayi wani zuru-zauru?" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, Ba dole kaga na rame ba?Salisu ina cikin tashin hankali?wallahi akwai damuwa sosai a tattare da ni, banga Inteesar ba tun jiya da safe rabo na da ita, tunda aka kira ni da sassafe a Asibiti akayi mani kiran gaggawa na tafi na barta tana barci, koda na dawo gida da rana banganta ba, abu kamar wasa har yau ba ita ba labarinta." "Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un,kunyi fad'a da ita ne? yasa ta tafi ta barka?sannan yakamata ka je gidan iyayenta dan ba zata wuce can ba." "Salisu bata gidan iyayenta kuma bata gidan iyayae na, nasa Mufida ta kira dukkan k'awayensu ta tambaye su ko ta je can, nan ma sun tabbatar da cewa bata gidansu, duk inda yakamata ace ta je bata nan." "Kuma bansan inda ta shiga ba, kuma ni fargabar da nake kada ya kasance ta fad'a mugun hannu, idan wani abu ya same ta bazan iya jurewa ba." Ajiyar zuciya Salisu yayi tare da cewa "To yanzun neye mafita?" "Ko zamuje police station ne da gidan redo ko Allah zaisa a dace." Take Muhdeen yayiwa motar key suka tafi police station, sukayi report daga nan suka nufi gidan redio ,bayan sunbar gidan redio ne suna tafiya akan hanyarsu ne yayi parking a gefen hanya, Salisu ya kalle sa ya ce, "Lafiya ka tsaya ko akwai wata matsalar ne?" Girgiza kansa yayi cikin yanayi na damuwa da yake ciki ne ya kalle shi ya ce, "Wane lafiya kuma zaka tambaye ni? bayan kasan halin da nake ciki ai ba lafiya, har sai ranar da naga mata ta sannan hankali na zai kwanta." "Kada ka damu ka kwantar da hankalinka addu'a ce kawai mafita a gare ka, duk abunda yayi tsanani sauk'i na zuwa, insha Allah zamu same ta cikin k'oshin lafiya Allah zai bayyana muna ita aduk inda take, nasan yadda kake ji a zuciyarka amma amma ka daure kayi ta addu'a har Allah ya bayyana mata." Murmushi Muhdeen yayi tare da cewa "Naji dad'in kalamanka Salisu har cikin raina, hak'ik'a tunda wannan abun ya faru ba wanda ya ta'ba fad'a mani magana mai dad'i kwatankwacin wanda ka fad'a mani, ba wanda ya nuna damuwarsa akan lamari na sai kai, hatta aminina Jabeer bai damu da halin da nake ciki ba, babbar abunda zai baka mamaki ma Mummy da Dady cewa sukayi wai na nemo ta duk inda ta ke." Haka Salisu yayi ta bashi baki yana kwantar masa da hankali, sai da ya tabbatar ya d'an saki ransa kafin suka cigaba da tafiya, sauke shi yayi a k'ofar gida inda ya ajiyae shi kafin yaja motarsa ya nufi gidansa. Koda ya shiga ba kowa a falo don ko motsin Sumayya bai ji ba, da alama bata gidan ta fita kenan, kai tsaye d'akinsa ya nufa, lokacin k'arfe d'aya na rana komai baici ba bai sha ba, rabonsa da abinci tun jiya da yasha yoghurt bai sake saka ko da ruwa a cikinsa ba, gashi wani masifaffen yunwa yake ji na addabarsa amma baya jin zai iya cin abincin duk da yunwar da ta addabe shi, toilet ya shiga yayi wanka ya fito ya saka kaya ya nufi masallaci, bayan an idar da sallah ne yayi addu'a sosai akan Allah ya bayyana masa Inteesar. Daga masallaci gida ya dawo a falo ya d'an kishingid'a, ba abuda yake tunani sai Inteesar, tuna yadda ya dinga wahalar da ita da azabtar da ita tun kafin aurensu har ya zuwa bayan aurensu, ya tuna irin biyayyar da take masa duk k'untatawa da yake mata bata ta'ba tsallake maganarsa ba, duk abunda ya umarce ta da tayi sai tayi shi koda hakan zai zama bak'in cikinta ne, zata yi masa indai zai faranta ransa, bata damu da halin da zata shiga ba. Nadama ce ta kama sa tare da danasanin abunda yayi mata a baya, tabbasa da zai ganata yanzun zai gyara kura kuransa ne, ya nuna mata kulawa da k'aunar da yake mata, yana nan zaune ya shagala da tunani bai ankara ba sai jin Kiran sallar la'asar yayi, mik'ewa yayi ya d'auro alwala ya nufi masallaci, kuma har lokacin baici komai ba a cikinsa, bayan idar da sallar ne ya d'auki motarsa ya koma gidan iyayensa. Da sallama ya shiga falon Mummy ce zaune a falo, amsa sallama tayi masa tare da kallonsa, ganin yadda ya rame cikin k'ank'anin lokaci yiyi zuru-zauru kamar ba shi ba, mamaki ne ya kamata ganin ramar da yayi, a tunaninta baya son Inteesar kamar yadda ta sani, amma yanzun ganin yadda ya koma ne yasa ta shakku akan abunda ta sani, domin kuwa don idan baya sonta bai kamata a ce ya shiga damuwa har haka ba, kenan yana sonta? to me yasa ya wulak'anta ta alhalin ya damu da ita har haka, uwa uwa ce duk da tana fushi da shi amma bata ji dad'in ganinsa haka ba. K'arasowa yayi ya durk'usa a gabanta "Ina wuni Mummy?" Ba yabo ba fallasa ta amsa masa "Lafiya lau" Zama yayi a saman center carpet dake falon, daga shi har Mummy ba wanda yayi magana, ganinsa tayi da alamar yunwa a tattare da shi, dan haka ta kalle shi ta ce, "Ka zo ka ci abinci" Bata jira cewarsa ba ta nufi dinning area, bin bayanta yayi duk da ba jin cin abincin yake ba amma yaji dad'i, ganin Mummy wannan karon ta d'an kula da shi, zama yayi a d'aya daga cikin dinning d'in tayi serving d'insa, white rice and stew ne da ya ji naman kaza, kunun aya da ta zuba masa a cup ya fara sha, take gabansa ya fad'i, don tabbas idan har Inteesar tayi masa kunun aya haka yake jin d'and'anonsa, abincin ya d'eba da cokali yakai bakinsa ya tauna a zabure ya mik'a tsaye, kallonsa Mummy tayi tare da cewa "Lafiya kuwa?" "Mummy ina take?" Da mamaki ta kalle shi ta ce, "Wake nen?" "Mummy Inteesar tana gidan nan, me yasa aka mani haka?" "Waye ya ce maka tana gidan nan?" "Mummy ba wanda ya fad'i mani amma tana gidan nan, don wannan abincin da na ci tabbas ita ta dafa shi, wannan kunun aya ma ita ce ta had'a shi, tunda na d'and'ana abincin nan nasan ita ta girka shi wannan d'and'anon girkinta ne, nasan d'and'anon girkinta nasan naki wallahi Umma ita ce ta girka shi, kuma tana cikin gidan nan." Mik'ewa yayi ya nufi falo yana k'wala mata kira da k'arfi "INTEESAR! INTEESAR!! INTEESAR!!!" Inteesar dake zaune a akan sallaya sanye da hijab, tunda ta idar da sallar la'asar bata tashi ba ta zauna tana azkar, gabanta ne ya fad'i jin muryarsa yana k'wala mata Kira yasa gabanta ya fad'i ta furta kalmar "Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Dama ita kad'ai ce a d'akin Mufida ta fita Mummy ta aike ta gidan Aunty Abla, Gwaggo dake d'akinta ta fito tana cewa "Wannan kuma haukar me yake mana a gida ne? Kazo kana d'agawa mutane murya ." Ranasa a 'bace yake kallon Gwaggo, yana shirin bata amsa ne sai idonsa ya sauka akan dady dake saukowa, kallon fusakar Dadyn yayi a murtuk'e ya ce, "Muhammad fitar mani a gida." Da ya ke kallon Dady jin kalmar bakinsa, bud'e baki yayi da niyyar magana Dady ya d'aga masa hannu alamun dakatarwa ya ce, "Get out in my house" Yadda yayi maganaar a tsawa ce, da ganin irin 'bacin ran da ya gani a fuskar Dady yasa ya nufi hanyar fita. A harabar gidan ya had'u da Mufida da suka dawo da Direb, ganinsa ta tasan akwai damuwa, da har zai wuce sai ya tamabaye ta "Da Inteesar tazo gidan nan mai ta sanar da su Dady da Mummy ne?" "Nima ban sani ba" "Kada kiyi mani k'arya ki sanar da ni gaskiya, me ke faruwa da kowa ya d'auki zafi da ni." "Yaya ai dole kowa ya d'auki zafi da kai, da badon Allah yasa munje gidanka ba kuma Allah yasa tana da sauran numfashi ai da wani zancen ake ba wannan ba." Kallon rashin fahimta yake mata kafin ya sake tambayarta "Kamar ya please ki sanar dani abunda ya shige Mani duhu." Ajiyar zuciya ta sauke sanan ta bashi labarin yadda suka tafi gidansa ita da Mummy, suka tarar da Inteesar kwance bata numfashi, kanta na fitar da jini, ta kuma tabbatar masa da cewa Sumayya ce tayi yunk'urin kashe Inteesar, take idanunsa suka kad'a zuwa ja jikinsa gar rawa yake, ya. nufi motarsa cikin k'unar rai da fusata ya shiga motarsa, key yayi mata ya dinga danna horn sai da kiwa ya firgita da yadda ya dinga horn, Mallam Ibrahim mai gadi ya wangale masa gate ya fita a guje zuciyarsana masa zugi, Mallam Ibrahim ya kalli bayan motar ya ce, "Allah dai ya kiyaye hanya amma wannan tuk'in akwai hatsari a cikinsa." *DAGA ALK'ALAMIN*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don k'arin bayani* 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page6️⃣4️⃣ "Allah dai ya kiyaye hanya, amma wannan tuk'in akwai hatsari a cikinsa. Driving yake kamar zai tashi sama, gaba d'aya Allah kawai ne zai kaishi gida lafiya, gudu kawai yake akan titi kamar zai tashi sama. Sumayya kuwa tana cikin bedroom d'inta zaune saman gado, waya ne kare a kunnenta, tana magana tana cewa "Ba haka bane shila har yanzun mutumin a sama yake, tunda waccan 'yar matsiyata aka rasa inda take gaba d'aya hankalinsa na kanta, ko damuwa dani baya yi, ina naga sakin fuska a wajensa daga na fad'i magana akanta kinga yadda ya hauni da fad'a kamar zai cinye ni d'anya?" Banko k'ofara d'akin yayi da k'arfi, a firgice ta mik'e tsaye tana kallonsa ganin fuskarsa ba alamun rahama be yasa zuciyarta tsinkewa, ganin yadda yanayinsa da fuskarsa suka canza ne yasa ta fara ja baya, cikin k'arfin hali ta bud'e baki ta fara magana "Baby lafiya kuw..." Kafin ta kai k'arshen zancenta taji ya sauke mata tagwayen maruka biyu a kumatunta, d'ayan kumatun ma haka ya sake sauke mata tagwayen maruka biyu, jiri ne ya fara d'ibanta, don tunda take a rayuwarta ba'a ta'ba marinta ba sai yau, yau d'in ma maruka hud'u lokaci guda, k'eyarta ya rik'e ya buga goshinta a bango take sai goshinta ya fashe jini ya fara fita, wuyanta ya shak'e wajen mak'ogoronta ya rike take ta fara kakari idanunta suka fito waje miyau ya fara dalala daga bakinta, cikin kakkausar murya ya fara magana. "Zaki kashe ta ko? to kafin ki kashe ta ni zan fara kashe ki, a kin had'ani da iyaye na suna fushi dani duk ta sanadiyarki, baiwar Allah da bata maki laifin komai ba kike neman kashe ta, dama Gwaggo ta fad'a mani cewa ke ba matar aure bace amma na dinga k'alubalantarta, amma gashi naga gaskiyarta a yanzun." Jifa da ita yayi gefe sannan ya nufi hanyar fita yana huci, ita kuma yanda yayi jifa da ita ta zube wajen ko numfashi bata yi. A can gidansu Mummy kuwa bayan fitarsa ne da Dady ya kalli Mummy ya ce, "Waye ya sanar da shi cewa tana gidan nan?" Mummy ce ta kalle shi tare da cewa "Ba wanda ya fad'a masa , daga ya ci abinci shine fa ya ce wai ita ta dafa abincin nan wannan d'and'anon girkinta ne, daga nan ya dinga k'wala mata kira." Shiru Dady yayi yana nazari, tabbas ya gane cewa Inteesar ce ta dafa masu abincin, don shi dama haka ya ke tun yana yaro indai ya d'and'ana abincin da ba mahaifiyasa ce ta dafa ba ya sani, yana ganewa Dan a lokacin Dadynsa har yana mamakinsa sai yanzunn ya ke tunowa da wani abun, wato har girkin Inteesar ma yana ganewa, gajeren murmushi Dady yayi tare da komawa ciki, Mummy ce ta kalle Gwaggo ta ce, "Lamarin nan fa ya fara d'aure mani kai." Dariya irin ta su ta manya Gwaggo tayi tare da cewa "Ba abunda ke d'aure mani kai a lamarin su, ki zuba ido kawai kada ki ce komai." Da misalin k'arfe takwas na dare ne Sumayya ta soma tari a hankali, dak'yar ya iya tashi zaune saboda tana rik'e da mak'ogoronta da ke mata zafi, goshinta dake mata rad'ad'i ta kai hannu ta shafo shi,jin yadda ya fashe ya kumbura ga jini da ta shafo, kuka ta sake da shi mai cike da tsantsar bak'in ciki da takaici, jikinta gaba d'aya ji tayi yana mata ciwo, dak'yar ta lalla'ba ta shiga toilet, tana kuka tana wanka har ta gasa jikinta, har zuwa wannan lokacin mak'oshinta na mata ciwa ga goshinta sai zugi yake mata, raki da son jiki bai bari ta gasa wurin ba. Haka ta ta fito ta zube a Kan gado, don dama sallah bai dame ta ba ko da kafiyarta ballantana yanzun da ba lafiyar,kuka ta cigaba da yi, wayarta ta kalla inda ta fad'i k'asa lokacin da Muhdeen ya mare ta, tashi tayi ta d'auko wayar tare da lalubo number Dad dinta, sau uku tana jaraba Kira amma bai shiga ba, kuma ba zata iya kiran Mum d'inta ta sanar da ita ba, dan tunda ta lura Mum ta daina goyon bayanta ta daina sanar da ita halin da take ciki, kwanciya tayi a kan gadon har barci ya d'auke ta. A 'bangaren Muhdeen kuwa shima haka ta kasance a gare shi, ya kwana cikin bak'in cikin abunda Sumayya ta aikata, wanda a dalilin haka kowa na fushi da shi, duk da cewar shima da nasa laifin amma nata ya janyo wannan matsalar har aka kawo wannan matakin, dan shi yanzun yayi niyyar gyara zamantakewarsa da matarsa, ya mantar da ita rayuwarsu na baya. A haka dai bai samu isashshen barci ba har k'arfe hud'u na asuba, toilet ya shiga yayi wanka ya nufi masallaci. Daga masallaci ya zauna yayi azkar da karatun al'qur'ani mai girma, sai k'arfe bakwai sannan ya dawo gidan, yana tafiya yana tunanin yadda zai fuskanci Dady da Mummy da Gwaggo akan Inteesar, amma ko ba komai ya samu sassauci a cikin zuciyarsa, kaso hamsin ciki d'ari na damuwar da yake ciki ya ragu, domin yanzun yasan cewa Inteesar bata mugun hannu, duk da dai akwai babban aiki a gabansa. A falo ya had'u da Sumayya tana zaune kan kujera tana cin snacks da yogurt, don dama aikinta kenan tunda bata iya girki ba sai dai tayi ta fama da kayan su biscuits cake da sauransu, tana zaune tana tsaka da cin snacks ne ya shigo, sai da gabanta ya fad'i dan wani tsoronsa ne ya shige ta, ko kallonta baiyi ba har ya wuce ta zai nufi d'akinsa ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Kada ki sake kwana mani a gida, ki tattara naki ya naki kibar mani gida na." Daga nan ya shige d'akinsa, kuka ta saki tana cewa "Dan Allah kayi hak'uri ka gafarce ni wallahi bazan sake ba, kayi mani alk'awari na zamu rayu har k'arshen rayuwarmu ba zamu rabu da juna ba, wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba dan Allah kayi hak'uri, soyayyar da nake maka ne ya saka ni cikin wannan halin. Bai saurare ta ba ya shigewarsa d'akinsa. A guje ta ruga d'akinta wayarta ta d'auka tana kuka, lamabar Jumy ta kira bugu d'aya ta d'auka, tana d'auka Sumayya ta fashe da kuka ta fara magana "Jumy na shiga uku, Muhdeen ya kore ni ya ce nabar masa gidansa." Cikin mamaki ta ce, "What! akan me ya kore ki?" Cikin muryar kuka ta fara magana "Jumy ya gano gaskiya cewa nayi yunk'urin kashe Inteesar." "Me kika ce? ta yaya ya gano gaskiya? ko dai bata mutu bane?" Jinjina kai tayi kamar tana ganinta ta ce "Ina tunanin bata mutu ba, kuma ta sanar cewa nice nayi mata wannan aiki." "To yanzun ina ita yarinyar take?" "Nima ban sani ba, amma da alamar ya sani tunda har yasan nayi yunk'urin kashe ta, kinga ta sanar da wani kenan, Jumy wallahi jiya na d'and'ani k'amshin mutuwa, kwana na ne kawai a gaba." "To yanzun da ya ce kibar masa gidansa Ina zaki je? London zaki koma?" "Ba inda zanje Wallahi, bazan ta'ba rabuwa da shi ba, ni da shi takalmin kaza mutu ka raba." "Kada fa yazo ya wulak'anta ki." "A shirye nake da na fuskanci ko wane irin wulak'anci daga gare shi, amma bazan tabu da shi ba." Ajiyar zuciya Jumy ta sauke ta ce "Shikenan, Allah ya bada sa'a." Daga nan ta katse kiran ." Tana nan zaune har tsawon mintuna talatin, turo k'ofar yaayi ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Kada na dawo gidan nan na tarar da ke, don wallahi zaki sha mamaki a waje na." Daga nan ya fice tare da buga k'ofar da k'arfi,. kuka tan saki, domin Alah ya sani ba zata iya rabuwa da, gaba d'ya hankalin ta yatashi. Wayar ce ta k'ara d'auka tare da Kiran shila a waya, labarin abunda ya faru tabbata, sannan ta cigaba da cewa "Wallahi bana son rabuwa da shi, ya zanyi ya hak'ura ya barni, so nake mu cigaba da zaman mu, meye mafita? "Ajiyar zuciya shila ta sauke tare da dogon tunani ta ce, "Ina zuwa k'awa ta zan kira ki" Katse kiran tayi ta nufi k'ofar d'akinta da taji ana knocking. Acan gida kuwa tunda Gwaggo ta shiga d'akinta Inteesar ta bita a baya, Gwaggo na zama Inteesar ta fad'a jikinta tare da sakin kuka, cikin tashin hankali Gwaggo ta d'ago ta tana cewa "Yar albarka me ya faru kuma kike kuka?" Cikin kuka ta fara magana "Gwaggo kada ki mayar dani" Kada mu mayar da ke Ina?" "Gidan Yaya" Murmushi Gwaggo tayi tare da cewa "Akan wannan shine kike kuka? to ki kwantar da hankalinki tunda baki so ba zaki koma ba." Cikin kwantar da murya tayi magana "To kiyi mani alk'awari" Dariya Gwaggo ta sake yi sosai ta ce,. "Nayi maki alk'awari sai dai idan kece kika nuna kina kina son cigaba da zama da shi, idan ba haka ba ki d'auka aurenku ya rabu." Dariya tayi sosai tare da cewa "Ni ba abunda zaisa nayi sha'awar komawa gidansa, daga shi har matarsa basu da imani, kashe ni zasuyi idan na cigaba da zama da su." "Ba zasu kashe ki ba sai dai idan kwananki ne suka k'are." "Gwaggo kenan haka zancenki yake, amma ni kad'ai nasan wahalar da nake sha a gidansa." "Dalla matsa ki bani waje, kinsan da haka shine na je gidanku tsawon wata d'aya baki sanar da ni halin da kike ciki ba? " "Gwaggo yadda yake nuna mani so da kulawa, da nace zan fad'a maki ba zaki yarda dani ba, saboda wayau ne da shi,yasan me yakeyi shiyasa ya ya dinga mani abubuwan da yake dan ki yarda da shi " "Shikenan yanzundai ba inda zaki koma." Cikin jindad'i ta jinjina kanta alamar gamsuwa da maganar Gwaggon . Sumayya na zaune tana jiran Kiran wayar sha ta shigo wayarta, sai kuwa ga Kiran nan ya shigo, da saurinta ta d'aga tare da cewa "Yauwa k'awa ta naji kince mafita d'aya ce zaisa na cigaba da zama da Muhdeen me ne ne?" Ajiyar zuciya shila ta sauke tare da cewa "Nasan ko na fad'a maki ba zaki amince kiyi ba, amma nasan hakan ne kawai mafitar da zaisa ku cigaba da mallakar juna, idan kuma baki amince kinyi abunda nasa ki ba to lallai ba ke ba Muhdeen yafi k'arfinki kina ji kina gani." "Kinga kada kiyi shakka akan komai don ba abunda bazan iya aikawa ba akan na cigaba da mallakarsa." *DAGA ALK'ALAMIN*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman k'arin bayani* 09065327995 Love you oll😘😍 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan, duk abu d'aya, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kin shiga indai baki comments zan fitar da ke ne. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. Page6️⃣5️⃣ "Kinga kada kiyi shakka akan komai, don ba abunda bazan iya aikatawa ba akan na cigaba da mallakarsa." 'Dan jim Shila tayi kafin ta ce, "Ki shirya ki tafi gidan Dadynsa da Mummynsa ki nuna nadamarki, sannan ki rok'e su gafara kin tuba ba zaki sake aikata abunda kika aikata ba, nasan suna da mutunci da karamci, ba zasu banzatar da ke ba, musamman idan suka ga abunda d'ansu ya aikata maki, nasan zasu kar'be ki hakan zaisa suyi masa maga..." Tun kafin takai k'arshen maganar da zata yi Sumayya ta katse ta tare da cewa "Bazan iya ba." Sakin baki Shila tayi cike da mamaki ta ce, "Lallai kuwa baki shirya zama da mijinki bane, kuma baki da wani za'bi da ya wuce ki nemi wad'anda zasuyi masa magana ya hak'ura, kinga sai ku cigaba da zama tare da shi, amma idan ba haka ba yadda ya zuciya da ke bazai saurare ki ba." Nidai ki bani wata shawarar amma ba wannan ba, dan gaskiya bazan iya zuwa gidansu na sanar da su ba, dan ba k'aunata suke ba, musamman wannan kakarsa ta tsane ni sosai wallahi, dan haka nima na tsane ta." Dariya shila tayi tare cewa "Idan 'bera na da sata daddawa ma tana da wari, haka nan kawai ba yadda za'ayi dangin mijinki su tsane ki, sai dai idan halinki ne zai sa su tsane ki, nasan halinki fa kuma dangin mijinki suna da mutunci haka nan kawai ba zasu tsane ki ba, idan kika girmama su kika d'auke su iyaye suma zasu d'auke ki 'yarsu." "Kingama? to shawarki bata yi aiki ba ki kawo wata." "To kije ki nemi abokinsa Wanda kika san yana d'aukar shawaransa ki sanar da shi, kuma ki rok'e sa ya taya ki bashi hak'uri ya yafe maki." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa da shawar shila ta ce, "Yanzun kikayi magana mai kyau, zan nemi abokinsa Jabeer duk da shima ba wai jini na ya had'u da shi bane, amma zanyi amfani da shi wajen cikar buri na." Sallama sukayi ta katse kiran. Number wayar Jabeer ta lalubo zata danna masa kira, lokacin ya fito zai shiga motarsa ya fita kenan ya ji wayarsa na ruri, ciro wayar yayi daga cikin aljihunsa ya duba, mamaki ne ya kama shi ganin mai kiransa a bayyane ya furta "Sumayya?" Zuba ma wayar ido yayi yana mamakin ya akayi ta kira sa, har wayar ta katse bai d'aga ba sai da ta sake kiransa a ya d'aga, yana d'agawa yaji muryarta ta fashe da kuka, gabansa ne ya fad'i dan shi a tunaninsa wani abun ne ya samu Muhdeen, cikin tashin hankali ya ce, "Subhanallahi Sumayya me ke faruwa? wani abu ne ya samu Muhdeen?" Kai ta girgiza kamar yana ganinta ba tare da tayi magana ba "Me ke faruwa ki sanar da ni mana." "Jabeer kana ina ne?" "Ina gida yanzun nake shirin zuwa Asibiti, akwai matsala ne?" "Dan Allah ka jira ni gani nan zuwa." "Okay ki hanzarta dan ina sauri." Daga nan ya katse kiran ya koma cikin gidan zuciyarsa cike da tarin tambayoyi, Maryam da ke zaune a dinning room tana breakfast, ta kalle shi ta ce, "Kayi mantuwa ne?" "A'a Sumayya ce ta kira ni wai tana son ganina, shine na dawo na jira ta." "Lafiya take son ganinka?" "Yadda naji tana kuka kam ba lafiya, akwai wani abun da ya faru." Ta'be baki Maryam tayi tare da cewa "Allah ya kyauta" "Ameen ya rabbi" Bayan ta kammala ta dawo ta zauna kusa da shi, suna d'an ta'ba hira. Bayan kimanin mintuna talatin aka turo k'ofara aka shigo da sallama, dukkansu a zabure suka mik'e suka Zuba mata ido cikin mamaki, ganin yadda fuskarta a kumbure, ga goshinta ya ffashe ya kumbura, ga jini da ya bushe a goshin nata,a hankali Jabeer ya furta sunanta. "Sumayya?" Maryam kam da ba don da Jabeer ya ambaci sunanta ba ba zata gane ta ba, domin Muhdeen gaba d'aya ya sauya mata kamanni, kamar ba Sumayya 'yar k'walisa ba, hawaye ne kawai ke tsiyaya daga idanunta k'arasowa tayi ta zauna kan kujera ta fashe da kuka. Jabeer ne ya bud'e baki yayi magana ya ce, "Sumayya ya naganki haka me ya same ki? gashi ma ko treatment ba'a maki ba, Muhdeen baya nan ne da ya barki haka ba tare da ya maki treatment ba?" Sautin kukanta ta k'ara tana cewa "Shine da kansa yayi mani haka." Kallon Juna suka yi Jabeer da matarsa ya ce "Ban gane shi yayi maki haka ba ta yaya hakan ta faru?" Sunkuyar da kanta k'asa tayi, ta kasa magana, hakan yasa Jabeer ya gane cewa lallai Muhdeen ya gano abunda Sumayya ta aikata, dan haka ya ce, "Kan abunda kika aikatawa Inteesar ne yayi maki haka?" A hankali ta gyad'a kai almar eh Tambayar kansa yayi idan har Muhdeen ya iya aikatawa Sumayya haka akan Inteesar, to tabbas yana son Inteesar, duba da yadda ya sauyawa Sumayya kamanni dan tayi yunk'urin kashe Inteesar, Sumayya da yake masifar sonta zai iya 'batawa da kowa kanta amma yau shine yayi mata mugun duka haka? kuma akan yarinyar da ya tsana a rayuwarsa yau ya illata masoyiyarsa akanta? me hakan ke nufi? Shin yanzun ya koma yana son Inteesar ne ko meye?. Haka ya dinga sak'e-sak'e a zuciyarsa sanin ba mai amsa ne yasa ya kalli Sumayya tare da cewa "Ina zuwa" Tashi yayi ya nufi d'akinsa, ba jimawa ya fito da aid box yazo ya fara treatment nata, sai kuka take tana jin zafin goshinta, sai sannu suke jera mata gaskiya sun tausaya mata, Jabeer yayi mamaki dan bai ta'ba tunanin Muhdeen zaiyiwa Sumayya makamancin abunda yayi mata ba, bayan ya gama mata ne yayi mata allura, sannan ya kalle ta ya ce, "Me ke tafe da ke" "Ya kore ni ne ya ce nabar masa gidansa" Jinjina kai Jabeer yayi tare da cewa "Yayi dai-dai ko nine a matsayin da yake abunda zanyi kenan, na ga ma k'ok'ari da bai had'a maki da saki." Da sauri ta d'aga idanunta ta kalli Jabeer jin abunda yake fad'a, ranta ya 'baci sosai da hakan, kamar ta maida masa martanin maganarsa amma sai ta gagara, don nema tazo yi kuma mai nema baya fushi, dan haka ta kwantar da murya tare da marairaice fuska ta ce, "Dan Allah kada ka fad'i haka, wallahi nayi nadama Kan abuda na aikata, hakan ba zata sake faruwa ba, ina son ka taya ni rok'onsa da ya yafe mani ya barni mu cigaba da zamanmu, hakan ba zata sake faruwa ba." Girgiza kai Jabeer yayi tare da cewa "Sumayya wannan tuba da kika yi tuban muzuru ne, na tabbata sai kin sake aikatawa, sai dai idan ba'a 'bata maki rai ba, amma matuk'ar ranki ya 'baci to ba abunda ba zaki iya aikatawa ba, domin kuwa wannan d'abi'arki ce, shiyasa tun farkon auren Inteesar ba yadda banyi ba ya raba maku gida bai saurare ni ba." Zamowa tayi daga Kan kujera ta durk'usa akan akan k'afarta ta fashe da kuka ta fara magana. "Jabeer ka ji tausayi na mana wallahi idan Muhdeen bai yarda ya cigaba da zama da ni ba wallahi zan iya rasa rayuwa ta, shine farin ciki na walalhi zan kiyaye duk abunda zai kawo mana sa'bani, haka ta dinga kuka tana rok'onsa da kuka tare da alk'awari daban-daban har Jabeer ya amince zai saka baki akan maganar tunda tayi nadama, har ya amince zai kaita sukayi sallama da Maryam sannan suka fito suka nufi gidan Muhdeen. Koda suka k'arasa mai gadin ya sanar da su baya ciki, wayarsa ya ciro ya lalubo number Muhdeen ya danna masa kira, jin ya d'aga ne yasa ya ce, "Kana ina ne?" Muhdeen dake driving ya ce, "Sai yau ka tuna da ni?" "Dama mancewa da kai aka ce nayi?" "To yanzun dai mene ne?" "Ina gidanka ne yanzun" "Ni kuma ina hanya zanje gidan Dady ne, kazo gidan sai mu had'u ko?" "A'a kadai zo nan dan maganar ba ta can bane." "Me ke faruwa." "Idan kazo zaka ji koma mene ne" "Daga nan ya katse kiran ya maida wayarsa cikin aljihu, ya kalli Sumayya ya ce, "Yana zuwa mu k'arasa ciki kafin ya zo." Tana gaba yana binta baya suka wace zuwa falo. *KUYI HAK'URI DA WANNAN* *DAGA ALK'ALAMIN*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON K'ARIN BAYANI* 09965327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan, duk abu d'aya, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kin shiga indai baki comments zan fitar da ke ne. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. Page6️⃣5️⃣ "Kinga kada kiyi shakka akan komai, don ba abunda bazan iya aikatawa ba akan na cigaba da mallakarsa." 'Dan jim Shila tayi kafin ta ce, "Ki shirya ki tafi gidan Dadynsa da Mummynsa ki nuna nadamarki, sannan ki rok'e su gafara kin tuba ba zaki sake aikata abunda kika aikata ba, nasan suna da mutunci da karamci, ba zasu banzatar da ke ba, musamman idan suka ga abunda d'ansu ya aikata maki, nasan zasu kar'be ki hakan zaisa suyi masa maga..." Tun kafin takai k'arshen maganar da zata yi Sumayya ta katse ta tare da cewa "Bazan iya ba." Sakin baki Shila tayi cike da mamaki ta ce, "Lallai kuwa baki shirya zama da mijinki bane, kuma baki da wani za'bi da ya wuce ki nemi wad'anda zasuyi masa magana ya hak'ura, kinga sai ku cigaba da zama tare da shi, amma idan ba haka ba yadda ya zuciya da ke bazai saurare ki ba." Nidai ki bani wata shawarar amma ba wannan ba, dan gaskiya bazan iya zuwa gidansu na sanar da su ba, dan ba k'aunata suke ba, musamman wannan kakarsa ta tsane ni sosai wallahi, dan haka nima na tsane ta." Dariya shila tayi tare cewa "Idan 'bera na da sata daddawa ma tana da wari, haka nan kawai ba yadda za'ayi dangin mijinki su tsane ki, sai dai idan halinki ne zai sa su tsane ki, nasan halinki fa kuma dangin mijinki suna da mutunci haka nan kawai ba zasu tsane ki ba, idan kika girmama su kika d'auke su iyaye suma zasu d'auke ki 'yarsu." "Kingama? to shawarki bata yi aiki ba ki kawo wata." "To kije ki nemi abokinsa Wanda kika san yana d'aukar shawaransa ki sanar da shi, kuma ki rok'e sa ya taya ki bashi hak'uri ya yafe maki." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa da shawar shila ta ce, "Yanzun kikayi magana mai kyau, zan nemi abokinsa Jabeer duk da shima ba wai jini na ya had'u da shi bane, amma zanyi amfani da shi wajen cikar buri na." Sallama sukayi ta katse kiran. Number wayar Jabeer ta lalubo zata danna masa kira, lokacin ya fito zai shiga motarsa ya fita kenan ya ji wayarsa na ruri, ciro wayar yayi daga cikin aljihunsa ya duba, mamaki ne ya kama shi ganin mai kiransa a bayyane ya furta "Sumayya?" Zuba ma wayar ido yayi yana mamakin ya akayi ta kira sa, har wayar ta katse bai d'aga ba sai da ta sake kiransa a ya d'aga, yana d'agawa yaji muryarta ta fashe da kuka, gabansa ne ya fad'i dan shi a tunaninsa wani abun ne ya samu Muhdeen, cikin tashin hankali ya ce, "Subhanallahi Sumayya me ke faruwa? wani abu ne ya samu Muhdeen?" Kai ta girgiza kamar yana ganinta ba tare da tayi magana ba "Me ke faruwa ki sanar da ni mana." "Jabeer kana ina ne?" "Ina gida yanzun nake shirin zuwa Asibiti, akwai matsala ne?" "Dan Allah ka jira ni gani nan zuwa." "Okay ki hanzarta dan ina sauri." Daga nan ya katse kiran ya koma cikin gidan zuciyarsa cike da tarin tambayoyi, Maryam da ke zaune a dinning room tana breakfast, ta kalle shi ta ce, "Kayi mantuwa ne?" "A'a Sumayya ce ta kira ni wai tana son ganina, shine na dawo na jira ta." "Lafiya take son ganinka?" "Yadda naji tana kuka kam ba lafiya, akwai wani abun da ya faru." Ta'be baki Maryam tayi tare da cewa "Allah ya kyauta" "Ameen ya rabbi" Bayan ta kammala ta dawo ta zauna kusa da shi, suna d'an ta'ba hira. Bayan kimanin mintuna talatin aka turo k'ofara aka shigo da sallama, dukkansu a zabure suka mik'e suka Zuba mata ido cikin mamaki, ganin yadda fuskarta a kumbure, ga goshinta ya ffashe ya kumbura, ga jini da ya bushe a goshin nata,a hankali Jabeer ya furta sunanta. "Sumayya?" Maryam kam da ba don da Jabeer ya ambaci sunanta ba ba zata gane ta ba, domin Muhdeen gaba d'aya ya sauya mata kamanni, kamar ba Sumayya 'yar k'walisa ba, hawaye ne kawai ke tsiyaya daga idanunta k'arasowa tayi ta zauna kan kujera ta fashe da kuka. Jabeer ne ya bud'e baki yayi magana ya ce, "Sumayya ya naganki haka me ya same ki? gashi ma ko treatment ba'a maki ba, Muhdeen baya nan ne da ya barki haka ba tare da ya maki treatment ba?" Sautin kukanta ta k'ara tana cewa "Shine da kansa yayi mani haka." Kallon Juna suka yi Jabeer da matarsa ya ce "Ban gane shi yayi maki haka ba ta yaya hakan ta faru?" Sunkuyar da kanta k'asa tayi, ta kasa magana, hakan yasa Jabeer ya gane cewa lallai Muhdeen ya gano abunda Sumayya ta aikata, dan haka ya ce, "Kan abunda kika aikatawa Inteesar ne yayi maki haka?" A hankali ta gyad'a kai almar eh Tambayar kansa yayi idan har Muhdeen ya iya aikatawa Sumayya haka akan Inteesar, to tabbas yana son Inteesar, duba da yadda ya sauyawa Sumayya kamanni dan tayi yunk'urin kashe Inteesar, Sumayya da yake masifar sonta zai iya 'batawa da kowa kanta amma yau shine yayi mata mugun duka haka? kuma akan yarinyar da ya tsana a rayuwarsa yau ya illata masoyiyarsa akanta? me hakan ke nufi? Shin yanzun ya koma yana son Inteesar ne ko meye?. Haka ya dinga sak'e-sak'e a zuciyarsa sanin ba mai amsa ne yasa ya kalli Sumayya tare da cewa "Ina zuwa" Tashi yayi ya nufi d'akinsa, ba jimawa ya fito da aid box yazo ya fara treatment nata, sai kuka take tana jin zafin goshinta, sai sannu suke jera mata gaskiya sun tausaya mata, Jabeer yayi mamaki dan bai ta'ba tunanin Muhdeen zaiyiwa Sumayya makamancin abunda yayi mata ba, bayan ya gama mata ne yayi mata allura, sannan ya kalle ta ya ce, "Me ke tafe da ke" "Ya kore ni ne ya ce nabar masa gidansa" Jinjina kai Jabeer yayi tare da cewa "Yayi dai-dai ko nine a matsayin da yake abunda zanyi kenan, na ga ma k'ok'ari da bai had'a maki da saki." Da sauri ta d'aga idanunta ta kalli Jabeer jin abunda yake fad'a, ranta ya 'baci sosai da hakan, kamar ta maida masa martanin maganarsa amma sai ta gagara, don nema tazo yi kuma mai nema baya fushi, dan haka ta kwantar da murya tare da marairaice fuska ta ce, "Dan Allah kada ka fad'i haka, wallahi nayi nadama Kan abuda na aikata, hakan ba zata sake faruwa ba, ina son ka taya ni rok'onsa da ya yafe mani ya barni mu cigaba da zamanmu, hakan ba zata sake faruwa ba." Girgiza kai Jabeer yayi tare da cewa "Sumayya wannan tuba da kika yi tuban muzuru ne, na tabbata sai kin sake aikatawa, sai dai idan ba'a 'bata maki rai ba, amma matuk'ar ranki ya 'baci to ba abunda ba zaki iya aikatawa ba, domin kuwa wannan d'abi'arki ce, shiyasa tun farkon auren Inteesar ba yadda banyi ba ya raba maku gida bai saurare ni ba." Zamowa tayi daga Kan kujera ta durk'usa akan akan k'afarta ta fashe da kuka ta fara magana. "Jabeer ka ji tausayi na mana wallahi idan Muhdeen bai yarda ya cigaba da zama da ni ba wallahi zan iya rasa rayuwa ta, shine farin ciki na walalhi zan kiyaye duk abunda zai kawo mana sa'bani, haka ta dinga kuka tana rok'onsa da kuka tare da alk'awari daban-daban har Jabeer ya amince zai saka baki akan maganar tunda tayi nadama, har ya amince zai kaita sukayi sallama da Maryam sannan suka fito suka nufi gidan Muhdeen. Koda suka k'arasa mai gadin ya sanar da su baya ciki, wayarsa ya ciro ya lalubo number Muhdeen ya danna masa kira, jin ya d'aga ne yasa ya ce, "Kana ina ne?" Muhdeen dake driving ya ce, "Sai yau ka tuna da ni?" "Dama mancewa da kai aka ce nayi?" "To yanzun dai mene ne?" "Ina gidanka ne yanzun" "Ni kuma ina hanya zanje gidan Dady ne, kazo gidan sai mu had'u ko?" "A'a kadai zo nan dan maganar ba ta can bane." "Me ke faruwa." "Idan kazo zaka ji koma mene ne" "Daga nan ya katse kiran ya maida wayarsa cikin aljihu, ya kalli Sumayya ya ce, "Yana zuwa mu k'arasa ciki kafin ya zo." Tana gaba yana binta baya suka wace zuwa falo. *KUYI HAK'URI DA WANNAN* *DAGA ALK'ALAMIN*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON K'ARIN BAYANI* 09965327995 Love you oll😍😘 Comments & share Comments & shareCanFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan duk abu d'aya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Pa6️⃣6️⃣ Tana gaba yana binta a baya suka wuce zuwa falo. Zama suka yi suna jiransa ba jimawa ya k'araso tara da sallama d'auke a bakinsa, yana ganin Sumayya ya tamke fusaka tare da cewa "Ke me na fad'a maki?" Jabeer ne yayi magana ya ce, "Dan Allah ka saura..." D'aga masa hannu yayi alamar dakatarwa ya ce, "Please Jabeer kada ka shiga wannan maganar, ka barta kawai halinta sai ita." "Nasan girman laifin da kayi mata kuma na nuna mata kuskurenta, ta nuna tayi nadama dan Allah ka kar'bi tubarta, ko Allah da ya halicce mu idan munyi masa laifi yana yafe mana, ballantana kai bawan Allah, ka bata dama ta gyara kuskurenta insha Allah ba zata maimaita ba, nasan irin son da take maka kuma ba zata iya rabuwa da kai ba, don tasan idan ta sake hukuncin da zai biyo baya, kayi hak'uri dan Allah ko wannan dukan da kayi mata ai yakamta ace ka hak'ura ka huce haushinka." Murmushin takaici yayi tare da cewa, "Bazan ta'ba hucewa ba har sai Inteesar ta dawo cikin gidan nan matuk'ar bata dawo ba wallahi bazan ta'ba hucewa ba." Da sauri Sumayya ta kalli Muhdeen jin kalaman da suke fitowa daga bakinsa,wani bak'in ciki da takaici ya lullu'be ta, ta d'auka fushin da yayi da ita na yunk'urin kisan Kaine, wanda ko akan waye zai d'auki mataki dan babban laifi ta aikata, amma yanzun ta fahimci cewa akan Inteesar ne yayi hakan, take ta tsinci Kanta a wani yanayi na tsananin bak'in ciki, ji tayi kamar ta kurma ihu tayi hauka, amma tuna halin da take ciki yasa tayi k'ok'arin danne bak'in cikinta kada su fahimta, a zubiyarta tana ayyana irin abunda zata aikata, tana magana ita kad'ai a tunaninta a zuciyarta take magana bata san maganar zuciya ce ta fito fili ba, jin muryarta sukayi tana cewa "Kwantar da Hankalinki Sumy komai zai dawo dai-dai, kada wannan ya d'aga maki hankali kece zakiyi nasara." Jin muryar Jabeer na cewa "Nasara?" Yasa ta gane cewa a fili tayi maganar, dan haka ta wayance da cewa, "Eh mana ai mai hak'uri shine mai nasara." Muhdeen ne ya kalli Jabeer ya ce, "Jabeer a zahirin gaskiya bazan..." Jabeer yayi saurin cewa "Kada ka ce haka, na fahimci matsalarka, insha Allah zata gyara ka tuna baya da darajar iyaye da kuma soyayyar da ta nuna maka kayi hak'uri komai ya wuce." Murmushin takaici yayi tare da cewa "Ba zata ta'ba canzawa ba, na san wace ce ita duk da yanzun ta wuce sani na, kuma ka sani ba abunda zai wuce har sai Inteesar ta dawo." Danne bak'in cikinta tayi tare da k'ak'alo murmushi ta ce, "Bakomai duk da hakan nagode Allah ya dawo da ita lafiya, tana ina ne?" "Bai shafe ki ba, salon na fad'a maki kije ki k'arasa ta?" Murmushi tayi ta ce "Yanzun na Sumayya da ka sani a baya bace, wannan ta daban ce na sauya, ina son ka d'auki abunda nayi a baya kayi jifa da shi kada ka sake waiwayawa gare shi, hakan zaisa mu samu zaman lafiya." Durk'usawa tayi akan gwuiwarta biyu ta fara magana "Mijina ka yafe mani kuskuren da na aikata na tuba, ka gafarce ni hakan ba zata sake faruwa ba insha Allah." Bud'e baki yayi da niyyar magana, Jabeer ya ce, "Kada ka ce komai ka yafe mata dan albarkacin nabiyyin rahmati ." Murmushi yayi tare da cewa "Wato Jabeer kasan cewa duk fushin da nayi idan aka kira annabin rahama sai na hak'ura, dan ba za'ace annabi ba banyi ba, amma bakoma zaka iya tafiya." Sallama Jabeer yayi masa ya tafiyarsa, yana fita ta fad'a jikin Muhdeen ta fashe da kuka ta fara magana "Nasan zaka d'auke ni mace mara aji, mai nacin soyayya kada kaga laifi na zuciyata ce take assasa ni, I'm crazy about yor I love you more than everything." Kuka ta dingayi sosai shima kansa yasan tana masifar sonta, wanda had'uwarsu ta farko ita ce ta fara nuna masa so kafin shi ya nuna mata, kuma yasan zata iya 'batawa da kowa akansa, amma duk da haka d'abi'arta baya sonsu, kallon fuskarta yayi ganin yadda ya sauya mata kamanni kuma ya kore ta amma ta kasa tafiya ta dawo ta nemi yafiyarsa, wanda bai ta'ba tunanin hakan ba, yadda take ji da kanta amma wannan Karan ta aje ji da kan a gefe saboda sonsa da gudun rasa shi, tausayinta ne ya kama sa cikin tausayi ya ce, "Am so sorry" "Ka daina sona ko?" Murmushi yayi tare da cewa "Ban daina sonki ba, kuma bazan ta'badainawa ba, halinki ne bana so, idan kika sauya bani da wata matsala da ke." Goge hawayen fuskarta tayi tare da cewa "To naji zan gyara, ita fa kana sonta?" Ya gane abunda take nufi amma ya ce, "Wace ce nake so?" "Inteesar" "Dukanku mata na ne kuma dukanku ina sonku." 'Daga kanta tayi daga k'irjinsa ta kalle shi da sauri, k'walla ce take k'ok'ari zubo mata na kishinsa, amma sai tayi saurin maida hawayenta ta ce, "Kai da kanka ka sanar dani cewa kai baka sonta ka tsane ta, kuma nasan auren doke akayi maku daga kai har ita baku son juna, to yaushe ka fara sonta haka? dama saboda ita ce kayi mani dukan da kayi mani? saboda ita ce nemi raba ni da rayuwata?" "Ba saboda ita bane, ko da ma waye kika aikatawa abunda kika aikata mata hukuncin da zan maki kenen, yakamata ki gane kuskurenki." Jinjina kai tayi cike da k'unar rai ta ce, "Yanzun idan ta dawo gidan nan tare zamu dinga sharing d'inka ni da ita?" Jinjina mata kai yayi alamar eh kasa danne bak'in cikinta tayi ta fashe masa da kuka tana cewa "Ai ba haka mukayi da kai ba, cewa kayi ko an d'aura maka aure da ita ba ruwanka da ita, baka d'auke ta mata a gare ka ba, na d'auka 'yar aiki aka kawo mani, amma shine yanzun zaka canza magana?" "To yanzun maganarki zanbi, ko maganar Aah da manzonsa zanbi?" Kallonsa tayi da idanunta da sukayi jazir tabce, "Nidai na fad'a maka" Addinina ya halatta mani auren mata hud'u, koda kike ganin Inteesar auren had'i akyi muna amma ai tana da hakki akaina, kuma idan na fifita ki aknta ko kuma na fifita ta aknaki Allah zai tambaye ni, ko kina son ranar gobe kiyama na tashi 'barin jiki na a karkace?" Ba zata iya cigaba da saurarensa ba, dan haka ta ruga a guje zuwa d'akinta tana kuka, a tunaninta zai biyo ta ne kamar yadda suka Saba idan tayi haka ya bita shima a guje, amm ayau kam sai taga ba haka ba, ko a jikinsa ya fice a binsa, lokacin da taji tashin motarsa kukanta ya k'aru sosai Pillows dake kan gadon ta fara d'auka tana jifa da su zanin gadon ma ta yaur tayi jifa da shi, ta mik'e ta nufi dressing mirror kenan ta tuna da zancensa, na cewa halinta ne baya so, don haka ta dakata ta tsaya tana nazari fasawa tayi ta kwashe pillows din da bedsheet ta d'ora Kan gadon don bata ma san yadda zata gyara gadon ta shimfid'a sabon zanin gadon ba. A can gidan kuwa Inteesar tana cikin d'akin Mufida ta rafka tagumi, tunanin Ummanta kawai take yi, don tunda suka je asibiti dau d'aya ta gaida Ummanta bata sake zuwa ba, don bata san ya jikin nata ba ya kasance ba, ta dai san ance an sallame su tana gida, dan haka ta mik'e ta nufi falo don neman izinin zuwa gaida Mahaifiyarta. Zaune suke Gwaggo ce da Mummy suna fira, Inteesar ta k'araso wajen tare da sallama, durkuwa tayi tare da cewa "Sannunku" Gaba d'ayansu suka amsa da yauwa, Gwaggo ta ce, "Yar albarka kin fito? Kai kawai ta gyad'a alamar eh, Mummy ta zuba mata ido tana murmushi ta ce "Daughter ya dai kamar akwai magana a bakinki ko?" Sunkuyar da kanta k'asa tayi ta ce, "Eh Mummy" "Me ke faruwa?" Gwaggo ce tayi saurin cewa "Ki dai kin gaji da zama da mu ne mu maida je d'akin mijinki?" Tura baki tayi tare da yin narai da Ido kamar zatayi kuka, Mummy ta ce "Kwantar da hankalinki ba zamu maida ke ba kinji?" Kai ta jinjina cikin sanyin muryarta ta ce, "To Mummy" "Yauwa to ki fad'a mani akwai abunda kike buk'ata ne?" Kai ta jinjina "Dama cewa zanyi tunda aka sallamo Umma banje na gaishe ta ba, tunda tana gida muna kusa nake so naje na gaishe ta." Gwaggo ta ce "Akan wannan shine kike damuwa? ai uwa ba wasa ba, kuma ai ba nisa bane nan baya ne kije kawai amma dan Allah kada ki sanar da su halin da ake ciki kada hankalinsu ya tashi, kinga Ummanki ba lafiya ne da ita sosai ba, ki nuna mata daga gidan mijinki kika zo kika fara sauka nan sannan kika je gaishe ta." Kai Inteesar ta jinjina alamr to sannan ta nufi d'akin Mufida, ba jimawa ta fito da hijabinta jar k'asa, sallama tayi masu ta tafi. Ummanta na zaune tana wankin kayanta, Inteesar ta shigo da sallama, tana hangen Umma ta k'arasa a guje ta rungume ta, Umman nata tayi farin ciki sosai da ganin tilon 'yarta. "Umma Ina wuni?" "Lafiya lau wlh" "Ya jikinki?" "Jiki Alhamdulillah" "Mummy tashi na k'arasa wankin" "Ai na gama " Inteesar ce ta dinga daukar kayan tana shanyawa akan igiyar shanya, a haka har suka gama. A can gidan Mummy kuwa Inteesar na barin gidan sai ga Muhdeen yazo, bayan yayi parking ne ya gaisa da ma'aikatan gidan sannan ya nufi cikin gidan. A falo ya tarar da Gwaggo da Mummy, gaishe su yayi sannan ya durk'usa akan kadarsa ya ce "Mummy in wuni?" Ba yabo ba fallasa ta amsa masa, dubansa Gwaggo tayi tare da kauda kanta taji ya ce, "Ina wuni Gwaggo" "Wai yau Kaine ka gaishe ni? banza bata kai zomo kasuwa, abunda kake so na sani saboda matarka ka gaishe ni, kuma ta ba zata koma gidanka ba Dan haka kai kawo mata takardar saki." Ji yayi kamar an soka masa mashi a kahon zuciyarsa, bazai iya jure maganar Gwaggo ba da haka ya mik'e ya nufi k'ofar fita ba tare da cewa komai ba, a harabar gidan ya had'u da Mufida ya kalle ta ya ce, ."Inteesar tana barci ne?" Wallah nima yanzun na dawo gidan, kataf suka ju muryar mai gadin yana cewa "Bata jima da fita ba" Da sauri ya kalle shi "What!? ta fita zuwa Ina?" "Wai zata je gaida Mahaifiyarta da jiki" Bai Kara cewa komai ba yaja motarsa yabar gida. Inteesar tana gama shanya kayan Ummanta yaro yayi sallama ya shigo ya ce wai ana sallama da Inteesar, gabnta ne ya fad'i ta ce waye? yaron ya shaida mata cewa wani ne da mota yazo, ta ce ya ke ya sanar bata nan Umma ce ta ce , "Saboda me zaki ce haka, bayan kinsan idan ba mijinki ba ai ba Wanda zaizo nemanki, ko dai tare kuka zo ne ya tsasya jiranki waje?" Rasa ba Umma amsa tayi don bata son ta fahimci halin da take ciki da mijinta, bata gama tunanin ba ta ju Umma na cewa ki tafi ki same shi." Ba musu ta d'auki hijabi ta nufi k'ofar fita, gabanta ne ya fad'i ganin Usman zaune akan motarsa ya zuba mata ido yana sakar mata murmushi, a zuciyarta ta ce ya akayi yasan tana nan, k'arasawa tayi da niyyar idan ta je ta sanar da shi gaskiya an mata aure da wani. "Ina wuni? Murmushi yayi tare da cewa "Bazan amsa gaishwar ba tsawo kwanki kina wahalar da ni, kullun sai na kira wayarki bata shiga, na kasa hak'uri tsawon lokaci banganki ba zuciyata ta kasa jurewa." Dai-dai lokacin motar Muhdeen ya k'araso yana parking idanunsa ya sauka akan Inteesar da Usman, ji yayi jinsa da ganinsa sun d'auke na wucen gadi, Usman sai Murmushi yake sakar mata a fusace ya fito daga cikin motar ya nufe su, Inteesar na ganinsa sai da ta tsorata, amma ta daure ya Harare ta ya ce, "Kina da hankalinki kuwa, kinsan abunda kikayi kuwa" Kallonsa tayi ta ta'be baki ta ce, "Waye kai a ina ka sanni?" Juyawa tayi ta koma cikin gidansu, ya bita da kallon mamaki da al'ajabi, sannan ya kalli Usman ya tuna cewa shine wanda ya ta'ba ganin suna zance da Inteesar kafin tayi aure, kuma shine ya gani ya d'auko Inteesar a mota sunje ubasanjo complex tana zaune gaban motarsa suna sakarwa juna murmushi, rintse idanunsa yayi tare da bud'e su ya kalli Usman ya ce, "Waye kai?" Dariyar rainin hankali Usman yayi tare da cewa "Wanda yazo akeyiwa wannan tambaya ba wanda aka tarar ba" "Ina mai gargad'i a gare ka ka kiyayi matata." "Wace ce matarka? Inteesar kake nufi? to ai naga ita wacce kake Kira matarka bata ma sanka ba bata san kanayi ba, isaka ne ke wahalar da mai kayan Kara." *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don k'arin bayani* 09965327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan duk abu d'aya ne, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page6️⃣7️⃣ "Wace ce matarka? Inteesar kake nufi? to ai naga ita wacce kake Kira matarka bata ma san kanayi ba, isaka ne ke wahalar da mai kayan Kara." Muhdeen ne ya fusata ya shak'o wuyar rigar Usman ya ce, "Ka iya bakinka ka san kuma da wa kake magana, idan baka fita daga harkarta ba zan d'auki mummunar mataki akanta." Dai-dai lokacin Abban Inteesar ya k'araso K'ofar gidan, ganinsu a hakanan yasa ya k'araso wajensu da sauri "Subhanallahi Muhammad me ke faruwa ne?" Sakin wuyar Usman yayi tare da hankad'a shi gefe yana huci kamar wani mayunwacin zaki, Usman ne ya durk'usa ya gaida Abba. "Ina wuni Abba?" "Lafiya lau me ke faruwa ne?" Shiru suka yi ba wanda yayi magana, sai da ya sake tambayarsu a karo na biyu sannan Usman ya ce, "Dama nazo wajen Inteesar ne muna tsaye muna magana da ita, daga zuwansa ya fara mata fad'..." Abba ya katse sa da cewa "Yaushe Inteesar tazo gidan? kuma ka meye alak'arka da ita?" 'Dan sunkuyar da kansa k'asa yayi tare da cewa " Abba aurenta nake son nayi?" Kallon mamaki Abba yayi masa ya ce, "Bawan Allah kai musulmi ne?" "Eh ni musulmi ne Abba." "Kasan haramun ne ka nemi matar aure?" Da sauri Usman ya kalle shi tare da cewa "Matar aure?" "Bata fad'a maka bane?" Gaba d'aya jikinsa ne yayi sanyi, amma sai ya daure ya ce, "Bansan cewa tana da aure ba Abba, bata fad'a mani ba." "Tun yaushe kake tare da ita?" "Baka gane ni bane Abba? nine Usman wanda na muka ta'ba samun accident da Inteesar kimanin watanni hud'u da suka wuce." Sai a lokacin Abba ya tuna Usman ya ce "Allah sarki, sai yanzun na tuna, amma ya akayi kasan tana nan ko kuma kuna waya da ita ne?" "A'a Abba bamu waya da ita na dad'e ko na kira wayarta bata d'agawa wani lokacin bata shiga ko na kira a kashe." To Inteesar tayi aure akwai igiyar aure akanta, wannan da ka gani shine mijinta, kallon Muhdeen yayi tare da sakin murmushi ya ce, "Dan Allah kayi hak'uri ka gadarce ni rashin sani ne ya kawo haka, ina maku fatan alkhairi a rayuwar aurenku." Abba ya ce " Masha Allah, Allah ya baka wata macen auren tagari" Sallama ya masu ya bud'e murfin motarsa ya shiga ya bar wajen, Abba ne ya kalli Muhdeen ya ce, "Dan Allah kayi hak'uri Muhammad" "Bakomai Abba." Kai Abba ya jinjina tare da cewa "Mu shiga ciki ko? ka tsaya kana tsaye a waje." Shiga cikin gidan sukayi Abba na gaba Muhdeen na binsa a baya, da sallama suka shiga Inteesar da Umma na zaune a tabarma, Umma ce ta ce, "Muhammad sannu da zuwa" "Yauwa sannu Umma" Durk'usawa yayi k'asa ya gaida Umma "Umma ina wuni" "Lafiya lau Muhammad bya aiki?" "Aiki Alhamdulillah" Zama yayi akan tabarma da Umma ta shimfid'a masa, Abba ne ya kalli Inteesar dake gaishe sa "Abba ina wuni?" "Lafiya lau, waye yazo wajenki a waje?" Shiru tayi ta kasa magana, tsawa ya daka mata wanda yasa ta firgita ta matsa kusa da Muhdeen "Kinsan cewa kina da aure zaki tsaya kina magana da wani saurayi, kinci arzikin ya sanar da ni gaskiya baku waya amma da yazo shine kika tsaya da shi baki sanar da shi cewa ke matar aure bace?" "Abba ina k'ok'ari na sanar da shi ne sai ga yaya yazo." Salati Umma ta saka tare da cewa "Dama ba mijinki bane yazo? ai na d'auka shine yazo shiysa na barki kika fita." Abba ne ya ce, "Daga yau kada ki sake kula shi duk da shima naga Alamar yana da sanin yakamata, kuma nayi masa bayanin kinyi aure ya bawa mijinki hak'uri, kada na sake jin makamancin wannan abun ya faru idan kuma ba haka ba zakiyi mamanki na." Idanunta cike da k'walla ta ce, "Abba kayi hak'uri" "Bani zaki ba hak'uri ba mijinki zaki nemi yafiyarsa, tashi ku tafi." "Abba mu tafi ina" "Ina ne gidanku? Kina da wani gidan da yafi gidan mijinki ne a yanzun?" "Abba ba tare muka zo ba kuma ni sai anjima zan..." Kafin takai k'arshen maganar da tayi niyyar yi ne ya d'aga mata hannu "Tashi kibi mijinki" Wani bak'in ciki da takaici ne suka lullu'be ta, yayi da shi kuma zuciyarsa fara tas murna kamar ya zuba ruwa k'asa yasha, tashi yayi tare d masu sallama da godiya ya nufi hanyar fita yana jiran fitowarta, sallama tayi harda kukanta basu kula ta ba haka ta mik'e ta nufi hanyar fita Abba na binta a baya. Yana tsaye jikin motarsa yana ganin fitowarsu baisan lokacin da murmushi ya su'buce masa ba, kwana tayi don komawa gidansu Mummy taji muryar Abbanta na cewa "Ina zakije?" Haka yasa ta dawo don tuna maganar Mummy da suka ce kada ta sanar da Abbanta da Ummanta matsalar da ta faru, hakan yasa tayi shiru ta shiga motar ganin yana bud'e mata murfin motar, shiga tayi inda Abba ya k'ara bashi hak'uri ya nuna masa bakomai, Abba ya koma gida yayin da Inteesar ta d'ora kanta a saman cinyarata tana ta sakin kuka, tada motar yayi yabar layain, jin sautin kukanta yake har cikin ransa, amma shi baiga abun kuka ba, shi fa ta masa laifi baiyi kuka ba sai ita, saboda tasabar jin dad'i. Ganin tsawon lokaci suna tafiya ne kuma tasan gidan su day na Mummy ba nisa yasa ta d'aga kai taga ina suke, gabanta ne ya fad'i ganin wani hanya daban Wanda bata san da ita ba , da sauri ta kalle shi ganin ya tamke fuska ya fito mata a asalin Muhdeen d'insa yasa taji tsoronsa ya dawo mata sabo, d'aurawa tayi ta ce "Yaya ina zaka kaini? wallahi su Mummy zasu neme ni basu ganeni ba." Kamar kurma haka ya k'yaleta kamar baiji ta ba, sau uku tana magana ya share ta "Nidai gaskiya ka mayar Dani gida dan bazan koma gidanka ba." Nan ma shiru bata ankara ba taga yayi parking a k'ofar gidan wani tangamemen gida, horn yayi mai gadi ne ya fito ya ga Muhdeen sanna ya bud'e masa gate ya shiga yayi parking, mai gadin ya k'araso yana gaishe sa ya amsa tare da tambayarsa ya aiki, Nima ya gaishe ni amma duk rashin son magana da na ke na amsa, tsaye nayi ina k'arewa gidan kallo kamar wata bak'auya, ta shagala da kallon k'ayataccen gidan, ta mance da wai fushi take da shi, sai jin muryarsa tayi yana cewa "Idan kin gama sai kizo mu shiga ciki." Kunya ce ta kamata ta had'e fuska ta ce "Ba inda zan shiga." Ganin yana tattare hannun rigaraa ya sa ta ce "Me zakayi"? "Zan d'auke ki ne." Da sauri tayi gaba yana binta a baya tsayawa tayi daf da k'ofar yayin da shi kuma ya bud'e k'ofar ya shiga, tsayawa tayi ta coge ya kalle ta ya ce, "Ba zaki shigo bane? tura baki tayi tare d cewa "Ba inda zan ahiga har sai ka mayar dani gida." Baice da ita komai ba ya shige ciki abinsa, ya barta nan tsaye a wajen. Babban Babban falo ne mai d'auke da sofa sa set biyu na royal, waoyinsa ya ajiye Kan center table dake falon,. kai tsaye bedroom ya wuce ya inda ya fad'a toilet yayi wanka ya ya feshe jikinsa da turare mai dad'in k'amshi. Fitowa yayi sanye da kananun kaya a jikinsa, riga red color da wanda 3 quarter black , yayi masifar kyau yana tafe cikin takunsa na k'asaita da tafiyarsa irin na lafiyayyun maza, k'irarsa da cikar zatinsa irin na cikakken namiji suka bayyana, k'amshin turarensa ne suka fara sanar da ita ya k'araso, juyawa ta kalle shi k'wayar idonsa ta kalla da sauri ta janye idonta ganin wani irin kwarjini da yayi mata, bata ankare ba sai ji tayi ya d'auke ta cak kamar jaririya, wutsil wutsil ta fara yi amma rikon da yayi mata ba na wasa bane. Har cikin bedroom d'insa ya shiga da ita bai dire ta ko ina ba sai cikin toilet a bahon wanka dake cike da ruwa, ganin yadda ya saka ta tsamo-tsamo cikin ruwa gata ta jike sharkaf da ruwa, hakan yasa ta fashe da kuka bata San me zata cewa su Mummy da Gwaggo ba, kuka ta cigaba da yi tana cewa, "Ni ka kaini gida" "Wane gida zan kaiki? ai wannan shine gidanki." "Nikam ba gida na bane nan " "To naji ba gidanki bane bari nayi maki wanka sai ma tafi ? amma idan baki tsaya nayi maki wanka b a to muna na. gidan." "Ya zanyi da kayana da suka jike?" "Kada ki damu akwia sababbin kaya a gidan nan zan baki ki saka." Make kafada tayi "Ban yarda ba su Gwaggo zasuyi mani fad'a" Bai saurare ta ba ya fara cire mata rigar jikinta, bayan ya saura daga ita sai bra and pant ne ya rik'e bra d'in tare da rufe k'irjinta, 'balle bra d'in yayi dukiyar fulaninta suka bayyana cirko -cirko kamr su tsire idanunsa, cije le'b'bensa yayi tare da zare mata pant d'in, sabulun wanka ya d'eba yana sawa a hannunsa yana murza mata a jikinta duk da ta fahimci cewa bawai wanka zaiyi mata ba kawai yana so ne ya luguiguita ta Dan yadda ya dinga mata wasa da bra d'inta yana shafasu da sunan wanka, ganin abun nasa yayi yawa ne yasa ta saka masa kuka. Sannan ya d'aurayota ya d'aura mata towel, ita kuma kunya ce ke damunta ta da takaici,bayan ya nad'e ta cikin towel d'in ya sungumenta kamar jaririya sai gaban dressing mirror zai sha fa mata ta ce bata so, don haka ya dire ta a tsakiyar gadon shim ya kwanta tare da janyo masu bargo ya lullu'be su. "Baby nayi missing naki sosai." Kuka ta saka ta ce "Wallahi nikam bazan yarda ba sai ka..."kafin takai k'arshen maganar ta ya had'e bakinsu waje d'aya ya fara tsotson la'b'banta kamar ya samu sweet, hannunsa na kan bra d'in ta yana murza su. Nan fa ta nuna masa bata San zancenba sam ta fara k'ok'arin k'watar kanta. *Daga alk'alamin* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan *Don k'arin bayani* 09065327995 Love you oll😘😍 Comments &shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan duk abu d'aya ne, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page6️⃣8️⃣ Nan ta nuna masa bata San zancen ba sam, fara k'ok'arin k'watar kanta, amma ina bai bata wanna damar ba nan fa ya fara zaucewa, wayarsa ce ta fara ruri bai kula ba ya cigaba da abunda yake yayin da Inteesar kuma sai kuka take, hankad'e sa tayi zata gudu cikin zafin nama ya janyo ta yayin da wayarsa ta sake d'aukar wani ruri, tsuki yayi ya janyo wayar da niyyar kasheta gaba d'aya, amma suna Dadynsa ya gani zaro ido waje yayi ta kalli Inteesar sannan ya d'aga wayar tare da k'arawa a kunne, tun kafin yayi magana ya ji muryar Dady na cewa "Muhammad ina kake?" Cikin sark'ewar murya ya ce, "Ina gida Dady?" "Ina inteesar take?" "Tana tare da ni" "Na baka mintuna goma yanzun ka kawo mani Inteesar ko nayi mummunar 'bata maka rai." Bai jira cewarsa ba ya katse kiran, Inteesar da ke rungume a jikinsa tana jin duk maganar da Dady yayi ne ta saki murmushi ta ce "Thank you so much Dady" Zuba mata ido yayi ganin yadda take murmushi ga hawaye a idanunta, jefa mata tambaya yayi "Me yasa kika tsane ni ne haka kuma yaushe wannan k'iyayyar da kike Mani zai fita daga rayuwarki?" Kamar bata ji me ya ce ba towel d'in da ya nad'o ta ciki ta d'aura tare da cewa "Ka jik'a mani kaya na kuma mintuna goma aka baka ya zamuyi kenan?" Bai ce ta ita komai ba ya ya sauka daga daga Kan gadon ya nufi wurin closet dake cikin bedroom d'insa ya ciro mata wata Abaya purple colour da mayafinta ya bata, kallonsa tayi ta kalli sabuwar Abyar da ya bata ta saka tayi gaba yana binta a baya har suka fito ya rufe k'ofar, mai gadi yayi masu sallama ko amsawa baiyi ba hannu kawai ya d'aga masa, kallo d'aya zakayi masa kaga yana cikin damuwa, mai gadin ne ya k'araso wajen motar ya ce, "Yalla'bai lafiya dai ko?" Kallonsa Muhdeen yayi tare da cewa "Me ka gani Mallam Musa?" "Naga ka shiga cikin jin dad'i da annuri amma yanzun naga kana cikin damuwa, shine na ce ko wani abun ne ya faru?" "Bakomai kada ka damu" Kud'i ya d'ebo masu yawa ya mik'a masa, ya kar'ba yana godiya sanna yaja mota suka bar gidan . A can gida kuwa bayan Direban Dady yayi parking ne ya fito ya bud'e murfin baya Dady ya fito, yana shiga ya tarar da su duka a falo, ya kalli Mummy ya ce "Ina Inteesar take?" Gwaggo ce ta kalle shi ta ce, ",Meye haka Sani zaka shigowa mutane ko sallama." "Kiyi hak'uri Gwaggo ina dawowa ne na had'u da mahaifin Inteesar yake sanar dani cewa yanzun Muhdeen da Inteesar suka tafi sunzo gaida Ummanta." Gwaggo ta dafe k'irjj ta ce "Me nake shirin ji haka? ta yaya akayi hakan ta faru?" Girgiza kai Dady yayi tare da cewa "Ban sani ba gaskiya, dan ko da ya sanar dani cewa sunzo gaishe da Umma, yanzun suka tafi bazan masa wata tambaya ba tunda basu san halin da ake ciki ba." "To ina suke yanzun?" "Na kira sa na tambaye shi ya sanar dani wai suna gidansa." Salati Gwaggo ta saka tana tafa hannu yayin da Dady ya cigaba magana. "Na sanar da shi nan da mintuna goma ya dawo da ita, nasan yanzun suna hanya." Suna nan tsaye sai suka ji sallamarsu, gaba d'aya suka juya suka amsa sallamar tare da zuba masu ido, Gwaggo ce ta k'ara bude idanunta da kyau taga kayan da suka tafi da su ba shine a jikinsu ba, Inteesar atamfa ta fita da shi yanzun kuma gata da abaya shi kuma ya fita da manyan kanta yanzun gashi da k'ananun kaya, tafa hannu tayi ta ce, "Wato ke bansan wace irin yarinya bace, mu zaki rainawa hankali? dama kun shirya da shi akan zaku haɗu yasa kika mana k'arya ko? ai ba akai can ba badai namiji bane gaki nan gashi ranar da zai ƙuntata maki sai kinji duk duniya ba wanda ya tsane ki sama da shi, wacce ma suka same ta da wahala ya ta ƙare da namiji ballanta ke da ya ganki a sama, ana neman k'watar maki 'yanci baki ganewa ba, tunda haka kika zaɓa mun zuba maki ido kije ki tattaro kayanki kizo kibi mijinki ku tafi Allah ya kawo ƙazantar ɗaki." Kuka ta fashe da shi tana cewa "Wallahi Gwaggo ba yadda kike tunani bane, Abba na ne ya tilasta mani binsa shine na ce ya kawo Ni gidanku amma ya wuce da Ni can wani gida, ba yadda na iya ku fahimce Ni." Muhdeen ne ya durƙusa a kan gwuiwowinsa cikin ƙasƙantar da kai ya ce, "Gwaggo, Dady Mummy nasan nayi kuskure a baya wallahi nayi nadamar abinda na aikata a yanzun son Inteesar nekeyi har cikin zuciyata, dan Allah ku bani dama na gyara kuskure ne a karo na farko, insha Allahu ba zakuyi danasanin ƙin amincewa da ni ba, kuyi haƙuri ku mance da abinda ya wuce a baya, insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba, wallahi yanzun soyayyar da nake mata ni kaina bansan iya adadinsa ba kuma bansan yaushe ne na kamu da sonta ba, a yanzun ji nake bazan iya rayuwa ba ita ba." Zuba masa ido sukayi ganin hawaye a idanunsa tabbas kuka yake, kuma ya kamu da sonta ne ko shakka babu don sun hango soyayyar da yake mata a cikin zuciyarsa, Dady ne yayi murmushi tare da cewa "To me yasa a baya ka dinga ƙuntatawa rayuwarta bayan kasan cewa kana sonta? ai masoyi kyautata masa ake tare da faranta ransa ." "Dady dan Allah ku daina tuna Baya insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba, nidai ku bani dama ba zakuyi dana sani ba." Gwaggo ce tayi tsuki tare da cewa dana sani na nawa kuma? ai nice mai da na sani da naje da ƙafa ta har gurin ubanta na nema maka aurenta ba tare da sanin ka ba, kai dai kawai daga sama ka same ta, lokacin da na yi maka gata na aura maka ita madadin kayi farin ciki da godiya a gare Ni sai harara ta ka dinga yi da jin haushi na, sannan ka dinga wahalar da baiwar Allah da azabtar da ita akan laifin da ba ita tayi maka shi ba, ba ita ta ganka tace tana so ba, ballantana ka ɗora mata ƙaran tsana bata da laifin komai, Gara kai an sanar da kai a ranar da za'a ɗaura maka auren ita kuma ba wanda ya sanar da ita sai bayan auren ta sani, haka tayi haƙuri ta jure bata taɓa kawo ƙarar kayi mata wani abu ba, Dan dai na firar da suke yi da Mufida ta sanar da ita, har take roƙon ta kada ta faɗawa kowa Mufida ta nuna ba zata iya ba sai ta faɗa, da haryanzun kana nan kana cutar ita, baka san kana sonta ba sai da aka ɗauko ta zuwa nan, sannan ga wannan ifirituwar matarka tana neman kashe ta, ai idan muka bari yarinya nan ta koma gidanka ganin bayanta za'ayi, dan haka ka tashi kabar gidan nan sannan zuwa gobe ina buƙatar takardar sakin da kayi mata, don tabbas sai ka sake ta ba zata koma ba." Kuka ne ya kufce masa ba tare da sanin kuka na zuwa ba, kamar ƙaramin yaro ya dinga kuka wai yana roƙonsu da su bar masa matarsa amma ina kowa ya tafi yabar masa wurin, sarrafawa yayi inda Inteesar ke shirin barin wajen zata bi bayan Gwaggo, Ƙasar abyar ya riƙon yana kallonta da idanunsa suka rikiɗe zuwa ja ya ce, "Inteesar kada ki rabu dani wallahi yanzun sonki nakeyi da gaskiya, bazan cutar da ke ba tunda nake a rayuwa ta ban taɓa jin tsananin soyayyar wata ƴa mace kamar yadda nake jinki a cikin zuciya ta, kada ki rabu dani ki nuni muje mu gina sabuwar rayuwa mai cike da jin daɗin da kwanciyar hankali." Gwaggo ce ta buge hannunsa daga jikin Inteesar taja hannunta suka shige ɗakinta suka barshi nan durƙushe yana kuka. Haka ya zauna wajen ya cigaba da kuka, yana roƙonsu da su bashi matarsa, Mummy ma kam sai da taji tausayin yaronta sosai, dan kamar ta zubar masa da ƙwallon take ji, ɗanta namiji d take jinsa a ranta fiye da kowa yau gashi durƙushe a gabansa yana kuka akan mace ba wanda ya saurare shi. Ya kwashe awa ɗaya a wajen ba wanda tabi takansa, har Dady ya fito daga part ɗinsa yazo zai fita bani takansa ba yayi ficewarsa ko kallonsa baiyi ba, ƙarshe haka ya tashi har yana jin ciwon kai da jiri haɗa hanya yake idan yana tafiya, har ya ƙara da wajen motarsa ya tada yabar gidan. Tsaye take a kitchen tana yanka alayyahu yayin da Mummy ke tuƙa tuwon shinkafa suka ji sallamar Jabeer yana gaida Gwaggo "Assalamu alaikum Gwaggo Barka da warhaka" "Jabiru lafiya naganka haka kamar wanda aka jefo daga sama?" "Ina fa lafiya Gwaggo ga Muhdeen can yayi accident yana kwance a gadon asibiti." Jin haka yasa Inteesar ta saki ƙara tare da yarda wuƙar hannunta jini na tsiyaya daga hannunta, bata san ta lokacin da ta yanke ba sakamakon jin magamar da Jabeer ke faɗawa Gwaggo, ita dai Mummy bata ji maganar Jabeer da Gwaggo ba sai jin ihun ƙarar Inteesar da ta yanke hannu da saki wuƙa, da sauri Mummy ta ƙaraso wajen tare da kallon hannun Inteesar ta ce, "Subhanallahi garin yaya kikayi muguwar yankewa haka da wuƙa?" Girgiza kai tayi sai a lokacin Mummy taji muryar Gwaggo na ƙwala mata kira "Fatima! Fatima!! Fatima!!!" Jin yadda Gwaggo ke ƙwala mata kira tasan ba na lafiya bane, da hanzari ta fito kitcheen ɗin tare da Inteesar na biye a bayanta "Na'am Gwaggo meke faruwa" Kuka Gwaggo ta saka yana cewa "Na shiga uku yanzun haka ɓacin ran abinda muka masa ne yasa yayi hatsari, wayyo Allah na." Jabeer ne ya kalli Gwaggo ya ce, "Gaskiya kam Gwaggo indai akwai abinda kaka masa a gidan nan da ya ɓata ransa to shine ya jefa sa cikin wannan halin." Jinjina kai Jabeer yayi ya ce, "Gaskiya kam da alamar haka, domin mutanen da hatsarin ya faru a idanunsu sun tabbatar da cewa tuƙin motar kawai amma ba a cikin hankalinsa yake ba ababen hawa da ke kan tatin ma wasu sauka sukayi daga kan tatin ganin yanayin tuƙin nasa, sai daiAllah yasa ba bugu kowa ba motar ce dai ta kufce masa take da daki wata bishiya." Mummy ce ƙwalla ya cika mata ido ta kalli Jabeer ta ce, "Yanzun wani hali yake ciki." "Da sauƙi za'a ce amma yana can baisan wa ke kansa ba" Inteesar ce ta fashe da kuka ganin cewa duk alhakin faruwar abun akanta yake ita ce silar komai da ya same shi,Jabeer ne ya kalli hannunta dake zubar da jini ya nufi ɗakin Muhdeen ya fito da kayan aiki yazo yayi mata treatment na hannunta sannan ya kalli Gwaggo ya ce, "Dawa zamuje ne? tun ina asibitin na kira Dady na sanar da shi." Mummy ce ta kalli Inteesar ta ce, "Daughter ki tsaya muje mu dawo ke da Mufida ku tsaya a gida ita tana barci." Kai Inteesar ta girgiza tana kuka ta ce, "Mummy wallahi bazan iya tsaya ba zan biku mu tafi domin naga halin da yake ciki." Tana magana tana kuka, kafin ma Mummy tayi magana har ta shiga ɗauki ta ɗauko hijabinta don zuwa Asibitin, dole suka ƙyale ta suka tafi da ita inda aka bar Mufida tana kwance a ɗakinta tana barci. Ko a cikin motar ma kuka take Jabeer dake driving Ya ɗan juyo ya kalle ta ya ce, "Please kibar kukan nan haka insha Allahu zai warware anyi masa alluran barci ne, saboda yaƙi yarda a duba sa da kyau ga rauni a jikinsa amma amma sai cewa yake a barshi ya tafi wanda hakan yasa dole muka yi masa allurar." Kasancewar Mummy ce a gaba gefen Jabeer Gwaggo da Inteesar suna baya, Gwaggo ce ta kalli Inteesar ta ce, "Ke nifa bani son damuwa, duk kinbi kin cikawa mutane kunne da hayaniyar kuka." Jabeer ne ya ce, "Ba dole tayi kuka ba mijinta na cikin wani hali." Taɓa baki tayi tare da cewa "Ni ban gane kukan da take yi ba, mijin da ba wai sonsa take ba neye na ɗaga hankali? sai da na tambaye ta tana sonsa zata koma gidansa ta ce bata sonsa ba zata koma ba, to yanzun daga jin yayi hatsari tabi ta rikice har tana yanke hannunta da wuƙa bata damu da ciwon hannunta ba ta shi kawai take, ni gaba ɗaya na kasa gane inda yarinyar nan ta dosa, wato ke sawun keke ce ba'a gane gabanki ba'a gane bayanki, sonsa kike ko tausayin halin da yake ciki ne ban sani ba." Tura baki tayi tace, "Nifa kwai tausayinsa nake ji, gani nake nice silar komai shiyasa nake kuka ba don komai ba, kuma ko waye zan iya masa kuka indai ya shiga wani hali saboda ni." Daga nan ba wanda ya sake magana har suka ƙarasa Asibitin, bayan Jabeer yayi parking suka fito suka bi bayansa. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😍😘 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na buɗe wannan duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinin na ba *SANARWAR* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi da cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce Ni bada niyyar yin hakan nayi ba, rashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page6️⃣9️⃣ Daga nan ba wanda ya sake magana har suka ƙarasa Asibitin, bayan Jabeer yayi parking suka fito suka bi bayansa. Yana kwance yana barci sai rauni da ya ji a kansa, Jabeer ne ya turo ƙofar sai Inteesar da ke bayansa sai Mummy da Gwaggo, a guje Inteesar ta ƙarasa jikin gadon bata san lokacin da ta riƙo hannunsa ba tana kuka, Jabeer ne ya kalle ta ya ce, "Kada ki tayar da shi ana son ya samu isashshen barci kada ki damu zai tashi, zuba masa ido tayi tana tuna lokacin da ya riƙe ƙasar rigarta yana roƙonta da cewa, Inteesar kada ki rabu dani wallahi yanzun sonki nakeyi da gaskiya, bazan cutar da ke ba tunda nake a rayuwata ban taɓa jin tsananin soyayyar wata ƴa mace kamar yadda nake jinki a cikin zuciya ta ba, kada ku rabu dani ki bini muje mu gina sabuwar rayuwa mai cike da jin daɗi da kwanciyar hankali. Haka ta dinga tuna kalamansa da a cikin zuciyarta tana jin tausayinsa har cikin ranta. Mummy kuwa ita kaɗai tasan yadda take ji a zuciyarta tana tausayin halin da ya ke ciki akan mace, dan yanzun da daina jin haushinsa akan ƙuntatawar da yayiwa Inteesar a baya, dan yanzun ta fahimci cewa yayi nadama. Ɓangaren Gwaggo ma bata ji daɗin faruwar hakan ba duk da ita ce ta tunzura shi, amma tayi haka ne dan ta ƙwayar wa Inteesar ƴancinta a wajensa Sakamakon azabar da uƙuba da ya nuna mata a gidansa, duk da ya sauya amma yana da kyau ya gane kuskure da ya aikata kuma yasan mahimmancin da take da shi a wajensa. Nan dai Jabeer ya kwantar masu da hankali sannan ya nufi office ɗinsa, zama yayi ya ɗauki wayarsa tare da cewa "Bari na kira abokanmu na sanar da su halin da abokinsu yake ciki." Bayan yayi dialing number Salisu ya sanar da shi ne, sai ya lalubo ma Biliyaminu shima ya kira sa ya sanar da shi sannan ya lalubo number Bashir shima ya danna masa kira. Kwance suke a ɗakin hotel ɗin ba kaya a jikinsu suna kulluɓe cikin bargo, ta kwantar da kanta a ƙirjinsa kallonta yayi yana murmushi ya ce, "Yakamata ki tashi kiyi wanka ki koma gida kafin mijinki ya dawo ya tarar baki gida." Yamutshe fuska tayi tare da cewa "Ba yanzun ba don na gaji wallahi sai na huta" Wayarsa ce tayi ringing ya duba tare ɗagawa ya ƙara a kunne da ya ce, "Hello Jabeer yau ka tuno da ni ne?" Ajiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa "Abokinka fa ba lafiya yayi accident?" "Subhanallahi wane daga ciki Muhdeen ki Salisu ko..." Kafin yakai ƙarsen zancensa ne yaji muryar Jabeer na cewa "Muhdeen" Ita dake kwance a saman ƙirjinsa kasancewar ta ji muryar Jabeer cikin wayan ya ambaci Muhdeen da sauri ta miƙe zaune tare da cewa "Na shiga uku nala..." Kafin takai ƙarshen zancenta Bashir yayi saurin rufe mata baki da hannunsa ya ce, "Asibitinsa yake kwance?" "Eh" Ya bashi amsa a taƙaice daga nan ya aje wayar. Bashir ne ya kalli Sumayya sannan ya cire hannunsa daga bakinta ya ce, "Meye haka daga magana kina neman tona muna asiri idan ya gane muryarki fa?" "Kasan yadda naji ne?mijina fa aka ce yayi accident ya bazan ruɗe ba?" "Bari nayi sauri na tafi Asibitin" Ta ƙarasa magana tana sauka daga kan gadon, kallonta yayi tare da cewa Tunda basu kira ki suna sanar da ke ba yanzun idan kika je aka tambaye ki waya sanar dake me zaki ce? ni zaki ce ?idan suka tambaye ki ina muka haɗu na sanar da ke fa? Sai a lokacin ta tuna ta dawo ta ɗauki wayoyinta tare da kunna su ta ce, "Na mance na kashe wayoyi na duka kila ma ya kira ni bai samu ba" Tana kunnah wayar kuwa sai ga kiran Jabeer ya shigo kamar jira yake da sauri ta ɗaga tare da karawa kunnenta duk da cewar da wayar Muhdeen ya kira ta don baida number ta, ko ranar da ta kira shi ya roƙi Muhdeen ya barta akan ta cigaba da zama a gidansa baiyi served number ta ba, kallon Bashir tayi da ya zuba mata ido ta ce, "Da number Mijina ya kira Ni wayar na hannunsa ne." Ɗagawa tayi tare da cewa "Hello my sweet" Da sauri Jabeer ya ce "Bashi bane bani da number ki ne yasa na duba wayarsa na kira ki." "To Allah dai yasa lafiya da naga ka Kira da wayarsa hankali manya tashi." "Kina ina ne?" Gabanta ne ya faɗi kada dai ace yahe gidansu bai gabata bane, kafin tayi magana ta ji ya ce, "Kizo Asibitinsa muna nan" "Lafiya me ya faru da shi ne?" "Kada ki damu kizo kawai" Daga nan ya katse kiran yana girgiza kai. Suna nan zaune a ɗakin Dady ya shigo don duba halin da Muhdeen ke ciki, daga nan ya je office na Jabeer inda ya nemi jin ƙarin bayani daga bakinsa nan Jabeer ya kwantar masa da hankali cewa ba komai zai warware insha Allahu, sai dai akwai damuwa. zuciyarsa kuma samuwar akan Inteesar ce don haka ya dinga sambatu yana kiran sunanta kafin barcin yaɗauke sa, nan Jabeer ya ƙara jaddada wa Dady cewa su basa matarsa don gaskiya Muhdeen yabcanza, yanzun son Inteesar yakeyi da gaskiya ya kamu da matsancin soyayyar Inteesar, bazai taɓa cutar da ita ba ko ya bari wani ya cutar da ita, nan dai ya cigaba da masa bayani kuma Dady ya gamsu da bayanin Jabeer sannan sukayi sallama ya fita. Suna nan zaune a ɗakin sa aka kwantar da Muhdeen bayan tafiyar Dady sai ga Sumayya ta faɗo ɗakin kamar wacce aka jefo, ganin su Mummy da Gwaggo yasa ta shan jinin jikinta kunya ce ta dabaibaye ta, don tunda ta auri Muhdeen bata taɓa zuwa ta gaida su ba, lokacin da idonta suka sauka akan na Inteesar sai da gabanta ya tsananta faɗuwa, taji ƙiyayyar da take wa Inteesar ce ta dawo sabuwa a cikin zuciyarta, musamman da taga idanunta alamar tayi kuka kuma tana riƙe da hannun Muhdeen ta zauna a gefen gadon, take sai taji kishin mijinta ya taso mata, ga kuma kunya tana ji na abunda ta aikata na yunƙurin kashe Inteesar kallon Gwaggo tayi ta ce, "Ina wuni Gwaggo?" Kauda kai Gwaggo tayi tare da cewa "Bari na fita ɗakin nan kada Allah ya tashi turo ma wata bala'i ya shafe ni." Ta ƙara maganar tana kallon Mummy da Mufida tana masu alamar da suzo su tafi, Sumayya ta ƙalli Mummya ta ce, "Ina wuni Mummy?" Ba yabo ba fallasa ta amsa mata da "Lafiya lau ya gidan?" "Alhamdulillah" Gwaggo ce tayi saurin sawa gadon taja hannun Inteesar suka tafi zuwa waje, wani wuri suka samu suka zauna saman kujeru dake ajiye a wajen. A can cikin ɗakin kuwa turo ƙofar akayi tare da yin sallama, Salisu ne da Biliyaminu, sai Bashir, durƙusawa sukayi suka gaida Mummy tare da tamabar ta ya mai kiki, ta amsa da Alhamdulillah sannan Sumayya ta gaishe su suka amsa mata inda Bashir ya kashe mata ido ɗaya da sauri ta kauda kanta daga kallon sa don ta lura Bashir ba kunya ne da shi ba, yanzun sai ya nemi tona masu asiri bayan 'yan mintuna sai ga Gwaggo da Inteesar sun shigo ɗakin, yayin da Bashir ya kafe Inteesar da wani kallon ƙurilla ba wanda ya lura da hakan sai Sumayya da idanunta ke kansa, gyaran murya tayi ya kalle ta ta galla masa harara sosai kai yayi tare da gaida Gwaggo ta amsa suma sauran suka gaishe ta amsa masu. Bayan kamar mintuna goma ne Bashir ya miƙe ya ce "Bari naje na ɗauko abu a mota." "Salisu ya ce "Okay" Yana ƙoƙarin fita ne sukayi kiciɓis da Jabeer suka ƙara gaisawa sukayi sannan sannan ya fice, bayan fitar da da mintuna biyar Sumayya ta tashi ta fice, Yana zaune a cikin motarsa gani kawai yayi an buɗe murfin motar kafin yayi magana har ta shigo ta rufe murfin motar, da mamaki ya kalle ta ya ce, "Sumy! lafiya kuwa?" Kauda kai tayi tana taunar cingum ta ce "Ƙalau" "To me zaisa ki biyo NI har cikin mota idan wani ya hannu fa akwai matsala." "Yaushe kasan yarinyar can da naga kana binta da wani mayataccen kallo?" "Wata yarinya?" Kauda kai tayi bata ce komai ba sai a lokacin ya tuna cewa lokacin da yake kallon Inteesar Sumayya ce kaɗai ta kula da hakan, dan haka ya ce, "Oh Inteesar?" Taɓe baki tayi ba tare da ta ce komai ba "Ai Inteesar ta daɗe da shiga raina, ranar da akayi reception na aurenki da Muhdeen ne na fara ganinta ita da Jabeer wai daga tashi reception matarsa ta kira sa tana son agwaluma suka kai mata, to bayan sun dawo ne na ganta har na cewa Jabeer zan aure ta don banga maccen da ta haɗa abubuwan da nake so kamar Inteesar ba, gani na na biyu da ita munje gidan baki nan lokacin kina London tana amarya munje cin girkin amarya, munta ta santin daɗin girkinta sai Salisu ke bani labarin wai da kike amarya sunzo cin girkin ki wai kinyi masu daɗɗaɗan girki irin taki ba, wai taki ta musamman ne basu taɓa cin girki mai daɗinsa ba, sanin cewa tsokanarta yake yasa ta ɗaga hannayenta biyu tana kai masa dukan wasa riƙe hannunta yayi, kamar daga sama suka ji ana knocking glass ɗin motar da sauri suka juya cikin fargaba dan ganin waye. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DIN NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love u oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na buɗe wannan duk abu ɗaya ne, sannan idan kisan cewa bazakyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣0️⃣ Kamar daga sama suka ji ana knocking glass ɗin motar, da sauri suka juya cikin fargaba dan ganin waye. Sauke glass ɗin motar yayi sai yaga ɗaya daga cikin security na Asibitin ne ya a tsaye, kallonsa Bashir yayi tare da cewa "Lafiya?" "Yallaɓai dan Allah ka gayara parking ɗin motarka." Jinjina kai yayi tare da cewa "Okay" Sai a lokacin ya lura da inda yayi parking ashe ya a hanaya ne, kuma motocin da ke gabansa dole sai ya bada hanya kafin su wuce, don haka ya gyara parking ɗin motar sannan ya juya ya kalli Sumayya. "Waya ta na manta a motar shine na fito ɗauka yakamata ki fita ki koma kiyi jinyar mijinki ko?" "Ni wallahi tunda na ƙyallara ido naga yarinyar nan a Asibitin nan sai naji gaba ɗaya raina ya ɓaci, musamman da ta haɗu da waccan jarababbiyar tsohuwar Gwaggo, Wallahi na tsane su a rayuwa ta." "Me sukayi maku da kika tsane su?" Yamutshe fuska tayi tare da cewa "Ita wannan tsohuwar tun lokacin da na fahimci baya ƙauna ta ne, ita kuma waccan yarinyar haka nan kawai tun ranar da na fara ganinta a gidansu Muhdeen na tsane ta, Ni dama na tsani kyakkyawar mace,idan har naga mace ta haɗu ta ko ina bata da cikas wallahi sai naji na tsane ta musamman idan na fahimci ta fini ko akan hanya ne bana son ganinta ballantana wannan da ta aure mani miji." Dariya Bashir yake ta ƙyaƙyatawa har Sumayya ta fara jin haushinsa, dan haka ta buɗe murfin motar ta fice ranta a ɓace. Komawa tayi ɗakin ta tarar Salisu da Biliyaminu ne sai Mummy, zama tayi gefen gadon da Muhdeen yake tana cewa "Allah sarki Allah ya tasarmun da kai ya baka lafiya." Ta ƙarasa maganar idanunta na tara ƙwalla, gaba ɗayansu suka amsa mata da Ameen inda Mummy ta ce, "Dan Allah ku daina masa kuka haka, jikinsa fa da sauƙi insha Allahu zai miƙe kamar baiyi ba." Kuka ta sake rusawa tana cewa "Mummy ta yaya hankali na zai kwanta? mijina yana cikin wani hali l." A'a kinga wannan ba abunda tada hankali bane addu'a kawai zamuyi masa Allah zai bashi lafiya, nan dai Umma ta dinga kwantar mata da hankali akan ta cire samuwar dake cikin zuciyarta, ana haka ne Bashir ya shigo ko kallon inda yake bata yi ba, daga bisani suka fita zuwa wajen Jabeer, ɗakin ya rage daga Mummy sai Inteesar. Shiyoyin sallar magariba ne, Mufida ta shigo hannunta ɗauke da basket da aka jera kayan abinci a ciki. "Assalamu alaikum" Mummy da Sumayya suka amsa mata "Wa'alaiki salam" "Mummy ya jikinsa?" "Jiki da sauƙi Mufida" "Allah ya bashi lafiya." Suka amsa da Ameen, Mummy ce ta kalle ta ta ce, "Baki ga Auntynki bace?" Yamutshe fuska tayi tare da cewa "Mummy ni banga Aunty na anan ba gaskiya." Kallon gargaɗi Mummy tayi mata ba tare da ta ce komai ba, sanin dalilin kallon ne yasa ta kalli Sumayya murya ciki ciki ta ce, "Ina wuni?" Itama kanta Sumayya taji zafin abinda Mufida tayi mata, amma sai ta dake ta nuna hakan bai dame ta ba kasancewar a gaban Mummy suke, "Lafiya lau Mufida ya kike? Kauda kanta gefe tayi tare da cewa "Lafiya" Dan tunda suka je gidan Muhdeen da Gwaggo lokacin Sumayya na Amarya har tayiwa Gwaggo rashin kunya, tun daga wannan lokacin Sumayya ta fice daga zuciyar Mufida, ganin lokacin salla yayi ne yasa Mummy cewa zata tafi tayi sallah, Mufida ma tabi bayanta suka fice, sai a lokacin Sumayya ta samu dama ta kira Jumy take sanar da ita halin da ake ciki na hatsarin Muhdeen, daga can ɓangaren Jumy ta ce "Anya ƙawa ta babu sa hannunki a hatsarin nan kuwa?" "Na san halinki nasan abunda zaki iya aikatawa ." "Dariya Sumayya tare da cewa "Tabbas kinyi gaskiya ba abunda bazan iya aikatawa ba, amma ki sani wannan hatsarin masa ba saka hannuna a ciki, ai kinsan idan in son mutum bazan iya cutar da shi ba matuƙar kuwa kika ga na cutar da mutumin dake ƙaunata to haƙiƙa ya kainii bango ne wanda hakan shine masalaha." Taɓe baki Jumy tayi tare da cewa "Ba wata masalaha da sai an halaka wani, nifa nan da kika ganni duk iya shige da isakanci na wallahi bazan iya yin kisan kai ba." "Hmmm ba'a kaiki bango bane wallahi da ankaiki bango da ba zaki daɗi haka ba, sannan lokacin da zaki aikata hakan ma ba zaki sani ba, nayi yunƙurin kashe Inteesar a baya ta tsallake rijiya da baya, amma matukar ta kaimu bango to fa wallahi bazata sha ba, don idan raina ya ɓaci ko zuciyata bana saurara duk abinda yazo gaba na aikata shi nake." "To ki guji ranar da zakiyi nadama kuwa wanda lokacin nadamar ba zata maki amfani ba." Maganganun Jumy ba suyi mata ba dan haka ta katse kiran tare da kiran lamabar wayar shila, bugu biyu shila ta ɗauka suka gaisa zancen da yayiwa Jumy ita tayiwa Shila, sai dai shila tunzura ta ta dingyi akan duk abinda ta ce zata yi, a haka sukayi sallama ta kashe wayar . Sai da akayi sallar isha'i ne su Mummy suka dawo bayan sunyi sallar isha'i, Sumayya tana nan zaune bata tashi ta je sallah ba. Da sallma suka shigo ɗakin ta amsa masu, a tunanin Mummy Sumayya bata je. sallah bane saboda kada a bar Muhdeen a ɗaki ba kowa dan haka ta kalli Sumayya ta ce, "Sumayya tunda mun dawo idan zakiyi sallah ki tashi kije kiyi ko." Dai lokacin Gwaggo da Inteesar ta suka shigo ɗakin, Sumayya ta miƙe tare da cewa "Bari na tashi naje nayi sallah to." Kai Mummy ta jinjina tare da cewa "To sai kin dawo." Daga nan ta fice Gwaggo ta raka ta da harara, Mummy tayi magana cikin sigar lallashi ta ce, "Gwaggo don Allah ki fita harkar yarinyar nan, tunda yanzun dai bata sake wani laifi ba." Gwaggo ta nuna Mummy da yatsarta manuniya ta ce "Fatima ki kiyaye ni fa ki fita a ido na na rufe, saboda ba ke tayiwa na mi tayiwa rashin kunya da fitsara, ai idan mayar ya manta ai uwar ɗa bai ci ta manta ba, kina cewa wai bata sake wani laifin ba sannunki kenan, amma wannan yarinya duk inda kike neman kaba'ira takai." Ita dai Mummy bata ce komai ba har Gwaggo ta ƙaraci sababinta tayi shiru. Jabeer ne ya shigo da sallama gaishe da su Mummy da Gwaggo yayi yayinda Mufida ta gaishe sa,zama kusa da Gwaggo ya ce, "Ke wannan tsohuwar ba zaki tafi gida ki huta ba?" Kai ta girgiza "Ina naga tafiya ga miji kwance ko motsi baiyi ba." "Kada ku damu ina sa ran insha Allahu ya kusa farkawa" Mummy ce ta kalli Mufida ta ce, "Ki dubawa yayanki abinci mana" Mufida ta tashi da niyyar zuba masa abincin yayi saurin cewa "Am okay" Dan haka Mufida ta koma ta zauna inda Jabeer ya cigaba da cewa "Yanzun magana cin abinci Mummy." Sumayya kuwa tunda ta fita da sunan zatayi sallah sallah ta zauna gefen masallacin, tana tunanin ta ina zata fara, dan ko sallar asuba barayi na ballantana azahar da la'asar, wayarta ta ciro ta kira number Bashir bugu biyu ya ɗaya "Hello Sumy ya akayi ya farka ne?" "Tukunnah dai bai farka ba tukunnah" "Okay nan zaki kwana Asibitin ne?" "Wace ni da kwana a Asibitin alhalin wannan fitina miyar tsohuwar na nan ai ba mu zama inuwa ɗaya, gida zan koma da safe na dawo." "Okay ko nazo na taya ki kwana ne" Da sauri ta furta "What's" Dariya yayi tare da cewa "Wai sai na maye gurbinsu tunda baya nan ko?" "Kasan me kake faɗa kuwa? kazo gida na ka kwana bayan ga mai gadin gidan da sauran ma'aikatan gidan zasu ganka ka kwana bayan abokinka baya nan? me zasauyi zato?" Taɓa baki yayi tare da cewa "To ke kizo mana ki same ni idan har ba nan zakai kwana ba ba wanda zai san inda kika kwana, su a nan zasu ɗauka gida kika je kika kwana su can ma gidan zasu ɗauka asibiti kika kwana ba wanda zai sani." Shiru tayi tana nazari kafin ta ce, "Shikenan sai nayi tunani amma idan kaji ni shiru to ka tabbatar a Asibitin zan kwana tare da mijina." "Hmm ai naga dole zaki fi buƙatata saboda zanyi maki amfani a daren yau shi kuma fa meye zai tsinana maku?" "Kaga kada fa ka zaƙe da yawa dan zaka iya fuskantar tirjiya daga gare ni, kuma duk son da nakeyi maka baikai wanda nake masa ba, i love him more than everything dan haka kada ma kayi tunanin haɗa kanka da shi dan ya fika ta kowace fuska." "Kada ki nemi gaya mun maganar da zuciyata ba zata iya ɗauka ba." Tsuki tayi tare da kashe wayar Tashi tayi ta je ta jero dalilin da ake binta tun daga asuba har isha'i. Bayan ta idar ne ta koma ɗakin ta samu suna cin abinci, Mummy ta kalle ta ta ce, "Sumayya kin idar da sallar ko?" "Eh Mummy" Zama tayi ta fara daddanna wayar ta, Mummy ta kalli Mufida ta ce, "Ki zubawa Sumayya abinci mana" "To Mummy" Daga nan ta janyo Basket d'in da aka jera abincin tare da ciro plate ta zuba mata abincin, ta haɗa mata da ruwan sha, karɓar tayi don dama yunwa take ji sosai. Suna gama cin abincin ne Inteesar wacce rabin hankalinta na wajen Muhdeen ta lura da ya fara motsi yana juya kai tare da yamutshe fuska. Cikin tsananin farin ciki ta ce "Ya farka" Gaba ɗaynsu suka maida hankalinsu ga Muhdeen, gani sukayi yana juya kai amma idanunsa a rufe, da sauri suka ƙara da wajen gadon Jabeer ya riƙo hannunsa tare da kiran Sunansa. "Muhdeen sannu ko" Ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya amsa da yauwa, Sumayya ta ce "Sannu ya jikinka?" Ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya ce, "Yauwa" Sai a lokacin Inteesar tayi magana ta ce, "Sannu yaya ya jikin?" Jin saukar muryarta a cikin dodon kunne da yasa ya buɗe idanunsa da sauri dan tabbatar da abinda kunne da ya jiyo masa, idanunsa ne suka sauka akan nata yaga tana sakar masa murmushi, zuba mata ido yayi don tunda yake da ita bata taɓa yi masa murmushi ba sai yau, gani yake kamar ba gaskiya bane mafarki yakeyi dan haka sai ya miƙa hannunsa ya riƙo nata hannun, cikin muryarar da bata fita ya furta "Inteesar kece?" Kai kawai ta gyaɗa masa tana murmushi ba tare da tayi magana ba, sun kai mintuna biyu zuwa uku suna kallon juna suna sakarwa juna murmushi, kowa kallonsu yake yana murmushi saɓanin Sumayya wacce baƙin ciki da takaici duk ya ishe ta, ta gaishe sa amsawa yayi ba tare ba tare da ya ko kalle ta ba, amma daga jin muryar Inteesar ya buɗe ido ba shiri sai kallon juna suke kamar zasu haɗiye junansu, ƙoƙarin tashi zaune yayi yana cije leɓe har lokacin hannunsu na riƙe da juna, Gwaggo ce ta ce, "Muhammadu ya jikinka?" Kai ya jinjina tare da cewa "Da sauƙi Gwaggo" Nan ma Mummy da Mufida suka gaishe su ya amsa masu, Jabeer ne ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo da kofin shafi ya bashi daƙyar yasha sannan Jabeer ya bashi magani yasha. Haka farin ciki ya lulluɓe zuƙatansu Ganin ƙarfe goma tayi ne yasa yasa Jabeer ya ce su tafi gida shi yana tare da shi, hakan yasa suka tafi Gwaggo, Mummy, Mufida da Inteesar sukayi masa sallama zasu tafi, maraice fuska yayi alamar baiso tafiyarsu ba kuma duk saboda Inteesar ne, Mummy ce ta kalle shi tayi murmushi "Son kada ka damu da sassafe zamu dawo." Kai ya jinjina alamar gamsuwa daga nan sukayi masa sallama suka tafi, Jabeer ne ya kalli Sumayya ya ce, "Ke fa ba zaki tafi bane yanzun dare yayi." Fuskarta ba walwala ta ƙarasa wajen gadon Muhdeen ta ce, "Baby baka ganni bane?" Murmushi yayi ya tare da cewa "Ba kece kika fara mani magana bayan Jabeer ba? mun gaisa ai." Cikin ƙunar rai ta fara magana "Shine ko kallo ban ishe ma ka ba ko? amma daga jin muryar waccan bagidajiyar kucakar yarinyar ka maida hanakalinka akanta saboda tafini a wajenka ko?" Girgiza kai yayi tare da cewa "Bakwai ta fiki a wajena bane a'a matsayinku ɗaya ne ba wacce tafi wata" "Ba haka bane ka fifita ta a kaina mana, ki ta kaina ma baka bi ba sai da ta fita sannan ka kalle ni ka kuma kama hannunta ka riƙe kana kallon fuskarta kamar ka samu farin wata, me ta fini da shi da ka maida hankalinka akanta ka amsa mani." Dade kansa yayi jin yana sara masa don baya son hayaniya, lura da hakan yasa Jabeer ya ce, "Sumayya meye haka? mutumin da yake cikin wannan halin ne zaki saka a gaba kina damunsa da hayaniya? wannan ba dai-dai bane." "Yanzun ne kasan ba dai-dai ba? lokacin da nayi masa magana bai kalle ni ba ya zubawa waccan 'yar matsiyatar ido me yasa baka faɗa masa wannan ba dai-dai bane?." Muhdeen kam rintse idanunsa yayi tare da riƙe kansa dan maganar Sumayya ma ciwon kai yake saka sa. Fita tayi fuuu kamar wacce zata tashi sama, wajen motarta ta nufa ranta a matuƙar ɓaci ga zafin kishin da take ji akan Inteesar ɗin, kai tsaye wayar ta ciro a handbag ɗinta number Bashir ta Kira, bugu biyu ya ɗaga kafin yayi magana ta ce "Kana ina ne gidanka ko hotel?" Yana kwance a kan kujerar mai zaman mutum uku ya ce, "Ina gida ne ya akayi?" "Lahira zatayi baƙuwa" Cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa ya ce, "Ban fahimci inda zancenki ya dosa ba." "Am on my way" "Till you come?" Daga nan ta katse kiran ta tayar da motar tana ayyana yadda zata aiwatar da shirinta, tayar da motar tayi ranar Asibitin ta ɗauki hanyar gidan Bashir. *Saura pages guda 10 na kammala book 1 insha Allahu, zamu shiga book 2 amma book 2 paid book ne idan kin siya ki karanta* Daga alƙalamin ✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shara Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan kinsan cewa kina cikin group ɗin Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne Sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group dan ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣1️⃣ Daga nan ta katse kiran ta tayar da motar tana ayyana yadda zata aiwatar da shirinta,tayar da motar tayi ta ɗauki hanyar gidan Bashir. Horn yayi mai gadin gidan ya leƙo ganin ita ce yasa ya wangale mata gare ɗin gidan ta shiga, bata ma tsaya yin parking da kyau ba ta fito ta nufi hanyar da zata sada ta da falon, tura ƙofar tayi ba tare da tayi sallama ba, ƙamshin turarenta ne ya tabbatar wa da Bashir ta iso,miƙewa yayi daga kwance da yake ya tashi zaune tare da ware hannayensa duka biyu, alamun tazo gare shi, ƙara sawa tayi tare da faɗawa jikinsa ya rungume ta, ajiyar zuciya ta sauke. "Waye ya taɓa ki? ki kwantar da hankalin..." Kafin ya kai ƙarshen zancenta ta katse shi da cewa "Hankali na bazai taɓa kwanciya ba matuƙar tana raye, mutuwarta shine kwanciyar hankaalina." "Wace ce?" Wani tunani tayi dan haka bata amsa masa tambaya da yayi mata ba. "Nace wace ce, mutuwarta ne kwanciyar hankali a gare ki?" Ƙara tsuke fuska tayi "Bai shafe ka ba." "Ki faɗa mani wata kila ma akwai amfanin da zanyi maki." "Babu wani amfanin da zaka mani a matsayinka na abokin miji na." "Domin ina da yaƙinin zaka iya taimakonsa ta wata fuskar" "Badai Inteesar kike ƙoƙarin kashewa ba?" "Ba matsalarka bace" "Idan ma ita ce tun yanzun ki fidda abunda ke cikin ranki, domin Inteesar she is innocent.." "Me ye matsalarka da ita ce, naga matar abokinka ce, bayan haka nana tunanin akwai wata alaƙa a tsakanin ku" Jinjina kai yayi tare da cewa "Tabbas ba wata alaƙa a tsakanina da ita bayan ta matar aboki a gare ni, kuma ita ce matar da na fara tunanin mallaka a matsayin uwar ƴaƴa a gare ni." Da sauri Sumayya ta miƙa daga jikinsa tana masa kallon mamaki, ya cigaba da cewa "Tun kafin Muhdeen ya fara sonta nake sonta duk ƴan mata da nake da su da kuma waɗanda nake gani banaga wacce ta ta mallaki duk abinda make so a wuri ƴa mace ba sai ta, ita ce ta cika 💯 irin zaɓi na." Taɓa baki tayi tare da jan tsuki, jin taja tsuki ne ya kalle ta ya ce, "Kishi kike ne?" "Allah ya sauwaƙe, akan mijina da make so kamar raina zanyi kishi, shi kaɗai ne nake kishi akansa saboda shine wanda nake haukar so, bayan shi banga namijin da ya isa nayi kishi akansa ba." Dariya yayi tare da cewa "Kina kishinsa har haka amma kika kasa killace masa kanki, kike fita kina waufantar da kanki ga wasu mazan da ba baki ba?" Murmushin takaici tayi tare da cewa "Ba laifinka bane laifi na ne da na baka kaina dole kayi mani duk cin kashin da kaga dama." Ƙoƙarin tashi daga jikinsa tayi yayi saurin janyo ta jikinsa ya ƙara katse ta "Am sorry" Bata ce komai ba ta cigaba da ƙoƙarin ƙwatar kanta yayinda shi kuma bai sake ta b. "Don Allah kiyi hak'uri Allah ya huci zuciyarki sarauniyar mata, banyi niyyar ɓata maki rai ba, ke ai baƙuwa ta ce dole na girmama ki, kuma na fahimci matsalarki Inteesar ce ko? to kiyi tunanin hanyar raba da Muhdeen yadda zai sake ta Ni kuma na aure ta, kinga Shikenan ke kin samu damar mallakarsa ke kaɗai Ni kuma na samu mallakar macen da nake mafarkin samunta a rayuwata." Shiru tayi tana nazarin kalamansa, tabbas ba zata iya jure ganin Muhdeen da kowace mace na raɓarsa ba kuma tasan raba Muhdeen da Inteesar wani abu ne mai wahalar gaske, don ta lura da yadda yake tsaninin son Inteesar yanzun, ga danginsa suna sonta ba zasu taɓa yarda ya rabu da ita ba, mafita ɗaya ce mutuwar Inteesar, bata san lokacin da murmushi ya suɓuce nata ba har sai da Bashir yaji saurin murmushin nata, kallonta yayi yana murmushi. "Kin amince wane shawara kika yanke?" "Ka zuba ido kawai kayi jallo" Daga nan ta tashi ta shiga bedroom ɗinsa kai tsaye toilet ta nufa, wanka tayi ta fito ɗaure da towel zama tayi ta shafa lotion nasa mai ƙamshi bayan ta gama ta juyo ta kalle shi taga yana kallonta yana mata murmushi yayin da ya haye saman gadon tare da jan bargo, ya rufe jikinsa, bayan ta gama ne ya ƙarasa jikin gadon tare da hayewa saman gadon ya shige cikin barhon itama, janyota yayi jikinsa tare da warware towel ɗin da ta ɗaura shima ya cire kayan jikinsa suka soma saɓon Allah kamar yadda suka saba yi. Washe gari Inteesar na idar da sallar asuba tayi azkar ta nufi kitchen don haɗa breakfast. Farfesun kayan ciki tayi wanda yaji kayan ƙamshi kamar yadda ta lura Muhdeen yana son shan farfesun kayan ciki da safe, don haka tayi shi Musamman saboda shi ta fere dankalin turawa da plantain ta soya da ƙwai sai ruwan shayi da yaji kayan ƙamshi, tayi kunun gyaɗa da bayan ta jiƙa wake ta wanke ta zuba tattatasai da albasa tayi blendin tayi ƙosai. Koda Mummy ta fito ƙarfe bakwai ta tarar da Inteesar a kitcheen har ta gama komai, murmushi tayi "Daughter yau da sammakon aiki kika tashi? baki gajiya ne?" Murmushin tayi tare da sunkuyawa ta gaida Mummy, ta amsa mata cikin farin ciki buɗewa ta fara yi tana mamakin yadda cikin ƙanƙanin lokaci Inteesar ta gama ayyukan nan. "Sannu da ƙoƙari Allah yiyi maki albarka" Murmushi kawai tayi inda ta ɗauko basket ta fara shirya wanda za'a tafi Asibitin dasu, kallonta Mummy tayi tare da cewa "Waɗannan da?" "Mummy na yaya ne da za'a kai masa Asibiti." Murmushin jin daɗi Mummy tayi don taji daɗin jin hakan har cikin ranta, don yanzun ta lura tun lokacin da Muhdeen ya durƙusa a gaban Inteesar yana kuka yana riƙe rigarta tare da roƙonta tayi haƙuri ta koma gidansa, tun a lokacin Mummy ta hango soyayyar Muhdeen acikin idanunta, amma duk da haka zata gwada ta dan ta tabbatar da abinda zuciyarta ke faɗa mata, kallon Inteesar tayi tare da cewa "Oh yanzun abincin nasa ne kika haɗa? saboda shi kikayi wannan sammakon?" Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta, ba tare da ta ce komai ba Mummy ta cigaba da cewa "Idan kin kammala ki bawa Direba ya kai masa kiyi zamanki ki huta, ba wanda zai je." Da sauri ta kalli Mummy tana so tayi magana kuma tana jin nauyin Mummy dan haka ta nufi ɗakin Gwaggo, kallo ɗaya Gwaggo tayi mata taga yanayinta ya sauya, dan haka ta ce, "Lafiya kuwa?" Girgiza kai tayi ba tare da ta ce komai ba, Gwaggo ta ce "Akwai abunda ya faru naga duskarki ba walwala, daga ina kike? A takaice ta ce, "Kitcheen" Miƙewa Gwaggo tayi tare ta nufi kitchen, ta samu Mummy ta ce, "Fatima lafiya naga Inteesar ta fito daga nan kitcheen duk yanayinta ya sauya?" Dariya Mummy tayi tare da cewa "Dama ina son na tabbatar da hasashe na ne, yarinyar nan sammakon zuwa kitcheen tayi tana girkawa mijinta abinci, kuma inda zaki tabbatar saboda shi tayi duk abincin da yafi so shi ta girka masa, saboda na ce, Direba ne zai kai ba wanda zai je shine fa ta shiga wannan halin, nima na faɗa ne kawai dan naga yadda zatayi." Murmushin kawai Gwaggo tayi ta fita daga kitchen ɗin zuwa ɗakinta kallon Inteesar tayi tare da cewa "Kiyi wanka kiyi breakfast sai kibi Direban ku tafi ko?" Bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba,tayi saurin rufe fuskarta da tafin hannunta, Gwaggo dariya itama tayi tare da cewa "Wato dama can kina son mijinki kike nuna baki sonsa ko? to anyi walƙiya na ganki kina so kina kaiwa kasuwa, har kina roƙo kina kuka akan cewa baki sonsa a raba auren, to yanzun da an raba auren wa kika cuta idan ba kanki ba? don nima nasan cewa idan kika rasa miji irin jikana Muhammadu kinyi babban rashi, samun miji kamarsa sai mai Sa'a irinsa basu da yawa a wannan duniya, bawai ina faɗa maki haka a matsayin yana jikana bane a'a ina baki shawara ne a matsayi na na babba a gare ki wacce ta hango abinda ke baki hango shi ba, ki riƙe mijinki hannu biyu da kyau, kinga har kusan kashe kansa yayi a dalilin an hana sa ke yana masifar sonki fiye da yadda nake zato, don banyi tunanin cewa yana sonki har haka ba, shiyasa nima na sauko daga dokin fushin da na hau da shi, dan na fahimci irin son da yake maki, yanzun mahaifiyarsa ma tasan da hakan, mutum ɗaya ne nake tunanin zaku fusƙanci ƙalubale daga wurinsa wato Mahaifinsa, dan naga yadda ya ɗauki abun da zafi sosai, ni kuma bazan ce masa komai ba duk shawara da ya yanke akai Shikenan." Da sauri Inteesar ta kalli Gwaggo ta ce, "Idan bai amince ba fa?" "Sai kuyi haƙuri bana son nayi saurin saka masa baki, wannan karon zan barshi yayi iko akan ɗansa, ba kamar kwanakin baya ba da nake masa katsalandan na hana shi aiwatar da hukuncin da yayi niyya, amma idan naga abun yayi yawa zan taka nasa birki ne." Cikin sanyin jiki ta nufi toilet don yin wanka, Mufida ce ta shigo take tambaya ina Inteesar Gwaggo ta sanar da ita yadda sukayi tun daga kan girki har zuwa wankanta zata je Asibiti, dariya Mufida tayi tare da cewa "Lallai kuwa bari nayi mata kwalliya ta musamman, ina zuwa." Ta fita zuwa ɗakinta kasancewar Inteesar da ta farfaɗo daga Asibiti aka taho da ita nan, so ba kayanya ko ɗaya a nan kayan Mufida take sakawa tunda kusan jikinsu ɗaya duk da cewar akasarin ɗinkunan Mufida suna matse ta cif ita kuma bata cika son ɗinkuna da suka matse mata jikinta ba. Sai da Mufida ta zaƙulo wani wani leshi milk colour da broun yana da ratsin golding color, sai ta fito mata da mayafi golding colour sai hakka da takalmi broun ta kwashe su tare da kayan kwalliya ta nufi ɗakin Gwaggo, lokacin Inteesar har ta fito daga wanka tana shirin zuwa ɗakin Mufida sukayi karo da juna, komawa baya Inteesar tayi Mufida ta kalle ta ta ce "Kayan da zaki saka na kawo maku, dan so nake ki burge mijinki fiye da waccan matar tasa, dan naga juya da ta ganki kamar zata haɗiye zuciya ta mutu dan baƙin ciki, yau so nake ki kece raini ki fito kamar wata Amarya." "Kinga Mufida meye abun wani kwalliya a cikin zuwa asibita?ni ba shi zai kaini ba kibarshi kawai." "Wallahi sai kin saka." Bata jira sawarta ba kawai sai ta fara ƙoƙarin zura mata kayan, ganin haka yasa Inteesar ta karbi kayan tare da cewa "Bari nasa da kaina." Bayan ta saka kayan ganin yadda siket ɗin kayan ya matse ta tam a jikinta hatta hips nata sai da suka bayyana, kallon Mufida tayi tare da kwaɓe fuska kamar zata yi kuka ta ce, "Bazan iya fita da kayan nan ba." Dariya tayi tana kallon Inteesar ta ce, "Wow gaskiya Allah yayi halitta a nan kinga yadda kikayi kyau kuwa?" Yamutshe fuska Inteesar tayi "Kinga ni ban damu ba nafi son saka abaya gaskiya, wannan kayan takura Ni zaiyi baki ga yadda suffar jiki na suka bayyana ba?" "To meye?" Girgiza kai tayi "Nidai gaskiya bazan iya ba." "Wajen mijinki fa zaki" Bata saurare ta ba ta fara mata makeup duk da ta ce bata so amma sai da akayi mata na dole, sarƙa da ɗan kunne na gold ta saka mata duk yadda Inteesar tayi sai da Mufida tayi mata kwalliya ta fito kamar ba ita ba, wani kyau da kwarjini ta ƙara sai fitar da annuri take, kallon Gwaggo tayi tare da cewa "Gwaggo ni da zan tafi Asibiti meye na mani kwalliya kamar wacce zata je gidan bikin?" Taɓe baki Gwaggo tayi tare da cewa "Kunfi kusa Ni bani da lokacinku bari naje na cika ciki na." Daga nan ta fita Inteesar ma tabi bayanta, suka nufi dinning table, ruwan tea kawai Inteesar ta sha sannan ta ce, ta ƙoshi, hakan yasa ta miƙe ta kalli Mufida ta ce, "Ki bani hijabi na tafi." "Gyale na ɗauko maki ki saka?" "Haba kema kinsan bana son saka gyale" " To ni bani da hijabi gyale nake da su hijabi na guda biyu ne na sallah kuma yanzun na saka su cikin washing machine na zuba ruwa da sabulu zan wanke." Kallon ta kawai Inteesar tayi ta nufi ɗakin Mufida, kai tsaye toilet ta wuce ta duba cikin washing machine taga duka hijaban ta saka su ta jiƙa, daga gani tasan da gan gan Mufida tayi haka dan yasan dole zata nema ita kuma ba zata so ta saka ba, takaici ne ya ishe ta dole ta ɗauki mayafin ta saka ta zura takalmi da ɗauki hand bag ta fito, kallo ɗaya idan kayi mata sai ka sake sha'awar kallonta, tayi kyau sosai, ɗakin Mummy ta shiga ta sallame ta itama ta yaba da kyaun da Inteesar tayi, sannan ta nufi kitchen ta ɗauki basket ɗin ta nufi harabar gidan dan ta sanar da Direba ya Kaita Asibiti. Direban Mummy ya buɗe mata bayan motar ta shiga bayan ya saka abincin, sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa ya tada motar suka bar gidan *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, dan ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce, bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣2️⃣ Direban Mummy ya buɗe mata bayan motar ya shiga, bayan ya saka abincin sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa ya tada motar suka bar gidan. Ɓangaren Sumayya kuwa bayan sun gama abuda sukayi ne suka kwanta rungume da juna a haka barci ya ɗauke su, kiran sallar asuba ne ya tada Bashir ya janye ta daga jikinsa don yasa ko ya ce, ta tashi tayi sallah ba tashi zatayi ba, sai ta gama barcinta, buɗe ido tayi jin ya janye ta daga jikinsa ta ce, "Ina zaka je?" "masallaci zanje, tashi muyi wanka lokaci na tafiya" Gyara kwanciyarta tayi tare da cewa "Idan na tashi da safe zanyi wanka da sallar." Girgiza kai kawai yayi ya nufi toilet don yin wanka, bayan ya fito ne ya saka kaya ya nufi masallaci. Ana idar da sallar ya dawo ya kwanta ya cigaba da barcinsa, ƙarfe bakwai ta farka ta tayar da Bashir ya tashi zaune tare da kallonta "Lafiya Summy?" "Ka fita ka nemo Mani kayan da zansa idan nayi wanka, kasan banzo da niyyar kwana ba kuma ban ɗauki komai ba so kane ka siyo man.." Kafin ta kai ƙarshen zancenta ya ce, "Kwantar da hankalinki Baby akwai kaya ana sababbin waɗanda na tanada saboda irin haka, ke dai kawai kije kiyi wanka." Tashi tayi ta nufi toilet bayan kamar mintuna ashirin sai ta fito kanta na ɗaure da towel, ba tare da jin komai a ranta ba ta warware towel d'in ta shafa mai shaf-shaf t gama shiryawa ta ɗauki doguwar riga ta material da Bashir ya ajiye mata ta saka ɗan ƙaramin mayafinsa ta saka ta kwashi wayoyinta da jakarta ta nufi hanyar fita, har ta kai bakin ƙofa ta jiyo muryarsa yana cewa "Bako sallama?" "Sorry Dear may be na dawo ta nan, amma ba tabbas ko na koma gida sai shawarar da na yanke." "Okay sai munyi waya kenan?" "No kada ka kira waya ta idan ba nice na kira ka ba kada ka kira ni, idan ma akwai wani abu ne to kayi mani text message idan da yiwar nayi magana zanyi maka magana ta waya, idan babu kuma zaka ga text message ɗin a." Daga nan bata jira amsar da zai bata ba tayi ficewarta har ta kai tsakiyar falo ta ji ya ce, "Ba zaki tsaya muyi breakfast?" "Kai ta girgiza tare da ɗaga hannunta na hagu tana kaɗai yatsarta manuniya alamar a'a." Daga nan tayi ficewarta gurin motarta, shigewa tayi tare da tada motar ta bar gidan. Kwance yake bayan Jabeer ya taimaka masa yayi wanka, ya dawo ya zauna, Jabeer ne ya shigo hannunsa ɗauke da kayan Muhdeen, kasancewar dama a cikin office ɗin Muhdeen akwai bedroom da toilet don haka ya je ya bedroom nasa cikin wardrobe na kayan Muhdeen ya ɗauko masa wasu ƙananan kaya ya kawo masa ya saka, yana gama sakawa Jabeer ya fita da waɗanda ya cire shi kuma ya kishingiɗa, idanunsa ya lumshe kamar mai barci alhalin ba barci yake ba. Sumayya ce ta turo ƙofar ta shigo, shi dai ya ji motsin shigowar mutum amma baisan ko wace ce ba, kuma bai buɗe idanunsa ba, ƙamshin turaren da ya ji ne yasa ya yayi magana ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya ce, "Bashir kaine da sassafe haka?" Gaban Sumayya ne ya faɗi jin abunda Muhdeen ke faɗa, cikin rawar murya ta ce, "Nice kuma Bashir yau?" Da sauri ya buɗe idanunsa ya sauke a kanta, ganin ita kaɗai e yasa ya ce, "Bashir kaɗai nasan yana amfani da wannan turaren shiyasa nayi zaton ko shine, don naji ƙanshin turarensa ne, amma ke me ya haɗaki da irin turaren nan?" Murmushi tayi tare da zama dab da shi inda yake kishingiɗe, tashi zaune yayi ta ƙara matsawa dab da shi, tana shirin yin magana ne sai ga Inteesar ta turo ƙofar bakinta ɗauke da sallama "Assalamu alaikum" Jin muryarta yasa ya zubawa ƙofar ido idanunsa suka sauka akanta, subhanallahi, ai mutuwar zaune yayi sakamakon wani ƙayataccen kyau da yaga tayi, din tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin tayi nasa kyau irin na yau ba, ko lokacin aurensa da Sumayya da aka mata kwalliya a lokacin kallon arziki bata ishe shi ba, ko lokacin aurenta da shi ma bai ko kalli fuskarta ba, tabarakallu ahsanal khaliqin, shine kalmar da ya furta a zuciyarsa, ita kanta Sumayya sai da gabanta ya faɗi ganin irin kyau da kwarjini da cikar haiba irin ta Inteesar, don ko mace ƴar uwarta ta kalle ta sai ta sake kallonta ballantana namiji, tsananin kishi ne da baƙin ciki suka cika mata zuciya. Ita kuma Inteesar ganin basu amsa mata sallama bane yasa ta sake cewa "Assalamu alaikum" Daƙyar Muhdeen ya iya amsawa da "Wa'alaiki salam" Shigowa tayi hannunta ɗauke da Basket da aka jera abincin a jiyewa tayi a gefe ta sunkuya ƙasa ta gaida Muhdeen. "Ina kwana yaya?" Tsayawa yayi yana kallonta, don tun da yake a rayuwarsa ba mahaluƙin da ya taɓa durƙusawa har ƙasa ya gaishe sa sai ita, farin ciki ne ya lulluɓe masa zuciyarsa don haka ya ce "Kin tashi lafiya" "Lafiya lau ya ƙarfin jiki?" "Alhamdulillah" Miƙewa tsaye tayi tare da cewa "Allah ya ƙara sauƙi" Ya amsa da "Ameen" Kallon Sumayya tayi tare da cewa "Aunty Sumayya ina kwana?" Ganin Muhdeen ne yasa ta amsa mata da "Lafiya lau ya kike?" "Alhamdulillah" Zama tayi a ɗaya daga cikin kujeru da ke cikin room ɗin, Sumayya ganin Inteesar zaune yasa ta ƙara shigewa jikin Muhdeen musamman da ta lura ya mida hankalinsa ga Inteesar ita kawai yake kallo, sajensa ta shafa da hannayenta cikin kirsa ta ce "Nayi missing ɗinka sosai wallahi" Gajeren murmushi yayi tare da cewa "Nima haka". "Da gaske" Kai kawai ya ɗaga mata alamar eh, amma gaba ɗaya hankalinsa na ga Inteesar, ya mace a kallonta abubuwa dayawa yake ayyanawa a zuciyarsa game da ita, lura da hakan yasa Sumayya tayi ƙoƙarin ɗauke hankalinsa dan ya manta da Inteesar dake wajen. Bakinsu ta daɗe wuri guda ta tsotsansa, zaro ido yayi yana kallonta da mamaki, sanin cewa Inteesar na wajen ne yasa ya fara ƙoƙarin zame jikinsa daga nata amma ina sai ƙara ƙanƙamesa tayi a jikinta, hannu tasa cikin sumar kansa kamar maiyi masa susa. Inteesar tana ganin haka ta miƙe ta nufi ƙofar fita da sauri ta fice. Fitarta daga ɗakin ta nemi wani waje da aka tare kujeru ta zauna a harabar wajen, akwai 'yar tafiya tsakani, tagumi tayi tana tuna yanayin da ta barsu take taji wani ɗaci a zuciyarta ƙwalla ne suka taru a idanunta sai tayi saurin mayar da su, tsuki tayi tare da furtawa a fili. "To me yasa ma naji haushin abunda suka yi? ina ruwa na da su? me yasa nake jin kishinsa a raina?." Ita kaɗai take magana sanin ba wanda zai amsa mata yasa tayi shiru. A can ɗakin kuwa Jabeer ne ya turo ƙofar ya shigo,turus yayi yana masu kallon mamaki, kafin ya ɗaga masu murya da cewa "Meye haka!?" Sai a lokacin suka dawo hayyacinsu kallon Jabeer sukayi da yake kallonsu shima. "Nan Asibiti be meye haka? wai mara lafiya kenan, tashi ku tattara kayanku ku tafi can ku ƙarata." Kwanciya Muhdeen yayi ita kun Sumayya dama ba kunya ce da ita ba, dan haka ko a jikinta. Tsuki Jabeer yayi yayin da idanunsa suka sauka akan Basket da Inteesar ta kawowa Muhdeen breakfast. "Wannna basket na abincin fa wa ya shigo da shi, tunawa Muhdeen yayi da Inteesar dan haka ya miƙe da ƙyar tare da cewa "Inteesar ce ban ma san lokacin da ta fita ba." Da mamaki yake kallonsu "Kana nufin tana zaune a nan a gabanta kuke wannan abun?ko kunya baka ji ba wannnan ai cin fuska ne." Sai a lokacin shi kansa Muhdeen yaji kunyarta ya rasa yadda akayi ya biyewa Sumayya, duk da baiso biye mata ba amma shu'umancinta sai da tasa ya biye mata. Hanyar fita yayi ko zai ganta a wajen amma ba ita ba alamarta, to ko dai ta tafi ne, juyawa yayi yaga wayarta a inda ta zauna sai ya tabbatar da cewa bata bata tafi ba. Ɓangaren Inteesar kuwa tana zaune a inda take ne sai taga mutum tsaye a kusa da ita, da sauri ta ɗaga kai dan ganin waye sai ganin Auwal tayi tsaye a kanta murmushi yayi tare da cewa "Assalamu alaikum" Itama murmushi tayi tare da amsa masa sallamar da yayi mata. "Wa'alaika salam, Malam ina wuni?" "Lafiya lau Inteesar me kike ana ?" "Bakomai ina dai hutawa ne" "Ok masha Allah, classmate ɗinki ce ba lafiya" Miƙewa tsaye tayi tare da cewa "Subhanallahi wace ce Malam?" "Lokacin da nake teaching naku ba S.S 2 ba akwai wata yarinya da na kawo ta class naku ba,na ce cousin ɗita ce ba?" Shiru Inteesar tayi tare da yin nazari kafin tayi murmushi ta ce, "Maryam Kabir ko?" "Ƙwarai kuwa ita" "Ayyah to mu ƙarasa na gaishe ta." Yana gaba tana binsa a baya har zuwa inda aka kwantar da Maryam, suna zuwa ma tana barci bata samu gaisawa da ita ba, sai dai ta gaida mahaifin Maryam da mahaifiyar sannan ta juyo don komawa, Mallam Auwal ya bita dan mata rakiya suka jera suna fitowa. Muhdeen da ke tsaye ta hango Inteesar tare da Mallam Auwal, suna tafiya a hankali suna magana, zuciyarsa ce ta fara tafarfasa musamman da ya kura Jama'a da yawa masu kai komo da waɗanda suke zaune sai kallon Inteesar suke, sai ta zama kamar zara a cikin taurari, itama kanta bata sake ba saboda kayan jikinta da suka ɗan kama ta ga gyale da ta yafa bata saba sakawa ba, ta saba da hijabi don haka sai take jin kanta wani iri. Mallam Auwal ya ce "Wa kika zo dubawa Asibiti?" "Mijina" Da sauri ya kalle ta tare da yin murmushi ya ce, "Mijinki fa kika ce." "Eh Mallam haka na ce," "Masha Allah na taya ki murnar auren da kikayi Allah ya sanya alkhairi." Murmushin kawai tayi tare da cewa "Nagode Mallam bari na ƙarasa, idan Maryam ta farka a isar mata da saƙon gaisuwa ta." "Okay zata ji, muje na gaida mijin naki da jiki." Zatayi magana kenan sai ta hango shi tsaye a ya jingina da bango ya zuba mata ido, sai da gabanta ya daɗi ganin irin kallon da yake mata fuskar nan tasa a murtuƙe ba sassauci a tattare da shi. "Gashi can ma ya fito" Mallam Auwal ya ɗaga kansa yana kallon inda take kallo, ganin Muhdeen yayi tsaye kansa an naɗe masa da bandeji idanunsa na kansu. "Amma mijin naki accident yayi ko?" Kai ta ta gyaɗa masa kawai, ƙarasowa sukayi gaban Muhdeen fuskar Mallam Auwal ɗauke da murmushi ya miƙawa Muhdeen hannu tare da cewa "Assalamu alaikum" Tsayawa Muhdeen yayi yana kallonsa kafin ya miƙa masa hannu fuskarsa a tamke, ciki ciki ya amsa masa sallamar, idan ba kin kalli bakinsa ba ba zaki san ya amsa sallamar ba, Mallam Auwal ya cigaba da cewa "Ya jiki?" Kai kawai ya ɗaga ba tare da yayi magana ba, Mallam Auwal ya sake cewa "Allah ya ƙara lafiya ya kiyaye gaba." Nan ma kai kawai ya ɗaga masa, ganin hakan yasa Mallam Auwal tunanin ko Muhdeen baya magana ne dan haka ya ce, "Allah sarki baya magana ne amma yana ji." Ita dai Inteesar shiru tayi bata ce komai ba, har Mallam Auwal yayi masu sallama ya tafi, bayan tafiyarsa da ne ya kalli Inteesar tare da cewa "Waye wannan meye alaƙarki da shi?" "Malami ne a school namu." "To yanzun me ye haɗinki da shi kuma waye ya ce ki fita ballantana har ya ganki kuma daga ina kuke?" Haka ya jera mata tambayoyi kallonsa tayi tare da cewa "To wace tambaya zan amsa maka?" "Dukansu zaki amsa mani." "Maganar cewa meye haɗina da shi bani da shi bani da wata haɗu da shi, face a matsayinsa na musulmi ɗan uwa na kuma malamin da ya karantar dani." Kallonsa tayi cikin ido sannan ta cigaba da cewa "Maganar daga inda muke kuma ya ganni zaune ina hutawa shine yayi mani sallama, bayan mun gaisa ne ya sanar da ni cewa akwai wata classmate ɗina ce ba lafiya, shine na bishi dan na gaishe ta." Saura tamabarka ɗaya na cewa me yasa n fita? to zaman me zanyi bayan kana buƙatar sirri kai da matarka shiyasa na fita tunda ku baku ji kunya ta ba, ai ni naji kunya na fita na baku waje, dan na lura kunya baya kuka bashi ba gaba ba." Mamanki ne ya kama shi yadda ta tsaya tana gaya masa magana, ba tare da shakkarasa ba kamar yadda take yi wasu lokutan, kuma maganar da yadda take yinsa zaka gane cewa har da kishi ne,don cikin jin haushinsa take maganar. *Daga alk'alamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😍😘 Comments &shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan har kinsan cewa kina cikin group ɗin Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, dan ko kinshiga idan baki comments zan fitar dake ne. *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣3️⃣ Mamaki ne ya kama shi yadda ta tsaya tana gaya masa magana, ba tare da shakkarasa ba kamar yadda take yi wasu lokutan, kuma maganar da yadda take yinsa zaka gane cewa har da kishi ne, don cikin jin haushi take maganar. "Okay saboda haka ne yasa kika fita haka kike mani terere da jikinki? kalli kayan da kika saka yadda suka kama jikinki yaushe kika zama haka, ke da kina buduwa ma kullum cikin hijabi kike, sai yanzun da kina matar aure da yakamata ace kin ƙara killace jikinki shine kika fito haka ko?sai wannna mayafin wanda yake shara-shara da ajiye shima kawai kika yi kika fito haka nan, dan biada amfani." Jabeer ne da ya ƙara so wajen ya ce, "To Sarkin kishi." Girgiza kai yayi tare da nuna jama'ar da ke harabar wajen da masu kai kawo ya ce, "Jabeer ka duba ka gani cikin jama'ar da ke nan ta keto ta ta taho akasarin jama'ar da ke wajan duk idanunsu akanta, kowa kallonta yake yi da haka ta saba fita?" Wani ne ya gifto zai wuce sai Muhdeen ya kalle sa ya ce "Yauwa Mannir zonan dan Allah" Wanda aka kira da Mannir yazo cikin girmamawa ya ce, "Sannu yallaɓai ya jikinka?" "Da sauƙi" Cikin aljihun wandonsa ya ciro kuɗi ya miƙa wa Mannir ya ce, "Ka tafi yanzun nan ka siyo mani manyan hijabai guda biyar ka kawo mani." Karɓa Mannir yayi tare da cewa "To yallaɓai" Ya tafi Jabeer ya kalli Muhdeen tare da cewa "Ai taɓa sanin cewa kana da kishi ba sai yanzun, na ɗauka baka da kishi sam a rayuwarka." Kallon Inteesar Muhdeen yayi tare da cewa "Ki shiga ciki" Ba musu ta nufi room ɗin da Muhdeen yake ta shige. Kallonsa ya maida ga Jabeer ya ce, "Me yasa kake tunanin bani da da kishi?" Dariya yayi tare da cewa "Abunda a bayyane yake, ita Sumayya da take yawo da kayan da basu dace ba wanda kwata-kwata ba wanda zai ganta yayi tunanin matar aure bace fa? tunda nake ganinta ban taɓa ganinta da shiga irin ta mutunci ba, tun daga kan 'yan matancinta har zuwa aurenta, duk da cewar da tayi auren an samu sauyi amma duk haka banbancin kaɗan ne, me yasa ita Sumayya baka tilasta mata ta lulluɓe jikinta da hijabi ba? sai Inteesar da take shigar mutunci ce zaka saka a gaba? ai naga duka matanka ne meye banbanci?" Gajeren murmushi Muhdeen yayi wanda ya tsaya iya fatar bakinsa sannan ya cigaba da magana "Kasan akwai banbanci tsakanin Inteesar da Sumayya, Inteesar tana da nazari, nutsuwa, hankali da kuma tarbiyya, yayinda Sumayya kuma tayi hannun riga da waɗannan abubuwan sam bata da su, domin Sumayya bata samu tarbiyya daga wurin iyayenta ba, haka ta tashi ba mai saka ta ba mai hana ta duk abinda taga dama shi zatayi na wanda zai ce da ita me yasa ko mai tayi dai-dai ne a wajen iyayenta su kansu basu isa da ita ba, kasan icce tun yana ɗanye ake lanƙwasa shi idan ya bushe bazai lanƙwasu ba sai dai ya karye, to Sumayya ma haka take kaima ka sani, Inteesar kuwa ta samu cikakkiyar tarbiyya daga wajen iyayenta tasan darajar mijinta, ɗan zama na da ita ko ita ce na ajiye na ce kada ta tsallake sa to baza ta tsallaka ba, tana mani biyayya da jin magana ta koda ranta bai so ba bata tsallake magana ta, shiyasa kai tsaye nake iko da ita saboda nasan na isa da ita." Jinjina kai Jabeer yayi ya ce, "Hakane, ne ta girko mana ne dan dama kasan nan Asibiti na kwana banyi breakfast ba, nasan Inteesar wajen iya girki ba daga baya ba." Shiga cikin ɗakin sukayi inda Inteesar ta zauna da tazo yanzun ma nan take, kuma a kagare take da ta tafi tasan bazai barta ta fita haka ba dan haka ta tsaya jiran a kawo mata hijabi ta tafi, Sumayya kuma tana zaune bakin gadon. Jabeer ne ya kalli Inteesar ya ce, "Ƙanwata a bani abincin da aka kawo wa majinyaci naci ina son naci girkin nan naki mai daɗin gaske." Dariya tayi tare da ƙara sawa tayi wajen Basket ta ce, "Yaya Jabeer me zan fara zuba maka?" "Me da me kika kawo ne?" "Kunun gyaɗa da ƙosai sai shayi da bread da soyayen dankali da plantain da ƙwai, sai farfesun kayan ciki." Murmushi yayi tare da cewa "Masha Allah, ki bani kunun gyaɗa da ƙosai sai farfesun nan" Cup ɗaya ta ciro ta zuba masa ta ciro plate ta zuba masa ƙosai, tana buɗe farfesun ƙamshi ya gauraye ɗakin Sumayya har tana haɗiyar miyau. Bayan ta ajiyewa Jabeer nashi ta koma ta zauna ki kallon inda Muhdeen da Sumayya suke bata yi ba, dan sun ɓata mata rai, ganin ta zauna yasa Summary kallonsa ta fara Magana "Baby wai ba saboda kai aka kawo abincin nan bane? naga ko zuba maka naka bata yi ba ballantana ni." Kafin Muhdeen yayi magana ne Jabeer ya ce, "Ai tayi mai wuyan tunda ta girka ta kawo ke sai ki zuba masa ai." Kallon Jabeer tayi cike da jin haushinsa ta buɗe baki da niyyar maida masa martani ne taji muryar Muhdeen ya ce, "Ki zuba ki kawo mani" Kallon Inteesar tayi dan gani take kamar tafi ƙarfin hakan tunda ga Inteesar a wurin, taso a ce ita zata zuba masu ta kawo masu. Tashi tayi ta je ta zuba ganin zata cika ne yasa ya ce ta barshi haka nan, sai ta nuna masa cewa ita da shi ta haɗa, dan haka yayi shiru bai ce komai ba, tashi yayi daga kan gadon ya nufi sofa dake ɗakin ya zauna, Sumayya ta kawo da ajiye a Centre table dake gaban Muhdeen, komai da aka kawo sai da ta zuba masu ta haɗa a plate kunun gyaɗa da ruwan shayi ta zuba a kofi biyu ita da shi, kallonta yayi tare da cewa, "Ki zuba a kofuna uku" Kallonsa tayi zatayi masa magana sai ta tamke fuska dan yasan halinta yanzun zata yi masa gardama, ganin haka yasa bata ce komai ba ta zuba tana jiran taga ikon Allah. Zama sukayi zasu fara yin breakfast ɗin ya kalli Inteesar tare da cewa "Zo ki zauna kiyi breakfast nasan baki ci komai ba." Da sauri Sumayya ta kalle shi jin abunda ya faɗa, dan kwata-kwata ta tsani taga yana kula Inteesar kuma yanzun ta lura ya faɗa tarkon son Inteesar tsundum, amma baya yi tunanin zai haɗa matsayinta da na Inteesar ba, wai ita ce zaisa ta zubawa Inteesar abinci? takaici ne ya kamata sosai da sosai, kallon Inteesar tayi lokacin da taji Inteesar na magana tana cewa "A'a yaya na ƙoshi" Kallonta yayi "Me kika ci?" Girgiza kanta tayi tare da cewa "Bakomai" "Bana son gardama kizo kici abinci, " Cikin sanyinta da nutsuwarta ta taso tazo ta zauna a cikinsu, wannan ne karo na farko da ta zauna a tsakiyarsu dan yin breakfast, ko can gida lokacin da take masu girki sai dai ta jera masu ta ajiye su ci tare amma yau da kansa ya ce ta shigo cikinsu. Cikin jin haushinta Sumayya ke binta da kallo har ta zo ta zauna, kowa ya fara cin nasa banda Sumayya da baƙin ciki ya hana ta ci, ganin kallon da Muhdeen ke mata yasa ta fara shan kunun gyaɗa ita kuma Inteesar ruwan shayi kawai ta ɗauka take sha. Gaba ɗaya idanun Muhdeen akan Inteesar yake ita kuma bata ma kula da kallon da yake mata bane, idonta nakan kofin shayin da take sha, Sumayya da idanunta ke kansa ne ta kula da hakan, yayin da take cike da takaici, miƙewa Inteesar tayi zata bar wajen ta jiyo muryarsa yana cewa "Ina zaki je baki ci komai ba." Cikin sanyin Muryarta ta ce, "Na ƙoshi" "Dawo ki zauna " Sumayya ce ta kalle shi da sauri "Haba Dear tunda ta ce ta ƙoshi dole ne? cikinta ne fa ba naka ba, idan ma bata..." Kasa ƙara maganar tayi ganin kallon da ya jefa mata, domin tun ranar da ya gane cewa ita ce tayi yinƙurin kashe Inteesar ya mata dukan da sai da ta suma to tun daga ranar ne ta fara shakkarsa idan ta tuna ma takan ji tsoronsa dan haka koda taga kallon gargaɗin da yake mata sai tayi shiru. Ba musu Inteesar ta dawo ta zauna, da kansa ya ɗebi soyayyan dankali da ƙwai sai da bread ya aje mata a gabanta. "Ki cinye su yanzun nan tunda baki son cin abinci." Kwaɓe fuska tayi kamar zata yi kuka tare da tura baki tana magana ciki ciki ba wanda ke jin me take cewa Shagala yayi da kallonta yadda take yi sai ji yayi ta burge shi, murmushi kawai yake yana kallon bakinta yana tuna ranar da ya sumbaci bakinta da irin yanayin da ya shiga, da daɗin da baƙin nata ke da shi,gaba ɗaya ya shagala da kallonta yana cin wani nishaɗi a tattare da shi, ji tayi a jikinta ana kallonta tana ɗaga kai sukayi ido huɗu da shi ɗauke idanunsa yayi daga kallonta, abun mamaki sai yaga ba Sumayya a ɗakin ba alamarta, juyawa yayi gabas da yamma Kudu da arewa ba alamarta, sai a lokacin idanunsa ya sauka akan Jabeer dake ta dariya, itama Jabeer take kallo Muhdeen ya ce, "Kai kuma lafiyarka? Ba tare da ya kalle shi ba ya ce, "Lafiya lau nake" "Ina Sumayya ta shiga ko tana toilet ne?" Tsagaita dariya Jabeer yayi tare da cewa "Mallam ka warware ba abunda ke damunka ka tattara kabar Asibitin nan" "Pls Ina take?" "Kai da kake zaune tare da ita baka sani ba sai ni? naga lokacin da ka shagala da kallon tauraruwarka ita kuma lura da hakan yasa baƙin cikinku ya kore ta dana na lura ba zata iya jurewa ba" Ya ƙarasa maganar yana mai ƙara keta wata dariyar ya tashi ya fita yana cewa "Kada na dawo na tarar da kai dan yanzun kam ba abuda ke damunka ba zaka tare mani rikicin wannan matar taka ba." Daga nan Jabeer ya fita ya bar Muhdeen da Inteesar, yayin da zuciyar Muhdeen tayi fari fes dan a duka lokacin da suka keɓe shi da Inteesar sai ya dinga jin wani aminci ya lulluɓe shi, kallonta ya cigaba da yi don shi ba mai yawan kallo bane amma idan dai akan Inteesar ne baya taɓa iya ɗauke idanunsa daga kallonta, sam baya gajiya da kallonta. Daƙyar ta iya cinye abincin da ya zuba mata kamar zatayi kuka, dan ita ba mai yawan cin abinci bane, dan haka kishingiɗa tayi a saman sofa ɗin, matsawa yayi kusa da ita da niyyar kai hannu ya taɓa ta yaji anyi knock bada izinin shigiwa yayi, Mannir ne riƙe da leda babba a hannunsa ya miƙawa Muhdeen tare da cewa "Yallaɓai gashi" Amsa yayi tare da cewa "Nagode Mannir" Mannir ya miƙa masa sauran canji da da suka rage, kai Muhdeen ya girgiza tare da cewa "Na baka kyauta" Godiya yayi tare da addu'a ga uban gidan nasu ya fice. Miƙa mata ledan tayi tare da cewa "Ki ɗauki daya kisa yanzun nan idan kin koma gida zaki cigaba da sawa." Cikin sanyin Muryarta ta ce, "Nagode Allah ya saka da alkhairi, Allan ƙara huɗu." .tsayawa yayi yana kallonta har cikin ransa ya ji daɗin kalamanta, janyo ta yayi tare da manna masa kiss a gishi. Gwaggo ce ta turo ƙofar ta shigo, Mummy na biye da ita a baya. Cikin so da kula suka gaisa da Muhdeen, kuma shi kansa yaji daɗin yadda suka saki fuska da shi ba sun daina fushi da shi,yanzun Dady ne kawai ya rage bai daina fushi da shi ba. Bayan awa uku su Gwaggo da Mummy suka tafi, Inteesar ma binsu tayi . A rana r ne aka sallami Muhdeen ya tattara kayansa ya koma gidansa, bayan ya koma ko zama baiyi ba ya ɗauki wayarsa ya da nawa Jabeer kira, bayan ya ɗaga ne Muhdeen ya ce, "Dan Allah ka shirya ka raka ni mu roƙi Dady ya bani mata ta dan Allah, dan bani da matsala da Mummy da Gwaggo dan naga sun sauka zasauyi sauƙin kai amma Dady kam har yanzu bai sauko ba, dan Alalh ka raka ni Jabeer, a shirye nake da na fuskanci kowane ƙalubane ne ." *Daga alƙamimin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don ƙarin bayani* 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan kinsan cewa kina cikin group ɗin Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce bada niyyar yin hakan nayi barshi me mai kashe auren wawa *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣4️⃣ "Dan Allah kanshirya ka rakani mu roƙi Dady ya bamu matata don Allah, dan bani da matsala da Mummy da Gwaggo dan naga sun sauka zasauyi sauƙin kai , amma Dady kam har yanzun bai sauko ba dan Allah ka rakani Jabeer a shiryau nake da na fuskanci bko wane ƙalubale ne" Daga nan ya kashe wayar toilet ya shiga yayi wanka. Sumayya kam tana can ɗakinta sai cika take tana batsewa, ita a tunaninta tunda ya dawo zai shigo ne ya lallaɓa ta, amma sai taji shiru bai shigo ba kuma ba alamar zai shigo, haka ta dinga saƙa da warwara ita kaɗai a ɗauki, zuwa can sai ta ƙyalƙyace da dariya har tana kwanciya saboda tsabar dariya, ita kaɗai ta fara magana "Kwantar da hankalinki Sumayya komai zai tafi yadda kike so, kedai ki kasance mai juriya ki daure har sai kin kai ga nasara akan abinda kika saka a gaba, komai zai dawo maki dai-dai Sumayya da farko ki fara ajiye makaman yaƙinki a gefe." Haka ta dinga magana ita kaɗai, daga ƙarshe ta fito ta nufi ɗakinsa, tana tura ƙoafar taji wani ƙamari ya ziyarci ta tsaye ta same sa yana saka hula a kansa, bayan ya gama shiryawa kamar wani ango yayi masifar kyau ta cikin mirror ya hango ta tana sakin murmushi, mamaki ne ya kama sa dan dai shi ya sani Sumayya fushi take yasan ba zata saurare shi ba dan haka ya fita harkarta, amma abunda ya bashi mamaki ganin yadda take murmushi kamar ba ita ba, kamar ba fushi da kishi ne ke damunta ba, juyowa yayi yana kallonta yayin da ta ƙaraso wajensa wajensa tare da riƙe hannunsa biyu cikin murmushi ta ce, "Masha Allah ka ga yadda kayi kyau kuwa kamar sabo ango?" Murmushi yayi tare da cewa "Nagode" "Ina zuwa wannna kwalliya haka?" "Zamu je wani waje ne ni da Jabeer" "To idan kun je ku gaishe mani da ita" Da mamaki yake kallonta "Wace ce zamu gaisar maki da ita?" Dariya kawai tayi tayi sannan ta ɗora da cewa "Nasan zaka tafi wajen ƙanwata ce, shine na ce ka gaisar mani da ita." Tsayawa yayi yana kallonta yayi mamakin jin maganar daga bakinta, dan idan da ba don shine da kansa yaji ba wata ce ta faɗa masa zai ƙaryata, don ko a mafarki ta nuna masa wannan yanayin idan ya farka zaiyi sadaka. "Ke Sumayyata da na sani ce ko kuma an canza msni ke? ban taɓa tunanin jin hakan daga bakinki ba, sai nake ga kamar ba ke bace." Murmushi tayi yayin da ta ƙara matse hannunsa cikin nata "Kada kayi mamaki nice, na canza daga yadda ka sanni ne ka ɗauka waccan Sumayyar da ka sani a baya ta sauya, wanna ta banbanta da waccan." "Da gaske kike yi?" "Eh mana baka yarda da ni bane?" "Ba wai ban yarda da ke bane,kawai mamaki nake canzawarki lokaci guda, anya ba wata munaƙisa kike shiryawa ba?" Murmushi tayi tare da girgiza kanta "Dama nasan ba zaka yarda da ni ba amma da sannu zaka fahimci komai, yau da gobe." Shikenan na ji, amma mutuƙar wani abu mara kyau ko mara daɗi ya biyo baya to da ki sani bazan saurara maki ba ko kaɗan, dan wallahi sai kin ɗanɗani kuɗarki." "Allah sarki bansan me yasa kake mani mugun fahimtar nan ba" "Ai Sumayya kin wuce sani na, duk mutumin da zaiyi yinƙurin kisan kai da ba abunda bazai iya aikatawa ba." Dafe goshi tayi tare da rintse ido "Dan Allah ka daina dawo da abinda ya wuce, mu mance da shi kawai mu rungumi gaba, amma matuƙar zaka dinga tuna aibu na ba zaka taɓa ganin haske na ba, nayi nadamar abinda ya faru a baya dan Allah a daina tuno mani da shi, insha Allahu itama Inteesar zan roƙi gafararta ta yafe mani." Farin ciki ne ya lulluɓe shi ya rungume ta yana godiya ga Allah da ya sa Sumayyarsa ta gane gaskiya. Kiran wayarsa ne ya sa ya sake ta tare da ƙarasawa jikin gadon ya ɗauki wayar, sunan Jabeer ne ya fito, ɗagawa yayi tare da cewa "Ka fito ne?" Jabeer ya ce, "Mu haɗu a ƙofar gidan kawai" "Okay I'll be on my way" Kashe wayar yayi tare da kallon Sumayya ya ce, "Sai na dawo" "Oky tare da ita zaku dawo?" "Bani da tabbas ki taya ni da addu'a Allah yasa ya amince" "Ameen, thank you so much" Daga nan ya nufi ƙofar fita ta riƙe hannunsa tare suka fito ta raka sa har wajen motarsa, wannan karan ba shine Aiyi driving ba Ishaq ne ya ja shi suka tafi, tana ɗaga masa hannu har mai gadi ya wangale masa gate suka fice, sannan ta koma cikin gidan. Dady zaune a falo shi da Gwaggo suna fira yayin da Mummy da Inteesar suke cikin kitcheen suna aiki. A ƙofar gidan kuwa Jabeer ne yayi parking, yana jiran ƙarasowar Muhdeen, bayan Muhdeen ya ƙaraso ne Jabee yayi horn mai gadin ya buɗe masa gate, bayan ya shiga ne shima Muhdeen yabi bayansa da tasa motar parking suka yi sannan suka fito a tare suka shiga gidan, bakinsu ɗauke da sallama, Dady da Gwaggo suka amsa sallamar yayin da Muhdeen da Jabeer suka ƙaraso suka durƙusa tare da gaishe su, bayan sun gaisa ne suka zauna akan Centre carpet kowa yayi shiru Gwaggo ce ta katse shirun ta hanyar cewa "Muhammadu ya jikinka har ma warware ne da zaka fara yawo?" Murmushi yayi jin Gwaggo tayi magana kuma yasan kuma ta sauko dan haka ya samu ƙwarin gwuiwar yin magana "Dama nazo ne ina mai roƙonku a karo na biyu da kuyi haƙuri ku gafarce ni ku bani mata ta mu kom..." Tsawar da Dady ya daka masa ne yasa ya kasa ƙarasa maganar, wanda har Mummy da Inteesar da suke kitchen sai da suka jiyo tsawar, dan haka suka nufo falo dan ganin meke faruwa. "Muhammad ka kiyaye ni ka fita a ido na me ka maida mutane ne? idan ma kana tunanin cewa Inteesar zata koma gidanka ne? to kayi kuskure babba tunda Allah yasa ka zo yanzun nan ba sai anjima ba kamar yadda na umarce ka da ka aure ta ba tare da ka shiryawa hakan ba, to yanzun ma na umarce ka da ka sake ta ba tare da ka shiryawa hakan ba, kada kayi mani musu ko gardama kuma ba shawara bace umarni ne ka sake ta yanzun nan." Muhdeen da Inteesar jin kalaman Dady yayi masu tsauri ne lokaci ɗaya suka fara zubar da hawaye, Muhdeen ya durƙusa akan gwuiwar ƙafarsa biyu yana zubar da hawaye yana roƙon Dady da ya amince da nadamarsa. "Dady tun ranar na baku haƙuri na roƙe ku da ku yafe mani, ku amshi tuba na sannan kuma ku kafa mani kowace irin sharaɗi ne indai akan Inteesar ce zan cika su, idan har na sake aikata wani abu mara kyau a gare ta na amince ku raba ni da ita har abada, yanzun dai na gane kuskurena, wallahi bazan iya rayuwa ba Inteesar ba." Jabeer ya dora da cewa Dady zan faɗa maganar nan ne badan na bi son zuciyata ba kuma badon Muhdeen yana amini a gare ni bane a'a zan faɗi haka ne dan..." Dady ne ya ɗaga masa hannu alamun dakatarwa ya ce, "Kai Jabeer kayi magana kai tsaye bana son nuƙu-nuƙu." Kai ya jinjina alamar to sannan ya ɗora da cewa "Dady wallahi yanzun Muhdeen yayi nadama da gaskiya yake son Inteesar, nabtabbata idan kuka basa matarsa suka cigaba da zamansu, na tabbata ba zaka taɓa dana sanin hakan ba, kuma..." "Kai Jabeer wato ya ɗauko ka ne dan kazo ka wakilce shi ko? to daga kai har shi ku fita kubar mani gida na, kuma kada na sake ganinku kunzo nan da makamancin wannan zancen." Kuka ne ya ƙwace masa kamar ƙaramin yaro ya dinga roƙon Dady amma yayi biris da shi ganin Dady baida niyyar saukowa yasa Jabeer yaja hannun Muhdeen suka nufi hanyar fita, kuka ne ya ƙwacewa Inteesar da mamaki Dady yake kallonta dan yasan ko kukan ne takeyi, kafin yayi magana yaji muryar Gwaggo na cewa "Wai kai Sani wani irin taurin zuciya ce da kai, yazo na farko ka kore shi ya je yayi hatsari Allah yasa kwanansa na gaba, yanzun kuma ka sake koransa so kake ya je ya sake wani hatsarin ya mutu ko?" Ƙara sawa tayi bakin ƙofar ta janyo hannun Muhdeen suka dawo . Ajiyar zuciya Dady ya sauke tare da cewa "Gwaggo mu muka aura masa ita da kanmu a bisa umarnink, mun kai ya gidansa akan muna da yaƙinin cewa bazai watsa mana ƙasa a ido ba, amma ina muke a lokacin da suke zaune ya dinga azabtar da ita? ina muke lokacin da ya dinga ƙuntatawa rayuwarta ya maida ita baiwa? ina muke lokacin da uwar gidansa Sumayya ta mayar da ita tamkar baiwarta, ita ce yai mata wankin toilet gyaran ɗaki shara ta bata umarnin ta dafa mata abincin da ranta keso, ina muke lokacin da take rayuwar rashin ƴanci? ina muke lokacin da matarsa Sumayya tayi yunƙurin kashe ta?" Kaga ba wannan nake so naji daga gare ka ba, yaro ya gane kurensa ya kuma kowa ya fahimci yanzun yana son matarsa, abu ɗaya ya rage a nemi jin ta bakinta idan ta amince zata koma ɗakin mijinta kuma tana sonsa ai shikenan sai ku binsu da fatan alkhairi." Jinjina kai Dady yayi ta ce, "Shikenan Gwaggo yi adda kika ce haka za'ayi" Kallon Inteesar dake goge hawaye Gwaggo tayi tare da cewa "Zo nan ƴar albarka" Cikin sanyin jiki ta ƙara so ta durƙusa a gabansu, Dady ya kalle ta tare da cewa "Inteesar" Cikin sanyin murya ta ce "Na'am" "Kina son Muhammad kuma zaki iya cigaba da zama da shi matsayin mijin aure?" Gaban Muhdeen ne yake dukan uku uku yana fargabar ta ce bata sonsa, Mummy ma da ta kasa magana kallon Inteesar take tana addu'a Allah yasa ta amince, dan yasan cewa tayi sa'ar suruka. Tsawon mintuna biyar batayi magana ba sai da Gwaggo ta tambaye ta a karo na biyu ta ce "Eh zan zauna da shi" Daga haka ta ruga a guje zuwa ɗakin Mufida cikin jin kunya, dariya sukayi Muhdeen ya ɗaga hannu yana godiya ga Allah. Muryar Dady suka ji ya ce, "Akwai sharaɗi guda ɗaya, har sai ka raba masu gida da Sumayya, bazan taɓa bari ka haɗa su gida da Sumayya ba, dan kafi kowa sanin abunda ta aikata, dan haka zama da ita hatsari ne ga rayuwar Inteesar." Nan dai Mummy da Gwaggo suka amince da maganar Dady, dama yana da wani gidan da ya siya har Jabeer ya bashi shawara yakai Inteesar gidan ya nuna gida ɗaya zai aje su, an gama komai na gidan hatta fenti anyi saura a goge gidan kasancewar yayi ƙura a kuma zuba furniture's. Kai ya jinjina tare da cewa "To insha Allahu nan da gobe za'a goge gidan a zuba furniture's sai ta zauna a ciki." Nan sukayi masu fatan alkhairi farin ciki a wajen Muhdeen ba'a magana. A ranar yasa akayi fenti aka aka gyara gidan aka wanke, washe gari, washe gari kuma yasa aka saka labulaye da furnitures. Ɓangaren Sumayya kuwa taso ace gida ɗaya aka haɗa su da Inteesar, dan ko da ya sanar da ita yadda sukayi da Dady bata so araba masu gida ba, dan magana tayiwa Muhdeen akan ya koma ya roƙi Dady kan cewa su zauna tare ya nuna mata cewa Dady da Gwaggo ba zasu yarda ba, amma idan komai ya tafi dai-dai zuwa nan gaba zai haɗa su gida guda hakan yasa ta ɗanji sanyi a ranta. Mummy ta Kira Aunty Abla tare da ƙawarta Aunty Bilkisu, suka je gidan da Inteesar ta zauna da Sumayya suka tattaro kayan Inteesar duka aka zuba a mota suka nufi gidanta na yanzun. Matsakaici gida ne dan bai kai wancan gidan da Sumayya take ciki girma ba, don shi 3 bedrooms ne kowane ɗaki yana ɗauke da toilet sai wani toilet da akayi shi a falo saboda baƙi, sai kuma dinning room da kitcheen. Tsarin gidan yayi kyau komai nasa madaidaici ne gwanin ban sha'awa. Ana gobe Inteesar zata tare farin cikin da Muhdeen yake ciki baya misaltawa, sai wani rawar ƙafa ya ke kamar sabon angon da za'a kaiwa Amarya gobe, farin cikin da yake ciki ya kasa ɓoyuwa duk wanda ya kalle sa yasan yana cikin farin ciki. Ɓangaren Inteesar kuwa wani sabon gyara Hajiya Bilkisu ta yi mata a cikin kwana biyun nan, tun daga kan na wanka na shafawa na sha da na turara jiki da na tsugunno, sai wani ƙamshi na musamman take fitarwa a cikin kwana biyun nan ta sauya Sosai. Duk yadda Muhdeen yaso su haɗu da Inteesar Mummy ta hana, dan ko yazo bata bari ta fito su haɗu, yau da ya ƙagara da ya ganta ne ya nunawa Mummy cewa yana son zaiyi magana da ita ne, amma ta nuna masa cewa ya faɗawa Mufida abunda zai faɗa sai Mufida ta sanar da Inteesar, haka ya hakura ya koma gidan a zuciyarsa yana cewa ai daga gobe ne, ƙarshen tika-tika tik. *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K N.T (Maman Ihsan) *DON NEMAN ƘARIN BAYANI* 090 65327995 Love you oll😍😘 Comments &shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Idan kinsan cewa kina cikin group ɗin Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group dan ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne. *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izina ba. *SANARWA* Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣5️⃣ Duk yadda Muhdeen yaso su haɗu da Inteesar Mummy ta hana, dan ko yazo bata bari ta fito su haɗu, yau da ya ƙagara ya ganta ne ya nunawa Mummy cewa yana son ya ganta ne, amma ta nuna masa cewa ya faɗawa Mufida ta sanar da Inteesar, haka ya haƙura ya koma gidan a zuciyarsa yana cewa ai daga gobe ne, ƙarshen tika-tika tik. Rana bata ƙarya yau ne ta kama ranar da Inteesar zata tare a sabon gidan Muhdeen, musamman Mummy ta sa aka kawo mai lalle da kitso, inda aka tsantsare ta da ado da kwalliya, tun safe ya kira Mummy yake tambayarta wai zaizo ya ɗauki matarsa, ta sanar da shi cewa ba sai yazo ba su da kansu zasu kawo masa ita, godiya yayi tare da mata sallama. Da misalin karfe takwas na daren Inteesar tana zaune a ɗakin Gwaggo, bayan anyi mata kwalliya tana zaune cikin riga da zani na atamfa ta lulluɓe jikinta da mayafi, sai ƙamari ke fita daga jikinta, Gwaggo na ƙara mata nasiha Mummy ta turo ƙofar ta shigo bakinta ɗauke da sallama, Gwaggo ce ta amsa mata sallamar Inteesar sai kuka da take yi. Gwaggo ce ta ɗaga kai ta kalle ta tare da cewa "Sanin ya dawo zaku tafi ne?" "Eh Gwaggo ya ce mu fito" Kai Gwaggo ta gyaɗa alamar gamsuwa "To gata nan ku tafi, Allah ya sanya alkhairi, ya kaɗe duk wani sharri da fitina dake tunkarar rayuwarsu, Allah ya basu zuri'a ɗayyiba". Murmushi Mummy tayi cikin jin daɗin addu'ar da Gwaggo tayi tare da cewa "Ameen ya rabbil izzati, Allah ya amshi addu'ar ki." Jan hannun Inteesar tayi dan ta miƙe amma Inteesar bata miƙe tsaye ba ta cigaba da zamanta tana kuka, jin muryar Gwaggo suka yi tana cewa "Ki tashi ki tafi ɗakin mijinki bana son munafurci, kukan me zakiyi anan wa zakiyiwa kuka? lokacin da aka ce ba zaki koma ba aka kore sa ba ƙofar kitcheen kika rakuɓe kinawa mutane kuka ba?kika nuna kina son komawa ɗakin mijinki ba? sai yanzun za'a kaiki inda kika kika nuna kina so zaki dinga yiwa mutane kukan munafurci." Mummy ce ta dinga rarrashinta taja hannunta suka fice, bayan ta daina kuka. Dady ne da kansa yayi driving nasu yayin da Mummy ke zaune a gefensa, Inteesar na bayan Motar, har Dady yayiwa motar key zai ja sai ga Mufida ta ƙaraso a guje ta buɗe murfin motar ta zauna gefen Inteesar. Kafin Dady yaja motar wayarsa ya ciro tare da lalubo number Muhdeen. Muhdeen ya gama shiryawa kenan zai fito daga ɗakinsa wayarsa ga soma ruri, ganin Dady ne yasa ya saki murmushi dan yasan akan Inteesar ne, ɗaga kiran yayi tare da cewa "Assalamu alaikum, barka da dare Dady" Daga can ɓangaren Dady dake zaune a motarsa ya ce, "Yauwa barka dai, kana gidan ne?" "A'a Dady yanzun dai zan tafi gidan." "To kayi sauri mu haɗu a can gidan dan yanzun zamu kama hanaya." "To Dady gani nan zuwa." Bayan Dady ya kashe kiran ne ya ya ja motar suka bar gidan. Bayan Muhdeen ya gama waya da Dady ne ya nufi ɗakin Sumayya, domin yayi mata sai da safe tunda ba gidan zai kwana ba, tura ƙofar yayi tare da yin sallama. Kwance take akan gado tayi ruf da ciki, goga fuskarta tayi a jikin filon, tashi zaune tayi tare da ƙaƙalo murmushin yaƙe, ta ce, "Wa'alaika salam" Kallo ɗaya yayi mata ya gane tasha kuka, ƙara sawa yayi jikin gadon ya zauna tare da kiran sunanta "Sumayya" Kallonsa tayi yadda yasha kyau sai annuri yake fitarwa, take taji wani tuƙuƙuƙin bakin ciki da ya taso mata, zuciyarta sai tafarfasa take sunkuyar da kanta tayi ƙasa tayi dan bata don yaga halin da take ciki, magana ya soma yi "Kinga dan Allah ki..." Kafin ya kai ƙarshen zancensa ne ta ɗaga masa hannu alamar dakatarwa, ta kasa magana ƙofar fita kawai ta nuna masa alamar ya fice, mamaki yake kamar ba ita ce ta nuna masa rashin damuwarta game da zancen ba, amma yau gashi yana magana ta kasa jure sauraronsa sai korarsa take,hannu yakai zai taɓa ta sai ta ja da baya ta haɗa hannayenta biyu alamar riƙon sannan ta nuna masa ƙofar fita, hakan yasa ya fita tare da mata sai da safe duk da yasan na amsawa zata yi ba. Bayan ya shiga mota ya tayar mai gadi ya wangale masa gate ya fice, kai tsaye ya nufi hanyar gidansa, yana driving yana tunanin halin Sumayya bayan ta nuna masa ta sauya ba komai, amma yanzun yaga alamar ba abunda ya canza a tattare da ita, amma ko ma dai mene ne da sannu zai gano komai." Sumayya kam Muhdeen na fita ta saki kuka mai sauti, pillows dake kan gadon ta kwashe ta dinga jifa da su a ƙasa, bedsheet ma ta yaye shi tayi jifa da shi, idanunta ya sauka akan babban hoton da ke manne a bango ita da Muhdeen suna dariya, tashi tayi ta ciro photon tayi jifa da shi ya tarwatse a ƙasa Haka duk wani abun fashewa da ke ɗakin dangin su kwalabe da gilashi sai da ta tarwatsa su ta kwanta a saman katifar tana rera kuka. Kasancewar gidan Muhdeen baida nisa da sabon gidansa, hakan yasa ya riga su Dady isa gidan, ko da yayi horn mai gadin ya buɗe masa gate ya shiga kai tsaye cikin gidan ya nufa, shugarsa falon keda wuya sai yaji horn alamaun Dady sun iso, farin cikin da yake ciki ne ya ninku. Bayan Dady yayi parking ne suka gaisa da mai gadin dama yasan Dady shi ya kawo sa gidan, bayan sun gaisa da Dady ne suka gaisa Mummy da Mufida Inteesar dai ba magana. Shiga cikin gidan sukayi Mummy na riƙe da hannun Inteesar, Muhdeen ya buɗe masu ƙofar tare da yi masu iso zuwa cikin falon Dady da Mummy suka zauna kan kujera, yayin da Muhdeen da Inteesar da Sumayya ke zaune a ƙasa, Muhdeen da Inteesar da Mufida suna zaune a ƙasa , cikin girmamawa ya gaida iyayen nasa suka amsa masa kafin Dady ɗaura da cewa "Muhammad" Ɗago kansa yayi ya kalle sa ya ce, "Na'am Dady" "Ga Inteesar nan amana a wajenka, a baya na damƙa maka amnarta a karo na farko, to yanzun ma na damƙa maka amnarta a karo na biyu, amma idan har kayi gangancin maimaita makamancin abuda ka aikata mata a baya to wallahi zaka yi nadamar hakan a tayuwarka, dan sai na baka mamaki, ka riƙe ta tsakani da Allah kuma kayi haƙuri da ita, kasan yarinya ce ƙarama ita dole sai anyi haƙuri, idan tayi maka wani abinda ba dai-dai ba kada ka ce zaka ɗauki zafi a kanta, ka nuna mata kuskuren haka cikin ruwan sanyi, ida. Ka auri mace dole sai kayi haƙiri da ita, dan sabuwar rayuwa ce ta tsinci kanta a ciki, koda yake ba sai na tsaya dogon jawabi ba, a wancan karon nayi maka duk wani abinda yakamata na faɗa maka. Maida dubnsa yayi ha Inteesar ya ce " ke Kum na dawo gare ki, kibi mijinki sau da ƙafa kiyi masa biyayya idan har kina son samun rahamar uban gijinki, duk abinda ya umarce ki kiyi masa, indai har bai saɓawa uban giji ba, ki zama mai haƙuri da da biyayya ga mijinki, nan dai suka dinga mata nasiha mai ratsa zuciya daga bisani suka yi masu sallama suka tafi nan Inteesar ta fara Kuka. Bayan wucewarsu ya dawo rarrashinta ya dinga yi, sannan ya ja hannunta suka shiga ɗakinta a bakin gado ya zaunar da ita sannan ya ce ta jira shi yana zuwa, key na motarsa ya ɗauka ya fice daga gidan. Bayan kamar awa ɗaya ya dawo hannunsa ɗauke da ledoji guda biyu, ɗakinta ya nufa ya ajiye sannan ya nufi kitchen ya ɗauko faranti da wuƙa da cups kaji ne gasassu guda biyu sai fresh milk, kazar ɗaya ya saka a farantin ya tsiyaya fresh milk ɗin a kofi, bakinta ya kai zai bata naman kazar ta kauda kanta ta ce ta ƙoshi lallaɓa ta ya dingayi kamar ƙaramar yarinya kaɗan ta ci Tasha fresh milk ta ce ta ƙoashi , haka ya haƙura ya ƙyale ta, bayan ya tattara kayan ne ya kai kitcheen ya dawo ya umarce ta da tayi wanka ta ɗauki alwala suyi nafilar godiya ga a Allah. Shima ɗakinsa ya nufa dan gabatar don yin wanka, yayin da ta miƙe ta nufi toilet. *Kuyi haƙuri da wannan* *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DON NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😘😍 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89 *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page 7️⃣6️⃣ Shima ɗakinsa ya nufa dan yin wanka,yayin da ta miƙa ta nufi toilet. Bayan ta gama wanka ne ta fito man shafawarta ta ɗauko ta shafa da turare, rigar barcinta ta ɗauko ta saka iyakarta gwiwarta tunda ya ce sallah zasuyi hakan yasa ta ɗauko zanin atamfa ta ɗauka akan rigar ya rufe mata har ƙafarta, turo ƙofar yayi tare da sallama. "Assalamu alaikum" "Wa'alaika salam" Sanye yake da farar jallabiya fara, murmushi ya sakar mata yayin da ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, sallaya ya shimfida masu suka tayar da sallah. Raka'a biyu sukayi tare da addu'oi, bayan sun shafa addu'ar, ya juyo gare ta tare da riƙe goshinta yana karanta karanta addu'ar da manzo ya hore su da suyi, ita dai Inteesar jinsa kawai take ita dai a daren farko tasan ana wannan baiyi ba sai yanzun yake yi kamar yau suka tsinci kansu a matsayin mata da miji, kamar yasan tunanin da takeyi dan haka ta ji muryarsa yana cewa "Bana son kina tuna abunda ya wuce, ki mance da baya mu gina sabuwar rayuwa mai cike da jin daɗi da kwanciyar hankali." Murmushi tayi tare da jinjina kai, haka ya dinga faɗa mata kalamai masu daɗi da ratsa zuciya, ganin tana hamma yayi murmushi tare da cewa "Barci ko?" Kai ta gyaɗa masa alamar eh "To tashi ki kwanta" Ganin bata tashi bane ya ce, "Bari na ɗauke ki na kwantar da ke" Ganin da gaske yake yana shirin miƙewa ne yasa ta tashi da sauri ta haye gadon, dariya yayi tare da cewa "To ki cire hijabin mana" Kai kawai ta girgiza ta kwanta tare da yin addu'ar barci. Tashi yayi ya kwashe sallayar ya ajiye shima ya hau gadon yana cewa "Bari na cire maki hijabin zai takura maki" Bai jira cewarta na ya cire mata hijabin daga kanta, janyo ta yayi a jikinsa yana shaƙar ƙamshin jikinta, sumbatarta yayi a goshi yana shafa kanta, bakinta da nasa ya haɗe wuri guda yafara tsotsan laɓɓanta cikin wani irin salo ya zura harshensa cikin bakinta yana tsotson harshenta cikin hikima da ƙwarewa, zanin da ta ɗaura akan rigar barcinta ya zare tare da aje shi gefe, hannunsa ya zura cikin rigarta ya fara shafar jikinta mai laushi da ƙamshi hankalinsa ne ya fara tashi, zare rigar barcin da ke jikinta yayi ya dinga shafar fatar jikinta tun daga samanta har ƙasanta, Inteesar kuwa tsintar kanta tayi a cikin wata duniya da bata taɓa da bata san da ita ba tun da take a rayuwarta. Dukiyar fulaninta da suke tsaye kyam a cike ya fara tsosa kamar jariri, yana tsotson ɗaya yana murza ɗaya hankalinsa yayi matuƙar tashi. Itama kanta wannan karon ta amshi saƙon da yake aika mata, dan kwata-kwata batayi yinƙurin hana shi ba kamar yadda ta saba yi a baya idan yana wasa da ita, dan taji daɗin abun a wannan karon, dan haka ta kyale shi yayi yadda yake so da ita, haka ya dinga murzar dukiyar fulanin nata idan yasha wannan ya saki ya kama wannan ya murza wannan, sai wasa yake da su san ransa, ɗaya hannun yana wasa da brest ɗinta har zuwa ƙasanta ya koyar da ita wani sabon darasi mai wuyar ɗauka, ya nuna mata tsantsar soyayya da madarar ƙauna mai daɗin ɗanɗano,wanda har sai da Inteesar ta mance a wace duniyar take, sannan ya karanto addu'ar saduwa da iyali sannan ya shige ta. Duk da wannan ba shine karo na farko da ya shige ta ba na biyu kenan, amma duk da haka ta ɗan ji zafi dan a matse take ita kuma ga ƙarin gyaran da Hajiya Bilkisu tayi mata, dan haka ta ɗanji zafi kaɗan. Muhdeen kuwa sai nishi yake fitarwa mai kama da kuka, wanda baisan yana hakan hakan ba, sai godiya da sanya mata albarka yake yi, haɗu da sambatu na daɗi yake yi gaba ɗaya ya rikice akanta. Kusan awa biyu yana abu guda, har sai da ta kasa jurewa ta sakar masa kuka tare da ture sa kafin ya saurara mata, janyo ta yayi ya rungume ya kyam a jikinsa yana rarrashinta tare da sanya mata albarka. Wanka suka je sukayi suka tsarkake jikinta, zuciyarsa fari tas ya samu matarsa tana tare da shi, kuma gashi Allah yayi mata wata baiwa wanda ba kowace mace ke da ita ba, sonta ne da ƙaunarta da yake yi ne ya ƙara ninkuwa a cikin zuciyarta. Sumayya kama yadda taga rana haka taga dare, gaba ɗaya bata rintsa ba, ta koma kamar wata mahaukaciya sai wajen asuba ne ya samu barci yayi awon gaba da ita. Kwance suke a kan gado yayi mata filo da faffaɗar ƙirjinsa, jin ƙarfe haɗu na asuba ya farka daga barci, a hankali ya janye ta daga jikinsa gudun kar ta farka, toilet ya shiga yayi wanka tare da ɗauro alwala yazo yayi sallar nafila raka'a biyu, zama yayi tare da addu'oi yana miƙa godiyarsa ga Allah da ya mallaka masa Inteesar a matsayin mata, ya kuma yi addu'ar Allah ya basu zaman lafiya ya bashi ikon yin adalci a tsakanin matansa. Jin ankira sallah ne yasa ya ƙarasa jikin gadon, zan yayi ya rasa yadda zai tayar da ita, iska ya hura mata a kunne a hankali ta buɗe idanunta, ta sauke shi a kansa, murmushi ya sakar mata tare da cewa "Ki tashi kiyi sallah, lokaci yayi." Kai ta gyaɗa masa alamar to, fita yayi zuwa Masallaci ita kuma ta nufi toilet Dan gabatar da alwala, bayan ta fito ne ta zura doguwar riga ta material sanna ya saka hijabi ta tayar da sallah. Misalin karfe takwas na safe ne Jumy da Shila suka zo gidan, tura ƙofar falon sukayi suka ji ta a datse, zagayawa suka zuwa ƙofar kitcheen ya baya, sukayi sa'a kuwa a buɗe take, turawa sukayi tare da sallama, shiri ba kowa dan haka suka nufi ɗakin Sumaayya kai tsaye inda shila ta ce "Idan kuma muka shiga muka tarar da mijinta fa?" Jumy ce tayi tsaki ya ce, "Ai sai kiyi tunda baki yarda da zance na ba, na faɗa Maki ta ce jiya zai tare da Inteesar a sabon gidansa, na tabbata yana can gidan." Tura ƙofar sukayi tare da yin sallama, turus suka yi ganin ɗakin kaca-kaca yasa suka san abinda ya faru, Jumy ta ce, "Nayi tunani haka shiyasa na matsa sai munzo da safen nan, kallonta sukayi ko da ganin yanayin barcin kasan cewa bata shiryawa yinsa bane ya sace ta. Basu kula ta ba nan suka dinga gyara mata ɗakin, ita ko bata san me yake faruwa ba. Ɓangaren Inteesar kuwa tana idar da sallar asuba kuwa sai tayi addu'ar da zatayi ta haye saman gadon dan wani irin barci take ji tana cikin barcinta taji an rungume ya ta baya, buɗe ido tayi tare da yin narai-narai da idanun kamar zata yi kuka, dariya ta bashi ya ce, "Kwantar da hankalinki ba abunda zanyi maki muyi barci ko?" Kai ta gyaɗa masa alamar eh, kwanciya yayi tare da matse ta tsam a jikinsa, kamar kar wani zai ƙwace masa ita, a haka barci ya ɗauke su. Bayan su Jumy sun kammala gyara mata ɗakin ne ta farka, da mamaki ne ya kamata ya yadda suka shigo Shila e ta ce, "Dama nasan za'a rina, tunda aka ce wai amaryarki sun satanta da miji, nasan juya zasu tare a sabon gidansu nasan hakan ne zata kasance a gare ki, mai hali ai baya fasa halinsa, amma wannan hanyar da kika ɗauki ba mai ɓulkewa bace, ki kwantar da hankali kiyi amfani da shawarar da muka baki, domin hakan shine mafita a gare ki." Nan dai suka cigaba da bata shawarwari sannan suka shiga kitchen dan yin abun da zasuyi breakfast da shi Ɓangaren Inteesar da Muhdeen kuwa sai ƙarfe goma suka farka daga barci da suke yi, ganin time ya tafi yasa Inteesar shirin saukowa daga gadon, riƙe ta yayi tare da cewa "Lafiya saurin meye haka?" Cikin sanyin muryarta ta ce, "Zan je kitcheen ne na haɗa maka breakfast" Murmushi yayi tare da cewa "Kada ki damu Mummy ta aiko muna da breakfast, yanzun kiyi wanka kizo muje muyi breakfast ko?" Kai kawai ta jinjina tare da saukowa daga kan gadon ta nufi hanyar toilet, jin muryarsa yayi tayi yana cewa "Ko nazo muyi wankar tare ne?" Kai kawai ta girgiza dan ita har ga Allah kunyarsa take yi, shima yasan da hakan ba zata amince ba , tana shiga ya nufi bedroom d'insa don yin wanka. Bayan ta fito ta shirya cikin riga da siket na atamafa ne da ya karɓi jikinta, simple makeup tayi tana ƙoƙarin fitowa ne shi kuma yana shiga, rungumarta yayi tare da zagayowa da hannunsa a ƙugunta ya jata zuwa dinning area, zama sukayi suna fuskantar juna shi da kansa yayi serving ɗibta yana cewa "Kuna barci Mummy ta aiko Direba ya kawo muna breakfast, tasan zan gajiyar dake ne shiyasa ta taimako da abinci." Sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya, shi kuma yana mata dariya. Bayan sun gama breakfast ɗin ne shi da kansa ya kwashi kayan zuwa kitcheen, tana ƙoƙarin shigowa kitchen ɗin ne shi kuma zai fito ya ce, "Ina zaki je?" Cikin sanyin muryarta ta ce, "Zan wanke-wanke ne" "Zo muje ciki bar wanke-wanken nan tukunna." Ɗaukar ta yayi cak sai bedroom ɗinsa, a tsakiyar gadon ya dire ta, shima ya haura saman gadon, ganin take-takensa ne yasa ta buɗe baki zata yi magana, amma kafin tayi magana sai yayi saurin haɗe bakinsu waje ɗaya, ya fara tsotsa haka ya dinga rikita ta da zafafan salon wasanninsa nasu tsayawa a ƙwaƙwalwa. Cikin hikima da dabara ya raba ta da kayan jikinta, shima ya cire kayansa suka lula duniyar ma'aurata, suna tsaka da mu'amalarsu Inteesar ta ji ana knocking ƙofa, amma shi baiji ba sai sambatu da sanya albarka yake mata, sam baya cikin hayyacinsa ya gama ruɗewa, shiyasa baiji ana knocking ba, yadda Inteesar ta ji knocking d'in da alama ba ƙofar falo ake knocking ba, ƙofar bedroom ɗin da suke ciki ne. Girgiza da take tana cewa "Yaya ana ƙwanƙwasa ƙofa" Sai da tayi magana sau huɗu tana girgiza shi kafin ya dawo hayyacinsa, ya gane me take cewa, Cikin sarƙewar murya ya ce, "Koma waye ya jira mu, idan bazai iya ba ya tafi." Cigaba yayi da abinda yake yi yayin da aka cigaba da buga ƙofar ba kakkautwa, ganin haka yasa Inteesar ta tilasta masa ya sauka, jallabiya ya saka ya ce, "Bari na duba ko waye." Ya nufi ƙofar ɗakin yana magana cikin sarƙewar murya ya ce "Wai waye haka ne?" Yana buɗe ƙofar idanunsa ya sauka akan Sumayya da ke tsaye itama shi take kallo, idanunsa sunyi jajir Cikin mamaki yake kallonta tare da furta "Kece?" *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love You oll😍😘 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story &, writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izina ba. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣7️⃣ Yana buɗe ƙofar idanunsa ya sauka akan Sumayya dake tsaye, itama shi take kallo, idanunsa sunyi jajir Cikin mamaki yake kallonta tare da furta "Kece?" Taune laɓɓanta na ƙasa yayi cikin jin takaici ta ce "Eh ni ɗin ce dai" Haɗe fuska yayi tare da cewa "To me kika zo yi da sassafe nan" "Oh ji wata tambaya yau, ni da gidan mijina ban isa in shiga lokacin da nake so ko naga dama ba?" "Na riga da na raba maku gida ga naki can, ita kuma ga nata nan kowa ya zauna gidansa." Taɓa baki tayi tare da cewa "Ni kuma na ce ban yarda a raba muna gida ba, dan haka ko ka maida ta can ko kuma ni na tattara kayana na dawo nan" "Baki isa ba" Murmushi tayi tare da cewa "Alright, ba abunda ya kawo Ni kenan ba yunwa nake ji banyi breakfast ba, shine nazo nan naci abinci" Wani irin kallo ya watsa mata tare da cewa "Da can ina kike cin abincin nan gidan ne?" "Takeaway nake sawa akawo mani, kuma yanzun tunda gata ta dawo ai ba buƙatar haka" "Saboda ita baiwarki ce ko? to bari kiki bautar da tayi miki a baya yanzun baki isa tayi mako kwatankwacin makamancinsa ba, dan haka ki fita tun kafin kiga ɓacin raina." "Ganin ɓaci ran da ke kan fuskarsa yasa tayi murmushi tare da kwantar da murya ta ce, "Lah abun ai baikai haka ba, kasan cewa ni ba iya girki nayi ba, kuma ka ce kai baka son abincin waje sai dai a girka maka, kuma ka ce baka son 'yar aiki, shine nayi wani tunani mai zai hana na dinga zuwa wajen ƙanwata tunda ya iya sai ta koya mani, nan da sati ɗaya dai nasan na iya, shine kawai ba wani abu ba." Kallonta yayi yana nazatarta, dan dai Sumayya ba abin yarda bane a wajensa, kuma da ace da gaskiya ta daɗi haka shi kansa zaiji daɗin hakan dan har ga Allah baya don cin abincin waje, kuma yanzun dole idan ya gama kwanakin da zaiyi a nan dole gidan Sumayya zai koma, kenan abincin waje zai ci, kuma idan har ta iya zaifi don haka, amma ta yaya zata ce dole sai Inteesar? " Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Ga wajajen koyon girki nan da yawa me yasa dole sai nan?" Murmushi tayi tare da cewa "Naga dukanmu matanka ne, kuma idan kanmu ya kasance a haɗe komai namu ɗaya zaka fi kowa farin cikin hakan." Shiru yayi tare da cewa "Ki koma gida sai nayi nazari akan maganar da kika zo da ita." Daga nan bai jira cewarta ba ya maida ƙoafar ya rufe. Inteesar duk ta ji maganar da suke yi jikinta yayi sanyi, dan tun ranar da Sumayya tayi yaunƙurin kashe Inteesar ta ke tsoronta, dan bata son abunda zai haɗa su waje ɗaya da ita, tunani ta shiga yi yadda ta dinga ƙuntatawa rayuwarta zaman da sukayi tare da zagin iyayenta da cin mutuncin da take mata, duk da haka tayi yaunƙurin kashe ta ba tare da ta mata laifi ba, sannan yanzun tana maganar wai ya maida ta can ko ita ta dawo, hawaye ne ta ji suna bin fuskarta, bata ankare ba ta ji yada harshensa yana lasar hawayen da ke tsiyaya daga idanunta, cikin salo da dabara mantar da ita ɓacin rai da take ciki har ta mance ya cigaba da fataucinsa. Sumayya dake tsaye har yanzu a jikin ƙofa ne ta dinga jiyo gurnaninsa, da sambatun da yake yi yana ma Inteesar godiya da saka albarka, take taji zuciyarta kamar an wata mata garwashin wuta, idanunta suka fara ganin duhu jiri taji yana neman ɗibarta dan haka ta zuba a wajen tayi dirshan sai hawaye take zubarwa. Duk da dai yana surutu da gurnani ne amma bata jin me yake cewa, ta dai ji yana sawa Inteesar albarka yana mata godiya yana cewa bazai iya rabuwa da ita ba shi kaɗai ta ji sauran maganar bata gane me yake cewa, daƙyar ta tashi ta ƙarasa kan kujera ta zauna, zuciyarta na tafarfasa, tunda take da Muhdeen bai taɓa yi mata kwatankwacin irin wannan samabataun ba, bata taɓa jin yana sa mata albarka lokacin sex ba amma ji yadda ya ruɗe akan ƙaramar yarinya yake ta Suratu kamar mahaukaci, kenan hakan yana nufin shi baya jin daɗinta ne? ko dai yana surutu ita ce bata ji tunda iatama a lokacin bata cikin hayyacinsa?kai ta girgiza alamar cewa baya yi, amma ko ma dai mene ne zata binciko ko yana yi akanta ko baya yi, idan ko ta kasance baya yi to wallahi zata ɗauki mummunar matakin da batayi niyyar ɗauka ba.haka ta zauna tana jiran fitowarsu dan tasan baya wuce awa ɗaya ya gama. "Shiru ta ji awa ɗaya ya wuce basu gama ba, tana duba agogo awa biyu nan ma shiru, hankalinta ya tashi sosai dan tunda take da Muhdeen 50 minutes ko 1 hour then ya gama sex, amma yanzun awa biyu ya ɗauka yana sex shiru bai gama ba, tana zaune har awa uku baƙin ciki dabtakaici duk ya ishe ta, kamar ta tashi tabar gidan amma ba zaiyiwa ba dan idan ta tashi ta tafi shirinta zai wargaje, dan haka ta samu wuri ta zauna. A can cikin ɗakin kuwa sai da Inteesar ta gaji ta saka masa kuka sannan ya ƙyale ta yana rarrashinta, zuciyarsa cike da farin ciki da annashwa wani ƙaunarta ne ya ƙara ninkuwa a cikin zuciyarsa, da kansa ya ɗauke ta ya Kaita banɗaki, sukayi wanka, duk da bata saki jiki ba kunyarsa ne kawai ke dawainiya da ita. Bayan sun gama wanka ne suka fito, gaba ɗaya Inteesar yunwa take ji, a daddare ta saka doguwar riga na atamfa bata ma tsaya wane makeup ba, shi kuma yana ɗauke da towal a ƙugunsa dan ba kayansa a nan ɗakinsa zai je ya saka kaya, ganin yadda take sauri ne yasa ya kalle ta lokacin da ta jona handryer tana busar da suman kanta, nan da nan ta gama ta tufke suman a tsakiyar kanta bayan ta nannaɗesa saboda tsawonsa, bata ma tsaya ɗaura ɗankwali ba siririn mayafinta ta ɗauka ta yafa gana ƙoƙarin fita ne ya ce, "Saurin me ye wannan?" "Kitcheen zan tafi" "Me zakiyi a kitchen?" "Ƙarfe ɗaya ya kusa fa kuma ni yunwa nake ji" Da mamaki ya kalle ta dan yasan bata samu da cin abinci ba, murmushi yayi tare da cewa "Kece da jin yunwa har kina sauri haka? ko da yake abincin da kika ci na zazzagar da shi ko?" Ya ƙarasa maganar cikin tsokana, yayinda ita kuma kunyarsa ne ya sake dirar mata, dan hakan ta nufi ƙofar fita a guje ta buɗe ƙofar tana dariya, yayin da shima yabi bayanta. Tana zuwa tsakiyar falon tayi turus, sakamakon ganin Sumayya zaune ta zuba mata ido, shima tsayawa yayi yana kallon Sumayya da mamaki a fuskarsa. Murmushin ƙarfin hali Sumayya tayi tare da cewa "Kun fito?" Muhdeen dai bai bi ta kanta ba ya nufi ɗakinsa, yayin da Sumayya ta cigaba da cewa "Ance ka girmama baƙonka, amma ni naga kamar bakiyi farin ciki da zuwa na ba ko? shikenan bari na tashi na bar maki gidanki." Miƙewa tasaye tayi tare da kallon Inteesar, har ta kai baƙin ƙofa Inteesar tayi saurin binta ta riƙe hannunta tare da cewa "Kiyi haƙuri Aunty Sumayya ba haka bane, mamaki ne ya hana ni magana" "Mamakin me kike yi?" Ta ƙarasa maganar da sakarwa Inteesar murmushi, itama martani murmushi ta maida mata ta janyo hannunta ta ce, "Dawo ki zauna Aunty Sumayya nan ma ai gidanki na" Zama sukayi ta kalli Sumayya da ke murmushi ta ce, "Ina wuni Aunty Sumayya?" "Lafiya lau ƙanwata ya kike ya amarci?" Sunkuyar da kanta kawai tayi tana murmushi, yayinda Sumayya ke wata mata harara ji take kamar ta shaƙeta ta mutu. Ganin Inteesar ta ɗago da fuskarta ne yasa ta yi saurin sakin murmushi "Kunga ki saki jikinki da Ni kinji? ki ɗauke ni a matsayin ya a gare ki, ki mance da abubuwan da na maki a baya, nayi nadama insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba, ko makamancinsa ma na ɗauke ki tamkar ƙanwa ta da muke uwa ɗaya uba ɗaya da ita, haka nake so nima ki ɗauke ni, kinsan ba iya girki ba kuma mijinki baya son na masu aiki, saboda haka na yanke shawarar idan ba zaki damu ba zan dinga zuwa kina koya mani girki na tsawo sati ɗaya." Kallonta Inteesar tayi tana tunani kafin ta ce "Bakomai" Kin amincewa shawara ta?" Kai ta girgiza alamar amincewa ta ce "Na amince bari na sanar da yaya." Daga nan ta miƙe ta nufi ɗakinsa, ya gama shirinsa zai fita, murmushi ya sakar mata tare da cewa "Nazo na tayaki girkin ne?" Ya ƙarasa maganar yana murmushi "Ka barshi kawai ba aikinka bane, zamu shiga kitchen yanzun tare da Aunty Sumayya." Take fara'ar fysakarsa ya ɗauke ya ce, "Kinga kada daɗin bakinta ya ruɗe ki, Sumayya tafi ƙarfin ki ta wuce sanin tunaninki, nasan wace ce ita haka nan awai ba zata zo gidan nan da sunan ki koya mata girki ba, domin yadda masana da jinkai hakan zai zama kamar ƙasƙanci ne a wurinta, matuƙar ta ajiye jin kanta da taƙamarta yazo gare ki da sunan koyon wani abu to ki tabbata da biyu tayi hakan, akwai dalili da kuma wani buri da take da shi akanki, ki bita a sannu dan ta fiki wayo da dabara kina da saurin yarda da mutane hakan zai bata damar samun abinda take so daga gare ki cikin sauƙi, shiyasa kika ji na ce ban amince da ita ba, ni kaina zanso zaman lafiya da haɗin kai da junanku, amma tunda na ce maki a'a akwai abunda na hango." Murmushi tayi tare da cewa "Ta nuna mani nadamarta naga sauyi a tattare da ita, bazan shige mata ba sai dai bazan iya ƙin amincewa da alfarmar da tazo nema daga gare ni ba." Jinjina kai yayi tare da cewa "Shikenan Allah ya ya kaɗe fitina a tsakanin ku ya haɗa kanku." Murmushi tayi tare da cewa "Ameen ya rabbil izzati" Tare suka fito daga bedroom ɗin, suka tarar da Sumayya a falo, zama yayi a akan kujerar da ke kusa da Sumayya, ido ya zuba mata dan haka kawai bai yarda ba abinda ta zo da shi ba , dan yasan halinta sarai, ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta ce, "Wai Baby naga kamar baka so zuwa na gidan nan ba, ko baka son kaga kan matanka ya haɗu ne?" Murmushi yayi wanda iya fatan bakinsa ya tsaya "Idan akwai wanda zai so haɗin kanku da zaman lafiyarku a baya na yake, domin zaman lafiyarku shine kwanciyar hanakali na." "To me yasa naga yanayinka ya canza?" .Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Sumayya Inteesar ƙaramar yarinya ce a gare ki, dan Allah ki riƙe ta amana da zuciya ɗaya, bata da matsala idan kika kama girmaniki nasan zata maki biyayya, ke kanaki shaida ce akan biyayyar ta ɗan zaman da kuka yi da ita, ki ɗauke ta ƙanwa ba kishiya ba ki riƙe girmaniki a matsayinki na babba." Juyawa yayi ya kalli Inteesar tare da cewa "Inteesar Sumayya ba tsararki bace ta girme ki a shekaru da kuma gidan aure, ki bata girmanta a matsayinta na babba a gare ki, bana son raini ya shiga tsakaninki da ita, kuyi haƙuri da junanku banda ɗaukar zuga, duk wacce ta batawa 'yar uwarta rai kata ce zatayi faɗa da ita, ta same ta ta sanar da ita abinda tayi mata wanda bata ji daɗinsa ba su fahimci juna, Allah ya haɗa kanku." Amsawa sukayi da Ameen, daga nan ya tashi ya nufi masallaci, Inteesar ta kalli Sumayya tare da cewa "Aunty duk da rana tayi bari na dafa mana ko Taliya ce ko?" Murmushi tayi tare da bin bayanta tana cewa "Muje muyi tare na fara koya tun yanzun ." Tare suka shiga kitchen ɗin Inteesar na mata bayanin yadda ake komai, tana kuma yi a akace yadda zata gane, wani abun ma da kanta zata karɓa ta zuba, a haka har suka girka jallop ɗin taliya da yaji kayan lambu da busashshen kifi. Jin an tada sallah ne ya sa Inteesar cewa "Aunty bari naje nayi sallah ko?" Kai Sumayya ta jinjina tana murmushi ta ce, "To sai kin fito nima na je nayi" Inteesar ce ya fita daga kitchen ɗin ta nufi ɗalibta dan yin sallah,tana fita Sumayya ta bita da harara tare da yin tsuki. Bayan Inteesar ta shiga ɗauki ne ta faɗa toilet bayan ta ɗan gyara zanin gadon da ya yamutshe, ta kauda komai. Alwala ta ɗauro yazo ta gabatar da sallar azahar, bayan ta idar tare da yin addu'a sannan ta bar salllayar a wajen tare da ajiye hijabin akan sallayar dan Sumayya idan tazo tayi amfani da shi, dan ba da hijab tazo gidan ba. Bayan ta fita ne ta samu Sumayya a falo tana zaune a kujera. "Aunty na idar kije kiyi sallar sai muci abinci ko?" Jinjina kai tayi "Okay to" Miƙewa tayi ta nufi ɗakin Inteesar dan yin sallah, dan da ba don da Inteesar ta ce tayi sallar ba ba yi zata yi ba, sai da ta tsaya ta na ƙarewa ɗakin kallo yadda aka tsara shi, gwanin sha'awa, komai tsaf a mahallin da ya dace, taɓa baki tayi ta nufi toilet ɗin. Muhdeen ne ya turo ƙofar falo ya shigo tare da sallama, Inteesar dake zaune a falo ya amsa masa sallamar, ƙarasowa yayi tare da zama gefenta ya riƙon hannunta cikin nasa . "Ina Auntynki take? "Ta shiga tayi sallah, bari ta fito sai muci abinci." Yana rufe baki sai ga Sumayya ta fito daga ɗakin Inteesar, idanunta ne suka sauka akan hannun Muhdeen dake sarƙe a cikin na Inteesar, kauda kanta tayi gefe, Inteesar tayi ƙoƙarin zame nata amma sai ya sake riƙe hannun da kyau kallon sa tayi ya ɗaga mata gira ɗaya kauda kanta gefe tayi tare da miƙewa tsaye ta ce, "Muje Aunty dame ke nake jira." Jin hakan yasa Sumayya tayi saurin nufar dinning table dan ba zata iya sake kallonsu a haka ba, a haka suka nufi dinning room ɗin sai a lokacin da zai zauna ne ya saki hannunta. Ta dauki plate da zuba ma Muhdeen ta ajiye masa, sannan ta zubawa Sumayya itama ta tsiyaya masu lemo da ruwa ta ajiye masu, sannan ta zuba nata itama, kallonta yayi tare da cewa "Duk kiran yunwar da kike yi iya abincin da zaki ci kenan?" Dariya tayi ta ce, "Yaya wannan fa ya ishe ni." Nan suka fara cin abincin a tare har suka kammala, Inteesar ta tattara kayan Muhdeen yayi falo kan kujera ya zauna, Sumayya ma ta biyo shi kasancewar a doguwar kujera ya zauna hakan yasa itama ta zauna kusa da shi tare da kwantawa ta ɗaura kanta a saman cinyarsa, wasa ta fara yi da yatsun hannunsa, shima bai hana ta ba, har Inteesar ta kammala wanke kwanonin ta dawo falo ta same su a haka, bata nuna ɓacin rai ko damuwa ba ta zauna kujerar da ke gafensu. Sai yamma bayan sun kammala cin abincin dare ne sannan Sumayya ta shirya don zuwa gida lokacin da zasu raka ta wajen mota ta kalli Inteesar ta ce, "To ƙanwata sai kuma gobe idan na dawo ko? ango ma da zai mana kwana biyu biyu to na ƙara maku kwanaki biyar, ku ɗauka yau ne aka kawo ki gidan mijinki a matsayin amarya." Farin ciki a waje. Muhdeen ba'a magana dan har ya kasa ɓoyuwa, godiya yayi wa Suamya dan ya ji daɗin hakan da tayi, bayan ta ja motarta mai gadi ya buɗe mata gate ne ta bar gidan. Haka rayuwa tayi ta tafiya Inteesar tana samun kulawa sosai daga wajen Muhdeen, kuma kullun Sumayya tana zuwa gidan dan koyon girki, dan yanzun ba girki kawai take koya mata ba, har da gyaran gado da ɗauki da duk wasu aikace-aikace na cikin gida. Idan Muhdeen ya kwanaki biyu a gidan Inteesar haka zaiyi kawanki biyu a gidan Sumayya, yana ƙoƙarin kwatanta adalci a tsakaninsu, sai dai matsayin Inteesar na musamman ne a cikin zuciyarsa, idan tana aiki a asibita da zaran ya samu sarari zai kira ta suyi ta fira da juna, ko suyi Video call tsabar kwanciyar hankali da ta samu da kula daga gare shi har ta ɗanyi ƙiba tayi kyau sosai. Gidan iyayen Inteesar kuwa haka Muhdeen ya sa a rushe shi, a maida masu shi zubin na zamani, dama Umma tana shirin zuwa Gombe jikin mahaifiyarta ya tashi bata da lafiya, tana son zuwa ta gaida mahaifiyarta a Gombe, koda Inteesar ta ji labarin abinda za'ayiwa iyayenta tayi farin ciki sosai da jin wannan zancen taso ta bi Ummanta suje Gombe tare amma Muhdeen ya gama ya dai ɗaukar mata alƙawarin idan ya samu dama zasu je tare shima ya gaida danganta, a haka ya haƙura ana gobe Ummanta zatayi tafiyar ne daddare suka je ita da Muhdeen, inda ya kaiwa Umma sha tara na arziki, ya ɗaukar mata shatan mota da zai Kaita har Gombe tare da bata kudi masu yawa, sanan sukayi mata sallama, inda ta dinga saka masu albarka tare da godiya, Abba ma da ya shigo ya tarar da abinda Muhdeen yayi ya masa godiya sosai da tarin addu'oi. Bayan tafiyar Umman Inteesar da kwana biyu, Inteesar tayi waya da Ummanta, inda Ummanta ke sanar da ita jikin kakar ta Inteesar yayi tsanani, Inteesar hankalin ta tashi matuƙa har ta samu Muhdeen da zancen zata je kila su gana kafin ta rasu, amma duk da haka bai barta ba, Sumayya ce itama ta saka baki ta matsa masa, wanda hakan yasa ya bata izinin zuwa Gombe ya haɗa ta da direba da zai Kaita ya dawo da ita, inda Inteesar ta ƙara ganin girman Sumayya a idanunta, mutuncinta ya ƙaru sosai a idanun Inteesar. Ana gobe zata tafi ta je tayi sallama da su Gwaggo da su Mummy, haka nan kawai jikin Muhdeen ya bashi cewar akwai wani mummunan abunda zai faru da Inteesar, dan shi dama yakan ji a jikinsa indai wani mummunan al'amari zai faru da na kusa da shi jikinsa na basa, dan haka yaso hana amma Inteesar da Sumayya suka matsa dan haka yayi ta addu'a. *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI* 09065327995 Love you oll😘😍 Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *_Albishir! Albishir!! Albishir!!!_* *_Jama'ar Annabi inayi muku Albishir da cewa nakawo muku wannan shahararre Kuma ingantaccen gida, gidan da suka darje suka rairaye suke kawo Muku kayiyyaki masu dankaren kyau da Kuma inganci abisa farashi dai dai da Aljihun ku_* *_Hajiyata, kanwata, Aunty na, kinaso kisamu kaya Wadanda ba kamarasu? Kayanda idan kika shirya kika fito kizama abin kallo a wurin Yan uwanki?_* *_dama wadanda zasu ganki ahanya?_* *_sbd yadda Zaki fita daban da saura?_* *_Kinaso Idan kikayi shiri arinka tambayanki a ina kika saye wannan kayan?_* *_Zakije gidan biki ko gidan suna Amma kina tunanin kayan dazaki saka saboda kiyi fita ta Alfarma ta kece raini?_* ```ARZUQLANA GALLERY``` *_sunkawo muku duk Wani abu Wanda zakuna bukata kama daga:_* ```Laces Atampha Shadda Abayas Materials Gyale Takalma Jaka Kayan Kitchen Bangles n jewelries``` *And many more* ```GIDAN KYAU, GIDAN QUALITY, GIDAN SAUKI, GIDAN KWALISA, DA ADO``` *_Wani abin sedai kunbiyomu zaku Gani da idanunku_* *_sunayin kasuwancinsu bisa gaskia da Amana, ba cuta ba cutarwa_* *_koda bakida kudin Siya Muna gayyatarki dan ki tallata kema kisamu naki_* *_Yar uwa kasance a gidan, da abaki labari gwanda ki bayar_* https://chat.whatsapp.com/FRJAnQZXm0t7rAroZWlMnQ *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shiga ta kowace siga ba tare da izina ba. Page7️⃣8️⃣ Ana gobe zata tafi ta je tayi sallama da su Gwaggo da su Mummy, haka kawai jikin Muhdeen ya bashi akwai wani mummunan abunda zai faru da Inteesar, dan shi dama yakan ki a jikinsa indai wani mummunan al'amari zai faru da na kusa da shi, dan haka yaso hana amma Inteesar da Sumayya suka matsa dan haka yayi ta addu'a. Ranar da Inteesar zata tafi dama ba ita ce da girki ba Sumayya ce, da n hakan Muhdeen a gidan. Sumayya ya kwana, da asuba ya shirya ya tafi masallaci, bayan ya dawo ne yake sanar da Sumayya zaije suyi sallama da Inteesar, itama ta dage sai ta bishi, ba yadda zaiyi dan haka ya barta suka fito tare da zumar zuwa gidan Inteesar, Motarsa ya ɗauki ya tada suka tafi. A ƙofar gidan ne ya tarar da direban da zai kai Inteesar Gombe, kasancewa Ishaq Direban Muhdeen baida lafiya yasa aka samo masa wanan, abokin Ishaq ne sosai, bayan sun gama gaisawa da Direban kai tsaye ya nufi cikin gidan bayan yayi horn mai gadi ya buɗe masa, bayan yayi parkinga ne suka fito Sumayya na biye da shi a baya. Da sallama suka shiga falon zaune ta ke ta haɗa hannayenta biyu tayi tagumi, da alama tayi nisa a cikin tunanin da take ne, tsayawa yayi ya rungume hannunsa a ƙirjinsa, Sumayya ce ta ƙarasa ta zauna gefen Inteesar tare da cire hannun da tayi tagumi ta cire tare da zuba mata ido, sai a lokacin Inteesar ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula, dubanta ta fara kaiwa ga Sumayya da ta cire mata hannu, kafin ta maida dubanta ga Muhdeen, cikin sanyin muryarta bayan ta durƙusa cikin girmamawa ya ce "Ina kwana yaya? "Lafiya lau, kin tashi lafiya ya shirye shirye? "Alhamdulillah" Ta amsa masa, sannan ta maida dubanta ga Sumayya ta ce, "Aunty Ina kwana?" "Lafiya lau Inteesar ya shirin tafiya?" Ganin yadda yanayinta ne yasa Muhdeen cewa "Lafiya naga kamar akwai wani abinda ke damunki ko?" Kai ta girgiza "Ba abunda ya same ni, kawai dai ina jin jiki na wani iri, tafiyar ma ta fitar mani a rai, amma ba yadda zanyi dole na je, tunda suna can suna saka ran zuwa na ." "Kinga nima fa ba son tafiyar nan nake ba." "A 'a baby kada la kashe mata gwiwa, ka dai mata addu'ar dawowa lafiya." Jinjina kai yayi tare da jan hannun Inteesar, inda yake cewa "Zo mu shiga ciki muyi sallama da kyau ko?" Sumayya ce ta bishi da kallo tare da cewa "Baby ana jiranta a waje ga direban can yana jiran fiowarta," Murmushi yayi tare da cewa "Kada ki damu da yanzun zamu sallami juna." Daga nan bai sake magana na kuma bai daki hannun Inteesar ba. Suna shiga ɗakin ya murzawa ƙoafar key ya rufe ta ciki. Sumayya kuwa yana shiga da Inteesar tabi bayansa a hankali ta maƙale a jikin ƙofar dan ta dinga sauraron abunda zai faɗa ma Inteesar. Shi kuma bayan ya zare key ɗin kawai sai ya zauna kan kujera, tare da janyo ta ya ɗauka ta samun cinyarsa ya fara magana "Gaskiya zan ji kewarki sosai, dan kwanaki bakwai da zakiyi a can ji nake kamar shekaru bakwai zakiyi, dan rashinki a rayuwata babbar giɓi ce, amma ni naga kamar ke baki damu da ni ba ko? " Murmushi tayi tare da cewa "Nima fa zanyi kewarka sosai, dan dai kawai na fika dauriya ne." "Kinfini dauriya fa kika ce?" Kai ta gaɗa masa alamar eh, ta buɗe baki da niyyar zatayi magana kenan sai ya saka bakinsa cikin nata tare da cafke harshenta yana tsosa, cikin wani irin salo da ƙwarewa, ya ɗauki kusan mintuna uku a haka kafin Inteesar ta zare bakinta daga nasa ta fara magana. "Yaya kaga fa lokaci na tafiya ga driver yana jira na, kuma ga Aunty Sumayya tana jiranmu a falo." Kinga please ki barni na magance ƙishin ruwar da nayi kwana biyu ina fama da shi, dan bazan iya haƙirin sati ɗaya nan gaba ba dan sai ƙishin ruwan ya kashe ni." Cikin rashin gane zancensa ta ce, "Wani irin ƙishin ruwa ne haka yaya?" "Kece ruwan ai, kwanaki biyun da nayi bana kwana tare da ke ba ƙaramin ƙoƙarin nayi ba, dan haka yanzun ma bazan barku ki tafi ki barni cikin wannan halin ba." Kafin tayi magana ta ji ya fara aika mata zazzafar wasanninsa nasu tsayawa a rai. Sumbatarta yake yi ta ko ina zif ɗin rigarta ta zuge, cikin dabara ya raba ta da kayan jikinta, tun tana noƙewa har ta fara maida masa da martani, gaba ɗaya ya fita hayyacinsa sai wasa yake da breast ɗinta nasu ɗauke masa hankali, yana wasa da ɗayan breast ɗin yana tsotson ɗaya tare da wasa da niple ɗinta, gaba ɗaya ya fara fita hayyacinsa sai gurnani ya ke, Sumayya da ke laɓe jikin ƙofa sai cika ta ke tana batsewa, ko me ta tuna sai kuma tayi murmushi tare da cewa "Kuyi duk abinda zakuyi daga yau ne ai shikenan sai kuma yaushe?" Dariya tayi wanda har da sautin sai mutum ya ji, dan suma basa cikin hayyacinsu ne da sunji dariyar muguntar da take yi. Lokacin da Muhdeen ya karanto addu'ar saduwa da iyali ya shiga Inteesar ne yasa Sumayya yin shiru da dariyar muguntar da keyi sakamakon jin yayi wani ihu mai cike da gurnani da sambatu a guje tabar wajen tare da saka hannunta tana toshe kunnenta gabar wajen cikin ƙunar rai. Sai d Muhdeen ya ɗauki awa ɗaya kafin ya bar Inteesar, dan ma nan yaga ana jiranta ne Tare sukayi wanka kowa ya canza kayan jikinsa inda ya janyo mata kayanya ita ma ta janyo sauran kayan suka fito. Amma ba Sumayya a falo ba labarinta ta fita dan kada ta cigaba da jin abuda zaisa zuciyarta ta buga . A harabar gidan suka same ta tana jirnasu, Inteesar ta ji kunyar Sumayya, yadda ga shiga ɗaki da miji fiye da wa ɗaya, sannan yanzun ta fito ta sauya kaya, a zuciyarta ta ce, "Koda yake b zata gane ba tunda na saka hijabi har ƙasa" Kallon Sumayya tayi tare da cewa "Aunty kiyi haƙuri mun..." Bata kai ƙarshen zancen ta ba Suamayya ta ce "Haba meye m bada haƙiri?" "Ba sallama kuke yi ba kada ki damu yau ne kawai ai" Ta ƙarasa maganar fuskarta ɗauke da murmushi. Bayan sun fita da kayan ne direba yada a boot, Inteesar ta shiga baya ta zauna, nan suka dinga yiwa juna ɗaga hannu inda Muhdeen ya ƙara jaddada mata ta riƙe wayarta a hannunta saboda zai dinga yawan kiranta. Har suka ɓacewa juna bata daina ɗaga masu hannu. Bayan sun tafi ne Muhdeen ya sanar da Sumayya zai shiga ciki ya rufe gidan, yana shiga gidan ta ɗauki wayarta a handbag ɗin ta ta lalubo wani number ya danna masa kira, bayan ya ɗaya ta ce, "Hello Amaguwa kana jina? wani aiki zan baka, amma ka sani bana son akasi a yayin da na bawa mutum aiki..." Ganin Muhdeen ya fito ne yasa ta ce "Okay sai anjima zan kira ki" Daga nan ta katse kiran ta shiga mota suka bar wajen. Da yammaci misalin ƙarfe huɗe da rabi ne motoci guda goma sha ɗaya ne, sai dai ɗayar motar da ke tsakiya ta fita daban da sauran motocin, biyar ne a gaban wannan haɗaɗaiyar motar yayin da wasu biyar ɗin ke binta a baya, da alamar motoci biyar na gaba da biyar da suke binsa a baya rakiya suka yi masa, zaune yake a bayan motar yayin da direban motar ke tuƙi sai wani bafade a gefensa yayin da wannan matashin saurayin mai tsananin kyawu da kwarjini da haiba yake zaune a bayan mitar, sanye yake da farar shadda mai tsadar gaske, sai baƙar alkyabba da ya ɗaura a saman farar shaddar ga rawani da ya zauna a kansa kamar dan shi akayi shi, kallo ɗaya zakiyi masa kinsan cewa jinin sarauta ne gaba da baya, idanunsa a lumshe kamar mai barci amma a zahiri b barci yake ba sanyin A.C kawai ke ratsa shi, jin wannnan bafaden da ke gefen direba yayi salati ne yasa shi saurin buɗe idanunsa , yayin da wannan bafaden ya ce, "Ranka ya daɗe wata mace ce gata can kwance a jikin ƙaton dutsen can, kuma gata ita kaɗai ne a cikin wannan jejin, yarima ne ya maida sunansa inda wannan bafaden ke nunawa, hango ta yayi kwance kamar hawa, juyawa yayi ya hango wata mota daga can tsallake da je ci da wuta, sauran motocin duk suka tsaya suna kallon me yarima zaiyi, a hankali ya fito tare da basu umarnin suje su duba ko akwai mutum a motar ne. Cikin hanzari mutanen huɗu suka tsallaka dan cika umarnin yarima. Koda suka ƙara da motar duk ta ƙone ba kowa a ciki, yarima ya ƙara kusa da inda take kwance kanta sai jini je fita, da kansa ya ɗauke ta ya saka ta a bayan mota ya zauna gefenta, kowa ya shiga mota suka ja suka bar jejin *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Saura 2 pages book 1 ya ƙare book 2 paid book ne ki biya ₦300 kacal don cigaba da karantawa, zaki turo kuɗin ta wannan account ɗin* 2242538358 Zainab Abdullahi U B A sai a turo shaidar biya ta wannan number 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & share*INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *_Albishir! Albishir!! Albishir!!!_* *_Jama'ar Annabi inayi muku Albishir da cewa nakawo muku wannan shahararre Kuma ingantaccen gida, gidan da suka darje suka rairaye suke kawo Muku kayiyyaki masu dankaren kyau da Kuma inganci abisa farashi dai dai da Aljihun ku_* *_Hajiyata, kanwata, Aunty na, kinaso kisamu kaya Wadanda ba kamarasu? Kayanda idan kika shirya kika fito kizama abin kallo a wurin Yan uwanki?_* *_dama wadanda zasu ganki ahanya?_* *_sbd yadda Zaki fita daban da saura?_* *_Kinaso Idan kikayi shiri arinka tambayanki a ina kika saye wannan kayan?_* *_Zakije gidan biki ko gidan suna Amma kina tunanin kayan dazaki saka saboda kiyi fita ta Alfarma ta kece raini?_* ```ARZUQLANA GALLERY``` *_sunkawo muku duk Wani abu Wanda zakuna bukata kama daga:_* ```Laces Atampha Shadda Abayas Materials Gyale Takalma Jaka Kayan Kitchen Bangles n jewelries``` *And many more* ```GIDAN KYAU, GIDAN QUALITY, GIDAN SAUKI, GIDAN KWALISA, DA ADO``` *_Wani abin sedai kunbiyomu zaku Gani da idanunku_* *_sunayin kasuwancinsu bisa gaskia da Amana, ba cuta ba cutarwa_* *_koda bakida kudin Siya Muna gayyatarki dan ki tallata kema kisamu naki_* *_Yar uwa kasance a gidan, da abaki labari gwanda ki bayar_* https://chat.whatsapp.com/FRJAnQZXm0t7rAroZWlMnQ *GARGA'DI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izina ba. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣9️⃣ Koda suka ƙarasa ga motar duk ta ƙone, yarima ya ƙarasa kusa da inda take kwance, kanta sai jini ke fita da kansa ya ɗauke ta ya saka ta a bayan mota, ya zauna gefenta kowa ya shiga mota suka ja suka bar jejin. Muhdeen hankalinsa yakai ƙololuwar tashi, gabansa sai faɗuwa take yi sannan ga numberta da na direba duk basu shiga, ya kira Ummanta ko sun isa nan ma basu ganta ba, dan ko su Ummanta hankalinta ya tashi musamman da taga dare yayi shiru, ba Inteesar ba alamarsu. Gaba ɗaya hankalinsa na kanta gata kwance kamar gawa, kallon direbansa yayi tare da cewa "Idan mun shiga garin Gombe ka tsaya,dan bazai yiwu mu tafi zuwa Yola da ita a haka ba, muje mu kaita asibitin abokina Dr Abdulkarim." Jinjina kai direban yayi tare da cewa "Insha Allahu an gama ranka ya daɗe." Wayarsa ce tayi ruri ya kamar bazai kalli wayar ba, a hankali ya buɗe idanunsa da ya zuba akan wayar, ganin me kirar wayar ne ya daga tare da cewa "Assalamu alaikum" Cikin kunnensa ya ji saukar muryar mai kiran wayar . "Wa'alaika salam yarima kuna ina ne?" "Ranka ya daɗe muna gab da shiga cikin garin Gombe, amma ba zamu ƙarasowa yau Yola a daren nan ba." "Yarima lafiya? Ko akwai wata matsala ce?" "Allha ya taimake ka muna tafiya akan hanyarmu ta dawowa ne muka tsinci wata yarinya kwance a gefen titi, kuma sai ga wata mota daga can gefe tana ci da wuta, mundai ɗauko yarinyar yanzun da mun shiga cikin garin Gombe zamu kaita asibitin abokina da ke cikin garin." "To shikenan Allah ya tsare ku ya bata lafiya." "Ameen ya rabbil izzati" Daga nan ya katse kiran tare da juyawa ya zubawa Inteesar idanu, tsawon mintuna biyu yana kallonta, kafin ya ɗauke idanunsa. Lokacin da Muhdeen ya sanar da su Gwaggo zancen ba'a ga su Inteesar ba, hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, musamman Mufida sai kuka ta ke mksmar ance Inteesar ɗin ta rasu, Dady ne yayi ta ƙoƙarin kwantar masu da hankali. Sumayya kuwa wayarta ta kashe tunda ta tafi gidan Bashir, bayan sun gama abunda zasuyi ne sunyi wanka ta saka kaya tare da kallonsa ta ce, "Dare yayi mani anan yakamata na yafi." Kallonta ya yayi tare da cewa "To sai yaushe? ko kuma ni zan zo?" Da sauke ya kalle shi tare da sake baki tana cewa "Kazo ina? dan Allah rufa nani asiri, ko lokacin da kake zuwa kana kwana ai ranakun ba nice da girki ba, yana gidan Inteesar ne shine nake barinka kazo ka maye gurbinsa, banda wahalar da nake sha wajen shigar da kai." Kasancewar motarta mai baƙin gilashi ne sai ta ɗauko Bashir a bayan motar, haka zata shigo da shi cikin gidan, amma ba zatayi parking a filin da aka tana da dan ajiye motoci ba, sai ta ƙara da har kan hanyar da zata sada ta da ƙofar shiga falon, wanda ba mai ganinsu a cikin ma'auikatan gidan. "Bashir ne ya kalle tare da cewa to yanzun yau Inteesar ce da giki yau to ya zamuyi ne?" Murmushi tayi tare da cewa "Ai girkin Inteesar ya riga da ya ƙare." Kallonta yayi cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa. "Ban gane Inteesar gikinta ya ƙare ba, bayan ya gama kwanakin girkinki yau yakamata a ce ce ita ce da girki. Dariya tayi tare da cewa "Da sannu zaka gane." Ta ƙsrsasa maganar yana mai ɗaulko wayarta tare da kunnawa, dan dama wayar a kashe take, tana kunnawa sai ga kiran Muhdeen ya shigo wayar, da sauri ta ɗaga wayar tare da cewa "Hello babyna ya kake?" Daga can ɓangaren cikin yanayin damuwa da yake ciki ya ce, "Tun ɗazaun kika ce mani zaki je dubiya ƙawarki ba lafiya, amma shine har yanzun baki dawo ba kina can?" "Dan Allah kayi haƙuri na same ta tana ɗan jin jiki ne, amma gani nan dawowa." "To me yasa wayarki bata bata shiga? tun yaushe nake kiran wayarki a kashe?" "Am sorry bansan cewa wayar a kashe take ba, sai yanzun na kula na kunna ta." "Tunda ƙanwarki ta tafi kunyi magana da ita kuwa?" "Ni hankalina a tashe yake ne saboda yanayin jikin nata, sai yanzun ta samu barci shine ma na samu nutsuwa har zan dawo gida, hope dai dai ta isa lafiya dan nasan yanzun ta daɗe a Gombe." Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Wallahi Ina cikin tashin hankali tun ɗazu, domin tunda mukayi waya da ita ta ce mani suna Bauchi, basu isa Gombe ba daga nan ban sake samun wayarta ba, ko na kira bata shiga nayi tunanin matsalar network ne, to har yanzun dai shiru, daga ita har direban ba wanda numbersa ya samu shiga." "Inalillahi wa inna ilaihir raji'un, yanzun meye abunyi?na shiga uku." "Ki kwantar da hankalinki na kira Ummanta ma shiru har yanzun basu isa ba, suma kansu hankalinsu ya tashi." "Oh my God, Allah dai yasa ba wani abun bane ya same su." "Ameen ya rabbi, dole zuwa Gombe ya kama ni." "Nima idan har ban bika nasan halin da take ciki ba ai ba zan taɓa samun nutsuwa a rayuwa ta ba." "A'a bai kamata ki bini ba ki.." Kafin yakai ƙarshen zancensa ne ta katse shi da cewa "Gani nan zuwa yanzun nan." Daga nan ta katse kiran zama tayi akan gadon da ƙarfi tare da kwashewa da dariyar mugunta, ganin yadda take dariya ne yasa Bashir mata kallon mamaki, dan ya fahimci me ke faruwa, dan haka cikin ɓacin rai ne yayi saurin miƙewa tare da ƙarasowa gare ta, cikin ɓacin ya damƙo wuyarta, tare da ɗan riƙewa da ƙarfi wanda hakan yasa dole dariyarta ɗaukewa ƙoƙarin ƙwayar kanta tayi amma ina duk yadda tayi ƙoƙarin janye hannunsa daga riƙon da yayi mata ta kasa, magana ya fara yi cikin kausasa murya yana cewa "Ke! kina da imani kuwa me kika aikatawa Inteesar ne? me ta tare maki a rayuwar nan? tana zaune dake da zuciya ɗaya kuma tsarkakkiyar zuciyarta yayin da kika zama mai fuska biyu kina nuna kamar ba ruwansu yayinda kike da wata mummunar manufa a cikin zuciyarki, innocent people kike ƙoƙarin ganin bayansu Sumayya wai why?" Karye wuya tayi tare da gantsara masa cizo a hannunsa wanda hakan yasa ya saki wuyanta ba shiri, tari ta dinga yi sannan ta kalle shi ta ce, "Akan me zaka hukunta ni ta wannan hanyar?" "Kin cancanci ayi maki fiye da haka, dan kin fini rashin imani wallahi bazan taɓa iya aikata abinda kika aikata ba" Murmushi tayi tare da cewa "Okay ko kana da wata shaida ko hujja akan cewa ni ce na aikata haka? Idan kana da shi ka kawo hujjarka na cewa nice na aikata?" Sau nawa kina zuwa nan kina sanar da ni cewa zaki kashe Inteesar? sai da kika zauna kikayi nazari hanyar da zaki kashe tare da an zarge ki ba shiyasa kika shiga jikinta kika nuna kinyi nadama ashe kura ce ke lulluɓe da fatar akuya, kuma sai na je na samu Muhdeen na sanar da shi cewa kina da sa hannu a ɓatar matarsa." Dariya ta dinga yi kamar mahaukaciya sannan ta tsagaita ta ce, "Ai ban taɓa sanin cewa ƙwaƙwalwar kifi ne da kai ba sai yau, to je ka sanar da shi, kaga idan ya tambaye ka ya akayi ka sani sai ka faɗa masa cewa kaine kake maye gurbinsa a wuri na idan baya nan, ta hakan yasa kasan shiri na, saboda kana taɓa ta, dan idan ba haka ba ya akayi kasan shiri na? a matsayinka kawai na abokinsa." Daga nan bata sake cewa komai ba, sai ta tattara kayanya ta zuba a jaka tare da ratayawa a kafaɗarta, sannan ta matso dab da shi ta sumbace shi a gefen kumatunta tayi murmushi ta fice tana ɗaga masa hannu alamar bye. Lokacin da suka ƙarasa asibitin Dr Abdulkarim sun tarar da shi yana jiransa, kasancewar ya sanar da shi, ajere motocin suka suka shigo harabar asibitin, nan da nan aka shiga da ita. Abdulkarim ne ya mikawa yarima hannu suka gaisa tare da cewa "Da ba don lalura ba ba zaka zo nan mu gaisa ba ko?" Cikin yanayin damuwa Yarima yayi magana kamar baya so "Pls a fara duba ta cikin gaggawa zamuyi magana daga baya." Murmushi Abdulkarim yayi tare da cewa "Kada ka damu zamuyi bakin ƙoƙarin mu, to yanzun yakamata ka nemi masu ki ka huta, bari nasa akaika gida na ko?" "Kada ka damu zamu tafi hotel ne." "A'a Yarima ka bari kawai ga gida na ga asibita na, duk da cewar kai da jama'arka ne akwai isassun ɗakunan da zai ɗauke su, yadda muke da kai ai bazan bari hakan ta faru ba, tunda har kun shigo nan." Daga nan Yarima ya kira ɗaya daga cikin masu tsaronsa, inda yayi masa nuni da hannu alamar ya ƙaraso, ƙarasowa yayi tare da zubewa ƙasa a gabansa ya ce, "Allah ya taimake" Ka sanar da sauran jama'a zava kaisu masauki, zuwa gobe insha Allah sai mu kama hanya, kafin nan yakamta ayi order na abincin da zaku ci, ki ina Galadima ya ke?" "Ranka ya daɗe ya matsa can gefe yana amsa waya ne." Daga can gefe kuwa Galadima ne yake waya yana cewa "Tuba nake yi ranki ya daɗe, kinsan cewa Yariman ne akwai shi da taurin rai, duk wani tarkon da muka ɗana masa sai ya tsallake, bansan wane irin yaro bane shi, yadda kika san uwarsa haka yake, amma ina mai tabbatar maki da cewa wannan karon idan Yarima ya tsallake tarkonmu to wanda zamu ɗana masa idan mun koma bazai taɓa iya tsallake shi ba,yanzun haka muna Gombe ya tsaya ceton rayuwar wata ya..." Bai kai ƙarshen zancensa ba ganin wani bafade ya tunkaro shi, dan haka yayi saurin cewa "Ranki ya daɗi zan kashe wayar ga wani nan zuwa." Daga nan ya katse kiran tare da kallon mai zuwan ya ce, "Lafiya?" "Yarima ne ya bada umurnin cewa anan zamu kwana" Da mamaki Galadima ya kalle shi tare da cewa "To akan meye ya daɗi haka" "Idan dai har kintata dai -dai to akan wannan yarinyar ce." "Oh Allah to meye haɗinsa da ita?ya taimake ta ya kawo ta asibiti to me ya rage? tunda ba mu muka zama sanadin Hatsarinta ba sai mu kyale ta ba." Cikin takaici ya ce, "Wuce mu tafi" A tare suka ƙarasa yayin da Dr Abdulkarim ya bar wajen, Galadima ya kalli Yarima tare da cewa "Allah ya taimake ka ga ni" "Zamu kwana anan kafin zuwa gobe idan Allah ya kaimu, yanzun za'a kai kowa masauki ga wanda zaiyi jagora nan." Ya ƙarasa maganar yana kallon wanda Dr Abdulkarim ya turo dan yi masu Jagora, daga nan bai sake magana ba ya saka kai ya bi bayan Dr Abdulkarim Sauran masu tsaronsa suka bi bayansa, Galadima ma ya bi bayansa, wanda ganin hakan yasa ya dakata da tafiyarsa, suma bayansa suka tsaya kallonsu yayi tare da cewa "Bana buƙatar kowa a tare da ni" Galadima ne ya ce, "Allah ya taimake ka amma ai..." Kallon da yayiwa Galadima ne yasa shi yin shiru, dan haka Yarima ya ce, "Ga lokacin sallar sallar magrib tayi ga masallaci nan ana kiran sallah, idan kowa yayi Sallah zai iya zuwa masaukinsa ya kwanta bayan ya ci abinci, bana buƙatar kowa a tare da ni. Daga nan shima Masallacin ya nufa, ganin lokacin sallah yayi. Koda aka idar da sallar magrib bai bar masallacin ba sai da akayi sallar isha'i sannan ya bar masallacin. Kai tsaye office ɗin Dr Abdulkarim ya nufa, amma bayanan, dan haka sai ya zauna saman sofa da ke cikin office ɗin yana jiran shigiwarsa. Da misalin karfe tara na dare ne Dr Abdulkarim ya shigo office ɗin fuskarsa ɗauke da damuwa, ganin Yarima zaune a office ɗin ya ce, "Allah ya taimaki Prince." Zuba masa ido yayi tare da cewa "Ya jikinta?" Girgiza kai yayi tare da cewa "Ya kake da yarinyar ne?" "Tsintar yarinyar nayi a gefen hanya, maybe accident tayi." "Kana nufin baka san daga inda take ba?" Ataƙaice ya ce, "Bansan komai game da ita ba." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Da sauri y kalle shi cikin fargaba tare da cewa "Don't tell me that she's dead." Girgiza kai yayi tare da cewa "She is alive, amma gaskiya tayi loosing memory nata." A firgice ya kalle Dr Abdulkarim "What?" "Sai dai kayi haƙuri amma gaskiya ta rasa tunaninta." "Kana nufin ka ce mani ta mance wace ce ita?" Dr Abdulkarim ya gyaɗa masa kai alamar eh "Kana nufin ta mance sunanta iyayenta komai da ya shafi rayuwarta ta mance ?ba abunda ta sani yanzun?" Jinjina Dr Abdulkarim yayi tare da cewa "Kaina kasan wannan ba sai na fada maka ba, duk abinda ya faru da ita a baya ta manta sai dai ta gina sabuwar rayuwa, a halin yanzun ƙwaƙwalwarta ta koma kamar na jaririn da aka haifa yau." Dafe goshinsa yayi cikin damuwa ya ce, "To ko mu fitar da ita ƙasar waje ne ko Allah zaisa a dace?" Murmushi yayi tare da cewa "Ko ina zaka kaita abunda zasu faɗa kenan." "To ba wata shawa da kake ganin idan anyi amfani da ita za'a dace?" "Gaskiya babu sai dai idan Allah yasa ta ziyarci wuraren da ta taɓa sani a rayuwarta, ko kuma ta haɗu da mutanen da ta sansu a baya kafin faruwar hakan to tayiwu tunaninta ya dawo." "Ya salam, toyanzun ya zanyi da ita?' "Shawarar da zan baka shine ka Kaita gidan marayu" Girgiza kai Yarima yayi tare da cewa "Hakan ba mai yiwuwa bane, zan tafi da ita can." "Ina zaka tafi da ita? "Yola" Daga nan bai sake magana ba Kishingiɗa yayi tare da cewa "Allahu ya bata lafiya." Yadda Muhdeen yaga rana haka yaga dare gaba ɗaya bai iya rintsawa ba, dan ko gidan Sumayya bai je ba, a gidan Inteesar ya kwana gaba ɗaya hankalinsa ya tashi ba alamar barci ma zai iya ɗaukarsa. Ɓangaren Gwaggo da Mummy hankainsu ya tashi sosai, suna ta addu'ar Allah yasa duk inda suke suna lafiya Allah ya bayyana ta Karfe huɗu na asuba Muhdeen ya shiga toilet ya watsa ruwa tare da yin alwala yazo yayi nafila da addu'ar duk inda suke Allah yasa suna lafiya ya kareshi tare da bayyanar da su. Ƙarfe shida na safe Muhdeen da Jabeer suka shirya dan zuwa Gombe, Jabeer ne yayi driving ɗin su bayan sunyi sallama da su Mummy ne suka kama hanya, Muhdeen bai ma sanar da Sumayya zancen tafiyar ba, dan ya ji tana cewa zata bishi kuma ba zaiso tafiya da ita a wannan yanayin da suke ciki ba, dan haka bai sanar da ita ba daga shi sai Jabeer suka kama hanyar zuwa Gombe. *Saura 1 page book 1 ya ƙare, idan har kina buƙatar cigaba da karanta littafin Inteesar to zaki biya ₦300 kacal ta wannan account ɗin* *2242538358 Zainab Abdullahi U B A nagode* *INTEESAR* Story & writing by✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *_Albishir! Albishir!! Albishir!!!_* *_Jama'ar Annabi inayi muku Albishir da cewa nakawo muku wannan shahararre Kuma ingantaccen gida, gidan da suka darje suka rairaye suke kawo Muku kayiyyaki masu dankaren kyau da Kuma inganci abisa farashi dai dai da Aljihun ku_* *_Hajiyata, kanwata, Aunty na, kinaso kisamu kaya Wadanda ba kamarasu? Kayanda idan kika shirya kika fito kizama abin kallo a wurin Yan uwanki?_* *_dama wadanda zasu ganki ahanya?_* *_sbd yadda Zaki fita daban da saura?_* *_Kinaso Idan kikayi shiri arinka tambayanki a ina kika saye wannan kayan?_* *_Zakije gidan biki ko gidan suna Amma kina tunanin kayan dazaki saka saboda kiyi fita ta Alfarma ta kece raini?_* ```ARZUQLANA GALLERY``` *_sunkawo muku duk Wani abu Wanda zakuna bukata kama daga:_* ```Laces Atampha Shadda Abayas Materials Gyale Takalma Jaka Kayan Kitchen Bangles n jewelries``` *And many more* ```GIDAN KYAU, GIDAN QUALITY, GIDAN SAUKI, GIDAN KWALISA, DA ADO``` *_Wani abin sedai kunbiyomu zaku Gani da idanunku_* *_sunayin kasuwancinsu bisa gaskia da Amana, ba cuta ba cutarwa_* *_koda bakida kudin Siya Muna gayyatarki dan ki tallata kema kisamu naki_* *_Yar uwa kasance a gidan, da abaki labari gwanda ki bayar_* https://chat.whatsapp.com/FRJAnQZXm0t7rAroZWlMnQ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a giji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page8️⃣0️⃣ Jabeer me yayi driving nasu bayan sunyi sallama da su Mummy da Gwaggo, Muhdeen bai sanar da Sumayya zancen tafiyar ba dan ya ji tana cewa zata bishi, kuma bazai so tafiya da ita ba a wannan yanayin da suke ciki, dan haka bai sanar da ita ba daga shi sai Jabeer suka kama hanyar zuwa Gombe. Bayan ya dawo daga masallaci yana kishingiɗe a ɗakin Dr Abdulkarim, yayin da Dr Abdulkarim yake daga gefensa. Wayarsa ce ta fara ruri, ko kallon wayar baiyi ba ballantana yayi niyyar ɗauka, har ta katse bai ɗaga ba, kallonsa Dr Abdulkarim yayi tare da cewa "Wayar ma sai kaga dama kake ɗagawa?" Bai ce da Abdulkarim komai ba kuma bai ɗaga wayar, har sai da aka kira wayar sau uku sannan ya ɗaga. Gimbiya Anisa ce ta kira shi video call, kara wayar yayi a gabansa ya ajiye ta, tare da zubawa wayar idanunsa. Zaune take ta ɗaura ƙafa daya kan ɗaya, yana sanye da alkyabba irin ta 'ya'yan sarakai, masu mata hidima na zagaye da ita, yayinda wata take ƙara gyara mata hullar alkyabbar, ɗaya wata tana durƙushe a gabanta tana bata fruit a baki, tana taunawa cikin yana kamar bata son ci. Murmushi ta sakarwa Yarima Areef tare da cewa "Barka da safiya my prince, fatan ka tashi lafiya." "Alhamdulillah" "Yarimana tun jiya nake jiran dawowarka na ji shiru, sai kuma nake jin labari wajen Fulani cewa ka tsaya ne saboda wata yarinya, gaskiya ba girmanka bane wannan, duk da nasan cewa kai mutum ne mai taimako da tausayi, amma hakan bai dace ba kana ɗan sarki guda ka tare a asibiti kawai dan ka tsinci yarinya a gefen titi." "Ni waye da nafi ƙarfin taimako, ba wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yafi shi tsoronsa, shi Allah baya duba zuwa ga surar jikinmu da dukiyarmu sai dai yana duba ne zuwa ga zuciyoyinmu da ayyukanmu." Shiru kawai tayi ya zuba ma pink lips ɗinsa da ke matukar burge ta ido, inda ya cigaba da cewa "Ina nan tare da ita, har sai ta farka sannan zamu taho da ita." A zabure ta miƙe tsaye tare da cewa "Ku tafi ina." "Masarautarmu kina da matsala da hakan ne?" "Komawa tayi ta zauna, ba tare da ta sake magana ba, ta ce, "Yanzun yaushe zaka dawo na ganka?" "Maybe gobe ko jibi insha Allahu." Datsar tufa tayi tare da cewa "Gaskiya bazan iya haƙurin zuwa jibi ban ganka ba, idan har ba zaka samu dawowa yau ko gobe gaskiya sai dai kaga na zo nan." "Kizo ina wai?" "Gombe" "Koda wasa kada kiyi Wannan gangancin, ba hali na sanyi tafiya na kwana biyu ki ce zaki biyo NI?" Dariya tayi tare da cewa "Ai a hakan ma nayi ƙoƙarin n daure dan naga ba aure mukayi ba, amma idan mukayi aure su inda zaka je ƙafata ƙafarka, Allah dai ya kaimu ranar aurenmu. Ta ƙarasa magana tana murmushi. Kallonta yayi tare da cewa "Bissalam" Daga nan ya katse wayar, Dr Abdulkarim ne ya kalle shi tare da cewa "Gimbiya Anisa na masifar sonka sosai, gashi kun dace da juna dukanku jinin sarauta ne gaba da baya, Allah ya kaimu ranar aurenku" "Ka daina tunanin cewa zan auri Gimbiya Anisa, dan gaskiya bata da ce da irin macen da make da burin aure ba, tana da gadara ta taƙama, tana da sin mulki da sarauta, Ni kuma duk Waɗan nan abubuwa basu dame ni ba, kullun maganarta zata zama matar sarki, wai nine sarkin gobe, yayin da Ni kuma bana son sarautar nan." Jinjina kai Abdulkarim yayi tare da cewa "Sarauta kam ko kana so ko baka so dole ka karɓe shi, dan mahaifinsa bashi da wani burin da ya wuce yaga ka gaji kujerar sarauyarsa. domin kai ne mafi mafi soyuwa a gare shi." Daga nan ya mike tare da cewa "Pls muje mu duba yarinyar nan mana." "kada ka damu nurse zasu yi mata duk abinda ya dace." Daga nan ya miƙa shima Dr Abdulkarim ɗin tashi yayi yabi bayansa Masu tsaron Yarima Areef ne suka take masa baya, dakata yayi na tare da ya kalle su na ya daga masu hannu dakatarwa., sanin me yake nufi me yasa suka koma inda suka tsaya, dan dama sun saba da wannan idan suka fita yakan dakatar da su,amma idan a masarautarsu ne bai hana su dan ya laura mai Martaba baya son yana dakatar da su. Koda suka iso Gombe basu sha wahalar gane gidan ba, dan haka, autar su Umma ne yayi masu jagora, har cikin gidan Da sallama suka shiga gidan, inda suka gaida da kowa na gidan tare da tambayarsu ya mai jiki, aka masu jagora har ɗakin kakan Inteesar suka gaishe ta tare da yi mata ya jiki. Bayan an kawo masu abinci da ruwa ne Jabeer ne kawai ya iya shan ruwan, amma Muhdeen ko kallon ruwan baiyi ba burinsa kawai yaga Inteesar. Koda suka shiga ɗakin da aka kwantar da ita, har lokacin tana kwance idanunta a lumshe, ƙarasawa Yarima yayi kusa da gadon tare da zuba masa ido. A hankali ta buɗe idanunta ta sauke su akan na Yarima, kallon juna suka dingayi na na lokaci, kafin ta cire ƙwayar idanunta daga nasa, ta maida su ga sauran nursess guda uku da ke ɗakin. Yarima ya kalle ta tare da cewa "Sannu ya jikinki?" Shiru kawai tayi tare da zuba masa ido, ya ƙara cefa mata wata tambaya ya ce "Ya jikinki? Nan ma shiru tayi ba tare da ta ce komai ba, Kallon Dr Abdulkarim Yarima yayi tare da cewa "Wuni ɗaya da kwana ɗaya tana kwance ba abunda ta ci, yakamata a nemo mata Abinci. Murmushi Abdulkarim yayi tare da cewa "Kada ka damu an je kawo mata." Kallonta Yarima yayi tare da cewa "Zaki iya tashi ki shiga toilet ki wanke baki?" Kallonsa tayi kamar mai kiyon magana ta ce, "Toilet baki?" Dr Abdulkarim ya kalli daya daga cikin nursess ɗin ya ce, Ta raka ta ta nuna mata yadda zatayi, dan haka ta ja hannun Inteesar suka nufi toilet, sabon brush ta ɗauko tasa tooth paste ta miƙawa Inteesar, sannan ya sake saka wani a wani brush ɗin, ta ƙara da jikin tap tana riƙe da hannun Inteesar, ta dinga nunawa Inteesar yadda ake yi ta hanyar yiwa kanta, haka kuwa akayi duk yadda tayi sai Inteesar ta yi itama. Har suka kammala suka fito, dai-dai lokcin da aka kawo mata kofin tea, aka bata ta shanye tass. A ranar nan sai da Muhdeen da Inteesar suka dinga zagaye Gombe, suka kai report police station aka tabbatar masu akwai motar da tayi accident jiya amm mutanen da ke cikin motar sun ƙone kurkusa hankali tashe Muhdeen ya ce sune amma baya tunanin sune, kuma aka sana cikin tamabaya ne ko akwai wadanda sukayi accident, jagorancin autar su Umma da Mallam Habu, nan dai suka gano motar da Inteesar yayi hatsari, hankalin Muhdeen yayi matuƙar tashi ganin motarsa da Inteesar suka tafi da ita ta koma, ya tsaya yayi mutuwar tsaye sai jin muryar Mallam Habu na cewa "Innalillahi wa'inna ilaihir, duk sun ƙone ƙurmus." Ji sukayi tim Muhdeen ya daɗi wajen sumamme, a guje Jabeer ya ƙarasa gare shi tare da ɗago shi yana kiran sunansa. Autan su Umma ne ya kalli Malam Habu ya ce, "Haba mallam Habu ba haka ake magana ba, ta yaya zaka ce sun ƙone kurmus? ba wanda ya mutu a cikin motar nan, dan banga alamar ƙashin mutum a cikin motar ba." Jabeer ya ɗauko robar ruwa a mota ya yayyafawa Muhdeen a karo na uku ya farfaɗo, koda ya farfaɗo kuka ya ke yana cewa "Kada ka ce mani Inteesar ta rasu, dan idan ta tafi nima zan bita ne." Autar su Umma ne ya dafa kafad'arsa tare da cewa "Ka kwantar da hanklinka, ba alamar mutum ya ƙone a cikin motar nan, dan haka muje asibitoci mu duba ko Allah zaisa an samu waɗanda suka ceci rayuwarsu, suka kaisu asibitin, daƙyar suka lallaɓa shi ya shiga mota inda suka dinga zagaye asibitoci sun tambayar ko an kawo wasu mace da namiji da sukayi accident, ko ina sukayi tamabaya za'a ce masu ba nan bane. Yarima ne ya tara jama'arsa inda yake sanar da su cewa da zaran an idar da sallar la'asar zasu kama hanya komawa Yola, dan ya ce daga masallacin zasu tafi. Inteesar kuwa an shirya ta cikin Abaya blue tayi kyau sosai, Yarima ne yasa da Galadima dai Dr Abdulkarim suka cikin ɗakin da take, yayin da Yarima ke hanta da magana yana murmushi, yayin da Galadima kuwa zuciyarsa baƙa sai kallon Yarima yake yana kwafa a cikin zuciyarsa. Haka su Muhdeen suka dinga zagaye asibitoci amma shiru basu da ce ba, inda Jabeer ya kalli Mallam Habu ya ce, "Ba wani asibitin da kuka sani na kuɗi ko na gwamnatin?" "Jinjina kai kawai Mallam Habu yayi tare da cewa "Gaskiya waɗannan kawai na sani." Autar su Umma ne ya ce "Akwai dai wani asibitin kaɗai sanya taga bamu je can ba." Jabeer ya ce wa "Ina ne?" "Autarsu Umma ya ce can ne ta farkon shigowa gari, shine ma yakamta mun fara zuwa, dan yafi kusa da inda maka baro wajen accident ɗin." Kiran sallar la'asar akayi wanda Mallam Babu ya ce "Bari suyi sallar la'asar sai su tafi can Asibitin Dr Abdulkarim ko can aka kai su, da wannan tunanin sukayi sallah suka tafi masallaci dan yin sallar la'asar sai su je asibitin Dr Abdulkarim. Acan ɓangaren Yarima kuwa yada an ajiye komi da zasu tafi da shi a cikin mota, yayin da suke jiran a idar da sallar la'asar suja motocinsu ya ɗaga zuwa Yola. *Shin ya kuke gani Muhdeen zasu ƙara so asibitin nan su haɗu da Inteesar?;idan sun koma da ita ashirin Sumayya ya tonu ya makomarta a wajen Muhdeen? Wani irin hukunci zai ɗauka akanta?shin ina direban da ya ɗauki Inteesar yake? Bashir zai faɗa wa Muhdeen kamar yadda yayi wa Ikirarari? idan kuma Yarima ya tafi da ita Yola ya rayuwarta zata kasance a cikin gidan sarauta?kunsan dai gidan sarauta da makirci waye Yarima Areef wace ce gimbiya Anisa?meye makomar Sumayya*? *Dan cigaba da karanta littafin Inteesar book 2 ki biya kuɗinki naira ɗari uku kacal # 300 ɗan jin ƙarahen labarin, zaki tura kuɗi ki ta wannan account ɗin* 2242538358 *Zainab Abdullahi U B A bank sai ki turo shaidar biya ta wannan lambar 09065327995* *Don neman ƙarin bayani* 09065327995 Love you oll😍😘 Love you oll😍😘