*DAURIN GORO* SHAFI NA DAYA (1) ©️HAFSAT RANO ALKALAMI TV https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo WATTPAD: HafsatRano ********** *MAFARIN KOMAI*. A guje ta fito daga dakin jikin ta cikin shigar kayan ma'aikatan jinya, da sauri duk suka mik'e ganin ta nufo su "Ta sauka Dr!" Suka tambaya a rude kuma a tare "Ina maigidanta?" Ta maida musu ba tare da ta amsa tambayar tasu ba. Matsowa yayi da sauri yace "Gani." "Ok muna so ka saka hannu ne, ba zata iya haihuwa da kanta ba dole sai dai ayi mata aiki." "Innalillahi, aiki kuma Dr?" Ya tambaya a kideme "Shine kadai abinda zamuyi mu ceto rayuwarta data abin cikin ta. Kayi hakuri babu lokaci." "Shikenan, Allah sa ayi a sa'a." Bin bayan ta yayi, suka je ya saka hannu sannan ya dawo wajen sauran ya tsaya yana kaiwa da komawa. Bayan shafe tsawon mintuna arba'in da shigar su ta sake fitowa, wannan karon akwai alamun nasara a tattare da ita. Kafin ta k'arasa garesu sukayi saurin isa, fuskar su dauke da alamun tambaya, hannun ta ta mika alamun abata tukwuici kafin tace "Congratulations Your highness, an yi nasarar ciro muku dan saurayi." Da sauri ya kalle ta kamar be ji me tace ba, gid'a masa kai tayi alamun gamsarwa, maida kallon sa yayi wajen sauran da duk fuskokin su ke cike da farin ciki yace "Alhamdulillah ya ALLAH!" Ya furta da karfi A duniya bashi da wani buri da ya wuce yaga an haifa masa d'a namiji, yau sai gashi Allah ya cika masa burin sa, ba ma shi ba, duk wani makusancin sa yana masa sha'awar haka. Duba da irin tarin dukiyar da Allah ya bashi. Ya hakura ya barwa Allah zabin sa, sai gashi ya bashi a lokacin da beyi zato ko tsammani  ba. A take wajen ya kaure da murna, babu wanda ya tsaya tambayar lafiyar mahaifiyar, tuni kowa ya hau kokarin kiran waya domin sanar da yan'uwa da abokan arziki. THE ONE AND ONLY HEIR To *MARWAN DIKKO* FAMILY IS BORN. A daidai lokacin Inno na kwance a gadon asibitin, babu tazara tsakanin dakin da take da babban dakin da aka ajiye Matar Alhaji Marwan, saboda haka tana jiyo hayaniyar mutane me cike da tsantsar farin ciki, kallon jaririyar dake kwance kusa da ita tayi, zuciyar ta tayi rauni, anya? Anya bata zalunci yarinyar ba kuwa? Kallon gefen ta tayi taga jakar da aka hado mata tare da jaririyar, soyayyar ta da kudi abu ne me girma, babu abinda ba zata iya aikatawa akan su ba, sai dai tana tsoron abinda zai je ya dawo gaba, gashi babu ko digon soyayyar yarinyar a zuciyar ta. Abu daya ta sani shine rayuwar jaririnta, rayuwa me inganci da tsananin gata da zai taso da ita. Idan ta tuna wannan sai ta ji ta samu sauki, sai dai fa tana da kudurin komai daren dadewa sai ta karbo shi. Shigowar su Yalwati da sauran jama'a ne yasa ta ɗan saki ranta, suka shiga daukar jaririyar kowa yana yaba kyawun ta, ita dai Inno jin su kawai take ba tare da ta tanka ba, ganin zasu cigaba da chaja mata kai da hayaniyar su yasa ta rufe idon ta alamun bacci take yi, hakan ya bata damar cigaba da yin tunanin da take akan wannan babban al'amari ne cike da tarin matsaloli a gaba. Hmm **** *AMINATU* Kowacce rayuwa cike take da kalubale, sai dai ni tawa rayuwar da wani salon na sarkakiya tazo min. Rayuwa ta cike take da abubuwa masu yawa. Duk da haka  bazan ce nafi kowa shiga matsin rayuwa ba, sai dai ina da tabbacin ina cikin sahun farko na mutanen da za'a kirasu da wanda rayuwa tayi *Daurin Goro*. _Eh daurin da nake tunanin babu wani mahalukin da zai iya warwareshi, na riga na sare, na barwa Allah ikon sa, ina kuma kyautata zaton zai kawo min yankewar sa kafin barin numfashi na._ Ajiyar zuciya na sauke ina bitar Rayuwa ta daki-daki kamar a lokacin komai yake faruwa. Zaune nake a faffad'an tsakar gidan mu wanda ke dauke da dakuna hudu falle falle sai madafi daga gefe, randunan ruwa manya, daga dayan bangaren rijiya ce babba da makewayi a gefenta, gidan gidane babba daya hada da mutane da yawa sai dai kowa yana ɓangaren sa inda babban zauren gidan shi ya haɗa kowa da kowa. Dakin farko ya kasance dakin Baba, sai dakin Inno daga chan gefe, dakin yara matan gidan ne a kusa dana inno, daga dayan barin dakin Yalwati ne sai dakin samari dake daura da hanyar fita daga shashen namu. Tsintar shinkafa nakeyi tun kafin rana ta fito gashi har ina neman makara ban samu na gama ba, a gurguje nakeyi saboda lokacin makaranta kar na makara, cikin sa'a na kammala nayi saurin zubawa a ruwan waken dake ta tafasa bayan na tabbatar da dahuwar waken saboda gudun abinda zai je yazo. Gyara wutar nayi ganin ta fara zarewa na karasa gaban rijiya domin yin kwaskwarima. Cikin sauri sauri na zura uniform d'ina wanda duk ya tsofe wani wajen ma ya yage na sake fitowa, lokacin har yaran gidan sun fara fitowa ana layin alwala. Haka dabi'ar gidan mu take, tun tasowa ta kawo yanzu hakan bata chanja zani ba, kafin su gama alwalal sai sunyi fada kashi dari. Murmushi kawai nayi na fada dakin Inno dan gaishe ta, a tsaye na ganta tana kokarin daura dankwali tana ganina ta tsaya. "Ina kwana Inno.?" Na durkusa har kasa kamar ko yaushe. Bata amsa ba sai kallon kayan jiki na da tayi kadan kafin tace "Kin gama aikin naki ne da zaki wuce makaranta?" "Eh." Nace ina kallon ta. "Kin zuba ko kin gama?" Iya sani na Karime ke karasa wa idan na zuba, tun da ita ba makarantar take zuwa ba, a darare nace "Na zuba karasawa kawai zatayi a kwashe Inna." Dan bata fuska tayi tana yatsine baki kafin tace "Jeki jira ta karasa yau babu me karasa miki Karime bata jin dadi." "Toh." Kawai nace na mike jiki a sanyaye na koma bakin dakin mu na zauna ina kallon yadda rana ta d'aga sosai alamun na makara, ina nan zaune kowa ya fito aka hau hada-hadar shan koko, ban bi ta kai ba ni dai buri na na ganni a makaranta. Sai bayan wajen rabin awa sannan na kammala na sake dauraye kafata na fice daga gidan da sauri kafin Inno ta ankare ta kawo abinda zai hana ni zuwa duk kuwa da na kan yi mamakin dalilin da yasa inno take bari na zuwa makaranta, bayan haka bama kowa ne a yaran gidan ke samun zuwa makarantar ba. A babban zauren gidan naci karo da Nura, da alama lokacin zaiyi sallah, gaishe shi nayi na wuce ba tare da jiran amsar sa ba. Tafiya ce mai tsawo kafin ka isa makarantar guda daya jallin jal dake a kauyen,  Kamar kullum babu malamin daya shigo har nazo, haka dabi'ar makarantar take, a rana sai ka samu malami daya ne kawai zai shiga duk suna zaune a staff room suna hira, a haka dai muke dan samun abinda muke samu wanda bamu da tabbacin daidai suke koya mana sai dai saboda ba gane wa zamuyi a lokacin ba yasa muke binsu a haka. Musamman ma ni da na taso da son karatu da kuzun zama wani abu a kauyen namu tun bayan ganin da nayi wa jikokin mama Ladi makociyar mu dake zaune a birni, sun kawo mata ziyara, tun daga lokacin na sawa raina zama kamar su, sai dai hakan ba mai yiwuuwa bane duba da irin gidan dana taso. *** Haka rayuwa ta cigaba da garawa, babu abu daya daya sauya na daga al'adun gidan mu, tun da na taso nasan Inno ita ke ciyar da gidan mu ko nace shashen mu, shiyasa ko babanmu baya mata musu, Yalwati kuwa ta zama kamar ba kishiiyar ta ba, dan bayan na gama girkin shinkafa da waken da karime take fita dashi wajajen sha biyun rana, Yalwati ce zata dora alala, sannan tayi dambu da wake shima a sake fita dashi, duk kuma jarin na Inno ne. Inno mutum ce wadda tasan darajar nema, bata taba zama haka nan, yau ta buga nan gobe ta buga chan, bayan sana'ar saida abinci har kiwon akuyoyi take yi da kaji, ga sana'ar abin kad'i dangin su kuka da su kubewa, da sauran abubuwa, sai ya zama ma a kaf kauyen namu babu wanda zai kama kafa da ita Indai a samu ne, shiyasa kaf gidan mu suke shakkar ta, babu wanda ya isa ya daga mata yatsa balle Baba da Yalwati da suka zama kamar yaranta, sai abinda tace musu ake aiwatar wa. ******* Kiran da Karime ke kwala min yasa na ajiye kibiyar hannu na na fito, riko ni tayi da sauri tana haki "Lafiya dai?" Nace ina kallon yanayin ta "Ina fa, dalla kowa yana chan kallon bak'in gidan Bature sun zo ke kina nan kina tsifa." "Dan Allah!" Nace ina fad'ad'a fara'ar fuska ta "Wallahi ana chan duk ana ta kallon su abin sha'awa, na duba ban ganki ba shine nazo kirankii, kinga motar da suka zo acikin ta, har da wata yarinya kamar girman mu, kinga kayan jikin ta kuwa? Wayyo yan gayu sun ji dadi wallah" Ta fada tana rik'e haba, da sauri na koma ciki na dauko dankwali na na daura muka fice da gudu, dukkannin mu sirara ne babu kibar arziki, yadda muke gudun kadai zaka tabbatar da yarintar mu, dudu du a lokacin ba bazan bi shekaru goma sha biyu ba, tsiran mu da karime shekara daya ne saboda haka ba zaka gane wani banbanci me yawa a tsakanin mu ba. Tun kan mu karasa muka ga ana juyowa, hanne ce ta tsaida mu tana dariya "Ina zaku wai, kallo ya barku ai sun koma gida, sai wani jikon kuma." Haushi ne ya kamani, duk zuwan  da zasuyi ban taba samu na gansu ba har su tafi, a take na kudurce a raina wannan karon babu abin da zai hanani ganin su, ko nima na samu na dorar da labarin su. Kullum da safe idan na tashi ta kofar gidan nake bi, haka ma idan na dawo, ban taba samun nasarar ganin ko da cikin gidan bane. Gida ne me girman gaske, hade da babban gidan gona da tsayawa fasalta yanayin girman sa ba mai yiwu wa bane. Duk da karancin shekaru a lokacin da kuma yanayi na duhun kai da kauyanci na gane cewa ba karamin masu kudi bane mamallaka wannan wajen, duk a irin wannan lokacin suka zo gaba d'ayan su su jima sosai, idan suka tafi kuma shikenan sai wani lokacin me tsawo. Gidan Bature kamar yadda mukayi wa gidan da lakabi, sai dai a zahiri ba haka sunan me gidan yake ba, tsari da yanayin gidan da bamu taba ganin kamar sa ba yasa muke kiran gidan da gidan Bature. *** Tun gabanin magriba garin yake ta hadewa, alamun za'a iya samun ruwa a kowanne lokaci, muna daga kofar dakin mu dasu hanne muna hira da karad'i Inno ta kwala min kira, tashi nayi na karasa wajen ta ina kallon hannun ta "Yi maza kije shagon Umaru ki siyo min maganin sauro yanayin garin za'a iya ruwa kowanne lokacin." Karba nayi na juya da niyyar kiran me rakani, dakatar da ni tayi ta hanyar cewa "Ina kuma zaki koma?" "Su karime zan kira su rakani Inna." "Saboda ku tsaya min shiririta a hanya ko? Kin wuce da sauri ko sai na bugo ki?" Da sauri na juya nayi hanyar waje zuciya ta duk babu dadi, duk yawanmu na rasa dalilin da yasa ni kadai Inno take takurawa. Sanda na isa shagon ya riga ya rufe, juyawa nayi ina tunanin yadda zanyi, sama na sake kalla naga yadda hadarin ke sake hadewa nayi saurin daga kafata na kara sauri don zuwa shagon dake chan kasa kadan. Sauri sauri nake nabi ta wani lungu ina kokarin ganin na isa kafin ruwan ya sakko, cikin sa'a na samu shagon yana bude shima yana kokarin rufewa, da sauri na bashi kudin na karbi maganin sauran na juya na kamo hanyar gida a lokacin garin ya kara hadewa. *** *Gidan Bature* Dukkanin su suna zaune a babban falon gidan, kallo suke suna hira gwanin sha'awa, sun kusa a ƙalla su goma maza da mata, Ja'afar ne ya kalli Farouk da tun da aka fara hirar yana rike da waya be tanka musu ba, magana suke akan fitar da zasuyi gobe dan zaga gari. "Ya Farouk." Ya kira sunan shi yana kallon sa "Uhum?" Ya amsa yana yin kasa da wayar dake hannun sa "Maganar fita gobe, U haven't said anything bayan kuma kai kadai ne zakayi convincing Dada ta yadda." Be tanka ba ya sake maida kansa kan wayar kamar ba zai ce komai ba, ganin haka yasa Ja'afar zungurar Amal ya nuna mata bangaren Farouk din, duk ciki tasu tafi zuwa d'aya, babu wani abu da zata nema beyi mata ba sai dai idan bashi dashi din. Tashi tayi tsam ta isa gefen sa ta zauna ta marairaice murya "Dan Allah Yah." Hade hannayenta tayi waje d'aya tana sake kallon sa, hararar Ja'afar yayi kafin ya mike yana ware hannayen sa, duk sun maida hankalin su kansa suna jiran su ji me zai ce, takawa yayi a nutse har gaban window dake makale a falon ya zuge curtains din, sama ya kalla yaga yadda garin yayi, murmushi yayi ya tura hannun sa gaba daya waje yana kama sanyayyiyar iska dake kadawa a hankali. Wajen mintinan biyu yayi a haka kafin ya zaro hannayen nasa ya juyo ciki yana kallon su. "Zan yi magana da Dada, shikenan?" Ihu suka sa gaba daya cikin murna, yana jin su ya juya da sauri ya fada dakin su, ƙatuwar rigar ruwa ya dauka ya saka hade da takalmin sa na ruwa ya fito ya fice daga gidan gaba daya. ZAFAFA BIYAR KAUNAR MU: MAMUH GEE ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL DAURIN GORO:HAFSAT RANO. IGIYAR ZATO: MISS XOXO *_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_* 2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_ saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863* *_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇 *09032345899* _Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 DG Shafi na biyu (2) ****** Lokaci daya iska me karfin gaske ta taso, gaba daya bana ganin gaba na, wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ni, na sani sarai idan har na bari ruwan nan ya taba lafiyar jiki na kashi na ya bushe, ganin da gaske bana ko ganin hanya yasa na makale gefen wani shago na kudundune kaina ina jin matukar tsoro. Ina nan makale yayyafi ya fara sauka a hankali, tsoro na ya dadu, zuciya ta tayi rauni sosai, kamar daga sama naji an dafa kafada ta, cikin tashin hankali na dago kaina,ban samu nasarar ganin fuskar kowaye ba, saboda tsananin hasken torch light din da aka sa aka haske ni. Cikin muryar tsoro na furta "Waye!" Be amsa ba, ba shi kuma da niyyar amsawar, illa sake dalle ni da yayi, take hasken yayi tasiri rage kaso tamanin cikin dari na gani na, baya da ƙurar da ta riga ta cika min idon nawa, da sauri na mike ina kokarin daidai ta zaman riga ta, na fara alamun barin wajen, hannu naji an saka an riko ni, cikin wata iriyar murya mara fasali ya furta "Gidan uban wa zaki? Ai wallahi kinyi kadan tsuntsu daga sama gashashshe." Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskata jin muryar Garbati, mutumin da ko a mafarki bana fatan hada hanya dashi, waye be san shi ba kaf kauyen nan namu, tantirin dan iska ne, lamba daya, gashi babu wanda ya isa dashi kaf kauyen. Da sauri na ja da baya ina kokarin sake shiga cikin ruwan sosai, damko ni ya sake yi nayi kara da karfi jin zafin rikon da yayi min, ja na ya shiga yi yana kokarin turani cikin shagon da tun zuwa na wajen na lura da yar kofar dake bude, amma banyi tunanin akwai mutum ciki ba, da karfin gaske na hau kokarin kwatar kaina, sai dai ko kusa da hakan ban kai ba , duba da yanayin karfin ba daya ba. Tuni na hau kuka ina magiyar bashi hakuri, tunda ayi ƙarancin shekaru na nasan hakan da yake me yake shirin aikata min. Be saurara ba, ko ma nuna alamun yaji abinda nace, haka ya tura ni ta karfi ya maida kofar ya tura yana sakin wani shu'umin murmushi. Tuni na watsar da aiken Inno, na shiga ihu da dukkannin murya ta ko Allah zai sa a jiyo ni, dariya ya shiga yi ba kakkautawa. "Yarinya da kin hakura babu shegen da zaiji ki, uban me ya fito dake a wannan lokacin shegiya." "Aike na akayi wallahi." Nace ina sharbe hawaye da majina. "Daidai kenan, idan na ci ubanki zaki gane shayi ruwa ne." Ya fada yana kokarin matsowa kusa dani. Sosai na kara karfin murya ta, cikin tsananin tashin hankali, magiya nake masa ina rokon sa, sai dai hakan ba sa ya fasa aiwatar da abinda ya kudurta a ransa. Tun daga nan bansan me ya kuma faruwa ba😭😭 *** *** Tafiya yayi sosai yana mai jin dadin yanayin garin, kafin zuwa lokacin da iskar ta taso, sauri ya kara don ganin ya isa gida, be yi tunanin ruwan zai zo da iska haka ba. Saukar ruwan ne ya rage karfin iskar sosai, hakan ya bashi damar cigaba da tafiyar sa cikin kwanciyar hankalin ruwan na dan taba fuskar sa kad'an-kad'an. Kamar daga sama yaji ihu, ihun ma na mace me karancin shekaru, sai dai karar saukar ruwan yayi tasiri kwarai wajen kasa tantance daga ina ihun yake, hankali ya tashi ya hau neman ta in da muryar ke fitowa, kamar mahaukaci haka ya shiga kai kawo a cikin ruwan, hankalin sa ne ya kai wajen, da wani irin mugun guda ya nufi dan karamin shagon daya gama tabbatarwa daga nan ɗin ne yake jin kukan, beyi wata wata ba yana zuwa ya daki kofar da dukkan karfin sa. Abinda ya gani yayi mugun daga masa hankali, da gudu yayi kansa ya shiga dukan shi, duka me cike da tsantsar bacin rai. Yanayin rashin karfi da a tattare da Garbatin ya hana shi katabus, sai daya yi masa duka sosai sannan ne hankalin sa ya dawo kanta, tana kwance kamar mara rai, abinda ya dade yana jin labarin yana faruwa ga yara masu kananan shekaru ne ya faru da yarinyar nan, yarinyar da dududu ba zata wuce sa'ar Amal ɗin su ba, da sauri yayi kanta ya dago ta, tuni ta sume saboda tsabar firgicin data shiga, wani irin kuka ne ya taso masa, wannan wane irin rashin imani ne?. Da dukkan karfin sa ya daga ta ya sata jikin sa, be bi ta kan Garbati ba da yake kokarin tare shi, har ya kai kofa maganar shi ta dakatar dashi "Ni kayi wa wannan dukan? Akan wannan yar iskar yarinyar?" A halin da yake ciki ba zai iya magana ba, saboda haka ya juya da sauri dan ganin ya ceto rayuwar yarinyar. Yana juyo hargowar Garbatin me cike da gargadin abinda zai aikata masa. Gida ya wuce kai tsaye yana jin kamar zuciyar sa zata bar jikin sa. Har lokacin dukkan su suna falo ya shigo da sauri dauke da ita Baba maigadi na bin bayan sa, a tare duk suka mike suna kallon shi cike da mamaki. "Yah Farouk..! Amal ta fada tana zaro "Bude min daki na." Da gudu ta yi gaba suka take masa baya, dakin sa ya kaita, ya kwantar da ita saman gadon sa, sai a lokacin ya ga fuskar ta, kallon su yayi duk sunyi cirko cirko kamar sun ga abin tsoro. "Kira Dada Ja'afar." "Wacece ita Yah Farouk?" Ya tambaya ba tare da ya motsa ba. Kallon sa yayi rai a bace daa karfi yace "Will you go and call her or..." Da sauri ya juya ya bar dakin, dafe kansa yayi ya sake dagowa yana hararar kowa. "Duk ku fice min anan, Amal ki tsaya." Yar rige rigen fita suka hau yi, kowa zuciyar sa cike da tambayar abinda yake faruwa. Gefen sa amal ta zauna tana kura mata ido "Yah bata da lafiya?" Ta fada cikin tausaya wa. Daga mata kai yayi zaiyi magana Dada ta budo kofar cikin tashin hankali. "Babana,me ya faru?" Ta fada tana shigowa dakin, ganin da tayi mata yasa tayi saurin ƙaraso wa wajen "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me zan gani haka?" Hannun sa ya saka cikin na Dadan yana kokarin saita yanayin bugun zuciyar sa. "Bani ruwa da sauri ke Amina." Da sauri amal ta tashi ta dauko ruwan, karba ta shafa mata a fuska, sai data yi wajen sau uku sannan ta bude ido tare da sakin wani irin ihu wanda ya karade kusan kowanne lungu da sako na gidan. Bude ido na nayi wanda yayi min matukar nauyi ina kallon kowa na dakin, a lokaci daya zuciya ta ta shiga tariyo min abinda ya faru, kuka sosai na saka ina jin tsananin zafi kamar an watsa min barkono, riko ni dattijiwar tsohuwar dake kusa dani tayi tana kokarin sani a jikin ta. "Kwantar da hankalin ki, yi shiru, babu abinda zai faru kinji? Yi shiru karki karawa kanki ciwo." Abinda kawai naji tana ta maimaitawa kenan yana shiga kunne na cikin wani irin yanayi dana kasa tantancewa. "Dada asibiti zamu kaita, She's bleeding so Badly." Muryar sa ta daki kunne na, kallon sa Dada tayi kafin tayi magana cikin harshen turanci. "Who is she?" "It's a long story, babu time zan sanar dake komai, for now let's help her please." Ya karashe a marairaice. "Owk, Amma Ina son sanin amsar, kasan dai mahaifinku, kasan kuma labari zai kai masa zuwa gobe, i just hope ba kaine ba." Ta zura masa ido tana son ganin gaskiyar sa. Be yi magana ba, sai ma mikewa da yayi ya fice daga dakin, jim kadan ya dawo yana kallon Amal data makale a gefe tana mun kallon tausayi. "Zaki rakamu ko?" Da sauri ta daga kanta. "Dada ga driver ya dauko motar, muje ko?" " Shikenan." A hankali ta daga ni zata mikar dani, wata irin kara na saki me cike da azaba, da sauri ya waiwayo ya fasa kokarin fita daga dakin, da baya da baya ya dawo ya daga ni chak ya fita dani suna take masa baya. *** Tun Inno na zuba idon dawowa ta har hankalin ta ya fara tashi, ganin tasowar hadarin yasa ta sake shiga tashin hankali sosai, turawa tayi aka kira mata Nura a zaure ya bi bayana, lokacin iskar nan ta taso sosai. Safa da marwa Inno kawai take yi, duk wajen kowa yayi tsit ana jiran dawowar Nura, tsawon mintuna talatin ya dawo hankalin sa a tashe, babu ni babu dalili na, hakan kuma yayi daidai ta tsugewar ruwan, iya kar tashin hankali Inno ta shiga, bata fatan abinda zuciyar ta ke raya mata ya zama ya faru,bata da wata hujjar kare kanta a duk lokacin data shirya karbar muradin zuciyar ta, ko ma ba haka ba, baya cikin yarjejeniyar da sukayi tsakanin su, ko ba komai zata ci darajar nata dan. Tuni su karime da sauran yaran suka fara kuka, babu me rarrashin wani, ana haka ruwan ya fara tsayawa, gaba daya suka fito dan zuwa nema na, lungu da sako babu alamun za'a same ni, tashin hankalin da ba'a sa maka rana kenan, gida suka dawo kowa yayi jigum jigum ana tunanin ta in da zan ɓullo, duk da zuwa lokacin kowa ya gama saddak'arwa wani mugun abin ya same ni. Duk suna zaune sunyi cirko cirko, makotan da suka shigo duk sun tafi, yara sunyi bacci sai yan kadan, aka yi sallama a kofar gidan, da sauri su Nura suka fito tare da su Baba. "Garbati?" Nura ya fada yana kallon su. "Mune nan." Ilu ya amsa yana jingina a jikin garu "Lafiya dai ko?" Baba yayi tambayar ganin basu ce komai ba. Ilu ne ya kalli Garbati kafin ya shiga magana "Dama akan Aminatu ne." Da sauri a zabure suka hada baki. "Kun ganta ne?" Ilu ne ya dora "Bamu ganta ba, sai dai mun san inda take, dan munyi iya kar kokarin mu wajen ganin mun taymaka mata, garin haka ne ma Garbati yasha wannan dukan da zaku ga jikin sa haka." Ya fada yana haske Garbatin "Tana ina?" "Ina bakin gidan Bature? Daya daga cikin su ne muka kama shi, dan a lokacin da muka je ko numfashin kirki batayi, garin kokarin mu ne ma yasa masu gadin su sukayi wa Garbati mugun dukan nan, sannan ya dauke ta ya tafi da ita." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." ZAFAFA BIYAR KAUNAR MU: MAMUH GEE ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL DAURIN GORO:HAFSAT RANO. IGIYAR ZATO: MISS XOXO *_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_* 2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_ saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863* *_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇 *09032345899* _Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_ Mucigaba da shakatawa da wannan ©️Rano ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899                          (3) Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Suka hada baki suka fada a tare. "Yanzu ina ya kaita?" Baba ya tambaya cikin jimami. "Wallahi muma bamu sani ba, mun dai zo mu sanar ne dan a sani, amma abunda yafi shine mu dunguma muje gidan su, idan yaso sai a sa ya fito da ita. " "Abinda za'a yi kenan, kai Nura shiga kira min Yahya da Lawan duk mu dunguma, ba dan dare yayi ba ma wajen maigari zamu fara zuwa." A tare suka fito, Inno na tambayar su yadda ake ciki babu wanda ya tanka mata, suna fita ta sulale kanta na juya mata, tsananin tsoro ya hana ta motsi, idan ta tuna abinda zai faru. Babu kowa a hanya har suka isa gidan, haske fitilu ne tarwai kamar rana, buga kofar Ilu ya hau yi da dukkan karfin sa Garxali na taya shi, Baba maigadi ya taso a zabure yana tunanin ko sune suka dawo. Yana budewa yayi turus ganin mutanen da be wani waye dasu ba a wannan daren, kallon kallo sukayi wa juna kafin yayi karfin halin tambayar su "Lafiya dai?" Lawan da duk yafi zafi cikin su ya bata rai yana leken gidan "Yarinyar mu da kuka sace muka zo ku fito da ita." Da sauri Baba maigadi ya kalle su yana tuno abinda ya faru kafin isowar su, kar dai ace? Da sauri ya kauda tunanin yana mai tabbatarwa kansa hakan ba mai yiwu wa bane, yasan waye Farouk, yasan me zai aikata, duk da ance ba'a yabon yaran yanzu, sai dai yana kyautata masa zato ko ba komai yaro ne nutsattse. "Kayi magana mana, wallahi ko a fito da ita ko mu nuna muku mune muke da garin nan dan uwar mutum." Garbati ya katse masa tunanin da ya tafi na wucin gadi, kallon su yayi daya bayan daya yana yanke  hukuncin abinda ya kamata ya sanar musu. "Bansan me kuke magana akai ga gaskiya, babu kuma wata yarinya da tazo gidan nan, amma ku bari na shiga ciki na yi magana da masu gidan." "Karya ne wallahi, karku yarda Malam Ayubah, yaran gidan ne a gaban idon mu ya sungume ta ya tafi da ita, bayan ya gama da ita, Allah ma yasa ba yan yankan kai bane wallahi." "Subhanallah!" Sai a sannan Baba yayi magana yana jan murya "Kayi wa Allah idan diyata na hannun ku ku fito min da ita, hankalin mu gaba daya a tashe yake, dan Allah na roke ka." "Wallahi Baba bansan komai akan maganar da kuka zo da ita ba, amma me zai hana mu bar maganar zuwa garin Allah ya waye, a lokacin masu gidan ma sun tashi, kunga sai ayi magana sosai." "Kana nufin mu bar maganar yar mu har sai gobe, bamu san halin da take ciki ba, idan ma cinye ta za'a yi ko kashe ta zuwa goben kaga shikenan ko?saboda ba yarka bace ta bata ba. Toh wallahi ba'a isa ba." "Ni dai kuyi hakuri dan Allah." Zasu sake magana Baba ya dakatar dasu "Mu bar wa goben idan Allah ya kaimu, ita kuma Allah ya bayyana mana ita, ku muje dare na sake yi." Haushi ne ya taso wa Garbati, ba haka yaso a tashi wasan ba, so yayi su kutsa kai gidan ya samu damar cin uwar yaron nan, kwafa yayi a ransa yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai masa idan Allah ya haɗa su. Zai gane ya tana Gaza Boy. ***Karamin asibitin dake garin suka kaita, babu alamun ma ana aiki a asibitin, maigadi ne kawai yayi saura da yar karamar torchlight din sa babu isasshen haske, Farouk kamar zaiyi kuka haka yaji sanda maigadin ke musu bayanin babu kowa a ciki sai majinyata.  Juyawa sukayi suka dau hanyar fita daga kauyen baki daya. A lokacin jiki na ya kara tsami sosai, ko ina ciwo yake min zufa nake kamar wadda ta hadiyi kunama, babu abinda nake sai kuka Amal na tayani, Dada kam duk hankalin ta ya kara tashi, musamman ganin yanayin da na sake shiga daga fitowar mu zuwa yanzu. Juyowa yayi a hankali yana kallon bayan motar be ce komai ba sai kura musu ido da yayi yana jin kamar ya bude motar ya fita, yasan Amal  da raguwar zuciya da saurin kuka, kasancewar ta marainiya wadda bata san mahaifiyar ta ba yasa yake tausaya mata, baya son ko kadan yaji kukan ta, sai dai kukan yarinyar da yake ji yana neman danne kukan Amal din, har ya zama baya jin na Amal din sai nata kawai dake masa yawo a cikin kunnen sa, zuciya da ruhin sa. Suna zuwa asibitin aka karbe su, suka zauna a reception aka shiga da ita ciki, Farouk kasa zama yayi ya shiga kai kawo a wajen yana ayyana rashin imanin wasu mazan, basu da maraba da dabbobi. Fitowar Dr Iman yasa duk suka mike, kallon su tayi sosai taga babu alamun kauyanci a tattare dasu, dan bata fuska tayi kafin tace "Kuzo office Ina son magana daku ku biyu." Ta fada tana nuna Farouk da Dada, rufa mata baya sukayi suna shiga ta tura kofar tana jingina a jikin kujerar ta "Menene alakar ku da patient din nan?" Kallon Farouk Dada tayi zatayi magana yayi saurin katse ta "We are Family Dr." "Good." Tace tana zama "Kenan my guess was right, kunyi wa yarinya karama at her age aure, sannan saboda rashin imani ka kasa hakuri da kankantar ta, kayi forcing kanka akanta ko?" "A ah likita..." Dada tayi saurin katse ta, kafin ta k'arasa yayi maza ya sauke kansa kasa a hankali ya furta. "Haka ne Dr, I'm very sorry, kuskure ne." Biron hannun ta ta saka a bakinta tana kallon sa, shi a karan kansa ba wani babba bane, bata jin zai dora shekaru 20 idan ya dara to ba zai fi da biyu zuwa da hudu ba, yanayin jikin sa na girma da cika yasa zaka kasa tantance shekarun sa, sai dai duk da hakan ba za'a hada shi da yarinya yar shekara goma da doriya ba. Cire glasses din idon ta tayi ta fara magana a hankali cike da nasiha, dan a yadda tayi niyyar shigar dashi kara duba da yadda ta ga halin da ya saka yarinyar a ciki, sai dai yadda ya amsa laifin sa kai tsaye yasa ya sauko ta shiga nasiha da dukkan kokarin ta. Hannayen Dada a makale da ita ta zuba su akan Farouk din, mamaki ne karara kwance a fuskar ta, bata gane nufin sa ba, bata gane inda ya dosa ba, tasan shi da tsananin tausayi amma bata taɓa tunanin zai iya aikata daukar laifi a ajiye akansa ba, tuni zuciyarta ta sake tsinkewa, idan har hakan ne kuwa ya tabbata Farouk din ne ya bata musu yarinya, in kuwa hakan ta kasance bata san ya zatayi ba. Bayan sun fito daga dakin Dr yaki yadda su hada ido sam Dada, yasani sarai tana bukatar gamsasshen bayani, amma baya so ya sanar mata da komai sai ya samu nutsuwar zuciya. Dakin da aka kwantar da ita suka tura suka shiga, Amal na zaune kan kujera tana bacci, drip ne a daure hannun ta, bacci take sai dai yanayin fitar numfashin ta ya nuna tsantsar wahalar da take ciki, karasa wa yayi gaban gadon yana sake kallon ta. "Umar!" Dada ta kira sunan sa, yanayin Muryar ta kadai yasa ya gane abinda zata ce, kasa juyowa yayi har sa data maimaita kiran nasa. "Na'am Swthrt." "Ba wasa nake maka ba, kasan kuma ni ɗin ba sa'ar tsohon ka bace balle kace zaka maida ni mara hankali ko wata chan daban, wacece yarinyar nan? Menene alakar ka da ita?" Juyowa yayi yana fuskantar ta, ganin ta bata rai sosai babu alamun wasa yasa shi takowa har gaban ta. Sai da ya daidaita tsayuwar sa a gaban ta sannan ya fara magana cikin son gamsar da ita. "Kiyi hakuri idan na bata miki rai, hakan da nayi ba wai nayi ne dan na bata miki ba, wallahil azim bani da wata alaƙa da ita,hasalima bansan wacece ita ba, bansan komai game da ita ba." "Aina ka samo ta toh idan baka santa ba?" "A daidai lokacin da Allah ya saukar mana da daya daga cikin ni'imomin sa, a daidai lokacin wani mara imani ya aikata mata wannan aika aikar, babu digon tausayi ko imani a tattare dashi, bansan shi ba, bansan waye ba, ihun ta kadai naji, na taimaka mata." Kallon sa take har ya kai karshe, ganin bata ce komai ba yasa shi kama hannun ta "Ki yarda dani, ba zan taba iya aikata wa wata mace makamancin wannan ba." "Naji! Amma menene dalilin ka na amsa wa likitar nan a matsayin kaine mijin ta? Baka tsoron maganar ta fita, bayan kasan waye mahaifin kuma." "Hakan shine daidai, karki manta wannan abun babban tabo ne a tattare da duk wata ya mace, da zai iya zama wani babban gibi a rayuwar ta. Banyi hakan da wata manufa ba face don kare mutuncin ta." Turo kofar akayi, hakan yasa yayi shiru yana duban su, Dr Iman ce sai wata nurse a bayan ta. Dan dube duben su sukayi suka juya, har ta kai kofa ta juyo. "Af na manta, akwai alluran da za'a yi mata da safe gobe, , so ka zama around please." "In Sha Allah." "Good." "Kai zaka kwana kenan?" Dada ta fada tana kura masa ido, har zai ce eh sai kuma yayi wani tunanin daban "A ah, kece zaki taimaka." "Amal fa? Kalli a yadda tayi bacci." "Eh zanje na tambaye su idan akwai spare gado sai su bamu mu biya sai ku kwanta akai, dama dare yayi yanzu komawa hanyar nan akwai risk, in yaso ni sai mu kwana a mota." Dan jim tayi kadan kamar zatayi magana sai kuma ta girgiza kanta kawai ba tare da tace komai ba ta koma gefen gadon ta zauna tana kura mata ido kamar me karanto wani abu a tattare da ita. *** Da safe na bude ido na ina karewa dakin kallo, daidai lokacin aka turo kofar aka shigo hade da sallama, zuba masa ido nayi ina kallon sa har ya iso gaban gadon, shi din ma kallon nawa yake fuskar sa dauke da murmushi. Juyawa yayi yana kallon Amal dake bacci hankalin ta a kwance, karar ruwan da yaji a toilet yasa ya gane Dada na ciki.  Sake matsowa yayi gaban gadon ya furta a hankali "Ya jikin?" "Da sauki." Na amsa da sauri ina kallo sa "Sannu kinji." "Toh." Nace ina sake bin fuskar sa da kallo kamar me son tuno abu. Murmushi ya sake yi yana kallon drip din dake shiga cikin jikina a hankali, file din dake ajiye saman drawer saka magunguna ya dauka yana dubawa har Dada ta fito. ***Yanayin horn din kadai ya tashi kowa na gidan, a firgice su ja'afar suka fito falo kowa ya tsaya, ba sai an fada musu ba sun san kowa ye, tsoron su daya abinda ya kawo shi a irin wannan lokacin, iya sanin su ma baya kasar baki d'aya. Motoci uku ne suka shigo a jere, kai kawo Baba maigadi ya shiga yi har suka daidai ta a harabar gidan. Cikin shigar sa ta Babban sojin kasa ya fito daga motar fuskar sa dauke da yanayi marar misaltuwa. "Barka da zuwa." Kawai kake ji kowa na kawo gaisuwa. Jiki a sanyaye su Ja'afar suka dunguma zuwa harabar gidan kowa tsoro fal zuciyar sa. A daidai lokacin aka fara bugo da mugun karfi kamar za'a balla gate din gidan, hayaniyar mutane ke tashi da alama ba mutane ne kadan ba. Da sauri ya kalli Baba maigadi Yana neman karin bayani. ZAFAFA BIYAR KAUNAR MU: MAMUH GEE ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL DAURIN GORO:HAFSAT RANO. IGIYAR ZATO: MISS XOXO *_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_* 2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_ saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863* *_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇 *09032345899* _Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_ Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN😁👉🏻📻 *DG* ©️Rano ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 ALKALAMI TV https://youtu.be/LxY42ErBf_8                          (4) ***** Babu wanda yayi kwakwaran motsi a cikin su, kowa da abinda yake ayyanawa a ransa. Jin bugun na sake karfi ne yasa shi juyawa da kansa ba tare da yayi magana ba ya nufi hanyar gate din. Budewa yayi yana kallon mutane dake tsaye, wasu dauke da makami, ganin haka yasa sojojin sa suka yo wajen da sauri. Hannu yasa ya dakatar dasu yana bin mutanen daya bayan daya cikin tsananin tashin hankali, sai dai duk da hakan ba zaka tantance yanayin da yake ciki ba, fuskar sa tana nan kamar ko da yaushe. "A fito mana da yar mu!" Muryar daya daga ciki ta bakunci jin sa, daya bayan daya ya hau kokarin fassara kalmomin acikin yan sakanni. Take wajen ya kaure da ihun kalmar da yake da bukatar amsar ta cikin gaggawa. Sake daidaita kansa yayi, ya kuma saka dukkan jikin sa ya fito waje sosai yana sake duban su, mutane ne yawancin matasa sai wasu dattijai guda uku daga gefe, kai tsaye ya nufi wajen su, yana me sake daidai ta kansa. Yana isa ya mika musu hannu daya bayan daya, kwarjinin sa ya cika wajen baki daya. Lawan dake niyyar rashin kirki ya ji ba zai iya ba, girma da cikar haibar sa kadai ta isa ka girmama shi. Balle kuma da shigar sa ta nuna ainihin shi din waye ne. A nutse ya kai duban shi wajen sauran yaran kana ya maida kansa garesu "Me yake faruwa?" Ya tambaya yana nuna su Garbati, "Yar mu wadda take cikin gidan nan muka zo tafiya da ita." "Yar ku? Kuyi hakuri ban gane kan maganar ba, zuwa na kenan." "Alhaji jiya daya daga cikin yaran gidan nan ya dauke mana yar mu, bayan mun gaji da neman ta muke samun labari ta wajen daya da ga cikin matasan garin da abin ya faru akan idon sa, toh jiya munzo a daren bamu samu ganin kowa na gidan ba sai Maigadi, shiyasa muka shiryo muka zo yanzu, dan har mun sanar wa maigari ma." Hannu yasa yana shafa kansa, be tsinci komai a bayanin ba, sai dai ya fuskanci suna zargin batan yar su ne a gidan sa, a gidan nasa ma kuma cikin yaran sa, dan jim yayi kadan yana nazari kafin yace "Ku bani mintina biyu dan Allah ina zuwa." Juyawa yayi ya nufi cikin gidan, ya zo shiga Garbati ya daga murya yadda zaiji sosai yace "Wallahi sai an fito da ita, ga Fyade ga sata, haba ai abin yayi yawa." Chak ya tsaya da tafiyar da yake, wani irin bugu zuciyar sa tayi, babu abu daya daya ki jinin ji kamar kalmar fyade. Maganganun da suka cigaba ne suka shiga maimaita kansu a cikin kwanyar sa, da sauri ya fada gidan, suna nan tsaye duk a in da ya barsu, daya bayan daya ya shiga binsu da kallo kamar me lissafa su, duk sun tsure iya kar tsurewa sun gama sanin me hakan ke nufi. "Ina Farouk?" Shiru babu wanda yayi magana, a fusace ya sake tambaya cikin daga murya sosai. Da sauri har suna hada baki suka ce "Sun...sun fita da Dada da Amal." " Ina suka tafi da sassafe haka bayan kuma ku da alama ko dukkanku tashin ku kenan." "Asibiti suka tafi kai wata yarinyar." Dafe kansa yayi ganin zancen na fitowa. "Da yaushe suka tafi?" "Jiya da daddare." *** Zama Dada tayi tana jiran Amal ta idar da sallah, Farouk na zaune a kan kujerar dakin yayi nisa a tunani, shi kadai yasan me yake tunawa, alluran da ya kamata ayi mata duk anyi mata. Tana idar wa ta tashi ta je gaban gadon tana kallon ta "Ya Farouk ta samu sauki ko?" Ta tambaya tana nuna masa ita. Daga mata kai yayi yana murmushi "Amma mene sunan ta?" Girgiza mata kai yayi alamar shima be sani ba, murmushi tayi tana sake kallon ta. "Ina son ta da kawa, me kyau kamar ta cikin cartoon din nan." "Tashi zakiyi mu tafi ba surutu zaki tsaya yi ba." Sai kuma ta maida kallon ta wajen Farouk "Kai ma tashi zakayi muje, idan yaso sai a nemi iyayen ta a sanar musu suzo dan yanzu nasan hankalin su a tashe yake." "Da wai sai na zauna da ita har suzo ɗin, kinga be kamata a bar ta ita Kadai ba." "Farouk!" Ta bude idon ta sosai "Baka da hankali ko? Kasan abinda hakan zai haifar? Lallai kai yaro ne." "Dadah ki barmu anan nida Ya Farouk dan Allah, kinga idan ta tashi bata ga kowa ba zatayi kuka." "Toh uwar iya, wallahi tashi zakuyi mu tafi, ba zan iya da matsalar da zata taso ba, na riga nayi magana da wata nurse zasu shigo suna dubata har suzo iyayen nata." Kamar ya fashe da kuka haka yaji, shi be ga dalilin da zai sa Dada tace sai sun tafi ba, gashi idan ta kafe babu abinda zai sa ta hakura, tashi yayi tsam yana kallon gadon kafin ya juya ya fice da sauri. Kwafa tayi ta ja hannun Amal suka fito, a tsaye ta hango shi tare da Dr Iman suna magana, karasawa tayi wajen "Dr Barka da safiya." "Yawwa Mama, ya me jiki?" "Alhamdulillah, mungode Allah." "Allah ya kara sauki, zan shiga sai na duba jikin nata." "Ok Dr, nima zan dan je gida ne na dawo." "Ok yayi,ka same ni a office idan na gama round zan yi magana da kai, amma yanzu ka koma dakin karta farka taga babu kowa." Ta fada tana yin gaba,kallon Dada yayi yana marairaice fuska, ganin yadda tayi kicin kicin da fuska. "Sai ka zauna ai dama abinda kake so kenan, amma wallahi Babana ina ji maka tsoron abinda zai je ya dawo, ba fata nake ma ba, amma baka san halin mutanen mu ba." "Babu abinda zai faru sai Alkhairi Dada." Ya fada cikin gamsuwa. "Shikenan, Allah yasa." "Amin." Yace yana murmushi. "Zan tsaya wajen ka Yah." Kama bakin sa yayi da sauri yana kallon Dadan, tsaki tayi ta juya tana mitar sun raina ta. Ciki suka koma da sauri, har lokacin bata tashi ba tana sauke numfashi a hankali. **** Zagaye da hannayen sa yake kaiwa da komowa, wani irin tashin hankali me matukar girma yake hasasowa idan har abinda yaji ya zama gaske, ya zaiyi? Da wacce fuskar zai kalli mutanen kauyen. Tabbas idan hakan ta kasan zai dauki mummunan mataki akan Farouk, baya fatan zargin sa ya zama gaskiya dan zai iya yafe shi ba ma a cikin yayansa ba, a cikin dukkan ahalinsa. Duk kuwa da dimbin soyayyar da yake masa duk cikin ya'yansa. Jin tsayuwar mota yasa ya juyo da sauri yana kallon gate din da tun zuwan sa yake tsaye wajen ya rasa me zaiyi. Idanun sa akan gate din har aka gama budeshi. Ganin motar gidan yasa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, duk da baya hango cikin motar amma yasan sune suka dawo, a yau da ace ba tare da mahaifiyar sa suka tafi ba be san abinda zai iya aikata mishi ba, sai dai dole ya saita kansa yaji komai a baƙin ta. Hannun sa ya harde a kirji yana jiran daidaituwar motar da yake ganin kamar da gangan driver yake lankan jin ajiye ta a mazaunin ta. Dada ce ta fito tana me kallon harabar gidan cikin tarardadin abinda yake faruwa, farko mutanen da ke waje tsaye kamar masu jiran a fito musu da gawa su kaita kushewa, sunyi kungiya kungiya suna tattaunawa, yanzu kuma tsayuwar Janar a harabar gidan ya kara tabbatar mata da abinda take tsoro take gudu ne ya faru. Jiki a sabule irin na wanda yayi fama a filin daga ya isa gareta kafin ta ƙaraso. "Dadah.! Ya furta muryar sa a bude sosai me nuna yanayin da yake ciki. "Muje ciki." Ta fada tana kallon sojojin da sukayi dafifi a wajen suna tsaye cikin jiran cika umarnin uban gidan na su. Be musa ba, sai jan kafar sa da yayi da tayi matukar sanyi yabi bayanta. Ajiye mayafin ta tayi ta zauna tana daidata nutsuwar ta, dan tabbas ta hango tsananin tashin hankali da firgici a idon yaron nata, kasancewar sa babban soja hakan be sashi zamaar mata tamkar yaron goye a duk sanda yake tare da ita ba. Tabbas haka Farouk yake, a duk yayansa shine ya biyo shi, babu abu daya daya bari nasan tun daga dabi'a da yanayin yadda yake daukar a'alamri, abu daya tasani shine Farouk yana da sanyin zuciya da saurin yarda da komai, banbancin sa da mahaifinsa kenan wanda ya kasance mutum me tsauri sosai da rashin yarda a duk sanda abu ya gifta tsakanin ku, duk yadda kake dashi zai bar ka, barwa ta har abadah kamar yadda suka rabu da mata mafi soyuwa a gareshi bisa babban kuskuren data aikata masa. Ruwan da aka ajiye a gaban ta ta kalla tana kallon Ja'afar daya kawo ruwan. Dauka tayi ta zuba ta mika masa. "Sha ruwa Muhammadu, ko zaka ji saukin zuciyar ka." Karba yayi ba tare da yayi magana ba ya kafa kai ya shanye tas yana ajiye kofin. "Me yake faruwa?" Ta wurgo masa tambayar tana nakaltar nazarin sa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yayi magana cikin dakiya "Ni kaina na rasa me yake faruwa, zuwa na kenan, na tarar da wannan tashin hankalin, shin da gaske ne abinda mutanen garin nan ke tuhumar Farouk?." "Me suke tuhumar shi akai? Maganar yarinya ne ko?" Ta fada kai tsaye dan tasan kwanan maganar kenan. "Eh ita Dada, suna zargin Farouk da yi wa yarinyar su fyade sannan kuma ya sace ta, wannan wanne irin tashin hankali ne Dada." Shiru tayi tana maimaita innalillah wa inna ilaihi raji'un a ranta, abinda take gudar wa Farouk kenan, ya kasa ganewa. "Dadah dan Allah, ina ya kai yarinyar, kuma shin da gaske abinda suke zargin sa akai ya aikata?" "Yarinya dai tana asibiti dan yanzu ma daga chan nake, kuma tabbas yazo da yarinya a cikin mayuwacin hali, kuma nayi magana dashi na tambaye shi idan shine ya aikata mata, yayi mun rantsuwar dan musulmi bashi bane." "Shikenan, Farouk ya gama dani." "A ah kar kayi saurin yanke hukunci, ka tsaya kaji ta bakin nasa." "Haba Dadah, yaran yanzu fa sun wuce tunanin mutum, kuma ba'a shaidar su sam, dan wanda kake ganin ba zai aikata abu ba yafi aikatawa." "Yanzu menene abinyi?" "Tashi zanyi naje asibitin, gani gashi ga iyayen yarinyar, harda maigari ma." "Shikenan, amma kabi komai a sannu." **** Shigar su dakin yayi daidai da sake farkawar ta, a dan tsorace take kallon su, kafin ta maida idon ta da sauri ta kulle su gam. Amal ce tayi saurin karasawa wajen gadon ta rik'e hannun ta, jin an rik'e ta yasa ta bude ido ta sauke su akan ta. "Ya sunan ki?" Amal ta tambaya dan ta matsu tasan sunan ta. "AMINATU!" Da sauri ya juyo, sosai yaji sunan nata har cikin ransa, sauti da amon muryarta ya shiga masa amsa kuwwa, yana jin Amal na fada masa sunan su daya tana murna ya kasa amsa mata, sai ma binsu da ido kawai da yake yi kamar be san me yake faruwa ba. Hira sosai Amal ta shiga yi mata, kallon ta kawai take yi ba tare da ta gane komai ba, ido kawai tasa mata. "Zan sha ruwa." Ta furta a hankali, da sauri Amal ta tashi ta dauko mata ruwan, kokarin tashi tayi taji zafi, kuka ta saka yayi saurin tasowa, "Sannu." Daga masa kai tayi tana gogen hawayen da bayan idon ta. Ruwan ya bata Amal na tsaye kamar zatayi kuka. "Gida zan tafi." Tace tana kallon sa. Zaiyi magana aka turo kofar, wani irin faduwa gaban sa yayi yasa hannu ya rike wajen zuciyar sa da sauri. "Daddy!" Amal ta fad'a tayi wajen sa da sauri, rike ta yayi ya matsar da ita gefe bayan ya shafa kanta, Maigari ne ya fara shigowa,sai Baba, Inno na bin bayan sa, sai Lawan Da Yahya. Garbati da Ilu suna take musu baya. Da sauri Inno tayi wajen gadon tana sakin kuka. Gyaran murya maigari yayi, Inno tayi shiru duk aka nutsu ana kallon sa. "Garbah!" Ya kira sunan Garbati yana masa alamun ya matso. "Maimaita abinda kace." Gyara tsaiwar sa yayi cikin dakiya ya nuna Farouk da hannun sa "Gashi nan, jiya ana ruwan nan ta gefen daki na naji kamar ana kuka, da har na share sai na kuma jin kukan na tsananta, kamar wasa na dauko toci ta na leko, in haska sai ga tashin hankali, ido na cikin nasa yana aikatawa karamar yarinya, nayi kukan kura na rike shi, muka haure da kokawa, shine fa ya samu yayi min mugun duka, kuma ya dauke ta ya gudu, duk da haka sai dana bisu a baya, naga gidan daya shigar da ita, shine fa nayi gaggawar zuwa sanar da iyayen yarinyar." Tun da ya fara magana Farouk ke  kallon sa, gaba daya jijiyar kansa ta fito, numfashin sa ya shiga fita da sauri da sauri, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, Daddy kuwa kasa yayi da kansa yana jin kamar kasa ta zage ya shige, sai dai bashi da ta cewa, duk abinda gaskiya ta bayyana zai goyi bayan ta, ba zai taba goyon bayan zalunci ba ko da daga dan cikin sa ne. "Kaji abinda ake tuhumar ka dashi, shin kana da abinda zaka kare kanka, duk da dai ga zahirin ganin ku tare da mukayi anan, amma ko zaka fada mana dalilin da ya jawo hakan." Maigari ya fada yana duban shi, kokarin magana yake ya kasa, motsa bakin sa yake ya kasa, kallon Garbati kawai yake cikin tsananin bacin rai, bai taba tunanin akwai mutane masu aiki irin na dabbobi kamar shi din ba, kallon Amal yayi yaga ta zuba masa ido kamar me son ganin wani abu, ya sake maida kansa wajen Aminatu, itama shi take kallo, tana share kwallar dake zubo mata. Runtse idon sa yayi ya bude ya maida kallon sa wajen Daddy, yanayin daya ga fuskar sa kawai ta gamsar dashi abin da zai je yazo idan har ya kasa fitar da kanshi daga wannan daurin. Kokarin daidai ta kansa yayi ya shiga kokarin magana a nutse duk kuwa da tarin tashin hankalin da yake ciki "Allah ne..." "Kai ne kayi mata Fyade ko ba kai bane!" Daddy ya fada cikin k'araji dan ya gaji so yake kawai ya amsa da a ah ko Eh. "Daddy Wallahi tallahi Allah ne shaida ta..." "Will you shut your mouth, amsar ka kawai nake so kai ne ka aikata mata Fyade ko kuwa?" "Fyade!" Dr Iman da shigowar ta kenan ta karbi kalmar, duk suka juyo suka kalle ta. "I'm sorry to interrupt, kuna nufin dama yaron nan ba mijin ta bane, fyade yayi mata suka rufa min yace shi mijin ta ne?" Da sauri Farouk ya kalle ta zuciyar sa na sake tsinkewa. DAURIN GORO😢😢😥😥😓 ZAFAFA BIYAR KAUNAR MU: MAMUH GEE ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL DAURIN GORO:HAFSAT RANO. IGIYAR ZATO: MISS XOXO LITTAFI DAYA 200 BIYU 300 UKU 400 HUDU 450 BIYAR 500 *_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_* 2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_ saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863* *_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇 *09032345899* _Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_ : *DG* 5 *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo ©️*Rano*                               (5) **** Duk suka maida kallon sa gare ta, takowa tayi ciki tana kallon fuskar Farouk din. "Me kike cewa Dr?" Daddy ya tambaya yana kallon fuskar Farouk din "Nice likitar data karbi case din yarinyar, a yadda mukayi magana na zata matar sa ce, dan shi dinma ya nuna min hakan, duk da cewa akwai karancin shekarun ta da nashin ma kansa, sai dai ya amsa laifin sa kuma ya bada hakuri, amma kuma naji wata maganar daban duk da ba dani ake ba, amma ina da right na sani saboda matsayi na na likitar ta." "Babu wata matar shi, makaryaci fyade yayi mata kila ma sai daya sha ya bugu sosai sannan." Garbati ya fada yana huci. Kasa hakuri Farouk yayi ya kalle shi cikin konar rai "Sharrin da zakayi min kenan, kasan nasan komai shine kake kokarin jona min laifin da ka aikata?" "Ni? Ni zaka wa sharri, na ganka ido da ido, shine zaka maida abin kai na, na shiga uku, wallahi Maigari karya yake min so yake ya maida abin kaina." Sake duban sa Farouk yayi yace "Kaji tsoron Allah, ka sani akwai mutuwa akwai hisabi, kar kaga idon mutane anan, ka fadi gaskiya ko dan rayuwar yarinya karama." "Wallahi tallahi sharri yake min, shine ya aikata karya yake min wallahi." Garbati ya fada yana karashe wa da fashewa da kuka kamar gaske. Dafa kai Daddy yayi ya kalli farouk, ya gaji da wasan yaran nan da suke musu, magana daya yake son ji, idan shi ya aikata ya amsa eh ko a'ah. Rike masa riga yayi cikin bacin rai "I'm asking u for the last time, Kai ne ko ba kai ne ba?" Kukan Amal da Aminatu ne ya kara karfi a wajen, juyawa Farouk yayi ya dube su daya bayan daya, sosai kukan nasu yake taba masa rai, kallon Daddy yayi ya shiga girgiza kai. "Alhaji ina ganin tun da ga yarinyar nan a zaune, duk da karama ce amma ba zata kasa tantance wani abu ba, ina ganin a tambaye ta, idan yaso kowa ne ya aikata mata wannan abin, a cikin su, to fa dole ne a aura masa ita bayan hukuncin da shari'a ta gindaya ga wanda ya aikata irin wannan laifin, dan kaf kauyen nan namu babu wanda zai yarda ya karbi aurenta, musamman yanzu da zance ya zagaya ko ina, ina tsoron sai dai ta karasa rayuwar ta a haka." Maigari ya katse su, sakin sa Daddy yayi ya hankada shi har sai daya kusa bigewa da karfen gadon, dago idon sa yayi ya sauka cikin nata, wani irin abu yaji ya taba shi, wanda be taba jin irin sa ba, raunin da ya gani a cikin idon ta, yarintar ta da tsantsar tausayin ta suka hadu. Idan har yaji daidai abinda mai gari ya fada, yana nufin aura wa Garbati ita kenan, auren da yake nufin lalacewar rayuwarta har abadah, auren da yake nufin yanker war duk wani jin dadi na rayuwar ta, auren da yake nufin rayuwa da mutum wanda bashi da maraba da dabba, dabbar ma mafi kaskanci acikin dabbobi. Kasa dagowa yayi ya rasa me yake masa dad'i, yana jin sanda Maigari ya kira sunanta, yana jin lokacin da ya tambaye ta, kukan ta ya kara karfi, be san yaushe ba, be san yaya ba, kawai ya samu kansa da amsawa a maimakon ta tun kafin ta samu damar yin magana. Da wani irin karfi Daddy ya riko shi, ya shak'e shi, kakari ya fara kamar wanda yake shirin mutuwa cikin sauri Baba ya shiga tsakani. Yayi kokarin bangare shi daga rikon da yayi masa, "Alhaji kar kayi mishi illah." Ya fada cikin tashin hankali ganin yadda idon yaron ya kakkafe "Barni na kashe shi, ya cancanci haka, ko ma fiye da hakan, barni dan Allah, harbe shi zanyi kowa ya huta." Ya sake riƙe shi sosai, bugu ya fara kai masa ta ko ina, tun Farouk na kokarin kwatar kansa har jikin sa ya saki ya shiga fitar da jini ta ko ina. Lawan da sauran ne suka shiga tsakani, ganin haka yasa Garbati da Ilu sulale wa su bar dakin suna fita suka ci karo da sojoji, a darare suka gifta su suka bar asibitin da sauri. Ba karamin duka yayi masa ba, da kyar suka kwace su, duk da haka sai daya hankad'a shi da karfi kansa ya fashe, Amal ce tayi saurin isa wajen sa tana kuka taa dago shi. Haki kawai Daddy yake, kamar wanda ya shiga filin daga, cikin tsananin bacin rai ya nuna shi da hannu yana kallan su Maigari. "Maigari, Malam da sauran wanda suke wajen nan, ku zama shaida, ga shi nan, duk hukuncin da kuka yanke akansa bani da ja, kuyi masa duk abinda kuka ga dama babu ruwana, karku duba girma na, arziki na ko khakhi na, kuyi masa hukuncin daya dace daidai dashi." Ya dora... "Sai dai ina neman alfarmar kowanne hukunci za'a yanke ya zama cikin kwana biyu, dan zan koma in da na fito." Juyawa yayi ya nufi kofar fita da sauri yana jin ba'a taba bata mishi rai irin na yau ba. Daya bayan daya suke dinga zamewa suna barin dakin ya rage sai su Inno kawai. Tashi tayi ta dago shi tana kallon fuskar sa "Baka aikata abinda ake zargin ka dashi ba, amma me yasa ka dauki laifi me girma ka dora akan ka?" Ta tambaya tana karantar sa. Mik'ewa yayi yana goge bakin sa yana kallonta "Bansani ba, bansan dalili ba. Ina ganin hakan da nayi shine kawai mafita." Juyawa yayi ya bar dakin Yana rangaji, Amal ta bishi da sauri tana kiran sa. Kuka na fashe dashi, Inno ta harare ni tana zama a gefe na "Kukan uban me kike?" "Inno kinga fa kuka yake, duk kuma jini a jikin sa, yana da kirki sosai." "Toh sai akayi uban me? Ke yanzu karamar ki dake kinsan wani yana kuka, baki ji maganar da mai gari yayi ba, idan na yarda akayi miki aure idan ranar da nake jira tazo nayi yaya kenan?" "Na'am?" Na tambaya cikin rashin gane abinda take nufi "Manta kawai, abu daya nake so dake, idan aka tambaye ki kice ba zaki auri kowa ba, babu inda zaki matsa daga nan sai ranar da Allah ya yanke miki wahalar nan." Gid'a mata kai nayi ina share hawayen dake faman kaikawo a fuskata kamar an kunna fanfo. Tashi nayi ta taimaka min na wanke fuska ta, ina zama ya shigo fuskar sa anyi dressing ya dire kayan tea ba tare da yayi magana ba ya juya ya sake fita. *** A hargitse ya shiga gidan, Dada na zaune a falo tana jira shigowar sa, ganin yanayin sa yasa tasan komai ya ɓaci, be zauna ba, ya shiga kwala wa su Ja'afar kira, sai daya tara su duka sannan ya hau fada, sosai yayi musu fada sannan yace duk su shirya kaya zasu bar garin a ranar. Duk suka amsa da toh sannan ya sallame su. Zama yayi cikin kujerar falon yana zare butiran din hannun sa. "Dadah yaron nan ya amsa laifin sa, dan yau dama ka haife shi ne baka haifi halin sa ba." "Yanzu menene abin yi? Kana nufin shi baban nawa ya amsa laifin?" "Ya amsa har ma sun yanke hukuncin bashi auren ta." Da sauri ta tashi "Aure kuma? Dududu Baban nawa nawa yake? Karka manta alƙawarin da kayi wa Marigayi." "Toh ya za'a yi Dadah, tun da yasan ya bata wa yar karamar yarinya rayuwa ai gwara a aura masa ita kawai kowa ya huta, idan yaso sai ya hakura da karatun nasa su zauna anan ɗin tunda irin rayuwar da ya zaba ma kansa kenan." "Amma ka tabbata shi ya aikata?" "Nima da ina ta tunanin hakan, amma daga baya daya amince da laifin nasa kinga ai babu maganar tantama, ya aikata din" "Kai wannan abu beyi dadi ba, amma ita yarinyar fa? Bata fadi kowa ba?" "Kin ganta dai Dadah, karama ce sosai dan ko Amal ta fita girma da cika ido, ga kuma kauyanci da rashin wayewa, bayan haka ba'a kai ga tambayar yarinyar ba ya amsa laifin sa, kinga ai babu bukatar kuma wani dogon bincike da dai be amsa bane." "Toh Allah ya sauwake, amma sam banji dadin abin nan ba, amma dai ƙaddara ce dan sam ba haka halin babana yake ba kai ma ka sani, bansan dai me ya faru ba, Allah ya kara kiyaye wa." "Amin ya ALLAH." "Bari na shiga ciki, in sha Allah da an gama komai jibi zamu wuce baki daya, su yaran suyi gaba yau, nima ina da ayyukan yi da yawa, dalilin admission din farouk din ne ya shigo dani garin wallahi." **** Tafiya yake a kasa bayan ya bawa driver umarnin ya maida Amal gida, be san ina yake saka ƙafarsa ba, ya dai san kawai yana tafiya ne akan kasa, sai dai kafatanin tunanin sa ya tafi ne akan abinda ya faru a yan awannin da basu wuce ashirin ba, gaba daya rayuwar sa ta chanja, ya rasa duk wani girma da kima a idon mahaifin sa, haka Allah yake ƙaddara wa bawa ƙaddarar sa, ba tare da ya shirya ma hakan ko yayi tunanin hakan zai taba kasancewa dashi ba. Tsaiwar babur a gaban sa ce yasa ya dakata yana kallon na kai, Garbati ke da Ilu, cikin kazamar shiga irin ta yan Iskan kauye, sigari Garbati ya busa masa a fuska yana dariya. "Ango ango." "Lafiya?" " Ita ce ta kawo hakan, ka dai ga kadan daga aikin Garbati ko?" "Bani da lokacin tsayawa magana daku, kamar yadda ban dauke ku a cikin jerin mutane masu hankali ba." Da haka ya rabe ta gefen su ya wuce, yana jin Garbati na kutuntuma masa ashar, be bi ta kai ba, burin sa kawai ya isa wajen da babu kowa.    Kansa ya haɗa da gwuiwar sa, ba zan iya fadar yanayin da yake ciki ba, zuciyar sa ta yi nauyi, ta cunkushe kamar zata budo kirjin sa ta fito, so yake yayi kuka ko zai samu sauki, sai dai babu ko digon hawaye sai na zuci da ya ka faman yi. Da fari ya so ya tabbatar da gaskiyar sa, ko dan irinsu Garbati masu halin dabbobi, sai dai furucin auren da yaji ne ya rusa komai, ba zai iya barin yarinya karama Kamar Amal ta rayu da Garbati ba, rayuwa irin ta aure me cike da tarin matsaloli, dalilin hakan yasa yayi ma kansa mugun dauri, daurin da yake tunanin har karshen rayuwar sa zai cigaba da bibiyar sa.     Ya jima sosai a wajen, ba zai iya lissafa adadin awowin daya bata ba, ya dai mike ne kawai da niyyar zuwa gidan ko me zai faru ya faru. Sai a lokacin ya lura da irin nisan tafiyar da yayi. Har ya karasa gidan be bar fargabar haduwa da Daddy ba, ya san shi sarai yasan abin da zai iya aikatawa akan shi, abun mafi tsoro a tattare dashi shine bakin sa, baya son wata kalma ta muzantawa ta fito daga bakin sa, ba zai iya daukar hakan ba sam.    Tura gate din yayi yaji shi a bude, a nutse ya tura kansa cikin gidan bakin sa dauke da addua, jami'an tsaron dake zube birjik a gidan ya fara cin karo dasu, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, dauke kansa yayi ya haura kofar da zata sadaka da falon gidan. A dan tsorace ya tura kofar yana tarrradin abinda zai tarar, cikin tsawa aka dakatar dashi. "Tsaya anan!" Da sauri ya tsaya yana maida hannayen sa baya kamar me shirin arcewa. "John!" Daddy ya bud'e murya ya kwala kira, a guje ya shigo ya tsaya gaban sa. "Lock him up." Ya fada yana nuna masa Farouk dake tsaye kamar an dasa shi, yasan dama hakan zata faru. "Yes sir!" Ya amsa da sauri ya chakumi wuyan Farouk kamar kayan wanki. Tirjiya ya fara yi yana magiya "Daddy please ka saurare ni, dan Allah Daddy." Ko gezau beyi ba, sai ma hade rai da ya sake yi yana wa John mugun kallo "Me kake jira ne?" Da sauri ya karasa janshi, ya fita dashi. Tsaki Daddy ya ja ya tashi ya bar falon baki daya. DAURIN GORO😢😢😥😥😓 ZAFAFA BIYAR KAUNAR MU: MAMUH GEE ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL DAURIN GORO:HAFSAT RANO. IGIYAR ZATO: MISS XOXO LITTAFI DAYA 200 BIYU 300 UKU 400 HUDU 450 BIYAR 500 *_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_* 2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_ saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863* *_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇 *09032345899* _Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_ : *DG* *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo     ©️Rano                     (6) *** Ina kwance ina ta kallon inno tana hada kan abubuwa da suke dakin, Nura ne ya shigo ya karba sannan ya fita dasu, kamani tayi ta lulluba min wani babban Mayafi muka fito, a hankali nake tafiya cikin wani yanayi mara dadi da ba zan iya tantancewa ba, har muka isa gaban motar da ban taba ganin irin ta ba, soja ne ya bude mana gidan baya muka shiga, ya rufe sannan muka dauke hanyar kauyen mu, kasancewar motar rufe take ruf da bakin gilashi hakan ya hana mutanen gari kallon mu, sai dai na lura duk in da muka bi sai an bimu da kallo. A kofar gida ya ajiye mu, Inno ta sake jan mayafin ta kare min fuska ta sosai ta fito dani, mata ne a tsaitsaye kowacce ta fito jin mota, da sauri Inno ta ja hannu na muka shige gida tana hararar su. Muna shiga matan gidan mu suka taso, kowa yana min sannu wadda ta kasance da biyu, daki Inno ta tura ni ta dawo wajen su tana amsa gaisuwar da suke min ta munafurci da gulma. Sun dan jima ina jiyo sautin karadin su, har suka watse, daga nan bacci ya dauke ni, ban sake sanin me yake faruwa ba. A bangaren gidan Maigari kuwa ya aikata aka kirawo su Baba da Daddy. Inno najin hakan ta rufo ni a daki ta yafa mayafinta ta bisu, Baba be isa ya hanata ba sai dai babu yadda ya iya. Suna zuwa Daddy ma yana zuwa cikin shigar fararen kaya manya, cikin girmamawa suka gaisa gaba daya, Inno na makale a gefe tana jiran taji dalilin kiran. "Abin da yasa na tara ku anan..." Maigari ya soma "Maganar da mukayi akan yaran nan, da kuma alfarmar da shi Alhaji ya nema ta a yi koma a kwana biyu, ina ganin abu daya da zamuyi wa yarmu shine aure, dan babu wani mutum a kaf kauyen nan da zai karbi auren ta, dan hakan ta taɓa faruwa a baya, a karshe saboda yadda yaran gari suka sako ita yarinyar a gaba yasa ta aikata abinda duk beyi mana dadi ba, shiyasa muka yanke hukuncin idan hakan ta sake faruwa, toh duk wanda aka tabbatar da ya aikata hakan xa'a aura masa yarinyar." "Gaskiya ne." Duk suka amsa cikin gamsuwa. "Toh yanzu Alhaji idan ka shirya, sai a gabatar da komai a nan." "A shirye nake ranka ya dade, duk abinda ake bukata sai a sanar dani." "Gaskiya ina da ja wallahi." Maganar Inno ta katse su, "Ina dah ja maigari, ya kamata ace a matsayi na na uwar yar nan anyi shawara dani, amma ace kawai a yanke hukuncin yi mata aure babu izini na, yarinyar da dududu nawa take, gaskiya ni ban yarda ba." Da tsananin mamaki suke kallon ta, babu uwa daya a kauyen nan kaf da irin hakan zata faru har ta tsaya jayayya, kamar bata san kalar wulakancin da yarinyar zata fuskanta ba? "Menene dalilin ki, na kin abinda muka zo dashi?" Maigari ya wurgo mata tambayar "Allah ya taimake ka, ni dai kawai bana so ne, ban yarda ayi mata aure yanzu ba, batun maganar mutane kuwa suyi tayi, zan san yadda zan ɓullo musu." "Kaji abinda maidakin ka tace Malam Ayubah, yar nan dai yarku ce, ku kuka haife ta, duk soyayyar da zamu nuna mata ba kamar wadda kuke yi mata ba, menene ra'ayin ka akai?" "Ranka ya dade ni dai na amince da maganar auren, ina ganin hakan shine kawai sauki." Ya fada ba tare da ya kalli bangaren Inno ba, dan yasan idan ya yarda suka hada ido ba zata taba barin sa ya aikata zabin zuciyar sa ba. "Sauran yan uwan yarinyar, shin kun amince ko kuwa?" "Mun amince." "Masha Allah, toh ke sai kiyi hakuri, dama aure a hannun Iyayen maza yake." "Alhaji Bismillah." Matsowa Daddy ya sake yi ya zura hannu a aljihun sa ya ciro kudi, alama yayi wa da driver sa ya fito da sauran kayan dake booth ɗin, ganin haka yasa Inno fashewa da kuka ta yi saurin fadawa gidan mai gari. Bisa ga shaidu da wakilan kowanne bangare aka shiga gabatar da daurin auren da ya zamo tsanin farko na duk wata rayuwa da Aminatu zata taka a gaba. *** Cikin dare ta kasa bacci, babu abinda take sai juyi, bata san yadda zatayi ba, idan har auren nan na nufin katanga da cikar burin ta, zata iya komai akai, duk da babu wanda yasan abinda ya faru sai mutane uku kachal a duniyar nan, amma ba zata bari damar ta ta karshe ta kwace mata ba, wanda auren nan yana nufin rugujewar komai. Har akayi asubah tana bitar abu daya, bata jira gari ya gama haske ba, ta tashi Aminatu ta bata kunu, ta ballo mata magungunan ta ta bata sannan ta dauki yar karamar purse din ta da mayafin ta, ta fice daga gidan. Tafiya me nisan gaske tsakanin kauyen nasu da wanda ke makwabtaka dasu, sanda ta isa gari yayi haske sosai, mutum daya jallin jal data san sirrin ta, sirrin da yake shirin zama tarihi idan har ta aminta da wannan auren, wajen ta tazo, dan samun mafita. Da sallama ta shiga gidan duk matan gidan suka kalle ta cike da mamakin wannan zuwan nata da sassafe haka, gaishe su tayi a tsaitsaye bata damu da irin kallon da suke mata ba ta fada dakin wadda tazo wajen ta. "Akwai matsala kenan." Ta fada tana kallon ta har ta ƙaraso ciki. "Ita ce ta taso ni, ina cikin matsala wallahi harira, bansan ya zanyi ba." "Lallai ai naga alama, me ya faru hala? Ko dai wani abun ya samu yar mutane ne?" "Kusan haka." Ta cire mayafin ta ta zauna gefen gadon, sannan ta shiga bata labarin komai. Ajiyar zuciya Harira ta sauke bayan ta gama sauraron ta "Kema dai Inno kinyi sakaci, bayan kinsan dalilinmu da kudurinmu a nan gaba, amma kikayi sakaci da yarinyar mutane har wannan abin ya faru da ita, kina ganin zasu yarda ne su kyale mu duk ranar da gaskiya ya fito? Bayan irin rikon da sukayi wa namu d'an." "Duk nayi dana sani wallahi, zuciya ce ta d'ebe ni, amma yanzu na gano kuskure na, ki taymaka nidai da shawarar yadda za'a yi da auren nan, idan yaran nan ya dauke ta suka bar kauyen nan kina ganin zai sake dawowa da ita ne?" "Gaskiya dai, gashi kince an riga an daura auren." "An daura wallahi." "Toh mafita daya ce gaskiya idan zaki iya..." "Zanyi koma menene idan akan d'ana ne." Murmushi harira tayi ta matso kusa da ita. *** Kamar kayan wanki haka suka fito dashi, a kwana biyun da yayi duk yai baki ya rame sosai kamar ba shi ba, kauda kai Daddy yayi daga kallon sa, sun riga sun fito a shirye zasu tafi, Dada kawai za'a bari itama dan tace babu inda zata ne, gashi ba zai iya musu da ita ba. Su Ja'afar kuwa tuni suka tsufa a can sai dai Daddy ya ja musu kunne akan maganar, baya son kowa yaji har sai ya dawo da kansa zai sanar musu. Atm card ya ciro ya wurga masa, sai mukullayen gidan. "Gashi nan, tun da kalar rayuwar daka zaba ma kanka kenan." Da sauri ya kalli daddyn, sanin hakan me yake nufi ne yasa ya hau rokon sa "Daddy dan Allah ka tsaya ka saurare ni, wallahi ban aikata abinda ake zargi na dashi ba." Da wani mugun kallo ya dube shi "Ni sa'an ka ne Farouk? Ko ka fara shaye-shayen ne dai da gaske?" "Wallahi ban taba shan komai ba, ka saurare ni kadai nayi maka bayani, wallahi bani da laifin komai." "You must be a fool, nace baka da hankali sam, idan har kana ganin zan tsaya sauraran ka bayan da kanka ba wani ya matsa bakin ka ba ka amsa laifin ka a gaban kowa, sannan yanzu kazo min da wani banzan zancen ka, toh kayi karya wallahi." Riko ƙafafuwan sa yayi da sauri yana sake sakin kuka "Wallahi ban aikata ba, bansan me ya hau kaina ba na amsa, dan Aallah Daddy kar kuyi min haka." Buge hannun sa yayi ya janye ƙafarsa yana matsawa. "Idan ka gama haukan naka zamu wuce." "Daddy ka taimaka min, maganar karatuna fa dan Allah, wallahi ban aikata abinda kake tunani ba, taimakon ta kawai nayi, wanda na dauke ta tamkar Amal." Tsaki Daddy yaja, ya gaji da jin wannan shirmen nasa, bashi da lokacin da zai kara batawa ya saurare shi, duk wata hujja tasa bata da amfani tun da be kawo ta a lokacin da ya kamata ba, ko a gaban alkali ne to Tabbas ya tabbata mai laifi tun da har yayi saurin amsawa. Duban shi yayi, baya so ya karya masa zuciya, saboda haka ya nuna shi da hannun sa "Kai yanzu ai na gama da kai, ba zan iya tsayawa sauraren shirmen ka ba. Maganar karatu kuwa in kana so zaka iya neman admission ka soma karatun anan, kar dai ka manta akwai responsibilities na matar ka kanka, so you have to be very careful." Hannu ya watsa baya ya juya cikin takun kasaita ya fada mota, Amal ce suka fito da Dada tana kuka sosai akan dole ba zata tafi ba, da sauri ya rarrafa gaban Dadan yana sakin kuka me tsuma rai. "Dada kiyi min rai dan Allah, Daddy ya dau zafi sosai yaki saurarata." Dago shi tayi ta bude kofar falon ta tura shi ciki ta rufe, motar ta nufa rike da hannun Amal, daddy na ganin haka ya fito. "Ka barta ta zauna tare dani har zuwa lokacin da za'ayi resuming makarantar su, sai azo a tafi da ita dan Allah." "Duk yadda kika ce haka za'a yi, mu zamu wuce." "Allah ya kiyaye hanya, ka kara nazari akan hukuncin da ka yanke wa Babana, duk abinda ka shirya sai ka sanar min a waya." "Shikenan in Sha Allah." Matsawa baya sukayi motocin suka fice daya bayan daya, ajiyar zuciya ta sauke ta kama hannun Amal suka juya ciki. Kaiwa kawai yake da komowa a tsakiyar falon, yana jin an bude yayi wajen ta da sauri ya fada jikinta yana sakin kuka. Bata hana shi ba, tasan zuciyar sa a cunkushe take kukan kadai zai rage masa radadin da yake ji. Ya dau lokaci sosai yana kokawa da zuciyar sa, yana jin kamar ya hadiye ta ya huta da radadi da zafin da take masa, a hankali ta fara sanyi sakamakon addu'ar da yaji Dadan na tofa masa, da sauri shima ya kama yana karanto innalillah wa inna ilaihi raji'un. Sosai hakan yayi masa tasiri kwarai, zamewa yayi ya zauna akan tiles yana sauke kansa kasa. "Babana..." "Tashi ka shiga kayi wanka ka gyara jikin ka, dukkan tsanani yana tare da sauki, kuma komai zai warware cikin ruwan sanyi. Ka cigaba da addu'a." Be musa ba, illa mik'ewa da yayi yana nufar dakin sa cikin tafiyar da tafi kama da wanda ya kwanta jinya me tsawo. ***Ina kwance yau ma kamar ko yaushe tun barowar mu asibiti bana iya aiwatar da komai sai abinda Inno tace, komai yimin ake abinci ma sai ta bani a baki, shigowa tayi tana tura kyauren dakin namu, gefen da muke ajiye kayan mu ni dasu Karime ta nufa, ta jawo ledar kayana ta fito dasu, set uku ne an wanke su sai hijabi daya da mayafi yellow, wata ledar sabuwa da alamun ita ta shigo da ita ta bude ta zuba kayan, takalmi na guda daya samfurin sukwal ta jawo shima ta saka min, sai dan kunne da sarka duk suma na sallah ta ne, ina kallon ta har tapp gama tana jan tsaki. "Tashi kije ki watsa ruwa maza." Mik'ewa nayi na amsa da toh na nufi bayin dake tsakar gidan mu, su Hanne na gani da su Karime sun cin kwalliya sun sa sababbin kayan su na sallah, kamar na tsaya yi musu magana sai kuma na fasa na shiga wankan. Mintuna kadan na fito na sake wucesu na shige ciki, da hannu Inno ta nuna min kayan dake ajiye a gefen tabarmar dakin. Dauka nayi na saka na koma na zauna ina tunanin inda zamu ake ta wannan shirin. Fita tayi ta barni a nan, ina ta jiyo hayaniyar yaran gidan sama sama, da gudu naji karime ta shigo gidan tana kiran Inno "Ga motar chan tazo Inno." "Naji me bakin aku." Ta katse ta tana hararar ta, mamaki ne ya kamani, yau Inno ce ke cewa karime me bakin aku, lallai ba karamin bacin rai take ciki ba. Shigowar ta dakin ne yasa nayi saurin kallon ta "Tashi maza ku kama hanya, saura inji ko in gani, ba dadewa zakiyi ba zaki dawo." Da sauri nace "Ina zani Inna?" "Ban sani ba, tashi nace ki wuce suna jiran ki." Tashi nayi jiki a sanyaye na fito tsakar gidan, Yalwati da Babar su Hanne na gani a tsaye duk sun sha lullubi, kamoni sukayi muka nufi kofar fita daga gidan. Motar dake ajiye a waje aka bude mana muka shiga, sai a lokacin naga Hanne da Karime a gaba, ajiyar zuciya nayi na ɗan ji sauki tun da bani kadai bace. Ina ji aka tashi motar muka dau hanya. Wannan tafiyar tana daya daga cikin shafukan rayuwa ta da bazan taba mantawa ba. Rano 😍   ©️®️HafsatRano *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                       (7) ***Tafiya kadan mukayi muka isa gidan, da mamaki nake kallon gidan, gidan da nake da muradin zuwa a koyaushe, murna na hau yi Yalwati tayi saurin hararata, da sauri na nutsu, aka bude mana bayan motar ta gama daidaita a harabar gidan da nake wa kallon aljannar duniya. Tsallen murna su Karime suka hau yi Yalwati ta daka musu tsawa, sum sum sum suka dawo bayan ta suka makale, kofar dake kallon mu wanda ya kawo mu ya nuna mana. "Bismillah hajiyan na ciki ai." Sake riƙe ni gam sukayi muka nufi kofar, kafin mu karasa aka budo kofar aka fito, matar nan ce ta asibiti, da fara'a ta tarbemu,tayi mana iso cikin falon, wani irin azababben sanyi me hade da sanyayyen kamshi ya kaiwa kofofin hancin mu ziyara, ina kallon Babar su Hanne na sake bude kofofin hancin ta sosai tana shaƙar iskar da tayi mana maraba, duk muka rabe a kasa nida su Karime, aka shiga gaisawa cikin mutuntawa. Nidai ina ta son kallon ko ina a falon amma babu dama saboda yadda Yalwati ke kara rufa min fuskata, bansan dalilin da yasa take min hakan ba, bayan na ga su Karime da Hanne an bar su suna ta shan kallon su. Ina ta hasashen ina ma nice na more kallon nan. Chan na kurawa katotuwar talabijin din dake girke a bango ido ta cikin mayafin duk da ba wani sosai nake gani ba, wasu mutum biyu babba da yar matashiya suka shigo dauke da manya manyan farantai, ina kallo suka dire gaban mu aka sake gaisawa sannan suka juya suka fice. "Bismillah ga abinci." Matar ta fada tana nuna wa su Yalwati kwanukan da aka jere a gaban mu, wanda tuni kamshin ya fara sawa na manta yanayin dana baro, ina ji na kamar babu sauran damuwa ko takura a cikin rayuwa ta. Kamar su Yalwati ba zasu ci abincin nan ba, ina ta addu'a har sai dana ji matar ta sake musu magana, sannan suka sauko kowa ta hau diba dan dama nasan kawai kara sukayi wanda ni sam ban san su da ita ba. "Amal!" Ta bud'e muryar ta tana kwala mata kira, da sauri ta shigo, turus tayi ganin baki taki karasowa "Ƙaraso mana kika tsaya." Shigowa tayi tana sake kallon mu. "Ga kawar ki nan rike ta ku shiga ciki." Hannu na ta kama, muka bar falon, mayafin na cire muna yin gaba, kallo na tayi tace "Laaaaa Aminatu." "Na'am." Nace mata ina murmushi "Yaushe kika zo?" "Yanzu muka zo, nan ne gidan ku ashe." Daga min kai tayi "Zo muje kiga daki na." Da sauri na bita, muka shiga dakin nata, dan karamin gado sai single wardrobe da toilet, kan gadon muka fada muka saki dariya a tare. "Dakin ki mai kyau." Nace ina kallon ko ina, a raina ina raya dama nawa ne. "Thanks." Ta amsa tana murmushi "Bari na kawo miki chocolate din da Ya Farouk ya siya min." Ta fita da sauri, tashi nayi na bude kofar toilet din, tsayawa nayi ina kallon mamaki, bansan ina ne nan ba, na dai ga alamun akwai ruwa a ciki. Rufewa nayi na koma gadon na hau, na mike kafata ina murmushi. A raina na shiga raya dama daki na ne dana more. Dakin Farouk ta nufa tana kwala masa kira, yana zaune da waya a hannun sa suna magana da Ja'afar ta shiga, kallon ta yayi ya mata alamar tayi masa shiru, tura bakin ta tayi ta nufi in da ta bar kayan chocolate din nata ta dauka, har zata fita sai kuma ta dawo ta tsaya a gaban sa tana dariya "Kawata Aminatu ce tazo, tana dakina." A dan rikice ya kalle ta "Ina zuwa zan kira ka." "Me kika ce? Su waye suka zo?" Ya fada yana mik'ewa "Kawata Aminatu." Da sauri ya dafa kansa, da gaske kenan anyi aure, wani irin yar yaji tun daga kansa har tafin kafarsa, tunanin kalmar auren kadai na sa shi a wani yanayi. Ashe da gaske Daddy yak masa, kwata-kwata yarinyar nawa take, da har za'a yi mata aure. Gaban mirror ɗin dakin ya isa yana kallon kansa. He's to young for that, idan be manta ba next month zai cika 22years chif. "Ya Salam." Ya furta yana fadawa gadon "Me nayi wa rayuwa ta ne? Na daure kaina da kaina, yanzu idan Mummy ta samu labari ya zanyi?" Da sauri ya tashi, farar singlet ce kawai a jikin sa, sai dogon wando, ciwukan jikin sa na nan musamman na fuskar sa, dakin Amal din ya nufa da dan saurin sa, ya bude kofar da karfi. Suna zaune sun baje a saman gadon suna kwasar chocolate. Tsaye yayi yana kare musu kallo, da sauri yaga ta rufe idon ta ta sauke kafarta kasan gadon, kallon kansa yayi ya sake kallon dakin "Menene?" Amal ta tambaya tana kallon na. "Tashi ki rakani wajen su Hanne, kar naje ana jirana zamu tafi." "Kai dan Allah, ki kwana mana." Make kafada nayi, takowa ya shiga yi har ya ƙaraso gaban gadon, ya sa hannu ya rike ni, zaro ido nayi ina kallon sa, sai kuma nayi saurin rufe ido na "Tsoro na kike ji?" Ya fada yana kallon saman fuskata Da sauri na daga kaina, dariya Amal ta kwashe da ita har da tafa hannu "Tsoron Ya Farouk kike ji, ai baya suka fa." Bata fuskar sa naga yayi ya saki hannu na, be ce komai ba ya juya ya bar dakin. Ajiyar zuciya na sauke ina kallon Amal din "Ni dai muje ki rakani." Tashi taga nayi yasa ta mike itama ba tare da taso ba muka fito wajen Dada. Babu kowa sai ita kadai, kallon ko ina na hau yi da sauri alamun neman abu. "Kuzo nan yarana, Aminatu me kike nema naga kina ta kalle kalle.?" Ta fada cikin son ta yi min wayo "Ina su Hanne?" Nayi narairai da fuska kamar zanyi kuka. "Kinga ke anan zaki zauna ke da kawarki, kuyi wasa tare, kuyi komai tare har karatu zan sa ana koya muku, idan kika kwana da yawa sai ki koma gida." "Har karatu ma zamu dinga yi, kuma ba zanyi girkin shinkafa da wake ba ko??" Na tambaye ta ina kallon ta. "Girki! A ah banda girki, ai kunyi kankanta sai an kwana biyu, sai share dakin ku kawai da wanke toilet, sai kuma sallah." Washe baki na nayi, cike da murna na ce "Ni ba sai an maida ni gidan mu ba ma, ki barni ana kawai." Dariya suka sa gaba dayan su, nima na bisu mukayi ba tare da na gane dalilin dariyar ba. Abincin dazu aka zuba mana, muka hau ci muna kallo, tuni na manta da komai, muna gamawa Dada ta dauko magani ta bani na sha, sannan tace muje muyi sallah, bazan tuna rabon da Inno ta sakamu sallah ba, babu ruwan ta da munyi ko bamuyi ba, muna idar da sallar muka dora kallon mu, ranar gaba daya ji nayi kamar nafi kowa farin ciki a duniya. Sai gaf da magriba sannan muka koma dakin Amal da a yanzu ake masa lakabi da dakin mu. **** Gidaje biyu ne manya manyan gaske wanda suka cinye kafatanin layin tun daga gaba har baya, iri daya ne sai dai daya yafi daya girma da komai. Da dukkan alamu mamallaka gidan akwai alaka me karfin gaske a tsakanin su, ko ta yan uwan taka ko ta abota. Gidan farko da yake dauke da tafkeken gate me matukar tsawo da fadi aka yi saurin wangalewa sakamakon karar horn, da sauri mutane biyun dake zaune akan dan bencin zaman maigadin gidan suka tashi suka nufi wajen motar. Babban mutum ne dogon gaske, cikin shigar alfarma ya fito daga ciki, hannun sa dauke da wayar sa yana amsawa, yadda yake magana kadai zaka gane yadda arziki ya samu babban matsuguni a wajen, rike yake da murfin motar har ya gama wayar kafin ya maida duban sa bakin yana murmushi "Sannun da zuwa Alhaji." Suka ambata a tare cike da girmamawa. Amsawa yayi yana duban chan hanyar gate din. "Wai tun da mukayi waya kuke zaune kenan, sannun ku da zuwa, Bismillah." Gaba yayi suka bi bayan sa har kofar da zata sadaka da babban  falon gidan, daya daga ciki ne yayi saurin bude masa, godiya yayi sannan ya shiga da sallama, babu kowa a falon nasa, sai sautin  suratul bagra dake tashi daga cikin jerin speakers din da suka karawa falon kawa. "Bismillah, Ina zuwa." Wuce su yayi ya haura corridor din da zai maidaka part din matar gidan. Yana shiga yaron dake kwance akan sofa yana kallo ya taso da sauri "Daddy!" Ya rungume shi, "Kamal, kana nan kana sana'ar taka ta kallo ko, yau babu islamiyya ne." "Malam ne yace yau ba zai zo ba zai je garin su." "Ah lallai, yau ranar hutawa ce." Kallon ko ina yayi kafin ya sake shi yana cewa "Ina Mamyn taka ne? Naji gidan tsit." "Tana daki, wai kanta ne yake ciwo na dame ta da surutu shine ta koroni." "Toh zauna na dubo ta, kai ɗin ne watarana akwai zuba kamar..." Buga kafa ya fara yi irin ta shawagabbun yara, dariya kawai yayi ya nufi dakin gimbiyar tasa. Tana kwance ta juya bayan ta ya shiga, yadda yaga yanayin kwanciyar ta ta yasa ya gane da gaske kan nata ke ciwo, dan dama gwanar ciwon kance, fasa tada ta yayi ya juya ya koma wajen bakin sa. Sun jima suna tattaunawa kafin su tafi, daga nan ya bada umarnin kar a bar kowa kuma ranar yana so ya huta sosai. Watsa ruwa ya fara yi, yaci abincin da ke jere a saman dining din part din nasa, sannan ya nufi bangaren Hajiyar sa. *** Gaba daya ran Inno a jagule yake, ta rasa yadda zata bullo wa al'amarin, gaba daya ji take dama bata amince da bukatar su ba, da tuni zuciyar ta na nutse bata da wani tashin hankali. Babban matsalar ta ma zuwa da tayi wajen Harira da ta tambaye ta labarin yaron ta, yadda ya amsa mata ya nuna cewa bata san komai akan halin da yake ciki ba. Tun bayan abinda ya faru da Aminatu, kullum bata samun isasshen bacci, bare yanzu da ta koma wani gidan sai take ganin kamar babu ita babu cikar burin ta. Duk da sunyi alkawari da Harira akan haka sai dai bata jin zata samu nutsuwa kenan har idan ba dawowa din tayi ba. Ita da zai yiwu ma da sun hakura da komai ta maida ta wajen iyayen ta, hankalin ta ya kara tashi ne saboda samun ainihin labarin waye iyayen ta, kuma dadin dadawa babu hannun mahaifiyarta ko mahaifinta a bin da ya faru, Harira ta rufe ta, ba ta sanar da ita duk wannan ba, yanzu idan suka ki yarda suka hada su dukka suka kulle su fa, bata tunanin duk duniya akwai wanda zai iya fito dasu. Haka zasu kare rayuwar su a ba wan ba kanin. Ita kam abubuwan sun mata yawa. *** *Sati Daya* Wasanmu kawai muke nida Amal, bamu da wata damuwa ko kadan, ina matukar jin dadin zaman gidan. Wajen yanayin jikina kuwa sosai magungunan da nake sha suka taimaka min wajen samun lafiya ta. Har na murmure abu na, kaya kuwa na Amal nake sawa kafin nima a karo min nawa kamar yadda Dada tace. Muna zaune a falon Amal na karanta mana wani story book duk da ba gane wa nake ba, idan ta karanta sai ta fassara min da hausa. Sosai hakan ke min dadi. Shigowa yayi fuskar sa babu walwala kamar ko yaushe ya wuce, duk ya rame yayi baki, ina ji dai ranar Dada na masa fadan ya saukaka wa kansa, damuwa babu inda zata kai shi, duk da hakan be chanja ba. Kullum yana aikin waya, a rana sai ya kira Daddy sau nawa ba tare da ya kosa ba duk da hakan baya dagawa, daga karshe ma sai ya sashi a blacklist. Har ya gifta mu sai kuma ya dawo da baya ya tsaya a gaban mu. Duk muka kalle shi a lokaci guda dan ba kasafai yake shiga harkar mu ba. "Me kuke yi?" Ya tambaya yana zaman a hannun kujerar ta gefen da nake. Mika masa littafin Amal tayi tana matsowa "Story book muke karantawa." "Kuna son mu fara lesson?" Da sauri muka amsa, murmushi yayi ya mika mana littafin "Shikenan anjima zamu fara idan nayi bacci na tashi." Murna muka hau yi ya wuce ya bar mu yana girgiza kai. Bayan wani lokaci sai gashi ya fito cikin shigar kananan kaya, yanzun ma wayar ce a kunnen sa suna magana da wani, zama yayi yana wayar yana kallon in da muke, har ya gama be dauke idon sa daga kanmu ba, tashi yayi ya wuce dakin Dadah, yau duk wunin ranar a daki tayi saboda ciwon kafarta da ya matsa mata,daga mu sai masu aiki sai yanzu da Ya Farouk ya dawo. Jim kadan sai gashi ya fito dauke da mukullin mota yana jujjuya shi. "Kuzo muje ku rakani." Yace yana yin hanyar fita, da gudu muka yi daki, muka sako takalmi muka fito, yana tsaye jikin motar suna magana da driver, muna fitowa ya bude mana baya muka shiga shi kuma ya zauna a gefen me zaman banza driver ya data motar muka fita daga gidan. Tunda nazo yau ce rana ta farko dana fita, murna sosai nake ina jin kamar muyi ta dawwama a irin yanayin da muke ciki a yanzu, kadan kadan nake tunawa da yan gidan mu shima ba ko yaushe ba, yawanci nafi tunawa dasu idan Amal tayi bacci ta barni. Bani da sauran matsala komai muke so mukeyi, sai nake jin kamar nafi kowa sa'a a duniya.   Fita daga kauyen namu mukayi baki daya muka shiga cikin gari, a bakin wani babban shago muka tsaya,ya Farouk ne kaɗai ya fita ya bar mu a motar, chan ya dawo da kaya ya zuba a booth sannan muka nufi wani shagon, haka mukayi ta yawo daga nan zuwa nan wani wajen ya shiga damu wani ya bar mu a mota. Bamu muka dawo ba sai yamma likis cike da gajiya dan Amal tun a hanya tayi bacci ta barni. ****Tun daga ranar muka fara karatu da Ya Farouk, kullum da abinda zamuyi, chan baya muke tafiya mu saka babar darduma mu baje sai mun gaji sosai yake kyale mu musamman ma ni, dan mafi ya yawan lokuta ni yake wa karatun dan ita Amal ta wuce wajen.   Muna cikin wannan yanayin Daddy ya turo aka tafi da Amal, ranar nayi kuka sosai nace lallai sai an maida ni gidan mu, da kyar shi da Dada suka shawo kaina na hakura na zauna, amma bani da wani kuzari tun bayan tafiyar ta ta wadda Dada tace min sun koma makaranta ne kuma ba nan kusa bane. Haka dai na hakura na cigaba da daukar karatu da yanzu yafi min komai a rayuwata. Wata na hudu cif a gidan, sau biyu su Karime suka zo ita da yan gidan mu suka wuni, suka tafi, anan ne suke fada min ai aure akayi min shiyasa nake zaune anan, kuma Inno ce take hanasu zuwa shiyasa. Ban dauki zancen nasu da muhimmanci ba, haka na tattara na cigaba da sabgata saboda ba karamin sabo nayi da Ya Farouk ba, gashi kusan kullum sai ya kira min Amal da daddare munyi waya.    Ranar da bazan taba mantawa da ita ba, nayi bacci na tashi kenan, dakin ya Farouk na nufa da sauri na ina tunanin ko ya zo tashi na ya ga ina bacci ya gudu bayan yayi min alkawarin yau zai kaini gidan mu har na wuni, kwana yace zanyi na fafure nace sai dai yini, yayi ta min dariya yana tsokana ta, ban damu ba,dan zama na anan ɗin yafi min dadi musamman ma saboda karatun da nake yi.   Tura dakin nayi na shiga bayan na kwakwasa ya bani izini, Yana lullube a bargo ya rufa har kansa, kiran sunan sa na fara yi ina k'arasa ciki. Cikin muryar bacci ya amsa min, dariya nayi na haye kan gadon ina jan bargon dan nasan ba bacci yake ba, mafiya yawan lokuta ya saba yi min hakan. Rike bargon yayi yana ja ina ja har na samu na bude masa fuskar sa. "Laaa bacci karya fa kake ya Farouk." Nace ina dariya, bude idon sa yayi cikin yanayin bacci ya zuba su a kaina "Bacci nake fahhh..." Ya fada cikin wata irin murya kamar ba tasan ba, jan bargon yayi ya sake rufawa nayi saurin janye wa ina sake yin dariya "Ni dai ka tashi, ba kaine kace zaka kaini gida yau ba." "AMINATU pleaseeeeee..., bacci anjima zan kaiki." 'Dage kafada nayi na sake janye bargon ina bubbuga masa damtsen hannun sa. Da wani irin karfi nayi ya riko ni, gaba daya na shige cikin jikin sa, ya jawo bargon ya rufa akanmu. A tsorace nake kallon sa, idon sa a kulle ya sake maidashi ya rufe, zura wa fuskar sa ido nayi kamar wadda ta fara ganin sa, na kasa kwakkwaran motsi, balle na yi yunkurin tashi. Takun tafiya naji yana tunkaro dakin, hade da karar abu kamar ana jan wani abu, janye bargon nayi daga saman fuskar mu na zuba wa kofar shigowa dakin ido tun da dama dana shigo ban rufe ta ba ina sauri. Cikin wata irin shiga ta alfarma, me cike da haiba tayi wa kofar dakin tsinke, tsaye take janye da yar karamar jakar matafiya, sai handbag din ta dake sakale a sangalalin hannun ta. Cikin mintuna da basu gaza biyar ba nayi mata kallon tsaf, yadda naga ta buda idon ta sosai akanmu ya ɗan tsorata ni, cikin tsananin mamaki naji ta kira sunan sa da d'an karfi. "Son!" A firgice ya dago idon sa ya sauka a kanta, yayi wani irin tashi da dukkan karfin sa har yana ture ni daga jikin sa, cikin sakin bakin ya furta "Mom!" DAURIN GORO😢😢😥😥😓 ZAFAFA BIYAR KAUNAR MU: MAMUH GEE ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL DAURIN GORO:HAFSAT RANO. IGIYAR ZATO: MISS XOXO LITTAFI DAYA 200 BIYU 300 UKU 400 HUDU 450 BIYAR 500 *_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_* 2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_ saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863* *_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇 *09032345899* _Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_ ©️®️HafsatRano *ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                       (8) *** Kallon mu take babu ko dauke ido cikin wani yanayi, ranta a matukar bace, da sauri ya isa gaban ta yana mika hannu zuwa wajen jakar kayan ta "Welcome Ma. Ashe kina hanya." Kallon banza tayi masa, ta wuce shi ta shigo dakin, har in da nake, bina ta cigaba da yi da kallo tana tabe baki kafin tace "Yanzu akan wannan ka zabi ka katse rayuwar ka, ka hakura da komai ka anan, yaushe ka zama haka Farouk?" Ta fada tana buɗe idon ta sosai akan sa "Mummy Please, ki huta sai muyi magana." "Naki na huta ɗin, kana son ka kashe rayuwar ka abanza kana cemin ma huta, saboda kai kafi kowa tausayi a duniya ko? Abin da kuma nazo na tarar fa, ko shima tausayin ne? Kuna kwance tare amma a waya kana nuna min kai kawai kana son taimaka mata ne." "Ya Salam... Mummy bafa abinda kike tunani bane." "Toh mene?" Ya fada a harzuke Kallo na yayi ganin yadda nake ta binsu da ido kamar na samu tv yace "Jeki dakin ki Aminatu, anjima sai na kaiki gidan ko?" Zumburo baki nayi cikin jin haushi na tashi na bar dakin, sakin baki tayi tana dubanshi. "Farouk!" "Mummy dan Allah, here me out, idan kika ji komai sai ki yanke min hukuncin da kika ga ya dace dani." "Farouk wanne abu kuma zanje bayan wanda ka fada min, Ja'afar ya fada min, akwai wani sauran point ne da ban ji ba?" "Ja'afar...?" Ya ambata cike da mamaki "Ban isa ya fada min ba ne ko me? Ina chan ni sam hankali na ya kasa kwanciya kai kana nan kana baccin ka da yar yarinya karama, toh wallahi an gama, munafukar kakar taku sai tazo ta warware wannan kullin da tayi, ko da bana gidan naku amma ido na na kan duk wani motsin ku, kuma wannan karon bazan yarda ba wallahi." Dafe kansa yayi ya juya mata baya da sauri, matsalar mahaifiyar su kenan, ya rasa dalilin da yasa a komai take blaming Dadah, bayan babu wani abu da tayi mata, shi yasa yayi ta iya kokarin sa na ganin ya kwantar mata da hankali amma sai da Ja'afar ya kai mata gulmar,  yana jin ta tana sababi kafin ta nemi waje daya ta ajiye kayan ta tana zaman gefen gadon. Dakin ya bari ya nufi wajen Dadah dan sanar mata kar sai ta fito su hadu, tana zaune akan babbar darduma da alama ta gama sallar walaha kenan, tana dan bitar karatun Alkur'ani, gefen ta ya zauna har ta kai aya ta rufe ta juyo tana murmushi "Babana an tashi kenan." "Uhum." Yace yana tankwashe kafarsa "Dama Mummy ce tazo." Ya fadi maganar kamar wanda baya so, shiru Dadan tayi cikin nazari, tabbas tasan zuwan nata ba zai zame musu Alkhairi su dukka ba, sai dai abu daya ta take tsoro shine yadda zata dauki maganar Aminatu, tasan ta sarai mace ce wadda take da son kanta, ba lallai ta fuskanci maganar ba, shiyasa take ta kokarin ganin Daddy yasauko ya bar su sun tafi baki daya, idan yaso Farouk sai ya koma makarantar sa ita kuma a sata a ko tasu Amal ce, sai dai hujjar daya bata na cewa wa'adin daya deba wa Farouk din be cika ba yasa ta hakura, sai dai zuwan mahaifiyar shi a yanzu yasa ta ɗan ji tsoron abinda zai je ya dawo. Duk da haka ba zata shiga hurumin da bana ta ba, d'anta ne   tafi kowa sanin ciwon sa. "Ah sannun ta da zuwa, yaushe ta zo?" "Yanzu." Ya amsa yana kallon yanayin ta "Madallah, sannun ta da zuwa." "Uhum." Kawai yace ya tashi "Dan Allah Dadah... Kinsan halin Mummy, karki bari tayi abinda ba dai-dai ba dan Allah." Kallon sa tayi ba tare da tace komai ba har ya juya ya bar dakin, tashi tayi ta koma saman gadon ta tana tunanin yadda abubuwan zasu zama. *** Kwanciya na koma nayi ina jin haushin katse min zuwa gida da matar tayi, ido na a lumshe kamar ina bacci aka turo kofar dakin, da sauri na bude ina kallon kofar, yana tsaye ya rike hannun kofar yana kallon ciki, tashi nayi zaune ina saukowa da kafata kasa "Ya Farouk wacece datazo?" "Mamana ce." Ya amsa min yana sakin kofar, ciki ya shigo ya zauna gefen gadon yana matso dani kusa dashi ssosai. "Kina son ta ko?" Ya tambaye ni yana kallon fuska ta, da sauri na girgiza masa kai alamun a'ah, ware idon sa yayi gaba daya akaina. "Are you serious! Mamana ce fa." "Eh ni bana son ta." Na faɗa cike da yarinta Da sauri ya rufe baki yana harara ta "Kar na sake ji kin fada, kice kina son ta." "Ni toh ba masifa take maka ba, ni bana son ta, ni kai kadai nake so sai Amal,sai yan gidan mu." Murmushi naga yayi, ya rike hannu na cikin nasa ya murza a hankali "Ni kina so na ko?" Ya tambaye ni "Eh mana, kana da kirki ai." "Toh idan kina son na, kiso mummy ma kinji." A cunkushe na amsa da toh "That's my girl." Yace yana mik'ewa. A nutse ya juya ya bar dakin ina kallon sa har ya gama ficewa. ***Waya ce a rike a hannun ta sanda ya shiga, yanayin da take magana ya gane akan sa take wayar, kai tsaye wajen kayan sa ya nufa ya tattara abubuwan da zai bukata ya kai chan dakin su Ja'afar ya zuba sannan ya shiga Kitchen yasa masu aikin gidan suka bashi breakfast ya kai mata dan yasan bata karya ba. Ko da ya koma ta gama wayar tana dan dube dube a cikin iPad. "Mummy gashi nasan baki yi breakfast ba, in Kika gama sai kije ku gaisa da Dadah pls tasan kinzo." Tabe baki tayi ta ja tray din gaban ta ta bude, juyawa zaiyi ta dakatar dashi "Ka daina gudu dole muyi magana kaji da abinda nazo, ba zama nazo yi ba ina da abubuwan yi da yawa." "Watsa ruwa zanyi sai nazo muyi maganar, kiyi hakuri." "Yayi, ina jiran ka." "Ok." Yace ya nufi dakin Aminatu, budewa yayi ya ganta tana kokarin zuge zib ɗin doguwar rigar dake jikin ta, karasawa yayi ya taymaka mata ta cire sannan yace tayi wanka ya kaita, da gudu tayi toilet shi kuma ya nufi dakin su Ja'afar da ya zama nasa a yanzu. A gurguje ya shirya ya fito dan baya so taje neman sa dakin sa, baya so sam su hadu ita da Mummy su biyu ba tare da shi din a tsakani ba. Aikuwa a hanya sukayi kicibis ta tafi dakin nasa, riko hannun ta suka juya zuwa hanyar fita murnar ta take tsayawa. Babu driver da alama Dada ta aike shi, sai driver mummy shi kuma baya so ya nuna masa gidan dan be san abinda mummyn zata iya aikatawa ba. Kawai sai ya yanke shawarar su tafi a kafa tun da babu nisa. Fita sukayi a kafa hannun sa sakale cikin nata, tana tayi masa hira duk yawanci akan wayar su da Amal ne, sama sama yake sauren ta, hankalin sa ya tafi akan yadda zai ɓullo wa Mummy. Sun kusa isa gidan suka yi kicibis da Garbati da Ilu, da mamaki suke duban su, sam Garbati be yi tunanin abin a iya nan zai tsaya ba, wani haushi ne ya taso masa, yayi saurin shan gabansu, da sauri ta koma bayan Farouk din tana buya. "Me hakan?" Farouk ya fada bayan ya haɗa girar sama data kasa. "Babu komai, kawai dai ajiya ta ta wajen ka nake dubawa, naga alama kuma dai babu wata matsala." Haushi ne ya kama Farouk, sai dai ba zai biye masa ba, dan yaga alama sam Garbatin baya cikin jerin mutane masu ƙwaƙwalwa, hannun ta ya damke sosai suka raba ta gefen su suka wuce kawai ba tare da yace komai ba. Haushi sosai ya kama Garbati, yaji kamar ya jawo shi ya ta bugun sa ko zai huce, haka yayi ta zage zage Ilu na bashi baki suka wuce in da zasu. A kofar gida ya tsaya ta shiga ciki ya tabbatar ta shiga sannan ya juya ya bar wajen. *** A tsaye na tarar da Inno wajen in da take kiwon ta, tana gani na ta saka min ido cike da mamaki, da sauri nayi wajen ta ina murnar ganin ta, murmushi ta k'ak'alo wanda ya zauna iya saman fuskar ta, ta ajiye abinda take "Ke kuma daga ina?" Ta tambaya tana yin gaba, bin bayan ya nayi lokacin su Karime suka ganni, ihu muka hau yi muka dane juna. Nan da nan aka fara shigowa daga cikin gidan namu zuwa gani na, hakan ya bata ran Inno ta kwala mana kira ni da Karime muka shiga dakin ta, waje ta nuna mana da hannun ta sannan ta fice ta bar mu a dakin bayan ta ja mana kunne akan karmu sake fitowa sai ta kiramu. Hakan da tayi ya rage masu shigowar dan sun sane abinda take nufi, hirar mu muka baje irin ta yarinta nida Karime ina ta bata labarin gidan Bature, murna take tana jin dama ita ce. Chan da azahar Inno ta kira Karime ta kawo mana dambu da wake, rabon dana ci irin abincin gidanmu an jima, ai kowa na saki ciki naci sosai harda k'ari, nasha ruwa nabi lafiyar katifar Inno na baje abina cikin jin dadi. **** Tun da ya koma gidan yaki yarda sam su hadu da Mummy, rufe kansa yayi a daki ya cigaba da aikin da yake na neman admission din sa tun wajen sati biyu da ya wuce, be samu gama wa shi yasa yau ya dage ya gama. Baya so ya kara bata wani zangon karatun a banza kamar yadda yayi wannan karon, shiyasa ya yanke shawarar chanja akalar karatun nasa zuwa abinda yake da tabbacin zai taimaka masa matuka wajen hukunta mutane irin Garbati. Knocking din dayaji a kofa yasa gaban sa ya fadi, kin magana yayi aka cigaba da knocking din, ya zata zata hakura ta tafi, ganin da gaske take yasa ya kashe komai ya mayar waje daya, ya nufi kofar cikin tafiya irin ta masu bacci. Budewa yayi tana tsaye ta harde hannun ta. Kallon da tayi masa ne yasa cikin sa murdawa, takardar hannun ta ta ware ta wurga masa. "Tun da kaki yarda muyi magana, sai ka duba wannan, kuma dole cikin biyu kayi daya, idan kuma ba haka ba, abinda da biyo baya ba zai maka dadi ba, dan na lura sam baka da hankali baka san ciwon kanka ba." "Mummy..." Juyawa tayi ta bar wajen bata ko sake kallon sa ba. Kasa ya tsugunna ya dau takardar hannun sa na rawa, layi cikin layi ya fara bin rubutun, gaban sa yayi wani mummunan faduwa, a take ya juya da mugun gudu ya nufi dakin da take, yana zuwa tana rufe kofar, bugawa ya hau yi yana kiran sunan ta da sauri "Mummy dan Allah karki fara, dan Allah Mummy, nasan me nake da hankali na wallahi, zanyi ko menene kika ce amma dan Allah karki min haka." Babu alamun zata saurare shi, zamewa yayi a wajen ya zauna kansa na juya masa. Manage 🙏😥©️®️HafsatRano *ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                       (9) ***Fitowar ta kenan zata dan taka kafarta ta hange shi a durkushe a kofar dakin sa, da dan saurin ta ta k'arasa "Babana?" Dagowa yayi idon sa sun kada sunyi ja ya kalle ta "Tashi muje daki na." Ta fada tana mika masa hannu, mik'ewa yayi cikin sanyi jiki yabi bayan ta, Mummy na jinsu ta tabe baki, babu wanda ya isa ya sata ta sauya ra'ayin ta akan abinda ta haifa, ba zata bari tana kallo a lalata masa rayuwa ba dan shi yafi kowa sauƙin kai. Suna isa dakin ya zame ya zauna kasan carpet din dakin yana jin zuciyar sa na tafasa. "Menene matsalar?" Ta saka masa ido, tana kallon yadda kirjin sa ke kaiwa da komowa. Shiru yayi ba tare da yayi magana ba ya mika mata takardar Mummy. Murmushi kawai tayi bayan ta gama karantawa ta mika masa, tasan zata aikata fiye da abinda tace ɗin, dan bata shakka ko kokonton hakan, sai dai babu yadda ta iya, musamman da babu wata alaƙa yanzu dake tsakaninsu da ita sai ta ya'ya, amma tana jan girman ta, bata so kuma wani abu ya shiga tsakanin shi da mahaifiyar sa. "Kayi mata abin da take so kawai Babana, shine zaman lafiyar kowa." "Dadah....?" "Shine maslaha, abu ne me sauki, kuma tabbas kayi kokari ma ladan ka yana wajen wanda kayi domin sa." Matsawa yayi jikin kafarta ya dora kansa a saman, zuciyar sa tayi rauni sosai, ba ya jin zai iya aikata abinda Mummyn tace, ya kuma rasa dalilin sa na son kin amincewa bukatar ta. Shafa kansa ta shiga yi tana ayyana yadda komai yake tafiya. "Babana..." Ta sake kiran sunan sa "Kana son Aminatu ko.?" Da sauri ya dago kansa jin tambayar a bazata, abinda yake ta kokawa da zuciyar sa kenan, ya rasa dalilin da yasa yake jin yarinyar har cikin ransa, komai nata yana jin kamar an haɗe shi da rayuwar sa ne, yanzu da Mummy ta kawo zancen rabuwa sai yaji kamar zare wani abu me muhimmanci ne a cikin rayuwar sa. Be san me haka yake nufi ba, sai dai yana daukar ta a matsayin wata babbar ƙaddarar sa. "Kana son ta ko?" Ta sake maimaitawa "Nima ban sani ba Dadah, kawai ina jin tausayin ta ne, She's too young for that, sannan na mata plan na good future,." "Shikenan, Ina da shawara, amma dole sai da taimakon mahaifiyar ta, kaga ni yanzu mahaifin ku ya matsa lallai sai na tafi saboda ciwon kafar nan tawa daya matsa min, da babu irin taimakon da ba zan baka ba, toh mahaifiyar ta ita kadai ce zata taimaka mana, wajen ganin mun samu abinda muke so." "Ta yaya kenan Dadah?" "Ka kai ta boarding school, ka damka amanar ta wajen mahaifiyar ta, ka sanar mata da kudurin ka nason ganin ta zama wani abu,nasan babu mahaifiyar da zata ki cigaban yar ta, kai kuma kaga sai ka dawo kayi wa mahaifiyar ka biyayya, kayi karatun ka, ka kara mallakar hankalin kanka, lokacin babu wanda zai fada maka yadda zaka yi da rayuwar ka, a lokacin sai ka dawo, ka cika burin ka." Da sauri ya tashi ya rungume Dadah, "Shisa nake sonki Granny, wallahi you are the best." "Ja'iri." Tace tana kai masa duka "Allah kuwa, gashi kin kawo solution cikin sauki, idan Daddy yaji labari sai nace masa makaranta na maida ita nima zan koma tawa, kinga ba zai ce komai ba." Daga masa kai tayi tana murmushi. Tashi yayi da karfi da kuzarin sa ba kamar dazun da ya shigo ba. "Bari naje na sanar wa Mummy na amince da komai data ce, sai na fara shiri." Ya fada cike da farin ciki. Fita yayi da sauri, a kofar dakin sukayi kicibis, basarwa tayi kamar bata gama jin komai ba tayi gaba ya bi bayan ta. Zama tai kawai ya shiga tsara mata zance. "Mom na amince da bukatar ki, amma dan Allah karki yi mata komai, bata da laifin komai bata san komai ba, idan ma hukuncin ne ni zakiyi wa, amma yanzu zan rabu da ita, zan biki mu tafin idan hakan zai saki farin ciki." Murmushi ta k'ak'alo wanda ya tsaya a iya saman fuskar ta tace "Madallah da kai, ka kyautawa kanka, ka kyauta mata, sai ka fara shirin tafiya dan bazan tsaya bata lokaci ba." "Kiyi gaba dan Allah, zan biyo bayan ki wallahi nayi Alk'awari, ki bari na dan karasa wani abu dana fara, ba zan dau lokaci ba." Dan jim tayi tana tunanin amince wa, kamar tace a'ah sai kuma tayi wani tunani. "Shikenan ni zan koma gobe, saura kaki abinda nace, kasan dai sauran ba sai na fada ba." "In Sha Allah hakan ma ba zata faru ba." "Jeka toh zan dan kwanta." Fita yayi ya ja mata dakin, ya wuce dakin Aminatu, budewa yayi ya haye saman gadon nata yana lumshe ido, tunanin yadda komai ya fara ya shiga yi, daga san da ya fita daga gidan zuwa yanzu da yake shirin daukar wani babban tsani a rayuwar su. Yadda komai ya zama kamar a film haka ya dinga bin komai daki-daki. Murmushi yayi ya mirgina gefe yana sake duban komai daya zama mamallakin ta a dakin sai yan abubuwan Amal. "My Destiny." Ya furta a hankali kamar me rada. Eh dole ya kira ta da Destiny dan shine kadai sunan da yake ganin ya dace da ita, ƙaddarar sa ce, wadda a yanzu yake jin babu wani abu da zai iya raba shi da wannan ƙaddarar. Haka ya jima a dakin har gabanin magriba kafin ya mike a kasalance ya fada toilet din dake manne a dakin. Alwala yayi ya fito ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskar sa. "A yau shafin rayuwar mu zai fara Aminatu, daga yau ba zan sake barin wani abun ki, ko cutarwa yazo kusa dake ba, nayi alkawarin zame miki babban tsanin cikar farin cikin ki ko da kuwa hakan na nufin... Ko da kuwa hakan yankewar nawa." A fili yayi maganar, sannan ya juya cike da karshashi ya bar dakin, sallah ya fara gabatarwa kafin ya nemi driver su tafi dauko ta. ***Ina zaune Inno na gefe tana ta aikin lissafin Kudi,yadda ta tsare ni a dakin gaba daya ya sa naji duk na gaji, tun Karime na tayani hira har itama ta gudu ta barni, gashi Inno ta kafa ta tsare ko ina, ina jin su suna wasa a tsakar gida kamar inyi ihu. Sai data gama ta tattare kan kudaden ta bude inda take ajiye wa tayi musu kyakkyawan boyo, har ta rufe sai kuma ta sake budewa da jawo wata jaka, bude cikin ta tayi ya dudduba sannan ta mayar ya rufe, ina kallon ta, ganin zata juyo yasa nayi saurin janye ido na, kallo na kuwa tayi tana juyawar. "Bacci kike?" Ta tambaya tana matsowa "Wasa nake son zuwa nayi nida su Karime dan Allah." "Ba zaki ba." Kawai tace tasa kai ta bar dakin, kuka na saka cike da jin haushi, duk sai naji dama ban zo ba, kallon tagar dakin nayi naga duhu ya fara zuwa alamun dare kenan, Ya Farouk be zo ya tafi dani ba, duk sai naji ina son tafiya. Addu'a na fara yi Allah yasa yazo. Jin shiru shiru yasa na kwanta lamo ina jin haushin kowa, da haka bacci ya fara fisgata. Sama sama naji Inno na taba ni. "Keeee...ke." Ta bubbuga min jiki na A gigice na tashi "Ya Farouk!" Na ambata ina mik'ewa, kallo na tayi kawai cike da mamaki. "Na'am." "Tashi maza ku wuce, kin hangame baki kina bacci ko tuwon baki ci ba." Da sauri na mike, na yayimi mayafi na na fito, a kan tabarmar gidan daidai kofar Baba na hange shi, kallo na yayi nayi saurin jan kafata zan karasa wajen, ji nayi an riko ni, Inno ce ta banka min harara, da sauri nayi kasa da kaina. "Ku wuce dare nayi." Tayi magana tana kallon bangaren su Baban. Tsam ya mike, yayi sallama da Baban sannan y fita, sai a sannan ta sakar min rankwashi a kai sannan tace su Karime su rakani. "Uwar rawar kai." Ta ambata tana jan tsaki. Daki ta fada cike da tunanin abin da zatayi. Ga maganar da yazo da ita wai makaranta zai sata ta kwana, kenan babu ranar da zai sake ta, bayan Harira ta karbi kudin ta tace ko wata biyu auren ba zai ba, sai gashi ana maganar wata biyar, idan tayi sake kuwa sai dai taji ana maganar suna. Dolen ta gobe ta koma taji in da aka kwana, ba zai yiwu ta zuba ido haka nan ba. ***Tun da muka fita bamu wuce gida ba, zakayi kawai muke tayi har bayan sallar isha'i, a mota suka barni suka yi sallah sannan ya je ya siyo mana tsire, sanda suka dawo har na fara bacci, tashi na yayi ya bani naman, ina ci na sake komawa na kwanta. Bansan yaushe muka koma gidan ba, ashe baya so mu hadu da Mummy ne shiyasa yayi ta jan komawar. Ban san me ya faru ba, nidai na farka naganni a dakin Dadah, tashi nayi na koma daki na na sake maida kai na cigaba da bacci na cikin kwanciyar hankali. Wajen bakwai da rabi na sake farkawa, sallah nayi na kwanta akan carpet din na cigaba da bacci. A hankali aka turo kofar, kallon gadon ya fara yi sannan ya hange ni a kasa. Banji takun tafiyar sa ba, kawai sai ji kayi an daga ni sama, dan karamin hijabin danayi sallah ya shiga kokarin cire min, na sake runtse ido na kamar me baccin gaske, ina ji a cire ya ajiye a gefe ya kwantar dani a gadon, ido na ne ya fara rawa alamun baccin karya ne. Murmushi yayi me sauti ya mintsine ni a hannu na "Wayyo." Na bude ido na ina kokarin yin kuka "Baccin karya ko?" "Na gaske ne fa, kaine ka tashe ni." "Umm amma idon ki yake ta rawa." Dariya nayi na tura baki gaba, kallo na naga ya tsaya yanayi sosai, babu ko giftawa, hannu nasa naja gashin idon sa cika da tsokana. "Ouch, kai kika min haka?" Ya tambaya yana taba idon nasa "Abu zan cire maka fah." "Karya ne." "Da gaske." Na saka dariya ina matsawa. Riko ni yayi ya dawo dani kusa dashi. "Kina son kiyi karatu ko?" Da sauri na daga masa kai na "Good... Zan saki a makaranta. Kina so?" "Ina so wallahi." Na faɗa cike da murna "Ok Tam, zan saki amma sai kinyi min alƙawarin zaki yi karatu sosai, sosai." "Zanyi Allah." "Good." "Toh yaushe zaka sani, kuma aina makarantar take." Shafa kansa yayi alamar tunani kafin yace "Yau zan fara zuwa neman makarantar, in Sha Allah zanyi kokarin ganin an samu, duk da ma anci term daya amma hakan zaki shiga ciki, sai kiyi kokari sosai ki kamo su." Murna na hau yi sosai kamar zanyi rawa, hannun sa ya rataye a saman kirjin sa yana kallo na, sauka nayi na jawo littafan da muke karatu dasu na fara jera su daya bayan daya. Be yi magana ba, sai murmushi kawai yake. Chan ya mike da sauri yana dafa kai, shaf yaso mantawa da tafiyar Mummy, abinda ma ya tashe shi da wurwuri kenan. Fita yayi yaja min kofar na cigaba da hada littafan cike da farin ciki. ***Har airport ya rakata, ba zatayi tafiyar mota ba wannan karon wai Lagos zata wuce akan wani kasuwancin ta, dole sai dai driver nata yabi bayan ta a mota ya koma gida, sanda suka isa ta kara jaddada masa alkawarin su, amsa mata yayi da toh da haka sukayi sallama. Be koma gidan ba, sai kawai ya bazama neman makarantar da zatayi daidai da Aminatun sa, makaranta yake so me kyau me tsada wadda zata taimaka mata kwarai wajen cikar burin ta, be damu da ko nawa za'a kashe ba, kudin da ya karba wajen Mummy da wanda yake dashi dana Daddy zasu ishe shi komai. Shi dai kawai ya samu ya tabbatar yayi wa dukkan su abinda suke so ba tare da ya fifita daya ba. Sai yamma sannan ya samu ya gama wasu abubuwan, duk da ba dukka ya gama ba amma yaci karfin komai, ya samu makarantar da tayi masa, har ma sun bashi damar ya kawo ta interview. A gajiye ya shiga gida, sallah kawai yayi yaci abinci ya sake shiryawa ya fita, gidan su ya wuce kai tsaye dan yana so su sake magana da mahaifiyar ta, a kafa ya taka a hankali kunnen sa sakale da earpiece suna magana da Ja'afar, har ya kusa karasawa gidan suna magana yana fada mishi yadda komai yake tafiya a gida. Daga nesa kadan yaga ta fito, cikin zulumi, kallo daya zakayi mata kasan ba a nutse take ba, da sauri ya kashe wayar yana kokarin tsaida ta yaga ta kara sauri, har zai juya sai kuma yayi tunanin ko babu lafiya, da sauri yabi bayan ta don tabbatar da babu wata matsala dan yanayin ta kawai ya nuna ba kalou ba. Tafiya take tayi  hakan kuma shima be fasa bin nata ba, kamar daga sama ta hango Harira tana nufo ta, ja tayi ta tsaya jikin wata bishiya har ta ƙaraso, ganin haka yasa yayi kokarin juyawa, sai dai kalmar da yaji yasa shi dakatawa yana kokarin ganin yaji komai "Wai Menene wannan kiran haka, kinga fa shiyasa kawai na yanke shawarar fitowa mu hadu a hanya dan yan gidan ma har sun fara zargin wani abu. " Hariran ta fada tana karasowa. "Maganar Aminatu ce kin sani ai, fisabilillah bayan kin min alƙawarin ko wata biyu ba za'a yi ba zai sauta ta dawo gida, shiru kake ji gashi ana maganar watanni biyar, kinsan me hakan zai haifar nan gaba." "Toh nidai bansan ina matsalar take ba, a gabanki na dauki kudin na bawa malam Tsalha da zauren gidan mu, ya tabbatar mana da ba za'a dau lokaci ba, toh ni bansan ina matsalar kuma take ba." "Ni duk ba wannan ba, yanzu gaba daya bani da kwanciyar hankali wallahi, ni idan zai yiwu kawai ki nemo Hajiyar nan, ayi magana, ta in da ake hawa ta nan ake sauka, na fasa wallahi gwara su karbi yar su." "Kamar ya? Abinda aka yi yarjejeniya, da zarar yaron nan ya kai matsayin da ake so ya kai din, sai ayi komai cikin sauki, amma yanzu daga farawa kice kin gaji, me ma akayi?" "Ba zaki gane ba, dalilin baki san yadda yaya suke a zuciyar iyayensu ba, ni kam gaskiya ba zan iya ba, nayi nadamar abinda kika sani na aikata, yanzu zuwa zakiyi ki bani addireshin su, na je na same su a warware komai, na maida musu da yar su, tun kafin ranar da nadama ta ba zatayi min amfani ba." Wani banzan kallo Harira tayi mata "Amma dai kamar ba a hayyacin ki kike ba ko? Kar ki manta su waye mutanen da kike cewa zaki je, kina tunanin zasu tsaya sauraren ki? Bayan haka ma wacce hujja kike da ita da zaki nuna musu?" "Jini ba karya bane Harira, wallahi suna ganin Aminatu ko ba'a fada ba zasu gane tasu ce, bayan haka kinsan dai ina da hoton mijin dana matar da muka dauka a saman file din asibitin su." Dariya Harira ta saka sosai hadda tafa hannu "Lallai Innaro, bansan ma kwata kwata tunanin ki baya ja ba sai yau, kinsan kuwa me kike shirin yi? Ina tabbatar miki da kina zuwa zasu kamaki su rufe ki, daga ke har zuri'ar ki kuwa babu wanda zai tsira." "Ki fuskance ni, akwai matsala ne idan aka cigaba a haka, wadda zamu shiga sai tafi ya yanzu wallahi, idan muka samu yaron nan ya tsinke igiyar auren, sai mu tattara mu mayar musu da yar su, in yaso ita matar data tsara komai sai su kare chan, nidai Buri na d'ana ya dawo, rashin sa ya fara tabani. Nayi nadamar komai wallahi." "Da kika gama kafa kanki da kudin da kika karba ba, ke fa wallahi san kanki yayi yawa, wato kinci moriyar ganga ko, toh bari kiji in fada miki gaskiyar magana, bansan in da suke ba, bansan aina za'a same su ba, rabona da su tun sanda muka rabu a asibiti, na yagi rabona, bayan wannan bansan komai akan su ba, ke wallahi ko sunan su ban sani ba, na sai tuna sanda Hajiyar take fada mana sunan da take so a sawa jaririyar, Aminatu MD. Daga wannan bansan komai akan su ba." Wani irin kukan kura Inno tayi ta  damki wuyan Harira, tuni kokawa ta rikice tsakanin su. Farouk dake tsaye a gefe yayi mutuwar tsaye tun sanda ya fara jin komai har zuwa sanda abubuwan suka dau zafi. Sosai maganar ta taɓa shi, wani irin mugun tausayin ta ya kara dirar masa fiye da wanda yake ji a baya, an cuci rayuwar ta, an raba ta da gatan ta, sai dai ya kasa gane dalilin daya sa suka aikata hakan, kenan babu sanin mahaifanta, toh wacece wannan data zabi rayuwar yarinyar ta lalace akan wani banzan burin ta mara tushe. Ya kasa gano hakan sai dai ya dau alwashin sai ya tabbatar da duk ya warware wannan daurin, ko da kuwa hakan na nufin.... Jin yadda suke abu kamar yara ne yasa shi magana cikin tsawa dan ba karamin bata masa rai sukayi ba. "Ku dakata!" A firgice suka juyo, wani irin bugawa kirjin Inno yayi, ta ɗora hannu a kanta kamar zata fasa ihu "Yanzu kune kuke kiran kanku matsayin iyaye? Masu tarbiyyar yayan su? Tir daku wallahi." "Faruku... Tsaya kaji, duk ba abinda kake tunani bane wallahi, yaudara ta akayi..." Katse ta yayi cikin tsananin bacin rai "Babu sauran girmamawa ko mutuntawa a tsakanin mu. A dah ina miki kallon uwa ne, wadda tasan ciwon kanta dana ya'yan ta, ina ganin girman ki,a matsayin wadda ta kawo Aminatu duniya. Sai dai a yanzu babu ɗaya daga cikin wannan da zai sa na cigaba da ganin girman naki, ki sani a yau ni Farouk, ni zan zame wa Aminatu uwa, uba da dukkan gatan ta, har zuwa lokacin da zan hada ta da iyayen ta, babu kuma daya daga cikin ku da ya isa ya raba auren mu, ƙaddara ce ta haɗa mu, kuma babu wani mutum da ya isa ya raba." Yana kaiwa nan ya juya a zafafe ya bar wajen, kwala masa kira take cike da tashin hankali, amma babu alamun zai tsaya balle ya saurare ta,kallo Harira tayi cike da tsana tace "Sai kin yi dana sanin abinda kika aikata min." Dariya ta saka harda tafa hannu tace "Ko ke kiyi dana sani ba, uwar yan son zuciya ai nice maganin irin ku." Ranoa: Hafsat Rano                          (10) *** Rai a bace ya shigo gidan, muka bishi da kallo nida Dada, be tanka ba, dan ko sallama a ciki ciki yayi ta yayi saurin wucewa dakin sa, yana zuwa ya maida mukullin kofar ya rufe, shiru mukayi baki daya babu wanda yayi motsi, ni a raina mamakin abinda ya sashi wannan tsananin fushin haka nake, ita kuwa Dadah ina kyautata zaton tasan tabbas koma menene akayi mishi ba karami bane. Har dare be fito ba, naje na buga dakin nasa yafi sau nawa baya budewa, duk na rasa ina zaka saka raina. Komawa nayi na shige cikin kujera nayi lamo na kasa ko cin abinci. Ina kwance na fara kuka kasa kasa, bansan dalilin kukan nawa ba, kila hakan na da na saba da yunwar da ke nukurkusata ne, jin karar bude dakin sa yasa nayi saurin tashi, shi dinne ya fito cikin shigar kananan kaya, fuskar sa tayi fayau kamar wanda yayi ciwo, tashi nayi na zauna sosai ban bar hawayen dake zuba a fuskata ba ya karasa sauka. Da sauri ya ƙaraso gareni ya zauna yana leka fuska ta "Kuka?" Ya tambaya yana mamaki. Daga masa kai nayi ina sake matsar kwallar. "Menene?" Ya furta yana matsar da hannu na daga fuskar tawa, goge min hawayen ya shiga yi yana girgiza min kai. "Karki kara kuka kinji? Babu abinda zai sake faruwa." Daga masa kai nayi ba tare da na gane abinda yake nufi ba, matsawa nayi baya kadan na sake kwanciya ina kokarin kama cikina da naji ya murda. "Kince abibci?" "Umm umm." "Ok Ina zuwa." Ya tashi tsam ya nufi Kitchen din, chan sai gashi da abinci a tray da ruwa, zama yayi a kasa ya tankwashe kafarsa ya nuna min kusa dashi "Oya..." Da sauri na sauko dama abinda nake jira kenan, tare muka shiga ci yana bani labarin makarantar da yaje, nan danan na ware na shiga yi masa hira nima, ni na kwashe kayan na mayar na dawo na zauna ina duban wayar sa dake saman kujera.. "Dan kira min Amal dan Allah na bata labari." Girgiza min kai yayi yana cewa "Karki fada mata, ki bari kawai sai dai tazo ta ganki da uniform." "Tohm shikenan." Nace ina murmushi. Mik'ewa yayi ya nufi kofar fita yana cewa "Kije ki kwanta kinji, gobe da safe zamu fita." "Toh." Nace ina mik'ewa dá sauri nayi daki. ***Da safe shine ya tashe ni, ya taimaka min na shirya muka fito, dakin Dadah muka wuce yana rike da hannu na, tana ganin mu ta riko ni tana sani a jikin ta, kallon shi naga tanayi cike da tsantsar tausayi. Girgiza kai kawai yayi yace "Zamu wuce Dadah, ayi mana addu'a." Hannu ta ɗora a kaina ta yi min addu'a, sannan ta rike hannun shi shima ta haɗa waje daya da nawa.. "Dan Allah Farouk karka yi wasa da abin da mukayi magana akai jiya, zan iya cewa kwana nayi ban runtsa ba ina tunanin komai." "In Sha Allah." Ya amsa mata Sakin hannun tayi tace muje Allah yayi mana albarka. Haka muka fito yana rike da hannun nawa har mota, wannan karon bayan shima ya shiga tare dani maimakon gaba, driver yaja muka dau hanya. Har muka isa makarantar be daina amsa waya ba, bansan da wa suke maganar ba amma tabbas maganar me matukar muhimmanci ce, lokaci zuwa lokaci yakan kalle ni ya sakar min murmushi. Sai daya ga mun doshi cikin makarantar sannan ya ajiye wayar, waje muka samu muka zauna har aka fara zuwa, ina ta kallon komai kamar almara, dandazon daliban dake kaiwa da komowa a cikin makarantar su suka fi jan hankali na, uniform dinsu ma kawai abin kallo ne, cikin tsafta da tsantsar nutsuwa. Sai wajajen goma da rabi sannan wani mutum yayi mana umarni da muka shigo, shiga mukayi muka zauna ya ɗan fita ya barmu. Kallo na ya Farouk yayi yace "Idan suka tambaye ki sunanki, kice Aminatu Farouk MD kinji?" Kafin nayi magana mutumin ya sake shigowa, zama yayi ya umarci ya Farouk ya ɗan jira a waje, fita yayi ya rufo mana kofar, kujerar kusa dashi yace na dawo, ya shiga yi min tambayoyi, da yawa ban san amsar ba, musamman bangaren turanci da lissafi, duk da na kan fuskanci wani abun saboda dan zaman da nayi da Ya Farouk da karatun da yake min dukka da turancin yake min su, sai dai ba komai ne nake ganewa ba duba da yanayi da makarantar da nake yi a dah. Tashi yayi ya leka ya sake kirawo shi. "Mr Farouk, mun mata interview sai dai fa she's left far behind, ya zata iya catching kuwa? I doubt so." Folding hannun sa yayi yana duban ya Farouk, murmushi yayi ya ce "Sir munyi duk maganar nan da principal, zamu biya kudin extra lesson da za'a dinga mata har Allah yasa tayi picking, and bani da doubt zata kamosu, tana son karatu sosai so ina da hope akan ta." "Ok Good, if that's the case, sai muyi komai yanzu, next week Monday ta zama full student, ina ga hakan zaifi." "Hakan ma yayi, thank you very much." "It's our pleasure." Tashi yayi yace ya mu biyo bayan sa, muka bishi wasu offices, duk wasu formalities bamu bar school din ba sai da muka gama su, a ranar aka bani komai har da uniform, murna da farin cikin da nakeyi ba'a magana, haka muka dawo gida ina rungume da komai kamar wani ne zai raba ni dasu. *** Dukkanin satin a cikin shiri muka karasa shi, sosai akayi min provision na dukkan abinda zan bukata, wannan karon Dada da kanta take tsaye akan komai, da ita aka gama shirya min komai. Sai dai ina lura kamar su ɗin ma hada kayan su suke tayi waje daya,sai dai ban kawo komai ba, na dauka ko wani abun dai zasuyi kawai, ana gobe tafiya makaranta dana matsu ina ji kamar na jawo ranar Dada tasa mai aiki ta rakani gidanmu. Gaba daya Inno tayi laushi kamar ba ita ba, ta rame sosai babu alamun walwala a tattare da ita. Kasa shiru nayi har sai dana tambaye ta ko bata da lafiya ne, ta bini da ido kawai ba tare da tace komai ba. Da muka zo tafiya ta dauko wata leda ta bani wai na makaranta ne, na karba nayi godiya na bawa mai aikin ta rike min, zamu tafi ta sake kirana daki ta hau min nasihar da bazan ce ga musabbinta ba, duk yawanci akan kula da karatu na ne, nidai kawai amsawa nake cike da mamaki, ban taba tunanin Inno zata min kwatankwacin hakan, duk sai naji babu dadi bana so na barta, da muka zo tafiya kuwa har da sharar kwalla ta cike da tausayin Inno da abinda yake damunta da bansan ko menene ba. Washegari da wurwuri na shirya tsaf cikin uniform d'ina sababbi kal, na zauna zaman jiran Ya Farouk, ina zaune shima ya fito, dan tsayawa yayi da baya yana kunshe dariyar sa, hatta jakar da komai na ajiye a gefe, zaman jiran sa kawai nake, karasawa yayi ya zauna yana dauke kansa. Ban gaishe shi ba, kawai na fara maganar tafiya, kin amsa min yayi ya wuce Kitchen ya hado tea ya fito. "Jeki nemi abu kici." Yace yana zama cikin kujerun falon, ganin fuskar sa babu wasa yasa na tashi tsam nayi Kitchen din, tea din nima na hado na dauko bread na fito, kamar magani haka nake ci cike da daukin tafiya, yana ta kallo na ta gefen ido har zuwa sanda ya gama ya maida komai Kitchen yazo ya fice, sauri sauri nayi na karasa na sake gyara komai na zauna ina kallon kofa. Chan sai gashi ya dawo dauke da wasu ledoji, a saman kujerar ya watsa su ya wuce dakin Dadah, jim kadan suka fito a tare itama ta shirya alamar tare zamu tafi. Da fara'a ta na gaishe ta, daga nan muka rankaya waje muka shiga mota ina ta murna kamar bakina zai yage. Uffan be ce min ba, yana dai noticing duk motsina. Haka nan yaji ba dadi, ko ba komai akwai matukar shakuwa tsakanin mu, amma hakan shine mafita ga dukan mu. Sanda muka isa makarantar sai naji duk babu dadi, Ina labe a bayan Dadah har aka gama komai, tuni fuska ta ta chanja dana ji an kirawo wata an ce ta tafi dani, da sauri na kankame Dada ina sakin kuka, dariya suka saka baki dayan su, hakan ya kara tunzura ni, hannu na ta kama cikin harshen turanci tace "muje ko?" Kwace hannu na nayi na sake saka kuka ina kallon Ya Farouk, shi dinma ni yake kallo, hannu yasa ya kirawo ni, da sauri na tafi gareshi, maimakon yayi min magana sai yaja hannu na muka fita daga office din, chan baya wajen wasu shuke-shuke ya kaimu, yana zuwa ya cika hannu na yana ja da baya. "AMINATU..." Ya kira sunana yana saka idon shi a cikin nawa, raw raw na sake yi da idon zan cigaba da kukan, da sauri ya furta "Ohh Ya Salam! Baki son makarantar ne?" Girgiza masa kai nayi na cigaba da kuka na. "Toh menene, kin fasa karatun ne?" Nan ma girgiza kai nayi "Bude baki ki faɗa min kinji." Ya fada yana sake matso wa sosai kusa dani, cikin muryar kuka nace "Ni ba tafiya zakuyi ku barni anan ba." Dan murmushi yayi kadan, yasan kwanan zance, lallashi na ya hau yi cikin son gamsar dani muhimmancin hakan, tare da alƙawarin zuwa duba ni kowanne lokaci, da kyar na sa kaina na amince, sai dai ban bar kukan ba, haka ya sani a jikin sa yana shafa bayana a hankali, lamo nayi na kasa kwakkwaran motsi, ina jin shi yana kokarin raba jikina da nashi jin takun tafiya, Dadah ce ta iso wajen tana nazarin mu. "Babana sallamar ta isa haka nan, karka manta fa muna komawa..." Kallon danayi mata ne yasa ta gimtse maganar tana yin gaba "Kuyi sauri dai ina mota ni, Aminatu Allah ya bada abinda aka zo nema, banda kawayen banza." Daga haka ta bar wajen dukkanninmu muka bi bayan ta da kallo babu ko kiftawa, a hankali ya kamo hannu na, ya ciro dan karamin akwati ja me masifar kyau daga aljihun sa, bude ta yayi dan karamin zoben azurfa ya bayyana, ya kama ring finger na ya zura min, yana kallon fuska ta. Babban harafin D cikin wata irin kwalliya shi ya karawa zoben kyau da kawa, kura ma hannun nawa ido nayi cikin tunani me tsawo da bansan me nake son tunawar ba. A hankali cikin wata iriyar magana ya furta... "Alk'awari kaya ne Aminatu, ki rike Alk'awari, nima zan rike, kiyi karatu, kiyi karatu har sai kin ji kamar kwakwalwar ki xata fashe, a sannan zan tabbatar da buri na ya cika, ina so ki zama cikakkiyar lawyer saboda wani kudiri nawa." Daga kai kawai nayi ina cigaba da kuka ganin da gasken tafiya zasuyi, gaba yayi kawai nabi bayan shi da sauri, haka muka jera har gaban motar, da wani irin sauri ya fada ba tare da ya sake kallon bangaren da nake ba, ina ji ina gani suka fice daga cikin makarantar. Jan kafafuwa nayi na wuce ina jin kamar wani babban bangare na rayuwa ta ya bar ni. ****Suna isa gida suka sauke Dadah, kai tsaye gidan su Aminatu ya wuce, Inno na zaune tana kulla kayan miya aka sanar mata da isowar sa, sai da gaban ta ya fadi, amma ta dake tace a shigo dashi dakin ta, shiga yayi ya zauna yana karewa ko ina kallo, a matukar sanyaye ta shigo dakin, bayan tasa Karime ta kawo masa ruwa, zama tayi daga chan gefe tana tunanin ta in da abubuwan zasu fara. ***Rayuwa na shiga yi sosai a makarantar, bani da wani lokacin kaina sai ka karatu, kawata daya ce Asma'u, tare muke karatu muyi komai, bani da wata matsala sai ta rashin Ya Farouk da nake matukar jin sa a jinin jikana. Lokacin visiting nayi sai gashi yazo, shi kadai yazo nayi ta murna, dariya kawai yake ina bashi labarin makaranta da wahalar karatun da nake, tun da ni kullum akwai wani extra lesson da ake min bayan normal lesson da muke yi baki dayan mu, hakan yasa nake shan wahala sosai, wani lokaciin ma sai naji kamar na sare, sai na tuna kalaman sa na ƙarshe, su ne suke sake zaburar dani dan ganin na cika masa burin sa kamar yadda yace. Lokacin da akayi hutun makaranta, sabuwar principal din da aka sake wadda na lura da zuwan Ya Farouk na karshe sun jima suna magana da bansan ta mecece ba tasa aka kirani, ta tabbatar min da ni bazan je gida ba, anan makaranta zan zauna wajen ta na cigaba da extra lesson d'ina, ranar wuni nayi ina kuka, haka ina ji ina gani kowa ya watse ya bar ni. Rayuwa ta haka ta cigaba da tafiya, ina iya kar kokari na wajen ganin nayi karatu, maganar zuwa gida hutu kuwa na rasa dalilin da yasa bana zuwa ɗin, tun ina damuwa har na hakura bayan munyi wata doguwar waya da Ya Farouk da wayar headmistress din, tun daga nan na watsar da komai na cigaba da karatu na ka- in- da-na- in. Lokacin da mukaje aji uku ne, akayi hutu sai ga mutanen da ban taba tsammanin ganin su ba, Ya Farouk ne tare da Amal, Dadah sai Inno da Karime, karamin hauka ne kawai banyi ba, amma tabbas zan iya cewa na jima banyi farin ciki irin wannan ranar ba, abu daya na kasa gane kansa, shine yadda Inno tayi laushi sosai, ta zama wata shiru shiru, duk in da nayi tana bina da kallo kawai, wani lokacin ma sai na ga kamar tana sharar kwalla, ban kawo komai ba, na cigaba da nan nan dasu, har suka zo tafiya, sosai naji son bin su, amma kuma nasan hakan ba me yiwu wa bane. Haka suka tattara suka tafi suka barni da tarin kewar su. Tun daga nan karatu na ya kara daukar zafi, babu wanda ya kuma leko ni, sai dai lokaci zuwa lokaci ya Farouk kan kira a wayar principal ta bani, kullum maganar sa daya nayi karatu, haka na cigaba da dagewa sosai. Zuwa lokacin zuciya ta ta gama sanin menene so, menene kauna, abinda nake ji game da Ya Farouk wani yanayi ne da zuciya da ruhi ne kadai zasu iya tabbatar dasu, baki na yayi kadan ya fasalta yanayin da nake ji game dashi din. Har muka shiga Ss2 be sake waiwayo ni ba, kiran da yake min sam ya daina, sai na dauki hakan a matsayin yana son yaga na yi karatu ne, aikuwa na sake jajircewa. Exams muka fara ta karshen Ss2, wadda zamu shiga ajin karshe, hakan ya sa na kara zama serious, bani da lokacin komai sai na karatu, sosai kuwa nake jin dadin exams din, ranar da mukayi final exams ne na fito ina tafiya a hankali, iska ake kadan kadan, yammaci ne me cike da ni'ima akwai alamun za'a iya ruwa kowanne lokaci, tafiya nake ina tunanin shi, iya sanin da nayi masa nasan shi mutum ne me matukar son yanayi irin na damuna, jin kamar ana min magana ne yasa na dan dakata ina juyowa, wata yarinya ce yar junior session, hannun ta rike da tarin littattafai. "Kiran ki ake a bayan garden din chan." Tace tana nuna min da bakin ta "Ni kuma, wake kira na?" Nayi tambayar cike da mamaki "Kije zaki gani." Ta amsa min tana wucewa abin ta, cike da mamaki na zuba wa hanyar garden din ido, mamakin me kira na nake, har zan wuce hostel sai kuma na fasa na juya zuwa hanyar da zata sadaka da dan karamin garden din makarantar, ina isa na shiga wurga ido na ko zan ga wanda yake kirana, ban ga kowa ba, tsaki naja kadan na juya da nufin barin wajen. Kamshin turaren sa ne ya daki kofofin hanci na, da sauri na juyo, ido na suka sauka akan sa, sanye yake cikin shigar Kufta baka, wadda tasha aiki sosai da bakin zare ɗinkin three quarter , kansa babu hula sai dai yana rike da ita a hannun sa. Cikin wani irin yanayi yake takowa gareni, na kasa ko da kwakwaran motsi balle nayi tunanin abin yi. Ya chanja kwarai, ya zama babban mutum, me cike da kwarjini da tsari, tsananin nutsuwa da tsagwaron hutu sun nuna kansu a tattare dashi, bayan wadannan abubuwan babu abu daya daya chanja a tattare dashi d'in, shine dai Farouk d'ina, wanda nake ganin sa a matsayin rayuwa ta, komai na. Hannun sa yasa ya murda a saman fuska ta ya bada sauti, da sauri na shiga kokarin boye fuska ta, tsananin kunyar sa ce naji ta rufe ni lokaci daya, wadda ban taba jin hakan ba sai yau din, wanda nake kyautata zaton hakan na da nasaba da yadda zuciya ta ke kara jaddada min matsayin da yake dashi a cikin ta. "My Destiny..." Ya kirani da sunan da dukkannin bangarorin jiki na sai da suka karbe shi, kasa daga kai nayi balle ya sa ran zan kalle shi, ina jin shi yana sakin dariya kasa kasa, kallon tsaf yake mun tun daga sama har kasa, a yau ya sake tabbatar da cewa Aminatun sa ta kai, ta isa dukkanin yadda yake da muradi. "Yau ni yar Aminene take jin kunya?" Ya furta yana dariya Da kyar na harhada kalmomin gaisuwa waje daya na furta "Ina... Wu..ni?" "Ah laillai, na yarda yau Aminatu na ta girma, kunya Aminatu? Ya farouk dinki ne fa, this is unbelievable!" "But I like it." Ya fad'a yana kawo bakin sa daidai kunne na. Da sauri na ja baya, hakan yayi daidai da zamewa ta, cikin zafin nama ya tare ni da dukkan karfin sa, ido na shiga zarewa kamar zan fita da gudu, hannun sa ya saka cikin nawa ya jani zuwa jerin kujerun dake zagaye a harabar wajen, banyi musu ba, na shiga bin sa, ina fatan abinda nake ji a yanzu ya zame min wani tsani da zan sake takawa na rayuwa, sai dai kash!. Rano: ONAR TASFAH                11 ©️®️HafsatRano *ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                       *** Hannun sa ya sabule daga jikin nawa ya zauna yana nuna min kusa dashi, a kunya ce na zauna, kafe ni yayi da ido na kasa koda kwakkwaran motsi, duk da hakan be dauke kansa daga kaina ba, yana so lallai sai yaga tasirin da idanun sa suke min, hannu nasa na kamo karshen hijabin nawa na shiga wasa dashi, bin hannun yayi da kallo yayi murmushi. "AMINATU... Wai Menene hakan ne? Kunya ta kike ji? Akan me?" Duk a lokaci daya yayi min wannan tambayar, ni kaina mamakin kaina nake ji yadda tsananin kunyar sa ta mamaye ni, na kasa kwakkwaran motsi, kwarjinin sa ne duk ya cika wajen, duk yadda naso na sake dashi na kasa, ina jin sa yana magana nayi kus kamar bana wajen, tashi naga yayi, ya zura dukkan hannayen sa cikin aljihun rigar sa, cikin jin haushi yace "Tun da haka ne, bari na tafi kawai tun da ba'a son gani na." Da sauri na rike hannun sa, "Dan Allah karka tafi." Hannun nasa ya kalla sannan ya kalle ni, ya kwashe da dariya, da sauri nayi kokarin zare hannu na amma sai ya rike "Baki isa ba ai, ana so ana kaiwa kasuwa." Dariya muka sa a tare baki daya, duk kunya ta sake kamani. Komawa mukayi muka zauna muka hau hira, mafi akasarin hirar shine yake min, duk da na dan sake kadan kar yace zai tafi. Acikin hirar ne na daure na tambaye shi karatun sa, wayar sa ya bude ya shiga gallery ya mika min, baki bude nake bin jerin hotunan nasa da suka gama bayyana irin karatun da yayi, no wonder na ganshi ya sake zama babba, ko ina na jikin sa ya murje, irin na ingarman namiji. "Soja Ya Farouk!"  Na faɗa ina kallon sa. Daga min kai yayi yana dariya "Burin both Daddy da Mom ne, sannan kuma burin Farouk dinki ne, saboda wani babban dalilin sa." Jinjina kai nayi ina sake kallon sa. "Ni da nake tsoron soja kuma..." "Sai ka mijin ki soja ba, sai ayi yaya? Karki manta fa ance... A wife of a soldier..." "Can never be a soldier." Nayi sauri amsa masa ina dariya. Dariyar shima ya saka ya kai hannu ya dungure min kai "Sarkin wayo, toh ba haka karshen yake ba." Muka kara saka dariya a tare. Hira muka cigaba ba dayi har zuwa sanda aka kira magriba, tashi yayi yana nannade hannun rigar sa. "Ya za'ayi?" Ya daga min kira sama, "Uhum." Nace ina tashi nima. "Kinga ba'a rufe makaranta ba sai gobe, wannan ma dan dai principal din ta hannun damar Mummy ce, kar mu shiga dokar makaranta, zan wuce, amma zan dawo gobe, kinsan da maganar zana waec dinki a Ss2 ko?" Daga masa kai nayi "Ok zamu je gida sai kiyi sati daya... Dagowa nayi da sauri, murmushi yayi min yace "Daga nan sai a dawo makaranta, kinga ba za'a dade ba zakiyi exams, kina gama wa..." Be karasa ba, yayi shiru yana sake fad'ad'a fara'ar fuskar sa "I can't wait ranar nan tazo, duk plans d'ina na ranar ne, Allah dai ya kaimu, zaki yi mamaki sosai." Bude baki nayi zanyi magana yayi saurin katse ni "Karma ki tambayi me zai faru ranar, kedai kawai ki shirya mata, it's going to be the biggest day of our lives." "Shikenan." Nace ina matsawa gaba. "Ba sallama?" Ya marairaice murya yana bude min hannayenku sa, sarai na gane me yake nufi, dariya nayi, na kara yin gaba, sosa kansa ya shiga yi yana kallo na, sai dana tabbatar nayi nisa daga in da yake sannan na daga mishi hannu ina masa gwalo, da hannu yayi min alamar zai kamani ne. *** Washegari tun da wuri na tashi, ina nan da d'abi'ata ta dauki idan zanyi abu na tashi da duku-duku na hau shiri, ina ji aka kad'a kararrawar assembly da ake yi a duk ranar da za'a rufe makaranta, a gurguje aka gabatar da komai da ranar da za'a dawo makaranta, kasancewar akwai sauran wajen sati uku kafin a fara Waec yasa aka bawa yan Ss3 hutun sati daya, sai kuma a dawo a fara karatun jarabawar kafin lokacin ta ya zo. Da haka kowa ya hau watse wa cike da farin ciki zuwa gida. Ina tsaye a saman barander classes dinmu na kafa wa gate ido naga shigowar shi, ji nayi kamar zan zame, haka dai na daure na nufi wajen motar, ina zuwa yana fitowa, idanun mu suka sarke waje daya, da sauri na janye nawa na hau gaishe shi, murmushi kawai yayi ya wuce wajen da aka signing, a gaggauce yayi signing din ya taimaka min na dau yan kaya na muka dau hanyar kauyen mu. Sanyin Ac da kamshin turaren da ya bulbula ne suka cika motar, lamo nayi jikin kujera ina jin wani yanayi ne wuyar fassara, magana yake min kasa kasa wanda zaka rantse ba dani ɗin yake ba, idon sa na kan titi sai dai hannun sa daya na rike da nawa yana murzawa a hankali. Har muka isa gida na kasa sakat, shi kuwa babu abinda ya dame shi, sha'anin gaban sa kawai yake cike da tsantsar farin ciki da ya kasa boyuwa a saman fuskar sa.   A kasalance na fito daga motar bayan ya tsaya, gaba nayi kawai dan Allah Allah nake na isa ciki na samu sauƙin abinda nake ji, ina shiga daki yana turo kofar, tsaye yayi kamar yadda ya saba a wanchan lokacin, hannayen sa jingina da makarin kofar, idanun sa na zagaya wa lungu da sak'o na dakin. "Garin sauri kin manta kayanki Madam." "Na manta wallahi." "Dole ki manta ai, kina gudu na, duk kin chanja Aminatu, what's wrong with you?" Ya fada yana takowa cikin dakin, saurin kasa nayi da kaina ina jin sanda yazo daf dani "Look at me." Ya furta a chan kasan makoshinsa, a dan darare na dago na kalle shin, sai naga ya cika gaba daya wajen. Tallafo fuska ta yayi ya dago ni "Kinsan matsayi na wajen ki ko? Kinsan dai ba zan cutar dake ba, then why are you behaving like this? Kamar kin ga bako." "Ni kawai kunyar ka nake ji Allah." Na faɗa kai tsaye. Dariya yayi ya saki fuskar tawa ya fada saman gadon dakin, tsaye nayi ina tunanin abin yi, ji nayi ya finciko ni na fado gadon kusa dashi, har saman keyata na buguwa da sangalalin hannun sa, matsowa yayi sosai yana kura min ido "Shekarar ki 17 if i'm not mistaken, ni kuma i'm 29, nasan abinda ya dace da wanda be dace ba, karki damu, babu wani abu da zan miki da nasan zaiyi hurting dinki, ki daina tsoro na ko kunya ta, ki dauke ni kamar dah, Ya Farouk dinki, ni a waje na,har yanzu yar karamar Aminene nake kallon ki." Dariya na saka, na kai masa dukan wasa, da sauri ya tare yana hade hannaye na waje daya ya murde su, yar kara nayi kamar zanyi kuka na shiga magiyar yayi hakuri, da kyar na samu ya hakuran, amma sam yaki barin dakin, ni kuma na matsu ya fita dan na samu na watsa ruwa na cire kayan jiki na, kiran wayar da akayi masa ce ta taimake ni, da sauri naga ya daga wayar yana kokarin fita daga dakin baki daya, da haka na samu damar saka key a dakin na aiwatar da abubuwan da nake so. ***Har dare be sake waiwayo ni ba, ina zaune a dakin ban fita falo ba, gidan tsit babu motsin kowa, kaina ke dan saramin saboda yunwar da ta fara addabata, ban dauko komai cikin provision dina ba, gashi naje Kitchen ɗin babu komai balle na samu abinda zan dan taba. Zamewa nayi na kwanta a saman tiles din dakin hannu na rike da wani story book ina karantawa saboda rage kadaita, turo kofar akayi, hannun sa dauke da ledoji manya guda biyu, tashi nayi da sauri na zauna. Ajiye ledojin yayi a gabana ya zauna. "Ya Farouk yunwa." Nace ina bata fuska. Tura min ledojin yayi "Kiyi hakuri abu ne urgent ya fitar dani." Matsawa nayi na bude na dudduba, kafin na tashi dan zuwa dauko abinda zan juye a ciki.   Bayan mun gama ci na tattare komai na maida na dawo dakin, ban tarar dashi a ciki ba, na shirin bacci na kashe wutar, ina cikin addu'a akayi knocking, tashi nayi na bude, yana tsaye cikin shigar bacci shima, rabawa yayi ta gefe na ya wuce ciki, tsaye nayi a jikin kofar ina kallon sa, har ya haye gadon nawa yana jan dubet zuwa saman kafadarshi. "Idan kin gama tsaiwar, ki rufe kofar kizo ki kwanta." Muryar sa ta daki kunne na, jim nayi kamar ba zan motsa ba, sai kuma na shigaa jan kafata da kyar kamar wadda kwai ya fashe wa na isa dayan bangaren, a darare na hau gadon na kwanta gefe daya, ina jin sa ya mirgino zuwa bangaren da nake, ya dora kansa saman pillow na yana saka ni cikin jikin sa. Jiki na ne ya hau rawa kamar mazari, a hankali ya dora bakin sa saman kunne na ya furta "Let sleep princess, Goodnight." Manage pls nayi typing ya goge 😥😥😢😓🙏 Comments yana taimakawa sosai wajen motivating writer🙏 Thanks All Jazakumullah bhi khaira: *ONAR TASFAH*                *OROG NIRUAD* *RIYAB AFAFAZ*                  *EGAP (12)* *** Kamar tsohuwar munafuka haka nayi ya raba idanu, gaba daya na rasa yadda zanyi, duk na takura,kasa koda kwakkwaran motsi nayi ina jin shi yana karanta mana addu'ar bacci. Bani da kuzarin da zan iya bude baki na, nayi addu'ar nima, haka nayi shiru ina tunanin abinda ke faruwa. "Princess." Ya kira ni da sabon sunan da ban san yaushe na same shi ba. "Uhum ." Nace kamar me ciwon hakori,. "Please ki saki jikin sa, bacci nake ji nasan kema haka, beside ni mijinki ne, mata da miji basa raba daki sai da kwakkwaran dalili, so kawai ki saki jikin ki dan ba fita zan ba, ina nan anan zan kwana atau." Ban tanka ba, ina jin sa yana ta kokarin ganin sai na saki jikina, wanda ni kuwa har ga Allah ba iya wa zanyi ba, a yadda nake ji ma yanzun Allah sa nayi runtsawa, yadda yabi ya kanainayeyi, bana jin zai barni na shaki iska me dadi yau kuwa. Har ya gama surutan sa ya fara jan numfashi sannan na sauke ajiyar zuciya, gaba daya bani da sukuni balle nutsuwa da zan iya runtsawa. Sake sake na shiga yi ina tuna wani Novel dana taba karantawa. Da haka bacci barawo yayi awun gaba dani ba tare da na shirya masa ba. *** Kira wayar sa ce ta farkar dani, baya dakin, na kai duba na wajen wayar, sunan da na gani yana yawo a saman wayar na kura wa ido, har ta gama ta katse wani kiran ya sake shigowa, ita ɗin ce dai, tsam na mike nayi hanyar toilet ba tare da na sake bi takan wayar ba. Tsawon mintuna talatin na dauka a toilet din, gaba daya na hado har da wanka na fito, a gurguje na hau shiryawa ina kallon kofa kar ya shigo, har na gama ɗin kuwa be shigo ba, sai a lokacin na lura ya dau wayar tasa kenan ya shigo ina toilet, ban shafa komai ba sai yar powder da wetlips, na dora hijabi na a saman sabuwar atamfar da na saka ta sau daya a makaranta, blue ce da adon baki anyi mata zanen ganye. Half covered shoe d'ina black na jawo a cikin kayan dana zo dasu na zura na yo waje. Yana zaune a saman kujerar falon, hannun sa rike da mug yana fitar da tururi alamun abu me zafi ne a ciki, shi dinma yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya black top da wandon su na sojoji, kallo ya hau bina dashi har na karasa ina zama a kasan carpet daidai wajen da kafafun sa suke. Zamowa yayi ya zauna kusa dani kafadarsa na gogar tawa yayi saurin cewa "Good morning princess." Murmushi nayi na gaishe shi da ina kwana? Amsawa yayi yana mika min mug din hannun nasa "Tayani sha wallahi cikana a cunkushe yanke." Mika hannu nayi zan karba ya girgiza min kai, hanyar bakina yayo dashi a kunya ce na bude ya kafe min cup din, a hankali na shiga kurbar kunun gyadar daya sha madara da sugar, ina sha ina tunanin in da ya samo shi, tas na shanye, ya jawo tissue ya mika min yana tashi "Anji dadi an shanye min." Dariya nayi ina karba shi "Ni kawai dan ka takura ne nasha, amma ba dadi." "Really!" Yace yana rike kugun sa. "Umm." "Ai shikenan, gobe ma rana ce, za'a kawo min ne ba zan baki ba." "Waya kawo maka?" Nayi saurin tambayar shi dan dama ina son sani. Make kafadar shi yayi ya juya hannun shi "Ba sai kinji ba." Murmushi kawai nayi ina ayyana a raina wanda ya kawo mishin, ganin zan bata wa kaina lokaci da tunani yasa na wuce Kitchen ɗin, na wanke mug din na gyara wajen na fito. A tsaye na tarar dashi yana kokarin saka p-cap a kansa "Muje na ajiye ki a gidan sai yamma na dawo, nima ina da abin yi yau din da yawa." Da sauri na juya, na dauko yar karamar jakata na saka tarkacen chocolate da sweet na fito, tuni ya shiga mota achan na iske shi muka dau hanya.   Muna fitowa yayi daidai da lokacin da Garbati yazo wucewa a saman machine din sa, gaba daya ya chanja kamar ba shi ba, riga da wandon jikin sa kadai sun isa su fada ma halin da yake ciki, duk yayi baki ya rame bakin sa yayi duhu alamar yasha sigari ya koshi. Kansa yayi da motar, ya ɗan taba shi, take ya fadi a wajen, balle murfin motar yayi idon sa yayi jawur ya fito, Garbati na kokarin mik'ewa cike da masifa ya dira a gaban shi. Kafa yasa ya take machine din, yana kallon fuskar shi. "Uban waye kai da zaka ture ni, kuma..." Maganar sa ta makale sakamakon wandon daya fara cin karo dashi bayan ya dago. Cikin in da in dah yace "Me nayi maka?" Farouk be tanka ba, sai kafa daya sa ya tardes shi, tuni ya baje a wajen bakin sa ya fashe, hannu yasa ya hau zare belt din jikin sa, da sauri na balle murfin motar na fito, na isa wajen, rike shi nake kokarin yi, ya juyo a fusace ya nuna min mota "Wuce ki koma ciki." Yadda yayi maganar da yanayin fuskar sa, yasa naji yan hanjin cikana sun juya, da gudu na koma na zauna ina rawar jiki. Be wani tsaya bata lokaci ba ya shiga laftawa Garbati belt din nan, ihu yake yana magiya amma sam yaki sauraran sa, Dukan sa yake da dukkan karfin sa, tuni abin ya fara bani tsoro, ganin yadda ya koma kamar ba Ya Farouk ba, ya juye gaba daya ya zama kamar wani horror, kuka na soma a hankali ina daga zaune a motar, sai daya tabbatar yayi masa laga-laga sannan ya ture shi ya nufo motar, da bayan hannu na, na shiga share hawayen fuskar ta. Be ko kalle ni ba, ya tada motar muka dau hanya, ta gefen ido nake satar kallon sa, yadda kirjinshi ke kaiwa da komowa. Sosai nayi mamakin tsananin zuciyar shi. Muna zuwa kofar gida nayi saurin kama kofar motar zan fita, naji ya riko hannu na. "I'm sorry." Ya furta yana kallon ido na, daga mishi kai nayi ina sake kokarin bude kofar dan har ga Allah na tsorata da yanayin sa.  Lock din kofar ya danna, ya matso daf dani, da sauri na kulle ido na zuciya ta na harbawa, tsoro na daya kar nima ya jibgen,  a hankali naji saukar light kiss a saman goshi na, sake runtse ido nayi na kankame jikina. "Ohh shit." Ya daki steering motar, "Kinga, pls karki ji tsorana, i can never harm you, shi wanchan kuwa zan masa fiye da wannan, wannan somin tabi ne, saboda haka kar na sake jin kinyi kuka idan ina abu makamancin wannan." "Toh." Nayi saurin cewa. "Zan tafi." Na nuna masa kofar motar. Dan karamin tsaki yaaja ya bude min da sauri na fita ina yin hanyar zauren gidan. Sai dana shiga sannan yaja motar ya tafi.   Sallama nake tayi a tsakar gidan namu, baki daya komai ya sauya, sosai gidan ya sake tsufa, duk kofofin sun lalace, dakin Inno na kalla naga an dan turo kyauren alamun bata nan, Yalwati ce ta fito daga dakin Baba, da mamaki take kallo na, sai kuma ta fadada fara'ar fuskar ta. "Wa nake gani kamar Aminene?" Dariya na saka na karasa ciki. "Ah laillai, maraba da yan makaranta." Kasa na tsuguna na gaishe ta, ta amsa sosai, kafin tace "Shiga wajen Baban naku, Inno dai ta je hayi karbo magani, kinsan duk ba dadi suke ji ba ita da shi." "Allah ya sauwake." Nace ina tura kofar dakin, yana kwance daga gani yana jin jiki, kallo na yake har na isa gaban sa na zauna. "Sannu Babah." Na gaishe shi cike da tausaya wa, hannun sa daya naga ya daga min, alamun na matso, matsawa nayi sosai na rike hannun sa ina jera masa sannu. Yalwati ce ta shigo rike da kofin silba cike da ruwan randa. "Tsautsayi ya gamu dashi ai, faduwa yayi a banɗaki shikenan barin jikin sa daya ya shanye, kin gashi nan baya ko magana." Kwalla ce ta zubo min cike da tausayin baba, mutum me sauƙin kai da hakuri, bashi da ta cewa kowanne lokaci sai abinda Inno ta gindaya masa, yau shine rayuwa ta juya wa baya haka, da ido yake min alamar nayi shiru, kasa kasa na cigaba da kukan nawa ina masa addu'ar samun sauki. Ban fito daga dakin ba, sai da Inno ta dawo. Tana gaban dakin ta ta baza ledar magungunan gargajiyar data karbo na fito, da ido ta kafe ni cike da mamakin gani na. "Yaushe kika zo.?" Tun kafin na gaishe ta ta watso min tambayar, murmushi nayi kawai dan hausawa sunce me hali baya fasa halin sa. "Sannu da zuwa, ina wuni?" Na bagarar da tambayar da tayi min na maye gurbin ta da gaisuwa, amsawa tayi tana cigaba da duba kayan data zo dasu kamar bata damu da zuwan nawa ba. Dakin nata na shiga, duk yayi kacha-kacha, ajiye hijabi na nayi na shiga kokarin ganin na gyara. Ina cikin gyaran ne nazo kan jakar da nake yawan ganin tana ciro ta, ta duba. Hannu nasa da nufin bude jakar ta shigo. "Kee!" Ta daka min tsawa, da sauri na saki jakar ta sabule daga hannu na "Me kike yi haka?" "Um.. um.. dama gani nayi dakin..um yayi datti shine nake sharewa." Zuwa tayi gabana ta dauke jakar ta bude sip dinta ta saka. "Yi sauri ki karasa sharar ki fito zaku gaisa da mutane." Daga haka ta fice ta barni, sauri sauri na karasa na fito, na shiga sauran gidajen dake cikin gidan namu. Bayan na dawo ina ta tunanin ina yan matan gidan suke, chan dai na tambayi Inna, sai a sannan nake sanin ashe duk an musu aure. Hanne ta haihu ma Karime kuma ta kusa. Sosai nayi mamaki, naso a ranar na samu me rakani, ana la'asar sai ga kiran Ya Farouk a waje, ban so ba, haka na shiga dakin Baba nayi masa sallama sannan na fadawa Inno yazo zan tafi. Shiru tayi kamar me nazari, sai kuma tace "Kice masa dan Allah yazo ina son magana dashi." Da toh na amsa mata na fito nayi wa sauran sallama. Waya yake yanzun ma, ina bude kofar yayi sallama yana dage min kira sama. "Ina wuni?" "Lafiya lou, kin gama ai ko?" "Eh na gama." "Ok." Ya hau kokarin data motar, "Dama inna tace na fada maka tana son magana da kai wai." Da sauri ya kalle ni "Kunyi wata magana ne?" Ya tambaye ni "A ah bamuyi ba." Na amsa. Ajiyar zuciya naji ya sauke kafin yace "Shikenan zan zo gidan gobe, yanzu ana jirana ne." Bance komai ba yaja motar muka bar kofar gidan. *** Tsawon satin haka mukayi shi, babu abu d'aya, daya chanja, kullum zamu kwanta kamar yadda muka fara a ranar farko, tun ina nokewa har na saki jikina ganin babu abinda ya faru, sai dan abinda ba za'a rasa ba.😜 Naje gidan Karime da Hanne, sannan na koma gidan mu sau biyu na sake duba Baba, bansan ko yaje sunyi maganar da Inno ba, ba ta kara dai yimin maganar yazo ɗin ba, sai kawai na share ban tambaya ba. Daren ranar da zan koma makaranta dukkan mu bamu da walwala sam,sai nace har gwara ma ni ina dan daurewa, amma shi ƙarara ya nuna damuwar sa, hira nake masa da son ganin ya ɗan saki ransa, amma fafur yagi, shinkafa da miya nayi mana a daren ranar, na samu yaci ba laifi dan tun rana be sa komai cikin sa ba. Da wuri yace muje mu kwanta, ranar babu petir a inji be fita ko nan da chan ba. Haka muka yi shirin kwanciya bayan na tabbatar da na gama hada komai nawa a waje daya. Wanka na fara yi saboda yadda garin ya hade rai alamun za'a yi ruwan sama, babu iska ko kadan sai kugin hadarin kawai kake ji. Ina fitowa daga wankan naji garin ya ɗan fara saki, doguwar rigar bacci kawai na zura na haye gado na kwanta, ina kwanciya ya shigo yana haska wa da torchlight ɗin wayar sa, rufe ido na nayi da sauri alamun bacci, wucewa yayi gaban mirror ya shafa roll on dina ya hawo gadon ya jawo ni jikin sa. Muna nan kwance babu wanda yayi wa wani magana, aka soma yayyafi, saki na yayi ya tashi ya bude windows din sosai iska ta shiga zagaye lungu da sako na dakin, yana tsaye ya zura hannayen sa yana kama yayyafin dake sauka kadan kadan. Cikin dan kankanin lokaci dakin yayi sanyi, ruwan da aka farayi da karfi yasa ya sake rurrufe glasses din windon ya saki curtains din. Da sassarfa ya hawo gadon ya kwanta yana ware hannuwansa. "Alhamdulillah, ni'imar Allah ta sauka." Ya furta yana mirginowa waje na. Shiru mukayi dukkannin muna sauraron saukar ruwan da karfi a nutse babu hayaniya, irin ruwan da za'a iya kiran shi da peaceful rainfall, babu tsawa babu tsananin iskar nan, hakan ya haifar da wani yanayi a tsakanin mu. Shirun da mukayi kowa da abinda yake ayyanawa, a daidai lokacin Ya Farouk na fama da zuciyar shi akan abinda take kokarin bijiro mishi dashi, duk kuwa da alkawari ne ya dauka wa kansa, amma a yadda yake ji yanzu, tabbas baya jin zai iya cika shi, yadda zuciya da ruhin sa ke azalzalar sa, da ingiza shi zuwa abinda ba haramun bane, sai dai shi din daya haramtawa kansa, bisa wani dalili nasa da yake ganin hakan shine daidai. Sake mirginawa yayi yana kokawa da zuciyar tashi, kaso saba'in cikin dari na tsarin zuciya da ruhin shi sun aminta da abinda yake ji ɗin, yana ganin ba zai iya kuma bata wasu dakiku ba tare da aiwatar da abinda suka riga suka yanke masa ɗin ba. "Princesssssss?" Ya kira ni yana sake matsowa. "Kina jina?" Ya sake maimaitawa yana lalubar hannu na. Runtse ido na nayi ina jin yadda numfashin sa ke sauka bisa saman fuskata. "Uhum." Nace ina kauda fuskata gefe yadda yage faman zagaye hannun sa a saman fuskar tawa. "Alhamdulillah." Ya ambata a chan kasan makoshinsa wanda ba karamin me kunne ne zai jiyo shi din ba. "I can't hold it anymore." Yace yana kokarin chanja karatun dana sani wanda na riga na gama dauka a wajen sa zuwa wani sabon shafi na daban. Tuni kwakwalwata ta tsaya tsak, ta daina aiki, komai ya shiga chanjawa, a hankali komai yake tafiya har zuwa sanda abubuwan suka sauyawa baki daya. Shafin rayuwa ta na baya ya sake maimaitawa kansa a karo na biyu a siga ta daban. ****Yar karamar ƙwaƙwalwa ta ta gaza aike min da komai zuwa ilahirin sassan jiki na, baki daya bani da kuzarin aiwatar da komai, na gaza tantance abinda nake ji a halin yanzu, karar kafuwar hakora na kawai ke tashi waje daya, tuni zazzafan zazzaɓi me cike da ma'anoni da yawa yayi min rufdugu, ina jin shi yana magana, da dukkan kalmar da zata zo bakin sa, kokari yake yaga ya fahimtar dani komai, bana fahimta, ba kuma zan fahimta ɗin ba. Kalma daya kawai nake iya tantancewa "hakuri" kalmar da yake ta nanatawa kamar a bakin sa aka halicce ta. Da kyar na bude baki nace "Zan sha ruwa." Da sauri ya tashi ya kawo min, ya taimaka min nasha, sannan ya gyara min kwanciya ta yana kara nanata kalmar hakuri. Bansan sanda bacci ya dauke ni ba, bacci me dauke da ma'anoni da yawa. A yau na sake taka wani mataki na rayuwa, matakin da ba zan iya sanar daku da yanayin da yazo min ba, abu daya na sani, yana cikin manyan matakan rayuwata dana gaza mantawa. ***Komawa ta makaranta ta ruguje, babu wanda ya tuna da hakan tsakaninmu, zuwa da safe naji dama dama, da taimakon sa na samu na sake komawa bacci a karo na biyu, wanda ban samu farkawa ba sai da rana ta daga sosai. Da fuskar sa na fara tozali, yana zaune a gefe na cikin shigar sabuwar shadda fara kal tana sheki , kansa babu hula kamar ko yaushe, yayi kyau ainun, da sauri na maida ido na na kulle. "Good morning My Dee." Ya ambata yana min peck a saman kuncina, dariya na saka ina rufe fuska ta da tafin hannu na. Tashi yayi ya fita, hakan ya bani damar saurin fadawa toilet, na sake gyara jikina da ruwa me dumi, kayan jikina na mayar na dora hijabi akai na fito, yana zaune gaban sa da babban tray, wuce wa nayi na dau doguwar rigar atamfa me karamin hannu na sake komawa toilet din na saka na dauro dan karamin mayafi a saman kaina na fito. Breakfast din ya tura min gabana yana ciro wasu jerin magunguna daga cikin leda. Sosai naci abincin ya bani maganin nasha na koma saman gado na kwanta. Shi ya tattare kayan ya fita dasu sannan ya sake dawowa dakin.   Kwana biyu muka yi a haka, komai shi yake mana, sosai nake jin kunyar sa, shi kuwa babu ruwan sa, budirin gaban sa kawai yake, a kwana na ukun ne aka matsa masa da kira, dole ya fara shirin tafiya nima na hau nawa shirin dan ma tuni yayi waya da principal dinmu.   A tare muka fito gaba daya, muka dau hanyar makarantar mu, har muka isa hannun sa na cikin nawa, da kyar ya kyale ni na tafi bayan doguwar sallamar da muka tsaya yi.   Sanda na dawo har sun fara wasu subjects din, haka na yi joining aka cigaba dani, kullum dare da tunanin sa nake kwana, dashi nake tashi, duk da hakan ban bari ya shafi karatu na ba, dan ina so yayi alfahari dani. Munyi waya sau biyu a wayar principal, daga ranar ban sake magana dashi ba. Bayan sati biyu muka fara Waec, tuni kaina ya dau zafi na ajiye komai, sai dai kullum da matsanancin ciwon kai nake kwana, nake tashi, a haka nake daurewa nake karatun. Wata guda muka dauka da yan kwanaki muna jarrabawar, a ranar da mukayi ta karshe ne jikina ya kara rikicewa, ban iya fitowa daga examz hall ba, sai da wasu seniors suka taimaka min zuwa clinic din makaranta. Tashin farko ta sani zuwa nayi fitsari na kawo a yar wata container, haka nayi fitsarin na kawo, ta rubuta min wasu magunguna tace su rakani hostel, gobe kafin mu tafi gida sai nazo na karbi result. Haka na koma hostel na kwanta, ban iya aiwatar da komai ba, sosai nake jin jiki, a daddafe nayi bacci har gari ya waye, wata roommate dina ce ta taimaka wajen karasa hade min kayana waje daya.   A nutse nake tafiya har na isa clinic din, Ina zuwa na samu waje na zauna dan bata ƙaraso ba. Can ina zaune tazo, tana gani na ta sakar min fuska "Shigo ciki ko." Ciki na shiga ta ban kujera na zauna, envelope ta ciro ta mika min "Test ɗin da akayi miki baya wani daukar lokaci, ina so dama nayi magana da principal ne shiyasa nace ki dawo yau, toh munyi magana ma kuma dai babu wata matsala tunda dama ashe kina da aure ko?" Daga mata kai nayi ina juya takardar hannu na. "Ok Masha Allah, Kinga sai kiyi rainon cikin ki a gida cikin kwanciyar hankali.' Kaina ne naji yayi wani gingirin, na bita da kallo kamar wadda bata jin Yaren da take min. "Yes! You are pregnant." Ta fada tana murmushi, wani yar naji tun daga kaina har tsakiyar kafata. Ni kuma? Ciki? Ikon Allah. Tashi nayi na mata godiya na dau magungunan data bani na fito. Sai na rasa ina zanyi, nayi ta zagaye saman barander daga farko zuwa karshen ta, ina kallo ana yayewa daya bayan daya, har ya zama na kowannne dalibi ya tafi, saura ni kadai. Tun ban fara damuwa ba, har abin ya fara damuna, ina tunanin abinda ya tsaida Ya Farouk, bayan yasan yau ne ranar, ranar dani dashi muke jira, ranar da yayi min alkawari da dama akan ta. Waje na samu daf da kayana na zauna ina kallon kofar. A hankali aka zuge gate din, wata bakar mota ta shigo, baka ganin komai na cikin ta saboda glass din ta me duhu ne. Tsayawa naga anyi daf da security man din dake tsaye daura da gate din. A hankali glass din motar ya shiga sauka, hannu ne ya fito, rike da wata farar takarda, hannun na mace ne, dauke da jerin awarwaraye masu matukar kyau da sheki. Takardar da mika wa security man din tare da sanar dashi wani abu. Ina kallo ta maida glass din motar ta rufe, ta juya ta fita daga cikin makarantar da mugun gudu. Ganin security man din ya nufo ni yasa na tashi ina sake riƙe takardar result d'ina, yana zuwa ya mika min takardar cikin harshen turanci yace "Sakon ki ne inji Farouk." Karba nayi hannu na na rawa, na bude ido na ya sauka akan abinda ke rubuce baro baro cikin manyan harafi. A take naji kaina na juya min, na fara ganin komai biyu- biyu, dafe kaina nayi da dukkan hannu na na kwalla kara da ta cika makarantar baki daya. Daga nan bansan me kuma ya sake faruwa dani ba. Rano ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                       ****Daurin Goro*              *13* ©️ Hafsat Rano ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                       *** Da kyar na bude idanuna da sukayi min matukar nauyi,na fara bin ko ina da kallo, kwance nake a dakin asibiti, hannu na daure da ruwan drip dake sauka a hankali. Fankar saman dake juyawa kadan kadan na kurawa ido ina son tuno me ya faru dani. Cikin yan dakiku ƙwaƙwalwa ta shiga dawo min da komai, kuka nasa da karfi zuciya ta na matukar suya. Me yasa zai min haka? Me nayi masa? Abinda na shiga tambayar kaina kenan ina kuka sosai. Shigowar principal ne da wata mata yasa na rage kukan da nake, har gaban gadon ta ƙaraso tana min kallo me cike da tausaya wa "Sannu Amina, kiyi hakuri kinji? Duk tsanani yana tare da sauki." Ban iya motsawa ba, sai hawayen da suka cigaba da sauka a saman fuskata kamar masu gasar tsere, a yau na sake tabbatarwa da sabon shafin rayuwa ta ne ya sake budewa, shafin da ban shirya masa ba, ban taba tunanin zan riskeni a irin wannan lokacin ba. Juyawa nayi ina runtse ido na ganin duk yadda na juya abinda ke rubuce a takardar nan nake gani, _"Ni Farouk Kabir Shagari, na saki matata Aminatu, babu sauran wata alaƙa a tsakanin mu, sannana babu wani abu daya shiga tsakani na da ita. Idan ta samu wani mijin, tayi aure."_ Tabbas rubutun sa ne, tun yana koya mana karatu na haddace zubin rubutunsa, kawo yanzu da ya zama duk wasu muhimman takardu na rubutun nasa ne akai. Hannu biyu nasa na rike kaina gam dake barazanar rabewa biyu saboda tsananin ciwo, tun ina yin kuka da hawaye har ya koma sai na zuciya kawai nakeyi. Duk maganganun da principal suke na gaza daukar daya a ciki, ina ji suka juya suka fita. Jim kadan wata nurse ta shigo dauke da ruwan allura, da kallo na bita kawai dan bani da wani karfin hana ta, duk kuwa da tsananin tsoron da nake wa allura yau sai ya zama na nafi tsoron kaina da rayuwar da zanyi akan komai. Ina jin ta tayi min, ban ko motsa ba, cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ne da karfin gaske. Wanda nake da tabbacin yana da alaka da allurar da tayi min, dan bana jin akwai wani abu da zai iya sani runtsawa a halin da nake ciki.   Ban farka ba sai da safe, na tashi da tunanin abinda ya faru, kukan na cigaba kamar jiya, dan ina ganin shine kawai zai rage min radadin abinda nake ji. Da taimakon matar jiya na samu nayi sallah, ina sallah ina kuka wiwi, zama tayi a gefe tana jiran na idar, da kyar na samu na kawo sallolin da ake bina,dan tuni jikina ya fara rawa, zuciya ta ta riga tashi, da gudu na fada dan karamin toilet din dake manne a dakin na shiga kwarara amai, babu komai a ciki sai ruwa, a galabaice na gama na fito bayan ta taimakin da ruwa. Kwanciya nayi jikina ya dau rawar sanyi, wani mugun zazzaɓi da ban taba jin irin sa ba ya dirar min a lokaci daya. *** Tsaye take a gaban desk din ta, wayar tace a hannun ta tana faman juyata, "Ya zamuyi da yarinyar nan ne? Sam wayar mijin nata bata shiga wallahi, tun jiya nake gwadawa, gashi babu wata hanya da zamu nemi iyayenta." Tayi maganar tana sake dialing number tasa a karo na ba adadi. "Akwai tashin hankali, ga saki gata dauke da juna biyu, maza basa kyautawa sam wallahi, wannan wane irin rashin adalci ne." "Hmm abun dai kam sai dai Allah ya kyauta, ina ganin jira zamuyi kawai ta ɗan ji karfin jikin ta, idan yaso sai a sata a motar makaranta a kaita gida, nasan tabbas zata san gidan iyayenta ai, in ba hakan ba bansan yadda zamuyi ba, kuma kinga ai ba zamu cigaba da rike yarinya a wajen mu ba." "Gaskiya dai, hakan kawai shine mafita." Shiru sukayi kowa da tunanin abinda ya ke, takardun biyu principal ta nannade ta hadusu waje daya, ta kwashi abubuwan da zata bukata suka fito. *** Ƙarar motar data tsaya a kofar gidan yasa yaran lekowa, ganin motar yasa suka hau tsallen murnar ga Aminatu, ga Aminatu, sanin su cewa ita kadai ɗin ake kawowa a mota, dan karamin yaron Yalwati ne yayi jikin motar da sauri, bude motar akayi, duk suka zuba ido suna kallo, a gadarance ta fito, ta tsaya tana karewa gidan kallo, yatsine fuska tayi ta shiga takawa a hankali har cikin gidan. Yalwati na gaban murhu tana gyara wuta, ruwan wankan jego ne akai da za'a yi wa Karime, ta dago da sauri jin takun tafiya haɗe da wani irin kamshin turare daya riga ya game dukkan lungu da sako na gida. "Maraba." Tace tana goge hancin ta da yayi shabe shabe da majina, kallon tsaf matar tayi mata batare data amsa ba. "Kece mahaifiyar Aminatu?" Tayi tambayar tana matsowa ciki. Sai a lokacin Inno ta fito, rik'e da kofin kunun kanwar da ta gama matsawa Karimen tasha. "Lafiya?" Inno tace tana kallon Yalwati da matar. "Wajen ki tazo wai." Ta amsa tana nufar dakin ta, tabarma ta dauko da sauri ta shimfida a yar inuwar wajen tana nuna mata "Bismillah ga waje." Kallon banza matar tayi mata sannan ta kalli Inno ta nuna ta da hannu "Kece mahaifiyar Aminatu kenan?" "Nice, me ya faru?" "Dama zuwa nayi na sanar muku, kuje ku dau yarku a makaranta dan yanzu babu wata alaƙa tsakaninta da d'anmu, asirin da akayi masa ya warware sai abi wani sarkin, saki ne ya riga ya sake ta, dawainiyar da yayi da itaa ya isa haka." Da sauri Inno ta matsa jikin bangon dakin ta, ta kasa cewa komai, kallo kawai ta shiga bin matar dashi har ta zaro takardar dake ninke a yar karamar jakar hannun ta ta yar a tsakar gidan, ta juya cikin takun ta na kasaita bayan ta tofar da yawu ta fice daga gidan. Da sauri Yalwati ta dauke takardar tayi wajen Inno tana mata magana ganin kamar bata hayyacin ta. "Lafiya Yaya? Ko jikin ne?" Ta fada cikin kulawa. Da kyar ta bude baki tace "Innalillah wa inna ilaihi raji'un.. Na shiga uku na lalace." Da sauri ta sa hannu ta karbi takardar, sannan ta juya ciki, Karime na zaune tana hawaye, bayan ta gama jin abinda ya samu Aminatu "Inno..." Tayi maganar tana kallon ta "Bari naje Karime, idan ruwan yayi Yalwati zata yi miki." Daga kai kawai tayi, tana share hawayen tausayin yar uwarta. Mayafinta ta dauka, ta dauka yan kudaden ta tayo waje, yara tasa suka kira mata Nura, suka nufi in da zasu samu mota. Har suka isa makarantar bata bar sake-sake ba, wani irin tausayin ta take ji, tabbas tasan ita ce Ummul abaisin halin da Aminatun ke shiga, sai dai tayi nadama, duk da nadamar bata da amfani, amma tabbas tayi dana sanin abinda ta aikata, gashi Baba tun lokacin daya ji komai ya kwanta ciwo, saboda tsabar kaduwar da yayi take barin jikin sa ya shanye, ko a iya haka Allah ya barta ta gane kuskurenta, ballantana tasan akwai wasu sakamakon masu zuwa nan gaba. *** Ina kwance kamar wadda aka zare wa dukka kashin jikin ta, cikina ke ta ya mutsawa kamar kayan cikin shi zasu fito, a wahalce nake fitar da numfashi ina murkususu. Budo kofar akayi na zuba musu ido, principal ce a gaba sai Inno da Nura, ganin su yasa na saki kukan da nake ta kokarin tsaida shi, da sauri suka ƙaraso wajena Inno tayi kokarin sani jikin ta. "Sannu kinji." Principal tayi maganar tana ajiye takardun a gefe na. Da sauri na runtse ido na ina jin kamar ta ajiye garwashi tunawa danayi da abinda ke ciki. Ina ji ta hau yi musu bayanin komai, "Naji dadin zuwan naku, dama muna ta tunanin yadda za'a yi, tun da kunzo sai asa hannu ku tafi da ita, Allah ya kara lafiya." "An gode Allah ya saka da Alkhairi." "Amin, dan Allah a kula da ita sosai, akwai karamin ciki a jikin ta, damuwa zata iya haifar mata da matsala, duk tsanani yana tare da sauki, komai zai zamo tarihi in Sha Allah." Da kallo Inno ta bita, ta kasa magana sai daga kanta kawai da take a hankali, har principal din ta juya ta fita. "Ni Nura a takardar nan ba yace babu abinda ya shiga tsakanin su bane?" Tayi tambayar tana kallon sa "Tabbas haka yake a rubuce." "Allah ya kyauta." Kawai tace tana kokarin tashi "Ki daina kuka kin daiji me firincifal ɗin tace ko?" Shiru nayi suka tattare komai da magunguna na Nura yasa hannu muka dau hanya. ***Tun da muka soma tafiyaa na jingina da kujerar motar, na lumshe ido na kamar mai bacci, babu wanda yayi min magana a cikin su har muka isa kauyen namu, sanda muka iso daidai gidan Bature, na bude ido na, jikina ya hau rawa na kura wa babban gate din gidan ina ganin kamar zai bude, gani nake kamar zai fito, kamar zan ganshi tsaye yana daga min hannu, sai dai kash, har muka wuce babu motsin kowa, babu alamun ma akwai mutane a ciki. Muna isa gida Inno ta gyara min hijabi na ta riko ni, ta taimaka min na fito, hannun ta cikin nawa muka shiga gidan, da sauri Yalwati ta taso, tana mana sannu da zuwa. Amsawa Inno tayi ta bude min dakin ta. "Jeki kwanta." Kawai tace ta rataye mayafin ta saman igiya ta nufi dakin Baba. Ina shiga na tarar da Karime da jaririnta, ta sauri ta taso ta rungume ni,sai a sannan naji wani sabon kuka ya taso min, kukan muka saka baki daya a tare, babu me yunkurin rarrashin wani, sai da mukayi me isarmu, sannan muka samu waje muka zauna, sai a lokacin Inno ta shigo, kallon mu tayi kadan ta wuce wajen daukar abu,har zata fita sai kuma ta tsaya tana duba na "Taso ki watsa ruwa kafin magriba tayi, ke Karime miki min yaron nan a goya shi magriba ta gabato." "Toh." Muka amsa a tare, ta karbi jaririn ta fita, cikin rashin kwarin jiki na mike, na rage kayan jiki na, na fito tsakar gidan, ruwa me dumi na tarar a bandakin na watsa na fito. Kayan Karime na saka na sake kwanciya a saman gadon Inno, har aka kira sallah sannan na tashi nayi na sake kwanciya, gaba daya bani da karfin jiki dana ruhi, komai baya min dad'i. A gefe na Karime ta zauna tana jijjigen yaron, kallon ta kawai nake ina hasaso hakan akai na. "Ya sunan shi?" Na tambaye ta ina mika mata hannu ta bani shi "Abubakar aka sa masa, amma saddiku za'a dinga ce masa." Shafa kansa nayi wasu hawaye suka zubo min, nima haka zan haifi abin ciki na, na raine shi ni kadai ba tare da uba ba, bansan wanne irin rayuwa kuma zan sake yi nan gaba ba,  hannu na dora a saman shafaffen ciki na bayan na mika mata shi don ta bashi nono. Na shiga tunanin kalar rayuwar da zanyi. Abinci Inno ta kawo mana, na d'an ci kadan dan har lokacin cikina babu dadi, na haye gadon na kwanta ina fatan bacci ya dauke ni ***Cikin dare na kaasa bacci juyi kawai nake, na rasa abinda yake min dadi, har aka kira sallah na mike da kyar na je nayi alwala,. Bayan na idar na zauna saman abin sallar ina fadawa Allah damuwa ta, nasan shine kadai zai kawo min sauki a dukkan al'amari ne. Sai da gari yayi haske sosai sannan na kwanta, bacci ya dauke ni a take. Ina cikin baccin ne naji hayaniya sosai kamar a tsakar gidan mu, da sauri na mike zaune, Karime na gani a zaune gefe na tayi wanka tana cin dumanen tuwo. "Sannu da tashi, ya karfin jikin?." Tace tana min murmushi "Da sauki, ya kwanan Saddik?" "Alhamdulillah." "Su waye nake jin hayaniya a waje?" Na tambaye ta ina sake kasa kunne na sosai, tabe baki tayi kafin tace "Dan iskan Garbatin nan ne yazo zai wa mutane hauka, amma Inno tayi maganin su ma ai, bashi da hankali wallahi sam." Gabana ne ya fadi nayi saurin lek'awa, lokacin suke fita daga gidan, hannu naga Inno tasa ta goge fuskar ta, ganin ta nufo dakin yasa nayi saurin komawa na zauna. Shigowa tayi tana maganganu kasa kasa, chan sai ga Nura yayi sallama a dakin. "Wai kina kirana ko?" Yace yana zama kasa. "Waye yayi maganar juna biyun da take dauke dashi? Kasan dai ni dakai kawai muka san maganar." Zaro ido yayi cikin rashin gaskiya "Wallahi dazu ne da asubah muke maganar dawowar Aminatun da su Iro(sauran samarin gidan) shine nake basu labarin abinda ma ya faru." "Toh gashi nan zance ya fita gari, har mutane sun zo neman ba'a si." Dafe kirjin sa yayi da sauri "Toh waya fitar da maganar kenan?" Ya tambaya yana zaro ido "Kaine, da baka fada ba ya za'ayi har a yada, tashi kaje ni kana abu kamar ba namiji ba." Sum sum ya tashi ya fita, Inno tayi tsaki ita ma ta bar dakin. Kallo na Karime tayi cikin son karin bayani "Me ya faru Aminatu? Bayan sakin akwai wani abu ne?" Share hawayen fuska ta nayi na zauna sosai zuciya ta na min daci, a hankali na ce "Bansan wacce kaddara ce ke tunkaro ni ba Karime, a lokacin da na gama tabbatar wa kaina da tsananin soyayya da nake ma Ya Farouk, a lokacin ya datse igiyar alakar dake tsakani na dashi, ya ruguza dukkan tanadin da mukayi wa juna. Kinsan bayan sakin har cewa yayi babu wani abu daya shiga tsakani na dashi? Bayan a daidai lokacin gwaji ya tabbatar min da ina dauke da ciki har na sati bakwai, Karime ya zanyi da rayuwata da abinda yake ciki na, bayan wanda zai tsaya min ya tabbatar da cewa babu abu tsakanin mu, ina kenan na samo cikin jikina? Wa zai karbe ni dashi?" Kuka yaci karfin mu dukka, tasowa tayi ta zauna daf dani tana sharen hawayen fuskata "Kiyi hakuri, tabbas ba'a kyauta miki ba, kuma an zalunce ki, amma bak'ya tunanin akwai sa hannu wani a cikin wannan al'amarin? Kina ganin Farouk zai miki haka kuwa?" Girgiza kai na nayi cikin kuka nace "Idan ma sharri akayi masa, yana ina yanzu? Me yasa be zo ya wanke kansa ba? Bayan haka rubutun dake jikin takardar nashi ne, rubutun sa ne Karime, ya kike tunanin bazan yarda ba?" "Duk da haka, ya kamata ayi bincike sosai." "Babu wani bincike da za'ayi, aikin gama ya riga ya gama, abu daya na kasa ganewa, laifin me nayi masa da har zai min wannan hukuncin? Menene matsalata?" Share hawaye nayi na mike ina komawa jikin tagar dakin, "Amma ba komai, na gode masa sosai da dukkan sadaukarwar sa gareni, hakika ba zan taba mantawa dashi a cikin jerin mutane masu matukar muhimmanci a rayuwata ba, ina jin kamar nunfashi na zai bar gangar jiki na Karime, zuciya ta tana min zafi." "Kiyi hakuri, karki tsananan ta damuwa ko dan abinda ki cikin ki." Sosai Karime ta shiga rarrashi na da ban baki, haka dai nake bin ta da ido kamar mutum mutumi, bata hakura ba har sai da saddiku yayi kuka sannan ta kyale ni. Wanka na fara yi na sha kunu wanda shi kadai ne zai iya zama a ciki na a halin yanzu. Wajen azahar sakon kiran maigari ya riske mu. Sai da akayi la'asar sannan Inno tasani a gaba tare da k'anin Baba muka tafi, duk inda muka wuce sai munga ana kallon mu ana magana kasa kasa. Haka muka isa wajen, daga gefe muka zauna muka gaida maigari sannan ya soma magana cikin dattaku." "Jiya wasu mata sunzo har nan sun same mu, sun gabatar da takardar sakin Aminatu daga wajen mijinta Farouk, bayan nan suka dora da bayanin su kafin sukayi sallama suka tafi. Toh bayan tafiyar su, nasa an karanta min abinda takardar ta kunsa, daga nan na yanke shawarar kiran mahaifin yaron, dan jin abinda yake faruwa, tunda ance ta inda aka hau ta nan ake sauka. Toh bayan kiran shi ne yake nuna min shi sam be san da maganar ba, hasalima shi rabon shi da yaron an kwana biyu, sai dai ya bani hakuri da alƙawarin zai samu lokaci ya shigo. Toh kuma yau sai ga maganar juna biyu ta riskeni, sai na sake komawa baya abinda yake rubuce a takardar nan da suka kawo, in da yaron ya nuna babu wata alaƙa data shiga tsakanin su, shine abin ya daure min kai, na bukaci naji daga gareku, kafin zuwa Mahaifin yaron ko yaron, mu san abinda ake ciki." Runtse ido na nayi ina karanto duk addu'ar datazo baki na, idan har Farouk be zo ba, be kuma ƙaryata abinda ya rubuta ba, ana nufin za'a sheganta min abinda ke cikina kenan? Wannan wacce irin masifa ce ta kunno min? "Aminatu..." Maigari ya kira sunana, ban iya amsawa ba sai dagowa da nayi kawai ina goge fuskata. "Abinda mijinki ya rubuta shin gaskiya ne ko ba gaskiya ba?" A hankali na bude baki na cikin tsananin kukan da ya soma cin karfi na nace "Ba... gaskiya bane." Gid'a kansa yayi cikin gamsuwa yace "Shikenan, in Sha Allahu komai zai warware kinji, kiyi hakuri." Da kai na amss kawai, ya karasa bayanin sa sannan ya sallame mu. *** Ransa a matukar bace yake kutsa kansa falon, tana zaune hannun ta rike da babban tasbah tana ja, tana ganin shi ta fadada fara'a ta "Soja mazan fama." Yake yayi kawai ya ƙaraso ya samu waje ya zauna "Dadah, me yaron nan yake so ya zama?" Ya ambata yana jan karamin tsaki "Wanne yaro hala? Ja'afaru ko wa?" "Farouk!" "Toh me kuma Babana yayi ehe?" Cire hular kansa yayi ya ajiye yana goge gumin kansa "Wallahi wai ya saki yarinyar nan." Da sauri ta dafe kirjin ta "Innalillah wa inna ilaihi raji'un! Saki!!! Yaushe?" Tsakin ya kara ja yana duban kofa "Dazu maigari ya kirani wallahi, kuma abin takaice wai aikawa yayi da takardar,ba shine da kansa yaje ba, gashi duk numbobin sa na kira a kashe balle nasan ta ina zan fara, ni rabona ma dashi tun zuwan da yayi karshe yace an tura shi wani aiki." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yau me zanji, wanne irin abu ne wannan? A lafiyar sa kuwa? Kai da sake gaskiya, bana jin Babana zai aikata makamancin wannan." "Dadah dan yau fa, halin su sai su." "Duk da haka Kabiru, sam ban yarda Farouk zai aikata ba, aikuwa ba dan dare yayi ba a yau zan bar garin nan, amma tabbas gobe da izinin Allah ina chan, hankali na ba zai kwanta ba sai na ji komai, ka cigaba da kiran wayar tasa ko zaka samu kaima." "Allah ya kaimu, nima zuwan ya kamani, ina ganin ki fara zuwa sai na biyo ki jibi, dan akwai ayyukan da zan karasa goben, amma idan na koma zan shiga gidan Aboki, zan sanar masa abinda yake faruwa, shine me yabon faruk yanzu sai yasan abinda ya sake aikata bayan na dah, idan yaso sai mu tafi taren musha kunyar a tare, dan bazan iya kallon mutanen nan ba wallahi, da kunya ana ganin mutuncin ka." "Duk yadda kayi yayi, amma ni kam gobe zan isa da izinin Aallah." "Allah ya kaimu, sai ku tafi Ja'afar da driver ko?." "Amin, yayi hakan." Ta amsa har lokacin bata bar mamaki ba, ina alkawarin da yayi mata na cewa duk ranar da Aminatun ta gama karatu zai dawo da ita wajenta, su zauna tare har zuwa lokacin da shima zai nemi transfer ya dawo nan ɗin, me ya faru da babban alkawarin da yayi na taimaka mata wajen hada ta da dangin ta? Kai akwai lauje cikin nad'i, tabbas wannan makirci ne aka shirya, sai dai kai tsaye Mum ce ta fado mata arai, tasan zata iya aikata fiye da hakan ba, amma dai koma menene, zata je taji. *** Alhamdulillah, nagode kwarai da addu'oin ku 🙏💯 Allah saka da Alkhairi. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                     : ©️ HAFSAT RANO     THE HEART BREAK💔💔💔💔                 (14) ***Dauke nake da Saddiku ina dan jijjigashi, rabi da kwata na hankali na yana kan tunanin abubuwan dake faruwa dani, sallama Karime tayi daure da zanin wanka ta lullube saman kanta da wani, kallo na yayi ganin yadda nayi firgigit jin sallamar ta. "Tunanin dai ko Aminatu, kifa saukaka ma ranki kar ki jawo wani ciwon kuma." Yake nayi wanda aka ce yafi kuka ciwo na zauna sosai ina kwantar da Saddiku, zaman tayi itama ta hau shiryawa bata sake min magana ba, tashi nayi na fito, nayi fitsari na dan leka dakin Baba, yana kwance idanun sa a bude, na k'arasa na tsuguna gaban sa "Sannu Baba." Nace ina maida kwallar ido na, bina yake tayi da ido babu halin magana, shiru nayi ina tunanin yadda mutum zaiyi rayuwa a haka, tabbas ba karamin jin jiki yake ba, gashi babu wanda zai taimaka masa da  zuwa asibiti, Farouk ne ya fado min, na tuna da yananan yanzu, xan iya neman alfarmar sa ya taimaka masa. Na jima a dakin ina zaune dashi har saida Inno ta kwala min kira, da sauri na tashi na fito, sai nayi turus ganin Dadah na kokarin shiga dakin Inno, gani na yasa ta dakata, ganin haka yasa nayi saurin isa gareta, bansan sanda na fada jikinta ba, na saka kuka sosai. Rike ni tayi muka karasa shiga dakin har lokacin kukan nake, gaishe ta Karime tayi ta tashi ta fita don bamu waje. Tabarma Babba na dauko na shinfida mata, na fita da sauri na debo mata ruwa na ajiye a gaban ta sannan na zauna ina sauke kaina kasa. "Aminatu, sannu kinji." Hakan data fada yasa naji zuciya ta ta sake yin rauni, tabbas ni ɗin abar a tausaya min ce, "Sannu da zuwa Dadah, ina wuni?" "Lafiya kalou Aminatu, mun same ku lafiya?" "Alhamdulillah." Nace ina wasa da hannu na. Inno ce tayi sallama ta shigo Yalwati na bin bayanta, a mutunce suka gaisa kafin su tashi su fita. Muskutawa tayi kadan tana dubana sosai. "Aminatu me yake faruwa? Me ya hada ki da Babana." Ta jeho min tambayar ta na riga nasan da ita, kallon ta nayi zan cigaba da kukan da nake ta dakatar dani, "Kul kina kuka, akan me? Fada min gaskiya me ya faru, kunyi fada ne ko kin masa wani laifin ne?" "Allah banyi masa komai ba, hasalima rabona dashi tun ranar daya maida ni makaranta, yace sai ranar da muka gama exams zai zo, toh kuma ni tun bayan nan sau biyu mukayi waya, daga nan bamu sake magana ba." "Zaki iya dauko min takardar da aka kawo miki?" "Eh." "Toh bani na gani." Tashi nayi na bude jakar da nazo da ita na dauko, na fito da takardun guda biyu, kura musu ido nayi a tare, sai kuma na juya na mika mata su dukka ina jin wani iri, karba tayi ta bude ta farko me dauke da sakamakon test result dina, a fuskar ta naga yanayin da take ciki, sosai naga ta sake sakin fuskar fiye da yadda take a baya, ninkewa tayi ta ajiye ta bude dayar, ta jima tana dubawa kamar ne son gano wani abu kafin ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya. "Waye ya kawo miki wannan?" Ta nuna takardar sakin "Bansan waye ba nima, nasan dai wata mota ce ta shigo makarantar mu, ina kallo ta bawa security man din dake wajen shi kuma ya kawo min, sai dai tabbas mace ce dan naga hannun ta." "Baki ga fuskar ta ba kenan?" Girgiza kai na nayi "Ban gani ba, amma ance tazo gida ma bayan ta je makarantar." "Nan gidan?" Ta tambaya da sauri. "Eh ance tazo, kuma maigari ma yace sunje chan wajen sa sun kai masa." "Good, kira min Maman taku." Tashi nayi tsam naje na kira Inno, a tare muka shigo na samu gefe na zauna. "Ko zaki iya gane matar data zo dan Allah?" Tayi maganar tana kallon Inno "Zan gane ta." "Yawwa." Ciro wayar ta tayi ta budo wajen hotuna ta fara nuna wa Inno, duk wadda ta nuna mata sai tace ba ita bace. Ajiye wayar tayi tana murmushi "Aminatu samu yaro yaje waje ya kira min Ja'afar, suna nan a mota." Tashi nayi na fito, babu yaro ko daya duk Inno ta kora su waje, hijabin jikin Karime na karba na leka da kaina na kirawo shi. Gabana ne ya fadi da ya fito, sosai yayi min kama da Farouk, sai dai shekaru da Farouk zai fishi da girman jiki. "Sannu, Dadah ke kiran ka." "Owk." Yace yana biyo bayana, tsayawa yayi a tsakar gidan na shiga na fada mata gashi, Inno ce ta daga labule tace ya shigo, a gefen tabarmar da Dada ke kai ya zauna yana gaida Inno din, amsawa tayi kafin Dadah tace "Kana da hoton Abidah a wayar ka ko?" "Ina dashi." "Yawwa mu gani." Budowa yayi ya mika mata, ta kalla ta mika wa inno, "Wannan fa?" Girgiza kai Inno tayi tace "Gaskiya ba ita bace." "Owk shikenan Ja'afar, zaka iya tafiya." Tashi yayi ya fita, Dadah ta cigaba da nuna wa Inno dukkan hotunan data ke tunani, amma sam Inno bata ga matar ba, a dole Dadah ta hakura da tunani shin wacece? Ganin ta kasa gane wacece yasa ta yi mana sallama bayan ta sa yara sun shigo da kayan data kawo min ta tafi, da nufin zata dawo gobe idan Allah ya kaimu. Har waje na rakata ina jin kamar na bita, sai dai nasan hakan ba mai yiwu wa bane. *** Sosai Dadah ta shiga damuwa, babu abinda yafi daga mata hankali sama da abubuwan da takardun nan guda biyu suka kunsa, abubuwa biyu dake da alaƙa da juna da siga daban, idan har ya tabbata Farouk shine yayi sakin ya kenan za'a yi? Bin Ja'afar tayi da ido har ya karasa shigowa cikin falon. "Wash." Yace yana fadawa saman kujerar. "Daga ina kake haka kai kuma?" "Wallahi Dadah zagaye nayi a gonar nan, sai naga girman ta ya karu sosai fiye da dah, ko dan na jima banzo bane ba oho." "Sai dai hakan, amma ai yadda take haka take, kawai son jikine irin naka." "Yawwa kai, nace yaushe rabon ka da Babana ne wai?" "Wai ya Farouk?" "Bansani ba." "Sorry, a satin nan ma munyi magana ai." "Da gaske ko da wasa?" "Wallahi, kinsan baya kasar sannan inda yake babu wani network me kyau, nima Amal ce ta bani number tasa lokacin da Mummy ta kirani akan bata samun shi a waya, shine na kirashi, wajen kwana huɗu ma ina gwada kiran kafin ta shiga." "Ina number, maza bani ita." "Owk bari na dauko wayata a ciki na barta." Mik'ewa sukayi a tare ya nufi dakin sa, a tsaye Dadah take har ya dauko ya dawo, hannun ta rike da wayar ta. Number ya karanto mata ta saka sannan tayi dialing, bugu daya ta shiga, zama tayi da sauri tana saka ta a handfree, sai dai har ta gama ringing din bai daga ba, cigaba tayi da kira, babu alamun za'a daga ɗin, haka ta hakura ta bari anjima ta sake gwadawa. "Be d'aga ba." "Kila baya kusa ne, idan ya gani zai kira nasan." "Ina ita Abidar take, tana Kaduna ne ko Abuja?" "Wai Mummy, ina ga tana Lagos, yanzu tafi zama a can ai saboda bussiness ɗin nata yafi a chan haka." "'Owk yayi, ka gwada kira min shi zuwa anjima idan ya dauka ka haɗa ni dashi." "Ok Tam, bari na shiga na huta." Barin falon yayi itama ta wuce dakin ta tana samun magana da Farouk din kafin wayewar gari. Tun tana saka ran zai kira har ta hakura ta kwanta, da safe wajen karfe goma Daddy ya iso, dama shi akwai shi da sammako saboda yanayin abubuwan nasa, zuwa sha-daya suka isa gidan Maigari, ciki maigari ya shiga dasu ya tura kiran su Inno. Lokacin ina zaune muna yar hira da Karime sakon kiran yazo, Hjabi na kawai na dora a saman kayan jiki na muna tafi gabana na ta faduwa. Cikin gidan muka shiga, yanayin takalman da na gani a kofar dakin tasa jikina ya ɗan soma rawa, rike ni Inno tayi muka shiga da sallama, duk suka zubo mana ido, a darare na zauna gefen Inno kaina a kasa na gaishe su, sannan suka gaisa da Kawu kanin Baba da Inno. Kamar wanchan karon yanzu ma maigari ne ya sake sabon jawabi, sannan ya bawa Daddy damar jin ta bakin sa. Wayar Dadah ce ta dau burari alamun kira ya shigo, dan dakatawa Daddy yayi ta ciro wayar, da sauri ta furta "Alhamdulillah." Ta daga ta saka ta a handfree "Assalamu alaikum." Muryar sa ta daki dodan kunne na, wani irin zabura nayi daga zaune, kowa ya zuba wa wayar ido kamar shi din ne a wajen. Daddy ne ya mika hannu ya karbi wayar "Kana jina?" "Daddy barka da warhaka, ina kwana?" "Lafiya, kana jina, ba wani dogon bayani muke bukata ba, ina fatan kana hayyacin ka dai ko?" "Eh daddy, a hayyacina nake." "Good, menene hakikanin gaskiyar takardar sakin daka aiko wa matar ka?" Shiru yayi, kamar baya kan layin, har sai da Daddy yace "Kaji abinda nace ko?" "Naji Daddy." "Toh ina jinka, me ya faru ka sake ta? Wani laifin tayi maka ne ko menene?" Kai tsaye yace "Babu laifin komai, kawai zaman mu ne ya kare." Da sauri na dago, Ina son sake tabbatar wa kaina wannan ba Farouk d'ina bane. "Haka kawai kenan ka sake ta ba tare da laifin komai ba ko me?" "Eh haka nan ne, babu laifin da tayi mun." Share zufa naga Dadah nayi, Inno kuwa kamar bata wajen, kuma baka isa ka gane yanayin da take ciki ba, ni kuwa sai naji kamar yanzu ne komai yake faruwa, jikina har rawa yake, na kasa yarda da abinda kunnuwa na ke jiye min, ina kallo Dadah ta karbi wayar cikin bacin rai tace "Babana kaine kuwa? Kasan me kake cewa? Kana nufin duk abinda ke jikin takardar kaine ka rubuta shi? Kuma shine gaskiyar abinda yake faruwa?" Babu ko digon tsoro balle damuwa a cikin muryar sa, kai tsaye yace "Ni ne da kaina, kuma duk abinda ke rubuce a ciki shine gaskiyar magana, kuyi hakuri idan na bata muku, Allah ya huci zuciyar kowa." Kafin ta samu damar sake wata magana kiran ya katse, da sauri tayi kokarin sake kira Daddy ya dakatar da ita. "Karki kirashi Dadah, barshi kawai, ni ya wulakanta ya nunawa duniya ban isa dashi ba, babu komai amma.." "Kayi hakuri Alhaji, yaran yanzu ne sai addu'a, idan ka biye tasu sai kayi musu mugun baki." Mai gari ya katse shi, sannan ya maida kallon sa wajen da muke zaune "Toh kun ji dai daga bakin yaron, duk da dukkannin mu babu wanda zancen nasa yayi wa dadi, amma dole haka zamu hakura, aure ya riga ya kare, dama shi raine dashi, idan kwanan sa ya kare ko ana so ko ba'a so dole a hakura." "Amma ba wai na katse ka bane, yarinyar nan fa tana dauke da juna biyu, ya kamata a duba lamarin nan." Kawu yace yana duban maigari da Daddy, "Juna biyu !" Suka hada baki a tare cikin tsananin mamaki "Tabbas tana dauke da juna biyu, ni da kaina naga sakamakon gwajin da akayi mata." A cewar Dadah tana duban Daddy. "Amma shine yaron nan zai maida mu yan iska? Lallai ma wallahi, dani yake magana." Yayi maganar a fusace "Mubi komai a sannu Alhaji, idan yaso sai a sake tuntubar shi yaron kan maganar cikin." A cewar maigari. "Babu bukatar hakan dan yaro ya riga ya nuna baro-baro babu wani abu da ya hada shi da ita, dan haka magana ta kare." Duk muka juyo da sauri, Mummy ce tana tsaye tayi kyau ainun cikin shigar alfarma, kallon juna sukayi ita da Dadah, kafin cikin bacin rai Daddy yace "Me kike yi anan Abidah?" A gadarance tace "Abinda ya kawo ka, shi ya kawo ni,kasan dai ina da hakki akan Farouk ko? Wanchan lokacin na kyale ka da kayi kokarin bata min rayuwar yaro, akayi masa sharrin da kai kanka kasan ba shine ya aikata ba. Shine yanzu za'a sake ruguza min rayuwar sa bayan Allah ya taimake ni ya gane gaskiya, naji komai a wajen Ja'afar tun ranar da abin ya faru, har zuwa zaman da zakuyi anan ɗin, dalilin zuwa na kenan saboda na karba wa d'ana yanci." "Danki? Ashe dama kina da d'a?" "Kafi kowa sani ai, bani da lokacin amsa maka wannan tambayar, maganar d'ana nazo, babu kuma uban da ya isa ya tilasta masa aikata abinda beyi niyya ba." Kasa magana Daddy yayi saboda tsananin kunyar data rufe shi, kasa yayi da kansa kawai yana jin kamar kasa ta tsage ya shige, jawabi ta shiga korawa maigari, a karshe tace Farouk ba zai karbi cikin jikina ba dan ba nashi bane. Tun da ake maganganun nan jikina yake rawa kamar mazari, tuni zuciya ta ta kekashe, hawayen dake faman kai kawo a saman fuskata ya bushe, cikin dakiya na tashi, na isa tsakiyar wajen, hannu na biyu na hada waje daya cikin wani irin yanayi nace "Ina rokon duk wanda yake wajen nan, da yayi hakuri, da abinda yake faruwa, ni kaina bansan menene matsalar ba, sannan ina neman wa Ya Farouk afwa wajen ku iyayensa, tabbas bashi da laifi ko daya a cikin duk wani abu da ake tuhumar sa, hasalima shi taimako na yayi. Daga rana irin ta yau na bar maganar nan, zan cigaba da rayuwa ta a matsayin wadda bata taba sanin shi ba, zan manta dashi, zan cigaba da rainon abinda ke cikina, har zuwa ranar da zai zo duniya, ina fatan hakan ya faranta wa kowa." Ina kaiwa nan na juya da sauri, zuciya ta na tafasa na bar dakin, ina ji suna kwala min kira, ban saurara ba, dan bana jin zan iya sauraron duk wani abu da zasu ce min, maganar da akayi da ya Farouk a waya kadai ta isheni, bana bukatar jin sauran wani bayani, a yau na tabbatar da na rasa shi, rashi na har abadah, zan sake sabuwar rayuwa, duk da bazan ce zan manta dashi a rayuwa ta ba, amma tabbas zan ajiye dukkan shafukan rayuwar mu tare a baya, zan bude sabon shafin rayuwar da bani da masaniyar in da zata kaini. _"Aminatu ina so kiyi karatu, ina so ki zama abar alfahari sanda zaki sadu da sanyin idaniyar ki."_ Wadannan sune maganganun sa a kullum gareni, wanda bani da masaniyar hakikanin abinda suke nufi, sai dai yau nayi wa kaina alkawarin, zan dauke su a matsayin wani tsani na matakin rayuwar da zan shiga anan gaba. Hanya kawai nake haɗawa da taimakon Allah na isa gida, da sauri Karime ta tare ni, tana kokarin rikeni na raba ta gefen ta, na shiga daki na hada kaina da guiwa ta cikin rashin sanin makomata. A kaina tazo ta tsaya tana min magiyar na sanar da ita abinda yake faruwa, ban iya ce mata kala ba, har ta gaji ta samu gefe na ta zauna tana rafka tagumi. A tare suka shigo gidan, kai tsaye dakin Inno suka shigo, Dadah ta ƙaraso gareni tana daga ni. "Aminatu tashi zakiyi mu tafi, mun gama magana da Maman ki, ba zan iya kyale ki ki raini cikin nan ke kadai ba, maza tashi kinji." Janye jikina nayi a hankali na matsa gefe ina kallon ta "Kiyi hakuri Dadah, ba zan biki ba, na gode da hallacin da kuka nuna min, sai dai na yanke shawarar nesantar duk wani abu daya danganci Ya Farouk, ina ganin hakan da zanyi shine kawai mafita a garemu, kiyi hakuri." "Ya zaki ce haka, kina nufin kin karaya, kin hakura kenan? Ni sam ban yarda da Farouk zai aikata ba, akwai dai matsala, ki bini muje in Sha Allah zamu gani bakin zaren." "Kiyi hakuri dan Allah, ba zan iya binki ba, hakan na iya haifar da matsala gagaruma a cikin ahlinki, sannan Mummy, ba zata taba karba ta ba, zan yi rayuwa ta, zan zauna anan, tare da yan uwa na dan Allah." "Aminatu..." K'asa na tsuguna ina kama kafarta "Kiyi hakuri Dadah, kiyi hakuri." Kuka ta saka, ba tare da tayi magana ba ta juya da sauri ta bar dakin. "Ya Allah!" Na furta da karfi ina zama a kasa, kaina kamar zai rabe biyu saboda tsananin ciwo. Matsowa Inno tayi tana kallo na "Kin tabbata ba zaki bita ba, zaman nan ba zai miki dadi ba, kinga yanzu da dah ba daya bace." Girgiza kai na nayi, "Kiyi hakuri, amma bazan bita ba." "Shikenan, ki daina kuka kar kanki yayi ciwo, tashi ki kwanta a saman gadon, zanje na yi mata bayani yadda zata gane." Tashi nayi jikina na rawa na hau gadon na kwanta ina lunshe ido na. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                       8/a:  ©️ Hafsat Rano         15 **** Duk hidimar da ake a gidan ban mik'e daga kwanciyar da nayi ba, sake juyawa nayi na maida kaina dayan barin, daga daren jiya zuwa yau na riga na gama yanke wa kaina hukuncin da nake ganin shine zaiyi daidai da rayuwata. Tsawon lokaci na dauka Ina kwancen har lokacin da Inno ta shigo dauke da kwano, a kusa da kafata ta ajiye ta. "Tashi maza, kici abinci sai kuje chan gidan ki dauko abinda zaki dauka." "Toh." Nace ina tashi, ajiyar zuciya na sauke na jawo kwanon, fara fita nayi na wanke hannu na da bakina na dawo na zauna na shiga cin abincin a hankali, ina gamawa na chanja kayan jikina, na zura hijabi da takalmi na fito. Dakin Baba na shiga na gaida shi na duba jikin shi sannan muka tafi nida Yalwati. Da yake safiya ce bamu hadu da wasu mutane masu yawa ba muka isa gidan, sojoji ne tsaye a gate din, sai Ja'afar dake magana da daya daga cikin su,yana hango mu ya taho yana fad'ad'a fara'ar fuskar sa. "Sannun ku da zuwa." Yace yana tsayawa a gabana, sai dana dan ji wani iri dan sosai suke yanayi da Ya Farouk, dakewa nayi muga gaisa, yanayin yadda yake kallo na yasa na dan ji babu dadi, nayi kasa da kaina har muka shiga gidan ban dago ba. Daddy na zaune suna magana da Dadah muka shigo, da sauri ta mike tana riko ni fuskar ta kamar zatayi ne saboda tsananin farin cikin ganin mu "Aminatu, kin chanja shawara ko?" . Yadda tayi maganar cikin farin ciki yasa naji kunya, a hankali na zame jikina na tsuguna a kasa na furta "Ina kwana Dadah?" "Lafiya lou Aminatu, nasan dama zaki chanja shawara, Nagode sosai da kika yarda zaki bini." Sai ta maida hankalin ta kan Yalwati cikin fara'a tace "Sannun ku da zuwa." "Yawwa ina kwana Hajiya." "Lafiya lou, ku zauna mana." Zama tayi a kujerar dake hanya ni kuma na sake gyara zamana a kasan da nake.Sabuwar gaisuwa suka sake sannan suka gaisa da Daddy da ya gama waya. A hankali na dago kaina na cikin girmamawa na gaishe shi, a sake ya amsa yana nazarina. Komawa Dadah tayi ta zauna sannan tace "Aminatu, zo matso kinji' Jan jiki nayi na matsa gaban ta, cikin rashin sanin yadda zata dauke abin nace "Dadah zan dau kayana ne, da abubuwan makaranta." "Ba zaki bini ba kenan?" Tayi tambayar tana bata rai Zanyi magana Daddy ya katse ni "Kiyi hakuri Dadah, tabbas tana da babban uzurin ta na kin amincewa ɗin, Aminatu, kiyi hakuri kinji, kowacce rayuwa cike take da kalubale, idan kayi hakuri sai kaga kaci riba, tabbas nasan ba'a kyauta miki ba, amma bani da yadda zanyi, kiyi hakuri kinji." Ban iya magana ba sai daga kai kawai da nake kamar kadangaruwa, nasiha ya shiga yi min sosai, sannan ya bani tabbacin duk yadda zaiyi zai nemi Farouk, yaji komai sannan magana ciki sun karba, sun tabbata bazan taba yin wani abu da zai bata sunana ba. Ɗorawa tayi "Zanyi kokarin ganin na kula da komai naki har zuwa lokacin da zaki sauka lafiya, mun riga munyi maganar jiya. Yanzu ki cire duk wata damuwa a ranki, ki fawwala Allah komai." "In Sha Allah, Nagode Allah ya kara girma." Wayar sa ce tayi kara, ya mike ya bar falon, hawaye naji ya zubo min, nayi saurin maida su ina bawa kaina k'warin guiwar bazan yi kuka ba, musanman a gaban Dadah. Bata ce min kala ba, sai kawai ta maida hankalin ta wajen Yalwati tana mata yan tambayoyi. Mik'ewa nayi tsam, suka bini da ido,a hankali na nufin dakin, cikin tarardadin abinda zan tarar ɗin. Turawa nayi, kamshin turaren sa ya daki kofofin hanci na, babu abu daya na dakin daya chanja, yananan tun ranar da muka bar shi, ba tare da sanin cewa na barshi har abadah ba. Kaina ne ya hau juyawa, nayi saurin dafe wa, na shiga har haɗa duk abubuwan dana san nawa ne, cikin dan kankanin lokaci na hada komai waje daya. Kallon wardrobe d'insa nayi, zuciya ta ta kasa hakuri, hannu nasa na bud'e, babban album din sa ya fado, tsugunawa nayi na dauka a hankali na shiga budewa, daya bayan daya nake bin hotunan da kallo, kwalla na taruwa a ido na. Jin takun tafiya yasa nayi saurin tashi, na ciri guda daya na tura cikin jakata na maida sauran tare da rufe wardrobe din. Juyowa nayi da nufin tafiya muka hada ido, tana tsaye ta zuba min ido tana murmushi, murmushi me dauke da ma'anoni da yawa Dauke kaina nayi na tattare kayana zan bar dakin, ta gefen ta nazo wucewa a hankali nace "Ina kwana?" Bata amsa ba, dama nasan ba zata amsa din ba, sai dai har lokacin idon ta na kaina, kallon da na rasa na menene, rab'ewa nayi na wuce kawai ba tare da na sake cewa komai ba. Ina zuwa falon na tarar da Dadah, tana zaune tana juya wayar hannun ta, kasa na tsuguna cikin dakiya nace "Na gama zan tafi Dadah." Girgiza kai naga tayi, ta miko min har karamar jakar hannu. Ajiye kayan hannu na nayi na karba ina kallon ta "Karbi ki ajiye wajen ki, in Sha Allah zan dinga zuwa ina duba ki lokaci zuwa lokaci, ki kula da kanki kinji? Allah yana tare dake." "Nagode sosai Dadah, bansan da wanne bakin zan gode miki ba, Ubangiji ya sake miki da mafificin Alkhairi." Da sauri ta tashi, ta shige dakin ta ba tare da tace komai ba, jiki na a matukar sanyaye na mike, ina karewa ko ina kallo, Yalwati ta tayani daukar kayan, muka fito. Da sauri ya tare mu, ya karbi kayan hannu na har lokacin idanun sa na kaina. "Daddy yace na mika ku saboda mutane." Ba musu muka bi bayan sa, ya saka kayan a booth muka tafi. Har kofar gida ya kaimu, sannan ya tayamu sauke kayan yara suka dauka muka shige ciki. Daki na wuce kai tsaye, na ajiye kayan na jawo jakar Dadah na bude, waya ce yar karama, sai kudi masu yawa, murmushi nayi na ciri wayar na ajiye jakar ina kokarin kunna wayar. Numbobi biyu na gani akai, daya an saka my number, sai dayar dake rubuce da babban baki, *BABANA* zuba wa number ido nayi ina kallo, babu shakka number Ya Farouk ce, shiru nayi ina tunanin abinda zanyi da ita da Dadah tayi min saving dinta akai, sai dai bani da amsar hakan. Ajiye wa nayi kawai na shiga wata sabgar ina kokarin ganin na manta da damuwa ta.    Kwana uku da tafiyar su Dadah sai ga kiran ta, da murna na daga muka gaisa ta tambayi ni idan akwai matsala, hira muka danyi sannan ta kashe bayan ta kara jaddada min kalmar nan ta hakuri ta na riga na gama haddace ta. Tun daga lokacin muke waya sosai, wani lokacin naga shiru nakan kirata muyi hira sosai. Wata rana muna waya take min maganar Jamb, tabbas nima dama ina son yi ɗin,sai dai idan na duba yanayin da nake ciki sai nace na jira wata shekarar, ko dana fada mata uzuri na bata amince ba, a wannan shekarar take so nayi, babu inda raino ko ciki ke hana karatu. Dole na amince na shiga tunanin yadda komai zai kasance.    *** *Bayan wata biyu* Ba tare da dogon nazari ba, tabbas yan watannin nan a cikin waha'a nayi su, wahalar rainon karamin ciki zuwa kokarin mantawa da dukkan rayuwa ta ta baya, bani da matsala da Inno, dan babu abun da yake hada ni da ita, iya kar kokari na ina yi ganin na kyautata mata, ita dinma a bangaren ta hakan ne, duk abinda tasan zan nema tana kokarin bani shi.  Ranar muna zaune muna hira da Yalwati, wadda yanzu ta zama abokiysr hira ta tun bayan tafiyar Karime, dan Inno ba kasafai take doguwar hira dani ba, kasuwancin ta da ya kusa durk'ushewa ta jajirce ganin ta farfaɗo dashi, dan hakan ya zama ma kowanne lokacin ta me tsada ne a wajen ta.    Nura ne ya shigo, kansa dauke da hular gini, ya zauna daga gefen tabarmar da nake zaune yana jingina da bango cikin matukar gajiya. Cikin tausaya wa nace masa "Sannu." ruwan dake gefe cikin kofi na mika nasa, karba yayi yasha ya ajiye sannan ya ciro takarda daga aljihun sa "Gashi Aminatu, dukkan bayanin yana ciki tace, ki shirya gobe sai na rakaki ki cike dan tace befi sauran kwana uku a rufe ba, Allah ne ma yasa aka danyi jinkiri wannan karon da sai dai wata shekarar." Da farin ciki na karba na duba, sannan nace "Kai amma naji dadi, nagode sosai Yaya Nura, Allah ya kaimu goben ." "Amin." Yace yana mik'ewa. "Bari na watsa ruwa a gajiye nake." "Gaskiya dai, ai da gajiya." Gyara zama nayi ina juya takardar principal din tamu cike da farin ciki. Ina shirin kwanciya Inno ta shigo, tsayawa tayi a kaina tace "Naji kuna waya ina tace miki ki saka?" Na gane Dadah take nufi, kai tsaye nace mata "Cewa tayi wai nasa Kano." Shiru tayi, sai chan kuma tace "Shikenan Allah taimaka." Daga haka ta fice tana jawo min kofar, ni kuma na gyara na kwanta ina fatan wayewar gari saboda tsananin farin cikin da nake ciki. Washegari da sassafe na shirya muka dau hanyar zuwa cikin gari dan cike jamb. Bamu sha wuya ba muka gama muka dawo. Ranar jarabawar tazo naje na zana cike da addu'ar samun abinda naje nema. Haka muka dawo gida zaman jiran tsammani. Kwana uku kuwa tsakani sakamakon ya fito, sosai hankali na ya tashi, haka dai na daure nasa aka dubo min. Ban taba zaton zanci haka ba, hamdala nayi ta wa Ubangiji dan nasan ba iyawa ta bace. Dana kira Dadah ma na faɗa mata sai ta hau murna, saura jiran post Utme kuma. A hankali cika na yana girma, ina kara tunanin yadda zata kasance min idan na haifi abinda yake ciki na, duk da yanzu bana shan wuya sosai sai dan abinda ba'a rasa ba.   Ranar dana gaji da zaman nayi gidan Karime, chan na wuni sai wajen magriba na dawo gida, washegari kuma nayi gidan Hanne. Sosai suke bani sha'awa, yadda suke zaune a dakin su, da dadi babu dadi, suna tare da mazajen su, hakan ba karamin sani tunawa da Ya Farouk yake ba. Haka dai nake bawa kaina k'warin guiwar komai zai wuce. *** BAYAN WATA SHIDA Haka rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Ubangiji  Ranar wata talata Inno ta fita sayo kaya,tun safe ta fita sai wajen Magriba ta dawo, yanayin ta kawai na kalla na tabbatar babu lafiya, a gefe kawai ta ajiye kayan ta fada banɗaki, ta jima ciki sannan ta fito, dakin ta ta wuce ta kwanta, ina ganin haka na mike na bita dakin, tayi nisa a tunanin ta na shigo, tana gani na ta tashi tana kokarin fita daga dakin, "Inna bak'ya jin dadi ne?" "Gajiya ce kawai, sai dan ciwon kai." "Allah ya sauwake, bari na dauko miki paracetamol kisha." Nace ina barin dakin, biyo baya na tayi, ni kuma na shiga daki dan dauko mata, a bakin rijiya na ganta tana alwala, tsayawa nayi ta gama sannan na bata maganin, balla tayi tasha ta wuce daki zuwa lokacin an fara kiraye kirayen sallah. Alwalar nima nayi na wuce daki dan yin sallah.   Tsawon sati guda kenan Inno na cikin zulumi, tun ina tambayar ta har na hakura na zura mata ido kawai ina alakanta hakan da yanayin jikin Baban.   Muna zazzaune a tsakar gidan ana yar hira, Baba na daga kofar dakin sa saboda yanayin da ake na zafi akan fito dashi shima yana shan iska. Shigowar bakuwar dauke da sallama ya saka Inno kusan sakin fitilar k'wan dake hannun ta. "Harira!" Ta furta cikin tsananin mamaki "Nice nan Innaro, kinga bakuwar daree ko?" Tayi maganar cikin wani irin salo dauke da yar karamar dariya. "Muje ciki." Inno tace tana saurin fadawa dakin ta, bin bayanta tayi, a hankali naji an turo kofar dakin alamun an rufo ta, mamaki ne ya kamani, na dan muskuta kadan ina tunanin abinda ya kawo matar, a yanayin Inno kawai ya nuna batayi maraba da zuwan nata ba. Tsawon lokaci suka dauka sai tashin magana k'asa k'asa, chan suka fito tare, Inno sanye da hijabi suka fita tare. Har wajen tara shiru bata dawo ba, ina ta sake-saken abinda yake faruwa sai gata ta shigo. Bata yi wa kowa magana ba ta wuce ciki, har zan bi bayan ta sai kuma na fasa ina kunna Radio cikin wayata. Washegari na tashi bani jin dadin jiki na kwata-kwata. Tun bayan dana shiga wata na takwas nake jin wani iri, haka dai na lallaba na d'anyi abinda zanyi, na koma na kwanta. Shigowar Inno dakin yasa na tashi da kyar ina kallon ta, zama tayi a gefen yar katifar tawa, hankalin ta sam baya jikin ta. Kallon idon ta nayi naga yayi ja, sai duk naji babu dadi. "Dan Allah menene yake faruwa inna? Kullum baki da nutsuwa kamar ma baki daa lafiya ne." Gyara zaman ta tayi, ta dube ni a nutse tace "Abubuwa ne da yawa suka tarar min Aminatu, sakamakon abinda na aikata ne yake bibiyata, dan Allah dan Annabi ki yafe min, na zalunce ki ban miki adalci ba, saboda son zuciya irin tawa, ki yafe min dan Allah..." "Inna? Me Kika yi min haka har zaki bani hakuri, ni wallahi bakiyi min komai ba, iyaye ai basa taba laifi a wajen ƴaƴansu, nice ma zan nemi gafararki, watakila na miki wani laifin ne da yasa ki a halin da kike ciki." "Kayya, Aminatu. Nidai dan Allah ki yafe min, kuma kiyi min alƙawarin zaki karbi hukuncin dana yanke akanki, shine kadai abinda zan miki na ceceki daga hannun azzalumai." "Ban gane ba inna." "Karki damu, yau in Sha Allah zakiji komai, banso sanar miki ba, amma ya zama dole idan ina so na samu sauƙin abinda na aikata." Daga haka ta tashi ta bar dakin. Kasa binta nayi kawai ina tunanin maganganun ta, ban gane komai ba sai ma toshewa danaji ƙwaƙwalwa ta na neman yi. Mik'ewa nayi da nufin binta naji marata ta rik'e. Komawa nayi na zauna ina yarfe hannu. A hankali naji ta fara saki, na yunkura da kyar na fito, dakin dana gani a rufe yasa na gane ta fita, komawa nayi na haye saman katifa ta na cigaba da juyi ina tunanin maganganun. La'asar likis ta shigo gidan a matukar gajiye, dakin da nake ta nufo, sallama kawai tayi ta shiga hade min yan abubuwa na waje daya, duk da dama ba wasu kaya bane masu yawa, cikin kankanin lokaci ta gama ta ajiye su a gefe sannan ta fita, cigaba nayi da kwanciyar kawai na zuba wa sarautar Allahu ido, chan ta shigo ta dauki kayan ta sake fita, bansan me hakan ke nufi ba. Da kyar na tashi na gabatar da sallah, idarwa ta kenan ko hijabin ban cire ba Inno ta sake shigowa, hannu na naga ta kama. "Tashi Aminatu, lokaci na kurewa." Mik'ewa nayi da d'an karfi na ta shiga jan hannun nawa, hanyar waje naga tayi dani, na cigaba da binta, motar dana gani ce yasa gabana faduwa, bude min tayi Na shiga sannan itama ta shigo, tana rufewa me motar yaja muka bar kofar gidan. Tafiya mukayi sosai babu wanda yayi magana a cikin su har sai da muka fita daga kauyen namu muka isa babbar tasha, gefe ya samu ya faka ya kashe motar ya fita daga ciki ya bar mu. Yana fita Inno ta juyo tana kallo na "Inna dan Allah me yake faruwa?" Kasan kafarta ta zura hannu, sai ga jakar da ta jima tana ajiyar ta, akan cinyata ta ajiye min tana kokarin maida kwallar fuskar ta "Gashi nan Aminatu, tabbas na zalunce ki, ban kyauta miki ba, na raba ki da dukkan farin cikin ki, ta hanyar rabaki da ainihin iyayenki...." Ras gabana ya fadi jin abin tace, wani irin juyi naji cikana yayi, nayi saurin dafe wajen ina zaro ido Bayan hannun ta tasa ta share fuskar ta "Labari me tsawo Aminatu, sai dai wallahi tallahi yaudara ta sukayi, ba tare da sanin komai ba, na amince musu, nayi dana sani Aminatu, nayi dana sani tun ba yau ba, Allah ne shaida ta. Kiyi hakuri da abinda zan sanar dake, bani na haife ki ba, hasalima bansan iyayenki ba. Rana daya muka haihu da mahaifiyar ki. Sai dai ni haihuwa nayi da kaina ita kuma aiki akayi mata. " "Watarana naje asibitin ganin likita, a lokacin cikina wata tara har da doriyar yan kwanaki, tare da kawata Harira data rakani, muka hadu da wata Hajiya, kana ganin ta kasan hamshakiyar mata ce, wadda ta jiku da kudi da jin dadi, yadda take ta kallon mu, yasa na dan zargu amma na share. Sanda muka zo tafiya ne ta tsaida mu, ta kira Harira gefe, sun jima suna magana har na gaji na zauna, sannan tazo muka tafi. Kwana biyu tsakani Harira ta bijiro min da maganar data firgita ni, da farko sam ban amince ba, amma yadda ya dinga kwadaita min abubuwan Alkhairin da zamu samu, naji na amince da bukatar su ta indai namiji na haifa zan basu, su kuma su bani tasu indai mace ce. Sai dai na kafa sharadin ba za'a dau lokaci ba zasu dawo min da d'ana, da farko matar bata amince ba, amma da Harira tayi mata bayani sai ta yarda. Bansan me ya faru ba ranar ina kwance sai ga Harira dauke da magani, ta kawo min wai nasha, ban kawo komai ba nasha, kafin wani lokaci na fara nakuda, da kanta ta dauke ni muka nufi asibiti, muna zuwa aka ce haihuwa ce aka shiga dani. Ban dau tsawon lokaci ba na haifo dana namiji, kukan sa kawai nake iya tunawa da yake min amsa kuwwa Harira ta dauke shi ta fita dashi, jim kadan ta dawo dauke da ke, da wannan jakar wadda ke dauke da manyan kudade masu yawa da tsoratarwa, haka ina ji ina gani aka tafi da d'ana, aka bar min ke. Bansani ba ashe Harira yaudara ta tayi, bata san su ba, bata taba ganin su ba sai ranar da muka hadun nan asibiti. Kiyi hakuri tabbas an zalunce ki, duk da bansan alakar ki da matar data tsara wannan abin ba, amma tabbas mahaifiyar ki bata da masaniyar abinda muka aikata." Saboda tsananin kukan da nake muryata ko fita batayi, bansan a wanne mazauni zan dauki zancen na ajiye shi ba, ji nake kamar zan haukace saboda tsabar firgice, sama sama numfashi na yake fita. Duk addu'ar data zo baki na na shiga karanto wa, ina kokarin ganin na saita kaina "Kiyi hakuri, tabbas na zalunce ki, ban kyauta miki ba. Bamu da lokaci Aminatu, ga jakar ki nan, da duk kudin dana karba wajen iyayenki, kiyi amfani dasu, domin sanar wa kanki rayuwa me kyau, Harira ta kulla wani babban abu, da bazan iya barin ta aiwatar wa ba, kuma bani da hujjar da zan ƙaryata ta, ko na nuna wa duniya ainihin wacece ita, rayuwar ki na cikin hatsari idan kika zauna anan, zan sauka na koma daga nan, ki kula da kanki, ki kula da kanki. Allah yayi miki albarka." Kukan ne yaci karfin ta, ta shiga yin shi babu kakkautawa. So nake nayi magana, so nake nace wani abu, amma na kasa, na kasa samun harafi kwaya daya da zai samu zama akan harshe ne har na iya furta shi. Ina jin ta ta bude kofar ta fita, cikin dakiya tace "Sai watarana Aminatu." Sai a sannan naji karfi yazo min, na yunkura da sauri na balle murfin motar na fito. "Inna..." Na kwala kiran da dukkan karfin muryar ta, chak ta tsaya, da tafiyar da take batare da ta juyo ba, k'asa daga kafa ta nayi, hankali naji wani abu kamar ruwa yana bina. Cigaba tayi da tafiyar ta, ina kallo ta bacewa gani na. A wajen na durkushe ina jin numfashi na yana barazanar barin gangar jikina. Sama sama naji wani mutum yana min magana, ban iya amsawa ba, sai nuna masa motar nake da hannu na. Barin gurin yayi da sauri, chan ya dawo tare da wata mata. "Taimaka Hajiya mu sata a motar chan bga kamar." Ina ji suka kamani, suka saka ni a motar, daidai lokacin me motar ya dawo. "Kaine me motar nan?" "Eh nina, tafiya zakuyi?" "Eh, amma ga passenger ka nan babu lafiya ai, ka taimaka a mika ta asibiti kusa." Lekowa yayi cikin motar, ganin yadda nake murkususu yasa shi firgicewa "Kuyi hakuri gaskiya ba zan iya ba, sai dai idan kunyi niyyar taimaka mata ne toh." Cikin bacin rai namijin yace "Ashe baka da tausayi, baka ga halin data ke ciki bane?" Da sauri ta dakatar dashi "Anas karka dau zafi, ina ganin haihuwa ce, ya kamata muyi sauri taimaka sai a biya ka malam." Tace tana kokarin shiga motar. "Muje toh tunda biya zakuyi." Kwafa Anas yayi a bude motar a fusace ya shiga. Ignore any error #Rayuwar Aminatu. 💔💔🙏 Nagode sosai da addu'oin ku gareni, kunsan matsalar ido sai a hankali, yau tun safe nake typing ɗin nan ina yi ina ajiye a hankali saboda idon. Please bear with me Dan Allah 🙏 Ranoa: ©Hafsat Rano                     (16) ★★★★★ Tsaki kawai yake har suka isa asibitin, zuwa lokacin na bana gane komai, tsananin azabar da nake ji tafi gaban a bayyana ta. Tun kafin motar ta gama tsayawa yayi saurin balle murfin motar ya fito yana kwala kira nurses din, da sauri daya ta ƙaraso wajen motar, suka taimaka aka fito dani, kujerar da ake dora mara lafiya aka saka ni akai, aka nufi labor room dani. Fitowa nurse din tayi ta bashi list ɗin abinda ake bukata, da sauri yaje ya siyo a cikin asibitin ya kawo.      Tsawon lokaci aka dauka ina fama, nasha matukar wuya kafin na haihu, ina haihuwa na suma cikin tsananin wahala. A wannan lokacin suka gyara min jikina ba tare da nasan me ya faru ba.    Sama sama naji suna kiran sunana, a hankali na fara dawowa, ido na ya sauka akan jaririyar dake kwance bisa kirjina, babu ko kaya a jikin ta, kura mata ido nayi, kuka take sosai da dukkan karfin ta. "Ga tana tabarakallah, lafiyayya kuwa." Naji nurse din na fad'a wa abokiyar aikin ta. Rasa a wannan  matsuguni zan ajiye wannan ranar, ranar da nake gudun zuwan ta, duk kuwa da na hakura na barwa Allah ikon sa, sai gashi tazo min a bai bai, cikin yanayin da ni kaina ba zan iya tantance shi ba, bani da kowa yanzu kenan? Sai wannan jaririyar da bata san komai ba, yanzu ne ma zata fara sanin abinda ke kunshe cikin duniyar nan. Hawayen da bazan iya banbance na farin ciki ne ko na bakin ciki ba suka shiga bin fuskata, ina ji suka cire ta daga jikina, suka shiga gyara ta. Dakin hutu aka maida mu, suka shigo a tare, kallon su nake har suka ƙaraso inda nake, Hajiya ta dauki yarinyar cikin farin ciki, ta shiga jera min sannu. "Masha Allah, Allah ya raya ta." "Matso ciki mana ka ga jaririyar." Tace tana kallon sa, yana tsaye jikin kofar yana kallon ciki, a hankali ya tako, ya ƙaraso gaban ta ya leka cikin shawul ɗin da aka rufe ta, murmushi naga yayi, a hankali ya furta "Tabarakallah Hajiya, kinga baby me kyau kamar a bani." Dariya ta saka "Kai fa Anas na manta son yara ne dakai." "Wallahi Hajiya. Ina son yara." "Allah ya baka masu albarka." Da sauri ya amsa "Amin Hajiya ta." "Ja'iri." Tace tana dariya. Kallo na tayi "Baiwar Allah ya kamata ki kira yan uwanki, kinga mu akan hanya muke, idan yaso ko zuwa gobe ne sai mu wuce, nasan ma dai goben zasu sallame ki tun da kalou kike ai." Ido na ne ya cicciko jin abinda tace, wa zan kira? Bayan bani da kowa a yanzu, wayar ma ko dauko ta banyi ba, ganin yadda duk suka kafa min ido yasa na wayance nace "Ba anan suke ba, a Kano suke." "Kano? Toh ai muna yan chan ɗin ne, idan kin yarda damu sai mu tafi tare gobe da safen, idan yaso sai dai su ganki da babyn ki." "Allah ya kaimu goben." Nace ina kokarin boye damuwa ta. Ido na ne ya sauka akan jakar nan, wani yawu me kauri na hadiye ina tunanin abin yi. Babu inda ta bar ya Farouk, komai nasa ne, hatta yatsun kafarta dana hannun ta nasa ne, hawaye na share a hankali ba tare da na bari sun ganni ba. Fita Anas yayi ya nufi masallaci, ya bar mu a dakin muka karasa kwana, da safe wajen tara aka sallame mu, mota yaje har tasha ya samo mana, aka zuba kayana muka dauki hanyar Kano a karo na farko a rayuwa ta. ***Isar Inno gida tana kokarin shiga yayi daidai da tsayawar motar, Harira ce ta fito kafin daga bisani matar da suke tare ta fito ita ma. Juyowa tayi tana kallon su, fuskar ta a yanayi me wuyar fassara wa. Karasowa sukayi suka tsaya mata a gaba, Harira tayi dariya sannan tace "Yau dai ga uwar yarinya nan, sai ki bata ita ta tafi da ita, ki gode wa Allah ma da bata ce zatayi karar ki ba wallahi, dan haka salun alum ba sai kowa yaji ba, shiga ki fito da ita." Kallon banza tayi masu a tare kafin tace "Ashe ma ni mahaukaciya ce kamar ke, kina tunanin bayan kinzo kin same ni da maganar banzar ki zan sake amince miki har na sake wani gangancin? Kije duk inda zaki ki tona min asiri, na riga na shirya wannan ranar tun kafin zuwan ta." "Kina nufin me kenan?" "Abinda kike tunani." "Baki yarda da abinda nace ba kenan?" "Ai yadda dake tun ranar da na gano cuta ta kikayi, a ranar na cire ki daga sahun mutane masu hankali, kuma a ranar na daina yarda da duk wani mutum a doran kasar nan." "Ina wai yarinyar take?" Matar ta tambayi Harira tana yatsine. "Kina ji ai ko? Ki shiga ki fito da ita, kinga shiyasa ma muka zo da daddare muyi komai cikin sirri, in Kuma so kike kowa yaji ne toh?" "Idan kinga dama, ki dauki abin magana ki zagaye duk garin nan ki sanar musu, a nan ne zan gane cewa baki da mutunci." Daga haka tayi shigewar ta gida, tsaye Harira tayi tana kallon matar, cikin bacin rai ta juya ta nufi mota tana mita "Kinsan bata min lokaci zakiyi kika kawo ni, bayan kin tabbatar min an gama magana." "Ja muje kawai aikin banza." Da sauri Harira tayi wajen motar, kafin ta k'arasa sun ja sun bad'e ta da kura, bin su tayi da gudu tana kwala kiran ta amma basu tsaya ba. Zage zage ta shiga yi cikin bacin rai. ★★★ A gurguje ya hada komai, ya rurrufe ko ina ya fito, baki daya tsawon zaman da yayi a wajen cikin rashin kwanciyar hankali yayi shi, kafatanin tunanin shi na wajen ta, duk da dai yasan ya bar ma mutane biyu amanar komai a hannun su wanda yake tunanin ba zasu taba yi masa ba daidai ba, amma hankalin nasa sam yaki kwanciya, har zuwa yau da suka samu yancin barin wajen, sosai yayi dana sanin shiga aikin soja, aikin da zai raba ka da kowa naka idan ba girma kayi a cikin sa ba, tsawon lokaci ba tare da anji daga gareka ba, babu service balle ka kira wani, idan ma akwai baka da kwanciyar hankalin kiran. Babbar mota ce sumfurin Hilux suka cika kayan su a ciki, suka dauki hanya. Ife ife ne kawai ke tashi a motar cikin yaren su na sojoji, kowa da abinda ya dame shi wasu ma waka suke bi cikin nishadi da murnar zuwa gida. Kallon su kawai yake ba tare da ya sa musu baki ba, daya gaji da hayaniyar tasu sai ya kwanta kawai ya lumshe idon sa yana jin farin ciki da daukin zuwan nasa gida. Sanda suka iso Abuja, dare ya soma yi sosai, bashi ya samu isa gida ba sai bayan sha biyu na daren. Rataye yake da jakar goyo irin babbar nan, sai yar karamar trolly daya riƙe yana jan ta a kasalance, ya ɗan buga gate din, sojan dake tsaye kofar ne ya leko, da sauri ya bude cike da mamaki sa, gaisawa sukayi ya wuce ciki kai tsaye, ganin dare yayi ya sa ya wuce bangaren su, ya tura kofar bakin sa dauke da sallama. Ja'afar na zaune a kan sofa Yana danne dannen waya yaji an turo , dagowa yayi da nufin ganin waye, cikin tsananin tashin hankali wanda yasa saura kadan ya saki wayar hannun sa ya furta "Ya Farouk!" Murmushi yayi, "Kana mamaki ne? Ko ka dauka na mutu ne?" "Wai yanzu kazo? Yanzu yanzu zuwan kenan?" "Ga zahiri ka gani, malam karbi kayan ka kaimin daki mana ka tsare ni da tambaya." "Auw." Yayi saurin karbar kayan yayi hanyar dakin dasu, shi kuma ya fada saman kujerar yana sakin ajiyar zuciya. "Home sweet home." Ya furzar da iska me dadi kafin ya tashi ya nufi fridge, ruwa ya dauka ya koma ya zauna yasha, sannan ya ɗan mike kafar sa. Jin shiru shiru Ja'afar be fito ba yasa shi kwala masa kira, a zabure ya fito kamar mara gaskiya. "Kai kuma daga ajiye jaka sai ka zauna, bayan kasan dole zan tambaye ka." "Bacci ne ya soma dauka ta, afwan, ya hanya ya komai?" "Normal." Dan zamowa yayi daga kujerar kadan yana fuskantar shi "Allah yasa dai abinda na saku kaida Amal kunyi min shi babu shirme ciki, nasan ma dai babu abinda zai sa kuyi min hauka, dan zan iya komai akai wallahi." "Na'am..?" Ya zaro ido "Yadda kaji, yanzu dai bari na kwanta, da safe ka shirya da wuri mu wuce, kasan i can't wait any longer." Tashi yayi wuce daki, a hankali Ja'afar ya zame a wajen yana jin wani mugun tashin hankali. Da sauri ya jawo wayar sa ya hau kiran Amal, har ta katse bata daga ba, haka yayi ta jera mata kiran duk kuwa da yasan ba dole ne ta daga ba, duba da dare yayi. A falon ya kwana, ba tare da ya runtsa ba, duk kuwa da yasan dole zai dawo dama, amma beyi tunanin dawowar shi a wannan lokacin ba. Lallai akwai matsala babba, matsalar da zata iya haifar da komai. Manage pls🙏 Yau ruwa yayi mun duka jama'a 😣😣🙄 Saura naji wata tayi min dariya🤫😬 8a:             Daurin Goro*              *17* © Hafsat Rano ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                 17 ★★★★★★ Cikin yanayin da ke bayyana tsantsar farin cikin sa ya tashi, mika yayi hade da salati, kafin ya fada toilet a gaugauce. Be dau lokaci ba ya fito, ya hau shiryawa cikin kaya mafi tsada da kyau, yana yi yana kallon kansa a mirror, murmushi ya saki da ya tuna inda zashi, shigar manyan kaya ce a jikin sa, wadda suka fito da zahirin kyawunsa na bakattsinen asali. Lekowa yayi falon da nufin kira Ja'afar, wayam babu kowa sai kalacin dake zube a saman centre carpet din dake ajiye a tsakiyar falon, tsaki yaja ya fito, ya nufi main part din gidan yana karewa ko ina kallo. Kicibis sukayi da Amal dake shirin fita a yanayi me wahalar fada, da sauri taja baya, cikin yanayin rashin gaskiya tace "Yahh..." Murmushi ya sakar mata kafin yace "Suprice!" "Saukar yaushe?" "Jiya kina ta bacci, nasan lokacin kin kai Australia ma dan nasan ki da shegen bacci." "Waye nake gani kamar Farouk?" Ta katse su tana fitowa daga kitchen rik'e da babban tea flask me dauke da kunun tsamiya. "Nine wallahi Mama, ina kwana?" "Ah laillai maraba da manyan sojoji, sannu da zuwa ya hanyar?" "Alhamdulillah walalhi ,sai kewar gida, sam aikin nan ba dadi wallahi." "Toh ya za'a yi, ka gaisa da Daddyn naku dai ko? dan yanzu yake shirin fita." "Aiko yanzu nake shirin shiga bangaren nasa, bari nayi sauri dan nima Kano zan tafi." "Za'a je a gano Hajiya kenan, toh karbi flask din nan ka tafi masa dashi, bari na dauko sauran kayan." "Ko da yake ma..." Ta kalli Amal dake tsaye kamar munafuka tana sauraron su tace "Daughter zo ki dau sauran kayan ki kai masa na karasa wani aiki anan." ***Tare suka jera yana tambayar ta bayan tafiyar sa, amsawa take har suka karasa part din Daddy, wayar ta dake cigaba da k'ara ta sake katse wa a karo na ba adadi, dariya Farouk yayi "Sirikin nawa ake wulakantawa ne?" Sai ta kalle shi da sauri, girgiza kai tayi suka shiga falon a tare, Daddy na zaune ya shirya cikin shigar sa kamar ko yaushe, da tsananin mamaki yake kallon Farouk din har suka ƙaraso ciki, ajiye kayan sukayi akan food mat din da ake jera masa kayan abincin kafin kowannen su ya zame ya zauna, Amal ce ta fara gaishe shi, kana ta mike kamar wadda ake mintsina ta fice da sauri, tana ji Ya Farouk yana bata sakon ta kira masa Ja'afar tayi gaba kawai ba tare da ta amsa ba. "Barka da Safiya." Ya furta cike da karsashi ba tare da ya gama karantar yanayin Daddyn ba. Be amsa ba, sai ma wurgo masa da tambaya yayi cikin dakewa yace "Sai yanzu kake nuna fuskar ka anan ko?" Kai tsaye yace "Ayi hakuri Daddy, wallahi tafiya ce ta taso a ranar, na sanar da Ja'afar amma ya fada maka, bayan na kirkira wayar ka ban samu ba, tun da muka shiga jejin nan babu service wallahi, sai jiya da Allah yayi muka fito lafiya." "Toh... Tafiyar ce ta saka ka yanke d'anyen hukuncin daka yanke kenan? Bayan haka ka nuna min kaine ka haife ni, ka watsa min k'asa a idon duniya ko? Ka kyauta.." Cikin rashin fahimta yace "Allah ya baka hakuri Daddy, amma sam ban gane abinda ake magana akai ba, ka gafarce ni dan Allah." "Rainin wayon naka har ya kai haka? Lallai wuyan ka ya isa yanka." Kasa yayi da kansa, yana ji Daddyn ya mike, ya shige bedroom d'insa, kasak'e yayi yana tunanin inda maganganun suka saka gaba, sai dai ya kasa gano ko daya. Fitowar Daddyn yasa ya dago, a fuskar sa ya jefa masa takardun guda biyu, kana yace "Idan kai kana shaye-shaye toh ni garau nake, kuma da hankali na idan kai mahaukaci ne, idan baka gane maganar fatar baki ba, ai zaka gane rubutu ko?" Da sauri ya dauki takardar ya hau budewa, bakin sa na karanto duk addu'ar da tazo masa, takardar shaidar cikin dake dauke jikin ta ya fara budewa, a take wani matsanancin farin ciki ya lullubeshi, wanda ba zai iya kwatanta shi ba, da k'warin guiwar sa ya bude dayar yana cike da yakinin abinda yace karo dashi a ta farkon na da alaƙa da ta biyu, a wani irin yanayi ya dago hade da mik'ewa tsaye. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya furta da karfi yana nuna wa Daddy hannu ba tare da ya iya furta kalma daya ba "Sannan bayan ka cimin mutunci ta hanyar sakin ta, ka kuma ƙaryata cikin dake jikin ta, shine har kake da gut din takowa inda nake, bansan kuma me kake so ka sanar dani ba." Da sauri ya dire akan ƙafarsa, yace "Ban aikata ba, ban aikata daya daga cikin abinda ake tuhuma ta dashi ba a karo na biyu wallahi ban aikata ba, bani da masaniyar komai.." "Rubutun jiki fa? Ko shima zaka ce min ba naka bane?" Ya watso masa tambayar yana masa kallon banza, sake kalla yayi da kyau, tabbas rubutun sa ne, me hakan ke nufi? Kira ne ya shigo wayar Daddyn, ya daga yana amsawa kafin yayi hanyar waje kawai ba tare da ya kalli jerin abinci da aka ajiye masa.   Kamar mahaukacin zaki haka ya fito daga shashen, da sassarfa ya isa bangaren su yana kwala wa Ja'afar kira. A zaune ya tarar dashi yana karin kumallo cikin kwanciyar hankali. Watsa masa takardun yayi a hargitse yace "Kayi min bayanin me ya faru, bayan tafiya ta, ina amanar dana bar maka?" "Ya Farouk calm down, nayi maka bayani." "Wanne irin calm down, kasan me kake fada kuwa?" Ya fada a hargitse "Owk, bayan tafiyar ka, ranar da ka fada min zasu gama exams, muka dau hanya, mun yi nisa sosai har mun wuce Kano ma amma da kadan, motar mu ta samu matsala, abinda yayi delay dinmu kenan gashi yamma tayi and wajen da muke babu abin hawa balle me gyara, da kyar muka sami wani bawan Allah ya juyo damu Kano, muka bar motar a can, washegari Daddy yazo da maganar sakin, bansan me ya faru ba naji dai suna magana da Dadah, the following day muka tafi Shagari tare da Dadah." Dafe kansa yayi cikin tsananin tashin hankali yace "Ja'afar, Saki ni? Na sake ta? When, how? Mesa bana tuna komai? Ka yarda zan sake ta kaima kamar Daddy?" Girgiza masa kai yayi "Ban yarda ba Ya Farouk, sai dai rubutun da ya zama naka, shi yafi bani mamaki, ya akayi hakan ta faru?" "Someone is behind this, WallAhi sharri aka kulla min, wani ke son ganin bayana." "Amma Ya Farouk..." Ƙarar shigowar messages wayar yasa yayi saurin kallon ta, ta saman notification bar ya ga alamun video aka turo masa ta whatspp, whatspp ɗin ma da ya manta rabon sa dashi, hankalin sa ne ya tafi zuwa son ganin abinda video din ya kunsa, a gaggauce ya danna load, ya zuba wa wayar ido yana jin kamar zuciyar shi zata fashe, cikin kankanin lokaci ya gama loading, videon ya bude. Shine zaune, gaban sa ɗan karamin centre table din dake falon su, rike da papper da biro, rubutun ya kura wa ido, take abinda ke rubuce a takardar hannun sa ya bayyana a faifan video ɗin, shine zaune yana rubuta wa Aminatun sa saki, cikin kwanciyar hankali, jefar da wayar yayi saman kujera yana sakin numfashi da karfi. "It's a trap Ja'afar, na shiga uku." Da sauri Ja'afar ya isa wajen wayar ya dauka yana kallo, rubutun tar hade da fuskar Farouk din sanda yake yinshi a cikin falon nan nasu, girgiza kai yayi yana shirin ajiye wayar sakon audio ya shigo, kunna wa yayi muryar Farouk din ta karade ko ina a lokacin da aka kira shi. Sanda yake ƙaryata maganar cikin, zabura yayi ya fisge wayar yana sake saurara, tabbas shine yake magana, amma yaushe hakan ta faru? Ya kasa tuna daya daga cikin ranakun da hakan ta faru. Da sauri ya fada dakin su, ya hau birkice komai na dakin, babu komai sai tarin kayayyakin su da takardun su na makaranta, a hargitse ya sake fitowa, rike da mukullin motar sa dake hannun Ja'afar tun tafiyar sa, da sauri ya tare shi ganin kamar ba a hayyacin sa yake ba "Barni Ja'afar, Kano zan tafi, daga can na dau Dadah mu tafi wajen ta, ba zan iya zama ba, idan har lissafin cikin jikinta da date ɗin da akayi daidai ne, toh tabbas ta haihu, ko kuma tana kusa da haihuwa, ya kake tunanin zata iya daukar wannan tension din da ciki." "Let me come with you, ba zaka iya driving ba." Mika masa car key din yayi ya fada saman kujerar idanun sa sun kada sosai, burin sa daya ya isa gareta, yayi mata bayanin komai. Cikin kankanin lokaci Ja'afar din ya fito bayan ya chanja kaya, suka dauki hanyar Kano. **** Dadah na zaune hannun ta rike da waya tana sake gwada kiran, karo na biyar kenan tana kira ba'a dagawa, gashi sam hankalin ta yake kwanciyar.  kanwarta Fatsim tayi wadda suke kira da Umma Fatsim, tace "Yaya wai kiran ne har yanzu?" "Kinga har yanzu ba'a daga ba, gashi sam hankali na yaki kwanciya wallahi, Allah yasa lafiya." "Toh amin, amma nake ga ai idan ba lafiya ba zasu kiraki su sanar miki, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru sai Alkhairi." "Allah yasa, anjima sai na k'ara gwadawa." Hira suka cigaba da yi sama-sama, har zuwa lokacin da aka bude gate din gidan, ta window ta zuge labulen ta leka, "Ja'afar ne." Tace tana sakin labulen, da sallama suka shigo, kallo daya zakayi wa Farouk kasan baya hayyacin sa, shine a gaba Ja'afar na take masa baya. "Babana!" Da sauri ya karasa gabanta, kamar karamin yaron dake gaban mahaifiyar sa, haka ya dora kansa a saman kafarta yana jujjuya kan kamar wanda ke shirin zaucewa "Me yake faruwa Ja'afar?" "Kamar yadda kike tunani ne Dadah." "Bani nayi ba wallahi Dadah, bani ne ba, sharri aka kulla min, I'm trapped bansan ya zanyi ba." Dago kanshi tayi "Mik'e Babana, nasan dama ba zaka taba aikata ba." "Nasan dama ba zaki yadda ba, ke kadai ce kika yadda dani, amma ni kaina yanzu Dadah ban yarda da kaina ba, na kasa tabbatar wa kaina bani ne na rubuta ba, rubutu na ne, magana tace Dadah, waye zai min wannan? Ko dai ni na aikata ban sani ba? Amma ta yaya? How comes bana iya tuna komai ne?" "Ba zaka taba aikata abinda zai zama cuta ga Aminatu ba." Ciro wayar sa yayi, ya mika mata videon yana girgiza kansa "Nine a videon nan, da hannu na na rubuta sakin Dadah, da hannu na na rubuta, bansan sanda na fara shaye-shaye ba, amma tabbas bana hayyacina sanda na aikata hakan, tabbas yaudara ta akayi, aka sani na rubuta ba tare da na sani ba, sai dai na kasa tuna komai, bana tuna komai Dadah, kaina kamar zai fashe nakeji, zuciya ta namun zafi, idan har akwai mutumin da yake son ganin bayana a duniyar nan, toh tabbas Aminatu tana cikin matsala, zanje na ganta, zan bata hakuri, nasan zata amince dani ko kowa be yarda ba." "Kaje ka ganta, tana bukatar ka fiye da kowanne lokaci, abinda ke cikin ta na bukatar ka." Mik'ewa yayi cike da karfin sa, ya juya ya bar falon Ja'afar na take masa baya. Shiru ne ya biyo bayan fitar su, zuciyar Dadah cike da farin cikin dawowar Farouk a lokacin data tabbatar Aminatu na bukatar sa. ★★★★ Tafiya ce mara daɗi musamman gareni, duba da rashin sabo da kuma danyan jegon da nake ciki, kuka yar jaririyar da bansan takamaimai sunan ta ba, ta saka tana wutsul-wutsul da kafarta, dauke kaina nayi daga ɓangaren Hajiyar, ina kallo ta hau jijjigen ta, sai dai bata da alamun yin shiru. "Aminatu, karbe ta ki sake gwada mata ko Allah zai sa a samu ruwan, kece ma dai kinki cin abinci, dole idan kika je gidan su tilasta miki sa wani abu a cikin ki, ruwan nono sai da abinci zaizo." Hannu na mika na karbeta, na dora ta saman cinya ta ba tare da sanin takamaimai ta inda zan fara mata. "Dauke ta ki sata jikin ki mana, shiririta." Kamar zanyi kuka na daga hijabi na na sata ciki, juyowa yayi bayan muka hada ido dashi, da sauri na janye ido na ina kallon kasan kujerar, "Hajiya ya za'a yi ne? Itan za'a fara kaiwa ko yaya?" Gabana ne ya fadi, nayi kasak'e ina jiran amsar ta, waigo ni tayi tace "Aminatu,wacce unguwar kuke? Kunga an kusa shiga Kanon mu fara rakaki gida sai mu wuce." Rau-rau nayi da ido na da ya cicciko lokaci daya, na daure na cije nace "Bansan kowa ba sai mutum daya, hasalima wannan ne karo na na farko dana zo Kanon, sai dai bansan inda zan same ta ba, wayar da xan kira ta na manta ta a gida." Bude baki sukayi a tare suka ce "Kina nufin baki san inda zaki ba?" Daga kai na nayi ina sharar kwalla, ransa naga ya ɓaci, ya kalle me motar "Idan kaje kwanar dawanau ka sauke mu, sai ta fada maka ita inda zaka kaita, nawa zamu biya gaba daya?" "Anas..." "Kiyi hakuri Hajiya, bana so daga taimako mu shiga matsala, kuma kinsan ni a rayuwata na tsani karya, me yasa zata boye mana gaskiyar ta? Sai data ga munzo zata ce bata san inda zata ba?" "Shikenan." Tace tana kallo na, kasa na sake yi da kaina ina kuka, zuwa lokacin jaririyar tayi baccin wahala, dan babu nonon sam yaki zuwa.   Sanda muka iso inda yace, inaji motar ta tsaya, ya fita da sauri aka bude masa booth, ya cire kayan su, bude mata kofar bangaren ta yayi yana sake daure fuskar sa tamau. "Fito Hajiya." Kallon da tayi masa ya dauke kai kamar be gani ba, ya maida kansa bangaren driver yana tambayar sa lissafin kudin tunda mu kadai ya dauko tun daga chan din. "Kudin dukka kujerar zaku bayar, ita kuma idan na isa tasha sai ta sauka ta nemi wani abin hawar, iyakata tashar ne kawai." Lissafa wa yayi ya ciro kudin ya bashi yana yin gaba, a hankali na furta "Nagode Allah ya saka da Alkhairi." Sarai yaji, dan har sai da yayi dan alamun kamar zai tsaya, kafin ya kara daga kafar sa Hajiyar na take masa baya. Kuka na saka sosai ina jin bani da sauran gata a duniyar nan. Rayuwata ta kare, ina ji a raina gab nake da mutuwa, sai dai idan na kalli yar karamar halittar dake hannu na, wadda yanzu dukkan rayuwar ta, na rataye a wuya na, sai naji komai ya sake min, zan rayu ko don sabo da ita, na kula da ita.   Ban yi aune ne na ganmu a tashar, sake rungume ta nayi sosai a jikina, motar na tsayawa na balle murfin na fito,ina sake karewa ko ina kallo, a karo na farko na zo Kano, ba tare da sanin inda zan dosa ba. Jakar nan ya fito min da ita, hade da sauran kayana, dauka nayi na matsa daga wajen ina neman inda zan fake don zuwa lokacin har ta kuma tashi tasa kuka, baccin nata baya nisa saboda yunwar dake damun ta. Chan na hango kasan wata bishiya, nayi saurin isa wajen, na rabe ina jijjigata. Nayi nisa a son ganin tayi shiru, kamar daga sama naji muryar sa a kaina "Kin tabbata ba wani mugun abun kikayi kika gudo ba?" Dagowa nayi idonmu suka sarke waje guda, da sauri na daga kaina alamun Eh "Idan kinyi alkawarin sanar dani gaskiya, zan taimaka miki." "Nayi Alk'awari." Hannu ya mika ya dauki kayan nawa, na tashi da sauri nabi bayan shi.Daurin Goro*              *18* © Hafsat Rano ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo                                         18 *** Adaidaita sahu naga mun dosa, muna zuwa ya mika kayan ciki yace wa Hajiya "Ku tafi bari na hau wani, zan sameku a gida." "Shiga." Yace yana nuna min ciki, shiga nayi Hajiya ta miko hannu ta karbi yar jaririyar. "Kiyi hakuri kinji?" Tace min tana kallo na. Murmushi kawai nayi muka dauki hanya ba tare da sanin takamaimai inda muka dosa ba. Unguwa ce tsaf tsaf babu cinkoso balle hayaniya, a kofar wani dan madaidacin gida naga mun tsaya, ni na fara sauka sannan ta fito, "Dauko kayan Aminatu." Kayan na kwaso ta bude yar karamar kofar jikin gate din muka doshi cikin gidan, da wata dattijuwar mata muka fara haduwa tana zaune gaban fanfo kayan wanke-wanke ne a gabanta tana yi, da murnar ta ta taso ta tare mu, "Sannu da dawowa Hajiya." "Yawwa Altine, ana ta aikin ne?" "Wallahi, jiya mukayi ta zuba ido shiru har dare sannan Ramlah ta hakura ta kwanta." "Wallahi kam." "Sannu." Tace tana kallo na, gaishe ta nayi ta amsa sannan muka dunguma zuwa cikin falon, ko ina a share tsaf na samu gefe na rakube ina jin su suna cigaba da hirar tasu inda na fuskanci ita Altinen me aikin Hajiya ce, mika mata kayana tayi tace ta shigar min dasu dakin Ramlah. "Jeki ki huta Aminatu, nasan kin gaji." Tashi nayi nabi bayan ta, a gefe ta ajiye kayan, dakin a hargitse duk an barbaza kaya, tattarewa ta hau yi tana mitar halin wadda aka kira da Ramlah ɗin, tana gamawa ta fita, da sauri na haye gadon na kwanta dan ji nake kamar zan fadi, anya ma ina da isheshen jini a jikina ma kuwa? Na tambaya kaina ina karewa ko ina na jikina kallo, na dashe nayi fari tas ga wani matsanancin ciwon kai da jiri da nake ji. Shiru nayi ina ayyana yadda zamu kwashe da Anas, dan da alama mutum ne mai zafi, zan yi kokarin sanar dasu gaskiyar labari na, dan na samu na makale kafin zuwa gaba naga yadda Allah zaiyi dani. Kukan da naji yana doso dakin yasa na tashi na zauna sosai, Hajiya ce ta shigo rik'e da yarinyar dake faman tsala kuka, zuciyata ce ta tsinke da tsananin tausayin ta, bata da damuwar komai sai ta cikin ta, yunwar dake damun ta itace ta hanata sakat, waya take da alama da Anas ɗin take yi, kafin ta ajiye yana mika min ita. "Karbe ta ki sake gwada mata, kafin a kawo mata madarar da tausayi sosai wallahi." "Toh." Nace na karbeta, fita tayi ta jawo mana kofar, yadda zan fara bata ne ma sam ban iya ba, kici-kici nake tayi na kasa, gashi sai kara karfin kukan nata take, duk na rikice na rude, a haka ta sake shigowa ta tarar dani, hannun ta dauke da bakar leda, da sauri ta ƙaraso tana ajiye kayan kafin ta karɓe ta, "Baki iya bata ba Aminatu? Na shige su, ai na zata kin iya, shiririta kenan." Sauke kaina kasa nayi, ta cigaba da jijjiga ta, shigowar Altine da tea flask yasa ta ajiye ta ta shiga hada mata madarar a sabuwar feeding bottle din da aka siyo tare da Madarar, ina zaune ina kallo har ta gama haɗawa sannan ta shiga bata, da sauri da sauri take sha gwanin tausayi, kwalla na share a ido na ta gefe ina godiya da Allah daya kawo min mutanen nan a lokacin da nake tsananin bukatar wani a kusa dani. Ana gama bata ta koma bacci, kwantar da ita tayi, tana dariyar yadda take fitar da numfashi a hankali. Kura mata ido nayi bayan fitar su daga dakin, murmushi na saki a hankali na kai hannu na saman kanta ina jin sabuwar soyayyar ta na bin dukkanin jikina. Ruwan wanka Altine ta haɗa min, ta kawo dakin, ganyen darbejiya naga ana shigowa dashi dakin, kuka yazo min, kukan farin ciki, bansan da wanne bakin zan gode wa wannan matar ba, da kanta ta shigo ta saka ni a gaba tayi min wankan, wankan jegon da iyaye keyi ma kowacce yarsu, a lokacin da nake tunanin na rasa wannan gatan, a lokacin Allah ya aiko min da ita rayuwa ta. Wankan da nayi ba karamin jin dadin jikina nayi ba, ina gama shiryawa aka aikon da abinci lafiyayye irin wanda ya kamata mutumin da yake irin yanayin da nake ciki yaci, sosai naci abincin dan rabona daci tun kafin komai ya sake canja min, dadin dadawar ta tabbatar min da idan ban ci abincin ba, jaririyar tawa ba zata samu ruwan nono ba, hakan ya kara min kaimi wajen ganin naci abincin sosai. Ina gamawa nabi lafiyar katifar, sam bana son nayi tunanin maganganun Inno, dan ba karamin hargitsa min lissafi suke ba, na kasa gasgata abinda ta sanar min, duk da na riga nasan ba zata taba min karya ba, amma kuma zuciya ta sam ta kasa aminta da maganganun. Dawowar shi naji yo muryar sa a falon, gabana ne ya fadi da tunanin yadda zamu kwashe dashi, ina nan kwance aka turo kofar, Hajiya ce a gaba sai shi a bayanta, yar karamar kujerar dake dakin yayi wa kansa mazauni, inda Hajiyar ta zauna a gefen gadon tana kallon jaririyar "Kinga ashe baiwar Allah yunwa ce, gashi yanzu sai baccin ta take." "Uhum." Nace ina kokarin daidaita zama na saboda yadda naji duk na kasa sakewa. "Ya jikin?" Ya jeho min tambayar, "Da sauki." "Good." "Kamar yadda kika ganmu, wannan mahaifiya ta ce, sai kanwata Ramlah, sai Altine dake taimakawa Hajiya da yan aike aiken gida, wadda ta zama kamar ma yar uwa ta jini. Babu bukatar dogon bayani mu, mu kadai ta haifa, mahaifin mu ya rasu, sai dangin sa dake Katsina inda muka hadu dake munje wata gaisuwar rashin da akayi, dangin Hajiya duk yan Kano ne, yan karamar hukumar Kibiya, kuma yawancin su suna chan. Ina aiki da federal mortgage bank, in da kanwata take matakin farko a jami'ar northwest." "Haduwar mu wani iko ne na Ubangiji, duk da haka, ina so ki sanar damu gaskiyar abinda ya dangance ki daya dace muji, ki sani bana bukatar komai sai gaskiya." Share hawayen dake faman bin fuskata nayi tun lokacin daya fara magana, a nutse na shiga sanar dasu rayuwa ta. Duk da ba komai na sanar musu ba, amma nayi kokarin sanar dasu abinda ya dace su sani kamar yadda ya nema. Ina kallon yadda yake girgiza kansa, Hajiya kuwa kuka ta saka cike da tausayi na, ina kaiwa karshe ta taso da sauri ta rungume ni. "Baa kyauta miki ba Aminatu, ba'a kyauta miki ba." Shine kawai abinda take ta nanatawa, mik'ewa yayi tsam ya iso gaban gadon, idanun sa cikin nawa, yasa hannu ya dauke ta, murmushi yayi min tare da girgiza min kai alamun nayi shiru. "Wanne suna za'a sa mata?" Ya fada yana tsura min ido, bance komai ba, na maida kaina kasa ina share hawayen fuskata hade da yiwa Allah godiya, sake maimaita wa yayi a karo na biyu, a hankali na furta "Duk sunan da ka sa mata yayi." Murmushi naga ya sake yi, sannan ya kara bakin sa a kunnen ta yayi mata huduba, dagowa yayi yana sauke ta a saman gadon kafin ya kalle Hajiya "Na sa mata Fatima." **** Har suka isa kauyen na Shagari babu wata magana data hada su, Allah Allah Farouk yake su isa gidan. Suna isa yayi saurin fitowa ba tare da ya jira Ja'afar ya gama daidaita tsayuwar motar ba, cikin zauren gidan ya shiga yayi sallama da d'an karfi dan babu yaron da zai aika. Inno na zaune taji sallamar sa, gabanta ne ya fadi ta mike da sauri, idan har ba gizo kunnenta yake mata ba, toh tabbas muryar sa ce, idan kuwa haka ne akwai gagarumar matsala. Sake sallamar yayi hakan ya sa ta kara tabbatar da shi din ne, da sauri ta ciri mayafin ta a saman igiya tayo zauren a rikice. Zagaye yake a cikin zauren ya kasa tsayawa waje daya, da sauri ya kalli hanyar shiga gidan jin takun tafiya, gaba daya tunanin sa ya tafi akan itace, bayyanar Inno a gaban sa yasa ya dan ji faduwar gaba, yanayin fuskar ta ya nuna akwai matsala, a gajarce ya gaishe ta, ta amsa kai tsaye tana gyara tsaiwar ta. "Dan Aallah ko zan iya ganinta? Duk da nasan ba lallai ta saurare ni ba, amma ina bukatar ganinta dan Allah." "Me yasa sai yanzu kake dawowa? Me yasa sai da lokaci ya kure, bayan kayi min alƙawarin zama da ita komai rintse, tabbas dawowar ka a wannan lokaci Farouk bata da amfani." "Nasan ni mai laifi ne, amma ina da uzuri, ina fatan idan mukayi magana da ita zata fuskance ni." "Ka makara Farouk, Aminatu ta tafi, bansan inda take ba, bansan ina za'a ganta ba, ya zanyi? Na jira ka, tsawon lokaci baka dawo ba." A wani irin yanayi ya kalle ta, kansa ya shiga juyawa, wani irin jiri ne ya kwashe shi, yayi taga taga zai fadi, Ja'afar yayi saurin tare shi, da karfin sa ya mike, ya kwace daga rikon da Ja'afar din yayi masa, kallon tsana da kiyayya yake bin ta dashi kafin ya nuna ta da hannu yace "Me tayi miki da kika watsa rayuwar ta haka? Wanne irin rashin imani ne wannan? Baki san inda take ba, me hakan ke nufi?" "Bani da zabi ne, zaman ta anan na nufin fadawarta mugun hannu." "Yanzu kika san a hannun da take? Eh?" "Ban sani ba." "Toh wallahi babu wanda zan kyale, bayan sanin alakar dake tsakanin ku, babu abinda zan tsaya jira ko kunya, idan har zaki iya rufe ido, ki koreta a halin da take ciki, wallahi ba zan yi kasa a guiwa ba wajen ganin na bi mata hakkin ta." "Ka saurare ni, banyi hakan don na cuce ta ba, bani da kowa da zai iya tsayamin, Harira ta wuce inda kake tunani, ya zanyi da raina? Kuskure daya tak, ya zama silar rugujewar dukkan farin ciki na." Sosai ya koma mata kamar bashi ba, maganganu ya shiga fada mata duk wadda tazo bakin sa, cikin tsananin fushi da bacin rai, da sauri ya juya ya fita, ya fada mota ya bar wajen ba tare da yabi takan Ja'afar da ya biyo shi yana kwala masa kira ba, zauren ya dawo ya tsaya kawai yana tunanin inda Farouk din zashi, "Dama nasan za'a yi haka, amma ya zanyi da rayuwa ta?" "Yaushe ta tafi?" Ja'afar ya tambaye ta "Shekaran jiya." Girgiza kai kawai yayi, yace Allah ya kyauta. A kafa ya shiga takawa, ya nufin gidan Bature, a hanya yaci karo da motar yan sanda, sai Farouk dake gaban su, da sauri yasa hannu ya tsaida shi, tsayawa yayi ya bude masa motar ya shiga suka cigaba da tafiya "Ya Farouk, kana ganin hakan shine daidai? Karka manta wacece a wajen ta fa." "Na fika sani, ai na fada mata, idan wani abu ya sameta, wallahi bazan kyale ba, wanchan karon taci darajar Aminatun bata sani ba, ba kuma naso na data mata hankali, amma yanzu sai inda karfi na ya tsaya." Duk da ja'afar be gane inda maganganun suka dosa ba, amma sai yayi shiru ba tare da ya sake cewa komai ba, suna isa gidan yan sandan suka fito, babu wani bata lokaci suka shiga suka fito da Inno, cikin kankanin lokaci kofar gidan ya dinke da mutane, yan kallo, Garbati na zaune a majalisar su labarin ya isar musu, da sauri sauri suka ƙaraso wajen, gaban sa ne ya fadi ganin Farouk ne, boya ya hau kokarin yi a bayan mutane be san tun zuwan sa wajen ya ganshi ba, yana kokarin guduwa yaji an chapke shi, turje turje ya fara yi, yana ihu ganin haka yasa kowa ya hau darewa, suka ingiza keyar shi suka sashi a bayan mota, Inno kasa dagowa tayi saboda tsananin kunya, kuka take har Karime ta ƙaraso wajen dauke da goyon Saddiku tana kuka, ganin Farouk yasa tayi wajen sa da sauri tana rokon sa, hakuri kawai ya bata ya basu umarnin su wuce zuwa kauyen da Harira take. Motar ya fada suka bi bayan su yana jin yau yayi abu na farko daya kamata ace yayi shi tun tsawon shekarun da suka wuce. Hajiya Inno za'a yi kwanan cell😂😂 #Manage 🚴🚴🚴🚴🚴🤫🤲:      Hansatu R                 19 ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo ★★★★ "Sunana Anas?" Hajiya ta tambaya cikin farin ciki, daga mata kai yayi "Sunan ki nasa mata Hajiya, ina fatan tayi gadon kyawun halin kirki da nagartarki." "Wai kin amince Aminatu?" Hajiyan ta juyo tana kallo na, da sauri na daga kaina sama, cikin wani yanayi na furta "Bani da ja akai, kin chanchanci fiye da haka." "Allah yayi muku albarka." Tace cikin farin ciki mara misaltuwa. Gefe ya koma rike da Fatima, ya zauna yana jujjuyata a hannun sa, daidai lokacin ta bude idon ta, hade da sakin kuka, da sauri ya mike "Iman ta tashi, kinga bakinta Hajiya?" Yace yana mika mata ita, dariya suka saka baki daya  kafin ta miko min ita tana faɗin, maza karbe ki sake gwada mata mu gani." Da sauri na sauke kaina kasa saboda kunyar data kamani, juyawa yayi da sauri ya bar dakin, sai a sannan Hajiya ya ankara, dariya kawai tayi ta cigaba da gwada min yadda zanyi, cikin sa'a kuwa aka samu sai dai babu yawa ga wani irin zafi, yarfe hannu na nake kawai ina cije baki Hajiya namun dariya.     Bayan ta koma bacci na kwantar da ita ina kwanciya a gefen ta, bacci ne ya dauke ni ba tare da na shirya ba.   Na jima sosai ina baccin har sai da mai dakin ta dawo, motsin tane ya data ni, muna hada ido ta sakar min murmushi, murmushi nayi mata kamin na mike ina gyara zama na. "Sannu da tashi." "Yawwa." Nace ina yar hamma, Altine ce ta shigo dauke da Kaskon wuta, ta ajiye ta koma ta kawo kayan wanka, komai sabo hatta bawon wankan da dangin su sabulu, daukar ta tayi, tayi mata wanka hade da gashin cibiya, kafin ta gama dakin ya dau dumi, turaren wuta Ramlah tasa mana ta zauna tana cin abinci tana yi min hira. ★★★ Harira na zaune rike da d'an karamin mudubi tana duba fuskarta, shirya take tsaf daga gani fita zatayi, ajiye komai tayi a gefe ta yafa sabon mayafin ta, tana yan wak'e wakenta cikin farin ciki ta fito, turus tayi ganin yan sanda a tsakiyar gidan nasu, kowa ganin abinda ya kawo su, bata kawo komai akanta ba tayi wajen su, cikin son nuna ita din wayayyace tace "Lafiya dai?" Maganar da tayi yasa Farouk juyowa, da sauri yace "Arrest her." Babu wani bata lokaci suka damke ta, tana ihu tana komai suka tusa ta cikin bayan motar, sai a sannan ta lura da Inno kanta a sunkuye ta rufe fuskar ta da mayafin kanta. Wani irin amsawa kirjin Harira yayi, cikin tsananin tashin hankali tace "Innaro?" "Ko ba ita bace?" Ta maimaita jin ta mata banza, bata amsa mata ba, har suka isa charge office, fito dasu akayi aka watsa su cikin wani ɗan karamin cell kafin ya tura Garbati a cikin nasa shi kadai. "Zan dawo, kar kuma ku bawa uban kowa belin su har sai sun bqyyana inda suka kai min matata da jariri na. Da sauri suka amsa ya juya ya bar wajen, Ja'afar na bin sa haka suka koma gida, be kula takan maganar da Ja'afar din yake ta masa ba ya fada daki da sauri ya saka key, misscals ɗin Dadah ya tarar, sai yaji zuciyar sa ta karye, yasan yadda ta damu da Aminatu idan taji labarin nan hankalin ta ba karamin tashi zai ba, fasa kiran ta yayi ya ma kashe wayar baki daya yana bin dakin nasu da kallo, dakin da sukayi rayuwa a ciki, rayuwar da yake ganin ta cikin wasu muhimman lokutan da yayi masa matukar muhimmanci a rayuwar sa. Ji yayi zuciyar ta ta bushe, ta k'ek'ashe, ba zai taba kyale duk wanda yake da hannu ba, ko da kuwa mutanen dake da kusanci mafi rinjaye dashi. So yake yayi kuka da idanun sa, ko yaji dadi a zuciyar sa, sai dai yasan abu ne me matukar wuya a yanzu, lallai zubar da hawaye idan kana cikin damuwa ma Rahma ne.   Sai yamma likis ya tashi daga inda yake, istigfari yayi hade da dauro alwala ya gabatar da sallar azahar da la'asar. Jawo wayar sa yayi ya kuna, ya danna kiran wayar Dadah don yasan tabbas tana cikin son jin abinda yake faruwa. Bugu daya ta daga, da sauri tace "Babana me yake faruwa? Kun barni cikin tashin hankali." Share zufar kanshi yayi, murya a ciki-ciki ya soma mata magana, salati kawai take har ya kai karshe, zuwa lokacin gaba daya komai ya fara tsaya mai, yunwa, tashin hankali da wani abu daya tokare masa makoshi ne suke barazanar kaishi kasa, kiran sunan shi take sai dai baya jin komai sai chan a saman kanss, ya gaza amsawa, a hankali idanun sa ke rufewa, kadan-kadan kafin su rufe baki daya yana sakin wayar wadda karar faduwar ta, ta saka Ja'afar tasowa da gudu ya hau dukan kofar. Jin shiru yasa shi firgicewa yayi dakin Dadah da gudu ya nemo spare keys, a gaggauce yazo ya bude shi, da sauri ya k'arasa wajen sa yana jijjigashi, ganin da gaske baya hayyacin sa yayi saurin dauko ruwa ya shafa masa a fuska, ajiyar zuciya ya sauke da karfi yana bude idon sa da suka rine sosai, taimaka masa yayi ya dora shi saman gadon kafin ya fita don dauko wayar sa. Daddy ya fara kira no answer, sai ya kira Mummy ita din ma babu amsa, shiru yayi yana tunanin wanda zai kira kuma, daga karshe ya yanke shawarar kiran Dadah, a rikice ta daga kiran nasa dan dama suna magana da Farouk din ne taji shiru.      Dakin Ja'afar ya komo bayan sun gama wayar, har lokacin idanun sa na bude ya kura wa saman dakin ido. "Ya Farouk!" Ya kira sunan shi, "Dadah tace karka sa damuwa a ranka, da cewa tayi ma xatazo nace a'ah zamu taho ma gobe." "Waye aka ce ya kawo takardar nan?" Ya jeho masa tambaya still idanun sa na kallon sama "Wacce kenan?" "Takardar dake rubuce da sakin, waye ya kaiwa Aminatu?" "Ban sani ba gaskiya, a yadda naji,makaranta aka je aka kai mata." Shiru yayi cikin dogon nazari kafin yace "Shikenan, koma waye zan gano ai." "Kabi komai a sannu Please." "Karka damu, zaka iya wucewa kawai, zan dan zauna anan ko na sati daya ne." "Babu matsala idan na Barka? Baka jin dadi naga." Girgiza masa kai yayi kafin yace "Idan ka fita ka jamin kofar Please ina son zama ni kadai." Juyawa dayan barin yana sake gyara kwanciyar sa, dan jim Ja'afar din yayi kafin ya ja masa kofar kamar yadda ya bukata      Dare ya tsala sosai, yayi zurfi a cikin tunanin sa,duk kokarin sa nason ganin ya samu ko da wani haske ne a binciken sa abun ya faskara, juyi kawai yake yana tuna halin da Aminatun ke ciki.     Da safe ya shirya sukayi sallama da Ja'afar ya tafi, duk da baya jin dadin jikin sa da zuciyar sa, amma haka ya danne ya nufi station din don yana son magana da Inno. Fito da ita akayi yayi mata yan tambayoyin da suka shige masa duhu, game da wanda ya kawo takardar sakin. Yadda ta sanar masa yasa kansa ya k'ara daurewa, wacece wannan da zatayi masa haka? Menene tsakaninsu? Mutun daya ya ke tunanin zata aikata hakan, Mummy, sai dai ya kara shiga matukar damuwa daya nuna mata hoton Mummyn amma tace ba ita bace.   Gidan Maigari ya nufa, sai dai shima bayanin d'aya ne mata ne su biyu suka zo wajen sa, sai dai shi be nuna masa hoton na Mummy ba ya daiyi godiya kawai ya tafi. Duk inda yake tunanin zai kai ga neman ta, yayi, ya sare sosai yana jin kamar rayuwar sa zata k'are. Gidajen Radio da talabijin duk ya kai musu cikiya hade da hoton ta, dan baya taba tunanin zatayi nisa da Katsina, duk binciken nasa a iyakar nan din ne.   Tsawon sati guda kenan yana bincike akai hade da neman ta, duk inda yake tunanin zai same ta har gidan principal yaje, gaba daya ya rame ya lalace kamar bashi ba.    Yana zaune kiran Daddy ya riske shi, a kasalance ya daga yana karawa a kunnen sa gami da sallama "Farouk, me kaje ka aikata a gidan su yarinyar nan, maigari ya kirani akan kaje har gida kasa an kama mahaifiyar yarinya tsawon sati daya kenan, wai kai yaushe zakayi hankali ne ehe?" "Daddy ba abinda kake tunani bane..." "Kai kullum abinda zaka sani magana shi kake yi, ya kamat kasan kai ba yaro bane yanzu." "Ba haka bane... Ayi hakuri dan Allah." "Awa uku na baka, kaje ka fitar dasu sannan ka baro garin, kayi abu ya dame ka shine zaka je ka huce akan bayin Allah, Awa uku ka bar garin nan ka dai ji na fada ma." Bin wayar yayi da ido, ya rasa me yasa har yanzu Daddyn ya gaza aminta dashi balle ya fahimce shi, har yanzu bashi da ikon kansa. Ba ya taba barin sa ya kare kansa, komai yayi bai iya ba, komai yayi sai fada. Mutum daya ke tsayawa ta saurare shi tun yana yaro har zuwa yau, mahaifiyar sa da ita da babu banbancin su kadan ne, bata san komai ba sai kasuwanci ta, bata da lokacin su tun ma kafin rabuwar su da Daddy balle yanzu da take ganin sun girma.   A gurguje ya shiga hada kayan sa, yana yi yana ayyana hukuncin da zai yanke wa kansa, hakan ne kawai mafita a garesa, baya jin zai iya sake zaman wasu awowin a cikin garin. Duk abinda yasan zai bukata ya tattare su, waya kawai ya daga ya kira sifetan yan sandan wajen yace ya sake su, loda koman sa yayi ya rurrufe ko ina ya damka wa Baba maigadi yan mukullayen gidan ya dauki hanyar Kano. Shigar dare yayi, Dadah na cin tuwo ya turo kofar ya shigo yana jan kafar sa, da kallo ta bishi cike da tausaya wa, har ya zauna gefen ta yana tankwashe kafarsa "Babu wani labari ko?" Tace tana tsame hannun ta, girgiza mata kai yayi bakin sa ya gaza furta kalma daya, tashi tayi ta wanko hannun ta tazo ta zauna gefen sa, da sauri ya dora kansa a saman ƙafar ta. Tun yana yaro haka yake mata, idan baya jin dadi ko kuma ransa ya ɓaci, fasa tambayar sa komai tayi. Sai daya gaji dan kansa sannan ya mike ya nufi daki, bata hana shi ba, tasan lallai yana bukatar kadaici, addu'a ta bishi da ita kawai tana fatan komai ya warware cikin sauki.     Ko da ta tashi da safe tuni ya fita, sai gabannin azhar sannan ya dawo gidan, kwana uku yana jeran fita a rana ta hudu yace mata zai je Lagos, bai sanar da ita abinda zai je yayi ba, haka ya tattara ya tafi, a ranar ne ita kuma ta dauki hanyar Shagari don samun magana da Inno.    *** Satin sa biyu a Lagos ya dawo ya wuce Kaduna gidan Mummyn su, duk ya sake ramewa kamar ba Farouk ba, ita kanta data ganshi sai data ji babu dadi, ta shiga tambayar shi abinda ya same shi. Wanka yayi ya shirya kafin ya same ta a zaune a falon ta na alfarma. Tana zaune kafarta saman tuntu tana hutawa.   Maimakon ya zauna a kujerar data ke nuna masa sai ya zauna a k'asa, cikin yanayin da ta kasa ganewa ya soma mata magana "Kiyi wa girman Allah Mummy, ki sanar dani gaskiya, ba zargin ki nake ba, sai dai zuciya ta, ta kasa nutsuwa, ina son sanin da hannun ki a duk wani abu daya danganci Aminatu? Dan Allah ki taimaka ki fadan gaskiya, kaina ya kule, na rasa waye zai aikata min hakan? Iya sani na ban sake ta ba, amma me yasa na kasa wanke kaina daga daurin da akayi min?" Murmushi tayi kafin tace "Farouk kenan, bani da masaniyar komai, haka zalika ban aikata abinda kake tunani ba, mesa zan boye kaina idan har ni ce na raba ku? Karka manta ni mahaifiyar ka ce, tsarin rayuwa ba zai sa na manta matsayi na ba, idan har ina son na raba ku, kai tsaye zan sa ka sake ta, bisa karfin iko na da matsayi na wajen ka." "Kiyi hakuri, ba ina zargin ki bane, kiyi hakuri dan ALLAH." "Karka damu, bani da masaniya akan ba kaine ka sake ta ba, bayan na samu labarin a wajen Ja'afar, ban yi niyyar zuwa ba, sai dai text message dana samu ne yasa ni zuwa dole, tun da sakon na nuna cewa ka saki yarinyar sannan Daddyn ku yaje domin ya maida auren, bayan kuma kace kai bakaa so, hakan yasa na tafi, a ganina hakan zai sa na hana abinda yake shirin aikata maka karo na biyu." "Text?Waye ya aiko shi?" "Ban sani ba, dan nima tun a ranar na kirkira number ba,tq shiga." "Zan iya ganin number." "Ok bari na duba, ina tunanin ban goge message ɗin ba ai." Gyara zaman sa yayi ta dubo masa number, da sauri ya dauki Number ya kira, ringing daya biyu aka daga, sai dai muryar data bayyana a wayar ta sake sashi a wani rudanin, bayerabe ne ya daga, cikin harshen sa na yarabawa, dole ya kashe yana jingina da kujerar dakin.   Kwana ɗaya yayi mata yace zai tafi, taso ya d'an kara zama sai dai yace mata zai dawo nan kusa, haka ya tattara ya wuce Kano, nan dinma kwanan sa biyu, ya komo abuja.    Jiran Daddy yayi har ya dawo ya same shi a falon sa, gaishe shi yayi a mutunce ya amsa kafin ya nemi izinin sanar dashi abinda ya kawo shi. "Na yanke shawarar ajiye aikina, zan koma karatu a karo na biyu, na nemi izinin ajiye aike, sai dai sam shugaban mu ya ki amince wa, shine nake rokon ka saka baki dan Allah." "A wanne dalilin zaka ajiye aikin ka?" "Akwai matsi da takura sosai, sannan ina son chanja akalar rayuwa ta ne, zuwa mutumin da zaka yi alfahari dashi a gaba." Da sauri ya kalle shi, sai kuma yayi murmushi "Kana tunanin yanzu bana alfahari da kai?" Be ce komai ba, ya sunkuyar da kansa kasa, "Shikenan, zan yi magana, duk abinda ka zaba wa rayuwar ka, ina fatan hakan ya zamo Alkhairi a gareka." Sosai yaji dakin maganar, da sauri ya amsa da amin yana jaddada kansa a k'asa cikin tsananin farin ciki "Sai dai akwai sharadi guda daya..." "Ina so ka amince da auren kanwar ka Amal, hakan shine kadai buri na akan ka yanzu, idan kayi min shi nasan ka cika d'a nagari." Da wani irin shock Farouk din yake kallon shi, daga mishi kai yayi cikin gasgata abinda yace ya dora "Idan har kana son ka samu damar barin aikin ka, ka tafi duk inda kake son tafiya tun da nasan kudurin ka na barin k'asar ne, toh tabbas sai ka auri Amal, idan yaso sai ku tafi tare, daga nan har karshen duniya bani da matsala da kai." Juyawa kansa ya hau yi, idan har shawarar sa ta kauracewa kowa na nufin auren sa da Amal, da kuwa ya sani be dauki wannan shawarar ba, sai dai ya sani Daddy ba zai taba kyale maganar ba, tun da har ya riga ya furta, idanun sa ne suka shiga dauko masa hoton Amal, duk da yana son ta, yana jin ta sosai a ransa, amma ba hakan na nufin zai iya auren ta ba, aure a irin wannan lokacin da bashi da nutsuwar zuciya, idan yayi haka be wa Aminatu adalci ba. "Zaka iya zuwa kayi shawara sosai, zuwa nan da lokacin da zuciya ka zata zaba maka abu daya, sai dai ka sani, abu daya tak zan iya yi maka, in ma ka hakura da kudurin ka naa son nisanta kanka damu, ko kuma ka yarda da auren yar uwarka, zabin ya rage naka." Tirkashi!!! Shin za'a yi auren nan? Yaya rayuwar Aminatu zata kasance a gidan data samu kanta? Sai yaushe zasu hadu da Farouk? Waye yake ma Farouk makarkashiya? Ina labarin d'an Inno ne wai? Yaushe a kuma wanne irin yanayi Aminatu zata hadu da iyayenta? Leggo🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚵🚵🚵🚵🚵🚵Hansatu R                 20 ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo ★★★★ Kasa tashi yayi har zuwa sanda Mama ta shigo, da kyar ya ja kafafun sa ba tare da yace komai ba ya fito. Amal na tsaye a gaban part din su kunnen ta sakale da waya tana amsawa, tsayawa yayi chak yana kallon ta daga nesan, ya sani sarai Amal bata da matsala, zai iya cewa ma rainon sa ce, amma ya gaza gano dalili d'aya da zai iya bashi damar auren ta, takawa yayi har wajen da take, ya tsaya daga bayan ta yana son ya gano wani abu, cire wayar tayi daga kunnenta cikin farin ciki ta juyo, ganin sa tsaye yasa ta dan yi sak, sai kuma ta fadada fara'ar ta "Yah Farouk, dama kana tsaye?" "Umm. Ina tsaye ina jinki kina waya da siriki na." "Ni?" Ta zaro ido tana dafe kirjin ta "Da fa Ilham muke magana." "Ahaap, idan ma dai boye min shi kike shikenan, anyway zo muje ina son magana dake." Gaba yayi ta bi bayan shi cikin tarardadin abinda zai ce mata ɗin, part dinsu ya shiga, ya zauna saman kujera cikin sanyin jiki ta zauna gefen sa tana kallon sa. "Kina da wanda kike so?" Tayi saurin dagowa, "Yes... Idan har akwai wanda kuke magana dashi, let me know, ni kuma zan yiwa Daddy maganar." Marairaice wa tayi kamar zatayi kuka tace "Ni dai babu kowa Allah." 'Dan jim yayi kafin yace "Kin tabbata?" Daga mishi kai tayi tana sake kwabe fuskar ta, girgiza kansa yayi ya furta "Shikenan ba damuwa, kije kawai." "Ya Farouk!" Ta kira sunan sa ba tare da ta tashin ba, maida kallon sa yayi kanta yana jiran yaji me zata ce, wasa ta soma da hannun ta kafin ta daure tace "Mamaa tace min zaka aure ni, shiyasa bana kula kowa." A mamakan ce ya bita da ido har ta bar dakin da sauri, janye hannun rigar sa yayi cikin rashin sanin madafa ya jingina kansa da jikin kujerar yana lumshe idon sa.   Kwana uku a tsakani yana ta tunanin mafita, ya rasa yadda zai ɓullo wa al'amarin, idan har yace ba zai aure ta ba, toh tabbas kamar ya dasa wani babban abu ne tsakanin sa da mahaifinsa, wanda bashi da wani buri sai na ganin ya faranta masan.   Muskutawa yayi yana sake kiran Number a karo na ba adadi,magana d'aya ce babu wani sabon bayani game da neman nata, tsaki yaja yana ajiye wayar, chan ya sake dauka ya danna wa Dadah kira, bata daga ba har ta gama ringing, zamewa yayi a wajen ya mike kafar sa yana fatan komai ya zama masa da sauki.   Yayi nisa cikin tunanin da yake na kokarin ganin ya samu mafita,  ganin yana kara bata lokaci yasa shi mik'ewa ya sauya shigar sa zuwa kayan motsa jiki, mota ya fada ya nufi wajen motsa jiki. A chan ya dade ba tare da ya dawo gida ba, sai daya ji ya gaji sosai sannan ya juyo gidan. Part dinsu ya wuce kai tsaye, Ja'afar ne zaune da sauran yaran gidan suna buga game d'in wot, idanun sa ne suka sauka akan Amal dake zaune cikin su ana yi tare da ita, ransa ne ya ɓaci, ya daka mata tsawar data saka dukkan su firgita, hannu ya nuna mata kofa yana jin kamar ya kikkifa mata mari, gaba daya wannan wani sabon hali ne da be san ta dashi ba, duk da sukan yi hakan a lokacin yarinta, amma yabzu fa? Sam ba zai yarda da wannan shashancin ba, dole ya taka wa Ja'afar birki dan shine babban banza, idan ba haka ba ace duk cikin su basu san abinda ya dace ba,yadda zamanin nan ya sauya, yan uwan da suke uwa daya uba daya ma shaidan na iya tasiri akan su, ballantana ita da take ba muharramar su ba, ya lura kanta na rawa sosai da yadda suke shige wa juna tsakanin su. Dole yayi wa tufkar hanci ba zai yarda su kara masa wani ciwon kan aakan wanda yake fama dashi ba. A kufule yayi hanyar daki wanda tun kafin ya kai ga yi musu magana duk kowa ya dare ya kama gaban sa.      ★★★ Idan nace ina da matsala ta zamantakewa ta da wadannan bayin Allah nayi karya, duk wani abu da zamu bukata nida Iman sai dai mu ganshi.   Sai dai har yanzu zuciya ta ta gaza daukar nauyin abubuwan da ke cunkushe a cikin ta, duk da ina kokarin dauke damuwa ta ko dan yawan fadan Hajiya a gareni, Amma Tabbas ba karamin abu bane a gareni, mutanen da ka sani a matsayin dangin ka, rana daya a tabbatar maka da babu wata alaƙa tsakanin ku, mesa tun da ta kasa daukar haske a kan hakan duba da yadda Inno take mata, sai a yanzu wata maganar da Babarsu Harira ta taɓa fada mata ke dawo mata, Inno bata taɓa shayar da ita ba, a lokacin ta dauki hakan a matsayin wata lalura kila data hana hakan, sai gashi yanzu ta gane babban dalilin ta nayin haka, ba zata ce ta cuce ta ba, amma tabbas bata kyauta mata ba, bata yi mata adalci da d'an data haifa ba.    Bata da wata hanya ta neman mutanen dake da muhimmanci a rayuwar ta, Farouk, Dadah, da mahaifanta. Yaushe zata gansu? Ta riga tayi ma manta alƙawarin ba zata sake komawa garin na Shagari ba har sai sanda ta tabbatar wa kanta shine daidai lokacin daya kamata ta koma din.   Turo kofar akayi aka shigo hade da sallama, dan gyarawa tayi tana kallon sa, a saman kujerar dakin yayi wa kansa masauki cikin kamala yace "Ya jikin naki?" "Alhamdulillah." Na maida nasa "Allah ya saka da Alkhairi." Na dora, nasan abinda yazo gani, tsam na mike na dauki Iman na isa gareshi, hannu ya mika da nufin daukar ta hannayen mu suka hadu waje daya, da sauri na janye nawa ina sauke kaina kasa, kallo na yayi na yan dakiku kafin yayi murmushi yana maida hankalin sa wajen ta, hanyar fita nayi daga dakin bakin daya saboda ba zan iya zama ni dashi kadai ba, yau ne ma rana ta farko daya taddani a dakin ni kadai, ban kai ga fitar ba ya dakatar dani da maganar sa "Dawo magana zamuyi." Da baya na dawo na koma inda na tashi na zauna, shiru ne ya biyo baya, ya cigaba da rikon Iman ba tare da yace komai ba, duk sai naji na takura, dagowa nayi da niyyar ganin abinda ya hana shi maganar, idanun sa a kaina suna yawo, da sauri nayi kasa da kan ina ji na a matukar takure. "Akwai abinda kike bukata ne?" Kai tsaye nace "A'ah..." Sai kuma na tuno da maganar kudin nan, tashi nayi na bude inda na ajiye su, na dauko na dire a gaban sa. "Dama... Dama idan ba damuwa ina so ko zaka ajiye min kudin nan, idan yaso duk abinda za'a bukata sai ayi a ciki." Da wani irin kallo ya bini "Kamar me za'a yi dashi?" Ya tambaya yana kallo na, kin yarda nayi mu hada ido nace "Amm.. ko za'a siya ragon da za'a yi mata hakika wai dama." "Aka ce miki ban siya ba? Bana bukatar kudin ki, nayi niyya ne ba wai dan wani dalili ba, nayi ne saboda Allah da ya halicce mu, kuma ya umarce mu da mu taimaka wa wanda yake bukatar taimakon." Daga kaina sama nayi, sai naga kamar ransa ya ɓaci, ajiye Iman din yayi a saman gadon ya juya zai bar dakin, sai kuma yaja ya tsaya yana juyowa "Idan kina bukatar inda zaki ajiye ne, zaki iya bude account sai kisa a ciki duk abinda kike bukata sai kiyi a ciki." Daga haka yasa kai ya fice, shiru nayi ina tunani, ni banga abin fushi a magana ta ba, sai dai dukkan alamun sa sun nuna haushi yaji, ya zanyi toh ni? Me laifin abinda nace?   Ko da Hajiya ta shigo, sai ta hau min fada, kar na sake maganar duk abinda za'a yi wa Iman din, dan shi mutum ne mai saurin harzuk'a, na bata hakuri tace ya wuce. Tun daga lokacin bana taba cewa komai har idan bashi ne ya yanke ba, sati ya zagayo  aka yanka mata abin yanka kamar yadda addini yace.    Sosai muke zaman mu lafiya da Ramlah, kasancewar ta mutum me faran faran da son mutane, Iman kuwa dukkan dawainiyar ta a wajen su take, idan tana makaranta Hajiya amma da zarar ta dawo shikenan ita zata dora. Slip dina na ciro na post Utme d'ina na duba, date da komai, Ramlah na bawa ta gani kafin tace zata je ta kaiwa Ya Anas, har ta tafi kai masan ina tunanin amincewar sa, ina zaune ta dawo da fara'ar ta, "Ya kukayi?" "Yace kije da kanki wallahi, dama nasan haka zai ce wallahi." "Na shiga uku, wallahi kunyar sa nake ji Allah." "Toh kuwa sai ki hakura wallahi." Tsaki naja na tashi ina daukar mayafi na, baki daya sun kasa gane yanayin da zuciya ta take ciki, kokarin su na son ganin lallai sai na sake dasu, bani da yadda zanyi, haka na fito falon ina wara ido, a hakimce yake a saman kujera ya ajiye laptop a gaban sa yana aiki, be dago ba duk da yaji sallamar danayi masa, a ciki ya amsa yana cigaba da danne dannen sa hankali kwance, rasa ta ina zan fara masa magana, sai dana juya iya kalmomin da zan iya fada masa sannan na soma magana a hankali, har na kai aya be fasa abinda yake ba, be kuma kalle ni ba, sai kawai ya ture laptop din yana daukar slip ɗin nawa, dubawa yayi ya ajiye, ya sake jawo laptop din sa ya cigaba da aikin gaban sa. Mik'ewa nayi tsam nayi hanyar dakin zan koma naji yace "Allah ya kaimu, best of luck." Cigaba da tafiya ta kawai nayi ba tare da na tsaya ba, nayi shigewa ta ina turo kofar, Ramlah na riƙe da Iman tana jijjigen ta, ba laifi akwai rigima idan ta fara kuka har sai kan mutum yayi ciwo, karbar ta nayi na yi mata abinda nasan zai sata shiru, da haka na dora sabon tunanin mutum daya tamkar da dubu wanda ya zama min kamar wata al'adah ta yau da kullum. **** Daddy be sake neman sa ba, kamar ma ya bar maganar gaba daya, har aka soma kiran sa na gaggawa a wajen aiki, ranar yana hanyar Kano kiran ya riskeshi, ba tare da sanin madafa ba ya isa gidan na Dadah. Sai daya ci abinci ya huta sannan ya sanar da ita halin da ake ciki, ta jinjina lamarin duk da ta fara cire rai akan ganin Aminatu nan kusa, sai dai ba zata taba hanashi auren Amal ba, da shi da ita dukkannin su nata ne, babu wanda zata zaba sama da wani, dadin dadawar maraicin yarinyar, duk da babu laifi Maman na kokarin kula dasu, sai dai rashin uwa tun kana d'an karami ba abu bane me sauki. Abu daya ta dogara dashi a halin yanzu shine Exams d'in da Aminatun zatayi wanda tabbas tasan idan har tana da rai da lafiya ba zata kasa zuwa ba, idan kuwa haka ne zatayi amfani da wannan damar wajen ganin ko za'a dace. Sanda ta sanar masa da kudurin ta, murna ya hau yi, kamar ance an ga Aminatun ne an gama, duk da babu sanin takamaimai ranar da zata je ɗin, sai dai a hakan zasu duba ko Allah zai sa a dace d'in. Bincikowa yayi ya samu date ɗin da za'a yi dukka Exams din da venue, ya had'a komai intact yana jiran ranar. ★★★ Ranar labari shine ranar da zatayi ta ta Exams din, tun ranar Monday suka fara jelar zuwa makarantar, daga nan suyi nan har la'asar babu alamun ta, haka suka koma gida washegari ya komo shi kadai ba tare da Dadan ba, nan ma haka ya gama zagayen sa daga nan zuwa nan har aka gama baki daya, ya sha wuya matuka sosai haka ya hakura babu komai a cikin sa ya koma gida yana fatan samun dacewa. Karfe 9 zamu shiga hall saboda haka da wuri na shirya, Ramlah ma ta shirya don dama sunyi hutun makaranta, shirya Iman akayi saboda zamu biya ta banki daga makarantar, tare muka fito suna zaune da Hajiya yana shan tea, kallo daya yayi mana ya maida hankalin sa kan abinda yake yi, zama mukayi ya karasa Hajiya na dan jana da hira, tashi yayi yana mika min kofin kafin yayi hanyar fita "Sai mun dawo Hajiya." "Allah ya bada sa'a, sai kun dawo." Kitchen na nufa na ajiye kofin na dawo mukayi mata sallama Ramlah na rungume da Iman muka fita. Yana zaune cikin mota ya kunna ta,muka shiga ya ja muka bar gidan. Karo na farko dana fito kenan tun bayan zuwa na, kallon unguwar nake babu hayaniya, layi ne Babba me dauke da shinfidaddiyar kwalta, daidai kofar wani madadaicin gida me kyau da tsari gate din gidan ya bude a hankali, wata bakar mota me bakin glass ta fito, da wani irin gudu ya hau kan dan karamin titin ba tare da ya kula da motar mu ba. Tsaki naji Anas yaja cikin kuluwa yace "Sojan nan yazo kenan!" Ramlah ce tayi tsagal tace "Jiya ma da Hajiya ta aike ni naga motar tasa, ba yau yazo ba." "Na tambaye ki?" Yace yana zare mata ido "Bana son gulma da sa ido kinji, ni da nake da grudges dashi daban, mind ur bussiness." K'us tayi tana turo baki, ya sake jan tsakin yana kallon mirror din dake saman motar, hada ido mukayi ya harare ni nayi saurin sauke kaina k'asa. Zuciya ta na tsananta bugu jin ambatar sojan da yayi, tunanin Farouk d'ina ne ya dawo min, shi kadai na sani da hakan. Tun daga lokacin na daina sauraron komai, na fada kundin tunanin sa. Rano😊🙏🏼:     DAURIN GORO        21 Gudu yake sosai muna biye dashi har makarantar, a wajen shiga suka tsaida shi ba'a barin me tinted glass shiga, kamar zai yi musu dasu sai kuma ya dawo da baya yayi wajen da aka tanadarwa masu irin glass din, shiga mukayi still Anas na ta mita, mitar yasan dokar kawai dan shi force ne zai taka, mu dai babu wanda ya tanka masa har muka isa gaban Hall d'in, fita mukayi ya nemi wajen parking mu kuma mukayi wajen gungun mutanen dake jiran zuwan examinars ɗin, zaman mu da kadan suka iso, nan dana aka soma screening ana shiga hall din, ba'a dau wani dogon lokaci ba aka fara, addu'a kawai nake duk wadda tazo baki na, saboda ba kowacce na sani ba, ba kowacce na iya ba, dama Farouk ne yamin alƙawarin sani a islamiyya da zarar ya dawo, ashe hakan ba mai yiwu wa bane.    Na gefe na ne muka hada ido dashi, ya bini da wani irin kallo kamar ya ga kashi, mamaki ne ya kamani ganin ba wai sanin sa nayi ba, shigar jikin sa kadai ta nuna waye shi, da inda ya fito. Ban sake kallon sa ba, dan na lura dan zafin kai ne, na shiga abinda ya kawo ni. Har muka gama ban sake kallon ko in da yake ba, hanyar fita nayi ina sauri sauri, ya cimmini yana tsaida ni, kamar bazan tsaya ba sai kuma na tsaya, cikin isa da kasaita ya tsaya a gabana yana min kallon up and down "Na sanki?" Ya tambaye ni looking as if ya taba gani na "Kamar ya?" Wani iri yayi da bakin sa, yana sake ware idanun sa a kaina, sai kuma yce "May be, may be." "Ban fa gane ba ." "Shit!, Kin tab'a attending birthday party haka or kinsan wani a abuja" Juyawa nayi da nufin barin wajen dan na lura bashi da abun fada sam, sai ya sake biyo ni da sauri, "I'm Kamal Marwan Dikko by name." "Baku gama bane?" Muryar Ya Anas ta kawo mana ziyara har inda muke, juyawa nayi na bar wajen da sauri ina tunanin yanayin da fuskar tasa ta nuna, inda na bar Ramlah na sameta, tana rik'e da Iman dake ta faman kuka, tana zagaye a wajen, tausayi ta bani ganin yadda tayi wujiga wujiga. "Kar dai kuka take tayi miki tun da muka shiga." Nace ina karbar ta, "Kuma kinsan batayi kuka ba sai yanzu, wannan da muka gani sojan nan dazu, har nan yazo, da yaji kukan ta har da karbar ta, yana da kirki na rasa me yasa basa shiri da Ya Anas wallahi, kinsan yana zuwa ya ganmu tsaye tare, ya haɗa rai ya karbe ta a hannun shi, dalilin barin wajen nan kenan da yayi, kuma dan mugunta irin ta Ya Anas yana tafiya ya dawo min da ita lokacin ta soma kuka,shine fa take tayi har yanzu, taki shiru." Dariya kawai na saka muna nufar motar "Kika san me ya hada su, kinsan ance wasu masu khakhi akwai iya shege, duk da ba dukka ba, Ya Farouk ba haka yake ba sam." "Toh wannan din ma bashi da damuwa wallahi, zafin rai ne irin na ya Anas." "Maza ya jiki wallahi, ba ruwana." Dariya ta saka "Nima wallahi ba ruwana nayi shiru." "Atoh, yafi dai." Jikin motar muka tsaya, tsawon lokaci sannan ya zo ya bude mana muka shiga, rannan nasa a jagule, kamar wanda akayi rigima dashi, banki muka wuce direct ya karbar min Form, na cike komai, wajen sa marital status ne har na zabi wajen Married, naga yayi min wani kallo, da sauri na gyara ina yak'e, na mika masa ya karba yana sake sakarmin harara. Dariya ma ya bani, na dan murmusa kawai, shi sam abin bacin rai baya masa kadan, komai abin ayi fushi ne, sai dai duk inda mutum me nutsuwa da kamala yake ya cika, bashi da hayaniya balle baragada, komai yana yinsa ne gently cikin tsantseni da takatsantsan. Yana ajiye mu a gida be ko shiga ba ya ja motar ya tafi, Hajiya bata nan taje Barka, Baba Altine ce kawai a gidan ta gama aiki tana kishingid'e tana jin radio, sai a lokacin muka samu muka ci abinci sannan muka zauna muna d'an tayata hira.     ★★★ Daya bayan daya mutanen dake cunkushe a harabar makaranta suka dinga yayewa, har ya zama na babu kowa sai yan tsirarin mutane, ran Farouk babu dadi ganin da gaske har ana neman gama wa babu alamar ta, hakan na nufin ta hakura da duk wasu muhimman abubuwan da suka dace da rayuwar ta kenan ko me? Baya so zuciyar sa tana raya masa wani abu mummuna ya faru da da ita, yana ji a ransa tana nan da ranta, kuma koman daren dadewa zata dawo gareshi. Amma yaushe? Yau? Gobe ko jibi? Babu rana balle wata, a duk sanda ya kira Shagari jikin sa kara mutuwa yake, a tunanin sa zata dawo baya, duk da yasan ba lallai bane tunanin ta ya kawo mata hakan, duba da yadda komai ya zo mata a lokaci daya.   Da kyar ya bar makaranta zuciyar sa babu dadi, yana zuwa ya rufe kansa a daki ya kwanta kawai, ba zai taba yafe wa Inno ba, da kuma duk wanda yake da hannu a ciki.    Sakon text message ɗin Ja'afar ne ya iso masa, ya bude yana karantawa "Daddy na neman ka, idan da hali ka baro komai ka dawo Please." Ajiye wayar yayi ya koma ya kwanta yana yanke hukuncin amsar tayin na Daddy. Saboda haka yana tashi da safe ya sanar wa da Dadah kudurin sa, addu'a kawai tayi masa tare da sake karfafa masa gwuiwar yayi wa mahaifin sa biyayya.    Haka ya tattaro koman sa ya dawo, ya kuma jewa da Daddyn da albishir ɗin karbar tayin nasa, tsabar farin ciki a take ya kira waya ya nemi alfarmar barin sa ya tafi karatu na tsawon wasu shekaru ba tare da ya bar aikin nasa ba, babu bata lokaci aka gama komai aka hau shirye-shiryen biki na alfarma. Shi dai sai ya koma gefe ya zuba musu ido kawai dan bashi da katabus akan komai zasu aiwatar. Da yake abun na gida ne sati biyu aka saka, tun daga lokacin Mama ta soma aikin gyaran amarya, aka shiga hidima sosai tun da wannan su shine karon farko da za'a yi aure a cikin gidan, auren kuma na mutum biyu. Wednesday suka fara events, dama sam babu wanda yasa ran Farouk din zai halarci abu ko daya a ciki, a harabar gidan dake manne da nasu da ya zama gidan shikiki kuma aminin Daddyn suke yin komai saboda girman sa. ★★★ Sanye take da takalmi me kamar slipers rigar jikin ta doguwa ce me budewa sosai, sai d'an karami mayafi data dora saman kanta, a hankali cike da farin ciki take taka harabar gidan har ta dangana da part din Mama, yan uwa ne cike kowa na zaune ana hada-hada, cike da karsashi ta karasa garesu, suka hau yi mata kirarin ga amarya ga amarya, bakin ta ya kasa rufuwa saboda tsabar farin cikin da take ciki, kan wata Anty ɗin su ta faɗa tana kunshe fuskar ta.   Tsokanar ta suka cigaba da yi, ta zame da kyar ta fada bedroom din su, sauran yan uwan su sa'annin ta ne da manyan ma da suka girme mata a zazzaune ana shafta, cikin su ta shige aka cigaba da yi dakin ya kaure da hayaniyar su.    Wayar tace tayi k'ara, ta daga da sauri, ganin sunan Yah Farouk yasa ta mike tayi saurin fadawa toilet tana saka key, shikiyanci suka hau yi mata tana jinsu ta daga wayar tana karawa a kunnenta "Kizo side dinmu yanzu ina jiran ki." Fitowa tayi ta fice tana ji su sake tsokanar ta, har ta isa bangaren nasu babu kowa,tura kofar tayi ta jita a bude, ta tura kanta kai tsaye, yana kwance akan cusion ya daga kansa sama sanye da farar singlet da dogon wando fari, wajen sa ta nufa yasa hannu ya dakatar da ita "Zauna a saman kujerar nan magana zamuyi." Jikin ta ne yayi sanyi ta zauna tana mamakin yadda yayi mata, tashi yayi zaune , idon sa sun kada sunyi ja sosai, gaban ta ya fadi da suka hada ido.   Takawa ya shiga yi yana kai komo tsakanin farkon falon da karshen shi ya gaza furta kalma daya, duk in da yayi sai ta bishi da kallo, har ya isa gaban system ɗin dake ajiye tana fitar da sautin suratul munafikun cikin kira'ar Ghamid'i. Kashe karatun yayi ya dauko d'an karamin Flash ya jona a jiki, hoton bidiyon da aka turo masa ne ya bayyana a saman screen din, dan zabura tayi, har ya iso gaban ta ya tsaya kusa da ita daf, ya kura wa videon ido yana masa kallon ssoai, hadiye yawu tayi cikin wani irin yanayi ta kalli fuskar sa, hankalin sa kachokam ya tafi kan kallon video, pause ya saka ya juyo yana hade hannayen sa suka bada sauti me dan karfi. Cikin shakakkiyar murya yace "Ina kika samu Flash ɗin nan?" "Ni... Ni? Na'am!" "Kinji me nace, bazan sake maimaitawa ba." "Ni ba nawa bane, bansan nawa ye ba." Wani irin kallo yayi mata shakeke, kafin ya tashi yana matsawa baya "Tun ranar da abin ya faru, ban taba hutawa daga binciken wanda zai min haka ba, I tried very hard na gano ranar da ni da kaina na zauna na rubuta takardar, sai dai na kasa." Dan sunkuyowa yayi daidai fuskar ta "Kin tuna ranar da kika zo kika kawo min juice Ina aiki, ranar dana fada miki zanyi tafiya ina so kuje wajen ta, kin tuna?" Daga kai tayi da sauri don har ta fara digar hawaye, "Bude baki kiyi min magana!" Ya daka mata tsawa "Na tuna." "Good, what did you do? I trust you the most, na kula dake na baki dukkan gata, kinsan komai nawa, what did you do?" Ya fad'a cikin daga murya "Ya Farouk, dan Allah." "Shissshhhhhhh..." Yasa hannu a saman leban sa "Don't say a word, bayan na amince miki, you betrayed me, kika bani juice da akayi mixing da abun da zai dauke min hankali, and you gave me this na rubuta same abinda ke jiki." Ya dago takardar yana nuna mata a fuskar ta da ita da kanta ta rubuta, karfin kukan ta ya karu sosai, wani irin harbawa jijiyoyin kansa suke, ba zai taba yarda idan aka ce masa Amal zata cuceshi haka ba, me yayi mata da yayi deserving wannan sakamakon? Tabbas abinda ya faru kenan ranar, amma yayi imani ba zata taba aikatawa ita kadai ba, dole sai dai idan da hannu wani babba,amma wa? Kokarin saita kansa yayi dan yana son jin komai. "Ki daina kuka, ina son sanin dalilin da yasa kika yi min wannan hukuncin, me nayi miki? Soyayyar dana nuna miki tun kina tsumma? Shine sakamako na?" "Ya Farouk dan Allah kayi hakuri." "Amal hakuri, is that all? Kinsan halin da kika samu dukka? Dalilin haka yanzu ba'a san inda take ba, and kice nayi hakuri?" Girgiza kai kawai take tana kuka sosai, tsugunawa yayi a gaban ta yana jin dama shima ya samu damar yin kuka, hannun sa ya dora a saman bakin sa, da sauri ta hadiye kukan da take tana ajiyar zuciya. "Waye ya saki?" Ya zare mata ido sosai yana sake hada ransa "Yaaahh..." "Waye ya saki!!!" Ya daka mata tsawa da karfn da ta kusa sakin fitsari a wando, babu bata lokaci ta shiga sanar mishi komai tana kuka sosai. Kansa ne ya hau juyawa, ya soma ganin dishi-dishi, bayan samun evidence din da yayi a jakar ta da yadda abin ya dawo masa kamar Flash back, duk da ya shiga kaduwa, sai dai bai taba tunanin zasu aikata masa hakan ba, mutane uku masu matukar muhimmanci a rayuwar sa, wanda ya aminta dasu, yake ganin su a matsayin wanda suka fi kowa a wajen sa, su suka taimaka wajen tarwatsewar rayuwar sa, da baya da baya ya shiga takawa har ya dangana da daki, ganin haka yasa ta fita da gudu tana kuka sosai kamar ranta zai fita. Daki ya fada ya saka kuka, kukan da ya jima yana neman sa, sai a yau ya samu damar yin sa, lallai ya chanchanci yayi kuka. Ya jima yana yi, sai da yaji kamar zai fita hayyacin sa, sannan ya tashi ya dauro alwala ya shiga gaya wa Allah kukan sa, yana sallar yana hawaye sosai, hawayen zallar bakin ciki yadda suka ci amanar sa. Asubar fari ya tattara komai nasa yayi wa gidan kallon karshe, ya dau hanya ba tare da tunanin zai sake waiwayo wa ba har abadah. Ranar data kasance ranar da za'a daura auren, a rana yayi bankwana da kowa nasa da dukkan memory d'insa da yayi tare dasu. Karfe sha daya kamar yadda aka tsara, dubunnan mutane suka shaida daurin auren Amal Adam Shagari, Da Farouk Kabir Shagari. A daidai lokacin yana kwance a dakin hotel din daya sauka, ya rasa inda zai saka kansa yaji dadi,ya san daga lokacin da Daddy zai gane yayi nisa, duk da yasan zai yi fada ssoai, zai kuma yi fushi dashi me tsanani, amma ba zai iya ba, ba zai iya zama ba, zai bi abinda zuciyar sa ta riga ta saka masa, ko da hakan na nufin zare shi daga cikin ahalinsa ne. Rano😍 Manage 🙋🚴 :      DG    22 ★★★ Kuka take sosai ta kudundune kanta cikin katon bargo, tana jin lokacin da aka sanar da daurin auren, amma bata da katabus, tana ji suka shigo baki dayan su, kowa na kokarin tsokanar ta, da sauri duk suka yo kanta ganin yadda jikinta ke faman rawa, suka shiga tambayar abinda yake damunta, kayan jikin ta ne tun na jiya, idanun ta sun kumbura sosai alamun kwana tayi bata runtsa ba, da sauri daya daga cikin su ta fita dan kiran Mama. A tare suka dawo dakin, ta dago ta tana karata jikin ta "Baki da lafiya ne dama aamal?" Kasa magana tayi, sai wani iri da take kamar zata shid'e, riko ta sosai Maman tayi suka fita daga dakin, dakin ta ta kaita babu kowa ciki, ta kwantar da ita tana kokarin kiran ko Ja'afar ne tun da tasan Daddy na cikin Jama'a. Be d'aga ba shi din ma, alamun shi ma ya shiga busy. Jawo mata kofar tayi ta dawo falon, daidai lokacin da Uncle Buhari ya shigo yana gyara zaman Babbar rigar sa. "Ina Amal?" Ya tambaya bayan ya amsa gaisuwar matan dake falon "Tana daki na, bata jin dadi ne." "Ok Ina son ganin ta. " "Lafiya dai ko?" "Eh kalou, magana zamuyi." Ganin da mutane wajen yasa tace ya biyo ta dakin nata,suna shiga ya matsa jikin gadon, ya duba ta kadan kafin yace "Kunyi magana da Farouk daga jiya zuwa yau?" Gaban ta ne ya fadi, tayi saurin girgiza kanta tana fatan ba wani abu yace ba, d'an jim Uncle Buhari yayi kamin yace "Farouk fa ya tafi, ya ajiye letter a dakin su, yanzu haka Yaya bai san inda zai sa kansa ba, matsalar ma ba'a ga letter tasa ba sai bayan aure ya dauro. "Innalillah wa inna ilaihi raji'un, mun shiga uku." Mama tace tana sallallami, karfin kukan Amal din ne ya karu, ta mike zaune tana sake bude muryar ta sosai, girgiza kai Uncle B yayi yace "Kinga yi shiru kar ki ankarar da mutane halin da ake ciki." Da sauri ta rage kukan nata, sai dai bata daina ba, dan ita kadai tasan dalilin faruwar komai, a yau da tana da iko da kanta, data sanar wa kowa komai, sai dai bata da wannan damar, kenan a haka zata kare rayuwar ta? Ko akwai sauyin da zai zo bayan nan? Kiyayyar Aminatu ce ta shiga ninkuwa a zuciyar ta, duk itace dalilin komai, ta raba ta da Ya Farouk dinta, mai sonta da kaunar ta tun bata san kanta ba. Cigaba da bayani Uncle B yayi, bata dauki komai a maganar tasa ba, sai data dawo daga tunanin da ta tafi taji yana yiwa Maman bayani "Abinda nake tunani ko menene akayi wa yaron nan me girma ne, da zai sa shi yanke wannan danyen hukuncin, idan akwai abinda ya haɗa ku ki sanar mana, idan yaso sai asan yadda za'a bullo wa al'amarin." Ya kalle ta yana sake tambayar ta a karo na biyu, sake girgiza masa kai tayi tana goge hawayen fuskarta "Bansan komai ba Uncle B, ni jiya ma tun bayan la'asar rabo na dashi." "Shikenan, ku kwantar da hankalin ku, kar a bari mutane su sani, idan kowa ya watse sai musan ta ina zamu ɓullo wa al'amarin." Fita yayi ya koma Falon da su Daddyn suke, waya ce a hannun sa yana ta making calls, babu wani information akai, yanke hukuncin kiran Dadah yayi duk da baya son d'aga mata hankali, amma yana tunanin xata iya sanin wani abu.    Yana gama mata bayani ta saki salati, sai kawai tasa kuka sosai, ta gaji da wannan abubuwan dake ta tasowa, ace daga wannan sai wannan? Idan fa wani ciwon ya kamashi? Ba taga ta zama ba.    Sosai maganar ta firgitata, iya sanin ta Farouk ba zai taba aikata abinda zai wargaza ahalin nasu ba, shiri ta soma yi, a yau bayan shekaru masu yawan gaske, zata sake taka garin na Abuja, garin da tayi wa kanta iyaka dashi saboda babban dalilin ta, tana shiryawa tana addu'ar komai yazo musu cikin sauki, dan ba zata juri wani abu ya sake bullowa a ahalin nata ba.    Driver ne ya iso, ya dauke ta da dukkan abubuwan bukatar ta, suka dauki hanyar birnin na abuja.    Tasbah ne ya hannun ta tana ja, bata jin dadin jikin ta kwana biyu, haka dai take daurewa tana yin komai, sai dai a yanzu yadda take jin jikin nata na neman rinjayar ta, addu'a take tayi tana rokon Allah ya daidaita al'amarin ya kare su daga sharrin masu sharri. **** Mummy na zaune suna meeting da clients dinta kiran Ja'afar ya risketa, message ta tura masa tana meeting ta kashe wayar baki daya.   A gajiye ta fito bayan sun gama, takardu ne masu yawa a hannun messenger ta,  hannun ta rike da yar karamar jakar hannun ta suka nufi motarta, sai data zauna a ciki gami da cilla jakar tata gefe sannan ta daga wayar ta kira shi tana kishingida a bayan motar. "Mummy, akwai matsala wallahi, Ya Farouk ya tafi, babu wanda yasan ina yake, bayan an gama daura auren shi da Amal na shiga daki duboshi na tarar da letter daya ajiye, dan Allah Mummy ko ya fada miki ina zaije? Hankalin kowa ya tashi." Tuni taji gajiyar da take ciki ta warware, tashi tayi zaune sosai tace ma driver ta ya rage gudn motar, "Kana jina Ja'afar? Ina yace ya tafi?" "Be fada ba, yace dai yayi nisa kada a neme shi." "Dama aure Daddyn naku zai masa? Bani da masaniya akai?" "Na zata kin sani naga yazo wajen ki before yayi accepting maganar ,shiyasa ma ban sanar miki ba." "Shikenan, ka kwantar da hankalin ka, bansan ina yake ba amma i ll try my very best naga na same shi, ka kwantar da hankalin ka." "Ok shikenan, sai anjjima." Ranta ne ya ɓaci, mamakin girman kiyayyar da Daddy yake mata har ta kai hakan, a karo na biyu ya sake aurar da dan nata ba tare da sanin ta ba, kwafa tayi tana lumshe idon ta, ta gaji da komai, dauriya ce kawai da karfin zuciya, amma wannan karon ya kamata ta nuna masa da gaske ita ta haifi Farouk ba wai shi kadai ɗin bane kamar yadda yake mata iko da gadara akan dukkan abin da ya shafe shi.    Maimakon ta wuce gida kamar yadda ta saba, sai ta sauya akalar motar zuwa gidan su, dan tabbas ba zata bar komai ba, zata nemo danta ta dawo dashi gaban ta, ta bashi dukkan kulawar da ta kamata. Dauriyar ta ta kare! ∞∞∞ Dadah basu isa Abuja ba sai daf da magriba, lokacin kowa ya watse sai yan tsirarin da suka zama dole, Daddy na zaune a masallacin gidan Aminin sa, tun bayan da aka idar da sallar la'asar suke ciki ba tare da sun fito ba, sosai tafiyar Farouk ta bige shi har yana jin kamar bashi da lafiya, zuciyar shi tayi sanyi,  tabbas yana tsaurara wa a duk abinda ya shafi Farouk din, ya rasa dalilin da yasa baya iya tsayawa ya saurare shi, ko ya bashi damar kare kansa.     Sai da aka yi magriba da isha'i sannan ya fito, ya nufi cikin gidan nasa yana takawa a hankali, da motar dasu Dadah suka zo ya fara tozali, da dan saurin sa ya nufi shashen nata da zama mallakin ta a dah, Wanda yake a rufe tun bayan tafiyar ta, taron biki yasa aka bude shi saboda mutane, bakin sa dauke da sallama ya shiga, suna zaune dukkan su, Mama na daga kasa wajen kafarta, sai Amal datayi matashin kai da kafarta tana kuka k'asa-k'asa.    Waje ya nema ya zauna, cike da girmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa kafin su fara zamewa daya bayan daya suna barin falon, su biyu sukayi saura, daga ita sai shi, kallon sa tayi a tsanake, da hango tsantsar ramar da yayi, wadda ba zata wuce a wunin yau ta same shi ba, Tabbas ba abu bane mai sauki ba tafiyar Farouk din, sai dai a yau zata nuna ma Daddy kuskuren sa, zata sanar dashi abinda ya gaza fuskanta. "Kabiru..." Ta kira shi da sunan shi kai tsaye, sai yaji zuciyar sa ta kara karyewa, tabbas ko menene zata fada masa yasan me girma ne, cikin girmamawa yace "Ina neman gafarar ki Dadah, idan na bata miki dan Allah." Gyara zaman ta tayi, cikin jan hankali tace "Idan nace kamin laifi nayi karya, tsakani na dakai, babu abinda zance maka sai Allah yayi maka albarka, ka zama baya goya marayu, ka rike kowa naka, ya'yan yan uwanka ka kula da su da al'amarin su, ba tare da ka duba abinda ya faru a baya ba, sai dai kayi kuskuren wofintar da naka duk da sunan son hukunta mahaifiyar sa, menene laifin sa a ciki abinda bashi da masaniya akai..?" "Baka taba bashi damar jin ta bakin sa ba, komai yayi laifi ne wajen ka, baka taba damuwa da halin da yake ciki ba, halin da zai shiga, duk da haka yana kokarin yi maka abinda kake so." "Ina ji a jikina a duk inda yake ba a dadi yake ba, akwai babban dalilin da yasa shi barin mu." "Nayi kuskure, ban taba jin abinda nake aikata masa laifi bane, sai yau, sai dana samu wanda zai fahimtar dani, tun safe maganar da muke kenan da MD, me yasa na kasa gane haka? Sai da lokaci ya kure min, ya zanyi da auren da ke kan Amal? Na rasa ina zan saka raina naji dadi Dadah, komai ya tsaya min." "Hakuri zamuyi, mu bar wa Allah komai, mu bashi lokaci muga yadda abubuwan zasu sauya, watakila ya waiwayo mu, idan ransa ya saki." "Allah yasa, bana son matsala ta sake faruwa, ina son yadda muka binne komai, kada wannan matsalar ta tono shi, zuciya ta ba zata iya daukar maimaituwar abinda ya shud'e ba." "In Sha Allah hakan ba zata faru ba." Cigaba sukayi da tattaunawa, a hankali cikin hikima Dadah ke kara nuna wa Daddy laifin sa, sosai jikin sa yayi sanyi, yaji tsoron abinda zai je ya dawo. Duk a dalilin rufe sirrin gidan nasu, ya bata wa d'an sa komai, da hannun sa ba tare da ya ankara ba. Tsaki yaja yana tuna shi,ba zai taba yafe mishi ba, duk kuwa da k'asa ta riga da ta rufe idanun shi a yanzu, amma tabbas ya bar musa tabo babba a zuciyar sa da ba zai taba iya goguwa ba.    Kwana Dada uku a daddafe ta tabbatar da komai ya lafa, ta hau shirin juyowa, rokon da suka dinga yi akan ta zauna dasu, ki tayi dan hakan shine abu na karshe da ba zata iya ba. Amal ce ta roki alfarmar zata bita, kai tsaye Daddy ya amince , ta haɗa kayan ta ta bita don samun nutsuwar zuciya. **** Hakimce take saman kujerar ta ta gado, me samfurin karagar mulki, farar tsohuwa wadda a ƙalla ta doshi shekaru tamanin da yan kai, bata da Abu mafi soyuwa a rayuwar ta fiye da jikin nata wanda ya kasance d'a kwaya d'aya tak.    Hajiya Turai kamar yadda sunan ta yake, wadda tsabar farin ta yasa aka saka mata sunan, gashi har tsufan ta tana nan da farin nata da ya sake haduwa da hutu da jin dadi.    Sanye yake da rigar sa marar nauyi da gajeren wando da be wuce masa guiwa ba, hannun sa rike da football yana dokata a hankali ya isa falon.    Fara'ar fuskarta ce ta dadu, ganin abinda yafi komai soyuwa a gareta, dukkan soyayyar da take wa mahaifin sa ce ta dawo kansa, da ya zama da d'aya tilo da ta haifa a duniya, bayan ta cire dai ta fitar da tsammanin samun sa.    Zama yayi yana cigaba da doka ball ɗin yana kamawa, ransa a bace babu walwala, tasan kwanan zancen,saboda haka ta shiga yi masa kirarin data saba masa a kodayaushe, biris yayi da ita kamar bai san tana yi ba, "Wanane ya taba min kai wai?" "Haba Old Woman kinsan fa dalilin fushi na, nace ku fada masa bana son karatun a Nigeriar ma baki daya kunki, ace a rasa ina zanyi University kamar ni sai a Kano, a Kanon ma ba Private Uni ba, chan ta kowa da kowa har da ya'yan talakawa, Allah ya gani an cuceni walalhi." "Ka kwantar da hankalin ka, ka fara chan ɗin tunda ya kafe, idan yaso a hankali sai na sashi dole ya fitar da kai wajen, amma sai ka fara rage rawar kan naka ya tabbatar ka nutsu sosai." "Ni wai wacce rawar kai nake, haka kullum Ammi sai faɗa take min, ke kadai ke sona sai Anty, ni na gaji da gidan nan ma baki daya duk babu dadi ayi ta yimin iyaka da abinda ya zama mallaki na." "Yo dama uwar ka ai ba sonka take ba, ka rabu dasu duk zanyi maganin su dan uban su, kaji shalele na, ka daure ka fara chan din tunda ya kafe." "Old Woman..." Ya kafe ta da ido "Wai bake kika haifi Dad bane?" "Nice mana, me ka gani." "Kawai ki tilasta masa kice kin gama magana ya kaini waje nayi karatu." "Ba za'a kai ka ba, dan gidan ku." Da sauri ya mike yana sosa kai, yayi wuri wuri da ido yana neman hanyar fecewa daga falon, matsowa yayi har gaban sa kafin ya sakar mishi rankwashi a tsakiyar kai, da karfi yasa ka ihu kamar karamin yaro, hakan yasa Hajiya Turai yin salati tana tafa hannu "Karka kashe min shi, rankwashin nan sai ya juya masa kwakwalwa ai." Kunkuni ya saka ya bar falon da sauri. "Hajiya duk ke kike biye masa wallahi, yanzu Kamal shekara nawa yake? Amma bai san abinda ya dace da wanda be dace ba, gashi kinga ni shekaru na kara hawa suke, yaushe zai yi hankalin da zai kular min da dukiya? Ya kula da mahaifiyar sa dani? Lokaci fa tafiya yake." "Ka kaishi wajen daya ke kulafuci mana, chan anfi saurin karatun nan danan sai yayi ya gama ya dawo." Girgiza kansa yayi "Hajiya dan Allah, mu bar wannan maganar, Kamal zan dauka na kai waje? A gaban mu ma ya yakare? No bazan taba wannan gangancin ba." Juya masa baya tayi, tana magana kasa-kasa, sallama yayi mata ya fita dan yasan idan ya biye mata rigimar da zata sashi a gaba tayi ba kadan bace. Bayan motar sa ya fada yana addu'ar shiriya ga tilon dan nasa, duk kuwa da yasan laifin na mahaifiyar sa ne, taki barin su sam suyi masa nagartacciyar tarbiyyar data dace dashi. Niko Nace hmm, Allah sarki su malam Kamalu an zake da yawa😂😂 *** Gaisuwa ta musamman gareki Oum Iman me comment da readmore😍😍 Allah ya bar kauna. Muna gani kuma muna godia. Sannu sannu dai bata hana zuwa sai dai a dade baje ba, kuyi hakuri a hankali zamu warware komai, *Daurin Goro* labari ne me rassa da zaruruka da yawa. A hankali zamu kawo inda muke son zuwa.🙋 Comments dinku na kara mana kwarin guiwa sosai, mungode.: DG              23 ★★★ Tun daga kan zauren gidan zaka tabbatar da san samu chanji ta kowanne bangare, tana zaune gaban kofar dakin ta, ta yi tagumi tana tunanin rayuwar baki daya, idan aka ce mata komai zai chanja rayuwar ta juya mata baya cikin dan kankanin lokaci zata musa. Tun bayan fitowar su daga police station bata sake samun nutsuwa ba, magana ta zagaye kowanne lungu da sako na kauyen nasu, bata da damar fita nan da chan, sai kaji ana yar mata da magana. Dalilin haka ta hana kanta fita, gashi komai ya tsaya mata na abinda ya danganci sana'ar ta. Jikin Baba ya sake matsawa sosai, haka dai suke jinyarsa ita da yalwati duk da karfin jinyar ma ta Yalwatin ce, ita kanta tana bukatar a kula da ita dan kuwa ba isashiyar lafiyar ce da ita ba. Karime ce ke dan lekowa lokaci zuwa lokaci tana duba su, ta tafi, da haka ake rayuwar cikin kankanin lokaci dan jarin nata ya kare sai yan dabbobin da suka rage mata. Tabbas ko a haka aka barta ta gane kuskurenta, tana ji a ranta bata kyauta wa Aminatu ba, duk da a tunanin ta ta aikata hakan ne don taimaka mata, amma tabbbas tayi kuskure, ta ina ma zata fara neman ta, ta haifi abinda yake cikin ta ko yaya! Wannan tunanin biyu ke sata sake shiga cikin matsanancin tashin hankali. Cikin dare jikin Baba ya sake rikicewa, babu wanda ya runtsa a gidan, wani irin abu yake fitar wa daga bakin sa, ala tilis da safe suka nufi asibiti bayan ta barwa Nura sallawun daukar guda cikin dabbobin ta ya kai kasuwa wajen mahauta su siya saboda kudin asibitin da za'a bukata. Ba'a karbe shi ba, har sai da Nuran ya kawo kudin,sannan aka bude masa file aka karbe shi, kafin kuma asan abun da za'a bukata a gaba. *** Duk hanyar da take tunanin zata same shi ta bi, tayi dukkan kokarin ta amma babu wani labari. Sosai zuciya da ruhin ta suka kosa da abubuwan, tana bukatar wanda zata fadawa damuwar ta, tun bayan rabuwar su da Daddy ta zama mace me matukar tsauri, bata barin kowa ya rabe ta, bata sabo da kowa balle ta saki jiki , agogo ta mayar da kanta,ko yaushe cikin aiki take ba dare ba rana, duk don son ganin ta manta komai. Sai dai a halin yanzu ta karaya, zuciyar ta tayi laushi ainun, tana son wani a kusa da ita, da zai jibanci al'amuran ta, ya saurari kukan ta, amma waye? Bata da kowa a halin yanzu sai babbar yayarsu data rage dake zaune a cikin garin na Kaduna, wadda itama girma da dawainiyar yaya da jikokinta kadai ya ishe ta, ranar data bar wajen meeting dinsu chan ta nufa, da niyyar ta sanar da ita kukan ta, sai kuma ta tarar da ita ma da tata matsalar, dole ta hakura ta boye natan har ta baro gidan. Kwanan ta kusan hudu bata sake leka waje ba, jinya take sosai, jiki da ruhi, komai baya mata dadi, tana jin ta kamar a yanzu komai yake faruwa, duk abubuwan data shafe su a babin rayuwar ta a baya, yanzu sun dawo mata suna mata amsa kuwwa a kanta. Rashin uzurin Daddy da yadda yake rufe idon sa ya kasa gano gaskiya komai,ya sake jefa rayuwar d'an su a wani hali. Ba zata taba bari rayuwar dan nata ta salwanta kamar yadda komai ya chanja mata a rana daya tak! **** Bai taba tunanin zai shiga damuwa kamar haka ba, sai gashi komai ya kakare masa, tafiyar Dadah ta kara sashi a wani yanayi, maganganun ta ne ke kai kawo a cikin ransa, babu abu daya data fada masa da bai zama gaskiya ba, sai gashi yana jin son sanin abinda ya faru a bayan, duk da ya rufe babin nan a rayuwar sa, amma kuma wani bangare na zuciyar sa na son sanin komai, watakila hakan zai taimaka wajen samun haske a wannan sabuwar matsalar data same su. Ita kadai ce zata sanar dashi komai, sai dai yasan ba zata taba sauraran sa ba, duk da kasan zuciyar shi na nan akan bakan sa na abinda ya aikata mata shine daidai da ita, amma kuma yana jin kamar bai mata adalci ba, kamar yayi tsauri wajen yanke mata hukunci, duk da abu ne daya shafi mahaifiyar sa da d'an uwan sa shakikinsa, amma kuma da ya bata dama, yaji wani bangare na labarin ta, sai dai kash, bai yi hakan ba, a lokacin ma sam baijin zai iya bata wannan damar, yadda zuciya da ruhin sa suka azabtu da abinda ta aikata masa. Bata kyauta masa ba, bata kyauta ba! Mirginawa yayi yana gyara kwanciyar sa, zai dora tunanin sa Mama ta turo kofar dauke da wayoyin sa da ya baro su yashe a saman teburin falon sa. Mika masa tayi ya duba kiran, misscals ɗin MD ne, shaf ya manta sunyi zasu hadu a yau din, tashi yayi ya shirya kansa ya sauya shigar sa daga doguwar jallabiya zuwa farar shadda da hula ya fita. Kai tsaye gidan sa ya nufa, ya shiga ya nufi babban Falon sa da yake ajiye duk wani bako mai muhimmanci a wajen sa. ★★★ Rayuwa ta a gidan bayin Allah nan rayuwa ce me cike da kyautatawa da mutuntawa. Na gama gane halin kowa a gidan naci kuma alwashin zama da su da halin su, zuwa ranar da zamu rabu, tunda nasan ba zamu taba dawwama a haka ba, dole watarana xan tafi. Iman bata da matsalar komai, girma da wayo kawai take karawa abin ta, duk wani abinda za'a bukata nata Anas na samar mata shi tun kafin a nema. Kunsan ance me d'a wawa, hakan ya kara mishi matsayi babba a zuciya ta, ina jin sa kamar wani uba ko babban wa a garemu, ina jin sa kamar wanda aka aiko shi dan ya taimaka wa maraicin mu nida ita a lokacin da muka rasa madafa. Ina zaune ina ninke kayan ta da na wanke da rana Ramlah ta shigo a gajiya ta fada saman gado tana sakin nishin gajiya "Makaranta akwai wahala wallahi." "Bayan wuya?" Nace mata ina dariya "Kafin dadin fa? Aiko kinga naji labarin ance Post Utme ta fito fa." "Innalillah, kinji yadda naji, Allah sa muna da rabo, karatun nan shine kadai hope d'ina." Na faɗa a sanyaye, "In Sha Allah zaki samu, akwai abokin Baban mu wani professor kuma nasan Ya Anas yayi masa magana, nima dan cut-off mark d'ina na jamb be kai na buk ba shiyasa na chanja northwest." "Toh Allah yasa,kinga har naji kamar bani da lafiya wallahi." "Allah sa muji Alkhairi." Amin nace ina cigaba da aikin da nake, sauya kayan jikin ta tayi ta nufi Kitchen dan samo abinda zata ci. Da daddare kamar yadda muka tsara Ramlah na koya min karatun daya shafi addini, ba laifi ina karuwa sosai da ita, duk abinda kake da interest akai kana tsayawa ka koya sosai, hakan ce ta faru dani, zama na dasu na gane bansan komai daya danganci addinin ba, daga karatun sallah sai dan abinda ba za'a rasa ba, bana mantawa a makaranta na koyi yadda zan kula da kaina yayin lokacin al'adah. Shiyasa na dage nake takura ta a kullum tana karamin sani a abinda ya shige min duhu. Da hannun sa rataye a bayansa abinda ya zama masa dabi'a ya shigo dakin namu da sallama, kusan sati guda kenan baya zama sosai a gidan aiki ya masa yawa kamar yadda naji Ramlah na fada, daina karatun mukayi muka maida hankalin mu wajen sa, be ƙaraso ciki ba ya tsaya yana kallon mu, a tare muka hada baki muka gaishe shi, ya amsa a sake kafin yace "Congratulations, sai jiran admission kinci postutme." "Alhamdulillah." Na shiga jerantawa, cikin tsananin farin ciki na hau yi masa godiya, rana ta farko dana ga babu wannan cunkushewar a fuskar sa, a sake yake amsa min yana yi yana min wani kallo. Yana fita muka rufe karatun muka yi dakin Hajiya, dan sanar mata, tayi murna sosai ta saka albarka. Daren ranar ban iya runtsawa ba, tunanin Farouk da yadda zaiji idan yana tare dani kawai nake, tun bayan tsawon lokaci yau naji alamun ina da rabo a rayuwar nan. Haka na tashi da safe cike da farin ciki da walwala, tsokana ta su Hajiya da Altine sukayi tayi ina dariya. Da wuri muka gama aikin mu da zamuyi ranar na bi Altine kitchen ina kara koyon abubuwan da ban taba sanin ma suna existing ba sai yanzun. Cikin hukuncin Allah Admission ya fito, sunana na jerin sunayen farko da suka samu, nayi farin ciki ranar nayi kuka sosai na kuma godewa Allah, saboda nasan ba wayo na bane ko dabara ta. Tun daga lokacin na tattara dukkAn damuwa ta na watsa ta a bayana na shiga shirye shiryen sabuwar rayuwar makaranta. Yadda Ya Anas ya soma chanja min ne ya shiga daure min kai, duk lokacin da yake gida ya kan tabbata da ina falon a zaune, duk hirar da za'a yi sai ya sako ni a ciki, ta karfi da yaji yake kokarin ganin sai na sake dashi, ina lura da yanayin Hajiya kamar bata son hakan, duk sanda zai min wata magana sai ta kawo abinda zai sauya akalar maganar zuwa wata daban da bata shafe ni ba. A haka aka fara registration da screening, shine dai wannan karon ma ya shige min gaba akan komai, sannan duk kudin da aka bukata shi ne ya bada su, duk da naso yin wani abun da kaina sai dai sanin halin sa yasa na hakura na zuba masa ido. Kwana wajen uku sannan na samu nayi screening din, na gama ina zaune karkashin wata bishiya me dauke da zagayayyun kujeru naji an zauna a gefe na, dagowa nayi da nufin ganin waye, hannu yasa ya nuna ni cike da mamaki yace "You!" Sai nayi kamar ban gane shi ba na juya kaina gefe. Gefen dana koma ya dawo ya sake zama yana leken fuska ta. "Ji mana." "Wa kake nema ne Please?" Na watsa mishi wani kallo, dan tsaf na karance shi dan rainin wayo ne na ajin karshe, sosa kansa yayi kafin yace "Shit! Kin iya rainin wayo wannan beb ɗin wallahi, kece dai ta ranar Exams din nan na gane ki." "And so?" "And so? And so?" Ya shiga nanatawa kamar karatu , sai kuma ya bigi gefen kujerar yana fitar da yar karamar iska daga bakin sa, sai kuma yayi murmushi m d'an sauti "Can we be friends?" Yace yana miko min hannun sa,bin hannun nayi da kallo, kafin na girgiza kaina ina sake matsawa kadan "Bana ƙawance da maza, infact ban ma tab'a ganin ka ba sai yanzu, sai kawai na saki jiki da kai?" "Kaji matsalar yan matan garin nan kenan, kauyancin masifa. Go to hell!!." Yace yana mik'ewa, da ido na rakashi har ya bar wajen cikin tafiyar sa ta ya'yan da suka jiku da hutu, murmushi na saki kadan ina mamakin sa. Gefe na kalla ina sake sakin murmushi, ido na ya sauka a cikin na Ya Anas, yana tsaye ya harde hannun sa, fuskar nan tasa a gimtse, da sauri na dauki tarkacen kaya na na nufi wajen sa, bansan tsawon lokacin daya dauka a wajen ba, ina karasawa yaja dan karamin tsaki yayi gaba, na bishi. Tada motar yayi muka fita daga makarantar, gefen window nake kallo ina ganin yanayin garin, tsaki yake tayi tun da muka fito, ban kulashi ba, haka ban kalli inda yake ba ma balle na san halin da fuskar sa take ciki. Murya a cunkushe ya soma magana "Idan har kinsan irin wannan ƙananan yaran zaki tsaya kulawa ba karatu ba, sai ki sanar dani tun farko na daina wahalar da kaina." Juyowa nayi da mamaki na kalle shi, idon sa na kan titi ya hade girar sama da ta k'asa, sai nayi shiru kawai na maida kaina waje ina mamakin fushin sa. Har muka isa gida be sake magana ba, fita nayi na barshi a motar don naga bashi da niyyar fitowa. Ina shiga na tarar da Altine na ta faman zagaye goye da iman, murmushi nayi na gaishe ta, ba karamin girman matar nake gani ba, kunto min ita tayi na karbe ta na shige ciki. Dakin Hajiya na leka, na sanar da ita mun dawo, kadaran kadahan ta amsa ta cigaba da abinda take, kwana biyu akwai chanji sosai a yadda take min, sai dai na dau hakan a matsayin wani ɓangare na dan adam, ba lallai ne koyaushe ya zama kamar yadda ka san shi ba, idan ma babu wata matsala ai akwai lalura, zata iya yiwuwa bata jin dadi ne. Sai ban wani damu ba, na cigaba da al'amura na yadda na saba su. *** *Bayan wata biyu* Cikin nasara na soma zuwa makaranta, bani da matsala da iman dan lokacin ta fara shan ceareal, wajen Altine nake barin ta bayan na tabbatar da tasha ta koshi, sauƙin ta ma babu ranar da muke wuni a makarantar, duk inda azahar tayi mun dawo, hakan shi yasa nake jin dadin karatun ina kokarin ganin na samu abinda naje nema. Bangaren Hajiya bani da wata matsala tun bayan rage shige min ɗin da Anas yake, sai ta sake muka koma kamar da, duk ban kawo komai ba. Ranar wata talata na sauka a titi na shigo layin namu ina tafiya a nutse, nazo daidai wajen wani me dan kiaosk na saida katin waya naji maganar ta, bazan taba mantawa da muryar ba,muryar da zan iya cewa na daya daga cikin abinda ke makale a raina na yarinta ta, da sauri na isa wajen, ido bude nake kallon ta da tsantsar mamaki, idan har idona ba gizo yake min ba, kunnuwa na ba karya suke min ba,toh tabbas Amal ce. A bayan ta na tsaya cikin tsananin farin ciki ina jiran su gama, juyowa tayi da nufin barin wajen, taci karo dani, da wani irin tashin hankali ta ja baya, kamar zata koma cikin kiaosk ɗin "Amal." Na kira sunan ta cike da farin ciki sai naga ta hau jujjuyawa kamar me neman wani abu "Amal baki gane ni ba? Aminatu ce fa." Gaba tayi da sauri har kamar zata fadi, nabi ta da sauri na cimmata ina kwala kiran sunan ta, ja tayi ta tsaya tana juyowa a fusace tace "Wai lafiya kike bina?" "Nice fa Amal, baki gane ni ba?" "Na gane ki, sai akayi yaya?" Washe baki na nayi ina tunanin matsala ta tazo karshe nace "Nasan dama zaki gane ni ai, ina su Dadah da Ya Farouk, Allah Nagode ma daka hada mu." Dariya ta tuntsire da, kafin ta hade fuskar ta cikin isa tace "Ke wai har yanzu baki manta da su ba, bayan sun manta da kina existing a duniyar nan, kinga karki takura min dan Allah, kar ma ki kuma nuna kinsan ni wallahi, ke da su kuma sai dai idan ana haduwa a lahira." "Me kike cewa Amal, kina nufin Ya Farouk ya manta dani, Dadah ma haka, idan kowa zai manta dani nasan su ba zasu taba mantawa dani ba,dan Allah ina Ya Farouk ina son haduwa dashi ko dan yar sa dake tsakaninmu?" Na fada murya ta na rawa, daga min kai tayi, sosai naga yanayin fuskar ta ya sake sauyawa, ambaton yar sa da nayi, ja baya tayi "Ya manta dake mana, tun da har ya aure ni, nice matar sa a yanzu saboda haka bana bukatar ki kusa da mijina da yan'uwa na, batun ya kuwa ke da kanki kinsan ya ƙaryata tun lokacin rabuwar ku, sai kije can ki nemi uban yar ki, idan kuma shegiya ce sai mu sani." Jiri ne ya soma dauka ta, na kalle ta ido na na ciccikowa nace "Amal?" "Abinda kunnuwanki suka ji haka yake, saboda haka karki bata min lokaci, kinga tafiya ta." Ina kallon ta ta juya tayi hanyar fita daga layin, kuka nasa sosai, na kasa daga kafata daga wajen, ina kallo ta haura daga layin, tun ina hango ta har na daina, durkushe wa nayi a wajen na saki kuka sosai kamar raina zai fita. Rano 8a: DG              24 ★★★ Da kyar na mike kafata da tayi nauyi na karasa gida, a waja na tsaya na goge hawayen fuskata na shiga gidan, da kallo Altine ta bini tana karantar yanayin fuskar tawa, ciki nayi ba tare da na tsaya yar hirar dana saba mata ba.    Ina shiga daki na sake sakin kuka, kuka me cike da ma'anoni da yawa, a yau komai ya dawo min sabo, ina ji kamar a yanzu komai yake faruwa dani, idan har da gaske Amal take, Farouk ya aure ta, to tabbas ya manta dani, ya rufe ni a cikin babin rayuwar sa kenan, idan ko haka ne bai kyauta min ba, bai min adalci ba, bayan ya koyo min yadda zan rayu da son sa, ya tafi ya barni a sanda nafi bukatar sa.    Amal yar uwar sa ce, nasan shakuwar da ke tsakanin su, ban taba kawo hakan a nufin soyayya suke ba, sai yanzu nake hango wasu abubuwan da suka dangance ta din, ta yadda yake yake bata lokacin sa.    Har Ramlah ta dawo daga makaranta ban bar kukan da nake ba, ina ji a raina ina bukatar nayi kukan, ko naji sauƙin zuciya ta, yadda ta tarar dani ne ya sa duk ta rikice, a dan zamana da ita na shaku da ita da har bana iya boye mata damuwa ta, ko ba haka ba ma ina bukatar wanda zai fada ma kuka na ko da ba da nufin a share min kukan ba, sai dai ko yaya na zanji sauƙin abinda ke damuna.    Yanzun ma ban boye mata ba, na sanar da ita komai, girgiza kanta ta hau yi tana dawowa kusa sani sosai kafin tace "Aminatu har yanzu baki san wasu matan ba, ya zaki yanke masa hukunci da abinda ta fada miki, ina kyautata zaton babu masaniyar sa a komai, a yaya kika ganta? A nutse take alamar wadda take cikin kwanciyar hankali tayi sabon aure, ko kuwa? Kuma baki yi tunanin abinda yasa ta yi miki haka ba? Bayan ko ni nasan yadda kika daukake ta a zuciyar ki? Abu daya ne, kishi take ko dai tayi kokarin samun abinda yake mallakinki bata samu din ba, ko kuma ta samu amma babu kwanciyar hankali." "Kin batar dani Ramlah, kina nufin Amal nada hannu a komai?" "Eh haka tunani na ya bani, ko da ba komai ba, amma a wannan lokacin akwai ayar tambaya akan, akwai babban dalilin da yasa tayi miki hakan." "Taki bani damar da zan san inda take, ballantana na rok'i alfarmar ta hadani dashi ko da na dan sakanni ne, akwai tambayoyin da nake son yi masa ne, sannan na nuna masa abinda ya tafi ya barni dashi, shine kawai buri na." "Shiyasa nace miki abinda tayi nada alaka da hakan, tabbas bata son haduwar ku dashi ne, idan har ya cire ki a ransa, ba zai ji shakkar haduwa dake ba, ita kuma kai tsaye zata hada ku dan tasan bashi da alaka dake, amma me? Sai taki ta hauki da cin mutunci, Allah ma yaso ta ba tare dani bane, wallahi da sai na saki shegiya na yar a wajen." Murmushi nayi ganin yadda ta hakikance, sai na zame na kwanta a wajen ina jin kamar wata dama na samu mai muhimmanci a rayuwa ta ta kuma kubce min. Yin ranar haka nayi shi sukuku, abincin kirki ma ban iya ci ba, daren wuri na lallaba Iman tayi barci ni kuma na hau kogin tunani.    Dan buga gadon tayi tana harara ta, sai a lokacin na lura da tsaiwar ta akai na "Allah ki rage tunanin nan, is not good for ur health,ki taso Ya Anas na kira." "Bacci fa na fara, Please kice masa nayi bacci kaina ke ciwo kinga kuma ina bukatar hutu." "Kinsan shi sarai, sai ya zo har dakin, babu ruwana wallahi ki taso ni nayi gaba." Ganin da gaske tayi ficewar ta yasa na mike da kyar na dauraye fuskata na zura dogon Hijabi na fito, idon sa kur akan kofar dakin namu, ina kallon yadda ya sauke ajiyar zuciya a boye ba tare da sun ankara ba, dauke kaina nayi na karasa na zauna a gefen Amal,. "Bak'ya gajiya da zaman daki?" Yace yana kallo na, da sauri Hajiya tace "Bata fa dade da tafiya dakin ba, kaine dai zuwan ka kenan shiyasa." "Duk da haka Hajiya, ta fiya takura kanta a daki, ya kamata ki dinga fitowa ana hira dan an riga an zama daya kin gane?" Daga kaina nayi bance komai ba, maida hankalin sa kan Hajiya yayi "Ina ganin shawarar siyan adaidaita sahun (babur mai kafa uku) ita kawai zamu dauka kawai, ko hudu ne a samu a siya sai a dinga kawo balance duk sati." "Hakan yayi, Allah ya taimaka." "Nace ba, idan tana da ra'ayin hakan sai a hada da ita, idan yaso ita ma sai a dinga kawo mata wani abu duk sati..." Ya karashe yana kallo na, "Kina da ra'ayin siyan abin hawa ana miki haya? Kudin ki zai isa ki sai guda daya ko ba sabuwa bace, idan Allah yasa miki albarka sai kiga kin maida kudin kin sayi wata." Dadi ne ya kamani, dama ina ta tunanin abin yi, tunda zaman ba zai yiwu haka ba, ko ba dan Iman ba ko dan makaranta ta, da sauri na amince, dan shine kawai abinda nasan za'a yi min ɗin ba tare da ya shiga lokacin makaranta ta ba. Murmushi yayi, daga ganin yadda na amince din yayi masa dad'i, dan shi mutum ne mai son a yarda shi, kuma kai tsaye yake nuna maka yadda yaji game da kai. "Shikenan, Nagode da damar da kika bani, sai a hada a siya dukka Hajiya, hakan ina ganin yayi ko?" "Yayi." Tace Muryar ta a dan ciki "Yauwa Anas, wai ya maganar da mukayi ne tun ranar? Shiru fa nake ji ya kamata kasan abinda kake ciki, shekarun ka kara ja suke." "Hajiya kenan, ai ina ganin lokaci kawai nake jira na bayyana miki komai, ki tayani da addu'a kawai ta karbi tayi na, dan nasan zaki yi farin ciki sosai da zabi na." "Ah masha Allah, shine tuni baka sanar dani ba? Ka barni ina ta tunanin wa zan binciko maka a dangi." "Na hutassheki Hajiya, ke zaki fara sani bayan ita, kuma nasan zaki yi farin ciki sosai dan yarki ce ma." "Toh madallah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." "Amin ya ALLAH." "Naji kamar kuka ko? Jeki duba ko tashi tayi." Mikewa nayi na musu sallama, kallon k'asan ido naga yayi min, nayi gaba da sauri ina jin faduwar gaba. **** Kamar wadda aka koro haka ta shiga gidan tana waiwaye, ajiyar zuciya ta sauke da karfi ganin bata biyo ta ba, lock ta saka wa kofar ta shige ciki. Kallon tuhuma Dadah ta bita dashi kafin tace "Ina kika je ne nake ta neman ki, baki fada min zaki fita ba kuma." "Kati naje na siyo, ina so nayi waya na kasa siya ta bank shiyasa." "Shine kike abu kamar baki da gaskiya?" "Ni ba abinda nake kece kika ga hakan." Tayi cikin dakin ta, tana shiga ta murda dan key din jiki ta cire mayafin ta ta haye gadon tana kiran number. Kasancewar akwai rata da tazara me yawa tsakanin su, sannan akwai banbancin lokaci yasa suka tsara sanda zasu dinga magana a waya, tun da tazo gidan sau biyu kawai sukayi waya. Kamar ba za'a daga ba, dan har ta fara cire rai, sai kuma taji an daga ɗin, cikin magana k'asa-k'asa ta shiga bayanin komai, bata wani dau tsawon lokaci ba ta ajiye wayar tana murmushi.   Duk ranar da Farouk ya gama boye-boyen sa zai fito, daga lokacin zai karbe ta a matsayin matar sa, dolen sa ne, tilas ɗin sane hakan,da shi kadai zata iya rayuwa.    Sam tafiyar sa bata dame ta ba tun bayan da aka tabbatar mata da ita din matar sa ce, aure ya dauro, zata jira shi komai daren dadewa, sai dai ba zata taba gangancin barin sa ya hadu da Aminatu ba, wannan Alk'awari ne tayi wa kanta, tunanin yadda akayi ma har Aminatu tazo nan ɗin, ayi sanin ta bata da wasu data sani a garin na Kano, sai gashi ta hadu da ita a lokacin da haduwar tasu tamkar yankewar farin cikin tane, kuma a unguwa daya da wadda take rayuwa a yanzu, shin dama tasan inda Dadahn take zaune ne ko kuwa co-incidense ne? Amma ta yaya? Idan har ta sani ba zata nemi ta kawo ta ba ai, toh amma? Kanta ya cunkushe ta rasa kalar tunanin da zata saka. Koma dai menene, ba zata taba barin ta ba, ko da kuwa hakan na nufin tonuwar asirin dake rufe shekaru masu yawa ne! ★★★ Riga ce karama da dogon wando a jikinsa ya dora doguwar Jacket a sama, kansa ruf da woody cap sai bakin glass me matukar duhu daya rufe ilahirin kwayar idon sa, tun sanda abin ya faru yake cikin garin na Lagos, bai taka ko nan da chan ba sai a yau da zai bar k'asar, bolt ya kira suka zo har gaban hotel din daya sauka ya fito suka dauki hanyar filin jirgi.    Sai da ya daidai ta a cikin jirgin sannan ya ciro wayar sa ya kunna, sakonni suka fara shigowa, sai daya tabbatar sun gama shigowa tsaf,sannan ya saka wayar a airplane mode ya shiga duba sakonnin. Daga na Daddy, Mummy, Ja'afar, Amal sai Dadah ne kowanne da abinda yake cewa, kai tsaye ya goge dukka baya son jin komai daga gare su, idan ba so suke su  k'arasa shi ba, dan a yadda yake jin zuciyar sa yasan tabbas ba daidai take ba.      Gyara kujerar sa yayi sosai ya kwanta, sakonnin su kadai sun sashi ya tuna da komai. Zuciyar sa ba zata taba daukar cin amana daga mutane uku ba, Ja'afar, Amal da Dadah! Sune mutanen da ya yarda dasu fiye da kowa a duniya, fiye da iyayen da suka kawo shi duniya. Amma ta yaya hakan ta kasance? A lokacin daya gane akwai sa hannun Amal bai shiga tashin hankali ba kamar sanda take sanar masa da komai, Dadah! Why? Ya kasa gasgata hakan, gashi ya gaza samun hujjar da zata kare daya daga cikin su, shiyasa ya gaza hakuri, ya kasa juriya, ya bar su, bari na har abadah, duk kuwa da yana sa ran haduwa da Aminatu komai daren dadewa, sai dai akwai lokaci, kafin sannan, yana fatan Allah ya bashi aron rai da lafiyar da zai iya fuskantar ta, ya kuma nuna masa gaskiyar komai.   A hankali sanda jirgin su ya lula sama sosai ya furta! "Sai wata ranah!" ★★★★★ Kullum idan na dawo daga makaranta sai nabi hanyar ko zan sake ganin ta, sai dai ko mai kama da ita ban sake haduwa da ba, tun ina saka rai har na hakura na cire na barwa Allah komai na rungumi karatu na, duk bayan sati biyu ake kawo mana balance, da su nake amfani wajen hidimar makaranta ta da abinda ba za'a rasa ba, tun Anas na fada har ya daina ya zuba min ido, daidai gwargwado yana kokarin sa a kaina duk da hakan, tun da mafiya yawancin lokuta shine yake ajiye ni a makaranta,bana cin komai har naje na dawo shiyasa ba wani kudi nake kashewa ba, nidai burina nayi karatun na taimaki kaina da yata.   Tun bayan fara zuwa na makaranta haduwar mu wajen bakwai da Kamal d'an gayu, duk sanda ya ganni sai yayi kokarin min magana a haka har na saki jiki dashi muke gaisawa, anan na gane course din da yake business adminstration. Na lura kwarai ba karamin dan masu kudi bane duba da yadda mutane keyi masa a duk lokacin da suka ganshi, bashi da girman kai ko kadan sai dai dan gayu ne na ajin farko, kullum cikin sabuwar shiga yake komai masa abin kallo ne tun daga kayan sawar sa har zuwa takalman da yake sawa. A hankali sabo ya shiga tsakanin mu, har mu kan zauna muyi hira duk da bata fita tsawo ba, kullum maganar sa guda daya ce Kakar sa, ko da zaman mintuna biyu kayi dashi zaka tabbatar da irin shakuwar da ke tsakanin su, tabara da tsantsar gata take nuna masa fiye da tunanin mai tunani. A off-campus yake zaune, gida guda ne yake zaune a cikin sa, duk da ba karamin takura yayi ba a yadda ya saba, amma hakan yake zaune ala dole bisa tursasawa mahaifan sa, duk weekend a gida yake yi, sai Monday da safe yake dawowa wani lokacin ma sai Tuesday, bashi da matsalar komai duk abinda yake so shi yake yi. Ina ta sauri zan fita daga makarantar ganin yau har la'asar ta taho ban isa gida ba, mota ce ta tsaya a gabana,na daga ido na dubeshi, daman nasan sai shi, fitowa yayi ya tako har wajen da nake, ina sanye da dogon Hijabi maroon har k'asa, sai jakata dake makale jikin sangalalin hannu na. "Gida kikayi ne irin wannan sauri Meena?" "Wallahi yau na dade, shiyasa nake ta sauri." "Lemme drop you mana idan ba damuwa." "A ah Ina, bashi na samu bus ta fita dani, see you." Nayi gaba ina nufar wajen da cincirindon mutane suka kowa na jiran abin hawa, dage kafadar sa yayi ya jingina jikin motar sa yana kallon mu, mota daya ce tazo, aka hau rububin hawa, kasa shiga nayi ina kallo aka cika ta, na sake matsawa gaba. Tsawon lokaci muka dauka shiru babu alamar zuwan wata motar, gashi ranar kudi na kenan, idan nace zan fita titi na hau normal abin hawa ba zai ishe ni ba, waigawa nayi gefe na hange shi still yana inda na barshi, muna hada ido ya saka dariya yana turo bakin sa alamar gwalo, da sauri na dauke kaina na yi gaba ina sauri ganin wata motar ta tawo, ita dinma hakan ce ta kasance, ina kallo aka gama shigewa aka barni, dafe kaina nayi dake ciwo na sake kallon sa, gani nayi ya fada motar sa ya bata wuta, yazo ya wuce ni, duk sai naji babu dadi, na hau takawa a kafa, ga yunwa gashi rashin nawa Iman abincin ta da banyi ba yasa duk sun cika sosai har na fara jin zazzaɓi na neman rufeni. Tafiya nayi mai nisa kafin na isa gate ina yi ina haki, a wajen gate din na hangi motar sa a fake a gafen titi, an bud'e kofar mai zaman banza daidai inda zan wuce, har zan dauke kaina muryar sa ta iso min tun kafin na karasa "Miss... da kin cire komai kinzo na ajiye ki, after all ba cinye ki zan ba, idan ma na cinye ki, za'a iya kamani ai tunda nasan za'a ce an ganni tare dake last." Bani da zabi, ila na shigan, a hankali na ja kafafuwana na zauna ina cin magani, dariya ya sa ya ja muka tafi yana yan kananan wake-waken sa da harshen turanci. Hanya na dinga nuna masa har muka isa, sosa kansa yayi yana kallon unguwar, "Kinga fa akwai gidan da Daddy yaso na zauna anan unguwar naki, babu nisa daga gidan ku." "Kafi so ka zauna Off-k kaci karanka ba babbaka ko?" "No ban saba squatting bane a rayuwa ta, kinga ba zan fara yanzu da girma na ba." "Yayi, nagode sosai, sai Monday idan Allah ya kaimu." Nace ina balle murfin motar. Daga min hannu yayi ya bar unguwar, na juya da nufin shiga gida, gabana ya fadi ganin shi a tsaye yau ma kamar ranar, ya harde hannayen sa a kirjin sa, fuskar nan tasa kamar wuta. Dakewa nayi naje zan wuce ta kusa dashi, hannun sa ya sauka a cikin hannu na, da wani irin karfi yasa ya fizgoni, ya tura ni cikin gidan, kamar zan fadi nayi saurin tsayawa a kafata fuska ta dauke da madaukakin mamaki. Da hannu ya nuna ni, cikin tsananin bacin rai ya soma magana "Baki isa ba wallahi,kinyi kadan kina kawo mana samari kofar gidan, samarin ma na jami'a, kanana yara wanda basu mallaki hankalin kansu ba, uban me wannan dan yaron zai baki, shiyasa kika yi zaman ki a makarantar bayan yau da wuri kuke gama lecture ko?" "Ban gane ba." Nace ina matsawa baya ganin yadda yake matso ni "Dama ba zaki gane ba,haka zaki ce kullum akayi miki magana, U act as if baki san me mutum yake ciki ba..." Dukan kirjin sa yayi da hannun sa biyu "Can't you see how much I love you? Nace baki gane ba? Ke makauniya ce? Baki da ido? Ko baki da wayo? Ba zan dauka ba, ke tawa ce, mine and mine alone! Kin gane? Get it straight to your filthy head, ni zan aureki saboda haka bazan dauki ganin ki da kowanne kazami ba." Daya bayan daya na hau kokarin fahimtar maganganun sa, kamar ya zare haka ya cigaba da magana yana sake nufo ni, yaki bari na sam na gama digesting kalaman nasa, wasu yake kara min akan wasu, a bayan mu muka ji salati, muka juya da sauri gaba daya "Na shiga uku,Anas mai zan gani? Tsintasshiyar magen zaka aura? Innalillah wa inna ilaihi raji'un, abinda nake gudu ya faru." Rano                  DG                    26 BARKA DA SALLAH!         ★★★ Asalin su shine jihar ta Katsina, tun yarinta shakuwar su babba ce tunda daya baya iya komai ba tare da daya ba, sun shaku matuka har zuwa girman su babu abinda ya chanja na daga yadda suke.    Asalin amintar su ta fara ne daga kusancin iyayen su maza, kar kawo yanzu.    Kabir Aliyu Shagari kenan da aminin sa Marwan Muhammad Dikko. Duk inda kake neman shakuwa da yarda da juna toh sun hada, tare suke komai tun daga matakin farko na rayuwa har zuwa shigar su jami'a.   Tafiyar su jami'a bisa mabanbantan ra'ayi be sa sun chanja ba, Kabir ya zabi bangaren aiki soji inda ya tafi makarantar horar wa dake garin na Kaduna, inda Marwan ya zabi tafiya jami'ar ta Ahmadu Bello dake garin na Zaria. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin nasara.    Kasancewar shi Marwan d'a daya tilo wajen iyayen sa yasa shi kara shakuwa sosai da aminin nasa, saboda babu wani wa ko k'ani da zasuyi shawara sosai. Masu arziki ne na gaske, abun kwatance a kaf fadin yankin su .     Kabir su uku ne wajen iyayen su duk maza, shi ne na farko sai kannen sa Adamu da Ahmadu. Mahaifiyar su da suke kira da Dadah mace ce mai kirki da sanin ya kamata. Tana da abokiyar zama guda daya sai dai Allah bai sa ta haihu a gidan ba har zuwa lokacin da maigidan ya rasu ta tattara ta kama gaban ta, duk da hakan har yanzu suna gaisawa da juna.   Bayan rasuwar mahaifin su komai ya dawo hannun Kabir, shine ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya kula da abinda mahaifin su ya bar musu, ya kuma cigaba da kula da yan uwan sa.   Cikin hukuncin Allah komai ya dinga tafiya musu cikin nasara da daukaka. *** A gaggauce ya shirya yana yi yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, karo na shida kenan da yake faman kiran sa akan an fara baya wajen, cikin sa'a ya gama shirya wa ya dauki hanyar jami'ar.   Yana isa yayi saurin dukawa kansa a k'asa yace "Tuba nake ranka ya dade."   Harara ya sakar masa, ya bigi saman kafadar sa cikin jin haushi yace "Allah ka iya jirga mutane, da ban azalzala ka ba da shikenan sai ayi babu kai." "I'm deeply sorry oga." Ya sara masa yana kokarin cire hular kansa, da wani irin shock ya tsaya yana kallon su, yan mata ne su biyu cikin shiga iri d'aya sai dai d'aya ta girmi daya duba da yanayin shekarun su "Kb!" Ya kira shi da d'an ƙarfi ganin yadda ya bada attention d'insa gaba daya wajen su. "Man nayi farin zuwa, wallahi naganta, no wonder naji sai na tsaya na tsara kwalliya ta ashe yau zan hadu da future d'ina." Dariya Marwan yasa ya kama hannun sa. "In dai Abidah ce kamar yadda naji ana fada ba sauraran ka zatayi ba, amma wacce kake so cikin su? Karamar ko babbar?" "Babbar, itace Abidah?" "Wai, toh ka gwada sa'ar ka, nidai babu ruwana idan ta wulakanta ka." Gyara wa ya shiga yi sosai "Aiko zan gwada, nasan nafi karfin wulakanci wallahi." "Owk best of luck, bari na matsa ciki kafin a fara, kuma wallahi ka zama kusa dan zan neme ka." "An gama my guy." A chan nesa ya hange su, suna tsaye gefe suna kallon yadda ake gabatar da taron convacation ɗin, magana suke kasa kasa da juna, kai tsaye ya isa wajen cikin gwarewa ya shiga introducing kansa, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, dan murmushi tayi kawai bata ce komai ba, karamar ce ta amsa masa suka shiga hira kamar sun saba, da haka ya hilace su har ta saki jiki dashi, cikin dan kankanin lokaci suka saba, ta ware sosai tana amsa masa,tun daga lokacin shikenan suka saba, soyayya ta shiga tsakanin su. *** Bayan Aure! Part uku ne sai na Dadah dake gefe, baya zama saboda yanayin aikin sa, hakan yasa ka shakuwa mai karfi shakanin ta da Adam da Aliyu, bata da matsalar komai duk sanda yazo yakan yi two weeks sai kuma wani dogon lokacin. Kasancewar Dadah mace wadda tasan ya kamata yasa suke zaune lafiya kowa yana mutunta kowa. A lokacin ne Marwan yayi aure ya auri wata yar zaria, basu wani dade ba auren ya mutu tun da ya ji tana waya akan yadda take so dukiyar sa ta dawo hannun ta, ya tattara ya watsar da duk wata maganar aure ya cigaba da zaman sa haka nan.   Rayuwar ahalin Dadah rayuwa ce mai dadi da kaunar juna. Shekaru biyar da auren Kabir da  Abidah Allah ya azurta su da samun d'a namiji, wanda take Dadah ta zaba masa sunan mahaifin ta Umar Farouk, dukkan soyayyar da d'a yake nema wajen mahaifin sa Uncle Aliyu kamar yadda Abidah take ce masa ya karbe ta, shine yake masa komai na uba saboda rashin zaman mahaifin sa.    A lokacin Marwan ya sake auren har mata biyu suma duk abu daya ne ke kawo su data farkon, gashi duk cikin su babu wadda ta haihu sai dai suzo su tafi.    Kanwar Abidah mai suna Safiyya ta gama karatun ta, ashe dama soyayya suke da Aliyun babu wanda ya sani, hakan ya kara faranta ma Dadah dan ta gamsu da Abidah saboda haka zata so su kara hada zuri'a.    Rikon Farouk ya koma kachokam wajen Aliyu da Safiyya bayan auren, su ka cigaba da zaman lafiyar su cikin kauna da kwanciyar hankali.    *** Cikin kankanin lokaci dukiyar Marwan Muhammad Dikko ta bunkasa. Samun aikin sa a PTDF ya sa dole suka tattara suka koma garin na Abuja, kasuwanci ya cigaba yana juya dukiyar su, daga shi sai mahaifiyar sa har lokacin baya maganar aure,  babu yadda aminin sa bai masa ba amma sam yaki maganar auren da uzurin har lokacin bai samu wadda tayi masa ba.    Gini ya fara a hade da juna guda biyu, komai iri daya sai dan banbancin girma, abun da akwai kudi ba'a wani dau lokaci ba ya kammala. Yanayin aikin Kabir yasa har aka gama ginin be san komai akai ba, mukullin gida kawai ya damka masa a matsayin kyauta ya zauna har karshen rayuwar sa. Ba karamin murna yayi ba, saboda bai taba zato ko tsammani ba, nan suka hau shirin tariya suka tattara komai suka koma garin na Abuja har Dadah, duk da Safiyya da Aliyu basu ji dadin tafiyar tasu ba, amma sun san hakan wani cigaba ne, dole suka bisu da fatan alkhairi suka rabu cike da kewar Farouk da ya zama tamkar d'an su.   **** Shekaru sun ja, abubuwa da yawa sun faru, ciki har da haihuwa da Allah ya azurta Aliyu da Safiyya ta d'a namiji, suka sa masa suna Ja'afar, lokacin Farouk na da shekara biyar a duniya. Har lokacin Alhaji Marwan Dikko bai yi aure ba, kuma bashi da niyyar yi, takanas Hajiya Turai ta aika aka kira mata Kabir (Daddy) ta sasu a gaba da fadan lallai ya matsa masa ya fitar da mata, dan zaman shi haka ya ishe ta babu da balle jika, hakuri suka hada baki suka bata, suna fitowa Kabir ya sake dora masa da nasa fadan, haka dai yayi masa alƙawarin zai yi kwanan nan babu jimawa. *** *Bakaken Ranaku* Yanayin aikin soja da rashin lokacin su ya kara saka shakuwa mai karfi tsakanin Adam da Abidah, a bangaren ta yake zama har dare ayi kallo ayi hira da wasa da dariya, wani lokacin ma har sai ta tafi ta kwanta ta barshi idan ya gama ya rufe mata kofa.    Watarana da daddare bayan ta tafi daki ta kwanta sai taji tana buƙatar dauko ruwa, kanta tsaye ta nufo falon, tun daga nesa take jin alamun magana a cikin fushi, d'an dakatawa tayi tana sauraron shi, "Kinsan Allah, kije chan ki nemi uban da yayi miki ciki, dan kin rainan wayo shine zaki kwaso cikin ki kizo ki na na min." "Eh nasan wannan amma sau daya shikenan sai kice ni, tab ai wallahi uban da yayi miki kije can ki neme shi, dan tsabar iskanci sai da kike gab da haihuwa sannan zaki kirani kina min wani banzan zance, karki kara kirana wallahi kinsan ni kinsan me zan iya." Tsaki yaja da karfi ya kashe wayar yana bugata saman kujera, rai a bace Abidah ta ƙaraso falon "Anty!" Ya fada cikin alamun tsoro tsoron ko taji, bata amsa ba sai ma zama da tayi kujerar dake kallon sa tana tallafe cikin ta dake wata takwas. "Adam, me naji kana cewa?" Ta watso masa tambayar tana kallon yanayin sa. Zai yi magana tayi saurin daga masa hannu "Ciki kayi ma wata Adam?" Juyar da kansa yayi gefe a ciki ciki yace "Tun da kin riga kinji, bani da damar boye miki, mistake ne ba wai hali na bane." A cikin tsananin mamaki take kallon sa, bata taɓa tunanin Adam da aikata abu makamancin hakan ba, fada ta hau yi masa ta inda take shiga bata nan take fita ba, tayi masa tas kuma tace tabbbas dole yan uwan sa da mahaifiyar sa su sani, da sauri ya zamo kasa ya haɗa hannun sa ya hau yi mata magiya, bata saurare shi ba tayi wucewar ta daki ta rufe da key. Tsawon kwanaki uku yana mata ziryar ta rufa masa asiri, kin bashi fuska tayi, ta daina sakar masa fuska ko kadan, tunanin yadda zata sanar wa Dadah take, bata son abinda zai daga wa matar hankali, haka tayi ta fama da abin a ranta ta rasa wanda zata faɗa wa.   Kwatsam sai ga Safiyya da Aliyu sun zo, hakan ba karamin dad'i yayi mata ba, bayan sun huta ne ta samu damar sanar musu abinda yake faruwa, sosai Aliyu ya dau zafi ya kirashi ya ci masa mutunci sannan ya ce dole ne Dadah ta sani sannan dole Kabir ma ya sani, shawarar yadda zasu fara fad'a wa ita Dadah sukayi musamman suka je har dakin ta, tare da Adam ɗin yana sunkuyar da kansa kamar munafiki, tun da taga yadda suke nuku-nuku ta gane akwai matsala, kafin su samu damar fada mata ta jefe su da tambayar,ala dole Aliyu ya daure ya sanar da ita, iya kar rudewa ta rude, bata san sanda ta rufe shi da duka ba, tana yi tana kukan ya cuce ta, da kyar suka lallaba ta, ta yi shiru suka shiga tunanin yadda za'a bullo wa al'amarin tun da dai ya tabbatar musu ba halin yarinyar bane shine ya yaudara ta da dadin bakin zai aure ta ita kuma ta amince masa.   Tunanin zuwan Daddy kowa ya shiga yi dan yasan ba karamin artabu za'a sha dashi ba, ranar da ya kira kuwa yace yana hanya duk jikin su a sanyaye, haka ya zo ya tarar dasu sukuku kamar wanda akayi ma mutuwa.   Wanka yayi ya fara hutawa kafin ya nufi bangaren Dadah, bayan sun gaisa ne suna d'an taba hira Alhaji Marwan ya shigo, yana zama aka shiga yin sallama a ɓangaren, Dadah ce ta yunkura ta leko, mata ne guda biyu cikin yanayin tashin hankali da rashin nutsuwa, hannun su tabi da kallo a take tasha jinin jikin ta jiri-jiri ne ya soma daukar ta, tayi saurin dafe bangon tana yi musu iso ciki, a d'arare suka bita, falon suka koma suka samu waje suka zauna. Hakan yasa suka katse hirar da suke suna kokarin mik'ewa Dadah ta dakatar dasu "Ku tsaya ayi komai a gaban ku, dan kuma ta shafe ku." Komawa sukayi suka zauna da tunanin abinda yasa tace hakan, "Sannun ku da zuwa." Tace tana mika hannu dan karbar jaririyar hannun su. "Gata nan, tabbas bamuyi tunanin ganin ku haka nan ba, ranmu a bace muka tawo sai dai a yadda kika yi mana yasa muka ji nauyi da kunya, gata nan, yar ku ce dan dukkan bincike ya nuna yaron gidan nan ne yayi mata cikin, sai dai ita Allah yayi mata rasuwa wajen haihuwar shiyasa ma muka jinkirta kawo ta har zuwa sanda akayi sadakar bakwai." "Allahu Akbar, Allah ya jikan ta, Allah ya raya mana, kuyi hakuri dan Allah, d'a ne ka haife shi, amma baka haifi halin shi ba, kuyi hakuri kuyi hakuri." "Me ya faru Dadah.?" "Kira min Adamu a waya, yazo nan bangaren sai kuji komai." Daga waya yayi ya kirashi, ya ajiye yana jin zuciyar sa kamar zata faso kirjin sa. Kan sa tsaye ya shigo falon, da kallo duk suka raka shi har ya samu waje ya zauna yana kallon matan. Tashi Dadah tayi ta mika masa jaririyar tana buɗe rufin da akayi mata da abin daukar yara "Ko da ace zaka ƙaryata, ka dube ta, babu abu daya data bari naka sanda kana karami, babu abu ɗaya, kaga ikon Allah ko? Toh haka rayuwa take, duk wanda yayi da kyau zai gani." Sai ta juya wajen su Daddy "Gashi nan ya ce aka kawo muku, sai yayi muku bayanin yadda akayi aka haihu a ragaya, sai dai wannan tsantsar kamar ta isa ta tabbatar da komai." "Ku kuma dan Allah kuyi hakuri akan abinda ya faru, bani da bakin da zan iya baku hakurin rashin kyautawar da akayi wa yarku, sanadiyar da har ta rasa ranta, Allah ya baku hakurin rashin ta." Mik'ewa sukayi a tare, sukayi sallama suka tafi. Suna fita Dadah ta karbi jaririyar tayi dakin ta tana jin kamar ta yi kuka, yau itace zata goya yar da ba ta hanyar sunna aka same ta ba, sai dai dole laifin iyayen ba zai shafe ta ba, zatayi kokarin ganin hakan bai shafi rayuwar ta nan gaba ba. ***Wata irin shaka Daddy ya kai masa, ya shiga bugun sa da dukkan karfin sa, da kyar Alhaji Marwan ya kwace shi dan tuni ya sauya masa halitta, da rarrafe ya fita daga falon saboda tsabar yadda ya daku.   Saman kujera ya fada yana dafe kansa, idan akwai abinda ya tsana take kyama a rayuwar sa ya kasance zina, abu ne da duk wanda zai iya aikatata to tabbas  bashi da sauran mutunci a idon sa.   Idan ya tuno yar jaririyar sai yaji kansa ya sake sarawa, komai daren dadewa dole ne gaskia ta fito. Ya zatayi da abinda bata da masaniyar komai akai? Shigowar matar dake dan taimakawa Abidah da aiki a guje ya maida hankalin su gareta "Alhaji ina tunanin haihuwar tazo." A kid'ime suka bi bayan ta, aka nufi asibiti da ita, lokacin ta riga ta gama galabaita sosai, har bata gane wanda ke kanta sosai. Sai data dau tsawon lokaci dan har an soma shirye-shirye shiga da ita theatre ta haihu sai dai abinda ta haifa bai zo da rai ba. Kwanan ta biyu a asibitin aka sallame ta. *** Bangaren Abidah Dadah ta nufa dauke da jaririyar a hannun ta, Abidah na zaune tana shan tea a kofi duk jikin ta babu dadi aka shigo, ajiye kofin tayi tana kokarin mik'ewa ta dakatar da ita "Zauna dan Allah. Ke da ba lafiya ba." "Ai da sauki Dadah, ashe sun zo ranar." Tace tana mai kallon hannun nata "Hmmm sun kawo ta gata nan, gashi sam taki karbar madara wallahi, kwana biyun nan kuka kawai take sai dai idan taji uwar bari ta karba tasha kadan, na rasa yadda zan." "Allah sarki." Tace tana kallon yarinyar, da sauri Farouk ya taso yana leka fuskar ta, daidai lokacin ta saka kuka sosai, da sauri ya kalli Abidah "Mummy kuka take, sabuwar bbyn da kika haifa mana ce?" Daga masa kai tayi, ta mika hannu ta karɓe ta daga hannun Dadah ta soma jijjigen ta. "Bari na dauko madarar a sake gwada mata, kukan ya soma yawa wallahi." "Mummy ya sunan ta? Itama kanwata ce kamar Ja'afar?" "Kanwar ka ce Farouk." "Yess!" Yace yana murna, yana kama dan karamin hannun ta, Dadah ce ta dawo dauke da madarar ta bata ta koma wajen bakin da tayi, karbar ta tayi suka shiga daki, ta sake hada mata madarar ta bata, kadan tasha ta yi bacci, shiru tayi tana tunanin taimakon yar jaririyar da bata san abinda duniyar ke ciki ba. Ba tare da shawara da kowa ba ta yanke abinda take ganin zai taimaka mata ya kuma farantawa Dadah. ***: *DG*                         27 Adam duk ya fita hayyacin sa, babu wanda ke bashi fuska a gidan, zaman daki ne ya zama abin yin sa tunda idan ma ya fito babu wanda ke kulashi, gefe daya yarinyar da yake mutuwar so da kauna, kwana wajen nawa kenan yana sintirin kiran ta a waya amma bata daga wa, daga karshe ma sai tayi blocking kiran sa baki daya, abin yayi masa zafi ssoai, dole ya shirya ya tafi gidan su, tun da ya hango motar yaji jikin sa ya soma rawa, ganin an bude gate din gidan yasa shi labewa a baya, itace tayi kyau ainun, cikin shigar ta kamar ko yaushe, ta nufi motar. Motar Alhaji Marwan ce, ji yayi numfashin sa ya soma ja da kyar, be kara shiga tashin hankali ba sai daya ga ya zuro kafafun sa ya fito, shi din ne kowa, fuskarsa dauke da madaukakin farin ciki, yadda tayi masa jagora zuwa cikin gidan yasa gama tabbatar da komai ya kare masa. Wayar sa ya sake kira yana son sake tabbatar wa, sai dai kamar ko yaushe ne, ba zai taba iya kiran nata.    Da kyar ya kai kansa gida, zuciyar sa na zafi, zafi irin na rabuwa da masoyin daka kwallafa rai akan sa, ka dora dukkan buri akan sa, shin me hakan ke nufi? Ta san abinda ya faru dashi ne yasa ta juya masa baya? Ko kuwa dai Alhaji Marwn... Tuni zuciyar sa ta hau tururi, yaji kamar ana zare masa sauran tausayin da ya rage masa a zuciyar sa, sai da ya zama babu digo ko sauran tausayin kowa a ransa, a take ya yanke wa kansa shawarar abinda yake ganin shine daidai. *** Zagayen dakin yake yana dan shafa saman kansa, tunanin sa ya tsaya tsak daga lokacin da ya tuna tabbas Abidah ta shayar da Amal nono, eh duk da ba wai ta shayar da ita bane har zuwa sanda ta isa yaye, amma tabbbas ta zama mahaifiyar ta ta shayarwa kamar yadda musulunci yace,ya akayi dukka suka manta da wannan? Duk da a lokacin ya hane ta ya gargade ta akan kadda ta shayar da ita bayan ya gano take taken ta, sai dai a yanzu yana hasaso hakan a matsayin wani ɓangare da yake bukatar dubawa. Da sauri ya jawo wayar sa, number ta da har lokacin ke ajiye a wayar sa, har ya danna kiran sai kuma yayi saurin katsewa, akwai sauran abubuwan da yake son ganowa, dan haka dole ya gama bitar komai daki-daki kafin ya kira ta. ***Babu bata lokaci aka shiga hidimar bikin Alhaji Marwan Dikko, zuwa lokacin Adam ya zama kamar wani tsohon mahaukaci, komai ya tsaya masa, babu kuma wanda ke bin takansa, kowa sabgar gaban sa yake akan abinda yake ganin wani kuskure ne da ya aikata da ya kamata su sassauta masa, idan yaje dakin Dadah bata wani sauraron sa, balle kuma Abidah da taso tafi kowa daukar zafi ita da mijin ta Uncle Aliyu da Safiyya na tayasu, sai yaji duk ya sake tsangwamar kansa.   Haka akayi biki aka watse aka kawo amarya, ranar bai iya baccin kirki ba, atleast yaso yaji ta bakin ta akan dalilin daya sa tayi masa hakan, sai dai duk cikin su babu wanda yake da niyyar sauraron sa. Hakan kuwa ya taimaka wajen dasa mummunar kiyayyar su a zuciyar sa. Zuciya bata da kashi, tuni ta shiga ingiza shi, da sunan daukar fansa wanda yake ganin haka ne kawai mafita. ***BAKAR RANA!*** Tana kwance ta bubbbude curtains din dakin ta saboda yanayin da ake ciki na zafi, gashi ranar babu wuta sai zafin ya kara yawa. Motsi taji kamar ana taba kofar ta, ta dan cire kanta ta dubi kofar na dan wani lokaci, maida kanta tayi ta rufe idon ta dan yadda baccin ke fizgar ta, ba zata iya hakura ba.   Yamma ce wajen karfe hudu da rabi, a ka'ida ba'a son baccin na rana, sai dai ita ta rasa dalilin jin nasa yau sosai, shiyasa ma ta kora Farouk da Ja'afar wajen Dadah tayi kwanciyar ta. Nan da nan bacci ya dauke ta me karfin gaske. ***Yau ranar daban take da dukkan ranakun da yake zuwa ganin gida, yau yana jin shi cike da son kasancewa da ita, yadda yayi kewar ta ba kadan bace shiyasa ma bai sanar da kowa zuwan nasa ba. A matukar gajiye ya shigo gidan, ya kalle bangaren Dadah sai ya wuce kai tsaye zuwa nasu bangaren, ta sallama ciki ciki ya tura kofar, yana son bata mamaki, shiru ko ina baka jin motsin komai. Ajiye kayan hannun sa yayi kai tsaye ya nufi dakin baccin su, da karsashi ya tura kofar ba tare da tunanin komai ba. Runtse idon sa yayi ganin komai na dawo masa a ƙwaƙwalwar sa, hoton da ya riga ya zama permanent a cikin zuciyar sa ya shiga dawo masa, numfashi ya soma ja cikin fitar hayyaci jikin sa ya soma rawa, kokarin tashi yake daga wajen bayan ya saki diary din hannun sa ya kasa, sai ya koma yaraf ya zauna yana kokarin saita kansa yana bawa kansa k'warin guiwar tsayawa yabi komai. Mugun gani kamar yadda ya kamata ya kira wannan rana, Abidan sa da kaninsa, a dakin sa na sunna cikin yanayin da zuciya da ruhi ba zasu iya dauka ba, da wani irin tashin hankali ya hau dukan su a tare dukka su biyun, duka irin na wanda yake jin kamar za'a zare masa numfashi ya bar duniyar.   Kallon cikin ido Adam ke yi masa, kwatankwacin kallon tsanar da Daddyn ke masa, jifa yayi dashi ya bugu da bango kansa ya fashe, a take jini ya shiga malala a wajen babu alamun rai a jikin sa.     Daidai lokacin ta kwalla ƙara tana kokarin neman abun da zata kare jikin ta, nufo ta yayi bayan ta samu nasarar jan dogon Hijabi ta zura ya shak'e ta, kakare ta hau yi kamar zata mutu, da kyar ta bude baki cikin galabaita tace "Ka... Tsaya.. ka saurare ni, wallahi ba abinda kake tunani bane." Wurgi yayi da ita ta fada a saman drower ya shiga kokarin zare belt din jikin sa, daidai lokacin Dadah ta fado dakin a hargitse, abinda ta gani ya firgita ta, bata san sanda tayi kan shi tana kiran sunan sa ba "Kabir!!! Zaka yi kisa, innalillah wa inna ilaihi raji'un." Sakin belt din hannun sa yayi yana ja da baya ya fita daga dakin da sauri, rudewa Hajiya tayi ganin jinin dake fita akan Adam, da sauri ta yo waje tana kiran Kabir ɗin. Chak ya tsaya lokacin har ya kusa fita daga gida, a gaban sa ta tsaya tana kuka sosai "Dan Allah karka tafi, kar ya mutu ka taimaka wa uwar da bata san komai ba sai lafiyar d'an ta, dan Allah." Hannun ta ya kama, ya rike gam yana sauke ajiyar zuciya, sakin ta yayi ya koma ciki da sauri, yana zuwa ya daga shi ya fito dashi, ya saka shi a mota yaja ya fita daga gidan. ***Da rarrafe ta isa gaban ta muryar ta ta dashe saboda tsabar kuka, ta rike kafarta "Dadah dan Allah kiyi min rai, ban aikata ba wallahi bansan komai ba, bansan mai ya faru ba, nasan kin yarda dani, nasan zaki fahimce ni." Ga mamakin ta sai gani tayi ta janye kafarta, ta bar wajen da sauri ba tare da tace komai ba. Daki ta koma ta fada toilet ta sakar wa kanta ruwa, kuka take a cikin ruwan tana tunanin abinda ya faru, wannan wacce irin bakar rana ce? Waye zai saurare ta ya yarda da abinda zata ce? Tana nan zaune jigum har suka dawo daga asibitin, da sauri ta mike jikin ta na rawa ta yo wajen, tun kafin ta k'arasa ya dakatar da ita "Karki ƙaraso nan, na sake ki saki uku! Keji ban yafe miki cin amanar da kikayi min ba." "Yaya!" Aliyu ya fada da karfi yana shigowa ciki, da sauri Safiyya tayi wajen ta ganin yadda take layi kamar zata fadi "Babu ruwan ka Aliyu, ta chanchanci fiye da haka ma, dan dai hakan shine karshen hukuncin da zan mata, taje na barta da Allah!" "Amma Yaya da ka tsaya kaji uzurin ta, haba yaya, Anty Abidah ce karka manta kafi kowa sanin halin ta, ya ba zaka bata damar kare kanta ba?" A zafafe Dadah ta kalle shi "Kayi min shiru Aliyu, babu ruwan ka." "Dadah kema baki yarda dani ba? Baki san abinda zan iya aikatawa ba? Iya zaman da mukayi?" Ta tambaya tana kuka sosai, girgiza kanta tayi "Bani da sauran zama a inda ba'a san daraja ta ba, ba'a taba tsayawa a saurari uzurin ka balle kasa ran samun sauki, tir daku nayi dana sanin shigowa rayuwar ku, a yau ni Abidah na yanke dukkan wata alaƙa tsakani na daku, babu sauran komai tsakanin mu sai ta yarana guda biyu, dan yar uwata da Farouk, wanda su kuwa kamar dole na ne  duk da haka zan tafi na bar su tunda ba dasu nazo ba!" Tana kaiwa nan taja hannun Safiyya dake kuka sosai ta fita daga dakin fita ta har a abadah.! ***     *DG*                 28 **** Da sauri ya rufa musu baya yana kwala mata kira, bangaren ta suka nufa, tana zuwa ta haɗa dukkan abinda tasan mallakinta ne, Farouk ne da Ja'afar suka shiga kuka ganin yadda iyayen su biyu ke kukan, tsaye uncle Aliyu yayi a dokin kofar ransa na mugun suya, mai yasa sam yayan nasu baya tsaya wa yayi bincike ne? Komai sai ya yanke hukunci a cikin fushi da bacin rai bayan ba haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya koyar damu ba, lallai duk wanda zai biye wa zuciya yayin da ransa ya ɓaci zai iya aikata komai, ciki kuwa har da aikin da mutumin da ya fita daga hayyacin sa.    Gashi yanzu ya aikata abinda har ya bar duniya ba zai taba daina dana sani ba, saki uku, a lokaci daya? Saki da aka ce idan akayi shi al'arshi ce take girgiza. Anty Abidah bata chanchanci hakan daga gare su ba, matar data tsaya da dukkan karfin ta wajen ganin ta kyautata ma kowa. Zuwa tayi zata wuce ta gefen sa yayi saurin tare kofar yana jin kamar alamun kukan shima "Anty yanzu tafiya zakiyi? Dan Allah karki tafi." "Uncle Aliyu kenan, zamana ya kare a gidan nan, karka manta da babu igiyar auren yayan ka yanzu akaina. Alfarma daya zakayi min, ka taimaka min ka kular min da Farouk da Ja'afar, yayana ne dukkan su saboda haka amanar su na hannun ku ku biyu." Girgiza kansa yake ya rasa ina zai tsoma kansa, gaba yayi ya sake baya ganin yadda yaran ke kukan fitar hayyaci, hannu yaga ta bude musu suka tawo jikin ta gaba dayan su. Runtse idon ta tayi hawayen da take kokarin makalewa suka shiga saukowa. "Allah yayi muku albarka!" Sai ta janye su tayi hanyar barin gate din Safiyya na take mata baya. *** A zafafe ya fada falon, wurga idon sa ya shiga yi har ya sauke su akan Adam dake jingine da kujera kansa na kallon kasa. Da sauri ya isa gareshi ya ci kwalar rigar sa, idon sa daya rine yayi ja ya sauke masa aka cikin matsanancin fushi yace "Me yasa zakayi mata haka? Me yasa zaka manta alkhairin ta gareka musamman, baka san halacci ba?" Kwace wa yayi daga rikon daya yi masa, cikin fushin shima ya taso masa "Just stay out of this idan ba so kake kaima ka shiga lissafi ba." "Idan naki fa? Me zakayi?" Murmushi yayi ta gefen bakin sa ya juyar da kansa "Ka shiga taitayin ka, na wuce yadda kake tunani wallahi, zan iya yin komai." Dukan kirjin sa yayi ya tura shi baya, "Babu abinda ka isa kayi sai abinda Allah ya ƙaddara akaina." Yana kaiwa nan ya juya ya bar masa dakin. Bangaren Dadah yayi yana riƙe da hannun yaran, tana zaune ta rasa ina zata saka kanta, da sauri ta dago tana ganin shine ta mike "Aliyu, dan Allah karka ce zakayi bincike akan abinda ya faru yanzu akan yayar matar ka, karka ce zaka tsaurara bincike na roke ka." Durkusawa yayi a k'asa ya kaskantar da kansa yace "Ke mahaifiya tace, idan har kike bani umarni dole nabi ko da hakan zai zamar min matsala, wajibi ne nayi idan har bai sabawa Allah ba, sai dai a wannan karon zan nemi afuwar ki tun kafin àbinda zai kasance ya kasance, zan tsaya wa Anty Abidah na bi mata hakkin ta, ba zan hakura ba har sai sanda gaskiya tayi halin ta. Ki yafe min." Kuka ta saka ta shiga yi mishi magiya ya bar komai kar ya tsaiwata bincike, babu alamun zai saurare ta, tashi yayi da nufin barin dakin tayi saurin rike shi tana kuka sosai. Yana tsaye kyam a bakin kofar dakin ya harde hannun sa a saman kirjin sa, cikin isa da gadara yacw "Barshi, wanda bai ji bari ba, shine zaiji hoho." Juyowa Aliyu yayi a fusace ya bar dakin da sauri, kukan yaran dana Dadah ya hautsina dakin, be bi ta kansu ba ya wuce uwar dakin ta, yar jaririyar sa na kwance tana jujjuya kafarta da alamun ta jima da tashi har tayi kuka ta gaji, yau ne karo na farko daya mata kallon tsaf tun ranar da aka kawo ta gidan, babu maraba tsakanin ta dashi sai ta banbancin jinsi. Shafa kanta yayi makogaron sa na kaiwa da komowa yace "I ll come back for you one day!" *** Tsawon sati kenan Daddy na rufe a bangaren sa, baya zuwa ko ina ko sallah ma a daki yake yin ta, sosai abin ya taba shi, yana ganin kiran Alhaji Marwan amma sam yaki dagawa, duk sanda ya runtse idon sa su yake gani, sun cutar da zuciyar sa, sun dasa masa wani babban al'amari da zai ta bibiyar tunanin sa.   Tsawon satin nan babu wanda ya leko tsakanin Aliyu da Adam, yaran uku dake gaban ta su kadai take kalla taji hankalin ta ya tashi, bata taɓa fatan ko tunanin abinda zai zo ya wargatsa musu kwanciyar hankali ba cikin d'an kankanin lokaci, gaba daya gidan ya fita daga kanta bata fatan cigaba da zama cikin sa, zaman da zai cigaba da yi mata famin abinda ya faru. Sai da Alhaji Marwan yayi da gasken gaske sannan ya samu Daddy ya fito, yayi muguwar rama da baki, fada yayi ta masa amma bai sanar dashi abinda ya faru ba, labarin yafi gaban a bada shi ba, duk kuwa da yadda suke da karfin abota amma ba zai iya ba.    Tubure musu Dadah tayi akan lallai sai ta bar gidan, ba kuma Katsina zata koma ba, bata son duk wani abu da zai tuna mata komai, ganin ba zata amince da kokarin kwantar mata da hankalin da suke kokarin yi ba yasa suka yanke shawarar sama mata gida a Kano, wannan shine asalin komawar Dadah Kano tare da Farouk, Amal da Ja'afar. *** Daddy na rurrufe ko ina na gidan dan komawa aiki Adam ya shigo, har lokacin kansa rufe yake da bandage, dauke kai Daddy yayi kamar bai ganshi ba, ya wurga masa keys din bangaren sa "Ka duba komai naka ka kwashe ka bar min gida." Dage kafadar sa yayi ya tsuguna ya dau keys din, bud'e dakin yayi ya dauke abinda zai dauka ya fito,kamar yadda ya wurga masa keys din shima hakan yayi, ya gefe shi dashi cikin keta yace "Sai watarana!" A kusan tare suka bar gidan, sai da Daddy ya fara biya wa ta Kano ya duba Dadah, kafin ya wuce wajen aikin daya dauki lokaci mai matukar tsawo kafin ya sake waiwayar gida.    Samun babban matsayin da yayi shi ya rage masa nauyin abubuwan da yake, ya tattara hankalin sa waje daya yayo gida, Dadah na ganin shi tasa masa kuka, kukan dake nuna tsantsar halin da take ciki, sai a sannan take sanar mishi ta mutuwar Adam din, hatsarin mota ne ya rutsa dashi daga Lagos zuwa Kano ko gawar sa ba'a kawo ba.   Babban tashin hankalin ta bai wuce daina ji daga Aliyu da Safiyya ba, tun bayan rasuwar, taje gidan yafi a kirga amma magana daya take samu daga makotansu shine sun yi tafiya. Takanas Daddy yaje da kansa har wajen aikin Aliyun, sai a sannan ne ma yake jin labarin ai ya bar aiki tun da jimawa, abun ya matukar daure masa kai, haka ya dawo a sanyaye gida ya sanar wa Dadah, wadda hakan ba karamin sake gigitata yayi ba,tun daga nan basu sake k'ara ji daga gare su ba, a hankali suka manta, kamar an cire musu su da abinda ya shafe su daga ƙwaƙwalwar su, babu wani daga cikin su daya sake yin maganar sa har kawo yanzu! **** Sake shiri yayi, ya fito a cikakken mutum mai cikar zati da haiba, sai dai yanayin fuskar sa kadai zata tabbatar maka da ba daidai yake jin jikin sa ba, bayan mota ya fada ya d'an kishingida kadan yana lumshe idon shi, tabbas yana bukatar ji daga gareta, yana so yaji komai daga bakin ta ko da kuwa ba zata saurare shi ba zai gwada sa'ar sa. Su biyu ne kaɗai daga shi sai driver sa, yau baya jin zai iya yin wannan tafiyar da masu kula dashi, bayan haka ma baya bukatar hayaniya yana so yaje mata a Kabir ɗin sa, Kabir ɗin data sani shekarun baya ba na yanzu ba.. "Ina zamu je ranka ya dade?" "Kaduna." Ya amsa mishi a gajarce yana sake mikewa sosai. *** Duk nauyin dake cunkushe a zuciyar sa yau yayi sauki har yana jin bukatar fara aiwatar da abinda ya kawo shi. Shigar manyan kaya yayi kamar ba a k'asar masu jajayen kunne ba, ya dora hula ya fito a cikakken bahaushe bakar fata, kai tsaye inda sukayi zasu hadu ya nufa da taimakon address din daya bashi. Daga d'an nesa ya hango shi, tabbas shine mutumin nan na ranar nan, ya akayi suka sake haduwa? Daga kafar shi yayi cikin sauri ya nufe shi, daf da zai isa gareshi yaga ya bude wata mota dake ajiye wajen ya shiga, bai iya ganin fuskar sa sosai ba sai rabi kamar wanchan lokacin, kamar an dasa shi a wajen haka ya tsaya yana kallon motar har ta bar wajen, jan ƙafarsa yayi zuwa shagon yana kokarin ganin ya yakice shi daga zuciyar sa, ya rasa dalilin ma da yasa yake jin wani abu game da mutumin. Ganin zai bata wa kansa lokaci yasa yayi saurin shigewa ciki yana duba agogon hannun sa, yasan baturen mutam da ka'ida, baya so ka saba masa alkawari. Tambaya yayi aka nuna masa inda zai same shi. Cikin aiki ya tarar dashi kacha-kacha, yana ganin shi yayi dariya, yana tura masa takardun gaban sa, da mamaki Farouk ya kalle shi amma kafin yayi magana ya riga shi "No time to waste." Gid'a kansa yayi a hankali ya furta "Nima bani da lokacin batawar ai, I'm here for it" Aikin ya shiga nuna masa,da yadda yake so komai ya kasance, babu wani bata lokaci ya fuskanci abubuwa da yawa sai dan abin da baza'a rasa ba wanda sai a hankali dama. Ranar a gajiye likis ya koma gida cike da farin cikin fara aikin da yayi da shugaban shagon wanda dalilin social media suka hadu tun da dadewa, sai gashi yayi masa rana a lokacin da bai taba tunani ba. Wanka kawai ya iya yi yasha tea ya kwanta dan sosai yake jin bacci, yana kwanciya kuwa baccin ya dauke shi wanda rabon da yayi irin sa ba zai iya tunawa ba. Gashi dama duk sanda yayi yunkurin baccin sai tunanin ta ya shigo masa, daga nan sai yaji sam baccin ya fita daga kansa, daga nan sai ya dasa sabon tunani har zuwa sanda baccin zai dauke shi ta karfin gaske ba tare da ya shirya ba. *** *AMINATU* Na cigaba da zuwa makaranta da taimakon Allah dana Baba Altine data zama wata babbar bangare na sabuwar rayuwa ta. Bani da matsalar komai gefe ga Kamal daya zama abokin shawara ta. Ban yi watsi da duk abinda Anas ya ce min ba ina matukar kokari wajen ganin na kare mutunci na. Lokuta da dama nakan tuna Baba, Inna da Karime, Yalwati da sauran mutanen da suka fi kowa kusanci dani a da amma babu ko daya cikin su yanzu a rayuwa ta, hakan ba karamin sani yake na kara tuna wacece ni ba, mara asali da tushe abar kyama ga kowa. *DG*              *29* ★★★★ Dukkan abubuwan bukatuwa na makaranta ta Kamal ya dauke min shi, tun ina fada har na kyale shi na zuba masa ido, ranar ina tsaka da duba wani handout ya iske ni wajen da muka saba haduwa, a dan gefe ya zauna yana leken cikin handout din "Kaga yan allazi boko." Yace yana dariya, harara na sakar masa ina janye handout din. "Wai dan Allah yaushe zaki kawo min Iman ne, I'm dying to see her kinsan abinki da hanta da jini, daga zuwa sau daya shikenan nasan ma ta kara wayo." "Sai dai ka shirya kaje da kanka, ni bazan iya dauko ta makaranta ba,dame zanji?" "Toh ai ni hakan ma zaifi min farin ciki, yaushe zaki gama da school?" "Lecture daya ya rage, nan da 30min zamu shiga." "Shikenan ki kirani idan kin gama." Yace yana mik'ewa, waya ta dake cikin jakata tayi k'ara, tsayawa yayi ya harde hannu yana jiran yaga mai kiran. Ina ciro ta naga ya kwashe da dariya "Yanzu zata nutsu kamar wani maka'ika." Yace yana bata fuska, ban bi ta kan shi ba na kara wayar a kunne na gami da sallama. A nutse na shiga amsa masa har ya ajiye wayar, ajiyar zuciya na sauke ina duban KAMAL da shi ma nidin yake kallo "Ya Anas ne fa." "Na sani, ai naga sunan, ki rage tsoro kamar zai yanka ki idan ya kira." "Kai ka sani, aka ce ma tsoron sa nake? Kawai ina respecting d'insa ne." "Daga baya kenan, ki cigaba da nuna masa tsoro, idan kika aure shi kisha wuya yarinya." Da sauri na ware ido ina murmushi "Yanzu Kamal har kasan wani aure? Inyeee." Dariyar shima yasa yana yin gaba abin sa, sai daya dan d'ara wajen kafin ya ce "Kinci sa'a ke sirikace zaki bani Iman amma da kinji magana gabza gabza wallahi." Murmushi kawai nayi ban kuma ce masa uffan ba na hau tattare kayan karatu na ganin lokacin shiga ajin ma ya kusa. A gaban Hall d'in na tarar dashi tsaye yana jira na, ni har na manta ma munyi maganar zamu tafi tare, babu yadda na iya haka na bishi muka dau hanya, sai dai kamar yadda ya san gidan a dah yau sai yaga mun chanja akalar tafiyar tamu, kallo na yayi yace "Kun chanja gida ne?" "Eh." Na amsa mishi a takaice, muna zuwa na shiga na sanar wa Baba Altine zai shigo, cikin daki ta koma na rik'e hannun Iman muka fito, da mamaki yake kallon mu, sai kuma ya ƙaraso ya daga ta sama yana dariya sosai "Baki da kirki Meena, haka matar tawa ta girma amma baki fada min ba?" "Shigo ciki dai sarkin zance, sai muyi maganar." Cikin muka koma, ya zauna a kan dardumar dana shinfida masa, ruwa na dauko masa na ajiye sannan na shiga daki na ajiye jakata na sake fitowa, yana zaune yana wa Iman wasa ita kuma tana ta dariya kamar ta sanshi, Kitchen na wuce na duba, shinkafa da wake Baba tayi, sai salak da tumatir dake yanke an tsaftace shi a cikin mazubi, hadowa nayi na jera komai na kawo masa ina zama. "Ga abincin gidan talakawa sai kasa albarka." "Kinci bashi wallahi." Murmushi kawai nayi, a gefen sa ya ajiye Iman ya bude flask din, ya dauki plate ya zuba abincin sosai ya shiga ci muna hira, sosai yaci dan banyi tunanin zai ci haka ba, ganin yadda yake d'an gayu sai na dauka a komai ma hakan ne, shiyasa Bature yace never judge a book by it's cover, tabbas haka ne, kar kayi saurin yanke wa mutum hukunci ba tare da sanin ainihin waye shi din ba.    Kiran wayar sa akayi, da murna ya daga yana sawa a handfree "Old Woman kinyi missing d'ina ne hala shisa kika biyo baya." "Sosai kuwa, sati nawa rabon dana saka ido na? Kana cewa baka son Kano sai gashi kayi luf har kana mancewa dani, ko kayi sabuwar mata ne?" Dariya ya tuntsire da yace "Aikuwa dai kin iya saurin gano abu, yanzu ma kin ganni wajen ta, nazo mamanta ta cika min ciki da Rice and beans me shegen dadi." "Da gaske kake yaron kirki?" "In bata ku gaisa ne?" "Eh bata naji." A kunne ya kara wa Iman wayar yana kunshe dariyar sa "Oya say hi to my boring Grandma kinji baby." Gwaranci ta soma yi, kamar yadda ta saba duk sanda Anas ya kira a bata wayar, dariya muka hau yi gaba dayan mu har granny din dake kan waya, "Ja'iri zaka zo har inda nake ka same ni." Tace tana katse wayar, tallafe fuskata nayi da hannu biyu ina kallon sa "Baka da dama kamal, Allah shirye ka." "Amin, naji, itama da gulmar tsiya ai maganin ta." Mik'ewa yayi ya mana sallama ya tafi, bayan tafiyar sa ina kokarin tattare komai na abincin ya shigo, bakin sa dauke da sallama, ido na cikin nasa nayi saurin yin kasa ina jin faduwar gaba, bai sanar dani zuwan sa ba dazu da mukayi waya, da gudu Iman ta rungume shi tana masa oyoyo, daga ta yayi ya manna ta a jikinshi har lokacin idanun sa na kaina yana yawo dasu. "Sannu da zuwa." Nace ina cigaba da tattare kayan, da hannu ya amsa min yana nazarin wajen zaman da kayan da nake kwashewa, sallayar na gyara masa ya zauna yana tankwashe kafar sa. "Bako kikayi ne?" Yace yana karanta ta, ban amsa na gaishe shi, a gajarce ya amsa daidai lokacin Baba Altine ta fito tana masa sannu da zuwa, da fara'a ya amsa mata ba kamar yadda yayi min ba, ta zauna tana tambayar su Hajiya, tashi nayi na kawo masa ruwa da ragowar abincin na wuce daki, ina jin sa ya jeho ma Baba Altine tambayar da yayi min ɗin, maimakon tace masa eh sai naji tace "Wata kawarta ce tazo bata jima da tafiya ba ma, ko kun hadu a hanya?" "No shikenan." Girgiza kai na nayi ina mamakin halin shi, kayan na sauya na fito na koma kitchen din na dora indomie dan ba karamar yunwa nake ji ba, zama na nayi a Kitchen din ba tare da na koma Falon ba, ina jiyo hirar su ya ware sosai yana wasa da Iman, wannan na daya daga cikin dalilan daya saka nake sake bashi girma, da gasken gaske yake kula damu kamar wanda muka zama masa dolen sa.    Zama na nayi bayan na gama dafa indomie na ci a Kitchen din na zuba ma Iman da Baba Altine tasu a dan flask na fitar da kwanukan na daureye sannan na koma ciki. "Mu baza'a bamu indomie ɗin ba ne?" "Za'a baku." Nace ina kokarin komawa kitchen din "Barshi sai da muka roka, dauko hijabin ki rakani unguwa." "Baba dauko nake kema kar mu barki ke kadai a gida." "A ah wallahi, shikenan kuma sai na biku godai godai dani, Aallah kiyaye sai kun dawo." Murmushi yayi kawai ya rike hannun Iman sukayi waje, ciki na koma na zura hijabin na fito. A jingine jikin motar na tarar dashi, yana gani na ya bud'e min bangaren mai zaman banza, shiga nayi sannan ya miko min Iman ya rufe mana kofar, zagaya wa yayi yaja muka tafi.    Zagaye ya dinga yi damu daga wannan titin zuwa wannan har zuwa lokacin magriba, tsayawa yayi a wani masallaci yayi Sallah sannan ya kaimu wani wajen cin abinci, nidai duk a takure nake haka yayi mana takeaway muka fito, shopping mall din dake manne da wajen abincin ya shiga, ya ɗan dade a ciki sannan ya dawo hannun sa dauke da manyan ledoji ya zuba a baya muka dau hanya.    Muna zuwa gida ya tsaya jikin motar yana nuna min kayan ciki "Kwashe kayan ki shiga dasu kizo muyi magana, dare ya fara yi." Kwashe wa nayi na dawo, na karbi Iman data fara bacci na kaita itama na sake dawowa na tsaya. "Ya karatun?" Ya tambaye ni "Alhamdulillah, yasu Hajiya? Kwana biyu bamuyi waya da Raudah ba nasan suna shirye shiryen finals." "Lafiya lou." "Ya maganar mu?" "Na'am?" "Kinji ai, ina so mu fara fuskantar juna, idan yaso sai nayi kokarin shawo kan Hajiya." Girgiza kai na nayi a nutse nace "Maganar iyaye magana ce mai matukar girma, kayi hakuri mu yi abinda tace, bana so ka sami matsala da mahaifiyar ka." "Zaki jirani zuwa lokacin da zata amince? Zaki jirani?" "Bani da zabi da rayuwa ta sai abinda Allah ya zaba min, idan kai din Alkhairi ne gare ni, nima kuma alkhairi ce a gareka, Allah ya sa ta amince, idan har ta amince ni bani da zabi." "Shikenan, in sha Allah zata amince, ki bani lokaci." Daga masa kai nayi, ya sakar min murmushi ya fada motar yana daga min hannu, sai dana ga fitar sa daga layin sannan na shige ciki ina saka key a kofar. Da daddare nayi ta juyi ina tunanin maganganun, bani da zabi face amince masa, wacece ni ma da har zai tsaya bata lokacin sa akai na, bani da asali bare tushe, bayan haka wannan ce hanya kawai mafi sauki da zan saka masa da dukkan alkhairin sa.     Sake juyawa nayi zuwa dayan barin ina tuna Farouk, mutum na farko daya so ni duk da karancin shekaru na, ban taba tunanin shi ma zai guje ni ba, haka dama rayuwa take shiyasa na bar wa Allah zabin komai na rayuwa ta, sau tari tunanin sa kan hanani sukuni har naji zuciya ta na zafi, tun ina sa ran haduwa dashi har na hakura na barwa Allah.   Ban cire rai ba amma, kila watarana ya waiwaye mu, ko ba dan ni ba, ko dan yarinyar sa, duk da yace babu komai tsakanin mu, amma ina fatan ganin da zai mata kadai ya isa ya gamsar dashi yar sa ce,shafa kanta nayi ganin yadda yake bacci cike da kwanciyar hankali, bata da damuwa ko matsala, tsoro na daya ranar da zata tambaye ni mahaifin ta, duk da ina fatan kafin ranar na samo gamsasshiyar amsar da zan bata. *** Shirin fita take taji ana mata knocking, ajiye abinda take tayi ta nufi kofar kai tsaye tana tunanin waye, turus tayi ganin shi, tayi saurin ja baya tana kokarin maida kofar "Karki rufe min kofa." Wani kallo tayi masa kafin tayi dariya "A matsayin ka nawa?" "A matsayi na na wanda kike jira tsawon shekaru." "Jira?" Tayi dariyar rainin hankali "Karka manta babu auren tsakanin mu." "Kema karki manta nasan kinyi auren kin fito, kin zata bani da labari?" Juyawa tayi kawai ciki ya bi bayan ta yana murmushi, falon yabi da ido, yadda aka kawata shi da kayan kawa da komai, sanyin Ac hade da kamshin turaren ta tun na fil'azal ne manne a falon, iska ya shaka ya fesar yana zama cikin jerin manya manyan kujerun da suka kara wa falon kawa. Ciki tayi ta barshi zaune, sai data dau tsawon lokaci sannan ta dawo ta sauya shigar ta zuwa simple gown ta rufe kanta, zama tayi chan nesa dashi tana kallon screen din wayar ta. "Me kake bukata?" Ta tambaya kai tsaye kuma a gajarce "Nazo ne nayi miki wasu yan tambayoyi, nasan tabbas kinsan amsar su." "Then..." Ta kalle shi cikin ido sosai "Kin shayar da Amal?" Yayi mata tambayar kai tsayen, kai tsayen itama ta amsa masa "Eh akwai wani abu ne?" "Akwai, kinsan auren Farouk dake kanta ko? Kuma kinsan musulunci ya hana auren wanda suka sha nono daya, amma ban manta ba tun a lokacin dana ga take taken ki na hana, saboda irin wannan ranar." "Na shayar da ita tun kafin kayi min magana, haka zalika na bari daga lokacin da ka hana." "Mesa baki fada min ba?" "Me yasa baka fada min da zaka hada auren ba? What is my fault anan? Wait saboda nice karkatacciyar kuka mai dadin hawa ko? Shine bayan komai ya kwabe muku zaka zo wajena." "Why are you like this? Kin chanja sosai." Dariya ta shiga yi sosai kafin tace "Mutane na chanjawa ne daga lokacin da wanda suke tare dasu suka chanja, baka ga komai ba indai nice." Mik'ewa tayi tana duban agogo "Ina da abin yi, can you please excuse me?" "I'm not done yet, ina son sanin ina d'ana?" "Shine tambayar da ya kamata nayi maka tun zuwan ka, ka sani ba wai nayi shiru bane, ina baka time ne kayi gaggawar fito min dashi duk inda kasa shi ya tafi." Ransa ne ya ɓaci, ya tashi tsayen shima zai maida mata martani wayar ta dake gefen sa tayi kara, kura wa wayar ido yayi da kuma sunan dake rubuce akan screen din kamar mai nazari, da sauri ta sa hannu ta dauke wayar tana sakata a silent. Shiru ne ya biyo baya ya kasa tantance abinda yake ji game da sunan da ya gani. Ganin ya kasa tunawa yasa ya share yana kokarin tausar zuciyar sa, sai daya dan ja lokaci yana tunanin yadda zai yi maganar kafin ya daure kamar an fuzgo maganar yace "Abinda ya faru shekarun baya, menene gaskiya? Menene tsakanin ki dashi? Me ya faru a ranar?" Dagowa tayi a dan zabure, sai kuma tayi saurin saita kanta tana sakin murmushi "Duk abinda zuciyar ka ta tsara maka, shine abinda ya faru,kuma ya riga ya wuce babu amfanin dawo dashi baya, bani da lokacin wannan maganar." Tana kaiwa nan tayi shigewar ta daki tana rufo kofar da sauri, kamar wanda aka dasa haka ya kame a wajen yana ayyana abun a ransa, yanayin ta da yadda ya hangi tsantsar tsoro a idanun ta bayan ya kawo mata maganar ta sashi shakku, ko dai ya aikata abu cikin fushi? Ya biye wa dokin zuciya? Yayi mata adalci kuwa a lokacin? Me yasa yanzu yake jin son jin gaskiya duk da tsawon lokacin da aka dauka? Bashi da amsar tambayoyin. Da kyar ya kai kansa mota yana shiga yace "Kano zamu je." **** Basu suka isa Kanon ba sai dare, Dadah na zaune saman abin sallah tana karatun Alkur'ani, ya shigo, da kallon mamaki ta bishi har ya dire a gabanta yana jin kamar ana sassara masa kasusuwan jikin sa. Da kyar ya bude baki ya amsa sannu da zuwan da take masa, shiru ne ya biyo baya sai kuma ya tuna yana bukatar suyi magana "Dadah kinsan Abidah ta shayar da Amal kuwa?" Kai tsaye tace "Na sani, amma ina ga ai ta daina tun lokacin daka hanata." Dafe kansa yayi da dukkan hannayen sa "Ya akayi duk ban san da haka ba? Kinsan musulunci ya hana aure tsakanin wanda aka shayar dasu nono daya, duk da malamai sunyi sabani, wasu sunce idan har an shayar da nonon sau uku, toh ta haramta ga duk wasu da suke muharraman wadda ta shayar da ita din, wasu suka ce ko sau daya ne idan har an bata tasha ta koshi, toh an haramta auren tsakanin ya'yan matar data shayar da ita, ko kannenta da suke uwa daya, ko uba daya, ko uwa daya uba daya, ko yayyenta da suke uwa daya, ko uba daya, ko uwa daya uba daya,ko mahaifinta. Duk dai wasu muharraman da babu aure tsakanin su da ya'yan matar data shayar da ita, toh sun haramta ga wannan wadda aka shayar ɗin. Wasu malaman suna ganin sai idan har ta shayar da ita na tsawon lokaci ne hakan zai kasance, toh amma dai ko yaya ne, nasan tabbas ta shayar da ita, na tsawon wata guda koma fiye, kinga kenan ta haramta ga Farouk." "Allahu Akbar, ilimi fadi ne dashi, ban taba sani ko ji ba wallahi, shiyasa ban kawo komai a kaina ba, bayan haka ko da ace na sani,bana ma tunawa da ta shayar da ita din." Ajiyar zuciya ya sauke yana jingina kansa da saman kujerar, komai ya chanja masa daga yan da yaso ya kuma tsara. *** Da baya da baya ta koma ta fada saman gadon ta tana sakin kuka, idan har abinda taji Daddy na fad'a gaskia ne, kenan ita da Ya Farouk shikenan? Kai ina bazai yiwu ba, yadda ta kwallafa ran nan dashi, ace kuma shikenan? Sai ta kara sautin kukan ta sosai. Da ido tabi wayar da kallo kafin ta shiga share hawayen fuskarta da sauri da sauri, dagawa tayi ta shige toilet bayan ta sawa kofar dakin key. Tsawon lokaci ta dauka suna magana kafin ta ajiye wayar ta fito, lamo ta kwanta tana tunanin mafita. ***Babu wanda yayi mata maganar daga Dadah har Daddy. Taso tayi ma Dadah maganar taji me zatace amma bata so ta tabbatar mata da gaskiyar hakan, duk abin duniya yabi ya dame ta, gashi ana maganar komawar ta makaranta saboda lokaci na kara tafiya, kamar marainiya haka ta zama, duk farin ciki da take dah idan ta tuno da auren dake kanta yanzu ya kau, tunanin ta yadda za'a samu mafita ace akwai aure tsakaninsu kawai take, idan haka ne Mummy ta cuce ta wallahi. Bata da aiki sai kuka, ranar da sukayi waya da Mama ta fada mata abinda ya faru, kwantar mata da hankali tayi, ta dan ji dama dama kuwa, har ta dan saki ranta. **** Tun ranar da ta fada mishi abinda ya faru be sake kiran ta ba, ya dai tabbatar mata da yana nan zai san yadda za'a yi. Sati guda ya dire a kasar, ya wuce kai tsaye Abuja, Daddy na zaune wajen daya saba shan iska ya shigo gidan. "Saukar yaushe?" Daddy yace yana fadada fara'ar sa, zama yayi kan katon carpet din yana mika masa hannu "Mun same ku lafiya?" "Lafiya lou mutanen Turai, Azeema kuwa tasan da zuwan ka?" "Ina bata sani ba ai, zuwan nawa kenan." "Lallai sannu da zuwa, ka shiga ciki toh nima yanzu zan shigo ai." "Ok." Yace kai tsaye ya shiga ciki, tana ganin sa ta rufe baki da hannun ta. "Ya akayi haka?" Tace tana zaro ido "Zuwan dole ne, akwai abinda zan duba ne ba jimawa zan koma." Ajiyar zuciya ta sauke "Na zata ai ko lokacin da muke jira ne yazo." "Saura kiris." Yace yana nuna mata hannun sa, dariya ta saka. Shigowar Daddy yasa su yin shiru, zama yayi suka sake sabuwar gaisuwa,kafin a gabatar masa da abubuwa ci da sha, kadan yaci ya yi musu sallama ya tafi. Yana fita ya tsura wa gidajen guda biyu ido kafin ya fashe da da dariya, motar sa ya shiga wadda ta kasance a rufe ruf da bakin glass, da karfi yasa hannu ya zare mask din fuskar sa, a razane na saki alkalami na ina sake duban sa da kyau "Adam!!!" Na furta baki na na rawa. Murmushin gefen baki ya saki kafin ya maida fuskar ta zama ta wani mutum daban ya ja motar ya bar kofar gidan da mugun gudu. Ranoa:                       *DG*                        *30* Kai tsaye garin na Kano ya wuce, yana isa ya mata text kafin ya karasa wajen da zasu haɗu. Tana zaune tana jira sakon ya risketa, dama a shirye take saboda haka mayafi kawai tasa ta fita. Kafin tazo ya cire mask din fuskar sa ya fito a ainihin kamar sa. Tana zuwa tayi saurin fad'awa jikin sa ta saka mishi kuka, shafa bayan ta ya shiga yi a hankali har ta tsagaita da kukan nata, tissue ya ciro ya mika mata "Menene matsalar ki?" Ya tambaya yana dago ta, "Ya Farouk." Tace cikin muryar kuka. Murmushi yayi mata yana jingina ta jikin kujerar motar "Karki damu, ki koma karatun ki, zan san yadda zanyi." "Yaushe? Daddy fa ya gama sanin komai, kuma ya fada wa Dadah." "Akwai lokaci, akwai lokaci." Yace yana tada motar. Shiru tayi tana tuna abubuwan da ya jima yana fada mata, haushin kowa take ji, babu wanda zatayi wa uzuri a cikin su, duk kuwa da sun yi mata sosai a rayuwa amma ba kamar mahaifin daya kawo ta duniya ba. Idan bata tsaya masa ba bayan kowa ya juya masa baya wa zai taimaka masa? Ita kenan daya mallaka a duniya dolen tane ta share masa hawayen sa. ***Tsawon makwanni biyu ya dauka a garin kafin ya tattara ya koma inda ya fito, itama Amal sai ta koma can Abuja don karatun ta ta cigaba da rayuwar ta kamar babu komai. Duk da lokaci zuwa lokaci sukan yi waya amma babu wanda ya san da hakan sai Mama kawai, shiyasa ma bata da matsalar komai dan kanta tsaye take abubuwan ta tun da sau tari ma a wayar Maman zai kira bayan sun gama magana sai ta bata. Alaka ce mai karfi tsakanin su, sai dai ta gaza gane wacce irin alaka ce hakan da har tasan sirrin sa. *** Dukkan kokarin Daddy na son ganin ya samu wani bayani ta wajen Mummy sam ta ki bashi fuska, rashin sanin yadda zai ɓullo mata ne da yadda yake mata gadara yasa ta kafe itama, zuciyar ta, ta riga ta k'ek'ashe shiyasa bata wani jin shakku ko wani abu game da hakan. Tun yana tunanin jan aji ne irin na mata har ya gane da gaske take ba zata saurare shi ba, duk baya jin dadin komai, tun bayan rabuwar su da auren da yayi bayan lokacin da kadan bai taba jin wani abu game da ita ba sai yanzu da girma yazo. Duk da Mama na kokari sosai wajen kula dashi amma ya kasa yakice ta daga ransa. Mai yasa ya kasa mata uzuri a wancan lokacin? Ya kasa gane dalilin sa na yin hakan, gashi yanzu ya fada kogin nadama da dana sani mara amfani. **** *Farouk* Aiki yake sosai babu kama hannun yaro, sosai yake jin dadin aiki da Mr Johnson shiyasa bashi da wata matsala da kasar. Zuwa lokacin da ya fara karatun sa ya riga ya tara kudade masu yawan gaske, duk da haka duk weekend yana zuwa ya zauna a wajen hakan kuwa ba karamin dad'i yake ma Mr John ba dan shi a rayuwa yana son mutum mai kwazon aiki. Da gangan Farouk ya zamar da kansa agogo baya bada lokacin sa a komai sai neman halal dan yayi wa kansa alkawarin ko zai koma gida ba zai taba bari ya rabi da kowa ba balle har ayi masa wata alfarma. Batun mutumin nan kuwa, tun ranar bai sake haduwa dashi ba, sai ya tattara shi ya watsar ya rungumi sana'ar sa da karatun sa. ***A gurguje ya sauko kasan shagon tun bayan daya samu sakon supervisor din sa akan yana son ganin sa, dole ya tattare aikin da yake waje daya ya nufi makarantar. A daidai gate din shiga ya hange shi, da motar sa ya fara gane shi, sai dai yau ba shi kadai bane hadda mace da yara, da sauri ya tsallaka bangaren su yana tsaida su, kamar ba zai tsaya ba sai kuma yaga yaja ya tsaya dage gefe, karasawa yayi cikin sassarfa yana kokarin ganin fuskar sa. "Assalamu alaikum." Yayi sallama kai tsaye, a tare suka amsa dukkan su, kafin namijin ya juyo da dukkan fuskar sa yana duban shi, duba na tsanaki. A wani irin yanayi suka hada baki a tare kamar wanda maganar tazo wa a lokaci daya cikin yanayin dake kama da an fuzgota suka ce "Farouk!" Ware idanun sa yayi, duk da karancin shekarun sa ba zai taba mantawa dasu ba, mutane biyu masu kusanci dashi, daya kani ne ga mahaifin sa, daya kuwa kanwa ce ga mahaifiyar sa. Mai suke anan? Me yasa babu wanda yake tunawa dasu? Babu wanda yake maganar su. Bayan har da d'an da suka tafi suka bari. Ja'afar! Mai yasa suka manta da kowa suka zo nan suka kafa sabuwar rayuwa. Bashi da amsar ko daya daga cikin wadannan tambayoyin, shaf ya manta da abinda ya kawo shi makarantar, da sauri ya fada motar yana kallon yaran guda uku dake zaune a bayan motar suma suna kallon sa. Sautin kukan Anty Safiyya ne ya sake dagula masa lissafi, kuka take sosai sai dai babu wanda yace uffan har suka isa gida. Daga kai yayi yana karewa gidan kallo, tsawon wannan shekarun suna rayuwar su su kadai ba tare da dangi ba. Mai yasa? ★★★★ Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Ubangiji, idan baku manta kuduri na ba, ba zai wuce na cikar buri na ba, karatu na nasa a gaba babu wani abu daya sauya na daga yadda rayuwar tawa take   Yadda komai yake wanzuwa cikin hukuncin Allah, zaka tabbatar da babu mai tsara bawa ƙaddarar sa face Allah SWA. Hakan ce ta kasance dani, a yau na rubuta jarabawar karshe ta makarantar horar da lauyoyi dake garin bagauda (law school). Idan na tuna matsayin karatun da nayi a daya daga cikin manyan jami'oin Nijeriya (BUK), na kan ji wani nishadi mara misaltuwa, ban taba hasashen hakan ba, sai gashi Allah ya hukunta min cikin manyan kaddarorin rayuwa ta. Anas ya zama wani babban jigo a karatu da rayuwa ta, sannan Kamal daya zama mafi kusanci dani da yarinyata Tun ina tunani ko hasashen zan hadu da wani daga cikin ahalin su Farouk har na daina sai dai har lokacin yana makale a kahon zuciya ta. Duk sanda na kalli Iman na kan tuna dashi da komai nashi. **Sanda sakamakon jarabawar ya fito sai dana yi kuka, kukan farin ciki saboda yadda result din yayi kyau ainun, wai yau nice rike da shaidar zama cikakkiyar lawyer, Anas yaso yafi ni farin ciki saboda a daidai lokacin ne Hajiya ta amince masa da aure na, duk da abin yazo min a wani irin yanayi amma nayi kokarin boyewa na biye masa wajen nuna farin ciki na, y'an kwarya kwaryar walima ya shirya min daga ni sai shi sai Iman, Baba Altine da Ramlah sai kawayen ta biyu, ban gayyaci kowa ba a yan makarantar mu, duk dama babu wata shakuwa tsakanin mu sai abinda ya shafi karatu. Kamal tun daya koma ban sake saka shi ido na ba sai dai muna waya sosai dashi. Komai ya sake chanjawa bayan gama karatu na, kai tsaye Anas yake zuwa a matsayin zance. Mutum ne shi da yake bin komai a tsare, dan haka bai taba ketare iyakar sa ba, komai yanayin sa ne a addinance babu jahilci. Hakan na kara birgeni dashi, yadda yake tafiyar da rayuwar sa cikin tsari abin so ne. **** *Waye Shi!* Hannu na sakale dana Iman muke zagaye supermarket din, Alk'awari nayi mata idan har ta iya wasu surori zan kai ta, ta zabi abinda take so, da kanta ta fada wa Anas aikuwa sai ga kudi ya aiko mana dashi. Doguwar riga ce bud'addiya a jikina, na yane kaina da madaidaicin mayafi, takalmin kafata irin flat shoe ne, babu yadda za'a yi daga kallo daya ka gane wacece ni ko daga ina na fito, jikina ya murje sosai na zama cikakkiyar mace ta kowanne fanni. Bamu da matsalar komai saboda Anas ya tsaya mana. Mun bata lokaci sosai kafin mu gama saboda yadda Iman ta tsaya ruwan ido,sai dana gaji nace tafiya zanyi sannan ta hakura, napep muka tara muka nufi gida lokacin duhu ya fara sauka. Muna cikin tafiya wayata tayi kara, ciro ta nayi ganin Kamal ne yasa na daga. Magana muke wanda ta dauke hankali na har muka kusa wuce inda zamu sauka, da sauri na tsaida me napep din muka sauko na mika masa kudin har lokacin wayar na makale da kunne na. Kasancewar har anyi magriba tasa layin babu kowa, da hannu daya na rike wayar da kayan dayan hannu na rike Iman dake min mitar na bata wayar su gaisa, tafiya muke a kafa ina cigaba da amsa wayata ban bi ta kanta ba. Kamar walkiya haka naji an fizge hannu na dake hade da nata, kafin nayi wani yunkuri an watsa min wani abu mai matukar yaji da radadi a idanuwa na, bansan lokacin dana saki kara mai karfi ba cikin tsananin azaba na durkushe a wajen. Ina jin sahun digadigan su, ina jin ihun Iman mai haɗe da kiran sunana, a birkice na tashi ina laluben ta, tsananin duhun daya mamaye ido naa yasa na kasa aiwatar da komai. Ƙarar tashin motar su kawai naji, na sake yunkura wa da dukkan karfi na, sai dai ban yi ko da taku daya ba naji an shaka min wani abu da yasa na daina gane komai. Rano Manage 🚴🚴🚴🚴🚴🏇🏇🏇 Dukkan masu kwamplain an daure su, kuyi hakuri za'a kunce ku a hankali, zaku gane kan komai. *DG*                        *31* ★★★★★ Kukan da nake ya dawo hankalin mutane wajen, da sauri wani makocin mu daya shaida ni ya karasa gida ya kira Baba Altine, a kideme ta fito babu ko mayafi, tana gani na ta hau salati tana kuka. Zuwa lokacin radadin da nake ji ba kadan bane a idanuwa na, kama ni aka yi da taimakon wani Alhaji ya bada aron motar sa aka dauke ni zuwa asibitin.    Kamal a rude ya fito daga dakin sa, part din Iyayen sa ya nufa riga a hannu yana kokarin sakawa, Ammi na zaune ta tallafe fuskarta da hannun ta ya shigo a kid'ime. "Ammi ina Daddy?" Yace a rude yana kallon ta. "Menene?" Tace tana tashi tunanin ta wani abun ne ya faru. "Kano zan tafi, akwai matsala." Yayi hanyar fita daga falon, da sauri ta riko shi, tana kallon yanayin sa "Kana da hankali kuwa? A daren nan? Wai menene ma ya faru?" "Ban sani ba wallahi, kawai muna magana da Aminatun,  naji ihu sai kuma na daina jin komai, ina ta kira kuma wayar bata shiga." "Yarinyar da ka bani labari? Har yanzu kuna tare kenan." "Ammi pleaseeeeee, suna bukatar taimako wallahi, bari kawai naje wajen Old Woman nasan ita zata fuskance ni." "Tsaya." Tace tana daukar wayar ta, Alhaji Marwan ta kira, bai dauka ba har ta katse, ta sake kira sai ya biyo ta da text message suna wani meeting ne zai kira. Ajiye wayar tayi tana kallon dan nata "Ka yi hakuri mahaifin ka ya dawo kamal, yanzu dare yayi." "Amma..." "Dan Allah, I can't risk loosing u, kasan dai yadda tafiyar dare take, ka bari kaje by flight idan Allah ya kaimu, yanzu ka duba available flight da time." Kamar zaiyi kuka amma dole ya hakura ya koma dakin sa, tsawon daren kiran wayar ta kawai yake amma bata amsawa, haka dai ya hakura yana ta Allah Allah gari ya waye ya je ya gani, ya rasa dalilin daya sa ya damu da ita sosai da al'amuran ta. *** Idan nace muku na runtsa tsawon daren toh nayi karya, kafin safiya idanuwan sun haye sunyi suntum, bana ko iya bude su ga bakar azaba, duk da wannan tunani na na wajen yata, waye wannan da zai sace ta, wai me nayi wa mutane ne har haka da ba zasu barni nayi rayuwa ta ba, iya sani ba bani da wani abokin gaba ko fada, amma me yasa hakan ke kasancewa dani.     Shigowar Anas dakin tare da yan sanda yasa nayi shiru daga kukan da nake na zuci, dan likita ya hanani kuka saboda idon nawa zai kara rikicewa.   Tambayoyi sukayi min suka fita, kamshin turaren sa daya sake kusantoni yasa na gane ya matso sosai "Sannu." Yace yana dora hannun shi saman goshi na. Bance komai ba,zuciya ta ta riga ta karye, ina ji kamar numfashi na zai yanke na bar rayuwar baki daya. Shiru ne ya biyo baya, ina jin motsin sa yana taba abu a jikin gadon, kafin yace "Ina zuwa." Yana fita Baba Altine ta shigo Kamal na biye da ita, kamar wadda wani dangi ko dan uwanta ne yazo haka naji, duk sai naji komai na sake bijiro min, mantawa nayi da kashe din likita na shiga rera kuka sosai suna bani baki, shigowar likitan ya katse min kukan da nake, tare suke da Anas, ganin Kamal a dakin ya dan sha jinin jikin sa kafin ya basar yana sauraron bayanin likitan.    Aiki za'a shiga dani na gaggawa, saboda haka aka wuce dakin gwaje gwaje, babu wanda ya matsa nan da can a cikin su har zuwa lokacin da sakamakon ya fito. Daga nan aka wuce dani zuwa dakin theatre domin gudanar da aikin. **** Daki ta shiga da sauri ta hau harhada kayan ta, har lokacin kuka take, yaran na tsaye bakin kofa kowa yayi shiru jiki a matukar sanyaye suke duban mahaifiyar tasu, idan da sabo sun saba duk lokacin da abin ya motsa sai anyi da gaske take hakura, sai dai yau zuwan wannan bakon ya so saka su a tunani, iya sanin su babu wanda yake zuwa musu da sunan dan uwa ko wani dangi, haka nan suke rayuwar su daga su sai iyayen nasu biyu.    Shigowar Abban nasu dakin hannun sa rike dana Farouk yasa suka matsa gefe suna jiran suji mai zai faru.    Anty Safiyya na ganin sun shigo tayi saurin rufe akwatin kayan ta tahau jan ta da sauri tana nufo su, kama hannun Farouk tayi cikin kuka tace "Wuce mu tafi, ba zan sake zaman ko da awa biyu bane a garin nan na gaji!" Gam ya rike hannun mata idanun sa na kadawa, duk da har lokacin ya kasa tunanin abubuwan da yadda suke sai dai tsantsar tashin hankalin da yake gani a idanun uncle Aliyu kadai ya isa ya gane akwai gagarumar matsala. Mai yasa tsawon wannan lokacin babu wanda ya nemu su?" A gefen gadon ya zaunar da ita, ya rike mata hannu yana durkusawa a gaban ta, ganin taki daina kukan yasa hannu ya shiga share mata hawayen kafin yace "Dan Aallah ki daina kuka, idan kina kuka mu fa? Dukkan mu zaki saka muyi kuka." "Ina Ja'afar?" Tace tana share hawayen nata "Ja'afar yana nan cikin koshin lafiya." Girgiza kanta tayi "An min adalci kenan? A rabani da d'ana tsawon wannan shekarun ba tare da ya ganni ba Farouk?" "Kiyi hakuri." Uncle Aliyu ne ya matso jikin gadon yana rike mata hannu "Safiyya... Nasan kina dauka ta a cikin mutane mara sa adalci da son kansu ko? Kina tunanin na rabo ki da kowa naki na kawo ki nan, ki sani bani da zaɓi da ya wuce hakan, ba'a son raina hakan ta faru ba." "Kullum magana daya kake, baka da zaɓi, baka taba zaunar dani ka sanar dani abinda ya kamata na sani ba, taya kake tunanin zan yadda da kai?" "Bani da ikon sanar dake ne, sai dai a yanzu komai ya wuce, ni kaina ina bukatar ganin dangi na, dana kasa kare su na tsaya musu sanda suke da bukata ta, musamman Anty Abidah." Cikin zumudi tace "Kana nufin zamu koma gida?" Daga mata kai yayi "Tsawon lokacin nan ina jiran wannan ranar ne, duk yayi min ikirarin ba zan taba ganin ranar ba, sai dai ban fitar da rai ba, ina ta addu'a Allah ya kawo min karshen halin da nake ciki, Safiyya ba haka kawai na zauna anan ba, akwai babban dalilin da ya rike ni har wannan lokacin." Juyawa yayi yana duban Farouk "Ya akayi kazo nan, ga dukkan alamu ba yanzu kazo ba,yanayin ka ya nuna ka jima a kasar, menene ya faru?" Ajiyar zuciya Farouk ya sauke yana jin an tabo masa tsohon mikin zuciyarsa, sai dai dole zai sanar musu komai saboda ga dukkan alamu Uncle Aliyu ya san wani abu dasu basu sani ba , sai dai kafin nan yana bukatar amsar tambayar dake nukurkusar zuciyar sa "Ina da dalili babba na barin kowa na dawo nan da zama, sai dai na kasa auna fahimta ta a sanda na ganka, tun zuwa na farko kasar nan na fara haduwa dakai Allah be sa zamuyi magana ba, me yasa tun bayan tafiyar ku, babu wanda ya kuma neman ku, yasan inda kuke ko yayi maganar ku?" Murmushi Uncle Aliiyu yayi ba tare da ya amsa ba ya jeho masa wata tambayar "Tun tasowar ku ka taba ji ance maka yau ga Kawun ka Adam yazo?" "Ina tunanin Uncle Adam ya rasu tun muna yara ai ko?" "Eh ya rasu a idon duniya sai dai be rasu a idanun Aliyu ba, yana nan da rai yana yawo a doran kasa." Zaro ido sukayi a tare da Anty Safiyya, ta tashi tsaye tana kallon mijin nata cikin rawar murya tace "Ya akayi hakan ta kasance?" "Babu amsar wannan tambayar taki sai a gaban mutanen da hakkin sanin hakan ya wajaba akan su, dole sai mun tabbatar da hakan ta hanya gamshashiya ba ta fatar baki ba, ƙaryata labarin mutuwar da ya dauki tsawon lokaci da wucewa ba abu bane me sauki. Musamman a wajen mutane irin su Adam wanda babu digo na imani a ransu." "Tabbas akwai rudani a cikin wannan maganar Uncle Aliiyu, sai dai hakan yasa na fara wani tunani da hasashen wasu abubuwa ciki har da abinda ya faru dani, ina so zan sanar maka da komai da ya faru bayan tafiyar ku, ina nufin abinda ni ɗin zan iya dorarwa akai ba wanda ban sani ba, daga nan zan baka labarin abinda ya sa na dawo nan ɗin, ina fatan hakan ya bani haske a abun da na jima ina tunani da hasashen wanda yake da hannu a ciki." "Madallah da kai, hakan ne zai taimaka mana kwarai wajen sanin ta ina zamu tabbatarwa da duniya abinda ya jima yana boye." "Ina fatan haduwar mu ta zama warwawar manyan daurukan da suka dade a daure, ina fatan ya zama silar wanzuwar farin ciki a zukatan mutane da suka dade da mantawa da yadda farin ciki yake." Madaidaicin study room din sa suka nufa, daga shi sai Farouk da Anty Safiyya, yaran na falo kowannen su ya samu abin tattaunawa da zuciyar sa, cikin gamsasshen bayani Farouk ya warware musu komai na abubuwa da zai iya sanar dasu, har zuwa lokacin da yayi bankwana da kowa.     Babu digon mamaki ko tashin hankali a tattare da uncle Aliyu bayan ya gama sanar dasu komai, a yadda ya nuna ma kamar dama yana da masaniya da dukkan abinda ya faru ɗin.    Da kyar suka barshi ya koma gida da niyyar zai dauko abubuwan bukatuwar sa ya dawo nan ɗin, sai a sannan ya tuna da maganar supervisor din sa daya ke kiran sa, a gaggauce ya tura masa mail na ban hakuri da bayanin uzurin daya riƙe shi, babu komai yace masa ya kuma sake bashi lokaci akan yazo ya ganshi gobe idan Allah ya kaimu. Kwanan sa biyu ya gama tattare komai ya dawo gidan nasu, Anty Safiyya da duk ta tashi hankalin ta ta dauka ba zai dawo ba, sai data ganshi sannan hankalin ta ya kwanta. Karatun sa daya zo gangara ya bada himma wajen hattama shi, shi kanshi a yanzu hankalin sa ya soma komawa gida, yana ji a ransa wannan lokacin zai hadu da Aminatu, duk da babu wani labari daya samu tun bayan zuwan sa game da komawar ta Shagari, amma kowanne lokaci cikin bibiya yake yana fatan Allah yasa ta koma. Shirye shiryen komawar su ya kankama, gefe guda yana cigaba da zuwa shagon dan ba karamin sabo yayi da mutanen wajen ba, tun da suka ji zai tafi suka shiga tashin hankali, barin ma Mr John daya sakar masa kusan dukka ragamar wajen shi sai dai ya dan duba abinda yake ganin zai iya amma komai a wajen Farouk ke kula dashi cikin kwarewa da kaffa-kaffa. *** Tsawon kwanaki hudu kenan tun bayan da akayi min aikin, sai dai ba'a cire ba sai zuwa karshen sati idan mai duka ya kaimu.    Kowacce uwa zata fuskanci yanayin tashin hankalin da nake ciki, batan d'a ba abu bane mai sauki, na rasa inda zan saka kaina, babu wani labari game da batan Iman, duk da kwantar min da hankalin da suke hakan bai saka hankalin nawa kwanciya ba, ji nake kamar na gudu daga asibitn na tafi neman ta da kaina,sai dai nasan daga Anas har Kamal suna iya kar kokarin su wajen ganin an samu ko da wani hint ne akan haka, kullum cikin jiran kiran su muke amma shiru kake ji kamar malam yaci shirwa, babu wani bayani gamsashe. Addu'a muka dukufa yi babu dare babu rana, ba ta kaina nake ba, buri na kawai naga yata, ita kadai ce dangin da nake dashi na kusa, duk wani da zai rabe mu da sunan kauna ba kamar ni da itan ba. *** Ranar da za'a cire min abinda aka saka aka nannade idon dashi duk jikina yayi sanyi da tunanin abinda zan tarar. Dishi-dishi na soma ganin komai, nayi saurin runtse idon ina jin kamar sun sake kankancewa akan yadda suke a dah, a hankali na sake bude su ina duban mutanen da ke dakin daya bayan daya, har lokacin bana ganin su tar sai dai ina iya banbance komai da kowa, glass likitaan ya saka min hakan ya taimaka wajen kara karfin ganin nawa, sai dai babu kaso hamsin ciki dari na gani na adah.      Kuka nake so nayi amma babu hawayen ma balle har na saka ran zasu zubo, da zuciya ta na shiga kokawa cikin yanayi mara misaltuwa, an cuce ni an lalata min rayuwa yanzu kuma an kashe min baban jigo na rayuwar mutum, idan aka taba maka ganin ka an gama da kai, makanta babbar musiba ce sai wanda ya sami kansa a ciki ne kawai zai gane. Kai tsaye na yanke wa kaina hukunci na kira kaina da Makauniya, eh makauniya mana tunda menene banbanci na da wanda basa gani gaba daya, illar ido daga ranar da ya riga ya tabu toh daga lokacin sai dai hakuri saboda yadda zai tayin gaba. *** Kai tsaye gida muka wuce bayan an sallame ni, babu Anas babu Kamal sai keke napep muka samu ya kaimu dauke da kayan mu, waya ta dake saman cinyata tayi kara, na dauka ina duban screen din, bazan iya karanta rubutun ba, dole na jawo glass din na saka na shiga bin rubutun a hankali ina kokarin karantawa, ji nayi idon ya fara ruwa, dole na rufe na kira shi kai tsaye ina manna wayar da kunne na " Kina ji? Gamu nan tare da Daddy da Uncle Kabir, zasu duba ki sai kuma yayi miki maganar Iman, ina tunanin zai iya taimakawa idan yasa baki a kara tsaro sosai wajen neman nata, sai mun ƙaraso." "Ai an sallame mu ma, muna gida." "Kash, shikenan bari na fada musu, zan kira ki." Kashe wayar yayi ya juyo baya "Daddy Ashe an sallame su ma, wai suna gida." "Toh, babu damuwa sai muje station din da kace case din na hannun su, idan yaso sai muji yadda za'a yi." Kallon Daddyn su Farouk yayi yace "Friend ban taba ganin Kamal ya zama so serious akan abu irin wannan lokacin ba, shiyasa nake so nayi supporting nasa with all I can." "Hakan nada kyau, ban taba tunanin yara na bukatar support dinmu ba sai bayan na rasa Farouk, ban taba bashi dama yayi wani abu da kansa ba, i always find fault a kansa bansan me yasa ba, sai da kuma ya matsa nake dana sani." "Suna bukata sosai, idan yaro yazo ma da abu ka fara bawa abun big thought,idan kaga akwai fault a ciki sai ka zaunar dashi ta cikin hikima ka fahimtar dashi illar abin, amma idan kace zaka zama tough toh yaran ka zasu na tsoron ka, ba kuma zaka taba sanin halin da suke ciki ba, komai a boye zasu dinga yin sa sai abu ya kwabe kuma sai kaji ana wallahi wallahi." "Haka ne." Yace yana girgiza kansa. Hirarrakin su suka cigaba har suka isa station din, waya Daddy ya daga ya kira commissioner of police na gaba daya Kano state ɗin ya sanar masa abinda yake so ayi, kai tsaye ya amince ya kuma hada su da head na station din da case din ke hannun su, a take aka chanja case din zuwa Babbar headquater su. Dukkanin su a gajiye suke dan ba karamin yawo suka sha ba akan case din da kuma wasu harkoki na bussiness da suka shigo dasu garin na Kano, a gidan Dadah suka yada zango la'asar likis, zarewa Kamal yayi ya nufi gidan Aminatu dan tare zasu koma da Daddy sablda yadda ya ke kokarin ganin ya dora kamal ɗin akan komai na kasuwancin sa. Har dare suna gidan sai da suka ci tuwo sannan suka tafi driver ya ajiye su a airport, abin ka da tafiyar manya cikin yan mintuna suka isa Abujan. Dukkan abubuwan daya saba gabatar dasu sai daya kammala su kafin yayi shirin kwanciya, be iya zuwa ganin mahaifiyar sa ba yau kamar yadda ya saba idan ya dawo yakan je suyi hira yaji bukatar ta, har ya kwanta ya tuna da wani mail da wani abokin cinikayyar sa dake birnin London yayi masa tun rana, ya kuma kirashi akan lallai ya duba a yau din dan abin nada muhimmanci. Tsam ya mike Ammi dake kwance ta bishi da ido tana gyara kwanciyar ta, hutun sa koda yaushe kadan ne, daren da yake samu ya huta ma sau tari yana kwanciya zai mike ya shiga wata sabgar kuma da na'ura mai ƙwaƙwalwa. Shiyasa wani lokacin akan ce mara arziki yafi mai shi kwanciyar hankali da nutsuwa. Zama yayi yana dora computer a saman dan karamin table din dake cike da tarkacen takardun sa, kunna tayi ya runtse idon sa yana jin kansa a cunkushe. Email ɗin sa ya shiga ya fara dubawa a hankali yana nazarin komai. Tsawon lokaci ya dauka yana dubawa kafin ya kashe komai, wayar sa dake ajiye saman bedside drawaer ya dauka yana kokarin sata a flight mood sakon dake yawo a saman notification bar din sa yaja hankalin sa, budewa yayi ya soma karantawa _"Cikar buri shine samun abinda zuciya ta kwadaitu dashi. Haka ma abu mai matukar muhimmanci na faruwa na da mutane masu muhimmanci.Kunyi tarayya akan abu guda, ba tare da sanin ku ba, saboda ku ɗin wawaye ne mayaudara. A yau abinda yafi komai muhimmanci a gareku kai da wanda kake kira aminin ka na hannu na. Ina fatan ku samu karfin zuciyar iya fuskantar abinda ke tunkaro ku!"_ Be fuskanci abu daya da sakon ke nufi ba, sake karantawa yayi ko zai samu wata amsa aciki, sai dai a yadda sakon yazo babu wani abu da zai iya fassarawaa ciki har ya gane inda maganganun suka dosa. Menene sukayi tarayya da aminin sa akai? Abu kuma mai muhimmanci gare su? Dole yasa a bibiyar masa number sakon da safe idan Allah ya kaimu. Gaba daya sai yaji dan guntun baccin dake idon sa ya kaurace masa, dole ya nufi toilet ya dauro alwala ya shiga nafilfili yana rokon ALLAH ya kare su daga sharrin masu sharri. *Rano**DG*                        *32* ★★★ Da safe ya tashi yana shiryawa sakon na cigaba da yi masa yawo a kwakwalwa, be wani tsaya karya wa ba ya karasa ya gaida Hajiya Turai a tsaitsaye ya fita.    Daddy shirye yake shima tun bayan da sukayi waya saboda haka yana fita suka hadu suka dau hanya, wayar sa ya ciro ya mika masa ya duba sakon, shi din ma bai wani gane komai ba, sai ya kashe ya mika masa yana kallon sa "MD ban gane komai akan sakon nan ba." "Nima hakan ce, kuma iya tunani na na kasa gane waye zai tura dashi?" "Shine, hanya mafi sauki ayi tracing sakon,daga nan sai mu san yadda zamuyi." "Shikenan." Yace yana lumshe idon sa, daren jiya bai wani runtsa ba, ba wannan ne karo na farko daya fara cin karo da irin wannan sakwannin ba, sai dai na yanzu yasha banban da sauran, idan har ya fahimta komene yana da alaka da abokin sa, hakan ya kara saka shi a taraddadin waye zai masa wannan? Lokacin da PA d'insa ya bashi statement din dake kan sim card din yayi mamaki kwarai, suna da duk wani information da akayi register sim din dashi bashi da alaka da wanda ya rubuto sakon, ga dukkan alamu ma irin sim card masu register akan su ne sai dai kawai ka siye su a haka. Shafa kansa yayi ya mikawa Daddy result din yana sake resting sosai akan kujerar office din nasa, dogon nazari Daddy yayi kafin yace "Ina ganin so ake ayi wasa da hankalin mu, a shagaltar damu da abinda yake mai muhimmanci, karka damu zan san yadda za'ayi." "Ok duk yadda kace haka za'a yi." Wayar sa ce ta hau burari, duba wa yayi ganin KAMAL ne yasa ya dan tura hular sa baya "Kamal ba zai barni na huta ba idan ban tashi tsaye akan case din nan ba." "Da gaskiyar sa, atleast he's willing to help." "Haka ne." Yace yana bin kiran, magana sukayi kadan ya ajiye wayar ya cigaba da duba abubuwan da zai duba suna hira jefi jefi. *** Duk motsin Farouk na kan idon Anty Safiyya, gani take kamar zata sake rasa babbar damar da take ganin ita kadai ce zata sata komawa ƙasar ta, ta gaji ainun, tana bukatar wani dangi a kusa da ita, ace rayuwa daga kai sai miji sai yaya. Tunanin da kachokam ya tafi akan Ja'afar, kullum kwanan duniya da tunanin sa take kwana take tashi, ba abu bane mai sauki a raba uwa da danta tun be san waye shi ba,tana bukatar ji daga gareshi, tasan matsalar sa, abinda yake so da wanda baya so. Karatun Farouk ya kare, saboda haka uncle Aliyu ya shiga shirye shiryen dawowar su a boye ba tare da sanin kowa ba sai shi Farouk din. Sai da komai ya kankama sannan ya sanar ma Anty Safiyya, ranar bata iya runtsawa ba kwana tayi tana duban ticket din tana hawayen farin ciki Jirgin karfe sha biyun dare zasu hau, saboda haka sai bayan sun gabatar da sallar isha sannan suka fito, yaran duk basu da walwala idan ka cire mahaifiyar su da har nema take ta manta wasu abubuwan nata sai da Uncle Aliiyu ya ankarar da ita. Duk da Farouk ba a wannan lokacin yaso ya koma ba, amma shima yana bukatar jin amsoshin dake dan kare a zuciyar sa. *** Kuka nake na zuci na rasa wanda zan fadawa damuwa ta, yau tsawon mako guda kenan da kwanaki biyu babu labarin ta, Hajiyar su Anas sunzo sun duba ni ita da Ramlah da wata kanwarta sai dai yadda naga Hajiyar tayi min sai nake jin kamar akwai lauje cikin nad'i, ina kyautata zaton ba a son ranta ta amince wa Anas ba. Hakan kuwa be dame ni ba, dan ni yanzu ba ta aure nake ba, buri na daya shine naga yata na kuma san wanda yake kokarin kassara mana rayuwa ba tare da mun aikata masa komai ba.     Duk da Kamal ya bani tabbacin maganar tana hannu manya amma na kasa aiwatar da komai, magana ma idan ba Baba Altine tayi da gaske ba sai na wuni bance komai ba, daga uhum sai um um.      Murmushi na saki me matukar ciwo, bayan na dawo daga dogon zangon dana tafi na tunanin rayuwa ta,tun daga lokacin dana budi ido na na ganni a wannan duniyar me cike da mutane marasa tausayi da imani.     Mutane biyu masu matukar muhimmanci a rayuwa ta a yau na rasa su, ciwon da zuciya ta ke ciki ba zai misaltu ba, da kyar na mike daga kwanciyar da nayi,waya ta dake yashe a saman gado ta dau ruri a karo na uku, karamin tsaki naja kafin na mika hannu na dauka, kamar yadda na zata shi din ne kuwa, *Kamal*. Murmushi nayi daya fi kuka ciwo  na katse kiran ina jingina da jikin dan madaidaicin fridge din dake daura da kofar shigowa dakin.    Sake shigowa kiran yayi na daidai ta zaman glass din ido na ina dagawa cikin muryar data fi kama da wadda bata da gata ko galihu nayi masa sallama cikakkiya kamar yadda manzon Allah (SAW) ya koyar damu. "Ina ta kiran ki tun dazu." Yace kai tsaye bayan ya amsa sallamar tawa. "Sorry na tafi wani dogon tunani ne kamal." "Zaki fara ko? Gani nan zanzo na dauke ki muzo nan station din, Daddy ma sun kusa ƙaraso wa shida Uncle Kabir." Dan dum naji gaba na ya fadi nan da nan, dakewa nayi na amsa masa da toh na fito falon, Baba Altine na zaune tana tunani gefen ta karamar jikar tace data dauko ta tun zuwan da tayi ganin gida zaune tana barar gyada.   Zama nayi a gefe ina juya wayar hannu na, tunanin haduwar da zanyi da mahaifin kamal nake, duk sai naji na damu, kasan zuciya ta cike take da tsoron haduwar mu, ina jin karar tsayawar mota a kofar gida duk sai naji kamar an tsaida gudun jinin jiki na, a kasalance na mike ina kallon kiran sa ba tare dana daga ba na yi hanyar wajen. Yana zaune ya zuro kafuwan sa wajen motar ya dago jin fitowa ta, bai tsaye wata doguwar magana ba ya tada motar muka bar layin. Mun riga su isa station din saboda haka muka samu waje muka zauna zaman jiran su, basu iso da wuri ba sai bayan mun dade da isa, a waje Daddy ya tsaya yana amsa waya baban su Kamal ne kawai ya shigo, kaina a kasa ina kara jin abu mai kamar tsoro tsoro na fizgata, wuce mu yayi kai tsaye ya shige office din DPo ɗin, a dan rada rada nace ma Kamal "I'm nervous." Dariya ya saka yana duba na "Kin cika tsoro." Shiru nayi ina tunanin abinda yasa nake jin hakan, takun tafiya muka ji nayi saurin sake nutsuwa har suka ƙaraso gaban mu, a hankali na dago yayi daidai da duba na, kura min ido yayi cikin wani irin yanayi me kama da kallon sani, da sauri na furta "Ina wuni?" Kada kansa yayi a kajarce ya amsa yana maida hankalin sa kan Kamal "Itace?" "Eh itace Daddy." "Ina iyayenki?" Ya wurgo min tambayar a bazata, da sauri Kamal yayi karaf yace "Sun rasu ai Daddy." Boyayyiyar ajiyar zuciya na sauke, ina jin dadin yadda Kamal ya cece ni, bansan amsar da zan bayar ba hakan kuma na iya jefa shakku a zuciyar sa, ina ji suka cigaba da magana da Dpo akan yadda za'a yi. Daidai lokacin Daddy ya gama wayar da yake ya shigo ciki, dukkan su suka mike cike da girmamawa suka sara masa, hannu ya daga musu ya ƙaraso inda muke yana kokarin fahimtar maganar da suke. "Ina fatan akwai wani improvement akan batar yarinyar?" Da sauri na dago jin irin maganar Farouk, sai dai wannan girma ya yi mata rufi sosai inda kai tsaye zaka gane mamallakin muryar Baba ne, yawun bakina ne ya kafe a diririce nace "Daddy?!" Sai a lokacin ya lura dani, ware idanun sa sosai yayi akaina cikin tsananin mamaki yace "Kamar Aminatu ko?" Sai na fashe da kuka da karfi ina daga mishi kai "Ikon Allah." Ya furta yana dubana duban tsanaki "Ko zuwan mu wajen Dadah sai data yi min maganar ki, ina kika shiga tsawon wannan lokaci?" Ban iya bude baki nayi magana ba, sai kuka na daya karu sosai, ganin duk mutanen wajen sun juyo suna kallon mu yasa Dpo yace mu koma office din sa. Alhaji Marwan da Kamal sun shiga tunanin abinda ya hada mu, saboda haka muna shiga ciki Alhaji Marwan yace "Me yake faruwa ne Kb? Ka santa ne? Ko shi yasa nake ji kamar na taba ganin ta tun shigowa ta wajen nan." "Matar Farouk fa, wadda muke maganar ta ranar da Dadah." "Ikon Allah." Yace yana bi na da kallon tausayi, kamar an mintsini Daddy yayi saurin cewa "Yarinyar da ta bata... Menene alakar ki da ita?" " 'Yata ce!" Na amsa kai tsaye ina sake sakin wani sabon kukan, tashi yayi yana zagaye dakin hankalin sa a matukar tashi, kenan da gaske bayan rabuwar su Da Farouk ta haifi abinda ke cikin ta har ma ta girma, idan haka ne yarinya ce wani tsani na warwarar wasu daurukan da har yanzu ya gaza warware su. Da wani irin sauri ya mika hannu ya karbi wayar dake hannun Alhaji Marwan, kai tsaye ya shiga jerin sakonni ya fara dubawa, a kan sakon ya tsaya yana sake dubawa duban tsanaki, "abin da sukayi tarayya akai, ba tare da sanin su ba..." "MD!" Ya kira shi da d'an karfi "Yarinyar Farouk ce, ita ce ake magana a wannan text message ɗin, waye shi? Me mukayi masa da yake son ganin bayan mu?" "Kana nufin abinda text ɗin ke nufi kenan?" "Eh duba kaga, ya zama dole mu nemo shi ko waye, shine yake da amsar dukkannin tambayoyin mu." Shiru nayi lokaci daya naji kukan ya dauke min, nauyin dake lullube a zuciya ta naji ya soma raguwa a hankali, sai dai ido na daya ke min wani irin zugi kamar na zuba masa yaji, su kadai yanzu suke maganar su sai Kamal daya zuba ido baya fuskantar komai, ni ɗin ma ba wani fuskanta nake ba, sai dai tabbas akwai wata kullaliya da ta saka aka sace min yata, kenan akwai me bibiyar rayuwa ta har bayan barin kauyanmu. Amal ce ta fado min, da ita kadai na taba haduwa har ta nuna min babu wata alaƙa tsakanin mu, ance zato zunubi sai dai a take zuciya ta ta shiga ayyana min ko tana da hannu a cikin batan Iman? *** A kofar gidan Driver ya ajiye ta, fuskar ta sanye da bakin glass, ta sakala earpiece a kunnenta da alama waya take amsawa, sai data gama amsa wayar sannan taja jakar kayan ta ta shiga gidan, da mai aikin Dadah suka fara karo, bata ko bi ta kanta ba tayi hanyar falon tana yatsine, da gudu da fada jikin Dadah tayi saurin ture ta tana matsawa gefe "Yar nema karki karya ni." "Nayi missing dinki ne Dadah." "Naji, tare kuke da Baban naku ne? Yayi min waya sun shigo garin tun dazu nake baza ido." "Wai Daddy, ban masan yana nan ba, sai anjima kila idan ya gama abubuwan da ya kawo shi." "Haka ne, ya mutanen gidan ya kowa da kowa?" "Lafiya wallahi, bari n huta nazo naci abinci dan yunwa nake ji." Ta mike tana jan jakar ta ta nufi daki. *** Sai da suka gama komai sannan muka fito, Daddy ne ya dubi Farouk yace "Kasan gidan Dadah ko?" Soso kai ya hau yi yana kallon Alhaji Marwan, da sauri yace "Yanzu duk zaman ka garin nan baka taba zuwa ba?" "I'm sorry Dad." Yace yana matsawa dan yasan sauran bayanin "Toh sai ku biyo mu a baya, chan zamu wuce Aminatu, ba zan iya bawa Dadah labarin da nake so na bata ba tare da ta ganki ba." Amsawa nayi da toh muka bi bayansu zuciya ta na wani irin bugawa ina jin tsoron abinda zan tarar. **** Sanye yake da dogon wando da riga longsleeve ya nade wuyan sa da abu mai kauri, hannun sa rike da Amir karamin dan uncle Aliiyu, bayan sa rataye da Jacket ɗin sa daya zare tun da suka ido Nigeria, cikin kankanin lokaci suka gama komai a airport dib suka tari cab kai tsaye suka nufi gidan Dadah bisa umarnin Uncle Aliiyu. Kallon ko ina yake babu abinda ya sauya a dan tafiyar da yayi, kai tsaye unguwar suka shigo daidai lokacin da motar su Daddy ta tsaya a kofar gidan, runtse idon sa Farouk yayi yana tuno abinda yasa shi barin kasar gashi ya dawo dashi ba tare da sanin yadda zai tunkari mutanen da suka zama masa wani jigo na rayuwa ba. Two hearts are about to reunite🏌️🏌️🏌️🏌️🏌️🏌️🏌️🏌️ idan kun shirya nima na shirya, let the game begins 🏇🏇🏇🚴 Idan na samu chargy zaku jini anjima. Manage dis wayata 3%*DG*                *33* ★★★★★ Tun kafin su k'arasa suka fito, Daddy ne a gaba Alhaji Marwan na biye dashi, sai kuma motar Kamal da ke tsaye a bayan tasu Daddyn, wani irin farin ciki ne ya lullube Uncle Aliiyu ganin mutanen da yake da muradin gani tsawon lokaci.   Rufe ido Farouk yayi ya kwanta sosai a jikin kujerar motar, a daidai lokacin Kamal da Aminatu suka nufi cikin gidan, har suka gama fita daga motar be dago ba sai da Uncle Aliiyu ya tab'a shi, kamar ba zai sauko ba sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya fito yana kallon sararin samaniya. Anty Safiyya ce a gaba yaran na binta sai Uncle Aliiyu da suka jera da Farouk yana mishi bayanin sauye-sauyen da ya gani. A daidai lokacin Dadah na tsaye gaban fanfo tana daura alwala, da fara'a ta tarbe su maganar da take kokarin yi ta makale ganin wadda bata taba tunanin gani ba. "Wa nake gani kamar Aminatu?" Tace a dan kideme, tana matsowa inda nake tsaye kamar an dasa, tsananin farin cikin da nake ciki bazai misaltu ba. Murmushi Daddy yayi "Yau sai a bani tukwuici na ga Aminatu na kawo miki har gida." Kukan farin ciki ta saka ta rungume ni jikin ta, kukan da nake kokarin rikewa ya kwace min muka shiga yi a tare, a yau na kara tabbatar da kaunar da matar take min, kenan sun koma nema na bayan na bar kauyanmu, wannan shine soyayya ta gaskiya ba tare da wani abu ba. Sallamar Anty Safiyya ta katse dukkan me shirin magana, duk suka zuba mata ido cike da tsantsar mamaki, takawa take kamar wadda take tsoron yadda zasu karbe ta. Har ta tsaya a gaban Dadah babu wanda ya iya furta komai, shigowar Uncle Aliyu, Farouk biye dashi kansa a kasa kamar baya son ganin kowa ya kara jefa su cikin rudani, saki na Dadah tayi tayi wajen Anty Safiyya bakin ta a bude, yaran dake gefen ta, ta shiga bi da kallo daya bayan ɗaya tana kallon fuskar mahaifiyar tasu. "Kabiru me yake faruwa, wa nake gani kamar Aliyu, Safiyya da Babana? Ban gama dawowa daga mamakin ganin Aminatu..." A rikice Farouk ya dago jin an ambaci Aminatu, a lokaci daya ya dira a gabana, idon sa cikin nawa yake duba na, cikin wani irin yanayi da bazan iya misalta shi ba, rawa bakin sa ya soma kafin da kyar ya samu nasarar furta kalmomin a rarrabe, "De..s...ti..ny." Sai ya rike hannu na da sauri ya shiga jana yana kokarin barin gidan, Alhaji Marwan ne ya dakatar dashi ta hanyar rike shi, ya kuma bata rai sosai yana nuna masa ciki, daya bayan daya ya shiga bin mutanen dake tsaye a wajen kowa da kalar kallon da yake mana, sai kuma ya sauke idon sa akan Dadah dake kuka sosai, kukan daya sanyaya jikin kowa har aka rasa wanda zai iya cewa komai. "Mu shiga ciki." Alhaji Marwan daya fi kowa karfin hali yace yana nuna masa hanyar falon, mai aikin Dadah ce ta rike ta muka dunguma zuwa cikin falon har lokacin hannun sa sarke yake da nawa, kaina a kasa na gaza kallon sa, wani irin yanayi ne ke shiga ta yana bin kowanne lungu da sako na magudanar jinin jikina.    A kasa muka zube tare yaki saki na kuma, idon sa akaina baya tuna duk mutanen dake falon da matsayin su gareshi. Kan Uncle Aliiyu na saman cinyar Dadah yana share hawayen dake faman reto a saman fuskar sa, girma da shekarun sa basu hanashi zubar da hawaye a wannnan lokacin ba, domin yana bukatar hakan. Saboda haka babu wanda yayi yunkurin tsaida shi sai daya gaji dan kanshi ya zauna sosai yana duban dukkan yan falon.   "Na tabbata duk wanda yake gurin nan yayi mamaki ganin mu, bayan shudewar lokaci da ina kyautata zaton babu wanda ya sake tunawa da Aliyu da matar sa Safiyya, sai dai mu bamu taba kwana ba tare da mun tuna da ku ba, duk da ba wai ina tuhumar ku bane, hakan ya faru ba tare da sanin daya daga cikin ku ba, haduwar mu da Farouk shine silar dawowar mu, wanda dama abinda muke jira kenan tsawon wannan lokaci da muka kasa dawowa din." "Kamar yadda kuka sani, ni Aliyu na bar gida ba tare da sanin daya daga cikin ku ba, sai dai bani da zabi illa na tafi, dan a lokacin da na tafi bana cikin hayyaci na, ji nayi ba zan iya zama ba dole sai na tafi, da fari jihar fatakwal na fara yada zango duk da ba a bisa son raina ba, so nake kawai na bar kasar a lokacin, daga bisani Allah ya taimake ni na nemi gurbin karatu a jami'ar Cranfield dake birnin London, na samu, hakan ya saka na tattara na bar kasar ba tare da tunanin sake waiwayar kowa ba.    "Tafiyar da nayi da Safiyya ita ta taimaka min wajen tuna wanene ni, sanda na dawo hayyaci na hankali na yayi matukar tashi naji bana son sake kwana a kasar, bayan mun gama shirye shiryen komai ranar da zamu tawo na dan fita ina karasa siyan abinda zamu bukata na hadu da Adam, nayi mamakin ganin sa a kasar kuma ga dukkan alamu ba bakon kasar bane, take abinda ya faru ya dawo min, rai bace na tare shi zan soma magana yace "Sako nazo baka, ka tabbata kai da barin kasar nan sai bayan cikar buri na, duk ranar da ka hadu da wani cikin mutanen dake da kusanci dakai, a rana zaka iya komai, sai dai ina maka albishir kai da haduwa da wani sai bayan ranka, kamar yadda kaso ka tona min asiri haka zaka kare rayuwar ka cikin kunci da dana sani." Juyawa yayi ya bar wajen ban iya ce masa komai ba, kiran daya shigo wayata na maida hankali wajen dauka, kukan dana ji Safiyya nayi yasa jikina ya hau rawa, a nan take sanar min da an shigo an kwashe komai da zamu bukata wajen barin kasar, hatta yan kudaden da suka rage mana an kwashe komai, tun daga lokacin bamu sake samun damar barin kasar ba, haka muka cigaba da zama a kasar muna addu'ar Allah ya kawo mana karshen wannan musibar.   Toh kamar yadda kowa ya sani, Adam ya mutu a idon duniya, amma yana nan yana yawo a doran kasa yana aikata mugayen abubuwa, ina fatan wannan bayanin nawa zai saka Dadah ta sanar da kowa wani boyayyen sirri da ta sani, wanda sanin dana yi ya jefa ni a matsala, amma kafin nan ina neman alfarma ya zama a gaban Anty Abidah, domin a lokacin nake so komai ya warware, ina son na cika mata burin alkawarin dana yi mata na wanke ta daga zargin da ake mata." "Kana nufin Adam yana raye?" Daddy ya jeho masa tambayar kansa a daure cike da mamakin abinda Aliyun yace, "Yana nan da ransa." Ya amsa kai tsaye "Ikon Allah." Ya dora "Sai dai nasan yarda da hakan ba mai yiwu wa bane lokaci daya, ina bukatar lokaci dan tabbatar da haka." "Me akayi masa haka mai zafi da yake kokarin ganin bayan mu?" Yace yana duban Dadah data sauke kanta kasa, murmushi Uncle Aliiyu yayi, ya kalli Dadah ya kama hannun ta ya rike cikin nasa "Ki taimaka ki sanar da kowa abinda kika sani, ke ce mahaifiyar mu dukka, ke kika haife mu saboda haka karki ji tsoron komai babu abinda ya isa yayi miki sai abinda Allah ya ƙaddara miki." Kuka ta saka tana tuna abubuwan da suka faru, wanda take ganin kamar a lokacin suke faruwa ko kuma taso da maganar na iya saka komai ya kara tabarbarewa. "Zan neme ku, kuyi hakuri yanzu." Tace tana goge fuskar ta "Shikenan Allah ya kaimu." Suka hada baki a lokaci daya, kallon Farouk Daddy ke tayi ganin yayi biris da kowa na falon kamar be san da zaman su ba, idanun Dadah na kansa haka ma Uncle Aliiyu na lura dashi tun zuwan su. "Farouk!" Ya kirashi Dagowa yayi yana duban sa cikin girmamawa yace "Na'am." "Baka gaida kowa a falon nan ba, ina fatan baka manta su waye a zaune a gaban ka ba ko?" Kwarjini yaji yayi masa, idan ba haka ba bashi da niyyar tanka kowa a cikin su, musamman Daddy Da Dadah, wanda yake ganin sun fi kowa rashin son shi bayan yana da yakinin su suke fi kusanci dashi. Bai manta abinda Dadah tayi masa ba, ya kuma kasa tantance a wanne matsayi zai ajiye ta, ganin da yayi mata a yanzu kawai yaji yana bukatar tuntubar ta akan abinda ta aikata masa, yana so yaji dalilin ta na yin haka, a darare kamar wani bako yace "Fatan na sami kowa lafiya." Tsananin mamaki ya kama Daddy, ya gaza cewa komai sai Dadah ce da Alhaji Marwan suka amsa masa. ****Kiran sallar magriba yasa kowa ya mike domin gabatar da sallah, daki Dadah ta nuna min tace naje na yi alwala nayi sallah, ban mata musu ba sai dai ina so na tafi gida, nasan duk inda hankalin Baba Altine yake ya tashi yanzu, dan ma na sanar da ita in da na tafi ne.   Tana kwance na shiga dakin, ta ɗora kanta a saman pillow da alama bacci take kuma tana jin dadin baccin nata, kofar dana gani dake nuna alamun toilet na wuce ina tuna ranar dana hadu da ita da abubuwan data fada min.    Mik'ewa tayi jin wayar ta dake gefen ta nata vibration, ba tare da sanin ina ciki ba ta daga, "Kina jina? Tashi maza ki duba min bakin da akayi a gidan, ki gani idan akwai Namiji Babba da matar sa da yara uku, yi maza ina jiran ki." "Toh..." Tace tana mik'a, mikewa tayi ta tsaya tana duba fuskar ta a gaban mudubi kafin ta fita, babu kowa a falon sai Amir da Amrah babban yabi su Daddy masallaci, kallon su tayi kallon su waye ku kafin ta wuce dakin Dadah ta leka, Anty Safiyya na kan sallaya tana sallah dake gefe Dadah na gabatar da tata sallar ita ma, dan jim tayi kafin ta juya zuwa dakin nata, bata lura dani akan abin sallah ba, ta dauki wayar ta ta kira shi "Na duba, naga yara biyu a falo sai wata mata a dakin Dadah tana sallah." "What!" Yace cikin k'araji "Da gaske kenan Aliyu ya dawo, Amma how comes?" "Waye shi?" Tace tana zama "Shine wanda ya raba ki da mahaifin ki tun kina tsumma, yanzu ma kuma zai sake wargaza min aikin dana jima ina yi, Amal so yake ya kashe miki uba ki zama marainiya gaba da baya, will you allow that?" Da sauri ta girgiza kai "Ba zan taba barin shi ba, nima ina bukatar uba kamar kowacce 'ya." "Then zaki yi yadda nace?" "Zanyi." Tace kai tsaye "Good girl, zan kiraki anjima." "Ok." Ta ajiye wayar, wayun bakin tane ya makale ta hau murza idon ta da sauri, kallo na tayi, nima na zuba mata ido babu ko daukewa bayan na gama sauraron wayar da tayi zan iya alakanta hakan da maganganun da naji anayi dazu. "Me kike yi anan, yaushe kika zo gidan nan, waye ya kawo ki gidan nan?" "Wanne kike so na amsa miki aciki?" Nace mata ina murmushi "Ni na kawo ta!" Ya shiga takowa cikin dakin yana kallon ta, sake shiga rudu tayi da sauri tace "Ya Farouk!" Daga mata hannu yayi "Karki kuskura, kinji na fada miki." Kasa nayi da kaina, ya iso gaban sallayar ya zauna yana tankwashe kafar sa, leka fuskata ya shiga yi, ganin naki yarda na kalle shi yasa shi sa hannu ya daga min fuskar. "Gudu na kike Aminene? Nine Farouk dinki fa." Gefe na kauda fuskata ina jin zafin abinda yayi min a baya, na farko saki na biyu ƙaryata abinda yake tsakani na dashi, wanda shine Ummul aba'isin jefa ni cikin gararin rayuwa. "Please dan Allah kiyi min magana, shekara nawa? Kinsan yadda na azabtu da rashin ki? Kinsan wacce irin rayuwa nayi bayan na rasa ki? Dan Allah kiyi min magana." Kamar tatsuniya haka nake jin maganar tasa, idan har abinda yake fada gaskiya ne me yasa ya rabu dani, yunkurawa nayi da nufin tashi ya sa hannu ya maida ni baya "Wallahi baki isa ba, duk tsawon lokacin nan dana yi ba tare dake ba amma kiki cewa komai, haushi na kike ji? Me nayi miki?" A zafafe nace "Baka san abinda kayi min ba Ya Farouk? Baka sani ba? All this while ni kasan irin rayuwar da nayi? Why are you selfish? Shikenan nice me laifi saboda bani da gata balle galihu, daka tafi ka barni da ciki ka taba tunanin halin da zan shiga? Ka taba? Ka sake ni bayan ka koya min sonka, na shaku da kai na soka,amma nice abar tuhuma ko..." Kuka ne ya taso min, na sake shi ina saka fuskata cikin cinyoyi na, be hanani ba, ina jin yadda numfashin sa yake kai kawo a saman kaina, tashi naji yayi, ya isa wajen da Amal ke zaune tana sharar kwalla yasa hannu ya fizgota ya dire ta a gabana "Ki faɗa mata, ki faɗa mata komai da kula kulla ke da munafukan da suka tayaki, kin fi kowa sanin bani da laifi akan abinda take tuhuma ta, ki faɗa mata ko na kakkaryaki a wajen nan wallahi Allah." "Ni...ni bansan komai ba." Tace cikin kuka, shaka ya kai mata ta shiga kakari, da sauri na shiga tsakani ina masa kallon mamaki "Me kake yi haka? Dukan mace ya Farouk!" Jin haka yasa shi sakin ta da sauri yana zama gefen gadon hannun sa rike gam da kansa, juyawa nayi na bar dakin da sauri, lokacin duk sun dawo suna zaune a falon, a gaban su Daddy na durkusa Ina share fuskata "Zan tafi Daddy, dare yanayi." "Eh kuma haka ne, na manta shaf Aminatu, ina farouk sai ya maidake, duk da zanso ki dawo nan ɗin amma for now tunda munsan inda kike shikenan." "Aminatu." Dadah ta kira sunana, matsawa nayi gaban ta ta kamo hannu na "Naji abinda ya faru, in Sha Allah za'a ganta, ki cigaba da addu'a kinji, sannan zaki dawo waje na zanzo da kaina har inda kike, kiyi hakuri kinga abinda kika tarar karki ga ban baki lokaci ba." "Babu komai." Nace ina musu sallama, har waje ta rako ni kafin ta koma ciki. "Wai kinsan matsalar idon ki amma kike ta kuka haka, me yasa?" "Kamal dole nayi kuka, yanzu muje kawai zan maka bayanin komai ko a waya ne, Baba Altine na chan na jira na." "Shikenan." Yace yana bude min motar, shiga nayi ya tayar muka tafi. Muna zuwa kofar gida na ga motar Ya Anas a ajiye da alama yana ciki kenan, fitowa nayi na masa sallama ina shirin shiga gidan najii yace "Kinyi mantawa fa a bayan mota." "Mantuwa?" Nace ina kallon shi "Zo ki duba ki gani." "Ni da ba idon kirki ba, duba min menene?" "Ki zo dai ki duba." Yace yana kunshe dariyar sa, hararar sa nayi na dawo na bude bayan motar na zura jikina sosai a ciki, ji nayi an jawo ni gaba daya ciki, har glass din idona na nemam faduwa nayi saurin rike shi, fuskata daf da tashi har ina iya jin sautin fitar numfashin sa "Kina tunanin zaki guje min ko?" Kokarin kwace wa na hau yi ya rik'e ni gam, baki na bude zan sa kuka yayi saurin sa hannu a saman bakin nawa "Kina kuka sai na baki mamaki wallahi." Da sauri na hadiye kukan, ya sake ni nayi saurin fita daga motar, fitowa yayi shima ya leka yace "Kanina zaka iya wucewa ni sai gobe." Dariya Kamal ya saka yaja motar sa ya bar layin "Muje ko?" Yace yana kallo na, kasa daga kafata nayi saboda tunowa da nayi Anas na ciki, ganin naki motsi yasa shi kama hannu na ya shiga jana har cikin zauren gidan "Shiga zakayi?" Nace ina tsayawa ganin da gaske ciki yake son tura kansa "I want to see my daughter dan jikina ya bani baby girl kika haifa min, baki da right na hanani ganin gudan jinina kuma." Ya cigaba da jana, da karfi nasa na fizge hannu na ina sa masa kuka "Ohh shit.!" Ya dawo baya yana duba na "Kina so idon ki ya kara ciwo? Naji kamal na miki maganar ido." Cikin shassheka nace "Anyi kidnapping Iman, an kuma bata min ido na, bansan inda take ba." "Me!!!!!" Yace yana zaro ido waje, girgiza ni ya hau yi da karfi "Tell me wasa kike min dan Allah." Sai kuma yasa hannu ya shiga shafa saman ido na "Me yasa na tafi? Me yasa ban kara jira ba, menene amfanin rayuwa ta!" Yace a rikice yana jawo ni jikin sa, da sauri na fada ya saka hannu ya rungume ni sosai yana kokarin boye hawayen sa. "Waye Anan?" Yace yana haske mu da torchlight ɗin wayar sa. **** Hello mutanen arziki, I'm sorry for yesterday duk da dama nace idan na samu chargy zaku jini. Ga wata yar tambaya zuwa ga malaman zafafa "Wai shin idan namiji ya saki matar sa ba tare da sanin sa ba, shin ta saku ko kuwa? Menene hukuncin sakin da Farouk yayi wa Aminatu a littafin DG? Shin ta saku tun da da kansa ya rubuta sakin duk da baya cikin hayyacin sa, kuma ba da gangan ya sha abinda ya gusar masa da hankalin ba, ko kuma bata saku ba?menene hukuncin hakan a musulunce. Nasan muna da manyan malamai cikin mu. I ll be reading ur comments. Nagodea: DG*                *34* ★★★★★ "Waye anan?" Yace yana haske mu da torchlight ɗin wayar sa, da sauri nayi kokarin janye wa daga cikin sa amma sai yaki, ya sake kankame ni yana duban Ya Anas "Baka iya sallama bane ko me?" Wani banzan kallo Ya Anas yayi masa yana matsowa ransa na matukar suya da abinda ya gani, Aminatu rungume jikin wannan gardin, be taba tunanin ta a irin wannan yanayi ba, yana zuwa yasa hannu zai raba su Farouk ya nuna shi da yatsa yana maida ni gefe "Karka kuskura kasa hannun ka jikin matata wallahi." "Matar ka? Idan naki fa? Iskancin ya kai har ka biyo ta cikin gida saboda tsabar rashin mutunci ko?" "Waye wannan?" Yace cikin bacin rai "Ya Anas ne!" Na furta a dan tsorace dan duk na gama tsorata da yanayin sa "Ya Anas, me yake anan? Me ya kawo shi?" "Baka da bukatar sanin abinda ya kawo ni." Yace yana duban shi, sai kuma ya dube ni rai a bace yace "Zo ki wuce ciki." Ina kokarin daga kafata naji Ya Farouk ya rike ni "Don't you dare, idan kika daga kafarki anan wallahi sai ranki yayi mugun ɓaci." "Idan kai ka haife ta ba? Sai ka hanata, zo ki wuce kafin kiga fushi na." A hasale na dakatar dasu ganin suna neman charja min kai, cikin kuka nace "Dan Allah ku kyale ni da abinda yake damu na, ku dukka kuna da dama a kaina, dan haka babu wanda zan wa abun da yake so na bar daya." "Ya Farouk wannan shine Ya Anas, mutumin da ya tallafi rayuwa ta ya dubi maraici na ya rik'e ni tsakani da Allah dani da 'yata." "Ya Anas wannan shine Ya Farouk, tsohon miji na kuma mahaifin Iman." Tana kaiwa nan tayi saurin fadawa ciki tana rufe kofar da zata sadaka da zauren gidan, da sauri Anas ya fice daga gidan ba tare da ya sake duban inda Farouk yake tsaye ba kamar an dasa shi. Iska me matukar zafi ya furzar yana sake kallon gidan maganganun ta na masa yawo a tsakar ka, kenan tana nufin bata da alaka dashi a yanzu kenan? Da kyar ya iya jan kafafun sa ya kai kansa bakin titi ya tari abin hawa ya wuce gida. A zaune ya tarar dasu dukan su, magana suke a tsakanin su, kai tsaye dakin daya saba sauka ya wuce yana jin kansa na matukar sarawa. Har ya kwanta ya tuno da Kamal, dakin daya san zai same shi ya wuce kai tsaye, yana kwance yana kallon wani video a wayar sa yaji an turo,tashi yayi ganin Ya Farouk yasa shi dan sosa kai yana murmushi "First time na kwanan ka gidan nan right?" Daga mishi kai yayi yana dariya "I see." Sai ya mika masa waya "I need her number please." "An gama." Yace yana dariya, karba yayi ya saka masa, yayi godia ya juya ya koma in da ya fito. Sai daya fara duba jakar sa ya ɗan samu cookies yaci sannan ya kuskure bakin sa ya kwanta yana kashe komai na dakin. Aminatu na kwance ta rasa me yake mata dadi kiran sa ya shigo, kamar kar ta tashi haka take ji saboda yadda ko ina na jikin ta ke mata ciwo, ga wani irin ciwon kai me tsanani daya addabe ta tun ranar da aka rasa iman, duk da tana ji a ranta yarinyar ta na nan da rai sai dai hankalin ta ya gaza kwanciya musamman data fuskanci kamar akwai wata rigima data shafi Daddy da wanda ya dauke tan, da tunanin ta masu garkuwa da mutane ne su nemi kudi, sai dai a yanzu ta tabbatar wani game ne ake so a buga da rayuwar yar ta. Tun tana kuka da hawaye ta dawo na zuci, ta dukufa fadawa Allah dan shine kadai zai iya kawo mata dauki a cikin halin da take ciki. Ganin me kiran da gaske yake yasa ta lallaba da kyar ta jawo wayar, bata iya ganin me kiran ba saboda babu glass a idon ta, saboda haka daga kawai tayi tana maida kanta saman filon data tashi. "Assalamu alaikum." Tayi sallama a hankali, shiru ya biyo baya ta sake maimaita sallamar karo na biyu, jin babu alamun amsawa yasa tayi yunkurin kashe kiran yayi saurin katse ta "Karki kuskura ki kashen waya wallahi." Zare wayar tayi daga kunnen ta, ta kalli saman screen din kafin, kafin ta maida kunne ta "Tell me, me ya sami 'yata,wanne progress aka samu neman ta " "Ban sani ba nima, su Daddy ne akan case din." "Yasan yarmu ce?" "Ya sani jiya." Ajiyar zuciya ya sauke da karfi "Me yasa kika ki jin magana a gaban trash din nan, kinsan yadda maganganun ki sukayi hurting din na?" "Uhum " "Kiyi hakuri." Yace murya a kasa, bata amsa ba ya sake cewa "I'm sorry for everything." "Uhum." "Talk to me Dan Allah, ki min masifa ma if you like, in ma duka na zakiyi ki dake ni idan zai sa ki hakura." "Iman." Tace muryar ta na rawa "Taci abinci? An mata wanka? Lafiyar ta lau, She's just a child ya kake tunanin zata iya coping without her mother,abinda ya damen kenan Please Farouk!" Ta fadi sunan sa kai tsaye, tashi yayi zaune zuciyar sa na zafi yace "Nayi miki alƙawarin dawo miki da ita sound and in a good health, karki manta 'yata ce nima, responsibility nace ba tasu Daddy ba, zanyi duk yadda zanyi." Kukan ta na ya kara tsananta ya dafa kansa yana daidai ta zaman sa sosai "Tell me anything da kike tunanin zai bani hint wajen neman yata, fada min komai." Shiru tayi tana nazari, chan Amal ta fado mata da wayar data ji tana yi dazu "Adam, shine first suspect yanzu duk da bansan takamaimai alakar su da Daddy ba, Ina tunanin game ne yake so yayi playing da su, yasan wace ni yasan alaƙa ta daku tsawon lokaci yana bibiyata." "Sannan..." Sai kuma tayi shiru "Sannan me?" Yace "Amal, naji jiya tana waya, ban yarda da wayar da take ba." "Will you be my personal lawyer?" Yace yana murmushi Murmushin tayi kadan tana runtse idon ta "I love everything about Aminene ta." Yace yana jan numfashi, wani iri taji ta sake danna kanta sosai a saman filon data ke kai, tana jin sautin fitar numfashin sa a hankali. "Goodnight, kiyi mafarki na da Iman mun saki a tsakiya kinji?." Daga kai tayi kamar yana ganin ta ta ajiye wayar tana lumshe idon ta. File din ta dake kusa da ita ta daga filon tasa ba tare da ta buda shi ba kamar yadda tayi niyy. *** Yana ajiye wayar ya shiga zagaye a dakin, badan dare ba sai yaje dakin Amal. System ɗin sa ya ciro cikin kayan sa ya kunna ta, e-mail ɗin da akayi masa wajen 3days back yaja hankalin sa sosai, a tsanake yake bin komai yana gid'a kansa cike da tsananin farin ciki *** Kukan da take ne ya katse sakamakon wayar ta data dauki suwwa,da bayan hannun ta ta goge fuskar sannan ta daga tana karawa a kunnen ta. "Baby kina jina? Karki bari asan muna waya dake, zan dan daina kiran ki kwana biyu amma ina so kizo address din da zan turo miki akwai abinda nake so na baki kiyi min wani aiki akai kinji?" "Toh." Ta amsa a cunkushe "Me ya faru?" Yace jin muryar ta a shake "Ba komai." Tace tana kashe wayar, ba'a jima ba text message ya shigo, bata bude ba ta cillar da wayar tana kwanciya a kasa, babu abinda yanzu take bukata face ace auren ta da Ya Farouk na nan, ganin Aminatu da tayi yau ya kara dagula mata lissafi. Kishin ta take sosai kamar zata mutu. Da kyar ta samu bacci barawo ya sace ta ba tare da ta shirya ba. Da safe ta tashi a makare idon nan duk ya kumbure, tana jin maganganu a falon tayi tsaki ta fada toilet, wanka tayo tazo ta gyara fuskar ta kafin ta duba text message ɗin da yayi mata, duba address din tayi ta ajiye ta karasa shiryawa ta fito falon. "Idon ki kenan Amal? Duk jiya baki ji alamun akwai baki gidan nan ba?" Dadah ta tuhume ta cike da mamaki "Na shigo da magriba kuna sallah, bacci nayi da wuri kinsan na kwaso gajiya." "Okey yayi kyau, baki ga bakuwa ba?" "Ina kwana?" Tace a gajarce "Lafiya lou." Anty Safiyya ta amsa kafin tace "Girma ba wuya Amal an zama yan mata." Haushi ne ya kama Amal ta tashi ta koma daki ta zauna tana tunanin yadda zata fita ba tare da kowa ya gane ba. Duk tunanin ta ya tsaya ta rasa ya zatayi gashi daga ganin alamun zaman da Dadah tayi a falon babu ranar tashi. Curtains ta yaye jin alamun za'a ta da mota, Kamal ne tsaye suna magana da Farouk, jingina tayi da bangon tana kare masa kallon tsaf, zuciyar ta bata san komai ba sai soyayyar sa, yayi kyau ya sake mirjewa kamar bashi ba. Ganin ya juyo yasa tayi saurin sakin labulen tana sauke ajiyar zuciya. Cigaba tayi da tunanin mafita har zuwa sanda ta sake jin maganganu sun sake karuwa a falon Alamun taba kofar dakin taji kafin tace wani abu ya budo ya shigo kai tsaye. "Come out!" Yace daga bakin kofar kafin ya juya, hadiye yawu tayi da k'yar ta tashi kamar wadda kwai ya fashe wa a ciki ta fito falon. Daya bayan daya ta shiga raba idanun ta tana binsu d kallo, kafin ta shiga jan kafar ta isa gaban su tana zama kasa. Daya Daya ta gaishe dasu Daddy zuciyarta na cike da tsoron kiran da aka mata "Ina wayar ki?" Ya Farouk ya mika mata hannu alamun ta bashi, gaban tane ya fadi ta hau rawar jiki. Daka mata tsawa yayi data firgita ta tayi saurin miƙa masa wayar, kai tsaye call log dinta ya fara shiga ya duba numbers din datayi waya da call duration kafin ya fita ya shiga messages, da sakon shi ya fara cin karo ya yi shiru yana karanta sakon, tabbas hasashen da Aminatu take gaskiya ne, Amal nada masaniya akan komai, number ya dauka akan wayar shi da message ɗin ya isa gaban Alhaji Marwan ya mika masa wayar yana komawa wajen zaman sa. "Menene dalilin tara mu da kayi anan Farouk?" Alhaji Marwan yace yana kallon wayar Amal din ba tare da ya duba ba. "Daddy ka rike wayar ko da za'a kira, ina da maganar da zanyi kafin a gangaro maganar wayar." "Toh muna jinka." "Da farko dai ina neman yafiya a bisa laifin dana aikata na tafiya na bar kasar,hakan ya faru ne a bisa dalilai na da nake ganin sun kai na zartar da komai. Sai dai ni kaina bani da masaniyar takamaimai abinda ya faru, tun bayan da ƙaddara ta haɗa ni da Aminatu har aure ya shiga tsakanin mu zuwa sanda na bar gari zuwa wani aiki da dawowar da nayi na tarar da mugun labari da bani da masaniya akai." "Naso kwarai Daddy ya bani dama ko sau daya na kare kaina amma hakan be samu ba, a dole na tsananta bincike anan ne na gano akwai hannun Amal a cikin abinda ya faru daya jawo rabuwa ta da Aminatu." "Na kirata na tuhume ta da laifin dana kamata dumu dumu na kuma bukaci na ji wanda ya sakataa, to my surprise sai gashi ta kira sunan mutanen da nafi kusanci dasu, Dadah da Ja'afar wanda duk duniya ina ganin idan akwai wanda na yarda dasu toh su biyo bayan su,wannan dalilin shi yasa ni tafiyar dole dan bazan iya zama ina kallon su da abun ba." "Innalillah wa inna ilaihi raji'un." Dada tace tana kallon Amal kallon tsantsar mamaki. "Muna sauraron ka." Uncle Aliiyu yace "Na tafi da clip din da aka dauka lokacin da nake rubuta sakin da kuma voice recording din da akayi lokacin da aka kirani a gaban kowa dan a tambaye ni dalilin abinda na aikata. Da fari na shiga rudani sosai dan bani da hujja da zan ƙaryata hakan, na farko dai murya ta ce gata nan, na biyu ni ne zaune ina rike da takarda da biro." "Tsawon lokacin nan nayi shi ne cikin binciken yadda akayi hakan ta faru, ban samu ba, haka na hakura na bar wa Allah komai. Sai gashi jiya cikin hukuncin Ubangiji mutumin da ya taimaka min kwarai wajen bincike na yayi min e-mail inda yake tabbatar min da duk abin da yake cikin clip din da kuma abinda yake a recording din nan shiryayye ne anyi amfani da lastest technology da wasu set of intelligent agencies dake ƙasar Amurika ke amfani dashi wajen sauya abin, yana so na tsananta tunani na gano abinda ya faru a rana makamanciyar da abin ya faru." "Tsawon daren jiya ban runtsa ba ina tunanin abubuwan da suka faru, tunani na ya dawo nan take sanda nake tuna tabbas Amal ta kawo min abu nasha a ranar sannan munyi hira data shafi Aminatu tana min tambayoyi ina amsawa sannan tabbas ranar ina rubutu ne ta tarar dani, wannan abubuwan su aka juya aka sauya zuwa komai, ba dani aka yi waya ba sai dai tabbas murya ta ce,magana ta ce aka hada yayi daidai da abinda Daddy zaku tuhume ni akai." Murmushi yayi me ciwo yana janyo system ɗin sa ya tura ta gaban Daddy kafin ya dora "Ina fatan wannan shaidar kadai ta isa ta wanke ni daga zargin da ake min sannan ina so ta fada a gaban kowa gaskiyar abinda yake faruwa. Me yasa lokacin dana tuhume ta ta nuna min tabbas na rubuta takardar kuma bana hayyacina, me yasa ta boye min gaskiya ta sake nisanta ni da matata da yata, me nayi mata haka mai zafi ta na chanchanci wannan?" "Annamimiyar Allah!" Dadah tace tana saka kuka, kukan Amal take sosai itama ta kasa cewa komai, girgiza kai Daddy yayi cikin yanayi mara daɗi yace "Adam yayi amfani da yarintar ta ya bata mata tunani." Wayar ta Alhaji Marwan ya duba kafin ya mika wa Daddy shima yaga text message ɗin "Amal me yasa ki aikata haka?" "Daddy kayi hakuri." "Tell me, zan saurare ki, me yasa? Saki yayi ko? Me yace miki?" "Daddy ni tausayin sa nakeji, babana ne, ina son sa yace kuma kashe shi zakuyi tunda kai soja ne." "Haka yace miki?" "Eh." "Shikenan daina kuka, mesa zamu kashe shi, ba haka bane kinji? Shiryawa zamuyi dashi mu nemi gafarar sa laifin da mukayi masa, can you help us?" Shiru tayi tana tunani, kallon fuskar Daddy take, babu alamun karya a maganar sa, bayan haka ma be taba musu alkawari ya saba musu ba komai shi yake musu, sai ta samu kanta da daga mishi kai. "That's my girl, bata wayar ta MD, text him kice kina hanya kinji? Kije ki gan shi babu damuwa." Kallon sa tayi ya dage mata kai cike da gamsar wa "Kije Allah yayi miki albarka, karki sanar dashi munyi maganar nan a waya sai kinje yanzu text kawai zakiyi masa." Tashi tayi tana goge fuskar ta ta wuce daki. "Me hakan ke nufi?" A cewar Uncle Aliyu "Shine kawai mafita, bin ta zamuyi dole sai an kama Adam a hannu komai zai warware." "Lallai akwai banbanci, na kara tabbatar da kai din jami'in tsaro ne, kudos." Duk sukayi murmushi banda Farouk da yake kallon su kawai. **** Kiran wayar ta ya fara yi bata daga ba, kai tsaye ya shiga gidan bakin sa dauke da sallama, shiru gidan lokacin Baba Altine ta shiga makota siyo koko, Aminatu na toilet tana wanka saboda haka bata ji shigowar sa ba, sakon da Ya Farouk ya bashi ya ajiye a gefe yana kallon falon, idon sa ne ya sauka akan file din dake yashe a kasa, garin sauri ta manta ta dauke filon bata dauke shi ba, kamar kar ya taba sai kuma yaji yana son ganin date of birth din ta ganin file ne na asibiti. Kai tsaye yasa hannu ya dauka, sunan asibitin dake rubuce a saman file din dayayi daidai da irin sunan dake jikin birth certificate d'insa shi ya kara jan hankalin sa, murmushi ya saki yana jin dadin ganin ashe ma asibiti daya aka haife su,yana budewa yan kananun passport din dake ciki suka fado be bi takansu burin sa kawai ya ga date ɗin ta dan suna yawan musun ta girme shi sanda suna makaranta. Mamaki ne ya kamashi ganin hatta date da time na haihuwar su daya ne, be kula da sunan ba yana dariya ya rufe ya tsuguna ya tattaro hotunan guda biyu, cikin tsananin mamaki yake kallon hoton yana sake kalla, hoton Ammi ne da Daddy, duk da dadewar da akayi da daukar hoton wanda idan ba sanin su kayi sosai ba ba lallai ka gane su ba, a birkice ya sake bude file din ya shiga bin sunan ta dake rubuce cikin babban harafi "AMINATU MD" Sakin file din yayi ya fadi a wajen daidai lokacin da Aminatu ta fito daga dakin a shirye tana kiran Baba Altine, ganin shi tsaye cikin wani irin yanayi yasa ta ƙaraso da sauri tana tambayar sa menene, be tsaya bata amsa ba ya juya da sauri ya fice daga gidan zuciyar sa na wani irin harbawa. Masha Allah... Duk naga bayanan ku, kuma zanzo insha Allah da hukuncin hakan a musulunce, Nagode kwarai Allah saka da Alkhairi. Allah ya taimaka ya bamu Sa'a baki daya. Rano DG*                *35* ★★★★★ Tsaye tayi cikin tarardadin abinda ya faru, sai kuma ta bi file din nata dake yashe kasa da kallo kafin ta tsuguna ta tattara komai tana sake dubawa. Ledar daya ajiye gefe me tambarin Shoprite ta dauka ta bubbbude breakfast ne me rai da lafiya sai yar karamar red rose me kyau sosai, dan karamin note din dake ciki ya fado, murmushi ta saka "I love you" Aka rubuta da wani irin rubuth me matukar birgewa, wato ya zama baturen karfi da yaji kenan, wani iri ta dinga ji kamar tana tafiya akan gajimare. ***Yana fita ya shiga motar sa ya kifa kansa saman sitiyari, fuskar Aminatu da bata da maraba da ta Ammin sa ta shiga yi masa yawo a saman ƙwaƙwalwar sa, tsawon wannan lokaci ashe da Ammi take masa kama ya kasa ganewa sai yanzu, hoton fuskokin iyayen nasa ya dinga kokarin haɗawa da nasa dana Aminatu sai dai ko kusa babu digon kama da sukayi dashi, sau tari yakan tambaya kansa da wa yake kama cikin iyayen nasa ganin babu yasa ya bawa kansa amsar kila wasu ya biyo a cikin dangin nasu tunda dama hakan na faruwa. Tunanin sa ne ya tsaya chak, idan har Aminatu diyar Daddy da Ammin sa ce, shi kuma fa da yake da shekaru da komai irin nata ballantana yace ko kanwar sa ce, ji yayi zuciyr shi ta sake karaya da kyar ya lallaba ya bar kofar gidan ba tare da sanin kowa ba ya bar garin domin yana da bukatar sanin komai. *** Ammi na zaune tana kallon talabijin cikin daya daga cikin jerin kujerun alfarmar dake zagaye da babban falon nata, rashin yara na matukar damun ta, tun tana yawon asibiti har ta hakura ta daina, babu wata matsala ta kai tsaye da za'a kira ta dashi daya hanata haihuwa. Yanayin yadda ya shigo mata a firgice yasa tayi saurin ta tashi zaune tana kallon sa. "Kamal!" Ta Kira sunan sa, kallon ta yayi sai kuma yayi saurin tattaro nutsuwar, tunowa da yayi bazai bari kowa ya san komai ba har sai ya gano ainihin abinda yake faruwa yasa shi sakin fuskar sa sosai ya zauna kusa da ita yana dora kansa a saman kafadar ta "Ammi nah." "Karka cemin dogon tuki kayi, ina Daddyn ya na ganka kai kadai?" "Ammi ji nayi ina so nazo gida, ga Old Woman ta matsa shisa kawai na gudo gida Daddy ma be san na taho ba." "Maganar yarinyar ce har yanzu Kamal?" "Ki taya mu da addu'a Ammi, komai zai daidaita." "Shikenan, amma gaskiya na soma gajiya da zaryar da kake tsakanin nan da chan, hanyar nan da babu kyau akwai risky." "Babu abinda zai faru In Sha Allah." "Allah yasa." Ta amsa ba don taso ba. Bedroom d'inta ya shiga, ya dubo dukkan takardun sa masu muhimmanci, ciki har da birth certificate d'insa original din, da address din asibitin da aka haife shi ya wuce dasu dakin sa. Be zauna ba ya tafi wajen Hajiya Turai, har dare yana chan suna hirar su gwanin sha'awa sai dai rabi da kwatan hankalin sa baya wajen yana tunanin yadda zai soma binciken kansa ba tare da sanin kowa ba. *** Sai data fara sauya shigar jikin ta sannan tayi masa text message gata nan ta fito, handbag dinta dake ajiye saman drawaer tayi nufin dauka bata ganta ba, dubawa ta hau yi kafin da kyar ta gano ta, ta kusa shigewa karkashin gado, ba tare da tunanin abinda ya kai jakar wajen ba ta tura wayar ta fito, duk basa falon hakan yasa tayi ficewar ta kai tsaye, bata bi takan driver dake gidan ba ta fita titi ta tari abin hawa ta fada masa inda zai kaita. Motoci biyu ne masu tsaron lafiyar Daddy sai motar da suke ciki su hudu wadda Farouk yake tukawa sai Uncle Aliiyu a gefen sa, Daddy da Alhaji Marwan na baya, tracker da Farouk ya sa mata a jikin jakar ta suke bi har zuwa sanda ta isa gaban building din da yake incomplete, saukowa tayi ta sallami me napep ɗin kai tsaye ta kutsa kanta ciki tana kokarin kiran number tasa. A daidai lokacin ya saka Iman a gaba ta ƙatuwar wayar charger, ko ina na jikin ta duka ne beyi la'akari da kankantar shekarun ta ba, duk da yana bata abinci amma idan tayi mishi kuka dukan ta yake kamar ya samu babba, shigowar Amal wajen ya saki wayar hannun nasa yana dora hannun sa a saman bakin sa "Shissh." Da sauri ta hadiye kukan ta saka dukkan hannayen ta biyu ta rike saman bakin ta "Daddy, yarinya ce fa." Amal tace tana matsowa kusa da su "Bani da time na tabbata by now Ali ya sanar dasu ina raye, ina so ki bawa Hajara wannan sakon, zata san yadda zatayi dashi." "Toh yarinyar fa?" "Itace makamin da zan yi amfani na yaki Kabir da MD, ina bukatar dukiya ta, ina so komai ya dawo waje na, na maida su abin kwatance kamar yadda suka zalunce ni." "Idan har kana da damar hakan ba?" Farouk ya shigo kai tsaye fuskar sa babu digon Rahma ko sassauci,kallon Amal gyatumin nata yayi cikin yanayi na tuhuma, "Amal yaudara ta kikayi? Duk abinda nake ba saboda ke nake ba?" "Bansan zai zo ba ai." Tace tana matsawa gefe gami da riƙe hannun Iman "Idan bake kika fada musu ba, ya akayi suka san nan?" "Duk yadda kake kafkaf tsawon wannan lokaci baka taba tunani wannan ranar ba?" Zai yi magana sai kuma hankalin sa ya kai kan jakar hannun ta "You are good as nothing Amal." Yace ganin abinda ke jiki ba tare da ta sani ba. Sosai hankalin sa ya tafi kan yar karamar kyakkyawar yarinyar dake tsaye tana raba ido, fuskar ta har dan tashi tayi saboda marin da take sha wajen Adam, babu tantama itace yar sa, yar da bata san mahaifin ta ba, very cute and innocent soul kamar Aminatun sa, takowa ya shiga yi yana zaro bindigar dake jikin gefen wandon sa daya karba wajen Daddy, kafin ya karasa Adam ya ciro tasa cikin zafin nama yayi kokarin riko hannun Iman, da sauri Amal ta hankad'a ta wajen Farouk yayi saurin riƙe ta yana sake dagowa. "Amal!" Ya ambaci sunan ta da dan karfi ganin abinda tayi masa, cikin zafin nama ya fizgota ya saita bindigar sosai a kanta "Karka kuskura ka matso, idan ka matso zan saka bindiga na harbe ta har lahira." Kuka Amal ta saka cike da mamakin abinda mahaifin nata ke shirin aikatawa. Dariyar rainin hankali Farouk ya saka kafin yace "Wa zakayi fooling? Yar ka ce fa. Idan ka ga dama ka kashe ta yanzu waya damu?" "Ok." Yace yana saita bindigar sosai yana kokarin jan kunamar bindigar Daddy ya dakatar dashi. "Me kake bukata? Me kake so damu Adam? Me muka yi maka haka?" "Ita tsohuwar bata fada muku abinda tayi min ba?" "Yanzu me kake so?" "Duk abinda kuka dade kuna tarawa, ina nufin dukiyar ka baki daya data MD, shine kadai zai fanshi duk abinda kukayi min ." "Kazo muje gida a zauna sai a san yadda za'a bullo wa al'amarin, hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar Adam." "Ni na dade da sa gatari na yanke nawa, bani da alakar komai daku, babu abinda nake so fiye dana ga kun wulakanta, wulakanta mafi kaskanci." "Daddy wanda yayi nisa baya jin kira, koma me akayi masa ya kamata ya zama mai yafiya, ka daina lallaba shi ba zai taba fahimta ba." "Farouk kai yaro ne, Adam zaka karbi tayina kazo muje gida mu yi sulhu?" "Har abadah." Yace yana sake riƙe bindigar sa sosai akan Amal dake kuka sosai har da majina. "Well then, bani da zabi face na yake ka." Yace yana nuna wa yaran sa hannu, kafin kace me sun zagaye Adam sun saka tsakiya, "Retreat or die!" Dariya ya saka "Ka zata bani da cover, baka taba mamakin yadda na iya surviving this long years ba tare da na taba haduwa da wani ba, while I'm leaving right under ur noses? Ba kayi tunanin hakan ba? Adam bazai taba kamuwa cikin sauki ba, hatsibibine ni fiye da yadda kake tunani, sannan yanzu zamu fara wasa, best of luck Gen!" Daga sama aka rufe su da kasa, nan da nan idon su ya rufe ruf kowa ya hau kici-kicin yadda zai ya kare idon sa, a lokacin ya samu ya gudu ba tare da sun ankara ba, sai da komai ya lafa suka neme shi suka rasa ya gudu. *** A mota Farouk be iya tuki ba dole daya daga cikin sojojin suka karbi tukin ya rike Iman da ta galabaita sosai, Amal na gefen sa ta cusa kanta tsakiyar kafar ta tana faman shassheka, haushi da bacin rai kukan nata ke kara masa,ji yake kamar ya ce su tsaya a sauke ta. Kai tsaye asibiti suka wuce da ita, domin tana bukatar a duba lafiyar ta. Sosai ta galabaita da yawan kukan da take sai rashin abinci ne suka haɗar mata, gashi da alama sauro yayi mata mugun cizo da har ya saukar mata da zazzaɓi me zafin gaske. Drip aka daura mata da allurai sannan aka gyara mata wajen da duk taji ciwo. A gefe Amal ta rakube bayan su Daddy sun tafi, Farouk be sake bin ta kanta ba ya shige dakin da aka kwantar da Iman din yaja kujera ya zauna ya zuba mata ido, babu abu daya daya raba ta dashi har duhun fatar shi dauka, idanun ta ne kawai irin na Aminatu da dan karamin bakin da zakayi tunanin karamin chokalin tea ne kaɗai zai iya samun sukuni shiga ciki. Sosai ya shagala da kallon ta yana jin farin ciki mara misaltuwa, da zarar ta dawo daidai zai kwashe su su bar kasar ba zai iya zama ba, dan ya lura fadan na su Daddy me karfi ne dan haka bazai yarda a kara involving rayuwar aaminatu ko Iman ba. Wayar sa ya ciro ya lalubo number ta, tana bukatar sanin halin da ake ciki ko dan lafiyar ta ita ma. A lokacin zaune Aminatu take ta kunna karatun suratul Bagra tana saurara, sau uku kenan tana kiran Kamal baya picking sai ta hakura ta bari ta sake gwadawa anjima, saboda haka data ji karatun ya tsaya alamun shigowar kira ta zata shine. Number data gani a saman screen din ta sakata komawa ta lafe sosai a jikin katitar kafin ta daga "Ina miki albishir da na cika alkawari, gani ga Iman." A zabure ta mike "Dan Aallah!" "Allah." Yace cike da gamsarwa Sai ta saka kuka "Kukan me? Ke da zaki gode wa Allah." Da sauri ta kai goshin ta k'asa cike da farin ciki tayi wa Allah godiya kafin tace "Kuna ina yanzu? Lafiyar ta kalou? Me ya sameta? "Duk wannan tambayoyin? Muna nan premier clinic an sa mata ruwa." "Owk gani nan." Tace da sauri tana kashe wayar. "Baba!" Ta kwala Kira "An ga Iman." "Alhamdulillah, Alhamdulillah." "Dauko hijabin ki muje suna asibiti." "Ina jiran ku a mota." Yace yana juyawa. "Yaushe Ya Anas yazo?" "Sanda kika fara waya, yana tsaye nace ma ya shigo falon yaki yace na miki magana." "Ok." Tace tana yin gaba. **** Da kallo yabi motar kafin ya kada kansa yana kara waya a kunnen sa "Itace?" "Ok done!" Yaja motar ya bar layin. ***Kamar kurame babu wanda yayi wa wani magana har suka isa Asibitin, tambaya sukayi aka nuna musu dakin, da Amal suka fara gamuwa tana daga kofar dakin akan wani benci ta kasa shiga ciki, sallama sukayi mata ta dago tana kallon su, amsawa tayi ta maida kanta gefe. Idon sa akan kofa yaji an turo, idanun su ne suka hadu waje daya, tayi saurin janye nata ta isa gaban gadon da sassarfa, kuka ne ya taso mata tayi kokarin tsaida shi sai dai duk da haka sai da ya zobo, Baba Altine ce ta karasa cike da jimami take kallon Iman din "Allah sarki." Cikin takun kasaita ya shiga takowa har ya iso gaban su, kallon kallo sukayi wa juna kafin Farouk ya dauke kansa yana jan karamin tsaki, hannu Anas yasa ya dafa kan Iman din akayi saa kuwa ta bude idon ta,tana ganin shi ta saka kuka tana kiran Abba tana mika masa hannu. "Yi shiru kinji my angel." Yace yana shafa kanta Riko hannun Aminatu tayi dana Anas tace "Karku tafi ku barni kai da Ummi, kullum sai nayi kuka yayi ta min masifa kuka ki zuwa ku tafi dani." "Karki damu kinji? Ba zamu kuma barin ki ba." Sosai ran Farouk ya bci, ya hade girar sama data kasa ya shiga watsa ma Anas harara, ita kanta Aminatu bata bi ta kansa ba kamar ma ta manta dashi a wajen, murya ya shak'e yace "Ba'a wa yaro hayaniya aka musamman wanda ba lafiya ce dashi ba, tana bukatar hutu an gode da dubiya." Sarai Anas ya gane dashi yake, be kula shi ba ya sake shafa kan Iman din "Baby Bari na dauko miki chocolate a mota ?" "Uhum uhum..Karka ki dawowa." "Zan dawo yanzu kinji?" Daga mishi kai tayi tana lumshe ido "Ina so muyi magana." Yace yana duban Aminatu, kallon Farouk tayi da sauri taga yadda yayi, fuskar nan tasa kamar wuta haka ya tamke ta. "Baki ji bane Aminatu, yayanki Anas yana so kuyi magana." Baba Altine tayi tsagal, yaki Aminatu tayi ta tashi da nufin bin sa dan tuni yayi hanyar fita Farouk yasa hannu ya finciko ta da karfi har sai da glass din idon ta ya cire ta fado jikin sa. Da hannu ya nuna ta cikin bacin rai yace "Karki manta akwai igiyar aure na akan ki, ke idan ma babu ban yarda ki kebe da wani gardi ba wallahi, zan baki mamaki idan kikayi gigin aikata haka." "Idan kai ne ka haife ta sai ka hana, dame kake takama ne wai?" Anas ya katse shi a hasale, da hannu Farouk yayi masa nuni da Iman dake kwance "Kaga abar da nake takama da, ba kuma zaka taba samun irin ta ba har abadah sai dai abi wani sarkin." Cikin bacin rai Anas ya bar dakin, ko motsi Aminatu batayi ba, ita mamakin yadda Farouk ya zama take, kamar ba Farouk dinta na baya ba me saukin kai da son mutane ba. *** Duk tsare tsaren da zaiyi ya gama shi, hatta address din asibitin da komai ya gama haɗawa waje guda, baya so Ammi tasan shirinsa saboda haka sai yayi mata karyar Kano zashi akan wasu harkokin Daddy da yake so ya fara duba wa, sosai taji dadi ta bishi da addu'a. Kai tsaye tasha ya nufa karo na farko a rayuwar sa daya shiga motar haya, kamar akan kaya haka yake jin sa, sai dai bashi da wata hanya sai hakan. Kano suka fara zuwa kafin ya kuma samun wata motar zuwa Katsina. Madam Inno😂 na zaune ta zabga uban tagumi tunanin rayuwar baki daya take, abubuwa da yawa sun faru, wasu ma nakan faruwa ciki har da yanayin da suke ciki yanzu na matsi da babu, duk jarin nata ya kare, ta dawo ta tsuguna sauran mazan gidan ne ke kokarin taimaka musu wani zubin da abinda zasu ci. Nan da chan bata iya zuwa saboda yadda abinda ya faru ya gama zagaye ko ina na kauyen hatta ƙananan yara sau tari idan ta fita sai dai taji suna maganar hakan yasa ta tattara fitar baki daya ta watsar ta zauna ta fawwala Allah komai tana cigaba da jinyar Baba da ke cikin mawuyacin hali tsawon wannnan shekarun babu wani sauki sai godiyar Allah. **** Yinin yau baki daya be duba wayar sa ba, aiki suke sosai akan wani kamfanin man gyada da yake son budewa a Niger, rabon da su hadu da Daddy yau kwana biyu kenan, shima ya zama busy sosai yana shirye shiryen ritaya ma saboda ya tattara hankalin sa waje guda, tun bayan abinda ya faru basu sake maganar Adam ba, sun barshi a matsayin ihu bayan hari ne kawai amma babu abinda zai iya, sun tuntubi Dadah da maganar tace su sake nata lokaci dole suka tattara suka ajiye komai. Bayan ya gama duba komai ya tattare su waje guda, sakatariyar sa ya kira ya bawa ta kai office din Admin human resources sabida yana so komai ya kankama. Babbar rigar dake jikin sa ya cire ya rataye ta a saman hanger kafin ya isa gaban dispenser ya tsiyayi ruwa ya sha sosai, sannan ya koma ya zauna yana jawo wayar tasa domin suba sakonni. Karon farko daya ji zuciyar sa tayi wani irin bugawa da karfin gaske, yasa hannu ya dafe ta yana kara bude idaon sa sosai akan sakon. _"50million na dan ka dake amsa sunan ka KAMAL MARWAN DIKKO , 100million kuma na yar da baka san tana rayuwa ba, wadda jinin ka ke yawo a cikin jijiyoyin jikin ta, bata san kanta ba, bata san wacece ita ba,tayi rayuwar kunci da bakin ciki duk ta sanadi na."_ _"Dukkan wannan zabi ne ya rage naka ka zaba, idan kuma ba zaka iya sadaukar da million 150 ga yayanka ba, ina fatan zaka iya sadaukar da matar ka ba tare da sisin ka tayi kuka ba. Zabi ya rage ga shiga rijiya!"_ Adam Rano 😍😍💯DG*                *36* ★★★★★ Number ya kira da sauri, ringing d'aya aka daga "Adam, kana jina?" Yace jikin sa na rawa "Ina jinka." Ya amsa a gadarance "Yawwa, me kake nufi da sakon nan? Ban gane komai ba, me hakan ke nufi." "Ina da tabbacin kai cikakken bahaushe ne ko? Lokacin boye boye ya kare ina so kaje kayi bitar abinda ka karanta da kyau zaka gane inda maganganun suka dosa, sai dai ka sani rayuwar Kamal na cikin hatsari, haka ma rayuwar yar ka da ni kadai zan iya tabbatar da hakan." "Ya..." Katse kiran yayi ba tare da ya jira abinda zai ce ba, hanyar fita daga office din Alhaji Marwan yayi yana kokarin neman number Kamal, a kashe take cikin tsananin tashin hankali ya juya akalar kiran zuwa ga Ammi, fitowar ta kenan daga banɗaki taji wayar ta dake saman mirror na neman agaji, karasa wa tayi ta dauka "Ina Kamal?" Yace a kid'ime "Be dade da tafiya ba ai, na zata kunyi magana dashi kafin ya tafi, wani aiki ka bashi?." "Ina ya tafi? Ban aike shi ko ina ba, be kuma fada min inda zashi ba, subhanallah!" "Me ya faru?" "Ina zuwa." Yayi saurin katse kiran yana neman layin Daddy Hankalin ta ne ya tashi ta hau kiran layin Kamal din sai dai duk a kashe, tunanin Aminatu ne ya fado mata, bata raba daya biyu yarinyar ce tasa shi tafiya ba tare da izinin mahaifin shi ba, sannan yayi mata karya akan aikin Daddy xai je yayi, take tsanar yarinyar ya shiga zuciyar ta, ta hau zagaye a dakin tana tunanin mafita, alk'awari tayi ma kanta idan wani abu ya samu danta ba zata taba barin ta ba. Gaba daya Alhaji Marwan ya birkice wa Daddy, tunanin sa kar wani abu ya samu Kamal d'insa, dan be san yadda zai iya dauka ba, a gefe guda kuma tunanin wacce yar tashi Adam yake nufi, iya sanin sa bashi da wata 'ya kawai Adam naso yayi wasa da hankalin sa ne tunda ya riga yasan tun bayan haihuwar Kamal din Ammi bata sake ko da batan wata bane, shiyasa kawai ya share maganar fatan sa kawai ya samu Kamal a waya yaji inda yake dan kwarai ya fara tsorata da lamarin Adam,ya soma tunanin komene akayi masa haka toh me girma ne a wajen sa. **** Isar su Katsina ana ta kiraye kirayen sallar isha'i, hotel ya samu ya sauka da nufin da safe ya karasa garin na Shagari, baya jin dadin komai burin sa ya gano wani abu da yake da alaka dashi da Aminatu. Be wani iya baccin kirki ba da sassafe ya shirya ya fita, asibitin ya fara zuwa da yake shi ba a cikin garin yake ba, ya tarar da wani mutum a reception, sallama yayi masa gami da mika masa hannu sukayi musabiha kafin yace "Wani muhimmin abu ne ya kawo ni, takanas daga Abuja, ina fatan zan samu information din da nazo nema." "Ok me kake bukata?" "A asibitin nan aka haife ni, ga date nan da komai a jikin birth certificate d'ina, idan babu damuwa ina so ka binciko min file din da mukayi amfani dashi sanda muke zuwa Asibitin." "Menene file number din?" "0023." "Ok ka dan zauna mu binciko shi, an kwana biyu zai danyi wuya." "Owk." Yace yana samun waje. Yana zaune mutumin ya dawo, hannun sa ya kalla ganin babu file din yasa shi cewa "Ba'a samu ba ko?" "Wallahi ba'a samu ba, abin mamaki duk daadewa ba'a rasa file amma wannan babu shi kwata-kwata." "Dama nasan ba za'a samu ba. Amma dan Aallah ko zan iya sanin adadin mutanen da aka haifa a asibitin nan ranar da aka haife ni?" "Da kamar wuya gaskiya, kaga an jima kuma mu ba wai muna da record bane cikin computer, manually ake komai dan haka gaskia ba zai yiwu ba." "Idris ina aka ajiye file din Samira ne?" Maganar ta ta riga ta ƙarasowa wajen, babba ce a kalla zatayi kusan sa'ar Ammi, kallon kamal tayi kadan kafin ta maida hankalin ta wajen wanda ta kira da Idris din tana masa magana, "Wallahi Sister Asibi bansan inda aka sashi ba, ko yana wajen Lawal a tambaye shi." "Sister Asibi?" Sunan ya shiga masa yawo aka, idan har be manta ba shine sunan da ya gani akan file din Aminatu, sannan shine same sunan dake jikin nasa takardar, da sauri ya ciro ta ya duba, hakan kuwa ne, murmushi yayi ya bita da sauri ganin har ta kusa shiga wani office "Dan Allah tambaya ce dani." Ja tayi ta tsaya tana duban sa "Ya akayi ɗan saurayi?" "Am nidai sunana Kamal Marwan Dikko..." "Anan aka haife ni, ranar 5 ga watan February, 1996." "Kaga akwai ayyuka da yawa kaina, ina ganin ka nemi wani sai kayi masa bayani." Tayi gaba da sauri, shan gabanta yayi yana bata rai sosai ganin da gaske so take ta gujewa maganar dan tun sanda ya ambaci sunan sa ta nuna alamun tsoro a idon ta "Ki tsaya muyi magana ta fahimta kafin na sanar da hukumar asibitin, kece kika karbi haihuwa ta ko? Dan sunan ki ne a rubuce jikin takardar haihuwa ta." "Shigo ciki." Tace tana yin gaba, bin bayan ta yayi har wani office, suna shiga ta rufe kofar tana kallon shi "Me kake so?" "Ina son sanin waye ni? Me yasa sunana yayi daidai da na wadda aka haife mu rana daya, lokaci daya da ita, me hakan ke nufi?" "Kai zan tambaya dan ban gane me kake nufi ba." Tace tana juya masa baya, murmushi yayi me ciwo kafin yace "Ina bukatar sanin gaskiya, karki boye mun komai ki sanar dani, idan kuma ba haka ba..." "Me kake so ka sani?" "Waye ni? Wacece Aminatu? Ko ana so ace min mistake akayi wajen rubuta mana sunan mahaifi daya bayan an haife mu a lokaci daya a rana daya kuma asibiti daya? Ko ana so a cemin mu ɗin yan biyu ne, nasan ana iya samun suna iri daya, sai dai ba irin namu ba, hoton Daddy da Ammi dake jikin file dinta fa? Shima kuskure ne? Ba zai taɓa yiwuwav ba." Hadiye yawu tayi me kauri ganin yadda yaron yake so lallai sai ya tono abinda ya dade da shudewa, abinda ta aikata wanda ta jima tana dana sanin amincewa zuciyar ta da tayi, kwanakin baya Inno da kanta tazo mata da rokon ta sanar da ita ko da address din inda aka kai mata dane, amma ita kanta bata sani ba. Idon sa ne yayi ja sosai, ya sake duban ta a karo na ba adadi "Shirun ki na nufin wani mummunan al'amari ya faru a ranar da aka haife mu, shirun ki ya tabbatar min da..." "Tabbas nayi kuskure wajen amincewa zuciya ta, nayi dana sani mara amfani, ban taba tunanin wannan ranar zata zo ba." "Kayi hakuri Kamal, tabbas mun zalunce ka zalunci me yawa, sai dai akan Aminatu kai gata mukayi maka, tun bayan lokacin ban sake haduwa dasu ba, sai dai har zuwa yanzu ina rayuwa ne da tunanin makomata." "Me kike nufi?" Yace cike da dauriya dan zuwa lokacin zuciyar sa ta fara shiga mawuyacin hali "Nice na chanja ka da Aminatu, nice sanadiyyar zaman ka duk abinda ka zama a yanzu, kuma nice sanadiyyar saka Aminatu a cikin mawuyacin hali, ba tare da sanin mahaifanta ba,son zuciyar mahaifiyar ka shine mafarin komai, da bata amince ba babu yadda zatayi hakan ta yiwu tunda ita lafiya lau ta haife ka tasan me ta haifa." Dip ya daina ji kwata kwata, tsawon dakika biyar tana cigaba da jera masa bayanin da baya iya jin komai, a hankali jin sa ya soma dawowa, jiri ne ya kwashe shi yayi saurin dafa bangon office din, da sauri ta sa hannu zata tare shi ta dakatar da ita "Menene kwatancen gidan?" "Idan kaje ka tambayi gidan Inno babu wanda be santa ba." "Waye ya saki aikata mana wannan mummunan aiki?" "Bansan shi ba, sai dai na san sunan sa a lokacin da naji matar ta fada masa, Adam idan har ban manta ba, shi ya bamu kudi domin mu yi masa wannan aiki, ni, harira da mahaifiyar ka sai mace daya da suka zo tare, wadda ta zama wakiliyar sa dan ita muka sani bashi ba ." Girgiza kansa yayi cikin sarkewar murya wanda yake jin numfashin shi na kokawa da gangar jikin shi ya soma magana "Allah ya isa tsakanin mu daku, bazamu taba yafe muku abinda kukayi mana ba, ina rokon Allah ya wulakanta ku tun a duniya, ya bi mana hakkin zaluncin da kukayi mana." Kofa ya nufa yana layi, kafin ya juyo yace "Ki jira abinda zai biyo baya dan ba zan yafe miki ba, Shari'a ce zata raba mu." "Dan girman Allah ka tsaya ka saurare ni." Bugo kofar yayi da karfi, ta zauna dabas a kasa tana rike kanta, ina zata kama? Shari'a da Marwan Dikko ba abu ne me sauki ba tasan tabbas zai iya sakawa a rufe kaf dangin ta. Da sauri ta mike ta zari jakar ta ta fita da kofar baya. ***Da taimakon wani direbab mota daya dauka shata suka isa cikin garin, duk da dauriya kawai yake yi amma bashi da karfi da kuzarin tunkarar abinda yake tunkaro shi din. Tambaya sukayi aka nuna musu gidan, da ido ya shiga duban gidan da ya sake lalacewa ainun, yanzu mutane ne ke rayuwa a ciki? Ya tambayi zuciyar sa, a take ta bashi amsa da mutanen ma iyayen da suka kawo ka duniya, chije bakin sa ya yi ya fitar da iska mai zafi yana tuna girma da kyawun gidan su na Abuja, tabbas Aminatu ita aka cuta, aka sata rayuwa a muhallin da har ta bar duniya ba zata taba rayuwa a cikin sa ba, kwalla ce ta zubo masa yasa hannu ya goge. "Sannu da zuwa." Nura yace yana fitowa daga cikin gidan, saurin daidai ta kansa yayi ya mika masa hannu,tunanin Abinda zai ce mishi yake, sai yaji yace "Wa ake nema?" "Nan ne gidan su Aminatu?" Yace "Nan ne, kana da labarin inda take ne dan Allah?" Ya amsa cike da zumudi, "Zan iya ganin mahaifiyar ta?" Yace yana dauke wanchan maganar "Bismillah shigo ciki." Yayi gaba da sauri, dan jim yayi kadan kafin ya kutsa kansa cikin makeken zauren gidan daya cika da yana. "Inna, inna fito ga wani yazo ganin ki kuma da alama yasan inda Aminatu take." "Yana ina?" Ta tashi a zabure, tsaye yayi a bakin kofar ya kasa karasowa ciki, wannan itace mahaifiyar sa data zabi kudi akan sa, mahaifiyar data raini Aminatu a cikin kaskanci da tozarci bayan nata dan na cikin gata da jin dadi Sararo tayi tana kallon sa, cikin sakannin da basu gaza biyar ba, ta kare masa kallo, kallon daya tabbatar mata da zargin ta, da sauri tayi kansa tana duban damtsen hannun sa dake bude cikin riga me gajeren hannun daya sa, katon tabon da aka haife shi dashi wanda shine abu na farko data fara gani sanda yazo duniya ta shiga bi da kallo, da hannu ta shiga nuna shi sai dai ta gaza furta kalma daya, tana kokarin riko hannun nasa yaja baya da sauri "Kamal MD kamar yadda kike hasashe! Ina fatan kina cikin koshin lafiya bayan abinda kika aikata." "Na shiga uku Nura, wallahi tallahi dana ne, shine dana wallahi shine, wallahi shine." "Inno me kike fad'a, ni ban fahimci komai ba fa." Cigaba da matsowa tayi tana kokarin riko shi yayi saurin ja baya yana bata fuska sosai "Karki taba ni, karki fara! Ba abinda ya kawo ni kenan ba, ina so naga kalar rayuwar da kike yi, alhamdulillah na gani, yanzu zan koma inda na fito." Yana kaiwa nan yayi waje da sauri, biyo bayan shi tayi tana kwala kiran sunan shi amma ko waiwayowa bai yi ba, motar ya fada da sauri ya umarci me motar su tafi. "Na shiga uku Nura, wallahi tallahi dana ne, kana gani ya tafi amma baka tsayar dashi ba." "Idan har da gaske shine, kina zaune zai dawo da kafafun sa, waye ya kawo shi yanzu? Ra'ayin kansa ko? Toh shi zai dawo dashi kiyi shiru karki tara mutane." "Shikenan nayi shiru." Tace tana kama bakin ta kamar yarinya karama. Ciki suka koma duk ta kasa komai data rufe idon ta hoton fuskar sa kawai take gani, ta girma sosai ya zama babban saurayi me ji da kyau da gayu, shigar sa kadai ta tabbatar mata da shi din waye, anya zai karbe ta a matsayin mahaifiyar sa kuwa? Yanzu da bata da maraba da mahaukaciya duba da yadda duk ta lalace ta koma kamar wadda tayi jinya ga babu suturar arziki. *** Ganin an kwana babu labarin Kamal yasa Alhaji Marwan baza jami'an tsaro sosai aka shiga neman sa, banda kuka babu abinda Ammi take, hakan ya karawa mishi damuwa sosai dan ba Hajiya Turai bata san wainar da ake toyawa ba. Dakin sa ta shiga ta tarar dashi yana waya, zama tayi a gefen sa idon ta duk ya ɓaci saboda kukan dataa sha, ajiye wayar yayi bayan ya gama ya dube ta cikin kulawa yace "Ki kwantar da hankalin ki in Sha Allah za'a ganshi." "An kira yarinyar da yake zuwa gani a Kano? Ina zargin ta dama ni chan hankali na be kwanta da ita ba." "Sirikar Aminini ce ashe, yarinyar da muke ta fafutukar nema ashe jikarmu ce, dan haka bani da matsala da yarinyar, idan kika ganta ma nasan kema irin ta Kamal din zakiyi, ki ji ta kwanta miki." "Bana son ta gaskiya, karo na farko dana fara jin mijina yana yabon wata bani ba." "Kishi?" Yace yana murmushi, gefe ta kawar da kanta tana bata fuska. "Kinsan Adam yana raye?" Yace yana duban ta, duburburce wa tayi tace "Ban gane ba?" "Hello inspector." Yace yana daga wayar "What!!!" Ya mike tsaye da sauri "Gani nan zuwa." Ya katse kiran yayi hanya da sauri : *DG*                        *37* ©Hafsat Rano ★★★ Tafiya yake ba tare da yasan inda yake taka ƙafarsa ba, so yake yayi kuka ko zaiji sauƙin zuciyar shi, sai dai ashe kukan ma samu ne, tsawon shekarun nan yana rayuwa ne da mutanen da bashi da alaƙa takusa ko ma ta nesa dasu, mahaifiyar data kawo shi duniya na rayuwa a wani waje cikin tsananin talauci, da kunci, tabbas ba'a kyauta masa ba, sai dai akan Aminatu kusan shi gata akayi masa, rayuwa ce yayi ta cikin tsananin gata da dadi, ita kuwa aka dora mata rayuwar da bata dace da ko da me aikin gidan ba balle ita, ya ɗaya tilo da take buƙatar dukkan gata, gata mace me rauni.    Tunanin ta yadda zai fara sanar da kowa komai yake, idan har ya cigaba da boye gaskiyar abinda ya sani be kyauta wa Aminatu ba, haka be yi adalci ga iyayen da suke rikeshi bisa amana ba, suna bukatar yar su, itama tana bukatar iyayen da zasu nuna mata gatan data rasa.    Idon sa ya runtse tuno labarin rayuwar ta data bashi, da irin abubuwan data fuskanta, ya tausaya mata kwarai sai dai a yanzu shine abin a tausaya wa, rashin sa'ar iyayen k'warai masu nagarta. "Baka gaji da tafiyar kasan bane?" Ya tsinkayi wata murya a saman kansa, juyowa yayi ya kalli mutumin "Ya kamata ace ka dan huta ai, bayan ka gano komai me ya kamata kayi?" "Me kake nufi?" Ya katse shi yana duban shi "Ina biye dakai tun barin ka gida, na kuma san abinda ya kawo ka, ina fatan bayyanar gaskiya be saka ka yanke hukunci da rayuwa ba." "Me yasa kake bina, ina kuma ruwan ka da rayuwa ta, waye kai ma a takaice.?" "Wanda ya chanja maka rayuwa daga ta tsantsar talauci zuwa mafi kuloluwar daraja." "Adam!" Yace yana zaro ido "Nine, Ina fata haduwar mu ba zata zamar wani babban al'amari ba." "Me nayi maka? Me yasa ka zabi da kayi wasa da rayuwa ta?" "Idan kace wasa da rayuwa kana nufin ban kyauta maka ba, dubi suturar jikin ka, ka dubi kanka, kana tunanin ban maka gata ba? Toh ka bude kunnen ka kaji.." "Ina so abin da ka binciko ya zama tarihi a ranka, wajibi ne ka boye komai ka cigaba da rayuwar dana zaba maka, idan baka sani ba, MD ne ya zabarwa yarsa irin rayuwar da take, shine silar komai, ya rabani da abubuwa guda biyu mafi soyuwa a gareni, shiyasa na zabar wa abinda zai haifa rayuwa mafi kaskanci." "Karya kake wa Daddy, babu abinda yayi maka karya kake, kuma wallahi sai na tona komai ko da zan dawo rayuwa ta ta asali." Murmushi yayi gami da cije lebensa na kasa "Idan har na bar maka damar yin hakan ko? Yaro kenan, sunana kawai kake ji amma na wuce tunanin ka." "Ta Allah ba taka ba, duk abinda kake kullawa sai ya koma kanka." Hannu Adam ya harde yana duban shi, tafiya Kamal ya cigaba da sauri da sauri ba tare da ya sake waiwayo wa ba.     A wani irin yanayi iska ta dauki karar motar ta kai masa kunnuwan sa,da sauri ya juyo kafin ya iya tantance komai tayi sama dashi. Ƙarar daya kwalla ita ta jawo hankalin mutanen dake wucewa ta wurin jefi jefi.    ***** A kid'ime yayi waje yana kwala wa Driver sa kira, kuka Ammi tasa tana binsa ganin kamar baya hayyacin sa "Dan Allah ka sanar min abinda ya faru." "Kamal ne ya hadu da accident a Katsina." Abinda kawai ya iya cewa kenan ya fada mota, kuka ta saka me karfi ta fado motar.    Wani irin gudu driver yake kamar zai tashi sama, babu abin da kake ji sai sautin kukan Ammi, ikon Allah ne kawai ya kaisu, direct asibitn da aka kai shi suka wuce suna zuwa kasar tsaye suka nufi accident and emergency unit.    A lokacin ya riga ya zama unconscious be san wanda yake kansa ba, dukkannin fuskar sa an rufe ta da bandage sai karaya a hannun sa na haggu.     Tsananin tashin hankalin da suka shiga ba zai misaltu ba, sai ga Alhaji Marwan na share hawayen tsananin tausayin dan nasa, ba'a ta Ammi da kowa yasan yadda uwa kan shiga tashin idan abu ya samu danta.    Isowar Daddy ya d'an saukaka abun, kwarai ya tausaya wa aminin nasa yadda yaga ya koma a lokaci daya kamar wanda yayi kwanciyar shekara.   ***** Tun bayan fitar Anas babu wanda ya sake magana a cikin su, kamar kurame sai dai idon sa na kanta duk sanda ta dago sukan hada ido sai yayi saurin basarwa yana maida kallon sa kan yar sa. Fita Baba Altine tayi ta basu waje dan sam bata ji dadin yadda akayi wa Anas ɗin ba, gefn Amal tayi zaman ta tana kallon yadda mutanen asibitin ke kaiwa da komowa.   Kiran wayar Farouk din akayi, kamar bazai daga ba ganin Iman na kokarin farkawa yasa shi dagawa dan kar a tashe ta, Ja'afar ne, baya kasar shima ya tafi karatu sai yanzu yake samun labarin dawowar Farouk din a wajen Dadah da sukayi waya shine ya gwada kiran tsohon layin sa na Mtn aikuwa sai gashi ya shigo. "Da gaske ka dawo? Wow nayi mamaki wallahi." "Uhum... Na dawo, kana lafiya?" ya amsa masa "Lafiya lou, sai dai banji dadin tafiyar ka ba Allah, ina tunanin baka san halin da Mummy ta shiga ba bayan tafiyar ka." "Ja'afar, kana ji? Ina wani abu yanzu very important, muyi magana anjima." Be jira amsar sa ba ya katse kiran yana jan dan karamin tsaki. Kallon ta yayi yaga shi take kallo, harara ya sakar mata "Dan na kori dan iskan chan kike share ni ko?" Yace yana baro kujerar da yake kai "Ba haka bane..." "Yaya ne? Ina lura dake har wani tasowa kikayi da ya kiraki." Ya zauna kusa da ita sosai a gefen gadon kafadarsa na gogar ta ta, wani iri taji tayi kokarin matsawa ya sake matso ta sosai. "Ni ba haka bane." Tace tana tashi tsaye, saurin chapko hannun ta yayi ya maida ita ya maida ita wajen da ta tashi yana dora kafadarsa a saman ta ta "Mesa kike gudu na, bakiyi missing d'ina bane?" "Ya Farouk?" Ta kira sunan shi "Ehen ina jinki." "Dan Allah ka daina wa Ya Anas haka, kaga babu dadi, yayi min kokari sosai a lokacin da na fitar da tsammani da samun wani jin dadi ko cigaba a rayuwa, shine ya rike mu tamkar nasa, ya kula da dukkan al'amuran mu, ya tsaya tsayin daka wajen ganin na samu ilimi me amfani, wanda idan babu shi da tuni rayuwar mu ta lalace, watakila ma da tuni na zama mabaraciya ko na mutu saboda wahala." Tashi yayi sosai ya kalle ta idon sa na kankancewa "Kina nufin dai yanzu ya fini wajenki ko? Saboda ya kashe muku kudi ke da Iman, shikenan, Ina so ki tambaye shi nawa ya kashe akan ku tun daga ranar farko zuwa yanzu sai na biya shi, tun da abin ya zama gori..." "Subhanallah, kar kayi misunderstanding d'ina, ba abinda nake nufi ba kenan." "Me kike nufi? Shikenan dan yayi wahala daku sai ya bashi damar shiga hurumin da bana saba? Nayi magana kuma kin juya min magana ta, alamun ma ni yanzu bani da wani amfani wajenki." "Ya Salam!" Tace tana kallon shi, "Wannan ba Ya Farouk d'ina bane, Ya Farouk d'ina me saurin fahimtar rayuwa ne kuma me yiwa mutum uzuri ne ko da yayi ba dai-dai ba." Kin tankawa yayi ya sake hade rai shi a dole an bata masa rai, ganin haka yasa tayi shiru itama saboda ta lura neman rigima kawai yake, ba kuma zata biye masa ba balle har ya samu galaba akanta.   Dogon zango suka dauka ba tare da kowa ya sake magana ba, sosai ranta ya ɓaci, dan bata ga abinda tayi masa da zai sashi reacting haka ba, ganin zaman ya ishe ta yasa ta mike don zuwa waje dan ba zata iya cigaba da zama dashi haka yana share ta ba "Zan koma gida." Tace tana mik'ewa, da sauri ya kalle ta "Iman din fa?" Yace cike da mamaki Idon ta ne ya ciko da kwalla tayi saurin sa hannu ta goge "Ba kana nan ba?" Ta amsa masa kai tsaye "Akan nace masa dan iska ko?" Yace yana kura mata ido, kin amsa masa tayi saboda yadda ranta ya ɓaci, ya gaza fuskantar ta s ranaram kishi ya rufe masa ido, gaba tayi kawai tana ji Iman din na kokarin tashi ta bude kofa tayi ficewar ta. "Ya jikin nata?" Baba Altine tace "Da sauki, ina ga idan drip din ya kare su sallame ta, muje gida." "Kamar ya? Muje gida ko naje gida? Na zata zaki zauna a sallame tan ne ko?" "A ah, zai iya kula da ita ai, muje kawai." "Fada kukayi?" Baban tace Gefen da Amal ke zaune Aminatu tayi saurin kallo ganin hankalin ta na wani wajen daban yasa tace "Ya kasa fahimta ta." "Shikenan sai kuma kiyi zuciya da yarki? Wannan ai shashanci ne." "Toh ya zanyi? Tsawon lokaci ina zaman jiran dawowar sa, ya dawo kuma amma ba da halin da na sanshi ba." "Aminatu ita fa rayuwa da kika gani ba zaki ce mutum ya zama yadda kike sanshi a koyaushe ba, mutane na iya chanjawa, Sai dai chanjawar su ba zai sa kema ki chanja ba." Jikin ta ne yayi sanyi, ta zauna tana tunanin mafita, suna zaune likita yazo ya wuce su, ya shiga ciki, jim kadan ya fito yayi nasa wuri. Ba'a wani jima ba sai ga Farouk ya fito rike da Iman a kafadarsa ya wuce su, ido Aminatu ta zubawa bayan sa ganin be ko bi ta kansu ba, ji tayi kamar ta tashi tabi bayan sa sai dai bata da wannan karfin halin, tsam Amal ta tashi tabi bayan sa, Baba Altine ta yanka mata harara cikin bacin rai tace "Me kikayi kenan?" "Ya zanyi toh?" "Muje." Tace tana mik'ewa Fitowa sukayi reception babu alamar su, suna fitowa parking lot suna fita daga asibitin. Wani iri taji ta rasa dalilin da Ya Farouk zai mata haka. Gida suka wuce Baba Altine nata yi mata fada akan abinda tayi, ko gaba kar ta sake irin wannan wautar. Ita dai jin ta kawai take bata iya cewa komai ba. ****Kwata-kwata ta kasa sukuni, tana yi tana duba wayar ta ko zata ga ya kira ta amma shiru kake ji, gashi kwarai tana so taji lafiyar yar ta, wannan shi ake kira a dakeka a hanaka kuka, yayi mata laifi amma ya fita daukar zafi. Ganin wankin hula na neman kaita dare yasa ta ajiye komai ta kirashi, lokacin ya gama shirya Iman cikin sabon kaya ya bata abinci da chocolate ta gama rigimar ya kaita wajen Ummin ta ya samu tayi shiru bayan ya bata wayar shi yayi mata downloading wani cartoon, shigowar kiran ya katse mata kallon ta, kuka ta saka masa hakan yasa shi saurin rejecting kiran. Sororo tayi rike da wayar a hannu, mamaki ne ya cika ta , dan son sake tabbatar wa ta kuma kira a take akayi rejecting, Sosai zuciyar ta ta sosu, ta zame ta kwanta ranta na mugun suya. Shigowar Dadah dakin uku tana son daukar Iman din Amma sam taki yarda, a shigowar ta na karshe ne take ce masa ina Aminatun bata bukatar yarta ne? Duba da rashin ta da tayi kwana biyu? Da yake har yanzu be gama sakin jiki da ita ba yasa yace mata yanzu zai zo ya kai mata ita. ****Ja'afar na ajiye wayar yayi saurin kiran Mummy dan yasan bata san da dawowar Farouk din ba, lokacin tana tsaka da aiki a system ɗin ta, da sauri ta ture komai ta shiga kiran layin Farouk din. Kura wa kiran ido yayi, a hankali ya zare wayar daga hannun ta ganin har tayi bacci wajen kallon, katse wa kiran yayi ya cigaba da bin wayar da ido har sanda wani kiran ya sake shigowa. "Farouk!" "Na'am." "Yanzu Farouk ka bar kasar nan tsawon lokaci sannan ka dawo duk ban sani ba? Ka kyauta min kenan? Kasan yadda naji dana samu labarin tafiyar ka? Amma shine har ka dawo baka neme Ni ba?" Shiru yayi duk sai yaji babu dadi, kallon tasa yar yayi ya tuna yanzu shima fa uba ne, idan tasa yar tayi masa haka ya zaiji? Cikin kankan da murya yace "I'm very sorry, kiyi min afuwa." Share hawayen fuskar ta tayi cikin dakewa tace "Ina son ganin ka yaushe zaka zo?" "Gobe ko jibi in Sha Allah." "Kazo gobe." "In sha Allah." Ajiye wayar yayi yana sauke ajiyar zuciya, kura wa Iman ido yayi yana jin soyayyar ta na bin kowanne lungu da sako na jikin sa. Tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Aminatu yayi, sai yaji duk be ji dadi ba, atleast idan bazai bi ta a yadda ta ke tunani ba kada ya kuma bata mata rai. **** Duk sunyi jigum babu wanda yake iya magana da dan uwan sa, gashi har an kwana babu alamun zai farka, dakin likitan ALHAJI Marwan ya shiga ya nemi a basu transfer,zai tsaya yi masa dogon bayani yace shi sam be yarda ba, dole ya amince ya sallame su suka dauke shi suka yi Abuja dashi ba tare da yasan me yake faruwa ba. A chan gidan kuwa Hajiya Turai ta tada bori bayan ta samu labarin abinda ya faru, gaba daya masu aikin gidan sun taru a kanta tana ta kuka da kururuwa a kaita wajen jikanta, duk sunyi jigum jigum motar su ta shigo gidan, da sauri ta tashi daga zaman dirshan din da tayi ta nufi kan motar tana kuka. Duk wanda ya ga Kamal a lokacin sai ya masa kuka, tuni Alhaji Marwan yayi nisa a shirye shiryen fitar dashi waje. Cikin dare ya farka, duk suna kansa, da wani irin abu ya soma kafin ya fara magana da k'yar irin ta wanda ya galabaitu da wahala. Babu wanda yaji me yake cewa saboda yadda maganar tayi kasa, Ammi na kuka Hajiya Turai na yi, cikin yanayin kamar an fuzgo maganar ya furta "Dad..dy.. A...mm..i.. itace." "Karka takura ma kanka da magana, dan Allah." Ammi tace tana kuka sosai, kukan shima yasa yana mika mata hannu, da sauri Daddy ya isa gareshi yana riko hannun sji "Kamal, look at me, menene? Kayi shiru kaji?" "Daddy... Ami...natu." "A kira maka ita?" Yace yana shafa kansa, daga kansa yayi alamun eh "Toh shikenan, kayi hakuri gobe zatazo kaji?" Daga kansa yayi yana maida idon sa ya rufe. "Kaga ni? Yarinyar nan me tayi masa? Yana wannan halin yana kiran sunan ta? Wannan wacce irin masifa ce? Wallahi bazan yarda ta lalata min rayuwar yaro ba." "Ya kamata ki duba lafiyar shi kafin ki tsaya tunanin komai, ni yanzu ta lafiyar sa nake, ba ta komai ba." Ran ammi ne ya ɓaci, ta kara jin haushi ta tsanar yarinyar da bata taba gani ba. Rashin Sani!!!! Yafi dare duhu Rano 😍: *DG*                        *38* ©Hafsat Rano ★★★ *K*amal be sake farkawa ba saboda yadda karfin allurar yake, da safe ya farka amma sai dai har lokacin ba a hayyacin sa yake ba, dole aka sake masa wata allurar saboda ciwukan da ke jikin sa ma.   Abincin kirki Ammi ta kasa ci saboda yadda abin ya dake ta, Hajiya Turai kuwa sai da aka bata magungunan ta na hawan jini sannan aka samu ta dawo daidai, dukkan su sun kasa matsawa daga in da yake, hakan kadai ya isa ka gane irin gata da soyayyar da suke masa.   Babban likitan da aka hada su dashi dake nan Abuja Dr Ahmad (Ruhi Daya) ne ya iso cikin shigar sa data dace da tsari da zubin hallitar sa, tun fari shi Daddy yaso ayi wa magana ganin Alhaji Marwan din ya kafe da son dole sai ya fidda shi waje yasa ya kyale, sai dai tsaikon da za'a samu yanzu kafin a fitan yasa dole ya amince aka kira shi.    Har wajen motar sa Alhaji MD ya k'arasa ya yi masa iso zuwa katafaren part d'insa inda aka ajiya Kamal din, har suka karasa suna tattauna wa akan abinda ya samu Kamal din da kuma abubuwan da Daddyn yake so ya taimaka masa dashi, a nutse ya amsa da zai yi iya yinshi sannan suka karasa ciki.    Cikin kwarewa da sanin makamar aiki na cikakken consultant a bangaren ƙwaƙwalwa ya shiga bincike da son gano ko akwai wani damage a brain d'insa, a haka dai physically babu wani abu da zata nuna ko ya samu wata matsala ,sai dai yana bukatar bincika shi sosai, kai tsaye babban asibitn sa dake Maitama ya umarci a kaishi, anan yayi undergoing several tests kuma Alhamdulillah babu wata matsala internally sai wadda ta bayyana kowa ke ganin ta. Cire glass din idonsa yayi bayan yasa tsaftacecen handy ya share zufar dake saman goshin sa ya kalli Alhaji MD yace "Ina ganin zaman sa anan ɗin zai fi samun kulawa fiye da gida, sannan ka bamu dama muyi aiki sosai in Sha Allah zaka ji dadin aikin mu fiye dana kasashen wajen, please let give it a try, for now a ajiye fita dashi." "Shikenan, na yarda da ingancin aikin ku da asibitin ku, please kayi iya kokarin ka wajen ganin yarona ya samu lafiya, shi kadai nake dashi i can't bear...." Saurin katse shi yayi "Babu abinda zai faru dashi in Sha Allah, ya riga yayi passing danger stage din so mu cigaba da addu'a." "In Sha Allah. Mun gode Dr." Fita yayi ya samu su Ammi ya sanar dasu abinda ya faru, cikin kankanin lokaci asibitin ya soma cika da yan uwan Ammi da abokan harkar Alhaji Marwan na kusa dana nesa, tuni labari ya game ko ina sai dai ba'a bar kowa ya ganshi ba sai ta window saboda yadda yake bukatar hutu. **** Hasken ranar daya risketa har inda take kwance yasa ta gane gari ya waye sosai, da sauri ta tashi tana laluben wayar ta da glass din ta da sukayi nasu waje, sakawa tayi tana duba wayar cikin tsananin mamaki take kallon lokacin , karfe bakwai har da mintuna, a zabure ta mike tayi saurin fadawa bandaki ta dauro alwala tazo ta gabatar da sallah tana rokon Allah gafara akan makarar da tayi.   Bayan ya idar ta zauna a wajen tana tunanin abinda Farouk yayi mata na regecting kiran ta da ya dinga yi, a takaice dai yayi fushi, fushin da bashi da dalili ko tushe.   Tashi tayi ba tare da ta cire hijabin jikinta ba ta koma daki ta tashi Baba Altine, zaman dirshan tayi a kasan dakin bayan Baban ta fita ta shiga azkar a nutse, tana cikin yi ne Kamal ya fado mata, jiya ta kirashi babu amsa duk sai taji babu dadi hankalin ta kuma ya gaza kwanciya, be taba tafiya hakan ba ba tare da sallama ba, sannan yanayin daya fita a ranar ya tsaya mata a rai sai dai ta kasa gane dalili ko hujjar da ya sashi aikata hakan.    Gefen gado ta koma ta haye ta kudundune a cikin Hijabin ta shiga kiran layin nasa tana fatan ya daga duk da dai tasan safiya ce. Babu amsa dole ta hakura ta ajiye wayar ta rufe idon ta. Bata tashi ba sai wajen goma, lokacin Baba Altine ta gama gyaran gidan har ta siyo kokon ta da ya zama mata kamar al'adah tasha abinda. Wanka ta fara yi ta shirya a cikin wata doguwar rigar atamfa koriya wadda Anas yayi mata da sallah sannan ta wuce kitchen ta hado tea da biscuit ta zauna tana ci. "Kwana biyu Kamalu shiru nace, lafiya kuwa?" "Wallahi nima abinda ke raina kenan, shirin yayi yawa gashi na kikkirashi baya dagawa." "Toh, Allah sa lafiya, ki kara gwadawa Allah sa ba kuma sace wayar akayi ba." "Toh Amin dai, bari na sake kira." Ta danna kiran tana ajiye cup din hannun ta. Lokacin wayar na hannun Ammi suna zaune da wasu mata kiran ya shigo, sunan data gani yasa ta jan tsaki ta mike ta dan matsa gefe kafin ta daga "Ya daga." Tace wa Baba Altine "Kamal. Ina ka shige kwana nawa ina ta kiran ka, wallahi baka ji yadda muka damu ba." "Toh munafuka, kin tura min yaro in da zai halaka ba ki masan matsalar da kika saka shi ba ko? Na tabbata abinda ya kaishi Katsina ya gamu da wannan mugun abun ya na da alaƙa dake, tun da kika shigo rayuwar sa shikenan ya chanja, komai ke komai ke, sai ki zuba ruwa kisha tun da kin kassara masa rayuwa." Ta karashe tana share kwallar data zubo mata "Dan Allah kiyi hakuri, me ya samu Kamal din? Wallahi bani da masaniya." "Karki sake kiran sa, baya bukatar ki mu iyayen shi kadai mun ishe shi,ki fita daga rayuwar sa ba zan juri rasa shi ba zan kuma iya yin komai akai." Tana kaiwa ta katse kiran tana komawa wajen zaman ta kamar babu abinda ya faru. Kuka Aminatu tasa tana fada wa Baba Altine abinda ya faru, duk ta rude idan wani abu ya faru da Kamal ba zata taba yafe wa kanta ba, me ya kaishi Katsina bayan tasan bashi da wani abu da zai kaishi chan din tunda ya taba fada mata tun bayan barowar su Daddy basu sake komawa da sunan zama ba, dama aiki ne ya kai su garin, yan uwan su da sukayi saura basu da yawa a garin ba kuma ma zuwa wajen su suke ba. Rasa inda zata sa kanta tayi, zaman ma sam ya gagare sai zagaye take,ita kenan duk wanda zai rabe ta sai ya shiga matsala, kamal ɗin da take ganin shi a matsayin dan uwa na jikinta shima ana neman illata masa rayuwa. Dole ta kyale shi kamar yadda mahaifiyar sa ta buƙata amma kuma tana son sanin halin da yake ciki gashi bata san wa zata tuntuba da maganar ba. ***Wanka yayi mata ya chanja mata sannan ya riko hannun ta suka fito falon, Dadah na zaune da anty Safiyya suna hira akan tafiyar da Anty Safiyyan zatayi Kaduna, miƙa hannu Dadah tayi da murnar ta, make kafada Iman din tayi tana buya a jikin baban ta. "Zo kinji." Tace tana sake gwadawa "Barka da safiya Anty." "Barka Farouk, ashe anan ta kwana shine baka miko mana ita ba, ko da yake ba yarda zatayi ba." Murmushi yayi "Ni dinma da kyar, zuwa zan na kaita na dawo sai mu wuce, Mummy na son gani na." "Sannu da gida Dadah." "Har yanzu fushin ne Baba na? Baka yarda dani ba ko?" Shiru yayi yana gyara wa iman zama a jikin sa "Komai yazo karshe in Sha Allah, dani zaku tafi ina so na sanar da kowa abinda baku sani ba, dama dazu baban naku ya kira akan Kamal ya gamu da hatsari yana asibiti ma toh kaga zuwa ya zama dole." "Subhanallah, accident yayi? Banji ba wallahi." "Wallahi wai mota ce ta buge shi a Katsina yana tafiya a kafa." "Ikon Allah, garin yaya? Allah ya bashi lafiya bari na maida ta sai na dawo." Yace yana tashi, da sauri ta mike tana sake riƙe shi. "Ja'ira kamar za'a kama ta." Sukayi dariya gaba daya. ***Da gudu ta bude motar ta shige gidan tana kwala kiran Ummi, da sauri ta goge kukan da take ta fito ran ta fari kal ta rungume yar ta ta cikin wani irin yanayi "Ummi nah." "Umm." "Ina ta neman ki, har kuka nayi." "Toh gani ai, no more kuka ko?" Tace tana shafa kanta cikin tsantsar kauna. Hannu ya harde yana kallon su, ji yake kamar ya je garesu ya haɗa su ya rungume su, dagowa tayi ya kanne mata ido daya yana murmushi. Sai ta turo baki tana tashi daga durkusan da tayi. "Muje ciki." Tace tana rike hannun Iman din. Shigewa sukayi suka bar shi a tsaye, ƙasaitaccen murmushi yayi ya bi bayan su. Kai tsaye daki suka shiga ta kwantar da ita saman gadon tana zame mata riga, ita kuma tana mata surutai. Budo kofar yayi ya shigo ta dago tayi masa kallo ɗaya ta dauke kanta, ya lura da yadda take share shi duk haushin jiya ne, matsowa yayi har cikin tsakiyar dakin yana karewa ko ina kallo kafin ya sauke idon sa akan kayan ta na lawyers dake ajiye a gefe guda, takawa yayi har wajen ya dauka yana jin sabon nishadi na ziyartar sa. "Barrister AFS ( Aminatu Farouk Shagari)." Ya furta cikin wani irin shauk'i. Bata kula shi ba ta sauya wa Iman kaya zuwa marasa nauyi ta rike hannun ta suka bar dakin, zaman sa yayi yana sake duba kayan karatun ta yana jin dadi mara misaltuwa. Wajen Baba Altine ta kaita bayan taje ta rufe gidan da sakata sannan ta komo dakin da niyyar daukar wayar ta. Ta gaban sa ta wuce ta dauki wayar zata bar dakin yasa mata kafa kadan tayi lu zata fadi yasa hannu ya taro ta, ido ta zaro a tsorace tana kallon sa numfashin sa na yawo a saman fuskar ta. Kici kicin kwacewa ta hau yi ya rik'e ta gam yana sake saka idon sa sosai a cikin nasa domin ya gane irin tasirin da hakan ke dashi.. "Ka kyale ni." Tace tana sake yunkura wa tana kokarin dole sai ta kwace. "Wai karfi kika fini? Karki manta da soja kike magana, just keep calm babu abinda zan miki." Juyar da kanta tayi gefe ya sa hannu ya juyo da fuskar yana cije baki kadan kadan "Fushin ne?" Sshiru tayi masa "I'm very sorry, bansan me ya hau kaina bane, bana iya controlling kaina duk sanda na ganshi kusa dake. Nasan yayi min halaccin kula min daku kuma in Sha Allah zanyi kokarin controlling kaina kinji?" Bata tanka ba. "Say something." "Ka daga ni be dace ba." Tace tana hadiye yawu da kyar, murmushi yayi yana sake dora mata nauyin sa sosai "Babu rashin dacewa dan miji ya kebe da matar sa, zan tabbatar miki da bani da hannu akan wannan takardar bogin da aka kawo miki, ban saki matata ba saboda haka babu wanda ya isa ya hanani kebewa da ita, kinsan yadda nayi kewar ki kuwa?" "It's still doesn't change anything, please ka kyale ni." Kura mata ido yayi cikin kankan da murya, ya sa hannu a saman fuskar ta yana bin ko ina kafin yace "Ba zan taba iya kyale ki ba, ko da ace saki nayi miki ai na uku bane ko? Balle wallahi ban sake ki ba, kuma zan tabbatar miki da haka." Shiru tayi cikin rashin sanin me zata yi, bata so ta yarda dashi ya zurma ta ta riga tasan hukuncin hakan, motsawa tayi da dan karfi bakin ta ya hadu waje guda nasa, da sauri irin na wanda yake a matuƙar buƙace ya shiga kokarin ganin ya fanshe abinda yake ji game da ita. Sai daya dau lokaci me tsawo yana aika mata da sakon da yake isa kowanne lungu da sako na zuciya da gangar jikin ta. Bata iya hana shi ba sai ma sakin jikin ta da tayi sosai tana karbar sakon nasa. "Ummi." Muryar Iman ta dawo dasu daga dogon zangon da suka tafi, da sauri ta ture shi tana sakin kuka, kallon ta yayi ya zura mata ido yana jin ransa fes, kukan me kuma zatayi bayan da gaske tayi enjoying abinda ya faru. "Ki share hawayen ki kafin ta shigo ta ganki kina kuka, ta zarge ni." Harara ta balla masa tana goge fuskar ta daidai lokacin Iman ta shigo. Mik'ewa yayi yana zura hannun sa cikin dogon wandon sa, "Zanyi tafiya zuwa Abuja, zan dawo gobe ko jibi, daga nan zanzo da kowanne hukunci dake tattare da auren mu." "Ya jikin Kamal?" Tace tana kallon sa "Alhamdulillah duk da bansan ya ake ciki ba..." Wayar sa ce tayi kara ya zaro ta yana dubawa "Barka da warhaka Daddy." "Barka dai, ya gida?" "Lafiya lou, ashe kamal be ji dadi ba, Allah ya kara sauki yanzu zamu tawo in Sha Allah." "Alhamdulillah WallAhi, tsautsayi ya hadu dashi, gashi ya dage da son ganin Aminatu, idan babu damuwa kazo da ita dan Allah, bamu san me yake son fad'a mata ba." "Babu damuwa, zamu zo tare in Sha Allah." Ajiye wayar yayi "Ki shirya baban Kamal ne ya roki alfarmar muzo tare wai Kamal din nason ganin ki." Dan jim tayi tana tuno warning ɗin maman shi, sai kuma ta tuna tana bukatar ganin shi sosai, gida mishi kai tayi alamar toh ***Kuka ta kwana tana risga cikeda nadamar abinda ta aikata, ganin danta yasa komai ya dawo mata sabo, bata kyauta wa Aminatu ba, bata kyauta ba ta zama daga cikin mutane masu son kansu, da tayi hakuri da duk yanzu babu abinda ya faru, tsantsar kiyayyar data gani a idon sa kadai ya ishe ta gane a wanne bigire a ajiye ta azuciyar sa.    Dauki da ledar magani Nura ya shigo ya zauna gefen tabarmar dake ajiye a wajen yana duban ta "Kiyi hakuri Inna, ina kyautata zaton zai sake dawowa." "Tunanin da kake kenan? Ka kuwa duba banbance banbancen dake tsakanin mu? Kalle mu cikin tsantsar talauci da kauyanci, ka tuna yadda jikin sa yake da ke fitar da tsantsar hutu da jin dadi, me zaiyi dani? Bayan ban zame mishi uwa ta gari ba." "Duk wannan daban, kasancewar ki mahaifiyar sa ya kore komai." "Nura kenan." "Dan Allah Inno mu bar maganar nan haka, karbi ga magungunan nan kisha kin daiji shafi'u me chemis yace jinin ki ya hau sosai, ki sha sai ki kwanta ki huta dan Allah." Bata sake magana ba ta karbi maganin ta balla tasha ta koma ta kwanta kanta kamar zai rabe biyu saboda azabar ciwon da yake mata. ***Tun daya koma office ya kasa aiwatar da komai, baki daya ya rasa gane inda dai ajiye alakar shi da Aminatu, da kuma billowar Farouk a lokacin da bai dace ba. Ba yaro bane shi dan a ƙalla ya doshi shekaru talatin da biyar, yana bukatar mace a kusa dashi, dan haka ya zama dole ya tuntube ta yaji matsayar sa dan bazai yiwu su dinga yi masa wasa da hankali ba.   Lambar ta ya lalubo zai kira sai kuma ya fasa ya ajiye yana sake gyara zaman sa sosai, gwara kawai ya bari weekend yaje face to face ayi magana yasan matsayar sa.    Wulakancin da Farouk yayi masa ya kasa barin ransa, a takaice dai ba'a taba masa abinda ya tsaya masa haka ba irin na Farouk din, ko dan dama tun asali ba wani shiri suke ba oho.    Kiran Hajiyar sa ne ya shigo masa, ya daga da sauri don wanna zuwan da yayi be samu ya leka su ba bacin ran Farouk yasa ya dawo ba tare da ya shirya ba. "Barka da safiya Hajiya." Yace cike girmamawa "Barka dai, ya aikin?" "Alhamdulillah babu dadi." "Haka ne dama sai hakuri, Allah ya bada sa'a." "Amin." "Na zata zaka shigo wannan satin ina ta jiran ka dan akwai muhimmiyar maganar da zamuyi sai kuma naji shiru." Sosa kansa yayi "Abubuwan ne suka sha kaina, satin nan zan shigo in Sha Allah." Ya samu kansa da boye mata zuwan da yayi wanchan karon. "Shikenan sai kazo." Shafa kansa ya dinga yi yana nazarin dalilin kiran mahaifiyar sa, ya santa sarai bata wasa da al'amuran da suka shafe shi, last zuwa da yayi sai data yi masa korafin maganar Aminatun ***** Wayar da take tayi saurin katsewa saboda shigowar Daddyn da bata yi tunanin a lokacin zai shigo ba. "Sannu da zuwa." Tace cikin rashin gaskiya, be fuskanci komai ba ya amsa mata a sake yana wucewa dakin sa, dazu da suka tsaya a Kaduna ya hangi Mummy a motar ta, gaba daya sai yaji ya gaza sukuni da ransa, ya rasa dalilin da har yanzu ya kasa mancewa da ita a zuciyar sa, gashi ta kafe sosai ta hanashi rabar ta balle har ya samu nasarar shawo kanta. Turo kofar tayi dauke da tray din abincin sa, ta ajiye gami da dora wayar ta saman mirror kafin ta juya ta fita. Kallon abincin yayi sam bashi da appetite ya matsar dashi gefe ya saka abin sallah ya gabatar da sallar da ta tsere masa. Yana sallar ta leko ta koma ta cigaba da wasu aikace aikacen Yana zaune yana addu'oin sa wayar ta dake ta faman kuka ta ishe shi, dan buɗe murya yayi da nufin kiran ta shiru sai kawai ya yanke hukuncin dagawa ba tare da tunanin komai ba. Wanda ya kira ya soma magana kai tsaye ba tare da tunanin tsayawa ya saurari wanda ya daga kiran ba *"Zan shigo gobe da safe, zanzo kamar yadda na saba zuwa a matsayin Ibrahim, ina so na tabbatar na katse numfashin Kamal kafin ya farfaɗo ya sanar da MD wacece asalin yar tashi, ba yanzu nake bukatar ya sani ba har sai na tabbatar da duk dukiyar sa ta dawo hannu na."* "Kina jina?" Yace bayan ya gama maganar, tsaki yaja kadan ya katse kiran yana tunanin network ne "Adam." Daddy ya furta da karfi Tsawon wannan lokaci dama shine yake raina masa wayo yana takowa har cikin gidan sa bisa amincewar matar sa? sanin cewa wanda ya riga ya mutu baya dawowa yasa be taba kawo komai ba, ya yarda dashi fiye da yadda ya yarda da kowa har ya amince da tayin auren Maman da yayi masa kai tsaye babu ko dogon bincike, ashe??? Ya zama dole ya shigo hannun sa a goben nan, ba zai taba bari damar ta kubce masa ba. A gaggauce ya rubuta masa text message da wayar Maman sannan yayi saurin gogewa yana ajiye wayar a mazaunin ta. Rano 😍😍*DG*                        *39* ©Hafsat Rano ★★★★ Da sauri ya jawo wayar sa ya kira MD, yana dagawa be jira komai ba yace "Zaman Kamal a asibtin nan akwai hatsari, zan iso asibitin yanzu, kafin zuwa na a tabbata babu wanda ya shiga in da yake." "Shikenan sai kazo." Ya ajiye wayar, duba lokcin yayi dare ya soma yi ya fito. "Lafiya Alhaji?" Ta tsare shi cikin kulawa "Eh babu komai, wani aiki ne ya taso da yake bukatar fitar tawa." Yayi gaba dan ko fuskar ta baya son gani. Yana isa asibitin ya ja MD gefe ya sanar masa da abinda yake faruwa, hankalin sa ya tashi, dole suka tuntubi likita a aka basu sallama a take sannan ya haɗa su da wanda zai kula da Kamal din kafin yazo da safe.   Dukkan su babu wanda be yi mamakin dalilin da yasa za'a dauke Kamal, haka suka nufi gidan kowa da tunanin sa, matakan tsaro sosai aka kara a kowanne gida sannan Daddy ya samu ya kwanta da tunanin abinda gobe zata haifar. **** Komawa yayi ya haye gadon ya mike kafa, "Ku shirya mu wuce toh, amma ya za'a yi da Baba?" Daga kanta tayi cikin nazari kafin tace "Ko taje gida?" "Ummm anya? Why not taje gidan Dadah, idan yaso sai suyi zaman su da mai aikin ta har mu dawo." "Ok bari na fada mata." Tace Rakata yayi da ido yana lumshe su kamar na wanda ya sha wani abun, sarai ta ganshi sai ta basar dan ita yanzu ya soma bata tsoro. Jim kadan ta dawo ta sauko da yar karamar trolly dinta ta jera musu kayan su ita da Iman da duk abinda tasan zasu bukata.   Juyowa tayi tana kallon sa, so take ta chanja kayan jikin ta sai dai ganin yadda ya kafa ya tsare yasa ta fasa ta zaro hijabi ta ɗora a saman doguwar riga, dama chan Iman a shirye take. "Na gama." Tace tana kallon sa "Kin fasa chanja kayan jikin naki?" "Ni nace zan chanja kaya?" "Na gane ai." Yace yana mik'ewa "Oya baby muje ko?"  Ya riko Iman din "Ina?" Ta kalli mahaifiyar ta da sauri tana matsawa kusa da ita "Ummi ina zamu?" Tace tana kallon jakar dake ajiye "Unguwa zamu, kije wajen sa Daddyn ki ne babu abinda zai miki kinji" "Har dake?" Tace tana sake matsawa kusa da ita "Har dani." Murna tayi ta kama hannun sa "Muje uncle." Shiru yayi duk sai yaji babu dadi, yana bukatar lokaci da zai shaku da yar sa, sai a yanzu yayi dana sanin barin garin da yayi. Kada kansa yayi yaja jakar tare da kama hannun ta suka fita. "Nace ba, ko zaki kira Anas ki sanar masa kar yazo bama nan?" Baba Altine tace tana daukar yan kayan ta "Ok zan kira shi." Tace sannan suka rufe gidan. Kai tsaye gidan Dadah suka nufa, Iman ce a gaba sai Baba Altine da Aminatu a baya, suna zuwa suka tarar dasu shirye, da murna Dadah ta tarbe ta ta rungume ta cike da jin dadin ganin ta. Bayanin komai Farouk yayi mata sannan suka fito. Babbar mota ce me kujeru biyu a baya saboda haka basu wani takura ba, Uncle Aliiyu da Farouk ne a gaba, sai Anty Safiyya, Dadah, Aminatu da Amal a baya sai yaran Anty Safiyyan guda uku.' da Iman   Hira suke tsakanin Dadah da Anty Safiyya, sai Farouk da uncle Aliyu dake tasu a gaba wadda ta shafi siyasar kasar mu ta gado.   Aminatu da Amal kamar basa motar babu wanda ya bude baki yayi magana duk da kuwa suna manne kusa da juna. Ta gefen ido Amal ke satar kallon Aminatun tana jin wani iri game da ita, tunanin yadda za'a kwashe da maganar auren ta da Farouk da take ganin ya kamata ace akwai mafita a ciki, gashi babu wanda ya kuma daga zancen a cikin su Daddyn sunyi biris kamar basu san da auren ba, gashi ita ba wani take kulawa ba kuma ita sam bata ma yarda da aka ce wai Mummy ta shayar da ita ba, idan har haka ne ba zata yafe wa Mummy ba dan ta cuce ta iya cuta. *** Daddy be iya bacci ba, jira yayi ta yi gari ya waye kar ma yazo ko yana bacci. Kiran farko a kunnen sa ya yunkura da kyar ya fada toilet ya daura alwala ya fara gabatar da raka'atanil fajr kafin ya wuce masallacin dake kan layin su dan gabatar da sallah.   Bayan an idar ya dawo gidan, jami'an tsaron dake tsaye a gate gidan ya tattara waje daya ya sanar dasu abin da yake so suyi masa, sun amsa da toh kafin ya koma ciki ya hau shiri dan yana ji a ransa yau komai zai waka na. Wajajen takwas na safe ya fito harabar gidan ya samu kasan rumfar da ya saba zama musamman da yammaci ya zauna, sannan ya aika aka karbo masa breakfast din sa a wajen.   Tun yana zaune yana duban lokaci har rana ta soma dagawa da tasa dole ya koma ciki yana tunanin abinda ya katse shi da zuwa bayan yayi masa reply a matsayin Maman ce.   **** Yammaci ne me cike da ni'ima, sake fitowa Daddy yayi ya zauna yana kallon ko ina a harabar gidan komai na sake dawo masa kamar a lokacin yake faruwa. Idan bai manta ba, a irin wannan lokacin ya same shi, cikin kankan da murya ya shigar da kansa, be san ya akayi ba,be san me ya faru ba, kawai ya samu kansa da amince masa kai tsaye, ya sakar masa ragamar komai na harkokin sa, a halin yanzu shine yake juya alakar dukiyar sa mafi yawa. Dan karamin tsaki yaja ya shiga shafa kansa, tabbas idan ka biye ma zuciya zata kai ka ta baro ka, gashi shima ya biye wa tasa, ba tare da dogon bincike ba ya afka ga tarkon da yake tunanin fitar sa akwai kalubale babba.    A daidai lokacin motar su ta kunno kai, duk a gajiye suke saboda tafiyar musamman Aminatu da ba sabawa tayi ba, yaran sunyi bacci yafi sau nawa suna farkawa.   Da kallo ya shiga bin motar har suka samu waje sukayi parking, Ido ya zura sosai ganin da gaske Dadan ce yasa ya mike da sauri cikin mamaki yace "Dadah." Fitowa tayi tana kallon gidan, karo na biyu bayan lokacin ta sake dawowa. "Barka da zuwa Dadah, ashe kina tafe." Yace yana bayyana farin cikin sa a waje, "Barka dai, ya jikin Kamal din?" "Alhamdulillah." Hannu ya mika wa uncle Aliyu sannan su Aminatu suka gaishe shi kafin su dunguma zuwa ciki. Duk Aminatu a darare take ta kasa sakin jikin ta, kai tsaye Amal ta wuce dakin ta dan dama a gajiye take da zama waje daya da su. Farin cikin Mama ya kasa boyuwa, dama haka take chan kirkin masifa ne da ita, haka ta shiga hidima dasu kamar zata goya su, a take ta saka umarnin a gyara tsohon bangaren Dadah daya ke a rufe.   Dakin Amal maman ta nuna wa Aminatun. Dago kai tayi jin an bude kofar, ganin wace yasa ta maida kanta ta cigaba da abinda take, gefe Aminatu ta samu ta zauna tana tunanin yadda zama zai yiwu ita da Amal a daki daya.    Tana nan zaune har aka kira sallah, kofar dake nuna toilet dake manne a dakin ta nufa, murya a shake Amal tace "Bana sharing toilet da kowanne trash." Juyowa tayi da sauri ta tsaya tana mata kallon mamaki "Amal nice trash?" "Mu nawa ne a dakin?" "Ok nagode." Tace sannan ta bude toilet din ta shiga, hakan ya bata wa Amal rai ta tashi tana fadan maganganu, tana jin ta sarai har ta dauro alwala ta fito, bata kula ta ba ta tada sallah a kan dankwalin ta.   Tana zaune tana addu'a Mama ta leko "Kin idar? Taso zaku shiga chan gidan." "Owk tom." Ta mike "Dota kema ki taso." "Zan je gobe kaina ke ciwo."   "Ayya sannu, gajiya ce kisha magani."   Fita tayi Aminatu ta tashi ta nufi kofar fita, har ta kama kofar sai kuma ta tsaya tana juyowa "Wai ke bak'ya sallah ne?" Waro ido Amal tayi, kafin tayi magana ta yi ficewar ta. **** Tsananin faduwar gaba ne ya ziyarce ta sanda suke shiga cikin gidan, haske ne ko ina kamar rana, haka ya bata damar karewa tsarin gidan kallo da yafi kama da irin wanda ake gani a Film.   Dukkan sautin sahun digadigan ta na fita ne tare da tsanantar bugun zuciyar ta, idan tace tasan musabbabin da yasa take jin hakan tayi karya, haka nan take ji kamar ta zura da gudu saboda tsabar zulumi   Haka suka shiga wuce bangare bangare na tafkeken gidan a kasan zuciyar ta tana tuna yadda suka saba da Kamal bata taba tunanin girma da yawan dukiyar su ta kai haka ba sai yanzu.    Babban falo ne daya kawatu da kayan more rayuwa, a hankali bakin ta dauke da sallama ta shiga takawa tana bin bayan su Dadah hannun ta damke dana iman.    Ammi na zaune, tallafe da kumatun ta bayan ta sha kuka, zuwan Dr Ahmad yasa ta fitowa daga ciki ta zauna a falon tana dakon fitowar su da labarin halin da gudan d'an nata yake ciki.    Zamewa tayi da sauri ganin su ta mike tana sakaya yanayin da take ciki ta maye gurbin sa da yar fara'a. "Dadah!" "Sannu kinji." "Bismillah." Ta nuna musu wajen zama, kamar munafuka haka Aminatu ta rabe a bayan Anty Safiyya, sam Ammin bata lura da ita ba, suka shiga gaisawa. A darare Aminatu tace "Ina wuni?" "Lafiya..." Maganar ta makale a makoshin ta, wani irin abu taji ya bige ta, ta kura mata ido sosai tana kallon ta, tsoro ne ya kama Aminatu ganin yadda matar take kallon ta, gashi daga ganin matar taji kamar ta taba ganin ta, kamar ta tashi ta isa gareta ta zauna kusa da ita. "Wacece?" Ta tambaya still idon ta na kanta "Oh wai Aminatu, matar babana ce ga diyar ta nan ma Iman, itace ai wadda Kamal din ke son gani." "Aminatu..." Ta maimaita sunan Sai ta bata rai ta nuna ta da hannu "Kece ki ka samun rayuwar yaro a matsala ko? Kece mukayi waya nayi miki kashedin fita daga rayuwar sa, me kuma kika zo yi nan?" "Me ya faru ne?" Dadah tace "Gata nan tafi kowa sanin halin da take ciki da dalilin da yasa ya shiga, idan ba haka ba me yasa dukkannin farkawar da zai yi da sunan ta a bakin sa, me kikayi masa haka?" "Haba Hajiya, ba haka bane Aminatu ba irin mutanen nan bace, kila baki fahimce ta ba." "Haka ne ma, komai a bayyane yake yadda ya damu da al'amarin ta ko ni be damu dani." "Kiyi hakuri." Tace cikin muryar kuka, hadiye abu Ammin tayi da ya tokare mata makoshi tace "Please kije i can take care of him, an gode da dubiya." "Haba Hajiya, haba Hajiya, bansan ki da son kai ba, karki manta ita ma mutum ce da iyayen ta, idan kika yi haka kamar baki yarda da ƙaddara ba." "Kiyi hakuri Dadah na gama magana." Tace tana kauda kanta gefe cikin son danne abinda yake taso mata kasan zuciyar ta, yadda take jin yarinyar a ranta ya sata cikin wani irin yanayi mara dadi. Mik'ewa Aminatu tayi, ta rike hannun Iman,ta soma takawa ta nufi kofa, ta kasa boye kukan ta saboda haka sai ta sake shi kawai, ita kenan kowa baya son ta kowa kyamatar ta yake, idan ba haka ba menene laifin ta. "Ummi ki daina kuka kinji?" Iman ta fada tana son fara kukan, tashi su Dadan sukayi, suka mata sallama suka bi bayan Aminatun cikin rashin jin dadin abinda Ammin tayi. Dr Ahmad ne ya leko yana duban Ammin da take jin kamar bata kyauta ba sai dai ta kasa yarda da hakan, "Hajiya yaron ku ya farka..." "Alhamdulillah." Tace cike da farin ciki "Yana bukatar ganin ki, mahaifin sa sai kuma Aminatu, idan tana kusa ki kirata please." "Aminatu!" "Eh haka yace, dan yafi damuwa da ganin nata ma akan kowa, ko dan lafiyar sa ki kirata please." Ya juya ciki, kanta ne ya hau juyawa, yanzu ya zatayi kenan? Da kunya ai ta koma tace suzo kuma, sai ta basar ta shiga ciki.   Yana kwance idon sa a bude fes, da sauri ta karasa tayi saurin kama hannun sa. "Allah na gode maka." "Ya jikin naka? Me yake maka ciwo yanzu?" "Ammi ina Aminatun? Dan Allah ki ce tazo." "Kamal wai menene ka damu da sai tazo? Baka murnar gani na sai ita?" "Inayi Ammi, sai dai..." "Bana son maganar ta Kamal, ka bari ka sake samun lafiya sai kaje ka ganta." Yake yayi ganin yadda ta dage, a hankali ya dora hannun sa a saman nata, ya kalli Alhaji Marwan dake tsaye bayan su ya harde hannun sa tun bayan shigowar Ammin yana duban su, baya so ya sa musu baki shiyasa yaki magana. "Tabbas kinfi kowa bukatar maganar ta Ammi, saboda kinfi kowa chanchanta da hakan, ƙaddara ce ta haɗa ni da ita, haka ma ƙaddara ce ta kaini Katsina har na shiga cikin wannan halin, babu sanin ta ko izinin ta kamar yadda kike tunani, komai da ya faru tsarin Allah ne, idan ka duba yadda ya kasance. Dan Allah a tura tazo idan har tana nan, bana so nace komai sai a gabanta." "Bari na kira ta son, sun iso yanzu ta bar falon nan bisa korar da mahaifiyar ka tayi mata." Sai ya ciro wayar sa ya shiga neman layin Farouk, yana zaune a dakin sa tun zuwan su, gefe jakar akwatin Aminatun ce daya ajiye a wajen sa, yana shirya wani kuduri a ransa.    Shigowar kiran ya katse masa tunanin da yake "Ina gida, ok tom gamu nan." Rigar sa daya rataye ya jawo ya saka ya fito, ganin part din Dadah a kunne da haske yasa ya nufi chan, sallama yayi ya tura kofar, duk sun zagaye Aminatun dake ta faman kuka suna bata baki, da sauri ya isa ciki yana neman ba'a si "Me ya faru?" "Matsala suka dan samu da Maman Kamal, kamar tana zargin ta da jefa Kamal din cikin halin da yake ciki." Anty Safiyya ta amsa masa tana matsawa gefe "Zancen banza kenan, akan me? Dan kawai ya taimaka mata sai kuma cin mutunci ya shigo? I can't tolerate cin mutunci daga kowa." "Bata kyauta ba kam, na rasa kuma me ya sa ta hakan bayan ba halin ta bane." "Tashi." Yace yana mika mata hannu, dagowa tayi ta kalli hannun kafin ta maida kanta kasa ta cigaba da kukan ta.   Damko hannun nata yayi ya mikar da ita tsaye yana girgiza mata kai "Karki sake kuka, kin bar kuka tun daga ranar dana dawo gare ki, wannan ya zama na karshe." "Me yasa kowa yake min haka?" "Muje." Yace yana nufar kofa da ita "Me zakayi Farouk?" "Alhaji Marwan ke kiran mu, yanzu zamu dawo." Yace yana fita da ita. ***** Shiru kawai Ammi tayi bata sake magana ba ta zauna tana matsawa Kamal din gefen kafadar sa. Shigowar su yasa ta dakata, kallo daya tayi musu ta dauke kanta zuciyar ta babu dadi. Fuskar Kamal ce ta washe sosai ganin ta, ya lura da yadda idon ta yayi, ya san kuma hakan na da nasaba da abinda Ammin tayi mata, duk da bai ji dadi ba amma yasan hakan baya daga cikin halayyar Ammin, be san me yasha kanta ba, har ta iya aikata abinda be yi tunani ba. "Ammi, Daddy, Ya Farouk da Aminatu, ina so na sanar daku abinda ya kaini Katsina, da abinda yasa na takura da son ganin Aminatu da har ya jawo matsala tsakanin ta da Ammi." "Go ahead, karka ji komai kaji, muna sauraron ka." "Nagode Daddy." "Duk da bansan takamaimai alakar Adam da ku ba, bansan me kukayi masa ba da har yake bibiyar rayuwar ku, ya kuma yi abinda yafi komai muni, Ammi ki dubi Aminatu da kyau, kiyi mata kallo ba irin kallon da kikayi mata a yanzu ba, zaki gane abinda zan fada." "Daddy I'm sorry, I'm very sorry to say, ni din ba danku bane, baku kuka haife ni ba." "Kamal!!!!" Alhaji MD ya daka masa tsawa "Me kake so kace? Kana da hankali ko ka tabu, waye ya gaya maka wannan banzan labarin?" "Daddy ka yarda dani, bani da ikon boye muku gaskiya tun bayan dana san gaskiya, Daddy wallahi ni ba danku bane, Aminatu ita ce yarku, yar da kuka haifa da cikin ku, aka chanja muku ita, duk a bisa umarnin Adam." "Kamal me kake shirin cewa ne wai? Ban gane ba!" "Ammi ki yarda dani, akwai kwararan hujjoji, komai na cikin waya ta nayi recording din sa, ina fatan idan kun gani zaku yarda dani." Juyawa dakin ya hau yi, daga Aminatu har Ammi babu wanda yake iya tantance komai, komai na dakin ya shiga rarrabe wa Aminatu, lu tayi zata fadi Farouk da maganar ta dake shi shima yayi saurin tare ta, lumshe idon ta tayi tana son tantance mafarki take ko kuwa gaskiya ne? "Baka da hankali Kamal, ka haukace ko ƙwaƙwalwar ka ta tabu?" "Idan kuka duba wayar still baku yarda ba ,daga nan zaku iya daukata a mahaukacin ma." "Bani wayar!" Ya karba a hannun Ammi da ta soma kuka ta kasa magana, hannun sa har rawa yake ya bude wayar ya shiga wajen, sautin muryar Kamal ɗin ce ta karade dakin cikin tattaunawar su da sister Asibi, zuwan sa Shagari, haduwar sa da Adam kafin accident din ya faru. Da baya da baya Alhaji Marwan ya shiga ja har ya isa kujerar dake daura dashi ya fada yana dafe kansa. Kuka sosai Ammi take, haka ma Kamal da Aminatu da bata masan a wanne matsayi zata ajiye abinda yake faruwa ba. Me ya kamata tayi yanzu? Me zata ce? Tsawon rayuwar ta tayi shi ne da tunanin ranar da zata hadu da iyayen ta, bata taɓa tunanin ta wannan yanayin zata hadu dasu ba, dukkan su kowa ya kasa motsawa daga in da yake, nauyi kunya da wani irin yanayi Ammin ke ciki, yarta! Yar cikin ta tayi wa abinda bata taɓa tunanin ko mai aikin gidan zata yiwa ba, ina tunanin ta ya tafi, ina hankalin ta, so take ta sake kallon ta, ta tabbatar da gaskiyar komai,amma ta kasa, ta gaza mik'ewa ta aiwatar da abinda yake cin ta. Waje Farouk ya samu ya zaunar da ita ganin duk sun rikice ya isa gaban Kamal din ya dafa shi "Me ya faru da har ya saka ka yin tafiyar?" "File ɗin ta, file dinta dake dauke da sunan ta, Aminatu MD, sannan da passport din dake jiki na Ammi da Daddy, sai kuma labarin ta data taba bani, tabbas ba abu bane me sauki garemuba dukka, amma wannan shine gaskiya. Asibi, Adam, Inno kadai sun isa shaida, za'a iya neman su a tabbatar da haka." "Na yarda da kai." Yace yana shafa kansa. "Kira min mahaifin ku farouk, kira shi yazo nan na rasa yadda zan ɓullo wa al'amarin na." "Ok tam." Ya zaro wayar sa, ya kira Daddy. "Daddy..." "Ku taho nan Farouk, Adam na hannu yanzu haka, yana cikin gidan nan a dakin horo na, ka gaya wa MD kuzo yanzu, komai yazo karshe!" *** Assalamu alaikum Kuyi hakuri pls na shiga hidimar biki ne, kunsan yadda biki yake musamman idan aka ce naku ne.. Bikin best friend d'ina ne kuma zata auri dan uwa na. Ku sanya musu albarka da bakunan ku masu albarka Allah sa ayi a sa'a Sai kuma ku shirya suburbudar Adam dan ni har na samu muciyar da zan sambade shi da ita.😂😂😂 Shegen Goraa: *DG*                        *40* ©Hafsat Rano ★★★★ "Bani shi." Yace yana karbar wayar "Ina ganin ko zaku zo nan ɗin saboda barin Kamal shi kadai anan ɗin matsala ne, idan yaso sai ayi komai nima akwai abinda ya shigo min yanzu haka, na ma rasa yadda zan." "Shikenan ina ganin mu bari zuwa gobe, bari nazo yanzu ni." Ya ajiye wayar yana nufar bangaren Dadah, yaji dadin zuwan da Adam ɗin yayi da daren dan hakan yayi masa sauki wajen kamashi.    Kamar yadda suka saba ya shigo cikin gidan kai tsaye babu shamaki saboda matsayin sa na kanin matar gidan kuma sananne tsawon lokaci, Daddy na zaune a falo yana tunani yadda za'a yi ya turo kofar ya shigo, da murmushi ya tarbe shi kamar kowanne lokaci ya kuma bashi wajen zama yana tambayar shi kwana biyu. Bayan tattaunawa da sukayi kadan Daddyn ya tashi ya bashi wuri gami da kira Mama ta fito da mamakin zuwan nasa.   Bangaren su Farouk ya nufa ya tura kofar, baya nan saboda haka ya dawo wajen securities din daya bawa umarni tun safe yace Ibrahim na fitowa su kama mashi shi, sannan ya koma ciki. *** Kuka Aminatu take sosai wanda ta gaza boye shi, sam bata taba tunani ko kawowa a ranta wani abu makamancin haka zai ɓullo mata a irin wannan lokacin data cire rai da komai, mahaifiyar ta? Yau ita ce gaban ta cikin yanayin da ta gaza fuskanta yadda zata ajiye shi.   Kadan kadan yake murza hannun ta cikin salon son rarrashin ta, sai dai ta gaza tsaida hawayen, idan da za'a fada mata cewa zata riski irin wannan ranar zata iya karyatawa, sai gashi ta risketa cikin yanayin da bata taba zato ko tsammani ba.   Shigowar Daddyn ya tsaida komai, da sauri Alhaji Marwan ya tare shi da abinda ya ke faruwa, sosai maganar ta dake shi, ya tsorata ainun da lamarin Adam, ashe zai iya aikata haka garesu? Tabbas Adam yayi nisa cikin kiyayyar su, ya zama dole su ajiye duk wata alaƙa su hukunta shi hukunci me tsanani. "Ina ganin dole a samu sauran mutanen da suka taimaka wajen bashi hadin kai, tabbas suna bukatar hukunci me tsanani." "Abinda nayi tunani kenan." "Dole gobe kowa ya zo, ya zama yana nan kuma ya zama dole Dadah ta fayyace wa kowa babban sirrin dake lullube a zuciyar ta." "Ina fatan ya zama abu mai sauki da zamu iya dauka." Alhaji Marwan yace yana kallon Aminatu da yake jin kamar ya dauke ta ya saka ta jikin sa, tun ranar daya fara ganin ta ya kasa tantance abinda yasa yaji wani iri game da ita, ashe jinin sa ne yake yawo a cikin jikin ta. **** Tashi Ammi tayi da kyar bayan ta gama bawa kanta k'warin guiwar tunkarar ta, tashi Farouk yayi ya bata wajen yana komawa gefen Kamal.   Da k'yar ta d'aga hannayen ta, ta ɗora su a saman kan Aminatun, kuka ya kuma kwace mata, "Wacce irin rayuwa 'yata tayi, wacce irin wahala tasha? Wannan wacce irin ƙaddara ce." Dago fuskar ta tayi wadda ta cika da hawaye ta rungume Ammin da dukkan sauran karfin ta, abinda take jira kenan itama tayi saurin sa hannu ta zagaye ta tana shafa bayan ta "Ki yafe min, ki yafe min dan Allah, an cuci rayuwar ki, an saki maraicin karfi da yaji tun a karancin shekarun ki bayan baki da hakki akan kuskuren da muka aikata." "Ammiiiii....!" Ta ja sunan cikin tsananin kuka da ta kasa tantance na farkin ciki ne ko na akasin haka? "Shissshh! Karki yi kuka, kukan ki ya kare, ke yar gata ce ta kowanne bangare, ba zan taba yafe wa Adam ba, ya cuce ni cuta mafi muni, akan me zai raba uwa da yarta tun zuwan ta duniya, wannan wanne irin rashin imani ne? Akan kuskure daya? Daya tak? Waye baya kuskure a rayuwa dan Allah?" Idon Alhaji Marwan ya kada sosai yayi ja, tabbas Adam yayi masa cuta mafi muni, ba zai taba yafe masa ba, ba zai taba kyale wa ba sai ya nuna masa akwai banbanci, matsawa yayi har gaban su ya riko Aminatu ya mikar da ita, girgiza mata kai ya shiga yi alamun tayi shiru, da sauri ta fada jikin sa tana sakin kuka muryar ta ta soma dashewa, murmushin karfin hali kawai yake dan yadda yake jin zuciyar sa zai iya kukan. Ta jima a jikin sa tana kokawa da zuciyar ta.   Ta gefe Farouk ya rabe ya fita yana jawo musu kofar, kai tsaye gida ya nufa domin dauko Iman, a yau yafi kowa murna. Anty Safiyya ta gama shirya su kenan shirin kwanciya bacci ya shigo, dagowa tayi ta kalle shi "Kar kace min dauke ta kazo yi." "Anty!" Yace yana murmushi "Naga aalama ne ai, yaran zamani." Sosa kansa yayi yana dariya kasa kasa "Zan kaita ne wajen Ammi da Anty!" "Auw toh mana, na zata ko rashin ta idon ne ya motsa." Murmushi yayi ya kama hannun Iman din suna barin dakin. Yanayin tafiyar sa kadai zata gamsar dakai da irin yadda yake ji,farin cikin sa ya gaza boyuwa kwata-kwata, har ya dangana ta da dakin da suke, yasa hannu kadan ya bude yana nuna mata ciki "Shiga wajen Ummi kinji?" Daga mishi kai tayi ta sa kai tana kallon ko ina, duk suka juyo suka zuba mata ido, da sauri Ammi ta tashi ta nufe ta tana goge fuskar ta "Alhaji kaga, ikon Allah kalli Alhaji,." "Alhamdulillah." Yace yana mika mata hannu , "Zo naji ki kusa dani, matso nan sabuwar amarya ta." Ya karashe cike da barkwanci, duk sukayi dariya har Kamal da yake jin kamar ya gama cika burin sa. *** Dakin Ammi ɗin ta jasu, ta rasa ina zata saka su, komai ta dauko sai ta mayar, kamar a mafarki Aminatu take ji, yau itace tare da mahaifiyar ta cikin yanayi me dad'i beyond her imagination.   Basu samu runtsawa ba, daren ranar ta fayyace mata dukka rayuwar da tayi,ba karamin girgiza Ammin tayi da labarin ba, tayi kuka sosai sannan kuma ta gode Allah da ya sa yarta bata fada mummunan hannu ba har ta samu tayi karatu irin na yanci. Zata so taga Anas, ya tallafi rayuwar yarta, yayi mata gata. A halin yanzu ita zata tsayawa yarta, ta bata kulawar da zata manta radadin abinda ta kunsa. **** Duk da bata da tabbacin zai zo kamar yadda yayi mata, sai dai ta gaza aiwatar da dukkan ayyukan ta na ranar tana dakon zuwan sa, ganin da gaske babu alamar shi yasa ta dauki wayar ta kirashi, hakuri ya bata yayi mata alkawarin zuwa gobe da ikon Allah.    Tashi tayi zata wuce zuwa daki kiran Ja'afar ya shigo, ta so sha'afa da dawowar tasa, sai data ga kiran sannan ta daga a gaggauce "Son..." "Mummy yanzu zamu taso, zuwa dare in Sha Allah xamu iso." "Ok dear, Allah ya kawo ku lafiya, karka manta da kun sauka ka sanar dani, Idris zai jira ka ku taho direct nan Farouk ma zaizo." "Shikenan, sai mun zo." "Owk bye." Ta ajiye wayar tana dan bubbuga bayan ta da ke dan mata ciwo. Tun bayan gano in da yar uwata take ta hau shirye shiryen zuwa takanas wajen ta, bata sanar da kowa ba har dan gaban goshin nata, so take ta basu mamaki kawai, shiyasa ta gama shirya komai take so su je su hudu, ita, Ja'afar, Farouk da babbar yayarsu Anty Lami.           ****Kwanan tsananin wuya Adam yayi, basu raga masa ba ko kaɗan dan Daddy yace kar su saurara masa bayan abinda Alhaji Marwan ɗin ya sanar dashi ya kara tunzura da lamarin Adam ɗin, tabbas babu digon tausayi ko rahma a zuciyar sa, dan haka suma ba zasu raga masa ba.     A gajiye Daddyn ya tashi kamar wanda aka yi wa duka, kwana yayi yana tunane tunanen yadda abubuwan suka dinga faruwa a karkashin ikon shi, rainin hankalin da adam yayin masa yafi komai taba shi, sai kuma rashin bincike kwakkwara da beyi ba akan case ɗin Mummy, a yanzu babu wadda yake so kusa dashi sama da ita, sai dai yasan taurin kan ta da kafiyar ta ba lallai ta sauko da wuri ba, idan ma ta sakko ɗin, dole ana bukatar ta a yau, ta zama tana wajen komai zai bayyana, amma waye zai kira ta ta yarda tazo? Babu shi. Shiru yayi cikin tunani kafin ya mike da sauri, Safiyya ce kadai zata sata zuwan dole. A gaggauce ya shirya ya fito, Mama na ganin shi ta mike da sauri "Alhaji, yau lafiya ka shige ciki tun wuri ka rufe kanka, duk hankali na ya tashi ban iya baccin kirki ba." "Baki da hurumin sanin abinda nake." Yace yana rabe wa ta gefen ta, baki ta rike cikin tsananin mamaki take kallon sa, sai daya kai kofa sannan yace "Akwai meeting na gaggawa karfe sha biyu, idan lokacin ya cika ki same mu a gidan MD." Yasa kai ya karasa fita yana jin kamar ya dawo da baya ya faffasa mata baki da hanci yadda yake jin haushin ta.    A harabar gidan ya tarar da su a tsaye suna jiran sa, duk suka sara masa da sauri, dakin ya nufa  suna take masa baya daya daga ciki yayi saurin bude masa kofar, kansa ya tura ciki yana kare ma ko ina kallo, yana kwance d'ai-d'ai yana fitar da numfashin wahala, fuskar sa ta haye tayi sumtum kamar bashi ba, babu mask din da yake sawa sai ainihin fuskar sa. Dagowa yayi ya zuba wa Daddyn ido har ya ƙaraso gaban sa, babu digo na sassauci a fuskar tasa "Iya kar abinda zaka yi min kenan?" Adam ɗin yace yana murmushin karfin hali, "Damage din da nayi muku kadai aka barku dashi nayi winning, na lalata maka dukiya na kuma cire hakki na daga ciki, sannan na raba ka da matar ka da kafi so, na hada ka danka tillo a duniya na kuma sauya masa tunani akan ka, yana maka kallon mara tausayi, na raba shi da matar sa, abubuwan da na aikata maka suna da yawa, kana tunanin Wannan hukuncin kadai ya ishe ka ramawa?" Wuya Daddyn ya riko masa ransa a matukar bace "Menene haɗin ka da Hajara!"" "Matar mu ce da mukayi tarayya akan ta!" Da wani irin karfi Daddyn yasa hannu ya hankad'a shi, ya bugu da bango ya bishi ya take yana nuna masa hannu "Sai na kashe ka!" "Kuna ina!" Ya fada cikin k'araji Da sauri suka shigo "Karku raga masa ko kadan, kuyi masa dukan da zai kasa magana, but i want him alive har sai yayi confessing dukkan laifukan sa." "Yes sir." Suka amsa a tare suna yin kan sa. **** A yadda ya shigo kadai yasa suka sha jinin jikin su, zama yayi yana dafe kansa da hannu bibbiyu, matsowa Dadah tayi gaban sa ta riko hannun sa "Lafiya?" Idon sa da suka soma kadawa ya dago mata cikin dashewar murya yace "Adam yana cikin gidan nan, za'a hadu da kowa karfe sha biyu na rana, ina rokon ki da ki sanar damu abinda kika sani idan an zauna." Da baya da baya ta koma ta zauna ba tare da tace komai ba. Girgiza kai kawai yayi ya maida duban sa wajen Anty Safiyya yace "Safiyya." "Na'am yaya." "Dan Aallah ki kira Abidah kiyi convincing din ta tazo yau, idan ni na kira ta ba lallai tazo ba." "Toh Yaya." Ta tashi dauko wayar, duk da tana tsoron yadda zasu kwashe idan ta samu labarin tana garin amma bata nemo ta ba, Amma dole ta kira dan ba zata iya ce masa a ah ba.     Kira tayi ta makala wayar a kunnen ta cike da fargaba "Rage min volume din chan Ja'afar." Tace kafin ta daga tana gyara zaman ta, "Hello Assalamu alaikum." Ta ce kai tsaye,hawaye ne ya taru a idon Anty Safiyya ta kasa magana, sai data sake maimaita sallamar kafin tayi karfin halin furta "Anty Abidah." A zabure ta mike shima Ja'afar sai ya mike "Safiyya, Safiyya kece?" "Nice." Sai ta sa kuka "Kina ina? Yaushe kika zo Nigeria, fada min yanzu zan taho innalillah." "Ina Abuja Anty gidan su Farouk, Please kizo Anty yanzu." "Wait what! Kina nufin chan Kika tafi? Dadi miji Safiyya,? Suwa ya kamata ki fara nema, tun yaushe ma kike garin kenan? Don't tell me kin kwana biyu sai yanzu kike kirana." "Kiyi hakuri duk tambayoyin nan idan kika zo zan amsa miki, nidai dan Allah kizo." "Shikenan, zanzo na dauke ki right away, ba xaki sake zama achan ba kuma, gani nan zamu kamo hanya da Ja'afar yanzu." Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace "Allah ya kawo ku lafiya." "Amin." Juyawa tayi wajen Ja'afar ba tare da ta zauna ba tace "Tashi Ja'afar, a dauko mota mu wuce Abuja, dole ta baro gidan nan yau yau." "Mummy wace haka?" Ya tambaya "Zaka gani idan munje." "Owk." **** Maganganun Iman ne ya tashi Aminatu, tana buɗe idon ta abinda ya faru ya dawo mata, kallon dakin ta hau yi zuwa lokacin ta tuna a inda take, kan gadon mahaifiyar ta, sosai taji dadin baccin fiye da wani bacci da ta taɓa yi a rayuwar ta, glasses din ta ta dauka ta saka tana saukowa daga gadon.   Budo kofar akayi, Ammi ce da Daddy cikin shigar alfarma, kowannen su bakin sa ya gaza rufuwa suka ƙaraso tsakiyar dakin suna duban ta, zamewa tayi da sauri zata sauka Ammi tayi gaggawar riko ta, a kunya ce tace "Ina kwana Daddy?" "Lafiya lou yar albarka, wannan amaryar tawa sai data tashe ki kenan." Dariya suka sa gaba daya, sannan ta gaida Ammi ma. Toilet ta shiga da yake tana fashin sallah, tayi wanka ta fito daure da sabon towel, a gefen gado taga wata haddiyar riga me masifar kyau, hade da sababbin underwears, murmushi tayi ta hau shirya wa cike da dauki.   Ba karamin kyau kayan sukayi mata ba, ta jima gaban mudubi tana kallon kanta.    Flat shoe ta zura sabo me kamar slipers ta yane kanta da dan siririn mayafi.   Idon ta ne ya sarke da nasa sanda ta fito, yana hakimce akan kujera Iman na saman cinyar sa tana masa surutu, zuba mata ido yayi kamar zai lashe ta, tayi k'asa da kanta ta ƙaraso. "Kinyi kyau sosai." Yace murya kasa, ta jishi sarai amma sai ta basar ta nemi waje daya ta zauna a hankali tace "Ina kwana?" "Lafiya lou princess, ko nace queen, dan yanzu kin zama kamar kwai nasan ni dan kallo zan zama." Murmushi tayi me aji, tabbas tana jin ta a yanzu ta kai ta isa gogawa da kowa, tunanin Shagari ya fado mata, lokacin komawar ta yayi.     "Ya kika ji? Kamar a film ko novel ko?" "Ina jin kamar I'm the most happiest being on Earth, farin ciki na bazai misaltu ba ya Farouk." "Alhamdulillah ya Allah! Allah shine kadai abin godiya." "Haka ne." "Akwai meeting by 12, komai zai bayyana." "Allah ya kaimu." Tashi yayi yana makale hannun sa a baya, ya tako har inda take, sunkuyowa yayi daidai kunnen ta a hankali yace "Get ready, patience dina ya soma karewa, i need u by my side." Turo baki tayi, yasa hannu a saman bakin. "A adana su against next time, yanzu ina gidan surukai ne I have to behave." "Ya Farouk!!!" Tace tana rufe ido "Me nayi? "Ba komai." Tace turo baki. "Yarinya taji tsoro." Yace yana murmushi kafin ya juya ya bar falon. Lumshe idon ta tayi ta bude su, kiran Anas ya koma shigowa a karo na uku, jingina tayi sosai da kujerar kafin ta daga. "Ni kike wulakantawa ?" Yace Muryar shi a shake "Ba haka bne ya Anas, bana kusa da wayar ne." "Shikenan kince kina Abuja ko? Ki tura min address din zanzo." "Naa...am?" "Sai kin turo." Ya kashe. "Ya akayi?" Ammi data fito daga wajen Kamal ta tambaye ta "Wai Ya Anas ne yace na tura mishi address,bansan ya zan ba." "Tura masa mana dama ina son haduwa dashi, idan har aka tabbatar da babu aure tsakanin ki da Farouk toh fa baki da miji sai shi, dan ni yaron yayi min." Murmushi tayi, ta rubuta address din Ammin na fada mata, bata son jayayya da ita, amma ita ta riga tasan hakan ba mai yiwu wa bace, Farouk ba zai taba kyale ta ba, gwara ma Ya Anas ɗin yazo ayi ta ta kare.a: *DG*                        *41* ©Hafsat Rano *RANAR WANKA....!*     *Ba'a boyen cibi* ★★★★ Dukka ahalin biyu sun hallara a babban Falon gidan Alhaji Marwan, kowa ka kalli fuskar shi yana cikin zulumin abinda ya tattara su haka waje daya, Mama tafi kowa shiga tashin hankali ko kwakkwaran motsi ta kasa yi sai rarraba ido take kamar tsohuwar munafuka, a gefen kafarta Amal ta zauna, Anty Safiyya da Mummy a kujera two seater Ja'afar da Farouk a kasan su, sai Alhaji Marwan da Uncle Aliiyu, suma a waje daya, Dadah da Hajiya Turai sai Ammi a kujerar ta ita kadai Aminatu zaune daf da ita, Kamal na zaune shima a gefen Ammin yaji karfin jikin sa.    Shigowar Daddy yasa kowa ya sake nutsuwa, a tsakiyar falon suka wurgar dashi kafin su juya su fice, dafe kirji Mama tayi ganin wanda bata taɓa tunani ba, kuka Amal tasa ta yunkura zata wajen sa Daddyn ya dakatar da ita "Kar wanda ya motsa daga in da yake." Komawa tayi ta zauna ta cigaba da kukan ta kasa kasa. Tasowa Dadah tayi, ta tsaya a kansa, yana dagowa ta taska masa mari, ta kuma taska masa kafin tasa kuka "Tir da kai Adam!" Komar da ita wajen zaman ta Daddy yayi yana duban kowa na falon "Alhamdulillah, kamar yadda kuka sani abubuwa da yawa sun faru ba tare da sanin takamaimai abinda yake kawo faruwar hakan ba, toh alhamdulillah, a yau komai zai bayyana kansa, duk wasu kulle kulle zasu warware." "Adam...Muna so kayi mana bayanin dalilin ka na raba Aminatu da iyayen ta ." "Cin amana ta suka yi." "Su waye?" "Mutanen da ke kokarin binne boyayyen sirrin su, su hau kai su zauna suna rayuwa ingantacciya ba tare da tuna komai ba, Marwan da Fatima kun yaudare ni, yaudara mafi muni...!" "Babu wanda ya tausaya min balle ya tsaya ya tambayi ba'a sin gaskiyar komai, tabbas nayi kuskuren aminta dakai, na daukake ka fiye da kowa...." "Soyayya mukayi me tsafta, babu wani abu me kama da rashin kirki a ciki, zuwa lokacin da muka riga muka aminta da juna, kai na fara tuntuba da maganar." Ya nuna Alhaji Marwan "Kai na shawarta har ma na baka  wuka da nama wajen neman ta, haɗe da address din gidan su, a matsayin ka na wanda na dauka babban wa, kuma uba! Me kayi? Me kayi min...?" "Kaje ka bata ni wajen ta, sannan ka nuna musu tarin dukiya, ka aure ta ka raba ni da ita, shin akwai adalci anan?... Tun daga lokacin na fara neman hanyar da zan lalata ma komai daka mallaka, ban samu dama ba." "Lokacin dana fuskanci Fatima na dauke da juna biyu nayi bakin ciki sosai, na kuma kuduri aniyar daukar fansa ta ko zan mutu a garin haka, hakan da nayi kadai nasan na gama da ku, rayuwar kunci da talauci da kaskanci yar ku tayi, sannan na sa aka rufe mahaifar ta saboda bana bukatar ku cigaba da haihuwa." "Ni na chanja ya'yan na dauki taku na bada ita a inda nasan ko kare kuke kiwo ba zai yi irin rayuwar nan ba." "Yanzu wannan dalilin ya isa ka lalata min rayuwar ya?" "Kai kasan zafin so? Kasan yadda yaudara take da ciwo? Baka sani ba ko?" Murmushin yayi "Ban taba dana sanin abinda na aikata muku ba, kun chanchanci fiye da hakan ma." Kuka ya hana Ammi magana, sam bata taba tunanin hakan zai zama babbar matsala a rayuwar ta ba, yanzu dama rashin haihuwar ta Adam ne? Bayan raba ta da yarta da yayi har da karin wannan, sama da k'asa kawai numfashin ta keyi, duk hankalin kowa ya koma kanta, Kamal duk ya rikice duk dauriyar sa sai yaji yana neman kasa wa. "Menene alakar auren Aminatu da Farouk da kai?" "Shiri na ne, ni na kulla komai, ban dauka zai sota ba, sai dana fuskanci yana son ta, sai nayi kokarin dora Amal akan turbar soyayyar sa, mu muka aika mata da takardar saki, mukayi komai cikin tsari, saboda ina so tayi rayuwa cikin kunci har sanda zata mutu!" Tashi Farouk yayi, Daddy ya sa hannu zai dakatar dashi, sam yaki ma kallon Daddyn har sanda ya damke shi. "Kai ne kayi min wasa da rayuwa kamar ka sami kwallo, ka bata min lokaci da komai, akan wani banzan dalilin ka mara tushe." "Sake shi Farouk!" Daddy ya daka masa tsawa. Sakin sa yayi ya koma ya zauna "Menene alakar ka da Hajara." "Ina tunanin na amsa maka wannan tambayar dazu, ko da yake bari na maimaita." "Zafin ranka yasa nayi amfani dakai wajen kawo maka baragurbi na kuma tabbatar da ka yarda dani, Hajara yarinya tace, ni nake sata komai, kuma da ita muke komai." "Ita ta taimaka min wajen ganin komai yazo min da sauki, ita ta kai takardar sakin Aminatu ita da Aminiyar ta sai dai bata bari aminatun ta ganta ba saboda bacin rana, haka ma dakikiyar matar data rike Aminatun." "A takaice dai duk wani abu kaine, kai ne ka raba Aliyu da kasar sa, ka raba ni da Abidah, kaine ka shirya komai." "Aliyu yayi kokarin shiga abinda babu ruwan sa, ganin zai kawo min cikas yasa na batar dashi ta hanyar da zai dade kafin ya waiwayo gida." "Ban aikata wa Anty Abidah abinda kake zargin mu ba, nayi amfani da hakan ne wajen saka maka zargin ta don nasan a irin zafin kanka ba zaka taba zama da ita ba. Duk wanda yasan sirri na nayi kokarin ganin na nisanta shi da ku, Anty Abidah ta shiga hurumin da ba nata ba, dole aiki ya biyo ta kanta." "Wanne irin sirri ne haka?" Dadah ce ta katse shi "Zan sanar daku, ina rokon gafara tun kafin kusan komai, zuciya ta cike take da nadama da dana sani, duk da bawa baya gujewa ƙaddarar sa, na dau hakan kuma na rungume ta hannu biyu ina kuma fatan mutane da yawa su dau darasi a cikin labarin da xan bayar amma ina so Amal da Kamal su dan bamu waje,da, idan yaso sai ku duba abinda ya dace." "Shikenan babu damuwa." Tashi sukayi suka shiga ciki sannan ta fara *** "Mu hudu ne a wajen mahaifan mu, mata biyu maza biyu, bayan aure na Allah yayi wa mahaifan mu rasuwa, tun daga lokacin rikon kanwata Habiba ya dawo hannu na da mahaifin ku muka cigaba da rayuwa tare. Bayan wani lokacin kanin mahaifin ku Adamu shima ya dawo gidan da zama, hakan ya bsu damar sabo da juna da kanwata har na fuskanci akwai soyayya tsakanin su.   A kwana a tashi har sanda zance ya fasu, mukayi murna sosai nida mahaifin ku, sannan aka hau maganar aure gadan-gadan.    Duk shirye shiryen da ya kamata iyaye suyi wa ya'yan su nida mahaifin ku mun yi, har zuwa lokacin da aka saka biki yazo, daga cikin gidan aka cire musu waje aka gyara musu suka tare abin su.      Mahaifin ku ya kasance me tafiye-tafiye, hakan ba karamin takura min yake ba, tun da a lokacin ina kan ganiyar kuruciya ta, haihuwa ta biyu kawai, sosai nake cutuwa da tafiyar sa, sai dai kunya da nauyi ya hanani sanar dashi, haka muka cigaba da zama ba tare da na sanar da kowa ba.      Watarana da daddare bayan kowa ya kwanta, na zabga tagumi ina tunanin abinda ya damen, Habiba ta shigo dauke da leda, kamar ko yaushe idan Adamu ya siyo mata wani abu nima sai sun miko min, hakan yasa na gane ko ledar mecece,a gefe na ajiye dan sam bani da ra'ayin ci a halin da nake. Zama ta danyi muka taba hira kadan kafin tayi min sallama, har taje kofa sai na tsaida ta nace ta turo min Adamu idan ta koma zan aika shi ya siyo min maganin ssuro, da toh ta amsa ta fita, bata jima ba sai gashi ya shigo rik'e da ledar maganin sauron, karba nayi na ajiye sannan na bukaci ya zauna muyi hira, dariya yayi ya zauna muna tattaunawa har zuwa karfe goma ma dare, kamar yadda addini yace, idan mace da namiji suka kebe toh lallai na ukun su shaidan ne, hakan ce ta faru dani da kanin mahaifin ku, bamu farga ba , har sai da mai afkuwa ta afku, shigowar Habiba da ihun da tayi ne ya ankarar damu kuskuren da muka tafka, lallai wannan itace bakar ranar da bazan taba mantawa da ita ba." Runtse ido sukayi yadda labarin ya bige su, baki daya kunya ta mamaye su,babu wanda ya iya cewa kala har zuwa sanda ta ɗora "Bazan iya tantance muku kalar tashin hankalin da muka shiga ba, washegari sai ga mahaifin ku ya diro, daurewa kawai muke muna farin ciki amma babu wanda yake ciki, kwana biyu tsakani Habiba ta hau ciwo me zafi, wanda zallar tashin hankali da firgici ne ya haifar mata dashi.    Haka mukayi ta faman jigilar asibiti da ita har mahaifin ku ya koma, ba laifi ta samu dan sauki sai dai bata umm balle a ah, kullum bata da aiki sai kuka, komai ya tsaya mana, walwala da farin ciki yayi kaura daga gidan mu, kwatsam sai ga ciki ya bullo, wanda bani da tantama cikin Adamu ne, tashin hankalin da ba'a sa maka rana, wannan wanne irin tsautsayi ne? Ashe itama Habiba tana dauke da nata cikin, abin ya hade mana sosai kullum sai dai mu zauna muyi ta kuka, har zuwa lokacin da haihuwa tazo mata, tsananin hawan da jinin ta yayi yasa ta jijjiga, bata kai ga haihuwa ba Allah ya karbi ranta da ga ita har abinda ke cikin ta.    Munyi kuka mun yi nadama mara amfani, kwana bakwai tsakani shima Adamu ya bita, nidai kamar zararriya haka na zama, ciwo ne ya taso min gadan gadan ciki wata bakwai, nayi ta addu'ar Allah yasa ya mutu kafin yazo duniya, sai dai kash, Allah ya ƙaddara sai ya taka doran ƙasa, haka yazo da rai,matsayin dan mahaifin ku.     Nayi nadama mara amfani, na rok'i Allah gafara nayi kuka har sai da idanu na suka kafe, na cigaba da boye gaskiyar saboda gudun kunyar duniya.     Bayan abinda Adam ya aikata ne yasa tsoron Allah ya dada kamani, dama nasan bashi da gadon mahaifin ku, sai dai na kasa sanarwa kowa, ganin lokaci na kure min yasa na yanke shawarar sanar da kowa waye Adam, amma kafin nan sai na fara kiran sa na sanar dashi komai, na kuma nuna masa Lallai kai da Aliyu kuna bukatar ku sani.    Ban sani ba ashe, ba zai taba amincewa ba, a lokacin yayi iya kar kokarin sa wajen roko na akan na bar maganar, ganin na kafe ne yasa shi ya shiga barazana da rayuwar ku.     Sannan abinda ya faru da Abidah sharri yayi mata, kasancewar taji dukkan abinda muka yi magana akai yasa ya bata mata suna, saboda yana so tayi nesa da rayuwar mu, na san komai sai dai ba zan iya budewa kowa ya sani ba, barazanar sa ce ta hanani aiwatar da komai, na cigaba da zama da tabon a zuciya ta.   Dan Aallah ki yafe min Abidah, ban kyauta miki ba na saka Alkhairi da sharri. To be continued.....*DG*                        *42* ©Hafsat Rano ★★★★★★ "Ki yafe min, ban kyauta ba, ban yi halacci ba, sai dai babu yadda zanyi ne shiyasa, hakan shine kadai mafita a garemu baki ɗaya." "Alhamdulillah." Uncle Aliiyu yace yana murmushi "Tabbas wannan ranar na jima ina jira, ko a yau Allah ya karbi raina zanyi farin ciki matuka." Shiru wajen ya dauka kowa da abinda ke masa yawo akai, ta gefen ido Daddy ke kallon Abidah cike da nauyi da kunyar ta, juyowa tayi suka hada ido tayi saurin hade fuska ta mike "Ina ganin bani da hurumin shiga rayuwar ku, wannan abune da ya shafi family dinku, saboda haka ni zan wuce, Allah kara rufa asiri." "Haba Anty Abidah, dan Allah kar kiyi haka, kiyi hakuri ki yafe wa Dadah, tabbas ba'a kyauta miki ba, amma nasan ki da hakuri da yafiya, dan Allah kiyi hakuri." "Aliyu karka damu, ni dama ai na dade da yafe wa duk wanda ya zalunce ni, shi kanshi Adam na yafe masa, saboda ko a yanzu haka aka barshi bashi da wani amfani, kaga kenan tun a duniya ya ga sakamakon sa." Baro kujerar da take tayi, ta iso gaban ta, ta riko hannun ta, "Ina neman alfarmar da ki yafe min, ban kasance me adalci ba, amma wallahi bani da zabi ne, kowanne bawa baya wuce ƙaddarar sa." Zuciyar Mummy tayi sanyi ganin yadda matar da girman ta take hawaye, tunanin rayuwar da sukayi a baya da irin zaman da sukayi na dadi da mutunta juna, ba zata iya fadar aibun ta ba ko ko rashin kyautawar ta, dan adam ajizi ne, kowa kuma nayi laifi. Kasa jurewa tayi, ta riƙe ta sosai tana kokari boye nata kukan tace "Na yafe miki Dadah, Allah ya yafe mana baki daya." Sai ta sake ta tana maida fuskar ta gefe ganin Daddy na shirin tasowa "Safiyya, Ja'afar, Farouk ku tashi mu tafi." Tace tana yin hanya "Dakata!" Ya tsaida ita "Ki tsaya a k'arasa komai, abinda ya shafi rayuwar Farouk ne, idan ma ni kike gudu karki damu, ba zan tilasta miki ba ai." Da wani kallo ta jefe shi, yayi murmushi yana komawa wajen zaman sa, a darare ta koma ta zauna kafin Daddy yace "Dukkan sirrikun dake rufe sun bayyana, kowanne da musabbin aikata shi, tsakani na da Adam da Hajara sai dai nace Allah yayi min sakayya, sannan maganar 'yayan da muka haifa tare kotu ce kadai zata tabbatar da nawa ne ko nashi ne, sabo..." "Wallahi tallahi karya yake min, duk abinda ya fada da sa hannu na a ciki, chanja yara, takardar saki da duk wani abu nice me kai masa rahoto, amma wallahi maganar yara naka ne, babu wani abu makamancin haka da ya shiga tsakanin mu tun bayan auren da mukayi." Ta katse shi cikin kuka, murmushin takaici Daddy yayi ya cigaba da bayanin sa "Saboda haka na saki Hajara saki uku! Ba zan iya zama da mace irin ta ba. Alhaji Marwan kai akafi yiwa cuta mafi girma da kai da mai dakin ka, ina baka damar bin diddigin duk wanda suke da hannu cikin rayuwar Aminatu, a nemo su ayi musu hukunci daidai dasu." "Sannan na riga na kirawo yan sanda, su tafi dasu daga nan sai a kai maganar kotu, idan yaso sai ayi musu hukunci daidai da abinda suka aikata, saboda daukar doka a hannu ya saba ma sharia, Farouk kayii musu magana su shigo." Yace yana komawa baya, tashi Farouk yayi, ya fita jim kadan suka shigo tare da yan sandan su biyar maza hudu mace daya, suna zuwa suka sara wa Daddy, suka koma gefe daga musu kai kawai yayi sannan yace "Gasu nan ku tafi dasu." Yaa nuna Adam da Mama. Tsit wajen yayi sai ihun kukan Mamaa tirje tirje ta hau yi tana magiya, babu wanda ya saurare ta, rike hannun Daddy tayi ya fisge yana dauke kansa, bashi da bukatar ganin ko da me kama da ita ne a yanzu, iyakar cutar wa sun masa, sai dai yace Allah ya saka masa.   Babu wanda ya iya magana har aka fita dasu, Adam nata zage zage da cin mutunci, jikin kowa yayi sanyi musamman Amal data yi tunanin za'a hada da ita, bata taɓa sanin mahaifin nata ya kai haka ba, he used her ya samu abinda yake so, ya kuma nuna mata shi aka cuta, bata san abubuwan daya aikata sun kai haka ba, hatta sharrin data yi wa Dadah da Ja'afar akan maganar sakin shi ya sakata, bayan babu sanin su duk dan ya riga ya gama juya mata tunani. Kunya da nauyin mutumin daya riƙe ta da amana take, Daddy yayi mata halacci be nuna banbanci tsakanin ta da ya'yan shi ba. Ganin shirun yayi yawa yasa Alhaji Marwan daurewa duk da baya jin dadin komai yace "Ina bawa kowa hakuri bisa abinda ya faru, lallai akwai rashin kyautawa ga kowanne bangare, sai dai hakan ba zai hana hukunta masu laifi ba,ina fatan duk wanda hukunci ya biyo ta kansa yayi hakuri, mu dukka abu daya ne, kuma zamu cigaba da rike juna da mutunci. Sannan ina sanar da dawowar ya ta, duk da wasu a cikin ku sun santa, sai dai wannan sanin yasha banban dana baya, Aminatu yata ce ta cikina, kowa yaji yadda aka chanja mana ita, ina fatan kowa ya karbe ta hannu bibbiyu, ba wai a matsayin matar Farouk ba, a matsayi 'ya ga Marwan Dikko!" Da sauri Mummy ta dubi Aminatun, duba na tsanaki kafin ta dauke kanta tana mamakin yadda abin ya zama.     Hajiya Turai tafi kowa shiga farin ciki, takanas ta taso ta dawo wajen Aminatu, ta sata jikin ta tana murna, tabbas jinin tace, babu tantama ko shakku. Duk da kasancewar Dadah tayi farin cikin samun labarin, sai dai bata da kuzarin nuna hakan duba da yadda kunya da nauyin ahalin ta mamaye ta, saboda haka bata iya cewa komai ba sai kokarin danne abinda ke taso mata na nauyi da kunya kawai take.     Amal kanta sai da maganar ta girgiza ta, ta shiga duban Aminatun da wata kama daban ba wadda tasan ta a baya ba,duk da amintar dake tsakanin Alhaji Marwan da Daddy, sai dai nisa da tazarar dake tsakanin su ta fannin arziki ba abu bane karami, ta ko ina MD ya yaga wa Daddy. Gashi ita bata ma da tudun dafawa kasancewar uban da take tunkaho dashi da babu duk daya, hakan ne yasa ta jin shakku, tabbas Aminatu ta yaga mata ta ko ina, tayi mata nisan da har abadah ba zata taba kamo ta ba, gashi ita yanzu bata ma san makomarta ba,ko Daddy zai cigaba da rike ta kamar yadda ya fara? Shine bata sani ba.      Duk da Ammi ta kadu sosai jin cewa Adam na da hannu a rashin haihuwar ta, sai dai taji dadi, atleast ta samu hanyar da zata nemi maganin matsalar ta a addinance. A kasan ranta ta tausaya masa, duk abinda yayi a dalilin son da yake mata ne, wanda ita kanta tasan bata kyauta masa ba, amma kuma abinda yai mata yayi tsauri sosai, sai dai tana fatan hakan ya zama izina ga yan baya, wani zai iya jure ma yaudara amma wani ba haka ba, zai iya salwantar da rayuwar wadda ta yaudare shi kamar yadda Adam yayi mata ko ma fiye da haka.    Ganin an tafi wata maganar daban yasa Farouk daurewa yace "Am...am... Daddy dama maganar    da kace na bari a zauna..." "Auw kaga naso na manta." Alhaji Marwan yace yana murmushi "Game da maganar auren su, ya kamata asan halin da ake ciki, tun da dukkan bincike ya nuna bashi da masaniya akan komai, dukkan abin da ya faru plan ne babu abu daya daya kasance gaskiya, bayan haka ma ko da ya kasance da gaske ya aikata sakin a bisa tirsasawa aka gusar masa da tunani, ko bisa rashin sani toh akwai maslaha akai kamar yadda yazo idan har ya tabbata bashi ya sha kayan mayen da kansa ba kuma ba'a cikin hanyacinsa yayi haka ba, to hakika sakin baiyi ba domin alkhalami ya sauka daga kansa sakamakon baya hayyacinsa, Sannan ya tabbata acikin hadisi Manzo s,a,w yana cewa:_ *ان الله تجاوز عن امتي الخطا والنسيان وماستكرهواعليه* _Ma'ana Allah ya daukewa al-ummah ta laifuka guda uku (3) Na farko: Abinda sukayi bisa rashin sani. Na biyu: Abinda sukayi bisa Mantuwa. Na uku: Abinda sukayi bisa tilastawa Abinda aka tilasta mutum yayi kenan ba'a Son ransa ba. Sai dai dukkan shaidu sun nuna bai aikata ba, bashi da masaniya ma akan abinda ya faru, hakan ya tabbatar da auren su yana nan, da ace dai tayi wani auren ne toh fa tabbas ta kubce masa. *WALLAHU A'ALAM*👏🏻   Ina fatan hakan zai wanke duk wani kokonto daga zuciyar kowa. Aminatu ta koma dakin ta su cigaba da zaman su. Kasa Aminatu tayi da kanta tsananin kunya duk ta rufe ta, babu wanda maganar batayi wa dadi ba in ka cire Amal, Ammi da  Mummy da ba zaka iya tantance abinda ke ransu ba.    Mik'ewa Ammin tayi tana kama hannun Aminatun kafin tace "Ayi min afuwa, ina bukatar yarinya ta a tare dani, saboda haka sai na sake bincike sosai akai, ba zanyi saurin saka rayuwar ta a matsala ba." Tana kaiwa nan ta jata suka shige ciki,rai bace Alhaji Marwan ya mike Daddy ya dakatar dashi "Tana bukatar yar ta, karka manta shekara ashirin da doriya ba kwana ashirin bane, ka kyale ta dan Allah." "Shikenan." Ya koma ya zauna, kasan zuciyar shi farin ciki ne dan shima yana bukatar hakan, yana so ya nuna mata gatan data rasa, ya sa mata sabo dashi kafin ta koma wajen Farouk din.   Ita dai Mummy bata ce komai akai ba, ta umarci Anty Safiyya, Ja'afar da Farouk da su tashi su tafi tun da an kare maganar, zancen zuwa kotu kuwa ita ta yafe, bata bukatar komai idan aka tsaya a haka ma Adam yaga ishara.    Farouk be so ba, yaso ko ganin Aminatu ne yayi kafin su tafi, amma baya so Mummy ta ga kamar baya damuwa da ita da lamarin ta, haka suka dunguma har Uncle Aliiyu da yaransu suka bita zuwa Kadunan.   Har sun dau hanya uncle Aliyu ya dakatar dasu yace yayi mantuwa, Iman yaje ya dauko ya fito da ita, da ido Mummy ta dinga bin sa har ya ƙaraso ya bude saitin da take zaune a mota ya mika mata ita "Ya kamata kiga jikata kafin mu tafi." Kallon Iman din tayi kai tsaye ta gane wace, duban Farouk tayi daya gaza boye farin cikin sa tace "Son?" "Yes Mum." Murmushi tayi ta kura wa yarinyar ido tana jin kaunar ta a cikin zuciyar ta. "Very cute, Masha Allah." "Uncle Aliyu ka bar min ita mana." Tace tana murmushi "Anty ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, sai dai da kyar idan Hajiya Fatima zata bar miki dan naga take taken ta." "Waye yafi kusa da ita?" Tace tana bata fuska. "Kece." "Shikenan na kwace ta, hakan zai sa tayi gaggawar dawowa da Son matar sa, dan nagano ta so take ta wahalar min da shi." Dariya suka sa baki daya, har Iman din da zuwa yanzu ta saba dasu. "Zaki bini na baki chocolate?" Tace tana shafa kanta, make kafada tayi tana kallon Farouk "Tare zamu tafi na riga na tambayi Ummin ki kinji dota." Yace dan yasan me take so tace masa, a tambayi Ummin ta, bata kara magana ba ta kwanta a jikin Mummyn, dadi ne ya lullube ta, har bata san sanda ta rungume ta a jikin ta ba.   Dole Uncle Aliiyu ya koma ya sanar wa Daddy sun tafi da Iman kafin ya dawo su dauki hanya.*DG*                        *43* ©Hafsat Rano ★★★★★★ Shiga daki sukayi, Aminatu ta zauna a gefen gadon tana sunkuyar da kanta, zama Ammin tayi tana daukar wayar ta, mita take tayi tun dazu, hakan ba karamin dad'i yake wa Aminatu ba, wai itace yau ta samu me tsaya mata, lallai uwa me dad'i, tana jin Ammin tana ta waya da yan uwan ta na jiki, tana sanar dasu taron da ta shirya na murnar dawowar Aminatun wanda sai a lokacin Aminatun ke samun labari, ita dai bata ce komai ba har ta gama ta ajiye wayar kafin ta zauna gefen ta "Kinsan dalilin da yasa naki amincewa da komawar ki? Ba wai bana son Farouk bane,ina tunanin nafi kowa son ki dashi, sai dai ba zan yarda da abinda ya faru a baya ba, dole ne yanzu ya zama kamar sanda zan aurar dake na farko, sai na gyara ki, yadda babu raini tsakanin ki da miji ko kuma uwar miji, zaki fito a cikakkiyar ya ga Marwan Dikko, zan shirya miki gagarumin bikin da kowanne lungu da sako na kasar nan zai dauka, ina fatan kin fahimce ni?" "Na fahimta Ammi." "Good." Tace tana tashi, "Ammi..." Ta dakatar da ita "Umm??" "Ina so muje Shagari dukkan mu, nayi wa kaina alkawarin ba zanje ba har sai sanda na hadu da iyaye na." "Yaushe kike so muje? Duk da nasan dole binciken da za'a yi yabi ta kansu, dole ne za'a kama ita matar da ta rike ki, da duk wanda yake da hannu, amma dole sai zuwa sanda aka tura case ɗin Adam ɗin kotu, so yanzu kike so muje ko bayan nan?" "Yanzu dai." "Shikenan, bayan taron sai muje, ina da bukatar ganin ta nima." **** Kamal na kwance duk da yaji dadin yadda abubuwan suka kasance, amma ya kasa manta fuskar Inno sanda ta biyo shi tana kiran shi, dukkan motsin da zai yi sai ya tuna, ransa babu dad'i amma kuma kasan zuciyar shi na kwadaita masa sake ganin ta. Shigowar Ammi yasa ya saita kansa ya k'ak'alo murmushi. "Ya jikin naka?"  Tace tana zama a gefen sa "Da sauki Ammi." "Sannu." "Ina ganin zamu je chan garin, nan da kwana uku, zuwa lokacin ka kara samun karfin jikin ka, sannan akwai taron da za'a yi gobe a gidan nan na murnar dawowar Aminatu." "Owk Allah ya kaimu." "Amin." Tace tana mik'ewa. "Ammi..." "Kana bukatar wani abu ne?" "A ah, babu komai." Yace yana had'iye wani abu, dawowa tayi ta zauna tana duban sa "Menene?" "Nagode Allah ya saka da Alkhairi Ammi, duk da kun gano bani da wata alaƙa daku amma baku chanja min ba, kun cigaba da kula dani kamar..." "Ya isa!" Ta daka mishi tsawa "Yanzu Kamal ni kake wa godiya? Har kake cewa baka da alaƙa dani? Kasan me kake cewa kuwa? Haihuwar kace kawai banyi ba amma baka da maraba da dan dana haifa da cikina, ni nan na shayar dakai, nayi maka tarbiyya, duk wani abu tsakanin uwa da d'a Kamal kai nayi wa, ko musulunci ya tabbatar da ni ɗin mahaifiyar kace ta shayarwa, saboda haka ka zama muharramina, kai dana ne, har duniya ta nade ba zaka daina amsa sunana a matsayin mahaifiyar ka ba." Tashi tayi ta fice daga dakin da sauri dan bata so tayi kuka a gaban sa, kukan ya saka shima, dan ba karamin tabashi maganganun sukayi ba, da yasan haka zai bata mata rai da be ma fara ba. **** Da daddare sai ga Anas ya iso, tana ganin kiran sa ta sanar wa Ammin, shigo dashi falon tasa akayi, ta fita da kanta wajen sa, cike da girmamawa ya gaishe ta, ta amsa a sake dan tun kafin zuwan sa take daukin haduwa dashi, bayanin kanta tayi masa a matsayin mahaifiyar Aminatu, wanda hakan ya ɗan sashi zama shock, ta lura da hakan sai kawai tayi murmushi ta tashi.   Yana zaune ya kura wa tangamemiyar Tv ido hankalin sa na ga tunanin maganganun Ammin ta fito, sanye take da Hajabi dogo, da ido ya bita har ta samu waje ta zauna. "Sannu da zuwa Ya Anas." "Aminatu, idon ki kenan." "Kayi hakuri, ya aiki? "Alhamdulillah, gashi muna ta fama." "Allah ya taimaka." "Amin." "Menene alakar ki da gidan nan Aminatu? Kinsan waye me gidan kuwa? Ba karamin me kudi bane karki je kisa kanki a matsala." Murmushi tayi "Ya Anas Allah ya amsa addu'a ta, ya haɗa ni da iyaye na." "What! Kina nufin Alhaji Marwan Dikko mahaifin ki ne?" Daga mishi kai tayi "How comes?" Yace cike da mamaki A nutse ta bashi labarin yadda komai ya kasance, jinjina kansa kawai yake har ta kare, "Allah mai iko, na tayaki murna sosai, zan sanar wa Hajiya kuwa gobe gobe dama zan je." "Nagode sosai da karamcin ka gareni." "Babu komai, wannan labarin yayi min dadi, nasan tabbas Hajiya zata ji dadin labarin." "So ya maganar mu? Ina muka kwana?" "Kayi hakuri ya Anas." "Me ya faru? Karki cemin ba zaki aure ni ba after all this time dana dauka ina jiran ki." "Ba laifi na bane, a yanzu dana san hukuncin da ke kaina kar mu saba wa Allah, ina da aure a kaina, kayi hakuri na cigaba da kallon ka a matsayin babban ya'ya na." Mik'ewa yayi da sauri, yayi mata wani irin kallo kafin ya juya kamar zai tashi sama ya fice daga falon.   Dafe kanta tayi, tasan dama za'a yi haka,sai dai bata so suyi rabuwar rashin dadi dashi, amma tasan fushin sa, dole dama zaiyi abinda yafi haka, zata bashi lokaci har zuwa sanda zai huce.    Tashi tayi ta koma ciki, tana duba wayar ta ko Farouk ya kira ta, amma babu kiran sa ko daya, gashi Ammi tace kar ta kuskurat ta kirashi, ita abin ma dariya yake bata, yadda Ammin ta dage sosai akan lallai sai ta ja ajinta. **** Gagarumin taro akayi, duk yan uwan Ammi da kawayen ta matan kushoshin gwamnati sun halarta, gift kuwa Aminatu ta shashi, har sai data daina gane masu bata saboda yawansu.    Kyautar sabuwar mota dalleliya Ammin tayi mata, Hajiya Turai kuma ta bata wani dankareren gold sarka da da kunne hade da bracelet me kyau. Kamal ma ba'a barshi a baya ba sabuwar waya yayi mata order ya bata,kukan farin ciki ta saka saboda yadda rayuwar ta ta chanja a cikin awanni kadan da a cikin awannin da tayi na rayuwar ta ba komai bane.    Daddy kuwa ba'a maganar tasa kyautar dan ta musamman ce, kokarin kiran manyan Drs na kashashe daban daban yake akan matsalar idon ta dan yana so ayi mata aiki me kyau, be fada wa kowa ba, so yake sai komai ya kammala ya sanar musu, yawan shakatawa zasu tafi gaba daya gidajen biyu, daga nan sai Aminatun taga likita, suna dawowa sai a hau shirye shiryen gagarumin bikin da suke shirya mata irin na ya'yan gata. *** Kwanan Farouk uku a Kaduna duk ya gundura, babu abinda yake son gani sai ita, gashi ko ya kira ta wayar da suke kadan ce zata ce Ammi na kira, dole yayi wa Mummy dabara ya lallaba ya taho bayan ya bar Iman din a chan duk kuwa da kashedin da Ammin da kanta ta karbi wayar tayi masa akan lallai idan zai dawo karya kuskura ya dawo babu Iman din, gashi Mummy ma ta kafe shi kam be san ya zai musu ba, abu daya yake ganin shine kawai Mummy tayi hakuri ta dawo gida, in yaso sai su dinga shifting idan tayi kwana biyu ana sai ta koma nan.    Har ya iso Abuja be daina tunanin yadda zasu kwashe da Ammin ba, sai da yayi wanka ya huta sosai, ya duba Dadah da bata jin dadi tun abinda ya faru,sannan ya nufi gidan kanshi tsaye.    Ta window ta hango shigowar shi, tayi saurin tashi daka kwanciyar da take, ta fada toilet, wanka tayi a gurguje ta dauro towel ta fito, kai tsaye wajen mirror tayi ba tare da ta lura da shi ba, ta cikin mirror ta hange shi, gaban tane ya yanke ya fadi ganin mutum a zaune a kan gadon ya zura mata ido ba ko kiftawa, da sauri tayi hanyar toilet din cikin zafin nama ya rigata k'arasa wa ya chapke ta. "Karki manta soja ne ni, ba zaki fini gudu ba." "Dan Aallah..." "Shissh karma ki fara wallahi, ba a isa a hanani abinda Allah ya halatta min ba." "Ammi zata shigo fa." "And so? Shine daidai ma ai." Yace yana zagaye hannun sa a saman fuskar ta, runtse idon ta tayi da sauri, ta rike hannun shi. "Pleee... Please kayi hakuri." "Please kayi hakuri." Ya kwaikwayi muryar ta yana dariya. Hannu ta kai chest din sa ta dake shi, ya rike hannun yana ɗorawa a saman kirjin nasa "Kiji yadda zuciya ta ke bugawa da sauri da sauri, I'm dying to be with you, please do something." Saurin zare hannun ta tayi, tana juyar da kanta. Zagayo wa yayi bangaren fuskar ta ta "Bari naji yadda take take bugawa." Da sauri tasa hannu ta kare saman chest dinta, ta lura so yake sai ya kure ta dole, ga wata masifaffiyar kunyar sa da take ji, Allah yaso ta ma towel din da dan girman shi, duk da haka ana iya ganin fiye da rabin jikin nata.   Baya ya ja ya harde hannu yana karewa ko ina na jikin ta kallo. He just can't wait...: DG*                        *44* ©Hafsat Rano ★★★★★★ Maganar Ammi ce ta iso musu tun kafin ta ƙaraso tana bada order, a diririce ya hau neman wajen da zai boye, duk rashin kunyar sa yana tsoron tazo ta ganshi a haka, dariya Aminatu ta shiga yi masa ba kakkautawa, be kula ta ba, yayi saurin samun corridor dake jikin wardrobe ya makale daidai lokacin ta shigo, tsaye tayi tana karewa dakin kallo kafin idanun ta su sauka akan kafafun sa dake bayyana a fili, basarwa tayi ta dubi Aminatun tana hararar ta "Me kuma kika tsaya kamar wata soja, ko ba wanka kikayi ba?" Da sauri ta juya ta shige toilet tana kunshe dariyar ta, rigar data cire ta maida ta saka, "Me haka? Ba sune jikin ki ba dazu?" "Auw sune." Tace a diririce, wajen wardrobe din tayi ta bude ta dauki kayan ta koma toilet din.  Sanda ta fito Ammin bata dakin, kallon inda yake a makale tayi ta kwashe da dariya yayi saurin fitowa, rankwashi ya kai mata ta goce tana dariya "Maganin me satar hanya kenan." Tace tana masa gwalo, "Yarinya bashi kika ci, xan dawo ne." Ya juya ya bar dakin, sai da ya fara tabbatar da babu kowa a falon sannan ya fice daga gidan da sauri yana murmushi. ***Hajiya Turai ce ta aiko aka kira ta, a chan ta tarar da Kamal ta zauna aka cigaba da hirar da ita duk da ba wani sake wa tayi dasu ba amma yadda suke jan ta a jiki yasa ta saki jikin ta itama, har Daddy ya dawo suna wajen,anan suka ci abincin dare gaba dayan su, cikin farin ciki, duk motsin da zatayi sai an samu wanda zai tambaye ta ko akwai wani abu da take bukata? Ta kanyi murmushi tace babu, dan ita a halin yanzu babu kuma abinda zata nema, sai fatan cikawa da duniya lafiya. Sai data gama shirin kwanciya tsaf, tayi wa Ammin sallama ta haye saman sabon gadon ta, wanda ya kawatu da abubuwa na jin dadi da more rayuwa, cikin kwana biyu aka shirya mata dakin duk kuwa da sun san ba dadewa zatayi ba, babu ce kawai babu a dakin.   Sama sama taji motsi kamar ana bude kofar, shiru tayi tana sake ji, tunanin ta ko Ammin ce, ta tashi tana kunna bedside lamp, idon ta ya sauka a cikin nasa ya zura hannayen sa cikin aljihun dogon wandon sa, fuskar sa na fitar ta bayyananan murmushi me sanyaya zuciyar wanda ake yi wa shi. "Yaaa F..." "Shissh!" Ya dora hannun sa alamun tai shiru, juyawa yayi ya murza key ɗin dakin sannan ya dawo, ba jiran komai ya haura saman gadon ya kwanta akan bayan sa, ƙafafuwan sa da suke mike sosai ta kalla, ta maida kallon ta kan fuskar sa. "Kashe wutar nan please bana kwana da haske." "Kwana? Anan zaka kwana?" Ware idon sa yai, ya daga mata kai "Akwai damuwa ne!?" "Ammi fa..." Tace da sauri, "Haram na aikata?" Girgiza masa kai tayi, "Oya kashe ki kwanta, gudnight." Ya juya bayan sa, yawu ta hadiye ta kashe wutar tana kwanciya a chan gefe, ƙasa ƙasa yace " Karfi da yaji an maida mutum gauro." "Na'am?" Tace tana sake matsawa "Babu." Shiru ya sake biyo baya, kowa da abinda yake ayyanawa a ransa, yadda komai ya sauya daga abun da ba zaka taba tunani ba zuwa me wanzuwa a yanzu a wani bigire na daban, sauyawar akalar rayuwa zuwa wani abu daban abin birgewa da sa farin ciki. Lallai komai ya faru da bawa mukaddari ne, haduwar su da taimakon da yayi mata ya zama wani tsani na rayuwar ta, tsanin da zai yi wuya ta taka shi idan ba wannan dalilin ba. Mirginawa yayi har ya isa gareta, ya raba hannun sa biyu ya toge dayan da kanta yace "Bani labari." Ajiyar zuciya ta sauke kadan, ta gyara kwanciyar ta sosai, a hankali tace "Gobe zamu je Shagari." "Daddy ya fada min." "Owk zaka je? I'm feeling nervous." "Yes zanje, dole na zama by your side ai, yadda zanji daɗin karya wuyan duk wanda yayi miki kallon da ban gamsu dashi ba." Murmushi tayi "Can you do that?" "Kina mamaki? Zan iya abinda yafi haka ma ai." "Ummm." "Allah dai ya kaimu goben.'" Yace yana sake matsowa jikin ta sosai, hira suka cigaba me dad'i, gaba-daya abinda ya faru a tafiyar sa, da abinda ya faru sai da suka sanar wa juna, wani suyi dariya wani kuma babu dad'i, ba tare da sanin su ba ashe dare yayi sosai, ganin idan suka biye wa hirar zasu kai asubah yasa suka hakura suka kwanta, duk da haka sai da ya tabbatar da ya aika mata sakonnin sa masu tsayawa a zuciya, duk da sakonnin kanana ne ba'a kai ga babban sakon ba,amma hakan yayi tasiri k'warai wajen sake dasa kyakkyawar alaka tsakanin su.     Kiran asubah ne ya tashe shi, yayi saurin tashi ya gyara mata kwanciya, saboda yasan tana fashin sallah, shiyasa be tashe ta ba ya fice bayan ya tabbatar da babu kowa daya ganshi. **** Karfe sha daya suka bar Abuja, suka isa Kano cikin yan mintuna da yake a jirgi suka tafi, suna isa suka dauki hanyar Katsina, daga Kamal har Aminatu babu wanda yake magana a cikin su, jifa jifa Farouk ke sako shi a cikin hirar tasu, bashi da kuzarin amsa musu sai dai yayi murmushi kawai.   Hankalin Ammi ya tafi ne ga kallon hanya, tana fatan su isa lafiya ta samu damar ganin Inno, matar da bata san a wanne bigire zata ajiye alakar su ba, sai dai tana jin ciwo da haushin irin rikon da tayi wa Aminatu, duk kuwa da tasan ba komai Aminatun ta faɗa mata ba. Idan ta tuna wacece a wajen Kamal sai taji tana kokonton irin hukuncin daya dace da ita, ko banza ance uwa uwa ce ba zata so abinda zai bata wa Kamal din ba.    Haka dai ta cigaba da tunanin abinda take ganin shine, amma bata iya jin zata saurara mata dole ne zata nuna mata kuskuren ta ko dan gaba.    Shigar bayan azahar sukayi wa garin, kai tsaye gidan suka nufa hakan ya kara tsananta bugun zuciyar Aminatu da take ji kamar zata huda kirjin ta, ta fito, tsoron abinda zata tarar ne dankare a zuciyar ta, bayan tafiyar ta tasan dole abubuwa sun sauya, sai dai ba zata iya daukar rashin wani a cikin mutanen da tayi rayuwa dasu ba ko da kuwa Inno ce.    A kasalance ta fito daga motar, rantsattsen lace ne a jikin ta wanda yasha ɗinkin k'warriyar telar nan pink couture, kallo daya ya isa ya gamsar da kai matakin da ta taka ko kuma take shirin takawa a yanzu.    A sanda Ammi ta bata kayan ita kanta sai data jinjina, dan tasan ba karamin kaya bane, duk sai taji ta kasa sawa tana tantamar wai itace? Sai da Ammin ta sake dawowa sannan ta matsa mata ta saka.     A waje su dukka suka tsaya, kowa ya zuba mata ido kafin Ammi tace "Ki shiga muna waje." Rau-rau tayi da idon ta, ta soma takawa a hankali, duk takun da zatayi sai zuciya da gangar jikin ta sun amsa, idon ta ta wurga gefe, matan dake makwabtaka dasu tuni sun fara lekowa jin tsaiwar mota, sai dai daga kallon da suke mata basu gane wacece ba, kada kanta tayi ta kutsa cikin zauren gidan nasu, yana da tsantsar talauci sunyi wa zauren k'awanya, inda zaka yi tunanin an dauki shekaru masu tsawo ba'a bi ta cikin zauren ba.   Bakin ta dauke da sallama ta shiga, Karime da tazo ganin gida ta saki tsintsiyar dake hannun ta, idan har ba gizo idanun ta ke mata ba, tabbas Aminatu ce. "Amin..." Bata karasa ba tayi saurin isa ta rungume ta, kukan da take boye wa ya taso mata gaba daya "Inna, Inna fito ga Aminatu." Tace a gigice, da mugun gudu Inno ta fito, sai tayi turus ganin Aminatun cikin shiga ta alfarma, tsoro ne ya kamata, ta tsaya jikin kofa ta kasa karasowa.   Kallon yadda ta koma Aminatu keyi, idan za'a gaya mata Inno zata zama haka zata iya musawa, babu fiye da rabin jikin ta, ta rame ainun, daga gani tana cikin mawuyacin hali. Da sauri Karime ta dauko tabarma, ta shimfida. Takowa tayi ta zauna tana kallon dakin Baba, sai ta mike ta isa dakin ta tura kyauren daya gama lalacewa ta shiga, yana kwance akan tsohuwar katitar sa data kara lalacewa, duk yayi baki ya rame abun tausayi, a gaban sa ta durkusa tana sakin kuka me tsuma rai, kukan da take ya farkar dashi daga baccin wahalar da yake, a cikin mawuyacin hali ya kira sunan ta, da ace ma ba a kusa dashi take ba, babu yadda za'a yi taji Hannun shi ta kama ta rike cikin nata, ta cigaba da kuka. Da kyar ta saita kanta tace "Sannu Baba! Ya jikin?" "Alhamdulillah." Shigowa Yalwati ta yi dan tabbatar da abinda aka gaya mata, turus tayi ganin da gaske Aminatun ce "AMINATU kece?ikon Allah." "Nice, mun same ku lafiya? Ya jikin Baba?" "Lafia lou, tare kuke da mutanen dake waje?" Da sauri ta tashi "Bari nace su shigo,tare muke." Tayi waje da sauri, Inno na tsaye in da ta barta, matsawa tayi gaban ta, ta tsuguna har kasa "Ina wuni Inna?" "Tsawon lokacin nan kina ina ? Shine kika ki waiwayo wa? Sai yanzu." "Kiyi hakuri, tare muke da baƙi bari nace su shigo." Tayi saurin ficewa, suna tsaya tace su shigo, ta juya suka bi bayan ta Ammi jikinta ya gama sanyi dan bata zaci lalacewar ta kai haka ba. Sallamar su kadai tasa cikin Inno kadawa, bata jira ta gama tantance su ba ta zari buta da sauri tayi banɗaki, zama sukayi akan tabarmar Yalwati ta zo suka gaisa kafin ta tashi ta kawo musu ruwa tana satar kallon Kamal. Jimawa tayi sosai a ciki, da kyar ta fito, sakin butar tayi ta fadi, ta kwala kiran "Yalwati, Yalwati! Zo kiga wallahi dana ne, shine yazo ranar zo ki gani karya ƙara tafiya." "Na ganshi yaya, ki nutsu ku gaisa." Tsugunnawa tayi a gefe duk jikin ta sai rawa yake kamar mazari. Cikin dakiya Aminatu tace "Inna wannan itace mahaifiya ta." Zumbur ta mike ta hau waige waigen inda zata buya dakatar da ita Ammi tayi "Ki tsaya muyi magana ta fahimta tun da ni dake a yanzu mun hadu akan abu guda, cuta dai kun riga kun cuceni, babu abinda zance muku sai dai na barku da ALLAH." "Babu abinda ya rage na boye boye,komai ya bayyana, Aminatu ta hadu da iyayenta na asali, cikin mutunci. Ko ban fada ba kinsan a yauzu ta wuce kallon banza balle a daga mata murya. Ina fatan hakan ya zama izina gare ki dama duk wani me irin wannan tunanin, Kamal da Aminatu dukkannin su yayana ne, ni nan na shayar da shi saboda haka baki da hurumin sake shiga rayuwar mu." Dagowa tayi da sauri, ta sauke idon ta akan Kamal din, yayi mata nisan da za'a iya misalta shi da tsakanin sama da kasa, ita dama tasan ko da Hajiyan bata ce haka ba, abu mawuyaci ne ya dawo gareta, share hawayen dake faman yawo a fuskar ta tai tace "Hakika nayi kuskuren da zai cigaba da bibiyata har sanda zan koma ga mahalicci na, ban chanchanci daya daga cikin su ba, na zame masa uwa, ina rokon da ki yafe min, ki dubi halin da muke ciki ko da shi kadai aka barni ya ishe ni ishara." "Bani zaki roka ba, Aminatu kika cuta, kika batawa rayuwa, idan nace zan daureki akan laifin da kika aikata mata bana jin igiya zatayi saura." "Aminatu ki yafe min dan Allah!" "Na yafe miki inna, na jima da yafe miki." "Idan har ita ta yafe, ni da Daddy ba zamu yafe ba." Ya fada rai bace "Kamal?" "Babu ruwanki Aminatu, wannan ba maganar ki bace." Tashi yayi ta fita, suka bi bayan shi da kallo, babu wanda yayi magana. Wajen Farouk ya koma yana ta waya, jingina yayi da motar wani abu me daci ya tsaya mishi a makogaro. Tsayuwar motar yan sandan yasa Farouk aje wayar da yake, tuni unguwar ta soma cika jin karar jiniya, Harira, sister Asibi ne a bayan motar kowacce an saka mata handcuf. Durgowa police din yayi, ya tsaya gaban su "Wacece dyr?" Yace yana kallon shi Shiru Farouk yayi ganin KAMAL ɗin a tsaye, ganin haka yasa Kamal din yace "Bismillah, muje na nuna muku ita, dama munyi yawa da Daddy akan haka." Gaba yayi suka bi bayan shi, yana shiga ya nuna Inno "Gata nan arrest her." A zabure Aminatu ta tashi tsaye tana wa Kamal kallon mamaki, "Menene haka?" Tace rai bace tana duban sa. "Ku tafi da ita officer." Yace yana dauke kansa. A gaban sa Aminatu ta tsaya tana masa duba irin na wanda be san abinda yake ba, cikin bacin rai tace "Me kake shirin yi?" "Babu ruwan ki." Kuyi hakuri da short page na aje wayar oga Affan ya dauka yanzu screen din ya tabu da kyar na iya rubutun inayi yana gogewa wlhia: *DG*         45 ©️Hafsat rano ★★★★ "Officer ku tafi da ita " "Hajiya you are under arrest " ya saka mata handcuf, jujjuya kanta kawai take cikin tsananin tashin hankali, a gaba suka sata Kamal na bin bayan su, kukan da take yana shiga cikin kunnuwan sa yana masa amsa kuwa, tsayawa yayi daga nesa yana duban motar, da gudu Karime tayi inda yake tsaye ta durkusa ƙasa tana kama kafuwan sa "Dan Allah karka yi mata hukunci data aikata...Mahaifiyar ka ce ka taimaka bata da lafiya." Dauke kansa yayi dacin da yake ji na sake taso masa, ko tantama babu ita ɗin kanwar sa ce, sai dai bashi da hurumin hana hukuma aikin ta, na hukunta duk mai laifi.     Ciki ta koma da gudu tana kiran Aminatu, tare suka fito yana ganin su ya yi saurin buɗe mota ya shige dan ba zai iya jure ganin su ba. Duban Farouk tayi, magana suk' da daya daga cikin yan sandan, kenan duk sun san da plan din kamasun shisa ma ko a ciki Ammi taki cewa komai duk kuwa da magiyar da tayi ta mata.    Karasowa akayi Garbati da Ila aka watsa su ciki suma, jan hannun Karime tayi suka koma ciki tana kuka, suna jin sanda motar ta daga ta bar unguwar, yara da manya aka samu abin magana.     Daki suka shiga, ta hau rarrashin Karimen da maganganu masu dadi, sosai take jin zafin Farouk da Kamal har ma da Ammin shisa da suka ce ta taso a tafi taki, tace zata tawo.   Babu wanda ya matsa mata tunda dama a garin zasu kwana. Suka tattara suka tafi suka kyale ta. Da tashin hankali Nura ya shigo gidan labari ya kai masa, lokacin jikin Baba ya kara rikice wa saboda abinda ya faru, mota ya tafi ya kirawo suka kwashe shi zuwa asibiti.    Duk abinda za'a bukata Aminatu ce ta biya, kudade ba kadan ba saboda ba karamin asibiti bane, ganin za'a iya bukatar wasu kudin gashi bata dashi yasa ta kira Kamal, lokacin yana zaune duk abin duniya ya dameshi "Kudi nake bukata muna asibiti da Baba." Tace kai tsaye, "Ina ne asibitin? zanzo." "Ok." Tace tana kashe wayar Cikin kankanin lokaci ya isa asibitin, a barandar ya hange ta tana tsaye ta zuba wa gate din ido, karasowa yayi ta nuna masa wajen biyan kudin bata ce mai komai ba, zuwa yayi ya biya abinda ake bukata ya dawo in da take, da hannu ta nuna masa dakin da Baban yake ta koma wajen da Karime ke xaune.    A darare ya bude dakin da aka kwantar da Baban ya kura masa ido, idon sa ne ya cicciko da kwalla ganin mutumin da ya kasance mahaifi a gareshi cikin tsananin wahalar talauci da tsananin ciwo. Har gaban gadon ya taka ya na kare masa kallo, bacci yake me wahalarwa numfashin sa na fita da kyar ta cikin oxygen. Dukkan su ba'a yi musu adalci ba sam duba da yadda abubuwan suka kasance.    Lallai Aminatu nada karfin zuciya idan wata ce ba xata kalle su ba balle har ta tausaya musu, sai gashi har fushi take dasu akan abinda ya xama dole. Sai da Ammi ta kirasu sannan suka bar asibitin, har lokacin Aminatun na fushi dasu.   Washegari suka sake dawowa asibitin, ta bawa Nura kudin da Kamal ya bata sannan ta bawa karime wani abu tace ta rike a wajen ta ko zata bukaci wani abu sannan suka tafi.    Taso kwarai su kara kwana amma Ammi taki. Dole suka hakura suka tafi. Kwanan su biyu da komawa rai yayi halinsa, mutuwar Baban ta girgiza both Aminatu da Kamal, be san mahaifin shi ba, magana ta fatar baki bata taɓa hada su sai gashi Allah ya karbi ransa a lokacin da yake da burin sanin sa.   Dole suka tattaro suka sake dawowa garin na Shagari amma wannan karon su biyu, sai Farouk da Ja'afar da suka biyo bayan su sukayi taaziyya.   Da zasu tafi kwarai Karime ta bawa Aminatu tausayi, ashe mijin ta ya rasu har tayi takaba, inda dangin mijin suka karbe dansu akan taki ta auri kanin mijin nata. Hakan ya kara wa Aminatu tausayin ta ba tare da shawara da kowa ba tasa ta haɗa kaya ta bisu saboda tana bukatar hutu sosai.    Bata ki ba, ta amsa tayin ta dan dama zaman yayi mata zafi gashi babu Inno tun da har yanzu ba'a shigar da case ɗin nasu kotu ba.    Zuwan Karime Abujan ya kasa ta dan saki jikin ta, tayi mamakin girma da Yalwar gidan da ya kasance mallakin su Aminatun, ta kuma kara karaya da lamarin shari'ar ganin ba kananan mutane innar ta tabo ba.   Duk yadda taso ta shige wa Kamal ya bata damar da zata yi masa maganar Inno yaƙi. ***** Safa da marwa Ya Anas ke tayi a tsakiyar falon ya gaza cewa komai. A kufule Hajiya tace' "Wai Anas menene haka? Ka sani a gaba ka gaza cewa komai, me ya faru?" "Hajiya Aminatu ce." Tabe baki tayi "Dama nasan tatsuniyar gizo bata wuce kok'i, wai har yanzu ba zaka hakura ba?" "Hajiya hakuri ya zama dole ai, Aminatu tayi min nisa sosai, bayan haka kuma da mijin ta." Tashi tayi rai bace tace "Dama rashin jin magana ne irin na dan yau, abinda na dade ina hasaso maka kenan, wahalar banza." "Hajiya bama wannan ba, ko da ace babu wani, zanji tsoron shiga saboda mahaifin ta ba karamin mutum bane, kina ji ana maganar Alhaji Marwan dikko?" "Eh! Inaji, me ya faru?" "Shine mahaifin ta." Da sauri ta dafe kirji "Kana nufin uba mahaifi?" "Eh Hajiya." "Na shige su ni Bintu, kasan kuwa me kake cewa?" "Wallahi Hajiya." "*Hukumullah, kaji ikon Allah ko? Kai masha Allahu, amma ya akayi haka?." "Yadda kika ji haka yake Hajiya, ni kaina abin ya dauren kai." "Alhamdulillah, Allah na gode ma da babu wani abu dana taba mata, shiyasa aka ce karka wulakanta mutum wallahi." Murmushi yayi kawai,yana duban Hajiyan, sai ya kada kansa kawai ya bar falon, har yaje kofa tace "Allah yasa tana da kanwa kaga sai ka shiga kawai ko dan hallacin da kayi wa yar su xasu baka, su kuma daga ka kaima ka samu wani abun." Sarai yaji, bece komai ba kawai ya karass barin dakin yana mamakin chanjawar Hajiyar,kudi masu gidan rana kenan. ★★★★ Cikin shirin farar shadda kal, ya dora hular jaddara, sosai ya fito a cikakken bakatsine me cike da kamala da haiba.   A gurguje ya shiga bangaren Dadah,ya gaishe ta ya sanaar da ita abinda yake shirin yi, addua tayi masa da fatan alkhairi.    Bayan mota ya fada, ya zauna sosai yana hasaso yadda xasu kwashe da ita, sai dai duk runtsi ba xai sake barin ta ba.    Sanda suka isa kadunan be ma sani ba yyi xurfi a tunani, sai da motar ta tsaya a kofar gidan sannan ya dago yana karewa unguwar kallo. "Oga xamu shiga ciki ne?" "No ka tsaya anan." Yace yana fitowa, da kafa ya isa gate din ya tura, da Iman ya fara cin karo tana wasa a harabar gidan kan sabon keken ta. Murmushi yayi ganin ya samu weak point din gimbiyar tasa. Kai tsaye falon ya nufa, yayi knocking yana maida hannayen sa baya.    Ta gama tattare duk ayyukan da ta yi kenan taji ana knocking, fasa shiga ciki tayi,ta nufi kofar a tunanin ta ko Iman ce ta gama wasan, turus tayi ganin shi taja ta tsaya ba tare da ta ce komai ba "Ba zaa ce na shigo ba?" Sai ta matsa masa,tana jingina da bango, har ya kai ya zauna bata motsa ba, sai daya sake magana sannan ta karaso ta zauna a darare.    Hakuri ya soma bata,cikin kankan da kai ya kuma yi mata alkawarin ya chanja xai dinga xurfafa bincike kafin ya zartar da hukunci.    Da fari taso kin bashi fuska, amma daga karshe sai ta sakko,dama chan tana son shi, kawai yadda ya rufe Ido ya wulakanta ta ne ya kasa barin zuciyar ta.     Be baro gidan ba sai dare bayan yayi dinner cikin farin ciki da annashuwa, anan sukayi maganar komawar ta, tace ya bata lokaci, kin yarda yayi yace mata sati daya kawai ya isa tun da yanxu su ba yara bane. Dole ta amince akan babu yadda ta iya. Dadah ya fara sanarwa yana isa, sosai tayi murna dan dama babban burin ta kenan.   A daren ya sanar da MD, ji yake kamar lokacin xasu fara aure. Sati daya kuwa na cika aka daura auren Alhaji Kabir da Hajiya Abidah a karo na biyu. Babu wata bidia da akayi ta tare a sabo kuma tsohon gidan auren ta. **** Gadan gadan aka shiga kotu bayan hankalin su ya kwanta, babu bukatar dogon zama da bincike tun da dukkan su sun amsa laifin su, adam yayi laushi sosai ya kuma gane ramin kura ba wajen bakin yaro bane, iyakar horo da wahalarwa ya shata a hannun yan sandan da ba wani isheshen imani ne da wasun su ba musamman akan mai laifi, hakan ya sashi gane kuren sa ya shiga magiya da ban hakurin da bashi da amfani.    Aminatu duk ta damu shi yasa ta tsaya kai da fata wajen ganin Inno ta samu sassauci, kamar yadda aka gindaya wa kowannen su iya adadin shekarun da zai yi gidan kaso ko tarar kudi, kai tsaye ta hau shirye shiryen biyan kudin da aka gindaya wa Innon ba tare da sanin kowa ba. *Sati biyu* ****Bangaren Farouk da Aminatu wasan buya kawai ake, sam Ammi ta hana shi ganin ta,hadaddiyar me gyaran jiki aka kawo take mata. Wani irin kyau da sheki take,santsi da kyawun fatar ta ma abin kallo ne. Ita kanta sai ta zauna tayi ta kallon kanta a mudubi, komai ya chanja a dan kankanin lokaci, haka rayuwa take dama.    Gidan ya soma cika sosai, da yan uwa da abokan arziki. Karime da Hanne sun zo tun kwana biyu, hakan yayi mata dadi sosai, da farko sunki sakin jikin su ganin girma da haduwar gidan basu taba ganin irin shi ba ko da a mafarki ne, a hankali suka saki jikin su aka shiga hidimar bikin dasu.   Walima kayatacciya aka yi a harabar gidan, in da aka gayyato wata babbar malama tayi fadakarwa akan zamantakewar aure.    Washegari akayi mother's eve, in da aka hada manyan matan kusoshi da masu fda aji na kasar nan. A gajiye take sosai, sai dai ba zata iya ketare kiran Dadah ba, dole ta sauya kayan ta xuwa marasa nauyi ta ja hannun Karime.     Gidan babu hayaniya sosai hakan ya basu damar isa kai tsaye bangaren Dadah. Amal ce ta amsa sallamar su, cikin sakin fuska tace "Amarya." Mamaki ne ya kama Aminatun ta , zatayi magana Dadah ta fito, hannun ta, ta kama suka shige bed room. Nasiha sosai tayi mata akan rayuwa sannan ta bata kyautar sarka da yan kunne masu azabar kyau. Taji dadin kyautar, soyayyar da take mata daban ce, tun bata san kanta ba, tun tana abar kyama ta nuna mata soyayya. Bata da bakin da zata gode mata,sai dai tayi mata adduar gamawa da duniya lafiya.    Part din mummy suka shiga, sanyayyen kamshi ne ke tashi, komai tsaf, mummy ba karamar yar gayu bace, shisa komai na falon sai da aka chanja shi, ya tafi daidai da zamani.    "Amarya." Tace tana murmushi, karon farko data fara sakar mata fuska. "Barka da dare Mummy." "Barka dai Aminatu, ya hidima?" "Alhamdullah." "Masha Allah, ashe tafiya xakuyi? Sai jiya nake samun labari." Shiru Aminatu tayi ba tare da ta gane me take nufi ba. Tashi Ammin tayi ta shiga kitchen. Harde hannun sa yayi a kofar yana kare mata kallo, jin kamar ana kallon ta yasa ta dago, da sauri Iman ta kwace daga rikon da yayi mata tayo wajen ta. "Ummi na." Shafa kanta tayi tana murmushi. "Iman, kin manta dani ko?'" "Eh... Ina wajen Mummy, tan bani kayan dad'i." Murmushi tayi "Lallai kinji daɗin ki." "Ummi baki gaishe da Daddy na ba." Tace tana nuna mata shi da yake tsaye "Zan gaishe shi ai anjima." Tace tana basarwa Fitowa Mummy tayi rike da tray sheke dq snacks. Kallon Farouk tayi "Son tsaiwar me?" Sosa Kansa yayi "Fita ma zan yi Mummy." Ya juya sai ya makale a waje "Zamu tafi Mummy." "Toh shikenan sai kun shigo sallama kenan?" Murmushi tayi suka fita, da sauri yabi su, takun tafiyar sa sukaji a bayan su, Karime ta tsaya ya ƙaraso tana rike da hannun Iman, gaisawa sukayi idon sa akan Aminatun kafin suyi wata magana. "Kuje wajen Ammi kinji dota?" Ya shafa kan ta "Tohm Daddy." Tace sukayi saurin wuce Aminatu. Da sassarfa ya k'arasa gareta, yasa hannu ya jata, be tsaya ko ina ba sai a bangaren su, tura ta yayi ciki ya maida kofar ya rufe, ya jingina da jiki yana dariya kasa kasa "Kin gama guje gujen kenan?" "A ah." Tace tana dariya Matsowa yayi ya manna ta jikin sa, murya kasa ƙasa yace "U look very beautiful, the soft skin, the perfume and everything are very nice!" Dukan chest dinshi tayi ganin yadda yake yawo da hancin sa ko ina yana lumshe ido. "Naughty boy." Tace tana dariya. "Kira ne koma mene, i just can't hold it anymore, haba babu tausayi ne? Kalle ni fa duk na zama maraya." "Yafi ai." Tace tana ture shi "Please ki taymaka min I'm dying." "Ka yi hakuri Please." "Shikenan." Ya janye jikin sa yana matsawa gefe alamun yaji haushi "Akwai dama yarinyar da muka hadu a Nottingham, Dr Teema gabas, kuma ta nuna interest dinta akaina sosai, tunda baki sona zan neme ta, dama ina da contact d'inta." A razane ta kalle shi, zatayi magana ya juya ya shige daki da sauri,p tsaye tayi saroro cikin rashin sanin abin yi, tana tsaye Ja'afar ya shigo, a kunyan yace ta amsa gaisuwar sa, tana ganin yadda yake blushing tasan akwai wata a kasa, sai ta juya kawai ta bar part din zuciyar ta babu dad'i. Tun da ta koma take gwada kiran sa amma wayar a kashe, dole ta hakura suka cigaba da hira dasu Karime.   Ko da tazo kwanciya ma sai data kara kira amma a kashe, duk babu dad'i, sai ta dinga hasaso budurwar da yace, tasan tabbas me aji ce ta karshen karshe, kishi ne ya taru ya cika mata zuciya har ta kasa baccin ma. ***Sai data makara sosai, sanda ta tashi har su Karime sun gama shirin komawa, duk sai ta sake jin babu dad'i. Sukuku ta dinga yin komai har zuwa sanda zasu tafi, da kyar suka rabu bayan Ammi ta haɗa su da sha tara na arziki tun daga kan dangin sutura zuwa kudi. Sunji dadi sosai, har mota Kamal ya rakasu sannan ya kara musu da nashi. Tasha aka kai su suka tafi cikin kewar Aminatu da sabuwar rayuwar ta. ***Waje daya Ammi ta hade mata komai, duk abinda zata bukata ta haɗa shi a cikin jakar. Tana kwance tayi rigingine Ammin ta leko ta kira ta, falon Daddy suka je, yana zaune daga shi sai doguwar jallabiya fara yana kallon news, remote ya dauka ya rage volume din yana duban su cikin kulawa. "Maraba da Uwata." Sunne kanta tayi ta zame ta zauna a kasa tace "Daddy ina kwana?" "Lafiya lou mamana, ya sabon waje." "Alhamdulillah." "Toh Masha Allah, mamana abubuwa da yawa sun faru, wanda dukkan mu babu wanda ya ke da ikon hana faruwar su tunda Allah ya riga ya tsara, toh Alhamdulillah duk da haka mun gode wa Allah, dan bamu san abin da hakan ke nufi be, ina fatan komai da ya faru ya zama tarihi a wajen ki, sannan ina horon ki da ki zama me hakuri da juriya a duk yanayin rayuwar da kika riski kanki." "Ki riƙe addinin ki, ki riƙe mutuncin ki, ki zama uwa ta gari ga yayanki, ki girmama mijin ki,ki kiyaye dokokin Allah, ina fatan ki shiga sabuwar rayuwar ki cikin amincin da yardar Allah, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka." Kuka ta saka, yau ita ce a gaban mahaifin ta yake mata faɗa irin wanda iyaye ya kamata suyi wa dan su, abun da ta rasa a rayuwar ta kenan, lallai babu abinda zata ce sai godiya ga Allah, shi ya ƙaddara mata komai. "Menene na kuka kuma? Kinji sokonta Ammi." Murmushi Ammin tayi dan itama zuciyar ta ta karaya, ta kuma gane dalilin kukan nata. "Auw kema kukan zakiyi? Toh bari na gyara zama na sha kallon uwa da 'ya suna kuka." Dariya ya basu gaba daya, hakan yayi masa dad'i ainun, sai ya mike yana cewa "Bari kiga mamana, akwai sakon ki da ya kamata na baki." Ya shige daki, jim kadan ya fito rike da manyan files ya aje gefen sa, ya hau bude su daya bayan ɗaya, sai daya gama dubawa sannan ya mike mata "Gashi uwata, wannan shine kyautar ki, abubuwa da kika rasa  a baya ina fatan zai isa ya rufe komai." Hannun ta na kakkarwa ta karba ta bude, jiri ne ya soma dibar ta ganin tarin abubuwan da files ɗin suka kunsa, da sauri ta dago ya sakar mata murmushi cike da gamsar wa yace "Karki yi tantama dama chan naki ne. *DG* *Fourty End * "Nagode Allah ya saka da Alkhairi.". Tace Muryar ta na sarkewa. Murmushi yayi cikin jin dadi yace "Allah yayi miki albarka." "Amin." Suka amsa baki daya. Daga nan gidan su Farouk ta shiga wajen Daddy, yayi mata nasiha sosai ya kuma bata kyautar kudi masu tsoka, daga nan sukayi sallama da Mummy ma, ita yar madaidaiciyar leda ta bata me kyau tace zata kira ta a waya, godia tayi ta wuce shashen Dadah, anan ta shantake ganin Ja'afar ya kuma ta kwasar ta da hira tun tana basarwa har ta saki jiki dashi, Amal na gefe bata sa musu baki sai dai tayi murmushi kawai ,Aminatu na lura da ita, tayi laushi sosai kamar ba ita ba, hakan yayi mata dadi, ko da ma chan tasan vata da matsala, kawai anyi amfani da ita ne da kuma yarintar ta.    Da kyar ta bar shashen Dadah ta wuce gida rike da Iman da ke ta faman bata labarin abubuwan da suka faru wanda ma bata tambaye ta ba, ganin surutun na neman wuce gona da iri yasa ta dakatar da ita.   A tsanake ta hau shiryawa tun da Ammi tace mata jirgin karfe biyu zasu hau, tana yi tana tunanin Farouk, bata san zai iya fushi da ita har haka ba, ita sam bata ma ga abin fushin ba, haka ta k'arasa tana ayyana yadda zasu kwashe dashi tunda dai tare zasuyi tafiyar.    Juyawa tayi ta sake kallon kanta a mudubi, shigar ta cikin ɗinkin lace white and red riga da zani yayi matukar yin kyau da dacewa da yanayin jikin ta, mayafi ta ɗora a saman red bayan ta daura dankwalin, tayi kyau ainun kamar ka sace ta, turo kofar akayi ta dakata da abinda take, Kamal ne hannun sa makale cikin dogon wandon sa, murmushi tayi ta zauna saman stool din gaban mirror tana duban sa har ya ƙaraso. "Sis, kingan ki kuwa? Wannan ai sai ki rikita Ya Farouk din." "Toh sarkin tsokana." Ta saka dariya "Allah dagaske nake, kin fito a amaryar ki, ga angon chan a falo sai kizo muje wajen Old Woman kinsan tun dazu take zuba wa hanya ido, yau kafar ta matsa mata shisa bata fito ba." "Allah sarki Hajiya, muje toh." Tace tana zura takalmin ta. Idon ta akan sa suka fito, ya shirya tsaf cikin shigar manyan kaya da suka dace da tsari da yanayin sa, kamshin turaren sa ya gauraye ko ina na falon, idon sa akan Tv har suka gifta shi be kalle su ba, hakan ya kara sata a wani yanayi mara dadi, haka ta daure suka dangana da bangaren Hajiyan, sukayi mata sallama har da kwallar ta sannan ta fito.    A tunanin ta zata tadda shi a falon, suna shigowa ta ga wayam babu shi, sai ta zame ta zauna a saman kujerar da ya tashi, ta soma tsorata da fushin nasa, amma babu komai zata san yadda zata bullo masa dan ba zata jura ba.    Da suka tashi tafiya kowa ya fito, har gaban motar iyayen suka rako su, kowa yana musu fatan alkhairi, kasa duban kowa tayi zuciyar ta ta karye, kuka ta soma kasa ƙasa ba tare da ta bar kowa ya gane ba. Sai da driver ya kunna motar sannan ya ƙaraso wajen, yayi sallama da kowa ya fada bayan motar, sanyayan turaren sa ya cika kofar hancin ta, a dan kaikaice ya kalle ta, yayi murmushin mugunta ya maida kansa window yana duban hanya, har suka isa airport ɗin babu wanda yayi wa wani magana, shi ya fara fita ya sauke kayan su, sannan ya buɗe mata kofar yana duban chan wani waje, a kasalance ta fito tana kokarin sai ta kalle shi amma sam ya hana ta hakan, jan kayan nasu ya shiga yi ta bi bayan sa tana sake sake.    Har aka gama duk arrangements din da za'a yi bata kara ganin sa ba, sau daya ta hange shi chan suna magana da wani agent, zuwa chan jirgi ya sauka suka dunguma zuwa ciki, She's feeling nervous saboda lokacin ta na farko kenan data tako cikin airport, jiri take ji ga wani mugun tsoro daya cika mata zuciya, daurewa tayi ta cigaba da bin sa a baya, har suka dangana da cikin jirgin zuwa lokacin tsoron ta ya dada karuwa.     Bayan sunyi settling aka yi a announcing kowa ya saka belt jirgi zai tashi, hannun ta ne ya hau rawa, yana lura da ita, tana kokarin sawa taji hannun sa saman nata, ta dago da sauri, sunkuyowa yayi daidai fuskar ta, yayi mata kallo ɗaya ya maida kansa kasa, ya daura mata belt din, sannan ya saka nasa, ya zauna sosai ya kwantar da kanta saman kafadarsa kusan rabin jikin ta na saman nashi a hankali ya furta "Stay still matsoraciya." Tsit tayi kamar ruwa ya cinye ta, tayi lamo tana jin tsoron na barin ta a hankali, she feels so comfortable a yadda yayi mata, har bata san sanda jirgin ya daidai ta a sararin samaniya ba. Shi kansa ya kasa tantance yanayin da zuciya da gangar jikin sa suke ciki, be ki su zauna a haka ba. "Ya Farouk." Ya tsinkayi muryar ta kamar me rada a saman kunne sa, lumshe ido yayi ya buɗe ya zuba mata su "Uhum?" Yace ya kasa buɗe bakin sa saboda yadda yake ji "Ina zamu je?" "Siyar dake zan, Allah sa ma zakiyi tsada." Shiru tayi bata kuma cewa komai ba, har zuwa sanda suka isa, hannun ta ya kama suka fito, yanayi da tsarin filin jirgin kadai ya isa ka gane ka bar Nigeria kasar mu ta gado, fararen Larabawan da suka yi wa airport ɗin ado yasa ta gane kasar da suke, bakin ta ya gaza boye farin cikin da take ciki, yau itace a birnin na Makka da take hasashe da burin zuwa, a hankali ta soma takawa a ƙasar me tsarki, tana biye dashi kamar ragumi da akala, taxi ya samar musu har zuwa masaukin da zasu sauka wanda ya riga yayi booking din sa tun kafin zuwan su kasar.      Da kallon manya manyan gine-ginen da suka kawata garin ta shagala, har bata san sun iso ba sai dayayi magana, a kunya ce ta sauko tana kara kallon ko ina cikin tsananin mamaki.    Girman hotel din kaɗai abin kallo ne, ya tsaru ta ko ina, komai tsaf tsaf kamar ka kwanta a kasa, wani a cikin ma'aikatan ne yayi musu jagoranci zuwa masaukin nasu, wanda ya kasance aljannar duniya, falo ne babba sai bed room me dauke da madaidaicin gado.   Sallah suka fara gabatarwa daga nan sukayi order abinci suka ci. Farouk ne ya fara wanka ya sauya kayan sa ya fita, hakan ya bata damar watsa ruwan ita ma, ta bi lafiyar gado tana jiran dawowar sa.    Ya jima sosai kafin ya shigo dauke da manyan ledoji, kayan da zasu bukata na dan zaman da zasuyi ya samo, da sauri ta tashi ta karbi kayan, tana yi masa sannu da zuwa. "Sorry na barki ke kadai." "Ba komi." Ta ambata a hankali. "Gobe idan Allah ya kaimu zamu fara Umrah, saboda next week zaki ga likitan ki, so get ready." Yace yana wucewa daki, kwanciya yayi ya huta, ita kuma ta kunna Tv tana kalla duk kewar gida ta taso mata.    Sai da aka kira sallah sannan ya fito, da alamu ma bacci yayi, alwala kawai yayi ya fita, hakan yasa ta tashi itama ta gabatar da sallar sannan ta dan sake cin abinci ta zauna tana cigaba da kallon.   Makale da waya a kunnen sa yana magana ya shigo, zare wayar yayi ya mika mata, yana cewa "Ammi ce." Da sauri ta karba ta tashi tayi ciki ya bita da kallo yana murmushi, so yake sai yayi mata horon da zata kawo kanta gareshi, gashi duk ya soma gazawa amma haka zai daure dan yaga alamar wasan zaiyi dadi, mimmikewa yayi a saman kujerar har ta dawo ta mika masa wayar sa, chan gefe ta koma ta zauna tana satar kallon shi, ranshi fes yana ta danna wayar sa yanayin fuskar sa ya nuna yana jin dadin abinds yake, sosai ranta ya sosu ganin ya share ta, tashi tayi ta wuce daki tayi shirin kwanciya kawai dan ta ga abin nashi ba na kare bane.    Anan falon yayi kwanciyar sa, tun tana sa ran shigowar sa har ta hakura ta kwanta.   Washegari suka soma Umrah, hakan ya kara haifar da nisa tsakanin su, dukkan su sun shagala wajen Ibadah musamman Aminatu da take ganin dama ce da zata bautawa Allah sosai ta kuma yi masa godiya bisa sauya sauyan da ya samu rayuwar ta.   Sati guda sukayi suna Ibadah, a ranar da suka sauke Umrah da daddare tana zaune tana duba wayar ta, gama maganar su kenan da Iman da Hajiya Turai ta zauna tana tunanin rayuwa, shigowa yayi ta bishi da ido, ya wuce kai tsaye wajen kayan su ya dauki bathrobe ya daura, ta gefe take kallon duk abinda yake yi, toilet ya fad'a ya jima a ciki yana wanka, ta lura dama yana da dadewa a toilet, tashi tayi ta fiddo masa doguwar rigar sa da boxer ta ajiye a saman gadon tayi hanyar barin dakin daidai lokacin ya turo kofar toilet din ya fito. "Bani karamin towel." Yace yana k'arasa wa gaban mirror, da baya ta dawo ta dauko ta mika masa kanta a ƙasa, kin karba yayi ya zuba mata ido, material ne a jikin ta silk anyi masa ɗinkin riga doguwa me fadi daga kasa, saman ta kuma ya tsuke, yawo ya  shiga yi da idanun sa, dagowa tayi da nufin sake mika masa idanun ta suka shiga cikin nasa, rage musu karfi yayi saurin yi zuwa kanana masu bayyana asirin zuciyarsa, da towel ɗin da hannun ta ya hade ya riga yana dage mata gira "Taimaka pls, tayani rage ruwan kaina." Zame hannun ta tayi, ta ja masa kujera ya zauna ta saka towel din tana share masa kai, lumshe ido kawai yake yana buɗe su tana lura dashi ta mudubin "Na gama." Tace tana mika masa, langabe kai yayi cikin shagwabe murya yace "Ki karasa ladan ki, get me dress ba zan iya ba." "Sai kace Iman?" Tasa dariya "Eh karki manta I'm the first and last born wajen Mummy da Daddy na, dole nayi shagwaba ai" "Soon za'a haifo twins ai,ka daina feeling kanka, bayan haka ma ai Ja'afar ne dan gaban goshin Mummy not u." Matso da ita yayi ta zauna saman cinyar sa, a kunne ya rada mata "Kece zaki haifa mana twins ai, Mummy ta tsufa sai mu bata kawai, ko mu bawa Ammi daya itama daya mu karbe Iman." Dariya tasa tana zamewa jin ya fara chanja salon, matse ta yayi gam ya hana ta motsi, kansa na saman kafadarta ya shiga aika mata da sakonnin sa, shiru tayi kamar ruwa ya cinye ta, ta gaza yin komai duk ya kanainaye ta, maganganu yake mata masu dad'i da sa kwanciyar hankali, sosai hakan yayi tasiri akanta. A hankali komai ya shiga chanjawa zuwa wani bigire me cike da farin ciki da kaunar juna, it was a memorable night a wajen dukkan su, hakan ya sake haifar da shakuwa mara misaltuwa a tsakanin masoyan biyu.    Da safe suka tashi so happy and energetic, tsokanar ta yake taki kulashi, kunya da nauyin sa take ji, kasan zuciyar ta cike yake da kaunar sa, kauna me sanyi, mutunci da karamcin sa gareta abu ne me matukar muhimmanci a wajen ta, he's the perfect husband da duk wata mace zata yi muradin samu.     Tare suka shirya suka wuce asibitin, domin ganin likitan idon nata da ya basu appointment yau, hannun su sarke da juna suka shiga asibitin, da fara'a ya karbe su, babban mutum ne dan a ƙalla zai girmi su Daddy, tests ya saka aka fara yi mata, daga karshe ya dora ta akan strong magunguna da zasu taimakawa idon wajen karo karfin ganin, kwana uku tayi tana shan magungunan suka koma, akayi mata aikin idon, cikin nasara akayi aikin aka gama, cikin hukuncin Ubangiji sai ga idon ta ya dawo ras tana ganin komai tar ba kamar da take amfani da glass ba, farin cikin da suka shiga mara misaltuwa ne, haka sukayi ta kiran mutane suna sanar musu cike da farin ciki.   Daga nan Dubai suka wuce, anan suka mori amarcin su sosai, suka yi yawon wajejen shakatawa kafin su tattaro su dawo. **** Yana zaune bayan yaje sun Alhaji Marwan, yaji dadin yadda ya karbe shi sosai, ya kuma yi masa godia bisa alkhairin da yayi wa Aminatu, sannan yayi masa tayin aiki a kamfanin sa dake Kano, yaji dadi ssoai kuma ya amsa tayin babu wani dogon tunani don aiki a kamfanin sa aiki ne me kyau da tsoka, gashi kuma permanent and pensionable ne.     Ji yayi yana bukatar yaje yayi shopping saboda gobe yake sa ran shiga Kano domin ya sanar wa Hajiya labarin, tashi yayi ya sauya shigar shi zuwa kananan kaya, ya fito. Kai tsaye supermarket din daya saba siyayya ya shiga, ya wuce direct inda yasan zai samu abubuwan da yake bukata.    A daidai lokacin wata hadaddiyar beb ta turo kayan data siya tana ta mitar bata musu lokaci da wadda suke tare tayi,ji tayi tayi karo da mutum ta dago a zaton ta ameerah ce, bude idon sa yayi sosai akan ta, chubby cute little girl da ita, she looks so young and naive. "Sorry." Yace mata a gajarce ya raba ta gefen ta ya wuce, da kallo ta bishi, zubin sa irin na first class guys din nan, masu nutsuwa da kamala, a take taji ta kamu, kamuwa me karfi, yayi mata 💯 ba karya, tana tsaye har ameerah ta karaso dauke da wani lotion da ta tsaya nema, "Sheshe na samo shi fa, sorry nasan kin gama shaka." Ta kama kunnen ta tana dariya alamun ban hakuri "Karki damu,jiran yayi amfani, muje." Ta tura bsket ɗin tana yin gaba. Cike da mamakin ta bi bayan ta, ganin sudden change a wajen Raheenat sheshe, kada kai kawai tayi ta san koma menene zata sanar mata.   A wajen biyan kudin suka sake haduwa, satar kallon juna sukayi tayi har suka gama. Tare suka fito ya shiga motar sa suma suka shiga tasu, bin su ya dinga yi a hankali har suka isa gida, sai da yaga shigar su sannan ya fito ya karasa wajen maigadi ya tambaye shi akan ta,be boye mishi komai ba ya sanar dashi komai, kai tsaye ya nemi izinin ganin mahaifin ta, lokacin yana garden din sa yana hutawa maigadi ya sanar dashi, yace ya shigo dashi     Bayan sun gaisa ya fada mishi abinda yake tafe dashi, tare da neman izinin magana da yar shi, hakan yayi wa mahaifin nata dadi kwarai, dan ba'a taba masa haka ba, yawanci sai sun gama daidai wa da yaran sannan iyaye ke samun labari.    Hakan da Anas ɗin yayi shine koyarwa addinin musulunci, idan kaga yarinya kana so ka fara neman izinin iyayen ta. Tambayoyi yayi masa masu yawa, ya kuma fuskanci abubuwa game da Anas ɗin, yaron yayi masa sosai, zai kuma so ya hada shi da Raheenatu dama ita kadai ta rage duk ya aurar da yayyenta. Waya ya daga ya kira ta yace tazo garden ta same shi, hijabi ta ɗora a saman kayan ta fita, gaban ta taji yana faduwa tun da ta doshi wajen, kamar wadda kwai ya fashe wa haka ta karasa, tana ganin shi gaban ta ya fadi, tayi saurin durkusawa a wajen cikin rawar baki tace "Gani Baba." "Yawwa auta ta, ga bakon ki nan ki kaishi wajen zaman chan sai kuyi magana ko." A kunyace ta amsa hakan ya kara dilmiyar da Anas cikin kogin son ta. Shi dinma kunyar yaji ya tashi da kyar yabi bayan ta, kanshi tsaye ya gabatar mata da kansa da abinda ya kawo shi, sosai ta jinjina karfin halinn sa, sai dai hakan ya kara birgeta, nauyin sa ya hanata cewa komai, sai kawai ya karbi number ta yayi mata sallama ya tafi.    Sanda Hajiya ta samu labarin har da taka rawar farin ciki, ga aiki me kyau ga mata, amfanin Alkhairi kenan, baya faduwa kasa banza. **** Bayan shekara daya da rabi Cikin hukuncin Allah bowayi gagara misali, abubuwa da yawa sun faru, rayuwa ta chanja komai ya cigaba da wakana da wanzuwa kamar yadda yake, sauye-sauyen da aka samu basu sa karaya ko kosawa ba, zaman lafiya kowanne bangare suke cikin so da kaunar juna, Dadah da Mummy komai ya wuce, ba zaka taba tunanin akwai wani abu daya taba faruwa tsakanin su ba, yadda take mutunta ta a da har yaso yafi haka.    Bangaren masu laifi kuwa kowa ya girbi abinda ya shuka, a zaman gidan yarin ne Adam yayi fada da wani kasurgumin dan bashi, cikin dare kuwa ya biyo shi ya luma mishi wuka a ciki inda ya kashe shi har lahira ya kuma haka rami ya binne shi a wajen, sai da aka tsananta bincike sannan aka gano. Duk da labarin be ma kowa dadi ba, amma sun tabbata hakan shine abinda Allah ya tsara, shiyasa a rayuwa komai kayi me kyau, kuma karka biyewa rudin duniya da zuciya domin zasu kaika su baro ka. Ko babu tsufa akwai mutuwa! Bangaren Inno tayi nadama sosai inda Aminatu da Kamal suka tsaya mata sosai suka chanja mata komai na gida da rayuwar ta sannan Aminatu ta bata jari me tsoka ta cigaba da juyawa, kasancewar ta mace me zafin nema, nan da nan ta kara bunkasa ta cigaba da juya kudin tana cire riba, duk yadda Kamal ya so share ta ya kasa,dole ya saki jiki ya ke shiga duk wani al'amuran ta,dolen sa ce shiyasa ma da auren Karime ya tashi shine akan komai, yayi uwa yayi uba ta tare a gidan sabon mijinta me kirki da yakana, ba laifi yayi karatun sa na boko dana arabi, matar sa daya suna zaune lafiya da Karimen tunda dama chan bata da matsala. Jarin itama Aminatun ta bata take yan kulle kullen ta a tsakar gida tana siyarwa. Da bikin ya Anas ya tashi da amaryar sa Rahee da suka dade da daidaita junansu har gida ya kawo wa Aminatu ita ta wuni, ta kuma gayyace ta bikin.    Da ya dawo daukar ta sai ya kira hajiyan sa ya aika da wayar sukayi magana da Aminatu ta bata hakuri sosai ta kuma gayyace ta bikin da za'a hada dana Ramlah, Aminatu taji dadi sosai ta kuma yi mata alkawarin zuwa idan lokacin yayi, anan sukayi exchanging number da Raheenatun da alƙawarin zata zo koyon hadaddun dishes don ita ɗin k'wararriyar chef ce. **** Cikin shigar doguwar riga baka me adon pitch ta sauko, babu kowa a kasan ko ina tsaf an gyara shi, Kitchen ta nufa kai tsaye ta tarar da Baba Altine na aiki, a jikin babban freezer dake ajiye gefe guda a Kitchen din ta tsaya tana dora jakar ta a sama gami da files ɗin da  zata buƙata. "An fito? Ina kwana?!" Baba Altine tace tana goge hannun ta da madaidaicin towel "Barka da safiya Baba, kin ga naso makara akwai cases da yawa da ya kamata nayi clearing yau, gashi me gayya me aiki yace yana hanya yau, amma zanyi kokarin ganin na dawo da wuri." "Ah kice yau wajen Hajiya zan gudu maigida zai dawo." Dariya ta saka bayan ta gama jera abinda zata bukata akan dan karamin tray ta dauka ta wuce falo, a gaggauce ta karya tayi mata sallama ta fito, a baya ta watsa kayan hannun ta ta fada motar ta kirar Camry ja me gadi ya wangale mata gate.    Sai data daidaita a titi sannan ta daga wayar ta dake faman reto ta sa a handfree "Maman Iman, hala har kin fita." "Wallahi Anty Rahee, kinga amma da wuri zan dawo, snacks din ya zama ready ne?" "Eh ya zama, nama yiwa oga magana ko zai biya ya aje, kinsan shi sai yace wai ba hanyar zai ba." "Ya Anas hoo! shikenan ki ajiye anjima Kamal ko Ja'afar wani zai zo sai ya karba. Nagode." Zata ajiye wayar kira ya kuma shigowa, dagawa tayi tana shan kwanar office din nata, "Sis, kin fita ko?". "Na fita Amal, anything?" "Ok zanzo gidan nida Iman, akwai maganar da nake so nayi miki ne." "Shikenan sai na dawo." Ta aje wayar, tana kashe motar, da sauri messenger ta ya iso wajen yana bude bayan motar "Sannu da zuwa Hajiya." "Sannu Ila, ina fatan an yi duk abinda ya dace ko?" "Anyi dukka, wasu mutane biyu ma da yar yarinya karama tun dazu suna zaune sunce wai wajen ki suka zo." "Ok." Tace tayi hanyar office din, suna zaune rike da yarinyar suna hango ta suka tashi, da fara'a ta tarbe su, ta bude office din suka shiga ciki, ajiye komai tayi a muhallin sa kafin ta zauna ta ji me ya kawo su, duk da dama tatsuniyar gizo bata wuce koki, maganar dai daya ce kullum fyade wa kananun yara, zare glass din idon ta tayi,ta goge saman goshin ta tana duban yarinyar da dududu bata wuce 7years ba, she was raped by her own family member,kamar uncle ma yake a wajen ta..    Rubuce rubuce tayi sannan ta kira Dr Rumaisa ta tura su domin ta duba ta sosai ta kuma bata report na damage din da aka mata before tayi proceeding further.     Shekara guda kenan da kafa kungiyar tata me suna FAR-AM INITIATIVE (HELPING THE NEEDY AND FIGHTING AGAINST RAPE, VIOLENCE AND OTHER MARITAL ISSUES) Alhamdulillah babu abinda zata ce sai godiyar Allah, sosai kungiyar ta samu karɓuwa ta kowanne lungu da sako na kasar nan, hakan kuma idan baku manta ba shine burin Aminatu, dan haka komai na tafiya cikin tsari, duk wanda ya kawo kukan sa wajen su suna kokarin share masa hawaye, da kanta take tsaya wa mata d a yara a kotu, ta kwato musu hakkin su ba tare da sisin su ba. Wajen azahar ta samu barin office din, ta riga tayi wa Kamal text message na abinda take bukata na taron babban bakon nata.    Sai zata fara watsa ruwa domin ana rana, sannan ta sauko kasan, lokacin Amal tazo, abinci taci suna dan taba hira akan wanda zai auri Amal din turad, Kitchen suka wuce saboda lokaci na ja, anan suka ci-gaba da maganar wadda Amal din kece tayi wa Farouk magana akai dan bata so damar ta sake kwace mata, so take itama tayi aure gashi har an saka bikin Kamal da Ja'afar shisa itama take so a hada da ita dan ta soma gajiya da zaman.    Cikin kwarewa Aminatun ta shiga sarrafa hadaddiyar jollop rice me veggies, gefe guda kuma tana gasa kaza a gudar ta, sai hadin coleslow da yaji kayan hadi sosai. Kunun aya me rai da lafiya ta haɗa masa bayan ts rage aikin ta saka a freezer, (don't mind me yunwa nake ji yasin 😭😂😂😂) duk da aikin yayi sauri saboda taimakon Baba Altine da Amal amma basu samu gamawa ba sai la'asar lis, sama ta haye da ya zama out of boundary daga ita sai chubby dinta ke rayuwa a ciki, komai yana kasa saboda haka babu wanda yake hawar mata domin fadar ta wuce ajin kowa.   Kayan da zata saka ta ciro a wardrobe ta kunna hadadden turaren kayan data yi order a wajen Yerwa(Na Mss Xoxo) ta saka a kasan kabbasa ta shiga turara su, hatta undies da shegun nighties din da zata saka sai da komai ya dau kamshi, ajiye su tayi a saman bed ta wuce toilet domin gyara kanta, sai data fara rage pubic hair sannan ta wanke kanta da hadaddun mayukan wanke kai masu masifar kamshi, sannan ta yi wanka, ta bata kusan mintuna arba'in kafin ta fito ta jona handdryer ta hau busar da kan nata. Tana gamawa tayi oiling nasa da mayuka masu dadin kamshi sannan ta raba shi biyu tayi parking kowanne da ribbon daban. A tsanake ta shirya kanta cikin wata ubansun half gown pink daga wajen kirjin anyi tattara da wani silk din zare, hakan ya fidda shape din wajen, sosai tayi kyau kamar yar tsana, parking din ya kara taimakawa ta fito kamar baby doll. Hijabi babba ta ɗora a saman shigar ta,ta sauko ta tarar da Ja'afar, Kamal, Amal da Iman suna kwasar gara a saman dinning. "Sai Anty!" Ja'afar yace yana dariya "Anzo za'a cinye wa mijina abinci ko? Toh wallahi gwara a matso da bikin nan naku kowa ya kama gaban sa." "Haba wa, Madam ai ko munyi auren muna manne da gidan Ya Farouk, wannan dabge haka." Kamal yace yana kurbar kunun ayar da yayi sanyi sosai. "Allah dai ya aurar damu nan kusa kawai alaji." Suka saka dariya baki daya, tattare warmers din da ta zuba wa ya Farouk nasa tayi ta kai sama, sannan ta dawo lokacin sun gama, sallama sukayi mata suka tafi har Iman din da ta zama ta Mummy dan sam taki basu ita har sun hakura. Sallar magriba tayi, ta sake gyara fuskar ta ta feshe jikin ta da wasu turarrukan ta sauko ta zauna jiran zuwan sa. Ganin shirun yayi yawa yasa ta kunna Tv tana kallon shirin dadin Kowa na arewa 24, sosai ta shagala da kallon har bata ji bude gate din ba sai tsayuwar mota, kafin ta isa kofar har ya turo kofar ya shigo, da sauri ta isa gareshi, ya bude mata dukkan hannun su ta fada ciki, rumfa yayi mata ruf yana sake kankame ta. "Welcome home chubby." "I missed you hayatyy.” "Missed you more." Tace tana zare kanta, peck tayi masa a kumatu taja hannun sa suka haye sama, a gefen gado ta zaunar dashi ta zare masa takalmin da safa ta ajiye su a wajen daya dace sannan ta dawo ta zauna a gefen sa tana masa murmushi me tsada tace "Sannu da hanya." Mika yayi yana komawa baya kafin yace "na gaji sosai wallahi." "Sannu, ai dole, bari kasha ruwa sai ka yi wanka zaka ji dadin jikin ka." Mik'ewa tayi ta kawo masa ruwa da kunun aya, ta zuba masa yasha sosai yana lumshe ido, ganin ya kusa shanye wa ne yasa ta matsar gefe ta rage masa kayan jikinsa sukayi bathroom, ita ta taimaka masa yayi wankan sannnan ta fito ta barshi ya karasa.     Bayan ya fito ya shirya cikin kaya marasa nauyi, alamun garin akwai hadari shiyasa zafin yayi yawa, sallah ya fara yi sannan ya hau kan food mat ta shiga serving dinshi.    Yana ci suna hira gwanin sha'awa, duk yawanci akan hirar inda yaje ne da kuma harkar NGO dinta. Yana gamawa ta tattare komai, ya jasu sukayi isha'a dan har an idar a masallaci lokacin an fara yayyafi kadan kadan.     A saman cinyar shi ta kwanta ya zura hannayen shi cikin gashin kanta dake fitar da wani annurin kanshi ya shiga ya mutsa shi a hankali cikin salo, hira suke gwanin sha'awar hannun su sarke da juna, a lokacin ta kawo masa maganar Amal, yace zai yi magana da Daddy, taji dadi sosai tayi addu'ar Allah ya bada sa'a, amin yace yayi kissing dinta a forehead kafin ya daga ta zuwa babbar fadar tashi data sha gyara da sabon lallausan zanin gado wanda ya dace da yanayin da masoya zasu kasance a ciki.       Da light and romantic kiss ya fara, a hankali xukatan masoyan biyu suka cika da muradin kasancewa da juna, a hankali cikin deep husky romantic voice d'insa ya kama kunne ta ya rada mata "Ina son yanayin damina, ya kan haifar da wani yanayi me wuyar fassarawa, its all started bayan na fito daga gida, fitowar da ta zamar min abin alfahari, ƙaddara ce ta fito dani, ƙaddara me karfi da ba za'a iya ketare mata ba, abu na biyu haduwar gangar jikin mu waje guda, sanda ruwa yayi karfi a lokacin komai ya wakana, har Allah ya bamu rabon haihuwa ta sanadiyyar haka, ina ji a raina hakan zai sake kasancewa a daren yau, ina so naga wani babyn, wanda zai amsa sunan Farouk da Aminatu. Ina son ki har bansan iya yawan sa ba, I love You with all I am." "I love you beyond everything Ya Farouk, ka soni a lokacin da bani da abinda za'a soni, ka inganta min rayuwa ka nuna wa duniya nima zan iya, i love You chubby nah." "Shissh say no more, xamu yi rayuwa me inganci, tare zamuyi kuka, muyi dariya tare, I'm your best friend kema haka, we shared our sorrows and everything, for you are my eternal peace of mind, my everything, both of our hearts will be bound forever, together we will see tomorrow." "In Sha Allah my chu...." Dariya yasa yana kokarin hade bakin su waje guda yace "Soon zan fara exercise gaskiya, I want to be slim again, ta karfi da yaji an samun chubby." "No haka nake son ka." "Shikenan, Allah ya barmu tare Mrs Farouk Kabir Shagari, soon to be Captain Kabir Shagari." Kankame shi tayi sosai cikin jin dadi tace "Allah ya tabbatar da Alkhairi." "Amin." Na amsa ina murmushi ******** Alhamdulillah ya ALLAH,ina godiya ga duk masoya ZAFAFA Biyar, na fili dana boye, Allah ya saka.da alkahiri. Kuskuren da ke cikin littafin nan ina rokon Allah ya gafarta min. Allah ya bamu Sa'a ya biya wa kowa bukatar sa ta duniya yasa mu cika da imani. Hafsat Rano ke cewa sai wani lokacin idan me dukka ya kaimu.     ZAFAFA BIYAR KAUNAR MU: MAMUH GEE ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL DAURIN GORO:HAFSAT RANO. IGIYAR ZATO: MISS XOXO *_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_* 2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_ saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863* *_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇 *09032345899* _Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_